*KWANTAN ƁAUNA* October/FitattuBiyar 2023. ©️ *Nana Haleema.* _*Da Sunan Allah mai rahma mai jinqai, Tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad S.A.W. Godiya ga Allah mad'aukakin sarki da ya bani iko da damar sake d'ora alqalami na akan sabon labarina mai take KWANTAN B'AUNA, ba dabarata bace, ba wayona bane,ikon sane shine ya nufa da bai nufa ba da bamu zo nan ba. Ina rok'on Allah yadda ka bani damar farawa lafiya ka bani ikon gamawa lafiya.*_ _Masoyana gani na sake dawowa a cikin wani sabon salon ina fatan zaku bani had'in kai fiye da wanda kuka bani a baya wajan ganin mun isar da sak'on da yake cikin labarin nan yadda ya kamata. Wannan tafiyar daban take da ko wacce, kuma doguwa ce sai kun shirya, salon daban yake ina tabbatar muku da hakan. Kunce kunyi kewata ko? To gani na dawo zan gani da gaske anyi kewar ko kuwa dai dad'in baki ne.😅 Gabad'aya labarin fiction bai faru a gaske ba, in yayi kama da naka ko naki to ayi hak'uri rashin sani ne._ _Warning: Ban amince a canja min labari zuwa wata siga daban ba, documents, audio ko a d'ora akan wani blog ba batare da izini na ba, a kiyaye dan Allah._ *001.* *BAUCHI STATE,* *MASARAUTAR AZARE KATAGUM.* *Mafari.* *1994.* Dare yayi duhu ya mamaye gari hannun ka baka gani sabida yadda garin yayi duhu matuk'a yayi tsiitt baka jin motsin komai ko ba'a fad'a ba yanayin garin zai tabbatar maka da dare ya tsala. Mata ne guda biyu suke tafiya da sassarfa cikin siririyar hanya mai d'auke da ciyayi da shuke-shuke, sauri suke sosai babu kamar wacce take a gaba ta bayan biye take da ita duk inda ta jefa k'afar ta itama nan take saka ta ta. Hasken aci balbal suke hango a gaba hakan ya saka ta k'ara kaimi wajan sassarfa har suka iso inda suke gano hasken ta kalli wacce take bayan ta tace, "Dakata a nan." Cikin girmamawa tace, "An gama ranki ya dad'e, ki fito lafiya." Gaba tayi zuwa inda hasken yake da sauri kamar zata kifa domin burin ta ta isa wajan, dutse ne babba a wajan sai yadi kalar ja da aka yane dutsen dashi da kawunan rago a sak'ale anyi ado dasu wasu suna zubar da jini wasu sun fara bushewa wasu kuma sun zama k'ashi. Zubewa tayi a k'asa tace, "Ta haihu! Ta haifi yara maza har guda uku a lokaci d'aya!" Yadda take fad'ar maganar muryar ta rawa take yi kana ji kasan cikin tashin hankali da d'imauta take. Baza ka d'auka akwai halitta a wajan da take ba sabida yadda wajan yake da duhu sosai aci balbal d'in a farkon wajan take kana shiga ciki babu hasken ta. "Ha!Ha! Bana fad'a miki daman zata haihu ba?. Mun riga mun ga haka zata haihu kuma y'ay'an zasu girma." Ya fad'a cikin murya mara dad'in sauraro mai bada tsoro da firgita wanda yake sauraron ta. Abin mamakin bata tsorata ba sai sake gyara zaman ta da tayi tace, "Ya zanyi? Bazan iya jurewa hakan ba ko kad'an, ka nema min mafita kaine k'arfin guiwata. In y'ay'an nan suka girma na shiga uku." "Me kike so a yiwa yaran?, A kashe su? A haukata su? A lalata rayuwar su ta gobe? A juyar da tunanin su? A sace su?. wanne kike so ayi musu a ciki? Ko wanne kike so zamu taimaka miki." D'aure fuska tayi alamun rashin imani ya d'arsu a zuciyar ta cikin kaukasar murya tace, "Bana so a kashe su; ina so su rayu su d'and'ana irin kalar rayuwar dana tanadar musu, bana so su haukace sabida so nake da hankalin nasu amma su kasa sarrafa shi, bana so a lalata rayuwar su domin da nutsuwar su nake buk'atar su, bana so a sace su; domin a gidan su nake so su tashi inda suna ji suna gani su da gidan su zai bare ya fisu daraja da mahimmaci a cikin sa. Ina so su rayu amma ko wanne su asan abinda za'a saka masa wanda dalilin hakan suna ji suna gani sarautar zata fi k'arfin su nan gaba. Bana son jinin Rabi yayi wani kwakwkwaran motsi sai naso, bana son jinin Rabi ya d'aukaka a duniya, yadda take jin tafi kowa ina so na nuna mata ita ba kowan komai bace face farcen susa a wajena." Ya kuma sakin dariya mai munin sauraro yace, "ki d'auka wannan an gama, ki jira girman su ko wanne a cikin su zaki ga da kalar dabi'ar da zai tashi, nine nace zanyi in na fad'a bana fasawa sai na tabbatar. Amma da sharaɗi!." Murya na rawa tace, "Meye sharaɗin?." "Komai zai faru daga baya babu ruwan mu, aikin mu mun riga munyi in kika ga wani canji to ki tabbatar kin sab'a abinda zan fad'a miki nan gaba." Farin ciki ya mamaye zuciyar ta tace, Na amince da ko wanne irin sharaɗi, duk wahalar sa, duk qalubalen sa, duk tashin hankalin sa na amince zanyi. Godiya nake, inda kai bazan zubar da hawaye ba ni na sani." "Tashi kije, abinda kike so zai biyo baya!" ya fad'a a firgice ta mik'e da sauri ta juya ta bar wajan da sassarfa zuciyar ta cike da farin cikin ta samu cikar burinta. *☆☆☆* Sarki Dr Nasir Sa'ad Muhammad shine sarki na goma sha uku a masarautar Azare dake cikin garin bauchi a arewacin Nigeria, jika ne wajan Mai martaba sarkin Azare Muhammad Nuhu mahaifin Sarki na goma sha d'aya. Mahaifin sa Sarki Sa'ad shine sarki na goma sha biyu a yankin fulani, bayan shi sai Nasir Sa'ad wanda ya kasance na goma sha uku. Yana da tarin y'an uwa da dama wanda suka had'a da uwa d'aya uba da d'aya da kuma uba d'aya, shi kad'ai Allah ya zab'a a cikin su ya baiwa sarautar Katagum duk da tarin y'an uwa manya da yake da. Sarki Nasir Sa'ad sarki ne mai ilimi da wayewa a matakin boko yana da matakin PHD a b'angaren addini ba'a cewa komai domin yafi zurfi a wannan b'angaren, shugaba ne mai ilimi da kuma adalci da sanin ya kamata da tausayin talakawan sa ta ko wacce fuska, baya lamuntar zalunci ta ko wanne b'angare ko waye kai ko kuma d'an waye yayi ba dai-dai ba masarauta zata hukunta shi sai dai an b'oye ba'a bari labarin ya bayyana yazo kunnen sa ba. Yana da yawan taimako da sadaka musmaman ga wanda basu dashi, y'an mata da za'ayi aure babu kayan d'aki yana k'ok'ari wajan yi musu dan daman can mai kud'i ne bada aljihun gwamnati ya dogara ba, Wannan dalilin ya sanya mutanen Azare da kewaye suke matuk'ar k'aunar sa dashi da iyalan sa baki d'aya kowa fatan alkhairi yake masa sabida in alkhairin sa bai same ka ba zai sami wanin ka. Matan sa uku babbar cikin su itace Fulani Sa'adatu itace uwar gidan sa auren saurayi da budurwa, tun kafin a bashi sarauta ta aure shi suna da yara biyar hud'u mata d'aya namiji wanda ya kasance shine k'arami cikin yaran ta. Mace ce makira a bayyane zata nuna maka duk duniya babu wanda take so sama dakai amma a b'oye tafi kowa cin dunduniyar ka. Burin ta guda d'aya ne tal yadda d'an ta namiji ya kasance k'arami bazai gaji sarautar katagum a wannan lokacin kada wani ya gada a cikin y'ay'an abokan zamanta. Matar sa ta biyu itace Fulani Rabi'atu y'ar sarki kuma jikar sarki sannan matar sarki, y'a ce a wajan sarkin Kano wanda mahaifin ta ya gaji sarautar a wajan mahaifin sa, Ya aure ta bayan an bashi sarauta ba jimawa. Mace ce mai izza da k'asaita da nuna zallar iko a kan komai, kai da ka ganta da yanayin maganar ta da yanayin takun ta kasan jinin sarauta ne yake yawo a jikin ta. Fara ce tass kyakykyawa domin ta b'angaren mahaifiyar kyawawa ne sosai. Tana da ilimi a waye take idanun ta sun bud'e kar take kallon kowa domin duk wata harqalla ta gidan sarauta ta santa dan a gidan ta tashi. Yaran ta hud'u maza uku mace d'aya haihuwar ta uku kacal a duniya domin haihuwar ta ta farko yara uku ta haifa duka maza, bayan su ta sake haifar wani namijin Allah ya yi masa rasuwa daga nan ta haifi mace a wannan haihuwar ta dakatar da haihuwa a cewar ta ta samu abinda take so, domin a ganin ta da tunanin ta haihuwar y'ay'a maza a gidan sarauta shine riba. Yaran ta sune manyan maza a kaf gidan kasancewar wad'an can mata ne kuma sun yi aure nata sune a kan gaba komai za'a yi na sarauta tabbas dasu za'a dama. Ta raba y'ay'an ta da y'an uwan su ta kebence su waje d'aya har ta kai ta kawo da d'aya a cikin su zaiga yaran y'an uwasa mata sai dai su yaran su gane su amma su baza su gane su ba sabida basu san su sosai ba babu zumunci a tsakanin su sam, a ganinta ba daidai suke dasu ba nata daban suke. Fulani Rabi'atu babban burin ta a rayuwa bai wuce ta kasance babar sarki kuma kakar sarki ba, burin ta d'an ta ya gaji sauratar garin Katagum ya mulke ta yadda ta tsara masa sannan jikan ta ma ya gada. itace zatayi mulkin domin yadda take so komai ya tafi sai abinda tace shiyasa ta zab'i mafi soyuwa da yi mata biyayya a cikin yaran ta, wanda yafi ilimi da kud'i a hannu kamar ba matashi ba, sai dai me?, manyan mazan da suke kasance guda uku sun kasance dukkan su basu da qualities d'in da za'a basu ragamar al'uma amma duk da hakan bata hak'ura ba kullum gani take yaran ta sune zasu gaji sarauta koda basa so, ko da tsiya koda tsiya-tsiya sai hakan ta kasance. Fulani Rukayya itace matar sa ta uku mace mai sanyin hali wacce bata d'ora ranta abinda wand'an can suka d'orawa kansu ba, y'ay'an ta hud'u itama mata uku namiji guda d'aya tal itama kuma shine k'arami a cikin y'ay'an ta duka manyan mata sunyi aure d'aya ce ta rage a gabanta. *☆☆☆* Babban falo ne na isa da girma da kuma k'asaita da alfarma, kana kallon falon kasan na manyan mutane ne masu tak'ama da aji da kuma sarauta, domin kuwa kalar adon da akayi masa da kalar kujerun cikin sa kana kallon sa kasan bana talaka bane sai na mai arzuk'i arzuk'in ma irin na y'ay'an masarauta. A zaune take ta d'ora k'afar ta akan pillow mata guda biyu suna matsa mata k'afafun ta a hankali hannun rik'e da waya tana dannawa hankalin ta a kwance. Fara ce sosai mai kyau kana ganin ta kasan ta manyan ta amma kasancewar kud'i da hutu bai nuna ba in ka ganta baza ka d'auka tana da manyan yara ba, mulki,k'asaita, izza, ko in kula ya ratsa jikin ta sosai dan ko yanayin da take danna wayar da izza take yin ta. Maza uku ne masu kama sak da juna samari matasa masu jini a jika suka shigo cikin falon nata da sallama. A k'alla zasu yi shekara ashirin da tara zuwa da talatin da haihuwa dogaye kyawawa masu kama da mahaifiyar su masu zagayayyen gashi bak'i a fuskar su. Farare ne dukkan su kana kallon su kaga y'an uku domin kamar da suke ta b'aci musamman guda biyu a cikin su babu abinda ya banbanta su sai adon gemu, dukkan su manyan kaya ne a jikin su irin na sarauta sun d'ora riga mai zanen sarauta a sama ko wanne da kalar tasa sunyi kyau sun amshi jikin su sosai duk da yanayin fuskar ko wannen su ya banbanta. Zubewa bayin gaban ta suke suna kwasar gaisuwa amma babu wanda ya kula su a cikin su k'asa suka zauna kusa da k'afafun mahaifiyar su suka gaishe ta a tare ta amsa tana kallon su, Murmushi take tana kallon su alfahari yana sake mamaye zuciyar ta, ko a wannan b'angaren tasan ta yiwa abokan zaman ta fintinkau itace da gida, itace da katagum, ta kalli bayin nata sai jikin su ya fara k'yarma suka mik'e suka fita da sauri domin yanayin kallon da tayi musu sun fahimci me take nufi. "Tun d'azu na aika kuzo dukkan ku sai yanzu kuka ga damar fitowa?." Wanda yake danna waya ne ya d'ago ya kalle ta yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, Lokacin ina wanka ne." Hararar sa tayi jin abinda yace ta gane waye a cikin su tace, "kodai kana waya da y'an matan ka?." Baice komai ba ya d'auke kansa ya kalli k'asa. Girgiza kai tayi kafin ta kalli na gefen ta tace, "Kai nasan daman indai kiran yazo wajan ka zaka iso kai bana jin ka Hydar" ta fad'a tana kallon sa. Asad ta kalla wanda yake kallon k'asa yana wasa da gashin carpet d'in falon da farin hannun sa mai d'auke da azurfa kalar golden ta haska hannun sa sosai, shi kansa hannun nasa abin kallo ne. Tasan kome za'ayi bazai furta komai ba kallo ma bazai kalle su ba balle magana. "Asad!." D'ago idanu yayi ya kalle ta amma bai amsa ba, ta san bazai amsa hakan ya saka tace, "meyasa baka je zaman fada ba d'azu?." Kansa ya mayar k'asa baice komai ba tace, "ba magana nake maka bane?, meyasa baka je fada ba matsayin ka na magajin wannan gida ko hukuncin mai martaba bai zo kunnen ka bane?." "Allah yaja da ranki Mama ni banga dalilin da zai saka kina kiran sa magaji ba bayan nine babba a cikin mu, baki tab'a kira na magaji ba meyasa sai shi?" Aliyu ya fad'a yana kallon k'asa da alama ya gaji da jure yawan kiran sa da magaji da take yi. Kallon sa tayi tace, "A hakan zaka zama magajin sarauta Aliyu? A hakan zaka mulki katagum?." Shiru yayi bai amsa ba ta dawo da kallon ta ga Asad tace, "Ko baza kayi magana ba nasan kana ji na Asad, duk wani abun da kake ji dashi a kanka ka ajjiye shi ka dinga zama kusa da mahaifin ka kana fahimtar yadda tsarin sarauta yake, kai kad'ai ne damar da nake da ita na zama mahaifiyar sarki kasan shine burina ya zamar maka dole ka cika min ita." Rausayar da kansa yayi cikin muryar sa da bata fita sosai sabida taushin ta yace, "Allah yaja zamanin ki Mama, Bana so!." "Dole kaso tunda ni ina so, kai kad'ai ne burina domin cikin y'an uwan ka gasu a zaune duk ka fisu quality, kai mahaifin ka ya zab'a har ya furta kai zai bawa kujerar sa sabida kullum k'arfin sa k'arewa yake dole kayi abinda nake so Asad koda kai baka so." Runtse idanun sa yayi ya sake mayar da idanun sa k'asa Aliyu da yake ji kamar ya shak'e wuyan Asad sabida bak'in ciki yace, "Mama wai meye laifina ne ni da baza'a bani ragamar rik'e magajin masarautar katagum bane?, Asad baya so ni ina so meyasa baza'a bani ba ni?" Ya fad'a a tausahe duk da ransa a b'ace yake bai bari yayi mata magana da k'arfi ba sabida girman biyayya. "Sabida baka dace ba Aliyu, baka da wadattacen ilimin addini, banzayen dabi'un ka na neman matan tsiya waye zai baka ragamar al'uma a hannun ka?. har bayin gidan nan baka bari ba badan na saka an binne zancen baiwar da ka lalata ba na saka a mayar da ita k'auye da yanzu mahaifin ka bai hukunta ka ba?." Shiru yayi bai amsa ba ta ja tsaki ta nuna shi da yatsa tace, "kar ina maganar sarautar gidan nan ka sake saka min baka, baka dace ba ba kuma zaka dace ba Aliyu. Asad shine magaji shine zai gaji mahaifin ku shine zai mulki masarautar katagum ba kai ba!." Ran Aliyu ya kai k'ololuwa wajan b'aci ya cize bakin sa yace, "in kinyi min izini zan iya tafiya?." Mama ta bishi da kallo tace, "Tashi ka bani waje." Ba musu ya mik'e yace, "A huta lafiya" ya fad'a yana fita daga falon zuciyar sa a cushe. Dawo da kallon ta tayi ga Asad tace, "kaji abinda nace maka ko?." D'aga kai yayi alamun eh tace, "tashi kaje anjima zan neme ka." Mik'ewa tsaye yayi baice komai ba ya fita aka bar Hydar a zaune kusa da ita. Hydar ta kalla ta ga yana ta murmushi itama tayi murmushin tace, "Hydar Allah ya baka lafiya, bana son yawan ciwon nan naka ko kad'an" Murmushi yayi yace, "Amin Mama. Amma Allah yaja da ranki sai nake ganin da ki k'yale Deaf da batun sarautar nan baya so." D'aure fuska tayi tace, "ka daina kiran sa da kurma na fad'a maka rashin magana yake da ita amma shi ba kurma bane ba, sarauta kuma sai yayi da izinin Allah." Yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ina neman afuwa." Numfashi ta sauke ta koma ta jingina da kujera tana kad'a k'afar ta, babban burin ta a rayuwar ta a yanzu shine Asad ya gaji sarautar masarautar katagum kamar yadda mahaifin sa yake son hakan, bata so sarautar ta fita daga gidan domin matuk'ar ta bar gidan zata cigaba da zaga dangin mahaifin sa ne maimakon y'ay'an ta da jikokin ta, "dole ma Asad ya karb'i mulkin nan koda baya so, tunda har mahaifinsa ya furta shi zai bawa mulkin nan komai zai tafi yadda na tsara." Asad koda ya fita fadar cikin gida ya nufa domin amsa kiran mahaifin sa, tafiya yake a nutse kana kallon sa izza da k'asaita da tak'ama ta gama ratsa ko wanne b'angare na jikin sa, kasancewar sa mai nutsuwa sai akayi sa'a aka had'a nutsuwa da sarauta sai suka bada kalar izza ta musamman wacce kafin ka samu mai irin ta sai ka tona. Dak'yar yake taka k'afar sa sabida sarautar da ta gama ratsa jijiya da tsokar jikin sa, kamar yana tausayin k'asa haka yake tafiya bakin sa na motsawa a hankali yana furta kalmar da ta zame masa jiki a koda yaushe wato Astagafirullah. Zubewa ake ana gaishe shi sai dai ya kad'a kai ko ya d'aga hannu amma magana koda motsa bakin sane baya yi sai lazimin da yake yi, Ba jimawa ya k'araso k'aramar fada yasan tabbas mahaifin sa yana ciki ya shiga da sallama cikin muryar sa da bata fita sosai. Ga mamakin sa mahaifin nasa baya nan sai dogarai da alama bai jima da tashi ba, "barka da shigowa Yarima mai jiran gado, barka da zuwa magajin masarautar katagum, Allah ya tsare mana kai, ya kare ka daga dukkan makiyan ka, takawar ka lafiya......" D'aga masa musu hannu yayi hakan ya saka su jan bakin su sukayi shiru ya kalli kujerar mahaifin sa ya kalle su nan take suka gane mai yake nufi cikin girmamawa suka ce, "mai martaba ya shiga ciki" suka fad'a suna sunkuyar da kansu suna yi masa jinjina. Baice komai ba ya juya yana ji suna kwara masa kirari ya yatsine fuska ya nufi babban falon sa na cikin gidan, da gajeriyar sallama ya shiga mahaifin sa na hango shi annunirin fuskar sa ta bayyana yana zaune su biyu kacal daga shi sai k'anin sa da suke ciki d'aya wanda ya kasance wambai katagum suna tattaunawa, k'arasowa yayi da girmamawa ya gaida mahaifin nasa ya amsa yana fad'in, "Asad zaki na, barka da zuwa." Murmushi yayi wanda ya k'ara saka fuskar sa annuri da kyau ta fito da zallar k'uruciyar sa amma baice komai ba, wanda yake a zaune shima murmushin yake yace, "Asad ikon Allah." Mai martaba yana kallon sa yace, "ya akayi ne Asad? Akwai wani abun ne?." Kai ya girgiza kai alamun babu komai yana murmushi amma baice komai ba, "in anjima kazo ina neman ka." Kai ya d'aga kafin yace, "to in sha Allah zan amsa kira." Mahaifin nasa yace, "Zaka iya tafiya." Ya sake duk'ar da kansa yace, "Godiya nake. A tashi lafiya" Daga haka ya mik'e ya fita suka bishi da kallo kafin mai martaba yace, "Mubarak ya kake ganin ranar dana ajjiye sarautar nan Asad zai iya mulkin nan kuwa?." Wanda aka kira da Mubarak yace, "zai iya mana ranka ya dad'e, Allah ya ja zamanin mai martaba ai kaf dangin mu Asad shine ya cancanci kujerar sarautar katagum sabida ilimi da halayen sa masu kyau. A madina fa yayi karatun addini suka rik'e shi suka hana shi dawowa sabida tsabar ilimin da ya tara, gana zamani gana addini. Allah yaja da ranka ina jin an manta da cewa Asad shine wanda k'asar Saudia ta yiwa takardar shaida zama d'an k'asa dan akwai basa so suyi asarar sa?." "Haka ne wambai, amma baka duba yanayin sa na k'in magana, ta ya shugaba zai kasance baya magana da wanda suke k'ark'ashin sa?. Sai abu ya k'ure sannan yake iya furta kalma guda d'aya fa." Murmushi Wambai yayi yace, "zai koya ne koya ne mai martaba. Allah yaja da ranka ai a haka ma maganar tasa ba kamar daba, tunda ya dawo Nigeria ai yana magana a can fa in ba karatun alkur'ani ba to yana masallacin madina yana limanci." Murmushi yayi mai cike da izza kana yace, "Sai yanzu nake ganin ganganci da nayi wajan furtawa y'an uwana Asad zan barwa mulkin Katagum, tabbas nayi kuskure a wannan b'angaren dana bar abin a zuciyata sai dai aji na aiwatar hakan zaifi." Wambai yace, "Allah yaja da ranka abinda aka riga aka furta ya wuce, sai dai dole mu dage da taya Asad da addu'a dan wannan maganar da mai martaba ya furta wasu suna nan da ita suke kwana suke tashi burin su bai wuce su samu hanyar da zasu kawar dashi ba dan cikar burin su." Mai martaba yace, "Nasan da wanann, makusanta na sune suke wannan k'ok'arin na san da hakan. Amma in Allah ya amince babu abinda zai faru sai alkhairi. Dan ma Asad d'in ba baya bane wajan addini da yanzu sun haukata shi. Allah zai kiyaye." "Da izinin Allah." Daga haka suka canja hirar zuwa wata daban. A guje ta shiga cikin babban falon jikin ta na rawa sosai ta zube a gaban wata babbar mace mai ji da jiki mara haske sosai tana fad'in, "Allah ya ja zamanin uwar gidan mai martaba, Allah ya ja zamanin ki, Allah ya ja da ranki ya saka ki fi haka, Allah ya albarkace ki da iyalan ki. Ranki ya dad'e" ta fad'a tana mata jinjina hannun ta na k'asa. Kallon ta tayi daga inda take zaune tace, "Ramma lafiya?." "Ranki ya dad'e yarima mai jiran gado na gani........" "Duk sanda na sake jin kin kira shi da wannan suna sai na saka an k'ona bakin ki" ta dakatar da ita a fusace. "Allah ya wuci zuciyar ki, tuba nake, nabi Allah na biki ki yafe ni." Tsaki ta ja sannan tace, "Ina jin ki." "Asad na gani a k'aramar fada shi da mai martaba sunyi ganawar sirri." "Ganawar sirri?" Ta fad'a tana mik'ewa zaune sosai tana kallon ta. "Na tabbatar ranki ya dad'e, domin daga shi sai wambai a ciki ko dogarai babu, kuma ya jima a ciki kafin ya fito." Jinjina kai take yi kafin ta mata alamu da hannu taje ta mik'e tana godiya ta fita. Tashi tayi tsam ta shiga cikin d'akin ta ta d'auki waya ta kira number Waziri. Duka biyu aka d'auki wayar yana d'auka tace, "Kana da masaniyar ganawar sirri da mai martaba yayi da Asad?." Daga can b'angaren yace, "Bani da masaniya, meya faru?. Waye ya kawo miki wannan labarin?." "Na tab'a kawo maka mara tushe ne?." "Baki tab'a ba." "Nifa kwata-kwata bana son mulki yaje hannun jinin Rabi'atu, tana yi mana kallo y'ay'an talakawa dan kawai ta kasance jinin sarauta, da zarar d'an ta ya zama sarki tabbas mun shiga uku zaman gidan nan sai ya gagare mu, dole nida kai mu san abin yi domin kuwa Asad ne kawai burin ta shima mai martabar shine burin sa ya zama dole muyi maganin sa." Dariya wanda ta kira da Waziri yayi yace, "Ina raye, ina numfashi, ina da wayo, ina ji, ina gani, ina da lafiya, wani bai isa ya mulki masarautar katagum ba face ni. Nine na dace kuma nine zan yi, babu wanda ya cancanta sama dani. Rabi'atun banza da wofi balle wasu y'ay'an ta?, ki bar ni dasu zaki ga yadda zan b'ullowa lamarin matuk'ar ina raye karagar nan tafi k'arfin ta!?." "Haka kake cewa koda yaushe amma ka kasa yin komai, da zafi-zafi ake dukan k'arfe amma kana barin sa yana wucewa, tun kafin mai martaba ya furta maganar murabus kake fad'ar haka yau gashi har ya riga ya furta ya kuma ambaci sunan Asad, da zarar an tabbatarwa da Asad mulki nida kai dole mu bi babu yadda zamuyi. A daina d'aukar lokaci in za'a yi kawai ayi bana son a dinga mayar da hannun agogo baya." Daga can b'angaren yace, "ki bani lokaci Asad bai isa yayi mulki ina da rai ba, yaron akwai tsari a jikin sa sosai dama kad'an nake so na samu nayi masa shigar sauri, zamu gani za kuma muji, kema kuma zaki gani" yana fad'a ya yanke wayar tabi wayar da kallo tana sauke numfashi zuciyar ta tana tafasa cike da bak'in ciki da b'acin rai. A shirye take da ta salwantar da duk abinda ta mallaka wajan ganin jinin Rabi'atu bai mulki katagum ba, zata iya salwantar da rai da lafiyar wani domin burin ta ya cika. *☆☆☆* K'aramin gida ne kana kallon sa kaga gidan talakawa wanda basu dashi yanayin sa da komai nasa ya nuna zallar talakawa ne suke rayuwa a cikin sa, ko a yanayin unguwar kasan ta masu k'aramin k'arfi ce amma tana da babbar hanya wanda mota zata zo har k'ofar gida. Daga cikin gidan tsakar gida ne mara girma duk turb'awa ko arzuki siminti babu sai d'akuna a tsakar gidan guda uku sai d'akin girki da kuma band'aki. "Rauda! Rauda!! Rauda!!" Gajeren Dattijo mai duhun fata da farar furfura ya ke fad'a yana shigowa gidan. Maimakon mutum d'aya ta fito kamar yadda yake fad'a sai mata uku suka lek'o, biyu daga d'aki d'aya guda d'aya kuma daga wani d'akin daban. A hankali ta tako ta k'araso inda yake ta durk'usa tace, "Baba gani." Kallon ta yake cikin harara yace, "uban me ya hana ki fita wajan waccan yaron mai mota da yake son ki?." Shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa ganin hakan ya saka shi ya fusata yace, "ba magana nake miki ba?." D'ago idanu tayi ta kalle shi kafin tayi magana yace, "ke ba kyau ba amma ki dinga wulak'anta manyan mutane masu kud'i irin wad'an nan? Dan kin samu zasu d'auki irin ki....? a ka'ida a mai aikin gidan sa zaki je amma yayi miki adalci yana so ya d'auke ki matsayin mata kike ja masa aji, ina aji a wajan talaka..? Nace miki ina aji a wajan talaka...?." A hankali tace, "Baba kayi hak'uri." "To tashi kije ki ku tattauna bana son jan magana." Bata musa ba ta mik'e taja mayafin ta a kan igiyar shanyar da take tsakar gidan ta saka takalmi ta fita. D'akin da mata biyu suka lek'o ya kalla sai suka koma ya ja tsaki yace, "haka dai, ke munafuka y'ar ki ma munafuka." Rauda lokacin da ta fita ta tarar da wanda zuciyar ta ta bata tabbacin ganin sa a tsaye a jikin motar sa yana facing gidan su. Yana hango ta ya saki murmushi sab'anin ita da face d'in ta take a cushe ba walwala ko kad'an ta k'araso tace, "Ina wuni." Sai da yayi murmushi sannan yace, "lafiya lau Rauda, ya gida da mutanen gidan?." "Lafiya." "Kiyi hak'uri na saka Baba ya fito dake." Bata bashi amsa ba daman yasan hakan yayi murmushi yace, "Ina son ki Rauda, Ina burin ranar da zaki ce min kema kina sona" Bata ce komai ba ta kalle shi tace, "Sai anjima." Har zata juya yace, "minti d'aya Rauda." Cak ta tsaya ya zagaya mota ya d'auko leda k'arama ya dawo ya mik'a mata yace, "ga tsaraba babu yawa." Kallon ledar tayi ta kalle shi tace, "na gode" daga haka ta juya ta shiga gida ko waiwayen sa batayi ba. A kan idanun Baba komai ya faru tana shiga soron gidan ya yi mata dak'uwa yace, "uban me yasa baki karb'a ba?." Kamar zatayi kuka tace, "Umma ta hana ni." "Keda Umman ba nine a gaba da ku ba? Dallah malama koma ki karb'o, ka ganar min yarinya y'ar bak'in ciki." Idanun ta yayi rau-rau zatayi kuka tana kallon sa yace, "in baki koma ba sai na fyad'a ki da k'asa, ka jimin yarinya mai bak'in ciki, zaki koma ko sai na b'alla ki?." Juyawa tayi hawaye na zubo mata ta kalli inda motar take taga babu shi alamun ya tafi ta sauke numfashi ta juyo ta dawo ta kalli Baban tace, "Ya tafi." Harara ya banka mata ya ja tsaki yace, "a nonon uwar ki kika tsotsi bak'in ciki dan ni kam ba haka halina yake ba, na rantse da Allah duk ranar da kika sake aikata wannan kuskuren sai ranki ya b'aci. Banza mummanar banza da wofi, ke ba kyau sai tsinanan bak'in ciki da mugun hali. Duk wanda ya kwashe ki matsayin mata ya shiga uku." Shiru tayi kanta na k'asa yace, "wuce muje ki d'auki d'anwake ki tafi bakin kasuwa rana tana yi." Babu yadda ta iya haka ta shiga cikin gidan yana bayan ta ya wuce cikin madafar da kansa ya had'o mata kayan abincin ya fito dasu yace, "D'auki maza ki wuce kar lokaci ya k'ure, kuma wallahi kika dawo kika ce min baki siyar ba duk inda zaki nemo kud'i sai kin nemo kin kawo min, domin ke bak'in halin ki har akan kayan sana'a ta yake." Umman ta da ta fito daga d'aki tace, "Malam dan girman Allah ka daina d'orawa yaran nan tallah, yaran nan sun girma sun kai munzalin aure maimakon ka tura su makaranta sai ka dinga basu talla.....? Nace maka ni ka barni zan siyar maka a gida amma kak'i, gani kake kamar baza'a siya ba, tura yara talla kamar su Rauda ba komai zai jawo ba sai lalacewar rayuwar su." Da kallo yake binta har ta kai k'arshe yace, "to uwar iyayi ita y'ar uwar ki bata yi magana ba sai ke?, yaran nan dai nine na tsuguna na haifi kayana ba wani ya haifar min ba, kema da kike tutuyar y'ar kice nine nayi miki cikin ta ko? To ki saka min matsaya a lamarina da y'ay'ana na amince da tarbiyayyar dana yi musu, in ma bak'in ciki kike dan ina samun arzuki da talla sai dai ki mutu." Shiru tayi Rauda ta sunkuya ta d'auki kular da yake mai marik'i ce kuma bata da girma can ta kalli mahaifiyar ta ta da mahaifin ta tace, "Sai na dawo." "Allah ya kiyaye" Umma ta furta a sanyaye tana kallon ta ta fita daga gidan jikinta a sanyaye......... *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023. ©️ *Nana Haleema.* *002.* Bayan fitar Rauda Umma ta kalli Baba ta girgiza kai tace, "Dan Allah Malam ka daina d'orawa y'ay'an ka talla ka bar mu mu matan ka mu dinga siyar maka kome kake so a gida, tura yaran nan tallah babu abinda zai haifar sai d'a mara ido." "Kedai kiyi masa amma ni kam gwara a d'ora musu tallan, yadda za'ayi rububin siya a wajan su mu baza'a yi a wajan mu ba. sune y'an mata wani saurayin ko dan su kula shi ma ya siya a wajan su" wacce take fitowa daga d'aya d'akin ta fad'a tana kallon Umma. Baba yace, "bar ta Asabe ita ai baza ta tab'a ganewa ba shiyasa, indai akace an tab'a mata Rauda shikenan babu zaman lafiya, ko da yake tun lokacin yayyen Raudan ake fama da ita y'ar bak'in ciki ce bata so taga nayi arzuk'i." Murmushi Umma tayi ta kalle su cikin takaici tace, "Amma bakwa gudun wani abun ya faru dasu ta silar tallan da ake basu?, kun manta y'ay'a mata ne dukkan su sun kai munzalin aure?." Baba ya nuna ta da yatsa yace, "Kinga Binta bana son mugun fata a kan yarana, ina yi musu addu'a ba dare babu rana Allah zai kare min su duk inda suke, kar na sake jin kin furta wata magana mara dad'i a kan su in ba so kike ranki ha b'aci ba." Umma bata kuma cewa komai ba ta koma d'akin ta. Tana jiyo shi yana fad'in, "kuma wallahi kika cigaba da hure mata kunne akan yaron nan Anas da yake son ta take k'in sauraron sa ki kiyayi hukuncin da zan miki, ban tab'a ganin uwa y'ar bak'in ciki kamar ki ba. Ace y'ar ki ta samu mai kud'i amma ki dinga bari tana wulaƙanta shi....? ita ba y'ar kowa ba ba kuma jikar kowa ba, gata ita ba kyau ba balle ace shi ya gano ya nace amma ki dinga hure mata kunne." Tana jin sa tayi shiru ta zauna a kan ledar da take shinfid'e a d'akin tana girgiza kai. Lamarin sa kullum sake gaba yake duk da girman da yake cimma masa, indai akan kud'i ne ba sani ba sabo, ko meye zaiyi indai akace kud'i zance ya k'are, tun lokacin baya haka yake gashi shekaru har sunyi nisa halayyar sa tana nan. Malam Adam haifaffan garin azare ne mazaunin unguwar Katsalle, y'an uwan sa da kowa nasan y'an Azare ne a nan aka haife su a nan kuma suka tashi suke kuma zaune. Yana da mata guda biyu Asabe da Binta y'ay'a kuma yana da goma takwas mata biyu maza, Asabe tana da guda shida biyar mata namiji d'aya, Umma kuma uku mata d'aya namiji shine auta a gidan gabad'aya. Suna zaman lafiya babu laifi wata ran ka gansu kamar y'an uwa wata rana kuma da kaga yanayin su kasan kishiyoyin juna ne. An aurar da mata biyar uku suka rage a gidan, Rauda wacce ta kasance itace babba wanda suka rage a d'akin su sai k'anwar ta Ummulkhairi sai k'anin ta Khalil. D'aya d'akin kuma sa'ar Rauda mai suna Rahma sai k'anin ta Garzali. Talakawa ne gidan wani lokacin abincin da zasu ci gagarar su yake sai dai kowa ya san abinda zai ci shida y'ay'an sa, mai gidan Allah ya d'ora masa san abin duniya baya jin kunyar rok'o haka baya jin kunyar cewa a bashi, koda sirikan sa ne mazajen y'ay'an sa indai Allah ya had'a su koda a hanya ne da wahala su rabu bai tambayi wani abun ba duk da suma ba masu kud'i bane ba. Tun y'ay'an nasa mata suna nuna rashin jin dad'in hakan da yake yiwa mazajen su har suka gaji domin ba zai daina ba. Tunda su Rauda suka kammala secondary school suka sauke a islmaiyya ya ajjiye batun karatu daman dak'yar aka k'arasa shi, dak'yar da sid'in goshi da ya hana su cigaba da karatu yace bashi hali suka koma islmaiyya suna hadda shima dan kyauta ce wani d'an siyaya ya d'auki nayi. Shekarar farko aka kori Rahma ita kuma Rauda ta cigaba da yin haddar ta tana sake sanin littafan addini dan Allah ya bata kaifin basira. Bayan ta kammala hadda a cikin shekara d'aya ta dawo gida sosai ta samu ilimi ta k'aru ta kuma san abubuwa da yawa a fanin addini, burin ta ta zama y'ar jarida amma kuma Baba ya daqile wannan burin nata domin yace bashi da halin da zai kaita jami'a dole ta jinginar da burin ta badan taso ba. Daga nan ya fara dafa musu abinci yana d'ora musu talla su shiga kasuwa su siyar su kawo masa kud'in ya d'aga pillow ya ajjiye dan babu wanda zai ci kud'in koda abinci ne babu a gidan sai dai a hak'ura. Dangin sa babu wanda bai masa fad'a akan basu tallan nan da yake yi ba amma ya shafawa idanun sa toka yace shifa ya haife su baiga wanda zai dakatar dashi da neman kud'in sa ba dole aka hak'ura aka k'yale shi. Babban yayan Umma babban malami ne a garin kowa ya sanshi har shi sai da ya yiwa Baba magana a kai amma ya nuna shifa y'ay'an sane yana da iko dasu dole aka zuba masa idanu. Masifar son kud'in sa ya amince ya ajjiye kud'in kar ya ci kar iyalan sa su ci amma zai ajjiye yayi ta kallon kud'in yana jin dad'i a fad'ar sa yace kallon kud'in ma rahama ne, da kansa yake girka musu abinci suna shiga kasuwa suna siyarwa gudun ma kar matan nasa su b'ata masa rai akan hakan shiyasa yake zagewa ya hura wuta ya dafa. Rauda yarinya ce y'ar shekara ashirin da hud'u bata da wadaccen kyau haka baza'a ce mata mummuna ba ba laifi dai zata shiga kadaran kadahan, tana da farin jinin samari sabida ilimin addinin ta kowa abinda yake kwad'ayi kenan a tare da ita amma bata sauraron su burin ta karatun jarida ne amma mahaifin ta ya hana shiyasa bata kula su musamman masu kud'i Umman ta takan ce mata kar ta d'ora buri a zuciyar ta domin duniyar ta koma kwarya tabi kwarya. Rauda wayayyiya ce in suna hira da Umma baza kace babar ta bace hira suke sosai suyi shawara kamar yaya da k'anwar ta. Sam Rauda bata da duhun kai in taga abu bata sani ba zata tambayi wanda ya sani ya fad'a mata sabida gaba hakan ya saka take a waye in taci kwalliya ka ganta baza kace yar Malam Adamu bace ba. Tana da kirki da girmama na gaba amma fa bata da kunya in aka tab'a ta, bata bari ko waye yayi mata sai ta mayar musamman a tab'a mata iyaye bata jure wannan. Duk girman mutum in ya latsa ta bazata bar masa ba sai ta mayar a cewar in babba bai ja girman sa ba dan k'arami yabi ta kan girman nasa ba wani abun bane, Allah bai halicce ta da tsoro ba ko Baba ne yayi wani abun ba daidai ba zata same shi ta fad'a masa sai dai yayi mata fad'an ya gama tunda ta fad'a shinkenan, halitta d'aya take tsoro a duniya shine doki. Anas ya jima yana bibiyar Rauda amma bata sauraron sa bai gaji ba duk sati sai yazo k'ofar gidan su koda bai ganta ba zai gama zaman sa ya tafi sabida Allah ya d'ora masa k'aunar ta, nutsuwar ta da ilimin ta yana daga cikin abinda yake sake jawo hankalin sa zuwa gare ta, kowa yana kaf unguwar itace mai haddar alkur'ani sau da dama y'an matan unguwar wajan ta suke zuwa tayi musu k'ari abinda yake sake burge Anas kenan da ita. In Baba yana nan ne yake tilasta mata zuwa wajan sa kawai dai ya bata wani abun ya kwace ya ajjiye gobe ma in ya dawo ya sake turata shine burin sa kawai. *☆☆☆* Aliyu tunda ya bar cikin gidan sarauta ya nufi wani plat house mai kyau da ya tsaru da falayoyi da fitala masu kyaun gaske, yana zaune a falon yayi shiru yana aikin jan tsaki ba komai ne yake k'ona masa rai ba sai zancen mahaifiyar sa akan Asad, pillow da yake ajjiye a kan kujara ya d'auka ya cillar cikin fushi yana jan numfashi zuciyar sa na mugun tafasa sabida bala'in b'acin rai da bak'in ciki. Cize lips d'in sa yayi ya koma ya jingina da kujera yana jin d'aci yana tasowa daga cikin zuciyar sa har kan harshen sa yana jin sa. "meyasa komai sai Asad?, meyasa ni ba'a maganar zan yi sarauta sai shi?!" Ya fad'a da k'arfi yana d'aukar remote yayi jifa dashi ya daki bango ya tarwatse a wajan. "Ya dai prince lafiya?" Wani matashi wanda bazai wuce sa'an sa ba ya fad'a yana shigowa falon yana bin sa da kallo, bai magana ba sai sake runtse idanun sa da yayi matashin ya zauna a kujerar da take kallon sa ganin yanayin da yake ciki ya saka yace, "Prince yane?." Nan ma bai masa magana ba bai kuma d'ago ba ganin hakan sai ya ja bakin sa ya tsuke baice komai ba sai da ya ga dama sannan ya d'ago ya sauke numfashi yana kallon sa shima yana kallon sa. "Sarkin mu na gobe, kaine yarima mai jiran gado, masarautar katagum taka ce, kai sarki, mahaifin ka sarki, kakan ka sarki, mahaifin mahaifiyar ka sarki. Allah ya ja zamanin Aliyu gadanga k'usar yak'i, daga kan ka an gama sarauta, kaine zakayi ko basa so sai ka hau karagar mulkin katagum." Lumshe idanu yayi jin kirarin da yake masa bai san lokacin da murmushi ya sub'uce masa ba ya kalle shi sai kuwa ya sunkuyar da kai yace, "Duk mai shirin bamu matsala akan hawa karagar mu zamuyi maganin sa ko waye, kar yarima ya damu muna tare dashi za kuma mu bashi goyan baya duk wahala duk dad'i, ko da tsiya koda tsiya-tsiya sai Aliyu ya gaji katagum koda Za'a rasa rai." Jin hakan sai Aliyu ya bud'e bakin sa a hankali yace, "Asad." "Shi d'in wa? Ana zancen mutanen k'arfafa wa yake zancen rago Asad?, mulki naka ne sai dai Asad ya duk'a a gaban ka ya kwashi gaisuwa, shi waye da zamu duk'a masa?, wane mutum balle aljan?. Mulki na k'arfafa ne ba irin Asad ragwaye ba, mulki na madu dakakkiyar zuciya ne ba irin Asad maau rauni ba. Allah ya ja zamanin yarima bai kamata Asad ya dinga damun ka ba domin ta ko ina kaine a sama bashi ba, waye zai d'auki mulki ya bawa kurma...?" wanda yake amsa sunan Hashim yake fad'a yana kallon sa cikin girmama irin wacce ake yiwa sarakai. Murmushin jin dad'i Aliyu yake yi duk duniya babu abinda yake k'auna sama da hawa karagar mulkin gidan su, babu abinda yake so sama yaga manya da yara suna duk'awa suna gaishe shi duk tsufan su haka duk yarintar su, yana so yaji ana buga masa tambari ana buga masa bindiga ana bud'e masa lema ana binsa a guje ana yi masa fifita. Asad yana neman zama cikas a cikin lamarin sa, burin sa da yake mafarki kullum Asad yana k'ok'arin ganin ya tafi a banza ba tare da ya tabbata basketball, sake kallon Hashim yayi har zaiyi magana sai kuma ya fasa ya d'auki wani pack a gefen sa ya bud'e ya d'auki kwayar da take bugar dashi yasha ya kora da ruwa yana sauke ajiyar zuciya. Murmushi Hashim yayi ya mik'e ya fita dan yasan ba kasafai yake son magana ba shi kuma ya lumshe idanun sa zuciyar sa na kawo masa abubuwan da ya kamata yayi a kan Asad. *ASAD.* A zaune yake a k'aramin falo ya hard'e yatsun sa waje d'aya yana kallon wani wajan daban idanun sa a kulle kamar mai tunani, wanda yake zaune kusa dashi kallon sa kawai yake yi kafin yace, "Asad hak'uri zaka yi fa babu yadda zakayi." Numfashi ya sauke ya buɗe idanun sa ya kalle shi kamar zai magana sai ya fasa ya koma ya jingina da kujera ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa. "Kai kad'ai ne ka dace da sarautar garin nan ka fi kowa ilimi da girmama talakawa, kai kad'ai ne kaf gidan nan baka yiwa bawa tsawa sai dai murmushi koda bakayi magana ba, kai kad'ai ne zaka cigaba da gunadar da mulki kamar mai martaba, matuk'ar sarautar nan ta bar hannun ka sarautar garin ta lalace gabad'aya" wanda yake zaune kusa dashi ya fad'a yana kallon sa. Lumshe idanun sa yayi ya buɗe ya kalle shi a hankali ya furta, "ni kuma bana so, why sai ni?." Jin yadda yayi maganar ya saka Suhail yayi murmushi yace, "kamar ba yanzu na gama fad'a maka qualities d'in ka ba?, bazan b'oye maka ba ko mahaifi na da yake k'ani a wajan mai martaba matuk'ar ya karb'i sarautar nan sai ya lalata komai, domin kansu kawai suke hange ba talakawan su ba, kaine ka dace dole ka hak'ura." Jijiyoyin kansa ya dafe yana murza wajan a hankali zuciyar sa na kawo masa abubuwa da yawa. _Meyasa ma suke zancen shine zaiyi sarki bayan mahaifin sa na raye kuma yana kan mulkin?._ ya tambaya a zuciyar sa yana so ya furta a bakin sa amma baya tunanin zai iya hakan ya saka shi ya sake yin ajiyar zuciya baice komai ba. Mik'ewa Suhail yayi ya k'arasa wajan fridge ya d'auko fresh milk ya had'o da glass cup ya dawo kusa dashi ya zuba masa madarar ya mik'a masa yace, "karb'i ka sha zaka ji dad'i a zuciyar ka." Bai motsa ba kuma bai karb'a ba hakan ya saka Suhail yace, "please ka karb'a." Baya son magana hakan ya saka shi ya karb'a ya rik'e a hannun sa ba tare da ya sha ba. Cigaba da magana Suhail yayi yace, "burin Mama ne ka daure ka cika mata shi nasan an tauye ka da yawa, burin ka na zama babban malamin addini a k'asar Saudia ya rushe ta dalilin sarautar nan amma ya zakayi abinda Mama take so ne, kayi hak'uri ka dinga bin abinda tace in Allah fa yayi baza kayi mulkin nan ba sai kaga baka yi ba." Dai-dai lokacin da ya kai kofin madarar bakin sa zai kenan daga bayan sa aka ce, "Asad!." A firgice ya fasa sha ya juyo yana kallon wanda ya shigo ya juya idanu dan daman yasan sai shi d'in ya d'auke ido daga kan sa dan ya tsorata shi. Abokin sa Hafiz kuma MD na kamfanin Asad ya fad'a yana shigowa cikin falon yana kallon sa yana kuma kallon Suhail. Zama yayi a nesa dashi yana kallon sa yace, "lafiya kake?." Fuska ya d'aure sosai domin yasan Suhail da Hafiz basa jituwa ko kad'an koya suka had'u zasu so suyi hayaniya shiyasa baya so su kasnace waje d'aya suna bashi ciwon kai, ganin hakan sai Suhail ya murmusa ya mik'e yace, "Deaf zamu had'u anjima." Fita yayi daga falon Hafiz ya kalle shi yace, "u know what deaf?, sam zuciya ta bata amince da wannan Suhail d'in a kusa da kai ba, u have to be very careful kasan yanzu kowa kai zai dinga hari tunda mai martaba ya furta zai sauka a mulki ya baka kowa burin sa yaga ya kawar da kai." Kallon Hafiz kawai yake yi kafin ya tab'e baki yace, "I trust him." "Kai ai daman zuciyar ka ta amince da kowa shiyasa ake cutar ka a ko wanne lamari, lamarin sarauta ba abu bane mai wasa kar ka manta mahaifin sa na neman mulkin nan za'a iya had'a baki dashi a cuce ka." Kallon sa yayi har ya bud'e baki zaiyi magana sai ya fasa ya d'auke kansa kafin ya d'auko waya yana dubawa. Hafiz ya kuma cewa, "ya dai kamata ka nutsu kasan abinda kake yi yanzu da kake gani kowa neman ganin bayan ka yake yi. Baka san komai ba a gidan kasancewar rayuwar ka Madina ka yita shiyasa kake d'aukar yarda ka bawa kowa." Nan ma bai amsa masa ba yasan daman bazai bashi amsa ba hakan ya saka shi baice komai ba shima ya cigaba da danna wayar sa. Gajiya da zaman Asad yayi ya mik'e ya shiga ciki bai sake magana ba shima kuma Hafiz bai kuma ba. Da daddare kamar yadda mai martaba yace yana neman sa bayan sallar i'sha ya tabbatar yana cikin gida ya nufi cikin gidan da yake da girman gaske, tun daga k'ofar da zata kai ka B'angaren mai martaba dogarai ne bila adadin har da jami''an taaro da suke gadin wajan sabida abinda zai zo wanda zai cutar dashi. Tunda Asad ya doshi wajan ake kwasar gaisuwa sai dai ya d'aga kai kawai har ya iso babbar k'ofar da zata kai shi falon mai martaba, Sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga da sallama a nutse yake takawa har cikin falon. Bai ma kula da wacce take zaune ba ya duk'a ya kai gaisuwa kafin ya zauna har lokacin bai d'ago ba, "Asad!" Mai martaba ya kira shi ya d'ago yace, "Na'am, Allah ya ja da ranka." "Gobe in Allah ya nuna mana zamuyi tafiya zuwa Kaduna dakai." Kai ya d'aga kafin yace, "Allah ya nuna mana goben." "Amin. Kaje shine neman da nake maka daman." "Nagode, a tashi lafiya" ya fad'a yana mik'ewa ya fita. Da kallo uwar gidan sarki ta bishi tana murmushi ta kalli mai martaba tace, "Takawa in Asad ya karb'i mulkin garin nan talakawa zasu huta zasu ji dad'i domin kuwa har ya fika zuciyar tausayi." Murmushi jin dad'i yayi babban burin sa a nuna masa kulawa ga Asad shiyasa koda yaushe Sa'adatu take burge shi tana son Asad sosai tana kuma yabon kyawawan halin sa yace, "Shine fatan da nake yiwa masarautar nan domin Asad shine kad'ai zai gyara duk wata b'arakar da take cikin ta, amma sam baya so shiyasa na dakata da batun ajjiye sarautar zuwa nan gaba." "Zai so ma tunda yana jin maganar ka na tabbata zai so, mu kam mu Asad ya karb'i mulkin garin nan ai jin dad'in mu ne balle kuma talakawan sa." Murmushi mai martaba ya kuma yi yace, "zai kasance in sha Allah." "Muna fatan hakan, shiyasa tun yanzu na fara nema masa maganin tsari daga garin mudan maganar da ka furta na zaka bashi mulki Allah kad'ai yasan magautan da suka sako shi gaba. Nasan mai martaba yana nema masa shima kuma yana yiwa kansa tawa gudunmawar nake so na bayar." Mai martaba yace, "Shiyasa nake alfahari da kasancewar ki babba cikin matana, kinyi tunani mai kyau dan a yanzu haka Allah kad'ai yasan adadin jifan da ake masa." "Allah zai kare mana shi koma waye zai koma kansu." Shiru tayi kafin kuma tace, "Takawa in an bamu izini zan shiga gida na dawo." Kallon ta yayi ya d'aga kai tayi godiya ta tashi ta fita. B'angaren ta ta koma ranta a matuk'ar b'ace jikin ta har rawa yake sabida bak'in ciki da hassada ta wuce cikin d'akin ta hannu na rawa ta d'auki waya, duka biyu aka d'auka tace, "Matuk'ar ba kawar da Asad mukayi daga doron duniya ba tabbas masarautar nan sai ta gagare mu shigowa nan gaba, mai martaba yana nan a kan bakar sa na bashi mulki ya dakata ne sabida wani dalili nasa amma ko gobe yaso zai sauka ya bashi karagar ya hau, bana fatan wannan bak'in labari ya tabbata ina raye ka san abin yi." Daga can b'angaren ya sauke numfashi yace, "kawar da Asad abu ne mai sauk'in gaske a waje na, amma bazan yi yanzu ba zamu bari a d'an kwana biyu sai mu kawar dashi bayan shi sai a kawar da mahaifin sa mu siye kwamnatin Bauchi ta yadda dole mu za'a bawa mulki koda bamu cancanta ba." "Meyasa sai an kwana biyu?, meyasa baza'a yi yanzu ba?, a kawar dasu duka biyun meye amfanin mai martaban?." "Bana son yin gaggawa domin za'a iya gano mu." "Babu wanda zai gano mu, kayi kawai mulki ya dawo hannun ka, tunda d'ana namiji ya kasance yaro k'arami banga d'an wacce zaiyi mulki a cikin mu ba, dan haka a kashe su duka mulkin ya koma hannun ka sai me!." Murmushi yayi mai sauti kafin yace, "kwantar da hankalin ki uwar gidan mai martaba sarki komai zai zo yadda muka tsara, ki cigaba da jan Asad jikin ki kina nuna masa so da k'auna a gaban mahaifin sa ki ture mahaifiyar sa kome zakiyi baza ta gani ba, tasan sarauta tasan makircin dake cikin gidan sarauta, a hankali zamu saka bakin nasa ma ya kulle duka ya daina maganar gabad'aya kowa ya huta, kinga ai baza'a bawa kurma ragamar al'umma ba. Kashe shi ba mafita bace mu bar shi a raye ta yadda Rabi'atu tana ji tana gani y'ay'an ta maza uku zasu zama hoto basu da wani amfani." Numfashi ta sauke ta lumshe ido ta bud'e tace, "Haka ne, bana so a d'auki lokaci a fara gabatar da komai domin ko wanne lokaci mai martaba zai iya canja shawara." "Kar ki damu yanzu aka fara wasan ai." "Sai na jika" tana fad'a ta yanke wayar tana wuci ita kad'ai kafin ta dai-daita kanta ta fito ta koma b'angaren mai martaba. A can b'angaren Waziri bayan ya yanke wayar da suke yi da ita ya kalli d'an sa Suhail da yake zaune yana kallon sa shima yace, "kana jin duk abinda yake faruwa, meyasa kayi wasa da maganin da na baka har bai sha madarar nan ba?." Suhail da ya fi mahaifin sa jin takaicin hakan yace, "Na bashi har zai sha abokin sa ya shigo sai ya fasa sha ya ajjiye, kasan kuma yana da basira ina na matsa akan yasha zai gano ni shiyasa na fito na barshi. Ka k'yale ni dashi Abbah ya riga ya amince dani a hankali zan shiga jikin sa na lalata duk wata garkuwar jikin nasa." Dogon tsaki yaja yace, "aikin banza, inda ka san daga inda aka kawo wannan maganin da baka yi wasa dashi ba, yanzu kafin a sake samo shi sai an kwana biyu sabida hatsarin sa ya saka ba'a bayar dashi ko yaushe. Ka lalata komai Suhail." Suhail ya cize bakin sa yace, "Abba zan gyara komai kada ka damu indai ina da rai mulki ya bar gidan su Asad ya dawo gidan nan, sai ka yi sarkin garin nan nima kuma sai nayi, burina kenan burin ka kenan, kada ka damu Abba alqawari na d'aukar maka sai naga bayan Asad, bai isa ya mulki garin nan ina numfashi a duniya ba, zan kawar dashi, zai zama bashi da amfani kamar y'an uwan sa. Asad zai zama tahiri sai dai a tuna shi ace Allah sarki." Murmushi mahaifin nasa yayi cikin jin dad'i yace, "Ina alfahari da kasancewar ka jinina Suhail, nasan zaka iya Allah ya bada sa'a." Mik'ewa tsaye yayi kafin yace, "Amin Abba, ka zuba idanu zaka yi kallo" yana fad'ar hakan ya mik'e zai fita Waziri yace, "Suhail." Ya juyo ya kalle shi yace, "Kar kaji tsoro, kar kaji tausayi, kar kaji d'ar a zuciyar ka. Ka manta dani da mahaifin Asad uwa d'aya uba d'aya muke, ka manta da kai da Asad y'an uwane ka d'auka baka tab'a sanin sa ba a wannan lokacin aikin ka zai tafi yadda kake so." Suhail ya girgiza kai cikin gamsuwa da maganar ya fita daga falon mahaifin nasa zuciyar sa na k'ullawa masa abinda ya kamata yayi a kan Asad domin cikar burin sa. *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023. ©️ *Nana Haleema.* *003.* Asad da ya bar wajan mahaifin sa wajan mahaifiyar sa ya wuce duk da dare ya fara yi amma yasan bata yi bacci ba,kamar koda yaushe a hankali yake takawa ma'aikatan dare na ta kai gaisuwa wasu yayi murmushi wasu ya d'aga musu hannu wasu ma ya share dan baya son takura. Lokacin da ya shiga ya tarar da Aliyu a zaune a kan kujera ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa ga ma'aikata a zagaye dashi ya bar su a tsaye bai sallame su ba yana aikin danna wayar sa. Sallamar da yayi suka amsa duk suka duk'a suka gaishe shi ya d'aga musu hannu bai kalli inda Aliyu yake ba kai tsaye d'akin mahaifiyar sa ya shiga, Jim kad'an ya fito samun da yayi tana wanka ya zauna shima a kan kujerar da ta kasance suna zama in bata wajan bai magana ba. "Dan girman Allah ranka ya dad'e kayi hak'uri bana jurewa tsayuwa kayi min wani hukuncin dan Allah" wani daga cikin ma'aikatan da suke zagaye dashi ya fad'a k'afar sa na rawa sosai. Kallon sa Aliyu bai yi ba balle ya bashi amsa cigaba yake da abinda yake yi, gumi ne yake ketowa daga dukkan kafofin tsohon k'afafun sa sai rawa suke haka jikin sa idanun sa yayi ja sabida wahala, baya yayi zai fad'i Aliyu da yake danna waya yace, "in ka fad'i k'asa ka tabbata yau a tsaye zaka kwana." Dafa kujera yayi jikin sa na cigaba da rawa hawaye na zuba daga idanun sa. Dukka sauran ma'aikatan jikin su yayi sanyi dan ya fisu shekaru a cikin su kowa yasan bashi da lafiyar k'afa balle ya iya tsayawa, Asad da ya ke jin komai yaso ya basar sabida ba shiri suke da Aliyu ba amma ganin abin yayi yawa ne sosai ya saka shi ya kalli tsohon yace, "Zauna!." A sama dukka suka ji maganar tasa Aliyu ya juyo ya kalle shi amma kamar ba shine yace na hankalin sa ma baya wajan su. Tsohon ya kalli Asad suka had'a ido da idanu yayi masa alama da ya zauna, kallon Aliyu yayi yaga shi yake kallo ya kuma kallon Asad yaga shima shi yake kallo duk sai ya rud'e ya rasa abinda zaiyi, maganar wa zaibi a cikin su duk sai ya diririce. Aliyu yace, "ka sake ka zauna wallahi gobe sai na saka an zane k'afafun ka an ji musu ciwo yadda zaka jima baka taka ba." Asad ya mik'e tsam ya k'araso inda tsohon yake ya kama kafad'un sa ya zaunar dashi a k'asa kafin ya kalli Aliyu su had'a idanu ko wanne fuska a d'aure zaiyi magana Asad ya d'aga masa hannu yace, "Bana son hayaniya pls." Kallon ma'aikatan Asad yayi da hannu ya musu alamun me suke a wajan, d'aya daga ciki yace, "muna jiran ya bamu umarnin abinda zamuyi ne ranka ya dad'e" ya fad'a cikin girmamawa yana kallon Asad. Da hannu yayi musu alamun duk su fita daman sun gaji babu b'ata lokaci suka fita tsohon da ya zaunar ya mik'e ya tafi kamar zai fad'i yayi saurin rik'o hannun sa ya tsaya cak sannan ya sake shi tsohon ya duk'a yace, "Allah ya kare ka a duk inda kake, ya baka kariya daga duk ka masu nufin ka da sharri, ya sanya ka zamo sarki a wannan gidan. Allah ya taimake ka ya biya maka dukkan buk'atun ka mai zuciyar alkhairi." Kai kawai ya d'aga masa ya fita da sha'awar rayuwar Asad duk da sarautar da izzar ta ratsa shi amma baya wulak'anta na k'asa dashi. Kamar jira Aliyu yake su fita ya mik'e yana nuna Asad yace, "Kaga Asad ka fita daga rayuwata tun kafin ka tunzura ni nayi maka abinda har ka mutu baza ka manta dashi ba, me kake ji dashi har da zan kira ma'aikata ka saka su fita?, kawai rainin hankali kake ji dashi ko kuma tsabar raini ne?" Ya fad'a a fusace yana kallon sa. Bai ce komai ba sai ma waje da ya samu ya zauna ya cigaba da danna wayar sa dan shi baya son hargagin Aliyu ko kad'an. Hakan da yayi ba k'aramin sake harzuk'a Aliyu yayi ba ya koma gefe yana jan wuci yana k'arewa Asad kallo yana hasashen irin abinda ya kamata yayi masa wanda zai saka ya wuce takaicin da yake ji a zuciyar sa. Sallamar Hydar ta katse su Asad ne ya iya amsawa kawai banda Aliyu Hydar ya k'arasa ya xauna kusa da Asad kafin yace, "Our king how far." Kai ya d'aga masa kawai baice komai ba ganin hakan shima sai ya share ya kalli Aliyu da yake wuce yace, "Ya dai bro?." Ji yayi kamar ya make Hydar ganin rainin hankalin da yayi masa, a gaban idanun sa ya kira Asad sarkin su sannan shi kuma ya kalle shi ya ce masa wai bro, k'wafa yayi yana jijjiga kansa dai-dai nan mahaifiyar su ta fito. "Ya dai triples" ta fad'a tana kallon su ganin haka duk suka mik'e tsaye ta k'araso ta zauna a kan kujera suka zauna a kan carpet ta kalli Aliyu dashi bai zauna ba tace, "Aliyu wai me yake damun ka haka ne?." "Ranki ya dad'e Asad shine yake damuna, har yana da ikon da zan kira ma'aikata zan saka su aiki ya ce su tafi?, me yake tak'ama dashi wanda bana tak'ama dashi?, ki ja masa kunne har ya harzuk'a ni nayi masa abinda bazai manta ba" Kallon Asad tayi tace, "Ina ruwan ka da ma'aikatan sa? Asad Aliyu fa yayan kane why zaka dinga masa halaye irin wad'annan kamar ba jini ka ba?, meyasa bakwa shiri ne?." Asad ya kalli Mama yace, "wulak'anta su yake Mama, bana jure ganin ana wulaƙanta na k'asa dani." "To ina ruwan ka dan na wulak'anta su?, kai na wulak'anta ko wani naka?, kai lallai mai zuciyar tausayi da Imani wa kafi a cikin mu!?" Aliyu ya fad'a da ihu yana kallon sa. Yatsine fuska Asad yake yi ya mayar da idanun sa ya kulle Mama tace, "Aliyu bana son shirme zauna ka daina min shouting a kai na. Wannan halayen naka suna bani mamaki kamar ba jinin sarauta ba." Ba musu ya zauna yana jijjiga kai Mama ta kalli Asad tace, "Ina ruwan ka in ma dafa naman su kazo ka samu yana yi? Ba bayin sa bane?, yana da ikon yi musu duk abinda yake so babu abinda ya shafe ka a ciki, bana son shishshigi Asad dalilin da ya saka bakwa shiri kenan kai da shi." Asad bai ce komai ba daman kuma itama tasan bazai ce ba tace, "Ku had'a kan ku dan Allah bana son wananan tashin hankalin a tsakanin ku, yadda kuke zaune lafiya da Hydar shima da Aliyun ku zauna lafiya." Aliyu ya girgiza kai yace, "ki gafarce ni Mama, Ba'a nemi zaman lafiya ba matuk'ar aka bawa Asad mulkin garin nan, Ba'a nemi kwanciyar hankali ba ko kad'an." Mama ta kalle shi a gajiye da magana irin ta tace, "Wai kai Aliyu waye zai baka mulki ne?, baka kwana a gida sai sanda kaga dama, koda yaushe cikin yawon banza kake da shaye-shaye na banza da wofi, a haka za'a baka mulkin ragamar al'uma?. Ka ajjiye wannan tunanin a ranka ka taya d'an uwan ka neman sarauta domin indai yana raye kai baza kayi mulki ba sai shi." Kallon mahaifiyar tasa yayi da jajayen idanun sa yace, "indai yana raye mahaifiyata tace?." "Eh indai yana raye baza ka mulki garin nan ba, da ace babu shi ne babu kuma Hydar zan shiga na fita wajan ganin ka zama sarkin garin nan kodan cikar burina, amma kash! Asad ya fika duk wani 'karko da ake nema a wajan wanda za'a bawa mulki dalilin da ya saka mahaifin ku ya furta zai bar masa karagar kenan. Hydar ya fila qualities d'in mulkar garin nan tunda shi rashin lafiya ce kawai kuma sai lokaci zuwa lokaci take tashi kai fa?." "In kin min izini zanje na kwanta" ya fad'a muryar sa har sark'ewa take sabida bak'in ciki. "Mu tashi lafiya" ta furta bata kalle shi ba yace, "Godiya nake." Mik'ewa tsaye yayi yana kallon Asad da ba shi yake kallo ba ya lumshe idanun sa kalaman mahaifiyar sa na dawo masa cikin kansa a zuciyar sa sak'a yadda zaiyi da Asad tunda ta furta da dai baya raye ne sai ta san yadda zatayi tabbas zai zama baya rayen kuwa nan kusa, baice komai ba ya girgiza kai ya fita. Asad ya kalli Maman nasu yace, "in anyi min izini zan tafi na kwanta nima." Da kai tayi masa alama da an bashi ya mik'e sannan ya duk'a yace, "Sai da safe" abinda yace kenan ya mik'e Hydar ma haka suka fita tare. Tare suke tafiya Hydar yace, "Deaf bana son mulkin nan ya sub'uce daga hannun ka ya koma hannun Aliyu, babu abinda bro bazai iya ba indai a kan sarautar nan ne." Asad ya sauke numfashi kawai baice komai ya kalli Hydar har zaiyi magana sai kuma ya fasa cewa komai ya d'auke kansa. Murmushi Hydar yayi yace, "ka koyi magana deaf domin nan da wasu kwanaki kad'an zaka zama shugaban wannan gari ba kuma za'ayi shugaba wanda baya magana ba." "Hydar ya zanyi?!" Ya furta da wata irin murya da ya sanya Hydar kallon sa har lokacin tafiya suke yi yace, "Kai kad'ai ka cancanta Deaf, in ba kai ba duk wanda aka bawa mulkin nan komai sai ya lalace, kayi hak'uri domin ya zamar maka dole." Bai bashi amsa ba daman shima yasan iyakacin maganar da zai samu kenan hakan ya saka shi jan bakin sa yayi shiru kawai yana kallon sa. Yana son Asad sosai baya son ganin abinda zai cutar dashi kamar yadda shima yake son sa, yayi alqawarin taya shi yak'i da duk wani mak'iya da suka sako shi a gaba, zai taya shi nemawa kansa kariya a duk inda kariyar take. A haka suka k'arasa babban b'angaren su suka shiga daman sun san baza su samu Aliyu ba kowa ya wuce d'akin sa Hydar yana murmushi ya shiga nasa d'akin. *☆☆☆* "Rauda! Zo ki bani kud'in ciniki na, rainin hankali ne ma irin naki kin san ban karb'i kud'ina ba ina ke ina bacci?" Baba ya fad'a da k'arfi a k'ofar d'akin su. Rauda da bacci ya d'auke ta ta jiyo amon muryar sa ba jimawa ta mik'e tana laluben k'aramar touch light d'in Umma ta d'auko ta kunna tana haska inda zata ga kud'in. Muryar Umma taji tace, "Suna cikin kayan ki kinyi bacci kin barsu shiyasa na b'oye miki." "Wai baza ki kawo min bane?!" Ya sake fad'a cikin d'aga murya yana d'aga laluben d'akin. "D'auko maka nake Baba" ta fad'a cikin muryar bacci tana dube ghana must go na kayan ta ta d'auko kud'in a bak'ar leda ta mik'e ta kawo masa ya karb'a ya kwance yana lissfawa, kallon ta yayi yace, "babu naira hamsin tana ina?." "Fad'uwa tayi Baba." "Kinci uwar ki keda fad'uwar, kaji min yarinya ni zaki kalla kice kin naira hamsin ta fad'i? Ina laifin ma biyar ta fad'i sai ki yarda har hamsin?." "Kayi hak'uri Baba wallahi ban sani ba sai bayan na dawo dana irga naga babu." "Daman ai kin saba, rik'e min canji ba wannan ya zama sabon ki dan kinga ina k'yale ki. Y'ar uwar ki cif ta kawo min kud'ina amma ke da yake bakya son tallah uwar ki ma bata so shine ake rik'e min canji dan nace na daina d'ora miki, to baki isa ba talla yanzu kika fara kuma wallahi sai kin biya ni hamsin d'ina." Yana fad'a ya saki labulen ya tafi nasa d'akin yana mita. Umma ta kalle ta tace, "ya akayi kika yar masa da kud'i?." Idanun Rauda suke ciko da hawaye tace, "Banyi da niya ba Umma ban san ta fad'i ba wallahi." "Da safe cikin cinikin alawar madarar da kike yi ki d'auki hamsin ki bashi in b haka ba kin shiga uku." "To Umma." "Kwanta sai da safe" komawa tayi ta kwanta tana share hawayen ta. Ko kad'an bata son wannan dabi'ar ta Baba baya d'aga k'afa akan kud'i ko waye kai. Kamar kullum da asuba duk ya tashe su kowa ya fito sallah bayan an idar aka jira ya shigo kowa ya gaishe shi sannan aka koma aka kwanta. K'arfe bakwai Rauda ta tashi ta tashi Khairi da Khalil suka fara shirin tafiya makaranta ita kuma ta fara gyare-gyaren gidan. Bata gama aikin ba ta shiga ciki wajan Umman su tace, "Umma gasarar Koko ta k'are gashi su Khalil zasu tafi makaranta." Umma ta mik'e zaune tace, "bai baku kud'in awarar bane?." "Bai bayar ba." Umma ta mik'e tace, "to bara naje naji yadda zamuyi dashi." Ta fad'a tana fitowa shima a lokacin Baba ya fito daga d'aki. Ganin tana nufo shi ya saka yace, "ban kwana da ko sisi ba kar kizo min da maganar kud'i." Umma ta karyar da wuya tace, "ba batun kud'i bane gasara ta k'are ne gashi baka bada kud'in awara ba ga y'an makaranta suna shiri basu ci komai ba." "Ki tafasa musu ruwa hamsin d'in da nake bin Rauda ku siyo ganyen shayi da sikari su sha su tafi." "Bak'in shayi Malam? Kar ka manta fa in suka tafi sai azahar ta yaya zasu gane karatu basu k'oshi ba?." "Kar su gane mana wani ma ai bai sha bak'in shayin ba, tun yaushe nake cewa ki dinga tura su gidan sarki suna karb'o sadakar taliya baki tab'a ba. Ita y'ar uwar ki ai gashi yanzu sun dafa sun ci har sun tafi sun bar naki suna kale." Umma tace, "yanzu malam kana da kud'in da zaka bamu muci baza ka bayar ba har sai munje karb'o sadaka har gidan sarki? Ka duba nisan dake tsakanin mu mana." "Ita wacce taje bata san ciwon kanta ba kenan? Da asuba Rahma take tafiya amma ke y'ar ki y'ar gwal ce baza taje ba sai ku zauna haka ni kinga tafiya ta" ya fad'a yana ficewa ya bar Umma a tsaye. Ummulkhairi ta taso tace, "Umma barshi ba sai munci komai ba ni zan iya dawowa haka in kina da wani abun ki bawa Khalil kawai." Girgiza kai tayi tace, "A'a Ummulkhairi muje ina da naira d'ari biyu ku siyo awara kuci ku tafi." D'aki ta shiga ta d'auko musu Khalil ya siyo musu awara suka ci suka tafi makaranta. Rauda bayan ta gama aikin gidan tayi wanka shiga wajan mahaifiyar tata ta same ta a zaune tayi tagumi tace, "Umma ki daina saka damuwa a ranki, indai batun abinci ne zan dinga zuwa ina karb'owa sai muje tare da Rahman mu dawo." "A'a Rauda ban amince da fitar asuba d'in nan ba, ban kuma amince da ki nemo abinda zaki ci da kanki ba Allah bazai hanani abinda zan baku ba in ya hana mu. Kin san bana son rok'o ne ko yawan cewa a bani da y'an uwana duk wanda na tambaya sai ya bani, yanzu ma ina da shinkafa kwano guda da aka aiko min dashi har gida wanke ki dafa canjin awarar da suka kawo ki siyo mai na hamsin yaji na hamsin muci har dare." Da to ta amsa ta mik'e ta tayi abinda mahaifiyarta ta ta saka ta. Gab da azahar Baba ya dawo ya kwab'e babbar riga ya shiga aikin dafa d'an wake ya gama nan da nan ya kwashe ya lissafa na nawa ne ya zuba masu ya fara kwala musu kira, ita da Rahma suka fito ya kalle su yace, "to gashi nan na naira dubu biyu ne ko waccen ku, wallahi Allah biyar d'ina baza tayi ciwon kai ba." Komawa Rauda tayi ta d'auko hijjabin da tayi sallah ta d'auki abincin ta fita itama Rahma ta fita ba wacce tace kanzil. Daga can inuwa ta hango motar Anas ta ja tsaki a zuciyar ta ta sake d'aure fuskar ta dan ma kar yaga fuskar da zai kulata, hango ta yayi ta tawo ya fito daga motar yana murmushi tazo zata gifta shi kenan ta jiyo amon sautin muryar Baba yana fad'in, "ki tabbatar sai kin biya ni hamsin d'ina ta jiya dan ba bar miki na yi ba!." Runtse idanun ta tayi cikin takaicin dizgi irin na Baba ganin wanda yake tsaye ya saka Baba k'arasowa yana fad'in, "Anas yau kaine da rana haka?." Murmushi Anas yayi ya duk'a har k'asa ya gaida Baba ya amsa da fara'a yana fad'in, "Gashi mutuniyar zata tafi wajan sana'ar ta, kana jina da ita ko? Jiya ta yar min da hamsin shine nace sai ta biya ni shine duka ranta a b'ace." Rauda kamar ta matse bakin Baba haka take ji amma babu dama ta d'aga k'afa zata bar wajan taji Anas yana cewa, "Baba har yanzu Rauda bata daina yawon siyar da abincin nan ba?." "To ya za'ayi Anas dashi muka dogara ai." "Bana son yawon Allah ya sani Baba, inda dama a siyar a gida in ya zama dole, in kuma akwai sana'ar da za'a canja a canja basai sun dinga fitowa ba." Baba ya gyara tsayuwa yace, "Daman sana'ar keke napep d'in nake so to ance kud'i ne dashi tsububu shiyasa muka ganewa abincin." "Babu damuwa Indai za'a daina bata abincin nan ta fita zan siya maka napep Baba." "Kai amma nagode d'an albarka, wannan abu mai shegen kud'i za'a siya min? Wallahi na rasa ma me zance maka dan murna." Anas yace, "Babu komai ai Baba." Baba yace, "talla ai daga yau ta daina zuwa yau d'in ma dan kar ayi asara ne" ya fad'a yana murmushi yana kallon sa. Kallon Rauda yayi yace, "Rauda na nawa ne abincin?." Kafin ta bada amsa Baba yace, "Na dubu uku ne." Da sauri ta kalle shi shima ya kalle ta ya d'auke kai Anas ya zaro dubu biyar ya bawa Baba yace, "na siye na yau, dan Allah Baba a daina bata tallan nan bana so wallahi." Hannun Baba har rawa yake ya karb'a yana zuba godiya Anas yace, "Babu komai Baba, zanyi tafiya yau bazan jima ba zan dawo dana dawo za'a kawo maka napep d'in in sha Allah, amma dan Allah a hak'ura da tallan nan dan Allah badan ni ba." "Ai an gama Anas baza a kuma ba in Allah ya yadda." "Na gode Baba." Baba ya kalle ta yace, "bani kular na shiga ciki ku gaisa" ya fad'a yana karb'a ya wuce ya tafi gida ita kuwa ji take takaici kamar ya shek'e ta. Kallon ta Anas yayi yace, "kiyi hak'uri nasan na takura miki Rauda, Ina son ki ne da zuciya d'aya kuma auren ki zanyi." Bata ce komai ba ya kuma cewa, "Dan Allah kice wani abu mana Rauda." "Me zance to? Na fad'a maka ni ba aure zanyi ba ka fita daga rayuwata ka nemi dai-dai kai amma kak'i." "Kece dai-dai Rauda ko shekara nawa zakiyi nan gaba zan jira ki har ki shirya yin auren, Ina son ki Allah ya sani." Bata ce komai ba yace, "ki bani number wayar ki zanyi tafiya ina so muryar ki ta dinga debe min kewa." "Bani da waya, na gode da abinda ka bawa mahaifina Allah ya saka alkhairi, sai anjima" ta fad'a zata wuce yayi saurin cewa, "Dan girman Allah ki tsaya." Ba musu ta tsaya ya ya bud'e mota ya d'auko farar envelop ya mik'o mata yace, "ki karb'i wannan kya sha ruwa." Kallon sa tayi ta kalli takardar tace, "na gode." "Dan Allah ki karb'a." "Kayi hak'uri bazan iya ba." "Da hannu a jikin ki kice baza ki iya karb'a ba?, Rauda meyasa kike.mayar da hannun kyauta baya bayan kin san babu kyau hakan?!" Baba ya fad'a yana k'arasowa wajan yana kallon ta. *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023. ©️ *Nana Haleema.