GIDAN ARO *01* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM _Abuja, Nigeria_ National Police Headquarters. _Criminal Investigation Department (CID)_ Cikin k’warewa da sanin makamar aikinta budurwar mai kimanin shekaru 29 taci gaba da kwararo bayanai tana mai nuni da Farin allo wanda hasken k’wan wutan projector ya haskesa, Ko ba’a fad’a maka ba zaka fahimci cewa cikin d’akin gudanar da binciken manya manyan laifuka suke musamman irin laifin da ya shafi kisan kai, fyad’e, Garkuwa da mutane da sauransu.. Hoton wani matashi ne na’urar Ta hasko, kwance yake a k’asa tamkar bai numfashi, ga dukkan alamu babu rai tattareda shi.. Ko ina na wajen a kewaye ne da Doguwar igiya mai launin ruwan d’orawa, jikin igiyan an rubuta _Restricted Area_ da manyan bak’ak’e... Budurwar ta k’urama hoton idanu Wanda ya bayyana Babba gabansu kasancewar da na’uarar projector ake hasko hoton.. Ta matso sosai tana mai rage girman idanunta tana kallon hoton, a hankali take furta “Da hannun hagu ya rik’e bindigar, direction d’in da bindigar Ta kalla bai kamata harsashi ya samu k’irjinsa direct ba, ya kamata harsashin ya huda ribs d’insa kafin ya ratsa cikin k’irjinsa indai har da hannun da aka sami bindigar a ciki yayi harbin..” Wani matashi mai kimanin shekaru 32 ya taso yana k’arasowa kusanta wanda shima d’aya ne daga cikin ‘yansanda masu gudanar da bincike da suke zaune a madaidaicin Zauren gudanar da binciken.. Hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa, idanunsa naga hoton yake furta “Well done Agent Maleeka.. But wani hanzari ba gudu ba.. Baki tunanin idan mutumin nan ya kasance bahago zai iya karkata hannunsa har harsashin ta iso daidai tsakiyar k’irjinsa ta hudasa..?” Karkatowa Maleeka tai tana duban wanda Yai maganar kafin ta d’an tab’e baki tace “Bani da tabbaci Inspector Assad.. Amma hakan nake tunani..” Bata Kai aya ba wata murya ta katsesu da fad’in “Oh shut up.!” Gaba d’aya suka juyo suna dubansa, kusan tun shigowarsu d’akin kansa a k’asa yana aikin murza zoben dake mak’ale yatsarsa guda wanda yin hakan kusan d’abi’arsa ce musamman idan yana nazarin bincike.. Ya d’ago kai yana dubansu, kallon da yake sanyata daburcewa ta rasa mai take ciki, tunaninta duk su sakwarkwace shi ya jefata dashi kafin yace “Tunani kikeyi.? Ko kuwa kin tabbatar..?” Kasa furta komai tai sai yin k’asa da idanunta da tai Hannayensa biyu sakale cikin aljihun wandon jeans d’insa, yana tsaye gabanta yana iya hango tsakiyan kanta sabida ratan tsawo dake tsakaninsu.. Cikin muryarsa da yake tsakanin kashe mata jiki lak’was wanda yake sanyata losing kanta gaba d’aya ya soma furta “We are investigating a murder here, in case you forgot.. There’s nothing like you thought, everything here must be known.. You must Know.. I want results and not assumptions.. Kin fahimta..” Ya k’arashe yana kwanto da fuskarsa kusan nata, idanunsa da suke matuk’ar furgitata dab kusan nata... A hankali take jinjina kai cikin yanayi na d’an daburcewa “I..I’m sorry Inspector, Sir..” “I don’t need your apology.. Just do your work correctly.. Or else, you’ll be kicked out of this team..!” Yanda yake maganar cikin tsananin zafin rai zaka fahimci ransa a matuk’ar b’ace yake.. Mutumin dake tsaye gefen Maleeka ya d’an girgiza kai kad’an kafin yace “But..” Katsesa yai da fad’in “What do you mean but.?.. You know me quite well Assad, you know I hate incompetence.. And I easily get irritated by people like her around.” Assad ya d’an shafi kansa dan yasan Wanene abokin nasa da kuma yanayin da yake ciki “MU’AZZAM.. will you please calm down.. I was only asking you to go easy on her..” “Oh really..! Da gaske Assad.. Am I really being too strict?.. Let me remind you idan ka mance.. Mutuwar k’anwata muke bincike a nan Assad.. K’anwata was found dead tareda wannan d’an ta’addan.. And you’re asking me to go easy on her... My sister Assad.. My only Sister.. An kasheta in a cold blooded murder.. Someone murdered her Assad.. Sannan na kasa aiwatar da komai domin wad’anda suka kasheta su biya abinda suka aikata.. Tell me, a haka ne kake ce min na natsu.. A haka ne kake ce min I should calm down and go easy on her Assad.!” Ya k’arashe cikin tsananin d’aga murya gashin jikinsa na kuma mimmik’ewa D’akin yai shiru sai hucin fitar numfashin Mu’azzam kakeji.. Cikin rarrabewar kalma yake ci gaba da furta “If she’s not competent enough to work with this team, the door is widely open..” Cikin zafin nama Assad ya katse sa da fad’in “But the man who killed your sister is dead too.. He committed suicide after he killed your sister Mu’azzam..!” Ya k’arasa jikin k’aton allon ya shiga nunawa yana fad’in “Look.. Look here, look at the suspect, ya kashe kanshi bayan ya kasheta.. Bindiga d’aya yayi amfani dashi.. Ga finger prints d’insa a jikin bindigar an samu.. Duk iyaka binciken da za’ayi anyi Mu’azzam but still babu wani abinda yake canzawa.. Until now we couldn’t figure anything out sabida bamuda wani dalili Ko hujja...Amsa d’aya muke samu a k’arshe shine mutumin nan kashe kansa yayi bayan ya kashe Ikram.. Sannan inaga ya kamata mu saki mutumin nan dake tsare cikin interrogation, babu amfanin detaining d’insa a nan..” Wani irin duba yake ma Assad da idanunsa da suka gama rinewa zuwa ja, lokaci guda yake jinjina kai kafin ya mik’a hannu saman Table dake gefensa ya d’auko k’aramar bindiga piston.. Cikin tsananin huci yake furta “I’ll proof to y’all that that man didn’t kill himself.. Someone killed him..” Yai maganar yana pointing Assad da bindigar zuciyarsa na kuma tafarfasa.. Maleeka kame baki tai idanu a warwaje take duban Assad da Mu’azzam.. “Sir.. What are you doing.. Please don’t..” Maleeka tai maganar cikeda tsoro.. Ko kallo bata ishi Mu’azzam ba balle ya amsata.. Pointing bindigar yai daidai saitin k’irjin Assad, yana kallonsa yana huci kaman mai shirin d’ana harsashi.. Lokaci guda ya karkato da bindigar saitin ya juyo da Ita saitin nasa k’irjin, bindigar tana rik’e ne cikin left hand d’insa kasancewarsa left handed, shid’in bahago ne.. Bai daina sakin huci ba yana rik’e da bindigar idanunsa tar akan fuskar Assad. Maleeka Ta kuma zaro idanu waje ganin Mu’azzam yayi pointing kansa da bindiga, cikin tsananin daburcewa take girgiza kai tana k’ok’arin rintse idanunta, dan gani take kaman d’ana ma kansa harsashi yake da niyya D’aya mutumin dake zaune saman kujeransa wanda shine cikon na hud’unsu a cikin d’akin wanda ya d’an fisu gaba d’aya a haife dan shi zai kusan shekaru 39 sai sannan ya taso ya k’araso yanda suke a tsartsaye.. Ya isa jikin board d’in yana nuna hannun mutumin yanda ya rik’e bindigar ya d’ana ma kansa harshashi cikin hoton, kafin ya kaikaito yana duban Mu’azzam dake rik’e da bindiga yayi pointing kansa daidai yanda wannan mutumin yayi.. A hankali ya saki murmushi yana ma jinjina kafin tunani da jajircewa a aiki irin na Mu’azzam.. Rik’e bindigar da yayi so yake ya masu proving cewa mutumin nan baiyi committing suicide ba kaman yanda ya bayyana masu cikin hoton.. Wani ne ya kashesa sannan ya saka bindigar cikin hannunsa dan idan ba haka ba babu yanda za’ayi ya harbi kansa a wannan position d’in... Tafe hannunsa mutumin ya shigayi yana furta “Impressive.. Bravo Officer MA Gamji..” Yai maganar yana mai tafe hannayensa lokaci guda yake duban Mu’azzam.. Assad ya kai dubansa ga hoton yana yanda mutumin ya rik’e bindigar sannan yakai dubansa ga Mu’azzam, ko shakka babu wannan rik’on bindigar saka masa akayi sannan ya tabbata bashi ya harbi kansa ba.. Jinina Kai Assad yai murmushi saman fuskarsa yake duban aminin nasa.. Lokaci guda ya k’araso gabansa kafin ya d’aga hannu yana sara masa alamun jinjina. Officer Maleeka ma wani irin murmushi ne taji ya kufce mata cikeda jin dad’i dan har Ta fara tunanin idan basu samu komai out of this case ba watsi za’ayi da binciken and bazata samu lokacin da take so Ta samu dan Ta kasance da Mu’azzam ba.. Sabida son kasancewa taredashi ne yasa tayi yanda tayi akayi assigning nata to case d’in... A hankali mutumin ya zare bindigar daga hannun Mu’azzam yana mai furta “Weldon Mu’azzam har na fara tunanin idan bamu samu komai ba anything can happen.. Za’a iya rufe case d’in...” Sai sannan Mu’azzam ya dubesa ya sara masa kafin yace “Believe me Yusuf babu wanda ya isa ya rufe case d’in nan until I get to the bottom of everything.. Is a promise, Alk’awari ne da na d’aukarwa mahaifiyata dake cikin tsananin jinya wacce batasan d’iyarta Ta mutu ba.. Wacce duk randa ta farka daga wannan jinya nata zata farka ne ta tadda babu d’iyarta.. Babu Ikram..” Ya k’arashe wane irin gumi na karyo masa tin daga cikin sumarsa har zuwa karan hancinsa da ya dace da kyakkyawan fuskarsa... Lokaci guda yaci gaba da furta “Yanzu da duk muka fahimci abu guda nida ku.. I’m goin to make that imbecile talk..!” Daga haka cikin sauri ya juya ya fice daga cikin d’akin.. Assad yabi bayansa yana kiran sunansa inaa Ko zarafin tsayawa bai samu ba balle ya amsa sa.. Yana isowa ya bud’e k’ofan interrogation d’in ya shige ciki saidai yana shigewa ya maida k’ofar ya danna mata lock yanda Assad Bazai iya shigowa ba... Girgiza kai kurum Assad yayi dan yasan waye abokin nasa idan ransa ya b’aci.. Wani mutumi ne zaune saman kujera nan cikin interrogation d’in, Mu’azzam ya d’ibi lokaci yana dubansa cikin tsananin tsimewa.. Murmushi ne saman fuskar mutumin, yana murmushin yana shafa hab’arsa, cikin muryarsa da yafi kama da ta ‘yantadda yake furta “Officer MA Gamji, you’re not going to get anything from me.. zaifi kyau idan ka sakeni nayi tafiyata dan idan ba haka ba zan iya shigar da k’ara an ajiyeni a police station babu dalili..” Cikin takunsa irinta cikakkun mazaje da suka sha training suka k’oshi ya soma takowa, hannayensa dafe da belt d’in wandonsa.. Saida ya k’araso har gaban mutumin kafin ya zauna a kujera mai fuskantar mutumin.. Zoben dake hannunsa ya cire ya wainata saman table d’in da ya raba tsakaninsu da mutumin, saida yayi hakan kusan sau uku k’afarsa d’aya bisa d’aya kaman bazai ce komai ba, har lokacin idanunsa naga zobensa da yake faman wainata saman table.. Mutumin ya kuma murmusawa kafin yace “Mr Officer, if you think you’re goin to get something from me you’re quite mistaken..” Cak ya katse maganar nasa sakamakon ganin hoton da ya aje masa saman table d’in.. “Im gonna ask you for the last time.. Tell me everything you know about this guy..!” Mu’azzam ya k’arashe yana mai matso da fsukarsa dab kusan na mutumin yatsarsa manuniya na saman hoton yana nuna hoton da Ita.... K’uri mutumin yai yana dubansa kafin ya saki murmushi kad’an yace “You won’t get anything from me, Mr Officer..?” Wani irin zabura Mu’azzam yayi saida yai fatali da table d’in da ya raba tsakaninsu da mutumin.. Ya finciko wuyan mutumin ya matse ya had’uda da garu yana mai ci gaba da sakin huci “I am not playing games with you.. Now tell me.. Ka fad’a mun mai ka Sani akanshi..? Wanene shi..?” Mutumin da yaji matsa idanunsa sun firfito waje yana neman hanyar da zai shak’i iskan numfashi ya fitar da k’yar yake jinjina kai ma Mu’azzam alamun ya sakar masa wuya zai fad’i abinda ya Sani... Jifa dashi Mu’azzam yai yana yarfe hannunsa kafin ya isa gabansa ya d’an duk’a kad’an “Tell me..” Ya fad’i idanunsa akan mutumin.. Da k’yar mutumin ya d’an iya mik’ewa ya zauna dirshan a k’asa kafin ya soma fad’in “Baida kowa.. D’an ta’adda ne.. Baida kowa a garin nan, sannan bansan daga Ina yake ba.. Amma nasan a nan yake running businesses d’insa..” Cikin zak’ewa Mu’azzam yace “Ya akai kasan d’anta’adda ne...?” “Sabida ni kad’ai yake zama yayi min firan da bai wuce mintoci....” Ya jinjina kai kafin yace “What was his business..?” Girgiza kai mutumin yai kafin yace “Komai ma business d’insa ne as far as wannan kasuwancin ta’addanci ne...Iyakacin abinda zan iya fad’a maka kenan..” Mu’azzam ya kuma gyara tsugunonsa idanunsa nakan mutumin kaman mai tsoron kar yayi losing sight d’insa kafin yace “Baida kowa.? Baida tak’amammen aboki ko wani abu mai kama da haka.. Tell me..” “As I told you , mutumin nan ganinsa kawai muke yazo ya sai sigari yasha ya k’ara gaba.. Amma wata rana naji yana waya kaman da wacce zai aura ne..” “Wacce zai aura..?” Mu’azzam ya tambaya cikin son jin yaji komai. Mutumin ya jinjina kai yace “K’warai wacce zai aura.. Dik a wanann daban ni kad’ai yake zama yayi hira dani da bai wuce na tsawon minti uku zuwa biyar.. “ Tura masa kujera Mu’azzam yai yace “Tashi ka zauna sannan ka sanar dani firan taku..” Saida mutumin ya d’an fuzar da huci kafin yace “Amma Rankaidad’e bazaka bari a ajiyeni a police station ba dan ka gani da idanunka shago na bana sayar da komai, bana sayar da tabar wiwi sannan bana sayar da k’waya.. Karan sigari kawai nake saidawa Rankaidad’e.. Dan Allah ka taimakeni kar a ajiye ni a nan.. Bana komai illegal I promise..” “Kar ka damu idan muka tabbata baka running wani illegal business na maka alk’awari bazamu ajiye ka a nan ba.. Yanzu ka fad’a mun hiranku na k’arshe da wannan mutumin..” Saida ya gyara zamansa kafin ya soma fad’in “A satin da ya gabata yazo k’ofan shago na, as usual ya sayi sigari na kyauta masa lighter.. Kaman ko yaushe bai shiga cikin mutanen dake zama a daban k’ofan shago na ba.. Ya koma gefe ya soma zuk’ar sigarinsa.. Ya gama shan sigarinsa yazo wajena karb’an canji dan dama sanda ya sayi sigarin ban basa canji ba dan babu canji, nace masa ya gama sha kafin a samu canji.. Toh tsayuwarsa yana jirana na had’o masa kan canji na basa yai daidai da fara ringing d’in wayarsa..Ya ciro wayar yana amsawa. Cikin maganganun nasa a waya na fahimci da wacce zai aura yake waya.” Mu’azzam yace “Bakaji wani abu ba gameda budurwar tasa.. Maybe a ina take kokuma wani abu mai kama da haka..?” “Inspector I told you I was only his smoking buddy.. How would I know all the details..!” Murmushi Mu’azzam yai kafin yace “Do you really want us to play this game..? I can assure you I know exactly when to throw my card..” Ya k’arashe yana mai waina zobensa saman table. Lokaci guda yake ci gaba da furta “Nasan baka Sani ba, but I do know a lot of things about you.. I know about your criminal records.. Nasan abubuwan da kake aikatawa wanda zasu kaika jail ka shafe shekaru da Dama.. But If you cooperate with me, zanyi iya k’ok’arina a kotu to make sure anyi reducing sentences d’inka.. So ina shawartanka don’t let me lay my cards first.” Ya k’arashe yana tsaida zoben dake faman wainuwa saman table da yatsarsa guda... Murmushi mutumin yayi yana mai jinjina kai dan yasan business na drugs da yakeyi zai iya kaisa gidan yari.. Yai k’uri wa Mu’azzam yana dubansa wanda babu alamun tsoro Ko d’ar a tattare dashi.. Kaman bazaice komai ba Sai kuma yace “I need protection..” Mu’azzam yai masa k’uri yana dubansa kafin yace “So you do know something..?” Yai maganan yana jinjina kansa yana kuma tabbatarwa plan d’insa really works.. Gyara zamansa yai had’ida d’aura k’afa d’aya bisa d’aya still yana fuskantar mutumin yace “I knew it.. I was right all along..” K’uri mutumin yai masa gajeriyar murmushi saman fuskarsa “But you need to guarantee my safety first, Inspector..” Mu’azzam ya jinjina masa kai yana mai furta “We will give you protection here.. I promise.. Just tell me what you know..” Ya jinjina kansa a hankali idanunsa akan Mu’azzam sann ya tura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya ciro k’aramar takarda a nannad’e.. Lokaci guda ya mik’a ma Mu’azzam yace “Wannan zai iya amsa maka duka tambayoyin ka.. Duk abinda kake so ka Sani gameda mutumin nan..” Mu’azzam yasa hannu ya amshi takardan ya warware.. Address ne na wani gida a jiki.. Ya d’ago yana duban mutumin da alaman tambaya.. Jinjina masa kai mutumin yayi yace “Kaje wannan Address d’in zaka sami amsoshin da kake nema...” Mik’awa tsaye Mu’azzam yayi yana juya address d’in wanda yake a garin SULEJA... Bai kuma ce ma mutumin komai ba yasa kai ya fice kaman zai kifa da k’asa.. Mutumin na kiransa yana fad’in yaushe za’a sake shi ya tafi gida.. Inaa ko zarafin juyowa Muazzam baiba balle ya amsa Sa.. Yana fitowa ya tadda Assad yana jiransa.. Cikin sauri Assad ya take masa baya yana fad’in Ina zasuje.. Bai tsaya amsa Assad ba har saida suka k’araso yanda motocinsu Ke ajiye.. Ya dubi Assad yace “You drive..” Assad yace “Destination.?” Takardan dake hannunsa ya d’an warware ya nuna masa.. “Suleja..?” Assad ya maimaita a hankali kafin ya girgiza kai kad’an yana mai capke d’an makullin da Mu’azzam d’in ya jefo masa.. “Do we have a mission there Inspector.?” Cewar Assad dake k’ok’arin key wa Mota.. “Idan munje zaka gani..” Mu’azzam ya basa amsa yana mai kuma duban takardan dake hannunsa.. Maleeka da tin fitowarsu take hangensu, Ta nufo waje cikin sauri amma saidai bata cimmasu ba, cikeda takaici take ciza baki kafin Ta koma cikin building d’in.. ** SULEJA Wata matace zaune tsakar gida tana tsintar wake, yara guda biyu maza zaune gefenta saman tabarma suna cin abinci.. D’aya bazai gaza shekaru 12 ba d’ayan kuma bazai gaza 9 ba.. Sai cin abincin suke hannu baka hannu k’warya alamun yunwa taci ta cinyesu... “SADIYA..! SADIYA..!! Ke SADIYA..!!” Matar Ke fad’i daga nan yanda take zaune tana tsintar wake.. Ganin wacce ta kira d’in bata fito ba ya sanyata yin k’wafa tana mai gyara zamanta saman kujerar had’ida daidaita zaman parantin da waken Ke ciki saman cinyarta “Kar Allah Sa ki fito daga cikin d’akin nan.. Idan yunwa ta azalzaleki zaki fito.. Ke kanki farau ake saka aure a fasa..? Ai ke abinma ki gode ma Allah ne da yanzu kin je kin auri wanda ba’a san danginsa ba.. Wa yasani ma ko d’anta da ne Ko d’an fashi da makami ne, ko kuma ma Dan garkuwa ne da mutane.. Ki gode ma Allah baki da rabon shan wahala ne tinda gashi har shagulgulan bikunku aka fara d’aurin aure kad’ai ya rage aka nemesa aka rasa sa, Allah kad’ai yasan shid’in wane irin mutum ne dan ko danginsa bamu tab’a gani ba sai wannan Kawun nasa.. Da yanzu kin aure shi d’in Allah kad’ai yasan irin masifar da zai janyo miki, ke da gidanki saidai ki rayu ciki tamkar kina a GIDAN ARO ne..” Ta k’arashe tana bushe waken dake cikin parantin... Tana busar waken take ci gaba da furta “Ni duk bama wannan ba uban bashin da mukaci ne na fitan biki ya tsaya min a wuya da yanda zamu kwashe da d’inbin mutanen dake binmu bashi... Oh Allah dai ya fiddamu..” Bataji sallamar ba sai Muryar data jiyo tana furta “K’warai kuwa Uwani gwara ki nemo hanya tun wuri dan yau bani fita cikin gidan nan sai kin lale min kud’ad’e na.. Yo Ai ni bani nace kiyi bukin k’arya ba.. Harda cewa d’an gidan Babban k’usa a k’asar Amurka ‘yarki zata aura.. Toh maza maza idan ma guduma ne ba k’usa ba a fiddo mun kud’ad’ena yanda suka shiga suka fita ehe..” Ta k’arashe tana wane irin jijjiga Mata mai tsintar waken murmushi ta saki wanda hausawa Ke ce ma kafi kuka ciwo “Tabawa kece tafe, k’araso k’izauna mana, ga wajen zama..” “Ank’i a zauna d’in.. Nace bazaa zauna d’in ba.. Yo ni naga wajen zama ne a nan..” “Haba Tabawa mu shiga daga ciki sai muyi maganar..” “Bazan shiga ba..!” Tabawa Ta fad’i tana mai fatali da parantin waken da matar Ke tsincewa Ai ko sai cikin abincin da yaran ke mamuk’a... Wane irin kuka k’aramin ya fashe yana birgima yana fad’in sai an biyasa abincinsa da aka b’ata... SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *02* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tagumi Ta rapka tana duban yaran yanda suke kukan basu k’oshi ba. “Oh ni Uwani naga takaina, yanzu ta Ina zan samo kud’ad’en nan..” “Umma bamu k’oshi ba..” K’aramin yaron ya fad’i yana mutsuke ragowar hawayen dake idanunsa.. Janyo yaran tayi jikinta tana lallashi tana fad’in suyi hak’uri yanzu zata girka masu ragowar waken data tsince.. “Umma nidai ba zanci wake ba, ni abinci mai dad’i da Aunty Sadiya take kawo mana zanci.. Kuma ai Umma kince idan tayi aure Gidanta zamu koma dukanmu.. Kince gidan Babba ne kuma zai d’auke mu gaba d’aya.. Abba kawai zamu bari a nan gidan..” Ya k’arashe daidai sanda wani magidancin mutumi ya fito daga wata d’aki dake can gefe, goge bakinsa yake da karar aswaki ya isa ya d’auki buta ya d’ebi ruwa a famfo dake filin tsakar gidan ba tareda yaceda matar komai ba.. Ta bisa da idanu tana jira taga ko zai mata magana amma shiru baice komai ba, kodashike tasan za’a rina haka.. Bazai ce komi d’in ba dan tinda aka soma hidiman bikin baya saka kansa ciki dan Dama ba’a saka shi ba dukda duwa cewa Sadiya d’iyarsa ce ta cikinsa amma baida ta cewa a gidan sai abinda Sadiya da mahaifiyarta Uwani sukace akeyi.. Uwani irin matan nan ne masu bala’in son abin duniya wanda kwad’ayi ya rufe masu idanu basa gane daidai daga abinda yake ba daidai ba koda kuwa gaskiyar Ta bayyana masu k’arara.. Tun aurensa da Uwani haka nan take, da yana dashi da baidashi sai ta tursasa masa ya kawo mata, koda suka haifi yara ma Uwani bata fasa halinta na kwad’ayi da tsaban son abin duniya had’ida hangen na sama da ita ba.. D’iyarsu Ta fari itace Sadiya Sai Ashiru da Habib d’an autansu.. Sadiya kyakkyawa ce ta gani a fad’a dan tun tana k’arama ake mata lak’abi da Sady pretty a layinsu.. Tinda ta soma zama budurwa Uwani mahafiyarta da suke kira da Umma ta maida ita hanyar samun kud’inta.. Tuni Umma ta hure ma Sadiya kunne cewa ta dinga karb’o masu kud’i hannun samaruka, hakan yasa Sadiya bata raina samari hardai zata samu ta tatsesa ta rariki rabonta.. Kowa a unguwar yayi shaida ma Sady pretty da Ummarta indai akan tara samari barkatai ne da amsan abin hannunsu.. Babu yanda Malam Ibrahim mahaifin Sadiya da suke kirada Abba baiyi ba wajen ganin ya karkatar da Uwani da kuma mummunan d’abi’ar data d’aura d’iyarsu amma abu yaci tura.. Tsaf Uwani take tsefe masa ruwan bala’i tace bazata zauna tanaji tana gani d’iyarta ta k’are a auren matsiyaci ba kaman yanda ita ta k’are.. A haka har Sadiya ta sami gurbin karatu a Jami’ar babban birnin Tarayya.. Idanun Sadiya sun kuma bud’ewa yanda Ta soma gogayya da manyan ‘yanmata masu ji da kansu da kuma yaran masu hannu da shuni.. Tuni Sadiya Ta kumaji Lallai batada miji sai mai Kud’i ko d’an mai kud’i musamman ganin yanda daga shigarta samaruka sukai mata chaa sabida kyaun halitta da Allah yayi mata.. Idan tayi wanka ta shiga makaranta sai ka rantse d’iyar wani hamshak’i ne, daga nan duk wasu situru da abubuwan more rayuwa da take amfani dasu maza Ke bata su.. Daidai da registration da kud’in samari tayi.. Hoto kuwa idan zatayi posting a social media saidai ta tafi can layin bayansu gidan su wata k’awarta Sabeera a nan take hoto dashike mahaifin Sabeera yanada d’an rufin asiri dan babban d’an canji ne cikin Abuja amma gidansa na nan Suleja.. Gida mai d’an karan kyau ya cancad’a.. Kullum Sady pretty tana gidansu Sabeera dan dama tare suka sami gurbin karatu a nan Jami’ar Abuja, course d’aya suke tare suke tafiya tare suke dawowa, a motar gidansu Sabeera ake kaisu a d’auko su wasu sunyi zaton ma ‘yan gida d’aya ne wasu kuma sukanyi zaton Sady ce d’iyar mai Kud’i Sabeera ce ‘yar k’wak’warta.. Bugu da k’ari Sabeera irin ‘yanmatan nan ne da abun hannun iyayensu bai rufe masu ido ba, Sam abun duniya bai d’ad’areta ba kaman k’awarta Sady pretty.. Sady sam bata bari k’awaye suzo gidansu saidai Su had’e a gidansu Sabeera.. A haka Sabeera Ta zamto Aminiyar Sady, sau tari Sabeera takanyi nasiha ma Sady kan irin rayuwar data d’aukar ma kanta amma ko a jikinta takan ce lokacinta gwara taci duniyarta da tsinke.. Bazata bari kyaun da Allah yayi mata ya zamto a wofi ba tinda basu da kud’i zata iya amfani da kyaun da Allah ya bata ta sama masu rayuwa mai inganci itada iyayenta.. Duk wasu kayan more rayuwa da Sady zata kawo gidan Abba baya amfani dasu bai kuma fasa masu nasiha ba musamman ga Uwani mahaifiyar Sadiya.. Ita kam Sadiya ya mata nasihar ya mata fad’an har duka yasha mata amma babu abinda ya canza dan Tuni mahaifiyarta ta hure mata kunne.. K’arshe Umma ce masa tai idan dai bazai bar mata d’iya ta sakata ta wala ba toh wllhi zata kwashe yaran ta tafi taredasu kuma bazai sake ganinsu ba Eritrea zasu koma da shike dama Mahaifiyar Sady ‘yar asalin k’asar Eritrea ce, haka nan take kyakkyawa kaman mutanen k’asar Eritrea masu kusanci da Ethiopia dan a wajenta Sady ta samo tsantsan kyaun halitta da Allah yayi mata, saidai Ita Sady har ta d’ara mahaifiyar tata. Sosai Malam Ibrahim ya samu matsala da Umma akan Barin Sadiya da tai sakaka tana Yawo dan har Dattijan unguwa sun gaji sun soma masa magana, yayi dik yanda zaiyi ya hana hakan abu yaci tura..K’arshe dai shine yace saidai Sady ta fiddo da miji a mata aure kafin ta k’arasa shekararta ta farko a jami’a.. Ana haka ta had’u da wani saurayi mai suna Sagir a Yanargizo.. Nan da nan Sagir ya samu gurbi mai girma a zuciyar Sady dan sosai yake mata b’arin kud’i kuma yace da aure yake nemanta.. Sady ta gama sakankacewa ta yarda ta amince Sagir masoyinta ne Tuni tace masa ya turo ayi maganar aurensu dan Dama Abbanta ya saka mata takunkumi.. Nan Sagir yake sanar da ita cewa iyayensa US suke basa zama a Nigeria.. Shima abinda ya kawosa zuwa yayi dan ya nemi mata ‘yar k’asar Nigeria ya aura ya d’auketa su koma can US suci gaba da zama.. Haba nan fah Sady da Umma suka kuma susucewa akan Sagir.. Ya turo masu wani mutumi guda d’aya a matsayin Uncle d’insa akai maganar aure.. Sagir yace kar suji komai shi zaiyi komai na aure, nan suka kuma jin dad’i.. Nan da nan zance ya d’auka Sady zata auri d’an gidan k’usa bama cikin Abuja suke zama ba cen k’asar Amurka suke da zama shida iyayensa neman macen aure ya dawo dashi gida Nigeria, iyayensa zasu Zo da zaran ya samu mata an soma shagulgulan biki.. Hakan yasa Uwani cin alwashin yin Bikin kece raini ga Sadiyarta, Ta shiga ciwo bashi dan tayi Bikin kece raini, Bikin yaran masu hannu da shuni Bikin nunuwa a shafukan sada zumunta na yanar gizo.. Ana biki kwatsam aka nemi ango aka rasa har rana mai kaman Ta yau basu san abinda ya faru da ango ba.. Ga wayar salulansa ta dena shiga.. Tun Sady na damuwa har dai Umma tace ta daina damuwa k’ila America ya koma dan ya taho da iyayensa tinda an soma shagulgulan biki.. Sabeera ma cewa tayi k’ila US d’in ya tafi kuma ba lallai wayarsa Ta shiga ba.. Hankalin Sady sosai ya tashi, taci kuka tana fad’in Maiyasa bazai kirata ba da zaran ya saka layinsa na k’asar Amurka, Sabeera tace k’ila surprise yake son mata.. Abu kaman wasa babu Sagir babu dalilinsa har zuwa ranan d’aurin aure da aka rasa ango aka rasa mai karb’awa ango aure.. Toh daga nan ne fah Umma da Sadiya suka fara shakku da yinin wane irin mutumi suka jajib’o... Umma Ta nusa tana duban Abba da har ya ida alwalansa yana d’auraye slippers d’insa da sauran ruwan butar har lokacin karan goge bakinsa na cikin bakinsa.. “Abban Sadiya yanzu bazakace komai ba.. Kana jin yanda ake shigo gidan nan sahu sahu ana d’aga min hankali sai na fidda kud’ad’en dana ciwo bashi..” Sai sann ya d’ago ya dubeta “Toh ki biyasu kud’insu mana sai su daina miki sintiri a gida..” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa. Ta k’walalo idanu waje “Ina zan iya kashin tulin kud’ad’en nan Abban Sadiya..?” “Aw dama Kinsan Bakida hanyar samu Kika ciwosu.. Kan wane dalili.? Dan ki birge mutane..? Ai sai ki jira mak’aryacin da ya yaudareku d’in yazo ya biya miki bashin dan nikam Kinsan Ko kud’in haya na shekara da nake biya idan an had’a bazasu isa ba..” Umma ta dafe fuskarta da hannu tana salallami tana furta “Oh ni Uwani na shiga uku, Sadiya kin d’ebo mana ruwan dafa kanmu..” Tana jiyo muryar mijinta na kiran Ashiru da Habib suzo su shige masallaci... Umma ta nufi d’aki yanda Sadiya Ke kwance tana aikin abu guda.. “Ki tashi ki daina wannan koke koken mu soma tunanin yanda zamu samo mafita.” Umma Ta fad’i tana mai zama gefen katifar da Sadiya Ke duk’unk’une tana zuban hawaye, sautin kukan ma ya daina fita.. Idanunta sunyi luhu luhu haka nan ma fuskarta tayi jajazir, tsinin hancinta shima yayi ja har kaman ya k’ara tsawo.. Kallo guda zakai ma Sadiya ka fahimci cewa tana cikin tsananin tashin hankali wanda tinda tazo duniya bata tab’a shiga irinsa ba. “Umma.. Sagir..” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka, sai kuma ta kasa ci gaba da magana sakamakon kukan da ya dad’a taso mata Nan ta kifa kanta tana mai isarta yayinda Umman tai tagumi Ta zuba mata Ta mujiya.. ** Suna tafe saman kwalta Assad naci gaba da jefo masa tambayoyi wanda akasari ba samun amsarsu yake ba shidai kawai damuwarsa su isa wannan location d’in da Danger ya basa.. Wayar Mu’azzam d’in Ta soma ringing.. Yai saurin ciro wayar a aljihu yana duban mai kiran nasa, a d’an kasalce ya k’arawa a kunnensa dan yasan mai kiran nasa matsala zai kunno masa.. Shiru yai ga dukkan alamu yana sauraren d’aya b’angaren ne.. A hankali ya lumshe idanunsa yace “Tell me your location..?” Alright alright I’ll be on my way.. Don’t call a cab just wait for me there..” D’if ya kashe wayar yana mai fuzar da fuci.. “Pull the car over Assad.” Assad da kacaukam hankalinsa kega kwalta d’an kaikaitowa yai yana dubansa “Wait what..?” “Stop the car, zan sauk’a a nan.. I need to go back..” “You mean to the station..?” Assad ya kuma tambaya yana k’ok’arin parking motar gefen kwalta.. Yana k’ok’arin ficewa daga motar yake fad’in “No..MUSADDIQ ne... Daga yanda yake mun magana nasan ba cikin hayyacinsa yake ba..” “Musaddiq kuma..? Na kwana biyu banji kana tare tare da gagaransa ba.. What really happened..?” D’an tab’e baki Mu’azzam yai kafin yace “How would I know.. Abunda na sani kawai shine ya kasa karb’an k’addarar cewa Ikram ta tafi kuma bazata tab’a dawowa ba.. I’m afraid rashin Ikram ka iya jefa Musaddiq halinda ya riga ya bari a baya..” Ya k’arashe damuwa saman fuskarsa.. Cikeda tausayawa Assad yake duban abokin nasa, yasan d’awainiya ne da dama zasu kuma hawa kan Mu’azzam d’in... Daidai lokacinda cab ya tsaya.. Mu’azzam ya shige yana fad’in “Kaje kayi sauri ka isa location d’in zamuyi waya..” Baki sake Assad Ke dubansa yana kuma juya ‘yar k’aramar Doguwar takardan mai d’aukeda address d’inmu.. D’an girgiza kai kurum yai kafin ya shige ya d’auki hanya... ** -Star lake street, Maitama_ Tsaye tayi saman kan matar dake kwance saman gado wacce idanunta Ke bud’e tarau saidai gefen jikinta guda tamkar a shanye yake, bakinta dake karkace miyau na fitowa.. A tak’aice dai kallo guda zakai mata ka fahimci matar tana cikin tsananin jinya ne... A hankali matar dake tsaye kanta ta duk’a tana mai ci gaba da k’are mata kallo, lokaci guda ta saki murmushi tana mai ciro tissue paper dake ake gefe cikin kwali ta shiga goge mata miyau d’in dake fitowa daga cikin bakinta. Lokaci guda take furta “Na shafe tsawon shekaru ina jinyar kishiya.. Shin zan samu riba nan gaba..? Shin hak’ata zata cimma ruwa.. They say everything in life has a price, Nuratu.. Could this be my punishment..?” Tai fasali tana mai duban matar wacce ta kirata da Nuratu kafin ta saki murmushi tace “No wait.. How could this be my punishment bayan ni ban aikata komai ba.. Kece kika aikata mun komai Nuratu.. Kece kika d’auke komai daga gareni.. A baya ked’in matar d’an uwan mijina wacce na miki lak’abi da kishiyar Dinga sannan Hausawa sunce ita d’in tafi zafi.. Kin kasance wacce tafi soyuwa cikin dangi musamman wajen Inne Mahaifiyar mazajenmu..” Ta k’arashe maganar tana mai disposing used tissue paper d’in kafin ta d’auko wani tana mai kuma goge wanda yake gangarowa, lokaci guda take ci gaba da furta “Nayi zaton idan mijinki ya mutu zaki fita daga rayuwarmu.. Zaki koma yanda kika fito.. But then I was wrong.. Ashe mutuwar mijinki ba komai zai k’ara mana ba face kusanci da juna..” Kukanta ya k’aru sanda taci gaba da fad’in “Kin aure mun miji Nuratu.. Kin aure mun miji bayan naki mijin ya mutu.. Kin zamto shalele mafi soyuwa a wajen mijina.. How could you.. Ta yaya zaki aikata mun haka..? Ta yaya Nuratu..” Tasa hannu tana goge hawayen da ya wanke mata fuska kafin taci gaba da fad’in “This is what you deserve.. Keda mijina bazaku tab’a kasancewa ba balle har Kuji dad’in yin rayuwar aure tare.. Bazan tab’a bari hakan ta kasance ba Nuratu.. Ked’in bazaki tab’a warkewa daga wannan ciwo ba.. Kar ki mance da furucina... Dama na gaya miki gidan mijina tamkar GIDAN ARO yake a wajenki... Babu Ke babu sukuni balle samun natsuwa a cikin gidan mijina.. Na fad’a miki aron gidan na baki na d’an wani lokaci.. Zaki fita daga gidan domin kuwa akwai babban shiri da nake miki.. Zaki fice daga wannan gidan kaman yanda na miki alk’awarin cewa shid’in GIDAN ARO ne a wajenki..” Tana kaiwa nan ta kece da wata irin dariya hawaye na fito mata.. Saida har dariyar nata ya koma tamkar kuka kafin ta kifa kanta gefen majinyaciyar tana kuma sakin kuka mai ban tausayi. K’amshin turaren mijinsu da yaima k’ofofin hancinta sallama ya tabbatar mata cewa shid’in ne ya shigo.. Nan fah ta dad’a narkewa tana sakin kuka mai ban tausayi.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:34 AM] My mom: *GIDAN ARO* *03* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ya d’auki mintoci yana tsaye kansu kafin ya duk’a a hankali ya zauna gefen majinyaciyar, yai amfani da hannunsa guda ya dafa matar dake duk’e tana sharb’an kuka “Hajara kukan nan ya isa haka, shi majinyaci ba kuka yake buk’ata daga wajenmu ba.. Abinda yafi buk’ata shine addu’o’inmu.. Kiyi hak’uri ki daina kukan nan kinji..” Ta d’ago fuskarta da tuni hawaye ya wanke ta janyo tissue paper tana share majinan da yazo hancinta alamun taci kuka. “Daddy gaba d’aya hankalina ya gaza kwanciya, ace ko yaushe ahalin nan cikin tashin hankali muke.. Babu k’asar da ba’a fita da Nuratu ba amma jikinta yak’i dad’i kullum ciwon nata ma kaman k’ara gaba yake.. An gama Bikin SAFEENAH da MU’AZZAM Ko tarewa basuyi ba wani tashin hankalin ya kunno aka tsinci gawan Ikram..” Ta kuma saka hannu tana share hawayen dake mak’ale cikin idanunta, a hankali takai hannunta ta dafa saman na majinyaciyar, cikin rawar murya take furta “Poor Nuratu, bata San da labarin mutuwar d’iyarta ba.. I’m sure duk randa ta farka daga wannan jinyar nata ta tadda wannan mummunan labarin zata shiga tashin hankali ne maras misaltuwa.. Na kasa daina tunani, mai Ikram tayima wannan mutumin ya kasheta , sannan Maiyasa shima ya kashe kansa.. Da ace shi D’an Garkuwa da mutane ne da ya nemi Ransom.. Ikram yarinyar kirki ce mai tsananin kamun Kai balle ace biye biyen maza take.. Ko shakka babu mutumin nan saceta yayi...Bazan tab’a mance rawar data taka a rayuwar D’amu Musaddiq ba.. Ikram Ta zamto tamkar wata fitila data haska rayuwar Musaddiq, bani mance lokacin da ya dawo daga k’asar England bai dawo da takardan komai ba.. Baiyi karatun ba Sai yawo da abokan banza.. Bani mancewa har kusan koranshi kayi a gidan nan.. Amma Ikram da Mu’azzam basu cire rai akanshi ba.. Mu’azzam ya shawo kanka ka yafewa Musaddiq, sannan Ita kuma Ikram ta taimakawa Musaddiq wajen ganin rayuwarsa ta inganta.... And now that she’s gone.. I don’t know what’s going to happen to our son..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka.. Alhaji Marwan Gamji ma hawayen da ya kasa rik’ewa ne ya sauk’o masa yana k’ok’arin dannewa..Ya rungume matarsa yana fad’in “Ya isa Hajara.. Allah yana nan da sannu zai daidaita mana al’amran ahalinmu kinji Ko.. Everything will go back to how it was before kinji koh..” Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Ta yaya Al’amara zasu koma kaman yanda suke da bayan babu Ikram a halin yanzu, Ikram ta tafi yanda bazata sake dawowa ba. Al’amara bazasu kuma kasancewa kaman da ba.. Ikram Fitila ce a cikin gidan nan, kowa tasan yanda zata zauna dashi.. Na shak’u da yarinyar nan fiyeda yanda na shak’u da Karimatu da Meema, kusan kullum tare muke yini nida ita wajen jinyar mahaifiyarta.. I saw how dedicated she was to her ailing mother.. Yarinyar kirki wacce ko wace uwa zatayi fatan samun irinta.. Bata tab’a banbanceni da mahaifiyarta ba.. Ikram rashinta zai bar gib’i Babba a gidan nan...” Ta k’arashe cikin tsananin kuka.. Hannu yasa yana mutsuke gajeren hawayen da ya mak’ale masa, lokaci guda yake furta “Wanda duk yayi ma Ikram wannan abun shine aiki yake gabansa domin kuwa itakam Ta sami shaida.. Sannan ita duniya dama takenta kenan GIDAN ARO, dik yanda ka kaiga sonta Ko k’inta wataran dole ka barta.. Yi k’ok’ari ka tanadi guziri mai kyau a GIDAN ARO domin ka inganta gidanka na lahira wacce itace tabbatacciyar GIDA...” Mommy ta d’an dubesa kafin tace “Wai kaima baka yarda wannan mutumin da aka tsinci gawarsu tare shi ya kasheta ba.?” D’an jan numfashi kad’an Daddy yayi yace “To be honest, I don’t know what to believe... Maiyasa mutumin nan zai kashe Ikram sannan ya kashe kansa..?” Mommy tace “Maybe baiso a kamasa dan yasan dole a kamasa shiyasa da yayi garkuwa da Ita ya kasheta sannan ya kashe kansa..” Daddy yai shiru kaman mai nazari sai kuma ya d’an girgiza kai yace “Still it doesn’t make any sense.. Maiyasa zai kashe kansa dan tsoron kar ya tafi gidan Yari..?” Mommy tai shiru tana nazari itama.. Fasali ya d’anyi kafin yaci gaba da fad’in “Inada tabbacin Muazzam bazai huta ba har Sai ya zak’ulo su Wanene Keda alhakin mutuwar Ikram.. Sannan Ina fata kafin zuwa wannan lokaci Nuratu ta sami lafiya domin taga yanda za’a hukunta ko su wanene suka aikata ma d’iyarta haka..” Wani irin bugawa k’irjin Hajiya Hajara yai lokaci guda.. Ta d’ago tana duban mijin nata Wanda da gani har cikin zuciyarsa yayi maganar.. A hankali ta shiga jinjina kai tana furta “Wannan gaskiya ne.. Ko su wanene suka aikata ma Ikram haka sun cancanci a gurfanar dasu gaban shari’a..” Ta d’an nusa kad’an kafin tace “Yau ‘yan Fufore Sun koma gidan Sai ya dad’a mana girma da shiru..” Jin baice komai ba ya sanyata kuma gyara zama tace “Jiya muke magana da Shema’u akan ciwon Nuratu, take ce min har yanzu Aunty Nurah dai shiru jiki yak’i dad’i nace mata wllhi anyi magani k’asashe da dama amma Allah bai nufa an dace ba.. Toh shine take ce min an gwada na gida.? Nace mata Ai baka faye yarda da maganin gidan nan ba.. Tace min akwai wata mata datayi shigen irin ciwonta, maganin wata bafulatana aka gwada dake wata Ruga cen gaba da Fufore.. Shine take ce min Ko za’a gwada nace mata gaskiya saidai idan na maka magana naji abinda zakace.. Magani kuma dace ne ba’a San yanda maganinta yake ba..” Ta k’arashe tana mai tsaresa da idanu cikeda kulawa.. Knocking d’in da akai a k’ofar d’akin ne ya katse masu tattaunawar tasu, Mommy Ta d’an janye jiki daga cikin nasa, tai k’ok’arin saita kanta kafin ta bada izinin shigowa.. Wata budurwar yarinya ce da bazata gaza shekaru 16 ba ta turo k’ofar ta shigo.. Yanayin da suka ganta ciki ya sanyasu zuba mata idanu suna jiran suji yau kuma menene ya faru a gidan “Kiki lafiya..?” Mahaifiyar tata ta tambaya Alhaji Marwan Gamji kaw cewa yai “Come here baby.. Zo ki fad’a min mai ya faru..” Cikin sanyi ta K’araso ga iyayen nata.. Ta dubi wannan ta dubi wannan.. Duban mahaifiyar tata tai tace “Mommy it’s Addah FEENAH.. Tace ita gidanta da Ya Mu’azzam zata tafi tinda ‘yan karb’an gaisuwar Ikram sun watse, ‘Yan Fufore sun koma itama zata tafi nata gidan..” Ta juyo tana duban mahaifin nata “Daddy you need to stop her, nida Meema mun ce mata Bride bata Kai kanta gidan Groom shine tace zataje ta sami Inne ta kaita tinda ita bata koma Fufore ba..” Mik’ewa yayi yana fad’in “Ina Safeenan take..?” “She’s in her room, probably parking her stuff..” Kiki ta fad’i tana matsawa kusan mahaifiyarta dan bama mahaifin nata hanya.. Cikin sauri yasa kai ya fice.. Kiki ta dawo da dubantaga mahafiyarta tana yatsina fuska tana duban Aunty Nurah dake kwance.. “Wai Ke Mommy bazaki daina damuwa akan matar nan bane.. Matar nan fah kishiyarki ce amma ko asalin danginta iyakacin abinda zasu mata kenan.. Ni ban tab’a ganin kishiya irinki ba Mommy wacce take ma kishiyarta jinya. Ko a sch idan ina labarin Mommy ta ita take ma step mom d’ita jinya mamaki suke sha sai suce Lallai Ke ta daban ce..” Tai fasali tana mai zama gefen mahaifiyar tata kafin taci gaba da fad’in “And Mommy tun tasowarmu a haka muke ganin matar nan, ciwonta bai gaba bai baya Ke kuma sai faman wahala kike da ita dik tulun maids d’in dake gidan nan basu isa jinyar nata ba sai kin saka hannu..” Murmusawa Hajia Hajara tai tana duban d’iyar tata “Kareema kenan, yaro dai yaro ne.. Bazaki fahimci komai ba yanzu sai nan gaba.. Mamarki kirki ne da ita bazata iya ganin wasu suna shan wahala ta k’yalesu cikin wahala ba.. Nuratu da kike gani ba kishiyata bace kawai, tamkar ‘yaruwa haka na d’auketa domin kuwa idan baki mance ba a baya Yayan Babanki mai rasuwa take aure.. Kinga nida Ita mun jima da sanin juna tun kafin Daddynki ya aureta..” Kiki Ta d’an turo baki tace “Amma Mommy Maiyasa da nata mijin ya mutu ta aure miki naki mijin..? Mommy nan gidanki ne bai kamata ta aure miki miji ba..” Murmusawa Mommy ta kumayi kafin tace “Nurah batada kowa a k’asar nan, batada dangi a nan.. Mijinta ne kad’ai danginta sai kuma yaranta, shiyasa koda mijinta ya mutu nawa mijin ya aureta..” Shiru Kiki tai tana sauraren mahaifiyar nata kafin ta tab’e baki tace “Even so Mommy, she shouldn’t have married your own husband.. Ita ta aure miki miji ga kuma d’anta Ya Mu’azzam ya aure Addah Safeenah.. Um nidai duk bana son irin wannan had’e had’en kusancin tai yawa... Shikenan namu family d’in sun k’are a cycle d’aya..Ni gwara ma da Addah Ikram Ta mutu nasan itama da yanzu an soma maganan nata auren da Ya Musaddiq.” “Ke Karimatu..!” Mahaifiyar tata ta daka mata tsawa wanda ya sanyata zabura babu shiri.. Mommy taci gaba da fad’in “Kina jina.. Koda wasa koda wasan wasa kar na kuskura na kuma jin wannan kalma ya fito daga bakinki balle har kiyi gangancin furtata cikin gidan nan kinji koh..!” Ta k’arashe tana mai nunata da ‘yar yatsa cikin tsananin b’acin rai.. Kiki baki a ture ta mik’e tana fad’in “Fine Mommy, kema kinfi son wannan matar da yaranta sama damu yaranki.. Kaman yanda Daddy yake nuna yafi sonsu.. This is not something new a gidan nan.. Dama Daddy ya saba nuna yafi sonsu tun kafin Ikram ta mutu..” “Kimin shiru da maganar Ikram nace and kindly leave this room kafin na b’ata miki rai..” Fuu ta fice fuska a kumbure kaman zata kurma ihu.. Tana ficewa Mommy ta dafe k’irjinta tana Sauk’e ajiyan zuciya.. Ta maidoda dubanta ga Nuratu da fuskarta ke duban wani b’angaren.. A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya kafin tasa kai ta fice... Tana fitowa d’akin Safeenah ta nufa yanda ta tadda Safeenar duk’e saman carpet tana fuskantar Daddy dake zaune bakin gadonta, kanta a k’asa da alama hawaye take.. “Daddy I’m sorry.. Kawai inaso na kasance da mijina ne.. Please understand me..” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Cikin kwantar da hankali yaci gaba da fad’in “Na fahimceki Safeenah.. But don’t you think yayi sauri ayiwa Mu’azzam maganar tariya yanzu..I mean, he recently lost his sister.. And he’s looking into the matter right now...Kuma Kema ‘yaruwarki ce..” Cikin muryar kuka Safeenah Ke fad’in “Daddy gani nake kaman Mu’azzam kufce min zaiyi.. Daddy kaga da k’yar ya yarda akayi aurenmu sabida jinyar Aunty Nurah toh mai kuma zai faru yanzu da Ikram ta rasu.. K’ila yace ya fasa auren ma gaba d’aya Daddy..” Ta k’arashe wani kukan na taso mata.. Cikeda tausayin d’iyar tasa yake dubanta dan yasan yanda take tsananin k’aunar Mu’azzam.. Hannunsa ya mik’o ya kamo nata kafin ya soma magana cikin kwantar da hankali “Safeenah an riga anyi aurenku da Mu’azzam kinji.. Shid’in mijinki ne, babu abinda zai rabaku ki kwantar da hankalinki kinji koh..” Izuwa lokacin sosai take kuka tana fad’in “Daddy you don’t understand.. Daddy Mu’azzam ba kaman kowa bane. Bata soyayya yake ba balle aure, baida lokacinsu Daddy I’m sure of it, yafi bada mahimmanci ga jinyar mahaifiyarsa da kuma aikinsa na d’ansanda.. Ba don Inne ta dage sai anyi aurenmu ba nasan k’ila da ba’ayi ba.. And yanzu da ya sami dalilin da zaice ya fasa.. I know him zai iya cewa ya fasa auren.. Daddy please kar ka bari aurenmu da Mu’azzam ya sami matsala..” Yanda take maganar gaba d’aya tamkar mai son fad’in wani abu duk ta daburce tama rasa mai take fad’i.. Shi kansa Daddyn da mamaki ya soma dubanta.. Cikin sauri Hajiya Hajara ta k’arasa ta rungume Safeenah dake sharb’an kuka tana sunbatu.. Shigowar Meema a birkice tana fad’in “Mommy..! Mommy kizo ga cen Ya Mu’azzam ya dawo da Ya Musaddiq.. And... he looks high..” Wani irin zafi Alhaji Marwan yaji zuciyarsa na masa, take ya shiga karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Yai saurin ficewa daga d’akin cikin tsananin damuwa... Mommy Ta dubi Meema dake tsaye daga bakin k’ofa tana duban yanda Safeenah ke cazgan kuka ta bud’e murya tace “Fita ki bamu waje..” Turo baki gaba Meema tai cikeda haushi kafin Ta juya tai ficewarta tana k’walla kira ma k’anwarta Kiki.. Cikin sauri Mommy ta isa rufe k’ofar had’ida danna mata lock.. Ta juyo tana duban Safeenah dake tak’ure waje guda tana cazgan kuka tana fad’in “I can’t lose him.. I love him so much.. No.. No I can’t lose him..” Jijjiga Safeenah take tana fad’in “Safeenatu Safeenah..Ke ki natsu nace..!” Safeenah kaw kaman cewa ake ta k’ara.. Mari maiji da lafiya Mommy ta d’auketa dashi Wanda ya sanyata yin tsit kaman an d’auke ruwa.. Tana sakin huci take duban Safeenar.. “Kina jina ki fad’a min mai kike son fad’awa mahaifinki.. Talk to me now..!” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya tana mai firfito da idanu waje.. Safeenah dake rik’eda k’uncinta wajen da Mommy ta mareta bata daina kukan ba take fad’in “Mommy idan Mu’azzam ya sani he will hate him.. Zai tsaneni Mommy.. Or he might even send me to jail..” Izuwa lokacin Hajiya Hajara ta fara daina gane mai Safeenah ke fad’i.. Cikin daburcewa ta shiga bud’e hannuna tana fad’in “Safeenah.. Ke Feenah mai kike fad’i.. Ban fahimceki ba..” Safeenah na hawaye take fad’in “Mommy I feel guilty.. I feel responsible..” Girgiza kai Mommy Ta kumayi tace “Har yanzu ban fahimceki ba Safeenah.. You feel responsible for what.?” “For Ikram’s death Mommy..!” Ta fad’i mata cikin tsananin rawar murya.... Izuwa lokacin bibbiyu Mommy Ke gani.. Cikin sauri ta janyo hannun Safeenah suka zauna saman gado Wannan karon cikin tsananin sanyin murya take magana “Safeenah.. Maiyasa kikace haka.. You did not kill Ikram, did you.?” Cikin sauri Safeenah ta girgiza kai alamun a’a tana fad’in “No Mommy I didn’t..” “Then how are you responsible..?” Kallon mahaifiyar tata tai kafin tasa bayan hannu ta goge hawayenta. A hankali Ta soma fad’in “Mommy Ikram tana zargin ban daina aikata wasu d’abi’u da nake aikatawa a baya ba, Ta d’auki wayata ta karance Adress d’in a lokacin shagulgulan bikina..” Kuka sosai yazo ma Safeenah Mommy jikina sanyaye take dubanta, Tai k’ok’arin saita kanta kad’an kafin taci gaba da fad’in “But Mommy abinda na sani shine I was to meet up with a client wllhi wllhi Mommy bansan Criminal bane... Bansan makashi bane..” Girgiza kai Mommy tai tana fad’in “Ni duk nan wani fahimceki ba Safeenah “Toh Wai kan wani dalili Ikram zata zargeki..?” Saida ta share hawayen da ya kuma gangaro mata kafin taci gaba da fad’in “Kin tuna lokacin da aka kaita University of Salford ina ajin k’arshe ne Ita kuma tana year one d’inta Musaddiq na aji uku.. Toh gida d’aya muka zauna nida Ikram, Mommy a nan Ikram tasan duk wasu abubuwa marassa kyau da nakeyi, Ina kawo maza su kwana a gidan..” Kuka ya sanyata katse maganar.. Mommy tace “Ina saurarenki Safeenah ..” Safeenah ta goge hawayenta kafin taci gaba da fad’in “Ikram witnessed everything, akan idonta komai yake faruwa.. Muka sami matsala a lokacin tace zata fad’awa Daddy da Mu’azzam duk abinda nakeyi.. Da k’yar na shawo kan Ikram nace mata friends d’Ina ne kawai and bama yin wani abu maras kyau.. Dukda haka Ikram bata yarda ba saida ta sanyani nai mata alk’awarin bazan sake yin abota da maza ba muddin Ina son kasancewa da Yayanta.. I promised her as she requested... And Mommy wllhi wllhi tin a Salford na daina bama Maza kaina..” Batakai aya ba Mommy Ta Kai mata mari tana hawaye take furta “Ashe duk tarbiyan dana baki kinje kin watsar a turai.. How could you..” Ta k’arashe tana mai kuma Kai mata mari.. Zata kuma Kai mata wani marin ne Safeenah tai saurin rik’e hannunta tana fad’in “What do you expect Mommy.. Kun tura budurwa k’asar waje.. K’asar da babu kowa nata.. Kun bata gida da ko wacce irin Gata.. Meye wannan budurwar bazatayi ba.. Mommy wannan kuskure ne da da yawan iyaye suke aikatawa.. Tura mace tayi karatu a k’asar da babu kowa nata ba birgewa bace Mommy.. Bance duka ba amma akasari lalacewa suke kafin su dawo.. Mommy ko a addini ma Babu kyau tura mace taje uwa duniya da sunan yin karatu ba tareda wani nata ba..” Cikin kuka Mommy Ta katseta da fad’in “Ai an tura Musaddiq.. Kuma Musaddiq d’an uwanki ne..” Cikin kuka itama tace “But kafin Musaddiq ya tafi Mommy I was all alone.. Har saida nayi shekaru biyu a UK kafin Musaddiq ya tafi.. Kuma Mommy Musaddiq shima nashi watsewar yake tareda ‘yanmatansa har saida Ikram ta taho Salford kafin ya rage wasu abubuwan da yakeyi sabida Ikram da nasihar da take masa... Mommy ki yarda akwai naku laifin daga ke har Daddy...” Cikin kuka Mommy Ta katseta da fad’in “Ke ni Kimin shiru ba guntun wa’azi nace Kimin ba tinda kin riga kin gama watsewarki da mazan turawa a turai.. So nake ki fad’a min Ta yanda alhakin mutuwar Ikram ya rataya a wuyanki..” Safeenah ta kuma k’unshe bakinta tana jin wani kukan na taso mata.. Daidai lokacin aka soma knocking.. Jin muryar mai k’wank’wasa k’ofar ya sanya Mommy da Safeenah ware idanu suna duban juna.. Cikin sauri Safeenah take k’ok’arin saita kanta Mommy na aika mata wane irin kallo.. Saitin kunnenta take rad’a mata “Kina jina..” Safeenah tai saurin jinjina kai Mommy taci gaba da fad’in “Koda wasa kar giyan soyayya ya d’ibeki ki bud’e baki ki sanar da mijinki wani abu.. Ke bama shi kawai ko Daddy bazai sani ba, sannan babu wanda zai san wannan maganar.. Daga ni sai ke kin fahimta..?” Nan ma saurin jinjina kai Safeenah tai kafin Mommy taci gaba da fad’in “Kisan yanda zakiyi ki b’oye wannan rawar jikin naki dan idan kika bari ya fahimci wani abu kashinki ya bushe Safeenah, Kinsan Wanene Mu’azzam kin fi kowa sanin zafin zuciyarsa.. Ba ke kad’aiba inaga har zuri’arki kaf Sai ya tura kurkuku muddin ya fahimci you’re somehow related to case d’in mutuwar ‘yaruwarsa..” Ta gyara tsayuwarta tana mai kuma yin k’asa da murya “ Kina jina..Zaki natsu kuma zaki nitsa kanki yanzu sannan kiyi abinda ya dace..” Ta k’arashe tana ware idanunta a fuskar Safeenar.. Cikin sauri Safeenah ke jinjina kai tana mai k’ok’arin saita bugun zuciyarta.. Lokaci guda ta koma kan Gado ta zauna tamkar marainiya... Mommy ma ta saita kanta kafin ta dubi Safeenah tace “Nidake bamu gama magana ba, zaki sanar dani komai..” Tai maganar tana kad’a d’an yatsarta a Fuskar Safeenar.. Safeenah Ta lumshe idanunta tana jin sanda Mommy Ta isa ta bud’ewa Mu’azzam k’ofar.. Haka kurum yaji wani iri da yanayi da yaga Mommy ciki dikda k’ok’arin saita kanta da take.. Sai ya jingina hakan da iftila’in da ahalinsu ke fuskanta a d’an kwanakin.. Gaisawa sukai da Mommy kafin tace “Gwara daka k’araso.. Gata nan kowa yayi shiru ya daina kukan rashin Ikram amma ita bata daina ba.. Nayi nasihan nayi lallashin duk tak’i dainawa nace k’ila sai kazo.” Haka kurum yaji bai gamsu da abinda Mommy tace ba abinka da Detective dukda cewa tin a waje Meema ta sanar dashi Addah Feenah nata kuka ta kulle kanta cikin d’aki, ya jinjina kai kad’an yace “Zan mata magana Mommy.. You can go now.. I think Musaddiq needs you..” Mommy Ta jinjina kai kafin tace “Mu’azzam.. Thank you for bringing him home..” Jinjina kai kurum yai ba tareda yace komai ba har Mommy Ta fice.. Cikin yanayin tafiyarsa yake takowa cikin d’akin, saida ya d’auki lokaci yana dubanta yanda ta tak’ure saman gado kanta kife saman gwiwa, a hankali yake takowa cikin d’akin.. Gefenta ya zauna har lokacin kanta na kife tana matsan hawaye.. Ya d’an fuzar huci yana shafe goshinsa kad’an, kana ganinsa kasan he must be completely stressed out.. Hannu yakai kaman zai tab’ata sai kuma ya janye hannun nasa yana mai d’an janye fuskarsa idanunsa a lumshe.. Jin alamun haka yasa Safeenah k’ara sautin kukanta.. Ya d’an rintse idanunsa kad’an kafin ya dad’a matsowa kusanta, hannayensa duka biyu yasa ya d’aura saman kafad’unta.. Kaman yace ta k’ara nan Ta kuma sake masa wani kukan.. D’an kauda kansa gefe yayi still yana rik’eda ita, kaman bazaice komai ba Sai kuma ya rungumota cikin jikinsa ga kukan nata dake k’aruwa “It’s okay Feenah.. Ya isa haka.. Ki daina kukan nan haka..” Yanda yake maganar tamkar wani d’an koyo sosai zai baka dariya.. Jin haka yasa Safeenah lafewa cikin k’irjinsa tana mai kuma sakin kuka.. Ba kukan tashin hankalin da take ciki takeyi ba.. A’a kukan Farin ciki da murna take yau Allah ya cika mata burinta Gata nan cikin jikin Mu’azzam d’inta kuma a matsayin matarsa.. Shid’in halaliyarta ne.. Cikin zuciyarta Ta furta _My Halaal_ . Tina haka da tayi ya sanyata had’e hannunta ta rungumo bayansa sosai tana kuma kwantawa cikin jikinsa tana kuma sakin kuka... SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *04* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* K’aran da wayarsa tai ne ya sanyasa k’ok’arin zame jikinsa daga nata, Safeenah kam da alama bama taji sautin wayar ba har saida taji Mu’azzam na k’ok’arin cire hannuwanta daga rik’on da tai masa.Ta d’ago tana dubansa idanunsa naga fuskar wayarsa yana ganin mai kiran nasa, caraf itama ta sauk’e idanunta kan screen d’in wayar tasa.. Sunan Assad data gani ya sanya gabanta wani irin fad’uwa.. Tasan Assad amininsa ne sannan abokin aikinsa ne a CID Office. Haka kurum taji wayar da Assad Ke masa nada alak’a da case d’in mutuwar Ikram.. “Excuse me, I’ve to take this call..” ya fad’i yana mik’ewa tsaye, lokaci guda ya tura dogon k’ofar glass da ya raba d’akin da balcony ya shige yana amsa kiran Assad.. Cikin sauri Safeenah tabi bayansa cikin sand’a ta d’an lab’e ta kasa kunnuwa tana san sauraron wayar tasa.. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “What do you mean Negative...?” Daga d’aya b’angaren Assad yace “You heard me right, negative..” Lumshe idanunsa yai kad’an kafin ya soma fad’i cikin b’acin rai “Assad kana so na koyar dakai aikinka ne.. you need to get ya act together, I have no time to babysit you..” “Mai kake so nayi Mu’azzam. Ka bani location without going through the details.. Naje wajen and guess what.. Wannan location d’in is an open waje, nothing suspicious.. Ba kowa babu komai a wajen.. Ban San mai zanyi a wajen ba..” Girgiza kai Mu’azzam yai cikin rashin yarda yace “No.. There must be something in that particular location,.. Danger ne ya bani location d’in nasan haka kawai bazai bani ba dole akwai dalili.. Look around, babu wani daba da mutane ke zama wajen, babu wani shago kodai wani abu..?” Assad yai shiru yana duban wajen da babu ko alamun mutane kafin ya fuzar da huci yace “He played you.. Wasa dakai kawai yayi Mu’azzam.. There’s nothing suspicious here.. Ga Maleeka ma ta taho tare muke da ita.. But we couldn’t find anything..” “Damn it..!” Ya furta yana jin zuciyarsa na masa wane irin k’una, idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa shine a raina masa hankali.. Fuzar da huci yai kad’an kafin yace “I’ll give him what he’s asking .. I’ll play his games.. Ka gane ku bar location d’in zamuyi magana..” Assad ya amsa masa da fad’in “Copy sir..” Yai maganan yana sarawa kaman Mu’azzam d’in na ganinsa.. Safeenah tana jin ya ida wayar tai saurin komawa mazauninta dikda cewa ba wai ta fahimci mai yake cewa bane cikin wayar amma kam ta tsinci wasu kalmomi kuma Ta fahimci bincike yake... Saida ya tsaya ya ida abinda zaiyi cikin wayar tasa kafin ya dawo cikin d’akin, Safeenah tana ganinsa ta mik’e tsaye, fuska fal damuwa take fad’in “Are you leaving now..?” K’arasowa yai kusanta hannayensa saman waist d’insa, ya d’an fuzar da fuci kad’an yana mai duba wristwatch d’insa “I have to.. Aiki na jirana..” Rau rau tai da idanunta tace “But you just got here.. Can’t you stay a little longer..” Tai maganar cikeda shagwab’a K’uri ya d’anyi mata kafin yace “Why..? Do you need something..?” Yanda Yai maganar yana bud’e idanunsa Sai ya koma mata Mu’azzam d’insa wanda a baya yake gwaleta a mafi akasarin lokuta.. Idan da Ta barsa ya gwansaleta sam bazata bari yanzu hakan ya kasance ba, shid’in mijinta ne kuma zatayi komai domin taja hankalinsa gareta.. Zatayi what ever it takes ta tabbata ta gina soyayyarta cikin zuciyarsa.. Matsowa ta kumayi kusansa.. A hankali ta isa ta d’aura kanta saman k’irjinsa, cikin raunanniyar murya tace “I need you here.. Please stay with me kaji..” D’an kauda kansa gefe yai yana son tureta daga cikin jikinsa amma sai yaji ta sakalo hannayenta saman waist d’insa ta rungumesa sosai tana ci gaba da fad’in “Please stay..” Tai maganar tana mai d’ago fuskarta idanunsu cikin na juna.. Bai iya tureta daga jikinsa ba sannan bai iya furta koda kalma ba saima samun kansa da yayi yana mai tallafe bayanta da hannunsa kad’an.. Inne Kakarsu mahaifiyar Daddy itace Ke k’ok’arin shigowa d’akin dashike Mu’azzam bai rufe k’ofar d’akin ba sanda zai shigo.. Safeenah tana hango Inne na dosowa d’akin Ta kuma mak’alewa cikin jikinsa dan tasan idan Inne ta gansu a haka zata hura wuta su tare a cen gidansu... Aiko Inne tana hangosu haka sai bata shigo d’akin ba tayi juyawarta.. Saida suka kwashi mintoci a haka kafin Mu’azzam yai gyaran murya yace “Safeenah, I need to go now.. They are waiting for me..” Yai maganar yana mai cireta cikin jikinsa.. D’ago fuska tai tana dubansa kafin tace “How long will you take..?” Ya d’an tab’e baki kad’an “I can’t say for sure.. It depends.. Kinsan yanda yanayin aikin namu yake..” Ta d’an rausayar da idanu kad’an lokaci guda tana mai kuma rau rau da idanun cikeda shagwab’a “My Inspector, nasan yanda yanayin aikin nan naku yake, very dangerous..Sannan kana bada mahimmanci sosai ma aikinka... Please promise me you’ll take care of yourself.. Always..” Yanda tai maganar sosai ya sanyashi jin sanyi can k’asar zuciyarsa, ya saki murmushi kad’an yana mai tallafo fuskarta da tafukan hannayensa, a hankali yake furta a hankali ya jinjina mata kai kafin yace “Zan iya tafiya..” Wani irin dad’i da mamaki ne ya cika zuciyar Safeenah Wai Mu’azzam ne yake mata magana softly haka ba tareda ya gwansaleta ba harma tambayarta yake zai iya tafiya.. Dad’i ya mamaye zuciyar Safeenah tabbas lokaci k’ank’ani zata d’iba ta dasa soyayyarta mai tsafta cikin zuciyar Mu’azzam.. Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Zan duba Mamy first daga nan zan shige..” Ta jinjina masa kai a hankali tana sakin murmushi.. Hannunsa guda dafe da b’angaren fuskarta yaje furta “You take care..” Ta jinjina masa kai a hankali su duka biyun suna masu sakar ma juna murmushi kafin Mu’azzam ya fice.. Yana ficewa Safeenah ta fad’a kan gado tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali.. Ta janyo pillow Ta kwanta ciki tana shafe fuskarta yanda Mu’azzam ya d’aura hannunsa.. Ta lumshe idanunta a hankali tana jin bazata tab’a bari wani abu ya datse mata wannan farin ciki da take ciki ba.. Zata kare aurensu no matter the cost.. Tana tsaka da tinanin wayarta dake gefen bedside Ta soma ruri.. Tai saurin d’agowa tana duban mai kira, lamba ce Babu suna.. Batasan dalili ba amma ta tsinci kanta da fad’uwan gaba... A hankali ta d’aga wayar tana mai k’arawa a kunnenta.. Lokaci guda ta mik’e tsaye sanda take receiving wayar “Barrister Ameer..Ina ka samu sabuwar layina..?” Daga d’aya b’angaren mutumin data kirada Barr Ameer murmusawa yai kad’an kafin yace “Ba damuwa bace sanin yanda na samu sabuwar layinki... Kawai na kira ne na miki murnan aure tinda ba’a gayyace mu biki ba..” Murmushin da yafi kama yak’e ta d’anyi kafin tai masa godiya Ta muka rok’esa da kar ya sake kiran layinta bata san duk wani abinda zai haifar da zargi tsakaninta da mijinta... Barr Ameer yace babu komai kawai dai dama ya kira ne ya mata murna tinda Allah bai k’addara shid’in zai aureta ba dukda tsananin k’aunarta da yake.. Barr Ameer Dikko yaso Safeenah sosai tun tana makaranta a Salford, da aure yaso Safeenah bada wani shashanci ba, tun Safeenah bata kulasa har saida yayi amfani da dabaru nasu na lauyoyi wajen iya tsara zance da kuma tsananin nacinsa da soyayyar da yake mata har dai ta soma kulasa, bata b’oye masa d’anuwanta Mu’azzam take so ba dukda kuwa cewa a lokacin bata gaban Mu’azzam d’in.. Barr bai karaya ba yace zai gwara luck d’insa.. A haka dai har Safeenah ta d’an basa dama cikin rayuwarta sabo ya shiga tsakaninsu sosai dukda cewa ita ba irin son da yake mata take masa ba, zuciyarta na Mu’azzam ne batajin zata iya had’a soyayyarsa da wani cikin zuciyarta, Barr Ameer yasan da haka amma bai damu ba a cewarsa nasa sa’an yake gwadawa.. Koda aka saka aurenta da Mu’azzam kuwa tuni tai cutting ties da Barr, ta yanke duk wata alak’arta dashi, dan sabida shi ma da nacinsa Ta canza layinta.. Bazata tab’a mancewa da furucin da Barr yai mata ba wata rana suna firan Mu’azzam shida Ita, tana sanar dashi irin soyayyar da take wa Mu’azzam d’in, Barr yace ‘Na saka a raina zaki zauna a gidan Mu’azzam ne na d’an wani lokaci tamkar dai kina a GIDAN ARO ko bajima ko na dad’e bazan tab’a cire rai ba, nasan watarana zaki dawo gareni..’ Batama d’auki maganar tasa da mahimmanci ba dan tasan irin son da takewa Mu’azzam zata iya shanye duk wani miskilancinsa ta tabbata aurensu ya d’ore har k’arshen rayuwarsu.. A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya tana mai kuma kwanciya saman gado.. Mu’azzam kaw a parlor ya hangi Inne Kakarsu da Daddy harma da Mommy, yanda yaga Mommy da Daddy sun gurfana ya tabbatar masa assembly Inne take, shi sam bai zaton ma bata koma Adamawa ba, hango Musaddiq da yayi duk’e gaban Innen ya sanyasa k’ok’arin janye jiki da niyyan ficewa ba tareda wani yayi noticing d’insa ba dan yasan fitinar Kakarsu.. Yana cikin sand’uwa zai fice ya sinkayo muryarta da girma ya d’an kama tana fad’in “Kai Kai Dansanda ina zakaje..? Zo nan kaima akwai namu da kai.. Bari na gama da wannan shashashan d’anuwan Naka..” Ta k’arashe tana dungure kan Musaddiq da yai zaman rak’umi gabanta, ya kuwa cika yayi fam kaman zai fashe... Dan dole Mu’azzam ya dawo ya tsaya daga bayan parlorn can wajen staircase.. Inne Dattijuwa da sam bazaka bata shekarun da take ba sabida kyaun k’ira da Allah yayi mata, ta dubi Musaddiq dake duk’e gabanta k’iris ya rage bai fashe ba Ta kuma dungurinsa tana fad’in “Sokon banza, ai bansan shashashancinka kawai kake a nan ba.. Mu dik zuri’armu babu mashayi baza’a fara samu cikin jikokina ba.. Kana jina Gida zan tafi dakai cen Fufore kaje kayi noma da kiwo naga alama gata ne yai maka yawa a nan shiyasa ka sangarce..” Musaddiq ya d’ago yana mata wani irin duba, Ta kuma dungure masa kai tana fad’in “Daina kallo na da wannan jajayen idanun naka.. Sabida azaban shan kayan maye jibi dik yanda kayi duhu ka lalace..” Mommy ta k’walolo idanu waje jin Inne tace zata tafi da Musaddiq Fufore yaje yayi noma da kiwo, ta dubi Daddy tana jiran taji mai zaice amma shiru baice komai ba... Musaddiq ma ganin iyayensa ba suce komai ba ya sanyasa soma girgiza kai yana fad’in “No.. No way.. Gaskiya bazan koma Gidan Gona ba..Ai dai kinsan ina makaranta Inne..” Ta kuma Kai masa bugu a kafad’arsa yana karewa, lokaci guda take furta “Rufe mun baki shashasha.. Yo makarantarka har wani makaranta ne, inji kaje can k’asar wajen ka gama yawon shashashancin Naka babu abinda ka tsinana, na tabbata nan d’inma ba abun arziki kake ba.. Idan ba an rabaka da shashashan abokan naka dake nan ba bazakayi hankali ba.. Ni tuntuni nasan cewa shashashancinka yakai har ruwan kwalba kake sha da ban Barka ka girma a bariki ba..” Ta dubi Daddy da kansa Ke kife k’asa tace “Kana jina Marwan, yaron nan zamu tafi tare.. Kayi magana da D’anuwaka Salmanu tinda shike kula da Gidan Gonar, ya samar wa Gidado aiki a nan Gidan Gonar.. Ya dinga kula da shanun dake gidan gonar..” Musaddiq baki sake yake dubanta shaye da tsananin mamaki.. Katseta yayi da fad’in “Amma Inne kinsan ni ba karatun kula da Dabbobi nayi ba koh..I’m not a Vet Dr..” Carbinta da ko yaushe yake nad’e hannunta wannan karon ta warb’a masa tana fad’in “Rufe mun baki idan bakayi karatun kula da dabbobi ba ai ka gada kiwo... Ubanka ma ya gada.. Gidan Gonan da Kakanka ya mutu ya bari arzikinsa kake ci..” Ta d’ago tana kuma duban Daddy “Kana jina ka kira Salmanu ka sanar dashi tun kafin mu koma Adamawa..” Jinjina mata Kai Daddy yai yace “Za’ayi yanda kikace Insha Allah Inne..” Mik’ewa ta soma k’ok’arin yi ta dubi Mu’azzam tace “Kai kuma shige muje..” Cikin rashin yarda da batun Musaddiq Ke fad’in “Haba Daddy.. You can’t be serious.. Daddy this is unfair.. Dan Allah kar ka bari hakan ta kasance..” Ya d’ago ya dubi Mu’azzam dake k’ok’arin bin bayanta yace “Officer dan Allah ka mata magana, you’re her favorite zata saurareka..” Ya k’arashe yana bin bayan Mu’azzam d’in cikin gudu gudu... Saitin kunnensa Mu’azzam Ke fad’i a hankali “Hakan yafi idan dai halinda zakaci gaba dayi kenan a nan..” Musaddiq ya girgiza masa kai yace “Wllhi na daina..” “Proof it then..” Mu’azzam ya fad’I yana mai bin bayan Inne.. Cikin sauri Musaddiq ya take masu baya.. Suna ficewa Mommy Ta dubi Daddy tace “Yanzu bazakace komai ba.. Haka zaka zuba ido Ta tafi dashi..” “Mai kike so nace Hajara.? Nace mata ba haka ba.. Ko kin mance cewa matar nan mahaifiyata ce.. Sannan idan hakan shi zaisa d’anki ya dawo cikin hayyacinsa I’d welcome the idea d’ari bisa d’ari.. If he stays here babu wani abinda zai tab’uka ma rayuwarsa..” Shiru Mommy tai tana mai kwantar da kai, hawaye ya ciko idanunta, k’ok’arin saita kanta tai sanda Daddy yaci gaba da fad’in “He’ll be better off there, tinda a nan dai kina gani yanda muke tare tare dashi, idan aka canza masa environment d’in na d’an wani lokaci k’ila Allah yasa hakan ya zamto sanadin shiriyarsa... Muyi masa addu’a kawai da fatan hakan ya zamto alkhairi..” Mommy dai bata ce komai sai mik’ewa da tai ta haura sama tana tinanin hukuncin cikin ranta.. Ita tanadinta shine Nuratu ta fice mata daga gida tayi nesa da ita da ahalinta ba Wai d’aya daga cikin yaranta yai nesa da Ita ba.. Daddy ya bita da kallo yana mai kwantar da kansa cikin kujera had’ida lumshe idanunsa kad’an.. Inne na gaba Mu’azzam da Musaddiq na biye da ita, Musaddiq naci gaba da magiyan cewa ta janye k’udirin ta.. “Kai Gidado (Kaman yanda take kiran Musaddiq d’in) bari kaji na fad’a maka.. Ko Marwan Ubanka bai isa ya hanaka komawa Gidan Gona ba.. Na riga na gama magana ehe, bazan zauna inaji Ina gani ka zame mun zakka ba.. Banyi shirin sallameka ba.” Musaddiq ya dubi Mu’azzam da yai kaman bashi a wajen a hankali kaman mai rad’a yake furta “Aren’t you gonna say anything.. Talk to her please.. She can’t do this to me... I mean she’s turning my life into a nightmare.” Bai Kai aya ba yaji sauk’ar ‘ya’yan carbi a k’eyarsa, yai saurin sosawa yana d’an sakin k’ara.. Kunnensa ta kamo dikda ratan tsawo dake tsakaninsu.. Nanma k’ara Musaddiq ya saki yana k’ok’arin k’watan kunnensa.. Inne Ta dage k’arfinta ta matse kunnen tana fad’in “Ni na gayyaceka d’akina..? Maza a k’ara gaba.. Fita ka bani waje jarababbe..” Ta k’arashe tana turasa waje.. Dik tsimewan da Mu’azzam yake saida yaji dariyar Inne da Musaddiq ya taso masa.. Ya sunkuyar da kansa gajeriyar murmushi saman fuskarsa.. Inne na hankalce dashi sannan sosai taji dad’in ya d’an saki ransa dan zata iya cewa tinda tazo bataga murmushinsa ba.. Abubuwa da dama Sun faru dashi d’in.. Ga mutuwar k’anwarsa bayan jinyar da mahaifiyarsa Ke ciki... Musaddiq na ficewa Inne ta K’araso ta zauna bakin gado, tai nuniwa Mu’azzam da kujerar dake fuskantar gadon “Modibbo zauna kaji muyi magana.” Ba musu Mu’azzam ya k’arasa ya zauna yana “Inne na zata kin tsufa a Adamawa..” Ta tab’e baki kad’an tace “Ina zanje bayan ban kai maka Matarka d’akinka ba..” Ba zata yaji maganan nata ya d’ago yana dubanta, dan shi harga Allah ya mance da wani maganan tariyar Safeenah.. “Kana jina.. Yau d’in zuwa dare.. Kokuma a barshi gobe yarinyar nan ta tare a d’akinta.. Zaman baida wani amfani..” D’an tura yatsunsa yai kad’an cikin sumarsa kafin yace “Inne Wai dama da dai an barshi sai zuwa gaba kad’an..” Shiru tai tana dubansa cikeda tausyawa, ta jinjina kanta a hankali kafin tace “Idan kace haka zan iya fahimtarka Modibbo.. Nasan har yanzu alhinin rashin ‘yaruwarka na tareda kai.. Amma idan kana tareda Matarka sai ta d’ebe maka wani kewan ka fahimta..” D’an shafe fuskarsa yai kad’an kafin yace “Inne ai akwai abubuwan da nake so su daidaita kafin nan.. Kinga yanzu babu Ikram dama itace take taimaka wa Aunty Hajara da jinyar Mamy na.. Aunty Hajara bazata iya kulada Mamy ita kad’ai ba dukda dai dama akwai ma’aikatan jinya da ake hayansu masu taimakawa.. Inaso idan al’amarin suka daidaita Sai mu tare mu koma cen gidan..” Katsesa tai da fad’in “Ni nan zanyi jinyar Nuratu.. Dama wannan karon nace zan d’auketa mu koma gida a jarabba jinyar gargajiya tinda na asibitin Allah bai nufa za’a dace ba.. Nayi magana da Baban naku dikda shima naga yafi son zamanta a nan amma haka dole zaku hak’ura a jarabba na gargajiyan.. Sannan zatafi samun kulawa a wajena sama da nan d’in..Watak’ila maganinta na gida bamu sani ba..” Shiru yai kaman mai nazari, harga Allah baison mahaifiyarsa tayi nesa dashi musamman duba da yanayin jinyar da take ciki.. Amma baida wani zab’i idan hakan shine Alkhairi.. Zaifi kowa son mahaifiyarsa ta sami lafiya.. Kaman kuma yanda Inne tace zatafi samun kulawa wajen Kakar tasa dukda kuwa cewa bai tab’a ganin gazawar Mommy ba sannan har kullum fatan alkhairi ne tsakaninsa da ita.. Ko dan mutuncin iyayen Safeenah Daddy da Mommy da yanda suka rik’esu amana shida ‘yaruwarsa da kuma mahaifiyarsu dake cikin tsananin jinya baiji zai iya wulak’anta Safeenah, koda ace baya sonta zaiyi hak’urin zama da Ita.. Mommy da Daddy sun cancanci ya rik’e masu d’iya da amana..Alk’awari ne da ya d’aukar ma kansa.. Muryar Inne ya sinkayo tana ci gaba da fad’in “Jinya yak’i ci yak’i cinyewa.. Idan ban b’ata lissafi ba yau a k’alla kusan shekaru shabiyar kenan Nuratu na fama da jinyar nan, ni ban tab’a gani ko jin had’arin mota irin nasu ba..” Mu’azzam ya d’ago yana dubanta “.. Ina makarantar Kwana a lokacin, aka sanar dani Mamy ta auri Uncle Marwan saidai a hanyarsu Ta tafiya Abuja daga Adamawa sunyi accident.. She survived the accident amma tana cikin critical condition.. Condition d’in da bata fice daga ciki ba har rana mai kaman Ta yau.. Ance motar da Mamy na take ciki kowa ya mutu ita kad’aice tayi rai a ciki..” Ya k’arashe cikin yanayi na ban tausayi. Sauk’e ajiyan zuciya Inne tai tana mai d’an goge hawayen da ya mak’ale mata cikeda tausayin Mu’azzam d’in.. “Modibbo ina k’aunar Mahaifiyarka tamkar d’iyar dana haifa a cikina wannan dalili yasa na umarce d’anuwan mahaifinka da ya aureta bayan da muka rasa mahaifinka... Ina tsananin k’aunarta kuma bana so ta bar cikin ahalinmu.. Nuratu yarinyar kirki ce mai tsananin biyayya.. Da ita da Baffanka Marwan sunyi min biyayya kuma Sun cika min burina sun amince da auren juna.. Saidai bansan wannan aure haka zai kasance ba.. Bansan a hanyar zuwa GIDAN Baffanka Nuratu zata had’u da wannan mummunan tsautsayi ba.. Ance had’arin motar bama irin wacce aka saba gani bane.. A samar bishiya aka tsinci motar da mahaifiyarka ciki... Mu’azzam inaji kaman alhakin ciwon mahaifiyarka a kaina yake.. Watak’ila da banyi masu umarni da su auri juna ba itada Marwan da yanzu lafiyarta lau.. Bazan daina jin zafin abun nan ba har na koma ga mahaliccina..” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka. Cikin sauri Mu’azzam ya taso ya duk’a gabanta, ya kamo hannayenta ya dunk’ule cikin nasa “Inne none of this is your fault.. Ki daina d’aura ma kanki alhakin ciwon Mamy, wannan wani abu ne da Allah ya K’addara.. Mutum baya shige k’addarar Sa a rayuwa.. Wani baya iya yi ma wani abin cutarwa ko na amfanarwa face Allah ya k’addari faruwar hakan,.. Baki nufi Mamy da komai ba face Alkhairi. Had’ari kuma ko ta auri Uncle ko bata auresa ba tuni Allah ya rubuta hakan zai faru.. Ki daina d’aura laifi ma kanki kinji Inne..” Ya k’arashe yana mai goge hawayen fuskar Kakar tasa da ‘yan yatsunsa.. Ta Shafa sumarsa murmushi saman fuskart “Allah shi maka albarka Modibbo na.. Ubangiji ya maka jagora a duk abinda kasa gabanka.. Allah tsare mun kai ya kareka daga sharrin mai sharri..” Sumbatar hannayenta dake rik’e cikin nasa yai yana furta “Ameen Inne na.. Allah ya bar mun ke..” Ya k’arashe yana mai d’aura kansa saman cinyarta.. Dik zafin da zuciyarsa Ke ciki idan yana tareda Kakar tasa Sai ya dinga jin wani sanyi can k’asar zuciyarsa, har wani shagwab’a yake mata, ga wanda yasan zafin sa a waje idan ya gansa da Innensa sosai zaiji mamaki.. Daga wajen Inne Kai tsaye wajen mahaifiyarsa ya nufa... SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *05* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ya jima tsaye bakin k’ofa yana dubanta, yana mai tina tattaunawarsu da Inne. A hankali ya soma takowa cikin d’akin har ya k’araso bakin gadon da take kwance.. B’angaren da fuskarta yake duba ya k’arasa, ga duk’a kad’an yana mai k’ura mata idanu.. Su kuma kalan tasu k’addarar kenan.. Da fari mahaifinsa ya rasa sannan mahaifiyarsa ta had’u da tsautsayi na jinya yanzu ga tilon k’anwarsa itama ta tafi.. Tinani yake lokacin ahalinsu ke cike, Daddynsa Mamynsa da kuma ‘yar k’aramar k’anwarsa Ikram.. Ahali mai cikeda Farin ciki da k’aunar juna.. Inama wad’ancan lokutan zasu iya dawowa.. Inama zai bud’e idanunsa yaga mafarki ne duk abubuwan da suke faruwa.. Amma saidai wannan itace gaskiyar, littafin k’addararka a kullum bud’e maka Sabon shafin rayuwa takeyi.. Rayuwar duniyar kenan, duk yanda ka kaiga ganin cewa dad’i kakeji a duniyar nan toh wannan dad’in k’ayadadde ne, aronsa aka baka akwai ranan da zaka wayi gari ka rasa wannan jin dad’in.. Sannan duk yanda ka kaiga ganin wahala kake sha toh wannan wahalan yanada wa’adi akwai ranan da zai k’are.. Duniya ba gidan zama bace gida ce ta jarabawa, dik yanayin daka tsinci kanka ciki a gidan duniya toh kuwa ko shakka babu jarabawa ce kake cikinta.. Gidan duniya gidace da aka baka aronta domin a jarabceka a cikinta, ba gidan Sharholiya bace sannan ba gidan baje koli bane.. Kai d’in tamkar matafiyi ne da aka baka Aron Gida domin ka yada zango na wani d’an lokaci k’ayadadde.. Babu komai a GIDAN ARO face tarin jarabawa da kuma k’alubale na rayuwa.. Mu’azzam ya lumshe idanunsa yana mai kamo hannayen mahaifiyarsa wacce ga dai idanunta a bud’e tarau amma wani b’angaren take duba.. Bata um bata um um.. A hankali ya soma furta “Mamy inada babban albishir da zan miki.. A yau d’in na soma gano wani abu gameda mutuwar Ikram.. Kuma na miki alk’awari in sha Allah bazan gajiya ba har sai na samo bakin zaren.. Mamy na Sani addu’arki da albarkanki suna tare dani.. Fatana shine Allah ya baki lafiya ya tashi kafad’unki.. Inada yak’inin cewa wata rana komai zai wuce ya zamto labari.. Wanda sukaci zarafin d’iyarki suka kuma kasheta zasu biya.. Zasu biya abinda suka aikata Mamy.. I won’t rest until I get to the bottom of everything..” Ya k’arashe yana mai sumbatar hannayen nata dake rik’e cikin nasa had’ida lumshe idanunsa siririyar hawaye ta gangaro daga cikin idanunsa guda... Yana duk’e wajen yaji hannun mutum a kafad’arsa, sanin ko wanene tsaye Kansan ya sanyasa k’ok’arin saita kansa kafin ya mik’e yana goge fuskarsa da duka tafukan hannayensa.. “Sorry Daddy banji shigowarka..” Ya fad’i yana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye. K’ak’aro murmushi Alhaji Marwan yai kafin ya girgiza kai kad’an yace “Babu komai Mu’azzam..” Ya kuma duban Mu’azzam d’un cikeda kulawa kafin ya maidoda dubansan ga mahaifiyar Mu’azzam d’in.. Idanunsu Su duka biyu naga mahaifiyar Mu’azzam d’in Daddy Ke fad’in “D’azu muke magana da Inne cewa tana so Nuratu ta koma Fufore.. Za’a gwada yi mata maganin gida ko Allah zaisa a dace.. Hajara ta fara mun maganar sai kuma Inne ma tazo da batun.. Toh amma a zahirin gaskiya Mu’azzam ni banyi Na’am da maganin gargajiyan nan ba.. Tinda ga abinda likitoci daga manyan asibitoci na duniya suka fad’i.. Zai matuk’ar wahala ta warke a bisa iya binciken da sukayi..So ina tunani kar aje a shiga bata wasu magunguna da babu dosage ba likita bane yayi prescribing aje a k’ara rikita jikin nata.. Toh amma kuma sai nayi tunanin likitocin nan ba sanin gaibi sukayi ba.. Cuta Allah Ke sakashi kuma shi Ke yayewa, saidai yakan bama wasu daga cikinmu ilimin sanin magani domin kuwa bai halicci cutan ba har saida ya sauk’ar da maganinta.. Ba Lallai sai ta hanyar likitoci wanda sukayi karatun ilimin zamani ba.. Wani dake rayuwa cikin daji ma sai Allah ya basa ilimin sanin magunguna a kumayi amfani dashi idan Allah ya nufa sai a dace...Amma Kai mai kake gani..” Shiru Mu’azzam ya d’anyi kaman mai nazari kafin yace “Haka ne Daddy..Abinda ka fad’a gaskiya ne.. And duk hukuncin da ka yanke zanyi na’am dashi.. Kaine mijin Mamy, and you’ve every right ka Kai Matarka jinya yanda kakeda tinanin za’a iya dacewa da magani.. Inne ta min maganar d’azu dana shiga wajenta.. Daddy duk hukuncin da kuka yanke yayi.. Fatanmu shine Allah ya Bawa Mamy lafia..” Murmusawa yai kafin ya d’an bubbuga kafad’ar Mu’azzam yace “Ka kasance d’a mai biyayya a wajena.. Ko Hamma ne yake raye yanzu iyakacin biyayyar da zaka masa a matsayinsa na mahaifinka irinsa kake min Mu’azzam.. Allah Ubangiji ya maka albarka ya dafa maka cikin duk abinda ka saka gabanka...” Kansa a k’asa kad’an yace “Ameen Daddy..” “Ya maganar binciken case d’in Ikram.. Ba wani abu da aka samu har yanzu..?” Mu’azzam ya d’an shafi sumarsa yace “Muna nan Muna bincike Daddy.. And da zaran mun sami wani haske zamu maka k’aran a Kotu..” Jinjina kai Daddy yai yace “Allah ya mana jagora, Allah kuma ya tona asirin duk wanda sukai mana wannan aika aikan..Zan kira Adnan yaje yai mana booking flight zuwa Adamawan within the week.. Zaka samu zuwa kuwa..?” “Idan Mamy zata tafi ya kamata nima ina wajen.. But I’m not sure idan zan samu damar hakan..” Daddy ya jinjina kai yace “Hakan yayi, kar ka samu damuwa zamuyi duk abinda ya dace in sha Allah.. Just concentrate on your job kaji koh..Allah ya shige mana gaba..” Mu’azzam ya amsa da “Ameen Daddy” wayarsa Ta soma ringing, sallama yaima Daddy ya fice yana amsa wayar.. ** SULEJA Sabeera na gefenta su duka biyun sunyi jigum jigum kowacce da kalan tagumin data zabga suna sauraro cecekucen dake tashi daga tsakar gidan Tabawa tana fad’in wllhi sai ta d’ebo masu ‘yansanda muddin wa’adin data basu ya cika basu nemo mata kud’ad’enta ba, dan itama kud’ad’en mutane ne da suka turo ta sai masu kaya ta had’a ta baiwa Uwani da shike Tabawa tana business na pre order irin na online d’in nan, ga mutane masu kaya Sun soma d’aga mata hankali, babu kaya babu kud’i ta tattara kud’in mutane ta bawa Uwani bashi dan tayi hidiman biki, da nufin da zaran Angon Sadiya ya biya kud’d’en events zata maida mata abinta harda k’ari ma tace zata mata, zata biya da interest kenan(K’arin nan kuwa ya zama kud’in ruwa, cin kud’in ruwa kuma haramun ne komin ka’ank’antarsa). A tak’aice dai itama Tabawa son banzanta ya kaita ya barota, babu uwar kud’i babu riba ga mutane Sun tasota gaba.. Komi zakayi yanada kyau ka tsarkake niyya.. Sabeera ta kuma sauk’e ajiyan a karo na babu adadi, ta canza position d’in taguminta yafi sau abinda yafi “K’awata kodai Police station zamuje ne muyi filing report na missing person Ko Allah zaisa a dace a zak’ulo mana Sagir yanda ya shiga ya fita..” Ai bata Kai aya ba Sadiya Ta shiga girgiza kai tana kuma goge fuskarta da tuni har ya kumbura sabida kuka “Haba Sabeera idan mukaje police station kuma ai shikenan mun kai kanmu, Tabawa ta samu daman maka k’arar Ummata a sauk’ak’e.. Ni bama wannan ba kin sanni da mugun tsoron duk abinda zai jawo mun tashin hankali.. Duk rawar kan nan nawa da san abin duniyata wllhi Sabeera ina mugun tsoron abinda zai had’ani da ‘yansanda balle har a kulleni.. Bana son ‘yansanda bana k’aunar abinda zai had’ani dasu..Sannan nasan Kema kina fad’a ne kawai dan naji sanyi cikin zuciyata, a gidanku akaji kin rakani police station Ko k’ofa baza’a sake barinki ki fita ba..” Sabeera ta kuma sauk’e ajiyan zuciya tace “Yanzu ma Mama ce na samu tamin hanya na taho nan dan wllhi Baba cewa yayi ko mai kamanni na aka sake gani na fito daga gidanku Dutse zai maidani wajen Kakata ya aurar dani a cen.. Dama tin ba yau ba ‘yan Sa idonsa ke kai masa gulman ni kad’aice k’awarki a unguwar nan, kowa bai Barin d’iyarsa tayi abota dake sabida rashin kamun kanki.. Kinsan ‘yan unguwar nan ‘yan unguwar nan da shegen gulma da saka ido, musamman wad’anda yake d’an masu alheri, suke Kai masa gulma tinda shi ba wani yini yake a nan ba, sai dare yake dawowa... Toh yanzu da batun auren nan ya faru abun Sai ya dad’a worse dan ance ma D’andamfara ne ya rud’eki bayan ya gama abinda zaiyi dake ya gudu ya barku da tulin bashi..” Sadiya Ta lumshe idanunta wasu hawayen na gangaro mata, Allah shine shaidanta dik kwad’ayinta bata saida mutuncinta ga wani namiji.. Amma saidai a rayuwa fuskar daka bayyana ma mutane da ita zasuyi kwatancenka sannan da ita zasu maka shaida.. Su mutane har kullum abun kushewa suke nema tattare da kai Sai su aibataka ba tareda Sun duba nasu aibun dake tattaredasu ba.. Tabbas Duniyar yanzu kiwon mutane ake bata dabbobi ba.. Sauk’e ajiyan zuciya tai tace “Nasan za’a rina haka, yanzu Ko k’ofa ban isa fita unguwar nan ba wllhi sai kiga har ‘yan yara suna nunani da yatsa, rufin asirin Allah ma makaranta ana strike nasan da na zama abin cecekuce da nunawa ana zancen angona ya gudu ran aurenmu...” Muryarta ya soma rawa sanda taci gaba da fad’in “Maiyasa al’amara suka kasance haka Sabeera.? Maiyasa Sagir zai rud’eni ya yaudareni..? Shin laifi ne dan naso ma kaina abu mai kyau.? Laifi ne dan na zab’awa kaina rayuwa mai inganci..? Sabeera ki dubeni ki gani wllhi ni ba matar k’anan mutane bane, matar manya ce ni.. Idan nace manya Ina nufin masu kud’i masu abun duniya Sabeera..Ni ba yawon banza nake ba kuma duk samarin da nayi k’arya yace na mik’a masa kaina, da yawansu burinsu suyi soyayya da kyakkyawar mace ce irina ni kuma nai masu wayo da dabaru irin tamu ta mata na amshe abin hannunsu, da zaran naga kana neman shige Gona da iri nake sallamarka ai ke shida ce.. Ni abinda nake so kawai shine na auri mai kud’i wanda zanji dad’i a gidansa na fantama na sakata na wala na baje koli na nayi Yawo k’asashen duniya mahaifiyata da ‘yanuwana suji dad’i.. Wannan shine mafarkin Sadiya a duniyar nan Sabeera....” Ta k’arashe guntun hawaye na zubo mata.. Hannayenta Sabeera ta kamo tana mai k’ok’arin k’ak’aro murmushi take fad’in “Kowa yanada ‘yancin da zai mafarkai da burukan da yake so ya cimma a rayuwa.. Amma saidai mukanyi kuskure idan bamu nemi zab’in Allah a ciki ba.. Ba tarin dukiya ba Sadiya, ki nemi farin ciki da kwanciyar hankali a gidan aurenki.. Aure is a lifetime commitment ba abu bane da za’ayisa jeka nayi ka, abu ne da yake buk’atar dogon nazari da bincike..” Katse ta Sadiya tai da fad’in “Dan Allah ni kiyi shiru kar ki karyar min da zuciya Sabeera, kud’i abin so ne kinji.. Maza kuma dik halinsu d’aya ne, da na auri talaka nayi kuka a bakin murhu wuta yana gasa ni gwara na auri mai kud’in nayi kuka a Dubai a rarrasheni da new brand of car..” Ta k’arashe tana kuma gyara zamanta.. Sabeera Ta murmusa tace “Saidai ba Sady pretty d’in ba.. Mai hali ai bazai fasa ba, yanzu ana tinanin mafita Ke baki daddara da zancen mai kud’in ba.. Koda shike I won’t judge you Sady sannan kuma bazan fasa gaya miki gaskiya ba, Kema Kinsan da hakan, bazan tab’a aibataki ba dan nima k’addara bata wuce kaina ba.. Babu wanda yake wuce k’addararsa a rayuwa kuma baka San da mai zata Zo maka ba, saidai a kullum ana so kayi fatan Allah ya nisantaka da mummunan k’addara...” Sabeera Ta kuma gyara zamanta tace “Sabida har yanzu baki had’uda true love d’inki bane shisa tinanin nan ya kasa barin kanki.. Bari kiga dik randa Allah ya had’aki da true love d’inki zaki k’aunacesa ba dan abin hannunsa ba.. Dashi ko Babu zakiyi hak’urin zama dashi..” Tab’e baki Sadiya tai kad’an tace “Babu wani true love Sabeera.. True love kawai nauyin aljihunka ne kin gane..” “We shall see..” Sabeera ta fad’i tana mai mik’ewa tsaye “Ni zan wuce naga magrib na hararowa kafin ‘yangulma su fara fito da bencinsu..” Ta k’arashe tana yane kanta da mayafin Doguwar rigarta.. Sady Ta mik’e tana fad’in “Ki tsaya na taka miki..” “A’a wllhi kiyi zamanki kawai, and please ki rage saka damuwar nan haka cikin ranki Allah zai kawo mana mafita kinji koh..” Jinjina mata kai tai tana fad’in “Toh K’awata na gode sosai sai munyi magana..” A tsakar gidan ta tadda Umma ta had’a tagumi, ta duk’a kad’an tace “Toh Umma na tafi saida safe..” Tsaban Umma na cikin tsaka mai wuya ko sallaman Sabeera bataji ba har saida Ashiru ya tab’ata yana fad’in “Umma Anty Sabeera tace miki ta tafi..” Umma ta nusa tace “Toh Sabeera ki gaida gida koh, mun gode sosai ki gaida Maman taki..” Sabeera Ta amsa da “Zataji Umma..” Kafin tai ficewarta.. ** K’arfe takwas daidai a Office yai masa, yana rik’e da disposable cups guda biyu wanda coffee ne cikinsu.. Danger yana hangosa ya soma murmushi yana shafa hab’arsa dan yasan Mu’azzam d’in dole ya kuma dawowa wajensa.. “Inspector.. Ban tsammaci ganinka da safen nan ba..” Ya fad’i yana duban Mu’azzam d’in.. Saidai ga tsananin mamakinsa shima Mu’azzam d’in murmushin ya sakar masa kafin ya zauna yana mai aje masa disposable cup d’aya na coffee, lokaci guda yake furta “Don’t you think drinking coffee together is much better than smoking cigarette.. Baka so ka zama abokin shan coffee d’ina..? Kaman dai yanda ka zamto abokinsa na shan sigari...” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da furta “After all, they say Smokers are liable to die young..” Ya d’an gyara zamansa yana tapping table d’in da ya raba tsakaninsu da yatsarsa mai zobe, sautin zoben saman table d’in na fitowa a hankali, lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Da alama zaka d’auki tsawon lokaci a nan sannan zamu jima muna shan coffee tare fiyeda lokacin daka kwashe kana shan sigari taredashi..” Yai maganar yana mai sipping coffee d’insa k’afa d’aya bisa d’aya.. Danger ya dubesa da mamaki ya kuma dubi coffee d’in da ya aje masa gabansa.. Murmusawa kad’an Mu’azzam yai kafin yace “Karka damu ban saka guba a ciki ba, because I want you to live long and spend your declining years in jail..” Ya k’arashe yana mai kuma sipping coffee d’insa still k’afarsa d’aya na kan d’aya... Danger ya murmusa kad’an yace “I’m not scared of your empty threats, Mr Inspector... Bakada wani hujja ko dalili k’wakk’wara da zaisa ka ajiyeni a nan..” Yai maganar yana juya cup d’in cikin hannunsa..” “Ka Sani wad’anda kake karewa bazasu maka haka ba, Dama kad’an suke jira su samu akanka sannan su gama dakai..Sannan ni kuma...” Ya d’anyi fasali kafin ya mik’e daga cikin kujerar ya kawo bakinsa saitin kunnen Danger yace “ Ka rubuta wannan ka ajiye, ni kuma Sai na tabbata ka tafi kurkuku tsawon rayuwarka..” Yana ida fad’in haka ya mik’e ya juya zummar ficewa.. Muryar Danger ya sinkayo yana furta “Gidan Alhaji Kabir Isyaku D’an canji dake Suleja..”Cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba.. Danger yaci gaba da furta “A k’ofar wannan gidan za’a d’aura aurensa, kaman yanda naji ya furta a lokacin da yake waya da budurwar tasa..” Juyowa Mu’azzam yai yana nanata sunan mutumin da Danger ya ambata, lokaci guda ya tako zuwa gaban Danger hannayensa saman kunkumi “Ya akai kasan duka wad’annan..?” “Believe me Inspector, iyakacin abinda naji kenan daga cikin wayar nasa.. Sannan Iyakacin abinda na sani kenan gameda wannan mutumin...” Mu’azzam yai masa K’uri kafin yai alama ma sergeant guda dake tsaye bakin k’ofa, yana k’arasowa ya sara masa.. Umarni Mu’azzam d’in yai masa cewa ya maida danger cikin cell d’insa.. Danger yana tarjewa yana fad’in “Rankaidad’e ai sai ku sakeni nayi tafiyata tinda na fad’i Iyakacin abinda na sani..” “You’re not off the hook yet..zamuci gaba da shan coffee tare na d’an wani lokaci...” Yai maganar yana mai sakar masa murmushi da gefen bakinsa.. Daga haka bai kuma tsayawa sauraron Danger ba yai ficewarsa ya nufi ofishinsu cikin sassarfa. A hanya ya had’uda da Yusuf da Assad, suka shige cikin Office yana sanar dasu yanda sukai da Danger.. Ana haka Maleeka ta shigo tana fad’in ai mata afuwa na rashin k’arasowarta kan lokaci.. Takaicin da take basa yasa bai Ko kalli yanda take ba.. Yaci gaba da shirya bindigarsa had’ida sanyata gefen suit pocket d’insa, lokaci guda yake fad’iwa Yusuf su tsaya nan zasuje shida Assad, idan suna buk’atan backup zasu sanar dasu.. Yusuf ya amsa yana mai sara masa kafin suka fice, Assad na kashe wa Maleeka idanu alamun tai hak’uri da abokinsa Ta sauk’e idanunta akan wani amma Mu’azzam kam bazata samesa ba.. Harar y’ar wasan da suka saba da Assad ta jefa masa, yabi bayan Mu’azzam yana rik’e dariyarsa. ** Tin farar safiya Tabawa take abu d’aya a gidan, banda zuba ruwan masifa da bala’i bata komai, ta shiga janyo Habeebu autan su Sadiya tana fad’in kodai a biyata kud’inta kokuma ta tafi dashi.. Sadiya kuka Umma kuka ga Abbansu bai gida ya fita.. Tsaban tashin hankali daga ita sai ‘yar T-shirt d’in dake jikinta da zani ta fito ko takalmi babu k’afarta balle d’ankwali.. Ihu kawai take cikin unguwar tana neman a kawo masu d’auki wata mata tayi Garkuwa da k’aninta.. ‘Yan unguwa da suka San cewa su Sady na cikin rikici tsamo tsamo babu wanda yabi takanta Sai kururuwa take tana tsalle hannu aka tana fad’in a taimaketa anyi garkuwa da k’aninta.. Dashike daga can bakin layin sukai parking motarsu hakan yasa suka shigo da k’afa.. Sam bata kula da mutanen ba gudu kawai take hannu aka idanu a rintse tana tsalle tana fad’in a taimaketa, taimako taimako. Ta karyo kwana kenan a wannan yanayin suma sun nufo layin kenan saiji tayi ta bangaji mutum ta fad’a cikin jikinsa.. Cak ta tsaya ta daina ihun saima k’ok’arin ware idanunta da take.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *06* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Idanunsa a rufe suke cikin bak’in glasses hakan yasa bata iya ganin k’wayar idanunsa ba, gaban Sadiya yayi wani irin yankewa ya fad’i, Ta kasa katab’us Ta kuma kasa janye hannunta daga saman k’irjinsa saima zuba masa idanu da tayi.. Mutumin yafi mata yanayi da taurarin cikin film. Shid’inma kallonta yake ba tareda ya janye idanunsa ba saidai sam Sadiya bata iya ganin k’wayar idanunsa amma shid’in yana ganin nata Ta cikin shades d’insa.. Assad ma zuba masu idanu kawai yai yana nazarin yarinyar data bangaje abokin nasa, gata dai kaman ba mai tab’in hankali ba amma yanayin da take ciki zai tabbatar maka cewa cikin tsananin tashin hankali take dan Ko takalmi babu k’afarta.. Tamkar wacce aka zabura haka Sadiya Ta soma janye hannunta tana mai matsawa da baya da baya ba tareda ta furta komai ba, Assad da Mu’azzam da mamaki suke dubanta har lokacin musamman k’afafunta da yayi fusufusu babu ko takalmi.. Ita kaw Sady kallo d’aya kurum tai masu sukai mata yanayi da Jami’an tsaro, Allah ya gani tana mugun tsoron jami’an tsaro bata fatan wani abinda zai had’ata dasu.. Lokaci guda Ta shiga k’yafta manyan idanunta masu tsananin haske da yalwan suma, takai idanunta k’asa tana kallon k’afafunta da sukai fusu fusu dan idon mutanen naga k’afafun nata ne, tai saurin d’ingile k’afafun tana mai sosa sumarta da ya barbaje, kaman mai shirin sakin kuka tace “Sorryyyy...” Lokaci guda ta saki murmushinda yafi kama da yak’e kumatunta suka lotsa, Ta soma jada baya a hankali.. Kan kace mai ta aune a guje ta juya ta bar wajen, har juyowa take tana kuma dubansu...Mu’azzam yabi bayanta da kallo har Ta b’ace masa yana mamakin yarinyar, wata zuciya tace k’ila mahaukaciya ce sabuwar kamu.. Assad ya bud’e murya yace “Ita kuma wannan ko meke damunta sai Allah..” Ya d’anyi fasali kafin ya k’arada “But she’s Pretty, very Beautiful..” Wani kallo Mu’azzam ya watsa masa had’ida d’an tab’e baki kad’an.. Ba tareda yace komai ba yasa kai yai shigewarsa. Assad ya biyosa da sauri yana fad’in “Amma kasan yanda kuka bige juna tamkar had’uwar taurarin cikin film.. You two zaku dace da juna sosai..” Da tsananin mamaki kurum Mu’azzam ke duban Assad.. “Wait, what rubbish are you talking about Assad..? What exactly has gotten into you.. Ta ya zamuga Mahaukaciya a hanya ka hau had’ani da ita... Baka santa ba ban santa ba, wannan wani shirme kenan Assad..” Ya d’an girgiza kansa kafin yace “Masu hankali ma basa gabana ballantana mahaukata..” Darawa Assad ya somayi kad’an dan dama so yake ya tab’o mutumin nasa “Kai waye yace maka mahaukaciya ce.. K’ila dai wani damuwarta ya fito da Ita haka.. Amma sam bata min kamanni da masu tab’in hankali ba.. Opps na mance ashe fah Kai ango ne, kafin Hajiya Safeenah tajini Ta sakani a blacklist tace na fara yima angonta tayin wasu matan tun kafin Ta tare a gidanta...”Ya k’arashe yana kame bakinsa da hannayensa biyu.. “Will you please stop being annoying and concentrate on your assignment..” Mu’azzam ya fad’i yana mai aikawa Assad d’in wani irin kallo.. Sara masa Assad yai yana mai fad’in “Sir, My apology.” Murmushi saman fuskarsa. D’an girgiza kai kurum Mu’azzam yai kafin suka nufi layin gidan Alhaji Isyaku D’an canji.. Wasu samari guda biyu suka tadda zasu shige k’ofar gidan, suka taresu suka tambayesu ko nan ne gida Alhaji Isyaku.. Sukai sa’a kuwa wannan gidan shine gidan Alhaji Isyaku, take suka soma knocking a k’ofar gate d’in... Maidagi Baba Dattijo dake bayima flowers cikin sauri ya k’araso ya bud’e yana tambayansu da mai zai taimaka masu.. Assad ya gaishesa cike da girmamawa kasancewar mutumin Dattijo kafin ya bud’e wallet d’insa ID d’insa ya bayyana, lokaci guda yake furta “Mu jami’an tsaro ne daga ofishin gudanar da bincike na manyan laifuka.. Muna son ganin mai gidanka idan yana gida..” Baba Dattijo ya d’an dubesu a tsorace yace “Amma saurayi inji lafiya koh..” Assad ya murmusa kad’an yace “Lafiya k’alau Baba aiki mukazo ba tashin hankali ba.. Kawai ka mana iso da mai gidan idan yana ciki..” Baba ya jinjina kai yace “Toh shikenan d’an nan.. Kuyi hak’uri, yau shekarata kusan ashirin kenan ina aiki gidan tin gina gidan ban tab’a ganin Jami’an tsaro sunzo ba shiyasa na tambayeku.. Ai Alhaji mutumin k’warai ne.. Duk anguwar nan an masa shaida..” Abinka da tsoho Sai ya shiga basu labarin abinda bai shafesu ba... Mu’azzam da ya riga ya gama k’osawa, k’ok’arin saita kansa yai kad’an kafin ya matso kusan Dattijon yana mai zare shades d’in dake mak’ale fuskarsa had’ida d’an rage girman idanunsa, ya d’an sosa sumarsa kad’an yace “Baba kodai mu tafi dakai ofishin ‘yansanda ne ka mana bayanin a can..” Tamkar mai rad’a haka Yai maganar Baba maigadi ya zabura ya zaro ido waje yace “Ofishin ‘yansanda D’an nan ka rufa mini asiri.. Ni Buba tinda nazo duniya ko hanyar ofishin ‘yansanda ban sani... Barin maku iso da Alhaji kunzo a daidai domin kuwa yau d’in bai fice ba..” Ya k’arshe yana mai nufan cikin gidan.. Mu’azzam da Assad suka dubi juna suna d’an murmusawa, lokaci guda Mu’azzam d’in ya tsume yana mai maida shades d’insa fuskarsa.. Jim kad’an Mai gidan ya fito mamaki fal saman fuskarsa, suka gaisa da juna had’ida gabatar da kansu.. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “A k’ofar gidanka, satin da ya gabata akwai taron d’aurin aure da aka gudanar a k’ofar gidanka.. Anyi haka..?” Da tsananin mamaki Alhaji Isyaku Ke dubansu kafin yace “Taron d’aurin aure kuma a k’ofar gidan nan..? Gaskiya ba’ayi haka ba..” Wannan karon Assad ne yayi maganar “Ko ba kai bane Alhaji Kabir Isyaku D’ancanji..?” Alhaji Isyaku ya jinjina kai yace “Of course k’warai ma kuwa ni ne Alhaji Kabir Isyaku.. Amma gaskiya babu wani taron aure da akayi a k’ofar gidana.. Babu ma auren da akayi kwata kwata..” Mu’azzam ya warware takardan dake hannunsa, sketch na fuskar mutumin da aka tsinta da gawan Ikram ya bayyana, ya nuna ma Alhaji Isyaku hoton yace “Wannan shine angon da za’a d’aura aurensa a k’ofar gidanka.. Ko zaka iya ganeshi..?” Alhaji Isyaku yai K’uri yana duban hoton lokaci guda yake girgiza kai alamun baisan mutumin ba.. “Yallab’ai a gaskiya bansan wannan mutumin ba, hasalima ban tab’a ganinsa ba..” Duk tattaunawar da suke Baba Maigadi dake tsaye gefe sai ware idanu yake yana so ya hango hoton da ake nunawa Alhaji Isyaku, dukda cewa shekarunsa sund’an ja amma tabbas yaso ya gane fuskar wannan mutumin... Mu’azzam ya jinjina kai ya mik’awa Alhaji Isyaku hannu sukai handshake kafin yace “Mun gode K’warai da lokacinka daka bamu.. Sannan ina fata idan muka sake zuwa zaka k’ara ara mana lokacinka.. Idan kuma Ta kama mu gayyaceka zuwa ofishin mu zaka amsa gayyatarmu..” Alhaji Isyaku ya jinjina kai yace “Wannan babu matsala Inspector, ko yaushe kuna iya zuwa da tambayoyinku..” Sukai sallama Alhaji Isyaku ya koma cikin gidansa.. Assad ya d’an fuzar da huci yace “Gaye nan ya rantse Sai ya bamu wahala..” Mu’azzam ya murmusa da gefen bakinsa yace “Muma kuma zamu bashi wahala.. Bazan barshi ba har sai yayi magana.. I’m positive yasan mutumin nan sosai ba abokin shan sigarinsa bane kawai kaman yanda yace.. Lets go..” Assad ya jinjina kai kafin suka juya da zummar Barin wajen.. Baba Mai gadi yai saurin biyo bayansu yana fad’in “Rankaidad’e.. Yallab’ai...” A tare suka tsaya suka juyo suna duban Baba Maigadi.. “Yallab’ai hoton mutumin nan da kuka nuna ma Alhaji..” Mu’azzam yai saurin zaro takardan cikin suit pocket d’insa, ya shiga warwareta yana nuna ma Baba Maigadi... Baba Maigadi yai K’uri yana duban hoton lokaci guda yake jinjina kai yana nuni da hoton yake furta “K’warai shine.. Shine wannan mutumin da Sabeera take kawosa suyi zance a gidan nan shida wata k’awarta.. K’warai shine wannan mutumin.. Shekaruna sunja amma idanuna garas yake.. Tabbas wannan mutumin ne..” Mu’azzam da Assad sukai saurin duban juna, Mu’azzam yace “Baba wacece Sabeera..?” “Sabeera ai d’iyar Alhaji ce, itace d’iyarsa ta biyu...” Assad yaji murmushi na zuwa fuskarsa, at last sun samu wani abu.. Cikin sauri ya shiga furta “Baba muna buk’atan muga Sabeera yanzun nan..” Shikam Mu’azzam tuni ma ya koma k’ofar gidan yana kuma bugawa.. Baba Maigadi da Assad suka dawo a tare, Baba na fad’in “Barin maka iso Yallab’ai ai inaga bata fita ba dan makarantarsu suna yajin aiki... Koda Baba ya shiga ya sanar da Alhaji Isyaku ga mutumin da suke nema sosai ran Alhaji Isyaku ya b’aci, ya tasa Maman Sabeera da fad’a Ta yanda yake shiga bata nan yake fita ba “Na fad’a miki bana son alak’ar yarinyar nan da k’awayen banza.. Har yaushe Sabeera take kawo samari zance cikin gidan nan banida labari.. Kullum ina ja miki kunne bakiji.. Ga irinta nan kinga abinda taurin kunnenki ya janyo mana.. Toh wllhi Nidai kinji na rantse idan aka rufeta bazanyi belinta ba, Keda kike d’aure mata gindi take tarayya da ko wasu irin mutane sai kije kiyi belinta.. Aikin banza Ina Sabeeran take yanzu..?” Maman data rapka tagumi cikeda tashin hankali take fad’in “Taje sayan Katin waya a bakin layi.. Amma yanzu zata dawo.. Oh ni Rahina na shiga uku.. Alhaji kar ka bari su tafi da Sabeera wllhi d’iyarmu yarinyar kirki ce..” Tsaki ya buga yana fad’in “Ai Kinga irin abunda kullum nake fad’a miki, idan kukayi wasa daga rana mai kaman ta yau makaranta ma Ta daina zuwa.. Rahina sanin kanki ne Gudun kar d’iyata ta lalace yasa nak’i kaita wani wajen tayi karatu nace saidai tayi a nan, ko hostel ban amince ta zauna ba na ajiye mota da driver nace kullum a dinga kaita, toh tinda a nan d’inma ban tsira ba cireta zanyi Ta gama karatun..” Cikin damuwa Maman Sabeera Ke fad’in “Alhaji kar kace haka, lalacewa ba daga nan take ba, Ko a d’aki kake rufe d’iyarka idan taso lalacewa sai ta lalace, tsananin tak’ura bashike tsare mana yaranmu ba, a’a ayi addu’a kuma a saka idon.. Nawa aka tak’ura masu kuma suka lalace d’in kaidai kawai addu’a shi zamuke masu.. Balle ma nasan Sabeera batayi komai ba..” “Ke ni ki rufe mun baki, ki shige muje ki bama ‘yansanda bayanin yanda d’iyarki taje..” Ya k’arashe yana mai sab’a babbar rigarsa kafin yai ficewarsa.. Maman Sabeera ta biyo bayansa tana kiranta inaa ko sauraronta baiba.. A b’angaren Sadiya kuwa tana isowa gida ta tadda k’aninta kwance jikin Ummansu, da k’yar Umman ta shawo kan Tabawa da fad’in satin da za’a shiga tayi alk’awari dik yanda kud’ad’enta suka shiga suka fita zata nemomata Su, da wannan yarjejeniya Tabawa ta saki Habeebu bata tafi dashi ba.. Sabeera dake tsaye gefe rik’eda k’aramar bak’ar leda a hannunta, recharge ne na waya saiko sai sanitary pad da ta sayowa Sadiyar, ta cire recharge card d’in ta mik’awa Sadiya ledar sanitary pad d’in tana fad’in “K’awata barin k’arasa gida kafin a soma nemata, Baba na gida bai fice ba.. Nasan Sai ya tambayi Ina nake kafin ya fita..” Sadiya dai tinda ta k’araso sai lek’e lek’e take a lungun, kaman mai jiran zuwan wani.. Sabeera ta d’an juya tana waige waige da mamaki tana duban mai ya d’auke hankalin Sadiyar.. “Wai lek’e lek’en me kike ne tintinin, Hajiya Tabawa dai ta tafi ba dawowa zatayi ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki..” Itadai Sadiya bata ce mata komai ba, dan tinda taci karo da wannan mutumin k’irjinta bai daina bugawa ba, sannan gabanta bai daina yankewa ba.. D’an murmusawa kad’an Sabeera tai tana fad’in “K’awata badai tsoro ba.. Kinga bara na k’arasa gida, sai munyi magana..” Juyawan da zatai ta hango ta hango Babanta da mamanta harma da wasu mutane guda biyu Sun karyo kwanan gidan Babanta sai masifa yake.. Ba Sabeera data kusan sakin fitsari a jikinta ba, harta Sadiya saida taji ‘yanhanjinta sun juya musamman data hango wannan mutumin da suka bangaji juna shida Ita... Sabeera tai saurin rik’o hannun Sadiya tana fad’in “Na shiga uku Sady wllhi Baba ne... