*KUDURAR ALLAH* *NA* *FATIMA ADAM* ******** ```Godiya ga Allah da ya bani ikon Fara rubuta wannan littafin wanda ya kasance littafina na farko Alhmdllh Masha Allah Godiya ga reki auntyna hassana iyayi (maman nuur) da Kika bani kwarin gwiwa akan rubutuna Allah ya bar zummunci amin. ______________ ```Page 1 ``` Bauchi unguwar dutsen tenshi. Unguwace ta masu k'aramin k'arfi wanda suke da wadatar zuci,lungu ne wanda baida wasu wadatattun gidaje gida huɗu ne kawai acikin lungun. gidana karshe shine gidan daya fi kowanne lalacewa aciki. Wani kyakykyawan dattijo ne wanda bazai gaza shekaru arba in da takwas zuwa hamsin ba yake k'ok'arin shiga gidan da yake da 'yar langa langar kofar gidan,ga dukkanin alamu bai da cikakkar lafiya, kafarsa yake takawa ! ahankali har yashige cikin dan matsakaicin tsakar gidan Wanda yake share Kal tamkar ba kasance na 'kasa ba, sai zabga kamshin kasa yake. Sallama yayi cikin wata kimtsatstsiyar murya da sauri ya karasa cikin wani karamin ɗaki dan jiyo sheshshekar kukan da yayi kutsa Kansa yayi cikin ɗakin gami da ambatan sunanta " Fatima Bintu subhanallahi !"da sauri ya ajiye ledar dake hannunsa cikin tsananin damuwa yasa hannu ya dago kanta. Kyakykyawar yarinyace me cike da wata irin baiwa da ilhama Wanda Rabbi ya bata, fuskarta me cike da kwarjini ta dago tare da zubawa mahaifin nata idanunta masu tsananin sheki. Cikin sautin muryarta me sanyi da dadin amo tace" Fafi fafi Ina katafi kabarni ? Inajin tsoro fafi kadena fita Ina matukar jin tsoran rasaka kabarni in fita Mana ni naje nasamo abin da zamu ci dan Allah fafi na rokeka karkasake fita zanyi duk abunda ya dace kaji fafina!". ta karasa maganar Tana mai hade hannuwanta biyu. Wani zazzafan numfashi ya fesar sannan cikin lallama yace. " Haba Bintu dani da ke wayafi cancanta da ya fita?ko kin manta keɗin macece me rauni ? Bintu kisani cewa babu wani abun tsoro sai Allah karki da aranki wani zai cutar dake face abinda Allah ya lamunce ya Zama kaddararki ke yarinya ce mafisoyuwa agareni lallaba rayuwarki nake Bintu kullum addu'ata Allah ya kauda idon Makiyaa akanki yakareminke tare da mahaifiyarki aduk inda take. " Yana kaiwa Nan yayi saurin goge kwallar da ya cika idanunsa Mik'a Mata ledar hannunsa yayi tare da cewa "maza tashi ki jika Mana garin rogone nasan kina jin yunwa" sosai yana faɗa da murmushi afuskarsa dan samar Mata da nutsuwa, aiko itama murmushi ta saki Wanda hakan yakara fito da zahirin kyanta ga hakoranta da yar siririyar wushirya da Kuma lobawar kumatunta " Ma sha Allah !".haka papinta yace bayan ganin mik'ewarta tana murmushi. ********* Abuja Tamfatsetsen gida ne irin gidajen nan nakasashen waje Wanda aka ɗauko tsarinsa tundaga US azo aka ginashi idan ka shiga cikin ainahin cikin gidan anan aljannar duniyar take. Birgima take tun karfinta tana Shure- shure tare da wani irin kuka me haɗe da ihu mutane, kusan goma ne akanta ana bata baki gami da rarrashi amma tamkar turata suke sai faɗin "Wooo jixos ka taimakeni ka dawomin da yarona ina son nagan shi cikin Addinina fatash ka dawo hankalinka, katemaki mamanka kaji kaina ko sau ɗaya ne a rayuwa ban turaka karatu dan kasauya ba na turaka ne dan kaji k'aina kadubeni da kulawa amma Kuma gashinka dawo min da abinda zai iyasawa zuciyata ta buga bazan iya laukar wannan abun ba." sai ta kuma kecewa da wani irin gigitaccen kuka. Dattijo ne ɗan kimanin shekara hamsin da ɗoriya yake saukowa daga upstairs yana karasowa yayiwa mutanen falon alama da su fice, sum sum ɗaya bayan daya suka fita. Zama yayi cikin k'awatattun kujerun da suka yiwa falon k'awanya Wani zazzafan kallo ya Willa Mata Wanda hakan yasa bashiri ta Mi'ke zaune tare da gyara zamanta dukda cewa Bata daina sheshshe'kar kukan ba. Zuba Mata Ido yayi na Yan wasu dak'ika kana ya numfasa tare da huro iska daga bakinsa ya ce. "Abigel kin kyauta kenan abinda Kika aikata kin tara mun jama a kina kokarin tona min asiri ko kina tunanin abunda ki kai zai canja shi daga Kan wannan ra'ayin nasa Kin manta waye shine ? Kin manta halaiyarsa ne? sirgiza Kansas yayi cikin takaici yace abigel Baki da tunani tunda harkika manta halaiyar wannan baudaddan Dan naki,se Kuma ya saki wani ɗan muafikin murmushi kana ya cigaba da cewa dama duk Wanda yase rariya yasan zata zubda ruwa muskutawa yadanyi Yana me hada hannayensa guri guda kana ya dubeta har yanzu hawayene suke satata daga idanunta, Shin kin manta baya ne ? Ko kin manta wahalar daya sha ahannun jams ? Kin manta ruɗanin da yasa kaki ? kin manta abinda yake Miki idan weekend yazagayo? Abigel be kamata ki manta duk wannan ba ballantana Kuma me Kan Kat yadda fatash be daukeki matsayin uwa ba". Azabure ta kalleshi idanunta cike taf da kwalla tace " Na rok'eka kadaina faɗan wannan kalmar tacewa fatash bai kallona amatsayin uwa ". kallonta yayi ya ce. " Ni dai yanzu shawara da zan baki ki sani duk abinda zakiyi ba fasawa zaiyi ba gara ki canja salo ko awannnan Karan Kya dace". Yana gama faɗin haka ya Mik'e tare da haye wa sama. Itama mik'ewa tayi cikin wani irin mutuwar jiki da wani irin fargaba dake yawan sawa zuciyarta na bugawa har haɗa Hanya take saboda yadda tsananin duhu ya mamaye idanunta. Adai dai wannan lokacin Kuma awannnan rana ta juma' a, ranar da kowane musulmin k'warai keyin haramar tafiya masallaci. Sai dai Kuma adaidai wannan lokacin ne wasu baragurbin dake cikin musulmai suka hada Kai da Makiya addinin Allah, suna Saɓa masa. Wata iriyar murya me tsananin Kara..... *KUDURAR ALLAH* *NA* *Fatima y Adam* Free book. *page 2* __________________________ Bismillahirrahmanirra Dajin me tsananin, duhuwa da dogayen bishiyu, babu abinda zakaji se amon muryar !" nan,wanda hakan yasa dajin yake wani irin gigiza bishiyu na, kadawa, tamkar iskar damuna. Sautin muryar nan ba daga ko Ina yake fita ba," illah cikin gidan Dake cikin tsakiyar dajin nan, shi daya kwallin kwal. Abun mamaki, acikin gidan babu wasu kayan kawa, banda wasu muggan ababan tsoro. duk 'ban garenda da ka kalla to akwai' abin da zakayi tozali dashi wanda ze kusa sa numfashin ka wuyar fita. Mutanene wanda akalla zasukai kimanin su ashirin,kowan' nen su Yana sanye da jan zani da kuma 'kwarya, ahannunsu, suna durkushe akan gwiwowinsu, babu me 'kwa'kw'kwaran motsi acikinsu dan sunyi amanna da abinda suke aikatawa shine ze basu nasara arayuwarsu. Shugaba azikwi Wanda shine yakasance shugaba acikin, kungiyar, Zaune yake Kan kujerarsa ta mulki, fuskar nan tasa, babu kyan gani gaba daya ya juye ya koma wata irin mummunar halitta, shi ba mutum ba Kuma ba dodo ba , ita kanta kujerar mulkin da kafar mutum akayita haka ma hannayen ta na mutum ne. Kai jama a idan daranka kasha kallo. Cikin wannan katuwar muryar ya bude baki !" se ga wani irin hayaki na ciccidowa tamkar hayakin turare. A haka ya Fara magana !" cikin daga sauti Wanda hakan yake nuni da Yana cikin tsananin fushi. 'Yace " haka dama mukayi daku ? bance ku kashe shiba? lallai kuwa to kusani, tun wuri d'an zaki ya riga ya girma , kunyi sake kunyi sakeeee" ya 'karasa fada cikin wani irin mummunan sauti, wanda hakan yasa gidan, da dajin suka Fara wata kakkarfar girgiza. Mutumin Dake fuskantar shugaba azikwi wanda yayi kokarin Fara goge!" zufar da take ta faman keto mashi tun Fara jawabin shugaba. Cikin tsananin rudewa da tashin hankali mabayyani Yace !" shugaba atemaka asamo mana mafita ayi mana afuwa akasi, akasamu' amma' tabbas, mun kasheshi. Wata irin tsawa shugaba 'azikwi yayi masa yace!" da da' akwai mafitar da' hankalina ze tashi ne? nayi iya'yina amma' nakasa ganin komai se tsananin duhu dodo jack, ma yayi fushi dan be taba, haduwa, da irin wannan matsalar ba. Yaci gaba da cewa!" tabbas nashiga rudani. wannan ba, karamar matsala bace dole se munyi wani abu akan wannan gagarumar matsalar." Gurin yayi tsit bakajin motsin komai se na ka'dawar da bishiyun dajin,sukeyi saboda razanin da muryar shugaba azikwi ya jefasu aciki. na kusa da wanda yay magana! afarko shine cikin tsananin biyayya yace ! "shugaba ayi Mana afuwa agafarcemu asamo mana fafita kasan komenene zamu aikatashi indai akan samun masarar mune. Yana rufe bakinsa wata kakkarfar guguwa ta taso gaba daya ta shiga zagayasu se da akadauki kusan mintuna biyu, sannan guguwar ta bace, Shugaba azikwi, ne yashiga babbaka wata mahaukaciyar, dariya wadda ta Kuma hargitsa jejin gaba daya tsuntsaye da namun jejin suka firgice kowa yashiga nemarwa rayuwar sa da dauki. Saida ya gama mummunan dariyar tasa, kana yace! " yayi dodon mu me share mana kukan mu bama taba shiga matsala baka, kawo mana mafita ba, mukuma munyi maka alkawarin baka duk abinda kanema awajen mu." Juyawa yayi ya fuskanci , mutanensa sosai gami da dayin wani shu'umin murmushi,wanda ya Kara munana fuskartasa,kana yace!"muna mika godiyarmu ga dodo jack, domin yakawo mana mafita bisa ga matsalar da Muke kokarin, antayawa' amma' Kuma akwai manyan sharadai, yaci gaba da cewa zamu bawa dodo jack jinin jarirai da yanmata da samari , dan haka kowannen mu ze kawo way'annan mutanen guda biyar biyar ragowar sharadan kuwa bani ne zan fada muku ba dodo ze fadawa kowa aikin da ze masa. A tare suka Mike suna wasu irin surutai !kowa da kwarya ahannunsa suna me ɗaukar alkawarin zasuyi biyayya ga dukkanin abinda aka' umarcesu. Acikin tsakiyar daren, ruhikansu suka koma zuwa gangunan jikinsu , Babu wanda zesan ba, mutum' amakwancinsu kasancewar kowannen, su gangar jikinsa na shimfide amakwancinsa... Bauchi Firgigit tafarka Tana Mai nanata "innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un" amatukar tsorace take da wannan' mummunan mafarkin da tayi aduk mafarkan da take Babu wanda yafi munana Kamar wannan, fargaba tashin hankali tsoro sune suka taru suka mamaye zuciyarta. dafe kahon zuciyar ta tayi saboda ji takeyi tamkar zasu Faso kirjinta su fito. Da gudu ta fito daga dan matsakaicin dakin nata duk da cewar dare ya tsala 'amma' hakan be sa taji tsoran fitowa ba. Dakin fafi ta nufa zuciyarta na wani irin bugawa da karfi cike da tsananin fargaba ta tura dan langa langar da akayi makari dashi. Sallama tayi can kasan makoshinta. da wani irin hanzari ta karasa inda ta hangoshi ayashe tamkar wanda yay danbe, cikin tsananin razana da kuka take jijjigashi tare da cewa!" fafi fafi katashi me yasameka? me'akayi maka ? baka da lafiya ne? dan Allah fafi katashi wayyo Allah na dan Allah fafi katashi karka tafi kabarni , Ina zanje? waye ze tallafi rayuwata ? kaddara karki biyo mun ta wannan hanyar karki rabani da bangona, rayuwata zata lalace. Gaba daya ta rude bata cikin hayyacin ta sambatu kawai take zubawa kasancewar ta yarinya me kana Nan shekaru gaba daya takasayin wani tunani me kyau dan akiyasi baza ta wuce sha shida zuwa Sha bakwai ba. Ta sashi tayi agaba Tana wani irin kuka me taba zuciya manyan idanunta sun kumbura sunyi suntum muryarta ta dashe , ba'akojiyo sautin kukan nata. Tana Nan zaune ahaka ta jiyo Kiran sallah ahankali ta zare hannuwanta Dake cikin nasa, so take taje tayi sallah ta roki Allah ya dawo mata da fafinta. Bayan tayi alwala ta dawo, ta zauna, agabanshi Tana me cigaba da sheshshekar kukan ta, ruwan dake fuskarta da Kuma hawayen dasuke ta ambaliya ne suka sami nasarar d'uga akan kyakykyawar fuskar fafin nata. Hakan kuwa yayi dede da Jan wata kakkarfar ajiyar zuciya da yayi kana alokaci daya yake bude idanunsa wanda suka sauka akan kyakykyawa Kuma kamilalliyar fuskar yartasa. hannunta ya kama, wanda jin haka yasa ta farga da farkawar fafin nata. cikin wani mabayyanin farinciki ta fada jikinsa tare da kankame shi tamkar za'akwace matashi. cikin dariya dariya kuka kuka take cewa !"fafina katashi? dama nasan bazaka tafi kabarni ba nasan kanasona kana tausayina baza kabarni ni daya ba fafina. yunkurawa yayi dan yana san tashi da sauri ta kamashi ta temaka masa yatashi tsaye, shafa kanta yayi yace jeki sallah bintu nima bari nayi alwala, a'a fafi muje na temaka maka kayi alwalar jikinka babu karfi bintu ta fada cikin tausayawa mahaifinnata. girgiza mata kai yayi yace!" kiyi naki lokaci Yana guduwa ni zan iya karki damu, to haka dai ta hakura badan tasoba gani take Kamar idan ya fita baze dawo ba hijabinta tasaka tare da daidaita nutsuwarta kana ta funkanci alkibla. Bayan sun idar da sallah ne sukayi karatun alkur' ani kamar yanda suka saba sannan ta bude haddarta tayi bayan yaji ya kara mata a inda yanzu tana kokari cika izufinta na hamsin da uku. ahankali ta mike ta mayar da kur anan inda suke ajiyewa ta dawo ta zauna agabansa tare da sunkwi da kanta saboda hawayen dasuke kokarin zubo mataasannu ya sa hannunsa ya dago fuskarta Yana me kada mata kai alamun kar tayi kuka haka nan ta daure ta hadiye shi. acikin kimtsatstsiyar murya da kokarin nuna mata babu abinda yake damunsa. yace mata!" fadima me yasaki kuka ? ko kinyi zatan na mutune ? da sauri ta gyada Masa kai Tana kokarin danne kukan dakesan kwace mata. murmushi yayi me cike da ma'anoni masu yawa, kana yace!" to kiyi hakuri ki dena kuka ko babuni akwai me temakon ki, cikin sauri ta kalleshi hawayen da takasa hana zubarsu suna tsiyayowa tace!" fafi waye yake da gwarin gwiwar temakona bayan kai? yace !"Fatima akwai shi Allah ne ze turoshi da sauri ta katseshi da cewa !" a'a fafi kana sani Ina cire tsammani, kana sani inaji araina na kusa rasaka fafi inajin tsoran faruwar wani abu ni banaso ka tafi kabarni a duniyar Nan me cike da azzalumai marasa tsoran Allah . Jawo ta jikinsa yayi yana bubuga bayanta alamun rarrashi shikaɗai yasan taskun da yake ciki rayuwarsa tana cikin barazana baya san tashin hankalin fatima kokari yake yana 'boye mata, dan yasan ita din me rauni ce tabbas yasan shi bame tsawan rayuwa bane zuciyarsa Tana cike da tsananin fargaba akan rayuwar salihar yartasa yana addu ar Allah ya cigaba da rufe idanun makiyansu akan salihar yartasa. ************** Abuja Alhj Balarabe estate zuri'ace guda babbar zuriya wadda tayi suna acikin fadin kasashen duniya. zuri'ace wadda zamu iya kiranta da zuriyar ban kashi zuri'ace ta tushen larabawa, amma' yanzu saboda aurataiya, an cakudata da wasu yarirrikan da kuma mutane ma banbanta ahalaiya da dabia ... Dan Kari har yanxu ba afara wasan ba. akwai, abubuwa masu tarin alajabi ,tausayi, bakin hali, Jarumta SADAUKARWA da Kuma KUDURAR ALLAH se uwa uba soyayya me taba zuciya dasa mutum cikin shauki Shin Wai waye fatash? Wacece fatima ? Meye asalinsu ita da fafinta? Ina mahaifiyarta ? Meye akunshe aziciyar fafi? Wai suwaye makiyansu shida diyarsa? Wacece abigel ? Me danta fatash yayi da har ya jefa rayuwarta atashin hankali ? Me pastor James yake nufi da kalamansa na cewa duk wanda yase rariya yasan zata zubda ruwa? Sannu sannu bata Hana baya ns zuwa duk zaku samu amsoshinku daya bayan daya ku dai kuci gaba da bibiyata tare da sambado comments danshi ze bani kwarin gwiwar cigaba da rubuta wannan littafin me cike da abubuwa masu tarin yawa Ina jiran comments kafun naci gaba da gashi...... Fatima yusha'u adam *KUDURAR ALLAH* *NA* *Fatima y Adam* Free book. *page 2* __________________________ Bismillahirrahmanirra Dajin me tsananin, duhuwa da dogayen bishiyu, babu abinda zakaji se amon muryar !" nan,wanda hakan yasa dajin yake wani irin gigiza bishiyu na, kadawa, tamkar iskar damuna. Sautin muryar nan ba daga ko Ina yake fita ba," illah cikin gidan Dake cikin tsakiyar dajin nan, shi daya kwallin kwal. Abun mamaki, acikin gidan babu wasu kayan kawa, banda wasu muggan ababan tsoro. duk 'ban garenda da ka kalla to akwai' abin da zakayi tozali dashi wanda ze kusa sa numfashin ka wuyar fita. Mutanene wanda akalla zasukai kimanin su ashirin,kowan' nen su Yana sanye da jan zani da kuma 'kwarya, ahannunsu, suna durkushe akan gwiwowinsu, babu me 'kwa'kw'kwaran motsi acikinsu dan sunyi amanna da abinda suke aikatawa shine ze basu nasara arayuwarsu. Shugaba azikwi Wanda shine yakasance shugaba acikin, kungiyar, Zaune yake Kan kujerarsa ta mulki, fuskar nan tasa, babu kyan gani gaba daya ya juye ya koma wata irin mummunar halitta, shi ba mutum ba Kuma ba dodo ba , ita kanta kujerar mulkin da kafar mutum akayita haka ma hannayen ta na mutum ne. Kai jama a idan daranka kasha kallo. Cikin wannan katuwar muryar ya bude baki !" se ga wani irin hayaki na ciccidowa tamkar hayakin turare. A haka ya Fara magana !" cikin daga sauti Wanda hakan yake nuni da Yana cikin tsananin fushi. 'Yace " haka dama mukayi daku ? bance ku kashe shiba? lallai kuwa to kusani, tun wuri d'an zaki ya riga ya girma , kunyi sake kunyi sakeeee" ya 'karasa fada cikin wani irin mummunan sauti, wanda hakan yasa gidan, da dajin suka Fara wata kakkarfar girgiza. Mutumin Dake fuskantar shugaba azikwi wanda yayi kokarin Fara goge!" zufar da take ta faman keto mashi tun Fara jawabin shugaba. Cikin tsananin rudewa da tashin hankali mabayyani Yace !" shugaba atemaka asamo mana mafita ayi mana afuwa akasi, akasamu' amma' tabbas, mun kasheshi. Wata irin tsawa shugaba 'azikwi yayi masa yace!" da da' akwai mafitar da' hankalina ze tashi ne? nayi iya'yina amma' nakasa ganin komai se tsananin duhu dodo jack, ma yayi fushi dan be taba, haduwa, da irin wannan matsalar ba. Yaci gaba da cewa!" tabbas nashiga rudani. wannan ba, karamar matsala bace dole se munyi wani abu akan wannan gagarumar matsalar." Gurin yayi tsit bakajin motsin komai se na ka'dawar da bishiyun dajin,sukeyi saboda razanin da muryar shugaba azikwi ya jefasu aciki. na kusa da wanda yay magana! afarko shine cikin tsananin biyayya yace ! "shugaba ayi Mana afuwa agafarcemu asamo mana fafita kasan komenene zamu aikatashi indai akan samun masarar mune. Yana rufe bakinsa wata kakkarfar guguwa ta taso gaba daya ta shiga zagayasu se da akadauki kusan mintuna biyu, sannan guguwar ta bace, Shugaba azikwi, ne yashiga babbaka wata mahaukaciyar, dariya wadda ta Kuma hargitsa jejin gaba daya tsuntsaye da namun jejin suka firgice kowa yashiga nemarwa rayuwar sa da dauki. Saida ya gama mummunan dariyar tasa, kana yace! " yayi dodon mu me share mana kukan mu bama taba shiga matsala baka, kawo mana mafita ba, mukuma munyi maka alkawarin baka duk abinda kanema awajen mu." Juyawa yayi ya fuskanci , mutanensa sosai gami da dayin wani shu'umin murmushi,wanda ya Kara munana fuskartasa,kana yace!"muna mika godiyarmu ga dodo jack, domin yakawo mana mafita bisa ga matsalar da Muke kokarin, antayawa' amma' Kuma akwai manyan sharadai, yaci gaba da cewa zamu bawa dodo jack jinin jarirai da yanmata da samari , dan haka kowannen mu ze kawo way'annan mutanen guda biyar biyar ragowar sharadan kuwa bani ne zan fada muku ba dodo ze fadawa kowa aikin da ze masa. A tare suka Mike suna wasu irin surutai !kowa da kwarya ahannunsa suna me ɗaukar alkawarin zasuyi biyayya ga dukkanin abinda aka' umarcesu. Acikin tsakiyar daren, ruhikansu suka koma zuwa gangunan jikinsu , Babu wanda zesan ba, mutum' amakwancinsu kasancewar kowannen, su gangar jikinsa na shimfide amakwancinsa... Bauchi Firgigit tafarka Tana Mai nanata "innalillahi wa'inna'ilaihiraji'un" amatukar tsorace take da wannan' mummunan mafarkin da tayi aduk mafarkan da take Babu wanda yafi munana Kamar wannan, fargaba tashin hankali tsoro sune suka taru suka mamaye zuciyarta. dafe kahon zuciyar ta tayi saboda ji takeyi tamkar zasu Faso kirjinta su fito. Da gudu ta fito daga dan matsakaicin dakin nata duk da cewar dare ya tsala 'amma' hakan be sa taji tsoran fitowa ba. Dakin fafi ta nufa zuciyarta na wani irin bugawa da karfi cike da tsananin fargaba ta tura dan langa langar da akayi makari dashi. Sallama tayi can kasan makoshinta. da wani irin hanzari ta karasa inda ta hangoshi ayashe tamkar wanda yay danbe, cikin tsananin razana da kuka take jijjigashi tare da cewa!" fafi fafi katashi me yasameka? me'akayi maka ? baka da lafiya ne? dan Allah fafi katashi wayyo Allah na dan Allah fafi katashi karka tafi kabarni , Ina zanje? waye ze tallafi rayuwata ? kaddara karki biyo mun ta wannan hanyar karki rabani da bangona, rayuwata zata lalace. Gaba daya ta rude bata cikin hayyacin ta sambatu kawai take zubawa kasancewar ta yarinya me kana Nan shekaru gaba daya takasayin wani tunani me kyau dan akiyasi baza ta wuce sha shida zuwa Sha bakwai ba. Ta sashi tayi agaba Tana wani irin kuka me taba zuciya manyan idanunta sun kumbura sunyi suntum muryarta ta dashe , ba'akojiyo sautin kukan nata. Tana Nan zaune ahaka ta jiyo Kiran sallah ahankali ta zare hannuwanta Dake cikin nasa, so take taje tayi sallah ta roki Allah ya dawo mata da fafinta. Bayan tayi alwala ta dawo, ta zauna, agabanshi Tana me cigaba da sheshshekar kukan ta, ruwan dake fuskarta da Kuma hawayen dasuke ta ambaliya ne suka sami nasarar d'uga akan kyakykyawar fuskar fafin nata. Hakan kuwa yayi dede da Jan wata kakkarfar ajiyar zuciya da yayi kana alokaci daya yake bude idanunsa wanda suka sauka akan kyakykyawa Kuma kamilalliyar fuskar yartasa. hannunta ya kama, wanda jin haka yasa ta farga da farkawar fafin nata. cikin wani mabayyanin farinciki ta fada jikinsa tare da kankame shi tamkar za'akwace matashi. cikin dariya dariya kuka kuka take cewa !"fafina katashi? dama nasan bazaka tafi kabarni ba nasan kanasona kana tausayina baza kabarni ni daya ba fafina. yunkurawa yayi dan yana san tashi da sauri ta kamashi ta temaka masa yatashi tsaye, shafa kanta yayi yace jeki sallah bintu nima bari nayi alwala, a'a fafi muje na temaka maka kayi alwalar jikinka babu karfi bintu ta fada cikin tausayawa mahaifinnata. girgiza mata kai yayi yace!" kiyi naki lokaci Yana guduwa ni zan iya karki damu, to haka dai ta hakura badan tasoba gani take Kamar idan ya fita baze dawo ba hijabinta tasaka tare da daidaita nutsuwarta kana ta funkanci alkibla. Bayan sun idar da sallah ne sukayi karatun alkur' ani kamar yanda suka saba sannan ta bude haddarta tayi bayan yaji ya kara mata a inda yanzu tana kokari cika izufinta na hamsin da uku. ahankali ta mike ta mayar da kur anan inda suke ajiyewa ta dawo ta zauna agabansa tare da sunkwi da kanta saboda hawayen dasuke kokarin zubo mataasannu ya sa hannunsa ya dago fuskarta Yana me kada mata kai alamun kar tayi kuka haka nan ta daure ta hadiye shi. acikin kimtsatstsiyar murya da kokarin nuna mata babu abinda yake damunsa. yace mata!" fadima me yasaki kuka ? ko kinyi zatan na mutune ? da sauri ta gyada Masa kai Tana kokarin danne kukan dakesan kwace mata. murmushi yayi me cike da ma'anoni masu yawa, kana yace!" to kiyi hakuri ki dena kuka ko babuni akwai me temakon ki, cikin sauri ta kalleshi hawayen da takasa hana zubarsu suna tsiyayowa tace!" fafi waye yake da gwarin gwiwar temakona bayan kai? yace !"Fatima akwai shi Allah ne ze turoshi da sauri ta katseshi da cewa !" a'a fafi kana sani Ina cire tsammani, kana sani inaji araina na kusa rasaka fafi inajin tsoran faruwar wani abu ni banaso ka tafi kabarni a duniyar Nan me cike da azzalumai marasa tsoran Allah . Jawo ta jikinsa yayi yana bubuga bayanta alamun rarrashi shikaɗai yasan taskun da yake ciki rayuwarsa tana cikin barazana baya san tashin hankalin fatima kokari yake yana 'boye mata, dan yasan ita din me rauni ce tabbas yasan shi bame tsawan rayuwa bane zuciyarsa Tana cike da tsananin fargaba akan rayuwar salihar yartasa yana addu ar Allah ya cigaba da rufe idanun makiyansu akan salihar yartasa. ************** Abuja Alhj Balarabe estate zuri'ace guda babbar zuriya wadda tayi suna acikin fadin kasashen duniya. zuri'ace wadda zamu iya kiranta da zuriyar ban kashi zuri'ace ta tushen larabawa, amma' yanzu saboda aurataiya, an cakudata da wasu yarirrikan da kuma mutane ma banbanta ahalaiya da dabia ... Dan Kari har yanxu ba afara wasan ba. akwai, abubuwa masu tarin alajabi ,tausayi, bakin hali, Jarumta SADAUKARWA da Kuma KUDURAR ALLAH se uwa uba soyayya me taba zuciya dasa mutum cikin shauki Shin Wai waye fatash? Wacece fatima ? Meye asalinsu ita da fafinta? Ina mahaifiyarta ? Meye akunshe aziciyar fafi? Wai suwaye makiyansu shida diyarsa? Wacece abigel ? Me danta fatash yayi da har ya jefa rayuwarta atashin hankali ? Me pastor James yake nufi da kalamansa na cewa duk wanda yase rariya yasan zata zubda ruwa? Sannu sannu bata Hana baya ns zuwa duk zaku samu amsoshinku daya bayan daya ku dai kuci gaba da bibiyata tare da sambado comments danshi ze bani kwarin gwiwar cigaba da rubuta wannan littafin me cike da abubuwa masu tarin yawa Ina jiran comments kafun naci gaba da gashi...... Fatima yusha'u adam *KUDURAR ALLAH* *Na* *Fatima y Adam* Free book page 3 Bismillahirrahmanirrahim Zuri'ar alhj balarabe zuri'ace daza a'iyakiranta da babbar zuriya. Ahline wanda yatara mutane kala kala masu hali da ban da ban dabi 'a kala da kala. ""Bazaka' iya fahimtar fuskar kowa ba bazaka iya, gane halin kowa ba me kyau ko mara kyau. Gidan alhj balarabe, zuriyace guda daya amma yaarika kusan hudune agidan saboda aurataiya da ta hada. Alhj balarabe balaraben maroko ne,kuma cikaken dan malamai dan abinnasu gadone. mahaifinsa babban malamine akasar ta maroko. "Mahaifinsa malam habu da mahaifiyarsa nana Wanda' asalin sunanta shine' aishatu. Asalin 'kaurarsu daga maroko, shine sanadin wata annoba da itace tayi sanadin kaurarsu zuwakasar nijer, daga nan suka sami masauki cikin kauyen agades. Balarabe mutumne, me tsananin zuciya da kokarin neman nakansa,shiyasa beyi kasa agwiwaba ya, bazama neman sana'a. Balarabe yayi sana' o'i da dama kama daga kayan gwanjo, kayan masarufi robobi da dai sauransu. "Yawo yakeyi gari' gari kasa' kasa yana kokarin kafa kansa. Alokacin da ya fara samun rufin asari se Kuma mahaifinsa yace !" yakamata yanemi yarinya me hankali ya aura, an dauki dan lokaci kafun ya gabatar da wata kanwar abokokinsa, safiya cikakkar buzuwa ce gaba da baya, me ilmi da sanin yakamata ga hakuri da kau da kai, Ba aja wani lokaciba aka daura aure' aka rufa, safiya' aka kaita gidanta wanda yake kusa da gidan iyayen mijinta. Shekara daya da yin auren yabawa iyayensa amanar safiya' yace!" shifa bega ta zama ba dole ze tafi neman kudi, mahaifinsa be hanashi ba sede ya gargade sa da ya dinga zagayo gida saboda matarsa. Haka kuwa balarabe ya, shiga duniya neman kudi Wanda be zauna ahaka ba ya se da ya hada da neman ilmin boko Be manta da gida ba Dan yana zuwa yayi, kwanaki se ya koma, ahaka ya hada masters dinsa Duk, fadi tashin da yake hakan besa ya manta da matarsa ba Yana me addu ar samun zuria ko sakara yawa dannyanaso yaga yatara zuri me yawa ko dan shi kadai ne oho? Kwanci tashi balarabe ya samunrufin asiri har ya gina musu gida, shida iyayensa suka koma. "Awata tafiya da yayi me duguri anan ya hadu da ya gana asalin babarbariya, kamar wasa se ga magana tayi karfi, rana daya balarabe yazo ya tafi da babansa da amininsa kuma makocin, su. aranar da sukaje washe gari aka daura auren suka juyo da amarya yagana. Alhj balarabe yafara tara kadarori ga kuma zuria me albarka "Bayan auren sa da yagana da wata biyu Allah ya albarkaceta da samun juna biyu, base na gaya muku irin murnar da, wannan' ahli sukayi ba, farinci kam iya farin ciki anyi awannan gida. "Bayan watanni, yagana ta haifi yarta mace' akasa mata sunan iya nana wato aisha Haka rayuwa tadinga gangarawa, kwanaki na zama watanni, watanni na zama shekaru yayin da arzikin alhj balarabe yake ta habaka, haka kuma yagana taketa ta hai famasa, yaya. ""Yayan yagana hudu kenan duk mata, ita kuwa safiya har lokacin Allah be kawo mata ba, Alokacinne kuma alhj balarabe ya kwashi, iyalansa da iyayensa suka koma nageria saboda ya riga ya kafa sana o'insa acan. Yana da manyan shaguna akano cikin kasuwar kofar wanbai wanda ake sauke dilolin, kayan gwanjo da kuma, kasuwar saban gari nan ma runfunane dashi kusan guda bakwai duk na dilolin gwanjo. se kamfanin sarrafa roba acikin garin abuja shima guda uku. se kamfanin shinkafa da na fulawa. ""Wannan kadanne daga cikin dukiyar alhj balarabe. Jigon dawowarsa nageria cikin garin abuja aiki yasamu ababbar kotun koli amatsayin alkali. "Ambashi katan gida da motar hawa duk da Yana da nasa. Daga nan rayuwa taci gaba da gungurawa alokcin yagana ta kuma, samun rabon da namiji. Alhj balarabe ya kara auren wata abokiyar aikinsa me suna zainab, wayayyar mace yar gayu, ita kuma zainab bafulata nar yolace iyayenta da danginta duk suna yola, Se dan' uwanta guda daya daya kenan abj shida iyalansa. shine yasamar mata aiki anan kotun kolin ta abj Matan alhj balarabe uku cas, yayin da mata biyu suke ta zazzago masa haihuwa, dan itama hjy zainab tuni ta jona da ya gana "Ayanzu haka yagana yayanta shida hudu Mata biyu maza, yayin da zainab take da hudu duka mata ita kuwa hjy safiya' buzuwar agades har yan zu shiru Babu rabo. Arziki fa se kara samun guri yake agidan alhj balarabe, dan' ayanzu shi kansa bazece ga' iya arzikin da yatara ba, yayansa kuwa duk sun tasa babbar yarsa wadda suke Kira da nana,karama itace me she kara goma se kanne, wanda duk ba wani taza_ rane 'atsaka ninsu masu yawaba dan dukan su da yagana da zainab din, kwai' nika sukeyi, dan haka tazarar bata wuce shekara daya zuwa da rabi. Cikin KUDURAR ALLAH hjy safiya' ta samu nata raban hakika alhj balarabe yayi farinciki tamkar ba ataba yi Masa haihuwa haka iyayensa mlm habu da nana sunyi, matukar farinciki da wan nan babbar kyauta ta, ubangiji. Kwanci tashi Allah me KUDURA ya sauki safiya' lafiya wadda yara suke mata lakabi da hijiya babba, ta haifi santalelen danta me kama da ubansa sak, saboda farinciki alhj balarabe kyautar kujerar makka yadingayi tare da hadawa da manyan kudade masu auki, hakika farin cikin wannan bawan Allah baze misal tu, ba. Abubakar yasamu soyayya ta wajen kakanni da kuma uba yaro mafi soyuwa acikin ahlinsa. "Daga nan kuma haihuwa ta bude tabangaren hjy babba, wato safiya yar agades, takara haifar yan biyu mace da namiji se kuma namiji me suna, aliyu Usman nabi masa se Kuma auta Ibrahim, maza biyar mace daya KUDURAR ALLAH, kenan, seda sukayi nasu suka gama sannan ita kuma. tazo tayi nata har taso, ta wucesu. Alhj balarabe,mutumne kamili, me tsananin riko da addini, me kokarin bin dokokin' Allah yana da, kyauta base lokacin zakka yake kyauta ba, kullum hannunsa abude suke akwai temakon addini, Yana kyautatawa iyalinsa balle kuma iyayensa,shi mutum ne me San gaskiya da fadin ta dan haka yake da farinjini cikin al umma talakawa sunyi kokarin jan ra ayinsa dan yatsaya musu amatsayin gwam nan jiharsu amma fir yace!" shi baze saka kansa aharkar da zatasa ya kauce hanya ba, dole haka suka hakura. Awannan tsukinne malam habu da matarsa nana sukace !"dole zasu koma gida, dan duba bayan ragowar yan' uwa, sede Kuma ashe ajali ne ya kirasu jirginda suka hau gaba daya ya tarwa tse' asakamakon birki da ya kwacewa matukin, "hakika alhj balarabe yaji mutuwar iyayen nasa, sede dole ce, Kuma rigace ajikin kowa yadda, mukazo haka zamu koma. Rayuwa taja, shekaru sun tafi, alhj balarabe ya samarwa yayansa in gan taccen ilmi na zamani da na boko. "ya' aurar da nana karama ga dan babban amininsa, salisu se sakina da ya aurawa yaransa rufa' i Alokacinne kuma'aka gama, gina babban estate dinsa wanda yakeso ya tasar da zuri' arsa ya hade su guri guda,duk kuma asannan ne yaje ya taho da danginsa na kasar maroko dan cika burin mahaifansa . "Baffansa 'kani ga malam habu, se kanwarsu wadda ta kasance' auta' adakinsu, sune danginsa najiki tare da iyalansu. "Baffa ali duk da ya tsufa amma' da dan kwarinsa , Se matarsa inna hafsatu, da da yayansa biyu,bab ban shine sa' an alhj balarabe sunansa hashir yana da matarsa daya yayansa uku se kaninsa me bi masa Mas' udu Shima matarsa daya da yaya hudu ahmad da, sadi se kuma nadiya da maryam. anan yazo ya hadesu' awaje daya kowa da bangarensa, ya bawa ko wannensu abunyi,kana kuma yayansu ya sanya su amakarantu ya basu' ingantaccen ilmi babu nuna san kai ya dauki yayan yan' uwansa tamkar nasa na cikinsa. Yayan hajiya yagana wadda' ake mata lakabi da hajjah sune nana karama, sakina hafsa, bilki, mansur, habibu Se yayan hajiya zainab ita kuma ana mata lakabi da inno, yaranta hudu mata sadiya,amina, zakiya, asiya Yayan safiya yar agadex wadda ake mata lakabi da hjy babba,sune' abubakar, hasana da husaini, se aliyu, usman, A yanzu gaba daya wadan nan iyali suna hade guri daya banda matan da sukayi aure awaje. Tofa anzo gun, ku gyara. zama domin jin me ake shiryawa,ake kullawa? suwaye masu shiryawar ? suwaye bosa bosan cikin estate din alhj balarabe? A, fage na gaba zamu zakuloka fatash dole ka fito muganka mujika ehe har yanzu ba'asoma wasanba. Dattijon bauci fafin bintu anya kuwa kana da gaskiya? ammafa bani na fada fans din, KUDURAR ALLAH ne.... Comments........ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GsLlgKf7MsD3M4Hoo7U65P 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 4 ``` 'Ya'yan alhj balarabe kaf dinsu, su goma sha biyar ne,maza takwas mata ta- ra, sai kuma na 'Yan uwansa hashir da mas'- udu guda uku-uku, Alhj balarabe Yana da abokai ko nace aminai guda uku, wa'yanda yayi matukar yadda dasu abokaine na amana matuka da gaske, alhj kabir me auduga da alhj nasir sai alhj shams, amintar dake tsakanin su ne yasa har suka hada au re tsakanin 'ya'yansu, alhj kabir 'ya'yansa uku namiji daya mata biyu, sai alhj shamsu shi yaran sa biyu'amma 'kananu ne kasancewar basu fara haihuwa da wuri ba sai bayan shekara goma sha biyar, sannan allah ya ba su yara biyu duk maza, alhj nasir ma babban dan sa guda daya ragowar guda biyu duka yarane shima tunda'aka haifi' ila wato isma'il saida aka ja shekaru kana aka samu kannensa, Ayanzu haka alhj balarabe ya dan man manyanta tunda har an fara aurar da jikoki amma baza ka taba gane haka ba, saboda tsufan alhj balarabe tsufane me kyau, wanda yake cikeda jin dadi gami da kwanci yar hankali, dan da 'kau yake,to baffansa Ali ma yake nan babu wata ta waya atare dashi sai na tsufa bare kuma shi da yake da manya 'ya'yan banki, Nana karama babbar 'ya agurin alhj balarabe ya aurarta ga dan amininsa alhj kabir me suna salisu suna zaune suma acikin garin abj da yaransu hud u khadija, haulat da Fa'iz da kuma ahmad, sai sakina da rufa'i yaran babanta alhj balarabe su kuma suna kano shi ya ke rike da shagonsa na daban gari,'ya'yansu biyar mata biyu maza uku, Sai hafsa ita kuma tana maidugu a 'bangaren mahaifiyarta tayi aure yaranta hudu itama duka mata rukayya fauziya kal tume da amina (amna) Sai Kuma bilkisu da nura hashim,yaransu uku najib da najiba sai hauwa'u, Habibu da saratu hashim yaransu hudu duk mata, farida zainab da sakinatu Husaini da nadiya mas'u d 'ya'yansu biyu mace da namiji, Ahmad da hasana yaran su uku duk maza nabil nazir da Kuma najib, Amina da bashir yayansu su kuma kananu ne basu haihu da wuri ba yaransu hudu, Zakiya kuma da dan alh nasir wato isma'il suma basu taba haihuwa suna nan cikin anguwar metama sule, Acikin 'ya'yan alhj balarabe e wadan dan sune sukayi auren zumunci, Abubakar shine da mafi soyuwa azuciyar mahaifinsa, kuma babba awajen mahaifiyarsa hjy babba, daya tashi sai bai tsaya, a ko'ina ba sai jihar gombe ya auro san kace ciyar bafulatanar matarsa zulaihat, kyakykyawar ba fulatanar gombe me kyak kyawan asali da tushe, ta kuma shigo cikin zuriya r alhj balarabe, taketa zaz zago masa kyawawan 'ya 'ya maza har guda biyar cur sai auta rahima, su shida ke nan, ayan zu haka biyar ne awajensu, mu'azzam muhamud abdurrahim da abdulsha- kur da Kuma auta rahima , Sai asiya itama tana kd da nata iyalin guda hudu Mansur abokiyar aikinsa ce me suna rabi'a yayan su uku Yar kanoce aikine ya kawota abj take zaune gurin yayanta, Aliyu Kuma kanwar aboki nsa ce" yayansu hudu maza biyu mata biyu Shi kuwa umar hjy zainab (inno) itace" ta hadashi da ' yar' aminiyarta hjy ladidi me suna nafisa, Hjy ladidi ' yar' salin garin minnace, aurene ya, kinki mota ya kawota garin abj da yarta guda daya tilo nafisa ba sai nace muku nafisa ' yar gata bace ku kanku zaku fada, kasan cewa kowa yasan yadda d'a guda daya yake agun iyayensa to irin wan nan son akewa nafisa agidansu, ""itaka kadaice'acikin suru kan alhj balarabe bata taba haihuwa ba ko batan wata kuwa, Yakamata musan meye halaiyar alhj balarabe, Alhj balarabe mutum ne me tsananin addini da ku ma amfani dashi yana da tausayi da hakuri haka kuma ya' iya mu' amala da mutane yana da san kyautatawa' al 'umma, ya gina makarantu da masallatai babu adadi, ga asibitocin da ya gina dan kawai tallafawa marasa karfi da Kuma marayu, wannan dalilin ne talaka wa su kaso ya tsaya musu amatsayin gomnan jiha amma sai yaki fur, acewa rsa" bazai taba iya shiga abinda zaisa yasa 'bawa mahaliccinsa ba, da wannan' hujjar tasa suka hakura badan sun so ba, Alhj balarabe baisan wace irin waina ake toyawa a,cikin estate dinsa ba,zuciyarsa daya yake kallan kowa baya kuma tunanin ana aikata wani mummnan ta adi, Yana can hadadden ban garensa shi da matansa dattijan da jin dadi da da ula suka boye tsufansu, Inaso makaranta kuyiwa labarin KUDURAR ALLAH kyaykywar fahimta, shine dalilin da yasa na fayya- ce muku sunayen ' ya'yan alhj balarabe da kuma wadànda suka rabeshi, Hali,dabi'a da Kuma manufa duk suna cikin labarin, CIGABAN LABARI ...…..Estate..... Wani kimtsetstsen falo ne me matukatukar gir ma da kyau wanda yaji kayan more rayuwa da dima- diman kujeru masu tsananin kyau da burge- wa,babu wasu yawan tar- kace acikinsa bayan sai- tun kujeru kala biyu sai kuma run dumemiyar placzima tv, Wani sanyayyen kamshin turaren wutane tare dana air freshener, wanda suka hadu suka bawa falon wani ni'imtaccen kamshi me san yaya zuci ya, Saidai duk wannan ni'ima hakan bai hana damuwar hjy zulaihat kassara ruhin ta ba, ""cikin tsananin damuwar dake cin zuciyarta tasa hannunta ta dafe saman kanta dake barazanar barin gan-gar jikinta sabi da tsananin sarawar da yakemata, Rahima dake tsaye akarshen matakalar da zata sadaka da falon ta bangaren hagu,yayinda hjy zulaihat ke ta bangaren gabas akan 'kawatattaun kujerun dining table din da ya ma maye gurin,ayanzu kanta a,kife yake dan haka batasan rahima ta zoba, sai kawai ji tayi andafa kafadarta, cikin tsananin tsoro da firgita!' ta dago kanta, ganin rahima ce yasa ta saki wata 'kak'kar far ajiyar zuciya, kana' ta yi saurin goge hawayen da suka 'bata kyakykya- war fuskarta tare da 'kirkiro murmushi akan fuskarta. Hannun rahima ta kamo tare da kokarin boye damuwarta, tace" rahima 'yanmatan Abbie ba ki koma bacci ba? rahima da tacika da tausayin ' ammin tata, tace" ammina yaza'ai na iya bacci bayan kina nan cikin wani'mugun yanayi da tsananin damuwar da take neman hargitsa farin cikina, "taci gaba dacewa" ammi tun ban mallaki hankalin kainaba nake ganinki cikin wannan damuwar, kuma duk sanda natam bayeki saikice mun bahurumina bane, ammi meyasa? ta fada cikin zubar da wasu zafafan hawaye, ""Cikin nutsuwa irin ta mata masu tsananin hakuri ammi tace"rahima kinutsu kidena wannan ihun haka!dan wani zai' iya shigowa ya Kuma fuskanci halin da muke ciki,hakan Kuma bakara min hatsarine agaremu ba dagani harke! wannan damuwar da kike gani' atare dani sirrin rayuwata ce"kuma jinsa ga wani fansane garayuwata da kuma rayuwar wasu,dan haka inaso kikama kanki da dakyau ki adana wadàn nan shir mammun tambayiyin'naki!takarasa maganar da wani irin hada rai dan karma rahima tasamu damar ragargazo mata wasu tambayiyin, Sai dai duk da hakan bata tsira ba,dan tana dasa aya,rahima ta dora da abinda yake cikin' zuciyarta tace" to ammi meyasa bazaki fadawa Koda 'ya'yan cikin ki bane? idan, ni kina ganin nayi kan-kanta da jin damuwa ko kuma sirrinki!kai tsaye ammi tace mata" saboda ban yarda da kowaba, ban' amince da kowaba, ban yarda, da amanar kowaba, haka kuma ban yarda da gaskiyar kowaba, da sauri rahima taca" ammi harda mu 'ya 'yanki ? wani' irin murmushi' ammi tayi me dauke da tarin ma'anoni kana tamike ta bar rahima zaune a agurin baki bude da madaukaki Yar mamaki!!!! Fatash........ Maman hamra rufe bakin taji nace fatash to se a page na gaba,😂😂😂 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GsLlgKf7MsD3M4Hoo7U65P 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 5``` Buga kofar dakin take iya karfinta,cikin kuka take fadin"fatash son ina hadaka,da allah kabude kofar nan kasaurareni, meyasa kake mun haka fatash?nifa mahaifiyarka ce" tafada cikin zamewa ajikin kofar tana kuma rushewa da wani kakkar fan kuka, ""Shiko wanda takeyi danshi baima san tanaiba, Fasto david shigowarsa kenan daga gurin bautar su, yaci karo da kukan matar tasa abigail, girgiza kansa yayi kana yanufi bangaren dansa fatash,dan ya tabbatar acan yake jiyo ihun abigail,hasashen sa kuwa ya tabbata, dan yana zuwa yatarar da ita abakin kofar se birgima take, tamkar wata karamar yarinya, tsaida idanunsa yayi akanta yana mai kiyasta irin, tashin hankalin da take ciki" jin kamar motsin mutum akanta, yasa tayi wata iriyar zabura, dan anata tunani tayi zatan fatash ne ya tausaya mata yafito daga dakinsa sai dai kuma taga akasin haka cikin sauri, ta wada jikin mijinta tana mai cigaba da kukanta,mai sosa zuciya, ahankali yasa hannu ya yi mata kyakykyawan masauki akirjinsa, yana mai ci gaba da dan bubbuga bayanta, cikin taushin murya yace"ya'isa haka kiyi shiru !' ko so kike ki kara tunzurashi? dasauri tasa hannu ta goge hawayen kan fus karta, Kana cikin karaya da da al'amarin dannata, tace'" david pls katemaka mun, karo'kar mun son yatemaka yabude yafito ina san magana dashi, yaufa kwana biyar kenan tun randa ya dawo ban gansa ba!' ta fada tana dan dukan kirjin david , cikin wani irin rudadden kuka me karya garkuwar jiki, cikin lallashi david yace" mata haba Abigail na gaya miki ki rage wannan damuwar da kuka,kinsan dai in har baki nutsuba dannaki bazai taba saurarenki ba dan kinfi kowa sanin halin abinki, to meyasa kikeso ki ruda kanki da kanki? cikin yadda da maganar sa, tace hakane david, to amma kasan abinda fatash yayi dole ne nakasa control din kaina, na shiga tashin hankali sosai yadda baka tunani!' david ya' gyada kanshi tare da cewa" muje ki nutsu tukun kafin na rakoki mu hadu mu lallabashi ko zamu samu ya canja ra'ayi!'cikin gamsuwa da shawarar mijin nata ta bi bashi suka nufi bangaren su". ......Bauchi....... Anan bauchi kuwa fatima ce zaune gefan fafi tana dama musu fura,tana dan jan fafin da hira shi kuma lokaci- lokaci yake amsawa saboda nisan da yake a tunani, can dai fatima ta aje furar tana dan tuttura dan karamin bakinta tare da cewa wai fafi tunanin me kake? ka barni ni daya inata magana ? yanzun da nice da yazu ka faramun fada,ta fada tana mai goge hawayen da suka gangaro mata kan kunci,cikin dawowa hayyaci fafi yace" batula ba tunani nake ba, ya.fada.da mur mushi a kan fuskarsa, dan yasan fatima bata son yana ce' mata batula, aikuwa tunzuro dan tattausan lip dnta tayi, cikin yanayin shagawabarta ta tsantsan yarinta tace" allah kuwa fafi ba sunana batula ba ,fafi ya danyi dariyar karfin hali, kana yace" a' a fa bintuna shima batula sunan kine kuma ai yana da dadi, meye abin rashin so cikin sa? tunzura bakin ta kumayi tace" fafi nidai banaso, yace to shikenan na daina fada, tafisu tafi sauran 'ya'ya, ya fada yana mai fadada murmushinsa, yace" maza miko mana furar musha kar yunwa ta karasamu,da sauri ta janyo kwanan furar ta bude musu suka farasha. Rayuwar fafi da diyarsa Fatima, rayuwace me cike da ban tausayi, rayuwa ce ta kunci da talauci, kasancewar shi fafi ba cikaken lafiya gareshi ba, fatima kuma yarinyace,mace abar tattali da killacewa, shiyasa fafi duk ciwon dayake damunsa haka zai daure ya fita yaje ya samo dan abin da zasuci, fafi ba sana'a yake ba sai dai dan ayyuka wanda basufi karfin girman sa ba, ahaka rayuwa take gungura musu cikin karfin gwiwa da taimakon ubangiji, Yayin da kuma ata wani bangaren, fafi yake fuskantar wani 'kalubale me tsananin sarkakiya, wanda shine dalilin dayasa yake kaffa-kaffa da rabin ranshi fatima,baya san tasan komai, kuma bayasan ta gane ko mai, ayanzu saboda acewar sa fatima tayi 'ka'kanta da shiga wannan babban al'amari aduk sanda ya tuna wata rana yana'iya barin bintu sai yaji tamkar zai shid'e dan tsananin tashin hankali, sai dai idan yatuna da allah da kuma irin addu'oin dayakewa diyar tasa sai yaji salama aransa, dan hakika fatima tana cikin jarrabawar rayuwa,wanda sam ita bata san da haka ba, yana koka mata'aduk sanda yatuna sarkakiyar da take cikin rayuwarta,sai dai yayi yakinin cewa Allah zai kawo mai taimakon ta, dan warware bakin kullin dake cikin rayuwar ta, yayi yakinin Allah zai kawoshi, tabbas mafarkinsa zai zama gaskiya,dolene ya bar rayuwarta kodan tseratar darayuwarta, bayasan shi dakansa yazamo silar karawa rayuwarta kacaccalewa,adai-dai lokacin dayazo nan atunaninsa, yasa hannu yashare hawayen dasuke ta damben saukowa saman fuskarsa, tare da cewa" fatima banasan kisan koni waye dole nayi nisa da rayuwarki!'ya fada abaiyane tare da kara sakin wani kakkarfan kuka wanda ya kasa boyeshi. .....Abuja..... estate Cike da nutsuwa hjy zainab (inno) ta dubi, aunty nafisa tace" yanzu nafisa kina ganin wannan halin da kika tsiri yi agidannan shine dai- dai awajenki!'ko kinaso kice mun rashin haihuwarki ne yajawo miki shiga wannan damuwar?to bari kiji na gaya miki gara tun wuri ki maida hankailinki jikinki, idan kuwa ba haka ba allura zata tono garma!' takarasa maganarta cikin nutsuwa da yanayin kamala, ta yadda idan ba kana gab da ita ba baza kataba cewa ga abinda take fadawa matar dan kishiyarta kuma 'yar aminiyarta hjy ladidi ba, Aunty nafisa taja wata doguwar numfashi me cike da fargabar bullowar wani gagarumin tashin hankali da kuma kwantacciyar damuwar da take kokarin tasowa ,tace" inno bazaki taba ganewa ba, ni kadai nasan yawan tarin damuwar da nake ciki da kuma tsananin fargaba, inno na rasa gane manufar mutanen gidan nan' idan ka dasawa wannan ayar tambaya daga baya sai kafara kokwanto, idan zargina yasauka daga kan wannan sai yafada kan wancan inno al'amarin gidan nan akwai rikitarwa da saka mutum cikin rudani, baka taba gane me amana bare me gaskiya, baza kataba gane mugu ba, bare makiyi!' tana dire maganarta inno ta dauka dacewa" kamar yadda kikeyi, ki boye fuskarki haka suma sukeyi harma sun zartaki a'iya taku, yadda bakisan zuciyarsu ba, suma basu san taki ba , yadda bakisan shirinsu ba, kema basu san nakiba, koni kaina da ke zaune gabanki matsayin surukarki ban san me kike shiryawa azuciyarki da rayuwarki ba!' tarufe zancanta tare da zubawa nafisar ido danjin abinda zatace" cikin kidima da bayyah nan nan tsoro!' tace'" ni kuma inno ? toni me zan kullah ? inno nima baki yarda dani ba? inno tayi wani dan murmushi !' kana tace" yo nafisa ai duk wanda ya kwana yatashi cikin gidan nan ba abin yarda bane, ko da bakone ya shigo ya fita saina dora masa ayar tambaya, bare kuma ke surukar gidan nan!' cikin tsananin mamaki aunty nafisa tace" to inno meyasa ? kuma saboda me? meyasa kowa yake zargin kowa aginnnan ? kuma suwaye ? inno tayi murmushi tare da cewa" nafisa nima bansani ba, bansan kuma suwaye ba, ban san a'ina bane ,da yaushe ne, duk ban saniba, shiyasa nace' miki ke kanki abar zargice agidan nan,'yayan gidan ma ba abin yarda mane bare kuma ke nafisa,kawai dai Ina baki shawara karki bari ta bare dake, shawarace kawai!'zukudi aunty nafisa tayi cike da matukar al'ajabin lamarin!' na cikin wannan estate wannan shi ake cewa" kowa tasa tafishshe shi". __________________ Wata hatsabiyar dariya shugaba azikwi ya buahe da'ita!' san nan cikin katuwar muryarsa, yace" nanuu kai kadai ne zaka shiga dakin nan dan cika ragowar bukatar dodo jack, bayan kai bama bukatar kowa yashiga, san nan Abu na biyu dolene mu nemo yarinyar nan domin itace ragowar cikar burin mu, rasata yana dai- dai da rushe rayuwarmu da farin cikin mu,haka kuma idan ba mubi 'ka'idoji ba shima kawota rayuwar mu, babban tashin hankali ne da rasa rayuka,dan haka bayan aiki da tsafi dole muyi aiki da tunani da lura da kuma tuggu!' yana rufe bakinsa wanda aka kira da nanuu yace" shugaba ina da yakini akan baza musaba umarni da san zuciyarmu ba, ita kuma yarinyar muna nan muna bibiyarta,datemakon jack bazamu kusre ba!' To fa waiya abin yakene? duk inda kuke zatansa ya wuce ku dan kucigaba da bina asannu. Comments........ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GsLlgKf7MsD3M4Hoo7U65P 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 6 ``` 'Dakine guda acikin estate din ta can wani bangare na musamman wanda ba kowane yakebi ta hanyarba, babu wanda yasan meye' acikin dakin da kuma mamallakan dakin,sai dai kuma wani abun mamaki babu wanda aka taba gani ya bude dakin ko kuma yabi ta hanyar,da dakin yake, dayawa-yawan zuciyoyi nakai komo da taraddadi akan dakin, haka kuma zuciya da gan- garjiki suna son kai kansu inda wannan dakin yake, amma kash,hakan ya kasa samuwa daga dukkanin bangarorin dake son sanin abunda aka 'kunshe acikin dakin da kuma amfanin zamansa anan, kai harma da mamallakan dakin. Adai-dai kuma wannan lokacin ne dije me aikin hjy madina matar mansur, tafito da wani kullin abu ahannunta sai yan dube-debe take kai kana ganin yanayinta zaka hango rashin gaskiya aidanunta,cikin sanda ta nufi can baya inda wannan dakin yake, alhj mansur da tun fitowarta ya hangota a lokacin da yake fitowa daga bangaren alhj baba(alhj balarabe)cikin sauri da azama ya mara mata baya dan ganin abinda take kokarinyi,abinka da namiji kakkarfa nan da nan ya taddata,cikin wata iriyar gugitacciyar tsawa,yace"ke dijeeee karki sake ki kara wani taku daga nan inda kike!'dije cikin tashin hankali da rawar jiki ta tsaya tare da juyawa dan ganin wanda yake neman fasa mata 'ya'yan hanji da wannan' razananniyar tsawar ,ganin uban dakinta tsaye yana aika mata da wani' shakurarren kallo me cike da gargadi da barazana,yasa ta kara kidimewa,da sauri ta karaso inda yake tsaye tana mai cewa"yallabai agafarceni wlh sani akayi bada niyar kaina nazo gurin nan ba, cikin tsareta da ido alhj mansur yace" dije.wani irin gan-gancine yakaiki ga zuwa gurin nan? kinsan kuwa komu bama iya zuwa hanyar nan amma ke kike kokarin saida ranki akan kudi!' wayasaka ki wannan aikin? kuma mezakiyi anan din?san nan meye wannan ahannunki? yayinda dady babba(alhj mansur) yakewa dije wadan nan tambayoyi ita tuni ta dade da antayawa' zuzzurfan tunani na yaya zatayi ta tseratar da rayuwarsu ita da yarta,tabbas idan bata kai wannan ajiyar inda akasata takaiba tana cikin tsaka me wuya,sannan kuma shima kaiwar wani tashin hankalinne wanda shima ya hada da rayuwarta, san nan fadin wanda ya aikota shima yana dai-dai da rasa rayuwar danta, to yanzu meye mafita agareta?kai suwaye anan gurin? ta ji wata murya daga bayansu ayayin da me maganar take nufosu saida ya karaso san nan ta fahimci waye alhj habib ne wanda ake masa lakabi da Abba 1,cikin nutsuwa ya dubi dady babba wanda yake ta faman muzurai yana wani hade rai,yace dashi yaya meke faruwane anan?cikin hargagi dady babba yace"kawai kaje babu ruwanka bana san saka ido da munafurci,Abba ane yayi murmushi cikin sanyiwa dan uwan nasa biyayya yace"yaya kayi hakuri ba Ina nufin wani Abu bane mara kyau amma kayi hakuri,dije kuwa hamdala tayi ganin ta samu hanyar kubuta daga wadan nan razannun tambayoyi daga uban gidanta,cikin sanda ta fece daga gurin ba tare da sun ankaraba. cikin fada-fada da yanayinsa na rashin hakuri yace"ai dama habibu dole ka bani hakuri tunda kasan baka kyauta mun,duk abinda zanyi idanka yana kaina ka daukeni tamkar wani mara gaskiya Ina amatsayin yayanka kuma babba acikin gidan nan idan ka dauke yaya nana da sakina da hafsa kaf gidan nan nine babba amma bani da damar da zan aiwatar da abu ya zauna acikin gidan nan, saika kai karata gurin alhj baba, to Ina mai tabbatar maka billahillazi idan baka fita harkata ba zaka ga abinda zai faru, babu ruwana da ciki dayan da muka fito dan wani lokacin rufin asirin da dan uba zaiyi maka dan ciki dayan bazai yi maka shi ba!' yana zuwa nan not azancen sa ya kada babbar rigarsa ya juya afusace ya bar Abba ane tsaye da tsananin mamaki da takaicin halin dan uwan nasa. Cike da razana da bayyanannen tsoro take duban nafisar, san nan cikin dan daga sauti tace'" nafisa kina da hankali kuwa? kinsan abinda kike shirin aikata mana kuwa!'sai kuma ta dan sassauta, cikin kwantar da murya tace" haba nafisatu yaya kike son bata rawarki da tsalle kinsan kuwa babban tashin hankalin da zamu dauwama aciki in dai ki kai saken da wannan' sirrin ya tonu,to bari in fada miki abinda har yanzu baki sani ba, alhj balarabe estate ta wuce duk inda kike tunani, ta wuce zatan me zato, a'iya tuggu da makirci, kowa yana' iya takunsa baza ki taba gane abinda ke cikin zuciyoyinsu ba,dan haka ki sake sabuwar damara indai har abinda kike fada gaskiyane!'ahankali nafisa ta dago kanta dake sunkwiye, idanunta sun kumbura sunyi ja tamkar garwashin wuta,tace'" mama na kasa!' damuwata tayi girman da bazata iya boyuwaba, Ina cikin mummunan tashin hankali aduk sanda naga dare yayi gari zai waye, damuwata 'karuwa take duk sanda na tuna lokaci yana zuwa da zan iya rasa umar,tsorona karuwa yake' aduk sanda na tuna, bansan wane rana bane wane lokacine, da wane yanayine wan can rudadden al'marin zaizo me cike da sarkakiyar da warware shi sai wanda ya kullah shi,mama ayanzu inajin garamun mutuwata da zuwan wan nan rana bazan iya kallon idanun umar ba, dana sani mama da na hakura da saukar KUDURAR ALLAH da ban kasance ahalin da nake ciki ayanzu ba!' ta karasa maganar da sakin wani rikitaccen kuka me bayyana abinda yake can cikin kasan zuciya,ita kanta mama kukan take yi wanda yake cike da cunkushewar zuciya na rashin tunanin mafita. Pastor David hause Kallo take masa me cike da tsoro,takowa yake gabanta cikin wani kakkarfan taku wanda duk takunsa daya ji take yana tafiya da bugun zuciyarta,fuskarsa me tsananin kyau da haiba da kuma tsananin kwarjini, ahade staf babu alamun murmushi bare dariya da dama ba al'darsa bace,tsayawa yayi akanta batare da ya tanka mata ba,dama tasan za'a rina da yaya ma tasamu yazo din,kallansa tayi sai dai ta rasa ta inda zata fara magana,tamkar ba itace me kururuwa da fade- fade akwanakin ba,daga kafarsa da yayi daniyar Bari wurinne yasa tayi hanzarin dawowa hayyacinta,tare da saurin kama tattausan hannunsa, san nan cikin rawar murya tace"FATASH...cikin wata murya me tsananin dadi wanda ta hade da yanayin fushi da muskilanci sai ta hadu ta bada wani daddan sauti,yace"don't coll me FATASH I'm doctor ABDALLAH,daga haka ya maida bakinsa ya tsuke tamkar bashine yayi maganar ba,cikin tsananin rudani da tashin hankali take kallallonsa, ga tarin maganganu da tashirya yi masa amma ta gagara furta masa Koda kalma daya saboda tsananin kwarjini da tarin ilhamomi da allah yay masa cikin kudurorinsa,tana kallo ya wuce cikin nisatstsan takunsa me cike da wani salo me burgewa, har ya bacewa idanunta, anan ne kuma takece da wani irin kakkarfan kuka me cike da ta kaici da tarin da nasani. FATASH. saurayine dan kimanin shekaru talatin zuwa talatin da daya, kyakykyawan gaskene fari amma ba tas ba, wata irin kalace dashi me wuyar samu, yana da saje wanda ya kara kawata kyakykyawar fuskar tashi,dogone me dogayen gabobi saidai kuma ba siriri bane acike yake babu rama ajikinshi,fatarshi cike take da gargasa me laushi yana da kyan tsari kwarai abangaren halitta,ta bangaren halayya kuwa zan iya cewa fatash murdaddan mutumne, tun yana karami iyayensa basu Isa su gane inda ya dosa ba, muskiline na karshe wanda baza kataba cewa ya ma taba magana ba ko dariya,yana da matukar zurfin ciki bai yadda da kowa ba sai kansa yana da tsentsami ta ko wane bangare,bai iya so ba baisan ya ake yi ba, shi dai kawai yaje asibitinsa ya yini aiki ya kwana aiki bayasan damuwa ta surutu, shiyasa baya shiga sabgar iyayen nasa musamman mamansa,tun yana yaro yake da muradin wani abu wanda ako da yaushe ake haska masa acikin mafarkinsa tun bay gane ba harya fahimta, kuma yasa aransa sai yabi wan nan hasken,tun yana shekara goma sha uku iyayensa suka kaishi can u.s dan yayi karatu dan kaucewa abinda suke zatawa yaron nasu, sai dai kash basu nan tuni Alllah ya saukar da KUDURAR sa akan fatash ba ya saukar da haskensa akansa,allah me kudura buwayi gagara misali, yayi cewa FATASH baze tashi cikin duhuba,zuwanshi u.s yasamar masa da nutsuwa ta yadda zai guda nar da rayuwarsa cikin haske, yashiga neman malaman addini manya-manya ya kuma dace,ashekarun da yayi a u.s ya haddace alkur'ani me girma ya haddace manya- manyan littattafan addini,ayanzu fatash yayi nisa kuma bazai taba jin kiran da mahaifan NASA suke masa ba. Mom abigail ce zaune tsakiyar rog capet din dake malale akasan falon,tayi kuka har ta gaji dan kanta, hawaye duk sun bushe mata,kofar falonce ta sanar da ita akwai bako wanda kesan shigowa ta hanyar wani Jan futula da yake kawo haske ta cikin falon,ahan kali ta jawo rumot din kafar ta danna nan take glass door din ta zuge, matar dake bakin door din ta shigo afuja atan kana ganin ta kasan tayi yar doguwar tafiya amma saboda bala'i naa cinta ko zama bata iya ba ta hau sababi,tace' ke abigail Ina wannan tsinan nan yaron naki? da baya ganin kan mutane da furfura maza ki fito mun dashi tun kan naci miki mutunci!' da sauri abigail ta mike tare da Jan hannun mamanta ta, cikin yanayin roko da magiya tace" mama kiyi shiru zo muje sama muyi magana fatash son yana nan kin san kuma bayasan hayaniya bare kuma irin wannan!'cikin hangame baki na matukar mamaki maman abigail tace" woo na wawoo abigail kene kika koma haka kinajin tsoran yarinyanki!'kasancewar yanzu cikin gurbatacciyar hausarta take maganar, abigail tace'"naji mama ni dai kizo muje sama zamuyi shawara dole sai mun hada da dabara kinsan halinsa yanzu fatash bazai murduba yana nan da halinsa saima wanda ya karu dakyar mama ta yadda da shawarar abigail,suka haura sama amma taki yadda tasa komai abakinta ,sai ta samu mafita, mama ta gyara zamanta tare da kara fuskantar yar tata,kana tace" abigail Ina mafitar?cikin yanayinta na damuwa race" mama aure zanyi masa Ina ganin shine kawai abunda zai canja shi daga wannan halayya,mama ta zuba mata ido kana ahankali ta furzar da wani zazzafan iska daga bakinta,tace'"kina ganin wannan itace' mafita agaremu? kuma kina ganin zai amince da wannan' din? cikin sauri abigail tace'"akwai hanyar da zanbi,Ina ganin niomy zan fara kawowa mu gwada akanta ko zamu dace, daganan sai mu fara addu'a akansa!' mama ta sauke tagumin da tayi,sannan tace' to allah yasa karyaa karya musu yarinya, dan haukan dankin nan kullum karuwa yake!'nan da nan mom abigail ta hada rai, tare da cewa" gaskiya mama kidaina cewa fatash mahaukaci,idan kika sake yajiki kuma wallahi babu ruwana!'ta fada ta na gunaguni. ...... BAUCHI..... Adame take kallon bakin fafi wanda yake tayi mata nasihu tun tashinsu a safiyar yau, ta fuskance shi yau kwata-kwata baya cikin walwala, duk da yanayin rayuwar dasuke ciki hakan bai hanasu walwala da farinciki ba,fafi yakance mata bintu duk wanda ya kasance me yadda da kaddara da tawakkali da jarrabawar rayuwa baya taba Bari asan damuwarshi Kuma baya bada kofar da za asan ahalin dayake ciki,shiyasa zaki ga Ina yawan janki da wasa domin kikasance me boye damuwarki aduk inda kika kasance!' rumtse idanunta tayi adai dai lokacin da taji fafi kana kiran sunanta,hakan ya nuna mata lallai tayi nisa atunaninta,fafi yace"da ita bintuna ban hanaki irin wannan zurfin tunanin ba kina karamarki dake ?cikin dan tura baki da kuma tarin kwallar da tacika fararan idanunta tace"fafi kaine,banaso,kadaina!'to bintu me kuma nayi? fafin ya tambayeta cikin sigar lallami, cikin gab da rushewa da kukan da ya tokare mata makoshi,tace"fafi wannan maganganun ne banaso jinake kamar wasiya kake ajiyemun!'shima cikin san rushewa da kukan yace " a'a bintu kar muyi haka dake ai ba yau na fara yi miki irin wannan zantukan ba!' cikin rushewa da kukan da ta kasa rikewa tace" fafi yau na musamman ne bantaba jin yadda nakejiba ayau,inajin wata kewa na mamaye dukkan sassan jiki da ruhina,fafi bazaka gayan abinda kake boyen ba har sai mun rabu, fafi kadaina boyen komai na girma fa,kar ka tafi kabarni baka gayan yadda zan fuskancesu ba,karka tafi baka gayan wadànda zan mamaya ba, kar ka tafi baka gayan inda zanje da abinda zanje dashi ba,fafi karka tafi baka bani tarin amsoshin tambayoyi na da suke kanka ba,kuka take sosai tamkar zata shid'e,fafi ma kuka take, kukan kewa kukan tausayi kukan fargaba,kukan wayyo rayuwa, yana matukar tausayin bintu,to yanzu me zaice mata? tayaya zai fara gaya mata?abu daya yasan zai iya nuna mata, wanda zai haska mata hanya,ta katse masa tunani da cewa'fafi kai nake sauraro,ahankali ya kama hannunta yace"bintu ba'abinda zan iya fada miki,sai abu daya,shine kije ki nemoshi aduk inda yake,zaku haska hanyar junanku dukkanin ku kuna bukatar temakon juna!'wani guri taga ya zubawa ido yana kuma girgiza kansa,yayin da bakinsa ya sarkafe ya kasa karasa mata,cikin kidima tashiga girgizashi tana cewa"fafi menene?ka fadamun a'ina yake yaza ai na ganeshi? meye sunansa?wane gari zan nufa?amma, Ina fafi shiru da alama dai fafi.... Tofa tafi-tafi dai akwai'fa murda-murda duk inda kuke zaton al'amarin ya wuce haka, soyayya zazzafa me cike da wani irin salo me ratsa,zuciya cin amana makirci, tausayi ga kuma curku dadden lamari..... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 7 ``` ...... ABUJA..... Pastor david ya zubawa mom abigail Ido yana sauraren tatsuniyar datake rangada masa,wai zata kawowa fatash matar aure,abin da matukar wuya,waisu mata meyasa kullum tunaninsu baya yakeyi,duba sai kace bata san halinsa ba,amma sai bai saurin gwasaleta ba,yace"yanzu kina ganin wannan mafitarce zata bulle miki?kina ganin yaron nan zai iya kallon macen da zaki kawo amatsayin matar da kikeso ya aura? abigail ina jiye miki aikin danasani akan abinda bazai amfaneki ba!'ya dire zancen da zuba mata Ido dan jin abinda zatace", cike da karfin gwiwa mom abigail tace"tabbas zanyi duk yanda zanyi dan ganin fatash awannan karon bai bani kunya ba,mace zan kawo mai wayo da kissa, wadda duk irin tsananin murdewa da kafiya da miskilancinsa sai ya sauko yabita, awannan karon bazanyi sakeba!'ta karasa maganarta cike da confidence,david yayi murmushi me dauke da ma anoni kana yace"shike nan amma kisani duk abinda ya biyo baya karki nemeni,sannan ina da sharadi bayan amin cewata!'da sauritace"meye sharadin?yace" nima akwai abinda nake shirin zartarwa akan fatash,yanzu na bar miki filin amma indai dabararki batayi ba zanyi abinda na shirya, kuma karki sake kice dan me? idan lokaci yayi kawai ki zuban Ido kamar yadda nayi miki karkiyi mun tashin hankali, karki daga mun hankali,Ina fatan kin amince!'batare da wani dogon tunani ba tace" ta amince. ....alhj balarabe estate.... Dijee ce agurfane gaban uwargijiyarta, babu abinda take sai kakkarwa da rawar baki,hankalinta amatukar tashe yake zuciyarta tana cike da alhini da danasanin shigowarta cikin wannan ahli,cikin wata irin gigitacciyar tsawa matar tace da'ita"amma dai ke dije ban taba sanin cewa bakyasan rayuwarki ba sai yanzu, kinsan kuwa abinda kika jamun?kinsan tashin hankalin da kika jefani?ko da ike dama naga take-takenki bakyasan wannan aikin da nasaki,to ki sani yadda aka fara dake to tabbas dake za'agama,kinriga kinsan sirrina ayanzu baki da fita dolene kisawa bakin ki linzami ko dan rayuwar yaranki, kuma dolene mu gyara wannan bar nar tare,dan haka yadda nake cikin tashin hankali dole kema ki dandana kiji ya'akeji!'daga nan tayi wani shu'umin murmushi tare da jefawa dijee wayar hannunta tana ci gaba da wata dariyar mugunta,da sauri dijee ta kawar da fuskarta daga kan allon wayar dan ganin yadda wasu katti zaratan maza majiya karfi kewa danta masduk wani irin duka nafitar haiyaci,jini suke fitar masa tako ina,ita kuwa kanwarsa azaba suke mata da ruwa me tsananin sanyi dasaka mutum tafiyar suman wucin gadi,cikin wani irin rikitaccen kuka me taba zuciyar me imani tace" dan allah rankishi dade ki taimakamun kisa arabu dasu, na daukar miki alkawari duk abinda kikasani zanyi batare da kuskure ba, kiji kaina, suka dai suka ragen aduniya, sune sanyin idaniyata!'ta fada tana rike da kafar hajiyar ,fuzge kafarta tayi taja baya gami da tamke fuska, kana tace"dije wannan alkawarin dakika dauka shi kadai zai taimaki yaranki daga fadawa tarkona,dan haka kije saina nemeki! D.A.D special hospital.shine asibitin dr abdallah (fatash) cikin takunshi na zaratan maza karfafa masuji da da tsantsar kyau da kwarjini yanufi lifter hawa na biyar inda anan office dinsa yake, yana shiga sakatariar sa me suna nabiha tayi azamar mikewa tare da tattaro nutsuwarta,tace" good morning sir!'ko gefan da take bai samu alfarmar kallonsa ba, bare ita, yana shigewa ta saki wata kakkarfar ajiyar zuciya ta tsabagen tsoro da kuma azababbiyar soyayya me cin zuciya da ruhi. Hadadden office ne wanda yake cike da duk wani nau'i na amfanin lafiyar dan' adam,zama yayi cikin kyakykyawar kujerarshi me kama da ta sarauta,kana cikin yanayinsa me cike da nutsuwa yasa hannu ya fara duba wasu muhimman fayal, cikakkun mintuna goma da shigarsa sannan nabiha ta yi kokarin fara gabatar da marasa lafiyar dasuke ta tsumayin jiransa, Agajiye yake taka dogayen kafafunshi akan tattausan carpet din dake malale akasan tan gameman falon,idanushi alumshe suke dan bazaka taba tsammanin yana kallon gabanshi ba, Mom dake zaune tun misalin bakwai na mangariba tana dakon shigowarshi, tayi saurin mikewa dan tarbanshi sai dai kuma wani kallo da ya bita dashi me cike da alamun gargadi shine ya dakatar da'ita daga niyarta na kama jakar dake a hannunsa,ganin yana kokarin shigewane yasa tayi azamar bin bayanshi dan tasan indai tabari ganinsa yanzu ya kufce mata ta tafka babbar asara dan kuma ganinsa zaiyi mata matukar wuya, yana jin takunta amma sam bai kula ba, danshi magana daya zuwa biyu ma gagararshi takeyi,zama tayi afalonshi kana cikin marairai tar murya tace fatash son dan allah zanjiraka anan ka gama bukatun ka inason zanyi magana da kai! ta fada tana mai hade hannayenta alamar roko dan Jim yayi sai kuma ahankali ya gyada kanshi gami da karasa shigewa, Rawa tayi harda juyi dan tasan tunda ya riga ya amsa to tabbas zai fito ya saurareta, danshi indai yace zaiyi abu da wuya kaga ya sauya magana yau agareta farar ranace me wuyar zuwa. Kukane irin kukan nan me wahala wanda haryi take tamkar zata shide tun tanayi da karfinta harya zamana karfinnata ya kare sai wani irin Jan ajiyar zuciya me tsananin karfi, ita dai tana ji tana gani tasan fafin nata bai mutu ba, to amma me? gaba daya jikinsa asake yake babu inda yake motsi ajikin nasa,sai'idanunsa daya kafesu awake daya kwayar idanne kawai take jujjuyawa sai kuma numfashi dayake fitarwa sasa-sama, amma bada ban wadannan alamu ba to dashi da gawa basu da maraba, hannunsa ta kuma rikewa tana jijjigawa cikin dasheshshiyar muryarta da bata fita , tace" fafi Ina rokaka da allah katashi karkamin haka bani da kowa sai kai ina zansaka kaina? ta inazan fara nemansa ?a'ina yake? wayeshi ? fafi duk bansani ba, bani da nutsumi bare da bara, ni ban san komai ba akan rayuwata,fafi bazan iya ba ,bansan ta ina zan fara fuskantar wadan nan cukurkudaddun al'amuran ba,wayyoni kam bansan ina zan nufa ba fafi kayi min magana mana kaji fafi kace wani abu bintun kace agefanka tanai maka magiya, kaji tausaina mana ko 'ka'kane kaji fafina!'maganganu take iri da kala da na hankali da na tsantsan yarinta,sai dai kuma duk abanza baisan ma tanayi ba, abinka da lungu ba wasu jama'ane dayawaba,ba kuma tayi tunanin neman taimako ba, dakyar ta iya tashi tayi sallar isha tare da nafilar wuturi,zazzabine mai zafi ya rufeta ga wani wahalallan ciwan kai dayake neman bara mata kan gida biyu. ..ABUJA.. Sai da tayi zaman kusan awa daya afalon tana jiranshi batare kuma da ta kosa ba, har saida ya gama yangarshi kana ya fito.sansanyan kamshin sa ne yasanar mata da zuwanshi,anutse yake takawa har zuwa inda luntsumemiyar kujerarshi ta zama take, zama yay tare da mike sambala-sambalan kafafunshi ya kwantar da kanshi saman kujerar yana mai lumshe manyan idanunshi,shiru falon yayi bakajin komai sai karar na'urar sanyaya waje, ahankali mom tadan muskuta cikin taka tsantsan,dan yanzu wani babban motsi zatai yace zai bar mata wajen ba kuma tare da ta fadi abinda ya zaunar da'ita tsawon awa daya ba,cikin kokarin kalato jarumta tace"son dan allah kasaurari abinda zan fada maka ka kuma fahimceni, tasan bazai tankata ba, dan haka taci gaba da cewa"kasan ni maman kace bazan taba son abinda zai cutar da kai ba ina neman alfarma awajenka inaso awannan karon kabani martabata ta mahaifiyarka ka mutuntani kayi min biyayya kasani farin ciki akaro na farko arayuwarka!' ahankali yake bude manyan idanunsa wanda suke cike da bacci da kuma gajiya,d'an tashi yayi zaune, yana d'an taune lip dinshi kana ya fara motsasu ahankali yace"mom please I'm very tried if you finish the talking I need a space!'yadda yake fitar da salon maganar ma abin kallone balle ka saurari muryar dake fita dai-dai cikin wani hadadden turanci,mom cikin sauri da son ta karasa maganarta tace"basai ka koreni ba fatash yanzu zan baka falonka amma kabari na isar da sakona!'shiru yayi mata dama tasan da haka,dorawa tayi da cewa fatash aure mukeso kayi na samo maka mata dan nasan zakace baka da girl friend!' wani irin rikitaccen kallo yake binta dashi idanuwan nan sun kara girma yayin da fuskar ta kuma hadewa tamkar hadarin da zai zubda ruwa,tuni jikin mom yashiga bari saboda idanuwan fatash masu hukunta mutum aduk lokacin da yaso ba tare da duka ko zagi ba,sun shiga hukuntata tako 'ina tsabgarta suke ,saida ya tabbatar ta ladabtu kana ya janyesu tare da mikewa ya nufi bedroom dinsa ba tare da ya tankata ko kuma duban inda take ba,da sauri akuma rikice ta bar apartment din nasa gaba daya, tana maijin babbar faduwa agareta da tazama shashashar uwa mai tsoran danta ....Bauchi.... Zumbur tayi ta mike tana mai nanata kalmar innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un,agigice tashiga laluben fafi saboda mummunan mafarkin da tayi, wanda bata fatan ya zama gaskiya,sai dai kuma ga dukkanin alamu mafarkinta nema yake ya zama zahiri dan bil hakki take neman fafi adakin amma yace daukar ni idan kin ganni babushi babu alamar sawunshi,loko da sako tamkar wani allura haka take bi tana dubawa acikin gidan, ta daina gane komai bata ganin komai tamkar wata zautacciya haka ta koma ,bata tunanin komai kawai hange da duba take a'ina zataga fafi har kiran sallar asuba tana abu guda sunturi kawai take tana shiga tana fita ita daya bata da mataimaki sai allah gwanin kuka gwanin tausai rayuwa tayi mata duhu kwakwalwarta da tunaninta duk sunjuye. ..…ABUJA.... Ayau asabar misalin karfe takwas na safiyar ranar, pastor david ya gama shirinsa tsaf dan kaiwa amininsa alhj habib ziyara da kuma isar da muhimmin kuduri da tarin manufofi acikin zuciyarshi wanda shine babban dalilin zuwanshi cikin estate din na alhj balarabe, ya dade yana bibiyar ahlin na alhj balarabe dan samun kusanci me karfi atsakanin sa da yayan gidan, yakuma dace yasamu abinda yakeso, dan ya 'kullah 'ka'k'karfar alaka tsakaninsa da alhj habib, hatta yaro karami indai a estate yake yasan pastor david sai dai a idanunsu pastor david ba Crista bane dan da sunan musulmi yaje musu, dady jafar shine sunan da ake kiransa dashi acikin ahlin alhj balarabe. Fakin yayi acikin katafariyar farfajiyar dake shashin alhj baba,bayan ya rurrufe kofofin motar da key din dake hannunsa, kai tsaye ya nufi katuwar kofar glass din da zata kaika har cikin falon alh baba,kafin ma ya taba madannin jikin kofar tuni ta wangale dan tuni CCTV ta nuna zuwansa. Yana shiga ya zube gaban alh baba yana gaishishi cikin tsananin girmamawa,alh baba yace tashi jafaru kazauna Allah yayi muku albarka!'ya amsa da amin baba muna godiya Allah ya kara girma yajikan magabata!'alhj baba ya amsa cikin jin dadi hakanan yake ganin kimar alhj jafar da mutuncinsa yana kuma girmama alakarsu sosai ya daukeshi tamkar d'an cikinsa,cikin mutumtaka da kamala alhj baba yace da alhj jafar, nayiwa duk wani wanda yakamata atattauna dashi magana dan haka yanzu zasu karaso baki dayansu!' yan halak kuwa yana rufe bakinshi sai gasunan kusan duk atare, kasancewar yau weekend kusan kowa yana gida danshi alhj balarabe duk yayansa yan bokone kalilanne suke kasuwanci acikinsu. Bayan gaishe-gaishe atsakanin su ne kuma alhj baba ya dubi alhj jafar yace"to jafar kace kana neman alfarma agurin ahlin gidan nan, kuma baza ka nema ba harsai na tara maka manyan yarana maza wanda dole sai da saninsu za'a'iyazartar da wani abu muhimmi acikin gidan nan,to gasu dan haka muna sauraronka!'alhj jafar yayi gyaran murya tare da gyara zamanshi kana yace"baba dama wata alfarmace nakeso ayimin acikin gidan nan wanda wannan alfarmar ba wani abu bane illa inaso d'ana abdallah zai dawo gidan nan da zama,wata zabura da alhj mansur yayi ita ta dakatar da dady jafar daga maganar da yakeyi, cikin wasiwasi da matukar shakku daddy jafar ya zuba masa ido dan yanaso ya karanto abinda yake kasan zuciyar mansur, alhj baba ne yace"munajinka jafaru kayi shiru!'numfasawa dady jafar yayi san nan yaci gaba da cewa"baba abdallah wani irin rikitaccen mutum ne kuma miskili me wuyar sha'ni,nayi-nayi ya fito da matar aure yakiya hasalima baya saurarona haka mamanshi duk wanda zaiyi magana ta bayan kunnenshi take wucewa,shiyasa na zauna nayi tunani me kyau akan abdallah naga dacewar kawoshi cikin ahlinka ko da bai samu macen da tayi masa ba zai dauki darasin rayuwa,kuma zai iya canjawa daga yanayin da yake ciki da kuma matsananciyar damuwar dayake ciki tunda nan wajene na jama'a da hada-hadarsu!'ya kare maganar yana mai tsurawa fuskar dady ane ido dan ganin yadda yake ta antaya masa harara tamkar idonsa zai fado,gyaran murya alhj baba yayi kana cikin nutsuwa yace"jafaru kan wannan dan batun ne kace sai na tara jama'a kamar gangamin daurin aure?kana ganin ko habibu kasamu da maganar nan bata isa ta wadatar ba?dady jafar ya sunjyiyar da kansa yana mai neman afuwa gurin alhj baba yace"baba ayi min gafara nayi kuskure amma naga kamar sai hakan yafi asanar da masu hakki!'alhj baba ya junjina kai,sannan yace"babu damuwa jafaru ni dai ta bangarena na amince abdallah jikana yazo ya zauna da yan uwansa, kuma duk yarinyar da yaga tayi masa indai babu maganar wani akanta to na bashi ita ya aura!juyawa yayi yana mai kallon yayan nashi da kuma yan uwanshi alhj Hashim da alhj mas'ud yace"idan da wani mai magana zai 'iya!' dady ane da dama kiris yake jira, ya zaburo cikin yanayinshi na zafi da ya shiga jikinsa yace"baba nifa Ina ganin kamar hakan bai dace ba bamusan manufarshi ta kullah wannan munafurcin ba to inba gulma ba haka kawai za'akawo katan gardi ace wai ya zabi mata bazai iya zuwa ya zaba ya koma inda ya fito ba!'ya karasa maganar cikin huci da hakilo shi adole baba ya fahimceshi, alhj hashir wanda suke kira da baffa ya dan numfasa kana cikin taushin murya da kamala irin ta manyan dattijai masu daddako, yace" haba mansur ya kana gima kana abun kananan yara duk ga kannenka nan zaune babu wanda yay irin wannan abun sai kai, dan allah ka dinga nutsuwa karka zama babban kobo meye abun tada hankali acikin wannan maganar, ka nutsu ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru sai alkhari insha allah!'abba mas'udu ma yace" hakane zancen ka yaya shi mansur baya daukar abu da sauki ne kamar yan uwansa, shiyasa kake jawowa kanka abubuwa da yawa ka nutsu dan Allah haka mansur kajiko!' ya fada cikin rarrashi da san kwantar mai da hankali,shi dai dady ane yayi shirune kawai dan anfi karfinsa amma ba dan yaji hankalin nasa ya kwantaba, Abba two wato alhj habib yace"to yaushe d'an namu zai karaso danni har na 'kagu naga zuwansa cikin ahlinmu!'ya fada yana sakar wa dady ane wani kayataccen murmushi tare da dage masa gira na irin to ya kagani din nan,dady jafar yayi dariya yace karka damu aboki insha Allah yana nan tafe!' Abba Ali yace" kaga sai asha shagalin biki dashi tunda yanzu baifi saura sati biyu ba bikinsu fa'iz!' abbi husain ne ya karbi zancen da cewa"tabbas zaisha hayaniya dan bikin mutum takwas ba wasaba!'nan dai suka cigaba da dan tattaunawarsu daga karshe kuma kowa ya nufi sabgarsa, dady jafar ma gida ya nufa kai tsaye da kudurin tunkarar abdallah da maganar komawa ahlin estate. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 8 ``` Yana zuwa yatarar da mom abigail zaune afalon idanunta sunyi jawur da alama taci kuka ta koshi, bai saurareta ba ya wuce apartment dinsa dan yasan ta tsuniyar gizo bata wuce koki,yasan abinda ta kawo ba mai yuwubane shi yasa ma bai fasa tun karar alhj baba da batun komawar abdallah gidan ba. Saida ya gama duk wani abu da ya danganci rayuwar sa ta yau da kullum kana daga cin abinci wanka da dai sauransu. yana kokarin fitowa daga bedroom yaci karo da ita tana kokarin shiga bedroom din nasa, dan haka sai shi ya dakata da fitar, wato ta ga bai da niyar fitowa shine ita ta biyosa, dama baya sawa akansa lallai sai tazo ta kula da al'amuran rayuwansa dan bai saba da hakan ba,murmushi yayi kana cikin dan tsokana ya kama hannunta yana cewa mom abdallah ya akayine naganki wata iri!'aiko tamkar jira take tasake masa kukan daya ke ta cin ranta tun shigowarsa, kamata yayi ya zaunar da ita abakin gado kana shima ya zauna agefanta, cikin san lallaminta yace" to kuma daga tambaya sai kuma kuka dan dai ke bakya girma kina fa da yaro kamar abdallah!'cikin Jan numfashi tace"abban fatash da kanka kake kiran fatash da wani suna ba fatash ba? me hakan yake nufi ?nifa gaba daya awatannin nan nakasa gane inda ka dosa idan kayi kamar kana bayana sai kuma kayi wani abun da zai jefani cikin shakka kamar da wani abu da kake boye mun abban fatash!'ta zuba mishi Ido tana jiran abinda zaice mata, hannu yasa yadan share fuskarsa kana yace"abigail me kike tunanin zan boye miki?kina zargina da aikata wani mummunan abune?da sauri ta girgiza kanta tace"bawai zarginka nake da wani mugun abuba abban fatash,kawai dai Ina maka kallon wanda yake boyen wani abu ko kuma kake wani shiri wanda ni ban sani ba!'da sauri ya tari numfashinta dacewa haba Abigail wane magana kikeyi haka ni Ina can Ina fafutukar nemar miki mafita akan danki ashe ke kuma kina nan kina saka mugun zato akaina!'bakinta har rawa yake wajen furta da gaske kake abban fatash ? kasamo mana mafita akan wannan lamarin? kasan ni yanzu aduniyar nan bani da wata babbar da muwa da tawuce damuwar fatash,yace"calm down mana ki nutsu muyi maganar da fahimta mana' ke matsalata dake kenan gaggawa!'tace" to naji Ina saurarenka!'cikin nutsuwa yace"abigail nasamo inda zan kai fatash horo akan abinda ya shafi addinin mu babu abinda bazai koya ba hatta da yanayin rayuwar duniya zai koya harma mata zai'iya samu acan,ko yanzu ma daga gurin nake fatan mu da burinmu yanzu ya amince!'mom abi tace"cikin sanyin jiki anya kuwa fatash zai amince da wannan zancen?ni dai bazan kara fuskantar yaron nan da wani zance ba, Dan ba saurarata yake ba hasalima baya ganin mutumcina,amma bana ganin laifinsa komi ya faru nice sila!'yayin da wasu zafafan hawaye suke sauka daga cikin idanunta tana mai danasanin abinda ta aikata masa amatsayinta na wadda akabawa amanarsa,to amma ai tayi na dama ya kamata ya manta ya kuma karbeta amatsayin mahaifiya.abban fatash ya katse mata tunaninta da cewa" bakece zaki masa magana ba ki barni da shi kawai nasan zai amince domin shima tafiyar karuwarsa ce da kuma babbar mafita arayuwasa,za kuma ta zame masa haske mai haska masa duhun da ya mamaye idanunsa!' ita dai mom bata fahimci inda zaurencen mijin nata ya nufa ba amma ta sami salama daga zababbakar da zuciyarta keyi. Baffa hashir ne zaune shida baba nura da kuma alhj nasir kana ganin yadda suka nutsu zakasan lallai tattaunawa suke mai matukar muhimmanci, baba nurane ya ce baffa kana ganin kuwa babu kamshin gaskiya akan maganar yaya mansur? kasan yaya mansur shine fitilar ganinmu mai haska mana hanya ni dai inaji kamar da alamar tambaya akan wannan jafar din!'alhj nasir ya dan muskuta tare da cewa"ni babu abinda yake dauren kai irin yadda yayi, yashiga jikin alhj baba yana matukar girmama jafar tamkar d'an cikinsa, alhj hashir yace abinda nakeso dakai nura lallai kayi kokarin binciko mana waye alhj jafar da kuma manufarsa ta kawo mana dansa cikin ahlinmu,dan tabbas kamar yadda ka fadane mansur shine fitilarmu mai haska mana hanya,kuma kasanarwa da salisu shima ya cigaba da yi mana binciken inda aka boye abubakar!'ismal yace maganar da nakeso nayi kenan nima dan wannan gabar ita tafi komai muhimmanci awannan zaman namu, ya kamata salisu ya kara azama akan wannan binciken, dan abubuwa karuwa suke kar lokaci ya kure mana!'dukka sunyi amanna da wannan shawarar,dan haka kowa yay damara dan aiwatar da kudurinsu me kyau ko akasinsa allahu a'alamu. ..... Bauchi..... Har aka kira sallah gari ya fara yin haske bintu na kan zagaye gidansu ciki da waje dan neman fafi, amma ba wata alama datake nuni da fafi yana cikin garin bauchi ma bare cikin gidan,tarasa me zatayiwa kanta kukan ma yanzu ya gagara,idanunta sun rufe sam bata kula da dan karamin diary acan gefe akasan dakin ba saboda bata iya ganin komai aidanunta ta zama tamkar makauniya,acan wani bangare na zuciyarta, tayi wani tunani a inda fafinta yakan yawaita yi mata nasiha akan dukkan cakudewar lamura saukinsu yana ga Allah kar ta nemi temakon kowa sai Allah domin shi kadaine mai jin kan bawansa shi kadaine mai kudura da irada kuma majibancin lamura, tunawa da haka yasa tayi azamar zuwa ta dauro alwala ta gabatar da sallar asuba, tare da mika kukanta gun allah buwayi gagara misali,tayi kuka tayi addu'a ta tayi a sujjada tayi atsaye tayi azaune tanayi tare da yakini da tawassali, ko da ta'idar wani irin kwarin gwiwa takeji tare da jin bata rasa kowa ba tunda tana da Allah buwayi mai kowa da komai, ahankali ta bude idanunta da suka kumbura saboda yawan kuka duk sun kan kance dishi dishi ta fara ganin dakin saboda dadewar da tayi idanun akulle ahankali suke washewa, can tashiga wurga idanuwan loko da sako na dakin tamkar dai tana tunanin zata ci karo da fafinnata, har ta kawar da fuskarta sai kuma ta kuma juyawa da sauri dan karamin diary din nan ta gani ,cikin sauri ta rarrafa ta daukoshi tare da zuba masa ido,budeshi ta farayi kamar amarki taci karo da zanzareran rubutun fafi jere reras akan farar takardar ,cikin nutsuwar da ta dan samu ta fara karanta rubutun. ..... ABUJA..... Sai misalin karfe 7 abdallah ya dawo, kaitsaye masallaci ya wuce saida yatsaya yay sallar isha kamar yadda yasaba kana ya shiga gida. baisamu kowa afalon ba dama koda ya samu ba damuwar shi bane cikin sassarfa da almun gajiya atare dashi ya wuce side dinsa,kayansa kawai ya cire ya daura towel ya fada toilet, kusan awa daya yayi kana ya fito,shiryawa yayi cikin wasu tattausan kayan bacci ya feshe jikinsa da turarukansa da yake amfani dasu wajen bacci daga nan ya nufi falo dan shan copy. da kansa yake hada kayanshi dan shi bai yadda wata kazamar arniya ta taba mishi koda kofar side ba bare taba abinda zaici, yana dora copy din akan tattausan lip dinshi aka murda handle din kofar, zubawa kofar ido yay yana tunanin ko momce tazo tacikashi da banzayen surutai,sai dai yayi kuskuren tunani, dady ne yashigo bakinsa dauke da sallama, ahankali ya sauke cop din copy daga bakinshi yana mai amsa sallamar dad din cikin taushin muryasa mai dadin sauraro,dady yace"abdallah ina fatan dai bakajin bacci dan magana nakeso zamuyi mai muhimmanci!'ya fada yayin dayake kokarin zama cikin daya daga cikin kujerun da suka kawata falon, abdallah yadan saki fuskarsa kadan amma ba murmushi yayi ba gata nan dai babu yabo babu fallasa,karasowa yayi kujerarsa dake fuskantar inda dad din ya zauna,ya hada hannunsa yana dan murzasu cikin salo da burgewa,kana ahankali yace da dady barka da dare!'dady ya amsa da alhamdulillah ya aikin naka?asaman labbah ya amsa dan wannan yar maganar har ta gajiyar dashi. Dady ya dan gyara zama tare da gyaran murya, kana yace abdallah wannan zaman da kakeyi cikin kunci ya isa haka duk danasan cewa ba azaune kake ba atsaye kake dan ganin ka cimma magauta ka kuma yakesu to amma kasan har yanzu lalube muke aduhu bamusan ko mai ba duk da kutsawar da nayi cikinsu to amma na gaza gane komai,abinda nayi tunani shine abdallah banine ya kamata na shiga cikin wannan ahli ba kaine ya kamata kaje kayi yakin da kanka wannan ahli ahlinka ne abdallah kuma idan kana zaune anan ta yaya za ka gano makiyanka da kuma inda suka kai mahaifinka?na fahimci wani abu guda acikin ahlin alhj balarabe wato shine akwai wata makar kashiya da yasa kwata-kwata ba'atunawa da mahaifinka ban tabajin habibu yayi alhinin rashin dan uwansa abubakar ba ban tabajin alhj baba yayi batun batan dansa mafi soyuwa agareshi ba kai hasalima babu wata alama dake nuna anyi wani babban rashi aciki wannan zuria ba,ban kai ga batunka bama tunda kai kana yaro karami,bansani ba kuma ko dai da akwai hakan ata wani bangare!'dan nisawa yayi kana yaci gaba da cewa abdallah dole kashiga cikin ahlinka kodan tseratar da wasu rayuka da basuji ba bare gani bayan mahaifinka na tabbatar akwai wadanda suke bukatar tai makonka dan haka ka shirya gobe sunday zamuje na rakaka!'gyada kanshi kawai yayi batare da yayi wani doguwar magana ba yace na gode dady!'dady ya shafa kanshi tare da cewa karka damu abdallah dole na taimaka maka domin nima ka,tai makeni dan tasanadin ka na samu haske arayuwata,yau gani amatsayin musulmi mai alfahari da musulunci,dole na tayaka da laluben neman masu san halaka ku kaida mahaifinka!' daga haka ya nufi kofa dan fita, harya dora hannu zai bude kofar ya tsinkayo daddadar muryar abdallah yana cewa dady bazasu ganeni ba saboda kamanni?dady yayi murmushi yana aiyanawa aransa lallai abdallah ya karbi batunnan da muhimmanci harda su tambaya,yace karkadamu abdallah Allah bazai bawa kowa ikon ganoka ba idanunsu zai rufe insha Allah,kayi itihara yau kafin ka konta kajiko!' jinjina kai abdallah yayi cikin nusuwa ya kuma cewa dady akara kwanakin tafiyar har sai na gama istihara!'dady yace hakane abdallah hakan yayi kyau,daga haka yabar falon, ..... bauchi..... Bintu kiyi hakuri abinda kikeso kiji daga gareni bazai samuba dan nima bansan komai ba amma abinda zan gaya miki yanzu shine fitilar da zai haska miki hanya, abu dayane zuwa biyu shine asalinki da kuma inda zaki nufa!' Dafarko dai bintu banine mahaifinki wanda ya haifeki ba amma uba nake agareki dan ciki daya muka fito nida mahaifiyarki uwa daya uba daya nine babba sai ita mu kadai iyayenmu suka haifa!' mu cikakkun fulanin adamawa ne,iyayenmu ba yan boko bane amma sun samar mana da ilmin boko dana addini mu bamasu kudi bane amma muna da rufin asiri dan bamu nemi komai mun rasa ba nayi karatun digree dina a maleshiya anan ne muka hadu da umar balarabe wanda yazamo amini agareni,ko da muka gama karatu bamu bar zumunci ba,har bikinsa naje nayi kwana biyu sai da aka gama na dawo. daga nan nima ban jima ba akayi bikina da yar uwata asma'u alokacin Ina aiki a wata babbar kotu dake nan cikin yola. Bayan shekaru kusan biyar Allah bai bamu haihuwa ba daga ni har aminina umar sai dai umar yafini shiga damuwa nine nake yawan bashi baki da yaci gaba da addu'a ,yana yawan cemun shi dai aure zaiyi da zarar yasamu matar da yakeso. Ana cikin hakane kanwata lailatu ta dawo daga makaranta, kasancewar akano take karatu a b.u.k tana zaune a hostel, tunda umar yake zuwa bai taba haduwa da Laila ba sai alokacin da ta kare karatunta, ranar da tayi exam din karshe aranar tayo gida tunda umar ya dora idonshi akan Laila shike nan yawada zazzafar soyayyarta,tun daga lokacin umar baya cikakken sati bai biyo jirgi yazo yola ba tun muna jin tsoro nida ita da iyayenmu har muka saduda, ba komaine yasa mukejin tsoron dangantakar umar da Laila ba illah tsananin kishi mai matukar zafi kuma na hauka wanda matarsa nafisa ke dashi agabana tasha alwashi iri da kala munana akan duk wadda tayi gangancin auren mata miji dan umar natane ita daya, wannan shine babban dalilin dayasa bamason wannan alaka ta soyayya. ana cikin wannan halinne kuma mahaifinmu ya rasu,bayan wasu yan watanni da rasuwar ne umar ya kuma dago da maganar sa da Laila wanda ni atsammanina ya hakura ashe wai mutuwar bafface tasa ya danyi shiru da zancen. Babban kuskuren da muka aikata alokacin ganin nine alwalin Laila yasa mukayi ganganci, nazo na kalallame hajjo mahaifiyarmu da zance mukace babu wanda zaisan da auren har sai ankwana biyu, umar ya kawo hujjar cewa idan alhj baba yasani kamar nafisa tasanine dan haka ayi auren daga baya sai ya kaita gida ya nunata yadda alokacin nafisa babu yadda zatayi dasu dole ta dangana, Haka kuwa akayi. aure tsakanin Laila da umar ya dauru, ya siya musu gida mai shegen kyau anan cikin yola suka tare duk sati yake zuwa yayi kwana biyu ya koma bansan me yake gayawa mai dakinsa nafisa idan zauzo . Haka rayuwa ta shuda har tsawon watanni biyar, alokacin matata asma'u ta haifa mun tagwaye harsuyi wayo. cikin ikon Allah Laila tasamu ciki acikin watansu na shida da aure, bazan iya kwatanta miki murnar da mahaifinki yayi ba domin ta wuce gaban kwatance, ahaka suka reni cikin atare cikin so da kauna har ya'isa haihuwa,aranarne mummunar kaddarar ta same mu kuma shine mafarin komai, lafiya kalau Laila ta haihu dama nace agida na zatayi wanka gaban hajjonmu dan haka daga asibiti can muka nufa dake umar saiwashe gari ne juma'a kenan zaizo dan haka nace kar agaya masa har sai yazo...... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 9 ``` Misalin karfe biyu na dare muna daki nida asma'u na dinga jiyo ihun kuka,zunbur muka tashi hankali atashe nida asma'u, tabbas kamar daga dakin su Laila nake jiyo ihun kuka da hayaniya , cikin sauri na fita, har asma'u ta biyo bayana, nace" da'ita ta koma ta kula da yan biyu karta sake tafito duk runtsi!' ba dan taso ba ta koma dakin, da sauri na zare key din dakin na rufe su, cikin sanda na doshi dakinsu Laila. Ina zuwa bakin kofar dakin na tsaya cike da tsoro da tarin fargaba, muryar Laila najiyo tana cewa" dan Allah kurufan asiri kubar mun yarinyata mahaifinta ko ganinta baiyi ba baisan ma'an haifeta ba!'muryar wani kato na kumaji ya daka mata tsawa yace" ke angaya miki ita kadai mukazo farauta?to harda ke uwarta da kuma wanda yai sanadin kulla alakar aure atsakanin ku wato munafukin yayanki, dolene yau dukanku ku ba kunci lahira!'yana kaiwa nan azancensa, kawai ni dai naga Laila ta fito aguje sabe da jaririyarta,cikin sauri na danki hannunta adai-dai lokacin naji wani yana cewa maza ku bisu karku bari su sha, ni kuma zanji da wannan tsohuwar!' wato hajjon mu ban tsayaba duk da haka sai dai addu'a danayiwa hajjona da kuma iyalina akan Allah ya karesu daga sharrin wadannan mutane da bamu san daga Ina suke ba. Allah ya bamu sa'ar fita daga cikin gidan, abinka da tsakiyar dare gari yayi tsit baka jin komai sai haushin karnuka,arewa muka nausa muna gudu iyakacin karfinmu amma abin mamaki mutanan nan suna biye damu, laila ta gaji iya gajiya dan haka na karbeki muka cigaba da nausawa cikin surkukin daji,bayan wasu bishiyoyi muka samu muka fake ganin yan ta addan nan na kokarin cimmana, gashi kuma da alamu karfin Laila yana gab da karewa yasa muka rabe abayan wasu ciyayi ganin mun bace musu yasa suka tsaya suna dube-dube,ji nai wani yana cewa kai washa gaskiya mutanen nan sunyi nisa kawai mucewa oga mun aikasu munjefawa namun daji gangar jikinsu sunyi fati!'sauran suka amsa masa da hakan yayi shashirgi!' dan suma sun gaji, muna jin komawar su sai da muka ja wasu mintoci kana muka fito,Laila duk tayi laushi ga danyen jego,kai tsaye muka dauki hanya batare da munsan inda muka nufa ba. Mun dade muna bulayi acikin dajin kafin muci karo da wata 'yar karamar rugar fulani anan muka ya da zango, baffa jauro shiyay mana masauki, ganin Laila da danyen jego yasanya kan kace kobo yasa matarsa inno tayi mata duk abinda ya dace dan gane da masu jego tayiwa yarinyar wanka ta gasa mata cibiya,akabamu abinci mukaci muka koshi,cikin kankanin lokaci muka dawo haiyacinmu, sai da muka nutsu sannan na bawa baffa jauro labarin abinda ya koromu daga gida, ya jinjina al'amarin tare kuma da tunanin suwaye wadan nan mutanen?zuwan kansune ko kuma turosu akai?mun kasa tsayar da tunanin mu akan kowa dan haka muka tattara al'amuran muka barwa Allah. Baffa jauro yace"amma yanzu ku dan dakata zuwa wani lokaci kafin ku koma!'nace"hakane baffa yanzu komawar mu gida bazai yuwu ba saboda bamusan masu neman rayuwar mu ba koda yaushe zasu iya kara farmakar rayukan mu!' ranar da kika cika kwana bakwai na rada miki sunan hajjonmu wato fadima amminki tana kiranki da hajjo ni kuma ina kiranki da bintu dan nace" bazan boye miki suna ba ko dan tunawa da mahaifiyarmu wadda bamusan halin da suke ciki ba haryau. Bintu nida mahaifiyarki muka baki ilmi na boko da na addini ko wanda yake zuwa makaranta bazai nuna miki ilmi ba,saboda kina da basira da kwakwalwa me.saurin daukar abu duk wani littafi da ake koyawa amakaranta mun koya mikishi haka ta bangaren addini duk wani littafi da aka koya manashi saida muka koya miki kama daga hadisi fiqhu akbari sira umdatul ahkam bulugu zaduzzau jaini da dai sauransu kuma alhamdulillah baki bamu kunya ba. Haka muka cigaba da rayuwa arugar baffa jauro bamu da wata matsala sai na tunanin gida da halin da su hajjo suke ciki, kina da shekara biyar muka fara shirin komawa gida sai dai kuma wani babban tashin hankalin ya kuma da katar damu,Laila ta gayamun tana wasu irin mafarkai mara dadi tana yawan mafarki da wasu mutane wadan da sam ita bata sansuba arayuwarta suna yawan zuwar mata awani irin suffa marakyan gani mun kasa gane inda mafarkin ya dosa,cikin wannan yanayin da amminki ta fada yau dadi gobe sai Allah baffa jauro baya zaune baya tsaye da nemar mata magani, ahaka muka kuma share wasu shekaru biyar din har me faruwa ta faru. Tunda Allah yasa muka shiga rugar baffa jauro Allah ya dora masa kaunarki, bintu dan haka baffa jauro yayi miki gata ya tsaya tsayin daka ya kula dake ya dafaki da kayan tsari kullum ta Allah da irin kalar rubutun da zaiyi miki ko tofi wanka kuwa ba dai ayi miki shi da ruwa normal ba sai anzuba masa abubuwa na tsari sauka kuwa kinshata bansan iya adadi ba, bintu kedin kudurar Allah ce kuma da sannu zaki zamewa wasu takalmin kaya!' babu wani abu da zaiyi tasiri akanki ke din kin riga kin gagara, anyi miki kuma ankoyar dake shiyasa bana shakka akanki domin duk wanda yanemi kariya da taimakon Allah to tabbas ubangiji yana tare dashi. Mafarkan da mamanki takeyi har nema suke su zautar da ita, dan har azahiri take ganin mutanen dasuke neman rayuwarta suna razanata, kalmar da suke yawan nanata mata shine, ta haifo abinda yake shirin rusa rayuwarsu sun kasa taba bintu ko inda take basa iya kalla, dan haka zasu dauke ta zasu rabata da ke so suke suyi maganin matsalarsu tun kan abin ya gagaresu, baffa jauro yayi iyayinsa amma dake kaddara tariga fata babu tsumi ba dabara dole abinda Allah ya nufa sai ya faru. kuma abincikensa yace"wadannan mutane ba jinnu bane sai dai kuma mushirukaine ma'ana manyan matsafane dasu kayi kaurin suna a har karsu ta shirka, haka muka dukufa da addu'a babu dare babu rana, sai dai kuma babu yadda zamuyi kaddarar amminki ahaka Allah ya shiryota. Awata safiyar juma'a ne muka tashi da gagarumin tashin hankali dan mun nemi Laila sama ko kasa mun rasata,na shiga tsananin rudani da tashin hankali kuka ya gagareni sai hadiyar zuciya kema da bawani wayo ne dake sosai ba saida kika tashi hankalinki kullum sai kinyi mana kuka akan mukaiki gurin amminki alokacin shekarunki basu fi tara zuwa gama ba, har yau har gobe ban dena kukan rashin yar uwata tilo danake matukar kauna ba. Sai da akayi shekara hudu da bacewar laila nima na fara fuskantar tawa matsalar,ni dakaina nayi tunanin mubar rugar baffa jauro, ko muna kusa dasune bamu sani ba, baffa shine yabani kudin da nazo na sai wannan dan gidan da muke zaune ya kuma bani kudi yace nayi wata yar sana ar kuma nasakaki amakaranta shi yabani shawara da muyi nisa da yola ko zamu samu nutsuwa, haka kuwa akayi baffa yasa nayi shigar da zan badda kama saboda samun akasi yakuma samo mana babur wanda zai kaimu har babbar tasha,munyi kuka sosai na rabuwa karma ke kiji labari dan har numfashin kine yake daukewa, dan alokacin shekarunki goma sha uku dan haka baki taba mantawa da baffa jauro ba kusan kullum sai kince na kaiki gurinsa da kyar nasamu kika daina yi min zancansa amma nasan badan kin manta dashi bane Bauchi shine garin da muka kuma Allah yasa na hadu da mutum me amana me suna gali, shiya kaimu gidansa har yasamo mana wannan gidan ya kuma bani shawarar abinda zanyi da dan jarin da baffa jauro ya bani yace na siyo kayan gwari kamar su mango data goba duk dai abinda yake lokaci, haka kuwa akayi, lokacin gobane da data dan haka su nake sai dawa, na kuma sami makaranta mai kyau nasakaki lokacin kina da shekara goma sha uku kasan cewar mun riga munyi miki kyakykyawan paundation kai tsaye aka kaiki aji uku na secondary nan dinma kawai an barkine dan ilminki yafi karfin aji uku. Ahaka muka dinga gungura rayuwar mu har kikayi candy wato ssce, ta bangarena wadannan mutanen suna ta bibiyata sai dai bantaba gaya miki ba saboda banasan damuwarki, alokaci daya kuma rayuwar ta tsaya mana cak dan jarin da nake tattalawa ya kare sai yawan rashin lafiya da nake Wanda duk baya rasa nasaba da irin ukubar da nakesha agun wadan can azzaluman kuma Nima sun sha alwashin sai sun rabani dake tunda na zame Miki katanga bayan su so suke su ga rayuwarki ta lalace shi yasa duk wanda take baki kariya sai sun ga bayansa dansu abatan basirarsu da duhun kansu indai babu wani garkuwa atare dake to hakkun zasu ci galaba akanki anasu karatun kenan anamu kuma basu san cewa Allah shine garkuwar bawansa kuma majibancin al'amuran sa lokacin da nake ta tunanin zuwansa bintu Ina ganin yakusa zuwa na dade da rubuta wannan sakon naki bintu dan nasan watakil alokacin da nakeso na sanar miki hakan bazai samu ba. Abu na biyu shine bintu Ina yawan sanar dake akwai wanda zai zamar miki jagora to tabbas naji ajikina zaku hadu kince na sanar miki waye? akuma ina yake? to ni kam duk bansan wannan ba!' hasali ma bantaba ganin fuskarsa ba andai nuna min shi amafarki na kuma inasa ran haduwarku insha Allah danshima yana bukatarki dan hada karfi da karfe ku tai maki junanku!' Abu na uku shine inda zaki nufa, to daga nan, ki wuce abuja duk yanda zaki ki samu koda aikine a estate din Alhji balarabe, Ina da tabbacin cewa duk wani abu yana cikin gidan nasan da wannan ki nutsu bintu karki sake ki nunawa wani ke din ahlin gidance, duk yanda zaki shaku da mutum karki yarda ki bashi yaddarki duk wanda kika gani ko shiga gidan yayi saka masa ido harsai kintabbatar da gaskiyarsa sannan ki barshi kuma kiyi hakuri da duk abinda zaki gani kibi ko mai asannu harki tadda gaci,akwai rudadden al'amari awannan ahlin dan haka kiyi taka tsantsan dan sai kin nutsu kinbi hanyo masu bullewa kafin ki fahimci komai mutanen gidan suna da ruda mutum, kuma ina da tabbacin mafarautanmu suna hade da alhlin gidannan. Bintu tana kawowa karshen bayanin fafi ta saki wata sassanyar ajiyar zuciya,tare da wani kuka me cike da shauki bege da kuma kewa data mamayeta, wani irin kewar fafi da mamanta ne suka hadu suka da baibaye zuciya da ruhinta, tanaji dolene ta shiga koma inane dan nemo fafinta da mamanta, kowane hadarine zata iya fuskantar sa indai akan wadannan mutanen guda biyune, ashe fafi bashi ya haifeta ba amma ya sadaukar da rayuwarsa ya bar iyalansa da mahaifiyarsa da dukiyarsa da abokansa yan'uwansa da komai nasa, kawai dan ya tserar da rayuwarsu ita da mamanta, shiko fafi wane irin mutumne haka da irin wannan babbar sadaukarwa?me zatayi arayuwarta dan saka masa da dinbin alkhairin da yaiwa rayuwarta? wani shashen na zuciyarta yace"fatima baki da abinda zaki iya sakawa fafi dashi arayuwarki sai dai ki bishi da addu'a da kuma binciko inda aka kaisu aka boyesu, da kuma rusa magautanku kamar yadda ya gaya miki, hannu tasa tashare hawayen da suka ki daina zuba daga cikin idanunta, kana ahankali ta bude wani page, dan taga kamar da wani sauran rubutu, aiko hasashenta ya zama gaskiya, ga abinda yace mata, bintu ki duba cikin kayana zaki ga kudi dubu biyarne na dade ina tarasu domin irin wannan ranar ki dauka kiyi kudin mota duk da nasan da.wuya zai isheki Amma dai nasan zai kaiki Abuja kuma kisamu ki danci abinci, Allah yabaki sa'a ya kuma kareki daga duk wani sharri ya kuma hadaki da mai taimakonki cikin sauki, Allah ya yiwa rayuwar ki albarka. Fatima ta kuma rushewa da wani rikitaccen kuka mai taba zuciya,duk wanda yaga halin da bintu take ciki awannan lokacin indai yana da imani da tausaiyi dole ya zubda mata da hawaye,tayi kuka tayi kuka har ta gaji sai wani irin masifaffan ciwo da kanta keyi mata tamkar zai tsage gida biyu,ahaka ta hakura ta lallashi kanta da mika dukkan lamuranta ga sarki Allah buwayi mai iko da komai,tare da fara kokarin shirin fuskantar gagarumin yakin dake gabanta. ......Abuja...... Kwanaki uku yayi cir yana istihara dan neman zabin Allah akan akan yakin da yake kokarin fuskanta,kuma alhdulillah yaji hankalinsa ya kwanta tare da samun kwarin gwiwa na shiga cikin ahlin Alhaji balarabe. Acikon kwana ukunne yagama shirinsa tsaf dan komawa estate din, dama dady ya kaimasa duk kayansa da kuma duk wani abu nasa mai muhimmanci tun kafin yau din tazo,dan haka yana tashi daga aiki ya nufi gida dan yiwa mom sallamar da taci albarkacin dady, da farko baiyi niyar yi mata sallamar ba, amma da yayi wani tunani saiya ga bai kyautatawa dady ba amatsayinsa na wanda yake ta kokarin dai-dai ta rayuwarshi da tarin kyautatawa da neman mafitawa rayuwarshi. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 10 ``` Koda ya shiga falon mom din zama kawai yayi batare da ya iya cewa da ita komaiba,sam shi baisaba da yin magana anyhow ba, shiyasa take matukar yi masa wahala har ga Allah sautari rasa abin cewane yake hanashi magana, kamar misali dady awasu lokutan yanaso yayi mishi magana kodan nuna masa irin jin dadin da yake shiga duk lokacin da yaga yana kokarin kawar da damuwar dake dankare azuciyarsa, sai dai kuma yana rasa tayaya zai iya hakan. Zuba masa ido tayi tana mamakin hali irin nasa, wai ace mutum da ransa da lafiyar sa amma sai yay awa biyu cur batare da ya bude baki yay magana ba, idan ma zaiyi bata wuce kalma biyu zuwa uku anya kuwa fatash zai iya rayuwa da mace?shin wace irin macece zata iya zama da fatash da wadannan halaye nasa?to shi tayaya ma zai iya wata soyayya?ita tana ganin ma bazai taba yin aure arayuwarsa ba tunda babu wanda ya ke shakka ko tsoro da zai tursasashi yayi auren, sai dai yay tazama ahaka tunda ya riga ya auri aiki, mom ita kadai da zuciyarta take mitar nan tare da cin alwashin bazata tanka masaba ko zasu kwana ahaka har sai taga iya gudun ruwansa. Banza tabawa ajiyarsa kamar yadda ta kudurta aranta,sai dai kuma abun neman fin karfinta yake, dan bata ga alamun yana da niyar tanka mataba, saima kokari yake ya bar falon saboda yasan dady ayanzu shi yake jira, saurin dakatar dashi tayi da cewa"haba fatash sai kace wadanda suke zaman gaba me yay zafi haka!' kake tsaurara tsanarka agareni?kai kana ganin ya kamata ka tafi wani guri zama na tsawon wani lokaci batare da munyi sallama wa juna ba?ya kamata ka sassauta min nasan ni mai tarin kuskurece agareka amma ai na nemi yafiyarka kuma kace kaimun afuwa!' to meye kuma acikin ranka game dani haka fatash? ta fada tana mai sakin wani dan marayan kuka gwanin tausayi. Ahankali ya koma ya zauna yana mai hada hannayensa biyu tare da lan kwasasu cikin kwarewa da sabo, suka bada wani sauti kakasss!' kana ya dubeta cikin dauriya yace" mom sorry and please forgive me, ni zan wuce Allah kaddara saduwarmu!'daga haka bai iya kara koda harafi daya ba yasa kai ya fice batare ya waigo ba. Sake da baki da Ido ta bishi, to meye amfanin neman yafiyarta ta?batare da ya saurari abinda zatace ba yai ficewarsa, ga tarin tambayoyin da tayi masa duk ya hada ya share tamkar ma batayi masa suba, ita dai tanaso taga ranar da za aiwa fatash tambaya ya amsa kai tsaye,wani lokacin idan kanasan amsar tambayarka agunshi sai dai kakula da aiyukanshi' a kanka ta nan ne kawai zaka gane amsarka amma ga wanda yasan hali. Acikin mota ya sami dady shi kadai, dan basa bukatar driver awannan gabar,yana shiga dady ya tayar da motar yaja me gadi ya wangale musu wawakekiyar kofar get din suka fita. Bayan shiru na dan wasu mintoci da fara tafiyarsu dady ya dan numfasa kana yace" abdallah ina mai baka shawara da kayi hakuri da duk abinda zaka gani ko katarar acikin gidan nan kasan shi gidane na jama'a da hada-hadarsu dan haka dole kajure hayaniya domin samun nasara akan kyakykyawan kudurinmu, anbaka bangare guda asashen kakarku hajiya zainab (inno) saboda itace babu kowa agabanta amma duk da haka kusan rabin yan mata da samarin gidan anan suke tarewa domin kamar nanne majalisarsu baccine kawai ke maidasu sashensu, to ni dai bansan meyasa aka baka masauki abangarenta ba,amma ni hakan yayi mun kasancewar kowa da kowa yana shiga bangarenta ma ana kowa nata ne tana kuma mu'amala da dukkan surukan gidan, kaga kenan a hasashena hakan wata babbar damace agareka da zaka samu kusanci da kowa na gidan zaka kuma kula da takun kowa, nasan kai mai basirane abdallah da kuma dogon hange bana jin ko dar akanka nasan insha Allah kaine da nasara akan makiyanku dan haka ka kula da ta kun kowa ko kallo mutum yayi agidan nan da ma'anarsa,ina maka fatan alkhari da nasara akan dukkanin rayuwar ka,san nan kayi min magana akan cewa kar gane wani abu akanka saboda kamannin ka da gidan da kuma mahaifinka, to wannan bako mai bane dan dukkanin su kansu ajuye yake anriga anmantar da dasu, sum manta wanene abubakar da wani gudan jininsa dan haka babu wanda zai ganeka sai wanda yay abun da kuma magoya bayansa dan haka inaso kasa ido sosai dan nasan su zasu iya ganoka amma bazasu taba nuna wata alama ba, suna da shiri akanka abdallah ka kiye!' Adai-dai lokacin kuma suka karaso dan kareran get din da zai shiga da kai cikin ainahin estate din manyan masu gadi sojoji kusan biyarne akofar, kasancewar babu wanda baisan dady jafar ba yasa suka barsu suka shige kai tsaye zuwa get na biyu wanda daga shine kuma zakai ta ganin get-get na bangare bangare, batare da wani dogon bincikeba kai tsaye akabarsu suka shige bangaren Alhaji baba. Alokaci daya abdallah yaji kansa yay wani irin mummunan sarawa da karfi tamkar ana buga masa guduma har sai da ya kai hannunsa ya dafe goshinsa, fahimtar hakanda dady yayi take yashiga karanto masa addu'a shima ahankali yake karanta innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un tare da allahumma ajirni fil musibati wa'aklifini khairan minha da la'ilaha'illa'anta subhanaka inni kuntu minazzalumin.kana ahankali sukayi sallama adai-dai lokacin da kofar ta zuge suka saka kai, yayin da sukaji wata kamilalliyar murya tana amsa musu, Guri suka samu gaba dayansu akasa suka zube, saboda tsananin girmamawa ga tsohon dattijo mai tsananin mutumci da kamala. Bayan sun gama gaisawa da dady ne, abdallah ya karayin kasa da kanshi kana ya gaishe da Alhaji baba, amsawa yayi cikin farin ciki da wani irin shauki na kauna da bege da lokaci daya ta saukarwa Alhaji baba. Hannu ya mikawa abdallah yana cewa"zomana jikana abin alfaharina matso kaji dumin jikin kakanka!'abdallah bai kasance ragon namiji mai raunin zuciyaba amma ayau akuma gaban dattidon nan jiyake tamkar zai zubda hawayen tsananin tausayinsa da kuma kewarsa tare da zunzurutun kaunarsa hakanan yaji yana fargabar ranar da zai san cewa ya haifi bara gurbi acikin yayansa ya kuma hada iri da gubatacciyar zuria yana tsoron kar saboda bakin ciki ya hadiyi zuciya arasashi kowa ya huta. Jin maganar Alhaji babane ya katseshi daga dogon tunanin da ya fada yace" abdallah jikana kasaki jikinka kadauka cewa kana cikin gidanku kuma cikin ahlinkane, duk abinda zakayi kayishi kai tsaye amatsayinka na dan gidannan na kuma baka umarni duk wanda yay ba dai-dai ba acikin kannenka ka hukuntashi amatsayinka na babban yaya tunda yanzu babu wani babba saurayi da yay saura agaban mu duk suna da iyali!'ya karasa fada yana mai shafa kan abdallah. Abdallah jinjina kai kawai yayi tare da kwantar da kanshi akafadar kakan nasa yana mai jin wata yar sangarta na shigarsa nakasan cewarsa tare da kakan nasa. Cikin lokaci kankani babban holl dinsu da suke taruwa dan taro muhimmi ya cika makil, saboda sanarwar Alhaji baba na cewar duk wanda yake nan kusa har yan kaduna yana bukatar ganinsu cikin gaggawa,wadanda sukai nisa kamar na kano ko wata kasa haka akayi connecting dan suma su sami damar jin abinda ya hada taron. Kowa ya nutsu yana sauraron bayanin Alhaji baba ta macrophon,kowa ya gamsu da abinda yasanar dasu har wasu suna cewa ai da ko awaya yasar musu ma ya wadatar. Alhaji baba yayi gyaran murya kana yace"dalilina na cewa lallai sai kowa yazo shine inaso ku dauki abun da muhimmanci kuma kowa yasan cewa abdallah shima jika naneeee (Waiyo ni fadima sauri nayi na zubawa mutanen dake dankare a holl din Ido ko zan samu nasarar riga su abdallah gano bara gurbin cikin zuriar Alhaji balarabe sai dai kash babu wanda ya nuna wani abu afuskarsa da zai sa na diga masa ayar tambaya,kai wadannan mutane ko suwaye akwai shu'umai) Abdallah ya zubawa fuskoki da yawa ido ko shima zai fahimci wani sauyi daga wata fuska saboda jin furucin Alhaji baba, sai dai shi din ma babu abinda ya fuskanta. Ahlin Alhaji balarabe sun karbi abdallah da hannu bibiyu, anan ya dinga ganin wata kauna akan fuskokinsu kansa ya daure matuka dan yakasa fuskantar gaskiyar kauna da akasinta, duk abu daya yake gani dauke a fuskokinsu, dady ane, ma da dady jafar yasan bai gamsu da zuwan abdallah ba, bai fahimci komai afuskarsa ba. Ahaka taron ya watse kowa na kokarin ganin ya nunawa abdallah shi mai kaunarsa ne baka da zuci, Alhaji baba da kansa ya rakashi har bangaren inno ya sadashi da hadadden dakinsa kana yace" yayi wanka ga abinci nan ya dade da rigashi zuwa sannan ya kwanta ya huta. Godiya abdallah yayi wa Alhaji baba,shi kuma ya juya ya fita yana mai tunasar dashi karya sake yi mai godiya. wadawa yayi bisa lumtsumeman gadon da yasamu wata iriyar shimfida ta alfarma da wani hadadden bedsheet,kansane yaji yana neman barewa gida biyu saboda yawan hayaniyar da yashaka yau shi tunda yake bai taba shiga hayaniya irin wannan ba dole dady yay ta bashi hakuri da tausarsa akan ya jure ashe yasan komai akan yawan hayaniyar gidan anya kuwa zai jura? Tashi yay yana layi ya nufi bayi jikinsa duk babu kwari hutu kawai yake bukata yanzu dan wannan hayaniyar tasa duk san aikinsa yaji ba zai iya fita aiki gobe ba. Tunda aka sauke ta atashar bulayi kawai take acikinta batasan ko Ina ba batasan kowa ba, batasan inda zata nufa ba, can kusa da wata mai abinci ta samu ta rabe sai baza manyan idanunta take taga ta inda Allah zai kawo mai agazamata, da dai taga zaman take ga yunwa na nukurkusarta kawai sai taciro naira dari biyu ta kara matsawa kusa da mai abincin tare da yi mata sallama!' alokaci daya kuma tana mika mata gudar dari biyu tace"abani abinci!matar mai abinci ta bi bintu da wani irin kallon yau naga India mai jin hausa,girgiza kanta matar tayi tana mai cewa' yi hakuri 'yan mata bamu da irin abincin ku anan sai dai kije restaurant' a canne suke yin kowane irin abinci!'ta karasa maganar da juyawa tana kallon mutanen da suka taru arumfar abincin nata, kallon bintu suke cike da farinciki yayin da wasu suke musun cewa ai amisha ce wasu kuwa suce ai pretty ce, Bintu ta rasa inda zatasa kanta kawai sai tafashe da kuka!' saboda ita bata saba shiga cikin jama'a ba, balle wadannan da suke tai mata surutu aka, ganin haka yasa wani babban dan union ya sa wasu samari suka kori mutanen, Matar nan mai abinci ta dubi bintu tace" yan mata Ina zakijene na ga kamar kin dade acikin tashar nan ko kin manta hanyane?da sauri bintu ta daga kanta!' matar tace"ayya to bari nasa yarinyata ta nuna miki hanya,juyawa tayi ta kalli budurwar dake tsaye agefanta tana saurarensu, tace" basira maza jeki ki nuna mata hanya ki saka ta a keke napep, ta fada masa sunan anguwar da zai kaita dan naga alama bakuwace batasan ko'inaba!'ta mikawa basira wata leda tana cewa" ga wannan sai ki bata idan zata iya cin abincin mu!'bintu cikin shagwababbiyar muryarta da ta riga ta sangarce agun baffa da fafi tace"na gode mama Allah ya saka miki da alkhari!' mai abinci cikin jin dadi tace"babu damuwa ki gaida gida Allah ya kiyaye!'ta amsa da amin tare da jin dadin karamcin da mama mai abinci tayi mata. Tun kan ma su fita daga cikin tashar suka samu mai napep,basira ta dubi bintu tace" wace anguwa za'akaiki? bintu shiru tayi tana son ta tuna sunan anguwar da fafi ya gaya mata amma ikon Allah shaf ta manta,mai keke yace"Ina gafa wannan hausarce tayi mata nauyi bari na lissafo mata sunan anguwanni ko zataji ta fada!'kafun ma basira ta tanka masa ya shiga lissafo manyan anguwannin masu kudi da fada aji, bintu tanajinsa har yanzu bai fadi makamanciyar sunan anguwar da zataje ba .gajiyar da tayine yasa yana cewa'mai tama sule tace"muje nan zani!'me napep yace au wai dama kinajin hausa kan uba alkur an ban zaci ta'iya hausaba kudurar Allah kenan!'basira tace da Allah mazarkwaila sarkin zaki wuce kuje ka kaita ka'ishi mutane da surutu kamar ba gobe!'dariya yayi kawai dan yasan gaskiya ta fada, mikawa bintu ledar take away tayi gami dayiwa junansu sallama,mai napep yaja suka wuce. Hajiya anzo mai tama a'ina zaki sauka?ahankali bintu take bin anguwar da kallo,tare da manya-nanyan gidajen da sukayi mata kawanya,tunani take idan ta sauka to Ina zata nufa?wa tasani acikin wannan haddadiyar anguwa ?amma abin da tasanine dole ta sauka tunda itane ta zabi akawota nan din, dan haka tace da mai napep ya sauketa,burki yaja akofar wani haddaden gida yana mai cewa" hajiya kudinki naira dari uku!' batare da tace"komai ba ta mika masa dari biyun dazu da mai abinci bata karba ba,yana amsa ya figi napep dinsa ya kara gaba. Tsuru tayi agefan gidan da ya ajiyeta tare da zabga uban tagumi,ji tayi cikinta yana wani kuuu sai alokacin ta tuna da yunwar dake dankare acikinta, gabas ta kalla kudu da arewa bata ga kowa ba dan haka a nutse ta juya baya taci abincinta, duk da bata wani ci mai yawaba cikinta ya riga ya cushe.zama ta cigaba dayi awajen ga tsoro da ya cika ta, fanfo ta hango daga dan nesa da ita da sauri ta karasa gun ta bude fanfon aiko ruwa ya zubo shaaa, cikin azama ta kafa kai tasha tayi nak, kana ta daura alwala ta dawo inda take, ta shimfida dan kwalin kanta tayi sallolin da ake binta kana ta dora da na filfilu, tana nan dai azaune har aka kira sallar magriba sai alokacin ta fara ganin mutane suna fitowa masallaci, wasu kuma sun dawo daga aiki, sai kuma taji hankalinta ya dan kwanta da taga jama'a musulmai suna hada-hadar shiga masallaci. Sai da akayi sallar isha dayawan jama'a suka dinga fitowa daga masallacin,motace ta dallareta yayin da aka bude wawakekiyar kofar get din gidan da take rabe ajikinsa, cikin sauri ta mike saboda yadda idanunta suka mutu saboda hasken fitilar, Bayan motar ta shige ne aka maida kofar aka rufe, sai kuma tsoro ya kamata, bintu sarkin kuka, take ta fara sana ar tata,sake bude kofar taga anyi da sauri ta zabura ganin wata girkakkiyar mata ta fito daga cikin gidan kai tsaye ta nufeta,bintu na ganin haka ta karawa kukanta sauti dan kuwa bintu matsoraciyace ta sosai, matar na zuwa ta jawo hannun bintu suka shiga cikin gidan, d'an da katawa matar tayi kana ta dubi bintu fuskarta babu yabo ba fallasa tace" kimin shiru ba wani abu zan miki ba mai gadine yasanar dani ya ganki ta CCTV tun dazu kina zaune banyi ma niyar kula kiba saida mai gidana ya dawo ya kuma yi min maganarki yace inzo na shigo dakeee... Tofa yanzu aka fara wasan Wai hannun wa bintu ta fadane? Shin zata samu nasarar shiga estate?idan ta shiga wace irin rayuwa take agidan ?a wane matsayin zata shiga? Shin ya rayuwar abdallah zata kasance acikin ahlinsa? Anya kuwa abdallah zai iya zama cikin hayaniyar ahlinsa ko zai fece? Da gaske zai iya zabar abokiyar rayuwa acikin jikokin Alhaji baba? Wai kuwa Ina labarin dije?meye shirinsu Alhaji hashir ne da suke neman inda aka boye Alhaji abubakar? Ina hajiya zulaiha ta shige shin itama Bata gane gudan jinintaba abdallah?meye hakikanin zuciyar alhaji mansur ?akwai tambayoyin da bamuzo gabar yinsuba, ku biyoni Dan jin tarin amsoahinku....... Comment....... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* Wannan page din kacokan na sa daukar dashi ga yan fans din KUDURAR ALLAH ina matukar godiya gareku Allah ya bar kauna love u lodi-lodi..,.. ```Page 11 ``` Tunda ya kwanta bashi ya farka ba sai da yaji kiran sallar asuba acikin kunnensa, ahankali ya bude manyan idanunsa dasuka koma wata kala mai matukar kyau da burgewa saboda baccin da bai isheshi ba, cikin yar kasala ya mike daga kan lallausan gadon nasa ya nufi hanyar toilet dan dauro alwala, yana fitowa yaji ana taba nock din dakin, ahankali ya karasa jikin kofar yana mamakin kowaye acikin wannan lokaci, ga tsananin mamakinsa Alhaji baba ya gani tsaye yana doka masa nutsatstsan murmushi wanda yake gauraye da wata irin mashahuriyar kauna,cikin tsananin kulawa yace" abdallah jikana fito mutafi masallaci ba nisa bane acikin estate dinnan yake dannasan haryanzu akwai gajiya atare dakai!'jinjina kai kawai abdallah yayi tare da kama hannun Alhaji baba yana cewa na fito, ai da kasani baka zo har nan ka wahalal da kanka ba sai mu hadu amasallacin!'Alhaji baba ya gyada kansa ayayin da suke jerawa yace" abdallah daka yanzu duk sanda kaga banzo na ta da kai mun tafi sallar asuba ba to ka kaddara aranka ba lafiya ba, dan tun daga yau na wajibtawa kaina, sai dai kuma idan baka nan ko na mutu ko kuma kayi aure kayi nesa dani!'adai-dai lokacin sukazo kofar masallacin dan haka zancen nasu ya yanke. Ko da aka idar da sallah sun jima aciki suna karatun alkur'ani Alhaji baba ba karamin dadi yajiba da yasamu abdallah yadda yake tsammata, wato mai tsananin ilmin addini da kuma aiki dashi,saida gari ya danyi haske kana suka fito Alhaji baba har kofar dakinshi ya kuma rakashi kana ya dubeshi cike da kauna, yace"abdallah kaje ka kwanta za'akawo maka kayan karinka idan katashi nasan yanzu kana bukatar hutu!' ahankali abdallah yace"na gode!' alhaji baba bai saurareshi ba ya wuce dan komawa bangarensa. Lumshe manyan idanunsa yayi wanda suke cike da zara-zaran eyelashes,yana mai jin kansa awata duniya ta daban, gashi dai acikin yan uwansa kuma mahaifarsa amma bayajin farinciki da walwala atare dashi, abu daya yaji tun shigowarshi gidan shine kauna da tausayin Alhaji baba sai kewa ta mahaifansa da ta lulllubeshi,yana jin kewar mahaifiyarshi saidai bazai iya haduwa da ita ba ahalin yanzu domin bazai iya jurar ganinta batare da ya nuna tsananin kewarta da dokinta agareshi ba,ko ita ma ta mantashi?ko tana tunanin sa ahalin yanzu?kwanciya yayi asaman gadonsa yana mai shafo tattausar sumar kansa da tai matukar kayatuwa wadda tai dai-dai da dan siririn sajen da ya kawata fuskarsa ma'abociyar kwarjini da haiba, rufe idanunsa yay yana mai kokarin gayyato bacci ko yasamu kansa ya daina masa ciwo. Kaiwa take tana komowa kamar mai safa da marwa, can dai kuma ta zauna,tana mai cije bakinta ta rasa ma wani irin tunani zatayi karfa garin sanyin jiki tabari abubuwa su cakude mata, kai Ina ai haka ma baza ta taba faruwa ba,duk yakin da nakeyi shekara da shekaru amma ace lokaci daya wasu banzaye suzo sucini da yaki ina bazan taba barin haka ta faruba, sai na ga abinda ya turewa buzu nadi!' takarasa fada tana fitar da wani irin zazzafan huci. Majalisar da take kasancewa afalon inno ce yau take ta tafka mahawara kowa da a bokin yinsa kasancewar bikin da yake ta da da matsowa dan yau sauran kwana goma afara shagalin bikin,shiyasa idan suka zauna basu da wani zance idan ba na yadda bikin zai kasance ba, amare hudu angwaye hudu sai dai dake da akwai zumunci tsakanin iyayen amaren da angwayen yasa komai za ayishi ahade dan haka suke cewa' bikin mutum takwas za'ayi 'acikin estate din na Alhaji balarabe, Khadija da haulat yayan nana karama wadda suke kira da hajiya mama sai kuma yarinyar aunty hafsa, ita kuma suna mata lakani da maman maiduguri, ita kuma zata aurar da rukayya babbar yarta, yayan maman maiduguri gaba daya su hudun suna nan cikin estate kamar yadda duk dan da aka haifa ba daga cikin estate ba to sai yay kaura ya dawo cikin yan uwansa, shiyasa yaran gidan gaba daya suka taso awaje guda, sai Abdurrahim d'aga hajiya zulaiha yayan rahima, suna matukar ji da bikin nan kasancewar sun kwana biyu ba'ayi biki a estate din ba. Hayaniya suke sosai sun cika falon da shegen musu, mazansu da mata kowa so yake asaurari zancensa dan haka hayaniyar tayi yawa har hawa kai takeyi, hatta inno da bata cika damuwa da harkokin hayaniyar suba yau sai da taji sun dameta, Ahankali yake bude shanyayyun idanunsa da har yanzu suke cike taf da bacci dan ko karyawa har yanzu baiyi ba tun da suka dawo daga masallaci da Alhaji baba wani bacci mai cike da mafarkai kala-kala yay awan gaba dashi, shine bai farka ba sai yanzu da wata iriyar gigitacciyar hayaniya mai fasa kwanyar kai ta farkar dashi, hannu yasa ya dafe saman goshinsa yana jin hayaniyar har tsakiyar kokon kansa,mikewa yayi ya nufi tailed, wanka yayi kusan minti arba'i kana ya fito yana sanye da rigar wanka sai karamin towel ahannu yana tsane kanshi,.cikin mintuna talatin yagama shirinsa tsaf cikin shigar kananun kaya wanda sukabi zubin jikinshi da kyakykyawar kirarshi ta sadaukan maza, yayi matukar kyau na ban mamaki tamkar ka daukeshi ka gudu, ya feshe jikinsa da manyan hadaddun turarukansa masu kamshi, falonsa ya fita, inda ya kara jin sautin hayaniyar tamkar afalon akeyi, runtse idanunsa yayi yana mai jin wani irin zafi aranshi tare da takaici,gashi ba gwanin magaba ballentana yace zai musu magana,Amma tunda hakane abun lallai yaran nan zasuci kaniyarsu tunda ba yadda zaiyi, zaman gurin dole ya kamashi dolene ya dauki mataki idan ba haka ba babu shakka yaran nan zasu kasheshi da wannan kadadinnasu mara tushe da ma'ana,dan bai dauki hakan ako mai ba sai tsabar rashin tarbiya. Kadan ya tattaba kayan karin da aka kawo masa, shima tea kawai ya sha, sakamakon rashin sanin daka Ina abincin suke, tashi yayi ya nufi hanyar fita babban falon cikin takunshi mai cike da nutsuwa da wata irin ta kama, kai kace sarkine amma shi bai san duk yana wannan ba, dan haka halittarshi take, Wani irin sassanyan kamshine ya farayiwa kofofin hancinsu sallama kana ginshirarren takunsa mai cike da nutsuwa sai kuma kwarjininshi da ilhama wanda rabbi ya bashi sai kuma kyakykyawar fuskarshi mai cike da haiba, kai bazakace ya taba sanin yadda ake murmushi ba, Tsit kakeji falon yayi ai tuni kallo ya koma sama ,mai sakin baki nayi mai zaro Ido nayi kan uban nan Allah mai kudura da irada tsarki ya tabbatar ga ubangijn da ya halicci wannan kyakykyawar surar cewar hauwa'u kenan da takasa kawadda da idanunta akan abdallah da yasamu wata kujera can nesa dasu ya zauna, zaman nasa ma kansa abin kallone, dukkanin su suka hadiye wani kakkauran miyau da ya daskare akan harshinansu,najib ne yay karfin halin cewa kai dalla dubesu duk kun wani rikice da ganinsa sai kace baku gansa jiya ba!'amna ce tai zakal tace" kai ya najib kaima ka rikice da ganinsa bare kuma mu mata, kuma jiyan ince kinbari yay aga fuskarsa tunda ya sunkuyar da ita har akatashi ataron bai dagoba!'rahima da zuciyarta take mata wani irin mugun bugu tace" kai amna baki sani ba dai irin wadannan ko kallo zasuyi basa bari afahimta, dan haka baki da hujja akan cewa bai dago ya kalli kowa ba!' abdurrahim ne ya kallesu cikin jin haushin maganganunsu yace"yanzun dan Allah wannan tarbiyace? kudinga yi da mutum agabansa kuma babu wanda yay tunanin gaidasa, karfa ku manta da jawaban Alhaji baba koma kai tsaye nace" umarninsa akan mubi Yaya abdallah domin shine babba ayanzu da zai tsawatar mana!' fa'iz ya harareshi gami da cewa to uban tsari kai yanzu gaidashin kayi? komu cewa akayi maka bazamu gaidashin ba me tarbiya!'yakarasa zancen da mikewa kai tsaye ya nufi kujerar da abdallah yake hakimce akai, ya kwantar da kansa idanunsa alumshe tamkar bayajin muhawarar da ake tafkawa akanshi,sallamar da fa'iz yayine yasashi dan bude idanunsa, nutsuwa fa'iz ya kumayi ganin tsabar kwarjinin abdallah, amsa sallamar yayi kamar wanda yake koyan magana,dan durkusawa fa'iz yayi tare da cewa barka da asuba ya abdallah!'barka dai ya fada asaman labbah danma fa'iz din yana kallon bakinsane da tabbas cewa zaiyi bai amsa ba, ahankali kuma suka dinga tasowa daya bayan daya suna gaidashin cikin kula da taka tsantsan tamkar ansanar musu halinsa sai dai kuma atabangarensu ba komaine yasasu wannan nutsuwar ba illa tsabar kwarjini da kamala irin nasa da kuma rashin ganin fuskar wasa, Tunda ya zauna ya hanasu sakewa karshe ma ahankali suka dinga zare jiki suna guduwa daga falon ba fada ba duka balle harara su da kansu sukaji sunyi tsarara abdallah yana zaune aguri suma suna zaune babu mai iya wannan karfin halin duk cikinsu,sai dai yan matanfa yau hirarsu ta canja zani dan gaba daya ayinin ranar hirar abdallah ce abakunansu karma amna da hauwa'u da kuma farida yar Alhaji habib suji labari... Da dai matar nan taji bintu takiyi mata shiru sai ta kuma juyowa afusace ta kwaza mata wata azababbiyar tsawa wanda nan take bintu ta kuma rikicewa, tsoro ya kuma da baibaye zuciyarta, saboda ta kaici matar figarta tayi sukayi ciki bintu kuwa binta kawai take batare da tashiryawa hakan ba saboda matukar tsoro,suna shiga tafkeken falon mai matukar haduwa da tsaruwa,wani dattijo wanda akiyasce zai iya kaiwa shekara hamsin da bakwai,yace'haba ladidi kiyi mata ahankali mana bakya ganin yarinyace karama,kinsan da nafisa ta haihu da yanzu kina da jikan da ya girme mata sosai!'sakin hannun bintu tayi tana cewa haba Alhaji ya daga ganin yarinya akwararo zakace lallai sai munshigo da'ita kai kana ganin kafurin kyau irin na yarinyarnan kasan ba abin arziki ta fito shukawa ba dan bana raba dayan biyu karuwancine ya fito da ita sannan gaka ganinta kaga balarabiyar karuwa!' Alhaji munir yace" ashsha haba ladidi bazaki daina aibata yayan al'umma ba kenan kullum Ina gayamiki Amma bakyaji, ki bar ganin daya kawai kika haifa...kafin ya karasa ta tari numfashinsa da cewa kaga ni banason wannan mugun bakin naka kaima dai yarkace na gani idan kayi mata baki ta lalace bani kadaice da asaraba harda kai ehe,!' jinjina kansa kawai yayi batare da yakuma cewa da 'ita komaiba, dawo da hankalinsa yayi kan bintu da kukanta ya mutu tun sa'ilin da kamilalliyar fuskar Alhaji munir tayi mata maraba,cikin nutsuwa yace yarinya ya sunanki? cikin Jan ajiyar zuciya ta wanda yaci kuka ya koshi tace"zahra ta sami kanta da canja suna wanda itama baza tace ga dalilin yin hakan ba, ya kuma cewa to zahra daga Ina kike kuma me ya zaunar dake kofar gidana kusan awanni hudu?bintu kasa tayi da kanta ganin irin buhu-buhun harar da hajiya ladidi take aikamata,tagane daga dazu zuwa yanzu matar da aka kira da hajiya ladidi bata kaunarta, itama kuma hakanan taji matar bata kwanta mata ba, Alhaji munir ne ya katse mata tunani da cewa muna jinki zahra!'hajiya ladidi tai zaraf tace"yo ba dole tayi shiruba tana kirkiro karyar da zata shimfida mana!' Alhaji munir yayi mata kallon ki kiyayeni ladidi......... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* Aunty hasana (maman nuur)wannan page din nakine kiyi yadda kikeso dashi Ina kara mika dunbin godiyata agareki Allah ya kara mana zumunci Amin ya Allah ```Page 12 ``` Alhaji munir ya juya yana dada fuskantar bintu tare da cewa Ina saurarenki zahra!'bintu cikin tsoron hajiya ladidi, tace"ni marainiyace iyayena duk sun mutu kuma a bauchi muke zaune, Ina zaune wajen kishiyar mamana na tsawon shekara daya da babana ya rasu, itace cina shana duk da Ina azabtuwa ahannunta,katsaham rana daya ta tada balli akan ta gaji da wahala dani alhalin babu dangin iya bare na baba dan haka saina bar mata gida wai itama tashi zatayi ta koma garinsu, hakan yasa na bar gidan da garin ma baki daya, Ina fita na nufi tashar garinmu dake bamu da nisa sosai da kafa naje, lokacin da na isa cikin tashar naji ana cewa Abuja dan haka kawai sai na hau motar Abuja ba tare da nasan kowa ba idan nazo, wata matace ta biya min kudin mota da muka sauka take tambayata inda zani ta ragemun hanya kasancewar anzo daukarta amota, shine kawai sai sunan anguwar nan ya fadomun da suka saukeni sai ta kuma taremin napep yakaraso dani nan, akofar gidan nan ya ajiyeni shiyasa na zauna awurin tun dazu har kawo yanzu da kasa aka shigo dani!' tayi saurin yin kasa da kanta ayayin da takawo nan akaryar da tasamu kanta da iya shararowa, Alhaji munir cikin tsananin tausayawa yace" ayya zahra karki damu insha Allah zaki zauna damu na dan wani lokaci kafin muyi shawara da mai daki na akanki!' bintu ta hada hannuwanta biyu tace"Abba na gode Allah ya saka maka da alkhairin sa ya kara tsawon kwana!' cikin tsananin jin dadin addu'ar ta yace"amin amin,!'tare da juyawa gurin hajiya ladidi da tayi wani irin sakalo tana kallonsa cike da mamaki da kuma takaicin wannan abu da ya aikata batare da neman amincewarta ba, batare da ya kula da kallon takaicin da take masa ba yace ladidi dan Allah kuje kisa iya talatu tayi mata duk wani abu da ya kamata, kama daga abinci wanka dakin da zata zauna,da duk dai abinda zata bukata awannan lokacin, yanzu zansa bawa driver yaje store yasamo mata kayan da zata bukata!'ya gama maganar da dauke kansa dan baya bukatar ta kawo masa wani buwaginta akan abinda ya bukata, hajiya ladidi ta saki wani dan murmushi, wanda da gani kasan da wani abu aranta,cikin ranta take fadin haba Alhaji nice fa ladidi idan kasan wata ai bakasan wata ba, bana aikata komai sai da manufa kuma wannan abun dakayi ni kaiwa danni zai amfana, Ganin yadda yabawa banza ajiyartane yasa ta mike ba dan ranta yasoba a fuskarta, kallon bintu tayi da wani irin kallon tsana ta rasa da lilin da yasa taji bata san yarinyar, ita kanta ta fara da sawa kanta ayar tamba tabbas akwai dalili amma babu kira mai zai kawo gawayi,ganin takiyiwa bintun magana yasa Alhaji munir yace" da bintu tashi maza diyata kuje kinji Allah yayiwa rayuwarki albarka!'bintu ta amsa da Amin tanajin kaunar mutumin da ganin girmansa da kuma mutuncinsa arayuwarta, sumi-sumi tabi bayan hajiya ladidi tamkar zakace kyat ta arta na kare. Can side din yan aiki suka nufa,wani daki taga hajiya ladidi ta konkwasa, wata dattijuwar matace ta fito daga dakin, tana yin arba da hajiya ladidi jikinta ya fara bari, kokarin rissinawa take hajiya ladidi ta dakatar da'ita cikin takama da izza, tace" talatu ga yarinya nan kiyi mata duk abinda ya dace!' daga haka bata kara ko'alif ba ta juya tai tafiyar ta,daga bintu har talatu bin bayanta sukayi da kallo,har sai da tabacewa idanunsu kana suka juyo alokaci daya suna duban juna, ahankali bintu ta durkusa har kasa ta gaida baba talatu,baba talatu ta'amsa cike da jin dadin girmamawar da bintu tai mata,sannan tace muje ciki kiyi wanka kafin nan na kawo miki abinci,bintu tace"na gode!'kana suka shiga cikin dakin na baba talatu, bayan ta nuna mata bathroom din sai ta fita dan samo mata abinda zataci, Zama bintu tayi akasa bayan tayi wanka ta fito ta maida kayan jikinta, tagumi tayizuciyarta cike da sake-sake da fargaba,to wai ita yanzu yaya zatayi?guduwa zatayi taje neman estate din nan Koko yaya? gashi ta manta sunan mai gidan balle tayi tambaya, to kuma idan ma tasani ta yayane zata kai ga matsayin da zata iya zama acikin gidan?rumtse manyan idanunta tayi, tana mai rokon Allah ya kawo mata mafita akan al'amuranta,bude kofar da akayine yasa tayi saurin bude idanunta, baba talatu ce ta shigo da leda ahannunta, mikawa bintu ledar tayi gami da cewa ga wannan kayane inji Alhaji sai ki cire wannan na jikinki kisaka sabbin!'karba tayi cike da ladabi tana mai yin godiya, zata shige bathroom kenan dan saka kayan, baba talatu tace a'a yar nan zo kisa kayanki anan ni fita zanyi na kawo miki abinci!"tana gama fadar haka ta juya tare da barin dakin, tashi tayi tasaka doguwar rigar wadda ta matukar amsar dirarren jikinta tabi kirarta ta cokacola tayi daram,komawa tayi ta zauna, tana zama talatu ta dawo hannun ta rike da plet shake da jolof din taliya wadda taji uban kifi kusan rabin abincin,ajiyewa tayi gaban bintu tana cewa ga abinci nan kici sai ki konta ki huta, aikinyi sallar isha'i ko?bintu ta daga kanta tare da cewa nayi sallah, baba talatu tace" to masha Allah maaza kici abincin kada ya huce!'bintu ta kuma amsawa da to na gode!'sannan ahankali ta sauko ta saka fock ta faracin jelop din supergatty, bata wani ci da yawa ba tacewa baba talatu ta koshi, baba talatu tace haba yar nan har kin koshi kenan? bintu ta jijjiga kanta batare da ta'iya cewa komaiba, da baba talatu ta fahimci dai bintu bata son yawan magana kawai sai taja bakinta ta dinke tare da dauke abincin ta fita dashi, konciya bintu tayi asaman gadon da take kai tare da lumshe idonta dan so take tayi tunanin mafitawa rayuwarta duk da bacci takeso tayi sosai. Hajiya ladidi tana shiga bedroom dinta ta dannawa aunty nafisa kira, tana dagawa batare da ta saurari gaisuwarta ba, tace"nafisa inason ganinki gobe da sassafe, arikice aunty nafisa tace"hajiyata me ya faru?meyasa kike nemana da gaggawa? Hajiya ladidi tayi murmushi mai fidda sauti tace"na samo mana dogon tsanin da muke nema dan hawa mu kai inda mukesan kaiwa da kuma hanyar dai-daita al'amuran rayuwarmu, ke dai kawai kiyo sammakon zuwa gida agoben!'jiki asanyaye aunty nafisa tace"to Allah ya kaimu!'amin hajiya ladidi tace gami da ajiye wayar, Zagaye dakin ta shigayi tare da cewa nafisa naga so kike ki lalata mana shirin mu da mukayi tsawon shekaru muna ginawa dan haka bazan taba barin haka ta faruba lallai so nake sai na cimma burikana bazan bari sanadin soyayya shirina ya wargaje ba domin kece tsanina awannan tafiyar to gashi yanzu na kuma samun wani tsanin, wani murmushi tayi mai cike da ma'anoni masu yawa, Waya takuma dauka tai kiran wata nomber kana ta danyi Jim, sai kuma tasaki wata mahaukaciyar dariya, alokaci daya kuma tana saurin sa hannu akan bakinta tana mai cewa' kai agida fa nake, kasani nake wannan dariyar kalan Alhaji ya jiyoni!'dan shiru tayi tana sakin murmushi sai kuma tace albishirinka!' batare data saurari abinda na wayar zaice ba ta cigaba da cewa munsami ma'aikaciya hargida burinmu ya kusa cika, zamuyi abinda mukeso nan kusa, yarinyace karama ta kawo kanta hargida, da ita zamuyi amfani dan cika burinmu da manufarmu sai dai akwai Abu daya danake tsoro!'ta dayan bangaren aka tambayeta da cewa mekike tsoro?tace"Ina tsoro kar nafisa taki bamu hadin kai da wannan shegiyar soyayyarta ta, shiyasa nace da ita inason ganinta gobe da sassafe!'a daya bangaren akace hajiya kin tabbatar yarinyar zatayi mana abinda mukeso batare da musu ko jayayyaba? hajiya ladidi tace" na tabbatar maka babu matsala saboda yarinyar tana da matukar tsoro kuma Ina matukar jin tsanar yarinyar araina shine ma babban dalilina, na tabbatar zamu juyata yadda mukeso idan mukai amfani da tsoronta!'yace tom shikenan karki damu da matsalar nafisa ni zanji da lamarin kawai ke dai ki sanar da ita tsarinmu sannan ni da kaina zan kai yarinyar estate dama nace zan nemowa inno yar aiki!' hajiya tace yauwa kaga shikenan babu mai zarginmu akan duk abinda zai faru!' daga haka suka yanke wayar. Alhaji baba yayi dan murmushi, lokacin da yagama sauraren maganar da dady jafar keyi masa,yace jafar indai akan samowa abdallah mai dafa masa abinci ne ni na dau wannan nauyin zansa abinciko min yarinya ko dattijuwa mai tsafta da amana saboda inno ma tana bukatar mai aikin da zata dinga gyara mata bedroom dinta, tace" jikokina dukkansu san gartattune!' yakarasa maganar yana mai fadada murmushin fuskarsa, daddy jafar shima murmushin yayi yana mai cewa' to babu damuwa baba hakan yayi Allah ya saka da alkhari!' Alhaji baba ya tari numfashinsa da cewa jafar na gaya maka kaida danka kude nai min godiya akan duk abinda yashafi abdallah saboda shima jikanane!'dady ya jinjina kansa yana jin wani abu yana taba zuciyarsa na tausayin Alhaji baba. Hajiya wai mene ya taso haka da gaggawa kike nemana? hajiya ladidi tayi saurin Jan aunty nafisa can karshen dakinta, ta kuma komawa tasawa kofar dakin key, kana ta dawo ta zauna tana fuskantar aunty nafisa wadda ta maida hankalinta kacokan akan gajiyar. Cikin kara san bawa maganar muhimmanci hajiya ladidi tace nafisa na samo yarinyar da zatayi mana aiki agidan Alhaji balarabe, abun nufi anan shine inason zaman zahra acikin estate saboda tadinga dauko mun duk wani abu dake faruwa acikin ahlin, sannan ni kuma ta dingayi mun duk wani abu da nasata batare da anzargeki ko anzargeni ba dan haka nake baki umarni da ki amince da wannan tsarin nawa!'ta karasa maganar da zubawa nafisar Ido, ga mamakinta sai taga nafin tayi dariya kana tace"haba hajiyata dan wannan yar maganar ne duk kikabi kika daga hankalinki bayan kinsan duk abinda kika umarceni dayi zanyi batare da musuba, karki damu akwai hanya mai sauki da zamubi batare da da wani zargi ba,!'cikin tsananin farinciki hajiya ladidi tace yauwa yar albarka shiyasa ako da yaushe nake alfahari dake amatsayin yata ta cikina, gayamun da sauri wace hanyace wannan? aunty nafisa tace"yanzu da zan fito saida na biya ta bangaren inno, shine take sanar dani wai Alhaji baba yasa anemo musu yar aiki mai tsafta da amana zata dinga da fawa wannan shegen yaron mai fi'ili da nunkufurci yawa fir.auna abinci, ita kuma inno zatana gyara mata bedroom shine tace" wai nima idan na samu ta bangarena na kawo duk sai azaba!'hajiya ladidi tai shiru tana dan wani tunani, nafisa batasan hajiya ladidi tana hada hannu da daya daga cikin yayan Alhaji balarabe ba dan haka dole ta dakatar dashi, akan cewa da yay shi zai kaiwa inno zahra, inyaso sai su mikawa nafisa wannan alhakin,firgigigit tayi lokacin da aunty nafisa ta girgizata dan tayi magana har kusan sau uku Amma no response shiyasa ta girgizata tace"hajiya wai lafiya kuwa? naga kinyi zurfi cikin tunani? me kike tunani haka? hajiya ladidi taja ajiyar zuciya kana tace" nafisa Ina tunanine akan yaron nan da kikace sunansa abdallah, ina tunanin Anya kuwa Alhaji dafar ba da wata manufa ya kawo dansa gidannan ba?nafisa ta danyi Jim kana tace tabbas hajiya na dade ina wannan tunanin kamar da kamshin gaskiya a maganarki Amma kina ganin kai wannan yarinyar zahra da kikace bazai bamu wata dama ta bincikar abinda suke nufi ba tunda kinga shine jigon wanda zatayiwa aiki kuma zata iya samun kusanci dashi inaga kamar zamu jefi tsuntsu biyu da dutse daya fa hajiya!'hajiya ladidi batasan sanda ta rungumo aunty nafisa jikinta ba saboda tsabar farinciki dan kuwa da gaske abdallah ya tsole musu ido, tace"kwarai kuwa yake yata mai basira da hngen nesa Ina matukar alfahari dake Allah yay miki albarka!'aunty nafisa ta amsa cikin jin dadin ganin farincikin mahaifiyar tata, sannan tace hajiya kirawo yarinyar na ganta Amma dai tare zamu tafi ko? Hajiya ladidi tace yanzu ma kuwa me zaki zauna kiyi nan din ? bakisan da zafi ake bugar karfeba, idan kuma wani ya rugamu fa?kin san dai mafarmakan gidan Alhaji balarabe suna da yawa dan haka bazamuyi sanyin jikiba!' Waya tayiwa baba talatu tace"kizo mun da yarinyar nan yanzu!'baba talatu ta amsa da to ranki ya dade!' batare da ta gama jin amsar talatu ba ta kife wayar. Kwankwasa kofar da akayine ya katse musu tattaunawar da suka cigaba dayi, aunty nafisa ce ta tashi ta bude kofar wanda budewarta ke da wuya suka hada idanu da bintu dake gefen talatu cikin shigar doguwar abaya wanda tayi matukar amsarta, tamkar dan jikinta akayo rigar, zuciyar aunty nafisa ce ta shiga wani irin bugu da karfi har sai da takai hannunta ta dafe saitin kahon zuciyarta,bin bintu da Ido kawai takeyi takasa tantance halin rudanin da tashiga ita dai tasan bata taba ganin bintu ba arayuwarta, kuma basu da wata dan gantaka ta jini, to miye hakan takeji aranta?me yasa take jin wata irin fargaba akan yarinyar? hajiya ladidi tace nafisa ya kuka tsaya ku shigo ke da zahra ke kuma talatu ki koma kan aikin ki!'talatu ta amsa da to hajiya na barku lafiya tare da fita daga dakin.... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* Aisha Ina godiya Ina jin dadin comment dinki, dan haka wannan page din nakine Ina godiya sosai. Yan group din KUDURAR ALLAH Ina godiya sosai Ina sonku irin sosai dinnan. ```Page 13 ``` Jiki asanyaye aunty nafisa ta karasa kan kujerar da ta tashi tare da zubawa bintu dake durkushe kan kafafunta Ido, abubuwa masu tarin yawa take kissimawa azuciyarta, sam zuciyarta taki yardan mata da bintu, sai dai kuma abun babu sauki sarayar da bukatar hajiya ladidi, hakan yana nufin dai dolenta ta zauna inuwa daya da bintu,wani zazzafan huci ta furzar, sannan ahankali ta daga kanta tana duban hajiyarta da ta zuba mata ido, tana mai karantar zuciyarta,hajiya ladidi tace"kyale ki nayi ki gama fita daga rudani da kuma kokwantan da zuciyar ki tashiga, wanda nima saida hakan ta faru dani ayayin da naci karo da wannan ko daddiyar fuskarta, sai dai kuma inaso duk wannan mu ajiyeshi agefe dan bai da wani amfani agaremu, zurfafa tunani akan zahra bashine damuwata ba, damuwata shine yadda zatayi mana aiki batare da faduwa ko samun akasi ba, ina fata kin fahimceni dakyau? ahankali aunty nafisa ta zare ta gumin da ta tafka, tare da cewa shike nan hajiya duk abinda kikace haka za ayi!' murmushi hajiya ladidi tasaki, kana ta juya tana fuskantar bintu yayin da take kara kokarin tsuke fuskarta, tace" kee" kisaurareni da kyau kiji abinda nakeso na gaya miki da farko dai zan tambayeki shin kina san rayuwar ki?afirgice bintu take duban hajiya ladidi, yayin da jikinta ya shiga rawa cikin zuciyarta tace" shike nan wayyo fafina bintunka ta shigo hannun yan yankan kai shikenan tawa takare!'wata masifaffiyar tsawa aunty nafisa ta daka mata kee" mahaukaciyar inace kinaji ana maki magana kina ji kina kallon mutane da wannan dakwalayen idanun naki masu kama da na mayu, nutsuwa zakiyi ki saurari umarnin da zamu baki, indai kuma har kina san cigaba da rayuwa aduniya, dole kibi umarninmu wannan shine ma'anar tambayar da hajiyata tayi miki, doluwa shashasha kawai!'ta karasa maganar tare da dora mata wani zazzafan kallo, mai cike da tsantsar tsana ta babu gaira ba sabar. Hajiya ladidi ta dora mata da zaiyano mata bukatarsu akan abinda sukeso tayi musu agidan da zasu kaita aiki, wani irin gumi ne yashiga ketowa bintu tako'ina yayin da zuciyarta tashiga wani irin tsalle tamkar zata hudo kirjinta ta fito, to me hakan yake nufi? ta addanci, zuciyarta tayi saurin bata amsa,to Ina makomar rayuwarta?Ina imaninta da tausayinta? Ina addinin ta na cikakkiyar musulma? Ina makomarta awajen ubangiji?Ina burinta nasan binciko mahaifiyarta da fafinta? ina burinta nasan tarwatsa makiyansu da tona musu asiri? lallai ni Fatima bintu ina cikin tsaka me wuya,anya ba gara su kasheni ba, da na aikata wannan mummunan aiki?to yaya zanyi?meye mafita agareni? tsinkayar muryar hajiya ladidi tayi akanta tana cewa tashi ku tafi inkin gama nazarin da bazai amfanekiba!'atsorece ta dago kanta cikin wani irin kuka tace hajiya dan Allah kimin rai..kafin ta kuma samun damar bude bakinta aunty nafisa ta dauke fuskarta da wani irin gigitaccen mari, wanda take agurin ji da ganin ta, suka dauke na wasu yan dakiku,aunty nafisa ta dora da cewa, indai har kikace gaddama zaki mana to tabbas rayuwar ki tana cikin hatsari, dan haka tun kafin na kara miki wanda yafi wannan ki goge wadannan shegun hawayen naki ki kuma shanye kukanki dan gaba zai miki amfani!'hajiya ladidi tace da kyau nafisa ni nasan ban haifi lusara ba, aikinki yanayin kyau yadda ya kamata kutafi kawai bani da haufi akan bar miki ragamar komai ahannunki!'tace karki damu hajiyata ko mai zai tafi daidai kamar yadda kikeso! bintu kuwa tun marin da aunty nafisa tayi mata tare da koro mata jawabai da manyan gargadi tayi dif sai zuciyarta dake wani irin zafi da tururi tare da wani irin tsanar aunty nafisa, sai dai tayi kokarin rarrashin zuciyarta kafin ta samarwar kanta mafita,kallo daya aunty nafisa tayi mata,aiko cikin sauri da rawar jiki tare da matsananciyar tsoron aunty nafisan ta juya ta fita daga dakin, yayin da nafisan ta bi ta abaya tana mai Jan wani dogon tsaki wanda ya shiga har tsakiyar kwakwalwar kan bintu. Suna fita hajiya ladidi ta dannawa Alhaji munir kira, tace Alhaji kayi hakuri na zartar da hukunci ban rigaya nasanar dakaiba!'ta can bangaren cikin yanayinsa na nutsuwa yace me ya faru ladidi?tace dama nafisace tazo yanzu tace Alhaji baba yana nemanwa inno 'yar aiki shine nace tunda ga zahra kuma yarinyar tana da nutsuwa me zai hana su karbeta, to kuma nafisan tana ganin ta ta dage wai dan Allah abawa inno din, saboda yarinyar ta shiga ranta da gani zatai hankali,nace tabari ka dawo taki, tace nai maka waya!'shiru tayi tana sauraransa,yace babu damuwa indai bazata takuraba kuma babu tsangwama, shikenan sa iya tafiyar? daga haka ya yanke wayar,ta wani tabe baki tana kwaikwayonsa kamar agabanta yayi maganar,babu damuwa indai bazata takuraba, kuma bazata tsangwama ba!'taja wani dogon tsaki waikai na Allah to muma ai bamuce bazamu tuba ba amma ba yanzu ba. Tunda suka fara tafiya bintu ta kunshe kanta tana Jan sheshsheka ahankali sabo da tsoron aunty nafisa, ahaka har suka karasa dan kareren estate din na Alhaji balarabe, ahankali bintu ta dago kanta tana bin mikakken titin dake shinfide, tamkar titin da zaikaika wani gari daban ba cikin estate ba,sunyi yar doguwar tafiya kafin su ratsa ta wani karamin titin wanda shine yasadasu da manya-manyan gidajen dake jere reras hagu da dama gwanin ban sha'awa,motar na tsayawa bintu tayi kokarin fitowa, sai kuma wani tunani ya zo mata karfa taje ba gidan bane fitowarta ya zama matsala, a'yan awannin da sukai da aunty nafisa ta fahimci jiran kiris take yi akanta, tasamu damar cimata mutumci harma da guzurin matuka, dan hakan zuciyarta cike take da tsoro dan hakika batasan me yakamata tayi ba, kafin takai ga samun mafita taji anyi mata wata kyakykyawar figa, hadi da ingizata, da kyar tasamu damar dafa jikin motar wanda shine ya taimaketa daga mummunar faduwar da take shirinyi, ahankali ta dago kanta da manyan idanunta da suka cika da ruwan hawaye, takalli aunty nafisa dake kallonta tamkar ta jawota tayi ta dukanta,cikin huci tace" mata tunda so kike na fito dake gashinan na fito dake saiki wuce muje!'jiki asalube bintu tabi bayanta zuciyarta cike da tsanar aunty nafisa, tana kuma aiyanawa aranta kome zasuyi mata sai ta gudu tunda su ba Allah bane. Wani Abu aunty nafisa ta danna ajikin kofar, sai ga kofar falon ta bude, hauwa'u da amna da rahima ne afalon,babu wata hayaniya dasukeyi kamar da, saboda yanzu basa samun damar watayawa abangaren inno kamar da,zaman ma basosai akeyi ba, sai dai su amna din saboda jarabar da suka dorawa kansu ta mahaukaciyar soyayyar abdallah, Sallamar aunty nafisa suka amsa tare da zubawa bayanta ido,rahima ce tace" waw aunty nafisa a'ina kika samo mana balarabiya?gaskiya wannan ko acikin larabawan ita mai kyauce!'aunty nafisa taja tsaki!' gami da cewa ke kam rahima kin ga takanki da surutu daga ganin abu sai ki fara zuba!'amna tace"kai aunty nafisa wallahi yarinyarce me kyau!'tace to aikwa barni na zauna kafin ku isheni da wadannan tambayoyin naku!'ta fada yayin da take samun gefen kujerar da hauwa'u ke zaune ta zauna, kana tace"hauwa'u Ina inno ?dan kifi wadannan taron yarintar hankali!' hauwa'u da hankalinta ke kan wayarta, tun kallo daya da tayiwa bintu bata kara daga idonta ba, tace"aunty nafisa kinsan ni ba komaine yacika yimin kyauba dan wani kyan ma ni tsoro yake bani, kamar dai wannan tayi nuni da inda bintu take atsaye har yanzu ba abata damar zama ba,aunty nafisa tayi wani kayataccen murmushi tace" yauwa yargidana duk muna gari daya kenan,amma dai yanzu bari na kira inno tukunna!'gani me akasamomin aketa nemana? inno ta fada yayin da take kawo kanta cikin falon, aunty nafisa tace" yauwa inno karaso kiga abinda nakawo miki!'karasowa tayi tana cewa to gani abani in abun dadine!'rahima tace" ke kam dadina dake shegen kwadayi to ba abun ci bane!ta fada ayayin da take juyawa gurin bintu dake kame atsaye kamar sojiya, kafafunta har sun fara rawa saboda gajiya, tace" me kyau zo ki zauna kinji Allah sarki mun barta atsaye tun dazu!'ta karasa maganar cikin tausayawa,sai alokacin inno ta lura da bintu data zauna adarare taki bari su hada idanuwa da aunty nafisa,inno tace" nafisa kar dai har kinsamo mana 'yar aikin?gashi kuwa kin gani inno!' cewar aunty nafisa,inno tace masha Allah yarinya karaso nan, meye sunanki? ahankali bintu tace" zahra!'cikin farin ciki inno tace kai masha Allah nafisa kinyi kokari yarinyar tana da nutsuwa da gani kuma zatai tarbiya,daga Ina aka samota nafisa Ina iyayenta? aunty nafisa tace inno wannan fa da kike gani marainiyace gaba da baya bata da kowa kishiyar maman tace ta kareta wai ta gaji da ciyar da ita, shine fa tazo garinnan shi kuma alhajinmu ya samota akofar gida dan ya taimaka mata!'inno ta kalli bintu tace 'yar nan kin tabbatar gaskiyar labarinki kenan? bintu ta daga kanta idanunta na zubar da hawayen tausayin kanta, inno tace" to taso ki biyoni ta dubi aunty nafisa tace" nafi bari na gabatar da ita gun babanku!' gyada kanta tayi tare da cewa to inno amma ni zan wuce gida bazaki sameni ba!'inno ta amsa mata da cewa shikenan nafi Allah yayi albarka!'ta amsa da amin!' tana mikewa dan fita alokaci daya kuma tana aunawa bintu kallon gargadi, inno tace" taho muje kinji!' ahankali tabi bayan inno cikin takunta na nutsuwa nutsuwa, Sallama sukayi afalon Alhaji baba, sai da ya amsa kana inno ta kutsa kai tana mai cewa da bintu shigo mana kidena dar dar nan ma gidane kamar kowane irin gida!' Alhaji baba dake kashingide cikin kujerarsa, yana kallon labaran duniya yace" ke dawa ne haka kike ta surutu!'inno ta zauna akujerar dake gefensa tana nunawa bintu wajen zama,tace aiko ma meye yanzu zakajishi, ni sarkin surutu kai kuma sanjin zance!'murmushi yayi yana maida dubansa kan bintu da kanta ke sunkuye, yayin da kuma ita kadai tasan halin da zuciyarta take ciki, ahankali ta kuma yin kasa da kanta cikin matukar girmamawa ta gaida Alhaji baba,shi kuma ya amsa cikin mutuncinsa da karamcin da yasaba yiwa duk wani wanda yazo gareshi, inno ya kalla da san karin bayani, ganin haka yasa ta dan muskuta, sannan cikin nutsuwa ta zayyana masa takai taccen tarihin zahra wanda nafisa ta gaya mata, cikin tsananin tausayawa yace" da zahra zonan fadima 'yar albarka na shafi kanki!'matsawa bintu tayi tanajin wata 'yar nutsuwa na shigarta, ayayin da tasamu karramawa ta mutumci daga wannan kamilin dattijo,dora hannunsa yayi akanta yashiga sharara mata addu'a, sai da ya gama kana ya dubi inno yace" kibata daya daga cikin dakunan dake gefanki sannan kuma fadimatu ba 'yar aiki bace rukon maraya yana da matukar alfanu garayuwar dan Adam, dan hakan zamu riketa tsakani da Allah zan sanar da abdallah komai!'duban bintu yayi ya dafa kanta tare da cewa fadima kema 'yace kamar kowa agidan nan amma zan rokeki wata alfarma, inaso zaki dinga dafawa jikana abinci sai kakarku da Zaki dinga taimakawa kina kama mata wasu aiyukan, inno gatanan azaune!'bintu wani nauyi ta dinga ji azuciyarta da gangar jikinta yana da baibayeta, yanzu dama irin wadannan mutanen akeso tazo tashiga jikinsu dan ta cutar dasu?yanzu kenan wannan mutumin mai tsananin kirki da karamci akeso ta cutar?shin sun san adadin mutane nawane suke amfanuwa ta karkashinsa?ko sun san adadin mutanen da sukeci sukesha akarkashinsa? dan basai anfada mataba wannan mutumin uban marayune da marasa karfi da rashin galihu irinsu,to ta yaya za ai ta iya cutar da mutumin da ya amsheta amatsayin jika dan butulci,muryar inno ta tsinkaya tana cewa zahra ko dai bazaki iya ba kikayi shiru, idan bazaki iya ba ki fada kanki tsaye karki damu sai asamo wata!'Alhaji baba ya dora da cewa abinda yasa bazan ce anemo wataba saboda nasan halin abdallah yana da tsantsani sosai kuma kinga ke kina da tsafta, Ina ji lallai zai iya yarda da abincin ki saboda kina da tsafta!' girgiza kai bintu ta shigayi alokaci daya tana cewa, wallahi ko abinda yafi girkine sau dari zan iyayi muku, dan hakan kudena tunanin bazan iyaba zanyi biyayya ga dukkanin umarninku!'Alhaji baba yace masha Allah fadima Allah yayi miki albarka, ya baki nasara acikin rayuwar ki!'cikin san rike kukan dayake makogoran ta take amsawa da amin,yace" da inno kutafi ta kwanta ta huta zuwa gobe!'inno ta amsa da Allah ya nuna mana goben, tare da riko hannun bintu tana cewa, tashi muje fadima kinji!' Kai tsaye dakin dake gefan nata ta kai bintu,dubanta inno tayi tace" yauwa zahra ga nan bathroom kiyi wanka ki huta zansa su rahima sukawo miki kaya!'bintu tace" na gode inno!'inno tace karki damu bari na kawo miki abinci!'ta fada tana fita daga dakin, Juyi kawai takeyi bisa dan ma daidaicin gadon da ayanzu ya zama nata, babu abinda zuciyarta takeyi sai kaikawo da tunanin mafita, jin ko Ina nata takeyi a daddaure tarasa makama, haduwarta da wadannan dattawan kirkin yasa taji tanason taimakon su,sannan ga tata matsalar yanzu yazatayi?shin zata gujewa mutanen da suka karbeta amatsayin jika ne ko kuma zata tsaya dan taimakon su?to idan ta tsaya fafinta kuma da mamanta fa tayaya zatayi ta samosu?ga kuma asalinta zatayi ta zama ahakane batare da ta damu da yin rayuwa da danginta ba?acikin wannan yanayin wani wahalallan bacci yay awon gaba da'ita. Maza-maza dije kizo kisameni ainda muke haduwa Ina bukatar ki cikin gaggawa karki zauna lusaranci kuma ki kula da hagunki da damanki ki tabbatar babu mai ganinki(Amma dai Allah na ganinku ehe) kashe wayar tayi tana cigaba da sunturi awajen, ita kadai tasan irin tashin hankalin da take ciki, hannu tasa ta gyara nikabin dake fuskarta. tsawon minti arbain saiga dije ta bullo ta wata hanya daban, da gani dai hanyar boyayyiyace, cikin sauri matar ta fizgo hannun dije saida suka dan bada ta zara da inda suke duk da bawai mutanene awajen ba, taja ta tsaya tana kallon dije cike da tashin hankali, duk da ita dijen ba ganinta takeyi ba dan haryanzu bata taba bari taga fuskarta ba,ahaka suke duk tsawon lokacin da ta dauka tanayi mata aiki, koda ace bata hada mata da barazanar idan ta fadawa wani zata kasheta ita da alhlin ta ba,bazata iya fada ba, to dame zata kwatanta ta? ko kwayar idanunta bazata iya kwatantawa ba, Matar ta girgiza dije cikin tsawa da tashin hankali tace" dije bakya jina wai Ina magana!' dije tayi firgigigit tace inajinki ranki ya dade!'zagaye gurin ta shigayi tare da cewa, dije aiki ya dawo min baya nasa anbinciko mun komai akan Alhaji jafar da abdallah abinda akasanar dani shine, Alhaji jafar aiki ya turo abdallah yayi masa, kuma suna cikin yan adawarmu yaki suka shirya yi damu kuma suna da kyakykyawan shiri akan hakan niyarsu duk abinda na shirya su kuma su rushe, duk da nasan cewa bani kadai bace nake laluban duniya,akwai wasu hadamammu Irina sai dai bakowa nasani ba,shiyasa kikaga bana zaune akan neman burina, ada hankalina ya tashi amma cikin yan mintuna nasamo mafita, kuma wani abun burgewa shine zan jefi tsuntsu biyu da dutse daya!'wata mahaukaciyar dariya ta saki, kana ta dubi dije tace"ankawo mun nama adai-dai lokacin danake bukata, dije nifa shu'umace yadda bakya zato,basu san komai dasukeyi idanunta na kansuba, sun lullubo yarinya sun kawota dan tai musu aiki amma sun fake da cewa, sun samowa inno da abdallah mai aiki ne, to ni suka kawowa mai aiki, dije na kuma samun tsanin aiwatar da abinda nakeso, ke zaki fake abayanta, kawo kunnanki wannan bazan bari Fatima taji ba dagani saike,,rada tayiwa dije wadda akalla tadaukesu kusan minti goma tana tsara mata bukatarta,daga nan tayi mata umarni da ta wuce tatafi gida. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 14 ``` Baffa hashir ya dubi Abba salisu yace"yanzu Salisu har yanzu babu wani bayani akan labarin Abubakar?nifa abunnan yana matuƙar ɗaure mun kai ni burina nasan suwaye suke da alhakin ɓatar dashi, idan ba hakaba kuwa tabbas muna cikin ruɗani baza kuma mutaɓa cimma burinmu ba, sanin mutanen nan shine samun mafita agaremu tunda kuna ganin dai yadda muke tufka ta baya tana warwarewa,Abba salisu yaja wani dogon numfashi kana yace" Baffa yanzu kafin na karaso nan maganar da muka gama da Alhaji na kenan (Alhaji nasir)kuma munyi maganganu dashi masu muhimmanci, akwai shirin da mukeyi A ƙasa, nasanar da yaya Nura komai dan haka kubamu lokaci!' Baffa Hashir yace to shikenan hakan yayi zamu saurareku muna fatan muji kyakkyawan sakamako!'daga haka sukayi sallama. Sun kasance suna yin mitin duk ƙarshen wata,manyan mutane ne masu faɗa aji,suna yin mitin ɗin ne saboda matsalolinsu da base ankai su gaban dodo jack ba,ko kuma idan sun sami nasara A wani aikin, sai su haɗa ƙwarya-ƙwaryar liyafa dan taya junansu murna, kamar dai yadda sukayi yanzu mitin ne me haɗe da liyafa don taya junansu murna sabida wata gagarumar nasara da suke ganin sun kusa cimmawa. Sai dai wani abin mamaki babu wanda zaka gani batare da face Mack ba duk rabin fuskar su A rufe take, ikon Allah wato abinda na fahimta kamar dai sunyi haka ne saboda sun san ina laɓe dan gano su waye daga cikin su ƴaƴan Alhaji Balarabe dan nazo nafesawa fans ɗin ƙudurar Allah, bayan Ni kuma suna tunanin da A kwai wanda zai'iya yi musu leƙen Asiri, gaskiya waɗan nan mutane sun iya takunsu. Wani ne daga cikinsu, ya fara magana cikin salon nau'in maganar su da bazaka taɓa iya gane muryoyinsu ba, yace" ya kamata ku saurara muyi Abinda ya kawo mu kar lokaci ya tafi!' tsit falon yayi,kana cikin nuna muhimmancin maganar da zaiyi yace" yanzu dai kowa A nan yana cikin farin ciki na kasancewar nasarorin da wasu daga cikin ƴan'uwan mu suke samu na daga manyan burukansu, to gaskiya muna matukar farin ciki da wannan lamari, kuma muna fata zamu ga ƙarshen lamarin cikin nasara!' yana direwa gaba dayansu suka ruɗe da shewa da wasu maganganu na nuna farin cikinsu,sai da kowa ya nutsu, kana wani ya ɗora da cewa lallai dole ne mu kasance cikin tsananin farin ciki kamar yadda abokina ya faɗa,kamar yadda kuka sani ne A kwai muhimman Abubuwan da mukesan haɗawa A cikin matakan aiyukan mu,wanda muka daɗe muna jira har muke ganin kamar hakan bame yiwuwa bane kuma muke ganin kamar rashin nasara ne yake tun karan mu, sai dai kuma da temakon dodo jack lamarin ya sauya daga faduwa zuwa nasara,dan A halin yanzu komai ya kammala sai aiwatar da aikin wanda shine mataki na biyu da zamu shiga, amma fa karku manta wannan aikin da muke shirin tunkara yana da matuƙar wahala zamu shiga ƙalubale masu yawa A kwai yiwuwar tonuwar asiri A kwai kuma yuwawar samun nasara, amma mun fi raja'a akan samun nasarar sai dai kawai wahalar aikin, dan yaran sarrafa su shine babban haɗarin da zamu fuskanta to amma munyiwa hakan kyakkyawan shiri kuma zamu cigaba da yin shiri!'gaba falon ya daɗa ɗaukar sowarsu, nan dai aka fara ciye-ciye da shaye-shaye, basa tare da wata damuwa bare kuma tunanin makomarsu. Alhaji Baba ne zaune shida Abdallah yana yi masa bayanin fadima da ainihin labarinta da inno ta gaya masa,da kuma irin hukuncin da ya yanke akan zaman nata, shi dai Abdallah ya amsa masa ne kawai batare da ɗaukar zancen da wani muhimmanci ba, sai dai jin cewar daga cikin estate din aka kawota dan yi masa aikin abinci, yasa yaji wani Abu can ƙasar zuciyarsa me kama da rashin yarda,duk da baisan wacece ainahin Anty nafisan ba, cikin salon maganarsa ta muskilanci da ɗaukar hankali yace" Baba Alhaji shikenan tunda ka gamsu da ita bani da matsala sai dai inaso ka haɗa ita yarinyar da dady dan ya gaya mata tsarina!'Alhaji Baba yayi murmushi irin nasu na manya, kana yace"a'a Abdallah basai na tambaye shi ba nasan abinda kake da damuwa dashi, ba dai hayaniya bane bakaso ita ma yarinyar bata da hayaniya dan abinda na fara dubawa kenan na tabbatar zaka amince da zamanta dan haka baka da damuwa da wannan, hatta da list ɗin Abincin da kake ci da lokacin da kake cinsu, da haɗin copy duk an sanar da ita fatana na gaba kawai Allah ya sa Abincin yayi maka!'jinjina kansa yayi kana ya miƙe cikin takunsa na ƙasaita da nutsuwa ya fita daga falon. Hajiya zulaiha ce tayi sallama falon inno,inno ta amsa sallamar tana cewa Ammin rahima kece haka da yamma!' Ammi ta amsa tana ɗan sakin murmushi tace" wallahi inno daga side ɗin Hajiya Babba nake kwana biyu jikin nan ya hanani zuwa dubaku!'inno tace haba Ammin Rahima ai mune zamu zo mu dubaki dan yanzu mun fiki jin karfi ke da ba wani cikakken lafiya gareki ba da kinyi zamanki!'ammin tace"inno ai da sauki jikin daga nan ma wajen Hajjo zanyi, naje na duba Alhaji Baba shima!' inno tarike haba tare da cewa to sannunki da kokari, ya kuma karfin jikin?Ammi ta amsa da cewa da sauƙi, inno yanaji gidan naki shiru ina sabon jikan naki?inno tace"wai Abdallah kike magana wannan baya nan yana can Asibitin sa ko da yana nan ma bazaki gane ba dan basan hayaniya yakeba, su kuma yaran duk sun daina zama saboda shi!'Ammi tayi dariya tace ai kam yayi mana maganin ƙiriniya yanzu shiru kikeji kunnan mu ya huta!' Zahra..zahra,inno tashiga ƙwala mata kira, yayin da take sanar da Ammi cewa bari na kira zahra ku gaisa yarinyar da Nafisa ta samo min dan debe kewa, sai dai kuma marainiya ce..shigowar Bintu ne ya katse mata zancen, sallama Bintu tayi cikin sassan yar muryarta me tsananin daɗin sauraro,A lokaci ɗaya kuma tana tsugunawa A gaban inno tare da rissinawa ta gaida Ammi,Ammi ta zubawa Bintu ido, kana cikin sanyin murya itama ta amsa gaisuwar, ta dubi inno tace masha Allah inno yarinyar ko kyakkyawa, ko itace'Rahima ta dameni da zancen ta?inno ta washe haƙora cikin jin daɗi tace" itace ai naga jininsu ya haɗu da Rahima tana sonta! Ammi tace"kinsan Rahima da son Abu mai kyau!'ta kare maganar da mikewa tsaye,tace" inno ni bari na wuce zan shiga wajen Hajjah!'to madalla Allah ya ƙara sauƙi!'ahankali Bintu tace"ki gaida gida Allah ya ƙaro sauƙi!'cikin ƙure bintun da kallo ta amsa ta da Amin na gode!'tare da barin falon gaba daya, Tafe take zuciyarta cike da da tarin tunaninnika, bata ga komai A game da yarinyar ba,haka nan kallon da tayi mata ta gano babu komai cikin idanunta sai tsananin kunya da gaskiya,tanajin wani ɓangare na zuciyar ta nasan amincewa da Bintu, to amma kuma me yasa takejin wani irin tsoro A kan yariyar? tanaji kamar da wata maƙarƙashiya A kan zuwan yarinyar duk da bata da wani zargi A kan Nafisa sai dai can ƙarƙashin zuciyarta tanajin wani Abu daban, amma dai komeye zan sakawa yarinyar ido,dan kaf gidan nan ba abin yadda bane dole ne na gano komeye Ake shiryawa. Yau ne ya kama, kamun Amare wanda yayi daidai da kwanan Bintu biyu A estate, ƴan matan Amare sai shirye-shirye suke, wasun su da yawa suna sashen inno,yayin da Bintu sai shiga da fita take, itace wancan itace wannan ko Abincin daren Abdallah sun hanata ta ɗaura, gashi yau A time table ɗin sa sakwara zata yi masa da miyar egusi, karma hauwa'u da amna suji labari, sun takurawa Bintu, kuma bakomai ne yake ɗawainiya dasu ba face kishi da hassada, duk da suma ba munana bane amma suna jin suna raina kansu A duk lokacin da bintu ta kasance A waje, shiyasa suka ɗauki karan tsana suka ɗora mata, hakan baƙamin faranta wa Anty nafisa rai yake ba,duk da har yanzu basu kuma haɗuwa ba tunda ta kawota. Saida duk ta sallamesu kana ta fara aikinta shima saida Inno ta fito ta tsawatar musu,cikin sauri take sarrafa duk abinda.yazo hannunta,duk da cewa basu taba haɗuwa ba har yau, amma tana ƙoƙarin kiyaye duk wasu ƙa'idojinsa da Aka lissafo mata,kai wannan mutum da shegen fi'ili yake komai bayaso,A haka ta gama aikinta lokacin babu kowa duk sun tafi wajen da Ake kamu shima A cikin estate ɗin yake,sai da ta gama jera masa komai kana cikin sauri ta nufi ƙofa dan fita, sam bataso su haɗu da wannan murɗaɗɗen mutumin, gashi yau har ta shiga lokacin dawowarsa shiyasa take sauri ta fice kar ya tarar da ita. Tana buɗe kofar tayi wani irin gware da wani irin faffaɗan ƙirji, duk da ita bata gama tan-tance da abinda tayi karon ba, runtse manyan idanunsa yayi dan haƙiƙa yaji zafi har cikin ƙahon zuciyarsa, Buɗe Manyan idanunsa yayi, A daidai lokacin ita kuma Bintu ta gama murza goshinta, ta ɗago dan ganin mugun da yai mata wannan aika-aikar, zaro manyan fararen idanun ta tayi tare da dagewa iya ƙarfinta ta kurma wani uban ihu, tare da komawa cikin falon da gudu tana neman gurin ɓuya,kira take wayyo inno yau nayi gamo, wa innahu sulaimanu, fafina yau nayi gamo, kuka takeyi sosai tamkar zata fitar da numfashinta, Mamaki haushi ta kaici duk sune suka cushe zuciyar Abdallah,yana nan tsaye ya kasa ko da motsawa, balle sanin abinda zaiyi, ga ƙararta da duk ta cika masa kunne har ya rasa me ya kamata yayi, kaji yarinya da rashin hankali, amma shi bai ce mata Aljana ba sai shi zata cewa Aljani,tsuka yayi kana yaja ƙafafuwan sa ya ƙarasa shiga cikin falon,ɗago idanunta tayi da suka fito waje kamar na preter, cak ya tsaya yana kallonta dan shi dai ba ma'abocin kallo bane amma sosai yaga kamar su da preter har zaro idon da yanayin tsoronsu amma azahirance bintu tafi preter kyau,hannu yasa ya finciko ta ransa A matuƙar ɓace, ya daɗe bai ji ɓacin rai makaman cin na yau ba,idanunta, ta kuma zarowa kamar zasu faɗo ƙasa saboda firgita da tsoro,ji tayi kawai yaja ta har bakin ƙofa ya turata waje,ya maida ƙofar da matuƙar ƙarfi ya rufe, Tsuru tayi A bakin ƙofar zuciyarta cike da fargaba,yanzu hankalin ta ya riga ya dawo jikinta,sai yanzu ta fahimci waye, A fili tace kai waini wace irin matsoraciyace? mutum da falonsa amma na kirashi da Aljani?cikin irin muryarta da ta saba yiwa fafi tace me yasa nake hakane? gashi najawo zai karya min hannu,to koma kurma ne ? kai inno dama tace sai ya kwana biyu baiyi magana ba, to kuma bakinshi baya yin komai? hannunta ta kalla taga har yayi ja ga shi sai raɗaɗi yake mata,kallon ƙofar tayi tana zabga mata harara tare da murguɗa ɗan ƙaramin bakinta, tace kuma ban yafe ba mugu!'ta arta A guje kamar wadda zai kama. Yana shiga bathroom ya sakarwa kansa shaya,yanayi yana sakin tsaki, kai wannan yarinya A kwai bagidajiya kawai tazo ta ƙaran ciwon kai, sai da yagama shirinsa tsaf, kana ya fito falon, wajen cin abincin ya nufa kai tsaye dan shi Abdallah yana cin binci sam baya wasa da cikinsa, shiyasa ma yasa a samo masa mai girkin, gashi kuma bai iya bin gidajen abinci ba saboda tsantsani, zama yayi ya zuba sakwarar yaci sosai dan sosai ɗanɗanon abincin yayi masa ɗari bisa ɗari, har ya shiga mamakin wannan ƴar yarinyar ce ta iya sarrafa abinci haka ga nau'in lemuka masu inganci da'A cikin kwana biyun suka kama zuciyar sa, A hankali ya miƙe ya koma cikin falon tare da zama cikin kushin, hannu ya miƙa ya ɗauki ɗaya daga cikin wayoyinsa, wadda take ta buruntun neman agaji, cikin hakimtacciyar muryar shi yayi sallama bayan ya dannata A amsa kuwa, muryar Dady ce ta ratso ta cikin wayar, bayan ya amsa sallamar tare da gaisuwar da Abdallah yayi masa,yace" Abdallah ina fata ko mai lafiya, batare da ya jira amsarsa ba ya cigaba da cewa anya kuwa Abdallah kanayin wani ƙoƙari kuwa dan najika shiru babu wani motsi,ina tsoron kar mutanen nan su sham mace mu,dan na lura A kwai mutanen da suke bin diddigina, amma bansan ko suwaye ba ban san kuma daga ina suke ba amma ga dukkanin alamu mutane ne mabanbanta shiyasa nakeso naji kai ta wajenka babu wani Abu? Cikin nutsuwa Abdallah yace" dady ka kwantar da hankalin ka babu abinda zai sameni da ikon Allah, kuma ina yin komai ne cikin lura, dady bamu ne zamu fara kai farmaki ba dole yanzu nasan bazasu zauna ba, da farmakin su zamu fara gano su kar ka damu babu wanda baza musawa ido ba insha Allah ko mai zai tafi dai dai!'hamdala dady yayi ya kuma tabbatar Abdallah yana yin komai da hangen nesa. Anyi biki angama cikin kwanciyar hankali, an kuma kai Amare gidajensu, an bawa ragowar ƴan matan inno fili suna zuba sha anin su, yayin da masu shiri suka fara shiri masu makirci suka fara shirin ƙulla makircinsu, Aɓangaren su Hajiya ladidi kuwa, yau Anty nafisa tayi sammakon zuwa gidan nasu,A yayin da suka ƙule A ɗaki suna ƙulla tsiyarsu, Anty nafisa tace"yanzu Hajiya taya zamu dinga isar da saƙonmu wajen wannan banzar yarinyar? kinga idan nace zan dinga kiranta muna keɓewa A kwai babbar matsala, kinsan gidan namu makiran suna da yawa, kuma baka ganesu kowa munafuncinsa yana cikinsa!'Hajiya ladidi tace" mafita ɗaya ce shine mubata waya!'to amma tayaya zamuyi hakan shima A kwai haɗari!'duk shiru sukayi suna tunanin mafita, can Anty nafisa tace yauwa na samo hanya!' Hajiya ladidi ta zuba mata ido tare da yi mata nuni da cewar tana sauraren ta,Anty nafisa tace" me zai hana nayiwa inno dabara na nuna mata ya kamata A bawa Zahra waya saboda ko wani uzurin zai taso na buƙatarta a kusa yayin da bata kusa!'tana direwa Hajiya ladidi tayi mata wani kallon bakya cikin haiyacinki,kana tace"nafisa A she baki da wayo so kike inno tayi wani tunani A kan haka?wannan ai ba dabara bace sam ki canza tunani!'Anty nafisa tace to Hajiya meye mafita?kinsan dai bazai yiwu mu bata waya A ɓoye ba,dan inno zata iya ganowa kuma kinsan bagidajiyar nan tsaf zata gayawa inno wanda ya bata!Hajiya ladidi taja iska ta furzar kana tace"mu bar wannan zancen nasan yadda zanyi!Anty nafisa tace dan Allah kigayamin me zakiyi kinji Hajiyata? Hajiya ladidi tace" Alhaji zan gayawa ya kamata ya kira Alhaji Baba yaji ya Zahra take, daga nan zai dinga kira akai akai danjin lafiyar yariyar, kinsan daga ƙarshe me zai faru? Anty nafisa ta girgiza kai, taci gaba da cewa daga nan zansa Alhaji ya siyo ƙaramar waya, zan sashi yaje gidan da kansa dan kaiwa Zahra wayar, wannan shirinane kuma zai tafi daidai da tsarina cikin sauƙi batare da zargin kowa A kanmu ba!wata shegiyar dariya Anty nafisa ta saki, tare da cewa, gaskiya Hajiyata kina da basira, wannan shirin yayi bari nayi sauri na koma dan gabatar da shirin mu na farko. Dije inaso ki kasance cikin shiri dan muna gab da kutsawa cikin lamarin!'daga haka ta kashe wayar tare da jan motar ta bar gurin cikin shigar ta ta kullum. A daidai wan nan lokacin, shi kuma Abokin aikin Hajiya ladidi bayan sun gama waya da'ita, ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya, yana mai cewa ladidi kin gama yawo tunda kika haɗa kai dani bayan Ni ɗin ma bani bane kin tabka babban kuskure kin kai kanki ga halaka, dan nasan yana gama samun Abinda yake so daga gareki sunanki sorry, Ni dai ana biyana zan canza sheƙa dama mu haka aikinmu ya gada, Hajiya ladidi kina ruwa, yayin da yakuma.sheƙewa da wata muguwar dariya, tabbas kinyi kuskure haɗa hanya da ƴan ƙungiyar jack masiface babba. A hankali take ta kawa cikin sanɗa da kiyaye wa dan kar wani ya ganta,kuka mara sauti ta farayi yayin da taga hanyar ta ɓace mata, guduwa take sanyi dan tunda tayi mafarki da fafinta yana ƙara jaddada mata abinda ta manta wato sunan kakanta yana kuma sanar da'ita ba bacci ya kamata tayi ba, domin gaba ɗayan ta A ɗaure take A tsakanin makiya, haka kuma babban yaki ne A gabanta wanda ya tun karota da zafinsa. Wannan shine dalilin da yasa take neman hanyar tserewa, domin zuwa ta fuskanci manyan ƙaddarorinta, sai kuma gashi kanta ya juye ta rasa hanyar tserewa. Tana cikin wannan zagaye ne tazo ta wajen wani ɗaki, sai lokacin kuma shegen tsoronta ya dawo, dan lokacin wajen misalin ɗaya da rabi na dare ne,juyawa tayi da niyar komawa,sai dai me wani irin jijjiga taji gaba ɗaya gurin nayi da sauri ta juya dan ganin meyake faruwa, dan saboda tsananin tsoro ji tayi ta kasa guduwa,wani irin razanannen ihu ta saki wanda A tunanin ta cikin mintuna zataga an kewaye ta, sai dai ga mamakinta ko kare baiyi haushi ba, zuciyar ta ce ta shiga wani irin bugu da sauri da sauri yayin da tayi arba da ɗakin nan yana wani irin juyi tare da fitar da wani irin hayaƙi, cikin kiɗimewa ta tattara dukkanin ƙarfinta ta sheƙa da wani irin A zababben gudu na fitar hankali wanda kawai tsintar kanta tayi A cikin ɗakinta...... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 15 ``` Tamkar A mafarki haka yake ganin Al'amarin,ihun da Bintun take har cikin tsakiyar kansa, juyi kawai yake tsakiyar tattausan gadon,bakinsa ɗauke da addu'o'i, lokaci ɗaya kuma komai ya tsaya cak tamkar ɗauke war nefa, A hankali ya tashi zaune hannun sa dafe da kansa, wannan Al'amari bakaramin hautsina masa tunani yayi ba, to me hakan yake nufi?me ya kawo wannan yarinyar cikin mafarkinsa?meye haɗin ta da wannan ɗakin? meye kuma A cikin ɗakin?Anya kuwa ba abinda yake zargi A kan yarinyar bane Allah ya nuna masa? tabbas hakan yana nuna masa turo ta A kayi, to amma waye ya turota? me aka turota ta aikata masa? komawa yayi da baya ya jingina da fuskar gadon tare da tattaro bedsheet ɗin ya ciku kuyeshi ya watsa shi ƙasa, miƙewa yayi ya fara zagaye ɗakin yana furzar da wani irin zazzafan huci daga bakinsa, idanunsa har sun sauya kala saboda tsananin zafin zuciya, lailai dolene ya binciki yarinyar nan,A sannu zai kamata da lefi dumu-dumu, bathroom ya faɗa ya ɗauro Alwala ya kama jera na filfilu. Tunawa da Abinda ta gani yasa ta kuma rikicewa jikinta ya shiga wata iriyar kakkarwa, cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi ya rufeta, A matuƙar tsora ce take da gidan nan, wannan wane irin gidane suka kawoni? ta faɗa cikin kakkarwar jiki da tashin hankalin da yaƙi barinta, raɓewa tayi can ƙarshen ɗakin tanajin kamar A lokacin abun yake faruwa, runtse idanun ta tayi, cikin tashin hankali tace"wayyo Allah katemakeni ka kuɓutar dani daga hannun waɗan nan mutane, ya Allah katemakeni ka tsareni daga shiga haɗarin gidan nan, ka kawo min mafita cikin gaggawa!'kuka tasaki me matuƙar bantausai da karya zuciyar mai imani,A hankali cikin jin tsoro da ɗar-ɗar take takawa har zuwa cikin bathroom,Alwala tayi ta fito ta shinfiɗa sallaya ta tada kabbara domin miƙa Al'Amuranta gurin sarki Allah buwayi gagara misali. Garau ta tashi washe gari tayi aikinta kamar yadda ta saba, ta haɗa karinsa ta nufi falonsa da tunanin ya fita motsa jiki kamar yadda ta saba zuwa ta tarar ya tafi, shi yasa basu fiya haɗuwa ba,tana shiga falon ta ɗan yi jim, kana kuma ta wuce ta jera kayan karin,juyowa tayi bayan ta A jiye da nufin ƙara Sachin ɗin falon dan ganin inda bai gyaruba ta kuma kimtsawa, saboda tun kan ya farka take shigowa ta gyara falon idan ya fita motsa jiki kuma sai ta gyara ɗakin da wankin toilet, dafe ƙirjinta tayi tare da saurin ja da baya ganin mutum kwance yayi luf cikin kushin, A kimtse yake cikin kayan motsa jiki damtsensa sai glowing yake idanunsa A rufe tamkar mai bacci, murguɗa ɗan ƙaramin bakinta tayi tare da motsashi A hankali tace"haka kawai sai mutum ya dinga bani tsoro kuma bani da damar yin ihu ko kuka sai A fizgeni a wulla waje,mutum sai kace kurma ba abinda ya iya sai ɗacin rai! A hankali ya shiga buɗe lumsassun idanunsa masu dawo da mutum cikin nutsuwar sa, ya ɗora su Akan kyakkyawar fuskar Bintu,tsaf yaji duk abinda tace, saboda shi Abdullah ya kasance daga cikin mutane masu tsananin ji, dan haka bai sha wahalar jin duk abinda take faɗa ba. Cikin rikecewar da kaifafan idanunsa masu tsananin maiƙo da sheƙi suka sakata,cikin yanayin fargaba da matsanancin tsoro da ya saukar mata A lokaci ɗaya, cikin sanɗa ta taka dan tsira daga waɗan nan shu'uman idanuwan nasa da suke neman kassara duk wata gaɓar da ke gudanar da jini A cikin jikinta, Wata tsadaddiyar murya taji tamkar amsa sarewa acikin kunnuwanta,wadda ta saka gaba ɗaya ragowar kuzarin dake tare da ita ya ƙarasa malalewa,cak ta tsaya A inda take batare da ta ƙara wani ƙwaƙwƙwaran motsi ba, cikin yanayin maganarsa na fitar da magana ɗai ɗaya tamkar wanda akasashi yi dole,yace"karki sake ganina ki tsorata,numfashinta bai gama dai dai tuwa ba ya kuma rigirgizo mata tambayar da ta motsa ƴan hanjin cikinta, tare da wata iriyar juyowa sosai tana fuskantar sa, yayin da idanuwan nan suka kuma fitowa cikin firgici da tsoro,sai da ya gama karantar yanayin ta tsaf kana ya kuma mai maita mata tambayar,yace" dake nake jiya misalin ƙarfe biyu me ya fita dake waje har kina neman fasawa mutane kunnuwa da shegen ƙaranki,me kikeso kishiga kiyi A wannan ɗakin? hantar cikinta ya kuma kaɗawa, to ma wai miyene na jin tsoron bayan nasan ban yi komai ba,wata ƙila ma shine yake wani mugun abun A cikin ɗakin, idan ba haka ba me yasa da yaji ihun nawa baizo ya tai makeni ba?kuma ya akai yasan na fita? kai wannan mutumin A kwai baƙin mugu!' gigitacciyar tsawar da ya buga mata ne yasa ta dawo haiyacinta,ya nunata da yatsa yana cewa duk ranar da na tabbatar da rashin gaskiyar ki to ki tabbatar da cewa sai nayi gutsi-gutsi da namanki A cikin gidan nan,wuce ki fitamin A falo!tun kan ma ya gama rufe bakinsa ta arta da wani shegen gudu,bata tsaya A ko'ina ba sai tsakiyar gadonta tana maida numfashi me cike da razanar da tayi da Abdallah, Allah kafitar dani daga cikin wannan gida na mutane marasa tsoron ka, kowa munafiki ne A wannan gidan, duk basu da gaskiya, duba Irin kallon da wannan Ammin Rahiman takeyi min dagani itama so take tasani wani mugun aikin!' Ammi ta dubi Rahima tace" auta ina ƙawarki kuwa zahra?Rahima ta saki dariya tare da miƙewa zaune tana cewa" wai ta gidan inno? ni wallahi ma banje ba tun washegarin da Aka kai Amare, faɗa mukayi da inno! ta ƙarasa maganar tare da ɗan turo baki, Ammi tace"to ai ba da ƙawar taki kukai faɗa ba ya kamata dai ki dinga zuwa kina ɗebe mata kewa!'to Ammi amma sai na huta sosai zan koma zuwa!' Ammi tayi murmushi kawai A ranta tanajin haɗa kusanci tsakanin Rahima da Zahra shine kawai hanyar da zata 'iya bi dan fahimtar abinda take so ta sani A game da Zahra,tasan ko bata tambayi Rahima ba zata dinga bata labarin Zahra,ita kuma zata dinga hankalta da inda yarinyar ta sa gaba idan A kwai wani Abu maka mancin na rashin gaskiya zata sani. Duk tsarin da Hajiya ladidi tayi shine ya kasan ce, sau biyu ne tasa Alhaji munir ya kira Alhaji Baba,ba tare da wani shan wahala ba tsarinta ya tafi yadda take so koma fiye da haka tunda A cikin kwana biyu Alhaji Baba yaji san sha'awar ya mallaka wa Bintu waya,ko dan sudinga gaisawa da bawan Allah Alhaji munir, tabbas yana jin daɗin yadda Alhaji munir ɗin yake nuna kulawarsa A kan ƴar marainiyar Allah Bintu,shi yasa yaji A ransa gwara ya bata waya dan shi Alhaji munir ɗin yasamu damar kiranta kai tsaye, Alhaji Baba da kansa ya kira Alhajin Nafisa, yasanar dashi ya bawa Bintu waya kuma layin da yaƙi rasa dashi shine layin Bintun, dan haka zai'iya kiranta kai tsaye, godiya Alhajin Nafisa yayi masa kana sukayi sallama, A lokacin suna tare da Hajiya ladidi ya kuma sanar da ita yadda sukayi da Alhaji Baba,yadda Hajiya ladidi ta nuna farin cikinta,har saida ya tsaya yana dubanta cike da mamaki,ganin haka yasa ta waske tare da cewa, kai masha Allah gaskiya Alhaji Baba ya kyauta,tare da ɗaukar wayarta ta bar falon. Ita dai Bintu kawai ganin inno tayi da ƙaramar waya ta bata,duban inno tayi tace"inno wannan wayar fa ta waye?inno tace nakine Alhaji ne ya baki saboda kurinƙa gaisawa da Alhajin Nafisa!'to inno kiyi masa godiya, yanzu zan ƙarasa aiki sai naje nayi masa godiya nima!'inno tace"aiko yace" karki sake kije da niyar yi masa godiya,yace kiyi masa addu'a kawai ita yake buƙata!'cikin sanyin jiki Bintu tace"inno ai addu'a tsakanina daku ba mai yanke wa bace, Allah Ubangiji yaja kwana me amfani!'inno ta amsa da Amin Batula,kana ta juya ta fita daga kiching ɗin. Tunda inno ta fita ta kasa ci gaba da aiyukan ta, gaba ɗaya ji takeyi mutanen nan suna ɗaureta, wai yaya ita da take neman hanyar tserewa suke ƙara yi mata da baibayi da zaman gidan,anya kuwa zata iya ci gaba da zama A gidan tana cin karo da shaiɗanun mutane da kuma Aljanu? Lokacin da Anty Nafisa ta shigo falon inno bata tarar da kowa ba,dan haka kai tsaye kiching tanufa, dan anan takesa ran ganin Bintu, cikin Sa'a kuwa tana shiga ta sameta tana kan tunanin mafita wa matsalar datake ta tun karo rayuwar ta, Tana ganin Anty Nafisa jikinta ya fara rawa, cikin sauri ta durƙusa ƙasa dan gaidata, batare da ta amsa ba ta ɗora mata da tambayar, ina inno? Bintu tace"ta tafi wajen Hajiya Babba,zata dubata da jiki!'saurin kamo Hannun Bintu tayi sukayi can cikin kiching ɗin,hannu ta mikawa Bintu tare da cewa ina wayar da inno ta baki?cikin sauri tace gata can, tanayi mata nuni da kan prezer,da sauri Anty Nafisa ta ɗauki wayar tare da buɗe ta tasaka mata wani layin A ciki, kana tasata A babiratin, sai da ta gama sannan ta dubi Bintu tace"ki kula da kyau, baki wayar nan yana daga cikin shirin mu dan haka ki kula da'ita tamkar yadda zaki kula da rayuwar ki,kuma duk wani shiri da kike na guduwa muna sane da hakan,zaro manyan idanunta tayi wanda idan tayi hakan baƙaramin kyau yake ƙara mata ba, Anty Nafisa tayi murmushin mugunta,kana tace" kina mamaki ko? to inaso kisani duk yadda kika zacemu mun wuce haka, mun zarta tunanin babban kaima barantana wannan ƙaramin kan naki, inaso kuma ki dinga sarrafa wannan shegen tsoron naki dan watarana zai iya hhhh gaiyato mana matsala cikin aikin mu, inaso kuma ki iya bakin ki A cikin gidan nan dan duk wanda kika gani ba Abin yadda bane ESTATE ƊIN ALHAJI BALARABE YA WUCE TUNANIN MAI TUNANI munanan munajira muga yadda ƘUDURAR ALLAH zata tarwatsa mugayen zukata da ɓara gurbin IYALEN ALHAJI BALARABE dan nasan namu ba komai bane shiyasa bana tunanin yin na dama akan abinda nake aikatawa ko kuma nace na aikata,A da har na fara karaya, na fara tunanin makomata sai Hajiyata ta nusar dani tare da ɗorani bisa hanya mai ɓullewa. Babu abinda zuciyar Bintu take sai wani irin bugu mai tsanani, Anty Nafisa idon ta ya rufe ko lura da yadda yanayin Bintu ya koma batayi ba,dan tana gama zantukanta ta juya ta fita da sauri tabar kiching ɗin,yayin da ta bar Bintu tamkar butun butumi A daskare, tuni ƙwaƙwalwar ta tafi hutun wuccin gadi,ji tayi an jijjigata da ƙarfi,wata Irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tayi tare da fashewa da wani kiɗimam man kuka mai razanar da zuciyar mai imani, dije ta zuba mata ido cike da mamakin meye yasa ta kuka kuma? ko dai irin matsalar su ɗaya? tabbas ta daɗe A laɓe tanajin Anty Nafisa sai dai bataji komai ba, tunda bata daɗe da shigowa ba Nafisan tafita,tsoron irin kukan da Bintun takeyi shiya kama dije,tsoron biyune ya haɗe mata na farko kukan Bintu wanda har yi take kamar zata shiɗe, na biyu tsoron kar A zo akamata ace ita tayiwa Bintun wani abu, wannan tunani da tayine yasa tayi saurin juyawa zatabar kiching ɗin, Amma kuma sai taji ta kasa wani irin tausayin yarinyar ne ya dinga kewayawa har cikin ɓargonta wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata, cikin sauri ta durƙusa inda Bintu take ta kama hannun ta tare da miƙar da ita tsaye,A hankali ta jawota jikinta ta shiga bub buga bayanta tana shafa kanta tana bata baki cikin taushin murya,tace" haba ɗiyata ko mai yayi zafi fa maganin shi Allah kiyi haƙuri ki daina kukan nan kowa kika ganshi yana da matsalarsa, wannan kukan da kikeyi ai sai ya cutar dake ki dena ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah shine zai yaye miki kinji!'Bintu da yanzu ta riga tayi shiru sai ajiyar zuciyar da take fitarwa ajejjere,sai da dije ta tabbatar Bintu ta samu nutsuwa kana ta janye ta daga jikinta tace maza jeki ɗaki ki wanke fuskar ki kar inno tazo ta ganki A haka baza taji daɗi ba!'A hankali Bintu ta fara takawa sai da ta kusan barin kiching ɗin kana ta juyo cikin muryar ta da ta dashe tace" mama na gode Allah ya biya ki dukkanin buƙatunki na Alkhairi ya kareki daga sharrin maƙiya!' da sauri ta ƙarasa fita daga kiching ɗin saboda wani kukan dayake ƙoƙarin kufce mata, Da ido dije ta bita tana ta nanata faɗin Amin akan harshen ta,haƙiƙa idan tace bata ji daɗin addu'ar da Bintu tayi mata ba tabbas tayi ƙarya, itama fita tayi jikinta A sanyaye, zuciyar ta kuma cike da tunanika iri-iri. Tana shiga ɗakin ta waɗa kan gadon tare da kecewa da wani sabon kukan, zuciyar ta cike take da ƙunci wanda bata san ranar gushe war sa ba,yau tayi da tasanin zuwa garin Abuja, Ashe dama wannan baƙin ahlin shine ahlina da fafi yake gayamin?tabbas iya abubuwan da na gani kawai sun isa tabbatar min da abinda fafina yake gayamin, yanzu wannan bawan Allah Alhaji Baba shine kakana? to wacece kakata kuma? wane ne mahaina?ya Allah hhhh kafitar dani duhu ka kawo min ɗauki, to ita Anty Nafisa wacece"?kuma matar waye?me yaya Abdallah yayi musu suke san cutar dashi?shi ɗan waye ne? wacece mamansa?ɗakin nan mallaki waye menene A cikinsa?shin me dame ake shiryawa da waye da waye masu shiryawar ?su waye suke neman halakani?suwaye suka ɗauke min mamana da fafina?ya Allah ka kawo min agaji, yanzu ta ina zan fara fuskantar wannan gagarumin yaƙin, fafi abin ya wuce zaton ka bazan iya ba bansan ta ina zan fara ba. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 16 ``` Hhhh sautin dariyar sa kawai kakeji amma baza kataɓa gane waye ba saboda yadda ya juya bayansa,waya ce kange A kunnen sa,ya kuma gyara zaman wayar yayi A kunnen sa,kana cikin wata murya me ƙarfi da wani irin sauti,yace"da kyau ɗan kaka aikin ka yanayin kyau,inaso kaci gaba da ɗora mun ladidi A kan hanya ita kuma tana ɗora mana yarinyar A saiti yadda zan samu biyan buƙatata batare da tasan mai nake shirya wa ba,kar kasake kayi abinda zata gane shirin mu A kanta!' Daga ɗaya ɓangaren, na kaka yace"ranka ya daɗe Hajiya ladidi baza taba gane dawa take aiki ba, saboda duk wata hanya na tosheta A binda kawai nasan tasani shine tana aiki da ɗaya daga cikin ahlin ALHAJI BALARABE, amma baza ta taɓa gane da waye ba in dai ba gaya mata A kayi ba, kuma ina da tabbacin babu yadda za'ayi ta sani dan mun toshe hanyar, kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya saboda mun haɗa kifayen mu A guri ɗaya, ba ƙaramar nasara nake ganowa A tafiyar nan ba, Ogan nasa ya sheƙe da wata muguwar dariya kana yace"naga fa kifayen nan suna da matuƙar wayo yaƙin suka fito da gaske, sai dai kuma ta yaro kyau take bata ƙarko basu san suna tun karar masifa da kansu bane, mutuwarsu suke kira, dan dazarar munci moriyar ganga zamu yada gauranta,ƙit ya yanke wayar tare da cire layin ya taune,cikin alfahari da kansa da yadda yake wasa da ƙwaƙwalwar mutane yace"shi yaƙi ɗan zanba ne idan baka iyashi ba zai kife da kai. A hankali ta tura ƙofar falon saida ta tabbatar baya ciki kana ta shiga, kimtsa falon ta farayi kamar yadda ta saba, sai da ta tabbatar da komai yayi daidai kana ta faɗa bedroom ɗinsa saida ta gama wanke toilet ta gyara ɗakin, tana cikin sharewa taji wani zumm zumm A ƙugunta,zabura tayi dan sam ta manta da wata waya A jikinta,cikin sauri ta ciro wayar ta danna ok A lokaci ɗaya tana ɗorawa A kunnen ta, muryar Hajiya ladidi ta doki kunnenta, cikin rawar murya tace" Hajiya ina kwana!'ta can ɓangaren cikin yin ƙasa da murya Hajiya ladidi tace"ke kina ina yanzu ina san zanyi magana dake? kamar zata yi kuka Bintu tace" ina falon ya Abdallah ina gyarawa!'Hajiya ladidi ta saki wani uban tsaki, tare da cewa kaji banza ƴar shishshigi A yaushe ya zama yayan naki? in dai har zaki fara tunanin ya zama yayanki ashe bazaki saki jiki kiyi mana yadda mukeso ba,to bari jiki da kyau inaso kisa A ranki wannan aikin da zakiyi shine rayuwarki gazawar ki A aikin yana daidai da ɗaukewar numfashinki, dan haka ki gaggawar fita daga inda kike zan magana dake!' tana gama faɗar haka ta kashe wayar,A dai-dai lokacin da Bintu take ƙoƙarin maida wayar ma adanarta shi kuma ya sawo kai cikin ɗakin,A matuƙar firgice Bintu take kallonsa ƙirjinta babu abinda yake sai wani irin bugu da ƙarfi tamkar zai fito waje, Abdallah sam bai gane me Bintu take ciki ba, Amma yanayin firgici da tsoro da ya gani akan fuskarta yasa ya gane bata da gaskiya, zuba mata ido yayi yana so ya ƙara karantar yanayin ta, A yayin da Bintu tayi ƙasa da kanta tana ɗan jajjan zara zaran yatsun hannunta,jikinta kuwa da za A ɓula baza a sami jini ba,saboda tsabar fargaba, (Allah sarki Bintu Abinka da wanda bai saba aikata rashin gaskiya ba) Cikin maganar shi ta ɗaukar hankali yace" da ita ina breakfast ɗina?wata sassanyan Ajiyar zuciya ta sauke cikin ƴan sakanni ta dawo haiyacinta,cikin shagwababbiyar muryarta tace" yanzu zan je na kawo!'cikin janye jikinsa daga bakin ƙofar yake cewa A ransa, meye wannan yarinyar take shiryawa suwaye ne suka turota? ƙwafa yayi hmm ko meyene zan kamaki da hannuna,ranar kuwa ta tabbata bata da mai ceto. Cikin hanzari ta gama shirya masa karin ta koma ɗaki tare da sawa kofar key,sauri tayi ta zaro wayar ta dannawa Hajiya kira, ko gama ringin batayi ba ta ɗaga tare da cewa,uban me kika tsaya yi tun dazu? cikin sauri tace" Hajiya ai ya kusa kamani ina waya,kuma kinga idan na tawo ban gama masa aikin ba dole inno zatazo nemana kinga ai da ta ganni ina waya zata tambaye ni dawa nakeyi! Hajiya ladidi ta katse ta da cewa na fahimta bar dogon sharhin nan ki buɗe kun nan ki kiji Abinda zan gaya miki,Bintu tace tom Hajiya ina sauraren ki!' Hajiya ladidi tace" kinsan dije ƴar aikin matar mansur?tace ban santa ba!' Hajiya ta ɗora da cewa zaki santa kuma dole kisanta saboda so nake ki shiga jikinta ki gano mun matar da take wa aiki A cikin ESTATE ɗin ALHAJI BALARABE,shine aikinki na farko na biyu shine Abdallah lallai inaso nasan abinda suke shiryawa shida ubansa daga nan zan ɗora miki babban aiki, zahra kiyi ta ka tsantsan da aikin nan duk ranar da kika yi sakaci wani ya gano ki to shike nan kin kaɗe, dan ina tabbatar miki bazaki taɓa iya ambatar ko da harafin L ba bare ƙarshen sunana dan haka ki kula da aikinki rayuwarki ina kuma jaddada miki shine rayuwarki (dake rayuwar A hannuku take ba.) Tunda suka gama wayar take kai kawo A cikin tsakiyar ɗakin sosai ta fara jin ƙwarin gwiwa,tana ganin Allah ne ya dubeta ya kawo mata mafita ta tsanin da zata hau dan kaita hanyar da zatabi dan binciko ƙullellen ƙulli mai cike da mugun zarge,cikin ƙarfin zuciya tace" Hajiya ladidi bani ce da kuka ba kece da kuka har da birgima kin jawo wa kanki da kanki tashin hankali shekarar tonon Asirinki dake da mabiya bayanki da sauran mutanen munafukan cikin estate ɗin nan yayi Ni ɗin nan sai na zame miki ciwon ido dake da duk wani azzalumi, ku shirya domin ƴar zakanya ta girma, gani nan gareku maƙiya Allah duk sai na binciko gaskiyar datake A binne, yanzu ne za a fara wasan. Inno ce zaune Bintu kuma nayi mata tausa yayin da Hauwa'u da Rahima ke zaune saman kujera, Rahima hira take ta zubawa inno da Bintu Ita kuwa Hauwa'u gaba ɗaya hankalin ta da tunanin ta yana kan scring ɗin wayar ta wanda ba komai take kallo ba sai hoton Abdallah,inno tace zahra ku tashi na aike ku wajen Hajjah dama baki taɓa zuwa kun gaisa dasu ba Rahima daga nan ki rakata wajen Hajiya Babba ta gaidata!'tun kafin ta rufe bakinta Rahima ta miƙe tsaye tana cewa ku taso muje, Hauwa'u da sai yanzu hankalin ta ya dawo kansu, ta wani taɓe baki gami da cewa Ni bazani ba!Rahima itama taɓe bakin tayi tana cewa Mutum dai wallahi ya gamu da aiki A rayuwar sa,tayi saurin jan hannun Bintu suka fita inno tana kiranta basu karɓi saƙwan ba, amma ina tuni sun ƙule,inno ta riƙe baki tare da cewa oh Ni zainaba jikar mutum biyu kome zasuje su faɗa oho. A hankali cikin nutsuwa suke ta kawa har suka kai ɓangaren Hajjah, da sallama suka shiga falon tsarinsa iri ɗaya da falon inno komai iri ɗaya ne sai dai kala ta ban banta, Hakimar macece kanuriyar asali mai matuƙar riƙo da Al'adunsu, tun daga yanayin ƙamshi na musamman da ya cika falon, tana zaune cikin kujerar ta ta alfarma, jikinta nan naɗe da lafaya mai asalin kyau da tsada,sai kuma Dady ane (Alhaji mansur)dake zaune kan kujerar data ke fuskantar ta, ga dukkan nin Alamu dai tattaunawa suke mai muhimmanci. Amsa sallamar sukayi A tare suna mai zubawa Bintu ido dan ganin baƙuwar fuskace A garesu,kamar yadda ya kasance ɗabi ar Bintu durƙusawa tayi har ƙasa ta gaidasu,haka Rahima itama tayi, Dady ane ne ciki yanayinsa na zafi da rashin sakin fuska, yace"ke Rahima ina kuma kika samo wannan kalar zabiyar? cikin yanayin tsoron sa da ya sabar musu Rahima tace" inno aka kawowa ita dan ta dinga taimaka mata kuma tana dafawa ya Abdallah Abinci da gyara masa sashe!'tana direwa Dady ane yasaki wata banzar dariya me ƙurar da zuciya, yana cewa ayyo haka zaki ce ƴar aikin inno ce kawai amma ba sai kinyi wani dogon bayani ba!' Hajjo ta ɗan gyara kashin giɗarta kana cikin girma da nuna isa tace" wai Mansur meyasa baka girma? wannan wane irin zance ne shi ɗan Adam ai ba abin tozartawa bane kadinga kiyaye harshen ka idan ba haka ba wataran zakayi da nasani!' dawo da hankalinta tayi kansu Bintu cikin sakin fuska tace" yarinya meye sunanki? Bintu ta amsa da cewa sunana Fatima zahra amma anfi kirana da Bintu!'Hajjah tace masha Allah Bintu suna mai daraja!'gani kawai Dady ane ya tashi fice A fusace,inno ta girgiza kai tana binsa da addu'ar shiriya,Rahima tace Hajjah bari mu kewaya sashen Hajiya Babba!'Hajjah tace"to madalla amma ku kujirani kaɗan ina zuwa,tana barin falon sai ga Yaya sagir ɗan gidan Alhaji mansur kasance war dashi da Nabil ɗan gidan Anty Asiya da take kaduna A wajen Hajjah suke, turus yayi ganin su Rahima zaune, A hankali ya ƙara so cikin falon yana da ɗa ƙure Bintu da kallo, zama yayi kana suka gaida sa,Bintu duk tabi ta takura da kallon ƙuril ɗin da yake Binta dashi, cikin ikon Allah sai ga Hajjah ta fito tana cewa na barku ku kadai ko? ko da ike ma ga Aku nan Sarkin zance zata ɗebe miki kewa!' tana mai nuni da Rahima datake ta zunɓura baki dan tasan da ita take,Ya Nabil yayi zaraf ya amshi zancen da cewa,aiko Hajjah kamar kin sani tana nan ta dami friter da shegen surutu!'gaba ɗaya suka dubeshi Rahimace tayi saurin tambayar sa wace kuma haka!'ɗage gida ɗaya yayi kana yace gatanan Bintu ko ke baki taɓa ganin kamar su ba?Rahima ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa Wallahi kuwa Ya Sagir so saima sai dai Bintu har tafi friter kyau!' yauwa ƙanwas ashe kin gane!' Hajjah tace karɓi nan kinji faɗima idan kika biye waɗan nan bazaki taɓuka ko mai ba zani ce ta tadda mujemu!'gaba ɗaya dariya sukayi har Bintun, karbar ledar tayi tana yi mata godiya, Hajjah tace" karki damu duk wanda ya shigo Ahlinmu yazama namu Allah yayi muku Albarka!'gaba ɗaya suka amsa kana sukayi mata sallama, har Sagir ya yunƙura zai bisu Hajjah ta dakatar dashi da cewa ina kuma zaka bayan kasan neman ka nake!' dole ba dan ransa yaso ba ya koma ya zauna. Cikin kulawa Rahima ta dubi Bintu tace"gaskiya Fatima na fahimci kina son sunan ki!' ɗan kallonta Bintu tayi, kana tace"saboda me kika ce haka? Rahima tace kawai dai nayi la'akarine da yadda idan an tambayeki sunanki kikan faɗi duk wanda yazo bakinki, Amma mu meyasa baki gaya mana ana kiranki da Bintu ba? Bintu ta saki ƙawataccen murmushin ta wanda har sai da gefan kuncinta duka suka loɓa,kana cikin sautin muryar ta me daɗi tace" kai Anty Rahima to bagashi yanzu kin saniba,kuma kin riga kin bawa kanki amsa,dan haƙiƙa inason sunayena duka ko Batula kika kirani dashi zan amsa!' ta ƙarasa maganar fuskar ta ɗauke da ƙayataccen murmushi,Rahima ma dariya tayi tare da cewa to Ai hikenan nima duk wanda yazo bakina dashi zan kira ki!'da wannan hirar suka ƙarasa sashen Hajiya Babba. Lokacin da suka shiga kimtsetstsen falon Hajiya Babba wanda yake cike da wani mayan ƙamshi mai sanyaya zuciya, samun ta sukai zaune akan sallaya da hijabinta fari ƙal sai casbaha dake hannunta tana ja, har gabanta suka je suka durƙusa suka gaida ta, Rahima cike da soyayyar kakar tata ta raɓa jikinta ta kwanta,cikin nutsuwa Hajiya Babba tasa hannu ta jawo Bintu jikinta tana cewa' ke kam Rahima anyi babbar kobo yanzu ai bakece autar jika ba,faɗima ce! Bintu tayi luf jikin Hajiya Babba, yayin da wata irin ƙauna me haɗe da kewa ta lulluɓe zuciyar ta tanajin kamar ta dauwama tare da wannan mata mai tsananin kyau kamala kirki da nagarta, muryar Rahima ce ta katse mata tunani da cewa kai Hajiya Babba dama nasan haka zaki min shi yasa tunda kike cewa na kawo miki Bintu naƙi kawota nasan fada zata ƙwacen A gurinki!'Hajiya Babba tayi ɗan murmushi irin nasu na manya tana ta ɗan shafa kan Bintu, yarinyar ta shiga ranta sosai tanajin shauƙin ƙaunarta tamkar su Raihana. Sun daɗe A sashen Hajiya Babba, Bintu ta sake sosai da ita saboda yadda Hajiya ta sakar mata fuska ta nuna mata ƙauna ta zahiri da ba ɗini, haka da zasu tafi Hajiya ta Haɗa mata kayan amfani sosai kana sukayi sallama, Hajiya taji kewar yaran sosai. Kewayawa sukeyi cikin Babban ESTATE ɗin, Raihana tana nuna mata kowane ɓangare da kuma me shi, sunzo dai dai ta wajen hanyar da zaka miƙa ka koma ta cikin wannan ɗakin, Bintu ta da kata, yayin da ta zubawa hanyar ido tana tuno abinda ya faru ranar tamkar A lokacin yake faruwa,sai da Raihana ta taɓata kana ta dawo haiyacinta tare da cewa Raihana gurin nan ya burgeni muje ta wajen mu zaga, naga kamar lambuneee...... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 17 ``` A tsorace Rahima take duban Bintu cikin tabbatar mata da abinda zata faɗa, tace" ke Bintu ki rufa mana Asiri kin san kuwa babu wanda yake iya bi ta wajan nan!' Bintu cikin tsananin mamaki tace" to saboda me? kuma waye ya hana zuwa gurin?Raihana tace" babu wanda ya hana, hasalima ba A taɓa yiwa kowa gargaɗi da zuwa wajen ba, nima haka nataso nagani ba wanda yake iya zuwa, sai dai ban taɓa tunanin yin tawajen ba kuma bantaɓa ganin wani yaje ba ko zancen babu wanda ya taɓa yi balle musan dalili!' tunda ta fara magana Bintu take kallon bakinta cike da maɗaukakin mamaki da tarin al'ajabi,to ya akayi ita taje wurin harma take tunanin ƙara kusan tar wurin? wai meyake faruwa A cikin gidan nan? dole ta saka ido akan ɗakin nan dan ita ɗin cikakkiyar shaida ce A kan rashin gaskiyar dake tattare A cikin ɗakin,dole tasan waye mai shi da yadda akayi aka samar da shi, Rahima ce ta dubeta cikin nutsuwa tace"yaya dai koda matsalane? Amma idan kinji kina san zuwa zaki iya zuwa amma Ni dai bazanje ba, da sauri Bintu tace a'a nima bazani ba muje kawai. Cikin takunsa na ƙasaita yake tun karar ƙofar da zata sadashi da office ɗin sa wayar sa dake ringin ya ɗora A kunnen sa kana ya fara magana cikin ingantacciyar muryar sa me daɗin saurare, yanzu zan shiga office ɗin inaso katuran dukkan bayanan ta cikin e-mail ɗina zan duba!' abinda yace kenan ya katse kiran, A dai-dai lokacin kuma ya ƙara so office ɗin da sauri sakatariyar sa ta tashi ta buɗe masa ƙofar tare da cewa good morning sir!' kamar dai kullum bai saurareta ba yay shigewarsa,binsa tayi da ido kana tayi ƙwafa tare da cewa kai Dr Abdallah matarka ta shiga uku da nunƙufurci,( niko nace ke kibar irin su Abdallah idan suka tashi basu iya soyayya ba) Bayan ya ɗan yi wasu muhimman abubuwa sai kuma ya janyo laptop ɗinsa ya shiga duba baya nan da Aka turo masa,lumshe idanunsa yayi A yayinda ya gama duba duk bayanan da aka turo masa akan binciken Bintu. Yarinyar nan kenan duk labarinta da ta bayar na ƙaryane? to me hakan yake nufi?gashi dai an binciko masa komai akanta sai dai Abu ɗaya ne basu samu ba, shine A salin inda suka fara zama,wato daga inda suka tawo,A yadda samu bayanan ance ba asan inda fafinta yayi ba kawai anwayi garine anga baya nan, daga nan ita ma Bintun ko kwana ɗaya bata ƙaraba ta gudu daga garin, hatta da gidan da suka zauna sai da aka ɗauka aka turo masa. Jinjina kansa yayi cikin takaicin da ya tokare masa maƙoshi yace"dolene nasan koke wacece!' ƙofar office ɗin aka turo tare da yin sallama, A hankali ya buɗe idanunsa dake alumshe har sun canja kala saboda ɓacin rai,Dady jafar ne ya shigo yayin da yake ƙoƙarin zama yace"Abdallah banaso kasaka damuwa mai yawa A cikin ranka har yayi maka sanadin wata cutar,ka riga da kasani koda ba Ahlinka bane bincike yazaman maka dole tunda aikin kane, kariga da kasan cewa aikin likitacin nan kaje kayi shine musamman dan ɓatar da hankalin mutane akan ainihin aikin ka amma kuma kaga hakan yazame maka aikin lada ta ɓangarori biyu, ga ladan nemo lafiya ga na nemo gaskiya,dan haka Abdallah ina baka shawara kasaki jikinka da mutane gidan nan musamu abinda muke nema, ko ita wannan yarinyar Bintu kamata yayi ka ɗan sake mata ko yayane dan hakan shine zai bamu damar sanin abinda yake tare da ita!' Ɗan furzar da iska yayi daga bakinsa kana yace" Dady bazan iyaba mukin dake cikin zuciya ta bazai bari ba ina jin ƙuna da gaske bazan iya sakar musu jiki ba Dady,ita kanta yarinyar mamakinta ƙara cushe min tunani yake!'Dady jafar ya dafa hannunsa kana yace"Abdallah karkayi saurin zargi dan bashi da kyau kafini sanin hakan,Ni inaji kawai kamar da abinda ya kawota gidan na daban bawai Abinda kake zargi ba,amma dai bincike shi zai nuna mana komai,bari na koma office ni!'Abdallah yace" nima fita zanyi Ni da Yahya akwai aikin da zamuje!'ok to ba damuwa sai mu fita tare kawai, Gaba ɗaya Bintu ta saka kanta cikin tunanin yadda za ai ta san wace ce dije,zama tayi A gefan gadonta,tana mai cigaba da lalubo mafita, can kuma sai tunanin wannan matar ya faɗo mata, to ita kuma wannan ko wace?gashi tun ranar bata kuma ganin ta ba, kamar an mintsine ta haka ta miƙe da sauri,tana ganin cewa tunani daga zaune bazai yi mata ba gara ta fita ko Allah ya taimaketa taci karo da abinda zai warware mata gaddama, Kai tsaye ta fita bayan ta sanar da inno zata ɗan zaga ta gaji da zaman guri ɗaya, har inno tana cewa ko duk kewar Ƙawarta Rahima ne ya dameta, saboda Rahiman sunje mai duguri ita da amna da Hajjah yayar amna ɗin ta haihu, murmushi kawai tayiwa inno ta fita daga ɗakin da cewa sai na dawo inno!' tafe take tana saƙa da warwara,cikin ranta harma batasan ta bangaji mutum ba sai dai taji kalmar subhanallah,da sauri ta maida hankalinta kan matar,wani irin farin cikine ya rufeta yayin da ta haɗa ido da matar nan,wanda hakan sai da ya nuna A kan ƙawa tacciyat fuskarta,Dije ma murmushine ɗauke A kan fuskarta,cikin fara'a Bintu ta duƙa har ƙasa ta gaida Dije,cikin farin cikin girmamawar da Bintu tayi mata ta amsa tare da cewa sarkin kuka ina kukan? Bintu tayi ƙasa da kanta tana murmushi, yayin da take tunanin ga mafita Allah ya kawo mata,to' amma ta ina zata fara wannan tambaya ba tare da tayi mata wani mummunan zargi ba, Dije ta katse mata tunani da cewa ƴan mata meye sunanki? wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Bintu ta sauke saboda jin tambayar da matar tayi mata,A hankali tace" sunana Bintu kuma Ni ƴar aikin inno ce,cike da gamsuwa Dije tace masha Allah duk da tariga tasan komai game da Bintun amma bata nuna mata haka ba, gabas ta duba ta dubi yamma kana cikin ta ka tsantsan dije ta miƙawa Bintun hannu kamar zasu gaisa amma sai Bintu taji ta bar mata wata yar takadda A cikin hannunta lokaci ɗaya Bintu ta fahimci Abinda Dije take nufi wato tana son isar mata da wani saƙo ne shiyasa tayi hakan,juyawa Dije tayi da niyar tafiya,Bintu tayi saurin cewa dan Allah mama meye sunanki? Sunana Dije! yayin da taci gaba da tafiya batare da ko waigeba, Abin baƙaramin mamaki ya bawa Bintu ba, dama wannan ce Dijen da take ta nema? Ita kam wace irin me Sa'a ce da A duk lokacin da take neman Abu sai taga ashema abin yana kusa da ita ko tana tare dashi, lallai wannan shi ake kira da ƘUDURAR ALLAH. Tana shiga ɗakinta kai tsaye toilet ta faɗa ta ɗaura alwalar azhar, bayan tayi sallah tayi addu'o'inta tare da ƙara miƙa godiyar ta ga sarki Allah jalla wa'azza mai iko buwayi gagara misali haƙiƙa tayi yaƙinin cewa Addu'ar Umminta da fafi da Baffa Jauro sune suke tasiri A kanta da kuma wadda take cigaba dayi dare da rana batare da ƙosawaba,kuma tayi yaƙinin Allah zai ci gaba da kareta da bata nasara A rayuwar ta har ta kai ga cin nasara A kan kyakkyawar manufarta,daga nan kiching ta nufa ta kama aikin shiryawa oganta Abdallah Abincinsa tanayi tana tasbihi, zuciyar ta na ƙara samun ƙarfi da nutsuwa. A can ɓangaren Hajiya ladidi kuwa ta hana Aunty nafisa yawan zirga zirga A ɓangaren inno, duk dan kar A gano tsakaninta da Bintu dan A cewar Hajiya ladidi yawan tsanar da tayiwa Bintu ma zata iya sawa A saka musu ido tunda bata iya ɓoye tsanarta wa Bintu ba,yayin da kuma take jin daɗin yadda Bintu ta karbi aikin hankali kwance batare da ta ƙara nuna musu rashin amincewa ba yake matuƙar yi mata daɗi, har tana ganin kamar dan Bintun taje taga daula ne yasa ta canja ra'ayin ta,tana ganin indai hasashenta ya zama gaskiya to lallai nan gaba idan aikin Bintu yanayin kyau batare da wani kuskureba zata iya jawo ta cikin tafiyar, saboda ta fahimci yarinyar tana da matuƙar baiwa ta basira da kaifin tunani. Tunda suka shigo farfajiyar gidan idanunsa suke kan hanyar ɗakin nan, in dai kuma idanunsa ba gizo sukayi masa ba sai yaga kamar giftawar inuwar mutum ta can bayan ɗakin, har Yahya ya buɗe masa ƙofa bai sani ba saida yahyan yace" sir Bismillah! kana ya zuro dogayan ƙafafuwan sa da suke sunƙe cikin wani arnan takalmi sau ciki sai sheƙi yakeyi,taku yake me cike da zallar ƙasaita kai kayi zatan sarkine, ko mai na Abdallah abin burgewane da ƙayatarwa,dai dai hanyar da zai ɓullah ya shiga ɓangaren inno sai ga Dady ane,(Alhaji mansur)kamar an jefoshi,ɗan kaucewa Abdallah yayi tare da cewa Barka da yamma Dady!' washe baki yayi tare da cewa Abdallah ne?ya naganka yau ka dawo da wuri? Abdallah bai samu damar bashi amsaba sai ga Dady nan ya ƙara so(Alhaji Habib)da murmushi A kan fuskarsa,yace"yana ganku anan ba shiga zakuyi bane?gaba ɗaya suka shiga falon inno bakunansu ɗauke da sallama, Inno suna zaune ita da Bintu harda ma Hauwa'u,ta amsa tana cewa sannunku kamar duk tare kuke!' Alhaji Habib yace"A'a inno duk Haɗuwar ƙoface yana maganar yana zama,ga mamakin Bintu da inno kai Harma Hauwa'u da tunda ya shigo ta daina gane na kusa da ita,zama yayi shima yana gaida inno da sannu da gida, Abinda suka sanine haka kawai bai cika zaman falon inno ba idan ya shigo ƙarƙarinsa ya gaidata ya wuce part ɗinsa,mamakin bai gama sakin su ba saida yasa tsadaddiyar muryarsa yace" ke ki kaimin wannan falona!' yadda yayi maganar bazaka taɓa fahimtar da wa yake ba ko kuma kayi tsammanin idanunsa abuɗe suke, saboda kansa jingine yake A jikin kujerar yayin da idanunsa suke A lumshe tamkar mai bacci,Hauwa'u ce tayi saurin tashi taƙarasa har inda yake, tasa hannu zata ɗauki jakar laptop ɗin kenan yace" bake nasa ba! cak Hauwa'u ta da kata yayin da wani irin haushi da takaici ya turnuƙeta,haka ta koma mazaunin ta jiki a saluɓe, Bintu kuwa tun sanda yace da Hauwa'u bake nasa ba, jikinta ya shiga baburashin dan ita kwata kwata bata san abinda zai kusanta ta dashi, dan ita kaɗai tasan irin bugun da zuciyar ta keyi da yadda take rikicewa duk saboda tsoronsa,A hankali ta miƙe kamar an zare mata lakar jikinta,zuwa tayi ta duƙa ta ɗauki jakar yayinda zuciyar ta kamar zata yi tsalle ta faso ƙirjinta,sai da ta raba kanta daga kusa dashi kana taji komai nata ya dawo daidai. Duk wannan diramar da sukayi hankalin Dady ane yana kansu, yayin da Alhaji Habib suke ɗan tattaunawa da inno,inno ta dawo da hankalin ta kan Abdallah yayin da take ce' masa yaya dai Abdallah naga ka dawo da wuri ince dai lafiya?ɗan motsawa yayi kana yace" inno ai yanzu zan dinga dawowa da wuri saboda na ɗauki hutun Asibiti yanzu ina ɗan wani aikine dan haka wataran ma babu inda zani zama zanyi muyi hirar soyayya!'yana gama faɗa inno ta ɗauka da wata shewa irin ta dattijan da sukaji daɗin wata magana, tace"haba ɗannan kamar bansan halinka ba,kaine zaka zauna nan kayi hira sai dai kaita lum-lumshe idanuwa kana taɓa waya!'murmushi kawai yayi batare da ya kuma tankawaba dan wannan ma da yayi ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba, muryar Dady ane ya tsinkaya yana tambayar sa wane aikine kuma zakayi shi a gida dan fi'ili? Alhaji Habib ya tari numfashinsa da cewa haba yaya bai kamata ba dan yace yana da aiki sai kaji ko wane irine? Afusace ya miƙe ya na nuna shi da yatsa yace" mansur ka dai nayi min katsalandan A cikin lamurana, ban isa na tambaye shi bane ko yaya?kana ƙoƙarin fa kadinga ganin ka zubda min da girma a gaban yara amma babu damuwa!' yayi ƙwafa tare da ficewa daga falon,inno ta dubi Alhaji Habib tace dan Allah Habibu ka daina shiga dabgarsa kasan dai ɗan uwan kane yadda Allah yayi mutum babu yadda za ayi wani yace zai canja shi!'numfasawa yayi kana yace" wallahi inno idan nayi kamar zan dinga ƙyale yaya mansur da halinsa sai naji sam bazan iyaba saboda yana zubarwa da kansa ƙima a idon mutane ba daga nan gida ba har can waje!'tace"to addu'a zamuci gaba dayi masa Allah Ubangiji ya shirya mana shi da dukkan zuri'a baki ɗaya!'da Amin ya amsa kana ya miƙe yace inno bari na shiga wajen Alhaji Baba!'to madalla afito lafiya, yace" Amin gami da fita daga falon. Yana zaune har suka gama faɗe-faɗensu suka fita bai ɗaga kai bama balle yasan sunayi,kamar jira yake dama su fita shima ya tashi yana cewa inno bari na ɗan huta kafin magriba! Inno tace au duk kun gudu? itama wannan daga aike shine ta sulale ta gudu, ita kuma wannan dama bata da amfani ta nuna Hauwa'u da tayi kamar bata falon saboda takaicin abin da yayi mata da kuma haushi da tsanar Bintu,binsa tayi da wani mayen kallo,yayin da shi kuma ya shiga sarrafa dogayen ƙafafunsa kan tattausan carpet ɗin dake malale bisa kafcecen falon,ba ita ta ɗauke idan ta daga kansa ba har sai da taga shigarsa falonsa. Ita kuwa Bintu dama tuntuni take neman hanyar guduwa,dan ta ƙagauta ta ji abinda takardar nan ta ƙunsa,tana zuwa kuwa ta zaƙulo takardar ta warwareta gaba ɗaya...... More comment... More, typing........ Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 18 ``` Ga abinda ke cikin saƙon, Bintu inason ganinki kuma kema nasan kina buƙatata dan haka daga yanzu ki fara shirin yadda zamuyi mu haɗu,dan bazata yiwu A cikin gidan nan ba, dole kisan yadda zakiyi ki fita daga gidan nan, Ni kuma daga yau zan fara tunanin inda zamu haɗu,sai dai matsalar ɗaya ce ke baki san ko ina A cikin garin Abuja ba,shiyasa ban san inda ya kamata na samu wanda bazakiyi wahalar ganewa ba,amma dai ko meye ma kikasance cikin shiri,da kuma lura dan gidan nan haka yake zaki ga kamar babu mai lura dake amma abun ba haka yake ba, koda ƙwarone yashigo ESTATE ɗin ALHAJI BALARABE,to shakka babu Ana biye dashi, sai dai bazaki taɓa gane hakan ba,ina mai ƙara tunatar dake da ki lura sosai. Bintu tana gama karanta wasiƙar ta koma cikin toilet tayi ploshin ɗinta,kana ta fito ta kwanta saman gadonta gami da rufe idanunta, cikin hasasowa kanta dabarar fita daga gidan batare da ankarar wasu manyan ƙayoyin gidan ba, wayarta dake kan bed side ta ɗan kalla har ta kawar da kanta sai kuma ta tashi da sauri tare da rarimo wayar saboda wata dabara da zowa ƙwaƙwalwarta A lokaci ɗaya,cikin sauri ta shiga latso lambar Hajiya ladidi,batare da jan wani lokaciba ta ɗaga kamar dama jiran kiran takeyi,yaya dai Zahra Ina fatan jin bayani mafi daɗi daga gareki!' cikin zumuɗi tace Hajiya wallahi an samu sai dai kuma akwai ƴar matsala!'Hajiya ladidi tace" ki gayamin, nasan ko wace irin matsalace bazata fi ƙarfina ba!' cikin murmushin samun nasara Bintu tace"Hajiya na samu hanyar haɗuwa da dije, dan ta bani baya nai akan matar da take yiwa aiki, sai dai tace bazamu haɗu acikin gidan nan ba dole sai dai mu fita can wajen gari domin haɗuwa,to kuma tayi min bayanin cewa kar na bari agane akwai wani shiri tare dani shine tun ɗazu tunanin da nakeyi hanyar da zan samu na fita batare da wata matsala ba!'Hajiya ladidi ta sauke wata Ajiyar zuciya tace" Zahra ai wannan ba wata matsala bace baga Nafisa ba ki kwantar da hankalinki zaki fita cikin salama batare da zargi ko bincike ba!' A hankali Bintu ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya,kana tace"to shike nan Hajiya na gode!' Hajiya ladidi,tace" ai nice da godiya!' daga nan suka ajiye wayar, Bintu tayi wani sassanyan murmushi,kana afili tace" Hajiya nice da godiya irin wannan aiki da kike min dole na gode miki. Zagaye falon yake hannayen sa goye A gadon bayansa, inuwar mutum da ya gani ta wajen ɗakin nan shine abinda yake taɓa zuciyar sa, tabbas yana ganin wannan binciken shine zai bashi wahala a dukkanin sauran binciken da yasa A gaba,to amma dai ba zai taɓa karaya ba,yana da tabbacin samun nasara akan kowane mara gaskiya. Alhaji Farouk ne zaune A gaban mahaifiyar sa Hajiya Babba,daga dukkanin alamu ma kuka yakeyi,cikin damuwa da alhinin halin da ɗan autanta yake ciki, cikin ƙauna da tausayi irin ta ɗan da ake matuƙar so,tace"autana kayi haƙuri banaso wani ciwon ya daɗa kamaka bayan ciwon zuciyar da kake dashi dan Allah Farouƙu ka daina wannan damuwar nima da fa karkamanta kwatankwacin irin damuwarka ce dani, amma nayi haƙuri na fauwala wa sarki Allah na miƙa masa komai A hannunsa shi zai yi mana maganin dukkan masifun da suka kewaye mu,banaso kaci gaba da nuna damuwar ka ne saboda nasan idan maƙiya zai koma kanka, amma idan ka ɓoye damuwarka wa maƙiyanka zaka samu salama baza A kuma ƙoƙarin cutar min da kai ba,kaji autana!'ta ƙarasa maganar cikin lallami da shaukin ƙauna da tausayi,ɗago kansa yayi yayin da idanunsa sukayi jawur kamar garwashi,cikin dishewar murya yace"Hajiya ina matuƙar ƙoƙari sosai,idan banzo gabanki nayi kuka na rage raɗaɗin dake cikin zuciyata ba tabbas wata rana za'a shigo miki da gawata, ke kaɗaice wadda zan iya zama gabanki inyi kuka kuma ki rarsheni koda ace bakisan silar damuwar tawaba, ballantana ke ka ɗaice kikasan damuwar dake binne cikin raina!'ya ajiye maganar cikin jan wata sheshsheƙa dake nuni da tsananin damuwar da mutum ke ciki,A hankali Hajiya Babba ta ɗora hannunta akansa tana shafawa tare da cewa, hakane Farouƙu,na gamsu da maganar ka,Ni dai fatana da addu'a ta Ako da yaushe shine Allah ya nunamin ranar tonan asiri ya nuna min maƙiya da idanuna ranar da za ayi walƙiya aga idanun kowa,ya kuma kawo mana haske da farinciki A cikin ahlin ALHAJI BALARABE!'Amin Hajiyata Amin ya Allah. Bayan kwana biyu da yin maganar Bintu da Hajiya ladidi,da misalin ƙarfe goma na safiyar asabar,Aunty Nafisa ta shigo falon Inno,lokacin da tashigo Inno tana cikin ɗakinta yayin da Bintu take kiching tana wanke kwanonin da oga Abdallah ya karya,kai tsaye ta nufi ɗakin inno tayi sallama daga bakin ƙofar,inno ta amsa tare da bata umarnin shigowa,Aunty Nafisa ta gaida Inno cikin girmamawa, kana ta ɗora da cewa inno runtsawa zakiyine? Inno tace"a'a kin san Ni banfiye zaman cikin ɗaka ba nafi son zama a falo saboda gurin baya rabo da baƙi,Gara ina kusa!' Anty Nafisa ta miƙe tana cewa to bari najiraki A falon!' Inno tace"babu laifi yanzu ina fitowa!' to A fito Lafiya!'Anty Nafisa ta faɗa tana fita daga falon. A falon ta sami Bintu tana ƙara kakkaɓe kujeru,zama tayi A kan kujerar da Bintun take kaɗewa, kana cikin ƙasa da murya tace" kizama cikin shirin fita,kuma kiyi dabarar sanar da dije tun wuri saboda itama ta shirya fitar tare da tsayar da gurin haɗuwa!' tana rufe bakinta wani sassanyan ƙamshi me tsananin daɗi ya game duka hancinansu,ita Bintu tana shaƙar ƙamshin tasan cewa oga Abdallah ne ya kusanto falon dan haka cikin sauri ta matsa daga kusa da Aunty Nafisa ta cigaba da abinda takeyi tamkar ma batasan da wata halitta A gurin ba, A dai-dai lokacin ya ƙara so falon cikin takunsa na isassun maza masu matuƙar aji kwarjini,kafin kace wannan tuni kwarjinin sa da ilhamarsa wanda rabbi ya bashi suka mamaye falon,wani irin kallo Anty Nafisa take binsa dashi har yasamu guri ya zauna ya hakimce tamkar basarake. Tap ɗin sa ya buɗe yashiga aikin dake gabansa batare da ko kallon ɓangaren da Aunty Nafisa take yayi ba,cikin kwarewar sa ya shiga sarrafa ta hankalin sa kwance,Anty Nafisa kuwa ina wuta tasaka Abdallah A ciki, iya ƙarshen ƙulewa ya ƙular da ita, Anty Nafisa tanasan A girmamata macece mai san ƙasaita dan haka jin zuciyar ta take tamkar zata kama da wuta saboda baƙin cikin wulaƙancin da Abdallah yayi mata,cikin ƙufula da jin tsanar sa A ranta ta ɗauke kanta tana duban inno dake shigowa falon bakinta ɗauke da sallama, tana cewa lallai kuce na haɗa manyan ƴan hira A falona amma ba Aje ansanar dani ba dan nayi saurin fitowa!"Abdallah da ya san dashi take ya ɗago kansa yana ɗan dubanta kana yace" my inno kin tashi lafiya!' inno tayi dariyar jin daɗin sakewar da Abdallah ya farayi da ita duk da dai bawai ya canja bane amma yanzu yana ƙoƙarin ganin yayi mata magana, tunda gashi har fitowa falonta yakeyi ya zauna,duk da ba wani magana yakeyi ba amma hakan na mata daɗi sosai,tace" lafiya ƙalau na tashi Abdallah,ina fatan dai babu wata damuwa tare da da kai? jinjina mata kai yayi kawai ya maida hankalinsa kan tap dinsa. Anty Nafisa tayi wani ɗan gajeren tsaki yadda baza aji taba,to amma batasan kunnen Abdallah da shegen ji bane,dan tsaf yaji tsakin da tayi tamkar A kunnensa ta raɗa masa,amma baza ka gane hakan ba saboda yadda hankalin sa kaf yake kan tap ɗinsa,juyawa tayi suka cigaba da hira da inno,saida ta samu kamar mintuna goma da fara hirar tasu,kana cikin girmamawa tace" inno wallahi tun jiya nake san faɗa miki amma ban samu shigowa ba sai yau,inno ta ɗan muskuta tare da cewa to lafiya daiko? Anty Nafisa tace"a'a ba wani abin damuwa bane,dama Hajiyata ce takeso ki ɗan ara mata Zahra zata tayata aikin abinci saboda zatayi baƙi daga can garinmu, to shine tace"bazata iya gaya miki ba dan kar kiga kamar tanaso ta nuna miki isa ne A kan Zahra shiyasa!" Inno ta shiga tafa hannuwa gami da sakin salati kana tace"kai amma dai Hajiya ladidi sai A barta, yanzu dama tsakanina da ita akwai irin wannan? gaskiya amma banji daɗi ba,kiyi kiranta kiji yaushe takeso Bintun taje? da sauri Aunty Nafisa ta shiga kiran Hajiya ladidi A wayarta. A can ɓangaren Bintu kuwa tana fita daga falon ɗakinta ta koma,sintiri ta shigayi tana neman hanyar haɗuwa da dije, sai dai kuma batasan ko ta yaya hakan zata faru ba, hasalima batasan A wanne ɓangare Dijen take aiki ba,san nan koda ta sanima ai baza ta iya zuwa kai tsaye ba, dan matsawa tayi jikin window ta ɗaga labulen window ɗin ta shiga rarraba manyan idanuwan ta A cikin harabar gurin,hannunta taji kamar yana taɓa wani abu,janye hannun tazoyi tare da kai idon ta kan abun,zaro idanunta tayi cike da wannan yanayin nata na tsoro dake matuƙar ƙarawa fuskarta wani irin sihirtaccen kyau,A hankali tasa hannu ta zaro cukurkuɗedɗiyar paper dake soke jikin window ɗin, sauri tayi ta mayar da cotain ɗin ta rufe,cikin hanzari ta buɗe paper,wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke yayin da tayi arba da saƙon Dije wanda take sanar da ita lallal ta samu hanyar fita A yau saboda itama ta samu hanya, dan Hajiya Rabi ta aiketa cikin kasuwa,A yayin da ta kuma ɗora mata da adireshin gurin da zata sameta tare da yimata gargaɗi da ta lura dan za a iya samun me bin bayanta dan haka sai ta kiyaye kar kuma ta bari drever ya kawota, kiran inno ne ya shiga kunnuwanta, cikin wani shegen gudu ta faɗa toilet tayi floshin ɗin paper kana ta fita tana cewa inno gani nan!' Dai dai Lokacin da ta ƙarasa falon, ita kuma Hauwa'u shigowar ta kenan tana gaida Inno da Anty Nafisa,cikin sanyin jiki ta dubi ɓan garen da Abdallah ke zaune har yanzu yana aikinsa tamkar bai san da mutane A falon ba, tace" Yaah Abdallah barka da safiya! A kan tausasan laɓɓan shi ya amsa da lafiya!' wanda ba daban idanunta na kallon bakin nasa ba da baza ta gane ya amsa ba ma,zama tayi kawai tana mai ci gaba da kallon sa tamkar zata cinye shi, A yayin da da Bintu ta ƙarasa gaban inno tace"inno gani!'inno tace"yauwa Batula maza ki shiga kiching ki haɗawa yayanku Abincinsa,tunda yana gida sai kije ki shirya Hajiya ladidi nasan ganinki!'ɗan ƙasa tayi da kanta kana tace"to inno!' har zata miƙe Hauwa'u tayi saurin cewa inno tunda aika zatayi Ni bari naje kiching ɗin na haɗa masa lunch ɗin!'kafin inno tayi magana sun tsin kayo kamilalliyar muryar shi yana cewa ba buƙatar hakan,tare da jefawa Bintu wani mugun kallo wanda bata san lokacin da ta ganta ƙofar kiching ɗin ba, ta dafe ƙirjinta tana maida numfashi tare da cewa kai wannan mutum kwai masifaffe, bada ban Musulunci ba alƙur an sai na bari su Anty Nafisa su hambuɗe ka kowa ma ya huta da bakin halinka!'sai kuma ta ɗan taɓe ɗan ƙaramin bakinta ta kuma cewa ke ma dai Anty Hauwa'u n nan kamar wata mara zuciya kullum mutum yana gwasaleki amma kina daɗa shige mai!'can kuma ta tuna da mutanen ta wani ƙawataccen murmushi ta saki,tanajin farinciki A ranta ta yadda akayi tayiwa mugayen nan da baibayi,yanzu tayi matuƙar gamsuwa da yardar da Hajiya ladidi tayi da ita. Sai misalin ƙarfe ɗaya kana duk suka bar falon saboda gabatar da sallar zuhur,lokacin kuma tuni Bintu har ta kammala aikinta ta kai masa falonsa,inno kuma ta jera mata A kan dining,ɗakinta ta shiga tayi wanka ta shirya cikin wata baƙar Abaya wadda tayi matuƙar amsar dirin jikinta,Bintu tana da matuƙar diri mai tafiya da hankalin jama'a tun yanzu ma ballantana kuma nan gaba idan ta ƙara girma za ayi kallon halittar ƙudurar Allah. Ɗakin inno ta nufa kai tsaye bayan tayi sallama, ta shiga inno tana zaune bisa sallaya tana lazimi,durƙusawa tayi Agabanta tace"inno na kammala shirin,inno tace"to ki duba driver duk wanda kika samu cikin su musa ko nafi'u kice ya kaiki, cikin yin ƙasa da kai Bintu tace"inno da zan tafi Ni ɗaya da naso saboda ina son ganin hanya kuma wallahi mota amai take sani!'inno ta riƙe baki tare da cewa ikon Allah to zaki gane gidan ne? kuma dai kinga kafin ki fita daga ESTATE ɗin nan zaki sha wahala,amma bari nace su fita dake get ɗin ƙarshe inyaso sai ki wuce! jakarta ta janyo ta fito da kuɗi kimanin dubu biyar ta miƙa wa Bintu tace"gashi sai kiyi kuɗin napep!' Bintu tace" Inno kuɗin yayi yawa ki rage,inno tace" a'a banason musu kije ko zaki ga abin da kike buƙata A hanya! godiya Bintu tayi tare da miƙewa ta fita daga ɗakin ita kuma inno tayiwa ɗaya daga cikin dirobobin waya tasanar da shi cewar ga Bintu nan ya fita da ita ƙarshen get ɗin estate..... Drivern yana A jiyeta sai da ta tabbatar ya koma, kana ta shiga ta kawa A hankali har ta fito bakin hanya,wani mai napep ne ya ja ya tsaya A gaban ta tare da cewa hajjaju ina zuwa ne? miƙa masa paper hannun ta tayi wadda ta kofe adireshin da Dide ta rubuta mata, yana dubawa kuwa yace" Hajiya kuɗin ki naira ɗari huɗu! Bintu ta hau napep ɗin tare da cewa Allah ya kaimu lafiya... Yana ajiye ta miƙa masa dubu ɗaya tace ya je kawai ta bar masa canjin, Allah dai ya biya Hajjaju godiya nake! jan napep ɗin yayi aguje, ita kuma ta fara gan garawa ɗan gidan da aka fara gina shi ba A gama ba, sai dai yana ta can baya ƙofar shiga wurin ita kuma ta bayan ginin aka sauketa,tana shiga kuwa ta ga Dije sai sintiri take, alamu ya nuna ta daɗe tana jiranta, tana ganinta kuwa ta zabura tare da kamo hannunta tana cewa kin tabbatar da babu wanda ya ganki ko ya biyo bayan ki? cikin tabbaci Bintu tace"na tabbatar babu wanda ya ganni dan kafin na shigo ma sai da na da ɗa dubawa sosai! ajiyar zuciya Dije ta sauke kana tace"na yadda dake saboda nasan kina da hankali da wayo! Sai da ya tabbatar da tashiga gurin kana ya ɗauki wayar sa ya daddanna san nan ya karata A kunnensa,jim kaɗan ya fara magana da cewa sir na kawota kuma na maida Napep ɗin yanzu haka ina ɓoye cikin gurin da suke! bansan me akace masa ta ɗaya ɓangaren ba naji dai yace"zan kunna sir ba ka da damuwa da wannan kuma bazan je ko ina ba har sai na tabbatar ta tafi...... Tofa Bintu duk taka tsantsan din da kikayi,waye yasa A biyoki waye ya gane shirin ji da har yasa Aka biyo sahun ki, sanin wannan sai A page na gaba 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 19 ``` Dije ta dubi Bintu cikin nutsuwa kana tace" Bintu ina so ki gayamin gaskiyar dake cikin zuciyarki ki yarda dani kamar yadda Nima na yarda dake,nasan cewa yadda da mutumin da yafito daga cikin ESTATE ɗin ALHAJI BALARABE,Abune mai matuƙar wahala,amma Ni inaso ki yadda dani ki bani amana Ni kuma zanyi miki alƙawarin bazan taɓa ci miki ba, kamar ƴa nake kallon ki kuma A cikin jikina nakeji ke ɗin ba Macuciya bace dan haka inaso ki gayan kaɗan daga cikin abinda ya kawo ki cikin ahlin ALHAJI BALARABE!' A hankali Bintu tasa hannu ta share hawayen da suka fara gangarowa daga manyan idanunta masu kyau da sheƙi, zuciyarta kuwa babu abinda take sai kai kawo da wasu wasi, anya zata iya amincewa da Dije da sauri haka kuwa,Fafinta fa yace"mata ko ƙwaro ne yazo zai fita daga ESTATE to ta tabbatar tasa masa ido har sai ta yadda da gaskiyar sa,bata sani ba ko dai Dije yau darar ta zatayi,Dije ce ta katse mata tunaninta da cewa, Bintu banga laifin ki ba lallai ke ɗin yarinya ce mai zurfin tunani da hangen nesa hakan kuma shi ya tabbatar min da cewa zamu haɗa hannu dake dan yaƙar maƙiya da azzalumai,dan haka Ni zan fara gaya miki sirri na ba lallai ne sai kin yadda dani A yanzu ba amma zan baki dama daga nan zuwa duk sanda kikaji zuciyarki ta gamsu dani ta kuma tabbatar miki da bazan taɓa iya cutar dake ba!' Cikin Ajiye numfashi ta cigaba da cewa Bintu Ni dai da kike ganina sunana Dije kuma ina da yara guda biyu marayu mace da namiji, sanadin mutuwar mahaifinsu shi ya kawoni aiki cikin ahlin ALHAJI BALARABE,inayiwa Hajiya Rabi matar Alhaji Mansur aiki kuma yau kimanin shekaru Ashirin ke nan ina aiki A gidan,ta ɗan da kata tare da goge hawayen fuskarta taci gaba da cewa A cikin wa ɗan nan shekarun ne na haɗu da matar nan wadda har yanzu ban san wacece itaba ko magana zatayi dani ba da ainahin Muryar ta take min ba na daɗe da sanin wannan kuma farko da na nuna mata bazan iya cin amanar ahlin ALHAJI BALARABE ba sai ta kwashe min yarana duka ta ɓiyesu har yanzu bansan ina suke ba, idan tasani wani abu nayi kuskure akansu take hucewa,kullum addu'a nake Allah ya tona asirin wannan baƙar ashanar ya kawo min ƙarshenta!' ta ƙara sa maganar tana toshe bakinta saboda kukan da yake son kufce mata, cikin wani irin tausayi Bintu ta kama hannuwan ta tana ɗan jijjiga wa, kana A hankali ta buɗe baki tace"mama Dije kiyi shiru dan Allah kar ki jawo hankalin mutane masu giftawa kanmu,ki saurareni zan gaya miki iya abinda nasani da dalilin zuwa na estate din nan!' shuru Dije tayi tare da nutsuwa dan fahimtar labarin Bintu. Bintu tace"mama Dije Ni marainiya ce ta ko wane ɓangaren bani da kowa, daga wani gari mukayi ƙaura Ni da mahaifina muka sauka A garin Bauchi,mutuwar da yayi ita ta takowoni garin ABUJA,nan ta ɗora mata da yadda akayi take gidan Hajiya ladidi da komai da ya gudana A tsakaninsu da aikin da suka sakata tayi da yadda sukayi mata bara zana da rayuwar ta,ta ƙara sa da faɗin mama Dije yadda na samu karɓuwa ta karamci da mutumci daga wannan bawan Allah Alhaji Baba da yadda matansa suka karɓeni suka nuna min ƙauna yadda Inno ta maida Ni mutum yasa na ji bazan taɓa iya cutar da ahlinsa ba,ranar da kika sameni da Anty Nafisa a kiching ina kuka,ba ko komai ne yasani kuka ba sai tsananin tausayin waɗanda ake shirin cutarwa batare da sunyi musu ko maiba, sai dan tsananin zalunci da ƙeta da haɗama, A fahimta ta kenan,mama Dije kinji abinda ya shigo dani cikin wannan gida sai dai yanzu,A shirye nake dan ganin kawo karshen ƙarya da tabbatar da gaskiya,indai zaki bani haɗin kai akan hakan!'Dije wani irin kamo Bintu tayi ta rungume ta tare da cewa Allah na gode maka tabbas na gari basa ƙarewa masu gaskiya basa to zarta Allah zai kuma kawo mana wani mai gaskiyar A kusa wanda zai tai maka mana da ƙarfin sa da rayuwar sa da kuma aljihunsa tare da mai kankat wato itace gaskiya!'Bintu tace" tabbas mama Dije zamuyi nasara sai dai amma akwai haɗari tare da fuskantar ƙalubale da kuma ƙoƙarin rasa rayukanmu saboda A yadda muka sani yanzu abokan yaƙin mu ɓangare biyune da ɓangaren Hajiya ladidi da kuma shu'umar matar da kikewa aiki, kuma ina da tabbacin da A kwai wata ko wani ko wasu Allah ne masani, amma da sannu zamu bin cikosu ɗaya bayan ɗaya,Dije ta ɗora da faɗin insha Allah karshen su yazo kuma mune zamu kawo ƙarshen nasu tare da taimakon Allah da ƘUDURARSA!'Bintu ta buɗe tafin hannun ta, Dije ta ɗora nata kana suka haɗa baki wajen faɗin munyi alƙawari babu gudu duk runtsi duk wahala sai dai maƙiya su gudu! Dije tace" maza Bintu fara fita daga baya sai na biyo bayanki! tace" to mama, ki bani nomban wayanki da sauri Dije ta karɓa ta saka mata ita kuma tayi mata Plashin, da sauri ta fita daga kan gon... Kamar walƙiya haka ya fita daga kangon,batare da ya bari Bintu ta gan shi ba, Tana fita kuwa ta samu dan sahu ya kaita har ƙofar ESTATE, tana sauka taga wata luntsumemiyar mota zata shiga cikin estate ɗin har zuciyar ta taji motar ta burgeta, bayan motar ta shiga itama tabi bayanta tana mai hango yawan tafiyar da zata miƙa. A hankali yace" Yahya tsaya yarinyar nan!' daga haka ya maida idanunsa ya kulle yana mai tambayar kanshi dalilin sawa a shigo da ita cikin motarsa,wani ɓangare na zuciyar sa yace" kawai dan ita ta kasan ce mace ne shine dalili,Yahya yayi ƙasa da glace ɗin motar tare da zura kansa waje ya ɗan ɗaga muryar sa yace"ki shigo mu ƙara sa dake!' kamar daga sama Bintu taji muryar Yahya da sauri ta juyo har zatayi gaddama sai kuma ta tuna zurfin tafiyar dan haka tayi shahada tare da addu'a A bakinta, kasancewar glace ɗin tintak ne shi yasa bata lura da oga Abdallah dake kwance A bayan motar ba,A hankali tasa hannu zata buɗe bayan motar Yahya yace" a'a shigo nan yana mai buɗe mata ƙofar,batare da tace" komai ba ta maida hannunta kan ƙofar gaba ta shiga da sallama tare da addu'ar da take ta nanatawa abakinta,tana rufe kofar wanan sanyayyan ƙamshin da ya zama hadda A hancinta yayi mata maraba, A hankali ta juyar da kanta zuwa bayanta,wani irin daram ƙirjinta ya buga dama shine A cikin motar nan to amma dai tasan bashi yace ta shigo ba dan A tunanin ta hakan baza ta taɓa faruwa ba, nutsuwa tayi sosai yayin da wannan yanayin da take kasancewa A cikin sa duk lokacin da sukayi kusanci da juna ya shiga mamayarta, ƙirjinta bugawa yake duk sakan da minti,fatanta kawai Allah ya kaisu lafiya. Suna ƙarasowa ta fita da gudu kamar walƙiya haka ta ɓacewa idanunsu, Yahya kasa daurewa yayi sai da ya ƙyaƙyale da dariya yace" kai wannan yarinya kwai zabuwa ga yadda ta kwasa a guje kamar ance za a saceta!'shiru yayi saboda kallon takaicin da yaga ogan nasa na binsa dashi da sauri ya dauko jakarsa yabi bayansa da ita. Dije kuwa kasuwa ta wuce tayi sayayyarta kana ta wuce gida,yayin da zuciyarta ta samu nutsuwa, damuwarta cikin kaso ɗari taji sauƙin kaso ashirin A ciki,dan haka lafiya ƙalau ta koma gida batare da tunanin wani abu ba. Tana shiga falon da sauran gudunta inno dake zaune ita da Najib wanda yake dakon dawowar Bintu,tace" Bintu lafiyar ki kuwa? ɗan tura bakinta tayi kafin tace" wani A bu ya shigo falon cikin sallama,inno tace au ko dai tare kuke ne? Bintu cikin gunguni tace" da inno a'a daga get suka ɗaukoni!'inno tace" ashe taimakonki akayi amma kike wannan shegan taka!'bi yayi ta gefanta ya shige batare da ya tanka ba, tana ganin ya wuce ta dubi inno cikin ɗan shagwaɓe fuska tace"Allah kuwa inno tsoro yake bani shi bashi da aiki sai bawa mutane tsoro!'inno tace" ikon Allah dama mutum yana bawa mutum tsoro? A to inno shi dai kam yana bayarwa!'ta faɗa tana shigewa ɗakinta,daga inno har Najib dariyar wautar Bintu sukayi.. Yana shiga bedroom ɗinsa kai tsaye ya wuce toilet bayan ya Ajiye jakar shi,ya ɗan jima kana ya fito ya shirya cikin gaggawa saboda kiran sallar la'asar da akayi,fes ya fito cikin shigar sa ta yau da kullum wato kananan kaya sai ƙamshinsa da ya game ɗakin gaba ɗaya, yana fitowa ya wuce Pert ɗin Alhaji Baba Dan yasan yana can yana jiransa dan zuwa Masallaci dan tunda ya fara zaman gidan kwana biyu suka koma tafiya tare kamar yadda sukeyi da Asuba, amma yanzu ba Alhaji Baban ne yake zuwa ba shi yake zuwa su tafi tare wanda da ƙyar da lallashi Alhaji Baban ya yadda da haka. Tofa yau dai kasuwar ESTATE ce take ci dan kuwa kowa da baya gida ya dawo yaran masu gida ƴan makaranta duk sun dawo ɗan gidan Alhaji Mansur saiyid da yaran Baba Ali guda biyu Sadik da lamin duk A yau suka dawo ƙasar su cikin gidansu kuma ahlin ALHAJI BALARABE, Sai mata da suka dawo daga b.u.k kano taufiƙa da siddiƙa ƴaƴan sadiya, kasancewar ita ba A Nigeria tayi aure ba tana can ƙasar camaroo jikokin inno kenan kuma duk A sashen inno zasu zauna, dama sunce idan suka gama karatu bazasu koma camaroo ba dan haka sai da Bintu tayi gyaran ɗakinsu, A yayi da su kuma samarin suke ɓangaren su daban A yanzu dai samarin gidan sun kai su shida, sai ƴan mata guda bakwai wanda suke rayuwa A cikin estate, Alhaji Baba ya aurar da jikoki kusan goma sha biyar maza da mata ba iya kacin na gabansa ba kawai har na sauran garuruwa. Rahima da amna suma sun dawo ita kuwa Hauwa'u dama tunda Abdallah ya dawo estate ta daina zuwa ko ina. A wannan rana Bintu ta aikatu iya aikatuwa, shi kuwa girkin oga Abdallah dama babu ɗaga ƙafa,ba ita tasamu zama ba sai ƙarfe tara na dare,yayin da jikinta yake A sanyaye saboda yadda ƴan matan suka dinga kyararta da nuna mata asalin matsayinta,ta fuskanci taufiƙa da siddiƙa suna da matuƙar jin kai da ɗagawa yayin da Farida take da mugun wulaƙanci kuma A kwanta da baƙar magana, itace auta A gurin babanta Alhaji Habib kuma A cikin ƴaƴan da ya haifa duka mata ita kaɗai ce bai aurar ba,Rahima da amna su kaɗai ne sukewa Bintu kallon mutum. Washe gari dawowar su, Bintu tana kiching tana ta sauri ta haɗawa oga Abdallah kayan karin kumallo saboda yau taso ta ɗan makara kasancewar gajiyar da ta tara A jiya, siddiƙa ce ta shigo cikin kiching ɗin tana mussika ido alamu dai ya nuna yanzu ta tashi daga bacci,A lokacin kuma Bintu ta gama haɗa komai tana shirin fara ɗauka dan kaiwa ta jera masa A falonsa,dubanta siddiƙa tayi tana wani ya tsina fuska kamar taga kashi tace"ke bani break ɗin nan da yunwa na tashi safiyar yau!' cikin nutsuwa Bintu tace"wannan ai na Oga Abdallah ne kuma ba a haɗa masa abinci da kowa shi kaɗai nakewa ki bari na kai masa sai nazo yanzu na haɗa muku wani!' tunda Bintu ta fara maganar take Binta da wani matsiyacin kallo irin na ke ɗin wacece,dan haka bata bari Bintu ta haɗiyi miyau ba ta fara sauke mata kondon rashin mutunci cikin ƙasƙanci tace" ke ɗin wacece?kuma ƴar gidan uban waye da har zaki hanani Abinda ya kasance ikona? ta daka mata wata gigitacciyar tsawa mutuniyar tuni ta gigice jikinta ya shiga rawa Bintu in da Akwai abinda ta tsana A rayuwarta to bai wuce tsawa ba, babu A binda ke saurin ruɗa ta kamar tsawa shiyasa take da matuƙar jin tsoron ruwan sama,kafin wani sakon hawaye sun fara mata ambaliya,ganin hakane yasa Siddiqa tayi saurin ƙwace tiren hannunta tana ci gaba da watsa mata ba zan kallo,cikin tsoro biyu da ya haɗar mata tace"dan Allah karki tafi dashi duka ki ɗiba iya wanda zai miki wallahi shima..bata ƙarasa ba taji tas an wanke kyakykyawar fuskarta da mari,runtse idanun ta tayi kana ta buɗe su a hankali saboda nauyin da sukayi mata,taufiƙa ce tayi mata wannan marin tana tsaye a gabanta tana mata kallon gargaɗi,tace" ke har kin isa ƴaƴan masu gida su buƙaci Abu ki hanasu ke ɗin wacece idan kikayi wasa sai na lalata wan nan banzar fuskar taki,idan baki sani ba to yau kisani mu ba A takamu ko A makaranta abinda muka gadama mukeyi bare kuma A cikin gidan mu!'kallon siddiƙa tayi tace maza kwaso mana break ɗin duka bari na yiwa Farida waya da Hauwa'u su zo mu karya anan!' siddiƙa ta bata hannu suka tafa kana suka kwashe komai sukayi waje dasu. Dur ƙushewa Bintu tayi A wajen ta saki kuka mai ban tausayi,ta yaya A cikin ɗan lokacin da Oga Abdallah yake bata ta kammala masa break zata yi ƙoƙarin sake haɗa wani, lafiya yan kunun gyaɗa tayi masa da farfesun kan saniya sai ƙosai da tayi masa wanda yaji attaruhu da albasa da kwai sai ruwan liptom data haɗa masa da kayan ƙamshi,ko ita ɗin injice ai dole ta ɓata lokaci,sauri tayi ta miƙe dan fara sarra fa kayan, wake ta kuma ɗebowa ta gyara ta zuba A blender kana ta ta ce gyaɗa ta ɗora akan gas, Shi ko Abdallah tunda yaga ya gama shirinsa ba a kawo break ba ya samu guri ya zauna yana ci gaba da aikinsa A laptop,wani irin yunwa yaji na nuƙurƙusar hanjinsa dan haka ya miƙe ya fito falon inno ko da zai ci karo da dalilin da ya hanata kawo masa break bayan yaga alamun ta gyara ko ina na falon da ɗakin bayan dawowarsa daga motsa jiki,zama yayi yana fuskantar ƙofar kiching ɗin.. Saura ƙiris ta kammala komai, su taufiƙa suka dawo kiching ɗin hannayensu ɗauke da kwanikan abincin saurin karɓar kwanikan tayi dan har da su a fargabarta tun da a cikin saitin kayan Abdallah suke, taufiƙa ce tace yauwa kinga Farida ba sai mun jira ba ma tunda ta kusa kammala wannan sai kawai muje mu ɗora dasu!' wani irin zaro ido Bintu tayi yayin da zuciyar ta ke wani irin bugu da sauri da sauri tasa hannu ta dafe ƙirjinta.. Comments.... Vote...... Share.... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 20 ``` Cikin tashin hankalin abinda suke san jawo mata tace" dan Allah kuyi haƙuri wallahi idan na kai masa zanyi muku wani irinsa amma dan Allah na roƙeku kar ku taɓa abincin nan!'Farida tayi mata wani kallon sama da ƙasa sannan tace" ke ƴar kwaɗayayyu ai taki taƙare tunda iyayen ki basu da zuciya suka turoki aikatau to dole ki shaƙi takaicin mu,dan haka baki isa ki hanamu ɗaukar Abincin nan A karo na biyu ba, shi wanda zaki bawa kwartankine da jikinki yake rawa dan zamu ci abincinsa? to daga yau ya daina baki abinda yake baki in baki bashi ba!' gaba ɗaya suka sheƙe da dariyar mugunta gami da ta fawa, siddiƙa tace" gaskiyar ki fa sister zan can nan haka yake babu kuskure A cikin sa!' wani irin runtse idanu Bintu tayi tanajin A rayuwarta ba'a taɓa ci mata mutunci kamar haka ba yau ita A kewa ƙazafi mafi muni A Rayuwar duk wata kamilalliyar mace, fuskarta tayi jawur saboda baƙin ciki da kuma wata azababbiyar tsana da ta taho tunda ga ƙasan zuciyar ta fararen idanunta sun juye sun koma wata kala, numfashinta da kyar yake fita saboda azabtar ɓacin rai,kafin ta ankara sun fara ɗaukar jikokin da fulas ɗin kunun gyaɗa,Farida tace" bari na kaiwa inno nata kar ayi babu ita Ana nan ana wadaƙa da hatsinta za akai wa kwarto!wani irin A zaɓaɓɓen mari mai matuƙar ƙuna da zafi taji an ɗauketaa dashi, kafin ta dawo haiyacinta ta fahimci wanda yayi mata mari ankuma sharara mata wani wanda har sai da nun fashinta ya ɗauke tare da anbaliyar jini ta hanci da baki. Bintu da kanta ke sunkuye tana wani irin kuka mai sosa zuciya, tayi saurin ɗago kanta tare da zuba masa ido cike da tsananin mamaki da kuma tsoron hukuncin sa A kanta, siddiƙa da Taufiƙa kuwa daskarewa sukayi A tsaye tare da zuba ma sabuwar halittar da suke gani ido, wanda take suka manta da abinda sukeyi hatta marin da aka shararawa Farida bashi ne agabansu ba, kallon da ya shiga yi musu, shiyasa su kusan sakin fitsari A tsaye, siddiƙa saboda tsananin farga ba da yadda yake hukunta su da idanunsa masu tsananin kaifi,yasa ta zame ƙasa dabasss ta zauna jikinta na karkarwa. Cikin takunsa na isa da ƙasaita ya ke takowa gabansu yayinda takun yake bada wani ɗan dadda ɗan sauti wanda ke nuni da zuwan cikakken namiji,wata irin tsayuwa yayi A gabansu, yayin da sukejin tamkar zuciyoyin su zasu faso ƙirjinsu saboda tsananin tashin hankali,Bintu ma da ba wajen ta ya tsaya ba jikinta karkarwa yakeyi tamkar mazari. Tsananin kyansa da kwarjini da tarin ilhama da ƙasaitar sa da kuma shu'uman idanuwansa suka haɗu suka ƙara firgita zuciyoyinsu da gangar jikinsu,Farida kuwa tunda ta ƙame bata ƙara motsi ba dan har yanzu bata dawo daga suman Ido biyu da ta tafi ba, Jin sautin kamilalliyar muryarsa mai cike da wani irin maganaɗisu shiya dawo dasu daga suman wucin gadin da sukayi, yace" zo nan!' kallon juna suka shigayi dan basu fahimci wadda ya kira A cikinsu ba, saida ya juya ya buga mata tsawa,kana ta fahimci da ita yake, cikin ɗaga sauti yace" ba dake nake magana ba?Bintu ta kuma rikicewa har ta rasa Abinda ya kamata tayi,wani ƙaƙƙarfan tsaki ya saki yana mai sheƙa mata wata muguwar harara wanda ta kaɗai ƴan hanjinta,saboda rikicewa har bata san lokacin da ta ganta A kusa dashi ba wanda har sai da hakan ya haifar mata da wata mummunar gullewa,runtse idanunta tayi tana shirin taji wani ta A ƙasa,shirun da taji bata kai ga kaiwa ƙasa ba, da kuma wani masifaffen ƙamshi mai kassara gaɓoɓi,da jinta A cikin wani yalwataccen ƙirji tamkar fadama shiyasa ta buɗe firgitattun idanunta masu matuƙar sheƙi da wani irin maganaɗisu,Aikuwa tana haɗa ido dashi ta kuma zarosu tamkar zasu daɗo ƙasa, tamke fuskarsa ya kumayi,ganin haka yasa da wani irin sauri ta zame daga jikinsa,kana cikin rawar murya da in ina tace" kakkayi-kayi haƙuri!' banza yayi mata tare da maida dubansa kan su Taufiƙa,kana cikin gajiyawa da yawan maganar da suka sakashi, yace"ki maresu!' da sauri ta dubeshi cikin nuna kanta da rawar murya tace" waini kake nufi na maresu?ko bazakiyi ba ya faɗa yana tsatstsareta da lulu eyes ɗinsa,girgiza kanta tayi ta juya tana fuskantar su,tana tunanin wannan shine abinda zatayi musu ta fanshe baƙin cikin da suka jefata,yadda suke taƙama da ji da kansu Ace ƴar aikin da suka raina ta sharara musu marika yaya mutum yake zaton zasuji,take taji wani ƙwarin gwiwa yazo mata dan haka batare da ɓata lokaci ba ta bude tafukan hannunta ta saita A kan fuskar Taufiƙa jikake tass kafinta dawo haiyacinta ta ɗorawa Siddiqa nata kana ta juya ta daddage ta shararawa Farida wanda yafi nasu ƙarfi da zafi, Aikuwa Farida kasa daurewa tayi kawai sai ta fashe da wani rikitaccen kuka ta fita daga ɓangaren gaba ɗaya tana kuka mai ƙarfi. Taufiƙa da siddiƙa suma fita sukayi suna mai ɗaukar alwashi da muguwar manufa A kan Bintu,zuba mata kaifafan idanunsa yayi,yayin da yakeji kamar zaiyi dariya saboda lamarin na Bintu akwai ban dariya da kuma takaici wato ta samu dama da ƙwarin gwiwa har wani dagewa take tana zabga maruka da kuma baizo ba ko ya zatayi dasu oho,fita yayi yana cewa ki kawomin karina yanzu nan idan kuma suka dawo sukayi miki duka babu ruwana!'kafin ya kammala rufe bakinsa ta zundumi fulas ɗin kunun gyaɗa da na ƙosai har ta rigashi fita daga kiching ɗin, binta yayi da kallo cike da mamakin tsoro irin nata. Kuka takeyi sosai wanda yake cike da san garta da kuma san ƙarawa miya gishiri,faɗawa falon nasu tayi tana mai ƙara zuzuta lamarin da shegen kukanta,Hajiya Saratu da ta fito daga kiching hannunta ɗauke da ruwan jarka,tayi turus tana kallon borin da Farida keyi cikin tsakiyar falon, cikin ɗaga murya tace"ke lafiyar ki kuwa? kamar wadda aka yiwa mutuwa!' Farida ta miƙe zaune,cikin rikici irin na auta,tace" momy wallahi garamin mutuwa da irin cin mutun cin da akayi min yau, ki duba ki gani marin ƴar aiki ne da marin ƙaton namiji A kan wannan kyakkyawar fuskar tawa!' A hankali Hajiya Saratu ta samu guri ta zauna tana bin Farida da wani irin kallon tuhuma,kawar da kanta tayi tana zunɓura baki dan tasan momin ta ba goyan bayan ta zatayi ba,aikuwa cikin ɓata fuska Hajiya Saratu tace"me kikayi mata dan nasan ruwa baya tsami banza, tabbas akwai abinda kikayi mata keda su Siddiqa, dan na tabbatar yarinyar nan baza ta mareki da gangan ba!' Dady ne ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, cike da kulawa yake duban Farida, kana yace" auta meke faruwa ne? da sauri ta isa gurinsa ta raɓa jikinsa,tace" Dady marar maka Ni Akayi,kuma nazo na faɗa wa momi ta rufeni da faɗa,ba tare da ta saurareni ba!'Alhaji Habib,ya maida dubansa kan H Saratu,yace" haba Saratu me yasa kike hakane idan baki rarrashe ta ba waye zai rarrasheta? gaskiya bana son haka!'Hajiya Saratu tayi murmushin takaici kana tace" Ni banyi mata faɗa dan wani abuba sai dan nasan bata da gaskiya,kuma kaima kasan halin ƴarka sai dai so ya rufe maka idanu,zama yayi tare da Farida kana yace" ai ban ce miki bata da laifi ba amma ai kya saurareta kiji ba'asi tunda ita aka mara!' juyawa yayi yana duban Farida yace" auta gayamin me yafaru aka mareki?nan kuwa Farida ta karkace ta shiga faɗar ƙarya da gaskiya,tana gamawa momy Sarah ta dubeta tace" yanzu ke bakiji kunyar ƙaryar da kika zauna kina sheƙa mana ba?tura baki tayi tace"nikam gaskiya na faɗa!'to munji nasu laifin ke kuma ina naki yake?shiru tayi batare da ta kula momin tata ba, Dadin Farida yace" gaskiya basu kyauta ba da suka mareki harsu biyu dan mugunta,amma kiyi haƙuri kar ki kuma shiga har karsu babu ruwan ki dasu kinji auta!' ta shi tayi ta nufi hanyar ɗakinta sai kuma ta dakata tare da juyowa fuskarta Babu alamun wasa sai tsantsan burin ɗaukar fansa tace Dady bana yafiya kuma bazan yafe musu ba har sai ranar da na ɗauki fansa na gansu suna kuka fiye da kukan da suka sani!wucewa tayi ɗakinta tayi cikin sassarfa,wani mugun kallo momi Sarah ta shiga wullawa mijin nata kallon kaga irinta ko,miƙewa tayi tabarsa nan zaune yana murmushi wanda Ni kaina ban san manufar murmushin nasaba. A ɓangaren su Taufiƙa ma kusan hakane ya kasance,sai dai su saɓanin Farida ne ita tasamu rarrashi da ga gurin Babanta,yayin dasu kuma har kusan marinsu saida inno tayi, ta ƙare musu tatas ta ɗora musu da cewa nariga nasan halin Bintu tun kafin zuwan ku babu wanda ya taɓa kuka da ita ko ya kawomin laifin ta yarinyace sam mara shiga sabgar mutane tana da nutsuwa da hankali,kuma nasan tunda har Abdallah ya shiga lamarin lallai baƙaramin rashin mutunci kukayiwa Bintu ba, dan haka abinda yasa tayi muku yayi dai dai naji daɗi,kuma bazan hanaku ci gaba da rashin mutuncin kuba zan kyaleku dan ina da mai gyara muku zama sangar tattun banza sangar tattun wofi,kutashi ku fitamin A ɗaki!'tashi sukayi suka fita suna mai cin alwashi A kan ci gaba da ƙuntatawa rayuwar Bintu baiwar Allah. A hankali take tafiya dan zuwa sashen Hajiya Babba,domin kai mata Masar da tayi mata alƙawarin zatayi mata saboda tana matuƙar son masa,tazo dai dai mahaɗar da zata sada ta da kori dan da zai kaita falon Hajiya Babba,sai kawai ganin mutum tayi A gabanta tamkar an jehoshi,da sauri ta ja da baya tana shirin sheƙawa da gudu,cikin hanzari Sayyid yasha gabanta yana cewa ke dalla matsoraciya mutum ne kuma ɗan uwan ki musulmi!'ɗan dakatawa tayi tana maida numfashi,kana cikin ladabi ta gaidasa,amsawa yayi yana Binta da wani shu'umin kallo,yayin da kwaɗayayyun idanunsa suke bin ko'ina najikin ta da kallo,hakan da taji ajikin tane yasa tayi ƙoƙarin zagaye shi dan wucewa, sai dai me wani irin figa taji yayi mata har yana ƙoƙarin mannata da jikinsa,A matuƙar fusace ta angijeshi tare da nuna sa da yatsa tace"kai wane ne A cikin halittu da har zakayi ƙoƙarin yin shishshigi ga halittar da tafi karfika halittar da ba ayita domin kaba kuma wadda take haramtacciya agareka? cikin cire tsoro da shirinta na fara yaƙi ga dukkanin wanda yake shirin zame mata annabo a rayuwa, taci gaba da cewa to A kul kuma A hir ɗin ka karka kuma yin wannan gangancin idan ba haka ba kuwa, hmmm,ta karkaɗa yatsan ta tare da ratsashi ta wuce ta barshi sake da baki da hanci,bashi ne ya motsa ba har sai da yaga shigarta falon Hajiya Babba kana ya jinjina kansa tare da cewa shike nan Bintu kike kowa kin jefo kanki komar Sayyid Mansur Balarabe muje zuwa muga idan zaki ci riba... Bayan ta kaiwa Hajiya Babba Masar sai ta biyo ta can bayan ɓangaren Alhaji Mansur, inda tanan zata miƙa ya maida ita ɓangaren wannan ɗakin tana kusan ƙarasowa ta shiga ƴan dube dube ko da da wanda yake binta duk da zuciyarta cike take da matsanancin tsoro amma tariga tasa aranta sai taje wajen nan yau dan ta daɗe tana neman wannan damar saboda tasan dole sai ta cire tsoro ta kuma fara ƙoƙarin tun karar haɗarin dake gabanta,jin wayarta na zumm zumm yasa ta dakatawa daga tafiyar da takeyi,ɗagawa tayi tare da yin sallama,ta can ɓangaren Hajiya ladidi tace"Bintu ya akayi meye labarin da kika samu daga wajen Dide?cikin ƙara duba bayan ta da gefen ta Bintu tace"Hajiya ki kwantar da hankalin ki na riga na gama samun kan Dije zata dinga sanar dani duk wani abu dake shiga da fita ta ɓangaren ta,kawai dai yanzu abinda nake buƙata daga gareki shine inaso ki dinga sanar dani duk wani abu dayake tafiya wanda kike da masaniya A kansa acikin gidan nan, saboda ta hakane zan dinga binciko miki abubuwa masu mahimmanci wanda zasu kasance miki matakin nasara A kan burinki!'wata irin dariyar farin ciki Hajiya ladidi ta saki kana tace"gaskiya yarinyar nan kin burgeni ashe haka zakiyi min rana amma naso yiwa kaina sakiyar da babu ruwa,karki damu wannan ai Abune mai sauƙi ai duk ƙaruwar muce!'cikin sauri,Bintu tace"au ai nasan Anty Nafisa zataji daɗin wannan lokaci,tunda dama daga mu sai ita mukasan mai muke shiryawa A cikin gidan nan!'Hajiya ladidi tace ke fice nan ai ita kanta Nafisa bata san manufar mu ba kawai dai muna amfani da ita ne,kamar yadda ita ma take da tata manufar batare da tasan mu mun sani ba,itace dai bata san komai kanmu ba!'cikin nuna halin ko inkula Bintu tace"to ai Hajiya Ni bandamu da duk abinda kuke ciki ba Ni kawai A yanzu burina nasamu kuɗin da zan gina rayuwata,to amma kuma Hajiya wani hanzari ba gudu ba kina ganin ba sai nasan waƴanda kuke tare dasu ba saboda gudun samun matsala ta ɓangarena? Hajiya ladidi ta saki murmushin ƙeta A ganinta ta riga ta gama dulmiyar da Bintu ta gama shiga hannunta dan haka ita yanzu lokacin baccinta ne yazo,tace" Bintu babu ruwan ki da wannan Ni kaina A yanzu bana ce miki ga wanda nake haɗa hannu dashi ba sai dai natabbatar shi ɗin ahlin ALHAJI BALARABE ne kuma bandamu da nasani ba burina kawai shine A gabana!'Bintu cikin gaiyato ƙarfin hali da san kawar da halin da tashiga na ruɗani tace" tom shikenan Hajiya baki da wata matsala da Ni komai zai tafi yadda kikeso!' Hajiya ladidi tace"amma Bintu ina so maganar Nafisa ya kasance tsakanin mune baza taji wannan magana ba mu cigaba da tafiya a yadda muke!'Bintu tace" haba Hajiya ko bakiyi min gargaɗi ba bazan taɓa gayawa Aunty Nafisa komai ba,Ni na gaya miki abinda nake buƙata dan haka babu ruwana da abinda kuke shiryawa ko kukesan cinmawa,idan hakane kuwa kinga babu ruwana da tsakaninku aiki na kawai zanyi na kauce,saura na zubawa ƘUDURAR ALLAH idanu!'Hajiya ladidi tace"yauwa Bintu na gode da fahimtar ki gareni sai mun sake waya!' to shikenan sai anjima!'duk wannan wayar da Bintu takeyi tana yine cikin ta ka tsantsan da ankarewa. da sauri ta bar gurin ta ma fasa zuwa gurin saboda yanzu tana buƙatar dogon tunani da kuma shawarar Dije,tana shiga ɗakinta tasaka mukulli ta rufe zama tayi tsakiyar ɗakin tana maida numfashin tashin hankali, kanta yayi matuƙar daurewa da wannan lamarin wato ita kanta ƴar da uwa munafuntar juna sukeyi lallai wannan al marin babbane, to yanzu yaza ayi na gano wanda suke haɗe da Hajiya?can kuma ta zabura gami da cizan yatsa A fili tace" tabbas Hajiya ladidi kin gama kashe kanki tunda kika yadda naji sirrin junanku ke da ƴarki,kuma da kanki zaki lalibo mugun da yake saki aiki!'sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya tana mamakin kanta,tare da mamakin Hajiya ladidi, dama sakarar mata ce bata da wani wayo? tana zaune jikarta tayi mata wayo ta bugi cikinta gaskiya abin nan yayi mata daɗi,abin yakowo citta...... More comment..... More typing...... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* Wannan page din nakine sister khadi ke da rufy AA COMMENT ɗinku yana bada citta. Fans ɗin ƙudurar Allah ina godiya da addu'ar ku gareni Allah ya ƙara mana zumunci da so da kauna,love U kwando kwando ```Page 21 ``` Yau gaba ɗaya jikin Bintu A san yaye yake kasan cewar tun safe mutanen nata suka haɗa dabar hira A falon inno, wani abin takaicin ma har da mazan suka gayyato,kuma ba komai ne yasa sukayi hakan ba sai dan kawai yau sun shiryawa Bintu buhu buhun rashin mutunci, saboda tun sassafe suka ga fitar do don nasu,yau kwana biyu da faruwar wancan abun, dan haka yau dama suka samu. Bayan ta gama jigilar kaiwa da kawowa tayi musu girkin dasuka buƙata, sai da ta jera musu komai na buƙata A gabansu kana ta wuce dan ƙoƙarin ta na barin falon,Sayyid ne yace"ke dawo nan uban waye zai savin ɗinmu? Farida ta yatsina fuska kana tace"Ni kije kisake min sakwara dan bazan ci wannan abincin ba!ita kuma Siddiqa tace" Ni kuma kiyi min danbun shinkafa! Bintu cike da takaici take duban su ta kasa cewa komai saboda mamakin ɗabi'ar su Hauwa'u ce tace"dalla Malama kije kiyi musu abinda suka buƙata kin tsaya mana akai yawa tsohuwar maiya!' juyawa tayi har ta fara ta fiya sai kuma ta ɗan da kata tare da juyowa jin Siddiqa na cewa banzar yarinya dama ai wan can uban shishshigi shine kwarin gwiwarta, ranar har da wani zagewa tana sheƙa mana mari to yau zakici ubanki idan kina dashi!'A hankali ta buɗe bakin ta tana son cire tsoronsu dake dan kare A ranta dan Allah ya gani Bintu tana tsoron taɓa lafiyar jikinta dan tasan zasu iya naɗa mata na jaki, amma badan haka ba sam batajin zata iya raga musu ta ɓangaren ragargaza musu magana ko wace iri ce, cikin san jawo ƙarfin gwiwa tace" to shikenan bazanyi girkin ba tunda aibaku kuka ɗaukeni aiki ba kuma ba asaminku A cikin albashi na ba balle kudinga wahalar dani kamar baiwarku,ta faɗa A yayin da take shirin bawa ƙafarta iska,dan tasan tsaf zasu naɗa mata duka,kamar ta sani kuwa Farida mai jiran ƙiris ita ta miƙe tayi wani irin tsalle ta sha gaban Bintu,da sauri Bintu ta matsa baya cikin yanayin ta na nuna firgici ,Nabil yace"ke Farida meye haka ne? Hauwa'u tace"idan bataya mu dukanta zakayi ba kayi shuru da bakinka inno bata nan tana ɓangaren Alhaji Baba Dan haka zaneta zamuyi la ada waje!' Sayyid yace" malam ka rabu dasu su zane bakin tsiwar duk da mugun sanda nake mata hakan ba zai hana nayi mata rashin mutunci ba!'Bintu tace"Ni dan Allah ku rabu dani babu ruwana daku,kuma ai gaskiya na faɗa ba aikinku nazoyi ba da haka sai ku rabu dani!kan ta rufe bakinta Siddiqa tasa hannunta ta doke bakinta,aiko Bintu taji zafi tuni idanun ta suka kawo ruwa wata zuciyar tace"da ita karki sake ki bari suga hawayenki daga nan zasu ƙara rainaki, dan haka sai tayi ƙoƙarin shanye hawayenta,A hankali ta shammace su ta angije Farida ta hankaɗata tayi ƙasa bata tsaya wata wata ba ta arta ɗakinta tasaka key, Farida ta lailayo wani uban ashar ta dan ƙara mata, Sayyid yace" kuzo kuji wani abu wannan duk ba mafita bace!' gaba ɗayan su suka zo suka haɗa kai yayi musu ƙusƙus, Siddiqa ta yi wata shewa tare da cewa lallai yarinya kin ɗauko ruwan dafa kanki kin shiga uku a gidan nan!'dariya suka saka gaba ɗayansu suka shiga ɗibar garar girkin Bintu maisa kunnen oga Abdallah motsi. Taufiƙa ce ta samu Bintu A kiching tana yiwa Abdallah abincin dare sai dai bata jima da ɗorawa ba saboda tsoron kar ta fito su haɗu su casata, Taufiƙa tace" Bintu me kike dafawane haka? batare da ta bata amsaba ta zuba mata ido cike da mamakin yadda tayi mata magana cikin kwantar da murya, murmushi Taufiƙa tayi tace"ko yau kin kurmance ne? girgiza kai Bintu tayi kana tace" yau tuwon semo nakeyi masa da miyar ɗanyan kubewa sai farfesun kifin ruwa!' Taufiƙa ta riƙe baki cikin mamaki tace" wai shi kam dan Allah Bintu meyasa yakeson irin wadannan abincin? Bintu tayi dariyar ta me kyau har kumatunta na loɓawa kana tace"wallahi Ni ma bansani ba kawai dai kowa kinsan da abinda ya fi burgeshi A rayuwarsa to shi dai yana san abincin mu na gargajiya!' Taufiƙa tace" kuma hakane fa maganarki!' yanzu dai ki kawo nayi masa girkin nan yau inaso yaji irin baiwa ta nima saboda nan gaba!' ɗan jim Bintu tayi cike da tunanin ta bata ko kar ta bata,Taufiƙa tace" Bintu bazaki bani ba?kinga dolene na koyi duk irin abibcin da yake so saboda gaba yadda nake mafarkin zama matarshi kinga hakan shine dai dai ko?Bintu cike da mamaki take bin bakin Taufiƙa da kallo kai wannan irin wawanci haka, sai yanzu ta gane manufar ta na yadda ta can ja mata lokaci ɗaya ashe ita da manufarta wato ashe ita ma ta faɗa komar soyayyar Oga Abdallah,tab amma lallai sun gamu da wahala in dai Oga Abdallah ne, Bintu tace to shikenan muyi tare!' Taufiƙa tace" Ni dai ki tsaya kawai ki tayani da hira har na gama sai ki ɗiba kikai masa!' Bintu tace Tom shikenan,amma fa ranta cike yake da tsoro kawai dai ta bayarne saboda kar ta jangwalo wa kanta wata rigimar bayan ta ɗazu da tasan ba ƙyaleta su Farida sukayi ba, Sunayi suna hira har Taufiƙa ta gama komai aka zuzzuba cikin kuloli, daga nan ta koma ɗaki sai da tayi sallar isha'i kana ta fito ta ɗibi kayan abincin ta nufi falonsa,bayan ta jera komai kamar yadda ta saba ta fito tashiga wajen inno suka fara taɓa hira. Sai da ya gama komai na aldarshi da yasa ba na yau da kullum kana ya nufi dining ya zauna ya fara savin ɗin kansa. lomar farko da yayi kasa haɗiye wa yayi sai da ya nufi sink ya zubda kana ya kuskure bakinsa ya koma ɗakinsa ya shiga yayi brosh,zama yayi cikin kujerarsa ya haɗa hannayen sa biyu ya rufe fuskarsa, yunwa yakeji sosai danshi bai cika san zama da yunwa ba, tun daya saba bawa cikinsa haƙƙinsa, wayar sa ya ɗauka ya dannawa inno kira,bayan sun gaisa yace" inno yarinyar nan tazo!'daga haka ya maida wayar ya ajiye,inno suna tare da Bintu har lokacin,duban Bintun tayi dan tasan ita yake nufi sanin cewar babu wanda yake shiga ɓangaren sa idan ba itaba,tace" tashi kije saraki na kira wataƙil wani abun yake buƙata!' dum,haka ƙirjin Bintu ya buga cike da fargaba ta tashi ta tafi tana fatan Allah yasa ba ganewa yayi ba ita tayi girkin ba. A hankali tayi sallama tare da ƙara sawa gabansa ta duƙa,kana tace" Barka da dawowa wani mugun kallo ya fara watsa mata kafin yace" wa kika bawa yayi abincin can? yana maiyi mata nuni da kan dining table,kallon gun tayi kana cikin tsoron abinda zai biyo baya tace" Ni nayi!' ɗan wara idonsa yayi akanta gami da cewa ko? gyaɗa kanta ta kumayi a tsammanin ta ya yadda, miƙewa yayi yace" zo nan!'tashi tayi tabi bayansa har zuwa dining ɗin, sai da ya zauna kana yayi mata nuni da itama ta zauna,A ɗarare ta ɗosana ta zauna gaba ɗaya idanunta sun fiffoto waje saboda tsananin tsoro,nuna mata wanda ya faraci yayi yace" oya maza kicinye su duka,zaro idon ta kumayi da sauri ya kawar da nasa,cikin ransa yace" yanzu zata fara firgita mutane da waɗan nan shanyayyun idanun,fuska ta kwaɓe tana shirin sakan mai san gar tattun hawayen ta,yayi saurin ɗora hannun sa kan laɓɓansa yayi mata alamun tayi mai shiru,haka nan ta haɗiye kukanta ta sanya hannu ta gutsiri tuwan tare da kaiwa bakinta,kasa haɗiyewa tayi tafara ƙoƙarin furzo shi,zaro mata manyan idanunsa yayi wanda suke da wani irin maganaɗisu acikinsu, ga wani maiƙo- maiƙo dake cikinsu tamkar manƙuli aka ɗiga musu,tuni ta kuma rikicewa dama ga yanayin da take shiga a duk lokacin da ta kasance tana shaƙar numfashi akusa dashi,sai ya kuma haɗe mata ya dinga bata wani irin yanayi mai wuyar fassarawa har wani sanyi sanyi take ji A can cikin ƙashushuwa da ɓargon ta,ƙasa tayi da kanta tana haɗiye tuwan daƙyar,haka ta dinga cusa tuwan cikinta tana kuma zabgawa Taufiƙa Allah ya isa saboda ita tajawo mata wannan tashin hankalin,bata taɓa zatan bata iya abinci ba ita A tata wautar tayi zatan kowa ya iya abinci mai daɗi shiyasa ta bata batare da tayi tunanin haka ne zata kasance ba, A nata yaritar kawai tunda bai gani ba ai bazai gane ba ita tayi ba. Sai da ta cinye wanda ya faraci, da ƙyar,kana ta ɗan saci kallonsa yana ta danna wayarshi hankalinsa kwance,cikin san rushewa da kuka tace" na cinye cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta mai fitar da wani sauti mai daɗin sauraro,kallo ya bi ɗan karamin bakin na ta dashi wanda bakowane zai fahimta ba sai ƙwararren munasiri (amma fa bani ba) A hankali yace" sauran fa? fashewa tayi da kukan da yake ta cin ranta,maida kansa yayi yajinginar tare da lumshe idanunsa yayin da zara zaran eye lashes ɗinsa sukayiwa idanun runfa,jin sautin kukan yake har can cikin ƙasan zuciyarsa,muryarta yaji tana cewa,Ni dai kayi haƙuri wallahi ita tace" sai na bata tayi maka saboda ta saba!' buɗe idanun yayi ya ɗorasu kan rigimammiyar fuskarta kana yace ita wace haka? Taufiƙa!' ta bashi amsa kai tsaye abinta, ya tsina fuska yayi danshi har yanzu bai fahimci shirman nata ba,batare da ya nemi ƙarin haske ba,yace" da ita kije ki samomin wani abu da zanci yanzu saura ki kuma bawa wata tayi min jagwalgwalo!' da sauri ta miƙe cikin share hawayen da ya ɓata kyakykyawar fuskarta,tace" me zan dafa maka? komai!' da ga haka ya miƙe ya barta tsaye tana faman tura ƙaramin bakinta. Washe gari sai ga Taufiƙa ta kuma biyo Bintu kiching Bintu tana ganinta ta haɗa rai tana gunguni, Taufiƙa ta zuba mata ido kana cikin san fahimtar abinda Bintun take faɗi tace" wani abu kike cewa bintu,?Bintu kuwa kai tsaye tace" Gaskiya Anty Taufiƙa bazan kuma baki girkin oga Abdallah ba jiya baki ga abinda yayi min ba,kuma dama kinsan baki iya ba kikace sai na baki kinyi kalan dama so kike kijamin masifar wannan yayan naku!'taƙarasa maganar cike da baƙin ciki kamar yanzu akayi abin tana tuna yadda yasa ta cinye Abincin nan mara daɗin ɗanɗano, Taufiƙa ta haɗe rai tare da cewa ke karfa kiga na sake maki ki rainani wannan abincin ne baiyi daɗi ba to ko yanzu nayi niya sai na karɓa nayi yadda nakeso, dama ai haka nakeso ya sauke fushin kanki! ta faɗa tana ɗage mata gira ɗaya da wani ɗan munafukin murmushi akan fuskarta,shiru Bintu tayi tana haɗiyar miyan takaici,ba ita taji dai dai ba sai da taga Taufiƙa ta bar kiching ɗin batare da tanemi ta bata girkin ba. Lokacin da ta kai masa yana zaune A falon cikin ƙayatacciyar shigarshi ta alfarma,ɗan jim tayi sai kuma ta wuce a saɗaɗe ta jera haka tayi har ta gama, tana shirin fita taji tattausar muryarsa yace" zo nan!' dawo wa tayi ta tsaya tana murza yatsun hannunta,tashi yayi ya nufi dining table ɗin ya zauna,bazakizo ba ya faɗa cikin da kakkiyar muryarshi ta zaratan maza mara sa son raini,ƙarasowa tayi batare data dubeshi ba tace"gani!' banza yayi mata ya cigaba da taɓa wayarshi kuma bai taɓa abincin ba, gajiya tayi da kanta ta fara savin ɗin sa ,wani haɗe rai ya kuma yi ya fuskanci yarinyar nan bata da kunya wato ta gane abinda yake nufi amma tayi mursisi nufinta sai ya gaya mata kenan, Sai da ya kusa cinye chips ɗin da ta zuba masa kana yayi mata nuni da ta wuce ta bashi guri,fita tayi tana mita cikin ranta. Alhaji Farouk ya dubi Anty Nafisa yace"inaso zan shiga wajen inno tunda na dawo daga tafiyar nan banje na dubasu ba! hakanan Anty Nafisa ta dinga jin faɗuwar gaba, shin meyasa take ta ƙoƙarin hana Farouk zuwa ɓangaren inno? tunda ya dawo take ta yi masa dabara wanda tasan bawai dabarar tace tayi mata aiki ba kawai dai shima yana daga cikin waɗan da suke da yawan sabgogi shine dalili sai dai kuma ita kanta bata san dalilin ta nayin haka ba,muryar sace ta katse mata zan can zucin da takeyi, yace" bari naje daga nan zan fita sai na dawo!' kasa magana tayi har ya fita daga ɗakin,jugum tayi ta rasa meke damunta sam ita fa bawai ta daina jin fargaba bane kawai abinda take son cimmawane yasa ta daina yawan damuwa da lamarinta na baya,tashi tayi ta fara zaga ɗakin cike da san samarwa kanta mafitar damuwar dake cin zuciyarta. Inno tarasa inda zata saka Dady Farouƙu saboda shi mutumne da bai fiye zama ba yana da yawan tafiye-tafiye idan ya tafi kuma yana daɗewa bai waiwayi gida ba, kuma haka baya rasa na saba da babban damuwar da ke cinye zuciyarsa,yaɗan jima suna taɓa hira da inno kafin yayi mata sallama ya wuce harkokinsa. Farida ta dubi Siddiqa tace"Siddiqa baza mu tsaya mu dogara da shirin Sayyid ba kinsan halinsa ɗan ɗauka da ajewa ne kawai zamu fara ɗaukar fansa ne ba sai mun zauna jiran gawan shanu ba!' Hauwa'u tace" amma duk abinda zamu shirya kar mu sake su amna da Rahima su sani dan zasu iya ɓata mana shiri!'Taufiƙa tace" hakane nima kinga shirin mu yana karɓuwa ta ɓangarena amma shegiyar yariyar bana tunanin zata kuma bani girkin nan amma inta san wata ai bata san wata ba!'hauwa'u tana wani dogon numfashi kana cikin yanayin karaya tace" Ni dai inaga burina bazai taɓa cika ba wallahi tunda nake a duniya ban taɓa tunanin zanyiwa wata halitta son da nakewa yah Abdallah ba,Ina son shi son da baki bazai iya faɗa ba!' sai kuma kuka ya ƙwace mata sosai (har ji nayi kamar na tausaya mata) Taufiƙa rufe idanunta tayi tamkar mai bacci sai dai kuma ita kaɗai tasan yawan wutar dake bab baka cikin zuciyarta da ruhinta, Hauwa'u shirme takeyi sai dai ita baza ta taɓa bari Hauwa'u tasan irin tarin ƙaunar da takewa Oga Abdallah ba,sai dai taci alwashin bin duk wata hanya da tasan zata mallaka mata Abdallah,wannan alƙawarin tane zata ɗagawa Hauwa'u ƙafa na ɗan lokaci kafin tayi maganinta dan tanajin zata iya yin komai a kan soyayyar Abdallah,wannan kenan. Cikin rawar jiki take karanta sakon Dijen wanda take sanar da ita cewa lallai tanaso ta kaucewa haɗuwa da Sayyid saboda Akwai abinda yake shirya mata kuma ita tasan wane Sayyid zai iya aikata komai akan biyan buƙatar zuciyarsa,Bintu ta ajiye wayar cikin zurfafa tunani akan abinda Sayyid ɗin yake shirin aikata mata,to wai meyasa sai ita? meyasa kowa ya kwaso ƙiyayyarsa da ɓakin halinsa sai kanta?me yasa suke san ganin bayanta? to ko sun gane ita wacece?girgiza kanta tayi tanajin waɗan nan basu ne A gabanta ba aikin dake gabanta ya fi sauran ƙananan ƙwarin nan. Bayan kwana goma da faruwar wannan lamari,rana tsaka inno ta shiga cikiyar babbar sarkarta wadda kakasance tun ta aurenta, yau kwananta bakwai tana nema batare da tayi cikiya ba saboda tana san ta tabbatar da sahihancin nemanta batason tayi cikiyar kuma tazo ta ganta, shiyasa taƙiyin maganar sam sai yau da ta ga dai da gaske ɗauke sarƙar akayi tayi ɓatan dabo,gaba ɗaya ta kira jikokin nata da wanda suke kwana da wanda zuwa kawai sukeyi,dukkansu bata zare kowa ba ta Fara duban su Taufiƙa tace" bari na fara ta kanku saboda daku nake kwana nake tashi,shin babu wanda yaga sarkata da yari A cikin ku? ware ido sukayi har da su Rahima da tambayar bata zo kansuba,kafin kace wannan kowa ya shiga rantse rantse, Siddiqa tace"inno kicaje ɗakinmu mana, yanzu har ta kai da zaki iya tuhumar mu laifin sata mu jikokin ki da KIKASAN bamu rasa komai ba me kuka rage mu dashi dazamuyi miki sata satarma ta abinda mukasan yana da daraja da muhimmanci a gurinki, gaskiya inno baki mana adalci ba!' Sayyid yace" nina ma rasa abin cewa da wannan gagarumin sharri da tsohuwar nan take san manna mana! Inno tace" bazaku fahimci abinda nake nufi ba amma tabbas an kwana biyu da soma yi min ɗauke ɗauke bana son zargi da yawan tashin zance shiyasa bana kulawa da irin wannan,amma yanzu dole nayi magana tunda abin yayi girman da bai kamata na rufe bakina ba!'Farida tace" to inno tunda haka ne ai bamu ka ɗai ya kamata ki tuhuma ba ai naga da ragowar wa anda baki tattaro ba!Nabil yace" tabbas wannan haka yake dolene suma ragowar ki tuhumesu indai gaskiya za abi!' kafin inno tace" komai Taufiƙa ta nufi hanyar ɗakin Bintu,can saiga ta sun fito tare,Bintu sai da gabanta ya faɗi ganin yadda suka zuba mata ido ga kuma ran inno A matuƙar fusace dagani Lallai laifin da akayi mata babba ne,durƙusawa tayi gaban inno tace" inno gani lafiya kuwa!A hankali inno ta kawar da kanta gefe saboda tanajin kunyar ta dubi idon Bintu tayi mata cikiyar sarƙa,Nabil ne ya gyara zaman shi kana yace" Bintu inno ce ta taramu take mana cikiyar sarkarta da ɗan kunne,tajima tana dubawa amma bata gansuba duk ɓangaren nan!' Bintu ta dafe ƙirjinta cikin tashin hankali tace" wallahi ban gani ba!'Sayyid ya katse ta da cewa inno kinsan dai duk cikin mu babu wanda yake shiga ɗakinki ko? ta gyada kanta, kana ya ɗora da cewa' dan haka ki sauke zargin ki daga kanmu ki maida shi kan wanda yake shiga ɗakinki kullum babu fashi!'Hauwa'u tace" inno babu wani ɓoye-ɓoye kawai mu tashi yanzu mu duba ko ina na cikin gidan nan har ɗakinki sai mun kuma dubawa dan haka mu rarrabu Sayyid Ni da kai da Farida mu shiga ɗakin su Siddiqa Taufiƙa da Siddiqa da Bintu su shiga ɗakin inno kai kuma Nabil da Rahima da amna ku shiga ɗakin Bintu kowa ya tabbata ya duba da kyau ke kuma inno ki zauna anan ki jira mu zamu nemo miki sarƙarki yan zunnan... ana wata ga wata ki a ina za aga sarƙar inno? Comment..... Share..... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 22 ``` Kafin kace meye sun bazama dukkanin dakunan dubawa suke sosai, sai da suka buncika ko ina basu gani ba,su Bintu ne suka fara fitowa daga ɗakin su Taufiƙa Hauwa'u tana cewa inno ɗakin su Taufi dai babu sarƙa!'kan ta gama rufe bakin ta, su Siddiqa suma sun fito daga ɗakin inno, Taufiƙa tace" wallahi inno babu inda bamu duba ba A ɗakinki bamu ganta ba!' shiru sukayi lokacin da suka ga su Rahima sun fito daga ɗakin Bintu jikinsu A matuƙar sanyaye,gaba ɗaya sukabi hannun Amna da kallo A yayin da take zube sarƙar a kan Centre table,waro ido sukayi gaba ɗaya A firgice, yayin da har haɗa baki suke wajen faɗin A ina kuka ganta? Nabil yayi nuni da Inda Bintu take tsaye,batare da ta fahimci abinda suke nufi ba, zuciyarta ɗaya bata taɓa kawo wai za aga sarƙa A ɗakinta ba tunda tasan bata ɗauka ba. Shiru inno tayi kanta a ƙasa babu wanda ya fahimci halin da take ciki,Farida ce tace"amma Bintu kin shammace mu ko da ba shiri muke dake ba amma bantaɓa yi miki kallon ɓarauniya ba!'sai kuma gashi ta bamu mamaki!'cewar Nabil da yake ta watsa mata mugun kallo,cikin ƙanƙanin lokaci Bintu ta fahimci inda zancen nasu ya dosa,suna dai nufin suce A ɗakinta aka gano sarƙar, to tayaya kenan?katse mata tunani Taufiƙa tayi da cewa haba Bintu tayaya zaki ɓata rawarki da tsalle tunda inno tayi mana faɗa naji A raina ban kyauta miki ba abinda mukayi miki shiyasa ma har na nemi kusanci dake saboda kwaɗayin kyawawan halayen ki,ashe kuma duk zatone!' A hankali take takawa har ta ƙara sa gaban inno ta durƙusa, cikin tashin hankalin da ta daɗe bata fuskanta ba A rayuwarta tace" inno ki ɗago dan Allah ki dubeni, zama tayi daɓar A kasa yayin da wasu zafafan hawaye suka shiga yi mata ambaliya,cikin san fidda kanta daga zargi ta riƙe ƙafar inno cikin wata irin murya me sawa mutum kasala saboda tausayi tace" inno ki yadda dani bantaɓa sataba bantaɓa ji A raina zan iya ɗaukar A bin wani ba bare kuma naki, wallahi inno bani na ɗauka ba! yadda inno take bata motsaba shine abinda ya kuma tayar wa da Bintu hankali,komawa tayi ta riƙe ƙafar Rahima ka tamau cikin wani irin ƙaƙƙarfan kuka take cewa,Rahima dan Allah ki gayawa inno bani bace wallahi ban ɗaukaba!' Rahima tasa hannu ta ture Bintu gami da matsawa gefe,tana share ƙwallan da suka cika mata idanu,tanajin Bintu har cikin ranta sai dai kuma wannan abinda tayi ya matuƙar sosa zuciyarta,ba wani ne ya shiga ɗakin Bintu ba balle taƙi yadda ita da hannunta ta zaro sarƙar A ƙasan katifar Bintun,dan haka bata da bakin yin musu ita ganauce ba jiyau ba. Ganin yadda Rahima tayi mata yasa taja gefe tana ci gaba da wani irin kuka mai tsuma zuciya,ta riga ta saddakar bata da fita bata da bakin cigaba da musan tawa tunda waɗan da take tsammanin zasu saurareta su goyi bayanta suma sun yadda da abinda ta aikata to meye amfanin maganar kawai ta miƙawa Allah ƙadiran wamaridan sarki buwayi gagara misali komai shi kawai take neman ɗaukinsa. A hankali inno ta tashi ta bar falon,batare da tabari ta haɗa ido da Bintu ba,inno tana shigewa Bintu ta kuma fashewa da kuka harda bubbuga ƙafa,Farida ce ta kallesu tare da cewa guys wai me muke jira ne ai zaman ɓarauniya ba zai yiwu A cikin estate ɗin mu ba dan haka kawai musan nayi da ita!'tana rufe bakinta gaba ɗayansu sukayi kan Bintu Rahima ce kawai da Amna suka kasa taɓuka komai jikinsu A sanyaye yake,kafin Bintu tayi wani motsi sun rufar mata da duka yayin da suke janta kamar ta barma suna ƙoƙarin fitar da ita daga falon duk girman falon nan da tsayinsa haka suka dinga jan Bintu tana kuka tana musu magiya amma sam basu saurare ta ba har sai da suka dan gana da bakin ƙofar falon, ɗagata sukayi suka jefata waje,runtse idanunta tayi tana jiran ganin ƙudurar Allah A kanta. Wurgatan da sukayi yayi daidai da tsayuwar shi a kofar falon dan haka tuni Bintu ta samu kariya daga faɗuwa A cikin faffaɗan ƙirjin sa,wanda jin ƙamshinsa yasa ta ɗago manyan idanunta da suka rikiɗe suka koma wata kala saboda tsabar kuka,tana ganin sa mai makon ta ji tsoro kamar yadda ta saba sai dai ma wata raruma da takuma kai masa yayin da ta kwantar da kanta kan kafaɗarsa ta zagayo da hannunta ta riƙe shi ƙam tana mai cigaba da sakin wani wahalallan kuka. Gaba ɗayan su sun kasa motsi daga inda suke bakamar Taufiƙa da Hauwa'u basu taɓa zaton zai iya dawowa A wannan lokacin ba,wani irin kallo yake musu mai wuyar fassarawa hatta da su Sayyid jikin su rawa yakeyi balle kuma su manya Farida da har yau bata mata da kaifin hannunsa A kan fuskarta ba,haƙiƙa dukkan su tsoro ya cika musu mara duk da suna da tabbacin shima idan yaji abinda Bintun ta aikata zai iya hukuntata,ganin ya motsa ne yasa suka shiga darewa suna bashi hanya,batare da ya janye Bintu daga jikinshi ba yashiga takawa,cikin nutsuwarshi da kamala har ya dan gana ga kujera,sai A lokacin Bintu ta farga da Abinda ta aikata cikin sauri ta sake shi kana kuma A hankali ta zame ta zauna A gabansa tana cigaba da sakin kukanta dayake yi mata matuƙar daɗi,haɗe hannunsa yayi waje guda ya shiga matsasu yayin da su kuma suka dinga bada wani sautin ƙara ƙasss ƙasss,cikin sanɗa suka shiga ƙoƙarin barin falon sai dai hakan bata samu ba saboda jin sautin muryar Abdallah cikin wani irin yanayi,yana cewa kar wanda ya sake ya bar falon nan!'kamar ansa inji an tsayar dasu haka duk suka koma suka ƙame A guri ɗaya,Nabil ne yayi ƙarfin halin yi masa bayanin abinda ya faru,jin yayi shiru tare da zubawa Bintu lulu eyes ɗinsa shiya basu ƙwarin gwiwar,cigaba da rattaba masa bayani,Bintu kallonsa itama ta shigayi da tsoratattun idanunta tana mai zubda hawaye ta rasa bakin magana komai ya ƙare daga bakinta bata da wani sauran kalami, Ɗaga musu hannu yayi alamun su saurara masa, miƙewa yayi tsaye ya cusa hannunsa cikin aljihun wandonsa, A hankali ya shiga ta kawa cikin nutsatstsan takunsa mai kama da takun sarakai,har yazo tsakiyar falon kana cikin kakkausar murya yace"ina mai ja muku kunne da kuma babbar murya duk wanda na ƙara gani ya bugeta wallahi wallahi!' wata irin ƙwafa yayi kana ya juya yabar falon, daga su har Bintun binsa da idanu sukayi,summ summ kowannen su yabar falon jiki A sanyaye amma bawai dan sunyi na dama ba, Bintu cikin tsamin jiki ta koma ɗakinta bayan tayi wanka tayi salla ta jawo wayar ta kira ta dannawa Hajiya ladidi,tana shiga kuwa ta ɗaga,ji tayi Bintu ta fashe mata da kuka,cikin tashin hankali tace" shikenan tamu ta ƙare Bintu me ya faru?da ƙyar ta saurara da kukan da takeyi kana ta zaiyanawa Hajiya ladidi abinda duk ya faru,cikin tsananin fusata Hajiya ladidi tace"kintabbatar dai bake bace ba ko? Bintu tace" wallahi Hajiya ban taɓa sata ba tunda nake A rayuwata!'to yi shiru ki kwantar da hankalinki,ki cigaba da walwalarki kamar da zanyi magana da inno ɗin wannan aini suke san yiwa,dan salam iskanci so suke kibar gidan kenan to dan ƙaniyarsu sai dai uwayensu da ubayensu su bar gidan amma bake ba sai mun kai ƙarshen manufar mu ina ai dasaura tukun bayanxu ba. Cikin nutsuwa ta gama haɗa masa break , zama tayi har ya gama karyawa yana sane da ita amma yayi kamar bai sanda ruwanta A gurin ba, A hankali ya tashi bayan ya kammala karyawarsa, zuwa yayi zai wuce ta, da sauri ta tare sa cikin kukan dayake son kufce mata tace"Dan Allah kayi haƙuri!'cike da mamaki yake duban ta,ganin kamar bai fahimci abinda take nufi ba yasa ta kuma marai raice fuska cike da san ya fahimceta tace' nifa banice na ɗauka ba, wallahi bantaɓa sata ba Ni bani bace"ta ƙarasa faɗa cikin sanyin muryar ta da haryanzu bata dawo daidai ba saboda kukan da tasha,dafa kansa yayi yanajin shikam baƙaramin takura masa akayi da zaman gidan nan ba, abinda baya cikin halinsa an sashi yinsa yanzu,shida bai damu da kowa ba bai damu da shiga sabgar kowa ba, amma tunda tazo gidan take sashi waɗan nan ɗabi'un,kome yasa ma yake yawan tausaya mata oho, amma dai yana ganin fita zaiyi daga sabgarsu suje koma me zasuyi mata suyi mata,dan A gaskiya yana takura da wannan sabuwar ɗabi'ar ta yawan magana tunda shi bai saba ba,(Malam Abdallah kenan A hakan shine kana yawan magana)kaucewa yayi zai fita,cikin kukan ta tace kaima baka yadda dani ba,inno bata yadda dani ba Rahima bata yadda dani ba duk masu sona basu yadda dani ba to Ni ya zanyi?ɗan dakatawa yayi kana cikin gajiyawa yace" sai kiyi yadda kikeso,ba dole su miki haka ba me inno tarageki dashi da za ki ɗunguma mata gagarumar sata haka? yana gama maganarsa yayi saurin barin falon gaba ɗaya. Wani irin yarfa hannu tayi gami da zubewa A gurin, hannunta tasa tashi ga mussike idanunta dasuka ƙi daina zubar ruwa,haka nan takejin wani mugun tashin hankali,to wai meyasa bata bi bayan inno ba sai shi? meyasa takeji A ranta yaddarsa kawai take buƙata A halin yanzu?kukan ta kuma fashewa dashi tana murza ƙafafuwan ta bisa tattausan carpet ɗin dake malale A tsakiyar falon,cikin dasashshiyar muryarta da babu sauti take cewa,kai kam meyasa ba A fahimtar zuciyarka bazakamin magana kafahimtar dani ba?Ni bazan iya gane abinda yake ranka ba,dan Allah-dan Allah meyasane? A nan bacci yayi awan gaba da ita batare data shiryawa hakan ba. Cikin kuka Rahima ke zaiyanawa Hajiya Babba dukkanin abinda ya faru, ta ƙare da cewa, Hajiya Babba yaza ayi Bintu tayi min haka? nakasa mantawa ina sonta sosai tausayinta nakeji wallahi!'Hajiya Babba ta shafa kan Rahima kana cikin nutsuwa da taushin murya tace"Rahima bakyason Bintu!'da sauri Rahima ta tashi zaune tare da cewa kamar ya bana sonta Hajiya? yanzu fa na gama gaya miki amma sai kice banason Bintu!'Hajiya Babba tayi murmushin su na manya masu hangen nesa tace"Ai da kinason Bintu da bazaki yadda da abinda ya faruba, domin Hausawa sunce so hana ganin laifi koda an aikatashi kuwa,dan haka ko Ni ɗin nan nafiki son Bintu tunda ban yadda da abinda A kace ta aikata ba,ko da kuwa A hannunta A kasamu sarƙar, kinga Ni ba tare nake da ita ba zuwa kawai takeyi shima zuwan ba sosai ba amma nayi mata yaddar da koke banyi wa ita ba,tana can ina nan amma da ita nake kwana nake tashi,inno bata kyauta ba in dai har ta yadda cewa Bintu zata iya yi mata sata,saboda watannin da tayi tare da ita yaci ace takaranci halayyar Bintu,wanda A cikin abinda nasani dan gane da ita nasan imaninta bazai iya barinta ta ɗauki abin wani ba Abu na biyu tausayinta san nan tsoro,dan haka Rahima ki je ki koyi yadda ake aminta ta gaskiya da amana kafin kiyi ƙawance da Bintu domin nasan idan itace baza ta taɓa yi miki haka ba!'daga haka bata kuma cewa komai ba ta maida hankalinta kan casbahar da takeja,Rahima kuka tasa tana mai jin tsananin kunyar haɗuwa da Bintu bata san da wane baki zata bata haƙuri ba, cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga ɗakinta tana mai jin nadamar abinda tayi. Nafisa wai meye amfanin ki A cikin gidan nan indai har kina kallo wasu banzaye daga can gefe zasu wargaza mana shiri,kin riga da kin san dai Bintu itace idon mu yanzu A gidan nan tun ba mu cimma abubuwan da mukesan cimmawa ba a keson A koreta!'Anty Nafisa tace"nifa Hajiya ban san meke faruwa ba saboda nima kwana biyu bana jin daɗi ban shiga ɓangaren inno ba dan haka bani da masaniya A kan komai dake faruwa!'Hajiya ladidi tace"shike nan amma inaso daga yanzu kisaka mana idanu akan masu kawowa burinmu farmaki!'Anty Nafisa tace"to Hajiya nayi miki alƙawarin bazan bari ƙananan maƙiya suyi tasiri A kan Bintu ba har sai mun cimma burinbu!'suna A jiye wayar Aunty Nafisa ta miƙe daga saman gadon ta, A fili tace"dole shirina bazai tafi yadda ya kamata ba sai da sa hannun Amintacce, kuma ba kowa bace sai Bintu ita kaɗai ce zan iya haɗa wannan al amarin da ita batare da fargaba ba, saboda Ni nakawo ta gidan nan Ni na buɗe mata ido, dan haka babu wadda ta can canta da Bintu ta zauna a ƙarƙashin ta face Ni, kuma tsari na baze yuwu Ni kaɗai ba dole sai da sa hannu dan haka yanzu lokaci yayi Bintu da zakiyi min amfani, bani da shakku akan ke ɗin zaki rufan asiri duk da tarin tsanarki me zafi ta dake ƙunshe cikin raina amma babu yadda zanyi dole na danneta A wannan karon. A hankali ta zauna gaban inno dake kan sallaya hannunta riƙe da ɗan ƙaramin ƙur'ani,Bintu ta zuba mata ido har ta ida karatun ta kana ta ajiye shi gefenta cikin nutsuwa,ƙara matsawa gabanta Bintu tayi tare da ruƙo hannunta cikin san haɗa ido da innon tace" inno kiyi haƙuri nasan ban kyauta miki ba da nakasance ɓarauniya A gareki duk da tarin halaccin ki A gareni!'hawayenta ne suka gangaro daga cikin idanunta tanajin zafin karɓar laifin da bata aikatashi ba, amma kuma tana ganin haka shine mafita A gareta,A hankali inno tasa hannu ta share mata hawayen, kana cikin taushin kalami tace"Bintu meyasa kike bani haƙuri? meyasa kika zaɓi karɓar laifin da baki aikata shi ba?da sauri Bintu ta kuma runtse hannun inno dake cikin nata,inno ta ciga da cewa,ba komaine yasa nakasa duban ki ba Bintu abu biyune, dalili na farko shine banaso na nunawa waɗanda suka saka miki sarƙa A cikin ɗakinki ban yadda ke kika ɗauka ba domin yin hakan shi zai basu damar cigaba dayi miki ƙullin da kowa zai iya tsanar ki koda kuwa Ni na yadda dake A banza wata rana abun zaiyi girman da ko Alhaji ba zai saurara miki ba,na biyu kuma shine tsananin kunyar ki kasancewar A cikin ahlina A kasamu waɗan da suka shirya miki wannan tuggun,amma wallahi Bintu ban taɓa zargin ki da zaki aikata wa wani ma mugun hali ba balle kuma Ni,Bintu ina ji A jikina ke ɗin wata fitila ce da tazo daga wata duniya dan haska mana abin da mu bama gani, dan haka ki saki ranki da zuciyar ki kici gaba da walwalarki Allah Ubangiji yana tare dake,sai dai ina mai sanar dake zaki ga canji A tare dani indai muna cikin jama'a saboda kawar da idon maƙiya A kanki!'wata kyakykyawar runguma Bintu tayiwa inno ta shiga sun batar ta tako ina tana cewa inno ilove U ina sonki da yawa ina yi miki son so inno, Allah ya barminke nasan idan ina tare dake bazaki bari hawayena su zubaba kece farin cikina garkuwa ta Allah Ubangiji yaja min kwananki domin kika ga ƙudurar Allah da idanunki!'A hankali inno tasa hannu ta sharewa Bintu hawaye itama tayi dabara ta goge nata ƙwallar kana tace"tashi kije Allah yayiwa rayuwarki Albarka!'Buntu ta amsa da Amin tana mai kuma sunbatar hannun inno,bayan ta fita inno tabita da kallon tausayi tana mai addu'ar Allah Ubangiji ya dafawa rayuwar Bintu baiwar Allah. Kafin wani lokaci Bintu ta shiga walwalarta tare da ƙwarin gwiwar inno mace da babu kamarta A wajen ta sai dai kuma can ƙasan zuciyarta tana jin A kwai sauran abinda ya daƙile farin cikinta na samun yardar inno, tana jin kamar hanyanzu A kwai sauran yaddar datake nema, zuciyarta ce ta rayamata Rahima, a'a ba ita bace ta kuma canja tunani,can kuma ta kuma yin wani tunanin Hajiya Babba tabbas tasan Rahima ta gayawa Hajiya Babba komai dan haka dole taje ɓangaren Hajiya Babba ko dan gano matar datake matuƙar ƙauna, cikin nutsuwa ta ɗauki ƙatan hijabinta ta saka har ƙasa kana ta nufi ɓangaren Hajiya Babba... Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 23 ``` Lokacin da tashiga falon inno babu kowa dan haka kai tsaye ta nufi hanyar ɗakinta,tana dab da shiga ɗakin taji daga bayan ta ance, wata satar kikazo ki kumayi A nan?da sauri ta juya Sayyid ta gani tsaye da alama yanzu shima ya shigo kamar ma ita ya biyo,ya tako ya ƙara so inda take, kana cikin san cimma wata manufa yace" dama zuwa kikayi na taimaka miki, da ki dinga yawan bin ɗaukar sarƙoƙin kakannin mu dan nasan yanzu ma zuwa kikayi ko zaki dace A nan tunda ta can ta suɓuce miki!'Bintu kallonsa kawai takeyi tana aiyanawa A ranta anya kuwa Sayyid baya daga cikin annobar gidan nan? to idan ba haka ba me tai masa meye haɗin ta dashi? meyasa ya uzzurawa rayuwarta? to lallai kuwa ya jawa kansa matsala domin tasaka masa ayar tambaya, tabbas da A kwai abinda zata iya samu ta ɓangaren sa Sayyid bai kai yayiwa kansa wani tanadi ba sai dai ayi amfani dashi haƙiƙa A kwai wani abu A ƙasa kuma da sannu zata bincikosa,yatsan sa yasa ya ƙyasta mata A kan fuska,bin hannun nasa tayi da wani irin kallo tamkar A cikinsa zata gano amsarta,murmushi yayi kana yace"kina tunanin yadda zaki samu kuɗi A gurinane? to indai wannan ne karki damu Ni ba matsala bace A wajena!'daddagewa tayi ta tattaro duk wani miyau dake cikin bakinta ta tofa masa A fuska tare da jan wani ƙaƙƙarfan tsaki tayi shigewarta ɗakin Hajiya Babba ta barshi tsaye yana binta da mugun kallo yana mai raya mugayen manufofinsa A kanta wanda babu wanda ya san manufar sai shi sai mai ƙudura da irada. Cikin sallama ta shiga ɗakin,Hajiya Babba dake jera kayan guga A kwabarta, ta amsa fuskarta cike da mabayyanin farinciki tare da saurin A jiye kayan hannun ta ta janyo Bintu jikinta wadda take shirin duƙawa, cikin ƙaunar yarinyar Hajiya Babba tace"Bintu na ina kika ɓuya kwana biyu ina ta cigiyarki? Bintu tayi ɗan murmushi tana aiyana wa A ranta wato Rahima bata gayawa Hajiya Babba komai ba kenan, Hajiya Babba ta katse ta da cewa Bintu ki daina dogon tunani ke yarinyace mai ƙananan shekaru idan kika bari yawan tunani ya aure ki zai iya haifar miki da wata babbar matsalar dan haka ki manta da abinda ya faru Ni nasan bazaki taɓa aikatawa ba,tashi maza ki gaya min inno ta yadda da satar da aka laƙa miki? da sauri ta girgiza kanta yayin da ƙwallar ƙaunar bayin Allan nan take ƙoƙarin zubo mata, Hajiya Babba tace"a'a Bintu bana son kuka fa ai komai ya wuce,zan cigaba dayi miki addu'ar neman tsari daga sharrin dake cikin gidan nan insha Allah babu abinda zai sameki kema ki dage da addu'a kinji? Bintu ta rungume Hajiya Babba amma takasa furta komai a kan harshen ta,wani littafi Hajiya Babba ta janyo dake kusa da ita ta miƙawa Bintu tare da cewa, karɓi wannan Bintu zai tai makeki duniya da lahira,Bintu ta karɓi littafin tana duba sunansa DA HAKA NA GAGARA shine sunan littafin,Hajiya Babba tace"kije ki duba kiyi wata addu'a tana nan A shafi na goma sha tara sunan addu'ar GAYAWA JINI NA WUCE bazan gaya miki komai ba sai kinje kin gwada Allah Ubangiji ya taimaki rayuwar ki!'Bintu ta buɗe baki zatayi magana sai ga Rahima ta shigo da sauri tazo ta rungume Bintu, tana cewa dan Allah Bintu ki gafarceni nayi nadamar abinda da aikata miki saida Hajiya Babba ta fahimtar dani san nan hankalina ya dawo jikina dan Allah kiyi haƙuri!'Bintu tayi murmushin ta mai sanyi tanajin farin ciki har cikin ranta ta kuma samu salama cikin zuciyar ta, tace"Anty Rahima na fahimceki!'tura baki Rahima tayi ta harari Bintu tare da cewa, ai gashi nan kin rama tunda kince min Anty!'dariya suka saka gaba ɗaya kana suka fita suka nufi ɓangaren inno. Duk da haka dai wannan abin yana zaune cikin ƙasan ranta,tanaji har yanzu A kwai wanda yayi saura ya fahimceta,tanajin rashin daɗi can ƙasan zuciyarta ɗan tura bakinta tayi cikin gunguni tace"shi wannan miskilin bazai yi maka alama ba kuma bazai fahimtar da kaiba,ji tayi kamar zatayi ƙwalla saboda bata sani ba ko kallon ɓarauniya yake mata,ko shima ya fahimceta oho,wata zuciyar tace da ita ya fahimceki kawai bazai nuna miki ba saboda karkiyi farin ciki,ɗan murguɗa ƙaramin bakinta tayi kamar yana ganinta,to ma meyene ta wani damu yaje can da halinsa tunda inno da Hajiya Babba da Rahima sun fahimceta to ai bata da wata sauran damuwa. Duban samuyal Abdallah yayi kana ya nuna masa gidan da yake ɗan nesa dasu yace"inaso nasan wan can gidan na waye kuma suwaye suke zaune A cikin sa?samuwal yace"don sir!: kana ya kuma cewa daga yau zuwa gobe nake buƙatar komai!'daga nan Yahya yaja motar, ɗan juyowa yayi yace sir ina muka nufa asibiti ko gida? yace"office ɗin sirri!' ok sir" Baba nura ya dubi Alhaji Salisu kana cikin tashin hankali yace,me mutanen nan suke nufi ne Salisu? kaga fa yaron nan ashe jami in sirrine, Alhaji sama ila ya ɗan ciza yatsa kana yace kun san abinda nayi tunani?gaba ɗaya suka zuba masa ido suna sauraren sa, ya ɗan ja ajiyar numfashi kana yace" inaga fa leƙen asiri yaron nan yazo yi!"Alhaji rufa'i (Babban yaron Alhaji Balarabe dake zaune akano yana auren sakina ƴar wajen Hajjah)takanas yazo har A buja saboda wannan zaman da zasuyi,gyara zaman sa yayi kana cikin nutsuwa ya fara magana,Ni ina ganin ba wannan dalilin ne ya kawoshi ba akwai dai babban dalili ta can ɓangaren Alhaji jafar!' wannan karon Alhaji Salisu ne yayi magana yace"duk abinda muke bibiya har yanzu bamu kai gacin nasarar tafiyarmu ba Ni dai aganina kama ta yayi mu maida hankali kan abinda ke gabanmu!'Alhaji Sama'ila yace tabbas maganarka haka take yanzu munajiran baya nai ne daga gurin Baffa Hashir daga nan zan bawa su ligidi aikin zasu yi shi batare da matsala ba!' Dady jafar, ya kalli Abdallah tare da cewa yanzu wa kake gani acikin ma aikatanka mata zaka danƙawa ragamar shiga rayuwar Alhaji salisu? Abdallah yace" Dady Anty Samira zan dan ƙawa aikin nan saboda kaga ita bazawarace kuma tana da hikimar aiki zamu tura ta wajen Alhaji Salisu,nasan zata ɗauko mana dukkan bayanan da muke buƙata!' yauwa Alhamdulillah masha Allah,sai kuma batun Dadinku Mansur!' A hankali Abdallah ya ɗan kwantar da jikinsa,kana cikin nutsuwa,yace" Dady wannan bana ta tashi,Dady yace" ya kamata kasaka yariyar nan cikin tafiyar nan zata iya yi mana amfani!' runtse idanunsa yayi yana hango rigimammiyar fuskarta,can ya ɗan nisa kana yace"rabu da ita rigimammiya ce!'murmushi Dady yayi batare da ya kuma tankawa ba. Wani irin shaƙurar ran kallo momy abigirl take bin Ayoyah dashi, tanason cewa wani abu amma ta kasa saboda maganar ta maƙale mata,can dai ta samu ta haɗiyi wani kakkauran miyau kana cikin tashin hankali tace"Ayoyah me kike nufi da wannan zan can naki? Ni kike sanarwar cewa ba gidan tiraning David ya kai Fatash ba? Ayoyah cikin tabbatar da zancanta tace"Abigirl banzo miki da maganar nan ba sai da na gama bincike, na kuma tabbatar da abinda naji kuma na gani, tabbas Abdallah yana ESTATE ɗin ALHAJI BALARABE,yana can yana rayuwa cikin musul mai yana kuma addininsa na Musulunci,hannu Abigirl ta ɗora aka ta kurma wani uban ihu, wayyo shikenan tawa taƙare asirina yana gab da to nuwa!'tashi tayi da gudu kamar mahaukaciya sabon kamu, sama ta haye bata tsaya ko ina ba sai tsakiyar ɗakinta zubewa tayi tana faman juya kanta ta rasa inda zata saka kanta saboda tsananin tashin hankali lallai idan batayi wani abuba, watan tonuwar asirinta yayi gashi nan garin neman gira zata rasa ido har da hanci da baki,zuface take keto mata ta ko ina, Abigirl tana cikin tsaka mai wuya me yasa David zai mata haka me yasa zai ci amanarta? ƙirjinta ta dafe da ƙarfi A yayin da wani tunani ya shige ta kaddai David ya gano sirrin da saninsa yake dai dai fansar rayuwar ta ?kai bai gano ba tabbas da ya gano da tuni sun daɗe da aikata lahira shi da Abdallah,to yanzu me zatayi dan cigaban rufuwar wannan mur ɗaɗɗen sirri? wani ɓangaren na zuciyarta yace mutuwar Fatash (Abdallah)runtse idanunta tayi ta na mai juyayin wannan shawara,idan kuma batayi hakan ba tabbas reshe zai juye da mujiya mutuwa biyu ce zata tabbata akanta,miƙewa tayi har zata fita sai kuma ta dakata ta ɗauki wayarta da mukullin mota ta fita. Yau tsawon kwanaki biyu kenan yana gwada zuwa wajen amma sai ya kasa shiga ɓangaren to wai meyasa hakane? hakan yana nuni da lallai an kewaye gurin da manyan sirrika,tunda ya auna ya gani kuma ya ankare tun da yazo gidan bai taɓa ganin wata halitta ta kusanci gurin ba,sai dai wannan inuwar da yake yawan gani lokaci lokaci,to ya akayi wannan matsoraciyar yarinyar take iya tun karar wajen? meye tare da yariyar nan ne? ko dai ta bakin Dady jafar ne dole sai sun sakata cikin wannan mugun haɗarin,anya baiyi ganganci ba idan yasaka Bintu cikin haɗarin gidan nan ba? to meyasa yake tsoron sakata bayan itama tana da burin tai makon ahlin gidan?to amma dai dole ya nutsu yayi tunani akan al'amarin. Gaba ɗayan su yau suna cikin ƙungurmin dajin da ko tafin hannun su basa gani, sai dai dake shu'umai ne su wannan shine cigaba agurinsu cikin gidan kansa din ɗin yake babu abinda kai baƙo zaka gani amma su dake sun san kansu da sirrinsu basu da wata da muwa da hakan, wutace A tsakiyar su take ci tamkar za'a babbaka mutum, wannan wutar itace idon su, dukkanin su sunyi tsit dagani zaka san cewa wani muhimmin aiki sukeyi wanda da gani yana basu wuya,cikin wata kakkausar murya shugaban nasu yace"nanu Akwai babbar matsala tunda har muka kasa hana kifanyan nan tun karar ɗakin iko,munyi nasara a kan kifin babu yadda zaiyi ya iya tsallaka wurin nan,kai ko tsuntsu ne yazo giftawa ta saman ɗakin nan sai ya fado ƙasa matacce,yanzu tashin hankalin mu kawai wannan fitinanniyar kifanyar,mafita ta ƙarshe itace..banji me sukace ba saboda ba da Yaren da nakeji yayi magana ba,daga nan kowa ya ɓace da ɗamarar sa ta fara yaƙi. Gudu take sheƙawa kamar zata tashi sama har ta kusa dan gana da inda zata, sai kuma taja wani uban burki wanda saura ƙiris ta angije wani me napep bata kula da zagin dayake antaya mata ba ta gangara gefe tayi fakin wayar ta dake ta neman ɗauki ta raruma,ta can ɓangaren cikin muryar ƴan daba akace mata Mr Devid ya akayine naga kiranki Ina cikin ɗaukar saiti!'ajiyar zuciya ta saki kana tace" Fire kana inane yanzu ina kan hanyar zuwa tsangayar ka!' yasa wata shegiyar dariya mai ban haushi, kana cikin maganarsa ta maye yace"hajjaju kenan kin so dakar gurbi saboda Ni yanzu bana Abuja na tafi ƙaddamar da ɗan wani aiki amma ba zan jima ba ki bani sati biyu kawai on my way!'momy Abigirl taja dogon numfashi kana tace"shike nan Fire Amma naso kana kusa saboda aikin na gaggawa ne amma babu damuwa zan jarraba wasu hanyoyin kafin dawowarka!'yauwa hajjaju sai nadawo ɗin!'kifa kanta tayi jikin sitiyarin tana maida numfashi,sai da ta ɗauki wasu ƴan mintuna kana taja motar A hankali kamar ba ita ta gama sheƙa gudu ba, Can cikin baccinta taji kamar motsi ta bayan ɗakinta har ma da sautin magana ƙasa ƙasa,cikin sanɗa da san cire tsoro ta tashi ta nufi jikin window A hankali ta manna kunnenta, abinda taji ana faɗa shiya matuƙar tayar da hankalin ta zama tayi daɓar aƙasan ɗakin yayin da zufa take yanko mata ta ko ina tamkar babu fanka A ɗakin,kafin kace meye idanunta sun jiƙe jagab da hawaye,yadda taga rana haka taga dare sai dai bata bari daren ya tafi abanza ba saida ta rayashi da kiyamul laili. Cikin mutuwar jiki ta gama haɗa masa karin kumallo,sai da ta gama komai ta jera,kana ta samu guri ta raɓe kamar munafuka,bata motsa daga inda take ba har ya dawo daga motsa jiki ya shiga ya shirya ya fito tsaf dashi tamkar wani fure sai ƙamshi yake zabgawa,sumar nan ta kwanta tayi luf sai ƙyalli takeyi, nan ma dai yayi mamakin ganinta amma sai ya share ta ya nufi dining,har ya gama karyawa bata tashi ba sai dai ido datake binsa dashi,ɗaki ya koma ya ɗauko jakarsa ya fito,zuwa yayi ta gabanta zai wuce, tayi saurin tashi tasha gabansa,idanunta cike taf da hawaye,tsayawa yayi yana kallonta cike da mamaki,har zai kuma wucewa sai kuma ya dakata jin ta biyoshi cikin ƙosawa da ganin yanayin da take ciki yace"lafiyarki kuwa? cikin kuka tace"karka fita zasu kasheka wallahi naji da kunnena suna faɗa jiya ta bayan ɗakina!'wani kallo yabita dashi kana A hankali ya taka ya koma ya zauna cikin kujera dubanta yayi da lumsassun idanunsa kana cikin taushin murya yace"zonan!'cikin sanyin jiki ta ƙara so inda yake ta durƙusa,A gabansa cikin nutsuwa sai dai fuskar nan a haɗe take ka tamau babu alamun ya taɓa sanin yadda ake murmushi,yace" ina jinki ki nutsu kiyi min bayani banason bana son hawayen Nan!' Samu tayi ta dai dai ta nutsuwar ta da ƙyar kana tace"jinayi suna cewa za'a sace tayar motarka da zaka fita da ita kuma ina tunanin sun sace"saboda alokacin umarni ake badawa da aje a sace!'cikin san tabbatar wa, yace" zaki iya shaida muryoyinsu?girgiza kanta tayi tare da cewa Ni ban taɓa jin muryoyin ba!'jin jina kansa yayi tare da cewa tashi ki tafi!'ɗan kallonsa tayi amarairaice,kamar zata fashe da kuka,bai ce mata komai ba ya ɗauki wayarsa saboda ya fahimci abinda take nufi,wayar yakara A kunnensa,jim kaɗan yayi magana,kakawo mota yanzu ina jiranka!' daga haka ya kashe wayar tare da maida idanunsa ya lumshe,ganin haka yasa ta miƙe A hankali ta fita daga falon ta ƙasan ido yabita da kallo har ta fice, Duban samuyal yayi bayan sun shiga office ɗinsa,yayi masa alamun yana sauraren sa, samuyal ya ɗan gyara zamansa kana yace sir wannan gida na Alhaji Nasir ne kuma an ta nade shine saboda zaman mitin da sukeyi idan hakan ta taso!'ya miƙa masa wata doguwar paper yana cewa ga bayanan waɗanda suke mitin ɗin da jerin sunayensu!'karɓa yayi tare da jinjina wa samuyal,daga nan kuma ya bashi umarnin tafiya da cewar sai ya neme shi..... Comment..... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 24 ``` Babbar mace ce, wadda baza ta gaza talatin da hudu ba,kyakykyawa ce bata da wata makusa,tana da kyawun jiki shiyasa idan ka kalleta zakayi tunanin bata kai shekarunta ba,A hankali ta zauna kan kujerar dake fuskantar sa,kana cikin girmamawa A matsayinsa na oganta,ta gaida sa,dubanta yayi cikin nutsuwa yace"Anty Samira ga wannan fayal ɗin kije ki duba shi ,A nutse,banaso A samu kuskure,saboda wannan aikin da zamu fara yana da ban banci da sauran aiyukan da muka saba fuskanta dole yana buƙatar shiri da kuma addu'a aikin yana da haɗari Anty Samira sai mun kula gaba ɗayan mu!'Samira ta ɗan ja dogon numfashi kana cikin nuna sadaukarwa tace"karkadamu sir,kafin na fara aikin nan nayi alƙawarin babu abinda zai tsoratani naji na karaya na sadaukar da rayuwata wajen kare rayuwar al umma dan haka zan je na duba insha Allah baza asami matsala ba!jinjina kansa yayi cike da gamsuwa,kana yace" shike nan zaki iya tafiya!' sallama tayi masa gami da fita daga office ɗin,shima kiran Yahya yayi,dan yana son shiga asibiti. Lokacin da ya dawo gidan A ɓangaren sa ya sameta duk da bai dawo da wuri ba yayi mamakin abin da ya hanata kammala girkin da wuri amma sai bai bawa kansa damuwa ba ya barshi kawai a yanayin yau da gobe,ita kuwa Bintu ba komai ne ya hana ta girkin da wuri ba sai ciwon marar da yake ɗan tsun kulinta Lokaci zuwa lokaci,A dai dai lokacin da take shirin fita daga falon mararta tai wani irin murɗawa da sauri ta durƙusa gami da riƙe cikinta yayin da gaba ɗaya ƙafarta ta riƙe katamau sai wani irin danƙa da marar take mata,abinka dama da wadda kuka baya mata wahala tuni fara rera abinta,yana fitowa yayi karo da sautin kukanta girgiza kansa kawai yayi yana mamakin yadda sam kuka baya mata wahala,zama yayi yaci haɗaɗɗen danbun shinkafar da yaji zogala da kayan haɗi sai zabga ƙamshi yake,sai da yaci yay ƙat kana ya kora da kunun ayarsa me shegen ɗaɗi goge bakinsa yayi da tishu,kana cikin yanayin takunsa na isassun maza masu kwarjini da haiba ya taka har zuwa kan luntsumemiyar kujerarsa,wani irin zama yayi mai cike da burgewa kai komai Abdallah yayi sai yayi masa kyau komai nasa abin burgewa ne, cikin wani irin salo mai cike da burgewa,ya zuba mata lulu eyes ɗinsa masu haske da sheƙi,jin idanunsa na yawo ajikinta yasa ta ƙara sautin kukan ta tana mai jin haushin yadda ya shareta,to ba sai ya tambaye ta abinda yasa ta kuka ba amma ya mata shuru sai kallon da ya ishe ta da shi kamar wani maye,jin ya ɗan lafa mata yasa ta miƙe A hankali zata lallaɓa ta bar masa falonsa inyaso sai yaci kansa,wani irin rawa ƙafarta ta shigayi yayin da marar ta kuma juya mata ai batasan lokacin da tasaki ƙara ba gami da zubewa ƙasa tana wani irin juyi wanda yake nuni da tsananin azabar da take sha, A hankali ya miƙe cikin takunsa na nutsuwa ya isa inda take kwance tana faman juyi,wani ɗan tsuguno yayi na burgewa A gabanta,kana cikin kamilalliyar muryarsa yace"me yasa ki kuka? duk da halin da take ciki amma hakan bai hana ta jin haushin tambayar tasa ba,har sai da ta ɗan yi musu-musu da bakinta tana ɗan murguɗa shi,sharewa yayi kamar baiga abinda tayi ba,idan bazaki magana ba ki tafi min A falo kin dameni da ihu!'ƙasa ƙasa ta wulla masa wani shu'umin kallo wanda ita aganinta hararace,ganin ya tashi zai bar gurin yasa ta kuma sakin ƙara wadda har sai da tasa ya runtse idanunsa,har ya rasa me Yakamata yayi,dawowa yayi tare da miƙa mata hannunsa batare da ya dubeta ba, cak kukan nata ya tsaya,yayinda ta ke bin hasken tafin hannun nasa da wani irin kallo,kusan sakanni ashirin kafin a hankali ta ɗaga hannunta ta ɗora bisa tafin nasa hannun,kamawa yayi ya miƙar da ita tsaye ,kana ya shiga takawa A hankali yana nufar ƙofar fita da ita,wani irin kallo take bin kwantaccen gashin da ya ƙawata ƙeyarsa dashi har bata san ya akayi ta shiga taka ƙafar data riƙe saboda ciwo ba, Bashi ya tsayaba sai da ya dangana da ƙofar ɗakinta kana A hankali ya saki hannunta ya juya ya barta A tsaye,saida ta ga yashi ge falon sa kana ta ji ciwon ya dawo sabo, komawa cikin ɗakinta tayi ta waɗa kan gadonta tana juyi,tsit tayi lokacin da taji alamun an shigo ɗakin,ɗago kanta tayi cikin yanayin jin ciwo,ɗan lumshe idanunta tayi kana ta buɗe su A hankali ta zuba su kan kyakkyawar fuskar sa mai cike da kamala,ta kowa yayi har gaban gadon,kana ya miƙa mata robar ruwan dake riƙe A hannun sa,karɓa tayi ya kuma miƙa mata wasu magunguna, suma karɓar tayi sai juyasu take A hannunta ta kasa sha, dan tsakanin magani da allura bansan wanda Bintu tafi ƙi ba,ganin taƙi shane yasa ya ɗan zaro mata idanu wanda dole yasa ta runtse idanunta ta afasu A baki,da farko kamar zatayi amai sai kuma ta koma tana maida numfashi,atunaninta juyawa zaiyi sai taga yana haɗa allura,tofa anan akeyinta cikin rawar murya tace"Ni ba sai an yi min allura ba naji sauƙi!'bai kula ta ba ya gama haɗa allurar,yay mata alama da girarsa data gyara zaiyi mata,tura baki tayi tana magana ƙasa ƙasa,mutun duk abinda zaiyi sai ya haɗa da mugunta,ga kuma bazai yi magana ba sai dai komai yayi wa mutum alama kamar wani bebe shi ko gajiya bayayi da rashin magana,bata aune ba sai jitayi kawai ya riƙe hannayen ta duka biyu yana ƙoƙarin tsira mata allura,wani irin zillo tayi sai gata gaba ɗaya A cikin jikinshi hakan kuwa ya bashi damar riƙe ta gam ya tsira mata allurar,ƙanƙame shi tayi tana kuka wanda harga Allah kukan zafin allurane, yana gama yi mata ya tura ta saman gadonta,ya tashi ya bar ɗakin yana mai jin mamakin sangarta da tsoro irin nata,ko ta yaya zata iya taɓuka wani abu da wannan shegen tsoron, Taufiƙa tana ganin zai fito tayi sauri tabar bakin ƙofar,sai da taga ya shige ɓangaren sa, kana ta shiga ɗakin,samun Bintu tayi tana kukan allura,tsayawa tayi A kanta tana fidda wani irin huci na tsananin kishi da tsana,tace" yanzu me zaki iya cewa game da wannan? sabo da sabon iskanci yau har sai da kikayi kisisinar da yashigo ɗakinki,wai Bintu me kike nufi da Yahh Abdallah ne?ɗan ranƙofawa tayi kana cikin tabbatar mata da abinda zata iya aikatawa taci gaba da cewa, Bintu idan har bakya son shiga tashin hankalin da baki taɓa tunanin zai kusan ci rayuwarki ba to lallai kar kibari zuciyar Yahh Abdallah ta fara sonki,san nan karki bari taki zuciyar tayi gangancin son Yahh Abdallah,wannan kashedi ne da nake miki saboda tsira da farin cikin ki, wallahi Bintu bantaɓa faɗar abu na karya shi ba muddin kika bari Yahh Abdallah ya soki to ki tabbatar da cewa zan iya saka wuƙa na yanka wuyanki, batare da nayi na dama ba,gara gara ma taki zuciyar tasoshi wannan ke zaki zauna cikin wahala,dan haka ina fatan zaki kiyaye!'daga haka ta fita ta bar Bintu sake da baki da wani irin maɗaukakin mamaki,meyasa wai bata gama da wani al ajabin ba wani yake danno kai, wai mace matashiya ce da irin wannan kaifin harshe,to wai shin gidan nan me yasa ɓara gurbin cikin sa sukayi yawa? meyasa mutanen kirki basu da yawa? wai waye silar gurɓacewar ahlin ALHAJI BALARABE ne,tabbas wannan shi ake kira da wata sabuwa,to amma ita ina ruwanta da Oga Abdallah meyasa take tunanin zai sota koda ita taso shi tabbas Oga Abdallah ba zai taɓa santa ba saboda babu gami babu alama wutsiyar raƙumi yayi nesa da ƙasa,miƙewa tayi ta ɗauro alwala ta fuskanci alƙibla domin miƙawa Allah kukan ta da kuma neman kusanci da shi. Washe garin ranar kuwa garau ta tashi sai dai al amarin da yake ɗan cizan zuciyar ta har yanzu shine mamakin Taufiƙa,tabbas taga matuƙar ƙoƙarin ta tare da ƙarfin halinta, haƙiƙa sai tayi hankali da waɗan nan mutane huɗu Taufiƙa Siddiqa Farida da kuma Oga Sayyid,dan tabbas ta fahimci mugayen marasa mutunci ne,kuma zasu iya kawo mata cikas gurin aiwatar da aikinta,da wannan tunanin ta ta fito daga ɓangaren Oga Abdallah,wanda kwata kwata basu haɗu ba dan sai yanzu taji ta na matuƙar kunyar haɗuwa dashi,saboda ta gano ya gane abinda yake damunta jiya,tunda gashi ya bata magani da allura kuma taji sauƙi,wato dai yana nufin yadda yake gane halin da mutum yake ciki, shima haka yakeso A dinga gane yaransa, na kurame,ai ko baze yuwu mutum da bakinsa yaƙi yin magana ba wannan kam sai shi Oga Abdallah. Tana shiga ɗakinta ta ji wayar ta na ƙara,da sauri ta ƙarasa inda ta ajiye wayar a ƙarƙashin fulo ta ɗauka,sunan Aunty Nafisa taga yana yawo saman fuskar wayar,ɗagawa tayi tana tunanin me kuma ake shirin ƙullawa dan dukkan kiran da Hajiya ladidi zatayi mata ko Anty Nafisa,kirane na sabuwar buƙata na baƙar manufa,batare da Anty Nafisa ta saurari gaisuwar ta ba tace"lallai ina buƙatar haɗuwa dake yau dan haka kizo ɓangare na kisameni!' ido Bintu ta waro tare da cewa lafiya dai ko? ba tambayar ki nake buƙataba ganinki nake buƙata dan haka ina jiranki!'sauke wayar Bintu tayi daga kunnen ta tare da cewa Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu sai na roƙi Allah ya bani ikon juriya akan sabon Al'amarin da zaki zomin da shi dan ina da tabbacin ba Alkhairi ne yasa kike nemana ba... Anty Samira ta dubi oga Abdallah tace"na kammala dubawa yanzu dai sa hannun sir Adebayo muke buƙata da sa hannun Babban sakataren kungiyar Dss,daga nan sai mu shiga bincike ka in da na'in!'Abdallah ya cire na urar dake saƙale A kunnensa,kana cikin tsurawa computer dake gabansa ido yace"duk bamu da matsala da wannan tunda munsami babban sahannu daga manyan su wannan ma ba zai gagara ba tunda duk muna tare dasu,yanzu abinda ya kamata muyi shine,inason hada mitin ɗin sirri wanda acikin sane nakeso na tace waɗanda basu can canta da wannan aiki ba saboda ina tunanin an samu ɗan leƙen asiri acikin mu, ma ana dai wanda yake fitar da sirrin mu saboda jiya ankawo min hari har cikin gida, A yadda tunani na ya bani tabbas an fitar da wani shirin mu shiyasa har aka fara shawarar kasheni,kuma daga haka zasu iya canja wani tsarin, dan haka tunda nasan yanzu sun san abinda muka shirya musu to mu kuma zamu canja namu tsarin binciken,dan haka zamuyi mitin yau sai anjima duk zanyi muku test ɗin a ina kuma ƙarfe nawa, Aunty Samira Dan Allah ki kula da kanki saboda A kwai haɗari cikin wannan aikin duk abinda kikaga baki yadda dashi ba kiyi gaggawar sanar dani'zaki iya tafiya kisanar musu da maganar mitin ɗin cikin kula!' shike nan insha Allah zan kiyaye, Allah ya bamu nasara!' Amin Ya furta A saman laɓɓansa.. Alhaji Nasir cikin tashin hankali yace" abinda na gaya muku tun farko shi ne yake san tabbata kunga dai wannan damar ta kufce mana dolene mutashi tsaye yaƙi biyune ya samemu kunga dai gashi nan mun tsaya wasa mu ba ga cimma burinmu ba,kuma baga tsira da rayuwar mu ba tunda gashi an fara bibiyar mu za adinga yi mana ɗauki ɗai ɗai!'ya dire maganar sa yana sakin wani zazzafan huci,Baba Nura ya ɗauki xan cen da cewa Baba Nasiru karka ta da hankalin ka yaƙi ne fa tsakanin mu dasu kuma idan ya tserewa wannan farmakin kana da tabbacin zai iya tsererewa na gaba? Alhaji Salisu ya ɗan ja numfashi kana cikin ta raddadi yace"nifa ina mamakin yadda akayi yaran nan ya mamayemu haka da sauri ashe kwantan ɓauna yayi mana!'Baffa Hashir da tunda aka fara maganar baice komaiba ya ɗan numfasa kana cikin yanayinsa nagirma yace"duk Habibu ne ya cuce mu da ya kawo mana jafar cikin ahlin mu,abunda ya ke ɗauren kai kuma bai wuce abinda ya haɗamu da wannan yaron ba ban san dalilin da yasa yake son tona mana asiri da kuma ƙoƙarin san yaga ya dakatar damu daga cikar burinmu ba,Alhaji Kabir da shima har lokacin bai ce komai ba ya ɗan gyara zaman sa kana yace"Ni ina ganin sashi akayi saboda idan kukayi la akari da cewa bamu kaɗai ne masu nema A duhu ba A kwai waɗanda mu bamu san su ba wata ƙil kuma su sun san mu kuma sun fimu shiri shi yasa suka haɗa da hannu da wannan shu'umin yaron!'amma kana ganin Abdallah zai iya amincewa A haɗa baki dashi dan cutar da BALARABE? cewar Alhaji Nasir kenan, Baba Nura yace kun san tunanin da nayi? duk suka zuba masa ido suna sauraran sa,ganin sun bada hankalin su gareshi yasa yace" bakwa zargin da haɗin bakin Habibu cikin wannan al'amari? Baba Nura yace tabbas ka kawo zance mai ma'ana kasan kuwa irin kallon zargin da Habibu yake yawan yi mun idan zama ya haɗamu?kuma ina zargin Habibu yana bibiyar mu dan duk cikin ƴaƴan Baba Alhaji yafi nuna masa tattali da ƙauna,kuma shi kaɗai ne halinsa yake daban da sauran ƴaƴan Alhaji Baba,dan ina ganin daga Abubakar sai Habibu A yaran sa masu tsananin ƙaunarsa da nuna kulawa A kan sa,dan haka babu haufi idan ance Habibu yana ƙoƙarin ganin ya kare mahaifinsa daga komar maƙiya!'dukkan su sun gamsu da wannan bayani na Baba nura kuma suna ganin A kwai ƙamshin gaskiya,Alhaji Salisu yace yanzu dai mu jira bayani daga wajen ɗanleƙen asirin mu idan yaso duk bayanan da ya bamu sai mubisu mu shirya tsari na gaba!' da wannan shawarar suka samu matsaya A tattaunawarsu, Tsaye take ta juya bayanta, fuskarta kamar ko da yaushe sanye take cikin liƙabi,magana takeyi amma kana jin maganar kasan ba itace ainahin Muryar mamallakiyar me maganar ba,cikin kaushin lafaxi take jaddada rantsuwarta ga Dije, wallahi wallahi Dije duk ranar da kika sake na kamaki daniyar cin amanata ko ƙoƙarin to na min asiri sai na yi miki mummunar illa A rayuwarki, bazance zan kasheki ba domin kisa A gurina ba hanyace ta ɗaukar fansa ba idan na kasheki kin samu salama to amma dai ina miki fatan kar hakan ta kasance!'cikin mugun tashin hankali Dije tace" ranki ya daɗe kin sameni da makamancin hakane?wani shu'umin murmushi tayi kana tace" Dije kar fa ki manta kifi naganin ka mai jarkowa,kina tunanin zakiyi wani motsine bada sanina ba? to indai kuwa hakan zata faru to lallai burina bashi da wani amfani da mahimmanci kuma bancika shu'uma ba, inaso ki sani Dije duk inda zaki shiga ki fita ina biye dake kuma!'Haɗuwar da kukayi da Bintu duk da tsarina ne amma kema dana ki tsarin A kwai abinda kuke shiryawa ke da ita wanda bakwa so nasani,shiyasa nake yi miki gargaɗi tun yanzu saboda duk abinda ya faru kiyi kuka da kanki, aiki kawai nace kiyi min ba fallasa ba!'daga haka bata ƙara magana ba ta wuce ta bar Dije san ƙame cikin matuƙar razana da tsinkewa da al a marin wannan shu 'umar mata kamar yadda takira kanta,to amma fa hakan baisa taji zata iya karya alƙawarin dake tsakanin su da Bintu ba sai dai dole zasu canja salon tafiyar,tasan Bintu tana da kaifin basira A sannu zasu haɗa ƙarfi da ƙarfe dan binciko wacece wannan mata, Kwance take tayi ruf da ciki gaba ɗaya tunanin ta ya tafi kan abinda ta gani daren jiya bata taɓa tunanin cewa Yahh Abdallah zai iya bawa wata mace kulawa ba,sai gashi ta gani da idonta yadda ya ta rairayo Bintu A jikinsa,duk da tana tsammanin tausayine kawai da kuma matsayinta Na mai dafa masa abinci,yasa shi kulawa da ita,to kuwa indai har zai iyai wa mai aikinsa haka to matarsa fa? wani irin filling ta dingaji yana ratsata tare da wani irin so mai girma ji take inama ita yayiwa haka ba Bintu ba, tabbas indai har tana san mallakar Yahh Abdallah sai ta tashi tsaye dole tayi wani abu domin samun farin cikin rayuwarta,domin Abdallah da ita kawai ya dace ko ƴar uwarta Hauwa'u bata jin zata ƙyale in dai A kan soyayyar Oga Abdallah ne, Taufiƙa,tayi shirin mallakar Abdallah ta ko wane irin hali.. To shin hakan zata kasance kuwa? Wace hanya zatabi dan mallakar gwarzan shekara kuma dodonsu ɗan zaki wato Abdallah? Me kuma Anty Nafisa take shirin ƙullawa? Shin Abdallah zai yadda kuwa ya haɗa hannu da Bintu ? Wai ma shin meyasa yake tsoron jefata cikin yaƙin? Wai waye mutumin da fafi yace Bintu zata haɗu dashi zai tai maka mata? Muje page na gaba yanzu aka fara wasan....... COMMENT.... More typing... Alƙalamin. Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 25 ``` Bintu sai da ta gama duk abinda zatayi kana ta nufi wajen inno dake zaune tare dasu Siddiqa A falo,durƙusawa tayi gabanta cikin yanayin tsoro tace" inno zan leƙa wajen Anty Nafisa tana kirana!'inno ɗauke kanta tayi cikin halin ko in kula tace" sai kin dawo!'ƙasa ƙasa su Siddiqa suka saka mata dariyar shaƙiyanci, su atunanin su yan zu inno ko fuskar Bintu bata ƙaunar gani,daga Bintu har innon babu wanda ya kulasu tashi tayi ta fita tana musu tata dariyar yadda suka maida su mahaukata ita da innon ta,ɗan kallon ɓangaren ɗakin tayi tanaji A ranta kamar ta nufi wajen yanzu amma sai wata zuciyar tace ki bari tukun har yanzu da sauran lokaci,gaba tayi tana mai ɗaukar shawarar zuciyarta, Can saman ɗakinta ta sameta sai kaiwa da kawowa take ga dukkanin alamu dai Bintun take ta dakon jira,tana ganin shigo war ta kuwa tayi saurin ƙara sawa ta jawo ta cikin ɗakin sosai kana ta murɗa key ɗin jikin ƙofar,shigowa tayi sosai ta gyagygyara labulayen ɗakin suma, ita dai Bintu tana tsaye tana binta da kallo har sai da ta gama tazo ta ja hannun Bintun ta zaunar da ita gefan gadon itama ta zauna, cikin yin ƙasa da murya tace"Bintu ki saurare Ni da kyau wannan karon taimakon ki nake nema,ina kuma fatan zaki taimaka min,jinjina kai Bintu tayi cike da zaƙuwar san jin taimakon da zatayi mata, Anty Nafisa tace"Bintu ciki nakeso nayi!'wata irin zabura Bintu tayi tare da zaro manyan idanunta,bakinta har rawa yake tace" ban ban gane me kike nufi ba? Anty Nafisa ta miƙe tsaye tare da goya hannayen ta A hankali take zaga ɗakin, kana cikin nutsuwa tace"Bintu ki nutsu ki saurareni banason wannan tsoron naki domin zai iya ɓata min shirina,na yadda dake ne shi yasa har zan gaya miki wannan sirrin saboda ko babu ke zan iya aikata ƙudurina,to kawai dai nayi tunanin abin yana buƙatar hannu biyu, ko Hajiya ta bata san da wannan ƙudurin nawa ba,juyowa tayi tana kuma fuskantar Bintun tace"Bintu na gaji da zaman jiran gawan shanu ban san ranar da zan samu ɗan kaina ba shiyasa naga ya dace na fara shiryawa rayuwata abinda zai amfane ta,Bintu baki sake take bin duk inda Anty Nafisa tayi da idanu so take taji ƙarshen labarin domin ita A ɓangaren ta labarine ko kuma tatsuniya,Anty Nafisa ta cigaba da cewa Bintu zan ƙirƙiri cikin ƙarya!'bintu cikin mamaki tace" idan kika ƙirƙiri ciki shima ɗan ƙirƙirar sa za kiyi ko yaya? murmushi tayi nasamun Bintu da tayi mai dabara da fikira,kana tace" Bintu ai cikin ba zai zo da rai ba balle a ƙirƙiri ɗan! cikin tarin mamakin dake shinfiɗe saman fuskar ta ta kuma cewa to meye amfanin ƙirƙirar cikin idan baza a haifi ƙirƙirar ran ɗa ba? good kinyi tambaya mai kyau Bintu,haɗe fuskarta tayi sosai kana tace" Bintu kafin a haifi ɗan za akashe uban ɗan!'wata irin miƙewa Bintu tayi cike da tsananin razana duk da bata gama fahimtar maganar ba,Anty Nafisa kiyi min bayani dan Allah ban gane komai ba ban fahimci komai ba ban san inda maganar ta dosa ba,dafa kafaɗarta Anty Nafisa tayi tana cewa ke dalla ki nutsu sai kace wadda nace ke za'a kashe,ina so ki fahimceni sosai Bintu wannan hanyar ce kawai zata samar min da abinda nakeso,manufa ta ta kashe uban ɗa kafin na haifi ɗan ba rai kuwa shine dole ɗan cikina ya gaji dukiyar ubansa, idan aka haifeshi bai zo da raiba dukiyar ɗana ta zama tawa,kinga kema daga nan zaki samu duk irin kuɗaɗen da kikeso, Tabbas alokacin nan da za'a tsaka jikin Bintu to kuwa baza asami jini na gudana ba ko mai nata ya tsaya cak hatta da numfashin ta da sauri da sauri yake fita tamkar ana fizgoshi, Anty Nafisa ta cigaba da cewa taimakon kuma danakeso kiyi min anan shine kece wadda zan bawa kwangilar kashe uban ɗan Bintu ke zaki kashe mijina!'waiyo masu karatu zan so kikaga yadda mutuniyar taku tayi a wannan lokacin,da ana mutuwa adawo to da sai nace Bintu mutuwa tayi ta dawo,idanunta ne suka tafi luuu kafin kace meye ta zube a gurin sumammiya,batare da wata fargaba ba Anty Nafisa ta shiga banɗaki ta ɗebo ruwa tazo ta sheƙa mata a fuska,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana mai buɗe idanunta tare da fatan ace duk abinda yake faruwa da ita mafarki ne zata buɗe idon ta ta ganta gata ga fafi ɗin ta da ummin ta tare da Baffa Jauro suna ce mata Bintu tashi daga wannan dogon baccin ya isa haka,amma kuma sai hakan bata samu ba dan tana buɗe idanunta sai caraf akan fuskar Anty Nafisa,tashi tayi da sauri tana ƙara murza idon amma dai still Anty Nafisa ce A gabanta ba fafi ba,wani irin kuka ne taji ya taho mata da sauri tasa hannu ta toshe bakinta, Aunty Nafisa ta zuba mata ido tana watsa mata wani mugun kallo tare da watsa mata tambayar da ta saka ta cikin tashin hankali tace" da kika damu haka ko ubanki nace ki kashe? duk da Bintu bata san waye ubanta acikin gidan ba amma sai da taji tambayar tamkar haka ne a cikin ranta sai takeji kamar uban nata akace ta kashe, katse ta tayi da cewa Bintu ki sani dole ne ki aikata abin da nasaki saboda kin riga kinji sirrina dan haka shawara ya rage naki ki aikashi ko kuma na kasheshi kema na kasheki sai ki zaɓa!'girgiza kanta take yi cike da tashin hankali mara misali, Aunty Nafisa tace" kije Ina jiran amsarki daga yau zuwa gobe,duk wanda kika gayawa wannan maganar shima zan haɗa dashi duk na aikaku inda ba A dawowa,cikin kuka Bintu tace" meyasa ke bazaki aikata ba tunda kuna tare a guri ɗaya? Anty Nafisa tayi wata shegiyar dariya kana tace"kema gashi kin faɗi dalili saboda muna guri ɗaya za ai zargina amma idan daga wani gurine babu wanda zaiyi zargina kuma kema ba wanda zai zargeki,ki sani mijina yana yawan cin masa a wajen Hajjah dan haka duk ranar da zai ci Ni zan sanar miki zan kuma baki gubar da hannuna kije can ki zuba ki gudu kinga babu wanda zaiyi zargin ki tun da ba zuwa ɓangaren Hajjah kike ba,idan kuma akayi zargin Hajjah fa? wannan babu ruwan ki tunda ke dai kinsha babu abinda yay miki zafi da wanda za azarga,maza ki tashi kije kar inno taga kin jima abinda kika zaɓa kiyo min test ba sai kinzo ba!nuna mata banɗaki tayi tare da cewa maza shiga ki wanke fuskar ki karki sake ki bar wata alama da zatai nuni da damuwarki!'cikin sanyin jiki Bintu ta tashi ta shiga banɗakin bata jima ba ta fito,batare da ta cewa Aunty Nafisa ko mai ba ta buɗe ƙoafar ta fice daga ɗakin,da wani irin murmushi tabita tana ji kamar burinta ya gama cika... Tun da tashiga ɗakin ta tarufe kanta take kuka har sai da ya saukar mata da mummunan ciwon kai,ko kiching bata jin zata iya shiga, )su Oga Abdallah yau fa sai haƙuri dan baza ka samu haɗaɗɗen girkin Bintu ba)shin yaya zatayi da wannan babban tashin hankalin da ya kuma dannowa cikin rayuwar ta? gaskiya A wannan karon bata da wata dabara ko mafita dole tana buƙatar shawarar wani,to tayaya kenan? bayan ta yi mata gargaɗin kar ta faɗa wa kowa,to hakan yana nufin duk wanda na gayawa shima sai ta kashe shi? runtse idanunta tayi yayin da hawaye suka ƙi dai na zuba mata,ita kanta tasan tana cikin tsaka mai wuya,domin baza ta taɓa iya kashe koda kiyashi ba balle mutum sukutun guda,idan kuwa hakane dole tayi gaggawar neman wa rayuwarta mafita,harma da wanda Anty Nafisa take shirin cutarwa. Ranar yini tayi A ɗaki tana fama da tunani da matsanan cin ciwon kai. Inno duk ta shiga damuwa ta rasa yadda zatayi ta duba Bintu, can sai wani dabara ya faɗo mata duban su siddiƙa tayi waɗanda suke ta buga game cikin ƙwarewa da nishaɗi yayin da Taufiƙa take can tana zurfafa tunani akan neman cikar muradinta,cikin haɗe fuska inno tace" dasu Farida wai ina yarinyar nan ta shiga ne ban ji alamar tafito shiga kiching ba? Siddiqa ta taɓe baki tana cigaba da sha'anin gabanta,Farida tace"yo inno kika sani ko yajin aiki ta tafi,yau tana muradin ɓatawa Yah Abdallah rai,miƙewa inno tayi ranta A ɓace ta nufi ɗakin bintu,dariya Farida da Siddiqa sukayi har da tafawa, A hankali ta tura ƙofar tare da sallama,cikin sauri ta ƙara sa gaban gadon,ta riƙo hannun Bintu,cikin tashin hankali tace" subhanallah Bintu baki da lafiya amma baki sanar dani ba? duba jikin ki kamar garwashi!'ɗago kan Bintu tayi ta ɗora kan cinyarta ta shiga shafa lallausan gashin kanta da ya baje har bayanta,cikin tausayi tace" sannu kinji Bintu tun ɗazu nake son dubaki amma ina tunanin ta ya zanyi hakan saboda yaran nan suna tare dani!'Bintu ta kama hannun inno cikin ƙarfafawa kanta gwiwa tace" inno karki damu ai naji sauƙi jiki nane kawai babu ƙarfi shi yasa kika ga ban fito ba!' inno tace" a'a Bintu ga jikin ki nan da zafin zazzaɓi amma kice min lafiya kike bari na duba ko Abdallah ya shigo nace yazo ya dubaki ya baki magani!'ai da jin haka Bintu tayi wata iriyar zabura sai gata zaune tana rarraba ido cikin rawar baki tace" Ni dai inno karki gaya masa naji sauƙi bari ma ki gani miƙewa tayi ta shiga dan tsalle,inno sakin baki tayi tana kallon Bintu cike da mamakin wannan tsoron da takewa Abdallah,kawar da tunanin tayi da cewa ke kam Bintu ban san wace irin matsoraciya bace!' ma rai raicewa tayi tare da cewa Wallahi inno zuwa zaiyi yamin allura gashi kullum fuskarsa A haɗe babu fara'a Ni kawai ki bani magani xan ji sauƙi!'numfashi inno taja kana tace" ai shikenan bari na kawo miki maganin kisha sai ki kwanta idan kika samu bacci zazzaɓin zai sake ki,shi kuma Abdullah bari naje nasamar masa wani abu da kaina ke ma sai ki ɗanci kafin kisha maganin! to inno na gode amma da baki wahalar da kanki ba zan yi masa da kaina!' inno ta miƙe tare da cewa a'a Bintu bana son gaddama ki kwanta ina dawowa!' daga haka tasa kai ta bar ɗakin.a hankali Bintu ta koma ta jingina da window tana mai jin ƙaunar inno har cikin ranta da kowa na gidan nan halinsu yayo ita da sauran kishiyoyin ta da kuma mai gaba ɗaya wato Alhaji Baba da tabbas sun zama abin koyi,wannan shi ake kira da ƘUDURAR ALLAH, Duk abinda ya kamata inno tayi mata sai da tayi mata ta kuma kaiwa Abdallah haɗaɗen jalof ɗin da tayi masa wanda yaji uban kifi sai gashin kaza da tayi masa mai shegen ɗaɗi,dan haka yaci abincin duk da dai bakinsa yaji cewar ba Bintu ce tayi ba, dake ya riga yasan ɗan ɗanon girkin inno sai bai damu ba amma ya ɗan yi tunanin abinda ya hanata yin girkin. Dole washe gari ta sawa kanta ƙarfin jiki ko dan saboda damuwar inno,da kuma gudun allurar Oga Abdallah,sai da ta gama kimtsa masa ko mai kana ta bar falon batare da ta bari sun haɗu ba tun da tasan shi tamkar Aljani yake wajen gano mutum baida lafiya, Abdallah ganin tayi masa karin kumallo yasa ya dai na tunanin komai,cikin sauri ya kammala saboda shima kwana biyu yana cikin busy, Aunty Samira tace"sir me yasa aka fasa miting ɗin jiya kamar yadda kace? cikin yanayin nutsuwarsa yace"Samira jiya an sanarwa dasu Alhaji Nasir zamuyi mitin hakan ya ƙara tabbatar min da akwai munafiki A cikin mu,dan haka yanzu inaso duk ki kira minsu a kwai binciken da zanyi akan ko wannen mu! ok sir Bari na sanar dasu!' Kallon su yakeyi ɗaya bayan ɗaya gaba ɗaya su goma ne suke ƴan team ɗin sa, sune Amin tattun da ya zaɓa dan yin aiki dasu sai dai bai san a cikin su wanda ya ke kware masa baya ba, amma dai yana da yaƙinin A cikin ƴan mintuna zai fito da ko ma wanene,ɗan gyaran murya yayi tare da gyara zamansa cikin haɗaɗɗiyar kujerar sa, kana ya fara magana cikin ƙasai tacciyar muryarsa wanda kana ji kasan babu wasa cikin dukan Al'Amuransa,yace"abinda yasa nace A yimin kiranku shine jiya nace zamuyi mitin amma hakan bata samu ba dalilin cin dunduniya da muka samu ɗaya daga cikin mu nayi mana!'shuru yayi tare da zuba musu ido ɗaya bayan ɗaya yana mai karan tar yanayin su,ci gaba yayi da cewa amma kusani na riga da na gama bin cikena A kan wanda yake fitar mana da sirrin mu na kuma gano kowanene!kallon kallone ya shiga giftawa tsakanin su kowa na tunanin waye? yayin da me aikata laifin ya fara fidda kansa wanda dama wannan duk shirin Abdallah ne yayi niyar kama kowaye A hannu shiyasa yay musu wannan hikimar,kuma Alhamdulillah yasamu abinda yakeso dan cikin hikimarsa da basirar da Allah Ubangiji ya fuwace masa ya gano mai laifin a cikin mutanen goma da ya amince dasu,ya ɗan daki table ɗin gabansa cikin wasu sakanni office ɗin yayi tsit,razanan nun idanunsa ya ɗora kan fuskar safyanu yana mai san ƙara tabbatar da zaton sa,mara gaski ance ko A ruwa gumi yake tuni safyanu ya shiga rawar jiki,cikin tashin hankali ya sauƙa ƙasa idanun sa na fitar da hawayen na dama yasan in dai a wannan harkar ne Oga Abdallah baida sassauci yana matuƙar girmama amana da gaskiya,cikin rawar baki ya buɗe baki zaiyi magana amma hakan bata samu ba saboda jin yadda wasu manyan ƙarti majiya ƙarfi suka da baibayeshi tare da sa masa sarƙa,ko su jabir baza suce ga lokacin da suka ga Abdallah yayi waya ba balle shigowar su Majid, kallon su Abdallah yayi fuskar nan babu alamar sassauci yace" ku tafi dashi karku saurara masa har sai na neme ku!'hankaɗa shi sukayi waje suka yi gaba dashi. Dukkansu nutsuwa sukayi dan babu wanda jikin sa baiyi sanyi ba,sun riga da sun san hukun cin Oga Abdallah ba mai sauƙi bane,sai da yaga ma shaƙar ƙamshin sa kana cikin kakkausar murya yace" ina so duk wanda yasan zai ci amanata A wannan tafiyar salin alin ya fita daga office ɗin nan idan kuma ba haka ba duk wanda na kama da makaman cin abinda safyanu yayi hukuncin sa sai ya nunka nasa sau goma!'shiru yayi yayin da office ɗin ya ɗau shiru na wani ɗan lokaci kowannen su zuciyar sa cike take da tsoro sai dai kuma akwai sadaukar wa tsakanin su saboda suna san ogan nasu,shima safyanu dan badashi aka fara tafiyar bane bai san irin gwagwarmayar da ogan nasu yayi dasu bane,shi yasa har yaci amanarsa. Dukkanin su sunyi alƙawari da kuma rantsuwa bazasu ci amanarsa ba, kuma zasu tsaya akan tabbatar da gaskiya ko mai runtsi komai wuya,daga nan ne kuma ya sallame su tare da sanar musu lokacin da zasuyi mitin ɗin ƙarfe shabiyu na daran yau in Allah ya kaimu da haka suka rufe tattatunawar. Haka nan taji tana buƙatar ganin Dide ko da baza ta iya gaya mata halin da take ciki ba to tasan zata iya samun shawara cikin hikima,fita tayi can wajen, lokacin ƙarfe takwas na dare dan saida ta kammala wa Oga Abdallah girkinsa kana ta fito, A hankali take takawa tana ɗan waige waige wanda har bata ankara ba sai jitayi an fincikota tare da toshe mata baki,A lokaci ɗaya kuma ana shiga da ita ta wani ɓangare wanda A halin da take ciki baza ta iya fahimtar inane aka nufa da ita ba.... Comments..... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 26 ``` Kiciniyar ƙwace kanta takeyi amma hakan ya gagara ƙarfin ba ɗaya bane,ji tayi an wulla ta saman gado bayan an shigo da ita ɗakin, ɗagowa tayi hankali A matuƙar tashe, Sayyid ta gani tsaye A kan ta riƙe da ƙugunsa yana binta da wani shu'umin kallo mai dauke da tarin manufofi,cikin ƙarfin hali ta miƙe A fusace tana nuna shi da yatsa cikin ɓacin rai da tsoron da ke cike taf A ranta, tace" wai me kake nufi dani? me zan maka da kakawoni nan?wani kallo ya bita da shi batare da ya bata amsaba yayi kanta gadan gadan,wani irin tsalle Bintu tayi ta yi hanyar ƙofa sai dai bata samu nasarar fita ba taji ya cafko gashinta, ƙara ta saka kafin kace meye sun fara dambe A cikin tsakiyar ɗakin,tun Bintu tana samun ƙarfin ƙwatar kanta har ya kai gacewa ta kasa kataɓus,har sai da ya samu nasarar kamata ya shinfiɗe ta asaman gadonsa, cikin dariyar mugunta yace" to yarinya me bakin fitsara ya kikaga wannan salon yau zan kwashe duk wani abu da kike ta ƙama dashi,babu mai ƙwatarki A hannun Sayyid Mansur Balarabe!'ya ƙarashe maganar da ɗage mata gira,yana mai ƙoƙarin zare rigar saman dake jikinsa wani irin ƙarfi ne yazo wa Bintu ta samu damar ture sa kana ta miƙe cikin hanzari har garin sauka a gadon tana bige ƙafar ta hakan yasa takasa tashi dan sosai ta bugu,shi kuma hakan ne ya bashi damar kusanto inda take tare da ɗauke fuskar ta da wani gigi taccen mari wanda har sai da bakinta ya fashe kuka tasa mai ƙarfi tare da fara masa magiya, Sayyid dan Allah kayi haƙuri kar ka ɓata min rayuwa Ni marainiya ce duk abinda kake so zan yi maka amma dan Allah kabarni da mutuncina!' jan yo ta yayi tare da hankaɗata saman gadon yana cewa dama kin san bada haƙuri?bakin rashin kunyar har ya mutu ne?to yau saina cimma burina ko mutuwa zakiyi!'kuka take tana yakushin sa da duka ta ko ina amma ina Sayyid yayi nisa baya jin kira ƙoƙarin sa kawai yaga ya cimma mummunan nufinsa A kan Bintu,duk yabi ya gajiyar da ita har yanzu ya kasa samun dama A kan ta amma hakan baisa ya saduda ba tun kukan ta na fita har ya zamana Muryar ta ta dashe baka iya jiyo sautin ta sosai,sun kai kusan awa ɗaya suna abu ɗaya. Tun da ya dawo ya ci abinci ya shirya,yake jin zuciyarsa na wani irin bugawa,komai yanayin sane cikin sanyin jiki har sai da yasamu ya ɗan yi karatun ƙur'ani kana yaji sanyi a ransa, amma duk da haka ji yayi gaba ɗaya gidan yayi masa zafi,dan haka tun kafin lokacin miting ɗin su yayi ya gama shirinsa tsaf ya zari key ɗin mota ya fita. Duk takun da zaiyi sai yaji bugun zuciyarsa ya ƙaru, yana kusan tar wajen ajiye motocin yana jin jikin sa na wani irin rawa da sanyi tamkar ana zuba masa ƙanƙara, A hankali yasa hannu zai buɗe motar amma sai yaji ya kasa, haka nan zuciyarsa ke sanar dashi da wani mummunan abu na shirin faruwa,to A ina kuma A kan waye? ɗan jim yayi yana sauraren bugun da zuciyarsa keyi,waywayawa yayi yana fuskantar ɓangaren su Sayyid kasan cewar ataɓangaren gurin ajiye motoci ɗakunan su suke,hakanan yaji kamar ana ingaza zuciyar sa da ya shiga ɓangaren, A hankali yake takawa yayin da duk taku ɗaya bugawar zuciyarsa ke tsanan ta,bai tsaya ba har sai da ya dangana da ƙofar ɗakin ɗaya daga cikin samarin,har ya ɗora hannun sa kan mariƙin ƙofar sai kuma yashiga tunanin abinda zai kaishi me zaiyi A wajen idan yashiga mai zaice da mamallakin ɗakin? dan haka zuciyarsa ta umarce sa da barin gurin. Bintu kuwa ta gama yin laushi ta kuma sadaƙar yau ƙarshen rayuwar tane yazo, dan tabbas Sayyid ya ɓata mata rayuwa baƙin cikine zai sa ta haɗiyi zuciya ta mutu,duk yaji mata ciwo ya kuma yayyaga mata kaya,lokacin da hannunsa ya taɓa lallausar fatar jikin Bintu ji yayi ya kuma ruɗewa idanunsa sun riga sun rufe baya sauraren kalaman Bintu na magiya wan da suke shige da waƙe saboda yawan jaddadawa,numfashin ta sai ƙoƙarin kumcewa yake saboda tsananin jigata da wahala da kuma yawan kukan da tasha,wani irin murmushi yayi na ganin yana dab da cimma burin sa. A dai dai lokacin kuma da Abdallah yake ƙoƙarin juyawa dan barin wajen,tamkar mayen ƙarfe haka yaji an fixgi zuciyar sa zuwa ga ɗakin da yake kusa da wanda ya fasa shiga. Yana gab da san cin ma manufarsa yaji tamkar duniyar tana juyawa dashi, yayin da kuma ya kasa tan tan ce duniya da lahira saboda wani irin mummunan naushi da ya bakunci fuskarsa wanda take haƙoran sa guda biyu suka biyo bayan naushin, kafin ya dawo haiyacin sa ya kuma ji anyi sama dashi tamkar ƴar tsana an wurgashi kusuwar ɗakin in da ya faɗo ƙasa tamkar kayan wanki, Abdallah dukan Sayyid ya shigayi tamkar ba ɗan Adam yake duka ba,hatta Bintu da bata hayyacin ta sai da taji tsoron kar Oga Abdallah yaje yay kisa, Sayyid ɗin ma ya daina motsi amma yaƙi daina dukan sa, A hankali ta rarrafa jiri na san yadda ita,tana kusan tar inda yake jiri ya ɗebeta ta tafi luuu, zata faɗi, babu shiri yay wurgi da Sayyid dake hannun sa ya tafi ya tarota, waɗawa tayi jikinsa numfashin ta na ƙoƙarin ɗaukewa,rigarsa ya cire ya rufa mata kana yay mata ɗaukan jarirai yabar ɗakin da ita. Cikin mota ya sakata ya kwantar da ita kana ya shiga ya figi motar da gudu kamar zai tashi sama,har yanzu bayajin yayiwa Sayyid hukuncin da yakamata,zuciyarsa tamkar zata faso ƙirjinsa haka yake ji saboda tsananin ɓacin rai,tabbas ba iya abinda ya kamata yayiwa Sayyid ba kenan dole ne yasa ayi masa horo mafi muni A rayuwar sa wanda sai yaji dama ba A haife shi ba. Da wannan tunanin yazo haɗaɗɗan gidan sa wanda yake A area 2, unguwar kanta abin kallo ce balle kuma gidajen dake cikin ta,guri ya samu yayi pakin bayan sojan mai gadin ya ɓuɗe masa get,buɗe bayan motar yayi ya ciro Bintu da har yanzu bata farfaɗo daga suman wahalar da ta tafi ba,ɗaukar ta yayi A kafaɗarsa ya nufi cikin gidan da ita. Duk kansu A falon ya samesu shi ko kula da motocin su baiyi ba saboda baya cikin nutsuwarsa,gaba ɗaya binsa sukayi da kallo batare da kowannen su ya iya yi masa tambayar dake zuciyar saba,har sai da ya shige ɗakin dake cikin falon da ita, kana suka shiga kallon junansu amma duk da haka basuce komai A junansu ba suna dai jira su gane koma meye dan sun san dai da wuya Oga Abdallah yayi musu bayanin abinda bai shafe su ba. Sai da ya fara shafa mata ruwa ta farfaɗo daga suman da ta tafi, kana ya saka mata ruwa saboda ƙwarin jikinta ya dawo duk da sai da sukayi artabu duk tabi ta cukwikwiye ta wahal dashi kafin ya soka mata allurar ruwan, saida yaga bacci ya ɗauke ta kana ya canja wasu kayan ya fita falo dan tattauna wa da yaran sa, bai ce musu komai akan Bintu ba dama suma basu sa ran zai faɗa ɗin ba,sun tattauna abubuwan da suka shafe su da kuma yadda zasu fuskanci wannan gagarumin yaƙin da suka tasa A gaba, kowa ya bashi ɓangaren da zai fuskanta yayin da ta ɓangaren Alhaji Salisu shima suka canja tsari dan yanzu A maimakon bibiyar Alhaji Salisu zatayi, yanzu Alhaji Sama'ila zata bi dan ƙulla alaƙar soyayya,duk da cewa yasan su Alhaji Nasir basu san da wannan shirin ba tunda daga shi sai Samira sukayi maganar A wan can ranar cikin office dinsa batare da sauran yaran nasa ba,sallamar su yayi batare da yayi musu ƙarin bayani a kan Bintu ba. Nabil ne yazo zai shiga ɗakin sa ya hango Sayyid A sheme kamar matacce da gudu ya ƙarasa cikin ɗakin ya ɗagoshi cikin tashin hankali, ya shiga jijjiga Sayyid da ko motsi baya yi dan kuwa matuƙar buguwa ya bugu,da gudu ya fita bai tsaya ko ina ba sai sashen Dady mansur,kiran da sukaji Nabil ɗin na kwarara musu shi ya fito da su A tuɗe kowa da irin tambayar da ya kewa Nabil, bai tsaya basu bayani ba kawai yaja hannun Dad suka fita yayin da mama ta shiga binsu Abaya cikin tashin hankali, Lokacin da suka ga halin da Sayyid ya ke ciki gaba ɗaya ruɗewa suka kuma yi,dan ita mama ta kasa daurewa kuka ta saka tana faman sanbatun tambayar waye yay mishi haka waya keson kashe mata yaro? haka dai take ta jefo zantuka cikin fitar hayyaci, Dady Mansur kuwa saɓa shi yayi A kafaɗarsa ya nufi wajen mota dashi cikin tashin hankali mara misaltawa duka nufi asibiti. Inno ta shiga ɗakin Bintu yayi sau ashirin, tun tana kasa magana har ta fito da tashin hankalin ta A fili bata san sanda ta fara tambayar su Taufiƙa ko sunga gilmawar Bintu ba,amma duk cikin su babu wanda ya bawa tambayar muhimmanci, saima cewa Taufiƙa tayi inno ki daina neman yariyar nan,dan ba yau ta fara wannan halin ba ke ce dai sai yau kika lura!' wani irin kallon takaici inno tabi Taufiƙa dashi batare da ta iya furta mata komai ba, ta ɗaga wayarta dan ta kira Rahima ta tambaye ta ko suna tare da Bintun. A hankali take buɗe idanunta da sukayi mata nauyi,tun tana ganin dishi dishi har suka buɗe tarwai,wata gigitacciyar ƙara ta saka tana ƙoƙarin fizge ƙarin ruwan dake hannun ta,gaba ɗaya ta fita haiyacin ta, A tsorace take gani take kamar har yanzu tana dakin Sayyid,A hankali ya turo ƙofar ɗakin ya shiga waya saƙale A kunnensa da ga dukkanin alamu da inno yake wayar dan naji ya na cewa ta farka karki damu idan mun dawo zanyi miki bayani!' daga haka ya katse wayar yana mai ɗora mata rikitattun idanun sa masu saukarwa da mutum nutsuwa,aiko take Bintu ta nutsu ta daina ihun da takeyi amma ba ta daina kukan ba,zare mata ruwan yayi kana ya juya da niyar barin gurin,riƙo hannunsa tayi gami da ƙara sakin wani marayan kuka,ɗan tsaiki yayi gami da juyowa A matuƙar fusace dan dama har zuwa lokacin bai gama hucewa ba,cikin tsananin fusata da ɓacin rai yace"meye ne kuma zan miki Ni nakai ki ɗakin nasa da zaki na cikan kunne da ihu?idan da banzo ba me kike tunanin zai faru?duk wannan tsoron naki amma bai hanaki shegen shige shige har sai kin kai kanki inda ake neman rayuwar ki!' cikin kukan tace Ni bani naje ba jana yayi ta ƙarfi ina cikin tafiyana!'ɗan tsuka yayi gami da zare hannun sa daga nata,cikin shagwaɓaɓen kukan nata ta kuma cewa dashi Ni dai yunwa nakeji!'sai ki tashi ki girka!' ya faɗa yana mai kawar da kansa gefe,tura ɗan ƙaramin bakin ta tayi tare da cewa" to ai Ni bani da lafiya!' bai saurareta ba ya fita daga ɗakin,shiru tayi cikin mamakin Al'Amuransa meyasa duk sanda take buƙatar taimako shi yake zuwa ya taimake ta? wani lokaci me kirki wani lokacin kuma akasin haka, tana cikin wannan tunanin har ya dawo hannun sa riƙe da take away miƙa mata yayi, hannu tasa ta karɓa tare da tashi zaune cikin sanyin murya tace" na gode!'bai dai tan ka matan ba ya kuma fita daga ɗakin,baki ta taɓe tare da buɗe take away ɗin ta. Inno ta samu kwanciyar hankali jin Bintun tana tare da Abdallah,sai dai zuciyarta da take tayi mata saƙe saƙe akan bintun, ko me ya faru da marainiyar Allah? ko ma dai meye dole ta ajiye ta barwa safiya. Sayyid kuwa yana can hannun likitoci suna kula dashi yayin da Alhaji Mansur yake Allah Allah Sayyid ɗin ya farka domin yaji uban da yayi masa wannan mummunar rauni har da cire haƙora, tabbas ba zai taɓa yadda ba dole sai ya ɗauki fansa wanda zata kasan ce ta ramuwar gayya. Washe gari Bintu garau ta ta tashi (yarinya taji hannun likitoci,)ko da ta farka banɗaki ta shiga tayi wanka tare da brosh,tana fitowa kuma taci karo da haɗaɗɗiyar doguwar riga A kan gado,dan haka ta shirya A nutse kana ta ɗauki rigar ta saka,masha Allah tubarakalla maƙi gani ya kau da ido tabbas Bintu kyakykyawar yarinya ce ta ajin farko Allah Ubangiji ya hore mata ƙira mai kyau da jan hankali duk sutturar da tasaka sai kaji kamar ka saceta,turarukan da ta gani ta ɗauka ta feshe jikinta dasu kana ta nufi bakin ƙofar da nufin fita,tana ɗora hannun ta kan mariƙin ƙofar, taji ana ƙonƙosawa A hankali,dan haka kawai sai ta ƙara sa buɗewa,wani irin wal hasken fatar sa ya haske mata idanuwa,babu shiri ta shiga rage girman idanuwanta A kan sa,yayi matuƙar kyau cikin shigarsa ta ƙananan kaya fuskar sa sai fitar da wani haske take da kwarjinin sa, ganin ta shirya kawai sai ya juya batare da yace mata komai ba,da sauri ta bi bayansa dan tasan tafiya gida zasuyi maganar ce dai ba zai iya ba saboda tana masa wahala. A can asibiti kuwa Sayyid ya samu farfaɗowa, Dady Mansur kuwa ba tare da wani jinkiri ba yashi ga watsawa ɗan nasa tambayoyi A kan wanda yaso kashe masa shi,gyara zama Sayyid yayi ya shiga sheƙa musu karya abinda ya faru da ban abin da ya faɗa musu da ban, Dady Mansur ya miƙe A matuƙar fusace yace" kai tashi mu tafi gida ai banga ta zama ba,ashe da ɗan ta adda muke rayuwa bamu sani ba!'batare da ya jira sallama ba ya tasa ƙeyarsu sai estate. Kamar tare suke lokaci ɗaya sukayi pakin suka fito gaba ɗayansu,Bintu tana arba da Sayyid kuwa ta zunduma wani uban ihu tare da komawa bayan Abdallah ta ruƙunƙumeshi,so sai fa Bintu ta firgita da ganin Sayyid dan A haƙiƙanin gaskiya ya dasa mata mugun tsoron sa,wani mugun kallo Abdallah ya shiga aika musu gaba ɗayansu kamar yadda Dady Mansur yake auna masa nasa mugun kallon tamkar idanun sa zasu waɗo, A hankali ya juyo da ita gaban sa tare da saka yatsansa guda ya ɗauke mata hawayen da suke ta gudu kan kyakykyawar fuskarta,cikin nutsuwa yace" mata, ke ki nutsu babu abinda zai sameki ina tare da ke!' daga haka ya janyo hannun ta suka wuce su Dady Mansur sake da baki,ɗaga murya yayi yace" Ni ba sa anka bane wannan maganar bazan ƙyale ta ba tunda ba jaki kasamu ba anjima kuzo falon Alhaji Baba kai da kilakin taka!'ko juyowa Abdallah baiyi ba balle yasa ran cewa yaji abinda yace masa,fuuu ya ja hannun Sayyid mama ta mara masa baya. Tunda suka shiga falon babu abinda Taufiƙa ke yi sai kallon hannayen su da suke saƙale dana juna,ji take tamkar ta kashe Bintu kowa ma ya huta, lokaci yayi da ya kamata tayi wani abu akan Soyayyar Abdallah,inno kuwa kasa ɓoye murnar ta tayi, sai da ta rugumo Bintu jikinta tana mai tsananin nuna farin cikin ta,kan ta kai ga cewa wani abu wayar Abdallah tayi ƙara ɗagawa yayi cikin nutsuwa,ɗan jim yayi kana yace" to yanzu zamuzo insha Allah!'kallon inno yayi yace" Alhaji Baba ne yake kiran mu gaba ɗaya!'tace"har dani kenan!'Taufiƙa yaga tana ƙoƙarin miƙewa, batare da ya dubeta ba yace" ban daku"daga haka yay tafiyarsa,inno ta ja hannun Bintu suka nufi part ɗin Alhaji Baba,yayin da su Taufiƙa suka bisu da wani mugun kallo tamkar zasu gaɗo da ƙwayar idanuwan su,Taufiƙa tayi wata ƙwafa mai cike da fassarori. Alƙalamin✍🏽 Fatimah y Adam 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 27 ``` Bayan ALHAJI BALARABE sai matansa da kuma yaransa maza wanda abin ya shafa Dady Mansur sai Dady Habib sai kuma Abba Hassan da bai jima da dawowa daga itali ba, shi kuwa dama Abba Aliyu ba A ƙasar yake ba yana can gana tare da iyalansa,sai dai yana yawan zuwa,sai kuma uban gayya Oga Abdallah da Bintu da Sayyid sai Dady jafar, dukkanin su sun nutsu suna sauraran Alhaji Baba da yafara magana cikin kamilalliyar muryarsa mai cike da hikimar zance,yace" Abdallah muna sauraren ka ka gaya mana abin da Sayyid yayi har kayi masa hukunci!'Dady Mansur da ya kasa jurewa ya ɗan zaburo yace" haba Baba,hukunci ko zalunci? wani kallo Alhaji Baba ya watsa masa wanda babu shiri ya kama bakinsa sai dai sam ransa bai gamsu da wannan salon tambayar ba, Ɗan sunkuyar da kansa Abdallah yayi kana cikin taushin Muryar sa mai daɗin sauraro yace" Alhaji Baba bani ya kamata na fara magana ba wadda abin ya faru akan ta ita zata faɗa mana yadda ko mai ya kasance!'Dady Habib yace"hakane maganarka to ke muna saurarnki!' ya juya maganarsa ga Bintu, cikin sanyin murya da kuma tsoron kallon da Sayyid yake ta aika mata ta buɗe baki tare da basu labarin abinda ya faru har zuwa lokacin da Abdallah yazo ya taimaketa daga hannun Sayyid,runtse idanu Alhaji Baba yayi,kana cikin rawar murya irin ta wanda yake cikin tsananin ɓaci rai yace" A cikin zuriya ta akasamu mazinaci? kaicona rayuwa baki da tabbas yanzu Sayyid kaine kake ƙoƙarin farma yarinya ƙarama marainiyar Allah?shiru yayi gami da sunkuyar da kansa ƙasa wanda shi ƙadai yasan irin takaicin da ke ƙunshe cikin zuciyarsa,Dady Mansur ya miƙe tsaye cikin yanayinsa na hargagi da rashin yin ko mai cikin nutsuwa yace" wallahi baku isah ba,kunyi kaɗan kuyiwa yarona ƙazafi, Sayyid ba mazinaci bane sai dai idan kune mazinata!'wata gigitacciyar tsawa Hajjah tayi masa tare da cewa kai me yasa baka da nutsuwa ne iye Mansur? me yasa kullum girma kake amma hankalinka yana da ɗa komawa na yara?bazaka dinga girmama mahaifinka ba yana magana kanayi duk cikin ƙannen ka gasu nan kaji wani yayi magana yayin da mahaifinsu yake magana? to akul ina yi maka gargaɗi akan wannan banzar ɗabi ar taka idan baka gyara ba zanyi mummunan saɓa maka!' ta dire maganar tana mai watsa masa kallon baƙin ciki,komawa yayi ya zauna dan duk abinsa yana shakkar mahaifiyar tasu tana da san mutane da jansu ajiki amma sam bata yadda da raini ba ko kaɗan bata ɗaukar sa, Tsit falon yayi suna jiran jin ta bakin Alhaji Baba,can dai ya ɗago kansa fuskarsa babu wasa ya dubi inda Sayyid yake a zaune fuska duk A kunbure,yace" Sayyid abinda yarinyar nan ta faɗa hakane?cikin in ina ya fara ƙoƙarin kare kansa,amma hakan bata samu ba saboda mugun kallon da Oga Abdallah ya watsa masa mai cike da gargaɗi,ai Sayyid bai san sanda ya saki baki ya gaskata zan cen Bintu ba, Dady Habib ne ya zuba masa ido cike da mamakin sa, Abba Hassan ma kawar da fuskar sa yayi dan baya son cewa komai saboda halin yayan nasu,inno ce tace"gaskiya Sayyid baka kyauta ba na rasa Abin da Bintu tayi muku kuke neman hana ta zaman lafiya ba, gaskiya banji daɗin wannan abuba!' Hajjah kuwa ƙwafa tayi tare da cewa aini Abdallah baka burgeni ba da har kayi masa dukan da ya tashi A kwana ɗaya, aikamata yayi ace har yanzu bai san inda kansa yake ba!'Hajiya Babba kuwa Bintu take ta kallo yayinda can cikin zuciyarta take wasu irin saƙe saƙe,me yasa ake bin yarinyar nan da sharri ka kala kala ne? anya kuwa babu wani abu aƙasa amma dai zata ci gaba da yiwa Bintu addu'ar kariya, Dady jafar ne ya danyi gyaran murya kana yace"Alhaji Baba kayi haƙuri yaran ne na yanzu sai dai addu'a kawai, babu tsumi ba daabara duk abinda Ubangiji ya rubuto to tabbas babu makawa sai ya faru,yanzu kawai jan kunne za ayiwa shi Sayyid babu shi babu Bintu!'da sauri Sayyid ya matsa gaban Alhaji Baba cikin nuna na damar sa yace" dan Allah kayi haƙuri wallahi ba halina bane sharrin shaidan ne kuma insha Allah hakan baza ta kuma faruwa ba,amma dan Allah ina rokon ku wata alfarma!'duk zuba masa ido sukayi kana Alhaji Baba yace" wace alfarma kake so muyi maka? ƙara matsawa kusa da Alhaji Baba yayi kana ya riƙe hannayen sa duka biyun cikin ƙanƙar da kai yace"alfarmar ita ce ina so a bani auren Bintu!' Shiru falon ya kuma ɗauka baka jin sautin komai sai na bugun zuciyoyi,shi kuwa Sayyid cigaba yayi da cewa dan Allah Alhaji Baba ka auramin ita wallahi santa nakeyi da gaske,zan riƙe maka ita amana ka taimaka ka bani auren ta!'yadda yake maganar babu yadda zakayi ka fahimci ainahin zuciyarsa,dan haka ko Ni ban san me Sayyid yake ciki ba a halin yanzu shin da gaske yake san Bintu yake ko kuma wani salon ne ya fito dashi na daban? wannan dai dole sai mun bibiyi Malam Sayyid tukun zamu sani. Baza ka taɓa fahimtar halin da Oga Abdallah yake ciki ba saboda wannan dama ɗabi'ar sace, ita kuwa Bintu bata da maraba da hoto baƙaramin shock ta shiga ba saboda jin abinda Sayyid yake faɗa, wai anya kuwa ita Bintun yake nufi ko wata ce can daban mai sunanta? nutsuwa tayi ta zubawa bakin Alhaji Baba Ido dan jin abinda zai furta, Alhaji Baba ne yayi gyaran murya kana cikin zubawa Sayyid ɗin ido yace"ka tabbatar abin da kake faɗa har cikin zuciyar ka ne babu wata manufa ko yau dara? cikin sauri Sayyid ya kada kansa tare da cewa hakane har cikin zuciya ta da gaske nake ina sonta kuma zan riƙe ta amana!'wani ƙawa taccen murmushi Alhaji Baba yayi tare da cewa to Alhamdulillah Masha Allah hakan yayi kyau kayi tunani mai kyau Sayyid ka fanshi kanka daga irin mummunan hukuncin da na tanadar maka!' shiru yayi yana bin mutanen falon da kallo sannu A hankali har ya dire idanun sa kan Abdallah da kansa yake sunkuye balle na gwada ƙoƙarina ko zan gano muku halin da yake ciki,har yanzu dai babu wanda ya tanka ko Dady Mansur bai tanka ba tun lokacin da Hajjah ta ƙare mai tanadi,kowa so yake yaji abinda Alhaji Baba zai ce,kamar ya karanci zuciyoyinsu,cikin dattijan taka yace"naji daɗin maganarka Sayyid sai dai nariga nayiwa Bintu miji ɗan lokaci kaɗan nake jira na gabatar musu da juna,duk da ban nemi shawarar ta ba amma nasan faɗima bazata watsan ƙasa A ido ba,bazan baka faɗima ba Sayyid wannan yarinyar bata dace da mutum irin ka ba,sai da na daɗe ina tunanin mijin da ya dace da rayuwarta kafin hankali na ya kai kansa,zasu dace da junan su matuƙar da cewa,dan haka kaje kanemi matarka cikin gidan nan ko wacece zan aura maka ita amma banda faɗima matar tsadadden namiji!' Wani irin ƙawa taccen murmushi ne ya shiga subcewa Hajiya Babba wanda ya fito tun daga ƙarƙashin zuciyarta, kuma ta kasa ɓoye shi kan kyakkyawar fuskarta,inno ma hakan yayi mata daɗi sosai dan ita kam tayi yaƙini cewa Sayyid ƙarya yake tunda tana sane da irin tsanar da sukayiwa Bintun,ta dai fi tunanin wani muguntar yake san shirya mata, Hajjah kuwa ita dariya tayi sosai tare da cewa haba Alhaji duk kasa fargaba ta rufeni dan kalaman ka sun fara nuni da kamar zaka amince da wannan maƙaryacin!'murmushi kawai yayi tare da cewa jafaru kayi shuru bazaka ce komai ba? ɗan muskutawa yayi kana yace"ai Alhaji Baba kaga ma faɗar komai muma abin ikonka ne barantana kuma yaran da muka haifa da kai da kaya duk mallakar wuya ne dan haka babu abinda zance sai fatan Alkhairi!'juyawa yayi ya kalli Dady Mansur da ya cika yayi fam tamkar zai fashe,yace mansur kana da magana ne? gyara zaman sa yayi dama abinda yake jira kenan samun damar magana, cikin gayyatowa kansa nutsuwa yace"nifa Baba Ina ganin gara abawa yaron nan dama tunda har yace"yayi nadama,duk wanda zaka bawa aurenta ai inaga bai kai matsayin Sayyid ba,kuma hakan babban rufin asirine A gareta tun da taimakon ta zaiyi!'Dady Habib yace"haba yaya me yasa baka tauna magana idan zaka faɗeta? ya mahaifin mu ya yanke hukunci amma ka nuna kamar baiyi dai dai ba!'a wannan karon Mansur bai tanka masa ba saboda yaga mugun kallon da Hajjah take aika masa, Alhaji Baba ba tare da yabi takan maganarsa ba yace" suje ya sallame su, Sayyid ta shi yayi yana kun bure kunbure tare da faɗar magana aciki babu wanda ya kula shi,Bintu kam ta riga kowa barin falon dan gani take kamar Alhaji Baba zai iya canja shawara yace ya bawa Sayyid aurenta,abinda bata fatan sa kenan ko da a mafarki ne, Part ɗin sa ya wuce kai tsaye,yana shiga banɗaki ya faɗa ya sakarwa kansa shaya ya jima ruwan yana sauka A kansa kafin yayi wanka ya fito,shirya wa yayi cikin doguwar jallabiya fara ƙal wadda tayi matuƙar dacewa da tsayin sa na ingarma kuma zaki,kwanciya yayi saman gadonsa tare da lumshe idanun sa, shi kansa yanzu ba zaice ga abinda yake damunsa ba bai san halin da zuciyar sa ke ciki a kan wannan lamari ba,dan haka kawai sai ya jawo casbaha ta dannawa ya shiga ambatan Allah, Bintu kam yanzu ta samu nutsuwar zuciyarta dan sam ita A ƙuruciyar ta bata saka maganar Alhaji Baba cikin ranta ba, ita atunanin ta ma yayi hakane dan ya kuɓutar da ita daga tarkon auren jikansa dan haka take jin mutumin har can ƙololuwar ranta,sai kuma mamakin Dady Mansur da ya kasa barinta,wato dai halinsa sak da ɗan sa babu abinda ya rabasu,a wannan lokaci fa tana buƙatar ganin Dije sosai kuma ya kamata tasan abin yi tunkan mutanen nan su cigaba da cutar da ita tare da mamaye ta ta ko ina. A ɗakinsa ya sameta sai sintiri take, yana shigowa ta tare shi cikin sauri tare da cewa Allah yasa dai munyi nasara?kawar da kansa yayi daga kallon ta kana yace"shirin nan baiyi ba Taufiƙa Alhaji Baba ya rufe idonsa yace bazai auramin Bintu ba saboda yayi mata miji!'zaro ido tayi tare da cewa wa ya bata? yarfa hannu yayi alamun bai sani ba,kana ya ɗora da cewa Wallahi Ni dama ina son yarinyar nan ban san ina sonta ba sai da Alhaji Baba yayi wannan furucin na ya bawa wani ita yanzu me kike ganin zamuyi? Taufiƙa taja Ajiyar zuciya tace" ai Ni dama dan kar Ya Abdallah yace yana sonta ne amma tunda Alhaji Baba yayi mata miji bani da matsala yanzu sai yaƙin samo auren sa dan Ni ban damu da sai ya soni ba !'wani mugun kallo ya watsa mata tare da cewa Ni zakiwa butulci makira to yadda ban samu Bintu ba ke ma bazaki taɓa samun Abdallah ba insha Allah!'Sayyid yanzun nan mutuncin dake tsakanin mu zai watse dan aduniya bani da maƙiyi sama da wanda zai shiga tsakanin soyayya ta da Ya Abdallah dan haka kasawa bakinka linzami tun kafin na fito maka da baƙin halina!' tsaki yayi gami da shigewa banɗaki ya barta tsaye tana saƙe saƙen yadda zata ɓullo wa al'amarin. Wayar da Anty Nafisa tayi mata ita ta tuno mata da tashin hankalin da take ciki,wayar na riƙe a hannun ta sai nombar Dije take gwadawa amma taƙi shiga to wai ta yaya zasu shawo kan matsalar nan ba yan basa haɗuwa da Dije? yanzu idan Dije yaudarar ta tayi ya zatayi kenan wa kuma zata tunkara dan ya taimaka mata?hannu tasa ta share hawayen da suke ta tsiyayowa daga idanunta, A fili take cewa fafi ina kake?ban san yaya zanyi ba al'amarin ya wuce duk yadda kake tunani,bazan iya ba,kai ne kace min zaizo ya taimakamin Amma har yanzu bai zo ba,a ina zan samo shi? Allah ka kawo min mafita cikin wannan cakuɗaɗɗen al'amari. Ka in da na in suka shiga bincike A kan su Alhaji Nasir, yayin da Samira har ta samu sa ar kama Alhaji Sama'ila a hannun ta,cikin hikimar su ta ƙwararrun ma aikata masu himma da ƙwazo,acikin kwana biyu suka sami babban cigaba sun sami baya nai masu yawa,kuma suna da tabbacin zasuyi nasara, Abdallah ya gano a kwai wani abu guda da suke san mallakar sa acikin estate ɗin kuma wannan abun ga dukkanin alamu yana da matuƙar muhimmanci a cikin ahlin ALHAJI BALARABE,to abinda yake so ya sani shine meye wannan abun? kuma A gurin wa yake? san nan mallakin waye?yanzu abu mafi mahimmanci dayake son ganowa shine inda mahaifinsa yake da kuma sanin sirrin dakin nan da ainahin abinda ake rigimar akansa,lallai dole ne ya tashi tsaye tun da yanzu ne za a fara wasan,kowa na cikin ESTATE sai yayi bincike a kansa dan ta hanyar ne kawai zai gano annamimai kuma gurbatattun iyalan ALHAJI BALARABE. Inno gaba ɗaya ta kasa gane kan Bintu kwana biyun nan hakanan take kallon ta kamar wadda take cikin matsala,hakan ne yasa ta sameta har ɗakinta ta ritsata da tambaya amma Bintu tayi fur tace" ita babu komai kawai dai yanayi ne, dole haka inno ta rabu da ita tare da binta da addu'a. Acan kuma ɓangaren Abigirl har yanzu tana nan tana jiran dawowar fire,yayin da takasa yin wani kataɓus dan bata da wata hanya ta ganin bayan Abdallah sai haya killers,Bata da damar ko zuwa get ɗin estate din bare ta kaiga shiga ciki,kwata kwata hankalinta ba a kwance yake ba, kullum ta Allah gani take kamar asirinta zai tonu,mutumin nan babu Allah a ransa duk lokacin da ya gano ta ha'inceshi tabbas sai buzunta gara tun bai ankara da Abdallah a duniyar ba ta kashe shi hakan ne kawai zai samar mata da kwanciyar hankali,ko haɗuwa da mijinta ta rage yi saboda tasan zai iya gano sirrin da take ɓoye masa,wayar tace ta fara ƙara ɗagawa tayi da hanzari a tunanin ta ko fire ne ya dawo,sai dai kuma ba haka bane dan wannan lambar ma an ɓoyeta,duk da haka batayi ƙasa a guiwa ba tana sa ran shi ɗin ne,wata mahaukaciyar dariya taji ansakar mata tamkar dodon kunnen ta zai tsage har sai da tayi saurin kawar da wayar daga kunnen nata,a amsa kuwa ta sakata dan bazata iya jurar jin wannan mahaukayar dariyar A cikin kunnen ta ba,ta can ɓangaren akace mata sannu tsohuwar kafura. A dai dai wannan lokacin kuma Daddy jafar yazo zai murɗa mariƙin ƙofar sai kuma ya dakata dan jin dariyar da ke fitowa daga cikin sifikar wayar,badan laɓe ya tsaya ba sai dan yana san gano wani abu game da matar tasa dan dama so yake ya gama kamata dumu dumu kafin ya sanar wa da Abdallah,dan yana matuƙar zarginta barin ma acikin kwana kin nan shi yasa yay matuƙar saka mata ido, Acan cikin ɗaki me wayar ya cigaba da cewa,kin ɗauka zaki iya yau dararmu,ai base kin kasheshi bane Asirinki zai rufu Ni awaje na Asirinki a tone yake,kinyi tunanin ban san me kike ciki ba to babu abin da ban sani ba game da rayuwar da na baki dan ki salwantar da ita amma kika yau dare ni,dan haka kisa ranki a inuwa ina nan tafe gareki dan yanzu ba ta taki nake ba babban aikine agabana!' ɗif aka datse kiran,hannu Abigirl ta ɗora aka zatasa kurwa sai karaf ya buɗe ƙofar ya shiga. Kallo yake binta dashi sai dai bai nuna mata yaji wayar da sukayi ba,cikin hikimarsa ta cikakken ɗan sanda wanda ba kowane yasan da hakan ba da gashi sai ɗan sa Abdallah,yace"lafiyar ki kuwa naga kamar zakiyi kuka, ko da wata matsalane?cikin ajiye wani wahalallan numfashi tace" dama mutuwa akayi mana A can garin mu yanzu zan shirya na tafi!' ta faɗa tana miƙewa ko ina nata rawa yakeyi saboda ruɗewa da tashin hankali, Dady jafar yace" to ai sai mu tafi tare nima na tarar da jana iza!'wata zabura ta kumayi kunsan dai yadda al'amarin su yake sam babu nutsuwa, a'a kabari zan je Ni kadai baza A bar gidan babu kowa ba!' ka faɗa ya ɗage cikin ransa yana cewa duk inda kikaje zaki dawo kitarar da tuhumar ɗanki Oga Abdallah,a fili kuma yace" shike nan amma gobe zaki dawo ko? cikin rashin san doguwar magana ta amsa masa da A,fita yayi dan yaga gaba ɗaya bata cikin hayyacinta. Gaba ɗaya tunanin sa ya tafi akan da wa Abigirl take waya me ta ƙulla dayake shirin komawa kanta? wa kuma take san kashewa? tabbas waɗan nan amsoshin suna gurin Abigirl kuma da sannu zata tono su da kanta da bakinta. Kwata kwata Oga Abdallah bashi da hutu yanzu,ka'in da na'in ya shiga zurfafa bincike A kan ahlin nasa, sai dai wani abu guda da yake tunani bai wuce yadda zai nemi karin bayani daga gurin Bintu ba,dan yayi yaƙinin cewa yarinyar ta san abubuwa da yawa wanda shi bai sani ba,to amma ta yaya zai saka yarinyar mutane cikin irin wannan haɗarin,anya idan yayi haka bai zalunci rayuwar ta ba bayan itama da tata matsalar ta ƴan iskan yaran gidan,to amma fa dole bashi da wata mafita sai hakan domin Bintu ita kaɗai ce zata iya keta ɗakin nan,furzar da iska yayi daga bakinsa ya zaiyi wannan ita kaɗai ce mafita agareshi amma dolene ya ɗauki matakin kare rayuwarta duk da cewa yasan Allah ne me rayuwar,amma ko mai yana da sanadi,dan haka zai jarraba. Kiran da yasamu daga Alhaji Baba shi ya katse masa dogon tunanin da yayi zurfi acikin sa,cikin takunsa na ƙasaita yayi sallama A falon Alhaji Baba,mamakine ya kamashi ganin Dady jafar da sauran yaran Alhaji Baba wanda sukayi wan can zaman dasu, sai kuma ƙarin Taufiƙa da aka samu,gai dasu yayi cikin girmamawa,kana ya samu guri ya zauna, Taufiƙa kuwa tamkar zata cinye shi saboda kallo, ga kuma farin cikin da take ciki kasan cewar itace Ummul aba'isin haɗa wannan taron. Abinda ya faru shine Taufiƙa ta gama yankewa kanta shawara akan tazo tasamu Alhaji Baba ta sanar dashi tana san Ya Abdallah tunda ta ga haɗa aure yake, ita dai ya haɗa ta dashi matsayin mijinta,Alhaji Baba murmushi kawai yayi tare da ɗaga waya yakira duk wanda suka san wan can zaman na Sayyid,farinciki ne fal ranta dan tasan tunda haka ta faru kamar ta samu Abdallah ta gama,kiran Bintu bai dame ta ba tunda tasan itama zai sanar da ita wanda ya zaɓa matane. Gyaran murya Alhaji Baba yayi kana yasa Abba Hassan ya buɗe taro da addu'a,bayan sun shafa ya kuma yin gyaran murya kana yace" nasan zakuyi mamakin kiran ku da nayi cikin gaggawa,to amma ta wani ɓangaren ba abin mamaki bane idan mukayi la'akari da cewa abu yana iya taso mana batare da mun shirya masa ba,dan haka yanzu ma abinda ya faru kenan, ina so nasanar daku zan haɗa auren Taufiƙa da.... Muje nest page Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 28 ``` Da Sayyid ko bayan raina na bar wannan wasiyyar!'wani irin kallo Taufiƙa take bin Alhaji Baba dashi,maƙoshin ta kuwa ya bushe ƙamas da ƙyar take iya haɗiyar yawu,maganar da yaci gaba dayi ce ta kuma sawa take tashiga wani irin tari me ƙarfi,yayin da Alhaji Baba yaci gaba da cewa, Bintu kuwa zan bada aurenta ga Abdallah, mutanen da suka shiga shock akan maganar nan ta Alhaji Baba suna da yawa,kamar dirar mikiya haka sukaji saukar zancen yayin da Bintu ta shiga matuƙar ruɗani da mamakin wannan haɗin na Alhaji Baba ta ya wannan haɗin zaiyi dai dai? Alhaji Baba bai san irin masifar da yasakata ba, yanzu ji take har ta gwammaci auren Sayyid ɗin, A hankali ta maida dubanta kan uban gayyar, kansa A ƙasa yake bata fahimci ko mai a yanayin saba amma ta tabbatar a yanzu jiyake kamar yayi aman zuciyarsa, Alhaji Baba ne yaci gaba da cewa, wannan haɗin yayi min har cikin zuciya ta Abdallah kai kaɗai nake buƙatar jin ta bakin ka!'cikin nutsuwarsa da ba ta yadda za ai ka fuskanci halin da yake ciki,yace"Alhaji Baba ni bani da ja akan umarnin ka kai naka faɗa ne Ni kuma cikawa ce tawa,dan haka na amince da umarnin ka!'shiru falon ya ɗauka na wasu ƴan daƙiƙa kana Alhaji Baba yace"to masha Allah Allah yayi muku albarka baki ɗaya Batula ke kuma fa ko kina da abun cewa? da sauri ta gyaɗa kanta,yace to me kike buƙata?cikin tsan tsan biyayya da kawaici tace"Baba dama Anty Taufiƙa ce take son sa, Ni kuma na amince ka haɗani da Sayyid ɗin!'tunda aka fara maganar nan banga Abdallah ya kalli ɓangaren da Bintu take ba sai yanzu,amma cikin sakanni har ya janye fuskar sa ba tare da kowa ya ankara da hakan ba, Alhaji Baba yace"a'a Bintu ke Allah ya bawa itama ga wanda Allah ya bata nan!' ya nuna Sayyid da shi kam ko ajikin sa zan iya cewa laba asa a haka yanayin sa yake,cikin wani irin kuka na fitar hayyaci Taufiƙa ta shiga yiwa Alhaji Baba magiya da rokon ya warware haɗin ta da Sayyid amma ina ko saurarenta baiyi ba,inno ce ta daka mata tsawa tare da cewa ke kam wai Taufiƙa wace irin macece haka mara aji da kunya?to tashi maza kibawa mutane waje idan an kaiki gidan Sayyid ɗin kiyi duk abinda kika ga ya dace da rayuwarki shashashar banza da ta wofi!'Dady Mansur ne ya tashi fuu ya fita yayin da duk suka bishi da kallo,Dady Habib ne ya kalli Alhaji Baba tare da cewa Baba yaushe akasa ranar auren? kai tsaye Alhaji Baba yace"sati me zuwa in Allah ya kaimu!'daga nan su Hajiya Babba suka saka albarka sukayi addu'a kowa ya watse, Tunda ta shiga ɗakinta take kuka wanda ita kanta tasan na tsorone yaza ayi ace wai Oga Abdallah shine wanda zata aura, har yanzu gani take kamar A cikin mafarki to ya zatayi da nauyin da yake kanta? tabbas tasan akwai ƙura ga Anty Hauwa'u ma da bata nan idan ta dawo tasan kashe ta zasu haɗu suyi kawai, wannan tunanin ne ya hana ta sakat duk tabi tayi sanyi, Watsi take yi da duk abinda yazo hannun ta, Siddiqa sai haƙuri take bata amma tamkar tunzura ta takeyi cewa take wallahi sai naga bayan yarinyar nan sai dai duk kowa ya rasa,tsinanniyar yarinya ƴar mitsiyata almajira macijiyar sari ka noƙe wallahi bazan ƙyale ta ba kai kuma Sayyid ko dame kake taƙama bazan aureka ba,idan kuwa hakan ta faru sai na kasheshi na kashe kaina kowa ya huta!'Siddiqa ce ta kama ta da ƙyar tana cewa zama zakiyi munemi mafita ba wai kizo kinayi mana hauka ba, dan wannan abin da kike bashine zai rage miki raɗaɗin dake cikin zuciyar ki ba!'da wannan kalamin ta samu kan Taufiƙa ta nutsu tana maida ajiyar zuciya. Cikin tashin hankali Hajiya ladidi ta tashi daga kashin geɗen da tayi tare da ƙara manna wayar akunnenta tace"aure kuma wani irin aure? Nafisa kina cikin hankalin ki kuwa yaza ayi maganar auren Zahra batare da sanin mu ba?ji tayi daga bayan ta Alhaji munir yace" Ni ai nasani kece dai baki sani ba!'kashe wayar tayi da sauri tare da juyawa tana fuskantar sa,tace"amma dai ko gayamin ayi ko ba dan neman amincewa ta ba tunda nasan ban isa ba!'Alhaji munir yayi dariya tare da cewa to yanzu baga shi kin sani ba,miƙewa tayi ta bar falon, Tana shiga ɗakinta ta danna masa kira bugu ɗaya ana biyu ya ɗauka, dariya kawai taji yasa tare da cewa nasan komai akan zan cen auren, ina so ki cire hannun ki daga kan wannan yaƙin dan yanzu yaƙin ya dawo na cikin gida ki zuba ido kiyi kallo yanzu wasan zai fara!'ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa yauwa har naji sanyi da hankalina ya tashi saboda ban san yadda zaka ɗauki maganar ba!'yace"kar ki damu ai hakan shine dai dai agurin mu!'daga haka suka katse kiran,Hajiya ladidi tace"wayyo Zahra inaji ajikina kece zaki zama silar warwarewar matsalolin mu. Ta mai maita saƙon Anty Nafisa ya kai sau goma,ta kuma karantawa A karo na sha ɗaya, Bintu har yanzu banji amsarki ba lokaci yana ƙurar mun kiyi gaggawar yiwa kanki da rayuwar ki sulhu bana son ki ƙara kwana uku ba tare da kin bani sakamakon buƙata ta ba!'share gumin da yake ta tsatstsafo mata tayi, kana ta samu guri ta zauna tare da zuba tagumi,matsalolin da suka sakata gaba sun fara neman zautar da ƙwaƙwalwar ta domin yanzu babu wani tunani dayake shiga yake fita A kan ta ko mai yatsaya mata cak,ji take kamar ta zauna tayi ta zunduma ihu,duk wata dabara ta ƙwace mata, Rahima ta zubawa Hajiya Babba ido tana sauraran labarin da take bata wanda take jinsa kamar alamara, wai Bintu da Ya Abdallah aure, kai ita zata iya cewa ma ta daɗe bata ji zancen da yayi mata daɗi kamar wannan ba,tace"Hajiya Babba wai wane irin ƙauna kikewa Bintu ne?kai tsaye tace"mata irin wannan ƙaunar da nakewa jikokina mafi soyuwa A zuciyata!'dariya Rahima tayi tare da cewa, gaskiya keda Inno ban san wanda yafi wani ƙaunar Bintu ba,sai dai kuma dukkan ku Alhaji Baba yafiku san Bintu!'hararar wasa tayi mata, tare da cewa ai shi ta huɗu yake nema ba dole yafi mu santa ba,amma mu kuma kishiyoyine kar ki manta,Rahima tace"lallai kam Hajjah ce kawai take kishi da Bintu dan dama duk tafiku kishi!'Hajiya Babba ta riƙe baki tana kallon Rahima cike da mamaki na gaske wai har ta fahimci Hajjah ta fisu kishi kai yaran yanzu sai abarsu. Ji tayi kawai an rufeta da duka ta ko'ina ta kasa kare kanta saboda shammatar da sukayi mata,Taufiƙa cewa take wallahi ko za'a kashe Ni sai na huce baƙin ciki na najiya akanki wannan somin taɓine na bijirewa magana ta da kikayi, sauran mataki yana gaba saikinyi namar zuwanki cikin ahlin mu saina gurgunta rayuwarki kin zama abin tausayi a idanun masu imani!'kuka take sosai Bintu dan wallahi tana buguwa,da gudu inno ta shiga kiching ɗin tare da salallami tace"amma wallahi yaran nan baku da imani uban me tayi muku zaku kashe ta?anya kuwa wannan mummunar ɗabi'ar da kuka ɗauka zata kaiku ga cin nasarar rayuwa? gaskiya ina tausaya muku nan gaba domin da hannun ku zaku shuke abinda kuka girba!'ta janyo hannun Bintu suka fita daga kiching ɗin,tana mai jaddada musu Allah saiya sakawa Bintun,ko ajikinsu dan wata uwar harara da suke ta bankawa Bintun kamar idanunsu zasu faɗo.. Bintu fa ta shiga cikin matsatsi da takurar Anty Nafisa,duk inda tayi motsi sai taji ƙarar saƙonta ya shigo mata har wata ƴar rama tayi, kana ganinta kasan tana cikin damuwa ga damuwar su Taufiƙa dan ma Rahima tana taka musu birki to yanzu Rahiman ma ba ƙyaleta sukai ba. Sunkuye take tana saka zanin gado a danƙareren gadon Oga Abdallah,jitayi wayarta na zumm zumm da sauri ta ɗauko ta buɗe saƙon Anty Nafisa ne kamar yadda ta canja salo har da barazana yanzu take aikomata, zubawa wayar ido tayi tamkar A cikinsa zata samo mafita,ya jima tsaye A bayanta duk da bai samu ganin saƙon ba amma yaci nasarar ganin sunan Anty Nafisa saman saƙon,ji tayi kawai anzare wayar daga hannunta,wata irin zabura tayi ta juya,tuni idanunta suka shige cikin nasa take kuwa jikinta yashiga rawa tamkar wadda ake kaɗawa ganga, idanunta har sun kawo ruwan hawaye tunda dama A kusa take,cikin rawar murya tace"dan Allah kabani wayana!'ko kallon inda take baiyi ba yaci gaba da sabgar gaban sa takalmin sa na motsa jiki ya shiga kuncewa, Bintu kuwa magiya har da kuka amma yayi funfurus,ƙarshe ma banɗaki ya shiga ya barta da tashin hankalin ta,ƙarshen zance ma dai tana kallo yasa wayar gaban aljihunsa ya fita da ita batare da ya kula ta ba,zama tayi taci kukanta kana ta koma ɗakinta. Dady jafar yace"Abdallah ya kamata mu fara zurfafa binciken mu akan Dadinku Mansur,dan gaskiya al'amarinsa akwai ayar tambaya,ko ya ka gani?ɗan kashin giɗa yayi jikin haɗaɗɗiyar kujerar sa kana cikin miskilar maganar sa yace"Dady ta manyan muke yanzu, ba tashi ba,nuna masa wayar da ya karɓa A hannun Bintu yayi tare da cewa wannan wayar zata temaka mana wajen samun abinda muke san sani, duk da ban binciki wayar ba me wayar nake san bincika domin iya waya baza ta gamsar damu komai ba!'Dady jafar yace"Abdallah dole kacire duk wani tunani A ranka game da yarinyar nan ka sako mana ita cikin al'amarin nan,kaga yanzu kana da iko A kan ta tunda ta kusa zama matarka nan da ƴan kwanaki!'ɗan lumshe idanunsa yayi kana ya fara da cewa, Dady nifa yarinyar nan zan aureta ne kawai saboda kariya ga haɗarin da nake san sakota aciki dan haka da komai ya dai-daita nan da wani ɗan lokaci zan rabu da ita ta samu mijin da yakeso ta aura idan ma Sayyid ɗin ne Ni zan tsaya mata ta aureshi tunda kaga saboda tana sonsa har Alhaji Baba takewa gaddama shine kuma zata haɗa shirinta dani ya ɗan ja tsuka tare da cewa dan haka ka daina yimin batun ta maras kunya kawai!'Dady jafar murmushi yayi tare da cewa to shike nan idan lokacin yayi ko Ni da kaina zan ne mawa Sayyid aurenta dan shine halaccin da zamu iya yimata bayan ta tai maka mana!'miƙewa yayi yana tattaro takardunsa ko yanzun ma zaka iya bashi ita!'daga haka ya fita ya bar Dadin A cikin office ɗin, murmushi Dady jafar yayi sosai tare da cewa Allah ya nunamin wannan rana. Wasan ɓuya sukeyi domin ta riga tasan yagama bincika wayarta hankalin ta tashe yake tasan kashin ta ya bushe a wajen Oga Abdallah,shiyasa duk hanyar da tasan zasu haɗu taƙi bi acikin kwana guda,shi kansa ya fahimci haka amma ya riga ya gama shirin sa na kamata A hannu duk wannan gudun da takeyi sai dai idan bai shirya kamata ba. Bintuna ki kwantar da hankalin ki ki natare da mai taimakon tsanin ki kuma mai tallafar rayuwarki,kuma muna nan araye Ni da mamanki gaskiya ce kawai zata baiyana mu ki dage da addu'a al'amarin gidan nan bai fi ƙarfin ƙudurar Allah ba,dan haka ina mai sanar dake ki cire tsoro ki tunkari matsalar ki,babu wanda ya isa yaga bayan rayuwarki sai lokacin ki yayi, wannan dai dayake taimaka miki cikin dukkanin matsalar da kika shiga shi zai cigaba da taimakon ki tare da taimakon Allah buwayi gagara misali,akwai ƙalubale a gaban ki Bintu karki wasa da addu'a Allah ya cigaba da taimakonki ya kuma kareki daga sharrin su!'zufa ce ta shiga keto mata buɗe idanunta tayi daga mafarkin da tayi da fafin ta tare da ambatan sunan Allah,a hankali maganganun da fafin yayi mata suka dunga dawowa cikin kunnuwanta,to me fafi yake nufi shine wa?waye wanda yake taimakonta?miƙewa tayi daga saman gadon cikin zurfafa tunani, Oga Abdallah kenan fafi yake nufi shine wanda yake yawan gaya mata zai zo dan tallafa mata?to ya akayi suka kasan ce guri ɗaya? Ƙudurar Allah kenan,duk abinda nake nema sai ya kasan ce yana tare dani kai masha Allah da ƘUDURARSA da kuma dogara dashi tabbas wanda ya maida lamuransa ga Allah zai ta ganin dai dai arayuwarsa, Allah kaine abin godiya,sai dai kuma tunani da ya sare mata gwiwa bai wuce wayar ta dake hannun sa ba,idan yaga saƙonnin dake ciki zai ɗora mata mummunan zargi,ko dai gaya masa zatayi?to kuma idan yaƙi yadda fa?tashi tayi kawai ta ɗauro alwala dan miƙa kukanta ga jallah wa'azza. Jinta tayi sawai saboda kusan kwana da tayi tana miƙa kukanta gurin Allah assamadu,shi yasa taji ƙuncin dake ranta duk babu ta tattara komai ta barwa Allah tasan zai kawo mata mafita mai kyau arayuwarta,cikin ƙanƙanin lokaci ta gama shiryawa ogan nata kayan karin kumallo wainar masa tayi masa wadda tayi matuƙar kyau da laushi sai kunun tsamiya da suyar chips da ƙwai ta haɗa masa ruwan liptom,kana taje ta shirya komai cikin nutsuwa, cikin ɗakin ta shiga ta fara da wanke toilet,sannan ta gyara ɗakin kan kace meye ya ɗauki ƙamshi da haske tsaftar Bintu ta musamman ce saboda bata da ƙwuya ko mai a nutse take yinsa shi yasa zaka ga komai tsaf bata barin datti ko ta allura ce, shiyasa duk ƙaƙalen Abdallah bai taɓa ganin kuskure a tsaftar Bintu ba,ya riga ya yadda da ita ta wannan ɓangaren ya bata maki ɗari bisa ɗari,ɗan dube dube ta fara so take ta gani ko zata ga inda ya ajiye wayar ta, har su ƙarƙashin gado sai da ta duba duk da gyaran ta har nan bata bari ba,me kike nema? taji muryarsa daga bayanta da sauri ta ɗago tana rarraba manyan idanuwan ta masu tamkar zaiba, tashi tayi tana son barin ɗakin,jingina yayi da ƙofar alamun dai ba zai bata hanya ba,tura ɗan ƙaramin bakinta tayi tare da cewa sharewa nayi!'ɗan ƙara girman idanunsa yayi akan ta batare da yace mata komai ba sannan kuma bai bata hanya ba,ɗan matsawa tayi daf dashi tace" zan tafi inno tana jirana!'saurin sunkuyar da kanta tayi saboda kaifin idanunsa,gaba ɗaya jikinta ya fara rawa saboda kusancin su yanayin da take shiga da zarar sun fara musayar numfashi shi yake ƙara yawa har wani sanyi takeji can cikin ƙashi da ɓargonta, da ta rasa mafitar ta tatserewa shu'uman idanunsa kawai sai ta fara sana ar tata,ɗan ɗage gira yayi yana ƙara zurfafa duban sa akanta,kana kuma ya taɓe bakinsa tare da cewa ke gyare sarkin kuka,tambayar ki nayi fa,cikin sangar tacciyar murya tace"to wuce wa zanyi!'bata hanya yayi batare da ya kuma tanka mata ba,da gudu ta fita,batare da ko waiwaye ba,jinjina kansa yayi tare da cewa lokacin kamaki ne baiyi ba. Sai da taga fitar sa kana ta koma ɗakin cikin sauri ta shiga dubawa, cikin Sa'a kuwa tayi karo da wayar ga alamu ma manta ta yayi,ɗauka tayi ta koma ɗakinta,lambar Dije ta fara gwadawa cikin sa ar datake da ita yau, wayar ta shiga,haba mama Dije hankalina ya tashi da rashin jinki gashi bani da wata hanyar da zan ganki!' cikin nutsuwa Dije tace"Bintu muna cikin masifa matar nan ta fara ganewa muna ƙulla wani abu Ni dake, Bintu rayuwar ƴaƴana nakeji shiyasa kika ga na ƙulle hanyar haɗuwa dake!'cikin tashin hankali Bintu tace"yanzu kina nufin kin karya alƙawarin da kikayi min? Dije taja wani sheshsheƙa tare da goge zufar dake sauko mata kana tace"Bintu ban karya ba kuma bazan karya ba,ina daiyin ta katsantsan ne saboda rayuwar marayun Allah, wannan matar shu'uma ce Bintu ta iya takunta, yanzu abinda nakeso na gano shine wai shin acikin gidan nan take zaune ko kuma daga cikin ahlinsa ne wanda basa zaune a gidan nan? daga nan zamu san yadda zamuyi mugano abinda suke wannan san zuciyar akansa dan tabbas a kwai wani abu daya dan ganci dukiya me razana zuciyar mutum a cikin estate ɗin nan!'jin kamar za a shigo ɗakin dan ta manta ba tasa key ba yasa tace"to shike nan mama duk abinda ake ciki ki kirani!'tayi saurin kashe wayar tare da cusa ta cikin zanin ta. Da wuri ta gama girkinta ta kai ta jera saboda bata san su haɗu da Oga dan tasan ita mai laifice A gurinsa,haka kawai take jin faɗuwar gaba jikinta duk a san yaye yake,shiyasa ko da Rahima tazo suka zauna A falon inno kasa gane mata tayi,tace"Bintu wai ko baki da lafiya ne duk na ganki wani iri? cikin faɗuwar gaban dake ƙara kusan tarta tace"wallahi Rahima kaina ne tun ɗazu yake sarawa kamar zai rabe biyu!'ayya sorry bari na kama maki sai kije kisha magani!'kama mata kan tayi kana ta miƙe tare da cewa bari na wuce sai Allah ya kaimu gobe!'Bintu tace"ki gaida min da Ammi na gode,daga haka sukayi sallama,zama tayi A falon ta kasa tashi har su Taufiƙa suka sameta,basu ce mata komai ba suka wuce ɗakin su, Sayyid ne ya shigo yana ganin Bintu ya fara washe mata baki zama yayi kujerar dake fuskantar ta ya shiga yi mata surutai bata tanka masa ba dan ita kaɗai tasan halin da take ciki,a haka Oga Abdallah ya shigo ya same su bai kalli inda suke ba ya wuce part ɗinsa,yana shiga ko ɗakin bai ƙara sa ba ya wuce dining dan wata muguwar yunwa ya dawo da ita,savin kansa yayi ya fara cin haɗaɗɗen tuwan farar shinkafa da miyar ɗanyen kubewa wanda taji ragargajejjen naman kaza sai ƙamshin daɗi takeyi. Acan falo kuma Bintu ta gaji da surutun Sayyid tashi tayi ta barshi ba tare da ta tanka masa ba tun zamansa,sai da ta shige kana ya ankara da wayar ta ɗauka yayi da niyar miƙa mata saƙon dayaga ya shigo wayar ne ya saka shi da katawa tare da zaro idanu cikin tashin hankali da firgici... Bintu kuwa tana shiga ta wuce wajen taga ta ɗaga labulen,dan samun iska ko zataji sanyi,takarda ta gani saƙale ajikin tagar da sauri ta ɗaga tare da warwareta,innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un da gudu ta fito daga ɗakin cikin tsananin tashin hankali... Turƙashi wani kaya sai amale,wane saƙo Sayyid ya gani A wayar Bintu?me saƙon wasiƙar Bintu ya ƙunsa da ya tayar mata da hankali haka?wane tashin hankali ne yake shirin faruwa da Bintu da har take jin faɗuwar gaba? amsar na cikin nest page insha Allah Alƙalamin✍🏽 Fatima y Adam More comment..... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 29 ``` Karo sukayi da Sayyid sauri tayi ta ɓoye takarda hannun ta tare da yagata ƙananu, bin yagaggiyar wasikar yayi da kallo,kana cikin sanyin jiki ya miƙa mata wayar tare da wani irin kallo na tsantsan tuhuma,karɓar wayar tayi hannun ta na rawa,da sauri ta wuce shi bata re da ta tsaya duba wayar ba. Paper da ta zubar ya tsaya ya tattara duk da bazai fahimci komai aciki ba haka yayi gaba dasu batare da nasan abinda zaiyi dasu ba. Da gudu ta ƙara sa ta tankoɓe hannun sa dayake shirin kai wa bakinsa, kallon ta yake cike da mamaki,ita kuma abincin tabi da idanu,cikin wani irin tashin hankali da ruɗani tace"kaci abincin? cikin mamakinta yace" ke meye hak...murɗawar da cikin sa yayi shi ya hanashi ƙara sa tambayar da yaso yi mata,ƙara riƙe cikin yayi cikin jin matsanan cin ciwo, Bintu wani irin kuka tasaka mai tsuma zuciya,kafin ta ankara Abdallah ya faɗo daga kan kujerar dayake kai yana wani irin juyi na tsananin azaba,riƙe shi tayi tana cigaba da kuka cikin matsanancin kuka tace"wayyo Allah na shiga uku yazanyi da rayuwata Ni Bintu wa zai fitar dani daga wannan mugun zarge?Allah kafitar da Ni banji ba bangani ba,bani da laifin komai ga bawanka da baiyi wa kowa laifi ba suna san ganin bayansa me yasa kuke san kasheshi me yayi muku? saboda tashin hankalin da take ciki har bata san lokacin da suka baiyana a falon ba Dady Habib ne yayi saurin cicciɓar Abdallah yana cewa maza muje asibiti Yakamata mu fara kaishi kar gubar tafara aiki har tayi ajalin sa!'Dady Mansur yace"kuje Ni ina nan saboda na kira police,inno kuwa dasu Taufiƙa harda Hauwa'u da bata jima da dawowa gidan ba,Dady jafar da Dady Habib ne suka tafi dashi asibiti, Bintu kuwa gaba ɗaya kukan ma ta neme shi ta rasa, sai yaune ta tabbatar ashe duk kukan da takeyi abaya na rahmane ashe kukan ma akwai ranar nemansa? Alhaji Baba ta kalla da tunda ya shigo ya zauna ya sunkuyar da kansa ƙasa,baice uffan ba,Hajiya Babba kuwa cikin nutsuwa ta ƙarasa kusa da Bintu ta dafa kafaɗarta wanda sai alokacin Bintu ta kula da ita,tace"Bintu gaya mana abinda ya faru kinji? ki kwantar da hankalin ki!' Dady Mansur yace"haba Hajiyarmu ai ba anan zata amsa tambayoyin ba sai taje can police station tukun dan mu baza ta gaya mana gaskiya ba!'Hajjah tace" kai bana san shashanci,ka bari yarinya tayi mana bayanin abinda ya faru kafin zartar da ko wane irin hukunci!'Hajjah ce tai mata magana a wannan karon cikin taushin lafazi tace"Bintu,gaya mana abinda ya faru? rawar murya ta farayi saboda ita bata san me zata ce ba,amma dai kawai zata faɗa musu gaskiya duk da dai tasan Allah ne kawai zai ƙwaceta daga wannan mummunar zargi,cikin tashin hankali tace" wallahi ban san komai ba Hajjah ɗakina na shiga na tarar an ajiye min wasiƙa,da na duba wasikar sai naga an rubuta an saka guba A cikin abincin Abdallah wallahi shine na fito da gudu dan nazo naga ko baici abin cin ba na zubar shine na haɗu da Sayyid ya bani wayata!'Dady Mansur yace"to lauya munji wannan ƙaryar shi kuma saƙon da Sayyid ya gani anturo miki fa? cikin mamaki tace" wane saƙo Ni ba wani saƙo da aka turan,(sanadin karbar wayarta da Abdallah yayi sai tayi tunanin tunda haka ta fara faruwa gudun tsautsayi gara ta goge duk wani saƙo dake cikin wayar,shi yasa Sayyid bai ga ko wane saƙo ba sai wanda aka turo A lokacin kuma da ɓoyayyar nomban)Bintu tayi mamaki ƙwarai dan bata san ta bar wani saƙo a wayar ba, Sayyid ɗin ne yace"Hajjah A karɓi wayarta a duba in dai bata goge ba za A ga saƙon wallahi ba sharri nayi mata ba!'Hajiya Babba ce ta karɓi wayar da kanta kana ta lalubo saƙon wan da bata sha wahalar ganin sa ba saboda dama Sayyid bai fita daga kan enbox ɗin ba,ga abinda saƙon ya ƙunsa Bintu kin tabbatar kin zuba masa gubar nan? bana so yau Abdallah ya kwana a duniya,shike nan abin da aka rubuta,wani irin juwa da layi Bintu ta shiga yi kan ka ce me sai gata yaraf aƙasa babu alamun numfashi,Abin mamaki babu wanda yayi ƙoƙarin tallafawa Bintu saboda dukkanin su sun shiga shock da jin wannan al'amari mai girma,wayar Dady Mansur ce tayi ringin ɗagawa yayi tare da cewa to to gamu muna ciki bari nasa a shigo daku!'kashe wayar yayi yana cewa maza jeka Sayyid kashigo da inspector lawan,da sauri ya fita dan shigowa dasu har zuwa yanzu babu wanda aka samu d yayi wani abu kan suman da Bintu tayi, Alhaji Baba ne ya miƙe tare da fita daga falon,har haɗa hanya yake kamar zai faɗi saboda har yanzu baya cikin nutsuwarsa, Siddiqa ce tayi saurin kamashi dan ta taimaka masa ita ta raka shi har part ɗinsa, Sai da su inspector lawan suka shigo kana Dady Mansur ya ɗauki ruwa ya sheƙawa Bintu A fuska, ajiyar zuciya ta saki kana ta buɗe idanunta da sukayi mata nauyi, Dady Mansur yace"to gata nan ku tafi da ita na gaya maka kisan kai take ƙoƙarin yi yanzu dai yaron yana asibiti bamu san halin da yake ciki ba duk abinda ya kamata zakuji daga baya!'wata ƴar sanda ce ta ƙara sa kusa da Bintu tare da kama hannun ta,batare da wata gaddama ba Bintu ta bita saboda tariga tasan bata da sauran kalamin kare kai ko da da akwai ma baza su yadda ba,suna kallo aka tafi da Bintu ba tare da sun iya dakatar wa ba,jiki A saɓule suka fita daga falon zuciyoyinsu cike da tunanika iri-iri. Tunda suka kaita suka rufe babu wanda ya ƙara bi ta kanta,saboda baza a fara taɓa fayal ɗin ta ba har sai anji sakamakon lafiyar Abdallah tunda su dai yanzu sun tabbatar Bintu mai laifi ce,ƙarewa gurin kallo tayi wai yau itace akarufe cikin magarƙama yanzu gaba ɗaya tunanin ta yana wajen san sanin halin da Oga Abdallah yake ciki, wani irin tsorone yake kamata idan ta tuna Abdallah zai iya mutuwa,ba kuma wai dan za'a kasheta ba kawai shiɗin ne bata san yabar duniyar yanzu,to wai waye yake san ganin bayan ta ita da Oga Abdallah shi waye acikin gidan? A cikin mutanen da suke nuna mata tsana bazata iya cewa ga wanda zai aikata haka A garetaba idan tayi duba da cewa wannan karon Abdallah suke so su kashe,to ko Anty Nafisa ce'zatayi mata haka saboda taƙi karɓar tayin ta? Anya kuwa itace? mugayen gidan nan fa suna da yawa ga hajiyar Dije ma da babu wanda yasan ta,ko ita ma zata iya aikata haka,to kuma waye ya kawo mata paper ya Ajiye dan ta gani? dafe kanta tayi saboda matsanancin sarawar da yake mata bata san wazata ɗorawa wannan alhakin ba zata iya zargin wanda bashi bane kamata yayi kawai ta barwa Allah shi zai saukar da ƙudurar sa da girman ikonsa kuma shi zai kawo mata ɗauki,tayi yaƙini wannan duk jarrabawa ce A gareta dan ya gwada imanin ta kuma zatayi ƙoƙarin cinyewa insha Allah. Likitoci ne akan sa kusan guda biyar ko wannensu da binciken da yake yi ƙoƙarin su shine suga sun fitar da gubar tun kafin tayi masa illah, to Alhamdulillah anyi nasara saboda bai kai ga cin ta da yawa ba shi yasa ma har akasamu rayuwar sa, allurori sukayi masa daga nan suka fita suka barshi dan jiran farfaɗowar sa,sunyi wa su Dady Habib bayanin komai dan haka suka samu nutsuwar da suka sami damar tattaunawa a kan al'amurin. What Nafisa wace irin magana kike yi ne hakaguba fa kikace? Aunty Nafisa ta dubi Hajiya ladidi tace" wallahi Hajiya da gaske nake gaba ɗaya yanzu ESTATE daga jiya zuwa yau zan can da ake yi kenan, Hajiya na shiga ruɗani dalilin da yasa kika ganni da sassafen nan kenan saboda ina tunanin koke kika bawa Bintu aikin nan ban sani ba!'Hajiya ladidi tace"wallahi Nafisa bani nasa ta ba,sam ban san da wannan maganar ba, Nafisa tace"idan kuwa hakane tabbas A kwai ƙura Bintu mu zata yau dara, taura biyu ta haɗa abakinta,nasan tunanin ta bazai taɓa bata kashe Abdallah ba sai dai A sakata,zama bai kama mu ba dole mu binciki Bintu ta gaya mana wanda yasa ta aikin nan, Hajiya ladidi tace"ta yaya bayan kin ce tana can A kulle!'Hajiya ganin ta ba zai bada wahala ba!' Nafisa kinsan kuwa laifin kisa kike cewa ganin ta bazai wahala ba? sai dai kawai ki jarraba amma ki kula dan zaki iya shiga cikin zargi!'ɗan jim tayi can kuma tace"hakane fa Hajiyata hankali na ne gaba ɗaya atashe,amma dai zamu jira muga abinda zai faru,tunda sai munji sakamakon da asibiti suka bayar akan lafiyar Abdallah. Har yanzu babu wanda yace wani abu tunda ƴansanda suka tafi da Bintu ba asami wanda yaji zai iya zuwa inda take ba bare yayi tunanin taimakon ta, shuru kake jin estate ɗin ta ɗauka sakamakon abinda ya faru,kowa kuma jira yake yaji labarin abin da yafi ƙauna a ransa,shin Abdallah ya mutu ne ko bai mutu ba? Alhaji Baba babu wanda zai ce ga halin da yake ciki,saboda tunda ya shige ɗaki ya rufe yaƙi bari kowa ya ganshi balle asan halin da yake ciki,inno ma kusan hakane ta ɓangaren ta duk cikin su dama Hajjah ce me iya magana to itama bakinta ya mutu dan batasan me zatace ba,a ɓangaren su Rahima kuwa tunda taji labari take kuka wanda baza ta iya cewa ga taka mai mai abinda yasa ta kukan ba tasan dai ta damu da Ya Abdallah matuƙar damuwa,haka kuma zaren tunanin ta yakasa tsaida ita A guri ɗaya,Ammin ta kuwa baza ka taɓa gane me take ciki ba wannan sirrin zuciyarta ne. Sayyid ya dubi Taufiƙa da take ta kuka kamar ranta zai fita yayin da su Farida suke ta bata baki tamkar wadda aka sanar da ita mutuwar mijinta,yace"Ni kaina duk sheɗancina bazan iya aikata makamancin abinda yarinyar nan tayi ba,ashe yarinyar nan kallon mu kawai takeyi babbar ƴar ta addace ɗaga mana ƙafa kawai takeyi!'Siddiqa ce tace"a'a fa Sayyid duk irin takun saƙar da kake da mutum karka sake kayi masa ƙazafin kisa saboda komai daran daɗewa sai hakkin ya dawo kanka!'cikin mamakin ta yace"to me kike nufi da wannan maganar Siddiqa?ok nagane me kike nufi kina tunanin kice Ni nayiwa Bintu ƙazafi ko? har yanzu dai bata bashi amsa ko ɗaya ba,gyara zamansa yayi kana yace"Siddiqa wallahi wallahi wallahi kinji rantsuwa so uku ko to ban san komai cikin lamarin nan ba sai abinda nasanar daku tun farko,nasan da akwai irin wannan tsakanin mu kuma ban Musa miki ba Bintu bata bar komata ba,kuma ba ƙyaleta nayi ba sai dai Ni ba wannan ne nawa tsarin ba dan Ni sam Abdallah bai dameni ba duk da dukan da naci a hannun sa balle har nayi tunanin kasheshi,dan haka ki dai na min wannan zargin, Bintu ita tasaka kanta cikin matsala, yanzu matsata ƴan sanda zasuyi kawai ta faɗi wanda yasa ta kashe oganta faƙat!'yana gama bayanin sa ya tashi ya fita daga falon. Anty Nafisa ta kasa hankalin ta biyu tana son ganin Bintu kuma tana tsoron kar ace ita tasakata, ko kuma idan wanda yasaka Bintu aikin yafita shu'umanci da iya barazana sai kawai Bintu ta ɗora mata,kan uba amma danayi asarar zuwa duniya na koma babu ɗa babu dukiya ai bazan ma ga wannan rana ba, dole na haƙura da zuwa police station har sai naga abinda hali zaiyi,da wannan tunanin ta samu mafita. Baba nura hankalin sa a tashe yace"wallahi Baffa, wannan lamari ya ruɗani,me yarinyar nan take nufi wai ma shin waya turota cikin estate?a kwaifa lauje cikin naɗi, tabbas,a kwai waɗan da suka fimu wayo da shiri A kan wannan al'amari,dan a iya tunani na tun farmakin farko da muka kaimasa bamu ƙara wani yunkuri na kasheshi ba!'Alhaji Salisu yace"dole ne fa mu samu yarinyar nan mu tursasa ta ta faɗi wanda yasa ta sakawa Abdallah guba!' wayar Alhaji Sama'ila ce tayi wani ɗan sauti na alamun kira na shigowa,tashi yayi ya fita yana ɗagawa daga can ɓangaren Samirace ta ja ajiyar zuciya tare da cewa, haba dear Ina kashiga nake ta neman ka tun jiya da dare nakasa samun ka ina fatan dai lafiya? cikin yanayin damuwa yace"ke dai bari wallahi mun ɗan shiga ruɗani ne akan wani harkar kasuwancin mu shiyasa kika jini ba dai dai ba!'ayya sorry to ina fata dai yanzu an gyara komai?ina fa muna dai kanyi dan yanzu haka ma miting muke na fito amsa kiranki!'to shike nan amma idan ka dawo ya kamata mu haɗu ko dan kagayamin damuwar ka koda A kwai abinda zan iya taimaka maka dashi duk da nima ina da tawa matsalar kuma dalilin kiranka kenan,Samira wace irin matsala ce kike da ita haka? a'a karka damu ai nace zan gaya maka saboda abokin kuka ba aɓoye masa mutuwa,kuma yadda nake jinka araina bazai bari na ɓoye maka komai akaina ba,dolene kasan Ni wacece saboda aure zamuyi,dan haka mu haɗu a copy,anjima sai muyi magana!'to shike nan zan kiraki anjiman, kashe wayar yayi ya koma,a inda ya tarar Baffa Hashir yana cewa yanzu dai bamu da ƙwarin gwiwar tun karar yarinyar nan A police station dole ne mu tsaya muga yadda zata kasan ce amma fa abin da ɗaurewar kai saboda ina tunanin kamar itace wadda akace Alhaji Baba zai aurawa shi Abdallah ɗin to gashi kuma tana ƙoƙarin kashe shi!'Alhaji Kabir da sai yanzu zai ce wani abu yace"kawai muje kowa ya baza ido muyi matuƙar saka ido a cikin dukkanin motsinta,tunda dai yanzu tana hannun hukuma dole mujira, Alhaji Sama'ila yace"to amma kun san ba lallai ne ta dawo gidan ba dan nasan daga can sai gidan kaso za a wuce da ita, laifin kisa ne fa ko da Abdallah bai mutuba tabbas hukuma ba zasu rabu da ita taci bulus ba!'waw to ai inaga mu kuma da wannan damar zamuyi amfani mu ɗauke ta tasanar damu wanda suka saka ta aikin kaga a ƙarshe ma mune da ribar aikin, wannan maganar taka tayi dai dai Salisu, cewar Alhaji Kabir kenan,da wanan maganar suka samu matsaya. Samira ta kalli Dady jafar bayan gama wayarta da Alhaji Sama'ila,tace"kaji dai komai da kunnen ka! jinjina kai yayi tare da cewa Samira kina ƙoƙari amma dagewar da zakiyi yanzu idan kun haɗu ki tabbatar kin jiyo mana sirrika masu yawa mafi mahimmanci ma shine ki jiyo mana idan dasa hannun su A kan zubawa Abdallah guba,idan ma babu sa hannun su na tabbatar sai sun bi hanyar da zasu binciko wanda yasa akayi,kinga mu kuma mun ƙara samun wata damar da sun sani sai mu sani,ya juya ya kalli Sabir yace"kai kuma Sabir kaci gaba da bibiyar Alhaji Nasir wannan abokan Alhaji Baban mugaye ne zasu iya cutar mana dashi,kai kuma samuyal aikin ka dama lura da shige da ficen duk wanda zai shiga ya fita daga cikin ESTATE,da lura da abinda suke aikatawa dan haka ina mai ƙara tunatar daku da bakin ogan ku,saboda haka ku kula kuyi aiki bisa amana da gaskiya,gaba ɗaya suka amsa da ƙarayiwa ogan nasu fatan samun lafiya. Tunda ya farka bai cewa kowa uffan ba sai zuwa duba shi suke yi, amma A cikin su bazai tan tance wanda yazo dan Allah ba,sallolin sa yayi yayi wanka ya kimtsa tsaf dashi kai bakace mara lafiya bane,tun lokacin yaso su barshi ya tafi sai kuma sukace da A kwai buƙatar ya ƙara samun hutu koda na awa ɗaya ne Dady jafar ne kawai ya samu ya lallaɓashi ya haƙura,dole likitoci suka dakatar da shiga inda yake sai Dady jafar kawai da yake tare dashi,Dady jafar ya ɗan zubawa Abdallah ido na ƴan wasu daƙiƙa,kana a hankali yace"wai Abdallah me kasani game da wannan batun ne?shiru yayi batare da ya amsa masa tambayar sa ba,idanunsa A lumshe tamkar mai bacci,Dady jafar bai daddara ba ya kuma cewa, kasan cewa tunda abin nan ya faru Bintu tana hannun ƴan sanda babu wanda ya leƙa bare asan hali...ganin Abdallah kawai yayi batara da yasan lokacin da ya yun ƙura ba,sai tsintar sa yayi yana ƙoƙarin fita daga ɗakin, cikin sauri Dady jafar ya riƙo shi,amma yadda yaga fuskar Abdallah lokacin da ya juyo shi kansa sai da ya razana matukar razana tunda yake da Abdallah bai taɓa ganin mummunan ɓacin rai tare dashi da kuma tashin hankali ba sai yau,wani irin kallo ya shiga watsawa Dady jafar wanda bai san ya a kai ya sake masa hannu ba,fita yayi cikin wata irin gaggawa kana ganin sa zakasan cewa a kwai gagarumar damuwa, me napep ya tare yace" kaini duk wata station da kasani,daga haka ya faɗa Napep ɗin me Napep yaja suka fara kewaya station, Saboda tsabar zuciya bai san station ɗin da aka kaita ba amma ba zai iya tambaya ba,a wannan lokaci bazan iya misalta muku zaɓaɓɓakar da zuciyar Abdallah take yi ba,tun shida suke abu ɗaya sune har takwas sallah ce kawai take tsaida su,yanzu ma sallar isha sukayi daga nan ne me Napep yace" da Abdallah to Oga Ni fa yanzu station ɗaya ta rage da nasani!'wata irin tsawa Abdallah ya buga masa tare da cewa to yanzu me kake jira ne?ai da wani irin gudu me Napep yaja jikin sa na rawa bai ƙara gangancin yiwa Abdallah magana ba,har suka isa station ɗin. A dai dai wannan lokacin kuwa Bintu tana cikin cell cikin wani irin yanayi me matuƙar ban tausayi, babu wanda ya dubeta da idon tausayi babu abinda taci ko tasha sai azabar kuka wanda shi ya zama ruwan shan ta, A halin yanzu ma tana zaune can loko ta haɗa kanta da gwiwa kuka takeyi me cike da tausayin Abdallah da kuma fargabar halin da yake ciki, wani ne ya taso ya daka mata tsawa, miƙe wa tayi a firgice,wata ƴar sanda mace ya kira tare da cewa dpo yace mu fara tuhumar yarinyar nan ta faɗi wanda yasa ta wannan mugun aikin!'to tace" tare da ɗauko wata sanda da suke dukan masu laifi.... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 30 ``` Wayyo Allah na dan Allah karku dake Ni bana son duka!'ɗan sandan yace"au dama wayake don duka ai sai dole, idan kika bamu haɗin kai ba wanda zai taɓa wannan lafiyayyar fatar taki idan kuma kikace gadda ma da taurin kai zakiyi yanzu zan farfasa lallausar fatar da kike tsoron kar ataɓa, cikin tsuke fuska yace"gaya min waya saka ki saka yin kisa?wani irin kuka ta fashe dashi tana wani irin girgiza kanta,tsawa ya daka mata tare da cewa ke nake jira ki bani amsa kuma ki faɗi gaskiya bazan ɗaga miki ƙafa ba idan kika yimin ƙarya!', numfashin ta har sarƙewa yake ta kuma kasa yin magana sai ruwan hawayen da da ace yana ƙare wa da yanzu na Bintu ya ƙare,kallon ƴar sandar yayi tare da yi mata alama Aikuwa ta dai daici kyakykyawar fuskar Bintu ta zabga mata mari wanda sai da taga giftawar wasu taurari,kamar zata shiɗe haka ta fixgo maganar daga bakinta,wal wal wal wallahi bani bace ban san komai ba kar ku dakeni bana son duka fafina kazo kabuge su kacire Ni anan gun ni ban san komai ba!'dalla Malama rufe mana baki duka kuwa kamar kin sameshi kin gama tunda baza ki gaya mana gaskiya ba!'cewar ƴar sandar nan,yace"rabu da ita yanzu zataci ubanta tunda bazata faɗa ba!' Suna shiga cikin ainahin station ɗin ya dinga jin bugun zuciyar sa na ƙaruwa,da ƙyar ya iya sauraran ƴan san dan suka bin cika masa sunan Bintu, duk da sun san nan aka kawo ta amma sai suka farayiwa Abdallah ƴan kewaye kewaye na nuna alamun suna san wani abu daga hannun sa,ai tun da Abdallah ya tabbatar Bintu dai tana cikin wannan station ɗin ya wuce su cikin wani irin ƙaƙƙarfan taku irin na jaruman maza masu ji da da kuzari,da sauri wani yazo zai tare masa hanya amma kallon da Abdallah yai masa sai da yasa shi sakin acawi a wando,ci gaba yayi da tafiya batare da ya saurari ƙananan maganganun da suke ba, Duka na farko da ya kaiwa Bintu akan idon Oga Abdallah, ya ɗaga zai kai mata na biyu,yaji anyi wata majaujawa dashi,wanda tashin farko yasamu karaya a hannun da yake dukan Bintu dashi,bai gama dawowa daga wannan azabar ba ya kuma jin wani uban naushi acikin sa wanda atake agurin ya zube,shi kuma Abdallah ya kuma samun damar take ƙafar sa itama atake tasamu karaya,kafin wani lokaci ƴan sandan sun gar zaya dan sanar da inspector lawan. Da wani irin azama ta ƙara so duk da jikinta babu ƙarfi amma ita ba wannan ne damuwar taba, farin cikin ganin sa A raye yafi mata komai arayuwarta,saurin tarar ta yayi ganin tana shirin faɗuwa, wata irin runguma tayi masa mai cike da wani irin salo da ɗoki da wani irin gawur taccen farin cikin da baza ta iya musaltashi ba,tallafo ta yayi tamkar jaririya wani irin kallonta yakeyi kamar wanda yake bincikawa dan ya ga ko ancire wani abu ajikinta,cikin sa'a yaga shatin marin da ƴar sandar nan tayi mata,cikin wata irin murya mai cike da wani irin amo da ya gauraye da ɓacin rai yace"waye ya mareki tun yaushe suka fara dukanki?cikin ɓoye fuskar a ƙirjin sa tayi nuni da inda ƴar sandar take A tsaye tamkar wadda aka liƙa tun lokacin da taga an zubar da oganta cikin halin mutuwa ko rayuwa,bata gama shiga tashin hankali ba sai da taga Abdallah yayi mata alama da tazo batare dashi ya motsa daga inda yake ba,cikin rawar jiki ta ƙaraso kafin tasan abinyi taji ya ɗauke ta da wani zazzafan mari wanda lokaci guda ya ɗauke mata ji da ganin ta na wasu mintuna,duk da sun kasan ce ƴan sanda amma basu da ƙarfin gwiwar sa insa da Oga Abdallah, kwarjinin sa da ilhamarsa sun wuce ka tsaya yana faɗa kana faɗa, ƙoƙarin gyara mata zama ajikin sa yake ɗan yaji daɗin tafiya,amma sai ta saki kuka ta saka tana ƙara cukume shi,dan atunanin ta tafiya zaiyi ya barta,ƙara sautin kukan tayi tare da cewa Ni bazan zauna ba duka na sukeyi tsawa suke min na ce musu ban san komai ba sunƙi yadda,gashi kaima baka yadda ba tafiya zakayi kabarni, wallahi bani bace,idan katafi kasheni zasuyi,idan baka yadda dani ba ban san wa zai yadda dani ba,yunwa nake ji basu bani abinci ba basu bani ruwa ba mugaye ne basu da imani,katai maka koda baka yadda dani ba kafitar dani daga nan na maka alƙawarin bazan koma gidan kuba!' Abdallah ya ɗan rumtse idanun sa saboda yadda kalaman ta suke dukan zuciyar sa, A rayuwarsa ya daɗe bai cikaro da abinda ya bashi tausayi ba kamar Bintu ba,wani ɗan danshi yaji cikin idanun sa wanda ya tabbatar ƙwalla ce amma bai bari ta zubo ba,saurin ɗaga ta yayi kamar wata ƴar tsana haka ya sunkuceta, Cirko cirko yagan su tsaye sun kasa yin ko tari da kyar ɗaya daga cikin su yace"yallaɓai yace kaji ra shi yataho!'ko kallo bai isheshi ba,sai da ya fita ya farfajiyar station ɗin kana ya tuna babu mota A hannun sa,babu waya. Motar da ta faka a gabansa ita tasa ya maida hankalinsa kan wanda ya fito daga motar, inspector lawan ne sai Dady jafar,ɗauke kansa yayi yana ƙoƙarin barin gurin dan baya bukatar ganin su balle yayi magana da su, inspector lawan ne yace"ka dakata wannan ba hurumin ka bane ya kamata ka barmu muyi aikinmu,dole kabamu ita saboda ka karya mana doka ka daki ma alokacin mu,dan haka bazan baka koda belin ta ba!cikin tsanaki yake binsa da kallon mahaukaci mara imani,wata Napep ce ta shigo dan haka ya daga ƙafa zai ƙarasa inda take sai yaga ashe ma wanda yakawoshi ne ya dawo karɓar kuɗin sa,shiga yayi ya kwantar da ita A bayan Napep ɗin,cikin hanzari yake ƙoƙarin shiga saboda yadda yaga Bintu bata numfashi saboda yadda ta gala baita ga yunwa da ƙishi duk A tare da ita, inspector ne ya kuma yi masa magana, Abdallah kar kasake ka fita da yarinyar nan batare da ka cika ƙa idoji ba!' cikin wata irin ɓacin rai Abdallah ya nuna lawan da yatsa cikin muryar sa dake fita ɗaiɗai yace"kar ka sake kakuma da Katar dani idan kuma ba haka ba zakayi da nasanin tsayawa agabana kana yimin umarni!'daga haka ya faɗa Napep ɗin ya bar inspector lawan da baki sake cike da mamakin kwarjinin Abdallah,saboda shika kansa ƙarfin hali yake wajen kallon idanun sa. Suna tafiya ya dubi Dady jafar da ya tsaya kawai yana kallon su, inspector lawan yace"bai kamata ka tsaya kana kallon mu haka ba kamata yayi ka da Katar dashi tunda kaima kasan abinda yayi bai kyauta ba!'Dady jafar ya ɗan ɗage kafadar sa tare da cewa hakan da yayi shine dai dai matsayin sa na wanda aka yiwa wannan laifin yazo ya fitar da wadda akace ta aikata laifin to kuma kai meye naka aciki,ko bakasan cewa matar da zai aura bace? cikin tsananin mamaki inspector lawan ya maimai ta kalmomin, matar da zai aura kuma!' Dady jafar yace"ƙwarai kuwa ko kana mamaki ne? girgiza kansa yayi yace" ai dole nayi mamaki matar da zaka aura kuma ta nemi kashe ka? gaskiya abin da kwai rikitarwa,da matuƙar al'ajabi!'Dady jafar yace"shi yasa nace maka ka rabu da wannan case ɗin, na cikin gida ne saboda Bintu ba itace tayi wannan laifin ba kasan dai matsayi na amma banyi amfani da hakan ba a matsayina na uban Abdallah,dan haka ina baka shawara ka fita daga wannan sabgar dan kar kazo kayi nadama!'daga haka bai sake cewa komai ba shima ya wuce ya bar station ɗin. Har cikin gidan sa na area 1 me Napep ya kaisu,kuma har lokacin Bintu bata farfaɗo ba ɗaukar ta ya kumayi a kafaɗa ba tare da ya tsaya ba yace" da me napep ɗin ya biyo shi, jiki na rawa yabi bayansa ko tsoro bayaji ko ɗan yankan kaine,suna shiga tangameman falon da ya kusa zautar da me Napep, Abdallah ya kuma cewa da shi ka dakata A nan ina fitowa!' amsawa yayi jikin sa na ɓari,shi kuwa Abdallah kai tsaye saman haɗaɗɗen benan da aka ƙawata shi a tsakiyar falon ya hau Bintu shimfiɗe A kan kafaɗar sa,kai masha Allah abinda nace kenan lokacin da naga ya kwantar da ita cikin wani lafiyayyan gado mai rai da lafiya tabbas idan kashiga ɗakin nan idan bakayi sa a ba sai kamanta a duniyar da kake,komawa yayi ya sallami me Napep da ɗaurin dubu hamsin bai tsaya sauraran doguwar godiyar da yake masa ba cikin gaggawa ya koma ɗakin tare da fara bata taimakon gaggawa,duk da shima har yanzu bajin daɗin cikin sa yake yiba amma saida ya tabbatar Bintu ta dawo hayyacin ta duk da dai bata farka ba,saboda allurar baccin da yayi mata bata cikin hayyacinta,dan da a dai dai take yasan sai yasha daru,gyara mata kwanciya yayi bayan yasa mata ruwa, Sai lokacin hankalin sa ya dawo jikin sa fita yayi ya koma ɗaya ɗakin shima ya ɗan watsa ruwa kana ya zura doguwar jallabiya me ruwan toka,san nan ya nufi wajen daya killace shi dan yin ibadarsa cikin nutsuwa. A can ESTATE kuwa Anty Nafisa ce zaune cikin ɗakinta tagumi hannuwa biyu,babu abinda take sai tunanin hanyar da zatabi tacika burinta, yanzu idan akace Bintu gidan kaso za a kaita wa zata samu ta maye mata gurbin ta?san nan taya zatayi tasan wanda yasa ta wannan aikin meye kuma dalilin da yasa ita batayi mata irin wannan aikin ba taje tayiwa wani?tabbas dolene ta samu waɗan nan amsoshin daga bakinta,domin taga haɗamammun gidan kullum ƙaruwa suke dole tayi hanzarin cika burin ta,to amma yanzu fatan da take yi Allah ya dawo da Bintu saboda A yanzu ne zata fiyi mata amfani dan tasan tabbas Bintu zata iya karɓar aikin ta yanzu,to kuma idan taji tsorofa?duk yanda zatayi dole sai tayi dan rufin asirin ta da kuma samun burinta,ɗan kashingiɗa tayi tare da tsurawa hotan mijin nata ido haƙiƙa tana matsanancin son mijin ta, A baya tayi tunanin bazata iya wata rayuwa ba idan babushi har tana tsoron ranar da asirinta zai tonu saboda gudun samun tangarɗa A cikin zamansu, sai kuma gashi katsam Hajiyarta ta nusar da ita tare da ɗorata A hanya wanda har ma ji take A yanzu tafi Hajiyartata sanin matakan aikin,kawar da kanta tayi daga kallon hotan dan bata so taji tausayi ko ɗugon imani A cikin dukan niyarta ta samun duniyar ta. Farida ta zubawa Taufiƙa ido tana sauraran ta cikin azalzalar da zuciyarta take mata take cewa, Wallahi Farida da zan samu dama saina bita har cikin station ɗin na kashe rayuwar ta ɗan bata da wani amfani!'Farida tace"Ni kuma ai atunanina an wuce gurin yanzu dan na tabbatar yanzu shi kansa Alhaji Baba bazai yadda da wannan auren ba, balle kuma uban gayyar bazai taɓa yadda ya auri matar datake son raba shi da rayuwarsa ba, Farida ta ɗan kalli ƙofar ɗakinsu sai da ta tabbatar babu wanda yake ƙoƙarin shigowa kana tayi ƙasa da muryar ta tare da cewa,dan Allah niko Taufiƙa na yi maki wata tambaya mana!'Taufiƙa tace"inajin ki"yauwa Dan Allah Taufiƙa bake kika haɗa wannan tuggun ba saboda kar Bintu ta auri Ya Abdallah?wani kallo Taufiƙa tayiwa Farida amma batace komai ba, saida Farida ta dafa ta tare da cewa kiyi haƙuri idan tambayar ta ɓata miki rai kawai dai abin da na sanine zaki iya aikata komai akan cikar burinki,shi yasa nayi miki wannan tambayar!'miƙewa tayi zata fita daga ɗakin cikin sauri Taufiƙa ta ruƙo hannun ta tare da cewa Wallahi Farida ban sani ba ban san waya aikata ba kuma banji haushin tambayar ki ba, kawai dai nayi mamaki ne duk wannan shedun da suka bayyana amma keda Siddiqa kuke san sawa zuciyar ku yadda da Bintu bayan kuma duk irin cika bakin da kika gamayi na ɗaukar fansa akanta,abu na biyu kuma banyi zatan zakiyi tunanin zan iya kashe abinda nake ƙauna da hannu na ba, koda kisan ne sai dai na kashe Bintu dan wannan alƙawarina ne indai Bintu ta auri Abdallah sai na hana rayuwar ta zama lafiya sai ta gwammaci mutuwar ta akan rayuwa,dan haka ki dai na tunanin Ni nayi wannan haɗin babu ruwana wannan macijiyar da take son mamaye dangin mu da salon ta na yaudara to itace ta haɗa komai,dan haka ki cire zargina da kika fara sawa A ranki!'tana gama faɗa ta saki hannun Farida tare da kwanciya saman gadon ta, Farida ta jin jina kanta tare da cewa na yadda da maganar ki Farida saboda nasan bazaki ɓoye min duk wani al'amarin da ya shafe kiba. Tunda asuba Bintu ta farka sai dai babu ƙarfi sosai a tare da ita, kasan cewar har yanzu bata ci ko mai a cikin ta ba yanzu ma da taimakon ruwan da yasa mata samu ɗan ƙarfin jiki,tana idar da salla ya shigo ɗakin hannun sa ɗauke da wani ɗan madai daicin cop sai madai daicin kwalanda,ajiyewa yayi A gabanta batare da yace"mata komai ba yayi mata nuni da takarya yanzu,miƙewa yayi ya fita yayin da Bintu ta ɗauki cop din nan da yake shaƙe da kakkauran shayi wanda yaji haɗi,tunda ta kafa shi abakinta ba ita ta ajiye ba saida ta shanye shi tas kana ta janyo kwalandar da take ɗauke da soyayya dankali da uban ƙwai sai zabga ƙamshi yake ta hau ci so sai taci tayi ƙat,daga nan kuma ta fara tunanin wanka dan har wani ƙayƙayi taji jikinta nayi saboda rashin wanka,tashi tayi ta shiga haɗaɗɗen banɗakin da sai da taja wasu mintuna wajen ƙauyanci da kalle kalle kafin ta fara gabatar da wankan ta sai da taji fatar jikinta har zafi take saboda gurza haka gashin kanta kana ta haƙura ta fito,kamar wancan lokacin yauma doguwar A baya ta samu saman gadon murmushi tayi tare da cewa,yau dai bazan ce wataran ne kake da kirki ba kana da kirki, kullum kai mai kirki ne mai tausayawa rayuwata Oga Abdallah kai na musamman ne gaskiyar fafina ne da yace" kai zaka zama jagora kuma garkuwa a gareni tabbas na haɗu da mai sharen hawayena,inayin ka ogana over!' tayi waɗi ɗan juyi mai cike da nishadin dake tattare da farinciki. Shi kuwa Abdallah bayan gama shirin sa Yahya ya kira yace"masa zasuje can office ɗin sirri saboda akwai buƙatar zuwan sa A yau ɗin,bayan gama wayar tasa ne ya koma ɗakin da Bintun take ciki,sai da ya ɗan yi knoc ta bashi izinin shiga kana ya shiga ,cikin wannan yanayin nasa na kirnewa wanda ita a yanzu bai dame ta ba, ya nufi wata durowa kai tsaye taga ya ɗauko magunguna har da allurai cikin sauri ta tashi zata shiga banɗaki, wanda kanta kai ga buɗewa ya danƙo hannun ta cikin zafin nama irin nasa na ƙarfaffan namiji,waro manyan idanunta tayi saboda ita tsoro ma ya bata dan bata san lokacin da har ya ƙara so ba,kwaɓe fuska tayi tana shirin sakin mai kuka saurin ɗora yatsun sa yayi kan jajayen laɓɓansa yayi mata alamar tayi masa shuru,batayi kukan ba amma bata saki fuskar ba, jawo ta yayi ya zaunar da ita gefan gadon,kana ya nufi ɗan ƙaramin frige ɗin da yake ɗakin ya bude ya ɗauko gorar ruwa ya ɓalle maganin ya miƙa mata tare da ruwan,karɓa tayi ta shiga juya sa cikin hannun ta,tunda ya shigo sai yanzu bakinsa ya motsa,Malama kina ɓatan lokaci ina da abinyi!'cikin tura baki tace"to kayi tafiyar ka zan sha!'kawai gani tayi ya shiga haɗa allura, cikin rigimammiyar Muryar ta tace"Ni dai banason allura zansha maganin ko kallon ta baiyi ba ya cigaba da abinda yakeyi,da taga dai da gaske yakeyi allurar zaiyi mata kawai sai ta miƙe zata gudu daga ɗakin, cikin azama ya fizgota ta faɗa jikin sa dama ya gama haɗa allurar riƙe ta yayi sasai ya tsira mata allurar kuka takeyi sosai hadda su kai masa duka a ƙirji amma bai rabu da ita ba sai da ya tabbatar allurar ta gama samun mazauni cikin jininta kana ya saketa yana watsa mata harara,juyawa yayi ya fice yana aiyana rigima da sakalci irin na Bintu A ransa, A nan kan gadon ta gama birgimar ta daga ƙarshe kuma bacci yayi awan gaba da ita. Tacan ɓangaren Alhaji Baba kuwa A safiyar yau ne ya A kuma cikin masallaci bayan idarwarsu daga sallar asuba ya umarci liman da yasanar da akwai ɗaurin auren da za A gabatar yanzu in Allah ya amince, tare da miƙawa Abba Umar kuɗi dubu ɗari biyu cif tare da ce masa Umar inaso kazama wakilin wannan marainiyar Allah Bintu nasan kai kaɗai ne zakayi min biyayyar yin haka batare da son jin ba asi ko kuma gar dama ba!' Abba Umar wanda ya sauka da asubahin ranar daga tafiyar da yayi duk da dai ba da ɗewa zaiyi ba, yasa hannu biyu ya amshi kuɗin da mahaifinsa yake miƙa masa,haka nan ya tsinci zuciyar sa cikin wani irin maɗaukakin farin ciki tamkar anyi masa bushara da aljanna,sauran yaran Alhaji Baba da ƴaƴan ƴan uwansa da jikokin sa da duk wanda yake zaune cikin wannan ESTATE kuma yasan abinda ya faru da Abdallah da Bintu saida ya shiga cikin tsananin mamaki da kuma tashin hankalin wannan al'amari,basu taɓa tsammanin cewa Alhaji Baba bai yadda da abinda yaji kuma ya gani akan gubar da Bintu ta zubawa Abdallah ba,sai gashi ya basu wani irin rikitaccen mamaki da ɗaurawa Bintu da Abdallah aure. A wannan rana ta juma'a da misalin ƙarfe bakwai nasafiyar ranar mutanen da suke cikin ESTATE da maƙota da masu gadi da direbobi da ma sauran manyan mutanen da Alhaji Baba duk ya riga yasanar musu, wanda wasu sai bayan idar da salla suka dinga shigowa wanda daga cikin su har da manyan Aminan sa su Alhaji Nasir Wanda su basu san kiran nasa na meye ba sai da suka zo,duk sun shaida Auren Fatima Bintu Zahra da kuma angonta Abdallah Jafar,kai wannan rana na kuma sakan kan cewa, imani ya kuma ratsani na kuma sallamawa ubangi ƙadiran Ala manyasha'u, na kuma jinjinawa ƘUDURARSA, da ikon sa tare da buwayar sa, abinda yaso ya kasan ce ko ta yaya sai ya kasance Alhaji Umar ya ɗaura Auren ƴarsa ta cikin sa da hannun sa batare da shima yasani ba,batare da sanin kowa ba Allah ya zartar da ƙudurar sa da buwayar sa. Wani irin farin ciki Alhaji Baba yake ciki dashi kansa bai san adadin sa ba, Abba Umar kuwa bayan farin cikin da ya tsinci kansa aciki hakanan sai tsohon mikin sa ya kuma tashi, can dakin mahaifiyar sa ya nufa ya sauke mata damuwar sa kamar yadda yasaba,ita kuma ta tarbe shi da tsantsan soyayya da tausayi wanda yake tsakanin uwa da ɗanta,duk da cewa itama tana cikin wani irin hali na damuwa da kewar gudan jininta da kuma farin cikin wannan Aure ji take kamar ta taka rawa saboda tsananin farin ciki,tana shafa kansa tana murmushi mai ɗauke da kishiyoyin ma'anoni, cikin taushin lafazi take cewa, Allah Ubangiji yasa Auren nan yazama sanadin wani haske da zai baiyana nan ba da jimawa ba cikin wannan ahlin, Allah Ubangiji yasa wannan Aure daka ɗaura ya zama sanadin kawo farin ciki A rayuwarka data ahlinka, Allah Ubangiji yasa wannan Aure yazama shine sanadiyyar ruguza duk wani ƙulli da aka ƙullashi acikin gidan nan!'da Amin Amin yake ta amsawa yanajin wani farin ciki da tun faruwar al'amarin bai kuma samun makamancin sa ba,(to nima dai ina yi muku fata da addu'ar ɗorewar farin ciki da kuma bayyanar gaskiya mu kuma Allah ya kawo mana ƙarshen masifun da suka addabi kasarmu ya kawo mana kuma farin ciki A cikin al'ummar mu yatabbatar mana da shugabanni masu adalci Amin Ya Allah) Tofa FANS Taufiƙa sai ku zama cikin shirin abinda zai faru idan taji wannan labarin Ko ya Abdallah da Bintu zasu ji idan suka sami labari? yaya Bintu kuwa zata karɓi aikin da Anty Nafisa ta bata?to wai ya zaman Aure zai kasance tsakanin waɗan nan taurari?Samira kuwa zata sami nasara akan Alhaji Sama'ila?kai dama sauran manyan tambayoyin da suke ƙulle acikin wannan rikitaccen labarin wanda da sannu zan warware muku zare da abawa dan haka sai ku shirya ku kuma kimtsa yan zu akasoma. Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 31 ``` A wannan rana zuciyoyi da yawa sun baƙanta wasu kaɗan daga ciki kuma sun faranta,taɓan garen,inno dai har yanzu zuciyar ta tana cikin zulumi da wasi wasi zuwa yanzu ta fara hararo tabbas A kwai wata maƙarƙashiya cikin al'amuran Bintu, da akwai wani ɓoyayyen sirri wanda bakowane yasan da shiba domin idan ba haka ba meye ruwan ahlin ALHAJI BALARABE da rayuwarta? meye yasa ake binta da sharri da makirci haka alhalin babu hurumin ta cikin mugayen al'amuran gidan, tabbas da A kwai wani ɓoyayyen sirri wanda insha Allah ita kuma sai ta binciko shi tare da taimakon Allah, amma bazata zuba idanu alalata rayuwar marainiyar Allah ba,tayi farin ciki da wannan Aure amma ta wani ɓangaren tana jin wata irin fargaba tanaji kamar wani abu zai iya samun Bintu ta rasa me mutanen gidan nan suke nema haka da kowa idansa ya rufe da salon mugunta da makirci na rashin imani idan ba rashin imani ba kamar Bintu za'a ɗorawa alhakin kisa har kuma a rufeta,ga kuma Abdallah da ba dan Allah yasa da sauran shan ruwan sa ba da yanzu batun wani ake bana saba, kai Allah ya kare mu daga sharrin zuciya ya tsare imanin mu. Ita kuwa Hajjah ƴar duk inda ta daɗi sha ce,bata zauna da Bintu ba bare tace" ga abinda zata iya aikatawa da wanda baza ta iya ba,kawai dai ita tana tsakiya babu ruwanta da duk wani al'amarin da yake gudana A cikin ESTATE ɗin ita abin da ya dameta shine damuwar ta, ba ruwanta da shiga shirgin da ba nata ba ko ba asata cikin saba,amma tana da zafi idan kataɓota,kuma bata fiye ɗaukar matsalar wani matsayin tata ba,amma idan ka zauna da ita tana da fara'a dan zan iya cewa duk cikin matan Alhaji Baba ta fisu sakin fuska da wasa da jikoki shiyasa dayawa jikokin nasu sun fiyi mata wasa akan su Hajiya Babba da Inno,kuma tun yaran gidan suna ƙanana idan sukayi laifi itace mai hukunci,shi yasa ta wani ɓangaren suke bala in tsiron Hajjah,dan haka yanzu ma tuni ita ta manta da batun Bintun sai da taji sanarwar Auren ne take cewa to shi Abdallah yaji sauƙine? Jabir da shi ya kawo mata tsegumin ya bata amsa da yaji sauƙi,daga haka bata ƙa ɗaga zancen ba sai fatan Alkhairi da tayiwa Auren. Ita kuwa Hauwa'u dama tuni tasawa zuciyarta dan gana, dan taga yanzu faɗan yafi ƙarfin ta na manyane sai dai ta koma gefe ta taya Taufiƙa yaƙin tunda ita taga zata iya amma zata bada gudummawa wajen ƙuntatawa rayuwar Bintu ita yanzu tuni ta haƙura ta amshi soyayyar Nabil da ya daɗe yana mata naci, ya fiye mata kwanciyar hankali akan taje inda ba asan da ita ba balle akai ga batun so. Hajiya zulaiha ta kai ta kawo yafi sau goma gaba ɗaya kanta ya ɗaure da wannan al'amarin,ta zurfafa tunani sosai akan Bintu kuma tabi duk wasu hanyoyi dan ganin ko zata kama Bintu da wani laifi amma bata gani ba, tabbas yarinyar nan ta shiga komar magauta akwai ayar tambaya fa meyasa suke bibiyar ta kamar yadda suke bibiyar duk wanda ya kasan ce ahlin ALHAJI BALARABE wanda yake da masaniya akan ɓoyayyen sirrin nan?gaskiya abin nan da matuƙar ɗaure kai ita yanzu sanadin wannan muguwar rayuwar da ake yi A cikin ESTATE ɗin nan yasa duk ta hana ragowar ƴaƴanta zaman cikin gidan ko wanne ya lula wata ƙasa shida iyalan sa Rahimace kawai ta rage mata a gabanta,anya kuwa da wanda aka cutar a cikin ahlin nan sama da ita, ansa ta rabu da yaranta wanda suke sune sanyin idaniyarta abin alfahari agareta duk saboda kar acutar mata dasu ko arabata dasu kamar yadda aka rabata da hasken zuciyarta da kuma mijinta abin alfarinta me share mata hawaye a koda yaushe da yawan lallashin ta,wani irin kuka ne ya kufce mata mai azabar raɗaɗi,me cike da kewa ta rashin masoya guda biyu. Wurgi takeyi da duk abinda yazo hannun ta, Siddiqa da Farida ne suke ƙoƙarin kamata duk tabi ta jiwa kanta ciwo saboda gilasan da ta fasa kuka take tare da wani irin ihu na tsan tsan baƙin ciki da takaici,da suka kasa tsaida ita sai suka ruga suka kira inno, inno tayi matuƙar mamakin wannan haukan na Taufiƙa,cikin muryar da take ɗauke da tsantsar baƙin ciki tace"Taufiƙa Ni dai wannan halin naku na ɓaƙin hali da shegiyar baƙar zuciya ba acikin zuriyata kuka sameshi ba,dan duk cikin yarana mata shida cas ban haifi me baƙar zuciya da mugunta ba sai dai acan dangin ubanku kuka kwaso wannan mugun halin, tur wallahi Taufiƙa kinji kunyar rayuwarki da babbar asarar da idan baki gyara halinki ba rayuwarki bazatayi kyau ba,kuma har abada ke da Abdallah dan ya riga yayi miki nisa wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa,baku dace ba ko ta wanne ɓangare, Bintun dai da kika tsana da ita ya dace Allah baya jarabtar kamilin mutum kamar Abdallah da Auren mace irinki, kina zaune a gidan nan zakiyi kallon yadda ake zaman Aure mai cike da mutunta juna kina zaune a gidan nan zakiga yadda Abdallah zai maida Bintu sarauniyar mata kina zaune a gidan nan zaki kalli soyayyar da baki taɓa ji ko gani ba arayuwarki, kina zaune a gidan nan zakiga yadda Abdallah zai durƙusa ya juya baya Bintu ta hau ya goyeta ya sa majanyi ya ɗaure kuma kina zaune zakiga yadda yarinyar da kika ƙasƙantar zata juya mijin da kikaso kike gani ya wuce ajinta, kina zaune kuma zakiga yadda Bintu za tayi taƙama da estate din nan kamar yadda kike mata borin tsiya,haka kuma kina zaune Bintu zata riƙe arzikin da baki taɓa mafarkin samun sa ba arayuwar ki, Taufiƙa Ni na gaya miki wannan wataran ko babu raina sai kin tuna da wannan kalaman nawa saboda da ikon rabbil izzati duk abinda nazana miki sai sun tabbata A kan rayuwar Bintu saboda ita ɗin kamar waliyiya take saboda wankakkiyar zuciya bata nufin kowa da sharri sai Alkhairi, wannan alkairin shine zai bibiyi rayuwarta da dukkanin zuriyarta insha Allah!'daga haka ta fita daga ɗakin cikin farin ciki saboda ji take ta fato Taufiƙa a kan yadda ta daɗe aranta, ta wanke takaicinta na tun ranar da suka dawo gidan akan abinda sukewa Bintu gashi tana jin abinda ta faɗa tamkar sun riga sun tabbata akan bintun duk da tasan a kwai ƙalubale cikin rayuwar ta to amma tayi yaƙinin cewa da sannu wannan lokacin zaizo. Sayyid ma yashiga halin ɗimauta da jin wannan al'amari, saboda akwai shirin da yasoyi kafin faruwar lamarin to amma dai ko yanzun ma babu abinda zai dakatar dashi daga aikin da aka saka shi duk da bai san wanda yayi wa Bintu wannan test ɗin ba amma dole zai bincika ya nemo wanda ta haɗa kai dashi ko wanda yasa ta aikin dan yanzu aikin da aka bashi kenan kuma da sannu zai zamu nasarar aiwatar da abinda yake aikin sane, dan ya ɗau alwashin ba zai bawa waɗan da suka sakashi aikin Nan kunya ba. Acan cikin copy kuma Samira ce tare da Alhaji Sama'ila zaune bisa kujerun ƙarfe sai ƴan kayan lashe lashe agabansu,Alhaji Sama'ila ne ya dubi Samira cikin zaƙuwa da san jin abinda zatace masa yace"Samira inajinki jiya da tunanin maganar da zamuyi nayi bacci!'murmushi tayi kana tace"abinda zan gaya maka wani Abune da ya shafi rayuwata wanda kuma naga ka can canta da nasanar dakai saboda yadda da zaman amana!'jinjina kansa yayi cike da gamsuwa da jin daɗin lafazinta,ta cigaba da cewa,shiyasa na shirya gaya maka duk wani sirrina wanda zaka iya zuwa kaji shi a wani baki na da ban, kuma hakan zai iya kawo mana saɓani cikin kyakykyawar mu'amalar mu!' katse ta yayi da cewa duk naji wannan na kuma fahimta ki sanar dani abinda yake faruwa kai tsaye karki samu damuwa!'ƙasa tayi da kanta kana cikin taushin murya tace"Ni dai na kasan ce ƴar babban gida kuma wadda take da tarin dangi da ƴan uba saboda mahaifinmu yana da tarin mata,shiyasa ya tara ƴaƴa da yawa,haka kuma yana da tarin dukiya wadda har ta zama abar kwatance cikin jama"a,amma abin mamakin sam mahaifinmu baya mora mana da ko biyar daga cikin arzikin sa kowa sai dai ya nema da kansa, matan mu da mazan mu hakan ne yasa har so muke muga mahaifin mu ya faɗi ya mutu,ganin abubuwan suna daɗa yawa sai kawai mukayi shawara a junan mu na me zai sa mu kasheshi tunda yaƙi mutuwa, wannan shawarar duk munyi amanna da ita amma iya mu waɗanda suke da buƙatar hakan,dan haka muka shirya da wasu ƴan daba mukayi ciniki dasu suka shiga har gida suka soka masa wuƙa, wannan shine sanadin mutuwar mahaifinmu kuma mun sami abin da muke nema na dukiya da kadarori!'sauke numfashi tayi tana dauke kanta ƙasa cikin sanyin murya tace" masa wannan labarinne bana so kazo kaji daga baya ka tsaneni shiyasa naga gara na faɗa maka da bakina saboda ka fahimceni!'shiru gurin ya ɗauka na wasu daƙiƙai daga bisani Alhaji Sama'ila ya gyara zamansa tare da goge zufar da ta ɗan taru saman goshinsa kana yace" Samira yanzu nadamar abinda kika aikata kike kome?shiru ta ɗan yi kana kuma tace"bazan yaudareka ba Alhaji Sama'ila sam bana nadamar abinda na aikata koda zuwa za ayi A tafi dani akan laifin kisan mahaifina!'ta ƙara sa maganar cikin nuna taurin zuciya, murmushi yayi tare da cewa gaskiya Samira kin burgeni wannan abin da kikayi shine ya nunamin zaki iya zama dani kuma zamu gudu tare mu tsira tare, tabbas zan iya saka ki cikin tafiyar mu,dan haka nima zan gaya miki kaɗan daga cikin aikin da mukeyi a yanzu amma ba yanzu ba sai mun sake zama!' tace"amma ko na jiya ne ka sanar dani saboda hankalina ya tashi sosai!'yace" kar ki damu ba komai bane wannan muna kan war ware matsalar tace" duk da haka dai yakamata ka faɗa koda taimakon da zan iya yi maka!'ɗan jim yayi kana yace"hakane,bata labarin abinda ya faru da Bintu da Abdallah yayi tare da yi mata bayanin abinda suke nema ya dai yi mata bayanin komai ataƙaice ya kuma ce zai sakata cikin tafiyar tasu,cikin farin ciki tace"amma da kasan da wannan business ɗin baka taɓa tallata min ba, Alhaji Sama'ila ya ƙyalƙyale da dariya cikin dariyar yake cewa to ai gashi yanzu na tallata miki har ma na siyar miki da ita!' itama dariyar tayi kana kuma ta ɗan maida fuskarta serios tace"kuma ku bakwa tunanin wani ko wata da zai iya sakata yin hakan?girgiza kansa yayi tare da cewa, gaskiya bama tunanin kowa,dan A binciken da muke kanyi kenan!'ta wacce hanya kake gani zanbi dan taimaka muku? yace" zamuyi maganar da sauran team ɗina idan ta kama ma ayi mitin ɗin dake duk zan sanar miki!'murmushi tayi tare da saurin danna sevin a recording ɗin da tasaka kana ta miƙe tace"to shike nan dear Ina nan inajiranka ni zan wuce gida!'muje nima ai wucewar zanyi!'daga nan suka taka har zuwa bakin motar Samiran, ya buɗe mata ta shiga suka kuma yin sallama kana ta ja motar sai da yaga fitar ta kana shima ya shiga tasa ya bar gurin. Sai da yagama sauraren recording ɗin kana ya ɗan yi wani muskilin murmushi,karkuso kuga fuskar Abdallah da murmushi saboda matuƙar kyan da yayi masa kumatunsa saida ya loɓa irin na Bintu,cikin daddaɗar Muryar sa yace"na gode Samira kinyi ƙoƙari sosai ina fatan mana nasara cikin dukkanin aiyukan mu dana yanzu dana gaba!'amin ya hayyu ya ƙaiyumu,ta faɗa tana ƙoƙarin ta shi sallama tayi masa,bayan fitarta ya ɗan jingina bayansa da makarin kujerar tare da lumshe shanyayyun idanun sa,ko ya waccen rigimammiyar take ciki? tun ɗazu ya bada take away a ka kai mata ko taci ta haƙura da kukan oho mata rigimammiya kawai, tsadadden agogon dake ɗaure a hannun sa ya kalla ƙarfe uku da arba'in miƙewa yayi ya kwashi tarkacen sa kana ya fita, masallaci suka fara shiga sukayi sallah daga nan suka nufi gidan sa na area 1. Lokacin da aka kawo mata take away ɗin tuni ta daɗe da tashi tayi wanka ta mayar da kayanta, dan haka ana kawo mata ci tayi ta ƙoshi,daga nan kuma sai duk tsoro ya rufeta ta kalli ko ina taga ita ka ɗai ce,sai tsoron ya kuma kamata tuni ta fara ruwan hawaye daga ƙarshe ma ta saki kukan gaba ɗaya,da taji motsi sai ta zabura acikin wannan halin ya shigo ya sameta wanda ita saboda rigima ba tasan yashigo ba kukan ta kawai takeyi tamkar wanda yake mata daɗi,ɗan tsayawa yayi yana dubanta wai ita kuka baya mata wahala ko yanzu me akayi mata kuma oho? ɗan tsaki yayi wanda shi ya ankarar da ita, da gudu ta miƙe zata gudu yayi saurin sa mata doguwar ƙafarsa aiko tuntuɓe taci ta zube ƙasa tana riƙe ƙafar cikin tura baki tace"to Ni me nayi maka kuma naga dai kai kabani tsoro!'harara ya zuba mata batare da yace"mata komai ba ya wuce dan shiga ɗaki, da gudu ta tashi tabi bayan sa,ɗan juyowa yayi yayi mata kallon ki kiyayeni ɗan marairaice wa tayi tare da cewa Wallahi Oga Abdallah tsoro nakeji!'ki shirya zamu koma gida da sauri tace"nan ba agida muke ba wane gidan kuma zamuje? ESTATE ya faɗa tare da cigaba da tafiya,tunda ya faɗi kalmar estate jikinta yayi sanyi zuba masa ido tayi har ya shige ɗakin sa, A hankali takoma ta shiga ɗakin da take ta ɗauko mayafin abayar jikinta, falon ta dawo ta zauna tare da zuba ta gumi anya kuwa zata iya ci gaba da rayuwa a cikin wannan ahlin? anya zata iya cigaba da zama ana ƙulla mata sharrin kisa?idan kuma basu karɓe ta bafa? inno fa ga Hajiya Babba itama tasan duk sun tsaneta yanzu kallon makashiya suke mata, ta tuna lokacin da ƴan sanda suka tafi da ita babu wanda yayi yunƙurin ceton ta babu wanda ya nuna alamun ya yadda da abinda ta faɗa,ya zatayi ta iya zama da inno cikin halin tsana da ƙyama? tabbas a wannan lokaci baza iya duban idon inno da Alhaji Baba ba, ga kuma Hajiya Babba matar da tabata yadda a rayuwa, kallon ƙofar ɗakin da yashiga tayi haka kuma zuciyar ta na cigaba da tunzura ta akan ta tashi ta gudu tun kafin ya fito ya mayar da ita cikin wannan gida mai kama da ramin macizai a wajen ta, cikin sanɗa ta miƙe batare da ta yadda tayi wani motsi mai ƙarfi ba, da sauri ta gangara ƙasa cikin Sa'a ta samu ƙofar falon babu security cikin hanzari ta fita, dai dai lokacin kuma mai gadin ya zaga baya, dalilin kenan da tasamu damar fita batare da kowa ya lura da ita ba. Cikin hanzari ya fito falon ganin bata nan sai ya ɗan ƙonƙosa ƙofar ɗakin nata jin shurun da yayi yasa ya shiga yana mai tunanin yanzu haka kuka take tunda ba gajiya take dashi ba idan tanayi har wata jiniya take masa da ado dan ya kuma yin daɗi,zubawa ɗakin ido yayi tare da ɗan kasa kunnensa ko zai ji motsi a banɗaki sai dai har kusan mintuna biyu baiji motsin komai ba, takawa yayi A hankali ya isa bakin toilet ɗin saida ya ɗan kasa kunnensa kana ya tura ƙofar,ga mamakinsa bata cikin toilet ɗin,da sauri ya fita tare da sauka babban falon ya shiga dubawa ko wane ɗauki daidaita duba kiching da sauran guraren dake cikin falon amma duk neman sa baiji koda motsinta tsorone yafara kama shi karfa a shigo har cikin gidan nan a sace yarinyar nan,a hankali ya fara kiran sunanta tun yana faɗa a hankali har ya koma ɗaga muryar sa amma shiru a yadda ya lurama babu kowa cikin gidan fita yayi can wajen get,sojan me gadin ya shiga ƙwalawa kira kamar zai dake shi,da sauri ya ƙara so inda yake jiki na rawa gani ranka shi daɗe!' cikin fusata Abdallah yace"wa kagani ya shigo gidan nan ko ya fita? cikin rawar jiki mai gadin yace"wallahi yallaɓai babu wanda ya shigo sai dai bansani ba ko lokacin da nazaga baya wani ya shiga!'wani mugun kallo Abdallah ya watsa masa tare da cewa ka tabbatar idan banga yarinyar nan ba saikayi na damar sakaci da kayi na barin aikinka kuma kabar get abuɗe! daga haka ya koma ya shiga mota tare da yimata wata irin wuta,ganin haka yasa mai gadin ya kwasa da hudu ya buɗe masa get,da wani irin azababban gudu ya fita zuciyarsa tamkar zata kama da wuta har ya rasa wane irin tunanin zaiyi, ita ta fita da kanta ko zuwa akayi aka tafi da ita?cikin wannan tunanin ya hango kamar Bintun tare da maza biyu sun zagaye ta da alama ma kukan nata na fama takeyi, cikin sauri ya taka burki tare da fita daga motar wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya saki lokacin da ya tabbatar da cewa Bintu ce. Ita kuwa Bintu tun lokacin da ta fito ta shati hanya batayi wata tafiya mai nisa ba wasu samari irin ƴaƴan manyan nan sangar tattu suka tare ta wai suna sonta, shine take ta fama dasu kan su rabu da ita sai kuka take amma sun ƙi rabuwa da ita acikin wannan yanayi Abdallah ya ƙara so ya samesu, Bintu tana ganinsa ta gudu bayan sa tare da cukyikyi sa tana sheshsheƙar kuka,ɗaya daga cikin sune yace" kai kuzo mu tafi wannan daga ninsa mijin tane!'ɗayan yace"ai inaga dai tabbas matar sace kawai mu fece!'Abdallah dai yana kallonsu bai kuma ce dasu komai ba ya juya da sauri tabi bayansa,buɗe mata motar yayi ta shiga sam ya kasayi mata magana saboda takaici, yarinyar nan tana bashi ciwon kai da yawa. Ganinsu a tan game man get ɗin ESTATE yasa ta kuma sakin kuka cikin tashin hankali tace"Ni kabarni na tafi bazan koma wannan gidan nakuba bazan iya rayuwa da mutanen cikin sa ba,dan Allah ka rabu dani na gode da taimakon ka bazan taba mantaka cikin rayuwata ba, wallahi idan nakoma kasheni zasuyi,ga su inno ma duk haushi na suke ji kowa bai yadda dani ba, kuma Ni bani bace wallahi ban san komai ba!' kuka takeyi sosai wanda har sai da yaji wani iri can cikin zuciyar sa,cikin wata irin taushin murya yace" da ita ki daina kuka ba wanda ya yadda da abinda ya faru har inno ma duk sun fahimce ki!',da sauri ta goge hawayen fuskar ta cikin farin ciki wanda ya nuna tsantsan ƙuruciya da yarintarta, tace"da gaske inno ta yadda dani Hajiya Babba ma ta amince ban aikataba?gyaɗa mata kai yayi kawai yanajin tamkar wani abu na faruwa da zuciyar sa sai dai bai san komeye ba,A hankali ya fita ya zagayo ya fito da ita tare da kama hannun ta, ji yayi ance kar kasake ka dawo mana da wannan annobar cikin ahlin mu bazamu zauna da ita ta dinga kashemu da ɗaɗɗaya ba, ka mai da ita inda ka ɗauko ta dan shi kaɗai ya fi dacewa da ita!' wani irin kallo mai cike da tsana ta kaici haushi shi Abdallah ya kewa Dady Mansur,batare da ya kulashi ba ya cigaba da tafiya dan shi baisa wannan mutumin cikin sahun masu hankali ba,haka ya barshi agurin yana kunfar baki tamkar wani zararre. Cikin nutsuwa yayi sallama falon Alhaji Baba,wani irin ƙayataccen murmushi Alhaji Baba ya saki ganinsu Abdallahn,yace"maza ku ƙaraso ƴan albarka Allah Ubangiji ya haskaka rayuwarku dan alfarmar shugaban mu Annabi Muhammad s.w.a.atare suka amsa masa da Amin Ya Allah, bazan iya misalta muku farin cikin Bintu ba ganin tabbas maganar Oga Abdallah ta tabbata, ga wata irin ƙauna ta bawan Allah da take ƙara mamaye jinin jikinta,gaidasa sukayi cikin girmamawa wanda bai bari sun ƙara wani magana ba ya ɗauko kuɗi a ɗaure cikin wata kyakykyawar leda wanda zaka iya hango abinda ke cikin ta, yace"matso nan jikata Faɗima!'matsawa tayi gabansa ya kuma kiran Abdallah shima ya matsa gab da Bintu hannun su Alhaji Baba ya kama ya haɗa dana juna ya sarƙesu daga bisani ya miƙa wa Bintu wannan kuɗin na hannun sa tasa ɗaya hannun ta karɓa cike da wani irin faɗuwar gaba wanda bata san dalili ba lokaci ɗaya jikin ta ya hau rawa,Muryar Alhaji Baba ce ta ratsa dodon kunnuwansu,Fatima karɓi wannan, sadakin Auren ki ne da Abdallah Allah Ubangiji ya baku zama lafiya ya kawo haske cikin rayuwarku. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 32 `` Hannun tane ya fara rawa saboda tsabar ruɗanin da maganar Alhaji Baba ta saukar mata, ji tayi tamkar an ɗora mata wani gungume man dutse akanta,wai dama da gaske Alhaji Baba yake ita zai ɗaurawa Oga Abdallah?anya kuwa wannan haɗin yayi?ya zatayi da farmakin Taufiƙa? Sannan taya zatayi ta cimma burin ta alhalin da igiyar Aure akanta?shin Abdallah zai tallafa mata kamar yadda fafi yasanar da ita?idan kuwa har zai tallafa mata to kuwa dole ta haƙura da Auren sa domin shima wata babbar dama ce agareta, wannan muskilalliyar Muryar tashi me tsananin daɗi ce ta katse mata tunaninta, Alhaji Baba mun gode Allah ya ƙara girma da lafiya,in Sha Allah zamuyi maka biyayyar da zakayi alfahari damu!'kut kaji wai zamuyi wannan ai aran baki ne,wato yau darar Alhaji Baba zaiyi dan tasan wannan muskilin ba abinda ya iya banda nunƙufurci da tsirawa mutane allura,duk gungunin da take da zunɓura baki akan idanun sa dan salon kallon Abdallah abin burgewa ne amma ga Bintu wanda shi kansa bai san yanayi ba,(amma koni alƙur an kallon na bani citta)Alhaji Baba yace"to masha Allah Ubangiji ya yiwa rayuwarku albarka ya baku zuri'a me albarka, Allah yasa wannan Aure ya kasance fitila ga rayuwar ku! da Amin suka amsa kana Bintu ta miƙawa Alhaji Baba kuɗi tare da cewa, Alhaji Baba kabar kuɗin nan Ni ban san me zanyi dasu ba!'yace"a'a Bintu wannan haƙƙin kine dole ki amsa idan yaso ga mijinki nan sai kibashi ya ajiye miki!'gyaɗa kai tayi kawai batare da ta kuma cewa komai ba,har zasu miƙe Alhaji Baba yace"au na manta ban tambayeka ba zaka zauna a gidan nan ne ko zaka tafi da matarka wani gidan daban? Abdallah ya ɗan rusuna yace"zamu cigaba da zama a ɓangare na har muga abinda Allah zaiyi!'hakan yayi kyau kuje Allah Ubangiji yayi muku albarka!'suka amsa da Amin kana suka fita daga falon, murmushin farin ciki Alhaji Baba ya saki tare da binsu da kyawawan addu'oi. Tarbar da Inno tayi mata ita tasaka kuka wanda dama a kusa yake,rungume ta tayi sosai tana ɗan bubbuga bayanta,cikin kalaman lallashi take cewa haba Batula to kuma meye na kukan bayan kina kusa dani, dan ban shiryawa rabuwa dake yanzu ba sai nayi miki biki irin na yargata amma ba yanzu ba akwai lokacin yana nan zuwa,idan kuma zan haɗa da suna ne shike nan!' Abdallah harara ya watsawa inno kana ya shigewarsa ɓangaren sa ya barta ita da sakalalliyar Bintun ta,hannun Bintun ta kama ta isa da ita har ɗakin ta da kanta ta haɗa mata ruwan wanka wanda sai da Bintu ta shiga taga kamar ba zallar ruwa bane dan sosai yake wani irin fitinan nan ƙamshi mai kama jiki da zuciyar wanda aka raɓa,sosai taji daɗin jikin ta, kwanciyar ta tayi saman tattausan gadon ta,ko minti biyu batayi ba wani nannauyan Bacci yayi awan gaba da ita. Tunda ya shiga ya gabatar da abubuwan da suka zama farilla agareshi, har ya kwanta saboda gajiyar dake tare dashi sai kuma wata gagarumar yunwa ta motsa masa, dan sai yanzu ya tuna rabon sa da abinci me nauyi tun kan wannan abin ya faru sai ƴan kame kame da yake dan bayajin zai iya cin kowane irin abinci idan ba na Bintu ba,ɗan tsaki yayi tare da tashi zaune ya dafe kansa dake ɗan sara masa,wayarsa ya ɗauka ya danna lambar inno bata jima ba kuwa ta ɗauka tare da yin sallama,amsawa yayi kana cikin takurawa kansa da magana yace"inno kisa yarinyar nan ta dafo ko noodles ne ta kawo min yunwa nakeji sosai!'inno tace"ai inaga sai dai Ni nayi maka dan Bintu tayi bacci!'ki tasheta inno yanzun nan!' saurin dafe kansa yayi saboda shikan sa bai san ya akayi ya faɗi hakan ba cikin san kawar da waccen maganar yace"inno bana son ki wahalar da kanki kawai ki tasheta bata da magagi!'murmushi inno tayi tare da cewa to gaskiya bazan sa ta girki daga farkawar ta ba sai dai idan na dafa maka in yaso na tasheta ta kawo maka, hakan yayi maka?shike nan inno yayi!'daga haka ya kashe wayar batare da yasan irin mamakin da yabar inno dashi ba,duk wanda yaga Abdallah ko yaji kalamansa dole zai gane halin da yake ciki amma a yadda ta lura sam shi bai san yanayin duk wannan ba,bai san yadda al'amuran sa suke tona asirin zuciyarsa ba,wani ƙawataccen murmushi ta saki gami da yunƙurawa dan zuwa kiching ɗin. Cikin bacci taji kamar ana tashin ta, cikin nutsuwa ta buɗe manyan idanunta da a yanzu suka bada wata kala ta musamman saboda baccin dake cikinsu,inno tace"yi haƙuri Bintu ta shi ki kaiwa Abdallah abinci, waya ya yimin yana jin yunwa!'tura baki tayi gami da gyara kwanciyar ta zata cigaba da baccin ta,inno tayi saurin ruƙota cikin lallami tace"haba Bintoton inno kinga fa cewa yayi na tasheki ki dafa masa amma saboda kar na tasheki sai ni nashiga kiching ɗin,kuma kin san dai halinsa tsaf zai biyoki har nan idan baki tashi ba!miƙewa tayi tana gunguni,ga bacci fal idonta amma saboda mugunta ance tana bacci wai atasheta,karɓar tiren da Inno ta zuba abincin tayi ta zura silifas saboda ba dai dai take ba sam ta manta da kayan da ke jikinta,ita kuma inno batace ta canja ba saboda taga cikin bacci take. Wani irin kuka ne ya kufcewa Taufiƙa lokacin da taga shigarta falon Abdallah daɗin abin baƙin cikin kuma kayan baccin da suke jikin Bintu wanda ko ita mace idan tacire hassada da kishi tabbas sai ta burgeta,gashi dai kayan ba wani nuna tsiraici sukayi ba amma yadda doguwar rigar mai shegen sulɓi da wani irin shep tabi lafiyayyan dirarran jikin Bintun shine abin kallo da burgewa, Siddiqa ce tayi saurin janye ta tare da toshe mata baki suka koma cikin ɗakinsu, Siddiqa tace"sai kin kawowa kanki maganar inno wadda itace zata iya fasa ƙahon zuciyarki!'cikin kukan fitar haiyaci Taufiƙa tace"wallahi bazan iya ba bazan iya kallon wannan macijiyar tana yawo tare da abinda nafi ƙauna arayuwata ba, tabbas Bintu kin janyowa kanki rigima da tashin hankali mara karshe dan sauna salwantar da rayuwarki!' Bintu baiwar Allah bata san ma tanayi ba, ita haushin ankatse mata baccin ta a yanzu shi yafi damunta,dan haka da haushin ta faɗa falon bata ganshi anan ba,dan haka cikin sauri ta ajiye tare da juyawa dan barin falon,cikin ƙasaitacciyar muryar sa yace"nan zaki kawo min!' ashe har yaji shigowarta kuma yana da yaƙinin abinda take shirin yi, Ai kuwa buɗe ƙofar ɗakin da yayi yaga tana sanɗar ajiyewa,da sauri ta ɗago ta ɗan dubesa kana ta duƙa ta kuma ɗauka ta biyo shi ɗakin babu abinda takeyi azuciyarta sai mita,tana shiga ta ajiye zata kuma fita nan ma dakatar da ita yayi da cewa ki tsaya ki tafi da kayan dan bazan kwana da ƙazanta ba!'ƙazanta kuma lallaima wannan mutumin wato kwanikan ne ma ƙazanta?kallonsa take cike da takaici saboda yadda ya basar kai bakace shiyayi maganarba, A hankali ta samu guri ta rakuɓe tana jira ya gama yangar cin abincin nasa. Wucewar mintuna huɗu zuwa biyar ya ɗan saci kallon ta sai yaga ta sheme ta cigaba da baccin ta hankali kwance,samun kansa yayi da zuba mata rikitattun idanun sa wanda har baisan iya tsawon lokacin da ya ɗauka yana binta da kallon ƙurilla ba,ɗan ƙaramin bakinta ya tsirawa ido haka nan yadinga jin wani abu na ratsa zuciyarshi wani irin mutuwa jikin sa yayi har wani sanyi-sanyi ne ke ratsa cikin jikinsa, lumshe idonsa yayi daga kallonta yayin da yarasa abinda ke damunsa wanda shi dai yasan bai taɓa jin Irin wannan yanayin tare dashiba,ɗan tsuka yayi tare da tashi ya shige toilet sabon brush yayi kana ya fito ya ɗauke kayan ya fita dasu kan dining table ya ajiye, Dawowarsa cikin ɗakin yayi dai dai da wani irin juyi da Bintu tayi, lokaci ɗaya santala santalan fararen cinyoyin ta suka baiyana,wani irin hajijiya yaji tana ƙoƙarin kada shi da sauri ya samu gefan gadon ya zauna tare da dafe kansa,ɗan satar kallonta yayi cikin sauri ya runtse idanunsa shifa sam bai saba ganin irin wannan abun ba, haka kawai tazo ta wani baje min aɗaki!'(Abdallah kaji tsoran Allah kaifa kace ta zauna tajiraka ka gama) tsakin ya kumayi kana ya yunƙura ya tashi, inda take ya ƙarasa tare da duƙawa runtse idanunsa yayi ya shiga bubbuga ƙasan carpet ɗin,amma tamkar ma nauyin baccin yake ƙara mata sai ma ƙafa da ta kuma ɗora masa a jiki,(kai dai kace bata da magagi ehe)janye ta yayi yana mamakin nauyin bacci irin nata wanda shi sam bai zaci tana dashi ba,da ƙyar ya samu ta farka amma duk da haka cikin magagi take,kamata yayi ya miƙar da ita tare da saita mata hanya,yace" tafi kije ki kwanta Sarkin bacci!'kamata yayi dan taimaka mata amma sai yaji gaba ɗaya ta yi kansa kasancewar suna tsaye ne a bakin gadon hakan yasa basu sha wahalar fadawa saman gadon ba,gaba ɗaya ta sakar masa nauyin ta saboda baccin da take sosai dan bata san komai yana faruwa ba, Bintu da shegen san jiki tuni tasa hannu ta kuma kanainaye shi tare da cusa kanta cikin ƙirjin sa tana shaƙar dadda ɗan ƙamshin jikinsa, rumtse idanun sa ya kuma yi tare da cewa ya Allah!'buɗe idan yayi tare da zubawa kyakykyawar fuskarta ido yayin da ita kuma take kwance saman jikin sa duk tabi ta duƙunƙune shi kamar wanda take tsoron kar asace shi,kasayin kataɓus yayi saboda yadda gaba ɗaya ta saukar masa da wata irin kasala da mutuwar jiki ki yayi ko ɗan yatsan sa ya kasa motsawa, kawai sai ya rabu da ita tare da ci gaba da kallon fuskarta, ko A baccin ma bakinta a ture yake saboda da haushin sa ta yi baccin samun kansa yayi da ɗan jan ɗan ƙaramin leɓenta yana mamakin rigimar Bintu ita damuwarta ta lokacin da Abu ya faru ne amma sam bata barin damuwa aranta sai dai idan A lokacin damuwar tazo ko ta tuna amma sabgoginta take hankalin ta kwance, (Abdallah ba haka bane Allah ne yabawa Bintu baiwa da wani irin hali na rashin barin damuwa tayi mata tasirin da har zata hana ta walwala, duk da tarin ƙaddarorin ta sai Allah ya sakamata tawakkali da amsar ƙaddararta a duk lokacin da ta kutso rayuwar ta) hannunsa akan tattausan lip ɗin ta wani daddaɗan bacci yayi awan gaba dashi,Abdubint asuba ta gari ayi bacci lafiya amma kar amakara sallar asuba. Labarin da Anty Nafisa taji na dawowar Bintu yayi mata daɗi sosai tana ganin matsalarta kamar tazo ƙarshe tanayiwa Bintu kallon maganin damuwar ta,ita Auren Bintun sam bai dameta ba dan aganinta bata ga abin damuwar ba wannan muskilin yaron da ba gane gabansa da bayan sa ake ba tsaf watarana zai iya sako Bintu,kuma da ɗin da ɗawa shi ba ahlin ALHAJI BALARABE bane balle abun ya dameta,kawai dai abinda ta sani ne dole a wannan lokaci Bintu tayi mata abinda take so dan haka ita kawai take jira ta gabatar da cikin ƙaryarta,daga tasamu abinda take nema babu wanda zai kuma jin ɗuriyarta sabuwar rayuwa zata buɗe ita da sabuwar soyayyar ta. Cikin juyi da tsananin daɗin bacci takuma shigewa jikin sa tare da ɗora kanta saman ƙirjin sa tan shaƙar dadda ɗan ƙamshinsa alokacin tuni ya farka saboda kiran sallar da aka ƙwala,shi da yake tashi kafin kiran sallar dan gabatar da nafila, amma yau shine da wannan nauyin baccin gashi idan baiyi da gaske ba zata iya sawa ya makara,a hankali yake ƙoƙarin zare ta daga jikinsa amma da ta kuma yin wani juyi sai gata gaba ɗayanta a ruwan cikin sa tare da zagaye hannuwan ta a ƙugunsa,runtse idanunsa yayi tare kiran Ya Allah!'wannan yarinyar so take ta kashe shi, bai mutu da guba ba gashi nan zata kasheshi da wannan juyin data keyi a ruwan cikin sa,daya ga dai da gasken makara yake neman yi kawai sai ya saka hannu ya ture ta kana ya miƙe,ita kuma a daidai lokacin ta farka tare da ware manyan idanunta ganin a inda take yasa tayi wata wuntsilowa daga kan gadon tare da zaro manyan idanunta, tace"na shiga uku anan na kwana?shine bai tasheni na koma ɗakina ba!' harara tabi bayansa dashi lokacin da ya fito daga toilet ya nufi ƙofa dan fita,bata daina hararar saba har ya fita daga ɗakin,tashi tayi ta ta fita, cikin sanɗa ta shige ɗakinta dan kar wani ya ganta amma Taufiƙa wadda tun daren jiya da taga Bintu ta shiga part ɗin Abdallah ta kasa ta tsare ko da rintse bata rintsa ba shi kuma wan da takeyi domin sa ma baccin sa yayi tare da matar sa hankalin sa kwance,komawa ɗakinsu tayi tare da ƙarfafa mummunan alwashinta akan Bintu. Alhaji Mansur ne zaune a falon Hajjah sai masifa yake zubawa kamar zai aro baki ya daɗa,Hajjah cikin takaici ta dubeshi tare da cewa kai kam Mansur ban san abinda yake damunka da yaran nan ba, duk kabi ka damu kanka kashiga cikin sabgar da ba taka ba kayi kane kane,shi Abdallah n da ya fito da ita bashi taiwa laifin ba? ina ruwanka da yaran da Ako da yaushe zai iya barin cikin ahlinka babu abinda ya tare maka wanda sai kaso zaka ganshi cikin gidan nan amma duk kabi ka damu kanka,Ni bana son wannan halin naka Mansur ka canja hali na gaya maka!'shuru tayi tana maida numfashi yayin da ran nan nata idan yayi dubu ya ɓaci da lamarin ɗan nata,ta rasa inda ya dosa cikin lamuran sa amma addu'a ita kaɗai ce zatayi maganin wannan matsala,cikin damuwa yace kiyi haƙuri Hajjah amma ina kan maganata bazaki gane abinda nake nufi ba yanzu sai nan gaba!'yana gama faɗa ya tashi ya barta,yayin da tabishi da wani irin kallo wanda yay kama da kallon tausayi, Ajiyar zuciya ta sauke tare da binsa da addu'o'in shiriya. Cikin iya taku da ƙwarewa akan aikinta Samira tace"dear gaskiya idan muna so musamu abinda muke nema sai kayi tunani akan mutanen gidan nan sosai,dan ta hakane kawai zamu iya fuskantar inda za mu ɗora aikin mu idan kuma ba haka ba zamuyi ta bulayine,kuma ina ganin hakan kamar wata sabuwar hanya ce da zamu kuma samun bayanai akan kishiyoyin ku, tunda duk abu ɗaya kuke yaƙin nema!'Alhaji Sama'ila yace"gaskiya Samira kina da fikira da ace aikin jarida kikeyi ko aikin bincike baƙarmin alfahari ma aikatarku zatayi dake ba, wannan tunanin da kikayi tunanine me kyau dan duk cikin waɗan da suke neman duniyar nan babu wanda muka sani, saboda idan mu ya rufe batasu muke ba!'Samira ta ja wani dogon numfashi kana tace"amma kunyi sake ai sanin su shine zai baku damar mallakar abinda kuke nema,saboda dolene kudinga sanin shirin su idan ba haka ba ku kuna zaune sai dai kuji sunyi nasarar mallakar koma meyene kuke son mallakan sa!'tsaye ya tashi yana zaga gurin cike da tashin hankali yace" me yasa bamu taɓa yin wannan tunanin ba? gaskiya mun tafka babban kuskure!'Samira tace"ai gyara shi ba Abune da zaiyi wuya ba tun da har munyi nasarar gane hakan yanzu tunanin mu zai juya ne kan masu nema wato kishiyoyin ku!' tafa mata yayi tare da cewa gaskiya Samira kin burgeni dolene nayi miki babbar kyauta dan haka na baki motar can da nazo da ita!'ido ta zaro cike da mamaki tace"da gaske kake Alhaji!'murmushi yayi tare cewa kin fi ƙarfin haka duk abinda nayi miki ban faɗi ba saboda kin kawo babbar gudunmawa cikin tafiyar mu!'wani murmushi ta saki kana tace"tabbas bazaka manta dani ba wanda sai nan gaba zaka kuma tabbatar da haka!' batare da ya fuskanci inda maganar ta ya dosa ba ya miƙa mata mukulli motar tare da cewa ki tafi da ita yanzu zanyi waya za'a zo a ɗauke Ni!' karɓa tayi tana cewa kamar na san da wannan babbar kyauta shiyasa ban zo da motata ba!'koda kin zo da ita har gida zansa akai miki kyautarki,daga haka ya tashi ya rakata har bakin motar kana sukayi sallama tana tayi masa godiya. Wata irin dariya ce ta ƙwace mata wato shi dai mutum duk girman sa da wayonsa bai isa ya kara da hukumar bincike ba,ga dai yadda tayiwa Alhaji Sama'ila wayo da ta shiga jikinsa,tabbas duk ranar da yagano ta zaiyi matukar mamaki saboda tanayin komai da lura bata zaƙewa yadda zai iya saka kokwanto akanta yanzu ta gama da wannan ɓangaren saura kuma jin sirrin abinda ya haɗa wannan rikitaccen al'amarin ita kanta tanason jin koda sunan abinda suke nemane, yanzun nan kuwa zata turawa Oga Abdallah recording ɗin da tayi saboda tana so yanzu yaji irin babbar nasarar da suka taka, lallai tana ji ajikinta baza su ɗauki dogon lokaci akan wannan case ɗin ba saboda duk wata hanya da ya kamata su kama dan samun nasara sun kama saura waccen tsohuwar Abigirl ɗin wadda tuni Oga Abdallah yasa ɗan leƙen asirin su yabi sahunta duk wani motsinta akan idonsa ne,gaskiya Oga Abdallah ɗan baiwa ne Allah ya hore masa basirar sanin makamar aikin sa shiyasa duk aikin da ya tunkara sai yaga bayan sa. Tun daga ranar da ta kwana a ɗakinsa bata kuma bari sun haɗu ba yau kwana biyu kenan da faruwar al'amarin,ta ɓangaren sa kuwa yanzu so yake ya haɗu da ita saboda manyan tambayoyin da suke ƙunshe cikin zuciyarsa,wanda a yanzu ne yake ganin ya dace ya sakata cikin wannan al'amarin,amma taƙi bari su haɗu ko meye dalilin ta oho, Yau rana ta uku kenan rabon da yasaka Bintu cikin ƙwayar idanunsa,haka nan yakejin son haɗuwa da ita saboda aikin ɓangaren ta da yake son fara gabatar da bincike akansa(hmmm su Abdallah manya daraktan wayo kayi sake dai fans ɗin ƙudurar Allah sun gano ka) Yau ɗin dai kamar yadda tasaba haka taje ta jera masa dinnar ɗin sa kana ta wuce tayi wanka tayi sallar isha tare da shafa'i da wuturi,wata kyakykyawar riga ta zura iya cinya mai shegen kyau wadda ta karɓi jikinta tamkar kasace ta ka gudu, dogon gashinta irin na fulani da sirkin Larabawa ta haɗa ta tufkeshi ya sauka kan bayanta fuskarta ce ta fito tayi fayau da ita yayin da jikinta yake wani irin santsi da ƙamshi mai tafiya da imanin mutum,wanda sam tunda ta dawo inno da Hajiya Babba basu ƙyaleta da kaye kaye ba, wannan ta bata wannan wannan ta bata wannan wai maganin baki ne da tsari, duk da wani maganin ma da ƙyar take iya sha,har ta kwanta sai ga kiran inno wai ta manta bata kaiwa Abdallah copy ba,ɗan tura baki tayi kana tace"Allah yasa dai bai dawo ba kalan naje ya kuma kamani ya wani riƙe ya sani kwana aɗakinsa dan iskanci kawai!'cikin wannan gungunin ta gama haɗa copy ɗin ta nufi falon,bayan ta ɗora doguwar buɗaɗɗiyar Abaya akan kayan baccin ta,tana shiga sai da ya tabbatar ta kai tsakiyar falon kana yasawa ƙofar lock batare da tasan lokacin da ya motsa daga inda yake ba,ƙin bari tayi su haɗa ido har ta ajiye masa cikin miskilar muryar sa yace"bani nan a hannuna!' miƙa masa tayi tana kawar da kanta gefe wanda hakan ne yasa taci tuntuɓe da ƙafarsa kawai sai jinta tayi cikin jikin shi batare da sanin sa ko sanin ta ba,da sauri ta ɗago dan tashi amma sai caraf fuskarta kan tasa hancinta na gogar nasa laɓɓanta na kan tattausan lip ɗinsa. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 33 ``` Da sauri ta miƙe tana yi masa hararar gefan ido,bai nuna ya ganta ba sai ma cewa da yayi ki zauna inason magana dake!'zaro manyan idanunta tayi cike da tashin hankali itafa bata son zama kusa dashi saboda zazzaɓin da yake sata, dan ji take wani sanyi na ratsa ƙasusuwanta har cikin ɓargonta,ɗan zama tayi daga can nesa dashi,batare da ya kalleta ba ya kuma cewa,ina wasa dake ne?girgiza kanta tayi kana ta miƙe ta koma gefan sa a mai makon ta zauna kan kujerar sai ta zauna ƙasa kusa da ƙafafunsa tare da sun kunyar da kanta sai jajjan yatsun hannunta take zuciyarta kuwa cike take da fargabar abinda zai ce mata ga kuma zazzaɓin kusancin ta dashi,zuba mata ido yayi na ɗan wasu da ƙiƙai wanda bazaka taɓa fahimtar kallon nata yake ba sai dai ita kuma a jikin ta taji alamun idanun sa akanta dan haka ta fara ɗan motsa bakinta a hankali kuma cikin shagawaɓaɓɓiyar muryarta tace"Ni kam dai bacci nakeji!'yaji ta sarai amma sai ya basar tare da ci gaba da tafa wayar sa,sai da yagama ƙulal da Bintu, kana cikin wata irin murya mai cike da nutsuwa da san nuna mata mahimmancin maganar da zaiyi yace" Duk abinda na tambayeki ina so ki nutsu ki bani amsa ta gaskiya idan kuma kika sake kika yimin ƙarya tabbas baza kiji daɗin hukuncin da zanyi miki ba!'ai tuni Bintu ta ruɗe iya ruɗewa dan bata shiryawa tutseyan Abdallah yanzu ba kuma bata gama shawara akan duk wani batu da zai tambayeta ba, cikin marairaice murya tace"dan Allah kayi haƙuri sai Allah ya kaimu gobe wallahi bacci nakeji sosai!'cike da alamun tashin hankali ta ƙara sa maganar,ba tare da ya dubeta ba yace"ki gaya min suwaye suka kawo ki cikin estate ɗin nan da kuma dalilin kawoki? duk da ya riga yasan wannan tun lokacin da yasa akabi masa ita tare da ɗauko masa tattaunawar su ita da Dije,amma yana buƙatar ƙarin bayani daga bakinta yana so ya tabbatar kuma yaji ko zata canja magana,ita kuwa Bintu tuni ta shiga wani hali na jin tsoran sanar da Abdallah wannan lamari duk da tanason sanar dashi amma idan ta tuna kashedin da suka yi mata duk sai taji tsoro ya kamata, fuskantar hakan da yayi ne yasa a matsayin sa na cikakken me binciken sirri kuma kwararre a wannan harkar yasa ya ɗan sassauta fuskar sa tare da muryarsa cikin tattausan harshe yace"Fatimah!'da sauri ta ɗago fuskar ta wadda take cike da fargaba ta dubeshi,saboda yanayin da kiran sunanta da yayi ya haifar mata ji tayi kamar shi ka ɗai iya kiran sunanta saboda salon da yayi amfani dashi gurin ambatar sunan,ganin tana kallon sa yasa ya kawar da fuskar sa saboda maganaɗisun da ke cikin idanunta wanda shine dalilin da yasa bai cika son kallon cikin ƙwayar idanun nataba, Cikin basar da abinda yakeji yace"ki kwantar da hankalin ki ki nutsu ki amsa tambayoyi na ki cire tsoron da ke ranki babu abinda zai faru,ko bakyason taimakon bayin Allah n da suke cikin matsala?da sauri ta kaɗa kanta kana tace"inaso mana!'yauwa to kinga dole idan haka zata faru saikin cire wannan tsoron dake addabar zuciyarki!'cikin gamsuwa da kuma samun ƙwarin gwiwa tace"Anty Nafisa ce da mahaifiyarta Hajiya ladidi sune suka kawoni, shuru ta ɗan yi kana ta faɗa mishi komai kamar yadda ta faɗa wa Dije har daga inda tazo babu abinda ta ɓoye masa labarin dai sak iri ɗaya da na Dije,yace"ki gaya min dukkan abinda ya faru daga lokacin da kika zo zuwa yanzu ina nufin har labarin gubar da aka saka min!kuka ta saka masa cikin kukan tace"wallahi ban san yadda akayi ba ban san komai ba!yace"Ni ba cewa nayi kin san komai ba kawai abinda nakeso dake ki gayamin duk wani shirin su da kuma abinda suke shiryawa da kuma bayanin da kika sani akan saka min guba da akayi!' Cikin nutsuwa ta bashi labarin ko mai hatta da haɗuwar su da sukayi da Dije da shirin da sukayi akan yaƙar magauta sai da takuma maimaita masa sai maganar guba wanda ta gaya masa gaskiyar abinda ta sani,abu ɗaya ne ta ɓoye masa aikin da Anty Nafisa takeso tayi mata, yace"ina wayarki take yanzu? shuru ta ɗan yi kana tace"Ni tun ranar ban sa ke ganin ta ba!'yace"a kwai ragowar abinda kika ɓoyen kuma idan baki gayamin ba na gaya miki zan yi matukar saɓa miki!'cikin lumshe idanu da tsananin baccin da ke cikinsu tare da fargabar da ta cikata,tace"Ni ka rabu dani bacci nakeji, Bintu tariga tayi alwashin baza ta gaya masa sirrin Anty Nafisa ba, saboda baza ta so Anty Nafisa ta kashe Oga Abdallah ba, lamarin cikin ahlin yana matuƙar bata tsoro tunda ta ga basu ɗauki cutar da mutum a komai ba,cikin wannan tunanin baccin da yake ta lallaɓowa idanunta ya samu nasarar surar ta, Abdallah cikin ƙosawa da yawan maganar yace"ke fa nake saurare!'shuru yaji daga ƙarshe ma sai ji yayi ta Kwaanto jikin ƙafafunsa,wanda shine da lilin da yasa ya ankara da abinda ke faruwa, ɗan tsaki ya saki kana ya shiga tashin ta dan ta koma ɗakinta. A hankali take buɗe idanunta wanda suka cik a fal da bacci,alama yayi mata da ta tashi,a hankali ta miƙe batare da ta ce komaiba ta nufi ƙofar falon a hankali ta murɗa ta fita yana tsaye yana kallon ta har ta maida ƙofar ta rufe,numfashi ya ɗan sauke kana ya kuma zama tare da ci gaba da aikin da yake cikin computer sa. Washe gari ta tashi cikin farin ciki saboda nauyin zuciyarta da ya ragu,sosai taji nishaɗi da nutsuwa, lokacin da ta kai masa break ɗin sa ya tafi motsa jiki dan haka cikin sauri ta haɗa masa komai tare da kimtsa masa sashen nasa,cikin sauri ta fito daga ɗakin ai yanzu kuma wasan ɓuya zata dingayi dashi dan ko mai zaiyi baza ta gaya masa ba, Tana shiga ɗakin ta tarar da Anty Nafisa zaune a bakin gadon ta, tana ta faman jijjiga ƙafa kana ganinta kasan tana tafe da rashin mutunci dan sai wani hura hanci takeyi kamar zata fashe,cikin sanyin jiki Bintu ta ƙarasa kusa da ita ta zauna a ƙasa tare da sunkuyar da kanta ƙasa,Anty Nafisa ta ƙare mata kallo sama da ƙasa kana tace"kin kyauta min Bintu na gode da abinda kika yimin!' cikin zaro manyan idanunta tace"me nayi kuma?au tambaya ta ma kike yi? gaskiya Bintu wuyanki yayi kauri naga alamar kin zama ƴar gari,yanzu har kin manta da yadda mukayi da ke? tunda kin samu waɗan da sukafi mu sakin kuɗi,shikenan sai mu ki saki namu aikin wallahi Bintu kin bani mamaki saboda yadda kika iya juyamin baya amma kikaje kika yiwa wasu,to ko meye hujjar ki tayin hakan?cikin damuwa Bintu tace"wallahi wallahi wallahi kinji rantsuwa ta har so uku bani bace na aikata ba, kuma ban san waye ba kuma ban zargi kowa da aikatamin haka ba na barwa Allahu jalla wa'azza dan shine kaɗai yasan sirrin dake ɓoye amma ki yadda dani bani bace ban san komai ba!'zuba mata ido Anty Nafisa tayi na wasu ƴan daƙiƙa kana taja Ajiyar numfashi tare da cewa shike nan na yadda mu ajiye wannan batun mu dawo kan asalin labarin domin yanzu shi yafi ko mai muhimmanci a gurina,shin zaki yi min abinda nasaki ko bazakiyi ba? idan har yanzu kina kan bakanki to nima ina kan nawa bakan bazan taɓa ɗaga miki ƙafa ba Bintu, saboda kin riga kin san sirrina kuma nasan tun da kika sani sai wani ya sani,dan haka ina sauraren ki wanne kika zaɓa? Wani irin gumi ne ya shiga ketowa Bintu ta ko ina bata da wata mafita a yanzu wanda ya wuce ta karɓi aikin nan inyaso daga baya sai ta nemi mafita,katse ta tayi da cewa kina ɓatan lokaci ki bani amsa!'a hankali Bintu ta ɗago kanta dake sunkuye tun ɗazu tace" na amince zanyi abinda kika sakani!'daga haka ta ƙunshe kanta cikin cinyoyin ta tana fitar da wasu zafafan ƙwalla masu tsananin raɗaɗi a zuciyarta, Anty Nafisa tayi wani shu'umin murmushi tare da cewa burina yana gab da cika, Bintu a hankali tace"nima nawa yana gab da cika insha Allah!'murmushi Anty Nafisa ta kumayi batare da tasan inda furucin Bintu ya dosaba,fita tayi da sauri ranta fari ƙal ji takeyi kamar burin nata ya gama cika, Bintu ta bita da wani mugun kallo tare da cewa insha Allah Asirinki ya kusa tonuwa da ɗai ɗai zaku fara girbar abinda kuka shuka wannan alƙawarin da na ɗauka ne!' hannun ta ta ɗora kan ƙirjinta tare da cewa Bintu ki kwantar da hankalin ki ki cire tsoro wannan yaƙin ba zai yiwu da tsoroba dole ki zama jaruma a filin daga. Taufiƙa ta kalli Farida tare da cewa idan kin san zaki lalata mana shiri ka wai ki bari tunda kina tsoron Abdallah, Ni dai nasan bazai kasheni ba kuma na gaya muku muna gamawa zamu gudu gidan Nana Babba!'Siddiƙa cikin yanayin tsoro tace"wallahi Ni dai babu Ni bazan dakar masa mata ba,saboda tun kafin ta zama matarsa idan mukayi mata abu rama mata yake ballantana kuma yanzu,dan haka Ni dai babu ruwana!'Taufiƙa ta kuma kallon Farida tare da cewa ke kuma fa meye ra'yinki? dake Farida kusan halin su ɗaya da Taufiƙa shi yasa batare da jin ko maiba ta amince da shirin da sukayi dan tarfa Bintu suyi mata shegen duka,daga nan su bar gidan sai komai ya lafa. Kallon ta take cikin tsananin baƙin ciki da tsana mara misali, ji take da zata samu dama da itace mace ta farko da zata fara ganin bayan ta, to amma yanzun ma bata fidda ran watarana wannan matar da har yanzu bata san ko wacece ba, zata kwashi kashinta a hannun ta ba,matar da take sanye da niƙab ta duƙa gaban mahaifiyar Bintu tace"lallai idan na bari kika cigaba da rayuwa a haka baƙaramin adalci nayi miki ba saboda ko ba komai zaki dinga jin labarin ɗiyarki kafin kiji labarin mutuwar ta wanda Ni kuma dashi ne zan samu damar gamawa dake dan nasan yadda kike son ɗiyarki da mijin ki zaki iya haɗiyar zuciya duk ranar da kika samu labarin barin su duniya!'Allah ba zai nuna miki wannan ranar ba sai dai keda zuri'r ki ku wula ƙanta amma ba dai kiga bayana nida ahlina ba,kuma ki sani cewa zalunci baya ƙarko dolene kuga ƙarshenku,kuma yaran da kuka zalunta sune zasu ga bayanki ke da duk wani me irin halinki, insha Allah Bintu ta fi ƙarfin shu'mancin ki saboda tana tare da Allah kuma shine zai zama garkuwar ta ya kareta a duk inda take!'wani gigitaccen mari ta watsa mata tare da cewa, mu zuba Ni dake da duk wanda yake son kawo min cikas akan samuwar cikar burina,bazan ƙyale ko da ɗan cikina bane in dai har zai kawo min matsala cikin burina ballantana kuma ke bafulatanar jeji sakarya kawai!'laila ta kuma ɗaga muryar ta tare da cewa bazan daina faɗar abinda ke raina ba kuma idan kin san wuta to tabbas Bintu ita zata zamar miki wuta me azabtar da rayuwarki kafin kije ki tarar da ta gaske me azabtar dake a lahira,in dai har bakiyi gaggawar tuba daga munanan aiyukan da kike aikatawa ba!'kuma ina mai kuma sanar da ke ki ƙyale ɗan uwana domin babushi cikin al'amarinki!wata muguwar tsawa matar me niƙab ta daka mata tare da cewa to idan baki sani ba ki sani ɗan uwanki shine babban jigo shine mutum na farko da idan na sassauta wa zan yi babban kuskure a rayuwata, ko dan baki san yaƙin da nasha gurin ƙwato ku daga hannun waɗan can mutanen ba?Laila ya kamata ki saduda ki zubda makamanki, ko karɓarku da nayi a hannun waɗan nan matsafan iya haka ya kamata ki jinjinawa shu'mancina ki san cewa Ni ba abar sa in sanki bace!'Laila tace" Aikuwa tun da kika kasa gane mutanen da suka ɗauke mu kika kasa gano babban shu'umin da kuke takara dashi wajen yaƙin neman Abu ɗaya to kuwa tabbas baki kai inda ya kamata kikai ba, kamata yayi kije cikin ESTATE ɗin ku ki binciko wannan takadarin da ya buwayi ahlinku tukun na, sannan kizo ki kama ƙananun ƙwari irin mu,kuma gashi duk kirarin da kike yiwa kanki kin kasa sanin inda mutum daya yake wanda dole shine zai haska miki hanyar samun cikar burinki, kinga kuwa kina da babban aiki agabanki tunda baki san inda ALHAJI Abubakar yake ba,kuma Allah ba zai taɓa baki nasara ba,dan haka ki sani wannan abun da kike kamar bulayi kike kina lalube a cikin duhu!'cikin matuƙar jin zafin maganganun Laila ta fita daga akurkin ɗakin, yayin da ta bada umarnin ci gaba da azabtar da Laila. Misalin ƙarfe bakwai na yamma ya dawo saboda yana son jin ƙarshen tattaunawarsa da Bintu, dan yasan baƙaramin aikin tane da ta gama abinda takeyi ta yi bacci ba,sai da yayi sallar isha kana ya nufi ɓangaren inno,yana dab da shiga hanyar da zai kashi ɓangaren wan da dole sai ka wuce ɓangaren wannan ɗakin kafin ka ƙara sa saboda shi wannan ɗakin ya kasan ce a tsakiyar ɓangarorin, sai ya zamana duk ɓangaren da zaka shiga sai ka wuce ta ɓangaren ɗakin, Kamar iska haka yaji wuce war Abu, juyawa yayi sai kuma yaga giftawar inuwar mutum al'amarin da yasa shi dakatawa daga niyar sa ta shiga ɓangaren inno,zubawa wajen ido yayi tare da ƙara nutsuwa ko zai kuma ganin wani abun, amma shuru kake ji sai da ya ɗauki kusan mintuna uku kafin ya bar wajen,amma zuciyar sa cike take da san ganin zahirin wannan inuwar,hakan ne yasa yaƙara sauri dan haɗuwa da Bintu tare da fatan Allah yasa batayi baccin nata na fama ba. A dai dai lokacin Bintu ta gama duk wani abu da ya dan ganci ogan nata,yayin da su Taufiƙa kuma tuni sun canja shirin su saboda sunyi tunani dukan Bintu ba mafita bace domin abin kansu zai'iya dawowa,wani yaron maƙotan su na ESTATE suka kira ya samo musu karara a makarantar su, dan haka sun shiryawa Bintu mugunta ta rashin mutunci kuma sun fasa barin gidan a cewar su dole su kalli rawar duskon da Bintu zatayi a cikin wannan dare,lokacin da suka zuba mata tana kiching dan haɗawa Oga Abdallah abincin sa, Tana shiga ta zame kayan ta, tare da waɗawa toilet, batare da tunanin ko maiba ta dauki sosanta wanda shima sai da suka zazzaga masa karara bayan wanda suka saka mata cikin bahon wankan,zuciyar ta ɗaya ta shiga cuɗa jikin ta, kaɗan kaɗan ta fara jin ƙaiƙayin sama sama tun tana daurewa har taji dai abin kamar gaba yakeyi,sauri tayi ta ɗauraye jikinta tare da ɗaukar tawul ta ɗaura,fita tayi daga toilet ɗin tana sosa dukkanin jikinta cikin ƙanƙanin lokaci ta fara fita daga haiyacin ta,gwanin tausayi haka ta shiga goga jikinta a bangon ɗakin ta rasa inda zata tsoma ranta gashi duk inda ta sosa sai ya tashi yayi wani irin ja kamar wanda zai tsatstsafo da jini,kuka ta farayi sosai tana kiran sunan Allah. Duk abin da ya kamata yayi ya gama sai dai kuma shiru kake ji Bintu ba ita ba alamar ta duk da dama yasan bawuyacin Abune tazo ɗin batare da ya kira taba,cikin azalzalar da zuciyar sa keyi masa ya yunƙura ya tashi,wata zuciyar tace masa mene ne dan kashiga dakin Bintu bayan tariga ta zama mallakinka, ɗan dafe kansa yayi tare da runtse idanunsa, haka nan yake jin wani irin yanayi atare dashi kamar ana taɓa wani ɓari na jikin sa,me ya hana yarinyar nan zuwa ne?ɗan takawa ya farayi har yaje bakin ƙofar sai kuma ya tsaya yana jin nauyi inno ta ganshi wanda shine dalilin da yasa ya kasa yi mata waya ta turo masa Bintun dan kar tayi wani tunani na daban ko ta fassara hakan da wata manufa,har ya juya zai koma amma sai yaji ba zai iya aikata hakan ba,dan haka ya juya tare da buɗe ƙofar yafita kai tsaye hanyar ɗakinta ya nufa wanda da ba dan yana ganin shigar taba da bazaice ga ɗakin ba. Kuka tayeyi sosai har da birgima duk ta yi wata iri shikansa tawul ɗin da ke jikinta gab yake da fita saboda duk cinyoyin ta a waje suke,gashi har ta rasa inda zata sosa, da ta sosa nan kafin ta ɗauke hannu wani ya fara,kai duk wanda yaga Bintu a wannan lokacin sai yaji ƙwalla cikin idanun sa. A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar tare da saurin faɗawa ɗakin saboda kukan Bintu da ya fara cin karo da shi cikin kunnuwan sa,a hankali ya ɗan lumshe idanunsa saboda yadda yakejin kukan can cikin jikinsa da zuciyarsa,ci gaba yayi da buɗe ƙofar har ya buɗe ta gaba ɗaya ganin da yayiwa Bintu cikin wannan halin shi ya gusar masa da duk wani tunani da rayuwar da ake yi cikin gidan da rikicin ahalinsa, cikin wani irin taku mai cike da ƙarfin izza wanda ya haɗu da fushin da yasame shi cikin wasu sakanni ya ƙarasa inda take kwance tana burgima tare da soshe soshe,durƙusawa yayi agabanta cikin wata irin murya me cike da sirri kan da har yanzu bai gane su ba,yace"me yasameki? Bintu da batasan da shigowar Oga Abdallah ba tayi wata irin zabura tare da afka masa kana cikin wata irin murya irin wadda take nuni da halin raɗaɗin da mutum yake ciki tace"wayyo Allah Oga Abdallah ka taimakamin jikina ko ina ciwo ƙaiƙayi ciwo zafiii!'ta ƙarasa faɗa cikin wani irin yanayi tare da ƙara shigewa jikin sa tana ƙara mustsika jikinta a cikin nasa, cikin wani irin yanayi da ya saukar masa alokaci ɗaya yace"ƙaiƙayi kuma a ina kika samo ƙaiƙayin!'cikin kuka ta kuma cewa wanka nayi ina cikin yi naji jikina yana ƙaiƙayi!'ta faɗa tana mai ɗaukar hannun sa tare da kaiwa jikinta tanaso ya sosa mata,shi kuwa Abdallah gaba ɗaya yanayin sa ya sauya da wani irin fillin da bai san daga ina ya taho masa ba, mamaki ne ya rufe shi to kuma me ya kawo ƙaiƙayi cikin toilet ɗinta?jin yadda tasakar masa wani azababban kuka yasa shi aje wannan tunanin a gefe ya fara neman hanyar magance wa Bintu wannan ɗan yan muguntar da akayi mata, Ɗaukar ta yayi cak tare da nufar ƙofa da sauri ya fita daga ɗakin yana dab da shiga falon sa yaji muryar Inno tana cewa Abdallah lafiya kuwa me ya faru da Bintu?cikin sauri yace" mata inno ƙaiƙayi aka sa mata cikin ruwan wanka!'bai saurari innalillahin da innon take zabgawa ba ya shige falonsa da Bintu ɗauke a hannun sa, Kai tsaye ɗakin sa ya nufa da ita ya shim fiɗeta saman tattausan gadon sa,da sauri ta riƙo hannun sa tare da cewa Ni dai ka sosa min zafi ƙaiƙayi wayyo fafina Bintun ka zata mutu Allah ka taimakeni na daina jin wannan azabar!'zama yayi gefanta yana cewa ke matsalarki ce kin cika raki idan kika ƙyaleni zan haɗo miki abin da zai gusar da kaiƙayin!'noƙe kafaɗa tayi tare da cewa Ni dai banaso ka sosa min kawai!'a hankali ya kai hannun sa kan wuyanta da yaga tana ta sosawa, shafawa ya shiga yi a hankali, cikin karaɗi tace"wayyo Ni dai sosa min zakayi ba shafawa ba!'dafa goshinsa yayi cikin yanayin damuwa yace"Ni ban iya susa ba saboda bani da farce!'ya faɗa tare da ƙoƙarin janye hannunsa cikin sauri ta riƙo hannun tare da mai dashi saman wuyanta, wanda saboda tsananin ƙaiƙayin da take ji bata san a yanayin da take ba na daga ita sai tawul, shammatar ta yayi ya tashi cikin sauri ya haɗa allurar gusar da ƙaikayi duk abinda yake bata lura ba sai da yazo ya kuma zama gefan ta ya ruƙo hannunta tare da janyo ta jikinsa gaba ɗaya, kafin tayi wani yunƙuri ya tsira mata allurar,kuka ta kuma fashewa dashi tare da bugun ƙirjinsa cikin yanayin anyi mata ba dai dai ba,kawai rungumota yayi tare da bubbuga bayanta a lokaci ɗaya kuma yana gyara mata gashinta da ya hargitse,a hankali wani irin bacci ya fara surar ta, sai can kuma ta firgita tare da saka wani kukan cikin haɗe fuska yace"meyene kuma dalla Malama ki mana shuru duk kin cika min kunne da wani shagwaɓaɓɓen kukanki!'cikin kukan tace" Ni dai ƙaiƙayi ka sosa min!'kafin ya ankara zafin ciwon ƙaikayi yasa Bintu ɗaukar hannun sa wanda lokaci ɗaya yaji shi cikin wani abu mai taushi da santsi,wanda a iya tarihin rayuwarsa bai taɓa jin abu mai taushin sa ba.... Ina mai ƙara nusar daku da cewa comments ɗin ku shine ƙwarin gwiwa ta,an fara shiga gundarin labari idan ba kwayin comments zan tsince waɗan da sukeyi na dinga tura musu ta pc More comments More confidence Alkalamin✍🏽 Fatima y Adam 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 34 ``` Runtse idanunsa yayi tare da kiran ya Allah me take shirin yi min ne? ƙoƙarin cire hannunsa ya farayi wani irin kuka ta kuma sawa me ƙarfi wanda dole yasa ya haƙura da ɗauke hannun sai dai ya rasa ta ina zai fara sosa mata wannan abu mai shegen taushi,yayi zurfi cikin tunanin ta yadda zai sosa mata,bai ankara ba yaji ta shiga mussika hannun sa akan bres ɗin ta, tare da cewa Ni dai kasosa min ƙaiƙayi nake ji!'cikin ɗauke numfashi Abdallah ya fara zagaya ya tsansa akan bres ɗinta, tabbas Bintu da tasan halin da tasaka bawan Allah aciki da batayi wannan sakalcin ba,tsayin mintuna biyu ya ɗan dakata tare da duban fuskarta dake kan cinyoyin sa,ashema tayi bacci wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke,kai wannan yarinya akwai shegen raki da shagwaɓa shi mamakin yadda akai yake biye mata wannan shirmen yakeyi,tunda yake bai taɓa tunanin zai iya tsayawa ya biyewa mace ba balle kuma me irin wannan shirmen,to amma kawai shi yana ganin dan zuciyarsa na tausayawa Bintu ne na kasancewarta marainiya wadda mugayen mutane suka kewaye ta da salon kaidin su,yana tunanin wannan shine dalilin. A hankali ya ɗauke hannun sa daga jikin ta tare da gyara mata ɗan ƙaramin towel ɗin dake jikin ta,yayin da idanuwansa suka kasa daina kallon kyakykyawar surarta me tsananin ɗaukar hankali baran ma wannan ƴan madai daitan lemukan da tasa ya sosa mata masu tsananin taushi da sheƙi, a hankali ya ɗan saki tsaki tare da cewa ƙwailar yarinya kawai babu abinda ta sani sai shirme da tsoro yanzu yauma ba zai ji komai daga bakinta ba kenan?Aikuwa insha Allah da safe baza ta bar ɗakin nan ba sai munyi magana!'zame ta yayi daga jikin sa tare da tashi ya faɗa toilet dan yin wanka,bayan ya fito ya saka kayan bacci masu kyau da taushi kalar sararin samaniya ya feshe jikin sa da turarukan sa na bacci masu cike da sirrika,falo ya fita ya ɗanci abinci kaɗan ya ɗora da kayan marmari kana ya koma ɗakin da Bintu take,fulo ya ɗauka ya sa a ƙasa ya kwanta can kuma yaji dai ba zai iya ba sai ya koma saman kujera nan ɗin ma kasa bacci yayi sai da ya dan gana da gadon kana ya samu nutsuwa,fuskan tar fuskar Bintu yayi tare da tsurawa ɗan ƙaramin bakinta ido wan da yasa yaji take yanayin sa yana sauyawa,wai meyasa kallon yarinyar nan yake dagula masa lissafi ne!'wan da shi bai ga abin damuwa a kan wannan ƙwailar yarinyar da ko ƙirgar dangi bata gama ba?rufe idanun sa yayi dan samun kariya daga kallon nata da yake saka shi cikin wani rikitaccen yanayi,sai dai kuma kafin ya gama mitar dake ransa, Bintu tayi wani kyakykyawan juyi wanda take ta nutse cikin yalwataccen ƙirjin sa tare da sa hannun ta gaba ɗaya ta zagaye ƙugun sa ta kuma ɗora fuskarta kan ɗan kewayayyen sajensa sai ya zamana goshinta yana kan haɓarsa,wayyo yarinyar nan da gaske so take ta kasheni ban cika burukana ba,numfa shinsa ya shiga saukewa kan goshin ta wanda ɗumin hucinsa yasa Bintu farkawa daga baccin ta, Zaro manyan idanunta tayi tare da saurin miƙewa zaune buɗe idanunsa yayi A hankali lokacin da yaji ta fizge jikinta daga nasa wani kallo ya shiga watsa mata,tura bakin ta shiga yi cikin gunguni tace"sai karinga barina ina kwana nan ɗakin ba sai ka tasheni na koma ɗakina ba!'nuna mata hanya yayi alamun ta tashi ta tafi ɗakin nata, ɗan satar kallon sa tayi taga yadda ya haɗe fuska babu alamun wasa, hakan yasa A hankali ta sauka daga kan gadon, har ta fara tafiya sai kuma ta tsaya cak kamar ance kalli jikin ki tana ganin a yadda take ta saka wata ƙara wadda sai da Abdallah yasa hannu ya toshe kunnuwan sa da idanun sa,da gudu ta dawo kan gadon tare da yaye bedsheet ɗin ta kanan naɗe jikinta cike da kunya da tsoro,gaba ɗaya ta rufe kanta bata ko san ƙara kallon Oga Abdallah,yanzu ke nan dama tun ɗazu A haka yake kallonta,A haka ya rugumeta ba kaya? na shiga uku ta faɗa da ƙarfi tare da sakin wani marayan kuka me cike da tsananin kunya da nadama yayin da ta tuna abinda tayi ɗazu cikin yanayin fitar hayyaci,hannunta tasa kan bres ɗin ta ta dafe shi tana mai jin tsananin ta kaicin kanta da har tayi sake Oga Abdallah ya taɓa mata bres, wayyo Ni wace irin yarinya ce haka ya Allah ka dubeni!'a fili take ta sakin maganganun ta, tana mai ƙara jin takaicin kanta dana oganta, Abdallah tun yana jin haushin yarintar Bintu har sai da abin ya koma bashi dariya haka nan ya dinga jin wani nishaɗin kallon diramar Bintun,jin shuru yasa ta ɗan leƙo da fuskarta amma sai karaf idanuwanta cikin na Oga Abdallah ai da sauri ta mayadda kan ta cikin bedsheet ɗin tare da ci gaba da kukanta,kwanciya yayi yana sakin wani ɗan muskilin murmushi wanda yayi matuƙar ƙawata fuskarsa da wani hasken annuri,tabbas Abdallah ya san idan yayi murmushi zai dinga kashe zuciyoyin mata da yawa ina ga shi yasa yake daga cikin abinda bai cika yi ba arayuwar sa,rufe idanun sa yayi kamar mai bacci tsawon mintuna uku yana sauraren sheshsheƙar kukan Bintu,ita kuwa jin shurun yayi yawa yasa ta kuma leƙo da kanta ganin kamar yayi bacci sai ta kuma tashi a hankali cikin sanɗa ta leƙa idanun sa har da sa hannu ta ɗan fifita idanun wai ta tabbatar yayi baccin ganin bai motsaba yasa ta kwashi fululluka ta shiga jerawa a tsakiyar su ta raba musu gadon biyu,ɗan kallon sa tayi tare da cewa dan ina jin tsoro ne amma da yanzu zan gudu ɗakina,tare da murguɗa bakinta,ko mawa tayi ta kwanta tare da runtse idanunta tayi addu'a ta tofa sai ta samu kanta da yiwa Abdallah addu'a shima ta tofa masa,kasancewar Bintu bata da wuyar bacci yasa cikin mintuna biyu ta koma baccin ta, A hankali ya buɗe idanunsa tare da zuba su kan saitin fuskar Bintu dake rufe cikin tattausan bargo,wani ɗan munafukin murmushi ne akan leɓanshi yayin da yake bin filon da ta jera da idanu yana ƙara mamakin sakarcin Bintu, amma kuma wani lokacin sai yaga kamar tana da tunani sai dai idan akace abu ya haɗa da yarinta dole sai a hankali,a hankali yasa hannu ya cire fulullukan ya maida su mazaunin su kana ya kwanta tare da lumshe idanun sa, shima addu'o'in yayi ya tofa mata, Bintu fa tana da matukar san jiki shiyasa take da yawan juyi cikin bacci matar da ta saka fulo tsakanin su sai gata garin juyi ta dawo da kanta har cikin ƙirjin wanda tayi kariya da fulo saboda shi,rungume ta ya kumayi tare da jan blanket ya rufe su daga haka shima wani bacci mai daɗi yayi awan gaba dashi,asuba ta gari Abdubint. Tun tana sauraran jin sakamakon abinda suka aikata wa Bintu har dai taji shurun yayi yawa, tashi tayi da niyar dubawa taga ko dai suma tayi saboda ƙayƙayin, zuciyar ta taji tayi wani irin fari tare da ƙara saurin shiga ɗakin tana fatan ganin Bintu cikin mummunan yanayi,turus tayi ganin babu kowa ɗakin toilet ta shiga ta duba nan ma babu Bintu babu alamar ta cikin sauri ta nufi kiching nan ma bata nan sai kawai tunanin ta ya bata Bintu ta gudu saboda azabar da taji tasan wannan ƙaiƙayin zai iya zautar da mutum na wani ɗan lokacin, da sauri ta koma ɗakin inno tana shiga taga inno tana nafilar dare ɗan zama tayi tana jiran ta ta idar da sallar,bayan inno ta idar ta dubi Taufiƙa tace"yaya dai cikin daren nan ince dai lafiya ko? Taufiƙa tace"Bintu nake nema bangan taba!' cikin wani tuhumammen kallo inno tace"mai zatayi miki Bintun ko kina tunanin muguntarku zatayi tasiri a gurin Bintu ne?idan ma wannan tunanin kike ki dai na dan Bintu kainuwace Allah ya riga ya kareta daga dukkan sharrin mai sharri,yanzu haka tana hannun mijinta yana can yana jinyar matar sa!'wani irin zufa ne ya shiga ke towa Taufiƙa tare da wani irin mummunan tashin hankali kallon inno tayi tare da cewa inno me yasa bakya ƙaunata me yasa kika fifita bare a kaina? inno ta katse ta da cewa mugun halinki shi na tsana bake ba da zaki gyara halinki da kinga soyayyata, Bintu kuma ba bare bace agurina kuma dalilin da yasa na fisonta halinta ne yaja mata dan haka dole naso Bintu fiye dake,kuma daga yau karki kuma yin tunanin zaki goge Bintu daga zuciyata saboda ta riga takafu na kuma yadda da ita ɗari bisa ɗari ki tashi ki bani ɗakuna zanyi bacci!'cikin wani irin kuka na tsantsan baƙin ciki da takaici tare da tsana me tsanani ta tashi ta fita daga ɗakin inno, tsayawa tayi saitin falon Abdallah kallon ƙofar takeyi tamkar wadda zata zuƙo Bintu ta ciki,wai me yasa rayuwa tazo mata da hakane me yasa duk lokacin da tayiwa Bintu wata mugunta take dawo wa kanta me yasa idan taso ganin Bintu cikin baƙin ciki da damuwa sai abin ya juya kanta? hannu ta ɗora a kanta tanajin kamar tayi ta zunduma ihu,to wai dama Abdallah yana son Bintu ne ko Yaya?me sukeyi idan suka shiga ɗakin?tunanin da tayi ne yasa ta zubewa a wajen tana mai ƙara sakin wani rikitaccen kuka mai sosa zuciya (wanda koni naji tausayin Taufiƙa wannan shi ake kira ƙaiƙayi koma kan masheƙiya haka nan kuma ramin ƙarya ƙurarrene kuma ƙarshen ta idan ka haƙa ramin mugunta kai zaka zurma) A wajen gari ya wayewa Taufiƙa har lokacin da Abdallah ya fito dan shiga ƙofar part ɗin Alhaji Baba dan tafiya msallaci,cike da ɗunbin mamaki yake bin Taufiƙa da kallo wanda sai yace tunda yake da ita da kuma haukan da takeyi akan sa sai yaune zai iya tan-tance kamanninta,ɗauke kanshi yayi lokacin da yaga ta zubo mashi jajayen idanunta da suka kumbura suntum ga rashin bacci ga kuka,ji takeyi kamar ta cinyeshi kowa ya huta Allah ne ya jarrabe ta da wannan ƙaƙƙarfar ƙauna me zafi dasa ta fita daga hayyacinta,cikin sauri ya bar gurin tare da waɗawa ƙofar da zata kaishi part ɗin Alhaji Baba,yana maiyiwa Bintu addu'ar neman tsari da wannan azzalumar yariyar,Taufiƙa ji tayi kawai gara ta shiga ɗakin taje ta kashe Bintu koda kuwa ita ma za a kasheta ta gwammace hakan da ace dai tana gani Bintu tana rayuwar farinciki ita da Abdallah,yunƙurawa tayi ta tashi ta ƙarasa bakin ƙofar falon, tana saka hannunta taji alamun a rufe ƙofar take wanda bata sani ba shi kuma Abdallah ya rufe Bintu ne dan kar ta tashi ta gudu bai samu labarin dayake buƙatar samu daga wajen ta ba,wata irin ƙwafa tayi wato ma har wani kulle kofa takeyi saboda samun waje,juyawa tayi cikin fushi da ƙuncin zuciya. Ita kuwa Bintu tunda ta tashi ta ta buɗe ƙofar falon yaƙi buɗuwa hakan ne ya tabbatar mata da cewa rufeta yayi,to ita yanzu da wane ido zata dubi Oga Abdallah me zata iya ce masa?gaskiya baza ta iya kula shi a halin da take ciki ba babu yadda zatayi haka taje ta ɗauro alwala tazo ta zurma doguwar jallabiyar sa wadda tayi mata tsayi sosai dubawa tayi ta ɗauki wani sabon towel babba ta rufa ta tayar da sallar ta, Tana idarwa ta cire rigar saboda yadda take taɗeta, towel ɗin ta mayar ta ɗaura kasancewar wannan babbane shi yasa ya rufe mata har ƙaurinta,zama tayi abakin gadon wanda tasan da aɗakin ta take da yanzu ta faɗa kiching,dole a yanzu tayi tagumi zaman jira, ko karatun da takeyi bata samu ba tunda babu suttura ajikinta sai dai tasbihi da sauran lazumukanta da tacigaba dayi cikin zuciyar ta, A wannan halin ya shigo ya sameta wanda bata san shigowar sa ba sai sallamar sa da taji akanta, wata irin zabura tayi tana neman gurin tsira daga tarkon da Abdallah ya ɗana mata,yana tsaye hannun sa soke cikin aljihun sa yana kallon yadda take ta dubi-dubi dan neman mafaka da ta rasa mafakar kawai sai ta fara tsiyayar da hawaye dan a hakikanin gaskiya tana matuƙar jin kunyar haɗa ido da Oga Abdallah,zama yayi kusa da ita wanda hakan ya kuma jefa zuciyar ta cikin wani irin bugu da fargaba,kawai sai ta sukuyar da kanta tana ta faman jajjan towel ɗin dake jikinta dan ya ƙara rufe mata jikin ta,cikin muryar sa da take fita ɗaɗɗaya da yanayin sa na muskilin namiji me tsananin aji da kwarjini yace"a karo na biyu zan kuma tambayarki idan kuma kika kawo min wasa sai na zaneki anan gurin tare da allura mai zafi guda biyar!'ɗagowa tayi ta ɗan saci kallon sa sai taga ashe idanunsa suna kanta,maida kanta tayi tare da cewa zan faɗa maka duk abinda ka tambayeni!'wai kuma sai yaji wani abu A ransa ganin yadda tayi magana cikin rauni, ya rasa me yasa yake da rauni da yawa akan yarinyar nan, cikin tausasa murya yace"ki nutsu ki cire tsoron ko mai ki bani amsa yadda ya kamata!'jin jina masa kai tayi tare da cewa to cikin rawar muryarta,ɗan gyara zaman sa yayi kana yace"wane irin aiki Nafisa ta sakaki kiyi mata san nan wanene mutumin da kike zargi suna aiki da Hajiya ladidi?da sauri ta dube shi cike da mamakin yadda akayi yasan abin da take ɓoye masa,ɗan ɗage mata gira yayi ganin yadda take masa kallon mamaki, sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya tare da cewa,Hajiya ladidi bata buɗe min zan can ba kawai tayi suɓutar bakine shiyasa nayi tunanin bayan Anty Nafisa a kwai wanda suke shirya wani al amarin tare, amma kuma nayi mamakin yadda akayi suke munafuntar junansu ita da Anty Nafisa,daga baya kuma nayi tunanin yadda zuciyoyin su suke babu abinda bazasu iya aikatawa junansu ba indai akan burukan sune,cikin ƙara yin ƙasa da murya ta fara bashi labarin yadda sukayi da Anty Nafisa tun daga farko har ƙarshe,cikin tsananin mamaki yake duban Bintun shi dama bai san komai a kan Nafisa ba kawai dai cikin salon aiki ne ya bigi cikin Bintun dan kar tayi tunanin ɓoye masa ko bashi labarin ƙarya,tashi yayi ya shiga zaga ɗakin hannun sa a dunƙule cikin juna kan sa ya kulle to amma idan hakane anya kuwa babu hannun Nafisa a saka masa guba?to kuma ta yaya zata kashe shi bayan cewa tayi sai Bintu taƙi yadda ko kuma ta gayawa wani sirrinta san nan zata aikata mata wani mummunan abu?kuma idan yayi la akari da yadda ita ma ta nunawa Bintu tana san sanin wanda yasa ta aikata wannan aiki sai kuma tunanin sa ya juya,kai wannan al'amari da matuƙar ɗaure kai yake dole ne ya bin ciki wanda ya saka masa gubar nan dan yana da yaƙini cewa shima zai zama jigo cikin binciken su zai ƙara faɗaɗa musu hanyar bincike cikin sauki tare da samun nasara,komawa yayi ya zauna inda ya tashi tare da duban Bintu da itama take ta binsa da kallo,yace"kin san me nake so dake? Bintu ta girgiza kanta ya ɗora mata da cewa inaso ki rage tsoro dan hakan shine zai kawo mana nasara cikin aikin mu,cikin sanyin murya tace"babu abinda zan iya taimaka maka dashi akan kyakykyawar niyarka ta binciko ruɓaɓɓun ƙwayayen dake cikin ahlinku?kallon bakinta yake dan baya iya jurar kallon ƙwayar idanunta,yace"kina ganin zaki iya taimaka mana?zan taimaka maka saboda raina fansane ga waɗanda aka cuta acikin ahlin nan!'a yanzun kallon idanun ta yake kai tsaye saboda yadda yaga wutar fansa na ci daga cikin kyawawan idanun ta yayin da suka cika da ƙwallar da take dauriya dan kar ta zubo saboda tun daga yanzu take san zama jaruma me yaƙi afilin daga,tunda yanzu ta samu tallafin gwarzan miji jarumi mara tsoro,dan haka ita ma ya zama dole ta cire duk wata fargaba domin fuskantar gagarumin yaƙin dake gabansu, cikin tausasa harshe yace"kin tabbata dai kin karɓi aikin da Nafisa ta baki ko?jinjina masa kai tayi,yace da kyau kin fara naki aikin tun daga yanzu da wannan ƙudurin nata zamu mamayeta,san nan ina so lallai zamu haɗu da Dije amma ba yanzu ba saboda haɗuwa da ita sai an saka lura da taka tsan tsan,ita kuma Hajiya ladidi cikin wayo zamu sa ta faɗi wanda suke tare dashi!'Bintu tace"oga a kwai tunanin da nayi akan mu amalar sirri tsakanin Hajiya ladidi da Anty Nafisa,taci gaba da cewa me zai hana tunda dukkan su basa son ɗayan su yasan sirrin ɗayansu mu kuma mubi wannan hanyar dan haɗa su faɗa, wanda Ni aganina zamu iya samun wasu muhimman sirrika ta hanyar tunzura zuciyoyin su,wanda zamuyi hakan ne cikin dabara batare da sun san daga inda abin ya fito ba!'duban ta yake cike da mamakin basirar ta tana da kaifin tunani tabbas ba karamin ci gaba zata kawo cikin wannan tafiyar ba,amma haka nan yake jin tsoron zaƙewarta cikin lamarin yana gudun kar wani abu ya yasame ta saboda ita yarinyace mai cike da ƙuriciya,hannu yasa ya shafa fuskarsa tare da jan dogon numfashi kana yace kinyi tunani mai kyau amma bake zakiyi wannan aikin ba!saboda me to wazaiyi?,ta faɗa duk alokaci ɗaya,haɗe fuskarsa ya kumayi tare da cewa kar su cutar dake kuma wadda ta san kan aiki zan saka tayi!'sakato tayi tana kallonsa yayin da ya tashi yana ƙoƙarin shiga toilet,har ya shige bata daina mamakin sa ba ita dai a iya sanin ta da shi bai cika bawa abu muhimmanci ba ballantana bada amsa amma yau shine ya zauna yake doguwar magana da ita har da su bata amsa kai harda ma ƙarin iyayi wai kar acutar da ita,ko da ike ai ɓangaren aikin sa aka taɓa wanda shi dama idan kaga dogon zan cen sa to akan aikin sane, taɓe baki tayi tana mai tuna ranar da tasan aikin da yake bayan aikin asibintin da tasan shine aikin sa, tasha mamaki lokacin da taga ID card ɗin sa tare da cikakken sunansa shi yasa abin bai dame ta ba tunda dama ta riga ta sani,ta shi tayi ta ɗauki ƙaramin tawul ɗin ta ta rufa kana ta fita daga ɓangaren. Wata irin mahaukaciyar dariya ya bushe da ita, tare da cewa lallai yaro bai san wuta ba sai ya taka yan zu aka fara wasan su atunanin su zasu iya rusani?tabbas kunyi gan yancin fara yaƙata domin bazaku taɓa cin nasara akaina ba,haƙiƙa naji daɗin wannan himma taku domin ta haka ne zan cimma burina dole kune ginshiƙin burina daku zanyi garkuwa domin sanin inda wannan ɓoyayyan sirri yake wanda ake tunanin bamu san dashi ba,hhhh ya kuma bushewa da wata ibilishiyar dariya tare da cewa Ni da nake da Jack ga kuma shugaba ai babu abinda zai gagareni samu adunayar nan (wa iya zubilla Allah ka shirya waɗanda suka ɓata dan Alfarmar shugaba)duk ta inda kuka ɓullo sai na ɓullo muku, Abubakar dole ka buɗe baki kasanar dani inda sirrin nan yake a ina aka ɓoyeshi?lokacin faɗarka yayi saboda fansar rayuwar yaronka da ƴar ɗan uwanka, lokacin ta shinka ya kusa saboda biyan buƙatata da nasamu kuma shikenan zan ƙara saka domin nasamu abinda ya hanani kasheka,ɗan taɓa kan kyakkyawan mutumin da yake a daskare kamar ƙanƙara yayi,sai ga wani irin farin hayaƙi na fitowa daga jikin sa idanun sa ne kawai keyin motsi sai bugawar zuciyar da ita ke nuni da har yanzu yana raye, zagaye shi ya shiga yi yana tafa hannayen sa ya cigaba da cewa babu wanda zai mallaki wannan abu idan har ina numfashi,duk masu bulayi da neman inda kake kallon su kawai nakeyi waɗan can mutanen da wani shu'umin ya sace su babu abinda zasu karan kawai dai ina ƙoƙarin rage yawan sune saboda zasu iya zama bara zana cikin samun farin cikina, Laila da ɗan uwanki duk ranar da na haɗa ido da wanda ya ɗaukeku gaba ɗayan ku zan haɗa na kashe bana so ki bayyana cikin ahlin ALHAJI BALARABE dake da shegiyar yariyar ki,duk da cewa ita ta bayyana amma tunda babu wanda yasan da labarin auren uwarta babu ta yadda za ayi ajingina ta da ahlin ESTATE ,kafun suma lokacinsu ya ƙara so ita da gwarzan mijinta,dariya yakeyi cike da farin cikin yana samun duk yadda yake so, tsarin sa yana tafiya dai dai da yadda ya buƙata,wani farin cikin ma sai nan gaba. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 35 ``` Tun ranar da Laila ta gaggaya mata maganganun nan masu zafi da nusar da ita abinda ta manta, bata ƙara samun nutsuwa ba gaba ɗaya hankalin ta atashe yake, tabbas ta amince da maganar Laila basu ya kamata ta tsare akan wani ƙaramin dalili ba ko da yake shima wani jigone sanin wannan mugun mashirikin na cikin ahlin ALHAJI BALARABE to amma ita Laila da ɗan uwanta sun ƙi bata haɗin kai su sanar da ita ko waye wannan mutumin dan sanin sa shima yana da matukar muhimmanci dan tana da tabbacin zai iya sanin inda aka ɓoye Abubakar, duk iya takunta a wannan karon ƙwaƙwalwarta bata aiki duk wanda zata yi tsammanin yasan inda Abubakar yake ba sannan inda zata lalubo shi ba bayan wannan dai shi umin da takasa gano waye duk iya binciken ta kuwa, da hakan ta jinjinawa taƙadirancin sa,ta riga ta sani kamar yadda ta iya takun ta haka suma ragowar masu neman suka iya nasu takun,babu wanda ta iya ganowa sai ƴan tsirarin mutanen nan su Alhaji Nasir da kuma Hajiya ladidi,to amma kuma yanzu duk bata tasu take ba dan ta riga ta gama bincikenta akansu tasan suma har yanzu lalube suke,shine dalilin da yasa ta kuma riƙe wuta gurin su Laila dan tayi yaƙinin sun san mutumin nan sai dai ta rasa dalilin su na ƙin gaya mata ko wanene,iska ta fesar daga cikin bakin ta dole Sayyid ya kamata ta kira tunda shi yayi mata binciken Bintun da waɗanda suka kawota gidan ta dalilin hakane yasa ta gano Hajiya ladidi da ƴarta Nafisa,wani shu umin murmushi tayi yayin da ta tuna shikansa Sayyid ɗin bai san fuskarta da Muryar ta ba balle ya gane WACCE ITA,dole shi zata saka yasawa ubansa ido cikin hikima zata sashi yayi mata aiki akan ubansa,har yanzu da akwai ragowar ƙwarin gwiwa atare da ita kuma baza ta taɓa sarewa ba har sai taga abinda ya turewa buzu naɗi, Ta ɓangaren su Alhaji Nasir tare da tawagar sa su Baffa Hashir sun miƙa cikin binciken kishiyoyin su, kamar yadda Samira ta tunatar dasu sai dai kuma basu manta da ci gaba da neman inda mukullin samun sirrin su yake ba wato Alhaji Abubakar,haka kuma sun kasa ɗauke ido daga kan Abdallah saboda suna matuƙar tsoron sa,kowa nema yake yi ido rufe, yayin da ta gefe Samira ta cika da ɗaukin san Alhaji Sama'ila ya sanar da ita wannan sirri,kamar dai yadda suka saba yauma sun haɗu a mahaɗar da suke haɗuwa,Samira cikin yanayin jimami tace"har yanzu babu wani da kuka samu wanda kuke tunanin yana da hannu cikin yaƙin nema,ɗan shuru yayi kana ya ɗan numfasa tare da cewa a kwai wanda muke zargin ana sashi bibiyar mu da kuma saka mana ido a dukkan al'amarin mu!'wani irin bugu zuciyar Samira tayi tare da zaro ido waje,Alhaji Sama'ila ya cigaba da cewa abinda yasa nace miki saka nace miki sakashi akayi shine saboda bai san komai akan wannan sirrin ba sai dai idan faɗa masa akayi,cikin zaƙuwa da kuma fargaba Samira tace"to waye wannan?kai tsaye yace" da ita Sayyid ɗan gidan Mansur!'wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta saki dan da atunanin ta ko ya gano wanda Oga Abdallah yasa shi aiki akan su ne,cikin mamaki tace'Sayyid kuma? tare da ƙara duban wayarta adabarance dan ta tabbatar bata kauce daga kan recording ɗin da take yi ba,yace"Sayyid shine wanda nake zargi abinda bansani ba kawai shine Mansur ɗin ne yake saka shi kokuwa wasune daban?jin jina kai Samira tayi tare da cewa shi kaɗai kake zargi yanzu?yace shikaɗaine kafin binciken mu ya kuma samo mana wani!'da kyau Alhajina yanzu zakaga komai naku yana tafiya kan tsari daga nan ma sai kuga kun samo wannan abu mai mahimmanci da kuke nema!'yace"tabbas hakane amma kuma wani abu da ban sanar dake ba Samira shi wannan abu da muke rububin nema mutum ɗaya ne yasan inda yake kuma an sace shi kusan shekaru talatin kuma tunda aka ɗauke sa ba akuma jin ɗuriyar sa ba hatta da ESTATE babu Wanda ya kuma tunawa shi,to a yanzu dole sai mun same shi kafin mu sami abun da muke hari dan shi kaɗai ne zai nuna inda aka killace abun!'jinjina kai kawai Samira takeyi saboda Al'amarin yayi matuƙar taɓata,tace"baku san inda yake ba kenan?da mun sani Samira ai da tuni an wuce gun kuma da yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba!'hakane to yanzu wane mataki kuka ɗauka dan cigaba da neman sa?Samira kenan ai baza mu zauna ba saboda duk abinda kikaga munyi dan shi mukeyi da zarar mun sami inda Abubakar yake,shike nan kakarmu ta yanke saƙa!'to Alhaji meye tabbacin ka na za a sameshi a raye?wani makirin murmushi ya saki kana yace"ai Samira Ina tabbatar miki da cewa da ankashe Abubakar da yanzu an fara kashe ƴan uwansa da mahaifin sa,Bama shi kaɗai ba duk wanda yake da ƙudurin samun wannan abu to wannan shine shirin sa na gaba koma waye ko su waye,dan magadan wannan abu su za akashe ko muma burinmu kenan,shi yasa nace miki ba akashe Abubakar ba,kuma Abubakar yana da matukar taurin kai ba zai faɗi inda abun nan yake da wuriba ba!'Samira da al ajabi yaƙi barin fuskarta da zuciyarta tace"ya akayi ku kasan da wannan abun kuma meye shi wannan abu haka da ake irin wannan ta asa akan sa? murmushi yayi tare da cewa Samira bazaki gane ba wannan amsar ba yanzu zaki san ta ba,amma,abinda zan gaya miki shine shi kan sa me abun bai san sirrin ya fita ba bayan Abubakar bai sanar da kowa ba, yadda akayi muka sani shima zaki sani nan gaba!'batayi masa musu ba saboda gudun karya ganota, wannan ma da ta samu ba ƙaramin babban nasara suka samu ba yanzu za ta kaiwa Oga Abdallah sai suji mataki na gaba da Yakamata su ɗauka,daga nan ta daure suka ɗan sha copy tare amma ji take kamar tayi tsuntuwa ta ganta office ɗin Oga Abdallah. Babbar macece wadda zata iya kaiwa sa ar inno zaune take bakin madafa daga dukkanin alamu dai girki takeyi,amma kana kallon fuskarta zaka iya hango ɓoyyayyiyar damuwar da ta kasa bushewa daga zuciyarta,wata makiman ciyar matace ta fito daga wani ɗaki a ƙiyasina baza ta wuce talatin da biyar zuwa da zuwa da bakwai ba,da sauri ta ƙarasa gaban matar dake gaban madafi tare da cewa haba Hajjo me yasa baki bari na fito ba kin san ba lafiyar idone dake ba amma kike zuwa gaban hayaƙi!'kama hannunta tayi tare da miƙar da ita tsaye sai da ta kaita har kan tabarmar dake shimfiɗe a makeken tsakar gidan,zama tayi akusa da ita,kana cikin tausayin surukar ta ta tace"dan Allah Hajjo ki daina yawan damuwar nan bana so ciwon ki ya tashi kin ga dai yadda Alhaji Umar yake damuwa idan yaga halin da kike ciki,bayan shima ba cikakkiyar lafiya ce dashi ba, gamu nida ƴan biyu duk ba mason rasaki saboda ke kaɗai ce muke gani muji sanyi idan kika bari lalura taci ƙarfin ki tabbas zamu shiga damuwa!'wani wahalallan numfashi ta sauke kana cikin muryar da take cike da damuwa tace"Asma'u ina matukar ƙoƙarin da dauriya wajen danne abinda ke taso mun,babu yadda zanyi ne Asma'u ƴara biyu har da jika babu su babu labarin su,kema nasan dauriyar kikeyi amma ki sani Ni dake a kwai banbanci ke da ragowar ƙuruciya atare dake Ni kuma girma ya fara cim mani dole yanayi na danaki su banbanta,hannu tasa ta share hawayen da suke ta ambaliya kan fuskarta tare da cewa,kullum addu'a ta da fatana shine inga Laila da Sulaiman,fafi take nufi (afwan ban faɗi sunan fafi na asaliba sunan sa Sulaiman)ina son ganin su kafin na bar duniya! Asma'u tace"Hajjo insha Allah burinki zai cika zasu dawo gida, kamar yadda suka tafi tare haka zasu dawo tare harma da jikallenki, ta ƙara sa maganar cikin san kautar mata da damuwarta. Tunda ya fara sauraran recording ɗin da Samira tayi na tattaunawar su da Alhaji Sama'ila,ya rufe idanunsa yana mai ƙara tasbihi ga Ubangiji tare da gode masa da yashirya rayuwarsa ya ƙawata zuciyarsa da tsoron sa da kuma ƙauna ta masoyin da babu kamarsa Annabi Muhammad swa,jin maganar ta tsaya yasa a hankali ya buɗe idanunsa da suka sauya kala saboda ɓacin rai me tsanani da ya mamaye zuciyarsa,duban Safwan yayi tare da cewa ina so a yau din nan a kamomin Sayyid ku kaishi can gidan sirri ku ɓoyeshi,ina so ku kula da aikin ku bana buƙatar Kowa yaga lokacin da kuka ɗauke shi!' Safwan yayi salut ɗin sa tare da cewa angama Oga insha Allah baza asamu kuskure ba!'jin jina kan sa yayi tare da mai da dubansa kan Samira yace"Samira na gode da taimakon ki!'da sauri ta katse shi da cewa haba meye na godiya kar ka manta da wannan aiki na ne kuma saida na ɗauki alƙawari kafin na fara, dan haka ya zaman min dole na jajirce dan taimakon al umma!'na sani duk da haka kin cancanci lambar yabo aikinki yana kyau sosai!'godiya tayi masa kana sukayi sallama ya sallame su,shima daga nan ya kira Yahya su tafi dan yana son leƙawa asibiti. Bintu tunanin ta hanyar da zata samu ta isar da saƙonta gurin Hajiya ladidi da Nafisa,ne hanyar da zata fara tarwatsa dangantakar su ko dan ta samu abin da takeso duk da tasan shiga tsakanin ɗa da uwa sai Allah, amma tanada yaƙinin Allah bazai kamata da haƙƙin su ba, tunda neman samun warware wani babban ƙulli take wanda zaiyi sanadin tar watsewar mutane da dama da kuma shiriyar wasu da dama, gashi bata san inda wayarta take ba tun ranar da aka kaita station, turo ƙofar ɗakin da akayi ne yasa ta dakatawa daga sintirin da takeyi tare da juyowa alokaci ɗaya tana kallon Anty Nafisa wadda ta shigo,ƙarasowa tayi gaban Bintu tare da miƙa mata wayar ta, Bintu kallon ta take cike da mamakin yadda akayi wayar taje hannunta ,kamar tasan tunanin da Bintu takeyi, tace"nima a wajen Hajiya Babba na karɓo lokacin na shiga gaida ta sai na tarar tana cewa Rahima tazo ta kawo Miki shine nace ta kawo zan baki nima nan nayo kinji dalili kuma nima rashin wayar taki ya dameni gashi babu halin na baki wata!'hannu tasa ta karɓa tare da cewa na gode nima yanzu tunanin wayar nake saboda ina buƙatar magana da Hajiyarki saboda...sai kuma tayi shiru da alamun kamar tayi suɓutar baki a zan cen nata, Anty Nafisa tace" ina jinki saboda me?shuru Bintu tayi tana ɗan kauce kauce alamun ta dai ya nuna rashin gaskiya,cikin da bar bar cewar zance tace"a'a babu ko mai fa wani saƙone da ban!'zuba mata ido Anty Nafisa tayi da alamun rashin yadda cikin idanun ta sai dai kuma ba tace komai ba amma yanayin ta ya nuna akwai Magana abakinta. Bintu ta kawar da wancan zan cen da cewa Anty Nafisa a kwai wani abu sabone? cikin wani yanayi Anty Nafisa tace"Bintu ai ko da yaushe gidan nan baya rabo da sabon labari wanda yake ƙunshe da sabuwar manaƙisa,na san da cewa burina ya sha ban ban da sauran burukan da ke zuciyoyin gidan nan,dan haka Ni bani da damuwa da sanin abinda suke hari burina kawai shine buri, tunda bani da kishiya ta wajen tarayya da abinda nake so to duk me sauƙine,shi yasa kikaga ban cika azarɓaɓi cikin aikina ba,dan nasan burina zai cika,to amma kuma yanzu wannan tunanin ya rushe saboda abinda na gano wanda Gara ace ina da masu tarayya akan dukiyar mijina, Bintu ta ɗan numfasa kana tace"yanzu me kike so dani ina cewa Ni aikina sai nan da watannin da kika ƙaiyadewa cikin ki zan fara? Anty Nafisa tace"hakane,amma akwai abinda yake son shigowa cikin burina shi yasa nake ganin gwara tun kafin cikin yayi ƙwari mu yi abinda ya dace kawai zaki aiwatar da aikinki acikin wannan lokacin!'duk da cewa Bintu ta girgiza da jin sauyin ra ayi daga Anty Nafisa amma sai ta dake ta nuna jarumta akaron ta na farko,dan haka cikin ƙwarin gwiwa tace"to amma kina ganin hakan ba zai zo da wata matsalaba,kuma meye abinda yake shirin kawo miki Barazana cikin burinki?wani irin kallon anya na gaya miki tayiwa Bintu, kana kuma tace"ina ganin babu wata matsala da zamu fuskan ta ki daina wannan tunanin fatan nasara ko da yaushe nakewa kaina ba faɗuwa ba,san nan kuma babu buƙatar kiji dalilin da yasa nake son janyo aikin nan kusa,kawai kiyi abin da nasaka ki ba wai tambayar abinda bai zama hurumin ki ba, wannan sirrinane da idan ba Hajiyata ba babu wanda yasani a duniya!'da sauri Bintu tace"shike nan na gamsu da bayananki amma nima ina da shawarar da zan baki!' Anty Nafisa tace"ina sauraran ki bamu da lokaci me yawa!'Bintu ta ɗan yi ƙasa da murya tare da cewa me zai hana ki fara ɗaukar matakin karɓar duk wasu manyan kadarorin mijinki cikin dabara kisa duk ya saka miki hannu su zama mallakin ki kafin mu kai ga sheshi"zubawa Bintu ido tayi cikin zurfafa tunani da mamakin manufar Bintu a kan wannan shawara,cike da mamakin tace"Bintu meye manufarki ta can ja min tunani?ɗan waige Bintu tayi tare da ƙara tabbatar da babu wanda yake musu laɓe, kana ta kuma yin ƙasa da muryar ta tace"manufata saboda koda idan ya mutu ƴan uwansa zasu iya handame dukiyar ke kuma wata ƙil dun haƙilon da kikayi akan dukiyar ya tashi Aban za saboda na fahimci gidan nan kowa haɗamammene basu da godiyar Allah duk irin tarin dukiyar da mahaifin su yake da ita amma kullum burin su shine ta yaya zasu ƙara arziki,ina ganin idan kika tsaya kallon ruwa tabbas kwaɗo zai iya yimiki ƙafa!'ta ƙara sa maganar tanayiwa Anty Nafisa wani kallo tare da fatan karɓuwar shawararta batare da tayi dogon na zari ba,ai kuwa cikin wani irin mamakin yadda akayi Bintu tayi wannan dogon tsinkaye,Anty Nafisa ta rugumota tare da cewa U are very smart, Bintu kina da fikira tabbas shigowar ki gidan nan ba ƙaramin cigaba da nasara zai kawowa rayuwata ba,na amince da sha wararki sai dai kuma a inda gizo ke saƙar yadda za ayi yasaka min hannun tunda mijina ba shanyayye bane atsaye yake da ƙafafun sa!'Bintu tace" masha Allah anzo gurin Nafisa kinga ta kanki tunda kika yadda dani sai na kawo ƙarshen makircin ku,taɓa tan da Anty Nafisa tayi yasa tayi firgigigit, Anty Nafisa tace"ya kikayi shiru?a hankali Bintu ta sauke doguwar ajiyar zuciya kana tace"mafita nake nemo miki!' cikin zaƙuwa Nafisa tace mecece mafitar? Bintu tace"mafitar itace in dai har kin yadda dani kuma kin gansu ba dan kuɗi zanyi miki aiki ba sai dai taimakon rayuwata da rayuwar waɗan da suke jirana dan taimakon ta su rayuwar, shine ina so ki dinga bi a sannu a hankali kina sace kadarorinsa, Ni kuma ki dinga bani zansa ka ayi fake ɗin takardun saiki maida masa fake ɗin ke kuma ki riƙe original ɗin!'ɗan jim Nafisa tayi daga bisani kuma taja wani dogon numfashi kana tace"kina da hanyar yin hakan yadda baza aganomu ba?da babu ai bazan kawo wannan shawarar ba!' ta faɗa tana ɗan goge fukarta, Anty Nafisa tace"ba dai Ni zaki bawa original ɗin ba idan akayi fake ɗin?tace"haba Anty Nafisa kamar bakya gane yaren da nake miki, ke zan bawa mana kinga idan ko mai ya faru koda sun so cutarki ke tuni kinyi maganin su,guduwa zakiyi abinki baruwan ki da tuhuma dama Ni ba asan meke tsakanin mu ba ina ga wannan hanyar itace mafi sauƙi wajen karya ƙwaɗayayyu!'Anty Nafisa tace"tabbas Maganar ki haka take bazan yi ƙasa a gwiwa ba tun daga yanzu zan fara nema da lalube tunda baya ƙasar!'juyawa tayi cikin sauri tana cewa Bintu bazaki ƙara ganina ba sai da wasu daga cikin kadarorin mijina!'daga haka ta fita daga ɗakin. Wani irin tsalle tayi tare da faɗawa saman gadonta ta rungume fulo tana sakin wani murmushi me cike da samun ƙarfin gwiwa da kuma hangen nasara wadda take tun karo su nan ba da daɗewa ba Anty Nafisa kin gama zuwa hannu watan cin ubanki da faɗuwarki yayi wannan farin cikin da takeji kamata yayi acce da me taya ta,babu wanda ya daɗi mata sai ogan ta shi yakamata ya ji wannan sarasa da suka samu ita kanta tayi mamakin yadda wannan tunani yazo mata lokaci ɗaya tare da tsara yadda zata tafiyar da komai cikin kwanciyar hankali da nasara. Duk mintuna sai ta duba agogon dake manne jikin bangon kiching ɗin Allah Allah takeyi ya dawo ta zaƙu ta sanar dashi wannan labari, ɗan tura baki tayi cikin karaya take cewa yanzu haka ma ya gwaleni ko yaƙi nuna farin cikin sa kuma ba lallai ya yaba min ba,bazan ma faɗa maka ba na fasa!'ta ƙare maganar tare da murguɗa ɗan ƙaramin bakinta. Kamar yadda ya saba saida ya tsaya ya gabatar da sallar magriba da isha kana ya nufo cikin gidan,kai tsaye part ɗin sa ya shige bayan yayiwa inno sannu da gida. Baƙaramin mamaki yayi ba ganinta a falon nasa amma sai ya basar yayi kamar bai ganta ba,ɗan harara ta watsa masa ƙasa ƙasa tana aiyana wa aranta dama tasan wulaƙanci zata sha gashi tun daga yanzu ta fara gani,ita sam bata ga wani abun faɗa da haƙilo da Taufiƙa takeyi kan wannan muskilin ba,wanda magana ma sai ya gadama zaiyita,ji tayi yana cewa idan kin gama bani saƙon hararar sai ki tashi ki tafi ko!'cikin dawowa hayyacinta tace"Ni ban harare kaba sannu da zuwa fa nake maka amma kace na harareka!'cigaba yayi da takun sa cikin nutsuwa batare da ya tanka mata ba ya dai san wannan zaman a kwai dalilin sa,shigewa yayi ɗakinsa ita kuma Bintu ta cigaba da zaman jiran sa, duk da tace ya bata haushi ta fasa faɗa masa cigaban da suka samu,(to Hajiya Bintu bari nima najira naga ya zata kaya muku keda jarumin naki wanda kika kira da miskili duk da naga kamar ke ba yayi miki miskilan cin) Yadda ya tafi ya barta haka ya dawo ya sameta,nan ɗin ma bai kula ta ba ya wuce kan dinning table dan bawa ciki hakkin sa,sai da ya gama tsaf kana ya taso ya dawo cikin falon,zama yayi kan hamshaƙiyar kujerar sa tare da ɗora ƙafafunsa kan ƙaramin Centre table ɗin dake gaban kujerar,rimot ya ɗauka ya kunna tafkekiyar placsiman da ta mamaye rabin bangon,Bintu dai kallo take binsa dashi ƙasa ƙasa haka nan taji ya mata kyau shigar da yayi ta wata Jessi da ƙaramin gajeren wando iya gwiwa ya burge ta ga wani sihir taccen ƙamshi da ya mamaye wajen tun fitowar sa yayi wani fresh dashi fatar sa sai wani glowing take,cikin ƙasai tacciyar muryarsa yace"ya dai kallon fa?wata irin kunya ce ta kamata kai wannan mutum kwai ƙwaƙƙwafi duk yadda tayi takatsan tsan wajen kallon sa amma sai da ya ganota,tashi tayi zata fita daga falon, ta kuma tsinkayar muryar sa yana cewa karki sake ki fita daga falon nan idan ba haka ba kin san karon mu dake ba zai kyau ba!'dawowa tayi tare da zama inda ta tashi,nuna mata gefan sa yayi ba tare da yayi magana ba,babu yadda ta iya dake yanzu ta fara gane yaran sa na magana da nuni ko da gira ko da ido, Rarrafawa tayi amma bata zauna kan kujerar ba sai ta zauna ƙasa jikin kujerar da yake zaune,cikin huskey voice ɗin sa yace"me kike son sanar dani?kawar da kanta gefe tayi tare da sa hannu ta rufe bakinta kamar ance mata zaiyi magana shi ɗaya batare da izinin ta ba,kawar da kanshi yayi daga kanta ya kuma cewa ina jinki,still dai batayi magana ba,kawai gani tayi ya miƙe tare da shigewa daki,binsa tayi da harara kana a fili tace"nima na zama miskilar ramawa zanyi kaji idan da daɗi idan akaiwa mutum magana yaƙi bada response dan haka bazan faɗa ba!'batasan fitowar sa ba sai kawai ganin sa tayi akanta yana ƙoƙarin haɗa allura,da sauri ta miƙe tare da neman hanyar guduwa amma kafin tayi wani yunƙuri ya cafko hannun ta cikin sanyin kuka tace"to Ni nace maka ban da lafiya ne kuma ba sai mutum bai da lafiya ake masa allura ba?cikin ɓoye murmushin da yake son kufce masa yace"ai naga kamar ciwon baki kike shi yasa zan miki allura sai bakin ya buɗe sosai!'cikin kiciniyar kwatar kanta tace"Ni wallahi lafiyana ƙalau ban son allura dan Allah kayi haƙuri kaji!'ta ƙarasa maganar cikin rarrashi kamar tana lallaɓa yaron goye,noƙe kafaɗa yayi tare da ƙara haɗa fuska yana mata nuni dole fa sai yayi mata allurar nan,tana ganin haka kawai sai ta shige jikin sa tare da cumimiye shi dan kar ma yasa mu damar ɗaga hannun sa danyi mata allurar....... More Comments More typing Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 36 ``` Zuba mata ido yayi yana kallon yadda take ta tura fuskarta cikin ƙirjin sa,cikin san ganin yanayin nan nata na tsoro ya shiga laluben inda zai soka mata allurar, jin haka yasa ta ɗago da sauri idanun nan duk sunyi waje yanayin nata gwanin sha'awa tace"plzzzz!' yayin da taja harafin ƙarshen da tsayi tana wani irin ƙifta ido wanda hakan yasa Abdallah shagala da kallon fuskar tata tare da ƙurawa tausasan lip ɗinta idanu,tura bakin ta tayi tare da kici-kicin ƙwatar kanta,wanda hakan yayi saurin ankarar dashi,cikin wani irin yanayin dayake ratsa duk wata kafa ta jikin sa tare da magudanar jini da ɓargonsa,ya zame ya zauna cikin kujerar tare da ita ajikin sa, cikin sanyin jiki yace"to zaki gaya min ko sai nayi allurar? da sauri ta kaɗa kanta kamar wata ƙadangaruwa, yace"ok bakin baiyi sauƙin ba kenan ya faɗa yana mai san kwace hannun sa da ta riƙe ka tau mau,cikin yanayin ta na shagwaɓa tace"Allah zan faɗa maka amma karkayi min allura na tuba bazan sake ba!'ta ƙarasa faɗa tana wani langaɓe kanta akan kafaɗarsa,yace"oya ina sauraren ki!' to ka cikani mana saina faɗa maka,da idanunsa yayi mata nuni da hannun sa da tariƙe da yadda take zaune akan sa tamkar wani kujera,da sauri ta sake shi tare da zamewa daga jikin sa ta zauna a ƙasa tana gun gunin yadda yake sata tana Hayewa jikinsa, Taɓe bakin sa yayi gami da gyara zaman sa yana fuskantar ta sosai kana yace" oya Tell me!' A hankali Bintu ta shiga bashi labarin yadda sukayi da Anty Nafisa bata tsayaba har sai da taxo ƙarshe,kana ta ɗago kanta dan ta kalli yanayin sa,ganin ya wani turɓune fuskane yasa Bintu cikin fargaban Allah yasa dai ba kwaɓa tayi ba garin san gyara,ganin yanayin ta ne yasa ya ɗan saki fuskarsa tare da ɗaga hannun sa ya dunƙule su kana yayi mata alamun jin jina,kawar da kanta tayi alamar dai bata gamsu ba, Cikin taushin muryarsa yace"kinyi ƙoƙari sosai,kuma duk yakar Dar da ta baki, ki dinga sauri wajen bani Ni kuma zansa A shirya mata ta kaddun bogi masu kyau sai kuma nasa ayi wanda bai kai na wajenta kyau ba A matsayin sune fake ɗin,sai na haɗa na baki ke kuma sai ki bata daga nan zamu dinga ajiye original ɗin a wajen mu har muga abinda Allah zaiyi,jin jina kanta tayi cike da gamsuwa,kana tace" kuma bazata gane bamu bata original ɗin ba,yace"insha Allah bazata gane ba Allah zai bamu na sara akanta zai rufe mata idanunta ba zai bata ikon ankara da abin da muka shirya mata ba har sai dubunta ta cika!'Allah yasa taimakemu ta faɗa tare da cewa, bacci nakeji!'kai tsaye ya nuna mata hanyar bedroom ɗinsa,kallon sa ta tsaya tanayi wato dai yauma aɗakinsa zata kwana kenan? ganin ya miƙe tare da nufar ɗakin sa ya sa itama ta tashi da sauri tare da nufar hanyar fita daga falon,bai ce mata komai ba yayi shigewar sa. A hankali ta buɗe ƙofar tare da saka kanta tana ɗan leƙawa, ganin gurin shiru ga duk fitilun falon innon a kashe suke baka iya ganin ko tafin hannun ka,tsorone ya kamata ji tayi kamar an taɓata,hakan yasa ta juya da gudu ta koma cikin falon Abdallah,wanda ba ita ta tsaya ba sai a tsakiyar gadon sa tana mai da numfashin gudun da ci, Abdallah dake tsaye gaban madubi yana fesa turare ya ɗan kalleta tare cewa Aran sa zabuwa kawai ko mai na tsorone da kuka a wajen ta,lulluɓe jikinta tayi gaba ɗaya amma fa ita tunanin ta ya za ayi ta iya bacci batayi wanka tasa kayan bacci ba gaskiya da sake hakan bazai yiwu ba agurinta, ganin yadda take ta juyi yasa yace"ko kina da buƙatar wani abu ne? cikin san zubar da hawayen taɓara tace"Ni banyi wanka ba kuma gashi babu kaya anan!'bai ce mata komai ba, ya buɗe wata akwati mai kyau ya zaro wasu kayan bacci masu kyau da ɗaukar hankali,miƙa mata yayi tare da cewa tashi kije kiyi wankan!'cike da mamaki tasa hannu ta karɓi kayan, sauri yayi ya fita daga ɗakin dan yasan sai tayi masa tambaya shi kuma bai shiryawa jin shirman nan nata ba,jiki asanyaye ta shiga bathroom ɗin sai da ta haɗa turarukan wanka kala kala amma duk da haka ba taji yayi mata yadda take so ba saboda haɗin inno na musamman ne dan ma ƙamshin ya riga ya kama jikinta ko nan da wata biyar zatayi bata sake wanka dashi ba wannan mataya taccen ƙamshin yana yana tare da ita,bayan ta fito ta zura rigar da ya bata tare da fesa matattun turarukan sa masu sanyin ƙamshi da kwantar da hankali,kana ta jera musu fulo a tsakiyar gadon,kwanciya tayi ta shige cikin tattausan bargo tare da lumshe idanun ta,shigowa yayi bakin sa ɗauke da sallama lokaci ɗaya yana mai bin saman gadon da ta jera fululluka da olido,wani irin tattausan murmushi ne ya suɓuce akan leɓan sa girgiza kan sa kawai yayi tare da ƙara sawa ya haye kan gadon. Hannu yasa ya fara zame fulon,cikin sauri ta buɗe idanun ta gaba ɗaya dan dama tana kallon duk abinda yakeyi takafar idanun ta da bata gama rufe shi ba,da hanzari tasa hannun ta ta riƙe wanda ya ɗauka yana shirin maida shi mazaunin sa,kallon ya bita da shi mai nuni da alamun tambaya,ɗan kawar da kanta tayi tare da cewa Ni kawai ka barshi anan raba mana nayi ba sai wani ya buge wani ba, kuma kai mirgin mirgin ne da kai!'kallonta kawai yake ya rasa ma abin da zaice mata wai shine yake mirgin mirgin lallai yarinyar nan taga gadon kwanan sa,bai ce mata komai ba ya cigaba da kwashe fulon yana gamawa yayi kwanciyar sa batare da ya tanka mata ba,gunguni tayi tare da ɗaukar fulon ta, ta komar da kanta wajen ƙafafun sa tana cewa to bari muyi sama da ƙasa!'still dai bai ce mata komai ba sai ma addu'a da yashiga yi,ganin haka yasa itama ta fara tofa tata addu'ar, Shi dai bai san ya akayi ba buɗe idon sa yayi kawai ya gansu manne da juna karma Bintu da tabi ta wani kanainaye shi kamar tana tsoron kar wani ya ƙwace mata shi,a hankali ya maida duban sa kan agogon da ke gefan sa saman gadon, ƙarfe uku saura,a hankali ya zameta ya miƙe ya shiga toilet bai ɗau lokaci sosai ba ya fito,wanda fitowar tasa tayi dai dai da farkawar Bintu,binsa tayi da kallo ta ɗan hasken ƙaramar fitila ganin kamar alwala yayi yasa itama ta yunƙura ta sauko tare da shigewa toilet ɗin,lokacin da ta fito yana ƙoƙarin tada sallar,sauri tayi ta ɗauki ƙatan tawul ɗin sa sabo ta rufa akanta, kana tabi shi yayi musu jam'i. Acikin wannan daren kuma su Safwan suka cafke Sayyid,ba tare da sun bari wani ya gansu ba kamar yadda Oga Abdallah ya gargaɗe su, Anty Nafisa fa da gaske ƙaramar yarinya tana neman buga wasa da ƙwaƙwalwal war ta,so sai shawarar Bintu ta shigeta tare da girgiza tunanin ta,har ji take yi aranta kawai ta fasa shirinta na saka cikin ƙarya tana ganin ma ta huta da sake-saken tsumma da fargabar samun akasi,amma kuma anya yarinyar nan ba wani ne yake ƙunsa mata wannan tunanin ba?amma kuma ai dama can tasan Bintu da tunani mai kyau, ko ita shine dalilin da yasa ta sakota cikin al'amarinta,duk da haka tayi mamakin ƙwaƙwalwar Bintu ko ita da ta kusan jika da Bintu batayi wannan tunanin ba, bayan kuma shine babbar mafita agareta,kai amma dai ita baƙaramar mai sa a bace na yadda batayi saurin sanar da Umar tana ɗauke da juna biyu ba,ashe wannan jinkirin alheri zai zamar mata, gaskiya ta jin-jinawa basirar Bintu. ɗan bin ɗakin tayi da kallo tana wani irin murmushi me cike da jin daɗi,tasan zata samu abin da takeso saboda mijin ta bai iya ɓoyo ba, dan haka tana da yaƙinin cewa bazata sha wahalar haɗa muhimman kadarorin sa ba,wani tunani ne ya faɗo mata wanda yasa ta ɗan cizan yatsa, ko wane abune Bintu zata gaya mata ta fasa? tabbas a kwai ayar tambaya akan wannan lamarin akwai abinda Hajiyarta ta gargaɗi Bintu da kar ta gaya mata shi,to meye wannan dahar Hajiyar ta zata iya munafuntar ta akan sa wane abu take son ƙullawa batare da sanin ta ba?wata zuciyar tace da ita kin manta halin ladidine? komai fa A kace ta aikata indai akan kuɗi ne tabbas zata iya ai katashi,to amma meye na ɓoye mata?wani ɓangare na zuciyarta ya kuma cewa da ita a'a Nafisa karkiyi saurin yanke hukunci ki bari ki lallaɓa Bintun ta sanar dake abinda yake da akwai, daga baya saiki yanke hukunci,da wannan tunanin ta tashi dan fara binciken abinda ya kasan ce shine burinta da buƙatar ta, Wai shin ina Abigirl ta lula ne? Tunda ta tafi garinsu can inugu bata ƙara waiwayar Abuja ba balle kuma tunanin mijin ta, ita dai kawai tunda tana ganin ta tsira da rayuwar ta to shike nan,sai dai abinda bata sani ba shine,tuni Dady jafar ya sanar da Abdallah yana zargin Abigirl amma bai sanar dashi ainahin abin da ya saurara daga gareta ba, dan yasan Abdallah idan ya sani ba lallai ne ya barsu subi aikin A sannu ba,cikin zafin zuciya zaibi lamarin na Abigirl tunda dama yana ciki da ita Abigirl ɗin,kuma hakan da zaiyi, shi zai ƙara bawa makiyan su damar da zasu iya cutar dasu ba tare da sun ankaraba,dan haka ya ɓoyewa Abdallah komai,shi kuma Abdallah batare da ɓata lokaci ba yasa akabi masa bayan Abigirl tare da ɗauko masa duk wani bayanan ta, da duk wani motsinta. Shi Dady jafar so yake sai Abigirl ta sakan kan ce kawai sai su sa aɗauko ta, dan ta amsa tarin tambayoyin da shima yake matuƙar buƙatar jin su daga gareta,lallai ya zaƙu yaji yadda akai tasamu Fatash wanda A yanzu ya koma Abdallah?kuma waye suke waya da shi?meye burinta akan Abdallah? me yasa kuma take ƙoƙarin kashe shi a halin yanzu? tunda tace kasheshi shine marufar asirinta,kuma gashi duk da haka sai da abin da take gudu ya faru,wanda shine dalilin da yasa tayi masa ƙaryar mutuwa ta gudu garin su?ɗan ƙara gyara kashingiɗar sa yayi tare da cewa, afili tabbas komai ya kusa ƙare muku duk wani munafiki an kusa yin walƙiya dan muga fuskokin ku,asirin ku duk ya kusa tonuwa,ɗan zakin da suka hana shaƙar numfashi tare da iyayen sa to shi zai ruguza tasirin su da duk wani makircin su,insha Allah lokaci ya kusa,shi kan sa ya ƙagu yaga ɓaƙaƙen fuskokin su,badan farin ciki ba sai dan san ganin ƙarshen su, insha Allah ƙudurar Allah ta kusa baiyana. Akan idon Taufiƙa Bintu ta fito daga sashen Abdallah, jikin ta sanye da rigar baccin da yabata ta saka a daren jiya,Bintu da ta fito a saɗaɗe dan kar inno ta ganta, sai tayi turus ganin Taufiƙa zaune akan kujera tana watso mata wani irin kallon tsana mai cike da ɓakin ciki mara misali,A hankali Bintu ta ɗauke kanta tare da cigaba da ta kawa dan isa ga ɗakin ta,tsayuwar da Taufiƙa tayi agaban ta shi yasata ɗan ja da baya tare da zubawa Taufiƙa ido kamar yadda itama Taufiƙan take bin duk ilahirin jikin Bintu da kallo na tsan tsan tuhuma da san gano wani abu, Bintu gefe taja da niyar canja hanya da sauri Taufiƙa ta wani sa hannu ta finciko ta ta dawo baya,tana wani irin huci na tsan tsan baƙin ciki da hassada, Bintu tsayawa tayi tana kallon ta cike da jiran ko takwana dan ta ɗau alwashin ta daina ragawa kowa dake cikin gidan, dan da hakane kawai zata samu ƴancin yin abinda ya kawota batare da tunanin wasu shirgin ƙwarƙwata ba. "Ke mahaukaya ƴar talakawa matsiyaciya,macijiya mai saran ƴaƴan masu gida da mugun dafin da yafi na kowace macijiya zafi da raɗaɗi,kinzo kin kanai naye wa mutane gida sai kace ramin macijin ubanta da na uwarta masu saran ɓoye,su noƙe su nuna tamkar basu taɓa saran ko wane ɗan adam ba,to ina mai tabbatar miki da cewa muddin baki fita hanyar ahlina ba saina kassara rayuwar ki yadda nan gaba bazaki iya moruwa ko ga makaho ba balle mai ido da cikakken lafiya,zan tabbatar miki da abinda nake faɗa in dai har baki san inda dare yayi miki ba!'wani mugun kallo Bintu take bin Taufiƙa dashi har ta kammala zantukan ta cikin wani irin huci da sauke numfashi,tsaki Bintu tayi tare da cewa,me kike da suna Taura ko Tofi? to inaso ki sani duk abinda kuke yi ba wai dan kun gagari Bintu bane yasa ta kasa yin komai ba, a'a sai dan ina da manyan kune ku kun yi min ƙanƙanta A sarah sai dai na sari na sama daku domin yaƙi na dasu nakeyi bawai daku ƙananan marasa kunya da abinyi ba,tabbas Ni macijiya ce amma inaso ki ɗan da ɗan lokaci dan in tabbatar miki da hakan, Taufiƙa Ni macijiya ce wadda idan tayi sara sai dai mutum ya mutu ko ya na ƙasa amma ba dai a warke ba,idan kina buƙatar sarana to ina so kibi ayari domin abin layin markaɗe ne bai zo kan ƙaramin kai irinki ba,idan na gama da manyan kawuna zan tsaya na saurare ki,kuma kisha kurumin ki ki daina haƙilo shi wanda kikeyi dan shi wallahi ko fuskarki ba zai tan-tance ta cikin ahlin ALHAJI BALARABE ba balle yayi miki duba irin na zumunci balle kuma duban soyayya, Oga Abdallah yafi ƙarfin ki dan ba dan irinku Aka halicce shiba Allah ya halicci bawansa Abdallah don mata masu kyakykyawar zuciya da tsoron Allah da kuma taimakon bayin Allah, zuciyar Oga Abdallah ta zinare ce ke kuma ta gawayi,to gaya min tayaya wannan haɗin gambizar zai yuwu,dan haka ki sawa zuciyarki shidin ba abokin rayuwar ki bane dan insha Allah Allah ba zai yi masa wannan jarabtar ta Auren ki ba ko iri-irin ki ba,ina so ki cigaba da saka ido akan wannan wasan Ni kuma insha Allah zanyi miki addu'ar tsawan kwana domin kiga ƙarshen wasan wanda zai zama gaskiya Abdubint for ever,ya kika gani?Taufiƙa ki kiyayi ranar na dama ranar da nasani ranar da sirrin ɓoye zai fito ranar da fuskoki da yawa zasu baiyana suna masu kaico da rayuwar da suka shuka,ki kuma kiyayi ranar da ƘUDURAR ALLAH zata baiyana,dan haka ina mai baki shawara da ki tuba tun kafin ranar dan karki kasance,cikin masu danasani wadda zata zamar miki ƙeya,kuma zaki kasan ce cikin mutanen da saran da nayi musu shi kaɗai ya isheki ba sai na kai ga asarar zubar da dafina ba!'har zata wuce sai kuma ta ɗan juyo dai-dai saitin kunnen Taufiƙa wadda ta tafasa kamar wuta saboda zafi da mamakin kalaman Bintu wanda suka matuƙar sakata cikin ruɗani da shakku mai tsanani akan Bintun,tace"abinda na manta ban gaya miki ba shine dafina baya cin wanda ya tsaya ga Allah ya kuma kiyaye dokokinsa,dafina ya tsaya ne akan mugaye ɓaragurbi masu ɗoyin baki da ƙwaƙwalwa,daga haka tayi shigewar ta ɗakinta tare da banko mata ƙofar da ƙarfi saboda ƙara tura mata haushi. Tabbas idan taufiƙa tace"maganganun Bintu basu taɓa ta ba tayi ƙarya,sosai kanta ya kulle tare kuma da san neman ƙarin haske ga kalaman Bintun wanda suke kama da magana mai harshen damo,a kwai manufa A cikin kalaman Bintun,cikin mutuwar jiki da zuciya taja jikinta ta shige ɗakin su. BaTaufiƙa ka ɗai ce ta shiga halin rikicewa da kalaman Bintun ba,hatta da Abdallah da Hajiya Babba da ta kawo kai dan sanarwa inno kiran gaggawar da ya same su daga Alhaji Baba sai da ta shiga wani yanayi na matukar zurfafa tunani,kasa shiga falon tayi ta koma saboda bazataso wani yaganta cikin wannan hali na kiɗima ba. Tun dawo war sa daga masallaci da ya wuce tiraning sai lokacin ya shigo, wanda shigar sa ke nan kunnuwansa suka fara jiyo masa kalaman Taufiƙa, tsaki yayi zai wuce saboda bai ga amfanin sauraren shashan cin Taufiƙan ba,amma kafin ya saka ƙafar sa cikin falon sa ya tsinkayo ɗaɗdaɗar muryar Bintu tana maida wa Taufiƙa Raddi cike da kar sashi da kuma san zuwan wata rana mai ɗinbin tarihi agareta,tabbas shima ya shiga halin rikicewa da wannan sabon Al'amarin, tabbas ya daɗe yana tunanin abinda Bintu takeyi bai ci ace wai dan taimakon musulunci kawai take ba, idan yayi duba da ranar da ta bashi tabbacin zata taimaka masa da dukkan rayuwar ta,tabbas ranar ya hangi yadda wutar fansa ke ci a tsakiyar idanunta,to ga kuma wannan kalaman nata masu shige da har shene damo,meye gaskiyar tarihin wannan yarinya meye gaskiyar,abinda ya kawota ahlin nan?kai akwai wani abun da Bintu ta ɓoye wanda ita kaɗai tasan shi sai Ubangijin ta,ta yaya zaiyi ya gano wannan gaskiya da ta ɓoye masa?anya kuwa Bintu bata da alaƙa da ahlin ALHAJI BALARABE?dafe kansa yayi A yayin da yake zama ƙasan carpet ɗin dake malale tsakiyar haɗadɗan falon nasa,tare da runtse idanun sa,wai meye yasa abin mamakin cikin gidan nan baya karewa?kafin ya gama da wani al amarin wani ya taso, tabbas al al'amari Bintu wani babban al amarine da dole sai ya nutsu dan gano shi,kuma shi kaɗai zaiyi wannan binciken batare da sa hannun kowa ba kuma zai bar shi a matsayin sirrin zuciyar shi, Hajiya Babba tunda ta koma ɓangaren ta take kaiwa da kawowa itafa a rikice take da wannan al amari na Bintu, tabbas A kwai wani ɓoyayyen sirri da Bintu take ɓoyewa,to me yasa takejin wani irin sabon kusanci A cikin jikinta game da Bintun? kuma tanaji ajikinta komeye agame da Bintu to Alheri ne,(Hajiya Babba macece mai matuƙar dogon hange da baiwa mai tarin yawa to ba wani abin mamaki bane dan shaidar Bintu jikar tace ta baiyana acikin jikinta da zuciyar ta duk da ita bata taɓa kawo wannan tunanin ba) amma tabbas tanaji ajikin ta Bintu haske ce ga ahlin ta kuma madubi mai haska baya, "Zama tayi tare da ɗaga hannuwan ta sama tana mai addu'a tunda ga ƙasan zuciyarta har zuwa kan bakinta,ya Allah ka zama gatanmu kajiɓanci lamuranmu Ni da dukkanin musulmi masu tsoronka,ya Allah ka sakawa waɗanda aka aka zalunta ya Allah ka war ware mana ƙullin da aka ƙulla mai wuyar kwancewa,ya Allah ka tsare mu daga sharrin kiɗan shaiɗan ka kiyaye zuciyoyin mu daga faɗa wa halaka katsare mu da aikata saɓonka, Allah kakiyaye mu da aikin na dama kasa kar mu tozarta a duniya da lahira, Amin Ya Allah. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 37 ``` Wayar tace tashiga neman ɗauki, cikin nutsuwa ta shafa addu'o'in ta, tare da janyo wayar ta kara a kunnen ta,cikin girmamawa tace"Alhaji wallahi wani ɗan saɓani aka samu amma yanzu zan kuma gwada wayar tata idan batayi ba sai na koma ɓangaren nata!'ta ɗaya ɓangaren Alhaji Baba yace"kizo ai na samu wayar tata tuni ke muke jira, Hajiya Babba tace"to madalla gani nan tafe!'bayan ta ajiye wayar tare da tafiya dan amsa kiran megidan nasu, suji abinda yake faruwa da sammakon nan kuma. Tana dosar coridon da zai sada ta da falon Alhaji Baban ta fara jiyo tashin Muryar Dady Mansur, a ranta tace"sababbe kaci kanka wato ma shine sanadin tarasu da wannan safiyar,to Allah Ubangiji ya shirya,ta faɗa tare da yin sallama cikin falon,amsawa sukayi gaba ɗaya kana sukayi gaisuwa a tsakanin su,cikin nuna halin dayake ciki na tashin hankali ya gaida Hajiya Babba, Dady Habib ma dake zaune ƙasan ƙafar Alhaji Baba yana ja masa yatsu ya gaida ta cikin tsananin biyayya, Hajiya Babba ta amsa fuskarta cike da ƙauna da kuma alfahari da yaron nasu wanda ya ya ƙwace girman Mansur tunda ya zubda girman to su sun ɗauka sun bawa Habib. "Ɗan gyaran murya Alhaji Baba yayi tare da cewa kai Mansur tun yaushe ne baka ga shi Sayyid ɗin ba?cikin ƙara san zafafa abun yace" Nabil yace"sam baiga ya shigo jiya ba, ma ana dai bai kwana gida ba,da farko ma yayi tunanin yana sashena sai da aka idar da Sallah kana nake ce masa ina Sayyid,to shine yake sanar dani,gashi tun alokacin nasa aduban duk inda akasan yana zuwa amma babu wani labari!'ya ƙara sa maganar cikin yanayin fargabar abinda zai faru da ɗan nasa, Alhaji Baba yayi gyaran murya kana yace"to Ni dai aganina Sayyid ba yaro bane da za ace ya ɓata,sai dai wani abu daban dan haka Ni aganina mu jira zuwa jimawa idan bai dawo ba sai mu ɗauki mataki!'inno tace"gaskiya Alhaji Ni dai ashawarata gara ayi saurin fara neman yaron nan tun da kasan duniyar yanzu ta zama abin tsoro,ba zai yiwu ace har sai wani lokaci mu fara ne man sa ba,kuma dai kaga yaran nan duk runtsi sai sun kwana a gida,barantana muce sun saba yin irin haka!'tana ajiye maganar ta Hajiya Babba,ta ɗauka ita ma dai shawarar da ta bayar ke nan kamar yadda inno tace" ita kuwa Hajjah tayi musu kara amatsayin ta na kakar Sayyid,dan haka batace komai ba baya ga fatan Allah ya baiyana shi da gaggawa,Dady Habib yace"yanzu yaya katashi muje mu bayar da cikiyar sa gida jen ƴan uwa da abokan nan sa,idan ba a ganshi ba zuwa gobe sai mu sanarwa ƴan sanda,tun da yanzu bamu da tabbacin ɓata yayi kaga bai kamata muyi saurin sanar da ƴan sanda ba!'Alhaji Baba yace"to madalla hakan yayi, Allah Ubangiji ya kareshi aduk inda yake ya dawo mana dashi cikin ƙoshin Lafiya,Amin suka amsa gaba ɗayan su,daga nan Dady Mansur da Dady Habib suka fita dan fara aiwatar da abin da ya dace,Hajjah da Inno ma tashi sukayi suka koma sashen su kasan cewar yau turakar ta uwar gida ce Hajiya Safiya buzuwar Agadez. Me sace Sayyid yake nufi?anya kuwa ba wani abune da ya dan ganci bin sahun ta ba? tabbas dole ne ta dawo da Dije cikin gidan nan tunda tasan itama Dijen bata da wani garanti akan ta bata san ko ita wacece ba,amma Dijen ce lamarin ta akwai sa shakku wanda hakan ne yasa tasa akayi nesa da ita daga estate ɗin gaba ɗaya, dan taga kamar tana shirin munafun tar ta ita da shegiyar yariyar nan,ga shi kuma rashin Dijen na son ya dameta,dan rashin ta shi yake sawa duk wasu abubuwa suke faruwa batare da sanin ta ba,gashi Sayyid ɗin ma ga dukkan alamu dai yafaɗa tarko, yanzu ya za ayi tasan waɗan da suka kama Sayyid idan ƙama shin akayi?tabbas a kwai ƙura,wata zuciyar tace da ita toke meye na far gaba bayan kin tabbatar da cewa Sayyid bazai iya bada baya nai akanki ba,tunda bai sanki ba,nunfashi ta ja mai tafe da ajiyar zuciya tana mai ƙara gaskata abin da zuciyar ta ta sanar da ita akan lallai su Alhaji Nasir su suka ɗauke Sayyid saboda suna tunanin yana aiki tare da wani akan buƙatar su,wanda basu san waye ba,shine suke son su sani ta hanyar ƙwamushe shi Sayyid ɗin,kuma suna tunanin zasu samu hanyar sanin inda Abubakar yake,wani ɗan murmushi tayi wanda alamun tane kawai ya nuna hakan,fulawar dake gaban ta Koriya shar ta cikin lambun da take ciki tasa hannu ta ɗan tsinka,tare da cewa Alhaji Hashir Alhaji Nasir Alhaji Kabir da sauran tawagar ku tabbas kunyi ta banza, domin ina da tabbacin babu abinda zaku iya ganowa game dani,saboda ban bar wata sheda da zata sa mai nemana ya sameni ba,kwayi ku gama ku dawo musu da ɗan su,Ni kam na riga nayi nisan da babu mai kamoni,(hmmm Allah mai kowa mai komai shi yake da ikon kamaki koma zai kamaki cikin ƙudurar sa,tafi-tafi dai ita dama akewa ai ƙarshen ta ƙasane)cikin ƙwarin gwiwa ta bar lanbun. Duk tabi ta birkita ɗakin duk wani waje da tasan yana ajiye muhimman abubuwan sa saida ta duba,ɗan dakatawa tayi tana mai cizan yatsan ta tare da bin ko ina na cikin tangameman ɗakin da ido,cikin sauri ta nufi wata ƴar jaka wadda baza ta wuce girman jakar mata ta rataya wa ba,buɗe jakar tayi tare da zazzage ta gaba ɗaya tana mai fatan samun abinda take nema,takardun da suka faɗo ta shiga dubawa da ɗaɗɗaya yayin da kuma bugun zuciyarta ke kuma tsananta,saboda tsananin tashin hankali da fargabar abinda ta gani rubuce cikin takaddun,goge idan ta ta kumayi saboda ta kuma tabbatar wa ba gizo yake mata ba,tabbas wannan sa hannu ne na mijinta akan ya mallaka wa ɗiyar sa gidan mansa dake cikin garin na Abuja,ta kuma buɗe wata itama ya sa hannu akan ya mallaka wa ɗiyar sa wani babban mension da bai daɗe da gama gina shi ba,sai ta ukun ita kuma kamfanin sa na auduga ya bata,hannu ta ɗora aka tare da zunduma wani ihu,da sauri ta rufe bakin tana mai fashewa da wani irin kuka mai tada hankali. "Wayyo rayuwa me yasa zakiyi min haka? Ni Nafisa naga ta kaina ashe shukar dusa nakeyi ban sani ba,me yasa banyi irin tunanin da Bintu tayi ba tun kafin zuwan wannan rana,kuka takeyi sosai tana san batu tamkar wata zararriya,anya zata yadda duk wannan wahalar da tayi ta tashi abanza,waifa wannan ke nan data gani,bata san iya adadin waɗan da yasaka hannun ba,dole tayi wani abu tun kafin ta zama asararriya dan kuwa ta rasa wannan uwar dukiya ta Umar ba iya asara tayiba ita kanta ta zama asararriyar,kwashe su tayi gaba ɗaya tana mai aiyanawa dole ta sami Bintu dan ita ka ɗaice zata kawo mata mafita akan wannan al amari. Ita ba sa hannun ne a yanzu ya dame taba,ƴar dayake iƙirarin ya bawa itace tafi damunta,to wai shin wace ƴar yake nufi?a i'na yasame ta a ina ya gano ta?idan ya gano ta yanzu tana ina?to ya akayi hakan ta farune dama matacce Yana dawowa?ko dai Umar tunani ya fara zautar shi?idan kuwa hakane ya zama dole agareta ta binciki Umar dan sanin inda ya dosa da kuma abinda yake nufi da mallaka wa gaibu dukiyar da ta jima tana farauta. Hello Samira!'daga ɗaya ɓangaren Samira tace"ya naji muryarka kamar ba dai-dai ba?Samira akwai matsala amma ki ɗan yi haƙuri zan kiraki,yanzu ina kan hanyata ta zuwa guest house zamuyi miting, ko da yake anjima mu haɗu kawai sai muyi magana!'daga haka ya kashe wayar dai dai kuma lokacin ya ƙara so gidan su da suke haɗuwa dan zaman tattauna matsalar su. Samira ta dubi oga Abdallah tayi masa alamun ko ya fahimci wani abu? dake wayar a amsa kuwa ta sakata,Safwan ne yace"kema dai kin san bazai wuce tashin hankalin an riga su ƙwamushe Sayyid ba,kuma zasuyi tunanin waɗanda suke tare dashi ne suka ɓoyeshi dan kar su sami damar samun bayanai daga Sayyid ɗin,samuyal yace"hakane sai dai ina ga tunanin su zai iya canjawa!'Abdallah ne cikin yanayin ƙasaitar sa ya ɗan motsa bakinsa kana yace"basu da wannan damar tunda muna tare dasu ta ko ina ko kun manta lawan ayanzu shine drivern Alhaji Nasir?mun mamayesu ta ko ina ga kuma Samira dan haka duk ta inda zasu ɓulla mu zasu gani!'Samira ta ɗora da cewa,kuma bana tunanin zasu iya canja hanyar da suke kai a yanzu domin mun riga munyi musu shigar sauri,mune muke juya tunanin su,koda sunyi tunanin hakan to tabbas Nice zan kuma ɗora su a hanya ta yadda zamu samu dukkanin abinda muke so!'Abdallah yace"mu saka ido akan motsin kowa domin ayanzu munzo gaɓar da zamu fara han kalta da motsin kowa ta hakane kuma zamu damar ɗora zargin mu akan duk wanda muka ga wata alama atare dashi,sace"Sayyid zaiyi matuƙar ɗagawa wanda suke sakashi aiki, kuma tanan zamuyi ƙoƙarin gano ko waye domin bibiyar sa. Hmmm Abdallah da sauran rina A kaba fa, gano wannan shu'umai sai andage da addu'a dan sun san takan ɓadda kama cikin mutanen kirki, sai su saka ɓaƙar fuskar su cikin fararen fuskoki yadda fararen fuskokin zasu haska su a kasa gane ɓakin fuskar tasu to Allah dai ya baku nasara Abdubint. A can kuma ɓangaren su Alhaji Hashir tare da Alhaji Kabir,sai Baba nura da Sama'ila da kuma,Salisu,yayin da Alhaji rufa'i ya kasance shine kaɗai babu acikinsu,kuma waɗan nan mutane sun kasan ce duk alhalin su ne suke musu wannan faɗi tashin, wato Alhaji Nasir da ɗan sa Sama'ila Sai Alhaji Hashir da ɗan sa Baba nura,sai kuma Alhaji Kabir shima da ɗan sa Salisu, dukkanin su sun yi zurfi cikin nazarin wannan lamari da ya taso musu,cikin dogon tunanin da Alhaji Nasir yayi yace"anya kuwa bamuyi gangan cin fita daga lamarin yaron nan Abdallah ba?nifa ina ganin kamar dasa hannun sa cikin wannan lamari!'Alhaji Sama'ila ne yayi saurin tarar sa da cewa haba Abba tayaya Abdallah yasan da wannan shirin namu balle har ya ɓullo mana ta haka? Ni ina ganin fa wannan fa bashine abinda Abdallah yake nema awajen mu ba dan haka ka daina sako shi cikin wannan sabgar!'Baffa Hashir yace"maganar Sama'ila akan hanya take Ni nafi tunanin mutanen nan sun ɗauke Sayyid ne kawai saboda suma sun gano muna bibiyar sahun su,dan haka sun ɗauke shi sun ɓoyeshi saboda kar mu samu wasu bayanai a tare da Sayyid ɗin!' wannan shine gaskiyar maganar cewar Alhaji Kabir kenan,kuma ina da tabbacin basu ka ɗai bane me amfani da Sayyid daban yake, kawai Ni aganina mu cigaba da bincike mubar maganar Sayyid, abu me mahimmanci agurin mu shine sanin inda Abubakar yake,dan haka mu cigaba da wannan binciken ta hakan zamu kuma gano waɗanda suke da irin manufar mu!tafi suka ɗauka gaba dayan su cikin nuna gamsuwa da batun na Alhaji Kabir,da wannan shawarar suka sami matsaya a tattaunawar su ta yau. Kaf Alhaji Sama'ila ya zaiyanawa Samira tattaunawar da sukayi awanni biyu da suka wuce,tare da ƙara wa da faɗin to kinji shawarar da muka yanke akan wannan al'amari,Samira ta ɗan ja ajiyar zuciya tare da cewa shawararka tayi wannan ma Abune mai kyau da Yakamata musani, dan haka idan kuna da buƙatar taimako na hanya A buɗe take!'murmushi yayi tare da cewa ki kwantar da hankalin ki Samira lokacin buƙatarki yana nan zuwa!'itama murmushin tayi tana mai ɗaukar ice cream ɗin dake gaban ta, haka suka cigaba da ɗan tattaunawa cikin ƙara bugun cikin sa ba tare da ya gano hakan ba. Alhaji Mansur fa yatashi hankalin sa,saboda har yanzu da rana take faɗuwa baiji wata alama da ke nuna masa cewa Sayyid zai dawo ba,ya tashi hankalin kowa dake cikin ESTATE da wan nan shegen kwakwazon nasa da rigima, to dama ya lafiyar kura, Hajjah ce tayi kiran sa ta zaunar dashi tare da yima sa nasiha yayi hakuri za aga Sayyid ɗin, amma tamkar tura shi takeyi,gajiya tayi ta sa masa ido dan fadan da yafi ƙarfin ka dole ka maida shi wasa, Ta auna kiran Bintu yayi so goma amma wayar yaƙi shiga, gashi duk sakanni tashin hankalin ta da ɗa girmama yakeyi,idan ta zauna ji take kamar ko mai zai iya zuwa ya faru,neman taimakon Bintu take cikin gaggawa,so take ta samu mafita kafin dawowar Umar,so takeyi ta samu hanyar da zata ɓullo masa dan Sanin abinda take ƙwaɗayin sani,gashi bata son yawan zuwa ɓangaren innon dan gudun shiga cikin zargi,amma dole nan da zuwa safiya tasan abinyi. Ta ɓangaren Abdallah kuwa yayi mugun saka ido akan al amuran da suke tafiya a cikin estate ɗin,amma abin da yake bashi mamaki har yanzu bai ga wata shaida da zai nuna masa wani yana da ɓoyayyiyar alaƙa da Sayyid ba,ɗan numfashi ya fesar yana mai cigaba da zame kayan dake jikin sa dan dawowar sake nan,ɗan ƙwanƙwasa ƙofar akayi batare da ɗaukar wani lokaci ba ya bada izinin shigowa, dan yasan babu mai shigowa ɗakin sa sai Bintu,sallama tayi cikin siririyar muryar ta tare da shigowa,kallon ta ya shigayi ƙasa ƙasa batare da yabari ta kula da hakan ba,tayi kyau cikin shigar riga da siket na atamfa wanda yayi ɗas ajikin ta, tamkar wata ɗawisu haka ya shiga kallon takun ta ga wani irin ƙayataccen ƙamshi da yagame ƙofofin hancin sa,samun kan sa yayi da ƙara buɗe hancin sa dan cigaba da shaƙar ƙamshin,yana wani lumshe idanun sa tamkar wanda yake jin bacci,Muryar tace ta dawo dashi hayyacin sa tare da saurin cigaba da abinda yakeyi,tace wai inno tace nazo kana kirana!'ko dai kike so kizo?ya faɗa batare da ya dubi inda take ba,cikin yanayin ta na sakalci tace"Ni kam Inno tace kana kirana!'yana ƙoƙarin shiga toilet ya ɗan dubeta kana yace"kawai kice kinzo gun mijinki ba sai kinyi wani kwana ba!'ya faɗa tare da shigewa toilet ɗin,kallo tabishi dashi kana tayi ƙwafa,wai miji Ni banga wani miji anan ba? Abdallah yana da matuƙar ƙarfin ji shiyasa bai sha wahalar jiyo abinda Bintu tace"ba,kaɗa kansa yayi tare da sakin wani murmushi yace"yarinya zakiga bakiga miji ba saikin gyara wannan kalamin naki. Ita kuwa Bintu tafiyar ta tayi ɗakin ta, tana cewa yau komai za ayi bazanyi kwanan wahalaba,mutum duk abi aka nainaye shi ya rasa ko hanyar yin numfashi mai kyau. Lokacin da ya fito bai ganta ba yayi tunanin tana falon sa,dan haka shiryawa yayi cikin kayan bacci masu kyau kana ya fesa turarukan sa masu sanyin ƙamshi,tare da fita zuwa falon,da idanu ya dinga karaɗe falon amma bai ga ko ƙyallin Bintu ba,ƙara sawa yayi dining yacika cikin sa da girkunan gargajiya irin wanda Bintu tayi matuƙar ƙwarewa akan su,sai kuma akayi dace Abdallah yana matuƙar san girkin gargajiya shi yasa bai taɓa gajiyawa da nau'ikan girkin da take shirya masa ba, dan har abincin Fulani yi masa takeyi,haka kuma kullum ji yake kamar ana ƙara wa hannun ta zaƙi,sai da ya gama ya koma falon ya zauna yana ɗan taɓa aiki a computer,tun yana tsammanin dawowar Bintu har dai ya fidda rai,saboda lokaci yaja yasan bazata taɓa fitowa a wannan lokacin ba,tashi yayi ya koma ɗakinsa ya kuma yin brosh kana ya kwanta, sai dai haka nan yake ji ya kasa bacci kamar da abin da yake buƙata akusa dashi,sai diramar Bintu dake dawo mashi wani yayi murmushi wani yayi tsaki da haka dai bacci ɓarawo ya sace shi. "Washe gari tunda ya dawo daga masallaci bai kuma fita ba yana zaune ta shigo tana ganin sa ta fara rarraba idanu kamar wata mara gaskiya,da ƙyar ta ƙara sa kusa dashi ta gaida shi amsawa yayi batare da ya kalli inda take ba,zata miƙe kenan wayar ta da sai yanzu ta kunna ta ta fara babureshon,juyowa yayi tare da zubawa Bintu ido, wadda ita kuma ta zubawa lambar da ake kiran da ita idanu,saboda wata irin nomba ce batafi guda uku ba kuma da wani irin yare ba da normal lambobi ba,ganin hannun ta yana rawa yasa Abdallah ruƙo hannun nata tare da karɓar wayar,shima zubawa nombobin ido yayi yana mai karanta addu'oi a bakin sa kana cikin yadda da Ubangiji da ka ɗaitakar zatin sa ya danna ok tare da saka amsa kuwa. "Wata mummunan dariya aka saki tare da cewa yarinya mai tunani to ya kike keda gwarzan angon naki?ko da yake ba sai na tambayeki ba tun da Ni masani ne akan duk wani motsin ku,bawani Abune yasa na kiraku ba sai dan nayi muku gar gaɗi akan ku kiyaye da shiga sabgata domin ban kaɗai wani sirrina da sanin ko Ni waye, domin duk abinda kuke nema baza ku same shiba a halin yanzu daku da duk wani me san shiga hurumi na,baku isa ganin bayana ba ƙananan kifaye,sai dai Ni naga bayan ku da duk wani mai burin ƙwatar burina,ku tsaya iya matsayin ku na neman iyayen ku wanda kuma ina tabbatar muku da cewa bazaku taɓa samun su ba,domin ku ɗin ma baku tsira daga tarkona ba, kune cika makon burina da ku zan yi amfani na samu cikar burina,daga nan kuma sai nayi mai yuwu daku da iyayen naku!' Wata mahaukaciyar dariyar ya kuma sheƙewa da ita, yana mai cigaba da cewa,yarinya mai hikima na yaba miki matuƙar yabawa da irin gudun mawar da kike bawa mijin ki dan ganin ya lalubo inda mahaifin sa yake,to ke mai yasa baki sanar dashi ya tayaki nemo taki mahaifiyar ba?kai ba daban zan ɓata shirina ba da na gaya miki inda mahaifiyarki take da kuma hannun wadda take riƙe dasu,ita da yayanta, FATIMAH UMAR BALARABE,DA ABDALLAH ABUBAKAR BALARABE,haɗin yayi kyau ina muku fatan shan wahala,daga haƙa ƙit wayar ta yamke, Tofa kar ku manta Abdallah bai san wacece Bintu ba Bintu ma batasan wanene Abdallah ba,kamar yadda yake mata kallon wadda zata taimaka dan ceto rayuwar wasu mutanen,haka ita ma take masa kallon wanda zai ceci ahlin sa daga wata babbar matsala,ko ya zasuji? ko wane hali zasu shiga bayan jin wannan murya? to mu antaya gaba ɗaya cikin fage na gaba dan jin yadda zata kaya........ Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 38 ``` Wani irin kakkauran miyau Bintu ta haɗiya wanda yake tafe da wani gishirin tashin hankali,to waye wannan mutumin?waye kuma Abdallah A cikin ahlin ALHAJI BALARABE?dama shima ƙaddarar sa shigen tata ce?to shi waye ya sace masa mahaifin sa? kuma me yasa aka sace shi?wai wannan wane irin ahline masu baƙin hali? me yasa san zuciya yayi yawa cikin wannan ahlin? Ɗagowa tayi a hankali tare da zubawa kyakykyawar fuskar sa idanun ta masu tsananin haske wanda suka suka fara sauyawa saboda halin ruɗani da take ciki, wani irin fargaba da tsorone ya kamata ganin yadda idanun sa suka sauya kala gawan nan maiƙon da yakuma tasowa wanda yake cike da zallar ɓacin rai,fuskar tayi wani irin ja,kana ganin sa kaga wanda aka tasowa da wani miki mai ɗaci,abin ya matuƙar bata tsoro,baran ma yadda yake mata wani irin kallo mai cike da tambayoyi marasa adadi. A hankali ta shiga ja da baya, ƙoƙarin samawa kanta gurin tsira take,saboda gani take a yadda yake ɗin nan tsaf zai iya bata kashi,to me ya ɓata masa rai haka?ko zan can mahaifinsa da akayi masa ne?tana ƙoƙarin silalewa taji yayiwa hannunta wani irin riƙo wanda har sai da ta saki wani marayan ihu,kallon sa tayi idanun ta cike taf da hawaye,kawai ji tayi ya janyo ta jikin sa tare dayi mata wata iriyar runguma mai cike da jin kewar wani sashe na rayuwar sa,rungumar da yayi mata runguma ce irin wadda mutum yake buƙatar lallashi,runguma ce irin wadda take nuni da halin da mutum yake ciki,samun kanta tayi da kwanciya luf cikin jikin sa wanda har baka iya gano ta aciki saboda lulluɓin da yayi mata,wani irin ɗumi taji saman wuyanta wanda yasa ta ɗan ɗagowa ta na fuskantar fuskar sa,ga mamakin ta Abdallah ne yake hawaye,wanda hakan ya kuma kiɗimata,tabbas duk abinda zai sa Oga Abdallah hawaye ba ƙaramin abu bane,kallon fuskar sa take tamkar tana san gano amsoshin ta cikin ƙwayar idanun sa, A hankali yasa hannu ya maida fuskarta kan ƙirjin sa tare da ƙara tsaurin riƙon sa A gare ta. "Cikin wata iriyar murya mai matukar sanyi da sanya kasala,yace"Bint!innalillahi kalmar da ta ambata kenan can ƙarƙashin zuciyarta,a yayin da taji wani irin yanayi ya lulluɓeta tare da wata iriyar kasala da wani irin sanyi da yagame dukkan sassan jiki da ɓargon ta,tunda take bata taɓa jin wanda ya kirata da wan nan suna ba,bata kuma taɓa jin wani ya kirata da wannan sigar da Abdallah ya kirata dashi ba,kuma bata taɓa shiga wani baƙon yanayi dan wani ya kirata ba sai yau, yau ɗin ma yanzu A cikin wannan lokacin,to ko dan bai taɓa kiran sunan ta bane yasa taji haka?ƙara kiran sunan ta dayayi ne yasa ta ida shiɗewa dan wannan karon kasa jurewa tayi sai da ta kuma shigewa cikin jikin sa tare dasa dukkanin hannuwan ta ta rungumo shi ta hanyar zagayo dasu ƙugun sa,ta kuma shiga murza kanta akan ƙirjin sa tana wata irin sheshsheƙa wan da ita kanta batace ga dalilin yin hakan ba,lumshe kyawawan idanun sa yayi masu kama dana mai jin bacci,cikin lokaci ƙan ƙani ya dinga jin wata nutsuwa na saukar masa abinda ya tokare masa a maƙoshi ya dinga faɗawa,sunkuyo da kansa yayi ya cusa hancin sa a wuyanta yana shaƙar wannan masifaffen ƙamshin da yake barazanar tafiya da tunanin sa,a wannan yanayin gaba ɗayan su wani nannauyan bacci mai cike da nutsuwa yayi awan gaba dasu batare da sun shiryawa hakan ba. "Dariya yayi cike da farin ciki,kana ya dubi tsayayyen mutumin da bashi da maraba da gawa,yace"ka gani ko ABUBAKAR saina watsa farin cikin waɗan nan ƴaƴan naka masu taurin zuciya,saina gama tsorata rayuwar su da barazana da tsafi na kuma mai dasu wawaye san nan na kawo su nan na na buɗe bakin ka agaban su ka gaya min inda ajiyar take,kai kuma A gabanka zan saka kawunan su cikin injin tsafi,wanda dole hakan zai sa ka buɗe baki ka gaya min inda aka ɓoye ajiyar zan gani shin riƙe amana yafi ɗanka da ƴar ɗan uwanka?dama na gaya maka zan yi ta ajiyar ka domin akwai ranar da kai da kan ka zaka tona abinda ka binne, ƴaƴan ka sune zasu zama garkuwar da zanyi amfani da ita dan nasaka tilas ka faɗa ko kaƙi ko kaso,duk da yanzu ma inada dama amma bazan yi ba saina jagwalgwala rayuwar su da tunanin su,yaro ke nan Abdallah kun kawo kan ku da kanku inda zaku zubda hawaye,agaban idanun ku baban ka zai faɗan abinda na daɗe ina binsa ya faɗa yaƙi faɗa,kuma agaban idanunka zan ƙarasa rayuwar sa dan bashi da wani amfani an riga anman ta da babin sa na rufe tunani kowa babu mai iya furta sunan sa sai maƙiyan sa,wata dariya ya kuma sheƙewa da ita yana cewa da kyau rashi kasheku tun farko yamin rana dan dana kasheku to da Jack Bai kawo min wannan mafitar ba,akan wannan burin ban san adadin rayukan da na kashe ba ƴan mata da samari da jarirai,dan haka ina da tabbacin burina ya kusa cika na mallakar duniya. A wannan daren baccin Dady Mansur ragaggene,dan ko mama sarah bata kaishi shiga tashin hankali ba ita da takasan ce uwa,babu irin alwashin da baici ba akan duk wanda yasamu da hannun sa akan sace masa gudan jinin sa ba,babu wanda baiyi zargi ba daga kan Baba Hashir har zuwa kan waɗannan mugayen munafukan aminan Alhaji Baba ɗin,koda yake duk tafiyar su ɗaya dasu Baba Hashir ɗin,shi yanzu tunanin sa kawai yadda zasu bashi ɗan sa batare da sun cutar masa dashi ba,tunda shi dai bashi da wani laifi ko wata masaniya akan duk wani abu da suke nema,tom dan mai zasuyi masa garkuwa da Sayyid duk yawan jikokin Alhaji Baba Amma su rasa wanda zasu ɗauka sai ɗan sa,juyawa yayi tare da ƙara gyara kwanciyar sa yana kuma Allah Allah gari ya waye dan yasan matakin da zai ɗauka tun kafin su cutar masa da yaro. "Anty Nafisa ma kusan haka abin yake agurin ta, kai ita ko da runtse bata runtsa ba, yadda taga rana haka taga dare,ji take kamar ta janyo safiya dan ta samu damar ganawa da Bintu,ji takeyi ganawa da Bintu kamar shine mafitar matsalar ta,shawarar Bintu itace abinda take buƙata,domin kuwa shawarar Bintu ce zata bata damar tunkarar Umar da abinda ke kai kawo azuciyar ta,zuwan ta ɓangaren inno kuwa ya zama dole ko da kuwa innon zata zargeta akan yawan ganawarta da Bintun. "Kiran sallar da aka ƙwala cikin danƙareran masallacin dake cikin ESTATE ɗin shi ya ta dashi daga baccin da ya kwashe shi batare da ya shirya ba,a hankali ya buɗe idanun sa da sukayi masa nauyi,bai sauke su ko ina ba sai kan kyakkyawar fuskar Bintu da ke ƙwaƙume cikin ƙirjin shi,zuba mata kaifafan idanun sa yayi masu matukar kyau da sheƙi,kallon abubuwan da suka faru a daren jiya yake tamkar a fai fan majigi,ganin ko mai yake tamkar shirin Film,lamarin Bintu ya matuƙar gigizashi da ɗaure masa kai,in dai har kunnen sa yaji masa dai dai ba kuma mafarki yake ba,to hakan yana nufin Bintu jikar ALHAJI BALARABE ce ƴar cikin ahlin sa kuma jinin sa mafi kusan ci da shi ƴa awajen Baffansa, Umar ƙani ga mahaifin sa,jika a wajen Hajiya Babba,to shi abinda bai gane ba dama Abba Umar ya taɓa haihuwa ne,shi dai yadda ya sani Anty Nafisa bata taɓa haihuwa ba kuma a iya sanin sa ita kaɗai ce matar da yake da'ita,dafe kan sa yayi wan da yake masa wani irin sarawa saboda tsananin ruɗani da kwan cewar tunani,ya shiga cikin duhu matuƙa da wannan al amari,ƙara kallon Bintun yayi yana ji tamkar ya tasheta yanzu ta war ware masa wannan curku ɗadɗen al'amarin,zame ta ya farayi daga jikin sa saboda yaji ana ƙoƙarin ta da Sallah,gyara mata kwanciya yayi saman faffaɗar kujerar tare da gyara mata dogon gashin ta da yarufe mata fuska,cikin hanzari ya ɗauro alwala ya fita bai nufi sashen Alhaji Baba ba dan dana yanzu ba kullum suke tafiya tare ba,a cewar Alhaji Baban wai yanzu ya zama magidanci ba zai dinga jiran sa ba dan kar ya makarar dashi,a lokacin murmushi kawai yayi yana aiyanawa a ran sa ko mai zai sa ya makara a masallaci oho, to kuma tun kan aje ko ina gashi shagwaɓɓiyar yarinyar nan tana saka shi fara makara, tun da duk ranar da ta kwana sashen sa sai dai yayi gaggawar alwala,da wannan tunanin ya isa masallacin. A hankali ta buɗe idanun ta tare da addu'a a bakinta,falon ta shiga bi da kallo,sai alokacin ta tuna abinda ya faru da sanadin kwanan su afalon,mai da idanun ta tayi ta rufe,tanajin wata iriyar kasala da wani irin fargaba cikin zuciyarta,tabbas kalaman mutumin nan sun tsorata ta,duk da bata fahimci wasu kalaman nasa ba,,tashi tayi taje ta ɗauro alwala kana ta nufi ɗakinta,zuciyarta cike da saƙe saƙe,da neman mafita ga kuma tsoron mutumin nan da san gano ko waye,tunda har yasan ko ita wacece ya kuma san inda aka ɓoye iyayen ta dole ne ta jajirce domin yaƙi da azzalumi irin sa dolene ya fito mata da iyayen ta, tabbas ya sauƙaka mata wahala yanzune yaƙin zai fara zafi tun da ta fara sun suno hanyar da zata samu kubutar da iyayen ta,to Abdallah kuma fa?hakan yana nufin da shima akwai tashi ƙaddarar mai kama da tata ƙaddarar?to idan hakane me yasa sai su?kuma meye dangantakar ta da Abdallah? lallai tana buƙatar waɗan nan amsoshin nata daga bakin Oga Abdallah, tunda ta fuskanci matsalarsu ɗaya,kuma ya riga yaji komai babu batun yi masa ƙunbiya ƙunbiya cikin tarihinta,dama tana tsorone dan kar wani acikin baƙaken mugayen suji su farmaki rayuwar ta,to amma yanzu tana da yaƙinin bata da wata da bara illa ta tonawa Abdallah sirrin ta,tunda ta tabbatar da shine wanda fafinta ya sanar da ita zai taimaketa,oho yanzune ta gano dalilin da yasa fafi yake yawan ce mata shima yana buƙatar ta akusa dashi domin tare zasu haɗu suyi yakin warware mugun ƙullin da yake sarƙafe da rayuwar Ahlin su,da wan nan tunanin ta shiga ɗakinta dan gabar da sallar asuba, Baiyi mamakin rashin ganin ta a falon ba,kai tsaye ɗakin sa ya shige dan shirin fita,dan baya tunanin ko karyawa zai tsaya yi,so yake yaje ya haɗu da Dady jafar ga kuma batun Sayyid duk da bai shiryawa ganawa da Sayyid ɗin yanzu ba,kuma bayajin zai sakeshi a ƴan kwanakin nan so yake ya haɗa faɗa gagarumi wanda zai kuma haska masa hanya,dan yasan abinda ya zama dole ne Dady Mansur ya tunkari wadan da bai yadda dasu ba yake kuma zarginsu da batun Sayyid, shi kuma da wannan dama zai kuma amfani dan gano mutum ƙwaya ɗaya da yafi addabar su ya kuma ɗauke mahaifinsa abin tunƙahonsa,duk da yana ganin ba lallai ne yasamu abin da yake so ta wannan ɓangaren ba,amma kuma tunanin sa ya bashi tunda duk abu ɗaya suke nema babu aibu dan yabi wannan hanyar hakan ma zai iya bashi wata hanyar ko yaya take tunda shi jam'i,in tsaro baya raina shaida ko mai ƙan ƙantar ta. Bintu kuwa ta riga ta gama shirya masa karin sa tsaf tare da shirya masa bisa dinning table,ɗakinsa ta nufa dan kimtsawa duk da basu kwana cikin sa ba, kuma bata da tabbacin dawowar sa, sai da tayi sallama cikin siririyar muryar ta da ta bada wani sauti saboda yanayin da take ciki na damuwa,sai hakan yabawa Abdallah wani salo acikin kunnuwan sa,ganin sa A ɗakin cikin shirinsa na fita yasa ta ɗan yi turus tunda batayi tunanin yana ciki ba,ɗan duƙawa tayi ta gaida shi,amsawa yayi ba tare da ya ɗauke kaifafan idanuwan sa akanta ba,hannunta tashiga murzawa,kanta a sunkuye,gaba ɗaya jinta take atakure cikin wani yanayi saboda kallonsa gareta,batasan meyasa yake mata wannan mayataccen kallon ba,da taga dai abin bana ƙare wa bane sai ta shiga ƙoƙarin yaye bedsheet ɗin dan canzawa,ƙarar zummm zummm da sukaji shiyasa su duka waiwayawa dan kallon inda wayar take,zaro ido tayi dan ganin wayarta ake kira,ita sam ta ma manta anan bar wayar,shi kuma Abdallah da ya dawo daga masallaci ya ɗauka ya shigo da ita ɗakin,sakin bedsheet ɗin tayi tare da matsawa kusa da Abdallahn daya tsurawa wayar ido,a tsorace ta raɓa ta gefan sa tare da riƙo hannun sa dayake ƙoƙarin ɗaukar wayar dashi,ɗan dubanta yayi fuskarsa babu walwala,girgiza masa kai tayi idanunta har sun cika da ƙwallah,bai saurareta ba ya ɗauki wayar tare da danna amsa kuwa,Muryar Anty Nafisa ce ta daki kunnuwan su,wata irin ajiyar zuciya Bintu ta sauke jin ba mutumin jiya bane,miƙa mata yayi,yai mata alamun ta amsa,cikin sanyin jiki, tace"inajinki Anty Nafisa!'Haba Bintu baki san irin tashin hankalin da nashiga ba tsakanin jiya da yau na rashin samun wayar ki, ga kuma babban tashin hankalin dayake tunkarar rayuwata koma nace ya tunkara,yanzu ina son ganin ki ɓangare na da gaggawa,ki hanzari dan Allah Bintu ki taimaka min ina cikin tashin hankali!'cikin saurin baki Bintu tace"Tom yanzu zanzo Anty Nafisa karki damu gani nan zuwa!'yauwa sai kinzo!'tana kashe wayar Bintu ta samu kanta da shigewa jikin Abdallah da yake sauraran maganar su da Anty Nafisa,wani irin numfashi take saukewa mai nuni da cewa tayi matuƙar razana,lumshe idanunsa yayi,lallai wannan mutumin sai sun dage da addu'a akan sa dan ya fahimci yayi matuƙar razana Bintu,to dama duk mutumin dayake mu amala da jinnu ai ya zama abin tsoro ballantana ga yarinya ƙaramar kamar Bintu,ɗago kanta yayi tare da cewa muje na rakaki,jinjina kanta tayi tare da sakin sa,gani tayi ya buɗe wannan jakar ya zaro mata dogon hijabi kalar blue mai tsananin kyau,miƙa mata yayi ta karɓa batare da wani bincike ba dan yanzu ba wannan ne agaban ta ba,sawa tayi sai yayi matuƙar yi mata kyau da haska farar fuskar ta wanda har sai da Abdallah yaso kasa ɗauke idon sa akanta,cikin tura baki da kuma gajiya da yawan kallon sa tace"to muje mana,hararar borin kunya ya sakar mata kana yayi gaba binsa tayi da sauri suka fita daga ɗakin. Lokacin da suka fito falon,tsayawa tayi tare da ɗan daga murya tace" baza ka karya bane?girgiza kansa kawai yayi yana cigaba da tafiya,cikin gunguni tace"kawai sai asa mutum yayi wahala kuma aƙi ci wannan ai al mubazzarancine,sarai yaji abinda tace"har zai fita sai kuma yaji ba zai iya fita bai karya ba ɗin kamar yadda ta faɗa gaskiya ne idan yayi haka yayi almu bazzaranci juyawa yayi ya nufi dinning table ɗin, zama yayi ya ɗan zuba chips kaɗan kana ya haɗa tea shima kamar na shan jariri, kallon tea din da ya haɗa tayi kana ta ɗan matsa gaban sa tare da ɗaukar ruwan zafin ta ƙara a cikin cup ɗin da ya zuba,ɗan kallon ta yayi ta gefan ido batare da yace"mata komai ba,ɗauka yayi ya ɗan sha kaɗan kana ya tura mata gami da yi mata nuni da ta ɗauka ta sha,tunawa da tayi akwai abinda ke gaban su yasa ta ɗauka ta shanye dan itama yunwa takeji,miƙewa yayi ya wuce gaba tabi bayan sa Taufiƙa ce zaune ita kaɗai a falon kamar tana jiran wani abu,idanunta yana kan ƙofar falon Abdallah,wanda hakan ne yaba ta damar kallon su yayin da suke fitowa,dukkan su babu wanda ya lura da Taufiƙa shi yasa suna kusan tsakiyar falon Abdallah ya ɗan dakata saboda jurwayen shayin dayagani gefan bakin Bintu,tana ƙarasowa kusa dashi ya dakatar da ita ta hanyar kama kafaɗun ta ya juyo da ita ya zamana tana fuskantar sa,kallon sa takeyi cike da alamun tambaya a kan fuskarta,kafin ta gama tunanin dalilin tsayuwar tasu,taji tattausan yatsan shi saman leɓanta yana goge mata shayin da batasan da zaman sa ba, Taufiƙa kuwa yadda kasan idanun ta zasu faɗo ƙasa saboda kallon da ta kuresu dashi,zuciyarta kuwa kamar zatayi bindiga ta faso haka takejin ta, Bata gama fita daga wannan tashin hankalin ba, taga Abdallah ya ɗora bakin sa saman na Bintu wanda yayi hakane saboda ankara da Taufiƙan da yayi da kuma irin kallon tashin hankalin da take musu,sai hakan ya bada wani salo na musamman Bintu kuwa kamar zata shiɗe saboda tsananin firgici da mamakin abinda Abdallah yake yi mata,shi kuwa Abdallah har ya manta manufar da tasashi aikata wannan ɗan yan aiki ga Bintu,shan bakin yake tamkar wanda yasamu alewar minti,wani irin kukan baƙin cikine ya ƙwacewa Taufiƙa wanda shine sanadin dawo da Abdallah cikin haiyacin sa,ɗan tsuka yayi tare da jan hannun Bintu da ta rasa inda zata tsoma kanta saboda kunya da takaicin wannan rashin kunya ta Oga Abdallah,bata iya kallon inda Taufiƙa take ba ta bishi kamar raƙumi da alaka suka fita daga falon,suna fita ya nuna mata hanya dayi mata alamun ta ƙara sa,shi kuma yaja ya tsaya yana son yaga kulewar ta dan tuni ya fahimci yadda tsoron mutumin nan yayi tasiri a zuciyarta,tafiya take A hankali tana waigen sa har dai ta ƙure ta kai hanyar da zata kaita part ɗin Anty Nafisa. Sai da yaga ɓacewar ta san nan ya nufi wajen motocin sa inda Yahya yake dakon jiran fitowar sa. Taufiƙa kuwa tashin hankalin da tashiga babu misali kuka take da idanun ta, tana jin fargabar tabbatar maganganun inno wanda gashi tunkan aje ko ina ta fara gani,wai Abdallah datake tunanin ba zai taɓa kallon macen da tafi Bintu ba, amma wai shi ne yakewa Bintu irin wannan sumba mai tada hankalin lafiyayyar mace,tunda haka ta faru tabbas abinda yake faruwa cikin ɗakin yafi haka,macen da ta raina kamar Bintu itace ta samu kiss ɗin miji kamar Abdallah,me yasa inno bata ƙaunar ta?har take mata bakin da yake neman tabbata,wai shin ya zatayi da soyayyar Abdallah ne?anya kuwa ba ƙas ƙantar da kanta zatayi taje tanemi soyayyar sa ba? tunda tabi ko wacce hanya taga babu riba,kawai abinda yafi mata a yanzu shine ta gwada kissa ko zata dace,da wannan shawarar ta goge hawayen ta, tare da komawa ɗakinsu ta ɗauko wayar ta dan ƙara neman sani a kan hanyar ƙwatar saurayi ta hanyar kissa. Tafe take tana ɗan waige waige, kasancewar safiya ce sosai shi yasa baka jin motsin kowa,sai na kukan tsintsaye,duk da cewa Bintu a tsorace take amma hakan bai hanata ƙarfin halin bi ta wajen ɗakin nan ba,kai tsaye taji tana muradin zuwa wajen koda bata shiga ciki ba ganin ƙofar ma zai iya zama abu mai muhimmanci,tafi-tafi saiga Bintu ta tsallaka inda babu mahaluƙin da yataɓa tsallakawa, wanda koda tsautsayi yasa ka tsallaka tabbas sai wani abu ya sameka,(a cewar su kenan masu gurin)ɗan dakatawa tayi agurin saboda wani abu da taga gilmawar sa kamar mutum,cike da mamaki ta fara ƙoƙarin tunkarar wajen da taga gilmawar,saboda yadda abin ya bata mamaki tunda tasan dai ance babu wanda yake iya zuwa wajen, to in dai hakane kuwa bai kamata taga wata alama ta mutum ba,da sauri tasa hannu ta toshe kunnuwan ta saboda wannan kiɗimammiyar ƙarar da ta taɓa ji a wan can karon wan nan karon ma ita ta kuma sake ji har taso tafi ta wancan karon, yayin da ta dinga ji wajen yana juyawa da ita,haka kuma tana ji tamkar ana son janta zuwa cikin wannan ɗaki ta ƙarfi,ƙara toshe kunnuwan ta tayi tana ciccijewa saboda a yanzu ta tabbatar da janta ake zuwa cikin wannan ɗakin sirrin... Bintu Allahu Ya kareki daga sharrin masu sharri ya kuma baku ikon bankaɗo mana abin da ba ason bankaɗuwar sa, Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 39 ``` Har Yahya ya tada motar tare da fara yi mata wuta,cike da azama Abdallah ya dakatar dashi,cikin sauri ya fito daga cikin motar,haka nan yaji zuciyarsa bata amince masa da tafiyar Bintun ba,tamkar ana ingizashi haka yaji yana son ganin ta,dan jikin sa ya bashi ba lafiya ba tun daga yadda zuciyar sa take wani irin bugu da sauri da sauri,dafe saitin zuciyar sa yayi lokacin da yaji tayi wani irin bugawa da ƙarfi,ƙara ɗaga ƙafafun sa yayi dan san isah inda zuciyar sa ke kai shi, Wata gigitacciyar ƙara Bintu ta saka lokacin da taganta gab da ƙofar ɗakin,wanda ƙarar da tayi tamkar acikin kunnen Abdallah ne,da wani irin sauri mai haɗe da gudu ya nufi inda yake jin sautin ihun na Bintu,lokacin da ya hango Bintu cikin wannan halin baƙaramin tashin hankali ya shiga ba, ƙoƙarin tsallakawa yake yi amma hakan ya gagara,(karku manta fa Bintu ce kawai take da damar shiga gefan ɗakin nan saboda fuwacewa ta Ubangiji da kuma taimakon Baffa Jauro). Buɗe idanun ta tayi lokacin da taji yana ƙwala mata kira,cikin yanayi na tashin hankali tare da karanto duk wata addu'a data zo bakin sa,cikin ikon Allah yana ɗaga ƙafar sa sai gashi Allah ya bashi ikon shiga wajen, cikin wani irin hanzari na ƙarfaffan namiji ya finciko hannun Bintu da ake shirin turata cikin ɗakin nan,tare da ce mata maza kiyi addu'a,amma ina tuni ai Bintu ta sume masa saboda tsananin razana da tayi da wannan al'amarin,ɗaukar ta yayi cak tare da fita daga ɓangaren,yana ƙoƙarin saka Bintu a mota yaji muryar Dady Mansur yana cewa kai kam ka zama wahalalle kai kenan ɗaukar mace"a bainar jama'a,to ai ba sai ka nuna mana Kai ɗin dan zamani bane, tuni mun riga mun sani dan duk wasu alamu sun nuna atare da kai!'tsayawa Abdallah yayi tare da zubawa fuskar Dady Mansur ido,yayin da tunanika sukabi suka da baibaye zuciyar sa tare da zargi mai ƙarfi akan Mansur ɗin,me yasa yake yawan ganin sa ta wannan ɓangaren ne?me yake yi a wajen?meye kuma haɗinsa da wajen?meye ne kake kallo na haka kamar zaka cinye Ni Ni dai na fi ƙarfin duka a wajenka babu yadda zakayi dani,Tom kuma ina mai sanar da kai idan har dasa hannun ka cikin ɓatan ɗana to kayi gaggawar sakar min shi idan ba haka ba duk abinda ya faru kayi kuka da kanka!'yana gama faɗar maganar sa yayi ciki tamkar zai tashi sama,saboda fushi da kuma sauri. A hankali Abdallah ya saka Bintu cikin motar, yana shirin shiga sai ga Anty Nafisa cikin sauri ta ƙara sa gaban sa tana cewa kamar Bintu na gani anan? me yasame ta?daƙyar kamar mai ciwon baki yace da ita,ta ɗan tsorata ne,shine ta suma!'da sauri Anty Nafisa tace"to ai ba sai an kaita asibiti ba ko ruwa aka zuba mata ya wadatar!'yahya ne yayi saurin miƙa masa gorar ruwa saboda alamar da yayi masa,ɗan zura kansa yayi ya yayyafa mata ruwan,bata wani jima ba kuwa ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya sai dai amma a tsorace take,ganin haka yasa shi shiga cikin motar tare da tallafo kanta saman cinyar sa,shafa kanta ya shigayi A hankali, tare da ɗan hura mata iska saman fuskar ta,buɗe idanunta da suke rufe tayi,ta zubasu kan kyakkyawar fuskar sa,sai kuma ta ɗan maida su ta lumshe saboda yadda wasu maganaɗisu ke fitowa daga cikin idanun nasa suna shigewa cikin nata idan. Anty Nafisa kuwa tana daga waje tana kallon sarautar Allah,ko tace wata iriyar ƙauna,wadda bata taɓa ji ko gani ba A tarihin rayuwar ta,ga kuma mamakin daya rufeta wai dama wannan muskilin mutumin zai iya tarairayar mace irin haka?to gashi dai ta gani da idanunta ba wai labari aka bata ba, duk da ta fahimci kamar Abdallah bai san da wannan zazzafar ƙauna da yake yiwa Bintu ba,fitowar Abdallah da Bintu ne ya katse mata tunani,bin su ta kuma yi da wani kallo saboda yadda taga Bintu tana wani narkewa Abdallah,shi kuma sai wani rirriƙeta yake duk da fuskar sa A haɗe take amma hakan bai hana damuwar halin da Bintu take ciki baiyana asaman fuskar tasa ba,ganin yana ƙoƙarin wucewa da Bintun part ɗin inno yasa tayi saurin ɗan matsawa kusa dasu tare da cewa,i can help her,ta faɗa tana duban Abdallah sama-sama batare da ta iya haɗa ido dashi ba,ci gaba yayi da tafiya batare daya kulata ba,ganin haka yasa Bintu ɗan dakatawa tare da duban sa tace"ka tafi kawai zamu ƙarasa da Anty Nafisa!'wani irin kallon yake mata wanda har saida ta kasa jurewa ta shige cikin jikin sa,ƙasa-ƙasa cikin miskilar maganar sa yace"kin tabbatar zaki iya babu wata matsala?ɗaga kanta tayi tana mai zamewa daga jikin sa,sakin ta yayi kana ya ɗanja da baya batare da ya ɗauke idonsa akanta ba,Anty Nafisa datayi mutuwar tsaye daƙyar ta iya ɗaga kafafunta tare da kama hannun Bintu suka fara tafiya dan shiga falon inno, Anty Nafisa ta shiga tsananin mamaki da irin wannan soyayyar da ta hango cikin idanun Abdallah da Bintu,anya kuwa soyayya zata bari Bintu tayi mata abun da ya dace akan wannan al'amari?to amma dai bazatayi saurin karaya ba tunda wannan tunanin tane ba tunanin Bintu ba,da haka suka dan gana har zuwa cikin ɗakin Bintu batare da kowa ya gansu ba saboda basu tarar da kowa A falon ba, inno tana sashen Alhaji Baba ita kuma Taufiƙa sun ƙule cikin ɗaki tana nemarwa kanta mafita,shi yasa suka shigo ba tare da kowa ya gan suba. Suna shiga ɗakin Anty Nafisa ta maida ƙofar tare dasa mata key,zama tayi gefan Bintun wadda ta shiga duniyar tunani, gaba ɗaya tunaninta yana kan wannan ɗakin itafa tasha alwashi ko zata rasa rayuwarta sai tagano sirrin ɗakin nan, wannan abin da akayi mata ba komai bane ba kuma ba zai sa taji ta karaya ba,ji tayi ma tamkar an zaburar da ita akan al'amarin,dafata Anty Nafisa tayi tare da cewa Bintu wai mai yafarune? tun ɗazu nake jiranki ganin bakizo bane yasa na biyo bayanki!'Buntu tace"ba wani abu bane ba fa Anty, A hanyar zuwa wajenki ne fa na ɗan samu tsautsayi,sauri tayi ta kawar da zan cen da cewa Anty Nafisa me yake faruwa ne kike nemana haka da gaggawa?take fuskarta ta sauya saboda motsuwar abinda yake ranta,cikin kama hannun Bintun tace"haƙiƙa ina cikin tashin hankali mara adadi,a hankali ta shiga zaiyanawa Bintu duk abinda ya faru ta ɗora da cewa,tashin hankali na bai wuce yadda zanyi nasan abinda Umar yake shiryawa ba,ban san me yake nufi da mallakawa, gaibu dukiyar sa ba,na shiga matuƙar ruɗani tare da duhun da naka sa ganin haske ko yaya yake!'tun da Bintu ta fahimci inda labarin Anty Nafisa ya dosa ta manta inda take saboda ruɗewa da tunani,me yake shirin faruwa ne?ba dai mijin Anty Nafisa shine mahaifin ta ba?wata irin zufa ce ta shiga keto mata,yayin da ƙwaƙwalwarta ta cigaba da yin zagaye tana auna abinda sa hannun yake nufi da labarin rayuwar ta,da kuma sunan mahaifinta da fafi ya gaya mata cikin labarinta wanda duk ta mantasu Abaya sai yanzu komai yake dawowa cikin ƙwaƙwalwar ta,ga sunan da ta ambata yayi dai dai da sunan da mutumin nan ya ambata, hakan yana nuni kenan mijin Anty Nafisa ita ya mallakawa dukiyar sa?to yasan da ita ne?kuma waya bashi labarin an haifeta,?tunanin tane ya kai kan matar Baffan ta fafi da mahaifiyar su,to ko mahaifinta ya same su dan ta hanyar sune kaɗai zai iya samun labari akan su ta hanyar sune ka ɗai zai san cewa Laila ta haifa masa ɗaya mace,to hakan yana nuni da cewa suna raye?idan suna raye to suna ina?Bintu fa ta ruɗe lallai tana buƙatar waɗan nan amsoshin a kusa,to amma ai zata iya samun wasu amsoshin wajen Anty Nafisa duk da tasan baza ta gaya mata ko mai ba,amma tabbas tana da yakinin Aunty Nafisa tasan wani abu akan mahaifiyar ta Laila,idan ba haka ba me yasa ta tashi hankalinta, saboda sa hannun?wata zuciyar tace Bintu ki nutsu kar Nafisa ta ganoki dan agurinta zaki samu,rabin amsoshin ki dan kuwa tasan abinda ke baki sani ba wanda kuma zai iya kasancewa wani ɓoyayyen sirri da batason kowa yasani,tabbas dole kiyi ƙoƙarin binciko wannan sirri, Anty Nafisa ta zaman miki tsanin hawa wanda zaki taka dan cimma kyakkyawar manufarki, da wannan tunanin ta juyo tana daɗa fuskantar Anty Nafisa wadda ta zuba mata ido ba tare da ta katse mata tunani ba dan atunanin ta ita take lalubowa mafita, ɗan numfasawa Bintu tayi tare da cewa"gaskiya wannan al'amari yana buƙatar dogon nazari!'cikin yanayin damuwa tace"haba Bintu Ni da nake ta sauri dan zuwa gareki ki bani shawara amma sai kice sai Anja lokaci,idan wani can shawarar baibgagareki ba me yasa wannan zai gagareki?kai tsaye Bintu tace"saboda ban san makamar zaren ba,bani na fara labarin ba dan haka ƙarƙareshi zaiyi min wuya!'cikin tashin hankali Anty Nafisa tace"me kike nufi Bintu?kai tsaye ta kuma cewa ban san ko mai akan batun yarinyar da aka mallakawa dukiya ba,ballantana nabaki shawarar yadda zaki ƙwaci dukiyar da A kasa hannu domin shaidar ta zama tata!' Wani irin gumi ne mai tafe da wani irin yaji ya shiga sauko mata tako ina,gaba ɗaya miyan bakinta ya ƙafe har wani ɗaci-ɗaci take ji saman harshen ta,hannu tasa ta ɗan share gumin kan goshin ta,kana cikin sarkewar da harshen ta yayi tace"yanzu kina nufin in dai zaki warware min wannan matsalar sai na gaya miki wani abu daya dan ganci yarinyar?jinjina kanta Bintu tayi cikin bata tabbaci,Anty Nafisa ta kuma cewa to idan kuma ban san komai ba fa?wani irin kallo Bintu ta wurga mata a fakaice,kana tace"ai nasan ba zai yiwu ace baki sani ba,kinga fa Anty Nafisa Ni taimakon ki nake yi kuma ina nema miki hanyar da zaki samu abinda kike nema batare da kinsha wahala ba,idan kina ganin wannan ba hurumi na bane babu wata damuwa sai mu canja shawara!'ta faɗa tana mai fargabar kar ta ɗauki maganarta ta ƙarshe,ai kuwa cikin sauri Anty Nafisa tace"gaskiya Bintu gwara mu canja shawara,saboda Ni kaina ban san komai game da wannan al'amari ba,kawai ki taimaka ki kawo shawarar yadda zan ɓullawa Umar ya faɗa min wani abu da yake ɓoyemin!'Bintu dai ba dan ranta ya soba Amma tasan a sannu zata samu abinda take so gurin Anty Nafisa,kuma ko ba komai itama samun bayanai daga wajen Abba Umar ɗin zaiyi mata amfani,dan haka cikin nutsuwa tace"shike nan amma ki ɗan bani nan da zuwa gobe,gaggawa bazai mana amfani ba a wannan gaɓar amma kiyi haƙuri zuwa goben idan Allah ya kaimu!'Anty Nafisa dai ba dan ranta yaso ba haka ta haƙura... Tana fita Bintu ta ƙwatar da kanta jikin gadonta tare da lumshe idanun ta,tana mai tasbihi ga Ubangiji tare da ƙara gine masa akan baiwa da Ni imar da yayi mata,ita da kanta tana mamaki idan ta duba taga yadda take juya rayuwar Anty Nafisa,duk da ba ason ranta ba,amma Allah mai ƙudura ya ɗora mata shakkar Bintu tare da bin duk abinda ta faɗa mata cikin hikimar sa tasan fidda gaskiyar mai gaskiya,gashi dai yabata ƙwaƙwalwa da tunanin abinda ta tsarawa Nafisan kuma har hakan ya zamo mata alheri,tunda gashi ta sanadin shawarar da tabawa Anty Nafisa ta san abubuwa da yawa wanda su yakamata tasani tuntuni amma bata sani ba saboda wani abu da Ubangiji ya ɓoye wanda babu wanda yasan shi sai shi mai kowa da komai,sai kuma wani irin farin ciki da ya mamayeta saboda kasan cewar ta samu mahaifin ta a raye, kuma wanda ya kasance kamili cikin wannan har gitsatstsen family mai abubuwan al ajabi iri da kala. A hankali Hajjah ta ɗora hannun ta saman kan ɗan nata, tare da cewa Habibu me yake damun kane? tun ɗazu kazo ka sanyani gaba da tagumi idan da wata matsala ba sai ka faɗa min ba!'ta ƙare maganar cikin yanayin damuwa da da muwar ɗan nata,ɗagowa yayi kana yace"wallahi Hajjah ba komaine yake damu na ba sai lamarin Yaya Mansur,na rasa me yasa idan zaiyi abu baya tunanin mai zai je ya dawo?cikin san jin abinda ya aikata Hajjah tace"me kuma yayi sababben?cikin jin takaicin abun yace"zuwa yayi har sashen Baffa Hashir ya ci masa mutumci wai yasan sune suka ɗauke masa Sayyid, to maza suyi gaggawar fito masa da ɗan sa ko ya ɗauki matakin da bazai yiwa kowa daɗi ba!'ya ƙarasa maganar yana ɗan huro iska ta bakinsa,shuru Hajjah tayi saboda tsabar takaicin halin ɗan nata,Dady Habib ne ya kuma cewa Ni abinda ya bani mamaki ma bai wuce yadda ya ɗorawa ɗan uwan mahaifin namu sharrin satar mutum ba,ko ta ina hakan zata faru?kuma duk yara sa wanda zai ɗauka sai Saiyyid ɗan Mansur mutumin da kusan shine ya raineshi da hannun sa,Hajjah da sai yanzu ta iya furta wani abu tace"anya kuwa Mansur baya shaye-shaye?idan kuwa har baya shan komai to tabbas yana da taɓin hankali,saboda abin nasa ya wuce makaɗi da rawa,kuma wan nan magana har gaban Alhaji dan wannan hauka ne da rashin kamun kai!'Dady Habib yace"nima abinda nayi tunani ke nan shi yasa na fara sanar dake dan kar yaje yayi abinda zai ɓata musu zumunci!'hakane Habibu Allah yayi maka albarka ya kuma shiryaku baki ɗaya kai da ƴan uwanka,da Amin ya amsa cikin jin daɗin addu'ar mahaifiyar tasa. Kallon ta take ta cikin miƙab ɗin dake sanye a fuskar ta,kallon da take mata kallone na tsana da ƙyashi, da kuma uwa uba baƙin cikin da take son yi mata na toshe mata hanyar samun burinta,tunda taƙi gaya mata inda Abubakar yake wanda ita kuma tayi yaƙinin cewa Laila tasan inda Abubakar yake kawai dai taurin kaine ya hanata faɗa mata,wanda tasan a ƴan kwanakin nan zata sauke mata shi,sunkuya wa tayi ta danƙi gashin kan lailan tare da cewa zaki iya gaya min ko har yanzu baki shirya ba?karfa ki manta kece kika dawo dani kan hanyar da da na kauce mata,wanda dama shine sanadin satoku daga wan can gurin amma sai wani dalilin ya sha kaina na sauka daga kan hanyar da nake da farko, amma sai gashi cikin tabbatuwar samun nasara ta sai ya zamana ke ɗin ke kika dawo da tunani na,to amma me yasa bazaki yi min abinda nake so ba?nace miki in dai kika gayamin suwaye mutanen dasuka ɓoyeku da kuma inda suka ɓoye Abubakar,to nayi miki alƙawarin zan kula da rayuwar Bintu ba zan bari wani abu ya cutar da ita ba!'tana direwa Laila ta ɗauka da cewa ke baki isa ki kare rayuwar wasu ba,tun da kema baki iya kare taki ba,kuma Bintu bata buƙatar kariyar wani bawa kariyar ubangiji take buƙata kuma ta riga tasamu,dan haka sai ki bi wani sarkin Bintu ta riga tafi ƙarfin shu'umancin ku gaba ɗayan ku macuta azzalumai insha Allah ƙarshen ku yana nan zuwa,Ni na gaya miki sai kun to zarta ke da duk wani mai kwatankwacin irin mugun halinki!'kafin ta gama rufe bakin ta matar ta ɗauke ta da wani mahaukacin mari,tana wani irin huci kana tace" ki kiyayeni Ni ba A faɗa ina faɗa,sai kinyi nadamar waɗan nan kalaman naki,dani kike zancen,daga haka ta fita daga ɗakin tamkar kububuwa,tana mai jin baƙin cikin yadda takasa samun abin da takeso,duk faɗi tashin da tayi kuma take kan yi,ko a iya binciken neman Abubakar ta tsaya ya isa a jinjinawa namijin ƙoƙarin da tayi,saboda ita farko neman ABUBAKAR takeyi amma sai tayi kacibus da su Laila,wanda sam da farko batayi niyar ɗauke su ba,amma sai ta canja shawara ta yaudaresu da nufin taimakon su zatayi sai da suka bata labarin su kaf ba tare da sun ɓoye mata komai ba,tun alokacin ta so su gaya mata ko waye ya ɓoye su sai kuma tayi rashin sa a suka gano nufinta,shine dalilin da yasa ta kwashe su gaba ɗaya ta killace da nufin zata iya gane ko waye ta hanyar neman su Lailan da zaiyi,amma sai taji shiru wanda hakan ne ya kuma tabbatar mata da cewa wannan mutumin baƙaramin shu'umi bane,saboda ya kulle duk wata hanya da zata sa agane shi, wannan shine dalilin da yasa tasan tarihin Laila da fafi kuma shine dalilin da yasa take faman ajiye dasu tsawon shekaru,gane Bintun bai yi mata wahala ba tunda tayi binciken ta yadda ya kamata,to kuma sai gashi itama Bintun tana yaƙin neman mahaifiyar ta,abu ɗaya ne yasa ta rabu da Bintu shine tana so ta gano musu wannan mutumin,da zarar tasame shi ita kuma lokacin zata samu kyakkyawar dama akan su su duka,dole tana buƙatar sanin waye wannan mutumin saboda shi kaɗai ne yake da fawar riga ta samun abinda take nema kuma tana ganin kamar Abubakar yana hannun sa,shi yasa take da tabbacin su Laila sun san inda yake tunda sun zauna tare da mutumin,duk da cewa ita bata yar da da wani zuwa wajen boka ba tafi yadda da kaifin basirar ta to amma alokacin sai da ta dangana da wani hatsabbin boka wanda shine ya bata tabbacin anan aka ɓoye Abubakar sai kuma gashi a maimakon ta samu Abubakar sai ta samu su Laila,wan nan abin shi yake matuƙar ci mata rai, kuma tana da tabbacin sun sani amma shegen taurin kansu ya hana su faɗa mata gaskiya,amma babu komai tunda ta haifi ɗiyar da zata nuna mata komai, batare da tasha wahalar da tasha a baya ba, Tun da ya shiga office ɗin bai huta ba,saboda aiyukan da ya tarar,sai dai lokaci lokaci tana yawan faɗo masa a rai,da tunanin ko ya take?ko wane hali take ciki yasan ta da shegen tsoro,shi yasa duk yake jin damuwa aransa,yana fatan dai Allah yasa bata cikin firgici, wayar dake salular dake cikin office ɗin ce tayi ringin ɗaga wa yayi tare da amsawa da ok ya ƙara so!'ajiyewa yayi tare da cigaba da duba wasu manyan fayal dake gaban sa,sallama akayi tare da turo ƙofar officce ɗin, Abdallah ya amsa sallamar yana mai ƙurawa mutumin da yashigo idanu dan san tuna inda yasan shi,har mutumin ya zauna Abdallah bai ɗauke idanun sa daga kansa ba,cikin tsuke fuska Abdallah yace"me ya kawoka officce ɗina? ƙoƙarin tashi yake ya bar officce ɗin saboda fes ya tuna fuskar mutumin idan bai manta ba wannan mutumin yana daga cikin tawagar su Alhaji Nasir,to me yake nufi da zuwa har cikin officce ɗin sa?Alhaji Rufa'i kamar yasan tambayar dake zuciyar Abdallah yace"Abdallah ka tsaya ka saurare Ni a kwai tarin manufofi da kuma ma ana da muhimmanci cikin wannan ziyarar tawa, wanda banyi wannan ziyarar kai tsaye ba har sai da na nemi izinin Dadyn ka jafar!'tabbas kuwa Abdallah sauraran Rufa i Abune mai matukar mahimmanci,dan haka ina baka umarni daka tsaya ka saurari abinda yazo dashi!'Dady jafar ne yake wannan furucin a yayin da yake sako kansa cikin Officce ɗin na Abdallah,zama yayi ba tare da yayiwa Dadyn nasa musu ba sai dai zuciyar sa cike take da mamakin yadda akayi zai samu wani abu mai muhimmanci daga bakin ɗaya daga cikin abokan gabarsa, wanda shi dai baya raba ɗayan biyu cewa yaudara ce,amma dai bari ya saurare shi ɗan yaji shi kuma da wace irin al mara yazo ko kuma tatsuniya... Tuna sarwa Alhaji Rufa'i shine babban yaron Alhaji Baba dake kula da kasuwan cin sa na Kano,kuma shike auren daya daga cikin ƴaƴan Alhaji Baba wato sakina,kuma ɗaya daga cikin ƴan kungiyar su Alhaji Nasir, To gashi dai yayi tattaki yazo har inda Abdallah yake, kome yakawo shi? Wannan duk sai mun haɗu cikin nest page.... Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 40 ``` Shuru officce ɗin ya ɗauka na dan wani lokaci,kana daga bisani Alhaji Rufa'i ya ja doguwar ajiyar zuciya tare da maida duban sa kan Dady jafar,yace" jafar akwai al'amari mai matukar ruɗarwa a cikin rayuwar iyalan mai gida,ɗan gyara zaman sa yayi tare da ƙara fuskantar Abdallah ya cigaba da cewa,tun a shekarun baya na fuskanci yadda al amuran ahlin ALHAJI BALARABE yake sauyawa da wani irin san zuciya da san duniya,kasan cewar Ni ba mazaunin Abuja bane ballantana na sa ido akan wasu miyagun abubawan da suke faruwa cikin ESTATE ɗin,to kuma ina cikin taraddadi da tunanin hanyar da zan ɓullowa al'amarin kawai saiga tayin da su Alhaji Hashir suka kawo min na san in shiga cikin su saboda sun san nima zan taimaka, kuma akwai manyan kadarorin Alhaji Baba A hannuna,ganin wannan ma wata dama ce na samu ta samun zaƙulo abinda ake ta ɓoyan sa da kuma makircin da ake son ƙullawa uban gidana kawai sai na amshi wannan tayin cikin nuna farin ciki,nan kuma aka shiga gwagwarmayar dani da faɗi tashin yadda za a samu wannan ajiyar da kowa yake harinta, A lokacin na samu na tara wujjoji masu yawa akan su Alhaji Hashir,sai dai har kawo rana irin ta yau na kasa gano abin da ake nema,duk iya bincikena da bin diddigina amma hakan ya gagara,kuma abinda na fahimta kamar dai nine kawai acikin su ban san wannan sirrin ba Ni kaɗai suka rufewa wanda nakasa gano dalilin haka, har ma na fara tunanin ko sun harbo jirgina ne nasan tona musu Asiri,sai kuma na lura sam ba haka bane kawai dai har yanzu basu gamsu dani bane,ba yanzu suka shirya sanar dani ba har sai sun gamsu da gaskiyata acikin su,kuma ina zargin Alhaji shamsi yasan ko mai akan abinda suke fafutukar nema, wanda shine baya cikin wannan kungiya tasu hasali ma nuna musu yake baza a haɗa baki dashi aci amanar ALHAJI BALARABE ba, duk da cewa zargina bai tsananta A kansa ba amma ya kamata abi sahunsa dan ina da tabbacin zamu sami wani abu daga ɓangaren sa!'yana tsayawa nan A bayanin sa Dady jafar ya ɗauka da cewa, Alhaji Rufa'i duk wan nan bayanan dakayi mana kamar tuni ne a wajen mu sai ɗan abinda ba A rasa ba,da kuma manufar ka ta shiga cikin su Alhaji Mansur,saboda ba a zaune muke ba kuma in Sha Allah muna gab da tonawa kowa asiri!'miƙewa Abdallah yayi tare da duban Dady jafar,gane abinda yake nufi da yayi ne yasa yace"Abdallah baka ce komai ba kuma kana shirin tafiya,ko baka yadda da gaskiyar Rufa'i ba?ɗan jim Abdallah yayi tare da cewa zan neme shi idan na tabbatar da abinda ya faɗa gaskiya ne!' daga haka ya fita daga officce ɗin ya barsu,Dady jafar yace" da Alhaji Rufa'i kar ka damu nasan zaiyi nazarine akan maganarka,saboda Abdallah mutum ne da bayayin abu cikin gaggawa komai yana yinsa cikin nutsuwa ne shi yasa ba zai saurin baka yarda nan take ba!'Alhaji Rufa'i yace" wannan shine halin manya,kuma hakan Abune mai kyau kayi dacen haihuwa yaron ka yana da ƙwazo da himma da kuma uwa uba san tabbatar da gaskiya, murmushin jin daɗi Dady jafar yayi,batare da yace komai ba,kana yaji daɗi da Alhaji Rufa'i bai san matsayin Abdallah a gurin sa ba,hakan yana masa nuni da cewa har yanzu su Alhaji Hashir basu san waye Abdallah ba,kuma hakan yana nufin sune da nasara akansu Alhaji Nasir ɗin. Fitowar sa daga officce ɗin kai tsaye mota ya shiga Yahya yajashi zuwa asibiti,duk da yadda ƙwaƙwalwar sa ta ɗauki zafi da wannan al'amari hakan bai hanashi nutsuwa ya duba marasa lafiyar da suke buƙatar sa ba,duk da a can ƙasar zuciyar sa ji yake kamar ya koma gidan awan nan lokacin ko dan duba lafiyar Bintu, sai dai kuma hakan ba mai yuwuwa bane dan da akwai ayyuka da yawa da suke gaban sa,wayar sa ya zaro daga gefan aljihun rigar sa, danna wa yayi tare da ɗora ta akunnen sa,ba ayi minti ɗaya ba aka daga wayar,cikin lafiyayyar Muryar shi yace"sani idan kana cikin Kano ina so kayi min wani aiki A nan!'banji mai akace ta ɗaya ɓangaren ba naji dai Abdallah ya ɗora da bashi bayanai akan Alhaji Rufa'i,ya ɗora da cewa inaso bayanan shigo da da sauri,ok kawai yace"tare da kashe wayar ya turata ma zaunin ta.. Dije kin san dalilin da yasa nace ki dawo ko?ba tare da ta jira amsar Dijen ba ta cigaba da cewa,gagarumin aikine ya taso min wanda dole sai da mataimaki,dan haka ina so ki maida hankali kan abinda zan sanar dake, ban ɗaukoki dan kici amanata ba ɗauko ki nayi dan kiyi min aiki,Dije lallai ina buƙatar ki shiga jikin Bintu ba dan kanki ba sai dan kaina da biyan buƙatata,danƙo kunnen Dijen tayi cikin ƙara yi mata kashedi da gargaɗi tace"wallahi wallahi wallahi Dije in dai na sameki da kuskewa daga kan maganata ko cin amanata to ki tabbatar da cewa ƙarshen rayuwar iyalan ki yazo ke nan,ke kuma sai na ƙarar da rayuwarki ta hanyar gana miki azaba iri iri wadda ita kaɗai ta ishi mai irin halinki na cin amana izina,salon da kika fara dashi nakeso ki ɗora ki barta a yadda tasan ki,sonake ki lulluɓeta da kalaman yaudara ki nuna mata kinatare da ita, ki tayata yaƙin nemo wancan shu umin,ni kuma abinda nake buƙata ke nan daga gareta tunda ita da mijinta suna da baiwar gano mugu to Ni kuma da ita zan jingina dan cimma burina!'babu abinda Dije take sai kuka wanda yake tafe da wani irin baƙin ciki na kasancewar rayuwar ta a haka, tabbas da tana da damar canja ƙaddarar ta ta zuwa aƙasan wannan shu'umar mata,sai dai ina, bakin alƙalami ya riga ya bushe Allah da yayo rayuwarta ahaka shi yasan dalilin haɗa ta da wannan mata,insha Allah sai ta zama sanadin bankaɗuwar asirin wan nan makirar mata,duk duniya babu abinda yafi ƙarfin Ubangiji dan haka bazata karaya da waɗan nan mugayen kalaman nata ba,ta riga tayiwa Bintu alƙawari kuma tayi alƙawari ita da Ubangijin ta saita tona asirinta,koda kuwa shine abu na ƙarshe da zatayi arayuwarta,wata gigitacciyar tsawa ta dakawa Dijen wadda har sai da ta toshe kunnuwanta,tare da runtse idanun ta tana kuma mai fatan Ubangiji ya bata dama da nasara akan wannan azzalumar mata,koma wacece,matar tace"kinaji na kina kumajin alwashina akanki dan haka ki tabbatar da cewa ba asamu matsala cikin wannan aikin ba domin shine kwanciyar hankalin ki da rufuwar asirinki da cigaban rayuwar zuri arki!'ki tashi yanzu ki koma cikin ESTATE ki gayawa uwar ɗakin ki cewa kin dawo daga zaman jinyar da kika tafi,daga karshe ina mai kuma tunasar dake muhimmancin amanata!' cikin sanyin jiki da kuma ƙwarin gwiwar rusa rayuwar ta, Dije ta miƙe tare da kama hanya ta fita daga gurin wanda kullum zasu haɗu sai ta canja gurin haɗuwar tasu kai wannan mata ta iya takunta. Dide ta dawo cikin ESTATE da kyakykyawar niya,da kuma burin hada hannu da Bintu dan su cimma kyakykyawar manufarsu wadda abaya ta dakatar dasu,zasu ɗora daga inda suka tsaya, saboda yanzu tana da cikakken ikon tarayya da Bintun zasu kashe su binne batare da tasani ba ta yadda ita take yiwa aiki amma ta wani gefan aikin rusa rayuwarta da farin cikin ta zasuyi ita da Bintu,cikin ƙudurar Allah gashi ita da kanta ta bata damar fallasa sirrinta da kuma rusa duk wani shiri da takeyi dan cimma mummunar manufar ta,ita da kanta ta bata lasisin tarayya da Bintu,tabbas lokacin karya alƙadarin waɗan nan azzalumai yayi lokacin banƙaduwar sirrin su yayi,zatayi abinda ya dace dan kuɓutar da bayin Allah da basuji ba basu gani ba,ko dan haka tasan Allah bazai taɓa bawa wannan tsohuwar azzalumar ikon cutar da ita ba,dan haka da ƙwarin gwiwar ta ta koma aikin ta ka in da na'in. Baƙaramin mamaki Bintu tayi ba lokacin da tajiyo Muryar Dije a falon inno,cikin sauri ta ɗauraye hannun ta datayi kwaɓin alkubus,haka kawai taji tana sha awar yiwa Oga Abdallah alkubus,duk da tasan ba gwanin ta ake masa ba amma tunda yana son waɗan nan nau'ikan abincin wataƙil idan yaga dama yaci batare da ya gwasaleta ba,fita tayi daga kiching ɗin cikin wani irin farin ciki dayakasa ɓoyuwa daga zuciyar ta har saman fuskarta,cikin wata dariyar farinciki ta zube A gaban Dijen tare da kama hannun ta,inno tarike baki yayin da taga itama Dijen fuskarta ta cika da farincikin ganin Bintun,tace"kai Bintu irin wannan farin ciki haka,Dije tayi saurin cewa ai inno Bintu tana da shiga rai saboda biyayyar ta ga manya kinga dai ba wani haduwa muke sosai ba amma mun shaƙu da juna!'inno tace"Dije haka maganarki take kuma kema ɗin Dije ai akwai daɗin zama kin san ance sai hali yazo ɗaya ake kulla abota shi yasa kuka shaƙu da Bintu!'Bintu da bakinta yaƙi rufuwa tace"Allah mama Dije nayi kewarki gashi kuma na rasa wanda zan tambaya ina kike,kullum sai nayi cikiyarki a raina nace Mama Dije balakuro babu sallama!'dariya sukayi gaba ɗaya inno tace"ai bakin kine balakuran!'ɗan tura baki tayi cikin yanayin ta na sakalci tace"Mama Dije mai zan kawo miki?Dije tace"babu komai ai ba yanzu na dawoba na ɗan jima a gidan kinga kuwa ai aƙoshe nake!'inno tasa baki da cewa Dije sai dai idan baƙunta zakiyi mana, ke Bintu je ki kawo mata ko lemo ne ta jiƙa maƙoshinta!'da sauri Bintu ta koma kiching ta haɗowa Dije ƴan kayan taɓa taɓe,tana ajiye mata tace"gaskiya Mama Dije ki dinga zuwa koni na dinga kawo miki ziyara!'inno tace" idan mijinki ya baki umarni ba!'Dije da bata san da batun auren da aka yiwa Bintu ba, ta ɗan zaro ido cike da san ƙarin bayani tace"kai haba yaushe akayiwa Bintu Aure?kunya ce ta kama Bintu dan haka ta gudu kiching dan karasa aikinta tabar inno da yiwa Dije bayanin Auren gaggawar da akayi mata,Dije tayi mamaki sosai da wannan al amari lallai wannan shi ake kira da ƙudurar Allah ƴar aiki da auren ɗan gida amma dai tayi musu fatan Alkhairi tare da kumajin matsuwar keɓewar ta da Bintu,to amma tasan ayanzu dai hakan bazai samu ba tunda dai sun riga su gaisa,sai dai zuwa gobe dan bata son suja lokaci batare da sun tattauna abubuwa masu mahimmanci da ita ba.. Ɗaya bayan ɗaya saida Dady Mansur yabi su ya kare musu tanadi da kuma basu tabbacin in dai basu fito masa da ɗan sa ba zaiyi abinda zai tada hankalin kowa da kowa,mutum ɗaya ya kasa tun kara wanda kuma yasan ko amafarki ba zai taɓa iya tun karar sa da makaman ciyar maganar nan ba haka ya dinga ɓaɓatu shi kaɗai yana harbin iska, Taufiƙa ce zaune A barandar ɓangaren inno,ta zauna ne a inda duk wanda zai shiga ko ya fita sai ta ganshi kuma ya ganta,tun bayan sallar magriba take zaune agurin,wanda ba kowa take jira ba sai Abdallah,shiga tayi take ce raini da ɗaukar magana wanda take ganin dashi zata karkato da hankalin Abdallah zuwa kanta,tun zaman yana mata daɗi har ya gundure ta,miƙewa tayi ta koma falon tana mai fatan Allah yasa inno bata nan dan dama saboda ita ta fito waje,fatanta ya tabbata dan kuwa babu inno a falon sai Bintu wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Taufiƙa ba,aganinta tasamu hanyar da zata rama bakin cikin da ta daɗe tana ƙunsa mata akan Abdallah, saboda a yanzu dai tayi yaƙinin Abdallah ba zai taɓa kaucewa tarkonta ba,dan shigar da tayi ba irin wadda lafiyayyan namiji zai gani ya kauda kai bace,bata kula Bintu ba itama Bintun bata kulata ba,zama tayi akujerar da take dab da ƙofar shiga falon, Cikin ƙasan maƙoshi yayi sallama tare da zuge ƙofar glace ɗin falon alokaci ɗaya yana sako dogayen ƙafafunsa kan tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a bakin ƙofar falon,cikin wani irin yanga da yauƙi Taufiƙa ta miƙe tare da cewa waw broth ur welcome iknow ka gaji sosai,tana faɗa tana karɓar bag ɗin laptop ɗin sa,shi bai masan wacece ba dan har ga Allah bai gane Taufiƙa bace,dan haka saboda gajiyar da yayi kawai ya sakar mata jakar tare da ƙarasawa falon sa, Bintu kuwa tana zaune tana kallon Taufiƙa da iyashegen da takewa Oga Abdallah,lokacin da taga tabishi falonsa,sai taji ta kasa jurewa,tashi tayi tabi bayan su,wanda shi Abdallah ma bai san tanayi ba dan baima san ta biyo shi ba, Taufiƙa baƙaramin kiɗemewa tayi da ganin haɗuwar falon Abdallah ba, ƙoƙarin zama take Abdallah ya ɗan juyo dan atunanin sa Bintu ce,cike da mamaki yake dubanta,yana tunanin wannan kuma wace zararriyar ce,kafin yasamu abin cewa Bintu ta shigo tana wani ciccin magani,wanda ita kanta batace ga dalilin da yasa takejin wannan yanayin ba.shigowar Bintu sai ya ɗauke masa hankali lokaci ɗaya ya tuna halin daya fita ya barta aciki,dan haka sai ya zuba mata lulu eyes ɗin sa,yana so ya tambayeta amma ya rasa ta ina zai fara, kawai sai ya ɗan ɗaga mata girar sa ɗaya,sai hakan ya bada wani salo na musamman,haka nan taji wata shagwaɓa tare ƙwalla sun cika mata idanu,ɗan duban Taufiƙa da tayi mutuwar tsaye agurin tayi tare da cewa to kace ta tafi mana,alamu yayi mata waye take nufi? da ido tayi masa nuni da Taufiƙan,ɗan duban inda take kallo yayi,lumshe manyan idanun sa yayi tare da cewa ba tare kuke ba?hararar gefan ido tayi masa kana tace"Ni ban san ta ba ma!'tafiya ya shiga yi dan shiga ɗakin sa yana cewa na gaji sosai zan ɗan huta!'daga haka ya shige ɗakin tare da kullowa, Bintu ta ɗan murguɗa ƙaramin bakin ta tare da cewa kin ji yace"zai huta,samun kanta tayi da binsa cikin ɗakin tare da yiwa Taufiƙa gwalo, Taufiƙa hannu tasa ta ɗan goge ƙwallar da suke san fallasa tarin bakin cikin dake kwance cikin zuciyar ta,ita da taso ta sa Bintu kuka yau, amma shine reshee ya juye da mujiya,anya kuwa Bintu ba asiri tayiwa Abdallah ba?dan taga kamar ma idonsa rufewa yakeyi idan Bintun na waje,baya tuna kowa sai bayan bata nan,anya kuwa zatayi nasara a wannan gaɓar ma?tunda gashi tunkan aje ko ina ta fara sarewa,wai bai ma gane taba ga kuma ita ƴar iskar yariyar da tasamu waje,wai itama bata santa ba,wata zuciyar tace"da ita Taufiƙa kawai kiyi haƙuri da Abdallah dan tuni yayi nisa bakuma yajin kira,cikin rushewa da wani mahaukacin kuka ta fita daga falon, A can dakin Abdallah kuwa, Bintu tana shiga taga yayi tik daga shi sai dan boxa ihu tasa gami da rufe idanun ta da duka hannuwanta,banza yayi mata bai ce mata komai ba, gashi ita kuma baza ta fita ba saboda kar Taufiƙa tace"korota yayi,ta gwammace tai ta zama da hannu saman fuska,bata buɗe idan ta ba har sai da taji shigar sa toilet ɗin kana ta saki ajiyar zuciya tare da cewa, shi mutum sam babu kunya a idanunsa, da zan shigo ba sai yace min ehemm ba sai nasan abinyi amma ya kama ya barni na shigo naga... sai kuma tayi shiru,tare da fita daga ɗakin dan tasan yanzu Taufiƙa ta gaji da zama ta fece... Zama tayi afalon tana jiran fitowar sa,kasancewar dare ya ɗan farayi sai garin yayi tsit ga kuma yanayin damuna dake sako kai,gari sai yayi kamar hadari,yanayin tsit ɗin da gari yayi shi yaɗan fara sakawa Bintu tsoran zaman falon, ƙoƙarin guduwa ɗakinsa take sai gashi ya fito,kai tsaye ya wuce tsakiyar falon ya zauna,tare da tanƙwashe dogayen ƙafafunsa,cikin miskilar muryarsa yace"kawo min abincin nan!'A hankali tace"yau kuma gargajiyar ce ta motsa? duk da yaji ta amma bai nuna mata alamun hakan ba tara ta kawai yakeyi duk ranar da ya rutsata baza taji daɗi ba,mata ɗin cin abinci ta shimfiɗa kana ta maido komai ta jera su cikin tsari da burgewa,har zata koma mazaunin ta sai kuma tayi wani tunani,dawowa tayi ta zauna gefansa tare da savin ɗinsa,loda alkubus ɗin tayi da yawa kana ta zuba miyar ta tura masa gaban sa,ɗan duban uban abincin da tazuba masa yayi tare da yin ƙwafa aransa, A hankali ya fara cin alkubus ɗin wanda take kunnen sa ya fara motsawa,tsayawa faɗar daɗin da Abincin yayi masa ma ɓata bakine,sai gashi yana neman cinye wanda ta saka mishi,gani tayi ya janyo kular ya kuma zubawa A tunanin ta daɗa wa zaiyi,har tana masa tsiya a ranta,sai taga ya turo shi gaban ta,zaro firgitattun idanunta tayi tare da cewa me za ayi?cinyewa za ayi!'ya bata amsa ba tare da ya dubeta ba,ɗan marairaice fuska tayi,cikin son ya tausaya mata tace"ai ya ai wannan yayi yawa na cifa nida inno!'juyowa yayi yana mai tsareta da kaifafan idanunsa wanda take suka saka mata nutsuwa,batasan sanda tashiga tura alkubus ɗin abakin taba,sai gani tayi kawai ta cinye wanda ya zuba mata tass,ganin ta cinye yasa shi miƙewa dakin sa ya nufa,zaro ido Bintu tayi dan ita dai har ga Allah tsoro take ji kuma sai ya ringa barinta ita kaɗai duk sanda tajita ta ita kaɗai, dakin nan take gani yana gilmawa ta cikin idanun ta,da gudu ta tashi tabishi cikin ɗakin,tana shiga ta shiga raɓewa kamar wata ƙadangaruwa,lokacin har ya gama shirin baccin sa, Zama yayi a gefan gadon tare dayi mata alamar da tazo,ita fa abin nan yafara damunta wai shi baya gajiya da yin magana da jiki ne?ta fahimci sam hakan baya damun shi dan tsaf zata iya irga maganar shi arana,a hankali ta ƙarasa ta zauna akasan ƙafafunsa,cikin kamar yanayin gajiya da jin bacci yace"bani labari,kallon shi ta shigayi tare da san sanin wane labari yake nufi?,katse mata tunani yayi da cewa komai nake nufi maganar ku da Matar nan da labarin rayuwarki da ko mai ma wanda ban sani ba,kuma bana son ki ɓoyen ko mai akan Asalin ki,inaso ki gayamin keɗin wacece acikin wannan ahlin? 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 41 ``` A hankali ta buɗe bakinta ta fara da gaya masa yadda sukayi da Anty Nafisa ba tare da ta ɓoye masa komai ba,shuru tayi bata kuma cewa ko mai ba,wanda shi kuma Abdallah so yake kawai yaji ta bashi labarin ta, Zuba mata ido yayi yana jiran jin ta ina zata fara,dan a haƙiƙanin gaskiya ya zaƙu da yaji wacece Bintu, wanda tun jiya shine aransa so yake ya tabbatar da abinda mutumin nan ya faɗa,idan har abinda ya faɗa yazo dai dai da wanda Bintun zata faɗa masa,to kuwa tabbas dole su san duk yadda zasuyi dan janyo hankalin Anty Nafisa ta buɗe musu sirrin da take ta ɓoyo, dan yana da yaƙinin cewa sirrin baya rasa na saba da Bintun,yana ji ajikin sa Nafisa itace sanadin komai,itace mafarin dukkanin abinda ya faru,dan ga dukkanin alamu tasan da zaman ɗiyar Umar ɗin,idan ba haka ba ba yadda za ayi ace ta tashi hankalinta kamar yadda Bintu ta sanar dashi,tabbas akwai lauje cikin naɗi akwai wani ɓoyayyan al amari me girma wanda ita Anty Nafisa bata son kowa ya sani, shine kuma sirrin datake muƙu-muƙun ɓoyewa,kuma da izinin Allah su sai sun sata ta faɗa ko ma meye da bakin ta,da kanta zata ɗauki wuƙa ta bur mawa cikinta,koma ace ta burma,tunda gashi bata iya aiwatar da komai batare da shawarar Bintu ba,wanda tabbas wannan wata alama ce data ke nuni da cewa ƙarshen Anty Nafisa ya zo, "Ganin yadda ya zuba mata ido yasa tashiga ƙif-ƙifta nata idanuwan saboda ta rasa ta ina zata fara, ita sam bata iya bada dogan labari ba,wani tunani tayi a ranta wanda yasa ta ɗan kalleshi,kana cikin sanyin muryar ta tace"zan ɗauko maka deary ɗin da fafi ya bani sai ka duba,ina ga zaifi sauƙi!'ta faɗa tana lumshe idanunta,cikin alamun nuna gamsuwa da Maganar tata yace"kije ki ɗauko yanzu ina jiranki!'ya faɗa yana ɗan kwanciya jikin makarin gadon,wanda shima faɗa kawai yayi amma yasan Bintu baza ta iya fita a wannan lokacin ba,shuru tayi a wajen batare da ta motsaba,juyowa yayi yana fuskantar ta tare da yi mata alamar me take jira?tura ɗan ƙaramin bakinta tayi batare da tace"ko mai ba,har zai share ta sai kuma yaji ba zai iya ba yana so a daren nan ya karanta labarin Bintun,dan haka ya tashi yana mai zura silifas ɗin dake bakin gadon wanda akayi shi da yadin dake shimfiɗe saman gadon,tashi muje! ya faɗa yana wucewa gaba. A hankali take bin bayan sa, wanda hakan ma ji take kamar za a ruƙota ta baya,lokacin da suka fita falon inno ne taji kamar anabin bayanta,tun tana daurewa har dai ta kumaji kamar an taɓota ta baya,cikin wani irin razana da tsinkewar zuciya ta ruƙo hannun sa yana juyowa ta faɗa jikin sa tasa hannu ta zagaye shi ta rikeshi katamau idanunta a runtse,hannu yasa ya ɗago fuskar ta,yana mamakin abinda ya tsorata ta lokaci ɗaya haka,sam taki bashi damar ganin fuskarta saboda yadda ta shigar da fuskar cikin ƙirjin shi, dalilin kusan cin su da juna ne yasa har yana iya jiyo bugun zuciyar ta wanda suke bugawa tare da tasa zuciyar, A hankali yasa hannun sa A gadon bayan ta yana ɗan partin bayan nata a hankali dan samar mata da nutsuwa,tana manne ajikin sa ya cigaba da tafiya da ita har suka kai cikin ɗakin ta,zama yayi da ita ajikin sa,cikin san yayi calming ɗin ta yace"buɗe idanunki, ki gani ba kowa mun shigo ɗakin ki,tashi ki nunan inda littafin yake!'A hankali yake mata maganar kamar wanda yake tsoran tashin jaririn da ya rasa uwar sa tashi daga baccin da yake,a tsorace ta ɗago kan nata tana bin ɗakin da ido a sace,kana cikin ƙara maƙale shi tace"yana cikin durowar can A cikin wata baƙar jaka, idan ka buɗe jakar zaka kuma ganin wata ƴar leda baƙa to aciki yake!'duk maganar nan da takeyi tuni ta daɗe da mai da kanta ta ƙunshe cikin jikin sa,ba dan Allah yayi masa ƙarfin ji bama da ba zai ji abinda take cewa ba,saboda yadda take yin maganar ƙasa ƙasa,kuma cikin tsoro. Zuba mata ido yayi ganin bata da alamar zata sake shi yaje ya ɗauko littafin,sai aukin yi masa kwatance da takeyi,ganin lokaci sai tafiya yake basuyi abinda ya kamata ba yasa shi fara ɗan janye ta daga jikinsa, haƙura tayi ta rabu daga jikin nasa amma bata rabu da binsa kamar jela ba,har sai da yaje ya buɗe durowar da ta kwatanta masa,ya ɗauko jakar tare da buɗeta ya ɗauko ledar itama kana ya maida su inda suke ya rufe,tana ganin haka tayi saurin matsawa jikin sa wanda dama jiran sa take ya gama abinda yakeyi ta ɗora daga inda ta tsaya,duban ta yayi cikin fuskarsa da take a haɗe yace"Bint wai wannan wane irin tsorone haka?ki rage tsoron nan yayi yawa!'ya faɗa yana ɗan janye ta daga jikin sa,ba dan taso ba ta rabu da jikinsa tare da raɓe a gefe kana ganin ta zaka gane cewa a matuƙar firgice take, durowar kayanta ya bude tare da ɗauko mata kayan bacci da hijabi, kana ya kama hannunta suka fita,har suka koma ɓangaren sa jikin Bintu bai daina ɓarin tsoro ba,wanda shi Abdallah atunanin sa kawai irin tsorone irin na Bintu,amma a haƙikanin gaskiya a kwai wani abu da shi Abdallah bai sani ba. Suna shiga ɗakin sa yasaki hannunta tare da miƙa mata kayan da ya ɗauko mata,karɓa tayi batare da ta motsa daga inda take tsaye ba,tana ta dai jujjuya kayan a hannun ta,ganin kamar bata gane abin da yake nufi ba yasa shi cewa kije ki canja kayan jikin ki idan bazaki iya yin wankan ba!'kamar wadda ƙwai ya fashewa haka take taka ƙafaunta dan zuwa toilet ɗin, zuciyar ta kuwa kamar zatayo waje saboda tsananin tsoron da ke cikinta,ƙoƙar tawa tayi ta fara karanto addu'oi bayan tashiga toilet ɗin,haka nan takejin wata kasala a cikin kwana biyun nan wanda ta rasa da lilin hakan,bata iya yin addu'oin ta yadda ya kamata, ko da ta fara sai bacci ya kamata,ga wani irin tsoron da take yawan ji,wanda ta san da ba haka take ba,duk da cewa tasan tana da tsoro amma ba kamar yadda takeji yanzu ba,cikin san dakewa da kalato jarumta ta cire kayan jikin ta,so takeyi ta ɗan yi wankan dan bazata iya bacci batare da tayi wanka ba,da tai makon addu'ar da ta samu ta zauna abakinta tayi wankan tare da ɗaura alwala kana taja ƙaramin tawul ta ɗaura ajikin ta,tana gab da fitowa taji kamar anja tawul ɗin da ta ɗaura ajikinta ta baya,ai da wani irin gudu ta ƙara sa fitowa jikinta yana wani irin rawa, Ganin ta yayi kawai kamar anjeho ta,da gudu ta faɗa jikin sa tare da ruƙun kumeshi,zuba mata idanunsa yayi zuciyar sa cike da saƙe saƙe,anya kuwa yariyar nan lafiya take?yasan cewa tabbas Bintu tana da tsoro amma kuma bai taɓa ganin tsoron ta kamar na wannan lokacin ba,take zuciyar shi ta fara kaikawo akan wannan al'amari,jin yadda take ta shigewa cikin jikin sane yasa shi dawowa daga nazarin al'amarin da yake,cikin nutsatstsiyar Muryar sa yace"lafiyar ki kuwa? me yake damun ki haka?alokaci ɗaya ya jero mata waɗan nan tambayoyin yana mai son ganin fuskar ta, ta hanyar ƙoƙarin ɗago da kanta da ta cusa a cikin kirjin shi, Zuba mata narkakkun idanunsa yayi A yayin da yasamu nasarar ɗago kan nata,itama kallon shi takeyi,da idanunta da suka cika da ƙwalla,cikin taushin murya yace"Bint gayamin meke damunki?girgiza kanta tayi saiga wasu zafafan hawaye sun sauka kan kumatunta,atare suka kai hannuwan su kan fuskar ta dan share hawayen,shi yana ƙoƙarin share mata itama tana ƙoƙarin gogewa,sai ya zamana hannun sa yana saman nata,kallon juna suka cigaba dayi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa,itace tayi ƙoƙarin fara janye idonta akan sa tare da janye hannun ta,kana shi kuma cikin sanyin murya da kasalar da tausayin ta yasaka masa ya yace" da ita,faɗa min damuwar ki!'salon da yayi magana dashi shine ya kuma karya wa Bintu zuciya kawai sai ta saki wani ɗan marayan kuka cikin muryar kukan da takeyi ƙasa ƙasa, tace"bana jin daɗi tsoro nakeji zuciya ta wani irin bugu take,ban taɓa jin abin da nakeji yanzu ba na kasa yin addu'a kayi min addu'a kaji Yahh Abdallah!'ta faɗa tana saka duka hannayen ta saman funkar ta tare da girgiza kanta,wani irin tausayine wanda yake gauraye da wani irin yanayi da ba zai iya tan-tance na meye ba ya rufe shi,cikin yanayin da bai sake shi ba ya gyara kwanciyar shi sosai kana itama ya gyara mata kwanciya ajikin sa tare da sa blanket ya rufeta,kana ya shiga tofa mata addu'oi har sai da yaji ta daina jan ajiyar zuciya tare da shaahsheƙar kukan da takeyi,kana ya janyo littafin da dama yana kusa dashi ya buɗe tare da Bismillah,ya fara karantawa, "Wani mudubi ne a gaban sa yake kallon duk abinda suke yi, amma Abdallah yana fara yiwa Bintu Addu'oi sai hotan su ya ɓace masa kamar walƙiya,dariya yayi tare da cewa,duk abin da zakayi nasara na gareni tunda har nayi nasara a kan matar ka to kai ma bazaka gagari dodo jack ba!'juyawa yayi ya dubi Alhaji Abubakar dake cikin wani irin yanayi na sihiri,yace"na gaya maka Abubakar sai nayi nasara akan ku,sai naga ƙarshen ku kaida duka zuri ar ka,wani shu'umin murmushi yayi tare da shafa ƙeyar shi da ita kawai nake gani yace"Bintu banyi niyar biyo miki ta haka ba ke kika jawo,saboda kina son ganin ƙarshe na kina son ganin bayana,koshi Abdallah baya ƙoƙarin kai kansa wannan ɗakin amma ke kullum burinki ki tona sirrin dake ɗakin,bayan kuma shine rayuwata shine garkuwa ta,bankaɗa ɗakin nan tamkar bankaɗa sirrina ne,tabbas duk ranar da nabarki ki ka samu nasara akan ɗakin nan to kamar kin samu nasara a kaina ne,wanda Ni kuma bazan taɓa baki wan nan dama ba,dan haka zan saka rayuwarki cikin wasi-wasi da halin razana, wannan tsoron da nasa miki shi ne zai rage miki ƙwarin gwiwa da tunanin tun karar ɗakin,ya kuma ƙyalƙyalewa da wata mahaukaciyar dariya yana cewa yarinya baki san wuta ba sai kin taka Ni ƙi gudune maganin sa gudu,murucin kan dutse ban fito ba sai da na shirya,ƴan jakar uba kwayi kwa gama rana ta tana nan zuwa,ranar da zan ganni gani ga burina a hannu na,Hhhhhh. " A ɓangaren Anty Nafisa kuwa tana cikin halin ƙaƙa niƙayi,ta kasa zaune balle tsaye,burinta gari ya waye taji abinda Bintu zata kawo mata,sai dai fargaban ta ɗaya,bata so Bintu ta kuma yi mata batun san jin mafarin al'amarin tana tsoron jin hakan daga gareta,lallai wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan hanya,wani ɓangare na zuciyar ta yace"to meye ne idan kin gaya mata abinda kika sani, bake kika ce kin yadda da ita ba,ai kamar babu wani abu dan kin sanar da ita ɓoyayyen sirrin ki wanda babu wanda yasa Ni daga ke sai ALLAH da ya halicce ta,zama ta ɗan yi tare da tallafe fuskar ta,wata kuma zuciyar nayi mata gargaɗi da aikata wannan gangancin,to ita dai tafi yadda da ɓangaren dayake mata gargaɗin sanar da Bintu ɓoyayyen ƙullin da ta ƙulla tsawan shekaru batare da ta kwance shi ko warware shi ba,to amma dai yan zu bari ta jira Bintu dan jin abinda ta yanke akan shawarar da ta nema ɗin. Tunda ya gama karanta littafin babu abinda yake yi sai tasbihi da ƙara kaɗaita Allah assamadu,tabbas ya shiga cikin ruɗani da wani irin tausayi me tsanani na gaba ɗayan su ahlin,tun daga kan Baffan sa Umar da mahaifiyar Bintu Laila da fafi da iyalan sa,sai uwa uba Bintu wadda yakejin tausayin nata har kamar zai saka shi kuka,kallon fuskar Bintun yake da take ta shaƙar baccin ta,ganin yadda take ta ɗan yatsine fuskane ya tabbatar masa da ba wai daɗin baccin take ji ba, addu'oi ya kuma tofa mata kana ya tafi duniyar tunanin yadda zaiyi ya nemo kakar Bintu wato Hajjon su Laila ita da iyalan fafi,wanda kuma yasan hakan ba zai taɓa yiwuwa ba har sai da tallafin Baffan nasa saboda ya riga ya tabbatar da cewa a yanzu haka Baffan sa Umar yasan inda suke, saboda bashi da wata hanya da zai iya sanin abinda ya faru da su Lailan sai ta hanyar su Hajjon,to ta yaya zai yi hakan batare da shi Baffan nasa yasan komai ba?wata zuciyar tace"dashi haba Abdallah sai kace" ba aikin ka ba, wannan ai ƙaramin aikine a wajen ka koda baka bi ta hanyar Baffa Umar ba zaka iya lalubo inda su Hajjo suke,da izinin mai duka da wannan tunanin ya samu ƙwarin gwiwa,to su kuma su fafin suna ina? A hannun wa suke?tunda dai ga dukkanin alamu suna raye,to ko suna wajen wannan tsinan nan da yake batun wai ba dan ba da ya faɗa musu inda su Lailan suke,lumshe idanun sa yayi yana mai jin kansa na sara masa saboda tsabar yawan tunani,cikin nutsuwa ya zame Bintu daga jikin sa ya tashi ya shiga toilet ya ɗauro al wala,har zai tashi Bintu sai kuma kawai yaji gara ya barta taɗanyi bacci,shimfiɗa sallaya yayi tare da fuskantar alƙibla dan kaiwa Allah ƙadiran ala manyasha'u kukan sa domin ya jiɓanci dukkan lamuransa na zahiri da na baɗini, Allah kabamu dacewa duniya da lahira. Tunda ya tasheta tayi sallar asuba tana cikin yin azkar bacci ya kuma surarta,a haka ya dawo daga masallaci ya same ta,ɗan tsayawa yayi akanta yana kallon ta cike da tunanin abinda yakamata yayi,ya fara tunanin ko dai asibi zasuje aduba lafiyar ta ɗan tabbas yana tunanin akwai matsala cikin wannan sabon Al'amarin na Bintu,da wannan tunanin ya nufi toilet da tsaf tace jikin sa, Tayi kiran wayar sau ba adadi amma duk abu ɗaya dai wannan matar ke sanar da ita,lambar bata yin aiki,cikin ɓacin rai Hajiya ladidi ta jefar da wayar can gefe tana cigaba da zabga tsakin da tayi shi yafi sau goma,yau kimanin kwana goma ke nan tana kiran mutumin nata wan da yayi mata bad da bami amatsayin wancan shu'umin mutumin,ta rasa dalilin da yasa ta kasa samun shi a waya,sai yanzu ne take ganin waw tar ta na kasa sanin komai akan sa,sai waya da nomber da ayanzu bata da wani amfani a gurin ta,to wai ita tun farko ma mai ya shiga kanta ne da ta kasa yin abinda yake daidai har ta bari wani ƙato can yana sarrafa tunanin ta?gashi ko Nafisa bata san komai akan tarayyarta da ɗaya daga cikin ahlin ALHAJI BALARABE ba,anya kuwa batayi shirme ba? ita da take neman dukiya sai gashi bata samu ko doki ba, tana nan daga zaune duk abin nan da tayi yana son tashi a banza,anya kuwa zata yadda ta tashi atutar babu?babu wan babu ƙanin,taɓ ai kuwa hakan ba zai taɓa yiwuwa ba dolene Nafisa ta cigaba dayi musu yaƙin neman dukiyar cikin ESTATE ɗin nan,tunda dai tana ji tana gani wan nan damar ta kufce mata, yanzu kuwa dole saban lale za a sake tunda suna da Bintu a hannun su,da wannan shawara ta ɗauko wayarta dan kiran ƴar tata dan su tattauna. A hankali ta zare ta gumin da Ammin nata ta rafka,tare da zama a kusa da ita tana kuma ƙoƙarin san taga sun haɗa ido,sai dai ina hakan bai samu daga gurin Hajiya zulaihat ba,ɗan shuru Rahima tayi tana kallon yadda Ammin ta haɗe mata girar sama da ta ƙasa,ta san ba dan komai takeyin hakan ba sai dan tayi garkuwa daga manyan tambayoyin da tasan zata yi mata,ƙara matsawa tayi kusa da ita kamar zata koma Cikin ta,abin da ya fusata Ammin ke nan,cikin hasala tace"waike kam Rahima meke damunki haka? gotai-gotai dake kin zo kina neman komawa ciki!'ta ƙara sa maganar amatuƙar fusace,dan so take ta kaucewa tambayar da Rahiman take son yi mata a duk lokacin da ta risketa cikin wannan yanayin,cikin marairaice fuska Rahima tace"kai Ammi ke ko irin kewan nan nawa bakyayi,tunda kika korani gurin Hajiya Babba baki taɓa cewa Rahima na ina kewarki yau kizo min mana ko kwana biyu kiyi min sai ki koma ,Ni kuma na gaji da kewarki da rashin ki nazo amma nazo kina korata da hantara!'ta faɗa tana mai goge hawayen da suka zubo mata akan fuska, Allah sarki uwa,sai kuma duk Ammi taji rashin daɗin abinda tayiwa autar ta ta,cikin sanyin murya tace"haba auta ya za ai nace bana kewarki,kema kin san faɗa ma ɓata bakine kawai dai inayin nesa dake ne dan bana son damuwata ta shafeki har ta sakaki cikin wani hali!'ta karasa maganar tare da jin tasowar wani ɗaci mai haɗe da zafi dake ƙunshe cikin zuciyar ta,kama hannun ta Rahima tayi tare da cewa,Ammi idan damuwarki bata saka min damuwa ba to rashin ki zai sa tabbas nima A rasani,domin tabbas kikaci gaba da ɓoye abinda yake ranki tare da baiyana damuwar ki to wataran sai dai nazo na tarar da babuke,yawan damuwarki ya kai mizanin da komai zai iya faruwa dake, Ammi Ni ban ce sai kin faɗa min damuwar ki ba,dan tunda na san bakya son faɗa min na haƙura, amma dai ina so ki rage yawan damuwar ko da ba duka bane nasan lafiyarki zata iya inganta!'murmushi Ammi tayi mai matukar ciwo kana cikin tausayin kanta da ɗiyar tata,tace"wallahi Rahima na rage damuwa tuni na fauwalawa Allah dukkan lamurana,dan da ace ban daina ba da bazan kai yanzu ba,to amma na riga nayi tawassali da tsarkakan sunayen Ubangiji na kuma san cewa ƙaddara jarabawar rayuwace,ta wani tafi ta wani ta wani bata kai ta wani ba, haka kuma ta wani kyakykyawa ta wani kishiyar hakan,dan haka ki daina damuwa,nima na daina damuwa tunda nasan Allah baya bacci yana ji yana kuma gani,kuma na roƙe shi cikin bacci na roƙe shi cikin ido biyu na roƙe shi da rana da dare da safe,haka kuma na roƙe shi cikin sakanni da mintuna da awowi,dan haka ina nan ina jiran Ranar da ƙudurar sa zata haɗu da irada,ranar da zaice ta kasan ce ita kuma ta kasan ce,domin nayi yaƙini tuni addu'a ta ta riga ta amsu sai jiran lokacin da zata baiyana!'Alhamdulillahi alakullin halin,da yayini a musulma na tashi cikin musulun ci kuma ya tsarkake zuciyata daga bin wanin sa ya bani kyakykyawar zuciyar da na kaɗaita shi shi ɗaya na kuma dogara da shi,cikin ma bayyanin farin ciki da samun nutsuwar zuciya Rahima tace"Allah ne abin godiya A ko da yau she!'daga nan Ammi ta zarce da yiwa Rahima nasiha tare da tunatarwa wanda suke shiga jinin jikin ta da ƙwaƙwalwar ta suna zagawa tare da samun wajen zama. Hajjah ta zubawa Taufiƙa ido A yayin da ta gama ratta ba mata jawabin ta, cikin kuka da wani irin baƙin ciki dake tasowa tun daga ƙarƙashin zuciyar ta,wani ɗan murmushi Hajjah tayi kana tace"yaro dai yarone,to yanzu Ni me kike so nayi miki da kika kwaso uban kaya kika dawo nan,ko so kike na kira shi Abdallah n nace masa gaki ya aure ki? Taufiƙa ta kalli Hajjah da jajayen idanun ta da suka rune saboda kuka,tace"Hajjah dan Allah ku taimakamin wallahi zai iya yadda idan kuka gaya masa saboda kema kin san Yah Abdallah yana da biyayya,tunda itama waccen ƴar matsiyatan bashi ita akayi kuma yakarɓa,nima idan kuka ce masa ya aureni wallahi Hajjah zai yadda, na yadda zan zauna da Bintu Ni dai kawai kusa shi ya aure Ni dan Allah Hajjah!'ta faɗa tana mai saukowa ƙasa ta riƙe ƙafar Hajjah tana wani irin kuka kamar ankashe mata duka dangin ta,kafin Hajjah tayi magana Dady Habib dake shigowa falon yace"Hajjah ya kamata a duba lamarin yarinyar nan kar taje ta shiga wani hali akan abinda zamu iya bata!'shuru Hajja tayi cike da yin dogon nazari akan maganar Dady Habib,can taja numfashi tare da cewa..... Fatimah y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 42``` Kai yanzu Habibu kana ganin wannan shine adalci?sunkuyar da kansa yayi kana cikin ladabi yace"Hajjah gani nayi kamar idan akai hakan shine hankalin ta zai kwanta, tunda kinga itama waccen yarinyar bashi ita akayi ina ga itama Taufiƙan idan aka bashi zai karɓa yayi biyayya!'wata irin harara Hajjah take zuba masa tun kafin ya ida maganar tasa,yana direwa kuwa ta ɗauka cikin faɗa tace"amma kai kam Habibu wallahi baka da kirki, wannan sankan har ina,saboda su bare ne a cikin mu shine zamu ƙuntatawa zuciyar su,wato tunda yayi biyayya a wan can to wan nan ma sai abashi koda ran sa baya so,ita kuma ƴarku a faran ta mata saboda itace ƴar dangi,to ba dani za ayi wannan sakarcin ba,kuje can kai da ita da wanda zai biye mata ku ƙaraci shirman ku amma banda Hajjah a ciki!'ta faɗa tana ƙoƙarin tashi dan barin falon gaba ɗaya,har ta bar falon bata bar mita ba, Taufiƙa kuwa gaban Dady Habib ɗin ta rarrafa tare da sakar masa wani ɗan kukan yaudara koda zai taimaka mata tunda taga alamun haka atare dashi,ɗago kansa yayi,kana ya dafa kanta cikin san kwantar mata da hankali yace"haba Taufi meye abin daga hankali? bayan ga ɗan uwanki nan Alhaji Baba ya baki,meye aibun Sayyid?cikin kukan da ya kuma ƙwace mata tace"Dady wallahi Ni bana son Sayyid a tunda can amatsayin abokai muke dan haka yanzu bazan iya zaman Aure dashi ba,dan Allah ka taimakamin ka sanar da Alhaji Baba halin da nake ciki,saboda kai ka ɗaine yake sauraran maganar ka, kuma kana gani Sayyid ɗin shima ya gudu saboda baya sona!'kul kar na kuma jin wannan maganar A bakin ki, wa yace miki Sayyid guduwa yayi? Sayyid ɓata yayi kuma insha Allah muna saran ganin sa anan kurkusa kar ki ƙara wannan maganar kinji,ki yi haƙuri maza tashi ki tafi ɗakin Hajjah tunda bakya son wajen innon ki kwantar da hankalin ki ki dai na yawan koke koken nan!'tashi tayi tana layi kamar wadda tasha wani abun,ta dai jine kawai amma ba dan ta yadda ba,itafa bata jin zata haƙura da soyayyar Yah Abdallah,saboda sonsa acikin jininta yake,da kallo Dady Habib ya bita cike da tausayi,dan tabbas da yana da damar da zai aura mata Abdallah da ya aura matashi ko dan samun nutsuwar ta Har ya gama shirin sa bata tashi daga baccin da takeyi na bayan asuba ba,ɗan tsayawa yayi akan ta tare da zuba mata ido,tunanika ne suke ta kai kawo cikin ƙwaƙwalwar sa,a yanzu babu abinda yafi buƙata kamar yagano wanene wannan mutumin sai kuma iyayen Bintu wanda yake ganin kamar duk hanya ɗaya ce zata kai su ga cimma wannan nasarar,kallonta yake tamkar wanda ke son samo amsoshin sa a kan fuskar ta,a hankali ta shiga buɗe idanunta saboda A can cikin jikinta taji kamar ana kallonta,tana buɗe idanun nata kuwa suka shige cikin na Abdallah,da sauri ta ɗauke kanta saboda yadda taji gaɓoɓinta na amsawa da wannan sihirtaccen kallon da Abdallah yake mata,a hankali ta ɗan motsa bakin ta tare da cewa"Barka da safiya!'sai A lokacin ya ɗauke kansa daga tsumamman kallon da yake mata,tare da amsawa asaman laɓɓan sa kamar wanda akayi wa dolen amsawa,tashi tayi tsaye tana ƙoƙarin fita daga ɗakin,cikin miskilar muryar sa yace,"baki sanar dani dawowar Dije ba!'juyowa tayi batare da ta kalli cikin idanun sa ba, tace"to ya akayi kasani!'bai bata amsar tambayar ta ba sai ɗora mata da yayi da cewa,ki tabbatar kin samu keɓewa da ita yau,ina son sanin abinda ke tare da ita duk da cewa ina zatan Alkhairi,ki kula da kanki!'binsa kawai tayi da idanu tasan dai mutumin nan ba zai daina kasheta da mamakin sa ba gara kawai ta haƙura da ɗorawa kanta nazarin al'amarin sa,sauri tayi tabi bayan sa lokacin da taga ya sa kai ya fita daga ɗakin. Yau kam har lokacin hira ta samu da inno,a cikin hakane ta samu damar gaya mata tana son zuwa gaida su Hajiya Babba da Hajjah,cikin kulawa inno tace"amma dai kin tabbatar kin sanar da mijinki ko?kai inno wai mijina!'cikin dariyar yarintar Bintun inno tace"au da meye idan ba mijinki ba?tura ɗan ƙaramin bakinta tayi tare da zura dogon jijabin ta,bata cewa innon komai ba saboda ita har ga Allah haushi takeji idan inno ta ambaci Oga Abdallah da mijin ta, wannan mai shegen nunƙufurcin,itafa tana ji bata taɓa ganin dariyar sa ba,gara dai suyi su kashe gobarar da take gaban su kafin daga baya su san yadda zasuyi da Auren da aka ƙaƙaba musu basa so daga shi har ita,da wannan tunanin ta nufi ɓangaren Hajjah, wannan karon bata ko kalli sashen da ɗakin yake ba balle taji son zuwa gurin. A hankali tayi sallama bayan ambata umarnin shiga,Hajjah ce zaune hakimce akan luntsumemiyar kujerar ta sai Dady Mansur da Dady Habib,wanda kallo ɗaya zakayi musu kasan cewa rayukan su duka aɓace yake,jikinta ne yayi sanyi da ganin su A cikin wannan yanayin sai kuma wani irin kallo da ta kasa gane ko na mene,da Dady Mansur yake mata,Hajjah ce tace"a'a Bintu ƙaraso mana kuma kin tsaya sai kace wata baƙuwa!'ta faɗa tana nunawa Bintu gurin zama kusa da ita,takowa tayi A hankali har ta zauna a inda Hajjah take nuna mata sai dai amai makon kan kujerar sai ta zauna ƙasan kujerar,cikin rawar murya ta fara gaida Hajjah kana ta gaida Dady Mansur da Dady Habib,shuru tayi yayin da zuciyar ta tashiga wani irin bugu wanda ta rasa na mene ne, Hajjah ce ta dubi Dady Mansur tace"na dai gaya maka karna kuma ji kaje wajen wani daga cikin ƴan uwan mahaifinka kayi musu rashin ɗa'a kaje kawai ka cigaba da addu'a Allah ya baiyana mana shi a duk inda yake,ku tashi kuje Allah yayi muku albarka ya shirya mana ku baki ɗaya,amsawa sukayi atare wanda hakan yasa Bintu ta ɗago kanta dake sunkuye da wani irin sauri tare da bugun zuciyar da zai iya yi mata illah,sai dai kafin tayi tunanin wani abu har sun fita daga falon,bayan su tabi da wani irin kallo mai cike da razani da tsoro da kuma san gano wani abu da ya ƙulle mata kai. Zubawa ƙeyar Bintu ido Hajjah tayi cike da tunanika bar katai,ita kuma wannan kome yake damunta? ta faɗa cikin zuciyar ta ganin yadda alokaci ɗaya duk ta firgice kamar wadda taga wani abin tsoro,ɗan dafa kafaɗar Bintun tayi dan san dawo da ita cikin hayyacin ta,a tsorace ta waigo ganin Hajjah ce yasa ta sakin wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciyar da takasa ɓoyeta, Hajjah cikin nuna tsananin damuwa da halin da taga Bintun tashiga tace"Bintu lafiyarki kuwa koda wani abun da yake damunki?ta faɗa cikin nuna kulawar ta,da sauri Bintun ta girgiza kanta tare da cewa,dama gaidaki nazo nayi bari na wuce ɓangaren Hajiya Babba!'ta faɗa tana miƙewa tsaye, Hajjah tace"to da sauri haka ko ɗan hira bazaki tsaya kimin ba tunda ita waccen kasan da tayo muku ƙaura bacci bazai barta tayi hira ba!'batare da Bintu ta nuna san sanin wa take nufi ba,tace"ai zan kuma dawowa!'Hajjah tace"to shike nan ki gaida Innon da kuma mai gidan naki da kika fishi kirki!'kafin Hajjah ta kai ƙarshen zan canta tuni ta nemi Bintu A falon ta rasa,riƙe baki tayi cike da nazarin Abin da Bintu ta gani afalonta ya razana ta haka. Tafe take dan zuwa sashen da Dije tayi mata kwatance,dan zuwa wajen Dijen,sai dai yanzu kwata kwata ba a nutse take kamar farkon fitowar ta ba,kafinta ta shiga ɓangaren Hajjah kenan,wai me yake faruwa da ita ne?ko dai zarar da ita ake son yi?me yasa yanzu take jin kamar mutumin nan yana kusa da ita?me yasa Muryar sa keyi mata gizo?wai wannan wane irin shu'umi kuma azzamin mutum ne,me yasa yake son cutar da ita ta hanyar son juyar mata da tunani? da wannan rikitaccen tunanin ta ƙarasa sashen da Dije take aiki,tayi sa a kuwa Dijen ce ta buɗe mata ƙofa,baƙaramin farin ciki Dije tayi da ganin Bintu ba,duk da cewa tana cikin ɗan yanayi na tsoron kar wani ya gansu,kama hannun Bintu tayi tana ƙoƙarin kaita cikin ɗakinta, Dady Mansur dake kallon su,cikin ɗaga murya yace"ina zaki kai min wannan annobar? cikin sauri suka juyo yayin da Bintu jikin ta ya shiga rawa haka kuma hankalin ta ya kuma tashi da jin muryar da taji yanzu ta kuma sake jinta,wai waye wannan ɗin ne?muryar Dije ce ta katse mata dogon tunanin da ta waɗa akan wannan al'amarin dake son zarar mata da tunani,Dije tace"a'a yallaɓai dama inno ce ta aikota zan bata saƙon goro da na kawo mata tsara ba!'bai ce mata komai ba sai wani kallo da yayi musu su duka kana yayi ƙwafa tare da fita daga falon,kallon juna sukayi kafin Dijen ta kuma jan hannun Bintu da sauri suka faɗa ɗakin ta. Cikin taka tsan tsan Dije ta gayawa Bintu duk yadda sukayi da uwar ɗakinta,sai dai ta ƙara mata da alwashin da taci da kuma alƙawarin da tayiwa Bintun duk suna nan sai ma abinda ya ƙaru,tace"Bintu dole ne mu tashi tsaye mu bada himma dan bankaɗawa waɗan nan mugayen mutane asiri,dole kuma musake yin ɗamara akan wadda mukayi da dan cimma nasara, Bintu da akwai mugaye da yawa acikin gidan nan don bazaki taɓa gane fuskar kowa ba,amma yanzu dole mu gane mu sakawa kowa ido,kar kiji cewa kin yadda da wane saboda haka bazaki bibiyi al Al'amarin sa ba, Bintu idan da hali Hatta inno da Hajiya Babba da Hajjah mu saka musu ido da duk wani motsin su,ba kuma wai na faɗi haka dan ina zarginsu bane a'a sai dai kin san Hausawa sunce idan allurar ka ta ɓata duba ta har cikin teku,nima zanyi nawa yin duk wata hanya zanyi bi dan ganin na samu abinda zan iya shaida wannan muguwar matar dashi!'Bintu tace"yauwa Mama Dije abinda zakiyi ƙoƙarin gano wa kenan ina ga sai mun fi saurin gano ko wacece A cikin gidan nan!'dije tace"Bintu ke dai kiyi abin da nace kiyi,saboda wannan aikin agurina yana da wahala kuma akwai hatsari,dan zata iya fuskantar cewa har yanzu ina nan akan bakana na yaudarar ta, kinsan wan can ma ganowa tayi da kanta,kuma da kike wannan batu ma Bintu idan kuma ba acikin estate ɗin nan take zaune ba fa,abin fa ba ƙarami bane saboda Ni har yanzu bata bani wata ƙofa da zan gane komai akanta ba, wannan matar ta iya takunta yadda bakya tunani shi yasa na gaya miki kar ki bar kowa da kuke tare hatta wannan nafisar ma ki kuma banƙaɗa cikin ta baza muka sa samun wani ɓoyayyan abu daga gareta ba!' Bintu tace"har Ammin Rahima?wani irin murmushi Dije tayi tare da cewa Bintu ke yarinya ce bazaki fahimci komai da nake son ganar dake yanzu ba,amma dan Allah kiyi abinda nace dake,na fiki daɗewa acikin gidan nan kuma tunani na da naki ba ɗaya bane,ko har yanzu baki yadda dani bane?cikin sauri Bintu ta girgiza kanta tare da cewa"kiyi haƙuri mama Dije ba haka nake nufi ba amma insha Allah zanyi abinda kikace fiye da yadda kike tunani!'dafa ta Dije tayi tare da cewa yauwa yariyar kirki, sannan ki dinga yi mana addu'a kinji domin komai baya tafiya dai dai sai da taimakon Ubangiji!'jikin Bintu ne yayi sanyi sai taji kamar ta faɗawa Dijen halin da take ciki a kwanakin nan sai dai kuma babu halin haka tunda har yanzu Dijen bata san komai akanta ba bata san ita wacece a cikin wannan gurɓatattun mutanen da suke son kawo ƙarshen suba,dan dole ta ƙirƙiro ƙaryar da ta sharawa Dijen tace"insha Allah inayi kema ki dingayi min addu'a mama Dije!'Dije amsa mata tayi cike da son ƙara mata ƙwarin gwiwa, duk da cewa ta fahimci cewa akwai abinda Bintun take ɓoye mata,amma dai ta ƙyaleta har zuwa ranar da zataji ta gamsu da ita A zuciyarta,sai da ta rakata har can waje kana sukayi sallama bintun ta nufi sashen Hajiya Babba cike da nazarin maganun Dijen. Tun Bintu ba ta ɗaɗe da fita ba Anty Nafisa ta shigo ɓangaren innon,tunda ta tabbatar Bintun bata nan shike nan ta ɗorawa hanya idanun ta,tana son ganin shigowar Bintu, sai dai har ta shafe awa ɗaya babu Bintu babu alamar ta,to amma tayiwa kanta alƙawarin bazata bar sashen ba sai da mafitar damuwar ta,gashi ta kasa tambayar inno inda Bintun ta tafi,har innon sai da taso fahimtar kamar ba anutse Nafisan take ba,sai ta ɗan shiga yi mata nasiha kamar yadda ta saba yi mata alokuta da dama,a tunanin inno har yanzu wannan damuwar ce aranta ta rashin haihuwa,duk da ta ga abin yayi sauƙi yanzu sosai bakamar lokutan baya ba,da take yawan riskar Nafisan cikin wani irin yanayi na matukar damuwa,to da taga inno tana son ranfota ne yasa ta ɗan nutsu,sallamar Bintu yayi dai-dai da wata ɓoyayyar ajiyar zuciya da Anty Nafisa tayi,gaishe da ita Bintu tayi,daga nan tayi shigewar ta ɗaki ba tare da ta kuma kallon inda Nafisan take ba. To ga dai biki kuma babu zanin ɗaurawa, Bintu ta dawo amma ta rasa hanyar magana da ita,tunda tasan cewa magar da zasuyi da Bintu ba ta mintuna bace,kuma maganar sirrice wadda ta shafi wani ɓangare na rayuwarta,to kuwa ta yaya zata iya yin wannan sirri inno tana cikin falon nan A zaune?tunanin tane ya tsinke lokacin da taji wayar inno na ringin,dawo da hankalin ta kan inno da ta ɗaga wayar tayi tana cewa to Alhaji gani nan zuwa!'runtse idanunta Nafisa tayi tare da yin hamdala ga Ubangiji abinda take daɗewa batayi ba sai idan takama,(sai dai kuma ba tasani ba wannan taimakon da ta samu daga Ubangiji ba na kowa bane sai na Bintu saboda Allah yana tare da ita akan niyar ta ta Alkhairi,da san taimakon bayin Allah) Inno tace"to Nafisa zan je Alhaji na kirana kuma gashi Bintu ta shige ƙurya bare ki samu ɗan taya hira!'da sauri Anty Nafisa tace"kije kawai inno bari na bita ɗakin, na rasa me yasa har yanzu Bintu bata sake dani ba,ko dan bamu cika zama guri ɗaya bane oho mata,ta faɗa tana miƙewa dan ƙara sawa ɗakin Bintun,inno ma dake ƙoƙarin shiga sashen Alhaji Babba ta ƙofar dake cikin falon ta tace"to ina ga dai haka din ne yanzu sai kije ki rutsata dan kiji dalili!'cike da farin ciki Nafisa ta faɗa ɗakin Bintu wanda ko sallama bata samu damar yi mata ba, Bintu na tsaye jikin windon ɗakin nata,har yanzu tunanin ta yana akan muryar nan datake tai mata kai kawo a cikin kunnuwa, ta kuma ci alwashin sai ta nemo shi kowaye indai yana cikin estate ɗin nan,ga kuma babban aikin da Dije ta bata, ko tayata zata fara bincikar inno da Hajiya Babba da kuma Hajjah?ita dai tasan bata zargin ko ɗaya daga cikin su,to amma idan tayi la,akari da maganar fafi ɗinta sai taga cewa wannan fa ita ce shawara mai kyau kuma abar bi,tabbas Dije tayi dogon tsinkaye,shigowar Nafisan ce ta dakatar da ita daga tunanin ta,juyawa tayi tana kallon Nafisan cike da jin tsanar ta acikin zuciyar ta tare yin tur da mugun halinta,zama tayi tare da cewa Bintun zo ki zauna saboda maganar mu bata buƙatar tsayuwa!' "A hankali ta ƙarasa kusa da Anty Nafisan ta zauna,shiru sukayi na wasu sakanni kana Anty Nafisa tace"Bintu kefa nake jira tun ɗazu kuma yanzu nazo kinyi min shiru!'to me zance dake yanzu?ta tambaye ta batare da wani shakka ba,me kike nufi ne Bintu?ɗan gyara zamanta Bintu tayi tare da ƙara yin ƙasa da murya tace"Anty Nafisa kin san yanzu duk shawarar da na baki ba zatayi kyau kamar ace nasan mafarin lamarin ba,amma duk da haka yanzun ma ba zan kasa ko mai a kan haka ba!'yauwa Bintu na san bazaki kasa yin kyakykyawan tunani akan matsala ta ba,kuma na gaya miki babu komai dana rufe miki da dawani abun kin san bazan ɓoye miki ba!'ta faɗa cikin san Bintu ta gasgata maganar ta,wani ɗan murmushi Bintu tayi wanda kana ganin sa kasan na yaƙe ne,kana tace"hanya ɗaya ce zaki bi dan mijin ki ya gaya miki abinda yake sirrin sa,hannu tasa ta ɗan shafa fuskarta kana taci gaba da cewa,in dai har kin san ya yadda dake ya kuma yadda bazaki taɓa cutar dashi ba,kuma da akwai amana da gaskiya a tsakanin ku to kawai ki tunkare shi kai tsaye ki tambaye shi,ina mai tabbatar miki da cewa indai yayi miki waɗan nan abubuwan dana lissafa to wallahi zai gaya miki batare da ya ɓoye miki komai ba!'shuru tayi ganin yadda Nafisan take mata wani irin kallo wanda kamar ma bata san tanayi mata shiba,can dai da ƙyar tace"Bintu kina da hankali kuwa ta yaya zan san duka waɗan nan abubu wan alhalin ban shiga zuciyar sa na gani ba,ban san meye a zuciyar sa game dani ba, ban kuma san wani irin kallo yake min ba, ban san wane irin zargi yake min ba? gaskiya Bintu ki sake tunani!'tsura mata ido Bintu tayi kana tace"Anty Nafisa ya akayi KIKASAN yana zarginki?bayan kuma kin ce baki san ta yadda za ayi kisan wane irin kallo yake miki a cikin idanuwan sa ba?tuni Anty Nafisa ta diririce gaba ɗaya Bintu yariyar cikin ta ta saka ta a kwana tamkar wadda take tuhumar ta da laifin kisa,ganin irin rikicewar da tayi ne yasa Bintu ta kuma tabbatar da zarginta tabbas a kwai Babban abinda Nafisa take ɓoyewa wanda kuma zai iya taimaka musu sosai cikin tafiyar su,kuma tayi alƙawarin sai ta faɗa mata kome taƙe ɓoyewa,yanzu zata bar ta da wannan sai kuma zama na biyu,miƙewa tayi tare da cewa,Anty Nafisa Ni zanje kiching ke kuma kije kiyi tunani akan shawarar da nabaki idan ta karɓu sai ki aikata ta,idan baki gamsu da ita ba,sai mu canja wata Kinga Nima sai na samu damar ƙara yin nazari,kinga dole sai kin yi haƙuri akan wannan aikin saboda ya ban banta da sauran ayyuka,su waɗan can na san komai shi kuma wannan sai dai nayi lalube,daga haka ta fita daga ɗakin batare da ta jira abinda Nafisan zata iya faɗa ba,ita ma tashi tayi jiki a saluɓe ta koma ɓangaren ta cike da tunanika iri-iri. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 43 ``` Tana shiga kiching ɗin ta fara ƙoƙarin ɗaurawa ogan nata sanwa, sai dai gaba ɗayan ta bata jin ta dai dai saboda tunanin da ya cika mata ƙwaƙwalwalwa, ƙoƙarin ta kawai a yanzu gano me wannan muryar,duk da cewa yanzu duk wanda yayi magana ji take kamar waccan Muryar to amma da izinin Allah hakan ba zai sa ta kasa gano me ai nahin Muryar ba. Wata tsawa shugaba azukyi ya dakawa Nanu, me kake yi haka ne?kasan wannan hanyar da ka biyo ba hanya bace me ɓullewa,me yasa baka tsaya akan wan can shirin namu ba, tabbas kayi gangan cin fallasa Muryar ka ga yarinyar nan,domin tabbas yanzu da abinda zata samu dama akanka ke nan!'ya ajiye maganar cikin wani irin huci na tsananin ɓaci rai da abin da nanun yayi,wanda aka kira da nanu yayi ƙasa da kan sa tare da cewa afuwa nake nema shugaba yanzu meye abinyi?babu wani abin yi nanu saboda ka nuna mana bamu da wani amfani a cikin wannan tafiyar dan haka sai kaje ka ƙara sa aikin ka kai ɗaya!'cikin tashin hankali nanu ya kwanta a ƙasa yana mai neman afuwar shugaba,nasan nayi kuskure amma ayi min afuwa!' shugaba yace"tabbas yanzu yarinyar nan zata dinga bibiyar ka ta muryar ka, don kuwa ka riga ka buɗe mata hanya da ace kayi haƙuri ka barta a iya tsoron da muka dasa mata da yanzu bamu da wata matsala yanzu ka riga ka rusa komai!'yanzu lalata wannan shirin yana da matukar wuya, saboda muryar ka ta riga ta zauna a cikin ƙwaƙwalwar ta,cikin ƙara yin ƙan da kai yace"yanzu meye abinyi shugaba?yace"dole sai mun nemi taimakon dodo jack dan haka yanzu kaje za muyi magana bayan na gana dashi!'nanu dai ya haƙora ne amma ba dan ransa yaso ba dan sai yanzu ya ankara da babban kuskuren da yayi baya son wannan abin da yayi ya zama shine sanadin tonuwar asirin sa, duk yadda zaiyi da yarinyar nan sai yayi dan samun cikar burin sa da kuma rufuwar asirin sa, Nafisa dai tana cikin tsaka mai wuya ta rasa inda tunanin ta zai tsaya maganganun Bintu ne suke ta kaiwa da kawowa cikin ƙwaƙwalwar ta,anya kuwa tana da wannan ƙwarin gwiwar a wajen Umar?duk da tana da tabbacin bai san komai akan abinda ta aikata ba,amma bata tunanin akwai wannan yardar da Bintu take faɗa a tsakaninsu,haka kawai take jin bata yadda da kanta a wajen Umar ɗin ba,to ko gwadawa zatayi ta gani ko zata dace?goge zufar dake ta tsatstsafo mata tayi,a fili ta furta,zan gwada Bintu zan ga yadda Umar ya ɗauke Ni da kuma kallon da yake min zan tambaye shi abinda yake damun sa zan gani ko zai gaya min indai kuwa ya faɗa min to tabbas zan ƙara kwantar da hankali na saboda na yadda ya amince dani ba kuma ya zargi na da aikata masa babban laifi. Abdallah ya samu duk wasu bayanai daya buƙata a kan Alhaji Rufa'i kuma ya gamsu da gaskiyar sa,yanzu yana tunanin kiran sa dan su tattauna akan batun Alhaji Shamsi tunda har yana tunanin shi Alhaji Shasin zai iya sanin kome ne ake rigima da neman sa ta kowace hanya,yinin ranar bai samu sukuni ba saboda yawan aiyukan da ya aiwatar a ranar duk wasu baya nai da yake bukata na mutanen da yake da alama akansu ya samu,dan haka ba tare da wani ɓata lokaci ba ya fara baza ma aikatan sa dan soma bincike akan su, Bai samu shigowa gidan ba sai misalin goma na dare,a gajiye ya shiga ɓangaren sa,kai tsaye ya faɗa toilet ya sakarwa kansa shaya,sai da ya shirya tsaf kana ya nufi dinnin dan samawa cikin sa wani abun, Tun ƙarfe takwas take duba agogo da leƙen window ko zataga dawowar sa amma shuru bai dawo ba ga yanayin garin da hadari alamu ya nuna dai yau zasu iya samun ruwa,dan ma dai damunar batayi nisa ba, hakan ne yasa taji duk ta damu da rashin dawowar tasa ko lafiya yake?ta riga ta daɗe da sanin baya wuce wannan lokacin,shi yasa duk tabi ta damu,dan hararar hanyar tayi tare da cewa ko me yasa ma na damu bayan ko ya dawo ba lallai ne yayi min magana ba!'ta faɗa tamkar yana kusa da ita har da dan murguɗa baki,sai dai kuma duk da hakan ta kasa haƙurin shi yasa tana jin karar mota tayi saurin bude labilan tana leƙawa,wata sassanyan Ajiyar zuciya ta saki lokacin da ta tabbatar da cewa shine ya shigo, komawa tayi ta zauna abakin gadon tana tunanin ta yadda za ayi taje ɓangaren nasa tunda bata da sauran wani abu da zatayi acan ɗin,ta gumi ta zuba,can kuma sai ta miƙe, toilet ta shiga tayi brosh tana fitowa ta saka wata rigar bacci wadda ta tsaya iya cinyoyin ta daga nan tayi kwanciyar ta dan ta rasa hanyar da zatabi dan zuwa ɓangaren nasa,kalan ma inje ya koroni ta faɗa tana tura baki tare da shigewa cikin ɓargonta saboda yanayin iskar da ake ga dukka nin alamu dai ruwa zai iya zuba ako wane lokaci. Abdallah ma dai a gurin sa kusan hakane,aiki yake amma hankalin sa yana kan duban hanya,tunanin zuwan ta yake akoda yaushe,sai dai har zuwa wannan lokacin baiji motsinta ba,ɗan tsaki yayi tare da janye laptop ɗin dake gaban sa,tashi yayi ya shiga toilet Jim kaɗan ya fito,ya ɗanyi abinda ya zama al dar sa,kana ya kwanta bayan yayi addu'oin sa,so yake ya kwanta ya ɗan rage bacci kafin ajima ya tashi yayi nafilfilu,sai dai kuma hakan ya gagara a wajen sa,mamakin yadda akayi ya kasa samun sukuni saboda yarinyar yake,ta wani bangaren kuma yana mamakin yadda ta iya kwanciya ita ɗaya,ya santa da tsoro gashi kuma yana gani kamar a kwai abinda yake damunta a kwanakin nan,lumshe idanun yayi yana jin wani irin yanayi a can cikin jikin sa,iska ce ta fara kaɗawa mai ƙarfi wadda take tasowa da ƙura,da sauri ya tashi ya kuma gyara windows ɗin ɗakin,duk abinda yakeyi zuciyar shi na wajen ta, gani yakeyi tausayin Bintu zai iya saka shi a wani hali,duba da yadda ya kasa sukuni ganin yau gaba ɗaya bai ganta ba,ga yanayin tsoronta dayake taɓa masa zuciya, ji yake tamkar yaje ya dubata,kasa zama yayi a ɗakin ya fito falo saboda yana ganin kamar zaifi samun kusanci da ita. "Can cikin baccin ta ta dinga jin kamar ana ta shinta a matukar firgice ta farka tana son yin addu'a amma hakan ya gagara saboda yadda taji tamkar an rufe mata baki, cikin zuciyarta ta ta dinga ƙoƙarin yin addu'ar yayin da duk jikin ta rawa yake,ga wata irin walƙiya da ake yi da tsawa saboda ruwan da akafara tamkar da bakin ƙwarya,kuka ta saka tana laluben hanyar da zata sauka daga gadon dan ta kunna hasken ɗakin,da ƙyar ta samu ta lalubo wayar ta ta kunna tare da saukowa daga kan gadon hasken ɗakin ta fara kunnawa,raɓewa tayi a can lokon ɗakin babu abinda jikin ta yake sai rawa saboda tsananin tsoro,ji take kamar ba ita kaɗai ce acikin ɗakin ba, zuciyarta kamar zata faso kirjin ta haka take ji, Gaba daya ya kasa samun sukunin zuciya ba ma kamar yadda yaga an tsuge da ruwa wanda yake tafe da tsawa da walƙiya,baya jin zuciyar shi zata barshi ya nutsu ya aiwatar da wani abu ba tare da yaje yagano amanar da Alhaji Baba ya bashi ba,cikin wani irin zafin nama ya miƙe tare da fita daga ɓangaren nasa,kai tsaye ya nufi ɗakinta yana kusanta ɗakin yanajin bugun zuciyar shi na ƙaruwa,a can lokon ɗakin ya hango ta a rakuɓe kamar wata ƙadangaruwa,tanajin buɗe ƙofar tasa ta ƙara ƙarfin kukan ta,tare da runtse idanun ta,cikin ta kun shi na zaratan maza ya nufo inda take,yayin da zuciyarta take ci gaba da wani irin bugu jira kawai take taji yadda Ubangiji zai yi ikon sa akanta,lokacin da ya ƙaraso kusa da ita sai taji yanayin bugun zuciyar ta ya sauya wani irin sanyi taji yana shigarta haka kuma hankalin ta yana kwanciya zuciyar ta na fita daga cikin mugun firgicin da ta shiga,zuba mata ido yayi batare da yayi mata magana ba,A hankali ta shiga buɗe idanunta saboda sassan yan ƙamshinsa da ƙofofin hancinta suka fara shaƙa wanda ya riga ya zama hadda a cikin hancinta,idanun ta ne suka sauka akan kyawawan ƙafafunsa da suke kwance luf cikin tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a ɗakin,cikin wani irin sauri wanda yake gauraye da wani irin shauƙi ta faɗa jikin sa tare da ƙankameshi tana kuma sakin wani marayan kuka mai cike da ban tausayi,riketa yayi sosai tare da ƙara gyara mata kwanciya,yana ɗan shafa bayanta wanda hakan yake nuni da calmin ɗin ta da yake son yi, bai ce mata ko mai ba sai ɗan sunkuyawa da yayi ya ɗauki wayar ta datake yashe a ƙasa,kana ya jawo hannun ta suka fita daga ɗakin,suna gaba da shiga falon sa,suka juyo muryar inno,ɗan tsayawa yayi saboda ƙarasowar innon gaban su,cikin yanayin damuwa tace"me yake faruwa ne Abdallah,me yasa mu Batular?ta jero masa tambayoyin tana riƙon Bintun da har yanzu hawaye basu daina saraftu akan kyakykyawar fuskarta ba, Cikin yanayin sa na ƙoƙarin ɓoye damuwar dake cikin zuciyar sa ya ɗan karyar da kan sa tare da cewa"inno tsoro ne kawai da ita san nan kuma,,sai ya ɗan yi shuru kamar yana lalubo abinda zai cewa innon,kana ya cigaba da cewa, sannan tana yawan tsorata ko mai tsoro ne yake bata,kamar dai bata jin daɗi!'ya ƙarasa maganar da ɗan kallon Bintun,inno cikin damuwa da tashin hankali tace"subhanallah me yake tsorata ki Bintu?ta juya tambayar ta kan Bintu, Bintu dai ta kasa magana sai hawaye,dan bata san mai zatace da inno ba,inno tace"anya ba makaraine suke san shafar ta ba?tayi maganar tana duban Abdallah,yayin da shi kuma ya zubawa Bintu idanu wanda maganar inno tayi saurin hasko masa wani abu makamancin abinda ta faɗa,(idan baku manta ba Abdallah yayi ilmin addini mai matukar zurfi,so dan haka yana da ilmin sanin sihiri ko jinnu saɓanin wasu ƴan bokon da zaku ga sam basu yadda da irin wannan abun ba, Abdallah yasan cewa sihiri gaskiya ne haka jinnu ma gaskiya ne,dan haka bai jahilci maganar inno ba)tsai yayi da ransa yana mai hasaso al al'amarin Bintu tabbas tana buƙatar addu'a,amma dai bai kawowa ranshi ga wanda yayiwa Bintu wani abu ba kawai dai yasan Bintu al'amarin ta yana buƙatar addu'a duba da yadda gaba ɗaya ta birkice ko addu'a bata son yi wanda shi kansa shaida ne akan Bintu ba haka take ba tun kafin suyi kusan ci da juna yasan tana da matukar riƙoda ibada,shi yasa yanzu bai sha wahalar gano yadda take sakaci da addu'a ba. A hankali ya ɗauke idon sa daga kallon da ya ƙure Bintu da shi,ya maida kan inno tayi zukuɗi tana jiran amsar sa,sai da ya ɗan huro iska daga bakin sa kana yace"hakane inno addu'a ya kamata ayi mata,insha Allah gobe zamu fita akwai wani malamina zamuje gurin sa!'murmushi inno tayi dan da tayi tunanin Abdallah ba zai yadda da abinda tace"ba,yauwa hakan yayi Allah Ubangiji ya kareku daga sharrin mutum da aljan ya tsare bayanku da gaban ku yasa kusa zama abin kallo da tsoro a idon maƙiayan ku,Amin Abdallah ya amsa yana mai juyawa dan shiga falon sa,yayin da inno ta bar zuciyar Bintu cikin wani irin hali na tunani da,tsoro mai tsanani,a hankali ta ta taka tabi bayan sa,tana waiwayen inno da take ta Binta da wani irin murmushi mai cike da ma anoni masu tarin yawa,a haka ta shige falon wanda shine sanadin rabata da kallon inno,tana rufe ƙofar ta zame ajikinta tare da saka wani irin kuka mai taɓa zuciya wai ya zatayi idan akace yau binciken ta ya gano mata inno cikin mugayen da take zargi,ya zatayi da rayuwar ta idan akace yau macen da take ƙauna,takewa kallon tafi kowa ƙaunar ta,a cikin gidan nan, tabbas wannan fargabar ita zata jefata cikin wani mugun hali na damuwa,jin an kamota yasa ta ɗaga jiƙaƙƙun idanun ta tana kallon sa wanda shima ɗin kallon idanun take bayan ya samu nasarar ɗagota daga zaunewar da tayi,cikin neman agajin makusancin ta ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kukan da take jin ta fara shi kenan har sai zuwa ranar da gaskiya ta baiyana,idan kuma gaskiyar ta baiyana a gaɓar da bazataso ba tabbas hawayenta bazasu taɓa daina zuba ba,tana ƙaunar inno har cikin ƙashi da jinin ta,kamata yayi suka fara tafiya har zuwa ɗakinsa zama yayi da ita ajikin sa,yayin da zuciyar sa take san gagarar ɓoye damuwar sa a wannan karon,wanda yake tunanin girman damuwar wannan lokacin ne yayi mata yawa,jingina yayi ya ɗan kashin giɗa ya kasa ce mata komai har yanzu dan bai san ta ina zai fara ba, Cikin tausayawa kanta da rayuwar da zata fuskanta nan gaba ta fara bashi labarin yadda sukayi da Dije,ba tare da ta ɓoye masa ko alif ba,ta gama maganar tana mai cusa kanta cikin jikinsa tana murzawa wanda hakan ne yake nuni da tsananin damuwar da take ciki,cikin muryar ta da ta dashe tace"Yahh Abdallah,yaya zanyi da wannan aiki da ya ɓullo min?kagayan ta ina zan fara bincikar matan da suka fi nunamin ƙauna ta gaskiya a cikin wannan duniyar,su kaɗai ne matan danasan sun fara ƙaunata bayan ƙaunar mahaifiyata,su kaɗai ne matan da suka karɓeni batare da ƙyama ba su kaɗai ne matan da suka fifita ƙaunata akan ƙaunar jikokin su batare da sun san Ni ɗin jinin su bane,su kaɗai ne matan da suka fara yarda dani alokacin da narasa yadda da amincin kowa a cikin gidan nan,sun maida Ni mutum sun maida Ni jikar su sun yi faɗa da jikokin su akaina,to kagayamin me yasa ba zan shiga wani hali ba duk ranar da akace wannan ƙauna ta munafunci ce ta yaudara ce ta ha inci ce,me kake tunanin zanyi a ranar, wallahi ba zan iya ɗauka ba,Ni bazan iya ba!'ta faɗa tana bugun ƙirjin shi tare da ƙara sakin wani marayan kuka mai ƙun tata zuciyar maiyin sa da kuma mai sauraren sa,hannun ta ya kama duka ya riƙe kana cikin wata irin murya da ta saukarwa da Bintu nutsuwa da kasala yace"Bint!'shiru tayi tare da yin luf tamkar wadda bata numfashi,hannu yasa ya shiga gyara mata lallausar sumar kanta wadda duk ta bar baje,kana yaci gaba da cewa',Bint injin ke musulma ce?jin jina kan ta yi batare da ta ɗago ba,yace"yauwa to kinga kuwa dole ki amshi ƙaddararki duk yadda yazo miki domin wannan shine cikar imaninki da cikarki musulma,kuma bawa baya taɓa tsallake wa ƙaddarar sa to ki ƙaddara haka taki ƙaddarar tazo kuma bazaki taɓa iya sauya ta ba,ko baki ga yadda Ni nake rayuwata ba?Bint kin san rayuwar da nayi kuwa kin san rayuwar ƙuncin da danayi kin san yadda aka ƙuntatawa rayuwata,kin san yadda nayi rayuwa a hannun kafurai alhalin Ni ina cikakken musulmi?kin san yadda zuciyata takeyi aduk lokacin da aka ƙuntatawa rayuwata da yin ibadar da batawa ba kuma addinin da ban yadda dashi ba, Bint amsar itace duk baki san wan nan ba baki san meye abinda na fuskanta a cikin rayuwata ba, taki kawai kika sani,dan haka ina so kiyi haƙuri,mu fuskanci abinda ke gaban mu abinda Dije ta gaya miki gaskiya ne,baka taɓa gane munafukin ka sai da dabaru,kuma baka taɓa gane masoyin ka na gaskiya sai kashi ga halin rayuwa,ɗago kanta yayi,yana kallon fuskar ta sauri tayi ta rufe idon ta saboda wani kallo da taga yana mata mai shiga cikin jiki da jini,ɗaga mata gira yayi cikin wani irin salo da shi kansa bai san ya iya shi ba, hakan ne ya bata kunya har ta maida kanta ta sunne ajikin sa, Ɗaga ta yayi tare da cewa bamu ga ta bacci Bint muna da babban yaƙi agabanmu muna da buƙatun da muke nema Allah ya biya mana,dan haka dole mutashi mu roƙe shi kiyi haƙuri ki Kore duk abinda ke kawo miki farmaki da wasu wasi cikin zuciyarki kinji ko!'ya faɗa cikin matuƙar nuna kulawar sa gareta, Kallon sa kawai take cike da mamakin sa,dama haka yake da matukar tausayi, tabbas tayi mamakin yadda akayi ya tsaya yana nuna kulawar sa akan ta kamar haka,mutumin da tasan baya yin shiri da duk wani abu da zai saka shi yin surutu mai tsayi,ta shi tayi kamar yadda ya Umar ce dan yan zu ya riga ya karya mata zuciya da kalaman sa, sai taji tana matuƙar san jin labarin sa dan ga dukkanin alamu ya sha gwagwarmaya da ƙalubale a cikin rayuwar sa. Sun daɗe suna salloli duk da dai Bintu dauriya kawai take yi, amma sam bata jin daɗin jikinta da dukkanin rayuwar ta,amma cikin taimakon jarumin mijinta mai tsananin riƙo da addinin sa mai kishin addinin sa ta samu ƙwarin gwiwar ganawa da ubangijin ta,cikin ƙarfin hali da miƙa lamuran su gare shi,basu suka kwanta ba sai misalin ƙarfe uku na dare,daga nan suka sami yin Bacci cikin salama da nutsuwar zuciya, A cikin wannan safiyar kuma da ta waye Abba Umar ya dawo daga ƙasar Italiya,wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Anty Nafisa ba, tunda ta riga ta sakawa ranta zata yi abinda Bintu ta shawar ta mata,hakan ne yasa tayi masa shirye-shiryen da ta daɗe bata yi masa irin sa ba,shi kansa sai da yayi mamakin hakan,amma dai bai kawo komai cikin zuciyar sa ba,lokacin da ya gama shirin sa ya fito tsaf dashi dan zuwa gaida mahaifinsa da iyayen sa mata har ta gama yi masa duk wani shiri,sai dai yace tayi haƙuri yaje ya gaida iyayen sa,dole tayi masa fatan dawowa lafiya duk da zaƙuwar da tayi suyi maganar datake cin ranta, Sai da ya fara zuwa ɓangaren Hajjah kana ya fito ya shiga ɓangaren inno,wanda a daidai lokacin ne kuma Bintu da Abdallah suka fito dan zuwa gurin malamin sa malam Nuhu da yace zasu je,tunda ta doso falon ta dinga jin zuciyar ta na wani irin bugu wanda har saida ta dafe ƙirjinta, cikin kulawa Abdallah ya ruƙota ganin tana ƙoƙarin faɗuwa,kallon sa tayi idanun ta cike taf da ƙwalla, ɗan girgiza mata kai yayi kana yasa hannu ya goge mata wadda ta fara zubowa kan fuskarta,tare da jan hannun ta suka fito falon tare da ƴar guntuwar sallama saman leban sa, A can ɓangaren Dije kuwa tun bayan rabuwar su da Bintu uwar ɗakinta tayi mata waya da ɓoyayyar nomba kamar yadda ta saba,ta sanar da ita a safiyar yau ɗin tana son su haɗu, sai dai bata gaya mata inda zasu haɗu ba, tasan dai sai tabar gidan zata faɗa mata kamar yadda ta saba yi,shi yasa tunda ta tashi take sauri dan tana son haɗuwa da Bintu,saboda tunanin da tayi,akan haɗuwar su da Hajiyar yau,zata gayawa Bintu ta yi ƙoƙarin biyota a baya,tunanin ta anan kuwa,tasan Bintu tana da tunani da wayo,idan taga koda bayan matar zata iya ƙoƙarin shaida ta aduk inda ta ganta, shi yasa take son lallai Bintu tabi ta ayau, tana ganin hakan ma kamar wata hanya ce zata sauƙaƙa musu aiki,cikin hanzari ta gama duk aiyukan ta,tare da kimtsawa ta fita dan zuwa sashen inno, A can ɓangaren inno kuwa,cike take da farin cikin ganin Umar ɗin,sai da ta cika gaban sa da kayan taɓawa,kana ta samu guri ta zauna,tana cewa Umari na saukar sassafe kenan kayo mana?ya buɗe baki daniyar bata amsa wayar sa ta fara ringin,dan haka ya fasa faɗar abinda zai faɗa tare da zato wayar,ɗagawa yayi duk da cewa ɓoyayyar nomba ce aka kirashi da ita,karawa yayi akunnen sa tare da yin sallama cikin kamilalliyar muryar shi,daga can ɓangaren akace, ina fata dai da Umar Balarabe nake magana?Abba Umar yace"nine Ina sauraren ka!'daga can aka kuma cewa,yauwa to ba komai ne yasa nakiraka ba sai kawai ɗan na tambayeka shin ka shirya haɗuwa da iyalansa da karasa su tsawon shekaru.... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 44 ``` Wata irin zabura Abba Umar yayi tare da miƙewa tsaye,cikin tashin hankali da rawar baki yace"waye kai?sai dai ina kafin ya kuma cewa wani abu tuni ankashe wayar ɗif, Abba Umar gaba ɗaya ya ruɗe ya kasa yarda ma wayar ta mutu sai nanata hello yake, sai da inno ta tashi ta kama hannun sa tare da zaunar dashi cikin nuna kulawa tace"Umarina me yake faruwa ne?ka nutsu ai ina tunanin ankashe wayar,waye yakiraka a waya,yake son tada maka da hankali?hannu yasa ya goge zufar da take sauko masa kamar wanda aka sheƙawa ruwa,ya kasa amsawa inno tambayoyin ta,gaba ɗaya antayar masa da tsohon mikin dake dan ƙare cikin zuciyarsa,inno karki damu wata ƴar matsala ce daga wajen aikin mune!'to dan Allah ka kwantar da hankalin ka kar kace zaka saka yawan damuwa aranka kaji ko!'murmushi yayi wanda kana gani kasan na yaƙe ne,yace"shike nan inno,bari na wuce wajen Hajiya Babba,daga nan zan ɗan shiga na kwanta, sallamar Abdallah ce ta katse shi daga sallamar da sukeyi da inno, yana tafe hannun sa sarƙafe dana Bintu,inno tace"yauwa Abdallah zo ku gaisa da Abban ku Umar shine kuma ya baka auren Bintu!'ta faɗa tana kallon Bintu da ta rakuɓe a bayan Abdallah,tunda inno ta ambaci sunan Abba Umar ta shiga wani Irin yanayi na matuƙar shauƙi da ƙauna, A hankali ta fito daga bayan Abdallah tana takawa har zuwa gaban Abba Umar tare da durƙusawa kamar yadda taga Abdallah yayi,ƙasa tayi da kan ta tana sauraren bugun da zuciyarta keyi. Abba Umar kuwa tunda ya zubawa Bintu da Abdallah ido ko ƙiftawa ya kasayi,kuma baya fatan abinda zai rabashi da kallon waɗan nan yara da yake kallon su tamkar wasu taurari acikin idaniyar sa,muryoyin su ne da suka gaida shi atare suka yanke masa tunani da ɗimuwar da ya shiga,cikin wani irin fillin da zuciyar shi ta shiga ya dora hannayen sa duka biyun a kawunan su,yana wani irin murmushi mai ɗauke da wani irin yanayi na tsananin tausayin kansa,yace"sannun ku ƴaƴana tunda kuke cikin gidan nan bamu taɓa haɗuwa ba sai yau,ko da yake Allah ne bai nufa tun can zamu gana ba sai yau ɗin,ina fata dai kuna lafiya? gaba ɗaya suka amsa atare har ɗan duban junan su sukayi saboda yadda suke yawan haɗa baki gurin faɗar abu alokaci guda, Abdallah ne ya fara tashi ganin Abba Umar ɗin yayi hanyar fita,itama tashi tayi tabi su A baya Abdallah yace"inno zamu tafi sai mun dawo!'tace"to Allah ya kiyaye ya bada sa'a ya amsa da Amin kana suka fita gaba ɗayansu. Suna tafe da Abdallah da Abba Umar suna taɓa hira,tunda yake cikin gidan bai taɓa yin hira ko wata doguwar magana da ƴaƴan Alhaji Baba ba,Amma ƙaunar Baffan nasa da ban take azuciyar sa,ji yake tamkar da mahaifin sa yake magana,shi yasa yakejin wani irin nishadi da farin ciki mai yawa a zuciyar sa,Bintu ma dai tana cikin shauƙin ƙaunar mahaifin nata ji take tamkar taje ta rungume shi tace Abbana ina sonka,acikin wannan hali Dady Habib ya same su,shima cikin biyayya suka gaida shi,am sawa yayi fuska cike da fara'a yace"kai kam Umar kaci sa ar ƴaƴan naka har rakiya suke maka,mu da muke tare da su kullum har yanzu sun kasa sakin jiki damu kamar waɗan da zamu cinye su!'ya fadi maganar cikin yanayin zolaya,ɗan ƙasa da kai Abdallah yayi bai ce komai ba haka nan fuskar sa ba yabo ba fallasa,Abba Umar yace"kasan haɗuwar jini ya faɗa shima cikin zolayar yana miƙawa ɗan uwan nasa hannu dan su daɗa gaisawa,daga nan dai sukayi sallama ya wuce part ɗin Hajiya Babba Dady Habib ma ya shiga falon inno, Abdallah ya kalli Bintu lokacin da yaga tabi bayan mahaifin nata da kallo,kamo hannun ta yayi cike da tausayi, suna ƙoƙarin shiga motar da Yahya tuni ya buɗe musu yana jira su shiga ya ja,sai ga Dije da sauri har da ɗan hakinta daga Ni dai tayi gudu kafin ta cimma su,tsayawa sukayi gaba ɗaya suna kallon ta sai da ta samu daidaituwar numfashin ta kana suka gaisa da Abdallah Bintu ma gaida ta tayi,Dije tace"ko zaku bani minti biyu zan ɗan yi magana da Bintu? Abdallah ya saki hannun Bintu tare da cewa babu damuwa!'motar ya shiga,ita kuma Bintu suka keɓe da Dije,duban Bintu tayi cikin nutsuwa tace"Bintu ko da hanyar da zaki bi dan bin sahu na A yau? Bintu tace"ban fahimta ba!' ɗan numfasawa Dije tayi tare da ɗan duba hagu da daman ta kana tawa bintu bayanin abinda take nufi da kuma manufar ta naso ta bi bayan nata a yau,sai a san nan Bintu ta fahimci Dije da manufar ta,cikin fargaba da sanyin jiki tace" anya kuwa Mama Dije babu matsala?Dije tace"Bintu wai me yasa kwana biyu naga gaba ɗaya baki da ƙwarin gwiwa ne? mai yake faruwa dake?ko tun maganar mu ta juya ne ya sauya ki haka?wato dai nasihuna basu shiga kunnan ki ba ko? Bintu ta goge hawayen da suke ƙoƙarin zubo mata tace"mama Dije kiyi haƙuri zanyi duk abinda kika Umar ce Ni,amma zan fara gaya masa sai musan shirin da zamuyi wajen bin naki,in yaso idan ta sanar dake inda zaku haɗu sai ki sanar dani ta hanyar kira ko text!'dije tace"insha Allah Bintu, kuma insha Allah mune da nasara lokacin mu ya fara, su sun gama nasu mu kuma yanzu muka fara namu,da haka suka rabu, tunda ta shiga motar tayi jugum ta kasa gaya masa komai,cikin taushin murya ya kira sunan ta tare da zuba mata narkakkun idanun sa, masu saka ta yin abu koda bata so ba,masu saka mata nutsuwa da saukar mata da kasala,hakan ne yasa ta shiga sanar dashi maganar dasu kayi da Dije,ba tare da yace"mata komai ba ya ɗauki waya ya kira, tare da cewa yauwa kazo min da mashin ɗin yanzu ina buƙatar sa cikin gaggawa!'daga haka ya kashe wayar, tafiya suka farayi domin fita daga cikin ESTATE ɗin. Tunda ya shiga ɓangaren Hajiya Babba bai samu wata cikakkiyar nutsuwa ba saboda hankalin sa ya rabu kashi kashi,ga tunanin wan da yayi masa waya ga kuma tunanin hotan Bintu da ta kasa ɓacewa daga fuskar sa da zuciyar sa,ba tare da ya cika lokacin da Yakamata ya kai ba,ya miƙe yana cewa Hajiya Babba Ni zan je na ɗan kwanta ina so zan ɗan yi bacci!'hajiya bata takura masa da tambayar sa meke damun saba dan tasan tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi, addu'a kawai tabishi da ita, Wayar Bintu ce ta ɗau haske alamar shigowar saƙo, tare suka kai hannun su kan wayar ita da Abdallah,wani irin musayar kallo suka tsaya yi ga hannayen su a haɗe kan waya, Bintu ce ta fara janye idanun ta da hannunta,tana kuma jin wannan yanayin na shigar ta,ɗaukar wayar yayi ya buɗe sakon da ya shigo,sai yaga daga Anty Nafisa ne saƙon,ɗan satar kallon ta yayi sai yaga gaba ɗaya hankalin ta baya kan sa,hakan ne yasa ya buɗe saƙon tare da karantawa A hankali batare da Bintu taji ba, Bintu na gamsu da shawarar ki zan tambayi Umar damuwar sa ko zai gaya min duk da cewa na aikata wani abu daban batare da sanin ki ba,ba dan komai kuma nayi haka ba sai dan inaso in zunguro damuwarsa tare da bugar cikin sa akan abinda nake tunani a game da shi,to bai shigo ba dai har yanzu ina jiran sa domin ganin ko aikina yayi kyau,ba lallai bane sai kinji komai amma dai nasa ankirashi awaya an bugi cikin sa tare da zunguro damuwar sa yadda idan ya shigo na tambaye shi ba zai taɓa iya ɓoye min ba,a wannan karon dai nayi abin kirki nayi abu da basirata ba basirar Bintu ba,daga haka ta saka alamar dariya,ɗagowa yayi daga kallon wayar sai karaf ya tsinci fararen idanunta akan sa,kawar da kan sa yayi tare da kashe wayar dan baiga amfanin wan nan saƙo ba kuma yana ganin kamar zai iya tada hankalin ruɗaɗɗiyar Bint ɗin tasa,kar bar wayar tayi daga hannun sa tana cewa waye ya turo saƙo?bai damu dan ta karɓi wayar ba kasan cewar ya riga ya goge saƙon,hakan ne yasa bata ga komai ba,sai dai kallon tuhuma da tabi kyakykyawar fuskar sa da shi,lumshe idanun sa yayi, yayi tamkar bai san me take nufi ba,ita kuma hakan ne yabata damar cigaba da kare wa fuskar sa kallo tare da kaifafa kallonta akan ɗan zagayayyen gemun sa da yake matuƙar burgeta, a rayuwar ta tana son wan nan Abu a fuskar Abdallah shi yasa take yawan satar kallon sa,dan sam bata gajiya da kallon fuskar tasa,jitayi yace"kallon fa?wani irin kunya ne ya rufeta wanda yasa tayi saurin rufe kanta cikin hijabin ta kuma shine dalilin da yasa bata kuma ɗagowa ba har suka je inda zasu,a nan ɗin ma daƙyar tafita daga motar sai faman sinƙe kai takeyi. Suna shiga zauren malam bayan anyi musu iso,ji tayi kanta yana juyawa har tana ƙoƙarin faɗuwa da sauri Abdallah ya tarota jikin sa,suka zauna, cikin girmamawa Abdallah ya gaida Malam,daga nan basu sake cewa komai ba,bayaga tsurawa Bintu ido da malam yayi yana nazarin al amarin ta,can ya ja dogon numfashi kana yace"Abdallah kayi tunani mai kyau da ka kawo yarinyar nan,saboda akwai al amari mai girma wanda yake a lullɓe tare da baiwar ta,ɗan sihiri ne yayi tasiri ajikin ta amma da baka kawota da wuri ba abin zai iya girmama!'shiru yayi na ɗan wani lokaci kana yaci gaba da cewa,yarinyar nan sai da aka sha wahala kafin wannan sihirin yayi tasiri ajikinta,kuma damar da aka samu akanta shiyasa baza a zaunaba ake kuma binta da abun,amma dai har yanzu ba ayi nasara akanta ba,saboda jikin ta ya ginu kuma tana cikin kariyar ubangiji,dan haka yanzu baza musha wahala akanta ba!'wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Abdallah ya sauke,yana kallon fuskar Bintu da bacci yayi awan gaba da ita,Tofi malam yayi mata tare da addu'oi sai magunguna da ya haɗa mata da yadda zata dinga amfani da su,ya miƙawa Abdallah tare da cewa gashi nan insha Allah kafin kazo karbar wasu ta samu lafiya, Allah Ubangiji ya daɗa karemu daga sharrin maƙiya, Abdallah ya amsa da Amin kana ya ajiye wa malam sadaka,ganin yawan kuɗin shi kuma yace"ba zai karɓa ba sadaka kawai yake buƙata,badan Abdallah yaso ba ya kwashe kuɗin sa kana sukayi sallama ya ɗauki Bintu kamar wata ƴar tsana ya nufi mota da ita,yana saka ta cikin motar ta buɗe idanun ta,gyara zaman ta tayi tare da kawar da fuskarta can gefe,suna fara tafiya wayar Bintu ta kuma yin alamar shigowar saƙo, wannan karon ma shine ya ɗauka,wan nan karon saƙon Dije ne,inda take sanar dasu ta fito ta kuma gaya musu inda Bintu zata zo ta same su,cikin sauri Abdallah yace"da Yahya maza faka motar nan kajira mu anan zamu dawo!'a kuma lokacin ne samuyal ya kawo masa a daidai ta,lokaci ɗaya naga Abdallah ya sauya kama wasu kaya ya saka baƙaƙe tare da wata hular gashi babu abin da zai sa ba zaka ce masa tsoho ba,dan sak ya juye wata suffar da ban,Bintu dai saboda tsabar mamakin sa tsayawa tayi tana kallon sa baki buɗe,ɗan ɗage mata gira yayi lokacin da suka haɗa ido da ita,tura baki tayi tare da cewa kai ka ɓoye kanka Ni kuma a ina zaka ɓoyeni?bata ankaraba taji ta cikin jikin sa yayi mata mayafi da rigar dake jikin nasa,cikin wata irin murya yace"anan zan ɓoyeki Bint duk San da kike buƙatar ɓuya kizo Ni zan ɓoyeki nayi miki rumfa yadda babu wanda zai ganki balle ya cutar dake!'wani irin rawa jikinta ya shigayi saboda wani shauƙi da ya lulluɓeta wanda ita karan kanta bata san komeye ba, ta dai samu kanta da matukar jin daɗin kalaman ogan nata wanda har saida ta kuma cusa fuskar ta tana shaƙar sassanyan ƙamshin sa me canja mata tunani,gaba ɗaya sun shiga cikin wani yanayi na matuƙar shauƙi,amma su duk basu san da haka ba, Bintu tana ganin kamar yadda yake matuƙar tausaya mata ne yasa takejin kanta a wannan yanayin,yayin da shi kuma yake ɗaukar haka amatsayin tausayi da kuma kasantuwar ta ƴar uwar sa ta jini wadda a yanzu ita kaɗai ke gare shi wadda zai kalla ya bigi ƙirji yace"ga ƴar uwar sa,ƙarar da wayar Bintu tayi ne ya dawo dasu cikin hayyacin su,cikin sauri ta ƙwace kanta daga riƙon da yayi mata tare da rarumar wayar tana karawa a kunnen ta, muryar Dije taji cikin faɗa faɗa tana cewa Bintu wai me kika tsaya yine?Ni fa har na kusa ƙara sawa wajen!'cikin rawar murya Bintu tace"ga,,, gamu nan mun taho!'kar ɓar wayar yayi daga hannunta bayan ya kashe,miƙa mata wata doguwar riga yayi baƙa me hula yace"maza saka kar mu ɓata lokaci!'karba tayi ta zura kana suka fito,a tunanin ta samuyal ne zai tuƙa nafef ɗin amma sai taga saɓanin haka,dan Abdallah wani mamakin ya kuma barinta dashi dan shine ya zauna a mazaunin draver ya kuma tada nafef ɗin,ganin ta tsaya taki shiga ya sashi cewa bazaki shiga ba kin san dai ba jiran mu zasuyi ba!shiga tayi batare da tace masa komai ba,sai dai zuciyarta cike take da mamakin sa da kuma tambayoyi. Cikin gwaninta da ƙwarewa yake jan nafef ɗin har suka zo inda Dije ta kwatanta musu,sai dai daga can baya ya tsaya da nafef ɗin, juyowa yayi yana duban Bintu cikin bata ƙwarin gwiwa yace"ga ta inda suke can na sanki kina da dabara ba sai nayi miki bayanin yadda zaki ɓoye kanki ba!'jinjina kanta tayi tana ƙoƙarin fita,kama hannun ta yayi kana A hankali yace"Bint ki kula kinji,kiyi addu'a nima zanyi miki ki,ba tsayawa zakiyi sauraran wani abuba kawai ƙare mata kallo zakiyi,koda Allah zai sa ki ki iya gane ta a duk yanayin da kika ganta!'fita tayi da sauri ta nufi wajen da take da yaƙinin cewa su Dije suna gurin,guri ya samu ya ɓoye kan sa, sai dai ji yake kamar yabi bayanta,amma dai haka ya daure ya shiga Binta da addu'oi na kariya da neman nasara, Lokacin da tazo dab da gurin sai ta shiga sanɗa da raɓewa ta yadda babu wanda zai iya ganin ta,cikin ikon Allah ta samu nasarar zuwa inda suke,waje ta samu mai matukar tsaro ta ɓoye kanta amma saida ta tabbatar da cewa zata iya ganin su sosai batare da ta samu matsala ba,zubawa matar ido tayi tana lura da duk wani motsinta da takunta, yayin da zuciyar ta kuwa ji take tamkar zata faso ƙirjinta ta fito saboda tsabar kiɗima,har yanzu tsoron gano wannan mata yana tare da ita,sai dai yayi sauƙi saboda samun ƙarfin gwiwa daga Abdallah, Matar ta tsurawa Dije idanunta ta cikin niƙaf,tana daɗa karantar yanayin ta,can dai tayi wani murmushi ta cikin niƙaf ɗin ta,kana tace"anya Dije babu abinda kike shiryawa nifa har yanzu ina kokwanto a kanki!' sai kuma tayi shiru tare da ɗan yin taku biyu zuwa uku,kana ta da kata,cikin nutsuwa da taka tsantsan dije tace"ranki ya daɗe babu wani abu da nake shiryawa face abinda kika sakani,aikin da kika sakani shi kawai nakeyi!'to Dije idan haka ne ya labarin mutumin nan shin kun samo shi ne ko har yanzu ita ma ya gagareta?Dije tace"ranki ya daɗe muna kan hanya kuma insha Allah mune da nasara mun kusa kawo ƙarshen komai ina tabbatar miki da cewa bazan kuma bari mu haɗu ba har sai na samo miki ko wanene wannan mutumin!'dariya tayi wadda ta shiga kunnen Bintu,kana tace"yauwa Dije yanzu ne hankalina ya kwanta da aikin da kike min kuma na samu tabbacin kina yin abinda ya dace,dan haka Ni kuma zan zuba ido na saurari ranar da zaki kirani ki sanar dani ko wanene wannan shu umin mutumin!'daga haka,ta cigaba da taku dan barin wajen tana cewa saboda yardar danayi miki yau Ni zan fara barin wajen nan Dije na baki amanar rayuwata!'ba tare da ta saurari abinda Dijen zata ce ba ta yi hanzarin ƙara sa fita daga gurin wanda har saida ta taka ƙafar Bintu ba tare da hankalin ta ya kai kanta ba. Runtse idanunta tayi cikin raɗaɗin da ƙafar ta take mata da kuma fargabar kar ta ganta, ga kuma ruɗaninda ta shiga na san tan-tance inda tasan me wan nan dariyar tabbas kamar taso ta gane Muryar matar duk da cewa ta rufe Muryar,haka kuma takun ta shima ya tsaya mata kai da duk yanayin jikin matar,tabbas tasan wannan mata kuma a cikin astate take rayuwa,lallai Dije tayi gaskiya kuma tayi babbar dabara da kawo wannan shawara,dan kuwa tabbas idan taga matar nan zata shaida ta Ali wane yanayi,sai dai kuma ta ina zata fara karaɗe ESTATE dan binciko ta?wata zuciyar tace ke Bintu biyota bai zama abu mai wahala a gareki ba sai duba ta a inda kike rayuwa,ko kin manta kina da jarumin maza kuma gwarzo a kusa dake,dan haka babu abinda zai gagareki a wannan karon kune da nasara,da wannan tunanin ta fito daga maɓoyar ta,wanda sai alokacin ne Dije ta san Bintu tazo,fita sukayi bayan sun tabbatar da tafiyar matar. Daga ɓangaren Abdallah kuwa kaɗan ne ya rage zuciyar shi bata buga ba,shi da yacewa Bintu kar ta zauna me ya kaita daɗewa a inda shu'umar mata kamar wannan take,yana ƙoƙarin Binta sai kuma yaga fitowar matar cikin sauri ta tari a dai daita ta shiga suka bar gurin,da sauri ya fito daga maɓoyar sa,yana tunkarar wajen sai kuma yaga Bintun sun fito ita da Dije,Dije tace"Ni bari na samu nafef na wuce dan ba zai yiwu mu tafi tare ba!'jinjina kansa yayi tare da duntso kuɗi cikin aljihun rigar sa ya miƙa mata,karɓa tayi tare da yin godiya,ganin Bintu na ɗingi sawa yasa shi ɗan duban ƙafar tata,cikin alamun tambaya ya kalleta,tuni hawaye suka fara zuba mata cikin shagwaɓar da take halittar tace, tace"ba itace ta take min ƙafa ba!'kawar da kansa yayi tare dacewa to muje gida ayi miki allurar tetonos tunda wajen yayi jini kuma Allah yasa bata ganki ba!'ya faɗa yana ƙara haɗe fuskar sa,shuru tayi batace masa komai ba amma dai ta ƙudurta a ranta babu allurar da zata tsaya yayi mata, A inda sukabar su Yahya a nan suka same su, nafef ɗin ya bawa samuyal,kana suka shiga motar, kayan jikin sa ya cire ya dawo Abdallahn sa na ainahi wanda har saida ya bawa Bintu dariya, sosai take jin dariya idan ta tuna shigar sa ta ɗazun wanda alokacin bata samu damar yinta ba saboda yanayin da suke ciki,kawai kallon ta ya tsaya yanayi saboda yadda yaga dariya tana mata kyau,ita kuma ganin ya zuba mata ido, sai ta bar dariyar tare da haɗe fuska wai dan karma ya ga fuskar da zaice zaiyi mata allura idan sun koma gida,wani ɗan murmushi ne ya suɓuce saman leɓan sa amma bai bari ta gani ba,ya gano ta sarai yasan abin da take yiwa gudu kuma allura ce sai yayi mata ko me zatayi,a haka suka karasa estate ɗin. Tunda suka sauka ta ɓangaren da ɗakin yake,sai gaba ɗaya tunanin da hankalin ta suka koma wajen,sai yanzu abin yake dawowa kanta wanda tun ranar da abin nan ya faru sai yau ta kuma jin shauƙin shiga ɗakin, wani irin ƙwarin gwiwa takeji a tare da ita, tabbas sai ta shiga ɗakin nan sai kuma tagano menene aciki,kuma sai ta gano mallakin waye,haka nan take jin kamar buɗe ɗakin nan shine wata buɗaɗdiyar hanyar sada ta da duk wani abu da take burin nema ko tace suke burin nema,ido ta zaro ganin mutumin da ya fito daga ɓangaren kamar almaraa haka take ganin al amarin wanda ya matuƙar hautsina tunaninta.... Karku damu komai ya kusa zuwa ƙarshe ku dai kuci gaba da bina sannu dan War ware muku turka turkar, 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 45 ``` Kafin ta fita daga mamakin ganin Dady Habib da tayi sai kuma ga Dady Mansur shima ya ɓullo ta can inda yafi kusanci da ɗakin,wai meke shirin faruwa ne,me yasa suke san burkita mata tunani?to acikin su waye?ko duka su biyun ne?me hakan yake nufi ne? runtse idanun ta tayi yayin da har shenta ya shiga nanata innalillahi tare da allahumma ajirni filmusi bati wakalifni khairan minha,a dai dai lokacin da Abdallah ya gama sallamar Yahya ya juyo dan su tafi, tsayawa yayi yana kallon ta cike da mamaki, yayin da ita kuma har lokacin idanun ta suna rufe tana maimaita duk addu'ar da takama, cikin nutsuwa ya juya yana kallon ɓangaren shima dan yasan komeye baya rasa nasaba da wajen,shi dai baiga komai ba dan haka kawai sai yaja hannunta suka fara tafiya,wanda sai alokacin ne ta buɗe idanun ta da suka kaɗa suka koma wata kala saboda tsabar damuwa,binsa kawai take batare da tasan inda take taka ƙafafunta ba,ita dai kawai tagan su cikin falon inno,basu samu inno a falon ba dan haka kawai sai ya wuce part ɗin sa kai tsaye, Suna shiga ɗakin sa ya riƙota jikin sa,wanda hakan ne ya kuma haifar da wani irin rauni azuciyar ta, a hankali ta kuma cusa kanta a cikin ƙirjin sa tana giga fuskarta a kai wanda ya riga ya gane wannan alamar tace"da take nuna masa yanayin damuwar da take ciki,hannun sa yasa a bayanta ya shiga fatin ɗin ta cikin salon rarrashi,A hankali ta shiga sakin wata ajiyar zuciya a jajjere tare da samun nutsuwa da salama,sai da ya tabbatar da nutsuwar ta kana ya saketa tare da nuna mata hanyar bayi,cikin body language ɗin sa yayi mata nuni da ta shiga tayi wanka,duk da halin da zuciyar ta take ciki sai da ta ɗan tura baki tana ƙunƙunin rashin maganar sa,bai kula ta ba ya fita daga ɗakin. ɗakinta ya shiga tare da ɗauko mata kayan bacci, da wasu abubuwan da yasan zata iya buƙata, ya fito yana ƙoƙarin shiga falon sa sai ga inno ta fito daga sashen Alhaji Baba,tace"a'a Abdallah ashe kun dawo?cikin girmama matar yace"mun dawo inno amma bamu jima ba,tace"to madalla ina fatan dai anyi nasarar abinda A kaje nema?yace"Alhamdulillah inno insha Allah an samu nasara tunda dai gashi nan yayi mata tofi da ya bata magunguna,ya kuma bamu lokacin komawa!'inno tace"to masha Allah Ubangiji ya sa a dace!'ya amsa da Amin kana ya shige ita kuma inno ta shige ɗakinta, Tunda ya koma ɓangaren sa,ya kasa samun nutsuwa,ita kanta Nafisar ta bata san shigowar sa ba,babu abinda yake damun zuciyar sa sai batun iyalan sa,yana son Laila da abinda ta haifa masa bai son so ba sai akan Laila Bai san ɗaɗin ɗa ba sai akan abinda ta haifa masa,wai waye yayi masa wannan mummunan cutarwa? tabbas duk ranar da yayi ido biyu da wanda yayi sanadin rabuwar sa da sanyin idaniyar sa,baya jin idan yakama shi zai iya barin sa da numfashi, babban abinda yake bashi mamaki ya akayi aka san ya auri Laila da inda take zaune kai harma da gidan Sulaiman ɗin da aka bisu,San nan wan nan mutumin daya kirashi waye shi?me yake nufi da wannan tambayar da yayi masa?san nan ya akayi yasan iyalan sa sun ɓata?anya kuwa ya kamata ya bar wannan magana? tabbas yanzu ba lokacin zama bane a wajen sa yanajin lokaci ne yayi da zai fita dan neman nasarar sa,yana ji ajikin sa ya kusa haɗuwa da farin cikin sa,ya dade bai samu nutsuwar da ya samu a wannan karon ba kuma a cikin wannan lokacin da ya gabata,fuskar Bintu da Abdallah ne suka gilma ta idanun sa murmushi ne ya suɓuce masa,yana jin ƙaunar yaran tamkar jinin jikin sa, yanajin mizanin ƙaunar su na ninkuwa duk sakan a zuciyar sa. Yana cikin wannan halin ne Nafisa ta ƙara so inda yake,zama tayi gefan sa,cikin nuna tsananin damuwar ta akan sa, tace"yallaɓai baka jin daɗi ne?girgiza mata kai yayi,ta kuma cewa to meke damunka naga dai kamar lafiya kafita,amma gashi ga dukkanin alamu ka dawo da matsananciyar damuwa?nan ma dai girgiza mata kai yayi,ƙara matsawa kusa dashi tayi tare da ɗan roƙo hannunsa tace"haba Umar yanzu kana da wanda yafini kusan ci da kai wanda zaka iya kai masa damuwarka bayan ni?dan Allah ka gayamin abinda ke damun ka yau ɗaya dai, ko ina da abinda zan iya taimaka maka dashi!'kallon da ya watsa mata ne ya ɗan so ya razana ta,amma duk da haka batayi ƙasa agwiwa ba ta kuma langaɓar da kai tare da cewa,pls Umar telk to me,ko baka yadda dani bane?wani rikitaccen kallo da ta kasa gane masa ya kuma watsa mata kana ya ɗauke kanshi daga kanta,shurune ya ɗan gifta,kowa da abinda yake saƙawa A cikin zuciyar sa,Umar ya san Halin Nafisa nesa ba kusa ba,ko ita bata san kanta yadda yasan ta ba,ya daɗe yana mugun tunani akanta game da al'amarin sa,idan yace baya zargin ta ma tabbas yayi wa kansa ƙarya,sai dai har yanzu bai kamata da wani laifi makacin wannan ba, bare ya tabbatar,to amma yanzu wayar wan can mutumin ta zaburar dashi daga baccin da ya kwanta yi,dole sai ya binciki Nafisa domin bai yadda da ita ba,ita kuma tunanin ta kawai bai wuce ta yadda za ayi ya sanar da ita ko mai akan lamarin sa ba,cikin san yi masa dabara tace"wai ni kuwa Umar baka tunanin lokaci yayi da yakamata mu nemi yarinya ko yaro a gidan marayu ba tun da har yanzu babu wani labari akan samun haihuwata!'kallon ta yayi cikin wani irin yanayi yace"me ya kawo wannan maganar kuma?anzo wajen dama so take ya magantu,tace"to ai ina ganin damuwar taka duk bata rasa nasaba da rashin haihuwar mu kuma kaga nima,ina buƙatar ganin ƙwaina a duniya kafin na mutu!'ta faɗa cike da alamun tausayawa kanta,irin tana cikin damuwar nan sosai,miƙewa yayi tare da watsa mata kallon tuhuma,ganin yana ƙoƙarin barinta agurin yasa tayi saurin cewa'cikin muryar dake son fashewa da kuka,yanzu Umar kana so kace baka yarda dani ba ke nan, da ba zaka iya gaya min damuwar ka ba?ban yarda dake ba Nafisa!'itace kalmar da ta daki dodon kunnen ta,kafin ta dawo daga ruɗewar da tatafi, ya kuma yanko mata wata da cewa,Nafisa tabbas ban yarda dake ba, saboda ina zarginki da aikata mun wani mummunan laifi,kuma wallahi duk wanda na samu da saka hannun sa kan aikata min wannan ɓarna to kuwa zan iya saka wuƙa na yanka maƙogaron shi ko wanene kuwa,shi yasa nake miki fatan kar ki kasan ce cikin waɗan da suka aikatamin wannan babban laifi,ko nace kar ki kasance kece kika aikata min wannan mummunan laifi,dan haka ki rabu dani,bazaki samu damar jin ko mai daga bakina ba yanzu har sai ranar da asiri ya tonu gaskiya ta bayyana!'daga haka bai ƙara cewa ko mai ba ya fice ya barta A zaune cikin tafiyar sumar wucin gadi,gaba ɗaya ƙwaƙwalwar ta tsaya ta daina aiki duniyar kanta ta tsaya mata,bata ganin ko mai bata jin komai, ayanzu dai acikin wannan yanayin. Lokacin da ya shiga ɗakin bata fito daga toilet ɗin ba,dan haka wayar sa ya ɗauka,ƙira ya tafi,bayan wucewar wasu ƴan sakanni,aka daga kiran nasa,daga can ɓangaren akace Yes ogah,a hankali yake magana cike da nutsuwa,yace"daniyal,aikin ka yazo,me wannan hotan dana turo maka ya dawo kamar yadda na gaya maka, a kwai inda muke so yayi mana jagora to kasan dai aikin namu na sirri ne,ina so duk inda ya shiga ya fita Kabi min shi har sai ka gano mun wannan gida danayi maka bayani a kan sa,dan haka ka inaso ka zama cikin shiri,ka kuma saka ido akan shiga da fitar sa, dan kar yaje batare da ka sani ba!'daga can ɓangaren daniyal ya amsa masa cikin ladabi,kana suka yi sallama. Yana sauke wayar daga kunnen sa tana fitowa,jikin ta ɗaure da ƙaramin towel,ta rufa wani a kanta, babu abinda take sai tashin ƙamshi me sanya zuciya nishaɗi,ganin sa a zaune a ɗakin yasa duk sai ta diririce,jan towel ɗin take a ƙoƙarin ta na ganin ta kuma sauko dashi ƙasa,saboda yadda cinyoyin ta da ƙaurinta duk suke waje,a garin san rufe ƙasa ta buɗe sama batare da sanin ta ba saboda hankalin ta yana kansa,bata so tayi wani motsin da zai sa ya gane mata jiki,ɗan lumshe idanun sa yayi yana mai jin wani abu na tsira masa har can cikin tsakiyar kansa da gan gan jikin sa,wani yamm yamm yake ji tsigar jikin sa na miƙewa,bai taɓa shiga cikin irin wannan yanayin ba bai kuma taɓa sanin zai shiga ba,a tunanin sa wannan ƙwailar yarinyar bata da abun da zata iya sawa yanayin sa ya sauya?miƙewa yayi dan ƙoƙarin kaucewa haɗarin da Bintu take ƙoƙarin saka shi,ita kuma ganin ya nufota a tunanin taq wajen ta zai zo saboda tana kusan kofar toilet ɗin,dan haka sai ta kuma jan towel ɗin ƙasa,wanda hakan yasa gaba ɗaya ƙirjin ta ya ƙarasa baiya ƴan madai daitan nn tane sukayi wa Abdallah ƙuri,batare da ta kula da hakan ba,gaba ɗaya ji yayi ya kasa control ɗin kan sa,anya kuwa yarinyar nan ba da gaiyya take yin abin nan ba? haushin abinda takeyi ne yasa Abdallah mai makon ya wuce ta ya shiga toilet kamar yadda yayi niya da farko kawai sai yasa hannun sa ya fizge towel ɗin data ke ta kanka bar rufe cinyoyin ta dashi,wata irin ƙara ta saka tare da waɗawa jikin shi ta cukyikyiye shi tana ɓoye halinntun ƙirjin ta ajikinsa,bai san sanda wani shu'umin murmushi ya kufce masa ba,wanda har sai da kumatun sa suka loɓa,hannun sa yasa ya zagayeta ajikin sa tare da ɗora haɓar sa kan jiƙaƙƙen gashinta data wanke yake ta zuba ƙamshi,cikin kuka tace"wayyo jikina dan Allah ka rufe min jikina bana son kana kallon min jikina!'a hankali ya gangaro da fuskar sa cikin wuyanta yana shaƙar ƙamshin jikin ta,tare da cewa me zan kalla ajikin naki?meye abin kallo ajikin naki?maza nunamin abinda bakyaso na kalla bint!'yana yin maganar yana saukar mata hucin numfashinsa cikin wuyanta da yake ta karaɗewa da fuskarsa,take jikinta ya shiga rawa har kafafunta na ƙoƙarin kasa ɗaukar gangar jikinta,kici kicin ƙwatar kanta take yi amma mai makon ya sake ta sai ƙara karfin riƙon sa yayi agareta,abubuwan da ya shiga yi mata masu wuyar fassarawa ne agareta, wani irin yanayi suka shiga gaba ɗayan su wanda tun tana son guduwa har ta kai da ta haƙura, sabo da wani irin susa da Abdallah yake bin sassan jikinta dashi da tausasan tafin hannun sa wanda yake neman shiɗar da ita,bata dawo hayyacinta ba taji hannun sa kan tausasan ma daidai tan nn,ta,shi kansa Abdallah bai san a wace duniya yake ba bai kuma san hakan ta faru ba,bai kuma san mai yake aikatawa ƴar ƙanwaliliyar tashi ba,( kai Abdallah babu ƙira me zai kawo gawayi ko kamanta tausayin Bintu kake yi ne) Laushi fatar jikin Bintu da taushin abinda yake latsawa a ƙirjinta su suka hana shi dawowa cikin hankalin sa,ita kanta Bintu ta sare da yanayin mutumin nata,wani irin tsorone yaka mata jin hannun Abdallah a pravet pant ɗin ta yana yawo dashi,da ta kasa ƙwacewa daga gareshi sai kawai ta saka masa kuka,wanda shine abinda ya dawo dashi cikin hankalinsa,da sauri ya saketa,ba tare da ya iya kallon ta ba ya shige cikin toilet,yana wani killer smell,wanda Ni kaina na kasa gane na meye,hmm shi dai yasan manufar abinsa,da sauri ta sunkuya ta ɗauki towel ɗinta ta ɗaura,kana ta nufi inda kayanta suke,ɗaga rigar da ya ɗauko mata tayi zata saka,amma sai ta da kata ganin ƙanƙantar rigar ita fa a iya ɗakinta kawai take saka irin wannan kayan amma shi ya kama ya wani ɗauko mata su, dan kawai yayi mata wayo yadinga taɓa mata nn,tura bakinta tayi tare da hararar kofar bayin tamkar manyan idanunta zasu faɗo,gaba ɗaya haushin kanta takeji da ta bari yayi mata irin wannan ta adi,a fili tace"yo ai dan yaga ina kwana ɗakin sa ne shi yasa duk yake min haka,kaga mutum sumi-sumi dashi kamar ba zai iya wannan iskancin ba,fitowar sa ce tasa ta yin shiru tare da hayewa saman gadon batare da ta saka rigar ba,rufe kanta tayi gaba ɗaya da tattausan blanket ɗin sa,bai kalleta ba yayi abinda ke gaban shi cikin nutsuwa ya gama shirin sa,fita yayi daga ɗakin,jin fitar tasa ne yasa ta tashi cikin sauri ta zura rigar tare da sake komawa ta rufe kanta ruf,dama sun tsaya a hanya sunci abinci dan haka bata da yunwa,tana jin lokacin da ya dawo, batayi wani motsi da zai nuna masa cewa idanunta biyu ba,amma shi yasan ba bacci tayi ba,a zuciyar sa yace"yanzu zanyi maganin ki,allurar tetonous ya haɗa asirinji kana ya dauko tofinta da malam ya bayar da magungunan da zai zuba aciki ya nufo kan gadon batare da ta san abin da yake yi ba,dan har bacci ya fara ƙoƙarin ɗauke ta,ji tayi kawai ya yaye,bargon yana cewa taso kisha magungunan ki!'a hankali ta buɗe idonta tana kallon hannun sa,sai a san nan ta gane maganin da yake nufi,shi yasa batayi musu ba ta tashi zaune tana ta faman jan bargon jikinta dan kar ya ganan mata jiki,haka kuma ta kasa kallon fuskar sa, shi ko gogan naku ko ajikin sa sai ma haɗa fuska da ya kuma yi,yana haɗa mata magungunan da zata sha,miƙa mata yayi tare da cewa tayi Bismillah tasha ta kuma shafa ajikin ta. Sai da ta gama shan tofin, har tana ƙoƙarin komawa ta kwanta,ya dakatar da ita,ɗan tsayawa tayi ba tare da ta dubi inda yake ba,shi kuma hakan ne ya bashi damar soka mata allurar batare da ta ankara ba,runtse idanunta tayi saboda jin shigar allurar cikin fatar ta,hannunta ta ɗora kan nasa hawaye wani na korar wani,sai da yagama ya leƙa fuskar ta,yaga yadda ta caɓe da ruwan hawaye,yace"yarinyar nan yaushe zaki daina kukan allura ne?tura ɗan mitsitsin bakinta tayi tana gunguni,kafin ta maida shi taji wani sabon Al'amarin daga ɗan gidan ABUBAKAR jikan BALARABE,kuma yayanta garkuwar ta mijinta Abdallah,sarrafa harshenta ya shiga yi cikin bakin sa da wani irin salo mai matukar tsayawa a rai da zuciya,yadda yake tsotsar bakinta har abin saida yaso fin ƙarfin tunanin ta,kokowa take dashi dan ta ƙwaci kanta,amma da abin yafi ƙarfin ta tuni ta miƙa wuya ga jikan BALARABE,har da saƙala hannunta ta ratayo wuyan sa,saiga Bintu da cafke ɗan madaidaicin laɓɓan Abdallah tana masa wata iriyar siɗa da ita kanta bata san ya akayi ta iya ba,dan sam bata cikin hankalinta,wani irin sweet bakin nasa yake mata kamar wadda aka lasawa zuma haka take ji akan harshen ta, Abdallah kuwa shi baya cikin wannan duniyar ma domin halin da yashiga da shauƙin da yake ciki ba Abune da zai iya kwatantawa ba, wannan yanayi da wannan rana ya barwa zuciyar sa da gangar jikin sa sanin halin da yake ciki,sun fi ƙarfin mintuna ashirin cikin wannan zazzafan yanayi me cike da sirrika da kuma tarihi a gare su dan dukkan su baƙi ne a wan nan fagen kuma a wannan ranar ne suka taɓa ɗanɗana garɗin soyayya,duk da su basu san da haka ba, bakuma su san cewa wannan abun da sukayi shine ƙauna ba,sun dai can ja masa suna daga tausayi zuwa shakuwa,e mana shaƙuwa ce tasa suka manta duniyar da suke ciki,(inji Abdallah da Bint ɗin sa fa,ba inji Fatimah ba)ɗaga kan sa yayi yana kallon ƙawatacciyar fuskar ta da take ta ƙyalli da sheƙi bacci take yi sosai tana tsotsar bakinsa da take jinsa tamkar zuma ana ta bakin, A hankali ya zame bakin sa tare da tashi zaune, tsura mata idanu yayi yana tunanin da duk koƙarina ban gano komai ba a wannan karon,yunƙurawa yayi ya tashi,toilet ya faɗa tare da sakar wa kansa shaya sai da yayi wanka daga nan,ya ɗauro alwala ya fito,dadduma ya shimfiɗa ya tada nafila,duk da cewa yaso tashin Bintu amma sai ya ƙyaleta,saboda tofin da zaiyi mata tana cikin bacci,asuba ta gari Abdulbint. A cikin wannan daren da Abdallah da Bintu suka samu nutsuwar zuciya,a cikin sane wasu kuma suka kasa bacci,kamar dai yanzu da nanu yake ta zagaye cikin ɗakin sa shi ɗaya,fargaba ce taf cikin ransa,da tashin hankali tabbas idan yace baya tsoron yarinyar nan yayiwa kansa ƙarya,dan gashi ga dukkanin alamu tana son ganin bayan shi,shin mai zaiyi a wannan karon dan dakatar da ita daga shirin ta na tunkarar ɗakin nan?yaya zaiyi duk ranar da ta samu nasar bankaɗa ɗakin nan?me yasa ƙarfin gwiwar shi yake sarewa ne?me yasa yake jin faɗuwar gaba duk sanda ya haɗu da yaran nan?shi da yake son su zamar masa garkuwa gurin samun mafarkin sa,to me yasa yake jin tsoron su? tabbas dole ne yayi gagagawa gurin cimma burin sa idan ba haka ba kuwa ko mai zai iya faruwa,cikin tashin hankali yace ABUBAKAR dole ka faɗa min inda mahaifin mu ya binne ajiyar nan,bazan ƙyaleka ba kai da iya Lanka, har sai na ga na samu abinda nake nema,badan ina da tabbacin ba a cikin ESTATE aka binne ba, ai da tuni na kashe kowa na tarwatsa estate din domin bin ciko abin da nake nema. A ɓangaren Nafisa ma dai kusan haka din ne,tarasa abin kamawa,ta kai mari ta kai gauro,duk wani shirin ta neman kwancewa yake,shin ya akayi ta bari har Umar yake zargin ta?wane irin sakaci tayi haka,da balli yake neman tsinke mata?shar ce hawayen fuskar ta tayi tare da cewa me yasa al'amuran suke ƙoƙarin dagule min?shin basu Babe sun bani tabbacin sun mutu ba,me ya jawo duk wan nan?idan sun mutu ai bai kamata na dinga jin tashin hankali irin haka ba!'wayar ta tayi saurin rarimowa lambar da tayi shekara kusan goma sha takwas rabon ta da ita, ita ta dan nawa kira a yanzu,bata jima tana ringin ba aka daga,cikin matuƙar ƙasa da murya tace"da Babe nake magana?wata irin dariya irin ta cikakkun ƴan daba akayi tare da cewa hajjaju Nafisa gaskiya baki da amana,ko dan kiran nan a gaisa baki taɓa yi mana ba tun bayan da buƙatar ki ta biya,yanzu ma wata buƙatar ce ta taso miki ko?cikin sauri ta dakatar dashi tare da cewa,babe ba wannan ne abinda yasa nakiraka ba,tambayar ka zanyi,shin a wan can ranar baka ce min kun kashe matar nan da ɗiyar taba? tabbas haka na gaya miki amma nima sai kwanakin nan naji yarana suna hirar gaskiyar yadda abin ya faru, ashe nima muna funtata suka yi,a taƙaice dai basu kashe su ba dan ɓace musu sukayi suka rasa su,dan haka gaskiya bani da tabbacin sun mutu ko basu mutu ba,,,wata razanniyar ƙara ta saki tare da sakin wayar ta faɗi ta tar watse,zubewa tayi tana wani irin kuka mai cike da tashin hankali da tunanin makomar,shike nan su baku kashe su ba Ni kun kashe Ni ƙarshe na yazo, tabbas tunda Umar yace"zai nemosu sai ya nemo su in dai suna raye,yanzu ya zanyi?kaicona,me ye amfanin abinda nayi tunda ban samu riba ba,yanzu kam anzo gaɓar da dole sai na gayawa Bintu abinda na aikata, da bakina,domin ta samo min mafitar da zan tsira koda da rayuwata ce,ranar idanun Anty Nafisa basuga bacci ba duk iya satar sa kuwa. Washe garin safiyar kuwa Umar ko ƙeyar Anty Nafisa bai gani ba,bai kuma neme taba shima, haka ya gama shirin sa na tafiya suleja,ai nahin inda ya mayar da su Hajjon Laila,shi yasa zuwa baya yi masa wuya,tunda ya dawo dasu cikin Abuja, ɓangaren Hajiya Babba ya fara zuwa su kayi sallama kasan cewar ita kaɗai ce tasan inda zashi,daga nan ya wuce sauran sashen suka gaisa, ya ɗan jima a bangaren inno dan kawai yana son ganin su Bintu sai dai ganin lokaci na ja basu fito ba yasa ya haƙura yayi sallama da inno ya ɗauki hanyar suleja, tare da ɗan rakiyar da bai san da yana bin sa ba. A can ɓangaren Samira kuwa yau ta tashi ne cikin farin cikin babbar nasarar data ke tunkaro su,don kuwa a yau ɗin ne misalin ƙarfe huɗu na yamma zasu haɗu da Alhaji Sama'ila,kuma da alƙawarin zai gaya mata abinda suke nema suke yaki suka hana idon su bacci dare da rana,suka zalinci wasu suka ha inci wasu duk akan sa,yayi alƙawarin saboda yar dar da yayi mata da kuma gudummawar da ta kawo masa,zai gaya mata wannan abun da suke nema,wanda Ni kaina na ƙagu da naji ko menene wannan abun da ake ta zaluntar bayin Allah akansa. Alhaji Baba ne ya zubawa kyakykyawar fuskar matar sa Hajiya Babba ido cike da son gano wani abu atare da ita, sam ya kasa gane mata kwana biyu kamar tana cikin damuwa,cikin taushin murya yace"meke damun ki ƴar Agadez?ɗan murmushi ta kalato wanda kana ganin sa kasan na yaƙe ne,tace"babu abinda yake damuna, halin rayuwa ne kawai,bai takura ta ba ya rabu da ita,sai ma can ja maganar da yayi da cewa,kin san dalilin kiran danayi miki? girgiza kanta tayi,yace"akan wannan ajiyar da na binne ne kin san dalilin da yasa naƙi gayawa kowa inda take,kuma bayan ke da Abubakar bana tunanin wani yasan da ita,duk saboda gudun fitina,to yanzu lokaci yayi da nake ga zan sanar da sauran ƴaƴana da matana, inda na ajiye wannan d....ɗan shuru yayi ganin kamar yaji motsi a tabayan ɗakin nasa,dan haka yace"Safiya mu bar maganar da sauran lokaci ban yadda da wajen nan ba kamar anyi mana laɓe a ta wajen nan.... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 46 ``` Hajiya Babba tace"shike nan Allah ya baka ikon sanar da zuri'arka wan nan sirrin,tunda kaga dai dani da kai duk ba dauwama zamuyi a duniyar ba,shekaru ja suke yi,shi kuma wanda ya sani bashi ba labarin sa Allah ne kaɗai yasan halin da yake ciki!'ta ƙara sa maganar cikin fashewa da wani irin kuka wanda daga ji kasan ya daɗe yana cin ranta da zuciyar ta,ta kuma jima tana son yin sa,Alhaji Baba shuru yayi yana kallon ta bai katse mata kukan ta ba,dan ji yake inama shine ya samu damar yin wannan kuka da ya ji sauƙin abinda yake cunkushe a zuciyar sa,ɗan jingina yayi da jikin gadon yana fidda wani irin nishi mai fita da tsananin wahala da damuwa,baka jin sautin komai sai kukan Hajiya Babba da takeyin sa cikin wani irin baƙin ciki da tarin damuwa,cikin rawar murya tace"ya Allah ya Ubangiji na roƙeka ka bayyana min farin cikina kafin ƙasa ta rufe idanuna,ina roƙon ka bayyana sirrin dake ɓoye,ka fiddani daga cikin duhun da na shiga,ka kuma kawo farin ciki acikin rayuwar ɗana Umar ka bayyana masa sashin sa farin cikin sa, Allah ka nuna min ranar da zanga farin ciki da walwala a kan fuskar sa wanda yake daga cikin zuciyar sa!'amin Alhaji Baba yake ta cewa yana jin tururin dake kwance cikin zuciyar sa na lafawa,saboda tasirin addu'ar dayake ta nanatawa a duk lokacin da wata damuwa ta taso masa,allahumma la sahlan,itace addu'a mafi sauƙaƙa damuwar zuciya. Dadyn Sayyid nifa na gaji da gafara sa har yanzu kuma banga ƙaho ba,kullum cewa kakeyi Sayyid zai dawo,amma har yanzu da muke cikin kwana na uku da ɓatan sa,babu wani labari mai daɗi akan sa, gaskiya ka nemo min yarona dan na gaji da wannan daɗin bakin naka!'Dady Mansur ya zaburo cikin masifa yace"au Nine nake miki daɗin bakin?ko kina tunanin kin fini shiga tashin hankalin rasa shi?ke baki san ko mai akan abinda nake tunani ba shi yasa bazaki gane tashin hankalin da nake ciki ba,amma saboda wuyan ki yayi kauri har Ni zaki duba kice ina miki daɗin baki!'ya faɗa yana ƙureta da kallon sa,bata ce masa ko mai ba sai da taje bakin step ɗin da zai kaita ɗakinta,ta juyo kana tace"ai dole hankalin ka yafi nawa tashi tunda kasan baka shuka gaskiya ba, yarona yana can za aɗauki fansar abinda kake yi akan sa,to kasani shi Allah babu ruwan sa, dan da wanda yayi zina da wanda ya tsaya akayi agabansa yana kallo duk ɗaya suke,tunda cewa yayi la taƙrabuzzina kada ku kasanci zina,to kaga kuwa baka da wata mafita laifin duk ɗaya ne kuma hukun ci daya,Ni dai kawai kasa waɗan da suka ɗauke min ɗana su dawo min dashi tunda shi baiji ba bare gani!'tana gama faɗar haka ta haura dakin ta da gudu,dan tasan kaɗan daga aikin Mansur ya faffalla mata maruka,a lallai wuyan ki yayi ƙauri,to zan ɗauki mummunan mataki akanki kuwa,da idan ba tsoro ba ki tsaya mana,da kuwa kin sha mamakin abinda zai biyo bayan waɗan nan mugayen kalaman naki!'fita yayi ran sa amatuƙar ɓace. A ranar nan ne dai kuma Abdallah yayiwa gidan sirri tsinke wanda tunda aka kai masa Sayyid aka ajiye bai waiwayen shi ba sai yau ɗin,zama yayi agabansa bayan Faisal ya saka masa kujera,kallon Sayyid ɗin yake wanda duk ya fita daga haiyacin sa duk da cewa ba dukan sa ake ba, kuma ba A hana shi ci da sha ba,kawai dai babu maganar wanka sallah dai ko ba yayi dole yayi ta,sai dai babu sakewa kuma ɗakin da aka saka shi aciki babu haske ko kaɗan,waɗan nan abubuwan sune suka sauya Sayyid tamkar ba Sayyid ɗan gayu da wanka ba,zuba masa ido yayi bayan yasa an haska masa wajen da wada taccen haske, Sayyid ɗin shima kallon sa yake cike da mamakin dama shine yasa aka kawo shi gurin nan,ɗan ɗage girar sa yayi kamar yadda ya zame masa jiki,kana yace"kayi mamaki ko? Sayyid yace"me nayi maka kuma da ka rabani da jin daɗi na?sai da Abdallah ya shaƙi ƙamshi,na ɗan wasu sakanni,kana yace"tambayar ka zanyi me by kasamu amsar taka tambayar acikin tambayar da zanyi maka, Sayyid bana so kayi min gaddama,saboda aikina na gaggawa ne,idan kuma har kana son fita daga gurin nan kaje kaci gaba da shaƙar iskar duniya kusa da mahaifin ka to ka gaya min gaskiya karkayi min karya!'kawar da kai Sayyid yayi tare da cewa me kake so ka tambaye ni?in dai na sani zan baka amsa!'ɗan tafa hannu Abdallah yayi tare da cewa yauwa kasamawa kanka lafiya,kana yace"waye yasaka shiga rayuwar Bint?kallon sa yayi da alamar bai gane Bint ɗin da yake nufi ba,gane hakan ne yasa Abdallah cewa Bintu my wife u understand,wani kafurin murmushi Sayyid yayi kana yace"au cewa zakayi bagidajiyar ƴar aikin inn...kafin ya kai ga ƙarasa abin da yake son faɗa Abdallah ya ɗebe shi da wasu mahaukacin marika hagu da dama wanda Sai da duniyar ta tsayawa Sayyid gaba ɗaya, lokaci ɗaya hancinsa ya fara zubda jini,cikin kakkausar murya Abdallah yace"tare da nuna shi da yatsa,kar ka sake ka bari wannan ruɓaɓɓen bakin naka ya kuma furta ƙazaman kalamai akan kyakykyawa mai kyakykyawar aniya kamilalliya mai kamilalliyar zuciyar matata,bana son raini ka mutunta Bintu tamkar yadda zaka mutunta iyayenka,koma fiye da haka,domin na tabbata tafisu kyan zuciya da mutuncin da za a mutunta ta,amsa kawai nake buƙata a gurin ka ba wasu ban zayen kalaman ka ba,ina sauraren ka,kabani amsar abinda na tambaye ka,saboda ina da abinyi!'ya faɗa yana duba tsadadden agogon dake ɗaure A tsintsiyar hannun sa,cikin wahala da nadamar shiga hurumin Abdallah da yayi Sayyid yace"nima ban san ta ba,a flazer muka haɗu da ita ta bani kwangilar sawa Bintu ido da kawo mata rahotanni akanta,amma wallahi ban san ta ba!'kamar ya baka santa ba?baka ga fuskar ta bane ko kuma kaga fuskarta sanin tane bakayi ba?girgiza kai Sayyid yayi cikin fitar da wahalallan numfashi yace"niƙabi ne a fuskarta, da ɓaƙar doguwar riga ban gane ko mai atare da ita ba,ban san komai A kan ta ba!'to meye manufarka ta karɓar tayinta? Abdallah ya tambaye shi cike da takaicin wawancin sa,nima saboda ina da manufa akan Bintun shi yasa na karɓa!'meye manufarka akanta? Abdallah ya kuma jefa masa tambaya,sunkuyar da kansa Sayyid yayi kana cikin rawar murya yace"sonta nake taƙi bani dama saboda tana da matukar kamun kai da nutsuwa,hakan ne yasa ko fuskar da zan yi mata wasan banza ban samu ba shi yasa Ni kuma nake jin haushin ta,kuma shine dalilin da yasa nayi saurin karɓar tayin matar saboda nima na ida manufata akanta,kamar dai ranar da ka ƙwace ta a hannuna!'ya ƙara sa faɗar maganar cikin fargaba,ji yake kamar Abdallah zai iya maimaita masa irin dukan da yayi masa ranar, wani ɗan huci Abdallah ya furzar batare da ya kuma cewa komai ba ya miƙe daga kan kujerar yana ƙoƙarin barin ɗakin,cikin saurin baki Sayyid yace"dan Allah tunda na gaya maka abinda kake so ka fitar dani daga nan gun!'Abdallah yace"da sauran lokaci daga haka ya ficewar sa ba tare da ya saurari surutan da Sayyid ɗin keyi ba. Tunda ya fita Bintu tana ɗakinta bata leƙa ko ina ba saboda bata jin fita ko ina ga kuma addu'oin da malam ya bata su ta yini tana yi,ko inno tunda suka haɗu da safe bata kuma ganinta ba,sai dai innon tana leƙawa ɗakin Bintu dan tabbatar da lafiyar ta,sai bayan sallar azhar ne ta fito falon dan samun abinda zata sakawa cikin ta,tana fitowa taci karo da bayan matar da take shirin shiga part ɗin Alhaji Baba,ta cikin ƙofar dake falon inno,zubawa bayan matar ido tayi zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri wacece wannan da ta shiga ɓangaren Alhaji Baba?wata zuciyar tace mata wacece take da ikon shiga idan ba inno ba,dafe ƙirjinta dake dukan tara-tara tayi,cikin sauri ta nufi ɗakin inno dan ganin ko tana cikin ɗakinta,sai dai abinda ya kuma tada hankalin Bintu sam bata ga inno a cikin ɗakin ta ba,hatta da toilet sai da ta duba amma bata ganta ba,kanta ta dafe,cikin tsinkewar zuciya tace"nashiga uku wacece wannan me irin takun matar nan da yanayin bayan ta, tabbas daga bayan matar nan ƙirar waccen shu'umar matar ta gani,to me hakan yake nufi?ji tayi kamar tabi matar sashen Alhaji Baba, Allah na roƙeka kar ka tabbatar min da abinda idanuwa na suke gani, Allah kar kasa zargi na ya zama gaskiya,haba inno anya kuwa zata iya aikata haka ta faɗa cikin yanayin ?tana son shiga falon Alhaji Baba Amma tana tsoron kar tayi mugun gani,wayar tace, ta fara haske alamar saƙo ya shigo, buɗe saƙon tayi tare da karantawa,Anty Nafisa ce take sanar da ita cewa gata nan zuwa yanzu da muhimmin saƙo gareta,kafin ma ta sauke idanun ta daga kan wayar taji ƙarar rawar falon tana ringin,hakan ne ya nuna mata ƙofar falon a rufe take,cikin jan jiki ta ƙara sa bakin ƙofar tare da cewa,waye?Anty Nafisa tace"nice Bintu buɗe min da sauri nasan inno bata nan saboda sai da na shiga ɓangaren Alhaji Baba na tabbatar tana can!'wani irin kakkauran miyau Bintu ta haɗiye wanda take taji bakinta ya gauraye da wani irin ɗaci, jikinta ya mutu murus, ta tabbata zarginta ne yake son tabbata,ke nan inno ce ta shiga falon Alhaji Baba, innalillahi'wa'inna'ilaihiraji'un,allahumma ajirni filmusi bati wakalifni khairan minha,abinda ta ambata kenan taji sauƙin abinda ya tokare mata a wuya,matsawa tayi Anty Nafisa ta shige ta mayar da ƙofar ta rufe,cikin sanyin jiki tamkar wadda bata da laka haka tabi Anty Nafisa zuwa cikin ɗakinta. Ganin irin tafiyar da takeyi ne yasa Anty Nafisa janyo hannun ta tare da rufe ƙofar har da saka key,kana ta je ta zuge window ta ƙara gyara labulen window ɗin,dawowa tayi ta kama hannun Bintu dake tsaye tana binta da ido cike da mamakin ta ga kuma wan can Al'amarin da har yanzu bai sake taba,zaunar da ita tayi a can ƙarshen gadon tare da zama a kusa da ita, Bintu dai har yanzu kallo take binta dashi ta kasa ce mata uffan,kama hannun ta Anty Nafisa tayi cikin matuƙar tashin hankali da neman taimakon Bintun tace"Bintu nazo gareki ne dan nasanar dake abinda ban taɓa sanar da kowaba, kuma sirrin rayuwata wanda cigaba da rufuwar sane kaɗai garkuwata,Bintu asirina yana neman tonuwa a gurin wanda bana fatan har duniya ta naɗe yaji sirrin nan,kamar yadda kika gayamin Bintu nayi amfani da shawarar ki kuma na aikata hakan,sai dai a maimakon samun nasara faɗuwa ce ta zomin domin kuwa allura ce take son tono garma,tsaf ta gaya mata yadda sukayi da Abba Umar,ta ƙare da cewa wannan dalilin ne yasa naji dolene nazo na sanar miki abinda baki sani ba dan ki samo min mafita wadda zan samu na tsira da mutuncina da kuma dukiyar Umar!'shuru ta ɗanyi tana haɗiyar miyan da ya daskare a maƙoshin ta,ita kuwa Bintu har yanzu cigaba tayi da saka mata ido,yayin da takewa Allah godiya cikin ranta dan tasan tasirin addu'a ne ya kawo mata ƙarshen Nafisa dan tabbas da zarar ta bankaɗa abinda ta shuka da bakinta to ta gama da ita fallasa ta ba zai zamar mata aiki mai wuya ba, wannan shi ake kira da dana sani wanda kamar shi ta fara hangowa a idanun Nafisa,sai dai lokaci ya ƙure mata,don kuwa a yanzu dana sani ce ta zame mata ƙeya. Kamar yadda kika sani sunana Nafisa ƴa ɗaya tilo a wajen Hajiya ladidi,shi yasa suke bala in sona,karma Hajiyata taji labari dan tafi Alhaji na ririta Ni da fifita soyayyar ta akaina,tun Alhaji na ganin gata ne take min har abin yazo ya fara damun sa,gashi Hajiyata bata jin maganar sa ko ɗaya,wan nan dalili ne yasa shi zuciya ya kaini makarantar kwana, Wan nan shine ɗan gajeren tatihina, ba zan jaki da nisa ba a takai ce dai dalilin aurena da Umar inno ce dan Hajiyata ce ta fara kawo mata maganar a matsayin ta na ƙawarta, to dake Allah ya ƙaddara nice matar Umar dole haka ya aureni ba dan yana sona ba!'Bintu ina da matukar kishi na hauka san nan ina son Umar da arziƙin gidansu,shi yasa nake matuƙar kishinsa,a haka muka ja shekaru ba haihuwa bare ɓari,Ni kuma alokacin sai na fara jin tsoro kar Umar ya fara tunanin ƙara aure ko Hajiya Babba ta saka shi yayi aure tunda dama kamar bata karɓeni amatsayin suruka ba,wan nan dalili ne yasa nayi matuƙar sawa Umar ido fiye da yadda kike zato,a kwai wani aminin sa Sulaiman tunda mukayi aure da Umar da shi kaɗai nasan shi kuma nasan yana zuwa Yola wajen sa dan haka sai da nasa aka yimin bincike ko yana da ƙanne dan ina tsoron kar shima yace zai bashi ƙanwar sa ya aura tunda yanzu kowa neman inda zaiji daɗi yake, A lokacin sai akabani tabbacin cewa yana da ƙanwa guda ɗaya amma anyi mata aure,hakan ne yasa hankali na ya ɗan kwanta kaɗan amma kullum ina cikin fargabar kar Umar yaje ya gano ƴar kyakykyawar bafulata na ya auro min,dan haka kawai sai na ɗauki wani salo na sakawa Umar tsoron yin aure da fargaba azuciyar sa sai na dinga yawan mugayen kalamai da alwashi kala-kala akan kishiya,har agaban Sulaiman nasha rantsuwa duk ranar da Umar yayi min kishiya sai na kasheta sai dai nima akasheni, Bintu duk wan nan abinda nakeyi ashe a banza nakeyi,dan katsaham na fahimci yanayin zuwan Umar Yola ya canja yana zuwa duk weak end a maimakon duk sati biyu ko wata, san nan Sulaiman shima zuwan sa ya ragu ba kamar da ba, anan ne nayi hanzarin tashi tsaye da bincike. "Hawayen da suka zubo mata tasa hannu ta share saboda tuno abin sai take ji tamkar yanzu yake faruwa,ta cigaba da cewa, bincike na ya tabbatar min da cewa,Umar aure yayi kuma ya ajiye matar a Yola,abinda ya kuma tayar min da hankali shine wai har ma matar tasa na ɗauke da ciki wanda zata iya aifuwar sa yau ko gobe,hankalina yayi matuƙar tashi saboda nayi mamakin yadda Umar ya shammace Ni har yayi aure yana shirin samun ɗa ko ƴa amma ban sani ba,sawa nayi a binciko min matar tasa ƴar wace mutane ce dan nasan irin matakin da zan ɗauka,amma amsar da aka dawo min da ita,ita ta kuma saka Ni cikin ruɗani wai ƙanwar Sulaiman ce,Ni da A kace min Sulaiman bashi da wata ƙanwa sai mai aure, to ina yasamo wata ƙanwar?ko dai sakota akayi ne?ƙarshe dai har da kaina saida nayi tattaki naje har cikin gidan Laila batare da tasan koni wacece ba, na kuma ganowa kaina tashin hankalin da ya hana Ni bacci ya hana zuciya ta sukuni ya hanani walwala cin abinci ya zama wahala agurina,saboda ganin turtsetsen cikin ta,tana rayuwa cikin ɗaula da jin daɗi, tunanin da ya fara faɗomin shine kawai nasa akashe Laila da ɗan uwanta harma da shegen cikin dake jikinta,tunanin hakan da nayi sai nayi ƙoƙarin kawar da abinda ke fuskata na barshi acan ƙasan raina yana cina,ban nunawa Umar ko mai ba,kamar yadda ya ɓoye min ban nuna masa na sani ba,sai dai kuma can gefe na koma nayi hayar haya killer waɗan da dama tun can mun daɗe dasu mutanen Hajiyata ne,su natura domin su kashe Laila da Sulaiman domin na tabbatar zaman sa a duniya bazaiyi min amfani ba,cikin daren suka bugo min waya cewa ai sun same ta da jaririya banyi wani tunani ba na basu umarnin sukashe su duka su ukun har jaririyar kar su bar kowa a raye,Bintu a cikin daren suka kuma kirana suka sanar dani sun kashe su duka dan haka na kwantar da hankalina,duk abinda nake yi inayin sa cikin taku dan alokacin ma ko ɗakin Umar banje ba ina ɗakina dan nasan da abinda na shirya. Bintu tun daga wannan rana na samu salama a zuciyata da kwanciyar hankali, amma sai dai kash mijina shi ya fansheni da ninkin baninkin damuwar da nashiga, wallahi Bintu halin da Umar ya shiga alokacin har saida na fara dana sanin abinda na aikata saboda idan nace miki bana son Umar tabbas nayi ƙarya,tun daga lokacin yake ciwo a tsaitsaye damuwa ta rafkar dashi ta wannan sanadin ya haɗu da ciwuka kusan kala uku, "A haka ne muka kwashi shekaru rabon dana ce miki Umar yayi dariya har na manta sai dai ban sani ba ko idan ya fita cikin ƴan uwan sa da iyayen sa,damuwar da yake ciki ita ta sani yawan damuwa akan abinda na aikata har inno da wasu da yawa suke tunanin ko damuwar rashin haihuwa ce na saka a raina,sai kawai na bari a hakan amma Ni a raina na san ba haka bane,ganin halin da nake cikine yasa Hajiyata tadamu ta tasani a gaba da cewa lallai sai na faɗa mata damuwata,banyi niya ko sha'awar gayawa wani sirrina ba,shi yasa kawai na canja labarin da ce mata,likitoci sun tabbatar min da cewa bazan taɓa haihuwa ba, Ni kuma shine nasa akayi masa asirin da bazai taɓa yin aure ba ko da yayi ma bazai taɓa haihuwa ba,kuma gashi hakan ya tabbata shi yasa nake nadama A yanzu ina ganin kamar zanje nasa a warware sihirin da nasa akayi masa!'alokacin Hajiya sai ta nuna min abinda nayi nayi daidai dan haka kar na sake na aikata abinda nake son aikatawa,idan dai har ba so nake asirina ya tonu ba,tayi min faɗan dan me ban gaya mata tuntuni mun san madafa ba, wallahi Bintu alokacin babu wan nan tunanin da burin a raina amma lokaci ɗaya Hajiyata ta ɗorani a hanya idanuna suka rufe ya zamana babu abinda nake nema sai dukiyar Umar ita kaɗai nake buƙata,dan kuwa tabbas huɗu bar mahaifiyata tayi tasiri a zuciyata fiye da yadda ita take zato,har ma sai burina yake son fin nata yawa,sai kuma gashi katsaham Allah ya kawoki,dan haka sai nayi amfani da wannan damar nayi duk abinda nayi ko nake kanyi,har zuwa yau dana baki labarin abinda Umar ya faɗa min wanda ban taɓa tunani ko zaton cewa Umar zai kawoni cikin zargin sa ba,dan ina da tabbacin cewa ban bar masa wata alama da zai iya gano abinda na aikata masa ba. Ba zan iya kwatan ta muku takaici da tsanar da Bintu ta ƙara ninkawa Nafisa ba,wai yanzu wannan matar dake gabanta ita ce tayi sanadin rabuwar ta da iyayenta,itace tayi sanadin da mahaifiyar ta take can cikin halin da bata sani ba,ke nan Nafisa bata san inda mahaifiyar ta take ba?to idan hakane waye ya kuma kawo musu farmaki na biyu?kuma shi meye nasa dalilin?kuma taya akayi suka san Lailan?da kanta ta shiga ta shiga hasaso komai dake faruwa, tabbatas tana zargin mutum ɗaya ne yake aikata duk wan nan,a yanzu ta gano me wayar nan shine ya ɗauke mahaifin Abdallah kuma shine ya ɗauke nata mahaifan,kuma shine masarrafin wan can ɗakin,to amma me yasa yace,bai san inda mahaifiyar ta take ba,domin ta tabbatar shine ya kira wayar ta wan can ranar,to meye yake ɓoyewa ko yake aikatawa a wan can ɗakin? tabbas dole lokaci yayi da zata farmaki wan can ɗakin ko ta wane hali kawai dai fatan nasara take gurin Ubangiji. Anty Nafisa bata katse mata tunanin taba har sai da taga dai Bintun dai bata da niyar dawowa cikin hankalinta,kana tayi magana a hankali tace"Bintu ya dai bakice ko mai ba!'sai alokacin Bintu ta kalli Anty Nafisa tare da ƙirƙiro murmushi tace"to ai ke nake jira ban ji ƙarshen ba tunda har yanzu ban san manufar kiba,shin kinyi na dama ne ko zaki ɗora daga inda kika tsaya!'tayi shuru tana jiran amsar da Anty Nafisa zata bata,cikin jan dogon numfashi tace"gaskiya Bintu da naso na haƙura ki nema min fafitar da zan samu na cigaba da rayuwata a gidan nan,sai kuma naga hakan ba zai taɓa yiwuwa ba,saboda duk daren daɗewa wata rana asirina zai tonu balle yanzu da Umar ya tabbatar min da cewa, sai ya nemo farin cikin sa a duk inda suke,dan haka shawarar da nayan ke kawai zansa akashe shi bakuma na buƙatar hannun ki a wannan karon,Ni da kaina zan sa su babe su kashe shi idan kuma zasuyi min kamar yadda sukayi min a baya to sai na kashe shi da kaina,ta faɗa tana miƙewa tsaye,Binta da wani irin kallo Bintu tayi,kana tace"kina ganin hakan shine dai-dai?kai tsaye ta bata amsa tare da ficewa daga ɗakin bata ƙara koda waiwayenta ba, "A wannan karon dai Bintu ta aro jarumtar mijinta,dan kuwa sam bata shiga tashin hankali akan furucin Nafisa na kashe mata mahaifi ba,zuciyar ta ta tsaida guri ɗaya da kuma naiman taimakon Allah,ta ɗaga wayar ta da tun shigowar ta ɗakin ta saka recording ta naɗe duk maganganun Anty Nafisa,wanda take fata su zame mata hujja ko anan gaba,yanzu babu abinda idanunta ke tun kara da hasasowa sai ɗakin nan zuciyar ta nan kawai take hanƙoro ta ƙagu da son ganin abinda ake aikatawa a cikin wannan ɗakin,da wan nan ƙwarin gwiwar ta tashi ta fara abinda ya kamata dan ida kyakykyawan nufin ta a yau. Tofa yau ake yin ta,muje nest page muji shin ko Bintu zatayi nasara a wan nan karon,shin daniyal zai ganowa ogah Abdallah gidan da su Hajjon suke,shin zargin Bintu zai tabbata akan inno kuwa,ina labarin Abigirl? Duk ku biyo NI domin dai anzo gun.... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 47 ``` Abdallah yana fita daga gidan officce suka wuce shida Yahya,bai daɗe da shiga officce ɗin ba sai ga Dady jafar, murmushi Abdallah yayi yace"Dady kafi Ni busy yanzu naga alama, tunda gashi har ina yin kwana biyu ban ganka ba!'wani irin murmushi Dady jafar yayi wanda yake nuni da tsan tsan farin cikin da yake ciki,farin cikin da yake ciki baya rasa nasaba da yadda yaga rayuwar Abdallah ta fara sauyawa kuma ga alamu sun fara nunawa suna samun nasara akan abinda suka saka gaba,cikin murmushin da yakasa gushewa akan kamilalliyar fuskar sa,yace"to ai naga ƴata Bintu ta fansheni tana kula min dakai yadda ya kamata,godiya mara adadi da yarinyar kirki!'ga mamakin sa sai yaga wani ɗan matashin murmushi ya baiyana akan fuskar Abdallah,a hankali ya lumshe idanun sa tare da jinginar da kansa a bayan kujerar,haka nan ya dinga jin maganar Sayyid na dawo masa daki daki,(taƙi bani dama saboda tana da matukar kamun kai da nutsuwa hakan ne yasa ko fuskar da zan yi mata wasan banza ban samu ba)kalaman da suka burgeshi sukayi masa daɗin sauraro ke nan daga bakin Sayyid, Dady jafar ne ya katse masa tunanin sa da cewa,to Malam Abdallah ina sauraron ka kayi min bayanin nasarar da muka samu tare da cigaban da aka kuma samu,ka kuma bani labarin da kace zai matuƙar bani mamaki!'ya ƙarasa maganar cikin ƙara dai daita zaman sa tare da taro nutsuwar sa kan Abdallah, "Cikin nutsuwa Abdallah ya gaya masa ko wacece bintu,cike da matsanancin mamaki haɗe da farin ciki,Dady ya taso ya rungume Abdallah tare da cewa,ikon Allah kaga ƘUDURAR ALLAH ko Abdallah, wato duk abinda Allah yaso tabbas sai ya faru, wannan abin akwai al ajabi amma ikon Allah ya wuce ga haka,!'Dady ya daɗe yana jin jina wannan ƙudura ta ubangi,yayin da soyayyar musulunci ta kuma kafuwa cikin ransa da zuciyar sa,ya kuma gasgata Allah da Manzon sa,ya kuma godewa Allah da ya kawo masa Abdallah cikin rayuwar sa da har ya zama silar zamowar sa cikin musulunci,hawaye ne ya shiga zubo masa saboda tsabar imani da tsoran Allah yace"Alhamdulillah alakulli halin, Allah na gode maka da wannan baiwa da rahama da kayi min Allah kashirya waɗanda suka ɓata, Allah ka ƙarawa Annabi daraja, Allah ka tsare zuciyoyin mu daga ruɗin duniya da ƙyaleƙyalenta ka kare mu daga faɗawa cin haram ka karemu daga cutar ƴan uwan mu,ka tsare idanuwan mu daga kallon abun da ba namu ba, Allah ya Ubangiji ka tonawa azzalumai asiri kasa suji kunya a duniya ka kuma sa su gane gaskiya ka shirya su idan masu shiryuwa ne!'amin Abdallah ya faɗa nima nace Amin Ya Allah,daga nan suka tattauna sauran maganganun da ya kamata Dady jafar ya sani,daga nan suka gangaro kan maganar Abigirl inda suka tsaida magana akan cewa zai sa aje ataho da ita,yayi wa ma aikacin su na can wanda yake kula da shige da ficen Abigirl waya ya sanar dashi zai sa azo ataho da ita,daga nan suka fara jiran zuwan sakamakon Samira. Kamma lallan guri ne me cike da nutsuwa, sam babu yawaitar jama a agurin saboda gurine na manyan mutane waɗan da suke buƙatar sirri dan hakane ba kowa ake bari ya shiga ba sai isu-isu manyan,Samira da Alhaji Sama'ila suna daga cikin mutanen dake zaune cikin gurin a kuma keɓantaccen guri,ga yanayin damuna da muke ciki wanda shine ya kuma ƙawata gurin da ƙamshin ƙasa dana furanni,zaune suke a kan ƙawatattun kujerun da suka zagaye gurin gaban su ɗan tebur ne wanda yake ɗauke da kayan sanyi kala-kala, Alhaji Sama'ila ya dubi Samira wadda ta nutsu ta kasa taɓa komai saboda ƙagauta da tayi taji abinda ta fi buƙatar ji a yanzu, murmushi yayi tare da cewa'haba My dear ki ɗan sha wani abu mana duk kinbi kin sawa kanki takura,ɗan murmushi tayi tare da ɗaukan drink ɗin da ya zuba mata,bata son ya fahimci wani abu atare da ita, shi yasa tayi saurin kawar da ɗokin dake kan fuskarta da yanayin ta,bata kuma ce masa komai akan abinda ya kawo su ba, sai da yagama jan ranta kana ya ɗan gyara zaman sa, tare da cewa, Samira zan fara da baki labarin asalin dangantakar dake tsakanin mutane huɗu,dan ki fahimci yadda abin yake tun farko, Alhaji Balarabe da Alhaji Nasir da kuma Alhaji Shamsi sai Alhaji Kabiru,asalin su aminai ne waɗan da suka haɗu ayawon fatauci,wato neman kudi,daga baya ne bayan kowa ya samu abinyi sai duk suka watse,amma abin Allah shine A lokaci ɗaya suka kuma haɗuwa da junan su,acikin garin Abuja ke nan,daga nan ne suka ɗora da amintar su wadda har tafi yadda suke a baya, dukkanin su babu wanda bai tara dukiya ba,sai dai amma arziƙin Alhaji Balarabe na daban ne acikin su,lokacin da suka fara ankara cewa Alhaji Balarabe yayi musu zarra,shine lokacin gina ESTATE, estate shine mafarin komai shi ya haddasa komai,tun daga lokacin ya zamana abokan nasa sun fara gane abinda yake zuciyar su na tsananin hassada da ɓakin ciki,abin yayi matuƙar tasiri a zuciyar su,amma basu taɓa nunawa Alhaji Balarabe ko mai ba hasalima nunawa suke sun fishi farin ciki da duk wani ci gaba da zai samu,tun daga lokacin suka fara haɗuwa su biyu suna mitin ɗin yadda zasu dinga cutar Alhaji Balarabe ta wajen kasuwan cin su,to amma dake shi zuciyar sa cike take da aminci da kuma kyautatawa talakawa,sai hakan bai girgiza komai a cikin dukiyar sa ba,duk kuwa da irin yadda mahaifina suke yagar dukiyar Alhaji Baba tamkar babu gobe,sai daga baya suka kuma samun karuwa saboda sun gano manufar su ɗaya da ɗan uwan Alhaji Baba wato Alhaji Hashir,dan haka sai abu ya kuma cin uban na baya ha inci suke masa batare da arziƙin sa na raguwa ba saima karuwa da yake samu Ako da yaushe,mutum ɗaya ne yasan abinda suke aikatawa shine Alhaji shamsi saboda shi babu hannun sa acikin duk wani abu da suke aikatawa Alhaji Baba,A lokacin yaso faɗawa Alhaji Baba abinda ke faruwa sai kuma yayi tunanin idan yayi hakan tabbas zasu iya cutar da shi da kuma Alhaji Baba,tunda ya fahimci cewa sunyi nisa acikin san duniyar su,idanun su ya rufe,tabbas idan yayi ƙoƙarin dakatar dasu ko ya sanar wa da Alhaji Baba zasu iya yin komai A yadda ya fahimcesu,sai kawai ya ƙyalesu tunda har yanzu babu abinda ya ragu ko ya samu tawaye daga dukiyar Alhaji Baba sai ma arziƙin nasa da yake kara haɓaka. A haka lokaci yaja suna kan wannan ƙadamin har zuwa yanzu da salon tafiyar ya sauya, Abin ya samune ta sanadin wani da ɗaɗɗen waje da Alhaji Baba ya saya domin ayi masa kamfanin robobi wajen kuma gini yake buƙata mai ƙarko,shi yasa kullum ta Allah sai Alhaji Baba yaje wajen, har aka gama ginin ma aikatar nan akazo kan hakar rijiyar da zata dinga bada ruwan amfani a cikin ma aikatar to anan ne ko mai ya faru a lokacin daga shi sai ɗan sa ABUBAKAR saboda yawanci tare suke zuwa irin wannan guraren,dama ance komai da sanadin sa sai kiga idan Allah yace da rabon ka to sai kiga sanadi ko mai ƙankantar sa ya kawo maka rabonka to hakan ce ta faru da Alhaji Baba ɗan abu ƙarami kuma mara tushe da dalili shine ya kawo masa wan nan rabon, indai ba rabo ba to haka kawai babban mutum zai zauna yana tona taɓo? haƙar rijiyar da aka fara batayi nisa ba wan nan ne dalilin da yasa Alhaji Baba tsugunawa yana taɓa ƙasar wajen yana ɗan tottonawa ramin badan wani abu ba sai dan nishaɗi,taɓo abin yayi a hannunsa hakan ne yasa ya ƙara tura hannun dan san ganin ko meye aaboda santsin da yaji abun ke dashi,abu kamar wasa sai gashi yana ta zaro abu wanda shi dai bai fahimci ko menene ba, Abubakar yace"Alhaji Baba me kake cirowa ne haka sai kajiwa kanka ciwo!'ya faɗa yana tsugunawa shima gaban ramin da bashi da zurfi, Alhaji Baba yace"ina tunanin dai wani babban dutsene kaga idan na ciro ai narage musu aiki ko? Abubakar ya kuma cewa'haba Alhaji duba kaga fa kana ciro abu da wahala kace zaka ragewa waɗanda zasu ciro shi da masarrafi aiki!' Alhaji Baba dai bai ce masa komai ba yaci gaba da tagagarin ciro mulmulen dutsen da ya kasa zaroshi saboda santsin sa,Abubakar babu yadda ya iya haka ya naɗe hannun rigar sa ya shiga taya dattijon nasa aikin da ya rikitowa kansa,kamar wasa Abubakar ya janyo wani ƙarfe dake can gefe irin na masu aikin haƙa,yace"Baba bari mu tona da wannan muragewa kanmu aikin da ka ɗauko mana!'Alhaji Baba yace"Abubakar bazaka gane ba jinake kamar wannan abun ba dutse bane saboda yana da santsi idan kayi la'kari da yadda yake saɓulewa daga hannun mu!'to bari na haƙo da wannan sai muga wane alherin ne yake kiranmu!'ya faɗa yana cusa abun dan zaƙulo abun daga cikin ƙasa,cikin sakanni saiga abun mai girma kamar ma dai dai ciyar boll,sai wani irin ƙyalli da sheƙi yake yana haske musu idanu,cikin ma daukakin mamaki Abubakar yace"Baba wan nan ai dimon ne,abu mafi ƙololuwar daraja!'sunkuyawa yayi da sauri ya ɗauke shi a hannun sa tare da nufar wajen da suka ajiye mota,cikin wani irin zafin nama yake takawa har ya isa motar ya buɗe ya saka dimon ɗin kana yace"Baba shigo mutafi da sauri!'shiga Alhaji Baba yayi tare da yiwa Abubakar ɗin wani irin kallo kana yace"bangane abinda kake nufi da wannan rawar jikin ba?sai da Abubakar ya tada motar ya ɗauki hanyar barin kamfanin kana ya ja ajiyar zuciya tare da cewa Alhaji Baba baka San akan wannan al'amarin yanzun nan sai a harbe mu ba? Ai yanzu ganin dimon ɗin nan tashin hankali ne a wajen mu dan duk wanda ya san dashi to wallahi sai an biyomu ankashe mu!'jijina kai Alhaji Baba yayi tare da cewa maganarka haka take kuma nima nasan da haka,da farko nayi tunanin farin cikin samuwar dimon ɗin agaremu ne ya hanaka nutsuwa, murmushi Abubakar yayi tare da cewa haba Baba kamar kamanta waye habunka kuma duk arziƙin da muke dashi sai na hangi wani,Alhaji Baba cikin tunanin yadda zasuyi da wannan dimon ɗin yace"ban mantaka ba habu,amma bana son samuwar wan nan abu ya sauyaka daga kan kyawawan halayyar ka dana riga na sanka da ita saboda shi wannan ɗin samuwar ƙololuwar arziƙine darajar sa ta wuce tunanin ka saboda wan nan dimon ɗin babban ne kuma kasan yanzu me shi a kullum shike neman daɗi!'baba ya akayi kayi saurin gane darajar dimon ɗin? Alhaji Baba yace"haba habu karfa kamanta kasuwan ci nane fa a baya kuma ido ba mudu ba ai yasan kima!ɗan murmushi yayi batare da ya iya cewa mahaifin nasa ko mai ba,sai can bayan sun kusa shiga estate Alhaji Baba ya dubi ɗan nasa yace"Habu bai kamata mu shiga estate batare da mun yanke shawarar yadda zamuyi da dimon ɗin nan ba!'Abubakar yace"nima abinda nake tunani ke nan amma ina ga ɓoyeshi zamuyi kar mu bari kowa yasan da shi idan ba haka ba kuwa tabbas duniya taji za a iya zuwa har gida a farmaki rayuwar mu akan sa!'Alhaji Babba ya jinjina kai tare da cewa amma kasan sai na gayawa ƴar Agadez ko!'naji Baba Amma kasan ta yadda zaka faɗa mata ba tare da ka bari wani yaji ba dan wan nan abun sirrin junan mune bayan zune lokacin bayyana shi ba,daga nan sukayiwa junan su raɗar inda zasu ɓoye dimon ɗin,babu wanda yasan inda suka ajiye shi sai su biyun nan bayan Allah da ya haccesu baki daya. Samira taja wani gauran numfashi tare da cewa to ku kuma ya akayi ku kasan da dimon ɗin? Alhaji Sama'ila yayi dariya tare da cewa,to ai wan nan ba Abune na mamaki ko wahala ba,yadda akayi mukasani kuwa shine ɗaya daga cikin mune yaji wato Nura ɗan Alhaji Hashir,alakacin da Alhaji ke faɗawa Hajiya Babba to shine yaji ya faɗa mana,amma ko ita Hajiya Babba bata san inda wan nan dimon yake ba,sai dai abinda ya ɗaure mana kai yadda akayi kwana kaɗan da faruwar al'amarin aka nemi Abubakar aka rasa tare da ɗan sa na biyu mai suna abdulraman,kuma tunda Aka ɗauke su har rana irin ta yau babu wanda yayi kukan rashin su ko cikiyar su,sai dai Alhaji Baba da ya fara cuta wadda har ta kaishi ga kwanciyar wasu watanni a asibiti!kinji abinda ya faru kuma yake kan faruwa kuma kinji akan abinda ake ta gumurzu akan sa!' Baƙaramar dauriya Samaira tayi ba gurin ƙoƙarin hana kukan dake idanun ta kufce mata ba,wani irin azababban tausayi ne ya cika mata ƙirji Allah sarki Alhaji Baba yana tare da maƙiyan sa bai sani ba,kalaman Alhaji Abubakar sun fi taɓa mata zuciya,wato abinda ya faɗa kuma ya guje musu tun A lokacin shine ya faru akan sa,cikin dabara ta goge hawayen da ya ɗan fara zubowa daga idanuwan ta,kana tace"gaskiya wannan al'amarin da ɗaure kai yake to waye ya ɓoye Abubakar?shi kuma ɗan nasa yana ina yanzu? Alhaji Sama'ila yace"ɗan sa dai babu labarin inda yake, shi kuma abubakar tunda muka rasa shi hankalin kowa a cikin mu ya tashi, ko da yaushe cikin nema da binciken inda yake muke ba tare da kowa ya sani ba,kuma har yau ba musamu damar sanin inda yake ba!'miƙewa tsaye yayi tare da cewa to Samira lokaci yayi bari na wuce kar suzo suna jirana!'tace"shike nan Alhaji sai munyi waya zanyi tunanin abin da ya dace!'yauwa sai mun haɗu daga haka ya fita daga gurin yana fita itama Samira ta wuce, officce ɗin Abdallah inda suke dakon jiranta.. Wannan karon Abdallah ya kasa daure abinda yake ji acikin zuciyar sa,dan haka kana kallon ƙwayar idanun sa zaka gane yanayin da yake ciki na azabar raɗaɗin zuciya,yana kuma tausayawa waɗanda suka aikata wannan mummunan kuskure ga mahaifinsa,miƙewa yayi ba tare da ya iya cewa dasu komai ba,ya tattara kayayyakin sa ya bar officce ɗin,Samira ta kalli Dady jafar tare da cewa, Dady anya kuwa babu wata matsala atare da Oga Abdallah naga yana yawan shiga tashin hankali akan wan nan aikin namu?shima kallonta yayi yace"baki san komai bane Samira,amma yau zan gaya miki abinda baki sani ba saboda amanarki da gaskiya da yadda kika tsaya mana akan aikin nan cikin nuna hazaƙarki da ƙwarewarki ta aiki,bai saurara da maganar da yake ba har sai da ya tabbatar wa da Samira cewa bashine mahaifin Abdallah ba wan nan mutumin da aka sace shine mahaifin sa, Wata irin zabura Samira tayi cikin matuƙar mamaki da tausayi har ta ma rasa abinda zata ce sai faman bin ƙofar da Abdallah yabi take bi da kallo baki sake da wasu tarin ƙwalla da suka cika idanunta,komawa tayi ta zauna cikin karaya da Al'amarin tace"innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un,astagfurullahi wa'atubu ilaihi, Allah alhakim Allah abin tsoro mugun mutum abin tsoro, tausayin Abdallah ne cike taf a ranta,sai ta kuma jin karsashin ci gaba da taimakawa rayuwar sa da dukkan ƙarfin ta da alajihunta da zuciyar ta. Duk da cewa tana ɗokin dawowar sa dan sanar dashi babban al'amarin da ya ɓullo daga gurin Nafisa amma tafi ɗokanta da lokacin da take hasashe dan ida nufinta,tayi ƙoƙarin danne duk wani al'amari dake cikin zuciyar ta,tayi kuma ƙoƙarin sakewa Inno tunda har yanzu hasashe takeyi bata tabbatar da abinda idanun ta da zuciyar ta ke gani ba, Al'amarin Anty Nafisa ma ta ajiye shi gefe,sai dai lokaci lokaci tana jin faɗuwar gaba idan ta tuna da mugun nufin Nafisar akan mahaifinta,amma kuma tayi matuƙar dauriya ta miƙawa Allah assamadu dukan lamuran ta tasan cewa rayuwar mahaifinta ba a hannun Anty Nafisa yake ba,dan haka tayi yaƙini azuciyar ta cewa bata isa ta katse rayuwar Abba Umar ba sai dai idan Allah ya kawo lokacin sa,da wan nan ƙarfin gwiwar na tasirin imani ga Allah Bintu take tsaye cikin aminci tana gabatar da al'amuran ta na yau da kullum, Lokacin da ya shigo falon inno babu kowa hakan ne yasa Bintu bata san da dawowar sa ba,amma kuma ga mamakin ta sai taji kamar zuciyar ta na gaya mata cewa Abdallah na kusa da ita,abin ya bata mamakin jin yanayin da ta saba ji aduk lokacin da yake gab da ita ya mamayeta,cikin yammacin nan tana tunanin mai zai dawo da Abdallah gida?sauri tayi ta zura doguwar hijiabi akan ƙaramin siket ɗin da ta saka bayan fitowarta wa daga wanka,fitowa tayi ta nufi part ɗin sa,kai tsaye duk da cewa bata tunanin shi ɗin ne ya dawo,babu kowa a falon dan haka ta wuce bedroom ɗin sa kai tsaye,tana shiga ta ganshi kwance ƙasan carpet babu abinda ya cire hatta takalmin sa yan ajikin ƙafafun sa,da cikin sanyin jiki da wata irin fargaba ta ƙaraso inda yake ta tsuguna,kana tace"baka da lafiya?shuru bai bata amsa ba ga idanun sa alumshe,Yahh Abdallah ta faɗa cikin wata irin murya mai matukar taushi da kwanciya,wanda hakan ya fito da wani irin amo mai tada tsikar jiki, Abdallah bai san ya akayi ya buɗe idanun sa ba,saboda yadda Muryar tayi matuƙar tasiri a zuciyar sa da gangar jikin sa,ganin sa zaune ya zuba mata idon sa masu sakata jin bacci yasa ta ɗan tura baki tana cewa yo hakan nan sai atayarwa da mutum hankali,ta faɗa cikin ɗan murguɗa bakin,tana farfari da fararen idanun ta,bata gama faɗar abinda ke ranta ba ta baƙumci bakin Oga Abdallah cikin nata wanda hakan ne ya hana ta ƙara sa faɗar abinda ke ranta, Zaro manyan idanun ta tayi tana mamakin wannan irin ta adi na ogan nata,ture shi ta fara ƙoƙarin yi amma sai taji ya tattarota jikinsa tare da yaye hijabin dake jikinta,zaro idanun ta kuma yi wanda shi Abdallah ma bai san tanayi ba,harshen sa yana sarƙafe da nata yana faman tsotse shi kamar wata sweet,hannu tasa tana dan ture shi dan kar ya yaye mata hijabin bayan shine kadai sitturar data suturce jikinta dashi bayaga dan guntun siket ɗin da tasaka,bata dawo daga tunanin yadda zata yi ba taji Abdallah yayi nasarar zare hijabin,runtse idanunta tayi lokacin da taji hannun sa nayawo bisa sassan jikinta,har yanzu kuma bakin sa yana maƙale da nata,ɗan cire bakin sa yayi anata yana goga fuskar sa a ƙirjinta,cikin kasalar da yake saukar mata tace"wai maye haka Ni ka rabu dani bana so nifa ba ƴar,,,,maganar ta katse mata lokacin da taji sanyin bakinsa bisa nn ta bata san sanda ta saki wani ɗan ƙaramin sauti ba oshhhhh,wai maye haka Ni karabu dani wayyo fafina ka taimaka zai cire min ƙirjina,dan ɗago fuskar sa yayi cikin ɗage mata gira yace"Bint kibar ni na rama mana,ke idan kina cikin damuwa ba ƙirjina kike shigewa kina goga fuskar ki ba,to Ni dan me yasa bazaki barni na rage damuwata da raɗaɗin dake cikin zuciyata ba?ki barni mana kinji Bint ya fada cikin wata irin muryar da yasa gaba ɗaya tsigogin jikin Bintu miƙewa,maida kansa yayi cikin wuyanta yana shaƙar dadda ɗan ƙamshin ta.. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 48 ``` Take nan Bintu taji duk jikinta ya mutu,ɗan zunɓura bakin ta kumayi cikin yanayin da take ciki tace" Ni yaushe nayi maka haka?kuma Ni ai ba haka nake maka ba!'cikin mutuwar jiki da wata irin kasala yace"ramuwar gayya Bint ita nakeyi idan kuma kika ƙara ambatar abinda nake miki da iskanci sai na cire bakin gaba ɗaya kowa sai ya huta!'ya faɗa cikin ɗan kama laɓɓan ta da haƙorin shi ya ciza a hankali,amma dake Bintu tana kan sharafin ta na taɓara,sai kawai tasa masa kuka wai ya cijeta,shine ka cijeni bayan Ni ban taɓa cizan kaba!'ya wani lumshe idanun sa tare da miƙa mata lip ɗin sa cikin wata irin kasalalliyar murya yace"Bint ram,,,,kafin ya ƙarasa maganar da zai faɗa tuni Bintu tayi caraf da lip ɗin sa a cikin bakinta daga ramuwa saiga Bintu ta koma tsotsewa bawan Allah harshe kamar ta samu alewa ko da ike ita a wajen ta daɗin bakin Abdallah yafi daɗin alewa, Abdallah har cikin jinin jikin sa da ƙwaƙwalwar kansa yake jin tsotsar da Bintu kewa bakin sa,kiran sallar da aka ƙwala cikin masallacin ESTATE shine ya dawo da su cikin hankalin su,zame jikin ta tayi daga nashi,shi kuma Abdallah so yake yaga idanun maras kunyar da take cewa ana iskanci, cikin wani irin farin ciki da ya cika zuciyar sa ya leƙa fuskar ta da take ƙasa,yace"Bint wan nan fa abinda kikayi min iskan,,,,da sauri ta rufe masa baki da hannun ta idanun ta cike taf da ƙwalla ji take kamar ta zane kanta saboda ta kaici,tace"dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba!'ta faɗa tana son fashewa da kuka,ɗaga ta yayi suka tashi tsaye,kana yace"gaskiya bazan haƙura ba,daga rama cizo sai kawai ki cinye min baki!' ya faɗa cikin rangwaɗar da kai kamar wanda akaci zali,cire ta yayi daga jikin shi tare da cewa bari idan nayi sallah zan zo sai ki faɗa min abinda ke bakin ki,amma kiyi sallah anan kar kije ko ina kinji ko!'gyaɗa kanta tayi tana ci gaba da ƙunshe kanta da tafin hannun ta,wucewa yayi ya shige bayi jim kaɗan ya fito cikin sauri saboda jin ana ƙoƙarin tada sallah,yana fita itama ta shige ta ɗauro alwalar ta tada sallar a nan cikin ɗakin, Kamar yadda ya saba saida ya gabatar da sallar isha'i kana ya nufo part ɗin su,a kan hanyar sa ta shiga ne daniyal ya kira shi a waya nan yake sanar masa cewa ya gano gidan da su Hajjo suke kuma bai dawo ba sai da yaga Abba Umar shima ya taho, Abdallah yace"yauwa daniyal idan Allah ya kaimu gobe zaka rakani muje san nan ina so kadinga kular min da Abba Umar bana so wani abu ya same shi!'daniyal yace"don worry oga i can take care!'daga haka suka katse kiran, Duk da bata da tabbacin zaici abinci amma hakan bai hana ta jera masa kayan abincin sa,duk da dai ba wani me nauyi bane dan tuwon semo tayi masa da haɗaɗɗiyar miyar kuɓewa wadda taji ragargajejjen naman kaza sai zabga ƙamshi take, Bintu dai aranta take rayawar ta gaji da waɗan nan girkunan dole ne idan ta samu nutsuwa taje koyan girkin ƴan gayu koda na kwanaki ne,wai dan ma shi Abdallah baya gajiya da cin nau'ikan abincin mu na gargajiya,a nutse ta kammala ko mai amma fa ta ƙagu ya dawo sabo da bata son Shirin ta ya ɓaci, a cikin wannan rana take son aikata ƙudurin ta,sallamar sa ce ta katse mata tunanin ta,tana ganin sa kuwa abinda ya faru awa biyu da suka wuce ya shiga dawo mata,cikin takaici da kunya ta sunkuyar da kanta,ƙarasowa yayi dinnin ɗin yaja kujera ya zauna,bai tanka mata ba,ya fara ƙoƙarin savin ɗin kansa,tana kallo ya saka tuwon sa ya fara ci, amma bata ce masa ba kuma ta kasa motsawa daga inda take tsaye,ɗan satar kallonta yayi yasan abinda ya hanata sakewa,amma yanzu zaiyi maganinta,kasan cewar ba wani tazara bace a tsakanin su ba,hakan yasa bai sha wahalar kamo hannun ta ba, Bintu jinta tayi kawai asaman cinyar sa,zabura tayi zata tashi,ya riƙeta cikin haɗa fuska yace"malama saurara ba abinda zanyi miki cizona kawai zan rama!'zaro manyan idanunta tayi bakinta na rawa tace"to ai ban cijeka ba!' amma aikin cinye min baki!'ya faɗa yana mai tsare ta da manyan idanun sa masu maiƙo tamkar an ɗiga musu man gyaɗa,ɓoye fuskar ta tayi a ƙirjinsa tana jin tamkar ƙasa ta buɗe ta shige ciki,ci gaba yayi da cin abincin sa,sai da ya gama kana yace"kinci abinci?girgiza masa kai tayi,tashi yayi da ita ajikin sa kana ya maida ita inda ya tashi ya zaunar yace"maza kici yanzun nan ki sameni a ɗaki muyi magana!'yasan idan ya zauna bazata iya sakewa ba shiyasa yayi mata haka,cikin sauri tace"bazan iya cin komai ba idan har banyi abinda zuciyata ke Umar tata ba a yau!'zuba mata ido yayi na sakanni kana yace"nace kici abinci ko!'ganin yadda ya tsatstsare ta da mahukuntan idanun sa yasa ta shiga tura tuwon da ya saka mata batare da tana gane ɗanɗanon sa abakinta ba,bai matsaba sai da yaga cewa tabbas ta ƙoshi kana ya janyo hannun ta suka koma ɗakinsa, brosh yaje yayi kana ita ma yasa ta tashiga tayi,yana sane da yadda yaga duk ta ruɗe bata yin komai cikin nutsuwa sai duban lokaci take yi,zama yayi abakin gadon yace"itama ta zauna,a ɗarare ta zauna,kafin yace komai ta miƙa masa wayarta tare da danno masa recording ɗin Muryar Nafisa wadda ta fito tar- tar tana bawa Bintu labarin tsiyar da ta shuka,bai tanka ba kuma bai motsa ba sai idanun sa da suke kan wayar Bintu tamkar wanda yake ganin Nafisa azahiri. "Recording ɗin yana zuwa ƙarshe Abdallah ya kashe wayar tare da miƙewa tsaye goya hannayen sa yayi yana ɗan zaga filin ɗakin,a fili yace"hakan yana nufin ke nan su Fafi suna waje ɗaya da Abbana,mutum ɗaya ne duk ya sace su?idan hakane meye hurumin su acikin wannan al,amarin?munji manufar Nafisa sai kuma manufar baƙin azzzlumin!'sanadin juya bayan da yayi ne yasa baiji fitar Bintu ba sai rufe ƙofar ta,cikin zafin nama yabi bayanta wanda tana gab da fita daga falon ne ya cimma ta,cikin zafin naman da bai san yana dashi ba ya kamota, cikin wani irin yanayin damuwa yace"Bint Ina zakije?me kike Shirin aikatawa ba tare da kin sanar dani ba?cikin wani irin azababban fushi da ƙwarin gwiwar da take ji,tace"t wan can ɗakin zani kuma a yau zan fiddo abinda aka ɓoye acikin sa ko akeyi aciki,tun tuni mafarki na ya nuna min cewa wan nan ranar itace ranar da zan baiyana abinda ke cikin ɗakin nan,kuma Allah ya bani ikon ganowa wan nan ɗakin shine zai kawo mana ƙarshen wannan mugun mutumin,Yahh Abdallah dan Allah kabarni naje inaji ajiki na cewa a kwai Babban Al'amarin dake ƙunshe cikin ɗakin nan!'kallon agogo tayi cikin tashin hankali tace"lokacin zai wuce,sha biyu ta kusa ƙara sawa bayan kuma shine lokacin da jikina da zuciya ta suke bani cewa Allah zai bani nasara,a mafarkina angaya min cewa da zarar biyu tayi banyi abinda ya dace ba komai zai iya faruwa saboda a wannan lokaci ne mai dakin yake fitowa dan aikata mugun nufin sa!'tana kawowa nan a maganar ta ta fita da wani irin sauri, Abdallah bashi da zaɓin da ya wuce yabi ta tunda taƙi sauraren sa ma balle yasamu abin cewa,addu a ce dai bata yankewa daga bakin sa da zuciyar sa. A cikin wannan daren kuma tuni ƴan aiken Abdallah sun cika aiki sun sanƙamo masa Abigirl wadda take ta ihun neman dauki,duk da cewa Muryarta bata fita saboda manne bakinta da sukayi da salatif,tun tana iyawa har ƙarfin ta ya ƙare ta haƙura, kasan cewar basu taho da wuri bane yasa suka kai har wannan lokaci na shabiyu da min tuna na daren ranar,samuyal ne ya dubi Safwan cikin gurɓatacciyar Hausar sa yace"Safwan baka lura da moto ɗin dake binmu tun fitowar mu daga cikin gari ba?ya faɗa yana mai leƙa bayan sa,Safwan dake gaba kusa da drever shima saita madubi yayi dan san gasgata maganar samuyal ɗin,sani dake tuƙi yace"tabbas maganar samuyal haka take ashe bani kaɗai na luraba, kawai nayi shuru ne saboda nayi tunanin ko hanya ce ta haɗamu!'Samuyar yace"nima daga farko abinda nayi tunani ke nan amma yanzu na fara zargin wani abu saboda da hanya ce ta haɗa mu to tabbas zasu iya wuce mu ko kuma mu muyi musu nisa!'shuru su kayi gaba ɗayan su kowa da abinda yake rayawa a zuciyar sa,sai daga can Safwan yace"ko Oga Abdallah zamu kira mu sanar dashi?sani yayi saurin cewa a'a ba haka za ayi ba bai kamata mu katse masa baccin sa ba,dabara zamuyi yadda zamu gane idan ma mu ɗin suke bi tunda kunga yanzu bamu tabbatar ba!'Samuwar yace"good i dea,hakan ne yasa suka ɗauke hanya suka canja daga hanyar da suke kai dama sun zo dai dai titin da zasu hau su shigo Abuja. Yanzu kam sun tabbatar da abinda suke zargi dan kuwa motar su ta kuma biyowa tare da ƙara gudu daga dukkanin alamu dai yanzu so suke su cimmasu, Safwan yace"sani ƙara gudu so suke su tare mu da alama dai wan nan abar dake tare damu suke son karɓa!' yana nufin Abigirl wai,cikin wani irin gudu motar ta ci gaba da biyo su wanda ga dukkanin alamu ma kamar so suke su bige motar su Safwan ɗin,ganin haka yasa hankalin Samuyal ya tashi,cewa yake kashemu suke sonyi!' sani yace ku kwantar da hankalin ku insha Allah muna tare da Allah kuma zai fidda mu ƙarshen sune yazo, ga dukkanin alamu Abigirl ta san sirrin su shi yasa suke son kasheta ganin bazasu sameta bane yasa zasu kashemu baki ɗaya!' A can ɓangaren su Bintu kuwa lokacin da Abdallah ya biyota har tayi masa nisa hakan ne yasa ya haɗa da gudu ya cimmata, ESTATE ɗin yayi shuru bakajin motsin komai saina iskar damunar da take kaɗawa A hankali,atare suka shiga wajen da taimakon addu'a A bakunan su,har suka je bakin ƙofar basu daina ambaton Allah ba,cikin ƙarfin gwiwa Bintu tasa hannu akan ƙofar tana ɗan turawa,cikin raɗa Abdallah yace"Bint ya zamuyi mu buɗe ƙofar nan duba ko wajen ɗan mukulli babu!'Yahh Abdallah angaya min yadda zamuyi ƙofar ta buɗu,ta tsafi ce ƙofar dan haka karya tasirin ta addu'a!'ta faɗa tana ƙara ɗora ɗaya hannun nata akan ƙofar,matsowa yayi shima tare da yin yadda tayi rufe idanun ta tayi shima sai yayi hakan, addu'oi suka fara karantawa a fili,cikin ƙudurar Allah saiga ƙofar na yin ƙasa tamkar wadda ake janye ta ta cikin ƙasa,bin ta sukayi da ido har ta nutse cikin ƙasan gurin,kallon juna sukayi alamu yayi mata da su shiga, cikin tsananta addu'a da miƙa lamura ga Ubangijin talikai suka afka ɗakin wanda yake dun ɗum da duhu baka iya ganin ko tafin hannun ka,da sauri Abdallah ya riƙo Bintu bakin su ya kasa daina ambaton Allah. Sosai fa mutanen ke son tura motar su Samuyal cikin rami,amma hakan ya gagara dan dukkan su addu'oi ne ɗauke abakin su, idan kacire Samuyal da ba Musulmi ba,shi kam amatuƙar ruɗe yake dan baya son mutuwa ko kaɗan,ji yayi kawai bakin sa ya kama innalihin da su Safwan suke ta ambata cikin ɗan ɗaga sauti yake ƙara nanata ta akan harshen sa,tun yana faɗa ba daidai ba har ya dawo yana faɗa dai dai,sai ya zamana duk addu'oin da suka kama marasa tsauri shima yana iya kamawa kamar allahumma ajirni filmusi bati wakalifni khairan minha, da la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin,lahaula da A uzu bikalimatullahittammati min sharril ma kalaƙa,cikin ƙudura ta ubangi da kiyaye bayin sa da suka tsaya gareshi suka nemi taimakon sa,a maimakon mutanen su sami na sarar jefa su Safwan sai kawai burki ya ƙwace wa drevern waccan motar kafin ƙiftawar ido sun afka dogon ramin da suke san jefa su Samuyal,ji kake bam motar ta tashi da wuta. Wata irin doguwar ajiyar zuciya suka sauke tare da faɗin Alhamdulillah!' a fili sai shima Samuyal ya kuma faɗa, sai lokacin suka samu nutsuwar tunawa da abinda Samuyal yayi, shi kuwa Samuyal tuni ya tafi duniyar tunanin ƙarfin mulki irin na Ubangijin sammai da ƙassai,ganin abun yake tamkar sihiri wato waɗan nan addu'oin da sukayi sune suka tseratar dasu daga hannun waɗan nan mugayen,suma dai su Safwan basu ce masa komai ba amma suna fata da buri wan nan abin da ya faru yanzu ya zama izina da kuma sanadin da Samuyal zai gane gaskiya,ita kuwa Abigirl saboda abin da suka shaƙa mata bata san duk wan nan abin ya faru ba, Wayyo Yahh Abdallah duhu babu haske ya zamuyi yanzu ta ina zamuga makunnin fitila?Bint ki nutsu Mana Ina ƙwarin gwiwar taki ya tafi?bakiga Allah yabamu nasarar shigowa ɗakin ba?kuma kina gani saboda Allah yana tare damu bamu sami wata matsala ba,kuma kin san abinda yake faruwa dake duk lokacin da kika zo wajen amma a wannan lokaci dake nasarar tana garemu babu abinda ya faru, kuma zamu fita lafiya insha Allah!'jikin sa ya shiga lalubawa,cikin ikon Allah kuwa sai gashi ya zaro karamar wayar Bintu,cikin farin ciki yace"Alhamdulillah,tare da kunna toch ɗin wayar. Kamar an min tsine shi haka ya farka, cikin matuƙar tashin hankali da kiɗima ya lalubo wayar sa, wajen kira ya shiga ya lalubo nombar dayake son kira,yadda ya saurara yake jiran aɗauki wayar haka yake sauraren bugun zuciyar sa,har wayar tayi ta katse ba'a ɗauka ba,kira yasake yi nan ma dai abu ɗaya ne No respond,zirga zirga ya shiga yi cikin ɗakin yana cigaba da kiran wayar,can bayan wasu ƴan mintuna sai aka ɗaga wayar,ba tare da ya saurara yaji mai magana ba ya hau surfa ruwan ashar da masifa,dan wulaƙan ci kunaji ina kiranku amma kunyi biris dani,shin kun ɗauko Abigirl ɗin kun kasheta? yallaɓai ba masu wayar bane ga yanzu aka tsinci wayar abakin ramin hanyar da ta tsaga ta shigo Abuja da Kano,ansami masu motar da motar sun faɗa ramin nan sunƙune gaba ɗayansu babu wanda ya tsira!'cikin rawar baki yace"motar ɗaya ce ko biyu?me maganar yace"a'a mota ɗaya ce"kashe wayar yayi tare da wulla ta gefe,ya shiga yarfa hannuwa,shike nan yanzu Abigirl tayi nasarar kubuta daga gareni yanzu wannan shegen yaron sai ya samu nasarar ganin bayana?tabbas na kaɗe idan har ya samu kan Abigirl yanzu me ya kamata nayi ke nan?ya tambayi kansa,cikin sauri yace"ya kamata naga shugaba domin yasamomin mafita,na rasa yadda zanyi da Abigirl ita ba musulma ba amma sai taurin rai ko me yasa na kasa kashe ta ta hanyar tsafi?ya kuma tambayar kansa kamar wani zararre,wani abu naga yayi tare da faɗin wasu ƙalasimai irin na waɗan da suka riga suka bata suka bar turbar gaskiya,cikin ƙanƙanin lokaci saiga shugaba azukyi ya bayyana agaban sa,durƙusawa yayi cikin magiya da tashin hankali yace"shugaba ka taimakamin duk wata dabara ta fara ƙwace min shegun mutanen nan sun tsira daga tarkon da na ɗana musu,yanzu kuma na rasa fafita, ka taimakamin na sace Abigirl daga hannun yaron nan!'shugaba Ezukyi yace"nanu ka sauka daga kan hanya ne shiyasa al'amuran suke ta zuwan maka a haka,amma bari na gwada na gani!'wani siddabaru yayi saiga su Safwan acikin mota suna gab da shigowa cikin gari,hannun sa ya miƙa dan ɗauko Abigirl daga cikin motar amma kafin ƙigtawar ido ya dawo da hannun da wani irin sauri yana yarfa shi ga dukkanin alamu wani abu ne ya samu hannun,cikin zafin da yakeji ajikin hannun yace"nanu a kwai matsala fa dan kuwa bazan iya taɓa Abigirl ba,kana ganin yadda suke ta addu'a ga kuma karatu da suka saka gaskiya bazan iya ba,sai dai mu canja wata hanyar!'nanu yace"to tunda hakane shugaba mu rufe mata baki mana,kaga idan sunje babu bakin da zata iya faɗar ko mai a kai na!'shugaba Ezukyi yace bari mu gwada wannan,saida yayi siddabarun sa na tsawon minti ɗaya kana ya dubi nanu da ya zuba masa ido yace"munyi nasarar wan nan, amma dai kasan duk sihirin da kayi yana zaune ne karkashin ikon wannan ɗakin dan haka ka daɗa kiyayewa!'ɓat ya ɓace ba tare da Allah ya bashi ikon gano matsalar da nanu yake ciki ba, ta shiga ɗakin nan da su Abdallah su kayi,sai alokacin hankalin nanu ya kwanta yasan kafin su Abdallah su ankara zai kashe Abigirl shi ke nan bakin sa ALAIKUM, Zuba masa ido Sarah tayi cikin tausayin mijin nata,kana ta ɗan numfasa tace"dan Allah yaya Habibu ka tashi daga kan sallayar nan kazo mu kwanta haka tun ɗazu fa kake abu ɗaya ai rai ma yana buƙatar hutu ga cofee ɗin na kawo maka,kazo ka ɗan sha ko zaka samu nutsuwa!'wani irin kallo yayi mata, kana yace"Sarah me kike faɗa hakane dama ana gajiya da ibada?to idan ma ana gajiya Ni dai bazan gaji da roƙon Allah da kai masa kukana ba,kuma kike batun nutsuwa ai tunda na ɗora goshina aƙasan gurin nan na miƙa lamurana gurin Allah to nutsuwa ta gama samuwa a gareni,dan haka kar ki kuma hana Ni yin ibadata,tunda ke bazaki yi ba!'ya faɗa cikin nuna ɓacin ransa da abinda tayi ɗin,cikin kwantar da murya tace"kayi haƙuri ba manufata ke nan ba ya za ai na hana ka ganawa da ubangiji amma kayi haƙuri insha Allah bazan sake ba!'ɗan murmushi yayi tare da cewa yauwa ko kefa kawai ki tayani da addu'a Allah ya kawo mana ƙarshen matsalolin mu!'tace" insha Allah yaya Habib!'daga nan suka koma suka kwanta kowa da abinda yake saƙawa azuciyar sa. Wani irin rawa jikin Bintu ya shiga yi cikin kiɗima da tashin hankali tace"Oga Yahh Abdallah kana ganin abinda nake gani? innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un!'shine abinda Abdallah ya shiga furtawa cikin nasa tashin hankalin,ɗakine wanda aka tara kayan tsafi dana siddabaru kala kala ko mai kagani da ɗigon ja ajikin sa,sassan jikin mutane kuwa yafi hamsin wasu an tsaface su a haka wasu kuma sun mutu sai gangar jikin ce ke aiki, idanuwan Bintu ne suka shiga ƙoƙarin rufewa saboda tsabar tashin hankali,da sauri Abdallah ya tarota yana goge mata fuska tare da cewa Bint ki tashi karki suma da akwai matsala zaman mu bazai yiwu agurin nan ba ki faɗa abinda ya kamata muyi yanzu,kamar wanda ya watsa mata ruwa haka tayi saurin buɗe idanunta saboda tunawa da tayi da wata ƙofa acikin ɗakin wadda aka bata tabbacin sai ta buɗe ta,saidai duk iya hangen ta bata ga wata ƙofa ba,cikin tashin hankali tace"Yah Abdallah mu duba a kwai wata ƙofa da matar tace"mu duba kuma Ni bangan ta ba anan!'cikin sauri yaja hannunta tare da cewa muduba sosai!'tace"sakeni na duba wani ɓangaren kaima kaduba wani wajen!'bint mu duba tare kawai bazan yadda ki keɓe ke kaɗai acikin wannan lokacin ba!'da sauri suka shiga tutture ƙwalangwal ɗin da suka yiwa ɗakin ƙawanya tare da cire duk wani abu da suka ci karo dashi ajikin bangon ɗakin,ɓanna sukeyi fa bata wasa ba,gaba ɗaya sun har gitsa ɗakin baka jin sautin komai saina karar zubewar abubuwa da fashewar su,kafin wani ɗan lokaci ɗakin ya turnuƙe da wani irin hayaƙi me shiga tsakiyar kai harda wani yaji me ƙarni da saka amai,cikin fitar da numfashi da ƙyar Abdallah yace"Bint zo mu fita kar dakin ya ƙone damu ko ki samu matsala da wannan hayaƙin!'itama numfashin take fitar wa daƙyar tare dacewa bazan bar ɗakin nan ba sai na ɗauko abinda aka ɓoye a ciki!'me akaɓoye aciki bayan kina ganin abubuwan da suke ciki!'Ya Abdallah bazaka gane ba kawai karabu dani sai na ɗauko shi koda bazan same shi a raye ba!'waye ne haka?bata bashi amsa ba saboda ganin wani waje daga can kusurwar ɗakin anyi shedar zanen ƙofa amma babu ƙofar,gurin ta tunkara gadan gadan tare da saka hannunta a tunanin ta bangone saboda babu wata alama da zata nuna maka ba bango ne gaba ɗaya ba,ashe ƙoface akayi mata kalar fentin san nan kuma ashafe take babu tudu, kamar yadda bangon yake haka take sak sai wannan shatin da Bintu ta gani, cikin sauri suka kalli juna da Abdallah,kana kuma atare sukayi Bismillah suka tura ƙofar saiga ƙofa ta buɗe. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 49 ``` Kamar an tsunkule shi haka ya tashi afirgice,zoban sa da yake ta faman wuta ya kalla abin baƙaramin ɗaure masa kai yayi ba,saboda tunda yake da zoban baitaba nuna masa wan nan alamar ba,da sauri ya tashi tsaye Saboda tunawar da yayi duk sanda zoben yayi wuta shike nuna masa cewar da akwai matsala,siddabarun sa yayi dan ya ɓullacikin ɗakin ba tare da yayi tafiya ba kamar yadda ya saba a duk sanda yaso,sai dai ga mamakin sa abin yaƙi yiwuwa hakan ne ya kuma tabbatar masa cewa da akwai babbar matsala,cikin sauri ya fita daga ɗakin nasa ya wuce falon sa ya fita duk cikin tashin hankali da fargaba,duk takun da zaiyi bugun zuciyar sa ƙaruwa yake. Ihu Bintu ta saka tare da kanƙame Abdallah cikin wata irin kiɗima da rawar jiki,riƙeta yayi ajikin sa tare da zubawa daskarerren mutumin ido, lulluɓe yake cikin wani abu kamar yana, babu abinda ke motsi ajikin sa sai ƙirjin sa dake nuna alamun bugun zuciya,ƙirjin Abdallah shima babu abin da yakeyi sai bugu dan har yanzu bai fuskan ci waye a cikin wannan dabai bayin ba amma dai tabbas ganin mutumin ya tsunkar mai da zuciya,Bintu ce tayi saurin dawowa cikin hankalinta lokacin da kunnuwan ta suka fara jiyo mata alamun taku ta can wajen dakin saboda tagar da ke kusa da ita wadda take agarƙame, jijjiga Abdallah ta shiga yi cikin tashin hankali tace"wayyo Yahh Abdallah lokaci yayi yana nan tahowa mu ɗauke shi mu gudu!'yace"Bint sai dai mu mu nemi gurin tsira tunda kinga bashi kadai bane,kuma idan mun ɗauke shi bamu san inda zamu kaishi ba!'cikin tashin hankali da kukan da ya kufce mata tace"Yah Abdallah saboda shi nazo saboda na fita dashi nazo idan ban fita dashi daga gurin nan ba to babu amfanin da zuwa dakin nan yayi mana!'shi dai har yanzu Abdallah bai fahimci abinda Bint take nufi ba,amma dai zaiyi ƙoƙarin yin abinda take so,kallon ƙofar tayi cikin wani irin tashin hankali da ketowar wata zazzafar zufa tace"musan abin yi Yahh Abdallah da akwai matsala idan mutumin nan ya gan mu fa!' Tun daga bakin ƙofar yasan cewa yau akwai babban tashin hankali,cikin matsanancin tsoron da ya fara fin ƙarfin zuciyar shi da gangar jikin sa ya faɗa cikin ɗakin, wayyo Ni kam Fatima saida na gwammace banzo wan nan tsurkun ba,tashin hankalin da nagani ya wuce abin misali,samu nayi na kuma raɓewa ajikin ƙofar ɗakin da su Bintu suke ciki kamar wata ƙadangaruwa,zuciyata kuwa tafi tasu bugawa dan Ni dai banga fitowar su daga ɗakin ba,wata irin gigitacciyar ƙara ce ta dawo dani hankalina,meye haka?waye yayi min wannan ɓannar?wani irin ƙara yake wadda take nuni da mugun tashin hankalin da yake ciki,hargitsa gurin yake yana wani irin juyi aɗakin,waye yake son ganin karshena?baku isa ba ko su waye kunyi kaɗan ku sabauta min burina na shekaru sama da talatin dole sai na cika burina,ɗakin ya nufa gadan gadan dan san tabbatar da ko ajiyar sa tana nan. Numfashin Bintu kaɗan ne bai zuƙe gaba ɗaya ba dan dai Allah yayi da sauran shan ruwan ta agaba amma mugun tsoro da firgicin da tashiga tsaf zai iya sawa ta haɗiyi zuciya,shi kan sa Abdallah ya shiga cikin firgici amma fa shi ba dan Bintu ba tabbas sai ya ga fuskar wan nan baƙin azzzlumin, cikin rawar baki da jiki Bintu tace"ga..g..gashi nan zai shigo!'ta faɗa tana wani irin jan numfashi kamar ta shiɗe,kamar daga sama taji Muryar matar da take zuwan mata amafarki wadda a yanzu ta gane ba Aljana ce kuma ba mafarki take ba, gani kawai take kamar amafarkin, tana mata magana, kin kakkausar murya tace"Bintu ki kwantar da hankalin ki insha Allah nasara na garemu ki nutsu kiji abinda zan gaya miki!'cikin sauri ta gyada kai duk da cewa ita bata ganin matar,matar ko nace aljanar taci gaba da cewa zan riƙe shi a bakin ƙofar nan amma na wasu ƴan daƙiƙa ne,kuyi gaggawar fita da mutumin nan ku kai shi wani ke ɓan taccen guri!' cikin tashin hankali Bintu tace"kina zan cen fita ta yaya zamu fita bayan yana bakin ƙofar,aljanar tace"zan riƙe ƙofar ne ta yadda zai ja lokaci bai buɗe ta ba,kuma dama ayanzu sihirin sa ba zaiyi tasiri ba tunda kun riga kunga sirrin sa,ɗan abinda yake dashi kuma bazai masa amfani yanzu ba,Bintu ta kuma cewa har yanzu dai baki gaya min abinda nake son ji ba,shin ta ina zamu fita?shi dai Abdallah sake da baki da hanci yake kallon abin al'ajabi agurin matar tasa dan shi kawai gani yayi tana magana amma bai san da waye take yi ba,ci gaba yayi da zubawa sarautar Allah ido,gani yayi Bintu ta bi wani ɓangare daga can lokon ɗakin da kallo tana cewa naga wajen!'aljanar tace"yauwa to a wajen ki duba akwai ƙofar da zata fitar daku har farfajiyar da ake ajiye dukan motocin gidan!'cikin sauri Bintu taja hannun Abdallah har zuwa gaban wannan mutumin da bashi da maraba da ice ta wani bangaren, tana cewa muyi sauri mu fita bamu da ishashshen lokaci!' ba tare da ya tsaya yi mata wasu tambayoyi ba kawai yayi abinda ta umarce shi bai sha wahalar ɗauke mutumin ba saboda babu wani nauyi atare da shi,sai dai kuma wani tashin hankalin da suka kuma riska har yafi na baya,saboda wata irin wuta ce ta fara ci a cikin dakin kamar wadda take jira a taɓa mutumin,kuma da sauri da sauri take ci,cikin wani sabon tashin hankalin Bintu ta nufi ƙofar daniyar buɗewa amma abin ya gagara kuka ta farayi tana jijjiga ƙofar da ko motsi batayi,yayin da wutar take tunkaro su ga kuma Abdallah saɓe da mutumin a kafaɗar sa,wutar na daɗa tun karo su Bintu na ƙara azamar da ɗa buga ƙofar,ji tayi matar ta kuma cewa da ita Bintu kiyi sauri ga can karfen dake jikin bangon gabas shi zaki ɗauka da Bismillah San nan ki buga ƙofar dashi kina ambatan sunan Allah insha Allah ƙofar zata buɗe!'cikin zafin nama Bintu ta tunkari wajen da ƙarfen yake wanda kuma wutar tana gab da isa wajen ƙarfan, Abdallah ne yayi ƙarfin halin cewa Bintu kina da hankali kuwa kina ganin wuta na tunkarar wajen amma kina ƙoƙarin kai kanki!'ba tare da ta saurari abinda yake cewa ba ta isa gurin tana daukar karfen, wutar na kamawa awajen cikin sauri ta matsa daga gurin ta koma bakin ƙofar tare da yin Bismillah ta daki ƙofar da ƙarfi tana ambatar sunan Allah cikin ƙudura ta Ubangiji ƙofar ta buɗe, tamkar walƙiya haka suka bar wajen wanda kuma suna fita ƙofar ta koma yadda take tamkar ba ataɓa taɓa ta ba,hakan ke da wuya kuma baƙin azzzlumin ya antayo cikin ɗakin tare da fara zazzare idanun sa yana bin wutar dake daɗa ruruwa da kallo,wanda hakan yake tabbatar masa da cewa mai faruwa ta gama faruwa, zubewa yayi a ƙasan wajen daɓas baiƙi alokacin nan wutar ta haɗa dashi ta cinye ba, tashin hankalin da yake ciki ba zai misaltu ba a wan nan lokacin,ya kasa yin komai banda zubawa wajen da ya ajiye ABUBAKAR da yayi da idanu ko ƙiftawa ba yayi,maƙoshin sa kuwa ya kasa haɗiye koda miyau ne. Wucin da ya rufe fatar jikin sa da wani irin zafi me shiga ɓargon jiki shine ya ankarar dashi halin da yake ciki,cikin sauri ya fita daga ɗakin zuciyar sa in banda balbala da wuta babu abinda take yi,yana fita daga gurin kuwa wata irin wuta ta mamaki ta mamaye dakin,wani abin al'ajabi kuma iya gurin ne kawai yake ci da wutar duk da cewa da akwai motoci ta bayan dakin, zubawa ɗakin ido yayi idanun sunyi wata irin kala tamkar garwashi,kamannin sa har sauyawa sukayi saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali, ƙoƙari yayi ya bar wajen tun kafin asirin sa ya ƙarasa tonuwa. Wata irin ƙaƙƙar far ajiyar zuciya Bintu ta saki lokacin da taga sun fita daga cikin ESTATE din lafiya ba tare da sun hadu da wata tuhuma ba,shigewa tayi jikin sa tana fidda wani numfashi wanda kana jin sa kasan na wahala ne,runtse idanun ta tayi saboda zugin ƙonuwar da sai yanzu tasan tayi ta ta ratsa fatar ta,A hankali yasa hannun sa guda ya shafa kanta da duk ya hargitse saboda wahala,zuciyar sa kuwa cike take da tausayi da tarin tambayoyi,agame da wannan al'amarin da yafaru akan idanun sa,ɗan zamewa tayi daga jikin sa dan san bashi damar ci gaba da tuki cikin nutsuwa,sai dai duk sakan da sai ta duba bayan ta dan tabbatar da cewa yana nan,gani take kamar har yanzu basu tsira ba,kamar za a iya ƙara ɗauke shi ta hanyar tsafi,amma idan ta tuna da cewa Allah yana tare da su kuma nasarar tasuce sai hankalin ta ya ɗan kwanta,tafiya suka ɗanyi mai nisa kana taga sun ƙara so wani ɗan madaidaicin gida mai kyau mota ma batafi biyu ce zata iya shiga farfajiyar gidan ba,fita yayi ya buɗe get ɗin kana ya dawo yaja suka shiga, Ga mamakin su sai kuma sukaji yanzu yayi nauyi bakamar da farko da Abdallah ya ɗauke shi ba,hakan yasa Abdallah ya ɗauke shi da nishi,a hankali suka shiga cikin madaidaicin falon da babu wasu kayan tarkace idan ka ɗauke tv da ec sai frige da kujeru, bai tsaya ba sai da ya dangana da can ƙuryar ɗakin dake cikin falon anan ya kwantar da mutumin da har yanzu bai san waye shi ba,tsayawa sukayi akan sa tare da zuba masa ido,tsuguna wa Bintu tayi agaban sa cikin fidda zafafan hawaye tasa hannun ta ta fara goge wan nan abun mai kamar yana ajikin sa da fuskar sa,cikin kukan da ya tsanan ta agareta tace"Allah sarki rayuwa ke nan yanzu ɗan uwanka ma sai ya zama abin farmaki agareka,ko kai ka farmake shi ko shi ya farmaki rayuwar ka,tabbas Dady kaga rayuwar da bantaɓa ji ko ganin irin ta a duniya ba,to amma hakan ba wani abune na mamaki ba duba da yadda duniyar ta koma duk abinda kake zaton ba zai yiwu ba yanzu shi yake yuwuwa, abubuwan al'ajabi da ɗaure kai su suke ta faruwa yanzu,sai dai muyi fatan Allah ya shiga tsakanin mu da shaidan ya kuma tsare zukatan mu da shiga mummunan rayuwa!'tana faɗa tana cigaba da yaye abin daga kan fuskar sa, Abdallah dama yaya lafiyar kura ai faruwar wannan lamari sai ya ƙara kurumtar dashi domin shi kansa so yake yaga yace wani abu amma hakan ya gagara,ga kuma tambayoyi fal aransa. Zama ko makaman cin haka bai same shi ba,tabbas yasan babu waɗan da zasuyi masa irin wannan muguwar ɓar bar sai yaran nan,wai ma tun asali mai yasa shi kasa ɗaukar mataki akan su?me yasa baiyi ƙoƙarin ganin bayan su ba?bazan taɓa barin ku kutona min asiri acikin ESTATE ɗin nan ba,bazan baku wannan damar ba kunyi naku kun gama saura nawa wallahi babu wanda zan ƙyale acikin ku kaf sai na ƙarar daku,saboda tsabar baƙin ciki baisan sanda wani kuka ya kece masa ba mai tsananin karfi da fitar da wani amon sauti wanda yake cike da abubuwa na bakin ciki masu tarin yawa. Cikin hawayen da suke ci gaba da wanke mata fuska ta ɗago da kanta tana kallon fuskar Abdallah da ya zuba idanun sa akan fuskar mutumin da yake jin wata iriyar faduwar gaba akan sa,kama hannun sa tayi ta jawo shi zama yayi gefan ta batare da yace kala ba,sai dai kawai yabi sawunta na jeruwa akasan gadon da mutumin yake kai,kamar saukar aradu haka yaji muryar Bintu nayi masa amsa kuwa yayin da take cewa Yahh Abdallah wannan shine Dadyn ka farin cikin ka burinka alfaharin ka wanda kake kwana dashi kake tashi kake kuma mararin san ganin sa da ganin bayan wanda ya sace maka shi ya hanaka jin daɗin mahaifanka!'ta ƙare maganar da zuba masa jiƙaƙƙun idanun ta,bakin ta kawai yake kalla sai ya koma ya kalli fuskar mutumin da Bintu kira da mahaifinsa,ya rasa da bakin da zaiyi magana,ya kuma kasa tan-tance halin da yake ciki tsakanin farin ciki da ɓakin ciki,to idan yace farinciki zaiyi ta yaya zaiyi farin cikin bayan ga mahaifin nasa a kwance bashi da maraba da gawa,idan kuma ɓakin ciki yace zaiyi ta yaya zaiyi shi bayan ga mahaifinsa agabansa wanda ya dauki shekaru yana faman neman inda yake,kawai sai ya kifa kansa ajikin Dady Abubakar yana fidda wani irin numfashi mai haɗe da wani irin zazzafan huci,yana kuma haɗiye wani abu mai girma da ya daɗe tokare amaƙoshinsa,shuru su kayi gaba dayan su,sai bayan wasu ƴan daƙiƙa ne Bintu ta samu kanta da ɗora hannun ta saman tattausar sumar sa tana shafawa cikin yanayin lallashi da tausayin kan su tace"yanzu me zamuyi agidan nan?ba tajira amsar saba ta ci gaba da cewa nayi tunanin muje mu kaishi gurin malam mu ajiyeshi,kaga za ayi masa magani sannan kuma ya samu tsaro, dan nasan tabbas sai yabi sahun mu,kuma ina ga mukai shi yanzu a cikin daren nan!'ta faɗa tana ɗan bin bangon ɗakin da idanu dan lalubo agogo,lokacin ta ga har ya tura ɗan yanzu baifi saura awa ɗaya akira assalatu ba,dawo da duban ta kan Abdallah tayi wanda har yanzu bai ɗago kan sa ba tun ƙifawar da yayi ajikin mahaifin sa,sai kuwa da yanzu maganar Bintu ta san yaya masa zuciyar sa tunanin sa kuma ya dawo kan hanya, kallon ta yayi idanun sa cike da wani ruwa wanda nake zaton ƙwalla ce ya hanata fitowa saboda tsananin bayaso yayi kuka agaban Bintu,yace"bari na kira su Safwan suzo su kaishi!'to me yasa mu baza mu kaishi ba?zuba mata ido yayi yana ganin yadda take cije bakinta har da wasu tarin ƙwallan da suka cika ƙwayar idanun nata,kamo hannun ta yayi babu zato ko tsammani saiji tayi ya kifa ta akan kafar sa da ya miƙeta, kafin ta gama tunanin abin da zaiyi mata kuma ta tsinci hannun sa kan gadon bayanta inda rigarta ta ƙone har ya shafi fatar jikinta,me yasa kike ɓoyewa?ya tamabeta cikin muryar sa da ta kuma yin ƙasa yana kuma zagaye yatsan sa agurin,cikin jin zafin ƙunar tace"na fiso mu gama da lafiyar Dady kafin tawa tunda ni mai sauƙi ne!'a gurin ki ko?ya faɗa yana zaro wayarta dake aljihun sa,cikin sakanni ya turawa su Safwan test saboda yana da tabbacin dai yanzu sun dawo Abuja,yana tura test ɗin ya tashi ya fara haɗa kayan wanke ciwo zuwa yayi ya wanke mata sai dai a wannan karon baƙaramjn dauriya tayi ba,ko dai dan taga ba allura bace,yana gamawa su Safwan suka bashi tabbacin sun ƙara so gidan cewa yayi su shigo,fita yayi dan buɗe musu ƙofa,yana bawa Bintu umarnin, ta shiga toilet zasu shigo su ɗauki Dadyn,daga haka ya fita daga ɗakin,jim kaɗan suka shigo gaba ɗayan su, yaji daɗi da bai samu Bint a ɗakin ba,kama Dady Abubakar su kayi tare da fita dashi,har cikin mota suka sakashi tare da gargaɗin Abdallah da kuma kiyayewar da yakeson suyi. A zaune ya same ta ta haɗa kanta da gwiwar ta,yanzu sun gama da ɓangaren Dady sai kuma mahaifiyar ta da fafinta Allah yasa suna cikin lafiya,fatan ta ke nan a kullum,shigowar sa ce yasa ta ɗago kanta,dukbdavba kallon shi take yiba amma dai tana kallon saitin da yake,tahowa yayi gabanta tare da kamo hannun ta miƙar da ita tsaye yayi,kana yaja ta zuwa toilet,cikin matuƙar kula yace"zaki iya wanka?daga masa kai tayi idanunta nasan fitar da ruwa,girgiza mata kai yayi yana cewa a'a Ni fa ba kuka nace kiyi ba, Bint meyasa kuka baya yi miki wahala ne?ya faɗa cikin yanayin zolaya duk dan san yaga ta saki ranta,ɗan tura bakin kuwa tayi zatayi magana ke nan ya ɗora bakin sa kan nata,sanyin harshen sa tare da ƙamshin da ya zauna da'iman acikin sa,yasa ta lumshe idanun ta,bata kuma yi ƙoƙarin ƙwace kanta ba ta saki jikin ta suna tanɗe bakin juna,saida suka dau tsawon mintuna biyu a haka kana ya janye yana mai kashe mata ido tare da cewa, Bint kin kuma ko?kallon sa tayi da alamun tambaya,dan langaɓe kan sa yayi tare da turo mata jajayen lip ɗinsa yace"kin kuma cinye min baki bayan ban rama wan can ba!'ai tana jin haka ta juya masa baya tare da rufe fuskar ta da tafikan hannun ta.wani dan murmushi ne ya suɓuce masa ganin yasamu abin da yake so sai juya zai fita,juyowa tayi ta zubawa bayan sa idanu,karaf sai gashi ya juyo,da sauri ta kawar da kanta,yace"ya dai ko nazo nayi miki wankan?kukan shagwaɓa tasa masa tana buga ƙafar ta aƙasa,fita yayi tare da ja mata ƙofar. Bayan fitowar ta shima shiga yayi yayo wankan,a bakin gadon ya same ta duk tabi ta kanannaɗe jikinta da bedsheet ɗin saboda babu abinda zata ɗaura towel kuwa tana ganin idan ta daura abinda ya faru ranar zai kuma maimaituwa,shi yasa taga kamar zama da bedsheet din yafi mata sauki,har ya gama abinda yakeyi yasaka kayan bacci bata motsa daga nan inda take ba,ɗan daga banta yayi kana yace"Bint kinji anfara Kiran sallah ina fata dai kin yi alwala? daga masa kai tayi,fita yayi daga ɗakin jim kaɗan ya shigo da sallaya da kuma doguwar jallabiyar sa wadda ta ɗan ɗage masa,miƙawa Bintu yayi tare da bata umarnin ta saka,tana daga zaune ta zura rigar san nan ta tashi tsaye,duk da cewa tayi masa kaɗan rigar amma saida tayi wa Bintu yawa,sabon tawul ya bata mai girma yace"maza rufe kanki muyi sallah!'karɓa tayi ta rufe jikin ta kana suka tayar da Sallah. Duk da matsanancin rashin hankalin da yake ciki amma haka ya daure ya ɓoye bai nuna wata damuwa akan fuskar sa ba,yabi ayarin da suke shiga sallah shima ya shiga yayi kamar yadda suka saba shida sauran ƴan uwansa,yana fitowa ya bar gidan dan yasan tabbas za ayi maganar ƙonewar dakin kuma bayaso ya tsaya ganin takaici,kamar yadda yayi zato don kuwa haka ce ta kasan ce,duk inda ka gifta zancan ƙonewar dakin akeyi,wasu dayawa basu ɗakin ya ƙone batare da sun san abinda ke cikin saba shekara talatin da ɗoriya,Alhaji Baba da kansa sai da yayi tu ajjubin Al'amarin. Bacci suke yi baccin da basu samu sunyi shi a daren jiya ba,idan kuga yadda Bintu da Abdallah suka cure guri ɗaya sai abin ya baka mamaki da da dariya ga kuma sha'awa, Bintun ce cikin jikin shi ya kanannaɗeta kamar wani zai ƙwace masa ita,wayar da ya karba a hannun Safwan ce ta fara ringin wanda shine dalilin farkawar sa daga baccin da yake yin sa ba tare da wani dadi ba,saboda mafarkan da suka da baibaye baccin marasa daɗi,da sauri ya dauki wayar dan kar ƙarar ta ta tashi Bintu,daniyal ne ya kira shi bayan sun gaisa daniyal yake cewa Oga nayi ta kiran wayoyin ka wasu suyi ringin wasu kuma akashe shine na sanar da Safwan ya bani wan nan layin!'Abdallah cikin yanayin bacci yace"haka ne Daniyal me ya faru? daniyal yace"Oga ka manta da tafiyar mu cikin suleja?cikin sauri Abdallah ya miƙe har saida Bintu ta farka a razane,yace"daniyal na sha'afa amma yanzu ka shirya kazo gidan nan na gari ka same Ni!'daniyal ya amsa cikin girmamawa kana suka ajiye wayar,Bintu da gaba ɗaya hankalin ta yana kansa cikin tsoro tace"me ya faru Allah yasa dai ba Dady bane!'ta faɗa cikin sanyin kuka,yace bashi bane amma dai yanzu mu shirya da akwai inda zamuje,bari nayi waya Safwan ya samo miki kaya ya bawa daniyal ya taho dasu, Sorry no edittin 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 50 ``` Ba tace dashi komai ba amma dai gani take kamar wani abun yake ɓoye mata,ba'A fi mituna goma ba sai ga kiran daniyal,ba tare da ya ɗauki wayar ba ya tashi ya fita daga ɗakin,jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da wata leda,miƙawa Bintu yayi tare da cewa sauri ki saka zamu tafi!'tashi tayi tana ƙoƙarin shigewa toilet sai taga ya juya ya fita daga ɗakin hakan ne ya bata damar saka rigar tare da yana mayafin ta asaman kanta,fita tayi falon gidan wanda suka ci karo da Abdallah shima ya fito cikin shigar sa ta ƙananun kaya wadda sukayi masa matukar kyau suka kuma fito da zallar kyawun jikin sa,ɗan kallon sa tayi kana ta ɗauke kai,yayi mata kyau sosai amma ita yanzu tsoron kallon sa ma takeyi dan kar yayi mata wata fassarar, Sarai ya gano ta amma bai magantu ba,fita sukayi tare, Daniyal yana ganin su yayi saurin buɗe motar suka shiga baya,ya rufe tare da komawa mazaunin drever,a hankali ya fara jan motar har suka fita daga gidan,fita yayi ya rufe get din kana ya dawo suka dauki hanyar zuwa gidan Hajjo. Hankalin shugaba azukyi idan yayi dubu to duk sun tashi,wai mai yasa nanu yake son zama sanadin mutuwar kasuwancin su ne?anya kuwa ba cire shi daga harkar zaiyi ba dan karya jawo musu abinda zaizo ya tarwatsa jin dadin rayuwar su ba,nanu ne ya dawo da shugaba daga duniyar razanin da ya fara shiga akan mummunan karshen da yake son jawo musu,yace"shugaba kayi magana mana, wannan al'amari fa ba ƙaramin abu bane sun riga sun karya Ni sun rusani sun kai rayuwata ƙasa tunda suka riga suka ɗauke Abubakar suka sami Abigirl a hannun su,na tabbatar da cewa duk sanda Abigirl ko ABUBAKAR suka farfaɗo daga suman sihirin da mukayi musu ƙaryar mu ta ƙare daga Ni harku dan haka dole mu haɗu mu nemowa kanmu da rayuwar mu mafita!'shugaba yace"lallai nanu ka haukace da waɗan nan kalaman naka ai yanzu kai wan nan ta shafa bamu ba, tunda dakin nan ba ajiyar muce acikin sa ba,kuma Abubakar da tarkacen dake cikin ɗakin basune tasirin mu ba kowa tasirin tsafin sa daban,kamar yadda kowannen mu matsalarsa da ban,yanzu ka gaya min taimakon da kake so muyi maka dan ayanzu shi kaɗai ne abinda ya rage tsakanin mu da kai!'duk da cewa nanu baiji dadin maganar shugaba ba amma sai ya danne abinda ke taso masa ya kwantar da kai yace"yanzu so nake asato min yarinyar nan daga nan zan janyo shi mijin nata yazo inda muke,kaga kashe su duka bazaiyi min wuya ba!'Shugaba yace"nasan saboda rufin asirin ka kake son yin duk wan nan abun ko?kamar wani gaula haka nanu ya daga wa shugaba azukyi kai,dariya shugaba yayi tare da cewa shi kuma Abubakar ɗin ya zakayi dashi?kasan idan ka kashe su baka kashe Abubakar ba tamkar ka sare reshe baka kashe miciji baka sare kansa bane?yayi shuru tare da zubawa nanu idanu yana jiran amsarsa,wani wahalallan numfashi ya fesar kana yace"shima Abubakar ɗin kashe shi zanyi!'ka haƙura da dimon ɗin ke nan!'cewar shugaba,shuru nanu yakuma yi cike da zurfafa tunani,can ya ɗago kansa da idanun sa da sukayi jajur saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki,shuga rasa dimon ɗin nan tamkar rasa rayuwata ne bazan iya haƙura dashi ba,zan sace wannan shegiyar yarinyar da ita zanyi garkuwa Abdallah yakawo min kansa da mahaifin sa!'idan kuma bai aminta da haka ba fa? tambayoyin shugaba fa neman zauta ƙwaƙwalwal nanu sukeyi duk hanyar da ya samo sai shugaba ya kawo lalacewar ta,wata irin zufa ce take karyo masa ta ko ina,yayin da zuciyar sa babu abinda take sai bugu, wanda kuma tsabar fargaba ce tasa hakan,da ƙyar ya tattara miyan da ya daskare cikin bakin sa ya haɗiye shi tare da cewa,shugaba zamu gwada wannan ɗin amma daga baya zan iya haɗawa da yaudara!'wata shegiyar dariya shugaba ya sheƙe da ita har da riƙe ciki kana ya ɗan saurara tare da cewa shegen kaya nanu ai dama in dai yaudara ce ka iya ta,tunda ka yaudari mahaifinka waye bazaka iya yaudara ba,amma dai yanzu na gamsu da wannan tsarin tunda naga yanayi,abinda ka faɗa ɗin shi za'ayi amma kasan wannan yarinyar baza mu hada ta da tsafi ba tunda tun farko dama ta gagaremu ballan tana kuma yanzu!'sai yanzu nanu yaji dan dama tunda shugaba ya bashi dama da kuma goyan baya. Sun ɗanyi nisa da fara tafiyar ya dube ta cikin dawowa yanayin sa na kullum yace"bani nombar inno a wayar ki mu kirata dan kar hankalin ta ya tashi!'miƙa masa tayi bayan ta duba sunan innon,ɗauka yayi awayar dake hannun sa ya kirata,ringin ɗin farko kuwa ta ɗaga,lokacin suna tare da Dady Habib,a hankali Abdallah yace"inno Barka da safiya!'cikin sauri inno ta amsa tana ɗorawa da cewa wai Abdallah ina kuka shiga kaida Bintu yau tun safe nake cikiyarku a cikin gidan nan?inno karki damu wani aikine ya taso mun cikin dare kuma tace bazata iya zama ba tana jin tsoro shine na tafi da ita!'jinjina kai inno tayi tana mamakin wai Abdallah ne da jero wannan dogon zan can duk saboda Bintu,cikin kulawa tace"aiyo ai hakan yayi kai da matar ka Allah dai ya baku nasara,saikun dawo,daga wannan sukayi sallama,juyowa tayi tana kallon Dady Habib da yayi shuru yana sauraren ta,tace"dama ai duk wanda ya samu mace kamar Bintu tabbas sai rayuwar sa ta canja tare da godewa Allah!'Dady Habib yayi murmushi tare da cewa jikokin naki ne?dariya tayi cikin farin ciki tace"sune kaga har sun hada kan su tamkar ba haɗa su akayi ba shi yasa nake cewa ita ma Taufiƙa zata haƙura duk ranar da taga bata da kowa A gefanta sai Sayyid, Allah dai ya baiyana mana shi cikin ƙoshin Lafiya!'da sauri Dady Habib ya amsa da Amin kana yace"to kuma ai baki tmbayesu inda sukaje ba!'inno tace rabu dasu mata da miji ne,kasan dai miji ba zai sace matar sa ba ko? murmushi kawai yayi b tare da yace"komai ba. A ɓangaren Anty Nafisa kuwa tuni ta bada aikin gamawa da Abba Umar amma tace aɗan saurara zata faɗa musu ranar da take so aikin ya kasance,ba dan komai ne yasa ta jinkirta ba sai dan tana son ta fara bibiyar sa dan ta tabbatar da ko su Laila suna raye suma ta aikasu tare gaba ɗaya, ko hankalinta ya gama kwanciya tasa mu tayi rayuwar ta cikin farin ciki ba tare da fargaba ba,wan nan shine tunanin Nafisa, A can kuma ɓangaren su Abdallah lokacin da suka gama waya da inno kallon Bintu yayi cikin haɗe gira dan karma ta kawo masa wasa cikin tambayar da yake son yi mata,ganin haka kuwa yasa ta nutsu tare da maida kanta daya ɓangaren,kamar daga sama taji maganarsa yana cewa Bint ke dawa kuke magana a cikin ɗakin nan kuma waya sanar miki da cewa Dady yana cikin dakin?kuma me yasa baki gayan ba tun asali kafin faruwar Al'amarin?cikin san tabbatar masa da gaskiyar abinda zata faɗa tace"wallahi ban santa ba kuma nima da farko ban sani ba saida ta sanar dani kuma yau baifi kwana uku da fara mafarkin da ita ba,tun ranar dai da mukaje wajen Malam ta fara zuwa kuma ita tace kar na gaya maka har sai mun shiga ɗakin munfito,kuma ita take min magana acikin ɗakin,Rimi Rimi ta faɗa masa maganganun da sukayi acikin ɗakin,cikin sheshsheƙar kukan da yake cinta tace"amma bata gayamin inda ummi na da fafina suke ba,inaso bagan su,amma bata gaya min ba,hannun sa har rawa yake gurin ƙoƙarin janyo Bintu jikin shi,ƙara shigewa tayi tana goga fukarta akan ƙirjin sa kamar yadda ta saba,rufe idanun sa yayi yana jin wani irin matsanancin tausayin bintu tare da wani abu mai girma da yake ratsa duk wata zuciya da gangar jikin shi,yana mamaye duk wata kafa mai muhimmanci dake cikin rukunin numfashin sa,hannu yasa ya ture ɗan mayafin dake kanta ya shiga shafa lallausar sumar kanta mai matukar santsi da ƙamshi,rufe idanun ta tayi wanda take anan bacci yayi awan gaba da ita,cikin mintunan da basu fi biyu da yin baccin Bintu ba suka ƙara so ƙofar gidan Hajjo. Hajjah ta zubawa Habib ido dan san gano halin da yake ciki, amma hakan ya gagara,cikin ƙaunar ɗan nata da ya zamar mata ɗaya tamkar da dubu tace"Habibu mai yake damunka ne naga duk kayi wani sukuku da kai kamar bakajin dadi,ɗan murmushi yayi tare da cewa Hajjah kin san dai yanzu bani da wani abu wanda yake saka Ni damuwa face maganar Mansur shi kaɗai ne damuwa ta,ina jin abin har cikin raina, wannan halin nasa ina fata ALLAH ya canja masa shi. Alhaji Baba ya kalli Alhaji Hashir cikin tsananin damuwar da ta taso masa a cikin wannan rana da tunawa da haziƙin ɗansa,wanda ya manta dashi tun bayan da akarasa shi, duk da cewa damuwar rasa shin yana tare da zukatan su,amma babu damar furtawa da baka,sai yau da yaji tamkar antashe shi daga bacci,ya tashi da azabar kewa da raɗaɗin rashin Abubakar ji yake tamkar yanzu aka neme shi aka rasa,so da yawa yakan kwana ya tashi da jin zafin abin amma ya rasa ta yaya akai ya kasa koda fita waje dan neman inda ɗan nasa ya shiga,abinda matuƙar mamaki ga kuma jikan sa da ya ɗauki soyayya ya ɗora masa shima ya rasa shi bayan rasa mahaifin sa,yanzu abin ne yake dawo masa tare da kaicon abin da ya hana shi yunƙurin neman ɗan sa da jikan sa,ɓatan Sayyid shi ya kuma saka zuciyar sa cikin wasu wasi da saka ayar tambaya akan lamarin gidan nasa,me yasa ake ɗauke masa zuriya?taɓa shi ɗan uwan sa Alhaji Hashir yayi tare da cewa ya dai Balarabe ka kiramu dan yin magana mai muhimmanci amma ka barmu kasa mana ido kai kuma ka tafi duniyar nazari,shin meke faruwa duk da nasan maganar bazata wuce akan ɗakin nan da aka tashi da gobarar sa ba!'ya faɗa yana duban dan uwan sa Alhaji Sa'ad da shima ya zubawa Alhaji Baba Ido dan son jin maƙasudin kiran da yasa akayi musu,Dady Mansur da Dady Habib da Abba Umar sai Baba nura da Ahmad da dai sauran ƴaƴan sa da ƴaƴan ƴan uwansa da suke tare aguri ɗaya cikin estate,yayin da kowa da abinda yake son ji daga bakin Alhaji Baba,wadan da suka san sirrin dimon suna fata ace abin da zai sanar dasu ke nan,wasu kuma saɓanin haka ne aran su. Hajjah ce tace"ya kamata ku bar Alhaji ya nutsu tunda ya kiramu kun san zaiyi magana mai muhimmanci ne,kuma duk lokacin da mutum zai furta wata magana anaso ya tattaro tunanin sa da nutsuwa da kuma nazari akan abinda zai furta,saboda tuntuɓen harshe,dan haka Dan Allah karku rikitashi!'wani mugun kallo Baffa Hashir ya wurga mata tare da cewa to ƴar iya,dama nasan ko kowa baiyi magana ba ke saikin yi!'murmushi Hajjah tayi dan tasan dama can kanwarsu bata juƙuwa da Baffa Hashir, Gyaran muryar da Alhaji Baba yayi ita ta sakawa kowa nutsuwa,tare da maida duk hankulan su kansa,cikin nutsuwar da bata hana damuwar sa baiyana ba,yace"duk hasashen ku bai zama daidai ba,domin nasan abinda zan fada muku bashi kuke tunanin zan faɗa ba,saboda nima yau tunanin ya fito daga zuciya ta zuwa kan harshena,ɗan shuru yayi,yayin da zuciyoyi suka ƙagauta da jin wannan batu,duk iya tunanin su akan dimon ne saboda su waɗan da suke abun sun san cewa Alhaji Baba bai san maganar dimon ɗin ta fita ba,balle yasan muguwar rigima da cutar data haifar a cikin zuri'arsa,Alhaji Baba yaci gaba da cewa,shi yasa zan sanar daku dan mu haɗu muyiwa kanmu da zuriar mu maganin abinda yake damunta,dan fitar da iska yayi ta bakin sa tare da sauke numfashin damuwar dake cunkushe a zuciyar sa,kana yaci gaba da cewa maganar Abubakar ce,,,wata irin zabura Dady Mansur yayi yayin da sauran mutanen ɗakin sukayi ɗif kamar babu wata halitta a falon,kowa da irin bugun da zuciyar sa keyi masa, Hajjah kuwa wasu hawaye ne suka sauko mata tana cewa Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah wanda yayi zuciya,kawai sai ta fashe da kukan farinciki nanatawa take Allah kasa lokacine yayi da gaskiya zata bayyana!'kowa ka kalla afalon nan da akwai abinda ke damun sa na matukar ruɗani da firgicin jin maganar Abubakar ta taso lokaci ɗaya, Dady Mansur kuwa kuka ya saka sosai wanda kana ji kasan kukane da yake fita tun daga ƙarƙashin zuciyar sa,ya kasa cewa komai sai sautin kukan sa dake fita gwanin tausayi,Dady Habib ne ya ɗan goge fuskarsa kana cikin nutsuwa yace"haba yaya bai kamata ba da girman ka kadinga abin yara!'wani Irin mahaukacin kallo me cike da fassarori da ma'anoni masu yawa Dady Mansur ya jefawa ɗan uwan nasa,ba tare kuma da ya iya ce masa komai ba,karon farko ke nan da yayiwa Mansur irin haka batare da ya tanka masa ba,ɗauke kansa yayi cike da mamakin wannan kallon da Mansur yake masa,ko me yake nufi da haka? Alhaji Baba yayi wani ɗan murmushi na takaici kana ya cigaba da cewa,a yau kuma a yanzu nasa afara rokon ALLAH ba dare ba rana idan Abubakar yana lafiya Allah ya baiyana mana shi idan baya cikin haicinsa kuma Allah ya bashi lafiya ya dawo min dashi cikin gidan nan,idan kuma ya mutu,,,,,kukan Hajiya Babba ne ya dakatar da shi daga barin abinda zai faɗa,cikin kuka da matsanancin tashin hankali tace"dan Allah Alhaji karka ƙarasa,inason ganin jagora araye (dake sunan da take gaya masa mafi lokata acikin mutane saboda karar ɗan fari)taci gaba da cewa Wallahi inaso yazo gidan nan araye inaso naga waɗanda suka gurgunta min rayuwar sa akan abin ɗun,,,,bata ƙarasa ba inno ta rufe mata baki tare da girgiza mata kai,alamun kar ta faɗi abinda ke cikin zuciyar ta,tunda shi Alhaji Baba baƙo ne akan sanin hakan,zai iya zurfafa bincike akan al'amarin,shurun kuwa tayi bata sake cewa komai ba,sai dai kukan da taci gaba dayi ƙasa ƙasa,yayin da Hajjah ta zuba musu idanun ayar tambaya da wannan sabon Al'amarin, wai meke shirin faruwa a gidan nan ne haka? Alhaji Baba yace"dama abinda nake son sanar daku kenan kowa zai iya tafiya!'daga haka ya miƙe ya shige can cikin ƙuryar ɗakin sa,jiki asan yaye suka dinga ficewa daga falon kowa ya kasa magana dan sun rasa abin cewa,wasu farin cikine ya hana su magantuwa wasu kuma bakin ciki,kowa ya fita daga falon sai Abba Umar da Aliyu,da kuma Dady Habib,sai su inno,Abba Umar yace"Hajiya Babba ku daina kuka komai ya kusa wucewa insha Allah tun da har muka samu Alhaji Baba da kansa yayi maganar yaya,kuma daga nan nima gurin wani malami na zan wuce Musa aƙara tsanan ta rokon Allah!'Dady Habib yace"tabbas maganar Umar haka take nima ina da malaman da zan saka cikin lamarin, san nan a ganina ya kamata a hada da cigiya gidajen rediyo ko za a dace!'Hajjah tace"hakan yayi Allah yayi muku albarka!'shi Abba Aliyu ma atake nan ya fara kiran malaman sa kasan cewar shi malamin addinni ne ya fara shela yana sanar dasu asaka almajirai sauka,yanzu zai taho da kayan sadaka,inno tace"masha Allah Ubangiji Allah ya baiyana mana shi cikin farin ciki da cikakken lafiya!'gaba ɗaya suka amsa da Amin summa Amin. Tunda ya fito yaji wani irin jiri na san kayar dashi,amma duk da haka sai da ya nufi ɓangaren ƙonannen dakin,zubewa yayi agurin yana cigaba da wani irin kuka mai matuƙar ciwo da saka mutum zazzafan zazzaɓi,Dady Mansur fa ya haukace da wannan al'amarin,shin ina Abubakar yake?ina kuma aka kaishi yanzu?kukan ya cigaba da yi,ya kuma kasa koda motsawa daga wajen,ji yayi an tsaya akan sa,da sauri ya juyo ganin Dije yasa shi saurin tashi tsaye yana kade jikin sa, ƙoƙarin barin gurin yake ta dakatar dashi da maganar ta data kusan saka shi fitsari a wando,shin yallaɓai Mansur wai meye haɗin ka da dakin nan ne?can kwanaki kai ne ka fara hanani zuwa gurin nan dan cika umarnin uwar dakina kuma har kayi min gargaɗin sake ganina agurin,san nan ina yawan ganin ka a gurin shin me ka ɓoye acikin ɗakin da yanzu rasashi yasa ka irin wannan kukan da tunda nake ban taɓa ganin magidan ci kamar ka nayin irinsa ba?Dady Mansur kallon Dije kawai yake amma bai bata amsar ko ɗaya daga cikin tambayoyin ta ba,saima kaucewa da ya kuma yi dan barin wajen,cikin sauri Dije ta kuma cewa,Mansur kaji tsoran Allah ka bayyanawa mutane abinda kake aikatawa!'ko da bai bayyana ba ai yanzu mun gane shi kuma ko baka faɗa ba Mansur a kwai mugun abinda kake aikatawa!'cewar Dady Habib ke nan da isowar sa gurin kenan,Dady Mansur sakato yayi yana buɗe Habib da wani shegen kallo,tsawan sakanni shuru ya gifta ratsa tawajen,daga baya kuma Dady Mansur ya ɗauke kan sa daga kallon Dady Habib,tare da cigaba da tafiya ba tare da ya tanka musu ba,yanaji Dady Habib yana cewa tabbas anfara yin walƙiya acikin estate ɗin ALHAJI BALARABE kuma da sannu zamu ci gaba da binciko irin ku!'ya faɗa yana mai juyawa dan barin gurin. Cikin sauri Dije ta koma ɗakin ta,ba abun da take sai kaiwa da kawowa, tabbas itama lokacin da tayiwa uwar ɗakin ta alƙawari yayi,so sai take son ganin ta dan sanar mata da abinda ta daɗe tana nema,yayin da ita kuma nata burin ita da Bintu zai cika na tona mata asiri dan sun riga sun shirya mata gadar zaren da baza ta iya fidda kanta ba,tun tuni wannan ranar take jira dan tabbas tasan idan ta kaiwa uwar ɗakinta wannan labarin ita kuma zata cika mata alƙawarin ta na bayyana mata fuskarta da kuma sakar mata yaran ta,ita kuma tuni ta shirya yadda wasan zai kasan ce,dan tasan yanzu matar ta sakan kan ce akanta dan kwantar da kanta tayi ta nuna mata tabbatas tana tare da ita ɗari bisa ɗari,dan haka tona asirin ta ba wani abun wahala bane agurin ta,wayar ta takalla tare da cizon yatsa dole sai dai ta jira kiranta,amma tasan dole zata kirata a cikin tsukin nan dan haka tana nan tana addu'a tare da jiran kiran ta ako da yaushe. A hankali ya ke tashin ta har ta buɗe idanun ta dasu ka kunbura saboda kuka da damuwar da take ciki, tashi tayi tana ɗan duban wajen da suke ,amma dai batace masa komai ba,ganin damuwar dake cikin fuskarta ne yasa duk yaji jikin sa ya mutu,haɗa goshin sa yayi da nata sai ya zamana dogon hancin sa na gogar tsinin nata hancin,cikin sanyin murya yace", Bint ba son damuwar Nan,na daukar miki alƙawarin kamar yadda kika zama sanadin farinciki na nima sai na zama sanadin farin cikin ki,bazan bari kiyi kuka ba zan toshe duk wata hanyar damuwar ki,zan kawar da duk wani abun cutuwa A gareki,Bint zan samo miki fafinki da ummin ki aduk inda suke a faɗin duniyar nan!'..... Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 51 ``` Ko yanzu ma na tanadar miki da abinda zai iya rage miki damuwa!'ya faɗa yana goga siririn hancin sa kan tsinin hancin ta,rufe idanun ta tayi tana ƙoƙarin maida hawayen da suke san zubo mata,A hankali yasa hannu yana goge mata fuskar tare da ɗan gyara mata ita,ɗage mata gira yayi tare da cewa har kin ɗan yi kyau,bana so su ganki cikin damuwa da yawa!'zata yi magana yayi mata alamar tayi shiru,haka ta haƙura da tambayar da take bakin ta,fita sukayi sai faman kallan anguwar take yi saboda har yanzu bata fahimci inda suke ba. Duban ta yayi tare da cewa ki shiga sai kiyi min iso!:ɗan jim tayi kamar tana tunanin wani abu,sai kuma ta gyada masa kai tare da saka kanta cikin madaidai cin gidan na bulo,sallama tayi cikin sassanyar Muryar ta,HAJJO dake zaune jikin bishiyar mango dake girke a faffaɗan tsakar gidan tayi wata irin zabura har zanin ta na ƙoƙarin kuncewa,cewa take yi, wa nake ji kamar Lailata Allah Ubangiji ka amsa addu'a ta na ganin Laila araye,idan mafarki ne kuma ka barni a haka karka farkar dani!'ta faɗa tana ƙarasawa bakin ƙofar da Bintu ta cokare agurin,zaro ido Hajjo tayi tare da dafe kirji bakinta har rawa yake gurin kiran Asma'u, Asma'u dake cikin daki tana haɗa wanki ta fito da gudu tana cewa lafiya Hajjo me yasa mek,,,,maganar ce ta maƙale mata sakamakon tozali da tayi da Bintu. Cikin kiɗima ta matso kusa da Bintu, ta taɓata tare da cewa Laila kece da gaske? Bintu dai ido tasa musu saboda ita bata fahimci abinda hakan ke nufi ba ta daiji suna ambatar sunan mahaifiyar ta, Asma'u ta jawo hannun Bintu tare da cewa Hajjo wannan ba Laila bece"sai dai idan yarinyar Lailace!'Hajjo ta kamo Bintu cikin wani irin kuka mai tsanani da ban tausai,ta rungume ta,tana cewa tabbas wannan jinina ce,ko aduhu na laluba naji wannan halittar sai nagane jinina ce saboda tsarin halitta da komai babu inda ta baro Laila,ta wani bangaren kuma sak Umaru!'Bintu jin an ambaci mahaifinta yasa taji wani kuka ya ƙwace mata, Allah sarki ko a wane hali yake yanzu,tunda ta san Nafisa tana nan tana shirin kashe shi,jin hon daga waje yasa Asma'u tace"kai Hajjo ko dai tare suke da yaya Umar ne?bari na da naje na gani tunda har yanzu baya iya shigowa gidan nan kai tsaye!'ta faɗa tana figar mayafi akan igiya,ta fita cikin sauri,Hajjo kuwa kama hannun Bintu tayi ta kaita har kan tabarmar datake zaune,tare da saka ta gaba tana kallo bata fata ace mata Bintu ba jikarta bace, Sallamar Abdallah yasa Hajjo ta dawo da hankalin ta kan bakin ƙofar tare da amsa sallamar,zubawa Abdallah ido tayi saboda hango kamannin Umar atare da shi,wani tabarmar Asma'u ta shimfiɗa masa ya zauna,idanun sa kan Bintu da yake son gano halin da take ciki, ji yake kamar bashi da lafiya saboda rashin walwalar Bintu, yarinyar da bata da batabarin damuwa tayi tasirin da zata hanata farinciki da walwala amma yanzu gaba ɗaya duk ta sauya,babu kunya Bintu ta matsa kusa dashi tare da langaɓe wuyanta a kafaɗar sa,tana ci gaba da yiwa su inno kallon rashin sani, cikin girmamawa Abdallah ya gaishe da Hajjo kana suka kuma gaisawa da Asma'u,Hajjo tace"bawan Allah daga ina duk da cewa ina maka kallon sani amma ina so kayi min bayani,amma dan Allah kar kace min wannan yarinyar ba ɗiyar Laila bace!'ta ƙarasa maganar cikin matso hawayen da suke kwarin idanunta, Asma'u ma shuru tayi ta zubawa Abdallah ido da kuma fatan jin kyakykyawan labari daga bakin sa,ɗan ajiyar numfashi Abdallah yaja tare da fesar da iskar da yacika bakin sa da ita,kana cikin nutsuwar sa da kuma salon maganarsa mai ratsa zuciya ya fara bawa Hajjo labari tun daga farkon zuwan Bintu ESTATE da irin gwagwarmayar da tasha da na nasa labarin da irin abubuwan da suka fuskan ta har kawo wannan rana da suka samu kuɓutar da Dady Abubakar daga cikin wannan ɗakin. Wani Irin mamaki da al'ajabi da kuma tsoron duniya shi ne abinda ya riski Hajjo da Asma'u ko magana sun kasayi sai taraddadi da kuma hawayen tausayin ƴaƴan ta dakuma jikokin ta,cikin zubar hawaye tace"zo nan Batula naji ɗumin ki , ki maye min gurbin kewar mahaifanki Sulaiman da Laila!'da gudu Bintu ta waɗa jikin ta saboda yanzu ta fuskanci komai,wato wajen kakarta mahaifiyar ummin ta da fafinta Yah Abdallah ya kawota,kwanciya tayi ajikin matar da takeji kamar ta kwanta A jikin ummin ta ne,wasu hawaye masu dumi suke ta sararowa bisa kyakykyawar fuskarta,goge fuskarta Hajjo tayi kana ta gyara zaman ta cikin nuna jinjina tace"Abdallah kayi ƙoƙari kunyi ƙoƙari kuma zamu cigaba da addu'a da sadaka domin Allah ya kuma ɗora mu akan maƙiya insha Allah nasarar na garemu kamar yadda kuka kuɓutar da Abubakar da taimakon Ubangiji suma su Laila zaku kuɓutar da su da izinin Ubangiji,Ni ai yanzu hankalina yafi kwanciya kan da, saboda yanzu ina ji ajikina kamar yadda Allah ya baiyana min Bintu to zai baiyana min Sulaiman da Laila!'Asma'u ta ɗora da cewa insha Allahu rabbi ya nuna mana wannan rana!'gaba ɗaya suka amsa da Amin,Hajjo tace"yanzu mai zamu baku irin naku na ƴan gayu? ta faɗa tana kallon Abdallah da murmushi akan fuskarta,shima dan murmushin yayi tare da cewa ai Hajjo sai dai ko Bint Amma yanzu nake son juyawa ina da aiyukan da zan gabatar dasu yanzu!'Hajjo ta riƙe baki kai ɗan nan da wuri haka? amma dai ko furar garin mu ka bari na dama maka zata rage maka wani abu inyaso ko tafiya sai kayi da ita!'shuru yayi bai ce komai ba sai murmushi da ya ɗan yi,yana duban Bintu da tayi zuru tana binsu da ido,kafin Hajjo tayi magana ma tuni Asma'u ta tafi dama furar dan haka sai ta kuma dawo da duban ta kan Abdallah tana cewa, amma dai anan zaka barmin kishiyata mudan kwana biyu ko?jin jina kai yayi tare da cewa gobe zanzo mu tafi idan Allah ya kaimu!'to goben nan to babu damuwa Allah ya nuna mana ai ganin ku yafi min komai!'ganin kamar Hajjon bataji daɗi ba yasa shi cewa Hajjo karki damu indai Bint ce har sai kun gaji da ganin ta, insha Allah baza mu dawo muku nan ba sai da fafi da Ummi Laila,Kinga yanzu zaman bint bazai yuwu ba saboda akwai abubuwan dake gaban mu!'cikin gamsuwa da bayanin Abdallah Hajjo tace"karka damu na gamsu da maganarka, Allah ya baku nasara akan aiyukan ku na alheri ya kuma baiyana mana su cikin aminci shi kuma Abubakar Allah ya tashi kaɗunsa ya bashi lafiya!'amsawa sukayi da Amin cikin rangwamen damuwar da tayi kaka gida A zukatansu. Lokacin da sukayi sallama har zai fita sai kuma ya ɗan yi jim da alamu dai akwai abinda yake son faɗa, inno tace" da akwai wani abu ne Abdullahi?cikin kwantar da murya yace"alfarma ce nake so kiyi min!'Hajjo tace"faɗi matsalar ka tsakanina da kai babu alfarma!'cikin ƙara tausasa murya yace"dan Allah Hajjo karki faɗawa Abba Umar komai kiyi shiru da bakin ki saboda ayanzu sanin sa zai iya haifar da wata babbar matsalar wan nan yazama sirrin mu har zuwa lokacin da Allah zai kawo mana ƙarshen komai!'Hajjo ta ɗan yi jim kana kuma tace" idan kana ganin hakan zaifi to babu damuwa game da hakan kuma wannan tunani ne mai kyau, insha Allah bazai san komai ba!'yauwa Hajjo na gode da fahimta!'daga haka sukayi sallama ya fita,Hajjo tace"kije kuyi sallama mana Batula!'cikin sanyin jiki Bintu tabi Abdallah wanda har ya shiga mota. A cikin motar ta same shi shi kaɗai,sai ta tsaya daga bakin ƙofar tana kallon sa idanuwan ta har sun cicciko da ƙwalla,miƙa mata hannun sa yayi alamar ta taho a hankali ta taka ta saka hannunta cikin nasa,janyo ta yayi cikin motar,yasa hannu ya rufe kana ya juyo da fuskarta gareshi,hmm gayamin wannan kuma na meye?ya faɗa yana lakato hawayen da suka zubo mata,fadawa jikin shi tayi tana ɗan sakin wata ƴar sheshsheƙa tare da ajiyar zuciya,shafa bayan ta ya shiga yi cikin ƙoƙarin samar mata da nutsuwa yace" ko bazaki iya zama ba mutafi?