* *004.* Runtse idanu Rauda tayi ji take ina ma k'asar wajan ta tsage ta shiga sabida kunya da takaicin abinda Baba yayi mata a wajan, ba'a b'ata yi mata abinda ta jishi a zuciyar ta kamar wannan lokacin ba, kafin ta gama wani tunani har ya k'araso kusa da ita daidai kunnen ta yace, "y'ar bak'in ciki baza ki karb'a ba?." Idanun ta ta bud'e ta kalli Anas da yake kallon su ta kalli Baba da yake ta yi masa murmushi. K'arasowa yayi ya sake mik'a mata kud'in ta nok'e hannun ta idanun ta na kawo ruwa Baba yace, "Ki karb'a mana ai ba'a mayar da hannun kyauta baya." Hawaye ya sakko daga idanun ta ta mik'a hannu ta karb'a hannun ta har rawa yake Baba ya washe baki ganin kud'in sun shiga hannun ta yace, "Madallah Anas ana ta shan hidima Allah ya saka da alkhairi." Murmushi yayi yace, "Babu komai Baba, zan koma a gaida mutanen gidan" ya fad'a da girmamawa har yana rage tsayin sa Baba yace, "to ba madallah, a gaida mutanen gidan dakyau." Anas ya amsa yana wucewa ya shiga mota ya ja ya bar unguwar zuciyar sa kamar sake kwarara masa son Rauda ake yi domin ya tabbatar in ya same ta ya samu wacce ta aure shi ba dan kud'in shi ba. A guje ya rufa mata baya ya tare ta a soro yace, "Ke Rauda! Bani kud'in mu ga." Ba musu ta mik'a masa ya b'are takarda ya ciro kud'in yana lissfawa. Dubu ashirin ne cif a ciki Baba baki yak'i rufuwa ya raba biyu ya d'auki dubu goma ya mik'a mata goma yace, "sai ku raba ke da babar ki badan na haife ki ba ai da baki samu ba" ya fad'a yana sokawa aljihu yana gyara zaman hular kansa. Babu yadda ta iya ta karb'a ta wuce ciki ta shiga d'akin Umman ta fuskar ta a chucule, a zaune ta same ta zauna itama Umma tace, "kiyi hak'uri Rauda babu yadda zakiyi da halin mahaifin ki bazai canju ba shekaru sun riga sun tafi, yace min wai saurayin ki ya siye d'an waken gashi nan mu ci har gobe da safe." Rauda ta goge idanun ta tace, "haka yaje ya saka shi a gaba fa Umma har yace zai siya masa napep bayan nan ya bani kud'i naki karb'a Umma yazo ya saka dole sai na karb'a ya raba kud'in biyu ya d'auki rabi wai in da bai haife ni ba ai bazan samu ba. Yanzu Umma dan Allah ko Anas d'in na aura bai riga ya zubar min da mutunci a idanun sa ba?." "To ya zakiyi ba'a canja mahaifi sai hak'uri, halin sane wannan mazajen yayyen ki ma da basu da kud'i ya suka cika dashi balle Anas mai kud'i?." "Ga kud'in Umma, ni gidan Yaya Ummi ma nake so naje" ta fad'a tana mik'a mata kud'in ta karb'a tana kallon kud'in tace, "Allah ya sani bana son karb'ar kud'i hannun saurayi musamman ma irin Anas, a haka dai bashi da hali mara kyau amma.....to Allah dai ya kyauta" ta fad'a tana ajjiye kud'in jikin ta duk babu dad'i. "Amin. Zanje gidan Yaya Ummi Umma, anjima zan dawo." "To d'auki d'ari biyar ki hau motar zuwa da dawowa kar kije can ki d'ora mata nauyin kud'in mota itama ba k'arfi ne da mijin nata ba." Ba musu ta karb'a ta tashi ta saka talamin ta ta fita. Bata jima ba ta samu abin hawa ta tafi gidan yayar tata, har k'ofar gidan ta abin hawan ya tsaya ta sauka ta basa kud'in sa ta shiga cikin gida. Tana tsakar gida tana aiki gidan shiru yara an tafi makaranta ta shiga da sallama, amasawa tayi ta d'ago tana kallon ta tana fad'in, "Maraba da amaryar Anas" ta fad'a cikin zolaya tana dariya. Sai kuwa ta d'aure fuska ta k'arasa kan tabarmar da ta gani a shinfid'e ta zauna tana fad'in, "Allah Yaya shiyasa bana son zuwa gida nan wani lokacin." Dariya tayi ta bar abinda take yi ta dawo kusa da ita ta zauna tace, "to k'arya nayi? Ke a tunanin ki Baba zai bar Anas ya kufce masa bai bashi ke ba?, ai wallahi ko auren dole ne sai Baba yayi miki sai dai ki mutu." "Hmmmm bari kawai Yaya, lamarin Baba sai shi." "Yanzu dai ya Ummana tana lafiya?." "Lafiya lau, tana gaishe ki." "Yau ina tallan?." "Na fito zan tafi Anas yana k'ofar gida shine fa ya siye har da ninkawa Baba kud'in yace a daina bani talla, wai Baba yace masa wai napep yake so ya siya kuma babu kud'i, a tak'aice dai yace zai siya masa." Yaya ta girgiza kai tace, "Allah ya kyauta, lamarin Baba sai addu'a." "Amin, kin san me Yaya." "Sai kin fad'a." "Mafarki nayi ina makaranta ina karantar aikin jarida." Yaya Ummi ta dara kad'an tace, "Wannan mafarki naki na aikin jarida Allah yasa ya tabbata Rauda." "Badai a gidan Baba ba." "Ha! Ha! Daman sai dai in kin auri Anas" Yaya Ummi ta fad'a tana dariya. Rauda tace, "Kin san kuma kwana biyun nan sai na dinga mafarkin mutane masu fuska iri d'aya ko wanne da rawani a kansa, d'aya yana b'angaren dama d'aya hana haggu, a tsakiya kuma nice in na tafi wajan d'aya sai na kasa k'arasawa in na koma wajan d'aya ma sai na kasa zuwa. Ina yawan wannan mafarkin amma har yanzu na kasa rik'e fuskokin mazan guda biyu." Yaya tace, "tofa, Allah mai hikima shi kad'ai yasan meya b'oye a cikin mafarkin naki, koma dai meye Allah yasa alkhairi ne shine fatan mu." "Amin Yaya." Daga nan suka cigaba da hirar su. *☆☆☆* Tunda garin Allah ya waye ya samu labarin mai martaba da Asad sun fita hankalin sa yayi mugun tashi, safa da marwa yake a d'akin ransa a b'ace zuciyar sa yske so ta bashi mafita akan Asad amma har lokacin ya kasa samun matsaya. Tashin hankalin sa da damuwar sa bai san me zasu tattauna da mai martaba ba abinda yake sake d'aga masa hankali kenan ya kasa zaune ya kasa tsaye, Suhail ne ya shigo ganin halin da mahaifin sa yake ciki ya saka yace, "Ranka ya dad'e lafiya?." "Asad ya fad'a maka dalilin fitar su da mai martaba?." "A'a bai fad'a min ban ma san zasuyi tafiyar ba." "Oh god! Laifin kane Suhail da ka bashi madarar nan jiya duk da ba haka ba, yanzu gashi sun tafi taro Kaduna ko ni ba'a nema ba matsayina na waziri a masarauta daga shi sai ni amma ya tafi daga shi sai Asad, me suke so su mayar dani ne a masarautar nan?." Yadda yake fad'a tashin hankali ya bayyana k'arara a tare dashi Suhail ya kwantar da murya yace, "Kayi hak'uri Abba ka bani lokaci matuk'ar ina raye babu wanda zai mulki garin nan sai kai." "Kana shirme a haka zan mulki garin?! Ka manta kane ka b'arar da damar da ya k'i shan madarar nan jiya?, kasan mahimmacin maganin da na baka kuwa Suhail?. Na baka sabida na yadda dakai amma sai ka bani kunya" Ya fad'a da fad'a sosai yana kallon sa. "Abba indai kaine ka haife ni nayi maka alqawarin zan yi duk abinda zanyi wajan ganin bayan Asad bama shi kad'ai ba dukka su ukun a hankali kowa zai k'are, ka bar komai a hannuna barewa baza tayi gudu d'an ta yayi rarrafe ba, zan baka mamaki Abba zan tabbatar maka da Jarumi ka haifa" yana fad'a ya fita daga falon ya ya bar mahaifin nasa a tsaye yana kallon sa. Murmushin jin dad'i yayi jin abinda Suhail yace ko babu kowa hankalin sa ya kwanta kad'an. Sai a lokacin ya samu dama da kwanciyar hankalin fita daga gidan. A cikin gidan sarki kuwa Mama tana zaune a falon ta ita da k'awar ta kuma aminiyar ta mai suna Sadiya suna tattaunawa Mama tace, "Sadiya bana son wani tsaiko ko katanga da zata shiga tsakanin Asad da mulkin garin nan, in wani daga cikin yaran nan baiyi mulki a garin nan ba na shiga uku Sadiya." "Baza ki shiga uku ba ranki ya dad'e, ai mulki ma kamar Asad yayi ya gama ne, in kika cire rashin son magana irin na Asad bashi da wani aibun da za'a hana shi mulki, to a tak'aice ma waye yake da qualities d'in da yake dasu kaf gidan nan da dangin mai martaban?." Mama tace, "Babu, amma kin san akwai y'an taka haye, tsaf waziri da Sa'adatu zasu shiga su fita wajan ganin buri na bai cika ba, zasu iya ni na sani hatsabibai ne sune suka mayar min da Aliyu na haka, sune suka mayar da Hydar haka, Asad ma ya gagare su ne shiyasa suka kasa yi masa komai. In kika duba su galadima da sauran y'an uwan mai martaba basu damu da sarautar nan ba harkar gaban su kawai suke banda shi. Sadiya idan Asad baiyi mulkin nan ba zan iya mutuwa." "Baza ki mutu ba ranki ya dad'e sai kin d'auki jikan ki d'an sarki kuma jikan sarki shima kuma sarki, Muma ai ba zuba idanu zamuyi muna kallon su muna da namu hanyoyin da zamu bi wajan ganin mun b'arar da duk wani hatsabiban cin su." Numfashi ta sauke tace, "ni bana jin wannan Sadiya, duk wani jifa da zasu yo mana su sun san nima ba kanwar lasa bace, abinda yake gabana a yanzu bai wuce Asad, baya son mulkin nan ko kad'an balle ya mayar da hankali a kai, ki duba inda yana da hankali yana kuma son abin yadda ake maganar nan da yanzu bai nemi matar aure an yi biki an gama ba?." Jin hakan sai Sadiya ta sake gyara zama tana murmushi tace, "Abinda ya kamata kenan Ranki ya dad'e, ki tilasta masa yazo yaga Jidda ayi komai a gama tunda sai yana da aure za'a bashi mulkin nan. Kuma Jidda y'ar gida ce ba buk'atar a tsaya bincike ko wani dogon jawabi ba." "Bari kawai Sadiya, Asad baud'ad'en hali ne dashi baya ganewa ko kad'an abinda yake gaban sa kawai shi yake yi, dole ma a dawo da maganar Jidda ko bai sani ba za'a d'aura auren sa da ita sai dai yaji labari kawai." Sadiya tace, "A'a ranki ya dad'e sai aita magana kuma a masarautar nan ace dan a bashi mulki kika yi masa auren dole, ki bar shi ayi komai da sanin sa na tabbata ai bazai k'i zab'in ki ba." Kai take girgizawa kafin tace, "Sadiya duk wanda zai shiga tsakani na da mulkin nan sai na kawar dashi, bana son wani tsaiko ko katanga a tsakanin Asad da karagar mulkin garin nan, burina na zama uwar sarki kuma zai ta tabbata, bazan lamunci wani abu da zai b'ullo daga sama ba, ko meye shi bazan lamunta!." Sadiya tace, "babu shi ranki ya dad'e, ko meye shi munfi k'arfin sa, ko aljan ne a gaba muke dasu balle mutum, haba shi d'in yasan karo da aljani ba dad'i." Kai take girgizawa ta lumshe idanu kafin tace, "Ina da buk'atar zuwa Kano." "Kina da iko ranki ya dad'e." Cize baki take zuciyar ta nayi mata tiriri bata son duk abinda zai hana Asad yin sarauta ko meye shi. A b'angaren waziri a zaune suke a katafaran falo na alfarma shida Hajiya uwar gidan sarki kenan sai Suhail a gefen su a zaune waziri yace, "kina da masaniya akan fitar da mai martaba yayi da Asad?." "Ina nake da ita a gaba dai ya fad'a masa amma bai ce ga abinda zai kai su ba. Nifa na gaji a wannan tafiyar da sukayi Allah kad'ai yasan abinda suka k'ulla shiyasa ko kai ba'a nema ba, a kawar da Asad kawai shine jin dad'i na." Numfashi waziri ya fesar yana kallon sama kafin yace, "farkawa rana d'aya tsaka a rasa Asad ba k'aramin abu bane sai dai muyi masa abinda zai bi jikin sa ta yadda koda mutuwar yayi ba wanda zai zargi komai." Tace, "to ya za'ayi kenan?." Wani abu ya jawo a gefen sa ya d'auko ya kwance ya fito da wata laya k'arama an nannad'e ta da bak'in zare ya nuna mata yace, "Wannan nake so a saka a k'asan kafitar da yake kwanciya, matuk'ar yayi kwana uku yana kwanciya a kai zance ya k'are. A hankali abin zai dinga shiga jikin sa rana d'aya kawai sai a neme shi a rasa." Kallon sa take yi hakan ya saka yace, "babban aikin shine wanda zai saka shi a k'asan katitar tasa, kin san ko a cikin nasu d'akin sa yana da wahalar shiga." Hajiya ta kalli Suhail tace, "Suhail shine zaiyi wannan aikin domin Asad ya amince dashi koda ya shiga d'akin sa bazai kawo komai ba." "Anya Suhail zai iya?, bana so a samu matsala ne kamar wancan lokacin" ya fad'a yana kallon Suhail d'in. Suhail ya gyara zama yace, "a wannan karon baza'a samu wata matsala ba Abba, zanyi iya bakin k'ok'arina wajan ganin na saka masa ina da tabbacin bazai kawo komai a ransa ba." Hajiya ta girgiza kai tace, "ni nasan zaka iya kai kad'ai ne daman ya cancanci ka yi wannan aikin in ka duba ko bayi basa shiga d'akin Asad, har kawo gobe ban san wacece ko waye yake gyara masa d'aki ba." Waziri ya girgiza kai yace, "gashi Suhail ka kula kar a samu matsala kamar wancan, ka tabbatar ka saka masa wannan layar a k'asan Katifar sa." Karb'a Suhail yayi ya juya layar a hannun sa sannan ya saka a aljihu yace, "babu damuwa an gama." "Shikenan tashi kaje" mahaifin sa ya basa umarni ba musu ya tashi ya fita. "Wai kana da tabbacin wannan abinda ka bayar zai yi mana abinda muke so kuwa?." Kallon ta yayi yace, "kar ki damu ni nasan abinda na bayar ai in kin amince da abinda zan iya to ki yadda." "Allah ya bamu sa'a." "Amin. Zan fita yanzu daga gidan daga baya sai ki fita kema." Kai ta d'aga ya fita ta bishi da kallo tana tunanin mafitar waziri ba mafita bace dole ta samo mafita da kanta. Suhail yana barin gidan cikin gidan sarki ya tafi yana zuwa kasancewar bashi da shamaki da ko ina b'angaren mazan ya tafi, nan ya samu Aliyu baya nan sai Hydar shida abokin Asad Hafiz suna zaune duk da ba hira suke ba, da sallama ya shigo ya samu waje ya zauna yace, "Hydar barkan ku." Amsawa sukayi dukkan su daga nan kowa yayi shiru. Can ba jimawa Suhail ya mik'e tsaye direct ya nufi k'ofar da zata kai shi d'akin Asad yana gab da shiga Hafiz yace, "Suhail Asad baya nan." Cize baki yayi tare da runtse idanun sa kafin ya juyo bayan ya daidaita fuskar sa yace, "yeah I know, zanyi amfani da toilet d'in sa ne." "Nooo ga public a falon nan in ma ba shi ba why not kayi using dana Hydar." Suhail ya kalle shi shima shi yake kallo kafin yace, "okay" abinda yace kenan ya juya zuwa band'akin da yake falon ya shiga badan zaiyi wani abun ba sai dan ya kawar da shakku. Babu wanda ya yi magana a cikin su har ya fito ya zauna nan ma babu wanda ya tanka kowa da abinda yake yi. Sun jima a haka babu wanda ya motsa kafin Hydar ya tashi ya shiga d'akin sa ya barsu a falo, shi Hafiz yana so Suhail ya fita dan baya son barin sa wajan shi kad'ai shima kuma yana so ya tafi domin ya cimma k'udurin sa. Dukkan su haushin juna suke ji babu wanda yake magana babu wanda kuma yayi yunk'urin motsawa. Ganin Hafiz yana yi masa wani kallo na rashin gaskiya kawai sai ya tashi ya fita ya bar masa falon da sabuwar niya da kuduri a zuciyar sa. *☆☆☆* Rauda kuwa bayan sallar azahar ta dawo unguwar su tana gab da shiga layin su ta had'u da k'awayen ta guda biyu Walida da Habiba suna fitowa ta tsaya tana kallon su tace, "ku kuma ina zuwa da rana haka?." Habiba tace, "Rauda manyan gari ke daga ina kike?." "Gidan Yaya Ummi naje." "Gidan sarki zamu je zan raka Habiba karb'o sak'o" Walida ta bata amsa tana kallon ta. "Sai kun dawo Allah ya kiyaye." Habiba tayi y'ar dariya tace, "banza matsoraciya, kizo muje." "Ni y'ar gidan baban mu, rufa min asiri babu inda zani." Walida tace, "ke kuwa kizo muje mana yanzu fa zamu dawo." Ta rausayar da kai tace, "kin san ni tsoron doki nake kuma wannan dogaran bulalar hannu su na bani tsoro wallahi." Habiba tace, "to ina ruwan ki da doki muda ba turken su zamu je ba?, dogarai kuma ai ba ciki zamu shiga bafa k'ark'arin mu wajan Gwaggo ta sai mu dawo." Rauda tace, "kedai Habiba dan kin saba dasu ne kina zuwa ni kam tsoro nake ji." Jan hannun ta Walida tayi tace, "Dallah can muje an fad'a miki baza mu shiga ciki ba ko banza kya kashe kwarkwatar idanun ki dan nasan baki tab'a shiga ba." Haka suka rankaya tafi suna hira Habiba tace, "Wallahi Rauda ke kam matsoraciya ce meye abin tsoro a doki da dogarai?." Dariya tayi kad'an tace, "to abinda baka saba gani ba mana Habiba ai dole naji tsoro, nifa ban tab'a shiga cikin gidan ba tunda nake, zaki ga ko hawan sallah ake bana lek'owa sabida tsoron doki kar yayo kaina." "Shiyasa muka ce kizo muje ai" Walida ta bata amsa suna cigaba da tafiya. Sun yi tafiya mai d'an nisa kafin suka iso babban gate d'in farko na gidan sarki. Ganin Rauda zata bayar dasu jiki har ya fara rawa ya saka ta suka rik'o ta suka shiga ciki, gate d'in farko suka fara wucewa na cikin masarautar suna ta tafiya domin da nisa kafin kaje gate na biyu, sun wuce gate na biyu suka zo wajan dokuna zasu wuce Rauda ta tsaya cak a wajan idanun ta na kawo ruwa tana girgiza musu kai, "Habiba tace, "kizo mu wuce Rauda babu abinda zasu yi miki." Kai take girgizawa tana kallo dokunan tace, "bazan iya ba nidai kuje, bazan iya zuwa ba." Walida ta kalli Habiba Habiba tace, "to ki jira mu a nan zamu je yanzu mu dawo, kar ki motsa." Kai kawai ta d'aga sukayi gaba suna waiwayon ta suka shiga gate na biyu. Doki d'aya ta gani kamar zai yo kanta ta zabura ta bi wata k'ofa da ta gani a bud'e a guje hawaye yana sakko mata daga idanun ta dan ta tsorata sosai bata son ganin doki ko kad'an hakan ya saka ta gigice har bata ganin abinda yake gabanta hankalin ta ya tafi wajan ganin ta nemi mafaka da zata b'uya. Ba zato babu tsammani tayi karo da mutum kafin ta dawo daidai tasan waye ta bashi hak'uri taji an shararawa fuskar ta mari......... *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023. ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *005.* Yadda ta gigice idanun ta ya firfito abin tausayi ne jikinta ya tsananta rawa haka hawayen idanun ta suka cigaba da zuba ta kasa koda d'ago kanta balle ma tasan wanda yayi mata kyakykyawan mari haka. A haukace Aliyu yake k'are mata kallo ransa a mugun a b'ace har wuci yake sabida b'acin rai yana binta da banza kallo yace, "Kuna ina!" Ya fad'a cikin murya mai amo har sai da Rauda tayi baya tana rutse idanun ta sabida yadda taji sautin har cikin zuciyar ta. A guje dogarai guda biyu suka shigo suka zube a k'asa ya bisu da kallon wulaƙanci yace, "wacece wannan?" Ya fad'a yana nuna musu Rauda da take tsaye idanun ta a rufe. Kallon ta sukayi wani daga cikin su yace, "ke y'ar talakawa durk'usa mana!." Jikin Rauda na rawa ta zube guiwa a k'asa jikin ta na rawa sosai duk tsoro ya gama kama mata zuciya. Kallon sa sukayi suka ce, "Allah ya ja zamanin Yarima ban mu santa ba." Aliyu ya kuma fusata yace, "kenan daman barin wajan kuke babu kowa duk wanda yazo ya shigo sanda ya ga dama?." Su kansu jikin su rawa yake domin tabbas zai iya sakawa a canja musu wajan zama hakan ya saka a tsorace d'aya yace, "tuba muke ranka ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ka, mun amsa kiran Gimbiya ne." Tunda suka ce gimbiya yasan Mama suke nufi hakan ya saka shi jan dogon tsaki yace, "ku d'auke ta kuje a hukunta ta tunda bata da bakin bada hak'uri" yana fad'a ya juya ya fita daga wajan a fusace. Har lokacin jikin Rauda rawa yake yi suka mik'e d'aya daga cikin su ya kalle ta yace, "tashi y'ar talakawa yau kin d'ebo ruwan dafa kan ki." Jikin Rauda na rawa ta mik'e har lokacin kuka take ta kasa cewa komai, ba wai tsoron sa take ji ba a'a tsoron doki da kuma masu bulalan nan shine yake sake hargitsa ta. Fitowa sukayi daga wajan daidai nan Habiba da Walida sun fito da alama neman ta suke yi ganin hakan ya saka tawo wajan da sauri Habiba tace, "Allah ya ja zamanin sarkin k'ofa." "Habiba kin san tane?" Ya fad'a yana kallon ta. "Na san ta Yallab'ai, k'awa tace rakiya tayi min tana jin tsoron dokuna shiyasa bamu wuce ciki muka ce ta jira mu." "Ta yiwa yarima Aliyu laifi yana tafiya ta bangaje shi kin kuma san tunda yace ayi mata hukunci babu wanda ya isa ya hana sai mutum biyu kuma basa nan." Habiba cikin girmamawa ta kuma cewa, "Wallahi Yallab'ai bata tab'a zuwa gidan nan ba yanzun ma nice na jawo ta dan Allah ayi hak'uri a sassauta mata." "Habiba ba daga ni bane daga shi ne ke kin san halin sa." Zata kuma magana suka hango shi ya tawo lokaci d'aya suka dare hanya yana zuwa zai wuce Habiba tace, "Allah ya ja zamanin yarima mai jiran gado, Allah yayi maka sarkin katagum, Allah yasa ka gaji mai martaba, kaine sarki na goma sha hud'u da izinin Allah. Ranka ya dad'e muna rok'on alfarma, k'awata ce bata tab'a zuwa gidan nan ba sai yau bata san hanyar da zata bi ba, na tabbata kuskure tayi ta shiga inda kake, ina ita ina yarima katagum?, ina ita ina sarkin mu?, ina ita ina shugaban mu baki d'aya?. Ayi mata afuwa ranka ya dad'e" ta fad'a da girmamawa bayan ta zube a k'asa tana tab'a Rauda da har lokacin jikin ta yake bala'in rawa. "Allah ya wuci zuciyar ka" abinda Rauda ta iya fad'a kenan murya na rawa jikin ta ma na rawa tsoron ta d'aya kar ya saka a kaita wajan doki. Kirarin da Habiba tayi masa ya shige shi hakan ya saka shi ya motsa yatsun sa biyu alamun su tafi kafin yaji ma mai zasu ce ya wuce ciki a abin sa. Wanda yake kusa da sarkin k'ofa ya kalle su yace, "Kinyi sa'a yarinya, maza ku tashi ku tafi kafin ya fito ya canja shawara." Ai kamar jira suke suka mik'e a guje suka yi hanyar fita Rauda na kuka sosai lokacin Hydar ya fito yaga gift giftwar su fusksr Rauda kawai ya gani tana hawaye daga nan kuma sai suka wuce. D'an lekawa yayi yana kallon su a ransa yana tambayar ko wacece take kuka oho. Tafiya suke har lokacin Rauda kuka take yi Walida tace, "mune muka ja miki Kiyi hak'uri dan Allah." Habiba tace, "badan mun tilasta ki ba da yanzu babu abinda ya faru, kiyi hak'uri dan Allah ki daina wannan kukan kinga a kan hanya muke fa sai aita kallon ki." Rauda kuwa ba kukan marin da yayi mata take ba kawai ita a tsorace take ne gani take kamar dokunan zasu biyo ta su kamata. Habiba tace, "kiyi hak'uri haka halin yarima Aliyu yake, bashi da kirki ko kad'an bai d'auki talaka a bakin komai ba ya mayar dasu kamar k'asar da zai taka ya wuce, yadda baya tausayin k'asa yake taka ta da zafin nama haka baya tausayin talaka. Kowa a gidan nan tsoron yi mata laifi yake domin duk tsufan ka koda furfurar ka tana jan k'asa wallahi sai ya saka an maka hukunci. A haka kuma shine zai zama sarkin garin namu." Walida tace, "mun shiga uku Habiba, akace d'an uwan sa ne." "Tabd'ijam naki wasa ne Walida, to yadda yake son mulki babu wanda ya isa ya hana shi mulkar garin nan, ke baki ga kirarin da nayi masa bane ya saka ya k'yale Rauda?, ai wallahi da yadda ya furta hukuncin nan sai ya hukunta ta. D'an uwan shine simple babu ruwan sa wallahi kika gan shi baza kice jinin sarauta bane sabida babu abinda ya dame shi, illar kawai shi bashi da lafiyar kwakwalwar in ciwon sa ya tashi sai yayi sati uku a sume." "Allah sarki abin tausayi, aka ce kuma y'an uku ne." "Eh uku ne ban tab'a ganin na ukun ba gaskiya kasancewar shi ba mai hayaniya bane ba, ace sai ya kwana ya wuni baice kanzil ba shiyasa ma baya fitowa sabida baya son gaisuwa. Ke kona ganshi bazan banbance su ba." Walida tace, "tofa lallai." "Bari kedai, kuma kinga yadda kika ga Aliyun nan haka babar su take ke tama fi Aliyu izza da k'asaita da saka tsinin takalmi ta murtsuke talaka. yar sarki ce kuma jikar sarki ce gata matar sarki, burin ta d'aya tak d'anta yayi sarki kuma zasu yi tunda sune kawai manya y'ay'an mai martaba maza a gidan." "In sha Allah baza suyi ba, wannan ya zama sarki ai mun shiga uku, taliyar da muke karb'owa kullum ma sai ya saka an daina bamu." Habiba tace, "kedai ki tsuke baki kawai dan wallahi in kinga yaran nan basu yi mulkin katagum ba sai dai in Allah ne ya nuna ikon sa, dan matar nan da kike gani sai addu'a kawai." "Allah muka ce ai muma." Habiba ta kalli Rauda da tayi shiru da alama har lokacin a tsorace take tace, "kiyi hak'uri Rauda dan Allah." Kai kawai ta d'aga suna tafiya suna hira sama-sama har aka zo k'ofar gidan su Rauda ta shiga su kuma suka wuce. Da Rahma suka yi karo ta dawo daga siyar da abinci tana ganin Rauda tace, "yau kin samu sake har da tafiya gidan Yaya Ummi ko?." Bata iya bata amsa ba ta wuce d'akin Umma har lokacin k'irjin ta bugawa yake. Umma da ta ga shigowar ta tana tsaye tana gyara labule tace, "ke kuma lafiya na ganki wujuga-wujuga?." Sai da ta zauna ta sauke numfashi ta kalli Khairi tace, "Khairi bani ruwa." Bata musa ba ta tashi ta kawo mata a kofi ta sha ta dire kofin tana ajiyar zuciya. Umma tace, "lafiya?." "Umma gidan sarki su Habiba suka jani na raka su." "A ina kika gansu?." "Lokacin da na dawo daga gidan Yaya Ummi suka ce nazo muje tunda ban tab'a shiga ba." Khairi ta fashe da dariya tace, "to Anty shine kuma kike wannan hakkin?." Umma taja tsaki tace, "ragwanta irin ta Rauda fa." Rauda tace, "Umma dokuna fa na gani zasu biyo ni na tsorata zan gudu naje na bangaje d'an sarki." Ta bud'e baki tace, "too! Amma dai ba'a yi miki komai ba ko?." "Marina yayi Umma ya dinga ci min mutunci wai y'ar talakawa ya saka a min hukunci Allah ya kawo Habiba ta dinga yi masa kirari sannan ya hak'ura. Wallahi bashi da Imani bai san darajar d'an Adam ba na tsane shi sam bana son sa. Kuma wallahi badan ina jin tsoron doki ba babu abinda zai hana ban mayar masa da maganar da ya fad'a min ba." Umma ta murmusa tace, "kedai tunda kin kub'uta Alhamdulillah, batun kina son sa ko bakya son sa ai bai tashi ba daman ke meye naki da zaki so shi? Ai sai kallo daga nesa. Naji ana labarin sa ance bashi da kirki sosai gwara da Allah yasa tsoron doki ya hana ki yi masa tsiwa ai." "Umma sai ma Habiba na baki labarin sa, nima gashi naga zahiri baya da kirki ko kad'an." Umma tace, "tunda dai lafiya Alhamdulillah, mari kuma Allah zai saka miki." Khalil da ya shigo yake cewa, "Anty d'azu Rahma tazo tana ta fad'a wai yau baki je siyar da abinci ba." Shiru tayi bata amsa ba ta kwanta a kan katifar Umma har lokacin k'irjin ta bugawa yake fuskar Aliyu na wulga mata a idanun ta. *☆☆☆* Mai martaba basu dawo ba sai dare har lokacin babu wanda yasan me suka tattauna a hanyar su, a gajiye Asad yake koda ya raka mahaifin nasa b'angaren sa nasu b'angaren yana shiga ya tarar da Suhail a falon shi kad'ai a zaune. Yana ganin sa ya mik'e tsaye yana fad'in, "Welcome back Prince." Kai kawai ya iya d'aga masa ya shiga cikin d'akin sa ganin hakan Suhail ya murmusa zuciyar sa fal farin ciki ya fita. Wanka Asad yayi ya canja kaya zuwa marasa nauyi a gajiye yake yana so ya huta amma kiran wayar Mama ya hana shi sukuni tun suna hanya take waya hakan ya saka shi fita ya nufi b'angaren ta. A zaune ya tarar da ita daga ita sai Suhaima ya shiga da sallama. Kallon sa take har ya zauna kusa da k'afafun ta ta kalle shi tace, "kun sha hanya." Idanun sa ya lumshe ya bud'e alamun sosai ma kuwa. "Me kuka tattauna a hanyar taku?." Kallon Mama yayi kafin ya buɗe baki yace, "Mama bamu yi komai ba." "K'arya bata tsarin halayyar ka Asad ka fad'a min me kuka tattauna." Juya idanun sa yayi kawai baice komai ba tace, "kafi kowa sanin bana jure wannan shirun naka kayi min magana kun tattauna game da sarautar ka?." Kamar zaiyi kuka ya kalle ta ya girgiza kai alamun a'a, ta fusata tace, "magana zakayi min malam!, kun tattauna ko a'a?." "Mama bamu tattauna akan komai ba, inda munyi mahaifiyata tasan bazan b'oye mata ba." abinda ya iya fad'a kenan yana dafe jijiyoyin kansa da suke harbawa a gajiye yake sosai ga maganar Mama tana sake d'ora masa damuwa. Suhaima da take kallon Mama kamar zata yiwa Yayan ta kuka tasan ya gaji gashi baya son magana ga shi sai tsawa take masa kamar ba ita ba. kallon Suhaima tayi tace, "kawo masa abinci yaci." Mik'ewa tayi ba jimawa ta kawo masa bai musu ba ya karb'a yaci abinda zaici ya bar ragowar ta kalle shi tace, "naji na k'yale ka yanzu amma gobe zaka fad'a min abinda kuka tattauna. Sannan nifa ban amince da Suhail ba mahaifin sa munafuki ne ka kula dashi bana so na gan ku tare dan komai zai iya faruwa, bana son ko meye a duniyar nan da zai kawo tangard'a a cikin sarautar da zata dawo hannun ka." Rausayar da kai yayi a hankali yace, "Sarauta again!." "Ehh, itace burina kuma matuk'ar ina raye sai kayi, kaje ka nutsu gobe zamu cigaba da tattaunawa." Kallon ta yayi ta wara idanun ta a cikin nasa ya sauke nasa k'asa tace, "Asad ko kai baka isa kace baza kayi mulkin nan ba matuk'ar na isa da kai, in kaga baka yi wannan sarautar ba ka tabbatar bana raye ne." Kai ya jijjaga kawai yayi mata sallama mik'e ya kalli Suhaima da take kallon sa ya d'auke kansa ya fita. Suhaima ma bata ce komai ba ta mik'e ta shige ciki itama Maman mik'ewa tayi ta shirya tsaf sai b'angaren mai martaba. Lokacin da ta isa yana zaune a gefe guda yana duba littafai kamar koda yaushe ta shiga da sallama ya amsa mata ta k'arasa ta zauna tace, "kun sha hanya, barka da dawowa." "Barkan ki, ya daren?." "Alhamdulillah, ya k'arfin jikin naka?." "Mun gode Allah." Shiru ya biyo baya babu mai magana kafin yace, "Aliyu baya gidan nan ko?." "Ban gan shi ba." Ya ajjiye littafin hannun sa yace, "ban san meyasa Aliyu yake halayya irin wannan ba, meye ribar abinda yake?, shi ko gudun zagi ma baya yi?. Ace yana daga cikin manyan y'ay'a na ace shine kuma wanda yafi kowa gurb'acewa?." Ajiyar zuciya tayi tace, "ban san meyasa Aliyu yake haka ba, kuma takawa kafi kowa sanin yadda aka sha wahala lokacin suna yara wajan kare su daga mugayen sihirin da ake musu. ni nafi tunanin akwai sihiri a jikin sa." "Koda yaushe ke Aliyu baya laifi asiri ne a jikin sa bakya duba yanayin dabi'un sa. Meyasa Asad shi baya yin abinda yake?, wanda suka yi asirin Aliyu kawai suka tsana?." Shiru tayi bata amsa ba ya kuma cewa, "Dabi'un Aliyu suna daga cikin abinda yake sake tayar min da hankali, da kunya ace d'an da na haifa a cikina shine yake irin wad'annan halayen mara sa kyau da dad'in ji, kuma a haka yake burin kasancewa sarki a garin nan." "To ya za'ayi sai hak'uri ai." Shiru ya biyo baya dan ita dai bata san maganar shiyasa ta katse ta kafin tace, "ya batun ajjiye sarautar taka?." "Na jinkirta zuwa nan da wani lokaci, ina so komai ya zama dai-dai kar a bar baya da k'ura. In kuma kafin lokacin na bar duniya shikenan." Nan ma shiru tayi bata ce komai ba zuciyar ta na cigaba da fad'a mata k'arya da gaskiya a kan komai da ya shafi lamarin gidan sarautar da take ciki. Washe gari. *☆☆☆* Rauda ko aikin gida bata samu ta tashi tayi ba duk da daman gyaran gidan Rahma ne ciwon kai ya mata mugun kamu dak'yar take iya juya kanta, har su Khairi suka tafi makaranta bata sani ba tana bacci sai goma na safe ta tashi tayi mamakin baccin dan bata saba jimawa haka ba. Sosai taji dad'in ciwon kan tayi wanka ta karya ta zauna a kusa da mahaifiyar ta suna hira. Har akayi Azahar babu inda taje tana kusa da ita duk da tana so ta fita taje gidan da take karb'o sarin alawar madara amma ta kasa fita. "Ke Rauda! Ke Rauda!!, maza fito" Baba ya fad'a daga waje. Mik'ewa tayi ta fito ta ganshi da kular da ta saba fita siyar da abinci tace, "Baba gani." Kallon ta yayi yace, "To maza a tafi, na dubu biyu da dari uku ne ki lisaafa dakyau in zaki bawa mutane." Kallon sa take yi da mamaki a fuskar ta ganin hakan ya saka shi yace, "Wai ke a tunanin ki dan jiya baki fita ba yau ma baza ki fita ba?, yo ko saurayin naki ya kawo min abinda yafi keke ai siyar da abinci yanzu kuka fara Rauda. Maza d'auki ki tafi bana son b'ata lokaci." Khairi da ta dawo daga makaranta ta fito daga d'aki tace, "Baba kanta ciwo yake." Ya harare ta yace, "ta sha magani kafin ta k'arasa zai warke, d'auko hijjabi ki maza ki wuce ki tafi." Jikin ta a sanyaye ta shiga suka had'a idanu da mahaifiyar ta da take jin su bata ce komai ba ta d'auko hijjjabin ta fito ta saka takalmi. "Kina wata tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki in baki hanzarta ba Rahma ta dawo ta barki wallahi ranki ne zai b'aci. In bakya son zuwa ai jiya saurayin ki ya baki kud'i d'auko su yanzu ki siye abincin ki bani kud'in kiga in baki zauna a gida ba." Bata ce kanzil ba ta sukunya ta d'auki kular ta fita daga gidan gabanta yana fad'uwa. Tsaki yayi ya fice babu wacce ta tanka cikin matan nasa kowa yasan halin sa shiyasa ko wacce taja bakin ta ta tsuke. Ko a can inda suke zama suna siyar da abincin Rauda ranar gabad'aya bata da walwala kana ganin ta kasan bata da lafiya duk da daman ba magana take da mutane ba, tana nan zaune Khairi tazo wajan ta tace, "Anty kije gida ni zan cigaba da siyarwa." Girgiza kai tayi tana kallon ta tace, "ya akayi baki je islamiyya ba?." "Yau alhamis ai babu shiyasa ban je ba." "Ki koma gida Khairi nima yanzu zan tawo." Zama tayi kusa da ita tace, "Zan jira ki a nan." Suna nan zaune ga abincin bai k'are ba Rauda taji jiri yana d'aukar ta ta mik'e tace, "Khairi d'auki kular nan muje kawai." Ba musu ta tashi ta d'auka suka tafi. A hankali suke tafiya dan sosai Rauda take jin jiri sabida yadda kanta yake sarawa. Titi suka zo tsallakawa Khairi ta tsallaka ta barta tana fad'in, "kya tsallako da kan ki dan nasan halin ki da tsoron titi bazan jira ki ba." Rauda bata ce komai ba ta saka k'afa a kan titi da niyar tsallakawa sai da tazo tsakiya ba zato babu tsammani taji anyi sama da ita an dawo da ita k'asa ta fad'i a gaban motar, wata razananniyar azaba taji a dukkan ilarin jikin ta musamman k'afar ta dalilin hakan ya sanya ta sumewa a wajan. Ihuu Khairi tayi a haukace tace, "Anty Rauda!" Ta fad'a a guje tana tsalkawowa daidai lokacin wanda yake zaune a cikin motar ya fito a gigice yana kallon Rauda da take kwance cikin jini hankalin sa a tashe............ *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023. ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *006.* A guje Ummulkhairi ta tsallako a lokacin Hydar yayi inda take kwance hankalin sa a matuk'ar tashe ya d'auke ta cak ya saka a bayan mota bai ma kula da Ummulkhairi da take kuka ba ya shiga motar ya ja a guje a hankalin sa tashe. Kasancewar titin babu jama'a sosai babu wanda ya lura da abinda ya faru Ummulkhairi ta kwasa a guje ko ta kan kwanikan abincin bata bi ba ta tafi gida. Babban asibitin kud'i na garin ya wuce da ita jikin sa gabad'aya rawa yake fuskar ta ta tasa lokaci d'aya har lokacin bata motsin kirki, k'ara gudun motar yake yi har ya isa asibitin nan take yayi waya akayi sa'a likitan da yake nema yana nan aka fito a guje aka d'auke ta aka wuce ciki. Gabad'aya ya kasa nutsuwa yana zaune a office d'in Dr amma zuciyar sa bugawa take da sauri, bai tab'a buge koda kaza ba tunda ya fara tuka mota sai wannan lokacin, shiyasa hankalin sa ya tashi sosai. Sun jima matuk'a a kan ta kafin Dr ya shigo yana ganin sa ya kalle shi alamun k'arin bayani nake nema, Dr ya zauna yace, "Prince ta samu karaya a k'afar ta munyi x-ray na k'afar mun gano k'ashin da yake rik'e k'afar ta baya wanda ya kasance bashi da k'wari ya karye shima, k'afar ta d'aya lafiya take sai dai buguwa da tayi amma d'ayar gaskiya tana da matsala munyi iya abinda zamu iya a yanzu in abin baiyu ba gaskiya dole sai anje Egypt." Hydar ya sauke numfashi ya lumshe idanun sa ya bud'e ya kalli likitan yace, "Yanzun jiran me za'a yi baza a tafi can ba?." Dr yace, "dole za'a jira ciwon ya warke in ka lura karaya ce mai jini ma'ana karaya ce mai had'e da ciwo, in ciwon ya warke in abinda muka yi bai ba shine za'a fitar da ita." Baice komai ba ya mik'e ya fita ya shiga d'akin da take yana kallon fuskar ta da ta kunbura amma kamannin ta basu gushe ba. Kallon ta yake k'irjin sa na bugawa ga k'afar ta a d'aure haka goshin ta ma an manne shi sabida ciwon da ta samu, numfashi yake fesarwa dana sanin fitowar sa daga gida gabad'aya ta damalmale masa zuciya ya fito daga d'akin suka had'u da Dr d'in a k'ofar d'akin yace, "A nemo family nata but bana so a sanar dasu nine na kad'e ta, a tabbatar musu da za'a tsaya ta samu lafiya ko nawa ne za'a kashe" abinda ya fad'a kenan kawai ya fita daga wajan bai jira ma yaji mai likitan zai ce masa ba. A can gida kuwa a guje Ummulkhairi ta shiga gida tana fad'in, "Umma! Umma!!" Umma da take tsakar gida ta kalle ta tace, "Khairi lafiya wannan wanne irin kira ne?." Jikin ta har rawa yake tace, "Anty Rauda!, Umma Anty Rauda!" abinda take maimaitawa kenan tana haki alamun ta sha gudu. Hankalin Umma ya tashi ta k'araso kusa da ita tana fad'in, "me ya sami Rauda d'in? Tana ina?, me ya same ta?." "Wani ne ya kad'e ta a mota tana kwance bata numfashi Umma, jini yana ta zuba daga jikin ta Umma" ta kuma fad'a har lokacin bata dawo dai-dai ba tana hakki. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wani ya kade ta fa kika ce Ummulkhairi?." "Eh Umma, ya d'auke ta a mota sun tafi." "Hasbunallahu wani'imal wakil, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Abinda Umma take fad'a kenan jikin ta na rawa itama Inna Babar su Rahma kenan ta fito itama tana salati tace, "To banda shirme kuma irin naki sai ki bari su tafi baki bisu ba?." "So nake nazo na fad'a muku, Umma Anty Rauda jikin ta duk jini ko motsi bata yi" ta k'arasa fada tana fashewa da kuka ta zube a wajan. "Kukan me nake ji haka?" Baba ya fad'a yana shigowa yana kallon su. Ba wanda ya iya magana yace, "Ya naga kunyi cirko-cirko kamar wad'an da aka yiwa mutuwa?, ke ina Rauda?." "Baba wani mai babbar mota ne ya kad'e ta ya d'auke ta suka tafi a mota." Baba yace, "Ya kad'e ta fa kika ce? A ina ya kad'e ta?, waye shi?." "Baba ban san shi ba, ya dai kad'e kuma ya saka ta a mota sun tafi." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" abinda Baba ya furta kenan ya fita daga gidan hankalin sa a tashe. Dukka mutanen gidan Hankalin su a tashe yake sun kasa koda zama musamman Umma Khairi kuma har lokacin kuka take sosai hankalin ta ya kasa kwanciya tunda a gaban ta akayi ba kuma ta tab'a ganin hatsari a zahiri ba sai a kan wannan. Baba ya jima da fita ya dawo Umma tace, "Malam an same ta?." Baba yace, "ban samu komai, inda aka buge ta d'in tabbas ga jini nan har yanzu yana wajan amma babu wanda yazo ya bada sanarwa koda y'an uwan ta zasu neme ta." Umma ta dafe kanta tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanzu a ina zamu same ta gashi har dare yayi?." Baba yace, "ki kwantar da hankalin ki ko waye ya buge ta zai nemi dangin ta ai kodan kula da lafiyar ta, kiyi hak'uri." "Ka gani ko?, kaga illar tallan da suke fita ko? Yanzu da basu je tallan ba da babu abinda ya same ta." "Tsautsayi ne ko tana gida sai ya same ta" ya fad'a yana fita daga gidan gabad'aya. Umma kasa magana tayi sai tagumi da tayi kawai zuciyar ta na k'una da zafi domin bata san halin da y'ar tata mai tausayin ta take ciki ba. *◇◇◇* Lokacin da Hydar ya shiga gida b'angaren mahaifiyar sa ya wuce a nan ya same ta a zaune ita da Asad ta saka shi a gaba tana ta jero masa tambayoyi amma guda d'aya ya gaza bata amsa, yadda ya shigo ya saka ta bishi da kallo tace, "Hydar lafiya?." Kusa da Asad ya zauna yayi shiru kafin ya kalle ta yace, "Accident nayi." Suhaima tace, "Accident a ina?." Kafin yayi magana Mama tace, "Babu abinda ya same ka?." "Babu Mama, but na buge wata yarinya yanzu haka ta asibiti unconsciously." "Da ranta dai ko?" Suhaima ta tambaya tana kallon sa. Kai ya d'aga alamun eh Mama tace, "A ina take yarinyar?." "I don't know, but zata tsallaka titi ne kawai sun fito daga kasuwa, I think tana sai da abinci ne." "Mtswww, to meye na damuwa? Ba ka kaita asibiti ba?" Ta fad'a tana kallon sa ganin yadda ya wani damu akan y'ar talakawa. Hydar yace, "Ranki ya dad'e Dr ya tabbatar min in abinda akayi bai yi ba sai an kaita Cairo an yi gyaran a can, taji ciwo sosai a k'afar ta kuma nine sila dole na damu." Mama ta tab'e baki tace, "Is okay tunda dai kai lafiya kake, kaje ka huta." Jikin sa a sanyaye ya mik'e sai a sannan Asad yace, "Sorry Bro." Kai ya girgiza kawai ya fita daga apartment d'in. "See him akan wata yarinya yar talakawa yake wannan damuwar, I hate dis" ta fad'a tana bin sa da kallo tana yatsine fuska kafin ta dawo da kallon ta ga Asad da yake kallon ta tace, "Dis time bazan d'aga maka k'afa ba Asad dole kaje ka nemo auren Jidda itace zab'ina a wajan ka sai kuma ka aure ta." Kai ya girgiza baice komai ba dan bai san me zaice mata ba. Baiyi magana ba Suhaima taji wayar ta na k'ara ta mik'e ta fita daga falon gabad'aya ta nufi can k'arshen gidan ta hango wanda ya kira ta a tsaye yana jiran ta, "Hello Suhail, I hope lafiya kake nema na haka?" Ta fad'a tana kallon sa. Kallon ta yayi yace, "lafiya lau Auta, akwai wani abu da nake so na baki ne ban sani ba ko zaki karb'a." "Meye shi?." "Magani ne nake so ki bawa Asad ya sha ba tare da ya sani ba." Wara idanu tayi tana k'are masa kallo mai cike da harara da mamaki ganin hakan ya saka shi yin murmushi yace, "bazan cutar da Asad ba kin sani, tunda kika ga na kawo masa kin san naji wata magana ne da take shirin faruwa." Hannu ta d'aga masa tace, "Bana daga cikin wad'annan shirmen naku kai ka sani, baza kuma ka hani wani abu kace na bawa Asad ba tare da ya sani ba, baza ka had'a kai dani a cutar dashi ba." Ya matso kusa da ita yace, "ba cutar dashi zanyi ba Suhaima, ke kin san baza'a tab'a had'a kai dani a cutar da Asad ba because he's my favorite cousin and he's my friend, wannan maganin da zan baki in ya sha zai karya dukkan abinda za'a aiko masa dashi, u know rayuwar Asad tana cikin hatsari a yanzu, kowa neman ganin bayan sa yake ki taimaka ki karb'a ki taimaki Yayan ki." Suhaima tayi masa kallon up and down tace, "Kai meyasa baza ka bashi ba?, kamar kai ma ya amince da kai ko?." "Eh ya amince dashi, amma kin fini kusa dashi kece zakiyi ba tare da kowa yasan hakan ba, sharaɗin maganin ba'a so wanda zai sha yasan an zuba. help us please in wani abu ya same shi dukkan mu ya sama." Numfashi ta fesar tana kallon sa a kaikaice zuciyar ta cike da tunani kala-kala. "Please Suhaima" ya fad'a yana sake marairaicewa yana kallon ta. "Sorry I can't" tana fad'ar hakan ta juya ta bar wajan ya bita da kallo yana cize bakin sa ji yake kamar ya jawo ta ya shak'e mata wuya yayi k'wafa ya juya ya bar wajan zuciyar sa cike da k'unar rashin samun nasara. Direct apartment d'in su Asad Suhaima ta wuce tana zuwa ta tarar dashi a zaune shida Hafiz ta shiga da sallama ta kalle shi tace, "Yaya ka amince da Suhail or not?." Hafiz yace, "what happened?." "He called me yanzu yana fad'a min akwai maganin da zai bani na bawa Bro deaf yasha wai zai protecting d'in sa daga abinda za'a aiko masa dashi, ban amince dashi ba gaskiya." "U see na fad'awa Asad Suhail ba abin yadda bane amma always sai yace min shi ya amince dashi, yanzu kin karb'i maganin?." "No, I'm not." "Ki kira shi yanzu ki karb'a sai ki zubar dashi in ba haka ba tabbas zai bayar a zuba masa ne, daga yau ko me zai baki akan Asad ki karb'a." Asad yace, "kar ki karb'a." Da mamaki ta kalle shi tace, "Why?." Idanun sa ya zuba mata akan fuskar ta yace, "abinda nace kenan" yana fad'a ya tashi ya shiga d'aki ta bishi da kallo. Hafiz ya kalle ta yace, "ban san me yake damun Asad ba akan Suhail, ya kasa gane inda ya dosa har yanzu but muje mu sanar da Mama ita kad'ai ce zatayi maganin abin." Kai ta d'aga alamun haka ne suka fita a tare zuwa wajan Mama. Asad lokacin da ya shiga d'aki zagaye kawai yake yi a cikin d'akin gabad'aya ya rasa tunanin me zaiyi cikin kwanakin mugayen mafarkai yake da mutane kala-kala suna k'ok'arin cutar dashi, dalilin da ya sanya gabad'aya baya sha'awar yin sarautar ko kad'an amma Mama ta dage shi bai ga abin so a cikin ta ba. Kan gadon sa ya kallah a gyare yake tsaf dan Suhaima ce kad'ai take shiga d'akin sa ta gyara sai Mama bayan su wani dogari ko baiwa basa zuwa cikin d'akin dan umarnin Mama ne. Tunda ya kwanta jiya a kansa yake jin kansa yayi masa mugun nauyi ga wasu abu kamar allura da yake ji yana sukar sa gabad'aya kansa ya kulle ya ma rasa tunanin me zaiyi. Ji yayi gidan gabad'aya yayi masa zafi ya d'auki makullin mota ya fita daga d'akin. Washe gari. Bayan gari yayi haske sosai Hydar ya d'auki mota ya tafi asibitin da Rauda take ya nufi office d'in Dr da sallama, yana ganin sa ya mik'e tsaye yana fad'in, "Barka da zuwa prince." "Ya jikin ta?." "Da sauk'i, mun samo dangin ta ma suna wajan ta a yanzu." "Good a cigaba da kula da ita ayi mata komai, but bana so suna na ya fito a maganar ka samu wani sunan but banda nawa." "Okay Prince in sha Allah." "Let's go" tare suka fito suka shiga d'akin da take nan suka samu Mama da Baba da kuma Inna suna zaune a kusa da ita. Da sallama suka shiga suka amsa Hydar ya kalle su dukkan su kana ganin su kasan talakawa ne duk da duk wanda yake k'ark'arin masarauta talaka ne amma nasu talaucin ya fito yace, "Ya mai jikin?, nine wanda na buge." Ganin babban mutum mai kalama da kwarjini kamar Hydar sai Baba aka gyara tsayuwa aka ce, "Jiki gashi nan dai har yanzu bata farka ba, sai dai fatan Allah ya bata lafiya." Kusa da gadon nata Hydar ya k'arasa yana kallon ta ya kalle su yace, "zata ji sauk'i, Dr zai mata komai babu damuwa." "Mun gode Allah ya saka da alkhairi" Umma ta fad'a tana kallon sa. Kai kawai ya d'aga baice komai ba ya fita daga d'akin daman burin sa a samo dangin ta. Gida ya koma ya shirya zai tafi aiki kasnacewar Friday ce, bayan ya gama ya shiga wajan Mama ta kalle shi tun kafin yayi magana tace, "Ina kaje d'azu?." Da girmamawa yace, "naje wajan wacce na buge ne." "Kaje kayi mata me? Ba ka bada komai Dr zai mata meye naka na zuwa inda take?." Shiru yayi Bai amsa mata ba tace, "Sunan ta Rauda iyayen ta talakawa ne suna zaune a unguwa Katsalle tana saida abinci a kasuwa meye naka da zaka dinga zuwa inda take?, wannan ba kalar wacce zaka je dubawa bace Hydar, zubar da kima ne a ganka a wajanta!, Tunda ka bar komai hannun Dr kar ka sake waiwayon ta kayi mata iya k'ok'arin ka." Kallon mahaifiyar tasa yake da zallar mamaki jin har ta binciko komai a kanta daga jiya zuwa yau kuma wai ya daina zuwa inda take tsakani da Allah ai babu adalci a cikin abinda tace shi kuma bazai iya ba, baice komai ba sai daga baya yace, "In kin min izini zan fita." Ta kalle shi da hannu tayi masa alama haka ya fice taja dogon tsaki tana fad'in, "meye nasa na damuwa akan wata banza y'ar talakawa oho?, har na tsani yarinyar" ta fad'a tana yarfe hannun ta tana tab'e bakin ta. *GRA.* Su biyu ne kacal a zaune a falon Sadiya da y'ar ta Jidda suna zaune suna tattaunawa kamar koda yaushe Jidda tace, "Mum u mean zan mallaki Asad matsayin miji na?." Sadiya ta murmusa tace, "of course Jidda, nan kusa bada jimawa ba zaki zama mallakin sa." "Wow!" ta furta tana juya idanun ta cikin jin dad'in abinda Mum d'in tace. Murmushi mahaifiyar tata tayi tana kallon ta tace, "Wannan kyauwu naki Jidda ai sai sarki, d'an sarki, jikin sarki ne zai d'auka." "But Mum kina ganin zaiamince?, kin san halin sa fa kamar ba mutum ba." "Babu abinda zai hana ya amince, yana jin maganar Maman sa fiye da tunanin ki, ko wuta ta nuna masa tace ya shiga zai iya shiga kuma ke kin san yadda take jin maganata ko ta iyayen ta bata ji, duk yadda zanyi sai nayi wajan ganin kin shiga cikin gidan nan matsayin matar sa. Wallahi zan iya k'arar da komai nawa wajan ganin hakan ya tabbata." Jidda bata ce komai ba Mum ta kuma cewa, "da sannu zan kwace duk wani jin kai da take ji dashi ya dawo hannun ki, da idanun ta zata kasa sarrafa d'an ta sai abinda muka ce shi zaiyi, tana muryar d'an ta zai zama sarki ne ni kuma ina murnar zaki mallaki sarki, zata kasance mahaifiya a gare shi zaki kasance mata a gare shi, duk wani sirrkan sa zai dawo tafin hannun mu daga nan Rabi'atu ta gama yawo." Murmushi Jidda tayi kyawun ta ya sake bayyana kana kallon ta kasan asalin iyayen ta ba hausawa bane tace, "Mum tana son Asad sosai fa, kina ganin zata bada wata dama kuwa?." "Nice damar ai Jidda sai abinda nace mata ke kin sani, duk wannan zafin kan da take ji dashi sai na sauke mata. Kin san wahalar da nasha kafin na mallake ta kuwa...? Na kashe kud'i ban san adadin su ba wallahi. Akwai tarin abubuwan da tayi min a baya na tabbata ita ta manta amma ni ban manta ba, kwantan b'auna kawai nake mata so nake ki mallaki Asad a nan zata gane wacec Sadiya." "Mum indai mallakar Asad ne lokaci ya kusa ai, ina so ma naje gidan na gaida ta." "Hakan yana da kyau Jidda, kije gobe ki wuni a can ki samu ku keb'e keda Asad duk da baya magana kiyi k'ok'arin ganin kunyi magana dashi." Shiru Jidda tayi Mum tace, "zan baki turare ki shafa a jikin ki duk wanda ya shak'i shi sai ya rikice Jidda." Dariya tayi tace, "da alama kin gama shirin ki Mum." "Murucin kan dutse nake ban fito ba sai da na shirya, lamarin Rabi'atu ba abu bane mai sauk'i ta wuce inda kike tunani. Kar take kallon kowa kanta na mugun ja sai da dabara da wayo zaka gano lagwon ta." Bata ce komai ba ta cigaba da danna wayar ta amma zuciyar ta cike take da farin cikin zata zama mata ga Asad kyakykyawa, mai aji, mai nutsuwa, mai kud'i, mai ilimi kuma sarki d'an sarki. *◇◇◇* K'asa-k'asa take magana kai da kaji kasan duk abinda ake fad'a babu gaskiya a cikin sa tana fad'in, "ka tabbatar Suhail ya saka layar a k'asan kafitar sa?." Daga can b'angaren yace, "na tabbatar domin inda bai saka ba Suhail bazai min k'arya ba." "Amma kasan ni bana son long process nafi son ayi abu a gama kawai a wuce wajen." "Ki kwantar da hankalin ki zancen da nake miki ma mai martaba ya jinkirta bayar da kujerar zuwa nan da wani lokaci." "Kai kamar baka san halin sa ba?, kwantan b'auna zai mana lokaci d'aya sai dai mu wayi gari muji ana bugawa Asad tambari, nifa in ba gani nayi an kawar da Asad ba hankali na bazai kwanta ba." "Ki kwantar da hankalin ki in abun bai yu ba a wannan karon zamu nemi master planer......." "Master planer!? Wacece Master planer?" Ta fad'a da mamaki tana jiran amasa. Murmushi yayi mai sauti yace, "Zaki Santa in lokacin hakan yayi, ita take tsara komai kuma yake tafiya yadda ya kamata, in abu ya gagare ni ita nake nema, ta wuce duk tunanin ki ta dame ki ta shanye a hatsabibanci, ta wuce tunanin ki da hankalin ki, in kika ji shirin ta sai kin san naki ba komai bane ba." Hajiya tace, "wacece ita?, a ina take?, meye alaqar mu da ita...?." Waziri yayi murmushi yace, "kamar yadda na fad'a miki zaki santa in lokacin yazo amma banda yanzu, ki cigaba da zuba idanu tabbas a kwanakin nan za'a wayi gari ace azo a fitar da gawar Asad, ki rubuta ki ajjiye na tabbatar da wannan" yana gama fad'ar hakan ya yanke wayar ba tare da ya jira yaji me zata ce ba tabi wayar da kallo zuciyar ta na hasaso mata Master planer amma ta kasa gane wacece................. *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023. ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *007.* Bayan sallar juma'a aka samu kiran gaggawa daga mai martaba duka iyalan gidan hatta matan da suke gidan mazajen su sai da aka kira su aka taru a fadar cikin gida duk wani da ya kasan jini a gidan sai da aka kira shi. Dukkan su suna zaune ana sauraren abinda mai martaba zaice kowa yayi mamakin kiran. A kamalance da k'asaita da zallar nutsuwa da hikima ya fara fad'in, "kamar yarda na saka a kira ku nasan da yawan ku kuna tunanin lafiya akayi kiran gaggawa haka kasancewar bai tab'a faruwa ba. Ba wani abun bane an kira ku ne akan murabus da nace zanyi a d'ora Asad." Kallon kallo aka shiga yi dukka mutanen wajan gaban su na fad'uwa matuk'a burin kowa yaji k'arshen maganar. "Babu batun ta a yanzu mu janye, amma nan da wasu kwanaki maganar zata dawo matuk'ar ina raye kuma abinda nace baza'a canja shi ba, in kunga abinda na fad'a bai faru ba ku tabbatar k'asa ta rufe fuska ta." Shiru fadar take ko masu kirari babu kasancewar magana ce ta cikin gida su kad'ai babu damar magana kuma sai ya bada dama. Fuskokin mutanen dake wajan zaka kalla zaka hango zallan farin ciki akan abinda yace, fuskar Mama ce kawai a d'aure cikin akasin farin ciki amma bata ce komai ba. "Bana son na sake jin wata magana akan wannan na yiwa tufkar hanci, in lokaci yayi komai zai bayyana amma banda yanzu." Nan ma shiru suka kuma yi kafin yace, "Akwai wanda yake da magana a cikin kuz?." Shiru akayi babu wanda yace komai sai daga baya babar y'a kaf gidan mai Maimuna wacce taci sunan mahaifiyar mai martaba ake kiran ta da Mummy tace, "Allah yaja da zamanin mahaifin mu, Allah ya kare mahaifin mu a duk inda yake. Hukuncin mai martaba shine hukunci a ko wanne lokaci, babu mai magana a cikin mu." Kai ya girgiza kafin yace, "Kowa zai iya tafiya." Kai k'asa sukayi da kansu a tare dukkan su suka furta, "A tashi lafiya." Dukkan su suka fita kowa ya nufi b'angaren sa zuciyar kowa fari kar sab'anin Mama da take cikin mayuwacin hali. Tunda ta shiga b'angaren ta take zagaye hankalin ta a tashe ta matuk'a ta kasa zama sai kai kawo take, ta d'auki waya hannu na rawa ta kira Sadiya tana d'auka tace, "Sadiya akwai matsala babba." Daga can b'angaren tace, "Ranki ya dad'e me ya faru?." "Mai martaba ya janye batun murabus d'in sa haka kawai babu wani dalili." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Ranki ya dad'e munyi sake gaskiya, duk yadda akayi wani abun aka yiwa mai martaba kuma ya shiga jikin sa. In fulani zata tuna akwai wanda zasu shiga su fita wajan ganin an tarwatsa mana abinda muka saka a gaba." "Shiyasa nace miki ina buk'atar zuwa Kano, dole ne na shiga garin Kano a kwanakin nan, babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da mulkin Asad, babu shi ko waye" tana fad'a ta yanke wayar hannun ta na rawa ta kira Asad. Yana zaune yaga kiran ta daman yasan sai Mama ta neme shi ya d'auki wayar baiyi magana ba ya sauke daga kunnen sa ya tashi ya tafi b'angaren nata, can ciki ya shiga inda ya kasance babu mai shiga sai su yana shiga kafin ma yayi magana tace, "a tafiyar da kuka yi dashi me kuka tattauna har ya canja shawara lokaci guda?." Ya d'ago ido kamar zaiyi magana sai ya fasa ganin hakan sai ranta ya sake ya b'aci tace, "bazan lamunci wannan shirun naka ba Asad! Ka fad'a min kaine kace masa baka ra'ayi?." Kai ya girgiza alamun a'a kafin yace, "wallahil azim Mama bamuyi magana irin wannan dashi ba, ki amince dani bazan yi k'arya dan na kare kaina ba" ya fad'a a sanyaye yana kallon k'asa. remote ta d'auka tayi jifa dashi ya tarwatse a wajan tana wuci tace, "koma dai meye Asad baka isa kak'i karb'ar mulkin nan ba indai ina da rai, Asad kaine zaka mulki garin nan babu wanda ya isa ya shiga tsakanin ku da mulkin nan, dole ka cika min burin." tana fad'in hakan ta wuce zuwa d'akin ta tana fad'in, "A shirya min tafiya gobe zan wuce Kano." Kai ya girgiza sai da ta shiga ciki sannan ya juya ya fita zuciyar sa gabad'aya babu dad'i ko kad'an. A falon Hajiya iyalan ta zagaye suke da ita maza da mata y'ay'an ta kowa ka kalla zaka hango zallar farin ciki a tare dashi barin ma ita da take ta murmushi ita kad'ai alamun hak'ar ta ta cimma ruwa. Wayar ta da taji tana k'ara ya sakata ta mik'e ta shiga d'aki ta barsu a wajan ta amsa wayar tace, "Abu kamar wasa yana ta zama gaske, sai ga mai martaba da kansa ya janye batun nan." Waziri yace, "Na sha fad'a miki ki kwantar da hankalin ki komai fa a hannun mu yake amma duk sai ki bi damu kan ki." Murmushi tayi mai sauti tace, "yanzu meye abu na gaba?." "Master planer tace mu had'u dake waje d'aya zamu tattauna." "Yaushe zaka shigo to?." "Zan shigo zuwa dare." Murmushi tayi tace, "Allah ya kai mu" tana fad'ar hakan ta yanke wayar zuciyar ta cike da farin ciki a bayyane. *◇* Amaryar Sarki Hajiya Rukayya wacce ake kira da Ammi a gidan itama tana zaune da nata iyalan babban d'an ta namiji mai suna Nazif a shekaru bazai wuce shekara sha hud'u ba ya kalle ta yace, "Ammi ni na rasa ganewa kamar kina goyan bayan sarautar Asad?." Murmushi tayi ta kalle su dukkan su tace, "To meye nawa da zanki goyan baya Nazif? Kai dai a musulunce baka kai minzalin jan ragamar al'umma ba to meye abin tayar da jijiyoyin wuya akan hakan?." Babbar y'ar ta mace mai suna Zainab wacce ake kira Yaya Zainab tace, "kin huta Ammi, koma waye zai mulki garin nan mudai burin mu ya kasance alkahiri a gare mu da kuma garin." Wacce take bin ta tace, "Shine kawai fatan mu amma ni banga abin tayar da hankali a lamarin nan ba. Asad kuma kaf gidan nan babu mai kirkin sa kawai shi rashin maganar sa ce illa amma kowa yasan halin sa ga san y'an uwan sa baya lakari da yanayin gidan namu kowa na sa ne. Duk da Mama bata son yana sauraren mu amma shi ko a jikin sa, ga ilimi da kud'i a hannun sa." Ammi tace, "Allah ya kyauta" duk suka amsa da amin suka cigaba da hirar su gabad'aya maganar mulkin katagum bata gaban su su kam. Hydar da Aliyu da kuma Asad ne a zaune a b'angaren su babu wanda yake yiwa d'an uwan sa magana dukkan su waya ce a hannun su suna dannawa hankalin su a kwance, waya Hydar ya d'auka ya kira Dr ya sake tambayar sa jikin Rauda ya tabbatar masa da komai daidai. Asad ya dafe kansa da yake mugun ciwo yana yatsine fuskar sa. Hydar ya kalle shi yace, "Deaf ya dai?." Yatsine fuska yayi yace, "nothing" yana fad'a kawai ya tashi ya shiga d'akin sa ya kulle k'ofar ya zaga baya ya bud'e varanda yana kallon harabar gidan ana ta hidima da shige da fice. Allah ya sani baya k'aunar mulkin da ake son k'ak'aba masa ga jifa da yake sha tun daga fara maganar sarautar nan yake ganin mutane da yawa wanda baiyi tunani ba a mafarkin sa ina ga an bashi sarautar?. Burin sa kasancewa a madina ba'a Nigeria ba a can yake burin yin aiki kuma burin sa ya cika amma Mama ta hana. Lumshe idanun sa yayi mafarkin da yayi a jiya ya dawo masa kansa ya wara idanun sa yana k'ok'arin tuno fuskar yarinyar da ya gani ta taimake sa a mafarkin amma ya kasa, furzar da iska yake yi jikin sa na kyarma hankalin sa ya tashi ji yake gidan gabad'aya yana juya masa sam baya son zama a cikin sa, duk yadda yaso daurewa kasawa yayi ya fito ya d'auki makullin mota ya fita har lokacin Hydar da Ali suna zaune. Hydar ma fita yayi aka bar Aliyu a zaune yana ganin fitar su ya mik'e ya shiga d'akin Asad yana k'arewa d'akin kallo kamar yana neman wani abun a ciki. Babba ne d'akin sosai komai fari ne a d'akin hatta tiles d'in d'akin fari ne labulaye carpet komai fari ne a d'akin, fari kuma tass babu alamun daud'a a tare da ko ina sai khamshi da yake yi. tab'e baki yake yana girgiza kai yana hasahen abinda ya kamata yayi a d'akin kafin ya fita daga d'akin. Hydar yana fita asibitin ya koma a lokacin Umma ce kawai a ciki ya shiga da sallama ta amsa tana kallon sa yace, "Sannu Mama, ya mai jikin?." "Da sauk'i gata bata farka ba har yanzu." Kallon ta yake yi ya runtse idanu ya rasa dalilin da ya saka gaban sa yake fad'uwa in ya kalli fuskar ta sai yaji wani abun yana shigar sa ya rasa meye. "Allah zai bata lafiya." "In sha Allah, ban san sunan ka ba." Murmushi yayi kad'an yace, "Aliyu suna na" ya fad'a yana ajjiye kud'i a gefen gadon ta ya fita bai kuma cewa komai ba. Kallon kud'in take yi ganin su da yawa a zahiri bata tab'a ganin mai yawan su ba balle kuma ta rik'e ta yunk'ura zata d'auka kenan Baba ya shigo. Idanun sa akan kud'in suka fad'a ya k'araso yana fad'in, "Ikon Allah wannan abin arzukin fa" ya fad'a yana k'arasowa wajan ya d'auki kud'in yana kallo. Kallon sa Umma tayi lokacin da yake juya kud'in tace, "Wanda ya buge Rauda ne yanzu ya fita shine ya ajjiye kud'in." "Tooo!" Ya fad'a da murmushi a kan fuskar sa yana sake kallon kud'in. Tab'e baki tayi tana kallon sa ya zuba kud'in a aljihu yace, "To shi wanne irin mai kud'i ne haka?." "Ban sani ba" ta bashi amsa a tak'aice tana kallon wani wajan daban. "Allah sarki daman in arzuk'i zai same ka sai Allah ya kawo silar faruwar sa, sai gashi silar arzuk'ina yazo ta hanyar hatsari" ya fad'a yana cigaba da murmushi ya saka hannu ya dafe kud'in. Shiru tayi kawai bata ce komai ba tayi tagumi tana kallon Rauda da take bacci har lokacin bata farka ba. Fita yayi yana ta dariya ta bishi da kallo kawai tana girgiza kai har ya b'acewa ganin ta. Fitar sa ba jimawa sosai Rauda ta farka rad'ad'in azaba ya kawo mata ziyara ta runtse idanun ta muryar ta bata fita tace, "Wayyo Allah!" Abinda tace kenan tana hawaye. Jin hakan ya saka Umma tasowa da sauri tana fad'in, "Rauda sannu kin tashi?." Kai take juyawa tana fad'in, "Umma k'afana!, k'afa Ummana!!, zafi take min zata cire" ta fad'a tana kuka sosai ga kanta na mugun ciwo. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, sannu Rauda, Allah ya baki lafiya." Kuka take sosai Umman ma sai ta fara hawaye tana rik'e hannun ta tana fad'in, "kiyi hak'uri Rauda, kiyi hak'uri." Bud'e k'ofar akayi aka shigo Umma ta kalli wanda suka shigo taga likita ne da Hydar likitan ya kalli Umma yace, "yaushe ta farka Mama?." Sai da ta goge idanu tace, "yanzun nan." "Rauda sannu, me yake miki ciwo yanzu?" Dr ya fad'a yana kallon ta. "K'afana, k'afa na zai cire, kaina zai fashe ku taimaka min" ta fad'a cikin tsananin azaba tana juya kanta. Gaban Hydar fad'uwa yake jin yadda maganar ta take fita tausayin ta ya sake kama shi jikin sa yayi sanyi matuk'a ganin duk fa da bai buge ta ba da hakan bata faru ba. Allura likita yayi mata ya d'aura mata ruwa har lokacin juya kanta take yi sabida ciwo. likitan ya kalli Umma yace, "Kiyi hak'uri Mama zata daina jin ciwo in sha Allah, sai a hankali zaki ga kamar batayi ba" Kai ta d'aga kai daga nan suka fita Hydar ya kalli Dr yace, "tana cikin ciwo sosai babu wani taimako da za'a yi mata?." "Prince daman ai sai a hankali zata samu sauk'i, yanzu farkawar ta kenan dole taji ciwo a jikin ta amma yanzu zai lafa." Hydar yace, "Dr ayi abinda ya dace please." "In sha Allah prince zata dawo kamar batayi ba." "Thanks" yana fad'a ya bar wajan da sauri shi kuma ya koma office. Haka Hydar ya koma gida gabad'aya jikin sa ya gama mutuwa tausayin Rauda yake ji na shiga jikin sa sosai, da ya kulle ido sai yaga yadda take kuka tana kiran k'afar ta sai hakan ya sake tayar masa da hankali sosai, muryar ta da kukan ta kawai yake ji a kansa da kunnuwan sa hakan ya sake saka jikin sa yin sanyi yana ji kamar yayi mata kuka. Lokacin da ya shiga b'angaren su Asad baya nan sai Aliyu yana zaune yana tauna chewing gum ganin yadda Hydar ya shigo ya saka yace, "lafiya kai kuma?." Hydar ya zauna yace, "yarinyar dana kad'e ce tana cikin ciwo abin tausayi." "Mtswww and so? I think y'ar talakawa ce ko?." "Ita y'ar talakawar ba mutum bace?." "Bata da banbanci da matattaciya." "Ban san me yake damun ku ba, shi d'an talaka ba mutum bane ba ko me?, ko kuma kai ka zab'i taka rayuwar a haka?." Aliyu ya tab'e baki yayi masa banza bai kuma kula shi da dan a ganin sa bashi da hankali in shine ya buge ta ko k'afar sa zasu gani ne balle ya dinga zarya haka akan kanta. Shima Hydar d'in banza yayi masa dan ya lura Aliyu da Mama halin su guda ne. A b'angaren waziri da Hajiya suna zaune kamar yadda suka saba a inda suka zaba had'uwa a sirrance waya na hannun waziri an saka speaker muryar mace babba mai cike da kamala tana fita daga cikin ta, Waziri yace, "kamar yadda na fad'a miki anyi komai an gama gashi har mai martaba yana cewa an jinkirta komai." Murmushi tayi mai sauti tace, "na raina wayon ka da kai da ita kanta Sa'adatun, yanzu ku har kun amince da abinda yace?. Wasa yake muku da hankali ya d'auke hankulan ku daga kan sarautar gabad'aya rana tsaka sai dai kuji sanarwa Asad ya zama sarkin ku dole ku duk'a ku gaishe sa. Kun manta tare suka fita ne a jiya?." Kallon juna sukayi kafin Waziri yace, "Haka ne, amma bakya ganin kamar wannan karon da gaske yake?." "Ina baka kana mik'o min hannu. Kai kasan babu wanda ya san sirrin mai martaba sama da Asad sai kuma Mubarak k'anin ka, ko lokacin da suka je Kano da shi Mubarak d'in suka tafi tare aka tattauna aka cimma matsaya ku baku san komai ba. Ku a ganin ku mai martaba zai bada dama kayi sarauta ne? Kuyi tunani dakyau zaku gano kwantan b'auna ne." Hajiya tace, "duk abinda kika ce haka ne tabbas tunani na bai kawo haka ba sai yanzu, tabbas kwantan b'auna mai martaba yayi mana yana so hankalin mu ya d'auke daga kan Asad ne shiyasa yace haka. Ya fahimci akwai masu nufi irin namu shiyasa yayi saurin dakatar damu." Murmushi tayi mai kyau tace, "Dad'ina dake kina da saurin fahimta. Ku nutsu ku kuma dawo hankalin ku in ba haka ba kuna ji kuna gani komai zai lalace muku. Suhail kuma tabbas ya sakawa Asad layar nan dana baka kuma ta fara shiga jikin sa zancen da nake muku yanzu ma zaman gidan ya fara neman gagarar sa, ciwon Hydar zai tashi a cikin kwanakin nan, ga Aliyu kuma daman ba zaman gidan yake ba. Matuk'ar bamu d'auke hankalin Rabi'atu ba to tabbas shirin mu bazai tab'a tafiya yadda muke so ba, rashin lafiyar Hydar da barin Asad gida ya isa ta fasa tafiyar da tace zatayi, dan matuk'ar taje Kano sai komai ya lalace." Waziri ya girgiza kai yace, "Wannan shine shirin mu na gaba kenan?." "Shiri na gaba a kan Asad ne ya zama dole ya bar gidan nan kota halin k'ak'a, ko kuma ya bar duniyar gabad'aya barin sa da numfashi barazana ne ga namu numfashin." Hajiya tace, "Abinda nake nuna masa kenan tun farko amma ya kasa ganewa, a kawar da Asad shine abu mafi mahimmaci a wajan mu." Tace, "kwantar da hankalin ki Hajiya baza mu gaggawa ba, a hankali zamu tafi da lamarin in muka ba bar Asad da Aliyu ma komai zai tafi yadda muke so, zakuyi mamaki idan nace Aliyu yana neman hanyar da zai bi wajan ganin ya zama sarki a garin nan, tabbas Ali zai iya kashe Asad abu ne mai sauk'i a wajan sa indai burin sa zai cika wannan ba komai bane ba. mu jira muga yadda wasan zai kaya." "Abinda nake so dake Sa'adatu ki cigaba da nuna k'aunar Asad a gaban mahaifin sa, ki jawo sa jikin ki yadda baya sakewa da uwar sa ke ya sake dake, kiyi duk abinda zakiyi ya fara cin abin hannun ki ana zuwa wannan gab'ar mun kamo wuyan sa, na bar ku lafiya" tana fad'a ta datse kiran wayar. Hajiya tace, "kirata naji ta yaya zan jawo shi jiki na, dan Allah ka kira ta." Waziri yace, "Bana tab'a samun ta a waya sai dai in ina taso zata kira ni sai ta bani lokacin da zamuyi magana." "Gaskiya ta cika babbar master planer, amma wacece ita? Naso na gane maganar ta amma na kasa ganewa, na santa kuwa?." "Ba lallai kin santa kedai kiyi abinda tace ta kai k'arshe wajan iya tsara plan. Ta wacce hanya zaki bi Asad ya zo hannun ki?." Numfashi ta sauke tana girgiza kai kafin tace, "Salad, zogale, lansir, wad'annan shine abinda Asad yafi so yaci tun mai babban d'aki tana raye, duk juma'a sai ta aiko masa da d'aya daga cikin su an masa lafiyayyen had'i zai ci kuma hankali a kwance. Bayan shi sai kunun tsamiya mai lemon tsami, sai kuma shayi ko coffee ko kuma chips Asad yana son wannan abubuwan dasu zanyi amfani na meye gurbin mai babban d'aki wajan aika masa dashi duk juma'a, babbar matsalar ita Rabi'atu kana ganin zata bada damar da zan jawo Asad jikina?." "Tabbas kinyi tunani mai kyau Asad yana matuk'ar son abubuwan da kika lissafa kuma shi halinsa daban ne dan kin bashi karb'a zaiyi yaci bazai kawo komai ba, yadda zuciyar sa take fara gani yake ta kowa fara ce, yarda baya nufin kowa da sharri gani yake kowa ma haka ne. Matsalar dai ita uwar sa kamar yadda kika ce." Ta daki kujerar da take kai tace, "Amma bar ni da ita nasan abinda zanyi zan biyo mata ta k'ark'ashin k'asa sai burin mu ya cika." "Ki dai yi a sannu kin san tana da wayo kuma ta dafu da magani ne tun tana yarinya ta kuma dafa y'ay'an ta, ki duba wahalar da muke ta sha tun suna k'ananu har yanzu akan abu guda muke, amma zamu kamo bakin zaren in Allah ya yarda." Hajiya ta mik'e tsaye tace, "ni na koma zaka ji bayani daga baya" tana fad'a ta fita shima bai jima sosai ba ya tashi ya tafi....... *ni kaina na shiga confuse fa, wacece Master planer kuma?.*🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🤣🤣 *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *008.* Washe gari ta kama ranar Asabar kamar jiya da wuri Hydar ya d'auki mota ya tafi asibitin da Rauda take duk da ciwon kan da yake fama dashi haka ya jure dan da ita ya kwana a ransa. Dak'yar ya iya k'arasawa yayi parking motar ya shiga cikin asibitin kansa na sara masa sosai. D'akin da take ya fara shiga da sallama a bakin sa cikin takun nutsuwa da izzar sarauta da k'asaita da take yawo a cikin jijiyoyin jikin sa. Yana shiga idanun sa ya sauka a cikin na Rauda da take kallon wanda ya shigo, bai d'auke idanun sa daga cikin nata ba ganin yadda idanun ta sukayi ja duk da bai san su a yadda suke a baya ba amma yadda ya gan su ya san sun canja. Kwarjini da fad'uwar gaban da ta ziyarci k'irjin ta ya saka ta janye idanun ta ta saukar k'asa duk da tsananin azabar da take ciki. Babu kowa a d'akin sai ita kad'ai ya k'araso yana yatsine fuska sabida kansa ba k'aramin sarawa yake yi ba, ko takawa yayi sai yaji takun har kwakwalwa sa. Kallon ta yake yi ganin yadda take juya kanta kana gani kasan tana cikin azaba jikin ta har rawa yake ga k'afar tata a d'aure goshin ta manne da flasta, k'arewa fuskar ta kallo yake a karon farko k'irjin sa ya cigaba da bugawa yayi saurin d'auke fuskar sa yana kallon gefe guda. Bud'e k'ofar akayi aka shigo ya kalli wanda ya shigo yaga Dr ne da kuma mahaifin ta ganin sa ya saka Dr k'araso yace, "barka da zuwa." Idanun sa ya lumshe ya bud'e kafin ya kalli Baba kafin yayi magana Baba yace, "Barka da safiya, da fatan an tashi lafiya." "Ya mai jiki?" Ya furta a nutse yana kallon Baba. "Mai jiki da sauk'i" Baba ya bashi amsa jikin sa har rawa yake yi. Hydar ya kalli Dr baiyi magana ba hakan ya sake yace, "Komai zai tafi dai-dai in sha Allah." Kai kawai ya girgiza ya juya zai fita cikin takun isa sai kuma ya tsaya cak ya juyo yana kallon Baba kafin yace, "ba wani damuwa?." Sai kuwa Baba ya gyara tsayuwa yace, "To Alhaji kasan lamarin abubuwan sai a hankali, ga gida ba abinci ga kud'in motar zuwa asibiti ga kuma......." hannu Hydar ya d'aga kawai baice komai ba ya saka hannun a aljihu ya d'auko d'aurin dari biyar guda biyu ya mik'awa Baba ya k'araso jikin sa har yana rawa ya karb'a baice komai ba bai kuma bari Baban yace komai ba ya fita. Baba yabi kud'in da kallo yayi murmushi yana shafa fuskar sa yace, "To ke Rauda ai sai ayi fatan ki ta zama a asibiti wannan abin arzuk'i haka?, tunda nake na d'auka zan rik'e kud'i manya haka nawa na kaina ni kad'ai? Ai ban tab'a ba sai silar kwanciyar nan taki. Yo ba sai nayi ta addu'a kita zama ba indai irin wannan zasu zo hannu." Rauda kallon Baba take yi duk da ciwon da take ciki hakan bai hana jin takaici da bak'in ciki a zuciyar ta ba, ji ta kud'i ma yake bata lafiyar ta ba gashi da ya shigo ko ya jiki bai mata ba dan ta fahimci shine ya buge ta. Hydar dak'yar ya iya zuwa office d'in Dr ya zauna kansa yana juyawa a ya saka duka hannayen sa biyun ya dafe kansa, ganin hakan hankalin Dr ya tashi dan masomin tashin ciwon Hydar kenan hakan ya saka shi ya rud'e yace, "Prince lafiya? Me yake damun ka?." Kansa yake nuna masa jikin sa har rawa yake hankalin Dr ya tashi ya kalle shi yace, "Prince kana buk'atar drip." Kai ya girgiza alamun a'a kafin kuma ya ja dogon numfashi jin yadda kansa yayi mugun sarawa daga nan idanun sa duhu ya mamaye su amma duk da haka yak'i kulle idanun nasa. "Prince! Prince!! Kana jina?, Prince!!!" Dr ya fad'a hankali a tashe amma lokacin idanun Hydar ya rufe ruf yana zaune idanun sa a kulle jikin sa ya saki duka. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" abinda Dr yake maimaitawa kenan jikin sa na mugun rawa ya bud'e k'ofar Office d'in sa yana fad'in, "Nurse!, Ashiir kana ina?!" Ya fad'a da k'arfin gaske wanda yake kira ya tawo a guje. "Zo ka taimaka min" ya fad'a yana komawa ciki suka shiga tare suka d'aga Hydar da jikin sa yake a sake kamar gawa suka d'ora shi akan gado Dr hankalin sa tashe suka tura gadon Hydar zuwa babban d'aki na musamman. Ta underground aka shiga babu wanda zaice akwai wani d'aki ko hanya a wajan aka shiga da Hydar aka jona masa ruwa na'urori sai da ya tabbatar yayi masa abinda ya kamata sannan ya fito da sauri yana kiran wayar Mama amma bata d'aukar wayar. Dafe kansa yayi hannun na rawa ya rika number Asad kamar yadda yayi zato bazai d'auka ba bai kuma d'auka d'in ba, "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta yana danna layin Aliyu shima bai d'auka ba har kira biyu. Suhaima ya kira na farko bata d'auka ba sai a na biyun yana ganin ta d'auka da sauri yace, "Princess where are you?." "At home." "Ina Mama?." "Lafiya?." "Ki sanar da ita Hydar yazo nan wajan yarinyar da ya kad'e kuma ciwon sa ya tashi yanzu haka yana kwance." "What!" Ta fad'a a firgice tana dirowa daga kan gado ta fito daga d'akin ta cikin sauri, bata yi tafiya mai nisa ba ta iso babban falon mahaifiyar tata bata same ta a shi ba ta nufi ciki ta ganta a tsaye tana amsa waya, "Mama ciwon Yaya Hydar ya tashi" ta fad'a a firgice bata jira ta gama wayar ba ma. Ba shiri ta sauke wayar daga kunnen ta ta zaro idsnu tace, "me kika ce? Ciwon Hydar? Yana ina?." "Dr Yasir ne ya kira ni yake sanar dani yanzu haka ma yana asibiti." "Oh my god!" Mama ta fad'a tana yin ciki da sauri. Ita da sauri ta koma ta canja kayan jikinta da sauri ta dawo ta tarar Mama har ta fita tabi bayan ta da saurin gaske, a mota ta samu Mama da sauri ta shiga kusa da ita aka ja motar aka fita da motar da saurin gaske. Hajiya tana tsaye jakadiyar ta ta shigo a guje tana haki ta zube a gaban ta, da sauri ta juyo ta kalle ts tana fad'in, "ke kuma lafiya zaki fad'o min ko sallama babu." "Tuba nake ranki ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ki." "Lafiya?." "Wato ranki ya dad'e ciwon yarima Hydar ne ya tashi yanzu zancen da nake miki gimbiya ta tafi asibiti wajan sa." Waje Hajiya ta samu ta zauna tace, "yanzu kenan abin ya faru?." "Yanzun nan ranki ya dad'e dan yanzu ta fita a gigice da ta shirya tafiya Kano amma a halin yanzu tafiyar ta watse." Kyakykyawan murmushi tayi tana cize baki tace, "jeki." "Na gode ranki ya dad'e, ki huta lafiya" ta fad'a tana fita jiki na rawa ta bita da kallo tana murmushi. "Master planer!" Ta furta a bayyane tana murmushi ganin duk abinda ta tsara ya tafi nan take taji farin ciki yana mamaye mata zuciyar ta. Y'arta Khaleesat sa'ar Suhaima ce ta shigo ta kalle ta itama ita take kallo tace, "Khaleesat kin san me nake so dake?." Kai ta girgiza kai Hajiya tace, "Jeki ki samo min zogale yanzun nan." Wara idanu tayi tace, "zogale? Hajiya a ina zan samo zogale yanzu?." Tsaki taja ta shige ciki ita ma tabi bayan ta da sauri. B'angaren Mama a gigice suka isa asibitin b'angaren da aka ajjiye shi shiru wajan babu motsin komai tsittt ko tsuntsu baya bi ta wajan ta shiga inda Hydar yake kwance, yana kwance sanb'al kamar koda yaushe ko ina na jikin sa baya motsi an jona masa na'ura a kan sa idanun sa a kulle ko wanne lokaci. Kallon Dr tayi ta kalli Suhaima da take gefen ta ta dawo da kallon ta ga Dr tace, "me yazo yi asibitin nan?." "Ranki ya dad'e yazo duba yarinyar da ya buge ne." "Yarinyar da ya buge? Kana so kace min a wannan asibitin ya ajjiye y'ar talakawar da ya kad'e?." Suhaima tace, "Mama muje waje kin san ba'a yi masa hayaniya." Ba musu duka suka fito ta kalli Dr tace, "Kai nake sauraro." "A nan ya ajjiye ta ranki ya dad'e, yau d'in ma yazo duba ta ne." "Ita wacece da zai zo duba ta da safe ko wajena bai shiga na gansa ba?, me take dashi?." Dr yace, "Bata da komai ranki ya dad'e." A fusace tace, "a kan me za'a ajjiye ta a nan? Meya zo yi wajan ta ko wajena bai shiga ba?, me yake nufi da yarinyar nan?." Shiru Dr yayi ya sunkuyar da kansa k'asa baice komai ba tace, "akan ta Hydar ya kwanta rashin lafiya, yasan ba'a son ya cika zirga-zirga mussmman da safe amma sabida ita yake fitowa har hakan ya kai shi ga kwanciya, y'ar gidan uban wacece?." Dr yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ba y'ar kowa bace hasalima iyayen ta talakawa ne." Dogon tsaki taja takaici da bak'in ciki na damalmale mata zuciya tace, "Ayi gaggawar sallamar su daga asibitin nan su koma asibitin gwamnati suje can su k'arata, bazai yu yana kwance a nan itama tana nan ba matsayin su ba d'aya bane ka gane ko?." Kai ya girgiza alamun eh cikin girmamawa tace, "a shirya komai zai tafi da Hydar gida" ta fad'a tana niyar komawa d'akin Suhaima tace, "But Mama zaman sa a nan zaifi samu kulawar da ake nema." Hararar ta tayi hakan ya saka ta yin shiru bata ce komai ba domin an gama magana ta shiga ciki. Suhaima ta kalli Dr tace, "please Dr ka bar yarinyar ta samu sauk'i in yaso sai ku sallame ta, a bata kulawar da ya kamata please" tana gama fad'a tabi bayan maman ta shima ya bisu da kallo. K'irji ya dafe yana fad'in, "Allah ya fidda ni lafiya" ya Fad'a shima yana bin bayan ta. Yana shiga ta kalle shi tace, "a had'a komai zamu tafi dashi gida." Kai ya girgiza da sauri ya fita aka had'a mota nan da nan aka turo gadon da yake kai aka saka shi a mota ita da Suhaima suka shiga bayan wata motar ta kalli Dr tace, "a tabbatar yarinyar nan ta bar asibitin nan." "In Allah ya amince ranki ya dad'e." Daga haka aka ja motar aka tafi. Har k'ofar apartment d'in ta aka je da motar aka bud'e da gaggawa aka tura gadon da yake kai zuwa cikin babban d'akin da yake kusa da nata, a kan gadon da yake kai aka barshi Dr ya jona masa abubuwan da aka tawo dasu ya tabbatar komai yayi sannan ya tafi. Kallon sa take ta zauna a gefe ta rik'e hannun sa jikin ta duk yayi sanyi domin abubuwan suna neman fin k'arfin ta. B'angaren Asad bai san abinda yake faruwa ba dan bai ma kalli wayar sa ba ya fito daga d'aki zuwa falo babu kowa daman dai yasan Aliyu baya nan amma yayi mamakin rashin ganin Hydar, numfashi ya sauke ya juya zai koma yaji maganar Hajiya a bayan sa tana fad'in, "Asad." Juyowa yayi yana kallon ta ya d'an saki murmushi kad'an yace, "barka da rana Hajiya." "Barka ka son, ya komai da komai." "Alhamdulillah" ya amsa yana d'auke kansa gefe. "Mafarki nayi da mai babban d'aki daren jiya sai ta tuna min da k'aunar ka da zogale hakan ya saka ni shiga kitchen da kaina na had'a maka, ina fatan zakayi farin ciki?" ta fad'a tana mik'a masa bowl da aka rufe shi da foil. Ba musu ya sanya hannu ya karb'a ya murmusa yace, "Godiya nake." Itama ta fad'ad'a murmushin ta tace, "Babu komai kar ka damu Asad" ta fad'a tana juyawa ta fita baice komai ba ya ajjiye bowl d'in ya shiga d'aki. Jim kad'an ya fito ya tarar da bowl d'in kamar yadda ya barsa ya zauna ya bud'e, zogalen ya burge shi sosai yaki kayan had'i yadda ya kamata hakan ya saka shi deba da hannun sa ya kai baki sai kuma ya dakata. _Hajiya kamar Mama take baza ta bani abinda zai cutar dani ba, yeah baza ta cutar dani ba tana sona._ ya fad'a a zuciyar sa ya kai zogalen bakin sa yana taunawa a hankali. Sosai yayi masa dad'i ba kad'an ba dan ya jima bai ci ba ya cigaba da ci har ya kusa cinyewa sannan yaji ya ishe shi ya tashi ya bar shi a wajan ya shiga d'aki. Yana fitowa daga d'akin yaga Mama a tsaye ita da Suhaima ya kalle ta ya durk'usa har k'asa yace, "barka da fitowa." Bata kalle shi ba tace, "Daman yau a cikin abinda ake kawo maka breakfast har da zogale?." Mik'ewa tsaye yayi ya kalli bowl d'in ya kalle ta yace, "A'a Hajiya ce ta kawo min d'azu." Mama ta wara idanu tace, "wacce Hajiya kenan?." "Hajiya dai." "Amma dai baka ci ba ko?." Kallon bowl d'in yayi ya kalli Mama yace, "ki gafarce ni,na ci." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Asad why" ta fad'a a gigice tana kallon sa kamar zata zubar da hawaye. Marairaicewa yayi baice komai ba yana kallon ta, "Asad meyasa baka ganewa ne kai? Meyasa kake d'auka yadda zuciyar ka take mai kyau haka ta kowa take da kyau?, meyasa yadda kake ganin baza ka cutar da kowa ba haka kowa yake?. Baka san a yanzu ba abincin kowa zaka ci ba?, meyasa kaci abin hannunta?, akan me baka sanar dani kafin kaci ba?!" Ta k'arasa fad'a cikin fad'a tana kallon sa. Runtse idanun sa yayi ya sunkuyar da kansa baice komai ba, sake tunzura ta yayi ganin yayi mata shiru tace, "baza kayi magana ba sai na mare ka?." D'agowa yayi ya kalle ta a sanyaye yace, "Allah ya wuci zuciyar ki." "Asad meyasa kaci yanzu in ta zuba maka guba a ciki ka mutu fa? Ya kake so nayi kenan?." Nan ma shiru yayi baice komai ba ta rik'e hannun sa tace, "muje duk yadda zakayi ka amayar da abinda kaci zai maka illa Asad" ganin duk ta rud'e sai ya rik'e nata hannun shima yace, "Calm down Mama, babu abinda zai same ni sai Allah ya nufa." "Asad tana so ta cutar da kai ba tun yau ba zata iya aikata komai wajan ganin ka cutu, kar ka kuma cin abin hannun ta dan Allah" ta fad'a kamar zata zubar hawaye tana kallon sa. Kai ya girgiza alamun to yana kallon Maman tasa da girmamawa kamar ko yaushe kallon sa take itama kafin tace, "Baka jin komai a jikin ka?." Kai ya d'aga alamun eh kafin tace, "jikin Hydar ya tashi Asad kazo muje ka gan shi" ta fad'a tana fita shima ba musu ya biyo bayan ta. D'akin da yake suka shiga yana kwance kamar ko wanne lokaci Aliyu na tsaye a gefen sa yana kallon sa Asad ya k'arasa d'aya barin yana masa addu'a yana tofa masa a fuskar sa. "Mama garin ya hakan ta faru?" Aliyu ya tambaya yana kallon Mama. Mama tace, "akan wata banza y'ar talakawa ya fita da safe, yarinyar nan da ya buge wai yaje dubawa da safe nayi masa warning akan zuwa inda take amma baiji ba gashi ya kwashi sanyi ciwon sa ya tashi." Aliyu ya tab'e baki yana kallon gefe baice komai ba. "Assalamu alaikum, surprise" aka fad'a daga baya ana shigowa d'akin. Dukkan su kallon k'ofar suka yi banda Asad da har lokacin yake wa Hydar addu'a, Suhaima ta wara idanu tace, "Sis oyoyo" ta fad'a tana hugging nata itama ta rike ta tana murmushi. Har k'asa ta duk'a ta gaisa Mama ta amsa da fara'a tace, "lallai kam surprise, ina Mum d'in?." Murmushi tayi wanda ya bayyanar da asalin kyaun ta tace, "Mom tana gida. Mama Yaya Hydar ne babu lafiya?." Kai ta d'aga mata kawai ta k'arasa inda Asad yake tsaye tana kallon Hydar. Sai kuma ta kalli Asad da bai kalle ta ba ta d'an bugi kafad'ar sa tace, "Kana gani na ko magana babu ko bro? I'm sorry in kaji babu dad'i jiya bance maka zan zo ba, ina so na baka mamaki ne." D'ago idanun sa yayi yana kallon ta nan take gaban ta ya fad'i ta d'an yi baya ta kalli Suhaima da take kunshe dariya tace, "deaf kenan, ga Bro Aly nan kina gani." Wara idanu tayi tana kulle bakin ta tana kallon Asad ya d'auke kansa daga kallon ta takaici kamar ya kashe shitace, "Sorry Boss." In ta samu kallon arzuk'i ma da ta godewa Allah ta bar wajan ta koma inda Aliyu yake shima bai kalle ta ba tace, "Yau sai naga kai ka koma min shi shi ya koma min kai." Irin kallon da ta samu daga wajan Asad shi yayi mata shima sai ta kalli Mama sai taga Mama tayi murmushi tace, "Yau suna so su rikita ki ne." Sai kuma Aliyu ya murmushi ya mik'a mata hannu alamun su gaisa. Sai tayi murmushi ta bashi nata hannun suka gaisa kafin yace, "Welcome" yana furta hakan ya mik'e tsaye har lokacin hannun sa na cikin nata yana binta da kallo itama haka kafin ya zame hannun sa ya fita. Mama ta kalle ta tace, "Jidda kije ki huta, Asad kaje ina zuwa." A hankali yake takawa ya fita ta bishi da kallo tana murmushi Mama na kula da ita itama ta murmusa bata ce komai ba suka fita aka bar Hydar dake kwance. Asad tunda ya bar wajan zuciyar sa take masa zafi har ya koma apartment d'in su ji yake kamar ya fashe da kuka sabida takaici. A bakin window ya tsaya yana furzar da iska mai zafin gaske jikin sa har zafi ya d'auka sabida takaici da zallar bak'in ciki. Ta yaya Mama zata ce wannan yarinyar ce zata kasance matsayin matar sa nan gaba?, yarinyar da a gaban sa take gaisawa da namiji wanda ya kasance yayan sa kuma jinin sa, kenan sun saba tunda gashi yana bata hannu ta bashi suka gaisa. dogon tsaki yaja lokacin da ya tuna dukan kafad'ar sa da tayi alamun sun saba ma irin wannan banzayen halayen da Aliyu. Kowa yasan shi yana da kishi ko takalmi akace wannan mallakin sane tofa bai aminta yaga wani da takalmin ba sai shi kad'ai balle matar aure, kai yake girgizawa a hankali yace, "Mama bazan iya auren ta ba, I'm sorry" ya fad'a yana barin wajan. So yake ya bar gidan yaje company amma ya kasa baya son fita gabad'aya wani irin abu yake ji a jikin sa kamar ana zare masa kuzarin jikin sa. Zama yayi a kan kujera yana furzar da iska kafin ya buɗe idanun sa ya mik'e zaune yana wara idanun sa a bangon d'akin, dafe kai yayi ya jingina da kujera ya rasa gane fuskar yarinyar da yake mafarki da ita amma yana jin tashin amon muryar ta a kunnen sa amma fuskar ta tak'i tsayawa a idanun sa. Ko yanzu yaji maganar ta zai iya ganewa amma banda fuskarta gashi ta maqale a zuciyar sa kowa ya motsa sai ya tuna da ita. B'angaren Mama suna shiga d'aki ta kalli Jidda tace, "Amma kwanaki zaki mana ko?." Ta yi farrr da idanun ta kana tace, "A'a Ranki ya dad'e anjima da daddare zan wuce." "To kije yanzu wajan Asad ku gaisa amma nasan Aliyu abokin kine ki daina nuna hakan a gaban Asad, lemme tell u something about your husband to be. yana da kishi, in ya nuna abu aka ce wannan naka ne yace kuma inaso to duk duniya babu wanda zaiyi amfani da abun nan sai shi kad'ai, in kuwa yaga wani ya rab'i wannan abin da yake so tabbas zai bar masa ne shi ya hak'ura. So u have to be very careful Jidda in kuna tare bakya ganin kowa sai shi koda Aliyun ne in ba haka ba zaku yi fad'a" ta fad'a tana kallon ta. Juya idanu Jidda tayi jin abinda akace mata sai farin ciki ya mamaye mata zuciya cikin muryar ta mai dad'in ji tace, "In sha Allah zan kiyaye ranki ya dad'e, bara naje wajan sa" ta fad'a tana ficewa Suhaima ta bita da kallo ta kalli Mama tace, "Mama Asad da Jidda sunyi bala'in dacewa, wannan suka tashi haihuwar yara za'a ga larabawa." Murmushi kawai Mama tayi dan ita badan kyau ta had'a su aure ba akwai manufar ta kafin ta fita ya koma d'akin da Hydar yake kwance. Asad yana zaune a inda yake aka shigo da sallama ya amsa ba tare da ya kalli wacce ta shigo ba yaji an zauna kusa dashi bai kalle ta ba tace, "barka da hutawa my Asad." Bai kalli inda take bama balle ta saka ran zai amsa. Daman tasan za'ayi haka tayi murmushi cikin shagwaba tace, "Kayi min magana mana." Nan ma bai kalle ta ba idanun sa a kulle suke. "Dan kai fa na baro gida nazo nan amma shine baza ka kula ni ba?" Ta fad'a a shagwab'e. Nan ma banza babu amsa ta kuma cewa, "My Asad please." Numfashi ya sauke ya juyo ya kalle ta baice komai ba ya sake d'auke kansa yana cize baki lokaci d'aya yaji cikin sa na k'ullewa. Ganin hakan sai tayi shiru bata sake magana ba dan tasan kallo na kin ishe ni ne hakan ya saka ta yin shiru tana kallon sa yana yamutsa fuska. Sun jima a haka a zaune kafin ya cize bakin sa ya furta, "Ya salam!." Mugun ciwo cikin sa yake yi bai san sanda ya furta hakan ba idanun sa lokaci d'aya sun canja kala zuwa jajaye haka fuskar sa ma tayi ja jikin sa har rawa yake yi. "Asad!, Asad me ya faru!?" Ta fad'a tana kallon sa ganin lokaci guda ya canja. Idanun sa da taga ya kulle yana sauke numfashi hannun ta na rawa ta kira number Mama tana d'auka tace, "Mama Asad zai mutu! Kizo Mama" ta fad'a da k'arfi tana kallon Asad da yake jingine a kan kujera kamar baya numfashi.. *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *009.* Tunda Mama tazo inda yake hankalin ta yake a tashe tana zaune kusa dashi tana fad'in, "Asad me kake ji a cikin naka? Kayi min magana dan Allah. Yaushe ya fara yi maka ciwo? Me kake ji?, zafi yake kome?." Bud'e idanu yayi ya zauna sosai yace, "Mama, I'm okay fa." "Ban amince ba Asad, kalli face d'in ka fa yadda ya koma, tashi muje asibiti da sauri daman nasan babu ta yadda za'ayi kaci abincin Hajiya ba tare da ka samu wani abun ba." Hannun ta ya rik'e duk da ciwon da cikin sa yake masa yace, "Mama kar ki tayar da hankalin ki." "Ta yaya bazan tayar da hankali ba Asad? Abincin fa ta baka kaci gashi har kana ciwon ciki wanda baka tab'a yi ba, hankalina kake so na kwantar ko me?." Shiru yayi bai amsa na kafin ya lumshe idanun sa yace, "bacci zanyi." "Baza kayi bacci ba Asad sai munje asibiti, kar ka kulle idanun ka ka bud'e mu tafi." Suhaima ce suka shigo tare da Dr Yasir Mama na ganin sa tace, "Zo da sauri ka duba shi." Da saurin kuwa ya k'arasa yana yanayin jikin nasa yana tambayar sa abinda yake ji duk da yasan babu lallai ya basa amsa. Allurar ciwon ciki yayi masa kafin ya d'ago ya kalli Mama yace, "Ranki ya dad'e ba wani abin tayar da hankali bane nayi masa allura zai daina ciwom." Jidda tace, "are you sure zai daina?." "I'm very sure." Mama tace, "in akwai damuwa muje asibiti ko scanning ne ayi masa." "A'a ranki ya dad'e zai ji sauk'i." Kai ta d'aga shi kuma ya fita da sauri baya so tayi masa maganar Rauda da take asibiti. Aliyu da ya shigo a lokacin ta kalls tace, "Ka rik'e shi ku shiga d'aki ya kwanta, please Aliyu take care of him bana so wani abun ya same shi." Mik'ewa Asad yayi ya tafi d'akin da kansa Aliyu ya kalli Mama yace, "basai na taimaka masa ba kin gani" yana fad'a ya shiga d'akin da yake kusa da na Asad d'in ya kullo k'ofa. Fita Mama tayi suma su Suhaima suka fito suka ga ta mik'e alamun b'angaren mai martaba zata je su suka kuma koma ciki. Mai martaba yana zaune shi kad'ai kamar ko yaushe aka mata izinin shiga ta shiga da sallama ta nemi k'asa ta zauna tana kallon wani wajan daban. Ganin hakan sai ya murmusa yace, "Rabi'atul adawiya ya akayi ne?." "Allah yaja da ran mijina burin mutanen gidan nan suga bayan y'ay'ana me suka tare musu? Hydar gashi can ciwo ya tashi, ga Asad ma Hajiya ta bashi zogale yaci gashi can a kwance yana ciwon ciki. Ya suke so nayi ne me na tare musu?." Mai martaba ya mik'e daga kashingidar da yayi yace, "Ciwon Hydar ya tashi baki sanar dani ba?." Ta kalle shi tace, "Na rud'e ne gabad'aya ana kira na naje asibitin da je duba wata yarinyar da ya buge a can ciwon ya same shi na dawo dashi nan, ga Asad ma a kwance ya suke so nayi ne?" Ta fad'a kamar zatayi hawaye. Mai martaba yace, "kar ki zubar da hawaye ban sanki da raguwar zuciya ba ki daure kamar yadda kike daurewa a koda yaushe. Yanzu ya jikin Asad d'in?." Idanunta ta goge tace, "yayi bacci. zogale yaci wanda Hajiya ta bashi daman na tabbatar ba da zuciya d'aya ta bashi ba, yanzu gashi can a kwance babu lafiya, burin su suga Asad ya mutu sai sun kashe sa hankalin su zai kwanta." Mai martaba ya kalle ta sosai yace, "bana son zargin da kike saurin yi ki fara tabbatar da abinda kika ga gani kafin ki yanke hukunci." Bata ce komai ba hakan ya saka ce sake cewa, "kar ki damu duka zasu samu lafiya babu wanda ya isa yayi musu abinda Allah bai nufa ba, Asad yana da ibada sosai k'aramin abu ko babba bazai kama shi ba sai wanda Allah ya nufa. Hydar zai samu sauk'i nan kusa ki daina tayat da hankalin ki." Bata ce komai ba a nan ma amma ta d'an ji sanyi a zuciyar ta yace, "muje na duba jikin su da kaina" ya fad'a yana mik'ewa tsaye ita kuma bata mik'e ba. Ganin hakan ya saka hannayen sa da kansa ya mik'ar da ita tsaye yana kallon fuskar ta da murmushi yace, "kar ki bada ni mana, ko yaushe ina fad'in ke jaruma ce samu mace mai irin tsayayyiyar zuciyar ki abu ne mai wahala ya zaki bani kunya kum?. Come on ban san ki da haka ba, muje." Tare suka fito ganin fitowar mai martaba babu tsammani aka tawo a guje aka saka masa takalmi aka bud'e lema tana takawa a hankali tana gefen sa ana zuba masa kirari har cikin d'akin da Hydar yake. Daga shi sai ita sai shamaki a gefen sa wanda aikin sa duk inda sarki yake yana kusa dashi sune kawai a d'akin kowa yana waje ya kalle ta yace, "meyasa ba'a bar shi a asibitin ba?." "Nan yafi safe."" ta bashi amsa a tak'aice tana kallon sa itama. A tare suka kuma fitowa ana ta kallon su bayi masu gulma suna yi tuni har an kaiwa sauran labari tun kafin su gama ma abinda ya fito dasu. Inda Asad yake suka shiga har cikin d'akin sa, mai martaba ne ya shiga d'akin kawai bai jima ba ya fito daga d'akin ana kirari aka raka shi har b'angaren sa. Bata zauna ba ta koma nata b'angaren mai martaba shi kansa abin ya d'aure masa kai sosai duk da yasan ciwon ciki lalura ce amma ya tabbata na Asad yana da sila baya so ya nuna mata ne ya sake tunzura zuciyar ta shiyasa yayi shiru. B'angaren Hajiya da labari yazo mata Asad yana kwance sai ta damu tana ta zaga d'akin ta cikin tunani dan dai ita ta tabbatar bata sakawa Asad komai a cikin zogale ba wanda ta bashi ko ita zata iya ci, amma meyasa akace bayan yaci yana ciwon ciki?, meye dalilin ciwon cikin nasa?, Anya babu wanda ya jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya?. Ta jima tana wannan tunanin kafin wayar ta d'auki k'ara, d'auka tayi taga sunan mai gidan ta Yana kiran ta ta d'auka a kunne ta saurari abinda yace kafin ta yanke wayar. Numfashi ta fesar ta fito cikin takun isa da k'asaita ta tafi amsa kiran mai martaba. Daga shi sai Wambai sai Mama a zaune ta shiga da sallama ta zauna gaban ta na fad'uwa sosai zuciyar ta duk ta cika da tsoro, mai martaba yace, "Rabi'atu gata." Mama ta kalle bowl d'in gaban ta da yake d'auke da ragowar zogalen a ciki ta fito da farar takarda tace, "wannan shine sakamakon gwajin ragowar zogalen nan da akayi ya tabbatar kuma an bawa Asad guba kuma itace wacce ta bashi yaci." Hajiya ta dafe k'irjin ta da yayi mugun bugawa fuskar ta tayi kalar tausayi ta kalli mai martaba shima ita yake kallo kafin yace, "Sa'adatu ya akayi haka?." "Allah ya taimake ka wallahi Allah ban bawa Asad wani abu a cikin zogalen nan ba, inda nayi niyar cutar dashi bazan bari yasan nice na bayar ba sai dai yaci. Ko ni zan iya ci ban san ya akayi hakan ta faru ba, mai martaba yasan bazan rantse a kan k'arya ba" ta fad'a muryar ta na rawa sosai. Mai martaba ya kalli Mama yaga ta kawar da kanta gefe alamun bata ma yarda ba kafin ya kalli wambai ya dawo da kallon sa a gare su yace, "zaku iya tafiya. Amma bana so na sake yin maganar nan a barta a wajan nan kar na kuma ji. Zaku iya tafiya." Ba musu suka tashi suka fita mai martaba ya kalli Wambai yace, "Mubarak mai ka fahimta game da lamarin nan?." "Allah ya ja zamanin ka abu ne a bayyane kai tsaye baza'a ce Hajiya ce ta bashi gubar ba, kai tsaye kuma baza'a ce Fulani itace ta mata sharri ba. Komai zai uya faruwa kowa yana da gaskiya a cikin su." Mai martaba ya sauke numfashi yace, "Sa'adatu bazata bashi guba ba ni nasan da hakan, koda ma ace zata bayar d'in kamar yarda tace baza tayi yadda za'a gane ba ta taka sahun b'arawo ne tabbas akwai wanda yake son ganin bayan Asad a cikin gidan nan, amma waye?." Wambai yace, "koma waye Allah zai tona asirin sa. Asad mutum ne mai addu'a kuma power of du'a tana canja destiny komai girman ta, kafin mummanar k'addarar ta samu Asad addu'a ta canja ta." Mai martaba ya girgiza kai zuciyar sa taf da tunani yace, "Rabi'atu dole ta shiga damuwa yau ta shirya zuwa Kano ga Asad ba lafiya ga kuma Hydar a kwance ba'a san ranar da zai farfad'o ba." "Gaskiya ta b'angaren yaranta tana karb'ar jarabawa daga Allah, amma in ta kwantar da hankalin ta Asad sai ya zamarwa makiya ciwon ido." "Allah yasa mu dace" mai martaba ya furta ya amsa da amin. B'angaren Hajiya tunda ta koma take zagaye hankalin ta ya tashi sosai ganin maganar har taje gaban mai martaba, babban tashin hankalin ta bai wuce yardar da mai martaba yayi da ita kar ta zube ba hakan ya saka ta shiga d'aki can k'arshe ta d'auki waya ta kira Waziri. kira 1,2 ya d'auka yana d'auka kafin tayi magana yace, "kin bawa Asad zogale yaci yanzu kuma yana ciwon ciki an yi binciken ragowar da ya rage an gano akwai guba a ciki, hankalin ki ya tashi domin kedai kin san baki saka komai ba kar hakan ya jawo rushewar yardar da kike so Asad yayi dake, shine kawai tashin hankalin ki amma bawai dan yaci guba ba haka ne?." Da zallar mamaki tace, "duk ya akayi kasan wannan bayan kai kana wani wajan daban ina nan daban?." Murmushi yayi mai sauti yace, "kar ki raina basira da y'an leken asirin da master planer take dashi a gidan nan, itace ta sanar dani duk abinda ya faru gashi kuma na tabbatar hakan ne." "Wai wacece master planer d'in nan? A ina take?, ya akayi ta san duk abinda yake faruwa a gidan nan bayan bata cikin sa?, su waye suke sanar da ita har abinda ya faru a falon mai martaba?. Lamarin ta ya fara bani tsoro fa na fara zargin tana kewaye damu a cikin gidan nan koma wacece" ta fad'a tana girgiza kanta. "Hhhhhh kar lamarin ta ya baki tsoro tsabar mayar da hankali ne akan abinda aka saka a gaba. Tace ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da abinda kika fara kar abinda ya faru ya baki tsoro, baki saka guba a cikin zogale ba itama ta sani kawai dai akwai wanda yake so yayi amfani dake ne a cikin gidan shiyasa ya d'ana miki tarko kuma kika fad'a. Tabbas bayan mu akwai wanda yake son ganin bayan Asad tambayar itace waye? Ko wacece? Ko kuma su waye?, ita kanta master planer bata gano waye ba." "Gano ko waye shine abinda ya kamata mu saka a gaba in ba haka ba akwai babbar matsala tunda aka fara haka." "Kada ki damu ki kwantar da hankalin ki komai zai zo mana da sauk'i tunda master planer tana tare damu, kedai ki cigaba da abinda yake gaban ki, ke kan ki kinga nasara a tafiya da master planer a jiya tace sai Hydar ya kwanta ciwo ya kwanta, a jiya tace za'a hana Rabi'atu zuwa Kano gashi kuwa duka ta faru. Ki mayar da hankali muyi abinda yake gaban mu nasara a tare damu take" yana fad'ar hakan ya yanke wayar tabi wayar da kallo. "Kenan akwai wanda yake son ganin bayan Asad bayan mu? Waye yake k'okarin shafa min kashin kaji?, wanne bak'in fenti yake k'okarin shafa min....?" Bata da wannan amsar hakan ya saka ta sauke numfashi tana sake tafiya duniyar tunani zuciyar ta cike da tsoro. A b'angaren Mama lokacin da ta koma kanta ta kulle a d'aki tana neman mafita dan zuwa lokacin kanta ya kulle, sai da ta jima sosai sannan ta fito ta tarar da Jidda da Suhaima a zaune bata ce komai ba ta shiga d'akin da Hydar yake. Yana nan yadda yake ta k'arasa kusa dashi tana shafa kansa tayi masa addu'a sannan ta fito ta sake komawa d'akin ta. Babban tashin hankalin da ya addabe su dukkan su shine su waye suke son ganin bayan Asad.....?. *☆☆☆* _Ina nan zan iso a gare ka zan baka kariya ga dukkan makiyan ka, makiya sun saka ka a tsakiya ka tashi tsaye kayi yak'i dasu kafin isowata gare ka, zan zo nan bada jimawa ba kafin na k'araso ka tabbatar ka tsaya da k'afafun ka, ina nan zuwa.....!_ a firgice Asad ya mik'e zaune yana zare idanun sa jikin sa yayi bala'in mutuwa ga ciwon cikin da yake damun sa har lokaci. Tuno mafarkin da yayi yake yi tiryan-tiryan suna dawo masa kansa ya dafe kai da duka hannu biyu yana yanutsa fuska. Kusan kwanaki goma kenan a jere kullum sai yayi mafarki da yarinyar da baya ganin fuskar ta sai dai yaji maganar ta itama kuma baya jin maganar tarrr dan baya tunanin zai iya gane mai maganar a zahiri, "who is she?" Ya tambaya a bayyane yana dafe cikin sa yana cize bakin sa. Tsaye ya tashi ya kalli agogo yaga har lokacii ya tafi yana dafa bango ya shiga band'aki yayi wanka da alwala ya fito ya tayar da sallah ya idar lokacin akayi la'asar yayi. Shiryawa yayi cikin manyan kaya maroon d'in yadi mai zane yayi masa bala'in kyau ya saka hula kalar aikin sumar kansa da sajen face d'in sa sai d'aukar ido suke yi. K'aramar riga mai zanen adon sarauta ya dauka kalar ta maroon itama ya d'ora akan ta saman hatta takalmin sa zanen sarauta ne a jiki. Cize baki ya kuma yi domin yana jin ciwo har lokacin ya furzar da iska ya d'auki wayar sa ya fita zuwa falo. a zaune ya tarar da Hafiz ganin fitowar sa ya kalle shi yace, "Prince ya jikin?." Kai ya d'aga alamun da sauk'i yana cize bakin sa har lokacin. Baice komai ba ya fita direct wajan mahaifinsa ya tafi aka masa iso ya shiga ya same shi babu kowa sai shi kad'ai yana duba littafan addini kamar koda yaushe. Ganin Asad ya saka shi ajjjiye littafin yana kallon sa ganin ya rame lokaci guda idanun sa sun fad'a yace, "Aliyu na, gadanga kusar yak'i, mai zuciyar maza, zaki mai firgita makiyan sa, ya akayi ne?." Murmushi yayi jin kirarin da mahaifin sa yake masa ya had'd'iye saliva ya kalle shima shi yake kallo mai martaba ya kuma cewa, "Yau sarautar ake ji da ita kenan ko?." Nan ma Murmushi yayi yace, "Barka da yamma." Mai martaba yace, "Ya jikin naka?." "Alhamdulillah" ya furta yana gyara zaman sa kafin mai martaba ya kuma cewa, "Naji dad'i da naga ka samu lafiya Asad, Kar ka saka komai a ranka Asad nasan mahaifiyar ka zata sanar dakai guba aka baka kaci a zogale amma bana so hankalin ka ya tashi domin duk mai son ganin bayan ka da iznin Allah kaine zaka ga bayan sa. Kana gani yanzu gashi an baka guda amma ko awa biyar ba'ayi ba ka tashi cikin k'oshin lafiya kamar ba kai ba. Ka cigaba da addu'a ka dage da addu'a kar kayi wasa da addu'a makiya sun saka ka a tsakiya kai kana gefe dole sai ka kai kukan ka wajan wanda ya halicce ka shine kawai zai kawo maka garkuwa da mafita nan kusa." Kallon mahaifin nasa yayi jin yana maimaita kusan irin abinda yarinyar da yake mafarki take fad'a masa hakan ya saka yace, "in an min izinin zan iya bawa mahaifina labari?." Mai martaba yace, "labari da kanka? Ina jinka." "Allah ya kara maka lafiya ina yawan mafarki da yarinya tana fad'a min kusan abinda mai martaba yake, amma bana ganin fuskar ta bana kuma gane maganar ta......" ya dafe mai martaba yace, "huta sai ka cigaba da fad'in min, Allah ya yaye maka wannan rashin son maganar taka kullum sai nayi maka addu'a akan hakan ina kuma da yak'inin Allah zai sassauta ka dinga magana koda bamai yawa ba." "Tana cewa zata zo gare ni nan kusa amma kafin nan na tashi nayi yak'i makiya na, Allah ya taimake ka ban san me hakan yake nufi ba" ya fad'a yana kallon mahaifin nasa shima kuma shi yake kallo. Da hannu ya masa alamu da ya matso kusa dashi ya matsa sosai ya rik'e hannun sa yace, "Asad kaine garkuwar wannan masarauta matuk'ar kamar yadda nake fad'a maka ko yaushe, in wani ya karb'e ta ba kai ba zata watse ta tarwatse talakawa zasu yi kuka. Ko bana raye ka tsaya kai da fata wajan ganin ka mallaki kujerar nan matsayin taka." Asad yayi shiru ya sauke kai k'asa. "A mafarkin ita yarinyar ta tab'a taimakon ka?." Kai ya d'aga alamun eh kafin yace, "ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba." mai martaba yace, "garkuwar kace Asad zata shigo rayuwar nan kusa sai dai bamu san da wacce fuska zata shigo ba, ina ji a jikina alkhairi ce a gare ka gashi bamu santa ba balle mu nemo ta. Tabbas itace zata kasance magani ga duk wani mak'iyin ka, itace zata kasance katanga a gare Asad. ka nemeta alkhairi ce a rayuwar ka, ba ko wanne mafarki ne yake zama gaskiya ba amma kwatankwacin abinda kake gani zai faru Asad." Numfashi yake saukewa a hankali ya dafe cikin sa mai martaba yace, "daure Asad nasan kana jin ciwo sosai an baka ne dan a kwantar dakai ciwo ko a kashe ka." "Abbana sai nake ganin kamar Hajiya baza ta cutar dani ba." Murmushi yayi yace, "Asad kenan, zuciyar ka wankakkiyar ce ka amince da kowa shiyasa kake ganin kowa irin taka zuciyar ce dashi. Bance zata cutar da kai ba amma ka kula da wanda suke kusa da kai da yawan suna yi ne dan su cuce ka, furta zanyi murabus da nayi shine kuskure babba da nayi dan daga lokacin mak'iya suka sako ka a gaba kowa so yake yaga bayan ka. Duk da daman kana dasu tun a da yanzu ne suka k'ara yawa." Asad ya girgiza kai mai martaba yace, "ka cigaba da addu'a duk abinda ya tunkaro ka ka fuskance shi ka daina cin abincin kowa sai wanda Maman ka ta baka itace kad'ai ce baza ta cutar da kai ba dan itace ta haife ka bayan ita kar ka amince da kowa hatta y'anuwan ka na jini ban d'auke kowa a cikin su ba sai kuma wanda zuciyar ka ta amince dasu." "In sha Allah Takawa zanyi abinda aka umarce ni" ya fad'a da girmamawa kamar ko yaushe kansa yana kallon k'asa. Mai martaba yace, "Allah ya bada iko. Kak'i kayi aure wata k'ila matar taka ce garkuwa a gare ka Allah yake nuna maka tun yanzu, ka daure ka nemo mata kayi aure a kwanakin Asad." "In sha Allah zanyi" ya bashi amsa yana murmushi. Murmushin shima yake yana kallon sa, kaf y'ay'an sa babu wanda yake so kamar Asad a baya yaso Aliyu amma a yanzu halayen sa sam sun saka ya fita a ransa amma Asad shine a kan gaba a kaf cikin yaran sa. Shi kad'ai ne zai zauna dashi yayi doguwar hira haka shima Asad d'in shi kad'ai yake iya fad'awa damuwar sa hakan ya saka in suka zauna waje d'aya sai su shafe awa d'aya mai martaba bai ga kowa ba sai shi kawai. Bai wani jima sosai ba ya fito yana takawa a hankali kasancewar yamma tayi iska na kad'a shi yana kallon kowa na aikin sa ana ta gaishe sa yana d'aga hannu ko ya d'aga kai. Wajan Mama ya tafi yana shiga duk da bayin da suke zaune a wajan bai hana ta tashi ta k'araso wajan sa ta rik'e shi tana fad'in, "Asad ya jikin naka?." "Mamana ta kwantar da hankalin ta naji sauk'i, ina Hydar?" Ya fad'a yana tafiya d'akin da hydar yake tabi bayan sa. Gadon Hydar ya dafa yana masa addu'a yana kallon sa dan kaf cikin y'an uwan sa yafi son Hydar dan shima yana son sa. "Asad ka daina jin ciwon cikin?" Mama ta tambaya tana kallon sa. Kallon ta yayi yace, "eh Mamana, da sauk'i." "Abinda nake nuna maka baka ganewa shine ya faru Asad, zogalen da kaci a cikin gubar take, da ka mutu ya zanyi...?.." Murmushi yayi yace, "Mamana ban mutu ba kuma na gane duk abinda mahaifiyata take fad'a min." Murmushi tayi tana kallon sa tace, "na gode Asad, Allah yayi maka albarka ya baka lafiya ya kare ka a duk inda kake." A iya labban sa taga ya amsa da amin. Tare suka fito tana gaba yana binga ta kalle shi tace, "yanzu ina zaka je?." Shiru yayi bai amsa ba tace, "kar ka fita ka huta Asad please." Ya d'aga kai a lokacin Jidda ta fito daga d'aki tana ganin sa tayi murmushi, "Mama Bro deaf ne right?." "Yeah, but ki daina kiran sa deaf fa." Murmushi tayi tana kallon sa tace, "ya jikin?." Kai ya d'aga kawai kafin ya wuce ya fita baice komai ba. Zuciyar Mama fal farin ciki ganin yaji sauk'i sosai kamar ba shi ba taji dad'i duk da kuma Hydar na kwance. Asad lokacin da ya fita jakadiyar Hajiya ta zube a gaban sa tana fad'in, "Allah ya ja zamanin yarima mai jiran gado, Allah ya kare zakin mu, Allah ya kiyaye ka ya baka kariya daga mak'iya." Shiru yayi jin hakan ya saka tace, "Gimbiya uwar gidan mai martaba tace ayi maka magana tana son ganawa dakai." Da hannu yayi mata alamun da su je, gaba yayi tana bayan sa tana kirari har sai da ya juyo ya kalle ta tayi shiru ya cigaba da tafiya tana bayan sa, yana zuwa ya shiga ita kuma tana tsaya a bakin k'ofa ya shiga da sallama. K'annen sa maza da y'an matan ta guda biyu Khaleesat da Juwairiyya ya gani suna ganin sa kowa ya mik'e suka gaishe shi ya amsa da murmushi kana yace, "kun b'oye." Mamaki suke jin ya musu magana Khaleesat tace, "naje duba ka d'azu kana bacci." Kai ya d'aga kai kafin Juwairiyya tace, "Hajiyan tace ka shiga ciki." Kai ya kuma d'aga ya shiga ya same ta a falon ta ita kad'ai tana ganin sa ta mik'e tana cewa, "Asad wallahi ban baka komai dan na cuce ka ba, ina kallon ka kamar d'an dana haifa akan me zan kashe ka kona kwantar da kai ciwo....? kayi hak'uri ban san waye ba" ta fad'a kamar zatayi kuka. "Babu komai Hajiya, na amince Hajiya tamkar Mamana." "In kai ka amince mahaifiyar ka baza ta amince ba Asad, gani take kashe ka zanyi." Kai ya girgiza yace, "babu komai" ya furta da murmushi yana kallon ta kafin tace, "na gode Asad, Allah ya baka lafiya. Zan cigaba da aiko maka da ganye kamar yadda nasan kana so, wallahi da zuciya d'aya nake maka badan wani abun ba." "Na gode." Tace, "Zaka iya tafiya." Baice komai ba ya juya zai tafi tabi bayan sa da kallo tana murmushi har ya fita kafin ta gyara tsayuwar ta tace, "Yanzu aka fara wasan Rabi'atu, yanzu kafcen ya fara, mu jira muga ni dake waye zaiyi nasara wa za'a bawa lambar girmamawa.....? Dan ni Sa'adatu bazan tab'a barin Asad ba sai naga bayan sa!" tayi murmushi ta shafa fuskarta ta shiga d'aki zuciyar ta kar......... *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *010.