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Shikenan yau kasheni kawai zaiyi wllhi..” Sadiya kam Ta kasa katab’us sai duban mutumin nan da suka bangaji juna take d’azu, zuciyarta taci gaba da bugawa idanunta akansa.. Har wannan lokacin idanunsa na rufe cikin bak’in glasses. Baban Sabeera dake gaba yana sab’a babbar riga yana nunasu da yatsa yake fad’in “Yauwa Inspector, ka gansu can, gasu can.. Dama na fad’a maku a nan za’a sami Sabeera.. Tana tareda wannan annobar.. Yarinyar ta riga ta zame mana masifa a unguwar nan, banda tara maza bata komai.. Duk ta lalata tarbiyan yaran layin nan..” Ya kuma sab’ babbar rigar yana jefo dak’uwa ma Sabeera tin daga nesan yana fad’in “Zakici gidanku ne yau..!” Sabeera Ta kuma rikicewa tana kuma b’oyewa bayan Sadiya daidai sanda suka k’araso k’ofar gidan.. Har lokacin Baban Sabeera bai daina bala’i ba mamar Sabeera na kwab’arsa hankalinta duk a tashe itama amma kaman cewa yake Ta k’ara... Sadiya tsoro Sabeera tsoro, Sabeera na tsoron Babanta Sadiya kuma gani take Baban Sabeera ‘yansanda ya d’auko mata zai sa a rufeta a police station tinda ya mata iyaka da d’iyarsa tak’iji.. Aiko suna k’arasowa ta finciki hannunta daga rik’on da Sabeera tai mata, tuni tai jifa da ledar sanitary pad dake rik’e hannunta wanda Sabeera ta sayo mata a shago... Aiko ledar nan bai sauk’a ko Ina sai Fuskar Mu’azzam, tim kakeji ya samesa a fuska sai da glasses d’insa ya gauce.. Ya saka hannu a hankali ya zare shades d’in yana mai sauk’e idanunsa k’asa dan ganin abinda ta jefesa dashi.. A hankali ya duk’a ya d’auka yana juyawa, bai ce ma kowa k’ala ba Sai d’age suit pocket d’insa da yai ya saka ciki.. Ya gyara zaman suit d’insa had’ida maida glasses d’insa kafin ya k’arasa k’ofar gidan ba tareda yabi takan su Sabeera da Babanta dake k’ok’arin janyota tana b’oyewa bayan mahaifiyarta Assad na k’ok’arin janye Baban Sabeeran. Hayaniyar da Umma ta jiyo daga waje ya sanyata fitowa bayan taga shigewar Sadiya d’aki a guje Ta maida k’ofa ta rufe.. Kana ganin yanda Umman Sadiya ta fito a birkice zaka fahimci suna cikin tsananin tashin hankali ne, dan ba’a jimaba Tabawa ta tafi da yarjejeniyar sati mai zuwa za’a mata kashin kud’ad’en mutane ‘yan group d’inta na online business d’inta.. Umma tana fitowa Baban Sabeera ya soma nunata yana fad’in “Yallab’ai gata nan, wannan itace mahaifiyarta.. Duk wani barikanci da tara maza Ita take koya mata, wannan mata mak’otaka da irinsu masifa ne.. Ka ganta nan..” Mu’azzam ne ya katsesa da fad’in “Kana iya Barin mu muyi aikinmu Alhaji..” Baban Sabeera ya jinjina kai yace “Amma nima Yallab’ai zan iya shigar dasu k’ara sabida Auren d’iyarsu da suka saka a k’ofar gidana ba tareda sanina ba.. Ina zaman zamana ‘Yansanda suka kawo min sammaci..” Assad ya d’anyi gyaran murya ya dubi Sabeera dake mak’ale jikin Mamanta tana hawaye yace “Ki daina tsoro kinji, tambayarki kawai zamuyi..” Sabeera tai saurin jinjina kai still tana hawaye.. Sketch d’in ya warware ya nuna mata yace “Kinsan wannan mutumin..?” Tai K’uri tana kallo, ta kuma d’ago kai ta dubi Assad kafin Ta dubi Umma dake tsaye gefe tayi zuru zuru.. Duban yanda Sabeera take kallo Assad yayi kafin yace “Saurayin k’awarki ce da take zuwa gidanku dashi zance. Am I right..?” Ta jinjina masa kai a hankali kafin tace “K’warai Sagir ne..” Jin Ta ambaci Sagir yasa Umma matsowa tana duban sketch d’in.. Umma ta shiga tafe hannaye tana salallami tana fad’in “Wannan Bawan Allah shi ya jefa mu a ukun da muke ciki.. Rankaidade dan Allah ina zamu samu Sagir yazo ya sanar damu abinda d’iyarmu tai masa ya mata wannan wulak’anci da cin kashi..” Assad ya jinjina kai yace “Bisa ga dukkan alamu kece mahaifiyar yarinyar da Sagir zai aura..?” Tai saurin jinjina masa kai tana jin hawaye na zuwa mata.. Jinjina kai Assad ma yai kafin ya dubi Alhaji Isyaku da iyalansa yace “Alhaji mun gode K’warai kuna iya tafiya daga nan..” Alhaji Iskayaku yace “Alhamdulillahi.! Muna iya tafiya koh..?” Wannan karon Mu’azzam ne yai magana “Kuna iya tafiya, amma kaman yanda muka fad’a maka idan Ta kuma kamawa mu nemeku zamu nemeku, muna kuma fatan ku sake bamu goyon baya da had’in kai..” Alhaji Iskayu ya jinjina kai yace “In sha Allahu Inspector.. Mun barku lafiya..” Ya k’arashe yana mai duban Sabeera “Ke kuma shige mu tafi..” Tana matsan hawaye ta shige Assad ya d’anyi kaman zaibi bayansu ganin yanda mahaifin nata ke k’ok’arin janyota, d’an girgiza kai kurum yai ya dawo da baya yanda Mu’azzam ya tsare Umma da tambayoyi.. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Ina mahaifin ‘yarki yake..?” Umma Ta girgiza kai tace “Ya fita tin safe..” Ya jinjina kai a hankali kafin yace “Toh zamu gayyaci d’iyarki zuwa ofishinmu domin gudanar da bincike had’ida amsa mana wasu tambayoyi..” Umma ta shiga salati tana fad’in “Na shiga uku ni Uwani.. Sadiya wane irin mutumi kika kwaso mana..Tinda nake ni ban tab’a zuwa police station ba.. Rankaidad’e wllhi bamu San mutumin nan ba, kuma kaman yanda na fad’a maka ba’ayi auren ba ya gudu.. Muma nan nemansa muke..” “Zaki iya shiga ki fito mana da d’iyarki domin ta amsa mana wasu tambayoyi..” Ya fad’i babu walwala tamkar ba hawaye yake hangowa fuskar Uwani ba... Jiki a sanyaye Umma ta shiga kiran Sadiya.. Har lokacin Sadiya tana kulle a d’aki, tana jin shigowar Umma tace “Umma Sun tafi ne..?” Umma tace “Ki fito magana sukazo dashi akan Sagir..” Ai Babu shiri Sadiya ta bud’e k’ofa ta fito tana fad’in “Umma mai ya sami Sagir.. An gansa ne.? Ina yake.. Ya dawo daga US d’in koh.. Ai dama ni na sani Sagir yana sona bazai tab’a watsa mana k’asa a ido ba.. Saidai ‘yan bak’in ciki su mutu.. Tabawa kuma harda abinda yafi kud’inta za’a biyata.. Event kuma Eagle square ma ya mana kad’an..” Fizgota da Uwani tai ne ya sanyata had’iye sauran zancen nata.. Ta shiga janyota tana fad’in “Shige muje kafin Babanki ya dawo ya tadda ‘yansanda k’ofar gidansa..” A haka Umma Ke janyota har suka fito k’afar gidan, shid’in Ta soma hangowa mutumin da suka bangaji juna shida ita d’azu, fitowarta yai daidai da lokacinda yake zare glasses d’in daga idanunsa... Sai wannan lokacin ta sami damar ganin fuskarsa complete, saidai fad’uwar gaban data tsinci kanta ciki har ya d’ara wanda tayi a baya domin kuwa a halin yanzu ya cire glasses da suka rufe masa idanu a lokacin da suka bangaji juna, fuskarsa ya kuma bayyana had’ida k’wayan idanunsa.. Tsoron jami’an tsaron da take ya ninku.. Har Mu’azzam ya soma takowa gabanta bata Sani ba.. Dan shima sarai ya genate yarinyar nan ce data bangajesa ta kuma gudu, sannan itace ta jefesa da ledar ultra pad yanzu a nan.. “Ke.!” Ya fad’i yana mai kuma tsimewa idanunsa tarau akanta.. Ta d’ago a zabure tana dubansa.. “Kinsan wannan..?” Ya tambaya yana nuna mata hoton Sagir.. A daburce ta shiga jinjina kai tana fad’in “Umma Sagir ne.. Umma wllhi Sagir ne.. Taho ki gani.. Na fad’a miki zai dawo gareni..” “Ke.!!” Ya daka mata tsawa sosai wann karon wanda ba Sadiya kawai ba harta Assad da Umma saida suka razana, Mu’azzam yaci gaba da takowa gaban Sadiya yana furta “Gawan kike jira..?!” Daga Sadiya har Umma mutuwar tsaye sukai suna duban Mu’azzam dake ci gaba da takowa gaban Sadiya cikin tsananin k’unan rai ya d’ago hoton yana nuna mata yake furta “Well wanann D’anta’addan ya mutu..! He’s found dead.. He’s gone..! Ya mutu, shid’in gawa ne.! Bazai kuma dawowa cikin rayuwarki ba.. Now you’re going to tell me everything you know about him..!” Sadiya dake dafe da k’irjinta tana jin maganganun D’ansandan sama sama, kalman ya mutu an tsinci gawarsa kawai take nanatawa cikin dodon kunnuwanta.. “Umma.! Umma.. Sa...Sagirrr..!” Luuu sai fad’owa tai jikin mahaifiyarta.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *07* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin tsananin tashin hankali Umma Ke jijjigata “Sadiya..! Sadiya.! Sadiya dan Allah Ki tashi, kar ki tafi ki barni.. Sadiya ki tashi dan Allah..” Assad ya k’araso yana mata fifita da takardan dake hannunsa... Kaman daga sama sai ji sukai an watsama Sadiya ruwa a saman fuskarta.. Suka d’ago idanu suna duban Mu’azzam dake tsaye saman kansu rik’eda bottle water. Dama tinda Sadiya ta sume ya nufi yanda suka aje motarsu ya d’auko ruwan gora a cikin motar.. Wani irin dogon numfashi Sadiya Ta saki tana mai k’ok’arin bud’e idanunta.. Daidai lokacin Mu’azzam ya d’an duk’a kad’an saitin fuskarta.. Aiko tana bud’e idanunta tai tozali dashi duk’e gabanta ya tsareta da wannan idanun nasa masu furgitarwa, fuskarsa sam babu alamun walwala.. Rungumeta Umma tai tana fad’in “Alhamdulillah.. Sadiya kar ki tafi ki barni kinji.. Ked’in nake so d’iyata.. A halin yanzu ban damu ki auri mai kud’i ko Talaka ba, idan dai zamu kasance tare...” Wani irin kuka Sadiya ta fashe dashi had’ida fad’awa jikin Umma sanda ta tuna abinda D’ansandan nan yace Wai Sagir ya mutu gawarsa aka tsinta.. “The drama is over.. Tashi ki fad’a mana komai da kika sani akansa..” Mu’azzam ya fad’i yana mai mik’ewa tsaye had’ida zira hannayensa cikin aljihun wandonsa.. Umma ta taimakawa Sadiya suka mik’e a tare “Rankaidad’e wllhi bamu San mutumin nan ba kaman yanda na fad’a maka, yaudara rum yai ya gudu ya bar d’iyata tana jira.. Wllhi bamu San daga yanda yake ba..” “Ta yaya zaku d’auki ‘yarku ku bada aurenta ga mutumin da baku sani ba..? Shin dama irin haka na faruwa..?” Assad yace yana mai tsare Umma da idanu.. Mu’azzam kam har wanann lokacin idanunsa na kan Sadiya, yanai mata wani irin duba.. Maganganun Alhaji Isyaku Baban Sabeera na Yawo a dodon kunnuwarsa cewa yarinyar Ballagaza ce mai bibiyan maza dan neman abin duniya.. Baima sauraron tambayoyin da Assad Kema mahaifiyar Sadiya dan Sadiyar kam har lokacin rawa kawai jikinta yake Ta kasa katsb’us sai kuka da take har lokacin. Tana cikin tsananin shock har wannan lokacin. Cikin tambayoyin da Assad yayima Umma ya fahimci cewa su kansu basu san tak’amaimen wani abu gameda Sagir ba, son abun duniya ne da ya rufe masu idanu ya sanyasu amincewa da Sagir har ta kaiga suna yunk’urin aura masa d’iyarsu.. Ya d’an girgiza kai yana duban yanda Uwa da d’iyar suka rungume juna suna hawaye.. Yaji tausayinsu dan tausayi amma something was amiss a cikin labarin, something wasn’t clicking, the math wasn’t mathing.. shi bai tab’a jin yanda akayi aure haka ba.. “Hajiya baku San kowa nashi ba kuka amince zaku basa auren d’iyarku..?” Assad ya kuma fad’i yana dubanta.. D’an jim Umma tai dan bata fatan wani abu ya jefata cikin fitinan da Sagir yake ciki.. Uban bashin da Tabawa Ke binsu ma kad’ai ya ishesu.. Hakan yasa ta girgiza kai alamun a’a.. “Kina nufin bai turo magabata ba haka kurum kuka amince zaku d’auki d’iyarku ku basa..?” Assad ya kuma jefo mata tambayar.. Umma ta daburce ta shiga girgiza kai tana neman kalaman da zata had’o saman harshenta.. Sai sannan Mu’azzam ya k’araso gaban Sadiya da kanta Ke kifi cikin jikin mahaifiyarta tana aikin kuka Cikin kuka Umma Ke fad’in “Rankaidad’e dan Allah kuyi hak’uri d’iyata Ta dawo cikin hayyacinta.. Dan Allah enough with the questions for now..” Kafin yakaiga magana wayarsa Ta soma ruri, Chief Inspector Officer ne Ke kiransa daga ofishinsu can headquarters.. Ya matsa gefe yana amsa wayan.. Neman gaggawa da Chief Ke masu yasa ya k’araso yanda suke.. Ya d’an fuzar da fuci kafin ya dubi Umma yace “Ku tsammacemu ko wani lokaci daga yanzu..” Daga haka Assad yai yace suje... Suna tafe Assad Ke fad’in “Maybe they’re telling the truth.. Maybe basusan komai akansa ba.. Kwad’ayin abin hannunsa ya rufe masu ido har sukayi tunanin basa auren d’iyarsu ba tareda sunyi bincike sunsan shid’in waye ba..” “And you believe them.? Well idan ma haka d’in ne ita yarinyar dole tasan wani abu, dole tasan yanda ta had’u dashi.. I believe through wannan yarinyar zamu samu wani abu..” Assad yai shiru yana nazari “You’re right.. Zatai linking d’inmu to gaskiyar al’amarin..” ** Su Mu’azzam suna tafiya Umma ta janyo Sadiya suka shige gida harda saka ma gidan sakata.. Ita kanta Sadiyar sai sannan ta warware ta shiga rabe raben idanu tana fad’in “Umma yanzu ya zamuyi idan ‘yansandan nan suka sake dawowa.. Mai zamu ce masu..?” Umma ta yarfe gumin dake kwance saman goshinta tace “Gwara mu barsu akan cewa bamu San komai ba kafin muje mu saka kanmu a UKU.. Allah kad’ai Yasan Sagir d’in nan wane irin gasunk’umin D’anta’addan ne..” Umma ta nusa tace “Ni Anya bazamu bar garin nan ba, bazamuyi hijira ba kuwa.. Tashin hankalin tayi yawa, bamu gama da Tabawa ba yanzu ga wani ya kunno Kai..” Sadiya tace “Umma mu tafi muje ina.. Bamuda wajen zuwa.. Kuma Tabawa bazata tab’a k’yalemu ba dik yanda muka je..Umma idan ma muka tafi bamusan wani irin fitina da tashin hankali zamu kuma fuskanta gaba garemu ba.. Sannan Umma ga Ashiru ga Habeeb yaya zamuyi dasu..? Sud’in fah yara ne Umma.. Tafiya dasu yana nufin jefa rayuwarsu cikin garari, and Umma bana fatan abinda zai b’ata rayuwan yaran nan.. Dik abinda nakeyi Umma inayi ne domin na inganta rayuwarsu.. Ina son mai kud’i ne domin su sami rayuwa mai inganci su kuma girma cikin gata.. I don’t want my little brothers to experience what I have been through in the past...Umma bana son ‘yanuwana su sha wahala irin wahalan da ni nasha a baya a lokacin muna cikin tsnanin talauci Abba kuma yana cikin tsananin jinya..” Ta kasa ci gaba da magana sabida rawa da muryarta keyi.. Umma tai saurin k’arasawa ta rungume d’iyarta su duka biyun suna hawaye.. Cikin zuban hawaye take furta “Sadiya I don’t want you to suffer the same fate da mahaifiyarki na auren Talaka Shiyasa na dage sai kin auri mai kud’i.. Amma bayan abubuwan da suke faruwa yanzu, na yarda mutum baya wuce k’addararsa.. K’addararka tamkar inuwarka ce duk yanda kaje sai ta bika.. Ki yafe min ‘yata.. Ina ji kaman ni na saka rayuwarki cikin wannan gararin..” Sady ta kuma rungume mahaifiyarta su duka biyun suna kuka mai ban tausayi.. ** Da tsananin mamaki Mu’azzam ke duban Chief Inspector, ya kasa yarda da abinda yake ci.. D’an girgiza kai yai kafin yace “Chief you need to believe me mutumin nan ba Iyakacin gaskiya yake fad’i ba.. Sir, I’m positive shid’in yasan Sagir sosai.. And yes munje location d’in da ya bamu and we found something.. Mun sami yarinyar da Sagir was about to marry.. Sir idan ka amince mun we are so close to finding the truth.” Girgiza kai Chief Inspector yai yana mai duban Mu’azzam d’in idanu a kannare yace “I can understand you’re desperate to get to the bottom of this case.. And According to your team report Officer Gamji, mutumin nan ya sanar dakai Iyakacin hiran da yaji daga tattaunawar shi Sagir d’in yake da budurwarsa.. And kaima ka fad’a da kanka kaje wannan location d’in ka tabbatar da hakan, harma ka samu yarinyar.. So tell me, wani hujja kakeda shi da zaisa kaci gaba da ajiye shi a nan..?” Huci kurum Mu’azzam yake yana duban Chief Inspector wanda yayi imani biyansa akayi ya kare mai laifi.. A hankali yake takowa gaban Chief kafin yace “Sir, I know my job.. I know exactly what I’m doing.. I only need a little more time to prove to you that..” Katsesa Chief yai da fad’in “All the decisions are taking by me Inspector Gamji..! Now I’m ordering you to process his release immediately...!” Cikin tsananin daka tsawa Yai maganar.. Mu’azzam dake ci gaba da sakin huci ji yake kaman ya shak’o wuyan che of inspector ya matsesa Sai ya fad’a masa uban wa yake karewa.. Assad ya kula da hakan, a hankali ya soma k’ok’arin janyo Mu’azzam yana fad’i cikin rad’a “Control yourself, don’t do anything foolish..” K’ok’arin saita kansa Mu’azzam yai kafin ya jinjina kai yace “Yes, Sir.. Permission to leave, Sir.” Chief ya jinjina kai yace “Good.. Dismiss now..” Sara masa Mu’azzam d’in yai kafin yasa kai ya fice daga office d’in zuciyarsa na masa wani irin zafi...Shi kad’ai Sai wani irin tsuma yake.. Yana isowa ofishinsu buga benci yai yana sakin huci.. Maleeka ne da wasu abokan aikinsu guda biyu.. Suna ganinsa a haka duk suka mimmik’e. Cikin tsananin huci yake furta “Out.. Everyone out..!” Babu shiri duk suka fice daga ofishin suna duban yananyin da yake ciki mai ban tsoro.. Assad ya turo k’ofar ya shigo kafin ya maida ya rufe yana mai fuzar da huci a hankali, lokaci guda yake furtawa cikin tsananin b’acin rai “What do you think you’re doing Mu’azzam.. What exactly is wrong with you.. You almost got yourself into trouble back there.. Ko kasan a gaban wa kake.. Chief ne fah Mu’azzam.. Ba case d’in nan kawai ba, harta aikinka zaka iya rasuwa Mu’azzam.. C’mon get a grip.!” Cikin b’acin rai Assad Ke maganar “Shut up..! Just shut up Assad..!” Yai maganar yana mai d’ago kansa dake kife kafin ya k’araso gaban Assad d’in su duka biyun suna sakin huci... Mu’azzam yaci gaba da fad’in “To hell with everything.. I don’t give a damn about his so called position.. I’ve always known mutumin nan is a corrupt police officer.. Nasan akwai wanda yake karewa.. Sanin kanka ne Assad sabida mutumin nan da gurb’atcciyar zuciyarsa wanda cin hanci da rashawa suka masa katutu munsha losing cases da Dama.. Criminals sun sha tsallake laifukansu. Da irin wannan mutumin a police force baza’a tab’a cin galaba ba.. Sune ‘yansandan da suke b’ata mana suna kuma suke walak’anta aikinmu takai matakin da Uniform d’in mu baida wani daraja a idon mutane.. But I promise you.. Ka rubuta wannan ka ajiye Assad, idan b’era na Yawo mage tana Yawo wata rana zasu had’e.. Sai na kawo k’arshen cin hancinsa da rashawarsa.. Kuma sai na kamo wannan mutumin da yake karewa..” Daga haka bai kuma cewa komai ba ya bud’e k’ofar yai ficewarsa, yanda yake tafiyar kad’ai zai tabbatar maka ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci.. Daga bakin cell d’in Danger ya tsaya suna aika ma juna kallo.. Danger sai sakin murmushi yake yana shafa hab’arsa.. Lokaci guda yake furta “Mr Inspector.. It looks like nida Kai bazamu d’auki dogon lokaci a nan muna sha coffee ba..” Ya d’anyi fasali yana mai girgiza kai had’ida tab’e baki kad’an kafin yace “Too bad you don’t smoke da mun had’e a mashaya.. So get off my neck already..!” Baikai aya ba Mu’azzam dake tsananin huci ya zira hannunsa guda ta cikin k’arfen cell d’in ya fincikosa yana fad’in “This is not yet over.. I’ll make sure you rot in jail, you criminal..” Cikin sauri Assad ya shiga janyesa, sai sakin huci yake.. Lokaci guda sergeant guda ya k’araso ya bud’e cell d’in Danger.. Aka fito dashi aka nufi bakin kanta dashi yanda Su agogonsa da wasu kayansa suke.. Sai sakin murmushi yake yana kashe ma Mu’azzam idanu.. Mu’azzam bai iya zama cikin wajen ba sai ficewa da yai cikin sassarfa.. Kafin Assad ya cimmasa har yayi key wa motarsa.. Yana isa gida baibi takan kowa ba ya nufi part d’insu shida Musaddiq dake cikin gidan.. Safeenah dake zaune balcony d’in d’akinta tana ganin shigowar motarsa ta mik’e.. Dama dawowarsa take jira, taci gayunta cikin navy blue Dubai material mai d’aukan idanu.. d’inkin fitted gown akai mata da ya mugun mata kyau ya zauna jikinta sosai.. Dikda bata faye fad’in kwankwaso ba amma ya mata kyau dan ko babu komai Safeenah tanada kyaun fuska da hasken fata.. D’aki ta komo ta isa gaba dressing mirror tana kuma k’yalk’yale fuskarta da kwalliya.. Ta sakar ma kanta murmushi ganin yanda tai kyau kafin Ta nufi b’angaren Mu’azzam... Shi kaw yana fad’awa d’aki bathroom ya shige ya sakar ma kansa shower.. D’umin ruwan na ratsasa yana tuno abubuwan da suka faru dashi a ranan.. Na farko buge juna da sukai shida wannan ‘yar tashan yarinyar da jifa masa ultra da tai a fuskarsa... Sai kuma Chief Inspector da yasa aka saki Danger.. Lokaci guda ya bud’e idanunsa ya saka hannayensa biyu ya maida sumarsa da ruwa ya jik’a zuwa bayan kansa.. Fuzar da fuci yai yana mai kuma lumshe idanunsa.. Bai Sa a ransa zai losing hope ba.. Binciken mutuwar Ikram yanzu ya fara koda hakan na nufin zai rasa komai nasa ne including his job as a police officer... Safeenah da tin shigowarta d’akin Ta fahimci wanka yake dan tana iya jin zuban ruwa daga cikin bathroom d’in hakan yasa Ta zauna saman gado tana mai mik’e k’afafunta alamun tana jiran fitowarsa.. A nan saman gadon ta hangi suit d’insa da ya cire.. Murmushi ta d’anyi kafin ta mik’e tana furta “Maza Feenah tashi Ki fara gudanar da duty d’inki as a wife..” Tai maganar tana sakin murmushi kafin ta isa ta d’ago suit d’in nasa.. Jin kaman da abu gefen rigar ya sanyata kuma shafawa tana jin kaman soso.. Nan dai ta zira hannunta ta ciro abun.. Cak Ta tsaya tana juya ledar cikin hannunta.. Daidai lokacin Mu’azzam ya fito daga bathroom d’aure da towel saman kunkuminsa, hannunsa rik’e da k’arami yana tsane sumarsa.. Kallo d’aya yai mata yaci gaba da abinda yake, tana tsaye tana kallonsa ba tareda ta janye idanunta ba.. Zai iya cewa zama a turai yasa Safeenah take wasu abubuwan kaman dai k’arancin kunya, amma yasha mamaki da har Ta gansa a haka bai Ko d’ad’areta ba saima ci gaba da dubansa da take.. Ganin ko tarewa basuyi ba.. Ya d’an kuma satan kallonta still bai daina abinda yake ba, sai sannan yaga abinda ke rik’e hannunta... Baice da Ita komai ba saima k’ok’arin nufan closet da yake.. Cikin sauri ta take masa baya har lokacin tana rik’e da pad d’in... “Mu’azzam what is this doing in your pocket..?” Ya d’an dubeta kad’an ba tareda yace komai ba yaci gaba da abinda yake... Zata kuma magana ya soma takowa gabanta, ganin yanda ya had’e rai yana nufota ya sanya gabanta wani irin fad’uwa ta shiga matsawa baya baya cikeda tsoro... Saida ta isa jikin gini kafin ta daina matsawa har lokacin pad d’in na rik’e hannunta.. Rank’wafo da kansa da yai kaman zai sumbaceta yasa Safeenah saurin rintse idanunta tana jin sanyin ruwan dake jikinsa had’ida hucin numfashinsa.. Saitin kunnenta yake fad’i tamkar mai rad’a “I hate it when someone messes with my stuff..” Daga haka zare ultra d’in yai cikin hannunta ba tareda ya kuma cewa komai ba.. “But I’m not someone.. I’m your wife.. And dan na tambayi ina ka samo ai banyi laifi ba..” “Safeenah Zo ki fice min a d’aki..” Ya fad’i yana nuna mata k’ofa. Idanunta suka kawo ruwa, zuciyarta ta shiga mata zogi, meke shirin faruwa da aurenta tin baaje ko Ina ba.. Auren data d’au alwashin protecting d’insa no matter the costs.. “But you know this is not fair..” Ta fad’i cikin rawar murya irinta mai kuka.. “Get out please...” Ya kuma fad’i yana nuna mata hanya.. Jinjina kai tai kafin ta tako gabansa tana goge siraran hawayen dake gangarowa saman fuskarta “Wannan shine dalilin da yasa kak’i mu tare har yanzu.. Do you have another woman in your life..?” Da tsananin mamaki yake dubanta, shine Safeenah take kallo tana fad’a masa magana haka, mai ta d’aukesa mai Ta maidashi.. Idan baiyi k’ok’arin rik’e kansa ba yanda ransa yake b’acen nan zai iya mata komai l.. K’ofa ya kuma nuna mata “Leave now..!” Zata k’ara bud’e baki kenan taji ya fizgota da k’arfin gaske ya nufi k’ofa da Ita.. Har waje ya fitar da Ita kafin ya maida k’ofan ya rufe.. Safeenah taji wani irin kuka na zuwa mata, durk’usawa tai wajen tana cazgan kuka.. Allah ya gani bazata iya sharing mijinta da wata shegiya a waje ba... Da wannan tinanin ta tashi ta nufi side d’insu.. A k’ofar parlor Ta had’u da Meema zata fito waje.. Meema ta dubi Safeenah da har lokacin da ragowar hawaye a fuskarta.. “Addah Feenah lafiya.. Ya na ganki haka.. Keda kika koremu d’azu kikace kwalliya kike wa Ya Mu’azzam mu fice mu baki waje.. Ya kuma naga Fuskar Ki haka..?” Harara ta raka Meema dashi “Mind your own business..” Ta fad’i tana mai shigew.. Meema ta tab’e baki kad’an kafin tabi bayanta tana fad’in “Aaaa badai Meeman ba, I don’t mind my own business.. Duk abinda babu ruwana a gidan nan shi nake shiga.. I love to meddle with other people’s lives..” Tana ida fad’in haka ta nufi bayan Safeenah.. Kafin Safeenah Ta rufe k’ofa Meema ta shige.. “Addah Feenah Wai meke faruwa ne.. Sai fah kin fad’a mun.. You know bazan k’yaleki ba har sai naji komai..” Feenah ta isa saman gado ta zauna tana jin hawaye na kuma zuwa mata, cikin muryar kuka take furta “I thought babu ruwansa da mata.. I thought baida lokacinsu.. But then I was wrong..” Kuka ya hanata ci gaba da magana.. Meema ta tab’e baki kad’an tace “Dama ke Addah Safeenah wani namiji ne mai lafiya zaice babu ruwansa da mace.. Wllhi k’arya ce kawai.. Ai haka aka haliccesu da son mata.. Ke yanzu jinki Ya Mu’azzam zaik’i amincewa da tariyarki ne idan baida me d’ebe masa kewa.. Ahap.. Allah yasa ma ba a Gidanki yake cin amanarki ba dai..” Cikin kuka Safeenah ta katse Meema da fad’in “Enough Meema.. Ya isheki haka.. I know my husband is not like that..” Tab’e baki Meema tai kafin tace “Aw really..? Shisa naga kinzo nan kina kuka ai.. Addah Safeenah you need to face reality.. Your Husband is a cheater.. Abinda ya kamaceki shine ki tashi tsaye, and fight for what’s rightfully yours kafin kiyi latti.. That’s if you really love him..!” Ta k’arashe tana ware idanunta fuskar Safeenar.. Shiru Safeenah tai kaman mai nazari sai kuma tace “What do i do now Meema..?” Meema Ta tab’e baki kad’an tace “Baki sanar dani abinda ya faru ba ta yaya zan samo miki solution..” Safeenah ta karanto mata tiryan tiryan abinda ta gani wajen Mu’azzam da yanda suka kwashe.. “Tabb amma wllhi Adda Feenah gayen nan ya raina miki hankali.. D’an anjima ma ce miki zai is a piece of evidence na wani binciken da yake.. Wllhi mata yake bi idan ba haka ba babu abinda zai had’asa da ultra.. Kinsan me..?” Safeenah Ta girgiza kai alamun a’a.. Meema ta jinjina kai tace “Kin bincika wacece budurwar tasa ni kuma na miki alk’awarin shirya miki wulak’ancin da zaki mata wanda ko kallon yanda mijinki yake bazata k’ara ba koda kuwa Colleague d’insa ce a wajen aiki..” Safeenah tai saurin d’agowa tana duban Meema, lokaci guda ta shiga jinjina kai tana fad’in “Itace.. Junior colleague d’insu ce a police Academy bani mancewa dik tare sukayi da best friend d’insa Assad.. And yanzu kuma tare suke aiki a CID.. Ta jima tana son Mu’azzam..” Meema ta dara kad’an tace “Ahap wllhi itace take neman rabaki da mijinki..” Safeenah tace “Toh amma ai shi baya sonta, kuma ita d’in ba ajin Mu’azzam bace..” Gajeren tsuka Meema tai tace “Wllhi idan kikayi magana Sai naga kaman Bakida experience na rayuwa.. Shi namiji ina ruwansa indai zai samu abinda yake nema.. Wllhi Ko kaffara bazanyi ba itace tinda kullum suna tare wajen aiki..” Safeenah ta jinjina kai tana huci “Wllhi sai na mata mugun wulak’anci.. Sai nasa ta soma jin kunyar kanta a ofishin nasu.. Sai naci mutuncinta a bainar jama’a..!” Ta k’arashe tana sakin huci.. Meema ta murmusa tace “Good. Now you’re talking like my real sister.. Ni ko a sch ban tab’a losing battle ba.” Safeenah tace “Mai zan mata Meema ta fita daga rayuwar mijina..?” Meema ta matso kad’an tace “Kawo kunnenki kiji.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *08* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Umma tana kallo Abba ya ida shirya yaransa Ashiru da Habib, tambayan duniya ta masa ya sanar da ita yanda zai kaisu yak’i kulata, ko kallon arziki ma bata ishesa ba balle ya amsata.. Har saida suka gama shiryawasu tsaf kafin yace suje waje su jirasa. Yaran sukai kaman yanda mahaifinsu yace.. Abba yai gyaran murya yana duban Umma “Uwani.” Ta d’ago a raunane tana dubansa. Lokaci guda yaci gaba da furta “Bazan bar yarana suna ganin tashin hankalin da kuka janyo ma kanku Keda d’iyarki ba, a shekarun Ashiru da Habibu sunyi k’anana su dinga ganin ana sintiri cikin gidan nan ana Fad’a da mahaifiyarsu ana fad’in sai ta biya kud’ad’en data amsa, sannan bazan bar yarana sunaji ana cewa ‘yansanda na sallama da mahaifiyarsu ba.. Tsuntsun da yaja ruwa dama shi ruwa yake duka.. Kuma abinda ka shuka ko shakka babu shi zaka girba. Ashiru da Habib sun gama yini a gidan nan, idan Kinga mun dawo toh dare ne Yayi amma sam bazan barsu su yini a layin nan ana cewa ga abinda mahaifiyarsu da ‘yaruwarsu sukai ba.. Kunje can Keda d’iyarki ku warware abinda kuka sak’a..” Umma cikin rawar murya take furta “Haba Abban Sadiya yanzu ficewa zakayi ka k’yalemu.. Idan ‘yansandan sukace zasu tafi damu fah..? Dan Allah ka tsaya ka zamo mana rumfa ka zamo mana Katanga.” Da tsananin mamaki yake dubanta kafin ya murmusa yace “Wanda Allah ya zama gatansa shikeda cikakken Gata Uwani.. Amma yau naji dad’i da kika yarda duk talaucin miji da rashinsa akan iyalansa shi Katanga ne kuma rumfa ne..? Ashe yau kin amince ki tabbatar da hakan Uwani.. Na gode ma Allah da ya nuna mun wannan rana da kika furta hakan da bakinki kafin na bar duniya.. Ko kin mance abubuwan da kike fad’a mun a baya, cewa ni ban isa ba a gidan nan.. Idan inaso na zamto isasshe a gidana na maku abinda ranku ke so. Toh Alhamdulillah ban maku abinda ran naku ke so ba amma ku kunyi da kanku dan haka a wannan fanninma na kasa Uwani, saidai ku kuyi da kanku.. Ubangiji ya fiddaku..” Yana ida fad’in haka yasa kai zai fice.. Sadiya dake mak’ale bayan k’ofa tana sauraren tattaunawan iyayen nata wane irin kuka ne taji na taso mata, tai saurin fitowa daga mab’oyarta ta nufi Mahaifinta.. Durk’usawa tai ta kamo k’afarsa tana kuka tana fad’in “Abba dan Allah ka yafe mun.. Abba nayi imani hakkinka da rainikon da muka maka nida Umma shike bibiyanmu.. Dan Allah ka yafe mana Abba, kar kayi fushi damu ka yafe mana.. Wllhi na tuba Abba bazan sake ba..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana mai rungume k’afar mahaifin nata... K’uri yai mata kaman zai magana, sai kuma ya duk’a ya zame hannayenta daga rik’on da tai masa, lokaci guda yasa kai ya fice daga gidan.. Sady ta d’aura hannu aka tana kuka da duka zuciyarta tana fad’in ta shiga uku.. Ficewan Abba da kaman wasu mintoci wani yaro ya shigo ya sanar dasu ‘yansanda suna sallama a waje.. Sady ta kuma fashewa da sabon kuka tana fad’in “Shikenan Umma k’ila kud’ad’en da Sagir yayita bamu na shan jini ne.. K’ila ma kud’in kan mutane yayita bamu bamu sani ba Umma.. Na shiga uku ni Sadiya ina zan saka kaina..” Umma ta girgiza kai tace “Aikin gama ya riga ya gama Sadiya, shige muje mu sami ‘yansandan dan ko bamu fita ba zasu shigo su samemu..” A b’angaren Sadiya Ita bama fitan bane, ganin wannan D’ansandan ne bata sonyi wanda kallonsa kad’ai ba komai yake haifar mata ba face tsananin fad’uwan gaba.. Addu’a take Allah yasa kar tayi tozali dashi.. Aiko tayi sa’a domin kuwa yau d’in babu wancan D’ansanda Sai d’aya abokin aikin nasa da sukazo tare jiya saiko wata mace wacce itama tayi shiga cikin bak’ak’en kaya.. Shi wannan Officer d’in kam nada kirki ba kaman abokin aikinsa da sukazo jiya ba, haka Sadiya tace cikin zuciyarta dan ko yanzu ma a natse yake masu tambayoyi shida abokiyar aikin tasa.. Tambayar k’arshe ne da yayi masu yasa Sadiya da Umma duban juna.. Assad yana hankalce dasu, d’an gyaran murya yai kafin yace “Zaki iya gane mutumin da ya turo a matsayin Uncle d’in nasa..?” Umma Ta girgiza kai tace “Gaskiya nikam bazan ganesa ba, dan sau d’aya na gansa kuma da Mahaifin ita Sadiyar sukai magana..” Maleeka ta d’an matso kad’an tace “Bazaki iya suffanta mana yanda kamanninsa yake ba..? Kiyi dogon tinani da nazari..” Girgiza kai Umma ta kumayi alamun a’a.. Sadiya dake gefe ta bud’e baki tace “Officer idan kuka sami wannan mutumin zaku k’yalemu..?” Assad ya dubeta kad’an yace “Kinga mutumin ne..?” Jinjina masa kai tai kad’an tana furta “ Eh na gansa kuma zan iya ganesa.. A tsakar gidan nan sukai magana da Abba ni kuma ina lab’e kitchen ina hangensu.. Zan iya gane kamanninsa...” Jinjina kai Assad yai yana mai zira hannayensa cikin aljihu “Da kyau, yanzu zaki bimu can ofishinmu dake headquarters, akwai masu ilimin zana kamanni cikin bayanan da aka masu wanda su aikinsu kenan.. Zamuje ofishinmu tareda ke zaki masu bayanin kamannin wannan mutumin su kuma zasuyi sketching d’insa..” Sadiya jin ance zaa tafi da ita police station ya sanyata zaro idanu waje tana duban mahaifiyarta “Umma Wai tafiya dani zasuyi..?” Maleeka da kanta ke kife tana rubutu cikin wata ‘yar k’amar littafi mai yanayi da jotter d’agowa tai Ta dubi Sadiya tace “Kar ki d’aga hankalinki ba tsareki za’ayi a can ba, wasu tambayoyi kawai zaki amsa mana sai kiyi bayanin wannan mutumin..” Assad ya murmusa kad’an ganin yanda tsoro ya cika Sadiyar yace “Ki daina tsoronmu.. Police are your friends kinji koh.. Had’in kanki kawai muke buk’ata domin mu cire gurb’atattu cikin al’umma..” A hankali Sadiya Ta jinjina kai har lokacin tsoro bai bar saman fuskarta ba.. Umma Ta matso da sauri tace “Rankaidad’e dan Allah zan iya raka d’iyata.. Dan Allah ku taimakeni ku barni na tafi tareda d’iyata..” Shiru Assad yai yana dubanta kafin ya jinina Kai a hankali yana mai nuna masu yanda motar take pake.. Gaba d’aya suka d’unguma suka tafi police headquarters.. Zuciyar Sadiya sai tsinkewa take, ta d’aga idanu tana duban dogon ginin.. Oh yau kuma Ita Sadiya ce a ofishin ‘yansanda, abinda takeji take kuma ganina finafinai sai gashi yau yana faruwa da ita.. Tabbas a rayuwa kar kayi ma k’addaran wani dariya domin bakasan da mai gobe zata Zo maka ba.. Tana ganin yanda mutane ke shige da fice. Assad na gaba yana masu jagora yayinda Maleeka ke take masu baya.. Sady dai sai rabe raben idanu take tana kallon kanta a wajen da bata tab’a tsammanin zatazo ba.. Suna tafe ta hangosa yana tsaye k’ofan wani Office kansa kife yana duba wani file.. D’ago kan da zai suka had’a idanu.. Take taga annurin fuskarsa ya kuma d’aukewa, Ta lura mutumin kaman haushinta yakeji, Ta kula baik’i ya sami wani dalilin da zaisa ya jefata kurkuku ba.. Take ta shiga b’oyewa bayan Maleeka tana k’ok’arin b’oye fuskarta tana lek’ensa.. Tana ganin Assad ya isa garesa yana nuna masa wani k’aramin d’aki mai kaman office.. A tare suka shige Assad d’in nayima Maleeka alama da hannu kan su k’araso.. Office ne madaidaici mai d’aukeda table guda biyu, d’aya table d’in wani mutum ne zaune da computer gabansa wanda take tinanin shima d’ansandan ne.. Sai d’aya table d’in kuma wani mutum ne zaune da takardu gabansa da k’aramar cup wanda pens ne da dangin abin rubutu ciki. Umma bata shigo office d’inba saiko Sadiyar. Addu’a take Allah Sa kar wannan mutumin ya shigo.. Aiko bata ida addu’an ba Ta gansa ya shigo yana amsa waya.. Assad yai mata nuni da wani kujera yace ta zauna.. Babu musu ta k’arasa ta zauna. Mutumin dake gaban computer shike tattara bayanan da Sadiya keyi cikin computer d’in yayinda d’aya Mutumin dake zaune gaban table d ya shiga shirya takardunsa alamun yana jira ta suffanta masu kamannin Kawun Sagir.. Assad yai mata umarni data fara bayani.. Yanda take masu bayanin a tsorace yasa mutumin bai fahimci komai ba, tana kuma d’agowa idan ta dubi Mu’azzam sai ta kuma daburcewa ta rasa bayanin da take.. Assad ya lura da hakan, ya d’ago yana duban Mu’azzam ya kuma dubi Sadiya dake satan kallonsa. D’an sosa kunnensa kad’an Assad yai kafin ya dubeta yace “Are you alright..?” Girgiza masa kai tai alamun a’a.. “What’s the matter then.?” Ya tambaya yana dubanta. Satan kallon Mu’azzam da ta kumayi yasa Assad murmusawa kad’an kafin ya k’arasa yanda Mu’azzam yake ya d’an janyo Mu’azzam d’in da har lokacin waya yake yana tsaye jikin window.. Cikin dabara Assad ya fiddashi daga cikin office kafin suka samu full attention d’in Sadiya.. Ai kuwa suna fidda Mu’azzam daga office d’in suka samu full attention d’in Sadiya, tai masu bayanin kamannin Kawun Sagir tiryan tiryan.. Mai zana hoto ya zano kamannin data fad’i.. A daidai lokacin Mu’azzam da ya ida wayan da yake ya turo k’ofa ya shigo.. Bai wata wata ba ya isa table d’in yana duba zanen wanda ba fuskan kowa bane ya bayyana face Danger.. Wani irin huci kurum Mu’azzam yake yana dunk’ule hannunsa, lokaci guda ya bugi table d’in yana furta “I knew it.!” Lokaci guda ya fuzgi takardan ya fice daga office d’in cikin tsananin b’acin rai sai sakin huci yake kaman zai kifa k’asa... Cikin sauri Assad yabi bayansa dan yasan komai ka iya tsakanin Mu’azzam da Chief Inspector. Hankali tashe Assad ke k’ok’arin taresa ko kula Assad baiba har saida ya daki k’ofan Office d’in Chief.. Chief na cikin waya yana kwance cikin kujerarsa mai juyawa sai ganin Mu’azzam yai akansa yana sakin huci kaman wani mayuwancin zaki.. Babu shiri Chief ya katse wayar da yake yana duban Mu’azzam da tsananin mamaki “How dare you barge into my office.. Who do you think you are..!” Cikin tsananin b’acin rai Chief yake maganar yana duban Mu’azzam dake tsaye gabansa idanunsa babu alamun tsoro.. Lokaci guda Mu’azzam ya d’ago Sketch d’in yana nunama Chief “Do you still have any reason to depend this criminal..?!” Ko ba’a fad’a maka ba tsoro ya bayyana a fuskar Chief Inspector amma Sai ya dake yace “Kai k’aramin maras kunya. Kasan da wanda kake magana.. Naga irinka dubu kuma na gama dasu..” Baikai aya ba Mu’azzam ya katsesa da fad’in “Bakaga irina ba kuma kafin kaga irina sai na tabbatar na gama dakai..” Wannan karon murmushi Chief yai yace “Mind your language boy.. Bakada hujjan cewa na kare mai laifi domin kuwa dani da kai bamu San wanene Danger bamusan he’s connected to crime d’in nan ba sai yanzu...” Ya murmusa kad’an kafin yace “Har yanzu kaid’in yaro ne a gidan nan.. Har yanzu bakasan yanda Al’amara ke gudana a gida irin wannan ba.. You’re lucky, you’re from well known and respective family, I should’ve thrown you out cikin k’ask’anci . Now, get out of my office befor you lose everything .. Including your career as a police officer..!” Ya k’arashe muguwar murmushin saman fuskarsa.. Daidai lokacin Assad ya shigo a rud’e yana neman afuwan Chief on behalf of friend’s behavior.. Mu’azzam kaw har lokacin huci kurum yake yana duban Chief Inspector da idanunsa da tuni sun gama rinewa.. Chief ya dubi Assad d’in yace “Take him out.. Fitar dashi daga nan..!” “Don’t touch me.. Don’t you dare touch me..!” Mu’azzam yai kashedi ma Assad kafin ya dubi Chief yace “Wata rana zamu had’u..! Alk’awari ne..!” Daga haka juyawa yai ya fice zuciyarsa na masa tsananin k’una.. Assad zai magana Mu’azzam ya d’aga masa hannu alamun dakatarwa “Not now Assad.!” Fuzar da fuci kurum Assad yai kafin yabi bayan Mu’azzam d’in... Su duka hud’in suna tsartsaye sunyi carko carko.. Suna kuma duban hoton Danger da ya bayyana cikin sketch d’in.. Assad ya nusa yace “What do we do now.. Danger must be in a hide tinda yasan dole za’a nemesa... Bazai tab’a zama nan kusa ba.. Allah Sa ma bai gudu ya bar gari ba..” Yusuf yace “Ba Lallai Danger yasan ana nemansa ba, so ba lallai ace tsakanin jiya zuwa yau ya gudu ba..” Muryar Mu’azzam suka sinkayo yana fad’in “We will track him down before yayi making move.. I know by now informer d’insa ya sanar dashi muna nemansa..!” Gaba d’aya suka jinjina kai.. “Zamu fita yanzun nan zamuje unguwarsu Danger, but zamu fita ne a shirye dan nasan wannan area d’in territory d’insa ne komai ka iya faruwa..” Suka jinjina kai suna amsawa.. Tuni ko Wannen su ya soma shirya weapon d’insa.. Maleeka ta d’an saci kallonsu yayinda suke ci gaba da tattaunawar yanda zasu tunk’ari al’amarin.. A hankali ta silale ta fice daga Ofishin gaba d’aya sai sauri take waya manne kunnenta tana faman waige waige.. A haka take gangarowa har ta d’anyi k’asa kad’an daga Building d’in nasu still tana ‘yan waige waige tana amsa waya.. Safeenah da k’arasowar motarsu wajen kenan Ta hangi Maleeka tsaye waya mak’ale kunnenta... Wani irin wawan birki ta taka saida Meema dake zaune kujerar mai zaman banza ta saki ihu. Hakan yayi daidai da k’aran da Umman Sadiya Ta saki wacce tayar Mota guda tabi mata kan k’afarta dan dama tin fitowarsu suke tsaye wajen suna neman abin hawa.. Umma ta sunkuya tana kame k’afarta dake mata zogi Sadiya na mata sannu.. D’agowa Sadiya tai tana jiran tagafitowar maras mutuncin matuk’in motar nan da yabi mata kan k’afar mahaifiya.. Wasu ‘yanmata ne ‘yangayun gaske guda biyu ta gansu Sun fito.. D’ayar fad’i take “Meema ki bud’e backseat ki d’auko.. Kiyi sauri mu k’arasa muci uwarta wllhi itace.. Bazan tab’a mance munin fuskarta ba..!” Safeenah Batakai aya ba taji an rik’ota, ta juyo da mamaki tana duban wacce ta rik’eta.. Saida gabanta yayi wani irin fad’uwa da ganin kyakkyawar yarinyar data rik’ota tana sakin huci.. “Baiwar Allah baki gani ne kika bige min mahaifiya..?” Sadiya tace tana duban Safeenar.. Wani irin wualak’antaccen kallo Safeenah da Meema suka raka Su Sadiya dashi kafin Meema tace “An bige ku d’in, ku makafi ne zaku tsaya bakin kwalta.. Ko kuma kurame ne ku da bazakuji sautin mota na zuwa ba..!” Safeenah Ta finciki hannunta tana fad’in “Ke kika tsaya biyesu Meema, Ai shi Talaka dik yanda yaga mai kud’I hassada dashi yake.. K’iris yake jira ya hau d’aura masa laifi.. Muje kafin wancan shegiyar Ta tsere mana..” Suka nufi d’aya length d’in cikin sauri yanda Maleeka take.. Sady tai kaman zatabi bayansu Umma ta rik’ota tana fad’in “K’yalesu Sadiya muji da rikicin dake kanmu bana fata mu kuma shiga wani fitinan..” Sady tace “Amma Umma baki ganin abinda suka mana.” Umma ta katseta da fad’in “K’yalesu Sadiya, ni mu samu mu bar wajen nan ma..” Ta k’arashe tana mai jan k’afar nata da k’yar Sadiya na mata sannu.. Maleeka tana tsaye taji an fincikota an fuzge wayar hannunta anyi jifa dashi had’ida kwasheta da wane irin mari mai walk’iya... SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *09* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Dafe da k’unci Maleeka ke dubansu da tsananin mamaki “Lafiya su waye ku..?” Cikin azama Meema ta b’arke Babban roll d’in sanitary pad dake rik’e hannunta, kan kace mai sun shiga jifan fuskar Maleeka dashi. Maleeka ta duk’a tana kare fuskarta da hannuwanta tana kuma tambayarsu su waye su mai ta masu.. Meema ta kuma jefa mata a fuska tana fad’in “Kinji Munafuka Adda Feenah tambaya ma take su waye mu.. Toh uwarki ne mu, ‘yar iska kawartuwa mai bin mazan mutane.” Safeenah ta cab’i zancen da fad’in “Gashi nan kece matsiyaciya mai jiran namiji ya mata hidima, ki tattara duka.. Idan shi guda d’aya Yayi niyyan baki toh ga roll an baki.. Matsiyaciyar banza sauran kwalta..” A hankali Meema ta soma jada baya sakamakon hango su Mu’azzam da tai sun fito daga building d’in.. Meema ta aune a guje ta nufi mota, tana bud’e marfin motar ta shige backseat.. Yanda ake aje k’afafu a wajen ta kwanta tai flat yanda babu mai iya hangota.. Safeenah kaw ta yanda take shiga bata nan take fita ba Sai jifan Maleeka take da sanitary pads tana kwashe mata albarka.. Mutane dake shigewa jefi jefi sai kallonsu suke da tsananin mamaki.. Assad ne ya soma hangosu.. Babu shiri ya tab’a Mu’azzam yace “Ai gacen Officer Maleeka.. But wait what’s going on..? Itada wacece..?” Daidai lokacin Mu’azzam ya juyo, Assad na furta “Kaman Safeenah ce fah.. Mai take a nan..?” Cikin sassarfa suka nufo yanda su Safeenah suke.. Da tsananin mamaki kurum Mu’azzam ke dubanta, bai zaici Safeenah zatayi abu makamancin haka ba.. “Safeenah.!!” Ya kirawo sunanta cikin tsananin b’acin rai Cak ta tsaya ta dena abinda take.. Mu’azzam ya tsareta da idanunsa da suka kuma rikid’ewa zuwa ja, dama ransa a b’ace yake dan har ya kamo Danger Chief yasa ya sake shi gashi yanzu ya tabbata Danger nada alak’a da crime d’in da yake bincike.. Kallon wajen yake da mamaki, Wato abinda Safeenah ta gani cikin aljihunsa shine ta biyo Maleeka har Office taci mutuncinta dashi, watau a haukan Safeenah Maleeka budurwarsa ce.. Muryar Maleeka ne cikin kuka ya katse masa tinanin nasa “Sir, wllhi ni bansan mai na mata ba.. I don’t even know her, kawai gani nayi Ta soma attacking d’ina..” Assad ne ya tari Maleeka da fad’in “Kiyi hak’uri Maleeka let’s talk somewhere else.. Kiyi hak’uri please..” Maleeka ta d’ago tana duban Mu’azzam dake ci gaba da tururi ga Safeenah tsaye gabansa sai faman huci itama take tana ture turen baki.. Assad ya tasa Maleeka gaba yana fad’in suje.. Bataso tafiyan ba taso taga yanda Mu’azzam zasu kwashe da matarsa.. Ta kula matar Mu’azzam ce wannan wacce akayi aurensu sati biyu da suka shige, dama an fad’a mata cuna masa ita kawai akayi Mu’azzam ba sonta yake ba, Lallai yau ta tabbatar da hakan. Wani irin sanyi mai gauraye da annashuwa ne suka gauraye Zuciyarta.. Watau matar Mu’azzam tana tinanin Ita d’in budurwarsa ce, aiko bazata tab’a losing hope akan Mu’azzam ba tinda har ta zamto babban threat ga matarsa irin haka.. Da wannan rashin hankalin matar tasa tsaf zata iya samun gurbi a zuciyar Mu’azzam.. Ta saki murmushi mai sanyi tana biyeda Assad.. Wane irin duba kurum Mu’azzam ke aika mata, kallo guda zaka masa ka fahimci zuciyarsa a tsananin b’ace take, daga wannan sai wannan “Are you out of your mind..? Have you lost it..?! Kin kuwa San mai kikazo kika aikata a nan Safeenah.. Kinsan inane nan wajen kuwa.. Kinsan wa kikayi attacking da haukarki..?!” Da tsananin mamaki Feenah ke dubansa wai tasan wa tayi attacking Wato ta wancan shegiyar yake bama ta ita ba.. Watau budurwarsa yake defending.. Ita kuma tayi laifi since she attacked his girlfriend.. Cikin muryar kuka take furta “Yes. Yes na San abinda na aikata.. kuma nasan wacce nayi attacking she’s nothing but your mistress wacce kake cin amanan aurenmu da Ita, kak’i na tare a GIDANA dik sabida Ita...” “Feeeenahh..!” Ya daka mata wane irin tsawa had’ida d’ago hannunsa kaman zai kwad’a mata mari.. A hankali kuma ya sauk’e hannunsa nasa ba tareda ya mareta ba, yaci gaba da dubanta zuciyarsa ba masa zogi.. Cikin kuka Safeenah ke fad’in “Go ahead and hit me, nasan baka mance a k’ofar ofishinku muke ba.. Hakan zai zama hujjan cewa kaid’in maci amana ne kana cin amanata da wancan ‘yariskar so called Colleague d’in taka...!” A hankali yake jinjina kai still yana dubanta da rinannun idanunsa “Wannan shine hujjarki na zuwa har wajen aiki na kici mutunci na.. Fine, Yayi kyau Safeenah.. Zan tabbatar kin biya duk abubuwan da kika aikata.. You’ll pay dearly Safeenah.. Daga rana mai kaman ta yau kin gama rashin kunya, Idan kuma ba haka ba sunana ba Mu’azzam Abubakar Gamji ba...!” Ya k’arashe yana sakin murmushin nasa da gefen baki wanda tasan idan yayi wani sharrin nasu na ‘yansanda zai k’ulla a cewar Safeenah.. Tai raurau da idanu tana dubansa yanda ya tsime kaman ba shine ya saki muguwar murmushin nan ba.. “Shige muje..!” Ya fad’i yana nuna mata hanya. Jiki a matuk’ar sanyaye Safeenah tabi bayansa tana goge hawayen dake kwance idanunta.. Front seat ya bud’e yace ta shige, babu musu ta shige kafin ya zaga mazaunin mai driver ya shige.. Dik wannan drama Safeenah tama mance tareda Meema suke.. Ita kaw Meema tana jin shigowarsu Ta kuma mak’alewa k’asan Seat tana addu’an Allah ya ceceta yasa kar Ya Mu’azzam ya ganta.. Ita batasan Addah Safeenah wace irin sokuwa bace da har zata bari Ya Mu’azzam ya kamata gashi yanzu shi zai driving d’insu home, ai kuwa wllhi saidai ta kwanta k’asar motar har su isa gida a haka.. A rashin hankalin Meema Mu’azzam bai ganta kwance k’asar motar bane, saidai Ta kula kaman da gangan ya dinga tsalle saman speed bumps da motar.. Idan Meema taji zafi saidai ta toshe bakinta kar tayi ihu ya jita ya gane tana motar.. Haka ya dinga gwarata saman kwalta tana matse bakinta dan azaba.. Ga tsananin mamakin Safeena gidansa da akai mata jere ya kaisu.. Ta d’ago tana dubansa da Mamaki... “Mai Zamuyi a nan..?” “Isn’t it obvious. Gidanki na kawoki.. Ki zauna har lokacin da gidan zai gundureki..”Ya bata amsa kai tsaye yana mai ficewa daga cikin motar.. Meema dai taji anyi parking batasan Ina akazo ba har saida taji Muryan Mu’azzam yana Fad’iwa Safeenah gidanta ya kawota.. Safeenah kaw tab’e baki tai kad’an zuciyarta na mata sanyi, tana ganin ya bud’e motar ya fice Ta soma furta “Weldon Feenah.. Kinyi daidai..Ko banza kwalliya Ta biya kud’in Sabulu gashi da kanka baka jira wani ya kawo maka ni ba ka kawoni da kanka..” Ta saki Murmushi tana k’ok’arin bud’e motar taji wani irin haushin police dogs irin manya manyan nan masu kaman kuraye.. Wani irin k’ara Safeenah ta saki ta jawo marfin motar babu shiri.. Ihun da Safeenah ta saki ya sanya Meema mik’ewa zaune cikin motar tana kallon yanda suke... Itakam Safeenah har Ta mance Wai tare suke da Meema saida Meemar ta taso daga mab’oyarta.. Meema ta soma salati tana fad’in “Mun shiga uku mun mutu mun lalace.. Addah Feenah Police Dogs d’insa ya kwance mana ya barmu rufe cikin Mota yayi tafiyarsa..” Idan karnukan sukai haushi sai Safeenah da Meema sun manne waje d’aya dan tsoro suna sakin ihu.. Wane irin haushi mai diri da ban tsoro suke..Gashi babu hali Su bud’e glass d’in motar Karnukan zasuyi tsalle su shigo motar, gashi Mu’azzam ya kashe motar ya cire key balle su kunna motar ko AC ne Su kunna.. Ga zafin cikin Mota ga Karnuka waje sai haushi suke jikin motar suna zagaye motar.. K’iris ya rage Meema bata saki fitsari ba ganin Mu’azzam ya fice daga cikin gidan ya kullesu ya barsu rufe cikin Mota police dogs na kewayesu suna shawagi a jikin motar.. Meema ta saki ihu tana fad’in “Adda Feenah wllhi ficewa zaiyi dan Allah ki kirasa ya dawo ya cecemu ya fitar damu.. Wllhi suffocating zamuyi cikin motar nan idan ya tafi ya barmu.. Dan Allah ki tsaidashi.. Na shiga uku ni Meema Wllhi ni tsautsayi ne dama ya sani biyoki.. Mun shiga uku wllhi horo zai mana irin tasu Ta ‘yansanda mu ba criminals ba.. Adda Feenah dan Allah ki ceceni a fiddani daga gidan nan dama ke gidanki ne..” Cikin kuka Feenah tace “Ke ni Kimin shiru duk na kece kika kawo shawarin ba.. Wayyo na shiga ukku..” Ta sake sakin k’ara a daidai lokacin da karnukan suke kuma haushi.. Shi kaw Mu’azzam Ko ajikinsa yana ficewa ya tari cab ya nufi location d’in da abokan aikinsa ke jiransa.. ** A b’angaren su Sadiya saida suka biya wani chemist aka duba k’afar Umma aka d’aure mata cikin bandage kafin suka nufi Gida.. Saidai suna dosowa layinsu gabansu yayi wani irin yankewa ya fad’i.. Cincirondon mutane suka hango, hakan ya sanyasu d’an k’ara sauri dikda cewa Umma d’ingishi take Sadiyar ce mai taimaka mata.. Gabansu bai ida yankewa ba saida suka hango mutanen tare suke k’ofar gidansu, ga mutum kwance cikin jini Habeeb da Ashiru sun kifa Kai saman k’irjin mutumin suna kuka.. Take Sadiya taji duniyar na juya mata, Ta rasa tafiya take kan k’afafunta kokuwa a iska take, zuciyarta yaci gaba da tsinkewa suna mai kuma tunk’aran dandatson mutanen.. Duniyar Sadiya bata ida juyewa ba saida ta sinkayo muryar Ashiru yana jijjiga mutumin yana fad’in “Abba..! Abba dan Allah ka tashi.. Abba ka tashi dan Allah.. Abba naaa..!!” “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un” Shine kalman da Umma ta iya furtawa.. Sadiya kuwa hannu biyu Ta saka aka had’ida sakin wani irin k’ara tana mai silalewa wajen.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *10* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* FUFORE _Adamawa State, Nigeria_ Ta kasance ranace na cin kasuwar garin, mutane daga ko wacce lungu da sak’o sai tururuwan zuwa kasuwar suke domin saye da sayawarwan hajojinsu. Mutane da rugagen da suke kusa dasu sukan shigo garin domin cin Kasuwa.. Wata kyakkyawar budurwa ce zaune k’asar Rumfar azara wacce bazata gaza shekaru 18 ba, ga tulin k’ulli k’ullin magunguna gabanta. tana karkad’a karan barankaci tana fad’i cikin wak’e irin yanda masu saida magani suke “Azo a sayi magani.. Sai an gwada ake sanin na k’warai. Magani ko wacce iri ce zaka samu wajenmu.. Azo a sayi maganin AJIDDE d’iyar Kyallu mai warka warka.. Ina saurayi mai shirin yin wasan shad’i Ina budurwa mai neman Farin jini.. Ina me neman lak’anin kariya daga mugun baki ko maita, toh ga Ajidde ta taho maku da warka warka...Azo a gwada maganin Ajidde d’iyar Kyallu mai Warka warka.. Dik garin nan babu wanda baisan amincin maganinmu ba.. Azo a gwada..!” Cikin harshen fillanci take tallan magungunan nata.. Kan kace mai an wawushe magungunanta.. Ajidde ta Washe baki tana k’irga cinikin da tai, ta kuma turo kallabinta gaba tana kuma k’irga kud’ad’en “Wo ni Ajidde wllhi Inna Kyallu yau dole ki saka mun albarka.. Kai jama’a watau dai idan kana so kayi kud’i nan take ka zamo macuci..” Ta shek’e da dariya tana tura kud’d’en cikin lalitarta “Ahab wawayen banza ku kuka sani idan maganin bai maku aiki ba.. Heheheh wllhi nidai babu ruwana Inna Kyallu ce ta d’auran talla..” Tana ida fad’in haka ta mik’e daga Rumfar tata ta nufi gida tin kafin Kasuwa ta watse sabida ta gama saida kayyayakinta.. Tana isowa gida ta hangi d’akinda Kyallu take duba majinyata wata mata mai tsohon ciki Ta fito.. Kyallu na biyeda ita cikin shigarta ta bak’ar riga.. Wannan kakkauran bak’ar riga itace rigar Kyallu duk zafi duk sanyi. Ga uban daud’a da rigar tayi.. Ita kanta Kyallun idan ka dubeta sai ta baka k’yama sabida tsaban datti da daud’anta.. Hannayen mata mai cikin rik’eda guraye da layu Kyallu naci gaba da fad’in “Ki tabbata ki d’aura gurun nan dan shine maganin mugun baki harma da mayu.. Shi zai baki kariya Keda abin da ke cikinki daga duk mai nemanki da sharri bama kishiyoyinki da suka saka ido kan abin dake cikinki ba, zai baku kariya daga sharrin mugu... Shi kuma layan da zaran kin haihu a d’aura ma jaririn a wuyarsa shi zai zame masa kariya..” Matar cikeda jin dad’I had’ida amincewa da abunda Kyallu ta fad’I mata take jinjina kai tana ma Kyallu godiya cikin tab’ewa da dulmuyewar basira. Matar sukai sallama da Kyallu kafin Ajidde ta k’arasa wajen Kyallu. “Inna Kyallu albishirinki.. Yau dai kaf na saida komai dole ki saka min albarka..” Dariya mai sauti Kyallu tai da muryarta mai gwab’in gaske kana tace “Ai babu albarka tattareda ke Ajidde.. Ki daina mafarkin samun albarka daga wajena.. K’irgo kud’ad’ena ki mik’o mun..” Jikin Ajidde ya d’anyi sanyi.. lokaci guda ta shiga fiddo kud’ad’en tana mik’a ma Kyallu.. Kyallu ta k’irgaga kud’ad’enta ta soke a hamnatarta. “Yauwa kina jina..?” Ajidde ta gyad’a kai a hankali Kyallu taci gaba da fad’in “Gobe zakije Gidan Gonar nan dake wajen gari ki kai maganin matar nan..” Nan fah Ajidde Ta soma Washe baki dan sau d’aya kawai da sukaje gidan gonar nan taji tana son wajen.. Ga shukoki koraye gwanin ban sha’awa ga kuma dabbobi masu yawan gaske kama daga shanunmu na gida har zuwa irin na turawan nan iyaka ganinka dan yawansu.. Kai gaskiya a cikin noma da kiwo akwai albarka mai tarin yawa.. Tuni Ajidde Ta soma murna ta mance fushin da take na rashin saka mata albarka da Kyallu batayi. ** ABUJA Kaman yanda sukai tsammani basu tadda Danger ba, majalisar k’ofar shagonsa ma babu kowa babu komai kaman anyi shara.. Shiru Mu’azzam yai yana nazari sanda suka keb’e su biyu shida Assad. “I told you so.. Mutumin nan must be in hiding, an sanar dashi muna nemansa.. Idan bai fice a gari ba Toh kuwa shakka babu yana b’oye wani wajen. Idan ba Chief Jaja bane ya sanar dashi waye zai sanar dashi.. Who could be his informer Assad.?!” Ya k’arashe yana sakin huci a hankali. Assad ya nusa yace “Ba Lallai ya zama Chief Jaja ba, sabida Chief ma bai san da hakan ba har saida abin ya kasance.. And it could be anyone from our Department.. Kasan yanda Al’amara suke a wajenmu..” D’an jim Mu’azzam yayi kafin ya girgiza kai yace “No way.. Binciken nan is classified, there’s no how wani daga department d’inmu zai zama snitch... The only Rat here is Chief Jaja.. And don’t forget a aiki irin namu wanda ya d’auraka kan bincike zai iya maka zagon k’asa domin ya b’afar da basirarka..” Girgiza kai Assad yai yace “I don’t think Chief Jaja zai aikata wani abu mai kama da haka sabida idan baka mance ba kafin Chief yasan da labarin anyi sketching fuskar Danger a matsayin Uncle d’in Sagir saida ka nufi Office d’insa ka sanar dashi.. Da ace yau ne Danger yasan da labarin an zana fuskarsa a matsayin Uncle d’in Sagir da mun samu wani trace ko alamun cewa yau ne ya gudu.. At least da mun samu mutane a majalisar.. Amma bamu samu trace ko wani alama na hakan ba.. It’s possible Danger yana cikin shirinsa tintini.. Ba Lallai ya kasance yanada agent a CID ba..” K’urama waje guda idanu Mu’azzam yai yana nazari.. A hankali ya soma girgiza kai “No Assad.. Those people are smart, ‘Yanta’adda k’wararru bazasu bar wani trace ko alama ba.. I’m positive akwai snitch a department d’inmu..” Assad ya d’an nusa kafin yace “Who do you have in mind..?” “Mutum d’aya ne kuma ba kowa bane face Chief Jaja.” Ya fad’i yana duban Assad d’in. “Be careful who you’re up against.. Kabi komai a sannu Mu’azzam har ka gano bakin zaren komai.. Ba komai bane da ya bayyana maka zai zamto gaskiya.. Nasan kasan da hakan..” Assad ya fad’i yana duban abokin nasa.. Fuzar da huci Mu’azzam yayi kafin yace “I trust my team members, you’re my best friend, Yusuf ma amintaccenmu ne.. Sannan Maleeka..” Assad ya ida maganar da fad’in “Maleeka you’re her all time crush.. Muna tare da ita tin a police Academy.. And I guarantee you wannan yarinyar babu abinda take buri face taga Tayi abinda zai burgeka Ta samu karb’uwa wajenka.. She’ll never betray you. Inada guarantee akanta. She loves you so much..” Mu’azzam ya d’an fuzar da fuci kad’an yana duban Yusuf da Maleeka daketa k’ok’arin neman trace na Danger dik yanda ya shiga ya fita.. A hankali yace “We’ve one option idan munaso mu kamo Danger da accomplices d’insa..” Assad ya dubesa yace “Wani option kenan..?” “The girl..” Ya fad’i yana duban Assad kafin yaci gaba da fad’in “Through her muka San cewa Danger nada saka hannu a crime d’in nan.. I believe through her zamu samo yanda Danger yake..” “Kaman yaya.? According to her statement ita kanta da family d’inta basusan waye Danger ba.. Ta yaya zata samo mana yanda yake..?” Assad yace yana duban Mu’azzam d’in. Murmusawa kad’an yayi kafin yace “Kana magana kaman ba ma’aikacin bincike ba.. Ai yanzu na tabbata Danger bazai bar family d’inta ba muddin yasan ansan wani abu akansa.. Nasan dole zai hanasu magana ma ‘yansanda ta ko wacce hanya.. Sannan zai saka masu ido idan yaga jami’an tsaro na zarya wajensu.. Zai making move d’insa.. Mu kuma zamu buga wasan idan yayi losing.. Caraf sai kama wuyarsa..” Assad ya jinjina kai yace alamun gamsuwa sai kuma yace “But don’t you think rayuwar yarinyar da ahalinta zai zamto yana cikin garari..?” Mu’azzam ya jinina Kai yace “Already cikin had’ari suke tinda sukai involving kansu da wannan criminal d’in.. They are in this mess already..” Assad ya d’an nusa kafin Mu’azzam yace su tafi gidansu yarinyar. Assad ne yai alama masu Maleeka da Yusuf yace Su k’araso su tafi.. ** Har lokacin Sadiya kife kanta yake kan gawan mahaifinta da tuni an gama shiryasa cikin suturarsa na gidan gaskiya.. kuka take da duka zuciyarta, cikin kuka take furta “Abba Maiyasa zasu maka haka.? Su waye suka maka haka..? Abba Dan Allah ka tashi.. Kar ka tafi ka barmu.. Abbbaaaa..!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka Tinda suka doso layin ya tsaya yana duban cincirindon mutanen dake tsartsaye k’ofar gidan nasu ana jajanta lamarin.. Wani mutumi da hatsarin ya faru gabansa yaci gaba da bama sauran labari “Ai mai mashin ne ya fara bugesa, kansa na rufe cikin rawani.. Malam Ibrahim tareda yaransa guda biyu yake tafiya sai mai mashin d’in ya bigesa ya cillasa wani gefen.. Yana cillasa gefe guda mai mota yabi kansa.. Wllhi abun abin tashin hankali kaidai..” Mu’azzam kam bai iya sauraron tattaunawarsu ba Yusuf da Assad ne sukai sallama kafin suka ja mutumin gefe suna tambayarsa yai masu bayani dalla dalla yanda had’arin ya kasance.. Shikam Mu’azzam tuni ya kutsa Kai cikin gidan Dan tabbatar ma idanunsa abinda ke faruwa.. Cak ya tsaya yana dubanta yanda ta kifa kanta saman k’irjin mahaifinta tana kuka mai ban tausayi ga mahaifiyarta gefe rungume da k’annenta suma duk kukan suke. Cikin sautin kuka Sady taci gaba da fad’in “Abba Dan Allah ka tashi kace ka yafe mun.. Nasan nayi maka laifuka da dama Abba, Abba dan Allah ka tashi kar ka tafi ka barmu bazamu iya ba.. Maiyasa suka kad’e mun kai Abba na..” Muryarsa ne ya katseta da da fad’in “Because they believe your father knows something shiyasa suka kashe shi Dan kar ya tona masu asiri..!” Cak Ta tsaya da kukan nata sakamako sinkayo muryarsa da Tai... Ta d’ago rinannun idanunta ta sauk’esu tsaf akansa, zuciyarta na mata wani irin zogi take dubansa.. Take tsanansa ya ninku cikin zuciyarta.. Cikin kuka ta mik’e tana furta “This is all your fault.. Ku kuka jawo aka kashe mana Abbanmu.. Maiyasa bazaku k’yalemu ba.. Bamu San mutumin da kuke nema ba, bamu San komai akansa ba.. Mun sanar daku Iyakacin abinda muka sani.. Mahaifina Bai cancanci a kashesa mercilessly irin haka ba... Just leave us alone already.. Ka tafi Dan Allah.. Kuje can ku nemi criminals d’in da kuke nema.. And leave us in peace..!” Ta k’arashe tana mai had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o had’ida zubewa saman gwiwoyinta.. Dubanta kurum yake yana jin zuciyarsa na masa wani irin k’una.. Yana duban yanda hawayenta ke zubowa da sautin kukanta had’ida rok’onsa da takeyi ya tafi ya k’yalesu suji da rashin mahaifinsu da sukai.. A hankali ya soma jada baya still idanunsa akanta.. Cikin sauri Mu’azzam ya juya ya fice daga gidan gaba d’aya yana duban yanda Sadiya ta zube saman gwiwoyinta tana kuka mai tab’a zuciya.. Har ya shige su Assad dake faman tattare bayanai daga wajen mutanen unguwa basu lura dashi ba.. Sautin tashin motarsu kurum sukaji.. Assad ya saki baki yana dubansa.. Maleeka dake faman rubuce rubuce itama baki sake take duban Mu’azzam d’in.. A yanda sukaga ya kwashi motar sunsan komai ka iya faruwa.. Assad ya girgiza kai yana mai furta “Oh no..! Mu’azzam mai kake shirin aikatawa..?” ** Ko parking mai kyau bai ida ba ya nufi ofishin Chief Inspector Jaja... A lobby ya iske Chief tareda wasu abokan aikinsu ‘yansanda suna tatauna wani matsalan.. Mu’azzam duban Chief kurum yake yana kuma sinkayo kukan yarinyar da yanda take fad’in an kashe mata mahaifi ba tareda ya aikata laifin komai ba.. Fuskar yarinyar yake hangowa cikin idanunsa yanda Ta duk’a tana zuban hawaye.. Baiyi wata wata ba yana isowa ya dunk’ule hannunsa yakai ma Chief naushi maiji da lafiya a Hanci wanda saida takai Chief har k’asa.. Ba Chief da yaji sauk’an naushin kaman a mafarki ba harta sauran ‘yansandan saida suka tsaya suna duban Mu’azzam cikin tsananin Shock Dan kaf d’insu babu wanda yaga zuwan Mu’azzam sauk’an naushin kawai suka gani.. Mu’azzam ya cakumo wuyan Chief yana fad’in “Lets end it now.. You better tell me waye kake karewa.. Ka sanar dani Manzo Jaja.. Waye kake karewa.. Do you know how many innocent lives are stake here.. Shin kasan rayuka nawa ka jefa cikin garari da gurb’atacciyan zuciyarka.. Tell me.. Tell me Chief Manzo Jaja..!!” Yanda yake jijjiga Chief dole ya baka tsoro.. Wane irin fincika Chief yai yana tsananin huci yayinda sauran ‘yansandan suka janye Mu’azzam daga jikin Chief.. Huci kurum Chief yake yana nuna Mu’azzam da ‘yar yatsa ga bakinsa dake fidda jini sabida naushin da Mu’azzam d’in yai masa “You’ll pay.. You’ll pay for this..!” Ya k’arashe yana mai shigewa ofishinsa cikin tsananin b’acin rai.. Daidai lokacin su Assad suka k’araso duk a birkice suke.. Yanda Assad ya hango Mu’azzam yasan mai aukuwa ya auku.. Saurin k’arasawa yai wajen abokin nasa dake faman yarfe hannuna wanda ya naushi Chief dashi.. Hannun Mu’azzam d’in kawai Assad ya duba da yanda yake yarfe hannun nasa ya fahimci cewa mai aukuwa ta auku.. Assad ya k’araso yana duban yanayin mutanen dake wajen yanda kowa yasha jinin jikinsa.. Dafa Mu’azzam d’in dake zaune saman kujera ya kifa kansa k’asa yai.. Ko baa ce kasan zuciyarsa ce ke tafarfasa “Can you tell me now.. What really happened here..?” Baikai ga basa amsa ba sukaga ana mik’owa Mu’azzam d’in Doguwar takarda cikin envelop.. Saida ya dubi mai mik’o masa takardan kafin yasa hannu ya amsa takardan ba tareda ya amsa tambayar Assad ba.. Lokaci guda ya shiga warwareta.. A hankali ya lumshe idanunsa Dan yasan za’a rina haka.. Suspending d’insa akayi har na tsawon makonni biyu... Cikin sauri Assad ya amshi takardan yana karantawa.. Dafe kansa kurum Assad yai yana mai fuzar da fuci.. Cikin tsananin b’acin rai Assad ya soma fad’in “You see.. Kaga abinda nake fad’a maka Mu’azzam.. You never listen.. You’re so stubborn Mu’azzam.. Yanzu ga irinta nan kaja an dakatar dakai..” Bai k’arasa sauraron Assad ba ya mik’e yai ficewarsa waje.. Assad ya biyo bayansa yana ci gaba da magana cikin tsananin b’acin rai.. Idan jacket d’in dake jikinsa ya amsa shima zai amsa.. Yanda motarsa ke ajiye ya isa ya shige, har lokacin Assad na masa magana yana k’ok’arin dakatar dashi suje dubawa Chief hak’uri ko rage masa tsawon wa’adin suspension d’in ne ayi amma ko ranka Assad baiba.. Tuni ya shige Mota ya fuzgeta.. Yana driving amma kukan yarinyar da rok’onsa da take su fice masu a rayuwa bai daina Yawo a kwanyarsa da dodon kunnuwarsa ba.. An kashe mata mahaifi dik akan binciken da yake na neman gaskiyar mutuwar ‘yaruwarsa.. A hankali ya lumshe idanunsa yana mai jin motar bayansa na danna masa horn.. Cikin sauri ya ware idanun nasa yana k’ok’arin saita kansa Dan k’iris ya rage baiyi causing accident ba.. Traffic ne ya tsaidasu, a daidai k’ofar wani kanti yake hango k’aton takardan Sanitary pad irin na advert d’in nan.. Lokaci guda ya tuna sanda Ta jefe shi da gidan abin.. Nan yake tina farkon had’uwarsu.. Yayi nisa duniyar tunani yaji ana masa horn motar bayansu alamun traffic light ya basu koren wuta.. Lokaci guda ya soma tafiya cikin tsanaki.. Bai zarce ko Ina ba Sai gidansa.. Saida ya iso gidan ya tina ashe su Safeenah na gidan ya kwance masu karnuka.. Ya ida shigo da motarsa yai parking a gefe Karnukan har sun koma gefe, suna ganinsa suka taso suna shinshina k’afarsa.. Yakai dubansa ga motar Safeenah, a hankali ya janyo chain d’in dake d’aure wuyan karnukan ya maidasu d’akinsu.. Lokaci guda ya isa jikin motar Safeenah.. Ta cikin glass yake dubansu yanda sukai laushi, d’an kad’an suka zube glass d’in ta d’an sama kad’an yanda iska zaike d’an shigo masu kad’an..Safeenah kam kamar ma bacci tai dan azaba, tana tak’ure jikin seat ga bushesshen hawaye kwance saman fuskarta.. Meema ce batai bacci ba amma har lokacin hawaye ne cikin idanunta.. Tana ganinsa ta mik’e wani kukan na zuwa mata.. Saman gwiwoyinta ta duk’a nan kan seat d’in, Ta had’e hannayenta biyu waje guda tana fad’in “Ya Mu’azzam dan Allah kayi hak’uri.. Wllhi na tuba bazan sake ba.. Dan Allah ka k’yaleni na tafi gida na rok’eka...” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da sabon kuka.. Cikin ransa yace ashe k’aryar rashin kunya kike.. A fili kuwa bai furta komai ba.. Kukan Meema ya tada Safeenah.. Tana ganin Mu’azzam ta wani zabura ta mik’e zaune.. Take ta fashe masa da wani irin kuka ba tareda tace komai ba.. Saida tai mai isarta kafin ta tsagaita, cikin rawar murya take fad’in “please take us home..”. Ta fad’i tamkar zata kuma kurma wani ihun.. Basu baya yai kafin ya ciro wayarsa cikin aljihu.. Dialing layin driver d’in gidan yai ya sanar dashi ya shigo Cab yazo ya samesa.. Jim kad’an kuwa driver d’in ya iso da shike gidan nasu babu wani tafiya sosai tsakani.. Car keys d’in motar Safeenah ya mik’a masa bayan ya iso yace ya kaisu gida. Driver d’in ya amsa cikeda girmamawa kafin ya bud’e motar ya shige mazaunin driver. Abin sosai ya sosa ran Safeenah watau bazai kaisu gida ba dikda yanda ya basu azaban nan sukai Laushi saidai ya kirawo driver ya kaisu.. Tana fama da kanta bazata iya tanka masa sannan wani sabon shakkarsa ne ya d’arsu a zuciyarta hakan yasa batace komai ba Sai mutsuke ragowar hawayen idanunta da take.. Ita dai Meema bata damu ko uban waye zai maidasu gida ba. Burinta kawai ta fice daga gidan ta ganta a gidan mahaifinta.. Suna isowa gida kai tsaye upstairs suka haye a jikace dan dama gidan ba kowa daga ma’aikata sai Mommy da Kiki. Su Daddy da Musaddiq da Inne harmada Aunty Nurah sun tafi Fufore a jiya.. Mommy ce kawai ma a gidan Sai ma’aikata dan Kiki tana WAEC Lesson zatayi trial a SS2.. Meema kuma dama jiran admission d’inta take ya fito a UK amma bayan Mommy taji yanda Safeenah ta watse da mazan turawa ta fara shakkun Barin Meema ta fita karatu waje. Ummati Dattijuwa cikin ma’aikatan gidan ne ta had’u dasu zasu haura sama a jigace. Tana tambayansu lafiya suke ko iya amsata basayi Meema kam ma da rarrafe take k’ok’arin shigewa d’aki.. Ummati ta girgiza kai kad’an ta shige sanar da mahaifiyarsu.. Domin kuwa babu lafiya tinda har Meema da Safeenah ne zata masu magana basu darara mata tsawa ba. Koda Mommy ta taddasu Safeenah ke labarta mata duk abinda ya faru.. Tamkar ta rufe Safeenan da duka dan takaici haka Mommy taji.. Ta rasa wace irin wauta ne kan Safeenah.. Wai har Meema ce zata bata shawari ta d’auka. Mommy tai k’wafa tana duban Safeenar cikeda takaici “Ya miki kyau ai.. Ki godema Allah da bai baki takardanki tin a titi kafin ki tare gidansa ba.. Banda shashanci da dolanci irin naki ta yaya zaki bisa har wajen aikinsa kici masa mutunci kici ma abokiyar aikinsa mutunci without any solid evidence..” Cikin kuka Safeenah ta katseta da fad’in “Mommy I’ve proof... Sanitary pad d’in is enough evidence.. And Mommy you should have seen her face sanda nake cin mutuncinta ita karuwar.. Wllhi Ko kaffara bazanyi ba cin amanata yake da Ita...” Dak’uwa Mommy ta dunk’ula mata tana fad’in “Kimin shiru kafin na tashi na tattakaki a wajen nan.. Banda ke shashasha ce sokuwa, idan ma da gaske cin amanar naki yake ta haka ne zaki samu gaskiyan lamarin..? Ta haka ne zaki kare auren naki..? Wannan dolancin da kikayi bashi zai hana ya fasa abinda yake ba idan ma yanayi d’in..Kusanci ma zaki K’ara masa da ita.. Yanzu haka zaije ya lalasheta bayan ya gama cin k’aniyarki.. Kinga wa gari ta waya..” Safeenah tai shiru tana duban mahaifiyarta tana jin zuciyarta na mata k’una. “Mommy yanzu ya zanyi..?” “Ya kuwa zakiyi banda ki k’yaleshi har ya sauk’o kafin ki basa hak’uri kan abinda kikai..” A zabure take duban Mommy “Mommy shi fa ya mun laifi amma kike cewa na basa hak’uri..” Ta shiga bubbuga k’afafu tana turo baki tana kuka take fad’in “Wllhi dama an jima ana nuna wariya gidan nan.. Daga ke har Daddy bakwa tab’a ganin laifin Mu’azzam, dik abinda yayi daidai ne wajenku.. Wllhi Mommy this is not fair..!” Tana maganganun tana kuka ta shige bathroom.. Tsaki Mommy tai cikeda takaicin ‘yar nata.. Ita batasan ba dan komai take so Ta auri Mu’azzam ba sai dan watarana Fortune d’in Mu’azzam d’in wanda Mahaifinsa ya mutu ya bar masu ya dawo hannunsu.. Mahaifin Mu’azzam shike Babba cikin yaran mahaifinsa.. Su Uku ne yaran Jauro Gamji, Abubakar wanda shine Babba kuma shine mahaifin Mu’azzam da marigayiya Ikram, sai Marwan Wanda shine mahaifin Safeenah Musaddiq Maryam(Meema) da kuma Karimatu (Kiki). Sai Salman wanda shine autan Inne kuma shine cikon na ukunsu.. Shi yana zaune ne a can Fufore dan kula da gidan gonar su dake Fufore d’in da kuma Kampaninsu na GAMJI MEAT FACTORY dake Adamawa.. Kaman yanda Daddy ke kula da Kampaninsu na GAMJI DIARY DISTRIBUTION FACTORY dake a birnin tarayya Abuja.. Gidan Gonar da kakansu Jauro Gamji ya mutu ya bar masu shine yake samar da nama da kuma madaran da companies d’insu ke producing.. A halin yanzu Uncle Salman shike kulada Gamji Meat Factory dake Adamawa wanda a baya mahaifin Mu’azzam shike kula dashi. Sannan shi Uncle Salman d’in shi ke kula da Babban gidan gonar nasu dake garin Fufore. A can gidan gonar suke zaune gaba d’aya dan mahaifinsu saida ya k’era gini maiji da lafiya a cikin gidan Gonar wanda tafiya mai d’an nisa zakai kafin ka isa ginin sabida tsaban girman da gidan gonar kedashi bama zakai tunanin a gidan gona kake ba idan ka shige cikin Mansion d’in.. Shuka da shanu suna cen gefe yanda ake kula dasu.. Uncle Salman da iyalansa harma da Inne a nan gidan Gonar suke zaune.. Uncle Salman yanada mata guda d’aya mai suna Shema’u tareda yaransu guda uku duka mata. Babbar zatai tsara da Meema sai sauran k’annenta guda biyu wanda Twins ne... A lokacin da mahaifinsu Mu’azzam ya rasu Uncle Salman yaso a cire kason Su Mu’azzam da k’anwarsa Ikram a basu tinda dole sunada kaso a both companies d’in.. Kason mahaifinsu.. Ya zaman babu sauran kason mahaifinsu cikin dukiyar.. Babu yanda Uncle Salman baiba Daddy yak’i amincewa da hakan.. Yace wannan kasuwanci ta ahalinsu bazai tab’a yuwa a cire kason Su Mu’azzam a basu ba dole za’a ci gaba da juya musu dukiyarsu ba tareda an bari dukiyar ta salwanta ba, idan shi Salman bazai iya kulada dukiyar ‘ya’yan d’anuwansu ba Wato Mu’azzam da Ikram shi Daddy zai kular masu dashi zaici gaba da juya masu har lokacin da zasu buk’ata.. Koda Mu’azzam ya girma Uncle Salman baisan Ina Daddy ke kai kud’ad’en Mu’azzam d’in ba amma yasan duk budget da za’ai sai an cire nasu.. Yasan har wannan lokacin Mu’azzam da ‘yaruwarsa harma da mahaifiyarsu sunada kaso cikin dukiyarsu.. Wannan kenan.. ** A b’angaren Mu’azzam kusan kwana yai yana tinanin Abinda ya samu mahaifin Sadiya. Baisan dalili ba amma tinanin nasa mahaifin ne ya fad’o masa..Mahaifinsa da ya rasa a Meat cold Room wanda ya shiga inspecting freezer d’in tsautsayi da ajali ya ritsa dashi a can Meat Distribution Factory d’insu dake Adamawa.. Mahaifinsa yayi stucking a cikin meat cold room wanda har yayi ahalinsa sai gawarsa aka cire.. Mu’azzam ya lumshe idanunsa a hankali yana tuna irin mutuwar da mahaifinsa yayi, lokaci guda ya tina jarabawa na cuta da mahaifiyarsa ta had’u dashi ya kuma tuna rasa ‘yaruwarsa Ikram da yayi... A hankali ya shafi fuskarsa da tafukan hannayensa biyu.. Babu abinda yake so a halin yanzu kaman ya kasance da mahaifiyarsa.. Sosai yaji yana so ya tafi Fufore. Bazai mance sanda aka ciro gawan mahaifinsa da ya sandare da k’ank’ara ba, kwanciya yai saman gawan mahaifin nasa yana kuka kaman dai yanda Sadiya ta kwanta bisa gawan mahaifin nata itama tana kuka.. Bazai tab’a mance kalaman lallashi da mahaifiyarsa ta fara furta masa ba ‘Kai hak’uri Mu’azzam, Duniya GIDAN ARO ce yanda mukazo cikinta kaman bak’i haka wataran zamu tafi mu barta.. Kayi hak’uri kayima Daddynka addu’a muma duka ma tafiya ne idan lokaci yayi’ A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya kafin ya mik’e ya nufi motarsa.. Wajajen k’arfe shabiyu da rabi na dare ya shigo gidan. Baibi takan kowa ba ya nufi side d’insa ya soma shirya kayansa jirgin Washe gari yake so yabi zuwa Adamawa. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *11* *©️Sameena Aleeyou...* Tin farar safiya Safeenah ke kitchen, duk abinda tasan Mu’azzam naso shi take instructing ma’aikatan kitchen d’in su girka.. Su kansu sunyi mamakin ganin Safeenah a kitchen dan kitchen ba wajen zuwanta bane.. Ko mi Suka dafa sai ta tasting, idan ya mata tace yayi idan bai mata ba tayi fatali dashi tace su sake girka wani.. Gaba d’aya sun gundura da kasancewarta a kitchen d’in.. Saida ta tabbata komai ya kamata kafin ta haura sama sauri sauri ta shirya dan bataso ta makara har Mu’azzam ya fice aiki basu had’u ba. Tasan shi da respecting time musamman lokacin aikinsa sam bai wasa da abinda ya shafi aikinsa, hardly kaga ya makara saidai dan ajizancin d’anadam. Tasha kwalliyarta sai watsa k’amshi take ta nufo k’asa, ta kuma duba dinging area ta tabbatar an jera komai yanda ya kamata kafin ta zauna saman kujera guda tana mai juya k’afafu d’aya bisa d’aya..Lokaci zuwa lokaci take duban agogon bango dake manne cikin parlorn tana mamakin rashin fitowar Mu’azzam d’in.. D’an mik’ewa tai ta lek’a window tana tinanin kodai bai dawo gida jiya bane.. Amma ganin motarsa da tai a parking lot ya tabbatar mata ya dawo gidan.. Ta d’an fuzar da fuci a hankali tana mai kuma duban agogo.. Toh kodai ta dubasa a d’akinsa ne..? Ta tambayi kanta tana mai d’an tsuke fuska.. Lokaci guda kuma ta tina yanayin da suka rabu jiyan.. Anya ita ya kamata ta fara dubasa.? Toh amma idan bataje ba tasan yana iya ficewarsa without checking on her.. Ta kuma fuzar da huci kafin ta yanke shawrin dubasa a d’akinsa. Ta d’auki lokaci tsaye bakin k’ofarsa tana tinanin yanda zasu kwashe.. Sai tazo kaman zatai knocking sai kuma ta fasa.. Ji tai kaman Ta juya Ta koma amma sai taji bazata iya ba, tana tsananin son Mu’azzam kuma abinda take k’ok’arin Yi kare aurensu take.. Tai k’ok’arin saita kanta had’ida d’ago hannunta da zummar knocking, saidai kafin takaiga k’onk’osa k’ofar taga ya bud’e k’ofar.. Tai tsaye tana dubansa, Shima d’in Ita yake duba saidai sam babu walwala saman fuskarsa.. Kallon mamaki take masa dan gashi dai cikin shiri da alama fita zai amma ba shirin da ya saba Fita office ta gansa ciki ba, bai faye saka Tshirt ba idan zaije aiki saidai lokutan zafi. Most of the time suit yafi sakawa.. Red Armani shirt ne jikinsa da ya fito da yanayin suffar jikinsa sai wando cream chinos.. Tana cikin k’are masa kallon ne taga luggage d’insa gefensa.. Tai saurin d’agowa tana dubansa da mamaki.. “Where are you heading to.. And why are you with your suitcases.?” Ta tambaya cikin tsananin mamaki “To the airport.” Ya bata amsa kai tsaye hannayensa duka biyu sakale cikin aljihu ya d’an turo k’irjinsa kad’an. “Ban.. Ban gane ba..” “Meye baki gane ba..” “Airport fah kace.. Mai zakajeyi airport.. Wait idan akan abinda na maka jiya ne I’m here to apologize.. You can’t just leave..!” Agogon dake d’aure tsinstiyar hannunsa ya duba kafin yace “Safeenah bani hanya, I want to catch my flight..” Unbelievably take rolling idanunta, murmushin da za’a iya kiransa da murmushin takaici saman fuskarta “Seriously.. Are you leaving us to go live with her..” Wannan karon cikin tsnanin b’acin rai yake dubanta “Don’t start.. Don’t even start Feenah..!” Yai maganar cikin rarrabewar kalamai. Lokaci guda ya janyo jakarsa ya matsar da ita gefe da hannunsa guda kafin yai shigewarsa.. Mutuwar tsaye tai tana dubansa.. Ita bata yarda ba tarewa zai da wancan ‘yariskar ba.. Yak’i ya tare da ita yaje zai tare da Karuwar banza.. Take taji jiri na neman kifar da ita, taji wani irin hawaye na ciko idanunta.. Cikin sauri Babu shiri ta biyo bayansa. Sauk’owar Mommy k’asa kenan Mu’azzam ya shigo parlorn ya gaisar da ita kafin ya sanar da ita Adamawa zai tafi.. Mommy zaida taga wani walk’iya ya gifta mata dan firgici, a fili kuwa cewa tai “Toooh Fufore kuma Mu’azzam.. Lafiya inji..? Ko sun sanar dakai wani abu gameda jikin Mamyn taka ne.. Amma kuma munyi waya jiya da Daddyn naku bai sanar dani wani abu kan haka ba.. Yace ma gobe yake saka ran dawowa in sha Allah, jikin Nuratu kuma da sauk’i sosai Alhamdulillah..” “No bamuyi waya dasu ba Mommy.. Kawai dai Zanje ne..” Muazzma ya bata amsa.. Daidai lokacin Safeenah Ta shigo tana kuka “Mommy tafiya zai ya barni ya koma zama da Ita.. Mommy I’m sure of it.. Dan Allah kar ki barsa ya tafi Mommy..” A tare Mommy da Mu’azzam suka juyo suna duban Safeenah dake shigowa parlorn cikin kuka tana surutai.. Mik’ewa Mu’azzam yai yana fad’in “Toh Mommy ni na wuce..” “Bazakaci wani abu ba..?” Mommy ke k’ok’arin dakatar dashi amma tuni Safeenah ta kuma fashewa da wani kukan tana fad’in Mu’azzam bai sonta.. “A’a Mommy zanci idan na fita..” Mommy tai masa addua’an sauk’a lafiya da kuma sak’on gaisuwa.. Baibi takan Safeenah ba ya fice cikin sassarfa, yana jin yanda Mommy ke mata fad’an wauta irin nata.. Bai tsaya sauraren mai zasuce ba yayi ficewarsa. A b’angaren Mommy ma yau ba ta shashashancin Safeenah take ba, Mu’azzam zai tafi Fufore tsoronta d’aya kar yaje ya b’ata masu shirinsu.. Ya zama dole ta kirawo Shamau ta sanar da ita cewa Mu’azzam na hanya tasan irin takan tsantsan da zasuyi kar ya fahimci wace irin mai magani aka d’aukarwa mahaifiyarsa. Ko takan Safeenah dake zube wajen tana kuka Mommy batabi ba Ta haye sama tana dialing layin Shamau matar Uncle Salman.. Bugu biyu a na uku Shamau ta d’aga. Ko gaisuwarta Mommy bata tsaya amsawa ba ta soma fad’in “Kina jina.. Mu’azzam na tafe yau.. Anya kinaga bazai fahimci matar da aka d’aukar wa mahaifiyarsa matsayin mai magani ‘yar 419 ce ba mai maganin gaskiya bace.. Idan ya fahimci haka zai saka ayan tambaya kanki Shemau dan kece kika kawo matar.. Idan kuma ya soma bincike nasan zai iso kaina.. Shemau bana so na sami matsala da mijina kan wannan nakashesshiyar matar tasa.” Mommy Ta k’arashe tsoro fal fuskarta Daga d’aya b’angaren Shemau ta murmusa tace “Aunty Hajara kenan.. Ni wllhi Mamaki kike bani.. Ta yaya Mu’azzam zai fahimci wani abu ba sanin kan magani yayi ba.. Mu’azzam fa D’ansanda ne ba Likita ba. Babu abinda zai fahimta koda yazo d’in.. Kyallu kuma mutane da yawa sunyi Na’am da maganinta amma ni nasan mak’aryaciya ce rufa ido kurum take wa mutane.. Idan da maganin Kyallu za’ai ma Nuratu jinya Ina mai tabbatar maki saidai ta k’arasa rub’ewa a turata rami taje ta had’e da tsohon mijinta Kinga ta fice daga rayuwarki har abada..” Mommy ta Sauk’e ajiyan zuciya hannu dafe a k’irji “Toh shikenan Shemau, ni nasan I can always count on you.. Wllhi banida burin da ya wuce Nuratu ta fice har abada daga rayuwar mijina.. Yanzu kiga yanda ya d’ibi jiki yai mata rakiya.. Ai ki gode ma Allah da wannan jarabebbiyar uwar tasu bata tura ma Salman ita ba sai ta tura ma mijina.. Koda dai nasan ma Babba za’a lik’a ba ma k’arami ba..” Aunty Shamau tace “That’s why I’m helping you Aunty Hajara, baki cancanci haka ba.. I can feel your pain, ciwon d’iya mace ai na d’iya mace ce.. Amma Ina mai tabbatar miki Nuratu bazata sami lafiya ba balle har tayi aurattaya da mijinki.. Gidanki kuma ta barosa kenan babu kome kaman yanda wanda ya mutu baya dawowa..” Mommy ta Washe baki cikeda jin dad’i tace “Toh yanzu hankalina ya kwanta sai munyi magana..” Daga haka sallama sukai Mommy na kuma jin zuciyarta ya mata wasai Ta yarda k’wallan mangoro ta huta da k’uda.. ** FUFORE Tsaki yai a karo na babu adadi yana mai kuma danna kansa cikin pillow, masu buga masa k’ofan basu fasa ba. Da mugun tsaki Musaddiq ya mik’e yai zaune saman gadon, ya janyo wayarsa yana duba time.. Wani irin tsakin ya kuma bugawa yana ayyana kalan rashin mutuncin da zaima duk mai buga masa k’ofar nan.. Bai ida tinanin ba ya sinkayo muryar Kakarsa Inne tana fad’in “Toh Uban ’yan gadara, Hakimi mai Sarauta sai ka tashi garin ya waye.. Nan ba gidan Ubanka bane daka saka baccin asara, aiki zakayi a nan kuma Kowa daka gani a nan nada amfani.. Idan ka bari na shigo wajen zanci mutuncinka Gidado..” “Goodness..! Musaddiq taka Ta k’are.!” Ya fad’i yana mai zubewa kan gadon daga zaunen da yake. “Kai Jume Zo ka bud’e min k’ofar nan da k’arfin tsiya na shiga na samesa..!” Ta fad’i tana duban Matashin da ta kira da Jume wanda ke tsaye gefenta.. Ai Musaddiq na jin haka ya mik’e ya k’araso ya bud’e k’ofar baki a kumbure.. Harara ta rakasa dashi shid’inma a dunk’ule yake aika mata hararan k’asa k’asa.. Kafin ya samu zarafin gaisheta taceda Jume mik’a masa kayan ya saka ya fice aiki.. Ma’aikata tintinin suke Gona shi yana kwance a nan yana baccin asara..” Da tsananin mamaki Musaddiq ke dubanta, da gaske uniform d’in ma’aikatan gidan gonar Inne ta basa tace ya saka.. Kan uba ai wllhi saidai duk abinda za’ayi ayi bazai saka wannan uniform d’in ba.. Bazawarin murmushi yai yana furta “You must be kidding.. Who’s going to wear those...?” Yai maganar yana nuna uniform d’in da Jume ke mik’a masa.. “Zaka amsa ka saka ne ko sai na tub’eka na saka maka da kaina..” Inne ta kuma fad’i a hasale. Ya d’ago idanu ya danna mata harara.. Dungurinsa tai tana fad’in “Ka sake hararata zan tsiyayi wannan jajayen idanun naka..” “Inne Wai dan Allah maiyasa kike mun haka ne.. Ni wllhi kawai ki fito fili kice kin tsaneni Inne, baki sona baki k’aunata..” “Eh an tsaneka d’in ba’a son naka.. Ka tashi ka shirya ka fita aiki. Kar ka bari na sake maka magana..” Ta dubi Jume dake tsaye gefe yana k’unshe dariyarsa tace “Ka tabbata ya shirya ya fito kuma ka nuna masa komai.. Sannan ka sanar da shugaban Laburorin idan Gidado yai latti ko na minti d’aya ne a hukuntasa.. Sannan koda wasa kar a basa kulawa ta musamman.. A kula dashi kaman yanda ake kula da ko Wanne ma’aikacin gidan gonar nan kaji koh..” Jume ya risina yana jinjina kai “Toh Inne in sha Allah za’ayi kaman yanda kikace..” Inne ta jinjina kai tana watsa wa Musaddiq da yai sakare yana dubansu mugun kallo.. Carbinta dake nad’e hannunta Ta zabga masa yana kaucewa “Jarabebbe kawai..” Tana ficewa Musaddiq ya dawo da dubansa ga Jume, wani irin mugun kallo kawai yake watsawa Jumen musamman da yaga irin dariyar da Jume yake bayan Inne ta fice.. “Kaci gaba da biye ma wannan matar kuna shiga hakkin rayuwata.. Wannan matar na jima da sanin cewa Ta tsaneni kaf cikin jikokinta babu wanda Ta tsana irina..” Jume yai k’ok’arin tsagaita dariyarsa yace “Wllhi Inne tana k’aunarka kuma so take ka zama good boy shiyasa ta sakaka gaba.. Gata take maka Musaddiq.. Yanzu dai ka shirya muje kai breakfast ka fice kafin kayi latti ka jaza min dan nasan nima harda ni Zata had’e tai mana d’add’aya..” Tsaki Musaddiq yaja yana mai janyo towel d’insa, ya tsani wannan gidan Gona tamkar akan K’aya yake haka jinsa “Let her do her worse..” Ya fad’i yana shigewa bathroom.. Jume dai murmusawa kawai yana fad’in “Ka fad’a a gabanta idan ka isa..” Jume second cousin d’in Su Musaddiq ne, Babansa cousin d’in su Daddy ne. Baban Jume kaman d’ah yake ma Inne dan D’an d’anuwanta ne.. A cikin Yola gidansu Jume yake shima bai jima da zuwa Gidan Gonar ba dan Industrial Training ne ma ya kawo sa aiki nan cikin Gidan Gonar dashike fannin da ya shafi noma da kiwo yake karantawa.. Musaddiq zai d’an girme ma Jume da shekarun da bazasu wuce biyu zuwa uku ba amma tin can dama sun saba da juna tin suna zuwa hutu Fufore hakan yasa da suka sake had’uwa yanzu abotansu na Tun baya ne yake k’ok’arin sake k’ulluwa.. Babu yanda Jume baiba Musaddiq ya saka kayan ma’aikatan gidan gonar amma fir yak’i sakawa.. Yace a haka zaije saidai Inne tayi abinda zatayi.. Aiko yana isowa k’ofar parlorn zai fice ya ganta tayi k’ebebe tsakiyar k’ofa tana aika masa mugun kallo.. Lumshe idanunsa kurum Musaddiq yai yana furta “Kai.. Kai.. Kai jama’a.. Shikenan kuma ai..!” Tin kafin ma tace ya juya ya juya d’in, d’aki ya komo ya sauya shiga cikin uniform d’in.. Ya fito yana tafiya awkwardly cikin uniform d’in kaman zai kurma ihu, shi babu abinda yafi basa takaici kaman wannan k’atoton boot d’in da ya zurma k’afafunsa ciki.. Aunty Shemau da ahigowarta section d’in kenan taci karo da Musaddiq a haka, dariyarta ta k’unshe itama tana mai k’ok’arin gaida Inne.. Zai fice Inne tace “Zo nan tsaya..” Yaja ya tsaya fuska a tamke Irin hular fulani makiyaya mai kaman malfar sak’a ta d’auko ta d’aura masa akansa tace “Toh maza aje ayi aiki.. Ayi noma ayi kiwo Allah ya bada sa’a..” Jume da Aunty Shemau ne suka amsa da Ameen shikam Musaddiq tuni ya fice cikin k’unan zuciya.. Sai sannan Inne ta dawo da hankalinta ga Shemau.. Suka kuma gaisawa Shemaun na tambayarta jikin Aunty Nurah.. Inne ta amsa mata da fad’in “Jiki Alhamdulillah, Hindatu na ciki tana kula da ita..” (Hindatu ma’aikaciyar Inne ce dake tayata kula da Nuratun) Aunty Shemau Ta d’an murmusa tana kuma sanne kanta k’asa had’ida gyara zaman mayafinta, Ta d’an muskuta tace “Nace ko mai maganin ta iso, ko yau batazo ba..?” “Ai yaushe garin ya waye Shemau, zatazo ne k’ila zuwa anjima..” Inne ta bata amsa.. Aunty Shemau ta jinjina kai tace “Haka ne.. Bara na lek’a na dubata..” Inne ta amsa mata da fad’in “Toh madallah.. Ki shiga tana ciki..” Shemau ta mik’e cikeda girmamawa kafin Ta nufi d’akin Aunty Nurah. ** Gaban madubi ta tsaya tana kuma zana gazal da janbaki saman fuskar nata da sunan kwalliya.. Lokaci guda take fari da idanu tana juyi gaban madubin.. Ita da kanta take kirari ma kanta “Yarinya mai kyau.. Had’uwa iya had’uwa.. Ba farar k’afa kike dashi ba kaman yanda Inne Kyallu ke fad’i.. Tsaban had’uwarki ne shiyasa samarin garin nan basa iya tunk’ararki.. Albarka na gaba gareki ko Inne Kyallu bata furta miki ba...” Ta k’arashe tana kuma juyi hannayenta saman kunkuminta ga uwar d’amara da tayi kaman zata tashe... Lokaci guda ta d’auko d’ankwalinta ta nannad’e kafin ta d’aura saman goshinta, ta turo kallabin gaban goshi, ta zubo da kitsonta guda biyu b’angaren dama da hagu.. Ta kuma duban kanta tana sakin murmushi.. “Wo ni.. Gaskiya kin had’u Ajidde..” Dundun da Kyallu Ta d’und’uma mata a gadon bayanta ya sanyata mik’ewa babu shiri tana sakin ihu had’ida sosa bayanta. “Uwar mi kika tsaya yi a nan da bazaki tafi ba..?” Ajidde Ta turo baki gaba kad’an tace “Inna Kwalliya fah na tsaya ko Allah zaisa ki sami Sirki a hanya..” Kyallu ta janyota waje ta jefa mata buhun maganin tana fad’in “Kinajina ki bud’e kunnuwanki da kyau ki saurareni.. Idan kikaje kice a fita a baki waje keda majinyaciyar zaki had’a mata magninta ki bata.. Idan an watse an barku ku biyu tinda babu abinda take iyawa bama zata fahimci kin d’auko wani abu ba.. Ki bincika d’akin taro da sisi da duk wani abinda zaki samu na arziki ki k’unso cikin buhunki ki kawo man Kinji koh.. Idan kika dawo min gidan nan babu abin arziki a turke zan d’aureki ki kwana.. Maza Tashi ki shige..” Ajidde ta jinjina kai a hankali baki a ture tana kuma sosa dundun da Kyallu tai mata wanda take ji kaman ta rabe mata k’ashin baya ne.. Lokaci guda ta mik’e ta d’au jakan buhu na maganin Ta rataye saman kafad’arta.. Kyallu ta zuba mata jajayen idanunta tana huci “Babu uban da zai tab’a sonki Ajidde dan ked’in Anno ba ce mai farar k’afa nima dan inada makarinki ne da tuni kin gama dani da mugun farar k’afarki..!” Ajidde dake lab’e jikin k’ofa dik kalaman Kyallu a kunnuwarta ne, cikin sanyin jiki ta soma tafiya rataye da jakan maganinta dan Idan da Sabo Ta saba da jin wad’annan kalamai daga bakin Inna Kyallu.. ** Koda ya iso motar da zai kaisa garin Fufore ya shiga, dan dama bai sanar dasu yana tafe ba balle ya sanar dasu isowarsa azo a d’aukesa.. Da shike Gidan Gonar wajen gari take hakan yasa shi ya soma sauk’a cikin motar tasu.. Yai tsaye yana k’are ma gidan gonar kallo, abubuwa da dama na ziyartan zuciyarsa.. Wajen da yafi so yafi k’auna a rayuwarsa.. Wajen da yake jefa zuciyarsa cikin nishadi da annashuwa.. Garin da aka haifesa ya kuma taso cikinta.. Gari mai tarin albarka da kwanciyar hankali.. Babu fitintunun da ya baro babu komai sai kukan tsintsaye da dabbobi dake sanyasa nishad’i.. Ya lumshe idanunsa yana shak’an iskan dake kad’awa. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *12* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali yake takowa yana kuma k’arema wajen kallo, memories d’in baya suna dawo masa.. Daidai jikin wata bishiyar mangoro ya tsaya ya d’aga kai yana duban bishiyar, lokaci guda yake tuna zamanin yarintarsa, sukanyi wasa da mahaifinsa wasan Corps da Bad guys, dama tin yana k’arami yake mafarkin zama D’ansanda domin ya kama masu laifi.. Ya tina wasu lokutan yakan d’ale bishiyar yayi kwanton b’auna Babansa na k’asa yana nemansa.. Sai ya bari Babansa yazo daidai jikin bishiyar Sai ya d’ago bindigar robarsa ta wasa yana pointing Baban nasa dashi yana fad’in ‘Na kamaka.. Freeze or I’ll shoot..’ Ya saki murmushi yana tuna moments masu dad’i da suka kasance ciki shida mahaifinsa.. A hankali ya aje jakarsa jikin bishiyar kafin ya dafa bishiyar ya d’ale.. Sai yana ganin hoton abubuwan cikin idanunsa kaman yanzu suke faruwa, komai yana nan yanda yake babu abinda ya canza Sai rayuwarsu data canza.. Akwai wani d’an hole jikin bishiyar yanda yake b’oye k’aramar bindigar robar tasa dik sanda zasuyi wasan hide and seek da Dad d’insa, ai kuwa nan ya hangota ciki tana nan a wajen har wannan lokacin.. Mu’azzam ya saki murmushi mai bayyana hak’wara yasa hannu ya d’ago bindigar yana juyawa, lokaci guda yake kuma tuno abubuwa da dama murmushin bai bar saman fuskarsa ba.. Yana nan zaune saman bishiyar yana tinani rayuwar baya ya hango wata yarinya Ta nufo wajen.. Tana tafe tana cillo da jakan dake hannunta tana ‘yan wak’e wak’e.. _”Mangoro.. Mai Mangoro kawo musha.. Idan da kud’i ma zamu sha idan babu kud’i ma zamusha.. Balle ma mu na bati zamu sha..”_ Mu’azzam ya mik’e daga kishingid’en da yake nan saman bishiyar yana kuma duban yarinyar dake nufo bishiyar tana wak’e Mangoro.. Cak Ajidde ta tsaya sakamakon hango bak’in jaka da tai aje k’asan bishiya.. Ajidde ta shiga wage baki tana furta “Allah ya kashe ya baki Ajidde, tsuntsu daga sama gasasshe.. Wannan jaka da gani Kud’i ne a cikinki..Idan nayi nasaran bud’eki na d’ibi kud’in ciki na kaima Inna Kyallu ko shakka babu zata yabeni za kuma Ta saka mun albarka..” Taci gaba da Washe baki tana kuma nufo jakan... Tana isowa ta soma ‘yan waige waige dan ta tabbatar babu mai ganinta.. Saida Ta tabbata babu kowa wajen kafin ta duk’a ta soma kiciniyar bud’e jakan... Mamaki ya cika Mu’azzam Ganin k’amar yarinya na k’ok’arin sata.. Ajidde bata fasa kiciniyar bud’e jakar ba tana fad’in “Dik taurin kanki sai na bud’eki jaka..!” Ta k’arashe tana mai daddage k’arfinta tana kiciniyar bud’ewa harda wani bada balance tai.. Tana kiciniyar bud’e jakan taji mangoro guda ya fad’o mata akai timm.. “Kai Kai Kai..” Ta fad’i tana dafe kanta.. Ta d’auki mangoron da ya fad’o ta shiga nunasa da yatsa tana fad’in “Tind kika buga min Kai zan miki shan azaba Alk’ur’an.” Lokaci guda kuma ta saki Tsaki tana mai furta “Ke mangoro yau bata taki nake ba.. Ki bari na samu abinda zan samu cikin jakan nan kafin na dawo kanki, nidake akwai amana ai..” Ta k’arashe tana mai kuma janyo jakan.. Fad’owar wani mangoron ne data kumaji ya sanyata tsagaitawa.. Ta soma k’ok’arin mik’ewa tana tinanin kodai mai jakan na saman bishiyar ne.. A hankali ta soma k’ok’arin d’ago kanta.. Ai a zabure ta saki wani irin k’ara sakamon hango mutumin datai saman bishiyar rik’eda bindiga “Bindiga.. Bindiga..” Kalman data iya furtawa kenan jikinta na k’yarma. Ajidde batai wata wata bata ta suri takalmanta da jakan maganinta a hannu ta soma gudu. Mu’azzam dake rik’e da bindigarsa tin na yarinta dirk’owa yai daga saman bishiyar ya soma k’ok’arin bin bayan b’arauniyar yarinya wacce bai tab’a ganin ko mai kamanninta a Gidan gonar ba dik zuwansa.. Gudu take tana waige waige tana hango alamun mutumin na nufota.. Rumbun da ake aje abincin dababbobin tai wuf ta shige had’ida turo k’ofar.. Musaddiq dake cikin d’akin aje abincin an basa aikin gyaran d’akin yanayi yana turb’une fuska kaman daga sama yaji an turo k’ofa an shigo.. Ya dakata da abinda yake yana dubanta da mamaki yanda take lek’en mutumin dake casing d’inta.. Motsin da taji bayanta ya sanyata juyawa babu shiri.. Razana tai da ganin yanda fuskar Musaddiq ya b’aci da k’ura shima ya razana da kwalliyar dake fuskarta da yanda duk ta dame kwalliyar ya b’ata mata fuska sakamakon gudun famfalak’i da tai.. Suka saki k’ara a tare kowa na tsoron juna.. Kowa gani yake gamo yayi.. Sai kuma Ajidde ta soma matsowa kusansa tana kuma zuru zuru da idanu, Musaddiq bai daina binta da kallon tsoro da mamaki ba.. Kan ya ankara ta duk’a ta soma k’ok’arin janye boot d’in da k’afafunsa ke rufe ciki.. Musaddiq yana janye k’afarsa yake furta “Hey what are you doing.. Who are you.. Ke ki sakar min k’afata..” Ajidde bata fasa janye takalmin cikin k’afar Musaddiq ba, harga Allah tsoro ya kamasa sosai ganin yanda wannan halittar ke janye masa k’afa.. Bata fasa janye Boot d’in ba har saida ta cireta gaba d’aya.. K’afar Musaddiq ya bayyana.. Ajidde na ganin k’afar Musaddiq ta sauk’e ajiyan zuciya hannu a k’irji tana fad’in “Wai Allah na.. Ashe mutum ne..!” Mamaki bai saki Musaddiq ba ganin itace ya kamata yace ashe mutum ce amma shine take masa zaton ba mutum bane.. Ya kafe yarinyar da idanu cike da mamaki yana mai kuma turb’une fuska.. Ajidde ta d’ago idanu daga duk’en da take tana duban Fuskarsa da dust ya b’ata masa yayi fusufusu.. Lokaci guda ta tintsire da dariya tana nuna fuskarsa take fad’in “Wllhi saikace Kuran tashe..” Tana maganar tana nunasa tana dariya.. Yanda ta wage hak’waranta tana dariya ga janbaki har kumatunta ya mugun bawa Musaddiq dariya, Ai take shima ya b’ige da dariya yana nunata yana dariyar.. Itama bata fasa nunasa tana ci gaba da dariya ba.. Cak ta tsaya da dariyar da take sakamon jiyo motsi da tai daga waje kaman wani na zuwa, tasan bazai wuce mutumin da taso b’alla jakarsa bane.. Fit ta had’iye dariyar tai saurin yin alama wa Musaddiq da hannu kan yayi Shiru.. Musaddiq ya daina dariyar da yake, yai shiru yana dubanta, lokaci guda take masa alama a hannu kan ya duk’a ya b’oye shima.. Babu musu ya duk’a ya d’an b’oye shima.. Sunajin motsin na kuma matsowa yanda suke.. Sukai likimau suna sauraron tafiyan.. Har kaman an tab’a k’ofar sai kuma sukaji an koma ba’a shigo ba.. Saida suka tabbata sun bar jin tafiyar kafin Ajidde ta sauk’e ajiyan zuciya tana furta “Allah ya ceceki Jidde yau da kin sha harsashi..” Musaddiq yace a fili “Ke Wai gudun me kike ne..? Wacece ke ma Wai..?” Ajidde ta mik’e tana fad’in “B’arawo ne ya biyoni.. Da k’yar nasha harda bindiga hannunsa..” Musaddiq yace “B’arawo kuma a nan.. Bayan duka masu gadin dake tsaron babban k’ofa..?” “Auho baka yarda ba amma ka biye mun ka b’uya.. Na fad’a maka har bindiga nadashi Allah ne ya kare bai ganmu ba da ya had’a da kai..” Musaddiq ya d’anyi tsaki a hankali sanda Ajidde taci gaba da nuna fuskarsa tana dariya tana fad’in “Yauwa ashe dariya nake ya kaste min..” Girgiza kai Musaddiq yai yace “Ke are you crazy.? Wait waima mai kike a nan ne..?” Sai sannan Ajidde ta tina bada magani tazoyi.. “Jaka na..!” Ta furta tana shafa bayanta.. Lokaci guda taci gaba da furta “Na shiga uku.. Na zubar da maganin.. Shikenan yau Inna Kyallu halak’ani zatayi.. Wayyo Na shiga uku na mutu na lalace..!” Tana maganar tana kuka tana kuma lalumen maganin.. Dariyar da Ajidde take ya koma kuka.. Harga Allah yanda dariyarta ya bawa Musaddiq dariya kukanta ma dariyar ya basa.. Hannayenta biyu ta saka aka tana kukanta. Tin yana dariyar kukan nata har kuma ta fara basa tausayi. Yai k’ok’arin saita kansa yace “Ki nastu ki fad’a mun meke faruwa..” Ajidde ta kuma fashewa da kuka tana fad’in ta zubar da maganin. Musaddiq yace “Wani magani.?” “Maganin masu Gidan da Innata ta aikoni na kawo.” Sai sannan Musaddiq ya fahimci d’iyar mai maganin Aunty Nuratu ce. “Toh yanzu ya kike so ayi..?” Musaddiq ya tambaya. Ajidde naci gaba da kukanta take fad’in “Ni wllhi ban Sani ba.. Abu d’aya na sani shine yau zan yabawa Aya zak’i hannun Inna Kyallu..?” “Wacece Inna Kyallu..?” “Inna ta ce.” Ta bashi amsa kai tsaye “Toh yanzu mai zakice wa mutanen gidan da kika zubar masu da maganin.?” “Nima ban Sani ba.. Kai zaka ce masu..” Ta fad’i hakan abinta. “Ni kuma.. Ta ina na sansu da zan shiga na sanar dasu kin zubar masu da magani..” Cewar Musaddiq yana dubanta “Toh ba Kai kana masu aiki ba Ai ka sansu..” “A’a ni aiki kawai nake masu.. Kuma masu gidan basuda kirki balle na shiga na miki cover.. Nima aikin da ya shafe ni kawai nake ko shiga gidan banayi..” Ajidde tai zururu da ido tace “Toh yanzu ya zanyi..? Dan Allah ka taimakeni ka shiga ka tsara masu zance ni naje naji da Inna Kyallu.. Dan Allah Kuran Tashe ka taimakeni..” Sunan data kirasa dashi ya sanyasa dubanta kad’an yace “Ke mai kikace..?” Tai saurin kama bakinta tace “Toh bansan sunanka ba..” “Ba Lallai ki sani ba.. Makeup abuser..” “Sunanka kenan..?” Ta tambaya tana dubansa.. “A’a naki dai..” Ya bata amsa kai tsaye.. “Ni sunana Ajidde Jidde Jiddodo d’iyar Kyallu mai Warka warka.. Ka fahimta..” Musaddiq ya zuba mata idanu ya da take jero sunaye. “Toh ai sunayen naki da yawa wanne zan d’auka.?” “Duk wanda ka d’auka ma yayi.” Ta basa amsa kai tsaye. Musaddiq ya murmusa kad’an sai kuma yace “Toh yanzu ya za’ayi ki fice B’arawon nan na nemanki..” Ajidde ta zaro idanu tace “Bazan fice ba sai ka min alk’awari zaka shiga gidan nan ka kareni kafin gobe Inna ta nik’o gari tazo da kanta..” Ya girgiza kai yace “Bana alk’awari.” “Toh ka taimakeni kaman yanda Allah ya taimakeka..” Tai maganan tana mai k’ok’arin duk’awa.. “Ke tashi basai kin durk’usa ba.. Naji zanyi magana ma abokin aikina shi yana shiga gidan.. Toh amma mai zance masu..? Nace masu b’arawo ya biyo mai maganin..” Baikai aya ba tai saurin dakatar dashi da fad’in “A’a kar kace haka..” Musaddiq ya tsareta da idanu yace “Toh k’arya kika mun kenan..” Ajidde ta shiga raba idanu tana twisting ‘yanyatsunta.. Murmushin yak’e tai yellow teeth d’inta da basu ganin brush suka bayyana kafin tace “Dama ai k’arya na maka.. Barin fad’a maka gaskiyar.. Kanaji tsinkar mangoro zanyi shine ya biyo ni a guje harda bindiga..” Musaddiq yace “Toh kece b’arauniyar kenan..” Ajidde ta fito da harshenta ta dangwala da yatsarta manuniya tace “Aradun Allah ban d’auki mangoron ba.. Ai kai shaida ne da ka ganni da ita..” Sosai ta basa dariya musamman rantsuwar tata.. Ya jinjina kai yace “Shikenan yanzu kije ni nasan mai zance ma abokin nawa Sai ya fad’a masu..” Ajidde ta jinjina kai tana masa godiya. Har zata fice yace tsaya.. Ta dawo da baya tana dubansa. “Idan kika fita haka mutumin da yake chasing d’inki zai ganeki.. Bari na miki dabara yanda bazai ganeki ba..” Ya k’arashe yana mai cire malfar kansa.. Lokaci guda ya d’aura mata akai yace “Yauwa he won’t be able to recognize you now.. Kina iya tafiya..” Ya k’arashe yana mai sakar mata murmushi.. Murmushin itama ta sakar masa tana mai furta ta gode.. Yanda take murmushi tana sanne ido ya mugun bawa Musaddiq dariya, Aiko nan ya tintsire da dariya.. Take Ajidde ma ta tintsire da dariya tana kuma duban fuskarsa mai lullub’e da hazon k’ura.. A haka ta fice tana dariyarsa yana dariyarta.. A b’angaren Mu’azzam kuwa tinda yabi bayan yarinyar bai cimmata ba Sai ya yanke shawarin tambayan securities na gidan gonan Ko sunga yarinyar da yake nema.. Saidai kafin ya isa wajen securities ya hango Daddy da Uncle Salman sun fito daga wani babban Office suna tattaunawa Uncle Salman d’in na nuna ma Daddy wasu documents.. Ko ba’a ce ba Business suke tattaunawa.. Suna hangosa fari’ar Daddy ya k’aru, yama daina sauraren Uncle Salman wanda shima tuni ya tsaya da bud’e takardun yana duban D’an d’anuwan nasa wanda sam inuwansu Bai jituwa.. Mu’azzam na K’arasowa Daddy ya tafi ya d’an basa light hug yana fad’in “A’a Inspector sauk’an Yaushe..?” Mu’azzam na murmushi ya d’an sadda kai yana gaida Daddy.. Su duka biyun annuri ne saman fuskokinsu.. Uncle Salman ya d’anyi gyaran murya yace “Sirki na rungumar Sirki nan dai ba Abuja bane..” Murmushi bai bar saman fuskar Daddy ba yake fad’in “Mu’azzam D’ah na ne ba Sirki na ba..” Mu’azzam ya d’an kaikaito yana duban Uncle Salman, irin duban da yake masa tin yana yaro shine dai saman fuskar tasa.. Ya gaishesa cikeda girmamawa yana tambayan ya samesu lafiya.. Uncle Salman yace “Lafiya lou Mr Officer.. Saima bautan dukiyar ka da nake Kanyi wanda Yayana ya hana a cire maku Shares d’inku tun kafin rashin ‘yaruwarka..” Take annurin fuskar Daddy ya d’auke cak.. Ya dubi Uncle Salman yace “Salman ya isa haka..” Uncle Salman ya d’an tab’e baki kad’an yana maida hannayensa baya.. “Ni zan shige Meat Factory aiki na jirana..” Uncle Salman ya fad’i yana mai k’ok’arin shigewa.. Lokaci guda kuma ya kaikaito ya dubi Mu’azzam yace “Ina maka Barka da zuwa D’ah na Mu’azzam..!” Yai maganar murmushi saman fuskarsa. Murmushin Mu’azzam ma ya sakar masa yana mai jinjina kai ba tareda yace komai ba.. Uncle Salman na shigewa Daddy ya kamo kafad’an Mu’azzam guda yana fad’in “Mu k’arasa ciki Inspector..” SameenaAleeyou 📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *13* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Inne tana ganinsa Ta soma masa lale kaman ta goyasa dan murna, Aunty Shemau ma na zaune wajen tai masa Barka da zuwa cikeda kulawa. Take ta tina wayan da sukaida Mommy, bazata tab’a bari Mu’azzam d’in ya fahimci wani abu ba. Kakarsa sai nan nan dashi take dan Farin ciki, tuni ta soma masa tayin abinci daban daban harma tambayarsa take ko akwai abinda yake so a girka masa a gurguje. Mu’azzam yace “A’a Inne zanci duk abinda ya samu, amma zanyi wanka na duba Mamy first idan yaso sai muci dinner gaba d’aya..” “Har dare bakaci komai ba, yammacin da saura fah..” “No Inne babu komai ai ba wani yunwa nakeji ba ma.. Zan duba Mamy sai na d’an huta..” Mik’ewa tai tana fad’in “Mutum yayi tafiya bai saka komai cikinsa ba inyi.. Badai a gidan nan ba..” Ta k’arashe tana mai kiran ma’aikatan. Mu’azzam yabita da kallo murmushi saman fuskarsa zuciyarsa Cikeda k’aunar ahalinsa. “You must be jet lagged.” Musaddiq ya fad’i murmushi saman fuskarsa yana mai k’ok’arin k’arasowa cikin parlorn. Juyowa Mu’azzam yai sanda Musaddiq d’in ya k’araso fuska fal fari’a sukai handshake suna d’an hugging juna. “Wai dama kana tafe.. Kuma shine baka fad’a mun ba.. I would’ve arranged something for you. You know this place is boring and annoying..” Da mamaki Mu’azzam ke duban Musaddiq dake sanye da uniform na ma’aikatan gidan gona“I can see you’re better off here.. And to be honest, naji dad’in ganinka haka da uniform kana aiki..” Musaddiq ya fuzar da fuci kad’an yana ‘yan waige waige dan ya tabbatar Inne bata wajen “Ai ni kawai matar nan ta gama dani.. Wllhi wnn jarabbebbiyar tsohuwa Ta gama dani.. Musaddiq Marwan Gamji no longer exists.. I guess fate has decided for me.. Ni kuma kalan nawa K’addaran kenan..” Yai maganar sanda suka jera suna tafe hanyar d’akin Aunty Nuratu.. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Haka shine da kyau Musaddiq, kaga one day you’ll takeover the family business. After all, Wannan shine mafarkin da a Kullum Daddy yake.. Wani daga cikinmu ya kula da kasuwancin Ahalin.. Saidai ni tuni Allah ya k’addari ba d’an kasuwa bane kaman yanda Daddy yaci min buri ni D’ansanda ne.. Naji dadi sosai da naga kai d’in zaka cika burin Daddy.. I’m so proud of you Musaddiq..” “Kawai ka fito fili kaima kace kana Farin ciki da k’untata rayuwata da akai..” Musaddiq yace yana kuma b’ata fuska Murmusawa wann karon Mu’azzam yai ya kaikaito yana duban Musadddiq sosai “Watarana zaka fahimci Inne gata ta maka Musaddiq.. We all love you, and we want what’s best for you..” Yai maganar kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Gajeren murmushi Musaddiq d’in ma yai yace “Sai ka shafe watanni Abuja kaji bana nan sannan ne zakace a dawo maka dani and your Grandma bata kyauta ba data d’auke ni..” Mu’azzam ya d’an daga fuskarsa suna ci gaba da takawa a hankali, ba tareda ya dubi Musaddiq d’in ba yace “At least zan d’an huta da rashin jinka..” “Au haka kace. Zamu gani ai.. I know rashina a gareka tamkar rashin police force ne..” Cewar Musaddiq daidai sanda yake tura k’ofan d’akin Aunty Nuratu sallama saman bakunansu. Aunty Shemau suka tadda ta gama kintsa Mamy ta d’aurata saman wheelchair.. Ta fad’ad’a murmushinta tana duban Mu’azzam d’in “A a Mu’azzam ka shigo, Aiko har na gama shiryata zan kawota wajenka.. Sai gashi ka shigo ma..” Cikeda jin dad’in yanda Aunty Shemau ke kulada mahaifiyarsa yace “A’a dama zan shigo Aunty.. Sannu da d’awainiya fah..” Aunty Shamau tai saurin katsesa da fad’in “A’a Haba dai Mu’azzam wani d’awainiya kuma.. Kawai na d’aura daga yanda ‘yar uwata Aunty Hajara ta tsaya ne. Aunty Nuratu ai ‘yaruwa ce a garemu.. Ka daina mana godiya kaman wani hidiman muke.. Ciwo ai na kan kowa, fatan mu dai Allah ya bata lafiya ya tashi kafad’unta..” Gaba d’aya suka amsa da Ameen daidai sanda Mu’azzam ya k’araso gaban wheelchair d’in ya duk’a Aunty Shemau na kuma gyara mata kanta da ya tank’washe a karkace. Mu’azzam ya zuba mata idanu zuciyarsa fal k’aunarta gauraye da tsananin tausayinta, Allah sarki inama wani na iya yaye ma wani cuta da ya bada duk abinda ya mallaka koda rayuwarsa ce dan mahaifiyarsa Ta sami lafiya.. Saidai ba haka abin yake ba. Allah shine yake jarabtan bayinsa da cuta ba Don ya k’isu ba saidai dan ya jarabci imaninsu da wannan cutan sannan ta kuma zame ma bayinsa na k’warai kankarewar zunubi.. Inne ce ta shigo tana tambayar ko mai maganin ta iso.? K’irjin Musaddiq ya buga dan sai yanzu ya tina da Ajidde da yanda sukai.. Inne taci gaba da fad’in “Shemau ki kirata muji ko lafiya bata iso ba har yanzu.. Ni bana son ana sako shiririta cikin lamarin jinyar nan..” Aunty Shemau ta d’an daburce tana fad’in “Ai Inne tace tana tafe.. Inaga abin hawa ne bata samu ba..” Musaddiq yayi caraf yace “Wait. Wai mai maganin Mamy.. Ai kuwa tazo amma saidai akwai maganin data mance bata taho dashi ba wanda za’a bata yau d’in.. So sai ta koma, and I don’t think zata iya dawowa yau dan wajen da take zuwa akwai nisa daga nan.. And kaman hadari ne a garin..” Duk suka juyo suna dubansa kafin Inne tace “Wannan ai shirita kenan..” Inne ta fad’i tana duban Musaddiq. Taci gaba da fad’in “Kuma sai ta rasa nawa zatai bayani sai kai..” “Toh ai ni ta samu Inne shisa ta fad’a mun..” Baikai aya ba tace “Kai rufe min baki..” Ta dubi Aunty Shamau tace “Shemau ki kira matar nan kiji bayani daga bakinta dan ban yarda da zancen Gidado ba.” Aunty Shemau ta jinijina kai tana fad’in “Toh Inne zan kirata..” Shidai Mu’azzam bai bi tankasu ba hannun mahaifiyarsa rik’e cikin nasa har lokacin.. A haka har d’akin ya rage saura shi da mahaifiyarsa.. Addu’o’i ya dinga mata har Shemau ta shigo ta taddasa. Nan take sanar dashi mai magani tace ko zuwa gobe za’a iya bata idan Allah yakai rai dan lokacin ma ruwa ake tsulawa.. Ta kuma k’arasowa tana fad’in “Kaje ka huta kaci abinci Mu’azzam gani nan ga Hindu zamu kula da ita...” Gajeren murmushi ya d’anyi had’ida mik’ewa yana ma Aunty Shemau godiya.. Yana ficewa Shemau ta Sauk’e ajiyan zuciya had’ida fuzar da fuci a hankali. Ta maidoda dubanta ga Aunty Nuratu tana aika mata mugun kallo “Nakasasshiyar banza.!” Ta fad’i tana mai hankad’a wheelchair d’in da Aunty Nuratu ke kai.. ** A b’angaren Ajidde kuwa koda ta koma gida ma Kyallu ba taro ba Sisi jibaganta tai Ta jefata d’akin Tumakai tace ta Kwana dasu, D’akin da Kyallu ke aje dabobbinta harda turke tayi ma Ajidde Wanda idan tai mata laifi take d’aureta a nan itama Ta Kwana tareda dabbobin.. Haka tayi lamo jikin turken da Kyallu ta d’aure mata k’afafu tana rungume da hular da ma’aikacin Gidan Gonar ya bata wanda bata San koda sunansa ba. Saidai tuni Ta masa lak’abi da Kuran Tashe.. Dikda azaban da take ciki hakan Bai hanata sakin murmushi ba sanda ta tina had’uwarta da mutumin wanda ko sunansa bata sani ba.. Tanaji can k’asar zuciyarta tana son ta sake ganin wannan fuskar tasa mai lullub’e da hazon k’ura wanda ya sanyata dariya da nishad’i har ya mantar da Ita ukuban da Inna Kyallu ke mata.. Washe gari bata aiki Ajidde ba da kanta tai shiri Ta nufi gidan dan bama Majinyaciyar maganinta.. Kyallu tana fita Ajidde ta samu ta k’ok’arta ta tsinke Turken data d’aureta. Gefe da Gidansu akwai wata mata wacce malama ce kuma har matan aure tana koyarwa, wasu lokutan idan Kyallu Ta fice tsiddabarunta da bokancinta gidan Malama Hafsatu take zuwa domin ta taimaka mata da abinci.. Yau d’inma hakance ta kasance da Ajidde.. Malama Hafsah na aji tana ma matan aure karatu Ajidde ta shigo da k’yar da k’yar kaman zata kifa k’asa.. ‘Yan aji suna ganin Ajidde suka soma k’ok’arin mik’ewa kowacce tana neman hanyar gudu dan an canfa ance tanada Farin k’afa dik yanda taje Sai bala’i ya auku wajen.. Malama ta tsawatar masu da fad’in “Shin ba yanzu muka gama karatu kan yarda da canfi ba.. Canfi haramun ne a musulunci.” Wata mata Ta d’aga hannu tace “Malama inada tambaya” Malama Ta jinjina mata kai tace “Ina sauraronki..” “Amma malama ai akwai Kambun baka.. Shin shi ba canfi bane..?” Malama ta jinjina kai tace “K’warai Al’ainu haqqun. Akwai Kambun baka, harta a musulunci an yarda akwai Kambun baka, yazo kuma a sunna cewa akwai Kambun baka har an bamu addu’a da zamu dinga yi domin neman tsari daga sharrin Ido wanda ake cema kambun baka.. D’aura laya ko wani abu mai kama da haka da sunan neman kariya daga sharrin ido haramun ne a musulunci.. Yin hakan shirka ne inji Manzon Allah SAW, hadisin yana nan a cikin Musnad Ahmad 16969.” Malama ta d’an tsagaita kafin taci gaba da fad’in “Wacce dik take neman kariya daga sharrin ido ko Kambun baka ga abinda zatace ‘A’uthzu bi kalimatillahit taammaati min kulli shaid’anin wa haammaa wa min kulli ainin laammaa.’ Wannan addu’a ce ingantacciya datazo a sunna sannan zaki iya karanta ma yaranki ko wacce safiya da maraice domin nema masu kariya daga sharrin ido dama duk wani shed’ani ko abin sharri.. Babban darasin da nake so mu d’auka a nan shine wani baya tab’a sauk’ar maka da bala’i sai idan Allah yaso haka wani baya tab’a kawo maka nasara sai idan Allah yaso Kun fahimta..” Gaba d’aya suka amsa da “Na’am Malama mun gane..” Malama ta jinjina kai tace “Monita ki bud’e shafin da muka k’ara jiya ayi bitarsa kafin na dawo muyi k’ari.. Ku d’an ara min lokaci naji da Ajidde..” Gaba d’aya suka jinjina kai suna amsa mata.. Malama ta janyo Ajidde suka fice zuwa tsakar gidanta.. Dik karatun kore shirka da aikata tauhidi da malama tai tsaf Ajidde ta saurareta, gaba d’aya jikin Ajidde yayi sanyi domin kuwa abinda Inna Kyallu ta d’aurata Kai kenan.. Malama ta nufi kitchen ta d’auko ma Ajidde abinci Ta bata tace ta zauna taci.. Saidai yau gaba d’aya jikin Ajidden a sanyaye yake babu sokancin data saba yima Malama.. Tak’i zama taci abincin ta fice sai waige waige take tana kuma duban Malamar rungume da kwanon abincin. Sauri sauri ta fice dan kar Inna Kyallu ta dawo ta tadda bata nan.. Malama Ta bita da kallo cikeda tausayawa har Ta b’ace ma ganinta.. Allah ya gani rayuwar yarinyar sosai yake bata tausayi.. ** Koda Kyallu ta isa gidan gonar sassafe tasa aka rufesu a d’aki daga ita sai Aunty Nurah, tai mata hayak’i da surace na magani.. Ta ciro wasu layu guda biyu ta bama Aunty Shemau tace a saka cikin matashin da Aunty Nuratu ke kwanciya.. Shemau Ta amsa tanai mata godiya.. Nan take sanar da Aunty Shemaun idan bata sami zuwa Washe gari ba zata turo d’iyarta ta bata maganin dan ita kusan ko yaushe fama take da masu karb’an magani.. Aunty Shemau tace babu damuwa za’ayi dik abinda Kyallu tace d’in.. Koda suka fito Daddy na parlor yana jira ya shiga yayi sallama da matarsa dan a yau d’in zai koma Abuja.. Koda Daddy yaga Kyallu tsareta da idanu yayi dan haka kurum yaji mata mai maganin bata wani kwanta masa ba amma yasan ba daga appearance na mutum bane kyaun magani.. Kuma basu san a Ina maganin Nuratu yake ba.. Idan aka dace sai maganin wannan matan yayi mata aiki.. Shemau dikda tasha jinin jikinta da ganin Daddy zaune yana jira a parlor hakan bai hanata wayancewa ta risina tana gaida Daddy had’ida introducing Kyallu mai magani.. Daddy ya amsa masu da sakin fuska ya kumayi ma Kyallu godiya.. Har zasu shige Daddy ya tsaida Shemau, ya ciro kud’ad’e da dama yace a k’ara wa mai maganin.. Kyallu ta kanne idanu tana duban tulin kud’in da aka bata.. Tuni ta Washe baki ta shiga yima Daddy godiya da addu’an girma.. Lokaci guda tana kuma gwad’a maganinta da fad’in nan da k’ank’amin lokaci zasuga canji jikin Nuratu.. Daddy yace Allah yasa haka kafin ya nufi d’akin.. Kwance take fuskarta Ta kuma yin fayau Sai hancinta da d’an bakinta kake hangowa, Ya k’ura mata idanu k’walla fal idanunsa.. A hankali ya duk’a ya d’aura hannunsa guda saman nata. Cikin rawar murya yake furta “Bansan ko na cika alk’awarin da na d’aukar ma d’anuwana ba cewa zan kula da bayansa.. I don’t know why I’m feeling this way.. Like I failed somehow.. Ban cika alk’awarin dana d’aukar ma d’anuwana cewa zan kula da bayansa ba.. It’s been 15 long years kina kwance cikin jinya ba tareda Kinsan a Ina kike ba.. And.. And Ikram..” Kuka ya hana Daddy ci gaba da magana, kansa kife gefen Nuratun, yake furtawa cikin murya irinta mai kuka “I failed to protect his family.. Na kasa kula dasu as I promised to.. Na kasa..!” Mu’azzam yai tsaye bakin k’ofa yana duban yanda Daddy ke kuka kan mahaifiyarsa yana fad’in ya kasa kula dasu.. A hankali yake takowa cikin d’akin har ya k’araso yanda Daddy ke duk’e.. Yakai hannu ya dafasa. Daddy na d’agowa da yaga Mu’azzam d’in sai ya kuma jin rauni can k’asar zuciyarsa.. A hankali Mu’azzam ya duk’a ya rik’o hannayen Daddy cikin nasa “Baka gaza ba Daddy.. What was meant to happen happened. Kuma Ka kula da bayan mahaifina kaman yanda kayi alk’awari.. Daidai da rana guda baka fasa cika alk’awarinka ba.. You’re true definition of a good brother Daddy... You’ve been taking care of us ever since my father passed.. You’ve become a father to his children and a husband to his wife wacce tin sanda ka aureta Allah ya jarabceta da jinya.. I’ve seen a lot of men wad’anda idan matansu Sun kamu da cuta irin haka har gida suke maidasu suje suyi jinya wasu ma auren ya k’are.. But bakayi haka ba Daddy.. Kai d’in ka d’auki d’awainiyar jinyarta kuma ka kula da ita daidai da rana guda baka gaza ba..” Saurin girgiza kai Daddy yai yana mai duban Mu’azzam d’in “Don’t say those words Mu’azzam dik abinda nayi nauyi ne da ya rataya a wuyana and it’s not a favor kaji koh.. Come here..” Ya k’arashe yana rungumar Mu’azzam d’in. Uncle Salman dake tsaye jikin k’ofa da ido ya tsaresu, lokaci guda ya koma da baya ba tareda ya bari sun gansa ba. ** SULEJA Tashin hankali goma da ashirin shine abinda Sadiya da ahalinta ke fuskanta, a yayinda mahaifinsu ko rufa kwanaki uku baiyi ba da mutuwa Tabawa ta kuma sakosu gaba da maganan biyan kud’inta.. Babu yanda Umma batai ba ta bari ko takaba ne ta gama idan yaso sai ta fita ta nemo mata kud’ad’enta ko wani aikin ne sai tayi ta samo mata kud’ad’enta.. Tabawa tace atafau ita bataji ba bata gani ba. Yo wani irin aiki ne ma zatayi ta samo mata kud’ad’enta idan ba Sana’ar bin maza data d’aura ‘yarta akai zasuyi Su biyata kud’ad’enta ba.. Wanann magana na Tabawa sosai ya tab’a Zuciyar Umman Sadiya.. Abinda batayi tin k’uruciya ba shine Tabawa take jifanta da munanan kalamai irin haka.. Ya zama dole Ta nemo wa Tabawa kud’ad’enta dan abin ya zama akwai tab’a mutunci da tozarci bazata bari Ta kuma traumatizing yaranta ba bayan tashin hankalin rashin mahaifinsu da suke ciki already.. Hakan yasa Umma yanke shawarin tink’aran Committee na masallacin unguwa ko da akwai irin taimakon da zasu masu su rabu da Tabawa.. Malam Liman ya gyara zama had’ida nusawa kad’an yace “Da farko nasiha zan fara maki da ita.. Ita wannan rayuwar da kuke gani duka ba yawa bace da ita, sannan dik halinda bawa zai tsinci kansa ciki jarabawa ake masa.. Bazai yuwu ace koda Yaushe mun samu abinda muke so ba.. Sannan Ko yatsunmu muka duba ba daidai bane wani yafi wani toh haka Ubangiji ya tsara mana rayuwarmu.. Wani yafika kaima kafi wani.. Kai wani arzikin lafiya ma kawai yake nema dikda d’imbin tarin dukiyar da yake dashi wanda zai iya kashe ko nawa ne domin ya samu wannan lafiyar amma bai samu ba.. Ga dukiyar Allah ya basa amma babu lafiya da zaiji dad’in dukiyar.. Kaikuma idan ka dubi kanka kaga Allah ya huwace maka wannan lafiyan sai kayi tunanin ya gama baka babban arziki.. Har kullum idan zamuke duba rayuwar na sama damu toh fah bazamu tab’a gode ma Allah da tarin ni’imomin da ya mana ba.. Amma idan muka dubi na k’asa damu sai muyi masa godiya da ni’imominsa garemu.. Shi kuma Sai ya k’ara mana domin fad’insa da yace _’Idan kuka gode Mun Ni kuma Zan k’ara maku_.’ “ Umma na matsan k’walla cikin hijabinta take jinjina kai “Haka ne Malam.. Kuma in sha Allahu mun d’auki darasi.. Ina kuma fatan masu halin kwad’ayi irin nawa abinda ya faru dani da d’iyata ya zamto izna garesu..” Kuka ya hanata ci gaba da magana Malam Liman yace “Ki daina kuka in sha Allah Committee na masallaci zatayi iya k’ok’arinta ta had’o abinda za’a iya samu a baku ku rage bashin.. Ubangiji ya dafa mana gaba d’aya..”Ya k’arashe yana mai mik’ewa ya kuma yima Umma ta’aziya kafin ya fice. Sadiya tai tagumi tana duban mahaifiyarta, ga k’annenta dake gefe har lokacin kuka suke. Hawaye suka kuma gangaro mata tana tina mahaifinta da k’alubale na rayuwa da suka fuskanta.. Inama mahaifinta zai dawo gareta da ta kasance irin d’iyar da yake so ta zama.. Amma saidai shi lokaci baya jira, idan ya wuce ya wuce kenan har abada.. Koda Malam Liman yaje ma Committee na masallaci da wannan batu suma sun tausaya ma Sadiya da mahaifiyarta dukda a baya basa k’aunar kasancewarsu a Layin.. Amma saidai kaf kud’ad’en dake asusun masallaci bai kai ko kwatan kud’ad’en da ake bin Umma da Sadiya ba.. Bazasu isa ba balle a biya masu dashi Sabida falalar dake cikin biyan bashi ga musulmi.. Haka Liman ya tara jama’a ya masu wa’azi kan falala da ladar da mutum zai samu idan har ya cire d’anuwansa musulmi daga k’unci na bashin da ake binsa ya biya masa wannan bashi.. Saidai ba’a samu wanda yace zai iya biyan bashin ba.. Ana haka saiga Alhaji Isyaku Dancanji mahaifin Sabeera Aminiyar Sadiya ya shigo, ya nemi ganawa da Malam Liman.. Bayan sun keb’e ne ya dubi Malam Liman yace “Malam naji sanarwan da kake na neman kud’i da yarinyar nan Sadiya da mahaifiyarta suke.. Zan biya masu bashin amma fah da sharad’i.. Liman ya fad’ad’a murmushi yana fad’in “Alhamdulillah.. Masha Allah.. Allah dai ya biyaka da gidan Aljannah Alhaji.. Taimakon da kake a layin nan Allah ya dad’a bud’e maka k’ofofin arziki.. Inaji mecece sharad’in naka..?” Alhaji Isyaku yace “Zan biya masu bashin da ake binsu amma fah saidai idan za’a bani auren ita yarinyar Sadiya..” Liman yai shiru yana dubansa “Alhaji kana nufi Sai za’a baka auren yarinyar ka biya masu bashin..?” “K’warai kuwa Malam Liman yanda dai kaji haka ne.. Ai dama bashin na shagulgulan Bikin yarinyar ne.. Kaga Shagali bai tashi a banza ba Malam Liman shikenan sai a d’aura aure dani..” SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *14* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Da tsananin mamaki Umma take duban Malam Liman “Malam Alhaji Isyaku fah kace.. Shine yace zai biya bashin idan za’a basa auren Sadiya.? Malam Sadiya fah k’awar d’iyarsa ce Aminiyarta ce Wanda sam baya k’aunar tarayyarsu shine zai zago yace yana sonta da aure.. Allah mai iko..” Malam ya nusa kad’an yace “Ni kaina banji dad’in cewa da yayi har sai idan za’a basa auren Sadiya ne zai biya bashin, domin kuwa naso ya biya dan Allah Allah ya basa ladansa toh amma ya kawo sharad’i sharad’i kuma shine a basa auren Sadiya..” Umma ta katse Malam Liman da fad’in “A’a Malam wannan ma bazai tab’a yuwa ba, Ko lokacin da nake ganiyan son kud’ina da abin duniya bazan tab’a bari Sadiya ta auri mutumin nan ba balle yanzu da duniyar da abindake cikinta suka fita kaina.. Yajesa mun gode da niyyan taimako Allah zai kawo mana wani hanyar amma banda auren Alhaji Isyaku..” Liman ya nusa yace “Toh shikenan dama ni ga abinda na Fad’i idan na tuntub’eku zaiji ba’asi.. Allah Ubangiji ya huwace ya kawo wani hanyar..” Umma ta amsa da Ameen Malam Liman yai mata sallama... Ta rapka uban tagumi tana mamakin halin mutanen duniya.. Lallai kaga d’an mutum ka barsa, yanzu dik kushe Sadiya da hanata k’awance da mutumin nan keyi da d’iyarsa ashe idonsa nakan Sadiyar ce.. Ashe zai zago bayan ya rabata da d’iyarsa yace zai aureta.. Oh Lallai duniyar yau Ta zama abinda Ta zama.. Wai mutum bazaiyi taimako dan Allah ba sai idan zai sami wani abu in return.. Taimako dan Allah yayi k’arancin har sai idan kaima zaka sami wani abu. Ta yaya kuwa Allah Bazai barmu da halinmu ba idan har na sama bazai tallafi na k’asa ba.. Kai Allah ka kawo mana sauk’i a wannan duniyar tamu.. Ta k’arashe tinanin nata tana mai sauk’e nannauyan ajiyan zuciya. A d’aki ta iske Sadiya ta gama lallashin Habib yayi bacci dan yaron tinda yaga yanda aka kad’e mahaifinsa akan idonsa Sai ya dinga wani irin firgita idan yana bacci yaita surutai, har sai sunyita masa addu’o’i kafin su samu ya d’anyi baccin.. Umma ta k’ura ma yaran nata idanu cikeda tausayinsu da k’aunarsu, ta k’udiri niyyan da zaran ta gama iddarta zata nemi Sana’a domin ta rufa ma kanta da iyalanta asiri.. Har kullum hannun da yake bayawar yafi hannun da yake karb’a, tayi kuskuren fahimtar rayuwa a baya da tayi tinanin Lallai sai ta hanyar namiji mace zata sami kud’i, yau da ace tanada sana’arta da zai rufa mata asiri da ba sai ta tsaya hangen abin hannun namiji ba balle har taje ta jefa rayuwar d’iyarta a tsaka mai wuya.. Juyowan da Sadiya zatai suka had’a idanu.. Murmushi suka sakar ma juna kafin Sadiya ta gyara ma Habib abin rufuwarsa ta mik’e ta nufo bayan Umma. Yanayin da taga Umman ciki ya tabbatar abubuwa sunci gaba da tafiya babu dad’i, Ta taimaka ma Umman ta zauna da k’yar saman tabarma sakamakon ciwon dake k’afarta wanda Safeenah ta kuskureta da mota.. “Umma lafiya na ganki haka..? Umma ko wani abin ne ya faru..?” Sadiya Ta tambaya cikeda kulawa tana mai duban mahaifiyar tata.. Umma ta nusa tace “Sadiya wani magana zan fad’a miki amma bana so ki d’aga hankalinki, sannan Inaso ki sani dik abinda kike so, dik abinda zai faranta miki rai nima shi nake so kuma ki sani muddin Ina numfashi Ina tareda ke a Ko menene a matsayina na mahaifiyarki kinji koh...” K’ak’aro murmushin da yafi kama da yak’e Sadiya tai “Haba Umma ki daina magana haka dik sai kina sa naji wani iri haka nan.. Bazamu sake rasa kowa ba da yardar Allah kinji koh.. Sannan Tabawa Allah zai kawo mana yanda zamuyi da ita...” Umma Ta kuma nusawa tace “Haka ne Sadiya.. Toh yanzu idan nace miki an samu hanyar rabuwa da tashin hankalin Tabawa amma bisa sharad’i shin zaki amince da sharad’i..?” Wani irin Farin ciki ne ya mamaye zuciyar Sadiya.. Ta fad’ad’a fari’ar ta tana jinjina kai take fad’in “Umma nasan sharad’in nan bazai tab’a mutuncinki ba sannan bazai tab’a nawa ba, nasan da ace zai shafi mutuncinmu ko sab’on Allah da baki Zo mun dashi ba, da kin watsar tin a inda kikaji.. Umma mecece sharad’in.? Aikatau ne zan masu babu biya ko kuwa wani aikin k’arfi zanyi.. Umma ki sanar dani ko menene zan k’ok’arta na aikata muddin Tabawa zata daina d’aga miki hankali..” Sauk’e ajiyan zuciya Umma tai cikeda tausayin d’iyar tata, saida ta nusa kafin ta kirawo sunan Sadiya cikin wane irin siga da yanayi.. Sadiya ta d’ago fuska Jiki a sanyaye wann karon ta amsa “Na’am Umma..” “Zaki iya auren mahaifin Aminiyarki..?” Dummm! Haka k’irjin Sadiya ya buga, taji batun wani irin gantsagarau wanda zatace ba don daga bakin Umma ya fito ba zasu hau sama Su fad’o da dik wanda yazo mata da wannan batu.. Mahaifin Aminiyarta.. Wacece ma Aminiyarta ai ita tama mance tanada wata Aminiya.. Kai Aminiya fah k’awa mafi kusanci ake nufi.. Wacce kuka d’auki yarda kuka aza ma junanku.. Ita ko lokacin da take Sady pretty d’inta mai son dukiya da abin duniya Ai bazataso ta auri Baban Aminiyarta ba dan idan akwai abinda tafi tsana shine cin amana.. Ita bazata tab’a cin amanan K’awarta irin haka ba.. Muryar Umma ne ya katse mata tinanin nata.. Ta d’ago tana duban Umma tamkar mutum mutumi.. “Umma wacece Aminiyata.. Umma mai kike fad’i... Ban gane komai ba Umma..?” Ta k’arashe gaba d’aya a daburce take. Umma ta jinjina kai tace “K’warai dole ki shiga rud’u amma ya zama dole na fayyace miki komai yanda mukai da Malam Liman..” Cikin tsanaki tiryan tiryan Umma ta karanto mata dik yanda sukai da Liman. Da tsananin mamaki Sadiya ke duban mahaifiyarta “Umma Abban Sabeera fah kikace, Sabeera dai Sabeera aminiyata.. Haba haba Umma.. Wllhi ni koda ace ban tsani mutumin nan ba bazan auresa ba Ko dan Sabeera.. Bana k’aunar ko ganin mutumin nan balle ace aure ya shiga tsakaninmu...Haba Umma ai akan bar halal dan kunya.. Balle ma mutumin nan Umma wllhi ayarsa yake shek’ewa cikin Abuja shisa yake tak’urawa ‘yarsa yake kaffa kaffa da ita dan kar a lalata masa ita kaman dai yanda yake lalata yaran mutane.. Saidai ya mance abinda yakeyi bashi ne kuma adashi ne da dik daren dad’ewa sai ya d’iba.. Ai dik Wanda ya faye kushe da aibata wasu shima d’in na aikatawa ne.. Bayan dik cin mutuncin da ya mana shine yanzu zai wani zago ko kunya babu yace ni zai aura.. Wllhi Allah ya sawak’e min Allah ya tsari gatari da saran shuka..” Umma ta katseta da fad’in “Nima abinda na fad’iwa Malam Liman kenan, yaje can da taimakonsa bama so Allah zai kawo mana wani hanyar.. Allah yana jin addu’an bayinsa kuma bai mance damu ba, da sannu zai yassare mana kinji koh.. Kar ma Ki saka wannan abu a ranki balle ya dameki.. Kuma kar ki nunawa Sabeera komai dan yarinyar da mahaifiyarta sunada mutunci.” A hankali Sadiya ta jinjina kai ba tareda ta iya furta komai ba dan har lokacin cikin Shock take, Wai Baban Sabeera Alhaji Isyaku Chanji ke sonta.. Ikon Allah kenan.. Kai jam’a sai kaga mutum ka barsa.. D’an Mutum sai Allah. ** Ita kad’ai sai zagaya d’akin take tana kuma duban wayarta ta rasa yama akai Barr Ameer ya kuma samun sabon layinta, layin data canza tin lokacin mutuwar Ikram.. Ta masa kashedi ya daina kiranta it’s over between them amma yak’i daina kiranta, ta kula so yake ya kashe mata aure tako ta halin k’ak’a bacin haka mai yasa zai damu da kiranta a waya har yana ce mata yasan bata tare a gidan Mu’azzam ba.. What if Barr Ameer yanada masaniya kan sak’on da aka turo mata a daren da ya gabata kafin safiyar da aka tsinci gawan Ikram.. K’irjin Safeenah yai wani irin yankewa ya fad’i.. Idan kuwa Barr Ameer yasan wani abu tabbas tasan zai dik yanda zai ya tabbata aurenta ya k’are kafin tariyarta da Mu’azzam.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ya zama dole ta tabbata Barr baisan wani abu akan wannan sak’on da ya shigo wayarta ba.. A fili ta furta “Enough Feenah.! You can’t get convicted.. After all, you’re innocent.. You didn’t kill her.. Shegen san sanin k’wak’waf d’inta shi yayi ajalinta..” Ta k’arashe tana mai cusa yatsu cikin sumarta.. Fuzar da fuci tai tana tinanin toh yanzu mai zatayi, ta Ina zata soma b’ullowa Al’amarin.. Idan Mu’azzam ya soma zarginta shikenan itakam tasan tata ta k’are.. Gaba d’aya Safeenah Ta fice a hayyacinta ko Dairy Company d’insu da take aiki a nan bata iya zuwa.. Ita yanzu babban damuwarta shine ta tabbata Barr Ameer baisan komai kan alak’arta da mutuwar Ikram ba sannan ya fice daga rayuwarta ta har abada.. Lokaci guda ta yanke shawarin kiran Barr. Bugu biyu ya d’aga kaman wanda yake jira “Mrs Mu’azzam Gamji. Matar Officer.. To what do I owe this pleasure..” Cikin tsananin huci Safeenah ke furta “Enough with your games Ameer.. Na gaji da kiran wayata da kake.. At first ka kirani ka min murnan aure na fad’a maka kar ka sake kirana amma bakaji ba.. And now ka kirani ka tayani jajen rashin tarewata gidan mijina.. Wannan ba matsalarka bace Ameer.. Na tare ko ban tare ba duk bai shafeka ba.. Mu’azzam is still my Husband and I’m his wife.. Idan munga dama zamu iya zama cikin gidanmu basai munje wani wajen ba. After all, Gidanmu gidansu Mu’azzam ne.. Kar ka mance Nida shi are first cousins so ka daina b’ata ma kanka lokaci da har kake cewa kanada sauran hope akaina.. I was never yours and I’ll never be.. Ka fahimta..?! And Remember you’re messing with the Corps wife.. You don’t want to get arrested. Do you..?” A hasale ya katseta da fad’in “Don’t you dare threaten me..!” Ya murmusa kad’an kafin yaci gaba da fad’in “And remember, I’m a lawyer. I can defend myself and easily incriminate you.. Kar ki damu ina k’aunarki Safeenah.. And I’ll never give up on you..” Yana ida fad’in haka ya fashe da dariya had’ida katse kiran.. Bibbiyu Safeenah ke gani.. Zuciyarta taci gaba da tsinkewa.. Da dafe dafe ta zauna saman gado, wani irin rawa jikinta keyi.. Ta kuma duban wayarta jikinta naci gaba da rawa.. Tama nemi kukan Ta rasa sai tsananin rawa da illahirin jikinta ke mata.. Har ji take Tamkar zazzab’i ke shirin sauk’o mata.. Ashe kuka ma rahama ne dan ta nemi kukan ta rasa.. Tsoro take kar Ameer ya zamto silan mutuwar aurenta.. Ya zama dole ta kare aurenta at any cost. She needs to be with her husband idan har tana so ta gyara aurenta. Amma mijinta baya nan yana can Fufore dan saida tayi waya da Assad taji Ba’asin abinda ya sami Mu’azzam ya tafi yai abandoning aikinsa tinda Ta sansa kan batun aikinsa.. Sanin cewa Safeenah matar Mu’azzam ce da kuma magiyar data tayiwa Assad d’in ya kuma san halin Mu’azzam d’in ba lallai ya sanar da ita an dakatar dashi na wani d’an lokaci ba yasa shi sanar da Ita suspending nasa da akai.. Tai zaune saman gado tana juya wayar cikin hannunta “What do I do now.. It’s too bad he got suspended.. But he sure had it coming da wannan zafin zuciyar tasa.. Yanzu idan inaso na kasance dashi saidai na bisa cen kenan.. Oh shitt.. I don’t like it there gaskiya bazanje ba.” Muryar Meema ce ya katseta “You have to.. Ya zama dole kije Adda Feenah and be with your Husband idan har kinaso ki sami kusanci da mijinki.. If not you’ll end up losing him..” A zabure Safeenah ke duban Meema. Nunata take da tsananin mamaki “How long have you been standing there.. Did you hear everything I said..?” Tai tambayar idanunta na firfitowa waje.. Meema taci gaba da takowa cikin d’akin murmushi saman fuskarta “Why.. Did you say something that I shouldn’t hear..?” Murmushin yak’e Safeenah tai tace “Sabida na sanki da shegen gulma ne da shiga abinda babu ruwanki shiyasa.” Meema ta murmusa tace “That’s my personality I guess. And I’m sure you’re used to it.. Addah Feenah you need to follow your husband.. Shawari nake baki..” Hararata Feenah tai tace “Last time I check komai lalacewa yai da nabi shawarinki..” D’an tab’e baki Meema tai tace “I’ve done my part tinda na baki shawari, it’s up to you Ki d’auka ko kar ki d’auka..” Ta k’arashe tana duban Safeenar murmushi saman fuskarta. Lokaci guda tasa kai zata fice. Feenah ta dakatar da ita da fad’in “We are going together Meema.” Meema ta zaro ido waje tace “Wa ni. Spare me Adda Feenah.. Wann mijin naki lamba d’aya ne a rashin mutunci. Bansan mai zai aikata mana ba wann karon. Chabd’i. Who knows what he might do to us.. Inaga kuraye zai kwance mana wann karon.” Feenah tace “Kar ki damu we’ll act smart wann karon. Yanzu mai zamuce wa Mommy ga Daddy ma yau na hanya.. Nasan definitely Mommy bazata barmu mu tafi ba..” Meema ta murmusa tace “Haba Adda Feenah kar ki badani mana, Keda kike da dalilin zuwa k’wakk’wara. Kawai cewa zakiyi mijinki ne yace yana so kije can ki samesa and yana jin kunya bazai iya kiran Daddy ko Mommy ya fad’I ba.. He wants you to have your first honeymoon a garinku..” Ta k’arashe tana kashe mata ido.. Pillow Feenah ta jifa mata tana fad’in “Zaki sani ne.. Well shawarinki yayi, zan fad’awa Mommy Mu’azzam yana so naje Fufore and inaso ke kuma ki rakani.. Ita kuma Mommy tasan mai zata cewa Daddy.. Nasan bazata yarda muje ba amma sai mun fama arranging komai mu sanar da ita.. Ke sai mun isa ma mu sanar mata dan Nasan babu yanda ta iya idan taji Muna cen dole kawai tasan abinda zata nemo ta fad’awa Daddy..” Meema ta murmusa had’ida mata jinjina da babbar yatsa “You’re genius Adda Feenah.” Ita kaw Feenah sai murmusawa take tana jin yau d’in ta tsara zance ya tafi daidai. ** Koda Malam Liman ya samu Baban Sabeer da batun cewa Sadiya da mahaifiyarta basu amince da buk’atarsa ba huci ya dingayi cikin zuciyarsa yana ayyana bai tab’a neman abu ya rasa ba balle ma mace, bazai fara akan Sadiya ba.. Dik yanda zai Sai ya tabbata ya aureta.. Koda ita da mahaifiyarta basa so.. Tabawa ce ta fad’o masa ransa, ya saki wata irin muguwar murmushi kafin yai sallama da Liman yace idan sun canza shawarinsu shi dai yana nan akan bakansa, zai sauk’e masu nauyin bashi a matsayin Sadakin Sadiya.. Baban Sabeera yana ficewa daga Zauren Malam Liman bai zarce ko ina ba sai gidan Tabawa. Tabawa taji mamakin jin Alhaji Isyaku na sallama da ita. Ta fito mamaki fal saman fuskarta, bayan Ta masa gaisuwan mutunci irin wanda ake ma masu abin duniya.. Ta kuma risinawa tana fad’in “Alhaji inji dai lafiya koh, ko wani abin ne ya faru..?” Alhaji Isyaku ya gyara babbar rigarsa yana fad’in “Toh lafiya ne ya kawo haka kuma babu komai sai alkhairi..” Tabawa ta Washe baki dan a tinaninta Alhaji Isyaku zaice yana sonta ne bayan tsawon shekarun data kwashe a unguwar tana zaman kanta. Tabawa ta shiga sanne kai tana mad’e. Alhaji Isyaku yai gyaran murya yace “Nasan kina so a biyaki kud’ad’en da kike bi bashi.. Musamman wanda kike bin iyalan Malam Ibrahim mai rasuwa..” Jikin Tabawa ya d’anyi sanyi, ta dubi Alhaji Isyaku tace “Toooh zaka biya masu ne Alhaji..?” “K’warai kuwa zan biya masu amma fah inada sharad’i..” Tabawa ta dubesa da mamaki wannan karon “Alhaji sharad’i kuma ni da hakkina.. Hakkin d’imbin jama’a dake kaina ace sai an gindaya min sharad’i a biyani.. Wannan batu ma ai hankali bai kama ba.. Haba haba dai jama’a.. Wllhi Alhaji ina ganin mutuncinka a layin nan dan rufin asirin da Allah yayi maka, kar kasa na daina gani.. Ka gode ma Allah wannan maganar da dare kazo min da ita dan da ace da rana tsage tsage kazo min da ita da na daina ganinka da wannan mayafi na mutunci da nake ganinka da Ita ehe..” Ta k’arashe tana jijjiga had’ida huci.. Alhaji Isyaku ya murmusa cikeda jin dad’in halin rashin mutunci da Tabawa keda shi yasan bazai sami matsala daga wajenta ba. “Hajiya Tabawa kenan.” Hannu ya zira cikin aljihunsa ya ciro kud’i bandir ‘yand’ari bibbiyu ya mik’a mata “Ungo karb’i wannan..” Tabawa ta k’yalla idanunta akan kud’i sai kuma tai wani murmushin rainin hankali tace “Haba Alhaji nice za’a min biyan ‘yan tasha a bani kud’ina gutsiri gutsiri.. Ko kasan kullum k’Arya nake wa mutane masu kaya cewa Kaya yana saman ruwa bai iso ba.. Ni fa na gaji da k’anan Murya. Wllhi bazan karb’i kud’i kad’an kad’an ba.. Dubu ashirin fah kake mik’o min..” Alhaji Isyaku ya murmusa yace “Wataran ma Daloli za’a mik’o miki.. Yanzu ki amshi wannan kiji na Menene..” Tabawa ta dubesa a yatsine sanda yaci gaba da fad’in “Wnn kud’ad’e da kike gani ba bashin da kike bi bane.. Sune mabud’an hanyar da zaki bi Ki sami kud’ad’enki..” Tabawa ta dubesa da mamaki, hanu har na rawa Ta amshi kud’ad’en. Alhaji Isyaku yaci gaba da fad’in “So nake ki saka masu pressure.. Ki matsa masu ki tak’ura masu.. Idan ta kama kice zaki d’ebo masu ‘yansanda kuma zaki maka Su a kotu. Dik yanda kud’ad’enki suka shiga suka fita su nemo su baki. Ni kuma na miki alk’awarin baki wasu kud’ad’en bayan bashinki da za’a biya..” Mamaki ya cika Tabawa Ta shiga Washe baki tana fad’in “Idan dan wannan ne kar kaji komai Alhaji.. Wllhi rashin mutunci yanzu zan soma masu irin wanda ma ban masu a baya ba.. Kuma babu ubanda ya isa ya dakatar dani..!” Alhaji Isyaku ya murmusa yace “Da kyau Tabawa.. Sai naga sakamako..” Daga haka sallama sukai shida Tabawa ya wuce yanda ya aje motarsa.. ** Kyallu ta gyara tsayuwarta sosai tace “Kina jina..” Ajidde dake duk’e gabanta Ta jinjina kai a hankali alamun eh. “Zakije wannan gidan kuma zaki rufe kanki a d’aki da wannan nakasesshiyar matar, idan ta kama ki shige har cikin drawer kin binciko mana ‘yankunnayen zinari da a warwaro ne zakiyi.. Wannan karon kar ki dawo min gidan nan babu komai Ajidde.. Ke idan ta kama ki saci jiki ki shiga sauran d’akuna nan ne toh fa sai kin shiga kin sato mana abin duniya da ‘yankud’ad’e kinji koh..” Ta ciro wani laya cikin bujenta Ta mik’a ma Ajidde “Ungo nan amsa.” Ajidde Ta mik’a hannu Ta amsa da k’yar.. “Layar zana ce da zaran kinga za’a kamaki kafin su shigo cikin d’akin sai ki matsata da k’arfin gaske yanda bazasu ganki ba..” Nan ma Ajidde jinjina kai tai kafin Kyallu Ta shureta da k’afa tace “Tashi ki daina kallona da wannan zuru zuru idanun naki..” Ajidde Ta mik’e da k’yar rataye da jakan maganinta Ta fice.. Tana tafe tazo dai dai k’ofan gidan Malama Hafsah, tai tsaye tana duban k’ofar gidan.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *15* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* K’arfe shida na safe sukaji ana bugun k’ofan gidan kaman za’a b’alla.. Bugu ake da k’arfin gaske ana jijjiga k’ofar, bai tsaya a bugun k’ofa ba tuni aka soma jefo duwastu cikin gidan. Umma dake bisa sallayarta wanda tinda tayi sallan asubahi bata tashi kan sallayar ba tana zaune tana Lazimi da kai kukanta ma Sarki da babu kamansa, majib’icin lamiransu, Mai mulkin sammai da k’assai wanda babu abinda yafi k’arfin ikonsa da buwayarsa.. Babu shiri Umma ta mik’e tana mai linke abin sallarta, Ta aza cazbahan dake hannunta saman abin sallar kafin ta nufo waje.. Kusan cin karo sukai da Sadiya wacce Ta fito daga kitchen tana kalata masu abinda zasuyi karin kumallo dashi. “Umma bugun k’ofa ake..” Batakai aya ba aka kuma jefo wani Dutsen sai a goshin Ashiru da fitowarsa kenan yana mutsuka ido. Aiko nan ya saki k’ara yana rik’e goshinsa. A tare Sadiya da Umma suka nufosa dan tuni ya kwanta wajen yana dafe da goshinsa yake fad’in “Kaina kaina Umma.. Wayyo Allah kaina.!” A fujajan Sadiya taje Ta nemo tsumma ta d’aure masa goshin nasa dan k’ok’arin tsaida jinin.. Umma kaw babu shiri ta nufi k’ofa ganin basu fasa abinda suke aikatawa ba. Tana bud’e k’ofar ta hangi Tabawa na tsaye wasu k’artan maza guda uku sun sakata a tsakiya ga duwastu a hannunsu. Sai faman sakin huci Tabawa take. “Yauwa kunaji ku shiga ku fito da dik abinda yake mai amfani ne a cikin gidan.” Tabawa tace tana duban k’artan mazan. Da tsananin mamaki Umma ke dubanta “Amma Tabawa bakida mutunci.. Shin wace doka ce ta baki daman ki shigo har cikin gidanmu kici mana mutunci dan kina binmu bashi.? Jifan da kika tashemu dashi har kikaji ma d’ah na ciwo bai isheki ba shine zakice ma wad’annan K’artan banzan su shiga gidan mata mai takaba su kwaso miki kayanta.. Anya Tabawa akwai zuciya cikin k’irjinki.. Anya zaki wanye da duniya lafiya..?” “Toh sai ki hani wanyewa da duniyar lafiya idan kece mai Ita... Ke har zakiyi ma wani wa’azi. Yaushe ma kika tuban.. Yaushe kika daina zuwa wajena kina rok’ona Allah Annabi na samo ma d’iyarki manyan Alhazawa shine yanzu dan duniya ta juye daku zaki bud’e tsartsaman bakinki kice zaki min wa’azi.. Toh wama zai saurari wa’azi daga bakinki.. Koda shike ba laifinki bane ke d’in dama ai tsintacciyar mage ce baki da dangi sai na bariki.. Kai Over Wai mai kuke jira ne.. Ku shige kuyi aikin da na sakaku.” Suka amsa da Toh Hajiya Tabai. Umma bata iya furta komai ba Sai hawaye dake ambaliya a fuskarta. Sadiya ce Tai k’ebebe bakin k’ofar ta hanasu shiga “Babu Wanda ya isa ya keta mana haddi ya shige mana gida ba tareda izinin mahaifiyata ba.. Hajiya Tabawa kar ki bari na maka k’ararki a ofishin ‘yansanda.. Tin muna saida juna ki tattari body guards d’inki ku b’ace mana a k’ofar gida bamu neman tashin hankali..” Shewa Tabawa tai harda rangad’a guda “Tashin hankali ai cikinta kuke dumu dumu..” Ta k’anne ido tana nuna Sadiya da yatsa “Ke k’aramar maras kunya ni kike ma barazanan zaki kai k’arata wajen ‘yansanda.. Cikin ni da ku wanene yake da abin kaiwa k’ara wajen ‘yansanda.. Ga fili ga doki maza.. Zo ki shige kije kikai k’arata wajen ‘yansanda.. Nasan dikda asarar da na maku bazai kwatan kud’ad’en da nake binku ba... Jeki Sadiya jeki ki kai k’arata ni kuma nayi alk’awarin jaza maku wulak’ancin da ban maku ba a baya.. Over ku shige nace ku tattaro.. Idan bata matsa maku a hanya ba ku had’a da Ita dan nasan zata maku amfani ko rage dare kwayi da Ita dama sauran titi ce..” Wannan karon Umma ce ta dakatar da Tabawan, cikin tsananin huci take nuna Tabawan da yatsa, lokaci guda take fad’in “Koda wasa kar ki sake aibata d’iyata a gabana.. Idan kuma ba haka ba..” “Idan kuma ba haka ba Sai k’ak’a..?” Tabawa tace tana ci gaba da jijjiga “K’arya aka mata Ko ba abinda ta saba yi bane..?” Hawaye ne kawai suke gangarowa daga idanun Sadiya da Ta tare k’ofar gidansu cikin tsananin huci.. Jin kalaman Tabawa take kaman ana dab’a mata wuk’a tsakiyan k’irjinta.. Yayinda su Over ke binta da mayen kallo suna wani shafa hab’a suna fad’in “Kuma fah wllhi dama ta jima a ranmu.. Muna ganin yanda masu manyan motoci suke safara a unguwar nan suna kwasanta... Kawai dan bamuda kud’i ne da muma mun jima da d’anata ai..” Suka k’arashe suna masu sakin shewa irin na cikakkun ‘yan daba.. Daidai lokacin Alhaji Isyaku ya doso lungun yana aza babbar riga yake fad’in “Yaya yaya kai yaya dai meke faruwa ne Wai..?” Kafin Alhaji Isyaku ya k’araso ‘yan daban Tabawa suka aune a guje dan sunsan wanene Alhaji Isyaku yanzu Sai ya kwaso masu ‘yansanda yasa a tafi dasu. Tabawa sai huci take tana kuma balabala wutan masifa. Alhaji Isyaku ya k’araso yana tambayan Tabawa ba’asi tamkar baisan komai ba.. Tabawa kaw nan taci gaba da masifa tana fad’in “Toh Wai biya masu zakayi ne Alhaji da zaka wani Zo ka dakatar dani.. Rashin mutunci yanzu na fara ehe idan har baza’a biyani kud’ad’ena ba..” Ta maidoda dubantaga Umma dake tsaye Jiki a matuk’ar sanyaye tana hawaye, lokaci guda Ta kad’a ‘yar yatsarta tace “Kunci sa’a wannan karon.. Had’uwar mu na gaba sai yafi wanann muni idan har baku biyani kud’ad’ena ba..” Ta k’arashe tana mai janye mayafinta fuuu ta wuce.. ‘Yan lungun kaw kaman ba safiya ba Sai lek’e ake anyi cincirindo ana bama ido abinci.. Alhaji Isyaku ya risina yana bama Umma hak’uri kan abinda ya faru, idanunsa rabi naga Sadiya wacce maganganun ‘Yan daban Tabawa ya sanyata zama sukuku da ita, gaba d’aya bama ta fahimci su waye a wajen ba, maganganun ne kurum suke Yawo a kwanyarta da dodon kunnuwanta.. Irin kallon da illahirin mutanen unguwarsu ke mata kenan, Fanko, sauran kwalta. Bata tab’a yin danasanin rayuwar da tai a baya na rashin kamun kai irin yau ba.. Ashe mutunci yafi komai.. Mutunci yafi kud’i.. Yau da ace ta rik’e talaucinta ta tsaya a matsayin da Ubangiji ya ajeta da babu wanda zai dubeta ya mata irin wannan mummunan k’azafi maras dad’in sauraro.. A nasu tinanin samaruka da suke d’aukanta a manya motoci mutuncinta take saida masu, yanda take shigan gayu ta rik’e babban waya ita ba d’iyar kowa ba dole suyi tinanin mutuncinta take saidawa ta samu. Abinda bata tab’a kuskuran koda aikatawa ba.. Ta lumshe idanunta hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro mata. Kaman Umma tasan tinanin da take tai saurin k’arasowa Ta rik’e hannunta tana girgiza mata kai take furta “Komi kikayi sai an zageki a duniyar nan.. Kar ki bari maganganun su ya dameki kinji koh..” Alhaji Isyaku na tsaye gefe ya kannare idanu yana dubansu. Sadiya bata iya furta komai ba har lokacin saima duban Umman da take cikin wane irin yanayi. Ana haka Ashiru ya fito rik’e da kansa dake jini har lokacin kuka yake.. Kukansa ne ya dawo da hankalin Sadiya, tai saurin ta nufesa tana tambayarsa ko kan nasa ke masa ciwo. Ga mamakinta Alhaji Isyaku ne ya k’araso yana fad’in “Subhanallahi.. Garin yaya haka Ta faru.. Wannan Ai sai an kaisa asibiti..” Da tsananin mamaki take duban Baban Aminiyar nata yayinda mak’ota ‘yan lek’e suka ci gaba da bama ido abinci wasu na k’usk’us ganin yanda Alhaji Isyakun duk ya wani susuce kan abinda ya samu su Sadiya saikace ba shi bane kwanaki yazo masu da ‘yansanda.. Tabbas akwai wata a k’asa.. Ba tareda Sadiya tace komai ba ta shiga janyo hannun k’aninta tana fad’in “Umma zan kaisa chemist d’in Ema..” Alhaji Sabi’u yai karaf yace “A’a ai bazai iya tafiya kan k’afafunsa ba jini ya zuba jikinsa.. Motata na bakin layi barin d’aukesa in kaisa..” Umma tai saurin girgiza kai tace “A’a Alhaji.. Kawai kaje mun gode Sadiya zata iya kaisa.” Alhaji Isyaku bai tsaya sauraron Umma ba ya sunkumi Ashiru yana fad’in “Haba dai Umma ai ciwo irin haka da zuban jini ba’a wasa..” Tuni ya shige da Ashiru rungume cikin hannunsa yana masa sannu.. Daga Umma har Sadiya da tananin mamaki suka bi bayan Alhaji Isyaku da kallo babu kaman Sadiya wacce ta kuma komawa tamkar mutum mutumi.. Wai Abban Sabeera da baya k’aunan ganinta da Sabeera shine ke wannan rawar k’afar duk dan sabida Ta yarda da aurensa.. Ikon Allah Wai dama haka mutane suke ne.. Lallai mutumin nan yakai mak’ura a rashin kunya.. Babu kunya har na kiran mahaifiyarta da Umma.. Tabd’i.! Wannan abu da matuk’ar mamaki yake.. Duban juna sukai itada Umma cikinsu babu mai iya cewa komai sai tsananin mamaki da ya lullub’esu.. Umma ta kamo Sadiya Ta maida k’ofar gidan Ta tura dan har lokacin ‘yan lek’e basu daina ba.. Su duka biyun sukuku suka nufo tsakar gidan babu mai iya cewa komai dan har lokacin mamaki bai sakesu ba.. Sadiya ta taimaka ma Umma ta zauna nan tsakar gidan saman tabarma.. Sauk’e nannuyan ajiyan zuciya Umma tai tace “Hmmmm Ikon Allah..! Lallai a gaisheda namiji..” Umma tace tana kuma canza position d’in taguminta a karo na biyu.. Sadiya kam tsaban mamaki tama rasa bakin magana. Kitchen kawai ta nufa yanda take jiwo k’aurin girkin data d’aura alamun ya soma k’onewa.. Bayan kaman shud’ewan awa guda saiga Ashiru ya shigo rik’eda robar Ice cream yana sha ga goshinsa an rufe da bandage. Baban Sabeera na biye dashi hannunsa nik’i nik’i da manya manyan ledodi shak’e da kaya. Bakinsa har kunne ga malum malum d’insa dik sun sauk’e sun rufe ledar.. Tsaban takaici Sadiya mik’ewa tai Ta shige d’aki dan bazama ta iya duban fuskarsa. Umma na nan zaune tsakar gidan saman tabarma Ashiru ya k’araso ya zauna gefenta sai lasar Ice cream d’in yake. Shafa kansa Umma tai tace ya kan naka. Ya daina ciwo.?” Ya jinjina mata kai yana bud’e ledar biscuit d’in dake d’aya hannunsa. Umma ta Shafa kansa tace “Tashi ka shiga ciki koh ka bamu waje.” Ya mik’e yana jinjina kai.. Yana shigewa Sadiya ta fuzge tarkacen da ya shigo dashi tai watsi dasu. Kuka ya shigayi yana bori yana fad’in Maiyasa ta yar masa abinsa.. Ko takan kukan Ashir batabi ba ta shige d’aki zuciyarta na mata d’aci. Umma da Alhaji Isyaku dik sunji abinda ya faru a kunnuwarsu.. Dikda jikin Alhaji Isyakun ya d’anyi sanyi bai fasa sanar da Umma buk’atarsa na son auren Sadiya ba.. Umma Ta murmusa cikeda takaici “Alhaji da ka daina wannan wahalan dan hukunci dai mun riga mun gama yankewa daga ni har Sadiya.. Kaje mun gode da niyyan taimako.” Alhaji Isyaku yace “Baki fahimta ba Umma..” “A’a ni dan Allah ka kirani da Uwani menene wani Umma.. Kaga Alhaji Takaba nake ba don tashin hankalin da muke ciki ba Ko barinka ka shigo gidan nan bazanyi ba.. Mun gode da kai Ashiru asibiti da kai dan Allah ina rok’onka ka tashi ka tattari kayyakinka ka tafi bamu buk’ata kuma kar ka sake dawo mana.” Alhaji Isyaku ya murmusa kad’an yace “Umma kenan.. Barin fad’a miki kuna buk’ata na..” Da mamaki Umma ke dubansa. Alhaji Isyaku ya murmusa yana mai jinjina kai “ K’warai kuna buk’atana Umma.. Ya kamata ki sake tunani akan wannan al’amari.. Ki tuna makomar rayuwarku musamman yanzu da babu mahaifin yaranki.. Ki tuna halin rayuwa da zaku fuskanta.. Shin kina tunanin Sadiya zata samu miji ne bayan duk abubuwan da suka faru..? Kindai ji da kunnuwanki irin maganganun da mutanen unguwa keyi akan d’iyarki.. Kina tunanin akwai wanda zaizo ya aureta a haka..?” Ya kuma kannare idanu yana kuma duk’ar da kansa yace “Amma ni zan biya maku bashinku sannan zan auri d’iyarki na d’auketa daga garin nan, zan kaita can da nisa yanda babu wanda ya santa, gaba d’aynku ma zaku bar nan zaku koma sabon waje ku soma sabuwar rayuwa a can yanda babu tashin hankali babu komai..” Umma da hawaye ke gangaro mata kafin takai ga furta wani kalma suka jiyo sallama daga waje.. Babu shiri Ta mik’e dan ba muryar kowa bane face Aminu dillalin da ya basu hayan gidan da suke ciki.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai Umma ke nanatawa cikin zuciyarta.. Ta d’aga idanu tana duban glasses na window da Tabawa da ‘yandabanta suka fasa.. Umma murya na rawa take fad’i da Aminu “Malam Aminu Barka da Safiya..” “Uwani ba wannan ya kawoni ba.. Zuwa nai dan na tabbata Kun fice daga gidan nan. Bazan d’auki asara irin haka ba.. Zamanku a gidan nan babu alkhairi dama baku biya kud’in hayan bara ba ga na bana.. Sabida mutuwar mijinki yasa na d’an d’aga maku k’afa. Nayi niyyan maku mutunci na barku ku zauna har ki ida takabanki kafin na sallameku amma Tunda abun ya zama haka gaskiya zaku tattara ku fice a gidan nan dan amana Alhaji ya bani.. Tinda nake masa dillancin gidajen hayansa a unguwar nan bamu tab’a samun matsala ba.. Bazan fara akanku ba, na kula masifa da tashin hankali bibiyarku suke Dan haka kawai ku biya kud’in hayanku ku k’ara gaba tin kafin Alhaji Sadi yaji wannan batu..” Cikin rawar murya Umma ke fad’in “Malam Aminu dan Allah kai hak’uri ka taimakemu.. Ka rufa mana asiri yanda Allah ya rufa maka.. Idan muka tashi a nan bansan Ina zamuje ba.. Dan Allah kaji tausayinmu.. Ka bari Ko Takaban ne na gama.. Inada yara Malam Aminu bansan ina zan kaisu ba idan muka tashi a nan..” Girgiza kai Malam Aminu yai yana duban wani gefen dan karma Ta basa tausayi “A’a Uwani.. Gaskiya bazan iya ba.. Gidan nan nima amana ce a hannuna, kawai ki daina rok’ona dan bazai yuwu kuci gaba da zama a nan ba.. Maganar gaskiya kenan..!” Ya k’arashe yana mai jaddada maganar tasa.. Alhaji Isyaku dake gefe gyaran murya yai yace “Aminu kayi hak’uri kar ka tashesu.. Ni zan baka kud’ed’en da ake binsu zan kuma biya damages d’in da Tabawa tayi ma gidan.. Mu k’arasa gidana ka amshi kud’ad’en..” Umma baki sake take duban Alhaji Isyaku, Ta rasa wanne zatayi dan batada bakin maganar a halin yanzu.. Tana ganin Alhaji Isyaku da Aminu suka wuce Aminu yana fad’in “Wllhi ba don kai ba Alhaji saidai su bar gidan nan a yau dan na lura tsautsayi ke bin ahalin..” Juyowan da Umma zatai taga Sadiya na tsaye bayanta hawaye na bin fuskarta.. Su duka biyun babu wanda ya iya cewa komai sai rungume juna da sukai had’i da sakin kuka mai ban tausayi.. ** Hindu ce taima Ajidde iso zuwa parlorn Aunty Nuratu. A nan suka tadda Inne harmada Aunty Shamau. Ajidde ta risina ta gaishesu sai kalle kallen kayan alatu take wanda aka k’awata d’akin dasu. Tab lallai da ace zata iya kwashe wannan kaya takaima Kyallu da ta gama saye zuciyar Kyallu da imaninta.. Yanda take kalle kalle tana d’aga kai yasa Shemau zuba mata idanu fuska a yatsine “Ke.!! kiyi abinda ya kawoki ki tafi kin tsaya sai faman kalle kalle kike..” Tsawan da Shemau ta daka mata saida ya sanyata zabura Ta k’ame waje guda. Inna kaw a hasale Ta katse Shemau da fad’in “Haba Shemau ki bita a hankali mana.. Meye abun fad’a a nan inyi. Baki ganin yarinya ce..” Shemau Ta d’an sassauta murya tace “Inne babu wani yarinta muguwar k’auyanci ne kawai..” “K’auyanci.? Ked’in yaushe ne kika waye..! Koda wasa ni Kinsan bana d’aukan wulak’anta d’an Adam.. Ki k’yale yarinya tayi aikinta a natse, Zo ki fice ma bansan zaman mai kike a nan ba..” Shemau ta d’an b’ata fuska ta fice ranta baiso ba Inne naci gaba da sababi.. Ajidde taima Shemau gwalo cikeda jin dad’in bayanta da Inne tabi... Mamaki ya cika Shemau dan taga sanda Ajidde ta mata gwalo harda kashe mata ido guda.. A ranta tace lallai wannan yarinya sai ta gyara mata zama. Tana ficewa Ajidde ta saci kallon Inne saidai itama Inne ita take duba murmushi saman fuskarta. “Taho muje.” Inne tace sanda ta mik’e ta nufi k’ofar d’akin da Aunty Nuratu ke kwance. Ajidde tabi bayanta rungume da jakar maganinta still sai kalle kalle take tana k’are ma gidan kallo. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *16* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Suna ficewa daga lungun Alhaji Isyaku ya mik’a ma Aminu hannu saka tafa yana sakin muguwar dariya. “Kai Aminu naji dad’in yanda ka masu barazana, na tabbata yanzu basuda yanda zasuyi face su amince dani.” Aminu ya dafe kud’ad’ensa yana k’irgasu yake fad’in “Toh kai d’in ai bana wasa bane Alhaji. Na gode K’warai. Idan kanaso na koma gobe ma zan koma na kuma masu barazana.” Alhaji Iskyaku ya kuma aza babbar riga yana sakin dariya “Aminu Aminu.. Ai bayan abinda ya faru yanzu dole zasu amince dani dan idan ba haka ba basuda mahalli, kaga basuda sauran zab’in da ya wuce su amince dani.” Suka kuma k’ek’yata dariya Aminu na kuma godiya, nan yai sallama da Alhaji Isyaku ya wuce. ** Tinda Inne ta tura k’ofar d’akin gaban Ajidde ke yankewa, batasan mai zata gani cikin d’akin ba amma kam zuciyarta ya tsananta bugawa. Bugun zuciyarta ya k’aru sanda Ta hango matar dake kwance saman gado idanunta a lumshe. Sumarta da yake tamkar na Indians ya rufe b’angaren fuskarta. Fuskar nata yayi fayau irinta marassa lafiya. Dan koda gani ba wata fara bace can tsananin Jinya ne ya sanya fuskar nata yin fari. Saidai ga dukkan alamu tanada Yalwan suma irin mai tsananin tsantsin nan.. Ajidde taci gaba da takowa a hankali tana jin zuciyarta na wani irin fuzga tana duban matar. Kyallu tasha kwantar da majinyata a gidanta tana masu magani da rawan Bori wanda akasari mutuwa suke amma ko kusa bata tab’a karo da matar da ganinta ya mugun raunana zuciyarta irin wannan matar ba. Taci gaba da takowa zuwa gadon da matar ke kwance bisa. Inne na hankalce da ita har ta k’araso. Ganin ta zubawa Aunty Nuratu idanu Ta kasa janye idanunta yasa Inne gyaran murya ta soma fad’in “Shekaru goma sha biyar kenan tana kwance haka. An gwada magunguna da dama, anje k’asashe da dama amma babu wani abinda yake canzawa haka za’a hak’ura a dawo da Ita.. Mun yanke shawarin dawowa gida ko Allah zaisa a dace.” Ajidde tasa hannu Ta share hawayen da taji na ziraro mata. Inne ta kuma dubanta tace “Ban tambayeki ba. Ya sunanki.?” Ajidde ta d’ago tana duban Inne “Suanana Ajidde.” “Ajidde.” Inne ta nanata, sai kuma ta saki murmushi tace “Ina fata maganinki ya mana aiki Ajidde.. Ina fata Ubangiji yasa mu dace da maganinki.. Allah ya nufa maganin Nuratu na cikin tafin hannunki.” Ajidde Ta d’ago manyan idanunta da suke farare k’al masu gauraye da hawaye tana duban Inne dasu. Bata iya furta komai ba Sai duk’awa da tai gaban gadon tana k’ok’arin bud’e jakan maganinta. “Amm Hajiya ko zan d’an sami k’aramar kwano.?” Ajidde ta tambaya tana duban Inne. Murmushi Inne Ta sakar mata Tace “Ki kirani da Inne kinji koh..” Ajidde ta maida mata martanin murmushin tana mai jinjina kai tace “Toh Inne..” Inne ta kuma murmusawa kafin ta bud’e murya tana kiran Hindu. Hindu ta shigo cikeda risinawa tana fad’in “Gani Inne.” “Kije ki kawo mata kwano k’arama.” “Toh Inne.” Hindu ta amsa tana mai ficewa. Ajidde tai zuru tana jiran taga ko Inne zata fice amma bata fice ba, dik addu’an da take cikin zuciyarta matar ta fice daga d’akin domin ta gudanar da abinda Kyallu ta turota tayi amma tak’i ficewa. Har Hindu ta k’araso da k’aramar kwano ta mik’a ma Ajidde. Ajidde ta amsa tana mata godiya. Har lokacin dai Inne na zaune saman kujera mai kallon gadon Aunty Nuratun Ita kaw Ajidde tana zaune gaban gadon tana k’ok’ari ciro had’in maganin.. Wani ruwa cikin gora irin wanda ake fafewan nan ta ciro.. A hankali ta soma zuba ruwan cikin kwanon.. Saida ta ida zubawa kafin ta ciro had’in maganin tana tina bayanan yanda ake had’a maganin daki daki.. Tana ida had’a maganin ta rik’e cikin hannuwanta guda biyu tana duban matar dake kwance, hannayenta sai rawa suke, zuciyarta na wani irin tsinkewa. ‘Ke Ajidde kiyi k’ok’arin saita kanki idan ba so kike asirinki ya tonu ba.’ Ta fad’i haka cikin zuciyarta. Ta d’an juyo ta dubi Inne wacce itama Ajidden take duba “Inn Inne nace Ko za’a d’an tallafa mun kanta zan bata magani." Dai dai lokacin Mu’azzam yai sallama ya shigo, kayan training ne jikinsa, ga dukkan alamu daga morning jugging ya fito. A tare Inne da Ajidde suka dubi mai sallaman. Zuciyar Ajidde yai wani irin yankewa, k’iris ya rage bata tintsirar da ruwan maganin dake rik’e cikin hannunta ba, dikda ba da wannan shigar ta gansa ba fuskarsa bai b’ace mata ba, tana tuno sanda ya nunata da bindiga daga yanda yake a saman bishiya. Gaisawa Mu’azzam yake da Inne amma Ajidde bata janye idanunta daga dubansa ba. Har saida Inne tace “Yauwa Modibbo na tinda ka shigo sai ka taimaka mata ta bawa Nuratu maganinta dama zan kira Hindu ne tinda ni banida k’arfin d’agata amma tinda ka shigo sai ka taimaka mata.” Mu’azzam ya juyo yana duban yarinyar da zata bawa mahaifiyarsa magani, K’uri yai mata yana so ya d’ago a ina yasan fuskar tata.. Taso ta masa kamanni da fuskar da ya sani amma ya kasa tuna ina yasan fuskar. Haka kurum yanayinta yai masa Zubi dana criminals abinka da wanda ya saba cin karo da masu laifi.. Shi bama wannan ba mamaki yake Wai wannan k’aramar yarinyar ce zata bawa Maminsa magani..? Jiyo muryar Inne da yai tana fad’in ya tallafo kan mahaifiyarsa a bata magani kar lokaci ya k’ure ya dawo dashi daga duniyar tinanin da ya tafi. A hankali yake takowa har ya iso kusan Ajidde.. Ajidde dai sai kauda fuskarta take alamun bataso mutumin nan ya ganeta. Idanunsa naga Ajidde yake k’ok’arin tallafo kan mahaifiyarsa. Dik iya tinaninsa dan ya tina a ina yasan wannan fuskar ya kasa. Maidoda dubansa ga mahaifiyarsa yai yana k’ok’arin d’ago kanta. Ajidde sai rawa hannunta yake tana k’ok’arin kai kwanon kusan bakin Aunty Nuratu. “Dakata.!” Ya fad’i yana duban ruwan maganin da yake bak’ik’irin. Cak Ajidde ta tsaya zuciyarta naci gaba da tsinkewa. “Wannan ruwan za’a bata.?” Ya tambaya yana kuma duban ruwan. Inne tai karaf tace “Maganin kenan za’a bata. Kasan had’e had’e ne.” “But Inne wannan zai iya cutar da lafiyarta dan bamusan da mai da mai aka had’a ba.. Sannan wannan yarinyar itace mai maganin dama.?” Inne ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Banda abinka Modibbo jinjiri ma ai sai ya baka magani kuma a dace idan Allah ya nufa. Karka damu da yanayin wanda zai baka magani kawai kai add’uan dacewa.. Mudai fatanmu shine Allah yasa a dace.” Ya jinjina kai a hankali yana mai maidoda dubansa ga ruwan maganin. Idanun Ajidde naga hannayen Mu’azzam da ya tallafi mahaifiyarsa wanda suke fresh dasu. Ta kasa janye idanu daga duban yatsun hannunsa da suke dogaye tamkar dai yanda yake da tsayi... Tsaban kallon yatsun hannayensa da take k’iris ya rage bata d’urawa Mamy magani a hanci ba. Mu’azzam yai caraf ya rik’e hannun nata wanda ke k’ok’arin Kai magani hancin mahaifiyarsa.. Jin hannunsa saman nata ya sanyata d’agowa a zabure tana dubansa zuciyarta na wani irin yankewa. Shiko yasha mur sosai yake dubanta “Concentrate.. Ki kula..” Ya fad’i fuska babu walwala. Ajidde ta jinjina masa kai amma jin bai sakar mata hannu ba ya sanyata kai idanunta ga hannayen nasu.. Sai sannan shima ya dubi yanda take kallo. A hankali ya sakar mata hanunta kafin ya kuma tallafe kan Mamy sosai.. Wane irin nannauyan ajiyan zuciya Ajidde ta sauk’e kafin ta soma k’ok’arin bawa Mamy maganin, a daidai sanda ta kawo maganin dai dai saitin bakinta tana jin sanda Mu’azzam ya furta Basmala a hankali. Batasan dalili ba amma taji wani irin natsuwa na sauk’o mata a lokacin da yake ambaton Allah. A haka Ajidde ke bata maganin, rabi na shiga bakinta rabi na zubowa jikinta. Inne ta taso ta gyara mata napkin d’in dake d’aure wuyanta har saida Ajidde ta ida bata ruwan maganin kafin Mu’azzam ya maida kanta ya kwantar, ya dafa goshinta da gumi ke tsartsafowa tin sanda aka soma bata maganin. A hankali ya share mata zufan yana mai kuma gyara mata kwanciyar. Ya jima yana duban fuskar mahaifiyar tasa yayinda Ajidde ke k’ok’arin tattare kayyaykinta. “Allah baki lafiya Maami.” Ya fad’i yana maida mata sumarta cikin hulan da aka rufa mata. Ajidde samun kanta tai tana mai furta “Ameen.” Yai saurin dubanta dan yaji Ameen d’in data ce, ya soma k’ok’arin tino yanda yasan irin muryar amma nan ma shiru bai iya tuna komai ba. Ganin zai bawa kansa wahala babu dalili ya sanyasa mik’ewa yana duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu. “Abinci fah ko sai zuwa anjima.?” Inne ta tambayesa cikeda kulawa. “No sai zuwa anjima Inne, zanyi wanka yanzu dai.” Yana ida fad’in haka ya nufi k’ofa. Inne ta jinjina kai tace a fito lafiya. Ajidde kaw alla alla take ta gama abinda take ta fice daga gidan kafin wannan mutumin ya kamata dan ta lura sam bai d’auko kamanninta ba. Ta murmusa cikin zuciyarta tana fad’in ta Ina zai d’auko kamanninta bayan yau d’in gaba d’aya ta canza yanayi, yau d’in jan powder ta shafa Wanda ya k’ara ma bak’in fuskarta haske sannan bata cika kwalliya ba kad’an tayi kuma harda hijabi Ta saka ba kaman wancan ranan ba, gaba d’aya dai ta sauya yanayi yanda ba lallai a ganeta ba. Canza yanayi da kamanni dik na cikin d’abi’ar Ajidde tinda dama damfaran mutane Kyallu ke sanyata yi, mai Sana’a irin nata dole yanada dabaru na b’adda yanayi daban daban.. Ta kuma murmusawa tana fad’i cikin zuciyarta Wo ni Ajidde gaskiya na iya shashashantar da mutane tinda na shashantar da wannan k’aton.. Muryar Inne ta sinkayo tana fad’in “Ajidde idan kin gama da maganin nata sai kici abinci ko.. Hindu zata baki abinci.” Ajidde ta girgiza kai tace “A’a Inne na gode, sauri nake akwai yanda zanje na kai magani.” Inne tace “A’a ai kuwa dole zakici abinci dan ba’a zuwa gidan nan a fita ba’aci komai ba kinji koh.. Jirani a nan Ina zuwa.” Ajidde ta jinjina kai tana murmusawa. Inne tana fita Ajidde ta mik’e tana k’are ma d’akin kallo.. Ya zama dole ta nemi abinda zata d’auka takaima Kyallu.. Saidai sam idanunta basu gane mata wani abinda zata d’auka ba. Sannan bata jin zata iya satar ma Kyallu wani abu a d’akin majinyaciya irin wannan.. Yanzu ya zatayi.? Bata isa ta koma ma Kyallu hannu banza ba dan Ta tabbata muddin ta koma mata haka a d’akin awakai zata kwana. Tana tsaka da tinanin ta hangi k’ofar d’akin a bud’e a hankali cikin sand’a ta fito daga d’akin. Doguwar corridor ta hanga da ya mik’e zuwa b’angaren hagu, ga wasu k’ofofin kana iya hangowa. Cikin sand’a Ajidde ta soma bin wad’annan k’ofofin.. Tana tafe ta hangi wata kaman bata ida rufuwa kirif ba. Ta Washe baki tana fad’i a hankali “Sa’arki tazo Ajidde.” Cikin sand’a ta isa jikin k’ofar tana turata a hankali. D’akin tas tas Sai k’amshin ‘yan gayun da take shak’a kaman dai yanda tace a cikin zuciyarta. Ta lumshe idanu tana shak’an k’amshin. “Kaji k’amshin Turawa.” Ta fad’i tana gyad’a kai. Ga kuma zuban ruwa tana jiyo daga wani wajen amma batasan daga ina bane. Kar dai ma ana kallanta.? Ta tambayi kanta cikin zuciyarta. Kafin takai ga nemo amsar tambayarta ta hangi wannan bak’ar jakan Ta mutumin nan data so masa sata dan sam bazata mance jakan ba, sannan shine mutumin da ya taimaka mata suka bama matar nan magani. Ajidde ta Washe baki tana fad’in “Jaka jin nace sai na sata ma Inna Kyallu abinda ke cikinki.. Watau yauma saida kika biyoni. Toh Bari dai muga Meye a cikinki.” Tana ida fad’in haka ta k’araso kusan jakan tana mamakin yau a bud’e ta sami jakan. Saidai k’arasowarta jikin jakan kenan taji an turo k’ofar d’akin an shigo. Cak Ajidde ta tsaya ba tareda ta iya juyowa ba, jikinta sai rawa yake. Ta nemi layar zana da kyallu ta bata ta rasa. Tana cikin dibi dibin ta sinkayo muryar mutumin da ya shigo d’akin yana fad’in “Who are you.? What are you doing in here.?” A slow motion Ajidde ke juyowa. Musaddiq ya ware idanu yana duban yanda ta zaro k’wayar idanunta, dikda babu janbaki da jagiran data zana wancan lokaci tsaf ya ganeta dan bazai mance wannan k’wayar idanun nata masu tsananin haske da kyau ba “You again.?” Ya furta yana nunata. Daidai lokacin aka soma tab’a k’ofar bathroom alamun mutumin dake ciki zai fito. Ajidde ta rikice ta rasa wanne zatai dan tuni Mu’azzam ya fito d’aureda towel, rufin asirin Allah hannunsa na rik’e da k’aramar yana goge fuskarsa zuwa sumarsa sam bai an kare ba balle ya gane da mutane cikin d’akin. Cikin azama Musaddiq ya finciko hannun Ajidde da ta saki baki da hanci tana duban Mu’azzam ya turata cikin wardrobe. K’aran rufe wardrobe Mu’azzam yaji ya d’ago fuskarsa yana duban Musaddiq dake tsaye wajen cikin wani irin yanayi na daburcewa. “Hey are you with someone.? Ina wanka kaman naji murya..” Mu’azzam yace yana k’arasowa. Musaddiq da gaba d’aya yake a rikice sabida Ajidde dake b’oye cikin wardrobe saurin girgiza kai yai yace “Me. A’a no.. Yanzu shigowarta.. Mu’azzam you need to come, wani mutumi ne naga ya dirk’o ta Katanga shine nazo kiranka.. You need to hurry kafin ya b’ace mana..” Yanda duk yake a birkice yasa Mu’azzam zuba masa idanu yana karantarsa “Musaddiq will you calm down please..” “Wane irin calm down kake magana. Inace maka b’arawo ne kaman naga ya shigo kana ce min calm down.. I know you’re a Corp shisa nazo wajenka direct.. Please you need to hurry..” Ya k’arashe yana mai janyo Mu’azzam d’in suka nufi k’ofa. “Wait Musaddiq.. I need to get dressed first.” Mu’azzam ya dakatar dashi da fad’in haka. Sai sannan Musaddiq ya tina towel ne jikin Mu’azzam d’in. Mu’azzam ya d’an girgiza kai yana k’ok’arin nufan wardrobe. ‘Oh shitt.. He can’t see her in there.’ Musaddiq ya fad’i cikin zuciyarsa. Kafin Mu’azzam d’in ya bud’e wardrobe d’in wanda tuni Ajidde dake dubansa ta d’an tsakanin da bai ida rufuwa ba ta sadak’ar kawai ya kamata dan har toshe bakinta tai ta rintse idanunta tana jiran mai afkuwa ya afku. Kwatsam Musaddiq ya k’araso ya damk’o hannunsa ya hanasa bud’e wardrobe d’in lokaci guda yake fad’in “Dan Allah kazo muje kar ya gudu.. Zo ka gansa ta window..” Ya k’arasa da Mu’azzam jikin window yana yaye curtains yake nuna masa “Look look duba tacan ka gani..” Girgiza kai Mu’azzam yai cikeda k’osawa yace “Musaddiq I can’t see anything..” “Ok wait muje wajen ka gani..” Ya d’an fuzar da fuci hannayensa saman kunkumi “Bani jallabiyata cikin wardrobe I just hang it there.” Cikin sauri Musaddiq ya jinjina kai yayinda Mu’azzam d’in ya d’an girgiza kai yana mai fuzar da fuci. Musaddiq na bud’e wardrobe d’in sukai ido hud’u da Ajidde da k’iris ya rage bata saki fitsari ba dan tsoro.. Ya aika mata mugun kallo kafin ya zaro jallabiyar dake lank’aye jikin hanger. Ya maida wardrobe d’in ya rufe kafin ya kawo wa Mu’azzam jallabiyar ya zira. Lokaci guda Mu’azzam d’in ya nufi waje ba tareda ya kuma bi takan Musaddiq ba.. Mu’azzam na ficewa ya dawo ya bud’e Ajidde yace “Kina jina kar ki sake ya ganki dan idan ya kamaki kashinki ya bushe.” Cikin sauri Ajidde da tuni Ta had’a gumi take jinjina kai alamun taji. Sauri sauri ta fice ta nufi d’akin Aunty Nurah tana sauk’e nannuyan ajiyan zuciya. Tana shiga ta tadda Hindu ta kawo mata abin kari. Hindu ta dubeta tace “Ina kika fito ga abin kari na kawo miki tuntuni..” Murmushin yak’e Ajidde tai tace “Oh wllhi makewayi na fita inata nema ai.” Hindu ta murmusa tace “Banda abinki Ajidde ai da tambaya kikayi muje na kaiki.” Ajidde tai saurin girgiza kai tace “A’a ki barshi kawai ai yanzu ma zan tafi bana so nayi rana.” Hindu Ta d’an tab’e baki tace “Toh shikenan.. Abincin fah..?” Ajidde ta juya taga kayan dad’in da aka kawo mata. Sai kuma ta dubi Hindu tana wage baki alamun tanaso taci. Hindu ta murmusa tace “Ki zauna kici abincinki kafin ki tafi..” Aiko Hindu na ficewa Ajidde ta shiga yagan pepper soup d’in kaza tana turawa bakinta, hannu bibbiyu takeci kaman wanda za’a k’wace.. K’arshe bud’e jakarta tai tana tura sauran ciki. Kaman wacce ta tina wani abu sai kuma ta d’ago tana duban matar nan majinyaciya. A hankali ta k’arasa kanta ta tsaya gabanta “Na gode kinji. Ba don ke ba da bazan shigo gidan nan har naci dad’i irin haka ba.” Ta k’arashe tana wage baki. Lokaci guda ta mutsuke hannayenta jikinta ta sab’i Jakarta ta nufo k’ofa. Sauri sauri ta fice tana lek’e tamkar maras gaskiya. Koda Mu’azzam ya fice baiga alamun kowa ba baiga alamun komai ba gajeren tsaki yai yana girgiza kai yasan bazai wuce shak’iyancin Musaddiq bane suka motsa. Ya yanke shawarin tuntub’ar securities ko sunga wani abu suspicious. Har zai nufa gate Musaddiq ya k’araso yana d’an haki alamun yayi gudu. Mu’azzam ya dubesa yace “Are you sure kaga wani ya shigo.” Sosa kansa yake yana duban Mu’azzam d’in “I think it’s just my imagination.” Kafesa da idanu Mu’azzam d’in yai yana karantarsa “Are you alright.?” “Of course.. I’m absolutely fine, Inspector.” Jinjina kai Mu’azzam yai yace “Lets go and ask the security men Ko sunga mutumin da ka gani..” “No no no.. Nace maka Ina tunanin imagination d’ina ne.. Babu kowa.” Yai maganar yana d’an ciza lab’e bakinsa kad’an irinta masu laifi. Takowa Mu’azzam yake zuwa gabansa yana mai tsaresa da idanu “Wait. Are you sure you’re not on drugs.?” Mu’azzam ya tambaya yana duban Musaddiq d’in. “Kasan na daina tin ba yau ba.. kuma bazan k’ara komawa ruwa ba in sha Allah. Dik da ban maka alk’awari ba amma nace In sha Allah.” Jinjina kai Mu’azzam yai yana mai kuma karantarsa ba tareda yace komai ba. Daidai nan Jume ya k’araso suka gaisa da Mu’azzam kafin ya dubi Musaddiq yace ana nemansa a wajen aiki. A tare Musaddiq da Jume suka wuce yayinda Mu’azzam ya nufo cikin gida yana jin dad’in yanda Rayuwar d’an uwan nasa ya Inganta a gidan gonar cikin ikon Allah. Can Ajidde ta hangosa zai shige, gabanta yai wani irin fad’uwa dan ba komai Ta tina ba sai ganinsa da tai d’aure da towel. Tai saurin rintse idanunta ga k’amshin wardrobe d’insa da ya kama illahirin jikinta. Koda ta rintse idanun ma shi take hangowa. Ta kuma bud’esu tana furta “Wayyo Ajidde shige shigen ki ya kaiki kika gano sa a haka.” Jikinta ta shiga shinshinawa tanajin k’amshin wardrobe d’insa da ya kasa barin jikinta. Muryar data sinkaya daga bayanta ya sanyata juyowa babu shiri. Musaddiq ne ke tsaye bayanta ya tsareta da idanu. Ta ganesa shine mutumin da ya taimaketa ya sanyata cikin wardrobe. Kan kace mai ta duk’a saman gwiwoyinta ta d’ago hannu tana rok’onsa ya rufa mata asiri. “Kin ganeni..?” Tambayar da ya mata kenan. Tai K’uri tana dubansa, sai kuma tai saurin girgiza kai alamun a’a Yashin dake wajen ya d’iba cikin hannunsa ya kakkab’e had’ida shafa sauran saman fuskarsa. Take fuskarsa tai hazon k’ura. Ajidde na zaro idanu waje tace “Kuran tashe.!” Sai kuma ta soma dariya tana nunasa. SameenaAleeyou 📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *17* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Harga Allah ta bawa Musaddiq dariya yanda tai maganar amma Sai ya gimtse yace “Zaki min bayani yanzu, what exactly were you doing in there..? Mai kike cikin d’akin mutumin nan..?” Zaro idanu waje tai sai kuma tai dariyar yak’e tace “Ban d’aki nake nema kawai sai tsintar kaina nai a wannan d’akin.. Kai kuma fah.. Ba kace min baka shiga wannan gidan ba.. Ya na ganka a cikin gidan.. Kuma da alama ka saba shiga.. Watau dai k’arya ka min kenan..?” Ta k’arashe hannayenta saman kunkumi tana mai tsaresa da idanu tamkar wacce zata kai masa bugu. “Wait what.. Ke ni nake miki k’arya..?” Ajidde ta d’an murgud’a masa baki tace “Toh ni bance kayi k’arya ba amma Maiyasa kace min haka..?” Tsareta da idanu yai dan a yanda ya d’auketa shashasha bai zaci zata iya d’ago zancen da sukai ranan ba.. Ya gyara tsayuwarsa yace “Tsaya ai idan ban mance ba nace miki inada aboki d’an gidan..” Ajidde Ta zaro ido Tace “Wannan ne abokin naka..? Ai shine mutumin da ya biyoni ranan..” Musaddiq ya zuba mata idanu da tsananin mamaki “Toh kin dai aikata laifin kenan.. Na tabbata ke mai laifi ce.. Zaki fad’a mun mai kike a d’akin ko kuma yanzu na shiga cikin gidan na sanar dashi komai..” Cikin tsananin damuwa Ajidde take rok’onsa “Dan Allah ka rufa mun asiri.. Ka rufa mun asiri kar ka tona mun asiri wajensa.. Idan ka tona mun asiri shikenan bazan bawa matar nan magani ba.. Dan Allah ka barni na gwada sa’an magani na akan matar nan.. Nasan zakaso mahaifiyar abokinka ta sami lafiya..” Ta k’arashe cikin tsananin nuna damuwa. Musaddiq ya jinjina kai yace “K’warai kuwa nafi kowa so Aunty Nuratu Ta sami lafiya.. Zan rufa miki asiri amma sai kin sanar dani gaskiyar Al’amarin..” Ajidde ta had’iyi miyau da k’yar tana mai kuma zaro idanu “Zan fad’a maka amma saidai idan zaka mun alk’awari.” Cikin wane irin yanayi yake dubanta wannan karon. Lokaci guda yananyin nasa ya canza, cikin wane irin kakkausar murya yake fad’in “I thought I’ve already told you.. I don’t make Promises.. Bana Alk’awari.. Ban tab’a cika Alk’awari ba.. Kuma bazan tab’a cika alk’awari ba... Kuma na rasata ne ta dalilin rashin cika Alk’awari na.!” Ya k’arashe siririyar hawaye tana gangaro masa. Cikin tsananin tsoro Ajidde ke dubansa, idanunta Sun firfito waje sabida tsoro. A hankali Ta soma k’ok’arin jada baya.. “Ina zakije.. Bazaki bar wajen nan ba sai kin fad’a mun sirrinki..” Ya fad’i yana dubanta. Cikin sauri take girgiza kai “Banida Sirri.. Ni d’in kawai magani nake kawowa..” Tana ida fad’in haka tasa kai zata shige. Musaddiq yasha gabanta yana binta da wani irin kallo wanda ya kuma haifar mata da tsoro “You are a thief..! Ke b’arauniya ce.. Wancan ranan sata kika so yi masa sai ya biyoki kika b’uya.. Wannan karon ma sata kika shiga d’akinsa zaki masa sai Allah ya kawoni kafin ki ida nufinki.. Now you tell me.. Shin wacece ke.. Mai magani ce ke kokuwa b’arauniya ce.?!” Idanun Ajidde suka kawo ruwa, Ta soma girgiza masa kai tana fad’in “Dan Allah ka rufa mun asiri wllhi nima umarni nake bi..” “Umarni kike bi.. Umarnin wa..?” Ya kuma tambaya yana dubanta. Ajidde ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubansa “Zan fad’a maka komai amma zaka yi shiru.. Bazaka fad’a ma kowa komai ba.. Idan har kana so na bawa matar nan magani.. Sannan zaka taimakeni..” Musaddiq ya jinjina kai yace “Zanyi duk abinda kikace Idan kika fad’a mun komai..” K’asar wata bishiya suka zauna Su duka biyun, Musaddiq ya dubeta yace “Ina sauraronki..” A hankali Ajidde Ta soma karanto masa sana’ar da Kyallu ta d’aurata bisa, ta kuma sanar dashi k’udirin kyallu na cewa muddin tazo gidan bata sato masu wani abu ba ga uk’ubar da zata mata.. Wannan dalili shiyasa take k’ok’arin aikata satan da yace tana yi. Musaddiq ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana dubanta “Toh ita Inna Kyallu bata tinanin watarana a kamaki.?” Ajidde ta girgiza kai tace “Inna kyallu bata yarda da fad’uwa ba.. Dik abinda zatayi sai ta masa shiri sosai domin kuwa har layar zana ta bani.. Sannan idan aka kamani babu damuwarta dan cewa zatai dama tin can ni b’arauniya ce.” Musaddiq yace “Ke kuma kin yarda layar zata taimaka miki..?” Ajidde tai shiru tana dubansa “Ban sani ba..” Ta basa amsa kai tsaye. Sauk’e ajiyan zuciya yai kad’an yace “Zan taimakeki.. Kuma zamuyi aiki tare.. Aunty Nuratu zata sami lafiya in sha Allah.. Sannan Inna Kyallu bazata fahimci komai ba..” Tai masa K’uri tana dubansa kaman yanda shima ya zuba mata idanun. ** Zaune take a uwar d’aki ta rapka uban tagumi tana tinanin rayuwa da yanda Al’amara suke kasance masu tun bayan had’uwarta da Sagir. Tana jin Tabawa da Umma yanda Tabawan ke yab’a wa mahaifiyarta maganganun marassa dad’in sauraro saikace ba d’azu tai masu kaca kaca da gida taci mutuncinsu ba, a rana guda karo na uku kenan kafin yammaci Tabawa ke kawo masu samame.. Wannan shine ake kira K’addara ya riga fata, da ace wani zai iya zab’an k’addararsa tabbas da bata zab’i K’addarar sanin Sagir ba balle har ta kasance dashi. Amma saidai tuni K’addararta tazo da hakan a rubuce. Ji take ta dalilinta komai ke faruwa, duk wasu iftila’i da ahalinsu ke fuskanta itace sababi.. Wasu hawayen masu tsananin k’una suka gangaro mata. A daidai lokacin Umma ta shigo. Ta jima tana duban Sadiyar kafin ta k’arasa gefe da Ita ta zauna, saida suka d’ibi lokaci babu wanda yace ma kowa komai kafin Umma ta nusa tace “Bana San kina saka damuwa ma ranki Sadiya, cuttutuka sunyi yawa yanzu Sai kije kisa ma kanki hawan jini ko ciwon zuciya a ‘yan shekarun nan naki..” Sadiya ta goge hawan dake kwance saman fuskarta “Umma Wai ni dan Allah ina dangin Abba suke da bazasu waiwayemu ba.. Umma shin basu san d’anuwansu ya mutu bane bazasu dubi bayansa ba Ko dan albarkacin zumunta. Umma kodai baida dangi ne..?” “Waye kika tab’a ji baida dangi Sadiya. Mahaifinku yanada dangi saidai tin lokacin da yace zai aure ni sukayi farrak’u da danginsa.. Iyayensa sun jima da rasuwa sai ‘yanuwan ne suka rainesa. Sunso su aura masa d’iyarsu shi kuma yak’i amincewa yace sai ni yake so.. Tin daga wannan lokaci suka ciresa daga cikinsu sukai rantsuwa babu shi babu su bazasu tab’a waiwayansa ba har abada.. Sadiya mahaifinki ya sadaukar da abubuwa da dama a sabida ni.. Banida kowa a k’asar nan sai shi.. Na shigo k’asar nan a wahalce a matsayin ‘yar cirani.. Kuma na rasa kowa nawa amma mahaifinki shi kad’ai ne ya tsaya min ya taimaka min ya zamto min sutura..” Muryarta ya soma rawa sosai sanda taci gaba da fad’in “Na k’are ina mai masa butulci da raina arzikinsa.. Mutumin da ya sadaukar da komai nasa sabida ni.. Ciki harda danginsa wanda suka guje shi sabida ya zabi ya kasance da matar da bata da kowa a k’asar nan.. ‘Yar cirani data shigo k’asar nan a wahalce.. Shin ki fad’a mun ta yaya bazan ga ba daidai ba.. Ta yaya wacce ta aikata irin wannan butulci zataga da kyau...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Sadiya dake hawaye Ta matso ta rungume mahaifiyarta su duka biyun suna kuka mai ban tausayi. Cikin zuban hawaye Sadiya ke duban Umma “Umma ki daina fad’in haka.. Bawa baya wuce k’addararsa.. K’addarar ka tamkar inuwarka ce dik yanda ka kaje saita bika sannan idan ka tsaya itama zata tsaya.. In sha Allah zanyi abinda ya dace wannan karon.. Bamuda sauran zab’i da ya wuce na amince da auren Alhaji Isyaku..” Kuka sosai ya kufce mata. Cikin zuban hawaye Umma ke dubanta lokaci guda take girgiza kai alamun a’a “A’a Sadiya, bazan bari ki sadaukar da rayuwarki da farin cikin ki sabida zunubaina ba.. Nasan bansan yanda zanyi ba.. Amma inada tabbacin Allah bazai bar mu haka ba da sannu zai kawo mana wani mafitan..” Sadiya tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka gangaro mata “Watak’ila mafitan kenan Allah ya kawo mana Umma. Watak’ila Alhaji shine mafitan angaremu.. Umma idan muka zauna haka bamusan mai Tabawa zatayi gaba ba.. Bamusan ko Malam Aminu zai bar muci gaba da zama a nan ba.. Umma ‘yan uwana nake tunani.. K’anne na nake tunani, bana so suna ganin irin wannan tashin hankali.. Umma abin yayi yawa.. This has to end Umma.. Ni kad’ai ce ya kamata nayi abinda ya dace.. Umma ki sanar da Malam Liman ni Sadiya na amince ya aurar dani ga Alhaji Isyaku... Zan rabu da Sabeera rabuwa Ta har abada.. Bazan k’ara kallon cikin idonta ba.. Watak’ila Wannan shine hukuncina a rayuwa.. Hukuncin abubuwan da nayi ma Abba a lokacin da yake raye.” Ta k’arashe cikin tsananin kuka... Umma ta rungumeta su duka biyun suna masu fashewa da wani irin kuka mai tab’a zuciya. ** Koda labari ya iski Alhaji Isyaku cewa Sadiya da mahaifiyarta sun amince da batun auren Zo kaga Farin ciki wajensa, jinsa yake sabon ango.. Lallai tarkonsa ta d’anu ko banza zai mallaki wannan kyakkyawan yarinyar da ya jima yana kwad’ayin kasancewa da Ita.. Bayan isha ya shirya tsaf yasha wankansa ya fesa kwalliya da babbar riga ya nufo gidansu Sadiya. Da k’yar Umma ta shawo kanta tace taje su gaba taji da mai yazo. Haka badon taso ba ta zira hijab d’inta ta fito. Yana ganinta fari’arsa ya k’aru “Assalamu alaki kyakkyawa ma’abociya annuri..” Ya fad’i yana mai k’arasowa. Sanin darajan sallama yasata ta amsa ciki ciki kanta na duk’e k’asa.. Ta soma k’ok’arin duk’awa da niyyan gaishesa. “A’a tashi tashi kayanki.. Haba ai saidai ni na duk’a miki Gimbiyata.” Takaici ya turnuk’eta, ta rintse idanunta a hankali tanajin zuciyarta na mata zafi. “Ki saki jikinki. Kuma ki saka a ranki cewa ni masoyinki ne..” “Masoyi kuma Baba..? Kodai b’atan kai kayi ne.? Ni ce fah Sadiya k’awar Sabeera wacce ka datse alak’armu da Sabeera sabida banida kamun kai.. Ko ka mance ne..?” Murmushin da yafi kama da yak’e yai kana yace “Yaro dai yaro ne. Toh banda abinki Sadiya ai ba komai yasa bani k’aunar alak’arku da Sabeera ba Sai dan bana so ku shak’u ku samu kusanci da juna gudun kar randa duk nazo miki da wannan batu nawa da ya jima a birnin zuciyata kice bazaki iya ba sabida k’awance da d’iyata da kuke.. Idan kika cire wanann ni babu wani abinda zaisa na rabaki da Sabeera.. Ki yarda dani Sadiya, ni wllhi ba sabida komai na rabaku da Sabeera ba sai dan kar ta zamto mana cikas a tsakaninmu.. Banaso ta zamto shamak’i ma soyayya ta dake..” Ya d’an nusa yana mai gyara zaman babbar rigarsa “Wato Sadiya na jima Ina k’aunarki saidai bansan Ta yanda zan tunk’areki da wannan batu ba har sai zuwa wannan lokaci..” Sadiya dake dubansa cikeda tsananin mamaki, dan itakam kunya ma take ji masa, murmusawa tai tace “Sai wannan lokacin ka sami dama. Lokacin da banida wani zab’i da ya wuce na amince da buk’atarka koda ace bana so. Shin ko ba haka bane Baba.?” Saurin katseta yai da fad’in “Ko d’aya.. Ba haka bane.. Kuma dan Allah ki daina kirana Baba, mud’in zamu kasance k’ark’ashin inuwar ma’aurata ne, matata zaki zamto nan da kwanaki biyu rak, dan ni asabar d’in nan mai zuwa nake so a d’aura Kinga yau Alhamis ne already..” A zabure ta d’ago tana dubansa “Asabar mai zuwa fah kace.!” “K’warai kuwa Amaryata, rashin jan lokacin yafi a’ala, shi dama jan lokaci a aure Baida wani alfanu..” “Ka sani auren nan da zanyi sadaukarwa ne ga ahalina amma ba don inaso ba.” Ta fad’i idanunta na raurau. Murmusawa yai yana mai kuma gyara tsayuwarsa “K’warai kuwa nasan da hakan, kuma ina mai tabbatar miki da sannu zaki soni ki k’aunace ni.. Idan har da gaske auren sadaukarwa zakiyi toh kuwa ya kamata ki amince ayi auren nan as soon as possible.. The earlier the better. Sabida ahalinki zasu huta da tashin hankalin Tabawa harma da Malam Aminu.. Bai kamata ayi Jinkiri ba a situation d’in da ahalinki ke ciki.. Bugu da k’ari Nifa d’aukeku zanyi Cak daga garin nan dan ku mance komai ku mance duk wasu tashin hankali da kuka fuskanta cikinta.. Amma ke ya kika gani..? Ki tuna you are doing this for your family.” Ya k’arashe yana mai zuba mata idanu. Hawayen da take rik’ewa ne suka soma gangaro mata. Ta shiga jinjina kai tana furta “Yes.. Yes I’m doing this for my family.. For the sake of my Family... Zan sadaukar da komai nawa ciki harda Farin cikina sabida Su.. Sabida ni ce duk na ja masu halinda suka tsinci kansu ciki..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Juyawa yai yana sakin murmushin cin nasara kafin ya maidoda dubansa gareta “C’mon Baby ki daina kukan nan haka, wllhi har cikin zuciyata nake jin zafin zuban hawayenki.. I promise you kukan ki ya k’are Baby.. Da zaran kin auren zan mantar dake komai.. Zan baki irin rayuwar da kika jima kina mafarkin samu... I’ll spoil you and pamper you kinji Baby na..” Jin kalaman nasa take kaman Ana hura mata wuta cikin kunnuwarta, babu kunya babu tsoron Allah Wai Baban Sabeera ke jero mata wad’annan kalamai hardasu kiranta Baby.. Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana girgiza kai tace “Wancan rayuwar mafarkin Sadiya ce a baya.. A halin yanzu babu abinda nake so face peaceful world for my family. I want my family to have peace.. Iyakacin abinda nake so yanzu shine peace.. Zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ahalina.. Mafarkina da buruka na sun jima da mutuwa.. An birnesu tareda mahaifina.. Kuma ina neman wani alfarma a wajenka.” Ya jinjina kai yace “Kin wuce neman alfarma Gimbiyata, abinda kike so kawai zaki fad’a ayi.” Sadiya tace “Kar ka biya Tabawa har sai randa akazo d’aura aurenmu domin akwai rayuwa akwai mutuwa bamu San mai zai faru kafin ranan ba..” Ya murmusa yace “Idan dan wannan ne banida matsala. Yanda kikace haka za’ayi Amaryata.. Wllhi na k’agu ki zamto tawa..” Katsesa tai da fad’in “Ni zan shige gida..” “A’a tsaya mana..” Yai maganar yana zaro kud’ad’e cikin aljihunsa. Saurin girgiza kai Sadiya tai tace “Bazan karb’i komai daga hannunka ba.. Na gode..” Bata tsaya sauraron sa ba tasa kai ta shige cikin gida. Yabi bayanta da kallo zuciyarsa fari k’al, kad’a Kai yai yace a fili “Bari dai naita lallab’a ki har ki shigo...” Yana ida fad’in haka ya gyad’a Kai yana mai kuma Washe baki ya shige. ** Washe gari sassafe Tabawa tai kiran Asabe mai kayan Koli. Tabawa ta k’irgo kud’ad’e cikin wanda Alhaji Isyaku ya bata, Ta mik’awa Asabe Mai kayan Koli tace “Kina jina dik abinda na sanar dake haka zaki sanar da matarsa.. Asabe koda wasa kar ki ce ni na sanar dake..” Asabe Ta jinjina kai tana tura kud’in cikin posar ta. “Haba Hajiya Tabai, indai dan wannan ne ai bakida matsala, da Asabe fah kike zancen..” Tabawa ta murmusa cikeda jin dad’i tace “Yauwa tawan.. Idan har hak’ata ta cimma ruwa zan k’ara miki wani abu..” Asabe Ta Washe baki cikeda farin ciki.. Tuni ta aza kayanta na Koli aka ta nufi layin gidan Alhaji Isyaku. Tabawa tabi bayanta da kallo zuciyarta fari k’al. A fili take furta “Alhaji Isyaku kenan ai wllhi bazan bari ka auri yarinyar nan ba, auren nan saidai ayi dani Koda zaka biya masu bashin amma bakada mata sai ni Tabawa. Zan d’aga masu hankali dan ka biya masu bashi sannan zan sa matarka da d’iyarka su d’aga masu hankali suk’i amincewa da buk’atarka bayan ka biya masu bashin..” Tana ida fad’in haka ta bushe da muguwar dariya kafin ta shige gida. ** Maman Sabeera na zaune parlor tana kallon shirin good morning Nigeria da ake nunawa da sanyin safiya a tashar NTA Asabe mai kayan Koli tai sallama. Iyatu mai masu aikatau ce ta amsa mata sallamar tace ta jira ta shiga ta tambayi Hajiya idan zata sayi wani abin. Asabe tace “Dakata ba saye da sayarwa ya kawoni na ba.. Alhaji na gida Ko ya fice..?” Iyatu tai jim kafin tace “Ai Jiya Alhaji bai dawo gida ba inaga wajen aiki ya kwana..” Asabe ta zaro ido waje tace “Bai kwana gida ba..? Ikon Allah Toh ki shiga kice mata magana nazo mata dashi mahimmiya kan maigidanta.” Iyatu ta dubeta da mamaki amma sai ta jinjina kai tace “Shikenan.” Lokaci guda ta shige ta nufo parlor ta tadda Maman Sabeera ta sanar da ita abinda Asabe mai Kayan Koli ta fad’a mata. Mamaki ya cika Maman Sabeera jin Wai magana Asabe tazo mata dashi kan mijinta. Ta nusa tana tinani kafin taceda Iyatu “Kice mata Ta shigo.” Iyatu ta jinjina kai kafin ta fice yin iso ma Asabe. Jim kad’an Asabe ta shigo d’aikeda kayan Kolinta, ta nemi waje daga k’asa ta zauna tana gaida Maman Sabeera. Maman Sabeera Ta dubeta da mamaki tace “Asabe kikace yau ba talla kikazo ba.. Toh wani magana ne ya kawo ki kan maigidana.?” Asabe Ta d’an Tab’e baki tana ‘yan waige waige tace “Hmm ai Hajiya abinda nazo dashi yau yafi k’arfin talla.. Amma Hajiya jiya Kinsan yanda mijinki ya kwana..?” Da tsananin mamaki Maman Sabeera ke dubanta ganin basu saba irin wannan batu ba, iyakaci ta shigo da kayan kolinta ta tallata ta fice. Amma yau Asabe tazo mata da batu mai girma. Girgiza kai kad’an Maman Sabeera tai “Ban.. Fahimceki ba Asabe.. Mai kike nufi..?” Asabe ta kuma gyara zama tana duban Maman Sabeera “Hajiya wllhi wllhi abinda zan fad’a miki Sai ya firgitaki.. Idan dai har bakisan yanda mijinki ya kwana jiya ba kuma bakisan da wa ya kwana ba ni zan sanar dake dan na sani..” Zuciyar Maman Sabeera yaci gaba da bugawa cikin sauri, mijinta ya saba kwana cikin Abuja idan dare ya masa sabida tsananin holdup da cinkoson Abuja yakan sa wataran ya kwana ga yanda k’asar Ta koma babu tsaro, wataran yakan ce aiki ya rik’esa zai kwana cikin Abuja da safe ya dawo. Amma koda wasa bata tab’a saka ma ranta cewa mijinta na ha’intarta ba tuni ta kyautata masa zato tinda ma kafin ya kwana cikin Abujan Sai ya kirata ya sanar da Ita cewa zai kwana aiki ya rik’esa gudun Karma zargi ko abu mai kama da haka ya shiga tsakaninsu. Cikin rashin yarda da batun Asabe Ta mik’e tana nuna ma Asabe k’ofa “Kinga Asabe tashi kawai ki fice.. Kafin ranmu gaba d’aya ya b’aci.. Tashi ki fice min a gida ni bana shiga gulma da gutsiri tsomen unguwar nan.. Tashi ki fice min a gida kuma kar ki sake dawowa idan da irin batun nan zaki Zo..” Asabe Ta murmusa tace “Hajiya wllhi Allah na rantse miki da Allah daren jiya mijinki na unguwar nan kuma nasan da wa yake tare.. Ni ganau ce ba jiyau ba, na gansa da yarinyar nan Sadiya kuma yau kusan kwanaki uku kenan yana zarya k’ofar gidansu.. Ina mai tabbatar miki d’aukanta yayi suka fice suka kwana tare.. Ai dai Kinsan wacece Sadiya a unguwar nan Sadiya Sady Pretty da tai k’aurin suna wajen rab’an maza masu abin duniya.. Toh ta fad’o kan mijinki zata k’wak’wale abin hannunsa.. Dan wllhi jiya tare na gansu kaman zai mata sijadda dan biyayya..” Bibbiyu Maman Sabeera ta soma gani, hazo hazo da wani irin duhuwa ne suka gifta k’wayar idanunta. A yayinda Sabeera da fitowarta kenan daga kitchen rik’eda mug dik taji tattaunawarsu a kunnuwanta.. Wani irin k’ara ta saki had’ida sake mug d’in dake hannunta ya watse saman tiles.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *18* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Da kuka Sabeera ta k’araso gabansu tana fad’in “A’a badai Babana ba.. Badai k’awata Sadiya ba.. Mama kar ki yarda da maganar wannan matar I’m sure k’arya take.. Ki tashi.. Tashi ki fice mana daga gida..!” Tai maganar tana k’ok’arin finciko Asabe dake duk’e wajen ta zuba masu ta mujiya. Maman Sabeera kam tama kasa tantance abinda ke faruwa. Kaman daga wani duniyar take sinkayo kukan Sabeera da maganganunta. Asabe ta mik’e tana fad’in “Idan k’arya nake maku ku tare mutanen lungunsu ku tambayesu ko kuma kuje da kanku dan ance zuwa dakai yafi sak’o. Nidai na gama nawa tinda sanar daku.. Ya rage naku ku yarda ko kar ku yarda. Allah bamu alheri.” Tana ida fad’in haka ta mik’e ta aza bahon kayan Kolinta aka Ta nufo waje, tuni Ta cika ma rigarta iska aka bar Sabeera da Mamanta babu mai iya ba ma wani hak’uri. Cikin muryar kuka Sabeera ke duban mahaifiyarta tana fad’in “Mama k’arya take kar ki yarda da ita.. Wllhi nayi imani Sadiya bazata tab’a aikata haka ba.. Nasan Sadiya nasan halinta wllhi sharri ne kawai irinta mutanen unguwar nan.. Mama dan Allah Kema kice min baki yarda ba..!” Maman Sabeera bata iya furta koda kalma ba sai hawaye dake zarya saman k’uncinta. Cikin sauri ta mik’e ta nufi d’aki tana jin kukan da gaske na zuwa mata. Sabeera tabi bayanta da sauri tana kiranta amma inaa bata ko tsaya ba balle ta saurari Sabeera ta shige d’aki kayanta. Silalewa Sabeera tai a wajen kukanta na k’aruwa itama. Hiran wasu course mates d’insu take tinawa data sinkaya wataran a makaranta cewa akasari ba duka ba iyaye da suka faye tak’ura da tsanani ka bincika ta yuyu shima watsewarsa yake da yaran wasu baiso ayi da nasa shiyasa yake masu mugun tsanani. Tai saurin toshe kunnuwanta tana girgiza kai dan bata so ta amince da hakan.. Wani tinanin ne ya kuma d’arsuwa mata a zuciya.. Ita kad’ai ta aminta da Sadiya, itace bata mata kallon da sauran mutane suke mata a unguwar.. Ta yarda da ita d’ari bisa d’ari sannan ta saka ma ranta cewa Sadiya ba mutuniyar banza bace but Maiyasa yanzu take jin shakku akan hakan.. Kardai da gaske Sadiya cin amanarta take.. Take taji zuciyarta na wani irin bugawa, gwara taji labarin mahaifinta na neman wata daban badai Sadiya k’awarta data d’auki yarda ta d’aura mata ba.. Waima tsaya mahaifinta ya mata iyaka da Sadiya ta ya za’a ce su biyu d’in suna tare.. Cikin sauri ta shiga girgiza kai tana furta “No.. no .. no I can’t take this anymore.. I need to find out myself..” Tana ida fad’in haka Ta mik’e Ta nufi nata d’akin dan shiryawa. Cikin kuka Maman Sabeera ta kirawo k’awarta Ramatu a waya tana sanar da ita tashin hankalin da suka wayi gari dashi, a fujajan Ramatu tace gata tafe maganar yafi k’arfin ayita a waya dan dama basuda nisa unguwar tasu. Sabeera kaw tuni ta fice dikda mahaifinta ya mata iyaka da waje balle gidansu Sadiya tin bayan abinda ya faru. Ta’aziyan mahaifinsu ne kawai Mamanta Ta mata cover suka tafi tare. Tafiya Sabeera take a layin tana jin zuciyarta na mata wani irin d’aci, babu addu’an da take cikin zuciyarta face Allah yasa duk abubuwan nan da taji k’arya ne babu gaskiya ko guda a ciki.. Bata jin zuciyarta zata iya d’aukan cin amana daga babban aminiyarta irin Sadiya wacce ta d’auki yarda da komai ta d’aura mata. Tana tafe tana tinanin tazo wuce shagon Maman Emeka ai kuwa saiga wasu ‘yanmata ‘yan unguwar a k’ofar Kantin sun Sai bredi da dangin abin kari kumallo.. D’ayar ta tab’a d’ayar tana nuna mata Sabeera dake had’a hanya zata nufi lungun gidansu Sadiya. Cikin azama suka nufo Sabeera suna kiran sunanta, taja Ta tsaya tana dubansu da idanunta da tuni sun kod’e sunyi ja dan kuka.. “Laa Sabeera ina kika nufa..? Kardai gidansu Sady Pretty..” Ta d’an tab’e baki kad’an yace “Ai kuwa ko Jiya naga Babanki k’ofar gidan yana zance kuma kaman Sady Pretty na gani..” D’ayan ta cab’i zancen da fad’in “Ni da naga motar Babanta bakin lungun ma nayi zaton Sabeerar ce ashe ashe dai Baba ne..” Cikin tsananin huci Sabeera ke dubansu, ta kasa magana sai dubansu da idanu da take.. ‘Yanmatan suka dubi juna kafin d’ayar ta tab’e baki ta janyo hannun ‘yaruwar tata tana fad’in “Kinga k’awata Zo muje.. Allah dai ya kyauta k’awancen cin amana..” Tamkar wacce aka dasa dutse haka Sabeera ta tsaya a wajen.. Shikenan dai Wato ta tabbata da gaske Mahaifinta saurayin Sadiya ne.. Kuma ko da wasa bata tab’a hasasho hakan ba, bata tab’a tunanin hakan ka iya kasancewa ba.. Da k’yar take d’aga k’afafunta tana ganin hanya na rabe mata bibbiyu.. A haka Ta k’araso gidansu Sadiya. Sadiya da Umma na zaune tsakar gidan tana duba k’afar Umma da har yanzu yake d’an mata ciwo, tamkar wacce aka jefota haka sukaga Sabeera akansu.. Zuciyar Sadiya yai wani irin tsinkewa yayinda Sabeeran ta zuba mata idanu. Umma ce tai k’arfin halin cewa “A’a Sabeera kece tafe.. Sannu da zuwa.. K’araso ki zauna.” Ko gizau Sabeera batai ba saima duban Sadiya da take. Umma ta dubi Sadiya ta kuma dubi Sabeeran da irin kallon da take ma Sadiya. Kafin Umma tai wani aune Sabeera ta k’araso ta duk’a yanda Sadiya ke duk’e suna fuskantar juna saidai kan Sadiyar a k’asa yake. “Ki fad’a mun gaskiya da bakinki.. Shin da gaske ne..? Sadiya da gaske ne abinda nake ji tsakaninki da mahaifina..?!” Izuwa lokacin hawaye sun soma ambaliya saman fuskar Sadiya, ta kasa d’agowa ta dubi Sabeera sai hawaye dake zarya saman fuskarta. Cikin zuban hawaye da tsananin d’aga murya Sabeeran ke ci gaba da fad’in “Talk to me Sadiya.. Tell me the truth.! Ki fad’a mun gaskiya.. Wacece ke a wajen mahaifina..! Ki fad’a mun Sadiya..!!” Ta k’arashe tana damk’o kafad’un Sadiya tana mai jijjigata da iya k’arfinta hawaye na ambaliya saman fuskarta a yayinda kukan Sadiyar ma ya k’aru. Umma dake gefe ta kasa tab’uka komai sai hawayen da itama taji suna zubo mata. Cikin muryar kuka ba tareda ta d’ago ta dubi Sabeeran ba take furta “I’m sorry.. I’m sorry Sabeera.. Please forgive me.. Dan Allah ki yafe mun..!” Take jikin Sabeera ya sake gaba d’aya.. Maiyasa Sadiya take bata hak’uri.. Kenan da gaske ne.. Kenan maganganun da mutane suke fad’i gaskiya ne.. Sadiya da mahaifinta... Ji tai Ta kasa k’arasa tunanin sabida wani irin jiwa dataji na neman kaita k’asa. Take taji wani irin k’arfi yazo mata.. Ta hankad’a Sadiyar da k’arfin gaske Wanda saida ya kaita k’asa.. Sadiya ta buga kanta had’ida gwiwan hannunta da tuni ya karje ya soma jini.. Babu shiri Umma ta mik’e da k’yar dikda k’afarta dake mata ciwo Ta nufi kan d’iyarta. Sabeera ta kuma yowa kan Sadiyar tana kuka sosai take fad’in “Sai na kasheki kafin ki zama matar Babana..!” Tayo kanta tana k’ok’arin fuzgota saidai tuni Umma ta raba tsakaninsu ta tallafi Sadiyar dake kuka sosai tana duban Sabeera dake k’ok’arin funcikota.. Cikin kuka Sabeera ke furta “I trusted you.. I believed in you.. I never doubted you.. I never judged you.. Duk abinda mutane zasu fad’i akanki Sadiya dai dai da rana guda ban tab’a yarda ba.. Ashe duk ba haka bane.. Ashe ked’in da gaske macijiyace mai bak’in guba.. Ta yaya zaki min haka.. Ta yaya zaki aminiyar data aminta dake irin haka Sadiya..!” Ta kuma yowa kanta tana kuma janyota tana fad’in sai tayi ajalinta. Daidai lokacin Baban Sabeera ya shigo da shopping bags hannunsa, nan ya tadda wannan hargitsi dake tashi cikin gidansu Sadiyar. Da tsananin mamaki yake duban Sabeera dake k’ok’arin kaima Sadiya duka Umma na tarewa. “Ke Sabeeraa.!!” Ya fad’i cikin daka tsawa yana mai fuzgo Sabeeran had’ida d’aura mata mari maiji da lafiya.. Sabeera ta tsaya Cak tana duban mahaifin nata cikeda tsananin mamaki hannunta guda dafe da k’uncinta. Sadiya kaw tuni ta rungume mahaifiyarta tana kuka sosai.. “Dan gidanku ashe bakida hankali.. Ashe ke shashasha ce ban Sani ba.. Uban wa ma ya baki izinin fitowa daga gida.. Matar nawa zaki daka dan bakida kunya bakida hankali Ko..!” Baki sake kurum Sabeera ke duban mahaifinta da kalaman da yake, tana ganin kaman mafarki take ba gaskiya bane.. Tanada tabbacin ba don zafin sauk’ar marin dataji a k’uncinta ba zata iya cewa mafarki take ba gaskiya bane.. A guje Sadiya dake tsananin kuka ta shige parlor yayinda Baban Sabeera yai yunk’urin bin bayanta yana fad’in “Baby.. Baby kiyi hak’uri dan Allah I’ll deal with her myself..” Cikin hawaye Umma Ta katsesa da fad’in “Ya isa dan Allah..!” Tai saurin bin bayan Sadiya tana ambato sunata ga k’annenta da tuni sun fito suna kallon abinda ke faruwa. Baban Sabeera kaw hannunta ya damk’o yana fad’in “Shige muje ki sanar dani ubanda ya koya miki rashin kunya..” Haka ‘yan lungun sukaita lek’e wasu na k’us k’us d’in an fara dan kaf lungun gidansu Sadiya ne bai rabuwa da hatsaniya da tashin hankali.. Daga wannan sai wancan.. Sadiya kam kulle kanta tai a d’aki tana kuka sosai kaman ranta zai fice. A b’angaren Maman Sabeera kaw Ramatu tazo sun k’ule a d’aki suna tattauna lamarin tareda neman mafita. Ramatu Ta nusa tace “Ai wllhi Rahina Kema da naki, idan b’era da sata daddawa da wari.. Ni tin yaushe nace ki raba ‘yarki da wannan yarinya Sadiya mai shegen kyau kaman aljana.. Wannan yarinyar tana shigo miki gida Ta shnatak’e kaman gidan Ubanta, santaleliyar yarinya irin wannan kice min mijinki bazai d’aura idanu kanta ba..” Maman Sabeera tace “Wllhi Ramatu ban tab’a kawo haka ba tinda naga bama ya son alak’arsu.. Kuma ni ban tab’a yarda yarinyar lalatacciya bace kaman yanda ake cewa _Never judge a Book by its cover_ toh ban tab’a munana ma yarinyar nan zato ba dan wataran wanda kake zaton mutumin kirki ne bashi ne mutumin kirkin ba, wanda kayi zaton na banza ne sai kaga shine mutumin kirkin.. Ni da har ina sha’awanta ma Abdallah (yayan Sabeera dake karatu k’asar waje..) Amma ni koda wasa ban zaci Wai Alhaji zai d’aura idanu kanta ba...Yayi aurensa ni bazan hanasa ba ya auri ko wacece amma kam banda Sadiya k’awar Sabeera... Ina zan Kai wannan d’imbin bak’in ciki da tashin hankali ga uwa uba Sabeera taji komai..” Ramatu ta tab’e baki tace “Rahina zama fah bai ganki ba, tashi zakiyi muje har gidansu yarinyar nan muci uban uwarta da kyau dan itace tsararmu ba d’iyarta ba.. Ki daina wannan simi simi d’in nan naki ki tashi ki karb’a ma kanki da yaranki ‘yanci idan kuma ba haka ba ki zuba ido ki zama ‘yar kallo cikin gidanki.. Kinaji kina gani yarinya ‘yar cikinki Ta k’unsa miki bak’in ciki. Keda gidanki yafi k’arfinki.” “Ramatu sanin kanki ne ban isa na hana namiji son mata ba dan a halittarsu ne amma damuwar shine kar ya nemi na banza, yayi auren dan shine mafi a’ala tinda Allah ya huwace masa daman auren mace sama da guda. Sannan ni idan zai auren ya auro ko wacece amma tsakani ga Allah banda Sadiya.. Idan ni zan iya jura Sabeera fah.. Sabeera bazata iya jura ba.. Ni wllhi tashin hankalin da ‘yata zata shiga nake tunani.. Yaran nan fah bacci ne ke rabasu sanda suke makaranta kafin su tafi yajin aiki har karatu tare suke..” Ramatu Ta katse Ta da fad’in “Ni dan Allah kin isheni, kin cika ni da surutun da babu gaira babu dalili.. Dik kin San da wannan shine kika d’add’agoni ko karin kummalo banyi ma mijina ba.. Dama Kinsan wa’azi zaki kirani kimin shine baki sanar dani tin a waya ba.. Ni wllhi indai hakane kar Ki sake neman shawari daga wajena.. Kije can ki k’arata da sanyin zuciyarki aita cutanki bak’in ciki ya turaki rami.. Idan kin canza shawri kya nemeni.. Ni Kinga tafiyata..” Bata ida rufe baki ba sukaji kukan Sabeera na tashi Babanta rik’e da Ita yana fad’in ta gama rashin kunya daga yau.. A tare Maman Sabeera da Ramatu suka nufo parlorn. Sabeera ta fad’a bayan mahaifiyarta a guje tana kuka.. Yayinda Babanta yaci gaba da aza babbar riga yana k’ok’arin ciro igiyar decoder yake fad’in “Har ni zakije ki wulak’anta.. Kije kici wa matar da zan aura mutunci sabida bakida hankali.. Yau zakiji a jikinki..” Ramatu kaw yab’e baki saitin kunnen Maman Sabeera Ta rad’a mata“K’awata ni na wuce kafin mijinki ya had’a dani yace ni ce uwar zigi..” Maman Sabeera da tuni Hawaye ya wanke mata fuska Ta tare d’iyarta tai tana fad’in “Wllhi bazan Barka ka daketa ba..” Lokaci guda ta tura Sabeerar d’akinta ta maida k’ofa ta rufe.. Tare k’ofar d’akin tai tana hawaye alamun bazata barsa ya shige ya daki Sabeera ba.. Sai sakin huci yake yana duban Maman Sabeera yana fad’in “Rahina ki bani hanya na koya ma yarinyar nan tarbiya.. Tarbiyar da kika kasa bata..” Cikin zuban hawaye Maman Sabeera ke dubansa, lokaci guda take furta “Wane tarbiya kake magana..? Wane tarbiya ne zaka bata wanda na gaza bata..? Tarbiyar rufeta a gida ka hanata fita Ko k’ofa dan kana tsoron kar a lalata maka Ita Ko mai..?” Da tsananin mamaki yake dubanta “Rahina kike fad’awa magana irin haka.. Kina cikin hankalinki Rahina..? Dan kawai nazo da batun zan k’ara aure sai ki nemi ki jefeni da sharri..!” Cikin zuban hawaye Maman Sabeera ke fad’in “Ni ban jefeka da sharri ba, sannan ban tab’a zarginka da aikata abu maras kyau waje ba, na sani idan kana gida Kai nawa ne amma idan ka fice zaka iya zama na kowa idan ka zab’a hakan.. Saidai ka Sani yaran nan kanadasu.. Idan ka lalata na wani ko cikin Tandu kake saka Naka ka b’oye wllhi sai an rama irin abinda kayi ma na wasu akansu..” Katseta yai da fad’in “Anya Rahina kina cikin hankalinki.? Ni kike yab’awa magana dan nace zanyi aure.. Toh bari kiji na fad’a miki Asabar d’in mai zuwa d’aurin aurena tareda Sadiya, Idan an kawota idan Kinga dama kar ki zauna..” Da tsananin mamaki Maman Sabeera ke dubansa hawaye basu daina zarya saman fuskarta ba “Aure kace.. Aure wannan asabar d’in.. Yarinyar da kak’i jinin alak’arsu da Sabeera shine zaka zago kace ita zaka aura nan da kwanaki biyu rak..” Tai maganar tana mai d’ago yatsun ta guda biyu hawaye na gangaro mata.. Cikin sanyin jiki Ta nufi d’akinta ta maido k’ofa ta rufe ba tareda ta kuma cewa komai ba, amma kam kaida gani kasan da zata samu ta fidda bak’in cikin dake k’unshe cikin k’irjinta ko ta hanyar kuka ne da Ta d’an ji sanyi cikin zuciyarta. Tsaki Alhaji Isyaku ya buga yana fad’in “Aikin banza aikin wofi.. Ni ma na tsaya Ina miki bayani.. Idan na aurota idan kinga dama kar ki zauna a gidan.. Aure kuma babu fashi.” Ya juyo ya dubi k’ofan d’akin Sabeera yace “Ke kuma k’ofa na kumaji kin lek’a balle har kije kici mutuncin matata sai na aurar dake sadaka a masallaci..” Daga haka sa kai yai ya fice daga gidan fuu kaman zai tashi sama yana aza babbar rigarsa. ** Sadiya na kwance saman gado ta kasa cin komai har yamma, banda aikin kuka bata komai, harta k’annenta su Ashiru da basu wani fahimci wainar da ake toyawa ba saida suka taru suna bata hak’uri Ta tashi ta saka wani abu a cikinta.. A ‘yan kwanakin tun bayan fasa aurenta da Sagir idan kaga Sady Pretty sai ta baka tausayi musamman idan ka santa a lokutan baya lokacin da tashen kyaunta. Gaba d’aya Ta rame tayi duhu kaman ba Sady ba.. A haka Umma ta shigo ta taddata da k’annen nata sai aikin lallashinta suke. Umma ta shafa kansu tace su fita su basu waje. Babu musu Asiru ya ja hannun k’anins Habeeb suka fice. Suma yaran duk sun koma abun tausayi.. A hankali Umma ta zauna gefen kan Sadiya tana shafa kwantattun sumarta wanda suke a kwance luf ga sulb’i ga tsawo. “Sadiya ki tashi kici wani abu kinji, zama haka bazai taimaka ba.. Ki tashi dan Allah idan nima ba so kike nak’I ci ba..” Umma tace tana kuma gyara mata sumar nata wanda ke zube saman pillown da take kwance bisa. Bud’e baki tai da niyyar magana amma sai taji kuka na zuwa mata, da k’yar Ta iya furta “Sabeera gaskiya Ta fad’i Umma.. Nid’in tamkar macijiya ce.. An yarda dani nayi yaudara... An aminta dani naci amana.. Umma I’m nothing but a betrayal.. Tell me please Umma, am I really a bad person.?!” Tai maganar tana mai mik’ewa zaune had’ida fuskantar mahaifiyar tata. Hannayenta Umma Ta rik’e tana mai share mata hawayenta “You are not a bad person Sadiya.. You are only human.. Dukkanmu muna kuskure, mafiya kyawun masu kuskure a cikinmu Sune wad’anda idan sun gane kuskurensu sai su tuba su gyara.. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Inada tabbacin Sabeera will come to understand cewa baki ci amanan ta ba.. Da sannu lamura zasu daidaita kinji koh..” Ta k’arashe tana mai janyo Sadiyar cikin jikinta. Sadiya bata iya furta komai ba Sai lamo da tai cikin jikin mahaifiyarta tana mai lumshe gajiyayyun idanunta. ** Yamma lis ana kiraye kirayen sallar magrib suka shigo gidan gonar, ko waya basuyi ba balle suce aje airport a d’aukesu dan dama tafiyar ‘yar solo ce. Motar haya suka yo shata suka taho garin. Meema sai mita take tana fad’in yau sai tayi ciwon jiki dan ita Allah ya gani bata tab’a shiga motar haya ba sai yau.. Safeenah tai gajeren tsaki tace “Toh wai da kika damen da mita nid’in na saba shiga ne.. Ni bama wannan ba Allah yasa muna shiga Inne tace duk mu tattara koma gobe gobe.. I’m sure zata goyi bayana wann karon.” Meema ta danna mata harara cikeda takaici tace “Malama returning flight zuwa Abuja sai an shiga next week.. Zamuyi weekend mu kwashe kwanaki kawai kiyi shirin zaman garin nan..” Tai tsuka tana kuma jan suitcase d’inta “Ni wllhi Adda Feenah kin gama dani dan banyi niyyan zuwa ba ga jaraban wannan masifaffiyar tsohuwar na jiranmu..” Feenah tabi bayanta cikin sauri tana kiran sunanta tana jan nata jakan da k’yar gashi babu kowa da alama ma’aikatan dik sun tafi sallah da alama. Safeenah Ta kuma sakin tsuka tana jan jakan. A daidai mashigar da zai sadaka da k’ofar babban parlorn Ajidde dake rik’eda bak’in ruwa mai kaman black ink cikin kwano sukai karo itada Safeenah wacce shigowarta kenan tana kokawa da Jakarta, ai kuwa bak’in ruwan nan bai shek’e ko Ina ba Sai fuskar Safeenah da yake fari tas Wanda lokaci guda bak’in ruwan nan ya maidasa bak’ik’irin kaman tayi wanka da ruwan da aka wanke bayan tukunya.. Meema dake gefe baki sake take duban fuskar Safeenah da yai bak’ik’irin yayinda Ajidde ma ta saki baki da hanci rik’e da kwanon tana duban matar data wanke mata fuska da maganin Kyallu. “Wow.! What a nice welcome gift you’ve received Addah Feenah.” Meema tace tana mai tintsirewa da dariya. Ajidde kaw tuni Ta arce a guje tana fad’in “Kai wllhi Allah bazanyi dariya ni kad’ai ba.. Kuran tashe dole yaga wannan.” Safeenah da har lokacin ta kasa koda motsawa da tsananin mamaki take duban yarinyar kafin ta maidoda dubanta ga Meema da ke ta faman k’yalk’yala dariya harda ciro waya tana fad’in Ta tsaya tai mata video.. A daidai exit d’in da sukai zasu had’u ta taddasa, da alaman isowar Ta yake jira.. Musaddiq na hangota ya kuma duba agogon dake d’aure hannunsa yana girgiza kai “Ya na ganki haka.. Ina maganin..?” Ajidde bata amsa sa ba sai dariya da take har tana zama a k’asa. Takaici ya cika Musaddiq jin har an kusa sallamewa a masallaci “Ke Crazy Dove ki tashi kimin magana kafin su fito daga masallaci su samemu a nan.. Ina maganin yake..?” Ta kuma tintsirewa da dariya tana fad’in “Ka tab’a ganin dodanniya..?” Mu Sadiq ya girgiza kai yace “Dodanniya kuma..” Ajidde ta mik’e tana fad’in “Kai sauri ka biyoni kar ta b’ace..” Da tsananin mamaki Musaddiq ke dubanta, sai kuma ya girgiza kai yana furta “Crazy Dove, you truly are crazy..” Lokaci guda ya take mata baya. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *19* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin tsananin b’acin rai Safeenah da har lokacin ta kasa koda motsa ‘yar yatsar k’afarta take duban Meema da har lokacin dariya take tana mata video sa waya “Meema you know I’m a very sensitive person, and I don’t take things lightly...Don’t make me take it out on you..!” Tai maganar tana bud’e hannayenta cikin tsananin b’acin rai da huci. Daidai lokacin Ajidde ta k’araso hannu biyu aka tana dariya. Cikin tsananin mamaki Safeenah Ta karkato tana duban mahaukaciyar yarinyar wacce tai mata wannan aika aikan sannan bama tasan ta aikata ba balle Tai tinanin bada hak’uri waima dariyarta take tana duban fuskar tata.. Wani irin wawan birki Musaddiq yai ganin wacce Ajidde ta wanke da ruwan maganin nan ba kowa bace face Safeenah, dikda bai ganeta daga fari ba har saida yaji tana fad’in Meema ta damk’o mata shegiyar mai aikin nan taci uwarta ta koya mata manners. Baki sake Musaddiq yake duban Safeenah da sam baisan da zuwansu ba yana duban yanda Ajidde ke dariya kaman sabuwar Kamu. Meema ta yatsina fuska tace “Ni ce zan tab’a jikin wnn mahaukaciyar Adda Feenah.. Chabd’i God forbid.! You know I’ve a very sensitive skin. I might easily catch infection.. Kawai ki rungumi k’addara kizo muje ki wanke. Ana haka Hindu ta k’araso jin hayaniya daga parlorn. Musaddiq ya dafe goshinsa kad’an yana jinjina rashin hankalin Ajidde wacce taima Meema gwalo tana rataye jakarta tana fad’in “Ni kuma sai na tsaya ki kamani. Tab lallai kina ruwa.. Ko banza naci dariya wllhi.. Allah bamu Alheri dodanniya.” Tana ida fad’in haka Ta kuma arcowa a guje tana ma Meema gwalo. Daga Meema har Safeenah da tsananin mamaki suka bita da kallo yanzu kam sun gama yarda Tanada tab’in hankali. Saida tazo daidai yanda Musaddiq ke lab’e ya janyo jakanta da k’arfi ta dawo da baya. Ihu ta saki tana fad’in “Dan Allah Dodanniya kiyi hak’uri.” Dik a zatonta Safeenah ce ta biyota. “Ke Crazy Dove.!” Musaddiq ya fad’i cikin daka tsawa. Jin Musaddiq ne ya sanyata sauk’e ajiyan zuciya ta bud’e idanu tana fad’in “Wllhi kallo ya shige ka.. Kaga..” Katseta yai da fad’in “Waike lafiyarki kuwa.. Kinsan abinda kika aikata kuwa.. Yanzu idan ‘yanmatan nan suka biyoki suka lakad’a miki duka waye zai ceceki..?” Ta sakar masa murmushi tana kashe masa idanu guda, abindake mugun basa dariya idan tai. Lokaci guda tace “Toh ba gaka nan ba.. Na San zaka tsare min kaman yanda ka tsare min sanda mugun abokin nan Naka mai bindiga ya biyoni wanda baya dariyar nan.. Mutum kullum kaman shed’an kasan d’azu ma na gansa ya fito wancan k’ofar fuskar nan babu annuri..” Ya tsareta da idanu kafin yana mamakin halin Ajidde, lokaci guda ya girgiza kai yace “Watau sabida ina nan shine kike taro masifa ki gudu kice zan tsare miki koh.. Toh randa banzo aiki ba fah..” “Zan jiraka har kazo ai..” Ta bashi amsa kai tsaye kayanta. D’an girgiza kai yai yace “Kina jina idan baki daina shiga abinda babu ruwanki ba wataran zaki taro abinda yafi k’arfinmu daga ni har ke..” Yai maganar cikin yanayin b’acin rai. Ta d’an dubesa da kulawa wannan karon “Kayi fushi ne..?” “Banyi ba.. Inaso kimin alk’awari gobe zaki bama matar nan da kika b’ata mata fuska hak’uri.” Tsuke fuska tai ba tareda tace komai ba. Musaddiq ya tsareta da idanu babu walwala wann karon. “Tau naji ince Dodanniya.. Anji anji.. Anji d’in.. Za’a bata hak’urin.. Hankalinka ya kwanta.” Tsareta da idanu yai yana duban yanda take maganar tana duban wani b’angare. Harga Allah mugun nishad’i take saka sa, shirmenta da shiriritar ta mugun nishad’i yake saka Sa. Hannu yasa cikin aljihunsa ya ciro kud’ad’en ya mik’a mata ”Oya take this..” Bata karb’a ba sai dubansa da take a kaikaice alamun tana fushi dashi yace sai ta bawa Dodanniyar cen hak’uri wanda bama tasan ‘yanuwansa bane. “Karb’a mana ya kuma fad’i yana dubanta.. Ko sai na baki hak’uri nima..?” Wannan karon murmushi tai tana wani kad’a kai dan sosai take jin dad’in yanda yake damuwa da damuwarta abu ne da ba’a tab’a nuna mata ba a rayuwarta sai akansa tasan hakan. Ta girgiza masa kai tace “Ai yau Inna Kyallu batace na sato mata wani abu ba, wanda ka bani jiya kace na bata kuma na bata..” Tsayuwarsa ya gyara yace “Ke baki gane ba, Idan kika kai mata a jere kwana biyu a matsayin sato mata kike zata rage duk wasu abubuwan da take miki tinda imaninta kenan..” Ajidde ta tsaresa da idanu tana dubansa “Toh randa bakadashi fah..?” “Kar ki damu badai ina aiki ba.. Zan tara mana na baki ki kai mata..” Ta murmusa kad’an tana mai rufe fuskarta da tafukan hannunta. Shima kafeta da idanu yai yana mai sakin murmushin. Harga Allah Ajidde na d’aya daga cikin dalilin da yasa garin ke masa dad’i baya fatan abinda zaisa ya daina ganinta a gidan gonar.. Zaiyi dik yanda zai ya taimaka mata Ta daina mummunan d’abi’a na sata da Innarta ke koya mata koda hakan na nufin yayi aikin k’arfi ne ya samu Kud’i ya bata Ta fanshi kanta wajen Kyallu. “Maza Jeki kar dare yayi.” Ya fad’i yana dubanta. Ta jinjina masa kai a hankali kafin tai masa sallama. Yana nan tsaye yana dubanta tana tafiya tana cilla Jakarta. Murmushi saman fuskarsa. Lokaci guda itama take juyowa tana sakar masa murmushi, har saida Musaddiq yaga shigewarta kafin ya nufi masallacin dake nan cikin Gidan Gonar da zummar gabatar da nasa sallar dan already sun sallame. ** A can cikin gida kaw Inne ce ta tsaresu tanai masu d’add’aya dan babu wanda yasan da zuwansu sai ganinsu akai kaman sauk’an aradu dikda cewa Meema tace da sanin Mommy da Daddy suka zo. Inne tai k’wafa tana mai kuma furta “Idan da sanin iyayenku kuka taho ke Safeenah mijinki yasan kina tafe ne.. Ko kuma saran da kuka d’auko kenan, shi yazo ke kin biyosa.. Zai shigo ne ya sameni, dukkanku Ina dai dai daku nikam..” Meema ta mik’e tana fad’in “Nidai na gaji d’aki nake son zuwa na huta.. And I’m starving already.. Hindu..! Hindu.. An gyara mana d’akin..” Inne da Ta saki baki tana duban Meema dak’uwa tai mata tana fad’in “Kinci gidanku.. Baza’a gyara maku d’akin ba, idan baku da hannaye kuna iya kwanciya a haka.” Ta dubi Hindu da k’arasowarta kenan tana fad’in “Ummilo tana can tana gyarawa..” Lokaci guda Inne tace kije kice mata ta bar d’akin mata ne, zasu gyara da kansu..” Baki sake Meema ke dubanta kaman zata kurma ihu “Haba Inne Haba Inne.. Dan Allah fah we just arrived here, and I’m pretty tired wllhi Ko hanuna ban iya d’agawa.. Please mana Inne, I can’t do any house chores wllhi..” “Ni kike ce ma kin gaji baki iya ba idan ban tashi na jefaki cikin turmi na dakaki ba, sangartacciyar banza a rasa da wa za’a mun takwara sai ke.. Matsa min a nan kafin na tashi na daddakeki.. Kuna mata kuce komai sai an maku saikace ba gidan wani zaku ba.. Ba dai kunzo nan ba, toh har girki sai kunyi ni bazan lamunci goyon sangarci da iyayenku sukai maku ba.. Kun sanni sarai ba a nan zakuyi iya shegenku ba..” Meema ta shige tana bud’e murya kaman mai kuka “Wayyo Wayyo na shiga uku.. Wllhi this is all your fault Adda Feenah.. I shouldn’t have followed you here.. Wayyo Allah na..” Haka Meema ta dingayi kaman wacce ake bugunta, ta shige tana tafiya tana jefa k’afafu tana fad’in dik Safeena ce ta jawo mata. Ana haka Musaddiq yai sallama ya shigo. Kallo d’aya yaima Inne ya fahimci a d’ane take yau ko ba’ace ba su Safeenah suka kunnata.. Ya nufo parlorn yanda Inne ke zaune tana girgiza k’afafu. Musaddiq da ya hango Safeenah zaune da bak’in fuska tana yatsina fuska dariya ya soma yana fad’in “OMG! Who do we have here.. Hey yaushe kikazo..? And what’s that on face..?” Ya k’arashe yana kuma k’unshe dariyarsa. Harara Feenah ta watsa masa “Kaga babu ruwanka dani.. Mind your own business..” Musaddiq ya kame bakinsa yana fad’in “Allah baki hak’uri Dodanniya..” “What..? Mai kace.. What did you just call me..?” “Abinda kunnenki yaji..” Ya bata amsa kai tsaye. “Inne Kinga kice ya fita hark’ata..” Safeenah tace tana kuma turo baki. “Ke rufewa mutane baki ank’i ace d’in..” Sakaryar banza. Musaddiq ya k’unshe dariyarsa yana k’ok’arin k’arasowa kusan Inne dan yanzu har wani shiri ne na musamman ya shiga tsakanin Musaddiq da Innen tinda ya fara watsar da rayuwarsa ta baya. “Gidado na Zo ka shige abinka kaji fita sha’aninta..” Inne tace tana duban Musaddiq d’in. “Toh Inne na..” Ya fad’i yana gwalo ma Safeenah had’ida kashe mata idanu. K’wafa Safeenah tai ba tareda tace komai ba dan harga Allah alla alla take Masoyinta Mu’azzam ya shigo Ta gansa. Aiko bata ida tinanin ba ta hangosa yana tafe ya nufo k’ofar parlorn, yana sanye cikin k’anan kaya dark blue polo shirt da faded pants. Idanunsa na kan wayar salularsa dake hannunsa, hasken k’wan wutan manya manyan wutan lank’arki da suka k’awata gaban gidan sun haske masa fuska tarau, gani tai kaman ma zuwansa nan ya k’ara haske da kyau ne babu damuwar CID akansa babu komai.. Ta saki murmushi a hankali dan tama mance da abinda ke fuskarta. Idanunta akansa tana sakin murmushi har yai sallama ya shigo parlorn. , idanunta naga masoyinta wanda shima ita yake duba cikeda mamakin bak’in dake fuskarta dan sam bai fahimci wacece ke zaune wajen ba har saida ta bud’e murya tace “My Halal.!” “Safeenah.!” Ya furta a hankali yana mai kuma shigowa parlorn mamaki fal fuskarsa, har lokacin idanunsa na kanta. Bama mamakin bak’in fuskar nata yake ba, mamaki yake yaushe Safeenah tazo. Inne ce takatsesu da fad’in “Yauwa k’araso dama kai nake jira.. Kazo ka sanar dani idan kai ka bata lasisin Ta dinga gantali saman kwalta da sararin samaniya Ita ba tsuntsuwa ba, tana a matsayin Amarya wacce ko tarewa batai ba.. Ai Iyayen naku ma basuda hankali da suka zuba maku idanu haka.. Toh ni bazan lamunci wannan asaranci ba.. Kafin Dangi su fara k’anan magana tinda shi Marwan ya zuba maku idanu kuyi yanda kuke so da rayuwarku ni zan masu abinda suka kasa.. Zaku tare a nan. Idan yaso a miki sabon jere a nan..Tinda abin naku ya zama haka sai a gyara maku d’aya b’angaren ki tare a nan.” Ta k’arashe tana duban Safeenah da ta saki baki tana jin Innen Wai zasu tare a nan. Safeenah zatai magana Inne tace “Rufe mun baki.. Ba shawarinki nake nema ba.. Bazaku bar mun abun fad’i a dangi ba.. Na riga na gama magana.” Ta k’arashe tana mai mik’ewa da zummar barin parlorn. Sai kuma ta juyo ta dubi Safeenah tace “Ke kuma Ki tashi kije ki wanke wann bak’ar fuskar taki kafin Ki razani mijin naki da ita..” Sai sannan Safeenah ta tina da bak’in dake fuskarta, tai saurin Kai hannu zata tab’a sai kuma ta kasa ta shiga muryar kuka tana fad’in “Oh my gosh.. Eww.. I can’t touch it, It stinks.. My Halal please help me get rid of it.. Wllhi I can’t touch it..” Yanda take da fuska da hannu Kai kace kashi aka watsa mata. “Meye a fuskarki..?” Ya tambaya yana dubanta. “I don’t know.. Wllhi wata mahaukaciya ce ta watsa min.. Inne tace wai magani take bawa Mamy.. My Halal wllhi Mahaukaciya ce ka koreta.. I don’t trust her around Mamy..” Ta k’arashe tana kuma yatsina fuska da hannu. “Biyoni..” Ya fad’i yana mik’ewa tsaye. Babu musu Safeenah ta biyo bayansa.. D’akinsa suka shige ya maida k’ofan ya rufe. Ya nuna mata hanyar bathroom “Shige muje..” Ta d’ago tana dubansa da mamaki sai kuma ta shige sim sim.. Mu’azzam ya take mata baya. Washbowl suka nufa yace ta saka fuskarta, tanaji ya d’auko sabulu yana wanke mata. Yana ida wanke mata ta d’ago fuskarta tana duban mirror saidai to her surprise Mu’azzam ta hanga ta cikin mirror d’in yana rage tufafin jikinsa.. K’akk’arfan suffarsa da yasha training irin na Force ya bayyana. Ta zaro ido a tsorace had’ida juyowa tana dubansa, tana ganin ya soma nufota Ta soma k’ok’arin komawa da baya.. Fincikota yai ta fad’o jikinsa hakan yai daidai da tab’a makunnin shower dake kansu ai kuwa ruwa ya soma zubowa kansu. Tana jin hannunsa saman zip d’in rigarta yana k’ok’arin zugewa.. Har lokacin ta kasa janye idanunta daga duban fuskarsa da ruwa ya wanke tas Wanda sam babu walwala.. Zuciyar Safeenah yaci gaba da tsinkewa.. Cikin sauri kaman wacce aka zabura, tamkar wacce ta tina wani abu tai saurin rik’e hannun nasa ta hanasa tana mai girgiza masa kai ga idanunta da sukai rau rau. Wani irin duba yake mata, lokaci guda ya kamo hab’arta had’ida d’ago kanta kad’an ruwan na zubo mata a fuska. Tsoro da tsananin firgici ya hango saman fuskar tata wanda dik a nasa tinanin tsoran kasancewa dashi take a matsayinta na budurwa sabuwar aure da bata tab’a sanin wani d’a namiji ba.. “Why.? Ba abinda kike so bane..? Ba abinda kike bibiyata sabida shi ba kenan.. Well na shirya baki yanzu a nan idan har zaki k’yaleni na gama binciken mutuwar ‘yaruwata da nake in peace ba tareda Kinyi causing mun distraction ba.. Fine zan baki sai ki daina bibiyata har na natsu na ida binciken da nake..” Lokaci guda hawaye ya soma zarya saman fuskar Feenah.. Ta shiga girgiza kai hawaye na gangaro mata “No ni dai ba haka bane.. Dama dama kawai I was missing you ne.. That’s why I followed you here..” Tai maganar hawaye gauraye da ruwa saman fuskrta. Ya tsareta da idanu yanda take shivering.. Janyota jikinsa ya kuma dikda tsananin rawa da jikin nata keyi, saitin kunnenta yake rad’a mata “Really..? Did you miss me that much..” Ya fad’i yana mata wasu salo irin nasa wanda tuni sun kashe mata jiki.. Lokaci guda yaci gaba da furta “Dama baki shirya ba kiketa bibiyata..?” Tai saurin girgiza masa kai tana hawaye.. Zatai magana ya rufe bakinta da nasa. K’arar wayarsa dake cikin aljihun wandonsa ya dawo da hankulansu.. Yai saurin zaro wayar yana duba mai kira, ba kowa bane face abokinsa kuma colleague d’insa Assad. Yai saurin kashe ruwan kafin ya shiga janyo Feenah yana fad’in “Zo ki fice..” Ta dubesa da mamaki yanda yake fuzgota saikace ba shine ya nuna San kasancewa da Ita yanzu yanzu ba “Mu’azzam a haka zan fice.. Duba fah ka gani from head to toe a jik’e nake fah..” Har saida suka k’araso k’ofa kafin ya turata ya janyo k’ofar ya rufe ba tareda yace mata komai ba.. Baki sake Feenah ke dubansa da tsananin mamaki. Yana rufe k’ofar ya d’aga wayar Assad “Hey Officer, hope all is well with you..” Mu’azzam yace yana mai tsane jikinsa da towel. Saida suka gaisa kafin Mu’azzam d’in ke tambayarsa “How are things at the CID.. Mai da mai kukai discovering so far..?” Assad ya d’anyi gajeren tsaki yace “Things are getting tougher here, tinda ka tafi.. And Chief Jaja ya bud’e mana wuta mu kawo Danger within 2 days... Jiya ya mik’a team report d’inmu office d’in Chief Superintendent a General meeting d’in da akai, and babu wani progress har yanzu and he was even insisting bamuda case against Danger.. Saifa da nai presenting final report d’inmu ne ya tabbata Danger’s involved toh shine ya hura mana wuta mu kawo masa Danger yanda ya shiga ya fita..Ga dukkan alamu so yake case d’in ta lalace a haka ba tareda an sami wani improvement ba.. And Danger is no where to be found.. Dik wani hideout da muke tinanin zamu samesa bamu samesa ba, duk wasu masu criminal records da muke tunanin zasuyi linking d’inmu to Danger still babu wani haske har yanzu..” Fuzar da huci Mu’azzam yai yana tura yatsunsa a sumarsa da suke wet.. “That scumbag I’m pretty sure he’s up to no good again.. Babu wanda ya isa ya rufe case d’in matuk’a ina numfashi.. Sai mun Kai har k’arshe yana so ko baya so.. Assad yarinyar nan itace kad’ai key d’inmu.. Inada tabbacin Babanta kashesa akai ba ordinary accident bane da ya saba aukuwa.. They’re after her family, I’m pretty sure bazasu k’yalesu haka nan ba.. Ya kamata muyi monitoring duk wani abinda ahalinta ke ciki.. Sannan Kai zaka fara tinda ni bana nan.. Go there, find out everything about them.. Dik information d’in da ka samu nasan zai ma investigation d’inmu amfani.” Assad ya jinjina kai kaman yana ganinsa “Copy Sir..” Lokaci guda ya k’arada “Baka tambayeni mutuniyar ka Maleeka ba.. Ita kaw kullum cikin missing d’inka take.. Tana counting days har zuwa randa zakai Reporting back to work.” Gajeren tsaki Mu’azzam yai yace “Banida lokacinku daga kai har ita..” Assad ya tintsire da dariya dan dama tsokanan abokin nasa yai niyya. Sallama sukai kafin Mu’azzam ya zauna saman gado rik’e da wayar yana fuzar da fuci.. Zama bai gansa ba, yasan da biyu Chief yasa aka dakatar dashi dan ya samu sauk’in cimma burinsa cikin sati biyun idan baya nan, yasan muddin yana nan sai yanda k’arfinsa ya k’are bazai tab’a iya stopping d’insa ba.. Fuzar da fuci ya kuma yana jin zuciyarsa na masa zafi. A b’angaren Safeenah kaw kafin ta isa d’aki wayarta ce dake cikin jakarta tai ruri, Meema da fitowarta kenan daga shower taji sautin waya na tashi daga cikin jakan Feenah. Kaman bazata d’aga ba dan tasan bazai wuce Mommy ba k’ila sunyi waya da Inne. Bata shirya ma fad’an Mommy ba. Amma jin wayar ta k’ara ruri ya sanyata k’arasawa jikin jakan ta d’ago wayar tana dubawa. Lamba ce Babu suna.. Meema dai samun kanta tai tana mai sliding kiran da ake.. Lokaci guda ta k’ara a kunnenta ba tareda tace komai ba. Daga d’aya b’angaren Barr Ameer ya murmusa yace “Kin zaci zaki gudu mun ne Safeenah.. Dik yanda kikaje sai na biki.. Bazan tab’a barinki ma D’ansandan nan ba Safeenah.. You are mine.. Ked’in tawa ce ni Barr Ameer.!” D’if Meema ta katse kiran tana kuma duban wayar k’irjinta na wani irin bugawa. “Barr Ameer..?!” Ta nanata a hankali. Daidai lokacin Safeenah ta turo k’ofa ta shigo da jik’akk’un kayanta sai rawar d’ari take. Da mamaki take duban Meema da tai tsaye rik’eda wayarta. Ta soma saurin nufo Meemar tana fad’in “Meye kikai wani tsaye a wajen sororo haka.. And why are you holding my phone.. bani kayata..” Saidai kafin ta mik’awa Feenah wayar saida ta tabbata ta goge kiran.. Feenah ta fuzge wayarta tana aikawa Meemar mugun kallo “Waye ya kira..?” “Babu mana.. Naji kaman wayar tayi ringing ne nazo zan d’auka, nayi tinanin Mommy ke kira Kinsan tawa babu charge.. Nasan dole zata nemu..” Meema tace tana mai bud’e suitcase d’inta. Tsaki Feenah tai tana mai neman towel take fad’in “Sabida kin mata sallama sanda zamu taho Ko..” Meema ta d’an tab’e baki tana duban ‘yaruwar tata. Sai sannan ta kula da jik’an dake jikin Feenar.. “Addah Feenah.. Ya haka..? Ya na ganki a jik’e..?” Tsaki Safeenah tai tana mai nufa hanyar bathroom.. Dariya Meema Ta soma tana fad’in “Kardai horon watsa ruwa yai miki a sanyin daminar nan.. Amma wannan miji naki anyi bak’in mugu wllhi duk wani salon mugunta ya Sani.. Koda yake ba laifinsa bane dama D’ansanda ne ya karanci sharri Da mugunta.. Allah ya cecen wann karon ba’a had’a dani ba..” Ko amsata Safeenah batai ba ta shige toilet kayanta. ** Washe gari sassafe Safeenah ta nufi d’akin Mu’azzam, dan tasan ya fice sallar asuba. Tana shiga ta fad’a kan gadonsa ta lume cikin bargo ta lumshe idanunta kaman mai bacci. Tasan babu yanda za’ai idan ya dawo sallar asuba ya samu tana bacci d’akinsa ya koreta dole ya k’yaleta su k’arasa kwanan tare. Aiko koda ya dawo yasha mamakin ganin Feenah na bacci saman gadonsa, bai tasheta d’in ba ya kwanta daga can gefenta dan jiya bai wani samu bacci ba kusan kwana yai yana tinani tin bayan wayar da Assad yai masa yanda zai b’ullowa al’amarin Danger da Chief Jaja wanda idan yayi wasa zai iya rasa case d’in mutuwar k’anwarsa da ya d’aukarwa mahaifiyarsa alk’awarin kafin ta farka daga wannan jinya nata da izinin Allah sai ya gano waye ya kashe mata d’iyarta. Hakan yasa tuni bacci yai awon gaba dashi. Safeenah tanajin alamun bacci yayi gaba dashi ta mirgino ta dawo jikinsa, zuciyarta fari k’al ta mak’ale cikin jikin mijinta tana shak’ar k’amshinsa dake rikitata.. Baccin ne itama yai gaba da ita.. Ba ita ta farka ba sai wajajen k’arfe bak’wai da rabi na safe sabida iska da aka soma sosai alamun za’ai ruwa hadari ya rufe sama gaba d’aya.. Ta saki murmushi tana duban yanda Mu’azzam ya rik’eta sosai cikin jikinsa alamun shi kansa yana enjoying baccin nasa. Ta k’ura ma kyakkyawan fuskarsa idanu tin daga sumarsa da suke kwance luf har zuwa idanunsa da suma suke a rufe, ta gangaro da idanunta tana duban hancinsa zuwa lips d’insa. Iskan da akeyi shi ya bud’e k’ofar d’akin.. Ajidde da Ta biyo corridor d’in dan zuwanta kenan, nan tazo zata shige k’ofar d’akin Mu’azzam dan kafin ka isa d’akin mahaifiyarsa sai ka wuce wasu k’ofofi ciki harda d’akin Mu’azzam.. Da mamaki take hangan k’ofar a bud’e ta tina sanda ta shiga zata masa sata ya kusa kamata.. Ta soma sauri tana fad’i cikin zuciyarta bari tai sauri ta shige k’ofar d’akin kafin ta hango wannan jakar tasa.. Tana tafe bata fasa lek’en d’akin ba aiko nan ta hango matar nan ta jiya data watsa mata ruwan magani zaune gefensa saman gado tana shafa sumarsa zuwa fuskarsa.. Ajidde ta saki baki da hanci tana duban ikon Allah.. Ji tai bakinta na furta “Kaga ‘yaniska.. Toh asirinku ya tonu tinda kuka mance k’ofa a bud’e..” Bata ida shan mamaki ba saida taga matar nan ta kifa fuskarta kaman dai sumbatar juna suke.. Jikin Ajidde ya d’auki rawa babu shiri ta kwasa a guje ta nufo parlor.. Tana k’arasowa tsakiyar parlorn ta saki wani irin azabebben k’ara wanda idan akwai masu bacci da basu tashi ba ma tabbas sai Sun tashi.. Ihu Ajidde take tana tsalle tsakiyar parlorn tana fad’in ta shiga uku.. Inne dasu Hindu dake kitchen suna karin kummalo Inne na monitoring nasu kaman ko Yaushe, babu shiri suka nufo parlorn.. Mu’azzam cikin bacci shima yaji ihun har tsakar kansa.. Ya mik’e yaga Feenah tareda shi itama da alama ta firgita da ihun da ake.. Cikin sauri ya mik’e yana janyo jallabiyar sa yana fad’in “Mamy.. Mamy na.. Something happened to Mamy..” Abinda yake fad’i kenan yana k’ok’arin zira rigar dan itace maras lafiya a gidan dole kowa yai tunanin jikinta ne ya tashi koma aka rasata gaba d’aya. Ko tsaya bi takan Feenah dake tambayarsa Ina zaije bai ba ya matsarta gefe kad’an ya nufo yanda yake jiyo ihun cikin sauri.. Tuni Feenah ma ta take masa baya tana mai rufa siririn rigar baccin nata da na saman. Musaddiq ma dake bacci a nasa d’akin babu shiri shima ya fito a birkice.. Aunty Shemau da tayo rakiya wa Uncle Salman zai wuce Factory dan wataran da wuri yake zuwa, nan Suma suka soma jiyo ihu daga sashen Inne. Babu shiri suka nufo sashen suma duk a birkice dan a tinanin Shemau Nuratu ce Allah ya mata cikawa. Harta Meema dake ta faman susa ta kasa bacci dan dama tanada allergy irin na daminan nan balle tazo gidan Gona ga dabbobi ga shuke shuke tuni allergy d’inta ya tashi.. Ta d’an samu baccin kenan itama ta soma jiyo ihun.. Ta fito rai b’ace tana soshe soshe.. Gaba d’aya aka hallara parlor ana duban Ajidde dake ihu tana tsalle idanunta a rintse. Musaddiq kam daga nesa yaja ya tsaya yana jiran yaji ruwan da Ajidde ta b’allo wannan karon. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *20* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ikon Allah, wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan kowa na mamakin haukar yarinyar. Inne Ta k’arasa ta rik’eta tana fad’in “Ke Ajidde.. K’alau kike..? Lafiya kiketa zunduma ihu haka..? Ko wani abu ne ya faru..?” Ajidde ta Ware idanu tana kallon mutanen da sukai cincirindo a parlorn Kowa ya zuba mata idanu. Ta kai dubanta ga Mu’azzam wanda yakai mak’ura wajen had’e rai kafin ta maidoda da dubanta ga Safeenah wacce ke tsaye tana aika mata mugun kallo ko ba’a ce ba kasan shak’e take da ita. Inne ta dubi Mutanen da Ajidde ke duba Wato Safeenah da Mu’azzam, sai kuma ta maidoda dubanta ga Ajidden “Ajidde lafiya kike.. Wani abu ya faru ne..?” Ta tambaya tana mai tsareta da idanu. Cikin sauri Ajidde ta jinjina kai alamun Eh.. Inne tace “Mai ya faru.. Ko wani abin ne ya sami Nuratu..?” Ta girgiza kai a hankali tana duban Safeenah da har lokacin huci take tana aika mata mugun kallo ga Mu’azzam dake gefe shima yana aika mata razanannen kallo hannayensa hard’e ta baya. Matsawa bayan Inne tai cikeda tsoro still idanunta naga Mu’azzam da Safeenah take fad’i a hankali “Inne Allah ne ya toni asirinsu..” Inne ta kuma dubanta da mamaki “Asirin Su Wanene ya tonu..?” Ajidde tai saurin shigewa bayan Inne tana lek’en Mu’azzam da Safeenah wanda kallon mutanen parlorn ya dawo kansu. Mamaki ya mugun cika Mu’azzam ganin yanda yarinyar nan ta tara masa jama’a sunata kallansa babu gaira babu dalili. Aunty Shemau baki sake take duban Ajidde Cikeda takaici tace “Da sukayi mai..?” Ajidde Ta dubi Inne sai ta kuma dubansu, lokaci guda take girgiza kai.. A kufule Safeenah tayo kanta tana fad’in “Ke yarinyar nan na kula kanki rawa yake.. Tin zuwanta gidan nan kike shiga hurumina.. Cikinmu wanene sa’anki da zaki tara mana jama’a.. Zo nan ki fad’a Uban mai mukai..” Inne Ta tare Ajidde tana fad’in koda wasa kar Safeenah ta tab’ata.. Lokaci guda Ajidde dake tsalle bayan Inne take fad’in “ Inne wllhi Allah ne ya toni asirinsu, ni ba lek’ensu nayi ba k’ofa suka mance bud’e shine na gansu suna abinda ‘yaniskan turawa suke a tv.. Wllhi Inne Shi naga sunayi bari ma kiga..” Ta juya Ta manna ma garu kiss tace “Wllhi Inne haka naga sunayi...”Tai maganar cikeda gadara irin ita ga mai gaskiya. Cikin zuciyarta kaw duban Mu’azzam take tana ayyana dama dik wannan famkam famkam d’in nasa na K’arya ne da bogi iskancinsa yake a b’oye. Meema baki sake take dubansu ta kuma dubi Ajidde ga wani irin dariya dake taso mata Wai abinda ‘yaniskan Turawa keyi a tv.. Kai wann yarinya anyi shashasha Ta bugawa a jarida. Babu hali Meema tai dariya ganin yanda Mu’azzam ya gumun had’e rai yana aikawa yarinyar razanannen kallo.. Sad’af sad’af Meema ta shige tana kuma k’unshe bakinta da dariya keta k’ok’arin kufcewa. Uncle Salman ya girgiza kai kafin ya dubi Mu’azzam dake tsaye kaman wanda aka dasa idanunsa sunyi jazir, ya maido da dubarsaga matarsa Shemau yace “Ni na wuce Office.” Musaddiq ya dafe goshinsa cikeda takaici kafin Shima ya juya d’aki dan yanzu kam ya gama yarda haukar Ajidde yafi k’arfinsa. Haka aka dinga barin parlorn cikeda takaici da kunyar abinda Ajidde tai. Hindu ta janyo Ajidde tana fad’in “Zo muje Ajidde lokacin maganin Aunty Nuratu yayi..” Ajidde ta saki baki tana duban yanda babu wanda ya kuma tankata a parlorn, ta dubi Mu’azzam da idanunsa suka kad’a sukai jajir yana aika mata razannan kallo.. Safeenah kaw ta Kasa yarda haukan yarinyar ya kai har wannan matakin. Hindu ta janye Ajidde parlorn ya rage saura Inne Mu’azzam da kuma Safeenah. Mugun kallo kurum Inne ke aika masu “Banaso naji wani ba’asi daga wajenku, ya maku kyau.. Ni bazan zuba maku idanu haka nan ba.. Na riga na gama magana, yau d’in nan zanyi magana da Salman a soma gyara maku b’angaren can gefen. Abin ya isheni haka..” Ta dube Safeenah dake ture turen baki tace “Tashi ki bamu waje kije ki saka sitira jikinki zanzo naji dake idan na gama dashi..” Baki a ture Safeenah ta tashi ta bar parlorn tana kuma gyara zaman rigar baccinta ta nufi yanda takeda tabbacin Zata cimma shegiyar Ajidden nan. Mu’azzam daketa faman murza zoben hannunsa yana sakin huci yana hango fuskar Ajidde sanda take nunasu tana fad’in asirinsu ya tonu, saurin d’agowa yai yana duban Inne data tasa sa gaba “Inne Yarinyar nan is a complete lunatic.. Mahaukaciya ce Inne. Bai kamata a barta ta kusanci Mamy ba in the first place, wayasan mai zata aikata mata idan haukarta ya tashi.. Gaskiya Inne lokaci yayi da za’a kori yarinyar nan daga gidan.” Katsesa Inne tai da fad’in “Kai tafi can ka rufe mun baki dama tin can kana son kasancewa da matarka kak’i a Kai maka ita.. Kaketa wani hanya hanya.. Ai gaskiyar Ajidden ne da tace Allah ya toni asirinka..” Mu’azzam ya shafa kansa kad’an yana kuma sakin huci “Inne, nifa bance Safeenah bazata tare ba, kawai banso a raba mun hankali ne a halin yanzu.. And Inne gaskiya yarinyar nan zata daina zuwa gidan nan daga yau ni ban ma yarda da maganin nata ba.. Idan har tana bada magani ma kanta ya kamata Ta fara yi.. Because she’s sick in the head.!” Inne Ta kuma katsesa da fad’in “Kanka farau.? Nace Kanka farau..? Wane D’ansanda ne Aure ya hanasa bincike.. Kuma bari kaji da kyau na Fad’a maka Ajidde lafiyarta lau ehe, tanada hankalinta yarinta ce kawai ke d’awainiya da ita.. Sannan jikina na bani cewa maganin Nuratu na tattare da ita da izinin Allah..Babu wanda ya isa yasa a sallami Ajidde ko a hanata zuwa.. Ai Kai da matar taka kune manyan mahaukata da zaku shige d’aki ku bar k’ofa bud’e, ku ya kamata ayima magani ba Ajidde ba.” Da mamaki Mu’azzam yake duban Inne yanda ta dage tana kare yarinyar nan da k’arfin gaske, ga gaskiya amma tana kaucewa. Inne Ta mik’e tana ci gaba da sababi ta shige ta barsa nan zaune kaman an dasa sa .. Lallai zai karya yarinyar nan, zai mata horon da bazata sake gangancin shiga huruminsa ba. Idan ma wauta ne ko hauka duk sai ya cire mata Su. Ya mik’e a fusace ya fice daga parlorn. Banda iskanci gaban kowa da kowa harda ma’aikatan gidan zata dubesa tace ta kamasu suna aikata abinda ‘yaniskan turawa suke aikatawa a tv, wai Ta gansu suna suna kiss shida Safeenah harda manna bakinta jikin garu tana nuna yanda sukai Wato.. Lallai ma yarinyar nan Ta samu waje, kuma dik Inne ce ta sakar mata da yawa har wannan raini yake yunk’urin shiga tsakaninsu, yarinyar da yakeda tabbacin ko hak’orinsa k’wara d’aya bata tab’a gani ba..Aiko kafin ya bar gidan Sai ya cire mata haukar nan nata. Ji yake gaba d’aya ransa a jagule, ya kuma tsanar yarinyar fiyeda misali. A can d’akin Aunty Nuratu kaw Safeenah ce keta kokawan kamo Ajidde Hindu na raba tsakaninsu “Yau sai na koya miki manners dan ubanki.. Sai na cire maki wannan k’auyancin naki..” Safeenah ta kuma fad’i tana kuma yowa kan Ajidde da tuni ta daka tsalle ta b’oye bayan gadon Aunty Nuratu. Hannayen Aunty Nuratu ta kama tana fad’in “Dan Allah kar ki bari ta daken kinji dan Allah.. Nice dai Ajidde mai baki magani.” Yanda take maganar kace Aunty Nuratu na sauraronta ne. Hindu kaw Sai k’ok’arin dannar Safeenar take.. Daidai nan Inne ta shigo.. Ba tareda tace komai ba ta janye Safeenah tana fad’in “Shige muje kece ya kamata ki fara koyan manners d’in kafin ki koya mata.” Inne tana janye Safeenah Ajidde ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana furta “Wai Allah na tsira..” Hindu ta dubi Ajidde tace “Ajidde Maiyasa kika aikata hakan.. Kan mai kika kunyata Safeenah da Baban Hajiya a gaban jama’an gidan nan..” Ajidde ta dubeta da mamaki irin ita batayi laifi ba sune masu laifi “Ah Toh ni mai nayi.? wayace su aikata tinda sunsan babu kyau.. Naga dai wannan jiya jiya tazo gidan nan.. Dodanniya.” Hindu ta girgiza kai tana mai jinjina shashancin Ajidde “Toh ke baki San matarsa bace, bakisan sud’in sunyi aure bane..” Baki sake Ajidde ke dubanta tana nanata kalman aure cikin zuciyarta.. Tinani take Meye ma auren.. Sai kuma ta kame baki ta rufe da duka hannayenta biyu tana zaro ido waje. Hindu ta girgiza kai tace “Ai dai nasan a shekarunki Kinsan mai kalmar aure yake nufi.. Ajidde ke macece ya kamata ki rage wannan wautan naki Kinga kefa budurwa ce da wanann sakarcin naki babu wanda zaice yana sonki, nan gaba kad’an Kema auren nan zakiyi ya kamata kike natsuwa kinji koh..” Baki sake Ajidde ke kallonta “Chabb kujita Wai nima aure zanyi.. Wllhi har kin bani kunya.. Tabb ni koda nake ce ma Inna Kyallu zata sami surki k’arya nake, ni wllhi kunya ma nake ji.. Ni dik kinsa inata jin kunyarki.. Ni yau Allah bazan iya duban fuskarki ba.. Na shiga uku.. Kujita Wai aure..” Ta k’arashe tana tura kanta tsakankanin cinyarta Wai kunya takeji.. Hindu ta girgiza kai kurum tana mai gauraya maganin kafin ta isa ta tallafo Aunty Nuratu tana fad’in “Kizo ki bata ko itama kunyarta kikeji yau..” Da k’yar Ajidde ta iya mik’ewa Wai kunyar Hindu take. Ta Kasa d’agowa ta tallafi maganin “Toh ni dan Allah ki daina kallo na wllhi kunya kika bani..” Da k’yar Ajidde ta iya mik’ewa Wai ita kunyar Hindu take, d’agowar da zatai kaw ta hangesa bak’in k’ofa fuskar nan tasa tamau kaman ma yafi na ko yaushe.. Wani irin tsalle Ajidde tai ta haye bayan gado jikinta sai rawa yake. “Na shiga uku na mutu na lalace, shikenan harbeni zai.!” Tana maganan tana duk’e lungun Gado jikinta sai rawa yake idanunta a rintse. Hindu Ta rik’e baki tana fad’in “Oh yau naga ikon Allah ni Hindu.. Wai meye yanzu kuma kika gani..?” K’ofa Ajidde ke nuna mata tana fad’in “Gashi can a k’ofa Mama Hindu wllhi harbeni zai.. Ki ceceni..” “Shi wane..Ni banga kowa ba..” Sai sannan Ajidde ta bud’e idanunta a hankali sai kuma ta dubi k’ofar taga baya nan.. Toh kodai gizo ya fara mata ne.. Sabon tsoro ya bayyana a fuskarta.. Itakam tak’i jinin mutumin Allah ya gani tsoro yake bata. A b’angaren Mu’azzam kaw tinda yaga ganinsa kawai da tai ya firgitata ya bata tsoro Sai ya shige d’akinsa dan yayi shirin tafiya masallacin Juma’a da shike ranan Juma’a ne babban Rana. Cikin zuciyarsa yake furta ‘Ashe k’aryar rashin kunya da k’auyanci kike.. Tinda kika shiga gonar muazzma kin b’ata yarinya.’ Yana cikin shirin ne wayarsa ta soma ringing Assad ne mai kira.. Cikin sauri ya janyo wayar ya d’aga dan yasan update Assad zai basa gameda bincikensu. Saidai baisan sanda cufflinks d’in dake rik’e hannunsa yana k’ok’arin mak’alawa hannun rigarsa ta fad’i ba.. Cikin rarrabewar kalma yake furta “What do you mean she’s getting married Assad..? I mean.. She can’t get married now.. We still need her for our mission..!” Ya mik’e babu shiri yana mai zagaya cikin d’akin sanda Assad yaci gaba da fad’in “And that’s not the case Muazzma.. Mutumin nan idan ya aureta d’auketa zai daga garin nan, idan ma Danger bibiyarta da ahalinta yake kaga shikenan bazamu cimmasa cikin sauk’i ba..” Muazzma ya fuzar da wani fuci yana girgiza kai alamun a’a “No Assad.. We can’t let this happen... Danger is still on the loose.. Hakan na nufin bazamu samesa nan kusa ba..” Ya d’anyi fasali kafin yace “Wai ma tsaya waye mutumin da zai aureta d’in..?” Assad ya sauk’e ajiyan zuciya yace “Bazaka yarda da abinda zan fad’a maka ba.. Amma bari na baka labarin komai in details..” Mu’azzam ya k’urama window idanu yana sauraren Assad dake labarta masa yanda auren Sadiya da Alhaji Isyaku zai kasance a gobe Asabar.. Wani irin gumi ne ke tsartsafowa Mu’azzam, Wai gobe auren yarinyar da Alhaji Isyaku “Wait Assad mutumin nan ba shine ya dinga sanar damu munanan halayyar yarinyar na kwad’ayin abin duniya da bin maza masu abin duniya ba.. Ba shine ya sanar damu irin shaidar da akai ma yarinyar na rashin kamun kai a unguwar ba.. Ba shine ya rabata da d’iyarsa ba..? Idan duka yayi wad’anann abubuwan Maiyasa zai zago yace zai biya mata d’inbin bashin dake kansu idan za’a bashi aurenta.. Ni fah ban yarda da mutumin nan ba Assad, idan baka mance ba bincikenmu ta Kansa ya fara biyowa kafin mu isa ga yarinyar domin kuwa Danger sunansa ya soma mentioning mana.. Assad I won’t let this happen.. I’ll stop this marriage from happening no matter the cost.” Assad ya nusa yace “Bashin zaka biya masu kokuwa d’auke yarinyar zakai..? Muazzma kar fa ka mance You’re still on your suspension, you’re not allowed to go to work ko kuma Kai wani abu ba tareda umarnin NPF ba.. Nasanka Mu’azzam, I know exactly how your mind works.. Don’t get yourself into another trouble.. Mubi hanyar da ya kamata musan yanda zamu b’ullo wa al’amarin..” Katsesa Mu’azzam yai da fad’in “Idan bazan Yi da yarda da amincewan NPF ba then I’ll have to do it my way..” Daga haka katse kiran yai ya k’arasa shiryawa a gurguje yana tina Wai auren gobe gobe ne.. Baisan mai zai aikata ba, baisan mai zai iya faruwa ba. Ya San yayi nisa da garin. Hakan na nufin baisan ko zai iya dakatar da wannan aure ba.. Yana ficewa bai zarce ko Ina ba sai Factory.. Nan ya nemi ganin Uncle d’insa Salman. Sectary d’insa ya ma Mu’azzam iso.. Mu’azzam yana zaune yana k’are ma Factory d’in kallo, yana kallan workers sai shige da fice suke, yakai dubansa ga office d’in Uncle Salman wanda Office d’in Mahaifinsa kenan a baya.. Ya tina sanda yake k’arami mahaifinsa na zuwa dashi Factory d’in wasu lokuta, lokaci guda kuma ya tuna a wannan wajen ya rasa Mahaifinsa.. Ya tina sanda aka kawo masu gawan mahaifinsa a daskare ya k’ank’are bayan yayi jamming kansa a D’akin K’ank’ara da ake aje nama.. Lokaci guda yaji wani irin rauni na ziyartar zuciyarsa.. Sam sai yaji baison kasancewa cikin Factory d’in.. Ya soma k’ok’arin mik’ewa kenan Sectary d’in Uncle Salman ya k’araso yai masa iso yace ya shiga. Mu’azzam ya jinjina masa kai kafin ya nufi office d’in. Can saman kujerar mahaifinsa ya hango Uncle Salman yana zaune yana juyi cikin kujerar.. Wannan murmushin tasa saman fuskarsa. “To what do I owe the honor..?My dear Nephew..” Ya k’arashe yana mai daidaita zaman nasa saman kujerar lokaci guda ya nunawa Mu’azzam d’in kujera mai duban table d’insa. Mu’azzam ya k’araso ya zauna “Uncle, Barka da rana..” Ya fad’i yana mik’a masa hannu alamun musabaha. Babu musu Uncle Salman ya mik’a masa hannu suka gaisa kafin yace “Har ka gama da commotion d’in da ka tayar a gidan..?” Mu’azzam ya fahimci mai Uncle Salman yake nufi amma Sai ya kawar da zancen da fad’in “Uncle ever since my father passed away, ban tab’a tambayar wani alfarma daga wajenka ba.. Wannan karon nazo na tambayeka alfarma If I’m really your nephew..” Gyara zama Uncle Salman yai yana duban Mu’azzam d’in wanda ga dukkan alamu magana ce mai girma yazo masa da Ita. Sannan babu tsoro ko kad’an cikin idanunsa wanda kusan ko yaushe idan ya dubi idanun yaron abinda yake iya hangowa kenan.. Rashin tsoro. Ya kuma gyara zamansa kafin yace “Allah yasa ba Kud’i kazo nema ba dan idan kud’i ne zan iya cewa wanda Sirkinka ke tara maka yayi yawan da har zai iya fin nawa. You know you’re lucky Mu’azzam, dikda ka zab’i career wanda ba wani kud’in arziki zaka tara da wannan career d’in Naka irin D’ansanda, You still have your inheritance a wajen Baban matarka.. Saidai kuma idan kaima baka yarda dashi bane..” Mu’azzam ya d’an murmusa kad’an kafin yace “I trust Daddy with my life.. Ko mai zaiyi da dukiyata na yarda dashi d’ari bisa d’ari kuma na yarda bazai tab’a yin abinda zai cutar dani ba.. Kar ka mance Wannan shine karo na farko da zan tambayi alfarma daga wajenka, Uncle Salman. And inaso ya tsaya between us.. Juts the two of us.. Let’s call it uncle to nephew gift tax..” Ya k’arashe idanunsa akan Uncle Salman d’in, gajeriyar murmushi wacce yake yinta da gefen bakinsa saman fuskarsa. Lokaci guda ya kuma gyara zamansa cikin kujerar kafin yaci gaba da fad’in “If you consider me your Blood, Uncle.. Zaka min wannan alfarmar.. Just this once..!” Wannan karon gumi ne ke gangarowa daga cikin gashin sa zuwa goshinsa sanda yai maganar.. Kana gani zaka fahimci har cikin zuciyarsa yake maganar. A hankali Uncle Salman yake jinjina kai tamkar wanda ya tina wani abu yana duban Mu’azzam d’in wanda shima dubansa yake. “Alright fine.. Yes.. Zan maka wannan alfarmar my dear nephew, and you have my word it will stay between us.. Babu wanda zaiji, not my mother, not my brother, not even my wife..” Mu’azzam ya sakar masa murmushi da gefen bakinsa su duka biyun suna duban juna “Thank you.. Uncle..” Ya fad’i still yana dubansa. A hankali Uncle Salman ya jinjina masa kai shima murmushin ne saman fuskarsa. ** Aunty Shemau ta d’an girgiza kai tana mai saita zaman wayar a kunnenta “Wai dama Aunty Hajara kinaso kice min Safeenah da Meema basu sanar daku zuwan nasu ba.. Toh mai Daddy yace.?” Mommy ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tace “Wllhi nasan bazai wuce shawarin Meema ba dan Safeenah dai bata amfani da k’wak’walwarta sai abinda Meema tace shi takeyi.. Tin jiya Daddy ke fad’a Maiyasa ba’a sanar dashi ba sai bayan Sun tafi. Nadai samu nace munyi ta neman wayar Office d’insa ance yana meeting nasa wayar kuma bata shiga.. Sannan da nace Mu’azzam ne yace saidai Safeenah taje can ta samesa sai baice komai ba, Kinsan wannan d’aniskan yaron yacce kika San ya lashe zuciyar Alhaji ne.. Duk abinda za’a ce indai Mu’azzam ne bai cewa komai.. Sami’ina wa’ad’a’ana ne. yanda kika San ya masa asiri wllhi.. Wani irin so yake ma Mu’azzam wanda tuni ya rufe masa idanu baya ganin laifinsa duk kalan laifin da zai..” Aunty Shemau Ta nusa tace “Yanzu dai Kakar tasu zata masu section a nan, jarabebbiyar tsohuwa.. Kuma sanin kanki ne Aunty Hajara zaman Mu’azzam a nan ka iya kawo mana cikas..” Mommy ta share gumin dake goshinta tace “Dik Safeenah ce da jarabar tsiyarta ta ja mana, amma inada tabbacin zaman Mu’azzam a Fufore bazai yuwu ba domin kuwa bazai tab’a barin aikinsa ya tare can ba.. Kafin ya ankare sai mun Kai uwarsa rami..” Aunty Shemau tace “Bakida wannan matsalar Aunty Hajara.. Aiko maganin Kyallu zai mata aiki mahaukaciyar yarinyar dake tareda Nuratu Itace zatayi ajalinta..” Suka shek’e dariya a tare kafin Aunty Nuratu taima Mommy sallama, Mommyn na cewa Ta saka mata idanu akan yaranta. ** SULEJA A daren ranan ma iya cewa Sadiya kwana zaune sukai daga ita har mahaifiyarta, Umma na saman sallaya tana kai ma Ubangiji kukansu yayinda Sadiyar ta kasa tab’uka komai dan tuni zazzab’I mai zafi ya rufeta tsaban kuka da tsananin tashin hankalin da take ciki.. Muassman idan Ta tina Washe gari Wai Ita d’in Ta zama Matar Alhaji Isyaku Baban Aminiyarta Sabeera.. Haka ta tak’ure cikin bargo tana rawar d’ari dikda tasha pcm amma kaman bata sha komai ba.. Tak’i daina Kukan tak’i taci komai.. Kallo guda zakai mata ta baka tausayi. Lallashin duniya Umma tayi amma abu yaci tura haka dole ta hak’ura ta fawalla wa Ubangiji lamarinsu dan shi kad’ai ne zai iya kawo masu d’auki a halin da suke ciki.. Washe gari sallar asuba ma da k’yar Sadiya ta tashi tai, ko k’wakk’waran tsayuwa bata iya yi sabida yanda take jin jikinta babu k’arfi.. Haka ta jima saman sallaya tana kai ma Ubangijinta kukanta.. Wasu almajirai ne sukai sallama rik’eda manya manyan kwalayan juice da dangin ruwan gora da dai abubuwan tab’awa irin na tarban biki.. Dikda Umma ta hanasu shigowa da kayan hakan bai Sa Almajiran sun fasa dire masu kayayyakin ba.. Sadiya tana jiyo yanda Umma ke fama da almajiran kukanta ya k’aru.. Shikenan da gaske yau ne aurenta da Alhaji Iskyaku. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *21* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Rana ce mai tsayi ta kasance a gidansu Sadiya, wajen Sadiya da mahaifiyarta. Ga duk wanda ya sansu zai fahimci tashin hankalin da suke ciki ya ninka wanda suka shiga a lokacin da Sagir ya tafi ya bar Sadiya a ranan bikinsu. Aure ne da basu san Mecece makomar auren ba. Iyakacin abinda suka sani shine K’addarar su rubutacciya ce tuntuni. Kuma bazasu tab’a tsallake K’addarar da Ubangiji ya gindaya masu ba. ‘Rabbi yassir wala tu’assir’ shine kad’ai abinda bakin Umman Sadiya ke iya nanatawa a wannan rana mai matuk’ar tsawo a garesu. Wai abin mamaki saiga Tabawa gidansu Sadiya harda d’ibo masu kid’an k’warya.. Da baya da baya ta shigo gidan tana tik’an rawa, tin daga lungun ma take tik’an rawa har suka iso gidan.. Baki sake Umma ke dubanta da tsananin mamaki. Tabawa kaw ko ajikinta, sai tik’an rawa take tana sabada harda k’awayenta ‘yan rakiya su Asabe mai kayan Koli. Umma ta zuba tagumi tana duban Tabawa da k’awayenta daketa faman juya mazaunanai suna tik’an rawa. Masu kid’i da rawan da Tabawa ta kawo kaw tuni yaja hankalin mutane akai cincirindo a gidan. Tabawa taci d’amara ta shiga rabon drinks da ruwa ma bak’i harda snacks danginsu cake da donuts Tabawa tazo dasu kwali kwali tana rabo wa mutane. Umma ta k’arasa tana k’ok’arin janyo Tabawa amma Sai k’ok’arin janyota Tabawar ma take fad’i take “Yauwa Uwani dan Allah ki saki jiki ki tik’a rawarki na yau d’aya.. Mance kina takaba ai dai biki ne.. Bikin tilon d’iyarki mace.. Kaman yanda aka fasa wancan auren nata bamu fata wannan ma a fasa shisa muke nuna Farin cikinmu.. Yo dole ma na nuna Farin cikina za’a biya ni hakkina, zan yarda k’wallan mangoro na huta da k’uda “Anyiiirriiirii.. Ungun mai kid’a saka mana Sabada kinji..” Hakan bai hana Umma janye Tabawa ba tana fad’in “Kiji tsoron Allah Tabawa gidan mata mai takaba kike.. Nasan kina Farin ciki za’a biyaki kud’ad’enki amma dik abubuwan da kikazo kinayi mu bama buk’ata..” Dogon tsaki Tabawa taja tana mai kuma turo kallabi gaba “Aifa saidai kiyi Uwani, yau kwana da kwanaki ina bin sahun kud’ad’ena na samu yau za’a biyan ki wani ce kar na nuna Farin ciki.. Wllhi ko kece kika mutu ba mijinki ba sai na nuna Farin ciki da sauk’e nauyin bashin nan da za’a maku.. Kai Kai Kai aci gaba da gashi.. Aci gaba da kid’a aci gaba da juya mazaunai wacce batadashi haushi ya kasheta.. Ahayyee yiririri nanaye sama mataaa..!” Ta k’arashe tana mai juyi da baya. Cikin zuban hawaye Sadiya ta fito zata janye mahaifiyarta aiko nan Tabawa ta fincikota ta jefata tsakiyar fili suna rawa suna zagayeta.. Duk’awa tai wajen tana kuka mai ban tausayi tana rok’onsu su fice masu daga Gida suji da abinda ke damunsu amma kaman cewa take su k’ara. Umma ta isa ta janye d’iyarta suka koma gefe suka rungume juna suna hawaye, Azo har gidansu afi k’arfinsu sabida kawai basu dashi. ** A can gidan Alhaji Isyaku kaw yaci uban wanka yasha gayu cikin sabuwar d’inkin babbar rigarsa, yadai zuba shiga irinta angwaye sai zuba k’amshi yake bakinsa har kunne sabida Farin ciki. A haka ya fito ya tadda Maman Sabeera da Sabeera a parlor sunyi jigum jigum hawaye saman fuskar Sabeera dake kwance cinyar Mamanta. Kallo guda ya masu ya wani d’auke kai irin ko a jikinsa. Maman Sabeera ta mik’e ta nufesa “Alhaji Wai yanzu dan Allah bazaka fasa auren yarinyar nan ba..? Fisabilillahi yarinyar nan fah ‘yar cikinka ne..” Katseta yai da fad’in “Kar ki sake cewa ‘yar cikita ce balle ki haramta min matata.. Ni ban haifeta ba bani ne ubanta ba kin fahimta..” Maman Sabeera ta goge hawayen da suka gangaro mata “Amma ko baka haifeta ba ka haifi Aminiyarta, Kai yanzu ko gudun maganan mutane bakayi kawai ka tashi ka auro mana k’awar d’iyarka aminiyarta.” “Gudun magana.? Toh waye yake sauraron maganganun mutane.. Ai bari kiji Rahina Idan kika ce zaki tsaya sauraren abinda mutanen duniya zasu fad’i akanki ne kina tareda babban aiki.. Ke bari kiji na fad’a miki babu uban da ya isa ya hanani Auren Sadiya.. Ko Ubanta ne ya taso daga kabari bai isa ya hana auren nan ba.. Matsa ki ban waje kar Malam Liman suyita jirana an had’a mutane a masallaci.. Shirirtar banza da wofi.” Ya k’arashe yana bangajeta gefe. Maman Sabeera ta fad’i nan k’asa wajen tana mai sakin kuka tana kiran mijinta ko kulata baiba ya sunkumi bak’ar leda wanda kud’ad’en da zai biya bashin Sadiya da mahaifiyarta ke ciki.. Sabeera tuni ta K’araso ta duk’a ta rungume mahaifiyarta su duka biyun suna masu sakin kuka mai ban tausai. Yana fitowa daga gidan nasa ya shiga aza babbar rigarsa shi kad’ai ya nufi motarsa dan dama a waje hai parking d’inta, Baba Mai gadi yace dashi a dawo lafiya.. Baban Sabeera yana shiga Mota sai gani yai wasu k’artan maza guda uku fuskoki rufe da bak’ak’en masks sun bud’e motar suma sun shigo.. Cikin tsananin firgici da tsoro Baban Sabeera ke fad’in “A’a.. A’ah su waye ku.. Mai nai maku..? Dan Allah kar ku cutar dani.. Wllhi nid’in Sabon ango ne yau ake Bikin aurena.. Dan Allah Kuji tausayi na kar ku cutar dani..!” Yai maganar hularsa tana karkacewa hannayensa rok’onsu dasu sai rawa suke. Wanda yake zaune a backseat ya buga ma Alhaji Isyaku k’asar bindiga a k’eyarsa yana fad’in “Shut up.! Rufe mana baki and keep on driving..!” Jiki na matuk’ar rawa Alhaji Isyaku ke tuk’a motar, a haka har suka fice daga layin. Sun d’auki hanyar barin gari kenan motar dake bayansu tasha gabansu, lokaci guda suka firfito daga cikin motar suna pointing d’insu da bindigogi suke fad’in “This is the police, freeze..!” Tuni suka soma bata kashi da mutanen da suka kira kansu ‘yansanda wanda suma ba kayan ‘yansandan bane jikinsu da kuma mutanen da sukai abducting Alhaji Isyaku. D’aya gardin ya finciki ledar kud’in Alhaji Isyaku suka ci gaba da harbi tsakaninsu da ‘Yansandan kafin suka nufi daji a guje.. D’aya D’ansandan yai k’ok’arin bin bayansu yayinda d’ayan ya k’arasa wajen Alhaji Isyaku dake duk’e hannayensa ta bayan kansa ya kifa Kan nasa Sai b’ari jikinsa yake sabida tsaban tsoro da hargitsin Bindiga da yaji ya kuma gani. D’aya daga ‘yanta’addan ya harbi D’asandan da yabi bayansu a hannu wanda hakan yasa dole ya dakata da bin ‘yanta’addan ya dafe hannunsa dake fitar da jini yana cije baki. A haka ya dawo wajen d’aya D’anuwan nasa da Alhaji Isyaku dake duk’e wajen. Alhaji Isyaku ya d’ago yana dubansu yana fad’in “Na gode na gode maku.. Kun ceceni hannun ‘yanta’addan nan.. Wllhi nid’in sabon ango ne yau ake d’aura aurena. Muyi sauri Mu k’arasa Amaryata da Malam Liman suna jirana, dikda B’arayin nan sun sace kud’ad’en zansan yanda zan nemo wasu kud’ad’en..” Kafin yai shiru d’aya mutumin cikin wanda sukai acting kaman ‘yansanda suka kuma taimakesa ya murmusa yace masa “Not too fast Alhaji..!” Yana ida fad’in haka ya buga ma Alhaji Isyaku k’otar bindiga a k’eyarsa. Tuni Alhaji Isyaku ya fad’i sumamme. Nan take suka jefasa cikin motarsu sukai tafiyarsu. ** Tun su Malam Liman suna jira har dai suka gaji da jira, Tun ana k’irga mintoci hardai aka koma k’irga awanni, babu Alhaji Isyaku babu dalilinsa, su Tabawa kaw ana can gidansu Sadiya ana tik’an rawa. K’arshe Malam Liman ya dubi ‘yan committee na masallaci yana basu hak’uri kan rashin zuwan Alhaji Isyaku da ya tarasu a wajen nan ya kuma sab’a alk’awari.. Malam Liman yaci gaba da fad’in “Mai yuwa ya canza shawari ne bazai iya biya masu wannan tsugugun kud’ad’en matsayin bashi ba.. Yanzu bansan mai zance wa yarinyar nan da mahaifiyarta ba.. Bansan mai zan sanar dasu ba domin kaw mahaifiyarta ta damk’a min ragamar auren yarinyar a hannuna matsayin awalinta.. Bayin Allah Kuji tausayin wad’annan bayin Allah ku biya masu wannan bashi zaku sama lada wajen Ubangijin..” Shiru babu wanda yakeda wad’ann tsugugun kud’ad’e, babu wanda zai iya biyan wad’annan kud’ad’e.. Kud’i ba naira dubu ba wuri na gugan wuri har Naira Miliyan d’aya da rabi.. Nan fah mutane suka soma k’ok’arin watsawa daga masallaci Liman na k’ok’arin dakatar dasu ko Allah zaisa Alhaji Isyaku ya canza shawari yazo ya biya masu bashin nan.. Ana tsaka da watsewa Malam Liman ya mik’e yana fad’in “Bayin Allah ku dakata.. Ku dakata Kuji tausayin na k’asa daku idan akwai mai kud’ad’en nan ya taimaka ya biya bashin nan.. Shin babu wanda zai iya sauk’e nauyin bashin nan..?” Kaman daga sama Malam Liman yaji wata murya “Akwai wanda zai biya bashin..!” A tare Liman da ‘yan tsirarun da suka rage a masallacin suka juyo suna duban mutanen da suka shigo cikin masallacin. Wani matashi ne sanye da bak’ak’en kaya suit fuskarsa rufe da bak’in glasses saidai suna shigowa harabar masallacin saurayin ya zame glasses d’in dake mak’ale idanunsa fuskarsa Ta bayyana, taredashi wani mutumi ne wanda shi ya d’an manyanta sannan manya kaya ne sanye jikinsa shi. Cikeda tsananin mamaki Assad dake zaune wani b’angare a harabar masallacin ya b’adda kama yana monitoring duk abindake faruwa cikin masallacin gameda auren Sadiya da Alhaji Isyaku kaman dai yanda Mu’azzam ya saka sa, ya mik’e in a shock yana duban Mu’azzam da sam baisan yaushe ya iso garin ba. Assad ji kawai yai bakinsa na furta “Unbelievable.!! You.. Are.. Unbelievable.. Mu’azzam Gamji..!” Mu’azzam da Uncle Salman suka ci gaba da takowa cikin masallacin a natse, suna K’arasowa suka mik’a ma Malam Liman hannu sukai masabaha. Malaman Liman ya koma ya zauna yana nuna masu waje cewa su zauna suma. Uncle Salman a Mu’azzam suka zauna daga gefe. Fari’an Malam Liman ya k’aru, lokaci guda yake furta “Allahu Akbar, nasan na kirki bazasu k’are ba.. Dikda cewa taimako dan Allah yayi wuya a duniyar nan tamu na k’warai bazasu k’are ba.. Bayin Allah yanda kukayi niyyan taimakon nan Ubangiji ya biyaku da Aljannah, Allah ya saka maku da mafificin Alheri. Yanda kuka yayewa wad’annan bayin Allah damuwarsu Ta Gidan Duniya Ubangiji ya yaye maku damuwarku ta lahira..” Uncle Salman yaji addu’o’i tuni ya d’aga hannunsa biyu yana amsawa da “Ameen Malam..!” Mu’azzam ne ya d’anyi gyaran murya yana mai matso da bakinsa kusan kunnen Uncle Salman, cikin sigan rad’a yake furta “Uncle let’s finish the deal.” Uncle Salman ya jinjina kai kafin ya tura hannu cikin babbar rigarsa ya ciro kud’ad’e cikin leda ‘yan dubu dubu.. Lokaci guda ya ajiyesu gaban Malam Liman “Wannan Naira miliyan D’aya ne da dubu d’ari biyar bashin da ake bin iyalan marigayi Malam Ibrahim.” Malam Liman ya jinjina kai cikeda jin dad’i, harda sujudu shukur yai yana d’aga hannaye sama yana Godiya wa Ubangiji “Alhamdulillahi Allah yayi yau an cire ma wad’ann bayin Allah k’angin bashi.” Baikai aya ba Uncle Salman ya kuma ciro wasu kud’ad’en cikin aljihunsa, wannan karon rapan ‘yan dubu dubu ne bunch d’aya wato hundred thousand Kenan.. Ya kuma ajewa gaban Malaman Liman. Baki sake da mamaki Malam Liman ke dubansa wannan karon “Alhaji wannan kuma na menene.? Uncle Salman ya gyara zaman babbar rigarsa kafin ya soma fad’in “Sunana Alhaji Salman Gamji.. Wannan d’an D’anuwana ne Mai suna Mu’azzam Gamji.. Bakada dogon binciken da zakai akanmu domin ahalinmu sananne a fad’in garin Abuja da kewaye..” Ya d’aura hannunsa guda saman kud’ad’en da ake bin Su Sadiya bashi yace “Wannan bashin da ake bin Sadiya da mahaifiyarta ce.” Ya kuma d’aura d’aya hannunsa kan Naira dubu d’arin yace “Wannan muma Naira dubu D’ari ce Sadakin D’ah na Mu’azzam ga d’iyar da aka mik’a maka jagorancin ragamar aurenta Wato Sadiya..” Kafin Malam Liman ya kuma wani magana Uncle Salman ya zaro Doguwar takarda ya mik’awa Malam Liman “Wannan takarda ce kuma shaida ce dake tabbatar da cewa d’ah na Mu’azzam lafiyayye ne baida wata cuta da zata hanasa aure, sannan genotype d’insa AA ne wanda a k’a’ida zai iya auren mace mai ko wane irin genotype koda kuwa SS ce domin na sani a akasarin masalattanmu ana ci gaba da wayar da kai cewa idan za’ayi aure a auna jini asan wani irin jini mutum ke d’auke dashi domin guje ma tsautsayi na samun yara da za’a Zo aita faman jinya suna shan wahala iyayen na shan wahala wanda ansan akwai k’addara amma idan akwai hanyar da za’a iya bi a kiyaye faruwar hakan yin hakan shi yafi alfanu dan ko a musulunci akwai rigakafi kuma an amince da hakan..” Tinda Uncle Salman ya soma magana Malam Liman ke dubansa, ya d’an girgiza kai yace “Alhaji idan na fahimceka kaima ka biya bashin ne domin ka amsar wa d’anka auren Ita Sadiya..?” Uncle Salman ya jinjina kai yace “K’warai kaw Malam Liman, ai idan ban b’ata ba dama aurarta zakayi ma Alhaji Isyaku ko ba haka ba..” Malam Liman ya jinjina kai a hankali kafin yace “Haka ne Amma Ai da yardar ita yarinyar da mahaifiyarta mukai za’a bada aurenta ga Alhaji Isyaku amma bamuyi dasu za’a aurarta ma d’anka ba.. Alhaji Aure ai ba abun wasa bane..” Uncle Salman ya murmusa yace “K’warai kuwa aure ba abin wasa bane shiyasa na gabatar maka da komai tin kafin ka tambaya.. Sannan na tabbata Ita yarinyar dama auren sadaukarwa zatai dan a biya masu bashi da don soyayya ba.. Bana ko haufi yarinyar bata son Alhaji Isyaku.. Amma fah idan bazaka bamu auren ba muma zamu tattara i namu i namu.. Allah bamu Alheri..” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin janyo kud’ad’en.. Liman ya tsunduma tunanin alk’awarin taimaka masu Sadiya da yayi, yana tsoron kar wannan itace damarsu ta k’arshe kuma ta kufce masu.. Idan yarinyar da mahaifiyarta suka tafi gidan yari baijin zai tab’a yafe ma kansa bayan alk’awarin taimaka masu da yayi.. Sannan mahaifin yarinyar marigayi yana d’aya daga cikin members na committee na masallacin, bazaiso Hakan Ta faru ga ahalin marigayi ba.. Toh amma idan ya aurarta ga wannan matashi ba tareda saninsu ba shin yayi daidai..? Gaba d’aya kan Malam Liman ya cunkushe ganin dama na k’arshe na k’ok’arin kufce masa.. Take yaji b’angare mafi girma na zuciyarsa tana fad’in Kar ka bari mutanen nan su fice daga masallacin nan bakada Sauran zab’I, zaka jima kana jin ciwo idan Tabawa ta kai iyalan marigayi gidan kasu.. Lokaci guda Malam Liman ya dakatar dasu.. Mu’azzam ya saki murmushi da gefen bakinsa. Take Malam Liman yace ya amince idan zasu sauk’e masu Sadiya nauyin bashin nan.. Uncle Salman ya juya ya dubi sauran tsirarun mutanen dake haraban masallacin dan dama ba cikin masallaci suke ba zaune suke haraba yace “Bayin Allah ku zama shaidu..!” Nan take cika cikan aure suka had’u, aka samu waliyi, Wakili, Siga da kuma Sadaki da shaidu nan aka d’aura auren Mu’azzam Marwan Gamji da amaryarsa Sadiya Ibrahim kan sadaki Naira dubu d’ari lakadan ba ajalan ba. Assad Daskarewa kurum yai dan ya kasa yarda da abinda Mu’azzam ya aikata kawai dan ya cimma burin bincikensa. “You.. Are a Savage Mu’azzam Gamji.!” Assad yace yana mai girgiza kai cikin rashin yarda da abinda Mu’azzam d’in ya aikata. Ana haka Wasu matasa ne suka shigo masallaci a hargitse.. Gaba d’aya su Malam Liman suka mik’e harmadasu Mu’azzam suna duban matasan daketa faman haki.. Malam Liman ya soma tambayarsu “Kai lafiya.. Lafiya kuka shigo masallaci haka nan.. Subhanallahi..!” D’aya daga cikin samarin ya duk’a yana haki “Malam Alhaji Isyaku Chanji ne..!” Malam Liman ya juyo ya dubi su Mu’azzam kafin ya dubi saurayin yace “Subhanallahi.. Mai ya sami Alhaji, taron nan fah isowarsa muke jira Allah baiyi za’ayi auren dashi ba.. Dan dik munyi zaton janyewa yayi..” “Malam wllhi wasu mutane ne mukaga Sun sakasa a mota sunyi wancan hanyar dashi.” D’ayan ya fad’i yana haki. Malam Liman dasu Mu’azzam suka dubi juna cikin kad’uwa, Sai kuma Liman ya dubi Matashin yace “Wasu mutane ne kenan suka d’aukesa.” “Malam ina tunanin ‘yan Garkuwa ne domin duk sun rufe fuskokinsu da bak’ak’en yadi babu wanda yake iya ganin fuskokinsu..” “Subhanallahi..! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!” Abinda Su Liman ke iya fad’i kenan.. Wannan karon Assad ne ya k’araso yana tambayar saurayin ta Ina Su Alhaji Isyaku sukai.. Malam Liman yace “Ai kuwa kafin a watse daga taron nan ya zama dole a sanar da ‘yansanda.” Mu’azzam ya dubi Malam Liman yace “Kar ka damu Malam ni d’ansanda ne zamu kula da wannan..!” Lokaci guda ya ciro wayarsa yana neman backup dan dama yasan masu bibiyan Su Sadiya ba lallai Su k’yale Alhaji Isyaku ba muddin sukaji zai aureta tinda yarinyar da ahalinta suke targeting.. Lokaci guda ya fice a harabar masallacin waya manne kunnensa. A can gidan Alhaji Isyaku kaw labari ya isa masu cewa anga wasu mutane fuskokinsu rufe da bak’ak’en masks sun sace Alhaji Isyaku hankalin Maman Sabeera da Sabeera ya kuma tashi.. Babu shiri Sabeera ta fice ta taho gidansu Sadiya. Masu kid’an Tabawa suna tsaka da kid’a su Tabawa na rawa Sabeera ta shigo a birkice, tayo kan Sadiya Ta cakumota tana jijjigata take fad’in “Ina mahaifina Sadiya..? Ki fad’a mun su wanene suka sace Babana.. Ki fad’a mun Sadiya..!” Toh fah Wannan shine ana wata ga wata Wai an sace Alhaji Isyaku Ango. Cak sautin kid’an k’waryar ya daina tashi, su Tabawa kaman wad’anda aka zare masu battery tuni suma suka dakata da rawar da suke.. Kowa ya juyo yana duban Sabeera dake jijjiga Sadiya tana fad’in ina Takai mata mahaifi. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *22* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Su Tabawa da ayarinta tuni suka fice Tabawa tana fad’in “Ku tashi muje zama bata ganmu ba an sace ango.. Wayyo Allah kud’ad’ena. Na shiga uku ni Tabawa waye zai biya bashin nan yanzu.. Wayyo Allah na shiga ukku. Gaskiya Sadiya farar k’afa gareki.. Ace aure biyu ana fasawa kaman bakin uwa.. Koda yake dama ‘yar bakin uwar ce ke.. Matsiyata masu bak’in k’addara..!” Haka Tabawa ta dinga ihu a lungun hannu aka tana tsine masu Sadiya, Ita damuwarta ba b’acewar Alhaji Isyaku bane bashin su Sadiya ne da zai biya shine damuwarta.. A nan cikin gidansu Sadiya kaw kuka kawai Sadiyar take tana duban Sabeera dake ci gaba da jijjigata wacce itama kukan take, cikin kuka Sadiya ke furta “Sabeera ban sani ba.. Wllhi ban San komai ba, ki yarda dani ina zan d’auki Mahaifinki na kaisa..” Cikin kuka Sabeeran ma ke girgiza kai tana ci gaba da jijjiga Sadiyar take fad’in “No you are a liar Sadiya.. You lied to me once.. What makes you think zan yarda dake wannan karon.. You are nothing but a gold digger, I was so stupid that I couldn’t see your true color tuntuni.. I no you never loved my father.. Sabida kud’insa ne kika amince da aurensa.. Kawai kud’insa kike so shiyasa kika sa aka sace shi Dan kar ki aure shi dan ki karb’i kud’ad’e masu yawa daga wajensa.. I feel like I don’t know you Sadiya. Tinda kikayi tarayya da D’antadda irin Sagir, zakiyi da ‘yan Garkuwa ma. You planned all this Sadiya.. Just admit.. Why can’t you admit it already..!” Ta k’arashe tana mai tura Sadiyar da k’arfin gaske.. Sadiya bata fad’a ko Ina ba Sai jikin Mu’azzam da shigowarsa kenan gidan.. Hannayesa duka biyu yasa ya tallafota. Sadiya ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban mutumin data fad’o jikinsa wanda ba kowa bane face wannan D’ansandan wanda sukai karo kwanaki kuma shine mutumin dake bincike kan mutuwar Sagir. Su duka biyun suka k’ura ma juna idanu.. Lokaci guda taji ya rik’o hannunta yana fad’in “Let’s go, you are no longer safe here.. Let’s go now..!” Ya k’arashe yana k’ok’arin janyo hannunta da k’arfin gaske. Sadiya da tsananin tsoro ya gama cikata Ta soma k’ok’arin k’wace hannunta tana fad’in “Wait.. Ina zamuje..? Ina zaka kaini.. Just let me go.. Ka sakar min hannu.. Ka sakeni Ina zaka kaini..!” Ta finciki hannunta da k’arfin gaske tana huci take dubansa, lokaci guda take furta “Just because you are a Corp doesn’t mean you can arrest me without any allegation. Mr Inspector..!” Mu’azzam dake tsananin huci yana dubanta, lokaci guda ya kuma takowa gabanta, wani irin duba yake mata wanda za’a iya kiransa da duban tsana “You wanna know who am I to you..?” Ya kuma matsowa kusanta sosai kafin yace “Well, I’ve every right over you.. Idan nace maku ni ne mutumin da ya biya bashin da kuka ciwo ma kanku fah..!” K’irjinta ne yai wani irin bugawa tana dubansa da idanunta wanda har yanzu hawaye ne kwance cikinsu. Lokaci guda kuma taji wani irin k’arfin zuciya na zuwa mata bayan tulin iftil’ai na rayuwa data gani.. Hawaye ne a cikin idanunta amma murmushin takaici ta sakar masa tana duban cikin idanunsa ba tareda wani tsoro ko d’ar ba tace “A cheap low life police officer like you.. Wanda bai dogara ga komai ba face cuku cuku da karb’an cin hanci da rashawa bashida wad’annan kud’ad’en da kake mafarkin ka biyasu a matsayin bashi na ni Sadiya.. Ka fahimta..?!!” Ta k’arashe tana sakin huci. Da mugun mamaki Mu’azzam ke dubanta idanunsa na kuma kad’uwa,wani wulak’antaccen kallo yake mata daga sama zuwa k’asa yana tuna duk maganganun da ake fad’i na rashin kamun kai gameda da Ita ya kuma tuna maganan da yanzu Ta fad’i masa cewa cheap low life police Officer mai karb’an cin hanci da rashawa irinsa bai isa ya biya bashin da ake binta ba. A hankali yake kad’a kai idanunsa na kuma yin jazir “You’ll repeat this..! Zaki maimaita wannan idan sunana Mu’azzam Abubakar Gamji.. Zaki maimaita..!” Daidai lokacin Umma ta K’araso tana k’ok’arin janye Sadiya, Ta d’ago ido tana aika wa Muazzma mugun kallo “Kaga Bawan Allah ka fice daga gidan nan dan kana a matsayin D’ansanda babu dokar data baka damar shigowa har cikin gidanmu kace zaka ci mana mutunci Dan muna talakawa. Fita nace..!” Umma ta k’arasa tana nuna masa hanya. Idanunsa da suka kad’a sukai jazir yanaga Sadiya yana aika mata wani irin kallo kafin ya maidoda dubansa ga Umma, sai kuma ya sadda kansa k’asa kaman wanda ya tina wani abu duban cikin idanun Umma da yai.. Lokaci guda ya juya yasa kai ya fice daga gidan.. A daidai k’ofa ya had’u dasu Malam Liman suna sallama alamun zasu shige gidan.. Bai iya furta masu komai ba sai sa kai da yai ya wuce cikin sauri.. Malam Liman ya bisa da kallo yana jin zuciyarsa na masa wani irin rauni.. Anya baiyi gangancin bada auren Sadiya ma wannan D’ansandan ba.. Take yaji yana tuhumar kansa da aikata babban laifi.. Ji yai kaman bazai iya duban Sadiya da mahaifiyarta ya fad’a masu abinda ya aikata ba.. Mu’azzam kaw yana ficewa daga gidan ya nufi yanda Assad ke tsaye, Uncle Salman kam tuni ya cika ma rigarsa iska. Mu’azzam na k’arasowa wajen yaga Assad ya k’ara waya a kunne yana fad’in “Yes Yusuf, we have a situation here.. I’ll send you our location..!” Ji yai an fuzge wayar kafin yakai aya. Ya karkato yana duban Mu’azzam, da mamaki Assad ke duban Mu’azzam “Backup nake kira Mu’azzam ya kamata musan su waye suka d’auki mutumin nan..” Ba tareda Mu’azzam ya basa amsa ba ya shiga janyo hannunsa yana fad’in “You ain’t calling anyone.. Just come with me..!” Assad ya dubesa da mamaki har suka isa mota Mu’azzam d’in ya bud’e ya shige yayinda Assad d’inma ya bud’e d’aya b’angaren ya shige.. Shi yanzu harga Allah tsoro Mu’azzam ke basa bayan wannan birkitaccen auren da yai yanzu yanzu.. Assad zuba masa idanu kurum yai yanda yake kwasansu saman kwalta tamkar zasu bar gari. ** Tabarma Umma ta shimfid’a wasu Malam Liman, ko daga yanayin da tagansa ciki ta fahimci akwai matsala mai girma, saidai ta jingina hakan da Sace Alhaji Isyaku da akace anyi. Ta zauna daga d’aya b’angaren suka gaisa, bak’ar ledar viva aje gaban Malam Liman. Saida ya d’anyi gyaran murya kafin ya soma fad’in “Watau Uwani ita rayuwar nan da kike gani komai rubutacce ne tun kafin a samemu, Idan Ubangiji ya k’addari faruwar abu Toh fah bawa bai isa yaja da hakan ba.. Sannan inaso ki sani mutum baya tsallake matarsa, muddin matarsa ce toh ko a ina take kuma ko menene sanadi sai yaje ya cinma matarsa a duk yanda take..” Jikin Umma yakai matuk’a wajen yin sanyi. Ta jinjina masa kai a hankali tana mai furta “Haka ne Malam.” Malam Liman yaci gaba da fad’in “Alhamdulillah naji dad’i da kika fahimci haka Uwani.. Sannan akwai magana mai girma da nake tafe inaso na sanar daku daga ke har Sadiya. Nasan Kunji cewa an d’auke Alhaji Isyaku yau a k’ofar gidansa bayan ya fito zai halarci wajen d’aurin aurensa da Sadiya.” Umma ta jinjina kai a hankali tana jin k’irjinta na tsananta fad’uwa. Malam Liman ya d’an kifa kansa kad’an yana ganin girman maganan da zai fad’a masu, ya d’an muskuta kad’an yana gyara zaman rawaninsa “Toh Uwani aure dai bai yuwu da Alhaji Isyaku ba..” Umma ta dubesa da mamaki sai ta d’an murmusa tace “Allah sarki Malam ai Babu komai haka Allah ya nufa, dama kullum cikin kai masa kokenmu muke muna rok’onsa yama zab’in abinda yafi alkhairi ya kuma dubi lamarinmu.. Na tabbata idan bai k’addari wannan aure ba k’udirarsa da Buwayarsa su suka dakatar da aukuwan wannan aure, inada tabbacin hakan shine abinda ya zab’arwa d’iyata.. Mun kuma gode da jarabawar da yake aiko mana daki daki.. Fatana Allah ya nufa muci wad’annan jarabawa.. Malam kar ka damu nasan kayi iyaka k’ok’arinka wajen ganin an sauk’e mana wannan nauyi na bashi dake bisa kanmu, Ubangiji ya saka maka da alkhairi duniya da lahira.. Idan Allah ya nufa zai turo mana wani hanyar da zamu samu mu biya wannan bashi dake kanmu..” Malam Liman ya d’an share k’wallan da ya zubo masa, lokaci guda yake furta “Sadiya d’iya ce a wajena Uwani, ki daina min godiya ni babu abinda nayi mata.. Sannan idan babu damuwa inaso ta fito itama domin abinda zan fad’a maku yanzu ya shafi rayuwarta kacaukam. Sannan zai iya canza rayuwarta gaba d’aya..” Wannan karon bugun zuciyar Umma ya k’aru. Ta dubi Habeeb dake zaune daga can gefe yana ‘yan wasansa abinka da yaro tace “Habeeb shiga ka kira Addarku..” Habeeb ya jinjina kai kafin ya mik’e ya shige ciki kiran Sadiya. Jiki a matuk’ar sanyaye Sadiya Ta fito, ga zuciyarta data tsananta yankewa tinda Habeeb yace su Malam Liman da Umma ke kiranta. Sadiya ta fito sanye da hijabinta ta duk’a daga can gefe kusan Umma ta gaida Malam Liman. Malam Liman ya amsa zuciyarsa cikeda tausayin yarinyar, bazai gushe ba yana mata add’uan samun Farin ciki mai d’orewa cikin gidan aurenta. Yana fata wannan aure nata da ya had’a da Mu’azzam ya zamto alkhairi gareta da mahaifiyarta harma da ‘yanuwanta. Malam Liman ya dubeta yana jin rauni sosai had’ida tuhumar kansa “Halimatu.!” Ya ambato asalin sunanta wanda babu mai kiranta da wannan sunan sai mahaifinta. “Na’am.. Baba..!” Taji bajinta na furta haka ba tareda tasan dalili ba, saidai tafi danganta hakan da cewa ya kira sunanta ne da sigan da mahaifinta ke kiranta shiyasa ta kirasa da Baba itama. Malam Liman yaji dad’in ambatonsa da Baba da tai, a hankali ya soma furta “Inaso ki sani, da ace inada halin da zan sauk’e wannan bashi da basai kin kaiga sadaukar da Farin cikin ki ba kin auri wanda baki so.. Halimatu kin d’aukeni a matsayin mahaifi..?” Sadiya ta dubesa sai kuma ta dubi mahaifiyarta, a hankali ta jinjina masa kai.. Malam Liman ya share hawayen da suka gangaro masa “Bansan ya zaku d’auki al’amarin ba.. Amma inaso ku Sani ina mai neman yafiyarku.. Musamman ke Sadiya.. Ki yafe mun kan had’a aurenki da nayi ba tareda saninki ba bayan kin d’auki matsayi mai girma kin bani.. Ki yafe ni d’iyata banyi haka dan wulak’anci ko cin zarafi ba saidai nayi haka ne gudun kar dama na k’arshe ya kufce mana.. Sannan inaso ku Sani ni d’an adam ne ajizi wanda yake kuskure.. Kar ku dubeni a matsayin malami ko limami.. Ku dubeni a matsayin D’anadam kuma Bawan Allah mai kuskure..” Izuwa lokacin hawayen Sadiya ya k’aru.. Girgiza Kai take tana fad’in “Baba Liman dik abinda ka yanke akaina zanyi na’am dashi kuma zaka sameni Ina mai maka biyayya kaman yanda zanyiwa mahaifina.. Zanji dad’i matuk’a ace na samu damar yi maka biyayya irin wacce banyiwa mahaifina ba a lokacin da yake raye.. Hak’ik’a zanji dad’in hakan.. Duk hukuncin da ka yanke kayi daidai nasan bazakayi abinda zai cutar dani ba..” Malam Liman da abokin tafiyarsa suka share hawayen da ya gangaro masu, da k’yar Malam Liman ya saita kansa kafin yace “Halimatu a yau sanda mukayi zaton Alhaji Isyaku ya janye aurenki ne gudun kar ya biya bashi na bada aurenki ga wani..” Umma da Sadiya suka dubi juna cikin tsananin sanyin jiki.. Malam Liman ya mik’a wa Umma dubu d’ari sadakin Sadiya dasu Mu’azzam suka biya “Wannan shine kud’in auren Sadiya..” Sadiya Ta kuma duban Umma cikeda kad’uwa. Cikin rawar murya Umma tace “Malam ko zamu iya sanin wanene mijin nata.?” Malam Liman ya d’an gyara zamana kafin yace “Mu’azzam Abubakar Gamji. Shine sunan mijinki Halimatu.” “Mu’azzam Abubakar Gamji.!” Sadiya ta nanata a hankali zuciyarta naci gaba da tsinkewa.. Take ta tina tattaunawarsu da Mu’azzam da ko minti talatin baiba kalamansa na k’arshe take tunawa _Idan Sunana Mu’azzam Abubakar Gamji ne zaki maimaita abinda kika fad’i_ A hankali Ta furta “The Corp!” Sai kuma ta mik’e tana jin wani irin kuka na zuwa mata.. Babu shiri ta shige d’aki a guje tana mai k’unshe bakinta da kuka gadan gadan ke shirin fitowa. Umma ta dubi su Malam Liman tace “Malam kuyi hak’uri zan shiga na kula da Sadiya.” Malam yace “Babu komai.. Ga kud’in Tabawa nan sun biya idan yaso sai a had’u tareda ku da shaidu a biya Tabawa kud’inta.. Babu sauran maganan bashi..” Jinjina masa kai kurum Umma tai kafin sukai sallama ta shige wajen d’iyarta da sumewa ne kawai batayi ba sabida firgici. Malam Liman suna ficewa ya dubi abokin tafiyarsa suka tafe hannu. Abokin Tafiyarsa yace “Kai Malam Wato dai harta ku malamai kuna d’an tab’a wuru wuru..” Malam Liman yace “Kai Munkaila rayuwar nan tayi wuya fah, ai muma Malamai sai mun d’an had’a da cida addini bacin haka bazamu kai labari ba. Kai badon zan sami nawa kason ciki ba maizaisa na dage nayita wa’azi ina rok’on a biya masu bashin da suka ciwo, bashinma da ashararancinsu na buki kawai sukai dashi.. Ai tsuntsun da ya jawo ruwa shi ruwa yake bugu Munkaila, ni ko tausayi basu bani ba kuma nima kasuwancina nai dasu..Yanzu kaga kud’ad’en nan Tabawa tamin alk’awari akwai Kaso na ciki shiyasa dole na aurar da yarinyar nan ma koma wanene.. Yo zanyima d’iyata irin wannan auren ne..? Mutane suzo bagatatan babu bincike babu komai a d’auki d’an mutum sukutum a basu.. Kai ina ka tab’a jin anyi irin wannan aure idan ba don zan sami kaso na ciki ba.” Suka kuma k’yak’yata dariya a tare Munkaila na fad’in “Nima kuma zan sami nawa ba..” Malam Liman yace “Bani son zari Munkaila ka jira na dafe nawa tukuna..” Munkaila yana murmushi yake jinjina kai kafin suka wuce. ** Wani uncompleted building sukazo, Assad sai dubansa yake cikeda tsananin mamaki dan shi har wannan lokacin ya gaza yarda da abinda abokin nasa ya aikata. “What are we doing here..?” Assad ya fad’i yana duban Mu’azzam d’in. Mu’azzam bai kaiga basa amsa ba saiga su Yusuf team mate d’insu da kuma wani abokin aikinsu a CID mai suna Jabir sun fito daga building d’in. A tare Yusuf da Jabir suka k’araso suna sara ma Mu’azzam da Assad.. Baki sake Assad ke dubansu, ya kuma dubi Mu’azzam kafin ya sake duban Yusuf yace “Wai ba yanzu na kiraka nake sanar dakai abinda ke faruwa ba..” Murmusawa kurum Yusuf yai yana mai mik’a masu hannu alamun musabaha. Jabir ma ya k’araso suna gaisawa. Mu’azzam ya dubi Yusuf da hannunsa ke d’aure alamun an kuskuresa da bindiga yace “Wait.. What really happened.. Why are you wounded..?” Yai tambayar cikeda kulawa yana duban Jabir d’in. Jabir ya d’an murmusa yana duba hannun nasa dake d’aure da bandage yace “This.? It’s nothing Sir, just a scratch.” Mu’azzam ya girgiza kai yana duban Yusuf da Jabir d’in.. Lokaci guda ya kuma duban Yusuf yace “What really happened Yusuf..?” Yusuf ya soma basa labarin abinda ya faru “Bayan ka turamu Mu d’auke Alhaji Isyaku, koda muka isa k’ofar gidansa munga wasu mutane Sun shiga motarsa.. Muka bi bayansu Toh Sai suka tsere mana, a nan ne abductors d’in suka kuskuri Jabir da Bindiga..” Da tsananin mamaki Mu’azzam ke dubansu kafin yace “Kuna nufin wasu sun rigamu, wasu suna targeting Alhaji Iskyaku.?” Yusuf ya jinjina kai yace “K’warai kuwa wasu sun rigamu.. And I’m suspecting zasu iya zama yaran Danger..” Mu’azzam yace “Kun kub’utar da Alhaji Isyakun..?” Suka jinjina masa kai a tare Jabir na fad’in “Yana cikin building d’in nan, saidai bamu fara interrogating nasa ba muna jiran isowarka.” Mu’azzam ya jinjina masu kai kafin yace “Muje ciki..” Saurin rik’osa Assad yai, ya dubi su Yusuf yace “Officers ku k’arasa ciki muna zuwa..” Suka jinjina kai kafin suka shige ciki. Aka bar Assad da Mu’azzam tsaye a wajen.. Huci kurum Assad yake yana duban Mu’azzam wanda shima fuskar tasa tamau take. Assad ya fuzar da fuci kafin ya d’ago yana duban Mu’azzam cikin tsananin b’acin rai “What the hell have you done Mu’azzam.. What has gotten into you.. Bayan auren yarinyar can da kai ashe kai ka d’auke Alhaji Isyaku.. Maiyasa na kasa gano hakan ma..? Mu’azzam anya lafiya kake.. Maiyasa zaka auri yarinyar nan idan ba sonta kake ba.. Kafi kowa sanin cewa marriage is a serious commitment.” Katsesa Mu’azzam yai cikin tsananin b’acin rai “You know perfectly well that I didn’t marry that girl because I wanted to be with her.. Abu d’aya ne yasa na aureta because she’s the key to finding my real sister’s murderer.!” Cikin b’acin rai Assad ya katsesa da fad’in “Kan wannan dalilin ne zakai making huge decision na aurenta..” “Yes Assad..!!! If that’s what it takes me to do.. Then I’d marry her just to find my real sister’s murderer.. Ka fahimta..!” Ya k’arashe idanunsa na firfitowa waje tsananin b’acin rai. Assad ya fuzar da huci yace “Don’t you think you’re ruining the girl’s life aurenta da kai ba tareda kana sonta ba Sai dan ka cimma burinka na binciken da kake..” “Her damn life has already been ruined tin lokacin da ta zab’i kasancewa da wannan d’aniskan criminal d’in..! And just to remind you, dama ‘yar tasha ce rayuwarta lalatacce ne tuntuni..!” Assad ya shafi kansa yana mai fuzar da huci kafin yace “Toh shi kuma Alhaji Isyaku daka d’aukosa ka ajiye sa nan fah..? Ta yaya zaka aikata abu makamancin wannan Mu’azzam, karfa ka mance you’re still on your suspension, sanin kanka ne mutumin nan can file a case against you d’aukosa da kai ka ajiyesa a nan, sannan baka tinanin Yusuf da Jabir zaka iya jefasu cikin matsala.. And.. waima da ka aje mutumin nan mai zai maka.. kanaji sunce anyi abducting d’insa sukai bata kashi da ‘yanta’addan suka k’wacesa.. Idan na fahimta Alhaji Isyaku baida masaniya akan abinda ke faruwa he’s only caught in the middle of all this a matsayinsa na wanda zai auri yarinyar.. Ya kamata ka saki mutumin nan ya tafi Mu’azzam kafin ka janyo ma kanka wani matsalar bayan wanda kake ciki.” Mu’azzam dake dubansa da rinannun idanunsa yace “I thought I told you, idan banzanyi k’ark’ashin umarnin NPF ba I’d do it my way.. And this is my way of doing things Assad.. Kafi kowa sanin hakan.!” Assad ya d’an shafi kansa kafin ya d’ago cikin tsananin b’abin rai yace “Baka tinanin mutumin nan Danger ke targeting d’insa.. He’s innocent Mu’azzam you can’t keep him here.. You’ll be charged with kidnapping..” Assad Bai Kai aya ba Mu’azzam dake tsananin huci ya katse sa da fad’in “Assad, If I keep doubting everybody then my real sister’s killer will never be found.!” “Then what..! So is it okay to abduct an innocent person if it means finding the killer..?” Assad yace cikin tsananin b’acin rai. Ya d’an sassauta murya yana duban Mu’azzam d’in “I know how frustrated you can be to wait for justice to come through.. We can’t take laws to our hands Mu’azzam.. You’re a police officer, you should know better..!” Da tsananin mamaki wannan karon Mu’azzam ke dubansa, ya bigi bonnet d’in Mota kafin yace “What the hell has happened to you.? Because you used to be so determined on solving this case.. Tell me Assad.. Are you backing off now..?!” Ya k’arashe cikin tsananin zafin zuciya gumi na karyowa daga sumarsa zuwa goshinsa. Girgiza kai kurum Assad yai dan ya gama yarda Mu’azzam yayi nisa.. Zai dik abinda zai domin ya gano waye ya kashe masa ‘yaruwa. A hankali Assad ke furta “Just don’t do anything that you’ll later regret Mu’azzam.. Please..! Let’s do everything the right way.. Hanyar da doka ta aminta dashi..” Da gefen idanu Mu’azzam ke dubansa kafin yace “I’ll interrogate that man.. Zaka shigo ne ko zaka tafi..?” Assad ya girgiza kai kad’an yana mai fuzar da huci kafin yabi bayan Mu’azzam d’in, suka shige cikin ginin yanda Alhaji Iskyaku ke zaune saman kujera Jabir da Yusuf na tsartsaye b’angarorinsa guda biyu.. Mu’azzam na shigowa ya janyo kujera da k’afarsa ya saita Ta gaban Alhaji Isyaku kafin ya zauna suna duban juna. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *23* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* K’ura masa idanu Mu’azzam yai yana duban yanda Alhaji Isyaku ke rarraba idanu kaman an jefa mage a tukunya. “Alhaji, nasan ka gane ni, domin kuwa munje gidanka a satin da ya gabata Nida abokin aikina domin gudanar da bincike..”Ya k’arashe yana d’ago kai had’ida duban Assad dake tsaye saman kansa. Alhaji Isyaku yai saurin jinjina kai yana duban Mu’azzam d’in harma da Assad “Eh K’warai Yallab’ai.. Na ganeku.” Mu’azzam ya jinjina kai kafin yace “Good, bazamu cutar dakai ba.. Hasalima mu Jami’an tsaro ne, inada Tabbacin ka fahimci cewa bazamu cutar dakai ba bayan abokan aikina sun Kub’utar dakai daga hannun wad’anda sukai garkuwa dakai..” Cikin sauri Alhaji Isyaku ke jinjina kai yana fad’in “Wannan haka ne Rankaidad’e, wllhi kud’in aurena suka sace nid’in sabon ango ne Yallab’ai..” Fuzar da huci Mu’azzam yai cikeda takaici kafin yace “Wannan ba matsalata bace Alhaji, tambayoyin da zaka amsa mana yanzu sune damuwata.. And I suggest that you cooperate with us dan muji dad’in gudanar da aikinmu kuma kaima mu maidaka gida a mutunce.” Alhaji Isyaku ya zuba masa idanu kafin yace “Maiyasa baku kaini police station ba kuka kawo ni nan wajen..?” Mu’azzam dake murza hannayensa kad’an yana duban Alhaji Isyakun gajeren murmushi ya kumayi kafin yace “Kasan da cewa yarinyar dake yunk’urin aura ‘yantadda suna bibiyarta..?” Alhaji Isyaku ya zaro idanu waje yana mai tuna kalan tashin hankali da iftila’in da ahalin Sadiya ke ciki dik dalilin tsohon saurayinta Sagir.. Idan ya fahimta Wato yarinyar suke hari shiyasa sukai yunk’urin d’aukesa. Yai saurin d’ago kai yana fad’in “Yallab’ai wllhi tsautsayi ne ya sanyani neman auren yarinyar nan.. Wllhi bansan komai ba.!” Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Baka San komai ba..? Then Maiyasa ka firgita..?” “Yallab’ai satan mutane ya zama ruwan dare a k’asar nan dole na firgita..!” Alhaji Isyaku ya fad’i jikinsa na rawa. Mu’azzam ya jinjina kai yace “Wannan shine dalili...?” Shiru ya gifta gumi na tsartsafo ma Alhaji Isyaku yana kuma zaro idanu waje, lokaci guda yanajin babu abinda zai kuma had’asa da Sadiya balle yai tinanin aurenta.. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Alhaji idan muka kaika ofishinmu dole sunanka ya shiga record sannan hakan ka iya shafan reputation d’inka harmada sana’arka.. And once you’re proven guilty dole a maka ka a kotu akumayi shari’a dakai.. Amma ni na maka alk’awari idan ka sanar damu iyakacin gaskiyar abinda ka sani zamu sakeka tin daga nan basai mun tafi ofishinmu ba.. Just cooperate Alhaji and tell us how you’re connected to this man.!” Ya k’arashe yana mai aje masa hoton Danger saman hannunsa. Da mamaki Alhaji Isyaku ke duban hoton kafin ya d’ago yana duban Mu’azzam, lokaci guda ya girgiza kai yace “Rankaidad’e wllhi kaji na rantse maka bansan wannan mutumin ba.. Wllhi Allah shine shaidata ban sansa ba ban kuma tab’a ganinsa ba sai yanzu daka nuna min hotonsa.” Mu’azzam ya jinjina kai kafin yace “Amma kanada masaniyar mutumin nan sunanka ya soma ambata mana a lokacin da muke bincikensa.. Ta yaya zaka ce baka sanshi ba bayan shi d’in ya sanka..” Alhaji Isyaku ya girgiza kai yace “Wllhi wllhi Allah d’aya ne ban sanshi ba, bansan yaya akai ya sanni ba.. Koda yake ba abun mamaki bane dan ya sanni dan ni mutum ne mai huld’a da mutane da dama. Sannan Allah ya rufa mun asiri a unguwarmu inada tabbacin idan ka shigo layin gidana na d’aya daga cikin gidajen da ake kwatance dasu.. So ba abun mamaki bane dan ya kama sunana Rankaidad’e..” Mu’azzam ya tsaresa da idanunsa da suka gama kad’awa sukai jazir “Alhaji zan sake tambayarka nicely ka sanar dani abinda ke tsakaninka da mutumin nan.!” Jin zai fice a giya yasa Assad saurin kamosa suka fice daga wajen. Dukan garu Mu’azzam d’in yai da hannunsa yana duban Assad “What now..! Mai kuma na aikata..? I was only questioning the man..” Fuzar da huci Assad yai yace “Baka aikata komai ba Mu’azzam, amma kana shirin aikatawa, ka d’auko mutumin nan ba bisa k’aida ba kana interrogating nasa, and not only that. you’re forcing him to admit to the crime he’s not committed. Bayan cewa koda ya aikata laifin yanada damar da zai k’i yin magana har sai an barsa ya gana da lawyer d’insa..Anya Mu’azzam ka d’auko hanyar da zai b’ulle.. Don’t allow your anger to consume you.. Kabi komai a sannu.. I’m positive mutumin nan Iyakacin gaskiyarsa yake fad’i babu abinda ya Sani. Kaman yanda na fad’a maka he’s caught in the middle ne sabida auren yarinyar da ya tassama yi, Toh haka d’in ne.. Instead mu tsaya muna b’ata lokacinka kan tuhumarsa da neman mutanen da suka tassama kidnapping d’insa mukai.. Dan na tabbata babu abinda zamu samu wajen mutumin nan..” Mu’azzam ya d’ago fuskarsa data rine zuwa ja sabida tsananin tashin hankali, lokaci guda ya shafi goshinsa da hannunsa guda kafin yace “Kai baka tunanin mutumin nan had’a baki sukai da mutanen da suka tassama sacesa.. Baka tunanin hakan na iya kasancewa cikin plan d’in Danger.. Danger is a very dangerous person Assad, he’s capable of everything.” Assad ya jinjina kai yace “Na sani Danger is Dangerous, amma tambayar da zan maka a nan shine idan bakinsa d’aya da Danger Maiyasa zai sacesa.. Sannan idan bakinsa d’aya da Danger bazasu amshe kud’ad’en dake hannunsa ba..” Mu’azzam ya zuba masa idanu kaman mai nazarin sai kuma ya murmusa yace “Kana magana as if you can’t read criminal minds and how smart they can act.. Yanzu dashi da Danger duk zasu iya shirya haka dan su karkatar da hankalin jami’an tsaro dan kawai abun yayi kaman Su d’in suna bibiyar Alhaji Isyaku ne sabida Auren Sadiya da yake yunk’urin yi.. I believe ka amince zasu aikata fiyeda haka.” Assad ya nusa yace “Everything is possible in a situation like this saidai hanyar da ka d’auko zai iya sakamu cikin matsala gaba d’aya.. Maimakon muyi solving case d’in zamu iya b’ata komai da wannan hanyar daka biyo ba bisa k’a’ida ba..” Shiru Assad ya d’anyi yana mai tsaresa da idanu kafin yace “But wait, idan har kana tinanin Danger da mutumin nan bakinsu d’aya ne Maiyasa ka hana mutumin auren yarinyar..? Sannan Maiyasa kai ka aureta.. Kana tunanin zasu iya cutar da ita ne..?” Shiru Mu’azzam bai basa amsa ba sai mugun kallon da yake aika masa. Lokaci guda Assad yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Now I get it.. Ka aureta ne to give her protection..!” “O C’mon just shut up Assad..!” Assad yaci gaba da fad’in “Yes gaskiya ne Mu’azzam dan ka bata kariya daga sharrin su Danger ka aureta.. Because she’s there target.. Ko baka fahimci hakan yanzu ba I’m positive gaba zaka fahimci haka.” Da mugun mamaki Mu’azzam ke kallonsa yanaji yanda yake k’ok’arin k’irk’iro wani zance, kan mai zai bama wannan yarinyar protection Iyakacin abinda ya Sani shine he still needs her for his mission ne. Gajeren tsaki yai yana mai girgiza kai yake furta “You are not serious Assad. Bansan ya akai kake aiki k’ark’ashin NPF ba. You should be a clown and not a police officer..