ɗan tura ƙaramin bakinta tayi tana ɗan bugun saitin zuciyar sa tace"kaima ka zauna mana sai goben mu tafi tare!'zaro idanuwan sa yayi tare da cewa kai Bint ya za ayi gan sameme dani na kwanar musu agida sai kace wanda mukazo wani garin!'shuru tayi batace komai ba,ɗago fuskarta yayi tare da ɗora bakinshi kan nata,A Hankali ya shiga tsotsa kamar mayunwacin da ya kwana baici ba,sun ɗau tsawon mintuna biyu kafin ya saketa,cikin muryar sa da ta sauya yace"maza shiga gida ina kallon ki!'cikin sanyin jiki kamar bata so, haka ta fita ta shige cikin gidan tana waiwayen sa, saida yaga shigar ta kana ya kira Daniyal,yazo su tafi,sai da suka fara tafiya kana yace"gidan sirri zaka kaini!'ok sir Daniyal ya faɗa yana ƙarawa motar gudu. Sosai fa Anty Nafisa tasa ake mata bincike akan shiga da fitar Abba Umar, wanda garin haka ne aka binciko mata gidan su Hajjo,daga nan tace yaran da tasa su aikin su duba tanaso agano mata suwaye acikin gidan,to wannan aikin ne dai ya ɗan dauki lokaci dan har yanzu jiran sakamako take,sai kuma yau katsaham da aka tashi da gobarar wan can ɗakin da itama ta daɗe tana son kai masa ziyara dan sanin ko me aka ɓoye acikin sa,ana cikin wannan jimamin kuma sai ta samu kira daga yaran da tasa suyi mata bincike,suna tabbatar mata da cewa sunga baƙin fuska sunzo gidan har mutum uku,amma dai babu Abba Umar acikin su,cikin tashin hankali tace"wane jinsi ne?yaron ya sanar mata cewa mace guda ɗaya sai maza biyu take zuciyar ta ta hau bugu,cikin rawar baki tace"lallai kuma cikin gaggawa inaso ku turomin da fuskokin su,a yau ba sai gobe ba!'daga haka ta kashe wayar tare da yin jifa da ita,tana fitar da wani irin zazzafan hucin ta shin hankali, Allah dai yasa ba shegun nan ne suka dawo ba,duk da cewa bata tunanin hakan zai tabbata amma tana matuƙar jin tsoron faruwar hakan. Yana yawan shiga ɓangaren inno dan kawai ya duba yaga ko su Abdallah sun dawo,sai dai kuma har yanzu da lokacin ranar ya kusa wucewa shuru kake ji babu alamar dawowar su,har inno sai da taso gane wani abu atare da shi saboda yawan shigo mata yake yi duk minti bayan minti,a shigowar sa ta wajen biyar ne inno tace" wai kai lafiyar ka kuwa ɗan nan ko dai da wani abu da kake jira ko kake nema?yace"ba wani abu inno kawai dai ina ɗan duba lafiyarki ne!'ya faɗa tare da ficewa daga falon,inno ta bishi da wani mugun kallo tare da fidda wani ɗan sauti kamar irin ƙwafa ɗin nan,a bayyane ta furta cewa komai ya kusa zuwa ƙarshe ayi dai mu gani!' Samuyal yace"wallahi Oga tun da muka dawo taƙi yin magana daga ƙarshe ma sai ta yi suman da muka kasa gane kanta,tun jiya muke sheƙa mata ruwa amma taƙi farfaɗowa,gashi kuma tana numfashi da'a lama dai ba mutuwa tayi ba!'Safwan ne ya ɗora da bawa Abdallah labarin abinda ya faru dasu ajiya wajen tahowa da Abigirl ɗin,shuru Abdallah yayi tare da tsurawa fuskar Abigirl ɗin idanu,ɗan jin jina kansa yayi kana ya fita daga ɗakin,ɗakin Saiyyid ya shiga yaja kujera ya zauna yana fuskantar Sayyid ɗin,cikin matuƙar kaushin murya Abdallah ya shiga korawa Sayyid gargaɗi yace"wallahi Sayyid idan ka sake ka kalli inda nake Acikin estate to zakayi nadama balle kuma ka ambaci sunana,kuma bawai ina maka gargaɗi dan ina jin tsoro bane a'a sai dan kawai inason kammala aikina lafiya,zan mai dakai gidan ku amma idan kana sha'awar cigaba da zaman rashin ƴanci to ka gwada yin abinda bana so!'daga haka ya kira Daniyal tare da bashi umarnin ya ɗauki Sayyid ya maida shi ESTATE kar kuma ya bari aganshi yasan inda zai ajiye Sayyid ɗin, Daniyal ya amsa cike da girmamawa kana ya juya ya fita daga ɗakin,Yahya ya kirawo dan ya mayar dashi estate, Hajiya zulaiha kuka take nasamun rangwamen abinda ke damun zuciyar ta,jin wannan al'amari take kamar almara wai yau Alhaji Baba da kansa ya tara mutane dan sanar musu zai sa afara neman ABUBAKAR,tabbas ta daɗe tana jiran wannan rana me ɗin bin tarihi,hakanan kuma take jin wani farin ciki tun bayan gobarar dakin can,wanda ta rasa dalilin haka, Rahima da bata jima da dawowa daga can egift wajen yayan ta ba,ta matso kusa da mahaifiyar tata,cikin tausayi irin na ƴa ga uwa tace"Ammi yauma dai har da kuka kuma duk da kince kar na kuma magana akan damuwar ki!'da sauri Ammi ta jawo ta jikin ta,tana cewa yau insha Allah zan baki labarin mahaifin ki da ɗan uwanki, alokuta da dama inason yin magana amma sai hakan ya gagara ban san meye dalilin ba, amma yanzu kamar wadda aka cirewa wata ƙaya daga cikin maƙogaro haka nake ji,amma ina fatan hakan ya zama silace ta warware mana dukkan matsalolin mu!'kuka Rahima take yi sosai kamar zata shiɗe bayan ta gama jin labarin mahaifinta da dannuwanta wanda ita a tunanin ta mahaifinta ya mutu,ta kanƙame Ammin kamar zata koma cikin ta,wayyo Ammi na dama wannan baƙar damuwar kike shaƙa shekara da shekaru ke kaɗai ban sani ba,dan Allah Ammi na ki yafe min gurguwar fahimtar da nayi miki Abaya,duk rashin sani ne wanda yafi dare duhu!'ta ƙare maganar cikin ƙara ƙanƙame Ammin,shafa kanta Ammi take cikin san lallashin ta,tace"ba laifinki bane nima kuma ba laifina bane,wan nan abinda ya sameni ba Ni kaɗai bace duk ahlin ALHAJI BALARABE ne,kamar anrufe baki da idanuwan mu babu wanda yake iya furta sunan mahaifinki acikin gidan nan,sai dai kabar damuwar ka cikin ranka tayi ta kassara lafiyar ka,dan haka yanzu godiya zamuyiwa Allah da ya bamu ikon tunawa dasu wanda hakan ma wata babbar nasara ce,a garemu,kinga zamuyi addu'a da bakunan mu mu roki Allah ya baiyana mana su aduk inda suke. Ta gumi ta zuba ɗan duk sai taji ranta babu daɗi akan abinda Inno da Hajiya Babba sukayi ɗazu a falon Alhaji Baba,ko me hakan yake nufi kuma?dama da akwai wannan kishin tsakanin su?duk sai taji ta tsargu to me Hajiya Babba take shirin faɗa Inno ta tareta?miƙewa tayi tsaye tana cewa tabbas bazan iya haƙuri ba sai na je nasamu inno da maganar dan Ni ban iya ƙunbiya ƙunbiya da munafunci ba dan haka bazan bari ayi min ba,ta zari mayafinta tayi waje dan zuwa sashen Inno, Daniyal yayi nasarar kawo Sayyid gida ba tare da kowa ya ganshi ba,daƙyar Sayyid ya iya ta kawa zuwa cikin estate ɗin saboda daure war da ƙafafunsa sukayi wajen zama guri ɗaya,yana shiga get ɗin farko ya cikaro da Dady Habib zai fita amota,ɗaga masa hannu yayi kasan cewar baƙin glace ne yasa shi Sayyid ɗin bai gano Dady Habib ɗin ba ya dai gane motar sa kawai,cikin sauri Dady Habib ya taka burki tare da fitowa daga cikin motar jikin sa har rawa yake saboda farin cikin ganin Sayyid, rungumo shi yayi yana duba jikin Sayyid ɗin tare da cewa Sayyidi ina fata dai kana lafiya babu abinda ya same ka suwaye suka sace ka?duk ya jero masa tambayoyin ajere, Sayyid yace"Dady nima ban san su ba,muje ciki a gajiye nake sosai!'cikin rawar jiki Dady Habib ya saka shi cikin motar kana ya zagaya ya shiga yaja suka nufi cikin estate ɗin. Wata irin zabura Anty Nafisa tayi yayin da taci karo da hotan Bintu a kan scring ɗin wayar,jikinta da zuciyar ta babu abinda sukeyi sai rawa,zubawa hotan ido tayi tana kallon wata fuska acikin fuskar Bintu,shin WACECE BINTU,me tazo yi ESTATE kuma meye haɗin ta da waɗan nan mutanen da Umar yake zuwa wajen su, su ɗin su waye?wai mai ke shirin faruwa da Nine?yana ke ganin fuskar Bintu na juye min da wata fuska da na sani?me yasa tun farko ban fara buncikar yarinyar nan ba na yadda da ita haka?me yashiga kaina alokacin?cikin sauri ta ta danna kira,ana ɗagawa tace"cakewa kayi gaggawar buncikomin asalin mutanen da suke zaune agidan nan, da matsayin su agurin Umar bana son ɓata lokaci kamar yadda katuran hotan nan a yau shima ina so wannan ayau ka bincikon abin da nake da bukatar sani!'yace"angama Hajiya karki damu zaki samu yadda kike so!'ajiye wayar tayi tana ci gaba da kaiwa da kawowa aɗakin dan batajin yau zata iya zama batare da taji sakamakon binciken da tasa ayi mata ba. Dady jafar ya dubi Dady Mansur cikin mamakin sa yace"dama wannan shine kiran da kayi min amma kuma me yasa kake son kasan inda Abdallah da Bintu suke,meye damuwarka da hakan, kuma me zakayi musu?Dady Mansur yace"Jafar bazaka ne komai ba yanzu amma dan Allah inaso ka taimaka kagayamin inda yake saboda ina buƙatar ganin su da gaggawa!'wani mugun kallo Dady jafar ya watsa masa kana yace"amma Mansur baka ji daɗi ba Nima ka biyoni ne dan kayi min yaudarar da kasaba yiwa mutanen gidan ku?to bari kaji na gaya maka Mansur tuntuni anyi walƙiya na ganka kuma sauran mutane ma zasu ganka insha Allah sai asirinka ya tonu a idon duniya,kuma zaka girbi abinda kake shukawa,saboda ɗan zaki ya riga ya girma shine zai cinye dukkanin mugayen kananun namun daji!'yayi wani irin murmushin takaici me ciwo ya cigaba da cewa Allah ya riga ya nufi zakaran da cara babu yadda zakuyi dashi sai dai kallo!'shuru Dady Mansur yayi saboda ayanzu dai bashi da ta cewa duk bakin sa amma yanzu ya baya iya maida magana,dan haka ne bai tankawa Dady jafar ba har yayi ya gama ya barshi awajen, Dady Mansur yayi mamaki lokacin da ya koma gida ya samu Sayyid tsaf dashi duk gida ya ɗauka da barkar dawowar sa, sai zuwa sashen Dady mansur akeyi barka kamar wanda akayi wata haihuwa,cike da farin ciki ya rungume ɗan nasa duk da halin da zuciyar sa take ciki a yanzu na rashin walwala da tsananin damuwa amma hakan bai hana shi jin dadin ganin ɗan nasa ba,duk wanda yayiwa Sayyid tambayar waye suka sace shi,to amsar dai ɗaya ce,shima bai sani ba,dole kowa ya haƙora da tambayar ya kama sabgogin sa. Kamar daga sama ta samu wayar uwar gidan ta, Cikin rawar jiki Dije ta ɗaga, daga can ɓangaren matar tace"Dije ya batun alƙawarin mu?ina fata dai zan samu kyakkyawan labari?cikin farin ciki Dije tace",tabbas kin kira lokacin da ya dace dan kuwa cike nake da ɗokin haduwa dake dan sanar miki abinda zai matuƙar faranta zuciyar ki!'wata dariya ta saka daga can kana tace"shi yasa nake matuƙar ji dake Dije, kuma na koma inuwa nayi zamana hankalina kwance saboda nasan ina dake,yanzu yamma tayi kuma kinga akwai al'amuran da ake dan gabatar wa a cikin gidan dan haka gobe kiyi sammakon fita zan tura miki da wajen da zamu haɗu bayan fitarki!'Dije tace"to ranki shi daɗe,Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya,tana kashe wayar tayi wani murmushi wanda yake baiyana ƙwarin gwiwar ta tare da cewa ko ke wacece taki ta kusa ƙarewa gobe i War haka kina nan kina zaman makokin kanki da kanki. Tun daga farkon shigowar sa gidan yasan cewa komai yana tafiya yadda suka barshi,ga wan can al amarin ga kuma dawowar Sayyid,kai tsaye ya wuce part ɗinsa dan komai dake faruwa ba baƙon sa bane,yana shiga duk sai yaji falon yayi masa faɗi har cikin jinin sa yake jin damuwar ta da kuma kewar ta,ga kuma uwa uba tausayin ta dake neman zauta zuciyar sa,cikin sanyin jiki ya gabatar da al'amuran sa na yau da kullum,wayar sa ce tayi ringin, har zai basar da kiran sai kuma yaga Dady jafar dan haka ya daga tare da yin sallama,ba tare da ya saurari gaisuwar da Abdallah yake masa ba, yace"Abdallah tun tuni na gaya maka ka saka idanu akan Mansur amma ka banzar da maganata,to yanzu umarni nake baka kasa ka ido sosai akan sa dan ina matukar zargin sa,nan ya bashi labarin yadda sukayi ɗazu da yadda ya damu sai yasan inda suka je shida Bintu,numfashi Abdallah ya fesar kana yace"Dady karka damu zan kula da komai!'kafin ya sauke wayar daga kunnen sa wani kiran ya shigo ba tare da ya duba ba ya ɗaga, dan azaton sa ko Dady jafar ɗin ne ya sake kira. Sannu ɗan zaki to idan kana buƙatar zakanyar ka,ka taho da zakin ubanka ka fanshi zakanyar matarka,idan kuma baka buƙatar ta yanzu saina fasa kanta da bakin bindiga, zanga irin naka halaccin idan ka gama tunani zan kuma kira dan yi maka sauran bayani inda zaka same mu kuma muddin kasarwa na jami an tsaro to wallahi ina tabbatar maka da cewa sai na kashe matar ka koda za akamani, na barka lafiya kayi tunani mai kyau matar ka ko mahaifinka?daga haka ƙit aka datse kiran. Fatimah Y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 52 ``` Wani irin rawa jikin Abdallah ya shiga yi,ɓacin rai da tashin hankali shi kawai zaka iya hanga akan kyakykyawar fuskarsa,wani irin miyau yake haɗiyewa mai tsananin ɗaci da kauri,gaba ɗaya kansa ya kulle ya rasa ina zai nufa,da abinda ya kamata ya farayi yanzu,kiran Dady jafar yayi wanda tuni shi har yayi bacci,cikin yanayin bacci ya daga wayar tare da cewa lafiya dai ko Abdallah?kasa magana Abdallah yayi saboda abinda ya tokare masa aƙirji da ƙyar ya iya cewa Dady sun ɗauke Bint!'Dady jafar dake kwance bai san sanda ya miƙe tsaye ba cikin tashin hankali da kiɗima yace"kagani ko Abin da nake gaya maka,Mansur ya sace yarinyar nan,shine dama dalilin da yasa yazo yana min tambayar inda kuke? Abdallah yace"Dady yanzu ya zamuyi ban karbi lambar su Hajjo ba bare na tambaye su naji gaskiyar maganar!'Dady jafar yace"kaga Abdallah fito yanzu mu haɗu ai bamu ga ta zama ba idan ma can sulejan zamuje sai muje mu duba!' Abdallah yana fita motar sa ya faɗa yana shirin tayar da ita,aka dallare shi da futula,kare fuskar shi ya shiga yi,ba kuma tare da ya saurari me haske shin ba ya fixgi motar da wani irin mugun guda, Dady Habib dake tsaye hannun sa riƙe da fitila ya zubawa hanyar da Abdallah yabi ido cikin tunanin inda zashi da wannan daren, sai kuma yayi tunanin ko wani aikine ya taso masa,dan haka ya juya ya koma ɓangaren sa. Gudu yake tamkar zai tashi sama bayan ya dauki Dady jafar,magana wannan ta gagara a tsakanin su kowa da abinda yake tunani acikin ransa, zuciyar Abdallah kuwa ko shiga kayi to tabbas sai ka ƙone,saboda tsananin zafin da take masa ƙirjin sa har wani sama da ƙasa yake yi,a cikin wannan halin suka ƙara sa gidan Hajjo,ko kashe motar baiyi ba,ya fita da wani irin saurin gudu,Dady jafar ma binsa yayi dan bayajin zai iya tsayawa jiran iso,buga gidan ya shiga yi cikin wani irin sauke numfashin fargabar abinda zai tarar,daga ciki kuwa atsorace, Asma'u ta kalli Hajjo tace"Hajjo yau mun shiga uku, wannan wace irin rayuwa ce,wai yanzu idan kana da arziƙi ashe baka huta ba,idan baka dashi ma baka huta ba,ta faɗa tana fashewa da wani matsanan cin kuka,da ƙyar Hajjo tace"insha Allah babu abinda zai faru da Batula,ki duba wannan bugun ƙofar da akeyi ko da bamu buɗe ta ba za a iya ɓallata,aiko bata rufe bakinta ba, Abdallah ya saka mata karfi ya doke kofar sai ga ta aƙasa,shiga yayi ya tarar da su Hajjo atsaye cirko cirko cikin tashin hankali,zubewa yayi agaban Hajjon tare da sunkuyar da kansa ya kasa ce mata komai,Dady jafar ne ya iya cewa garin yaya haka ta faru?shin da gaske ne,an sace Bintu?ya jero musu tambayar cikin san amsar su da gaggawa,A hankali Asma'u tace"da gaske ne ku waye yasanar daku?miƙewa Abdallah yayi ya fita daga gidan ba tare da yace"kan zil ba,Dady jafar ne yayi ƙoƙarin yi musu tambayoyi ba tare da ya amsa mata tata tambayar ba,yace"ya akai haka ta faru?Hajjo da sai yanzu ta iya magana amma da tausayin kanta dana Abdallah ya hana ta cewa komai,ita kam anyi mata taleƙo ta koma,tace"bayan sallar isha babu jimawa suka zo, duk da gidan mu arufe yake amma bugun da sukayi mana cikin nutsuwa da jan hankali shine abinda ya kwashe mu har muka buɗe musu,abinda ya biyo baya ne baiyi mana daɗi ba dan kuwa ta ƙarfi suka ɗauke Bintu tare da saita ta da bindiga acewar su duk wanda ya motsa acikin mu sai sun fasa kan Bintu da bindiga!'ta faɗa tana mai ƙara fashewa da matsanancin kuka,Dady jafar yace"shike nan bari muje nasan zasu iya kara kiranmu zamu san me zamuyi ku kwantar da hankalin ku insha Allah babu abinda zai faru!'daga haka yabi bayan Abdallah,ya bar su Hajjo cikin rashin nutsuwar zuciya... "Abdallah ya samu, ya kifa kansa da styarin motar har yanzu ko fitar numfashin sa baka jin sautin sa,Dady jafar yace"Abdallah dawo nan na tuka motar!',baiyi masa musu ba ya fito ya koma sit ɗin mai zaman banza. Tafiya suke kawai ba tare da sun san inda zasu nufa ba gashi har yanzu sun rasa tunanin da zasuyi akan lamarin,kamar daga sama Dady jafar ya tsinkayo Muryar Abdallah yana cewa Dady na samo mafita!'Dady ya danyi slow da tuƙin,kana yace"da Abdallah mecece mafitar?lumshe idanun sa yayi tare da maida kansa ya kwantar yace"zamu kai Dady kamar yadda suka buƙata!'daga nan ban kuma jin abinda Abdallah yake cewa ba, ban ankara ba kawai sai gani nayi Dady jafar yayi ɗan murmushi tare da cewa wannan mafita ce mai kyau!'wayar Abdallah ce ta fara dan wani sauti mai daɗi, dagawa yayi tare da kaita kunnen sa,kamar yadda zuciyar sa ta raya masa wanda ya kira hakan ne ya tabbata, cikin shaƙewar muryar da kanaji kasan sauyata akayi,yace"ya dai ɗan zaki ka shirya?me kake da bukata matarka ko mahaifinka?zan kawo maka mahaifina idan shi kake buƙata,amma ina da sharaɗi!'wata dariya ya sheƙe da ita kana yace"ina jin ka ɗan zaki faɗi sharaɗinka!'Abdallah yace"karka kuskura ka taɓa Bint ko cizon sauro na samu ajikin ta baza kaji daɗin abinda zai biyo baya ba,kuma Ni zan baka lokacin da zan zo dan haka ka bani layin da kasan zan same ka!'nanu yace"lallai yau na kuma yarda ɗan zaki ya girma tunda gashi har kana shirin yi min wayo,to ban yarda da wannan sharaɗin naka na ƙarshe ba,zan kiyaye kiranka akai akai shine kawai abinda nasan zan iya yi maka!'daga haka ya kashe wayar,dan murmushi Abdallah yayi wanda yafi kuka ciwo, Ƙara gudun motar Dady jafar yayi kana yace"tabbas Abdallah ina zargin Mansur sai dai kuma na rasa dalilin da yasa zuciyata take ƙin karɓar abun!'cikin wata irin murya wadda take cunkushe da ɓacin rai da baƙin cikin kasa kiyaye rayuwar Bintu,yace"Dady a yanzu ba mune abun tausayi ba sune abin tausayin tabbas rayuwar makafin zuciyoyin mutanen nan tana cikin hadari,nan gaba kaɗan zasu zama A baban tausayi a idanun waɗan da basu san abinda suka shuka ba!'daga nan gidan su na asali gidan Dady jafar nan suka wuce, Washe gari da sassafe Dije ta fito daga cikin babban birnin estate,cike da ɗokin wannan rana, wadda take fatan tazo mata da nasara,wayar tace tayi haske alamar shigowar saƙo,dubawa tayi daga Hajiya ne tana sanar mata cewa taga fitowar ta ga kuma in da take so su haɗu,tana gama karanta wa ta fara kiran Bintu,sai dai kuma kash wayar akashe take,cikin cizon yatsa Dije ta juya akalar kiranta kan Abdallah,shi kam bata sha wata wuya ba ya ɗauki kiran, alokacin Dady ya tasa shi gaba da ƙyar sai ya sha koda ruwan shayi ne,da sallama ya fara,Dije ba tare da ta tsaya wata doguwar magana ba ta shiga zaiyano masa abinda ke faruwa da abinda take so su shirya ayanzu,da sauri Abdallah ya tashi tare da ce mata gashi nan zai zo yanzu,ta ce amma kayi hattara fa bana so ta ganka balle yaddar dake tsakanin mu ta rushe!'yace"insha Allah karki damu!'daga haka suka aje wayar,ɗan kallon Dady jafar yayi wanda tunda ya fara wayar yake kallon sa cike da san gano wanda yake wayar dashi,hanya ya kama zai fita yana cewa Dady yanzu sauri nake idan na dawo zanyi maka bayanin abinda ke faruwa!'jinjina kanshi Dady jafar yayi tare da cewa Abdallah fatan nasara!'yana zuwa ya shiga mota ya ja da mugun gudu, A cikin kuma safiyar nan ne dai Anty Nafisa ta samu mugun saƙamakon da ya nemi zaucewar ta,wato yaran ta sun tabbatar mata da cewa mutanen nan daga Yola suka taso,kuma sunan Hajjo raɗau ya zauna mata da sunan Asma'u wanda bata manta su ba tun a wancan lokacin,tashin hankali wanda bazai misaltu ba agurin ta,da ta rasa yadda zatayi kawai sai ta ɗora hannun ta aka ta fasa wani gigitaccen ihu wanda yake haɗe da kukan tashin hankali,Abba Umar dake shirin fita dan tafiya gidan Hajjo,da sauri ya buɗe ƙofar dakin nata ya shigo yana cewa'lafiya dai Nafisa?meke damunki?bata iya bashi amsa ba sai wani irin mugun kallo da tabishi da shi a fakaice,tashi tayi ta wuce shi ta faɗa toilet tare da banko ƙofar,ɗage kafaɗunsa yayi tare da ficewa daga dakin,tana jin fitar sa tayi saurin fitowa tare da kiran yaran ta,yana daga wa tace"kawai kusa wa gidan wuta amma kutabbatar da cewa Umar yana gidan, ku saka masa ido dan yanzu ya fito kuma ina tunanin nan suleja zai nufo,kar ku sake kubar wata halitta da rai acikin gidan!'yaron yace"Hajiya Nafisa aikin nan ba zai yiwu da safe ba dole sai cikin dare, zamu saka wuta a gidan!'Anty Nafisa cikin tsawa tace"ni dai koma mai zakuyi ku tabbatar da cewa kun kashe mutanen nan ayau ba sai gobe ba,idan yaso shi ku kama shi a hanya ku fara kashe shi daga baya sai ku koma ku ƙona gidan!'tom ranki ya daɗe an gama in dai mu zaki bamu kuɗaɗe to baki da matsala da mu!'daga haka suka yanke wayar, Abba Umar dake jikin ƙofar ɗakin Anty Nafisa,babu abinda yake sai zufa jikin shi kuwa wani irin kyarma yake saboda tsabar razana,wani irin tashin hankali ne ya rufe shi tare da mamaki tsanani,me hakan yake nufi?kashe su Nafisa tasa ayi shida su HAJJO?to akan me?me sukayi mata?a ina ta san su?ya akayi tasan inda suke?wai meke shirin faruwa ne?ko dai zarginsa akan Nafisa daidai ne?tabbas Nafisa itace ta salwan tar da rayuwar iyalan sa,ita ce Ummul aba'isin shigar sa wannan halin,cikin sauri ya sauka tare da wani irin gudu,motar sa ya faɗa tare da jan ta da wani irin mugun gudu. Tunda aka dauko ta bata san inda kan ta yake ba,sai yanzu da ta farfaɗo daga suman da tayi,tun bayan shigowarta cikin ƙungurmin dajin,wanda komai akan idonta ya faru,ko rufe fuskar da ake yi wa wanda akasato basuyi mata ba,hakan ne ma ya bata damar gane cewa daji mai tsananin haɗari suka shigo,razar da tayi ne yasa ta suma,shine bata far faɗo ba sai yanzu wajen misalin ƙarfe tara na safiya, bin ɗan tsukakken dakin tayi da kallo kana ta tsaida idanun ta akan basamuden dake tsaye akanta da sunan gadi,kawar da fuskarta tayi,yayin da idanun ta suka ciko da ƙwalla,ko ya Yah Abdallah zaiyi da wannan sarƙaƙiya da aka saka shi dan komai da yafaru akunnen ta ya faru sai dai ba akan idanun ta ba tunda har yanzu batayi ido hudu da Oga kwatakwata ba,wanda ita kuma fatan ta kenan ganin wanene wannan baƙin azzzlumin,ko da daga haka ƙarshen numfashin ta yazo,yanzun ma bata karaya ba saboda tasan halin gwarzon mijin ta tasan bazai batta agurin nan ba,kuma bazai bari su kashe ta ba,indai har ba Allah ne yayi zata mutu ba,kuma tasan bazai kawo masa Dady Abubakar ba,kuma ko anan ba zata fasa ƙoƙarin ta na ganin bayan azzalumai ba,insha Allah alƙadarin su ya karye karshen zaluncin su yazo.. Ya dade da samun guri ya fake,tun daga zuwan ta har shigar ta ɗan tsukakken lungun da bai wuce kamu goma ba, duk akan idon sa,nutsuwa ya sake yi wajen miƙa hankalin sa kanta,sai da ya tabbatar ta shiga ciki kana shi kuma ya bi bayan ta cikin nutsuwa da sanɗa irin ta ɓarayi,Dije ta samu zaune akan ɗan kututturen dutsen dake girke a wajen tana saƙa da warwara,da sauri ta tashi tare da cewa ranki ya daɗe kin ƙara so?duk da bata ga fuskar matar ba ta tabbatar da cewa murmushi tayi,cikin ƙasai tacciyar Muryar ta ta isa da taƙama tace"Dije tawa Dije aikin ki na kyau yadda ya kamata,maza tashi ina saurarenki ki sanar dani inda Abubakar yake da wannan mutumin ko waye!'cikin yin ƙasa da kai Dije tace"ai ranki ya daɗe Abubakar yana hannun Mansur kuma man sur shine wannan mutumin dakike ta son sani tsawon shekaru amma hakan ya GAGARA,,daɓas taga ta zauna akan ƙasar gurin jikin ta yana wani irin kyarma kamar ana kaɗa mazari,shuru ne ya gifta ta ta wajen kamar babu wani halitta agurin,yayin da Abdallah ya kuma gyara tsayuwar sa yana mai kafe fuskar matar da ido zuciyar shi na dokin ganin fuskar ta ta ainahi. Yana zuwa yasa su Hajjo suka fito da komai nasu ba tare da ya amsa musu tambayoyin da suke ta jera masa ba,sai da suka shiga mota kana yace"da Anty Asma'u ƴan biyu suna Yola ko? tace e suna can basu dawo ba!'daga haka bai kuma cewa komai ba yaja motar suka fara tafiya,tunda ya fara tafiya ya kula da motar dake binsa,kuma zuciyar shi ta aiyana mashi cewa mutanen Nafisa ne suke binsa,A hankali ya dinga rage gudun motar har ya tsaya agefan hanya,yana kallo suma sukayi fakin abayan motar tasa,Hajjo da ta kula da abinda ke faruwa tace"Umaru mai makon mu guje musu sai kuma kanemi guri ka tsaya!'yace"Hajjo da akwai abinda nake son aiwatarwa!'ƙwanƙwasa glace ɗin window sa da akayi shi ya maido da hankalin sa wajen,zuge glace ɗin yayi,yana kallon yaron da ya tsare shi da jajayen idanun sa da suka sha sukayi tatil,yaron ji yayi kawai ya kasa aiwatar da abinda yayi niya akan Abba Umar,wani irin kwarjini yayi masa,wanda har bai san sanda Abba Umar ɗin ya fito daga cikin motar ba,sai ji yayi yana cewa ɗan samari nasan abinda ya kawo ku gurina ko nace yasa kuke bina!'dafa kafaɗar sa yayi suka fara tafiya, ɗan nesa da su Hajjo suka tsaya,daga nan sukayi magana da Abba Umar wanda sam basu bari naji abinda suka ce ba,na dai ga kawai sunyi hannu da Abba Umar, da sauri, Abba Umar ya koma motar sa yaja ba tare da yayiwa su Hajjo bayanin komai ba.. Sai da taja mintuna a haka kana ta tashi ta kaɗe jikin ta,idanun ta sunyi jajur saboda yanayin firgicin da tashiga,kallon Dije tayi tare da cewa, Dije na gode da ƙoƙarin ki gareni kuma yanzu zan cika miki alƙawarin da nayi miki,daga nan ba zamu wuce ko ina ba sai inda na ajiye miki yaran ki,kuma suna nan babu abinda ya same su kamar yadda na alƙawarta miki!'Dije tace"naji wannan ranki ya daɗe saura ɗayan alƙawarin!'Hajiya tace"ina sane da wannan ma amma shi ina so kiyi min alfarmar bari muje inda yaranki suke sai na buɗe miki fuskata acan!'Dije ta jinjina kanta alamar gamsuwa,sai dai kuma Abdallah fa ya zatayi dashi?wata zuciyar tace"da ita, kema kin san kowaye Abdallah ba zai rabu da ku daga nan ba dole zai biku ko dan sanin manufar ki ta bin matar bayan ba haka kukayi ba,hakan yasa ta sauke guntuwar ajiyar zuciya,tare da bin bayan matar da ta ƙauta taga fuskar ta, Sai dai kuma abinda Dije bata sani ba shine komai akan kunnuwan Abdallah suka faɗe shi, dan kuwa Allah ya bawa Abdallah ji tamkar maciji,dan haka yana jin haka yayi saurin fita daga inda ya ɓoye,motar sa ya koma yayi shirin bin bayan su Dije ba tare da ya bari matar ta gano shi ba. Sai da suka ɗan yi nisa kasan cewar a Nafef suke shi yasa basuyi masa nisa ba,haka kuma ya dinga binsu cikin nutsuwa ba tare da ya bari sun kula da hakan ba,tafiya sukayi doguwa sosai,kana suka shiga wata hanya kamar hanyar da zata iya kai ka zuwa wani ɗan ƙaramin ƙauye,wajen shuru babu kowa sai gidan ƙwalli ɗaya a gefan gonakin mutane,tsayawa sukayi ta sallami mai adaidai ta sahun su kuma suka shige cikin ma daidaicin gidan, Abdallah baiyi gangan cin binsu ba sai da yaga mai Nafef ɗin ya fito kana,ya bisu bayan yayi fakin ɗin motar sa acan baya,shiga yayi gidan cikin sanɗa da kiyaye wan da zai iya ganin sa. Duk ma aikatan da suke mata gadi acikin gidan bin ta sukayi suna girmamata tare da bata bayanai akan cigaban da akasamu na aikin da yake wakana A cikin gidan,hakan ne ya bawa Abdallah damar shiga gidan ba tare da sun ganshi ba,sai dai kuma ɗakin da suka nufa ne ya ɓace masa kamar wasu walƙiya haka suka ɓace masa,ko magan ganun su baya ji,ɗan jim yayi cike da tunanin abinda ya kamata yayi,fara tafiya yayi cikin sanɗa yana bin bango,wani ɗaki ya hango yana facin ɗinshi,ƙara sawa yayi bakin ƙofar ya ɗan kara kunnen sa ko da zaiji sautin maganar su,sai dai maimakon haka sai sautin kuka da yaji da kuma addu'oin da akeyi, Allah ina rokon ka ka kawo ƙarshen matar nan, ka kawo me kuɓutar damu daga wajen nan dan girman annabin da alƙur ani!'ji yayi kawai ya murɗa mariƙin ƙofar ga mamakin sa kuwa sai yaji ta buɗu,ba tare da tsoro ko shakka ba ya saka kansa dan ya tabbatar ba dakin su Dije suka shigo ba. Da sauri ta ɗago kanta da yake sunkuye tana ta malalar hawaye,kallon kallo suka shiga yi tsakanin ta Abdallah,wan da shi kuma Abdallah tuni ya shiga wani irin shock mai ƙona jinin jiki,kallon fuskar matar sa Bintu yake yi acikin fuskar dake gaban sa, sai dai kawai wahala da girma su ban banta Bint da wannan matar dake gaban shi,da sauri Laila ta miƙe tana cewa zuwa kayi ka fitar damu ko? Allah ne ya turoka,maza mu tafi mu dauko yaya, dama naji ajikina yau addu'a ta zata karɓu yau Allah zai fitar damu daga cikin wannan uƙubar!'ta faɗa tana kama hannun Abdallah da ya rasa abin cewa saboda tsabar mamaki da al'ajabi,idan tunanin shi ya bashi dai dai kenan wannan itace Laila mahaifiyar bint ɗin shi,tunanin sa ne ya katse lokacin da yaji muryar ta kuma dukan dodon kunnen sa tana cewa mai ka tsaya yine ko ba mu kazo taimako ba?za fa ta iya zuwa ta same mu idan bamuyi gaggawar barin gidan nan ba!'hakan da ta faɗa ne ya zaburar da Abdallah yaja hannun ta da sauri yana cewa ina fafy yake?duk da tayi mamakin ambatar yayanta da fafi da yayi amma hakan baisa ta tsaya yi masa tambayoyi ba,cikin san ɗa suka fita daga ɗakin,A hankali suka murɗa mariƙin dakin dake kusa da na Laila,cikin ikon Allah shima suka samu A buɗe yake,da sauri suka kamo fafi da ko magana baya iya yi saboda tsananin cuta da jigata ko kansa bai san inda yake ba,sunkutar sa Abdallah yayi tare da kama hannun Laila,cikin ƙudurar Allah da nasarar dake bin rayuwar su,suka fita daga gidan ba tare da ko tsuntsu ya gansu ba.. Da gudu Dije ta ƙarasa ta rungume yaran ta da sukayi zuru zuru saboda tsabar kewa da zaman guri ɗaya, duk da dai an kwana biyu ba ayi musu wata azaba ba,sun daɗe suna kuka ita da yaran ta,yayin da su kuma su Hajiya suka tsaya suna kallon su duk da bawai tausayi ne ya sa su kallon na su ba,abin mamaki babu wanda yayi musu magana ko tsawa wanda dalilin hakane yasa suka kwashi kusan minti ashirin A haka,daga bayane Hajiyar ta kalli yaranta tare da cewa ku ba mu guri zamuyi magana,kuma ku tabbatar kun kula da ragowar Ajiyar dake gidan!'fita sukayi tare da jawo musu kofar,dan taku tayi biyu zuwa uku kana ta tsaya tare da cewa Dije ko kin san cewa mahaifiyar Bintu na cikin gidan nan?maganar ce ta zowa Dije a wani irin bazata bata gama fita daga wani shock din ba ta shiga wani, sakamakon saka hannun ta da tayi akan fuskar ta tana yaye liƙabin fuskar ta,miƙewa Dije tayi tana nuna ta da yatsa cikin tsananin firgici da kiɗima da mamaki da tashin hankali,bakinta na rawa tace"in........... Kar ku manta ganin COMMENT ɗinku shike bani ƙarfin gwiwa... FATIMAH Y ADAM✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 53 ``` Innalillahi'wa'inna ialaihi raji'un,t faɗa tana da ɗa murza idanun ta cike da mamakin wadda ta gani,ba ƙaramin shock ta shiga ba ganin matar dake tsaye gaban ta,cikin tsananin ruɗani da mamaki gami da tashin hankali take nunata da yatsa bakinta yana rawa ta gaza furta abinda take son furtawa,zuciyar ta babu abinda take sai ta riyo mata irin karamci da Mutuncin matar,kai ita Dije ma zata iya cewa duk gidan Alhaji Baba babu macen da tafi kirki da mutunci a idanun ta kamar wan nan dake tsaye agaban ta,ta tuna lokacin da tazo gidan amatsayin mai neman masauki,itace wadda ta fara karbar ta,tare da bata masauki kafin daga baya ta haɗa ta da ɓangaren Dady Mansur,to hakan yana nufin duk shiri ne?dama da manufa tayi mata hakan?lallai kuwa idan haka ne wannan mata ta cika cikakkiyar makira kuma shu'ma,zilwaja haini,katse Dije tayi da cewa,kinyi mamaki ko Dije?to amma kuma idan kika bi ta wani fuskar ai ba wani abun mamaki bane,yanzu dai duk ba wannan ba abinda nake so dake shine ki tashi ki tattara yaranki da komatsanki zan baki kuɗin aikin ki,ki bar garin Abuja gabaki daya kiyi nesa da ita,bana buƙatar ganin ki acikin garin nan,saboda hakan shine rufuwar asirina!'Dije bata ce komai ba, sai miƙewa da tayi ta haɗa hannuwan ƴaƴan ta suka fara tafiya,matar tace"Dije baki ce komaiba me shurun ki yake nufi?Dije ta ɗan dakata ba tare da ta juyo ba tace"babu abinda shuru na ke nufi sai Alkhairi,kuma bana buƙatar komai daga gareki tunda kin riga kin cika alƙawarin da kika yi min haka ma na gode!'daga haka ta ja yaran ta suka yi waje, zuciyarta cike da baƙin cikin rashin Bintu ko Abdallah a wajen,gashi yanzu bata san yadda za ayi ta haɗu dasu har ta fayyace musu abin da ke faruwa ba. Wata mashahuriyar dariya ta fito tanayi wadda ke nuni da tsananin farin cikin da take ciki ji take kamar ta samu Abubakar ta gama,gashi kuma ta toshe duk wata hanya da zata iya tona asirin ta,dariyar tace ta tsaya lokacin da tashiga dakin Laila,zubawa ɗakin Ido tayi cike da razani da tunanin inda Laila ta shiga,da sauri ta buɗe ƙofar toilet ɗin dake ɗakin, dubawa ta shiga yi loko da sako,amma babu Laila babu labarinta,cikin wani azababban sauri ta fito tana ƙwalawa masu tsaron su kira,cikin rawar jiki duk suka nufota yayin da ita kuma ta waɗa dakin da fafi yake ciki,ga tsananin mamakinta shi ma baya nan, babu komai aɗakin sai tarkacen kwanikan da ake basu abinci,ihu ta saka tare da zunduma musu wata iriyar gunndume miyar ashar,cikin tsawa da yanayin hauka hauka na zaucewar tunani take cewa,me kuke yi suka gudu? kuna ina aka sace su?ɗaya daga cikin sune yace"ai Hajiya lokacin da kuka shigo gidan nan daga dakin su nake na kai musu abinci!'babban cikin su ma yace"tabbas Hajiya lokacin da kuka zo gidan nan ajiyar ki suna nan,sai dai idan bayan shigar mu dakin nan ne suka gudu!'zubewa tayi agurin cikin ɗora hannu aka take cewa shike nan asirina ya tonu,ya akayi na bari haka ta faru?ya akayi akasan da gidan nan duk takatsan tsan ɗin da nakeyi?dungu yace"Hajiya anya kuwa matar nan tana da gaskiya?anya bata haɗa miki gadar zare ba?wata irin zabura tayi cikin ihu tace"ku bi Dije ku samo min ita duk inda take,ku kawo min ita nan!'ta faɗa tana sharce gumin da yake ta wanke mata fuska,da gudu suka bazama neman Dije. To ya akayi Dije ta shammace ta haka?tabbas babu wanda ya isa yazo gidan nan sai wanda ya biyo bayan su,to waye ya biyo bayan su?wata zuciyar tace mata Dije ta riga ta shirya komai kafin haɗuwar ku,tabbas wannan shirin dagaDije ne makircin daga Dije ne,dama sun shirya yin komai ita da Bintu,to ya akayi BINTU tasan cewar iyayen ta suna wajenta?a kwai fa matukar ɗaurewar kai a cikin wannan al'amari,bata ga ta zama a wajen nan ba,dole ta tafi estate ta kasa ta tsare taga daga inda al'amarin ya ɓullo. Dije tana fita ta ɗauki hanya, sauri suke tamkar zasu tashi sama,saida sukayi dan nisa daga gidan kana suka tsaya maida numfashin gajiya,kamar daga sama suka ga mota A gaban su,kafin ta gama mamakin yadda akai mota tazo nan,taji Muryar Abdallah yana cewa yi sauri Mama Dije ku shigo!'Dije bata tsaya sanya ba da a zama ta tura yaran ta cikin motar kusa da fafi,itama ta shiga,da wani azabar gudu Abdallah yaja motar kafin ƙiftawar ido sun bace sai ƙurar motar sa,a daidai lokacin kuma yaran Hajiya suka ƙaraso gurin basu ga mota ba sai ƙurar mota,a take kuwa zargin su ya tabbata,juyawa sukayi jiki a san yaye,dan sun san zasu sha bala'i gurin Hajiya. Wai Abdallah har gida nawa ne dashi ne?nice nayi wa kaina wannan tambayar,ganin ya kuma kawo su Dije da Laila wani gidan mai shegen kyau, A hankali ya fito da fafy daga cikin motar,Laila ta kama hannun sa suka shiga takawa su Dije na binsu Abaya,sai da ya kai fafy har cikin daki yayi masa duk wani abu da ya kamata,kama daga karin ruwa allurai da sauran su,kana ya Umarci hafiz ɗan Dije da ya zauna a dakin tare da fafy ya dinga kula dashi,su kuma ya wuce dasu sama inda ya bawa Dije da salma ɗiyar ta daki ɗaya,daga nan kuma ya kai ummi Laila lafiyayyan ɗaki,sai alokacin yayi magana da ita,duban ta yayi cikin nutsuwa da girmamawa yace"Ummi ga nan dakin ku zauna a gidan nan gaba dayan ku,saboda kuna bukatar tsaro gaba dayan ku!'juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya sakamakon jin muryar da yaji tamkar Bint ɗinsa na magana, tace"samari ya kamata kayi min bayanin ko kai waye da kuma dalilin taimakon mu da kayi? ɗan murmushi yayi wanda sai da zuciyar Ummi Laila ta buga sakamakon ganin tsananin kama da ta hanga kan fuskar sa da kuma yanayin sa da mutumin da baza ta taɓa mantawa dashi arayuwarta ba,yace"karki damu ummi yanzu kuna buƙatar hutu zakiji duk abinda kike bukatar ji,amma kiyi haƙuri yanzu da akwai babban matsalar da nake son warwarewa,yanzu zan aiko muku da abinci!'ya faɗa yana ficewa daga ɗakin,zuru tayi tana daɗa kure bayan shi da takun shi da kallo,sak Umar ɗina ta faɗa tana waɗawa toilet dan yiwa jikin ta kyakykyawan wankin da ya dade bai samu ba. Abdallah bai bar gidan ba sai da ya tabbatar su ummi basu da wata matsala,har satar kallon ummi Laila yake saboda yadda take masa tsananin kama da Bintun sa gashi kuma tayi wanka tayi fes da ita cikin doguwar abayar da ya siyo mata,shi yasa duk damuwar sa ta karu ya ƙagu da yaga lafiyar Bint,tazo ta ga ya cika mata alƙawarin da ya ɗaukar mata akusa,yana matuƙar san ganin farin cikin ta wanda kuma hakan bazai taba samuwa ba har sai ya kuɓutar da ita daga hannun wani can azzalumin ya kuma kawo ta gaban ummin ta da fafyn ta, Daniyal ya kira ya kawo musu take away,kana ya umarce shi da ya zauna tare da su ya kula dasu A matsayin sa na namiji kuma ma aikacin tsaro,daga nan fita yayi shi kaɗai ya ɗauki Dady jafar A gida suka nufi inda suke son zuwa,tashar jirgin sama suka nufa inda suka haɗu da wani farin Bature, daga Ni ma dai ya ɗan jima yana jiran zuwan nasu,bayan dan gaisuwa ta mintuna ya miƙawa Abdallah saƙon hannun sa yana cewa gaskiya kayi sa a, sosai da samun wannan sakon a cikin kwana ɗaya da yini ɗaya! murmushi kawai Abdallah yayi ya juya suka bar tashar. Dady jafar ya ɗan dubi Abdallah kana ya maida kansa zuwa hanyar da suke bi,yace"yanzu meye mafita ta ɓangaren samun kiran nasa,kaga mun gama shirin mu yanzu shi muke jira!'abdallah yaɗanyi slow da motar kana yace"nima tunanin da nake kenan!'bai gama rufe bakinsa ba, sai ga wayar mutumin,da sauri Abdallah ya ɗauka yana mai fatan samun nasara tunda ya gane ko waye yake kiran,ba tare da ya bari ya saurari abinda zaice ba Abdallah ya tari numfashin sa da cewa,ɗan zaki ya shirya zuwa karbar zakanyar sa!'wata irin dariyar mugunta ya sheƙe da ita kana yace"yauwa ɗan zaki ka kyauta,ke nan ka shirya zuwa inda zaka samu zakanyar ka!'yace"kai nake saurare?cewar Abdallah ke nan,da zuciyar sa ke wani irin tuƙuƙi saboda sauraran Muryar wannan baƙin ƙumurcin,nanu yace"ina mai kuma yi maka gargaɗi akan zuwa da wasu mutane ko kuma jami an tsaro,yin hakan daidai yake da rasa matar ka da mahaifinka,nayi alƙawarin kashe su koda zan rasa rawa rayuwar kuwa!'cikin ƙosawa Abdallah yace"ina jiran address wannan duk na dade da kiyaye su!'hakan yayi kyau ɗan zaki,ka kalli fuskar wayarka zata haska maka inda zaka same mu ba tare jinkiriba!' Dady jafar ya dube shi da sauri yace"maza muje mu dauko Abubakar ɗin kar lokaci ya ƙare!'cikin hikima suka karbi Dady Abubakar daga wajen Malam na zaure,daga nan kuma sai suka dauki hanya,yana tafe yana waya dasu Safwan akan shirin kama su Alhaji Hashir da Alhaji Nasir da dai duk sauran ƴan tafiyar su, A can kuma su Abba Umar wani ɓoyayyen gidan sa ya kaisu su Hajjo,tare suka ɓoye kansu,dan gabatar da shirin da suka shirya, Da sauri ta ɗaga wayar da tun ɗazu tana hannun ta dan ta kasa ajiye ta gani take kamar labarin wani abun zai iya wuce ta,cikin sauri tace"ya akayi ina fata dai komai ya kammala?bansan amsar da aka bata acan ɓangaren ba sai kawai ta sheƙe da dariya cike da farin cikin samun nasara akan burin rayuwarta,tace"Barka" inawa kaina Barka kafin nayi muku Barka da arzikin dake bunku yadda kuka cika min burina nima zan cika muku alƙawarin da nayi muku dan haka yanzu ina jiran shaidar kashe su da kuma asusun bankin ku!'kashe wayar tayi ta bar su da sakin baki gaba dayan su wayar suke kallo yayin da suka shiga tunanin yadda za ayi su tura mata shaidar kisan da tasaka su aikata,sai dai kuma abunka da ƴan ta adda waɗan da suka saba aikata kisa a kowane lokaci kuma su ajiye record saboda wata rana,shi yasa basu sha wuyar turawa Nafisa fake ɗin gawar Abba Umar ba,sun tura mata kuma shirin su yayi daidai da irin ƙwaƙwalwar Anty Nafisa dan bata gane komai ba tunda ita dai taga gawar mutum kuma taga ƙonannen gida bata da wata damuwa,take ita ma ta tura musu kudaden su, zuciyarta fes bata da wata sauran damuwa sai ta cin duniyar ta da tsinke. Cikin sauri ya gaida Hajjah ba tare da ya zauna ba,hakan ne ke nuni da irin saurin da yake dan fita daga gidan, zuba masa ido Hajjah tayi ganin yadda yake ta share gumi ga kuma yawan kallon agogo da yake yi,cikin tsare shi da ido tace"wai Mansur saurin me kake yi ne haka,gaba ɗaya ka kasa zama ba daban Ni nayi kiran ka ba ma ina ga bazaka zo ba!'ta faɗa tana daɗa tsare shi da mahukuntan idanunta,cikin ɗan sosa kai yace"wallahi Hajjah da inda zani kuma zuwan yana da muhimmanci!'tace"shi wajen bashi da suna?girgiza mata kai yayi yana ƙoƙarin tashi,ba tace"masa komai ba sai ido da tabi shi da shi. Yana fita ya shiga mota wanda da alama bashi kadai ne cikin motar,kasancewar duhu ya farayi shi yasa ban kula da wanda ke zaune a bayan motar Ba,figar ta yayi da matsiyacin gudu,itama cikin sauri ta shiga motar ta tare da figarta a tsiyace,tana cewa Mansur bazan bari ka tseremin ba dole sai na ga inda kakai Abubakar kuma sai na kwato shi a yau ba sai gobe ba!'ta faɗa tana ɗan danna wayar ta,wanda da alama kira takeyi,cikin sakanni kuwa aka daga wayar,ba tare da ta saurari wani zance ba tace"ina fatan kuna nan inda nasa ku tsaya!'daga can aka amsa mata kana tace"yauwa to gamu nan yana fitowa kubishi Abaya Ni kuma zan biyo ku kar ku sake ku bari ya tsere muku haka kuma kar ku bari ya fuskanci ana bin bayan sa!'daga haka ta kashe wayar ta ci gaba da bawa motar ta wuta. Dady jafar ya kalli Abdallah cikin gajiya da shiga wannan uban surƙuƙin dajin,yace"anya kuwa Abdallah ba yaudarar mu yayi ba? Amma ace dan Adam ne yake shiga gurin nan babu gida gaba babu baya!'abdallah ya dage kanshi tare da cewa tunanina kawai shine halin da Bint take ciki!'daga haka basu kuma magana ba har suka zo wajen da yayi daidai da zanen kwatan cen da yake kan wayar sa,ɗan slow suka farayi tare da yin ƴan dube dube saboda ko bukka basu gani awajen ba bare gida,gashi kuma inda aka zana taswirar akwai gida a wajen,tsayawa sukayi tare da zubawa dajin ido wanda yayi tsit baka jin kukan komai sai na tsuntsaye,kamar daga sama sukaji ance, sannun ku da zuwa ɗan zaki,munayi maku maraba kaida jajirtaccen uban riƙon ka,ku fito daga cikin mota ai kun zo inda kuke nema!'daga haka gurin ya kuma ɗaukar shuru kamar yadda yake a farko,da ambatan Bismillah da addu o in tsari suka fito daga cikin motar,ga tsananin mamakin su suna fitowa suka ga tafkeken gidan da babushi a farkon zuwan su,ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗauko Dady Abubakar dake san ƙame kamar gawa,suka shiga cikin gidan ba tare da sun tsagaita da ambatan Allah jalla wa'azza ba. Wani fili suka fara tararwa kafin su dan gana da ƙofar da suka gani tana kallon su,itama kai tsaye suka shigeta ba tare da jin tsoro ko wani ɗar atare dasu ba,sosai suka shiga gidan da yake da wani irin zurfi ga wani irin duhu da ya mamaye gurin gaba ɗaya, da taimakon Allah kawai suke samun inda zasu jefa ƙafafunsu,gajiya sukayi da shiga inda basu sani ba kuma basu da tabbacin akwai mutane agurin,suna tsayawa haske ya gauraye wajen,bin ko ina suke da kallo cikin mamakin mutanen da suka gani agurin,kallon juna sukayi kana suka maida kallon su kan mutanen da suke zaune wasu kuma a tsaye,da wasu irin jajayen kaya ajikin su sai zane dake kan fuskar su,zasu kai kimanin su ashirin da ɗoriya,babu wanda ya tanka acikin su duka, sai daga can baya akayi magana da cewa Barka da zuwa ɗan zaki tabbas kacika ɗan halak wanda ke saka Alkhairi da halacci,ga kuma soyayya mai tsanani wanda bantaɓa jin ta ko ganin irinta ba,maza ka miko min mahaifin ka Ni kuma na miƙa maka matar ka!'Abdallah yace"ba haka mukayi da kaiba,dole sai naga lafiyar Bint kafin na baka mahaifina!'wata shegiyar dariya ya sheƙe da ita kafin yace"yaro kar ka manta fa fada ta ka shigo dan haka gaddama ba taka bace,kawai kayi abinda na saka ka inda ba haka ba zan nuna maka ƙarfin iko na,ko dake ma bar shi dama na sha alwashin ta hanyar ku zan samu cikar burina dan haka yanzu agabanka mahaifinka zai buɗi baki ya sanar dani inda suka ɓoye wannan dimon ɗin!'take ya shiga yin wasu siddabaru duk da yasan ba lallai ne yayi ba,yana kuma daga inda yake ba tare da ya fito su Abdallah sun ganshi ba,kafin ƙiftawar ido Dady Abubakar ya fara wani irin jijjiga kafin wani lokaci jikin shi ya saki yana fitar da wani irin numfashi,da sauri nanu ya fito daga inda ya ɓoye cike da mamakin farfaɗowar da ABUBAKAR yayi ba tare da yayi masa wani aiki ba dan siddabarun da yayi yanzu gwadawa kawai yayi tunda yanzu bashi da karfin siddabaru kamar da. Cike da tsananin mamaki Abdallah ke kallon shi cikin rawar baki ya nuna shi tare da cewa"Dady Mansur kai ne dama?Dady jafar yace"haba Abdallah me na gaya maka ai Ni ban yi mamaki ba saboda duk wasu alamu sun gama nuna Mansur a fili!' cikin wani taku irin na taƙama ya ƙaraso gaban Dady Abubakar wanda ya buɗe idanun sa tsaf yana bin Mansur da wani mugun kallo,hannu yasa ya ɗago habarsa yace"dan uwa yau fa ka dawo mutum ina tayaka murna,ya faɗa yana jifan su da wani shu'umin murmushi, Abdallah kuwa kallon da yakewa Dady Mansur hatta Dady jafar saida ya nutsu dan son gano ma'nar kallon. Tun da suka zo suna bakin gurin sun rasa inda Mansur yashiga basu san ta hanyar da yabi ba,domin su dai basu ga gida ko wani waje dake nuna alamun da mutane a wajen ba,tashin da tashiga ba mai misaltuwa bane, wannan aishene ta tasamu yanzu kuma tana shirin ganin rashi,to ina wannan shu'umin ya shiga da har ya ɓace musu,gashi dai tabbas basuyi kuskuren hanya ba,daga ita har yaran nata cirko cirko sukayi suna jiran tsammani. Ɓangaren Abba Umar kuwa,sai da suka ɗan samu nutsuwa,kana yake bawa Hajjo labarin abinda ya faru tsakanin sa da mutanen nan masu kashe su,yace"Hajjo na fahimci cewa kudi shine matsalar su dan haka sai na siye su dashi kamar yadda aka basu aikin kisa akan su to barin aikata kisan ma bazai gagara su barshi ba,dan haka sai nace dasu ya fadi farashin da akabasu Ni kuma zan ninka musu sau biyar,yadda dai ya sanar dani za abasu dubu ɗari biyar dan haka ni kuma nace zan basu miliyan biyar, su rabu dani kuma suje su cewa wanda ya saka su sun yi abinda aka umarce su,to kinji dalilin da yasa basu kashe mu ba!'Hajjo tace"ikon Allah idan kana da kuɗi babu abinda zai gagareka haka kuma idan kana dasu kana cikin tashin hankali, Allah dai yasa mu dace!' da Amin suka amsa shida Asma'u. A ɓangaren su Safwan kuwa sunyi abinda ogansu ya umarce su,dan kuwa cikin kankanin lokaci suka kama su Alhaji Hashir da tawagar su,lokacin da Alhaji Sama'ila ya ga Samira acikin jami'an tsaro na farin kaya,sai da ya suma,Samira ce da kanta ta zuba masa ruwa ya farfaɗo amma yana kuma haɗa ido da ita sai ya kuma shekawa,da ta kuma zuba masa ya farfaɗo zai koma kenan ta daddage ta sheƙa masa marika har guda biyu hagu da dama,wani irin ƙayataccen murmushi ta saki na samun nasara da cin gari,tace"Sama'ila sakarai ko da yake sakarcin ka ya matuƙar taimakamin,dan da baka kasance wawa ba da nasan ba lallai ne nasamu nasara kamar yadda nasamu yanzu ba!'zuba mata ido yayi idanun sa na ruwan hawaye ga wani irin yaji kamar zasu waɗo ƙasa,ta cigaba da cewa,Ni ɗin ƙaryace gabaki ɗaya na gaibuce labarina gaibune amma awajen ka,rayuwata tare da kai ka ƙaddara amafarki kayita yayin da gaskiya ta bayyana a farke,kuma ƙaryarka ta ƙare a farke,dariya tayi irin ta tura haushin nan,kana ta miƙe daga durkusan da tayi a gaban sa,tana cewa Sama'ila na gode fa da aikin da kayi min nasaka wahalafa da yawa to amma dai babu damuwa tunda gashi yanzu soyayya tayi rana,tunda ta ƙure ƙaryar masu ƙarya!'daga haka suka fita daga ɗakin da aka lodasu,wani irin ihu Alhaji Sama'ila ya saka tare da rushewa da wani irin kuka mai cike da nadama da takaici,sauran kuwa basu da bakin magana duk da suna so su magantu saboda tonuwar asirin da Sama'ila ya jawo musu,da kuma zubewar mutuncin su,gemai gemai dasu an watsa su a kurkuku kamar wasu karnuka,hmm kaɗan ma kuka gani dan indai akan ha inci da hassada da yaudara ne to baku ga komai ba kwarankwatsa dubu.... Daga ɓangaren su Laila kuwa tunda Abdallah ya fita suka taru gaba dayansu a falon,Laila ce ta fara neman da su gabatar da junan su,dan tana son sanin su Dije da kuma abinda ya kaisu gurin nan,Aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba Dije ta bawa Ummi Laila duk kanin labarin abinda ke faruwa a cikin zuri'ar Alhaji Balarabe,abinda kawai da bata faɗa ba shine Bint saboda Dije har yanzu bata fahimci inda maganar matar ta nufa ba bare zuciyar ta ya kawo mata cewa mahaifiyar Bintu ce wannan,sai kuma labarin Nafisa wanda bata san duka al'amuran ba,kuma ganin ta bai shafi Lailan ba,ita dai ummi ba tacewa Dije komai akanta ba tunda ta fuskanci bata sani ba. Cikin son nuna ƙarfin ikon sa,da kuma aiwatar da ƙudurin sa yasa afito da Bintu,lokacin da aka fito da ita hannayen ta ɗaure bakinta kuwa duk yayi alamun jini jini kana dubanta kasan tasha marika,da wani irin sauri Abdallah ya nufeta,sai dai kan ya kai ga ƙara sawa yaji an riƙeshi ta baya ita kuma Bintu wani ya saita wuƙà amaƙoshinta,Dady Mansur yace"yaro ka tsaya iya matsayin ka na gaya maka nan fadata ce"idan ka kuskure abinda nake so yanzu zan sa afarke min wuyar wannan ƙwailar matar taka!'Dady jafar ne yayiwa Abdallah alama da yayi hakuri su gabatar da shirin su ba tare da sun samu tangarɗa ba,hakanne yasa Abdallah danne zuciyarsa, Bintu kuwa duban Dady Mansur take ita ma cike da mamaki dan tunda aka kawo ta gidan bata taɓa ganin shiba,dawo da hankalin ta tayi kan Dady Abubakar da yake magana ƙasa ƙasa irin ta majinyata yace"bazan taɓa sanar da kai abinda kake son sani ba sai dai ka kasheni!'dariya Dady Mansur yayi tare da cewa yo ai bakai zan kashe ba kaga waɗanda zan kashe,wata ƙilma na haɗa da ɗan raino!'ya faɗa yana kallon Dady jafar,cikin abinda bai wuce sakanni ba, Bintu ta dinga tariyo Muryar a ƙwaƙwalwar ta tana kuma auna a wajajen da take jin muryar da kuma fuskar mai Muryar,kamar an fuzgo maganar daga bakinta,haka kuma tamkar dirar mikiya su Abdallah sukaji maganar,nunashi tayi da yatsa bakinta na rawa tace"YAH,,,ABDALLAH WALLAHI,,,,WANNAN BA DADY MANSUR BANE DADY HABIB NEE,,,...... Wash Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 54 ``` Cikin matuƙar mamaki da razana gaba ɗaya suka kalli Bintu hatta da shi kansa uban gayyar,zuba mata ido sukayi yayin da A hankali kuma suka maida duban su kan nanu suna so su gano ta yaya ya zama Habib bayan fuskar Mansur suke gani,cikin tashin hankali Bintu ta kuma cewa Wallahi ba shi bane,ga Muryar sa nan!'daga bayan su suka ji ance tabbas Bintu wannan ba Mansur bane Habib ne,gaba ɗaya suka juya dan ganin mai wannan maganar,cike da mamaki suke duban sa ba kowa bane sai Alhaji Rufa'i,wanda ita Bintu bata san shi ba,ya cigaba da cewa kai kam Habibu ka gama taɓewa duniya da lahira domin Allah ma ba zai yafe maka laifin hada shi da wani ba gakuma haƙƙi wanda shima bazai yafe maka ba har sai waɗan da kacuta sun yafe maka,kuma suma bazasu yafe maka ba har abada!' Cikin tashin hankali ya nufo Alhaji Rufa'i yana cewa kai kuma daga ina waya kawoka gurin nan?kuma a ina kuke da shaidar cewa Habib ne agaban ku ba Mansur ba?daga bakin ƙofar shigowa suka ji wata Muryar tana cewa Nine tabbaci!' gaba ɗaya suka kuma ɗibar idanun su suka mayar kan Dady Mansur da yake sako kansa falon,kai wannan abun mamaki da yawa yake,to wai me yasa kuke san ruɗa mana tunani,cewar Dady jafar ke nan da ya rikice da mamaki,Dady Mansur yace"karkadamu jafar abun afili yake Nine nan Mansur na ainahi wanda kuke zargi da laifin ɗan uwana!'Dady Habib ma yace"au wai ku kun yadda da abinda kidahumar yarinyar nan ta faɗa da wannan maƙaryacin?da sauri ya dawo kusa da Dady Mansur ya kamashi suka haɗe guri ɗaya dan ya kuma ɓatar musu da tunani,yana cewa Nine Mansur ko kunƙi ko kun so yana so kawai yayi amfani danine dan cimma burin sa!'bintu tace"wai ko dai ka zare ne Baba Habibu?ga Abu afili Amma kana kokarin maida shi rainin hankali,kasani cewa muryarka bazata taɓa ɓoye min ba,idan ka ɓoye fuska to muryarka ta tona ka,dan bata ɓoye ainahinka ba!'Abdallah kamar mutum mutumi haka ya zama a gurin saboda shi dama can bai iya irin wannan surutan ba,sai dai yayi aiki a aikace,da ba dan Dady jafar da ya dakatar dashiba da tuni ya daɗe da ɓalle hannu da ƙafar mutumin da yake kiran kansa da matsayin Mansur, wanda shi dama tun da ya ɗora idanunsa akansa yasan cewa ba Dady Mansur bane Habib ne,yana shirin bayyana hakan sai kuma Bint ta tiga shi bayyana wa,dariya Dady Habib yayi tare da cewa ku kiyayeni saboda yanzu a fadata kuke dan haka ina tabbatar muku da cewa duk wanda yazo gurin nan ba zai fita da ransa ba!' Har dani mahaifiyarka ta faɗa tana ƙarasowa cikin gurin,kallo ya koma sama''' wan nan shi ake kira da Ali yaga Ali,shuru gurin ya dauka sai fuskokin da suke ɗauke da matsanan cin mamaki, cikin ƙarfin hali da tsananin mamaki Dady jafar yace"Hajjah me kika zo yi nan gurin,cikin nuna damuwa da tashin hankalin da take ciki tace"lokacin da Mansur ya shiga ɓangarena na fuskan ci da wani abu da yake ɓoyemin kuma daga dukkanin alamu abin ba ƙarami bane,shi yasa nayi tunanin biyosa,sai kuma nazo na kasa samun gurin tun ɗazu ina daga waje ina neman hanyar shigowa sai kuma yanzu katsam na ga kofar gurin ta bayyana!'ta ƙara sa maganar cikin rushewa da wani matsanan cin kuka, ta ci gaba da cewa Habibu ka zama ɗan kunama agareni mai harbin uwarsa,me yasa kayi duk wannan?me yasa ka kauce daga hanyar dana ɗoraka?ina ganin Mansur shine jarraba ta ashe kaine bansani ba,tabbas ka yaudaremu dan bani ka ɗai ka yaudaraba,har mahaifinka da sauran ƴan uwanka, mahaifinka yana ganin zaka maye masa gurbin ɗan uwanka da yarasa amma ashe abun ba haka yake ba!'ta faɗa tana durƙushewa a gurin cikin kukan fitar haiyaci,kama daga kan Fatima Bintu har zuwa kan Dady jafar da Alhaji Rufa'i da Mansur saida suka kusa zubdawa Hajjah hawayen tausayi, Abdallah ne dai ba kasafai ake gane masa ba indai damuwa ba akan Bintu ko mahaifinsa ba ne,dan haka bazaka gane kallon da yakewa Hajjo ba, Cikin tausayawa ta tsakanin ɗa da uwa, Dady Mansur yace"dan Allah Hajjah ki daina kukan nan bana son kina tada hankalin ki!'mansur dole ne na tada hankalina ya za ayi ace duk tsawon shekarun nan da mukayi zuciyoyin mu cikin kewar Abubakar ashe wai yana tare damu bamu sani ba,ya haɗu da sharrin ɗan uwa, ko duk akan me yayi masa hakan oho,har kuma ya dinga ikirarin kashe dansa da surukarsa!'me kake nema a wajen sa haka da yafi girman zumuncin ku?ta faɗa tana kafe Dady Habib da idanun ta wanda sukayi jajir saboda kuka,bai ce mata komai ba sai kawar da idanun sa da yayi ya mayar kan Dady Abubakar da yayi sakato yana kallon abun al'ajabi,yace"to tunda duk kunyar da Nine Habib naji amma fa bazan taɓa nadama akan abinda na aikataba,kuma bazan taɓa saurarawa akan abinda nake da burin aikatawa ba,dan haka aɗaure kuke anan zan iya yin komai ba tare da kun hanani ba,ya cigaba da kallon Dady Abubakar yana cewa ABUBAKAR ƴan fansa sun ƙaru dan haka inaso ka zaɓa, ko ka faɗa min inda dimon yake ko na kashe duk mutanen dake zagaye da kai!'zaro idanu Hajjah tayi cike da mamakin ɗan nata,tana cewa Habibu dama shu'u mancin ka ya kai haka? to Ni kuma ina tabbatar maka da cewa bazan bari ka aikata mugun nufi akan ƴan uwanka ba!'tana gama faɗin haka ta nufi gurin da Dady Abubakar yake zaune akan wheel chair,kama wa tayi tare da fara turawa,ganin haka yasa da sauri Abdallah yace"ki barshi kawai Hajjah zamu san abunyi!'Hajjah tace"bazan bari ba Abdallah ku kuna da karfin da zaku iya ƙwatar kanku kubari na tafi da Abubakar!'zai kuma magana,Dady jafar ya girgiza masa kai,hakan ne yasa ya dakata daga abinda yake son faɗa,Dady Habib yace"kema bazan bari ki fita dashi ba,bare kuma su!'Hajja bata saurare shi ba ta tunkari ƙofa gadan gadan,Dady Mansur kuma ganin abinda yaran Habib suke shirin aikatawa na ƙoƙarin isa isa inda Hajjah take, yasa ya shammace su yayi wata hanya inda makun nan gidan suke take ya kashe duk fitulun gidan,kafin wani lokaci gurin ya ɗin ke da wani irin duhu mai tsanani,cikin ruɗewa da tashin hankali Dady Habib yake bawa yaransa umarnin kar su sake su bar wani ya fita daga gurin,sai dai kafin su aikata hakan tuni Hajja ta daɗe da ficewa da Abubakar, da ke ba ita kadai bace shi yasa,saka shi amota bai jasu lokaciba sukayi gaba dashi ita da yaranta,zuciyar ta cike da farin cikin nasarar dake tasamun rayuwarta,tana ganin tunda tayi nasarar samun Abubakar to bazata gaza wajen shirya yadda mutuwar sa zata kasance ba,bayan ta samu abinda take nema kenan.. Daya daga cikin yaran ne yayi saurin kunna wutar, sai dai hakan baiyi rana ba, dan sun rasa Hajjah da Abubakar ko ƙurar motar basu gani ba,hakanne ya kuma hargitsa zuciyar Dady Habib tare da tunzura shi cikin ɓacin rai yace"karku bari kowa ya bar gurin nan!'Dady Mansur yace"yanzu Habibu akan abin duniya zaka kashe ƴan uwanka?kuma meye dalilin ka na saka fuskata amatsayin mugu?wani kallon baka da wayo yayi wa Mansur kana yace"an gaya maka Ni mara wayo ne irinka?zagaye shi ya shiga yi kana ya cigaba da cewa Mansur baka san yadda kayimin amfani arayuwata ba, na samu damar fakewa A bayanka Ina aikata mugun nufina,duk da nasan kasan komai akan abinda nake aikatawa,hakan yasa da yawan mutane suke zarginka suna maka wani kallo,dalilina nasaka fuskar ka kuwa shine ko da zan kashe Abdallah da ubansa da kuma wannan uwar tona tonan matar sa,zasu tafi ne da sanin kaine ka kashe su bazan mozanta azukatan su ba ko acan ƙiyama zasu bada shaida akaina,kai kuma kisan su ya rataya akanka!'tir wallahi tur da wannan jahilin tunanin naka,ilmin ka bai AMFANA maka da komai ba indai har ƙwaƙwalwal ka zata zana maka yiwa Allah wayo,shin karatun da akai maka bai shiga kanka bane kokuwa idan Alhaji Baba ya turaka makaranta laɓe kake yi?gaskiya na tabbatar da cewa kai ba karamin sunduƙi bane mai karkataccen tunani!'tau kakeji ya ɗauke fuskarta da wani lafiyayyan mari,zabura Abdallah yayi wani ya rikoshi amma dake zuciyar maza ta ɓaci antaɓa rabin rayuwar sa,da hannu ɗaya ya kama hannun mutumin da ya riƙe shi jikake ɓass ya karya shi, cikin sauri ya ƙaraso inda su Bintu suke da mutumin da ya saita maƙoshinta da wuƙa,cikin azababban fushi yace"ba gaskiya ta faɗa ba da zaka mareta, Dady Habib da yake fitar da wani irin huci na tsananin ɓacin rai yace"idan yasake ya ƙaraso inda take na baka dama ka farka maƙogwaranta!'yake fadawa wanda yake rike da Bintu. Cak Abdallah ya tsaya jin an riko hannun sa ta baya, muryar Dady Mansur ce ta shiga kunnuwan sa yana cewa karkaje Abdallah kana nan tsaye Allah zaiyi mana maganin sa idan yafi ƙarfin mu ai baifi ƙarfin wanda yayi shiba!'a hankali Abdallah ya koma ya jingina da bango mafi kusa dashi,idanun sa akan Bintu da take ta kallon sa gani yake kamar kallon tuhuma take masa na Kasancewar ya kasa yin komai na taimakonta,shi ne yasa duk yaji zuciyar sa ta kasa nutsuwa,da barin ta a hannun wannan ƙasurgumin dan ta adda,ga yadda yake jin zuciyar sa na masa suya saboda kusan cin Bintu da wannan ƙaton, A hankali Dady Habib yasa hannun sa ya ɗaye fuskar da yasaka, yana cewa babu amfanin zama da wannan a yanzu tunda kun gane shirin,sai kuwa ga fuskarsa ta zahiri ta bayyana,babu wanda yayi mamakin haka a cikin su sai Bintu tunda ita bata taɓa sanin anayin fuskar wani asakaba,cikin ƙosawa Abdallah yake ɗan duban agogon hannun sa wanda yake traking ɗin in da mutum yake,lumshe idanun sa yayi wanda sai buɗe su yayi yaga mutane zagaye dasu an dasawa kowannen su bindiga,wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke,Muryar wani jami'in tsaro ne ya karaɗe wajen da cewa kar wanda ya motsa duk wanda ya motsa kuwa saina fasa kansa da bindiga! cikin mamaki Dady jafar yace"to me yakawo ku nan?ina tunanin gurin da ake aikata laifuka irin ku suke zuwa?to nan kuma naga tattaunawa ce tsakanin zuri'a ɗaya Dady jafar ya faɗa cikin nuna pretending!'Safwan da ya ɗorawa Bintu bindiga yace"babu ruwan mu da abinda kuke tattaunawa binciken mune ya nuna mana da akwai matsala babba a ta ɓangaren nan, dan haka gaba dayan ku abin tuhuma ne!'ya faɗa yana tafiya da Bintu wajen da Abdallah yake tsare da bindiga,yayin da Dady Mansur da Alhaji Rufa'i da basu san shirin su Abdallah ba hankalin su duk ya tashi,haka kawai Habib zai shafa musu jakar tsaba,cikin tsari da sanin makamar aiki suka dinga fita da yaran Dady Habib,sai da aka fita dasu gaba ɗaya sai shi kaɗai yayi ragowa, Abdallah yasa hannu ya ture hannun wanda ya ɗora masa kan bindiga kana yashiga takawa A hankali tamkar wani Basarake da yake kan ganiyar mulki,gaban Dady Habib ya ƙaraso tare da zuba duka hannayen sa cikin aljihunan dogon wandon jins dake jikin sa,wani irin kallo ya fara watsa masa wanda Dady Habib yajishi har cikin hanjin cikin sa,ganin Abdallah agaban sa baƙaramin kyarmar jiki yasa shi ba,tabbas kwarjinin Abdallah abun tsorone ga maƙiya da kuma marasa gaskiya,Dady Habib baisan sanda ya sunkuyar da kansa ƙasa ba,ya kasa haɗa idanu da shi,wani zazzafan huci Abdallah ya furzar kana cikin maganarshi mai fita ɗai ɗai da kuma salon iya sarrafa harshe,yace"Habibu ga ranarka nan, sakamakon ka kuma yana nan tafe,gashi dai ɗan zaki yazo har fadarka kuma zai tafi da kai cikin ƙasƙanci,kuma mutuncin da kake dashi zai zube a idon duniya,ina nan kuma zan aiko maka da ragowar mutanen ka da kuke aikata shirka dan babu wanda zai tsira a cikinku da izinin Allah!'yana gama faɗar haka yayi musu alama da su tafi dashi,hankaɗa ƙeyarsa Safwan yayi suka fita dashi cikin ƙasƙancin da yake gudu,bakin sa dai bai mutuma alwashi yake ci iri da kala akan sai ya ga bayan zuri'a Hajiya Babba gaba ɗayan ta. Da wani irin gudu haɗe da kuka-kuka dariya dariya Bintu tazo ta waɗa jikin sa,ba su Dady jafar ba hatta Ni da nake sakaɗe abayan kofa sai da naji ajiyar zuciyoyin da suka sauke atare kamar an irga musu,riƙeta ya kuma yi ajikinsa yana shafa gashin kanta da duk ya watse a gadon bayanta,Dady jafar ne ya dubi Dady Mansur tare da cewa Mansur afuwa fa, saɓanin fahimta ne!'murmushi Dady Mansur yayi kana ya kama hannun Dady jafar yana cewa babu komai baka da laifi kai mutumin kirki ne, da duk mutane zasuyi koyi da halayenka da tabbas ansamu ƙaruwar jin dadi da zaman lafiya!'fita sukayi suna ƙara maida maganar. A hankali ya kamata suka fara takawa yanayi yana duba lafiyar jikinta duk da ta tabbatar masa da cewa babu abinda ya same ta ko sukayi mata sai marikan da tasha,motar da su Abdallah suka zo da ita shine ya shiga shida bintu sai Safwan da zai ruƙasu,su kuma su Dady Mansur suka shiga wadda suka zo shida Alhaji Rufa'i da Dady jafar,cikin nutsuwa suka jero motocin suka fito daga wan nan mugun wajen. A hankali ta matsa jikin sa tare da saƙala hannunta ta bayansa,ta kwantar da kanta A ƙirjinsa,ji take kamar wadda ta shekara ba tare da shi ba,ɗan tura ta yayi yana cewa matsa tsamin datti kikeyi!'a zubure ta ɗaga kanta tana kallon sa,sai kuma ta shiga ƙoƙarin ƙwace wa daga gareshi,riƙe ta yayi yana sakin wani sassanyan murmushi wanda yake fitowa tunda ƙasan zuciyar sa,da ta kasa ƙwacewa sai ta ɗago kanta dan yi masa magana,,,amma ina hakan ba ta samu ba sakamakon jin ya haɗe bakinsa da nata,a hankali cikin wani irin salo na ƙwarewar da bai san a inda ya sameta ba,yake sarrafa harshenta acikin bakinshi,tun tana son ƙwacewa har ta haƙura ta bada kai bori ya hau,sai da ya hango fuskar Safwan ta cikin miro kana ya ankarar da shi abinda yake gaban yaran sa,zare bakin sa yayi daga nata yana binta da wani kasalallan kallo,rufe fuskarta tayi akirjinsa tana tura baki,cikin gunguni tace"me yasa to kayi wannan bayan wari nakeyi?bai amsa mata ba sai kallon da yake ci gaba da yi mata,ganin haka kawai sai ta canja maganar ta,ta da cewa yanzu da Hajjo ta tafi da Dady ina zata kaishi?karfa ta kai shi ESTATE,bayan bamu shirya komawarsa yanzu ba?dan sunkuyawa yayi ya sumbaci goshinta kana yace"kar ki damu shi yasan yadda zaiyi zaiyi mata bayanin komai!'da wannan maganar ta gamsu duk da dai tanajin wani abu aranta game da tafiyar tasu,cikin sanyin murya ta kuma cewa dashi dan Allah ka kai Ni gidan Hajjo Ina son daukar wayana,kuma,,,,katse ta yayi da cewa shuru Malama da surutun!'tura baki tayi amma dai bata kuma cewa komai ba, Ganin su A kofar gidan Hajjo ba ƙaramin farin ciki ya saka ta ba,sai dai kuma abin mamakin da suka tarar gidan babu kowa gashi abuɗe sakayoshi kawai akayi,cikin fargabar abinda zasu shiga su tarar suka shiga cikin gidan,a kideme Bintu ta kalli Abdallah tare da cewa to ina suka je dukan su haka?ɗakin Hajjo ta faɗa da gudu anan ta samu wayarta a yashe ƙasan ɗakin durƙusawa tayi ta ɗauka,cikin rawar jiki ta kunnata,tayi sa a kuwa da ragowar caji tunda mutuwa tayi,lambar da Anty Asma'u ta saka mata ita ta kira,zuciyar ta kuwa sai bugawa take saboda tsananin fargaba,ɗan matsowa yayi kusa da ita tare da kamata ganin yadda ƙafafun ta suke rawa, yace"Bint ki nutsu Mana me yasa haka da ruɗewa,tun kafin kiji dalilin barin su GIDAN!'kar ɓar wayar yayi yasaka ta a amsa kuwa,daidai lokacin da Anty Asma'u ta rangaɗa sallama,wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya suka saki atare kamar yadda suka saba,kana cikin nutsuwar sa ta kullum yace"Anty Asma'u mun dawo kuma bakwa nan!'da sauri tace"kai da waye?ina Batula hankalin mu ba akwance yake ba, Allah yasa kar kace mun ba a sameta ba? cikin ƙosawa da yawan maganar yace"tare da ita muke!'miƙawa Bintu wayar yayi ta karba da sauri tare da cewa'Anty Asma'u gani kuna ina ku?sai kuma taji Muryar Hajjo har da kuka tana cewa Alhamdulillah Allah abin godiya, Abdallah Allah yayi maka albarka tabbas kacika gwarzo kuma jarumi Allah Ubangiji ya taya maka ya dafa dukkan al'amuran ku,ya cigaba da kareku daga sharrin maƙiya da dukkan abin ƙi!'amin Hajjo me yafaru ne wai?'ya faɗa yana matsawa jikin Bintu don yaji maganar sosai,nan dai Hajjo ta bashi labarin abin da ya faru gaba ɗaya har yadda sukayi da yaran Anty Nafisa da Abba Umar,hamdala yayi,yana sakin murmushin farin ciki da nasarar da suke samu adukkan abinda suka tunkara, lallai Allah mai ƙudura ne,shi kaɗai yasan ta hanyar da zai kare bayin sa wanda suke tare da shi,cikin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa ya da ɗa rungumo Bint jikin sa yana cewa to Hajjo Allah abin godiya ne ko da yaushe agaremu Allah ya ƙara wa Annabi wasila da fabila,gaba ɗaya suka amsa da Amin,Bintu tace"Ni kam ma Hajjo dama kukan gulma kikeyi bana rashina bane,tun da gashi har yanzu kin kasa yimin magana!'ta faɗa tana share hawayen da ba wahalar zubo mata sukeyi ba,dariya Hajjo tayi cike da madaukakin farin ciki,tace"wace ni naƙi kula ƴar lelena,mijin nawa ne dole na tsaya na yabeshi dan ya cancanta!'ɗan kallon Abdallah tayi wanda yake ta zuba mata wani munafukin murmushi da kallon da yake haifar mata da mutuwar jiki,abinda ya shiga yi matane yasa ta fara yiwa Hajjo in ina, tace"haj,, haj, Hajjo to zamu taho inda kuke kiyi mana kwatan ce!'karɓe wayar yayi yana cewa Hajjo ba yanzu ba kin san dai abinda nake shiryawa,dan haka sai mun sake waya!'daga haka ya kashe wayar, yana yiwa Bintu sigina A lokaci ɗaya kuma yana cigaba da yimata tafiyar tsutsa a gadon bayanta,kanƙame shi tayi jikin ta na wani irin rawa,cikin rawar murya tace"Ni Ni dai mu tafi gida!'cikin hura mata iska a kunne yace"nan A daji muke?a bazata taji wani irin sanyi cikin kunnen ta, ƙafin ta dawo hayyacin ta, Abdallah ya shiga tsotse kunnenta loko da saƙo,wani irin kyarma jikin Bintu yake yi, wannan abun da Abdallah yake mata wani baƙon al al'amari ne a gareta wanda take, taji duk wata tsiga dake jikinta tana miƙewa cikin biyayya da karban saƙonnin da Oga Abdallah yake basu,bata gama kiɗimewa ba sai da taji hannuwan Abdallah biyu akan nn,ta wanda yasa ta kusa shiɗewa, Ringin ɗin da wayar ta tayi shi ya dawo dasu hayyacin su duk da cewa Abdallah yaƙi sakin ta,ganin lambar Dije ya sa ta ɗauki wayar da sauri,ajiyar zuciyar da Dije ta saukar shi ya shiga kunnuwan ta da Abdallah yayi musu wankin babban bargo da miyansa,Dije tace"Bintu ina kika shiga haka kwana biyu nayi kiranki har na fidda rai da samun ki!'Bintu tace"Dije na shiga matsala ne amma yanzu komai yayi daidai,ya ake ciki kuwa?Dije tace"sakon da nake ta son baki ke nan,amma yanzu a gurguje abu ɗaya mafi muhimmanci zan gaya miki sauran bayanin sai mun haɗu!'Bintu tace"ina jinki!'Dije ta ɗan ja ajiyar numfashi kana tace"kin san wacece wannan matar Bintu?cikin fargaba, Bintu tace"wallahi ban sani ba Mama Dije!'Dije tace"abin da matukar mamaki da ɗaure kai,ba kowa bace wannan shu'umar matar ba sai Hajjah matar ALHAJI BALARABE ta biyu,kuma uwa ga ALHAJI Mansur da Alhaji Habibu....... Ɗit ɗit ɗit .... FATIMAH Y ADAM✍🏽 More Comment 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 55 ``` Wayar ta saki, ta faɗa ƙasa,ita kuma ta koma jikin Abdallah saboda jirin da ke neman kayar da ita,riƙe ta yayi,kana cikin taushin murya yace"Bint calm down Mana me yasa bakya ɗaukar abu da sauƙi? cikin kukan da yake tasan ƙwace mata,tace"ya Abdallah ta tafi da Dady fa,kuma kasan fa ita ma tana son ta ɗauki dimon ɗin nan,dan haka zata iya cutar da Dady!'A hankali ya shiga jijjiga ta kamar wata ƙaramar jaririya,sai da yaga ta ɗan nutsu kana ya kai bakinsa saitin kunnen ta yayi mata raɗa, wanda hakan yasa naga ta saki wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tare da kuma ƙankameshi har da guzurin wani sassanyan murmushi,shima murmushin yayi tare da kama hannun ta suka fita daga gidan,kullewa sukayi kana suka dau hanyar komawa ESTATE, Cike da farin ciki suka isa gidan da ta ajiye su Laila,shi dai Dady Abubakar yana kallon ikon Allah ne kawai amma baice komai ba, tun daga yadda suka ɗauke hanyar shiga cikin gari yasan cewa akwai wata manufar, Fito dashi sukayi suka tura shi har zuwa cikin dakin da aka ajiye fafi,daga nan Hajjo ta yi musu kashedi da jan kunne akan su kula su kuma kiyeye kar suyi saƙen da zata rasa Abubakar akaro na biyu akan sakacinsu, dan akan wannan bazata taɓa raga musu ba, saboda samun Abubakar shine cikar burinta,da wannan kashedi ta tafi ta barsu da niyar sai gobe zata dawo saboda yanzu dare ya raba kuma bata son shirinta ya wargaje na yadda zatasanar dasu kufcewar ABUBAKAR daga hannun ta. Kai tsaye falon inno suka nufa,wani abun tausayin inno suka tarar tare da Hajiya Babba daga dukkan alamu ko da rintse basu runtsaba,gaba ɗaya hankalin su atashe yake,da gudu Bintu ta ƙarasa ta zube jikin inno kana ta koma jikin Hajiya Babba wani shaukin kaunarsu ne ke da ɗa kwarara cikin zuciyarta,inno ta dubi Abdallah dake zama kusa da ita cikin damuwa da kulawa tace"Abdallah ina kuka shiga kwana biyu hankalin mu duk ya tashi? tun ranar da kayi min waya ban kuma jin duriyarku ba!'Hajiya Babba ma saka mashi idanu tayi suna jiran amsar da zai basu, jingina yayi da jikin kujerar da yake zaune tare da lumshe gajiyayyun idanun sa,kana A hankali yace"inno na gaya miki aiki ne ya fitar damu shine na tafi da ita!'kallon da suka ci gaba da yi masa ne ya tabbatar masa da cewa basu gamsu da abinda ya gaya musu ba,hakanne ya sa shi mikewa cikin nuna gajiyar dake tattare dashi ya nufi falon sa,da kallo suka bishi har sai da ya shige kana suka dawo da duban su kan Bintu dake kwance jikin Hajiya Babba idanun ta alumshe da alamun dai itama da gajiya da kuma bacci atare da ita, a hankali Hajiya Babba ta shafa kanta tare da cewa Bintu me ya same ki ne haka dubeki kamar wadda aka tsamo cikin shara duk kayanki sunyi datti ga idanunki sun faɗa,wai ina kuka je ne haka da kuke ɓoye mana?kallon jikin ta tashigayi wanda ta riga tasan ya Abdallah bai tsammaci zaiga su Inno a nan ba da tabbas bazasu shigo a haka ba,murza idanunta ta shigayi ta rasa abin cewa,kallon juna su Inno sukayi kana inno ta kuma dawo da dubanta kan Bintu tace"Bintu na nasan da akwai abinda kuke ɓoye mana kawai dai kuna tsoran faɗa ne saboda sirrin junan kune!'cikin sauri Bintu tace"a'a inno kar zuciyar ki ta raya miki wani abu mara kyau,sirrin mu sirrin kune,koda babu dangantaka tsakanin mu zan iya fada muku sirrina!''kallon da taga suna zurfafawa akan ta ne yayi saurin ankarar da ita katoɓarar da tayi,dan haka cikin dabara ta sauya zancen da cewa,inno wallahi kun riga kun zama dangina kuma iyayena shi yasa har nake manta koni wace a gurinku ji nakeyi tamkar nima daga tsatsan ku na fito dan haka babu wani sirrina da bazan iya sanar daku ba,amma kuyi haƙuri ku bamu lokaci!'ta ƙarasa faɗa cikin marairaice fuska,Hajiya Babba tace"shike nan tashi kije kiyi wanka ki kwanta!'tace to tare da tashi sai da tabi kowaccen su da runguma ta tsantsan ƙauna da farin cikin basu zamo daga cikin taɓaɓbuba,kallo suka bita dashi ganin ta nufi falon Abdallah hankali kwance ba tare da tasan suna kallon nata ba,sai da taje bakin ƙofa kana ta juyo tare da huro musu sumbata,san nan ta shigewar ta tana kuma yi musu sai sa da safe, murmushi sukayi kana inno tace"Hajiya Babba ki wuce na rakaki dakin Alhaji!'Hajiya Babba tace"yi kwanciyar ki ba sai kin raka Ni ba abinda ta kofar falonki kawai zan shige!'inno tace"to shike nan Allah ya tashe mu lafiya!'amin Hajiya Babba ta amsa tana shiga falon Alhaji ta falon inno, sai dai dukka su zuciyoyin su cike take da damuwa akan al'amura masu yawa, dake wakana acikin gidan kwana biyu. A zaune kan sallaya ta tarar dashi kamar yadda ta tafi ta barshi,zama tayi a gefan gadon har ya shafa addu'a itama ta shafa, cikin nutsuwar sa ya juya ya dubeta kana yace"sun dawo?tace"sun dawo amma alamu ya nuna a kwai wani abu da suke ɓoyewa a junan su!'nan dai ta gaya masa yadda sukayi da su Bintu,ta ɗora masa da cewa, wallahi Alhaji haka nan nakeji araina kamar da wani gagarumin abu dake shirin faruwa acikin gidan nan,kuma zuciya ta tafi raya min Alkhairi shi yasa nakejin wani irin farin ciki!'murmushin su irin na kamilan mutane yayi,kana yace"kice munyi ɗaya dake amma Ni dai farinciki na baya rasa nasaba da irin mafarkan da nake yi da Abubakar wanda nake ganin sa cikin halin jinya amma duk kwanan duniya idan na kumayin mafarkin to sai na ga samun sauki da lafiya a tare da shi, kuma inaji ajikina ya kusa dawowa garemu,sai dai kawai mu cigaba da tsananta addu'a akan lamarin!'Hajiya Babba tace" hakane Allah ya shige mana gaba!'... Turus tayi ganin Dady Mansur zaune a falon ta, ya zuba ta gumi kana ganinsa kasan yana cikin damuwa matsananciya, cikin sanyin jiki ta ƙaraso cikin falon sai kuma duk taji damuwa da tausayin MANSUR ɗin ya kamata,tasan damuwar da yake ciki bata rasa nasaba da halin da ɗan uwansa ya shiga,to yake nan zaiji idan yaji cewar uwarsa ma tana daga cikin waɗan nan mutanen masu matukar san zuciya da san abin duniya?wane irin hali zai shiga duk ranar da ta bayyana cewa mahaifiyar sa munafuka ce mai fuska biyu?kai ina bata ma fatan zuwan wan nan rana, baza ta taɓa bari hakan ta faru ba,duk yadda zatayi zatayi dan rufuwar asirin ta,baza ta bari ta tozarta gaban mutanen da suke matukar ganin girma da darajar ta ba,zama tayi a kusa dashi tare da dafa kansa cikin san cire damuwa da fargabar da suke san rufeta tace"Mansur ya haka da zama mai makon kaje ka kwanta ka huta sai kazo ka zauna anan, ko kana nufin kwanan zaune zakayi?wata irin ajiyar zuciya yayi cikin sanyi jiki da murya yace"Hajja bazan iya bacci ba,ba na yau kawai ba har da na gobe da jibi,abun nan bazai taɓa fita daga raina ba,na dade ina tuhumar kaina dalilin da yasa ina ganin ana aikata ɓarna amma bazan iya kataɓus akan hanawa ba,Habibu ya cuceni ya cutar da ƴan uwan taka yaci amanar zumunci!'ya faɗa wasu zafafan hawaye na zubowa daga kwarin idanun sa, cikin mamaki Hajjo tace"kana nufin tun tsawon lokacin nan kasan abinda Habibu yake aikatawa kuma kasan ABUBAKAR yana hannun sa?jinjina kansa yayi tare da cewa tabbas Hajjo Ni ganaune kuma jiyau akan dukkan abinda Habibu yake aitawa,sai dai kuma sanin nawa bai da wani amfani tunda baiyiwa ɗan uwa na ABUBAKAR rana ba!'Hajjah tace"meye dalilin ka na rufawa wannan bugun asiri?cikin damuwa da tsananin takaici yace"Hajjah ban sani ba,amma yanzu na sani,nasha yunƙurin zuwa dakin nan dan fito da Abubakar amma sai hakan ya gagara,wanda nasan hakan baya rasa nasaba da ƙarfin sihirin dake tare dani ko nace tsafi dan yanzune nake da tabbacin Habibu tsafaceni yayi,nasha yunƙurin zuwa gurin, wanda tasanadin haka da yawa mutanen gidan nan suke zargina da alaƙa da wannan ɗakin,ranar da aka sace Sayyid ma nayi tunanin shine ya ɗauke shi saboda yasha min kashedin idan ban daina yunƙurin zuwa dakin nan ba to zai kashe min Sayyid,hakan ta farune agaban matata shi yasa ita ma take min kallon wanda ya sadaukar da rayuwar ɗan ta akan wata buƙata,Hajja Habibu ya sakani acikin haɗarurruka da dama,ranar da naga gobara a ɗakin da Abubakar yake baƙaramin tashin hankali na shigaba dan atunanina Abubakar ɗin ne ya ƙone, sai kuma ƙonewar ɗakin nan tamkar shine tashin rayuwa ta,da baibayin da aka yiwa bakina da zuciyata duk ya kama gaban sa,wanda kuma tun daga ranar na saka idanu sosai akan duk wani motsi da Habibu zaiyi saboda ina son tona masa asiri,na rasa da wanda zan hada kai domin ya zamar min shaida,sai kawai Alhaji Rufa'i ya faɗo min dan haka na tare shi da maganar ban sha wuya ba ya fahimceni muka haɗa hannu,daga nan shi ya bani labarin su Abdallah da binciken da suke akan wanda ya ɗauke Abubakar, duk da nayi mamakin hakan sai dai kuma da nayi tunanin shifa jami'i ne sai na daina mamaki, A hankali muka cigaba da bibiyar Habibu har muka gano abinda yake shiryawa na sace Bintu na kuma gano Abubakar yana gurin su Abdallah,shine dalilin da yasa naje wajen Alhaji jafar dan yasanar dani inda su Abdallah suke, tunda na tabbatar a ranar Habibu zai sace"Bintu amma sai yaƙi bani haɗin kai daga ƙarshe ma ya fito ya nuna min zargin da yake min akan Abubakar,Ni kuma hakanne yasa na rabu dashi ba tare da na gaya masa shirin da Habibu yake ba,daga baya ne na tabbatar Habibu ya sace"Bintu kuma na bibiyi Abdallah nasan cewa zai kai masa Abubakar kamar yadda suka shirya,duk da nasan wata ƙil da akwai wani shiri da sukayi a ƙasa, amma hakan baisa nayi kasa a gwiwar isa wajen ba,duk da kema kin so ki ɗan bani matsala gurin tafiyata gurin!'ya tsaya da maganar shi daidai nan,yana ɗan ajiyar numfashi,alamun dai yaji daɗin fidda abinda ke cikin ranshi shekara da shekaru,Hajja dai jugum tayi tana al ajabin yadda ɗan ta ya yaudareta,domin duk mugun halinta taso ace yaran ta sun kasance na arziƙi ko zata iya cin albarkacin su ranar lahira,amma yanzu ma ai ga Mansur nan,wata zuciyar tace da ita"ai kuwa kin san barewa bazata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba,halin ki ne sak Habibu ya ɗebo sai kuma yace kauce ki ban guri,tashi tayi tana cewa Mansur dan Allah in dai na isa da kai kaje ka kwanta ka ɗan yi bacci kafin kiran sallah!'shima tashi yayi yana cewa shike nan Hajja amma dai yanzu bazanyi ba sai nayi salla tunda kinji har har n fara kiran farko,idan na kwanta zan iya makara dan haka sai nayi sallah!'daga haka ya fita daga falon zuciyarshi sawai ta rage mugun nauyin da tayi masa, sai dai kuma tunanin inda Hajja ta kai Abubakar yake wanda yana sane dashi azuciyar sa,kawai dai yayi shurune yaga abinda Hajja zata shirya akan fitowa dashi, yasan wata ƙila ta kaishi wani gidan daban dan akula da lafiyar sa kafin dawowar sa gida. A ɓangaren Anty Nafisa kuwa, A cikin daren ta yiwa Hajiyarta waya tasanar da ita ta shirya tarbar ta tare da arzikin da zata zo mata dashi,Hajiya ladidi da ta haƙura ta saduda ganin babu hanyar samun arzikin gidan Alhaji Balarabe,tace"me kike nufi nafisa? maimakon ta bata amsa sai kawai ta sheƙe da wata irin dariyar farin ciki kana tace"Hajiyata labarin mai tsayi ne abin da yasa ma bazan ce gobe zaki ganni ba saboda ina so sai jibi zan fasa kukan mutuwar sa daga nan na haɗo kan dukiyata nayo gaba!'ita dai Hajiya ladidi jin Nafisan take kamar almara wace irin kukan mutuwa kuma zata fasa?kafin ta samu damar yiwa Nafisan tambayar afili tuni ta katse wayar tare da kasheta gaba ɗaya,takaddun da take ta haɗawa na kadarorin Abba Umar su taci gaba da haɗawa,wanda daƙikiyar ƙwaƙwalwar ta tabata tabbacin cewa na gaske ne,sai da ta gama haɗa su tsaf kana ta tashi ta koma ɗakinta tayi kwanciyar ta tana juyin farincikin samun sabuwar rayuwa.. Kai tsaye ɗakin sa ta nufa,shiga tayi tare da ƴar sallama saman fatar bakinta,zaune ta ganshi kan sallaya da alama dai sallolin da baiyiba ya rama,wuceshi tayi ta shiga toilet ɗin itama,wanka tayi mai rai da lafiya wanda ta daɗe tana durzar fatarta,dan ji take kamar ta shekara ba tayi wankan ba,dan haka ta zage ta dirji fatar jikin ta da gashinta,har sai da fatar ta ta fara zafi ga jan da ta farayi abunka da farin mutum,alwala tayi ta ɗauro towel mai dan girma ta fito,wadrob ɗin sa ta bude wanda take da tabbacin ba zata rasa guntun kayanta anan ba,ilai kuwa ta samu wata doguwar rigar bacci mai santsi har da hijab dan haka ta ɗauka ta zura tare da saka ɗan turare kana ta zura hijab ɗin itama taje bayan shi ta tayar da sallar,saida sukayi sallar asuba kana suka koma biyan bashin baccin da suka ci... Tun bakwai take zuba ido ko zataga daya daga cikin su yazo mata da maganar Abubakar,amma shuru take ji,gashi ta ƙagu taje tayi abinda yake gabanta,har daga baya ta yanke shawarar fara tafiya ta gabatar da babban ƙudurin ta,sai kuma ga sallamar Dady jafar a kofar falonta,duk da cewa ta riga ta shiryawa fuskantar kowanne daga cikin su amma sai da taji faduwar gaba,(Hajja kenan to ina batun kwanciyar hankali akan abinda babu Allah acikin sa)sauri tayi ta ƙara burkita yanayin ta tare da gaiyato tashin hankali kan fuskar ta,idanun ta kuwa ta shirya musu tun adaren jiya gasu nan sunyi jawur kamar gaske,zama yayi bayan ta amsa sallamarsa cikin wani irin yanayi da kukan da take ta san ƙirƙirowa kanta,Dady jafar yace"Hajja lafiya dai ko?cikin kukan da ta gama shirya zuwan sa tace"jafar ina fa lafiya,tun bayan dawowata gidan nan bayan rabuwar mu da Mansur yaran da na bawa ajiyar Abubakar da kuma likitan da na kai masa dan ya duba lafiyar sa,suka kirani suke sanar dani cewa Habibu ya tura abokan nan sa matsafa sun tafi da Abubakar ɗin!'ta ƙara sa maganar tana fyace hanci da haɓar zaninta,idanunta kuwa kai kace kukan tun daga ƙasan zuciyarta yake fitowa,da sauri Dady jafar ya mike cikin nuna mata tsananin tashin hankalin sa yace"innalillahi'wa'inna'ilaihi taji'un yasa hannu ya share zufar da ta tsatstsafo masa kana yace"shi kenan Hajja karki damu ai shi Habibun yana wajen su Abdallah dan haka zamu sa ya fito da Abubakar ko ta halin yaya fatana dai kar yasa sukasheshi!'Hajja ma mikewa tayi tana ɗan share hawayen fuskarta tare da cewa shikenan Jafaru amma kar wanda yasan da wannan maganar har sai mun sami nasarar kuɓutar da Abubakar daga hannun waɗan nan azzalumai!'yace"insha Allah Hajja karki damu komai zai tafi daidai!'daga haka sukayi sallama ya fita yana sakin wani ƙayataccen murmushi,yanzu ne ya kuma yadda da shu'umancin wannan mata,saboda shima yasan itace wannan matar me niƙaf tun ajiya Abdallah ya kirashi ya sanar dashi,ji yadda take yi tamkar wata ƴar wasan kwaikwayo,cikin ƙwarin gwiwa ya faɗa motar sa ya bar estate din ba tare da ya shiga ko ina ba. Tana tabbatar da tafiyar sa,ta sheƙe da wata muguwar dariya,cikin jinjinawa kanta tace"saini Hajiya yagana mai buga gangar shaiɗan A bayan gida!'cikin takun ta na ƙaisa da alfahari ta shiga ɗakin ta,shiryawa tayi ta fito dan kaiwa ga inda zata cimma burinta. Wayar sa ce ta tasheshi daga nannauyan baccin da ya kwashe su,kamar ba zai daga ba,sai kuma ya daga ganin Safwan ne akan layi,baiyi magana ba,sai daga can ɓangaren ne Safwan yace"sorry sir Abune ya taso na gaggawa,dama wannan Abigirl ɗin ce ta farka!'cikin sauri Abdallah ya ɗan zame Bintu daga jikin sa tare da miƙewa zaune,yace"Safwan kuyi mata duk abinda ya kamata kar kubarta cikin mummunan yanayin da zata kasa amsamin ɗinbin tambayoyin da nake son yi mata!'cikin girmamawa Safwan ya amsa kana suka katse wayar. Cikin kanƙanin lokaci ta isa gidan saboda uban gudun da take sheƙawa,kai wannan tsohuwa akwai ƙarfin hali,ko da ike matan Alhaji Baba suna da matukar kyanjikin da bazaka iya tan-tance shekarunsu kai tsaye ba,shi yasa Hajja take jin kanta har yanzu da sauran ƙuruciyar ta,tana shiga suka shiga miƙa mata gaisuwa,yadda take amsawa ma kaɗai ya isa ya baka tabbacin yadda ta dauki KANTA,kujera aka dasa mata gaban Dady Abubakar wanda yake zaune hankali kwance,kai bakace saceshi akayi ba, murmushi tayi kana tace"da kyau yarona,da ganin alamu dai zaka iya bani haɗin kai cikin sauki ba tare da ka wahalar da hajjan ka ba!"ta faɗa tana wani shu umin murmushi,shima murmushin yayi tare da cewa,Hajja kar ki manta fa Ni ɗan ki ne ko nayi gaddama wa Habibu aike bazanyi miki ba,dan haka tambayeni duk abinda kekeson tambayata!'dariya tayi wadda ke cike da farin ciki kana tace"yauwa my son, shi yasa tun farko ka shiga raina ban taɓa kuma tunanin cutar da kaiba,inda dimon ɗin nan yake kawai nakeso ka faɗa min sai na mayadda dakai gida gaban iyayenka da ƴaƴan ka!'wata irin dariya ya sheƙe da ita, sai da yayi mai isarsa kana cikin muryar sa ta ainahi yace"kai wannan tsoho akwai shashasha!'sororo sukayi gaba ɗaya suna kallonsa cike da ɗin bin mamakin yadda akayi muryarsa ta canja lokaci guda,kafin ta gama fita daga mamakin da ya sakata ya kuma jefa ta cikin wani irin firgici da tashin hankali,sakamakon yaye fuskarsa da yayi,yacire fuskar ABUBAKAR da aka saka masa,fuskarsa ta cikakken bayerabe ta bayyana. Wata irin zabura Hajjah tayi tare da dafe ƙirjinta da yake wani irin bugu,cikin rawar hannu da na baki ta shiga nunashi da yatsa,yayin da bakinta ya kasa furta abinda take son furtawa,da ƙyar ta iya fuzgo maganar tace"kai kaiwaye? ID ɗin shi ya curo ya nuna mata yana mai ɗage mata gira,yace"wannan duk lissafin yaro mai ƙwazone, Abdallah yayi nisa babu mai iya taradda dashi,tunanin sa yana tafiya daidai kuma aikin sa na tafiya daidai da abinda yazo tunanin shi,ku da kuna nufin a jakar kwaƙwalwar ku ke da ɗanki Abdallah zai dauko mahaifin sa ya kuma mayar da shi inda ya kubuta da ƙyar? girgiza kanshi yayi yana wata dariyar tura haushi,Hajja kuwa tsugunawa tayi tare da dafe kanta ta rasa abinda yake mata daɗi, wannan shine taga samu taga rashi,yanzu ya zatayi ke nan,kashe mutumin nan zatayi ko zata rabu dashi ne in yaso ta rokeshi ya rufa mata asiri ta hada masa da manyan kuɗaɗen da zai jima yana amfanarsu?kai anya kuwa hakan zata yuwu?Gara kawai tasa sukashe shi hakan shine zai zama rufin asirinta,to amma ya zatayi da ƙaryar data zubawa Jafar?meye manufar sa da bai gaya mata cewa ba ABUBAKAR ne suka zo dashi ba?tunawa da wannan yasa takuma shiga tashin hankali,sosai ƙirjinta ke bugawa tamkar wanda ake kiɗan ganga acikin sa,miƙewa tayi tare da yanke shawarar kawai ta cigaba da rike mutumin nan anan har sai ta tabbatar da cewa ba ganota Dady jafar yayi ba da har ya ɓoye mata,abinda suka aikata akan Abubakar,fita tayi tana cewa ku ci gaba da riƙe shi anan,koda ta zauna cikin motar ma kasa ja tayi jikin ta duk yayi sanyi,amma gaskiya yaron nan ya shammace ta da yawa,ko ina Abubakar ɗin yake oho?ita yanzu da zata samu tasan inda dimon ɗin nan yake ai da komai ma zata iya ɗauka,A hankali take jan motar tunani fal cikin ƙwaƙwalwar ta... FATIMAH Y ADAM✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 56 ``` Yana gama waya da Safwan ya tashi ya faɗa toilet,wanka yayi ya shirya tsaf,kana yazo ya tsaya akan Bintu da har yanzu take ta shaƙar baccin ta hankali kwance,a hankali ya sunkuya ya kai bakinsa kan ɗan ƙaramin bakinta ya sumbata,wanda hakan ya farkar da ita, zuba masa ido tayi kana kuma ta ɗan tura baki tare da cewa nifa bacci nake ka tasheni!'ɗage mata gira yayi,ba tare da yace"mata komai ba yaja hannunta ya miƙar da ita tsaye, sannan a hankali ya kuma janta har zuwa cikin toilet duk bata ce mashi komai ba,sai da taga yana ƙoƙarin cire mata kaya,kana tayi saurin riƙe hannun damansa cikin tura baki tace"wai mi zakayi ne? cikin haɗe fuska yace"wanka zanyi miki!'zaro manyan idanunta dake matuƙar burgeshi tayi,kana cikin san ya tausaya mata,tace"dan Allah kabari zanyi da kaina!'ba tare da ya tanka mata ba,ya rabu da ita tare da ficewa daga toilet ɗin,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kana tashiga tsaftace kanta. Bata sameshi a dakin ba sai kayanta da ta tarar har da mayafi da alamu dai yanzun ma fita yakeso suyi,a nutse ta shirya duk da yunwar dake sakaɗar ƴan hanjinta,tsaf ta fito da ita cikin doguwar rigar atamfa mai kalar kore da baƙi, sai hakan ya kuma haska kyawunta da ƙuruciyar ta suka kuma bayyana,takalmin ta ta zura bayan ta feshe jikinta da sassanyan turarukan sa,fita tayi cikin wani irin taku tamkar wata ɗawisu. Zuba mata ido yayi yayin da yake zaune bisa kujerar dinning table,shigarta,da nutsatstsiyar kwalliyarta da babu hayaniya, ƙamshinta da yanayin takunta shi ya fi tafiya dashi,A hankali ya lumshe idanunsa tare da kwantar da kansa jikin kujerar,jinta dafdashi yasa shi ƙara buɗe idanun yana binta da wani irin kallo wanda ita kuma yake karya duk wata laka dake jikin ta,zama tayi tana bin jerin kwanayen abin karin dake kan table ɗin da kallo,zatayi magana ya rigata da cewa,inno da Hajiya Babba ne suka aiko dashi!'ya faɗa idanunsa na kanta bai ko rissuna su wajen kallon nata,ƙasa tayi da kanta tana jan yatsunta,ita kam ta rasa wannan kallon ko na magani da meyene?katse mata zancan zuci yayi da cewa,ki zuba mana ina saurine!'tashi tayi ta fara saven ɗin sa kana ta zuba itama,yunwa take ji dan haka ba ta tsaya nawa ba ta zage ta cika cikinta,shi dama Abdallah ba baya bane wajen bawa ciki haƙƙin sa,sai da suka gama kana suka fita falon inno,azaune suka sameta ita da taufiƙa wanda rabon da Bintu ta ganta har ta manta, Abdallah kuwa baima shaida ta ba,amma ita idanun ta tamkar zasu faɗo wajen kallon sa,har sai da Bintu ta samu kanta da zabga mata harara,gaishe da inno yayi,ya na gyara zaman agogon hannun sa, Bintu kuwa zuwa tayi jikin innon ta kwanta tana zuba mata shagwaɓa,inno tace"nikam zaki ƙarasani ne? jikina ba irin na mijinki bane mai ƙwari!'ta faɗa cikin dariyar farin cikin ganin su cikin walwala,tura baki Bintu tayi ba tare da tace" komai ba sai idanun ta dake kan Abdallah da take ganin kamar yana kallon Taufiƙa,kawai ji tayi idanunta sun kawo ruwa wanda kuma bata san dalilin hakan ba,Muryar Taufiƙa ta tsinkayo tana gaida Abdallah, ai ko da sauri ta kuma maida hankalinta kansa dan taga yadda zai karbi gaisuwar,amsawa yayi yana ƙoƙarin ɗora waya A kunnen sa,duk da taga yadda yayi amma hakan baisa taji nutsuwaba,juyowa yayi yace"da inno zamu fita amma bazamu jima ba!'inno ba ta tsaya tuhumar inda zasu ba,tayi musu fatan nasara,tashi Bintu tayi ta bi bayansa tana jin kamar ta tsinkawa Taufiƙa mari,Wanda ita kuma Taufiƙan fiye da haka take ji akan Bintun,duk sanda zata ga Abdallah to kuwa sai taji ana ƙara iza wutar san sa a zuciyarta,dan ma bata nan kwana biyu ita da Siddiqa da tasan abin sai yafi haka yawa azuciyar ta. Yana kula da yadda Bintun ke ta faman cin magani,saboda duk wani motsinta akan idanun sa ne,shi dai bai ma gane Taufiƙa ba bare ya gane dalilin hararar da Bintu ke antaya mata,shiga mota sukayi duk da yaso yashiga ɓangaren Hajiya Babba da Alhaji Baba Amma hakan bai samu ba sakamakon saurin da yakeyi,Bintu na ƙoƙarin shiga suka haɗa idanu da Anty Nafisa,ɗauke kai tayi tare da rufe ƙofar,tana mai ci gaba da kallon Anty Nafisa ta cikin baƙin glace ɗin window motar,sosai ta hango tashin hankali kwance kan fuskarta da kuma asalin mamakin da ya rufeta wanda Bintu bata san na meye ba,ji tayi ya jiyo da kanta saitin sa,cikin al'adar sa ta dage gira yace"Ni zaki kalla ba itaba!' so tayi ta harareshi saboda haushin sa da tasamu kanta da ji,amma sai taji baza ta iyaba hakan ne yasa ta juya hararar zuwa wani irin kallo na musamman da bata san ta iyashi ba,kuma batasan halin da yasaka wanda aka yiwa kallon ba,kawai dai taga ya koma ya kwanta sosai yana ɗan lum-lumshe idanunsa tamkar wanda yake shirin komawa bacci,A hankali ta tsinkayi Muryar shi yana cewa,me haka Bint?me nayi Makine?ita zaton ta fushin da takeyi yake tambaya,dan haka sai ta kuma tura ƙaramin bakinta tana magana ƙasa ƙasa,ba waccen Taufiƙan ce take ta kallon ka ba!'sam Bint bata fahimci komai akan abinda tayiba hasalima bata san manufar yin hakan ba,buɗe ido yayi sosai yana kallon fuskarta dake a kwaɓe da alama dai har yanzu da haushin abun atare da ita,dogon hannun sa yasa ya jawota jikinsa gaba ɗaya,ya kuma haɗa fuskarshi da tata,ba tare da yace"da ita komaiba,sai numfashinsa da yake saukar mata kan fuskarta,kwantar da kanta tayi sosai tana jin abinda ya tsaya mata na sauka A hankali,sai kuma ta shiga fitar da numfashi mai ɗauke da manufar samun nutsuwa. Hajiya zulaiha dake tsaye itama ta lumshe idanun ta tare da cewa,insha Allah ka kusa dawowa gareni,inajin haka ajikina,tun sanda na fara ganin Abdallah nake jin wani abu game dashi wanda nake fata ya zama gaskiya!'Rahima dake bayanta tace"Ammi kamar me?kuma dama baki taɓa haɗuwa da Yah Abdallah ba tun tsawon zaman shi agidan?Hajiya zulaihat tace"ban taɓa haɗuwa dashiba ban taɓa ganin sa ba,sai a daren jiya da suka dawo akan idanuna!'Rahima tace"wallahi Ammi nima inajin kwatan kwacin abin da kike ji,to komeye dalilin hakan?kama hannun ta tayi suka shige falon tana cewa,Rahima Allah ne masani shi kaɗai yasan abinda ke ɓoye,sai dai muyi fatan duk abinda zai biyo baya ya zama Alkhairi!'.. Cikin wani irin tashin hankali da sauri mai haɗe da gudu ta koma ɓangaren ta, cikin karkarwar jiki ta zaro wayarta daga jaka har tana neman faduwa,wajen kira ta shiga ta nemo nomber da zata kira,wayar sai ƙoƙarin faɗuwa take saboda yadda jikin ta ke rawa,da ƙyar ta samu nasarar karata a kunnen ta,sai da ta daɗe tana ringin har ta kusa tsinkewa kana aka ɗaga,Ya dai Hajjaju aiki ya samu kenan?cikin wata irin muryar da take nuni da tsananin tausayin kanta tace"wai mai yasa bani da sa'a ne a rayuwata?me yasa duk abinda na saka agaba sai ina murna na kusa cimma shi sai ya kufce daga gareni?me yasa nake haɗuwa da mayaudara ma ha'inta acikin dukkan sabgata?dariya yayi kana ya shiga bata amsar tambayoyinta,da cewa abinda yasa baki da Sa'a saboda waɗan da kike neman sa ar halaka su basu da alhakin cutar da kowa ballan tana ke, sannan kuma abinda yasa duk abin da kika kama yake kufcewa daga gareki,saboda ba dan kyakykyawar manufa kika riƙeshiba,amsar ki ta ƙarshe itace" saboda kema mayaudariya ce kuma maha'inciya maci amana, dan haka babu ta yadda za'ayi kiyi abota da mai gaskiya da amana dole sai irinki!'ya ƙare da cewa, Hajjaju meye aikin ki? cikin wani irin baƙin ciki da ɓacin rai ga kuma damuwa tace"mai kake nufi da waɗan nan maganganun naka?yace"Hajjaju ke nan nifa tambayata kikayi kuma na baki amsa,kuma kema kinsan gaskiya na gaya miki,kawai dai dan mun kauce ne amma ko yau muna fatan shiriya!'babu yadda zatayi da wannan taƙadirin dolene idan tana so ya bata amsar abinda take nema agurinsa sai ta haɗiye fushin ta,dan haka cikin ƙoƙarin maida mugun fushi da haushin sa da takeji tace"aikin da na baku ba kunce kun gama dasu ba?kai Hajiya Nafisa yaza ayi ki dinga dawo mana da aiki baya,bayan har shaida sai da na turo miki,ki daina haufi akan aikina,ko kinga wani kuskurene?a jiyar zuciyar samun ƴar nutsuwa tayi kana tace"yarinyar da kuka turomin hotunan ta na gani yanzu acikin gidan nan,ita me yasa baku kashe ta ba?yace"sai dai idan lokacin da muka gabatar da aikin bata cikin gidan wannan itace amsar ki,kin gama ina da abinyi yanzu?shike nan dama abinda zan tambayeka ke nan!'kashe wayar sa tayi tare da cire layin ya taune shi kana ya haɗiye,yana cewa,bazaki ƙara ganina ba a rayuwarki har abada,ita kuwa Nafisa baƙaramin kwanciya hankalin ta yayi ba,tana ganin Bintu koda bata kasheta ba bazata bata wata matsalaba,tunda babu wanda yasan ko ita wacece,duk da ko ita har yanzu bata tabbar da abinda take zargiba.. Tun daren jiya baiyi bacci ba,duk inda ya juya tashin hankali yake fuskanta,yanzu abinda su shugaba zasuyi masa kenan? duk yadda aka daɗe ana gwagwarmaya tare,amma shine yanzu zasu juya masa baya har da ƙoƙarin razana rayuwarsa,juyawa yayi ya zubawa gurin da yake idanu duk da ba gani yake ba saboda tsananin duhun wajen,yanzu ɗan ɗan uwansa ne ya jefashi cikin wannan halin?abinda zuciyar shi ke ta tambayar shi ke nan,ji yake tamkar yasa hannu aka yayi ta zunduma ihu,abin duniya ya dameshi,zuciyar shi tamkar ana babbakata da wuta haka yakeji,sai dai kuma sam har yanzu babu alamun nadama atare dashi sai hanyar kuɓuta da samun cikar buri. Zubawa kyakykyawar fuskar ta idanu yayi wanda sam baya gajiya da kalla,A hankali yayi magana cikin miskilar muryar sa,yace"sleeping beauty wake up!'ya faɗa yana ɗan taɓa tattausan kumatunta,buɗe idanun ta tayi wanda suke cike da baccin da Bai isheta ba,ɗage mata gira yayi tare da cewa,yarinyar nan na kula sam bazaki iya kwanan zaune ba!'a hankali ta zame daga jikin sa tana ɗan bin farfajiyar gidan da kallo,dawo da kallon tayi kansa tana shirin tambayar sa,nuni yayi mata da su fita kar tace komai,dole ta haƙora da abin da take son cewa suka fita daga motar,kai tsaye cikin falon suka nufa,bin ko ina takeyi da kallon baƙunta da kuma mutanen da bata san su ba,gaisuwa suke ta miƙa wa ogan su suna haɗawa da gaida Bintu yarinyar da yanzu suka gama gasgata cewar matarsa ce,ɗakin da Abigirl take suka nufa yana rike da hannun Bintu tamkar ance za a kwace masa ita. Zaune take ta haɗa kanta da gwiwa kana kallon ta zaka san cewa cikkakiyar kafura ce,jin motsin da tayi ne yasata ɗagowa da sauri,wata irin zabura tayi ganin Abdallah wanda bata taɓa tsammanin gani a daidai wan nan lokaci ba, cikin rawar harshe ta kira sunan da tafi ƙware wa da faɗarsa, Fatash!'wani irin mummunan kallo ya shiga watsa mata,yayin da Bintu ma ta kuma bude idanun ta jin sunan da aka kira Abdallahn ta dashi, cikin tsanar sunan da wadda ta ƙirƙiri sunan yace"ba tun yauba kuma batun yanzu ba nake miki jan kunne akan kirana da sunan kafirai,yanzu kina cikin tarkona ne,dan haka idan na kuma jin wannan baƙin sunan a bakin ki sai na zubda hakoranki gaba ɗaya!'shuru tayi tana kallon sa babu abinda ya sauya daga halayyar dayake nuna mata tun asali,zama yayi ya turawa Bintu kujera itama dan ta zauna, amma sai ta kasa zama ita kawai so take tasan wani abu akan matar nan da kuma sunan da ta ambacesa dashi,gane hakan da yayi ne yasa yayi mata banza,ba tare da yakuma duban inda take ba,ya juya kan Abigirl wadda tayi tsumu- tsumu da ita,tabbas ta daɗe tana fargabar wannan rana da Abdallah zai zo ya tutsiyeta dan sanin abinda take ta ɓoyewa tsawan shekaru,kallon da yake mata yasa ta kuma rikicewa duk ta rasa wata nutsuwa, zuciyar ta cike take da tsoron Abdallah da irin hukun cin da zai yi mata,dan ta san tunda ya rutsata dole sai ta faɗa masa asalin labarin ko taki ko taso, Abigirl yadda ya kira sunan ma kansa abin firgici ne,dan hatta da Bintu dake tsaye idanun ta kan Abigirl ɗin sai da ta juyo ta dubeshi,fuskar nan babu alamun wasa ko wani annurin dake nuna zaiyi sassauci A al'amarin sa da Abigirl ɗin, cikin ƙara kiɗimata da sautin muryarsa yace"waye yabaki Ni kuma a wane dalilin sannan da wace manufa aka bakini?zatayi magana ya dakatar da ita,da hannun sa tare da cewa ba yanzu nake buƙatar amsarki ko musuntawarki ba,ina miki tambayar ne dan ki shirya amsata agaban dimbin jama'a da kuma wadda ko wanda yasaki aita aikin da zai zamo miki danasi wanda Hausawa suke kira da ƙeya,ina mai tabbatar miki da cewa duk ranar da nazo dan karɓar amsar tambayoyina ki kayi min gardama to wallahi sai kin gane kurenki sai kin gwammaci baki zo duniyar ba,dan haka ki shirya zuwa cikin ESTATE dan fallasa sirrin da kike ta sirrintawa tsawon waɗan nan shekarun!'daga haka ya mike tare da hanƙada kujerar da ya tashi akai zuwa fuskar Abigirl,wanda badan tayi saurin kaucewa ba da tuni ya cire mata wani abun daga sassan fuskarta. Binsa Bintu tayi ganin ya fita, zuciyar ta cike da tunanin ko ita wannan wacece kuma,tana da tarin tambayoyin da take son yi masa amma yaƙi bata damar hakan,ko meye dalilin sa na hana ta tambayar sa kuma oho?bayan ita duk abinda ya tambayeta tana amsa mashi dai dai da abinda yake son sani,ji tayi wani haushinsa ya kamata tare da kewar fafinta,ko wane hali suke ciki, yace" ta kwantar da hankalin ta zai kawo mata ummin ta da fafi amma har yanzu shuru ko maganar ma bayayi,sai ma can wasu al'amura da yakeyi wanda bata gane musu ba,wani kuka taji yana taho mata wanda hakan yasa ta saka hannun ta ta toshe bakinta,juyowa yayi tare da zuba mata ido sai dai baice komai ba,cikin kallon nata ya fahimci damuwarta da kuma dalilin kukanta,ji yayi jikin shi ya mutu tare da wani irin tausayinta ya kan rasa meke damun shi akan Bint indai lamari akanta ne bashi da wani sukuni ko pawer, hakan yasa ya jawota jikin sa suka ci-gaba da takawa har zuwa bakin motar su,da sauri Yahya ya buɗe musu suka shiga,shi kuma ya zaga ya shiga mazaunin drever,sai da suka fara tafiya kana ya ɗago fuskarta dake kwance kan kafaɗar sa,zaro oily eyes ɗinsa yayi cikin san kawar mata da damuwarta,yace"me yafaru da idanunki haka wannan ai sai ki bani tsoro!'sai ya ɗan rufe idan sa alamun wai baya son gani tana bashi tsoro,sanin tsokanarta yake da kuma yadda yayi da fuskarshi sai hakan ya bata dariya,ga kuma tsananin mamakin yadda yake mata wanda tasan da wannan duk ba halinsa bane,amma yanzu wai duk dan yasata farinciki yake yin abinda bai saba dashi ba,ganin hakoranta sai ya samu kansa da samun nutsuwa har shima ya saki wani ɗan ƙawattacen murmushi da ya ƙawata kyawunshi da kwarjinin shi,wanda har bata san da ta zubawa fuskar tashi idanu ba,ɗan gemunshi dake matuƙar burgeta ta mai da hankali wajen kalla,ji tayi yace"kinaso ne?da sauri ta maida kanta ta ɓoye a ƙirjinshi saboda kunyar da taji ta rufeta, cikin taushin murya yace"Bint kiyi haƙuri Ina sane da abinda nakeyi na kusa cika miki burinki,ki ɗauka tamkar kina tare da Ummi da fafi ne,kinji ko bana son ganin damuwa akan fuskarki!'ya faɗa yana jan lafiyayyan kumatun ta,A hankali tace"to ya Abdallah ka kaini naga Dady mana dan Allah!'zan kaiki shike nan? Ɗan ƙif-ƙif tayi da idanun ta kana cikin sanyin murya tace"wacece wannan matar da take kiranka da wani suna?kawar da kanshi yayi sam baya san abinda zai dan gantashi da wannan kafurar matar,yace"matar da ta riƙeni ce!'wata irin zabura tayi tana kallon sa cike da mamaki,ganin yaƙi kallonta sai ta ɗan langaɓar da kanta bisa kafadunshi tare da cewa,ayya to meyasa zaka kawota nan?ko itama tasan wani abu game da barinka gida?sai da tayi wannan tambayar ya juyo da fuskarsa inda take,yace"inye kaga yarinya tayi gadon basira,tayi tambaya ta bawa kanta amsa kuma!'dariya tayi wanda saida fararan haƙoran ta suka baiyana,haka nan takejin wani irin nishadi da farinciki duk lokacin da ta kasance da oganta Abdallah, bare yanzu da yake ririta farincikin ta yake gudun damuwar ta yake neman duk wani abun da zai cire kunci a zuciyarta ga shi kuma ta gama fahimtar halayyar sa tsaf sai ɗan abinda ba arasaba,yace"Bint zakisan abinda ya faru dani da kuma irin rayuwar da nayi tare da wannan kafurar matar,amma sai agaban dukkan ahlinmu, acikin falon Alhaji Baba,tare da Dady da Ummi da fafy,da kowa da kowa da yake buƙatar sanin rayuwar da mukayi Abaya!'jinjina masa kai tayi cike da gamsuwa da bayanin sa,daga nan kai tsaye gidan malam suka nufa. Baƙaramin farinciki sukayi ba ganin yadda aka samu ci gaba a lafiyar Dady Abubakar,sosai yake samun kulawa a gurin malam da sauran ɗaliban sa,duk da dai yana kwance har yanzu bai buɗe ido ba, amma tsaf yake tamkar idanun sa biyu,Bintu ce ta matso kusa dashi tare ɗora hannun ta kan hannun sa ta riƙe a hankali ta shiga karanto addu'oin samun sauƙi gareshi,tanayi tana tofa masa asaman kansa da idanun sa, Abdallah kuma magana suke da malam dan haka sai hankalinsa ya rabu biyu,kamar almara Bintu taga hannun da tarike yana motsawa,nutsuwa tayi tare da zubawa hannun ido dan tana son gasgata abunda idanunta suka gani,ganin bai kuma motsawa ba sai ta dawo da kallon ta kan kyakkyawar fuskarsa wadda asalinta da kwarjinin ta suka bayyana,zubawa fatar idonsa ido tayi saboda ganin kamar tana motsawa,tabbas kuwa ba gizo idanunta kemata ba,kafin tayi wani abu kuwa sai ga idon Dady Abubakar akanta ya buɗe su fes yana kallon ta,wata irin zabura tayi tare da sakin kuka da kabbara duk alokaci ɗaya,wanda hakan yasa malam da Abdallah suka zaburo zuwa inda take, Abdallah jikin sa na rawa yake tambayar ta lafiya?kafin ta bashi amsa ya hango amsar da idanunsa,ɗurƙushewa yayi gaban gadon da Dady yake kai kusa da Bintu,yayin da malam yake ta kabbara tare da hailala, Bintu kuwa cikin wani irin yanayi na tsantsan farinciki take cewa Alhamdulillah masha Allah,Dady kana gani? kayi magana ga Ya Abdallah ga kuma Ni Bintu ɗiyarka ɗiyar ɗan uwanka Abbana Umar!cak taga ya tsaida ƙwayar idanun sa akanta,yana mata wani irin kallo, Abdallah kuwa kwantar da kanshi yayi jikin Dady yana fidda wani sassanyan murmushi wanda yake fitowa tun daga asalin zuciyarsa,A hankali Dady ya shiga jan hannunsa cikin nutsuwa da rashin ƙwarin jiki ya ɗora bisa kan Abdallah yana shafawa wanda hakan ya kuma jefa BINTU cikin wani irin shauƙi jin farin ciki take har ƙoƙon ranta,sai kuma taji wasu hawaye masu ɗumi suna gangarowa kan fuskarta,sha awar Dady da Abdallah taji ta mamaye ta,ina ma itama zata ganta jikin Abbanta yana shafa kanta cikin so da ƙauna,tunanin tane ya katse lokacin da taji Muryar Dady duk da ba fita take sosai ba amma zaka fahimci abinda yake cewa,yace"tashi ka bawa ɗiyata gurin ta ba kanka naso na fara taɓawa ba kanta ne saboda itace bata taɓa jin ɗumina ba bata taɓa zama tare dani ba,ba ta taɓa yin wasa dani ba,kai kuwa ka hau jikina kafin azzalumai su rabamu,kayi wasa dani kafin mu rabu kuma kaci abinci dani,dan haka matsawa ɗiyata ta fara samun nata gatan tun yanzu kafin Allah Ubangiji ya bani ikon miƙewa gaba ɗaya na nuna mata gatan da babu wata diya da ta taɓa samun shi a cikin duniyar mu!'wani irin kuka ne ya ƙwacewa Bintu mai haɗe da wani irin shauƙi da jin ta yau tacika ƴa, ƴar gata,waɗawa jikin sa tayi shi kuma yasa hannu a gadon bayanta yana bubbugawa cike da san rarrashinta,ko Ni tunda nake ban taɓa ganin dariyar Abdallah da hawaye ba sai yau,jarumtar shi ta ƙare ba zai iya jurewa ba,farinciki tare da tausayin su baki ɗaya da kuma kalaman Dady suka saka shi hawaye,malam ma sai da ya share hawayen tausayin waɗan nan bayin Allah,shi tun da yake arayuwar sa bai taɓa cin karo da abin mamaki da tausayi ba kamar labarin bayin Allah nan, Allah ka ƙaremu daga makircin shaidan kayi mana tsari da faɗawa halaka,a hankali Bintu ta ɗago kanta kana tace"Dady na ina son ka,dama haka kasancewa da uba yake? dama haka waɗan da suke tare da iyayensu sukeji? murmushi kawai Dady yakeyi kana yace" fiyema da haka suke ji kema zakiji fiye da haka tukun na dai Allah ya bamu aran lokaci!'amin suka amsa, Abdallah cikin marairaice fuska yace"tunda abun wariyace,nima yanzu zanje na nunawa Abbana ɗan sa da ya daɗe yana bege sai kowa ya riƙe nashi!'dariya sukayi baki daya cikin tsananin farin cikin da ya mamayesu a wannan rana mai ɗinbin tarihi. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 57 ``` Bazan iya misal ta muku irin farin cikin da waɗan nan mutane suka shiga awan nan rana mai matukar muhimmanci ba,A hankali sai da suka sanar da Dady duk wani labari da gwagwarmayar da suka sha,abu ɗaya ne bai sani ba Yadda aka saceshi sai kuma labarin rayuwar sa a hannun Abigirl wanda shima yace a bakinta zasu ji,kuka Dady yake da idanun sa kukan bakinciki da ta kaicin zamowar ɗan uwansa da step mom ɗin sa maha inta a cikin zuri'ar su,su waɗan can nasu mai sauƙine,tunda danganta kar bata kai wannan ba,da ƙyar suka rarrashe shi yayi shuru,daga nan suka yi sallama, Bintu tace"Dady sai gobe zan dawo!'Abdallah ya harareta tare da cewa bazaki kuma fitowa ba,saboda shima goben nake son mai dashi gaban tsohon sa!'bata san lokacin da ta ɗane shiba cikin farin ciki tace"yauwa ya Abdallah hakan ma yafi ko Dady tunda dai kasamu sauƙi!'dariya yayi cike da samun nutsuwa yace"hakane ɗiyata ina son ganin tsoffina nima naji daɗin da kikaji!'da wannan suka bar gidan zuciyoyin su fes, Yaso ya kaita gidan da su Ummi Laila suke,sai dai kuma ya fasa saboda so yake yayiwa Bintu bazata dukan su ma,gashi dama Fafi ma ya samu sauƙi,dan haka kawai sai ya ƙyale Yahya ya maida su estate. Abba umar ma dai yana can Itali,babu wanda yayi tunanin wani abu akan sa tunda babu wanda yasan abinda Anty Nafisa take kurdawa,kuma kowa yasan shiɗin ba mazauni bane,amma dai shima goben yake shirin dawowa dan san yiwa Nafisan tasa bazatar,(to Allah dai ya kaimu goben nan dan da alama ranar fallasace da fasa muggan ƙwayaye,ranar da zata yiwa wasu daɗi san nan ta zamo wa wasu ranar jin kunya da mozanta a idon ƴan uwa da abokan arziƙi,(nima dai zanso naga goben nan dan kuwa zata zo da abubawa masu yawa na kuka da na dariya mamaki da al'ajabi) Suna fitowa daga mota suka ci karo da Dady Mansur wanda yake shirin shiga ɓangaren Alhaji Baba,har ƙasa suka durƙusa suka gaida shi, abinda Abdallah bai taɓa yiba,daga Bintun har Abdallah samun kansu su kayi da jin kunyar Dady Mansur ɗin,shima dai kunyar tasu yakeji saboda kasancewar ɗan uwan sa na jini da ya zama azzalumi agaresu,cikin tsananin ƙaunar yaran da tausayin su, ya dafa kawunan su,kana yace"Allah yayiwa rayuwar ku albarka, Allah kuma ya kawo mana ƙarshen duk wata musiba!'Amin suka amsa cikin jin daɗin yadda Dady Mansur ya koma mutum mai nutsuwa,da kama girman sa,yace"ku tashi mu shiga ko ba gurin Alhaji Baba zaku shiga ba? Abdallah yace"nan zamu shiga Dady!'daga nan suka rankaya suka shiga falon Alhaji Baba,shi kaɗai ne a falon yana kallon tashar aljazira hannun sa riƙe da tasbaha,yana ganin su fuskarsa ta kuma washewa da wani irin annuri,hannu ya miƙa wa Bintu da Abdallah yace"kuzo nan kwana biyu kunyi min ƙaura ban san dalilin da yasa hakan ta faru ba!'cikin girmamawa suka gaida shi,kana Abdallah yace"kayi haƙuri Alhaji Baba wasu aiyukane suka shamin kai kwana biyu shi yasa!'ya juya ga Bintu da take ta zuba murmushi saboda yau wani irin farin ciki takeji wan da tasan baya rasa nasaba da samun lafiyar Dady da kuma tabbacin da Abdallah ya bata na bayyanar ummin ta da fafinta akusan nan,yace"Batula ke kuma fa meye uzurinki?da sauri tace"ai tare muke yin komai!'ji tayi sun saka dariya shi da Dady Mansur,yace"wato kun zama ƴan biyu ke nan tare kuke yin komai?sunkuyar da kanta tayi saboda kunyar da ta ɗan kamata, Alhaji Baba yace"to masha Allah hakan yayi kyau!'cikin nutsuwa Abdallah yace"Alhaji Baba akwai alfarmar da nake nema awajen ka!'Alhaji Baba ya gyara zaman sa yana daɗa fuskantar Abdallah da bashi dukkan hankalin sa,kana yace"Abdallah ka faɗi buƙatar ka kai tsaye babu batun alfarma dan nasan ko me zaka zo dashi Alkhairi ne insha Allah!'ɗan kallon Dady Mansur yayi sai yaga ya gyada masa kai alamun ya faɗi abinda yake son faɗa babu matsala,dan haka sai Abdallah ya maida hankalinsa kan Alhaji Baba tare da cewa,dama ina sone gobe idan Allah ya kaimu katara duk mutanen gidan nan acikin falon ka,hatta da surukai ban ɗauke su ba,idan nace kowa ina nufin kowa da kowa sai dai wanda baya nan,ƙarfe huɗu bayan sallar la asar akwai abinda nake son GABATAR muku dashi mai matukar muhimmanci,amma dan Allah acikin waɗanda basa nan ina buƙatar Abba Umar a wan nan zaman saboda zuwan nasa yana da muhimmanci!'jinjina kai kawai Alhaji Baba yake sai da yaji Abdallah ya kawo karshe a maganar sa, kana yace"wannan ba abin damuwa bane Abdallah fatana kawai Allah yajiyar damu Alkhairi Allah yasa taron da zai amfanemu ne baki ɗaya,gaba dayan su suka amsa da Amin,daga nan suka bar falon shida Bintu suka bar Dady Mansur. Tun bayan dawowar ta daga gidan ta rasa sukuni gaba ɗaya cikin fargaba take,duk motsin da zataji sai ta zabura,ta kasa zuwa ko ina,ta kuma rasa ta hayar da ya kamata ta binciki su Abdallah ko sun gano makircin ta,duk da ko tasamu hanyar baza ta iya aikatawa ba saboda kar taje allura ta tono garma,sallamar Taufiƙa ce"ta dawo da ita hayyacinta,zama tayi akusa da ita tana cewa Hajja me yake faruwa ne naga kamar ba anutse kike ba? murmushin yake tayi tare da cewa bana dan jin daɗi ne kwana biyu!'Taufiƙa tace"ayya sannu Hajja Allah ya sauwaƙe!'tace"Amin tana ƙoƙarin miƙewa ta bar falon dan tafi buƙatar kaɗaici a wannan lokacin,kafin ta kai ga mikewar ta kuma tsinkayar muryar BINTU tana rangaɗa sallama cikin sassanyar Muryar ta,wani irin tsinkewa zuciyar Hajja tayi tare da komawa ragwab ta zauna ba tare da ta shiryaba, duk wan nan tashin hankalin nata baya rasa nasaba da shigowar Abdallah cikin falon ba,yanayin takunsa na isasshen namiji da kuma kwarjinin sa, shine abin da yaso rikita ta da saurin fallasa rashin gaskiyar ta,zama yayi ba tare da ya ce komai ba sai hankalinsa dake kan wayarsa, Bintu ce ta tsuguna a gefan Hajja ta gaida ta,amsawa tayi cikin fara'ar da bata taba yiwa Bintu irinta ba,gaba ɗaya a ruɗe take saboda bata shirya komai akan tuhumar da Abdallah zaiyi mata ba,da ace ba tariga tayiwa Jafar waccen ƙaryar ba ne,to da zata iya samun abin cewa dan kare kanta,shuru falon ya ɗauka sai da Abdallah ya gama shan ƙamshin sa, kana ya juyo yana fuskan tar Hajja tare da gaishe ta,amsawa tayi cikin wani irin bugun zuciya,wanda har mamakin kanta take saboda bata taɓa tsammanin a kwai wani mahaluƙi da zataji tsoron fuskantar sa ba, sai kuma gashi har tana jin fiye da zaton ta akan jikan ta, cikin haɗe fuska da dauke kai yace"Hajja ta ɗan bamu guri!'duban Taufiƙa tayi wadda tasan cewa da ita yake,tace"Taufiƙa tashi ki bamu guri!'cikin sanyin gaddama ga umarnin da aka bata,tace"Hajja mu tashi dai ai naga bani ka ɗai bace a gurin!'wani irin rikitaccen kallo ya watsa mata wanda yasa ta tashi babu shiri har tuntuɓe take ci da ƙafar Bintu, Tana shiga ɗakinta tayi sufa saman gadon ta,tare da saka wani irin kuka mai sosa zuciya,ko yaushe ne Bintu har ta samu irin wannan soyayya mai zafi daga gurin Abdallah?karfa bakin da inno tayi mata ya tabbata dan kuwa gashi nan ta fara ganin alamu, Taufiƙa sai dai hakuri fa dan daga dukkan alama dai Abdallah ya rufe ƙofa, A can falon Hajja kuwa bayan da ya tabbatar da Taufiƙa ta bar wajen,sai ya ɗan kuma gyara zaman shi cikin nutsuwa yace"Hajjah dama nazo ne akan maganar Dadyna!'yadda ta zuba masa ido da yanayin ruɗewa shine yaso bashi ƴar dariya,sai dai kuma yayi ƙoƙarin maida ta tunda dama ba al aldarshi bace,cikin ɗan ruɗewar da ta farayi tace"Abubakar ke nan?yace"wanda kika tafi dashi jiya!'ya faɗa idanun sa akan Bintu wadda ita kuma ta zubawa Hajja nata idon dan har yanzu al'amarin mamaki yake bata, bata taɓa yiwa Hajja kallon muguwaba amma sai gashi ya tabbata cewa itace makirar cikin zuri'ar Alhaji Baba,Hajja kuwa da kyar ta iya aro jarumta wanda duk da haka tsoran ta da rashin gaskiyar ta bai kasa bayyanuwa ba,cikin kasa haɗa ido da ɗayansu tace"Abdallah an samu akasi fa ban san ta inda abun ya juya ba saboda wannan mutumin ba Abubakar bane,kuma ina tunanin duk daga sharrin Habibu ne!'ta juya maganar dan san tabbatar da zargin ko sun gano makircinta,cikin dabi ar sa ta rashin gano ainahin abinda yake zuciyarsa,yace"Hajja yanzu kina nufin mun kuma rasa Dady?cike da mamaki take kallon sa,kana tace"amma ai na ɗauka duk ku kuka shirya hakan?ya akai kika san haka?ya kuma jefo mata wata tambayar,cikin ruɗewa da san kama kanta tace"ai shi ya faɗa da bakin sa!'a wannan karon Bintu ce ta jefo mata tata tambayar da cewa to Hajja ya akayi ya faɗa miki bayan wannan abun sirrine tsakanin su su uku?cike da tashin hankali take duban Bintu ta kasa bata amsar tambayar ta,Bintu bata saurari abinda zata ce ba ta cigaba da cewa,kinga hakan yana nufin an so yi masa wani abune da zai iya cutar dashi shi kuma yaga kawai gara ya bayyana cewa bashi ne Dady ba!'wani irin kallon tashin hankali tabi Bintu dashi kana tace"yanzu me kike nufi?nice zanyi ƙoƙarin cutar dashi?da sauri Bintu ta girgiza kanta tare da cewa abun ne akwai mamaki da ɗaure kai Hajja saboda mu ba irin bayanan ki Dady jafar yayi mana ba, hasali ma munzo ne dan sanar dake abin da ke faruwa,sai kuma muka ji saɓanin abin da ya kawo mu daga bakin ki,bayan kuma kince an ɗauke Dadyn!'Bintu ta ƙarasa maganarta da tsare Hajja da idanuwan ta irin na Abdallah,wata irin zufa ce ta shiga ketowa Hajja tana kuma mamakin yadda yara ƙananu suke son mozanta ta a fakaice,gashi sunƙi bata damar gano manufar su,ganin halin da tashiga ne yasa Abdallah miƙewa tare da cewa,shike nan Hajja yanzu ina shi wan can da muka saka a madadin Dady?da sauri tace"ai yana nan zan sa akawoshi!'Bintu tace"meyasa da kikaga ba Dady bane baki barshi yay tafiyarsa ba?a yanzu kam anzo gaɓar da take neman fito da kanta, kasa bawa Bintu amsa tayi saboda bata da amsar,dan haka shuru tayi tana rarraba ido, Abdallah ya kama hanyar fita daga falon ba tare da ya kuma tankawa ba. Suna fita taji kamar an zareta daga cikin masifa,kai yaran nan sun iya tambayoyin da zasu saka mutum ya kama kansa sai kace wasu lauyoyi ko ƴan jarida,karma yarinyar nan taji labari,hatsabibiyar yarinya kawai,gaba ɗaya dai a wannan rana nutsuwar Hajja ta ƙare ta rasama ta kaimaiman tunanin da zatayi akan wannan al'amari,bata taɓa tunanin cewa akwai ranar da zata kwaɓe mata ba,bata taɓa tsammanin asirin ta zai iya neman tonuwa ba,kuma ko a yanzun ma bata tunanin haka a ranta dole zata san mafitawa rayuwarta, Ɗan tsayawa yayi Bintu ta ƙaraso,kallon juna sukayi Sai kawai suka saka dariya,abinda ban taɓa gani ba a fuskar Abdallah,lallai yau farin ciki yay farin ciki,A hankali Bintu ta shiga gwada yadda Hajja tayi tun shigar su falon, Abdallah kuwa Binta kawai yake da wani kasalallan kallo yana murmushin gefan baki,da dai yaga ba da katawa zatayi ba kawai sai ya ja hannun ta suka cigaba da tafiya har zuwa sashen Hajiya Babba, Kallo take binsu dashi wanda yake nuni da tsananin ƙaunar da take musu kuma har ta kasa ɓoyuwa cikin idanun ta,rungume Bintu tayi tana shafa kanta,ita kuma kamar wata mage tayi wani luf sai faman lum-lumshe idanuwa takeyi,sun ɗan daɗe a ɓangaren Hajiya Babba daga nan sukayi mata sallama suka koma sashen inno,sai da yaje yayi Sallah ya dawo kana ya samu Abincin inno najiran shi,ita Bintu tuni ma har taci nata saboda yunwar da take ji,shima zama yayi yaci, kana ya miƙe tare da ɗan kallon inda Bintu take zaune,so yake ya ɗan fita yaje gidan da yakai su Ummi,ƙarasowa yayi inda take zaune ta ƙurawa tv Ido kamar tanaso ta ciro mutanen dake ciki,zama yayi a kusa da ita tare da ɗan taɓa ta zabura tayi cikin tura baki tace"nikam ka bani tsoro ma!'yace"fita zanyi amma bazan jima ba!'da sauri tace"ba tare zamu tafiba?girgiza mata kai yayi tare dayi mata alama da girarsa, karyar da kai tayi kamar wata sabuwar marainiya,kana tace"ayya Yah Abdallah kasan fa ko ina tare muke zuwa meyasa yanzun bazaka dani ba? kai tsaye ya bata amsa da cewa nan ba gurin zuwan matan aure bane!'zaro idanu tayi tare da cewa to ai kai ma mijin aurene nikam tsoro nakeji bazan iya zama ba!'tashi ki tafi wajen inno!'ya faɗa yana miƙewa,tashi tayi jiki a sanyaye sai murza idanu da takeyi alamun dai tana son yin kuka,tsayawa yayi tare da zuba mata ido,shifa sam bashi da wata zarra akan abinda ya shafi BINTU,shi yasa yake kokarin ganin yayi abinda zai faranta mata,itace sanadin farin cikin sa da duk wata walwala da ya tsinci kansa aciki,kamo hannun ta yayi a hankali yayi mata masauƙi cikin faffaɗan ƙirjinsa,wani abu yake ji game da ita yana daɗa tsikarar zuciyarsa,mutsu mutsun da take ne yasa shi ɗago kanta sai yaga hawaye shaɓe shaɓe kan kyakkyawar fuskar ta,bakinsa ya kai kan fuskarta ya shiga share mata hawayen da harshensa, wanda ɗumin harshen nasa ya saukar mata da wata irin kasala da mutuwar jiki, cikin wata irin murya yake cewa ke Bint kin san zafin wannan kuwa kin san raɗadin zubar wayenki kuwa?bata fahimci mai yake nufi ba dan haka sai ta shiga girgiza masa kai,ɗan ware idanun sa yayi akan ta,daga nan kuma ya samu kansa da zura harshen sa cikin bakinta,take jikin ta ya shiga karkarwa,ganin ƙafafunta na san kasa ɗaukar ta yasa ta kuma rikoshi da kyau daga nan salon ya kuma sauyawa da wani irin mayataccen sumba mai ruɗa zuciya da gangar jiki,ba ga ogan ba,baga yarinyar ogan ba,wani irin mahaukacin salo yakewa Bint din tasa wanda shi kansa baibsan daga ina ya iyasaba,nema yake ya kasa control ɗin kansa akan Bintu,duk wani ƙarfin shi ƙare wa yake a duk lokacin da ya kasance da ita,suna cikin wannan halin basu ankara ba saijin kiran sallar magriba sukayi a tsakar kansu,wanda dole ta sa su rabuwa da juna,kawar da kanta tayi saboda kunyar abin da tayi,leƙa fuskarta yayi tare da cewa my ukty, na fasa fitar bazan barki ke ɗaya ba,da sauri ta juyo da fuskarta gareshi sai caraf ta kuma tsinkayar bakinsa cikin nata,amma ba sha yake ba tsayawa yayi yana kallon cikin idanun ta da ta kasa kallon sa,a hankali ya miƙe da ita ajikin sa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa,sai da ya shiga kana ya sake ta tare da shigewa toilet,yana fitowa yace"kiyi alwala masallaci zanje yanzu zan dawo!'kai ta ɗaga mishi kamar wata ƙadangaruwa dan bakinta da jikin ta duka amace suke da irin zazzafan kulawar Abdallah agareta. Duk da cewa zuciyar ta ba anutse take ba hakan bai hanata son aiwatar da niyar ta ba,shirinta takeyi ta haɗa duk wani abu da zai iya zame mata arziki dan wucewa dashi,jira takeyi kawai gari ya waye ta fece,tana cikin wannan shirin kuma katsaham ta samu waya daga Alhaji Baba cewa yana buƙatar ta gobe da misalin goma a falonsa,(kasancewar Abdallah ya dawo da taron da safiya saboda wani tunani da yayi)jikin ta asanyaye ta amsa tare da ajiye wayar,ta gumi ta zabga tana tunanin abinda yasa ake hada taro rana tsaka,wata zuciyar tace mata ko dai mutuwar Umar ce ta samesu shi yasa ake son sanar da ita cikin nutsuwa, wannan tunanin da tayi ne yasa ta kwashewa da wata shegiyar dariya,wadda ita agurin ta ta cin nasara ce,yanzu hankalin ta ya kwanta sai kuma tsimayin abinda zai faru gobe. Yana cikin filin jirgin sama na malam Aminu Kano ya samu wayar mahaifin sa,nasan kasancewar sa a gobe ƙarfe goma na safe cikin falon sa,cikin ladabi ya sanar da Alhaji Baba ai yana Kano saukar sa ke nan dan haka insha Allahu zai halarci taron,daga nan jirgin da zai kaishi Abuja ya wuce,yana sauka bai wuce ko ina ba sai gidan dasu Hajja suke,cikin girmamawa ya sanar da Hajjo cewa su shirya zai zo ya ɗauke su gobe dan zuwa estate zai gabatar dasu a wajen Alhaji Baba, Duk wanda ya kamata yasan da wannan gagarumin taron ya sani har ma waɗan da Abdallah baicewa Alhaji Baba ya sanar dasuba, duk saida yasanar dasu ƴaƴan Hajja waɗan da suke nesa da yawa ne kawai bai ce lallai sai sunzo ba,Hajja kuwa ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba,babu yadda batayi da Alhaji Baba ya sanar da ita ko taron na meye,amma yaƙi cewa da ita komai, hasalima sai ya ɓoye mata cewa Abdallah ne ya haddasa taron,ganin yaki sanar da ita dalilin kawai sai ta rabu dashi dan bata son ta tsaurara bincike har ya ɗora mata ayar tambaya,waɗan da basu razana da kiran Alhaji Baba sune masu zuciziyar zinare, zuciyar da babu komai acikin ta sai Alkhairi,to Allah dai ya jiyar da mu Alkhairi a wannan zama na falon Alhaji Baba cewar da yawa daga cikin ahalin wannan estate ke nan. A wannan rana da yawa daga cikin alhalin Alhaji Baba baccin su ragaggene daga na cikin gidan har na wajen irin su Baba nura kenan dasu Alhaji Hashir waɗan da kowa yasan da wannan taron dan duk da cewa suna garƙame amma saƙon ya tarar dasu,dan Abdallah bai bari Alhaji Baba yasan cewa ƴan uwan sa da ƴaƴan sa basa cikin gidan ba shi yayi uwa yayi makarbiya yace"zai sanar dasu,dan haka gaba ɗayansu hankalin su atashe yake, dukkanin su suna cikin halin nadama domin babu wanda ya tsammaci zuwan wannan rana agaresu, Alhaji Hashir kuka yake da idanun sa yana kaicon rayuwarsa da tsufan sa da gemun sa amma yabi ruɗin zuciya da kiɗan shaiɗan,yana matuƙar tsoro da jin kunyar haɗa ido da ɗan uwan sa,ji yake yi inama Allah zai ɗauki rayuwar sa kafin wannan rana ta jin kunya da mozanta ta waye, Shi kuwa Dady Habib, bai san komai da yake faruwa ba, Abdallah bai bi takan sa ba,dan yasan shu'uman cin sa zai iya neman hanyar kufcewa daga garesu,tunda har yanzu baiga alamun nadama atare da shi ba,shi yasa ya rabu dashi sai agoben zaisa arufe masa idanu a shiga dashi har cikin falon Alhaji Baba, Misalin ƙarfe takwas na safe Abdallah ya fito cikin shirin sa tsaf,sai zabga ƙamshi yake kamar wanda yayi ɓarin turare ajikin sa,Bintu dake ta sharar baccinta hankali kwance sai buɗe idanu tayi taga yana shirin fita,ai kuwa wata irin wuntsilowa tayi daga kan gadon tare da fara murza idanun ta,dan ba sai yayi mata bayani ba tasan cewa fita zaiyi ya barta,bai san ta farka ba sai takunta da yaji abayansa,tsayawa yayi tare da juyowa,kallanta ya shiga yi tun daga sama har ƙasa sanye take cikin wata ƴar figigiyar riga iya gwiwa gashinta kuwa duk yabi ya baje a kaɗarta,kana ganinta kaga wadda ta tashi daga bacci,da gira yayi mata nuni da jikinta,sai tashiga bin jikin nata da kallo amma dai ita bata ga komai ba,dan haka ta ɗago ta kalleshi da alamar tambaya,ɗan lanƙwashe kansa yayi a kafaɗarsa kana cikin taushin muryarsa yace"ba bina zakiyi ba?da sauri ta ɗaga mashi kai,yace"A hakan zaki bini me yasa yanzu bakya son zama a gida?tura ɗan bakinta tayi tare da cewa aiya nikam tsoro nakeji!'matsowa yayi gab da ita kana yace"Dady zanje na ɗauko kafin ki shirya ko kin manta da taron da muke dashi anjima?girgiza kai tayi tare da cewa to amma ka tsaya nayi wanka sai mu fita tare Ni sai na zauna wajen inno kafin ka dawo!'jan hannun ta yayi har zuwa cikin toilet ɗin kana ya shiga zare mata rigar jikin ta,duk da ƙoƙarin hanashi da tayi amma hakan ya gagara a wannan rana kuma a wannan lokaci sai da Abdallah yagane mata sirrin jikin ta, dan kuwa wanka yayi mata mai sunan wanka,tare da nan naɗota a tawul ya fito da ita,kana ya shirya ta kamar wata ƴar baby, ko da yake shi baby ce awajen sa, Bintu dai ta kasa haɗa ido da Abdallah har sa ilin da ya kaita ɗakin inno shi kuma ya juya ya bar gidan,dan zuwa ɗauko Dady Abubakar. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 58 ``` A FALON ALHAJI BABA. Damisalin ƙarfe goma daidai falon Alhaji Baba ya ɗauki haramar al'ummar da suke zaune a ƙarƙashin sa,ciki kuwa har da Dady Habib wanda yayi tsumu-tsumu,dan shi sam bai taɓa tsammanin zai fuskanci wannan rana ba,tunda asirin sa ya tonu bai taɓa jin wani abu mai kama da jin kunya da nadama ba sai yanzu, wannan dalilin ne yasa ya kasa haɗa ido da kowa dake zaune cikin falon,a ta ɓangaren su Alhaji Hashir da Alhaji Nasir ma kusan hakane a gurin su,da sauran ƴan tawagar su ma baki ɗaya,Bintu dake kallon su ɗaya ɗaya,duk ta fahimci abinda ke zukatansu,abinda ya so bata dariya kenan wai kunyar duniya sukeji,bata lahiraba,kunyar Alhaji Baba sukeji ba ta ubangijin su ba,kaico da irin wannan rayuwar,da babu tsoran Allah acikin ta,kallonta ta maida kan Anty Nafisa wanda tana kallonta ta fuskanci tana farin ciki acan cikin ƙasan zuciyar ta,yayin da kuma azahirinta fuskar ke ɗauke da alhinin abinda take tsumayin ji cikin kunnuwanta, rashin ganin Umar shi ya kuma tabbatar mata da abinda take fata ne yake son tabbata,falon yayi tsit baka jin ƙarar komai sai ta na'urar sanyaya ɗaki da kuma fankokin dake kaɗawa,sai fitar numfashin waɗan da suke da nutsuwar yin sa. Gyaran muryar da Alhaji Baba yayi yana tafe ne da bugawar zuciyar wasu da kuma samun nutsuwar wasu,A hankali ya fara gabatar da addu'a cikin tsananin nutsuwar sa da kamalarsa,bayan shafa addu'oin ne ya kuma gyara zaman sa tare da maida hankalinsa kan Abdallah kana yace"to Alhamdulillah Abdallah na cika maka alƙawarin ka kamar yadda nayi maka gashi nan na tara maka duk al'ummar dake cikin ESTATE ɗin nan,dan haka yanzu zaka iya fara gabatar da dalilin da yasa kasa aka tarasu!'rufe bakin Alhaji Baba dai dai yake da ƙara ƙarfin bugun zuciyoyi,sai kuma nutsatstsiyar Muryar Abdallah ta ƙara sa ruguza ɗan ragowar ƙarfin halinsu,yace"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Ubangijin halittu,sai kuma ya ɗan yi shuru yana tunanin ta inda zai fara,idanunsa ne suka sauka akan Dady Habib dan haka ya cigaba da cewa'Alhaji Baba ina fata zakayi min afuwa game da abubuwa masu yawa da suka faru ba tare da saninka ba,san nan ina fata ka zama jarumi mai ƙarfin hali da yadda da duk wata ƙaddara da ta zo maka mai kyau ko akasin haka!'wani ɗan murmushi Alhaji Baba yayi kana yace"Abdallah baka da damuwa dani akan haka ai duk Musulmin ƙwarai dole ya kasance mai yadda da ƙaddara dan haka ka faɗi duk abinda yake tafe da kai insha Allahu zan kasance mai haƙurin ɗauka!'ya faɗa yana maida kallon sa kan matansa dan ya tabbatar da cewa suma haka take agaresu, Hajjah ce ta saki murmushin ƙarfin hali duk da bata da tabbacin zaman ya shafe ta ko bai shafeta ba,amma ya zama dole ta cigaba da yin pritendin dan tsira da ragowar mutuncinta,Anty Nafisa kuwa ji tayi zaman ya fara gundurar ta tunda yanzu ta fara hasaso wani abu daban,tunaninta ya fara bata cewa lallai wannan taron bai dangance ta ba kuma bai shafeta ba,tunda taga alamun duk mutanen cikin falon basu da wata masaniya akan abinda za a tattauna a wannan taron gaggawar, muryar Abdallah ce ta dawo da ita cikin hayyacinta inda ya cigaba da cewa,a kwai abubuwan mamaki wanda zan fara gabatar maka dasu yanzu,amma sai dai kuma banga Abba Umar ba ko bai ƙarasoba?wata mummunan faɗuwar gaba ce ta samu Anty Nafisa sai dai tayi saurin shiryawa abinda zata faɗa game da mutuwar Umar ɗin idan har saƙon bai tarar dasu ba,sai dai kuma Muryar da taji daga bakin ƙofar falon ALHAJI BABA ita taso zautar da tunaninta,Abba Umar ne yake shigowa cikin ɗan gaggawa tare da cewa afuwan ku gafarceni na makara ne saboda wani dalili mai ƙarfi!'mutanen da suka biyo bayan shi su kaja hankulan mutanen dake cikin falon har da Bintu wadda tayi saurin miƙewa cike da farin ciki ta rungume Hajjo da Anty Asma'u,take kuma kallo ya koma sama hatta da shi kansa Abba Umar ɗin da mamakin inda Bintu tasan su Hajja yake kallonsu, Abdallah kuwa wani irin murmushi ne ke fitowa daga bakinsa zuwa saman leɓansa,Alhaji Baba ne yace"Batula kin san sune?da sauri tace"Baba wannan kakata ce,da yayar ummina!'wata irin zabura Anty Nafisa tayi tare da cewa ƙarya kike wannan abun ba zai taɓa tabbata ba,bazaki taɓa zama ƴar Umar ba,kamar yadda ban taɓa haifa masa ɗa ba!'Abba Umar kamar wani dolo haka ya tsaya yana bin Bintu da su hajjo da Nafisa da kallo,gaba ɗaya ya rasa tunanin da zaiyi komai nashi ya tsaya, Murya yaji daga bayanshi Muryar da ba zai taɓa mantawa da itaba Muryar da ko a mafarki yajita sai ya ganeta,Muryar da yake kwana yake tashi da begen sake jinta,itace take cewa ƙarya kike yi Nafisa ba'a taɓa canja Ƙudurar Allah,kuma baza a taɓa sakewa tuwo sunaba,kin yi sake domin kuwa Bintu ta zama zakanyar dake juya akalar rayuwarki, Bintu Umar Balarabe kenan ƴar da kika so salwantar da rayuwarta,itace ta dawo gareki domin tona asirin ki na mugun nufi akan bawan Allah!'cewar fafi kenan da ya ɗora maganarsa daga inda Ammi Laila ta tsaya,tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Hajja dai bata san sanda jikin ta ya jiƙe da fitsari ba saboda tsabar tashin hankali dan tasan zuwan Dije taron nan tare kuma da su Laila ba Alkhairi bane a gareta,wato dama Dije ce ta gudu da su Laila ke nan?daɓas haka Nafisa ta koma ta zauna yayin da zufa ke ta zubo mata tamkar wadda ake ruwan sama akanta,yayin da fafi ya rugume Bintu tare da mahaigiyarshi da matar shi ciki kewa da shaukin ganin juna,shi kuwa Abba Umar sunkuyawa yayi tare da yin sujjadar shukurr,yana ɗagowa ya tarar da Bintu tsakiyar su shi da Laila ta rasa wajen wanda zata fara nufa,sai wasu irin hawaye da take fitarwa wanda ta tabbata na tsananin farinciki ne,yau gata ga iyayenta duka biyu babu hijabi tsakaninta dasu,ba ta ankaraba taji sun lulluɓeta duka su biyun sun rungume ta atsakiyar su,baka jin komai sai koke koken dake fita ƙasa ƙasa, wasu kuma da yawa mamaki ya hanasu kataɓus wasu kuma har yanzu basu fuskanci kan lamarin ba,Alhaji Baba kuwa yana zaune yana kallon ikon Allah, sai kuma ya jiyo da kallon sa kan Abdallah tare da cewa, Abdallah me nake gani haka mai ke faruwane?ya kamata ku FAHIMTAR dani, na shiga ɗimuwa da ruɗani na kasancewar ganin Umar ɗina da ɗiya har da mata idan banyi kuskuren fahimta ba!'Abdallah yace"Alhaji Baba ka kwantar da hankalin kazaka fahimci komai dan kuwa yanzu za a warware maka zare da abawa kuma abinda ka fahimta ba kayi kuskure ba,Bintu jikarka ce ta cikin jinin ka ɗiyar ɗan ka Abba Umar!'kabbara akasa tare da tu ajjubin wannan al'amari,inno da Hajiya Babba kuwa kukan farinciki suka saka,ko wacce na san ƙarajin Bintu ajikin ta A matasayinta na cikakkiyar jikar su,shima Alhaji Baba ɗagowa yayi ya kalli iyaye da ɗiyar tasu da suke cikin wani irin shauƙi na kasancewa da junan su,yace"Umar ku zauna kayi min bayanin abinda ka lulluɓemin!'zama sukayi gaba ɗayansu sai dai Abba Umar ya kasa haɗa ido da mahaifin nasa domin yasan shi ɗin mai laifine a gareshi. Acan gefe kuma Hajiya zulaihat ce rabe babu abinda take sai kukan tunawa dana ta iyalan kuma gudan jinin ta,tausayin Bintu da ƙaunarta take ji har cikin zuciyar ta,yayin da Abdallah yakeji kamar ya tashi yaje ya rugumeta ya lallasheta yace"yi haƙuri Ammina kema naki farincikin yana kusa dake,amma ya fisan gabatar da komai daki daki idan ba haka ba abun zai cuɗe da yawa har a rasa abinda za 'aji dashi,amma dai ai sannu bata hana zuwa,mai da idanunsa kan Bintu yayi wanda yaji ajikinshi cewa itama idanun ta na kansa,ai kuwa suna haɗa ido yaga tayi masa wani irin kallo mai haɗe da wani irin shauƙi da kewa da bege gami da jinjina,lumshe idanun yayi tare da aika mata da sakon da ya kusa shiɗar da ita, Muryar Abba Umar ce ta karaɗe falon da fara bawa mahaifinsa hakura da neman gafarar sa dana mahaifiyar sa,kana ya ɗora da basu ainahin cikakken labarin haɗuwar sa da Laila da aurensu,kamar dai yadda Fafi ya sanar da Bintu,yana rufe bakin sa,Anty Nafisa ta zunduma wani irin ihu tamkar wata zararriya, Abdallah ne yayi mata tsawar da tasaka ta nutsuwa ba tare da ta shiryawa hakan ba,kana ya ɗora mata da cewa,muna jiran jin ta bakin ki ki sanar damu yadda akayi kika sa aje a kashe Bintu da mahaifiyar ta harma da Fafi?shuru tayi tamkar wadda ake magana da kurma,daga ƙarshe ma tace"ita sam sharri za ayi mata bata san komai akan wannan batu ba,kallon Bintu yayi tare da yi mata wata alama,cikin ƙan ƙanin lokaci kuwa akaji sautin Muryar Anty Nafisa ta cikin waya tamkar alokacin take magana,tsit falon yayi masu al'ajabi nayi masu fargaba nayi dan Hajjah ƙiris ya rage ta fara zawo bayan fitarin da ta lantaya,ta riga ta saddakar da cewa yaufa babu mafita kuma ranar tonon sililice,ranar jin kunya ranar nadama wadda bata taɓa tunanin cewa zata risketa ba,haka abin yake a ɓangaren Dady Habib da sauran makiran estate. Wani irin kuka Nafisa takeyi kukan kaico da nadama,babu abun da ya kuma haukatata da wani irin fitinan nan kuka sai labarin da taji ya ɗora musu akan yadda yayi da saban aikin da ta bayar na kashe su shida su Hajjo da Bintu,da yadda ya kuɓutar da rayuwar su dake Allah yayi da sauran rayuwar su agaba sai ya bashi dabara da tunani da nasara akan mutanen har yayi nasarar juyar da hankalin su. Tsit falon ya yayi baka jin komai sai fitar numfashi, wasu mai daɗi wasu na fargaba wasu kuma na tunanin makoma,kamar dai Anty Nafisa da tata ta riga ta ƙare acikin ESTATE ɗin Alhaji Baba,gyaran murya Alhaji Baba yayi tare da cewa zo nan ƴata Laila nasa Miki Albarka!'a hankali Laila ta ja jikinta ta matsa kusa da Alhaji Baba Wanda ya ɗan dafa hannun sa akanta ya shiga yi mata addu'oi da fatan Alkhairi arayuwarta baki ɗaya,haka abin ya kasance a wajen Hajiya Babba da inno,sai dai Hajjo ta kasa kataɓus bare ta samu damar sawa Lailan albarka kamar yadda sauran ƴan uwanta ko tace kishiyoyin ta sukayi,itama Lailan bataji zata iya kar ɓar Albarkar bakin Hajjah ba dan haka sai ta koma mazaunin ta ba tare da ta ƙarasa gaban Hajjan ba,masu ƙarfin halin magana ne suke iya tofa albarkacin bakinsu,Alhaji Baba yayi gyaran murya tare da ɗan gyara zaman sa kana yace"Abdallah ka gama gabatar da abinda kake son GABATAR wa ko da sauran bayanai a tare da kai?jinjina kansa yayi cikin ɗan motsa bakin sa yace"Alhaji Baba a kwai abubuwa masu tarin yawa da kuma mamaki acikin wannan zaman namu ƘUDURAR ALLAH CE take kan bayyana har yanzu da sauran mu,sai dai yanzu na miƙa ragamar bayanin Hannun Baffa Hashir ko Alhaji Nasir ga kuma Alhaji Kabir duk wanda yayi magana acikin su ya wadatar tunda bakin duk ɗaya ne!'yayi shuru yana mai zubawa kyakykyawar fuskar Bintu idanu,sunkuyar da kanta tayi saboda yadda kallon nasa ke tasar mata da duk wata tsiga ta jiki da kasala,yayin da su Alhaji Nasir suka shiga share zufa wanda basu san ma ta inda take zubo musu ba,haka kuma gaba ɗaya falon su aka sawa idanu Baba Ahmad da dai sauran ahlin Baffa Hashir duk tsumayi suke suji abinda tosffin nasu su kuma suka aikata,dan kuwa ga alamun rashin gaskiya nan tsaf akan fuskokin su,shima dai Alhaji Baba ido ya sawa ɗan uwan nasa da kuma aminan sa guda biyu mafi kusanci agareshi,Dady Mansur ne yace"ku muke sauraro ku wakilta ɗaya daga cikin ku idan kuma bazaku iya fada ba muna da hanyar sanin komai ba tare da mun wahalaba!'Abdallah yace"Dady inaga kawai a kunna wayar!"Dady jafar ne ya miƙowa Dady Mansur wayar dake hannun sa,karɓa yayi tare da kunnata cikin sakanni sai ga muryar Alhaji Sama'ila na fitowa tun daga farkon fara aikin da Samira tayi na sirri har zuwa inda ya sanar da ita komai akan diamon,wayar tana tsayawa falon ya rude da surutai daga masu Allah wadai sai masu fatan shiriya iyalan su kuwa kuka suke sosai da irin wannan tozarcin da Baffa Hashir da Baba nura suka janyo musu,gaba ɗaya sai sukaji duk sun mozanta acikin mutane,da ƙyar Alhaji Baba ya tsawatar falon ya kuma ɗaukar shuru na wasu ƴan sakanni kana cikin wata irin murya wanda take nuni da tsananin halin baƙin ciki da takaicin da yake ciki yace"sannu Nasiru sannun ku Hashir!''' ɗan shuru yayi saboda wani abu mai ɗaci da ya tokare maƙogaran sa,daga bisani yaci gaba da cewa, abokai na da ƴan uwana sune suka zama masu ha intata muna fukaina masu san ganin bayana,hannu yasa ya ɗan goge ƙwallar dake son fallasa halin da zuciyar shi take ciki,kana ya cigaba da cewa nasan akan wannan dalilin ne na rasa gidan jinina ɗan da babu kamarsa sai dai kwatankwacin sa zan iya yafe komai amma banda wanda ya rabani da ɗan da kuma jikana,amma ku kuje babu komai rayuwace,na barku da Allah tunda yanzu ma ba dabarata ce ta fallasaku ba ƙarshen makircin kune yazo,dan Allah ba ya barin mai zalinci,na gode Allah da rahamar sa agareni na gode Allah da ya kawo min Abdallah cikin zuri'a ta!'ya faɗa yana sakin wani ɗan murmushi na samun sukuni da yayi azuciyar sa a sakamakon yawan ambatan Allah. Baffa Hashir cikin tsananin jin kunya da nadama wadda take neman karya garkuwar jiki da ruhin sa, yace"ɗan uwa ina mai neman gafarar ka da kafemin cin amanar da nayi maka duk da cewa ban cutar da rayuwarka ko wani daga cikin ahlinka ba, amma naci dukiyar ka kuma naso aikata babban kuskure akan abinda ba nawa ba ba kuma na ɗana ba,a yanzu ina mai cikin tsananin nadamar abinda na aikata,tabbas na kasance maci amana mai saka Alkhairi da sharri,ka yafe min ɗan uwana ina cikin wani hali na na rashin samun yafiyar ka!'ya ƙarasa maganar da rushewa da wani matsanan cin kuka wanda har saida Alhaji Baba ya runtse idanun sa,daga nan suma suka samu damar neman gafara da yafiya magiya da kukan da suke shi ya tabbatar wa da jama ar gurin cewa sunyi taubatun nasuha,dan haka Alhaji Baba yayi gyaran murya tare da cewa haƙika kunyi kuskure a cikin tafiyar da al'amuran duniya da rayuwarku,kamar ba kuyi karatuba kai Hashir kamanta da hadisin da mahaifina yake yawan yi mana maimaicin sa,cewa Annabi Muhammad (s.w.a) yace"duk jikin da ta ginu da haramun ba zata shiga aljanna ba,haka kuma duk mai annami manci ba zai shiga aljanna ba,kai kuma gashi a wannan gaɓar duk sai gashi ka aikata waɗan nan laifukan,dan haka ina mai jan hankalin mu anan da mu gujewa cin haram komai ƙan ƙantar ta,mugujewa ha'inci,da cin amana,domin Allah baya yafe laifin da akayiwa bayinsa,daga ƙarshe ina mai tunatar daku muhimmancin gaskiya da rikon amana,na yafe muku Allah ya yafe mana baki ɗaya,amma ku sani duk wanda yake aikata wani mummunan laifi to ya dinga tunawa da mutuwa san nan kuma duk abinda yake yi Ubangijin sammai da ƙassai yana kallon sa,ko da ka mutu asirin ka bai tonuba to tabbas a lahira za a nuna maka dukan aiyukan ka,da kunyar lahira kuwa gara ta duniya,zanso idan ina aikata mugun aiki asirina ya tonu ko hakan zai iya zama sanadin shiriyata, Allah yasa mu dace ya kuma karemu daga ruɗin zuciya ya tsare imanin mu!'da Amin suka amsa yayin da jikkuna su kayi sanyi zuciyoyi suka mutu hankula suka fara dawowa jiki,kiran sallar da akayi shi ya dakatar dasu daga ci gaba da gabatar da al'amuran da suke faruwa,Alhaji Baba yace"ya kamata muje muyi sallah ina yaso sai mu dawo mu ɗora daga inda muka tsaya idan akwai wani abun kenan!'Abdallah ne ya fara miƙewa idanun sa suna shawagi akan Dady Habib da Hajjah gani yake kamar zasu iya guduwa dan haka kawai sai yace" da Dady Mansur da Dady jafar su tafi suyi Sallah da Dady Habib saboda yanayin jikinsa su sun fahimci abinda yake nufi,yayin da wasu sukayi tunanin ko Dady Habib ɗin bai da lafiya ne,a hankali aka shiga watsewa daga falon, Abdallah yana fitowa ya kira wayar Safwan yace"su ke waye gaba ɗaya estate din Nan kar su bari ko ƙwaro ya fita,har gefan Hajjah bai bari ba sai da ya tabbatar da tsaron wajen. A bangaren Anty Nafisa kuwa tunda ta fita sai taji bata da kwarin gwiwar shiga ɓangaren ta,tunanin makomar ta a wajen Abba Umar shine abinda ya da baibaye ƙwaƙwalwarta,jikin ta asanyaye haka ta shiga falon tana mai jin tsananin faɗuwar gaba akan abinda zai biyo bayan tonuwar asirin ta, Duk da cewa kowa ɗokance yake da ya keɓe da iyalan sa,tsakanin Abba Umar da Fafi,amma hakan suka hakura suka nufi masallaci bayan sunyi alwala da tunanin ai yanzu komai ya wuce babu abinda zai kuma rabasu da iyalansu idan ba mutuwaba,lokaci lokaci zaka ga murmushi kan fuskar Abba Umar wanda yake nuni da tsananin farincikin da yake ciki ga matar shi Laila ga gudan jininshi Bintu babu abunda zaice da Allah sai godiya Alhamdulillah masha Allah. Su inno dai da Hajiya Babba su sukayi ma sauƙin baƙi,Hajiya Babba kamar yadda ta saba tayiwa inno kara da alkunya ita tabarwa ragamar karrama surukar tata tare da ririta ta tamkar basu taɓa yin suruka acikin ESTATE ba,Hajiya zulaihat ma tana manne da Laila,dan ko ɓangaren ta bata koma ba,Bintu kuwa gatan har nema yake yayi mata yawa sai dai duk da haka ta kasa sukunin rashin ganin Oganta Abdallah maganin kukanta,wata irin kewar sa takeji tare da tsananin bege,wanda har kawo yanzu ta kasa fassara hakan da cewa ƙauna ce mara algus, Bayan idar da sallar ne mazan duk suka hallara a falon Alhaji Baba,yayin da ya bada umarnin akawo abinci a fara ci kafin ci gaba da tattaunawa,a lokacin ne kuma ya saka waya yayi kiran Alhajin Nafisa ya sanar dashi yana buƙatar ganin sa tare da Hajiya ladidi,kowa yana sabga cikin walwala amma banda Dady Habib wanda bugun da zuciyarsa take yi tafi ƙarfin a misalta,yanzu yafi kowa shiga tashin hankali tabbas da ya samu hanya sai ya gudu dan yana ganin guduwar ita ce kadai mafita agareshi da kuma samun sauki a gareshi. Hajja kam tun komawarta bangaren ta take zawo har sai da Nana karama tace"wai Hajja lafiyar ki kuwa naga sai sunturin banɗaki kike?bata iya bawa ƴar tata amsa ba sai komawa da tayi ban dakin dan ta ga alama zaman cikin sa sai yafi mata sauƙi,a kwai abinda take ɓoyewa wanda babu wanda yasan shi kuma tana ganin lallai lokacin tonuwar wannan sirri yayi shi yasa abun ya haɗe mata bata jin cewa duk sanyin zuciyar Alhaji Baba zai iya yafe mata wan nan al'amari,a yanzu kaico da nadama take,shin tayaya zata iya fuskantar Alhaji Baba da wannan sirrin wanda tasan cewa koda su Abdallah sun san wancan to tabbas basu san wannan ba,yaya duniya zata kalleta da sauran ƴaƴan ta idan sukaji abinda ta aikata,dole tasa ta ci gaba da zaman banɗakin domin tun yanzu ta fara jin kunyar haɗa idanu da iyalanta, Oga Abdallah kuwa mai gaiya mai aiki duk yadda ya kai ka san yin juriyar hakura da ganin Bintu abun gagara yayi, cikin rashin sukuni ya nufi ɓangaren inno,yana shiga falon yaci karo da Dije zata shiga kiching inda suke hada hadar dafa abinci,tsayawa tayi tare da cewa,a'a yallaɓai ko kana buƙatar wani abunne? cikin ɗan basarwa da farincikin da yaji na samun dama yace"ki bawa Bintu ruwa ta kawo min!'daga haka yayi saurin faɗawa falon sa,wani ɗan murmushi tayi tare da shigewa ɗakin inno inda Bintun suke tare da su Laila da Hajjo,yafito Bintu tayi,suna fita ta miƙa mata ruwan da ta ɗauko,ba ta haɗa da komai ba,dan tasan ba wai ruwan yake buƙata ba,tace"maza jeki kaiwa mijinki yana cikin falonsa!'ai kafin ta kai ga rufe bakinta tuni ta tsinci Bintu abakin kofar falon Abdallah,riƙe baki tayi cike da dariyar yarintar Bintun. Kamar an jehota haka ya ganta a gabansa kasan cewar tun shigarsa bai zaunaba,zuba mata idanunsa masu saukar mata gajiya yayi,haka nan ta dinga jin wani irin sanyi har cikin kashinta sunkuyar da kanta tayi tana jin wasu ƙwallan da bata san daga ina suke ba,ɗan ware idan sa ya kuma yi akanta,kana a hankali ya riƙota kamar wanda yake tsoran kar yaji mata ciwo,ɗagowa tayi ta shiga yi masa wani irin kallo daya fara sashi kokuwa da numfashinsa, cikin wani irin salo da shauƙi ya haɗe ta jikin sa,tare da ɗora fuskarshi saman kanta,zame ɗan kwalin kanta yayi ya shiga shinshina gashinta kamar wanda ya samu turare,Bintu cikin wata irin kasala ta kuma lafkewa cikin faffaɗan ƙirjinsa,can kasan maƙoshi ta tsinkayi Muryar sa yana cewa my Bint,sai kuma me kike bukata? Ummm faɗa min!"ya faɗa cikin cusa kanshi a wuyanta yana goga fuskarsa da ɗan gemun sa akan uyan nata, cikin wata iriyar kasala da yake saukar mata ta shiga goga fuskar ta a kan ƙirjin sa tare da cewa"Ni kam ka gama min komai bani da wata sauran damuwa,ka cika min burina ka dawo min da farin ciki na, wannan ma kaɗai ya isheni!'ɗan murmushin gefan baki yayi tare da cewa a'a faɗa min dai ina sauraren ki da akwai wani farin cikin da kike bukata!'girgiza kanta ta shiga yi jikin ta yana kuma mutuwa da salon da ogan nata yake mata,kamar daga sama taji bakin shi cikin nata wata doguwar sumba yayi mata tare da cewa hmm Bint ki duba mana bakya bukatar wan Nan?a ruɗe ta kuma girgiza masa kanta,ya kuma sumbatar idanunta yana cewa da wannan ma,ya sumbaci goshinta da wannan ma,daga nan ya zarce da yiwa bakinta wata irin tsotsa tamkar wanda ya samu sweet..... Mu haɗu a falon Alhaji Baba zama na biyu Fatima y Adam✍🏽 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 59 ``` "Kiran da yaji a wayar sa dake soke gaban rigar sa ita ta fara dawo dashi hankalin sa,amma duk da haka bai saki Bintu ba,a hankali ya zare bakin shi daga nata,tare da zuba mata ido,hannu tasa ta rufe fuskarta saboda kunya,leƙa fuskar ya shigayi tare da cewa duk bakya buƙatar waɗan nan eye Bint?janye jikin ta tashiga yi a ƙoƙarin ta nasan guduwa,domin ita sam bata gane inda maganarsa ta dosa ba,riƙeta yayi ganin zata gudu yace"baki bani amsa ba,ko sai anjima zaki gaya min?da sauri ta daga kanta kamar zatayi kuka, murmushi yayi tare da sumbatar dogon hancinta,kana ya saketa,sai da taje bakin ƙofa kana ta ɗan dakata tare da juyowa tace"kayi sauri ka fito kazo falon Alhaji Baba saboda ina buƙatar ganin farincikin Ammi da Oga Abdallah!'tana gama faɗa tayi waje da gudu fuskarta dauke da murmushi,zubawa kofar idanu yayi hannuwan sa zube cikin aljihun shi,ɗan shafa cikinsa yayi dan shi sai yanzu ne ma yake jin yunwar gashi kuma su kaɗai ake bukata a falon Alhaji Baba,kafin ya samo mafita sai ga Bintu ta dawo hannun ta ɗauke da plat wanda yake shaƙe da jelof ɗin shinkafa da uban kifi wanda kusan rabin abincin kifine,sai ƙamshi take gwanin da ɗi da burgewa,har tazo gaban shi ta janyo dan Centre ɗin tsakiyar falon ta ajiye yana kallonta,sai da ta ɗago taga kallon da yake mata,sai kuma ta tura baki tare da cewa wai miye ne haka da kallo?bai bata amsa ba sai zama da yayi yana maida duban shi kan abincin,cikin kasalar da ganin ta ke saukar masa yace"abun burgewa mata tana son mijinta yaci abinci kamar kinsan yunwa nakeji!'kamo hannun ta yayi ya zaunar da ita kan cinyar sa tare da cewa ke kinci abincin ne?girgiza kanta tayi,bai ce komai ba ya shiga miƙa mata abincin bayan ya ɗebo a spoon,Bata son yawan yi masa gardama hakan yasa ta buɗe bakinta ya shiga bata abincin,sai da ya tabbatar ta koshi kana shima yaci,yana gamawa ya ɗaga ta yana cewa muje Bint kar muga dakarun Alhaji Baba akanmu!' dariya tayi kana ta zagaya hannun ta ta saƙalo hannun shi,a haka suka fita dan zuwa falon Alhaji Baba. Kamar yadda akayi a farko haka yanzu ma kowa ya hallara har da ƙari,saboda yanzu da akwai Alhjin Nafisa da kuma Hajiyar ta Ladidi,kowa ya nutsu,shigowar Abdallah da Bintu kawai ake jira,yayin da Hajjah take cikin wani irin hali duban farko zaka san cewa a kwai tsoro da tarin fargaba a tare da ita, Anty Nafisa ma tun da ta ga zuwan baban ta da kuma Hajiyar ta cikinta ya kuma durar ruwa,cike take da tashin hankalin abinda zai biyo bayan abinda ta shuka, Hannun su rike dana juna sukayi sallama,wanda su sun manta a yanayin da suke,sai da Bintu taga kallon da Inno take watsa mata kana ta ankara,da sauri ta zare hannun ta daga nasa,can wajen Ummin ta ta nufa ta zauna tare da kwantar da kanta a kafadar ta,shi kuwa Abdallah daga nan gefan Dady Mansur da Dady jafar ya zauna,Alhaji Baba ne ya bawa Abdallah umarni da ya buɗe taro da addu'a,bayan sun shafa addu'ar ne Alhaji Baba ya dubi Abdallah tare da cewa,har yanzu kai muke bi Abdallah meye abu na gaba da zaka gabatar mana dashi?wayar Safwan ya kira yace"ku shigo dashi!'baiyi minti ɗaya da kashe wayar ba,akayi sallama a ƙofar falon tare da sako kai alokaci ɗaya. Kaf mutanen falon sai gasu a tsaye,daga mai murza idanu sai mai zaro su dan san da ɗa tabbatar da abinda idan nasu yake gani,A hankali Alhaji Baba ya shiga takowa har zuwa inda Dady Abubakar yake tsaye cikin kyakkyawar shiga ta kamala kai baka ce shine wanda yayi tsawon shekaru ba tare da yasan inda kansa yake ba,kama hannun sa yayi cikin nasa jikin sa har rawa yake gwanin tausayi, zuba masa idanu yayi sai ga hawaye shar suna tsartuwa daga idanun Alhaji Baba jarumin namiji,sai ga Hajiya Babba ma tazo saboda ta kasa daurewa tsayawa daga nesa ga Ni take kamar zata iya yin saken da zata kuma rasa ɗan nata,ita kanta Hajiya zulaihat alkunya tayi amma idanun ta tamkar zasu faɗo ƙasa saboda kallon Abubakar kuka take yi mai tsanani wanda yake tafe da wani irin kewa da shauƙi,duk ƴan uwansa dake zaune a falon babu wanda yake son ko ƙifta idanun sa yayi dan kar ya buɗe yaga babu Dady Abubakar,Abba Umar ne yazo da sauri tare da cewa, Alhaji Baba yayane fa ko baku gane shiba?bai sauraren su ba ya tafi ya rungume ɗan uwan sa tare da sanbatun farin cikin sake kasancewar sa acikin su, cikin ƙanƙanun lokaci falon ya dau sautin kukan mutane,Hajiya Babba kuwa kama su tayi gaba ɗaya shida Umar ɗin ta rungume ta kasa cewa komai sai wani irin murmushi wanda yake haɗowa da wasu zafafan hawaye,shafa kawunan su takeyi kamar baza ta sakesu ba,A hankali Alhaji Baba ya zaresu daga jikin ta shima yayi musu kamar yadda tayi,duk kan su sun rasa bakin magana sai zubar hawaye ,cikin nutsuwa yajasu suka koma inda yake a zaune daga nan yabawa sauran ƴan uwan sa damar raɓar Abubakar ɗin dan nuna farin cikinsu na dawowar sa,cur cur haka zaka ga duk wanda suka rungumi juna ya koma yana hawaye kai abun dai gwanin tausayi,rarrafawa yayi har gaban inno matar da ta so shi ta nuna masa kauna tamkar ita ta haifeshi,ɗora kanshi yayi bisa ƙafafunta,hannun ta tadora a kansa tana mai cigaba da zubar hawaye,A hankali tace"Abubakarina Allah ya nufi ganawar mu,yau ƙudura ta hadu da irada,ƙudurar Allah ce take ta wanzuwa acikin wannan zuri'a tamu,dama inaji ajikina zuwan Bintu da Abdallah cikin ESTATE ɗin nan haskene da warwarewar duk kanin matsalolin mu,na daɗe inajiran wannan rana mai ɗumbin tarihi a garemu, Allah ya karemu ya kuma shiga tsakanin nagari da mugu!'ɗagowa yayi cikin san kwantar musu da hankali,yace"inno ku daina kuka godiya ya kamata muyiwa Allah da ya nufemu da sake haɗuwa!'A hankali Bintu ta tashi taje har gaban Ammi ta kama hannun ta ta miƙar da ita,kowa sai ya maida kallonshi kanta,bata tsaya da Ammi ba sai a gaban Dady Abubakar,hannun shi ta kama ta haɗa dana Ammi idanun ta cike taf da hawaye tace"duba nan Dady kar kamanta da macen da ta ɗauki tsawon shekaru idanun ta na tsiyayar da hawayen rashin ka da na gudan jininta,Ammi kenan macen da tashaƙi ɓacin ran da ya kusa illata rayuwarta, duk saboda kai,Ammi ki kawar da fulako ki tarbi Dadyn mu,saboda abinda ke zuciyar ki ya wanku,abinda ya tsaya a ƙahon zuciyarki ya faɗa!'kuma takawa tayi taje ta kamo hannun Abdallah, tana zuwa ta haɗa dana Ammi da Dady Abubakar cikin hawayen tausayin su,tace"ya Abdallah inaso kayi farin ciki kamar yadda kasani, kaji irin abinda naji lokacin da ka haɗani da Ummina da Abbana,kaima yau gaka ga Dady ga kuma Ammi,ta ɗan kalli Ammi da ta zuba mata ido tana san fahimtar inda zancan BINTU ya dosa tace"Ammi ga nan Ya Abdallah shine ɗanki da suka ɓace lokaci ɗaya da Dady,wata irin zabura Ammi tayi sai kuma ta koma tare da riƙe hannun Abdallah kamar zata ɓallashi, Allahu Akbar tabbas naji ajikina kullum fatana kenan abinda nake tunani akan ka ya zama gaskiya, Alhamdulillah,yau haske ya baiyana duhu ya yaye,yau ranar farin ciki ce a cikin wannan ahlin,ta faɗa cikin zubar da wasu zafafan hawaye wanda zamu iya kiran su dana farinciki, Dady Habib kuwa tamkar zararre haka ya koma yana zaune amma duba ɗaya zakayi masa kasan cewa baya hayyacin sa,cewa yake yi nayi sake nayi sake yau gashi ƘUDURAR ALLAH ta baiyana,Dady Mansur dake hankalce da shi da Dady jafar sune kawai suka fahimci halin da yake ciki ga kuma maganganun da yakeyi,wanda basu ji abinda yake cewa ba,amma dai tabbas alamu sun nuna Dady Habib yana cikin wani yanayi na tsaka mai wuya,kowa a cikin falon nan farinciki yake, amma banda waɗan da suka shuka suke jiran girbewa,idan ka duba zuciyoyin su tamkar ƙabari haka suke,su kuwa su Alhaji Hashir sun shige cikin masu taya ɗan uwan su murna da samun ɗan sa da jikokin sa,tunda su sun samu salamar yafiyar wanda suka yiwa kuma nasu ƙullin makircin bai kai na su Dady Habib ba, wannan dalilin ne yasa suka samu nutsuwar zuciya. A hankali Abdallah ya rungume mahaifiyar sa ya haɗa da Dady,Rahima da ta ƙaraso itama ta rungume ɗan uwanta,ɗago idanunshi yayi ya ɗorasu kan rigimammiyar fuskarta kamar yadda yake faɗa,nuni yayi mata da ta share hawayen fuskarta, murmushi ne ya suɓucewa Ummi da sauran waɗan da suka kula da abinda Abdallah yayiwa Bintu,ita kuwa Bintu umarnin mijinta tabi tasa hannu ta goge hawayen da suka ɓata kyakykyawar fuskar ta,zama yayi ya zaunar da Ammi da Dady Abubakar,kana ya koma mazaunin sa,fuskar sa ɗauke da wani ɗan maƙalallan murmushi,shuru falon ya kuma ɗauka yayin da zuciyar Dady Habib ta cigaba da bugawa da sauri da sauri, zufa kuwa tamkar wanda ake sheƙa masa ruwan zafi. Abdallah ya buɗe baki zaiyi magana kenan, sai Dady Habib ya riga shi cikin yanayin fita daga haiyaci da tashin hankali na birnin kunya, yace"me zakace? me kuma yayi saura?kai dai wan nan yaro bakaji da kyauba,na tabbata dama zaka zama annoba arayuwata shi yasa tun farko naso wan can shegiyar ta kashe min kai,amma sai ta munafunceni saboda wata manufa tata,to gashi nan dai itama bata tsira daga tarkonka ba, wallahi bazan ɓoye muku ba na tsaneka kai da mahaifinka da wannan tsinanniyar yarinyar me kwana ido biyu,duk kece kika jawo komai!'ya faɗa yana nuna Bintu da kamar zai je ya rufeta da duka,a tsorace kowa yake kallon Dady Habib,Alhaji Baba kuwa bakinsa buɗe da tsananin mamaki yake duban ɗan nasa,haka jama ar da basu san komai akan abinda ke faruwa ba, Abdallah kuwa waya ya yiwa Safwan tare da bashi umarnin a shigo da Abigirl,ci gaba yayi da kallon Dady Habib da ya kasa zama sai muzurai yakeyi yana kuma faɗar maganganun da tun ba a fahimta har mutane suka soma fuskantar inda tashin hankalin nasa ya dosa. Safwan ne yayi sallama ya shigo tare da Abigirl wadda tayi firi firi da ita kana ganin ta kasan cewa alhaki na biye da ita,tsakiyar falon Alhaji Baba ya zaunar da ita,kana ya juya ya koma inda ya a fito,kowa sai hankalin sa ya dawo kan Abigirl ita kuma hankalinta yana kan Dady Habib da ya zuba mata ido kamar wanda yake son aikamata da wani saƙo na gargaɗi,kawar da kanta tayi ta maida kan Abdallah da ya farayi mata magana cikin nutsuwar sa ta ko da yaushe,yace"kamar yadda na gaya miki ranar ne bana so kiyi min gaddama ko kuskure acikin abinda nake son sani daga gareki,nasan kin san abinda zai iya biyowa baya akan rashin bani haɗin kai da zakiyi,dan haka inaso ki faɗi komai da komai da kika sani akan yadda kika sameni, da yadda kika raine Ni da kuma manufarki akaina!'daga haka yayi shuru tare da maida kallon sa can ɓangaren da Bintu take,yayin da kuma ɗaukacin mutanen dake falon suka maida hankalinsu kan Abigirl, wadda ta zubawa Dady Habib ido,shi kuma yana maida mata da kallon gargaɗi, harma ya manta abin da yagama faɗa yanzu cikin fita hayyaci,kawar da kanta tayi daga gareshi tare da share hawayen da suke ta rige rigen sauka kan fuskarta,Dady jafar ne yace"ke muke sauraro!'duban shi tayi cikin saddaƙarwa tace"zan faɗa,zan faɗi duk wani abu da nasani,amma dan Allah karkuyi min komai,kubarni na koma garin mu bazan kuma waiwayar garin nan ba, ko da me maƙwaftaka dashine!'Dady jafar yace"idan har kika faɗi gaskiya kuma waɗan da kika aikatawa laifi suka yafe miki,to babu abun da za ayi miki,dan haka muna sauraranki!' SHEKARA TALATIN da suka gabata, Sunana Abigirl Adebayo ina zaune acikin garin Abuja nida mijina pastor David,tun da mukayi aure bamu taɓa haihuwa ba,tun bamu damu ba har muka fara nuna damuwar mu afili, mutane suka fara fuskantar halin da muke ciki,wala agida ko choch kullum addu'oin mu shine Allah ya bamu haihuwa,sai dai abin yaci tura shuru kamar ba roƙo muke ba,har ta kai da cewa na fara bin manyan bokaye da matsafa,amma duk abin da nakeyi mijina David bai sani ba,dan Ni nafishi damuwa da rashin haihuwar mu,mahaifiya ta ita ta kuma ƙara iza mun wutar san haihuwa saboda huɗu bar da tayi min wanda a da sam ba tunanina kenan ba,tayi min nuni da yadda David yake da arziki,ta nuna mini cewa idan ban haihuba,bazan taɓa samun abinda nakeso daga David ba,tace"min ai yanzu dan ban aihu bane yasa baya sakimin kuɗaɗe masu yawa,amma duk randa na samu baby to zanyi arziƙi ta sanadin baby,huɗubar ta tayi tasiri gareni,hakan ne yasa na kuma tashi tsaye gurin neman aihuwa ba dare ba rana,a kuma cikin lokacin ne komai ya faru,a ranar da bazan manta da ita ba,naje gurin bokana yake sanar dani Lallai sai na samo ƙaramin yaro na raine shi tsawon shekara talatin sa an nan zan samu abinda nakeso wannan shine laƙanin da bokana ya bani,kuma shine dalilin da yasa na taho ina tunanin hanyar da zanbi dan samun yaro karami. Ina cikin wannan tunanin sai kawai na tsinkayi kukan yaro tamkar al mara,kasancewar daji ne sai na fara tunanin ko dai aljanu ne suke san zautani Saboda sun san laƙanin da boka ya bani,sharewa nayi na cigaba da tafiya,amma sai naji kukan yaron yaƙi tsagaitawa kamar dai anayi masa wani abu ne,dan haka sai kawai nabi kukan da sawayena,banji tsoro ba saboda na saba shiga irin dajikan nan saboda neman biyan buƙata ta,daga ɗan nesa na tsaya dalilin hangen wani mutumi da nayi da jajayen kaya na riga da wando da kuma yaro a hannun sa yana shirin yanka shi,abin ya bani mamaki har kuma lokacin ban daina tunanin ko jinnu bane,amma dake sam bani da tsoro sai kawai na tunkari gurin da niyar idan ma jinnu ne ai Ni ina da buƙatar su cikin rayuwata,ina zuwa nasa hannu na tare hannun mutumin dake shirin yanka ƙaramin yaron da bai wuce shekara uku ba,ɗagowa yayi a fusace,ganina sai kawai ya kasa magana ya tsaya yana kallona da mamakin abinda ya kawoni cikin wannan dajin,zaiyi magana ke nan na tari numfashin sa da cewa,kaiko mutum ne ko aljan? sai naga ya tuntsure da dariya tare da cewa ke kiji min da shegiyar mata,ai Ni zan tambayeki bake ZAKI TAMBAYENI ba,ko da yake ai idan aljana ce ke to tabbas zanji ajikina domin duk da cewa Ni ba aljan bane,amma ina gane su,saboda tsananin tarayyata dasu!'nace,to meyasa zaka kashe yaron nan?kai tsaye ya bani amsa da cewa saboda zai zama masifa arayuwata zaman shi tare da mu acikin ESTATE zai iya rusa duk wani burina!'sai nace masa'mai zai hana ka bani shi domin cika wani buri nawa!'girgiza kai yayi tare da cewa Ni kashe shi nake son yi,lallai sai ya mutu!'da na ga alamun dai ba zai bani shi haka nan ba kawai sai na bashi labarina da abinda yasa nake son ya bani shi ɗin,amma da na fahimci cikin gaggawa yake son mutuwar yaron, sai kawai na juya maganar mai makon nace shekara talatin da boka ya bani, sai nace shekara biyu,na kuma bashi tabbacin da nayi shekara biyu da shi zan kasheshi,a nan dai mukayi yarjejeniya,bai kuma ɓoyemin daga inda yaron yake ba har sunan kakansa sai daya sanar dani amma duk a matsayin gargadi ne,dan ya tabbatar min da cewa duk ranar da nayi kuskure cikin alƙawarin mu sai ya kasheni har lahira,da wannan batun muka rabu,da sauri na juya na koma gurin boka na na nuna masa yaron da na samu,yana ganin Abdallah sai kuwa ya zabura tare da cewa zaki iya rainin sa amma duk ranar da na bari ya karbi Musulunci shikenan duk abinda nayi ya tashi a banza, kuma shima sihirin da zaiyi min na tsawon shekara talatin ɗin duk sai ya karye,dan haka sai na kula da tarbiyyar sa da kuma waɗan da zai dinga mu'amala dasu, wannan shine sanadin zuwan ka hannu na,kuma koda na dawo gida sai nacewa David gidan marayu naje na karɓoka,dake shima san yaran ya rufe mashi ido sai kawai ya karɓe shi ba tare da bin cike ko tsaurarawa ba. Ɗan shuru tayi kana ta cigaba da cewa,tunda nazo da yaron a cikin kwana biyu nafara fuskantar ƙalubale daga gareshi, saboda wani irin shegen taurin kai da kake dashi da baƙar zuciya,Ni kuma ganin nawa zan haifa sai kawai na shiga gallazawa rayuwarka,idan ina dukan ka kuwa tamkar na samu jikin wani ƙaton saurayin,kusan kullum sai munyi faɗa da David akan ka,da yaga naƙi dainawa ne sai yayi min barazana da zai ɗauke ka ya maida ka can gidan marayu,Ni kuma da naji haka nasan kuma ba da wasa yake ba,sai na dai nayi maka agaban sa,amma bawai dan na daina ba,a kwana a tashi da irin wannan wahalar da nake baka na gina tsanata acikin zuciyarka,a lokacin Ni duk ban damuba saboda burina kawai nake hange,mun saka ka amakaran mai tsada kayi karatunka na primary,a Turkish,Wanda anan ne kuma na fara fuskantar ɗabi unka suna kuma sauyawa kana abu kamar na Musulunci,sai hakan kuma yaɗaga min hankali na fara tasaka gaba muna tafiya choch,wanda kai kuma anan ne kake nunamin asalin taurin kai,da baƙar zuciya,Ni kuma sai abin ya haɗe min ga tsanar ka ga kuma fargabar halin da kake nunamin,hakan ne yasa na tashi tsaye haiƙam da cusgunawa rayuwarka,duk saboda kana ƙin zuwa choch,sai na saka ka aɗaki na rufe yini guda baza kaci komai ba ko da ruwa kuwa sau ɗaya nake baka, shima dan kar ka mutune,daga nan na kaika makarantar horas wa ta kiristoci,a nan ma kasha azaba iri da kala,amma duk da haka baka sauko daga kan dokin naƙin da ka hauba,Ni kuwa alokacin tuni na manta da wani wanda ya bani kai da sharaɗin sa,burina kawai naga lokaci ya cika nima na samu ɗan kaina,da naga abun ya ci tura sai kawai muka yanke shawarar kaika waje dan kayi karatu wataƙil idan kana cikin waɗan da ba Musulmi ba ka haƙura da addinin Kirista,haka kuwa akayi sai dai ban sani ba ashe tuni yaɓe nakeyi akan suminti dan alokacin ma tuni Abdallah ya riga da ya musulunta tun yana primary,sai lokacin da ya tashi dawowa Sai kawai ya dawo min da wannan guzurin da yasa na kusa zaucewa,daga baya kuma da naga yadda ya maida Ni mara amfani da kuma wani tsoransa da nakeji na tsananin kwarjini da hasken Muslunci yasa nazo ina nadama da abinda na aikata masa wanda nadanamar bata da wani amfani alokacin,daga baya na fara tunanin yi masa aure amma hakan baiyuwuba,shine daga baya David ya kawo shawarar sa ta cewa zai kaishi gidan horaswa,wanda Ni kuma bansani ba ashe cikin ahlinsa ya kawoshi,daga nan ta ɗora da labarin yadda akayi ta fara ƙoƙarin kashe shi da wayar da sukayi da mutumin da ya bata Abdallah,har kawo yanzu bata ɓoye komai ba,sai dai kuma har lokacin bata faɗi kowayeba,wanda su kuma da yawa mutanen dake cikin falon abinda suke ɗaukin ji kenan, Tana yin shuru Dady jafar ya ɗora musu da tarihin musuluntar sa da yadda akayi ya fara zargin Abigirl, da yadda akayi suka binciko asalin Abdallah har sukayi dabarar kawoshi gidan dan aiwatar da aikin sirri,gaba ɗaya falon aka ɗauki kabbara masu share hawaye nayi masu kuka nayi,wanda da yawa labarin Abdallah ne ya ɗimauta su ya kuma gigizasu har yasa su zubda hawaye,Bintu kuwa numfashinta har ɗaukewa yake,saboda matsanancin kukan da take na tausayin rayuwar Abdallah,haka Dady Mansur da Dady Abubakar da Abba Umar da su Ammi Ummi Hajiya Babba da inno kowa kuka yakeyi da kuma Allah wadai da wannan baƙin azzzlumin can ƙarƙashin zuciyar su kuma suna jin bazasu iya yafewa mai wannan alhakin ba, Abdallah kuwa gaba daya neman kasa riƙe kansa yake saboda yadda kukan BINTU ke kiɗima tunanin shi,idanun shi suna kanta so yake kawai ta ɗago kanta daga jikin Ammi dan yasamu damar rarrashinta koda da ido ne,a jikinta taji cewar yana kallon ta hakanne yasa ta ɗago kanta a hankali ta ɗora rinannun idanunta akan kyakykyawar fuskar shi,sai kawai taga ya lumshe idanun shi haɗe da budesu duk alokaci ɗaya,kana ya shiga yi mata nuni da ta share hawayenta,yanzu lokacin kuka ya ƙare,yana gama yi mata nunin sai ya tallafe fuskarsa a cikin tafikan shi yana ci gaba da yi mata wani irin narkakken kallo,wanda tuni ya tafiyar da gajiyarta da kuma damuwarta,hannu tasa ta shiga share hawayen tana ci gaba da kallon sa ƙasa ƙasa dan bata jin zata iya shigar da idanun ta cikin nasa,kamar yadda taga alamun yanaso suyi,Muryar Alhaji Baba ce ta katse musu hirar kurman da sukeyi,cikin dishashshiyar Muryar da kanaji kasan cewa tayi kuka, yace"baiwar Allah muna sauraren ki har yanzu baki sanar damu wanda duk ya kitsa wannan munanan aiyukan ba!'a hankali ta ɗaga hannun ta tayi nuni da inda Dady Habib yake rakuɓe kamar ɓeran da mage ta tarfa.... 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 60 ``` Kowa sai ya maida hankalinsa saitin da take nunawa, cikin fatan kar abinda yake zargi ya kasance Alhaji Baba yace"ban fahimceki ba? kiyi mana bayani sosai yadda zamu fahimta!'ya ƙare maganar tasa cikin bugawar zuciya da fargaba, Abigirl ta buɗe bakinta cikin yanayin tsoro tace"gashi nan Habibu shine mutumin da na karɓi Abdallah a wajen sa!'ɗuf falon yayi lokaci ɗaya,A hankali Alhaji Baba ya shiga jan innalillahi'wa'inna ilaihi raji'una,kansa a ƙasa yana tsiyayar hawayen da ya kasa daurewa rashin zubar su,a halin yanzu kuwa bazan iya ce muku ga misalin halin da Dady Habib da Hajjah shuke ciki ba,ƙwaƙƙwaran motsi an rasa wanda zai farayi a wajen, wannan shine ana zatan wuta a maƙera,su Baffa Hashir sunyi matuƙar girgiza da jin wannan batu,dan aduk bulayin su da hasashen su basu taɓa kawo Dady Habib a cikin mummunan tunani ba,inno da Hajiya Babba kuwa gaba ɗaya idanun su yana kan Hajjah,Dady Abubakar ne yaga gara kawai ya ƙarasa musu da abinda basu sani ba ayi ta taƙare,dama mahaifinsa kawai yakeji,amma yasan Alhaji Baba a ko da yaushe mai tawakkali ne da haƙuri da ƙaddara,dan haka cikin nutsuwa yayi gyaran murya tare da cewa, Alhaji Baba ka gafarce Ni ka kayi haƙuri kuma da duk abinda zaka ci gaba da ji har lokacin da komai zai dai-dai ta!'ɗan shuru yayi kana ya cigaba da cewa,tun tsawon lokacin da aka nemeni aka rasa agidan nan,ina kusa daku kuma A cikin gidan nan,cikin damuwa da kaicon rayuwar da ɗan uwan nasa ya saka kansa a ciki, ya basu labarin duk abinda ya faru iya wanda ya faru acikin tunanin sa, har kawo lokacin da Bintu da Abdallah sukayi nasarar fito dashi zuwa yanzu da ya dawo cikin ahalinsa,yana ajiye numfashi Dady Mansur ya ɗora da nashi labarin kamar yadda ya sanar da Hajjah, Da ƙyar mutanen dake falon nan suke iya jan numfashi saboda tsananin mamaki da tu ajjubi,babu kama abun da su Alhaji Nasir suke faɗa kenan,sunji kakansu a san duniya,Nana ƙarama kuwa kuka take sosai da jin abinda ɗan uwanta ya aikata,da yawan ƙannen sa da kuka sukeyi da jin matsananciyar kunyar Ahlin Hajiya Babba, Alhaji Baba ne ya ɗago kansa bayan yaci nasara akan zuciyar sa da idanunsa,da kallo ya dunda bin ƴaƴa da jikokin nasa,kana kuma cikin wata irin murya mai kama da wadda aka shaƙe, yace"Alhamdulillah masha Allah,Ni kuma jarraba ta akan ka take Habibu,to wai duk akan wannan diamon ɗin ake wannan ta asar acikin ahlina ba tare da na sani ba? Ni kam wane irin uba ne?Habibu mai na rageka dashi da har kake ƙoƙarin gina jikinka da haramun kake son kashe ɗan uwanka da ɗanka?ko dan baka san zafin ɗa bane shi yasa kake raba tsaka nin iyaye da ƴaƴan su?ka rabani da ɗana shi kuma ka rabashi da ɗan sa,ita kuma Laila ka rabata da iyayen ta,ka rabata da ƴarta, duk da cewa ba kaine ka fara rabasu da farin cikinsu ba,Habibu ka bani mamaki na dade banji makamanciyar rayuwa irin taka ba!'ya ɗan tsagaita da maganar yana jan wani wahalallan numfashin da yake ne man gagarar yin shi,kana ya cigaba da cewa,Habibu me kake nema?anya kuwa diamon kaɗai ya isa ka salwantar da rayukan ƴan uwanka? Ɗago jajayen idanun shi yayi da shi kaɗai yasan irin azabar radaɗin da zuciyar shi take mishi,girgiza kanshi yayi tare da yin magana cikin wata razanniyar murya,wadda take cike da nuna tsananin da yake ciki,yace"Alhaji Baba duk kaine ka jawo wannan ƙiyayyar da nakewa dan uwana,saboda fifita shi da kayi sannan gashi Ni ban taɓa haihuwa ba,a asalima likitoci sun tabbatar min da cewa bazan taɓa haihuwa ba, sannan tun ina yaro Nakasance mutum mai san duniya da ganin nafi kowa kuma ansoni fiye da kowa,sai dai kash duk ban samu hakan ba,dalilin da yasa na fara cusawa zuciyata neman kuɗi ta kowace irin hanya,da ɗin da ɗawa kuma ga abokai ƴaƴan manya wanda ake sakar musu da dukiya ina tare da su,a hankali burika na kullum da ɗuwa suke ina girma burina yana da ɗuwa,gan da bikina sai katsam na haɗu da abokina Saddam wanda shine sanadin duk wani arziki nawa da kuma kaucewa ta,tun da yakawo mun tayin sama ar sa,banji ko dar ba na karɓa saboda alokacin nayi nisa idanuwa na sun gama rufewa,tun daga lokacin na faɗa harkar tsafi nayi tsundum har mukami aka bani,babu wanda zai iya gane halin da zuciyata take ciki saboda na iya taku na,nasan ta kan yaudara,da wannan halin da rufe zuciyar kowa,na saka ƙaunata da yarda a zukatan dangi da ƴan uwana,na samu arziki wanda bazai kwatan tuba sai dai kuma ban bari kowa ya fuskanci daular da nake ciki ba,a hankali nake tafiyar da al amurana cikin dabara da salo na wayo,da kuma sihirin da nakeyi,sai kuma katsaham rana ɗaya na samu labarin diamon ɗin nan wanda nasan idan nasame shi na gama shahara a duniya tunda yanzu sunan da nayi a harkar tsafine kawai kuma har kar sirri ce,Ni kuma burina bai gama cika ba sai na ganni ina damawa da manyan ƙasashe da ƙusoshin masu kuɗi wanda sukayi suna a faɗin duniya,amma sama ar da nakeyi ba zaiyuwu na cika wannan burin nawa da itaba tunda arziƙin nawa ma na kasa bayyana shi saboda gudun zargi,labarin diamon kuwa da yazo kunne na,shine ya sa na fara jin cewar burina zai iya cika ta sanadin sa,dan haka banyi ƙasa a gwiwa ba,nayi duk yadda zanyi cikin shu uman cin tsafi na sace Abubakar,daga baya na sace ɗan sa Abdallah saboda,a nawa tunanin gani nake idan Abdallah ya girma zai iya gadar mahaifinsa ta wajen mallakar diamon ɗin, sam na manta da cewa yana da ƴan uwa,saboda idona ya rufe da tsanar Abubakar da ta shafeshi,sai kuma daga baya muka gano zulaihat ɗin na da wani cikin,alokacin na riga na gama shirya yadda zanyi,da sabon dan fasaha haifa sai kuma ta haifi mace, ƴaƴan Abubakar kaf ɗin su Nine sanadin tarwatsasu,saboda yadda nake razanasu tare da mahaifiyar su,akan rayuwar su,a haka suka rayuwa cikin tsoro da fargaba har dai sukayi aure,mahaifiyar su ta turasu can wata duniyar dan kar a salwantar mata dasu,kamar ma ba a haiyacin sa yake ba haka ya cikagaba da zaƙulo magana yana haɗar duk wani abu da yayi hatta da irin matan da suka kashe da ƙananan yara da sukayi aiki dasu,bai ɓoye ba sirrin su kaf na cikin ƙunya sai da ya faɗa ya daɗa da faɗar inda suke zaman mitin da sunan dajin da suke aikin tsafinsu. Tun abin na basu mamaki har ya koma basu kuka daga nan ya koma san yayayar musu da jiki da zuciya da ƙara san miƙa wuya ga ubangijin talikai,cikin wani irin yanayi na tsananin tausayin kai da tsinkewa da al'amuran duniya, Alhaji Baba yace"Habibu a ina kaji zancen diamon?tsit falon yayi masu kuka suka tsaida kukansu masu ƙus ƙus suka tsaya da gulmarsu,sai ido da yayiwa Dady Habib yawa,shi kuwa cikin yanayin alhakin da ya fara kamashi, yace"wata rana can shekarun baya nazo zan shiga ɗakin Hajjah sai naji tana surutai cikin ɓacin rai wanda da alama anyi mata wani abu da ya bata mata rai,to har zan shiga sai kuma na dakata sakamakon abinda naji tana cewa,yanzu Alhaji har san kan nasa ya kai ya ware Hajiya Babba ita kaɗai ya gaya mata wannan sirri mai matukar muhimmanci da hatsari ba tare da mu ya nemi ɗaya daga cikin mu ba,kuma har ita da ɗan ta,ƙwafa naji ta ɗan yi kana ta ci gaba da cewa yanzu yana nufin zaice ya barwa Abubakar diamon ɗin saboda tare suka tsinta,kuma ya bashi ya ɓoye baya gudun yayi masa halin ɗan yau,inajin wannan ban bari naji wani batun ba,nayi hanzarin barin falon nata,acikin zancen ta na fahimci cewa ABUBAKAR ya san inda diamon ɗin yake,shi yasa kai tsaye na saceshi saboda na kuma samun tabbaci!'Alhaji Baba ya maida duban sa kan Hajjah wadda kanta yake ƙasa daza a buɗe zuciyar ta kuwa da anyi mamakin irin bugun da takeyi,saukar Muryar sa a kunnen ta daidai yake da wata irin tsinkewa da zuciyarta ta kumayi wanda har saida ta dafe ƙijinta da yake barazanar fasowa ya waje, Alhaji Baba ba tare da ya kula da yanayin ta ko halinda take ciki na fargaba ba,yace"Ya gana ya akayi kika san da wannan maganar alhalin nasan Ni dai ban gaya miki ba?wata irin zufa ce take ta wanke mata jiki,a haƙiƙanin gaskiya Hajja tana cikin wani irin hali wanda bata taɓa tunanin zata shiga ba,da tasan wannan rana zata zo mata da bata aikata abinda ta aikata ba,da tasan asirinta zai tonu da batayi abinda tayi ba,da tasan a kwai ranar da zata mozanta a idanun ƴaƴan ta da mutanen da suke ganin kimarta da ba tayi abinda tayi ba,maganar da Alhaji Baba ya kumayi mata cikin ɗan fusata da tsawa shine ya dawo da ɗan guntun hayyacinta kansa,yace"ba magana nake miki ba Yagana?cikin karaya da saddaƙar da cewa yau ranar dubunta ce,yau ranar banƙada da tonon sililice,yau ce ranar ƙindillanci ranar jin kunyar duniya,tace"kayi haƙuri Alhaji!'Ya gana ba haƙuri zaki bani ba so nake ki gayan yadda akayi kiji wannan sirrin da har kika jawo na kusa rasa ahlina!'cikin rawar murya da tsoron Alhaji Baba da ya kuma kamata saboda ɓacin ransa da yafito sosai,tace"kamar yadda Habibu yaji ina sambatu na Ni kaɗai to nima haka nazo naji kuna maganar kaida Hajiya Babba. Kuka ta fashe dashi mai tsuma zuciyar wanda bai san abinda ta shuka ba,tana cewa dan Allah kugafarceni Alhaji kayi haƙuri nayi maka gagarumar laifin da banajin zaka iya yafe min amma dan Allah kayi haƙuri!'na kasance mayaudariyar mata a gareka mai fuska biyu,ban taɓa zama da matan ka da zuciya ɗaya ba,da da farko hankalina a kwance yake ganin inata haihuwa Ni kaɗai Safiya bata haihuba,amma daga baya da ta fara haihuwa kuma ta fara da namiji sai hankalina ya fara tashi,daga nan nasha alwashin Safiya bazata rayu da ɗan ta ba,dan tun yana ciki naso ɓarar da cikin Abubakar amma hakan bata samu ba,to kuma ashe nima ina da cikin Mansur alokacin ban sani ba sai daga baya na fahimta,hakan ne yasa na dakatar da kokarin zubar da cikin Safiya, na riga Safiya haihuwa dan ita sai da cikin ta ya haura wata goma, namijin da na haifane ya ɗan sanyayar min da zuciya har na ɗan fara haƙura da abuwan da nakeyiwa safiya ta bayan fage,sai dai kuma wata sabuwa,rana tsaka na kuma ganin Safiya da ciki wanda hakan ya matuƙar tada min da hankali,gashi Ni kuma bani da wani cikin kai ƙarshe ma tun a haihuwar Mansur likita ya tabbatar min da cewa mahaifata bazata ƙara iya ɗaukar ciki ba,saboda lokacin da na haihu ALHAJI ba ya nan,dan haka na ce da likita yayi shuru kar ya sake ya faɗa maka saboda hankalinka zai tashi,ya ɗauka da gaske nake hakan yasa shi yimin alkawarin ba zai taɓa sanar da kaiba,to shi yasa da safiya ta kuma samun cikin shima na shiga damuwa me tarin yawa wanda daga nan na fara saƙa mugun nufi akanta da yadda zanyi nima na samu ƴaƴa maza dan aganina soyayyar da kakewa Safiya har da dalilin yaran da ta fara haifa maka Abubakar ne,ban damu da zainab ba saboda itama kamar nice ƴaƴa mata take haihuwa naso mu haɗa kai da ita sai kuma naga kamar tafiyar ba zatayi daidai ba dan naga yadda takewa safiya biyayya abun har mamaki yake ban, duk yunƙurin da nake yi akanta da cikinta ban samu nasara ba,dan shima wannan cikin na Aliyu yaƙi barewa. Wata rana ne na tashi da tsananin farin ciki saboda tunanin da nayi na samowa kaina mafita ta hanyar tara ƴaƴa maza ba tare da wata matsalaba a tunanina ke nan,shawarar da na bawa kaina tayi min ɗari bisa ɗari,tun daga lokacin sai nima na tsiri laulayin ciki,na fara amaye amaye da ɗan kwaɗayi irin na masu ciki,har dai Zainab ta fahimta take cemin Hajjan yara ko dai ankuma kamuwa ne na ga yanzu tsere kuke keda Hajiya Babba!'daga nan sai na samu hanya, kafin kice meye gida ya ɗauka nima ina da ciki,ban fara laulayi ba sai da na tabbatar na gama shirina kuma ya tafi yadda nake so,sai da muka zo daf da haihuwa nida Safiya ita cikin gaske Ni kuma na ƙarya,sai na ce da Alhaji dan Allah ya barni na tafi garin mu can maiduri na haihu saboda matsalar da na gaya masa na samu a mahaifa kuma a kwai buƙatar zuwa gidan a wannan lokacin,duk da Alhaji ba mai san irin wannan al ada bane,amma sai na samu nasara a wannan lokacin ya barni na hada kayana na tafi maiduguri,wanda dama duk acan na riga na kammala shirina,salamatu reza karuwar gida wadda take cin karenta a lokacin,ita najewa da buƙatata amatsayin ta na karuwa,ai kuwa tun alakocin ta sanar dani ai faduwa tazo dai dai da zama dan kuwa tayi sake a wannan karon ta ɗauki ciki,dan alokacin zubar dashi take ta faman yi yaƙi zubuwa,daga nan dai muka shirya me yuwuwa,muka tsara komai cikin dabara,dan haka lokacin da naje Maiduguri dan aihuwa,sai na sharawa mamana ƙaryar cewa a gidan mai magani zan haihu,na nuna mata ina da matsala kuma nice na samo mai maganin likitace ƙwararriya,ita zata karɓi haihuwa ta kuma ba aso haihuwar tazo babu ita akusa saboda matsalar da ka iya faruwa,ras ƙaryata ta yi tasiri azuciyar ka da na mamana,daga nan na shirya muka koma gidan da na karɓi hayar kwanaki, cikin ikon Allah kuwa sai salamatu reza ta haihu a cikin satin sai dai kuma tana haihuwa tace ga garin ku nan,duk da cewa naji mutuwar ta amma hakan bai hana Ni farin cikin cewa bani da wata sauran barazana arayuwata ba,babu wanda yasan me na shirya daga Ni sai ita sai Allah da yafimu sani,na dawo gida da yarona,daga nan kazo kayi masa huɗuba kace kuma mu zauna muyi arba'in saboda bai kamata nayi tafiya mai nisa ba,ka sakawa yaron suna Habibu!' Innalillahi'wa'inna ialaihi raji un abinda yake fitowa daga bakuna mafi hankali kenan, daga ciki harda uban gayyar Alhaji Baba,wata irin zabura Dady Habib yayi kamar mahaukaci ya nufo Hajjah yana cewa ke muguwace Hajjah yanzu kina so kice Ni ba ɗan Alhaji Baba bane?Ni dan ban zamo ɗan ki ba ba abin damuwata bane,amma dan Allah kar kice Alhaji Baba ba mahaifina bane,duk irin mugun halina Ina fatan zama ɗan mutum na gari kamar Alhaji Baba!'sai ga Dady Habib yana zubda waye kamar ƙaramin yaro, Hajjah tace"Habibu sai dai kar a kuma domin kuwa ba kazamo ɗan Alhaji ba san nan kuma baka zamo ɗana ba,domin Allah bai bawa Alhaji gurɓataccen ɗa ba,kasancewar sa mutumin da yatsaya ga Allah,kuma ko ban fada ba dole anzo gaɓar da zaka sakawa mutane kokwanto azuciyar su,domin abinda kayi ya wuce hankali ya ɗauka cewa ɗan uwa zai iya yiwa ɗan uwan sa irin abin da kai kayi,Ni kaina habibu na ji daɗi da yakanance bani ce na haifeka ba domin mugun halinka ya zarta nawa nesa ba kusa ba!'wani irin kuka ne ya kufce mata tana mai cigaba da basu labarin abinda ta aikata ba ta ɓoye komai ba, ta ƙare da ɗurƙushewa gaban Hajiya Babba tana kukan neman gafarar ta, Alhaji Baba kuwa ya kasa cewa komai,sai kansa da yayi ƙasa dashi Allah kaɗai yasan halin da zuciyar sa take ciki,a hankali ya miƙe ya fara ratsa taron ƴaƴan sa da jikokin sa ya wuce can cikin ɗakinsa ya kulle,babu wanda yayi ƙoƙarin dakatar dashi saboda sun san a wannan lokaci dole ayi masa uzuri dan ma ya kasance mutum mai tsananin tawakkali,da juriya akan ƙaddarar da tasameshi. Kuka Dady Habib yake da idanun sa wanda bai taɓa tunanin zaiyi shiba, wannan lamarin shi kaɗai ya karya lagon sa,tabbas idan yace ya ya taɓa jin makamancin wannan tashin hankalin yayi ƙarya, cikin kukan yake cewa Hajja kin cuceni,me yasa baki barni na taso a hannun dan gin uwa ta ba koda kuwa za a dinga yimin girin uba?yanzu duk taran mutanen nan da da suka kasance ƴan uwana yanzu na zama bare acikin su kenan?maganganun da yake yi har sai da takai da cewa wasu sun fara tausaya masa karma Dady Mansur yaji labari,dan abun shi yawa yayi masa ya mutukar razana da jin wacece Hajjah da iri n abinda ta shuka,kallon Habibu yake cike da haushi da kuma tausayi Sa dai shi kansa yasan cewa Habibu ba abin tausayi bane,saboda ya cutar da mutane masu yawa arayuwar sa,wanda kuma alhakin sune ya fara bibiyar sa,tun da gashi har ƙaddarar sa ta juya sama ta koma masa ƙasa,tabbas duk wanda bai ji tsoran Allah ba ɗaiɗaicewa tana tare da rayuwarsa,Dady Habib yana cikin halin nadama wadda ta zame masa ƙeyar baya, yaji an damƙi hannun shi yana ɗagowa yaga Safwan ne da ankwa a hannun sa da alamu dai zai koma inda ya fito ne,dan Nana ne kaɗai ya fi dacewa dashi kafin ya fara ganin sakaiyyar Allah,saboda tsananin tashin hankali da zaucewar tunani bai iya yin musu ba haka ya tashi ya bishi idanun sa na zubar da zafafan hawayen nadama. Duk wanda ka gani afalon Alhaji Baba zakayi tunanin mutuwa akayi masa mai shiga jiki,sai dai kuma sam ba haka bane tsabar damuwa da tashin hankali da kuma tsinkewa da al'amuran duniya ne,Hajiya ladidi da akayi komai agaban idanun ta,tuni jikinta yayi sanyi nadama ta shigeta,tare da fara itgfari akan abun da taso yiwa rayuwarta,Alhajin Nafisa ne ya ɗan ja numfashi kana yace"ai wannan al'amari wanda ya shafi ahline,bai kamata kuyi kirana ba,duk da dai ban san dalilin Alhaji Baba nayin haka ba!'Alhaji Rufa'i ne ya ɗan share gumin dake saman goshinsa,kana yace"ai Alhaji kaima wannan zama ya shafeka matuƙa,kawai dai Alhaji ya ɗan shiga cikin wani yanayi ne da ya kamata ya keɓe kansa shi yasa bai iya tsayawa yayi maka bayani ba,to amma tunda wakilan sa suna nan na kuma su ai nahin waɗan da abin ya faru akansu to ai ina ganin za a iya sanar da kai komai!'ya rufe bakin sa yana mai duban inda Abdallah yake kwance idanunshi a lumshe dan bazaka taɓa iya fahimtar halin da yake ciki ba,Dady jafar ne ya karbi zancen dan yana ganin waɗan nan ahlin yanzu dole ayi musu uzuri dan suna cikin halin da a yanzu bazasu iya wata doguwar magana ba,har sai lokacin da zuciyar su ta fara mantawa da gagarumar ƙaddarar data keto cikin rayuwar su,babu wanda ya motsa ko yayi wani ƙwaƙwƙwaran tari,har sai da Dady jafar ya dire ƙarshen labarinsa da yake bawa Alhaji munir na abinda gudan jinin sa Nafisa ta aikata,sai gashi shima yabi layin kurame,dan tunda ya ɗora tafukan hannun sa akan fuskarsa,bai ce komai ba har na tsawon wasu mintuna,sai daga can ne kuma ya saki ajiyar zuciya tare da cewa,kuyi haƙuri dan Allah kuyi Allah ya huci zuciyarku,bansan da irin bakin da zan rarrashi zuciyarku ba,haƙika Nafisa tayi min ƙarshen tozarci a rayuwata,ta kuma aikata mummunan kuskuren da bazai taba kankaruwa ba!'yana maganar yana share hawayen da ya kasa hana su zubowa,miƙewa yayi ya bawa su Alhaji Hashir hannu kana ya nufi hanyar waje yana cewa Umar kayi haƙuri ka'ida dukkan iyalanka,amma bance sai ka yafewa Nafisa ba,kabbarta taje ta koyi darasin rayuwa,kuma karki sake ki nufo gida na,ki haƙura dake har abada!'wani irin kukan ihu Anty Nafisa ta saka tana magiya wa Mahaifinta da ya yafe mata ya bawa Umar hakuri,amma ina tuni shi yayi ficewar sa,yana ƙara goge ƙwallar idanunsa,Abba Umar ne yace"Abdallah ya kira Safwan ya tafi da Nafisa dan barinta ba tare da ankoya mata darasi ba hadarine, Abdallah kuwa kamar jiran umarni yake haka ya kira Samuyal,yace"yazo cikin falon,yana shigowa ya zo gaban Abdallah ya duƙa kansa a ƙasa yace"Oga kafin inyi abinda ka umarceni inaso na fara karɓar kalmar shahada a bakinka,domin naje nayi bincike akan addinin Musulunci na kuma gamsu cewa shine addinin gaskiya,dan haka ina so ka musuluntar dani!'gaba ɗaya falon ya ɗauki kabbara, Abdallah kuwa bazan iya ce muku ga halin farin cikin da ya shiga ba,ba tare da wani jinkiri ba,ya bawa Samuyal kalmar shahada,yana faɗa har saida ya maimaita sau uku,kana aka kuma yin wata kabbarar, Abdallah yace"wane suna kake so?kai tsaye yace"Abubakar!'dady ya miƙa masa hannu cikin murmushin farin ciki,yace"Alhamdulillah masha Allah, Ubangiji ya sa musulunci da musulmai su amfane ka,ya kuma baka ikon kiyaye DOKAR sa!'da Amin suka amsa kana Abdallah ya bashi umarnin ya tafi da Nafisa har sai ya nemeta. Wannan abun da yafaru na karɓar kalmar shahadar Samuyal shi ne ya sanyaya musu zuciya har aka samu damar tattauna abinda ya faru,sai dai har yanzu babu wanda ya kula Hajjah hatta da ƴaƴan ta sunƙi duban inda take, addu'oi masu yawa aka gabatar kana kowa ya fara watsewa jiki a sanyaye,Dady jafar ne ya ciro madaukar da yasaka ya bawa Dady Mansur saboda waɗan da basa nan,domin wannan zaman yana da muhimmanci ace duk wani ahlin ALHAJI BALARABE ya san abinda ya faru acikin ESTATE ɗin sa, Hajjah kam ta zama tamkar wata mujiya dan kaf ƴaƴan ta waɗan da suka sami halartar taron basu koma ɓangaren ta ba kowacce sai ta wuce gidan mijinta,domin a halin yanzu basa jin zasu iya fuskantar mahaifiyar tasu,duk da cewa itama Nana ƙarama da mijinta a cikin maha intan,to amma dai tanajin gwarashi tunda har ya samu yafiyar wanda suka zalunta,Abba Umar kuwa matarshi ya janye suka nufi sashen sa,Dady Abubakar ma Ammi yabi, dukkanin su suna maijin sabon farin ciki tamkar a lokacin suka mallaki junan su,inno dai itace ta wuce dasu Hajjo bangaren ta,ita kuma Hajiya Babba sai ta janye Bintu saboda dalilinta na cewa sai sunyiwa BINTU auren gata,dan haka da ga yau tabar zaman ɗakin Abdallah,Dady jafar kuwa kai tsaye yacewa da Abigirl ta san inda dare yayi mata dama shi yanzu basu da wani haɗi da ita,ya daiyi mata taimako daya ya bata kuɗin mota ta tafi garin su. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 61 ``` Alhaji Baba kuwa tunda ya shige ɗakinsa ya saka fuskarsa gabas ya shiga miƙa lamuaransa ga Allah,bayaso yayi wani abu da zaisa ace ya zama daga cikin mutane marasa tawakkali da yarda da ƙaddararsu, wannan dalilin ne yasa ya tsaya tsayin daka domin nemarwa kansa nutsuwa,tabbas yasan ko bai fada ba an san cewa dole ya koka da irin wannan lamari da ya samu ahlinsa, amma kuma yanzu dole ne ya zama mai godiya ga ubangiji domin kuwa yanzu ba dabarar sa ce tasa ya warware masa matsalolin ba,yana ji cewa yanzu lokacine da ya kamata ya ƙarfafa zuciyarsa ya janyo farinciki dan farincikin iyalansa,dan kuwa yasan kasancewar sa cikin walwala shine zai basu damar mantawa da mummunar ƙaddarar da ta same su,tun da su sukayi hakuri ai yana ganin shi ba komai bane,ganin cewa su ne jigon waɗan da akayiwa laifin tare da cuta mafi muni, wannan tunanin da yayine yasa shi sakin wani ɗan murmushi tare da faɗin Alhamdulillah aka kulli halin, Allah ya karemu daga sharrin zuciya ya mana tsari da shaiɗan,ya kuma bamu farinciki mai ɗaurewa ya kuma kawar da duk wani abu da zai ƙara cutar da rayuwar iyalina!'Alhaji Baba yayi ƙoƙari sosai gurin cire abinda Hajiya Babba tayi masa a ransa tare da kitsa irin hukuncin da ya kamaceta,Habibu kuwa bashi yayiwa laifi ba Allah yayiwa laifi mai girma, laifinda ya faɗa cewa ba yayiwa bawansa a fuwa akan waɗan nan abubuwa, laifin wani akan wani laifin shirka,to shi kuma Habibu duk ya aikata waɗan nan laifukan,ba zaice yaji daɗi ba dan Habibu ya kasance ba ɗan shi ba,saboda ya riga ya sawa ranshi Habibu ɗan sa ne dan haka yanzun ma bata sauya ba,sai dai yabishi da addu'ar fatan shiriya da neman sassauci gurin Ubangiji. Tsakanin Dady Abubakar da Abba Umar ban san wanda yafi wani dokin amarcewa ba,dan kuwa tunda suka kule a ɓangaren su babu wanda ya kuma jin ɗuriyar su,suna can suna sabunta soyayyar su,Nafisa kuwa ba zan iya misalta halin da ta shiga ba,saboda rashin tsuntsu da tarko,kuma gata a kulle cikin gurin da ko tafukan hannayen ta bata iya gani,gurin da bata taɓa tunanin zata zoshiba,(to dama Nafisa ai ƙarshen mugun abu kenan, Allah dai ya tsare mu daga masu irin halin ku) ESTATE ɗin tayi shuru tsawon kwana biyu,kafin kuma su koma da walwalar su, Abba umar tuni ya maida su Hajjo gidan da ya kaisu kasancewar gidan babban gidane,sai ya miƙa wa Fafi takardun gidan yace"ya bar masa ya cigaba da zama da iyalan sa,ƴan biyu kuwa tunda suka ƙyalla idanu suka ga ƴar uwar su Bintu shike nan suka samu nayi duk da cewa sun girmewa Bintun,Hassan ya zama macen dole a cikin su,sunƙi barin estate ɗin gaba ɗaya sun tare anan sunce sai angama bikin Bintu zasu koma gida,fafi dai yana can shima shida ma'unsa ana sabunta soyayya. Yayin da duk ake wannan budurin Abdallah yana can yana fama da soyayyar da a yanzu yake kokarin gasgata ta,ya rasa dalilin da yasa a ka hana Bintu dawowa sashen sa,shi kuma tsabar miskilanci ya kasa tambayar ko Ummi Laila ce,wadda a kwana biyun kusan kullum yana bangarenta,haka yake sunturin zuwa wajen Alhaji Baba ko da zaiyi masa maganar Bintu amma shuru kake ji,sai yayi tunanin ko dai baisan abinda yake faruwa bane?tun yana daurewa zuciyar sa har ya fara bin iyayen nasa maza amma,duk yawan zaman da zasuyi tare baya jin maganar Bintu abakin su,to wai me ake nufi da wannan abun ne?sai kuma ya shiga fargaba kar dai ko Dady jafar ya faɗa musu abinda yace"akan cewa da yayi idan komai ya daidaita zai saketa ta auri wanda takeso,tunawa da hakan yasa yaji zuciyar sa na bugawa da ƙarfi,kamar zata faso ƙirjinsa ta fito. Ita kuwa Bintu tana can Hajiya Babba da Ammi da inno kai harma Hajjo da bata gidan suna faman yi mata gyaran da bata samu ba,gyaran gata wanda suke san zautar da jikan nasu a ɓangaren fadamar Bintu,tana yawan tunawa dashi tana kuma mararin ganin sa,sai dai kuma yadda su Inno suka kasa suka tsare yasa bata da hanyar ganin sa ko da daga nesa ne. Yau kimanin kwana biyar kenan da warwarewar ƙullin dake cikin gidan Alhaji Baba,hankula sun fara kwantawa farinciki ya fara wanzuwa a zukata,yayin da wasu suke cikin halin tsaka mai wuya,kamar dai su Hajja ke nan,wadda tunda abun ya faru babu wanda ta kuma gani a ɓangaren ta,tun daga kan ƴaƴan ta har zuwa ƴaƴan kishiyoyinta da surukanta,dan kuwa Alhaji Baba yayi jan kunne mai tsauri akan kowa dake cikin estate din,duk wanda yaji koda labarin ya kalli hanyar ɓangaren Hajja to bai yafe masa ba, wannan shine hukuncin da ya fara zartarwa akanta,a halin yanzu kuwa kaf ahlin ALHAJI BALARABE babu wanda labarin abinda ya faru bai same shiba,su abdulraman da abdulshakur duk sun dawo cikin ahalinsu farin cikin ganin mahaifinsu da ɗan uwansu shi ya saka su cikin farin cikin da ya hana su alhinin abun alhinin da ya faru,kowa ya dawo da iyalan sa ya kafa sabuwar rayuwar tafarinciki tare da ƴan uwansa,a ɓangaren Taufika kuwa tunda labarin ya sameta ta rude tare da shiga wani irin hali na damuwa, wato dai yanzu ana nufin ace Ya Abdallah ya haramta a gareta,bata jin zata iya wannan jihadin hakan ne yasa ta tattaro daga ziyarar da suka kaiwa mahaifansu suka dawo Abuja cikin ESTATE. Abdallah ya koma bakinsa,kamar yadda ya saba a baya,ya na cigaba da tafiyar da asibitin sa,amma duk wannan abun da yakeyi ƙarfin hali yake,dan dai kawai Abdallah ya kasance muskilin mutum ne,amma fa haƙika zuciyarshi tana cikin wani yanayi na rashin Bintu, wanda a kwana kin ne ya tan-tance tsakanin ƙarya da gaskiya,ko yanzu dawowar shi daga asibiti kenan,ya shiga shawagi a tsakanin part ɗin iyayen nasu ko Allah zaisa yaci karo da Bintun,sai dai har ya gaji ya yada zango a part ɗin Hajiya Babba wanda ya fi bada tabbacin cewa Bintu tana nan bai ga ko usainar fafi ba bare kuma buntu,yana kwance jikin ƙatuwar kushin ɗin falon idanunshi a lumshe kana ganin sa kasan da akwai gajiya a tare dashi gakuma ƙishin ruwan Bintu da ya addabeshi,Muryar Hajiya Babba ce tasa ya ɗan bude gajiyayyun idanun sa,kai kuma lafiyar ka kazo nan ka kwanta cikin kin kayan aiki?bai kulata ba,sai dai can kasan zuciyarsa yake cewa ina fa lafiya Hajiya Babba kun kama matar mutane kun riƙe,amma a fili sai yayi mata banza dan gaba ɗaya haushin su yake ji,bata nuna ta gane komai a tare dashi ba, tace"ai ya kamata kaje ka kwanta ka huta tunda da alama yanzu ka dawo!'tamkar ba dashi take ba,ko kallon inda take baiyi ba, sai ɗan gyara kashingiɗar shi da yayi,hakan da yayi ne yasa ta gane bai da niyar tashi,ƙwafa tayi tana cewa dani kake zan can!'ta tafi tana ƴan miticinta,bata san kunnen Abdallah da ji ba, har da su cewa ita sam bazata yadda da zaman Bintu dashi ba,dan Bintun bazata iya da wannan halin nasa ba,a saman laɓɓan shi yace"da data zauna dani har zuwa yanzu ke kika zauna mata dani? kamar anjehota haka ta ta fado cikin falon,dawowarta kenan ko hutawa ba tayi ba,tazo ganewa idanunta abinda taji,turus tayi ganin wanda yake hakimce acikin falon,sai kuma take jikinta ya shiga rawa,har ta ma manta abinda ya kawota,itafa bata jin zata iya daina san Ya Abdallah sai dai idan mutuwa tayi,duk lokacin da ta ganshi saitaji tamkar ana ƙara mata wutar sanshi,cikin sanyin jiki ta ƙaraso tsakiyar falon,kana ta nemi guri kusa da inda yake ta zauna,tare da gaida shi cikin kiɗimewar murya,da lafiya ya amsa mata shi ma badan kallon ƙuril ɗin da take binsa dashi ba,da bazata san cewa ya amsa ba,sai kawai ta samu kanta da ƙarfin halin fara yi masa jaje akan abinda ya faru da kuma fatan Allah ya tsare gaba. Buɗe idanun ta tayi a hankali,idanun ta nadan komawa suna lumshewa,ita kam ta rasa wannan abu na magani da meyene,gaba ɗaya nema suke su zamar da ita ƴar ƙwaya daga sun banka mata wancan sai wan Nan,wai duk maganin sanyi ake bata,a fadarsu dai,gashi wasu da yawa idan ta sha sai sun sata bacci kamar dai yanzu da wannan ya sakata baccin yamma,saida ta ɗan huta kana ta miƙe har zata shige toilet,sai kuma taji jikinta ya dauki wani sanyi,haka zuciyarta ta shiga bugawa da sauri da sauri,fasa shiga tayi ta juya akalarta zuwa ƙofar da zata maida ita falon Hajiya Babba,a hankali ta buɗe tare da cusa kanta,sai dai kuma tozalin da tayi da Taufiƙa durƙushe gaban Abdallah shi ya nemi hautsina tunaninta,da sauti ta ƙarasa fitowa,sai a sannan ya kula da abinda Taufiƙan takeyi,ruwa ne take tsiyayawa Ya Abdallah a glace cup,tana ƙoƙarin miƙa masa,da sauri BINTU ta rike cup ɗin, ɗagowa tayi dan ganin waye sai tayi ido huɗu da fararen idanun Bintu da kyakykyawar fuskarta da take wani irin glowing na tsananin gyaran da take sha, murmushi tayiwa Taufiƙa da ta daskare a gurin, tana cewa ayya Anty Taufiƙa saukar yaushe ashe kin dawo?ta faɗa tana mai shanye ruwan,yayin da idanunta suke san kallon idanun ogan nata amma sam hakan ya gagara,sai ɗan tura bakinta da tayi,wanda batayi aune ba, taji Abdallah ya sunkuceta cikin sauri sai waje,wani irin kuka Taufiƙa ta shiga yi mai tsanani da ban tausayi,ita kuwa Bintu magiya ta shiga yi masa ya sauke ta kar su haɗu da wani,ba dan hujjarta ya sauketa ba,sai dan baya son kwakwazonta ya janyo hankalin Hajiya Babba,kama hannun ta yayi suka fara tafiya wanda a da taso yi masa gardama saboda tsoran fadan Hajiya Babba,sai kuma taji baza ta iya ba, Cikin nasara da fatan Abdallah basu tarar da inno a falonta ba,hakane ya ƙara bashi ƙwarin gwiwar jan Bintu har can cikin ƙuryar ɗakunsa,suna shiga ya juyo da ita gareshi yana fuskantar ta,sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta,a hankali ya matso daga da ita,kana ya ɗago fuskarta,ita kuma tayi saurin rintse idanunta,zubawa eye lashes ɗin ta ido yayi,yana kissima abubuwa masu yawa can kasan zuciyarsa,a jikinta taji irin kallon da yake mata,dan haka ta shiga ɗan ware idanun nata dan ganin abinda yake kallo a jikinta,idanunta ne suka shige cikin nasa,yayin da ita kuma gaba daya ta diririce,cikin sanyin murya da tura baki tace"zan tafi kar Hajiya Babba ta nemeni!'haɗe fuskar ta yayi da tashi kana ya fara magana cikin shu'umar Muryar sa,me saka lakar mutum narkewa,yace"Bint""me kuke nufi dani ne ke da kakanninki?cikin rashin fahimta tace"kamar ya?cikin tura kanshi cikin wuyanta yace"da suka ƙwace minke ke kuma kika biyesu saboda baki damu dani ba,ya kuma tura kanshi a wuyanta yana shaƙar ƙamshin ta da yake neman zauta tunaninsa,yana faɗin Ummm Bint na gaji haka bazan iya ba,bazan iya nisa dake ba,bazan iya raba makwanci dake ba,bazan iya nisan tar numfashinki ba,Ina son halinki,inason kyawunki,inason nasabarki,Bint Ina son wannan ƙamshin naki,komi naki abinso ne,ya ƙara sa faɗa yana sauke mata numfashin sa,wanda yake hadewa da ƙamshin jikinsu yana bada wani irin yanayi mai wuyar fassarawa, maganganun Abdallah sun rikitar da tunaninta sun kuma jefa ta cikin tunanika iri iri,ji tayi ya ɗago kanta cikin wani irin sanyin jiki,ya sumbaci saman lip ɗin ta,kana yace"my Bint,kije Amma ki sani zaki bar mijinki da kewarki da muwar rashinki zata iya jefani wani hali!'daga haka ya saketa ya faɗa toilet,binsa tayi da ido,tana jin wani irin abu na mata yawo a tsakar kanta,cikin mutuwar jiki ta fita daga ɗakin,tana ƙissima yawan damuwar ta akan damuwar Abdallah, Dady Habib fa yana cikin kin tsaka mai wuya,duk inda ya motsa sai yaji kukan jarirai,babu hali bacci ya ɗan fizge shi sai yayi mafarki da wasu daga cikin ƴan mata da samarin da ya salwantar da rayuwarsu,ko ina yayi babu daɗi,ji yake inama yana da halin ta riyo rayuwar sa da yayi domin ya goge duk wasu kura kurai da ya aikata,idan ka ganshi baza kace wannan hamshaƙin mai kudin bane mai ji da dukiya,su kansu masu tsaran shi sun fara tausayawa halin da yake ciki,dan ganin tun kan aje ko ina Allah ya fara kama shi da irin abubuwan da ya shuka. A yanzu dai Alhaji Baba ya samu nutsuwa,hankalinsa ya kwanta, duk inda ya juya ƴan uwanshi da ƴaƴan shi da jikoki ne suke walwala,babu wani abu dake damunshi sai ɗan damuwar Habibu,shi yasa yake tunanin kiran Abdallah dan afito dashi haka,a ganin Alhaji Baba ai idan aka barshi da hukuncin Allah ma ya isa,su Alhaji Nasir kuwa tuni ya yanke ma amalar a minta a tsakanin su,sai dai mutumci,har kar kasuwanci da duk wani abu da ya shafe su ya yanke,ta kanas Alhji Salisu mijin Nana ƙarama yazo ya gurfanar agaban Alhaji Baba ya roƙe shi gafara,tare da neman masa gafarar Nana ƙaramar,dan tunda suka koma gida take borin sai ya saketa tunda baya san mahaifinta shi da mahaifinsa,kuma dama ba dan Allah ya aureta ba,dan haka sai ya saketa, Alhaji Baba a take ya kira wayar Nana ƙarama ya bata baki tare da nasiha mai ratsa jiki,babu yadda zatayi dole haka tayi hakuri ta ɗan gana ta zauna a gidan mijinta, Tun ranar da suka rabu basu kuma haduwa ba,dan kuwa sosai ake shirin bikin ƴaƴan gata dan harda su Farida da Hauwa'u sai Taufiƙa da Siddiqa har da Rahima,kowa ka kalla shirin bikin yake,gyara kuwa tamkar za a canja musu halitta,dan fatar su har wani jaja da sheƙi takeyi,duk wannan abun da akeyi BINTU da Abdallah basa cikin haiyacinsu,bukace suke da ganin juna, amma Abdallah tsabar miskilanci ya haɗa yayi fushi da kowa ya ma bar gidan gaba ɗaya ya koma wajen Dady jafar, BINTU kuwa sai tsabar damuwar da take ciki sai ana acikin yi musu gyaran jiki sai dai kawai kaga hawaye na tsiyayowa daga idanunta,kamar yauma da suke cikin tafkeken dakin da aka zuba masa kayan gyara nau'ika iri iri,Rahima ta dubeta yayin da taga tana faman goge hawaye da bayan hannunta,ƙunshe dariyar ta tayi kana tace"Ya dai yarinyar Ya Abdallahn ta,me yafaru haka?tura baki tayi tana hararar Rahima saboda taga dariyar da take yi mata,Rahima ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa,gaskiya Batula salon nan naku na burgeni,wai amma idan an cewa mutum ya faɗa tafkin soyayya sai yace ba haka ba,hasalima shi bai san soyayya ba!'ta ƙare maganar da sheƙewa da wata muguwar dariyar tura haushi,shigowar Ammi ce ta tsayar da ita tana rufe baki da hannun ta,Ammi tace"ke Rahima bana son sakarci,wan Nan dariyar ta lafiya da meye? da sauri BINTU ta koma jikin Ammi tana ci gaba da tsiyayar hawaye, cikin san fashewa da kukan da ya tokare mata maƙogaro,tace"Ammi da take,tun ɗazu take tsokana ta!'Ammi ta kuma jefawa Rahima harara,kana ta dawo da duban ta kan Bintu cikin lallashi tace"rabu da ita mamana,jeki zauna a ƙara sa miki,idan angama kizo zan baki abun daɗi banda su oo!'tura baki Rahima tayi kana tace"da ɗin abun dai yanzu nima ina da tudun dafawa!'gwalo Bintu tayi mata,daga nan Ammi ta fita ta barsu ana ci gaba da gyara su. Tunda taji kira daga falon Alhaji Baba taji duk bata da nutsuwa,da sassarfa ta ƙarasa falon,inda ta tarar da Abbanta da Dady Abubakar da Dady Mansur sai inno,ga kuma uban gayya Oga Abdallah a hakimce tamkar wani sarki fuskar nan a cakuɗe,sai da ta zauna sannan ta kula da Taufiƙa da ke durƙushe gaban Alhaji Baba tana ta sheshsheƙar kuka,a san yaye tace"Alhaji Baba gani!'ɗan gyara zaman shi yayi tare da gyaran murya kana yace"yauwa Alhamdulillah, Taufiƙa ga shi nan na kira duk wanda yake da ruwa da tsaki akan al'amarin aurenki dan haka ki maimaita abinda kika faɗa min kafin shigowar su!'sunkuyar da kanta kasa tayi tana fatan dacewa Allah yasa kar Bintu ta kunya tata, Allah yasa kar ta ƙarya tata, cikin kwantar da murya tace"dama naje na samu Bintu munyi magana ta fahimta nida ita,tace"ta amince na auri Ya Abdallah zamu zauna lafiya amma bazata iya zuwa ta faɗa ba,sai dai Ni nazo na sanar da kai idan yaso in aka kirata aka tambayeta zata amsa cewa ta amince!'ta ƙarasa faɗa tana mai yiwa Bintu wani irin kallo na neman ɗauki da taimako,har da hada hannayen ta biyu bata tare da kowa ya luraba,sai Bintun da takewa Taufiƙan kallon mamaki da tambayar yaushe mukayi haka dake?maganar Alhaji Baba ce ta dawo da hankalinsu kansa,yace"to kinji ke Bintu shin wannan magana gaskiyane?kuma kin amince da auren Yara uwar ki da mijinki?wani irin duka ƙirjin Bintu yake,ga kuma tashin kallon da take jinsa a jikin ta na Abdallah,wanda sai kayi da gaske zaka san cewa kallon nata yakeyi,Dady Mansur ne yace"ke muke sauraro faɗima!'sam bata san lokacin da ta shiga gyada kanta ba,idanunta kuwa sunyi jawur,ƙiris suke jira su zubar da zafafan hawayen da suke cikin su,bata gama dawowa hayyacinta ba taji Abbanta yana cewa to tunda ta amince Alhamdulillah!'shi dai Dady Abubakar kallon Bintu kawai yake cike da san ta ɗago su haɗa ido, Alhaji Baba yace"Abdallah tashi ka dauki matarka ku tafi gida na baku sati ɗaya,wanda shine ranar da za a ɗaura auren ku kaida Taufiƙa,idan yaso sai a zarce da bikin gaba ɗaya!'Dady Mansur yace"hakan yayi Allah yayi muku albarka,amma Alhaji Baba wane gida zasuje nayi zatan suma a nan cikin ESTATE zasu zauna?Alhaji Baba yace"a nan zasu zauna amma sai angama gyaran sashen nasu dan haka suje ta ɗan anyi bikin sa tare gaba ɗaya!'a hankali Abdallah ya miƙe ya ɗan rissina yayiwa Alhaji Baba rada kana ya fita,inno tace"idan tayi tsami Maji!'Dady Abubakar yace"tashi maza ƴar albarka kibi mijinki!'tashi tayi jiki a sanyaye tabi bayan Abdallah, Taufiƙa kuwa kamar zata taka kanshege da farin ciki itama ta fita burinta ya kusa cika zata auri rabin ranta,su kuma suka cigaba da tattauna abinda yake sirrinsu ne. Tunda suka shiga motar take kuka har suka fara tafiya,shi kuwa Abdallah babu abinda yace"mata,saima wakar ɗawisu da yasaka ya shiga bi a hankali cikin sassanyar Muryar sa,mai daɗin sauraro,inda yake cewa,zana sanar miki amsar tambaya a cikin zuci babu kowa sai ke ɗaya,ɗif tayi da kukan da takeyi sai Muryar sa dake ratsa duk ilahirin sassan jiki da jinin ta,lumshe idanunta tayi kamar mai bacci tana ci gaba da sauraro tare da mamakin yadda akayi ya Abdallah ya iya waka haka, [11/15, 5:17 PM] F Y ADAM: 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 62 ``` [11/15, 5:19 PM] F Y ADAM: 💫💥💫💥💫💥💫💥💫💥💫 *_ALBISHIRINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE , SHAHARARRAR KUMA KASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TANA YI MAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE CIKIN FADIN NIGERIA DA NIGER KARKU MANTA MACE MAI KYARA KANTA BATA BORANCI_* 💃💃💃💃💃💃💃 07069711327 _Akwai zafafan kayan Mata masu kyau da arha cikin sauki da rahusa Kuma duk inda kike zamu aika maki kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa don a Dade anayi sai gaskiya uwargida da amarya ku garzayo Kar abaku labari_ Munada kalolin Kaya kamar haka💥💫💥💫💥💫👇🏻👇🏻 Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin gargajiya da bashida illah ajiki Maganin hips Mai tado da hips cikin kankanin lokaci Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau kema ki shigo cikin jerin Mata masu aji Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar dai dai abin alfaharin kowane namiji, Akwai kalolin gumbuna masu kyau da saukar da ni'ima Maganin matsi masu ciko da gaba da matseki Kamar Yar budurwa uwa uba zasu Baki dandano Mai gamasar da maigida Kalolin garrika masu bawa mace niima da jimawa ajiki Kalolin tsumi Sha yanzu magani yanzu dasa Mai gida ihun Dadi Zumar mallaka Zumar goron Tula Zumar ridi Zumar Mai rubutu Hadin mallaka Turaren mallaka Shu'umar humra Turaren AL'AJABI Matan gaske Ak 49 Sirrin tafin k'afa Turaren fuska Hatsabibin turare Kwallin mallaka Zoben mallaka Jigidar maida tsohuwa yarinya Maltinar Mata Karya gado Yajin Mata (yajin Mai ciko da mace) Yajin maza (domin Karin k'arfi) Muna dahuwar Kaya kamar haka💫💥💫💥👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 Dahuwar zabo (mallaka) Kazar Yar gata Yan shila Ciccibi Dambu Zuciya Yan ciki Kwai ukku Tsoka Tara Kifi Da sauransu Akwai sirrika sosai da muke hadawa ga wacce kishiya ta addabeta ko wadda take fama da butsarin namiji ko mafadacin namiji ko namiji Mai yawon dare ko Wanda yake bin Mata insha Allah duk zaku samesu Kuma da yardar Allah za'asamu biyan bukata Muna bada magani ga yarinyar da tsautsayi ya fad'a Mata ta rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji Kuma insha Allah zaadace da yardar Allah Abubuwan da yawa gsky Wanda in nace Zan lissafasu sai nakwashi tsawon lokaci maiso tabini PC don ganin kalolin kayan da muke dasu , Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman yusuf Yar mutan sokoto 07069711327 . Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan tayimun magana🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼ngd 07069711327 Pg 62 A haka suka ƙara so wani hadaɗɗen gida mai hawa biyu,yana yin fakin ta fito tana bin gidan da kallo,tsabar yadda gidan ya burgeta yasa bata san sanda ta fara washe fararen haƙoran ta ba,juyowa tayi tana son yi masa magana amma ganin yadda ya haɗe fuska yasa tayi shiru tare da dawowa hankalinta,takawa ya farayi tabi bayanshi abinda ya faru ɗazu yana dawo mata,nan da nan saiga hawaye sun cika idanunta,bata samu damar ƙarewa ran tsetstsan falon kallo ba saboda yanayin da take ciki,hayewa sama yayi ya barta nan tsaye tana fama da hawaye,take wasu tunanika suka fara tsere a zuciyarta,yanzu haka ma haɗa baki sukayi da Taufiƙa shi yasa baice komaiba,kuma gashi yanzu yana ta haɗe mata rai,zama tayi tare da zuba tagumi,zuciyarta cike da tsoran zama da Abdallah,tunda tasan dama can ba wai sone ya haɗa su ba,wata ƙil yana ganin yanzu amfaninta ya ƙare ne shi yasa zai auri matar da yake ganin ta dace dashi,kuka ta fashe dashi mai tsanani tanajin wani irin tafasar zuciya,da zafin ƙaunar da ta riga ta gasgata cewa tanayiwa Oga Abdallah,wanda a da sam bata tsammaci haka ba,kuma idan za a rutsata da wuƙa bazatace ga yadda so yake ba,amma yanzu ta hakikancewa zuciyarta cewa dole ta yadda da zazzafar soyayyar da ta kamata,yanzu ke nan ta zama mai son maso wani kamar yadda takewa Taufiƙa kallo? yanzu reshe ya juye da mujiya kenan?zamewa ƙasan tattausan carpet ɗin dake malale tsakar falon tayi tana cigaba da kukan tausayawa kanta,ji take gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi tausayin kanta kuwa sai ratsata yake yi, Sai da yayi wanka ya fito,kana ya lura fa har yanzu Bintu bata biyoshi ba,ɗan tsaki yayi yana mai jin haushin yadda zuciyarshi ke azabtuwa akan yarinyar da sam bata damu dashiba,shi yana can yana fama da azabar zuciya da rashin sukuni akan ta,ashe ita kuma tana nan tana neman yadda zatayi ta cuso masa wannan baƙar kunamar cikin rayuwarsa, cikin jin haushin abun ya fita,can ya hangota ta maƙure guri ɗaya kamar maijin sanyi,sai kuma yaji wani iri a ransa,sam baya da wani kwarin gwiwa ko karsashi akan ganin Bintu cikin damuwa,hakan na sa yaji duk ya tsani kansa,ko a tarihi bai tambajin makamanciyar ƙaunar sa da Bintu ba,wani irin sone ya shige shi wanda lokaci daya yayi masa mummunan kamu,lumshe idanunsa yayi yana tuna lokacin da ya fara sauraren waƙoƙin soyayya duk saboda Bintu da kuma binciken da yasha akan gane launinso,da yadda yasha fama da bince kafin ya yadda da soyayyar da tayi masa kamun kazar kuku, A jikinta tajishi, taji irin kallon da yake mata na tsantsar so da tausayi,ɗago kanta tayi a sukwane dan tabbatar da shi ɗinne,kallonshi take idanunta na tsiyayar hawaye,tanajin zuciyarta na bugawa,tare da kuma jin wani rauni na shigarta,ji tayi bazata iya ba,sam bazata iya dakon soyayyar shi ita kaɗai ba,ita macece mai rauni bazata iya jumurin barin zuciyarta cikin halin neman ɗauki ba,tun farko shine me taimaka mata a duk kan abun da ya shafi rayuwarta,dan haka yanzun ma shi zai taimakawa zuciyarta,da wani irin gudu mai haɗe da sassarfa ta isa gareshi,wanda shi kuma take yayi gaggawar yi mata masauƙi acikin faffaɗan ƙirjinshi,a hankali ya shiga sunsuna gashin kanta,yayin da ita kuma take murza fuskarta a ƙirjinshi,cikin wata iriyar murya wadda kana ji kasan tana neman ɗauki ne a cikin soyayya,tace"wayyo,wayyo bazan iya ba,ya Abdallah na gaza zuciyata baƙuwa ce akan wan nan yanayi,ban san komaiba sai asanadinka,ban fahimci komai ba sai a kwanakin na,ban gane manufar bugawar zuciyata akanka ba sai a kwanakin nan,ban gane ma anar damuwar da zuciyata tayi akan ka ba sai a kwanakin nan,ke nan na daɗe ina shan wahalar da na kasa gane kota mece ce,na daɗe ina azabtuwa akan abinda bani da masaniya akan sa,sai yanzu na gane ya Abdallah dan Allah kar ka juyan baya,ka dauka cewa har yanzu Ni marainiya ce,ka dauka cewa har yanzu bani da gata kai kaɗaine gatana mai share hawayen fuskata majinginata,kuma farin cikina!'ɗaga ta yayi ba tare da yace mata komaiba,bai dureta a ko ina ba sai katafaren ɗakin da yake dim ɗim da duhu,sauke ta yayi tare da kunna wutar ɗakin,zaro idanu tayi tana bin kwalliyar da aka ƙawata dakin da ita,wasu jajayen fulawowine a ka yi kwalliya dasu a kowace kusurwar ɗakin,shi kanshi gadon abun kallone,zaunar da ita yayi a gefan gadon kana ya fita,jim kaɗan ya dawo hannun sa ɗauke da wani plat wanda aka wrapin ɗinsa, ajiyewa yayi a kusa da ita kana yayi mata alama da ta sauko,saukowa tayi jikinta a sanyaye har yanzu zuciyarta bata daina bugu ba,ganin bata samu amsa daga ya Abdallah ba,fuskarshi take kalla tamkar zatayi kuka lokacin da taga ya buɗe plat ɗin,wasu irin kaji ne masu maiƙo da kyan kallo kana gani kasan gashin ma na musamman ne,har lokacin bai yi mata magana ba,sai tura mata da ya shiga yi a bakinta,tayi ƙoƙarin kawar da kanta aniyarta na ƙinci amma sai ta hadu da hukuncin kaifafan idanun sa,wanda dole tasa ta buɗe baki ta shiga karba,duk da cewa ba ƙaramin daɗi gashin yayi mata ba amma hakan bai hana ta ci gaba da tsiyayar hawaye ba,yana kallonta bai ce mata komai ba,har sai da yaga tana yin kamar zatayi amai kana ya ƙyaleta,daga nan ya kuma yi mata umarnin bebaye akan taje tayi alwala,haka ta kuma tashi taje tayi wanka ta ɗauro alwala,a kan sallaya ta sameshi,dan haka ta bishi sukayi salla daga nan suka fara nafilfilu wanda har saida ƙafafun Bintu suka fara hajiya,bayan sun idar ya daɗe yana addu'oi,itama ya kama kanta yayi mata addu'a,idanunta ne sukafara lumshewa alamun bacci,ji tayi kawai ya zare hijabin dake jikinta,ɗaukar ta yayi cak ya nufi gadon da yasha shimfidar alfarma da ita,kwantar da ita yayi kana ya janyo igiyar ƙwan dakin ya kashe,sai dakin ya bada wata kala mai kyau,jinshi tayi ya kwanto jikinta tare da yi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa. Kallon fuskarsa take yi ta cikin ɗan hasken da ya haska ɗakin,kamar yadda yake kallon cikin idanunta,wani sassanyan kis taji a saman idanunta, cikin wata irin kasalalliyar murya yace"kin gama naki saura nawa,Ni abinda yake raina yafi ƙarfin baki ya fadeshi, ya fi ƙarfin misali,yafi kuma ƙarfin tunaninki, sai dai nayi a aikace,abinda kikeso ki sani shi zan nuna miki yanzu,kisan cewa zuciyata ta musamman ce akanki kuma baƙuwa wadda bata iya karɓar abinda ya danganceki da wasa ba!'daga haka wasan ya fara sauyawa,tun Bintu naƙin karɓar tayin ogan nata har ta koma responding,wata irin sumba yake mata tamkar zai tsinke harshenta,a hankali yasa hannu ya tsinke madaurin rigar da dake jikinta,sai ga komai na Bintu ya baiyana a cikin idanun jarumin mijinta,laushi da santsin fatar Bintu da ƙamshi shi yake neman zauta ƙwaƙwalwal Abdallah,bin ko inan ta yake yana sunsunawa,ya rude ya kuma ruda Bintu ƙaramar yarinya da bata san komai ba,lokacin da hannun shi ya kai kan na shanunta sai da numfashinsa ya nemi daukewa, Abdallah farin shiga ne a taba halittar mace dan haka ji yake kamar ba a duniya yake ba,ita kanta Buntu duk yabi ya gigitata,karɓar sakonnin sa take ta ko ina,tafiya tayi tafiya Bintu bata ankaraba sai tsintar Abdallah tayi yana karanto addu'ar saduwa,bata gama tan-tance me ke san faruwa ba,taji wani abu mai kauri na ratsa tsakiyarta,kuka ta saka mai ƙarfi,tana ture shi,amma ina Abdallah bai san tanayi ba,(karfa kuyi zatan wai karfi yasaka mata)shi fa Abdallah duk wani abu da yasan Bintu zata ji zafi azuciyarta ko jikinta baya sonshi kuma ƙoƙarin kiyayeshi yake,amma tsabar raki irin na Bintu da shegen tsoro sai gata tana kuka wurjanjan,bakinshi ya saka a kunnen ta,can cikin wata irin murya yace"my Bint kiyi haƙuri ki barni,bazan Miki mai zafi ba,zan tattala gonata tamkar ƙwan da ba ason fashewar sa,zan kiyaye samuwar ciwo da raɗaɗi a jikinki da zuciyarki,bazan bari kiyi kukan bakinciki ba sai dai na farin ciki,ki amince dani kinji my jewel!'yadda yake kalaman da yadda yake sarrafa harshensa shine ya kashewa Bintu jiki,bazata iya hana ya Abdallah abinda zai kasance farinciki da jin daɗinsa ba,tana zubar hawaye tace"na bari ya Abdallah na bari kayi komai kakeso haƙƙin kane!'cikin sanyin jiki ya haɗe bakinshi da nata tare da yi mata rumfa yana kallon cikin idanunta,itama shi ɗin take kallo wanda har ya fara ratsata a hankali ba tare da ta ankara ko taji wani mugun zafi ba,iya dauriya dai yau Bintu tayi ta duk da cewa Abdallah baiyi mata mugunta ba,son abin da yake bai rufe masa ido ya kasa tausayawa Bintun tasa ba,mirgina wa yayi gefanta yana maida numfashin gajiya,ga wani zazzaɓi da yake son kamashi,Bintu ma numfashi take maida wa a hankali yayin da ta kasa rufe ƙafafunta sai warasu da takeyi saboda ta samu iska,ga wani irin ciwon kai da ciwon jiki da yake saɗadarta,a hankali ya sa hannu ya janyo ta jikin shi,zafin da taji a jikin shi shi ya rudata, kamashi tayi tana goga ƙafafunta cikin nashi,cikin sanyin murya tace"wayyo ya Abdallah kaina jikina ciwo!'kara janyo ta jikin sa yayi,kuka ta saka tana shishi da baki kamar wadda taci yaji,sauri yayi ya rufe bakinta da nashi har saida yaji ta nutsu kana yayi ƙarfin halin tashi,sauka yayi daga kan gadon kana ya shige toilet,ya ɗan jima sannan ya fito jikinsa ɗaure da ƙaramin towel,yana zuwa ya dauketa cak,bai direta ko i na ba sai cikin zazzafan ruwan da ya haɗa mata,kasancewar bacci ya fara daukarta sai abun yazo mata kamar a mafarki,kuka ta saka masa saboda zafin da taji yana ratsata,a wannan gaɓar dai Abdallah bai tausayawa Bintun tasa ba dan yasan hakan shine gatan da zaiyi mata tasamu sauƙin abinda takeji,duk da yasan cewa abun na Bintu har da raki,sai da yayi mata ruwa uku ƙwarara,san nan ya tsaya akanta tayi wankan tsarki dana sabulu,naɗo ta yayi kamar ƴar baby, ya kwantar da ita saman sofa,yaje ya zare zanin gadon tare da canjawa,kana ya dauko ta ya maida ta kan gadon ba tare da ya nemi saka komaiba ya kwanta a gefanta,tare da nadeta cikin jikinshi. Kamar daga sama yaji sheshsheƙar kukan ta, ɗago fuskarta yayi yana mai yi mata kallon tambaya,ɗan tura baki tayi cikin yanayin shagwaɓarta,tace"ba kai bane!'alamar tambaya ya kuma yi mata akan me kuma nayi?hawaye suka kuma sauko mata tace"kaida Anty Taufiƙa mana dama kana santa shi yasa kuka haɗa baki zaka aureta ko?wani ɗan murmushi ne ya suɓuce masa,kana yace"ai ke kika ce na aureta ko kin fasa tunda na ga alama yanzu kin san daɗin auren ko?da sauri tace"bani nace mata ba ƙarya tayi min Ni bana magana da ita ma!'dariya yayi wadda ta kuma kayata fuskarshi da annurin amarcin dake fita,a hankali ya raɗa mata wani abu a cikin kunnen ta, wanda basu bari naji ba,kawai dai naga Bintu ta ƙyalƙyale da dariya gami da rufe fuskarta alamun dai taji kunya a abinda ya faɗa mata,daga nan bacci suka koma ba tare da wata damuwa a zukatansu ba, A can ESTATE kuwa Taufiƙa ce take ta zuba haukanta, a sashen inno wai murnar zata auri wanda takeso zata cika burinta, Sayyid yana zaune yana kallonta bai ce mata komai ba,dan shi tunda yaji al'amuran da suka faru acikin gidan nasu ya saduda ga kuma ji nasabarsa da BINTU da Abdallah wanda shine ya kara kashe masa jiki,kuma yanzu ne ya tabbatar da cewa soyayyar da yayiwa Bintu ta jini ce, dan haƙikanin gaskiya bai taɓa jin ƙiyayyar Bintu da Abdallah ba komai ya faru ne sanadin huɗu bar sheɗan,dan haka yanzu ma kallon mahaukaciya yakewa Taufiƙa dan ya tabbatar da cewa Abdallah ba zai taɓa auren ta ba,zurata kawai su Alhaji Baba sukayi,to inno ma dai kusan kallon da takewa Taufiƙan ke nan dan ita dariya ma lamarin ya koma bata,ita kuwa Taufiƙa tsakaninta da Allah take sabon shiri, dan yanzu ta sake tana komai cikin walwala da farinciki,hatta su Farida sun haƙura tuni sun karɓi Bintu a matsayin ƴar uwar su kuma ƙanwarsu, dan idan ka gansu a tare bazaka yi tunanin sune mutanen nan da suka cusgunawa rayuwar Bintu ba,duk kan al'amuran da suka kafaru cikin ESTATE din ya zame musu izina,kowa ya dawo hankalinsa. Aunty Nafisa kuwa tana cikin wata iriyar rayuwa ta ganin ishara, dan tunda mahaifinta yaki karbarta,sai garin su ta koma can lafiya,wanda kuma ba wani arziƙi ne dasu ba kowa ta kansa yake,kuma lokacin da take dashi babu irin wulaƙancin da batayiwa danginta ba,shi yasa yanzu babu mai tausaya mata,idan ka dubeta baza ka ganeta farar ɗaya ba,abinda ta shuka shi take girbewa,ga dai kudin mahaifinta amma hakan bai sa taki ganin hukuncin Allah da sakamakon cutarwa ba,ita kanta tasan sakayyar Allah ce ke bin rayuwarta. A ɓangaren tawagar Dady Habib ma,dai zamu iya cewa gayyar ta watse dan dukkan su sai da su Abdallah suka tarwatsasu,suka ƙona gurin da suke shuka tsiyar shirkar tasu,daga haka dai kowa ya fece wasu an kama su wasu kuma tun daga nan suka sami taɓin hankali, Dady Habib ma kusan zan iya cewa ya zare,dan yanzu bashi da aiki sai surutai da fadin abinda ya aikata,kukan mutane kuwa har yanzu ya kasa rabuwa dashi wala a farke ko a bacci,(to wan Nan dai kadan ne daga ikon Ubangiji ita sakayya dama ba lallai sai anje can ba,tun a duniya Allah ya kan nuna sakamakon masu mugun hali dan ya zama izina garemu amma duk da haka sai mai rabo ne yake gane hakan Allah Ubangiji ya shiryemu kuma ya ganar damu tun da sauran numfashin mu Amin Ya Allah) Inno tana gama shirya kayan karin da za a kaiwa su Abdallah ta kira Yahya a waya,jim kadan ya shigo bayan ta amsa gaisuwar sa,tace"yauwa Yahya ga abincin ogan naka nan na kammala sai a miƙa masa!'ta ɗan dubi Taufiƙa da taci uban ado kamar me shirin zuwa gidan fati,tace"Taufiƙa ko zakuje ki kaiwa angon naki abincin kari?cikin rawar jiki ta mike tunda dama tsoran gwaliyar innon ne ya hanata tace"zataje,tace"me zai hana inno? ya dauko mu tafi!'duban Yahya inno tayi tace"kuje tare tunda kaine kasan gidan!'amsawa yayi cikin girmamawa kana ya kwashi kulolin da zai iya dauka,itama Taufiƙan ta dauki wasu bayan ta dauko yalolon mayafinta,da kallo inno ta bita, tana ganin fitar su tayi dariya, tare da cewa idan da rabon kin dawo da kukan jinine ai shike nan,dan nasan hawayen ruwa sunyi wa idanuwanki kaɗan idan kikayi tozali da zinaren masoyan da tauraron su ke haskawa,wataƙil hakan yasa kiyi haƙuri ki saduda ki karbi mijin da yazo a ƙaddararki!'Siddiƙa dake fitowa daga daki,itama cikin dariya tace"gaskiya dai inno kin iya shirya wasa nasan da biyu kika turata gidan ya Abdallah!'inno tace"yo idan ba ta kaici take shaƙa ba banga zata haƙura da Abdallah ba,idan ma ba wauta da hauka irin na Taufiƙa ba ya za ayi kizo kiyiwa yarinya kamar Bintu sharri kice ta amince ki auri mijinta,yo mu haukane ya sake mu da zamu bari hakan ta faru,ai duk da cewa hakan ba haramun bane,amma ai ana barin halas dan kunya,kuma Taufiƙa zata iya cutar da Bintu dan haka wannan abun ma tamkar kwado haka yake!'Siddiƙa tace"to amma inno me yasa kuka amsa mata kun yadda da aurenta da ya ABDALLAH,?inno tace"Siddiqa idan ba haka mukayi mata ba bazata bari ayi auren nan cikin kwanciyar hankali ba,amma kinga hakan da akayi mata ai mun samu saukin fitinarta,in yaso idan an daura auren da Sayyid ta ya galgala naman jikinsa faƙat, Siddiqa tayi dariya tana cewa ai inno Ni tuni na dawo daga rakiyar Taufiƙa dan naga abun nata nema yake yashiga tsakanin zumuncin mu da ƴan uwana,wanda Ni kuma a halin yanzu bana fatan haka, so nake mu haɗa kanmu mu zama tsintsiya madauri ɗaya!'cikin farin ciki da jin daɗi inno ta rungumo Siddiqa tana shi mata albarka tare da yiwa taufiƙa fatan shiriya da gane gaskiya. 💕 *KUDURAR ALLAH* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page 63 ``` Zumudi da rawar jiki ya hanata tayi tunanin abin da zata je ta iya tararwa,gaba ɗaya idanunta sun rufe, danunta da zuciyarta shi kawai take hangowa,bata hango mata cewa Abdallah baya sonta bai kuma taɓa sonta ba,san nan bazai taɓa sonta ba, A daidai lokacin ne kuma Bintu take ta faman zubawa Abdallah shagwaɓa da sangarta,tun da suka tashi a bacci sukayi wanka suka shirya tsaf tamkar wasu taurari,sai kuma ta dasa masa rigimar wai ita ciwo takeji ajikin ta,hakanne yasa shi fitowa da ita ƙasa suka baje a faffaɗan kushin ɗin da yayiwa falon ƙawanya,matsa mata jikin ta yakeyi a hankali cike da taka tsan tsan ɗin samuwar ciwo ko jin zafi ajikinta,sam taɓarar Bintu da san jikinta baya damunshi,saima alfahari da yake yi da hakan. Ɗan bude idanunta da suke lumshe tayi,tana kallon kyakykyawar fuskar shi,ɗage mata gira yayi,sai tayi saurin rufe idanun tana sakin wani sassanyan murmushi,can cikin kunnen ta ta fara jiyo sassanyan Muryar shi yana rera mata waƙa(a tsakanin mu Ni dake babu sabawa baƙon zuciyar ki Nine gani nan zaune, kyakykyawa kece kike rikitani na kasa ganewa, ashe kece kike kiɗima Ni ina ta dubawa, nai ƙoƙarin na gyara ganina amma na kasawa, guguwar son aciki na cake zuciyata saitawa)kallon da bata taɓa masa ba shi yanzu take masa,ji tayi kawai bakinta ya kama rera wata waƙa da take matukar so, tana yawan ji Rahima najin waƙar Sarina,(Bintu ta kace in dai da alƙawarii rabamu zai wuya indai a soyayya ne)gaba ɗaya suka saka dariya,kwanciya yayi a kusa da ita yana cewa my jewel yaushe kika iya rangaɗa waƙa haka?shimfiɗe kanta tayi a ƙirjinshi tana cewa kai yaushe ka iya?kai tsaye ya bata amsa da cewa,tun sanda na gano na faɗa komar ki!'murmushi tayi tare da da cewa Ya Abdallah ka goyani idan ba haka ba ciwon jikina ba zai warke ba!'saukowa yayi ya juya mata baya tare da cewa da zani kikeso ko haka?kafin ta bashi amsa sun ji knoc ɗin kofa,kasancewar inno ta shaida masa za akawo musu kayan kari sai hakan bai bashi mamaki ba dan yasan Yahya ne,yana tashi tabi shi,buɗe ƙofar yayi kafin yace komai sai ga murmushin Taufiƙa na haske mashi fuska,zakuyi mamakin yadda lokaci ƙanƙani fuskar Abdallah ta haɗe yawa hadarin da ya haɗo gangami,gaisuwar da Yahya yake masa ce ta ɗauke masa hankali har ta shige cikin falon tana wata tafiyar kwarkwasa, karɓar kulolin hannun Yahya yayi ya rufe ƙofar tare da nufar dinnin, anan ya samu amarya Taufiƙa yayin da Bintu ke ta faman bunshi kamar jela dan ko duban inda Taufiƙan take ba tayi ba,cikin sanyaya murya ta gaida shi,amma tamkar ba da shi take ba,saima hankalin shi da ya maida kan Bintu yana kallon rigimammiyar fuskarta da take a kwaɓe ƙiris ya rage ta fashe masa da kukan da baya buƙatar shi a ko da yaushe,zama yayi saman kujerar tare da janyo ta ya zaunar da ita saman cinyar shi, cikin san lallashin ta yace"me kuma ya faru my princess jewel?ɗan tura ƙaramin bakinta tayi tana kuma hararar gefan da Taufiƙan take a tsaye kamar zata haɗiyi zuciya da wulaƙancin da Abdallah yayi mata,gane abinda take nufi ne yasa shi miƙewa da ita a jikinsa yana cewa cikin miskilar muryarshi da ba yayi agaban Bintu,my wife,goyon kike buƙata ko abinci?girgiza kanta tayi tana murza idanunta irin yadda shagwaɓaɓɓun yara sukeyi,tace"Ni bancin abincin yanzu ka fara goyona!'da sauri ya durƙusa a saitin ta yayi mata alamar ta hau saman bayansa, cikin farin ciki da wata rigimammiyar dariya ta haye gadon bayanshi tare da zagaya duka hannayen ta ta cikinshi, Taufiƙa dai bata san sanda hawayen baƙin ciki sukafara saraftu akan fuskarta ba,sai kuma take taji sha'awa Ina ma itace akewa wannan soyayya,to ta yaya za ayi miki haka bayan ke kikeso bake ake so ba,zuciyarta tacigaba da bata shawara da cewa Taufiƙa kiyiwa kanki faɗa tabbas kika bari Abdallah ya aureki to hoto zaki zama a gurinsa hoton ma mara amfani,kije ki auri Sayyid tunda shine yake sonki,ki canja rayuwarki,tunda gashi kina kallon duk abinda Inno ta zaiyano akan zai faru da rayuwar Bintu shi kike gani yana faruwa tamkar wadda a kasanar da ita,bayan kuma ba haka bane kawai dai tayi mata fata ne na kasancewar zuciyar zinaren da Bintu take da ita, Taufiƙa kiyi haƙuri ki karɓi zabin da ya zamo naki tun kafin a haifeki, Maganar Bintu ce ta dawo da ita daga tunanin da ta lula,tace"Ya Abdallah sauke Ni haka ka gaji,zo muje muci girkin inno!'yadda ta faɗa ɗin haka yayi, sauke ta yayi tare da nufar kulolin a hankali ya fara savin ɗin su a plat ɗaya,sai kuma Bintu duk daji babu daɗi abinda sukayiwa Taufiƙa hakan ne yasa ta ɗan dubeta a sanyaye tace"Anty Taufiƙa bazaki zauna bane?jin haka da tayi daga bakin Bintu sai tayi saurin durƙusawa kasa tare da kama hannun Bintun cikin kuka wanda ke tafe da hawayen nadama tace"dan Allah ƴar uwata ki haƙuri ki gafarceni!"cike da mamakinta Bintu take dubanta,kama hannunta tayi suka miƙe janta tayi har zuwa falon kana suka zauna, cikin sanyin murya Bintu tace"Anty Taufiƙa shin wane irin tuba kikayi?cikin kukan Taufiƙa tace"wallahi wallahi wallahi kinji rantsuwa har uku ta musulmi,nayi tuban da bazan kara komawa ga aikata ko wane irin zanuɓi ba,Bintu rayuwarki ishara ce ga mutane masu san zuciya kuma abar koyi ce,ƙaddararki ƙaddara ce wadda take cike da darussan rayuwa ga mutumin da ya gane,dan haka na tuba na janye duk wani batuna zan auri Sayyid dan uwana tunda shi Allah ya zaba min matsayin abokin rayuwa!'cikin farin ciki Bintu tace"Alhamdulillah masha Allah Allah shine abun godiya,kana ta ɗan gyara zamanta tana cewa Anty Taufiƙa ki sani cewa duk wanda yayi imani cewa a kwai wuta kuma akwai aljanna dole ne ya kiyaye kansa daga fadawa daga halaka ta sharrin shaidan wanda zata kasance masa azaba a gurin ubangiji,muna aikata kuskure mai girma a cikin rayuwar mu wanda sam hakan bai kamata ba,duk wanda ya dauki burin duniya ya saka a ransa to kuwa tabbas yayi ƙawance da shaidan,domin shi shaidan babu abinda yake so irin yaga ana aikata saɓo,manzan Allah s.w.a ya tambayi shaidan cewa shin mai yake sawa ƙashin bayansa ya karye? sai yace,yaga ana tuba dan komawa turbar gaskiya, San nan a kwai lokacin da mala'ika jibrilu yazo yana bawa Annabi a,w,a labarin jahannama har yazo kan ƙofar wuta ta bakwai,irin azabobin da Annabi yaji za ayiwa waɗan da suka kasance a cikin wannan ƙofa sai da ya suma,bayan ya farfaɗone yake cewa da maka'ika jibrelu dama akwai wata al umma ta da zasu shiga cikin wuta? shin zaka bani labairin waɗan da zasu shiga cikin wan nan ƙofa?sai mala'ika jibrelu yace"masu manyan zunubai ne wadan da suka koma ga ubangiji basu tuba ba sune zasu shiga wannan kofar wutar!'wa iya zubilla alla ka kiyashemu da ita,dan haka duk wanda ya tuba daga wani aiki na saɓo da yake aikatawa ba ƙaramin rabone dashi ba,kin ga yanzu ke kin dace muna fatan dacewa har acan ƙiyama!'cak taji an ɗaga ta sama,ƙamshinsa da taji ne ya kuma tabbatar mata da cewa shine,duk da tasan shine kadai zai iya yi mata haka, yace"princess mun gode da wannan ta ƙaitaccen wa"azin haɗe da tunatarwa Allah yasaka da Alkhairi ya bamu dacewa da kuma babban rabo na Alkhairi,yanzu muje ki karya ki bar amaryar Sayyid itama taje gida ta fara shirin sabuwar rayuwa mai cike da daɗi da sirrika da kuma ɗumbin lada gurin Ubangiji!'sai kuma Taufiƙa taji duk tana jin kunyar Abdallah dan haka ta miƙe cikin sanyin jikin da kalaman Bintu suka ƙara saukar mata, cikin nutsuwar da da bata da ita, ta ce dan Allah ya Abdallah ka yi hakuri ina fata zaka dinga kallona kamar Rahima dasu Shakur!'jinjina kanshi yayi cikin jin dan tausayin Taufiƙan yace"kar ki damu Allah ya kaimu ya kuma yafe mana baki ɗaya!'suka amsa ita da Bintu daga nan ta fita daga falon Bintu ta ɗan daga murya tana cewa sai munzo shan biki dan nima ban yafe nawa ba sai anyi mun!'tana dariya a hanyar ta ta ƙarasa fita tace"ai ke angama da babinki tunda komai yayi daidai,shine ƙarshen maganarta da ta faɗa ta kai waje, Zaunar da ita yayi kan cinyar sa ya fara bata abincin,ganin kamar bata son ci,sai kawai ya shiga ɗurawa abakin shi sai ya tauna sai ya ɗura mata,tamkar dai cin abincin tsuntsaye,(wai ko Ni nan Fatima ƴar uwar Bintu ban taba tunanin Abdallah ya iya irin wannan salon soyayyar mai kashe gaɓɓai ba sai yau)a haka suka gama daga nan kuma ya sunkuceta suka koma daki, Inno tayi matuƙar mamaki da yadda taga yanayin taufiƙa,ta shigo cikin fara a da walwala,dan haƙiƙa ita kanta tafi jin sakewa da rashin nauyin zuciya a yanzu da ta sauke nauyin damuwarta ta kuma nemi gafarar Bintu,zama tayi gefan inno da take Binta da kallon mamaki,cikin sanyin murya ta gayawa inno abinda ya faru da kuma hirarasu da Bintu ta ɗora da cewa inno dan Allah kema ina neman yafiyarki san nan zanje na gayawa Alhaji Baba da kaina cewa na haƙura da auren Ya Abdallah a ɗaura da Sayyid ɗin!'inno ɗaga hannunta sama tayi tace"Allah na gode maka da wannan hasken Alkhairin da yake ta shigowa zuriyar mu,duk a sanadin su Bintu wan Nan shi ake kira da ɗan Hakin da ka raina, Allah yayi muku albarka ya baku zuri'a mai albarka ya kuma ciga ba da nuna mana hanya mai kyau, ya bamu ikon binsa cikin tafarkin musulunci,Amin Taufiƙa ta amsa zuciyarta fes babu sauran damuwa. A cikin wannan kwanakin ne ake ta shirye shiryen auren jikokin Alhaji Baba,yayin da su Bintu suna can suna shan soyayya duk da dai har lokacin Abdallah bai kuma neman wani abu a gurin ta ba,saboda so da tausayi,ita kuwa sai zuba sangarta da taɓara takeyi, amma fa Abdallah yana da burin maida Bintu makaranta,in Sha Allah,babu abinda yafi burge shi a gurin Bintu sai irin tsananin ibada da miƙa lamura ga Allah duk abinda zatayi sai ta saka Ubangiji a ciki, komai zata aiwatar sai kaji tana addu'a ko tasbihi da ya riga ya zauna abakinta,to dake shima Abdallah ba baya bane sai suka haɗu suke raya rayuwarsu da yawan ibadu ga sadaka da taimako,wan nan duk halinsu ne wanda suka koya daga gurin iyayensu, Yau ake ɗaura auren su Taufiƙa da su Hauwa'u,abin yayi amarshi sosai,kaf iyalan Alhaji Baba babu wanda babu,a ranar da yamma akayi ƙayatacciyar walima,Amare sunyi kyau har ba a magana, Bintu tamkar ka saceta ka gudu fans din ƙudurar Allah kuwa kamar kiyashi haka suka cika babban holl ɗin ESTATE duk wanda ka kalla bakinta har kunne sunci atamfarsu mai zaiba sai wawar kajin walima suke su maman hamra da su Ummu banat kai harda su saudee iyayen rawar ƙafa,su Maryam cika ga su fati nan duk anci gayu an ƙafe aguri ɗaya ana muzurai,gasu nan dai da yawa mutanen idan nace zan lissafo su abun zai ci lokaci, Allah sarki yayata maman nuur tana wajen su Ummi Laila ana shirin kai Amare da ita,kai abu dai yayi kyau haka taro ya watse lafiya,daga nan kuma su Alhaji Baba suka wuce gidan su Anty Samira a ƙa ɗauro aurenta da Dady jafar,Ni kaina bazata akayi min wannan abu baƙaramin daɗi yayi ba, Abdallah zan iya cewa yafi kowa farinci,ikon Allah ya wuce da haka to mu dai sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya ya kawo ƙasantar dakuna, Tsit kake jin estate din tayi,kowa yana ɓangaren sa ga kuma ƙaruwar Amare da aka samu duk da cewa suna da tazara sosai tsakanin su da iyayen nasu, haka tsakanin su da juna ma a kwai tazara me yawa,dan haka za kayi tsammanin kowa a guri daban yake,tamkar yadda a kayiwa kowacce amarya itama Bintu haka akayi mata basuyi duba da cewa ita ta daɗe da aureba,zaune take bakin haɗaɗɗan gadonta da yasha shimfiɗu na alfarma kai kace gadon sarautane,sallama yayi tare da shigowa ɗakin fuskarsa tamkar wata ɗan daren goma sha huɗu,kana kallon sa kasan cewa yana cikin farinciki mara misaltuwa,takowa yayi cikin nutsatstsan takunsa mai cike da iko kamar wani saraki,zama yayi a gefan ta tare da dage mayafin lafayar da aka yane dukan fuskarta,cikin taushin muryarsa yace"Alhamdulillah!'kana ya sunkuyo da fuskarshi daidai saitin tata,yana binta da wani narkakken kallo mai cike da shauki,cikin sanyi da lallaɓa ya janyota cikin jikinshi yana sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya,tallafeta yayi gaba ɗaya cikin jikinshi yana bin ko ina na jikinta da sunsuna,shigewa jikinshi ta kuma yi tana matsarshi saboda yanayin da take tsintar kanta aciki aduk lokacin da ya kusanto jikinta,ɗago kanta yayi mata ana bin lumsassun idanunta da eye lashes ya kwanta yayi zara zara,har shensa ya kai saman idanun ya shiga lasa tamkar ya samu alewa,wani irin numfashi taja tamkar wadda zata shiɗe,bata gama da wannan yanayin ba,ta tsinci bakinshi cikin nata,yana yi masa wani irin tsotsa tamkar wanda yake shirin tsinke harshen gaba ɗaya,sai ga Bintu na tallafar ƙeyar Abdallah domin taimakawa bakunansu wajen daɗa kusantar juna,a hankali ya shiga ware lafayar jikinta yanayi yana scuizin ɗin jikinta da tafukan hannunshi,saida ya warwareta gaba ɗaya kana ya buɗe idanunshi da suke lunshe tare da zare bakinshi daga nata,kallon shigarta data ɗimauta shi yake,wata fitinanniyar rigar bacci ce wadda akayi mata ado da bakin less baƙa kuma iya kacinta cinya,abunka da fara sai ga Bintu na walwali cikin rigar,wanda take Abdallah ya kuma rikicewa tsumammiyar ƙaunar ta ce takuma tashi tare da shawa awa da ɗokin kasancewa da ita,yana kwadayin kara zuwa wannan burnin na fadama,yana son ƙara zuwa gurin nan da tunda ya shige shi har yau daɗinsa bai bar cikin ƙwaƙwalwa da gangar jikin shi ba,duk da cewa bai je ko ina ba, bai kuma kai inda ya kamata ace ya kaiba,amma dai a yau yana fatan zuwa ƙoramar Bintu mai wuyar mantawa, cikin kunnenta ya shiga raɗa mata wasu kalamai wadanda suke neman zautar da tunaninta kalaman da bata taɓa tunanin zata jisu daga gwarzon maza irin Abdallah ba,kalaman da bata taba sanin cewa Abdallah zai iya fadawa wata mace su ba,lallai ta taki sa a ta zama mace mai sa a arayuwarta,da abun yayi mata yawa kawai sai ta yi masa wata irin runguma da ita kanta bata san taya tayi hakan ba ji take yi kamar ta maida shi cikin zuciyarta kowa ya huta,tana sonsa tana kishinsa tana kuma mararinsa, Da ƙyar suka iya control ɗin kansu,ya tashi ya zare kayan shi,daukarta yayi cak sukayi toilet,wan Nan wanka kam ya ajiye wa rayuwarsu tarihi domin kuwa sun wanzar da wata irin ƙauna mai tsayawa azuci,tun Bintu na kunya da sunkui da kai har dai ta bada kai bori ya hau, Abdallah yayi mata cuɗin kauna itama haka ta dage ta murje masa jikinshi da tausasan tafikan hannun ta,daga nan suka ɗauro alwala suka fito,sallah suka fara gabatar wa sukayi karatu kamar yadda suka fara sabarwa kansu, Tana ganin fitarshi tayi saurin tashi ta goga turaren da Inno ta bata na humra,kana Takoma kan gadon tayi luf tamkar mai bacci,A hankali ya ƙaraso bakin gadon yana magana cikin nutsuwa,yace"my ukty ba dai bacci kikayi ba?a hankali ta ɗan buɗe idanunta tayi masa alamun irin ta fara baccin nan,ya durƙuso kanta yana cewa tashi kici wani abu kinji ukty!'ɗan tura baki tayi hade da janyo hannun shi ta rungume a ƙirjinta,tana cewa Ni dai bacci zanyi ya Akiyy!'lumshe ldanunshi yayi saboda saukar da hannunshi yayi akan na shanunta, cikin san fita daga hayyaci yace"umm ummm ki tashi kici wani abu karki min musu kinji ukty,tashi tayi zaune amma bata sauka akan gadon ba,hakan da tayi ne yasa ya ɗauko plat din da ya shigo dashi ya hauro kan gadon yana cewa, kinga irin naman da kikeso ne zakiji dadinshi!'ba tace komai ba ta fara karbar wanda yake kaiwa bakinta,tana taunawa sai ta fito dashi akan harshenta tana tura masa,a hankali ya kai bakinsa kan harshen ta ita kuma sai ta tura masa naman da ta tauna,da wan Nan salon kaunar suka gama cin naman ya bata tatatacciyar madarar shanu tasha,daga nan suka sake yin brush, Fitar da yayi ta sakanni kafin ya dawo har tayi bacci,a hankali ya hauro saman gadon kamar wanda yake tsoran tayar da ita,kashe fitilar dakin yayi kana ya kwanta ajikin ta,kanshi ya ɗora saman ƙirjinta,kana ya shiga yawo da hannunshi cikin jikinta,jin kamar anayi mata tafiyar tsutsa ne yasa ta ɗan buɗe idanunta kaɗan duk da dai dama baccin baiyi mata nisa ba,sai dai batayi motsin da zaisa ya gane idanun ta biyu ba,zame ƴar karamar rigar jikinta yayi tare da ɗora fuskarshi da hannunshi saman na shanunta, wanda hakan yasa ta motsawa ba tare da ta shirya ba,dama abinda yake buƙata kenan dan haka ya kai bakin shi kan na shanunta,wani irin zullo Bintu tayi tare da bankaro ƙirjinta tana wani irin shan yaji,kamar zata shiɗe,lokaci ɗaya Abdallah ya burkita mata lissafi da salon soyayyar sa mai tsayawa a rai,a hankali yake bin jikinta yana mata wani irin lasa yana tsotse duk inda yaci karo dashi ajikinta,cikin yanayin da ya gama saka ta aciki ta fara maida masa martanin salon da yake koyar da ita,wanda a take anan taso zautar da tunanin sa akan abinda shi ya koya mata, cikin nutsuwa ya nufi hanyar da yake ta ɗokin zuwa bayan ya gama rikita lissafin ta da ƙauna mara algus, wanda har bata san ya kai ga wajen da take ta kaffa kaffa dashi ba,runtse idanunta tayi yayin da taji Abdallah ya ratsata ratsin da baiyi mata shi a wan can ranar ba,kuka ta farayi a hankali tana son tureshi ɗaga jikinta,cikin wata irin murya can kasan maƙoshin sa yace"my ukty kiyi haƙuri ki barni daga yau bazaki kuma jin zafi ba,kar kiyi min shamaki da wannan jin daɗin da bazan sameshi a jikin kowa ba saike,karki hanani zuwa garin daɗin da nake mafarkin zuwa tun ranar dana fara ɗan ɗanashi,ya faɗa yana jan wata irin shaahsheƙa kamar wanda yake shirin shiɗewa, cikin rawar murya tace"na bari my Akey,na bari amma kar kabari naji zafi,kar kayi min da zafi,kar ka bari naji ciwo,kaji my hubby!'ta ƙarasa faɗa tana tallofo kanshi tare da shafa kyakykyawan sajenshi da yake matukar burgeta,haɗe bakinshi yayi da nata yana mai shigewa jikinta a hankali dan kar taji zafi,duk da cewa Bintu taji zafin sosai sai dai tayi matuƙar dauriya dan Abdallah yayi tattalinta ya kuma nuna mata tsantsar ƙauna wadda babu surki a cikinta, Bai bari sun kwanta da najasa ba,sai da ya dauketa sukayi wanka tas, kana ya dawo suka koma bacci mai daɗi,wanda yake cike da mafarkai masu dadi da Alkhairi. A ɓangaren su Sayyid da Taufiƙa ma an samu zaman lafiya, dan Taufiƙa da gaske ta saduda tayi nadama,hakanne yasa ta karɓi mijinta suka raya daren da soyayyar da basu san suna yiwa junansu ita ba, Haka a bangaren Dady jafar ya samu Anty Samira yadda yake so matarsa ta kasance,dan haka sun fara ƙoƙarin shimfida kyakykyawar rayuwa me cike da amana da fahimtar juna. 💕ƘUDURAR ALLAH💕 NA FATIMA Y ADAM PG 64 AND 65 Momy Abigirl dai taga ishara dan daga yawan bara a can garinsu a ka markaɗe mata ƙafa,yanzu haka tana nan tana fama da ƙafa daya wadda aka rasa yadda za ayi ma a sai mata maganin da zai dinga rage mata raɗaɗi,to dai ga yadda karshen masu zalunci ya kasance. Anty Nafisa ma dai ba acewa komai dan rayuwarta abar tausayi ta zama ga wanda bai san tsiyar da ta shuka ba,da ƙyar ta samu aka shawo kan mahaifinta yace ya hakura amma ba dan ya haƙora ta dawo masa gida ba,yace sai dai idan zata fidda miji yayiata aure amma bazatazauna masa a gida ba,dole uwar naƙi ta hakura ta kawo wani musakin bazawarinta da shi kaɗai ne me dan dama cikin zawarawan nata,matansa uku,ita ta zama ta hudu,gashi ba wani dukiya gareshi ba sai dai ɗan rufin asirin sawa ana bakin salati,haka nan ta haƙora ta zauna acikin ƙazaman matansa,idan ta zauna tana tuna baya sai tayi ta kuka,gashi nan akan kishiya guda ɗaya ta biyewa san zuciyarta har ta kasance yau itace da kishiyoyi uku,garin san dukiya ta biyewa shaidan yau itace a gidan da ko ƙofa mai kyau babu bare kuma a kai ga gyata gyatai,ai dama Nafisa duk wanda ya daka ta kaɗan sheɗan to tabbas zai kaishi ga ramin danasani, Dady Mansur sunje sun fito da Dady Habib,sai dai kuma labari ana cikin wani hali na rashin lafiya da kuma haukan da ta soma ta azzara a gurinshi, Alhaji Baba kuka yayi da idanun shi saboda tausayin halin da Habib yake ciki haka sauran ƴan uwan shi babu wanda bai tausaya masa ba,ganin halin da yake ciki ne yasa sukayi tunanin kaishi gidan mahaukata dan abashi kulawa ta musamman, Sa dai kuma kash laifin shirka da haƙƙin ɗan adam su suka hana Dady Habib samun nutsuwa duk da cewa kulawa ake bashi sosai,amma a banza saboda akwai haƙƙin mutanen da bai nemi gafarar su ba,a kwana na biyu ne bayan uwar wahalar da ya sha duk yajiwa kanshi ciwo hatta da kunnen shi zubar jini yake saboda abubuwan da yake ji cikinsu,daga ƙarshe dai yace ga garinku nan, Allahu Akbar, tabbas duk wanda baiyi ƙoƙarin gyara rayuwarshi ba yana tare da yin mutuwar wulaƙanci ga dai yadda rayuwar Dady Habib ta kasance nan,duk abinda ya tara ya tafi ya barsu,kuma yaje ya tarar da ubangiji sai yayi bayanin yadda akayi ya tarasu,gashi kuma bai moresu ba,saboda tsoro da gudun tonuwar asirin sa,to Allah ya shiryi bayin sa waɗan da suke da rabon shiryuwa. Da ƙyar da sidin gishi da lallami da naci da ƴaƴan Hajja su dasu inno da Hajiya Babba suka saka Alhaji Baba ya sauko daga kujerar nakin da ya hau,ya hakura ya dan sake da ita amma dai ƙimarta ta riga ta zube a idanunsa da kuma kishiyoyinta kai harma da ƴaƴan cikinta,ga dai abin da take gudu nan ya faru zubewa kuma da mutunci, Allah ya ganar damu gaskiya ya rabbil alamin, Katsam kuma sai ga kira daga Alhaji Baba,ba kowa yakewa kiran ba sai Amare da angwayen jikokin sa da ya aurar,nan yake sanar dasu cewa bizar su ta fito na tafiya Saudiya,sunyi murna sosai kuma sunyi godiya,haka suka tattara suka fara shirin keta birnin Madina, Tafe yake yana waya akan hanyar su ta dawowa daga ɓangaren Alhaji Baba,sai dai kuma hankalinshi na kan ƴar lelanshi ta gaban goshi wato Bintu, cikin tura baki tace"Allah Ni dai kam ka daina kallona sai kaje ka fadi!'dan murmushin gefan baki yayi kana ya kuma maƙale hannun ta cikin nashi,sauke wayar yayi daga kunnen shi yana cewa idan ina tare da ke banaso idanuna su dauke daga kallon baby face ɗin ki!'ya faɗa yana dage mata gira,rufe fuskar ta tayi tana dariyar ta mai kyau,wash ya Akey na gaji ka goyeni!'tsugunawa yayi a gabanta ita kuma ta haye gadon bayanshi tana ƙyalƙyala dariya,a Hankali yake takawa,sai da suka shiga katon falonsu wanda yake cike da kayan ado marasa yawa sai ƙamshi yake zabgawa saboda ya gamu da masu tsafta,sauketa yayi yana ɗan rike bayanshi,alamar dai ya gaji,zuwa tayi ta zagaya hannunta ta bayanshi tare da kwantar da kanta akan tsakiyar gadon bayan shi, tace"wai ka gaji ne my hubb? bani da nauyi fa!'juyowa yayi ta koma Cikin ƙirjinshi yayin da yasa hannunshi da jikinshi gaba ɗaya yayi mata mamaya, kana yace"wannan goyan fa sai an bani tukyicin sa!'ya faɗa yana yi mata raɗa cikin kunnenta,take ta shiga buga ƙafar ta aƙasa cikin sangarta da salon shagwaɓarta dake matuƙar burge Abdallah da sakashi cikin wani yanayi, take cewa Allah Ni dai naƙi wayon me yasa baka faɗa ba kafin ka goyani?ban fa warke ba jikina yana ciwo!' cikin nutsatstsiyar dariyarshi yace"haba my Bint wan Nan karon babu zafi sai daɗi!'ya faɗa yana kashe mata ido daya,kuma tura kanta tayi cikin ƙirjinshi saboda kunyar daya bata,ɗaukar ta yayi cak suka nufi bedroom ɗinsu dan raya sunnar Manzo s,w,a. Yau dai jirgin su Abdallah da sauran ƙannenshi ya tashi tare da rakiyar iyayensu da abokan arziƙi,tunda suka je Madina babu abinda suke sai bautar ubangiji,a cikin kwana goma sha biyar da sukayi a garin na Manzo s.w.a ba ƙaramin nutsuwar zuciya suka samu ba,gashi su Bintu kansu ya haɗe kula suke da junan su basa so ko kusa da a taɓa daya daga cikin su saboda tsananin zumuncin da suka riƙe,ga mazajensu da suke tattalinsu da kaffa kaffa dasu,dukaninsu suna cikin farin ciki da walwala,daga nan kuma kowa ya nufi ƙasar da ya zaɓa A matsayin cin amarci,shi Abdallah dake yana da wani bincike akan wani criminal da ya gudo daga can naija,ya dawo nan kasar Siriya,dan haka kawai sai suka wuce can da niyar Bintu zatayi karatun wucin gadi anan kafin su koma,hakan kuwa ba ƙaramin farinciki ya saka Bintu ba, dan haka ta nunawa Abdallah sha awarta na koyon nau ikan girkuna, saboda ko ta koma naija abinda zata karanta ke nan,yayi na am da buƙatar ta dan haka sukayi ban kwana da ƴan uwansu kowa ya nufi inda yafi wayo, Rayuwar Abdallah da Bintu, rayuwa ce da kai tsaye zamu kirata da rayuwar farinciki da fahimtar juna,komai yayi farko haka yana da ƙarshe,Bintu bata taɓa tunanin zata kai irin wannan matsayin ba a rayuwarta, to amma dake abun ƙudurace ta Allah sai gata a inda batayi zato ko tsammani ba,ta fara karatunta na catering cikin nasara,shima Abdallah a gefe ɗaya yana gudanar da aiyukan sa wanda yake saka ran San n nasara insha Allah... Bayan wata biyar,sai ga ciki ya baiyana a jikin Ummi Laila,waiyo zakuso kuga farincikin ABBA Umar,abin dai ba a cewa komai, Allah ya nufa Laila da Umar ɗan su yafi ɗaya a duniya,sai kuma wani abin al'ajabin, ko da yake kaɗan daga ƙudurar Allah ke nan,sai ga Anty Samira ma da cikin Dady jafar, Allahu Akbar bayan cire rai da samun wannan kyauta tsawon shekaru sai gashi Allah ya nuna masa ikonsa da buwayarsa,lallai bawa kar ya taba cire tsammani da rahamar Ubangiji, A hankali kuma sai ciki yay ta ɓullowa jikin jikokin Alhaji Baba,su Taufiƙa su Farida Hauwa'u, Rahima, kai abun dai masha Allah sai fatan duk Allah ya sauke su lafiya. Lokacin da Bintu taji labarin cikin da ummin ta take dashi sai da tayi kuka tayi suddar shukurr,sai kuma na ƴan uwanta wanda hakan yasa ta farinciki da kuma jin kwadayin samun ciki, ,fafy ne yake faɗa mata lokacin da suke waya,ya kuma sanar da ita an saka ranar usainar sa,daɗi kan daɗi ke nan,ganin tana ƙoƙarin fasa masa dodon kunne kawai sai ya kashe wayar yana dariya,wato dan bata san shima ya kusa zama Baba akaro na biyu bane, da ji zatayi kamar tayi tsuntsuwa, kawai ta taho naija, Abdallah yana dawowa da zan cen da ta fara tararshi ke nan,sai da ta gama faɗa mashi kuma wai sai ta saka masa kuka itama sai yayi mata ciki tunda su Taufiƙa ma suna dashi, bayan kuma ta riga su yin aure amma suka zo suka rigata,a kullum wautar Bintu mamaki da dariya take bashi amma kuma da yayi wani tunani sai yaga ai shi gaba ta kaishi,dan haka sai ya matseta cikin jikinshi yana cewa yi shuru my ukty ciki kike so ba?ta daga kanta kamar wata ƙaramar yarinya,yace"to maza share hawayenki insha Allah yau zan miki ciki,bazan ƙyaleki ba har sai na tabbatar da cewa na dasa ƙwaina a nan!'ya faɗa yana shafa kan mararta,dariya tayi cike da farin ciki tana da ɗa rungumo shi jikita tace"yauwa my zauji!' Allah mai ƙudura da irada gagara iko gagara misali,sai ga shi maganar Abdallah ta tabbata dan kuwa tsakanin ranar da yau da ta zagayo wata ɗaya cif, Abdallah ya tabbatar da cewa ya dasa ɗan sa ko ƴarsa a marar Bintu,shuru yayi dan yana so sai ya tabbatar da hakan,yau tunda ta dawo daga makaranta take kwance ta kasa tashi ko da abinci taci,dan ma gurinta tsaf yake kamar babu halittar dake motsi acikin gidan,saboda tsananin tsaftarshi da ƙamshin da yake tashi,a gurin,a haka ya shigo ya same ta kamar ruwa,cikin sauri ya ɗauke ta yana dubata kamar wanda akace masa wani abu ya sameta,yace"my Bint meke damunki?langaɓar da kanta tayi akafadarshi tana cusa kanta a wuyanshi,ba tare da ta bashi amsar tambayara shi ba, tace"wayyo my zauji, inason wan nan ƙamshin naka dan Allah kabarni in kwana ina shakarshi!'ba tare da yace"mata komai ba ya ɗaga ta suka nufi bedroom kana yace"anya my zaujaty babu ajiyata acikin nan naki? bari dai na bin cike ki sai hankalina yafi kwanciya!"zaro manyan idanunta tayi tace"amma dai ba allura zaka mun ba ko? yace"haba my jewel ya kamata ace kin daina tsoran allura tunda kinga fa kin kusa girma!'bata gane abinda yake nufi ba dan haka sai tayi rau-rau kamar zatayi kuka,cikin sauri yace"nifa bance zanyi miki allura ba,duba ki kawai zanyi!'hakan da yafaɗa sai ta hakura yayi mata duk wani binciken da yakamata,bata ankara ba sai ji tayi yana juyi da ita a tsakar dakin tare da bin ko inan ta da wani zazzafan kiss,wanda har sai da ya ruɗa ya sauya mata yanayinta abinka da dama wadda take kusa saboda cikin da ke jikinta yana ɗan sata jin bukatar mijinta,ai kuwa dai biye masa tayi suka jika junansu da ƙauna mai tsayawa a zuciya da ruhi,bayan sun sami nutsuwa ne ya mamayeta da dukkan jikinsa yayi mata rumfa da faffaɗan ƙirjinsa, kana cikin so da kulawa yace"my ukty sai ki shirya dan kin kusa zama Ummu nan da wata takwas!' ya faɗa yana yi mata nuni da yatsunsa,ganin kamar bata fahimceshi ba sai ya kama kunnen ta yayi mata raɗa dariya ta saka tare da ƙanƙame shi tana mai jin farin ciki na mamaye duka nin ruhinta. Wata sabuwar kulawa da soyayya Abdallah ke bawa Bintu yayin da duk gida ya ɗauka kowa murna da farin cikin ƙaruwar da suka samu yake,burin Alhaji Baba ya cika zuri'arsa ta kasance cikin walwala da jin daɗi, Abdallah ya samu nasarar aikin da yaje yi, acikin wata takwas dan haka ya zauna Bintu ta ƙarasa karatunta kafin nan suka jiyo gida naija, Taufiƙa ce ta fara sauka ta haifi dan ta namiji sai Rahima, daga nan kuma sai Ummi Laila,kamar layi abin sai ya zama abun burgewa saboda yadda suke ta haihuwa ajere,Anty Asma'u ma ta haifi ɗanta namiji,sai Anty Samira da ta haifi namiji itama,Bintu dai itace karshe dan da akwai tazara tsakanin su, Alhamdulillah masha Allah bayan wata uku Bintu ta san kato yarinyar ta mai kama da Abdallah da Ammi,bazan iya fada muku irin farin cikin kin da bayin Allah nan suka shiga ba, sai dai kawai mutaya su da addu'a,an sakawa yariyar suna yusra, Bayan daidai tuwar al'amurane,Alhaji Baba ya Tara dukkan alhalin sa,ya sanar da su cewa duk ana so su bada shawara, mai kyau akan diamon ɗin,yace"na zauna nayi dogon nazari akan al'amarin diamon ɗin na kuma na gano cewa cigaba da zamansa acikin zuri a ta ba karamar fitina bace"dan haka nake neman shawarar ku akan yadda za'ayi,amma kuma Ina so ku tuna cewa diamon ɗin nan ba mallakina ne Ni kaɗai ba,nida Abubakar ne dan haka inajiran shawarwarinku!'Baffa Hashir ne ya ɗanyi gyaran murya tare da ƙara daidaita zaman sa,kana yace"Ni dai aganina tunda abun ya zama haka me zai hana a kira masana sirrin diamon ɗin a sirran ce su siya tunda kai kasan kan harkar in yaso sai ku kasa kuɗin gida biyu kowa abashi haƙƙinsa!'alhaji Baba yace"wannan shawarar tayi ko da wani mai magana ya tambaya yana bin ƴaƴan sa da matansa da kallo,kowa dai ya yi na AM da shawarar da Baffa Hashir ya kawo,bayan Alhaji Baba ya tabbatar da gamsuwar su,sai ya dora da cewa,to Ni kuma insha Allahu idan An bani kasona zan rabawa iyalina duka!'Dady Abubakar yace"Alhaji Baba ni idan anbani me zanyi da ita?dan haka na bar maka ka haɗa duka ka rabawa zuri'ar ka!'gaba ɗaya falon yayi tsit ana jiran jin ta bakin Alhaji Baba,cikin nuna daddako yace"a'a Habu baza ayi haka ba ai kaima kana da magada, ga matarka ga ƴaƴan ka har da mahaifiyar ka dan haka baza a shiga haƙƙin su ba!'cikin sauri Hajiya zulaihat tace"wallahi Alhaji na yafe dani da yara na baki daya har ga Allah!'cikin tabbatar da hakan su Abdallah suka jinjina kai, dan haka sai ya juya gurin Hajiya Babba dan fitar da nata haƙƙin,kafin yace"komai ta rigashi da cewa haba Alhaji yanzu dan Abubakar yayi maka kyauta sai na amince zaka karɓa? bayan ina da tabbacin cewa bakai zakayi amfani da ita ba,kuma Hausawa suna cewa da kai da kaya duka mallakar wuya ne!'murmushi yayi cike da farin ciki,kana yace"za araba kudin da aka sayi diamon ɗin nan gida uku,kashi ɗaya za akai gidan marayu,kashi daya zamu gina asibitoci da masallatai da kuma makarantu, ɗaya kuma zan kasaftawa dukan ahlina ban cire kowa ba har surukai!'gaba ɗaya falon suka dau kabbara,a hankali ya kuma maida duban sa kan Dady Abubakar tare da cewa habu a ina wan nan diamon ɗin yake?so nake ka faɗa da bakinka kamar yadda akaso ka faɗa ɗin!'Hajja ji tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige dan tasan bakar magana Alhaji Baba ya yaba mata,Dady Abubakar cikin bin umarnin mahaifinsa ya ɗanyi gyaran murya tare da cewa a bayan ɗakin Hajja muka binne shi Ni da kai kuma har rana irin ta yau yana gurin,kuma a yau da izinin Allah na tanoshi!'ya faɗa tare da ɗauko diamon ɗin ya nunawa dukan al'ummar dake zaune a gurin Hajja kuwa kamar ta nitse dan har gobe bata daina nadama da danasanin abin da ta aikata ba, tabbas ko yanzu Allah ya kuma nuna mata ishara ashe duk wahalar da ake kan diamon ɗin yana cikin wannan estate din kuma abayan ɗakinta,gaba ɗaya falon ya dauki kabbara saboda imanin da ya kuma shigar su,idan ba Allah me ƙudura da irada ba waye zai yi haka,(gashi dai duk sun gama bulayi da daukar zunubi kuma ƙarshe abin ya dawo wajen su su zasu amfane da dukiyar,Hakika hakuri shi yake tadda rabo,kuma duk abinda haƙuri bai baka ba,tsiya bazata taɓa baka shi ba, Allah ya kiyaye mu da aikata mummunan aiki, Allah ya bamu ikon tuba tun bamu rasa damar tuba ba Amin) addu'oi sukayi kana daga nan suka watse kowa jikinsa a sanyaye. To alƙawari dai ya cika duk abinda suka shirya akan diamon Allah ya basu ikon gabatarwa, Alhaji Baba ya cika alƙawarin da yayiwa iyalansa,dan kowa sai da ya tashi da kusan miliyan biyar biyar,to Allah dai ka bamu dukiya mai amfani. BAYAN SHEKARA HUƊU,,, Abdallah ya cikawa Bintu burinta dan kuwa ya bude mata dan kareta gidan abinci wanda suka zuba masa manyan ma'aikata. Bintu ce zaune a cikin gadin ɗin da yake mamaye da korayen ciyayi da fulawowi, rubuce-rubuce take tayi tana lissafin kayan da za ayi mata order na restorent ɗin ta wanda a yanzu ya zama guda uku saboda nasara da cigaban da aka samu a kasuwancin abincin,Bintu bata zuwa ko ina ta ɗora mutane masu amana wadanda suka karanci abun,wasu daga danginta ne na ɓangaren ummin ta,wasu ƴaƴan ƴan uwa ne aka tallafa musu,shi yasa kullum har kokinsu suke ci gaba ita da jigon ta uban ƴaƴan ta wato Abdallah Abubakar Balarabe,A,A,B ke nan,duƙufar da tayi ne har bata san sanda yusra ta zo gurin ba, Sai dai tashin rigimar ta da taji,ɗago kanta tayi cike da gajiya tace"o my yus Ina abbun naki kika taho nan ki dameni bayan guduwa nayi saboda ku!'kin gudu baki tsira ba ke nan!'abdallah ya faɗa yana takowa inda take,ɗan tura bakinta tayi kana tace"kai ya Akey ku ɗan barni mana na kusa gamawa fa!'zuwa yayi ta bayanta ya zagayo da hannayen sa kan cikinta yana shafawa a hankali,yusra kuwa ture takaddun da suke kan cinyar ummin ta tayi ta haye cinyar tana cewa, Ni ci kaini gidan cu fadil jamuyi washa!'dan matsa bakinta Bintu tayi, tana cewa aike ce washan, baga Abbunki nan ba sai ya kaiki!'lumshe idanunta tayi jin tafiyar tsutsar da yake mata kan cikinta,yace"hi my princess zuwa mukayi mu ganki sai mu koma,amma kiyi haƙuri da distorbing ɗinki da mukayi,kin san idan bamu ganki ba ne baza mu sami natsuwa ba,ga kuma new baby dake son jin muryar Abbun shi da yayarshi!' ya faɗa yana tura hannun shi ikon mararta,shafa kyakykyawan sajen shi tayi tare da cewa,shi ke nan anyi muku AFUWA,kana ta janye hannun shi daga jikita tanayi mishi nuni da yusra,ɗan shafa sumar shi yayi,kana yace"zan kai yusra wajen su fadil,dan haka sai ki shirya tarbata!'tace"naji kuje kafin ku dawo na gama shirya order ta!'lan gaɓar da kanshi yayi,kamar wani maraya tare da hade hannayen shi,yace"ai baki ce kin yafe mana ba!'tace"na faɗa mana, Sa dai idan mai-maici kikeso?dage mata gira sukayi shida ƴar tashi,lumshe idanunta tayi tana jin farinciki na shigarta ta kowane ɓangare,a hankali tace"My zauji and my princess yusra,kuje nayi muku AFUWA,amma SANADIN ƘADDARAR MU DATAZO DA HASKE!"yeeh shi da ƴar tashi gaba ɗaya suka saka ihu,dariya Bintu tayi tana mamakin Abdallah da yadda rayuwar shi ta canja,duk da cewa wannan halin nashi yana nan amma sam ita baya yi mata,ya maida kanshi yaro soko a gabanta,ita kam babu abinda zatace da Allah sai godiya Alhamdulillah masha Allah,a fili ta faɗa sai suma suka ɗauka da faɗin Alhamdulillah masha Allah,nima Fatima y Adam nace Alhamdulillah masha Allah, Godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon kammala wannan littafi Mai suna ƙudurar Allah,ina fatan mu amfanu da darasin dake cikin sa,kuskuren dake cikin sa kuma Allah ya yafe min, Allah ka yafewa dukkan al'ummar musulmi, Allah ka bamu ikon bin abinda yake daidai, Sai mun haɗu a sabon littafina mai suna ƘADDATA SANADIN HASKE, I DAN ALLAH YA BAMU ARAN RAI DA LAFIYA,,,, INA ƘAUNARKU MASOYANA ADUK INDA KUKE,,,, KADA KU MANTA DA SUNAN SA NA KUƊIINE AKAN FARASHI MAI RAHUSA ,,,,ƘADDATA SANADIN HASKE.....ZAIZO MUKU NAN BADA JIMAWABA..... TARE DA ALƘALAMIN✍🏽 FATIMA Y ADAM