* Asad lokacin da ya koma d'akin sa gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa fassarar mafarkin da mahaifin yayi masa yana dawo masa cikin kansa tiryan-tiryan, kenan akwai mace da zata shigo rayuwar sa matsayin mata? Wacece ita?, a ina take Allah ya had'a su tun a mafarki?. Shin ita tana mafarkin sane ko batayi?. Sam baya so wata mace ta shigo rayuwar sa ko kad'an sabida shi kad'ai yasan illar dake tattare da hakan. Lumshe idanun sa yayi tuno Jidda ce zab'in Mama ya bud'e idanun a zuciyar sa yana tambayar kansa kodai Jiddan itace yarinyar mafarkin...? Numfashi ya sauke a hankali kammanin ta suke bayyana a idanun sa kamar lokacin yake mafarkin. Wara idanun sa yayi yana hango zubin ta da kammanin ta amma basa fita tarrr amma yana iya hango ta a idanun sa kamar almara, agogo ya kalla yaga yamma tayi sosai bazai yu yaje Abuja ya dawo a ranar ba da babu abinda zai hana shi zuwa Abuja wajan abokin sa Zaid ya zana masa fuskar da yake gani a mafarki ko zai iya gane ta in ya ganta, da ace yana kano ma a lokacin zai tafi amma yasan yana Abuja.. Haka yayi ta zaune da wannan tunanin kafin ya tashi ya d'auki makullin mota ya fita. *☆☆☆* "Dan Allah Malam ka bani koda duba d'aya ne a kud'in na siyo mata kayan marmari ta sha bata iya cin abinci, koda tana ci ma ba'a son mai karaya tana cin abu mai nauyi sabida zagawa band'aki" Umma ta fad'a tana kallon Baba da yake tsaye a cikin d'akin. Baba ya gyara zaman hula yace, "Kinga ni babu komai a jikina kud'in ma da aka bani na adana su sai auren ta yazo sai ayi amfani dasu, ga shinkafa da manja nan ai nasan tana san cin abinci da manja shiyasa na saka aka dafa mata." "Yanzu Malam mai karayar ce zata ci shinkafa da manja? Kazar gida fa ita ake so masu karaya suci sabida tabi jikin su." "To ba'a haifo ta inda zata ci kazar ba in baza ta ci shinkafar ba ta hak'ura." "Amma Malam kud'in da aka bayar fa duk nata ne tunda itace take jinya." A fusace yace, "Amma ji kikayi nace ai na adana mata sai lokacin bikin ta ko? Ko saka su a gaba nayi naci banza da wofi dasu?." Jin yadda yake magana Rauda dake kwance tace, "Umma a bar shi zanci shinkafar." Umma tace, "ta ina zaki ci shinkafa Rauda?, baki san ba'a san mai karaya ya dinga cin abu mai nauyi ba sabida yawon band'aki?. Dan Allah malam ka bani koda naira d'ari biyar ce." Tsaki yayi ya saka hannu a aljihu ya d'auko naira d'ari biyu yace, "gashi nan a siyo mata." Ba yadda Umma ta iya haka ta karb'a ta kalli Khairi da Khalil da suke gefe tace, "Khairi ina za'a samo mata kankana da lemon zak'i tasha?." Khairi tace, "Umma wajan asibitin nan akwai amma da gani zaiyi tsada tunda kinga asibitin manya ne." "Jeki dai ki duba mana ko za'a samu" ta fad'a tana bata kud'in ba musu ta karb'a ta tafi. Tana fitowa wajan asibitin kuwa suna nan masu kayan zak'in ta tsallako ta nufo su tunda ta tawo kowa ya tashi dan daman an san siyayya za'ayi ta k'arasa wajan d'aya tace, "Sannu Baba." Yayi murmushi yace, "yauwa y'ata me za'a baki?." "Kankana nake so ta naira d'ari lemo ma na d'ari" ta fad'a tana mik'a masa kud'in. Kallon ta yayi ya kalli kud'in ya kalli asibitin da ta fito sai ta girgiza kai yace, "yarinya babu na kud'in sai dai na baki lemo guda biyu ko wanne naira dari." Wara idanu tayi tace, "a unguwar mu naira ashriin-ashirin ne, bar shi bara na tambayi na gaba." Koda taje na gaban ma shima haka sukayi ta je na kusa dashi shi ce mata ma yayi babu ta tsaya cak kawai tana kallon su cikin rashin sanin abin yi. Mota ce ta faka a kusa da ita aka sauke glass dai-dai lokacin da take cewa, "Yayata aka kwantar a nan kuma bata iya cin abinci dan Allah ku taimaka min ku bani kankana da lemo na d'ari biyu ita kad'ai ce damu itama dak'yar Baba ya bayar." "Dallah malama bamu dana kud'in ki ki wuce ki bawa mutane waje, y'ar aiki kawai" daya daga cikin su ya fad'a ta juyo idanun ta ya fad'a kan Asad da yake kallon su mai siyar da Apple yana masa magana ma amma baiji ba. Gaban Asad ya fad'i haka kawai ya tsaya yana kallon fuskar ta kamar dai yana so ya san mai irin ta amma bai a ina ba, ya motsa bakin sa ya kalli wanda yake masa magana yace, "ku bata komai." Jiki na rawa yace, "an gama alhaji" ya fad'a yana komawa ya fara had'a mata kaya da yawa. Murmushi tayi tace, "na gode sosai Yaya Allah ya saka da alkhairi, Yayata ce aka kwantar da ita a nan bata iya cin komai akace nazo na siyo mata kuma d'ari biyun kenan damu itama dak'yar Baba ya bayar" ta fad'a tana kallon sa. Kallon ta shima yake jin tana magana kamar ta had'd'iye radio ba commer babu full stop zuba kawai take yi, kallon asibitin yayi ya dawo da kallon sa gare ta ganin asibitin da suke zuwa ne kuma wanda yake k'ark'ashin kulawar Mama to meya kawo yarinya kamar wannan cikin sa bayan yasan hundred percent na kud'i ne kud'i ma kuma ba kad'an ba..?. A lokacin aka kawo mata manyan ledodoji guda uku an cika su da kayan marmari da murna ta kalli ledar lokacin da yake karb'ar tasa ta apple tace, "na gode Yaya, dan Allah ya sunan ka?." Sai ya samu kansa da yin murmushi a hankali yace, "Aliyu." "Na gode Yaya Aliyu, kuma wallahi kana da kyau kamar mutanen nan na tv da nake gani a gidan Yaya Ummi, kuma gashi kana jin hausa, dan Allah d'an garin nan ne kai?." Shi dai Asad kallon ikon Allah kawai yake ganin yarinya mai shegen surutu kamar wata y'ar tsana. Sai kuma tace, "Umma zata min fad'a tace ina na samo kud'i na siyo wannan zata kuma ce rok'ar ka nayi." Shi kam ya gaji da surutun ta ya d'aga glass sama bai ce komai ba yaja motar sa ya tafi ta bishi da kallo ta kinkimi ledojin dak'yar ta shiga asibitin. Tana tafiya tana hutawa har ta shiga d'akin ganin ta da leda har uku Umma tace, "Ke bashi kika karb'o ne?." Tana haki ta ajjiye tace, "Wani ne ya siya min ganin suna tayi min wulaƙanci sunce baza su bani duka a d'ari biyu ba wai sai dai lemo guda biyu d'ari biyu, shine ya siya min duka. Umma baki ganshi ba mai kyau kamar baya jin hausa ya kuma cemin sunan sa Aliyu." "Ummulkhairi yaushe zakiyi hankali ne wai ke? Baki da girma sam ke sai na jikin ki? Akan me zaki karb'i abin hannun wanda baki sani ba?, rok'on sa kika yi ko?." "Wallahi Umma ban rok'e sa ba shine fa ya bani, kuma ban tambaya ba muje a tambayi masu siyarwar." Baba da yake sauraren su ya bud'e leda d'aya ya d'auki apple ya ci yana lumshe ido yace, "ni nasan halin ki baza ki tambaya ba, d'auki ki sha kema ki dandali arzuk'i." Umma ta kalle shi kafin ta girgiza kai ta tashi ta d'auki wuk'a ta yankawa Rauda kankana da gwanda da tufa d'in ta k'arasa kusa da ita tana bata tana ci a hankali. Sai da Baba ya cika cikin sa dam da kayan marmari ya goge baki yace, "oh yarinyar nan dai ana ta samun alkhairi tunda kika kwanta a asibitin nan, a haka ma fa wai dan Anas baya nan ai da nasan kullum sai munci kaji wallahi. Kai Allah ya dawo dashi kafin a sallame mu." Babu wanda ya tanka ya mik'e yace, "to zan koma Rahma zata kawo muku abinci inda wani abun sai amin waya." "Basai an kawo komai bama wannan zai isa muci." "To Khalil, Ummulkhairi muje, sai da safen ku." "Allah ya tashe mu lafiya." Bayan fitar su Umma tace, "tsabar san kud'i ya dinga fatan wai kar a sallame ki har sai wani ya dawo kawai dan a basa kud'i, Allah ya kyauta ni ban san irin zuciyar baban ku ba nikam ba haka nake ba wallahi." Rauda tana ji bata ce komai ba idanun ta a rufe tana tauna kankana. *☆☆☆* Asad haka ya gama zagayen sa a gari bai koma gida ba sai bayan sallar i'sha sai da ya shiga wajan Mama yaga Hydar sannan ya wuce d'aki yana shiga d'akin Ummulkhairi ta fad'o masa a rai ya murmusa tuno surutun ta baice komai ba ya shiga band'aki yayi wanka tare da alwala ya fito yayi shafa'i da wutur ya jima yana addu'a sannan ya kwanta. Abu yaji kamar yana shiga jikin sa ya tashi ya yaye zanin gadon da yake shinfid'e a kan gadon ya dawo zallar katifa yana kallon tsurar katifar amma baiga komai ba, mayarwa yayi ya yafa zanin gadon ya koma ya kwanta ya rasa meyasa yake jin hakan duk sanda ya kwanta a kan gadon sa. Ya jima kafin bacci ya d'auke shi yana juyi yana jin abu na shiga jinin sa kamar tiriri ne yake fitowa daga katifar yana shiga jinin sa. K'arfe uku na dare ya tashi kamar ko yaushe yayi alwala ya tayar da sallah, ya jima yana sallah sai da assalatu ya rage mintina arba'in sannan ya fara addu'a yana rok'on Allah har akayi kiran Asuba ya fito daga d'akin. Masallaci ya shiga akayi sallah yabi mai martaba har cikin b'angaren sa suka gaisa sannan ya shiga wajan Mama ya gaishe ta ya duba jikin Hydar sannan ya fita da niyar komawa d'akin sa. Kamar giftarwa mutum ya gani da sauri ya tsaya cak ya kalli dan lungun da yaga an bi da sauri, ya taka a hankali ya k'arasa wajan amma duhun asuba bai ga kowa ba ya shiga yana takawa a hankali yana bin wajan haka kawai yaji bai yadda da wajan ba, a hankali ya jiyo tashin murya ana fad'in, "na saka, na saka dak'yar" sai kuma ya daina jiyo maganar bai ga kuma kowa ba. _me aka saka? Wa kuma aka sakawa?._ ya tambayi zuciyar sa amma babu mai bashi amsa ya koma da baya sai kuma ya sake kallon wajan amma babu kowa. D'akin sa ya wuce ya tarar da Aliyu a zaune da alama dawowar sa kenan ma gidan dan gashi nan da kayan jiya da daddare ga warin sigari na tashi a falon, kallon sa yayi ya girgiza kai kawai ya shiga d'akin sa ya d'auki alkur'ani ya karanta suruti yasin yayi azkar sannan ya kwanta. _na saka, na saka dak'yar._ abinda ya dawo masa zuciyar ya juya yana tunanin abinda aka saka ake cewa an saka dak'yar da wannan tunanin bacci ya d'auke shi. _k'atuwar kujera ce ta tsakiya ita bata sauka ba kuma bata sama k'asa wuta ce gefe namun daji ne ko wanne ya bud'e bakin sa, Asad ne a kan kujerar saura kiris ya fad'i k'asa in ya fad'a wuta ce in kuma ya zauna a kai namun dajin nan sai sun cinye shi, ya rasa yadda zaiyi gashi babu kowa a wajan. k'ato kuma k'osasshen zaki ya kawo masa cizo Asad ya runtse idanun sa gab da cize shi yaji kamar anyi sama dashi an d'auke shi daga kan kujerar. Fad'a sosai yaga yarinyar sun fara ita da namun dajin nan suna k'ok'arin cizon sa tana tarewa duk sun cize mata jiki cikin d'aga murya tace, "Ka kashe wutar kai kuma! Ka kashe ta!! Kar ka bar ko kad'an!!." Ba musu ya d'ebi k'asa yana zubawa wutar tana sake yin sama kamar zata kamo hannun sa yana sake zubawa a hankali take mutuwa zuwa lokacin ta kusa k'arar da namun dajin da take fad'a dasu. Lokacin da ya gama kashe wutar ya hango wani k'atoton maciji ta bayan zai sare ta ya yayi tsalle ya janye ta ya tura ta baya ya fillewa macijin kai da takobin da bai san daga ina take ba ya ganta kawai a hannun sa. Kallon tarin namun dajin da ta kashe yake yi ya kalle ta yaga wasu sun yakushe ta a fuska wasu a hannu har da cizo a hannun ta, da sauri ya rik'e hannun ta yana kallon cizon ta fizge hannun ta tace, "Meyasa baka son nemawa kanka kariya ne? Meyasa kake yadda da kowa? A halin da kake ciki bada kowa zaka amince ba..... Kai sarki ne ya zama dole ka kula....in ba haka ba za'a ga bayan ka cikin sauk'i....!." Asad da yake kallon ta yace, "Wacece ke? Meyasa kike son ki taimake ni? Meyasa kika tsaya suka cutar dake sabida ni? Ban san ki ba a ina kike?." Kai take girgizawa tana yin baya tace, "zaka sanni amma kafin lokacin yazo za'a jima, za'a sha qalubale kafin nazo rayuwar ka, kayi abinda nace, ka tashi tsaye ka bar batun zuwa na ka yak'e su kafin su kashe min kai......" zai kuma magana yaji an rik'e hannun sa ta baya yana juyawa yaga Mama tace, "Zo mu tafi Asad, baza ka bita ba zo mu tafi." Kallon ta yake tana sake yi masa nisa Mama na jan sa yana sake waigawa yana kallon ta daidai lokacin da ta juyo ta ta masa alamun jinjina._ A firgice Asad ya sake tashi yana kallon jikin sa amma bai ga wani tabo ko alamun wahala ba kamar a mafarkin, kammanin ta yake so ya tuna amma ina ya kasa ya runtse idanun sa ya nutsu ya tsayar da kwakwalwar sa waje d'aya cak a hankali yake ganin kammanin suna washewa a idanun sa, iya idanun zuwa goshin yake iya gani sujjud mark d'in dake goshin ta bak'i shi yake sake gani a idanun sa sai idanun ta. So yake ya tuna ta gabad'aya amma ya kasa iya abinda yake gani kenan ya daki kansa yace, "Why?." Mik'ewa tsaye yayi ya tsaya a jikin mirror yana kallon kansa a madubin muryar ta nayi masa amsa kuwa a kunnen sa, sosai yaji ya gane maganar ta rasss kamar ma ya tab'a jin mai irin ta amma ya manta a ina. "Meyasa a koda yaushe take taimako na? Wacece ita?,A ina take? Yaushe zata zo inda nake? Meyasa Mama ta janye ni daga gare ta a mafarkin...?" K'aramin tsaki yaja ya d'auki wayar sa yana dannawa jim kad'an ya ajjiye ya shiga band'aki. Bai jima ba ya fito yana fitowa ya shirya cikin shigar sa ta manyan kaya ya saka d'auki key d'in mota da wayar sa ya fita, direct airport d'in Bauchi wuce yana tsayawa ya bayar da mota ajiya ya shiga ciki ya hau jirgin k'arfe sha d'aya na safe zuwa Abuja. Mintina kad'an suka kawo shi Abuja yana sauka ya d'auki waya yana kiran wajan wanda yazo, ba jimawa aka zo da mota aka d'auke shi suka wuce. Har cikin gidan aka shiga dashi aka masa iso har cikin gidan kafin a k'yale shi ya shiga shi kad'ai, babban falo ne katafare ma kuwa yana shiga ya hango Zaid a zaune daga shi sai wando three quarter sai bodyhop a jikin sa yan zaune yana danna laptop, ganin Asad ya shigo ya saka shi jan tsaki yace, "Ina jin dai bashi kake bina ka dame ni da waya?." Asad ya zauna yana sauke numfashi yayi masa banza ya kalle shi ganin hakan sai ya tab'e baki ya cigaba da aikin danna laptop d'in sa. K'aramar yarinya ce ta shigo doguwa mara jiki mai kyau wacce zata kai kimanin shekaru takwas ta shigk ya kalle ta yace, "Amani kawowa masa drinks." Ba musu ta k'arasa kitchen ta kawo ruwa da lemo har da cake ta ajjiye sannan tace, "morning uncle." Jin hakan sai Asad ya bud'e ido ya kalle ta yayi murmushi amma baice komai ba ita kuma ta wuce ciki. "U no Zaid i can't believe that beautiful girl is your own daughter" Asad ya furta a hankali yana kallon Zaid. Idanu ya d'ago ya kalle shi ya tab'e bakin sa ya shiga ba da aikin laptop kafin yace, "ka fad'a min meke tafe dakai ina da aikin yi. Ka ishe ni da waya kamar wanda yake bina bashi, kuma wallahi kar ka saka min larabci a maganar ka." Nan ma banza Asad yayi masa sai ruwan da ya sha sai kuma Zaid ya kalle shi ya d'auki wayar gefen sa ya kira aka d'auka yace, "Precious Asad is here, please make him some breakfast" yana fad'a ya kashe wayar ya ajjiye a gefe. Ba jimawa sai ga ta ta fito da k'aton tray a hannun ta sanye da hijjab har k'asa ta k'araso ta ajjiye a kan center table zatayi magana ya d'aga mata hannu ya mata alamun da ta koma kar tayi masa magana, murmushi tayi ta girgiza ta wuce shi ta koma ciki. Asad da yake kallon sa shima murmushin yayi kafin yace, " is that really you Zaid." Murmushi shima yayi ya kalle shi yace, "Ai naga sarautar kake ji dashi kar tayi magana kayi mata banza like yadda ka yiwa Amani bazan d'auka ba" ya fad'a yana kallon sa. Tea d'in yasha hankali kwance babu tunanin an zuba masa wani abun sai da ya gama ya kalle shi yace, "friend Hameed fa?." Wara hannayen sa yayi alamun oho Asad ya runtse idanu yace,"Daddy fa?." "Kano" ya bashi amsa a tak'aice. "You know what friend? i need your help." Kunne ya nuna masa alamun yana jin sa basai ya kalle shi ba. Allah ya sani Asad bazai iya bashi labari ba hakan ya saka shi danna wayar sa yana rubuta masa text dan shima d'in ba mai son magana bane ba. K'arar shigar message yayi ya kalle shi kafin ya d'auka yana karantawa Zaid ya tab'e baki ya kalle shi yace, "prince Asad, na fad'a maka akwai abinda ya maqale a throat d'in ka, kana buk'atar ayi maka surgery wannan rashin maganar is too much." Asad yace, "please." "Can you explain?." "I can." Tsam Zaid ya tashi ya yi masa alama da shima ya tashi ya kuwa mik'e suka shiga wani babban d'aki dake cikin falon sai gasu a baban d'akin zane da manyan boards da k'ananu da yawa ga pencils da paints na zane babu adadi a wajan. Zama yayi a kujera d'aya ya kalli Asad alamun ya fara masa bayanin ta. Asad ya runtse ido yana tuno ta a hankali ya fara fad'a masa yanayin face d'in, Zaid ya zana ya kuma kallon sa Asad kafin ya jawo wata drawer ya d'auko samples na idanun mutane alamun ya nuna masa irin nata, Asad yayi lucky kawai ya zab'a ya saka nuna masa hanci da baki nan ma ya zab'a shi kuma yana zanawa. Juyo masa da zanen yayi Asad yana kalla yana wara idanun sa ganin sakk irin yadda yake ganin ta a mafarki yadda yake ganin rabin face d'in ta haka ya zana rabin ya kuma k'arasa hanci da baki da kansa. Asad ya kalle shi alamun ya akayi Zaid yace, "Yeah indai har a yadda kayi min bayani fuskanta yake then definitely that's how her face should be seen." K'arewa face d'in kallo yake amma Asad shi sam bai amince da k'arasawar da Zaid yayi ba kawai babu yadda zaiyi dashi ne amma tabbas saman fuskar nata ne k'asan ne bai amince dashi ba dan haka bai yarda face d'in ta ya fita tasss ba. "Thanks friend" ya furta yana kallon Zaid ya d'age kafad'a yana tashi daga wajan. Tare suka fito hannun Asad rik'e da board d'in. Zaman kurame suke yi a falon har akayi azahar wata maganar kirki bata had'a su ba sai da Asad yayi azahar har abinci yaci sannan ya kalli Zaid yace, "Yaran ka nawa yanzu?." "Four, maza biyu mata biyu, sun ishe ni" ya fad'a yana kallon sa Asad yayi murmushi baice komai ba Zaid yace, "Asad soon kai ma zaka tara naka yaran dakai da dream girl d'in ka dan nasan kana son tane. You're in trouble tunda ka bari ka fara soyayya it's not easy and sometimes it's painful." Asad ya murmusa zuciyar sa na harbawa Zaid yace, "Nan gaba wannan murmushin u can't do it, forget about kai prince ne zata mayar dakai like crazy sai kaji ina ma baka san teste na love ba." Murmushi sosai Asad yayi dan ya bashi dariya shima ya sake yin dariya yace, "Dariya na baka right..? In akace soyayya ina dariya ne nima a baya i thought babu wata soyayya a duniya but daga baya fa...? ina fad'a maka hakan ne saboda ya faru dani kayi addu'a akan yarinyar taso ka idan ba haka ba you're doom wallahi" ya fad'a yana clapping hannun sa yana girgiza kai. Asad da yake dariya kad'an ya daure cikin muryar sa da take da dad'in ji yace, “Did you think I'm also that type of guys...? actually u are mistaking don't forget who am I." Zaid yace," well, we shall see.. soyayya dai ba ruwanta da mulki ko sarauta... taqamar ka kai din dan sarki ne u think you're sufficiently akwai ranar da zata zo wanda sarautar da kake taqama da ita da duk abin daka mallaka basu isa su baka wannan soyayyar da kake yi mata ba zaka ce na fad'a maka." Asad ya mik'e tsaye ya ajjiye kud'i a kan table kana yace, "beside let me remind you one thing, I'm not in love with d girl. A bawa baby ta siyi chocolate." Shima ya mik'e yace, "fad'ar gaskiyar ka shine abin da saka muka zama friends few years back, and now you're trying to deny the fact. I'm telling u, you go wipe your own tears my friend." Asad ya gaji da magana sosai yana daurewa ne kawai ya lura Zaid ya koyo surutu baice komai ba murmushi zaid ya rako shi har gate driver Zaid ya d'auke shi a mota sukayi sallama ya koma. Da board d'in da aka zana fuskar yarinyar har cikin motar sa bayan ya sauka daga jirgi yana k'arewa hoton kallon sam bai amince da zanen ba gabad'aya sabida sanin halin Zaid d'in shiyasa bai nuna masa ba, kuma mutum yayi maka abu babu ko sisin ka bai kamata kace masa baiyi daidai ba. Window ya sauke ya cilla board d'in ya bi ta kansa ya wuce zuciyar sa na sake hararo masa kammanin yarinyar dake cikin mafarkin sa. Yaro dake wasa a harabar wajan ya tsallako da gudu ya d'auki zanen fuskar Rauda sa aka cillar a wajan ya d'auka yana kallon face d'in yana murna ya tsinci hoto kafin ya k'arasa a guje ya shiga mota su bar wajan. Asad baiyi nisa ba ya ja ya tsaya ya wara idanun sa tuno da yarinyar da suka had'u jiya kamar fuskar tace complete a cikin zanen ya juya kan motar ya koma amma yana zuwa wajan babu board d'in da ya cillar ya daki sitiyarin motar yace, "Ya salam!." Sai kuma ya lumshe idanun sa komai ya tuna kuma ya sake juya kan motar ya nufi Katagum kai tsaye. *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *011.* Maimakon ya wuce gida samun kansa yayi da nufar gusset house d'in mai martaba da yake hannun sa ya shiga ya faka motar ya shiga cikin gidan, a kan kujera ya zauna yana sauke numfashi a wannan lokacin kiran Zaid ya shigo wayar sa, d'auka yayi dan yasan maganar guda d'aya ce ya ya sauka kuma daman abinda ya tambaya d'in kenan. Ajjiye wayar yayi yana kallon wani waje daban kafin ya kulle idanun sa hoton ta yana gifta masa a idanun sa. Tuno fuskar da aka zana masa yayi ya tuno fuskar yarinyar da ya taimakawa a bayyane yace, "Akwai kama sosai, kenan suna da relation?." Sai kuma ya dafe kansa a zuciyar sa yace, _Why Asad meyasa wannan zai dame ka?, kawai dream ne fa ba gaskiya bane, ka manta da wannan tunanin ko zaka samu peace of mind._ numfashi ya sake saukewa a bayyane yace, "but why nake ganin ta a mafarki always tana taimako na?." Sai kuma ya mik'e tsaye yana fad'in, "ya kamata na nemo wannan yarinyar" Sai kuma yaja ya tsaya ya kama k'ugu ya fad'a kan kujera ya zauna yana furta, "Oh Asad!" Ya dafe kansa yayi shiru yana sauke numfashi a hankali tunanin yake barin ransa ya runtse idanun sa yana goge fuskar ta mafarki da wacce aka zana masa a hankali suke barin idanun sa yana ajiyar zuciya. Ya jima a haka sosai har magariba tayi a nan yayi sallah kafin ya mik'e ya d'auki key da wayar ya fita ya shiga mota ya fita daga gidan. Baiyi gida ba babban company sa ya wuce ya tarar da Hafiz yana ta kai kawo har lokacin ganin sa ya shigo ya saka shi bin bayan sa zuwa office suna zama Hafiz yake cewa, "Asad what happened?." Bai bashi amsa ba yayi shiru ya jawo laptop d'in dake kan table d'in gaban sa yana dannawa. Ganin hakan sai Hafiz ya bar shi ya fita bai jima sosai ba ya fita daga office d'in yaja motar ya fita gabad'aya. Gida ya wuce kai tsaye wajan Mama ya shiga kasancewar magariba ce bai same ta ba Suhaima take sanar dashi tana d'aki ya shiga wajan Hydar yana nan kamar yadda yake koda yaushe ko hannun sa baya motsawa yayi masa addu'a ya zauna a kan kujera yana kallon sa. A nan ya kwashe lokaci da yawa har i'sha tayi ya fita yayi sallah ya sake dawowa a nan ya ga Mama a wajan Hydar ya k'araso gaban ta ya tsuguna da girmamawa yace, "Barka da dare Mama." "Ina kaje yau?" Ta tambaye shi ba tare da ta amsa ba. Kallon ta yayi sai kuma ya d'auke idanun sa wannan tun yana ganin wani abu kan tambayar nan da Mama take masa ta ina kaje, ina zaka, me zakayi in ka fita, wa ka tambaya har ya daina ma domin ya saba. "Naje Abuja" ya bata amsa a tak'aice. Bata ce komai ba tayi jim kafin tace, "yaushe zaka je wajan Jidda kasan dai ita zaka aura ko?." Kallon Maman yayi baice komai ba tace, "in baka ce ba nasan ai ka jini, nan da lokaci kad'an za'a d'aura muku aure ta." Kai ya girgiza kafin yace, "Mamaa......" Sai kuma yayi shirun jin hakan sai tace, "kar kace min baka sonta ko baku dace ba, itace zab'ina ya zamar maka dole ka sota." Kai ya jinjina alamun gamsuwa kafin ya mik'e jikin sa a sab'ule ya fita. Sallama akayi aka shigo falon ana fad'in, "y'ar sarki, jikar sarki, matar sarki, babar sarki kuma k'anwar sarkin garin Kano in sha Allah." Jin muryar tasan wacece k'anwar mai martaba kenan Rabi'a kaf cikin dangin mai martaba tasu ce tazo d'aya suna shiri sosai ta juya ta kalle ta ta fad'ad'a murmushi tace, "babbar bak'uwa." Murmushi tayi mai sauti itama ta k'araso tana fad'in, "Zaman kujera ya gagare ni ni Rabi in dai har gimbiya na zaune a kai." Kan Mama ya sake fashewa izzar ta ta ninku ta saki murmushin k'asaita tace, "keda kika b'uya ko ganin ki ba'a yi." "Yanzun ma dole ce ta saka na taso nazo domin naji abubuwa suna ta faruwa marasa dad'in ji." Mama ta sauke numfashi tace, "bari kawai Rabi'a komai yana neman lalace min lokacin da ban shirya ba." "Shiyasa nazo ai naji ya akayi hakan take faruwa." "Sharrin Hajiya ne, itace ta bama Asad guba a ganye yaci." Murmushi Tayi tace, "Zata aikata ai, in kince badaqalar da suke yi da waziri kare bazai ci ba. Waziri yayana ne amma bazan b'oye miki ba baya son ki baya son me son ki, kinga dashi da galadima dama kawai suke jira a kan ki su kawar da y'ay'an ki sabida a lalata maki goben ki." "Na sani takwara, na sani. Duk abinda suke yi a kan idanuna suke yin sa. Nan Suhail fa ya kira Suhaima yana bata wani abu wai ta bawa Asad na tsarin jiki ne, kiji rainin wayo da y'ar uwar sa yake son yin amfani yaga bayan sa." Tace, "shiyasa dana tashi tawowa na biya wajan malamin nan na karb'o garin magani da rubutu, kinga lamarin Aliyu ma wallahi saka masa hannu akayi haka Hydar ma. Asad ya gagare su ne kawai sabida ibadar sa amma shima zasu iya nasara a kansa nan gaba tunda ya kasance mai rauni ta wani fannin." Mama tace, "ta b'angaren yarda da mutane Asad yana da rauri, ta b'angaren magana Asad yana da rauni. Amma fa wani abun kwantan b'auna yake yi kallon kowa yake kawai bar shi da rashin maganar sa. Amma wani lokacin in yayi wani abun sai ki d'auka Aliyu ne." Mama Rabi tace, "na sani, namijin duniya kenan kallon su yake yi ta wani b'angaren na san da hakan. Ga rubutun da maganin ko wanne da bayanin sa akwai na Asad akwai na Hydar dana Aliyu harda Suhaima." Mama ta ja ledar kusa da ita tana dubawa tace, "ai yanzu ma zan tashi na shafawa Hydar nasa dan wancan lokacin rubutun da kika kawo aka shafa masa yayi amfani sosai." "Mai martaba baya aiko da nasa?." Mama tace, "Da kansa yake zuwa ya bashi kin san gidan ya yake baya barin kowa yazo da kansa yake zuwa, shi da Asad kuma kin san ai ba'a jin sirrin su." "Haka ne. Wai kuwa Rukayya da Sa'adatu sun zo duba Hydar kuwa?." Mama ta tabe baki tace, "Sun zo." "Ki dai kula da Sa'adatu zata iya goga masa wani abun a hannu ko a k'afa wallahi." Murmushi tayi tace, "na sani fa rasss nake kallonta." Mik'ewa tayi tace, "ranki ya dad'e ki shafa masa zan shiga ciki na dawo." Kai ta girgiza kawai ita kuma ta fita. *Bayan Kwana biyu.* Babu abinda ya ragu ta b'angaren harin da ake kawowa Asad bai kuma fasa addu'a ba mafarkin da yake kullum k'aruwa yake, tunda aka zana masa fuskar ta kuma sai ya koma ganin fuskar a mafarkin amma yak'i bari mafarkin yin tasiri a zuciyar sa yana k'ok'arin mantawa dashi koda yaushe. Fuskar ta ta zama masa tamkar hoto a idanun sa da ya kulle sai ya hango ta hakan ya saka yake jin wani iri a zuciyar sa. Hydar na kwance har lokacin amma an samu cigaba dan zuwa lokacin yana motsawa alamun ya kusa farfad'owa kenan. A zaune take a babban d'akin ta wanda aka k'awata shi da kayan gado na alfarma waya na hannun ta, kamar wacce aka tunawa ta danna number Dr ta kira shi bata jima tana ringing ba ya d'auka yana fad'in, "Allah ya ja da ran Mama." "Ka sallami yarinyar nan kuwa ko tana nan?" Bata amsa gaisuwar ba abinda ta fara tambaya kenan. D'an dabarbarcewa yayi kana yace, "Na sallame ta Mama." "In ka min k'arya na gano gaskiya kai kasan sauran." "Ba k'arya nake ba tun lokacin na sallame ta." "Ka kyauta. In Hydar ya farfad'o kasan sometimes yakan manta wasu abubuwan na baya sai daga baya ya tuna in ya manta batun ta koda zai tambaye ka bana so ka sanar dashi kace komai bai faru ba ka gane ko?." Kamar yana gaban ta ya girgiza kai alamun to kafin yace, "zanyi in sha Allah." Bata kuma cewa komai ba ta yanke wayar yabi wayar da kallo yana sauke numfashi. "Wannan mata masifaffiya ce, ta yaya zan iya sallamar Rauda bayan har yanzu bata ji sauk'i ba?. In kuma na barta ta gano na shiga uku." Tsaki yaja ya mik'e ya tafi d'akin da Raudan take ya same ta a zaune tana karatun alkur'ani a bayyane. kallon ta yake da birgewa domin da wuya yazo ya same ta haka kawai bata karatu ko lazumi. Sallama yayi ta katse karatun ta kalle shi tace, "Dr shigo mana." Umma da bacci ya fara d'aukar ta ta mik'e zaune ya k'araso ya tsaya yana kallon k'afar tata yace, "Ya k'afar?." "K'afa da sauk'i yanzu bata min ciwo ai sai dai gajiya da zama." Ya sauke numfashi yace, "Rauda kud'in wanda ya kawo ki asibitin nan ya k'are kuma shima yana kwance babu lafiya tun zuwan sa na k'arshe nan shine na rasa yadda zanyi." Gaban Umma ya fad'i itama Raudan haka ta rufe alkur'anin tace, "To sai mu koma gida." "Eh ko kuma ku biya kud'in." Umma da take gefe tace, "mu biya me likita? Ina muka ga wannan halin?, gwara dai mu koma tunda Allah yayi k'afar tayi kyau." Jikin sa sai yayi sanyi ya sauke numfashi yace, "to in kun shirya zan saka a kai ku a mota sabida k'afar tata kafin kuje ku saka a gyara mata inda zata zauna, zan baku magungunan da zata dinga sha da abubuwan da ya kamata ta cigaba da ci in sun k'are a kuma siya. Kuyi hak'uri dan Allah na rasa yadda zanyi ne." "Haba likita meye na bada hak'uri? Ai kayi k'ok'ari ko kaine ka buge ta ai sai haka." Rauda ta tab'e baki tace, "Daman su y'ay'an masu kud'in nan babu abinda suka sani sai kansu, yanzu inda girmamawa ai yaci ace wani nasa yazo ya cigaba da d'aukar nauyi na tunda sune silar komai. Tunda bashi da lafiya an bar maganar daman ba gata ne dani ba sun yiwa banza. Allah wadaran wasu masu kud'in" Rauda ta fad'a a fusace. Dr yace, "Wallahi Hydar bashi da wannan halin baki ga yadda ya tsaya akan ki ba rashin lafiya ce dashi in ta tashi sai ya kwashe sati uku a sume bai farfad'o ba, yanzu zancen da nake miki tun da yazo nan ciwon ya same sa bai tashi ba har yanzu." Umma tace, "kai ka biye mata ai likita ai ko iya haka aka tsaya yayi k'ok'ari sosai, wanda in sun buge ka suke guduwa fa su kuma ace musu me?." "Umma maganar da ta fad'a gaskiya ce ya kamata ace wani nasa ya tsaya, amma da zaku san waye shi ku kuma san abubuwan da suke faruwa da ku kan ku kun tausaya masa shida y'an uwan nasa." "Allah ya kyauta" Umma ta fad'a. A wannan lokacin aka had'a magungunan Rauda da komai nasu aka saka Rauda a ambulance Umma ma ta shiga aka wuce da ita gida. Kafin suje Inna ta gyara d'akin Umma an yiwa Rauda shinfid'a aka shigo da ita a akan gadon aka zaunar da ita aka basu maganin ta suka koma. Umma ta cire mayafi ta ajjiye tace, "Daman na gaji da zaman asibitin nan, zaman asibiti sai dole." Rauda tayi shiru bata ce komai ba haka kawai take jin haushin wanda ya kad'e ta a ganin ta bai d'auki lafiyar ta da mahimmaci ba tunda ita talaka ce. Ummulkhairi da Khalil sai dawowa sukayi suka ga su Umma a gida suka dinga murya Umma ta dawo. K'arfe biyu na rana Baba ya diro gidan ganin k'ofar Umma a bud'e ya saka shi ya lek'a ya gansu a zaune Rauda tace, "Baba sannu da dawowa." Kallon su yake da mamaki kafin yace, "Me kuma ya dawo daku?." Umma tace, "Kud'in wanda ya kad'e tane ya k'are a asibitin kuma bashi da lafiya shiyasa aka dawo damu gida." Baba yaja dogon tsaki yace, "Kai amma ban so hakan ta faru ba, yanzu shikenan bazan kuma ganin sa ya bani wani abun ba? Abin takaici wallahi." Rauda tabi mahaifin nata da kallo da mamaki kafin ta d'auke kanta Allah ya sani abinda yake yi yana bata takaici kawai dan babu yadda zatayi ne uba uba ne. Juyawa yayi ya fita yana fad'in, "To Rahma a fito." Ba musu Rahma ta fito da hijjabi ya nuna mata kular yace, "gashi nan na dubu uku ne ayi aje a dawo." Da to ta amsa ta d'auki kular ta fita ranta a b'ace. Inna ta fito daga d'akin ta ta kalle shi tace, "Tsakani da Allah malam nima da nake goya maka baya na gaji da wannan tallan da kake d'orawa yaran nan, ka duba halin da Rauda take ciki ta dalilin talla ni na d'auka zaka saduda sabida hakan amma ko gezau bakai ba." Kama k'ugu yayi yace, "To uwata kama kunne na zakiyi ki fad'i maganar nafi fahimtar ki sosai." Inna ta d'auke kanta gefe yace, "in ban d'ora musu tallan ba a gida kike so su zauna naita kallon su su ba aure ba ba kuma samari ba?, meye amfanin su in basu yi tallan ba?." "Abinda kake sakawa suna yi ba shine zai kawo musu miji ba, aure kuma ai lokaci ne in yazo kamar ba'a zauna ba." "To bazan daina ba, tallah yanzu suka fara siyar da abinci ba ki d'auka yanzu aka fara wallahi sai sunyi. Inda Allah ya bani manyan y'ay'a maza ya za'ayi na saurare su?, haihuwar y'ay'a mata a farko ma ai asara ce." Umma da take d'aki tace, "Haba malam, da kanka kake furta wannan maganar?, abinda Allah ya baka ne fa kake cewa asara?." "Asara mana inda wad'anda na aurar suke gidan mazajen su ne y'ay'ana maza da yanzu sune suke taimaka min ko d'awainiyar ku suka d'auke min ai na huta amma duka mata ne kuma suka auri talakawa ba uwar abinda nake mora, su kuma wannan da suke zaune ba miji sai na zuba musu idanu haka kawai ina ciyar dasu a banza bana k'aruwa?." "Daman hakkin ciyarwa a kanka yake ba kan su ba" Inna ta fad'a tana kallon sa. Yace, "wannan kuma ku kuka jiyo tallah dai yanzu na fara in kunji haushi bakwa so suyi ku dinga ciyar da kan ku kuga zan basu tallah ko bazan basu ba" yana fad'ar hakan ya fita Inna tace, "nidai na gaji da wannan dabi'ar wallahi." Umma bata kuma cewa komai ba balle kuma Rauda da take zaune. Ba jimawa Yaya Ummi tazo ta fara shiga d'akin Inna ta gaishe ta sannan ta shiga d'akin Umma tana fad'in, "Allah ya taimaka banje can ba kika min waya Umma." Ta fad'a tana zama Umma tace, "Shiyasa na sanar dake ai dan nasan tsaf zaki iya wucewa." Gaisawa sukayi ta kalli Rauda tace, "Sannu Rauda, kin ajjiye k'iba kinyi haske da yake babu inda kike zuwa." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba. "Ni gwara ma da kuka dawo gidan wallahi k'afar taki ai tayi kyau da yake asibitin kud'i ne kamar ba karaya ba." Umma tace, "haka nace nima wallahi, ai yayi k'ok'ari yaro." Ledar da ta shigo da ita ta bud'e ta mik'a mata tace, "karb'i kazar hausa ce kici ance ana so masu karaya suci kaza." Karb'a Rauda tayi tace, "Na gode Yaya Ummi, Umma kici." Umma tace, "ki ci k'oshi tukunna, naji dad'i ma dasu Khalil sun tafi islamiyya." Ba musu ta fara ci suna hira sama-sama kawai sai ganin Baba sukayi kamar an cillo sa. Kafin suce wani abun ya saka hannu a kwanon hannun Rauda ya d'auki k'atuwar b'angare daga cikin kazar ya saka a baki yana fad'in, "Daman sai dana aiyana wani abun kika kawo kika k'unso a leda to Allah yayi da rabona, yaushe rabon da a gamu da kaza?" ya fad'a yana taunawa tare da lumshe idanun sa. Umma takaici kamar me haka take ji amma ya zatayi haka tayi tagumi tayi shiru suma haka ba wanda yace uppan ya cinye ta hannun sa ya kuma d'aukar wata yana ci. Yace, "Ke Mamana yaushe mijin naki yayi kud'in siyo miki kaza har kika bayar?." Yaya Ummi tace, "ba shine ya siyo ba bashi na karb'o a mak'ota na na dafa mata ganin mai karaya ce, ina yaga halin da zai siyo min kaza Baba?." Baba yana b'alla k'ashi yace, "yauwa koda naji" ya fad'a yana fita ya sha ruwa ya dauraye hannun sa ya fita. Umma tace, "Allah ya kyauta." Da amin suka amsa kafin Rauda tace, "Amma Yaya meyasa zaki karb'i bashi?." "Ke k'arya nake ba bashi na karb'a ba wasu y'an kud'i Abban su Islam ya samu ya siyo mana guda uku yace na kawo miki guda d'aya. Kin san halin Baba ina fad'a masa hakan gobe a gidana zaiyi sallama yace masa bashi da kud'in cefane." Dariya Rauda tayi tace, "kinyi farar dabara." Umma ma dariya tayi bata ce komai ba Yaya Ummi tace, "ke ai kece a ruwa kika auri wannan yaron Anas ai kun shiga uku da rok'on Baba wallahi." D'aure fuska tayi tace, "nifa bashi zan aura ba Allah zai kawo min miji na." "Allah ya kawo k'anwa ta burina naga anyi auren ki. Allah ya kawo wanda ya fishing mu sha biki." Da amin suka amsa ta cigaba da cin kazar kafin ta ragewa Umma. *☆☆☆* A zaune ya same ta kamar koda yaushe ya k'arasa ya zauna a kan carpet ta kalle shi tace, "tun yaushe nace kaje gidan su Jidda?." Yayi shiru bai amsa ba ta kuma cewa, "ba magana nake maka ba?." Asad yace, "tun kwanaki." "Sabida ban isa dakai ba ya saka baka je ba kenan ko?." Kai ya girgiza alamun a'a yace, "Tuba nake." "To me ya hana ka zuwa?." "Na manta ne." "Yanzu na tuna maka ai saura ka kuma cemin ka manta. Kunyi waya da mahaifin ka?." Kai ya d'aga tace, "yaushe zai dawo?." "Jibi" ya bata amsa a tak'aice yana kallon k'asa. Zatayi magana Aliyu ya shigo cikin k'ananu kaya mara sa tsayi a jikin sa ya mayar da gashin fuskar sa bak'i kamar na Asad daman shine yake banbanta su sai suttura kuma. Shima k'asa ya zauna Mama ta kalle shi tace, "Lafiya na ganka haka?." Ya cize bakin sa har zai magana sai kuma yace, "babu komai." "Kai dai ka sani" ta fad'a tana kallon Asad kafin tace, "na gama dakai zaka iya tafiya." Ba musu ya mik'e yace, "Ki tashi lafiya" ya fad'a yana fita. Aliyu ya kalle ta yace, "Allah ya taimaki Mamana maganar me naji kuna yi dashi?." Mama tace, "to wanda ya haife ni bani umarni sai na fad'a maka." "Allah ya wuci zuciyar ki, tuba nake. Ki tashi lafiya" ya mik'e yana girgiza kansa ya fita ta bishi da kallo cikin takaici. Asad yana fita mota ya hau ya tafi company dan akwai abubuwan da dole sai yaje da babu abinda zai kai shi, yana zama a office yaji kansa yayi mugun sarawa ya dafe kan da duka hannu biyu ya kulle idanun sa, "Prince lafiya?" Hafiz ya fad'a yana shigowa. D'ago kai Asad yayi ya kalli Hafiz da ya zauna ya girgiza kai kafin yace, "kaina." "Sorry." "Ina files d'in nan?." Hafiz ya mik'e ya kawo masa yana dubawa Hafiz yace, "akwai abinda yake damun ka deaf, tell me please." Baice komai ba ya koma ya jingina da kujera yana sauke ajiyar zuciya amma baice komai ba. Hafiz yace, "i don't know why yanzu baka sanar dani damuwar ka." Asad yace, "no ba haka bane, babu ne" ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya d'auki key da wayar sa yace, "in ka gama ka same ni gida." "Okay, akwai meeting da kamfanin k'asar Dubai yarjejeniyar suke so a k'ara musu tsahon lokaci." Asad yace, "Kuyi komai" yana fad'a ya fita Hafiz ya bishi da kallon tausayi gabad'aya ya canja kamar ba shi ba. Bai koma gida ba yawo yayi tayi a gari bai koma gida ba sai magriba, yana shiga apartment d'in su yaga giftawar mutum kamar iska alamun rashin gaskiya ya dawo da baya ya ganta ta juya baya tana waya ya k'arasa kusa da ita ya tsaya yaji ana cewa, "na saka tun wancan lokacin har yanzu kuma yana cikin d'akin nasa." Juyo da ita taji anyi ta zaro idanu waje shima nasa idanun ya wara ganin wacece ya Bud'e baki yace "Suhaima!." *Ba'a fara komai ba ku shirya kawai.* *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *012.* "Na'am Yaya Asad" ta bashi amsa tana kallon sa shima kuma ita yake kallo da mamaki shinfid'e a kan fuskar sa. kallon k'ofar falon yayi ya dawo da kallon sa gare ta sai tace, "Mama ce ta bani fresh milk tace na saka maka a fridge shine nake waya nace na saka." Kai ya jinjina kafin yayi gaba sai kuma ya tsaya ya juyo ya kalle ta yace, "bayan yau ta tab'a aiko ki?." Kai ta girgiza alamun A'a tace, "bata tab'a ba, yau d'in ma dan bata fito bane ba ya saka ta bani, ni kuma bazai koma ciki ba shiyasa nake sanar da ita a waya." Baice komai ba ya shiga d'akin wajan fridge ya nufa ya bud'e yaga madarar a ciki ya kulle ya shiga d'akin sa yana k'are masa kallo kamar wanda yake neman wani abun kafin ya sauke ajiyar zuciya ya tsaya a jikin mudubi yana kallon kansa. Wani abu ya gani ya gifta ta bayan sa bai juya ba ya cigaba da kallon mudubin ya sake ganin giftarwa abu hakan ya saka shi ya juya da sauri amma bai ga komai ba. Wajan da yake ganin abun yake nufa amma baya ganin komai hakan ya saka shi kulle idanu ya bud'e tunda ya fara mafarkan nan sai ya dinga ganin abun kamar a zahiri ne yake faruwa. Bai jima sosai ba ya kuma fita yaje masallaci ya dawo suka had'u da Hafiz a k'ofar shiga falon suka shiga tare, suna zama Suhail ya shigo da sallama Asad ne kawai ya amsa banda Hafiz ya samu waje ya zauna yana fad'in, "kwana biyu kowa ya b'uya." Asad girgiza kai kawai yayi Hafiz ya kalli Suhail yace, "ko zaka iya bamu waje magana zamuyi." Suhail ya kalli Asad ya kalli Hafiz ya murmusa ya mik'e tsaye yace, "okay babu damuwa." "Noo zauna" Asad ya fad'a yana danna wayar sa jin hakan Suhail ya koma ya zauna Hafiz takaici ya sake kama shi ya girgiza kai amma baicr komai ba Shiru wajan ya sake d'auka dan shi dai Hafiz bazai yiwa Asad magana Suhail yana nan ba shi kuma Asad bazai yi maganar ba, Suhail ya mik'e yace, "Sai da safe" yana fad'a ya fita Hafiz kamar jira yake ya kalli Asad yace, "Abinda kake yi fa sam ba mai kyau bane ba, kasan manufar Suhail a kanka amma ka dinga zak'ewa kana barin sa kusa dakai bayan nida kai mun san dama kad'an yake nema a kan ka ya halaka ka amma kake bashi fuska har haka." Shiru yayi kamar bazai amsa ba jikin sa wani iri yake ji cikin kwanakin gabad'aya baya son zaman gidan yana jurewa ne kawai sabida Mama amma da tuni ya bar k'asar, "Ka nunawa wanda yake neman ka da sharri baka san yanayi ba yafi riba" ya bashi amsa yana kallon sa shima yana kallon sa. "Amma kasan....." dakatar dashi Asad yayi yace, "Bana son magana a kan hakan. Muyi abinda nace." "Okay better" ya bashi amsa shima kafin ya mik'e ya fita dan bazai yi maganar ba shima ya fasa. Murmushi Asad yayi bayan ya fita cikin su biyun shi dai ya rasa wanda yafi sonsa ko wanne burin sa ya bashi kariya shiyasa yake ji dasu baya so yaga an tozarta wani a gaban sa. Duk da shi ba wani sakewa yake da abokai ba amma babu laifi su kan danyi hira sama-sama. Tashi yayi ya fita daga apartment d'in gabad'aya yana takawa a hankali kamar ko yaushe ana zubewa ana kwasar gaisuwa yana amsawa a ciki, zaga gidan kawai yake badan akwai abinda zaiyi ba sai dan haka zuciyar sa take bashi umarni, har yazo b'angaren da yake da duhu sosai har ya gota sai kuma ya dawo da baya jin abinda ake cewa, "ku bari kawai shima Asad d'in maganin sa zamuyi yadda muka kwantar da Hydar shima haka zamu kwantar dashi, ko muyi masa kurciya ya bar k'asar gabad'aya bazai sake dawowa ba har abada." Dariya yaji anyi kafin yaji ance, "Allah yaja zamanin Master planer, Asad bazai tab'a mulkar garin nan ba in sha Allah, jinin Rabi'atu baza suyi sarauta ba in Allah ya amince." Motsi yaji alamun za'a fito ya tsaya a wajan cak yana jiran yaga wacce zata fito, rad'ad'in da ya kawo masa ziyara a idanun sa ya saka shi kulle su ba tare da yayi niya ba yana juya kansa yana so ya bud'e amma ya kasa idanun nasa ruwa suke yi, hannu ya saka a aljihu ya d'auko tissue yana goge idanun nasa hankalin sa na wajan da yake jin maganar amma baya gani sosai, sai da ya d'an samu sauk'in idon ya d'auko wayar sa ya kunna haske ya sake haska wajan amma babu kowa alamun da gangan aka saka masa abu mai yaji a idanun sa. "Asad me kake yi a nan?." Jin tambayar daga bayan sa ya saka shi ya juya yaga Hajiya a tsaye tana kallon sa. Mamaki ya kama shi uwar gidan sarki mai zai kawo ta wajan a wannan lokacin da ba kowa yake yin hanyar ba..? amma bai nuna mata mamakin sa ba sai ya goge idanun sa yace, "babu komai" yana fad'a ya wuce tabi bayan sa da kallo ta murmusa kafin ta bar wajan. D'aki Asad ya koma yana zagaye hankalin sa a tashe matuk'a, bai tab'a jin tashin hankali akan abubuwan da suke faruwa ba kamar yadda yake ji yau. Babban tashin hankalin sa sunan Hydar da yaji suna ambata kenan duk rashin lafiyar da yake yi sune suka jawo hakan?. Suna saune suke kwantar dashi dan rashin imani..? Su waye ma a tak'aice....?. Kama k'ugu yayi ya furzar da iska mai zafi yana sauke numfashi, "me ya kai Hajiya wajan a yanzu?" Ya tambayi kansa nan ma babu amsa ya had'd'iye saliva a jikin sa yake jin lokaci yayi da kowa ya kamata yasan waye Asad. *Bayan wasu kwanaki.* "Malam dan Allah in ka fita ka biya ta wajan sarkin d'ori ku tawo da ko yaron sane yazo a duba k'afar Rauda. Gashi dai ta samu lafiya amma k'afar ta nakasa yazo ya gani in akwai abinda za'a yi" Umma ta fad'a tana kallon Baba. Baba da ya gama saka takalmi yace, "in aka d'auko sarki d'ori ke zaki biya shi?." Umma ta buɗe baki tana kallon sa shima yana kallon ta yace, "Nidai bazan biya ba in zaki biya yanzu za'a tawo dashi." Umma tace, "Shikenan azo dashi sai na biya d'in." "Zab'i mai kyau, kuma kin san dai biyan da tsada tunda gida zai zo sai ki tanadi kud'i." "Zan bayar ko nawa ne." Ya k'are mata kallo yace, "Da uwar kud'in ki a k'ugu amma asahana in ta kare sai a turo min yaro" ya fad'a yana fita ta bishi da kallo kawai. Ba jimawa ya shigo yace, "ku gyara gashi mun zo dashi" ya fad'a yana komawa suka shigo tare aka shiga d'akin Umma ya fara duba k'afar Rauda da take zaune. Mai gyaran k'afar da yake kusa da Rauda yana duba k'afar ta ya kalli Umma da Baba da kuma Inna yace, "Akwai sauran gyara a k'afar nan tata dole sai dai ayi mata aiki." Baba yace, "Aiki kuma?." "Eh aiki Baba, amma kuje asibiti ayi hoton k'afar a kaiwa likita shi kuma zaiga inda za'a gyara sai ya fad'i kud'in ku biya." Umma ta girgiza kai tace, "to kuma zata iya tafiya?." "Eh zata iya amma sai dai a bata sandina guda biyu, inda dama yanzu kuje asibitin ayi gaggawar duba k'afar tata in ba haka ba zai zama silar da za'a ce zata nakasa gabad'aya." Baba yace, "to mun gode." Fita yayi Baba ya kalli Umma yace, "ke kina da kud'in zuwa asibitin ne?." Umma ta girgiza kai a raunane tace, "bani dashi. Suke nan na hannuna kuma na bayar yanzu." D'an k'aramin tsaki yaja ya kawar da fuska gefe yna jin haushin ciwon nata kawai za'a saka shi kashe kud'i kafin ya fita. Inna tace, "abu kad'an zai zama sanadi." Umma tace, "Allah ya yaye." Rauda dai tana jin su jikin ta yayi sanyi ta tabbatar ta rasa k'afar ta kenan sabida tasan kud'in aikin da za'a fad'a babu mai kud'in da zai iya biya. Baba ya dawo yace, "ta tashi ta d'auki sandinan muje yanzun." Ba musu Umma da Inna suka kama ta ta tashi aka bata sandinan nata tana tafiya dasu a hankali har suka fita suka ga taxi Baba ya taro aka kwantar da ita a baya Umma ta rab'a ta zauna Baba ya shiga gaba suka tafi. Wajan hoton k'afar suka fara zuwa suka hau layi abin mamakin Baba baiyi k'yashi ba ya bada kud'in akayi hoton suka shiga asibiti wajan likita. Tun safe suke zaune har azahar layi bai zo kansu ba duk sun gaji da zama gata ita kuma a kwance tunda k'afar ba kwari tayi ba. Bayan azahar layi yazo kan su suka shiga duka su ukun aka bawa likitan hoton yana kalli hoton sosai ya gama Nazarin duk abinda yake jiki ya juyo ya kalle su bayan ya gama dubawa yace, "Akwai wani k'ashi da ya tsage a k'afar ta yanzu kuma nama ya shiga tsakiya jini ya shiga sosai dole sai anyi aiki zan cire an had'e wannan k'ashin." Baba yace, "to kuma aikin yana kaiwa nawa?." Likitan yace, da yake bani zanyi aikin ba amma dai gaskiya yana kaiwa miliyan d'aya da dubu d'ari biyu koma yaje miliyan biyu. Aikin babba ne gaskiya dan ba'a jima da fara yin sa Nigeria ba Egypt ne da Germany da India kawai suke yin sa." A tare gaban su ya fad'i suka kalli juna Rauda idanun ta tuni sun wanke da hawaye Umma tace, "Tabd'ijam." Likitan yace, "kuma gaskiya in ba'a yi wannan aikin ba tafiyar ta baza ta dawo ba sai dai ta cigaba da tafiya da sanda ko kuma kujerar marasa lafiya wheelchair kenan kamar yadda take yi yanzu, aikin ya zama dole." Baba yayi shiru kawai baice komai ba kafin likitan ya kuma cewa, "Wannan magungunan dana gani a katin ta da take sha tun a baya ta cigaba da shan su suna da kyau sosai zasu taimaka wajan rage mata rad'ad'i." Su dai babu wanda ya tanka jiki a sab'ule suka fito har suka koma gida babu wanda yayi magana. Umma ta kalli Rauda da ta jingina da bango tayi shiru tace, "kiyi Hak'uri Rauda taki k'addarar kenan rasa k'afar ki, kiyi hak'uri dan wannan kud'in bamu da hanyar sa kinfi kowa sani." Rauda ta goge ido tace, "babu komai Umma a hakan ma na gode Allah wani fa ko k'afar bashi da ita ni na samu ina takawa, nafi wasu da dama a duniya." Umma ta share idanun ta bata ce komai ba Baba ya shigo yace, "to kunji dai yadda mukayi kun sani bani da wannan halin koda ina dashi ma gwara nayi jari da dai na bawa wani banzan likita gwara mu kafa jari a gidan, Rauda sai kiyi hak'uri taki jarabawar kenan." Kai kawai ta d'aga kawai bata ce komai ba zai fita tace, "Baba magungunan sun k'are wancan lokacin ma kud'in rabi aka bashi Khairi ta karb'o wajan Bala mai pharmacy." Ya juyo ya kalle ta yace, "Wannan lokacin ma kije ya baki bashin in bazai bayar ba a hak'ura bazan iya siyan maganin dubu hamsin ba wallahi." "Yanzu haka za'a zauna babu maganin kenan? Ina kud'in da aka bata a asibiti?" Umma ta fad'a tana kallon sa. Ya juyo ya kalli Umma yace, "ki danne ni ki kwata in ta k'arfi ce" yana fad'a ya fita Umma ta bishi da kallo ta girgiza kanta tace, "Sam mahaifin ku yafi damuwa da kud'i akan lafiyar ku, bai damu da lafiyar mu ba gabad'aya kud'i kawai. Zan iya rantsewa yana da fin dubu d'ari kawai bazai iya bayarwa bane gani yake asara ce." Rauda batace komai ba dan bata ga laifin Baba ba hakkin siya mata magani akan wanda ya kad'e ta yake gashi ya nakasa ta tana zaune babu ruwan sa babu abinda aka isa ayi masa kuma. Tuna hakan sai ta fara kuka Umma tace, "kiyi hak'uri Rauda." Tace, "Umma yanzu kenan wandaya kad'e ni ya yiwa banza kenan? Gashi ya nakasa ni na rasa k'afata amma shi yana can gidan su hankalin sa a kwance bai sake waiwayo na ba, meye ribar masu kud'i da suke irin wannan banzayen halayen...? shin sun manta da lahira ne?." Umma tace, "Akwai Allah Rauda, kiyi hak'uri hakika an cutar dake amma ki daure k'addarar kice a haka." Hawayen idanun ta ta share ta mayar da kanta ta jingina da bango bak'in ciki da takaici yana shiga zuciyar da jinin ta. Yamma tayi Ummulkhairi da Khalil dasu Rahma suka dawo Ummulkhairi ta dawo da ciwon ciki Allah ya Umma bata rasa maganin ciwon ciki ta bata tasha Khalil ya fice Ball Rahma ma ta kwaso gajiyar siyar da abinci. Tsiko k'afar ta take mata tunda babu magani ta kwana biyu bata sha ba ta kalli Umma tace, "Umma zanje wajan mai pharmacy d'in nan da kaina ko zai bani maganin." Umma tace, "A'a Rauda keda ba k'afa ba ki zauna ni naje na bashi baki ko zai bamu." "Zan iya Umma gwara ni naje ki zauna" ta fad'a tana tashi tsaye ta d'auki sandinan ta guda biyu ta tsaya ta saka dogon hijjabi har k'asa ta saka face mask bak'i a fuskar ta. Umma da take kallon ta cikin tausayi tace, "Ki zauna naje da kaina Rauda ko muje taree." Rauda ta murmusa tace, "Umma babu abinda zai faru zan dawo in sha Allah." "To kije Rahma ta raka ki ko ki nemi Khalil a waje ku tafi." "Rahma a gajiye take kinga yanzu ta dawo daga kasuwa in naga Khalil d'in daman dashi zamu tafi." "Allah ya kiyaye, ki kula sosai Rauda." Ta amsa da amin ta fita tana tafiya a hankali har ta bar gidan. A waje kuwa taga Khalil ta saka shi a gaba suka tafi a hankali suke takawa har suka zo pharmacy da yake a tsallaken titi suka tsallaka suka shiga, da sallama suka shiga ta zauna akan benci tana haki mai pharmacy ya amsa a dakile yana kawar da kansa gefe. Sai da ta huta sannan ta kalle shi tace, "Ina wuni Bala." Fuska babu walwala yace, "Lafiya, kud'ina kika kawo nin dai ko?." Kai ta girgiza kana tace, "A'a Bala maganin nazo a kuma bani." "Da yake jarin na baban kine ai ko? Dan baki ma da kunya baki da mutunci ina binku kud'i har naira dubu ashirin da biyar kizo kice min wai na kuma baki bashin magani, ga asararre wanda bai san abinda yake yi ba ko?." Ranta ya b'aci sosai amma da yake nema take sai ta tausasa murya ta d'ago ta kalle shi tace, "inda ina da kud'in da zan baka kuma wallahi zan biya ka kud'in ka gabad'aya nan gaba in sha Allah." "To bazan bayar ba, kuma wallahi ko ki biyani kud'ina ko na kai k'arar ku police station." Rauda ta kasa jurewa tace, "Dan nazo neman alfarma a wajan ka ba hakan yana nufin ka fad'a min maganar da kaga dama ba." "Wannan kuma ke ta shafa wallahi sai an biya ni kud'i na, darajar babar ki ya saka nake bada maganin ban gano waye mahaifin ki akan kud'i ba sai bayan na baki magani dan da nasan haka yake wallahi bazan bayar ba. sai an biya ni in ba haka ba nakai k'ara wajan y'an sanda suzo su karb'ar min ta dole." Mik'ewa tsaye tayi Khalil ya bata sandar ta ta kalle shi tace, "Za'a biya ka kud'in ka in Allah ya yarda, kar ka sake kuma ka sake zagin iyaye na in ba haka ba zan nuna maka bani da mutunci nima." "Ai nasan ki waye bai san sanfurin rashin mutuncin ki ba?, duk zafin kan ki na fiki wallahi dan na dame ki na shanye tuni. Kud'i ne dole a biya; ki daina in Allah ya yarda ai dole ne ma ki biya ni in ba haka ba kuka ga hauka keda iyayen naki." Banza tayi masa ta kalli Khalil zuciyar ta nayi mata ciwo tace, "muje Khalil." Ba musu yayi gaba tana jin sa yana ta yi mata ihu bata juya ba tana tafiya bata kallon gaban ta bata san tazo kan titi ba sai horn d'in mota taji mai k'arfi hakan ya saka ta tsayawa cak ta runtse idsnun ta. Motar ta tab'a ta hakan ya saka ta fad'uwa sandinan suka zube katin maganin da yake hannun ta shima ya fad'i. Da sauri Khalil yazo wajan ta yana k'ok'arin d'aga ta yace, "Sannu Anty baki ji ciwo ba?." K'ok'arin mik'ewa take taji kwarjini ya mamaye wajan lokaci guda, sanyin khamshi da zazzafan izza da k'asaita ta bayyana a wanan mai d'auke tsantsar nutsuwa da kamewa. Tsayuwar mutum da inuwar sa take ji a kanta hakan ya saka ta d'ago kai ta kalle shi idanun su suka had'u dana juya ta wara idanu tana k'are masa kallo shima kallon idanun ta yake dan iya shi kawai yake gani ta rufe sauran da face mask. Saurin janye idanun ta taji jin wani abu kamr shocking da kwarjini yana ratsa cikin jijiyoyin idanun ta, jikin ta yayi sanyi lokaci guda taji baza ta tab'a iya jure cigaba da kallon sa ba ta dole ta janye idanun ta. A b'angaren sa shima hakan take zagayayyun idanun ta da ya kalla na wasu mintina sun masa kama da wanda ya sani amma kansa ya kasa tuna a inda ya san su hakan ya sama shi zuba mata ido yana so ya tuna. "Kai dan Allah shine ka buge min Antyna bayan wani ya kad'e ta ta karye ya daina zuwa ya duba ta ta koma wayo da sanda, yanzu ma fa wajan mai magani muka je dan bamu dankud'i shine har da zagin Baban mu yace bazai bada maganin ba" Khalil ya fad'a kamar zaiyi kuka yana kallon Asad da yake tsaye a kanta har lokacin. K'okarin mik'ewa take yi Khalil yana so ya rik'e ta amma ta kasa Asad da ya gama sauraron abinda Khalil yace ya dawo da kallon sa gare ta yaga tana kiciniyar tashi amma ta kasa, a hankali ya tsuguna a gaban ta khamshin turaren sa ya sake kawo mata ziyara cikin hancin ta ta runtse idanu gaban ta na fad'uwa ya kama kafad'un ta duka biyun ya mik'ar da ita tsaye, Khalil ya bata sandinan ta ta tsaya cak har lokacin kala baice ba. "Na d'auka iya mugunta da rashin sanin darajar d'an adam ka sani ashe ka iya taimako....?. A waccan ranar ka mare ni na k'yale ban tanka ba sabida akwai abinda nake jin tsoro a gidan bawai dan ina jin tsoron ka ba. Kana da kud'i ko mulki duka basa gabana indai mutum ya tab'a ni nima sai na tab'a shi dan bai fini daraja ba, mutum shi nima mutum ce. Sa'ar ka guda ni nasan darajar d'an adam da babu abinda zai hana na wanke maka taka fuskar da mari kamar yadda ka mari tawa, banbanci na dakai kenan na fika tarbiyya da sanin ya kamata, amma koda nan gaba kasan irin matan da zaka dinga wulak'antawa domin ni da kake gani na nafi k'arfi suya sai dai babbaka" ta k'arasa fad'a tana kallon gefe domin bazata iya jure kallon saba shima yana kallon ta cike da mamakin kalaman ta. Baki yake so ya bud'e yayi magana amma ya kasa cewa komai sai kallon ta kawai da yake yi tana zazzaga masa rashin kunya yana jin ta yana kuma kallon ta, sai da ta kai aya sannan ya kalli Khalil yace, "a ina kuke?" Ya fad'a cikin muryar sa mai taushi da ratsa zuciya. Gabanta taji ya fad'i jin kamar ba waccan muryar bace. Muryar Khalil taji yace, "A unguwar Katsalle muke." Kallon ta yayi sai ya kalli Khalil yace, "Muje." "Allah ya tsari gatari da saran shuka, ni Rauda na shiga motar wanda bai san darajar d'an adam ba sai kansa kawai ya sani Allah ya kiyaye ni. kaje can ka k'arata kai kad'ai tunda ku y'ay'an manya da y'ay'an masu mulki baku san kowa ba sai y'an uwan ku masu mulki. Dan kana d'an sarkin garin nan baka isa ka saka ni nayi abinda banyi niya ba, bada hak'uri ya gagare ka akan buge ni d'in da kayi a yanzu me zai kaini shiga motar ka?" Rauda ta fad'a cikin masifa lokacin hijjabin ta yake ja baya har tabon sallar dake goshin ta ya bayyana. A wannan lokacin suka tsallaka bai juya ya kalle ta ba bai kuma bar wajan ba amma kalaman ta sun tabbatar masa ta tab'a had'uwa da Aliyu ne yadda ta zayyano abinda ya faru yasan tabbas Aliyu ta gani take tunanin shine, katin maganin ya gani a k'asa ya d'auka yana kalla kafin ya juya sai yaga har sun b'ace masa, numfashi ya sauke ya shiga mota zuciyar sa na bugawa, kallo inda suka bi yake yi zuciyar sa na fizgar sa zuwa wani tunani daban ya runtse ido ya kunna motar ya buɗe idon sa ya ja ya bar wajan. *tofa fan's an gamu fa.*🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *013.* Rai a b'ace Rauda ta shiga gida Khalil ya taimaka mata ta ajjiye sandar hannun ta ta zauna a kan farar kujerar da take tsakar gida shi kuma ya zauna a k'asa. Yanayin ta Umma ta kalla tasan an tab'o ta kuma tasan bazai wuce akan maganin ba hakan ya saka tace, "ko baki ce ba nasan ya hana ki maganin ne shiyasa kike kunbura fuska, sai kiyi hak'uri." Rauda tace, "daga neman taimako Umma sai ya zage ni? Har yana cewa da yasan halin Baba tun farko bazai bada bashi ba." Umma ta murmusa tace, "ban ga laifin sa ba Rauda; yanzu kafin wannan kud'ad'e masu tarin yawa su fito daga hannun baban ki a shekara goma a fama. Yayi k'ok'ari fa da ya baki ma dan ba kowa ne zai bada magani mai tsada kamar naki ba, Allah yasa baki masa rashin kunya ba dan ya taimaka miki." Shiru tayi bata amsa ba Baba da yaji komai ya shigo yana fad'in, "In ma tayi masa rashin kunyar ita ta jiyo ai ita k'afar zata damu da ciwo sabida rashin magani bani ba." Shiru sukayi dukkan su kafin Khalil yace, "Umma wani kyakykyawa kamar balarabe ya kusa kad'e Anty yanzu har sai da ta fad'i k'asa." Umma tace, "Kuma dai?." "Amma ai bata ji ciwo ba ai. Umma ta yi masa rashin kunya yace muzo ya kawo mu gida tak'i kuma baki ga motar ba babba" ya fad'a yana fad'ad'a hannayen sa alamun girma. Baba da yake alwala a durk'ushe furzar da ruwan bakin sa yace, "A koda yaushe ke ai bak'in halin ki yake ja miki alkhairi yake tsallake ki ya koma kan wanin ki. inda kin shiga motar da bai siya miki maganin ba." Umma tace, "Rauda akan me zaki masa rashin kunya? Meyasa ke baka jin kunyar yiwa babba rashin kunya ne?." Rauda tace, "Umma nifa ba rashin kunya nayi masa ba na fad'a masa abinda yake raina ne. shine wanda nace miki ya mare ni lokacin da na raka su Habiba gidan sarki shine na amayar masa da abinda yake zuciya ta a lokacin ban samu dama ba ina jin tsoron doki ya hana ni mayar masa." Umma ta wara idanu tace, "D'an sarkin Katagum guda masu ji da kud'i da mulki kika yiwa rashin kunya Rauda?, Yaron da an masa shaida bashi da kirki ina ke ina shi?, in ya saka aka yi miki wani abun fa?." Rauda ta turo baki gaba tace, "To Umma dan yana d'an sarki sai yayi min abinda yaga dama na k'yale shi? Bafa haifata yayi ba da zai fad'a min magana na tsaya ina kallon sa, wallahi saina rama dan mutum ne shi nima mutum ce." "Sannu y'ar gidan dangote, nace sannu y'ar gidan shugaban masu kud'in duniya. Wato in ana neman talaka mai fad'in rai wanda aka fad'a a hadisi aka same ki Rauda an shafa Fatiha. Tunda bake ban tab'a ganin yarinya mai karanbani da nuna isa kamar y'ar wani ko y'ar wata sai ke da kanki yake rawa. D'an sarki guda kika yiwa rashin kunya, bakya jin tsoron wani abun ya same ki ke ga fitsararriya mai ji da fitsara. Har yace miki kizo ki shiga mota ya kawo ki kika ki sabida girman kai yayi miki yawa. To Allah ya isa abinda yayi niyar baki in ya kawo ki kika yi mana bak'in ciki da yau nasan kaji zamu ci mu kwanta, sakamakon rashin kunya duk abinda ya saka aka yi miki ke kika ja kar sunan Adamu ya fito a gaban sunan ki" Baba ya fad'a yana buge rigar sa ya fita. Umma ta girgiza kai tace, "Wai Allah ya isa, Malam har ya saka a ran sa ma za'a bashi wani abun bama illar shiga motar tasa yake hangowa ba kawai a bashi kud'i koma me yayi miki in kin shiga motar ke kika jiyo. Kai Allah ya kyauta" Umma ta fad'a tana murmushin takaici kafin ta kalli Rauda tace, "Kinga Rauda na raba ki da y'ay'an masu kud'in nan babu ruwan ki dasu in ba so kike ki jawo mana matsala muna zaune lafiya ba. Ina ke ina yi masa rashin kunya? In yaso a batar dake yana da damar yin hakan babu wanda yasan shine yayi, ki dawo hankalin ki dan Allah bana son wannan fitsarar taki." Rauda bata ce komai ba tayi shiru k'afar ta na ciwo rashin shan maganin da batayi ba. *☆☆☆* Tun a mota yake tunani har ya isa guest house d'in mai martaba ya shiga kamar yadda ya saba shi kad'ai ya zauna a akan kujera yana sauke ajiyar zuciya. kallon katin yake yana kallon sunan ta kamar a jikin sunan yana so ya gano wani abun. _Sa'ar ka guda nasan darajar d'an adam da babu abinda zai hana ban wanke maka taka fuskar da mari kamar yadda ka mari tawa._ kalaman ta suka fad'o masa a rai ya runtse ido jin abinda bai tab'a ji ba yana kawo barazana ga kunnen sa. "Ta tab'a had'uwa da Aliyu" ya furta a hankali idanun sa har lokacin a kulle zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri. "Wacece ita?" Ya tambayi kansa yana dafe kansa da duka hannayen sa idanun ta da goshin ta na sake dawowa masa cikin kansa da idanun sa a hankali. Sake kallon katin yake maganar Khalil na sake dawo masa zuciyar sa ya kai idanun sa sunan asibitin da aka rubuta mata maganin. Mik'ewa zaune yayi sosai mamaki ya kama shi ya wara idanun sa ganin sunan asibitin su ne ya tafi k'aramin tunani kafin ya d'auko waya daga aljihun sa da azama. Sai da ya danna number Dr Yasir ta shiga sai kuma yaji haushi ma akan me ma ya saka shi ya kira Dr, "Assalamu Alaikum, Ranka ya dad'e" muryar Dr ta katse tunani ya kalli wayar kamar bazai yi magana ba sai yace, "ehemmm Hydar" sai kuma yayi shiru jin hakan Dr yace, "Jikin sa ana samun ci gaba saura kiris ma ya farfad'o domin ana samun cigaba fiye da baya." "About yarinyar da ya buge fa?." Gaban Dr ya Fad'i jin abinda yace yayi shiru Asad yace, "tana ina?." Dr yace, "Prince Mama ta saka an sallame ta tun kwanakin baya." Asad yayi shiru cike da mamaki yasan tsaf Mama zata aikata abinda yafi haka ma hakan ya saka shi yin shirun kafin yace, "meye sunan ta?." A sama Dr yaji maganar hakan ya saka shi yin shiru kafin yace, "na manta ne prince abubuwan da yawa marasa lafiyar da yawa babu lallai na rik'e." Shiru dukka sukayi kafin Dr yace, "Na tuna, sunan ta Rauda sunan mahaifin ne dai na manta." Asad baice komai ba ya yanke wayar ya sake kallon katin yaga sunan da ya fad'a masa ya ajjiye katin a gefe yana kallo, _Mama meyasa?, ga yarinya yanzu a cikin yanayi mara dad'i, babu kud'in magani gashi har tana yawo da sanda a silar Hydar._ ya fad'a a zuciyar sa yana sauke numfashi shi jikin sa duka babu dad'i. Kiran magrib ya tashe shi yayi alwala ya fita masallacin estate d'in yayi sallah sannan ya dawo ya d'auki motar sa zuwa gida. Wajan Mama ya wuce kai tsaye bai same ta a falo ba ya shiga d'akin da Hydar yake a nan ya ganta a zaune kusa dashi kamar koda yaushe. Da sallama ya shiga ta kalle shi ta d'auke kai ya tsaya a kan Hydar yana kallon sa. Har zai mata magana sai kuma ya fasa ya d'auke kansa itama kuma bata ce masa komai ba. Ganin bata kallon sa ya saka yace, "Mama ko meyasa aka sallami yarinyar da Hydar ya buge daga asibiti?" Ya fad'a a tausahe kamar ko yaushe. Kallon sa tayi ta harde hannun ta a k'irji tana kallon sa alamun bazata yi magana ba kenan. "Na saka an sallame ta d'in sabida bata dace da zaman wannan asibitin ba akwai abinda za'a yi min ne?. kuma ahir naji kaje wajan ta da niyar wani abun, shima Hydar nice na dakatar dashi kar ka jawo abinda raina zai b'aci a kanta iya abinda aka yi mata a asibiti ya ishe ta" ta fad'a a kausashe tana kallon sa. Ajiyar zuciya yayi yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ban fad'a dan ranki ya b'aci ba." Kai ta kawar gefe tayi masa alama da ya bata waje ya kuwa fita kamar yadda tace. Masallaci ya fara wucewa yayi sallah kafin ya nufi d'akin sa jikin sa duk babu dad'i, zuciyar sa na bugawa sosai yana jin bak'on abu yana zaga jikin sa kamar yadda jini yake zaga jijiyoyin jikin sa. Yana tsallaka k'ofar d'akin yaji kansa yayi mugun sarawa ya tsaya cak yana bin wajan da kallo amma baiga komai ba ya runtse idanun sa. "Lafiya?" Aliyu ya fad'a daga bayan sa ganin yanayin sa duk ya canja. K'arasowa Aliyu yayi yana kallon sa yace, "baka da lafiya?." Asad ya cize bakin sa ya kalle shi yace, "Kaina" abinda yace kenan ya shiga ciki shima yabi bayan sa. Suhail da yake lab'e a bayan babban gate d'in da ya raba apartment d'in su da gidan ya fito yana murmushi ya bar wajan da sauri ya fiddo waya daga aljinun sa ya danna kira ana d'auka yace, "An zuba masa kuma tabbas ya taka yanayin sa ma ya canja." Waziri yace, "Good boy." Daga haka ya yanke wayar yayi saurin barin gidan gabad'aya. Shigar Asad falo keda wuya kansa yayi mugun nauyi ya rasa me yake masa dad'i bai san lokacin da yayi saurin dafa bango ba yana furta, "Ya salam!." Ganin hakan ya saka Aliyu ya rik'o hannun sa yace, "you're not okay deaf, zauna" ya fad'a yana jan sa kan kujera ya zaunar dashi yana juya kansa. Yadda kansa yake mugun ciwo da sarawa fita yayi daga hankalin sa idanun sa suka firfito waje ya saka hannayen sa biyu ya dafe kansa yana ji kamar ana saka guduma ana dukan kansa. Aliyu ganin abin yayi yawa sai hankalin sa ya tashi ya zauna kusa dashi ya rik'e kan nasa jin yadda jijiyoyin kan nasa suke bugawa a guje sune ya sake tayar da hankalin sa yace, "oh my God wannan wanne irin ciwo ne?." Da sauri ya lalubo waya ya kira Dr Yasir amma bai same shi ba ya tashi tsaye ya kira number Mama ya sanar da ita halin da ake ciki. A gigice Mama ta tawo apartment d'in nasu gab da zata shiga Hafiz ya tsaya a gaban ta yace,"Mama kar ki wuce nan wajan." Hararar sa tayi kafin tace wani abu yace, "Wani abu aka zuba masa ya wuce ta wajan, kalli kiga" ya fad'a yana nuna mata wani bak'in ruwa a wajan ga garin magani a cikin sa har yellow yake yi. Kallon wajan take gaban ta na fad'uwa da sauri ta k'arasa ta kunna hasken wayar ta ta sake haska wajan ta kalli Hafiz tace, "Waye ya shigo nan b'angaren?." Hafiz yace, "ban sani ba Mama." "Kuna ina! Kuzo nan" ta fad'a cikin d'aga murya sosai masu tsaron wajan suka k'araso a guje suka zube kafin suyi magana tace, "Kafin Asad ya shigo wajan nan waye ya shigo?." Jikin d'aya yana rawa yace, "Ranki ya dad'e Suhail ne ya shigo." "Suhail again" ta fad'a tana dafe kanta kafin ta juya da sauri ta nufi falon Asad d'in, bata sake bi ta kan maganin dake wajan ba ta tsallaka ta shiga ta same shi a zaune hannu sa duka biyu a kan sa jikin na rawa sosai. Da sauri ta k'araso ta rik'e shi ta d'ora hannun ta a akan sa tace, "Aliyu kayi wani abun please." Aliyu yace, "Mama na kira Dr yana hanyar zuwa yanzu." "Sannu Asad" ta fad'a kamar zatayi kuka tana kallon