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya koma cikin building d’in yanda Alhaji Isyaku ke zaune. Assad ya take masa baya yana mai girgiza kai kad’an. Suna k’arasowa Mu’azzam ya dubi Alhaji Isyaku yace “Alhaji zamu k’yaleka ka tafi.. Zamu maidaka Gida.. Motarka tana nan a waje wad’annan abokan aikin nawa sun taho maka da Ita nan.. Amma still idan kanaso zaka iya reporting ‘yanta’addan nan da suka tasamma saceka suka kuma sace maka kud’ad’enka.” Alhaji Iskyaku Yai saurin girgiza kai yana mai zaro idanu yace “Ni wllhi bana fatan abinda zai had’ani da ‘‘yanta’addan nan, yo a k’asa irin wannan da aka maida satan mutum kaman an d’auke ‘ya’yan kaji ai abun na gode ma Allah ne da bai k’addari zan sha wahala hannun mutanen nan ba.. Kuma tinda na tsira Alhamdulillah.. Sannan wannan yarinya ko a k’afa aka d’aura mun ita zan kwance na gudu dan na kula tsautsayi da bala’i ke bibiyarsu.. Ban tab’a jin k’aran harbe harbe ba saida nace zan aureta.. Na gode maku matuk’a da ceton rayuwata da kukai..” Assad ya mik’a masa hannu sukai musabaha kafin yace “Kar ka damu Alhaji, hakan aikinmu ne.. Kula da al’umman k’asa tsare masu rayuwarsu lafiyarsu harmada dukiyarsu.. Kuma kar ka damu da izinin Allah zamu gano mutanen da suka maka wannan aika aika and they will answer to the law. Ku daina karyar ma jami’an tsaron k’asar nan da fad’in cewa sun gaza Gwabnati ma sun gaza.. NPF tana iya k’ok’arinta a kullum domin taga Ta kawo k’arshen ta’addanci da rashin tsaron da ya addabi k’asar nan..A koda yaushe ku saka a ranku cewa mu ‘yansanda abokanku ne ba mak’iyanku ba.. Dukda cewa da yawa sun mana shaida cewa akasarin mu gurb’atattu ne ba haka abin yake ba domin kuwa akwai na k’warai a cikinmu.. Kaman dai ko wacce irin Sana’a akwai gurb’atattu akwai na K’warai..” Alhaji Isyaku ya jinjina kai a hankali yana duban matashin D’ansandan. Lokaci guda ya kuma masu godiya kafin suka nufo waje gaba d’aya. Suna fitowa waje Alhaji Isyaku ya kasa key ma Mota, jikinsa dik sai rawa yake.. Gani yake kaman ‘yantaddan zasu kuma dawowa. Ya lek’o da kansa ta glass yana fad’in “Rankaidad’e ko zaku taimaka min dan Allah.. Wllhi ban iya tuk’a motar.” Assad ya dubesa kafin ya dubi su Mu’azzam sai kuma yace da Alhaji Isyaku “I’ll drive you home Alhaji.” Alhaji Isyaku cikeda jin dad’i yake godiya wa Assad “Na gode matuk’a yallab’ai, aikam bazan iya tuk’a mota ba dan har yanzu tsoro bai sakeni ba.. Gani nake kaman idan ina tafiya ‘Yantaddan nan zasu dawo.. Na gode na gode k’warai.” Assad ya dubi Mu’azzam yai masa alama da hannu kan cewa zai kai Alhaji Isyaku gida. Jinjina masa kai kurum Mu’azzam yai kafin suka soma fitowa tareda su Yusuf suka nufi motocinsu suna basa update abinda ke faruwa a CID. Shiru Mu’azzam yai yana nazarin abducting Alhaji Isyaku da aka tasamma Yi wanda baida haufi idan har Alhaji Isyaku baida wani connection da Danger Toh ko shakka babu masu bibiyan yarinyar ne suka kuskuresa. A fili ya furta “Danger..! Zan kamaka dik yanda ka shiga ka fita.. Da k’udurar Ubangiji.!” K’aran shigowar sak’o cikin wayarsa da yaji ne ya sanyasa ciro wayar aljihu yana dubawa. Lamba ce Babu suna, sannan abinda kawai aka rubuta jikin sak’on shine _BAD_ Ya nanata alphabets d’in a hankali “BAD” sai kuma ya fad’a in word “Bad..!” Ya nanata yafi sau UKU. Lokaci guda ya yanke shawarin kiran lambar.. Kafin yakai ga kiran lambar wani sak’on ya sake shigo masa. Wannan karon ga abinda aka rubuta. _BAD is your enemy_ A hankali ya kuma furtawa “Bad is your enemy”. Yai shiru yana kuma duba. What does this mean.? Saurin sake danna kira yai amma wayar bata shiga, a kashe take. Take wata sak’on Ta kuma shigo masa da wata lamba ta daban _BAD is ruining your home._ Dafe kansa yai kad’an yana duban lambobin da aka turo masa wad’annan sak’on dasu wanda ko shakka babu wasa da hankalinsa mai turo sak’on yake shiyasa yake turo masa da lambobi barkatai dan kar yayi tunanin tracing lambobin. Bai ida tinanin ba wani sak’on ya kuma shigowa da wani lamba daban duk dai akan BAD. _BAD is very BAD_ A hankali ya fuzar da fuci yana duban lambobin kusan guda uku. Cikin natsuwa ya nufi motarsa lokacin ana kiraye kirayen sallar magrib. Tinanin Bad bai daina Yawo a kwanyarsa ba. Yana driving yana nanata kalmar Bad. Wata sak’on ta sake shigo masa da wata lamba daban duk dai akan bad _You need to find BAD_ A fili Mu’azzam ya furta “Who are you BAD..?!” ** A gidansu Sadiya kaw tana k’udundune a d’aki cikin bargo sai rawa jikinta yake alamun zazzab’i ya kuma rufeta, ko kukan ma ta kasa yi yanzu kam. Tabbas da ace zatai kukan da taji sa’ida cikin zuciyarta. Tana nan kwance tana kar karkarwa tana iya sauraro muryoyinsu daga tsakar gidan yanda yanda Malam Liman da Ummanta da shaidu guda uku suka had’u suna warware bashin da Tabawa ke binsu Wanda Wai mutumin da ya aureta ya biya masu.. Kuma Wai ba kowa bane wannan mutumin face d’asandan nan da Ta tabbata da zai iya samun daman harbeta da zai aikata hakan.. Ta yaya za’ace wannan mutumin shine mijinta.. Ta yaya za’ace an mata aure haka bagatatan saikace wata ‘yar tsana.. Shin talauci hauka ne kokuwa dai rashin mahaifinta ne yasa akai mata haka.. Allah sarki yau Ta kuma yarda cewa mahaifi Katanga ne mai k’arfi kan iyalansa duk talaucinsa da babunsa kuwa.. Ta tabbata da ace Abba yana nan sam bazai zuba idanu ai mata irin wannan auren ba.. Tabbas maraici akwai ciwo cikinsa.. Tabbas wanda bai d’and’ani d’acin maraici ba baisan rashi a rayuwa ba.. Yau taga ranan mahaifinta sannan taji ciwon rashin sa a gareta.. Gashi nan a aurar da ita saikace wata taguwar da aka ciwo a yak’i wacce batada wani daraja.. Wasu hawaye masu tsananin zafi suka zubo mata. Tana jin sanda Tabawa ke gud’a tana fad’in ta yarda k’wallan mangoro ta huta da k’uda. Saida su Malam Liman da shaidu suka fara ficewa kafin Tabawa ta mak’ale kud’ad’enta ta fice. A zauren gidan Tabawa Malam Liman da D’an Rakiyarsa Munkaila kuka tsaya suna jiran Tabawar. Tabawa tana shigowa tai wani birki tana bada balance dan bataga alamun mutane ba da shike dare ne. Rawanin Malam Liman ta hango ta gane sune. “Ahh Haba Malam yo ai sai ka razanen.!” Malam Liman ya Washe baki yace “Yo banda abinki Tabawa ai su kud’i ‘yan sirri ne..” Tabawa tace “Haka ne..” Lokaci guda ta juya ta basu baya Liman sai nad’e carbi yake cikin hannunsa yana gyara rawani yana ‘yan lek’e lek’e irinta marassa gaskiya. Tabawa ta k’irgo dubu biyar ta mik’awa Malam Liman. Malam Liman ya amsa yana juya kud’ad’en “Haba Tabawa. Haba Tabawa dubu biyar fah nake gani.. Dik wa’azin dana dingayi ina d’aga jijiyan wuya duba fah ki gani jijiyoyin wuyata da mak’oshi na har ciwo suke.. Ace duk a dubu biyar zasu tsaya.” Tabawa ta karkace tana dubansa “Toh Malam kazarka ce ta kama..? Kaga idan bazaka amsa dubu biyar d’inba kana iya dawo da ita dan wllhi dama da k’yar na baka.. Ni Tabawa kud’i basa fita hannuna idan bazan sami k’ari ba.!” Malam Liman ya girgiza kai yace “Ai shikenan kuma.. Dama idan da kwad’ayi da wulak’anci.. Allah amfan.. Kai Munkaila Shige muje..!” Ya tasa k’eyar Munkaila suka shige Tabawa na rakasu da bak’ak’en magana.. “Kaji min rashin kunya saikace da guminsa cikin kud’ad’en..” Tana nan tsaye tana sababi su Over suka shigo rungume da ledar kud’i suna ‘yan lek’e lek’e. Over sai bin bayan Su Liman da ficewarsu kenan daga lungun da kallo yake, yana wani duk’awa yana d’aura hannunsa saman gira irin idan haske ya maka yawa kana so ka tantance abu kai kace ba dare bane haka Over ke kannare idanu yana fad’in “Kaiiiii! wa nake gani a nan..! Kai bara’uba ashe Malam ma yana d’an capcapkewa kenan..!” Suka fashe da dariya shida abokansa suna fad’i cikin muryarsu Ta ‘yan maye “Wllhi mutumin nan yama raina mana hankali yake taramu yana mana wa’azi ashe yana zagayowa idan dare ya raba..! Toh wlllhi ya sake cewa zai mana wa’azi zamu fasa k’wai.. Fayaaa zamu masa harsashi d’aya ta mar..!” Tabawa tai saurin tura k’ofar tana fad’in “Kai Kai ya isa.. Wannan ba matsala Ta bace ku ta Shafa.. Ina labarin aikin da na sakaku..? ya ta kasance tsakaninsu da Alhaji Isyaku. Over ya d’ago mata ledar kud’i yana nuna mata kafin yace “Tin yaushe muka cika aiki.. Amma saidai ‘yansanda sun biyomu sanda muka d’aukesa..” Tabawa Ta zaro idanu waje tana dafe k’irji “Ince baku sakamu cikin matsala ba.. Allah yasa babu wanda yaga fuskokinku..” Over ya dara irinta basawa yace “Haba Over da yaransa ai ba na wasa bane. Mun cika aiki yanda ya kamata. Mun amshe miki kud’ad’en Uwar Daba.. Amma Uwar Daba ina kika samo bindigar da kika bamu ne..? Kodai safaran makamai kike ne.!” Tabawa Ta buge bakinsa tana fad’in “Kai over koda wasa kar na sake ji ka fad’I kalaman nan.. Bani bindigar ta k’arashe tana fuzge bindigar ta nad’eta cikin bak’in k’yalle. Lokaci guda kuma idanunta suka sauk’a kan hannun over dake rungume da ledar kud’in ta dara cikeda jin dad’I tana mai amshe kud’ad’en hannun Over, ta d’an tsakuro wani abu Ta basu tace su fara somin tab’i da wannan “Aikinku yayi kyau Over.. Sai mun had’e sauran bayanin.” Ta k’arashe tana rungume kud’ad’en. Over yace “Baji uwarmu Ta daba.. zamu had’e ai.. Ya toh Baabaa mu Ware mana..!” Ya k’arashe yana duban abokan nasa. Lokaci guda suka fice suna tangad’i irin yanda ‘yan maye suke. Suna ficewa Tabawa ta murmusa hannayenta biyu rik’eda kud’ad’en da ta dafe a ranan, d’aya hannun bashin Ta ne da Angon Sadiya ya biya, d’aya hannun kuwa kud’in Alhaji Isyaku ne data tura su Over suka sato mata. A fili take furta “Alhaji Isyaku kenan abokin k’ullawa da warwarewa.. Da Tabawa kake zancen.. Wanda baiyi sharan masallaci ba dama zaiyi na Kasuwa. Baka auri yarinyar ba kuma naci kud’inka naci banza.! Na jefi tsuntsu biyu da Dutse guda.” Ta k’arashe tana mai fashewa da dariya. ** Umma da Sadiya na zaune Umma tana mata fad’an ta tashi taci wani abu idan ba kashe kanta take son yi ba, Su rungumi k’addara Su fawwala wa Ubangiji lamarinsu. Yana sane dasu yake aiko masu jarabawa daki daki.. Tai k’ok’arin cin jarabawar kar tai ma rahamarsa butulci. Da k’yar Sadiya ta mik’e ta zauna Umma ta zuba mata paten dankalin hausar ta d’an soma tsakura kenan suka jiyo ana kwankwasa k’ofar gidan. Suka dubi juna a tare itada Umma suna kuma duban lokaci, agogo ya nuna k’arfe 8:30 na dare. Umma ce ta d’an soma k’ok’arin mik’ewa da dafe dafe dan itama k’afar nata bai warke ba. Sadiya ta dubeta taga yanda take k’ok’arin tashi da k’yar. Lokaci guda ta girgiza kai tace “A’a Umma zan duba.” Umma tace “Anya zaki iya kuwa.? Kiga fah kaman jiri zai kifaki.” Sadiya ta mik’e da k’yar tana fad’in “Babu komai Umma zan iya.” A haka ta nufo tsakar gidan tana tafe da k’yar tana dafa bango dan mugun juwa ke k’ok’arin kaita k’asa. koda Ta bud’e k’ofar da tsananin mamaki take duban wanda ke bugun k’ofar. “You.!!” Ta furta zuciyarta na wane irin tsinkewa idanunta suna kuma firfitowa waje. Lokaci guda kalaman Malam Liman ya soma dawo mata, sunan mutumin da aka aura masa ita.. Rawar da jikinta yake ya k’aru.. Babu shiri cikin tsananin tsoro da firgici ta soma k’ok’arin maida k’ofar zata rufe saidai kafin tai wani aune ya saka hannunsa guda ya tare k’ofar. D’aya hannun nasa yai amfani da ya damk’o arms d’inta yana fad’in “Don’t you dare try that.!” Su duka biyun huci suke suna duban juna, fuskokinsu dab da juna suna iya jin fucin numfashin junansu babu kaman Sadiya da take ji zafin jikinta na k’aruwa tin sanda ya kamota. Lokaci guda Mu’azzam yaci gaba da fad’in “You’re coming with me, wether you like it or not.!” Cikin tsananin huci itama take dubansa, lokaci guda taji Ta tattaro duk strength d’in da ya rage mata “I’m not going anywhere with you.. Kai baka isa ka tilasta min ba.. I’m not your wife and I’ll never be..!” Ta fad’i tana kiciniyar k’wace jikinta daga rik’on da yai mata. Da k’arfi take k’ok’arin turasa tana fad’in “Let go.. let me go.. Ka sake ni nace ko kuma na kira maka ‘Yansanda.!” Murmushi wannan karon ya sakar mata yana kallon yanda take kokawan k’wace kanta daga rik’on da yai mata wanda da hannu guda kurum yai hakan “Go ahead and call the police.. Let’s see waye yakeda bayanan da zaima ‘Yansanda.. For as far as I know ban aikata wani abu illegal ba.. On the contrary..” Wannan karon matso da fuskar yake sosai kusan nata kafin ya manna bakinsa saitin kunnenta guda yace “Don’t you think I should report you instead.? Sabida nayi wasting kud’ad’en da a garbage like you bata cancanta ba.!” Wannan karon sosai bugun zuciyarta ya k’aru k’walla masu zafi suka ciko idanunta.. Batasan sanda wani irin k’arfi yazo mata ba, ta turasa baya da duka k’arfinta.. Hawaye ne ke gangaro mata sanda ta shiga nunasa da yatsa “You stay away from me.. Kar ka sake zuwa nan..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. Daidai lokacin Umma Ta k’araso dan taji shirun Sadiyar yayi yawa. Da mamaki Umma ke duban Mu’azzam dake tsaye cikin tsananin tsimewa yana duban Sadiya dake kuka.. Umma tana k’arasowa Sadiya ta k’arasa ta rungumeta tana kuka “Umma kice ya tafi dan Allah.. Umma kar ki bari ya d’aukeni..” “Unfortunately, I’m not leaving this place without my wife..!” Suka sinkayo muryar Mu’azzam na fad’in haka cikin dakewa. Jikin Umma yai sanyi, musamman da ta tina cewa shid’in Wai mijin Sadiya ne sannan a shari’ance yanada cikakken iko akanta. Umma na hawaye take dubansa “Dan Allah kayi hak’uri abi komai a sannu.. Dan Allah na rok’eka..” Gyara tsayuwarsa yana duban Umma wannan karon “Tell your Daughter to come with me willingly.. Or else..” Katsesa Sadiya tai cikin huci “Or else what.. What are you going to do Mr Inspector.? Zaka janyoni da k’arfi ne ko zaka sanyani tafiya gidanka da k’arfi ne..!” Wannan karon bai kuma tsayawa sauraronta ba ya k’arasa ya shiga janyota, Umma tana kuka tana rok’onsa yai hak’uri ayi magana cikin natsuwa amma kaman cewa take yaci gaba da janye Sadiyar.. Sadiya na kuka tak’i sakin Ummanta Mu’azzam bai fasa janyeta ba. Kuka take tana fad’in “Umma dan Allah karki barshi ya tafi dani.. Umma ki taimakeni.. Kar ki barshi ya d’aukeni...!” Muryarta ne ya katse sakamakon sakewa da jikinta yai ta zube cikin hannunsa sumammiya.. Umma ta rarrafo da k’yar tana jijjiga ‘yarta tana ambato sunanta shiru bata tashi ba.. Babu shiri ta mik’e da k’yar ta tafi kawo ruwa dan ta zuba mata.. Saidai Umma na mik’ewa Mu’azzam ya sunkumeta cikin hannunsa...Daga haka Sa kai yai ya fice daga gidan d’aukeda Sadiyar cikin hannunsa. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *24* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Assad da fitowarsa kenan daga layin gidan Alhaji Isyaku bayan ya maidasa gida nan ya hango bayan motar Mu’azzam tana ficewa daga layin. Mamaki ya cika Assad mai ya kawo Mu’azzam nan kuma.? Shi zai iya cewa yama mance Wai Mu’azzam d’in ya auri Sadiya. Juyawa yai ya dubi lungun gidansu Sadiya nan ya hango Umma ta fito tana kuka tana ambato sunan Sadiyar.. Babu shiri Assad ya nufota.. Tambayarta ya soma abindake faruwa. Cikin zuban hawaye Umma ke sanar dashi dik abinda ya faru tin daga zuwan Mu’azzam har d’auke Sadiyar da yai. Dan ta gane Assad shine abokin aikin Mu’azzam d’in da suka soma zuwa bincike gidansu tare. Assad ya lumshe idanunsa a hankali yana girgiza kai “Mu’azzam! Mu’azzam.. Mu’azzam..!! Mai ka aikata kuma..” Yai maganar a hankali idanunsa a lumshe. Bai gama kashe wani wutan da Mu’azzam d’in ya kunna ba ga wani ya kuma tadawa. Muryar Umma ya sinkayo tana fad’in “Yallab’ai dan Allah ka ceceni.. Kar abokin aikinka ya cutar min da d’iya.. Ka taimaka min ka nemo min d’iyata.. Wllhi batada laifin komai..” Assad da zuciyarsa ta gama raunana ganin yanda matar ke zuban hawaye tana ambaton ya taimaka mata dik sai yaji zuciyarsa na kuma karaya. A hankali yake furta “Umma ki kwantar da hankalinki.. Nothing bad will happen to your daughter... Mu k’arasa gidan naku sai muyi magana.” Umma ta share hawayen da suka wanke mata fuska kafin Ta girgiza kai tace “A’a bazan iya ba sai nasan Ina yakai mun d’iya.. I don’t want to lose another family member.. Na yarda ni yakaini ya rufeni amma kar ya cutar min da d’iya..” Assad ya d’an kifa kansa kad’an kafin yace “Umma mu k’arasa gidan muyi magana a natse, na miki alk’awari babu abinda zai sami d’iyarki.” Duban Assad tai da idanunta masu zuban ruwa kafin ta samu kanta tana mai bin umarnin Assad d’in lokaci guda Ta juya suka koma gida. Sauk’in abun su Ashir dik suna bacci da batasan yanda zatai tama yaran bayanin abinda ke wakana ba. A nan veranda d’in Umma tai nuni ma Assad da tabarmar dasu Malam Liman suka tashi kafin Ta k’arasa saman kujera irin wanda mata ke amfani dashi a kitchen ta zauna, har lokaci sharan hawaye take da hijabinta. Tsananin tausayin bayin Allahn ya rufe Assad. A hankali ya soma furta “Umma da farko Ina mai baki hak’uri kan abinda abokina ya aikata.. K’warai Mu’azzam bai kyauta ba sannan bai biyo ta hanyar da ya dace ba.. Ina baki hak’uri Umma on his behalf kiyi hak’uri.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Umma Mu’azzam is not a bad person, yanada kurakurensa kaman ko wani d’an Adam, but I can assure you he’s not a bad person, and he’s not going to do any harm to your daughter.. Saidai ma ya d’auketa ne to give her protection daga mutanen da suke yunk’urin cutar da ita.. Mutanen da suke tunanin Sagir ya sanar da ita wani abu.” Umma ta dubesa da mamaki wannan karon kafin tace “Amma ai mun sanar daku Jami’an tsaro Iyakacin abinda muka sani gameda Sagir.. Maiyasa abokin ka bazai k’yale d’iyata ba.. Na tabbata da wani dalili nasa da nufi ya aureta ya biya mana bashinmu.” Assad ya jinjina kai kafin yace “Haka ne Umma, Kinyi gaskiya..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Umma Mu’azzam ya auri Sadiya ne to keep her safe from danger, itace target d’in ‘yantaddan da muke nema muke kuma bincike kansu.. Nasan kinada masaniya akan irin mutuwar da mijinki kuma mahaifin Sadiya yayi..” Umma ta d’ago tana dubansa wannan karon sai kuma ta katsesa da fad’in “Mijina had’arin mota yayi.. Mota ce ta bigesa.. Sannan tsautsayi ne kuma k’addara ne da bazai tab’a tsallakewa ba..” Tai maganar cikin tsananin rauni. Assad ya jinjina kai kad’an kafin yace “K’warai haka ne Umma, Tabbas tsautsayi ne da bazai shige ranansa ba.. But mu jami’an tsaro hasashenmu da bincikenmu sun tabbatar mana accident d’in shiryayye ne.. Shiryawa akai Umma and Sadiya suke hari sai suka fara daga kan Wanda yake sama da kowa a family d’inta which’s her father.. Sun kawar da mahaifinta sabida shine mutum na farko da zai bata protection ya zamto garkuwa a gareta. Zaman Sadiya a taredaku had’ari ne a gareta da kuma gareku baki d’aya.. Na tabbata bazaki so wani abu ya sake samun wani cikin ahalinku ba.. Inada tabbacin wannan dalili shiyasa Abokina ya d’auketa sabida ‘yantaddan Ita suke hari they believe Sagir ya sanar da Ita wani abu wanda zai iya exposing nasu..” Umma tai shiru tamkar mai nazari sai kuma tace “Idan na fahimceka Abokinka ya d’auke d’iyata ne domin yaja hankalin mutanen da yake nema.. Ba don ya bata kariya ba..” Assad ya d’an shafi kansa kad’an yana mai sadda Kai k’asa “Umma bazan so kiyi ma abokina mummunan fahimta ba Dikda cewa kinada cikakken damar da zaki masa irin wannan fahimtar... Wato Umma Mu’azzam mutum ne da ya had’u da tarin iftila’i na rayuwa.. Dikda cewa ansan musulmi da d’aukan k’addara.” Ya d’an kuma nusawa kafin yaci gaba da fad’in “Ya rasa mahaifinsa tin yana k’arami sannan a daidai wannan lokacin jinya mai tsanani ya sami mahaifiyarsa.. Bayan wannan yazo ya rasa tilon k’anwarsa wacce aka kasheta aka kuma tsinta gawarsu tareda Sagir.. Kinji dalilin da yasa bincikenmu ya gangaro har kanku.. Sabida tarayyar Sadiya da Sagir... Amma kawai abinda nake so ki yarda dashi kuma ki amince shine Mu’azzam is never going to do any harm to your daughter.. And He’ll protect her with his life.. Ki kwantar da hankalinki Umma ki natsa zuciyarki kuma ki saka a ranki d’iyarki tana safer place.. Kiyi takabarki cikin kwanciyar hankali ki kuma rungumi yaranki.. I’ll be checking on you time to time in sha Allah.. Allah ya gafarta wa Abba yasa yana Aljannah..” Jiki a sanyaye Umma ta amsa da Ameen tana mamakin tarayyar Assad da Mu’azzam, yanda wannan yakeda mutunci da sanin yakamata ba kaman abokin nasa ba. “Ina mahaifiyar tasa take..?” Umma ta tambaya tana d’an dubansa kad’an. Assad ya d’an risina kafin yace “Tana can garinsu ana mata magani. Shekaru goma sha biyar kenan tana kwance tana jinya..” Jiki a matuk’ar sanyaye wann karon Umma tace “Allah sarki Allah ubangiji ya bata lafiya.” Assad ya amsa da Ameen. Daga haka Assad sallama yai ma Umma kafin ya fito ya nufi bakin Babban kwalta.. Yana tafe yana dialing layin Mu’azzam. Mu’azzam na driving yaga kiran Assad na shigo masa, yana d’agawa Assad ya soma fad’i daga d’aya b’angaren “Do I always have to remind you that you are a big jerk..” Katsesa Mu’azzam yai da fad’in “Say what you want to say quickly, I’m busy right now.” “Who do you think you are Mu’azzam Gamji.! Ta yaya zakazo har gidan mutane ka d’auke masu d’iya.. Are you out of your mind.” “No you’re out of your mind Assad, for as far as I know I didn’t do anything wrong. Matata na d’auko tareda ni.. Did I commit a sin..?” “Is that how you take your wife..” Kafin Assad yakai aya ya katsesa da fad’in “We talk tomorrow. I’ll send you some numbers.. Tracking nasu nake so ayi since you’ve access to the tracking room..” Daga haka katse kiran yai yana k’ok’arin forwarding lambobin da aka turo masa sak’on BAD dasu.. Birki yai sakamon motar da bai kula wanda ke gabansa ba. Aiko nan Sadiya Ta hantsalo daga saman seat ta buga kanta.. A hankali ta soma k’ok’arin bud’e idanunta tana dafe goshinta dake mata zogi yanda Ta buga. Nan ta Ware idanu ta ganta cikin mota.. A firgice ta mik’e tana k’ok’arin bud’e k’ofar motar saidai tuni ya danna motar a central lock. Sadiya ta dubesa yanda yake driving hankali kwance lokaci guda Take furta “Malam ina zaka kaini..? Ka maidani yanda ka d’auko ni ko na maka ihun b’arawo.!” Shiru idan steering da hannayensa ke bisa ya amsa shima zai amsa. Hawaye suka cika idanunta, cikin rawar murya take furta “Please ka maidani yanda ka d’aukoni.. I promise ban aikata komai ba.. Please don’t hurt me.. Ka maidani wajen Umma..!” Nan ma shiru bai amsata ba. Lokaci guda Ta soma sakin huci tana dubansa, kaman wacce akanjefota haka ta tsallako ta dawo frontseat d’in.. Steering wheel ta shiga k’ok’arin janyowa tana fad’in “Either you take me back home ko kuma na jefamu a rami gaba d’aya.” Ya juyo ya dubeta da mamaki ganin yanda take ta kokawa da steering. Nan ma bai kulata ba bai sakar mata kan motar ba. Idanunta na hawaye take dubansa “You’re merciless.. This is police brutality, Mr Inspector. Idan baka maidani ba wllhi zan maka ihun b’arawo.” Ba tareda ya dubeta ba idanunsa naga street yake d’an rage girmansu, kafin ya saki murmushi kad’an yace “Go ahead and shout. Shout at the top of your voice.. Let’s see idan akwai wanda zai taimakeki..” Hango check point na ‘yansanda da tai ya sanyata sakin murmushi tana hamdala, kafin ta juyo ta aika masa mugun kallo “You won’t get away with this.. I promise you..!” Suna k’arasowa aiko yana zuge glass ta dubi ‘yansanda masu patrol d’in “Officers dan Allah ku taimakeni.. He’s a kidnapper, wllhi satoni yayi.. I know my Mum must be worried.. Dan Allah ku taimaka min.” Mu’azzam ne ya katse zancen da fad’in “Officer all is well, I just found out my wife is pregnant. And you know how pregnant women are like..” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa Daskarewa tai tana dubansa, for the first time da taga murmushinsa, sai kuma ta shiga girgiza kai tana fad’in “K’arya yake Rankidad’e wllhi satoni yayi.. You need to arrest him please..” Bata Kai aya ba taga ‘yansandan sun k’ame suna sara masa had’ida clearing masa hanya “SIR.!” Suka fad’i a tare suna masu nuna masa hanya. D’ayan har yana fad’in “Congratulations Sir.!” Yana wani Washe baki yana k’anwata Cak ta tsaya da bayanan nata kafin ta juyo tana duban Mu’azzam dake maida wallet d’insa cikin aljihu wanda ko shakka batayi ID d’insa masu patrol d’in nan suka gani. Tabi ‘yansandan da kallo baki sake yanda Suka k’ame masa har motar Ta shige.. Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Do you think zanyi asaran wad’annan kud’ad’en kanki a banza ne,.. I’ll only dispose you when I’m done with you..” Yai maganan tamkar dai bashi yake maganar ba dan ko duban yanda take baya yi. Cikin tsananin huci da zafin rai take dubansa, kalaman nasa masu zafi suna mata Yawo a dodon kunnuwarta. Wai zai disposing d’inta when he’s done with her saikace wata shara. Take kuma tsoro ya bayyana sosai saman fuskarta.. Ko lokacin da take Sady Pretty d’inta bata tab’a tsintar kanta da tsoron wulak’ancin d’a namiji irin wannan karon ba.. Tsoro take kar wannan mutumin ya mata babban wulak’anci.. Hijabin dake jikinta ta shiga duk’unkunewa ciki tana girgiza kai wasu hawayen na kwaranyo mata. “Don’t hurt me please.!” Ta fad’i cikin tsananin rawar tana mai rintse idanunta. Ko kallo bata isheshi ba saima bada mahimmanci da yai sosai ga tuk’in motar. Suna isowa k’ofar gidan taga ya bud’e motar ya fito kafin ya zagayo ta yanda take zaune. Bud’ewa yai yace “Fito.” Da rinannun idanunta take dubansa “No I won’t.!” Ta basa amsa kai tsaye. Gajeren tsaki yai kafin ya fincikota ya fito da Ita ya soma k’ok’arin janyota tana tarjewa. Bai fasa janyota ba har saida suka shiga gidan. Saidai suna shiga taji haushin wasu irin k’artan karnuka irin breed d’in turawan nan. Ai bata San sanda tai tsalle Ta mak’ale cikin jikinsa ba. Cikin tsananin rawar jiki take furta “Na shiga uku mai zaka mun.!” Kai tsaye ya bata amsa “Zaki gani..!” Yai maganar yana mai tsare fuskarta da kallo wanda cike yake tab da tsoro.. Sai rawa jikinta yake ta kasa sakinsa. Saitin kunnenta ya rad’a mata “Sakeni kafin ki Shafa min wani cutan zamani..” Dubansa tai zuciyarta naci gaba da yankewa sai kuma taga ashe shid’in ta rik’e tsananin firgicin haushin karnukan wanda bama tasan tayi hakan ba. Cikin tsananin huci da zafin nama ta turasa da iya k’arfinta wanda saida ta kusan kaisa k’asa “Idan kana tsoron na shafa maka cutan zamani Maiyasa ka sato ni daga gidanmu ka kawo ni nan.. Bari kaji na fad’a maka Allah bazai tab’a baka nasara akaina ba.. Nafi k’arfinka nafi k’arfin wulak’ancinka..!” Ta k’arashe tana mai kuma janye hijabinta tana sauk’ar sa sosai tana mai kuma rufe jikinta. Dubanta yake daga sama zuwa k’asa cikeda mamaki kafin yace “Ke.! Cut this nonsense. No one wants a trash like you..!” Yana ida fad’in haka yaci gaba da janyota. Ga tsananin mamakinta wani d’an d’aki mai kaman store taga ya k’arasa ya bud’e gefen na Karnukan nan daketa faman haushi. Tsoro ya soma cikata sosai, kardai da gaske ya kawota ne ma karnuka su cinyeta. Jikinta yaci gaba da rawa. Yana ida bud’e d’akin ya turata ciki. Sadiya na hawaye ta d’ago hannu tana rok’onsa “Please don’t.. Don’t leave me here please.. Na rok’eka.. If you have any good in your heart dan Allah kar ka barni a nan.. Dan Allah ka maidani wajen Ummata..Wllhi tsoro nake..” “Ina tsaurin idon naki da courage d’in suka tafi.? Maima kika ce..?” Ya kannare idanu yana dubanta kafin ya jinjina kai yace “Yauwa kika ce A cheap low life police Officer wanda baida komai bai dogara da komai ba face karb’an bribe baida kud’ad’en da zai sauk’e miki bashinki..? Ko ba haka kika fad’a ba..” Ta shiga girgiza kai still tana hawaye. Jinjina kai ya kuma kafin yace “Dama na fad’a miki Zaki maimaita. Well, wannan Matsiyacin D’ansanda ya biya bashin kuma harda sadakinki.. And yau zan tabbatar miki cewa ke d’in Low life ce. Wannan d’akin shi ya kamaci low life irinki.. You’ll spend the night here, tareda Karnukan nan dan na tabbata kema d’in Kariyace.!” Yana ida fad’in haka ya janyo k’ofar ya rufe yai ficewarsa. Daskarewa Sadiya tai cikin rashin yarda da abinda Mu’azzam ya mata. Rufeta yayi a wannan k’aramin d’akin dake jikin d’akin Karnuka wanda motsi kad’an sukai zataji balle suyi haushi. A hankali taji k’afafunta suna silalewa. Ta tak’ure waje guda tana duban d’akin mai tsananin duhuwa.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai take iya ambata.. Bata tab’a jin ta tsani wani mutum a rayuwarta irin Mu’azzam ba. Ta rintse idanunta tana fad’in “Allah na tuba.. Na tuba ka yafe mun.. Abba ka yafe min.. Umma kizo ki cecen.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Na shiga uku ni Sadiya..!” Tana jin sanda Mu’azzam ya fice daga gidan ya rufe gate. Da gaske barinta yai a gidan Ta kwana tareda Karnuka.. Wani wawan haushin da karnukan suka saki saida taji har tsakiyar k’wak’walwarta.. Ta saki k’ara dan tsoro tana mai duk’awa had’ida toshe kunnuwanta da duka hannayenta biyu, ta rintse idanunta dikda tsananin duhuwa dake cikin d’akin wanda ko tafin hannu baka iya gani. ** A can Fufore kaw anyi carko carko akan Safeenah wacce mai gyaran k’afa yazo ya yana d’aure mata k’afar tata. Sai kuka take tana fad’in ta shiga uku gashi sam batasan yanda Mu’azzam yake ba tin jiya basu had’u ba sannan bata isa ta tink’ari Inne ta tambayeta Ina Mu’azzam yake ba. Ga wayarsa sam ta kasa samu.. Safeenah sai kuka take tana fad’in zafi k’afar take mata. Inne na zaune saman kujera mai gyara na kuma jan k’afar Safeenah na ihu. Inne tace “Ki rufe mana baki.. Uban da yasa kika zuba ma yarinyar tsantsi a hanya.. Gashi nan da yake batada hakkinki ta tafi gida lafiya ke kuma kin taka abinda kika zuba mata kinji ciwo.” Safeenah tace “Inne amma ke Wai bakiga abinda yarinyar nan tayi bane.. Wllhi na tabbata akan abinda tayi Mu’azzam zai iya b’ace mana b’att a dena ganinsa a gidan nan.. Ai dai Kinsan halinsa Kinsan yanda yake abubuwa.. Wllhi Allah na tabbata kan abinda yarinyar nan tai zai iya barin gidan nan without informing anyone... Wayyo Allah Malam mai d’auri Kaja a hankali..!” Ta kuma fad’a tana k’ok’arin janye k’afarta. “Ki rufe wa mutane baki.. Allah k’ara. Gobe ma dan Allah ki k’ara..!” Musaddiq ya tina sanda Ajidde zata tafi tace masa anyi babu shi bayi kallon birgiman bijimi a k’asa ba.. Dik a tinaninsa D’aya daga cikin shanun gidan ne ya fad’i k’asa yana birgima ashe fad’uwar da Safeenah tai ne take son sanar dashi kenan.. Ya girgiza kai kurum yana ba tareda ya ce komai ba. Sai kuma ya dubi Safeenah dake ture turen baki tana motsa k’afar da k’yar yace “Next time sai a kiyaye.. Allah ya kara sauk’i..” Bata amsa ba ta rakasa da harara ga hawaye saman fuskarta. Bayan kowa ya mata sannu an watse Meema ta matso kusanta tace “Sannu Adda Feenah..” Harara Safeenah Ta aika mata kafin tace “This is all your fault you know.. Saida nace miki kar mu saka mata ruwan tsantsi ba lallai ta taka ba Kikace mahaukaciya ce bata tafiya a natse dole zata taka gashi nan ita bata taka ba ni na taka..” Meema Ta tab’e baki tace “Addah Feenah ni fa da nace ki zuba mata ai bance kibi bayanta ki duba ko ta taka ko bata taka ba, ke da kanki kiyi wannan shawarin naki.. Toh ki fad’a mun how am I at fault..?” D’an gyara zama Meema tai tana kuma fito da idanu waje had’i da kwantar da murya tace “Addah Feenah.. What if this is your Karma..! Kin tuna matar nan da kika taka mata k’afa da Mota ranan a k’ofan Police Headquarters.. Karma is backfiring you Addah Feenah..” Tai maganar tana mai d’aga gira sama had’ida jinjina kai alamun tabbatarwa. Safeenah ta aika mata harara tace “Don’t even start Meema..” Meema ta murmusa tace “Wllhi Addah Feenah it’s possible hakkin matar nan ne ya kamaki.. Gashi irin abinda kika mata ya sameki.. Now we have no option dole mu k’ara kwanaki a garin nan har ki warke.. Who knows mai rikiceccen mijin nan naki zai tareda budurwarsa yanzu da kika gurgunce a nan..” Pillow dake gefenta ta d’auka ta jifawa Meema tana fad’in “Get out before I kill you Meema..!” Tai maganar tana huci zuciyata na tafarfasa. Fuskar Maleeka kurum take hangowa tareda mijinta. Lokaci guda Ta saki k’ara tana mai jifa da pillow d’in. Dik shegiyar Ajidden nan ne ta jawo mata.. Wllhi babu abinda zai hanata cin uwar yarinyar nan.. Meema Ta k’unshe bakinta ta fice tana dariya. ** Misalin k’arfe 11:00pm ya shigo gidan, Kai tsaye sashen Daddy ya wuce dan ya hango wutan parlor a kunne alamun Daddyn bai kwanta ba kenan. Da sallama ya shigo saman bakinsa. Daddy dake zaune daga center d’aukeda wasu documents yana sorting. A hankali ya soma zame k’aramar gilashin dake mak’ale idanunsa yana mai amsa sallamar Mu’azzam d’in. Nan fari’arsa ta k’aru. “A’a Officer sauk’ar yaushe.” Daddy ya fad’I yana mai fad’ad’a murmushinsa. Murmushin ne saman fuskar Mu’azzam d’inma sanda ya k’araso saman carpet d’in. Gaban kujeran da Daddy ke zaune ya duk’a ya zauna yana mai gaida Daddyn. Da sauri Daddy ya mik’a masa hannu sukai musabaha kafin yace “Yanzu ne zuwan Naka kokuwa ka jima da shigowa garin..” Mu’azzam ya d’an girgiza kai yace “No Daddy tin da yamma na shigo na biya na kula da wasu al’amran ne..” “Oh toh toh Allah sarki.. Kun taho tareda iyalin taka ce...?” Tambayan da Daddy yai masa saida ya sanya k’irjinsa bugawa sannan sosai yaji nauyin Daddyn dan har cikin ransa ji yake abinda yake yima Safeenah bai kyautawa. Iyayenta sunada mutunci musamman Daddy. Gaba d’aya sai yaji bai kyauta ba. K’ok’arin saita kansa ya d’anyi yana mai girgiza kai “No Daddy.. Fitowar gaggawa nayi shiyasa na taho ni kad’ai..” Daddy yace “Allah sarki.. Toh yayi kyau Allah dai ya taimaka yai maka jagora..” Muazzma ya amsa da “Ameen Daddy.” “Ya ka baro mutan gidan Inne da ‘yanuwanka.. Ya jikin Mamyn naka kuma.. Ana samun progress..?” “Kowa lafiya Daddy.. Jikin Mamy Alhamdulillah da sauk’i sosai.. Mun sameku kafiya..” Daddy yace “Toh Alhamdulillahi... Lafiya lou an gode Allah.. Gashi ka shigo ka samu ina duba takardu..” Mu’azzam ya soma k’ok’arin mik’ewa yana fad’in “Barin Barka kayi aikinka Daddy..” Daddy yace “No zauna abinka.. dama akwai maganar da nake so muyi amma yanzu naga dare yayi so zamuyi maganar gobe idan Allah ya kaimu.. And akwai yanda nake so muje dani dakai..” Mu’azzam ya jinjina kai cikeda risinawa yace “Okay Daddy Allah ya kaimu.. Mommy ta kwanta koh..” Daddy yace “Eh kasan Mamar taku kaman kasa ce nan da nan tayi bacci..” Ya k’arashe cikeda barkwanci irin tasu ta manya kafin Muazzma ya mik’e yana d’an Murmusawa. Saida safe yaima Daddyn kafin ya fice ya nufi side d’insa. Saidai tinda ya shiga d’akin tinanin yarinyar ya addabesa. K’ok’arin kauda tinanin yai kafin ya fad’a shower. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *25* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali take k’ok’arin bud’e idanunta da suka mata nauyi, tas ta Ware idanun nata tana duban yanda take. Wani had’add’en d’aki ne da ya tsaru iyaka tsaruwa. Tsoro ya kuma bayyana saman fuskarta, itadai tasan a wani d’aki mai kaman store ya barta wanda Tim wani haushin kare dataji bata kuma sanin meke wakana ba. Zumbur Sadiya ta mik’e tana duban d’akin.. Kallo guda zakai ma d’akin ka fahimci cewa d’akin Amarya ce. Ta saka hannayenta biyu tana kuma mutsuke idanunta ganinta da tai kwance saman gado har an rufeta da duvet. Kalle kalle ta soma tana kuma Shafa gadon dan dai ta tabbatar da gaske ne.. Toh ya akai tabar wancan d’akin yaushe aka kawota nan..? Tambayoyi ne da batada amsoshin su.. Gefen bedside ta hango hoton wata mata kyakkyawa an aje cikin k’aramar frame. Ta matso tana duban Matar.. Gani tai kaman ta tab’a ganin fuskar matar amma saidai sabida heavy makeup dake fuskar matar bata iya ganeta ba.. Bata kuma gane ina tasanta ba. Hasken rana data hango ya tabbatar mata gari ya waye. Tsalle tai ta diro daga saman gadon tana kuma juye juye zuciyarta naci gaba da yankewa “A ina nake..?!” Ta tambayi kanta cikeda firgici. Sallar asuba da batayi bane ta soma tinawa.. Babu shiri ta nufi wata k’ofa dake nan cikin d’akin wanda takeda tabbacin bathroom ne. Aiko tana tab’a k’ofar ya bud’e, kaman yanda take zato bathroom d’in ne komai na buk’ata akwai a ciki sannan komai Sabo ke sealed ba’a bud’e ba.. Harta toothpaste da toothbrush dik sabbi ne jere a wajen. Ta tab’e baki kad’an ba tareda tace komai ba.. Ita a halin yanzu babu abinda take so face ta ganta a gida.. A gurguje tai alwala ta fito tana tinani ina zata kalla ya zamto mata alk’ibla.. Bata ida tinanin ba ta hangi k’aton darduman turkey an shimfid’a ready to pray.. A ranta tace k’ila mata mai d’akin ne ta shimfid’a.. Sauri sauri ta isa saman darduman ta tada sallah.. Koda ta idar mik’ewa Tai tana kuma bin d’akin da kallo wanda ya tsaru iyaka tsaruwa, harta wardrobe d’in da yake transparent tana iya hango kaya jere cikinsa. Ta d’an tab’e baki a hankali kafin ta nufi k’ofa tana tinanin toh ina ne nan.. A hankali ta tab’a k’ofar d’akin ta bud’e.. Nan taga corridor ne madaidaici da k’ofofin da bazasu gaza guda uku ba. Tana tafe ta hango stirs wanda zai sauk’arta k’asa kenan. Nan take ta nufo staircase d’in zuciyarta bai daina yankewa ba. D’aga idonta da zatai ta hango wani k’aton hoto da akayisa in full kaman ka kira mutanen ciki suzo.. Mu’azzam ne da wannan Matar da taga hotonta a d’aki. Take ta tina walak’acin da ya mata a daren jiya. Ganin fuskar tasa take kaman wani bak’in kumurci. “Rascal..!” Ta fad’i a hankali tana aika masa mugun kallo dukda kuwa cewa Sunyi kyau sosai kaman ka sure ka gudu, ko ba’a ce ba hoton ran aurensu ne dan sunyi shiga ne irinta Amarya da ango. Dikda manyan kayane a jikinsa tsaf ta ganesa, sky blue shadda da akai mata d’inkin babbar riga mai gajeren hannu daga ciki sai hular dake kansa navy blue zanna bukar mai k’anan zane tasha tangaran sai k’yalli take. k’afarsa rufe cikin bak’ak’en covers.. Yayi kyau sosai dan ba k’aramin karb’ansa manyan kayan sukai ba. Ita kaw matar bridal gown ne jikinta all white tayi kyau sosai itama fuskarta cikeda annuri wanda da gani zaka fahimci tana tsananin k’aunar mijin nata.. A fili Sadiya tace “Bakiyi dacen miji ba.” Sadiya ta k’ura masu idanu tana tinani Wato gidansa ne kenan nan.. Toh ina matar tasa..? Rashin samo amsar da batai ba ya sanyata tab’e baki a hankali tana mai kuma dubansa cikin hoton, dan a hotonma fuskar nan tass babu wani annuri.. Ta tab’e baki kad’an kafin ta furta a fili “Mugun banza azzalumi.!” Tai maganar tana dungurinsa cikin hoton. Mu’azzam dake zaune dining area dik yana kallonta ta cikin k’atoton mirror d’in da aka k’awata dining area d’in dashi. Yi yai kaman bai ganta ba kuma baiji mai take cewa ba, yaci gaba da abinda yake yana kallon yanda take sakin huci tana dungurin hotonsa tana fad’in mugun banza Yai murmushi yana dubanta ta mirror, saida yai sipping tea d’in sau biyu kafin ya bud’e murya yace “Welcome to GIDAN ARO.. Where everything here doesn’t belong to you..!” Sadiya ta juyo a razane dan sam batasan da mutum a wajen ba.. Mu’azzam ya taso yana takowa a hankali har dai ya k’araso kusanta.. Hannayensa sakale cikin aljihun jeans d’insa yake furta “Take your eyes off my photo, I’m not the rich husband you’re looking for..!” Yai maganar yana mai mata nuni da hotonsu shida Safeenah da idanunsa. Murmushin da yafi kama da yak’e tai tace “Correction Mr Inspector, bani na kawo kaina nan ba, as a matter of fact kidnapping d’ina akai.. Zan fi kowa Farin ciki idan ka maidani yanda ka d’aukoni.!” Ta k’arashe cikin tsimewa itama. Ya murmusa kad’an da gefen bakinsa yana mai kuma takowa gabanta.. Lokaci guda ya tsime kaman dai bashine mai murmushin ba. Nan yaci gaba da furta “If you cooperate with me and do exactly as I say zaki koma yanda kika fito, because I don’t intend to keep you here for good.. Like I told you gidan nan tamkar GIDAN ARO yake a wajenki.. Kinsan ance ba’a baje Koli a a GIDAN ARO.. Toh kar kiyi gangancin baje naki kolin domin dik gidan da akace na aro ne any moment any time za’a iya sallamanka without notice..” Ya k’araso jikin hoton yana mata nuni da Safeenah “Kin ganta nan, she’s the lady of this house.. Aro aka baki na wutin gadi..” “Ban nema ba balle a bani Aro.. So don’t delude yourself.!” Da mamaki yake dubanta, dik ajiyeta a wannan store d’in da yayi jiya a matsayin warning ashe bai shiga kanta ba. Ya kula bakinta sam bai mutuwa. Ya tina yanda daren jiya baiyi bacci ba har saida ya dawo ya d’auketa cikin hannunsa ya kaita d’aki ya kwantarta ya tabbata ta samu sound sleep. Da yasan wannan bakin tsiwar nata bazai mutu ba da barinta yai a wannan d’akin ta Kwana ko zatafi shiga hankalinta. Takowa kusanta yake tana jada baya, bai tsaya ba har saida ya k’araso kusanta sosai ya tabbata bata da sauran wajen gudu kafin yai mata rumfa da kansa ya bud’e duka hannayensa ya tareta dasu yanda ko k’wakk’waran motsi bazata iya ba “Mai Kikace.. Maimaita abinda kika fad’a.!” Kasa magana tai Sai k’walla dake k’ok’arin ciko idanunta. Dubanta yake tin daga fuskarta mai cikeda rauni gauraye da tsoro kafin ya murmusa kad’an yace “Be careful how you speak to me.!” Yai maganar yana duban d’an bakinta wanda kaman ba daga nan maganganun ke fitowa ba. Saida ya tabbata tsoro ya shiga jikinta kafin yaci gaba da fad’in “Kar ki damu everything here is free of charge.. You can sleep in my wife’s bedroom, free of charge.. You can use her kitchen, free of charge.. You can watch her television, free of charge.. You can have all the luxury here free of charge.. You don’t need to pay with your body.. Kaman dai yanda kika saba..!” Ya k’arashe yana mai dubanta daga sama zuwa k’asa. K’walla masu zafi suka ciko idanunta.. Ta lumshe su a hankali hawaye suka gangaro mata. “I can’t take this insults anymore.. Tell me.. Ka sanar dani mai kake nema wajena.!” Ya murmusa kad’an kafin yace “Worse abinda zai faru dani a rayuwata shine a ganni tareda ke... Amma idan har sai nayi hakan na gano makashin ‘yaruwata, zanyi.. Zanyi dan na gano gaskiyar komai yanda akai aka samu gawan ‘yaruwata tareda watsettsen saurayinki who was about to marry you.!” Sadiya ta murmusa hawaye na gangaro mata lokaci guda tace “Ashe K’anwarka ma tanada connection da Sagir tinda har aka gano gawansu tare.. Ashe bani kad’ai bace dai watsettsiya...! Katseta yai da fad’in “Don’t you dare mention my sister..! I forbid you..!” Yai maganar yana mai nunata da yatsa hannunsa har rawa yake. Taji tsoron yanayin da taga ya shiga, lokaci guda kuma sai taji kaman bata kyauta ba ganin cewa k’anwar tasa ta rasu bai kamata tai magana irin haka akanta ba koda Mu’azzam ya gaya mata maganganu marassa dad’i.. bata iya k’ara furta komai har ya fice daga gidan cikin sassarfa.. Haka Mu’azzam ya fice da tinanin maganganun Sadiya cikin zuciyarsa. Cewa k’anwarsa tana da connection da Sagir.. Bazai tab’a yarda Ikram tana da connection da wannan d’anta’addan ba... No no no baima so ya amince da hakan.. Wasu irin hawaye ne yaji suna k’ok’arin ciko idanunsa.. Maiyasa all of the sudden yaji ya fara tunanin binciken k’wak’waf da yake yi.. Ji yake cikin tone tonensa zai digging abinda zuciyarsa bazata iya d’auka ba.. Hawaye ne yaji from no where suna gangaro masa.. Ya shiga girgiza kai yana furta “No no.. Sace Ikram akayi.. Batada wani connection da wannan mutumin.. Babu wanda yakeda connection da wannan d’anta’addan dik cikin ahalina...” Birki yai had’ida kifa kansa saman steering yanaji zuciyarsa na barazanar tarwatsewa. A b’angaren Sadiya kaw yana ficewa itama Ta nufo waje da zummar ficewa daga gidan.. Saidai tana sako k’afa taga k’artan karnukan nan suna nan a harabar gidan suna shawagi.. Ta koma da baya had’ida jinginuwa jikin garu Ta lumshe idanunta hawaye na gangaro mata. Umma da ‘yanuwanta kawai take tunawa tasan dole suna cikin damuwan rashinta. Jiki a matuk’ar sanyaye ta mik’e ta komo cikin gidan, ga wani irin yunwa dake azalzalanta.. Nan saman dining table d’in taga mug na tea, da alama dai shima a nan yaci karin kumallon nasa.. Ta tab’e baki kad’an kafin ta nufi hanyar da take tinanin kitchen zai kaita.. Aiko kitchen d’in ne wadatacce wanda shima aka k’awatasa da kayan alatu irin na zamani kana gani kaga gidan Amarya. Tai tsaye tana k’are ma kitchen d’in kallo sai kuma taji hawaye na k’ok’arin ciko idanunta, bata son tab’a duk wani abu da ya shafi wannan gidan amma batada wani zab’i cin abinci dole ne a wajen ko wane rayayye abin halitta.. Fridge ta bud’e tagansa shak’e da abubuwan buk’ata.. Ala dole ta had’a mai zata had’a dan ta saka a cikinta.. Saida ta koma d’aki ta d’auki sabbin abubuwan da takeda tabbacin shi ya aje su kafin tai brush ta fito taci sandwich d’in data had’a Wanda take jinsa kaman magani take taunawa. Zama tai ta rapka tagumi tana tinanin rayuwa da yanda yake zuwa mata.. Mahaifiyarta da ‘yanuwanta suna buk’atar ta bazataso taita zama a wannan kurkukun ba.. Zatayi k’ok’ari taga Ta bar wannan gida Ta koma ga ahalinsa as soon as possible. ** A b’angaren Mu’azzam kaw saida suka had’u da Assad ya basa update cewa basu iya gano masu lambobin da ake tura masa sak’o dasu ba.. Lambobin basa kan waya sannan ta iya yuwa ma mai turo sak’on ya karya SIM cards d’in yayi disposing d’insu. Nan yake sanar dashi tareda Maleeka sukai k’ok’arin gano mai lambobin amma basu samu ba. Mu’azzam ya d’an dubesa yace “Maleeka kuma.?” Assad ya jinjina kai yace “Kasan itace computer guru.” D’an Jim yai sai kuma ya jinjina kai ba tareda yace komai ba. Shiru ne ya gifta tsakani kafin Assad ya tambayesa Sadiya dan ko a daren jiya ya kira Mu’azzam d’in yaji hayaniya lokacin yana Passion Trust Super market yana mata sayayya a daren. Bai iya basa amsa ba sai cewa da yai zaijesa yaga Daddy yana jiransa akwai yanda zasuje. Assad ya jinjina kai kafin sukai sallama... Ya kula da gaba d’aya jikin Mu’azzam d’in a mace yake. Dukda bazaice ga abinda ke damun abokin nasa ba b’angare na zuciyarsa na raya masa mutuwan jikin Mu’azzam nada nasaba da shigowa rayuwarsa da Sadiya tai... A k’ofan parlor ya had’uda Daddy fitowarsa kenan, yana k’arasowa Daddy ya fad’ad’a murmushinsa sanda suke gaisawa. “Officer ka iso..” Daddy ya fad’i yana mai sab’a babbar rigarsa. “Eh Daddy Allah sa ban makara ba.” Daddy yace “A’a no baka makaraba.. Kace ma Adnan kar ya fito da Mota zakai driving d’inmu.” Mu’azzam ya jinjina kai cikeda risinawa yace “Alright Daddy..” Lokaci guda ya shige ya sanar da Adnan sak’on Daddy. Mu’azzam ya k’araso da motar tasa zuwa yanda Daddy ke tsaye. Daddy ya shige suka d’auki hanya. Ta saman bene Mommy ke hangosu.. Ta jinjina kai ita kad’ai tana tinanin toh Ina zasuje su biyu rak. Cikin tsanaki Mu’azzam ke driving Daddy ma basa direction har suka iso wani makeken gida mai babban gate. Aka bud’e masu gate masu tsaron k’ofa suna ma Daddy sannu da zuwa. Shidai Mu’azzam sai kallon gidan yake wanda yake kashi kashi flats da dama. Sai kuma ya soma ganin mutane nakasassu masu deficiency suna fitowa daga wasu ginin nan cikin building d’in, wasu da wheelchair wasu da crutches wasu ma kaman rarrafe suke.. Tunanin mahaifiyarsa ce ya fad’o masa sanda yaga wata mata saman wheelchair kanta a karkace kaman dai yanda mahaifiyarsa take saidai ita wannan matar tana iya motsa hannayenta. Mu’azzam yaji rauni ya cika zuciyarsa. Yana gani ma’aikatan wajen suna k’arasowa suna gaida Daddy wasu ma cikin nakasassun Sai tururwar zuwa gaida Daddy suke.. Take yaji wani irin nastuwa had’ida sanyi na ziyartar zuciyarsa.. Wani yaro mai karkataccen k’afafu ya k’araso yana janye Mu’azzam d’in.. A hankali ya duk’a yana shafa kan yaron murmushi saman fuskarsa. Da yawan yaran ko magana basu iya ba wasu kuma gwalamniya suke.. Duk yanda ka kai ga taurin zuciya idan kaga wad’ann bayin Allah dole kaji rauni ya ziyarci zuciyarka, ka kuma tina cewa kai d’an Adam ba komai bane, yanzu labarin rayuwarka zai iya canzawa.. Wad’ann mutane basuyi laifin komai ba ba wai kuma dan Allah yak’isu ba ya jarabcesu da irin wannan jarabawa. Sannan kaima ba wai dan yafi sonka bane ya baka cikakken lafiya.. Saidai dan ya jarabceka da lafiyar nan da ya baka yaga zaka gode masa ne ko zaka bijire ma rahamarsa. Muryar Daddy ya sinkayo yana fad’in “Mu’azzam my Son, this is where I invited your inheritance.. Ban Sani ba ko na maka katsalandan amma tin lokacin da na fahimci bakada interest akan tara dukiya da abin duniya sai nayi tinanin bud’e wannan cibiya na taimaka ma nakasassu, da nusar dasu cewa nakasa ba gazawa bace.. Ana koyar da yaran karatu wasu ma ana koya masu san’a sannan wanda dik ya k’ware a sana’arsa ana tallafa masa da kayan sana’a sai a sallame sa a kuma d’iban wasu.. Wannan Cibiya taimakon masu jarabawar nakasa take domin a rage yawan barace barace da nakasassun mu keyi saman kwalta wanda zaka samu wasu ma a garin wannan barace baracen sun rasa rayukansu, wasu an sace su anyi tsafi dasu wasu idan sun fita shikenan ba’a sake ganinsu..” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Ko wani budget na Company Naka kason nan yake zuwa..A halin yanzu kayi aure .. And very soon zaka fara tara iyali so ban Sani ba ko zaka ci gaba da tallafa ma wad’annan yaran, amma daga wannan lokaci kasonka a company zai ci gaba da tafiya asusun ajiyarka ne.. Idan kanada interst d’in ci gaba da taimaka masu falillahil hamdu idan kuma kanada wani tunanin in mind shima Alhamdulillah..” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Kai hak’uri idan nayi maka katsalandan..” Saurin girgiza kai Mu’azzam yai hawaye na ciko idanunsa. “Haba Daddy.. Mutumin da ya nema maka Aljannah kana gadon baccinka irin haka har zai nemi yafiya wajenka.. Daddy ni ya kamata nai maka godiya bisa wannan sadaukarwa da kai min.. Allah ya saka maka da gidan Aljannah Daddy. And wad’annan mutane masu jarabawar nakasa zasuci gaba da samun kulawa daga wajena in sha Allah da duk mai niyyan taimak masu. Allah yasa manyanmu a k’asar nan suyi koyi da irin wannan tinani da kayi Daddy.” Daddy ya murmusa yana mai kamo kafad’un Mu’azzam d’in suka nufi cikin building d’in yana saka ma Mu’azzam d’in Albarka. Har kusan azahar suna foundation d’in. Basu bar wajen ba har saida suka amshi list d’in kayan amfani da nakasassun bayin Allahn nan ke buk’ata musamman na sana’ar hannu da ake koyar dasu. A wannan ranan Mu’azzam ya kuma ganin girman Daddy da jin nauyinsa. Ya kuma yarda Daddy uba ne na K’warai a wajensa. ** Koda Sadiya tai wanka bata yarda ta tab’a kayan dake jere cikin wardrobe d’in ba dan tasan bazai wuce na matarsa bace. Tai tsuka a hankali tana furta “Yanzu ya zanyi..? What do I do now..!” Tai maganar cikeda shagwab’a kaman wani yana ganinta. D’aura hijab d’inta tai a k’irjinta ta nufi toilet da rigar nata tana fad’in “Zaka gani kayana zan wanke.. I’m not wearing your wife’s cloth Mr Inspector.!” Ta tab’e baki tana kwaikwayon maganarsa “You can use everything here free of charge.. Mtsww Mannerless.!” Ta k’arashe tana mai tura k’ofar bathroom d’in. Ta shiga ta wanke rigar ta fito ta nufi balcony tana bibbige rigar.. Sam bataji ko alamun shigowarsa ba balle rufe gate.. Tana nan tsaye wajen tana aikin bige rigarta. Shiko Mu’azzam koda ya shigo bai ganta parlor ba, tab’e bakinsa yai kad’an kafin ya nufi upstairs yasan ba lallai dama ta zauna a parlorn ba. Kai tsaye upstairs ya haye. Sautin buga abu da yake jiyowa daga d’akinta shi ya janyo hankalinsa. Yai tsaye yana duban k’ofan d’akin yana tinanin Toh meke faruwa da Ita. Lokaci guda ya yanke shawarin tura k’ofan d’akin.. Bai ganta cikin d’akin ba amma ga k’ofan balcony a bud’e. Lokaci guda ya nufi balcony d’in mamakin sautin k’aran buge abu da yake jiyowa bai bar saman fuskarsa ba. Da tsananin mamaki Mu’azzam ya tsaya yana duban Sadiya dake d’aure da Hijab tana buge jik’akk’en rigarta. “What.!” Ya furta da d’an k’arfi. A wani irin birkice ta juyo tana mai sakin k’ara dan bataji shigowarsa ba sai muryarsa. Ta shiga manna jik’akk’en rigar jikinta tana kare Jikinta dashi.. Cikin huci take furta “What are you doing here..?” “This is my house, and I don’t remember asking for your permission idan Ina son shiga ko Ina a cikin gida na.. Get ready we are going out..!” Ya fad’i yana mai juyawa. Kaman kuma wanda ya tina wani abu ya juyo yana dubanta k’asa k’asa musamman k’afafunta da take ta k’ok’arin d’ingilesu tana b’oyesu yace “And don’t think of wearing that thing you are holding.. wear something nice and decent..” Daga haka Sa kai ya fice ba tareda ya kuma cewa komai ba. Rausayar da idanunta tai tana mai rakasa da mugun kallo.. “Tyrant.!” Ta fad’i tana jan gajeren tsaki. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *26* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Rigar nata ta maida dikda cewa bai bushe ba, Allah ya gani bazata saka kayan da yace ta saka ba. Ta window take hangensa yana tsaye jikin motarsa waya mak’ale kunnensa. Tai tsuka a hankali tana tinanin ina zai kaita.. Allah yasa gajiya yai da zamanta a gidan, Allah yasa gida zai maidata wajen Ummanta. Wannan tinanin ne ya d’arsu a zuciyarta. Haka ta nufo waje sai rawan d’ari take dan harta hijab d’in ma da danshi jikinsa. Da mugun mamaki yake kallonta, ya rasa wane irin taurin kunne take dashi, watau dai baza’a fad’a mata abu tai ba. Katse wayar yai yana dubanta yanda take k’ok’arin k’arasowa bakinta a ture tana kallon k’asa. “Ke, Meye haka..?” Ya fad’i yana dubanta. “Mene kenan..?” Ta tambaya tana d’an dubansa itama fuska a dame. “Bance miki kar ki saka jik’akk’en kayan nan ba.. Do you want to fall sick.?” Tab’e baki tai kad’an tace “Idan ma nayi rashin lafiyar ai jikina ne..” Ya jinjina kai yana dubanta, a hankali ya furta “She’s so stubborn..” Ya d’ago yana dubanta kafin ya bud’e murya yace “And waye kike tinanin zai d’auki asaran saya miki magani.. Wuce kije ki canza kayan nan or else..” “No I won’t change.. Kayana kenan..!” Ta fad’i tana mak’e kafad’a still tana rawar sanyi dan a lokacin ma hadari ne a garin iska na kad’awa. Fuzar da huci yai kad’an kafin ya nufota, kafin ta ankara ya shiga janyo hannunta.. Tarjewa take tana fad’in “Malam ni ka sakeni.. Ni bazan saka wasu kaya ba bayan na jikina.. Bana so kuma bazan saka ba.” Bakinta bai mutu ba haka nan shima Mu’azzam bai fasa janyota ba har suka shigo cikin d’akin. Tana gani ya bud’e wardrobe ya ciro wata Doguwar riga abaya kalan shud’i. Ta soma matsawa da baya ganin yana nufota. Cikin rawar murya take furta “What are you doing.? Don’t come near me.. Dan Allah kayi hak’uri ka k’yaleni..” Ta k’arashe cikin rawar murya tana kuma matsawa baya. Fuzgota yai ta fad’o cikin jikinsa fuskokinsu suka had’e waje guda.. Jikinta sosai ya soma rawa.. Ta shiga k’ok’arin turasa amma Ta kasa.. Kafin ta ankara taji hannunsa saman zip d’in rigarta yana k’ok’arin zugewa.. Kuka Ta soma tana girgiza masa kai “Please don’t.. Please..!” Tai maganar tana mai rintse idanunta jikinta bai daina rawa ba. Mu’azzam kaw fuskarta yake duba musamman idanunta da ta rintse su da kuma bakinta da take motsawa a hankali tana rok’onsa ya k’yaleta. A ransa yace ga tsoro ga tsaurin ido. Jin ya tsaya Cak ya dena abinda yake ya sanyata tattaro sauran k’arfinta tai k’ok’arin turasa.. Aiko nan yai losing balance saidai bai yarda ya fad’a kan gadon shi kad’ai ba fuzgo hannunta yai suka fad’o gadon tare k’irajensu suka had’e waje guda. Su duka biyun suna iya jin bugun zuciyar junansu.. Jikin Sadiya yaci gaba da rawa hawaye na gangaro mata. Tai azaman mik’ewa amma sai taji ya rik’eta ya hanata tashi. Saitin kunnenta yake fad’i a hankali “Stop acting like you’re new in the system.. Like I told you everything here is free of charge.. Ba sai kin biya da jikinki ba.. I’m not interested.. Get dressed now.. And don’t make me wait..!” Daga haka mik’ewa yai ya fice ya nufo k’asa. Tai saurin tattaro rigarta ta tak’ure waje guda wasu hawayen na zubo mata. Har lokacin bata dawo daidai ba.. Rintse idanunta tai sosai tanaji kaman har lokacin cikin jikinsa take.. A hankali ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka wanke mata fuska. Ta Ware Doguwar rigar tana gani.. Ya zama dole ta bar wannan gidan, bazata iya ci gaba da zama ba, ba Karnuka ba ko kuraye ne zai sake mata zata gudu.. Bathroom ta koma ta d’auraye fuskarta ta goge da towel.. Dama sumarta tupke yake cikin ribbon. Ba don taso ba Ta zira rigar wanda yake daidai ita kaman an auna. Ta rufa mayafin rigar akanta tana duban kanta cikin mirror a nan toilet d’in.. Dikda bata shafa komai a fuskarta ba Ta fito tas Sady pretty d’inta saidai fuskarta da yake kaman Ta maras lafiya. Ta sadda idanunta k’asa kafin ta nufo k’ofa, nan taga takalmi flats mai kyau a bakin k’ofar da alama shi ya aje mata. Ta zira k’afafunta ciki a hankali kafin Ta nufo motar tasa. Tai tsaye kaman bazata shiga ba har lokaci idanunta na k’asa bata d’ago ta dubesa ba. “Ke shige mu tafi we don’t have the whole day..” Ya fad’i yana key ma motar. Bai tsaya biye mata ba ya mik’o hannunsa ya bud’e mata front seat.. Ta d’an d’ago ta saci dubansa amma sai taga idanunsa naga wayarsa ko kallon yanda take baiyi ba. Tai k’wafa cikin zuciyarta kafin Ta shige motar. Kaman wanda yake jira nan yaja motar suka fita daga gidan.. Ya sauk’o ya rufe gate d’in gidan kafin suka d’au hanya.. Suna tafe babu mai cewa komai. Addu’a kurum take cikin zuciyarta Allah yasa ya maidata gidansu.. Bata ida addu’an ba ta sinkayo muryarsa yana fad’in “A ina kuka had’u keda Sagir.. ? Allah yasa ba club bane ko Hotel dan ni banyi miki kama da mutumin da za’a gansa a irin wad’ann wajajen ba..” Ta dubesa da mamakin tambayar sai kuma ta girgiza kai tace “Wannan ba matsalarka bace koma a Ina muka had’u..” Jinjina kai yai yana duban kwalta “Baki so ki koma gidanku ashe..” Ya fad’i ba tareda ya dubeta ba. Jin abinda ya fad’i ya sanyata saurin fad’in “A park muka had’u..” Ya tambayeta sunan park d’in nan ta sanar dashi. Jinjina kansa yai a hankali yana mai maimaita sunan park d’in..Lokaci guda ya d’auki direction d’in da zai kaisu Park d’in data fad’i masa. Ta kuma sinkayo muryarsa yana fad’in “Kina jina.. We are on a mission.. If you mess everything up delay d’in komawarki gidanku zaki ci gaba da ja ma kanki.. We’ll go to the park, and we’ll act like a real couple.. Don’t mess up kinji abinda na fad’a miki koh.. Idan kika b’ata komai lokacin zama a GIDAN ARO kike k’ara ma kanki.. The sooner we are done with this mission, the sooner you get your freedom back. Did I make myself clear..?” Ya k’arashe yana dubanta da gefen ido. A hankali ta jinjina kanta har lokacin fuskarta a hard’e.. Suna tafe tana jinsa yana waya wanda dagaji da abokin aikinsa yake wayar.. Har suka isa Park d’in waya yake.. Saida sukazo yanda zai parking kafin taga yaja jikin Seat d’insa ya ciro bindiga.. Ganin bindiga da tai ya sanyata ta razana “Na shiga uku.. Mai zakayi da bindiga..?” Bai amsata ba yaci gaba da shirya bindigar kafin ya d’aga jacket d’insa ya mak’alata ciki.. Ya d’ago yana dubanta har lokacin a tsorace take “Don’t mess up na fad’a miki.. We will act like a real couple.. Kinji abinda na fad’a miki ko bakiji ba..?” Tai saurin jinjina kai alamun taji. Sauk’owa yai ya zagayo yanda take zaune ya bud’e mata.. Hannu ya mik’a mata alamun ta kama hannunsa ta fito.. Ta dubesa ta kuma dubi hannun nasa. Tsareta da idanu yai alamun ta rik’e hannunsa ta fito. Zuciyarta sai tsinkewa yake, tai k’ok’arin saita kanta kafin ta mik’o masa hannun nata ya rik’o yana mai sakar mata murmushi.. “My lady..!” Ya fad’i yana sakale hannunta tsakankanin arms d’insa da k’irjinsa. Lokaci guda ya d’an janyota cikin jikinsa da k’arfin gaske yai k’asa da kansa saitin kunnenta yana fad’in “Remember this is all acting.. So you better cooperate.!” Tai murmushin yak’e tana dubansa “Of course My Detective..!” Ta k’arashe tana d’aure fuska kaman ba itace mai fake smile d’in ba. Sunata wuce mutane a haka sai ka rantse wasu masoya ne.. Saman grass carpet suka k’arasa suka zauna gefen wasu furanni.. Nan wayarsa ta soma ringing.. Assad ne mai kira.. Lokaci guda ya mik’e yana mai amsa wayar idanunsa akan Sadiya. Daga d’aya b’angaren Assad yace “Kana nufin kaida Sadiya..? Toh mai kuke a park.?” “We’re on a mission..” Ya basa amsa kai tsaye. “Mission kuma.. Wane irin mission..?” Assad ya tambaya. “Dama da nace maka aurenta da nayi mission ne baka yarda bane.. Well yanzu sai ka yarda.. Abun shine itada Sagir a nan suka had’u so kaga definitely ta iya yuwa shida accomplices d’insa suna zuwa nan.. Idan har suna hunting d’inta zasu making move” Assad ya girgiza kai dan ya dena mamakin abokin nasa “You’ve got to be kidding me Mu’azzam.. What if she gets hurt.. What if suka mata wani abu bakada backup bakada komai..” Katsesa Muazzma yai da fad’in “They’ll have to pass through me before they lay a finger on her..! Kaidai kawai stay alerted zan iya neman backup daga wajenka.” Assad ya jinjina kai yace “Shieknan.. Be careful Mu’azzam.. Allah ya tsare.” Mu’azzam ya amsa da Ameen kafin sukai sallama.. Yana dubanta yanda take ta wasa ma wani yaro shida mamansa sunzo sun zauna a wajen. Yanata kallonta yanda take wasa ma yaron har dai suka mik’e zasu wuce shida mamansa yaron har waving yake mata itama tana masa kyakkyawan murmushi saman fuskarta.. Sosai Mu’azzam ya shagala da duban yanda take murmushi. Yana nan tsaye wayar Safeenah ya shigo masa.. Ya d’aga cikeda kulawa, saidai yana d’agawa da kuka Safeenah ta fara masa tana fad’in taji ciwo ya tafi ko sallama basuyi ba gashi nan taji ciwo kuma mai gyaran k’afan yace zata iya kaiwa sati guda kafin Ta fara taka k’afar.. Sai kukan shagwab’a Safeenah take masa.. Lallashinta ya soma idanunsa na kan Sadiya yana kuma matsowa kusan Sadiyar yanda zataji wayar da yake da matarsa. Abin ya mugun dad’i ma Safeenah ya kuma bata mamaki Wai Mu’azzam ne ke lallashinta irin haka ba tareda ya gwaleta ba ikon Allah.. Lallai ta yarda yanzu kam tana da matsayi mai girma cikin zuciyarsa.. Ta fara Mitan ita ta gaji Abuja take son dawowa su tattara su koma gidansu. Mu’azzam yace “I had to attend to some urgent matters ne shiyasa na dawo cikin gaggawa but Kar ki damu soon zamu koma.. I promise you kina dawowa zamu koma gidanmu.. But for now kiyi abinda mai gyaran yace kar azo a sami matsala..” Sadiya kaw d’auke kanta tai kaman bata a wajen.. Yanda kasan tafiyarsu ba d’aya bane haka tayi.. A ranta tana fad’in ita tausayin matar tasa ma take dan wllhi sam batai dacen miji ba. Wasu samari ne guda biyu suka dosota d’ayan yana wani fad’ad’a murmushinsa ya k’araso yanda take zaune “Miss Beautiful are you alone..?” Ya fad’i yana mai k’ok’arin duk’awa. Ai kafin yakai k’asa Mu’azzam yai ma Safeenah sallama a gurguje yana sanar da ita zai koma bakin aiki.. Lokaci guda ya k’araso yanda Sadiya ke zaune.. Ya sakalota cikin jikinsa yana fad’in “Sorry Wife na barki ke kad’ai..” Saurayin ya d’an sha jinin jikinsa ya mik’e yana basu hak’uri yana fad’in baisan matar aure bace. Mu’azzam baice komai ba Sai aika ma Sadiya mugun kallo da yake.. Suna shigewa ta cire jikinta daga nasa su duka biyun suna sakin huci “So abinda kika saba zuwa yi park kenan.. Dan kiyi new catch masu kud’i koh.. Kina wani zaune wancan d’aniskan yaron mai suma kaman na shed’an yana k’ok’arin zama kusa dake.. Kuma ko a jikinki koh.. Da kin bari ya zauna da na had’eku duka biyu na harbe..” Rausayar da idanunta tai cikeda k’osawa take k’ok’arin mik’ewa “Mr Inspector da alama babu wani abinda zaka samu a nan.. Kaga ruwa zai iya sauk’owa any moment.. Dan Allah ka maidani wajen Ummata tinda nayi abinda ka umarceni..” “Ank’i a maidake d’in..!” Ya fad’i yana tsareta da idanu dan zuciyarsa tafarfasa take tin lokacin da yaga samarin nan sun nufota. Fuzar da fuci tai kad’an kafin tasa kai kaman zata shige.. Saidai tuni taji ya janyota ta dawo da baya.. Hakan yai daidai da soma zuban ruwan sama.. Mu’azzam ya mak’aleta cikin jikinsa yana mai kallon yanda ruwa ke zubowa.. Dubansa take da idanunta da sukai rau rau hawaye gauraye da ruwa cikinsu.. Drops d’in ruwa saman fuskokinsu su duka biyu.. Wani mutumi ne mai tallan lema ya k’araso yana fad’in “Rankaidad’e saura d’aya ce ta rage ya kamata ka siya.. Kar Amarya tayi mura..” Mu’azzam ya dubi mutumi mai saida leman yace masa “Nawa ne..?” Mutumin ya fad’i masa kud’in leman.. Zaro kud’ad’en yai cikin pocket d’insa ya mik’a wa mutumin yana fad’in “Keep the change.” Mutumin ya masa godiya had’ida mik’a masa lemar.. Saida ya bud’e masu ma kafin ya mik’awa Mu’azzam d’in.. Lokaci guda ya kuma janyota cikin jikinsa sannan ya rufa masu lemar akansu.. Ta dubi hannunsa yanda ya rungumota ya rik’eta, zafin kalamansa akanta kurum take tunawa da wulak’ancin Sa take tunawa.. Lokaci guda taji wani irin k’arfi yazo mata.. Tai k’ok’arin turasa dashi da lemar tasa.. Saidai sam bai saketa ba saima dad’a matseta da yai.. Saitin kunnenta yake fad’i a hankali “Don’t get wrong ideas dik cikin acting ne..!” Lumshe idanunta tai hawaye na gangaro mata. Ganin tana rawar d’ari ya sanyasa zame jacket d’insa ya rufa mata.. Still saida ya sake tina mata cewa a cikin acting ne. Ruwan na k’aruwa dole suka nufi mota, ya bud’e ya shigar da ita.. Nan wani mutumi mai hoto ya tsallako a guje yana tare Mu’azzam d’in.. Envelope ya mik’o masa yana fad’in “Yallab’ai hoto aka maku d’azu kaida Madam baku Sani ba.. Yayi kyau sosai bud’e ka gani..” A hankali Mu’azzam yasa hannu ya amshi envelope d’in.. Lokaci guda ya soma zaro hoton kaman mai tsoron ganin hoton.. Fuskokinsu ya gani su duka biyun suna murmushi sanda yake ce mata ta nastu tayi acting d’inta da kyau idan tana son komawa gidansu.. Sunyi kyau sosai like a real couple.. Kud’in hoton ya zaro ya mik’a wa mutumin kafin ya saki tsaki a hankali ya tura hoton cikin aljihunsa.. Ya kaindubansa ga Sadiya dake zaune cikin Mota ta kifa kanta da alamun kuka take. Ya d’auke kansa yana sakin gajeren tsaki.. Lokaci guda ya shige cikin motar ya tada suka tafi.. Sam baiji dad’I ba dan babu wani abinda suka samu gameda Su Danger ko masu bibiyan Sadiya. Suna isowa gida tai shigewarta tana matsan k’walla. “My jacket.” Ya fad’i yana dubanta. Babu musu ta cire ta mik’a masa abunsa kafin tai shigewarta. Shima shigewar yai nasa d’akin dan yin wanka dan duk a jik’e suke. Yana cikin rage kayan jikinsa yaga hoton da akai masu a park.. Ya jima yana duban hoton, lokaci guda ya k’arasa dustbin zai disposing sai kuma ya tsaya kaman wanda ya tina wani abu.. Drawer ya janyo ya jefa hoton ciki kafin yai shigewarsa bathroom.. Yana fitowa daga wanka yaga kiran Assad na shigo masa. Daga d’aya b’angaren Assad ke sanar dashi Sun sami wani clue regarding the search for Danger.. “Are you serious Assad.. Did you find his whereabout..?” “No not really... But mun samu abinda zai iya leading namu to his hideout..” Assad yace yana juya flash drive d’in dake hannunsa. Lokaci guda yaci gaba da fad’in “I’ll tell you about the details idan muka had’u.. Yanzu dai ya kamata muyi aiki akaine.. Ina zamu had’u..?” “Let’s meet up here at my place..” Mu’azzam yace yana k’arasa shiryawa. Assad yace “Alright zamu taho tareda Yusuf dan d’aya location d’in shi yaje yai spying mana..” “Alright sai Kun k’araso..” Daga haka sallama sukai kafin ya ida shiri a gurguje ya fito ya nufi masallaci dan kiraye kirayen sallar magrib ake. Yana dawowa daga masallaci d’akinta ya nufa ya tadda Ta ida sallah kenan tana k’ok’arin linke darduman. Bata ko dubi yanda yake ba taci gaba da abinda take. “My friends are coming over tonight, kar ki damu ba masu kud’i bane balle kice zaki samu wani attajirin cikinsu.. ‘Yansanda ne irina masu fafutuka.. So karki kuskura ki sauk’o downstairs har sai Sun bar gidan nan...” Daga haka Sa kai yai ya juya ya fice a d’akin.. Ta girgiza kai ba tareda tace komai ba. Zama tai nan saman carpet tana tinanin abinyi.. Take taji ya kamata Ta karanta Alk’ur’ani dan zuciya da karatun alk’urani ne kawai take samun nastuwa.. A hankali cikin tsanaki ta soma rero karatun ta cikin suratu Maryam daka dan dama ta haddace suran. Bayan su Assad da Yusuf sun iso tuni sukai connecting na’urar aikinsu a nan parlorn gidan. Mu’azzam yai masu offering coffee da tea Assad yace “Tab Inaa wannan ai sai ku turawa.. ni wllhi yunwa nakeji.. Idan zan samu something solid I’ll be glad..” Bai kai aya ba Mu’azzam ya katsesa da fad’in “The kitchen is right there Sai ka shiga ka girka dan dai nikam k’asan ban iya girki ba.” “Toh matar gidan fah.. Haba Malam Officer gidan Amarya fah muka zo.. Ni wllhi kafin a fara aikin nan sai an bani abinci idan ba haka ba bazaku tab’a gane kaina ba..” Mu’azzam ya aika masa mugun kallo yasan da gangan Assad yai maganar nan kawai dan dai ya had’asa magana da yarinyar ne.. Car keys d’insa ya d’auka yana fad’in “Barin sayo maka a nearby eatery..” “A’a wllhi.. No gaskiya bazanci na restaurant ba na Amarya nake so idan kuma ba rowar abincin gidanka zaka mana ba.. Ko ya kace Yusuf..?” Ya k’arashe yana duban Yusuf wanda tinda suka fara tattaunawar murmushi kurum yake yana k’ok’arin connecting computer. Fuzar da huci yai kad’an yana aikama Assad mugun kallo “Damn you..!”Ya fad’i yana hayewa upstairs. “Oho dai naji koma menene..” Assad yace yana darawa kad’an. Mu’azzam na hayewa ya tadda karatu take. Ya d’an tsaya jikin k’ofa yana sauraronta. K’amshin nan nasa da taji ya tabbatar mata yana tsaye wajen. Ta dasa aya ma k’aratun nata kafin ta juyo a hankali. Cikin zuciyarta tai tsaki tace mutum kaman goyon maguzawa Sai ya ringa shiga waje babu sallama. “Abokaina suna jin yunwa.. I told them ba’a dafa abinci a gidan nan amma sunk’i amincewa.. Can you cook something simple for them..?” Jin bata amsasa ba ya sanyasa fad’in “Nasan kin San matsayin girman miji a wajen matarsa. So idan har kinada karatun addini kaman dai yanda naji kina karatun nan zakiyi abinda mijinki ya umarceki.. Idan kuma Bakiyi ba Kinsan mai hakan yake nufi.. And please do not embarrass me.” Daga haka ficewa yai ya barta nan zaune ba tareda ta tankasa ba. Watau yanzu kuma da Ubangijinta zai had’ata bayan ya gama mata barazana da mission. Taji wasu k’walla masu zafi suna zuwa mata... Tasha jin ana cewa ko Wanne gidan Aure da nasa k’alubalen wata nata dangin miji ne wata uwar miji ne nata k’alubalen wata kuwa shi mijin kansa ne k’alubalen kaman dai yanda nata ya kasance dikda kuwa Auren nata ba mai d’aurewa bane. Tina cewa da tai koda auren na d’an lokaci ne shid’in mijinta ne kuma umarni yake bata ya sanyata mik’ewa ba dan taso ba. Ta nufo wardrobe d’in tana duba mai zata rufa akanta.. Wani shud’in mayafi ta d’auko yalwatacce ta rufa akanta kafin ta nufo k’asa ta shige kitchen d’in.. Tana jin hayaniyar su shida abokan nasa har tana mamaki ashe dama ana jin muryar sa haka.. Wata zuciya tace ai indai bincike yake kam tsaf zakiji muryarsa.. Ta tab’e baki kad’an kafin Ta nufi kitchen d’in. Store ta soma dubawa taga store d’in shak’e da kayan abinci. Ga dangin su pasta da couscous.. Tai tinanin dafa masu abinci mai sauk’i kaman yanda yace. Couscous d’in ta d’auko ta dawo kitchen d’in ta bud’e fridge ta duba groceries nan taga gasu veggies sealed cikin leda irin yanda ake saidawa a super markets harda minced meat dasu sausage dik Suma sealed... Minced meat d’in ta d’auko kafin ta dafa white couscous tai garnishing d’insa da veggies sannan tai soma had’a masu sauce d’in minced meat d’in wanda za’aci white couscous d’in dashi.. Suna zaune parlor suna aikinsu k’amshi ke dakan k’ofofin hancinsu. Assad yace “Kai wannan k’amshi ai sai ya cika mana ciki kafin muci.. Gaskiya da alama Amarya ta iya girki..” Gajeren tsaki Mu’azzam yai ya kuma duban Yusuf dake k’ok’arin saka flash jikin computer yace “Ina sauraranka Yusuf go ahead.” Yusuf yaci gaba da fad’in “Kaman yanda na fad’a maku shi wannan footage d’in wajen security d’in da suke kula da restaurant d’in na samu bayan na shafe kwana biyu ina bincike ina tambaya people around the area ko sun tab’a ganin mai kama da Danger wajen.. Toh shine na samu har mutum uku suka ce Sun tab’a ganinsa sau kusan uku yana zuwa wannan restaurant d’in yana sayan abinci.. Da alama Danger yana son abincin wannan restaurant d’in.. Toh sai na tambayi CCTV Footage daga wajen securities bayan na sanar dasu matsayina da binciken da nake.. Bari mu gani gaba d’aya mu tabbatar..” Suka jinjina kai a tare sanda Yusuf ya soma playin videos d’in har kashi Uku wanda yake tabbatar da cewa Danger ne yake zuwa Restaurant d’in sayan abinci dikda yana saka rigar sanyi mai hood dan kar a ganesa. Sanda akazo daidai fuskar mutumin Mu’azzam yace “Stop. Yi zooming muga.” Yusuf yai kaman yanda yace d’in. Jinjina kai yai yace “It’s him.. Danger ne.. So Ta tabbata yana zuwa wannan restaurant d’in tinda har yaje sau uku..” Yusuf ya jinjina kai kafin Assad y ciro wani flash drive d’in yace “Wannan kuma wani super market ne da aka ga wani mai kama dashi once.. But nima I’m not sure idan shi d’in ne domin wannan kaman yafi Danger girman jiki saidai kuma idan camera ce ta k’ara masa girman jikin.. Footage d’in na k’ofar super market d’in ne wanda fuskarsa ta d’an fito amma is not that clear..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Saka mu gani..” Lokaci guda Assad ya saka ya soma playing.. “Wait.” Mu’azzam ya dakatar dashi yace masa yai zooming.. Lokaci guda ya k’ura ma lambar motar da mutumin zai shiga idanu a nan k’ofar super market d’in..Lambar motar tayi daidai da motar da aka basu bayanan cewa itace motar data buge Baban Sadiya. Mu’azzam ya shiga jinjina kai yana fad’in “That Scumbag.! Shi ne.. Shine ya kad’e Babanta.. Danger ne ya kad’e mahaifin Sadiya..!” Ya shafa sumarsa a hankali yana jin zuciyarsa na masa zogi.. Cikin sauri Yusuf ya shiga d’aukan plate number d’in motar dan suyi comparing da wancan... Assad yace “Yanzu ya tabbata Danger yana nan cikin garin nan yana hunting dik wani wanda yakeda alak’a da case d’in nan.. By all means yake so ya rufe bakin kowa.” Ya dubi Mu’azzam yace “Surely Danger will come after your wife..!” Mu’azzam ya jinjina kai yace “I’ll kill him if he attacks her..” Yai maganar yana murza hannunsa a hankali. “What’s plan now.?” Assad ya tambaya yana duban Mu’azzam d’in. Jinjina kai Mu’azzam yai kafin ya soma fad’in “Yanzu dole mu rabu muje wuraren da muke tsammanin Danger na zuwa. Kunga ni bazai yuwu na tafi aiki under NPF ba since I’m still on my suspension.. Naji ASUU sunyi calling off warning strike d’in da suka tafi.. So Sadiya zataje makaranta gobe.. Ni zan kaita dan nasan Maybe Danger yai tinanin attacking nata idan ta fita makaranta.. Kai kuma Assad kaje wannan Super market d’in.. Kai kuma Yusuf ka tafi wannan location d’in.. Restaurant d’in sai muga ina danger zai fara zuwa.. We should all stay alerted wanda dik ya soma ganin Danger cikinmu Sai muyi alerting juna mu nemi backup..” Gaba d’aya suka jinjina masa kai suna fad’in “Yes sir..!” Daidai nan Sadiya ta fito daga kitchen rik’eda plates ta nufi dining table.. Tin daga nesa Assad ke zolayarta ta cika masu ciki da k’amshi. Mu’azzam sai satan kallanta yake cikin zuciyarsa yana addu’an Allah yasa kar Ta basa kunya. Saidai ganinta da yai sanye da tufafin da ya zuba mata a wardrobe yasa hankalinsa d’an kwanciya. K’ila bazata basa kunya ba. Daga can yanda take tsaye ta d’an duk’a ta gaidasu Assad gajeren murmushi saman fuskarta jin yanda Assad ke Zolayarta ta cika masu ciki da k’amshi had’ida yi mata godiya. Ko duban yanda Mu’azzam ke zaune bataiba tai juyawarta kitchen ta kawo masu sauran abincin. Harda pineapple drink Ta had’a masu.. Sai dubanta yake cikeda mamaki. Ita kaw yi tai kaman batasan yana parlorn ba, tana gama jera komai tai hayewarta sama. Yabi bayanta da kallo har Ta b’ace ma ganinsa.. Muryar Assad da tuni ya nufi dining area ya soma bud’e warmers d’in shi ya dawo da hankalin Mu’azzam. Assad yai ma Yusuf tai baibi takan Mu’azzam ba. Suka soma cin abincin yayinda Mu’azzam ke ci gaba da duba footage d’in dikda kuwa sosai k’amshin ya cika masa ciki. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *27* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Haka su Assad sukaita santin abinci Mu’azzam bai tankasu ba. Sanda zasu tafi Assad harda cewa a kirawo Amarya suyi mata godiya. Mu’azzam ya aika masa mugun kallo yace “Congratulations for ruining my evening Detective Assad.!” Assad ya dara kad’an yace “Wait baka bani labari ba.. How did your mission go Inspector..? Ko da yake bari dai nai shiru, maybe everything is classified for now, but we’re not in a hurry. In due time zamu San komai..” Ya d’an kashe masa ido guda yana fad’i a hankali “Bari dai muga yaushe za’ayi accomplishing mission d’in.” Fuzar da huci kad’an Mu’azzam yai kafin yace “Get out before I blow your brains out.” Darawa ya kumayi kafin yace “Sai mun had’u goben.. At the meeting place.” Daga haka sallama sukai kafin Assad ya fito ya tadda Yusuf dake jiransa. Mu’azzam kaw yana dawowa cikin gidan tsayuwa yai a dining area yana duban saman table d’in lokaci guda yana tunanin maganganun Assad.. Gajeren tsaki yai yana shafa sumarsa a hankali.. Lokaci guda idanunsa suka kan clean plate da spoon d’in dake aje wajen. Wato harda plate d’insa ta kawo da cup.. Kenan harda shi tai serving abincin. Gajeren tsaki yai kafin yasa kai zai shige.. Sai kuma ya dawo da baya kaman wanda ya tina wani abu..A hankali ya shiga bud’e warmers d’in yana d’an tab’e baki kad’an.. A ido abincin wasn’t that bad. Ya jinjina kai a hankali kafin ya janyo kujera d’aya ya zauna.. Lokaci guda ya soma serving kansa abincin.. Ya zuba kad’an saman plate kafin ya janyo jug d’in ya zuba drink.. A hankali ya soma sipping drink d’in kaman mai tsoron kar yaji taste maras dad’i.. Saidai drink d’in na shiga bakinsa yaji wani irin taste mai dad’i ya gauraye cikin bakin nasa har yana lumshe ido.. Saida ya kusan shanye glass d’in kafin ya aje ya janyo plate d’in ya soma cin abincin. A hankali yake jinjina kai cikin zuciyarsa yana fad’in not bad. Wasa wasa saida ya cinye abincin tas, ya lumshe idanunsa yana tinanin yaushe rabon da ya k’oshi haka. Daga nan kitchen d’in ya nufa dan yaga wasu abubuwan girki ya kamata ya k’aro since she can cook like this. Ya shiga store yana dubawa. Sadiya kaw sam batasan yana kitchen d’in ba, Ita a nata tunanin ma ya fice tareda abokansa. Ta d’an lek’a parlorn kafin ta tab’e baki ta nufo dining table d’in tana tattare plates d’in da suka ci abincin.. Sam batasan Mu’azzam na cikin store d’in ba Ta aje plates kenan aka d’auke wuta a daidai lokacin shi kuma ya fito daga store.. Lalume ta soma tana neman hanya tana fad’in “Oh no I’m scared of the dark..!” saidai kaman daga sama taji ta fad’a jikin mutum.. A razane ta bud’e murya tana sakin razannan k’ara.. Ya janyota sosai cikin jikinsa tana kiciniyar k’wacewa lokaci guda ya rufe bakinta da hannunsa guda. “You scream over every little thing..!” Ya fad’i cikin sigan rad’a..Cizo ta gantsara masa a tafin hannunsa wanda ya sanyasa sakin bakin nata babu shiri.. “Malam ka sakeni na tafi..” Bai saketa ba Sai yarfe hannunsa data ciza yake. Daidai nan aka kawo wuta, hasken wutan lantarki dake kitchen d’in ya haske fuskokinsu. Fuskar nan tasa a tsime yana duban nata fuskar Wanda itama babu wani walwala saima sakin huci da take. Ya d’ago hannusa data ciza wanda har ya d’anyi ja yana nuna mata “Baki ciza banza zan rama kuma nasan a ina zan rama..” Ya k’arashe yana tallafota sosai.. Ta shiga turasa tana fad’in “What are you doing..? Just let me go.. Let go..” Batakai aya ba taji ya rufe bakinsa da nata. Ta zaro idanu k’irjinta na wani irin bugawa.. Jikinta ya d’auki rawa ganin bak’on al’amarin dake faruwa da ita.. Ta soma kiciniyar k’watan kanta amma ta kasa.. Batasan sanda hawaye suka soma gangarowa daga idanunta ba.. Saida ya tabbata ya razanata sosai kafin ya cire bakinsa daga nata.. Saitin kunnenta yake rad’a mata “W’ll continue with our mission tomorrow, ki shirya da wuri Kinsan ban son jira..” Daga haka ficewa yai ya barta nan tsaye tana goge bakinta da duka hannayenta biyu kaman wacce zata cire bakin nata. A guje ta nufi washing base ta bud’e famfo tana wanke bakinta still hawaye bai daina zuba mata ba.. A fili take furta “Allah ya isa mun mugu kawai..” Can k’arshen kitchen d’in Ta k’arasa ta durk’usa ta tak’ure waje guda hawaye na kuma gangaro mata. Yana haurawa sama tsaki ya dingayi yana tinanin irin maganganun da ake fad’I akanta, Allah kad’ai yasan yawan mazan da tai mu’amala dasu dan Ta sami kud’i da abin duniya.. Kai tsaye bathroom ya shige ya soma brushing bakinsa kaman zai cire bakin yanajin zuciyarsa na masa k’una. ** Koda Daddy ya koma gida babu yanda Mommy batai ba ya sanar da ita yanda sukaje shida Mu’azzam amma yak’i sanar da ita, abin sosai yake damunta.. Uwa uba rashin kwanan Mu’azzam a gidan, tana tsaka da tinanin Aunty Shemau Ta kirata. Taji yanayin Mommyn cikin damuwa nan Mommy take sanar da Ita abinda ke faruwa. Shamau tace “Nifa zaman Safeenah a nan ma duk bata taso ba, gashi nan Inne ta saka anata gyara section d’in dake gefenmu tana cewa a nan Fufore zasu tare.. Aunty Hajara idan har muka bari Mu’azzam ya zauna kusa da uwarsa akwai damuwa.. Ya kamata Safeenah Ta dawo gida Ta tare gidanta.” Mommy tace “Haka ne.. Nima nayi wannan tunanin.. Ni abinda nace ma kawai su Safeenah su tattara su dawo idan yaso sai ace wa Inne likitan gyaran K’ashi Safeenah zata gani a nan Abuja kuma visiting Dr ne daga k’asar waje ba ko yaushe ake samunsa ba.. Kinga idan so samu ne ma gobe gobe Ta dawo kawai ta tattara ta koma Gidanta.. Ni wllhi gantalin da take da aure bata tare ba ya soma damuna.. Ita ba matar aure ba ita ba bazawara ba.. Ni wasu lokutan Sai inke ganin anya ba abinda naima Nuratu bane yake bibiyata ta hanyar d’iyata Safeenah..?” Ta k’arashe cikeda tsoro. Aunty Shemau tace “Haba Aunty Hajara, ki daina damun kanki.. Karma ki saka wannan tinanin a ranki, Safeenah zata tare gidanta tsaf. Abinda kikace d’in kawai shi za’ayi.. Yanzu zan samu Uncle Salman da maganar, shi Sai ya samu jarabebbiyar uwarsu ya sanar da ita.. Gobe idan Allah ya kaimu sai muyi fitowar sassafe idan yaso Muasaddiq sai yai driving bama sai an tsaya ana jiran wani driver ba.. Sassafe zamu fito dik tsiya dai zuwa yamma mun iso.. Ni zan taho da dik wani kayan buk’ata na gyaran Amarya saidai kawai a shirya Safeenah a kaita d’akinta idan yaso tai jinyar nata a can..” Mommy Ta nusa tace “Shikenan ma kuwa.. Kai Shamau ni wllhi kin gama min komai.. Ko ciki guda muka fito iyakaci..” Aunty Shemau tace “Haba Aunty Hajara ai yima kaine.. Ki daina wani min godiya.. Kawai ki zuba idanu ki jira isowarmu gobe in sha Allah..” “Toh shikenan Shemau. Allah ya kaimu goben.” Shemau ta amsa da Ameen kafin sukai sallama. Daga nan ta shiga ta tadda Safeenah da Meema da batun. Meema kam hakan yafi mata dan dama ta gaji gida take san komawa. Safeenah ce dai tace sunyi waya da Mu’azzam kuma yace Ta bari har ta ida recovering zuwa next week. Aunty Shemau ta aika mata mugun kallo kafin tace “Ke kuma sai Kika biyeshi da shike bakida hankali koh.. Ke ko tinanin wani yanayi mijinki ka iya kasancewa ciki bakiyi..” Meema tace “Fad’a mata dai Aunty.. And wllh mijin nan nata Allah kad’ai yasan mai yake aikatawa.. Kinsan Daddy bai ganin laifinsa..” Aunty Shemau ta jinjina kai tace “Ahtoh kinji har ‘yaruwarki Ta fiki tinani.. Maza a wannan zamanin ba abin yarda bane.. Kana kaffa kaffa ma ya ka k’are balle ke da kike uwa duniya yana wata duniyar.. Taimakon ki ake idan kina san mijinki a hannunki idan kuma baso kike tin kafin ki tare aurenki ya k’are a titi ba..” “Gaya mata dai Aunty..” Meema tace tana mai chatting da wayarta “Nifa Aunty Shema I trust my husband completely, especially yanzu da muka fara fahimtar juna yake nuna min k’aunarsa.. Amma ni kaina nafi so na koma kusa dashi.. I’ll surprise him kawai saidai ya ganni..” Aunty Shema tace “Ahtoh Kema dai kya fad’i kina san kasancewa kusan mijinki.. Yanzu bari Muasaddiq ya shigo sai na sanar dashi ya fara shiri dan shi zai maidamu.. Idan Uncle d’in naku ya shigo sai na fad’a masa yanda mukaida Mommy shi zai sanar da Inne komai cewa Visiting Dr zai duba Safeenah dole mu tafi gobe gobe.. Sai ku shirya dan fitar sassafe zamuyi..” Meema tace “An gama Aunty..” Tuni Ta mik’e ta soma shiri Safeenah na fad’in ta kirawo mata Hindu ta shirya mata nata kayan. * Washe gari kaman yanda suka shirya komai hakance ta kasance. A b’angaren Musaddiq kuwa tinaninsa guda shine tafiya da zai ya bar Ajidde na kwana biyu. Yau d’in ba Uniform d’in ma’aikatan gidan Gona bane jikinsa, tsaf ya shirya cikin k’anan kaya, dark blue shirt mai d’aukeda k’atoton hoton Paris tower sai jeans, yayi kyau sosai dan zamansa a gidan gonar babu shaye shayen kayan maye har haske ya k’ara asalin color d’insa ya kuma fitowa jajayen idanunsa duk sun koma fafare yanzu. Safeenah ta dubesa tana fad’in “Ina kuma zaka. I thought we are leaving now..” iWatch d’in dake d’aure hannunsa na hagu ya kuma dubawa kafin yace “I need to see someone.. I’ll be back soon..” Cikin sauri ya fice.. Safeenah tana kiran sunansa ko amsata bai ba yai saurin shigewa. “Goshhh.! What kind of driver do we have.. Yau dai wnn tafiya Allah dai kawai ya kaimu lafiya..” Ta fad’i tana rausayar da idanunta. A daidai yanda suka saba tsayuwa ya tsaya yana jiran k’arasowarta. Can kuwa ya hangota tafe ta nufo yanda yake.. Tana tafe tana cilla jakan maganinta sama as usual. Wani irin wawan birki Ajidde taja ganin mutumi D’an gayu tsaye gabanta, gashi dai amma irin murmushin Kuran tashe yake mata. “Hey Crazy Dove..” Ya fad’i yana kuma sakin murmushi. Ta shiga mutsuke idanunta tana kuma dubansa “Wai kaine haka..? Toh ina kayan aikin Naka yau..?” Murmushi ya sakar mata kafin yace “Na d’auki hutu ne.. Zanje garinmu..” Sai kuma take ta daina murmushin da take idanunta taji suna k’ok’arin kawo ruwa. Ta girgiza masa kai a hankali kafin tace “Da gaske kake..?” Shid’inma sanyi yaji jikinsa yayi, a hankali ya jinjina mata kai “Yes.. Da gaske.. But kar ki damu ba jimawa zanyi ba, juts two weeks at most..” “Ni ban gane mai kake fad’i ba ka fad’a mun da gaske tafiya zakayi ka barni..?” Tai maganar siririn hawaye na gangaro mata daga idanu guda. D’an shafa sumarsa yai yana jin zuciyarsa na masa wani irin rauni, shi kansa bai San yayi sabo har irin haka da Ita ba.. K’ok’arin saita kansa yai Kafin yace “Sati biyu.. Bazan wuce sati biyu ba..” Ya d’an murmusa kad’an yace “Kin tuna nace miki bana alk’awari.. Amma yau zan miki alk’awari.. Bazan wuce sati biyu ba.. Kinji koh.. So you behave while I’m not here..” Izuwa lokacin kukan da Ajidde take rik’ewa ya fara fin k’arfinta “Kayi alk’awri zaka dawo gareni.. Dan Allah kar ka sab’a alk’awari..” Duk k’ok’arin Musaddiq yaga baiyi hawaye ba saida yaji hawayen na fita masa daga idanu guda, ya d’an matso kusanta kad’an yana sassauta murya “I promise you.. I’ll come back.. Zan dawo.” Murmushi ya d’an soma dikda hawaye dake zubo masa daga idanu guda yace “Kin manta bamu k’arasa abinda muka fara ba.. Bamu k’arasa bama Aunty Nuratu magani ba.. So definitely zan dawo.. Kimin alk’awari zaki ci gaba da abinda muke.. Zaki ci gaba da karb’owa Aunty Nuratu magani wajen Malama Hafsah sannan zaki ci gaba da zubar da maganin Kyallu..” Hawaye Ajidde take tana jinjina masa kai “Zan ci gaba, kuma na maka alk’awari bazan fasa ko d’aya ba..” Ya sakar mata murmushi kafin ya saka hannu a aljihunsa ya ciro kud’ad’e “Take this.. Dik randa Inna Kyallu tace ki sato mata kud’i Sai ki bata wannan kafin na dawo kinji koh..” Girgiza masa kai tai tana mai mak’e kafad’u alamun bazata karb’a ba. Musaddiq ya d’an sha mur yace “Look, idan baki karb’a ba zamu b’ata.. Nasan bazaki so na tafi Ina fushi ba.. So tun wuri ki karb’a..” Ya k’arashe yana mai janyo jakanta ya saka mata kud’ad’en ciki.. Gani taci gaba da kuka yasa Musaddiq cewa “Hey is not like I’ll be gone forever.. Zan dawo ai ki daina kuka kinji koh..” Shafa sumarsa yai kad’an dan yasan bazata daina kukan ba a yanda yasan halin Ajidde. Ji yai gaba d’aya ya kasa juran sauraren kukan nata. Ya saka tafukan hannayensa biyu ya shafa fuskarsa yana fuzar da fuci. “You take care Crazy Dove.. I’ll surely miss you.. Kina jina kar kiyi abinda zai saka ki a matsala idan bana nan kinji koh.. Zan wuce yanzu.. Till we meet again..” Ya k’arashe yana mata waving yana tafiya.. Cak Ajidde ta tsaya tana kallon yanda yake d’aga mata hannu kukanta na k’aruwa... Bata iya koda motsawa ba Sai duk’awa da tai wajen kukan na zuwa mata gadan gadan.. Haka rabi Misaddiq da kallo har ya b’ace ma ganinta. Shid’inma goge k’wallan da suka cika idanunsa yai had’ida saurin shigewa yana jin wani abu can k’asar zuciyarsa. A hanya ya had’u da Jume, Jume ya taresa da tambaya.. Nan Musaddiq ke sanar dashi sallama sukai da Ajidde.. Ya dubi Jume yace “Bansan na saba da yarinyar har haka ba.. Na zaci dariya da nishad’i kawai take sakani.. Amma yau da zamu rabu na d’an kwanaki sai naji kaman duka duniyar babu dad’i..” Jume ya murmusa yace “Sabo da dad’i amma idan za’ai rabo da zafi.. Kar ka damu abokina.. In sha Allah zakaje ka dawo ka sami Ajidde lafiya.. Allah dai ya nuna mana lokacin biki..” Musaddiq ya dubesa da mamaki yace “What.. Mai ka ce.. Haba Jume.. Ajidde k’aramar k’anwata na d’auketa so don’t get wrong ideas..” Jume ya jinjina kai yana murmusawa yace “Munsan irin wad’ann k’annen ai.. Allah dai ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya ya kuma dawo daku lafiya..” Musaddiq ya amsa da Ameen kafin suka k’arasa yanda sauran jama’an ke jiransu. Dama Musaddiq d’in kawai suke jira nan aka soma sallama da juna kafin suka shige Mota suka kamo hanya.. Mutan gidan na masu fatan sauk’a lafiya. Haka sukazo suka shige Ajidde tana duk’e wajen tana kuka, Musaddiq ne kurum ya kula da Ita, ko Ita kanta Ajidden ma batasan shine mai tuk’a motar ba dan har wnn lokacin bai sanar da ita shi jikan gidan bane.. Ta dai zaci ma’aikacin gidan ne kaman yanda ya sanar da ita. Ta mirror yake dubanta yana driving. Cikin zuciyarsa ya furta “I’ll miss you and your Crazy jokes.. My Crazy Dove..!” ** ABUJA Zama yai cikin Mota yana jiran sauk’owarta, waya yake da Assad yana sanar dashi yanzu zasu fita kenan. Daga d’aya b’angaren Assad yace “Mission continues kenan.” Gajeren tsaki Mu’azzam yai yace “Don’t you think is too early for this.. Kaga zamuyi magana.. Ka sanar dani idan Kun isa location..” Daga haka katse kiran yai yana mai d’ago kai nan ya hangota tana tahowa cikin doguwar rigar abaya kalan peach Wanda y dace da skin color d’inta. Ya tsareta da idanu yana dubanta har ta k’araso jikin motar.. Saurin kauda kansa yai ganin Ta d’ago fuskarta. A hankali ya mik’a hannunsa ya bud’e mata frontseat. Bata shiga ba sai mugun kalllon da take aika masa. “Get in..” Ya fad’i yana tsareta da ido. “Tell me first, ina zaka kaini.. I’m so tired of your games, you know..” Ta k’arashe cikeda tsiwa “Do you always talk this much.?” Ya fad’i cikin d’an d’aga Murya. “Only when I’m forced to..” Ta basa amsa kai tsaye tana mai kauda Kai gefe. Fuzar da huci yai kad’an kafin ya bud’e motar ya fito “Ko ki shiga ko na shigar dake da k’arfi..” Ya fad’i hannayensa saman belt d’insa. “Get in now..” Ya kuma fad’i yana mata alama da idonsa cewa ta shige motar. K’walla ne cikin idanunta amma sai tai k’ok’arin rik’e kukan nata ta shige motar. Lokaci guda ya zago ya shige suka fice. Suna tafe babu mai cewa k’ala saima duban samb’ala samb’ala hanyoyin cikin garin Abuja da take.. Inama taga ya kaita gidansu wajen Ummanta.. Tana tsaka da tinanin taga ya d’auki hanyar sch d’insu.. Ita kam bama tasan an janye yajin aikin da aka tafi ba. Ta dai yi shiru ta zubawa sarautar Allah idanu. Bata ida tinanin ba taji yana tambayarta course d’inta. “And why does it matter..? Ko dik cikin mission d’in Naka ne..?” Ta tambaya tana duban wani b’angaren. “Wani department kike..?” Ya sake tambaya ba tareda yabi takan wancan tambayar nata ba. Jin Ta masa shiru ya sanyasa kad’a kai yana fad’in “Seems like you’re enjoying zaman GIDAN ARO..” Jin abinda ya fad’I ya sanyata saurin cewa “Quantity Survey nake karantawa.. And first year nake.” Bai kuma bi takanta ba har saida suka isa yanda suke lectures.. Mutane kaw mak’il k’ofan department d’in nasu ciki harda ‘yan ajinsu. “Wait..” Ya fad’i yana mai ciro waya cikin aljihunsa. “Take this.” Yai maganar yana mik’a mata sabuwar waya gar k’irar Samsung. Rausayar da idanunta tai tace “No.. no need for it I guess, Mr Inspector.” Tai maganar tana k’ok’arin bud’e k’ofa. Saurin janyota yai cikin tsananin b’acin rai “Why are you so stubborn..?!” Yai maganar yana firfito da idanunsa waje cikin b’acin rai. “Take it now..” Ya fad’i yana mik’a mata. Baki a ture ta amsa ba tareda ta kuma dubansa ba. “Incase of emergency.. Don’t go anywhere idan ba tareda ni ba. Idan buk’atar hakan ya kama dole, ki kira lambar dake cikin wayar ki sanar dani... Kije ki zauna da ‘yan ajinku I’ll be waiting for you here.. I repeat don’t think of going anywhere without me.. Understood..?” A hankali ta jinjina masa kai.. Lokaci guda ya bud’e motar ya fito kafin ya zagayo ya bud’e mata. Zata shige ya tare gabanta had’ida bata light hug... Daidai saitin kunnenta yake rad’a mata “This is also part of our mission..” A hankali ta k’ak’aro fake smile ta sakar masa tana mai jinjina kai. Murmushin Shima ya sakar mata yana mai d’aga mata hannu “Take care wife..!” Ya fad’i yana d’aga mata yatsa guda had’ida kashe mata ido guda. Fuzar da huci tai tana mai rausayar da idanunta ba tareda tace komai ba. Lokaci guda Mu’azzam ya zaro shades d’insa ya rufe idanunsa dashi kafin ya zauna saman motar yana jiranta. ‘Yan matan dake zazzaune k’ofar wajen kuwa Sai awwn awwn suke masu dan sunyi bala’in burgesu yayinda wasu suka shagala da kallan mijin nata.. K’ananan maganganu na tashi musamman bayan rumor d’in abinda ya sami saurayin Sadiya Sagir ya isa masu wasu na gulman bata auri Baban Aminiyarta ba ta sami wani had’add’en matashi kuma daga gani He’s loaded . Da yawa cewa suke Lallai Sady Pretty nada sa’a. Yanda taga anata kallonta yasa dik ta tsargu, haka ta shige sukuku kaman ba Sady Pretty da idan tazo waje sai kowa ya sani ba.. Haka nan da yawa ma shakkun magana suke mata. Can ta hango Aminiyarta Sabeera zaune cikin lecture hall. Gabanta yai wani irin fad’uwa ganin irin kallon da Sabeerar ke mata.. Lokaci guda Sabeera ta wani d’auke kanta kaman bataga Sady ba. Cikin sanyin jiki Sady ta nufi cikin hall d’in wajen k’awarta. Sabeera tana Ganin Sady ta nufota ta mik’e zata fice.. Cikin sauri Sadiya ta k’arasa ta rik’o hannun Sabeerar. “Dan Allah ki tsaya muyi magana Sabeera..” A wulak’ance Sabeera ta juyo tana dubanta, lokaci guda tana duban sutiran dake jikinta had’ida wayar dake hannunta. Murmusawa tai tace “Your true color has finally showed up, dear friend.. Bansan ya akai van fahimci haka ba tuntuni.. Dik ja min kunne da ake akanki ban tab’a sauraronsu ba amma yanzu na yarda.. Kuma Ked’in da alama tsautsayi binki yake Sadiya..” “Shut up Sabeera..! You know perfectly well abinda kike fad’I ba haka bane...!” “No you shut up.. Kin mance saura k’iris ki auri mahaifina.. I’ll never forgive you for that Sadiya..” “But I didn’t marry him.. Did I.?” “Badon ‘Yantaddan da suke bibiyan ki ba da tuni kin zama matar Babana.. How dare you..? You have no idea wane irin tashin hankali muka shiga nida Mama.. Bakisan yanda Baba ya juya mana baya ba duk akanki.. Sadiya Kinsan irin k’uncin da kika saka ahalina ciki.. My parents almost got separated all because of you Sadiya.. How could you expect me to forgive a betrayal like you..!” Ta k’arashe cikin kuka su dukansu biyun kuka suke. “Sabeera hear me out first.. Kema kinsan idan ba dole ba bazan tab’a yin abu makamancin haka ba.. Kin sani Sabeera.. Please let’s talk this out first please..” Girgiza kai Sabeera tai tana hawaye tace “Na yaushe Sadiya.. Bayan duk abubuwan da suka faru Baba yace bazamu ci gaba da zama a garin nan ba.. Dutse zamu koma kuma da zaran mun koma zai sami wani cikin family ya aurar dani..” Sadiya taci gaba da hawaye tana girgiza kai. Lokaci guda Sabeera Ta jinjina kai tana murmushin da za’a kirasa da yak’e wanda yafi kuka ciwo.. “Kinfi kowa sanin yanda nake son karatuna Sadiya.. Yanzu shikenan bazanci gaba ba.. Dole na sato k’afa na fito domin nayi bankwana da karatuna na k’arshe.. Na tabbata mazajen zuri’ar mu basu bari matayensu suyi karatu.. But at least ke kin samu mai supporting d’inki.. Had’add’en miji mai sonki da k’aunarki wanda zai iya ajiye komai nasa ya biyoki har makaranta ya zauna ya jiraki.. Wacece ake mata haka Sadiya.. Da alama ke d’in kinada sa’a bayan duk abubuwan da kikai, mafarkin ki na auran mai kud’i ya tabbata, not only that he’s every girl’s dream..” Ta k’arashe maganar tana mata nuni da Mu’azzam dake zaune saman mota ya d’aura k’afarsa d’aya kan d’aya yana shafa waya. Sabeera taci gaba da furta “I don’t know ko zamu sake had’uwa ko bazamu sake ba.. But for now, ni Sabeera ina ce miki Goodbye..!” Ta k’arashe tana mai juyawa.. Cikin tsananin sanyin gwiwa Sadiya Ta silale ta zauna saman kujera.. Hawaye suka ci gaba da gangaro mata, cikin zuciyarta take furta “Allah sarki Sabeera bakisan abinda ke faruwa da rayuwata bane.. Baki San wane irin walak’antaccen aure nayi ba duk da bazaki fad’I haka ba.. A fili kuwa Fad’i take “Ki yafe min Sabeera.. I never wanted any of this to happen.. Ki yafe mun k’awata..” Ta k’arashe tana mai kifa kanta saman desk hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta. Mu’azzam dake zaune waje waya ya samu daga Assad, lokaci guda yace “Alright I’ll be on my way..” Yana katse kiran ya shiga kiran wayan Sadiya. Sadiya da kanta ke kife tana mance da wani waya saida taji ringing har cikin kanta da shike wayar na saman desk d’in ne. Tasan shi kad’ai ne zai kira tinda shi ya bata kuma bata saka lambar kowa ba sannan bata bama kowa ba. Batace komai ba koda ta d’aga, daga d’aya b’angaren yace “Zanje yanzu ana nemana.. Don’t step a foot out of that hall.. Ki zauna a nan ki jirani kinji koh..” Ya d’anyi fasali kafin ya k’ara jaddada mata “Kar ki fita ko k’ofa ne Sadiya.. You wait for me right there kinji koh..!” Daga haka katse kiran yai kafin ya shige Mota ya d’au hanya. Yana katse kiran Ta kuma fashewa da sabon kuka.. Ai kuwa koda ta tabbata ya fice a makarantar Mik’ewa tai tana goge hawayenta “Ka rabani da kowa nawa Mr Inspector.. This is the perfect opportunity for me to escape..!” Tana ida fad’in haka tai fitowarta itama lokaci guda ta nufi gate tana neman abin hawa.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *28* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A cikin Mota suka had’u da Sabeera, saidai cikin dukansu biyun babu wanda ya fahimci suna cikin motar har saida Sady Ta fad’i destination d’inta. Sabeera ta waigo suna duban juna, sai kuma ta kauda kanta ba tareda tace komai ba. A haka har suka iso unguwar tasu babu mai cewa k’ala.. Da shike waje guda suka sauk’a Sadiya Ta dubi mai motar tace “Malam dan Allah kai hak’uri lungun can kawai zan shiga na amso maka kud’inka.. Akasi aka samu ban fito da Jaka ba.” Mutumin ya dubeta ya girgiza kai yace “Hajiya Kinsan ba’a haka.. Ki biya kud’in ki kawai ki tafi..” Zata kuma magana Sabeera ta ciro kud’i ta bawa mai taxi d’in tace “Malam namu ne mu biyu, ‘Yaruwata ce tare muka saba tafiya dama..” Daga haka Sa kai tai zata shige. Sadiya ta dubeta murmushi saman fuskarta “Na gode..” Sabeeran batace mata komai ba sanda suka soma takowa daga nan bakin babban kwalta yanda aka ajesu. Sadiya ce ta soma fad’in “Ina fata wata rana ki sami gurbi a zuciyarki ki yafe mun Sabeera.. Nasan Kinsan maganan bashin Hajiya Tabawa dake kanmu wanda Baba yace zai biya mana amma saidai idan zan amince da aurensa.” Katseta Sabeera tai da fad’in “Basai kin maimaita ba na sani tinda har ya kiraki da Baby a gabana.” Sauk’e ajiyan zuciya Sadiya tai kafin taci gaba da fad’in “Ba auren jin dad’i nai ba Sabeera. Dan ni ko a labarai ban tab’a karo da labarin irin aurena ba.. Auren Mission nai.. Sannan a GIDAN ARO nake zaune gidanda sam ba nawa bane kuma ko wane lokaci za’a iya sallamata.. Mr Inspector ya aureni ne ba wai dan yana k’aunata ba Sabeera.. Da zaran ya ida mission d’insa zai sallameni daga rayuwarsa Wanda zanfi kowa Farin ciki da hakan..” Sai sannan Sabeera ta d’an dubeta da mamaki.. Sadiya ta murmusa Wanda yafi kuka ciwo taci gaba da fad’in “Sabeera amfani dani kawai yake domin ya cimma burinsa ya samu wani clue da zai had’asa da abokan ark’allan Sagir.. Yau da zai samu abinda yake nema zai rabu dani.. Amma idan bai samu ba haka zai Ta wahalar da rayuwata.. Kinji irin jarabawar da Sadiya ta sake samun kanta ciki..!” Ta k’arashe gajeriyar hawaye na gangarowa daga idanunta. Sabeeran ma hawaye ne ya gangaro mata amma Sai batace komai ba. Sadiya Ta k’ak’aro murmushi ta sakar mata daidai sanda suka iso layin gidansu Sabeeran dan dama sai an fara samun gidansu Sabeera dake sarari kafin a isa nasu Sadiya dake can k’asa. “Ki gaida Mama Sabeera.” Ta fad’i murya can k’asa. Juyowa Sabeeran tai ta dubeta kad’an kafin ta jinjina kai. Ba tareda tace komai ba ta shige hanyar gidansu. A hankali Sadiya Ta lumshe idanunta tana ji can k’asar zuciyarta bazata tab’a bari abinda ya faru ya lalata zumuncinsu da k’awancensu itada Sabeera ba.. Tare suka taso tin suna yara bata da wata k’awa bayan Sabeera.. Tasan Sabeera na k’aunarta deep inside, kawai dai zuciya ce da batada k’ashi amma da yardar Allah zasu koma kaman da. Da wannan tinanin ta nufi layin gidansu.. Zuciyarta fari k’al zataga Umma dasu Ashir da Habeeb. Saidai murmushin nata ne ya tsaya Cak sanda Ta hango Mr Inspector tareda abokan aikinsa ga mutane sunyi cincirindo a k’wanan lungunsu da alama bayanai suke d’auka. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa dan dama tinda ta fito daga makarantar gabanta ke tsananta fad’uwa kaman dai wani mugun abu zai faru da ita.. Saurin girgiza kai Ta soma kafin ta nufi lungun nasu cikin sauri.. Kaman ance ya d’ago kai nan ya hangota ta nufo lungun.. “Oh no..! What’s she doing here..?” ya furta yana k’ok’arin nufota.. Bai tsaya saurarenta ba ya shiga janyota yana fad’in “Mai ya fito dake..? Didn’t I tell to wait for me there.. What exactly is wrong with you.. Baki jin magana koh.. What if something happens to you..!” Cikin fad’a fad’a yake maganar. Girgiza kai take tana duban lungun nasu “I need to see my Mom and my brothers.. Bazaka hanani ba wannan karon Mr Inspector.!” Ya shafi goshinsa kad’an yana k’ok’arin rik’ota. Fuzgewa tai ta nufi lungun nasu a guje tana ambaton Ummanta.. “Damn it.! She can’t find out about this.!” Ya fad’i yana mai bin bayanta cikin sauri shima, lokaci guda yana kiran sunanta yana fad’in “Idan kika shiga gidan nan sabon mission zamu fara daga farko..! Just stay right there.!” Ko sauraronsa batai ba ta tura k’ofar gidan ta shige a guje tana kiran Umma.. Su Assad tsaiwa kawai sukai suna duban Sadiya da Mu’azzam d’in wanda yabi bayanta cikin sauri. “Umma gani nan na dawo. Ina kuke..? Ashir.. Habeeb.. Umma wai kuna ina..?” Tana maganar tana bud’e k’ofofin gidan Mu’azzam na biye da ita yana k’ok’arin dakatar da ita.. Cak ta tsaya sanda ta kula ga dukkan alamu babu kowa cikin gidan.. Babu Umma sannan babu Ashir da Habeeb. Cikin rarrabewar murya tana Ganin gidan na juya mata take fad’in “Umm..Umma.. Umm.. Habeeb.. Ashir... Ina kuke.. Umma wasan b’oyo kuke mun.. Dan Allah ku fito gani nan na dawo gareku.. Babu abinda zai sake rabamu.. Umma dan Allah ki amsa mun.. Kinji na rok’eki..” Kasa jura Mu’azzam yai ya shafi goshinsa a hankali kafin ya shiga janyo hannunta yana fad’in “Let’s go, we are going home now..!” Ya fad’i a tsare kaman yanda ya saba. Bama tasan mai ke faruwa ba.. Bata gane mai take ciki ba, batama lura da Mu’azzam dake janyota ba har saida suka fito waje.. Sannan ne ta soma tuna wai babu kowa cikin gidansu. Babu mahaifiyarta sannan babu k’annenta guda biyu... D’agowa tai tana duban Mu’azzam wanda zata iya cewa yau d’in Ta hango tsananin damuwa cikin tsimammen fuskar nan tasa.. Wani irin fincika tai daga rik’on da yai mata, ta soma jada baya ta nufi gidansu tana fad’in “No.. I’m not going anywhere with you.. Ina Mahaifiyata da ‘Yanuwana..? Tell me.. Ina suke..?!” Ta k’arashe cikin tsananin tashin hankali jikinta na wani irin rawa.. Mu’azzam ya shafi kansa a hankali kafin ya k’araso ya kuma kamota “Shige muje nace..!” Fincika tai tana huci take dubansa “Nace maka bazanje ba..! Ina Umma ta Ina Habeeb ina Asheer.. Ina suke.. Ka fada’a mun Ina suke.. Just tell me.. Tell me now ina suke..?” “I don’t know..!! Ki wuce mu tafi nace miki.. Let me remind you, you still owe me.. You are still on your mission.. You must finish your assignment and help me catch Sagir’s accomplices.. Kin fahimta.!” Yai maganar cikin daka tsawa. Shaye da tsananin mamaki take dubansa, bataga mahaifiyarta da ‘yanuwanta ba but he stills talk about his stupid mission. Girgiza kai take wasu irin hawaye masu k’una na zubo mata cikin rashin yarda “My Mother and my two little brothers are gone missing.. Yet you still have the audacity to talk about your so called mission..!” Taci gaba da girgiza kai hawaye na zubo mata “You are so Selfish..You are so mean Mr Inspector..!” Daga haka gidan ta kuma komawa a guje tana kirawo Umma da ‘yanuwanta. A guje shima ya bita ya fincikota “You will not find them here..Bazaki samesu a nan ba.. Just let the police do their Job..!” Cikin tsananin k’unan rai yake maganar. Wannan karon da rinannun idanunta take dubansa “Damn the police..!” Ta fad’i tana dukan k’irjinsa.. Lokaci guda taci gaba da kai masa duka a k’irji da duka hannayenta biyu tana ci gaba da fad’in “This is all your fault..! Dik laifinka ne.. Laifinka ne na rasa kowa nawa..! Na tsaneka..! Na tsaneka.. I hate you l..! I hate you..!!” Dikda zafin kalamanta da yake ji hakan bai hanasa kame duka hannayenta biyu da take dukansa dasu ba, lokaci guda ya rungumota ya kwantar da ita saman k’irjinsa, ya matseta sosai yanda zai iya hanata bige bige. Lokaci guda yake furta “I’ll find them..! I promise you I’ll find them..!” Yana jinjina kai still tana cikin k’irjinsa crying her heart out yake ci gaba da fad’in “Zan samo Su ko Ina suke..!” Ya k’arashe yana d’aura hab’arsa kad’an saman kanta. Kuka take kaman ranta zai fice ba tareda tana iya fahimtar komai ba.. A haka ya rik’ota suka nufo waje yanda su Assad ke tsaye suna jiransu. Mu’azzam ya dubi su Assad da jikkunansu gaba d’aya yai sanyi yace “Take care of things here.. I’ll take her home..” Assad ya jinjina kai yace “Sure Inspector..” Bata sake sanin meke wakana ba, bata sake sanin meke faruwa ba.. Farkawa tai kurum ta ganta a d’aki a kwance.. Ta mik’e cikin sauri tana jin kanta na wane irin sara mata.. Dikda rawar d’ari da jikinta keyi hakan bai hanata k’ok’arin fitowa daga d’akin ba ta nufo k’asa. Saidai tana fitowa ta hangesa a kitchen, yana sanye cikin armless shirt ruwan shud’i da bak’i irin kakin da police ke sakawa sai bak’in 3quater.. Ya bada baya da alama aiki yake kitchen d’in.. Cikin sand’a ta soma takawa a hankali da zummar guduwa.. Saidai tana tab’a k’ofar Parlorn ta jita a kulle.. Ta kuma ja da k’arfi taji bata bud’e ba.. Nan Ta shiga dage k’arfinta tana jan k’ofar kaman zata b’alla. “Let me out please..! Dan Allah ka k’yaleni na tafi.. I need to find my Mom and my brothers.. Dan Allah ka k’yaleni.. Na rok’eka..!” Ta k’arashe sabon kuka na kufce mata tana mai juyowa. Ido hud’u sukai dashi yana tsaye bayanta rik’e da plate noodles ne cikin plate d’in. “Kinaso ki tafi..?” Ya tambaya yana dubanta. Cikin sauri ta shiga jinjina masa kai tana hawaye. Ya jinjina kai a hankali kafin yace “Come here.” Yai maganar yana mik’a mata d’aya hannun nasa. Ta girgiza masa kai alamun a’a tana mai ci gaba da hawaye. Ya fuzar da huci kad’an kafin yace “Idan kinaso na barki ki tafi zakiyi duk abinda nace.. Kinji koh..” Ta d’ago tana dubansa, sai taji wani kukan na zuwa mata gadan gadan.. Cikin muryar kuka take furta “Umma.. Ashir.. Habeeb.. They need me.. I need to find them.. Dan Allah ka barni na tafi yanzu..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka. K’arasowa kusanta yai kafin ya kamota yace “I know.. But idan na barki kika fita haka bazaki iya komai ba.. You’ll collapse. You need to gain your strength idan kinaso ki samu energy d’in nemansu.. Come with me now..” Ya k’arashe yana janyota cikin jikinsa. Lokaci guda taji wane irin rauni gauraye da tausayin kanta cikin zuciyarta. Rik’eta yai b’angaren jikinsa guda yayinda d’aya hannun nasa ke rik’eda plate na noodle d’in. A haka suka nufi upstairs tana binsa kaman rak’umi da akala. Suna shigowa d’aki ya zaunarta bakin gado kafin ya aje plate d’in gefen bedside. Kamo hannunta ya kuma suka nufi bathroom. Ya k’arasa wash bowl ya d’auki toothbrush d’inta ya wanke ya zuba mata toothpaste akai.. Lokaci guda ya soma k’ok’arin wanke mata bakin. Saidai bata bari yakai ga hakan ba ta tsaresa da fad’in “I can do it myself.!” Fuzar da huci yai yana mai kauda Kai gefe “Fine, do it then.” Ya fad’i a d’an hasale shima yana damk’a mata brush d’in cikin hannunta. Ta aika masa mugun kallo kafin tace “I need some privacy.!” Ba tareda ya dubeta ba ya fuzar da huci kad’an yana mai ficewa daga ciki bathroom d’in. Yana fita ta wanke bakinta kafin ta soma lek’e lek’e ta ina zata iya gudu saidai babu wani hanya da zata iya tserewa. Silalewa tai nan cikin bathroom d’in tana hawaye tana tina Ummanta da ‘yanuwanta. Ganin ta jima bata fito ba yasa Mu’azzam matsowa bakin k’ofan bathroom d’in ya kasa kunnuwansa yana tinanin ko tayi collapsing cikin bathroom d’in ne.. Ya d’an saka yatsarsa guda ya k’wank’wasa “Kina lafiya..? Or should I come in..?” Cikin sauri ta shiga share hawayenta tana fad’in “I’m almost done..” Ta mik’e tana d’auraye fuskarta da ruwa. Tsaki take cikin zuciyarta tana mamakin Wai duk jimawan nan da tai bai fice ba ashe, yana cikin d’akin yana jiranta. Tana fitowa ta gansa tsaye gefen k’ofar bathroom d’in ya d’an jinginu jikin garu had’ida d’ingile k’afarsa guda alamun fitowarta yake jira. Kallo guda tai masa ta d’auke kai. Shid’inma gajeren tsaki yai yace “Ke Zo ki zauna..” Ya fad’i yana mai k’arasawa had’ida d’aukan plate d’in noodle d’in.. Yai mata alama da ido kan ta k’araso ta zauna saman gadon. Ba don taso ba ta k’araso ta zauna nan yanda yace ta zauna d’in. “Eat up now..” Ya fad’i yana d’ebo abincin cikin fork ya mik’o mata saitin bakinta. Mak’e masa kafad’a tai alamun “A’a.. Ka kaini wajen ahalina na rok’eka.. Suna buk’atata..!” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya. “Zan kaiki amma sai kin cinye abincin nan.. You haven’t eaten anything since morning.. Kinga time kuwa yanzu..?” Ya k’arashe yana nuna mata smart watch d’in dake d’aure hannunsa na hagu. Kauda kanta gefe tai tana jin wani kukan gauraye da tashin hankali na zuwa mata. Mu’azzam yai gyaran murya yace “Police are doing all they can to locate them.. Na miki alk’awari zamu samesu.. Nasan baki yarda dani ba.. But please I want you to trust me on this..” Ya k’arashe yana tsareta da idanunsa. Bazatace ta yarda dashi ba amma ta samu kanta tana mai sadda idanunta k’asa ba tareda taci gaba da duban cikin fuskarsa ba. Ya kuma mik’o mata abincin lokaci guda yake furta “I cook for the very first time in my entire life. I hope you won’t disappoint me.. Zakici abincin nan koda babu dad’i.. Open your mouth now..” Ta d’ago ta d’an dubesa yana mata alama da kansa irin yanda ake ma yara idan basu da lafiya ana so suci abinci.. Gaba d’aya ita gani take ma being nice doesn’t suit him at all gwara ma yaci gaba da zama tyrant d’insa.. Bata iya kauda kan nata ba wannan karon dan Ta kula bazai k’yaleta ba har sai taci d’in.. A hankali ta bud’e bakinta ya saka mata abincin ciki. Saida tai spoon uku a na bud’u ta kauda kanta gefe alamun ta k’oshi. “Last spoon.!” Ya fad’i yana tsimewa wannan karon. Fuzar da huci tai kafin Ta furta a hankali “I’m ok..” “No you are not.” Ya katse da fad’in haka, kafin yaci gaba da fad’in “Idan baki ci wannan na k’arshen ba bazan kaiki ba..” Jin abinda yace ya sanyata bud’e baki a hankali ya saka mata. Lokaci guda taga ya ciro magani pcm ya d’auki bottle water d’in dake gefe ya mik’a mata yace tasha. Zata masa gardama taga ya tsareta da wad’ann idanun nasa. Ta kauda kanta gefe tana amsan ruwan da maganin.. Saida ya tabbata tasha kafin ya mik’e zai fice.. Tai saurin bin bayansa tana fad’in “Nayi duk abinda kace.. Yanzu sai ka barni na tafi please..!” Tsareta yai da idanu yana dubanta, kafin ya murmusa kad’an yace “And what makes you think zan barki ki tafi..? Ya d’an jnjina kai yana dubanta lokaci guda ya had’e rai yaci gaba da furta “Bayan juran duka tsaurin idonki na ‘Yan tasha da kika saba. Mu’azzam Gamji cooks for the very first time in his life.. He feeds a low life like you with his hand.. Bayan mahaifiyarsa bai tab’a ciyar da wata mace da hannayensa ba.. Kina tunanin mission mai sauk’i kikeyi da zai jure ya miki Duka wad’ann abubuwan..?” Ya jinjina kai kafin yaci gaba da fad’in “Nayi duka wad’ann ne don na tabbata kin tsaya cikin k’oshin lafiya har dai na ida mission d’ina... Idan kina mafarkin zan barki ki tafi ba tareda nayi accomplishing mission d’ina ba you’re so mistaken.. You are staying right here until the mission is finally accomplished..!” Yana ida fad’in haka ya fice ya janyo k’ofar. Girgiza kai take tana furta “No please.. Dan Allah kayi hak’uri..!” Ta k’araso a guje tana tura k’ofar amma ta kasa.. Kuka Ta soma tana rok’onsa ya bud’e mata Ta fice amma a banza.. Ta nufo balcony a guje tana k’ok’arin tura k’ofar amma saidai shima a rufe ta jisa.. Cikin sanyin jiki ta dawo da baya Ta zube nan saman gadon tana kuka mai tab’a zuciya.. Tinawa da tai ko sallar azahar da la’asar da tuni an soma kiraye kiraye batai ba ya sanyata Saurin mik’ewa ta nufi bathroom d’in da zummar d’auro alwala tana hawaye. Nan tazo ta tada sallah ta soma kai kukanta ga Sarkin da Babu kamansa. ** Kasancewar isowar yamma lis sukai yasa Aunty Shema basu nufi gidan Safeenar da niyyan gyare gyare da kakkab’e k’ura ba. Dan dama tace da zaran Sun iso a yau d’in zasu d’iba ma’aikata aje a share gidan a gyara tas. Mommy ma tace su bari kawai gobe idan Allah yakai rai da safe sai suje su gyara gidan idan yaso zuwa yamma sai akai Safeenah. Hakan kaw akai basu je gidan a ranan ba saima bada hankali da ‘yan gyare gyare da ake ma Safeenar wanda Aunty Shema’u tai tsayin daka tana fad’in sai Safeenah ta rikita angonta. Safeenah kaw jin hakan sosai yai mata dad’i.. Mommy ma taji dad’in hakan sanin irin abubuwan da d’iyarta tai kafin aure idan mijinta ya tunk’areta a haka sunada babban matsala. (Su Mommy kenan, sun mance ba’ayi ma Allah wayo.. Maganin bari dai shine kar a fara.. Allah ka tsaremu daga fad’awa aikin danasani.. Ameen) Safeenah Amarya Dikda ciwon dake k’afarta dan da crutches ma take tafiyar hakan bai hanata zumud’in shirye shiryen tafiya gidan mijin nata ba. Meema Ta dubeta tace “Waini Addah Feenah ina Ya Mu’azzam ne.. Tinda muka dawo ko ganin k’yallin motarsa banyi ba balle nayi tunanin ganinsa cikin gidan nan..? Toh kodai baisan kin dawo bane.?” Safeenah ta murmusa tana kuma kurb’an tsimin da Aunty Shemau Ta tilasta mata shanyesa tas a daren tace “I want to surprise him.. Kema Kinsan yanayin aikinsa k’ila sai dare ki gansa ya dawo.. I’ll wait for him in his room saidai kawai ya shigo ya ganni.” Ta wani k’arashe tana girgiza k’afarta mai lafiyar. Meema Ta tab’e baki kad’an tace “Toh amma idan kika taresa a d’akinsa ya b’ata miki shirin da akai na tafiya gidanki fah.. Ko so kike komai ya faru a nan gidan tin ba’aje gidan naki ba..?” Harara Ta aikawa Meema kafin tace “Na sake miki da yawa Meema.. Yaushe har muka fara irin wannan tad’in dake..?” Meema tace “Ahap na yaushe kuma Adda Feenah.. Ai bakida aminiyar da ta wuceni dan haka dole nasan komai..” Ta k’arashe tana kashe mata ido guda. Suka tintsire da dariya a tare Safeenah na fad’in “Of course my sister is my sidekick.. Zanyi missing shishiginki da gulmarki Meema.. Daga gobe I won’t be living here anymore..! Come here give your sister a hug..” Ta k’arashe tana turo baki gaba kaman zatai kuka. Cikin sauri Meema ma ta k’arasa ta rungumeta tana fad’in “I’ll miss you too Addah Feenah.. And this your Savage Husband shi zai ke hanani zuwa gidanki.” Safeenah ta dara kad’an tace “And I love him just like that.” “I know..!” Meema tace tana d’an tab’e baki. Lokaci guda Ta k’arada “And I hope he doesn’t surprise you instead..!” Daidai lokacin glass cup d’in dake hannun Safeenah ya fad’I k’asa ya tarwatse tsimin dake ciki ya zube. Jin abinda Meema ke fad’i mata. Meema ta zaro ido waje tana kame baki “Oh no.! This is a sign Addah Feenah... It’s a bad omen..! Something terrible is going to happen..!” Tai maganar tana kuma firfito da idanu waje cikin k’ok’arin razana Safeenar. Jifa mata pillow Safeenah tai tana fad’in “Shame on you Meema.. Fice min a d’aki I need positive vibes..” Ta k’arashe tana k’ok’arin kwad’a mata Sandar crutches d’in nata.. Meema ta fice tana dariya lokaci guda take furta “I’ll miss you Addah Feenah.. I love you..” Daga nan yanda Feenah ke zaune take fad’i da k’arfi itama “And I hate you little sis.. Ki turo wata cikin maids d’in nan Ta gyara nan..” ** Har safiya Safeenah bataga Mu’azzam a gidan ba.. Mamaki ya cikata, nan Ta yanke shawarin tambayar Mommy dan ko jiya da daren Ta kirasa yafi abinda yafi amma bai d’aga ba.. Ta fara tinanin ko wani abu ne ya faru dashi sanin irin had’arin dake tattareda aikinsa. Saidai tana k’ok’arin shiga d’akin Mommy Ta soma sinkayo tattaunawar Mommyn da Aunty Shemau. Cak Safeenah Ta tsaya tana jin Wai tinda Mu’azzam ya dawo bai kwana a gidan.. Idan ba sharholiyarsa yake waje ba mai zaike hanasa kwanan gida matarsa bata gari.. Sau d’aya ma suka had’u da Mommyn. Zuciyarta ne yai wani irin yankewa amma sai ta bawa kanta k’warin gwiwa da cewa aikinsa aikin Al’umma ne zai iya kasancewa a ko Ina any moment. Mijinta bazai tab’a cutar da ita ba.. Mata basu gabansa, sannan shima baida lokacinsu.. Bazata saka ma zuciyarta wannan damuwar ba musamman yanzu da ta samu Mu’azzam yake nuna damuwarsa akanta. Da wannan tinanin ta juyo ba tareda ta shige d’akin Mommy ba. Saidai gaba d’aya jikinta a mace ne.. B’angare mafi girma cikin zuciyarta yafi karkata ga zancen da taji Mommy nayi.. Take taji zuciyarta na son amincewa Mu’azzam ha’intarta yake. Da gaske sharholiyarsa yake a nan.. Toh amma tambayar da su waye yake sharholiyar tasa..? Take taji zuciyarta na bata amsa da matan banza mana.. Ji tai kaman sandar taimak ma tafiyar nata ya gaza d’auakrta. Tana tafe kaman mutum mutumi K’annenta Meema da Kiki dake haurowa saman suka hangota, Kiki sanye da sch uniform d’inta da safiyace da alama makaranta zata.. Meema kuma sanye da tracksuit da alama morning exercise ta fito. Sukai carko carko suna dubanta. Meema tai saurin zare earpiece d’in dake mak’ale kunnenta Ta k’araso Ta dafata tana fad’in “Addah Feenah lafiya..?” SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *30* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Musaddiq ya girgiza kai kurum kafin ya fice daga parlorn gaba d’aya. Meema dake Ta faman sosa fuskarta yanda Musaddiq ya mareta satan kallan Mu’azzam tai Ai kaw nan taga kaman jefo mata razannan kallon nan nasa babu shiri ta nemi hanyar ficewa daga parlorn itama. Gani take kaman daga kanta zai fara tinda ita ta kawo rahoton. Batama San ko kallon yanda take baiba balle yasan tana parlorn. Tsaban tsoro ne da imagination d’inta suka nuna mata hakan. Safeenah Sai kokawan k’wacewa daga rik’on da Aunty Shemau tai mata take “Daddy Mommy kuce ya fice bana son ganinsa.. I don’t want to see him.!” “Ki rufe wa mutane baki ki natsu ki daina haukar nan..!” Daddy ya katseta da fad’in haka. Lokaci guda Mu’azzam d’in ke k’ok’arin gaida Daddy kafin ya juyo yana duban Mommy “Mommy Ina kwana..” Mommy baki sake take dubansa bayan d’aga masu hankali da yai har yanda guts d’in dubansu yace masu ina kwana. “Da ban kwana ba ai bazaka ganni ba mugu kawai azzalumi macuci maci amana.. Kaji kunya Mu’azzam Bayan duk abinda naiwa mahaifiyarka a rayuwa, na d’auketa ‘yaruwa na kwashe shekaru ina mata jinya abinda zaka saka mun dashi kenan.. Ka rasa mai zakaiwa d’iyata sai ka dinga d’auko Karuwai kana kaiwa Gidan aurenta gidan da ko tarewa cikinsa batai ba.. Wllhi kaji kunya Mu’azzam.. Tirr.!” “Mommy I don’t know what you’re talking about.. Ni ban kai wata Karuwa ko ina ba..” Ya fad’i cikin dakewar Murya. Baki sake Su Mommy dasu Safeenah suke dubansa. Wai bai kai Karuwa ko ina ba.. Tsaban shi tacecce ne maimakon ya bada hak’uri ya amshi laifinsa denying ma yake hankalinsa kwance. A hasale Mommy ta mik’e tana fad’in “Kai bari kaji na fad’a maka ba tsoronka fa ake ba.. Ka bar ganin kana dik abinda kaga dama ana d’auke ido..” “Hajara ya isa haka..!” Daddy ya katseta cikin tsananin b’acin rai.. Da mamaki take duban Daddy kafin ta ci gaba da jinjina kai tana fad’in “Dama na sani bayansa zaka bi.. Ya cutar da d’iyarmu ya Zalinceta amma kana bin bayansa..!” “Nace kimin shiru Hajara.. Ta yanda kika b’ullo bata nan za’a gyara al’amarin ba..!” Safeenah dake kuka Ta bud’e murya tace “Daddy are you really taking his side..? Daddy karuwa fah Karuwa ya kai mun gida tun kafin na tare..!” Wannan karon Mu’azzam ne ya mik’e a zuciye yana nuna Safeenah da yatsa “Don’t you ever call her Karuwa again..!” Mommy ta soma salati tana tafe hannaye tana duban Daddy “Ka gani ko.. Ka gani da idonka.. Ya nuna mana shi tabattacene.. Goyon bayan Karuwa yake akan matarsa.” Ya juyo ya dubi Mommy “Mommy ita ba Karuwa bace..” “Idan ba Karuwa bace to mecece..?” Kafin Mommy takai aya ya bata amsa da fad’in “She’s my wife..! Matata ce kaman yanda Safeenah take matata..!” Yanzu kam gaba d’aya mutane parlorn in a shock suke dubansa kaman wanda aka danna masu pause aka hanasu motsi. Daddy ya girgiza kai wannan karon “Mu’azzam matarka fah kace..?” Ya jinjina kai a hankali yana mai sadda kai gaban Daddy. Daddy yace “But.. But how’s is this possible... Wane irin matarka kuma..?” Mu’azzam yace “Daddy I’ll explain everything..” Mommy ta shiga tafe hannaye tana fad’in “La’ilaha’illahu na shiga uku ni Hajara..! Mu’azzam ta nan ka b’ullo kuma.. Na shiga uku wata irin mata Mu’azzam..!” K’aran da Safeenah ta saki tana mai zubewa wajen yai daidai da soma kiran wayar Mu’azzam da akai. Gaba d’aya su Daddy Mommy harma da Aunty Shemau sukai kan Safeenah suna jijjigata suna ambato sunanta. Assad ne mai kiran nasa, ganin yak’i daina kira yasan dole abu ne mai mahimmanci.. Ya d’aga wayar yana sauraron Assad daga d’aya b’angaren “Mu’azzam you need to come right away.. Ka baro duk abinda kake kazo.. Mun samu abinda zai fayyace mana wanene Sagir..!” Ai Assad bai kai aya ba Mu’azzam yace “Alright.. I’m on my way there..!” Ya dubi Daddy yace “Daddy I need to go now.. I’ll explain everything later..” Shi kansa Daddy yau d’in bai iya amsa Mu’azzam ba sai zuba masa idanu da yai.. Safeenah wacce dama sumar k’arya tai jin zai fice bai ko bi takanta ba ta mik’e tana furta “Mommy Kun gani wajen Karuwar zai koma ya k’yaleni a nan bai damu ko mutuwa nai ba.. Daddy you need to stop him.. Wllhi wajenta zai koma..!” Ko tsayuwa sauraronsu bai ba ya fice cikin sauri. Safeenah ta saka hannayenta biyu aka tana k’walla wane irin birkitaccen k’ara. Mommy taci gaba da bala’i tana fad’in wllhi sai Sun tafi Kotu da Mu’azzam.. Yau d’in nan ba sai gobe ba zasu rubuta masa sammaci. Daddy ficewa yai a parlorn dan ya kasa controlling Safeenah da mahaifiyarta wanda gaba d’aya sun fice a giya sabida abunda Mu’azzam ya aikata masu. Aunty Shemau kaw tsananin mamakin Mu’azzam ne ya mugun cikata. Ita batai tsammanin rashin mutuncin Mu’azzam ya kawo nan ba.. Wai matarsa ce ba Karuwa ba.. Ikon Allah Toh yaushe akai auren..? Yaushe ya aureta har ya kaita gidan Safeenah.. gidan da akai ma Safeenah jere.. Kuma ko kunyar cewa matarsa ce baiyi.. Ita yanzu kam ta fara razana da al’amaran Mu’azzam.. Harga Allah tsoro ya fara bata koda wasa batai tsammanin yakai wannan matakin a rashin mutunci ba.. Ko a labarai bata tab’a cin karo da D’an iskan miji irin Mu’azzam ba ka d’auki wata mata ka Kai gidan Amaryar ka da iyayenta suka zuba mata dukiya sukai mata jere ko tarewa matar batai ba. Lokaci guda tausayin Safeenah na rufeta, bata tab’a ganin Amaryar da aka ci mutuncinta irin Safeenah ba.. Ace aure ko tarewa Bakiyi ba. Bama kiga kalan gidanki ba har an auri wata mace an kaita ta rigaki sanin gidanki da mijinki da kayyakin ki.. Ikon Allah wannan kayan mamaki da yawa yake. Ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tana mai ci gaba da danna Safeenah dan Mommy kam tuni tabi bayan Daddy tana jaddada masa tafiya Kotu, dan cewa tai bataga Uban da zai hanata maka Mu’azzam a kotu ba sakamakon cin mutuncin da yai ma d’iyarta. Safeenah ta mik’e ta d’au crutches d’inta Ta nufo waje.. Aunty Shemau ta biyo bayanta tana fad’in “Feenah ina zaki.. Bakida lafiya ki zauna a gida..” Ko tsayuwa amsa Aunty Shemau batai ba.. Kiki da Meema hayaniyar ya fito dasu, Kai kana ganin gidan kawai Kasan babu lafiya. Meema kaw da ta lab’e taji komai mamaki ya kasa sakinta ita kanta yanzu al’amarin Ya Mu’azzam ya daina bata mamaki ya koma bata tsoro.. Wai matarsa ce ba Karuwa bace.. Ikon Allah kayan mamaki baya k’arewa a wannan ahali nasu. Meema tai saurin rik’o Safeenah da tuni ta d’uko car keys d’inta tana fad’in “Adda Feenah what are you doing..? You can’t drive like this.. Dan Allah kiyi hak’uri abi komai a sannu.” Cikin tsananin huci Safeenah ke fad’in “Let go of me Meema.. I’m not listening to you today.. Ki sake nace Meema..!” Ta k’arashe cikin tsananin daka tsawa hawaye na tsartsafo mata. Babu shiri Meema Ta saketa ta shiga bin bayanta tana kiran sunanta. Kiki ma makarantar da bataje ba kenan ta soma bin bayan ‘yanuwan nata.. A haka har suka iso parking lot yanda motar Safeenah ke ajiye tana k’ok’arin bud’eta.. Meema taci gaba da rok’onta tana fad’in “Addah Feenah please you can’t drive like this.. Ki kalli condition d’in da kike ciki fah.. K’afarki babu lafiya how can you drive like this.. Ok bani key d’in I’ll drive you ko ina kike son zuwa..” Ta k’arashe tana mik’o hannayenta biyu alamun Safeenah ta bata key d’in. Huci kurum Safeenah take tana duban Meema. Lokaci guda ta dank’a mata key d’in tace “Take me to her..!” Meema Ta juyo da dubi Kiki dake tsaye bayansu tana zaro idanu waje dan tsoro sabida tsananin tashin hankulan da suka tsinci kawunansu ciki a gidan.. Kai da ganin yanayi Safeenah Kasan zata iya aikata koma menene. Kiki ta girgiza wa Meema Kai alamun kar ta kai Safeenah wajen matar da suka ganta tareda Ya Mu’azzam dan tsaf zata iya illatata komai ka iya lalacewa. Dama Kiki akwai tsoro. Tsawa Safeenah ta dakawa Meema “I said take me to her Meema..!” Lokaci guda Meema ta shiga jinjina kai kafin ta bud’e driver’s side Ta shige Safeenah ta shige mazaunin mai zaman banza.. Girgiza kai Kiki take tana furta “Oh no.. This is not good.. I must do something to stop them..!” A guje Ta koma cikin gidan tana k’walla kirawa Yayanta Musaddiq. A main k’ofan fitowa daga gidan sukai kusan karo da Musaddiq yana mata fad’an shi sa’anta ne da zatake masa kiran tasha. Kiki ta shiga girgiza kai tana fad’in “Ya Musaddiq Addah Feenah da Meema sun tafi gidan Ya Mu’azzam . Addah Feenah tace sai ta kashe matar da muka ganta tareda Ya Mu’azzam..! You need to stop them before Addah Feenah does something terrible..!” “Damn it..!” Ya furta yana mai komawa cikin gidan.. Sauri sauri ya d’auko car keys d’insa ya fito zaibi bayansu.. Mommy ya gani tsaye gabansa tana sakin huci “Koma babu yanda zakaje.. Ka koma ka k’yalesu suje sucimin uwarta.. Idan kabi bayansu ka taresu ban yafe maka ba Musaddiq..!” Musaddiq ya girgiza kai yace “Mommy idan sukaje suka kashe ‘yar mutane kamasu fah za’ayi, kulle yaranki za’ayi a prison.. Dan Allah ki bari na dakatar dasu kafin azo ana danasani gaba d’aya.. You don’t want your daughters to go to jail.. Do you..?” “Kafin su tafi gidan yari sai shegen nan Mu’azzam ya tafi dan dik abinda ya faru shine sila shi ya jawo.. Dan haka na basu goyon baya d’ari bisa d’ari suje suci uwarta kafin shima mu tafi kotu ya amsa nasa..!” “Mommy..!” Bai kai aya ba Ta katsesa da fad’in “ka sake kiran Sunana sai na tsine maka.. Shashasha kawai wanda baya kishin ‘yaruwarsa..!” Kiki dake tsaye gefe kuka itakam ta fara dan tashin hankalin yayi yawa.. Cikin sauri ta sad’ad’a ta fice ba tareda Mommy ta ganta ba. Bazatso Addah Feenah ta kashe wannan matar a kaita gidan yari ba.. Zatabi bayansu tai k’ok’arin dakatar dasu koda bazata iya ba. Mommy kaw tana nan tana jaddadawa Musaddiq cewa yana fita daga gidan sai ta kwashe masa albarka. A parlor Aunty Shemau ta tadda Daddy asthma attack d’insa ya tashi sai numfashi yake da k’yar oxygen na neman gaza masa.. Ta saki kururwa tana doka kiran Mommy.. A tare Mommy da Musaddiq suka nufi cikin gidan a guje hankali tashe. ** A can Headquarters kuwa Assad sai juya wayar da Sabeera Ta basa yake yana kuma dubawa. Ya d’an tsareta da idanu kafin yace “Zan so ki tsaya ki bada statement d’inki a gaban Mu’azzam..” Sabeera ta girgiza kai tace “Rankaidad’e Kasan yanda yanayin wannan case d’in yake, yanzu haka ni da na kawo wayar nan ta yuwu rayuwata na cikin had’ari.. Da fari jefar da wayar nayi niyyan yi dan bana son wani abinda zai had’ani da case d’in nan duba da yanda Aminiyata keta faman shan wahala dik a sabida tarayyarta da Sagir. Da ace Nasan yanda zan sami Sadiya da bazanzo ofishinku ba, da kai tsaye wajenta zanje na kai mata wayar. I don’t want anything to associate me with this case.” Assad ya murmusa kad’an kafin yace “I understand where you are coming from.. And believe me wannan abinda kikayi zai taimaka mana matuk’a wajen solving case d’in nan.. I must thank you.. Mun gode k’warai.. Ba k’awarki kawai kika taimaka ba harda entire NPF kika taimaka.. Idan aka kamo accomplices d’in Sagir an rage mugun iri cikin al’umma.. Thank you miss Beautiful..” Ya k’adashe yana sakar mata murmushi. Murmushin itama tai kad’an tana mai sadda kanta k’asa. Cikin d’an daburcewa sabida irin kallon da yake jifanta dashi Ta mik’e tana fad’in “I.. I must leave now.. Goodbye..!” Ta k’arashe tana mai sa kai..” Saurin bin bayanta yai yace “Wait.. Barin saka a kaiki..” Tai saurin girgiza kai tace “No banso a ganni da wani d’ansanda balle naja ma kaina attention.. But thanks anyway.. I can manage..” Assad ya jinjina kai yana dubanta “You take care..!” Ya fad’i sanda take ficewa. Ta jinjina kai a hankali kafin tai saurin ficewa daga wajen. Yana nan tsaye Yusu ya k’araso ya samesa suna magana k’asa k’asa dan basu so wani ma yasan sun sami wayar Sagir a hannunsu har Sai Mu’azzam ya iso.. Aiko nan suka hangosa yana tafe ya kwab’e suit d’insa yai folding hannayen long sleeves d’insa wanda itace ‘yar cikin suit d’in nasa.. Da gani yanda yake tafiya Kasan ya shirya ma binciken. Yana k’arasowa suka nufi building d’in suna tattauna batun. Maleeka da k’arasowarta kenan nan ta hango Mu’azzam ya dawo aiki wani irin murmushi ne ya kufce mata ta k’araso gudu gudu tana d’ago masa hannu take fad’in “Sir....!” A tare suka waigo suna duban Maleeka dake nufosu.. Team d’in nasu sun had’e gaba d’aya. Yusuf da Assad suka saki murmushi suna duban Maleeka wacce suka rasa walwalanta tin bayan dakatar da Mu’azzam da akai. Sai yau suke ganin murmushinta. Ta k’araso da sauri tana k’ok’arin saita kanta gaban Mu’azzam wanda ya tsime sosai yana dubanta “I.. I’m sorry Sir.. I just want to say welcome back.. Munyi kewarka sosai.. Welcome back Sir..!” Ta k’arashe tana rungume files d’in dake hannunta cikin k’irjinta. Duk sukai tsaye suna duban Mu’azzam da ya tsareta da idanu wanda ba Maleeka dake Ta faman rarrabe idanu cikin tsoro tana addu’an Allah Sa ba wani laifin tai ba harta da su Assad saida suka d’anyi pause suna dubansa. Murmushi ya sakar mata da gefen bakinsa kafin yace “Thank you..” Daskarewa Maleeka tai tana jin Wai Mu’azzam ne ya ce da ita thank you har yana sakar mata wannan tsadadden murmushin nasa.. Bai kuma bi takanta ba yasa kai ya shige su Assad na biye dashi suna murmushin Daskarewar da Maleeka tai.. Lokaci guda Mu’azzam d’in ke fad’iwa su Assad “Let’s go.. To the tracking room and see what we can find inside..” Yusuf da Assad suka jinjina masa kai suna tafe cikin sassarfa. Saida har suka shige kafin Maleeka ta saki d’an k’aran murna tana cilla hannayenta sama “Yes yes.. He will fall for me eventually.. I’m sure of it.. Well done Maleeka kici gaba da hak’uri har ki saye zuciyarsa..” Daga haka saurin shigewa tai tabi bayansu. ** Meema tana ida parking a k’ofar Gidan Safeenah ta k’arasa tana buga gate d’in da sandar crutch d’inta. Bugu take da iya k’arfin da Allah ya hore mata Meema na fad’in Addah Feenah take ita easy..!” Bata ko saurari Meema ba tace “Ki d’auko min ultra pad d’in nan cikin mota nayi imani nata ne na gani wajensa ranan.. Ma ita ya saya zai kawo.. Wllhi I’ll make her eat it.. Sai na sakata Ta cinyesa.. Ki wuce nace ki d’auko mun Meema..!” Cikin sauri Meema ta jinjina kai ta shige mota ta d’auko ledar ultra d’in. Police man d’in dake gate ya bud’e yana duban Meema da Safeenah da mamaki.. Kafin yai magana Safeenah ta d’aga crutch d’inta ta shiga rabza masa aka kaman Allah ne ya aikota.. Dik k’ok’arin sa ganin ya hanasu shiga abu yaci tura dan Safeenah hauka tuburan take nunawa. Daidai lokacin Kiki ta k’araso ta ceci Police man d’in da k’yar wanda tuni jini ya soma zubowa daga goshinsa Sabida k’arafan da Safeenah ta dinga rabza masa. A haka suka nufi gidan Safeenah na sakin huci tana duban fad’in gidan da kalan cin amanar da mijinta Mu’azzam yai mata.. Gidanta ne amma wata ‘yar iska ce ciki har yana kiranta da matarsa. Suna isa ta shiga bugun k’ofar parlorn da iyaka k’arfinta. Sadiya da har lokacin tak’ure take waje guda tana kukan rashin sanin ina ahalinta suke kaman daga sama taji ana bugun k’ofar.. A d’ari ta mik’e ta nufi k’ofar dan a zatonta Mu’azzam ne ya dawo mata da labari mai dad’i ta bud’e tana fad’in “Have you found them already..!” Cak ta tsaya ganin ba Mu’azzam bane wasu ‘yanmata ne guda biyu.. Take ta juya tana kallon hoton auren Safeenah da Mu’azzam, nan ta fahimci matarsa ce wannan.. D’ayar kuma taso ganeta ta rasa a ina ne.. Lokaci guda ta tuna Sune ‘yanmatan da suka tab’a had’uwa dasu a Police Headquarters har suka take mata k’afar Umma da tayar Mota. Sud’inma dubanta suke suna son d’ago ina suka tab’a ganinta.. Meema ce ta soma d’ago hannu tana nunata alamun ta ganeta. “Addah Feenah itace.. Itace wacce muka bugesu a k’ofar police headquarters last two weeks itada wata mata.. Ta saba binsa har wajen aiki..!” Ai Meema bata kai aya ba Safeenah dake tsananin huci tana duban Sadiya ta yunk’ura takai mata wata jahilar mari.. Saidai Sadiya bata bari marin ya sauk’a a fuskarta ba Ta rik’e hannun Feenah tana sakin huci itama.. Tin kafin Feenah takai hannunta k’asa Sadiya Ta maida mata Martanin marinta tasss..! Lokaci guda take nunata da yatsa tana fad’in “Wannan shine sakamakon take mun k’afar mahaifiya da kikayi da Mota..!” Kan uban can.! Safeenah tai tsaye tana dubanta dafe da k’uncinta. Meema ma kame baki tai tana duban Sadiya data kashe Safeenah da mari mai lafiya har cikin gidanta.. “Idan ban kasheki yau ba sunana ba Safeenah Marwan Gamji ba.. Sai nayi ajalinki shegiya Karuwa..!” Tana ida fad’in haka ta shiga kokawan janyo Sadiya sabida k’afarta dake da ciwo yasa batai nasaran capketa ba takai mata duka da sandar hannunta Ta kauce.. Lokaci guda Safeenah ke fad’i da Meema “Tare mun shegiya Meema kar ki barta ta fice..!” Daidai lokacin Kiki ta shigo Safeenah tace su toshe mata Sadiya.. Sarkin yawa yafi Sarkin k’arfi aiko Meema dake duk Ta fisu jiki dama tuni ta k’arasa ta had’e Sadiya jikin garu ta matseta sosai Safeenah na fad’iwa Kiki Ta taimakawa Meema.. Kiki ta k’araso ta saka ma Meema hannu suka danne Sadiya a k’asa. Safeenah na huci ta b’arke ledar ultra d’in ta shiga turawa bakin Sadiya tana fad’in “Sai kin cinye yau tas dan uwarki.. Shegiya Karuwa sauran kwalta mai bin mazan mutane.. Yau sai kinyi nadaman sanin mijina da kikai har kika yarda ya kawoki gidana ya ajiye..” Sadiya tana kiciniyar k’watan kanta fa Safeenah na tura mata sanitary pad cikin bakinta.. Kiki Ta sunkuya saitin kunnen Sadiyar ta rad’a mata a hankali “Zan sakeki kiyi k’ok’ari ki tura Meema batada wani balance sai ki gudu..” Safeenah ta kamo sumar Kiki tana fad’in “Mai kike fad’a mata munafuka..!” Daidai lokacin Kiki ta saki Sadiya ta taimaka mata suka hankad’a Meema ta fad’i gefe tana sakin k’ara.. A guje Sadiya ta nufi upstairs ya maida k’ofa ta rufe.. Safeenah tayo kan Kiki zata jibga wayar Meema ya soma ringing dan dik tashin hankali da Meema zata shiga bata rabo da wayarta.. Kiki ce ta k’arasa ta d’auka dan Meema kam ta kasa tashi tana nan zube wajen tana ihun k’afarta. Ganin Aunty Shemau ce mai kira ya sanya Kiki Saurin d’agawa.. Cikin rawar murya Kiki ke fad’in “How’s Daddy doing Aunty Shema..? Alright gamu nan zuwa..!” Ta juyo tana duban ‘yanuwan nata sai kuma ta fashe da kuka tana fad’in “Daddy ne.. Daddy babu lafiya.. Aunty Shemau ce ta kira tace maza muje gida yanzun nan..” Babu shiri Safeenah ta finciki wayar tai jifa dashi “Babu yanda zamuje sai na kashe shegiyar nan..!” Meema ta mik’e da k’yar tana fad’in “Toh wllhi saidai kiyi ke kad’ai Addah Feenah.. What if Daddy ya mutu muna tsaye a nan.. Kiki shige muje I want to see Daddy..!” Ta k’arashe tana kamo Kikin cikin d’ingishi. Safeenah ta d’aga ido tana duban upstairs d’in “This is far from over..! Zan dawo dan Ubanki.. Kuma sai na kashe ki..!” Daga haka ta janyo crutches d’inta ta nufo bayansu.. Saidai suna fitowa sukaga d’akin karnukan a bud’e. Aiko nan karnukan suka soma haushi.. A d’ari suka arce suka nufo gate a guje suna ihu.. Harta Safeenah watsar da Crutches d’inta tai ta fito a guje.. har suna bangaje police d’in dake gate.. Dik gudun nan basu san k’ofar d’akin karnukan bane kawai a bud’e amma suna d’aure da chain d’insu. Police d’in ya tattaro sandunan Safeenah ya mik’a masu cikin Mota yace a sauk’a lafiya.. Aka barsa da kumburarren goshi yanda Safeenah ta jibgesa da sanda. ** CID Bayan wayar tai chaji suka soma binkicen k’wak’waf cikin wayar. Suka soma Retrieving dik wani sak’o ko kira da aka fitar daga kan wayar. Lamba d’aya suka samu cikin wayar da kuma kan SIM card din, sannan wannan lambar ita kad’ai aka tab’a contacting da SIM card d’in.. Sannan sak’o d’aya ce aka tura da wayar kuma ma lamba d’aya tak aka tura sak’on.. Sak’on Address ne aka tura da wayar. Location d’in da aka sami gawar Ikram da Sagir. Mu’azzam idanunsa sukai jazir yana karanta sak’on. Lokaci guda Assad ke fad’in “Let’s see idan zamu iya tracking lambar da aka aika ma sak’on..!” Bai Kai aya ba Mu’azzam da gumi ke tsartsafo masa yace ya basa wayar. Babu musu Assad ya mik’a masa duk suka zuba masa idanu. K’ura ma lambar da aka turama sak’on ido yai yana duban digits d’in yana karantsrsu one by one.. He’s familiar with number, for sure yasan wannan lambar... D’aukan lambar yai cikin wayarsa ya soma dialing yana jin bugun zuciyarsa na ninkuwa. Sunan da ya fito masa b’oro b’oro saman screen d’insa shine ya sanyasa tsayawa Cak yana duban fuskar wayar tasa, lokaci guda yana jin duniyar na juya masa. SameenaAleeyou📚 *GIDAN ARO* *31* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ji yai k’afafunsa suna barazanar kasa d’aukarsa, lokaci guda zuciyarsa na barazanar tarwatsewa. Assad Yusuf harma da Maleeka mik’ewa sukai suna dubansa cikin tsananin kad’uwa da tashin hankali. Zasu iya cewa yanayin da suka gansa ciki basu tab’a ganinsa cikin irin yanayin a baya ba. Assad ya matso yana jijjiga Mu’azzam wanda ya koma tamkar mutum mutumi “Mu’azzam.. Mu’azzam lafiya.. What’s wrong Mu’azzam..?!” Mu’azzam bai iya amsa Sa ba sai zuba masa rinannun idanunsa da yai yana dubansa har lokacin takara bashi a duniyar haka yake jinsa. Wayar hannunsa Assad ya amsa nan yaga sunan Safeenah ya bayyana saman wayar. Yusuf da Maleeka suka dubi juna bayan sunga sunan da fuskar wayar Mu’azzam ya nuna. Lokaci guda Yusuf yai alamawa Maleeka da idanu cewa su fice. Babu musu Maleeka tabi umarnin Yusuf suka fice daga d’akin. Gijif haka Mu’azzam ya zauna saman kujera idanunsa na k’ok’arin kawo ruwa . Cikin wane irin murya mai gauraye da tashin hankali had’ida rud’ani yake furta “It’s Safeenah’s phone number Assad..! That text message...was sent to her.!” Ya d’ago yana duban Assad wanda tsananin shock shima ya nuna a fuskarsa, lokaci guda Mu’azzam yaci gaba da fad’in “But Assad how’s this possible..? I mean.. Safeenah is my blood.. And Ikram... Ikram was like a sister to her...!” Ya mik’e yana girgiza kai yana duban Assad d’in yake damk’e wayar Sagir cikin hannunsa, lokaci guda yake jijjiga wayar yana fad’in “Assad lambar matata.. Matata Assad, sak’on ma ita aka tura.. She couldn’t have killed my sister right..?!” Yanda yake maganar zaka fahimci yana cikin tsananin rud’ani ne da tashin hankali. Kamo kafad’unsa Assad yai ya zaunarsa saman kujera yana k’ok’arin calming nasa “Please try to calm down Mu’azzam.” D’ago idanu yai yana duban Assad d’in wanda gaba d’aya shima ya zama lost and confused. Kauda Kai gefe kad’an Mu’azzam yai yana tinanin abubuwan da suka faru tun bayan rasa Ikram, lokaci guda yana dunk’ule hannayesa yana murzasu. Assad ya d’an shafi kansa kad’an yana duban Mu’azzam d’in cikeda tausayawa. Fuzar da fuci yai kafin ya isa jikin window cikin rashin sanin abinda zai fad’iwa abokin nasa.. Tabbas Mu’azzam yana cikin yanayi mai matuk’ar wahala. Ace kana bincike kwatsam sai ka samu Matarka itace prime suspect na binciken da kake.. Kuma k’anwarka ce aka kashe sannan matarka ‘yaruwarka ta zamto Prime suspect.. Tabbas al’amarin akwai matuk’ar tashin hankali. K’ok’arin saita kanta Assad yai kafin ya nufo Mu’azzam d’in wanda har lokaci ke zaune ya k’ura ma waje guda rinannun idanunsa. Lokaci guda Mu’azzam d’in ke furta “All this while.. The killer’s right in front of me. Makashiyar tana nan a gabana.. Ina can inata neman makashin ba tareda sanin tana nan tare dani ba.. Claiming to be my wife.. wacce tafi kowa kusanci a gareni bayan mahaifiyata..” Ya d’ago idonsa wanda siririn hawaye ke gangarowa daga ciki yana duban Assad. Lokaci guda yaci gaba da furta “She killed my sister Assad, and then she acts innocent.. Like she was also grieving for Ikram’s death.. She made me look like a complete idiot. Ina can inata bincike kaman wani wawa.. Tanata toshe duk wani hanyar da zanbi na samu gaskiya.. Assad she insulted my profession, you know.!” Saurin dafasa Assad yai yana fad’in “Try to calm down first.. please Mu’azzam..” Mik’ewa Mu’azzam yai yana fad’in “You’re not the one who’s being fooled by the woman you call her wife..! You are not the one who lost a sister in the most painful way.. So don’t.. even.. ask me to Calm down..!” Yai maganar jijiyar goshinsa na kuma fitowa sosai gumi na kuma tsartsafo masa. Kafin Assad yace wani abu Mu’azzam ya nufi k’ofa. Assad yai saurin take masa baya yana ambaton sunansa amma inaa ko sauraronsa baiba. Karo suka kusan yi da Chief Jaja wanda ya nufo Office d’in. Mu’azzam ya tsaya Cak yana duban Chief da idanunsa da suka gama kad’uwa. Chief yana murmushi yake shafa hab’arsa lokaci guda yana duban Mu’azzam d’in “Inspector Gamji, I hope you learned your lesson.. You should know there’s no right way to do wrong things.. Next time sai a kiyaye..!” Ya k’arashe yana bubbuga kafad’an Mu’azzam d’in guda. Maleeka dake tsaye gefe itada Yusuf sai aika ma Chief mugun kallo take musamman da taga yanayin Mu’azzam d’in. Mu’azzam baice da Chief komai ba har ya gama maganganunsa sai dubansa da rinannun idanunsa da yake. Lokaci guda Chief ya gyara tsayuwarsa had’ida gyaran murya “Any update regarding your case, Inspector Gamji..?” Ya tambaya yana tsare Mu’azzam d’in da idanu wanda ko motsi mai kyau ya kasa Sai dad’a damk’e wayar Sagir dake cikin hannunsa yake. Chief ya gyara tsayuwarsa yana karantar Mu’azzam d’in.. Lokaci guda Maleeka da Yusuf suka k’araso yayinda Assad ma gaba d’aya za’a iya cewa ya shiga missed call. Yama rasa mai zai yi sai duban Chief yake yana kuma duban Mu’azzam. Chief ya dubi Assad ya kuma duban sauran team members d’in Wato Yusuf da Maleeka. Nan yaga gaba d’ayansu kaman an cire masu laka. “Detectives..!” Chief ya fad’i yana dubansu d’aya bayan d’aya kafin ya tsaida idanunsa kan Assad. “Shattima.!” Ya kira surname d’in Assad. Assad ya sara masa “Sir.!” Chief yaci gaba da fad’in “Any progress..?” Duban Mu’azzam Assad yai cikin rasa mai zai fad’i. Yanzu kam ran Chief ya soma kad’uwa wajen b’aci. Cikin tsananin zafin nama yake furta “Why are you all mute.?” Ya girgiza kai yana ci gaba da furta “It seems we assigned this case to bunch of incompetent Detectives.. Am I right.?” Ya k’arashe cikin daka tsawa. Yayinda suka duk’ar da kawunansu k’asa idan ka cire Mu’azzam wanda har lokacin duban Chief yake bai daina murza hannunsa ba. “Give me updates now. Detectives.!” Ya k’arashe cikin tsananin daka tsawa. Zuciyar Chief fari k’al ganin basu ce komai ba, yanzu ya tabbata dole a gaji ai closing case d’in kaman dai yanda suka tsara. Ya wani gyara tsayuwa yasha mur sosai kafin ya soma jinjina kai cikin tsananin b’acin rai yana duban Mu’azzam d’in “I am going to warn you for that last time Inspector Gamji..! Bring all your team together to collaborate more effectively on this case.. Unless kana so ai maka retire before your retirement period.!” Lokaci guda Mu’azzam ya d’ago wayar daketa faman dunk’ulewa cikin hannunsa yana nunawa saitin fuskar Chief. “Meye wannan..?” Chief ya tambaya. “It’s Sagir’s cell phone.. Sir.!” Mu’azzam ya basa amsa kai tsaye. Dukda cewa zuciyar Chief ya yanke, ya kuma razana da ganin wayar Sagir d’in amma Sai ya wayance yace “Good.. At last something good came out of your investigation.! Good Inspector Gamji.. You’re one of our best agents. Nasan bazaka bamu kunya ba.. Let’s see what you found inside..” Ya k’arashe yana mai kad’a kafin ya nufi office yana fad’in su biyosa.. Babu musu suka bi bayan Chief. Zuciyar Chief sai yankewa take. Ya kula Mu’azzam bazai tab’a dakatawa ba har Sai ya tono komai. Ya tsani Mu’azzam.. Sannan zai komai in his power ya tabbata Mu’azzam ya bar aikin D’ansanda for good. ** Su Safeenah suna komawa guda suka tadda Daddy zaune harabar gidan saman kujeru na shak’atawa. Sai kallon kallo suke ma juna ganin Daddy ras kaman ba shine Aunty Shemau ta kira ta sanar dasu Baida lafiya sosai ba. Dan har kaman kuka sukaji tanayi cikin wayar. Gaba d’aya suka fito suka nufi mahaifinsu wanda Mommy ke zaune gefensa ta cika tayi fam sai girgiza take. A guje Meema da Kiki suka k’arasa suka rungumesa “Daddy wai bakada lafiya..? Daddy munji tsoro sosai.?” Murmushi ya sakar masu ya shafi fuskokinsu kafin yace “I’m fine now.. Ku kwantar da hankalinku Kunji koh...” Kiki ta kuma rungumarsa tana fad’in “Daddy banso mu rasaka.. I can’t even bear the thought of it..” Ya shafi kanta kad’an yana murmushi kafin yace “Ku shige ciki zamuyi magana da Addarku..” Babu musu suka shige dan Mommy kam basu ma ga fuskar mata magana ba tsaban tafarfasa da take. Safeenah dake tsaye daga baya tana hawaye suna shigewa ta k’araso ta zube kanta saman cinyar Daddy dake zaune kan kujera. Kuka take sosai tana fad’in “Daddy it is true..! Daddy Mu’azzam mace yakai cikin gidana.. Daddy zan mutu.. Mutuwa zanyi Daddy.. I can’t take this anymore..!” Bai hanata kukan har saida tai mai isanta kafin ya dubi Mommy yace “Can I have a moment with my daughter, Please.” Mommy Ta dubesa da mamaki kafin Ta soma magana cikin huci “Wllhi wllhi kaji na rantse maka da Allah sai na maka Mu’azzam a kotu.. Ko ka shawo kan Safeenah ka danneta wllhi sai nayi k’aran Mu’azzam kan abinda yayima Safeenah. Har ofishin nasu zan tafi na kai masa sammaci wllhi.. Babu ruwana da cewa shi D’ansanda ne.. Idan shi bakin bindiga ne k’arewar tsaro wllhi Sai na maka k’ararsa ehe..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye. Daddy ya d’ago yana dubanta “Kin gama.?” Bata basa amsa ba sai ci gaba da jijjiga da take. “Idan kin gama leave us alone with my Daughter.. Please..” Mugun kallo ta watsa masu daga shi har Safeenar kafin Ta wuce fuu kaman zata tashi sama. Aunty Shemau dake tsaye saman Balcony d’in Mommy akan idonta komai ya faru. Tana ganin Mommy ta nufo cikin gidan ta nufo k’asa itama. Daddy ya d’ago Safeenah ya zaunarta saman kujerar gefensa yanda Mommy ta tashi. Har lokacin Safeenah bata daina jan zuciya ba alamun taci kuka. Daddy yai gyaran murya a hankali kafin ya soma fad’in “I know you’re hurt.. And you’ve the right be angry.. Dole kiji zafi dan jin zafi.. Amma abinda nake so ki sani shine tashin hankali bai tab’a kawo solution wa matsala ba, saidai ma ya k’ara b’ata komai.” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Safeenah my Daughter, don’t allow your anger to consume you.. Kiyi hak’uri mubi komai a sannu.. Give your husband a chance to explain himself.. Bamusan dalilinsa na yin auren ba.. And yace zaiyi bayani, I’m sure Mu’azzam yanada bayanin da zaiyi.. You and I both know Mu’azzam is a good person.. He might have his faults as a human being, but he’s not a bad person.. Ba ina fad’in haka dan nafi sonsa ne ko nafi sonki ba.. No, I’m not taking sides here.. I love you both.. Kai gaba d’ayanku yarana ina k’aunarku kuma bazanso naga abinda zai cutar da d’ayanku ba.. Kiyi hak’uri Safeenah.. Da zafi na sani. Amma ki daure ki saurari mijinki kiji dalilinsa.. Allah ya miki albarka tashi ki shige..” Da tsananin mamaki Safeenah ke duban Daddy, lokaci guda take girgiza kai still hawaye na zubo mata. “Seriously Daddy.. This is all you can say..?!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka kafin taci gaba da fad’in “I can’t believe you are asking me to give him a chance to explain.. “ Ta girgiza kai kafin taci gaba da fad’in “Daddy what explanation kuma. Bayan abinda na gani da idanuna Daddy you still ask me to wait for his explanation..?” Taci gaba da hawaye tana girgiza kai “Daddy Mu’azzam fooled me.. He fooled us all. All this while wata ya aje gidana shiyasa yak’i amincewa na tare.. And yet you’re asking me to give him a chance to explain how he cheated on me with that prostitute he called wife..!” “Safeenahhh!!” Daddy ya daka mata tsawa yana mai d’auketa da mari mai ji da lafiya wanda ya haifar mata da gani giftawan walk’ila harda taurari. Ta d’ago a gigice tana duban Daddy dake tsaye kanta rik’eda k’uncinta. Yaci gaba da nunata da yatsa “Ban haifi ‘yarda zatafi k’arfina ba. Idanma mahaifiyarki ce mai zugaki.. kije.. Go ahead, ku shigar da Mu’azzam Kotu.. Ni kuma na rantse sai na tsaya masa tinda duk kayan jeren naki da kud’ina aka saya.. Shashasha kawai maras hankali..! Get out of my sight now..! B’ace min da gani.. Stupid kawai..!” Da d’ingishi Safeenah ta wuce rik’eda k’uncinta ko takan crutches d’inta batabi ba.. Tana tafe tana kuka tana k’wallawa Mommy kira. ** Mota guda suka d’auka ta ‘yan sanda irin yanda ake idan za’ayi arresting mai laifi, bayan Maleeka harda wata ‘yar sanda mace mai sanye da uniform d’in police. Lokaci guda Mu’azzam ya nufi nasa motar yana jin zuciyarsa na masa wane irin k’una. Assad ya biyosa dan bazai barsa yai driving a yanayin da yake ciki ba. Wayar Mu’azzam d’in ne Ta soma ringing, nan ya duba yaga Mommy ce mai kira. Ya d’aga without saying a word. Daga d’aya b’angaren Mommy ke fad’i cikin tsananin huci “Ka gama gudunka Mu’azzam wllhi wllhi kaji na rantse maka sai ka biya abinda ka aikata ma Safeenah.. Bazan dubi zumunci ba Mu’azzam ba kuma zan dubi alak’a Ta jini dake tsakaninku da Safeenah ba balle na duba matsayinka na kasancewa miji a wajenta.. Sai na maka ka a kotu saidai duk abinda za’a fad’I a fad’I.. Ka riga da ka ruguza ahalin da Kakarku tai k’ok’arin ginawa tsawon shekaru. Wllhi you will pay dearly for what you did to my daughter.. I don’t give a damn about your police uniform..!” Tana ida fad’in haka ta katse kiran ba tareda ta tsaya ta saurara daga nasa b’angaren ba. Tana katse kiran ya cire wayar daga kunnensa yana jinjina kai idanunsa na duban waje guda. A hankali yake furta “You’re right Mommy.. Ahalin ya tarwatse.! Kuma zamu tafi Kotu kaman dai yanda kikace.!” Suna shigewa Maleeka Ta silale Ta ciro wayarta Ta soma dialing layin Barr Amir. Bugu d’aya a na biyu Amir ya d’aga kaman wanda yake jira. Cikin sauri Maleeka ta soma fad’in “I’ve always known matar Mu’azzam tanada saka hannu a mutuwar k’anwarsa, tarayyar da nakeda Chief Jaja ba’a banza ba, Domin na mallaki Mu’azzam zanyi komai ni Maleeka. zance na ya tabbata gaskiya... Yanzu zaka yarda da batuna Barr.” Barr Ameer ya mik’e kad’an daga kishingid’en da yake “Tell me, mai kika samo mana daga wajen saurayin naki..? Ina nufin Chief Jaja.!” Ta d’an murmusa kafin tace “Ka shirya za’a tafi ayi arresting Safeenah Gamji. If you want to defend her in court, this is the perfect time for you to make a move..After all, I’ve done my part da na kiraka na sanar dakai. The NPF are on there way to arrest her so Sai ka zama cikin shiri idan har baka so Safeenah ta kufce maka.. I want her out of Mu’azzam’s life completely, ka fahimta.. Idan ta nawa ne bank’i ta tafi jail ba ta k’arashi rayuwarta a can.. Amma idan kana sonta dama ya sameka, sai ka tsaya mata ka kareta a Kotu dan na tabbata bayan abinda Mu’azzam yai discovering yau d’in bazai ci gaba da zama da ita matsayin mata ba.” Tana ida fad’in haka ta katse kiran tai saurin k’arasawa ta shige motar ‘yansandan. Barr Ameer yai wata k’asaitacciyar murmushi yana furta “Now it’s your time to shine Ameer..! Good Job Officer Maleeka.. I knew it from the very start. You and I would make a perfect team, nasan zaki min amfani.. Good job Officer.” Ya wani murmusa yana karkad’a k’afa guda kafin yaci gaba da fad’in “Yanzu za’a fara buga wasan tsakanin Lawyer da kuma Inspector.. I told you Safeenah, you are mine.. Ni Ameer ni ne mijinki nan gidan duniya.. Now it is time for me to play a perfect Attorney role..!” Yana ida fad’in haka ya bushe da muguwar dariya kafin ya mik’e yana sab’a suit d’insa. ** Daddy na nan zaune waje aka soma bud’e gate, motar ‘yansanda da ya hango na danno kai cikin gidansa shi ya bala’in d’aga masa hankali. Badai Safeenah taje ta aiwatar da wani mugun abin ga matar Mu’azzam ba. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum Daddy ke iya nanatawa cikin zuciyarsa. Bai ida tinanin ba ya hango Motar Mu’azzam biyeda na ‘yansandan. Daddy ya mik’e yana tambayar kansa meke faruwa. ‘Yansandan suna ida parking Mu’azzam ma yai parking a gefe. Saidai basuyi yunk’urin aiwatar da komai ba dan umarnin Mu’azzam d’in suke jira. Mu’azzam yana fitowa daga mota ya hangi Daddy tsaye yana dubansa cikin rashin gane meke faruwa. Take Mu’azzam yaji zuciyarsa ya masa wane irin rauni. Idanunsa suka soma k’ok’arin kawo ruwa. Ji yai k’afafunsa na barazanar gaza d’aukarsa.. Dik k’arfin hali irin nasa saida yaji zuciyarsa Ta gaza juran abinda ke faruwa. He looks shattered. A hankali yake takowa yanda Daddy ke tsaye. Yana k’arasowa ya kifa kansa ba tareda ya iya ci gaba da duban Daddy ba. Shi kansa Daddy ya Sani ba k’aramin abu bane zai jefa Mu’azzam cikin irin yanayin da ya gansa ciki. A hankali Daddy ya soma furta “Mu’azzam. Son, are you alright..? What’s the matter.. Talk to me Mu’azzam, meke faruwa..?!” Daga nan yanda yake tsaye kansa na kife sai sautin fitar kukansa Daddy yaji jikinsa na vibrating kaman dai wanda aka jona masa electric shock. Saurin kamosa Daddy yai cikin tsananin kad’uwa da tashin hankali “Mu’azzam.. Son.. Talk to me.. Mai ya faru Mu’azzam.. Dan Allah ka mun magana..!” D’agowa Mu’azzam yai yana duban Daddy sai kuma ya rungumesa yana kuka sosai, kukan dake tare cikin k’irjinsa wanda bai iya fitarwa ba. Jikin Daddy ya gama sanyi Mu’azzam d’in na rungume cikin k’irjinsa. Abinda kawai Daddy ya kawo shine kodai Nuratu ce ta rasu.. Kar dai Sun kuma rasa ahali. Daddy ya kasa jurewa, kafad’un Mu’azzam ya damk’e sosai ya shiga jijjigasa kad’an “Mu’azzam tell me.. Tell me it’s not your Mom.. Talk to me Mu’azzam.. Please talk now..!” Mu’azzam ya d’ago gajiyayyun idanunsa yana duban Daddy, tausayinsu gaba d’aya ya rufesa. Cikin rawar murya yake furta “It’s Safeenah..! I’m sorry Daddy.!” Ya sunkuyar da kansa ba tareda ya iya ci gaba da magana ba. Cak Daddy ya tsaya ya daina jijjiga Mu’azzam d’in.. Ya dai San yanzu Safeenah ta bar gabansa ta shige gida.. Toh mai kuma ya faru. Ya girgiza kai cikin rashin gane ina kalaman Mu’azzam suka dosa. “What happened to Safeenah..? I mean tana cikin gida, right.?” Mu’azzam ya d’ago ya dubi Daddy cikeda tausayawa “Unfortunately Daddy.. We.. We are here to arrest Safeenah. Bincikenmu ya gangaro zuwa kanta Daddy..!” Dummm!! Haka k’irjin Daddy ya buga. Mu’azzam yai saurin kama Daddy ya zaunar dashi. Daddy yaci gaba da girgiza kai yana fad’in “Tell me mai Ta aikatawa matarka.. Ta mata wani illan koh..?” Girgiza kai Mu’azzam yai yana duk’e gaban Daddy. Hannayen Daddyn rik’e cikin nasa yake fad’in “Bata aikata mata ba.. Amma ta aikata ma Ikram Daddy.!” “Ikram kuma..?!” Daddy ya tambaya cikin tsananin kad’uwa. Mu’azzam ya jinjina kai a hankali. “But.. But.. Mai kake nufi Mu’azzam.. Ikram ta rigayemu gidan gaskiya.. A ina Safeenah zata ganta.. What.. what is all this Mu’azzam.?!” Mu’azzam ya kuma damk’e hannayen Daddy cikin nasa kafin yace “Safeenah is now our prime suspect game da case d’in mutuwar Ikram Daddy.!” Wannan karon cire hannayensa Daddy yai daga cikin na Mu’azzam yana girgiza kai yake duban Mu’azzam d’in “No Mu’azzam.. You must have got this wrong.. Safeenah.. Safeenah would never do something terrible irin wannan.. Mu’azzam ka mun magana yanda zan fahimceka.. Ikram da Safeenah duka yarana ne.. Bazai yuwu hakan ta kasance ba.. Safeenah nada kurakurenta a rayuwa amma bazata tab’a zama makashiya ba.. Right Mu’azzam.. She’s your wife. You should know better, bazata iya kashe Ikram ba.. Mu’azzam wannan wasa ne ba gaskiya ba.!” Mu’azzam ya shafi fuskarsa da duka tafukan hannayensa kafin ya girgiza kai yace “Daddy I wish ba gaskiya bane nima.. But... Gaskiyan kenan..!” Daddy yaci gaba da girgiza kai hawaye mai zafi yana gangaro masa.. Daidai lokacin da Mu’azzam ya kifa kansa k’asa. Muryar Daddy ya sinkayo yana fad’in “Ku shiga ku tafi da ita a binciketa.. Go Mu’azzam.. Go ahead.. Jeka kayi aikinka..!” Mu’azzam ya d’ago yana duban Daddy.. Kafin ya kuma furta wani kalma Daddy yace “Bazan hanaka ka bincike Safeenah ba.. Sannan idan har an kamata da laifi nayi maka alk’awarin zata biya abinda Ta aikata.. Go ahead now.. Ku shiga ku tafi da ita.!” Yana ida fad’in haka ya kauda kansa gefe yana k’ok’arin maida k’wallan da suka taru idanunsa. Lokaci guda Mu’azzam ya juya ya dubi su Assad yai masa alama da kai. Jiki a matuk’ar sanyaye Assad ya jinjina kansa kafin ya dubi su Maleeka da d’aya ‘yar sanda macen mai sanye da uniform yace su shiga su fito da Safeenah. Maleeka ta jinjina kai kafin ta dubi sergente d’in tace suje. Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, yau Wai Safeenah aka Zo arresting ana tuhumar Ta da zargin kisa. Wane irin tashin hankula ne suka tsinci kawunansu ciki wanda za’a iya cewa yazo masu bagatatan babu zato balle tsammani. Aunty Shemau kam Ta kasa daina mamakin abubuwan tashin hankula dake kan faruwa tun bayan zuwanta. Babu wani abin arziki da faru tinda tazo. Mommy masu shirin maka Mu’azzam a kotu sai gashi su ake shirin makawa. Safeenah ta ci gaba da b’oyewa bayan Mommy tana fad’in “Mommy wllhi ba gaskiya bane.. Wllhi ban kashe Ta ba.. Mommy I can’t go to jail.. Na shiga uku.. Daddy please help me.. Na rantse da Allah bansan komai ba.. Wllhi Allah I’m innocent..!” Maleeka tayo kanta tana fad’in “Idan munje Headquarters zaki k’arasa bayananki.” Safeenah ta rapza mata crutch akai tana fad’in “K’arya kike k’aramar Karuwa kinyi kad’an kiyi arresting d’ina.. Bak’ar munafuka Kema kina cikin Karuwan nasa..” Sergeant Teena ta k’araso tana fad’in “Madam you’ll be charged for attacking the police officer.. Ki shige muje..” Mommy ta shiga tsakani ta tare d’iyarta tana fad’in “K’arya ne..! Wllhi babu ubanda ya isa yai arresting ‘yata.. My daughter is not a killer.. Ku fice mana a gida ko muyi suing naku for trace passing..!” Maleeka ta mik’o mata takarda a linke tana fad’in “Hajiya, we have the warrant of your Daughter’s arrest.” Mommy ta fuzge takardan ta yaga tai kaca kaca dashi tana fad’in sunci ubansu dasu da warrant d’in. Daidai lokacin Mu’azzam ya shigo, idanunsa kan Safeenah dake b’oye bayan Mommy tana kuka. Mommy taci gaba da k’are Safeenah tana fad’in “Mu’azzam ta nan ka b’ullo dan ka guje ma laifinka.. What kind of a monster are you.. You’re not taking my daughter.. Kai ko kunya bakaji ba ka tattaro ‘yansanda ka kawo mana gida.. Haven’t you thought of our family’s reputation.. Haven’t you thought of what people might say.. Zakayi arresting matarka kuma ‘yaruwarka kana tuhumarta da kisan k’anwarka.. So kake sunan ahalinmu ya lalace ko mai.. So kake mu tafi kotu muna shari’a ana nuna mu da yatsa.” Da rinannun idanunsa yake duban Mommy wannan karon kafin ya girgiza kai yace “Mommy, Safeenah should’ve thought about that before committing the crime..! And yes kafin nace za’a tafi Kotu kin riga kowa cewa zamu tafi Kotu muyi shari’a. Idan ban mance ba yanzu kika gama fad’a mun a waya, ashe idan mun tafi Kotu da sunan ahalin nan ba komai bane wajenki. Abinda kike so ne.. Kuma ina mai tabbatarki zamu tafi Kotu, kuma za’ayi sharia..!” Yana ida fad’in haka ya kamo hannayensa Safeenah yana zira mata handcuffs. Lokaci guda yake furta “You have the right to remain silent. Everything you say can be used against you in the court of law. Kinada damar da zaki d’aukarma kanki lauya.. Idan kuma baki dashi the Authority will assign one for you.!” Ya ida maganar sanda ya gama rufe hannayenta. Shaye da tsananin mamaki Safeenah ke dubansa. Bakinta na tsananin rawa take girgiza kai tana furta “I.. I didn’t do it.. Na rantse da Allah ban aikata ba Mu’azzam.. You need to believe me.. How can you arrest your wife..? Mu’azzam ni ce Safeenah.. Kaga abinda ka min.. Haba my Halal, Please don’t do this.. Wllhi I’m innocent. Maiyasa zan kashe Ikram..? What could be my motive.!” “Ki ajiye bayananki har sai munje ofishinmu.!” Ya fad’i cikin kad’uwa kafin ya dubi Maleeka yace “Take her.!” Wane irin k’ara Safeenah ta saki wanda saida ya firgita kowa dake cikin gidan. Su Kiki da dake d’aki basusan wainar da ake toyawa ba ihun Safeenah ne ya fiddo dasu gaba d’aya. Tashin hankali bisa tashin hankali. A fujajan Mommy tabi bayansu Safeenah tana fad’in Mu’azzam bai isa yakai mata ‘ya ofishin ‘yansanda ba. Dik abinda ake bama tai zaton Daddy na gidan ba. Ta zaci ya fice.. Ta dubi Meema hanaki tashe tace “Call your Dad right now..!” Ta kuma duban Aunty Shemau da tuni ta d’auko mata mayafi tana rufa mata. “Muje Shemau..!” Ta fad’i suna ficewa cikin sauri. Wani irin wawan birki Mommy tai ganin Wai da sanin Daddy Mu’azzam yazo d’aukan Safeenah. Kuka Mommy Ta fashe dashi sanda Safeenah ke sanar da Daddy cewa batada laifi cikin kuka. Daddy ya girgiza kai yace “‘Yansanda zasuyi aikinsu.. And if you are proven guilty.. Ki mance kinada mahaifi Marwan Gamji. I do not have a daughter for a criminal.!” Yana ida fad’in haka ya juya cikin gida yana matsan k’walla. Mommy Ta bisa da kallo baki sake. Lokaci guda ta isa tana janyo Daddy “She’s your daughter.. You should believe her.. Kasan Safeenah bazata tab’a aikata abinda ake zargin Ta ba.. Wllhi our daughter is not a killer.. She can be anything.. But not a murderer.. You can’t neglect your daughter.. She needs you now.. Kai tunanin sunan ahalinmu.. Wannan zai b’ata maka sunanka da sunan ahalinmu ne.. Mu’azzam ba d’an halak bane tinda har ya shigo da ‘yansanda cikin gidan nan akai arresting Safeenah.” Sai lokacin Daddy ya juyo ya katseta da fad’in “Ina jin kin mance cewa kafin Mu’azzam ya tsaya akan case d’in nan ni ne mutum na farko da yai failing case d’in mutuwar Ikram ma ‘Yansanda.. Kin mance cewa ni ne nan nai k’udirin za’a bincike mutuwar nata dukda cewa ga sakamon da ya bayyana cewa mutumin da ya kasheta ya riga ya kashe kansa.” Mommy cikin kuka Ta katsesa da fad’in “Amma ai duk mun amince mutumin da ya kashe Ikram ya kashe kansa.. Mu’azzam neman wanda zai d’aura ma Alhaki kawai yake..” Ta k’arashe cikin kuka. Daddy ya jinjina kai yace “Ki k’yale ‘Yansanda suyi aikinsu Hajara.” Daga haka Sa kai yai ya shige. Mommy ta soma kururuwa ta nufi mota tana fad’in driver yazo ya tuk’asu itada Aunty Shemau, dole subi bayan ‘yansandan idan Daddy bazaije ba. Meema da Kiki kaw kuka suka dingayi suna ganin Bak’on al’amaren dake faruwa cikin ahalin nasu. Wai Ya Mu’azzam yai arresting Addah Feenah kuma wai da kisan Ikram ake tuhumarta. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Cikin sauri Meema ta shiga neman layin Musaddiq dan Ta sanar dashi abindake faruwa dashike baya gida. ** Mu’azzam ya k’ura mata idanu sanda aka barsu su biyu a interrogation room saiko d’an mindow mai kaman glass wanda abokan aikinsa zasu iya hangosu daga nan. Idanunsa jazir yake duban Safeenah sanda ya nuna mata lambar wayarta da time da date da komai da komai na lokacin da aka tura mata sak’on. Safeenah taci gaba da girgiza kai tana furta “Na rantse da Allah bansan komai ba Mu’azzam..” Tsawa ya daka mata yana mai buga table d’in da ya raba tsakaninsu “Don’t you dare lie to my face.! You received this text message a ranan d’aurin aurenmu.. Admit it Safeenah.!” Yai maganar idanunsa tar akanta wayar Sagir rik’e cikin hannunsa yana mata nuni da sak’on. Safeenah taci gaba da girgiza kai tana hawaye ba tareda tace komai ba. Mu’azzam yaci gaba da furta “You were not yourself that day Idan ban mance ba. You were acting very strange.. I even asked you meke damunki, but what did you say..? Ce min kikai nervousness ne na barin gida sabida zakiyi aure.. Washe garin wannan ranan aka tsinci gawar Ikram... Haka ne..?!” Ta kuma girgiza kai tana hawaye “Na rantse da Allah ban San komai ba..” Wani Farin takarda Mu’azzam ya ajiye gabanta nan saman table d’in wannan karon cikin rawar murya yake magana “This is the autopsy result of Ikram’s death Safeenah..!” Muryarsa yaci gaba da rawa yana furta “Take a look Safeenah.. Ki duba autopsy result d’in.. Binciken da likita ta gudanar akan gawan Ikram.. She was raped Safeenah..!” Izuwa lokacin hawaye ne ke gangaro masa haka ma Safeenar wacce take girgiza kai tana duban takardan. Mu’azzam yaci gaba da furta “My sister was raped and then shot.. An mata fyad’e sannan aka harbeta da bindiga.. An kasheta a wulak’ance. Wulak’ancin da ko dabba baza’a masa ba.. Idan kinada zuciya cikin k’irjinki Safeenah zaki sanar dani gaskiyan al’amarin.. Zaki sanar dani gaskiyar da kika sani..!” Ya k’arashe gumi na gangarowa daga cikin sumarsa zuwa goshinsa. Safeenah taci gaba da girgiza kai tana hawaye “Wllhi ni bansan komai ba Mu’azzam.. Ka yarda dani.!” Buga table d’in ya kuma da k’arfin gaske wanda saida ya storata Safeenah “Isn’t it enough that you’ve been fooling me for almost a month now.. You insulted my intelligence and my profession as a police officer.. Safeenah let’s not make this difficult anymore.. Ki sanar dani mai kika sani..” Safeenah ta d’ago tana dubansa cikin huci wannan karon “Banfa mance abinda ka min ba Mu’azzam.. Dan Mommy tace zata maka ka a Kotu shine bari ka b’ullo ta nan.. Bazaka tsere ma laifinka ba.. Ka cuceni ka kai min mace cikin gidana.. Kana kwanciya da ita a saman gado na kai ko kunya bakaji ba.. Tell me mata nawa ka kai min gida ka kwanta dasu saman gadona.” “Feenahh..!!” Ya daka mata tsawa yana mai d’ago hannunsa kaman zai mareta. Sai kuma ya sauk’e hannun nasa a hankali.. Safeenah taci gaba da kuka tana fad’in “Kai mugu ne Mu’azzam.. Azzalumi ne kai.. Ka cuceni Ka cuceni.!” Tai maganar tana k’ok’arin turasa tana kuka sosai tana bige bige. Mu’azzam ya shiga k’ok’arin kame hannayenta dole Maleeka ta shigo tana taimaka masa da rik’e Safeenah dake Ta faman buge buge kaman sabuwar kamun hauka. Ficewa yai daga interrogation d’in to get some fresh air, saida Safeenah ta daina bige bigen da take kafin ya dawo cikin tsananin tsimewa. Tai zaune saman kujeran tana sakin huci. “Shall we continue.”ya fad’i yana dubanta. Kauda Kai gefe tai kafin tace “Ina son magana da lawyer na. Ko shima banida dama.?” Yai mata K’uri yana dubanta “Daddy yace lauyansa bazai tsaya miki ba. Kinada wanda kike so a kira miki in mind.” Ta d’ago da mamaki tana dubansa jin abinda ya fad’i. Kafin Safeenah takai ga magana sukaji an turo k’ofa an shigo. “I need to speak to my client. Mr Inspector.” Abinda ya fad’i kenan daga nan yanda yake tsaye cikin bak’ar suit d’insa. Daga Safeenah har Mu’azzam juyawa sukai suna duban Ameer dake tsaye kansu. Mu’azzam ya mik’e shaye da mamaki yana duban Brr Ameer dan tsaf ya ganesa tsohon saurayin Safeenah ne. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *32* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Mu’azzam ya girgiza kai yana duban Barr Ameer disbelievingly kafin ya kuma duban Safeenah wacce itama Ameer d’in take duba. Lokaci guda Ameer ke takowa gaban Mu’azzam d’in muguwar murmushi saman fuskarsa. Ba tareda wani b’ata lokaci ba ya mik’awa Mu’azzam dake tsaye gaban yana dubansa hannu alamun musabaha “Inspector, long time no see.” Ameer ya fad’i still murmushin saman fuskarsa yana mai mik’a right hand d’insa ga Mu’azzam d’in. Ganin Mu’azzam bai mik’o masa hannun ba ya sanyasa sakin wata k’asaitacciyar murmushin kafin yace “Nasan ka sanni by name so need na maimaita abinda ka riga ka sani. After all, your wife and I used to be very good friends.” Izuwa lokacin zuciyar Mu’azzam takai k’ololuwa wajen b’acin, hannayensa kaw sai faman dunk’ulesu yake jijiyon jikinsa na kuma fitowa sosai. Ameer ya kuma gyaran murya yana d’an gyara tsayuwarsa kafin yace “Aff ashe fa na mance ban maka murnan aure ba, everything happens so fast.. I couldn’t get the chance to congratulate you.. But wait.. Shin ka cancanci nai maka murna..? Wanne irin miji ne zai arresting matarsa..? What kind of a husband does that to his wife .? Aren’t you ashamed of yourself Inspector.? Kana tuhumar matarka da kisan k’anwarka..” Ya d’anyi fasali yana mai girgiza kai kafin yace “Don’t you have anything to say to me, Mr Inspector..?” Ya d’an tab’e baki kad’an kafin yace “Koda shike ba Kai bane abokin karawan nawa wannan karon. I rather speak with your Lawyer in court.. Sai muga waye kuma zai sha k’asa yanzu.!” Baikai aya ba yaji sauk’an naushi a hancinsa wanda saida ya kaisa k’asa. Safeenah ta mik’e da sauri tana k’ok’arin tare Mu’azzam yayinda Maleeka da Assad dake dubansu ta cikin glass sukai saurin shigowa. Assad ya k’arasa ya rik’e Mu’azzam d’in yayinda Maleeka ta duk’a tana tambayan Barr Ameer if he’s okay. Barr ya mik’e yana kame bakinsa da Mu’azzam ya basa naushi wajen.. Yana fad’ida Maleeka “I’m alright.. Kar ki damu Officer.” Assad yaci gaba da k’ok’arin janye Mu’azzam yana fad’in “That’s enough Mu’azzam..” “You Stay out of this Assad.. Let me teach this moron some manners.” Yana maganar yana fincika Assad na kuma rik’esa. Ameer yai wata k’asaitacciyar murmushi kafin yace “Can I speak to my client now..?” Yai maganar yana duban Mu’azzam dake aika masa razannan kallo. Ya kuma murmusawa kafin yace “In private.” Mu’azzam ya kuma yowa kansa Assad yai saurin janyesa ya fice dashi. Suna ficewa Mu’azzam ya finciki hannunsa daga rik’onda Assad yai masa yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Assad ya jinjina kai yana dubansa “Just what do you think you are doing..? What has gotten into you.?” Assad cikin fad’a fad’a yake maganar. Ya shafi kansa kad’an yana duban Mu’azzam da ya dafe benci ya kifa kansa kurum ba tareda yace komai ba Sai zuciyarsa dake tafarfasa. Assad yaci gaba da fad’in “You attacked her lawyer Mu’azzam.. What if wani yaga hakan.? Ka godewa Allah babu kowa wajen...” Katsesa yai da fad’in “I do not give a damn Assad.! Didn’t you hear what that imbecile was saying.? Ko bakaji abubuwan da yake fad’i bane..?” Ya fuzar da fuci yana duban Assad d’in “Kar ka sake dakatar dani Assad.. Idan kuma ba haka ba..?” Yaci gaba da girgiza kai kafin yace “I don’t know what I might do to you..!” Yana ida fad’in haka ya fice daga wajen gaba d’aya.. Yana ficewa ya hango Musaddiq ya fito daga motarsa. Sukai tsaye suna duban juna, kana ganin fuskar Musaddiq zaka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali ne wanda baki bazai iya fad’i ba. Mutuwar Ikram ya dawo wa Musaddiq sabo. Mu’azzam ya k’ok’arin danne nasa tashin hankalin kad’an yana mai k’arasowa kusan Musaddiq d’in. Cikin wane irin yanayi Musaddiq ke dubansa “Is it true.?” Ya tambaya yana duban Mu’azzam d’in. Mu’azzam ya d’an kauda Kai gefe kad’an yana fuzar da fuci a hankali. Musaddiq ya sake fad’in “Da gaske ne.. Safeenah itace prime suspect.. Did she kill Ikram..? C’mon Mu’azzam answer me talk to me now.?!” Jinjin kai Mu’azzam yai a hankali yana duban Musaddiq d’in “I’m afraid yes.!” Ya k’arashe yana jinjina kai alamun tabbatarwa. Kauda Kai gefe Musaddiq yai yana mai rik’e bakinsa da duka hannayensa biyu.. Safeenah ta kashe masa Ikram. Ta rabasa da Ikram.. His very own sister.. Ji yai kaman bashi a duniyar, k’afafunsa na barazanar gaza d’aukansa. Cikin sauri Mu’azzam ya tallafosa ya rik’esa sosai “She.. Killed her.. Ta kashe mun ita.. Ta rabani da ita.. Maiyasa zatayi haka.?!” Saurin rungume Musaddiq Mu’azzam d’in yai yana jin zuciyarsa na masa rauni shima “That’s enough Musaddiq.. Ikram bazata wuce lokacinta ba.. Amma wad’anda suka kasheta need to pay.. I promise you, I’ll make them pay for what they did to her. They’ll pay dearly.” Ya k’arashe yana mai janyo Musaddiq d’in suka zauna nan saman wasu kujeru dake gaban wajen. A can interrogation kaw Safeenah dai kasa cewa komai tai sai ma duban Ameer da take da matuk’ar mamaki. Ya akai Ameer yasan anyi arresting d’inta.? Waye ya sanar dashi.? Yama akai har yaji komai ya taho in a very short time..? “Did I surprise you.?” Ya fad’i yana dubanta murmushi saman fuskarsa. Dubansa take har lokacin tana mamakin yanda akai yasan tana ofishin Yansanda. Lokaci guda ta jinjina kai tace “And you know I don’t like surprises..” Ta d’an dakata kafin tace “Ameer ya akai Kasan anyi arresting d’ina.. How did you find out about this in such a very short time.?” Ameer ya murmusa yana mai d’aura k’afa d’aya saman d’aya “Let’s say I do my homework.” Safeenah Ta girgiza kai tace “Ameer what kind of game are you playing..? Bayan threatening da kakeyi cewa Kasan wani abu game dani.. Now you appear as my lawyer. What is this Ameer..? Tell me mai ka sani gameda abinda ke faruwa dani.?” Ameer ya rage girman idanunsa yana karantarta irin dai yanda lauyoyi keyi idan suna karantar mutum gaskiya yake fad’i ko k’arya. Lokaci guda yake furta “Na fad’a miki I do my homework Safeenah.. And idan zaki tsaya kina b’ata ma kanki lokaci da tambayoyin da bazasu amfaneki na zaki tafi jail ne a banza a wofi ba tareda kin aikata laifin da ake tuhumarki ba.. Safeenah even your family basu baki support ba. you are all alone in this battle, ya kamata ki taimaki kanki ki cire kanki a wannan mess d’in.. And ni kad’ai ne mutumin da zai cireki a mess d’in da kika tsinci kanki ciki Safeenah..” Ya gyara zama yana mai tsareta da idanu “Now you tell me everything.. I mean kar ki b’oye min komai.. Ki fad’a mun duk abinda ya faru.” “What if I don’t.” Ta fad’i tana dubansa “You’ll have to Safeenah.. Idan har kinaso ki fita daga wannan mess d’in.. Unless kuma kinaso ki tafi jail for the crime you did not commit.” Safeenah daketa murza tafukan hannayenta kauda FUSKA gefe tai kafin a hankali ta soma furta “Mommy zata turo min lawyer, a very good one.. I don’t trust you, and I don’t want you to handle my case.. Ka gane..” Murmusawa yai yana dubanta kafin yace “What if nace miki Mommy ce ta turo ni.?” In a shock take kuma dubansa, ta girgiza kai kad’an tace “Pardon..” Ameer ya d’an matso kad’an yana mai d’aura duka hannayensa saman table d’in “Feenah.. You need to cooperate with me idan har kina so ki ceci kanki.. Kema kin sani Mu’azzam zai komai Domin ya Turaki gidan yari.. Kuma ina mai tabbatar miki a halin yanzu zai wuya yaci gaba a zama dake matsayin mata da miji.. We are talking about his sister here Feenah.. Kina dai ganin yanda ya bada himma wajen ganin yayi nasara kan binciken da yake.. Kar ki bari bayan saye zuciyarki da soyayyarsa da yayi ya kuma saye miki freedom d’inki.. Ki tashi ma kanki kafin lokaci ya k’ure I’m sure baza’a d’auki lokaci ba za’a tafi kotu.. You don’t belong here Feenah.. You deserve a good life tareda mijin dake knaunarki.. Kar ki bari Mu’azzam ya d’auke miki wannan..!” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu. Hawaye ne Safeenah taji na zuwa mata. Cikin muryar kuka take furta “Ban aikata ba.. I swear I didn’t do it.. But I don’t know.. Ban San ya zanyi bayani Mu’azzam ya fahimceni ba..” Katseta yai da fad’in “Ba wa Mu’azzam zaki fad’i ba Safeenah.. Idan kuwa kikai gangancin fad’iwa Mu’azzam zaki k’ara kulle kanki cikin case d’in ne.. Kar ki mance cewa Mu’azzam shi yake gudanar da bincike kan case d’in nan.. Sannan Ikram ‘yaruwarsa ce.. So ko mai zaki ce bazai yarda ba Safeenah.. Kece kawai zakiyi duk yanda zakiyi ki zame kanki.. And don’t forget, You are well and fully entrapped in this case.. You’ve no way out domin kuwa Tabbas an tura miki sak’on address na location d’in da aka tsinci gawan Ikram.. And you received that text message.. But don’t you worry zan wanke ki a Kotu in sha Allah.. And I’ll do it to the best of my abilities.. I promise you.. Kawai abinda nike so dake shine ki bani had’in Kai Safeenah.. Hundred percent.. Kin fahimta..?” Ya k’arshe yana kuma tsareta da idanu. Safeenah ta share hawayen da ya zubo mata. Daidai lokacin Mu’azzam ya turo k’ofan ya shigo domin kuwa lokacin da aka d’ibar mata na ganawa da lawyer d’inta ya cika. Ya tsaresu da idanu musamman Safeenah dake matsan k’walla. Lokaci guda Maleeka ta kawo kujera ta ajiye ma Mu’azzam nan jikin table d’in. D’akin binciken ya zamto su uku kenan ciki.. Safeenah sai Ameer Wanda take lawyer d’inta ne saiko Mu’azzam mai gudanar da bincike. Ajiye wayar Sagir Mu’azzam yai saman table d’in kafin yace “An tura miki wannan sak’on da lambar ki a ranan 12 ga watan June.. You can’t deny it domin kuwa munada shaidan da zai tabbatar an tura sak’on zuwa layinki sannan Kinyi receiving.. Just admit it already..!” Ameer ne ya katseta da fad’in “Excuse me Mr Inspector.. Are you suggesting that my client committed that crime.?” Wani duban Mu’azzam ya aika masa kafin yace “I don’t remember asking you.. Safeenah nake tambaya kuma ita zata amsa min.!” Safeenah dake sakin huci tana duban Mu’azzam d’in lokaci guda itama take furta “I have the right to be assistant by a Legal Counselor.. And Ameer here, is my Lawyer.!” Ameer ya murmusa yana duban Mu’azzam d’in “Calm down Inspector.. Ina fata ka saurari matarka, I’m only her Lawyer. So don’t bring up your personal issues with me here.” A wulak’ance Mu’azzam ke aika masa wani irin duba kafin yace “I don’t give a damn about you, Mr lawyer. Now you tell your client to answer my question.!” Safeenah ta girgiza kai tace “Wannan layin tsohon layina ne.. Kuma ni banyi receiving sak’on ba.” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Amma bayan wannan ranan kika canza layin..? Haka ne.. So definitely wannan sak’on ya isa miki.” Wannan karon Ameer ne Yai maganar “You heard my client Mr Officer, batai receiving sak’on ba. Gidan biki ne kar ka mance kuma ita d’in Amarya ce wacce aka sani da zafin kai, so za’a iya tura sak’on wayar nata na hannun wani.. So ba lallai ita tayi receiving wannan sak’on ba. And da kake maganar canza layi ansan most of Amare suna canza layi idan sukayi aure.. So ina shawartanka da ka daina d’aura wa client d’ina laifi kai tsaye.. Sannan sauran tanbayoyinka zaifi kyau ka ajiyesu ka sanar da lauyanka har dai zuwa ranan da zamu tafi Kotu.” Ameer yana ida fad’in haka ya mik’e yana gyara zaman suit d’insa. Mik’ewa Mu’azzam d’in ma yai yana aika masu wane irin kallo “You must talk Safeenah.. Sai Kinyi magana tun kafin aje Kotu na miki alk’awari.. Zaki fad’i komai..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga room d’in. Koda aka fito da Safeenah za’a kaita cell d’inta a nan ta had’u da Musaddiq yayi tsaye yana aika mata wane irin duba. Safeenah ta rok’i sergeant d’in Ta barta tai magana da D’anuwanta. Musaddiq ya k’araso yana mai zuba mata rinannun idanunsa “Tambaya d’aya nake so na miki. Maiyasa kika aikata..? Why did you do it Safeenah..? Maiyasa kika rabani da Ikram..?” Girgiza kai Safeenah take tana duban Musaddiq “Wllhi ban aikata ba Musaddiq ka yarda dani.. And I know nothing about it..” Jinjina kai yai yana dubanta kafin yace “Idan ya tabbata akwai saka hannunki a kisan Ikram ki mance kinada D’anuwa Musaddiq..!” Yana ida fad’in haka ya juya ya fice Safeenah na kiran sunansa ko tsaya baiba balle ya tankata. Haka sergeant d’in ta tasa kanta ta turata zuwa cell d’inta.. Wai yau Safeenah Marwan Gamji ce a cikin cell, ‘yansanda na tsare da ita.. Abunda ko a mafarki bata tab’a hasasho kanta a irin wannan yanayi ba.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un. Tabbas idan Bawa bai mutu ba bai gama ganin jarabawar rayuwa ba.. Sai masifa Safeenah take tana fad’in azo a fiddata daga cikin cell d’in nan ita bazata iya ba. Sergeant ta darara mata tsawa “Ke Malama Ki mana shiru.. I know you live in a mansion, you better get used to staying jail.. Kin zaci a 5star hotel kike da zaki ishe mutane.. And don’t expect any VIP treatment Dan kina matar Inspector Gamji.. Yanda ake ma criminals d’in dake cikin cell d’in nan haka za’a miki.. Idan kina san samun rangwame shine ki bud’e bakinki ki fad’i Iyakacin abinda kika sani idan kuma ba haka ba. Yanzu kika fara zama behind bars har ki dangana ga Prison that is idan ba’a yanke miki hukuncin kisa ba.” Safeenah ta zaro ido waje tana girgiza kai “No.. Bazai tab’a yuwa ba wllhi.. Nayi imani da Allah ban aikata ba babu kuma wanda ya isa ya hukuntani akan laifin da ban aikata ba ban kuma San wa ya aikata ba.. Ameer do everything you can to get me out of this place.” Ta k’arashe tana duban Barr Ameer kaman zatai kuka. Ameer yace “Ki kwantar da hankalinki Safeenah. Zaki fita daga wajen nan.. I promise you.!” Ya k’arashe yana mai jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa. ** A b’angaren Mu’azzam gaba d’aya zuciyarsa a jagule take. Ji yai kaman k’irjin ya masa mugun nauyi. Tamkar dai ya gaza d’aukan abubuwan dake cikin k’irjin nasa.. Gaba d’aya baisan meke masa dad’i ba daga jikinsa har duniyar Tasa ga kansa dake wani irin sara masa tamkar dai kan nasa zai rabe gida biyu. Sun jima suna tareda Assad har dare, Assad na kuma shawartansa da ya d’auki abubuwa da sauk’i kafin daga bisani yai ma Assad d’in sallama. Bayan rabuwarsu da Assad Tsayawa yai a wani chemist ya sai maganin ciwon kai kafin ya nufo gida. Yana shigowa gidan ya zube a nan parlor had’ida lumshe idanunsa yana tinanin abubuwan da suka faru a ranar. Rana ce data kasance mai tsawo a garesa.. Kiraye kirayen sallar isha da aka soma ya sanyasa mik’ewa ya nufi d’akinsa. Saida ya tsaya ya dubi k’ofar d’akin Sadiya na d’an lokaci kafin ya maidoda dubansa zuwaga katafaren hoton aurensu shida Safeenah dake aje wajen. Take yaji zuciyarsa na kuma masa zafi kansa naci gaba da sarawa. Lumshe idanunsa yai a hankali kafin ya nufi nasa d’akin. Tana jin tab’a k’ofa ta mik’e daga zaunen da take tana aikin abu d’aya Wato kuka. Ba kukan abinda matar Mu’azzam da ‘yanuwanta sukai mata a ranan take ba. Kukan rashin sanin halinda ahalinta ke ciki take. Yinin ranan kuka take ga tsananin ciwon kai da ya addabeta itama. Ta fito da sauri tana lek’en ta ina zata gansa ta tambayesa ko an samu su Umma amma bata gansa ba. Baya kitchen sannan baya parlor.. Ta dubi k’ofan d’akin da take tinanin nasa ne. A hankali ta lumshe idanun nata wasu hawayen suka kuma gangarowa.. Bata shiga d’akin ba ta koma da baya ta nufi nata d’akin ta gudanar da sallar isha da tuni aka kira har wasu masallatan sun shiga. Ta jima tana addu’o’inta tana sauraron ko zataji bud’e k’ofan d’akinsa amma shiru bataji ba.. Ta soma tinanin kodai ya fice daga gidan ne bataji fitarsa ba.? Ai kuwa bataci ta zama ba, bazata bari ya fice ba tareda ya sanar da ita komai gameda neman mahaifiyarta da ‘yanuwanta da yai mata alk’awarin zai ba.. Bazai yuwu ya kulleta a wannan kurkukun ba ya hanata fita neman ahalinta sannan shi ya gaza yin komai.. Ta mik’e da sauri ta fito tana dubasa cikin gidan. Bai ko ina sannan ga motarsa a haraban gidan. Definitely yana cikin gidan kenan. D’akinsa ne kawai yai saura bata duba ba, yau kam zata shiga domin tasan wani hali Umma dasu Habeeb suke ciki.. Ta isa jikin k’ofar d’akin ta murd’a handle d’in a hankali nan taga k’ofar ya bud’e. D’ago idon da zatai ta hangesa kwance saman sallaya yana sanye da jallabiya mai ruwan sararin samaniya.. Take ta shiga sakin huci, Wato ma kwanciyarsa yazo yayi mahaifiyarta da ‘yanuwanta suna can ba’asan duniyar da suke ba. A zuciye ta shigo cikin d’akin tana fad’in “Mr Inspector ka tashi ka sanar dani Ina ahalina suke.. Bazai yuwu ka ajiyeni a wannan kurkukun da kake kira gida ba sannan kazo kai kwanciyar ka ba tareda sanin ina ahalina suke ba..!” Shiru taji bai amsa ta ba sannan ko motsawa daga yanda yake kwance bai ba.. Nan Ta soma rau rau da idanu cikin rawar murya take fad’in “Nasan tsiwa bazai saka ka kai abu ba.. But please na rok’eka ka k’yaleni na fice na nemosu da kaina.. Please Mr Inspector.. Just put yourself in my place.. Dan Allah please..!” Ta k’arashe kuka na zuwa mata. Har lokacin yana nan kwance bai ko motsa ba.. Abun ya soma k’ular da Sadiya ganin ya bata baya ko juyowa baiba balle ya amsata. Ta k’araso ta yanda fuskarsa ke kallo nan taga idanunsa a lumshe suke. Takaici ya kuma cikata. “Mr Inspector..!” Ta fad’i daidai saitin fuskarsa. Shiru bai amsata ba.. Ta shiga bubbuga gefen sallayar tana ambato sunansa, nan ma dai shiru bai amsata ba har lokacin idanunsa a lumshe suke. Nan ne fah tsoro ya soma kamata, gani tai tamkar ma bai numfashi.. Taci gaba da buga gefensa tana ambaton sunansa.. Ganin da gaske dai k’ila numfashi ne baiyi ya sanyata matso da kunnenta guda saitin hancinsa taji kodai numfashin ne baiyi.. Aiko nan taji tamkar dai bai numfashi.. Girgiza kai ta soma tana fad’in “Oh no.. He’s not breathing..! What do I do now..? Na shiga uku ni Sadiya ya zanyi..? Who do I call..?” Ta soma girgiza kai cikin birkicewa da tinanin mai zata aiwatar. “The gateman.. Shi zan kira.. Bara nai sauri na kirasa..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin mik’ewa saidai kafin ta ida mik’ewa taji Mu’azzam ya kamo hannunta ya janyota ta fad’o jikinsa. Zaro ido tai tana duban fuskarsa wanda har lokacin idanunsa a lumshe suke yana sakin murmushi a hankali. Still idanun nasa a lumshe yana shak’an k’amshin jikinta yake furta “Your perfume is nice.!” Takaici ya cika Sadiya, Wato dama duk yana jinta yai banza da ita, tana maganar neman ahalinta shi ta perfume ma yake, wai your perfume is nice.. Ita da ko turare bata saka ba bayan kayan wanka masu k’amshi da ya tara mata a toilet.. Inama taga wani nastuwan fesa perfume..Ta shiga kokawan cire jikinta daga nasa tana fad’in “You.. You scared me.. Let me go now.. Inspector.” Bai sakenta ba har lokacin saima sakin murmushin da yake still idanunsa a lumshe. Saitin kunnenta yake furta “Did I scare you..? Kin zaci kin rasani kenan..? Kar ki damu bazan mutu ba until our mission is finally accomplished..!” Turasa tai da k’arfi tana fad’in “Toh kama mutu mana. Who cares.. The only thing da na damu dashi shine kar ka mutu baka samo mun Ummata da k’annena ba.. I don’t care idan ka mutu..” Ya bud’e lumsassun idanunsa wanda da gani zaka fahimci baijin dad’i yana dubanta dasu. Still murmushin ne saman fuskarsa yana duban yanda take sakin huci “Don’t make the mistake of falling for me, because I’ll never love someone like you.” Ya fad’i idanunsa akanta. A yatsine ta dubesa kafin tace “I’d rather die than to fall for someone like you. Mr Inspector.! Now you let me out and look for my family.” Ya kuma murmusawa kafin yace “Kina son sanin ina ahalinki suke.?” Tai saurin jinjina kai tana dubansa. Ya jinjina kai kafin yace “I’m sick, and I need someone to take care of me.. Can you stay here in my room and look after me..?” Galala take dubansa kafin tace “Allah ya sawak’e mun..!” “Ashe baki son sanin ina suke.. Kin mance cewa yin hakan duk cikin mission d’inki ne..” Sadiya tai rau rau da idanu tana dubansa, dik wani salon mugunta ya sani, dik abinda zai yi ya k’untata mata shi yakeyi da sunan mission. Tasa bayan hannunta ta goge hawayenta “But you’re not a baby. You can move your hands and legs.. Mai yasa zan tsaya na kula da kai.” Duban fuskarta yake musamman d’an bakinta da taketa faman turo shi gaba kafin ya soma k’ok’arin mik’ewa zaune, yace Ta mik’o masa pillow. Baki a ture ta isa ta d’auko pillow d’in, ya d’an matsar da bayansa alamun ta saka masa pillow d’in jikin gadon. Nan ma fuska babu walwala ta k’arasa ta saka masa pillow d’in ya d’an jingina bayansa. “Sai mai kuma.?” Ta tambaya Cikeda k’osawa. Juyawa yai gefen bedside yanda magani da ruwan gorar ke ajiye yace ta mik’o masa. Babu musu Ta isa tai yanda yace d’in. “Saura cup.” Ya fad’i yana dubanta. Babu musu ta sauk’o downstairs ta haura masa da glass cup. Ya dubeta yace ta zuba masa ruwan ciki. Nan ma babu musu tai yanda yace Ta mik’a masa. Maganin ya d’auka ya b’alla yasha, lokaci guda ya maida kansa ya jingina jikin pillow d’in had’ida lumshe idanunsa. “Zan iya tafiya..?” Sadiya ta tambaya tana dubansa. Still idanunsa a lumshe yake fad’in “I might need something.. You stay here until I fall asleep.. Amma idan baki so na kaiki kuma fine.. Kina iya tafiya..” Idanunta sukai raurau, ta koma gefe ta zauna ta tak’ure cikin hijab d’inta Dan ji take sanyin AC d’in dake d’akin ya mata yawa ga sanyin damina.. Gaba d’aya sai kan nata yaci gaba da sarawa. Suka d’ibi lokaci a haka, yana nan kishingid’e idanunsa a lumshe. Sadiya kaw Sai rawan d’ari take tana daga can gefe tak’ure cikin hijabi. Maganin dake gefensa Ta hanga takeda tabbacin na rage rad’ad’in ciwon kai ne. A hankali ta sad’a’d’a ta d’auko maganin da ruwa ta b’alli guda biyu tasha ko zataji sauk’in ciwon kan dake damunta. Mu’azzam yana jinta saidai bai bud’e idonsa ba baice komai ba har ta dawo da maganin Ta ajiye. Ta koma taci gaba da tak’urewa tana rawar d’ari. A haka take jin ciwon kan nata na raguwa saidai kafin tai wani aune bacci yayi gaba da ita nan yanda take zaune. Ya bud’e idanunsa yana dubanta, nan yaga tayi bacci.. Ya dubi maganin yaga har guda biyu tasha, yasan dole zai mata k’arfi sannan zai sakata bacci. Yai mata K’uri yana dubanta yanda ta tak’ure tana bacci. A hankali ya mik’e ya isa ya d’aukota ya kawota kan gado ya kwantar. Lokaci guda ya rage sanyin AC d’in. Hijab d’in jikinta ya soma k’ok’arin zame mata Dan ta samu tai baccin a sake. Nan yaji bugun zuciyarsa na k’aruwa a lokacin da yake cire mata hijab d’in. Kasancewar duk English wears ya saya ya aje mata a wardrobe d’in yasa bata da wani tufafin sakawa face su. Saiko dogayen riguna dangin abaya. Nan yaga wata jan riga ce doguwa Wanda ta d’an kama daga k’irji zuwa ciki saiko k’asan dake baje shine a jikinta.. Yai saurin kauda kansa gefe yana jin zuciyarsa na kuma tsinkewa.. A hankali ya lumshe idanunsa yana furtawa a hankali “What’s wrong with you Mu’azzam.. Kar kyaun jikinta ya rud’eka Ta riga Ta rabar dashi ma wasu banzaye.. Ita d’in bata cancanceka ba.!” Tina hakan da yai Sai ya kuma jin zuciyarsa na masa zafi.. Cikin sauri ya janyo bargo ya rufa mata, ya sauk’o daga saman gadon ya dawo nan k’asa yanda ya tashi ya kuma kwanciya yana lumshe idanunsa, saidai duk rufe idon da zaiyi kyakkyawan surar jikinta yake gani.. Ya mik’e ya zauna yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa yana jin bugun zuciyarsa na k’aruwa.. Meke faruwa dashi..? Badai sha’awan yarinyar nan yake ba.. Kai never..! God forbid..! Ya kuma lumshe idanunsa, ji yai zaman d’akin na neman gagaransa. Ya mik’e ya bud’e k’ofar balcony yana shan fresh air na damina.. nan yaji k’aran hadarin dake sararin samaniya na k’aruwa. Kan kace mai an soma ruwa kaman da Bakin k’warya. Ya mik’a fuskarsa waje ruwa na zubo masa saman fuskar nasa, idanunsa a lumshe ko zai daina ganinta amma babu abinda ya canza Ita d’in dai yake gani.. Ya yarda sha’awanta yake sannan bai tunanin zai iya rik’e kansa har gari ya waye.. Toh amma ta yaya zai had’a jiki da fasik’a irinta..? Wata zuciyar tace masa ai kai ba fasik’anci zakayi da ita ba ka biya sadaki, ka fanshe sadakinka tinda dama Ta saba a biyata kud’i ta bada jikinta.. Kai Naka ta halattacen hanya zakayi akwai igiyan aurenka har guda UKU akanta wanda sun halatta maka Ita. Ya bud’e idanunsa yana fuzar da fuci a hankali.. Toh amma ta yaya zai soma tunk’aranta da batu irin wannan aima sai ta rainasa ta maidashi D’anhannu irinta.. Ya saka hannayensa biyu ya shafi sumarsa da suke wet ya maidasu baya.. Zuciyarsa tana fad’i masa this is the perfect opportunity for you Idan baka so ta fahimci wani abu ya shiga tsakaninku kaje mata a cikin barci bazata fahimci komai ba.. Besides tinda an samu suspect shikenan zaka rabu da ita bazata kuma dawowa cikin rayuwarka ba.. Da wannan tunanin Mu’azzam ya dawo cikin d’akin. Yana tina suffarta da kuma ni’imtaccen k’amshin da yaji cikin jikinta.. A cikin baccin ya dinga sarrafa sassan jikinta yana mamakin mace da ta gama yawon ta zubar jikin nata bai sake ba, komai zamzam kaman dai na sabuwar budurwa wacce bata tab’a sanin wani d’a namiji ba.. Tin daga nan jikin Mu’azzam ya soma yin sanyi yanajin zuciyarsa na masa wani irin rauni.. Bai ida shan mamaki ba saida yazo shiganta yaji kirif babu alamun ta tab’a tarayya da wani d’a namiji.. Cikin tsananin sanyin jiki ya tsaya cak ba tareda ya ida nufinsa ba.. Ya d’ago yana duban fuskarta wanda har lokacin idanunta a lumshe suke alamun bacci take.. Take yaji bugun zuciyarsa ya k’aru.. Toh kodai idan mace tayi tarayya da wasu mazan bayan wani lokaci idan ta jima batayi ba tana komawa budurwa ne..? Da kansa ya bama kansa amsa da fad’in no never.. Sabo Sabo ne.. Koda ace baisan halitta ‘ya mace practically ba ya sani a karance.. A hankali yaji bakinsa na furta “She’s verging..!” Cikin tsananin sanyin jiki ya mik’e kaman wanda aka zare ma laka. Ya shiga janyo mata tufafinta yana maida maida mata. Ya janyo bargo ya kuma rufa mata bayan ya gyara mata kwanciyarta. Yai zaune had’ida mata K’uri yana duban fuskarta lokaci guda yana jin wani abu mai kaman tausayinta can k’asan zuciyarsa.. Kalaman b’atanci da ya dinga fad’a akanta yake tunawa da irin wulak’ancin da ya dinga yi mata.. Toh kenan batabi mazan bane kokuwa dai sharri ake mata..? Toh Wai shin meke faruwa ne..? Ya kuma tambayar kansa yana dubanta. Tabbas ya shiga rud’u da rashin sanin abinda zai yarda dashi.. A hankali ya mik’e daga kan gadon ya nufi bathroom ya d’auro wankan tsarki. Ya dawo cikin d’akin har lokacin baccinta take. Drawer ya isa ya d’auki takarda da pen yai rubutu saman takardan ya linke ya ajiye mata nan gefenta. Sadiya kaw maganin bai saketa ba Sai wajajen k’arfe bakwai na safe, Ta mik’e taji idanunta sun mata nauyi.. Nan ta ganta a d’akin Mr Inspector saman gadonsa.. Take ta soma tuna abinda ya faru a daren jiya, ya sanyata zaman d’akinsa da sunan baida lafiya.. Tai saurin mik’ewa tana k’ok’arin sauk’owa daga saman gadon, nan taga takarda ya fad’o.. Ta mik’a hannu ta d’auko tana addu’an Allah yasa takardan saki ne ya ajiye mata. Allah yasa Ta gama mission d’inta kenan.. Da wannan tunanin ta warware takardan. Zuciyarta ne yai wani irin tsinkewa sakamakon abinda ta gani rubuce cikin takardan _Thank you for taking care of me last night. Dare ne mai cikeda rud’ani.. Dukda cewa babu abinda ya faru, but still kiyi wanka ki tsarkake jikinki_ Sai aka rubuta Mr Inspector daga k’asan note d’in. Jikinta ne ya d’auki rawa, ta k’unshe bakinta da duka tafukan hannayenta tana girgiza kai.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Mai ya faru da ita.. Mai Mr Inspector ya aikata mata.. Tasha magani ya sakata bacci.. Kenan Mr Inspector yayi attempting raping d’inta alhalin tana bacci.. K’ank’ame jikinta ta soma hawaye na zubo mata, cikin tsananin rawar murya take furta “Monster..! Monster.. How could you..? You are a monster..!!!” Ta fashe da wani irin kuka tana k’ank’ame jikinta. Ya mata abinda bazata tab’a yafe masa ba. Ta mik’e tana kuka ta nufi nata d’akin ta fad’a bathroom.. Haka tai wankan tana kuka tana darje illahirin jikinta.. Sosai take kuka tana jin tsanar Mu’azzam wanda bata tab’a yin irinsa ma wani bil Adam ba. Bayan tayi wanka tayi alwala tai sallah har lokacin kuka take tana jin zuciyarta na mata wane irin zafi.. Ya bud’e mata jikinta, sannan ya kalle mata jikinta harma yayi abinda yaga dama da jikinta alhakin tana bacci.. Cikin k’unan zuciya hawaye na zubo mata take furta “He’s a Rapist.. He tried to rape me while I was asleep.. How could he..?!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin wani kukan. Ta mik’e tana goge hawayenta. Lokaci guda ta koma d’akin nasa Ta d’auki pen d’in da paper d’in da ya rubuta mata note d’in. Can k’asan rubutun tana hawaye Ta soma rubutu itama. _I’ll never forgive you for what you did last night.! Aside from being a Kidnapper you are also a rapist, Mr Inspector. You are a Criminal, baka cancanci zama D’ansanda ba. Kai d’in D’antadda ne.. Zan iya yafe maka komai, all the insults wulak’anci and all.. But abinda kayi daren jiya abu ne da bazan tab’a yafe maka ba.. Har abada. The game is over, and the mission is accomplished. Mr Inspector_ Ta ajiye masa nan kafin Ta mik’e ta nufi gate tana hawaye. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *33* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Zaune ta tadda D’ansandan saman benchinsa, yana ganinta ya mik’e yana sara mata “Good morning Ma’am.” Ya fad’i cikeda risinawa. Sadiya tai k’ok’arin saita kanta kafin tace “Morning..” Shiru ya d’an biyo yana sauraron mai zatace. Kanta ta d’an dafe kana tace “Magani nake son zuwa saye zaka bud’e mun k’ofa yanzu.” Ya d’an dubeta yana girgiza kai “Ma’am I’m really sorry.. I was instructed not to let you out.” Ta tsaresa da idanu tana dubansa tana kuma kame kanta “I told you magani nake so, ko so kake na mutu maka a wajen nan.. Kai D’ansanda ne kafi Kowa sanin mai hakan ke nufi idan na fad’i maka a wajen nan.. So you better let me out now..” “Ma’am I’m sorry.. Idan na barki kika fice, Boss won’t sapere me. Kiyi hak’uri ki koma cikin Gida..” “Am I a prisoner da bazaka barni na fice ba.?” Ganin ya kifa Kai k’asa bai amsata ba ya sanyata dafe kanta tana ‘yank’ararraki kad’an tana k’ok’arin duk’awa k’asa alamun tana jin jiki. Police d’in ya matso a daburce yana tambayarta “Ma’am are you alright... Do you want me to call Boss..? Ma’am..” Bata amsa Sa ba Sai kame kanta da cikinta take tana fad’in idan bazai barta Ta fice ba shi yaje ya nemo mata maganin.. Yanda takeyi dole kayi tunanin da gaske batada lafiya. Cikin daburcewa ya mik’e yana k’ok’arin zaro wayarsa da niyyan kiran layin Mu’azzam. Sadiya ta kannare ido tana dubansa daga nan yanda take kwance nan ta soma fad’in “Hey what are you doing.? Can’t you see I’m in pain. Just go to any nearby pharmaceutical and get me medicine.. Wayyo cikina.. Kaina.. I can’t breath..!” Abubuwan da ta dinga fad’i kenan daga nan yanda take kwance wanda ya kuma birkita mutumin. Gashi ya gaza samun layin Mu’azzam.. Dole ya fice yana fad’in bari ya nemo mata magani. Yanda ya fice haka ya bar k’ofan a bud’e ko tinawa ya kulle baiba. Aiko sanda ta tabbatar ya fice ya bar ma layin sannan ta mik’e tana hamdalah. Ba tareda Wani b’ata lokaci ba tasa kai Ta fice daga GIDAN ARO. Ta juyo tana duban gidan bayan ta fice, hawayen da ya gangaro mata ta goge kafin tace “Wannan shine k’arshe bazan kuma dawowa cikinka ba in sha Allah.!” Tana ida fad’in haka tasa kai Ta soma sauri sauri tana mai ficewa daga layin gaba d’aya. ** Assad ya shigo Coffee shop d’in yana mamakin kiran da Mu’azzam d’in yai masa yace Su had’u nan da sassafe irin haka. Assad ya k’araso sukai musabaha still mamaki saman fuskarsa. Mu’azzam ya tambayesa abinda za’a kawo masa. Nan yace a kawo masa coffee d’in shima. Yai zaune yana duban Mu’azzam d’in yana jira yaji da mai zai fara. Bayan an kawo wa Assad nasa order d’in ya sinkayo muryar Mu’azzam na fad’in “Nasan ka tab’a aure zama baiyi dad’i ba Kun rabu da matar..” Assad ya dubesa da mamaki jin yau kuma da wannan batun yazo, shi ya zaci ma wani ci gaba suka kuma samu daga binkicen da suke. Assad ya jinjina kai yace “Haka ne.” Mu’azzam ya kuma sipping hot coffee d’insa kafin yace “Kanada experience, kasan halittan mata kenan.” Yanzu kam aje cup d’in dake hannunsa Assad yai yana duban abokin nasa da tsananin mamaki wanda a baya sam bai irin wad’ann zantukan. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Inaso na maka tambaya a matsayinka na wanda yakeda experience.” Assad ya jinjina kai yace “Umhum ina saurarenka. “Idan mace ta gama yawonta da biye biyen maza, after some time ta jima batabi mazan ba tana koma sabuwa ce kaman dai budurwar da bata tab’a sanin wani d’a namiji ba.?” Bagatatan Assad yaji zancen wanda har saida ya kusan fuzar da coffe d’in da ya shiga bakinsa sabida dariyan da yazo masa.. Da alama abokinsa ya shiga missed call.. Ya k’unshe bakinsa yana darawa a hankali dan Yanzu kam ya gama gane Ina tambayoyin Abokin nasa suka nufa. Mu’azzam ya aika masa mugun kallo cikeda takaici “You are not serious, you know. Ya ina tambayarka abu kana wani dariya..” “Toh kuka kake so nayi.. Abun ne abun dariya.. Budurci guda d’aya ne ai.. Halitta ne da Ubangiji ya Karrama ko wace d’iya mace dashi, wacce ta watsar da wannan karamci nata tin a titi bazata kuma samunsa ba, bazai dawo ba duk gyaran da za’ayi kuwa.. Bazata tab’a zama kaman wacce ta Martaba wannan karamci nata ta rik’esa da kyau ba.” Mu’azzam ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana mai sipping coffee. Lokaci guda Assad yaci gaba da fad’in “Shiyasa shaidar zina dai takeda matakai daki daki..Ku guje ma mummunan zato ma bayin Allah.. So tari wanda ka munana masa zato shine na k’warai d’in. Sannan so tari wanda ka kyautata masa zato shine na banzan. Amma ko yaushe ana so mutum ya kasance mai kyautata zato.. Ku guje ma d’aukan maganganun mutane domin shi d’anadam a Kullum aibunka yake nema ya yad’a, Sai ya yad’a aibunka sau d’ari kafin ya fad’i alkhairinka guda d’aya.. Ga aibun a tattare da shi amma shi bazaiga nashi ba sai yaje yana hangen na wani.. Allah yasa mu gane ya kuma datar damu.” Mu’azzam ya amsa da Ameen. Yana mai ci gaba da shan coffee d’insa. Time ya duba yaga Wai har tara na safe Ta d’an gauta ya kamata Su k’arasa Office.. A tare Suka mik’e Mu’azzam yai settling bill d’insu kafin suka nufo waje. Babu b’ata lokaci suka nufo ofishinsu. Suna isowa suka tadda Daddy a k’ofan Ofishin nasu. Assad ya dubi Mu’azzam “Wa nake gani kaman Daddy..? Allah sarki ni wllhi duk yafi bani tausayi a al’amarin nan.. Mutumin nan yana k’aunarka Mu’azzam, kaga yanda ya juya ma d’iyarsa baya yak’i ya bama k’arya goyon baya dukda cewa yanada halinda zai iya sakawa a kashe case d’in nan a rufe case d’in gaba d’aya sabida d’iyarsa amma baiyi haka ba.. Gaskiya na jima banga mutum mai dattako da kiman Daddy ba.” Mu’azzam ya jinjina kai yace “K’warai Daddy mutumin kirki ne.. Bai cancanci d’iya irin Safeenah ba.. Unfortunately bamu zab’en ahali, farkawa muke kawai mu ganmu tareda mutanen da Allah ya hukunta zasu zama ahalinmu.. Sannan ko wanne ahali sunada nasu k’alubalen da suke fuskanta.. Mu kuma irin namu k’alubalen kenan.. Mu k’arasa..” Assad ya jinjina kai kafin suka nufo yanda Daddy ke zaune. Gaisawa sukai gaba d’aya kafin Assad ya Shige ya basu waje. Daddy ya dubi Mu’azzam wanda jinkinsa ya d’anyi sanyi da ganin Daddyn.. Ko Babu komai Safeenah d’iyar Daddy ce jininsa ce dole zaiji wani abu can k’asan zuciyarsa dukda kuwa k’arfin halin da yai. Mu’azzam yace “Are you here to see Safeenah.? Mu k’arasa sai a kira maka ita..” Daddy ya girgiza kai yace “Ba Safeenah nazo gani ba Mu’azzam.. Kai nazo gani..” Mu’azzam ya d’an gyara zamansa yana duban Daddyn. Daddy yaci gaba da fad’in “Mu’azzam bazan hanaka hukunta Safeenah akan laifinta ba idan har an kamata da laifin.. Amma inada wata alfarma guda d’aya da nake son rok’a daga gareka.” Mu’azzam ya d’an d’ago ya dubesa “Alfarma kuma Daddy.. Ai ka wuce alfarma a wajena Daddy.. Umarni kawai zaka bani..” Daddy ya murmusa cikeda jin dad’i kafin ya jinjina kai yace “Allah ya maka albarka Mu’azzam.. Alfarmar da nake nema wajenka shine, dan Allah kar ka saki Safeenah har sai an gama bincike an sameta da laifi.. Kamin wannan alk’awarin cewa bazaka rabu da ita ba har sai an tabbata Tanada laifi.. This is the least I can do for my daughter bayan juya mata baya da nayi..” Ya k’arashe yana duban Mu’azzam d’in cikeda kulawa. Cak Mu’azzam ya tsaya ba tareda ya iya amsa Daddy ba, saima sadda idanunsa k’asa da yai. Daddy yai gyaran murya yaci gaba da fad’in “I know it’s not easy, ace kana shari’a da matarka.. But please do this for me.. For our family Mu’azzam.. Kar ka saki Safeenah until she’s proven guilty.. Ina rok’onka ne a matsayin mahaifin Safeenah.. Please Mu’azzam..!” Ganin Daddy na k’ok’arin had’e hannayensa biyu waje guda alamun rok’o yasa Mu’azzam saurin kamo hannayen Daddy ya hanasa aikata hakan. Yana girgiza kai yake fad’in “Dani da Safeenah Kai Babanmu ne gaba d’aya Daddy.. Yanda zaka umarce Safeenah tai abu ko Musaddiq haka nima zaka mun.. Daddy bazan saketa ba kaman yanda kace.. Safeenah zataci gaba da zama matsayin matata..” Daddy ya sakar masa murmushi yana k’ok’arin maida k’wallan dake k’ok’arin ciko idanunsa “Na gode Mu’azzam.. Thank you for this.. Allah Ubangiji ya maka albarka ya kuma maka jagora.” Mu’azzam ya amsa da “Ameen Daddy..” Daddy ya mik’e yace “Alk’ali ya sanar da Court Hearing d’in ne..?” Mu’azzam ya girgiza kai yace “Muna sauraro tukuna Daddy.” Daddy ya jinjina kai kafin yace “Ni zan wuce Company.. Sai na ganka a gida..” Mu’azzam ya jinjina kai yana mai rakiyawa Daddyn har zuwa yanda motarsa ke ajiye driver na jira. Suka kuma yin sallama kafin Mu’azzam ya dawo cikin ofishin nasu. Yana shigowa Assad ya K’araso yana fad’in “Barr Ameer Dikko, Safeenah’s lawyer is here.. Yana son ganawa da Safeenah..” Sunan Ameer da Assad ya fad’i in full shine yai ringing a k’wak’walwar Mu’azzam. Barr Ameer Dikko. Duban Assad yai kafin ya kuma duba Barr Ameer dake nufosu cikin takunsa na k’asaita. Ya k’araso yana gaisar da Mu’azzam cikeda izgilanci irin yanda ya saba. Mu’azzam bai ce masa komai ba Sai aiaka masa muguwar kallo da yake yana nanata sunansa cikin zuciyarsa. Assad ne yai masu jagoranci gaba d’aya zuwa interrogation yanda Safeenah ke zaune tana jira. A d’an Kwana guda da tai cikin Cell har kamanninta ya canza abinka da wacce bata saba da wahala ba. Farin fatar ta dik yayi wani irin jajaja alamun wahala da rashin sabo. Ameer ne ya soma shiga suka gana kafin daga bisani Mu’azzam ya shigo. Safeenah na ganinsa ta fashe da kuka tana fad’in “My Halal I can’t believe you are doing this to me.. Please ka k’yaleni na tafi gida.. This place is hell..” Ameer kaw takaici ya cikasa ganin yanda Safeenah ke shagwab’awa Mu’azzam tana wani kiransa her Halal. Zama yai gefe yana mai aikawa Ameer mugun kallo. Bai amsa Safeenah ba still idanunsa na kan Ameer yake furta “Barrister Ameer Dikko is your enemy.!” “Barr Ameer Dikko is ruining your home.!” “Barr Ameer Dikko is very BAD” “Barr Ameer Dikko you’re BAD” Cikin rashin gane kalman nasa suke dubansa daga Ameer d’in har Safeenah. Ameer ya girgiza kai yace “Ban fahimceka ba Inspector..?” Murmushi Mu’azzam yai kafin yace “Ba Lallai ka fahimta ba amma Iyakacin abinda na sani YOU ARE BAD..” Ameer ya kuma dubansa kai a k’ulle, lokaci guda Mu’azzam ya ciro wayarsa cikin aljihu yana nunawa Ameer sak’onnin BAD da akaita turo masa kwanakin baya. Ameer ya dubi sak’onnin da tsananin mamaki yana kuma duban Mu’azzam. Safeenah ma mamaki ne saman fuskarta cikin zuciyarta tana furta mai hakan yake nufi. Mu’azzam yaci gaba da furta “Ko Wanene mai turo mun wad’ann sak’onnin gargad’i yake mun akanka BAD.. And that means yasan Kun jima kuna k’ulla wani abu kenan kaida Safeenah.. Let’s say Ikram Ta fahimci wani abu taakaninku da Safeenah.. And you two silenced her sabida kar ta sanar dani.. Am I right..?” Ya k’arashe yana dubansu su duka biyun. Zuciyar Safeenah yai wani irin yankewa. Ta shiga girgiza kai tana fad’in “No.. Wllhi wlhi babu komai tsakanina da Ameer.. Wllhi bansan mai wannan sak’on ke nufi ba..” “Ai dama bazaki sani ba. Amma shi wanda ya turo min wani clue yake so ya bani game da ku biyun..” Mu’azzam ya fad’i yana tsare Safeenar da idanu. Ameer ya girgiza kai wannan karon yace “Excuse me Mr Office. Mai kake k’ok’arin fad’i.. What are you trying to accuse us of.? BAD everyone can be BAD.. You can also be BAD... Bad is just a word.. So don’t try to complicate things here..” Murmushi Mu’azzam keyi wann karon yana duban Ameer d’in “We shall see.!” Safeenah dake girgiza kai tana hawaye lokaci guda Ta soma fad’in “Wait Mu’azzam wllhi zan fad’i gaskiyar abinda ya faru.. Kar ka fara zargina da cin amanarka balle aurenmu ya lalace.. Wllhi zan fad’i komai koda bazaka yarda dani ba.” Mu’azzam ya jinjina kai yana mai gyara zamansa lokaci guda yai alamawa Maleeka cewa ta shigo ta tattari bayanan Safeenah. Maleeka kaw kaman wacce take jira, nan take ta shigo.. Ameer sai aika mata mugun kallo yake a sace, yana tinanin idan ba Ita ba babu wanda zai tura ma Mu’azzam sak’on BAD dan yasan duk wanda ya tura sak’on so yake ya raba Mu’azzam d’in da Safeenah.. Maleeka ita kad’ai ce takeda wanann Motive d’in. Mu’azzam ya dubi Safeenah yace “Ehen go ahead ina sauraronki.” Safeenah ta soma fad’in “Kafin ranan aurenmu nayi receiving phone call daga wani mutumi, he told me he was an investor, yana son sayan Dairy milk da companyn mu ke producing... Ni kuma banso muyi losing client since ni ce ke rik’eda fannin saye da sayawarwa na Company d’in.. I didn’t want to disappoint Daddy.. I wanted to be perfect in his eyes.. Dikda cewa lokacin na kusan aure amma sai nayi accepting business proposal d’in.. Yai fixing date d’in da zamu had’u Mu tattauna kasuwancin, ranan ya fad’o daidai da ranan aurenmu.. Nace mishi bazai yuwu mu had’u mu tattauna kasuwancin wannan ranan ba amma sai yace mun shi baida lokaci daga wannan ranan, saidai a fasa kasuwancin.. Bana so muyi losing client nace masa babu damuwa zamu had’u mu tattauna kasuwancin.. Toh a ranan nayi receiving wannan text message d’in saidai banje location d’in ba dan zuciya na bai kwanta ba maiyasa zaice mu had’u a wani waje ba a Ma’aikatanmu ba.. Ban tab’a business da wani outside the company ba.. Shiyasa zuciyata bata aminta ba.. Kwatsam saiji nayi an tsinci gawan Ikram a wannan location d’in.. Wllhi wllhi Iyakacin abinda na sani kenan Mu’azzam.. Bansan ya akai Ikram ta tafi wannan location d’in da aka turo mun a matsayin meeting place ba..!” Ta k’arashe cikin kuka sosai. Mu’azzam da yai mata k’uri Maleeka na gefe tana tattara bayanan cikin k’aramar littafi. Mu’azzam ya kuma duban Safeenah kafin yace “And you expect me to believe your story..? Ta yaya zan San you’re not making it all up..? Idan gaskiya kike fad’i mai ya hanaki fad’i tuntuni..?” Safeenah ta girgiza kai tace “Wllhi gaskiya nake fad’i wannan shine abinda ya faru.. Naji tsoron kar ka k’i amincewa dani ne shiyasa ban fad’i ba..