sa. Ya canja lokaci d'aya jijiyoyin kansa sun fito radau jikin sa na rawa sai juya kai yake alamun yana cikin azabar ciwo, hankalin Mama ya sake tashi ganin numfashin sa yana k'ok'arin tsayawa ta kalli Aliyu da yake a tsaye hannun sa rik'e da waya shima duk ya rud'e. Shigowar Dr Yasir ya saka Mama kallon sa tana fad'in, "yi sauri kazo ka duba shi." A guje ya k'araso ya tab'a kan Asad jin yadda yake bugawa sai da ya d'auke hannun sa da sauri. Hannun sa har rawa yake ya saka masa ruwa ya kuma yi masa allura ya fara auna bp sa, abinda ya bashi mamaki komai normal yake dan yadda yaji kansa yana bugawa ya d'auka ko jinin sane yayi k'asa hakan ya saka ya kalli Mama itama shi take kallo duk rauni ya bayyana a tare da ita kamar zatayi kuka. Hannu Asad ya saka ya cire ruwan da yake shiga jijiyoyin sa sabida ji yake kamar azaba tana shiga cikin jikin sa. "A'a Asad ya zaka cire?" Mama ta fad'a tana kallon sa hankali a tashe. Juya kan nasa yake yi cikin tsawa Mama tace, "Dr kana ganin abinda yake yi ka tsaya kana kallon sa!?." A firgice ya kalle ta yace, "Ranki ya dad'e na rasa gane kan matsalar, bara nayi masa allurar bacci" ya fad'a da gaggawa yana yi masa allurar bacci amma ko gezau baiyi ba. Aliyu yace, "Dr muje asibiti kamar zai fi." Hafiz yace, "No prince zaman sa a nan yafi safe, dan Allah Yasir kayi iya k'ok'arin ka a samu yayi bacci." Gabad'aya sun rud'a Dr ya rasa ma abinda zaiyi yayi masa allurar bacci baya son sake yi masa wata dan tabbas zai zama cikin risk domin abubuwan zasu yi masa yawa a blood d'in sa. "Prince in aka sake masa another injection abubuwan zasu yi masa yawa" ya fad'a yana kallon Aliyu. "Kayi masa mana, ko meye kayi masa abinda zai bar wannan condition d'in!" Mama ta fad'a a fusace tana kallon sa dan hankalin ta a tashe yake, bai san sanda ya balle kan allurar ya ja a sirinji ya dannawa Asad a jijiyoyin jikin sa. Lumshe idanu Asad ya fara yi har lokacin yana rik'e da kansa idanun sun k'i rufewa yadda ake so. Abin mamaki da al'ajabi Dr ya tsaya yana kallon ganin har lokacin bacci bai d'auke sa ba sai kansa ya kulle ya rasa abinda zai bashi kuma nan gaba. Domin allurar da yayi masa bata second biyar a jikin mutun bata saka shi bacci ba. Hafiz da yake tsaye ya lura da yanayin Dr hakan ya saka ya k'arasa wajan fridge da sauri ya d'auko ruwa ya bawa Mama yace, "Mama ki masa tofi ya sha zai fi samun sauk'i." Ba musu ta karb'a ta fara tofa masa duk ayar da tazo bakin ta kafin ta bashi yasha ta shafa masa ragowar a fuskar sa. Komawa gefe Dr yayi yana kallon ikon Allah har lokacin bacci bai d'auke Asad ba kuma kansa bai daina ciwo ba. "Hafiz kama shi mu kai shi d'aki ya kwanta" Aliyu ya fad'a yana kallon Hafiz. Tare suka d'aga shi aka kai shi kan gado ya kwanta har lokacin hannun sa na dafe da kansa idanun sa kuma a bud'e. Mama na zaune a gefen sa hannun ta guda d'aya ta rik'e nasa tana tofa masa addu'a a hankali, sun kwashe sama da mintina arba'in a wajan kafin bacci ya d'auke shi. Ajiyar zuciya Mama tayi ganin yayi bacci ta kalle su da suke tsaye har lokacin bata ce komai ba ta mik'e aka ja masa k'ofar aka fita ta kalli Dr hakan ya saka shi yace, "Ga magani na koma na d'auko masa in ya farka sai ya sha. Nayi mamakin ciwon nan nasa ban tab'a karo da ciwon kai irin wannan ba gaskiya" ya fad'a yana ajjiye maganin akan table. Bata ce komai ba ta fita da sauri ta dinga kiran masu tsaron wajan suka k'araso a guje suka zube ta kalle su tace, "Daga yau ban amince a sake barin kowa ya shigo wajan nan ba, ko waye ko wace ban amince ba in kuma aka sab'a abinda na fad'a....." Bata k'arasa ba ta girgiza yatsan ta guda kafin ta bar wajan da sauri. Tana shiga b'angaren ta d'akin da Hydar yake ta shiga yana kwance inda yake ta fita ta koma d'akin ta. Waya ta d'auka hannu na rawa ta zauna jikin ta duk yayi sanyi ta nemi number mahaifin ta ta kira shi. yanke kiran aka yi hakan ya bata tabbacin zai kira ta kenan bata ajjiye wayar ba kuwa kiran ya shigo, da sallama ta d'auka muryar ta na rawa sosai kafin tace, "Barka da dare Abbie." Jin maganar ta a haka ya saka yace, "Ban saba jin rauni a muryar Rabi'atu ba, me ya haifar da hakan?." Kuka ta fara yi mara sauti kafin tace, "Abie suna neman su kashe min Hydar da Asad. Hydar na kwance har yanzu baya motsawa ga Asad can yanzu na baro wajan sa kansa na ciwo dak'yar aka samu yayi bacci. Ban san me suke nema a wajan su ba so suke suga bayan su." Abie ya murmusa yace, "Babban kuskuren mijin ki da ya furta zai sauka daga kan kujerar sa ya bawa Asad wannan shine kuskure babba da ya tafka. A yanzu zakiyi mamakin adadin wad'an da suke harin rayuwar Asad sabida son mulki, mulki yana sakawa mutane suyi komai a kansa, mulki yana sakawa idon mutane ya rufe suga in basu samu abinda suke so ba zasu iya ganin bayan kowa. Baza su barki kiji dad'i ba sai kin dage da addu'a sosai dan itace maganin ko wanne mugu. Kiyi hak'uri ki bar lamarin a hannun Allah, nima kuma ina taya ki addu'a bama ke kad'ai ba dukka y'an uwan ki." "Allah yaja da ran mahaifina lamarin nasu ne yayi yawa na rasa inda zan saka kaina." "Zama uwa ga sarki ai ba abu bane mai sauk'i ba Rabi'a, duk inda kike tunanin wahalar sa ya wuce nan sai kin jure dole. ki cigaba da addu'a kawai ban amince kiyi shirka ba Allah kawai zaki rok'a zai miki maganin komai. Zan bada sak'o a kawo miki kuyi amfani da maganin dukkan ku." "An gode Takawa, Allah ya ja kwana, Allah ya tsare, Allah ya rufa asiri" ta fad'a da girmamawa kafin suyi sallama ya katse kiran ta sauke numfashi, ko babu komai hankalin ta ya kwanta da kalaman mahaifinta masu sanya nutsuwa. *☆☆☆* "Umma k'afa ta ciwo take min" ta fad'a tana hawaye mai zafi tana cize bakin ta. Umma hankalin ta duk ya tashi ta kunna k'aramar fitilar hannun ta tace, "Sannu Rauda, kiyi hak'uri kita yiwa k'afar addu'a zata daina in sha Allah." Kai take juyawa kawai sosai k'afar take ciwo rashin shan maganin da bata yi ba. "Gashi kin cillar da katin maganin balle na fita naje wajan mai chemist d'in nan na baya naji ko za'a samu wasu daga ciki na karb'o miki. Kwalayen ma kin watsar balle naje dasu." Ita dai bata ce komai ba sai juya kanta da take yi kawai hankalin Umma yak'i kwanciya. Addu'a ta dinga yi mata a k'afar haka suka raba dare sai gabanin biyun dare sannan bacci ya d'auki Rauda sai a lokacin Umma ma ta runtsa. Da asuba Umma taso makara Allah ya taimaka ta tashi bayan ta idar da sallah Baba ya shigo take shiga d'akin sa tace, "Malam daman magana nazo muyi." Yace, "to ina jin ki." "Akan k'afar Rauda ne jiya kusan kwana mukayi babu bacci tana ta kuka tana yi mata ciwo rashin shan maganin da bata yi ba kwana biyu, shine nace zamu shiga gidan radio ko muje gidan sarki tunda yana taimakawa mu nemi taimakon kud'in maganin." Baba yace, "gwara ma gidan sarkin yana taimakawa sosai da zarar maganar taje gaban sa, gidan radio sai aita yad'awa amma kaji shiru wani lokacin. zan tambaya anjima naji yana gari sai aje in sha Allah kuma zai taimaka." "Allah ya sa" Umma ta furta jikin ta a sanyaye ta juya ta fita. Baba yana ganin ta fita ya k'arasa wajan ajiyar kud'in sa ya tsohuwar riga duk ta yage baza ka tab'a d'auka akwai kud'i a cikin ta ba ya fiddo da kud'in yana kalla, murmushi yayi yace, "da zan iya da an siyi maganin amma bazan iya cire kud'i masu yawa akan magani kawai ba gwara a fita neman taimakon shima riba ce" ya fad'a yana tattare kud'in ya mayar dasu ma'ajiyar su ya fito daga d'akin. Da gari yayi haske Rauda ta tashi babu laifi taji dad'in k'afar ta yi wanka ta karya tana zaune a kan farar kujerar da take zama sabida sauk'in tashi tsaye. "Sallamu alaikum wai ana sallama da Rauda a waje." Yaro k'arami ya fad'a daga soron gidan. Umma ta d'ago labule ta fito tana fad'in, "Sallama da Rauda kuma? In ji waye?." "In ji Bala mai pharmacy" ya bata amsa yana kallon Umma. Umma tace, "to jeka kace gata nan." Yaron ya Juya ya fita Rauda ta kalli Umma tace, "Umma naje nayi masa me?." "Jeki Rauda bamu sani ba ko hak'ura yayi ya kawo miki maganin." "Ni dai Umma bazan je ba babu cin fuskar da bai min ba jiya." "To ni bara na je" Umma ta fad'a tana niyar juyawa ta shiga d'aki ta d'auko mayafi. Mik'ewa Rauda tayi tace, "Zanje" ta fad'a tana d'aukar sandinan ta tana tafiya a hankali har ta fita soron gidan ta tarar dashi a tsaye da leda a hannun sa. Yana ganin ta yayi murmushi yace, "Rauda sannu, ya k'arfin jikin?." "Da sauk'i, lafiya kake nema na?." "Lafiya lau. Maganin na kawo miki nazo kuma na shaida miki duk bashin da yake kan ki an biya an kuma siya miki maganin da zaki ta sha har ki warke, dan haka daga wannan ya k'are azo a karb'a a waje na." Kallon sa take tana kallon maganin da yake mik'o mata a leda kafin tace, "An siya min? Kuma an biya min bashi?, waye wanda ya siya har ya biya min bashi?." Bala ya gyara tsayuwa yace, "to wanda ya siya d'in aiko min akayi ba shi yazo da kansa ba, amma dai an siya miki." "Waye wannan wanda zai siya min magani?" Ta fad'a a bayyane fuskar ta d'auke da zallar mamaki. *Nima kaina abin ya bani mamaki waye ya siyawa Rauda magani kuma?.*⛹‍♀️⛹‍♀️⛹‍♀️ *KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *014.* A sanyaye ta shiga gida hannun ta rik'e da leda ta zauna a inda ta saba zama Umma ta kalle ta tace, "Lafiya yake neman ki?." Ledar hannun ta ta nuna mata kana tace, "Wai cewa yayi nayi hak'uri da abinda ya faru jiya ga maganin wani ya siya min kuma ya biya bashin baya ya kuma bada kud'in wanda zan karb'a nan gaba." Da mamaki Umma ta rik'e baki tace, "ikon Allah! Waye kuma ya biya?." "Ban sani ba Umma, na tambaye shi yace shima turo wani aka yi amma wanda ya siya d'in bai zo da kansa ba." "Wanne d'an albarkan ne da wannan aikin?." "Nima kaina ya kulle Umma." Umma ta nisa kafin tace, "to wama zai miki haka in ba Anas ba? Shi kad'ai ne saurayin da yake zuwa wajan ki yanzu shine zai shiga lamarin ki, Jikina yana bani shine ya siya miki." Rauda tace, "Amma kuma Umma Anas baya garin nan tun ranar da muka had'u had'uwar k'arshe ya cewa Baba zaiyi tafiya ban kuma ganin sa ba, bai ma san halin da nake ciki ba a yanzu." Umma tace, "Ke kamar ba y'ar zamani ba Rauda? Kin manta yanzu waya tana isar da ko wanne irin sak'o a kuma duk inda kake a duniya?." "Haka ne Umma, amma ina tantama gaskiya." "To in ba shi ba waye Rauda?." "Babu kowa" ta fad'a a sanyaye Umma tace, "to kin gani, amma Allah ya yi masa albarka ya raba shi da iyayen sa lafiya." Rauda ta murmusa har cikin zuciyar ta take jin farin ciki tace, "Amin Umma Karon farko kenan a rayuwar ta da naji ya burge ni" ta fad'a farin ciki na shiga zuciyar ta sosai. Umma tace, "kin ga bara na kawo miki ruwa ki sha maganin nan jiya kin sha wahala" ta fad'a tana mik'ewa ta kawo mata ruwa a kofi ta sha maganin ta shafa na shafawa ta ajjiye ragowar. Inna da take d'aki taji komai ta fito fuskar ba yabo babu fallasa ta wuce su bata ce komai ba daman Umma tasan baza ta ce ba dan idan magana ce akan Anas k'arara zata nuna miki tana bak'in ciki da ba Rahma yake so ba. Baba ne ya shigo a gigice fuskar sa taf fara'ar da basu tab'a ganin irin ta ba yana fad'in, "mutanen gidan nan kuna ina! Kuzo kuji abin arzuk'i da farin ciki" ya fad'a yana shigowa yana kallon su. Umma tace, "Malam lafiya?." "Bari kedai, ai babar ki ta iya haihuwa da ta haifo ki na aura kika haifo min Rauda. Bawan Allah shigo mana" ya fad'a yana kallon k'ofa. Mutumin ya shigo sanye da k'ananu kaya hannun sa rik'e da leda ya durk'usa har k'asa ya gaishe su kafin yace, "An turo ni akan na kawowa Baba keke napep guda biyu, sannan ance na bawa mahaifiyar Rauda wannan kud'in" ya fad'a yana d'auko kud'in daga leda. Da hanzari Baba ya kaiwa kud'in cafka mutumin ya hana shi ya kalle shi yace, "Ita aka ce na bawa Baba." Yak'e Baba yayi yace, "Daman zan mik'a mata ne ai." Mutumin ya k'arasa wajan Umma ya ajjiye kud'in a gaban ta yace, "sannan yace a gaida wacce bata da lafiya shima baya jin dad'i ne da ya zarar ya samu lafiya zai baro inda yake yazo in sha Allah. Gashi yace a bata" ya fad'a yana sake d'auko kud'i a rufe a takarda ya sake ajjiyewa Umma. "Sannan akwai kayan abinci da yace a tawo dasu gasu can za'a shigo dasu yanzu." Umma da ta saki baki tana kallon mutumin tace, "bawan Allah waye ya turo ka da wad'an nan abubuwan haka?." Kafin yayi magana Baba yace, "Anas mana, da shi mukayi maganar zai siya min abin hawan da zan dinga samun kud'i dashi, gashi kuma ya cika alqawari." Umma ta jinjina kai tana kallon mutumin tace, "Amma hidimar tayi yawa bai kamata mu karb'i abin hannun sa ba tunda babu wata magana mai k'arfi tsakanin sa da Rauda, gaskiya a mayar masa." Baba yace, "ai na riga na ba shi auren ta, ko bana raye shine mijin Rauda tun ba yau ba na mallaka masa ita" ya fad'a hakora a bud'e dan kar ma a mayar da kud'in. Mutumin ya murmusa ya mik'e tsaye yace, "Za'a shigo da kayan yanzu" ya fad'a yana fita jim kad'an aka fara shigo da kayan abinci babu abinda babu harda yankakkun kaji da d'anyen nama. Bayan an gama shigowa da su yace, "To Baba zan wuce ni." Umma tace, "Bawan Allah da gaske Anas d'in ne ya turo ka?." Zaiyi magana Baba yace, "Kina da matsala Binta, in ba shi ba waye zai aiko mana da wannan abin arzuk'in? Shine an fad'a miki sai faman maimaita magana d'aya kike yi." Umma tayi Jimm sai tace, "mun gode bawan Allah kayi magana godiya dan Allah. bamu da bakin gode masa sai dai muce Allah ya biya masa dukkan buk'atun sa na alkhairi." Ya amsa da amin Umma tace, "Tsaya bawan Allah a baka tukwici." Yayi dariya yace, "Haba hajiya ki bar shi na gode sosai. Sannan Baba yace a fad'a maka dan Allah kar kace zaka ja keken da kanka ka bayar a dinga yi maka ana kawo maka kud'i har gida." Baba yace, "In sha Allah hakan ce zata kasance, Allah ya biya buk'atar duniya da lahira." "Amin ya Allah. sai an jiman ku" ya fad'a yana fita Baba yabi bayan sa. Rauda dai ta kasa cewa komai bakin ta a bud'e tana kallon abincin da kuma kud'in dake kusa da Umma zuciyar ta na mugun bugawa da sauri-sauri bakin ta ya mutu murus ta rasa wacce irin kalma zata furta. Umma ta kalle ta tace, "Rauda baki ce komai ba bayan duk abinda ya faru ta silar ki ne." Kamar kuma an mata allura a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tace, "Umma na kasa magana ne gabad'aya ban san me zance ba." "Haka zaki ce kuwa Rauda domin duk abinda aka bamu ta dalilin kine." Kafin tayi magana Baba ya shigo fuska washe yana kallon kayan abincin yana fad'in, "yau ko fita kasuwar ma bazan ba a dafa mana kajin nan muci mu karya k'asusuwa." Umma ta kalle shi bata ce komai ba ya kalli Rauda yace, "Allah ya yi miki albarka Rauda, ke farar haihuwa ce wallahi ko cikin y'ay'ana ke ta daban ce." Inna da take tsaye tace, "Su kuma bak'ak'en haihuwar sai a zubar dasu ace ba'a so" tana fad'a ta shiga d'aki ya bita da kallo baice komai ba ya cigaba da santin kayan abinci. Umma tayi dariya tana girgiza kai jin yau Rauda ake cewa ko a cikin y'ay'an sa ita ta dabance, ita yake yiwa wannan fara'ar har yana ce mata farar haihuwa. "Allah yayi mana arzuk'i" Umma ta furta a bayyane tana sauke numfashi. Umma ya kalla yace, "Nawa ne kud'in da aka baki?." Yana fad'ar hakan ta d'auke takardun kud'in da nata dana Rauda ta rik'e bata ce komai ba ganin hakan ya saka yace, "Ga b'arawo zan sace miki kud'i shine kika d'auke ko?." Ita dai bata furta ba ya girgiza kai. Ranar Umma ke da girki abinda baya faruwa a gidan ranar shine ya faru, lafiyayar shinkafa da miyar kaji aka yi a gidan kowa y'an makaranta suka dawo cikin ikon Allah akayi bak'i a yayyen su mata duk suka zo aka ci aka sha kowa da farin ciki a zuciyar sa ana ta santin auren Anas da Rauda. Rauda sai taji alfahari a zuciyar ta ganin ana ta santin abinda ta dalilin ta ya samu lokaci d'aya taji Anas yana samu kyakykyawan gurbi a zuciyar ta. *☆☆* A jingine yake da fuskar gado idanun sa a lumshe kana kallon yanayin sa kasan bashi da cikakkiyar lafiya haka zalika baya jin k'wari a jikin sa dan fuskar sa da yanayin sa ya gwada hakan. kamar wanda aka yiwa magana ya bud'e idanun sa yana kallon d'akin kafin ya sauke numfashi ya kalli k'ofar da za'a shigo d'aki jin motsi. Mama ya gani ta shigo ya tashi zaune sosai yana kallon ta ta k'araso da sauri ta zauna kusa dashi ta tab'a fatar kansa tana kallon sa tace, "Asad ya jikin? Tun d'azu nake zuwa kana bacci." "Naji sauk'i, Barka da safiya." "Ka tabbata lafiya lau ka ke?" Ta furta ba tare da ta amsa gaisuwar ba. "Naji sauk'i" ya sake fad'a yana kallon ta. Fuskar sa ta rik'e tana kallon sa tace, "ka rame Asad yanayin fuskar ka ya nuna min akwai abinda yake damun ka bayan ciwon da kake fama dashi, meye?." "Mama kwana biyu ta daina zuwar min cikin mafarkina, ina so na ganta ban san inda take ba, ina kewar ta sosai" ya furta yana kulle idanun sa yana nuni da tsantsar abinda yake zuciyar sa kenan. Da mamaki mai had'e da fad'uwar gaba Mama tace, "Wacece take zuwa mafarkin ka har kake so ka ganta?." Bud'e ido yayi yaga ta kafe shi da idanuwa sai kuma ya dawo hankalin sa tunawa da wacece a zaune kusa dashi ya sauke kai k'asa baice komai ba. "Magana nake maka wacece?." "Margayiya Hajiya mai babban d'aki" ya furta a hankali ba tare da ya kalle ta ba. Nannauyar ajiyar zuciya tayi jin abinda yace sai ta murmusa tace, "Ka dinga mata addu'a itace zata amfane ta a yanzu. Ni har ka bani tsoro na d'auka wata ce take kutse cikin mafarkin ka." Shiru yayi bai amsa ba gaban sa mugun fad'uwa haka kawai ba tare da ya san dalilin hakan ba. Tashi tayi ta fita jim kad'an ta dawo da abincin sa da kanta ta zauna kusa dashi ta had'a masa duk abinda zai buk'ata ta bashi tace, "maza ka cinye akwai maganin da Abie ya aiko dashi zaka sha." Bai ki ba ya ci abincin daidai yadda zai iya ya bar sauran ya sha maganin da ta cika masa a k'aramin kofi. Kallon sa tayi bayan ya shanye maganin tace, "mahaifin ka ya dawo d'azu in ka samu lafiya sai kaje ku gaisa. Sannan na hana kowa shigowa apartment d'in nan koda Hafiz ne ko Suhail ban lamunci su zo nan ba, in suna son had'uwa da kai suje wani wajan amma banda gidan nan na lura masu son ganin bayan ka suna da yawa." Kai kawai ya girgiza dan bazai kuma iya cewa komai ba. Fita tayi daga d'akin ya sauke ajiyar zuciya ya d'auki ruwa ya sha, "Rauda!." Ya ji bakin sa ya furta ba tare da ya shirya hakan ba ya runtse idanun sa yana hango idanun ta da goshin ta ya bud'e yana cize bakin sa ji yake kamar ya tsinke kansa da mari. Yadda yake jin begun zuciya da fad'uwar gaba abin har tsoro yake bashi ya kalli gefen k'irjin sa yaga yana d'agawa a hankali. Tashi tsaye yayi yana dafe da kansa sa ya kalli agogo inda ya nuna masa k'arfe hud'u na yamma ya sauke numfashi a karo na babu adadi ya shiga band'aki, bai jima sosai ba ya fito ya shirya cikin manyan kaya kamar koda yaushe yayi kyau sosai duk da ya rame amma kyawun sa bai b'uya ba. K'ofa aka bud'e aka shigo bai kalli wanda ya shigo ba dan yasan bazai wuce jinin sa Aliyu ba shi kad'ai ne zai shigo babu izinin sa, "ya jikin ma?" Aliyu ya tambaya yana kallon sa. Juyowa yayi ya kalle shi da niyar bashi amsa sai maganar ta tsaya ganin abinda bai tab'a gani ba tun bayan girman su shi ya gani a tare dashi. kayan da yake jikin Asad irin sa Aliyu ya saka hatta hular kan su iri d'aya ce kamar su ta fito sak babu wanda zai banbance Aliyu babu wanda zai banbance Asad. "I'm fine, thanks you" ya furta a tak'aice bai kuma kallon sa ba. Aliyu bai damu ba bai kuma kallon sa ba shima ya fita daga d'akin. Sosai Asad yake cikin mamakin canjawar da Aliyu yayi ya koma sak irin sa, hatta yadda yake magana shima ya mayar da tasa hakan babu ta yadda zaka ce ba shi bane in kaga Aliyu a canjin da ya samu abin yana d'aure masa kai. Waya da key na mota ya d'auko duk da baya jin k'arfi a jikin sa ga jiri da yake ji amma baya son zaman gidan ya fito falo. Babu kowa a falon ya wuce ya fita zuwa harabar apartment d'in nasu. A sannu yake takawa sabida yadda kan yake masa ciwo cikin nutsuwa yake giftawa khamshi yana tashi. ganin yadda ake gaishe shi jiki yana rawa ya fahimci d'auka suke Aliyu ne dan shi ya fara fitowa sun gane kayan jikin sa hakan ya saka shi fita daga gidan da sassarfa. *☆☆☆.* "Khalil! Khalil!!, baka ji ina yi maka magana ne?" Umma ta fad'a daga d'aki tana fitowa amma babu Khalil babu dalilin sa. "Lallai ma yaron nan nace ya jira ni zan aike sa sai ya fice?." Rauda da take zaune tace, "yammar tayi ai ya tafi ball balle yau da garin yake a rufe ba rana" ta fad'a tana cigaba da karanta azkar. "Ina Khairi?." "Ta tafi kara Yaya Ummi bakin titi." "Rahma kuma basa nan?." "Duka sun fita" Rauda ta sake bata amsa tana kallon ta. Umma tayi k'wafa tana girgiza kai Rauda tace, "A kira miki shi ne?." Umma tace, "k'yale ni bara na fita da kaina na kira shi." Da sauri ta ajjiye littafin hannun ta ta mik'e tace, "Haba Umma bana so kina fita irin haka wallahi, bara na kira miki shi da kaina." Umma tace, "in yayi nisa ki k'yale shi kar ki yi nisa kema." Da to ta amsa ta saka hijjabi ta fita tana dora sandinan ta. Batayi nisa ba ta hango yara ana ta ball ta kalle su tace, "Ina Khalil?." D'aya daga cikin yaran yace, "Yanzun nan yayi titi." Rauda ta girgiza kai ta bi hanyar titin dan ta kira shi kar ayi magariba yana ball. Titi ta fito amma dai bata ganshi ba, ta dinga kallon titin amma baya nan taja tsaki ta juya da niyar komawa taji kamar tayi karo da mutum. Gaban ta yayi muguwar fad'uwa shakar khamshin turaren da bazata manta dashi ba tayi saurin d'agowa ta kalle wanda ta buge. dogon tsaki Aliyu ya ja ya saka hannu biyu ya bangaje ta ta fad'i k'asa ya cize bakin sa cikin takaici da tunanin irin hukuncin da ya kamata yayi mata. kallon ta ya kuma yi itama shi take kallo haushi da tsanar sa take ji a zuciyar ta yace, "Mahaukaciya!" Abinda ya furta kenan ya wuce ya bar wajan zuciyar sa cike da jin haushin zuwan sa ma wajan, in badan mai martaba ba mai zai kawo shi unguwar talakawa kamar wannan, badan mutane da suke kai kawo ba babu abinda zai hana bai sake b'alla mata k'afa ba. Kafin Rauda ta farga bata kuma ganin sa ba sai k'urar motar sa ta gani ta kyad'a kai tana jin zafi a hannun ta ta furta, "kaine dai mahaukaci bani ba, wanda bai san darajar na gaba dashi ba. Na tsane ka wallahi naso kuma ka tsyaa dana tabbatar maka da kaine mahaukaci bani ba." ta fad'a tana k'okarin Mik'ewa. A hankalin motar Asad kirar range rover ash colour take yin slow daga gefen ta, wajan yake kalla yaga tabbas a nan suka had'u ya sake kallon gefe yaga kamar itace take so ta tashi kamar kuma ba itace ba, zuba mata ido yayi ta jikin glass d'in motar ganin fa da gaske ta kasa tashi ga kuma babu yawan mutane a wajan sai ya b'alle murfin motar ya fito duk da zuciyar sa na hana shi hakan amma gangar jikin sa tak'i karb'ar umarnin zuciyar tasa ya tsallako. Khamshin da taji a kanta ya saka ta d'ago kai ta kalle shi mamaki ya hana ta magana har ya kama kafad'ar ta kamar jiya ya tasar da ita tsaye bata san anyi ba. Lallai ma wannan mutumin yana raina mata hankali, shi kuwa fuskar ta yake kallo da babu niqab ko face mask zahirin tace a bayyane. d'auke idanu tayi dan yana yi mata kwarjini jin baice komai ba ya saka tace, "wai fuska biyu ce da kai wani lokacin kamar mutumin kirki wani lokacin mutumin banza ne kai, in zaka yiwa mutane fuska biyu banda ni domin na riga na gama gano kai d'in ba komai bane face mahaukaci wanda bai san darajar d'an adam ba. ban tab'a jin tsanar halitta kamar yadda nake jin tsanar ka ba. Na fad'i duk abinda yake bakina in ka dama ka saka a kashe ni a nan shine zaka nuna min lallai kana da k'arfin ikon mulki da sarauta. Ni kuma zan nuna maka k'arfin sarautar Allah domin ahi kad'ai nake jin tsoro a duniyar nan" ta fad'a tana d'ago ido ta zuba masa banzar harara mai d'auke da zallar tsana da k'yama. Baice komai ba daman bazai ce ba dan ya gama fahimtar duk abinda take fad'a ba dashi take ba babban abinda yake d'aure masa kai a ina suke had'uwa da Aliyu?, "Lahh Yaya Aliyu!" Aka fad'a daga bayan sa cikin mamaki. Bai juya ba hakan ya saka Khairi k'arasowa da sauri ta tsaya kusa dashi tana dariya tace, "Ashe dai zan gane ka, ina wuni Yaya Aliyu?." Kallon ta yake yana so ya tuna inda ya santa ganin hakan ya saka Khairi tace, "Wacce ka siyawa Yayar ta kayan fruits a k'ofar asibitiiiiii....?" Ta fad'a tana jan kalmar asibitin lallai sai ya gano. Murmushi yayi kad'an alamun ya tuna ganin hakan ya saka tace, "Kaga yayar tawa nan ita ka siyawa. Anty Rauda ina lokacin da kina asibiti Baba ya bada d'ari biyu na siyo miki lemo a wajeeee.. Har Umma ta dinga min fad'aaaaaa? To kin ga wanda ya siya miki yace na kawo." Juyo da kallon ta tayi ga Asad tace, "Yaya Aliyu kaga Antyna ta koma mai yawo da sanda ko? Wanda ya buge ta ya daina zuwa inda take ance kuma sai an mata aiki zata warke mu kuma bamu da kud'in biyan kud'in, shikenan Antyna ta zama gurguwa" ta fad'a kamar zatayi kuka. Takaici, bak'in ciki, b'acin rai suka tararwa Rauda lokaci d'aya bata san sanda ta tsinke Khairi da mari ba ta jawo ta kusa da ita ciki fad'a sosai ta zare mata idanu tace, "in baki min shiru ba sai na fasa miki baki, banza wacce bata iya shiru a rayuwar ta. Wa kika tab'a gani yana kula wanda basu san darajar mutane ba irin wand'an nan? Wa kike ganin yana kula masu shaye-shaye da neman mata eyeee?." Khairi da take hawaye tace, "Wallahi yana da kirki Anty." Bai ji mai tace mata a gaba ba tafiya suke yi shi kuma ya juya zuwa cikin motar sa, duk da kalamai ta fad'a masu muni amma sam baiji komai a ransa ba dan maganar ta ta tabbatar masa da Aliyu yake bada shi ba. A kan sitiyarin motar ya saukar da kansa yana furzar da iska a hankali yana jan numfashi yana saukewa, kallon inda suke yayi yana hango su da alama fad'a take yiwa Khairi dan yaga tana magana a fusace, duk taku d'aya da take yi tana nisa dashi ji yake kamar ana d'igo masa kewa wacce bai san dalilin ta ba a zuciyar sa tana yin gaba yana sake jin kewar na k'aruwa har ya daina hango su. _Ya akayi ta san Aliyu?, a ina suke had'uwa haka?. Da gaske silar Hydar ta zama gurgurwa?._ tambayoyin da yake yiwa kansa a zuciyar sa kenan amma babu mai bashi amsa sai ita d'in. Sake kallon layin nasu yayi ya sauke numfashi sunan Rauda na yi masa amsa kuwa a cikin kunnuwan sa. "Inda Aliyu ta fad'awa hakan da me zai faru?" Ya furta a bayyane har lokacin yana kallon inda suka bi dan yasan tabbas sai dai wata ba ita ba, babu abinda zai saka Aliyu bai mata mummunan hukunci ba. Yarinyar cikin mafarkin sa yake tuno fuskar ta idanun ta da goshin ta yake ganowa kamar ko yaushe, bud'e ido yayi ya tuno lokacin da Rauda ta bud'e idanun ta tana yiwa Khairi fad'a gabad'aya yanayin ta ya koma irin na yarinyar mafarkin sa. "Itace ko A'a" Ya tambaya yana dafe kansa da duka hannayen sa guda biyu jin bak'on abu wanda bai tab'a jin irin sa ba yana cigaba zuciyar sa da ko ina na jikin sa. *KWANTAN ƁAUNA* ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *015* Fuska a had'e Rauda ta shiga cikin gidan su Khairi na bayan ta tana gurshek'en kuka sai Khalil da yake biye dasu a baya. Ganin su haka ya saka Umma ta kalli Rauda tace, "Tun d'azu Rauda sai yanzu?." Zama Rauda tayi kafin tace, "Sai da naje titi." Umma tace, "Ke kuma Ummin ce ta dake ki kike kuka?." Khairi tace, "Anty Rauda ce, dan kawai naga wanda ya siya mata fruits a asibiti na yi masa magana shine ta mare ni" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da kuka. Umma ta kalli Rauda tace, "Akan me zaki mare ta Rauda bayan abin arzuk'i tayi? Ai ba laifi bane da taga wanda yayi mata alkhairi ta nuna ta san shi. Inda arzuk'i kema gaisawa ya kamata kuyi dan taimakon ki yayi." Rauda tace, "Umma bai cancanci a kula shi ba, bai san darajar d'an adam ba kwata-kwata." Da mamaki Umma tace, "Ke ya akayi kika sani?." "Umma ina wannan d'an sarkin da muka had'u dashi a gidan sarki..? Wanda muka sake had'uwa dashi har Khalil yake cewa yace na shiga mota nak'i...?. dashi muka kuma had'uwa yau, shine fa wanda take cewa ya siyi kayan marmari dan tsabar k'arya." "Wallahi ba k'arya nake ba shine Umma" Khairi ta fad'a tana kuka. Umma ta kalle ta zatayi magana Rauda tace, "Sai sake marin fuskar ki sannan zakiyi mana shiru naga alama. Bashi da kirki fa ko kad'an Umma yau ma baki ga kalar rashin mutuncin da yayi min ba." Umma tace, "Kuma dai?." Rauda tace, "Kin san Khairi da shegen surutu ta dinga zuba a gaban sa maganar da ba'a tambaye ta ita take furtawa shiyasa na mare ta, wannan ai ba wanda za'a kula bane ba. Habiba tace min har neman mata yake yi garin haka in yayi mata wani abun fa tunda yasan babu abinda zamu iya?." Umma ta rik'e baki tana nuna Rauda da yatsa tace, "Ina raba ki Rauda da irin wad'annan zantuttukan wallahi, kinga ki kiyayi bakin ki kar ki jawo abinda zaki zo kina dana sani. Ina ruwan ki da sabgar sane wai? Ba abinda ya had'a ku ki dinga k'okarin gefa rayuwar ki a hatsari sabida tsiwa. Kuma kar na k'ara ji kince yana neman mata tunda kedai bai neme ki ba bai kuma nema a gaban idanun ki ba, ki kiyayi tsayuwa gaban Allah." "Wallahi Allah na tsane shi tsana mai muni Umma, ban tab'a jin tsanar wata halitta a duniya kamar sa ba, bana son ganin koda fuskar sa ce." Umma bata ce komai ba ta wuce tana d'aura alawar magriba dan bata ga amfanin yi mata magana ba. Bayan an idar da sallah suna zaune cikin k'aramin hasken fitilar tsakar gidan Baba ya shigo kamar an cillo shi har tuntub'e yake yi, "Ke Rauda maza jeki ga Anas can yana jiran ki." Abincin hannun ta ajjiye dan tasan ko bata ajjiye ba tunda yace ta tashi sai fa ta tashj tana k'okarin mik'ewa cikin fad'a yace, "ki k'arfafa jikin ki malama ki tashi." Babu wanda ya tanka ta tashi ta saka hijjabi ya d'auki kujerar da take zama da kansa yayi gaba tana bin sa baya. Sanyin khamshi taji tunda ta shigo soron gidan nasu Baba ya ajjiye mata kujerarya kalli Anas da yake tsaye yace, "Gata ta fito maka da ita da kaina, zauna mana" ya fad'a yana kallon Rauda. Ba musu ta zauna Anas ya duk'a har k'asa yace, "Allah ya saka da alkhairi Baba." Baba ya amsa da amin ya fita. Zama yayi kan irin tata kujerar yana kallon ta cikin hasken fitilar da aka ajjiye a soron ga hasken wayar sa da ya kunna gana waje wanda yake shigowa, bata d'ago ba shi kuma baiyi magana ba. Jin shirun yayi yawa ya saka ta d'ago sai suka had'a ido karon farko tayi murmushi mai kyau tace, "Ina wuni." Jinjina da kujerar Anas yayi ji yayi in bai jingina ba iskar soyayya da take kad'a zata iya d'auke shi ta kai shi wani wajan shiyasa ya nemi mafita tun da wuri. Bai jima sosai ba ya kalle ta yace, "Dan Allah ki sake min murmushi da kika yi yanzu." Bata san lokacin da murmushin ya sub'uce mata ba ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na gode my love, Allah ya biya ki da aljanna." "Baka amsa ba na gaishe ka" ta furta a hankali. "I'm sorry My love, murmushin da kika yi min a karon farko a rayuwa ta ya saka na manta duk abinda kika ce. Lafiya lau ya jikin ki?." "Da sauk'i." "Allah ya k'ara lafiya. Kiyi hak'uri na nemi wayar Baba lokacin da abin ya faru ban same shi ba, ina can hankali na yana kan ki Rauda duk da tarin aiyukan da suka min yawa." A sanyaye tace, "haka Allah ya k'addara, babu komai a hakan ma na gode sosai, mun ga abubuwan alkhairi Allah ya saka da alkhairi ya biya buk'ata. Umma tace nayi maka godiya sosai." Murmushi yayi yace, "Babu komai Rauda kar ki damu." Shiru ya sake biyo baya kafin yace, "Munyi magana da Baba akan aikin k'afar ki in sha Allah tafiyar ki zata dawo kamar dah indai ina da rai tunda aikin ba wani mai wahala bane indai aka bar nigeria, cikin satin nan in Allah ya amince za'a yi aikin." D'ago ido tayi suka had'a idanu yayi murmushi sai tace, "Na gode." "Haba Rauda ni dake babu godiya wallahi, fatana ki amince da soyayya ta ki yadda dani har ta kai mu ga aure." Murmushi tayi kad'an bata ce komai ba domin ita kam bata d'auka zai sake dawowa inda take ba sabida lalurar da ta same ta. "Naga kin gaji sosai ga sallah ana yi, zan koma amma in sha Allah gobe zan yiwa Baba bayanin aiki da za'ayi in sha Allah." Kai ta girgiza kafin tace, "Allah ya saka da alkhairi." "Amin. Amma kin san wacce irin addu'a nake so kiyi min?." Kai ta girgiza alamun a'a yace, "Ki min addu'a Allah ya mallaka min ke a matsayin matata." Murmushi tayi sai tace, "Ban d'auka zaka yi wannan fatan ba duba da irin iftila'in da ya same ni." Murmushi yayi yace, "Wai da sai na guje ki kenan?." Ya sake yin murmushi yace, "Ni Rauda nake so ba abinda yake tare da Rauda ba, zuciyar Rauda nake so ba gangar jikin Rauda ba. Ilimi, halayya, tarbiyya, nutsuwa, iya magana, girmama na gaba, su nake so a tare da Rauda ba k'afar ta ko hannun ta ba. Rauda a yadda nake jin ki a zuciyata ba fata nake ba ko ido da k'afa da hannu kika rasa wallahil azim ni mai iya auren ki ne, soyayyar gaskiya nake miki ba soyayya dan wani abun ba. Ina fatan ki fahimta?." Murmushi tayi mai d'auke da jin dad'in kalaman sa ko babu komai ta tabbatar da soyayyar ta ta gaskiya ce a zuciyar sa tace, "Na amince da duk abinda ka fad'a, ina kuma alfahari da hakan." shima yayi murmushi yana kallon ta yace, "A karo na farko da nake ganin murmushi a kan fuskar ki har kike min doguwar magana haka lallai addu'ar da nake ba dare ba rana Allah ya karb'a ya kuma fara biya min." Murmushi ta kuma yi ya kalli agogo yace, "Ana ta sallar i'sha zan tafi." "Ka gaida gida da mutanen gidan." "Zasu ji in sha Allah. A gaida Umma da kowa da kowa." Ta amsa da to kafin suyi sallama ta koma cikin gida. Sallah Umma ta samu tana Khalil ya d'auko mata kujerar ta ta zauna dan ita ba sallar zatayi ba, bayan Umma ta idar da sallah Inna ma na zaune ita da Rahma Umma tace, "Har ya tafi?." Kai ta d'aga alamun eh. Baba ne ya shigo da sallama suka amsa ya nemi waje ya zauna yana fad'in, "Ke Rauda Anas yace zai biya ko nawa ne ayi miki aikin k'afar ki, zuwa gobe zan nemi likitan da ya amince da aikin sa ayi komai a gama." Umma ta kalli shi tace, "Amma malam hidimar yaron nan bata yi yawa ba? Ka duna irin abubuwan da aka kawo mana fa yanzu kuma ya kuma biyan kud'in aiki...? Bafa ayi auren nan ba kar a fara zagin mu a gari." "Bafa rok'on sa mukayi ba shi yayi niya ya bayar." "Allah ya saka masa da alkhairi ya biya shi" Umma ta fad'a kawai dan babu yadda zatayi. Baba yace, "Abinda ya kamata kice daman kenan." Yana fad'a ya juya zai fita Inna tace, "motar kwadayi in ka hau zata sauke ka a tashar wulaqanci." Juyowa yayi ya kalle ta yace, "kinga munafurcin ki da bak'in cikin ki shine ya saka ga y'ar ki nan a zaune kusa dake babu wanda yake tayawa, kuma wallahi in baki kiyaye ni ba sai na bayar da ita sadaka a masallaci." Bata ce komai ba ta mik'e ta shiga d'aki Rahma ma ta bi bayan ta yaja tsaki ya fita. Umma ta kalli Rauda bayan sun bar wajan tace, "Rauda kin masa godiya yadda ya kamata kuwa?." "Nayi Umma." "To ya kike jin sa a ranki yanzu? Nidai ina miki sha'awar auren sa badan yana da abin hannu ba sai dan yana son ki, duk da abinda ya faru dake bai guje ki ba sai ma sake bibiyar ki da yake yi wannan alamu ne na masoyin gaskiya." Shiru Rauda tayi bata ce komai ba Umma tace, "kiyi tunani ki kuma yi addu'a in shine alkhairi Allah ya tabbatar, in ba alkhairi bane Allah ya watsar da maganar ya kawo miki mai alkhairi." Shiru nan ma tayi bata amsa ba ta lumshe idanun ta nan take fuskar Asad ta ziyarci fuskar ta sai ta bud'e idanun ta tana tsaki. Umma ta kalle ta ganin bata ce komai ya saka ta ja bakin ta itama tayi shiru. *☆☆☆* Asad yana barin wajan a mota gida ya koma dan ya samu kiran mai martaba, yana ajiiye mota b'angaren mahaifin sa ya nufa aka yi masa iso ya shiga ya same shi kad'ai kamar ko da yaushe a zaune a falo. Da sallama ya shiga yayi masa izinin zama ya zauna kafin yace, "Barka da dawowa, da fatan an dawo lafiya." Mai martaba yace, "lafiya lau, ya jikin naka?." "Na samu lafiya." "Amma yanayin ka bai gwada hakan ba." Shiru Asad yayi bai ce komai ba mai martaba yace, "Asad yanayin ciwon da nake ji a jikina kullum sake gaba yake yi, bana son Allah ya d'auki raina ban bada amanar talakawana a hannun nagartaccen mutum ba, dan haka zan dawo da bara bana." Asad yace, "Amma Takawa....." Mai martaba ya dakatar dashi yace, "Abinda za'ayi kenan Asad, kai kad'ai ne nayi istikhara akan haka yfi sau babu adadi tunda kaga ina ta maimaita maganar ka d'auka kaine alkhairin katagum. Har yanzu kana mafaran da ka fad'a min?." Asad yace, "Na kwana biyu banyi ba." Kai ya girgiza kafin yace, "ka cigaba da addu'a ka kuma cigaba da kula ba komai zaka yarda dashi ba, mak'iyan ka na kewanye da kai. wanda kake d'auka masoyin kanewani lokacin shine mak'iyin ka, wanda kake d'auka makiyin ka wani lokacin shine masoyin ka." Asad cikin gamsuwa yace, "in sha Allah za'a kiyaye." "Mahaifiyar ka ta sanar dani tayi maka mata za'a gaggauta maganar auren ka ana gama shagalin bikin zan sauka daga karaga na baka." Shi dai Asad bai iya cewa komai ba dan ba wannan ne a zuciyar sa ba, zuciyar sa bugawa take yi da sauri har sautin ta yana ji a kunnen sa. Mai martaba yace, "zaka iya tafiya." "Godiya nake, a tashi lafiya" ya fad'a da girmamawa ya fita mai martaba ya bishi da kallon burgewa da kuma sha'awa. Sai da akayi sallah ya shiga wajan Mama ya samu bata nan ya k'arasa ciki inda Hydar yake yana nan kwance kamar koda yaushe. Yana fitowa daga d'akin ya ganta a zaune a kan kujera tana waya yadda take maganar ya tabbatar da k'anwar ta take waya, zama yayi a gefen ta yana sauraron ta kammala wayar. Bata jima sosai tana wayar ba ta yanke ta kalle shi tace, "lafiya na ganka wani iri?" "An nemi a k'asar Dubai zanyi....." ganin yadda ta d'aure fuska sai ya kasa k'arasa maganar yayi shiru tare da sunkuyar da kansa. Fuska a d'aure tace"kalle ni." Ba musu ya kalle ta tace, "ko k'asar Dubai zasu d'auka su mallaka maka baza kayi ba Asad, zaman ka a nan shine burina ba barin ka k'asar ba. Akwai abinda ka nema ka rasa ne a nan d'in?." Kai ya girgiza alamun a'a tace, "to kar na sake jin irin wannan maganar a bakin ka, hukunci ne na yanke babu kai babu wani aiki sai na mulkin garin nan." "Toh. Allah ya wuci zuciyar ki." ya amsa a tak'aice. "Ya kuka yi da mahaifin ka?." "Babu komai." Ta d'auke kanta daga kansa kafin tace, "kaji sauk'i, yaushe zaka je wajan Jidda?." Shiru babu amsa hakan ya saka ta kalle shi kamar zaiyi kuka yace, "san da kika ce." "Gobe." "Allah ya kaimu" ya furta a sanyaye. Da hannu tayi masa alamar ya tashi ya bata waje kamar jira yake ya mik'e ya fita. B'angaren su ya tafi ya samu babu koma an k'ara masu tsaron k'ofa harda jami'an tsaro Mama ta ajjiye a wajan ya shiga d'akin sa yana mamaki a ransa yana aiyanawa tsoro bashi zai hana wani abun ya same shi ba, wanka yayi da alwala ya fito yayi sallah ya kwanta. Kasa jin dad'in kwanciyar yayi a kan gadon ya tashi ya jefa pillow a kan tiles ya kwanta yana kallon saman d'akin. _Sabida Hydar ta zama gurguwa_ zuciyar sa ta cillo masa wannan tunanin ya lumshe idanu a hankali ya bud'e, juyawa yayi ya d'ora kansa a kan hannayen sa yana kallon sama yana tuno yanayin fuskar ta da yadda take masifa akan laifin da ba nasa ba, a bayyane yace, "A ina suke had'uwa da Aliyu? Ya akayi ta san shi?, me ya had'a ta dashi haka?. Ta kira shi mazinaci ya akayi ta sani?." _ka sani ko itama ya neme ta? Kad'an daga aikin Aliyu zai iya zama dalilin yi masa rashin kunyar kenan._ zuciyar sa ta tambaye shi gaban sa yayi mugun fad'uwa ya mik'e zaune yana girgiza kansa yace, "nooo! In sha Allah hakan bai faru ba." K'irjin sa yaji yana duka a hankali ya saka hannu ya dafe b'angaren zuciyar sa ya lumshe idanun sa, "What!" Ya furta a bayyane jin abinda yake ji a zuciyar sa da gangar jikin sa mai kama da tsaninin kishi. Tsaki yayi ya koma ya kwanta ya fara k'ok'arin mantawa da tunanin amma ya kasa ko ya ya kulle idon sa sai ta fad'o masa a zuciyar sa, duk yadda yaso kawar da tunanin abin bai yu ba dak'yar bacci ya d'auke shi. Washe gari. Karyawa ake da shayi mai madara har da budori a gidan su Rauda bayan y'an makaranta sun ci nasu kowa ya tafi gidan daga Rauda sai Rahma da iyayen su ana karyawa, Umma ta kalli Rauda da take shan tea a hankali kamar an mata dole tace, "Rauda lafiya dai?." "Lafiya lau Umma" ta bata amsa tana kallon ta. "In kin gama ki daure ki lek'a gidan Alhaji Musa ki yiwa matar sa gaisuwa babban yaron ta ya rasu d'azu, har akayi jana'iza kina bacci shiyasa baki sani ba." Rauda ta zaro idanu tace, "Ishaq d'an tane ya rasu Umma?." Ta fad'a tana dafe k'irji. "Shi fa Rauda. Ki daure in kin gama kije tana son ki matar." "To Umma in sha Allah, ai ka gaida mai gaishe ka tana sona. Allah ya gafarta masa." "Amin, maza ki gama kije kafin rana ta bud'e sosai." Bata musa ba dan duk jikin ta yayi sanyi dan ta san wanda ya rasu d'in sosai suna gaisawa in sun had'u a gidan su tunda takan je ta gaishe da matar, mik'ewa tayi ta saka hijjabi mara tsayi sosai ta d'auki abin tafiyar ta ta saka takalmi ta fita daga gidan. Tafiya take a hankali babu ruwan ta da mutane da suke kallon ta dan in ta biye musu sai ta kifa sabida kallo, kasancewar da y'ar tafiya tsakanin su dan sai ka shiga layikan manyan gidaje zaka je gidan ga kuma yanayin tafiyar ta ya saka ta jima a hanya. Tana dosar layin taga manyan motoci da runfuna an kafa manya-manyan mutane a zaune ana ta fitowa da abinci kamar ba safiya ba. Daga farkon layin babu mutane sai kayi nisa zaka zo wajan mutanen, tsayawa tayi daga baya tana kallon mutanen tace, "Anya zan k'arasa kuwa? Gwara na koma anjima Khairi ta rako ni." Ganin kamar ana kallo ta sai ta b'uya bayan wata farar mota tana cigaba da yanke hukunci a zuciyar ta wata zuciyar tana taje wata tana ta bari sai anjima. "Gaskiya komawa zanyi bazan iya wuce mazan nan ni kad'ai ba" ta fad'a tana gyara zaman sandinan ta zata bar wajan. "Takawar ka lafiya d'an sarki jikan sarki, takawar ka lafiya yarima mai jiran gado, taka a sannu sikari bakai farin banza ba, inuwar kowa kake, dawisu sarkin ado, wallahi in kana wajan ba'a kowa sai kai kad'ai, d'aya kake tamkar da dubu." kirarin da ta jiyo kenan daga bayan ta kafin ta farga har an zo inda take duk sai ta rud'e ganin wanda take jin tsoro masu bulalai a hannun su. Tsawa d'aya daga cikin dogaran da suke take masa baya yayi mata yace, "gafara y'ar talakawa!" Ya fad'a da k'arfin gaske. Duk sai ta kuma gigicewa tama rasa wacce hanya zata bi zuciyar ta na rawa dan bata k'aunar ganin su ko kad'an gashi bata son tsawa. "Baza ki matsa bane?!" Aka sake fad'a mata kafin ta dawo hankalin ta. Aliyu face d'in ta yake k'arewa kallo ganin yadda ta rud'e ya kuma tabbatar itace fa ba k'arya idanun sa sukayi masa ba. "You!" Ya furta cike da mamaki yana k'are mata kallo tun daga sama har k'asa kafin ya cize bakin sa yana kallon motar sa wacce yafi so duk duniya tana jikin ta a tsaye har da dafawa. Sai a sannan ta dawo nutsuwar ta ta danne tsoron da take ciki tayi niyar barin wajan yace, "ke mahaukaciyar banza, ki kiyayi idanu na su sake tozali da k'aramar mummnar fuskar ki. Duk sanda na sake tozali da bak'ar fuskar ki wallahi sai na canja miki kamannin" ya fad'a a kausasahe yana nuna ta da yatsa. A fusace ta juyo ta zuba masa banzar harara tace, "indai har ni mahaukaciya ce tabbas kai kakana ne a hauka domin a wajan ka na gani na koya, kaine mahaukaci bani ba a zahirance ana ganin yanayin ka an san na mahaukata ne. Baka isa kayi min komai ba kuma wallahi nafi k'arfi wanda ya fika ma balle kai iskar titi" ta fad'a cikin salon rashin kunya tana hararar sa cikin tsana da b'acin rai. Kafin kace kwabo dogarin bayan ta ya zuba mata bulala a baya ta runtse idanu domin bulalar ta shige ta sosai ta hana idanun ta kuka amma tana jin zugin ta a gadon bayan ta, kallon ta kawai yake da mamaki ya rasa abinda zai mata ya wuce daga b'acin ran da ta jefa zuciyar sa a ciki hakan ya saka shi yin cak yana kallon ta. D'aga hannu yayi zai d'auke ta da mari ganin hakan ya saka ta runtse idanu yaji an rik'e hannun nasa daga baya bayyanar wanda ya rik'e hannun nasa ya sake b'ata masa rai yana kallon sa yace, "Aliyu why?." Jin shiru ba'a mare ta ba ya saka ta bud'e idanu tana kallon su, gaban ta yayi mummnar fad'uwa ganin sun zamar mata guda biyu hatta kayan jikin su iri d'aya komai nasu sak kwabo da kwabo baka banbance su. Murza idanun ta tayi ta sake kallon su a lokacin da Aliyu ya fizge hannun sa yana fad'in, "look Asad babu abinda ya shafe ka babu wanda ya isa ya hanani ganin waye uban yarinyar nan a kaf duniyar nan, babu wanda ya isa ya hana ni sakawa a sake b'alla mata k'afa." Asad ya kalle ta itama shi take kallo idanun ta a bud'e yace, "Jeki." Kasa motsawa tayi jin sanyin muryar sa har cikin kwanyar ta ta kasa koda motsi sai kifta idanu da take yi. "Kee y'ar talakawa baki ji abinda yarima yace ba ne!" Aka sake mata tsawar da ta firgita ta har sandar ta guda d'aya ta fad'i. "Kar ka sake!" Ya fad'a yana d'agawa wanda yayi tsawar tsayan sa tare da had'e fuskar sa. "Tuba nake ranka ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ka" ya fad'a yana zubewa a k'asa dan bai tab'a jin Asad yayi tsawa haka ba tunda suke. Asad ya sake kallon ta baice komai na kamar ta san me yake nufi ta duk'a zata d'auki sandar ta ya kalli dogarin sai ya zabura ya d'auka mik'a mata yana fad'in, "Wuce ki tafi baiwar Allah, Allah ya baki lafiya" ya fad'a a sanyaye yana bata hanya. Da yake babu mutane a wajan da suke masu zaman makokin suna can nesa ba hango su ake ba hakan ya saka babu wanda ya lura da abinda yake faruwa a wajan. A sanyaye take takawa jikin ta kamar an mata dukan tsiya tana tafiya tana waiwayon su taga d'aya daga cikin su yana ta masifa d'ayan kuma yama bar wajan da alama wanda yake k'okarin dukan nata ne yake fad'a, kallon gaban ta tayi ta cigaba da tafiya gaban ta na fad'uwa matuk'a zata iya rantsewa da Allah bata tab'a ganin y'an biyu masu kama da juna kamar su ba. K'arar mota taji a baya ta Aliyu ne ya wuce a guje ta sauke numfashi tana bin motar da kallo gaban ta na cigaba da fad'uwa tsoro duk ya mamaye mata zuciya. Tunani take son yi amma ta fi to ta samu waje tukunna ta zauna sai tafi yin tunanin dakyau. Tafiya take a kan hanyar babu kowa kamar yadda ta biyo tana tafe a hankali tana tunani, zafi bayan ta yake yi mata inda suka dake ta da bulala ta runtse idanun ta sosai har lokacin tana ji zafi sosai. Asad yana hangon ta yana tawowa a bayan ta a mota a hankali ya rasa me yake d'aukar sa akan yarinyar ya san tabbas tana bashi tausayi amma bayan tausayi yana jin wani abu amma ya kasa fassara meye. Yana ganin ta kamar yarinyar cikin mafarkin sa abinda ya saka bai tabbatar ba sabida har lokacin fuskar ta gabad'aya bata tab'a bayyanar masa a mafarkin nasa ba. Yana so ya k'arasa ya taimake ta ya kai ta gida amma kuma yana jin zai iya hakan gwara kawai ya k'yale ta. Waje yaga ta samu ta zauna a kan wani dutse dake kan hanyar tana sauke numfashi alamun ta gaji, tsayawa yayi a motar yana kallon ta zuciyar sa na angiza shi akan yaje ya taimaka mata abar a taimakawa ce. Taka motar yayi yazo kusa da ita ya sauke glass ya kalle ta itama ta kalle shi suka had'a idanu duk sai ta dabarbarce kamar mara gaskiya ta fara kallon gefen ta kamar wacce take neman wani abun da ta ajjiye a wajan. Wani abu take ji mai sanyi yana shiga duk ilahirin jikinta wanda ya kasance bak'o a gare ta shiyasa duk ta dabarbarce jin bak'on yanayi a tare da ita har tana sauke ajiyar zuciya ga bugun da k'irjin ta yake yi. *Akwai k'ura fan's.*⛹‍♀️⛹‍♀️🤸‍♀️🤣 *KWANTAN ƁAUNA* ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *016* Yarda take jin gaban ta yana fad'uwa shima haka yake ji bai mata magana ba kuma bai d'aga glass d'in motar sama ba balle ya bar wajan yana tsaye har lokacin ko motsi bayayi. kanta ta sunkuyar k'irjin ta na bugawa duf, duf, duf, kamar wacce tayi gudu mai nisan zango tana raba idanu a k'asa tana ji kamar ta tashi ta gudu daga wajan. Ya bud'e baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya d'aga glass d'in motar ya ja motar ya bar wajan a guje. Nannauyar ajiyar zuciya tayi har da dafe k'irji jin ya tafi ta bi motar da kallo har lokacin k'irjin ta bugawa yake yi tace, "Ni Rauda na shiga uku, na d'auko abinda yafi k'arfi na" ta fad'a tana haki har lokacin tana kallon inda motar ta bi. "Ke kuma zaman me kike a nan?" Aka fad'a daga gefen ta ta kalli inda taji maganart aga Habiba da Walida sai taji dad'i a ranta tana k'okarin mik'ewa suka zo suka kama ta ta mik'e tsaye. "Bari kawai gidan gaiswar can zan je fa har na shiga layin naga maza shine zan koma gida an jima Khairi ta rako ni." Habiba tace, "Mu ma can zamu je ai yanzu, muje to." Ba musu suka jera suna tafiya a hankali sabida yanayin tafiyar ta. Waiwaye suka ga tana yi suka juya suma suka babu abinda take kallo Walida tace, "Wai me kike nema ne?." Bata amsa ba suka cigaba da tafiya har suka shiga cikin gidan rasuwar. Ba jima suka fito bayan sun yi mata gaisuwa sunyi nisa da gidan Walida tace, "Oh yanzu in kin ga an cika a rasuwa to gidan mai kud'i ne an san za'a ci a sha, in iyayen mu suka rasu ko wani namu babu wanda zaki gani amma nan da yake akwai kud'i kalli motoci da maza dan Allah." Habiba tace, "Ai yanzu daman in kin ga gidan rasuwa ya cika to tabbas akwai wani babban mai kud'i a gidan, ki duba irin abincin dake fitowa dashi fa kamar gidan biki ga kaji ga naman rago ga kuma ruwa da lemo kamar bikin gidan gwamna. Har da gwamna fa akayi jana'iza d'azu." Walida tace, "An ce sarkin garin nan ma dashi akayi." Habiba tace, "A'a yanzu fa daga gidan sarkin nake bai zo ba baya jin dad'in amma ya turo wakilan sa Asad da Aliyu. Kuma shi ai yana da k'okari wallahi ko ba masu kud'i ba yana zuwa jana'iza, ki tuna ta gidan su Salima da baban su ya rasu shine ma ya ja sallar gawar, yanzu ne ance baya jin dad'i shiyasa ya turo wakilan sa kuma na jiki." Jin hakan sai gaban Rauda yayi mugun fad'uwa ta kalli Habiba tace, "Waye Asad a y'ay'an nasa waye kuma Aliyu?." Habiba ta kalle ta tace, "ke dai kina son labarin gidan sarkin nan. Aliyu shine babba shine baya ji bashi da mutunci ko kad'an bai d'auki talaka a bakin komai ba, shine ya mare ki ranar nan badan nayi masa wannan kirari ba wallahi sai yace a kai ki ki share turken dokunan da kike jin tsoro kuma wallahi sai kin yi in ba haka ba a zane ki" ta fad'a tana kallon Rauda ta cigaba da fad'in, "Bashi da mutunci ko kad'an ya raina talaka ganin talaka yake kamar ba mutum ba, in fa ya tawo bayi ko dogarai suka tawo wallahi sai kin koma can baya duk nisan wajan ya wuce sannan zaki wuce, ga shi kowa ya shaida a gidan shaye-shaye yake da neman mata shiyasa basa shiri da mai martaba. Naji ance a da yafi son Aliyun amma rashin jin sa ya saka ya fita a ransa tunda yayi yayi Aliyu ya shiryu yak'i kullum sake wastewa yake yi, gashi baya yafiya ko kad'an. akwai wani labari da naji y'ar sarkin Zamfara tayi masa rashin kunya ya saka aka d'auko masa ita yayi mata fyad'e na wulak'anci ya azabtar da k'arshe yarinyar rasa ranta tayi, amma da yake babar sa ba kanwar lasa bace wallahi tuni an manta da maganar." Habiba bata kula da halin da Rauda ta shiga ba tace, "Asad kuma shine Kamili mai kirki duk da baya fara'a amma kowa ya shaida a gidan nan shine ya fita zakka kamar ba jinin sarauta ba in yayi miki wani abun, bazai ga ana wulak'anta d'an adam a gaban sa ya k'yale ba, bazai ga ana cin zarafin wani a kyale ba, shiyasa ko hukunci Aliyu ya saka a yiwa wani da sun ga Asad zasu daina domin tasu tukunyar ce zatayi zafi a wajan sa. Ga taimako ko a hanya yaga tsoho zai tsallaka titi Asad yana iya parking mota ya fito ya tsallakar dashi ya bashi kud'i sannan ya koma mota yaje inda za shi, labari in yaji na gidan ku baku dashi ko kuna neman wani taimako sai ya taimaka muku wallahi, wani lokacin baza ma kusan shine yayi ba. Kuma kaf gidan nan babu mai kud'in sa hatta mai martaba bashi da kud'in da Asad yake dashI, sai dai mai martaba ya nunawa Asad kadarori amma zunzurutun kud'i Asad ne yake dashi tunda shi bada Nigeria yake aiki ba. Kullum fa sai ya bawa su Gwaggona dubu d'aya sadaka, sama da mata d'ari a gidan nan kowa sai ya samu yara da manya, in kana da buk'ata ma in Allah ya had'a ku ka nemi taimakon sa an gama shiyasa kullum yake gaba baya b'ata yin baya a rayuwar sa." "Shi bar shi da baya magana dan ya kwana uku ma bai fito daga d'aki ba abu ne mai sauk'i a gare shi tunda ba zaman k'asar yake so ba, duk inda kike tunanin miskili mara son magana da hayaniya ya wuce nan, shiyasa y'an gidan da dama kurma suke ce masa domin ance sai su zauna meeting na cikin gidan su a tashi bai ce kanzil ba, sam baya k'aunar magana shi yafi son shiru shiyasa ko gaishe ki kayi a hanya sai dai ya d'aga hannu in yaga dama yayi murmushi. Amma fa naji ance duk tsiyar Aliyu in Asad yayi fushi bai kama k'afar tasa tsiyar ba, ance duk ya fisu zafi ta Aliyu ce ta bayyana." Walida tace, "shi na ukun fa?." Habiba tace, "Hydar kenan gidan fara'a, shine kuma basa kama da y'an uwan in kika ganshi ma baza kice y'an ukun su bane, wad'ancan sune masu kama kwabo da kwabo kika ga Asad kika ga Aliyu baza ki banbance ba. A da adon gemu ne yake banbanta su na Asad bak'i ne sosai na Aliyu kuma ya shirka da ja, cikin kwanakin nan shima ya mayar da nasa bak'in kafin ki gane su zaki sha wahala. Hydar halin su d'aya da Asad kawai shi yana da wata cuta ce da in ta tashi sai ya shafe wata a kwance kamar yadda na fad'a muku ranar nan, yanzu haka ma ciwo ya tashi yana kwance ya jima ance ko motsi baya yi." "Allah sarki Allah ya bashi lafiya." "Amin. Ke Rauda lafiya kike kuwa?" Habiba ta fad'a ganin kamar ta fita a hayyacin ta. Rauda ta firgita ta kalle su hawaye ya wanke mata fuska tace, "fyad'e kika ce ya yiwa wata dan tayi masa rashin kunya fa, kuma y'ar uwar sa mai kud'i da mulki; Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Habiba na shiga uku ni yanka ni zai saka yi, bakina ya jawo min abinda yafi k'arfin dangin mu gabad'aya." Walida da mamaki tace, "Me kike nufi?." Sai kuma Raudan ta saita nutsuwar ta tace, "Wai da ranar da ya mare ni na tanka masa." Habiba tayi dariya tace, "ke me zai had'a ki da wannan? Yadda ya raina talakawa wallahi Allah kad'ai yasan mai zai miki. Banza matsoraciya shine har da kuka?" Ta fad'a tana kallon ta sukayi dariya ita da Walida. Habiba ta kuma cewa, "kuma baku san wani abu ba, a kaf gidan babu mai taka masa burki kamar Asad d'in, basa shiri fa amma kamar ba y'an uku ba sam Aliyu da Asad basa jituwa amma kuma in ya tsawatar akan abu ance Aliyun yana shayin aikatawa, dan Asad akwai slicent treatment." Walida tace, "Ke wai a ina kike jin wannan labaran?." "Ina fa kwana a gidan, kuma kin san labarin gidan sarauta baya tab'a b'uya ko me aka aikata sai ya bayyana." Basu lura da yanayin ta ba suka cigaba da tafiya har aka zo gida Rauda ta shiga gida suma suka wuce nasu gidan. Umma na zaune taga shigowar Rauda a gigice ta bita da kallo tace, "ke kuma lafiya?." Jikin ta har rawa yake tace, "babu komai Umma" tana fad'a ta shiga d'aki ta zauna gefen gadon Umma ta ajjiye sandinan ta a gefe kawai ta fashe da kuka. "Na shiga uku ni Rauda na jawowa kaina bala'i" ta fad'a a hankali gudun kar Umma taji. Bugawa k'irjin ta yake cikin tsoro da fargabar abinda zai je ya dawo hankalin ta ya mai k'arshe wajan tashi k'irjin ta har d'agawa yake sabida tashin hankali. Umma da ta d'aga labule ta shigo ta kalle ta tace, "Ki sanar dani abinda yake damun ki." Kuka take sosai bata ce komai ba Umma na tsaye tana kallon ta ganin yadda take kuka sosai sai tayi mata shiru tana kallon, sai da ta gaji da kukan sannan ta kalli Umma tace, "Tausayin kaina nake Umma lokaci guda na nakasa." Umma ta girgiza kai tace, "Wani lokacin kamar bake ba, kina mantawa da Allah yana canjawa bawa halittar sa komai tsufan sa, indai ba mutuwa kika yi ba'a gama canja miki halitta ba. Indai baza kiyi imani da k'addara ba kuka yanzu kika fara" ta fad'a tana komawa da baya ta barta. Kwanciya Rauda tayi cikin tashin hankalin da ya hana zuciyar ta sukuni, hangowa take ya saka an kamo ta itama anyi mata fyad'e kuma an kashe ta lokaci d'aya sai taji hankali ta ya kuma tashi. Tana kuka bacci ya d'auke ta bata sani ba. *☆☆☆* Tunda ya shiga falon Mama ya zauna bai ce kala ba ganin hakan sai Mama ma ta share shi ta cigaba da danna wayar ta dan duk a tunanin ta Asad ne ba Aliyu ba, shigowar Asad ya saka ta kalle shi taga fuskar sa tayi kama da ta Asad ta dawo da kallon ta ga Aliyu taga sak iri d'aya dai ta Asad d'in ce a d'aure ko wanne da alamun b'acin rai a tare dashi. Sanda Asad ya zauna lokacin ta kalle su ta ajjiye wayar a gefe tace, "Ikon Allah." Nan ma babu wanda ya tanka mata a cikin su sai suka sake rud'a ta. "Lafiyar ku kuka shigo min ko wanne fuska a d'aure? taz'aziyar da mahaifin ku ya tura ku kenan?." Nan ma shiru babu amsa ko wanne na kallon wani wajan daban sai suka fusata ta tace, "Malamai bakwa ji ina muku magana ne? Wanne irin iskanci ne wannan ina magana kunyi banza dani kamar sa'ar ku?. Ku banbance min kan ku tunda kun d'auko sabon iyayin saka kaya iri guda, banbancin ma da yake fuskar Aliyu ya shafe shi." Tab'e bakin da Aliyu yayi ya skaa ta kalle shi tace, "Kaine Asad kenan" sai ta kalli Asad taga bama ita yake kallo ba nan ta sake rud'ewa dan gabad'aya ko wanen su acting d'in Asad yake yi. Ganin ranta ya fara b'aci ya saka Asad yace, "Allahbya wuci zuciyar Mama, ya jikin Hydar?." Yana fad'ar hakan sai ta gano waye dan Asad yafi damuwa da jikin Hydar akan Aliyu daman kuma tun farko tasu tafi zuwa d'aya, ta kalli Aliyu tace, "baku tab'a rud'a ni kamar yau ba, kamar ku ta fito a zahiri sosai har ta bani tsoro tabbas Aliyu ka koma min Asad a yau." Aliyu yace, "ina neman izinin magana." Mama tayi masa alama da hannu yace, "Mama wata yarinya ce ta kira ni da mahaukaci a wajan ta'aziya amma Asad ya hana ayi mata hukunci. Ina rok'on Mamana da ta shiga tsakani na da Asad tun kafin raina ya b'aci hukuncina ya shafe shi, babu ruwan sa da duk abinda zan saka ayiwa wani a k'asana yake tunda talakan garin nan ne." Mama ta bud'e baki tace, "What? Mahaukaci! kaine mahaukacin?." Basu amsa mata ba tace, "y'ar gidan uban waye?." "Ba y'ar gidan kowa bace ba Mama, beside y'ar talakawa ce gurguwa mai yawo da sanda, sau uku kenan tana k'okarin raina min hankali amma na yau yafi na ko yaushe har ta kira ni da mahaukaci amma wannan ya hana a sake b'alla mata k'afafun ta" duk da fad'a yake amma bai fito fili ba sabida a gaban Mama yake dole ya tausasa harshe. A fusace Mama ta kalli Asad tace, "For what reason?. Mecece d'in ka da zaka hana a hukunta ta?." Shiru Asad yayi bai amsa ba ta kuma fusata tace, "meyasa kai baka san Allah ya banbanta ku da talakawa bane ba?, meyasa ka kasa gane kai da talaka sai dai taimako in kaga dama?, meyasa baka gane tazarar ku kamar tazarar sama da k'asa ce?. Ni y'ar sarki ce babana sarki ne, kakana ma sarki ne, miji na sarki. Baban ku sarki ne kakan ku sarki ne haka zalika a cikin ku akwai sarki. Ko a jinin sarautar naku daban yake, ko a y'ay'an sarautar ku daban kuke, ko a izza da k'asaitar taku daban take, meyasa kake mantawa da wannan Asad?!." "Allah ya wuci zuciyar ki, amma dukkan mu bayin Allah ne babu wanda yafi wani ko a wajan Allah. Tunda har ita yarinyar tace masa haka maybe akwai abinds ya fad'a mata ta rama." "K'arya kake Asad ko a wajan Allah akwai banbanci tsakanin talaka da mai kud'i nasan kasan da wannan. Kuma ko zane ta yayi ai matsayin da yake dashi a garin nan godiya ya kamata tayi masa ko babu komai ta samu k'imar da har ya tsaya ya dake ta." Yadda take magana da fad'a ya hana shi sake cewa komai yayi mata shiru. "Aliyu ko y'ar gidan uban wacece ina so ka saka ayi mata hukunci, ina so ka saka a nuna mata ruwa ba sa'an kwanbo bane sabida gaba, in ka k'yale ta wasu ma zasu gwada tunda sunga wata tayi tasha. Ka tauna tsakuwa ko dan aya taji tsoro" ta fad'a tana kallon sa. Cikin gamsuwa ya girgiza kai domin bayanin da tayi ya saka ya sake jin izza na mamaye masa jikin sa yace, "tabbas zata gane nida ita kamar wuta da ruwa ne baza mu tab'a zama waje d'aya ba, Mama zata san ni ba d'an sarkin Bauchi bane ni d'an sarkin katagum ne." "Good boy!" Ta fad'a tana masa jinjina. Asad yace, "Mama yarinyar nan fa ta silar....." Sai kuma ya fasa fad'a yayi shiru da bakin sa yana kallon gefe guda. Tsaki taja tace, "baka gado ni ba sam Asad, bakayi kama da jinin sarauta ba. Har wata yarinya zata kira d'an uwan ka mahaukaci a gaban ka ka hana ayi mata hukunci, ita d'in banza da wofi, ko baban tane ba sai a hukunta shi ba balle ita." Aliyu ya tashi ya fita zuciyar sa cike da tunanin hukuncin da ya dace da Rauda. Shima Asad d'in tashi yayi ya fita dan ya lashi takobin babu wanda ya isa yayi mata wani abun indai yana raye domin kuwa ta dalilin Hydar ta nakasa, ko babu wannan dalilin a yadda ya samu labarin ta tana da hankali baza ta saurari Aliyu ba sai dai in shine ya fara zagin ta shine ta rama bai ga dalilin da zai saka a dake ta a kuma hana ta kuka ba. *☆☆☆* Yadda suka nutsu suka bada dukkan hankalin su ga wayar hannun waziri zai tabbatar maka da abu nai mahimmaci ake sanar dasu a cikin wayar, motsin kirki basa yi hankalin su gabad'aya yana kan wayar sunyi shiru suna sauraron abinda ake fad'a daga cikin wayar. "Kamar yadda na fad'a muku mai martaba ya dawo da batun bawa Asad sarauta jiya sun tattauna dashi akan maganar, wanne tunani kuka yi game da hakan?." Suka kalli juna a tare kafin waziri yace, "bamu san hakan ta kasance ba dukkan mu mun saki jiki akan maganar ta jinkirta ne." "To bata jinkirta ba ku fad'a min shirin ku naji." Hajiya tace, "bamu da wani shiri sai abinda kika shirya mana." Master planer tayi murmushi tace, "Ina da shawara sai dai shawarar tawa tana da wahalar faruwa amma zata faru in kuka jajirce." Waziri yace, "muna sauraron ki." "Ku jawo Aliyu ya dawo cikin ku." A tare suka wara idanu Hajiya tace, "Wanne Aliyun kike nufi?." "Aliyu nawa ne daku a gidan?." Waziri yace, "to maganar ce na jita wani iri master kamar da kamar wuya, Aliyu fa jinin Asad ne ta yaya zai had'a kai damu." Y'ar dariya tayi tace, "Aliyu ya fi ku son ganin babu Asad a cikin gidan nan, domin Asad shine kawai wanda yake ganin zai hana shi mulkar garin nan. In kuka samu ya dawo cikin ku ya fiku yarinta yana da matuk'ar wayo idanun sa kuma a bud'e yake tafiya zata yu yadda ake so." Hajiya tace, "Amma in muka nemi Aliyu kamar tonuwar asirin mu ne, zai iya bijire mana yak'i amincewa bayan ya riga yaji sirrin mu." Waziri yace, "abinda na gani kenan, inda dama a bar maganar Aliyun nan." Master planer tace, "shigowar Aliyu shine nasarar mu." "Ta yaya zai zama nasarar mu bayan in ya shigo cikin mu mun kashe maciji ne basu sare masa kai ba?. Kar ki manta in ya shigo cikin mu kenan mun zubar da makanan yak'in mu na neman sarauta mun barwa jinin Rabi'atu." "Hhhh! wani lokacin bakwa saurin fahimtar inda na dosa. wato shi kan sa Aliyun amfani zamuyi dashi in mun gama burin mu ya cika mu ajjiye shi a gefe. Abinda nake nufi a nan zamu saka a b'atar da Asad amma za'a bayyanawa mutane cewa Aliyu aka batar ba Asad ba. Aliyu zai koma acting d'in Asad gabad'aya kamar yadda yake yi yanzu, zai dakatar da duk wani abu da yake yi ya dawo Asad a cikin gidan nan. Ko mahaifiyar sa bazata san bada Asad take zaune ba zai koma Asad sak babu wanda zai ce Aliyu ne. Da zarar hakan ta kasance kunga mai martaba zai bawa Aliyu mulki ba tare da yasan shi bane, mu kuma indai aka bawa Aliyun mulkin nan kwace goriba a hannun kuturu abu ne mai sauk'i a wajan mu. Wannan shine amfanin da Aliyu zai mana shiyasa nace ku jawo shi cikin ku." Waziri ya numfasa yace, "ta yaya Aliyu zai shigo cikin mu? Shine babban tashin hankali shigowar sa cikin mu, sannan in ya shigo an gama komai an bashi mulki ta yaya Aliyu zai amince ya bar mulkin cikin sauk'i bayan kema kin shaida wayon sa?." "Waziri kana da dawo da bara bana, nice nace zanyi ku gwada abinda nace muku ku gani in ban yi nawa ba." Hajiya tace, "Abun ne kamar da wahala master, Aliyu fa." Ta ja k'aramin tsaki tace, "nice nace kuyi in kuka tabbatar ya shigo tsagin mu an b'atar da Asad komai zai zo mana da sauk'i, in kuna ganin baza ku iya ba a nemo wata mafitar." Waziri yace, "A'a basai an kai ga haka ba zan san yadda zanyi." "Better" abinda tace kenan ta yanke wayar. Hajiya ta kalle shi tace, "da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, tabbas shawarar tayi amma in ka duba ta yaya zamu shigo da Aliyu cikin mu sai kaga gabad'aya maganar bata da ma'ana." Kai yake girgizawa yana nemo mafita a kwakwalwar sa kafin yace, "tunani ya kamata muyi game da lamarin, a ganin ki mu gwada neman Aliyu ko mu bar zancen?." Hab'a ta rik'e cikin tunani kafin ta kalle shi tace, "a rashin tayi ake barin arwa, haka zakila a yawan tayin ake shan duka. Wanne daga ciki zamu d'auka?." "Mu taya!" Waziri ya bata amsa yana kallon. "Allah ya bamu sa'a" ta furta tana kallon sa shima yana kallon ta. _ya kuke gani anya Aliyu zai karb'i tayin su?. Ina batun Rauda wanne hukunci zai mata?._🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️ *KWANTAN ƁAUNA* ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *017.* Rauda ta jima tana bacci sanin ba sallah zatayi ba ya saka Umma bata tashe ta ba sai bayan azahar ta farka ta firgice, ganin ta a d'akin Umma ya saka ta raba idanu tana sauke ajiyar zuciya ganin mafarkin da tayi ba gaske bane ba. Mafarki tayi sun had'u da Aliyu ya kai ta wani waje tana ta bashi hak'uri yak'i ya hak'ura bai kai ga yi mata komai ba ta farka shiyasa hankalin ta gabad'aya yake a tashe. Duk ta jike da gumi tana shafe fuskar ta Khairi ta shigo d'akin tana fad'in, "Umma ta tashi." Kallon Khairi tayi kafin tace, "k'arfe nawa?." Khairi tace, "K'arfe biyu." K'aramin tsaki ta ja Umma ta lek'o d'akin tace, "To Rauda zan fita su Khairi zasu je makaranta ki kula da gidan." "Ina zaki je Umma?." "Zan koma yiwa matar nan gaisuwa, daga nan kuma zanje gidan Baba Malam mu gaisa." "A dawo lafiya." Sakin labulen Umma tayi ta fita daga gida. Rauda ta kalli Khairi da take shiryawa tace, "Khairi in zaki tafi makaranta ki biya gidan su Habiba kice dan Allah nace tazo ina neman ta Umma bata nan." Khairi ta amsa da to ta gama shiryawa ta fita. Gidan shiru hakan ya bata tabbacin d'akin su Rahma ma basa nan kenan ta fito daga d'akin ta zauna a kan kujerar ta a tsakar gida inda babu rana. Yunwa take ji sosai amma baza ta iya cin abinci ba sai tayi maganin matsalar da ta d'aukowa kanta sannan zata samu abinci ya iya zama a cikinta, tana nan zaune taji sallamar Habiba ita da Walida sun shigo a tare. Amsawa tayi suka k'araso suka zauna a kan tabarma Habiba tace, "Naga fuskar ki a kumbure." "Bacci nayi" ta bata amsa tana yatsine fuska. Habiba tace, "y'ar hutu. Lafiya kike nema na?." Rauda tace, "Yan uwa ina cikin matsala ne." A tare suka had'a baki wajan fad'in, "Wacce irin matsala kuma?." Shiru Rauda tayi tana kallon su kafin ta kwashe duk abinda ya faru tayi ta fad'a musu kafin ta d'ora da fad'in, "tunda kika ce min har fyad'e ya yiwa y'ar sarkin Zamfara na tsorata ku taimaka min dan Allah." Girgiza kai suke yi cikin mamaki da tsoro Habiba tace, "Mahaukaci kika ce masa Rauda? Tabd'ijam na rantse da Allah bai k'yale ki ba kina nan a zuciyar sa sai ya d'auki mataki a kan ki, ya yiwa yar masu kud'i da mulki balle irin mu?." Sai ta fashe da kuka tana fad'in, "Dan girman Allah ku taimaka min ku nema min mafita wallahi tsoron sa nake ji, ni ko zuwa ne zanyi na bashi hak'uri indai zai yafe min." Habiba tayi shiru tana tunanin m a fita kafintace, "mafita d'aya ce kawai abinda za'ayi zuwa zamuyi mu samu Asad ki fad'a masa duk abinda ya faru tunda a gaban sa akayi, ki sanar dashi tsoro kike ji kuma kinyi dana sanin yi masa rashin kunya dan Allah ya bashi hak'uri kar yayi maki komai, in anyi sa'a zai iya k'yalewa in Asad d'in ya saka baki." Walida tace, "To kince sai ya kwana uku bai fito ba a ina zamu gan shi?." Habiba tace, "yana sadaka ai da kansa ranar juma'a bayan masallaci indai yana k'asar nan, ranar zamu je masa in ba ranar ba wallahi bamu da ikon ganin sa." "Juma'a yayi nisa Habiba, kafin juma'ar zai iya sakawa ayi min wani abun, dan Allah a canja shawara. Ni tsoron abinda zai min nake yi bawai tsoron sa ba, ga Ummana bana so ta shiga wani yanayi mara dad'i a kaina shiyasa hankalina ya tashi sosai" Rauda ta fad'a cikin tashin hankali tana hawaye tana kallon su. Cikin kwantar da murya Habiba tace, "Na rantse da Allah Rauda da ina da damar ganin Asad a yau zamu je wajan sa amma ban isa ba, Fulani ta saka an k'arawa b'angaren su tsaro sabida abinda ya faru dashi kwanaki kusa da wajan ma baki isa kaje ba sai da dalili. ki bari sai ranar jama'ar in Allah ya nuna mana sai muje ki same shi na tabbatar bazai bari a cutar dake ba, Kafin ranar ki ta addu'a Allah zai kawo miki sauk'i." "Habiba in ya yi min wani abun na shiga uku dan Allah ku taimake ni. Ba kaina nake ji ba Ummana nake ji, abinda Baba zai yiwa Umma shi nake jin tsoro" ta fad'a cikin kuka sosai. Tausayi ta basu suka dinga rarrashin ta Habiba tace, "Allah yana tare dake wallahi bai isa ya cutar dake ba. Amma zan je yanzu in naga yana nan zan roƙe shi zance masa zan kawo ki ki masa bayanin komai in yaso sai naje na dawo muje wajan sa dake." Rauda tace, "tashi kije Habiba." Habiba ta mik'e tsaye tace, "Walida zo muje, duk yadda ake ciki zan dawo" ta fad'a tana fita daga gidan suka barta tana sharb'ar kuka. Haka ta zauna zaman jiran su har la'asar basu dawo ba Umma ma bata dawo ba sai biyar sannan Khairi ta shigo ita da Khalil da Sammani, bayan shigowar su ba jima Habiba ta shigo tunda taga fuskar ta tana ba'a yi nasara ba. Kusa da ita ta zauna ta kalle ta tace, "Wallahi duk yadda naso ganin Asad abin ya gagara, amma kiyi hak'uri gobe zan same shi in Allah ya yarda." Idanun Rauda yayi rau-rau zatayi kuka Habiba tace, "kiyi hak'uri dan Allah, haba komai zai tafi daidai in Allah ya amince ki yadda dani wallahi zan masa magana. Kamar ba ke ba kinbi kin rud'e keda na sanki da dakakkiyar zuciya wacce babu tsoro a cikin ta." Kai ta girgiza tace, "Habiba wannan fad'an yafi k'arfina, bawai ina jin tsoron saba bane ina jin tsoron abinda zaiyi min ne Habiba." "In sha Allah babu abinda zai miki." "Na gode Habiba." Habiba ta mik'e tace, "Kar ki damu zan neme shi gobe in Allah ya amince." "Na gode" ta furta a hankali daga haka sukayi sallama ta tafi. Fitar ta ba jimawa Umma ta dawo su ma su Rahma suka dawo, bayan anyi sallar magriba Baba ya dawo bayan yaci abinci ya shigo tsakar gidan ya zauna ya kalli Rauda yace, "Rauda." Tace, "Na'am Baba." "D'azu Anas ya kira ni ya sanar dani tafiya ta taso masa ta gaggawa bai samu yayi magana da likitan naki ba, amma ba jimawa zaiyi ba da zarar ya dawo za'ayi komai a gama. Ya aiko da waya yace dan Allah a baki yana so ku dinga magana na kuma karb'a, gata" ya fad'a yana mik'a mata ledar Khairi da take kusa dashi ta karb'a ta mik'a mata. Umma ta kalli Baba ta kasa jure abinda take ranta tace, "Malam wai ka bawa yaron nan auren Rauda ne?." Ya kama k'ugu yace, "Me yasa kika tambaya?." "Sabida naga kana karb'ar hannun sa da yawa, tsakani da Allah bai kamata ba a dinga karb'ar kud'in yaron nan ko abin hannun sa ba tunda ba'a yi auren su ba, ko maganar aure fa bata shiga tsakanin su ba." Baba yace, "to fad'a min ke kika haife ta, dad'in ta nima dani aka haife ta ba ke kad'ai kika kawo ta duniya ba. Na riga na bashi auren ta koda bana raye shi zata aura ba wani ba, ko ban isa bane ba?" Ya fad'a yana kallon Umma. Umma bata kuma cewa komai ba ta kawar da kai yaja tsaki ya fita. Rauda tunda aka bata wayar ta rik'e a hannun ta ko bud'ewa ta kasa yi sabida ba wannan ne a zuciyar ta ba abinda yake zuciyar ta daban wannan daban, sai da suka shiga d'aki zasu kwanta sannan Khairi ta bud'e wayar a kwalin ta ta ciro ta kunna har da sim card a kai, Khairi ta kalle ta taga ba ita take kallo ba tace, "Anty Rauda keda kike da burin rik'e waya yau Allah ya cika miki burin ki amma ban ga kina farin ciki ba." Umma tace, "ta yaya zatayi farin ciki ana zubar mata k'ima wajan saurayi ana karb'ar komai daga hannun sa?, ai farin ciki ba nata ba." Rauda ta kalli wayar hannun Khairi ta ganta mai kyau babba ga bayan ta nan da logo d'in Samsung. D'auke kai tayi ta kwanta kawai bata ce komai ba domin ita ba wannan ne yake damun ta ba. *☆☆☆* Asad kuwa da ya bar gida gidan su Jidda ya tafi ya riga ya cewa Mama zashi baya son sab'a alqawari a rayuwar sa musmman ma maganar Mama. Kasancewar gidan sa ba bak'on sa bane Mama tana aiko shi wani lokacin har cikin gidan ya ajjiye motar. Fita yayi daga motar ya shiga cikin gidan da sallama ya samu falon babu koma sai k'anwar Jidda mai suna Eman. Ganin sa ta saka tayi murmushi tace, "Yaya Aliyu ina wuni." "Lafiya, Ina Mum?." "Tana sama bara na fad'a mata" ta fad'a tana hawa sama. Bai zauna ba ya tsaya a tsaye kafin ta lek'o tace, "Tace ka hayo." Ba musu ya k'arasa stairs d'in ya hau saman a nutse ba tare da wata fargaba ba. A babban falo ya tarar dasu ita da Jidda a zaune ganin sa ya saka Jidda mik'ewa ta k'araso gare shi da niyar hugging d'in sa. Baya yayi yana kallon ta ta k'asan ido, sanye take da riga da wando yan kanti kanta babu d'ankwali gashin ta ya sauka har kafad'a tayi kyau kamar baturiya, ganin kallon da yayi mata sai gaban ta ya fad'i ta kauce ya k'arasa ya zauna kana yace, "Mum ina wuni." "Lafiya lau Aliyu, Ya Maman?." "Lafiya lau" ya furta a tak'aice bai kuma cewa komai ba. Jin shiru ya saka Mum ta kalle shi dan tasan Aliyu baya wannan dabi'ar in yazo gidan da tuni ya rungume Jidda sun koma gefe suna hirar su tace, "Aliyu kayi shiru yau kamar ba kai ba." "Asad!" Ya furta a tak'aice bai kalli Mum d'in ba. Jin abinda yace ya saka Mum da Jidda suka kalli Juna Mum ta d'aga mata gira suna murmushi Mum tace, "Au daman Asad ne ka barni ina ta kiran ka da Aliyu?." Baice komai ba itama bata damu yace ba dan tasan bazai ce ba ta kalli jidda tace, "Jeki ki kawo masa abin tab'awa mana kin tsaya kina kallon sa." Da sauri ta juya ta sauka Mum tayi murmushi tana kallon sa tace, "nidai nayi mamaki nasan Aliyu baya irin wannan bakuntar a gidan nan." In table d'in dake gaban sa ya amsa to tabbas shima ya bata amsa sai ma kawar da kansa gefe da yayi yana jin sa a takure, bata damu ba dan tasna halin sa daman a lokacin Rauda ta dawo da tray a hannun ta ta ajjiye masa ta zauna a gefen sa Mum ta mik'e ta basu waje. Suna zaune shiru babu mai magana zuciyar sa ta tafi tunanin kenan daman ta saba hugging d'in Aliyu duk wanda yazo tunda gashi da ta ganshi ta d'auka shine har ta nufo shi da niyar hugging d'in sa. Cize baki yayi Allah ya sani baya son yaga wani ya rabi abinda aka ce nasa ne indai har da gaske nasa d'in ne baya so yaga wani abun ya rabe shi, baya son hakan sam. "My Asad" ta furta a hankali tana kallon sa. Bai kalle ta ba ya sauke ajiyar zuciya yace, "Zaki iya d'aukar wayar ki?" Ya fad'a da harshen laranci. Kallon sa tayi alamun bata gane ba tace, "Bana jin Arabic." Yamutsa fuska yayi yace, "Take your phone." "Okay." ta furta tana d'aukar wayar ta. Sai kuma ya tsaya kallon wayar tasa tunawa da yayi bashi ma fa da number ta balle suyi chart ya fad'a mata abinda ya kawo shi. D'an k'aramin tsaki yaja ya ajjiye wayar kamar zai magana sai kuma ya fasa. Sun d'an jima a haka kafin ya mik'e ta mik'e itama tana kallon sa yace, "my regard to Mum" yana furtawa ya sauka daga saman gabad'aya bai kuma kallon ta ba balle ta saka ran magana ko wani abun. K'ugu ta kama tana kallon sa tana fad'in, "Lallai ma wannan gayen ya raina min wayo da hankali, shikenan har anzo zancen an tafi?, wacce irin izza da k'asaita yake ji da ita har haka?." Mum da taga saukar sa take jin abinda take cewa tace, "D'an sarki ne fa, jikin sarki ne, shine yake niyar zama sarki. Wacce izza kike so ki gani a tare dashi in ba wannan ba?." Ta kalli Mum tace, "Amma Mum tunda fa ya zauna bai ce min komai ba haka za'a yi auren?." Dariya Mum tayi tace, "Sai aka ce miki haka zamu bar shi?, zamu sark'afo wuyan sa ta yadda ko uwar sa Rabi'atu sai dai ta sallama miki shi. Duk wannan kurmancin nasan zai shigo hannu ne sai ya zamar miki kamar rakumi da akala wallahi, barni dashi tunda har ya fara zuwa gidan nan da niyar zuwa wajan ki ai zance ya k'are duk da dai nasan itace ta turo shi." Jidda tace, "Amma Mum ya raina min wayo wallahi." Mum ta dafa ta tace, "k'yale ni dashi Jidda barshi ya shigo hannu tukunna, da zarar ya shigo hannu to wannan kuma lokacin mu ne." Jidda ta tab'e baki ta shiga d'akin ta duk ranta a jagule. Shi kam Asad ya kasa fassara yanayin da yake jin zuciyar sa haka ya tuk'a motar zuwa gida ransa duk ya b'aci sam baya son auren Jidda amma babu yadda zai iya Mama tace dole sai ya aure ta. Babban abinda yafi b'ata masa rai game da ita ya lura tana da kusanci da maza sosai wayewar ta tayi mata yawa shi kuma Allah ya sani irin matan nan basa cikin tsarin sa ko kusa. Ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga d'akin sa ya zauna ya kunna TV yana kallo. K'aramin tsaki yaja ya kashe TV ya hard'e hannayen sa waje guda, yana son barin Nigeria ko umra ce yaje ya dawo amma zuciyar sa tak'i k'arfafa masa guiwa a kan hakan, ya rasa abinda yake damun zuciyar sa bata tuna masa komai sai yarinyar mafarkin sa da kuma yarinyar da Hydar ya buge. Tsaki ya kuma yi ya jingina da kujera zuciyar sa nayi masa zillo akan abinda bai kai ya kawo ba yake jin d'aci da suka a cikin ta. Mik'ewa tsaye yayi ya kashe hasken d'akin gabad'aya sannan ya shiga band'aki. Washe gari. Tunda Rauda ta tashi take jin bata san zaman gidan gabad'aya sabida gani take kamar za'a zo a d'auke ta a kaiwa Aliyu ita, ko kuma a yiwa yan gidan su wani abun. zaman gidan yak'i mata dad'i komai nata sanyaye take yin sa har magana bata iyawa sosai. Umma na lura da ita bata tanka mata ba itama kuma bata ce ga abinda yake damun ta ba. K'arar waya taji a kusa da ita abin ka da ba'a saba ba sai ta manta an bata waya sai da ta katse aka kuma kira sannan ta kalli gefen ta taga ANAS a rubuce a kan screen d'in wayar. Numfashi ta sauke ta jawo wayar tana kallo tana tunanin ta yadda zata d'auka dan bata iya ba, garin ta d'auka ta katse kiran aka kuma kira bata san ya akayi ba taga seconds sun fara tafiya alamun ta d'auka. A kunne ta saka wayar bata ce komai ba daga can b'angaren yace, "Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya kyakykyawar matata." Murmushi tayi kad'an wanda iyakacin sa kan fuskar ta tace, "Amin, kaima amincin Allah ya tabbata a gare ka." Y'ar dariya yayi yace, "Ni mijin ki?." "Uhum" ta furta kawai bata ce komai ba. Jin hakan sai yace, "da fatan kin tashi lafiya." "Lafiya lau, ya aiki?." "Alhamdulillah, ya jikin ki?." "Da sauk'i" ta bashi amsa a tak'aice. "Allah ya k'ara sauk'i." Ta amsa da amin kafin yace, "Ina Umma, ina fatan lafiya take?." "Lafiya lau kowa yake." "To ma sha Allah, haka nake so naji." Shiru ne ya biyo baya kafin yace, "Kiyi hak'uri Rauda wallahi aiki ne ya taso min da gaggawa wanda dole ya saka ni tafiya Abia ban shirya ba, amma in sha Allah nan kusa zan dawo zan nemi wani likitan ayi aikin nan a gama dan wanda na sani ya sanar dani baya k'asar nan." "Babu komai, Allah ya taiamaka, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya biya buk'ata." ta bashi amsa a tare. "Amin. Amma k'afar bata miki ciwo ko?." "Bata yi" ta fad'a a hankali. "Naji dad'in hakan." Shiru ya sake ratsa tsakanin su kafin yace, "bara na barki ki huta anjima zan kira ki." Da to kawai ta amsa dan daman ta gaji ba wannan ne a gaban ta. Umma ta shigo d'akin ta kalle ta tace, "Da Anas d'in kuke waya?." Kai ta d'aga alamun eh kafin tace, "Umma ni gidan Yaya Ummi zanje yau zaman gidan bana jin dad'in sa, ko naje gidan Yaya Shamsiyya." "Sai kin dawo ai" Umma tana fad'a ta fita ta k'yale ta. Sai azhar ta fito daga gidan ta nufi titi da nufin shiga mota ta tafi gidan Yaya Shamsiyya. maza ne guda biyu a bayan ta suna ganin ta d'aya daga ciki ya d'auko waya daga aljihun sa ya danna kira ya kara a kunne, ana d'auka yace, "Allah ya ja zamanin yarima mai jiran gado, yanzu muka ganta ta fito daga gidan su." Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin yace, "To ranka ya dad'e, a huta lafiya" yana fad'a ya yanke kiran suka cigaba da bin ta. Rauda kuwa bata san ana binta ba tafiyar take har taje titi ta hau mota zuwa gidan Yaya Shamsiyya. Da nisa gidan sun jima suna tafiya kafin su zo unguwar babu jama'a sabuwa ce ba'a cika ba sosai. Tana sauka ta biya mai keken kud'i ta shiga layin gidan. Da sallama ta shiga gidan Yaya Shamsiyya na aikin ta amsa tare da juyowa ganin Rauda ce ya saka ta sauri tashi ta k'araso ta rik'o ta tana fad'in, "Rauda me ya fito dake da rana ke ba lafiya ba?." Sai da suka k'arasa ta zauna akan benci ta kalli Yaya Shamsiyya tace, "Ina wuni." "Lafiya lau, ya jikin naki?." "Da sauk'i Yaya, ina su Amir?." "Sun je gidan kakar su anjima zasu dawo, me ya fito dake ana rana haka Rauda?." "Na gaji da zaman gidan ne kawai Yaya." "Da gajiya kam gaskiya, sannu Allah ya k'ara lafiya." Ta amsa da amin suka fara hira har akayi la'asar tayi musu wainar fulawa suka ci Rauda bata fito ba sai biyar da wani abun. Har bakin titi Yaya Shamsiyya ta raka ta sai da taga ta shiga mota sannan ta juya ta koma gida. Napep d'in da Rauda ta shiga suna cikin tafiya suka ga an sha gaban su da mota k'atuwa bak'a mai tsaho, gaban Rauda ya fad'i ganin manyan zagage sun fito daga motar sun k'araso inda suke tsaye. "Kee fito!" D'aya daga cikin su ya fad'a yana kallon ta. Cikin k'arfin hali irin nata tace, "Akan wanne dalilin zan fito?." Mai napep din yace, "malamai lafiya muna tafiya zaku tsaya a gaban mu?." Bulala d'aya daga cikin su ya d'auko yace, "kana kuma magana sai ta sha jinin jikin ka. Zaki fito sai mun d'auko ki?." Ganin mai napep d'in ya tsorata yayi shiru dan ganin bulalar ma abin tsoro ce ya saka ta dogaro sandar ta k'asa ta sauko dan har lokacin bata daina jin zafin bulalar jiya ba. Sai da ta fito da sandar ta d'aya ya kalli d'aya. yace, "Zata b'ata mana lokaci fa" yana fad'a masa haka kawai ya sunkuya ya d'auki Rauda cak ya k'arasa motar ya saka ta shi kuma dayan ya kwashi sandinan ta ya k'arasa da sauri ya shiga motar suka ja a guje. Mai napep a kan idanun sa akayi komai ya koma da baya dan yaje ya sanar da wacce ta rako ta amma bai san gidan ba tunda a kan titin kawai ya gansu dole ya hak'ura ya kama gaban sa amma zuciyar sa babu dad'i ko kad'an. Gudu suke sosai da Rauda a mota sai ihu take tana kuka amma babu mai jinta tunda gilasan a kulle suke gasu bak'ak'e na waje baya ganin ka sai dai kai ka ganshi. sun yi nisa sosai sannan suka tsaya a kan titin da babu kowa sai motoci suma sai ayi mintina goma wata bata wuce ba. Tsayawar su babu wahala suka fito daga motar aka bud'e ta suka jawo ta suka fito da ita ta fad'i a k'asa. Kallon wajan take babu kowa kamar ma daji ne domin shiru ga duhun magriba hakan ya saka hankalin ta ya sake tashi ta sake rud'ewa lokaci d'aya. "Dan Allah kuyi hak'uri ban san laifin da nayi muku ba amma ku yafe ni dan Allah ku barni na tafi" ta fad'a cikin kuka sosai jikin ta har rawa yake sabida tsoro. Waya taji kusa da kunnen ta ana fad'in, "ke jinin talakawa, ni kika kalla kika kira da mahaukaci ko? Zan nuna miki dabi'un hauka yanzun nan, ko nan gaba aka sake cewa ki fad'awa wani irin abinda kika ce dani bazan ki kuma. Kuna jina?." Da sauri suka amsa da, "muna ji ran ka ya dad'e." "Ku yi duk abinda kuke so da ita in kun gama ki sakar mata Bobby ku k'yale ta a wajan, in kuka yi akasin hakan taku tukunyar ce zatayi zafi" yana fad'a ya yanke wayar suka kalli juna kafin su dawo da kallon su ga Rauda da take kuka tunda taji komai. D'aya ya kalli d'aya sannan yace, "Sako Bobby ya fara yaga naman ta kafin muyi namu." Ba musu suka k'arasa kusa da bak'ar motar su suka bud'e, Katon bak'in k'are ya fito daga boot d'in motar yana zaro harshe jikin sa har rawa yake sabida k'oshi da zallar mugunta a tare dashi. "Bobby ga nama can" d'aya daga cikin su ya fad'a yana nuna masa Rauda da yatsa yana dariya amma a zuciyar aa tausayin ta yake ji. Karen sai da yayi wata girgiza gashin jikin sa ya mik'e sannan ya fara nufo ta a hankali yana sake zaro harshen sa, idanun sa ma da jikin sa abin tsoro ne shiyasa tunda ya tunkaro ta ta runtse idanun ta tana salati dan ta tabbatar k'arshen tane yazo babu abinda zai hana Karen bai kashe ta ba. Razananniyar k'arar da tayi shine ya saka su kallon inda take da gaggawa. *KWANTAN ƁAUNA* ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *018.* Cizo ya kawo mata karen shine ya saka ta yin k'ara ta kulle idanun ta tana jiran taji sukar hakoran sa a a naman ta amma sai taji shiru, ta bud'e idanun ta a hankali taga karen baya gaban ta kamar d'azu ta juya gefen ta ta ganshi a tsaye ya juyo yana kallon ta kusa da wanda bata tantance waye ba. A hankali yake takowa yazo kusa da ita suka had'a ido sai jikin ta ya cigaba da tsuma ya had'e hannayen ta waje guda tana kuka amma ta kasa magana. D'auke kai yayi daga kanta ya kalli wad'anda suka sato ta sai suka zube a k'asa cikin girmamawa hannun su na jinjina d'aya yace, "Tuba muke ranka ya dad'e, zamu aikata abinda ka umarce mu yanzu, ka yafe mana zamu yi." "Aliyu ya saka ku kawo ta nan?" Ya fad'a a tausashe cikin muryar sa mara hayaniya wacce bata fita sosai yana kallon su. Sai a sannan suka gane bafa Aliyu ne a gaban su ba babar giwa ce da kanta sai jikin su ya k'ara kaimi wajan tsuma d'aya yace, "Kayi mana aikin gafara ranka ya dad'e. Yarima Aliyu ne ya umarce mu da mu kawo ta nan mu sakar mata Bobby ya cize ta sannan muyi abinda muke so da ita. Mun tuba wallahi baza mu sake aikata hakan ba." Kai Asad yake girgizawa kaf yasan plan d'in nasu sune da Aliyun basu san ya sani bane amma tunda yasa a fara tracking d'inta yasan da haka. Kallon da yayi musu ya saka jiki su rawa suka fara fad'in, "Kiyi hak'uri yarinya muma ba san ran mu bane ba wallahi saka mu akayi babu yadda zamu yi, kiyi hak'uri ki yafe mu." Kanzil Rauda bata ce ba sai kuka da take mai tsuma zuciya ya sake kallon su duk sai suka sake diriricewa dan basu fahimcin kallon na meye ba. D'aya ne ya mik'e da sauri ya kawo mata sandinan ta guda biyu yace, "kiyi hak'uri." Da hannu yayi musu alamun da su wuce su tafi a da sauri suka hau mota suka ja da gudu. Dawo da kallon sa yayi kanta yadda jikin ta yake tsuma tana kuka hakan ya tabbatar masa da ba k'aramin tsoro take ji ba sai ta sake bashi tausayi yana so yayi mata magana amma bai san me zaice ba. Yana tsaye tana kuka sai da ta gaji dan kanta sannan ta fara k'ok'arin tashi tsaye, bata iya tsayuwa da k'afafun ta hakan ya saka tashi yake gagarar ta ganin sai juyi take kamar wancan lokacin ya saka shi mik'ar da ita tsaye ya bata sandar ta rik'e sai kuma ta dafe kai da hannayen ta guda biyu jin yadda yake sarawa. Bata daina kuka bai kuma ce komai ya juya wajan motar sa ya shiga karen shiga mazaunin baya ya dawo da motar daidai kusa da ita amma har lokacin bai ce k'ala ba. Wajan take kallo babu alamun abin hawa in tak'i shiga motar ta cuci kanta dan bata san a inda take ba balle tabi hanyar da zata sami mota, tana so ta shiga amma rashin yi mata magana da baiyi ba ya saka take shakka kar ta shiga ya wulaqanta ta. Sauke glass d'in gefen ta yayi da hannu yayi mata alama da ta shiga a sanyaye ta ja handle d'in motar ya bud'e, so take ta fara saka sanda guda d'aya sannan ta shiga sai ta shigo da d'ayar amma ta kasa ta rasa yadda zatayi. Babu tsammani taga ya fito daga motar ya dawo inda take ya karb'o guda d'aya ya saka a ciki ta saka k'afar ta mai lafiyar ta shiga cikin motar, saka mata d'aya sandar yayi kana ya kulle k'ofar ya zaga ya shiga. Ganin ta yayi duk a tsorace tana kallon baya ya juya yaga Bobby ya san shi take jin tsoro bai ce komai ba yaja motar. kuka take cigaba da yi tana goge idanun ta har lokacin jikin ta bai daina rawa ba shi kuma bai ce mata ci kan ki ba tuk'i yi a nutse. Kukan ya dame shi har tsakiyar kansa yake jin kuka amma bai san me zaice mata ba shiyasa yayi shiru ya jure abinda yake ji ya cigaba da tafiya. Ba tare da tayi zato ba taji sun tsaya tana d'ago kai ta gan su a k'ofar gidan su d'an hasken kwan solar da ya haske wajan gidan nasu duk da babu wani haske sosai amma dai yafi babu ya haska wajan, kallon sa tayi ta kalli gidan nasu ta tabbatar fa nan ne mamaki da tsoro suka yi mata yawa tunanin ta a ina ya san gidan su?. "Kina da Yaya?." A sama taji maganar tasa ta juyo ta kalle shi sai taga kamar ba shine yayi maganar ba dan bama ita yake kallo ba. Idanu ta goge ta girgiza kai alamun a'a kafin tace, "Bani dashi." "Mahaifi?" Ya sake fad'a bai kalle ta ba har lokacin. "Ina dashi" ta bashi amsa muryar ta na rawa sosai. Sai da ya kusa kwashe sakan hamsin sannan yace, "kice ana sallama dashi" ya fad'a yana danna lock d'in motar ta bada sautin k'ut alamun ta bud'e. "Na gode. kayi hak'uri da abinda na fad'a maka a baya ban san kai bane ba, ka bawa d'an uwan ka hak'uri ya fita a rayuwata nasan nayi kuskure duk da laifin sane amma na karb'i laifin." ta fad'a murya na rawa sosai. Yadda maganar take rawa shine ya jawo hankalin sa ya kalle ta yaga yadda hawaye suke ambaliya daga idanun sa sai yaji rauni ya sake mamaye ko ina na jikin sa zuciyar sa na harbawa da sauri-sauri wani abu nayi masa yawo tun daga yatsan sa har cikin kansa. "Allah ya saka maka da alkhairi ya biya maka dukkan buk'atun ka na duniya, na gode ka taimake ni Allah ya taimake ka kai ma" ta sake fad'a tana bud'e motar ta saka sandar ta sannan ta sauka ta d'auki d'ayar ta kulle motar ta nufi cikin gidan su. Da kallo ya bita yana kallo ta cikin wani abu mai kama da kewa a zuciyar sa da shauki wanda bai tab'a jin makamancin sa ba a kan kowa sai ita kawai, duk takun da zatayi sai zuciyar sa ta buga hakan ya saka shi dafe zuciyar sa yaji tana harbawa a guje kamar zata faso k'irjin sa ta fito. Gidan yaga ta shiga ya sauke numfashi yana k'arewa gidan kallo tausayin ta na sake ninka na baya a zuciyar sa. A can gidan kuwa ana ganin shigar ta Umma ta mik'e tana fad'in, "Alhamdulillah! Malam gata ta dawo" ta fad'a tana nufo Rauda da idanun ta suke cike da kwallah har lokacin. Rik'e ta tayi tana kallon fuskar ta tace, "Rauda ina kika tsaya? Meya faru kike kuka?." Tare suke tafiya har suka k'arasa kan kujerar da take zama ta zauna Umma ta kalli Khairi tace, "Kawo mata ruwa." Da sauri ta tashi ta kawo ruwa a kofi Umma ta bata tasha ta sauke numfashi hannun ta dafe da kanta da yake mata ciwo. Baba yace, "Sannu Rauda, daga ina kike Shamsiyya ta sanar dani tun la'asar kika baro gidan ta gashi har anyi i'sha yanzu?." Numfashi take yi kafin tace, "Baba ana sallama da kai a waje." Baba yace, "Waye yake sallamar?." "Wanda ya taimake ni" ta fad'a tana haki jin hakan ya saka Baba fita bai kuma cewa komai ba. "Ummulkhairi kawo mata abinci taci" Umma ta fad'a tana kallon Khairi. Mik'ewa Khairi tayi ta d'auko mata abinci ta kawo mata ta karb'a ta bud'e dan taga meye a ciki, shinkafa ce da miya ta sauke numfashi tunda Anas ya aiko musu da abinci suke ci suke sha a gidan shiyasa take bashi babban matsayi a zuciyar ta. Kad'an ta fara cin abincin duk jikin ta babu dad'i haka ta fara ci gaban ta sai fad'uwa yake ba tare da tasan dalilin faruwar hakan ba. Shigowar Baba da sallama ya saka suka amsa har ya k'araso ya zauna ya kalle su dukkan su har da Inna da Rahma yace, "Yayan wanda ya kad'e Rauda ne. abin mamakin y'ay'an sarkin katagum ne." A tare k'irjin su ya buga har da ita Rauda d'in dan bata san waye ya buge ta ba daman. Umma tace, "ko da naji, yadda yaron da ya buge ta yake da izza kana kallon sa kasan jinin sarauta ne." Baba yace, "tunda ya buge ta ranar da ya dawo da safe ya kwanta ciwo har yanzu bai farfad'o ba yana kwance, shi wannan d'in yayan sane duk da kamar ana masa dole in yana magana har wani yatsine fuska yake yi yace min yana so a madadin k'anin sa zai saka ayi mata aikin k'afar ta a waccan k'asar ta larabawa meye ma sunan ta...." ya fad'a yana yin shiru alamun tunani. "Yauwa Misra, gobe zai aiko a d'auke ta a kai ta can ofishin da ake yin fasko na tafiya ayi mata cikin satin nan yake so ayi mata aikin. Yace kuma na baku hak'uri bai san da mara lafiyar da wuri ba da tuni anyi mata magani." Umma da take sauraren sa ta sauke numfashi tace, "Shi ya akayi yanzu ya san da ita?." Baba ya kalle ta yace, "Ai bazai miki k'arya ba." "nidai Malam ina jin tsoro aikin baza'a yi a k'asar nan ba har sai anje Misra? Kuma haka zamu bada ita daga shi sai ita aje ayi mata aiki muna nan baki sake?." Baba yayi shiru da alama duk kwadayin sa shima maganar bata shige shi sosai ba yace, "To nema mata lafiya za'ayi ai, kamar kuma kin san abinda yace dan ya fad'a a bada babba guda d'aya ko mace ko namiji da za'a tafiyar tare kin ga kenan ya san abinda yake yi. Kuma kina kallon sa kin ga fuskar sarki Sa'ad yadda ya fad'a min sunan sa Asad yafi kowa hankali da ilimj a gidan sarki, kowa ya sanshi da a k'asar saudia yake da zama bai jima da dawowa ba shiyasa na amince da maganar sa tunda nema mata lafiya za'ayi kuma daman sune da hakkin hakan." Umma dai bata kuma iya cewa komai ba ta ja bakin ta tayi shiru. Rauda kuwa sabon tunanin ta afka cikin mamaki da al'ajabi kenan daman yasan d'an uwan sane ya buge ta shiyasa yake k'okarin taimakon ta koda yaushe? Ya akayi yasan nice wacce d'an uwan sa ya buge? Ya akayi ya nemo ni yasan nice har ya san gidan nan?. Babu mai bata amsa sai ta ajjiye abincin dan ya fita daga kanta kuma ta tashi ta shiga d'aki tana shiga ana kawo wuta gidan ya haske d'akin nasu fanka ta fara kad'awa mai sanyi. Duk watsewa akayi daga tsakar gidan Umma ta biyo bayan ta tace, "Rauda a ina kuka had'u dashi wannan d'in? Wanne taimako yayi miki yau?." Bata b'oyewa Umma ba ta fad'a mata komai har k'arshe Umma ta jinjina kai tace, "Ikon Allah! Kinga illar rashin kunyar ki da nake fad'a miki ko? Yanzu badan shi yazo ba da me kike tunanin zaiyi miki....?." Rauda ta sunkuyar da kanta k'asa Umma ta kuma cewa, "Ki dinga fad'a har da maza akan wani abu kalilan wanda bai kai ya kawo ba, meye dan ya mare ki a gidan sarki basai ki manta anyi hakan ba tunda kin san yafi k'arfin ki...?. Har da kuka kuma had'uwa wai sai kika ce masa mahaukaci da yake bakya gudun abinda zai je ya dawo. Yanzu me gari ya waya da ya saka karen ya yaga naman ki sun kuma yi miki fyad'e fa?." Rauda a sanyaye tace, "Umma Allah ya rubuta faruwar hakan ne kawai." Umma tace, "Koma dai meye ke kika ja ai. kenan y'an ukun da ake zance akwai su a shigan sarki kin shiga rayuwar su dukka su ukun. to Allah ya kub'utar dake daga sharrin babban shi kuma wannan da ya taimake ki Allah ya saka masa da alkhairi, d'ayan kuma Allah ya bashi lafiya. Ke kuma nan gaba sai ki kama kanki." Da amin ta amsa a ciki ta shirya ta kwanta zuciyar ta cike da tunane-tunane. *☆☆☆* B'angaren Asad tunda ya bar k'ofar gidan su Rauda inda ake ajjiye karnukan ya kai Bobby ya ajjiye sannan ya nufi gida kamar koda yaushe. jin zuciyar sa yake da dad'i babu dad'i, in ya tuna yayi magana da iyayen Rauda akan ciwon ta sai taji dad'i a ransa, in kuma ya tuna da wani abun sai gaban sa ya fad'i a haka har ya k'arasa gida. Yana shiga B'angaren su ya samu Aliyu a zaune yana wuci yana shiga ya mik'e ya tare masa hanya yace, "Waye ya baka ikon hana yiwa wacce na saka a yiwa hukunci?." Asad ya kalle shi kamar zai magana sai kuma ya fasa ya rab'a ta d'aya gefen zai wuce Aliyu ya sake tare shi yace, "Magana nake maka Asad, me kake ji dashi har da zan yi hukunci ka saka a warware?." Asad ya kalle shi ido cikin ido yana juya nasa idanun yace, "Sabida baza'a yi d'in ba." "Har kai ka isa!, me kake ji dashi da zaka hana ni abinda nayi niya?. Wacece ita a wajan ka da zaka hana ni d'aukar mataki?." "Special one" ya bashi amsa a tak'aice yana wuce shi ya shiga d'aki ya bar shi a tsaye baki bud'e yana kallon sa. "Special one? Me yake nufi?, kenan ta musamman ce a wajan sa?. In na fahimta daidai kamar wata ce a wajan sa ko wacce yake so?." Sai kuma ya dafe kansa yace, "A'a Aliyu this is not possible kawai akwai dalilin nasa nayi hakan, tunda har kuwa baya so koda nayi niyar na rabu da ita na fasa, yanzu na fara sakawa a hukunta ta indai hakan zai b'ata masa rai shine fatana" yana fad'a ya fita daga falon da sauri. Asad kuwa wanka yayi ya saka kayan bacci ya fito zuwa falo, yunwa yake ji amma bazai iya cin abincin da ya gani a ajjiye ba haka kawai zuciyar sa bata yarda ba ya fita zuwa apartment d'in Mama. Bai same ta ba daman ba wajan ta yazo ba ya shiga ciki yaga abinci ya zuba yaci yarda yake so sannan ya tashi ya shiga ya duba Hydar ya koma. Koda ya koma d'akin sa kalmar da ua fad'awa Aliyu ce ta fad'o masa zuciyar sa, ya tsaya a jikin madubi yana kallon kansa a bayyane yace, "Da gaske special one ce?." Sai kuma ya murmusa sosai har hak'oran sa suka bayyana ya shafa gemun sa ya zauna a gafen gadon yana jin muryar ta mai sanyi tana sake rantsa dodon kunnen sa. Ido ya lumshe tunawa da ta bashi hak'uri sai yaji zuciyar sa tayi fess ya dinga murmushi shi kad'ai a haka har ya kwanta yayi bacci. Washe gari da misalin k'arfe goma na safe ake kwad'a sallama a k'ofar gidan su Rauda, Baba ya fita ba jimawa ya dawo ya kalli Rauda da take zaune tayi wanka yace, "gashi yarima ya turo zaku je, ki d'auko katin d'an k'asar ki kema ki d'auko naki kuje ke ya kamata ku tafi tare in tafiyar ce" ya fad'a yana Kallon Umma. Umma tace, "Ni da nace cikin yayen ta suje da guda d'aya." Baba yace, "Duka su kad'ai ne wajan mazan su basa yi doguwar tafiya irin wannan ba. ke dan fa aikin jinya za'ayi da wallahi bazan neme ki ba ni zanje kodan na kashe kwarkwatar idanu na, to jinyar mace sai mace ki tashi ki d'auko ku tafi ana jiran ku." Umma ba dan taso ba ta tashi ta saka mayafi ta d'auko katin d'an k'asar ta fito tana fad'in, "Amma malam kyau kaima kabi mu muje tare." Baba yace, "wannan a rubuce yake ai ba sai kin fad'a ba, d'an sarki fa da kansa wanda mai martaba yake ji dashi. na san abinda zai kunso muku ai gwraa naje nima." Umma ta kalle shi cikin takaici jin badan tsare lafiyar su zai je ba dan abinda za'a samo ne. Inna da ta lek'o daga d'aki tana kallon su tace, "duk wanda ya hau motar kwadayi zata juye su a tashar wulaqanci, daga uwar har uban har y'ar." Ba wanda ya tanka mata suka fita. Suna hango su jiki na rawa suka bud'e musu mota su uku a baya aka ja suka tafi. Da yake abu ne na manya an sanar da komai suna zuwa aka fara yi musu ashe Baba ma da nasa katin ya tawo wai bai san inda rana zata fad'i ba, kafin azahar an gama musu fasko an awa ashirin da hud'u zai fito da yake na manya ne babu b'ata lokaci. Suna baro wajan d'aya daga cikin dogaran ya kalle su yace, "Mai girma yarima Asad ya umarce mu da in mun gama mu kai ku inda zaku ci abinci sannan a mayar daku gida, yanzu zamu k'arasa wajan in zaku shiga ciki sai muje in zuwa za'ayi a kawo muku duk d'aya ne." Kafin Baba yace wani abu Umma tace, "A'a ba sai muje ba mu wuce gida hakan ma mun gode." "A'a ranki ya dad'e, yarima Asad bazai ji dad'i ba in muka ce masa bamu je ba, ku daure muje sai a kawo muku nan." "Babu damuwa" Baba ys fad'a da sauri suka cigaba da tafiya. Gaban babban gidan abinci suka tsaya kafin na gaban yace, "ranku ya dad'e me za'a kawo muku?." "Duk abinda ya samu" Umma ta fad'a kawai suka amsa da to suka fita. Basu jima sosai ba suka dawo da ledoji manya suka shigo motar suka mik'a musu sai khamshi ne yake tashi sannan suka wuce gida, sai da suka har gida sun shiga sannan suka wuce. *☆☆☆* A zaune ya samu Mama kusa da godon Hydar ya shigo tana ganin sa tace, "Asad Hydar ya motsa yau da alama yana gab da farkawa" ta fad'a cikin nishad'i tana kallon sa. Murmusawa yayi kad'an ya k'arasa kusa da gadon yana kallon sa. "Sadiya ta kira ni tace min kaje jiya naji dad'in hakan" ta furta a tak'aice tana kallon sa. Numfashi ya saukar a hankali yace, "kiyi hak'uri Mama, amma bata dace dani ba." "Ta dace dakai Asad ita na zab'a maka ita nake so ka aura." "Tohm Mama" Ya furta yana juyawa ya fita daga d'akin gabad'aya. Yana fita mota ya d'auka ya fita daga gida. Gidan da ya saba zuwa yaje ya zauna shi kad'ai yana tunanin da ya saba kansa a kulle kamar ko yaushe. idanun sa a kulle yana zaune ko motsin kirki bayayi babu abinda yake ji a zuciyar yake kuma gani sai Rauda ba tare da yasan dalilin hakan ba kawai ji yake zuciyar sa na motsawa a kan hakan. Ya sauke numfashi mai k'arfi ya tashi zaune sosai yana mutstsika idanun sa, jinin jikin sa yake ji tana shiga ko ina ya rasa gane tausayin ta yake ji sabida ta rasa k'afar ta ta dalilin Hydar ko kuma me? Bai sani ba bai san meyasa yake ganin ta always ba ko yaya ya kulle idanu ita yake gani; ya kasa banbance itace ta mafarkin sa ko ba ita bace?. "RAUDA!" ya furta a bayyane yana jin wani iri a jikin sa gashin jikin sa na rinsing ba tare da ya san dalilin hakan ba, wayar sace ta d'auki k'ara ta katse masa tunani ya kalle ta yaga sunan Hafiz ne yayi banza bai d'auka ba aka kuma kira ya kalla yaga d'aya daga cikin wanda ya saka su kai su Rauda ofishin yin fasko d'in ya d'auka, "Ranka ya dad'e, Allah ya taimaki yarima, Allah ya ja zamanin ka, ya baka tsahon rai ya taimake ka a duk inda kake." "Uhum" ya furta kawai ba tare da yace komai ba. "Ranka ya dad'e anyi abinda kace, yanzu haka mun sauke su sun shiga gida." "Good" yana furta hakan ya katse wayar bai tsaya yaji mai zasu ce ba. Lumshe idanu yayi ya tuno lokacin da take hawaye tana masa godiya sai yaji kasala ta saukar masa ya koma ya kwanta a akan kujera yana jin wani irin yanayi a jikin sa. 'You love her' yaji zuciyar sa ta furta hakan ya saka shi saurin tashi ya bud'e idanun sa yana ji zuciyar sa na gasgata masa abinda ta fad'a. "A'a ba haka bane" ya furta yana cize bakin sa. 'Da gaske Asad haka ne ka yarda.' zuciyar sa ta sake fad'a ya dafe kansa da duka hannayen sa jin yana juya masa. Tashi yayi ya d'auki makullin mota ya fita daga gidan da sauri jikin har shaking yake yi. *☆☆* "Uncle ka kira ni then kayi shiru ina da abinda zanyi" Aliyu ya fad'a yana kallon waziri da yake zaune yana facing d'insa. Numfashi ya sauke yace, "Wato Aliyu abubuwan ne suke d'aure min kai, ace kamar ka babba kaine namijin farko da mai martaba ya samu amma a dinga mik'a sarauta ga k'anin ka?. Kasan jiya mai martaba ya zauna da Asad kuma ya tabbatar masa da shine zai mulki garin nan?." Kafin Aliyu yayi magana yace, "ga kyau, ka k'ima, ga k'asaita, ga nagarta, ga izza, ga ilimi, ga wayewa, ga sanin ya kamata. Waye ya cancanci zama sarki in ba kai ba?. Kai ka san ina son sarautar nan amma sabida dacewar ka ya sanya na hak'ura na sallama; ranka ya dad'e wallahi inda zaka zama sarki zan cigaba da zama matsayin wazirin ka amma meyasa mai Martaba yake fifita Asad a kan ka? Meyasa kowa maganar sa a akan Asad take sab'anin ka?." Zuuuuu haka Aliyu yake jin k'asaita da zugar da ake masa na shiga cikin jikin sa, kansa yake ji a sama kamar shine yake mulkin duka duniya, wani irin yarrrr yake ji a jikin sa har bai san ya cize bakin sa ya kalli Waziri yace, "Kana so kace min kana bayana? Kana so kace min kaima ni kake so na zama sarki a garin nan kenan?." Murmushi waziri yayi yace, "Dari bisa dari, ni daman kaine nawa ai tun kana k'arami ba Asad ba, in kana musawa ka tambayi mahaifiyar ka zats baka labari." Wani irin kallo Aliyu yake masa na ka raina min hankali amma sai ya murmusa yace, "Ta yaya zan yadda bayan kaima kana harin mulkin nan?." "A bayyane yake ai ranka ya dad'e, indai kai zaka mallaka wallahi nidai na hak'ura." Murmushi Aliyu yake na kana mayar dani yaro k'arami bai ce komai ba ganin murmushin da yake yi sai Waziri yace, "shine nace me zai hana baza mu samo mafita ba; matuk'ar Asad ya mallaki garin nan shiga gidan sai ya gagare mu, ya kamata mu san abinda zamu yi." "Ina jinka." Ya gyara zama yace,"Na shirya wani abu a raina amma ban sani ba ko zaka amince." Da hannu yayi masa alama da yana jin sa. Gyara zama ya sake yi yace, "Daman mafita ce na nemo amma ina jin shayin fada maka." Aliyu ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa yace, "Go ahead." "Daman cewa nayi mai zai hana mu b'atar da Asad ya bar k'asar nan ma'ana ayi masa abinda bazai sake waiwayo mu ba, kai kuma sai ka koma acting d'in Asad a fad'awa duniya Aliyu ne ya b'ata ba Asad ba. Ni da kai mun san Aliyu ne yake nan amma duniya za'a ce mata Aliyu ne ya b'ata; kaga mai martaba zai mallaka maka mulkin katagum a matsayin Asad kaga shikenan ciki lafiya baka lafiya." Wani irin kallo Aliyu yake masa gaban Waziri sai fad'uwa yake yi yana b'oye tsoron sa babban burin sa kar yak'i amincewa da batun sa hakan ya saka tsoro ya bayyana k'arara a tare dashi duk da yana so ya b'oye amma hakan ya gagara sai da tsoron ya kwanta a fuskar sa. Numfashi Aliyu yayi kafin ya saki dariya mai d'auke da izza da k'asaita kafin ya kalli waziri yace....... *KWANTAN ƁAUNA* ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *019.* Irin kallon da yake yi masa jikin Waziri yayi sanyi qalau kuzarin sa ya ragu amma duk da hakan bai nuna ba ya daure ya cije baya so ya bayyanar da raunin sa kar Aliyu ya gano shi, Aliyu wani irin murmushi yake yi ya sauke k'afar daga kan d'aya ya kalle shi ta k'asan idanu yace, "kana ganin hakan zai yu kuma?." Jin abinda yace sai ya sauke ajiyar zuciya yace, "Mai zai hana ya yu ranka ya dad'e?, indai zaka bada goyan baya abu ne mai sauk'i faruwar hakan." Ya juya manyan idanun sa ya sauke su akan Waziri kana ya mik'e tsaye yana kallon sa yace, "Zan yi tunani a kan hakan" yana gama fad'ar hakan ya fita daga falon bai sake kallon waziri ba. Waziri ya dafe k'irji gaban sa yana fad'uwa sosai ya d'auko waya da sauri jikin sa har rawa yake, kiran yake ba'a d'auka ba ya cillar da wayar akan kujera ya mik'e yana zaga d'akin. "Me yaron nan yake nufi dani? Yaji sirrina a banza ya tashi ya tafi ya barni....? kenan yana nufin na jira shi?, in bai amince bafa?." Naushin iska yayi ya koma ya zauna jikin sa har b'ari yake sabida tashin hankalin da yake ciki. Kamar kuma anyi masa allura ya mik'e da sauri ya shiga d'aki dan bai ga ta zama ba. Aliyu lokacin da ya fita mota ya shiga ya zauna yana tuno abinda Waziri ya fad'a masa sai yayi murmushi yaja tsaki yace, "Wai ni zai yiwa wayo, an fad'a masa ni d'in shashasha irin sa?, ko kuma ya d'auka zuciya ta irin ta Asad ce?." Sai kuma ya tsaya da dariyar ya d'auki waya da sauri ya kira Waziri, kamar jira yake yaji an d'auka ya gyara murya yace, "Na amince da tayin ka." Yana jin ajiyar Wazirin a waya baice komai ba ya yanke wayar ya ajjiye wayar wayar yana kallon glass d'in gaban motar. Asad bai koma gida ba sai da ya gama yawon sa har dare yaci abinci sannan ya koma, ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga apartment d'in su ya tarar da Aliyu a zaune ya kunna sigari yana sha, har ya wuce ya dawo yana kallon sa har ga Allah baya son warin ta ko kad'an ya masa magana sau babu adadi amma yak'i. "Aliyu ko a lafiyar ka abinda kake yi ba daidai bane" ya furta yana kallon sa. D'ago idanun sa yayi ya kalle shi ya murmusa ya sake zukar sugarin ya fesar kana yace, "lafiya ta kace ba taka ba, a gani na ai hakan ba damuwar ka bace ba." Asad bai kuma cewa komai ba ya d'aga kafa zai wuce yaji yace, "kabi a hankali ka kuma taka tsan-tsan akwai lokaci Asad." Baice komai ba ya wuce ya k'yale shi ya shiga d'akin sa. Can k'arshen d'akin ya wuce ya janye labule sai ga k'ofa ta bayyana a wajan wacce in ba kasan da ita ba baza ka tab'a cewa tana wajan ba ya shiga ciki ya kulle k'ofar. K'aton wajan karstu ne mai d'auke da drawer na littafai manya-manya na addini dana karatun zamani, littafai ne sama da guda dari uku a wajan ko wanne rukuni da cover sa da sunan su a k'asa ga table da kujera mai guda d'aya a wajan da k'aramar lamp a kai. Kujerar yaja ya zauna ya dafe kansa da duka hannayen sa biyu kansa na juyawa ya rasa dalilin da ya saka yake jin hakan da zarar ya shigo d'akin sa, daurewa yayi ya tashi ya k'arasa jikin cover ya d'auki littafai guda biyu ya k'araso ya zauna a kan kujerar ya fara dubawa. Karantawa yake a nutse yana bin rubutun daki-daki yana Nazariin abinda yake yi. Rufe na farko yayi ya bud'e na biyun yana sake bi a hankali har ya kammala karanta inda yake da buk'ata ya kulle ya kifa kansa a kan littafin kamar mai bacci. Juma'a ce gobe kuma shine zai gabatar da hud'uba shiyasa yake ta dube-duben littafai amma zuciyar sa ta kasa bashi topic guda d'aya da zaiyi hud'ubar a kansa, d'ago kai yayi ya saka hannu biyu ya d'an daki kansa a hankali ya furzar da iska waje yana kallon d'akin gabad'ayan sa. Zuciyar sa yaji yana bugawa da sauri har yana jin sautin ta a kunnen sa ya runtse idanun fuskar Rauda ta bayyana a gare shi. "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta a hankali yana dafe da kansa har lokacin bai kuma daina jin bugun zuciyar ba. Cize bakin sa yayi ya runtse idanu kafin ya koma ya jingina da kujerar, sautin muryar ta yake tunowa a hankali tana shiga ilarin jikin sa, tasirin muryar da dad'in ta ya saka shi kulle idon sa yana sauke numfashi gashin jikin sa na tashi. sautin muryar yarinyar mafarkin sa yaji sai ya bud'e idanun sa; ya kasa banbance shin itace yake gani a mafarki ko kuma ba ita bace?, bai tab'a ganin waccan fuskar ta completely ba amma idanun ta da goshin ta irin na Rauda ne, akwai banbanci a maganar su waccan muryar ta tafi zak'i a kan ta Rauda, ita kuma ta Rauda tafi sanyi da taushi kamar mai mura in tana magana. Tashi yayi ya kashe hasken d'akin ya fita daga cikin da ya dawo d'akin sa ya zauna a gefen gado ya rasa tunanin ma mai zaiyi. Kiran wayar Suhail ya gani ya jawo wayar ya d'auka ya saka a kunnen sa yayi shiru alamun ana yi masa magana kafin yace, "Alright" daga haka ya yanke wayar ya tashi ya shiga band'aki. Sai bayan ya gama komai sannan ya kwanta da burin Allah ya sa yau yayi mafarki da yarinyar da yake gani ko zai gane ta. Washe gari da ya farka yaso yaje ofishin fasko amma sabida juma'a ce dole ya tsaya yayi hud'uba ya saka babu inda yaje har aka shiga masallacin cikin gari, kamar ko yaushe yayi hud'uba ya kuma yi sallah bayan an idar ya hau mota ya wuce office d'in. Da kansa ya karb'o faskunan nasu guda uku da hotuna yana shiga mota ya zauna yana kiran agent d'in su a waya, ana d'auka yace, "Egyptian visa nake so guda uku" Shiru ya kuma yi kafin yace, "Okay better" yana fad'a ya yanke wayar ya ja motar sa ya bar wajan. Gida ya wuce ya ajjiye faskunan ya fito zuwa wajan Mama kamar yadda ya saba. A hakimce ya same ta tana danna waya kamar koda yaushe ya zauna a gefen ta kana yace, "Barka da juma'a." "Barka Asad" ta furta kawai ba tare da ta kalle shi ba. Shiru ya biyo baya babu wanda ya kuma yin magana kafin yace, "Mama anyi inviting d'ina wani event a Cairo" "Kwana nawa zakayi?." "I think one week." "I'm not allow u to go." Kallon ya yayi itama ta kalle shi yace, "but Mah...." D'aga masa hannu tafi tace, "Na gama magana Asad, tafiya indai ba ta kwana biyu bace ban amince ka jeta a yanzu ba maybe kaje wani lokacin." Numfashi ya sauke ya tashi ya fita daga falon nata zuwa falon Hajiya kamar yadda ya saba duk juma'a, tana zaune ita da hidiman ta ya shiga da sallama, "Barka da zuwa Yarima, barka da zuwa fari mai farar wutsiya, fari mai farar aniya, indaroro sai kan soro, kaga tufa mad'aukar d'aki, sikari bakayi farin banza ba, walikiya kake duk inda kabi sai ka haska......" zasu kuma magana ya d'aga hannu sama sukayi shiru cikin girmawawa. Murmushin yake take tana kallon sa ya zauna a k'asa yana kallon yace, "Barka da Juma'a Hajiya" "Barka dai Asad, ya jama'a ya kuma k'ok'ari?." "Alhamdulillah, ina suke?" Ya fad'a yana kallon falon alamun yana neman kannen sa. "Sunje gidan Yayar ku sai zuwa anjima zasu dawo." Tunda tace Yayar ku ya gano wacce take nufi dan babar yar ta wacce ta kasance babba a gida gabad'aya bata fad'ar sunan ta daman. "Na barki lafiya" ya fad'a yana mik'ewa tsaye tace, "Na gode Asad." Bai amsa ba ya fita ya tafi b'angaren Umma, kamar ita tana zaune itama a zagaye da hadimai suka gaisa kamar waccan ya tafi. Kasancewar rana ce bai samu mai martaba ya bada kud'in da ake rabawa dan bazai samu damar yi da kansa ba ya koma apartment d'in sa. Sai yamma sannan wanda zai karb'i faskunan yazo ya bashi ya wuce Abuja dasu domin a buga musu visa. Bayan wanda karb'a ya tashi yana zaune Suhail ya kira shi, bai d'auka ba har ta katse bayan ta katse ya d'auki wayar ya kira hidiman k'ofar ya bada umarnin a bar shi ya shigo ya ajjiye wayar. Da sallama ya shigo ya zauna kusa dashi Asad yace, "Suna bin umarnin Mama ne." Suhail ya murmusa yace, "Hakan yana da kyau sosai tsoron lafiyar kace, sai naga kamar ka rame." Tab'e baki yayi baice komai ba kafin Suhail ya kuma cewa, "me yake faruwa?." Iska ya furzar a hankali yana sauke numfashi amma bai ce masa komai ba, jin hakan sai shima yayi shiru ya saka hannu a aljihun gaban rigar sa kamar mai neman wani abu, "me kake saka min?" Yaji muryar Asad a kansa yayi saurin janye hannun sa daga kusa dashi. Had'a idanu sukayi Asad ya d'aga gira alamun ya bashi amsa, nutsuwa ya aro ya saka a fuskar sakana yace, "me kuwa zan shafa maka Asad? Kalli hannu na mana" ya fad'a yana nuna masa tafikan hannun sa. Murmushin gefen baki Asad yayi kafin ya d'auke kansa daga kallon sa yace, "lafiya ka ke nema na?." "Normal ina so mu had'u ne kawai." "Really?" Asad ya fad'a yana wara idanun sa waje. "Sure, naga duk ka canja Asad kamar baka yadda dani ba, ko da Aliyu nake tare ne ban sani ba?." Baice masa komai ba ya shafa kai kawai kafin yace, "u can go." Suhail ya kalle shi yace, "Okay bye" ya fad'a yana mik'ewa ya fita yana mamakin canjawar Asad. Waya aka kuma yi masa ya kalla yaga masu tsaron k'ofar sane ya share kiran ya katse aka kuma kira ya ja k'aramin tsaki ya d'auka baice komai ba, daga can b'angaren suka ce, "Ranka ya dad'e Allah ya wuci zuciyar ka na dame ka, wata yarinya ce take so tayi magana da kai, tana ta magiya mu barta ta ganka." Jimm Asad yayi yana tunani kafin ya bada umarnin tazo, ba jimawa ta shigo da sallama jikin ta har rawa yake ta zube a kan carpet tace, "Barka da yamma ranka ya dad'e." "Wacece ke?" Ya furta a hankali yana kallon ta. "Sunana Habiba ni jikar Gwaggo Gambo ce da take gidan nan. K'awa tace ta samu matsala da Yallab'ai Aliyu to tsoro take ji kar ya mata wani hukunci shiyasa muka kawo k'ara gaban ka a taimaka a bashi hak'uri. " Shiru yayi bai amsa ba hakan ya saka tace, "Sunan ta Rauda tana da matsalar k'afa shiyasa bamu zo tare ba, mun tab'a zuwa gidan nan da ita ta buge shi bata sani ba ya mare ta, had'uwar su ta biyu kusan hakan ce ta faru, had'uwar su ta uku shine ta mayar masa da abinda ya fad'a mata. Yayi alwashin sai ya d'auki mataki a kanta duk taji tsoro sai kuka take hankalin ta ya tashi matuk'a. A bashi hak'uri ranka ya dad'e wallahi y'ar talakawa ce kar ya cutar da ita." Yana sauraron ta dan a hankali take maganar hakan ya saka shi nutsuwa yana jin ta, tunda ta ambaci Rauda gaban sa ya fad'i ya sake bata hankalin sa har taje k'arshe kafin, "kar ki damu." "Na gode ranka ya dad'e, Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana, ya ja da ran Mama da mai martaba." A lab'b'an sa ya amsa da amin ya sanya hannu a aljihun sa ya d'auko kud'i ya mik'a mata ta karb'a hannu na rawa zatayi godiya ya d'aga mata hannu ta tashi ta fita. Numfashi ya fesar kalmar ya mare ta tana yi masa amsa kuwa a kunnen sa nan take ransa yaji ya b'aci ba kad'an ba yaja tsaki baiyi niyar fita ba amma ya tashi ya fita daga gidan gabad'aya. Habiba na barin gidan wajan Rauda taje ta bata labarin duk abinda ya faru har kud'in da ya bata ta nuna mata, Rauda tace, "Bari kawai Habiba baki san me ya faru washe garin da kika zo nan ba." "Meya faru to?." Kwashe duk abinda ya faru tayi ta fad'a mata sannan ta d'ora da cewa, "Jiya ya saka aka kai mu ofishin fasko za'ayi mana zai kaini waje ayi gyaran k'afa madadin k'anin sa." Habiba tace, "ban sani ba ai da banje na same shi yanzu ba tunda komai ma ya wuce. Amma nayi murna da za'a yi miki aikin k'afar nan Allah ya sa ayi a sa'a." "Amin." "Kika dinga zagin wanda ya kad'e ki kina ganin kamar wasa ne babu wani rashin lafiya ashe gashi wanda muka sani ne ma." "Wallahi kuwa, na d'auki hakki." "Ina Anas ne wai?." Rauda tace, "Yaje Abia." "Masoyin ki kenan, wai har yanzu baki bashi dama ba?." "Na bashi Habiba tunda ina sauraron sa yanzu. Tunda ya siya min maganin da aka wulak'anta ni a kai ya kawo mana kayan abincin da ko rabin rabin sa bamu ci ba wallahi nake ganin k'imar sa sosai. Ta silar abincin nan Baba ya daina d'orawa Rahma tallah." Habiba tace, "Ai yana son ki wallahi zaiyi komai sabida ke; Allah ya saka masa da alkhairi." "Amin." "Kin fara son sa kenan?." "Ina fa, kedai Allah ya kyauta." Habiba tayi dariya ta amsa da amin kafin su cigaba da hira suyi sallama ta tafi. Maganar Habiba ta dinga tunawa musamman halayen Asad sai taji ya burge ta sosai ko babu komai baya wulak'anta talakawa kamar Aliyu. B'angaren Asad bai dawo ba sai dare direct ya wuce b'angaren mahaifin sa sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga, baya babbar fada ta farko ya shiga ta biyu nan ma baya nan hakan ya bashi tabbacin yana d'aki kenan. Shi kad'ai mai martabawa yake lamuncewa ya shiga amma gudun kar ya shiga ya tarar da wata matar tasa a ciki ya saka yaja tunga tunda ba girkin Mama bane ba. Kamar kuwa ya sani yana nan tsaye Ammi ta fito ganin sa ya saka tace, "Asad daman kai yake nema kuwa, kaje ciki" ta fad'a tana wucewa shima ya shiga d'akin da ya san mallakin mahaifin sane. A zaune ya same shi a kamalance ya k'arasa ya zauna a akan carpet yace, "Barka da dare Takawa." Murmushi yayi yace, "Barka dai Asad." "Ya k'arfin jikin?." "Jiki Alhamdulillah ana ta samun lafiya." "Allah ya k'ara lafiya yasa kaffaara ce." "Amin Asad. Allah ya yi maka albarka ka rayu cikin aminci da walwala." A labban sa ya amsa da amin kafin mai martaba yace, "Ya batun zuwa taron malamai masu shekarun naka a Dubai?." "Mama ta hana Abba" ya furta a sanyaye. Kai ya girgiza yace, "Rabi'atu manya, ko kad'an bata so kayi nisa dani gudun kar ka tafi a bawa wani sarauta ba kai ba, tana mantawa da Allah ya riga ya rubuta wanda zai gaje ni." Shiru Asad yayi bai ce komai mai martaba yace, "Ta hana ka aikin da kake mafarki tun kana yaro, ta hana ka komawa Dubai kamar yadda sarkin su ya nema, ta hana ka aiki da Saudia yanzu kuma ta hana ka zuwa taron kwana bakwai kacal; in kana so ka shirya ka tafi na baka damar hakan." "Allah yaja zamanin mahaifina, tunda tace na bari na bari d'in." Mai martaba yayi murmushi mai kyau yace, "Shiyasa albarka take baibaiye dakai a koda yaushe, indai nace kar ayi ko tace kar ayi baza kayi koda a bayan idanun mu. Amma tauye ka da take yi yayi yawa nan gaba indai aka kuma zuwa irin wannan gab'ar bazan bari ta tauye ka sai kayi abinda kake so." Shima murmushi Asad d'in yayi yana kallon mahaifin nasa. "Ya batun yarinyar da take nema maka?." Take fuskar sa ta koma yadda take a d'azu yace, "bata dace dani ba Abba, na sanar da Mama tace ba haka ba ita ta zab'a min, amma na karb'a." "Da zarar ka samo wacce kake so ko wacece a fad'in duniya ka sanar dani Asad, zan shige maka gaba wajan ganin ka mallake ta ko waye mahaifinta a garin nan ko a k'asar nan." D'ago idanu yayi suna had'a ido da Abban nasa kwarjini ya saka ya sauke kai k'asa ba tare da ya shirya ba yaji bakin sa yace, "Ko y'ar talakawa ce?." Mai martaba ya tashi sosai yace, "Ko y'ar wace Asad; shi talaka ba mutum bane? Ko y'ar shugaban k'asa ce indai ba y'ar gidan sarauta bace y'ar talaka ce a gidan sarauta. Indai da tarbiya da ilimin addini zance ya k'are. Inda za'a samu matsala in aka bincika aka gano wata dabi'a a tare da ita ko tare da dangin ta, kasan gida irin wannan baya d'auko irin wannan yaran." Jin abinda mai margaba yace sai kuma ya rud'e amma bai nuna hakan ba shima mai martaba ya lura bai san yayi maganar ba sai ya murmusa kawai baice komai ba. "Ina neman izinin tafiya" ya fad'a kai a k'asa. Mai martaba yace, "Dan kada a fad'a min wacece sirikar tawa ya saka zaka gudu?, to Allah ya tashe mu lafiya." Murmushi sosai Asad yayi har hakoran sa suka bayyana yana son zama da mahaifin sa shine yake damuwa da damuwar sa sab'anin Mama da kanta kawai ta sani. Mik'ewa yayi ya fita yana jin sanyi a zuciyar sa. _Na bayyana a zahiri na a gare ka yau Asad, kayi gaggawar kawo ni rayuwar ka kafin su hallaka, Asad kana da tarin mak'iya na jikin ka sune mak'iyan ka, zanzo gare ka Asad amma akwai tarin qalubale a gaban mu, sai ka jure sai kuma ka daure._ a firgice ya tashi zaune ya dafe kansa abinda ta fad'a masa yana dawo masa cikin kansa, tabbas Rauda ce domin fuskar ta yau ta bayyana sosai a gare shi, itace domin ya ganta ido da ido sosai ta fito tarr itace. "Meyasa take taimako na tun a mafarki?." Ya tambayi kansa gabad'aya a rud'e yake hankalin sa kuma a matuk'ar tashe. Agogo ya kalla yaga karfe biyu na dare ya tashi ya shiga band'aki ya d'auro alwala ya fito ya tayar da sallah. Ya jima yana sallah har k'arfe hud'u kafin ya koma lazimi yana zaune har lokacin k'irjin sa bugawa yake yi bai dawo daidai ba. Ana kiran sallah ya tashi ya fita zuwa masallacin cikin gida. Safiyar asabar yaji gabad'aya babu abinda yake so ya gani ya kuma saka a idanun sa face fuskar Rauda, ya kasa kai komai bakin sa Rauda kawai yake son gani, k'okarin daurewa yake amma abin yaci tura zuciyar sa sake azalzala masa take yi a kan haka dak'yar ya iya zama a gidan bai fita yaje gidan su ba. Koda ya fita daga gidan Company ya wuce ya tarar da Hafiz suna ta had'a kayan wanda sukayi order za'a kai ya wuce office gabad'aya jikin sa babu k'wari. Bai bar company ba sai yamma wajan cin abinci yaje yaci ya gito ya shiga mota ya nufi unguwar su Rauda kan sa tsaye. A k'ofar gidan ya tsaya yana kallon gidan nasu amma ya rasa me ya kawo shi sai kallon gidan yake kawai amma ya rasa dalilin da ya kawo shi, hango ta yayi a tsaye da sandinan ta tana dariya ita da wata babbar mace mai shigen maka da ita da alama Yayar tace. K'arewa mata kallo yake cikin hijjabi mara tsaho fuskar ta a washe da kyakykyawan murmushi a kan fuskar ta, lumshe idanun sa yayi gaban sa na fad'uwa sosai yana kallon ta domin ta k'ara yi masa kyau ga annuri da take fitarwa. Numfashi ya sauke mai nauyi bai daina kallon ta ba bai kuma sauke glass ba har matar da suke tsaye ta bar k'ofar gidan ita kuma koma cikin gidan. Sai da ta bar wajan ya lumshe ido ya dafe saitin zuciyar sa da take bugawa da sauri ya bud'e ido daidai lokacin da wayar sa ta sake cika masa kunne da ihu, sai da ya dawo hankalin sa ya dawo nutsuwar sa duk da zuciyar sa na bugawa, kallon wayar yayi yaga sunan Mama bai yi k'asa a guiwa ba ya d'auka ya saka a kunne, "Asad ka dawo gida Hydar ya farka!" ta furta daga can b'angaren baice komai ba ya yanke wayar ya tashi motar sa zuwa gida. _tirkashi fan's mai Asad yake nufi da Rauda ne?._ *KWANTAN ƁAUNA* ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *020.* Lokacin da Asad ya shiga falon Mama ya tarar da Hydar a zaune ya rame sosai yayi haske jikin sa babu k'arfi sai idanu da yake bin mutane dashi, a nutse ya tako ya zauna kusa dashi ya kalli Mama da take zaune itama a gefen sa sai Suhaima da take tsaye yace, "Sannu Hydar, ya kake ji?." Maganar sa bata fita sosai yace, "da sauk'i." "Asad ka taimaka masa yayi wanka ya sai yaci abinci." Asad ya kalli Hydar yace, "Zaka iya tashi?." Kai ya d'aga alamun eh ya rik'e shi suka tashi zuwa d'akin da yake kwance. A nan yayi wanka aka kawo masa kaya ya saka yayi sallah ya fara cin abinci. Suna zaune zagaye dashi ya gama cin abincin ya sha magani kana ya kalli Asad yace, "Akwai yarinyar dana buge deaf a tambaya min Dr Yasir tana ina." Ran Mama ya b'aci jin da abinda ya fad'a tace, "na saka an sallame ta." Hydar ya kalli Mama ya dafe kansa yace, "meyasa Mama? Yarinyar tana buk'atar taimako sai an mata aiki fa." Mama tace, "kuma indai nice na haife ka dole ka bar maganar ta ba, bana son sake jin zancen wata wacce ka buge a bakin ka ya wuce ka manta da babin ta." Zaiyi magana Asad ya d'an ja rigar sa sai yayi shiru ya saukar da kansa k'asa baice komai ba. Tsaki Mama tayi tace, "kana farkawa ka rasa da abinda zaka tashi sai maganar wata banza y'ar talakawa, kenan daman da ita ka kwanta a ranka da yake baka da hankali, na tsani yarinyar tsana mai muni." Babu wanda ya ce komai ba sukayi shiru zuwa lokacin magariba ta kawo kai. Tare suka fita da Hydar sai a sannan jama'ar masarautar suka san da farkawar sa aka dinga gaishe shi zai amsa duk da ba wani k'arfi ne dashi ba. Bayan an idar da sallah suka je wajan mai martaba daga nan suka dawo apartment d'insu. Aliyu baya nan Hydar ya zauna a falo jin jiri yana d'aukar sa yana sauke numfashi yace, "Deaf ban san inda zan ga yarinyar ba, basu da kud'in da za'a yi mata aiki in wani abun ya same ta Allah sai ya saka mata." "Relax" abinda Asad yace kenan daga nan bai kuma cewa komai ba. "Deaf ina cikin damuwa tunda na tashi itace tazo raina, ta yaya zan ganta ina so na ganta wallahi." Wani irin kallo Asad yayi masa jin abinda yace nan take sai gaban sa yayi mugun fad'uwa amma bai nuna masa ba bai kuma yi masa magana ba. Hydar ya yi shiru amma zuciyar sa gabad'aya tana ga tunanin inda zai ganta gabad'aya hankalin sa yana kanta gashi bai san inda zai nemo ta ba abin duk ya dame shi. Washe gari Asad tare da Hydar suka fita zuwa company dan ya samu k'arfin jikin sa suna tare har yamma, a yamman aka kawo masa passports d'insu Rauda an buga musu visa ticket ya rage a siya, bayan tafiyar wanda ya kawo passports Hydar ya kalle shi yace, "Passports d'in su waye?." Bai bashi amsa ba sai da ya gama abinda yake yi ya tashi suka shiga mota suka bar company. Gidan su Rauda ya wuce Hydar bai san gidan ba yaga dai sun tsaya a k'ofar gidan ya kalli Asad yace, "Ina ne nan?." Bai magana ba ya sauke glass d'in motar nan ya hango Khalil yana ta wasa ya yafito shi da hannu ba musu ya k'araso Asad ya kalle shi yace, "Abban ka yana nan?." Khalil yace, "Eh yana nan." "Jeka kace ana sallama dashi" yana fad'a ya ja bakin sa yayi shiru Khalil ya shiga cikin gidan. Hydar yace, "Asad ban gane ina muka zo ba fa." Kallon sa yayi baice masa komai ba a lokacin Baba ya fito ganin haka ya saka Asad ya fito daga motar shima Hydar ganin ya fita shima ya fito lokacin Baba ya k'araso, hango Asad sai ya washe baki ya k'araso da sauri yana zuwa yace, "Barka da zuwa ranka ya dad'e." Murmushin k'arfin hali Asad yayi suka gaisa da Baban Hydar ma ya gaishe shi kafin Asad yace, "Shine Hydar wanda ya buge ta jiya ya farka daga rashin lafiya" ya fad'a yana nuna masa Hydar. Baba ya washe bakiyace, "Allahu Akbar! Naso na gane fuskar sa yadda ya rame ya saka ban gane shi ba, sannu Hydar ya jikin ka?." Fad'ar hakan nan take sai Hydar ya gane shi shima yace, "Alhamdulillah, ya jikin ta?." "To jiki da sauk'i dai za'a ce." "Zan iya ganin ta?" Hydar ya fad'a yana kallon Baba. "Mai zai hana, bara na sanar dasu shigowar ku" ya fad'a yana komawa ciki da sauri Asad baice komai ba har Baba ya dawo yace su shigo. Yana gaba suna binsa a baya Hydar na k'arewa gidan kallo har suka shiga ciki. suna zaune dukkan su a kan tabarma a tsakar gidan suka shigo da sallama cikin takun nutsuwa da k'asaita, dukkan su manyan kaya suka saka sun karb'i jikin su sosai tunda suka shigo khamshi ya mamaye gidan. S tare suka amsa Rauda da take zaune a akan kujera ta d'ago ido suka had'a ido da Asad nan take gaban ta ya fad'i tayi saurin janye idanun ta. "Bismillah ku k'araso mana" Baba ya fad'a yana nuna musu wajan zama. Basu musa ba suka zauna suka gaisa da Umma kafin Hydar yace, "Mama ayi hak'uri nayi fama da rashin lafiya ne shiyasa ban kuma waiwayon ta ba, amma in sha Allah komai zai wuce yanzu." Umma tace, "Babu komai lafiya ai tafi gaban wasa, Allah ya k'ara lafiya." Hydar ya amsa da amin kafin ya kalle ta yace, "Ya jikin ki?." Sai da ta saukar da kanta k'asa kafin tace, "Da sauk'i." Bai kuma cewa komai ba Asad daman tunda aka gaisa bai sake magana ba. Khalil ne ya shigo yana fad'in, "Baba ga Yaya Anas yazo." Baba yace, "To ina zuwa." Hydar yana so ya basu kud'i amma bai fito da komai ba duk sai yaji kunya tana baibaye shi ganin hakan Asad ya d'auko kud'i a aljihun sa ya ajjiye kusa da Umma sannan yace, "ku fara shiri tafiyar ku baza ta wuce nan da sati ba" yana fad'ar hakan ya mik'e sai Hydar ne yayi musu sallama dan yasan Asad ya gama magana suka fita tare da Baba. A tsaye jikin mota suka ga Anas Baba ya k'arasa gare shi suna tare dasu Asad, har k'asa Anas ya gaida Baba kafin Baba yace, "Ranka ya dad'e wannan shine Anas mai neman auren Rauda, yana ta d'awainiya damu hatta maganin ta shine yake siya duk da lalurar da ta same ta bai saka ya guje ta ba" ya fad'a yana kallon Asad yana fad'a masa fuskar sa a washe da a nutsuwar magana da kamar Asad. Abinda Asad yake ji a zuciyar sa sabida abinda Baba yace bai tab'a jin irin sa ba tunda Allah ya kawo shi duniya, k'irjin sa har d'agawa yake sabida bala'in tashi hankalin da bai san zai same shi ba a lokacin, bai tab'a jin k'una da rad'ad'in da yake ji ba tunda yazo duniya. Suka yake ji a zuciyar sa in ya tuna kalaman Baba da yake cewa 'mai neman auren Rauda' nan take sai yaji kamar jiri zai d'auke shi ya fad'i k'asa. Kai kawai ya d'aga sukayi gaba Baba ya biyo bayan su yana godiya Asad ya bashi kud'i bai iya cewa komai ba suka shiga mota suka bar wajan. Gudu sosai Asad yake yi hakan ya saka Hydar kallon sa dan yasan shi ba ma'abocin gudu bane in kaga yans gudu ransa a b'ace yake ko kuma wani abun na damun sa,shiru Hydar yayi ya fara tariyo abinda ya faru tun daga farkon zuwan su har yazo inda yaga yanayin sa ya canja inda suke magana da Anas kenan dan shidai yasan har suka fito daga gidan su Rauda yanayin sa bai canja ba. Kallon Asad ya kuma yi yana nazarin sa kafin ya girgiza kai baice komai ba shima. Anas bai ga Rauda ba sai da akayi magriba aka kunna hasken soron sannan ta fito suka gaisa cikin soyayya yake kallon ta kana yace, "Naga wanda suka buge ki Baba yace min y'ay'an Sarkin garin nan, amma sun kyauta gaskiya abubuwan da sukayi ba ko wanne d'an mai mulkin ne zai shi ba; a ganin wasu da banbanci tsakanin su damu." Rauda ta d'aga kai tace, "Sosai ma kuwa sunyi k'ok'ari." "Yanzu yaushe ce tafiyar taku Egypt d'in?." "Ban sani ba gaskiya; ya dai ce bazai wuce sati ba." "Allah ya nuna mana, nima da ni za'ayi tafiyar in sha Allah." Murmushi kawai tayi kafin yace, "Rauda magana nake so zamuyi dake." Ta kalle shi tace, "Ina jin ka." "Tsakanin da Allah kina sona ko a'a?." Gabanta yayi mugun fad'uwa ta runtse idanun ta domin bata san me zatace masa ba komai ta fad'a tasan k'arya take, in tace tana son sa tayi k'arya in tace bata son sa nan ma tayi k'arya. "Kin yi shiru Rauda, ki bani amsa koda zata cutar dani gaskiya kawai nake son ji." Nan ma shiru bata bashi amsa ba yayi murmushi yace, "Na riga da na fahimci amsa ta Rauda, har yanzu baki bani wani matsayi a zuciyar ki ba, bazan sare ba zan cigaba da nemawa kaina gurbi har na samu ko za'a kai shekara goma nan gaba zan jure." Tausayin sa taji ya kamata ta kalli kanta ta ganta da k'afa guda d'aya gata ita ba kyau ne da ita ba amma namiji mai kyau da kud'i kamar Anas yana sonta duk da abinda ya same ta bai guje ta ba ya nuna shi dai ita yake so sai taji wani iri a zuciyar ta ta sunkuyar da kai a hankali tace, "Nifa ban ce ba." Murmushi yayi yace, "Nima ban ce kin ce ba ai Rauda, na fahimta ne kuma fahimta ta itace gaskiya." Zatayi magana Ummulkhairi ta fito zata wuce Rauda tace, "Ina zaki je da magariba?." "Zan je wajan Bala na karb'o miki magani Umma tace ya k'are." "Koma anjima sai muje tare." Ba musu ta koma ya kalle ta yace, "Ina ne wajan mai maganin na karb'o miki?." Rauda ta kalle shi tace, "babu nisa bakin titi ne, wajan wanda ka tura aka bawa kud'in maganin nawa fa." Anas yayi jim kana yace, "wanda na tura aka bawa kud'in magani? Yaushe kenan?." Rauda da mamaki ta kalle shi tace, "Wanda ka biya bashin maganin da yake kaina sannan ka siya kace na dinga karb'a har kud'in su k'are....? a ranar ka turo mana da kayan abinci da yawa da kud'i har da alqawarin Baba na keke napep, ka manta kenan?." Anas ya girgiza kai cikin mamaki ya rik'e bakin sa yace, "Rauda bani bane, duk abinda kika lissafa ban san anyi ba gaskiya sai yanzu da kika fad'a. Maganar keke napep d'azu muka magana da wanda zai kawowa Baba amma ban kawo ba tukunna." Rauda cike da al'ajabi tace, "Wai da gaske kake?." Ya d'aga mata kai yace, "Da gaske nake ban san anyi ba sai yanzu da kike fad'a min, abinda na sani na turo da da kud'i a baki kafin na dawo." Rauda ta sauke numfashi tana girgiza kai cikin tsoro da mamaki tace, "to waye ya aiko da wad'annan abubuwan haka?, duk a tunanin mu kaine shiyasa bamuyi tunanin kowa ba kaine kawai kazo ranmu a lokacin." Anas ya girgiza kai yana tab'e yace, "Damn it! Lallai akwai wani a gefe wanda yake neman shigowa cikin gwamnati na a shirye, tabbas ko waye ya aiko da abinda kika fad'a masoyin ki ne." Rauda kamar zata zubar da hawaye tace, "to waye?." "Allah ne ya sanshi Rauda" ya furta a sanyaye yana kallon ta jikin sa ya kuma yin sanyi jin abinda rauni a zuciyar sa. Shiru tayi shima haka tunanin ta waye wannan wanda yasan abinda yake faruwa da ita har yayi mata abinda yayi....? Koma waye tabbas yana bibiyar ta tunda har yasan da abinda Baba yake so yasan yanayin gidan su na rashin abinci yasan kuma da bashi a kanta wajan Bala mai magani, tabbas ya santa ko ya nemi sani a kanta. shi kuma tunanin waye wannan yake k'okarin shigowa rayuwar Raudan sa a b'oye...? Waye wanda yake k'okarin yin kutse a gwamnatin da yake so ya Gina...?, a ina yake? Waye shi?. Babu wanda zai basu amsa haka dukkan su suka rabu jikin kowa babu k'wari kowa da tunanin da yake zuciyar sa. Asad yana tsaye a jikin window d'akin sa yana kallon mutanen da suke shige da fice a gidan iska na kad'a shi kad'an kasancewar yanayin garin babu iska, ya rasa abinda yake masa dad'i gabad'aya hakan ya saka shi kallon waje ko zai ji dad'i, motsin da yaji a bayan sa hakan ya saka shi ya juyo yaga Hydar ne ya shigo ya k'araso kusa dashi ya tsaya yace, "Deaf akwai abinda yake damun ka tun lokacin da muka baro gidan su yarinyar nan na lura akwai wani abu, meye shi...?." Numfashi ya sauke baice komai ba ya cigaba da kallon window d'in kafin Hydar ya kuma cewa, "Ka sanar dani abinda yake damun ka ko zan iya maka maganin sa." Asad ya bar jikin Window d'in ya saka hannu a aljihu yace, "Ban san meyasa nake ganin ta ko haushe ba Hydar, even in my dreams I saw her lokaci zuwa lokaci." Jin yadda yayi maganar da rauni ya saka Hydar fuskantar sa yace, "Who is she?." Kallon idanun Hydar yayi kafin ya bar wajan yace, "Forget it." "Tell me please, bana so na ganka cikin damuwa ka sanar dani." Asad ya zuba masa ido na wani lokacin kafin ya tsaya jikin mudubi yana kallon kansa yace, "Hydar...." Sai kuma yayi shiru jin hakan ya saka Hydar yace, "Please in baka fad'a min ba wa zaka fad'awa?." "Ina ganin ta a mafarki Hydar tana taimako na ko yaushe tana bani kariya, after that na ganta a zahiri na tabbatar itace ta cikin mafarkina" sai kuma ya dafe kansa ya sauke numfashi yace, "ban san me nake ji ba but ina jin wani iri." ya fad'a yana dafe kansa ya jingina da bango yana lumshe idanun sa. "Wacece?." Shiru Asad yayi masa bai amsa ba Hydar ya sake maimaitawa sai daga baya yace, "Rauda!." Hydar gaban sa yayi mugun fad'uwar ya zaro manyan idanun sa waje yace, "What? Rauda!, I think yarinyar da muka je gidan su itace Rauda ba...?, yeah itace, oh my god!" ya fad'a yana dafe kansa yana kallon d'an uwan nasa da mamaki. Asad bai amsa ba daman yasan bazai amsa ba hakan ya saka yace, "deaf kana nufin kana son ta kenan?" Ya fad'a yana kallon fuskar sa. Ido Asad ya bud'e suka had'a ido yana kallon sa ya cize baki kafin ya girgiza kai alamun a'a, Hydar yace, "meye in ba so ba?." Asad ya d'age kafad'a alamun bai sani ba. Hydar yazo kusa dashi ya dafa shi yace, "Deaf kana sonta na tabbatar tun a mafarkin ka ka fara sonta naga hakan a cikin idanun ka, lokacin da mahaifin ta yake gabatar mana da wannan mutumin I saw so many changes on your face, like kishin abinda akace nake hangowa a kan idanun ka a kwanshe, that's mean kana son ta Asad." Zubawa Hydar ido yayi yana kallon sa har ya kai k'arshen maganar sa kafin yace, "A'a Hydar, hakan bazai yu ba." "It can be deaf, kai mutum ne kana da zuciya kana kuma da feeling ko da yaushe zuciyar ka zata kamuwa da soyayyar wacce ta aminta da ita. Kana son ta Asad ka amince dani." Numfashi ya fesar ya bar wajan ya koma gefen gado ya zauna ya jawo drawer ya d'auko passport d'inta ya bud'e yana kallon hoton jiki. Hydar ya murmusa ya k'araso gaban sa ya duk'a yace, "believe me your in love deaf, nasan tunanin ka ta ya zaka tunkari wannan yarinyar da batun love, ka bar min komai a hannu na zanyi komai." "Nooo Hydar ban saka ka ba, ban amince kuma da abinda kace ba." Hydar ya murmusa baice komai ba yana kallon sa taurin kan Asad shine yake cutar sa wani lokacin. Fita Hydar yayi daga d'akin yana murmushi yana kuma neman hanyar da zai gabatar da yayan sa ga Rauda. "How?" Ya furta bayan fitar Hydar ya kwanta a kan gado yana kallon sama yana jin zuciyar sa na bugawa da saurin gaske. Idanun sa ya kulle amma ita yake gani har lokacin ya bud'e ido sai yake jin sautin muryar ta a cikin kunnen sa hakan ya saka shi ya mik'e zunbur yana zaga d'akin. 'ta yaya zan fara son wacce aure na da ita bazai yu ba?, ta yaya zuciya ta zata so bayan Mama na raye?; oh my God ya zanyi?. firstly sai na cire ta a raina zan samu sauk'i, but itace take zuwa dreams d'ina bani na gayyace ta ba, meyasa take zuwa? Meyasa zuciyata take bugawa nake jinta a jikin ta?. oh my heart.' Abinda yake fad'a a zuciyar sa kenan ya dafe zuciyar sa da yake mugun gudu furta kalmaan da Hydar yayi ya saka zuciyar sa ta k'ara kaimi wajan gudu. A daren ranar Asad ya tabbatar da son Rauda yake ba tausayin ta yake yi ba, ya tabbatar da maganar Hydar tun ganin da yake mata a farki Allah ya ajjiye soyayyar ta a cikin zuciyar sa, ya tabbatar da itace macen da ta samu nasarar d'aukar kambun soyayya a zuciyar sa. A cikin daren ya fara tunanin nemo hanyar da fidda ta daga zuciyar sa tun kafin dare yayi masa. Washe gari. Mama na zaune tana karyawa ita kad'ai a falon ta Aliyu ya shigo ya zauna kusa da ita ya jawo kayan breakfast na gaban ta ya fara sha shima, bata ce masa komai ba sai da ya had'a tea yasha kana ya kalle ta yace, "Mamana kin san me Asad yake shirin yi kuwa?." Ta kalle shi tace, "kamar ya kenan?." "Mama ina wannan yarinyar da Hydar ya buge kika ce babu shi babu ita?." "Ina jin ka." "Itace dai yarinyar da ta kira ni da mahaukaci, at the end kuma kullum Asad sai yaje gidan su wajan ta, ya mata passport ita da iyayen ta zai kaita Egypt" ya fad'a yana kai grape bakin sa yana taunawa. Mama ta ajjiye cup d'in hannun ta tace, "Me kake fad'a ne haka Aliyu?." Aliyu yace, "Abinda mahaifita taji shi nake fad'a, ina da tabbacin Mamana tasan bazan mata k'arya ba." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, me ya had'a Asad da y'ar talakawa y'ar tallah har yake zuwa gidan su?." Aliyu ya kalle ta yayi murmushi yace, "sabida yana sonta ne, yana kuma tunanin auren ta!." "What? Aliyu kasan me kake cewa kuwa? Bana son shirme fa, wanne irin yana sonta Aliyu?." Aliyu ya mik'e tsaye yace, "Ba k'arya nake yiwa Mama ba, in kuma Mamana bata yadda ba zata iya sakawa a bincika zata gane maganar Aliyu gaskiya ce. but yana da kyau Mamana ta yiwa tufkar hanci tun kafin abun yayi nisa, mahaifita tasan in Abba yaji maganar nan babu abinda zai hana bai bashi ita ba. Faruwar hakan kuma daidai yake da Fulani mahaifita matar sarkin Katagum y'ar sarkin Kano jikar sarkin Kano zata zama inlaw d'in gurguwa, baka, kuma y'ar talakawa. At the end ita kuma zata zama matar sarki zata kasance a saman take Mamana, before Asad yayi sharawa da mahaifita sai ya fara da ita tunda itace sirrin sa!. Zata san abubuwa nasa da yawa kafin Mamana ta sani." Yana gama fad'ar hakan ya fita yana cize bakin sa alamun samun nasara dan yasan Mama ta cika tayi fammmm. #Vote #Share #Comments. *KWANTAN ƁAUNA* ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *021.* Hankalin Mama in ya kai miliyan ya tashi jikinta har rawa yake sabida tashin hankali ta tashi ta bar wajan da sauri ta nufi ciki hankalin a tashe sosai. Bata tab'a jin abu mai munin abinda Aliyu ya fad'a mata ba gabad'aya ya gigitata ta rud'e jikin ta har rawa yake yi sabida rud'ani. Kallon agogo tayi taga k'arshe sha d'aya na safe ya kusa ta saka takalmi da sauri ta fita zuwa b'angaren y'ay'an nata dan tana so ta tabbatar da abinda akace mata. Gab da zata shiga falon taji sautin muryar Hydar yana cewa, "Deaf in love, ban tab'a amincewa zaka fara soyayya da wata mace ba duba da yanayin ka da yanayin maganar, sai gashi ka fad'a ba tare da ka shiryawa hakan ba, wannan soyayyar taku itace silar accident." Asad dai baice komai ba Mama jin abinda ta jiyo ta sake firgicewa ta kuma tabbatar Aliyu bai mata k'arya ba abinda ya fad'a gaskiya ne tunda gashi har Hydar ya sani yana kuma kiran soyayyar da silar accident, har zata shiga falon sai kuma ta koma da baya da sauri ta koma b'angaren ta ta shiga cikin d'akin ta hannu na rawa ta d'auki waya ta kira Mum. Buga biyu Mum ta d'auki wayar kafin tayi magana tace, "Sadiya in kina da time ki shigo yanzun nan." Daga can b'angaren Mum tace, "An gama ranki ya dad'e, bani mintina goma zan iso." Mama bata kuma jin me tace ba ta yanke wayar ta cillar kan gado tana zaga d'akin hankalin ta yayi mugun tashi. Zagaye take daga nan zuwa nan ta kasa zama abinda bata tab'a tunanin zai faru ba shine yake k'okarin faruwa jinin ta wanda ya fito daga jikin ta shine da son y'ar talaka, jinin talakawa kuma nakasashshiya. Jinin nata ma kuma Asad da ta k'wallafa rai a kansa ace shine yake son y'ar talaka gurguwa mummuna wannan ba k'aramin abun kunya bane a wajan ta. Shigowar Mum ya saka Mama ta juya Mum ta k'araso da sauri tana fad'in, "Ranki ya dad'e lafiya kuwa?." "Ina fa lafiya; zauna mu tattara" Mama ta fad'a tana zama itama Mum d'in ta zauna. "Me ya faru?." "Meye ma bai faru ba Sadiya. Wani abu naji wanda yayi bazanar tarwatsa min zuciya ya jefa ni cikin wani hali wanda ban shirya tsintar kaina a cikin sa ba." Mum tace, "Ranki ya dad'e meye wannan d'in haka?." Mama tace, "Ace wai jinina wanda na haifa da kaina ne zai so jinin talakawa, y'ar talakawar ma y'ar tallah a titi bak'a kuma gurguwa? Ta yaya hankali na bazai tashi ba?." Mum ta dafe k'irji ciki da firgici tace, "mun shiga uku, gaskiya dole hankalin ki ya tashi domin kuwa wannan babban cin mutunci ne da cin fuska a gare mu duka ba ke kad'ai ba." "Bari kawai, yanzun nan naji maganar yanzun nan na tabbatar da ita amma zafi nake ji a k'irjina kamar ana tafasa min zuciya." Mum tace, "Amma waye da wannan d'anyen aikin? Nadai san Aliyu bazai aikata hakan ba sai dai Hydar dan nasan shine zai iya b'allo mana wannan ruwan." Mama tayi murmushin takaici zuciyar ta na sake cika taf da k'una da b'acin rai tace, "Wanne Hydar ana zaune qalau...? inda Hydar ne ai hankali na bazai tashi haka ba. Babbar giwar fa Asad; wanda yake jiran kujerar masarautar nan wai shine yake soyayya da yarinya irin wannan." Gaban Mum yayi mugun fad'uwa jin wanda aka ambata ta dafe k'irji cikin tashin hankalin da ya bayyana akan fuskar ta itama ta zaro idanu tace, "Asad! Mun shiga uku." Mama ta girgiza kai bata ce komai ba Mum tace, "Kuma kin tabbatar da maganar? In kika duba yanayin sa ranki ya dad'e sai naga kamar ba zai saurari irin su ba, Anya maganar nan daga majiya mai tushe take?." "Da Aliyu ya fad'a min ban amince sosai ba amma da naje na riska suna magana da abokin sirrin sa Hydar a sannan na tabbatar da Aliyu baiyi min k'arya ba. Sadiya jinina tafasa yake yi bazan lamunci wannan lamarin ba gabad'aya." Mum tace, "ni kaina jinin nawa tafasa yake ranki ya dad'e balle ke. Amma fa abinda mamaki anya kuwa ba asiri tayi masa ba? In ba asiri ba a yadda kika lissafo ta meye abin so a wajan ta har da yarima mai jiran gado guda zai d'aga kai ya kalle ta?." "Babban tashin hankalina kenan Sadiya." "To shi kin ji ta bakin sa?, ina nufin kun tattauna dashi akan lamarin?." "Bai san ma na sani ba." "Amma yana da kyau shima a tsawatar masa a kanta tunda yana jin maganar ki." "Wannan ba komai bane ba Sadiya na fara maganin yarinyar shi ba wani abin damuwa bane in nace bana so zance ya k'are; ita yarinyar ita nake so na jawa kunne ko dan tasan wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa. Ina so tasan ruwa fa ba sa'an kwando bane, ta banbance tsakanin zare da abawa." ta girgiza kai cikin gamsuwa tace, "Haka ne, yana da kyau mu tauna tsakuwa dan aya taji tsoro. Amma wanne mataki kika d'auka a zuciyar ki wanda kike gani zamu aiwatar dashi?." Mama ta kalle ta tace, "Shiyasa na kira ki domin inaso ko meye a aiwatar dashi yau bana son b'ata lokaci." Mum tayi jim tana tunani kafin tace, "Mu saka a d'auko ta a sace ta mu bata wahala sosai a sake b'alla k'afar ta ta kinga in aka mata haka zata shiga hankalin ta." Mama ta girgiza kai tace, "Shawara ce mai kyau wannan amma bazata yu ba, in labarin ya bayyana daga baya sunan mai martaba zai b'aci a garin nan za'a dinga yawo dashi ace nice na aikata hakan. Canja wata." Mum tace, "Haka ne. Mu tura mutane su je gidan ayi mata dukan tsiya ita da iyayen ta inda dama a b'alla ta a b'alla iyayen ta a kuma yi musu kyakykyawan warning wanda zai shiga jikin su, kin ga zasu ji tsoro dukkan su bama ita kad'ai ba har da iyayen ta." Mama tayi murmushi cikin jin dad'in maganar tace, "Wannan shawarar tayi d'ari bisa dari da kuma ita zamuyi amfani; amma fa bana son aje da wani dogari daga gidan nan dan tonuwar wannan maganar ma b'ata suna ne a idanun mutanen gidan nan balle mutanen gari, k'askanci ne a wajena ace yaron dana fi so cikin y'ay'ana yana bibiyar wata y'ar talakawa. Inaso aje dake domin kiyi musu kyakykyawan warning wanda zasu shiga hankalin su." Mum tace, "Wannan ki d'auka an gama ranki ya dad'e, zan samu mutane a waje muje muyi duk abinda kika ce ai abu ne mai sauk'i." Mama ta girgiza kai tace, "kuje a fara aiwatar da komai yanzu bana son b'ata lokaci Sadiya ke kin sani." Ba musu Mum ta mik'e tace, "An gama ranki ya dad'e" tana gama fad'ar hakan ta fita daga gidan da sauri. Mum na fita gida ta koma Jidda bata nan gidan babu kowa jikin ta har rawa yake dan tama fi Mama son d'aukar mataki a kan Rauda ta d'auki abinda zata d'auka ta fita daga gidan da sauri. Mata da maza ta had'a duka ta biya su aka tafi gidan su Rauda lokacin rana ta bud'e sosai. Rauda na zaune akan kujerar da ta saba zama ita da Umma da Inna bata nan sauran sun tafi makaranta, Baba ne ya fito daga d'aki bai fita da wuri ba Umma tace, "Malam kaji ashe duk abinda aka kawo gidan nan ba Anas ne ya bayar ba?." Baba ya kalle su yace, "kamar yaya kenan?." "Jiya take yiwa Anas mganar magani yake cewa shi duk abinda aka kawo bashi ya bayar ba, hankalina duk ya tashi ban san abin wanda muke ci ba wallahi, da alhairi yake neman mu ko akasin sa duk bamu sani ba." Baba yace, "Bashi bane ba? Kuma Rauda ba wasa yake miki ba kuwa?." Rauda tace, "Ya rantse min da Allah akan bashi bane ba." Baba cikin mamaki yace, "To amma dashi muka yi maganar ta kawai, da shi muka yi maganar keke napep d'in nan ya akayi wani daban yasan da ita?." Umma tace, "abinda ya d'aure min kai nima kenan." Shiru Baba yayi sai shiru can kuma yace, "Koma dai waye tunda ba sata nayi ba ai shikenan, ban kuma rok'i mutum ba Allah ne ya kawo min tsuntsu daga sama a gashe akan me zan ki ci ni kuwa?." Umma tace, "Amma malam ya kamata a bincika." Baba yace, "Na bincika ina? Nida ke da kowa bamu sanshi ba ina zanje na bincika nace ga wanda nake nema nida ban sanshi ba?; kar ki d'aga min hankali ina zaune lafiya dan Allah." "Assalamu Alaikum!" Aka fad'a daga soron gidan aka wuce Baba suka shigo cikin gidan mata uku maza biyu sai Mum ta hud'u. Baba da yake kallon ikon Allah ganin maza garada sun shige shi sun shiga tsakar gidan sa kai tsaye babu izinin sa ya k'araso yana kallon su yace, "Malamai lafiya kuka shigo min gida kai tsaye haka?." Mum ta k'are masa kallo ta kalle gidan tace, "Au wai wannan gida ne?, ni na d'auka wani kango wanda y'an zaman banza suke zama suna shaye-shaye da yiwa yara fyad'e muka shigo, wai ashe gida" ta fad'a tana kallon wanda suka shigo sai suka fashe da dariya har da tafawa. Rauda ta kalle su tace, "Malamai lafiya zaku shigowa mutane gida kai tsaye?." Jin yadda tayi maganar cikin tsiwa ya saka Mum kallon ta tace, "Oh kece gurguwar kenan, astagafirullah" ta fad'a tana dariya kafin tace, "Yadda aka kwatanta min munin ki ma ashe kin wuce wajan, wannan sai kace ragowar y'an wuta; wanne bak'in zunubi kuka aikata kuka haifo wannan?" Mum ta fad'a tana kallon Baba tana nuna Rauda. Rahma ta mik'e tace, "Dallah malamai me ya kawo ku gidan mu har kuke fad'a mana maganar banza?." Mum tace, "Koma gefe keda uwar ki y'an kallo ne. wajan ita da uwarta da uban ta muka zo ba ku ba, so ki tsaya kiyi kallo in kina da waya ki d'auko ki fara d'aukar video." "Wacece ke da zaki zo kina fad'a mana maganar banza da wofi?" Umma ta fad'a tana mik'ewa tsaye. Baba yace, "Malama lafiya me ya kawo ku gidan nan?." Ta juya ta kalli Baba tace, "Jan kunne nazo nayi muku gabad'ayan ku akan gangancin da kuke neman aikatawa, ina so ku jawa y'ar ku kunne ta fita hanyar wanda take cikin hanyar sa, babu shi babu ita domin shi d'in ba sa'an ta bane tazarar su kamar tazarar sama da k'asa ne. Yafi k'arfin ta ya kuma fi k'arfin dangin ku gabad'aya." Baba da gaban sa ya fad'i nan take Anas yazo ransa amma baice komai ba sai yace, "Akan wa kuke magana?." Mum ta gyara tsayuwa ta tofar da yawu tace, "Wannan gidan ai sai ka d'auki ciwo, bari kuga" ta fad'a tana d'auko facemask a jaka ta saka sannan tace, "Ina magana ne akan ASAD! Wanda kuka kamowa kurwa kuka asirice shi baya ganin kowa sai waccan bak'ar annobar, kaja mata kunne zata d'auko ruwan dafa kanta matuk'ar bata fita hanyar sa ba zatayi dana sanin da bata tab'a yin irin sa ba har abada." Rauda dake zaune cikin fusata tace, "Waye Asad? Meye shi suna ne ko gari?, mutum ne ko aljani?" Ta fad'a cikin masifa tana kallon Mum da ba ita take kallo ba. Mum ta juyo ta kalle ta tace, "kin sanshi ai basai na fad'a miki ba, tunda har kuka iya bin bokaye kuke so ku kamo zuciyar sa ai kinfi kowa sanin sa. ke banda tsaurin ido ma da kwad'ayi irin na jikar talakawa ina ke ina Asad?, kalle ki fa kamar wacce aka d'auko daga cikin bak'in gawayi, tsabar bak'in da yake fuskar ki sai a d'auka jikar shaid'an ce ke, kalli k'afar ki abinda ya rage miki hawa kan titi ki fara bara amma ki fara tunanin Asad dan talauci ya toshe miki kwakwalwar ki." "Kece dak'ik'iya mara hankali wacce bata san darajar d'an adam ba babu girma sai na jiki, shi wanda kike magana a kai bansan da zaman sa bama balle na d'aga idanuna na kalle shi, dan haka kija bak'ak'en k'afafun ki a fitar mana daga gida" ta fad'a cikin rashin kunya tana mata ihu. Mum ta girgiza kai tace, "lallai yarinya zan nuna miki ni ba sa'ar yin ki bace, ga sa'a ta nan" ta fad'a tana tsinkawa Umma dake tsaye mari ba zato babu tsammani. Baba ya yunk'uro zai zo wajan mazan suka rike shi gam ta juya yana kallon sa ransa a b'ace yace, "Ke wacce irin mahaukaciya ce shashasha? Ya zaki shigo har cikin gidana ki saka hannu ki daki matata?." "Dan na nunawa y'ar ka itace abokiyar yina ba ita ba, kuma....." saukar marin da taji a tata fuskar ya hana ta k'arasawa ta juyo a razane taga Rauda a tsaye da sandinan ta tana wuci cikin b'acin rai Mum na juyowa a fusace Rauda ta sake bata wani sabon marin da batayi tsammani ba. Cikin fusata da rashin kunya da yatsa ta nuna ta tace, "A kaf duniya babu wanda ya isa ya tab'a min iyayena k'yale shi ciki kuwa har dake, in zafin kai kike ji dashi na fiki, in rashin kunya ce itama na fiki, in iskanci ne shima na fiki, duk abinda kike ji dashi a tafin hannuna kike na dame ki na shanye. Na rantse da Allah kika sake dukar min uwa ko kika sake tab'a min uba sai na sake marin ki sai naga abinda zaki min. Banza babbar banza mara hankali mai tunanin jakuna" ta fad'a tana hararar ta cikin b'acin ran da ya bayyana k'arara a ka fuskar ta. Mum da take kallon ta hannun ta dafe da kuncin ta kasa cewa komai tayi sai jikinta da yake rawa sosai alamun b'acin rai tsanar ta na shiga ko wanne sak'o da lungu na jikinta, tunda take ba'a tab'a tozarta ta kamar yadda akayi mata yau, yarinya k'arama ta fad'a mata wannan magana mai zafi har ta mare ta..?. Hannu ta saka da k'arfi ta tankad'e Rauda ta janye duka sandinan ta kalli matan tace, "Me kuka jira ne ku fara aiwatar da abinda ya kawo mu ku nuna musu mu ba sa'anin su bace" ta fad'a tana marin Rauda da k'arfin gaske. Nan da nan suka shiga dukan Umma da Rauda kamar Allah ya aiko su Inna da ta shigo lokacin ita da Rahma suka zo ceto aka had'a dasu ana duka Baba yana hannu an rik'e shi ya kasa komai. "Asad yafi k'arfin ta ku sake b'alla k'afar tata dan uban ta" Mum ta fad'a tana daga gefe ana dukan Rauda kamar zasu kashe ta. Baba yace, "Waye Asad din nan da kike magana a kansa? Bamu sanshi ba balle muyi abinda kuke so. Dan Allah ku bar dukan su ko waye zata rabu dashi." "Ai ko baka ce ba sai ta rabu dashi, ka kuma ce mata ta karya asirin da ta yi masa in tana son zaman lafiyar ta da ta uwar ta har ma da kai ubanta. Ta fita daga sabgar Asad d'an sarki sai y'ar sarki ko y'ar mai kud'i ba d'iyar talaka y'ar tallah kamar ta ba." Ganin sun duku ya saka tace, "Guys ku shigo ku d'aye min kwanukan rufin gidan nan naga inda zasu kwana yau daman naga langa-langa ne kawai" ta fad'a daga k'arfi sai ga maza uku sun kuma shigowa suka hau saman d'akin suka farar b'alle kwanon rufin d'akin wanda yayi gardmar cirewa suna huda shi da abu mai kaifi. Mum ta saki dariya tana tafa hannu ta kalli Rauda da bakin ta ya fashe jini na zuba a gefe tace, "Ke ba y'ar marasa kunya ba...? yanzu kika fara gani, har ni zaki saka hannu ki mara da yake baki da mutunci ko? ai kin tarowa kanki bala'i da masifa har ki mutu. Ku k'yale su haka kuzo mu wuce ai ko yanzu sun ji a jikin su; sai ku ja mata kunne in bata fita daga rayuwar Asad ba wallahi nan gaba sai mun saka an rushe gidan nan an kuma yi musu abinda yafi haka, banzaye mahaukata masu kai kansu inda Allah bai kaisu ba" tana fad'a ta shige ta fita suma suka bi bayan ta mazan saman suka diro suka bi bayan ta. Suna sakin Baba yayo kan Umma a guje dan ita kamar bata numfashi ma gwara Rauda tana motsawa amma Umma na kwance sosai. Kuka Rauda take yi sosai Rahma da ta maku tana gefe ganin sun tafi ya saka tayo kan Rauda ta d'aga ta fuskar ta duk jini hawaye na bin fuskar ta. Baba ya fita da sauri hankalin sa a tashe ya yi sa'a mai chemist d'in yana nan ya tawo dashi gida aka fara duba Umma da take kwance. Fita yayi ya dawo da kayan aiki aka shiga yiwa Umma taimakon gaggawa aka samu ta farfad'o dukan fuskar ta aka gyara aka saka mata ruwa dan jikin ta yayi zafi sosai ga hannun ta an mata targed'e. Kan Rauda akayi aka gyara mata fuska aka bata maganin ciwon jiki dana ciwon da taji a fuskar ta har loksckn kuka take. Ba kukan dukan take ba kukan zuwa gida da akayi aka wulaƙanta su take yi in ta kalli Umman ta bata sanin sanda hawaye yake sake zubo mata. Yana fita aka zo da mai gyaran targad'e ya gyara hannun Umma aka d'aure hannun sannan suka tafi Baba jikin sa duka yayi sanyi. Kuka sosai Rauda take yi tana jikin Rahma Baba yace, "Rauda ban fahimci abinda matar nan take nufi ba, meye tsakanin ki Asad har hakan ta faru?." Kai take girgizawa tace, "Wallahi babu komai Baba, bansan wanda suke nufi ba; sun yi amfani da power sun zo sun wulak'anta mu sabida bamu da gata bamu da wanda zai bi mana hakkin mu. Wallahk Baba bazan yarda ba sai maganar nan taje gaban hukuma sai an bi mana hakkin mu, Baba sai an karb'a mana hakkin mu bazan amince da wannan cik mutuncin ba" ta fad'a tana kuka sosai. Baba yace, "Nima bazan bari ba Rauda cin kashin yayi yawa. Tunda sukayi maganar Asad d'an sarki zanje wajan mai martabar da kaina na kai masa k'arar abinda ya faru, ai talauci ba hauka bane ba. Meye tsakanin mu dasu in ba silar ciwon nan naki ba? Dan kawai yana sauke nauyin da yake kansu na nema miki lafiya kawai sai azo har gida ayi mana wannan shirmen...? To wallahi bazan amince ba." Kuka take ita dai har lokacin tana kallon saman d'akin Umma da aka kwashe kwanon kai rana tar a cikin sa sai wani b'angaren da aka huda, a hankali bacci ya d'auke ta Allah ya saka akwai inuwar rumfa a wajan. *☆☆☆* B'angaren Asad bai san me yake faruwa ba suna tare da Hydar a company dan bai koma aiki ba yana wajan Asad, sai da sukayi azahar suka bar company suka koma gida dan yunwa Asad yake ji. Suna b'angaren su Suhaima tazo ta kawo musu abinci ta ajjiye ta zuba musu kamar ko yaushe, Asad ya d'auki wanda ta zuba masa ya d'auka zai kai bakin sa Suhaima ta kalli Hydar tace, "Yaya Hydar wai me ya faru ne naga ran Mama a b'ace?." Hydar ya fara cin abinci kana yace, "Ina zan sani Suhaima nida na dawo yanzu?." "Naji tana waya tana a dake su bata kai matsayin yin soyayya da wanda ta haifa ba, na d'auka ma ko kaine ka fara soyayya da wata poor lady d'in ta saka ayi mata punishment." Gaban Asad ya fad'i ya ajjiye cokalin daman tunda ta fara maganar bai kai abincin bakin sa ya kalle ta yace, "Suhaima me kika ji tace?." "A yadda take maganar dai an tura gidan su yarinyar ayi mata duka amma ban san wacece ba. Naji tana a dake ta inda dama a sake b'alla k'afar ta babu abinda aka siya ayi." Mik'ewa Asad yayi ya d'auki key na mota da sauri ya fita, ganin hakan Hydar ma ya ture abincin ya mik'e tare da bin bayan sa suka fita Suhaima ta bi su da kallo. Mota suka shiga suka tafi gidan su Rauda gaban Asad sai fad'uwa yake yi har suka faka a k'ofar gidan, babban burin sa bai wuce Allah yasa basu illatata ko wani nata ba. Baba suka gani ya fito yana waige-waige ganin hakan ya saka Asad ya fito daga motar Hydar ma ya biyo bayan sa suka k'araso kusa dashi, Baba na ganin su tun kafin su gaisa yace, "Kamar kusan kune a raina, me muka yi muku haka da za'a aiko azo a ci mutunci na dana iyalai na?, me Rauda tayi muku har haka aka yi mata wannan hukunci....? dan Allah ku fad'a na baki hak'uri." Asad ya kalli Hydar shima ya kalle shi kafin Hydar ya kalli Baba yace, "Baba meye ya faru?." Baba yace, "Kuzo muje ku gani" ya fad'a yana yin gaba suka bi bayan sa gaban Asad sai fad'uwa yake yi sabida fargaba da tashin hankalin abinda zai gani a cikin gidan. *KWANTAN ƁAUNA* ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *022.* A hankali suke takawa zuwa cikin gidan suka shiga da sallama idanun sa ya fad'a na Rauda da take zaune cikin ranar da bud'e har taje inda suke fuskar ta duk taji ciwo musamman bakinta da ya fashe. Runtse idanu Asad yayi ya kawar da kansa gefe daga kallon ta kafin Baba yace, "Kunga irin abinda aka yi mana. kalli mahaifiyar Rauda har targad'e aka yi mata, ga ita kanta Rauda da ta kasa tashi tsaye tun da akayi abun bamu sani ba ko an sake karya mata k'afa ne; kalli saman d'akin babar Raudan sun cire kwanon bayan sun dake ta. Me muka yi muku haka?." Hydar ya gyara tsayuwa yace, "Kuyi hak'uri Baba bamu san abinda ya faru ba kenan sai yanzu muke jin labari shine muka tawo nan d'in kai tsaye dan muyu maganin abun, Mama kiyi hak'uri bamu san abinda ya faru ba kenan" ya fad'a yana kallon Umma. Rauda ta kalle shi ta zaro idanu waje cikin zallar b'acin rai da tashin hankali tace, "Ba tun yau ba daman in aka cuci mutum sai ace yayi hak'uri, in aka zalumci talaka sai ace yayi hak'uri ya yafe sabida bashi da gata da wanda zai shige masa gaba ya karb'i hakkin sa. dan an fimu kud'i da mulki ba hakan yana nufin an mufi daraja a duniya bane, muma mutane ne baza mu lamunci azo har cikin gidan mu a ci mana mutunci sannan a dake mu ba kuma ace muyi hak'uri; bazai yu ba wallahi. Meye ya had'a mu daku da za'a dake mu a kanku? Tsautsayi ne ya ratsa tsakani fa akwai shikenan sai ya zama abin tashin hankali?, naga tun kafin bayyanar ku cikin matsayin wanda suka bige mu ai rayuwar mu muke yi babu abinda muka nema muka rasa, daga shigowar ku rayuwar mu har an fara neman raywuar mu?" Ta fad'a cikin fusata da masifa tana kallon su dukkan ranta a b'ace ba. Hydar yazo wuya ba'a tab'a yi masa irin wannan fad'an ba a duniya sai yau nan take ransa ya b'aci amma babu yadda ya iya yayi k'okarin b'oye fushin sa kana yace, "Na fad'a miki ko meye ya faru babu sanin deaf babu sani na, inda mun sani hakan ai baza mu bari ta faru ba. Yanzu ake sanar damu muka tawo dan muga su waye amma bamu same su ba, meyasa baza ki fahimta ba?." "Zuwan ku d'in banza da wofi dashi gwara ku zauna a gida ku sha a.c yafi min wallahi. Sai da aka gama ci maa mutunci sannan zaku d'auko k'afa kuce wai kunzo to kuyi mana me? Ku bamu hak'uri kenan ko?. Ni abinda nake so naji ma akan wanne dalili zasu dake mu har su yiwa Ummana wannan rashin mutuncin?, suna zancen wani Asad ni meye had'ina da wani Asad?, su ya dama bani ba wallahi in ma wani sharrin aka je aka min can ta matse muku amma wallahi sai maganar nan taje gaba in ba haka ba na shiga radio na yayata abinda aka mana ko babu komai k'imar gidan ku zata ragu." Hydar ya kalli Asad da ya zuba mata idanu kawai yana kallon ta ya girgiza kai yana cize bakin sa cikin zallan b'acin ran da yake ji a zuciyar sa, in badan Asad ba ta isa ta dinga fad'a masa wannan kalmai marasa dad'in jin ya tsaya yana kallon ta bai hukunta ta ba?. Ya daure yace, "Ni da kaina nace kuyi hak'uri muje a fara yi muku magani kafin komai." Kafin Baba yayi magana ta kuma cewa, "Bama so ku rik'e kayan ku talakawan da ake rainawa sun yiwa kansu magani kuma zasu karb'arwa kansu hakkin kansu." "Wai ke meye haka ne? Ina baki hak'uri kina sake d'aga min murya kina fad'ar duk abinda yazo bakin ki?, wani dalili kawai ya saka nake tsaye a gaban ki ina baki hak'uri amma badan shi ba bazan zo inda kuke bama balle ki samu bakin fad'a min abinda kike so. Na fad'a miki kuyi hak'uri zaku ji abinda ya jawo hakan wanda ban sani ba shima wanda akayi dukan dan shi bai sani ba, meyasa kike haka ne?" Ya fad'a cikin fad'a yana kallon ta ransa a b'ace. Zata kuma magana Baba yace, "Muna so muji dalilin dan gaskiya sai maganar nan taje kunnen mahaifin ku sai naji dalilin dukan da aka yiwa iyalai na har cikin gida." "Firstly ku fara ganin likita a duba lafiyar ku, please Baba kuzo muje" Hydar ya sake fad'a yana kallon Baba. Rauda ta kalli Asad da idanun sa yake yawo a kanta amma in baka fahimta ba baza kace ita yake kallo ba taja dogon tsaki tace, "Wanda akayi dan shi d'in yana tsaye k'ikam shi bazai bada hak'uri ba sabida bamu kai ya bamu hak'uri ba an dake mu an daki banza kenan, to wallahi sai na d'auki mataki ina k'yale komai banda a tab'a min iyayena." D'auke kai yayi daga kanta Baba ya kalle ta yace, "Ya isa haka Rauda bana son sake jin bakin ki, ke Rahma tashi mu taimaka mata ta tashi aje asibitin." Tare da Baba suka fita Rahma da Inna suka fito da Umma da Rauda suka shiga bayan mota Baba ma ya shiga Hydar ya shiga mazaunin driver dan yasan Asad bazai iya tuk'i ba ya ja motar suka tafi asibiti. Babu wanda yake magana a cikin su har suka je asibitin ya saka aka duba su aka sake gyara ciwon hannu Umma aka sake wanke ciwukan fuskar su duk da ba masu yawa bane ba. A d'akin da suke suna hutawa bayan an gama Umma taji dad'in jikin ta su Hydar sunje sun dawo Asad ya kalli Umma yace, "kiyi hak'uri Mama." Umma tace, "To ya zanyi in ba hak'urin ba?, babu komai." Hydar yace, "Baba zaku koma wani gidan daman kafin a gama gyara wancan zan kai ku yanzu suma wad'ancan zan koma na kai su gidan, in kawai abinda kuke da buk'ata sai a d'auko muku." Baba yace, "to sai muje tare in yaso akwai k'anwar Rauda nasan zuwa yanzu ta dawo daga makaranta sai ta d'auko musu abinda zata d'auko." Rauda Hydar ya kalla da take kallon wani wajan daban ya kalli Asad da yake a tsaye baice komai ba shima ya d'auke kansa. "Baba muje" Asad ya fad'a yana kallon su suka tashi suka fito zuwa inda motar take suka shiga suka tafi. Kusa da unguwar su suka tsaya jikin wani gida babba flat mai maroon d'in gate da maroon d'in fenti yayi kyau sosai kamar sabo dan kana gani kasa ba'a zama a cikin sa kawai yana ajjiye ne. Asad ya fito Hydar ma ya fito suka cewa Baba shima ya fito. Gidan suka shiga Jim kad'an suka fito Baba yace, "Kuzo muje ciki." Umma ce ta fita Rauda kam k'in fitowa tayi Baba yace, "baza ki fito bane ba?." Ta kalli Baba zuciyar ta kamar ana tafasa ta sabida b'acin rai tace, "Zan fito daga baya." Shi da Umma suka shiga gidan ta bisu da kallo tana kiyasta adadin matakin da zata d'auka a zuciyar ta. Hydar ne ya shiga gaban motar ya zauna bai kalle ta bayace, "ki ajjiye abinda kike ji dashi a kanki ki fahimci abinda zan fad'a miki yanzu. Ina so ki fahimci abun dakyau kiyi tunanin kalaman da suka fad'a miki akan Asad ki gano me hakan yake nufi." Shiru tayi dan har lokacin a fusace take kafin ta girgiza kai tace, "A yanayin maganar su yayi kama da b'atan kai sukayi suna so suje wajan wacce take sonsa ko dai abinda yayi kama da haka." Hydar yace, "good girl. Ba b'atan kai sukayi ba Rauda tabbas kece." "Nice me?." "Kece wacce Allah ya d'orawa Asad k'aunar ta a zuciyar sa!." Gaban Rauda ya fad'i har ta dafe k'irji bata san tayi ba ta kalle shi cikij tsananin bugawar zuciya a firgice tace, "Me kake nufi?." Hydar ya juyo ya kalle ta yace, "Ina nufin Asad yana sonki yana kuma fatan auren ki dalilin da ya saka wanda basa goyan baya suka fara d'aukar mataki a kanki, dan farawa akayi in maganar ta cigaba tabbas akwai wasu abubuwa a gaba wanda zan iya cewa sunfi wannan. Na zab'i na fad'a miki ne ba tare da ya sani ba dan kisan dalilin da ya saka akayi miki haka." Shiru Rauda tayi ta kasa magana sai zuciyar ta da take bugawa da sauri-sauri tana sake maimaita kalmar yana sonta a zuciyar ta cikin mamaki da tsoro da ya bayyana a gare ta. "Sona fa kace? Ta yaya zan amince da hakan bayan matsayin sa da nawa akwai banbanci?, har yaushe mukayi had'uwar da zai fara sona?, har yaushe ya sanni? Yaushe ya ganni da zai soni?. Wad'an nan kalaman naka sun sake bani tsoro sun tabbatar min da akwai wani abun da kuke nema dani shiyasa tun yanzu kuka fata bayyanar da nufin ku a gare ni. Shin me nayi muku?." Murmushi Hydar yayi yace, "Inda akwai abinda muke nema dake da tuni mun aiwatar dashi babu wanda ya sani basai anzo yanzu ba. ki tuna abinda Aliyu yayi miki wanda babu wanda ya sani har kawo gobe kinga da munyi niya zamu iya aikata abinda yafi haka babu wanda yasan mune muka aikata, in munso har ranki zamu iya d'auka babu wanda sai san mune to a kan me dan muna da wata manufa a kanki sai biyo ta wannan hanyar?. In muna da manufa a kan ki bazan tankare ki da wannan maganar ba domin furta tama ba ga ko wacce mace ya dace ba sai wacce ta isa, ke kin san su waye mu basai an fad'a miki ba." Kalaman sa sun shige ta sosai bakin ta ya mutu murus ta kasa furta komai domin ta tabbatar da abinda yace gaskiya da akwai manufar da suke da ita baza su tunkare ta ba, kallon window tayi zuciyar ta na zillo a lokacin Asad yazo wajan shida Baba. Baba ya bud'e mata yace, "fito ki huta zamu jemu tawo da sauran." Jikinta ya mutu Baba ya rik'o ta suka shiga cikin gidan da ta kasa kallon sa sabida tunanin abinda aka fad'a mata ya tsaya mata a zuciya kamar an soka mata mashi a zuciyar ta haka take ji. Gida ne babba sosai mai babban ma'ajiyar mota sai babban tsakar gida sai kuma k'ofa guda uku a tsakar gidan. Guda d'aya suka shiga sai gasu a falo babba mai kyau wanda babu abinda babu a cikin sa har da a.c da duk wani abun buk'ata akwai shi a falon ya zaunar da ita ya koma. Basu jima ba suka dawo dasu Inna bayan sun d'auko kayan sawa da abin buk'ata suka shiga ciki Baba ya tsaya yace ya kalle su, "To mun gode muku Allah ya saka da alkhairi, kunyi bakin k'okarin ku akan mu badan ku ba da bamu san inda zamu je mu zauna ba. amma duk da haka inaso maganar nan tazo gaban mai martaba." Hydar yace, "Kar ka damu Baba mu da kanmu zamu sanar masa baza a bar maganar ba in sha Allah. Za'a kawo abinci yanzu." Baba ya amsa ya shiga ciki suma suka shiga motar Hydar ya fincike ta zuwa gida. A can gida kuwa Mum tana wajan Mama ranta a b'ace take zayyanawa Mama abinda ya faru tana had'awa da k'arya akan abinda Rauda tayi mata, "Wai ni yarinyar nan zata d'aga hannu ta mara? Har tana fad'a min wai me zatayi da Asad a fad'a masa shi da ya nace mata ya daina zuwa inda take?. Ranki ya dad'e meyasa Asad zai mana haka dan Allah? Kinga yarinyar kuwa?; ai duk yadda kike musalta munin ta ya wuce haka wallahi. kaf unguwar gidan su yafi na kowa lalacewa, gaskiya Asad bai kyauta mana ba wannan cin mutunci ne a gare mu gabad'aya." Ran Mama ya sake b'aci ta girgiza kai tace, "Ta mare ki!, lallai yarinyar nan tana buk'atar babban mataki ba k'arami ba. Zan yi maganin abun da gaggawa bazan d'auki wannan cin kashin ba, k'aryar Asad wallahi babu shi babu ita dole ya rabu da ita matuk'ar yana son zaman lafiya. Ina shi ina wannan yarinyar?" Ta fad'a tana dafe kai cikin zallar takaici. "Ai kuwa ranki ya dad'e bazai rabu da ita ba, Gwara ma mahaifiyata ta dajna tunanin hakan dan bazai yau ba" Aliyu ya fad'a yana shigowa ciki yana kallon su. Mum ta kalle shi tace, "Haba Aliyu! meyasa zaka ce haka?." Yace, "To abinda yake zahiri na fad'a ai Mum, kuna nan kuna tunanin kun d'auki mataki kunyi maganin ta shi kuma yana can yaje gidan su ya d'auke su da kansa ya kaisu asibiti an musu maganin ciwon da suka ji ya mayar dasu d'aya daga cikin guest house d'in sa, yanzu maganar da nake suna cikin gida mai a.c da TV kamar gidan ki." A fusace Mama ta tace, "da gaske kake ko da wasa Aliyu?." "Ni na isa nayi wasa da mahaifiyata? Abinda na fad'a gaskiya ne bazan yiwa Mamana k'arya ba." Mum tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. mun shiga uku, me yarinyar nan ta yiwa Asad ne haka?." Mama ta fusata tace, "ko me tayi masa dole ya sake shi bazan lamunci abinda yake niyar tunkaro ni ba, wannan raini ne da k'askanci a idanun mutanen gidan nan a gare ni. ya zama dole Asad ya bar maganar nan matuk'ar yana son zaman lafiya a cikin gidan nan." Aliyu yace, "ko kuma Mama ta hak'ura ba ta bar shi da ita domin kuwa da zarar maganr taje gaban Takawa zancen ta ya k'are kuma yanzu haka suna kan hanyar zuwa gare shi." A haukace Mama tace, "Kira min shi Aliyu, maza ka kira shi" ta fad'a jikin ta har rawa yake tana zaga falon tana ji kamar zuciyar ta zatayi bindiga ta fashe. "Mama baiyi picking ba nasan daman ko Mama ce ta kira shi yanzu bazai d'auka ba balle kuma ni" yana fad'ar hakan ya fita daga falon hankalin Mama da Mum ya sake tashi Mama kamar ta zubar da hawaye haka take ji. A b'angaren su Asad ana idar da sallar la'asar Asad ya shiga b'angaren su Hydar ya fita bai wuce ko ina ba sai wajan mai martaba ransa a b'ace. Basu san mai ya faru ba dukkan su sun samu kiran gaggawa daga gare shi har Asad suka isa b'angaren nasa ba tare da sanin abinda ya faru ba. A zaune Asad ya tarar da Mama ga Hydar a gefe nan take gaban sa ya fad'i abinda ya faru yazo ransa ganin su kad'ai ne a ciki ya samu waje ya zauna Mai martaba yace, "Asad abinda Hydar ya sanar dani haka ne?." Shiru Asad yayi dan bai san mai Hydar yace ba ya d'ago ya kalli Hydar d'in kafin ya girgiza kai yace, "Haka ne takawa." "To ma sha Allah. Bazan ce komai ba a yanzu zan tura aje a tawo min da mahaifin yarinyar da kuma ita yarinyar, Hydar kaje kazo dasu ka kai su b'angaren baya dan bana son cikin gida su san abinda yake faruwa in yaso in kazo dasu ka sanar dani zan zo da kaina." Hydar ya amsa da to ya tashi ya fita babu wanda ya kuma magana a cikin su mai martaba baice komai ba ran Mama a b'ace tana ta hararar Asad shi kuma kansa na k'asa baya ganin me take yi. Ba jima Hydar yazo da girmawawa ya sanar dashi gasu can yazo dasu ya yace, "Ku je can gani nan zuwa." Tashi sukayi Mama kamar ta shak'e wuyan Asad haka take ji sai binsa take da kallo tana kwafa suka fita shi kuma ya kasa ma had'a ido da ita. Ta wata k'aramar k'ofa mai martaba ya fita babu wanda ya lura da fitar sa sai gashi ya bayyana a harabar b'angaren da yace a ajjiye su ya shiga falon kowa ya mik'e tsaye banda Rauda da take k'okarin tashi ya kalle ta yace, "yi zaman ki" ya fad'a yana k'arasowa ya zauna a akan kujera duk suka zauna a k'asa. Mai martaba ya kalli Baba yace, "Malam Adam mun same ku lafiya?." Baba jikin sa har rawa yace, "Allah ya ja da ran mai martaba, lafiya lau." "To ma sha Allah. Ya akaji da abinda ya faru kuma?." "Mun gode Allah ranka ya dad'e." "Muna sake baku hak'uri akan abinda aka yi muku tabbas ba'a yi muku adalci ba. Meye sunan naki?" Mai martaba ya fad'a yana kallon Rauda. "Rauda" ta furta a hankali mai martaba yace, "Kiyi hak'uri kinji Rauda duk abinda aka aikata muku ga wacce ta saka nan, babu babu wanda yasan abinda ya faru sai bayan ta saka an aikata d'in da baza mu bari hakan ya faru ba" ya fad'a yana nuna Mama da take zaune a gefe kana yace, "Mahaifiyar su ce komai ya faru itace ta saka ayi muku. gaku gata nan in kun yafe mata a k'yaleta in baku yafe ba kuma a yi mata hukunci daidai da ita kowa yasan mulkina baya lamuntar zalunci koda jinina ne ya aikata." Rauda zatayi magana Baba yayi saurin katse ta yace, "Allah ya k'arawa sarki lafiya, babu komai mu hakan ma da akayi mana an nuna mana mahimmacin mu, an nuna mana muna muna da darajar da Mai martaba da kansa sai bamu hak'uri,ya wuce mun gode sosai." Mai martaba yace, "ka barta tayi magana ita aka yiwa ba kai ba, Fad'i abinda yake ranki." Rauda ta kalli Baba yana kallon ta tace, "Babu komai ya wuce." Mai martaba yace, "kin tabbatar ya wuce ba'a takura ki ba?." Rauda tace, "Ya wuce ranka ya dad'e." Mai martaba yace, ma sha Allah. Rabi'atu basu hak'uri" ya fad'a yana kallon Mama. A firgice ta kalli Mai martaba suka had'a ido kallon da yayi mata ya saka ta d'auke kai tana girgiza kai tare da taune leb'en ta na k'asa cikin wani abu wai shi bak'in ciki da taikaici ta kalli Rauda da take kallon ta itama ido cikin ido ta cize bakin ta kafin tace, "Ayi hak'uri." Murmushin jin dad'i Rauda tayi har cikin zuciyar ta taji abinda aka yi musu ya wanke tass ko babu komai mace mai izza ta basu ko iya nan sun ci riba. Baba ya washe baki yace, "babu komai ranki ya dad'e, ya wuce." Mai martaba yace, "mun samu labarin an buge wata yarinya kwanaki amma bamu san ba'a kula da lafiyar ta ba tunda Hydar ya kwanta ciwo, Shima muna neman afuwa a kan hakan kuma nasan Asad zaiyi duk abinda ya dace in sha Allah." Baba yace, "Allah ya taimaki Mai martaba, komai ya wuce mu a wajan mu. Kamar yadda mai martaba yace Asad yana iya bakin k'okarin sa akan rashin lafiyar Rauda." Mai martaba ya girgiza kai yace, "mun gode da karamcin ku a gare mu baki d'aya, muna tabbatar muku da babu abinda zai sake samun iyalan ku ta k'ark'ashin wannan gida in sha Allah." Shiru babu wanda yayi magana kafin mai martaba yace, "Tunda hakan ta kasance ina neman wata alfarma a wajan ka." Baba yace, "A wajena kuma Ranka ya dad'e?." "Eh wajan ka." "Umarni shine naka a gare ni ba alfarma ba." "Alfarmar dai nake nema ka amince na fad'i abinda nake so." "A shirye nake da sauraron ka, Allah ya ja zamanin ka." Mai martaba ya kalli Asad yaga kansa yana k'asa ya kalli Mama yaga tana kallon sa kafin ya kalli Baba yace, "D'ana Aliyu wanda nakewa lak'abi da Asad gashi a gefe yaga y'ar ka Rauda ya yaba da hankalin ta da kuma tarbiyyar yace yana so. Bama shi ba ni kaina na yaba da ilimin ta da kuma tarbiyyar ta da nuna b'acin ranta a kan abinda zai tab'a iyayen ta. Muna neman alfarmar a bashi ita inda damar hakan!." A take k'irjin mutane hud'u suka buga a wajan, Mama, Asad, Rauda, da Baba. A tare suka kalle shi shi kansa Asad d'in ya gigice bai san abinda zai fad'a ba kenan dan bai shiryawa hakan ba a lokacin kwata-kwata. Baba baki na rawa yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, maganar da naji ce nake kokwanto anya ba mafarki nake ba?." Mai martaba yace, "ba mafarki kake ba Malam Adam abinda kaji gaskiya ne. Amincewar ka da tata amincewar nake so a d'aura auren ranar juma'ar nan mai zuwa dan bana son a d'auki lokaci. amincewar ku kawai nake nema amma babu dole in taga bai mata ba karta takura kanta, in kaga kaima baza ka iya bashi auren ta ba duka ba abin damuwa bane. Ina tambayar ka a matsayin siriki ne ba matsayin shugaba a gare ka ba, ka kalle ni matsayin sirikin ka ka fad'a min amsar da take zuciyar ka. Zaka iya bawa Asad auren Rauda ko A'a?!." Tirk'ashi!🏃🏼‍♀️😂 #Vote #Share #Comments *KWANTAN ƁAUNA* Fitattubiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *023.* Kallon kallo ake tsakanin Baba da Rauda da kuma Mama kowa fuskar sa d'auke da rud'ani, Asad dai kansa yana k'asa ko motsin kirki ya kasa balle ya iya d'ago idanun sa yace wani abun yayi shiru yana jiran yaji abinda za'a ce dan zuciyar sa duka take kamar ana doka ganga. Baba ya kasa magana shud'ewar wasu dak'ik'u kana Baba yace, "Allah yaja da ra. mai martaba, abin ne naji shi wani iri shiyasa na kasa magana." Mai martaba yayi murmushi irin nasu na manyan mutane yace, "Kar ka damu na baku lokaci kuje kuyi shawara in tana sonsa Alhamdulillah haka muke fata, in kuma bata so kar ayi mata dole a barta da ra'ayin ta. Ina sauraren ku nan da wasu kwanaki da kun yanke hukunci a sanar dani ayi komai a gama cikin watan nan bana so a d'auki lokaci mai tsaho." Baba yace, "angama ranka ya dad'e, in sha Allah zaka ji komai daga bakina kamar yadda ka umarta. Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana, ya jiqan iyaye ya sanya suna Aljanna." Da amin suka amsa dukkan su kafin mai martaba ya kalli Hydar yace, "A mayar dasu gida, a kuma tabbatar an basu kulawar da ya kamata bana so su nemi wani abun su rasa." Ba musu Hydar ya tashi suma suka tashi akayi godiya suka fita. Falon ya rage daga Asad sai Mama sai mai martaba babu mai magana a cikin su kowa ta ciki na ciki, hawayen bak'in cikin da Mama take b'oye ne suka zubo mata daga idanunta ta share tana kallon wani wajan daban zuciyar ta nayi mata zafi da k'una sabida k'askantar da akayi a gaban talakawa. "Dole ki kawar da kai gefe ai domin abinda kika aikata kin san ba abu bane mai kyau, da ace yarinyar nan bata furta ta hak'ura ba wallahil azim ko wanne hukuncin da take so ayi miki sai an miki sai dai hakan ya zama silar bugawar zuciyar ki sabida bak'in ciki. Yarinyar da Hydar ya buge har ta samu matsala a k'afar ta ki saka a kore ta daga asibiti kawai sabida banza ra'ayin ki..? Ke kullum a idanun ki talaka da mai kud'i suna da banbanci, dan ta kasance talaka wannan Allah ne ya k'addara amma d'anki ne yayi silar nakasar ta amma ke ko yaushe tunanin ki daban yake dana kowa. kin kyauta ai abinda kika aikata yayi miki kyau" ya fad'a yana mik'ewa dole ta mik'e Asad ma ya mik'e tsaye. Ya sake kallon ta yace, "Ko nan gaba kika sake aikata wannan kuskuren Rabi'a sai na saka anyi miki hukuncin da baki tab'a tunani ba, sai na nuna miki talaka daidai yake dake a duniya tunda ke mutum ce shima mutum ne. Ki kuma ji tsoron ranar da zaki je neman alfarma a wajan talaka" ya fad'a da zallar b'acin raina tare dashi. Tare suka fita da Asad yana kallon irin kallon da take masa take gaban sa ya cigaba da fad'uwa har suka koma b'angaren mai martaba Asad baya tare da nutsuwar sa nutsuwar sa. Ganin hakan ya saka yace, "Kada ka damu Asad zan tsaya maka a wannan karon sai naga ka samu abinda kake so koda ita d'in bata so, bazata cigaba da tauye maka hakki ina kallo ba a wannan karon alqawari nayi maka." Kamar zaiyi kuka ya kalle shi yace, "Abba amma zatayi fushi dani kuma ni ban saka Hydar ya fad'a maka abinda yake faruwa ba, at least ban tabbatar da abinda nake ji akan yarinyar ba, a janye maganar Abba." Mai martaba ya dafa kafad'ar sa yace, "kana sonta, Asad na tabbatar da kana sonta. itace mace ta farko da saka kanka a cikin lamuran ta, kuma fuskar ta kake gani a mafarkin ka Asad. Akwai tarin alkhairi a zaman ka da ita nayi istikhara akan hakan Allah ya nuna min kaima yana da kyau kayi. Ka bawa zuciyar ka abinda take so kar ka cutar da kanka a wannan lokacin kamar yadda ka saba yi a baya, ka daure ka zama namiji ka Jajirce kar barazanar babar ka ta baka tsoro ka tsaya a akan ra'ayin ka. Shigowar ta rayuwar ka itace zata canja komai Asad, ka rubuta ka ajjiye koda bana raye hakan zata kasance amma dole ka jure, ka ajjiye wannan raguwar zuciyar taka ka zama namiji kamar kowa dan Allah" mai martaba yana gama fad'a yana kallon sa. Asad kansa yana sunkuye mai martaba ya kuma cewa, "Yau ba gobe ba ina so kaje gidan su yarinyar ka fara yak'in neman amincewatar, tana da ilimin addini babu abinda ban sani ba a kanta. Tana da tarbiyya mai kyau duk da ta kasance kuna da banbanci ta b'angaren matsayi amma itace daidai da kai tunda kana sonta. Ilimin ta da tarbiyyar ta shine ya saka na sake baka goyan baya d'ari bisa dari ta ko wacce fuska bata da aibu haka dangin ta. Ka nemi amincewar ta umarni nake baka Asad." Yana gama fad'ar hakan ya shige ciki ya bar Asad da sanyi jiki dole ya jawo k'afar sa ya nufo b'angaren Mama k'irjin sa na bugawa. Zagaye take hankalin ta a tashe ita kad'ai fuskar ta har ta fad'a sabida tashin hankalin da k'unar zuciyar da take ciki, jin motsin da taji ya saka ta juyo ta kalle shi ya sunkuyar da kansa k'asa baice komai ba ta gyara tsayuwa ta fuskance shi tace, "Asad kayi gaggawar samun mahaifin ka ka fad'a masa kai ba son yarinyar nan kake ba, ka janye maganar nan tun kafin nayi maka baki Asad" ta fad'a tana nuna shi. Asad ya sauke numfashi amma baice komai ba ta kuma cewa, "in ma asiri tayi maka zan warware shi amma baza ta tab'a zama mallakin ka ba ko bayan raina, babu kai babu ita tsakanin ka da ita taimako ne bayan shi babu maganar aure Asad!." Yadda ta d'aga murya ya saka shi runtse idanu zai iya cewa lokaci na farko kenan da Mama ta d'aga murya dan kowa yasan bata d'aga murya in tana magana a ganin ta fad'uwa ne a gare ta ya bud'e a hankali kana yace, "Ina sonta Mama!." Tassss shine sautin abinda ya sauka a kuncin sa daidai lokacin da kalmar mama ta gama fitowa daga bakin sa. Rai a b'ace take kallon sa tana nuna shi da yatsa da yake tsaye har lokacin tace, "K'arya kake Asad! Baka isa ba ba kuma zaka isa ba. Meye a wajan ta da zaka so ta?, me take dashi?, bak'a, gurguwa, y'ar talakawa, y'ar tallan abinci a kan titi me zaka nema a wajan ta wanda Jidda bata shi?. Meyasa baka son Jidda sai ita?." Yayi shiru zuciyar sa na zafi rana ta farko kenan da Mama ta d'aga hannu ta mare shi duk sai yaji duniyar tana yi masa zafi komai yana fice masa daga ransa. "Asad Jidda itace daidai kai mahaifin ta ambassador ne, na zab'e ta sabida ita kanta a k'asan ka take talakar kace dalilin da ya saka ban nemo jinin sarauta irin ka ba dan bana son matar da zaka aura ya zama tana had'a kanta da matsayin ka. Ita ta dace da rayuwar ka ba waccan banzar ba, ka tuna kai d'an sarki ne, wanda ya haifi mahaifin ka sarki ne, wanda ya haifi mahaifiyar ka sarki ne, wanda ya haifi mahaifin mahaifiyar ka sarki ne, kaine kuma sarki mai jiran gado me zakayi da y'ar talaka mara ilimi da wayewa!?." Ta bugi kujera ta cigaba da fadin, "Kask'anci ne a gare ni da dangi na gabad'aya matuk'ar ka auri yarinyar nan, baza ka aure ta ba indai ina da rai ka ajjiye wannan batun indai kana son farin cikina, in kuma ka dage akan kud'irin ka ka tabbatar min da y'ar talakawa ta fini a wajan ka." ta fad'a tana nuna shi da yatsa idanun ta a waje sabida bala'i da bak'in ciki. Muryar sa a tausashe kamar ko yaushe yace, "K'addara ce ta had'a ni da ita Mama ba soyayya ba, kece mahaifiyata wacce ta haife ni ta raine ni na tsahon shekaru da dama har gobe take kan bani tarbiyya. Ta yaya zan had'a matsayin ta da nata wacce na tsince ta a sama?, ta yaya zan fifita wata a kanta?. Ki amince min Mama ki yarje min kaddarar da ta had'a ni da ita na d'auke ta tamkar jarabawa ce wacce Allah ya k'addaro min, ki bani dama na amshe ta hannu biyu-biyu na rubuta nayi nasara. Agajin ki nake nema akan komai a wannan gab'ar ma yarjewar ki nake nema. ki duba yanayin da abin yazo ban shirya zuwan sa ba balle nayi rigakafi tun kafin lokacin, K'aunar ta nake ba sonta nake ba, ki amince min a wannan lokacin na gayyato ta zuwa rayuwata" ya k'arasa fad'a yana runtse idanun sa dan shi kansa ji yake kawai maganar na fitowa daga zuciyar sa zuwa kan harshen sa. K'are masa kallo take cike da dunbin mamaki jin doguwar maganar da ya tsaya yana yi mata akan wata mahaukaciyar yarinya da bata wuce mai bawa doki abinci a gidan su ba, ba k'aramin hasala ta sake yi ba tace, "baka isa ba Asad! wallahil azim baka isa ba, dole a wannan karon ma kaso abinda nake so in ba haka ba zaka jawowa yarinyar bala'i da masifar da baza ta iya fidda kanta ba; zan iya sakawa a kashe ta kuma na kashe banza da wofi kai ka sani, ina tabbatar maka matuk'ar ka bari abinda mai martaba ya fad'a ya tabbata wallahi sai kayi dana sani!." Idanun sa sunyi jahh sosai sabida tashin hankalin da zuciyar sa take ciki, zai iya rantse da Allah bai tab'a tsintar kansa a yanayi mara dad'i kamar wannan lokacin hatta yanayin fuskar sa ya koma ja. K'asa tayi da murya ta juya masa baya tace, "Yau ni kake fad'awa doguwar magana akan wata banzar mahaukaciyar yarinya ko Asad?, baka tab'a min irin wannan maganar mai tsaho ba sai yau sabida ta fini a wajan ka, ina cewa ga abinda nake so kana cewa kai ba shi kake so ba sabida ita ko Asad....?" ta k'arasa maganar a sanyaye sai kuma ta ta zauna akan kujera tana hawaye. Ganin hakan hankalin Asad ya tashi ya bita ya zauna a k'asan carpet yace, "Allah ya wuci zuciyar mahaifiyata, ina rok'on mahaifiyata akan tayi hak'uri ta daina zubar da hawaye akan Asad" ya fad'a a sanyaye yana dafa guiwar k'afar ta kamar shima zaiyi kuka. "Asad kar ka aure ta, bana sonta wallahi na tsane ta kar ka aure ta Asad" ta fad'a tana rik'e hannun sa gam hawaye na zuba a idanun ta. Kamar zaiyi kukan yake ji zuciyar sa tayi rauni matuk'a tana cigaba da bugawa rana ta farko da Maman sa take kuka a kansa hakan ya saka yace, "Zan iya hak'ura da komai akan Mamana duk k'aunar da nake masa, Allah ya wuci zuciyar ki." Hydar dake tsaye a bayan su ya shigo yana fad'in, "A karo na farko meyasa Mahaifiyata baza ta amince da ta amince da abinda Asad yake so ba....? ya bar aikin sa da yake buri tun yana yaro sabida Maman sa, ya bar damammaki da yawa a rayuwar sa sabida Mahaifiyar sa abinda Mama take so shi yake yi. Baya son Jidda amma ya amince da ita duk sabida Mama tana so yau kad'ai Mama ya nuna yana son Rauda meyasa mahaifiyar mu bazata amince masa ta bashi goyan baya ba?. Meye aibun ta kawai dan ta kasance ta fito daga jinin talakawa shikenan ba abar so bace ba?. Dan Allah dan annabi ranki ya dad'e a yiwa Asad adalci a karon farko a barshi ya aure ta tunda yana sonta" ya fad'a a sanyaye yana durk'usawa a gaban Mama cikin girmamawa. A fusace tace, "Hydar ba da kai nake magana ba dashi nake magana, ka fice ka bani waje." Hydar yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ina neman afuwa in abinda na fad'a ya b'ata miki rai" ya mik'e ya kalli Asad yace, "kazo muje takawa yana son ganin ka." Jin abinda Hydar yace ya saka Asad mik'ewa Mama tana rik'e da hannun sa har lokacin tace, "kar ka amince Asad, na yadda zan bar ku kuyi mata ko wanne irin taimako amma banda aure tsakanin ku bazan iya jure ganin wannan ranar ba, zuciyata zata iya bugawa a lokacin da hakan ta faru. Na rok'e ka matsayina na mahaifiyar ka Asad ka sanar dashi baka sonta." Kai Asad ya girgiza kawai ya fita Hydar yabi bayan sa. Hanyar wajan mai martaba Asad ya nufa Hydar yace, "Zo muje ba wani kiran mu da yake yi, na fad'a ne dan ka taso kalaman ta zasu karya maka zuciya ka hak'ura da abinda kake so" ya fad'a yana jan hannun sa suka nufi hanyar apartment d'in su. Bayan sun shiga Asad ya kalli Hydar a sanyaye sosai yace, "Hydar zan hak'ura kamar yadda Mama take so, bazan iya ganin Mama a halin da take ciki ba ina da damar cire ta kuma na barta; zan hak'ura kawai kome nake ji a zuciya ta zan jure Hydar; ba yau ne na fara rasa abinda nake so ba" ya fad'a a sanyaye yana zama akan kujera ya dafe kansa. Tausayin sa ya kama Hydar domin yasan soyayya tayi masa mugun kamu lokaci d'aya ba tare da ya shirya ba ya zauna kusa dashi yace, "Baza ka hak'ura ba deaf, sai ka mallake ta domin itace wacce kake so ba Jidda ba. Kana fa da hakki akan Mama ba itace kawai take da hakki a kanka ba tauyen ka da take yi yayi yawa a ko yaushe kanta ta sani bata duba kai halin da zaka shiga in ka rasa abinda kake kawai cikar burin tane a gabanta." Ya juyo ya fuskanci Asad ya rik'e hannun sa yace, "Deaf u lovers her right?." Ya lumshe ido yace, "Hydar!." Hydar ya katse shi yace, "Na tambaye kane kawai ka amsa min." Shiru yayi yana tunani kafin yace, "eh ina sonta Hydar, but yanzu na bar batun ta sabida Mama." "Baza ka bari ba abu nawa ka bari sabida Mama a duniya? Meyasa ita baza ta yi maka adalci a wannan lokacin ba?. Tana so ka auri wacce take so kaji zaka aura amma kaima zaka auri wacce kake so ba shikenan ba anyi equal why zata ce kai sai ka hak'ura?." "Hydar mu bar maganar nan dan Allah" ya furta yana dafe kansa da hannu d'aya kansa yana harbawa yana ajiyar zuciya. Hydar yace, "Na bari; amma inaso ka sani bazan zuba ido ka rasa abinda kake so a karo na babu adadi ba deaf, zanyi iya yina wajan ganin ka mallake ta" yana fad'a ya tashi ya fita daga falon ya bar Asad a zaune yana sauke numfashi. _Suna zancen wani Asad ni meye had'ina da wani Asad?._ kalaman Rauda suka fad'o masa a zuciyar sa ya runtse idanu zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri ya lumshe idanu yana tuno yadda fuskar duk taji ciwo, wani abu yaji yana masa suka a zuciya ya runtse idanun sa da k'arfi yana cize baki, bud'e ido yayi ya kalli falon kamar mai neman wani abun kafin ya tashi ya shiga d'aki jikin sa duk a sanyaye. *☆☆☆* Umma da take sauraron abinda Baba yake fad'a mata da mamaki take binsa da kallo jin abu kamar a shirin film ko a hausa novel tace, "Malam wai auren Rauda ake nemawa Asad d'in? Nifa ban gane ba ka saka ni a duhu wallahi." Baba yace, "Abinda kika ji na fad'a shine, Asad d'in ne da kansa yace yana son tane shiyasa mahaifiyar sa ta turo ayi mana wannan aikin dan daman nasan labarin ta ana cewa bata son had'a jini da talaka; shiyasa ta d'auki wannan matakin kafin abin yayi nisa." Umma ta rik'e baki tace, "Tabd'ijam, ni kuma fa gani nake kamar da wata manufa akace yana sonta in badan haka ba ina matsayin sa ina Rauda...?, banda abin su ina shi ina Rauda? Kalli yadda take fa?" Ta fad'a tana kallon Rauda da take zaune a gefe. Baba yace, "to Allah ne masanin gaibu ni bana ce komai ba." ya fad'a cikin rashin sanin mai zaice. Umma tace, "Ina zamu kaita inda za'a wulak'anta ta?, da ta aure shi azo ana wulak'anta ta wallahi gwara ta auri talakan da bashi da komwi zai kula da ita. To ita da bama sonsa take ba ina maganar aure?." "Ke kinji illar ki wallahi, meye to in ta aure shi? ai tunda yana sonta ko ita bata son shi magana ta k'are, kuma kaf dangin ki da nawa wacece ta taka matsayin da Rauda ta taka in ta aure shi?. D'an sarki fa kuma mai kud'i ki kuma tuna shine sarki gobe wannan ai abin alfahari ne a gare mu gabad'aya." Umma ta kalle shi da mamaki ta girgiza kai tace, "Shi kuma yanzu Anas ka dawo daga rakiyar sa kenan ko?." Baba yace, "ke muna so mu shiga aljanna amma a aljanna ma firdausi muke nema" ya fad'a yana wara hannayen sa. Umma ta d'auke kai daga kallon sa tace, "to ke Rauda wanne tunani kike akan wannan?." Rauda tace, "Umma wanne tunani zanyi?." Umma tace, "kece kike da tunani Rauda, amma a zahiri ina ke ina Asad?, Ga k'iyayayar da babar sa take miki tun kafin aje ko ina har ta fara turowa har gida ayi miki wulaƙanci dan kiji tsoro ke kya shiga gidan nan?. Ga badaqalar da take cikin gidan sarauta, da karancin shekarun ki a haukata min ke ko a kashe ki a barni da zubar da hawaye, bana fatan ma ki aure shi wallahi." Baba yace, "Sai ki hana ai in an tashi auren, ko in Allah ya rubuta kije ki goge." Umma bata ce komai ba Baba ya tashi ya fita ta kalli Rauda tace, "Rauda ke kina ji a ranki zaki iya zama dashi?." Rauda tace, "Bana kawo hakan Umma, hasalima ni haushi yake bani duk abubuwan nan da suke faruwa bai tab'a cemin yi hak'uri ba a haka kuma zan zama matar sa?. Bada ni ba yaje can ya nemi wata ni kam bazan iya ba dan ni zuciya ta ma hasaso mun take akwai wata manufa a son da yace yanayi min wata k'ila amfani zasu yi dani daga baya su wulak'anta ni dan sun ga suna da mulki da kud'i. Bana sha'awar hakan ma ni sam Umma." Umma ta sauke ajiyar tace, "ashe kin hango abinda nake hangowa. Meyasa ya zabe ki bayan tarin matan da suke son su aure shi? Dan nasan bazai rasa ba duba da girman da yake dashi a idanun mutane, duka ya tsallake su yazo kanki kuma yana tunanin zamu amince da zuciya d'aya yake son ki...?. ga rigimar gidan sarauta musamman ma ta katagum d'in nan da kowa yasan badaqalar da take ciki, Allah ya kawo miki wani daban amma ba shi ba yaje ya samu daidai shi amma ke kam yafi k'arfin ki." "Sabida tsabar mulki da sarauta bai tab'a min kallon arzuk'i bama sa wani ce yana sona dan kawai suna ganin zamu amince tunda suna da kud'i?, to ba haka muke ba yaje ya nemi daidai ahi nikam a kai a kasuwa." "Kedai tunda bakya ra'ayi ai shikenan babu wanda zai miki dole, amma yau kiyi addu'a ki kuma yi istikhara kafin ki kwanta wata k'ila akwai abinda Allah ya b'oye wanda mu bamu san dashi ba." Da to kawai ta amsa ta jingina da bango tayi shiru tana tunanin abubuwan da suka faru tsakanin ta da Asad d'in har kawo wanda ya faru yau sai taji tsigar jikin ta ta tashi har gashin kanta sai taji abin. Da daddare Asad yana zaune ya dafe kansa yana kallon wani waje daban b'acin ran da Mama take ciki gabad'aya ya dame shi ko yaya ya motsa ita yake gani tana kuka akan abinda yake da ikon rabuwa dashi, kuncin sa ya shafa ya tuna marin da tayi masa wanda ko yana yaro baya tunanin ta tab'a marin sa amma sai gashi yau sabida wata mace daban ta mare shi. "I'm sorry mah" ya furta a hankali yana sauke numfashi zuciyar sa nayi masa d'aci da k'una. Hydar ne ya shigo d'akin nasa ya kalle shi ya ganshi sanye da doguwar riga kalar orange mai hula a baya tayi masa kyau sosai yace, "Deaf ko zamu iya zuwa wani waje mu dawo?." Asad zai musa yayi saurin katse shi yace, "Please yanzu zamu dawo kaima kuma zaka ji dad'i stress d'in nan da kake ciki." Mik'ewa kawai yayi suka fita suka shiga mota Hydar yaja Asad bai san inda suka nufa ba. Babu zato yaga sun tsaya a k'ofar gidan da suka ajjiye su Rauda d'azu kafin Asad yace wani abu Hydar ya fita daga motar a lokacin Baba ya fito ganin su ya saka ya k'araso da fara'a yana fad'in, "A'a Hydar kaine tafe?." Hydar yace, "Eh, tare muke da Asad ma, ka fito mana" ya fad'a yana kallon glass d'in motar dole Asad ya fito badan yaso ba. Baba yace, "to ku shigo mana ciki ai bakwa tsaya a waje ba." Daman abinda Hydar yake so kenan suka yi gaba Asad ya tsaya a baya bai da niyar tawowa Baba yace, "Asad baza ka shigo ba kai?." Jin hakan sai ya tako ya biyo bayan su yana jin sa wani iri kamar bashi ba. Rauda na zaune da hijjabi tana nunawa Ummulkhairi assignment kasancewar gidan akwai hasken wutar sola ba duhu ko ina haske tarr suka ji sallama, amsawa sukayi kafin su kalli wanda suke shigowa. Asad shine k'arshe shigowa yana shigowa ya had'a ido da abar sonsa nan take yaji duk wata damuwa na yayewa a zuciyar sa a hankali tana tafiya kamar daman bata samu mazauni a ransa ba. "Lah Yaya Aliyu." Ummulkhairi ta fad'a tana kallon sa da murmushi ya kalle ta amma baice komai ba kafin tace, "Ance kaine ka kawo mu sabon gida mai kyau har da wuta ga tv ma, kai mun gode sosai" ta fad'a kamar yarinya k'arama. Ya murmusa kad'an baice komai ba kafin Baba yace, "ku zauna mana." Kafin Asad yace wani abu Hydar ya zauna Hydar ya kalli Rauda yace, "ya jikin? Ina Mama ya jikin ta?" Ya fad'a a tare yana kallon ta a nutse. Dumm haka Rauda taji a zuciyar ta tana ji tana yi mata zillo kamar tana rawa ta daure tace, "Umma ta kwanta bata jin dad'i jikinta." "Ayya" ya furta daga nan shima yayi shiru. Baba ya kalli Hydar yace, "Nikam Asad baya magana ne?." Hydar yayi murmushi yace, "yanayi amma ba sosai ba gaskiya, baya son magana bai k'i a kai gobe a haka babu wanda yace wani abun ba, haka Allah ya yisa magana bata cikin tsarin sa sosai." Baba yace, "Allah sarki." Hydar yace, "yace na rako shi su gaisa da Rauda amma naga duk ya canja kamar ba shine yace muzo ba" ya fad'a yana kallon Asad da shima kallon sa yake cikin mamakin k'aryar da ya yi masa. Baba farin ciki ya kama zuciyar sa ya washe baki yace, "To ai sai mu basu waje su gana" ya fad'a yana tashi Hydar ma ya tashi ya fita yana d'agawa Asad gira ya fita aka barsu daga shi sai ita dan Ummulkhairi ma ta shiga ciki wajan Umma. Shiru wajan yayi babu wanda yace kanzil a cikin su ita ta zuba ido taga k'arshen izza da k'asaitar tasa shi kuma yayi shiru dan bai san me zaice mata ba gabad'aya dan bashi ya kawo shi ba. An kwashe mintina a haka kafin ta yunk'ura zata tashi tana neman sandar ta ta mik'e tsaye tana fad'in, "Ina da abin yi ba zama nazo yi ba." Jin abinda tace sai ya kalle ta yace, "ya jikin ki?." Komawa tayi ta zauna tana hararar sa ta gefen ido tace, "Oh ashe kana magana." Shiru ya kuma yi baice komai ba itama bata amsa abinda yace mata ba. Tunawa da abinda mai martaba yace dak'yar Asad ya iya tattaro kalaman bakin sa ya had'e waje guda yana ji kamar ana turo kalmomin daga zuciyar sa yace, "I'm in love with you, but no forcing, no begging and no competition." Rauda da take kallon sa bata lokacin da ta furta, "ikon Allah!" tana kallon sa jin abinda yace. Mik'ewa tsaye yayi ya kalle ta itama shi take kallo dukkan su k'irjin su bugawa yake yi ba kamar shi da yake ji kamar ana jijjigo ta daga mazaunin da Allah ya ajjiye ta yace, "good night!" yana fad'a ya fita ta bishi da kallon mamaki mai d'auke da rainin hankalin da yayi mata. _K'asaitar so d'in kenan sunan wani littafi._⛹‍♀️🤣🤣 #Vote #Comments #Share. *KWANTAN ƁAUNA* Fitattubiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *024.* Asad baiga Baba ba da ya fita a mota ya tarar da Hydar kawai ya shiga ganin hakan Hydar yaja motar ya tafi yana satar kallon Asad da yake murmushi mai kyau kana gani kasan zuciyar sa fari tas take a wannan lokacin. Shima murmushi Hydar ya mayar da hankalin sa kan tuk'in kana yace, "in aka ce min deaf zai so wata mace lokaci d'aya haka bazan amince ba, amma sai gashi na gani na kuma tabbatar kana cikin soyayyar da baka san iyakar ta ba." Hannu Asad ya saka ya shafa kansa yana kallon titi shi kansa mamakin kansa yake yi domin bai tab'a d'auka akwai soyayyar wacce zata yi masa kamu lokaci guda kamar ta ba, bai kuma d'auka akwai macen da zai yiwa wannan son na farar d'aya haka ba sai gashi ya tabbata yana kuma kan faruwa a lokacin. "Ka fad'a mata kana sonta face to face dai ko?." Asad ya girgiza kansa alamun a'a Hydar yace, "to meyesa baka ce mata ba? Meye amfanin zuwan da mukayi?, dan fa ka sanar da ita kana sonta ya saka na d'auko ka muka zo nan." "Oho" ya furta ya shafa fuskar sa yana lumshe idanun sa. Hydar yace, "gashi ai yanayin ka ya dawo daidai da kazo ka ganta, kana cikin damuwa amma gashi daka ganta ka dawo normal. But da ka sani kayi mata bayanin yadda kake sonta, ina so ka sani Asad lokaci yayi da zaka ajjiye wannan rashin maganar taka, ka san ita soyayya ba ruwan ta da mulkin ka ko nasabar ka ko kud'in ka, a iya kwanakin da ka fada tarkon sonta nasan ka tabbatar. Ka fuskanci abinda zuciyar ka take so in ba haka ba zaka iya rasa ta, soyayya tana son kulawa sosai." Kallon sa yayi idanun sa a bud'e sosai yace, "babu maganar rasata" ya fad'a yana cize bakin sa cikin jin zafin kalmar rasa ta da yace zaiyi. Hydar yayi y'ar dariya kana yace, "na sani shiyasa nace ka dage Asad, a kan idon ka aka nuna mana wanda yake sonta zai iya kwace ta in ya fika iya kula da ita, na farko kai ga yanayin nature d'in ka ga kuma yadda abin yazo in ba mayar da hankali kafi ba zaka zama looser, kuma sun saba da wancan kai kuma kalma mai tsaho bata tab'a had'a ku ba." Murmushi kawai Asad yayi bai kuma cewa komai ba ya mayar da hankalin sa kan in ya tuna Mama gaban sa sai ya fad'i yaji komai ya fice masa a rai. Washe gari. K'arfe tara na safe Mum tazo ta d'auki Mama a mota suka fita su biyu kacal ko hadiman Mama bata bari sun biyo ta ba babu wanda yasan inda zasu je sai su kad'ai. Tunda ta shiga motar take k'wafa Mum da take tuk'i dai bata ce komai ba domin itama nata ran a b'ace yake sosai sai daga baya Mama tace, "Wai ni Takawa zai yiwa fad'a kamar zai dake ni akan wata banza y'ar matsiyata bayan hak'urin da ya saka na basu?, kamar ni ace na bawa wad'annan k'ask'antun hak'uri....? Me suke dashi a duniya da zan kalle su nace suyi hak'uri....? an cuce ni wallahi" ta fad'a tana dukan jikin motar ranta a b'ace. Mum dai bata tanka ba tafiya suke yi lokaci kad'an suka shiga wata unguwa da babu jama'a ko kad'an sai gidaje kad'an-kad'an kamar rugar fulani suka faka motar suka fito dukkan su suka shiga cikin gidan. Wani k'aramin d'aki suka shiga wanda yake baje da magunguna na itace dana gari da turarruka kana dosar d'akin kasan d'akin maganin gargajiya ne, wanda yake zaune a gaban faranti da aka zuba masa yashi da k'aton mudubi a kusa dashi yana ganin shigowar su ya murmusa yace, "Barka da zuwa Fulani." Waje suka samu suka zauna kafin Mum tace, "Malam mun same ka lafiya." "Lafiya lau Sadiya, ya yara suke?." "Lafiya lau. Matsala ta taso dole muka zo da kanmu shiyasa nace basai kazo ba zamu shigo nida Fulani." Mama ta kalle shi bayan ta d'age nikaq d'in fuskar ta tace, "kamar yadda ta maka bayani a waya Sunan yarinyar Rauda inaso a duba min aga kodai asiri ta yiwa Asad har ya furta yana sonta duk da tarin nak'asun dake tare da ita da kuma tarin y'an matan da suke so ya kula su ya tsallake su yaje wajan ta." Jin abinda Mama tace ya jawo farantin gaban sa ya fara dubawa kusan minti d'aya da wani abun kafin ya karkad'e hannun sa yace, "a abinda muka gani bata yi masa asiri ba had'uwar jini ce kawai." "Ka dai sake dubawa ko wani ne daban yayi masa asiri dan ya sota" Mum ta fad'a tana kallon sa. Malamin ya kalle su yace, "Kamar yadda na fad'a muku babu batun asiri a tare da lamarin nan soyayya ce daga Allah wacce ya dasa masa ita a zuciyar sa." Mama tace, "To meyesa yake sonta?." "Ranki ya dad'e soyayya ce da kuma had'uwar jini ce." "Ban amince da wani had'uwar jini ba dole akwai wani abun a k'asa. Kai kanka da zaka ga yarinyar na tabbatar zaka bada shaidar akwai abinda aka kulla." Mum ta kalle shi tace, "to yanzu ya za'ayi kenan?." Malam d'in ya sake duba farantin sa sannan yace, "Asad yana son yarinyar sosai lokaci guda Allah ya saka masa ita a ransa, yana sonta kamar ya had'd'iye ta. ita kuma yarinyar kamar har yanzu babu wani tsayayyen abu a ranta amma dai......" Mama ta katse shi ta hanyar fad'in, "Amma me..? A datse soyayyar kawai." Malam yace, "ranki ya dad'e kenan hakan yana nufin a yiwa Asad aiki ko?." Mama tace, "A'a ba tun yau ba kasan bana san a yiwa Asad wani abu a yiwa ita yarinyar amma bashi ba." Malam ya murmusa yace, "Ranki ya dad'e banda abin ki ita da babu abu tsayayye a ranta shine akwai soyayya a ransa sai dai in shi za'a yiwa aikin a cire ta daga zuciyar sa. "Mama ta girgiza kai tace, "A'a ko kad'an bana son hakan, a nemo wata hanyar." Malam ya sake bincikawa ya kalle su yace, "Kun sani bana fad'ar k'arya dan na samu wani abun a wajan kowa, haka zalika bana fad'awa mutum abinda zaiji dad'i koda bana jin dad'in na gani ba, ina fad'ar abinda Allah ya bani ikon gani ne komai d'acin sa. Maganar gaskiya auren yarinyar nan da Asad bazai lalatu ta sauk'i ba akwai wani abu mai k'arfi da yake rik'e dashi." A firgice Mama ta kalle shi tace, "A lalata shi ta k'arfi, a saka k'arfin da yafi nasu k'arfin a tarwatsa shibana son hakan ta kasance ne ko a mafarki." Malam ya jinjina kai kafin Mum tace, "A yiwa yarinyar asirin da zata ji ta tsane shi gabad'aya taji bata son ganin sa ko kad'an, kaga koda tayi niyar amincewa dashi zata fasa." Malam ya sake dubawa kana yace, "Yiwa yarinyar aiki ba abu bane mai sauk'i, tana da rik'o da ibada fiye da tunanin ki Hajiya Sadiya." Mama ta dafe kai cikin takaici tana cizan yatsa zuciyar ta na tafasa sabida b'acin rai jikin ta har zafi ya d'auka kamar mai zazzaɓi, bata k'aunar talaka ya rage ta balle kuma y'ay'an ta. Mum tace, "A kashe ta ko a haukata ta!." Malam ya yi murmushi yace, "Kar ayi gaggawa ranki ya dad'e, shawara a nan aje a same ta a tsoratar da ita har a cusa mata tsanar auren tak'i amsawa zata aure shi, a fitar mata da sha'awar auren jinin sarauta a zuciyar ta. A ganina wannan itace kawai hanya mai sauk'i in tak'i sai a dauki mataki." Mum tace, "Kenan mune zamu same ta?." "Kwarai ku da kanku zaku same ta in akayi sa'a hakan zaiyi aiki, domin indai ba ita tace bata so ba Asad bazai fasa auren ta ba haka mai martaba bazai fasa bashi ita ba." Mama ta sauke numfashi tace, "ya batun sarautar sa?." Malam ya bincika kana yace, "Tana nan, kamar yadda na sha fad'a miki shine zai mulki katagum har gobe maganar haka take; amma kamar koda yaushe akwai qalubale manya ma wanda suka fi na baya yawa. Na farko maganar auren nan zata sake dagula komai, na biyu wad'annan wanda nake fad'a miki suna aiki a kansa sun sake zage dantse sun k'aro makaman yak'in yak'ar ku, na uku suna gab da yin nasara a kanki da kuma kan Asad d'in." Mama ta sauke ajiyar kana ta sassauta murya tace, "ya batun tsarin jikin sa?." "Ranki ya dad'e komai lafiya yana k'ok'ari wajan ibada da rok'on Allah shiyasa suka kasa nasara akan sa har yanzu." Kai ta girgiza kafin ta mik'e tsaye tace, "Zamuyi waya, muje" ta fad'a tana yin gaba tare da sakin niqab d'in fuskar ta. Mum ta kalle shi bayan ta tashi tace, "Akwai maganar da zamuyi ma tattauna a waya" ta fad'a tana fita daga d'akin tabi bayan Mama da sauri. Suna shiga motar Mama ta kalle Mum tace, "muje gidan su yarinyar." Zaro idanu Mum tayi tace, "muje muyi me? Kin manta rashin kunyar ta dana baki labari?; marina fa tayi." "Zamu je mu gyara komai ne yanzu." "Kamar ya mu gyara Fulani? Kema in ta maren ki fa?." "Ko uban uban ubanta bai isa ya tab'ani ba balle ita; dalilin da Malam ya fad'a shine zai kai mu wajan ta." "Amma fulani......?" Dakatar da ita Mama tayi ta hanyar cewa, "Muje kawai. Zan nuna miki gidan da suka koma." Shiru Mum tayi zuciyar ta a wuya take tuk'in har suka zo k'ofar gidan su Rauda Mama ta fita daga motar tana kallon gidan ta tabbatar nan ne inda aka binciko mata ta nufi zuwa cikin gidan, juyowa tayi taga Mum bata fito ba ganin tana kallon ta ya saka ta fitowa suka shiga cikin gidan. K'ofa biyu suka gani suka tsaya suna kallon k'ofar cikin tunanin waccw zasu bi a ciki, bud'e d'aya akayi aka fito hakan ya saka suka kalli wacce ta bud'e k'ofar ta kalle su tace, "Bayin Allah daga ina?" Inna ta fad'a tana kallon su. Mum ta kawar da kanta gefe da alama baza ta bada amsa hakan ya saka Mama tace, "Muna neman wajan su Rauda." "Gashi nan" ta fad'a tana nuna musu d'aya k'ofar suka wuce ba tare da sun kuma kallon ta ba. Da sallama suka bud'e k'ofar sai gasu a falo Rauda na zaune ita da Umma da kuma Yaya Ummi suka amsa suna kallon su, ido Rauda suka had'a da Mum ta bita da kallo kana tace, "tofa kice shugabar y'an daba ce da kanta ta kuma dawowa, to yau kuma da me kika zo mana...? zauna ki bamu labari" ta fad'a tana kallon Mum cikin sigar rashin mutunci. Mama ta zauna ta d'age nikaq d'in fuskar ta ta kalli Umma tace, "Sannu ya jikin?." Umma tace, "lafiya lau Alhamdulillah. Amma ban sanki ba." Mama ta murmusa tace, "Sunana Fulani Rabi'atu mata a wajan sarki katagum ya a wajan sarkin Kano, jika wajan sarkin Kano, uwa a wajan sarkin Katagum mai jiran gado" ta fad'a tana kallon su. Yaya Ummi tace, "Allah sarki! To sannu." Mama ta kalli Rauda tace, "wajan ki nazo." Rauda da mamaki ta kalle ta tace, "gani ai kin ganni." Mama tazo wuya jin amsar da ta bata amma ta jure tace, "d'ana Asad ya furta kalmar so a gare ki a lokacin da ban shiryawa hakan ba, ya nuna ke yake yi kuma na riga da nayi masa mata tun ba yanzu ba, gidan sarauta gida ne na rikita-rikita kanki bazai d'auki abinda yake faruwa a cikin sa ba koda an baki labari, duk inda kike tunanin abun ya wuce haka gwara ki zauna a gefe hakan zaifi miki alkhairi. Nasan halin mahaifin sa tunda yace amsar ki ake jira ita ake jira indai kika amsa zance ya k'are in kuma kika yi akasin haka za'a fasa shiyasa nazo na shawarce ki akan karki kai kanki ga halaka matsayin da kike k'okarin takawa yafi k'arfin ki akwai mata sosai a gaban ki." Kallon Umma tayi kana tace, "Ke uwa ce baza kiso ki rasa d'iyar ki ba ki bata shawarar kar ta amsa batun Asad domin kuwa tana niyar shiga wuta ne da k'afar ta." Umma tace, "banda abin ki kinji ance y'ar mu zata auri d'anki ne?." Mama ta tab'e baki tace, "ko d'aya nasan baza tak'i tayin ba ai shiyasa nake fad'a mata gaskiya." "Ai kuwa sai muce a kai kasuwa domin kuwa tana da wanda yafi Asad d'in" Yaya Ummi ta fad'a tana kallon ta. Kyakykyawan murmushi Mama tayi tace, "tana da daidai ita dai amma bawai wanda yafi Asad ba ko yarinya..? Ta samawa kanta lafiya da kuma zaman lafiya." Rauda da take gefe tace, "in kuma na amince masa fa?." Mama ta kalle ta tace, "abinda ma bazai yu ba kenan, keda shi sai dai taimako amma yafi k'arfin ya zama mijin ki har Allah ya tashi duniya, Rauda sunan ki ko?" Ta fad'a tana kallon ta cikin k'ask'anci da rainin hankali Rauda tayi dariya tace, "kodai nafi k'arfin sa ba tunda shine yake jiran amsa ta bani nake jiran tasa ba, shi ya gani ya mato yace yana so har kika kasa dakatar dashi kinga kenan nice nafi k'arfin sa bashi yafi k'arfi na ba. Ki rike d'anki daman bana sha'awar auren kuramen maza ni." "Ke yarinya ki iya bakin ki! Ki san da wacce kike magana" Mum ta fad'a a fusace tana kallon ta Rauda tace, "in kuma nak'i fa akwai abinda za'ayi min ne?." Mama tace, "Naga alama kanki yana rawa sosai kina ji da y'an matanci, ki saita harshen ki tun kafin ya kai ki ya baro ki" ta fad'a tana nuna ta da yatsa. Umma tace, "Rauda ya isa haka." Mama tace, "ya kamata dai kija mata kunne ta san da wacce take magana." Rauda tace, "Ke kika tako k'afar ki kika zo har inda muke dan haka baki isa ki fad'a mana maganar da batayi mana ba kuma nayi miki shiru ba." Mama tayi k'wafa tace, "Ba wannan ne a gabana ba abinda na fad'a miki shi ya kamata kiyi, maganar auren Asad ki d'auka a mafarki kika tab'a ji ba a gaske ba" ta fad'a a kausashe. Rauda ta tab'e baki tace, "Umarni ne ko shawara?." "Umarni ne!" Ta fad'a a fusace tana kallon ta. "Dalili?" Rauda ta fad'a tana binta da kallon raini. Mama tace, "ke banzo wajan nan dan na fad'a ki fad'a ba, ina so kisan badan Jan kunnen da zan miki ba uban ki ma bai isa na fad'a ya fada ba balle ke y'ar k'aramar tsakuwa. naga alama baza kiji maganar a nutse ba sai an fad'a miki da yaren da talaka yafi ganewa wato duka. Ki samarwa kanki lafiya ki bar Asad in baso kike wani abun ya same ki ba." Rauda tace, "babu abinda zai same ni sai abinda Allah ya nufa. Sannan babu wanda ya isa ya saka ni yin abinda banyi niya ba, in naga dama kuma zan iya cewa ina sonsa na aure shi kodan naga yadda zaki koma a lokacin." A fusace Mama ta mik'e tace, "Kee! Kar ki sake hasashen wannan ranar a rayuwar ki domin baza tazo ba har abada. Ke wacece da zaki zama matar d'an sarki jikan sarki kuma sarkin gobe? Wacece ke? Banza kike, bak'a, mummuna, matsiyaciya, gurguwa mai tallan abinci a titi. Ke ko a mafarki akace zaki zama matar sa sai ki amince?." Murmushin rainin hankali Rauda tayi tace, "Da alama sirikata kina wasa da ikon Allah kinga ta inda muka samu banbanci kenan ni nasan duk wahalar abu a wajan Allah mai sauk'i ne." ta fad'a tana kallon ta itama tana kallon ta. Mum tace, "kul kar ki sake kiran ta da wnanan sunan bai dace a bakin mace irin ki ba, ki sani akwai matan da suka amsa sunan su mata sama da d'ari da suke son su furta wannan suna amma yafi k'arfin su." Rauda tace, "ba tsoron ta kar na amsawa Asad zan sa aure ba? To ina so ku sani da zarar lokacin da aka d'iba yayi zan tabbatarwa da mai martaba ina son Asad kuma zan aure shi kodan naga ya zakuyi a lokacin da Bak'a, mummuna, gurguwa, y'ar talaka, mai tallan abinci ta zama matar sarki Asad; kuma sirikar y'ar sarkin Kano babar sarkin jibi. Kunga sai ku d'auki bindiga ku harbe kan ku" ta fad'a tana kallon su one by one. A fusace Mama tayi kanta zata mare ta Mum ta rik'e tana girgiza mata kai Mama a fusace tace, "matuk'ar kika aikata haka zakiyi dana sanin da baki tab'a yi ba tunda Allah ya kawo ki duniya. Zan iya sakawa a b'atar dake daga duniyar gabad'aya wannan ba komai bane a wajena matuk'ar zan samu abinda nake so. Sai na tabbatar baki tako k'ofar gidan sarauta ba balle ki kasance a matsayin da kika lissafa domin yafi k'arfin kaf dangin ki gabad'aya. Zan miki biyu babu, babu Asad babu sauran wanda suka zo taimakon ki su aure ki tunda abin naki rashin kunya ce" ta fad'a tana nuna ta da yatsa cikin murya mai amo da alama kamar wani abun ma bata san tana fad'a ba sabida b'acin rai. Rauda ta tab'e baki tace, "Ina jira na gani sirika ta, in kuma nice naci wasan na shigo gidan matsayin sirikar ki nice nayi nasara bake ba." K'wafa tayi fuskar ta har ja tayi sabida b'acin ran da take ji a zuciyar ta wanda bata tab'a jin irin sa ba sukayi hanyar waje kafin Mama ta tsaya ta juyo ta kalli Umma da Anty Ummi tace, "Duk abinda ya samu y'ar ku kuyi kuka da kanku.." Rauda ta d'aga murya tace, "babu abinda zai same ni sai alkhairi. Kii gaida min mijina kinji sirika ta!." Juyowa tayi ta kalle ta Rauda tayi dariya kafin ta girgiza kai ta fita daga falon a fusace. Kallon Rauda Umma tayi bayan sun fita cikin fad'a tace, "Wannan wanne irin rashin hankali kike aikatawa haka Rauda?. Ke kuma babbar banza mai biye mata ina yi mata magana kina tab'a ni wai na k'yale ta tana yiwa wacce ta haife ta rashin kunya, Ni in aka yi min haka zaku ji dad'i ne?. Matar sarki ce fa bamu yi mata komai ba ta saka anzo gida an ci mana mutunci ina ga kun fad'a mata wad'annan maganganun marasa dad'i...? Ba kaina nake ji ba ke nake ji Rauda zata iya yi miki komai dan ganin bayan ki." Yaya Ummi tace, "Umma ai ke baza ki aikata abinda ita tazo tayi mana har cikin gida ba bayan wanda ta saka akazo har gida aka ji miki ciwo, ai wallahi munyi mata da sauk'i ma irin ta'asar da tayi kamata yayi mu kamata mu rama irin abinda ta saka akayi miki. gani take kud'i shine komai zata iya juya mu tayi mana rashin mutuncin da taga dama bata san bata isa ba wallahi. Dan tana matar sarki baza muji tsoron ta ba tunda ita ta d'auko k'afa tazo har inda muke ko zane ta mukayi itace ta jawo." Umma ta kalle su tace, "ya dai isa haka bana son tashin hankali da yiwa na gaba rashin kunya. Ku tuna a gidan d'anta muke ko a yanzu mun ci albarkacin ta dan ba bata haife shi ba damu zauna ba, da badan yazo inda muke ba da wataƙila yanzu bamu san a inda muke zaune ba. Kar na sake ganin kin yiwa wani haka koda nan gaba ne, wannan ba tarbiyya ce." Umma ta fad'a tana kallon Rauda kafin ta tashi ta shiga d'aki. Yaya Ummi ta kalli Rauda tace, "Ke me kika yanke game da auren shi Asad d'in?." Rauda ta kalle ta tace, "Ban yanke komai bani domin bana ra'ayin auren sa gabad'aya. Ya cika rainin hankali da yawa bazan jure ba." "Kuna tare da Anas har yanzu?." "Tun dai ranar yazo har yace min bashi ya aiko mana da kayan abinci ba ban sake jinsa ko a waya ba gaskiya." "Kuma baki neme shi ba?." "Na kira shi jiya amma layin a kashe." Yaya Ummi tace, "inda nice ke Rauda da Asad d'in nan zan aura badan yafi Anas kud'i da mulki ba sai dan na nunawa uwar sa ba'a ja da ikon Allah, duk k'ask'ancin mu da take gani in Allah yace yes bata isa tace no ba duk abinda take ji dashi sai dai tayi ta gama ta d'auki jikan da zaki haifar mata. Gurguwa, bak'a mai tallan abinci da take rainawa ta zama mata ga d'an nata da take ji dashi sai naga uwar abinda zatayi." Rauda tayi murmushi tace, "Nima zan so hakan Yaya kodan naga yanayin da zata shiga a wannan lokacin, amma sam ni bana ra'ayin auren sa." "Kiyi ra'ayin yanzu Rauda, kar ki manta tun ba yau ba kina yawan ce min kinyi mafarki da namiji mai rawani a kansa wataƙila Allah ne ya nuna miki auren sa tun a mafarki. sannan istikhara da kika yi Allah ya nuna miki a mafarki ko?." Rauda tace, "Haka ne Yaya Ummi amma hakan ba yana nufin shi zan aura ba. Nifa bazan iya zama matar sa ba gaskiya in na aure shi nayi ya da k'iyayayar mahaifiyar sa?." Yaya Ummi ta dawo kusa da ita ta dafa ta tace, "Shi zaki aura Rauda, ki saka a ranki shine mijin ki da zarar an tambaye ki kice kin amince." Rauda ta kalli Yaya Ummi tace, "Nifa bana son sa ta yaya zan amince?." "Sabida mu nunawa babar sa iyakar ta, mu nuna mata duk abinda kake ji dashi baka isa kaja da ikon Allah ba." "Ni tsoron gidan sarauta nake fa Allah ya sani." "Ki ajjiye tsoron ki saka a ranki a nan aka haife ki." Rauda ta kalle ta da mamaki tace, "Yaya Ummi in na amince da Asad Anas fa? Nayi masa adalci kenan duk tarin d'awainiyar da yayi dani dan na samu wanda ya fishi na watsar dashi...?." #Vote #Comments #Share. *KWANTAN ƁAUNA* Fitattubiyar 2023 ©️ *Nana Haleema.* *Book 1* *025.* Yaya Ummi tayi shiru alamun tunani kafin ta sauke numfashi ta kalli Rauda tace, "Tabbas Anas ba abin yarwa bane ba, in muka watsar da Anas bamuyi adalci ba." Rauda rausayar da kai tace, "Abinda na gani nima kenan, zan iya auren Anas na zauna dashi duk da bana jin sonsa a zuciya ta har gobe, amma halayyar sa da yadda yake nuna tsantsar so a gare ni zata saka naso shi nan gaba." Yaya Ummi tace, "Haka ne Rauda, ki cigaba da addu'a kedai kawai duk abinda ya zama alkhairi Allah ya zab'a maki." "Ina yi sosai." Yaya Ummi zatayi magana kenan aka bud'e k'ofar aka shigo Baba ne da kuma maza guda biyu a bayan sa ganin su waye ya saka Yaya Ummi tashi tsaye tana fad'in, "Sannun ku da zuwa." D'aya daga cikin su yace, "Yauwa Ummi, ya mai gidan naki?." Yaya Ummi tace, "Alhamdulillah." Gaisawa sukayi har Rauda kana d'aya daga cikin su yace, "Jiya nazo wucewa ta k'ofar gidan ku na tarar an baje gidan gabad'aya ya koma fili ana sabon gini na bulo, daman kuma ina ta ji a gari ban tabbatar ba sai dana gani da ido na; sai yanzu mahaifin ku yake shaida min abinda yake faruwa." Kawu Badamasi yace, "Ke daman kin san shi ne tun a baya har ya furta yana sonki?." Rauda ta girgiza kai tace, "A'a Kawu bansan shi ba." Ya girgiza kai yace, "ikon Allah kenan, abinda baka tsammaci faruwar sa ba sai kaga ya faru." Kawu Lawan yace, "To ke meye a ranki kenan?." Rauda tayi shiru bata amsa ba Baba yace, "ita bata yanke hukunci ba har yanzu; akwai wani yaro Anas da yake sonta yana hidima da ita sosai ina tunanin shine a ranta." Kawu lawan yace, "ba d'an gidan Alhaji Tasi'u mai farin gida ba?." Baba yace, "Shi." Kawu lawan yace, "to ai ni Alhaji Tasi'un ya aika min da mutane guda biyu na d'auka ma ko neman auren ta suka zo wajena sai suke shaida min shine ya turo su yace a sanar damu ya yiwa d'ansa mata kar a jishi shiru kwana biyu zai masa aure ne. Sun shaida min bazasu iya had'a ido da kai ba sabida kunya shiyasa suka je wajena kai tsaye." Baba yace, "ikon Allah! Amma baka sanar dani ba." "Na d'auka shi yaron ai ya sanar dakai ko ya sanar da ita." Baba ya girgiza kai ransa fari karr har hakan ya bayyana a kan fuskar sa yace, "basu zo inda nake bama shiyasa kwana biyu shiru babu motsin yaron, Allah sarki ni shaida ne yana son Rauda amma da alama iyayen sa basa son alaqar su tare shiyasa suka yanke wannan hukuncin, Allah ya zab'a mafi alkhairi." Kawu Badamasi yace, "Amin. Baza muyi saurin cewa iyayen ne basa son alaqar ba wataƙila alqawarin aure ne sukayi zasu had'a shi yaron bai san dashi ba shiyasa yake neman Rauds. Rauda karki yiwa kanki dole dan ganin kud'i ko dukiya ko kuma sarauta, yanzu maganar Anas ta k'are kinji duk abinda yake faruwa da kunnen ki, kar kice tunda babu batun Anas yanzu bara na amince da d'an sarkin kar kiyi haka kiyi addu'a ki kuma bi zab'in zuciyar ki." Kai ta girgiza alamun gamsuwa Baba yace, "Ai ana ta addu'a duk inda na bayar ayi mana istikhara sai kaji ance auren sa da ita alkhairi ne ba kad'an ba. Daman Anas d'in nan nake ji tunda abin yazo da haka wallahi nafi kowa farin ciki ya auri zab'in iyayen sa itama ta auri Asad d'in shikenan an huta." Kawu Badamasi yace, "A'a, ka barta ta zab'i abinda take so dan Allah kar abin duniya ya rufe mana idanu mu kaita inda zamu zo muna dama mun sani bamu kaita ba, dan ni Allah ya sani wani lokacin bana yi mata sha'awar shi yaron mai martaba sabida abinda zata tarar ba abu kad'a bane. Na farko da ga babar sa, na biyu ga sauran jama'ar gidan, na uku har abada gidan sarauta bazasu tab'a girmama ta ba k'ask'ance zata rayu dan su gidan sarauta indai ba y'ar gidan sarauta ka d'auko ba talaka sunan ka balle kuma Rauda." Umma da take zaune tace, "tun a yanzu ya fara bayyana kansa dan mahaifiyar yaron bata jima da fita daga gidan nan ba tayi b'adda kama ta shigo tana yi mata gargad'! akan auren d'anta, har da ikirarin in ta aure shi sai ta b'atar da ita daga duniya, ina dalili d'an sarki ai ba d'an wani annabin bane da za'a so a aure shi. Kuma shi yaron ita dashi bai ma ce yana son ta balle yace zai aure ta, haka zasuyi zaman auren?." Kawu Lawan yace, "sai a bar maganar in mai martaban ya nemi jin ra'ayin ta ace bata amince ba ai ba dukan mu za'ayi ba." Baba yace, "A'a bafa za'ayi haka ba zata amince ma in sha Allah, meyasa kuke haka ne ku? Alkhairi ya biyo mu kuna k'okarin saka mu guje masa?. Ni ina goyan bayan auren d'ari bisa d'ari kuma in sha Allah sai ta aure shi." Umma tayi murmushi tace, "Daman Malam ai baza ka k'i ba kai." Kawu Badamasi yace, "Muma bamu k'i ba muna fatan abinda yafi alkhairi Allah ya zab'a, in shine alkhairin Allah ya tabbatar da arzuk'i a gidan wasu ai gwara a gidan ku, kuma kowa yana so yaga nasa cikin jin dad'i da kwanciyar hankali, abin alfaharin mu ne gabad'aya ace Rauda ta auri d'an sarki dan kaf dangin mu ba'a tab'a ba sai a kanta. In kuma babu alkhairi Allah ya watsa lamarin waje duk kud'i ko mulki bazai saka mu kaita inda zamu zo muna dana sani ba." Baba yace, "Da alkhairi ma in Allah ya amince." Shiru sukayi dukkan su kafin suyi sallama su wuce. Baya fitar su Yaya Ummi ta kalli Rauda tace, "to kinji yanzu babu batun maganar Anas sai ki dawo da hankalin ki kan Asad." Rauda ta murmusa tace, "Wallahi Yaya sai nake jin zuciyata tayi min nauyi da akace ya fasa aurena, ashe shiyasa ya kasa nema na a waya." Umma tace, "Ni kaina zuciyata babu dad'i Rauda balle ke, Anas ya cancanci aso shi kodan soyayyar da ya nuna miki ashe Allah bai rubuta zai mallake ki matsayin matar sa ba, Allah sarki! Allah ya zab'a masa abinda yafi alkhairi ya basu zaman lafiya shida wacce aka zab'a masa." Rauda tayi shiru tana jin babu dad'i a zuciyar ta. *☆☆* Gudu yake sosai a motar yadda Mama ta kira shi a wayar tana kuka ta d'aga masa hankali sosai hakan ya saka yake gudu kamar zai tashi sama burin sa yaje yaji kiran da take masa. Ko gama faka motar baiyi ba ya fita da sauri zuwa wajan ta yana shiga falon farko bata nan ya shiga ciki ya tarar da ita ita da Mum a zaune sunyi jugum-jugum kamar an musu rasuwa. Hankalin sa tashe yace, "Mama lafiya?." Kallon sa tayi da jajayen idanun sa ta yafito shi da hannu ya k'arasa kusa da ita ya zauna ta rik'e hannun sa tace, "Asad dan Allah ka janye batun maganar auren yarinyar nan, bata da tarbiyya ko kad'an bata da kirki." Juya idanun sa yayi ya rik'e hannun ta da yake cikin nasa yace, "meya faru?." Mum da take gefe tace, "zuwa gidan su yarinyar mukayi da niyar ta rok'e ta kar ta amince maka; yarinyar ta dinga zazzaga masa rashin kunya har da k'okarin dukan mahaifiyar ka tana fad'in bata ga wanda ya isa ya raba ku ba. Bata da tarbiyya gabad'aya yarinyar in kaji cin mutuncin da tayi mata baza ka d'auka tana da hankali bama." Asad da yake jinsu yayi shiru kawai baice komai ba jin yayi shiru ya saka Mama tace, "Asad dan Allah ka fasa auren ta, ka aure ta zan iya mutuwa dan zuciya ta zata iya fashewa ko wanne lokaci." Asad sanyaye yace, "Mamana bazata mutu ba, Allah ya wuci zuciyar ki, I'm sorry" ya furta a hankali yana kallon ta. "Ka fasa d'in?" Ta tambaya tana kallon idanun sa. Kasa magana yayi dan bai san me zaice mata ba hakan ya saka shi yin shiru kana yace, "zan fad'a sanar da mamana in anjima, ina zuwa yanzu" ya fad'a yana tashi ya fita daga falon zuciyar sa duk babu dad'i. Mum ta kalli Mama tace, "bafa zai amince ba an riga an juyar masa da tunani daga kanki, in badan haka ba Asad ne kike rok'on abu a wajan sa amma yake cewa ki jira ya dawo anjima, yaron da kince zo kayi yake cewa to in ba asiri ba meye?." Mama sabida abinda take ji bata ce komai ba amma ta amince da asiri aka yi masa dan ga zahiri ta gani. Mum tace, "Ai hanya ta biyu dole zamu bi, ko a kashe yarinyar, ko a haukata ta. Cikin biyu zamuyi guda d'aya." Mama tace, "Kisan yafi haukan, ta b'ace bat daga duniyar yafi ace tana cikin duniyar hankali ne babu. Kije ayi duk abinda za'ayi aga bayan ta tsakanin yau zuwa gobe kin san bana son b'ata lokaci, sai dai bana so a samu matsala, bana so sunana na ya fito, bana so ayi mata kisan da za'a fahimci kashe ta akayi." Mum ta tashi tsaye tace, "Baki da matsala Fulani wannan ki d'auka an gama." Ta d'auki jakar ta da makullin mota kana tace, "Sai kin jini" tana fad'a ta fice daga cikin falon. Asad da ya fita daga wajan Mama daga gidan ya fice gabad'aya dan bazai iya jure abinda yake ji ba ya hau mota ya tafi gidan da ya saba keb'e kansa, yana zaune a falon gidan ya zubawa waje d'aya ido yana kallo zuciyar sa na bugawa da gudu ko ya ya kulle idanun sa Rauda yake gani. 'Ina sonta sosai, amma nafi son Mama da ita bazan iya ganin Mama cikin wani hali sabida ita ba, zan cire komai a raina.' Abinda yake fad'a a zuciyar sa kenan gabad'aya ransa a jagule yake. Motsi yaji a bayan sa ya juya suka had'a ido da Hydar ya k'araso kusa dashi ya zauna yana kallon sa kana yace, "Deaf indai zaka biyewa Mama baza ka tab'a samun farin ciki ba." Da sauri Asad ya kalle shi Hydar yace, "yeah sabida duk hanyar da ka biyo ta neman farin cikin ka sai Mama ta toshe ta, ka bar abubuwa da yawa sabida ita ya kamata zuwa yanzu kaima ka samu abinda kake so a karona farko, farin cikin ta kawai ta sani banda naka." "She's my mother tana da ikon zab'a min duk abinda take so, bana son rasa ta a cikin rayuwata" Asad ya fad'a a raunace yana kallon k'asa. "Even me i love her because itace ta haife mu bamu da wata kamar ta a kaf dunitar nan, but tana son kanta da yawa ne Asad musamman akan abinda ya shafe ka, tana tauye maka hakki ka always abinda take so kake yi meyasa wannan baza ta baka dama ba?." "I can leave anythings because of her" ya sake furtawa yana lumshe idanun sa. "I know Asad but ka aikata hakan zaka cutar da kanka ne fiye da lokacin baya, Sabida you loves Rauda so much itace ta farko da ka fara yiwa wannan son, lokaci d'aya Allah ya d'ora maka k'aunar ta a zuciyar ka cire ta ba abu bane mai sauk'i. Try to understand soyayya ba irin aiki da mukaman da ta saka ka bari a baya bane, wannan rayuwar kace domin soyayyar ta ta riga ta kama ka barin ta illa ce a gare ka." Asad ya furzar da iska ya kalli Hydar da idanun sa yace, "Meye mafita?." "Addu'a. Nasan kana yi but ka k'ara a kan wacce kake yi, in Rauda alkhairi ce a rayuwar ka Allah ya baka ita in ba alkhairi bace ya fitar da ita daga ranka." Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa da maganar Hydar kafin Hydar ya kuma cewa, "then yana da kyau ko number yarinyar ne ka nema sabida ku dinga gaisawa, hakan zai rage maka wani abun a zuciyar ka." Asad ya girgiza kai alamun a'a kafin yace, "I can't." "U can" ya bashi amsa shima yana kallon sa. Murmushi Asad yayi har hak'oran sa suka bayyana fuskar sa ta washe sosai annurin ta ya fito kyau da zatin da Allah yayi mata ya fito k'arara ba tare da ya shirya ba. Ganin hakan ya saka Hydar yayi murmushin shima yace, "Kayi murmushi mana nasan zaka iya sabida kana sonta." Baice komai ba Hydar daman yasan bazai ce ba sai yace, "Deaf nifa ina ganin rashin gaskiya a tare da Aliyu cikin kwanakin nan, bana amincewa da yanayin sa gabad'aya." Tab'e baki Asad yayi kawai baice komai ba dan shima ya fahimta musamman ma halayya da shiga da ya canja ya koma sak irin nasa kafin ya d'auki wayar sa ya fara dannawa. Haka suka zauna shiru babu mai magana a cikin su sai daga baya suka tafi suka bar gidan. *☆☆* Mum ce a zaune a gaban wani malamin daban ba wanda suka je wajan sa da Mama ba yana ta dube-duben sa kafin ya d'ago ya kalle ta yace, "Auren nasu yana da wahalar rabuwa amma za'a raba shi." Mum ta girgiza kai tace, "haka nake so naji Malam, so nake a raba auren a saka masa tsanar yarinyar itama a saka mata tsanar sa ta har abada." Malam yace, "wannan baki da matsala Hajiya Sadiya, sai dai za'a kashe kud'i." "Kud'i ba matsala ta bane ba Malam ayi kawai." Malam yace, "Zaki ga aiki kuwa nan bada jimawa ba." Gyara zama tayi tace, "Aiki na biyu so nake a saka masa k'aunar Jidda a ransa fiye da yadda yake k'aunar ita gurguwar, ya manta da kowa da komai Jidda kawai yake gani. Hatta uwar sa Rabi'atu ya manta da ita gabad'aya ya zama Jidda ce zata juya shi yadda take so duk abinda tace shi zaiyi." Girgiza kai tare da yin dariya kad'an yace, "Za'ayi hakan tabbas. Amma yana da wahala kasancewar sa mai ibada da zama cikin alwala muna buk'atar lokacin da ya kasance babu tsarki a jikin sa a sannan aikin mu zai tafi yadda muke so. Dan aikin da zamuyi masa akan Jidda ba k'arami bane ba gaskiya." Mum tace, "ta yaya zamu san bashi da tsarki?." Malam yace, "Wannan ba abin damuwa bane ba zamu gano hakan da kanmu." Mum tace, "to ma sha Allah haka nake so naji. Batun auren sa da Jiddan yana nan dai ko?." Malam yace, "yana nan kawai dai akwai sauran lokaci amma akwai maganar auren su kamar yadda nake shaida miki, kuma dole sai ita gurguwar bata tare dashi sannan zai kalli Jidda." Mum tace, "Za'ayi maganin ta ai. Ina maganin da mukayi zaka bani?." Malam ya juya gefen sa ya d'auko wani turare a k'aramar kwalba ya mik'a mata yace, "Wannan turaren zaki shafa in zaki je wajan ta ko in zaki had'u da ita a ko wanne lokaci, ina tabbatar miki tana shak'ar sa a lokacin babu wani sirrin ta da zata b'oye miki komai sai kinji sai kuma abinda kika ce mata shi zatayi." Mum ta karb'a ta saka a jaka ta fito da kud'i masu yawa ta ajjiye masa kafin tace, "Na gode Malam, a cigaba da aiki in komai yazo mana yadda muke so duka tare zamu ji dad'i, sauri nake mayi waya" ta fad'a tana mik'ewa ta fita da sauri. *☆☆* "Me kike so kice mana kenan master planer? Asad zaiyi aure?" Waziri ya fad'a a bayyane cike da mamaki da kuma al'ajabi. Daga cikin wayar Hajiya tace, "Nima dai jin abun nayi wani iri, kika ce kuma gurguwa zai aura?." Dariyar tayi tace, "tabbas Asad zaiyi aure nan bada jimawa ba zai bar k'asar Nigeria zai tafi can wata k'asar yaje kula da matar sa, a wannan lokacin muke da damar sake nisanta shi da k'asar gabad'aya." Waziri yace, "To ya maganar Aliyu kuma? Ya amince min amma har yanzu bai sake tuntub'a ta ba nima kuma haka." "Ya fika wayo wannan yaron raba k'afa yayi yana nasa aikin yana kuma naku aikin, duk maganar auren nan shine assasata badan komai ba sai don cikar burin sa. Zai mana amfani a tafiyar mu sosai domin kansa yana ja fiye da tunanin ku zai kawo mana mafita lokacin da abubuwa suka yi mana yawa." Hajiya tace, "Sai nake ganin kamar yaudara ce amma baya tare damu." Master tace, "yana cikin mu yana kuma saka idanu akan ku gabad'aya duk motsin ku ya sani, tafiya dashi zata yi mana amfani sosai amma sai nan gaba zaku fahimci inda na dosa. Tsarin da ya saka muka jawo shi cikin mu yanzu babu batun sa tunda shi Asad d'in zai bar k'asar nan da wasu kwanaki ba buk'atar mu canja shi da Aliyu." Waziri yace, "kuma kina ganin tsarin zai tafi yadda muke so kuwa?." "Sosai ma kuwa fiye da hakan ma ku dai ku shirya ta kusa fashewa mu samu abinda muke so, boom!" Ta fad'a tana yanke wayar compress call d'in ya rage daga shi sai Hajiya a kai. "kana ganin abinda tace haka ne kuwa? Nifa ban ji maganar aure a cikin gidan nan ba ta ya akayi ita ta san da ita?." "Tunda tace haka tofa haka d'in ne, zan bincika yanzun nan naji gaskiyar lamarin koma meye ai bazai b'uya ba, in da gaske akwai maganar auren ai sai munfi kowa farin ciki da hakan. Ki saurare ni zan sanar dake abinda na binciko" ya fad'a yana yanke wayar shima. *☆☆* Rauda haka ta wuni sukuku bata son Anas amma bata jin dad'in raba su d'in da akayi lokaci d'aya ba gabad'aya sai taji tana jin zafi a zuciyar ta hakan ya haifar da sanyin jiki a gangar jikin ta. Tana zaune a d'akin da suke kwana ita da Ummulkhairi tana juya wayar da ya bata gabad'aya wani iri take jin ta kamar ba ita ba zuciyar ta a jagule kamar ta zubar da hawaye. Shigowar sak'o taji wayar ta tayi kamar bata ta duba ba sai kuma ta duba ta bud'e tana karantawa. _Assalamu Alaikum Rauda ina fatan kin wuni lafiya ya jikin ki da jikin Umma?. Nasan kin ji labarin abinda yake faruwa wata k'ila zaki ji babu dad'i duk da ba sona kike yi ba amma nasan zaki tausaya min tunda kin san ke kad'ai ce a zuciyata ke kad'ai kuma nake k'auna. Wallahil azim ke nake so Rauda har gobe har jibi har na mutu amma iyayena sun nuna min wacce suke so na aura babu yadda zanyi na amince musu sabida matsayin su gare ni. Bazan ce ki jira ni nayi aure na dawo na aure ki ba nasan abu ne mai wahala shiyasa na saka a raina na rasa ki har abada, wallahi ina rubuta miki message d'in nan ina hawaye Rauda domin na tabbatar na rasa abinda nake so wanda bazan mayar da kamar sa ba har abada. Ina sonki Rauda, ina k'aunar ki har gobe, naso ace zan rayu dake har abada amma hakan bai yu ba duk da har yanzu ban cire rai dake ba amma ni kaina ina ganin wahalar hakan. Ki yafe min wallahi ba'a son raina ba banyi kuma dan na yaudare ki ba, kunyar ki nake ji shiyasa na kasa ko kiran ki a waya dan ban san me zance miki ba in na kira ki, ina fatan zaki yafe min za kuma ki dinga min addu'ar Allah ya bani ikon yiwa wacce za'a aura min adalci domin matuk'ar ba ke ba bana tunanin akwai wacce zan zauna da ita da zuciya d'aya. Ina miki fatan alkhairi Allah ya baki miji na gari ya baki lafiya Amin. ANAS._ Babu tsammani taji hawaye yana bin fuskar ta wanda batayi tunanin zasu zuba ba a wannan lokacin ba, ta ajjiye wayar tana kuka mara sauti tana fad'in, "Allah ya baka juriyar rashi na Anas, ni kaina zanyi rashin wanda yake sona da zuciya d'aya, ko bana son ka zan iya zama dakai Anas sabida kai me k'auna tane na tabbata bazan yi dana sanin zab'ar ka ba, Allah bai amince zan zama matar ka ba, Allah ya baka hak'urin rashi na" ta fad'a tana goge idanun ta jikin ta duk ya mutu murus. Asad ne ya fad'o mata a rai nan take gaban ta ya fad'i ta dafe k'irjin ta tana jin yadda yake bugawa tayi shiru ta nutsu tana sauraron bugun zuciyar tata a hankali, ta rasa meyasa in ta tuna shi take jin bugun zuciya ta rasa dalilin hakan. kawar da tunanin tayi ta d'auki wayar ta ta shiga mayarwa da Anas amsa da kalamai masu sanyaya zuciya da taushi had'i da tausasawa har ta kammala ta ajjiye wayar a gefe tana tunani. 'Matuk'ar bai bayyana min yana k'auna ta ba bazan amince da auren sa ba, a soyayya ba'a nuna mulki da izza shi na lura abinda yafi mayar da hankali kenan a kai, zan nuna masa ba'a samun ko wacce mace da k'asaita ko izza.' Abinda take fad'a a zuciyar ta kenan a bayyane tace, "to ma in ya furta zan amince kenan? Anya na dace da rayuwar sa na kuma yiwa kaina adalci..? ga abinda mahaifiyar sa take fad'a ban kai kaina inda za'a kashe ni ba kuwa?. To wai duk da nake wannan tunanin sonsa nake kome..?" Ta fad'a tana jan dogom tsaki tana kallon sama abubuwa sun mata yawa a kanta duk sun cushe mata zuciya. K'arar wayar ta taji duk a tunanin ta a Anas ne ta jawo ta ta d'auka bata duba waye ba ta d'aga wayar ta kara a kunnen ta tana jiran taji maganar Anas sai taji sab'anin hakan, nan take zuciyar ta ta sake bugawa ta cigaba da bugu kamar ana doka ganga tunanin ta ya tsaya cak lokacin da taji ance, "Ina sonki, na fara sonki lokacin da ban shirya ba........!." *End of Book1*🤗⛹‍♀️ _Waye ya kira Rauda wannan lokacin..? Asad ne ko kuma Hydar ne ya kira a madadin sa...?. Rauda zata amince da Asad tunda babu maganar Anas a halin da ake ciki ko a'a..? In ta amince dashi tayi ya da Mama wacce take shirin kashe ta? Anya auren su zai kasance Mama tana raye...?. In ya kasance kuma ta yaya ta wacce hanya hakan zata faru...?. Ina matsayin Jidda da kuma Mum da suke son ganin bayan Mama? Asad zai amince da Jidda kuwa har ya aure ta? In ya aure ta kuma ya kenan in suka raba shi da Maman sa?. Aliyu fa? Anya shima zai bar Asad zaman lafiya duba ds yadda ya koma acting like Asad..? Anya babu abinda yake shiryawa a kan hakan tunda dukkan mu mun shaida yana son ganin bayan Asad?. Wacece master planer? A ina take da zama da take sanin sirran cikin gida tun kafin na gidan su sani?. Ina makomar su Waziri zasuyi nasara ko a'a? Shin Asad zai mulki katagum ne ko a'a? Shin Rauda zata zata aure shi ko a'a? Shin Jidda zata aure shi ko a'a?. Akwai rikici, akwai makirci, akwai tashin hankali, akwai dana sani, akwai soyayya, akwai akasin ta duk a cikin book2._ _Duka amsar wannan tambayoyi suna cikin littafin kwantan b'auna book2 da zai fara zuwa nan bada jimawa ba in sha Allah akan naira 500 kacal. domin biya tuntub'e ni akan number via whatsapp 09030398006. Kar ku sake a baku labari tabbaci nake dashi akan KWANTAN B'AUNA salon sa ba irin wanda kuka saba karantawa bane, daban yake a cikin littafan sai kayi sa'a zaka samu irin sa._ Sai na jiku mutanen amana🥰 #Vote #Share #like #Comments #gidan sarauta #makarci #fuska biyu #Soyayya