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “And shi mutumin da zaku k’ulla kasuwancin tare baki da contact dashi ne ko kuwa contact d’in ne ya yanke.?” Ta girgiza kai tace “I don’t even know him..” “How is this possible..?” Tana bada amsa yana kuma rikitata da wasu tambayoyin. Ta kuma girgiza kai tace “I lost contact with him tin wancan lokacin.. Na karya SIM card d’ina bayan na canza layi dan naji tsoro sosai da aka ce an sami gawan Ikram a wannan location d’in wanda bansan ya akai taje wajen ba.” “We are in a Global world Safeenah.. Tracking mutumin bazai tab’a yin wahala muddin kin tab’a samun contact dashi.. Unless kuma bakinku d’aya ne Keda shi.. Maybe Kun datse duk wata hanya da zai nuna kun tab’a samun connection dan kawai ku rufe laifin da kuka aikata ke da shi na kisan Ikram.. Admit Safeenah.!” Ya k’arashe cikin tsananin tsawatarwa. Ameer yai saurin dakatar dashi wannan karon “Inspector ya kamata ka gyara kalamanka...” Yusuf ne ya katsesu da fad’in “Someone has just confessed to the crime.” Mu’azzam ya juyo yana duban Yusuf, gaba d’ayansu dake cikin d’akin ma duban Yusuf suke. Mu’azzam ya girgiza kai yace “Mai kace..?” Yusuf yace “Wani mutumi ya zo yanzun nan sannan ya amsa laifin kisan Ikram...” Mik’ewa tsaye Mu’azzam yai yana tambayan Yusuf “Where is he..?” Yusuf yace “Gashi nan a office d’in Chief ana tattara bayanansa..” Cikin sauri Mu’azzam yasa kai ya fice yayinda Yusuf ya take masa baya. Maleeka ma bin bayan abokan aikin nata tai. Safeenah Ta dubi Ameer tace “Mai hakan yake nufi..?” Ameer ya tab’e baki kad’an yace “Ta yaya zan sani..? Ai ke zan tambaya.. Kwatsam Ana tuhumarki saiga wani ya amsa laifin..? Watak’ila wancan investor d’in ne da kukai deal tare..” Safeenah ta mik’e tana huci “Ai kuwa wllhi sai na shak’e D’anbanza naji uban da yasa ya sakani a wannan ukun..” Ameer ya tare k’ofa yana dubanta kafin yace “Not too fast Safeenah.. Ki tsaya kiji da mai yazo.” Harara Ta aikawa Ameer kafin tace “And who do you think you are da zaka dakatar dani.. Wanda yayi crime d’in ya bayyana kansa hakan yana nufin zan zama free sannan zan koma gidan Mijina.. Babu wata alak’a tsakanina dakai dan haka kar ka sake kallon ko yanda nake ne balle kace ka sanni..!” Shaye da tsananin mamaki Ameer ke dubanta “Safeenah.! Ni kike gayawa magana haka dan wani ya ceceki ya amsa laifin..?” Dakatar dashi tai da fad’in “Correction Mr Lawyer. Dama ban aikata laifin ba kuma nasan Allah bazai barni na biya abinda ban aikata ba.. Da wannan b’ata lokacin da kake da ka fara processing releasing papers d’ina ne dan ni ba mai laifi bace.” Ameer ya jinjina kai yace “I see, toh dai kar ki mance ko da wani ya amsa laifin nan akwai wanda ya tura sak’on BAD wa mijinki a gefe.. Mu’azzam bazai kuma yarda dake ba musamman idan ya tina BAD.!” Ya k’arashe yana murmushi. Zuciyar Safeenah yai wani irin yankewa ta dubesa tace “You are behind this Ameer..!” Ameer ya murmusa yace “Maiyasa zan tura masa sak’on BAD bayan nasan hakan na nufin d’aure kaina zanyi wajensa.. Ai duk wanda ya tura masa sak’on BAD wani ne da ya fahimci recently ina damunki da waya sannan kuma yana so ya rabaki da Mu’azzam maybe dan shi ya samu kusanci da Mu’azzam d’in..” Yai maganar yana kashe mata idanu guda kafin yace “Aff! I mean ita.. Dan nasan definitely mace ce..!” Zuciyar Safeenah yaci gaba da yankewa. Ameer ya barta nan tsaye tana tinanin waye yasan tana waya da Ameer yake so ya sanar da Mu’azzam ta wannan hanyar. Waye mafi kusanci da ita wanda yasan komai nata..? Take taji bakinta na furta “MEEMA.!” *SameenaAleeyou📚* [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *34* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Mu’azzam yana shigowa ya damk’o mutumin da duka hannayensa biyu yana tambayarsa ma wa yake aiki. Assad da Chief suka janyesa bayan ya kaima mutumin naushi a hanci. Mutumin yaci gaba da fad’in “Tare mukai niyyan kidnapping Safeenah Gamji domin mu karb’i Ransom wajen Mahaifinta watau Alhaji Marwan Gamji. Ni lebura ne a Dairy Company d’insu dake nan birnin tarayya, a nan na sami contact d’in Safeenah Gamji kasancewarta ma’aikaciya ce a ma’aikatan. Mun tura mata sak’o a matsayin zamuyi kasuwanci da ita..” Chief ya kuma jefo masa tambaya “Kun tura mata sak’o ta wayarta.. Kaida waye kukayi hakan.?” “Nida accomplices d’ina.” “Su waye accomplices d’in naka.?” Wannan karon Mu’azzam ne ya jefo masa tambayar yana murza hannunsa. “Sagir da Muttak’a wanda akafi sani da Danger.” “Ya akai kuka sace Ikram..?” Assad ya jefa masa wannan tambayar. “Kaman yanda na Fad’a maku our target was Safeenah Gamji dan itace mukeda contact d’inta wanda na samo mana daga record na company.” “Kenan Safeenah kuka so sacewa sai baku sameta ba kuka sami ‘yaruwarta.? Maiyasa Ita baku nemi Ransom d’in ba kuka zab’i ku kasheta bayan kun keta mata haddi..?” Chief ya jefo masa wannan tambayar, Mu’azzam kam huci kurum yake yana aika masa wani irin duba yana jin zuciyarsa na masa zafi musamman da ya tuna saida akai raping Ikram kafin aka kasheta. Mutumin ya bada amsa da fad’in “Munso amsan Ransom d’in amma Sai muka samu abokin alk’allarmu wato Sagir ya riga ya mata fyad’e.. Bamu shirya haka a cikin plan d’inmu ba shiyasa Sagir ya harbeta. Sai muma muka harbesa muka saka masa bindigar cikin hannunsa muka saita bindigar zuwa k’irjinsa dan yayi kaman cewa suicide yai committing bayan ya kashe Ikram d’in..” “Maiyasa sai yanzu ka zab’i ka fad’i gaskiya bayan tsawon lokacin nan..? Why did you chose to turn yourself in now.?” Jaja ya jefo masa wannan tambayar. “Sabida naga an kama wacce batada laifi ana tuhumarta kan laifin da Tun asali itace target d’in, shiyasa na zab’i na fad’i gaskiya.. Dan harga Allah nayi nadaman abinda mukayi..” Chief Jaja ya kuma jefo masa tambaya “Dama kun saba sace mutane ne kuna karb’an kud’in fansa ko Wannan shine karonku na farko..?” Ya girgiza kai yace “A’a Yallab’ai Wannan shine karonmu na farko kuma shine karonmu na k’arshe dan nikam dai na tuba. Bazan sake ba shiyasa ma na zab’i na fad’i gaskiya.?” “Now tell us, where can we find Danger.?” Assad ya jefo masa wannan tambayar. Ya d’ago ya dubi Assad kafin ya murmusa yana mai girgiza kai “Kar ku b’ata ma kanku lokaci Yallab’ai dan bazaku sami Danger cikin sauk’i ba..” Mu’azzam da tun yana bayani sai faman dunk’ule hannunsa yake yana murzasu naushi ya kuma Kai masa a Hanci ya damk’osa wuyarsa ya shak’esa yana fad’in “We are not playing games with you.. Moron.!” Chief ya soma harzuk’a yana fad’in Assad ya fitar da Mu’azzam. Lokaci guda ya bada umarnin a d’auke D’an ta’addan a kaisa cikin cell a gark’ame. Fincika Mu’azzam yai daga rik’on da Assad yai masa, ya d’aura duka hannayensa saman table d’in Chief Jaja ya matso da fuskarsa kusan na Chief sosai kafin ya kad’a kai yace “I swear.! I swear I will get to the core of this case.. And believe me, I’ll give you the shock of your life.. Just you wait and see, Chief Jaja..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice daga office d’in Assad ya bawa Chief hak’uri yana mai takewa Mu’azzam d’in baya. Aka bar Chief Sai sakin huci yake yana rage necktie d’insa, Lallai ma wanann yaron baida kunya baida mutunci ya lura dik horon dakatar dashi da akai bai ishesa ba yanzu har yana duban cikin idanunsa yana fad’a masa magana.. Ya kula baida tsoro ne sam babu kuma abinda zai dakatar dashi dukda cewa gashi an samu wani yayi confessing. Yana tsaye yana tinanin Maleeka ta turo k’ofa ta shigo tana sakin huci. Kallo d’aya yai mata ya d’auke Kai ya k’arasa jikin k’aramar fridge ya ciro bottle water ya b’alle marfin ya shiga kwankwad’a ko zuciyarsa zatai sanyi. “Tell me now.. What have you done to Mu’azzam.? Naga ya fice kaman Zaki.. Ka sake aikata masa wani abun ne.. Suspension d’in da aka basa na tsawon makonni bai isa ba..” “Shut up Maleeka..!” Chief Jaja ya daka mata tsawa kafin ya matso kusanta sosai yana huci yake furta “D’aniskan yaron nan is driving me crazy.. Ina d’aga masa k’afa ne sabida ke.. Sabida kince akanshi zaki iya rabuwa dani kuma zaki iya rasa rayuwarki duk akan wanann D’aniskan yaron da ma baisan kinayi ba.. Bayajin bari ba’a hanasa ya dena.. Duk hanyar da za’abi a nuna masa cewa an isa k’arshen case d’in anbi yak’i ya amince yak’i ya dakata ya hak’ura da binciken da yake, anyi duk mai yuwa yak’i ya daina.. Ya rantse sai ya isa k’arshen case d’in nan.. Toh kuwa Ina mai tabbatar miki Maleeka Mu’azzam Gamji yana tono mutuwarsa ne da kansa.. Dan akwai BAT a sama dani duk randa ya isaga BAT Toh kuwa babu shakka mutuwarsa kenan..!” Maleeka ta shiga girgiza kai tana fad’in “No please.. Dan Allah kar ku kashe shi.. Kar ka bari a kashe shi.. Wllhi idan na rasashi mutuwa zanyi.. Wllhi mutuwa zanyi. Dan Allah kar ka bari a halak’ashi..” Chief ya murmusa da gefen baki yana shafan b’angaren fuskar Maleeka da hannunsa guda “Baby bani zan kasheshi ba BAT ne zai kashesa..” Cikin rud’ani Maleeka tace “Bayan BAD akwai BAT.. Toh Waye BAT..?!” Tai tambayar cikin rud’ani.. Murmusawa ya kumayi kafin yace “Jemage kikeji, baya farauta sai cikin dare.. BAT is worse than BAD.. Abinda zan iya fad’a miki kenan.. Idan ya ci gaba da Digging zai isa wajen BAT, idan ya isa nan kuma believe me ya hak’o kabarinsa da kansa.. Zaifi masa kyau idan ya yarda ya tsaya a nan domin BAT baida d’and’anin imani...!” Suna cikin maganar wayar Chief ta soma ruri, sunan BAT ya bayyana saman screen d’in. Zuciyar Maleeka yai wane irin tsinkewa ganin BAT ya bayyana. “Get out now..!” Chief ya fad’i yana dubanta. Yanda ya bud’e murya gaba d’aya yai maganar saida ya d’an firgita ta.. Tai saurin sa kai ta fice daga ofishin dukda taso taji abinda BAT da Chief zasu tattauna akai. Tana fitowa taga wayan Ameer na shigo mata. Tai k’ok’arin saita kanta kafin Ta keb’e domin amsa kiran Ameer. Tana d’agawa Ameer ya soma fad’in “Well done Officer.. Kinyi k’ok’ari da kika tura wa Mu’azzam sak’on BAD.. Tabbas sak’o ya isa ga Mu’azzam har ya nuna mun.. Well done..” Fuzar da huci tai kad’an kafin tace “Look Ameer, I don’t know what you are talking about..” “No no no.. Don’t you play dump with me Maleeka.. Ke kad’aice kikeda motive na turawa Mu’azzam wanann sak’on.. But koma yaya ne I must thank you domin kuwa sak’on zai taka babban rawa a auratayyan Mu’azzam da kuma Safeenah musamman yanzu da aka wanke Safeenah Banida chance d’in kareta a Kotu kinga sak’on BAD zai amfani domin kuwa na tabbata a halin yanzu Mu’azzam bazai tab’a yarda babu wata alak’a tsakanina da ita ba..” Ya k’arashe yana mai fashewa da dariya. Lokaci guda yaci gaba da furta “Good job Officer.. Keep it up.. Dole na baki kyautar kiss ta cikin waya..” Ya k’arashe yana mai kissing wayar yana kuma tintsirewa da shewa. Zama Maleeka tai gijif saman kujera abubuwa cunk’ushe cikin zuciyarta, ita yanzu bata Ameer da ahirirtarsa take ba. Damuwarta shine wanene BAT wanda Jaja yake tarayya dashi wajen ruguza Mu’azzam.. A baya tayi tarayya da Jaja ne dan tasan Tabbas Jaja nada masaniya kan case d’in mutuwar Ikram, dan ta tab’a tsintar text message wata rana cikin wayarsa bayan Sun gama aikata mai zasu aikata a hotel room, sak’on ya shigo wayar Chief.. A lokacin wayar na aje gefenta kan gado yayinda Jaja ke bathroom.. Nan taga an turo sak’on kuma zallan sunan Safeenah Gamji kawai taga an rubuta a sak’on shiyasa tai zargin Safeenah nada alak’a da case d’in mutuwar k’anwar Mu’azzam.. Hakan ne yasa ta nemi Barr Ameer suka had’a team ta sanar dashi abinda take zargi gameda Safeenar shi kuma Barr Ameer yai amfani da abinda Maleeka ta fad’a masa yana Barazana ma Safeenah da cewa yasan wani abu gameda ita. Amma a halin yanzu batajin zata iya, Dikda cewa tin farko bataci dunduniyar Mu’azzam ba, ita kawai abinda take so shine ta fidda Safeenah daga rayuwarsa ita ta samu gurbi, bayan wannan batada wani motive na ruguza Mu’azzam.. Yanzu da rayuwarsa ke cikin had’ari ta damu matuk’a.. Batasan mai zata aiwatar ba.. Idan ta sanar dashi ga abinda Jaja yakeyi tasan Tabbas ba Mu’azzam kawai ba harta itama zata rasa rayuwarta ne.. Zata rasa Mu’azzam domin kuwa Tabbas su Chief sai Sun karsa matuk’a bai dakata da binciken da yake ba.. A b’angare guda tasan Mu’azzam da kafiya akan duk abinda yasa gabansa.. Batajin zai dakata da binciken nan.. Gaba d’aya Maleeka ta rasa wanne zatai, zuciyarta ya gama karaya da hidiman Jaja.. Tana matuk’ar tsoron ta rasa Mu’azzam.. Lumshe idanunta tai hawaye suka gangaro mata.. Ji take tsaf zata iya bada rayuwarta ga Mu’azzam sabida tsananin k’aunar da take masa.. Wayarta ne ya kuma ruri nan taga Chief ne mai kiranta. Tana d’agawa yace da ita su had’u da dare. Ya sanar da ita sunan hotel d’in da zasu had’u daga haka ya katse kiran bai tsaya sauraronta ba. Ta goge hawayen da suka zubo mata.. Tabbas dole ta had’u da Chief a daren domin ta k’ara samun clue gameda BAT.. Ya kamata Mu’azzam yasan akwai BAT a sama da Chief wanda suke k’ok’arin kaisa k’asa. Da wannan tunanin ta mik’e ta nufi restroom ta gyara fuskarta kafin ta fito ta nufi ofishinsu. ** A can gidan Daddy kuwa murna ake kanyi ana Barka da juna, Safeenah kaw Mommy da Aunty Shemau sai nan suke da ita musamman data basu labarin daren jiya a cikin cell saida shugaban ‘yantaddan cikin cell d’in ta sanyata tai mata tausa tana a matsayin Safeenah Gamji babu halin tak’i yi taci bugu a banza. Meema kaw duk maganar da takewa Safeenah, Safeenar tak’i kulata, idan taga Meema a waje ma b’ata fuska take ko ta bar wajen gaba d’aya. Wannan karon zaune ta tadda Safeenar a d’akinta tana shan grapes. Tana duba wayarta da tai missing na kwana guda. Meema ta dubeta tace “Addah Feenah wai bazaki min magana bane inata binki ina miki barka..” Safeenah ta dakata da abinda take tana aikawa Meema wane irin wulak’antaccen kallo “Maiyasa zan amsa munafuka irinki wacce batada burin da ya wuce taga na dawwama a Kurkuku.. Ai nasan na ciki na ciki ba haka kika so ba, kinso na zauna a can don ki samu abinda kike so.. Algunguma traitor.. How could you Meema..? Inaji ana cewa a cikin wanda kuka fito ciki guda ma ana samun wanda zaike bak’in ciki dakai ban yarda ba Sai akanki Meema..” Cikin rashin gane ina kalaman Safeenah suka nufa Meema ta shiga girgiza kai tana fad’in “Adda Feenah where’s all this coming from..? Addah Feenah mai kike nufi..?” Safeenah ta kuma watsa mata wani kallon kafin tace “Munafuka, don’t act innocent. Kinsan sarai abinda nake nufi kuma Allah ya toni asirin munafuka irinki.. Dama kaf gidan nan an miki shaidan munafunci da gulma ni kad’aice ke yarda dake na baki dukkan yarda na da sirrina kikaci amanata.. Ko zaki ce bakisan Ameer na kirata a waya ba..?” Gaban Meema ya fad’i dan ta tina lokacin suna Fufore ta amsa wayar Safeenah sanda Barr Ameer ya kirata har ta goge kiran daga call log amma tayi hakan ne dan kar Safeenah ta jefa kanta cikin matsala wajen Mu’azzam ya zaci tana cin amanansa da wani ne. Tayi hakan ne domin ta taimaki ‘yaruwarta amma ba da wani nufi ba. Allah shine shaidanta. Safeenah taci gaba da jinjina kai ganin Meema nata amsata ba “Dama nasan kin sani, kuma kina son sanar da Mu’azzam.. I was such a fool da na Kasa gane ina kika nufa tuntuni.. Komai kece kike karanta mun yanda zanyi Meema ashe so kike ki rabani da mijina ban sani ba.. You are jealous of me..!” Ta d’an dakata kafin Ta kuma tsareta da ido tace “Tell me Meema.. Do you love Mu’azzam..?” Baki sake Meema ke dubanta cikeda tsananin mamaki.. Ta soma girgiza kai cikin rashin yarda da abinda ‘yaruwar tata ke fad’i mata “Addah Feenah.. Kin kuwa ji mai kike fad’i.. Why would you think like that..? I mean.. Kinsan mai kike fad’i kuwa..? Addah Feenah how on earth zan so mijinki..?” “Ai ba kanki farau ba.. Ana samun irin haka Meema.. Son Mu’azzam kike shiyasa kiketa k’ok’arin exposing d’ina wajensa dan ya sakeni ke kuma ki samu ya aureki koh..? Munafuka kawai algunguma.. Yau duk illahirin gidan nan sai sunji mai kika aikata..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa kafin ta bangaje Meema ta wuce. Mommy da Aunty Shemau suna d’aki suna kuma jinjina lamarin Aunty Shemau tana sanar da ita sunyi waya da Uncle Salman Daddy ya sanar dashi duk abinda ke faruwa amma yace kar a sanar da Inne. Mommy tace “Ai gwara da ba’a sanar da wannan jarababbiyar tsohuwar ba da yanzu ta d’agawa mutane hankali gaba d’aya.. Gashi Allah ya tak’aita, gaskiya tayi halinta Allah ya wanke Safeenah daga zargin da ake mata. Yanzu kuma lokacin mu ne da zamu d’au fansa kan Mu’azzam.. Wllhi Sai ya sakar mun d’iya kuma sai mun tafi Kotu akan abinda yaima Safeenah sannan muci taransa.” Daidai lokacin Safeenah ta turo k’ofa tana fad’in “Mommy babu wanda zai rabani da mijina.. I still love him dukda abinda ya aikata..” Baki sake Mommy da Aunty Shemau ke dubanta. Safeenah ta dubi Aunty Shemau tace “Aunty ku shirya yau d’in nan zuwa dare zaku kaini gidana.. Na kira Aunty Faty da Aunty Hadiza k’awayen Mommy zaku kaini gidana yau da dare.. Wllhi bazan bar ma wata shegiya can gidana da mijina ba.. Dan naga alama har a cikin gida ma akwai masu son su rabani da mijina su shige gidana..” Tana ida fad’in haka ta juya ta fice. Mommy ta mik’e ta biyo bayanta tana fad’in “Ke ke Safeenah.. Zo nan..” A parlor suka tsaya gaba d’ayansu harda Aunty Shemau. Mommy na tambayarta mai take nufi. Duban Meema dake rakub’e gefe tai tace “Mommy ‘yarki Meema son mijina take har sak’o take tura masa na cewa nida Ameer muna cin amanarsa.” Mommy harma da Aunty Shemau suka dubi Meema dake girgiza kai tana hawaye “Mommy na rantse da Allah ban aikata ba.. Wllhi banyi haka ba.. Maiyasa zan yiwa Addah Feenah haka.. Wllhi Mommy nasan dai na amsa kiran Ameer kuma na goge kiran amma wllhi ban turawa Ya Mu’azzam wani sak’o ba.. Mommy Addah Feenah fah ‘yaruwata ce Maiyasa zan mata haka.. Maiyasa zan rabata da mijinta..?” Safeenah tace “Kunji munafuka koh.. Ita Tai incriminating d’ina da sak’on da turawa Mu’azzam.. Mommy Meema itace silan kaini police station har na kwana a cell.. Meema son Ya Mu’azzam take Mommy..” Mommy ta darara masu tsawa da fad’in “Ya isa ni ko sunan D’aniskan yaron nan maras mutunci banson ji..!” Meema taci gaba da kuka tana girgiza kai tana fad’in wllhi ba ita bace bata aikata ba. Safeenah na huci take fad’in “Wllhi daga rana mai kaman ta yau ke ba ‘yaruwata bace Meema.. Babu ni babu ke.. Mommy kiyimin iyaka da d’iyarki mun raba jini daga yau..!” Tana ida fad’in haka ta shige fuuu.. Mommy Ta shiga salati tana tafe hannaye “Na shiga uku ni Hajara wannan wane irin Yaro ne haka..? Bayan duk abubuwan da yayi yanzu kuma ya shiga tsakanin yarana ya rabasu, Feenah da Meemah da ba’a rabasu sabida k’aunar juna yanzu saida Mu’azzam ya raba mun kan yara ya masu farrak’u.. Ga Musaddiq ma tin jiya da akace ana zargin Safeenah da kisan Ikram ni ban sake sakasa a idona ba.. Wannan duk laifin Mu’azzam ne.. Ya raba mun kan gida ya dasa gaba da tsana tsakanin ahalina.. Wllhi nima sai na masa farrak’u da duk wani masoyinsa..” Ta janyo hannun Shemau suka shige d’aki. ** Yamma lis ya iso gidan, ya jima yana horn kafin Gateman d’in ya k’araso ya bud’e masa. Yana sara masa yana gyara belt d’in wandonsa, hularsa ta ‘yansandan ma a karkace take ga uwar gumi duk ya wanke masa fuska. Mu’azzam ya dubesa da mamaki kafin yace “Patrick is all well..? Ya na ganka haka..” Patrick yace “Sir.. Sir cikina ne ya kunce amin afuwa Sir, zuwana toilet na goma kenan Sir.” Mu’azzam ya girgiza kai kafin yace “Kasha magani..?” “Eh..Eh.. Yes yes.. Sir, nasha ai..” Yanda yake maganar gaba d’aya a birkice yake.. D’an Jim Mu’azzam yai kafin ya jinjina kai yace “Idan cikin naka bai tsaya ba kana iya zuwa asibiti ai tinda ganin nan na dawo.. Ko barin kira azo akaika Asibiti.. Allah yasa ba abin naku kaje kasha ba..” Patrick ya girgiza kai yace “Sir ai na daina sha tinda ka kawoni nan.. Ba sai ka kira kowa ba Sir.. I’ll be fine..” D’an tab’e baki yai kad’an kafin ya jinjina kai yai masa fatan samun lafiya ya nufi cikin gidan. Yana shigewa Patrick ya zame hularsa ya d’aura duka hannayensa biyu akai yana fad’in “You are a dead man Patrick.!” Mu’azzam kaw yana shiga gidan bai tsaya nemanta ba dan yasan bazai wuce tana cikin d’aki ba. Kai tsaye nasa d’akin ya shige ya soma rage kayan jikinsa, Cak ya dakata da abinda yake yana duban saman gadon yana tuna abubuwan da suka faru daren jiya. Murmushi ne yaji yana kufce masa, duk zafin kan da ya kwaso a waje sai yana jin kaman dai zafin kan yana yayewa a hankali, zuciyarsa tai masa wasai ba tareda yasan dalili ba. Ya kuma sakin murmushi yana d’an girgiza kansa kad’an, lokaci guda ya fad’a bathroom yayo wanka. Ya fito yana goge sumarsa nan ya hangi takardan da yai mata rubutu gefen bedside. A hankali ya isa ya d’auki takardan yana dubawa. Wani abu ne yaji ya tsaya masa a k’irji a sanda ya soma karanta abinda ke cikin takardan. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *35* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Girgiza kai ya shiga yi yana furtawa a hankali “This is not happening.. No.. No.. Mai yarinyar nan ta aikata kuma yanzu.?” Cikin sauri yai jifa da takardan, a gurguji ya shirya cikin jallabiya ruwan toka kafin ya soma bincikata cikin gidan, babu ita babu alamunta hakan yasa ya nufo k’asa babu shiri. Patrick yana jin yanda Ogan nasa ke kiran sunansa cikin tsananin amo da gwab’in murya yasan mai aukuwa ya auku. “Where.. is my wife.?!” Ya tambaya yana duban Patrick daketa faman rabe raben idanu yana girgiza kai. “I ask you a question Patrick. Where is my wife.. Ina matata..?” Patrick yaci gaba da girgiza kai gumi na k’eto masa “Sir.. Sir.. Ehm..” Katsesa Mu’azzam yai da fad’in “Patrick, I’m at the edge of my patience.. Kar ka bari kaga other side d’ina.. Now you tell me. Where the hell is my Wife.?” Ya k’arashe idanunsa tar kan Patrick. “I’m afraid she’s not here, Sir...” Ya girgiza kai yace “What do you mean she’s not here..?” Patrick yace “Ta aikeni na sayo mata magani na dawo na tadda bata nan,I.. I’m sorry Sir..” Girgiza kai Mu’azzam keyi yana dubansa cikin tsananin tashin hankali “Aikinka ne sayo mata magani..? I thought I told you kar kaje ko Ina without informing me first.. What have you done now Patrick.?!” Ya girgiza kai yana duban k’asa “Sir I tried calling you but I couldn’t reach you..” Lumshe idanunsa Mu’azzam yai yana ambaton Allah. Bai San ta ina zai fara ba.. Baisan ta ina ta nufa ba.. Shin ta ina zai fara nemanta kafin ta fad’a cikin had’ari domin kuwa rayuwar tata na cikin had’ari ne. Cikin sauri ya koma cikin gidan ya d’auko car keys d’insa da wayarsa. Ji yai sam bazai iya zama ba ba tareda yasan yanda take ba. Yasan bazai wuce tace zata fita ta nemi mahaifiyarta da ‘yanuwanta ba. Toh amma ta ina zata fara neman nasu.? What if taje Ta fad’a mugun hannu.? Yai saurin kauda tinanin yana fatan ta kasance lafiya a duk yanda take. A haka ya iso jikin motarsa ya bud’e zai shige amma Sai ya juyo yana duban Patrick “You stay here and don’t go anywhere.. Ban gama dakai ba..!” Daga haka ya shige motar Patrick na jinjina kansa dake kife. Lokaci guda ya isa gate ya bud’ewa Ubangidan nasa k’ofa. Yana tafe a Mota yana kuma nanata sak’on da Ta ajiye masa cikin zuciyarta.. Ya lumshe idanunsa a hankali yana furtawa a fili “Dear Stubborn head, please be safe..!” Bai ida rufe baki ba wayar Assad ya shigo masa “A kasalce ya d’aga cikin rashin kuzari. Daga yanda Assad yaji muryarsa ya fahimci babu lafiya. “Mu’azzam are you alright..?” Assad ya tambaya daga d’aya b’angaren. “She has left..” Abinda kawai ya iya fad’iwa Assad kenan. “Ta tafi kuma.? Wacece ta tafi..?” Assad ya tambaya. “Who else Assad.? Wacece nake zaune tareda ita a gidan..” Ya basa amsa kai tsaye. “Kana nufin Sadiya ta tafi..? Toh ina ta tafi..?” Assad ya tambaya daga d’aya b’angaren. “Ta yaya zan sani Assad.. Ta bar gida bansan yanda taje ba.. Bansan yanda take ba..” Ya d’anyi fasali kafin ya k’arada “I don’t know what I’d do if something bad happens to her..” Assad ya shafi fuskarsa yana mai jinjina lamarin “Don’t think like that.. Babu abinda zai faru Mu’azzam ka kwantar da hankalinka kaji.. Ka sanar dani yanda kake zan sameka.. And we’ll look for her together.. Just text me your location.” Sauk’e deep breath Mu’azzam yai kafin yai parking gefen hanya yana mai turawa Assad location d’in. Lokaci guda ya kifa kansa saman steering wheel yana mai tuhumar kansa da alhakin ficewarta.. Da ace bai aikata mata abinda ya aikata a daren jiya ba maybe da bata tafi ba.. Idan wani abu ya sameta baijin zai tab’a yafewa kansa.. Ya lumshe gajiyayyun idanunsa yana nan gefen kwalta dan ji yai ma baida kuzarin tuk’a motar. ** Mommy ta kasa ta tsare tace sam Safeenah bazata tafi gidan Mu’azzam ba sai anje Kotu an k’watar mata hakkinta tinda ita batasan zafin kanta ba sai soyayyar wann jarabban yaron maras mutunci. Ana tsaka da wannan hatsaniyar Daddy ya shigo gidan. Ya dubi Safeenah dake tsaye da trolley d’inta tana fad’in koma Mommy ta hana k’awayenta kaita gidanta ita zata kai kanta ehe. Dan a halin yanzu batada burin da ya wuce ta kori shegiyar can da Mu’azzam ya aje mata a gida ta kasance da mijinta. Daddy ya kuma duban Mommy da Aunty Shemau dake tsaye gefe carko carko. Shemau tana ganin Daddy ya shigo ta shige ciki ta basu waje tana mai dialing layin mijinta, idanunta k’asa k’asa alamun zancen gidan D’anuwan nasa take sanar da mijinta Ta cikin waya. Safeenah tana ganinsa ta fashe da kuka tana fad’in “Daddy dan Allah kace Mommy kar tayi k’arar Mu’azzam wllhi ina son mijina.. Daddy na gaji da tashin hankali I want peace with my husband.. Dan Allah Daddy kace kar tayi k’ararsa.” Girgiza kai Daddy yai yana duban Mommy kafin ya dubi Safeenah yace “Ki kwantar da hankalinki babu wanda zaiyi k’arar mijinki..Kinji koh..” Mommy Ta katse zancen da fad’in “Naji baza’ai k’aran Shelelenka ba amma Safeenah bazata tare gidan Mu’azzam ba sai an kirasa an zaunarsa a nan gamu ga shi ya sanar damu matsayin karuwar da ya aje gidan Safeenah tin kafin ta tare dan ni ban yarda aurenta yai ba ehe. Kai banda ma wannan yaron asirce zuciyarka yai har yaushe zaka kuma aminta dashi bayan yaje yayi aure ba tareda saninka ba duk wannan kulawa da kake basa wanda ko ‘ya’yan cikinka albarkaci.. Da ace ya d’aukeka Uba wllhi da ya sanar dakai.. Amma bai sanar dakai ba.. Ko Wanne uban ya tura ya amsar masa auren sai Allah..!” Daddy ya jinjina kai yace “Kin gama..?” Mommy batace komai sai jijjiga da take ci gaba da yi tana sakin huci. Ya dubi Safeenah dake tsaye wajen tana goge hawayenta kafin yace “Safeenah zan kaiki gidan mijinki.. Amma zan hud’uba guda d’aya.. Kuma hud’ubar itace koda wasa kar ki d’auki halayyar wannan matar kije kina ma mijinki.. Kinji koh..” Safeenah ta jinjina kai tana kuma goge fuskarta da mayafin dogon rigarta. Mommy tai k’wafa tana kad’a kai “Eh yayi.. Dole ka mata hud’uba kar Ta d’auki irin halayyana.. Duk abubuwan arziki na alkhairi da nai a baya ba’a gani ba sai yanzu za’a sami bakin kasheni da shike na gama jinyar nakasasshiyar matarka ba..” “Hajaraa!” Daddy ya darara mata tsawa yana mai d’ago hannu kaman zai kai mata mari.. Lokaci guda yake nunata da ‘yar yatsa “Ki iya bakinki kuma kar ki sake zagar mun mata, a yanda take a nakashe tafimun ke sau babu adadi.. Kuma da sannu zaki gani Allah zai bata lafiya ta dawo cikin gidan nan.. Tamkar bata tab’a jinya ba..!” Ya dubi Safeenah yace “Shige muje..” Babu musu Safeenah ta janyo suitcases d’inta tabi bayan Daddy. Aka bar Mommy baki sake tana duban bayansu har suka fice.. Yau itace Marwan yake cewa nakasasshiyar can ta fi masa ita, matar da ma cushe aka masa ba cewa yai yana sonta ba tun fil azal.. Lallai tun kafin ta makara gwara ta tura Shemau ta koma ta duba mata wanne hali Nuratu ke ciki.. Da wannan tunanin Mommy ta haura sama tana kiran Shemau. Shemau tana jin Mommy na kiranta tai rounding up wayar da suke da mijinta Salman. Ta dubi Mommy dake sakin huci ta tambayeta ya akai. Mommy ta sanar da ita komai cewa Daddy yakai Safeenah gidan Mu’azzam dukda irin cin kashin da Mu’azzam d’in yai masu, harda cewa da Daddy yai Nuratu tafi masa Ita. Tab’e baki kad’an Shemau tai tace “Ai kuwa gwara ki tabbata Nuratu bata sami lafiya ba dan da alama mijinki ya fara sonta tin kafin ta warke daga jinya.. Ina ji miki tsoro kar ta dawo Gidanki a kan k’afafunta bayan an fitar da ita a kwance.” Mommy ta sauk’e fuci tace “Kin mance cewa gidan mijina tamkar dai GIDAN ARO yake a wajenta.. Ai yanda aka fitar da ita a kwance Saidai a turata rami a haka.. Gidana ya haramta a gareta.. Yanda idan aka mutu ba’a sake dawowa Gidan Duniya haka itama yanda Ta fice daga gidan nan bata kuma dawowa.. Shemau ya kamata ki koma gida tinda dai Safeenar ta tare ki duba mana halin da nakasasshiyar cen ke ciki.” Shemau ta jinjina kai tace “Gawa zakice dan kullum jikinta dad’a gaba yake yanzu haka wayar da nayi da Salman abinda ya sanar dani kenan cewa jikin Nuratu yak’i dad’i har Inne ta fara tinanin ko mai magani za’a canza..” Mommy ta zaro ido dafe da k’irji tace “Shemau kar ki bari a canza mai magani.. Asirinmu zai tonu.!” Shemau ta murmusa kafin tace “Baki da damuwa hakan bazai tab’a yuwa ba.. Bazan bar hakan ta kasance ba. Yanzu Salman yace zai taho Abujan gobe Ina tsammanin Business trip ne, zai kwana biyu sai mu koma tare. Kinsan nace miki Su Husna sunata shirin waec ga twins ma na barsu wajen mai aiki gwara na koma sai naci gaba da saka mana idanu kan Nuratu.” Mommy ta jinjina kai tace “Hakan yayi.. Allah yasa kafin gobe muji Labarin nakasasshiyar nan ta mirgina..” Suka saki shewa suna masu tafe hannaye. ** Assad yana k’arasowa yai masa knocking da yatsar saman glass, lokaci guda Mu’azzam d’in ya danna unlock Assad ya ya bud’e ya shiga.. Kallo d’aya yaiwa Mu’azzam d’in ya basa tausayi.. Kai da gani Kasan abubuwa sun taru sun masa yawa k’arfin hali kurum yake. Assad yace “Ya jikin Mamy..?” Lumshe idanunsa kad’an Mu’azzam yai a hankali kafin yace “Munyi waya da Inne da safe tace mun jikin nata da sauki an gode Allah..” Assad ya jinjina kai yace “Allah ya bata alfiya yasa kaffara ne.. Allah ya tashi kafad’unta..” Mu’azzam ya amsa da “Ameen ya Allah..” “Safeenah fah..? Wanne kake ciki da nata batun..?” Ya d’an tab’e bakinsa kad’an kafin yace “I still don’t know.. Ban Sani ba Assad..” Assad ya fuzar da fuci kad’an cikeda tausayin Mu’azzam d’in kafin yace “Kar ka damu Mu’azzam Ubangiji yana jarabtar bayinsa ta ko wacce hanya.. Ba wai yak’ika bane yake aiko maka da jarabawa daki daki, daga wannan sai wancan.. Kai hak’uri sannan kai addu’a Allah ya baka ikon cin jarabawarka Brother..” Mu’azzam ya d’an kaikaito ya dubi Assad d’in kafin ya jinjina kai a hankali ba tareda ya iya furta koda kalma ba. Assad yace “Ta ina zamu fara yanzu..?” Mu’azzam ya d’ago yana dubansa kafin yakai ga basa amsa wayar Daddy ya shigo masa. “I’ll take this call, Daddy ne mai kira.” Assad ya jinjina masa kai ba tareda yace komai ba. Mu’azzam ya d’aga da sallama yana mai gaida Daddyn. Daga d’aya b’angaren Daddy ya amsa cikin sakin fuska kafin yace “Baka gida ne, gashi munzo bamu taddaka ba sai gateman.” Ya d’an dubi Assad kafin ya girgiza kai cikeda mamakin jin Daddy yana gidansa “No bana gida Daddy. Ai na fice..” Daddy ya jinjina kai yace “Toooh da kuwa gashi na taho da Safeenah ce zan had’aku gaba d’aya harda d’aya matar taka nai maku nasiha.” Jin abinda Daddy yace ya sanya Mu’azzam ware idanu babu shiri yana jin wani abu na neman toshe masa mak’oshi.. D’an girgiza kai yai kafin yace “Daddy you mean, ka kawo Safeenah yanzu haka..?” Daddy yace “K’warai kuwa Mu’azzam, na kawo maka matarka dan zaman nata a gida can baida wani alfanu.. Kyaun mace mai aure ta kasance a d’akinta shine cikan mutuncinta.. Sannan kaima shine cikan Kamalarka..” Mu’azzam ya jinjina kai a hankali kafin yace “Haka ne Daddy..Amma yanzu bana gida and.. Bazan dawo gida nan kusa ba..” Yai maganar cikeda jin nauyin Daddy. Daddy ya d’anyi jim kafin yace “Tooh lafiya dai koh..?” Mu’azzam ya jinjina kai kaman Daddy na ganinsa “Eh.. Eh wani aiki ne ya taso mun shisa zan d’an makara.” Daddy yace “Af Toh ai babu komai, nan gaba sai na had’aku na maku nasiha.. Ina ita matar taka take..?” Mu’azzam ya dubi Assad dan baisan mai zai sanar da Daddy ba.. Baisan ta yanda zai soma fad’a masa cewa Sadiya ta gudu daga gidan ba. Ya d’an shafi fuskarsa kad’an kafin yace “Bata gida inaga taje can wajen mahaifiyarta..” Daddy yace “Allah sarki toh shikenan.. Allah Ubangiji ya zaunar daku lafiya ya had’e maka kan iyalanka.. Allah shi maku albarka gaba d’ayanku..” Mu’azzam yanata amsa masa da Ameen kafin Daddy yai masa sallama yana mai sanar dashi ya bar Safeenah a gidan shi kuma ya koma gida. Suna ida wayar Mu’azzam ya dubi Assad yana mai kuma tura yatsun hannunsa cikin sumarsa. Assad ya d’an girgiza masa kai alamun meke faruwa. Mu’azzam ya d’aura duka hannayensa saman steering yana mai kuma fuzar da huci, idanunsa naga glass na gaban motar yake furta “Daddy yakai Safeenah gidana..” Assad ya murmusa yace “Kaga mai tagwayen mata.. Baka Farin ciki da hakan ne..?” Da wutsiyar idanu ya dubesa kafin yace “If she’s still my wife it’s because of Daddy..” Assad ya d’an girgiza kai kad’an yace “Mu’azzam, Safeenah batada wani laifi.. Kawai dai she got trapped ne.. Gashi Allah ya wanketa. Su Danger sunso saceta ne suka sace Ikram. At least ka godewa Allah da ya wanke Safeenah.. Ko Babu komai ‘yaruwarka ce kuma matarka ce Still da wutsiyar idanu yake dubansa kafin yace “Ka mance text d’in BAD ne.. I’m pretty sure D’aniskan Lauyan nan shine BAD.. Ban kuma yarda da sak’on BAD ba har Sai na isa k’arshen binkicen nan.” Assad ya jinjina kai a hankali kafin yace “Ta ina zamu fara yanzu.?” “Suleja..” Mu’azzam ya basa amsa kafin yaci gaba da fad’in “Babu yanda zatai tunanin zuwa sai nan, na tabbata can zata tafi ta nemi mahaifiyarta da ‘yanuwanta.” Assad ya jinjina kai kafin yace “Let me drive..” Mu’azzam ya murmusa yace “Kai haba rangwancin nawa ai bai kai nan ba.” Yana maganar yana tada motar had’ida d’aukan hanya. ** Daddy yana tafiya Safeenah ta dinga zagaya gidanta tana imagining kalan cin amanarta da Mu’azzam yai a cikin gidan da wannan ‘yariskan yarinyar. Tai tsaye tana duban Parlorn sai taga kaman tana hangosu saman kujera Mu’azzam na zaune yarinyar tayi matashi da cinyarsa. Tai saurin rintse idanunta tana jin zuciyarta na mata wane irin zogi da k’una. Can taga kaman ta soma hangosu yana mata cakulkulkuli tana dariya tana zillewa.. Har kaman shewarsu takeji cikin kunnuwarta suna wasanni irinta masoya a parlorn gidan dikda kuwa tasan mislkilanci irin na Mu’azzam.. Ta sak’i k’ara tana mai toshe kunnuwarta “Enough Feenah..!” Ta daka ma kanta tsawa da fad’in haka “This is just your imagination.. Mu’azzam would never do something like this musamman da k’aramar yarinya irin wannan.. Asiri tai masa kawai shiyasa ya aurota ba tareda sanin kowa ba..!” Ta k’arashe zancen nata tana sakin huci kafin ta haura upstairs. Ta jima tana duban hoton su itada Mu’azzam na ranan aurensu dake lik’e a hanyar matakalan. Lokaci guda Safeenah ta isa jikin hoton tana sakin murmushi tana shafa hoton a hankali musamman b’angaren Mu’azzam. Sunyi kyau har sun gaji, sannan sun dace da junansu.. Ta kuma sakin murmushi har lokacin shafa hoton take “Hakan ya nuna tabbacin ni ce a zuciyarka My Halal.. Da ace wancan ‘yariskar tanada matsayi na tabbata da baka aje hoton nan a nan ba.. I’m the Queen of your heart Mu’azzam.. And I won’t allow any woman ta sace mun wannan matsayin a wajenka.. I’ll do whatever it takes to make sure banyi sharing d’inka tareda wata ba.. You are mine.. Alone..!” Tana ida fad’in haka ta nufi nata d’akin tana k’are ma d’akin kallo.. Kaman babu wanda ya zauna ciki, komai tas tas harda hotonta gefen bedside Mu’azzam ya aje. Ta kuma sakin murmushi tana duban hoton saidai hango kaya jere cikin wardrobe da tai ne ya sanya zuciyarta tsinkewa.. Ta isa ta bud’e ta shiga firfito da kayayyakin tana watsi dasu wasu tana kekketa su da hannayenta musamman da taga dik dangin English wears ne.. “I curse you.. I curse you.!! I curse you..!!” Haka ta dinga fad’i tana keta kayyakin tana watsi dasu. Taci gaba da sakin huci kafin ta nufi bathroom d’in tana k’are masa kallo.. Harda kayan wanka dasu shampoo.. A fili ta furta “Shegiya Karuwa.. Idona idonki sai na kasheki..!” Ta tattaro kayan wankan danginsu shower jell dasu Shampoo ta dinga matsesu tana zubar dasu cikin toilet seat saida ta zubar dasu kaf tai flushing d’insu tana sakin huci kafin ta fito ta nufi ta nufi nasa d’akin. Haka kurum taji gabanta yayi wani irin yankewa sanda ta hangi saman gadon.. Muasamman data lura saman gadon is kind rough alamun an kwanta ba’a gyara ba.. Take wani tunanin ya soma d’arsuwa zuciyar Safeenah.. Tai saurin rintse idanunta tana bud’e hannayenta take furta “Enough Feenah.. Nothing happened, kawai dai ya kwanta ne ya tashi bai gyara gadon ba.. And that’s all.. Yanzu sai ki gyara masa and play a perfect wife role..” Ta d’an rausayar da idanunta kafin ta haye saman gadon tana mai tattaro pillows d’in.. K’amshin da hancinta ya jiyo mata cikin pillows d’in shi tasa zuciyarta kusan bugawa, dan k’amshin shower jell da Shampoo d’in da ta gama juyowa cikin toilet taji.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Tare fah suke Kwana kenan.. D’akin mijinta wanda ko tarewa basuyi ba.. Gashi ya tare da wata Karuwa tana can baki sake.. Take taji kuzarin jikinta sun tafi gaba d’aya.. Ta koma ta silale tana jin wane irin kuka gauraye da k’unci na taso mata.. Haka ta dinga kuka tana fatali da kayayyakin dake cikin d’akin.. Saida tai mai isarta kafin Ta danni kanta da fad’in “Feenah kuka bai ganki ba.. You need to be strong if you want to get your husband back.. Think Feenah..!” Ta soma kame kanta tana tinanin abinyi tinda dai yanzu babu Meema mai bata shawari. Murmushi ta saki still hawaye na gangaro mata sanda ta tuna abinda zatai. Nan kuma ta hango takarda yashe a k’asa.. Ta rarrafa ta d’auki takardan tana juyawa, rubutun da ta gani jiki shi ya bala’in kashe mata jiki ya kuma haifar mata da bugawan zuciya. Na farko na Mu’azzam ne yana umartan Sadiyar da tai wankan tsarki dukda babu abinda ya faru.. Sai note d’in da Sadiyar ta bar masa a k’asa na cewa bazata tab’a yafe masa ba kan abinda yai niyyan mata sannan mission d’in ya k’are.. Safeenah ta gyara zama sosai tana nazarin rubutun, idan taso fahimtar wani abu kenan zaman mission wann ‘yariskar tai a gidanta..? Toh kodai da gaske ba zaman auratayya sukeda Mu’azzam ba..? Kardai auren yarjejeniya ne shiyasa yace wa Daddy zaiyi bayani..? Toh amma wane irin mission kenan..? Ta kuma tambayar kanta.. Toh koma dai menene mission d’in ta tabbata kusantar yarinyar yasoyi kenan.. Mu’azzam d’in da tai masa shaida babu ruwansa da mata ashe hauka take gashi har zai ma wata da k’arfi ita tana can tana bibiyarsa ko kallo bata ishesa ba.. Zuciyar Safeenah yaci gaba da harbawa cikin sauri.. Babu abinda ya tsaya mata kaman cewa da Mu’azzam yai cikin note d’in ‘Thank you for taking care of me last night’. Safeenah ta shiga keta takardan tana kuka tana birgima a wajen. ** Suna isa gidansu Sadiya suka tadda kaman Kufai, babu kowa sannan babu alamun kowa wajen, Mu’azzam yai tsaye yana tina farkon zuwansa layin wanda bincike ya kawosa, ya tuna had’uwarsu Ta farko a lokacin da suka bangaji juna, ya tuna jifarsa da ultra pad da tai, ya tuna randa ya aureta ya kuma sunkuceta ya tafi da ita.. Haka ya dinga tina every bit na abubuwan da suka faru tun bayan had’uwarsa da ita.. Saman dakalin k’ofar gidan ya zauna yana mai d’aura hab’arsa saman hannayensa da ya had’e waje guda. Assad da k’arasowarsa kenan bayan yabi layi layi yana tambaya ko sunga Sadiya amma babu wanda yace yaga Sady Pretty sannan Mahaifiyarta ma da ‘yanuwanta har yau basu san yanda suke ba, babu wanda ya kuma ganinsu a unguwar. Assad ya k’araso kusan Mu’azzam d’in yana mai girgiza kai “Mu’azzam negative..! Babu wanda ya ganta, da alama batazo nan ba.. Sannan k’awarta Sabeera sun bar gari..” Ya k’arashe cikin sanyin murya. D’agowa Mu’azzam yai ya dubesa kafin ya jinjina kai a hankali ya mik’e yana kuma duban gidan.. Inama ya ganta a gabansa, inama ya ganta tana fitowa daga cikin gidan.. Ya kuma fuzar da fuci kad’an kafin yace “I’m not leaving this place har Sai na ganta.. Nan kawai zatai tunanin zuwa. I’m hundred percent positive.. So you go Assad.. Ni zan tsaya a nan..” Assad ya d’an girgiza kai kad’an yana mai zama gefen Mu’azzam d’in nan saman dakalin. Wayar Mu’azzam ne ya soma ruri, ya ciro daga aljihunsa yana duba mai kiran, ba kowa bane face Safeenah.. Bai d’aga ba sai maida wayar da yai cikin aljihu. Bata fasa kira ba. Assad ya dubesa yace “Bazaka d’aga ba.. It might be something serious..” Gajeren tsaki yai yace “Assad, don’t you think I have a lot on my plate already. Banida lokacin haukar Safeenah..” “She’s still your wife Mu’azzam.. She’s your responsibility.. Ya kamata ka d’aga kaji meke faruwa.” Ya d’an fuzar da fuci kad’an kafin ya d’aga kiran. Kukan Safeenah ya soma jiyowa tana fad’in Tasan komai duk kalan cin amanarta da yai shida wancan ‘yariskar da sunan mission. Ya lumshe idanunsa kad’an kafin yace “Look Feenah.. I don’t have time for your stupid tantrums.!” Katsesa tai da fad’in “Bakada lokaci na amma kanada lokacin shirya mission a bayan ido na hardai ka tasamma raping d’in ‘yar mutane. Ko kunya bakaji ba kana da mata kaman Safeenah Gamji amma kaje kana k’ok’arin aikata fyad’e wa k’aramar yarinya.. Kodai shima cikin mission d’in naka ne..?” Assad kaw matsawa gefe yai yana amsa wayarsa wanda ya soma ruri. Da Mamaki Mu’azzam yace “Mai kika ce Safeenah..?!” “Kaji sarai abinda nace, Wllhi ko ka dawo gida ka kula dani ko na sanar da Daddy ga irin auren da kayi Kasan sarai Daddy bazai lamunci irin wannan auren ba musamman idan yaji cewa auren mission ne.. Sannan harda fyad’e ka tasamma yi a matsayinka na jami’in tsaro.” Gyara zamansa yai kafin yace “First of all kar ki sake cewa na tasamma yin fyad’e wa matata ta sunna.. Secondly, don’t you dare threaten me Safeenah, for as far as I know, I didn’t do anything wrong.!” Safeenah ta jinjina kai tace “I’m not threatening you, I’m only saying the fact.” Mu’azzam ya fahimci cewa Safeenah Ta tsinci note d’in da suka bari ma juna ne shida Sadiya. Hakan yasa ya jinjina kai yace “Okay, well.. Go ahead and tell Daddy.. Kije ki fad’a ma duk wanda kikaga dama cewa ni Mu’azzam Gamji nayi auren mission sannan idan kinje fad’a kice na tasamma kusantar matata wacce nai mata mummunan fahimta daga farko.. And after na fahimci cewa she’s a total opposite of duk abinda nake zato kanta sai na fasa kusantarta dan ba a haka ta cancanci nazo mata ba, because she deserves nothing but the best.!” Daga haka katse kiran yai Safeenah na kuma fashewa da wane irin kuka wanda batayi irinsa a baya ba. Daidai lokacin Assad ya k’araso yana fad’in “Shall we inform our team members ko zasu tayamu da search d’in..?” Girgiza kai Mu’azzam yai yace “Ni a halin yanzu ban yarda da kowa ba Assad, especially mutanen da muke aiki dasu, bayan abubuwan da suka faru nasan ba zakaga laifina ba idan na zargi kowa.” Assad ya d’an shafi kansa yace “Haka ne Mu’azzam, toh yanzu kana nufin ba komai zamu sanar dasu ba gameda case d’in..?” Ya jinjina kai yace “Ko Yusuf ne bazamu sanar dashi komai ba for the mean time har Sai mun fahimci waye mai mana zagon k’asa..” Assad ya jinjina kai yace “What do we do now..?” Mu’azzam Baikai ga basa amsa ba wayarsa ta soma ruri.. Unknown number shine ya bayyana saman screen d’in. Ya dubi Assad ya kuma duban wayar dake ci gaba da ruri.. Lokaci guda ya d’aga wayar. Daga d’aya b’angaren dariya aka fashe dashi kafin mutumin ya furta “Detective Gamji.. It’s been a long time.. Did you miss me..?” Sai aka kuma fashewa da dariya... SameenaAleeyou📚 *GIDAN ARO* *36* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* “Danger.!” Abinda Mu’azzam ya furta kenan yana jinjina kai a hankali. Dariya ya kuma kecewa dashi kafin yace “Correct.. Ashe dai baka mance ni ba.. Koda yake ta yaya zaka mance Abokin shan shayinka..!” “I’ll catch you.. Believe me I will..!” Mu’azzam yace yana sakin murmushi mai zafi. Danger ya kuma k’yak’yata dariya kafin yace “If I were you ba wann maganar zanyi ba yanzu.. Zai fi kyau ka bada mahimmanci ga neman matarka da kake..!” Ya kuma fashewa da dariya kafin ya katse kiran.. Yana katse kiran ya karairaya SIM card d’in yai watsi da ita. K’iris ya rage zuciyar Mu’azzam bata buga ba.. Mai Danger yake nufi.. Badai Sadiya tana hannunsa ba.. No no no. Baiso yayi tunani haka. Zagaye wajen ya soma yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa, Assad yai saurin bin bayansa yana tambayarsa mai Danger yace masa. Mu’azzam yai tsaye yana fuzar da fuci a hankali yana kuma shafe fuskarsa cikin tsananin damuwa “Assad that Maniac was asking me about my wife.. Assad what if..?” Sai kuma ya kasa k’arasawa yana jin harshensa na masa rawa cikin bakinsa.. Assad ya kame kansa yana mai karanto innalillahi wa inna’ilaihi raji’un a hankali. Lokaci guda Mu’azzam ya isa jikin mota yana mai kifa kansa cikin rashin sanin mai zai aiwatar. Assad ya dafa Sa kad’an yace “Let’s not think of the worse.. Bata tareda shi in sha Allah..” D’agowa yai yana duban Assad da idanunsa masu gauraye da tashin hankali, yana pointing Assad da ‘yar yatsa yake fad’in “If he lays a finger on her, I’ll kill him without showing any mercy..” Daga haka bud’e Mota yai ya shige Assad ya zagaya mazaunin mai zaman banza ya shige yana addu’an Allah yasa Danger bai d’auke Sadiya ba. Suna tafe wayar Mu’azzam d’in ta kuma ruri, wani bak’on lamabar ne. Yana d’agawa Danger ya soma fad’in “Don’t think of tracking me down Mr Officer, dan bazaka tab’a samuna ba.. Amma idan kana so ka samu matarka zaka nemi ni koda bazaka sameni ba. Ni kuma zan sanar dakai conditions d’ina..!” Babu shiri Mu’azzam ya paka motar gefen kwalta yana fad’in “Why can’t you face me. You coward..!” Dariya ya kumayi kafin yace “You haven’t changed one bit.. You are still a short tempered police Officer..” Yana maganar yana dariya irinta rainin hankali. Lumshe idanunsa Mu’azzam yai dan yasan yana fad’in hakan ne to provoke him. A halin yanzu baida burin da ya wuce ya ceci matarsa daga hannun wann d’an ta’addan “Wani salon wasan naka ne wannan..?!” Abinda kawai ya fad’i kenan. Danger ya kuma murmusawa kafin yace “Karka damu I play fair idan har zakabi abubuwan da zan gindaya maka.. Amma idan bakabi ba.. Believe me abinda ya faru da k’anwarka zai faru da matarka..After all, she’s as beautiful as your sister..” “If you touch her. I swear I’ll kill you.!” Mu’azzam ya fad’i idanunsa naga kwalta. Dariya Danger ya fashe dashi kafin ya katse kiran. Kifa kansa Mu’azzam yai saman steering wheel yana sakin numfashi a hankali. Assad yai saurin dafasa yana tambayar Mu’azzam d’in. Ga duhun dare da ya soma shiga Sai kiraye kirayen sallar magrib ake. Duk maganar da Assad yake masa bai basa amsa ba har suka tsaya wani masallaci sukai sallah. Yana nan calm kaman babu abindake faruwa harta Assad saida yaji mamakin hakan. Suka nufo motar bayan sun fito daga masallacin still Mu’azzam baice komai ba.. Suna shiga Mota suka d’auki hanyar cikin Abuja amma ga mamakin Assad Sai gani yai Mu’azzam murza kan motar ya canza hanya tamkar wanda aka tinzirasa. Yana ida kwana ba tareda ya dubi Assad ba yace “Get out Assad” Assad ya dubesa da mamaki kafin ya girgiza kai yace “No, a halin da kake ciki bazan Barka kai kad’ai ba Mu’azzam.. I know you so well, so bazan Barka kai kad’ai ba.” Murmushi yai da gefen baki still idanunsa naga waje guda “Ka fita Assad.” Ya sake fad’i yana damk’e kan steering d’in sosai. Assad ya kuma girgiza kai “Bazan Barka kai kad’ai ba Mu’azzam..” Jinjina kai Mu’azzam yai yace “Fine.. Ka zauna kai kallo..!” Daga haka ya ja motar suka soma falfala gudu saman kwalta. Basu zarce ko ina ba sai daban su Danger da Sagir k’ofar shagon Danger yanda Danger d’in yace Sagir sayen sigari ne kawai ke kawosa basuda wata connection. Suna isa yai parking Assad Sai dubansa da mamaki ganin babu kowa babu alamun mutum a k’ofar shagon Danger, tamkar dai anyi shara. Assad ya girgiza kai kurum yana duban Mu’azzam d’in “Kana tunanin zamu sami Danger a nan ne.?” Mu’azzam bai ce masa komai ba Sai k’urama k’ofar shagon idanu da yai. Assad bai kuma cewa komai ba sai kwantar da kansa da yai cikin kujera had’ida lumshe idanunsa. Kusan minti talatin suka kwashe a wajen babu ko tsuntsu da ya gifta. Assad ya d’an fuzar da huci yana duba agogon dake d’aure hannunsa. Ya bud’e baki kenan da niyyan magana suka hango wasu matasa sun nufo shagon. Mu’azzam zai bud’e Mota Assad yai saurin rik’osa yana fad’in “Mubi komai a sannu Mu’azzam..” Da tsananin mamaki yake duban Assad kafin yace “That Maniac has my wife yet kana cewa na bari ayi komai a natse..? Assad Wai shin ka mance cewa Sadiya itace target d’in Su Danger.. Ka mance cewa nemanta suke ruwa a jallo.. Ka mance cewa ta dalilin nemanta da suke kowa nata ya shiga had’ari..? If you can’t be at any help kar ka kuskura kai tunanin dakatar da ni..!” Daga haka sauk’a yai ya nufi matasan Assad yai saurin bin bayansa, kamo Mu’azzam d’in yai suka d’an lab’e suna sauraron tattaunawar matasan yanda suke jajen sun d’ebe kwanaki basa ganin Danger bai bud’e shago gashi akwai wata nau’i na k’waya a wajensa kawai suke samu. D’aya matashin yai tsaki yana fad’in kodai ya daina zuwa nan ne gaba d’aya.. Aiko zai rasa customers.. Muje kawai dallah..” Ganin zasu shige yasa Assad fitowa daga yanda sukai kwanton b’auna suna sauraron tattaunawarsu. Tuni d’ayan ya arce dan sun zaci ‘Yan kamen Drugs ne.. Assad ya juyo yana duban d’ayan wanda tuni Mu’azzam ya damk’o kafad’arsa ya sharb’e k’afafunsa ya zube k’asa. Saurayin ya shiga d’ago hannaye yana rok’onsu yana fad’in wllhi basu saye k’wayan ba kuma shi ba D’anta’adda bane. Assad yace “Munsan kai ba D’antadda bane amma kana Ta’ammudi da miyagun k’wayoyi, zamu iya kulleka akan haka Kasan da wannan.?” Saurayin wanda duka duka bai fi shekaru 20 ba ya shiga jinjina kai yana kuma rok’on Su k’yalesa.. Assad yace “Zamu sakeka idan ka amsa mana tambayoyinmu..” “Na rantse da Allah Yallab’ai wllhi Allah shine shaidana ni zan fad’i gaskiya, ina sayen abu wajensa amma ni ba D’antadda bane..” Mu’azzam baice k’ala ba Tunda Assad ya soma tambayar mutumin. Kafin Assad ya ankara sai gani yai Mu’azzam ya janyo saurayin ya jefasa cikin Mota. Assad yai tsaye kurum yana dubansa cikin rasa mai zaice. Bayan Mota Mu’azzam ya bud’e ya jefa saurayin ciki kafin ya d’auki hanya.. Assad yai saurin take masu baya saidai bai cimmasu ba mai taxi kurum ya tara yace Su bi bayan Motar Mu’azzam wanda Mu’azzam d’in keta wajajjaga gudu dasu shida wann matashin. Matashin ya shiga ihu ganin ana wasa da rayuwarsa saman kwalta d’in da babu yawan motoci yana fad’in “Rankaidad’e na shiga uku.. Dan Allah ka tsaya kar ka kasheni..” Idan motar Ta amsa Mu’azzam ma zai amsa, Sai wajajjagasu yake yana gwara mutumin nan. Lokaci guda yake jefo masa tambayoyi “Ina Danger yake..?” Saurayin yace “Wanene Danger..? Wllhi ban sanshi ba.. Dan Allah kamin rai..” Mu’azzam ya jinjina kai kafin ya kuma sharan wata kwana da motar wanda saida mutumin ya kuma buga kansa jikin marfin Mota “A ina zan sami Mutakk’a ..?” Ya kuma jefo masa tambayar daidai sanda suka shige wani bend yanda zai shigar dakai daji. Saurayin sai haki yake yana furta “Rankaidad’e kamin rai..” Parking Mu’azzam yai ya bud’e marfin motar kafin yasa hannayensa biyu ya fiddo saurayin wanda tuni ya gama jigata. Sai haki yake yana layi alamun an wajajjagasa. Daidai lokacin Assad da mai tasi ya sauk’esa a bakin hanya ya k’araso wajen.. Kasasancewar basu shiga can ciki ba yasa manya manyan kwan wutan streetlights ke haskosu tarau. Mu’azzam na k’ok’arin kicking bindigar. ya saita Saurayin da Ita yana kuma jefo masa tambaya “Tell me now, if you value your life.. Ina Danger yake..?!” Saurayin dake duk’e saman gwiwoyinsa hannayensa ya d’aga alamun rok’o yana girgiza kai yana Hawaye yake fad’in “Na rantse da Allah ban Sani ba Yallab’ai.. Ni tsautsayi ne ma yakai ni shagon yau.. Dan Allah kamin rai..” Assad ya girgiza kai dafe da kunkuminsa yana duban yanda matashin ke karkarwa dan tsoro kafin ya dubi Mu’azzam yace “Ka k’yale yaron nan haka, It’s obvious baisan koma ba..” Ya kuma duban saurayin dake duk’e yana rawan d’ari yace “Tashi kaje..” Saurayin ya mik’e yana godiya, har ya juya zai wuce Mu’azzam ya saitasa da bindiga. Lokaci guda yake furta “If you take one more step, I won’t hesitate to blow your brains out.!” Ya k’arashe yana saita kan saurayin. Juyowa saurayin yai in a slow motion yana had’o hannayensa yana kuka yana rik’on Mu’azzam yai masa rai. Mu’azzam ya shiga harbin k’asa gefen k’afafun saurayin, sai tsalle yake yana kaucewa bullets d’in yake fad’in “Na shiga uku.. Kamin rai..!” Yana tsalle yana sakin fitsari a wandonsa dan tsoro. “Believe me, the next bullet zai sauk’a ne a jikinka Idan baka sanar dani yanda Muttak’a mai saida maku kayan maye yake ba.. Talk now..!” Ya kuma fad’i yana harbin tsakankanin k’afafun saurayin abinka da wanda yasha training ya k’ware wajen saita bindiga da harbata. Take saurayin ya soma fad’in “Zan fad’i gaskiya wllhi..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Ina jinka.” “Wllhi dama Muttak’a mai shago syrup yake saida mana, da ‘yan chocolates (drugs) Toh wllhi wllhi abinda kawai muke saye wajensa kenan..!” Ya k’arashe yana sakin numfashi da k’yar. “Ina za’a samu Muttak’a..?” Mu’azzam ya kuma jefo masa tambayar. “Rankaidad’e wllhi ban Sani ba amma akwai wani abandoned warehouse da wasu lokutan yake cewa mu samesa a can idan zai saida mana k’waya dan kar idon jami’an tsaro yakai kansa.. Wllhi Yallab’ai Iyakacin abinda na sani kenan kansa.. Kuma k’wayar ma na daina sha na tuba wllhi daga yau.. Dama Mamata tayi tayi na dena nak’i amma daga yau wllhi na dena..” Ya k’arashe yana kuma matse k’afafunsa da tuni fitsari ya wanke wandon. Kana ganin yaron Kasan ya gama razana. “A ina ne Warehouse d’in yake..?” Babu musu saurayin ya sanar dashi yanda warehouse d’in yake. Bai kuma furta komai ba ya nufi Mota Assad ko ya dubi yaron kafin ya k’arasa ya d’aura masa Pcap d’insa da ta fad’i dan azaba yace “Sai kai nasiha ma abokinka Shima ya daina Ta’ammidi da miyagun k’wayoyi domin gobenku tai kyau..” Saurayin da gumi ya wankesa sai jinjina kai yake yana haki yana Godiya. Daga nan Assad take ma Mu’azzam baya yai cikin sauri, dan tuni Mu’azzam d’in ya kunna Mota. Suka nufi location saida k’wayan Danger da yaron ya sanar dasu. ** Maleeka ta d’ago tana duban Chief da tsananin mamaki kafin ta girgiza kai tace “I don’t get you.. Chief.” Ya kuma murmusawa yana mai zama saman gadon Otel room d’in kafin yace “You are on the path of no return Maleeka.. You know too much already..!” Ya mik’e tsaye yana zagayeta yana mata wani irin duba fuskarsa d’aukeda muguwar murmushi.. Lokaci guda ya kamo fuskarta mai cikeda tsoro kafin yace “Turning back will be dangerous for you.. Not only you, you don’t want drag your loved ones into this.. I mean your family..” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa. “Mai kuke so na maku yanzu..?” Ta tambaya tana duban Chief. Chief ya murmusa kafin yace “Inaso ki haifar da rashin yarda a tsakanin team d’inku..” “Mai kake nufi da haka..?” Maleeka ta tambaya tana dubansa. “Detective you know exactly what I mean.. Inaso ki haifar da rashin yarda tsakanin Mu’azzam da abokinsa Assad.. If those two are working together bazamu tab’a cin nasara wajen Kai Mu’azzam k’asa ba. Ina fata kin fahimci abinda nake nufi.” Girgiza kai Maleeeka tai tana sakin murmushin da yafi kama da yak’e “You know this is not possible.. Those are like brothers.. They always have each other’s back... Bazaku tab’a iya shiga tsakaninsu ba..” Chief ya murmusa kafin yace “Bazamu iya ba amma ke zaki iya..” “How..?” Ta tambaya tana dubansa lokaci guda taci gaba da fad’in “We are talking about Mu’azzam Gamji here.. Kasan shi d’in wane irin mutum ne..” “I don’t know how Maleeka.. Amma dole zaki samo hanyar da zaki saka shakku da kokonto tsakaninsa da amininsa Assad.. Idan kikayi haka, kinada reward mai girma daga wajen BAT..” Ya k’arashe yana mai k’arasawa yanda kayansa ke ajiye ya d’aga ya ciro bunch d’in ‘yan d’ari biyar biyar ya mik’a mata “Somin tab’i ne wannan.. BAT yace a baki kisha minti daidai..” Maleeka tai tsaye tana dubansa shida kud’in kafin ta girgiza kai tace “I can’t do this Chief.. Bazan iya cin amanan abokan aikina irin haka ba. I’m not a betrayal... I can’t accept your offer.. I’m sorry, Sir..!” Ta k’arashe cikin tsananin tsimewa tana duban fuskarsa. Chief ya kuma sakar mata murmushi kafin yace “Kin riga da kin shiga ciki Maleeka. Kuma Bazaki iya fitar da kanki ba.. If I were you zan karb’i kud’ad’en nan kuma nayi biyayya.. Idan har Kinyi valuing rayuwarki..” Maleeka Ta murmusa kafin tace “You and your accomplices can go ahead and eliminate me but I’ll never ever allow you to destroy Mu’azzam..” Chief yai wata dariyar rainin hankali kafin yace “I like your courage yarinya.. I wish yanda kike son kare Mu’azzam shi zai iya miki haka.. Shin akan Waye kike d’aga jijiyan wuya.? Mutumin da mata biyu zuk’a zuk’a ke garesa mai zaiyi dake Maleeka.. Dama kin daina b’atawa kanki lokaci ne dan Officer Gamji babu abinda zai dake.. Da wannan kumfan bakin da kike da zuwa kikai kika taimaka masa da neman matarsa da yake wacce aka saceta a safiyar yau..” Da tsananin mamaki Maleeka ke dubansa kafin ta girgiza kai tace “Kana nufin an sace Safeenah..?” Ya kuma murmusawa yana mai kishingid’uwa saman gado “Da alama Bakida labarin auren tsohuwar fiancée d’in Sagir da Mu’azzam yai.. And it seems your team members basu sanar dake komai.. Da alama suna zarginki..!” Ya k’arashe yana mai kuma fashewa da dariya. Zuciyar Maleeka yaci gaba da tsinkewa, Ta shiga girgiza kai tana duban Chief wanda keta kyakyata dariyar mugunta. Lokaci guda Chief yaci gaba da fad’in “You are Trapped Maleeka.. Idan akwai wanda Mu’azzam Gamji zai suspecting cikin team d’insa Toh ki sani kece.. Tun kafin ki bari ya fara zarginki gwara shi ki dasa masa shakkun Abokinsa Assad cikin zuciyarsa. Dan abinda ya miki saura a halin yanzu shine ki nemawa kanki mafita ba ki tsaya kina b’ata lokacinki kan Mu’azzam Gamji ba wanda sam ba samunsa zakiyi ba..” Gijif Maleeka ta zauna saman gadon tanajin Hawaye na gangaro mata.. Tanata fafatawa tana k’ok’arin taga ta cire Safeenah daga rayuwar Mu’azzam ashe haukarta take. Yaushe duk hakan ya faru batada labari.. Kenan Yusuf ma ya sani amma bai sanar da ita ba.. Toh mai suke nufi da ita ne wai.. Tana nan tana k’ok’arin karesu gaba d’aya team d’in daga sharrinsu Jaja ashe su suna can suna aiwatar da abubuwansu ba tareda saninta ba.. Tayi imani Mu’azzam Gamji ba son wannan yarinyar yake ya aureta ba saidai sabida ci gaban case d’insu.. Ta lumshe idanunta tana jin zuciyarta na mata d’aci hawaye na gangaro mata.. Dikda haka bataji son Mu’azzam ya ragu koda da percentage guda ne cikin zuciyarta. Tana jin hannayen Jaja a jikinta ta kuma rintse idanunta. ** Daddy yana zaune parlonsa na k’asa yana duba wasu takardu da suka shafi Kampaninsu yaji sallama kaman Ta d’anuwansa Salman. Ya bar abinda yake ya d’ago da tsananin mamaki yana duban K’anin nasa wanda sam baisan yaushe yazo garin ba. Murmushi saman fuskar Uncle Salman ya k’araso yana mai mik’awa Daddy hannu alamun musabaha. Tsananin mamaki ne saman fuskar Daddy dan ko hannu ya gaza mik’a ma D’anuwan nasa. Uncle Salman ya murmusa kafin ya zauna gefen Daddy yana mai kishingid’uwa cikin kujera “Aren’t you going to welcome your brother..?” Ya tambaya yana karkad’a k’afarsa wanda ke bisa d’aya. Daddy ya aje takardun dake hannunsa had’ida zame Farin gilashi wanda yake sanyawa idan zai karatu. Ya karkato yana duban Uncle Salman sosai. “Salman yaushe kazo garin nan.. Sannan ya akai baka sanar dani kana garin nan ba..?” Murmusawa Uncle Salman ya kumayi kafin ya gyara zamansa yace “First gaisuwa ya kamata mu farayi dan munga juna a matsayinmu na ‘yanuwa.. Sannan sauran tambayoyi su biyo baya..” Daddy ya girgiza kai yace “Salman bazaka tab’a canzawa ba.. You like to surprise people..” Uncle Salman ya kuma murmusawa kafin yace “Exactly.. No one knows me better than my brother.” Ya k’arashe yana sakin murmushi. Daddy ma murmushi ya sakar masa kafin ya mik’o masa hannu sukai masabaha. Gaisawa suka shiga yi Daddy na tambayarsa mutan gida. Nan Uncle Salman d’in ke fad’in ko Shemau batasan yana garin ba, sunyi waya yace mata zaizo sa amma tin lokacin da suke wayar ma yana cikin Abuja. Daddy ya kuma murmusawa had’ida girgiza kai kad’an kafin yace “Salman kenan. Bazaka daina wannan d’abi’ar taka ba.. Na tuna a baya haka kakeyiwa Inne duk lokacin hutunka sa’ilin kana makaranta.. Zakuyi waya da Inne ta tambayeka ya karatu ka amsa mata komai lafiya. Kuna ida waya saidai Inne ta ganka akanta..” Suka d’an dara gaba d’aya kafin Uncle Salman yace “Toh haka ai yafi.. ka dinga surprising mutane. Watarana zasuyi kewarka.. Gashi na samu Magaji a zuri’a mai irin halina Wato Mu’azzam.. Yaje yayi aure ba tareda saninku ba ya baku shock da surprise..” Daddy ya d’ago yana duban Uncle Salman da mamaki kafin yace “Kanada labarin auren Sirrin da Mu’azzam yai ne..?” Uncle Salman yai k’asaitacciyar murmushi kafin yace “Au dama bai sanar dakai cewa ni ya wakilta na karb’a masa auren ba..?” Daddy ya girgiza kai disbelievingly yana duban Salman d’in ba tareda ya iya furta komai ba. Uncle Salman ya murmusa kafin yace “It seems like bai yarda dakai bane shiyasa bai wakiltaka ba ya tsallakeka ya je wajena dukda cewa bama jituwa..” Daddy ya girgiza kai yace “Salman meye nufinka na karb’awa Mu’azzam wannan auren.. Na tabbata bakayi haka bane dan Farin cikin Mu’azzam.. Kanada dalili.. Because you never loved Mu’azzam..!” Mik’ewa Uncle Salman yai yana huci kafin ya soma fad’in “Idan akwai wanda baya k’aunar Mu’azzam da ci gabansa that person must be you dear brother.. Let me remind you har yau kak’i ka sanar da kowa ina kake kai dukiyar Mu’azzam.. Kar ka mance Mu’azzam ya kawo k’arfi da zai iya kula da dukiyarsu da mahaifinsu ya mutu ya bari.. Amma har yau kak’i la sanar da kowa harta shi Mu’azzam d’in.. Mai kake nufi da haka.. Ko auren mahaifiyarsa da Kayi ne kake tunanin ka samu cikakken dama da iko akan dukiyarsu..?!” A fusace Daddy ya mik’e kaman zai mari Uncle Salman sai kuma ya dakata yana nunasa da yatsa “Kar ka bari na tono abinda ya wuce shekaru masu yawa Salman.. Nayi shiru ne Salman sabida bana so ahalinmu Ta tarwatse.. Nayi shiru ne sabida bana so k’unci ya halak’a mahaifiyarmu.. Nayi shiru ne to protect Mu’azzam from you..!” Ya k’arashe yana nuna Uncle Salman hannunsa har rawa yake. Cak Musaddiq dake k’ok’arin shigowa parlorn ya dakata yana sauraron abinda Mahaifin nasa ke fad’i zuciyarsa na wane irin yankewa.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *37* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Shaye da tsananin mamaki Uncle Salman ke duban Daddy kafin ya girgiza kai kad’an “Mai kake nufi..?” Daddy ma jinjina kan nasa yake fuskarsa gauraye da tashin hankali yake furta “I lived with this Salman tsawon rayuwata.. I know exactly what happened that day.. Ranan da Yayanmu Abubakar ya rasu..!” Uncle Salman ya kuma girgiza kai kafin yace “I still don’t get you.. Shin mai kake nufi..?” Daddy ya jinjina kai yace “Naji sa’insan da kukai dashi.. Ka masa rashin kunya cewa ko ba dad’e ko jima sai ka karb’e position d’insa.. I was in his office that day, we were to inspect the factory together dan har mun saka rigunan leda irin wanda ake sakawa idan za’a shiga inspection.. Da naji tattaunawarku sai na fasa shiga inspection d’in nai niyyan komawa gida domin na samu Inne mu tattauna batun had’in kan ahalinmu dan tinda Baffah ya rasu kake rashin kunya wa Hamma.. Baka ganinsa da gashin ido ka kafa idanunka akan matsayin da yake rik’e dashi.. Na fito na barku a cikin Factory.. Koda na dawo gida labarin mutuwar Hamma ya riskemu cewa he was stuck in a cold room... I didn’t want to suspect you Salman because you are our brother.. Na aje wannan a cikin zuciyata ban sanar da kowa ba sabida banaso na raba kan ahalinmu ko na lalata zumuntar mu, sannan banaso bak’in ciki ya kashe mahaifiyarmu mu kuma rasa ahali... Nayi zaton idan ka samu abinda kake so Wato Company zaka rabu da Ahalin Hamma ka cire ido akan Kaso na dukiyar Mu’azzam.. But still ka d’auki tsana ka d’aura akan Mu’azzam kaman dai ba ciki guda kuka fito da Mahaifinsa ba.. Na zab’i na adana masu dukiyarsu sabida D’anuwa irinka Salman.. Shin ka zaci na rayu da wannan abun cikin zuciyata abu ne mai sauk’i..?!” Daddy ya k’arashe yana girgiza kai hawaye na gangaro masa. Uncle Salman murmusawa yai kafin yace “Is this how you welcome a guest, Dear Brother..?” Ya kuma murmusawa kafin yace “Matsalar shine baka da wata shaida da zata nuna cewa ni na kashe Yaya.. Quite alright na fad’i duk abubuwan da kace nace amma abinda bazan tab’a yarda na aikata ba shine kisan Yaya.. Ban kashsa ba lokacin sa ne yayi kuma shiyasa ya mak’ale a d’akin K’ank’ara..” Daddy ya jinjina kai kafin yace “What if baka aikata ba amma maganganun da ka fad’a masa sun janyo ya yanki jiki ya fad’i a cikin d’akin K’ank’ara hardai ya mutu ba’asan yana ciki ba.. What if wann maganganun Naka sune silar mutuwarsa shin kana tunanin alhakin mutuwarsa baya wuyanka..?” Uncle Salman ya kuma murmusawa kafin yace “Ko mai zakace bazan tab’a amsa laifin da ban aikata ba.. Sannan zaka iya fad’awa D’ansa after all shi jami’in tsaro ne.. Sai yai bincike kan mutuwar mahaifinsa wanda baiyi a baya, kaga yazo masa da sauk’i Sai ya had’a binciken tareda na ‘Yaruwarsa.. Zan d’auke matata mu tafi da alama ba’a maraba damu a gidan nan..!” Yana ida fad’in haka yasa kai fuuu ya fice ya nufi cikin gidan shashen Mamy yana dokawa Shemau kira. Musaddiq ya fito daga mab’oyarsa yana jin gumi na kuma keto masa.. Meke shirin faruwa da ahalinsu.. Menene wannan daga wannan sai wancan..? Mai hakan yake nufi..? Kaman dai ahalin nasu mummunan baki na binsu.. Bacin haka meke shirin faruwa dasu..? Idan har Uncle Salman yanada saka hannu a mutuwar Uncle namesake (Kaman yanda yake kiran Baban Mu’azzam dan sunansa Musaddiq yaci) Toh kuwa ya kamata Mu’azzam ya sani.. Idan har za’a binciki Safeenah Maiyasa baza’a binciki Uncle Salman ba.. Da wannan tinanin ya shigo ya tadda Daddy ya had’a tagumi da hannayensa duka biyu. Musaddiq ya k’araso ya zauna kusan k’afan Daddy, ya kifa kansa hawaye na gangaro masa. Lokaci guda yake furta “I heard everything Daddy.. Shin abinda ka fad’i kan Uncle Salman gaskiya ne..?” Daddy ya shafi fuskarsa da duka tafukan hannayensa yana mai fuzar da fuci “Musaddiq you didn’t hear anything..!” Daddy yace yana duban Musaddiq d’in. Musaddiq ya girgiza kai cikin rashin yarda kafin yace “Daddy that was a serious accusation, you know.. Tuhumar Uncle Salman fah kake da alhakin mutuwar Uncle namesake.. Daddy idan da gaske ne duk abubuwan da ka fad’i mai yasa bazaka bari a binciki Uncle Salman ba.. Karfa ka mance Daddy kai ka bada go ahead a tafi Safeenah a binciketa, tana a matsayin ‘yar cikinka.. Mai yasa zaka kare D’anuwanka idan har bazaka kare ‘yarka ba.. Daddy idan Uncle Salman shi yai sanadiyar mutuwar Uncle namesake then Mu’azzam needs to know..” “No Musaddiq..! Koda wasa.. Kar ka kuskura ka sanar da Mu’azzam.. Ko wani cikin ahalinmu idan har kana so ahalin nan yaci gaba da zama a dunk’ule waje guda...!”Daddy yace cikeda gargad’i. Musaddiq ya girgiza kai yace “But Daddy..” Daddy ya kuma katsesa “Kana so ka tarwatsa zuciyar Mu’azzam..?” Musaddiq ya girgiza kai a hankali kansa duk’e hawaye na gangaro masa. Daddy ya jinjina kai kafin yace “Kana so ka tarwatsa Zuciyar Inne..?” Nan ma girgiza kai Musaddiq yai alamun a’a. Daddy yaci gaba da fad’in “Do you think it’s easy for me to live with this..? Musaddiq baka tunanin Mu’azzam ya shiga k’unci da tashin hankali masu yawa.. Ya rasa mahaifinsa tin yanada k’anan shekaru.. Mahaifiyarsa Ta gamu da tsananin jinya wanda tana nan ne tamkar ga babu.. Ya rasa k’anwarsa wacce akai Garkuwa da ita aka kuma kasheta.. Yana tsaka da bincike matarsa da akai niyyan sacewa tun a fari ta zamto prime suspect.. Allah ya rufa asiri ya wanketa da shike batada laifi.. Kwatsam yanzu sai a sanar dashi wannan batu..? Kai ma Kanka adalci kaima D’anuwanka Mu’azzam adalci shin ya cancanci a sanar dashi sa’insan da Uncle d’insa yai da mahaifinsa kafin ya bar duniya..?” Musaddiq kuka yake sosai yana girgiza kai ba tareda ya iya furta komai ba. Daddy ya jinjina kai yace “Idan har kana k’aunar Mu’azzam a matsayin D’anuwa bazaka sanar dashi duk abinda kaji yau ba.. Sannan bazaka sanar da kowa ba.. Kamin alk’awari Musaddiq..” D’ago idanunsa masu zuban hawaye yai yana duban Daddy kafin ya mik’e k’unshe da bakinsa ya fice wani kukan na zuwa masa. ** Babu abinda suka tadda a wannan location d’in Sai kangon gini da wasu dangin karyayyun kujeru. Mu’azzam ya shafi sumarsa zuwa fuskarsa yana fuzar da fuci. Assad ma dafe kunkuminsa yai yana girgiza kai bayan sun gama searching entire location d’in “Mu’azzam stop being stubborn, let’s inform our team members about this..” Assad yace yana duban Mu’azzam d’in. Da wutsiyar idanu yake duban Assad kafin ya girgiza kai yace “No I think we should inform the entire FCID.” Ya basa amsa da fad’in haka Kafin ya kifa kansa jikin garu. Lokaci guda ya d’ago yana duban Assad d’in. Fuci ya kuma fuzarwa yana shafe fuskarsa da duka hannayensa biyu “She’s so stubborn you know.. Na gargad’eta cewa kar Ta fita ko k’ofa amma saida ta fita.. Yanzu ga irinta nan.. D’aniskan nan ya d’auketa..!” Assad yace “Ka kwantar da hankalinka Mu’azzam.. Babu abinda zai sameta and you ain’t gonna lose her..” Da mamaki yake duban Assad jin kalamansa na k’arshe. A hankali ya girgiza kansa kafin yace “I’m only doing my job as a police officer. And I’ll make sure na cire mata stubbornness d’in dake kanta..” Ya fad’i yana murza tafin hannunsa a hankali. Assad ya jinjina kai a hankali kafin yace “Yanzu Meye abinyi..?” Duban Assad yai without uttering a word.. Lokaci guda ya d’an girgiza kai yasa kai zai shige saiji yai kaman yai tuntub’e da wani abu. Dakatawa yai ya kuma haska abun da ya taka da hasken wayarsa. Hular sanyi ce yai tuntub’e da ita.. Ya duk’a a hankali yana kuma haska hular sanyin.. Assad ma ya duk’a yana duban abinda Mu’azzam d’in yake duba. K’aramar Karan dake gefe Mu’azzam ya d’auka ya d’an tura hular dashi, hular ta bud’u sosai.. Bak’ar hula ce irinta sanyi gaban hular an rubuta B.A.T da manyan harrufa.. Mu’azzam yai shiru yana duban hular yayinda Assad ya zuba masa idanu ganin yanda yake examining hular da idanunsa. “Assad nasan mai irin hular nan exactly..” Assad ya dubesa da mamaki kafin yace “Could it be hular Sadiya..?” Girgiza kai Mu’azzam yai kafin yace “Wait.” Ya shiga whatsapp account d’insa ya bud’e hoton dake display picture d’in Musaddiq, hoton su ne shida Musaddiq d’in da suka d’auka a cikin k’ank’ara a k’asar England ko wannesu yayi shiga irinta sanyi. Hular dake kan Musaddiq babu abinda ya rabata da wannan hular da suka tsinta a warehouse d’in da Danger ke business d’in drugs d’insa. Zuciyar Mu’azzam yai wani irin yankewa. Assad ya dubi Musaddiq da hular sanyin dake kansa ya kuma duban hular da suka tsinta nan gabansu. “What is this Assad.. Shin wannan zai iya zama hular Musaddiq ne..? Shin Musaddiq nada connection da Danger ne..? But how..?!” Ya k’arashe cikin tsananin rud’ani. Assad ya girgiza kai yace “Mu’azzam wannan hula ce kawai, ba lallai ta zama na Musaddiq ba.. Mutane da yawa company guda d’aya.. Ta iya yuwa hular wani ne..” Har lokacin duban hular yake kafin ya saka karan ya d’an bud’e cikin hular ya kunna hasken wayarsa yana haska cikin hular sosai, nan yaga alamun tsillin gashi cikin hular. Ya d’ago ya dubi Assad kafin yace “I have an idea.. Ga alamun gashi cikin hular.. We will conduct a DNA test.. If it matches with Musaddiq kenan hular na Musaddiq ne.. And that means Musaddiq nada connection da Danger.” Assad ya d’anyi shiru kafin yace “Toh amma wane connection Musaddiq zai samu da Danger..?” Mu’azzam ya d’an gyara tsugunonsa kafin yace “Ka mance Musaddiq used to be a drug addict. Danger kuma drugs yake saida wa matasa.. Ka mance musabbabin zuwanmu wajen nan d’aya daga cikin customers d’in Danger shi ya bamu location d’in nan.. What if Musaddiq customer d’in Danger ne..?” Ya k’arashe cikin wane irin yanayi. Assad ya shafi fuskarsa cikin rashin sanin mai zai furta. Mu’azzam d’in ma zuba ma hular idanu yai cikin tsananin sanyin jiki. Muryarsa na rawa yake furta “Meke faruwa dani da ahalina Assad.. First Safeenah ce yanzu kuma Musaddiq.. Assad mai hakan ke nufi.. Assad I’m lost.. I .. I don’t know what to do or what to think... Shin wannan duka na cikin wasannin Danger ne..?” Dafasa Assad yai kafin yace “We are still not sure idan hular nan ta Musaddiq ce Mu’azzam.. Ka kwantar da hankalinka zamuyi DNA test kuma zaka gani hular nan bata Musaddiq bace kawai kamanceceniya sukai kaji koh..” A hankali Mu’azzam ya jinina masa kai ba tareda yace komai ba. Lokaci guda ya mik’e. Assad ya dubesa yace “Ina kuma zaka..?” “I’ll be right back.” Ya fad’i yana mai shigewa. Motarsa ya bud’e ya ciro hand gloves da transparent zip lock bag irin wanda investigators ke storing evidence ciki.. Ya k’araso ya zira hannayensa cikin gloves d’in kafin ya d’auki hular ya saka a cikin transparent nylon d’in. Ya mik’e suka fice daga wajen jikinsa duk a mace. Idan yace zuciyarsa bata kusa daina aiki ba yayi k’arya.. Allah ya gani duk k’arfin hali irin nasa wannan bincike na nema ya zautar dashi.. Yanaji za’a iya isa wajen da Zuciyar tass bazata iya d’auka ba.. A b’angare guda ga Sadiya can hannun wannan D’anta’addan.. Gaba d’aya ya rasa Wanne zaiyi.. Ya rasa wane tunani zaiyi.. Assad ne yai driving nasa zuwa gida kafin shi ya nemi abin hawa ya shige nasa gidan. Safeenah tana jin shigowar motar Mu’azzam ta sauk’o parlor cikin kwalliya na d’aukan hankali tana jiran shigowarsa. Sanda ya turo k’ofar kallo d’aya yai mata ya d’auke kansa yai shigewarsa. Safeenah tabi bayansa da kallo shaye da mamaki ganin irin kwalliyar da tai wanda akai dominsa bata ma ishesa kallo ba. A fusace ta mik’e ta haura sama itama. Yana k’ok’arin shigewa bathroom ta shigo d’akin, tasha gabansa tana ture turen baki tana hawaye “Haba my Halaal.. Ka dubi tsawon lokacin nan da mukai bama tare a matsayinmu na ma’arauta.. And.. And yaufa na tare baka tashi dawowa gidan nan ba sai yanzu.. Sannan daka dawo ko kallo ban isheka ba. Wllhi this if not fair Mu’azzam..!” Ta k’arashe tana hawaye sosai. Da gajiyayyun idanunsa yake dubanta kafin yace “Safeenah it was a long day.. And I have a lot on my mind right now.. Please don’t add to it with your drama.” Zai shige Safeenah tai saurin taresa still tana kuka “Sabida mai kake mun haka Mu’azzam.. Idan akan text d’in BAD da aka tura maka ne wllhi nasan wanda ta tura maka..” Da tsananin mamaki Yanzu kam yake dubanta “Mai kike nufi..?” Safeenah ta saka hannayenta tana goge hawayenta, lokaci guda take furta “Wllhi nasan wa ta tura maka.. Kuma ta tura maka ne dan ta rabamu ita ta aureka..” Ta fad’i cikeda confidence. Ya gyara tsayuwarsa yana dubanta, idanunsa akanta ya kuma girgiza kansa a hankali alamun bai fahimceta ba. Safeenah ta shiga jinjina kai still hawaye bai daina gangaro mata ba “Meema ce Mu’azzam.. Meema ita ta tura maka sak’on BAD dan ka zargeni da cin amanar aurenka ka sakeni Ita kuma ta samu ka aureta.. Meema loves you Mu’azzam.. All this abubuwan da nake Meema ke bani shawari ashe so take naita provoking d’inka har ka gaji dani ka sakeni shine data fahimci Ameer na damuna da waya yana ce min shi bai hak’ura dani ba he still loves me Dikda cewa na zama matarka.. Ni kuma bana kulasa ina goge duk wasu sak’onninsa da kiransa tinda nasan implications d’in hakan zai haifar a matsayina na matar aure.. My sister took my phone and copied his phone number.. Shine take tura maka sak’onnin nan dan ka rabu dani.. Mu’azzam wllhi Allah shine shaida na babu komai tsakanina da Ameer. You need to believe me.. Wllhi I’m telling the truth..” Da tsananin mamaki yake dubanta kafin ya saki gajeriyar murmushi yace “Safeenah Anya lafiyarki..? Kin kuwa San mai kike fad’i.. Meema fah.. Meema ce take sona ni Mu’azzam Gamji.?” Safeenah tai saurin jinjina kai tana hawaye “Wllhi itace mai son rabamu..” Girgiza kai ya kuma dan Yanzu kam ya soma tunanin k’wak’walwar Safeenah ya samu matsala. Wai Meema ce mai sonsa, toh yaushe ma yake wasa da Meema da har wannan rainin zai shiga tsakaninsu.? “You are not well Safeenah..” Ya fad’i yana girgiza kai kafin ya rab’a ta gefenta ya shige bathroom. Kuka ta kuma fashewa dashi ta zauna dirshan a wajen tanayin mai isarta.. Ta mik’e ta nufi nata d’akin ta d’au waya ta shiga kiran Mommy dan gaba d’aya kanta ya cunkushe ta rasa mai zatai dan dama Meema ce mai bata shawarin ya abinda zatayi Toh gashi sun b’ata da Meemar akan Mijinta ya zama dole ta samar ma kanta mafita tinda babu Meema. Taita kiran wayan Mommy bata d’aga ba, Safeenah ta silale nan saman carpet tana kuka dan tasan Tabbas Mommy fushi tai da Ita tinda bataso ta tare gidan Mu’azzam ba. Shiko gogan yana fitowa da yaga Safeenah bata d’akin Sai ya danna lock ma d’akin ya soma shirinsa. Daga nan sallah yai shafa’i da wuturi ya jima yana kai kukansa ma Ubangijinsa a matsayinsa na bawa gajiyayye wanda ya gaza sai abinda Ubangijinsa ya masa.. Sosai ya k’ask’antar da kansa gaban mahaliccinsa yana rok’onsa ya kawo masa d’auki a al’amransa. Daga bisani janyo laptop d’insa yai da zummar bincika wasu files da kwanakin baya yai saving.. Amma gaba d’aya ji yai baida kuzari tamkar dai wanda aka zare ma laka. Ya tura laptop d’in yana mai lumshe idanunsa. Ita kurum yake hangowa cikin k’wayar idanunsa da zuciyarsa.. Memories d’in da sukai sharing a gidan da kuma fita waje da suke da sunan mission shi yaita Yawo a kwanyarsa idanunsa da kuma zuciyarsa. Kaman wanda ya tina wani abu ya mik’e ya nufi drawer d’in da ya aje picture d’in da aka masu a park. Ya k’ura ma hoton ido, su duka biyun murmushi ne saman fuskokinsu amma kana ganin murmushin dake bisa kyakkyawar fuskarta zaka fahimci akan dole takeyi.. A hankali yakai yatsarsa guda yana shafa saman hoton daidai fuskar Sadiya. Labb’ansa ne suka fara motsi, harshensa ya soma furta “Don’t you worry.. I’ll find you.. In sha Allah I’ll.. I promise you..” Ya k’arashe yana mai lumshe idanunsa da sukai matuk’ar masa nauyi. Safeenah kaw koda ta dawo taji d’akinsa a rufe nata d’akin ta koma ta fad’a kan gado tana mai kuma fashewa da wani kukan. Washe gari ma batasan fitarsa ba dan yanda Mu’azzam yai kusan kwana zaune yana sak’e sak’en mafita kan abubuwan da suka taru sukai masa yawa haka Safeenah tai kusan kwana tana aikin kuka itama. Bata wani samu bacci ba sai kusan asuba. Dama sallahn ba wai ya wani d’ad’areta sosai bane musamman sallar asuba wanda zai katse mata baccinta. Sai rana ta fito tangararau take sallarta. Allah ka shiryar damu ka datar damu ta farki mik’akk’iya. Ameen! ** Kana ganin k’wayar idanun Mu’azzam zaka fahimci dare ne mai tsawo ya kasance a garesa kafin wayewar gari. Abinka da Farin mutum nan da nan wahala damuwa ko jin dad’i yake nunawa tattare dasu koda kuwa sunyi k’ok’arin b’oye hakan. Suna zaune a ofishinsu gaba d’aya.. Maleey (In Halee’s voice. Lol) Maleeka idanunta akansa tun shigowarsa Office d’in. Tinanin maganganun Chief ne fal zuciyarta, a b’angare guda kuma ga wani irin kishin Mu’azzam d’in da take.. Ita da taji an sace Sadiya ma addu’a take Allah yasa Danger ya maida shegiya matarsa koma ya kasheta gaba d’aya. Mu’azzam d’in na tsaye gaban Farin allo wanda hotunan mutanen dake da alak’a da case d’in a jajjere anyi linking d’insu gaba d’aya da arrows ko Wanne da matsugunin da aka ajesa duk wanda ya tab’a samun alak’a da case d’in. Mu’azzam ya kuma Jan wata Doguwar arrow daga kan hoton Danger yai cycle, ya zana k’atuwar question mark a cikin cycle d’in kafin ya rubuta B.A.T a saman cycle d’in. Assad ne kawai ya fahimci mai B.A.T ke nufi, hular da suka tsinta ne jiya da dare a wajen saida drugs na Danger. Ita kaw Maleeka zuciyarta ne ya dinga bugawa tana tambayar kanta kodai Mu’azzam yasan da batun BAT ne.? Batakai ga samo amsar tambayar da zuciyarta ke mata ba wayar Mu’azzam d’in ta soma ringing.. Koda gani Danger ne mai kira, nan take yai masu umarni gaba d’aya su shirya tracing Danger da zaran ya d’aga wayar. Kowa ya zama in position. Duban Maleeka da ta zama wata sukuku da Ita yai yana karantar Ta kafin yace “Tap trace location.” Yai mata alama da ido kan computer d’in dake gabanta a d’an tsime kafin ya d’aga wayar. Cikin sauri Maleeka tai k’ok’arin saita kanta tana mai jinjina kai kafin tai abinda ya umarceta. Daga d’aya b’angaren Danger ya soma fad’in.... SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *38* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* “Kar ka b’ata lokacinka trying to trace my location. Dan bazaka tab’a samuna ba.!” Danger yace daga d’aya b’angaren. “What do you want.. Tell me..!” Mu’azzam yace cikin k’ok’arin tsawaita conversation d’insu da Danger. Danger ya dara yayinda Mu’azzam ya dubi su Assad yana son sanin ko sun samu location d’in Danger.. Assad yai masa alama da hannu saura ten seconds yaci gaba da jan Danger da surutu.. “Yarona da kuka kama nake so, ka bani shi na baka matarka in exchange..” Murmusawa Mu’azzam yai kafin yace “You know that’s not possible..” Danger ya jinjina kai yace “Your wife’s life is on the line here Inspector.. Da alama har yanzu baka yarda tana wajena bane.. Amma idan bakayi abinda nake umartanka ba zan zamar da ita tawa yanzu nan.. Nayi duk abinda naga dama da ita..” Ji yake zuciyarsa na wani irin tafarfasa, ga gumi dake tsartsafo masa “Don’t you dare.!” Ya fad’i cikin tsnanin karaji yana mai buga teburin gabansa. Danger ya shek’e da dariya kafin yace “Da alama har yanzu baka yarda matarka tana hannu na ba.. But let me put her through maybe zaka yarda..” Kukan Sadiya Mu’azzam ya jiyo tana fad’in “Please don’t.. Don’t hurt me please.. Have mercy dan Allah..” Danger yaci gaba da fad’in “Kaji koh.. Zan baka awa ashirin da hud’u ka saki d’anuwana da kuka kama, idan ba haka ba ka saka ma ranka wannan Beauty d’in ta zama tawa..!” “I’ll kill you...!” Mu’azzam ya fad’i zuciyarsa na tsananin bugawa yana sakin haki a hankali. D’if Danger ya katse kiran a daidai lokacin da sukaci nasaran samun location d’insa. Take Maleeka tace “Location found.” Tana maganar tana sanar dasu ga location d’in. Gaba d’aya suka soma zame headphones d’in suka mak’ala a kunnuwansu suka mimmik’e suna shirin ficewa operation. Daidai lokacin Chief ya shigo sanda suketa shiri cikin sauri babu kaman Mu’azzam wanda gani yake kaman bazai isa wajen ba, alla alla kawai yake ya ceceta ya kuma damk’o Danger da hannayensa. Chief yai tsaye yana dubansu yanda kowa ke sauri cikinsu sai shirya alburusai suke cikin bindigoginsu. Yusuf na sanar dasu wani tsohon building ne Danger yake can wajen gari. Assad ya sarawa Chief yana fad’in “We were able to trace Danger’s location, Sir.” Dikda Zuciyar Chief Ta yanke hakan bai hanasa nuna Farin cikinsa a fili ba.. Yana tafe hannayensa yake fad’in “Then what are we waiting for Detectives.. Move it, faster.. Let’s catch Danger.!” Ya fad’i yana tafe hannayensa alamun Su k’ara sauri. A haka suka dinga ficewa har dai Mu’azzam yazo ficewa, suka tsaya suna duban juna shida Chief. Murmushi Chief ya sakar masa kafin yace “Well done Inspector Gamji.. I must congratulate you and your team..” Murmushi da gefen bakin Mu’azzam ya sakar masa yana Soka bindigarsa jikin belt d’insa kafin yace “Tukunna ma Sir.. Sai kaga Danger da accomplices d’insa behind bars.” Yana ida fad’in haka ya sarawa Chief kafin yasa kai ya shige. Chief yabi bayansa da mugun kallo yana huci, lokaci guda yake duban allon binciken nasu nan yaga an zana circle an rubuta B.A.T a sama ga kuma question mark cikin circle d’in.. Anyi linking circle d’in da hoton Danger. Zuciyr Chief yai wani irin bugawa.. Gumi ya shiga ketowa Chief tako Ta ina.. Kar dai Maleeka ta sanar da Mu’azzam wani abu akan BAT.. Lallai Maleeka tana wasa da rayuwarta. Ya lura komai zatayi akan Mu’azzam. Cikin tsananin fushi mai gauraye da tashin hankali Chief ya daki garu kafin yasa kai ya fice daga ofishin. Kallon da Chief yaiwa Maleeka tasan cewa akwai matsala, tasa kai Ta shige cikin sauri zuciyarta na yankewa. Mu’azzam ne ya rarraba masu bulletproof vests ko wannensu ya aza saman rigarsa, gaba d’ayansu motar Office suka shiga. Assad ke driving Mu’azzam na gefensa Yusuf da Maleeka suna mazaunin baya. Saidai suna isa sukaji an soma kaima motarsu attack da harbi alamun su Danger Sun riga sun San da zuwansu an sanar dasu. Take sukai holding positions d’insu Mu’azzam na fad’in”No one shoot.. My wife is in there..” Suka jinjina kai suna fad’in copy. Su Danger suka ci gaba da harbi kafin daga bisani wutan ya tsagaita. Mu’azzam ne yai masu alama da hannu da ido kan su soma matsowa kusa suna nufan ginin cikin kwanton b’auna. Haka kuwa akai a hankali suka dinga matsawa kusa cikin bin umarnin Mu’azzam har suka isa ginin.. Wani mutumi sanye da bak’ak’en tufafi fuskarsa rufe da bak’in mask shine yai saitin Mu’azzam zai harbesa ba tareda Mu’azzam d’in ya gansa ba Maleeka ta k’arasa da sauri ta tare wa Mu’azzam harsashin tana kiran sunansa dan ita taga mutumin.. Take harsashin ya sameta a hannunta.. Gaba d’aya suka juyo suna duban Maleeka da ta karb’ewa Mu’azzam harsashi ta duk’a wajen tana cije lab’e rik’e da hannuta yanda harsashi ya huda jini na zuba.. Yusuf da Assad suka k’araso a guje suna ambato sunan Maleeka yayinda Mu’azzam yai Chasing mutumin a guje.. Gini ne upstairs mai tsawo irin abandon gini d’in nan wanda zallan Kango ne.. Haka mutumin ya dinga haurawa sama a guje yana sakowa Mu’azzam harsashai Mu’azzam na kaucewa yana kuma chasing d’insa dan a raye yake son capke Sa. Saida ya bari Mu’azzam ya isa sama saura kad’an ya kamasa kafin ya dirk’o yana kuma kai masa harbi.. Mu’azzam ya kama jikin bargwajajjen staircase din kenan zai dirk’o yabi bayansa yaji kaman kukan mutum cikin wani d’aki dake rufe .. Cikin sauri ya juyo yana duban d’akin ya daina chasing mutumin.. A hankali ya furta “Sadee.!” Da k’afarsa ya daki k’ofar saida ya b’allata.. Can ya hangota d’aure saman kujera idanunta a rufe haka ma bakinta.. Jikinsa har rawa yake ya isa a guje ya cire blindfold d’in da aka rufe mata ido dashi.. Suna had’a ido taji wani irin kuka yazo mata.. Lokaci guda yaci gaba da kwanceta yana fad’in “It’s okay.. You’re safe now..!” Ya k’arashe yana mai rungumarta cikin jikinsa. Wani kukan Ta kuma fashewa dashi jikinta sai rawa yake alamun bak’ar azaba yunwa da galabaita had’ida tsananin tsoro da tashin hankalin da Ta tsinci kanta ciki. Kaman wacce ta tuna wani abu tai k’ok’arin cire jikinta daga nasa ta shiga girgiza kai tana k’ok’arin matsawa da baya take fad’in “No no no.. Don’t touch me.. Kar ka tab’a ni kar kazo kusana..” “How do I save you idan ban tab’a ki ba.!” Yai maganar cikin daka tsawa.. Juyawan da zai yaji kaman abu na reading ashe bomb ne a gefe Danger ya aje ma Sadiya da niyyan k’onata. Mu’azzam bai kuma sauraronta ba ya shiga girgiza kai yana furta “Oh shit..! Come here now..” Ya sunkuceta tamkar Baby ya soma gudu da ita tana cikin hannunsa sai had’e stirs yake yana tsallakewa gudun kar bomb d’in Ta tashi dasu suna cikin ginin. A can waje kuwa Maleeka dai tana fama da hannunta da aka harba Assad da Yusuf ne sukai chasing mutumi mai bak’in kayan bayan ya samu fitowa daga building d’in.. Suna guje suna bata kashi tsakaninsu.. Nan harsashi ya samu Assad gefen wuyarsa kusan kafad’arsa yanda Bulletproof vest d’in bai rufe ba.. Ya duk’a a wajen yana kame wuyarsa da tuni jini ya soma kwarara.. Yusuf ya dakata da chasing mai bak’in kaya ya duk’a yana duba Assad dake cikin pain yana k’ok’arin taimakawa d’anuwansa. A can building d’in kaw wata jahilar tsalle Mu’azzam yai still tana rik’e cikin hannunsa daidai sanda Bomb d’in tai exploding.. Haka ya kwanta kan Sadiya ya rufeta ruf sand bomb d’in ta tashi dan ma kar wani abu ya sameta. Maleeka ma ta juyar da fuskarta tana mai kwanciya flat a k’asa sanda bomb d’in tai exploding. A hankali komai ke lafawa. Mu’azzam ya mik’e da k’yar yana jijjiga Sadiya dake kwance k’asar sa wacce ta koma tamkar bata numfashi. Maleeka ta bud’e idanunta da k’yar tana duban Mu’azzam dake ci gaba da jijjiga Sadiya yana fad’in Ta bud’e idanunta. Lokaci guda yaci gaba da jijjigata yana fad’in “No.. No.. Stubborn head.. Not now.. Please wake up.. Wake up.. wake up now..!” Yana maganar yana jijjigata. Dukda rad’ad’in ciwon dake jikin Maleeka bai hanata zuba idanu tana dubansu kaman Ta samu TV.. Tinda take bata tab’a ganin Mu’azzam ya birkice kan wata mace ba sai wannan yarinyar.. For the first time da zata iya cewa taga Mu’azzam Gamji dumu dumu cikin kogin soyayya.. Haka ya dinga jijjiga Sadiya yana fad’in Ta tashi.. K’arshe bakinsa ya d’aura saman nata yana hura mata iska.. Maleeka kaw ji tai wani abu ya tokare mata mak’oshi sanda tanga Mu’azzam ya saka bakinsa saman na Sadiya. Tai saurin rintse idanunta had’ida ciza labb’anta.. Shekara da shekaru tana kwad’ayin irin haka ya kasance tsakaninsu sai gashi yau d’in tanaji tana gani a gabanta yake saka bakinsa cikin na wata.. Ji tai zafin ciwon da taji dominsa na k’aruwa.. Ta kuma rintse idanunta da k’arfin gaske hawaye mai zafi na gangaro mata. Wani dogon numfashi Sadiya taja had’ida bud’e idanunta. Bai wata wata ba ya mak’aleta tsam cikin jikinsa kaman mai tsoron kar wani abu ya kuma raba tsakaninsu. Daidai lokacin Su Assad da Yusuf suka k’araso. Yusuf na tallafe da Assad wanda jini ke zuba sosai daga jikinsa. Cikin sauri Mu’azzam ya bud’e mota ya zaunar da Sadiya ciki kafin ya k’araso wajen abokansa. Assad ko iya bud’e idanunsa bayayi dan sosai harsashin ta shigesa gashi a waje mai had’ari harsashin ya samesa. Sai wannan lokacin Chief ya taho wajen da backup harda ambulance dan tinda aka harbi Maleeka dama suka nemi taimakon ambulance. Kan kace mai an soma basu taimako na gaggawa. Assad aka fara baiwa taimako dan yafi kowa buk’atan taimakon. Mu’azzam ya k’araso da sauri lokacin da aka d’aura Assad saman doguwar gadon tura marassa lafiya. Hannun Assad ya kama yana fad’in “Zaka samu lafiya brother.. In sha Allah..!” Cikin jin jiki Assad ya bud’e idanunsa da k’yar kafin ya murmusa ya jinjina ma Mu’azzam kai yace “Ina Sadiya.. Did you save her..?” Mu’azzam ya jinjina masa kai yace “She’s dafe now..” Ya d’aga masa babban yatsarsa alamun jinjina yana mai sakar masa murmushi da k’yar. Lokaci guda aka tura Assad cikin ambulance kafin aka saka masa na’uran oxygen. Yusuf ya dubi Mu’azzam yace “Zan kula da Assad.. Just go to your wife.” Yai masa nuni da ido zuwa cikin motar yanda Sadiya ke tak’ure waje guda. Jinjina kai Mu’azzam yai kafin ya d’an dafa kafad’an Yusuf alamun godiya. Lokaci guda Yusuf ya shige cikin ambulance d’in.. ** Safeenah da taga Mommy bazata d’auki wayarta ba sai ta yanke shawarin kiran Aunty Shemau. Da kuka ta soma ma Aunty Shemau tana fad’in Mommy tana fushi da ita bata d’aga wayarta. Aunty Shemau ta tab’e baki kad’an tace “Safeenah ni fah na baro gidanku tin daren jiya.. Your Uncle came ya d’aukeni mun taho masauk’insa tare.” Safeenah tace “Aunty Toh ni yanzu ya zanyi da Mu’azzam ne.. Wllhi Aunty ko kallo fah ban ishesa ba dan Allah kizo ki yanzu..” Ta k’arashe wasu hawayen na gangaro mata. Aunty Shemau Ta dubi mijinta dake zaune gefe kafin ta d’an sauk’e ajiyan zuciya tace “Shikenan Safeenah zan tambayi Uncle d’in naku idan ya barni zaki ganni..” Cikin kuka Safeenah tace “Aunty idan Uncle Salman d’in na kusa put him through zan tambayesa da kaina.” Aunty Shemau ta murmusa kafin tace “Kar Safeenah ina nan zuwa kinji koh.. Kiyi hak’uri. Yauwa sai nazo..” Daga haka katse kiran tai tana duban mijinta da ya kafeta da idanu. “Mai wannan shashashar kuma take buk’ata..?” Ya tambaya yana duban Shemau. “Banda akan Mu’azzam.. Kasan ita wannan batada tinani batada hankali sam indai akan Mu’azzam ne.. So take naje gidan nata ta rasa abinyi..” Uncle Salman ya jinjina kai kafin yace “A tak’aice dai zuwanki garin nan baiyi amfani ba Shemau.. Kin kasa d’auko min wad’annan Documents d’in.. Wad’anda idan na mallakesu tamkar na mallaki kaso na dukiyar Mu’azzam ne da d’anuwana ya handame..” Aunty Shemau ta murmusa kafin tace “Idan akan abinda ya shafi takardun kud’i ne babu wanda ya isa yama D’anuwanka wayo.. Dik k’ok’arina na rasa ina takardun suke.. Kuma da alama baya sanar da matarsa wasu abubuwan.. Amma mai zai hana ka cire idanunka akan dukiyar Mu’azzam tinda yanzu company dake Adamawa kai kake rik’e dashi harma da gidan gonar..” Katseta yai da fad’in “Samun mahimman takardun nan su zasu sa Company ta zama nawa gaba d’aya amma muddin ba’a samesu ba baza’a daina cire kason Mu’azzam da ‘yar uwarsa harma da mahaifiyarsa a cikin dukiyar ba. Wann takarda shaida ce zai tabbatar cewa basu da kaso cikin dukiyar.. Inada tabbacin lokacin da Yayanmu ya mutu Marwan shi ya d’auke takardun nan..” Ya k’arashe yana kuma zagaye d’akin lokaci guda yana kurb’an shayi. Aunty Shemau ta sauk’e ajiyan zuciya kafin tace “Yanzu kam da ka d’auko ni ai ka b’ata komai saidai mu dake gwada sa’an wani lokaci.” Fuzar da fuci yai yana mai jinjina kai a hankali. ** ‘Yansanda ne tin daga k’ofar asibitin har cikin asibitin. Tuni an shiga da Assad d’akin operation.. Sadiya ma Ta k’ara fainting a asibitin dole aka bata Gado dan gaba d’aya babu k’arfi da kuzari jikinta gashi har lokaci bata daina razana ba sabida abinda ya faru da Ita. Da alama tin safiyar ranan da aka d’auketa bata saka komai a cikinta ba.. Kwana guda kenan tai babu abinci ya tsoro da razana dole aka d’aura mata ruwa a nan asibitin. Mu’azzam yana zaune gefenta yana dubanta idanunta a lumshe, da gani baccin azaba take da kuma tsoro. A hankali yakai hannunsa saman goshinta yana shafawa a hankali “Bazasu k’ara samun damar cutar dake ba.. Na miki alk’awari..” Ya fad’i idanunsa akanta Lokaci guda kuma yai shiru yana nazari.. Maiyasa suke bibiyanki da ahalinki.? Maiyasa suke so su shafeki Keda ahalinki..? Zuciyarsa Ta basa amsa da fad’in ‘Sabida suna tsoro kar Sagir ya sanar da ita wani abu tinda har saura kad’an ya aureta.. Zasuyi tunanin yarinyar tasan duk wani shirinsu daga wajen Sagir.. Watak’ila harta ahalinta ma sun sani..” Shafe fuskarsa yai da duka hannayensa biyu kafin ya mik’e yana duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu. Fitowa yai daga d’akin ya dubi ‘yansanda guda biyu dake tsaye k’ofar d’akin yace su kula sosai babu mai shiga Sai likitan nan da suka gansu tare.. Suka jinjina kai suna sara masa. Lokaci guda ya shige nan ya hangi Maleeka ana rufe nata wound d’inta a dressing room. Kaman zaisa kai ya shige sai kuma ya dawo da baya. Da wutsiyar idanu Maleeka take dubansa.. Ganin ya tsaya yana dubanta ya sa Maleeka marairaicewa kaman yau ne bullet ya soma kuskuranta. Mu’azzam ya nufo d’akin still idanunsa akanta, daidai lokacin da aka fama rufe mata ciwon. Ta d’ago tana dubansa, k’warjininsa ya hanata duban k’wayar idanunsa, hakan yasa Ta sadda kanta a hankali. Hannayensa dafe da kunkumi yake dubanta “You shouldn’t have done that, you know..” Ta d’an d’ago a zabure tana dubansa jin abinda yace Mu’azzam ya kuma jinjina kai kafin yace “Maisa zaki karb’a mun harsashi.? Next time kar ki sake abu makamancin haka Maleeka.. Get well soon..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige. Maleeka Ta saki baki da hanci tana dubansa, Ta tare masa harbi harsashi ya sameta maimakon ya samesa amma ya rasa abinda zai fad’a mata sai wad’ann kalaman.. Maimakon yai mata godiya ko ya nuna kulawarsa akanta amma abinda zai iya fad’i kenan sabida tsaban girman kansa da isansa.. Tai k’wafa tana jin zuciyarta na mata wani irin k’una.. Nurse d’in ta k’araso tana fad’in bari a k’arasa rufe mata ciwon. Tsaki Maleeka tai tace “Barshi bana buk’ata..” Nurse d’in tace “But infection zai iya shiga ki tsaya a k’arasa rufewa.” A kufule Maleey tace “Ank’i a tsaya d’in.. Baza’a tsaya ba.. Infection d’in ya gama shiga a daidai lokacinda wanda akaji ciwon dominsa ya nuna rashin kulawarsa.” Tana ida fad’in haka ta mik’e tana huci. Chief ne ya shigo yace ma nurse d’in ta d’an basa Moment da Maleeka. Babu musu nurse d’in ta basu waje. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *39* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Chief ya k’ura mata idanu yana girgiza kai “Ban yarda baki sanar dashi komai akan BAT ba.. If you can take a bullet for him na tabbata zaki iya masa komai.. So you better tell me the truth right now.. Mai kika sanar da Inspector Gamji gameda BAT.?” Ya k’arashe kaman zai shak’ota. “Wane irin rantsuwa kake so na maka..? Na rantse maka da Allah ban sanar dashi komai ba.. Yanda kaga ya rubuta B.A.T jikin board haka nima na gani.. I’ve no clue mai hakan yake nufi..” Jaja ya jinjina kai ya d’an kuma matso da fuskarsa kusan na Maleeka. Cikin yanayi na gargad’i yake furta “You better be telling the truth.. Because once I find out k’arya kike mun Maleeka..?” Ya murmusa kafin yace “Ki fara k’irga kwanakinki..” Har ya juya zai fice ya kuma dawowa “Ki tabbata kin samo mai Mu’azzam ya sani gameda BAT.. Wannan shine next Assignment d’inki..” Murmusawa Maleeka tai kafin Ta girgiza kai tace “Da alama har yanzu bakusan da wa kuke dealing ba Sir.. Do you think this is an easy task..? We are talking about Mu’azzam Gamji here..” Ta gyara tsayuwarta kafin taci gaba da fad’in “Guy d’in nan is a complete savage. I risked my own life for him.. I took a bullet for him.. But a simple thank you ya gaza fad’a.. Irin wannan mutumin nan ne kuke tsammanin shiga jikinsa abu ne mai sauk’i..? Mu’azzam Gamji is not like every other guy.. Kuyi hak’uri amma zai matuk’ar wuya ku kaisa k’asa..” Chief ya murmusa kafin yace “Ko bai fad’a miki ba yasan he owes you a huge of gratitude.. And deep down ya gode miki.. Kuma bazai tab’a mance sacrifice d’in da kika masa ba.. Kawai kaman yanda kika ce ji da kansa bazai barsa ya nuna miki hakan ba ko ya furta.. But believe me kin samu yardarsa daga yanzu.. Mu’azzam Gamji will never doubt you bayan sadaukarwa mai girma da kika masa.. Ki ringa da kin samu yardar Mu’azzam, yanzu abinda ya rage miki shine kisan mai yake ciki, kiyi uncovering duk wasu abubuwan da ya sani especially akan BAT.” Ya murmusa kafin ya kuma furta “Get well soon sweetheart..” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice. Huci Ta kuma saki kafin Ta fito waje, nan ta hangi motar Mu’azzam a wajen. Ta d’an d’aga gira guda sama tana duban motar.. Toh kenan bai tafi bane ko k’ak’a.? Wata Zuciyar ta bata amsa da fad’in Ina zai tafi tinda Queen of his heart tana kwance anyi admitting nata.. Ta fuzar da fuci mai zafi tana furta “Goddamn your pride Inspector Gamji..!” Tana ida fad’in haka Ta nufi motar tasa dan a zatonta ko zata hangosa ciki. Tai tsaye tana k’are wa motar kallo.. A backseat ta hango wani abu cikin transparent nylon.. Tai saurin matsowa tana duban abun.. Hula ce d’auke da rubutun B.A.T a fuskar hular.. Take ta soma tina abinda taga Mu’azzam ya rubuta saman allon bincikensu.. Kenan wannan ne clue d’in da ya samu gameda BAT ko menene.. “I need to find out what he knows.” Ta furta a hankali tana mai ficewa daga asibitin lokaci guda ta tari Cab ta shige tana dialing layin Chief..” ** Kai tsaye bayan ya fito daga asibitin gida ya wuce dan ya samu yai wanka ya sake fitowa. Bud’e k’ofar parlorn da zai ya hangi used tissue papers baja baja a k’asa wanda Safeenah tasha kukanta ta goge fuskarta dasu, ya hangi dining table nan ma yaga a wargaje, ko ina very scattered.. Ga plates a saman dining table d’in ga abinci har saman table d’in tin daga cikin takeaway pack har k’asa.. Ga ledojin da aka sayo abincin ciki suma suna nan a wajen ba’ai disposing nasu ba.. Fuzar da fuci yai a hankali kafin ya nufi upstairs cikeda k’yank’yanin gidan gaba d’aya kaman ba kwana guda Safeenah tai cikin gidan ba ko Ina kaca kaca.. D’akinsa ya nufa ya soma rage kayan jikinsa. Daidai lokacin Safeenah ta shigo taci uwar gayu kai kace ba itace tai kaca kaca da gidan ba tsaban yanda Ta tsara gayu ma jikinta. Fuskar nan Sai k’yallin kwalliya take an zubo da gashi sai zuba k’amshi ake. Saurin K’arasowa tai tana k’ok’arin b’alle masa botiran rigar nasa. Ganin bai gwasaleta ba ya sanyata kuma rausaya idanu tana ci gaba da b’alle masa botiran cikin salo na jan hankali “My Halal banji zuwanka ba..” Ta fad’i cikeda shagwab’a. Kauda fuskarsa yai kad’an kafin yace “Ina zakiji kina can kinata tsara kwalliya ma jikinki kin bar gidanki kaman bola..” Ta d’an turo baki tace “Yanzu zan gyara.. Na kawo maka abinci ne... Nayi order online d’azu..” Girgiza kai yai yace “I’m Ok.” Ya d’anyi gyaran murya kafin yaci gaba da fad’in “Everywhere is scattered Safeenah.. Ya kamata ki kira gida kice a turo miki yarinya da zata ke tattara gidan nan.. Kinsanni, I’m obsessed with tidiness..” Safeenah ta kuma turo baki cikeda shagwab’a tace “My Halaal kasan bana son wata tazo ta zauna a gidana.. Ni kawai bana son wata ‘yar aiki a gidana, I can handle everything here..” Girgiza kai yai yace “No Safeenah, you can’t.. Bazaki iya kula da gidan nan ba.. Ki kira Mommy right this moment ki fad’a mata kina buk’atar help.” Ta kuma turo baki cikeda shagwab’a, kafin tai magana ya tsareta da rikitattun idanunsa yace “Now Safeenah..!” Babu musu ta d’auki wayarta da ta aje saman gadonta Ta soma dialing layin Mommy tana addu’an Allah yasa ta d’aga. Kaman kaw bazata d’aga ba, can ta d’aga ba dan tayi niyya ba Sai dan Aunty Shemau ta kirata ta sanar da ita halinda Safeenar ke ciki bayan taje gidan Safeenar. Bai tsaya sauraren wayar ba ya fad’a bathroom. Safeenah ta zauna nan saman gado tana gaida Mommy, Mommy na amsa mata da k’yar. Safeenah ta d’an kuma turo baki tace “Mommy are you still mad at me..?” K’wafa Mommy tai kafin tace “Ba dai kin tare gidan miji ba.. Ke ga mai miji ya miki kyau Safeenah.. Ni mai zan ce miki bayan Allah ya kad’e fitina tinda kedai bakisan ‘yancin kanki ba.. Ke gaki ‘yar dad’i miji.” Safeenah tace “Kai Mommy.. Let bygones be bygones.. My Halaal ma komai ya wuce wajensa.. And I don’t think yana tare da wancan shegiyar..” Katseta Mommy tai da fad’in “Ke dallah rufe mun baki shashasha.. Wani Your Halaal kika samu.. Indai namiji ne Sai ya baki kunya gaki ga shi.. Kin karb’ar ma kanki ‘yanci ma ya kika k’are hannun namiji balle ke da kika kai masa kanki Bayan duk kalan rashin mutunci da ya zabga miki..” “Mommy nifah bani na kawo kaina ba.. Daddy ne ya kawoni.. Mommy ni duk bama wannan ba.. Kira nai nace ki turo min d’aya cikin yaranki my Halal yace ina buk’atar Help..” Ji tai kaman ta buge Safeenah ta cikin wayar “Kinci ubanki dake da Halal d’in naki.. Baza’a turo ba..” Tai maganar tana dak’uwa da hannunta kace Safeenar tana gabanta ne. Safeenah Ta kuma turo baki tace “Ba damuwa Mommy zamuyi hiring a registered company.. Zan fad’awa My Halal..” Katseta tai da fad’in “Kika k’ara ce mun wani My Halal zan fasa bakinki ta cikin wayar nan.. Doluwar banza ya gama cutanki kin d’ibi jiki kinje kina zama dashi.. Ina Mu’azzam d’in yake..?” Baki a ture Safeenah tace “He’s having a shower.” “Toh idan ya fito ki kirani ki sanya wayar a handsfree zan masa magana kinji koh..” Safeenah ta jinjina kai tace “Alright Mommy..” Daga haka katse kiran tai ta kuma mik’e k’afafu nan saman gadon tana jiran fitowarsa. Jim kad’an ya fito yana tsane jikinsa, shi a zatonsa ma Ta fice a d’akin. Ya d’an dubeta da gefen ido kafin yaci gaba da abinda yake. “Mommy tace tana son magana dakai yanzu..” Tai maganar tana mai nufosa. “Tace idan ka fito I should call her back.” Jinjina kai yai yace “Ehen.. Kirata mana.” Safeenah Ta jinjina kai kafin Ta janyo wayarta ta soma dialing layin Mommy. Bugu d’aya a na biyu Mommy Ta d’aga. Safeenah tasa a handsfree kaman yanda Mommy tace d’in. A zaton Safeenah Mommy zatai maganar ‘yar aikin da Mu’azzam yace a turowa Safeenah ce saiji tai Mommy ta soma fad’a ta yanda take shiga bata nan take fita ba “Kana jina Mu’azzam koda wasa kar ka kuskura kazo kusan d’iyata ba tareda ka kawo min shaida daga asibiti cewa baka d’auke da cutan zamani ba.. Wllhi kaji na rantse maka idan ka kuskura ko rik’e hannun Safeenah kai ba tareda ka kawo min shaida daga asibiti cewa baka d’auke da cutar kanjamau ba Allah ya isa ban yafe maka ba..!” Safeenah Ta kame bakinta da hannu tana girgiza kai.. Kaman Mommy na ganinta tace “Idan kika katse wayar nan ke kuma sai na tsine maki.. Kuma Idan kika kuskura kika..” Basu k’arasa ji ba sai kururuwar Mommy suka jiyo tana fad’in “Dan na fad’i gaskiya.. Akan Mu’azzam ne yau zaka d’aga hannu ka ma...” Mu’azzam bai bari Mommy Ta k’arasa furta kalmar mari ba ya katse kiran d’if. Ashe Daddy ne ya shigo yajita tana wannan maganganu shine ya fuzge wayar ya had’a mata da mari. Safeenah ta sadda kai tana hawaye. Mu’azzam kaw kaman babu abinda akai yaci gaba da shirinsa. Zuciyarsa yana nanata kalaman Mommy wai shi Mu’azzam akema zargin cuta.. Har Mommy tana masa iyaka da d’iyarta bayan ma Safeenar albarkacin Daddy taci shiyasa aurensu bai k’are ba. “My Halal please talk to me..” Safeenah tace tana k’ok’arin matsowa kusansa. “Bakiji mai Mommy tace bane..? Kiyi hak’uri sai na kai mata takardan gwajin lafiyata kaman yanda tace..” Saurin girgiza kai Safeenah tai tace “Dan Allah kai hak’uri da Mommy my Halal..” Ta k’arashe tana k’ok’arin kamo hannayensa. Dakatar da ita ya kumayi ta hanyar d’aga mata hannu “Don’t Safeenah.” Ya fad’i yana d’ago hannunsa guda. Baki a ture Safeenah tace “But you are my Halaal..” Ya jinjina kai yace “Of course amma Mommy bata yarda da hakan ba..” Safeenah ta goge hawayenta tace “Amma ai Mommy batada hurumin da zata haramta mana juna.. Dan Allah kar ka azabtar damu kan maganganun Mommy..” “Bazan saka ma ‘yarta cuta ba.. Zo ki fita ..” Ya fad’i yana nuna mata k’ofa. Kuka ta fashe dashi daidai sanda wayar Mu’azzam d’in ya soma ringing. Daddy ne mai kiransa. Ya d’aga cikeda risinawa Safeenah Ta lab’e tana sauraron wayar. Jinjina kai yai cikeda girmamawa yace “Alright Daddy.. Zan taho yanzu..” Daga haka k’arasa shiryawansa yai cikin k’anan kaya gray polo sai blue jeans.. Bai bari Safeenah taji fitarsa ba dan baida lokacin dramarta. Yana isowa gidan Daddy ya hangi Musaddiq zaune balcony d’in side d’insu shida Musaddiq d’in. Ya k’urawa Musaddiq d’in idanu wanda ko ba’a ce maka ba cikin damuwa yake. Take tinanin hular B.A.T ya fad’o masa.. He needs to find out shin Musaddiq nada alak’a da Danger ne kokuwa dai wasa da hankalinsa Danger yake.. Da wannan tunanin ya nufi b’angaren Daddy. Yana dosowa ya soma jiyo hayaniyar Mommy tana fad’in tinda Daddy ya d’aga hannu ya Matera kan D’aniskan yaron nan wllhi sai ta bar gidan.. Saidai duk abinda zai faru ya faru.. Fasa shiga Mu’azzam yai ya nufi b’angaren Musaddiq. A balcony d’in ya taddasa.. Yai masa sallama. Da k’yar Musaddiq ya iya amsawa kana ganinsa zaka fahimci cewa he’s not himself.. Gaba d’aya a dama yake.. Ba komai yake tunawa ba face tattaunawar Uncle Salman da Daddy. Maganganun suketa Yawo a kwanyar Musaddiq kaman zasu tarwatsa masa kwanya ga Daddy yace ko da wasa kar ya sanar da Mu’azzam wani abu for their family’s sake. Ya k’ak’aro murmushi daidai sanda Mu’azzam d’in ke zama kujerar gefensa “Detective.. Yaushe ka shigo.?” Musaddiq ya tambaya yana dubansa. K’ura masa idanu Mu’azzam yai yana karantarsa kafin ya d’an girgiza kai yace “Are you alright..?” Haka kurum Musaddiq yaji tambayar ta mugun razanasa.. Gani yake kaman Mu’azzam yana iya reading mind d’insa.. Gaba d’aya a daburce Musaddiq yake.. Wata zuciya tana ce masa ya sanar da Mu’azzam abinda yaji wata zuciya tana ce masa kar ya fad’a domin kaman yanda Daddy yace hakan can destroy Mu’azzam harma da ahalinsu.. Ajiyan zuciya ya sauk’e yana mai d’an fuzar da fuci kad’an lokaci guda ya kuma d’agowa yana duban Mu’azzam d’in wanda shima idanunsa k’ar akan Musaddiq d’in yake zuciyarsa fal tunanin hular da ya tsinta a business location d’in Danger. “Musaddiq.. Are you alright..?” Mu’azzam ya kuma tambayarsa a karo na biyu. D’agowa Musaddiq yai yana dubansa kafin ya furta.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *40* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Musaddiq ya girgiza kai kad’an yana mai sakin murmushi “I’m good..” Jinjina kai yai a hankali kafin yace “Mun kwana biyu bamu kasance tare ba.. Do you have plans for tonight.. Let’s have dinner together..” Musaddiq ya murmusa kafin yace “Anya kuwa yau d’in nan..” Mu’azzam ya tsaresa da idanu sosai yana karantarsa, ya murmusa kafin yace “Why.. Ko Kanada wajen zuwa ne.?” Ya kuma sakin murmushi kafin yace “No Fufore nake son komawa gobe.. Na gaji da garin nan nafi sabawa da can a halin yanzu.. Yanda babu tashin hankali babu damuwa babu komai sai kukan dabbobi da tsintsaye.. Idaniya bata kallon rikici da tashin hankali Sai ciyayi masu kyau masu sanya natsuwa ma zuciya..” Mu’azzam yai masa K’uri yanda yake maganar. Jinjina kai yai a hankali kafin yace “Kayi gaskiya.. Tinda gobe kake son komawa ka tashi yanzu ka shirya sai Mu d’an fita tare maybe you can get rid of this negative energy.” Musaddiq ya murmusa kafin yace “I can’t say no to my brother.. Ya mik’e yana murmushi. Idanunsa akan Mu’azzam d’in. Shima Mu’azzam d’in murmushi yake yana dubansa. Musaddiq yace Bara ya shiga ya k’ara wanka.. Mu’azzam ya jinjina masa kai kafin yace “Zan duba Daddy kafin ka fito..” Musaddiq na shigewa bathroom Mu’azzam ya dawo closet d’in Musaddiq d’in yana duba ko zaiga hular Musaddiq mai d’aukeda rubutun B.A.T.. Bai gani ba dan cikin sauri sauri yake gudanar da komai.. Aljihunsa ya zira hannu ya zaro nylon k’arama ya zira hannayensa cikin gloves kafin ya isa yanda hair brush d’in Musaddiq ke ajiya ya zari gashi guda daga cikin hairbrush d’in yai saurin zirawa cikin ledar ya tura ledar a aljihunsa kafin ya fice daga d’akin yana zame gloves d’in da ya rufe hannayensa dasu. Yana isowa b’angaren Daddy ya tadda Daddy shi kad’ai ne wannan karon. Ya zauna daga can gefen k’afafun Daddy suka gaisa. Daddy ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kafin ya soma fad’in “Kai hak’uri da abubuwan da Hajara tai maka Mu’azzam.. Bata kyauta ba, kuma na maka alk’awari bazata sake shiga hurumin gidanka ba..” Mu’azzam ya girgiza kai yace “A’a Daddy babu komai.. Ai komai ya wuce.. Kuma ko meye Mommy zata mun bazan tab’a daina ganin k’imanta a idanuna ba ko dan shekarun da Ta shafe tana jinyar mahaifiyata.. Abinda yasa take haka yanzu ba komai bane.. Fushi take dani sabida abinda naima Safeenah.. Daddy dan Allah kuyi hak’uri. Nasan ban kyauta ba amma dan Allah kuyi hak’uri..” Daddy yai masa k’uri yana dubansa kafin ya girgiza kai yace “Dan kayi aure Mu’azzam bakai laifi ba.. Kuma bamu da hurumin da zamu haramta maka abinda Allah shi halatta maka. Ni wasilcin da zan maka shine adalci.. Tabbas Allah shine shugaban masu adalci, kowa saidai ya kamanta... Kai k’ok’ari ka kamanta adalci tsakaninsu.. Wannan shine nasihar da naso Yi maka.. Amma sai naji wani batu wanda ya girgiza ni Wai ka d’auki Salman ka wakiltasa ya karb’ar maka aure ina nan a garin nan.. Ka tsallake ni baka sanar dani komai ba sai ka tafi ka d’auko Baffanka Salman ka wakilta sa.. Mu’azzam ko na maka wani laifi ne..?” Jikin Mu’azzam yai matuk’ar yin sanyi.. Ya d’ago yana duban Daddy, duk sai yaji bai kyauta ba.. A hankali ya sadda kansa kafin ya soma fad’in “Daddy kai hak’uri.. Bazan iya tunk’ararka nace ka amsar min aure bane alhalin ko tarewa Safeenah batai ba shiyasa na tafi wajen Uncle Salman.. Banyi haka dan k gaza ba Daddy.. Sai don gani nake hakan tamkar ya zama cin fuska ne..” Daddy yai shiru yana mai duban wani b’angaren kafin ya jinjina kai yace “Shikenan babu damuwa.. Ai dani da Salman d’in duk d’aya ne.. Abinda yayi mahaifinka shi yayini ya kumayi Salman.. Bakai laifi ba dan ka baiwa Salman daman zama mahaifi a gareka.. Su waye ahalin matar ya kamata mu San dasu tinda an zama ahali a halin yanzu..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Marainiya ce Daddy batada kowa sai mahaifiyarta da k’annenta guda biyu.. A halin yanzu mahaifiyar tata takaba take da zaran ta ida in sha Allah zanyi maku introducing nasu..” Daddy ya sauk’e ajiyan zuciya kafin yace “Nasan bazakaje ahalin da ba decent ba Kai aure.. Babu damuwa Allah ya kaimu lokacin.” Mu’azzam ya murmusa yace “Ameen Daddy.. Ni zan wuce Daddy akwai yanda nake son zuwa..” Daddy yace “Tashi kaje abinka Allah shi maka albarka ya had’e maka kan iyalanka ya kuma azurtaku da Zuri’a wanda Al’umma zasuyi alfahari dasu kaman yanda muke alfahari dakai..” Murmushi kurum Mu’azzam yake kansa a k’asa yana amsa ma Daddy da Ameen kafin ya fice. Wayar Musaddiq ya kira yace something urgent ya taso masa su bar fitan sai wani lokaci. Musaddiq yace babu komai hakan shima yafi masa dan gaba d’aya ko kuzarin fita baidashi. ** Meema na tsaye Lambun gidan ta hangi ficewar motar Mu’azzam.. Tai tsaye tana tinanin abin yi bayan juya mata baya da ‘yaruwarta tai harda zargin da tai mata akan mijinta.. Meema ta jinjina kai tana fad’in “Safeenah ‘yaruwata ce.. Kuma wanda ya tura wa Ya Mu’azzam sak’on nan a bayyane take so yake ya raba Addah Feenah da mijinta.. I need to clear my name a wajen Addah Feenah.. Nasan tana buk’atata da shawarwari.. Saidai wannan karon shawari na k’warai zan bawa ‘yaruwata bayan na wanke sunana a wajenta.. Tabbas ishara Allah ya nuna mun da masu halayyan irin nawa wanda su a kullum basuda buri saidai suji abinda mutane ke tattaunawa su k’ara.. A koda yaushe yafi kyau mutum ka zamto mai minding business d’inka.. Hadisi ne guda manzon Allah (S.A.W) yace yana daga kyaun musuluncin mutum ya bar shiga abinda bai shafesa ba.. Toh matsala ta kenan ni Meema kuma na tuba na daina daga yanzu.. Babu horo mai tsananin da zan samu a duniyar nan kaman gaba da ‘yaruwata wacce muka fito ciki guda wacce nake matuk’ar k’auna irin Adda Feenah.. Da ace shawari masu kyau nake bawa Addah Feenah duk da hakan bata kasance ba.. In sha Allah zan gyara alak’armu Addah Feenah.. Kuma zan wanke sunana a wajenki ki fahimci cewa ni Meema ba ni na turawa mijinki sak’o ba sannan banida buri tamkar naga Kun zauna lafiya da Ya Mu’azzam..” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige gida tana tinanin abinyi.. Wani tunani ne ya d’arsu mata hakan yasa ta nufi d’akin Mommy ta d’au wayarta ta kofe lambar Barr Ameer dan lokacin da aka tsare Safeenah Barr Ameer d’in ya kira Mommy a matsayinsa na lauya da zai kare Safeenah a kotu. Meema tana kira ta sanar dashi itace Meema k’anwar Safeenah.. Tana so su had’u. Babu musu Barr ya bata lokaci da wajen da zasu had’u. Meema ta jinjina kai tace Babu damuwa zatazo wajen.. Sai Sun had’u.. Daga haka sallama tai masa tana kuma tabbatar ma kanta zata wanke kanta da sunanta da izinin Allah.. Sann sai ta gano wacece wacce ta tura wa Ya Mu’azzam wannan sak’on. Itama aikin Detectives zatai wannan karon (Wayaga Detective Meema.. Lol) ** A b’angaren Mu’azzam kaw yana ficewa shopping mall ya biya yai mata sayayya kafin ya nufi asibitin. Maleeka tana mak’ale wani b’angare cikin asibitin dan tasan dole zai dawo tinda Sadiya tana asibtin. Nan Ta hangesa sai jidan kaya yake cikin shopping bags ya shige ward d’in da Sadiyar take.. Maleeka ta rakasa da mugun kallo tana jin zafin yanda yaketa rawar k’afa kan wata alhali Ita ta ceci rayuwarsa baiko ga hakan ba. Tai k’wafa a hankali daga nan yanda take zaune Ta rufe fuskarta da nose mask tayi shiga irinta ‘yan asibiti harda Lab cot da hular da Malaman jinya ke rufe kawunansu dashi.. Sam bazaka fahimci Maleeka ba. A fili Maleeka take furta “Let’s see idan na shiga d’akin na dannawa matar taka Allurar mutuwa ya zakai.. Inspector Gamji..” Ta k’arashe tana sakin murmushi D’akin Sadiyar ya nufa yayinda suka had’u da likitan nata a hanya. Suka gaisa da Mu’azzam yana basa update kan jikin Sadiyar. Likita yace da sauk’i sosai dan yanzu haka ma ruwan da aka saka mata ya k’are kuma ya cire mata, yanayin fargaba kuma da take ciki sai a hankali traumatic experience d’in zai rabu da ita.. Sannan tanata nanata abu guda cewa a kaita wajen Ummanta da ‘yanuwanta. Mu’azzam ya jinjina kai yace “Yanzu za’a iya sallamarta kenan..?” Dr yace “Of course Inspector.. Amma da son samu ne a kaita wajen mutanen da take ta nanata sunayensu hakan sai ya zamto tamkar therapy ne a gareta..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Shikenan Dr.. Na gode sosai.. Zan iya shiga na ganta yanzu.?” Dr ya jinjina masa kai yana mai fad’in zai bada takardan sallamar nata in a bit.. Daga haka musabaha suka kumayi Mu’azzam na masa godiya kafin ya nufi d’akin Sadiyar. ‘Yansandan dake tsaye k’ofar d’akin suka sara masa kafin ya shige ciki. Tana zaune saman gadon ta nad’e k’afafunta, har lokacin ga alamun hawaye saman fuskarta. Kallo guda tai masa ta d’auke kai fuskarta a tamke saima kukan da taji na kuma zuwa mata. Ya k’arasa saman drawer dake gefen gadon ya aje shopping bags d’in dake hannunsa. Sai karantar yake ta wutsiyar idanu.. Yasan bazata masa magana ba dan baima saka ma ransa zata amsa gaisuwarsa ba hakan yasa bai mata sannu da jikin ba dukda cewa abinda zuciyarsa ta soma fad’i kenan sanda ya turo k’ofar d’akin. Ya soma fito da kayayyakin, toothpaste da toothbrush da set d’in shower ya soma fitarwa. Ya nufi bathroom d’in dasu a hannunsa ya duba komai need harta water heater akwai sannan akwai ruwan yin wankan. Dettol d’in dake hannunsa ya k’ara zubawa a bathroom d’in tai disinfecting dukda cewa ko Ina a gyare yake. Ya fito ya taddata har lokacin tana nan yanda ya barta. “Tashi kije kiyi wanka zamu tafi yanzu..” Kuka ne taji ya kuma zuwa mata gadan gadan.. Ya d’an shafi sumarsa yana mai kauda Kai kad’an.. Batace komai ba sai kukan da take tana ambato Umma dasu Habeeb. D’an duk’awa yai yana dubanta yanda ta kifa kanta tana kuka. “Kina son ganin su Umma..?” Ya tambaya idanunsa akanta. Batace komai ba sai dubansa da take. “Come here..” Ya furta yana mai janyo hannunta.. Ya nufi bathroom d’in da ita still bata iya furta komai sai dubansa da take tamke dai an canzata.. Hular da sumarta ke rufe ciki ya soma zame mata.. Yana k’ok’arin zame tufafinta tai saurin turasa tana girgiza kai take kare jikinta da hannayenta “Don’t touch me..” Ta fad’i jikinta har rawa yake tana kuka. Yanzu kuma tausayi take basa sosai domin kaw ka kasance hannun ‘yantadda abu ne mai matuk’ar tashin hankali. Zuciyarta ta shiga bugawa kardai Danger ya mata wani abu ne.. Ya matsa baya a hankali yana mai d’ago hannayensa alamun bazai tab’ata ba. “Did he do something to you..?” Ya tambaya yana dubanta.. Still tana duk’a wajen tana hawaye. Saurin girgiza kai tai alamun a’a kafin Ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa “He didn’t.. But you did.. I hate you.. And I’ll never forgive you for what you did.. Kaima bakada banbanci dashi.. Kaima D’antadda ne.. Harma ka fi shi.. Sabida shi bai mun abinda ka tasamma min ba..!” Wannan karon sosai bugun zuciyarsa ke k’aruwa, yana jin kalamanta suna masa zafi a kunnuwarsa da zuciyarsa. Cikin huci ya k’araso ya kamo arms d’inta, ya shiga jijjigata yana furta “Kar ki sake had’ani da wanann D’aniskan.. I’m your husband in case you forgot.!” Ya kuma jinjina kai yana mai ci gaba da furta “And I’ll touch you, not just once... As many times as I want.. Because you are my wife..” Ya k’arashe rik’e da ita har lokacin hawaye take. D’an saita kansa yai yana mai fuzar da huci kad’an kafin yace “Get ready now.. We are leaving.. That is idan kinaso ki sake ganin ahalinki..” Daga haka ficewa yai daga bathroom d’in tabi bayansa da kallo jin abinda ya fad’i mata.. Mai yake nufi ko ya samo yanda Su Umma suke ne.. Abinda zuciyarta ya dinga raya mata kenan. Tai saurin mik’ewa tana addu’an Allah yasa zata dake ganin Su Umma. Mu’azzam kaw yana fitowa ya fice gaba d’aya daga d’akin abubuwa fal zuciyarsa. D’akin hutu da aka kwantar da Assad ya nufa. Yanda ya tadda Assad d’in bacci yake bai tashi ba.. Likita ya basa update akan jikin Assad d’in. Ya jima kan Assad yana masa fatan samun sauk’i kafin ya nufo motarsa ya d’auki samples d’in sumar Musaddiq da ya d’auka da kuma hular da suka tsinta a wajen alk’allar Danger. Maleeka tana reception acting like a Staff ta hangosa rik’eda samples d’in ya nufi Lab. Shiru tai ta soma tinanin mai zai a Lab.. Lokaci guda ta soma binsa cikin yananyi na b’adda kama. Da shike asibitin is more of glass nan ta hangesa yana magana da ma’aikacin lab d’in Mu’azzam na mik’o masa samples guda biyu cikin leda.. D’aya hular B.A.T ne d’aya kuma bata iya hango menene a ciki ba. Tai saurin mak’alewa gefe sanda taga Mu’azzam da Mutumin sun fito yana jaddada masa cewa yana so komai ya tafi perfect. Mutumin yace baida matsala zai k’ok’ari result d’in ya fito da wuri.. Maleeka ta lab’ab’a ta shige burut cikin Lab d’in ta mak’ale a bayan k’ofa ba tareda sun kula da ita ba. Daidai sanda Mu’azzam sukai sallama da mutumin ta shige store d’in dake cikin Lab d’in. Ta ramin k’ofa take hango mutumin yanda ya d’auki Samples d’in da Mu’azzam ya basa da alama aiki yake so ya fara gudanawar kansu.. Maleeka Ta girgiza kai tace “Bazan bari ka samu result mai kyau ba Mu’azzam... Lokaci guda ta janyo wasu takardu nan cikin store d’in suka zubo k’asa wanda hakan yaja hankalin mutumin.. Ya shiga ‘yan dube dube yana neman k’aran mai yaji.. Nan wani ma’aikaci d’an uwansa ya shigo yajasa suka fice yana fad’in yazo ya tayasa duba wani result d’aya Lab d’in. Suna ficewa Maleeka Ta fito daga store d’in.. Tai saurin zaran handgloves ta rufe yatsunta ciki.. Lokaci guda ta bud’e drawer d’in da taga mutumin ya aje samples d’in ciki.. Tabbas d’aya hular BAT ne d’aya kuma tsillin suma ne ciki.. Ta saki murmushi tana furta “Kashe matarka zai zamto matsala a gareni.. But I thought of something more tangible Inspector Gamji.. Ka jira kaga yanda zanyi tempering Samples d’in nan..” Tai maganar tana murmusawa kafin Ta bud’e ledar da Mu’azzam ya saka sumar Musaddiq ciki.. Ta b’alli nata sumar ta saka ciki sannan ta cire na Musaddiq wanda Mu’azzam ya samu jikin hairbrush d’insa.. Tasan cewa babu yanda za’ayi nata yayi matching.. Mu’azzam bazai tab’a samun sakamako mai kyau ba.. Sauri sauri ta fice daga lab d’in kafin ta nufi wani store d’in yanda Ta canza kayan jikinta Ta koma Detective Maleekar ta. Sanda Mu’azzam ya koma d’akin Sadiya ya tadda har ta gama shiri cikin tufafin da ya aje mata. “Tashi muje..” Ya fad’i yana dubanta. Babu musu jiki a sanyaye Ta mik’e tabi bayansa. Ya bud’e mata front seat Ta shige kafin ya shige B’angaren driver. A k’ofar asibitin ya hango wata kaman Maleeka ta shige ciki cab.. Ya tambayi kansa ko mai take har lokacin a asibitin tinda dai ciwonta bai wani yi tsanani ba.. Wata zuciya Ta basa amsa da fad’in k’ila tana jira taji condition d’in da Assad ke ciki ne.. Da wannan tinanin ya d’auki hanya. Cikin su biyu babu mai cewa komai k’arshe ya kunna karatun Alk’ur’ani mai girma wanda ya sanya ma zukatansu Salaama had’ida natsuwa. Wani k’aton gini taga sunzo mai manyan Gates har guda biyu. Yai horn securities da suke tsaron k’ofofin suka bud’e masa cikeda girmamawa suna gaidashi cikin mutunta juna.. Ita har mamaki ma taji da taga yanda yake amsa masu kaman bashi ba.. Ta d’an tab’e baki kad’an ba tareda tace komai ba. A haka suka shigo cikin ginin wanda kaman gidaje ne da Wani gini daga tsakiya tamkar ma’aikata.. Nan kuma Ta hangi nakasassu na sintiri cikin wajen.. Tana ta duban buwayar Ubangiji.. Allah sarki wasu idan ta gansu sai ta kuma gode wa Ubangijinta da rahama na lafiya da yai mata.. Tabbas idan kana ganin irin wad’ann dole imaninka ya k’aru.. Kaima ba dan ka fisu bane Allah ya Barka haka.. Sannan suma ba wai dan yak’isu bane yaso ya gansu haka.. A’a dukkaninmu d’aya muke wajen Ubangiji wanda yafi wani shine wanda yafi tsoronsa.. Kowa jarabawa yake fuskanta a GIDAN ARO. Ya isa yai parking a k’ofar wani gida mai kaman apartment. Ya zagayo ya bud’e mata yace ta fito. Bata fito d’in ba sai dubansa da tai.. “Uncle Cop..” Abinda taji an fad’i kenan.. Muryar da ko a bacci tasan na k’aninta Habeeb ne.. Zuciyarta yaci gaba da bugawa sanda ta hango Habeeb a yazo ya taho a guje ya haye jikin Mu’azzam. Mu’azzam ya basa hannu sukai handshake harda wani d’an dunk’ule hannayen masu sukai suka tafa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.. “Ka kawo mana Aunty Sadiya ce as you promised... Ina take..?” Habeeb ya k’arashe yana waige waige.. Sadiya dake k’arasowa kusansu hawaye ne ke gangarowa daga cikin idanunta.. Mu’azzam ya jinjina masa kai yace “Of course little Cop.. Kalli wacece na kawo maka.” Ya k’arashe yana juyar da yaron zuwaga direction d’in da Sadiya ke tsaye tana hawaye. Ta rungume d’anuwanta tana hawaye. Ta shiga shafa fuskarsa tana jujjuyasa dan dai ta tabbatar “Habeeb kaine.. Ina Su Umma da Ashir..?” Ya nuna mata apartment d’in da ya fito daga ciki murna fal fuskar yaron “Munyi kewarki Aunty Sady kullum sai Uncle Cop yazo ya duba mu yace zai kawo mana ke..” Cikin sauri ta kuma rungume Habeeb tana hawaye. Lokaci guda ta mik’e tana fad’in “Muje naga Su Umma.” Ko takan Mu’azzam bata kuma bi ba tama mance tare suke. Murmushi saman fuskar Mu’azzam ya bisu da kallo har suka shige parlorn. Sadiya tana shiga parlorn ta hango Umma sanye da hijabi tana fitowa daga corridor tana kiran sunan Habeeb dan taji bud’e k’ofarsa tasan bazai wuce yace zaibi Ashir da Aunty Larai bane. Cak Umma da Sadiya suka tsaya suna duban juna.. Wani irin kuka Sadiya ta fashe dashi kafin ta k’arasa a guje ta rungume Umma. Umma ma ta rungumeta sosai tana matsan k’walla.. D’iya da Uwa sunga juna dole su baka tausayi idan ka gansu a yanayin. Umma ta d’ago fuskar Sadiya tana duba “Sadiya ta.. Zan k’ara ganinki ashe.. Alhamdulillah Allah ya kub’utar mana dake..” Sadiya ta murmusa tana hawaye tana sharewa Umma nata hawayen.. Lokaci guda take jinjina kai tana fad’in “Umma zan k’ara ganinku ashe.. Umma ki k’ara rungumata naji d’umin jikinki..” Suka kuma rungume juna suna hawaye cikeda shauk’in sake ganin juna. Daga yanda Mu’azzam ke tsaye ya zuba masu idanu cikeda tausayawa.. Bai shiga ba ya juya ya koma cikin mota yana amsa wayar Yusuf yana tambayarsa ko Assad ya farka. Yusuf yace “Har yanzu dai allurar bata sakesa ba, amma idan ya tashi zan sanar dakai.” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Alright Detective, sai na jika..” Daga haka sukai sallama kafin yaci gaba da shafa wayar tasa. A cikin parlorn kuwa Sadiya da Mamanta kaman kar su saki jikin juna. Sadiya tace “Umma ina Ashir..?” Umma tace “Ashir Sun fice da Aunty Larai sun shiga cikin foundation..” Sadiya ta d’an numfasa kafin tace “Aunty Larai kuma..? Wacece ita..?” “Mu’azzam ya had’amu da ita tin sanda suka kawomu gidan nan shida Abokinsa Assad...” Sadiya Ta d’an girgiza kai tace “Wai Umma dama ba saceku akai ba..? Toh ya akai kuka Zo nan..?” Umma ta murmusa kad’an kafin tace “Mu’azzam da Abokinsa Assad su suka kawo mu wannan gida bayan threats da akaita ajiye mana a k’ofar gida Tun bayan d’aukeki da Mu’azzam yai.. Wad’annan bayin Allah babu abinda zamu ce masu face fatan alkhairi” Sadiya ta girgiza kai cikin rashin fahimta “Umma mutumin da ya saceni ya rabani daku bisa tilastawa Shi kike yabo har da godiya..?” Murmusawa Umma tai tana mai girgiza kai “Allah sarki Sadiya.. Da ace Mu’azzam bai d’aukeki wannan lokacin ba watak’ila da yanzu bazamu kuma ganin juna ba..” “Umma maiyasa kikace haka..?” Ta tambaya cikin rawar murya. Umma ta numfasa tace “A daren da Mu’azzam ya tafi dake Washe gari da safe aka k’wank’wasa mana k’ofa, Ashir yaje ya duba babu kowa sai wani k’aramin akwati da aka aje mana an rubuta sunana da sunana su Ashir a Farin takarda da jan rubutu anyi crossing.. An rubuta a k’asa cewa za’a shafe ahalinmu gaba d’aya.. Abin ya firgitani sosai sai Allah yasa abokinsa Assad Wanda tin a daren da Mu’azzam ya tafi dake yazo ya dubamu kuma ya bar mun layin wayarsa yace idan wani abu ya taso na kirasa. Toh shine na kirasa na sanar dashi ga abinda muka samu k’ofar gidanmu.. A lokacin suka taho tareda Mu’azzam d’in ban b’oye masu komai ba na sanar dasu sanin cewa su d’in jami’an tsaro ne.. Suka kwantar mana da hankali tareda fad’in zasu kama mutanen dake bibiyan rayuwarmu da izinin Allah. Akai haka kusan sau biyu sai a k’wank’wasa mana k’ofa muje muga babu kowa Sai sak’o da ake bari mana wanda ba komai bane face threats daga mutanen dake bibiyarki. A daren ranan da su Mu’azzam zasu kawo mu nan harbi akaita mana a cikin gidanmu cikin dare. Cikin drum na b’oye k’annenki Habeeb da Ashir ni kuma na b’uya a cikin kaya a store..” Sadiya hawaye Umma hawaye.. Washe gari sassafe mijinki Mu’azzam da abokinsa Assad suka s’aukemu daga wancan gidan wanda ake kai mana hari suka kawo mu nan.. Sun rufe hakan suka bar abun akan cewa sacemu akai domin su b’atar da tunanin ‘Yantadda masu bibiyar ahalinmu... Kinji abinda ya faru damu Sadiya..” Sadiya na hawaye ta waigo tana duban motar Mu’azzam da alama har lokacin bai tafi ba.. Ta sadda idanunta a hankali tana jin wani kukan na zuwa mata.. Ta matso kusan Umma kafin Ta kamo hannayen Umma tace “Muna nan tare daga yanzu babu abinda zai kuma rabamu Umma.. Ku yafe mun duk ni ce na jefa ahalinmu cikin ukuba.. Watak’ila da banyi tarayya da Sagir ba duk da hakan bai samemu ba..” Umma ta girgiza kai tana duban Sadiyar lokaci guda take furta “Wannan duk muk’addari ne daga Allah tuni Allah ya hukunta hakan zai faru.. Saidai mu k’ara gode masa da baiwa da yai mana na had’amu da mutanen arziki da yai..” Sadiya dai bata kuma cewa komai ba Sai kwantar da kanta saman cinyar Umma da tai. Umma ta shiga Shafa kanta a hankali abubuwa fal zuciyarta.. Can k’asar zuciyarta wani tinanin ne ya addabeta.. Batasan dalili ba amma abubuwan dake faruwa suna tuno mata da bayanta.. Kaman d’ai abinda ya faru shekarun baya ne zai kuma faruwa. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *41* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Yana nan zaune a mota su Anty Larai suka k’araso.. Gaisawa sukai Anty Larai na zolayarsa ko ya kawo mata surkar tata ce. Ya murmusa yana shafa sumarsa lokaci guda suka nufi cikin gidan a tare. Aunty Larai ma’aikaciya ce a cibiyar sannan d’iyar k’awar Inne ce a nan Abuja take zaune da mijinta toh tinda mijin nata ya rasu take fama da rayuwa dama Sana’ar d’inki take gashi ta saba da zaman garin sam bata son tafiya Ta bar Sana’arta musamman da shike ba yara gareta ba, Daddy shi ya sama mata aiki a nan cibiyar, takan Zo cibiyar ta koyar da Sana’ar d’ink.. A nan suka kuma had’uwa da Mu’azzam shine har ya nemi alfarmar tazo su zauna dasu Umman Sadiya ko zata d’an d’ebe masu kewa. Yanzu haka a nan cikin cibiyar suke zaune taredasu Ummman Sadiya dashike Aunty Larai akwai sabo da saurin shiga rai tuni suka sake da juna kaman dai Sun jima da sanin juna. Gaisar da Umma Mu’azzam yai cikeda girmamawa, Umma ta amsa tana tambayarsa jikin Assad.. Yayinda Sadiya ke rungume da k’annenta.. Janyo hannunta ‘yanuwan nata sukai suka shige ciki. Mu’azzam yabi bayanta da kallo har ta b’ace masa. Umma ta k’ara masa godiyan d’awainiyar da yake da kub’utar da Sadiya hannun ‘yanta’adda da yai. Kansa a k’asa yaketa sakin murmushi a hankali. Aunty Larai na taya Umma. Daga bisani Umma mik’ewa tai Ta basu waje shida Aunty Larai, nan Aunty Larai d’in ke fad’in bari a kawo masa abinci. Ya d’an girgiza kai yace zai koma asibiti wajen Assad ne. Aunty Larai ta mik’e tana fad’in “A’a haba dai Malam D’ansanda da ganinka baka wani ci abinci ba.. Kaga barin turo maka Amaryar taka ta kawo maka..” Jin zata turo Sadiya ta kawo masa yasa baice komai ba Sai murmusawa kawai da yai.. Aunty Larai ta mik’e ta nufi ciki. Sadiya na tare da k’annenta Aunty Larai ta shigo.. Sadiya ta kuma gaisar da Aunty Larai cikeda girmamawa kafin Aunty Larai taceda Ita ta taso suje kitchen.. Babu musu Sadiya ta mik’e tabi bayanta.. Suna kitchen d’in Aunty Larai tana nuna mata abubuwan da Zata tayata dasu, Sai janta da hira take Dikda Sadiya ba wani amsawa take ba sai murmusawa da take.. Nan Anty Larai Ta hango alamun cannula hannunta tace “Na mance ashe fah sirkar tamu patient ce... Amma bara na tayaki da d’aukan masu nauyi Kinsan ba’a barin mai Gida da yunwa..” Sadiya dai batace komai ba sai murmushi da take wanda yafi kama da yak’e. Ta kula Matar akwai magana bakinta baya shiru sam. A haka suka nufo parlorn rik’e da trays na abincin. Bakin Aunty Larai bai shiru ba. Sadiya tana direwa Ta mik’e da zummar tafiya saiji tai Aunty Larai ta rik’ota ta dawo da ita.. “A’a Haba Amaryarmu.. A ina kika tab’a jin an k’yale maigida yaci abinci shi kad’ai.. Zauna gefensa kunaci tare yana kallon kyakkyawar fuskar nan taki haka akeyi.. Kakanninmu sunce hakan na k’ara dank’on k’auna tsakanin ma’aurata.” Mu’azzam ya saci kallonta jin abinda Aunty Larai Ta fad’i.. Kana ganinta kasan dan dole take aiwatar da komai.. Dan dai Babu yanda ta iya ne. Aunty Larai Ta mik’e Ta kunna masu tv tana mai fad’in “Yauwa na barku lafiya.. Ku cinye komai mu gidan nan ba’a bari mana sauran abinci..” Tana ida fad’in haka ta shige ta janyo k’ofar corridor d’in ta rufe aka barsu su biyu parlorn. Kaman babu mai cewa komai Mu’azzam ya d’an dubeta kafin yai gyaran murya yace “Aren’t you hungry..?” Ta girgiza masa kai alamun a’a.. “You must be.. Bayan drip babu abinda kikaci..” Ya fad’i yana dubanta kafin yace “Serve us now..” Ita mamaki ma yake bata yanda yakeyi kaman dai babu wani abinda ya faru. Ta d’an d’ago baki a ture tace “I’m Ok.. Ni bazanci ba..” Ya jinjina kai yace “Toh ni zan ci.. Serve your husband..” Gyara zamanta Ta d’anyi kafin tace “Mr Inspector.. As far as I know the mission is over now.. kuma na baro GIDAN ARO.. Why don’t you end this fake marriage once and for all.. Ka sanar dasu cewa auren mission mukai kuma ya k’are..” Murmusawa yai kad’an kafin yace “As far as I know, I didn’t sign any agreement.. Bamuyi haka a rubuce ba.. Iyakacin abinda na sani shine inada shaidu da zasu tabbatar da cewa ni mijinki ne, and that means zakiyi duk abinda na umarceki... And don’t get this wrong dan na kawoki nan.. I brought you here because of what the Dr said.. Ba dan yace a kawoki nan d’in ba da Gida muka wuce.” Ya nad’e hannaye kafin yai mata alama da ido zuwa plate d’in “Serve your husband..” Ta d’an juyar da kanta tana fuzar da fuci kafin ta juyo tana dubansa “Kana tinanin na mance abinda kai mun ne.. Bazan tab’a yafe maka ba kuma zanyi k’ararka a ofishinku na ‘yansanda..” Wannan karon dariya ne yazo masa, ya d’an ciza labb’ansa na k’asa kad’an had’ida kauda kansa yana mai danne dariyarsa. Lokaci guda ya juyo yana dubanta “Oh really..? Toh idan kikaje filing case d’in mai zakice..?” Tana huci tace “First I’ll file a case of kidnapping.. And second..” Sai kuma tai shiru kaman wacce aka rufe mata baki, Ta kasa duban cikin k’wayar idanunsa, sai ma kauda kai da tai tana sakin huci a hankali. Mu’azzam ya murmusa kafin ya janyo plate d’in ya soma zuba abincin yana ci gaba da fad’in “A ina aka tab’a k’aran miji dan ya d’auke matarsa..? As far as I know babu dokar data hana haka koda ta yahudu ce.. Na biyunsa zakiyi k’arar miji dan zai amshi hakkinsa wajen matarsa.. Wanann ma banaji akwai yanda za’a saurareki.. Am I right..?” Ya k’adashe yana dubanta. Idanunta sukai rau rau.. Tasa d’aya hannun nata tana gogewa.. Baice mata komai ba har ta gama goge hawayen kafin ya d’ibo abinci cikin spoon yace “You’re still weak, Oya open your mouth..” Ta dubesa a dak’ile, sai kuma ta mak’e kafad’ar ta alamun ta k’oshi. Ya tsime sosai wannan karon “Idan bakici ba Kinsan Allah zan d’aukeki mu tafi gida yanzun nan.. Kinsan zan kuma zan aikata hakan..” Jin abinda yace ya sanyata bud’e baki a hankali. Ya saka mata spoon d’in cikin bakinta. Ta lumshe idanunta a hankali wani hawayen na gangaro mata.. Yayinda Mu’azzam yai mata K’uri yana duban fuskarta. Ya sake d’ibo abincin ya kuma kaiwa saitin bakinta, ta kauda kanta gefe.. Tsareta da idanu wann karon yai ba tareda yace komai ba. Hakan yasa babu yanda ta iya ta kuma bud’e bakinta. Saida ya bata kusan five spoons kafin ta girgiza masa kai kaman zata saki kuka tana fad’in ita ta k’oshi. Ya k’ura mata idanu yana mamakin yanda tsiwarta ya ragu, da da ne ba kuka zata sakar masa saidai ta murgud’a masa d’an bakin nan nata da yafi komai d’aukar hankalinsa a kyakkyawan fuskarta. Wayarsa ce Tai k’ara ya duba yaga Yusuf ne mai kira. Ya d’an mik’e yana amsa wayar kaman zai fice da alama update yake basa kan Assad. Ganin haka yasa Sadiya saurin mik’ewa zata nufi corridor.. Kafin ta isa k’ofar yai saurin fuzgo hannunta ta fad’o jikinsa, still yana wayar.. Ta soma k’ok’arin cire jikinta dags nasa amma ta kasa dukda cewa da hannu guda kawai ya rik’eta. Sukai sallama da Yusuf yace masa yana nan tafe yanzun nan. Lokaci guda ya kashe wayar yana duban yanda take ta faman daddage k’arfinta tana k’ok’arin cire hannunsa daga jikinta. Harda ciza labb’a tai alamun Takai mak’ura wajen tattaro duka k’arfinta. Ya murmusa kad’an kafin yai amfani da d’aya hannun ya tallafo kunkuminta, ya matso da ita kusansa sosai had’ida k’ura mata idanu.. Wani irin fad’uwan gaba ne taji ya sauk’ar mata musamman da ta d’ago ido taci karo da murmushin dake bisa fuskarsa.. Ita zata iya cewa tafi sabawa da d’aure fuska da yake.. Ta alak’anta fad’uwan gaban nata da wannan fake murmushin da Ta gani samar fuskarsa. “Please let me go..” Ta fad’i kaman zatai kuka. Hannunsa guda yasa ya d’ago hab’arta suna duban juna, zuciyarta naci gaba da yankewa. Ya soma matso da fuskarsa kusan nata kaman dai zai kai mata sunba.. Tai saurin rintse idanunta tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa. Saitin kunnenta na dama taji sauk’an labb’ansa, cikin sigan rad’a yake furta “Lets go back home.. The house misses you..” K’ok’arin tattaro duka k’arfinta tai had’ida turasa baya “That house was never mine.. And it will never be.. Ka mance menene sunan gidan a wajena..? GIDAN ARO..” Ta jinjina kai kafin taci gaba da fad’in “You said it yourself, Mr Inspector..” Murmusawa yai da gefen bakinsa kafin ya soma matsowa kusanta tana jada baya.. Har saida taji kujera ya tokareta alamun wajen gudu ya k’are kafin Ta tsaya tana mai kwantar da bayanta saman kujerar alamun bataso ya matso kusanta.. Ya kwanto shima had’ida mik’a hannunsa guda ya rik’o bayanta yace “Give your husband a goodbye kiss..” Bugun zuciyarta ya k’aru ganin abinda yake, what if wani ya bud’e k’ofar ya gansu haka.. Bata ida tinanin ba tai saurin take k’afarsa guda da k’arfin gaske. Ya d’an saki k’ara yana kame k’afarsa.. Ya janyota ya d’agota tsaye yana fad’in “Hey That was a kick and not a kiss..” Ta k’unshe dariyarta ganin yanda ya rik’e k’afarsa yana d’an sakin k’ara a hankali kai kace zafi yaji da gaske. Lokaci guda Ta jinjina kai tace “I know.. Abinda ya kamaceka kenan.. Mr Inspector..” Ta turasa da duka hannayenta biyu kafin ta isa a guje ta bud’e k’ofar ta shige cikin sauri bugun zuciyarta na k’aruwa. Mu’azzam yabi bayanta da kallo yana murmushi kafin yasa kai ya fice daga parlorn.. Sadiya dake kallonsa ta ramin k’ofa yana ficewa ta Sauk’e ajiyan zuciya had’ida juyowa. Ido hud’u sukai da Aunty Larai.. Gaba d’aya sai taji kunya ya rufeta.. Aunty Larai ta murmusa tace “Har angon namu ya wuce ne..?” Sadiya ta sadda kanta k’asa kad’an kafin ta jinjina mata kai a hankali alamun eh.. Aunty Larai ta janyota tana fad’in “Ki saki jiki dani kinji koh.. Mu’azzam d’ah na ne amma babu wani surkunta tsakanina dake dan ked’in ma d’iyata ce.. Mu k’arasa ciki..” Suka shige ciki hannunta rik’e cikin na Aunty Larai suka nufi ciki suka tadda Su Umma. ** FUFORE Yau ma kaman kullum tana zaune tana tinanin mutumin da ko sunansa bata sani ba. Iyakacin abinda ta sani shine tayi kewarsa sosai sannan Gidan gonar ya canza tin sanda ya tafi garinsu. Mama Hindu Ta K’araso Ta sameta tana nan zaune batai wankan ba. Ta d’an girgiza kai ta k’araso ta dafata kad’an tace “Ajidde Wai bazaki tashi Kiyi wankan ki baiwa Aunty Nuratu maganinta ba.. Duba kiga lokaci nata tafiya.. Waima tunanin mai kike ne..?” Ajidde ta mik’e tana turo baki “Kai Mama Hindu Wai ni idan nazo gidan nan dole ne Sai nayi wanka.. Ni wllhi na gaji haba.. Wai dan Allah Mama Hindu waye ya saka mun wannan dokar a gidan nan..?” Mama Hindu Ta murmusa tace “Idan ban Fad’a miki ba ma kinyita damuna kenan.. Modibbon Inne shi ya bada wannan dokar.. Yace kullum kafin ki baiwa mahaifiyarsa magani na tabbata babu datti jikinki.. Toh amma ko kefa yanzu Kinga kina wanka kina wanke bakinki.. Gashi asalin kyakkyawar bak’ar fatarki ta kuma fitowa tas gwanin kyau.. Ga hak’waranki yanzu sun dawo farare tas tas.. Tsafta da dad’i ai Ajidde..” Ajidde ta saki baki da hanci tana duban Mama Hindu.. Sai kuma ta girgiza kai tace “Mama Hindu kina nufin ‘Yaniskan turawa shi ya bada wannan dokar..?” Mama Hindi Ta girgiza kai tace “Sunansa Mu’azzam.. Ki daina kiransa ‘Yaniskan turawa jami’in tsaro ne idan yaji kina kiransa haka zai kulleki a police station..” Takaici ya cika Ajidde ta gama kula mutumin Babban D’an rainin hankali ne.. Wato kar Ta tab’a masa mahaifiya da datti jikinta sai tayi wanka.. Ta tab’e baki tace “Shi wannan sam halinsu baizo d’aya da abokinsa ba.. Ni banma San ya akai sukai abota ba..” Mama Hindu ta girgiza kai tace “Waye abokin nasa..?” Ajidde tace “Kuran tashe mana..” Mama Hindu ta girgiza kai tace “Wannan wane irin suna ne kuma Ajidde..?” Ajidde ta dubeta tace “Toh oho nima bansan sunansa ba.. Amma ai a gidan gonar nan yake aiki... Gashi tinda ya tafi garinsu fah har yau bai dawo ba.. Mama Hindu kinaga zai dawo..?” Mana Hindu ta murmusa tace “Toh kodai shine ke sakaki tunani kwana biyun nan.. Da alama shine sirkin nawa..” Baki sake Ajidde ke dubanta sai kuma ta rufe fuska tana dariya “Kai Mama Hindu.. Ni wllhi har kin sa naji kunya.. Kuran tashe Abokina ne kuma Yayana mai tare mun fad’a ehe..” Mama Hindu Ta dara kad’an tace “Munsan irin wad’ann yayyen.. Da alama dama shine sirkin nawa.. Ke kaw ya akai bakisan sunansa ba.. Allah dawo dashi lafiya na had’u dashi..” Ajidde Ta kuma darawa kafin tace “Kai Mama Hindu ni wllhi dariya da kunya kike bani.. Kuran tashe fah d’an gayu ne.. Saima randa zai tafi garinsu da na gansa.. Wllhi yasha gayu cikin kayan da ‘yan gayu ke sakawa kuma ma fah ya fini kyau.. Kinga dukda shi ba fari bane amma ya fini haske.. Kuma ya fini tsawo..” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye tana gwada tsawonta da tsayin k’ofa lokaci guda tana bayanin tsawonsa ma Mama Hindu. Mana Hindu ta murmusa tana mai shigewa shiriritar Ajidde da yawa yake. Ajidde ta Sauk’e ajiyan zuciya tana duban kanta jikin madubi tana mamakin Mama Hindu tace ta k’ara kyau.. Ta murmusa kafin tace “Yo dama ai ni mai kyau ce Mama Hindu..” Idanunta suka sauk’a Kan Aunty Nuratu sai taga kaman ita take kallo.. A koda yaushe idanun nata saidai kaga Sun kafe waje guda amma yau Sai Ajidde taga kaman dubanta take.. Ta k’araso a hankali tana mai k’ura mata idanu, Ta duk’a tana duban idanun Aunty Nuratu ta d’an soma Yawo da tafin hannunta saman idanun Aunty Nuratu sai taga kaman idanun nata na motsawa ba kaman ko Yaushe da zaka ga idanun tamkar a kafe suke waje guda ba.. Ajidde tai shiru tana tuna bayanan Malama Hafsah cewa ko taga wani canji a tattare da matar da take Jinya ta adana hakan ma kanta, kar tai saurin sanar da mutane dan daga yanda Ajidden ke mata bayanin ciwon ya mata kama da asiri ko tsafi.. Amma da taimakon ayoyin Ubangiji idanma asiri ne ko sihiri zai lalace. A hankali Ajidde Ta furta “Tabbas akwai waraka cikin ayoyin Ubangiji..” ** ABUJA Assad ya murmusa kad’an yana dubansa kafin yace “I’m feeling much better now.. Damuwata kawai shine we couldn’t catch Danger.. We were so closed k’iris ya rage mu kamasa ya tsere mana..” Ya k’arashe yana d’an fuzar da huci kad’an. Mu’azzam ya girgiza kai yace “What’s important a halin yanzu shine lafiyarka.. Let’s all take a break.. Na tabbata a kwana a tashi zamu had’u da Danger watarana..” Assad ya jinjina kai kad’an kafin yace “Su Hajiya sun taso daga Nasarawa d’azu Shaheed ke sanar dani a waya, anjima kad’an nasan zasu iso.. Yarinyar nan ne mai shegen magana Humaida ita ta sanar da Hajiya. Kuma saida nai warning nata kar ta sanar dasu Hajiya amma ta sanar dasu..” Mu’azzam ya d’an murmusa kafin yace “Hajiya ai bazata iya bacci ba tareda ta ganka ba..” Mu’azzam bai rufe baki ba ‘yan gidansu Assad sukai sallama, Hajiyarsa wacce itace mahaifiyar Sai K’aninsa mai bi masa Shaheed wanda shi ya tuk’o Su Hajiyan sai ko k’anwarsa Humaida... Suka shigo duk a rikice.. Assad na wurga ma k’anwarsa harara ganin yanda mahaifiyarsa duk Ta rikice. Ta dubi Mu’azzam bayan sun gaisa tace “Ni wannan aiki naku harga Allah tsoro yake bani.. Shin bazaku aje aikin nan ba ku nemi wani. Aiki kullum cikin fargaba da tashin hankali..” Mu’azzam sai murmushi yake ba tareda yace komai ba, shi ko Assad girgiza kai kurum yake yana fad’in “Hajiya babu wani abu fah mun saba da wannan cikin aikinmu..” “Kai tafi can ka rufe mun baki.. Rai guda d’aya ce. Ba wannan ake jiye maku ba.. Aikin tsaro a k’asa irin wannan ai abin tashin hankali ne k’ananan suke shan wahalan ba manyan ba.. Allah dai ya kawo mana d’auki ya bamu shuwagabanni adilai..” Gaba d’aya suka amsa da Ameen kafin daga bisani Mu’azzam yai masu sallama Shaheed k’anin Assad yai masa rakiya zuwa waje. ** Bayan sallar isha ya dawo gidan, tin daga k’ofa yake jiyo hayaniyar Mommy tana fad’in sai Safeenah ta tattaro kayanta Sun tafi.. Yanda Ta bar gidan Daddy dole Safeenah ma Ta bar gidan Mu’azzam tinda dik abinda ke faruwa akan Mu’azzam d’in ne.. Yai sallama ya turo k’ofar parlorn. Safeenah tana ganinsa Ta nufosa a guje tana b’oyewa bayansa fuska shar shar da hawaye “My Halal pls don’t let Mommy do this.. Dan Allah kar ka bari Ta rabamu..” Mommy na sakin huci take duban Mu’azzam d’in “Kinaji Safeenah idan ni na haifeki kin gama zaman aure da wannan maras mutuncin.. Ki shige mu tafi bana son wani dogon bayani..” Safeenah Ta kuma fashewa da kuka tana fad’in “Mommy no please.. Wllhi I love my husband.. Please don’t make me choose between you..” Mommy Ta jinjina kai tana huci “Yayi Safeenah.. Duk Kun juya mun baya akan wannan maras mutuncin.. Yayi.. Baga mahaifinku ba bagaku ba.. Yayi kyau.. Kije Safeenah indai namiji ne gaki gashi nan.. Ina nan zaki Zo min kina kuka..” Ta juyo tana duban Mu’azzam.. Murmusawa tai kafin tace “Bokanka ya iya aiki matuk’a Mu’azzam.. Da alama ka lashe zukatan ahalina.. Bazan tab’a yafe maka ba tarwatsa mun kan ahali dakai..” “Ke kuma Safeenah na barki da namiji..” Tana ida fad’in haka Ta fice tana sakin huci.. Safeenah Ta fashe da wani irin kuka tana mai duk’awa wajen.. Hannun Mu’azzam taji saman kafad’unta.. Ta d’ago tana dubansa wani kukan na zuwa mata.. Mik’ewa tai Ta fad’a jikinsa tana kukan mai isarta. A hankali ya d’ago hannayensa ya rungumeta cikin jikinsa. For the first time da yaji tausayin Safeenah ya d’arsu cikin zuciyarsa tun bayan da binciken mutuwar Ikram ya biyo kanta. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:35 AM] My mom: *GIDAN ARO* *42* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Meema da Kiki suna zaune parlorn sunyi jigum jigum, harda guntun hawaye a fuskokinsu.. A haka Musaddiq ya shigo ya taddasu. Bai ce masu komai ba suma basu ce masa komai ba, ya haura sama ya nufi d’akin Mommy yana dubata, bai sameta ba sai wata mai aikin gidan guda d’aya tana tattara d’akin Mommyn yanda Mommy tai fashe fashen abubuwa masu fashewa a d’akin dangin su frames dasu flower vase. Musaddiq yanata bin d’akin da kallo cikeda mamaki. Lokaci guda ya girgiza kai yace “What happened here.. Ina Mommy..?” Mai aikin Ta girgiza masa kai alamun bata san yanda Mommy take ba. Bai kuma cewa komai ba ya fito ya sauk’o k’asa ya taddasu Meema dake zaune jigum jigum ko wacce da kalar tagumin da tai.. “Kai ina Mommy..?” Ya tambaya yana dubansu. Meema Ta girgiza kai tace “Bamu San ina ta tafi ba.. But she says bazata sake dawowa gidan nan ba..” Da tsananin mamaki Musaddiq yace “Mommyn.?” Suka jinjina masa kai. “Toh mai ya faru..? Maiyasa Mommy zatace haka..?” “Muma bamu sani ba kawai daga side d’in Daddy mukaga Ta fito tana kuka..” Kallo ya bisu dashi kafin ya zaro wayarsa ya soma dialing layin Mommy.. Bugu d’aya a na biyu ta d’aga. Musaddiq hankali tashe yake fad’in “Mommy ina kika tafi..? Nazo gida na tadda baki nan.. Yaran nan sunce min Wai kince bazaki sake dawowa ba..? Mommy what is happening..?” Maimakon ta basa amsa sai kukan da tai tana fad’in “Musaddiq Daddynku yaci zarafina.. Yamin abinda bai tab’a min ba tinda k’uruciya.. Ko kasan yau har marina yai akan Mu’azzam.. Ka kula da ‘yanuwanka amma nikam na gama zama gidan Mahaifinku.” Da tsananin mamaki ya saki baki yana sauraron Mommy abinda bai tab’a faruwa gidansu ba, Wai Mommy ta tafi ta bar gidan kuma bazata kuma dawowa ba “Mommy where are you now..?” Ya tambaya yana ficewa. “Ina Apo gidan Hajiya Faty K’awata..” Ta basa amsa kai tsaye. “Alright gani nan zuwa Mommy..” Daga haka katse kiran yai ya kuma ficewa daga gidan ya nufi gidan Hajiya Faty kawar mahaifiyarsa. Musaddiq yai jigum yana duban Mommy yanda take nuna masa farar fuskarta da zanen yatsun mijinta ya fito. “Daddy ne ya miki haka.?” Musaddiq ya tambaya yana dubanta idanunsa sunyi jazir sabida tsananin b’acin rai. Ta jinjina masa kai tana kuma matsan k’walla “Dashi da Safeenah duk sun juya mun baya kan Mu’azzam, nasan kaima bayansa zakabi sabida shi d’angata ne bai laifi a idanunku..” Mik’ewa Musaddiq yai kurum yana sakin huci yana duban fuskar mahaifiyarsa, jinjina kai yai kafin yace “Zaizo har nan ya baki hak’uri ya kuma d’aukeki ya maidake gidanki..!” Daga haka ficewa yai kaman zai kifa k’asa. Mommy Ta bisa da kallo kafin Ta murmusa tace “Ai jini ba K’arya bane.. Uwa kuwa Ta wuce gaban wasa..” Hajiya Faty ta fito tana dubanta tana murmushi “Ina Musaddiq d’in.. Ko har ya fice ne ba sha ko ruwa ba.?” Mommy Ta murmusa tace “Ya tafi yayi yak’i ma uwarsa..” Hajiya Faty Ta dara kad’an tace “Kaji D’an halak haka ake so d’ah ya kasance. Kinga ko baki samu goyon bayan Safeenah ba kin samu na Musaddiq..” Mommy ta jinjina kai tace “Ita dama wannan ai shashasha ce, kuma Ina nan dake zata Zo min tana kuka lokacin da zai gurza mata ya tabbatar mata cewa ya amsa sunan namiji..” Hajiya Faty ta murmusa kad’an ta zauna tana fad’in “Bata lokaci soyayya ke d’awainiya da ita.. She will come back to her senses soon.. Ina d’aya matar tasa ne Wai..?” Mommy Ta tab’e baki tace “Toh wa yasan masa ne Wai Kinsan bazai sanar da Safeenah komai ba dan bai d’auketa da daraja ba..” Hajiya Faty Ta jinjina kai tace “We need to do a background check on her.. Musan ‘yar wacece kuma daga Ina take sannan ina iyayenta suke dan Kinsan dai Safeenah bayi zatayi ba wannan fad’anta ne amma dole mu dafa mata tinda ita namiji ya lashe zuciyarta.” Mommy Ta jinjina kai tace “Kin kawo shawari.. Zan bar miki wannan a hannunki ki gano mana wacece ita sai musan ta yanda zamu b’ullo wa al’amarin.” “Bakida matsala idan dan wanann ne k’awata.” Hajiya Faty Ta bata amsa tana mai d’aura k’afarta d’aya bisa d’aya. ** Chief ya d’aga wayar ya k’ara a kunnensa yana furta “Yes BAT bakada matsala, komai ya tafi as we planed.. Mu’azzam Bazai tab’a samun sakamako mai inganci ba.. Yes munyi tempering samples d’in kaga hakan na nufin result d’in bazai matching ba..” Ya murmusa kafin yace “Bakada matsala BAT. We did a clean job.. I trust Maleeka, she’s good at everything.. Tana d’aya daga cikin best agents d’inmu a FCID. Yes alright shikenan sai na jika BAT..” Daga haka katse kiran yai kafin ya dawo yanda Maleeka ke kwance saman gado.. Alert ya nuna mata na naira dubu d’ari biyar ya shigo wayarsa. Maleeka Ta zaro idanu waje tana kame baki. Chief ya fashe da muguwar dariya kafin yace “Idan kika ci gaba da bamu had’in kai kina aiki damu yanda ya kamata haka Zakita receiving alert babu k’akk’autawa.. BAT yace a baki wannan tukurci ne for the job well done..” Maleeka ta fuzgo wayar hannun Chief tana kuma karance alert d’in lokaci guda Ta saki murmushi tace “Idan ka rasa soyayya sai ka kama Kud’i dan kar kayi biyu babu.. Mecece duniyar dama soyayya ne da kud’i.. A rashin d’aya sai ka samu d’aya domin kaji dad’in baje kolinka..” Suka b’uge da dariya Chief na shafa k’atuwar tunbinsa wanda kaman zashi labor room, lokaci guda ya hauro saman gadon yanda Maleeka ke kwance. ** Ko parking mai kyau bai ida ba ya fice daga motar, ya shiga tafiya cikin sassarfa ya nufi b’angaren Daddy.. Ko sallama Musaddiq bai ba ya tura k’ofar parlorn ya shiga.. Daddy na zaune tsakiyar parlorn yana shan shayi dan ko dinner bai samu yaci ba Musaddiq ya shigo parlorn cikin tsananin b’acin rai. “This has to end now Daddy.. Bazai yuwu akan Mu’azzam a tsaya ana wulak’anta kowa a gidan nan ba.. Especially Mahaifiyarmu.. Daddy I’m so disappointed.. Absolutely disappointed.. How could you hit our Mom kawai akan b’acin ran Mu’azzam.. Just yesterday ka hanani sanar dashi wani abu da ya shafi ahalinmu ba Don komai ba Sai dan gudun b’acin ransa.. And bai jima ba kanaji kana ganni Daddy Mu’azzam ya shigo har cikin gidan nan da ‘Yansanda yai arresting Safeenah.. Yanzu kuma Daddy ka d’aga hannu ka mari mahaifiyarmu duk akan gudun b’acin ran Mu’azzam.. Who the hell is he.. Shi waye da baza’a b’ata masa rai ba..! Shi waye da kowa zai sadaukarwa mai girma sabida gudun b’acin ransa.!” Yai fasali gumi na kuma tsartsafo masa yana kuma zaro idanunsa da suka kad’a sukai ja sosai “Daddy na rantse da Allah idan Bakaje ka basa Mommy hak’uri ba, ka d’auko Ta ka dawo da Ita gidan nan.. I’ll expose everything.. And when I say everything.. Ina nufin duk abinda na sani.. Idan yaso zuciyar Mu’azzam ya kumbura kuma ya fashe sabida bak’in ciki da k’unci..!” Yana ida fad’in haka yasa ya fice. Daddy da ya rapka uban tagumi yabi bayansa da kallo har ya b’ace masa.. Meke shirin faruwa da ahalinsa ne..? Mene abubuwan da suke faruwa.. Yanzu Hajara saida ta bak’anta Mu’azzam wajen D’anuwansa Musaddiq.. Yau shine Musaddiq ke masa barazana har yana cewa zai sanar da Mu’azzam tattaunawar da yaji sunayi da Salman.. Lallai shaid’an ya shigo masa kan ahali.. Bazai bari ahalinsa ya tarwatse ba.. Jiki babu k’wari Daddy ya mik’e ya haura sama. Ya shirya tsaf kafin ya sauk’o ya nufi b’angaren Musaddiq. Zaune ya tadda Musaddiq d’in hannunsa rik’eda pills yana k’ok’arin afawa bakinsa sai sakin huci yake. Daddy ya k’arasa da sauri ya buge hannun Musaddiq k’wayan suka watse k’asa. Cikeda tausayawa Daddy ke duban Musaddiq d’in.. Ya shiga girgiza kai yana duban yanda Musaddiq ke hawaye cikin tsananin k’unan rai. Daddy ya girgiza kai yace “Akan abinda ya faru shine kake k’ok’arin maida kanka ruwa Musaddiq..? Maiyasa..? Akan na samu matsala da mahaifiyarka..?” Musaddiq baice komai ba Sai hawayen dake ci gaba da fitowa daga idanunsa. Daddy yaci gaba da fad’in “Musaddiq mahaifiyarka ce ta turoka ka rama mata abinda bai mata.. Shin Ita tace kazo kamin rashin kunya abinda ba d’abi’arka ba..?” Musaddiq ya d’ago idanu masu zuban ruwa yana duban Daddy “Mahaifiyata ce Daddy.. Kuma dole nabi bayanta a lokacin da ahalin da take tink’aho dasu suka guje mata.. Daddy Menene matsalar Ahalin nan..? A koda yaushe matsalar guda d’aya ce shine Mu’azzam... Baga kai ba baga Inne ba.. Duk Kun d’auki son duniya Kun d’aura masa.. Shin Daddy mu ba ‘ya’ya bane.. Why always him..?” Ya k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Shiru ne ya d’an biyu tsakani kan Daddy a k’asa, kafin ya girgiza kai yace “Kar ka bari Shed’an ya sanya maka hassada cikin zuciyarka d’ah na.. Ba haka abun yake ba.. Banfi son Mu’azzam ba, dukanku Ina sonku daidai gwargwado.. Haka Inne ma na tabbata tana k’aunarku gaba d’aya.. Idan kaga anfi son wani ba shi d’in akafi so ba kyawawan mu’amalarsa da d’abi’unsa ake so.. Zuciya tana son abu mai kyau ne Musaddiq ba gurb’atacce ba.. Kai shaida ne lokacin da ka koma Fufore da yanzu ka duba Alak’arka da Inne kasan akwai banbanci.. Inne tana nuna maka asalin k’aunarta gareka a halin yanzu.. Ashe ba kaid’in bane bata k’auna.. A’a so take ka gyara d’abi’unka shiyasa take nuna tsauri akanka..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Musaddiq duk abinda nakeyi ba inayi bane don Mu’azzam.. A’a inayi ne domin ahalinmu.. Ko wani ahali sunada nasu k’alubale da suke fuskanta amma bana fata Allah ya jarabcemu da k’alubale na tarwatsewar ahali ko gaba mai muni ya shigo tsakani wanda wasu lokutan zaka samu ya shafi har ‘ya’ya da jikoki.. Musaddiq sabida wannan dalilin naketa k’ok’arin naga kan ahalinmu bai tarwatse ba.. Sannan na tabbata mahaifiyarka bata sanar dakai mai Ta aikata ba.. Amma naji dad’i da baka sani b, kuma bana so ka sani.. Sannan koda bakace naje na dawo da Hajara ba zanje na dawo da ita dukda cewa ita ta sallami kanta bani na sallameta ba..” Ya mik’e yana gyara tsayuwarsa still idanunsa kan Musaddiq d’in. Daddy ya d’an kuma gyaran murya kad’an kafin yace “Ya kamata ka koma Fufore, zamanka a nan bazai haifar maka da komai ba illa ya kuma maidaka cikin Rayuwar da ka riga ka baro a baya..” Yana ida fad’in haka yasa kai zai shige. Musaddiq yai saurin ambato sunansa. Daddy ya juyo yana dubansa. Ya k’araso yana sadda kansa k’asa, a hankali ya furta “Kai hak’uri Daddy ka yafe mun..” Daddy ya saki murmushi kafin ya d’an buga kafad’an Musaddiq kad’an yace “Babu komai Abubakar Allah shi maku albarka gaba d’aya.” Daga haka Sa kai Daddy yai ya fice ya nufo k’asa ya shiga motarsa dan already driver d’insa ya tafi, da kansa ya tuk’a motar ya tafi d’auko matarsa dake gidan Hajiya Faty. ** FUFORE Aunty Shemau Ta dubi mijinta dake zaune gefen gado yana duba wasu takardu.. Lokaci guda ya d’ago mata takardun yace “Takardun irin wad’annan ne.. A gabana Yayana Abubakar ya saka hannu cewa baison k’wandala na Kampanin, kuma zaiyi resigning daga wannan ranan.. Zai nemi nasa daga scratch..” Aunty Shemau Ta girgiza kai cikin rashin fahimta kafin yace “Amma Maiyasa zai haka bayan Dukiyar nan mahaifinku ne ya bar maku..” Murmusawa Uncle Salman yai kafin yace “Bakisan kalan Zuciyar Yayana Abubakar ba, yana da matuk’ar zafin zuciya da gudun duk abinda zai kawo masa magana ko raini..Yanda kika ga D’ansa Mu’azzam haka yake.. Maganganun da nake jifansa dasu kan cewa yayi tsaye akan dukiyar mahaifinmu yana son ya handame komai shiyasa yak’i barina na girma a Kampanin wann kalaman su suka tunzurasa yace na basa takarda da alk’alami ya saka hannu cewa daga wannan ranan baya buk’atar ko k’wandala na daga abinda mahaifinmu ya bar mana sannan zai tashi ya nemi nasa bazai kuma dogaro da abinda aka bar mana ba.. Shemau wad’annan takardun nake nema wanda D’anuwana Marwan ne ya b’oyesu na tabbata.. Sabida bayan rasuwar Yayanmu da aka Zo ana maganar rabon Gado sai cewa yayi babu yanda za’ayi a cire iyalan Yaya cikin Company.. Ni kuma sai na sanar dashi ga abinda Yayanmu yayi ya rubuta cewa baya son k’wandala amma sai Marwan yace “Gado Allah ne ya riga ya raba abunsa.. Ko Yaya yana so ko baya so yanada gadon mahaifinmu tunda mahaifinmu ya rigarsa rasuwa, sannan kasonsa za’a dinga bawa Iyalansa koda basa so... Bazai tab’a yarda da wannan yarjejeniyar ba kuma bazai bari na raba mana kan ahali ba.. Kinga idan na samu takardun nan ni kuma zan kai Kotu na tabbatar cewa iyalan Yayanmu basuda gado dan mahaifinsu shi da kansa ya ciresu daga cikin gadon.. Harma yayi furuncin idan inason nasa kason na had’a gaba d’aya shida Iyalansa basa kwad’ayin wannan dukiyar.. Kinga kuwa ai Shemau baki shi ke yanka wuya.. Zafin ransa ya jawo yayi wannan rubutun ya cire iyalansa daga cikin Dukiyarmu.. A yau idan na sami takardan yajejeniyar nan zan tafi Kotu kuma dole a daina cire kason su Mu’azzam a cikin Company dan Ubansu da kansa ya ciresu.. Balle ma Mu’azzam idonsa baya kan dukiyar na tabbata Marwan shima amfani yai da wanann damar yake handame nasu kason dan har yau bai d’aura Mu’azzam a hidimar Company ba.. Sannan shi Mu’azzam d’in idanunsa baya kan dukiyar sam.. Dan da alama Mu’azzam bai rage wa mahaifinsa komai ba na rashin son abun Duniya..” Aunty Shemau ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Tabbas Dukiya Itace mafi munin bala’i ga D’anadam a doron k’asa, za’ayi tsafi sabida a sameta, a kashe rai duk dan a sameta.. Za’ayi komai domin a tarata a GIDAN ARO.. Gidan da sam ba tabbata za’ayi ba balle a cinye abinda aka tara..” Uncle Salman ya d’an dubeta yace “Mai kikace..?” Ta d’an tab’e baki kad’an kafin tace “Toh ni meye role d’ina a wasan Naka daka sa na shiga jikin Hajara na samu yarda da amincewarta..?” Uncle Salman ya murmusa kafin yace “Ai kaman yanda kikace Dukiya itace mafi munin fitina ga D’anAdam a GIDAN ARO.. Kin manta wani abu guda d’aya wanda tare suke tafiya kunnen doki suke..” Aunty Shemau ta dubesa da mamaki kafin tace “Mai kenan kake nufi..?” “Mata..!” Ya bata amsa kai tsaye. Kafin yaci gaba da jinjina kai yana furta “Kud’i da mata tare suke tafiya.. Idan muka samu yardar matarsa Kinga mun samu kansa cikin sauk’i itace kawai wacce Ta hanyarta zamu iya samun wad’annan takardun..” Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai tana tinanin yanzu idan bata samu takardun nan Ta wajen Mommy ba. Hardai Alhaji Marwan ya fahimci ta taimakawa Mommy Sun d’auko wa matarsa mai rufa ido da sunan mai gani shikenan kashinta ya bushe Ta tabbata Mu’azzam jefata zai gidan yari ya kulleta.. A b’angare guda Mommy zata gane da biyu Ta shiga jikinta kenan dan Ta cimma burin mijinta na samun wad’ann takardun masu mahimmanci.. Kenan fah Ita tayi b’atan b’akatantan fah kenan.. Babu nan babu can.. Lallai tun wuri gwara tasan alk’iblarta.. ** ABUJA Yai tsaye yana duban yanda Safeenah Ta tak’ure cikin pillow tana bacci bayan ta gama cin kukanta. Ta zab’esa akan mahaifiyarta, shin wacce Ta zab’i zama dashi akan mahaifiyarta zata iya kashe masa ‘yaruwa..? Toh amma Maiyasa ahalinsa suketa shigowa cikin binciken nasa.. Kodai ahalin nasa ne zai bincika..? Kodai akwai abinda ke rufe cikin ahalin nasa bai sani ba..? Kai a’a wannan wasannin Danger ne.. Bazai tab’a zargan ahalinsa da aikata mummunan laifi irin wannan ba.. Toh amma...Zaici gaba da bincikensa daki daki har ya gano komai.. Ya k’arasa saman gadon nata ya zare pillow d’in yai mata matashi da k’irjinsa.. Safeenah da ba bacci take ba dama da taji shigowarsa ne Tai likimo kaman mai bacci nan ta saki ajiyan zuciya tana mai kuma shigewa jikinsa.. Plan d’inta yayi aiki dan tasan yanzu kam dole Mu’azzam ya koya ma kansa sonta koda bayayi tinda har Ta zab’esa akan mahaifiyarta. Turarrukan data shafe jikinta dasu wanda Aunty Shemau Ta bata sun taimaka sosai wajen kai Mu’azzam wata duniyar.. Dukda cewa idan ya rufe idanunsa ba Safeenar yake hangowa ba.. Sadiya yake hangowa suna raya wannan duniya mai tsafta tare.. Cak ya d’auki Safeenah suka nufi nasa d’akin yana nuna mata salon k’aunarsa wanda Ta jima tana mafarkin samu daga garesa. A b’angaren Mu’azzam kaw tin daga hanya ya fahimci akwai banbanci da lokacinda ya tasamma kusantar Sadiya.. Tabbas ba d’aya suke ba.. Abinda zuciyarsa Ya raya masa kenan.. Toh mai hakan yake nufi..? Safeenah tasan maza ne Ta saba da maza kokuwa..? Amsar da ya gaza bama kansa har komai ya lafa. Yai mata K’uri yana dubanta, duk sai tasha jinin jikinta dukda cewa bai furta mata komai ba.. Kukan da batayi tun daga farko ba shi ta fara bayan al’amra Sun lafa. Cikin kuka take furta “I’m sorry my Halal..” Ya dubeta da mamaki kafin ya girgiza kai yace “Why are you apologizing.. Maiyasa kike bani hak’uri.?” Safeenah Ta kuma sadda kanta kafin tace “Ko baka fad’a mun ba fuskarka ya nuna my Halal.. You are disappointed.. And believe me I feel ashamed..” Mu’azzam ya kuma girgiza kai yace “I still don’t get you Safeenah.. Stop beating around the bush.. Ki fad’a mun menene..?” Tasa bayan hannunta ta share hawayenta kafin tace “Lokacin ina Salford friend d’inmu Ta gayyacemu birthday party d’inta.. You know yanda parties suke kasancewa a k’asashen turawan nan.. Wllhi banyi niyyan zuwa ba friends d’inmu suka tak’ura man na bisu.. Shine boys d’in sukai drugging namu suka sanya mana k’waya cikin drinks sukai raping d’inmu.” Kuka ya kuma kufce mata tana fad’in “Amma wllhi daga ranan ban kuma zuwa parties ba koda birthday ne.. Please forgive me My Halal na kasa kare maka kaina.. Naje Party an k’eta mun haddi..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka. Dukda cewa haka kurum baiji zuciyarsa ya aminta da zancen Safeenah ba Sai ya fuzar da fuci kad’an da yai, ya d’an kauda fuskarsa gefe na d’an lokaci kafin ya soma fad’in “Laifinki d’aya na zuwa Party da maza. Da bakije ba watak’ila da abinda ya sameki bai sameki ba.. Shi kamun kai ya shafi mutanen da kike mu’amala dasu, wajajen da kike halarta da kuma yanayin shigarki.. Yanda kikai appearing ma mutane haka zasuyi addressing naki.. Na tabbata abokan ku na wajen Partyn zasuyi tunanin kuma irinsu ne shiyasa kuka d’ibi k’afafu kukaje irin wann wajen hardai sukai abinda sukaga dama daku.. Allah ya ganar damu baki d’aya ya hanemu aikin danasani.” Yana ida fad’in haka ya mik’e ya nufi bathroom ya bar Safeenah nannad’e cikin bedcover tana ci gaba da matsan k’walla nata wautan ita a dole yau tayi dabara ta tsara zance ba tareda taimakon Meema ba kuma Mu’azzam ya yarda. Haka ya tsarkake jikinsa ya fito daga bathroom d’in tana nan kwance, duba d’aya yai mata yace Ta tashi taje tai wanka. Babu ko irin tarairayan nan da ake ma ko wacce amaryar da takai mutuncinta da Martabarta. Safeenah Ta d’an turo baki tace “Gaskiya ni bacci nakeji zanyi da safe..” Mu’azzam ya girgiza kai yace “A’a bazaki kwana mun a gado haka ba.. Saidai kuma idan zaki tafi naki d’akin..” Badon taso ba ta mik’e tana ture turen baki Ta shige bathroom. Bai kuma bi takanta ba yai kwanciyarsa zuciyarsa na muradin sake kasancewa da Sadiya. ** Washe gari Safeenah batasan ficewarsa ba tanata sharan baccinta, tasan dai ya tada Ita sallar asuba. Tun kafin ya dawo daga masallaci ta kuma hayewa gado tai kwanciyarta. Ba ita ta farka ba sai wajajen k’arfe 8:30am. Ta shafa taji baya kan gadon Ta kuma lumewa cikin gadon tana mai canza position d’in kwanciyarta dan tasan definitely office ya tafi. Tasan sa da bama aikinsa mahimmanci. Shiko Mu’azzam tinda ya fice asibiti ya soma biyasa ya duba jikin Assad kafin ya nufi foundation. Sadiya na kitchen tana taya Aunty Larai da wasu ayyukan Ta sinkayo muryar Habeeb yana fad’in ga Uncle Cop. Cak ta daina abinda take jin k’anina nata na shelan zuwan Mr Inspector. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *43* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tana jinsu dasu Aunty Larai suna gaisawa Ta kasa fitowa daga kitchen d’in saima tambayar kanta da take “Toh mai yake a nan da sassafen nan..?” Bata kaiga nemo amsar ba Habeeb ya shigo rik’eda bindigar wasa ta roba yana fad’in “Aunty Sadiya Uncle Cop yace Wai yana kiranki.. Kinga bindigata da ya kawo mun.. Zanyi chasing bad guys nima..” Ya k’arashe yana saitata da bindigar. Fuzar da huci tai kad’an kafin tace “Shida waye a parlorn.?” “Shi kad’aine yace yana jiranki..” Ya bata amsa yana ci gaba da wasansa. “Alright je ka kawo mun hijab d’ina..” Batakai aya ba Aunty Larai Ta shigo fuska fal fari’a tana fad’in Yauwa had’a ma mijin naki abin kari.. Yana parlor yana jiranki..” Sadiya ta d’anyi rau rau da idanu ba tareda tace komai ba, ta lura wannan Matar tak’ura wa rayuwarta take son yi.. Akan dole tai abinda ta umarceta kafin tazo zata shige. Aunty Larai ta tareta “Ina kuma zakije.?” “Zan d’auko mayafi ne..” Ta bata amsa kai tsaye. Murmushi Aunty Larai tai tace “Yo banda abinki Sadiya mai gida fah akace.. Yo wane irin mayafi..? Wa yafi cancanta yaga kwalliyarki sama dashi, ai ko mu bamu kaisa cancanta ba.. Jeki abinki haka ni bana San wani k’auyanci.” Ta had’iyi miyau da k’yar kafin ta d’auki farantin tana mitan tak’ura mata da wannan matar tai cikin zuciyarta. Yana zaune saman kujera kansa kife yana aikin shafa waya Ta hangesa.. Kaman yasan shi take kallo ya d’ago idanunsa, Ya jima yana dubanta yayinda ta sadda kai k’asa taci gaba da takowa sallama saman bakinta. Murmushin da ba lallai ka fahimta ba saman fuskarsa yake dubanta har ta k’araso cikin parlorn. Ta dire tray d’in ba tareda tace komai ba. “Good morning..” Ya fad’i yana dubanta. Bata amsa ba sai k’ara masa sallama da tai cikin ranta tana fad’in mutum kaman goyon yahudu. Ya amsa mata sallamar . Yana kasheta da wani irin kallo wanda gaba d’aya ya hanata sukuni. Ta lura ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta. Alla alla take ta tashi ta bar wajen. Ta warware d’ankwalin dake kanta ta d’an yafa zuwa kafad’arta tana fad’in “Emm.. Aunty Larai tace na kawo maka breakfast..” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’ewa. “Wait..” Ya dakatar da ita da fad’in haka kafin yaci gaba da fad’in “Shikenan kuma sai ki tashi ki tafi.. Haka akeyi a garinku.. You haven’t even served me” Ba tareda ta kuma cewa komai ba Ta dawo da baya ta duk’a ta zuba masa abincin. “Don’t go until I say so..” Ya fad’i yana zuba sugar cubes a cikin tea. Ya tsareta da idanu kafin ya d’auki mug na tea yana kurb’a. Wane b’angaren take duba ba shi d’in ba. “You look good..” Ya fad’i yana dubanta. “Thank you..” Ta basa amsa cikeda k’osawa murmushin da za’a iya kiransa da yak’e saman fuskarta. Lokaci guda ta kuma d’aure fuskar tana mai duban wani b’angaren. Ya d’auki fork kafin ya janyo chips da liver sauce dake cikin bowl ya soma ci a hankali still idanunsa akanta “This food is delicious.. You made it..?” D’an gyara murya tai kafin tace “Well, actually yes.. But only the sauce.” Jinjina kai yai kad’an kafin yace “So you can cook like this..? I thought zama a gaban motar samari kawai kika iya..” Yai maganar yana cin abincin ba tareda ya dubeta. Ta had’iyi maganar nasa tana mai kauda fusk. Saidai ba shid’inba bazai zauna bai yab’a mata magana ba. Wai ya zaci zama gaban motar samari kawai ta iya tsaban wulak’anci. Babu wanda ya kuma tanka kowa cikinsu saima cin abincinsa da yake peacefully. Ya d’anci da yawa kafin ya d’auki tissue yana goge bakinsa.. Daidai lokacin wayarsa Ta soma ruri. Ya d’aga yana murmushi ganin Inne ce mai kira. Saidya tanaji yanda yake fira gwanin ban sha’awa da Kakarsa.. Tanata mamakinsa dan Ita sam batai zaton na magana haka ba.. Koda yake Ta lura da selected people yakeyi dan ta kula sosai sabo mai tsanani ya shiga tsakaninsu shida Habeeb. Tana tsaka da tinanin ta sinkayo Muryarsa yana fad’in “Alright Inne.. Zan fad’a mata cewa kina gaisheta..” Ya kuma murmusawa kafin yace “Soon zan kawo maki ita in sha Allah..” Daga haka sallama sukai kafin ya dubi Sadiya da Ta b’ace shiru tamkar bata a wajen. “Inne tace tana gaisheki.. And she wants to meet you soon..” “Inne..?” Ta fad’i tana dubansa. Jinjina mata kai yai yace “She’s my Grandmother.. Tace inada sa’a nayo mata kishiyoyi har biyu lokaci guda.” Yai maganar kaman ba daga bakinsa barkwancin ya fito ba. Murmushi ne ya kufce mata wanda yafi kama da yak’e kafin tace “Amma ka mance baka fad’a ma Inne ba.. Cewa you create your own luck yourself.. And aurenmu na mission ne.. Ba mai d’orewa bane..” Shiru yai yana dubanta kafin ya gyara zamansa yace “Look here.. Kalleni..” Ya fad’i yana tsareta da idanu. Dukda gabanta dake tsananin fad’i hakan bai hanata k’ok’artawa Ta juyo tana dubansa ba. Sai kuma ta sadda idanunta a hankali tana jin bugun zuciyarta na k’aruwa. “Sadiya..” D’agowa tai tana dubansa for the first da taji ya ambaci sunanta cikin wane irin siga da zata ce Ta tsinci kanta cikin yanayi mai wuyan fasaltuwa.. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “We’ve been wearing each other out for quite some time now.. I don’t want to have another stressful conversation with you..I want to try and make peace with you.. Let’s try to do this.. Mu mance duk abinda ya faru and start a fresh..” Jiki a matuk’ar sanyaye take dubansa, ji tai kaman ba shi bane mai maganan amma sai ta kauda kanta gefe tana jin wani abu kaman rauni na tasowa daga can k’asar zuciyarta. Lokaci guda wulak’anci da munanan maganganun da ya dinga jifarta dasu suna zuwa mata. “Don’t you think you are asking for too much.. Mr Inspector.?” Bai bata amsa ba Sai mik’ewa da yai yana gyara zaman d’amararsa “Don’t say a word.. Zamuyi magana da dare idan na dawo.. But for now.. Just come with me..” Bai jira cewarta ba ya shiga janyo hannunta. Ta soma girgiza kai tana fad’in “But.. But wait.. Where are you taking me to..?” “Don’t worry I won’t kidnap you again..” Ya bata amsa daidai sanda suka fito zuwa k’asar bishiyar da ya aje motarsa. Jikin k’ofar motar ya tsaya ya d’an jingunu kad’an yana dubanta a hasken ranan hantsi yana jin wani abu mai kamada shauk’i cikin zuciyarsa.. Dik sai ta kuma tsarguwa da irin duban da yake mata. “Do we have to stay here all day Inspector..?” Ta fad’i tana kuma ‘yan juye juye.. “ zamuyi magana da dare idan na dawo..And it’s about us.. Da makomar aurenmu..” Yana ida fad’in haka ya d’auko shopping bag k’arami mai kyau ya mik’a mata. Bata amsa ba ta tsaya tana dubansa gabanta ya fad’i.. Watak’ila sakinta zai tinda dama auren nasu na mission ne kuma mission d’in ya k’are. “Karb’a mana..” Ya fad’i yana kuma mik’o mata. Ta d’an d’ago tana dubansa kafin tace “May I know what’s inside..?” Ta tambaya tana dubansa. “You will see..” Ya fad’i yana mai kamo hannunta ya saka mata bag d’in cikin hannun nata. “Make sure you on the phone.. I’ll call you later..” Ya fad’i yana shigewa cikin motar. Ta d’ago bag d’in tana duba jin abinda ya fad’i kenan waya ya bata. Tai K’uri tana duban motar nasa.. Ta glass ya fito da kansa ya sakar mata murmushi kafin yace “It was a lovely breakfast.. Thank you..” Bata iya furta komai ba Sai dubansa da take.. Har ya maida kansa cikin motar ta dakatar dashi “Inspector.” Ya kuma ciro kansa yana dubanta. “Thank you.. For saving me and my family..” Murmushi ya sakar mata da gefen bakinsa kafin yace “You don’t need to thank me.. It’s my sworn duty as a police officer..” Ya bata amsa da fad’in haka kafin ya maida kansa cikin motar ya soma tafiya. Tai tsaye tana dubansa har motar tasa Ta b’ace ma ganinta kafin Ta sauk’e ajiyan zuciya, ta kuma d’ago jakar tana juyawa maganganunsa na Yawo a kunnuwarta cewa Ta kunna wayar zasuyi magana. Tana isa d’aki ta kulle k’ofar ita d’ayarta kafin ta soma bud’e jakan. Wani note ne Ta soma cin karo dashi. Ta d’auka a hankali tana warwarewa.. Saida ta nad’e k’afafunta kafin ta soma karantawa _You have no idea with whom you are dancing..! MISSION CONTINUES..._ Rausayar da idanu tai tana mai girgiza kai “I knew it.. Bazaka tab’a canzawa ba Malam Inspector.. Ka canza salon wasan Naka kenan.. Zamu gani waye ya iya rawan tsakanin ni da kai..” Ta k’arashe tana mai juya takardan cikin hannunta. Sauk’e ajiyan zuciya tai kafin ta linke takardan tana kuma ciro kwalin wayar. ** Daga cikin restaurant d’in yanda Ameer ke zaune ya d’agowa Meema hannu alamu ta k’araso table d’insa. Meema ta d’an janye shades d’in dake idanunta kafin Ta k’arasa teburin Ameer d’in. Yai mata K’uri yana dubanta har Ta zauna saman kujeran. “Good morning..” Ameer ya fad’i still idanunsa akanta. Ta saki murmushi da gefen bakinta kafin ta jinjina kai tace “Morning..” “What do you want to have..?” Ta girgiza masa kai “No I’m good.. Kar ka damu.. Magana kawai nazo muyi ba jimawa zanyi ba..” Ameer ya mik’e yana fad’in “A’a zaki sha ko tea ne ko coffee it’s still morning ai..” Yana maganar yana d’aga kai yana neman inda waiter d’in ya tafi. Meema tace “Da baka tak’ura kanka ba.. But since you insist, coffee will do.” Ta k’arashe tana mai d’aura k’afa d’aya bisa d’aya. Tuni Ameer ya shige neman waiter d’in yana fad’in mata yanzu zai dawo. Ta jinjina masa kai ba tareda tace komai ba. Barin Ameer wajen keda wuya wayarsa ta soma ringing. Sunan Maleeka CID shi Meema ta ga ya bayyana saman screen d’in Ameer.. Meema Ta zaro idanu sosai tana kuma ganin sunan.. Tabbas Ta gane Maleeka abokiyar aikin Ya Mu’azzam ce.. Kenan tasan Ameer ne kodai dama Ita ce ta turawa Ya Mu’azzam sak’on BAD tinda dama Meema tasan Maleeka na son Mu’azzam dan itace cop d’in da suka tab’a zuwa har ofishinsu suka ci mutuncinta itada Addah Feenah.. Toh idan kuwa haka ne.. Yanzu ta fahimci duk abinda ya faru, kenan Ameer da Maleeka sunsan juna probably suna aiki tare domin cimma muradin junansu. Har wayar Ta katse Ameer bai dawo ba, can ya dawo hannunsa rik’e da disposable cup. Ya ajiye gaban Meema yana fad’in “Your coffee..” “Thank you..” Ta fad’i tana sakin murmushi da yafi kama da yak’e. “Ina sauraronki.. Mecece tattaunawar da kike so muyi..?” Meema ta sauk’e ajiyan zuciya dan ta riga ta sami abinda take nema tinda taga Maleeka na ma Ameer waya. Gudun kar ya fahimci wani abu yasa Ta murmusa tace “It’s about my sister.. She’s living a happy life now with her husband.. Bana fatan abinda zai b’ata mata wannan Farin ciki da take ciki.. Nazo nan ne na rok’eka on behalf of my entire Family.. Dan Allah Barr ka k’yale Safeenah haka.. Ka fita daga rayuwarta ka barta da mijinta.. Ka tuna cewa kai musulmi ne sannan kasan matsayin musulmi dake bibiyan matar aure.. Kuma kaima bazaka so a bibiye matarka ba. Dan Allah ka rabu da ita haka nan.. “ Ta k’arashe tana had’e hannayenta biyu alamun rok’o.. Murmushi Ameer yai kafin yace “Safeenah ce ta turoki nan kizo ki gaya min wad’ann kalaman..?” Saurin girgiza kai Meema tai tace “No.. Addah Feenah bata San nazo nan ba.. Kawai rad’in kaina ne na tsara haka.. Sabida Ina k’aunar ‘yaruwata da kuma ci gabanta.. Kuma da Allah na had’aka ba da kowa ba.. Ka dubi girman Allah ka yada makaman yak’inka na neman auren Addah Feenah.. Ita d’in matar wani ce a halin yanzu..” Shiru yai kaman mai nazari yana duban wani b’angaren kafin ya murmusa yace “I love your sister like I never loved someone before.. Ina tsananin k’aunar Safeenah wanda yasa zan iya aiwatar da komai domin naga na mallaketa.. Amma tinda kikazo har nan kikace haka.. Zan gwada dannar zuciyata idan zata iya amincewa.. But I’m still not sure idan zan ita cire Safeenah cikin sauk’i daga zuciyata..” Daga haka mik’ewa yai ya saka glasses d’insa kafin ya cire suit d’insa da ya lank’aye jikin kujera ya saka a jikinsa “Zan wuce chamber.. Dik yanda mukayi da zuciyata zakiji ni..” Murmushi Meema ta sakar masa kafin Ta kuma masa godiya.. Ameer yasa kai ya shige. Yana ficewa Meema Ta sauk’e ajiyan zuciya kafin tai saurin zaro wayarta Ta shiga dialing layin Safeenah dan ta sanar da ita ha wacce ta had’ata da mijinta. Saidai kiran duniya Meema tayi Safeenah bata d’aga wayarta ba.. Ta lumshe idanu a hankali dan tasan zai wuya Safeenah Ta d’aga kiranta tinda tana tsananin fushi da ita. ** An gama dressing ma Assad kenan ya shigo.. Suka sakar ma juna murmushi kafin Mu’azzam ya k’arasa ya mik’a masa hannu sukai masabaha. “Detective, How are you feeling now..?” Ya tambaya yana duban Assad d’in. “Much better, Sir..” Assad ya basa amsa murmushi saman fuskarsa. Gaba d’aya murmushin suke kafin Assad yace “Ya meeting d’in naku da DIG ya kasance..?” Mu’azzam ya fuzar da fuci kad’an kafin yace “Believe me, It was so stressful..!” Assad ya murmusa kad’an kafin yace “Ba damuwa an karb’o Sady yanzu sann ga kuma Safeenah.. Zasu had’u Su d’auke duk stress d’in nan I believe..” Ya kuma murmusawa kafin yace “Mission zai ci gaba kenan.. I still can’t believe that Mu’azzam Gamji is finally falling in love..” Da wutsiyar idanu Mu’azzam ke dubansa kafin ya d’an tsime yace “You should stop watching those Indian movies.. They are filling your head with nonsense..” Ya k’arashe yana wani tsimewa. Assad ya murmusa yace “Mudai mun zuba ido mun zuba kunne muga yanda mission zata kaya..” Kauda zancen Mu’azzam yai da fad’in “Wai ina Shaheed ne..?” “Ya fice d’azu amma yace ba jimawa zai ba..” Ya jinjina kai kad’an kafin yace “Maleeka tazo ta dubaka..?” Assad ya d’anyi jim kafin ya girgiza kai yace “Yusuf dai yace min jiya Sun shigo ina bacci.. Why.. Maiyasa ka tambaya.?” Mu’azzam ya k’urama waje guda idanu kafin ya d’ago ya dubi Assad yace “Haven’t you noticed anything suspicious tareda Ita..?” Assad ya girgiza kai yace “Ban fahimta ba..?” Mu’azzam ya tako kad’an kafin yaci gaba da fad’in “Randa muka fita operation d’in nan.. Something was off with her.. She looked quite disturbed.. Kaman tana b’oye wani abu..?” Assad ya murmusa yana mai d’an girgiza kai kafin yace “Wacce Ta ceci rayuwarka ne zaka mata wannan zargin.. You owe her a huge debt of gratitude.. She saved your life Mu’azzam..” K’ura masa idanu Mu’azzam yai kafin yace “Da alama har yanzu baka fahimci abinda na gano ba.. Naji she saved my life.. But Maiyasa babu wanda yaga mai harbin cikin kai da Yusuf sai ita..? Sannan muna isa wajen aka soma attacking namu alamun informant d’insu ya sanar dasu muna hanya..” Assad yai shiru yana nazari kafin ya dubi Mu’azzam yace “Kana tunanin tana aiki dasu Danger.. And she could be the mole in our group..?” Ya jinjina kai a hankali kafin yace “Possibly..” Ya gyara tsayuwarsa kad’an kafin yace “Kawai ban yarda da ita ba Assad.. Inaji a jikina itace mai mana zagon k’asa..” Assad ya d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an kafin yace “Ban tab’a kawowa koda tunanin Maleeka zatai abu mai kama da haka ba..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “We are still not sure.. But they say mugu baida kama..” Assad yace “Haka ne..Kace wani abu..” Ya k’arada yaushe ne DNA result d’in B.A.T zai fito.?” “In three days time.. Nan zuwa gobe kenan..” Assad ya d’an gyara daga yanda yake kishingid’e yana fad’in “Nima dai bazan wuce kwana biyu a nan ba.. Na riga na warke.” “Hey don’t rush Detective.. Ka bari ka ida samun lafia babu abin hanzari.. Duk da cewa yau a meeting d’inmu da DIG mutuminka neman duk wata hanya da za’ai watsi da case d’in nan yake.. Amma babu abinda zai achieving bazan bashi wann satisfaction d’in ba..” Assad yace “Jaja will never backdown.” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Ka barshi idan b’era na Yawo mage na Yawo zasu had’e wata rana..” Assad yace “Kenan idan Jaja na kare ‘yanta’addan nan zai iya yuwa yana aiki tareda Maleeka.” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Exactly.. Nasan kamasu redhanded zai matuk’ar wuya but believe me, we will play myth games.” Ya k’arashe yana jinjina kai a hankali lokaci guda Ya duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu “I’ve to go now na maka hira da yawa ai..” Assad ya murmusa yace “Mai iyalai.. Aima kayi k’ok’ari.. Thank you very much..” Girgiza kai kurum Mu’azzam yai kafin yace “Don’t let me punch your wound.” Assad ya darara kad’an daidai lokacin Shaheed k’anin Assad ya shigo suka gaisa yana takama Mu’azzam d’in. ** Babu yanda Meema batai ba Patrick ya barta Ta shiga wajen Safeenah amma fir ya hana yace Safeenar ce tace ita bata San da zuwan wata Meema ba, bama ta da k’anwa mai wann sunan. K’arshe Safeenar da kanta Ta fito tana yatsina fuska take duban Meemar daga gate yanda Patrick ya hanata shiga. Meema da Ta hango Safeenah ta kuma saurin matsowa jikin gate d’in tana fad’in “Addah Feenah please let us talk.. I have something important to tell you..” Patrick ya dubi Safeenah yace “Ma’am, should I let her in..?” A yatsine Safeenah ke duban Meema kafin ta dawo da dubanta ya Patrick tace “Don’t you dare.. Kai ko mai kamanninta ce tazo kar ka barta Ta shigar mun gida.. I don’t know her.” Meema baki sake take duban Safeenah kafin tace “Addah Feenah ni kike kora haka daga gidanki har kina cewa ko mai kamanni na kar a bari ta shiga..? Addah Feenah ni ce Meema fah.. Your sister..” Safeenah ta juyo tana aika mata mugun kallo “I don’t remember having a sister like you..” Ta maidoda dubanta ga Patrick tace “Kai kuma idan ka barta ta shigo a bakin aikin ka.. Idan ta matsa sai ta shigo ka kwance mata karnukan nan..” Daga haka Safeenah sa kai tai ta shige cikin gida abinta. Aka bar Meema baki sake tana duban Safeenah har ta b’acewa ganinta. Fuzar da fuci kad’an Meema tai kafin Ta wuce ta shiga mota ta bar wajen. Tana isowa gida ta tadda Kiki tana jiran k’arasowarta. Jiki babu laka Meema ta zauna cikin kujera tana kwance belt d’in takalmin dake k’afarta. Kiki Ta dubeta tace “Ehen, ya kukayi da Adda Feenah..?” Meema ta tab’e baki kad’an tace “She wouldn’t listen to me.. Tama hanani shiga Gidanta.. Tayi instructing security man d’insu cewa idan na shiga ya kwance min karnuka..” Baki sake Kiki ke dubanta “Addah Feenah ce ta miki haka.. Anya kuwa Meema..?” Meema ta kuma tab’e baki tace “Kinsan dai na daina tsara zance.. Wllhi gaskiya nake fad’a miki.. Addah Feenah shut me off..” Kiki ta jinjina kai cikeda Mamaki “Yanzu kece Wai Addah Feenah ta kora daga gidanta..” Meema bata kai ga bada amsa ba suka sinkayo muryar Mommy tana fad’in “Wacece Safeenah ta kora..?” Kiki Ta dubi Mommy tace “Mommy Wai fah Meema ce Addah Feenah ta hana shiga gidanta.. Can you imagine..” Mommy ta jinjina kai tace “Ai Safeenah ta zama sallamammiya.. Ku k’yaleta bata cikin hayyacinta.. Gata ga namiji idan ya gurza mata guda d’aya k’wakk’wara zata dawo cikin hankalinta.. Sannan ne zata nemi ahalinta..” Mommy tana ida fad’in haka tai k’wafa kafin tai shigewarta zuciyarta fam takaicin Safeenah. Meema da Kiki suka dubi juna kawai ba tareda sunce komai ba. ** Tana jin shigowar motar Mu’azzam Ta mik’e tana gyara kwalliyarta. Abincin da tai googling Ta girka Ta shiga jerawa saman dining table.. Tayi kyau kam dan kyau dan Safeenah akwai iya gayu ma jiki da kwalliya. Saidai fah kana iya hango kwantattun k’ura cikin gidan Dikda kuwa ta daure tayi picking wanda idanu ke iya gani. Mu’azzam na shigowa Ta tafi Ta D’ale jikinsa tana masa sannu da zuwa. Ya sakar mata gajeren murmushi yana mai amsa gaisuwarta. “My Halal.. Nayi kewarka da yawa.. I thought zaka dawo da wuri.” Ta k’arashe tana turo baki. Murmushi ya sakar mata a d’an gajiyye kafin ya kai dubansa ga dining table yaga komai a shirye. Da mamaki ya juyo yana dubanta “You cooked all this..?” Ta jinjina masa kai tana juya idanu “Of course..” Ya d’an rage girman idanunsa yana dubanta “For real..?” Ta d’an turo baki tana juya idanu “Haba my Halal na maka girki instead kaji dad’i shine kake doubting d’ina..” Ya jinjina kai yace “Naji dad’i.. I’ll take a shower first Sai na sauk’o muci abincin..” Ya k’arashe yana mik’a mata k’aramar shopping bag irin wacce ya bawa Sadiya. Safeenah ta Ware idanu tana amsa “Wow.. Menene wann. A surprise gift.?” Ta k’arashe tana ciro kwalin sabuwar wayar. Mu’azzam yace “Nasan bata kai naki kyau da tsada ba.” Rungumesa tai tana fad’in “Duk abinda ya fito daga wajenka is priceless a wajena.. Thank you My Halal.” Ya sakar mata murmushi kafin yace bari yai wanka. Ta jinjina kai cikeda jin dad’i tana mai take masa baya. Da k’yar ta barsa yai wanka da kansa. Shiryawa ma ita ta tayasa.. Suka nufo parlor a tare ta mak’alesa tsam cikin jikinta. Safeenah Ita Ta janyo masa kujera ya zauna kafin Ta soma serving nasa. Kallo d’aya yaima abincin yaji ya k’oshi, bai dai ce komai ba har ta soma serving abincin. “Do you want me to feed you..?” Ta fad’i tana mai zama kujerar gefensa. “Kar ki damu I can feed myself.” Ya fad’i yana janyo plate d’in. Spoon d’aya yai ya dakata.. Safeenah ta tsaresa da idanu tana duban reaction d’insa. Yinin ranan a YouTube ta k’are tana checking recipes d’in da zata girka masa. Da k’yar ya had’iyi abincin da ya saka bakinsa yai saurin janyo ruwa ya tsiyaya a cup yana kwankwad’a “It’s too spicy.. Wann abincin baza’a iya ci ba Safeenah.. Ga gishiri ga yaji.. Ya kuma janyo ruwa yana sha yana hura iska ma bakinsa. Safeenah tai saurin matsowa kusansa ta amshe glass cup d’in Ta aje saman dining table tace “Nasan maganin yajin..” kafin yai aune ta rufe masa baki da nata.. Daga nan bata yarda Ta bar jikinsa ba har saida Ta tabbata an isa yanda take so. K’ara shiryawa yai cikin k’anan kaya kafin ya kuma ficewa. Safeenah fitowa tai daga bathroom taga baya nan.. K’aran ficewar motarsa kurum taji.. Tai saurin janye labule tana lek’e tana mamakin Toh ina ya kuma ficewa..? Kodai wajen wancan ‘Yariskar ya tafi ne..? Toh amma ai basa tare yanzu dama auren mission ne sukai ta tabbata Mu’azzam babu abinda zai da wann yarinyar tinda har Ta gama zamanta cikin gidan babu wani abinda ya shiga tsakaninsu.. Bazata saka ma ranta wani damuwa ba yanda Ta samu yanzu suke zaune lafiya tana samun kula da tarairaya daga mijinta. Sauk’owa k’asa tai tana duban abincin da suka kasa ci. Tai tsaki a hankali tana yatsina fuska “Kai Kai Feenah anya zaki iya wann d’awainiyar..?” Ta tambayi kanta tana duban gidan. Tsaki tai kafin ta isa dining table d’in ta shiga d’iban abincin tana juyewa cikin dustbin. Tanayi tana mitan bazata iya wann wahalar ba. K’arya da ciwo gwara taci gaba da yo masu order idan yaso sai tace ita ta girka. ** Duba d’aya Sadiya tai masa ta sadda kanta. Yai gyaran murya kad’an kafin yaci gaba da fad’in “Bazan k’ara tilasta miki komai ba, kuma bazan kuma d’aukan ki bada amincewarki ba.” Ta d’an girgiza kai kafin tace “Amma ai kai da kanka kace auren mission mukai kuma gidanka tamkar dai GIDAN ARO yake a wajena.. Maiyasa zan koma bayan an gama mission d’in.” Idanunsa k’ar akanta “Nayi alk’awari ma Inne zan kai mata ke.. Bani d’in bane mai son tafiya dake..” Murmushin da yafi kama da yak’e tai kafin tace “Maiyasa ka kasa sanar da Inne gaskiya cewa Auren Mission kai dani.. Kuma mission d’in ya k’are.” D’an kauda kansa gefe yai yana fuzar da fuci kad’an. Ya kuma dubanta yace “Wai ke baza’ayi peaceful conversation dake ba. Dan ma ana son tafiya dake.. Ba don Inne tace a kai mata ke ba Maiyasa ma zanyi tafiya dake bayan inada wata matar.. Kema Kinsan bake kad’ai gareni ba..” Ta d’an juyar da fuskarta kad’an kafin tace “Maiyasa bazaka tafi da matar taka ba.. Tinda kanada ita..” “Bakiji mai nace miki bane.. Badon Inne ba bazanje dake ba. Ita ke son ganinki kuma na mata alk’awari zan kai mata ke.. Nasan bazaki bari na sab’a wann alk’awarin da nai mata ba.” Ta d’an dubesa kafin tace “Is this my new assignment..? Is this another mission..? Idan mun dawo mission d’in ya k’are..?.” “Mai kike so ayi yanzu.?” Ya tambaya yana dubanta. “Zanje sabida kace Inne.. Amma idan na dawo mission d’in ya k’are.. Kuma inada condition d’aya kafin na bika..” Ya tsareta da idanu yana dubanta Wai sai ta gindaya masa sharud’a kafin Ta yarda Ta bisa. “Meye condition d’in naki..?” Muryarta ya sinkayo tana fad’in ”Sai ka rantse min da Allah zaka sakeni da zaran mun dawo kuma zaka fice daga rayuwata gaba d’aya.” Da tsananin mamaki Mu’azzam ke dubanta Wai sai ya mata rantsuwa zai saketa kafin Ta yarda ta bisa. Umma da Ta fito daga d’aki zata nufi kitchen Ta sinkayo tattaunawar nasu Sadiya na fad’in sai Mu’azzam ya rantse zai saketa kafin Ta amince ta bisa garinsu. Fasa shiga kitchen d’in tai Ta k’araso parlorn da sallama. Mu’azzam ya risina ya gaisheta. Ta amsa tana aika ma Sadiya mugun kallo nan take tambayarsa jikin Mamynsa Ta kuma sanar dashi sunyi waya da Inne jiya da dare tace jikin Mamyn nasa da sauk’i. Mu’azzam yanata amsa mata cikin girmamawa yana fad’in aima yanaso yaje ya dubasu idan abubuwa suka d’an lafa.. Umma tace “Aikam ya kamata.. Allah dai ya bata lafiya yasa kaffara ne.” Mu’azzam yanata amsawa da Ameen Umma yayinda Sadiya keta dubansu tana mamakin yaushe har sukai Sabo haka har Umma tasan ‘Yan gidansu suna gaisawa a waya. Bata ida tinanin ba Ta sinkayo muryar Umma na Ta taso suyi magana. Jiki babu laka Sadiya tabi bayan Umma dan taga irin duban da Umman tai mata. Tana shigowa d’akin taji sauk’an mari mai kyau a fuskarta. Ta kame fuskarta tana kuka. Umma na huci take nunata da yatsa “Ashe Bakida mutunci.. Ashe ke mahaukaciya ce ban Sani ba.. Mijin naki kike cewa yayi rantsuwa zai sakeki dan kawai yace yana so ya d’aukeki.. Ashe baki d’auki darasi kan abinda ya faru dani da mahaifinki ba.? Toh idan ya sakeki d’in sai muga ina zaki tafi dan nan ma alfarmarsa kikeci.. Yanzu Sadiya ashe duk karatun da duniya ta biya miki baki d’auki darasi ba.!” Cikin kuka Sadiya ke fad’in “Umma fah baki San mai ya mun bane sanda ya d’aukeni. Yace mun ‘yar tasha ya kirani da sunaye masu muni har had’ani da Karnukansa yai yace ni Kariya ce.” Umma ta kuma kai mata bugu tana fad’in “Sai mai dan yace miki haka.. Wa ya ja ma kansa.. Ke har kinada bakin magana bayan rufa miki asiri da yayi.. Mutumin da ya biya miki bashi ya tsare miki mutuncinki da na ahalinki ya kub’utar dake da ahalinki wannan mutumin kike k’ok’arin wulak’antawa.. Ashe idan baki gode masa ba har zaki wulak’antasa.. Ke bandama taimakon Ubangiji ina zaki samu miji irin Mu’azzam.. Har kina wani gindaya masa sharud’a shi bai miki haka ba.. Tun wuri ki wuce kije ki duk’a ki bawa mijinki hak’uri tun kafin Ubangiji baiyi fushi dake ba.” Ta mik’e tana goge hawayenta. Tin kafin Ta zauna Umma Ta lek’o tana fad’in “Mu’azzam ka dena biye ma wann taurin kan nata, ta shirya maza ka d’auketa ku tafi bazata kuma kwana mana a nan ba..” Ya murmusa kad’an yace “A’a Umma ba damuwa ai tafiyar ma zai kai zuwa thursday in sha Allah.. Ai hak’uri Umma..” Ya fad’i yana duban Sadiya dake goge fuskarta da mayafinta. Umma Ta aika mata mugun kallo kafin tace “Kinci albarkacinsa.” Tai k’wafa kafin Ta janyo k’ofar parlorn ta basu waje. Sai goge hawayenta take ba tareda Ta dubesa ba. Ya k’araso ya kamo kafad’unta ya zaunarta saman kujera. Hannunta ya cire ya shiga goge mata hawayen nata da yatsun hannunsa “I didn’t mean for this to happen.. I believe Umma bata San wasa kike ba.. Mission d’inmu bazai tab’a k’arewa ba har mu koma ga Ubangijinmu... Every day is another mission for us to accomplished..” Ya k’arashe yana mai mak’aleta gefen k’irjinsa na dama. Bata iya furta komai ba Sai lamo da tai cikin k’irjin nasa tana ajiyan zuciya. Bashi ya bar gidan ba saida yaci Dinner, ko bayan da ya tafi ma Sabon fad’a Umma ta dingayi ma Sadiya. Ta yanda take shiga bata nan take fita ba. Har saida Aunty Larai ta k’waci Sadiya hannun Umma. Umma Ta mik’e tana furta “Wanda duk bai gode ma Allah ba zai gode ma azabarsa barikiji na fad’a miki..” Daga haka shigewa tai ta bar Sadiyar da Aunty Larai tana lallashinta “Haba Sadiya har yaushe zaki bud’I baki kice mijinki ya sakeki, kin kuwa San zunubin dake cikin yin hakan.. Mutumin da kullum rawar k’afa yake akanki yana sintiri a nan safe da dare bama muzguna miki yake ba balle ace eh ga dalili.. Kar fah ki mance Mu’azzam mata biyu ke garesa kuma wacce duk tafi kyautata masa cikinku itace zata zamto mai babban matsayi cikin zuciyarsa koda bai furta hakan ba dan zuciya tana san mai kyautata mata ne..” Cikin kuka tace “Aunty wllhi fah ba sona yake ba kawai mission d’insa yake dani.. Umma bazata fahimci haka bane..” Aunty Larai Ta murmusa kafin tace “Salon nasa soyayyar kenan Sadiya.. Kuma Kema na tabbata kina son mijinki kawai dai halin namu na mata ne kike d’an masa.. Hakan nada kyau dan mu mata saida aji koh.. Amma ai a hankali kar ya zarce kima.. Ki natsu ki karanci mijinki kisan wanene shi Ina nufin d’abi’unsa da halayyarsa.. Idan kika karanci wad’ann kika San yanda zakiyi mu’amala dashi ina mai tabbatar miki zaki samu mijinki zaki tafiyar da gidanki yanda kike so.. Ba Wai asiri bane ko tsafi yake sa a mallaki Zuciyar miji.. A’a babu boka babu Malam idan kinaso zaki zama sarauniya wajen mijinki.. Tsananin biyayya da iya kula da buk’atunsa shi ke sa mace ta samu wann d’aukaka a wajen miji.. Sannan kafin ki iya wann sai kin karanci wanene mijinki.. Shiyasa wasu lokutan sai kiji ana cewa wasu matansu sun asircesu.. Wlhi babu boka babu Malam kawai sanin makaman rayuwa ne. Quite alright akwai masu mallaka da asiri amma kuma akwai masuyi da dabaru irin namu na mata da Ubangiji ya hore mana.. Idan yace mission bishi a mission d’in, ki rikitashi da naki salon mission d’in kinji koh.. Yana jefo miki assignment capke ki solving masa tun kafin ya kuma jefo miki wani yanda zaki zamto kece wacce kike basa assignments d’in bashi ba.. Ko wane d’an adam akwai halinsa da yake nature ne, wad’ann natural d’in sai kiyi adopting nasu since we can’t change what’s natural. Mace ita take raya gidanta kuma ita take kashe gidanta.. Duk wasu makaman yak’in Allah ya mallaka miki kawai saidai idan baki San yanda zakiyi amfani dasu ba. Kina jina.. Ki saki jiki ki tarairayi mijinki Mu’azzam na matuk’ar k’aunarki koda wasa kar ki bari gidanki ya kufce miki a hannunki.. Kula da miji ba gajiyawa bane sannan yi masa biyayya ba kasawa bane. Wad’ann sune zasu d’aga martabarki da Kimarki a idanunsa kinji koh.. Idan nace haka ina nufin tsafta kwalliya kula da muhalli iya sarrafa kayan abinci da girkasu Duk suna cikin tattalin gida kinji koh.. Muhimmi kula da buk’atarsa, so goma idan zai nemeki kar ko gwada masa kin gajiya, ko a fuskarki kar ki bari ya gane haka, wnn ba k’aramin kima da martaba zai k’ara miki a idanunsa ba Sanna k’aunarki zai ninku cikin zuciyarsa.. Ki gyara masa kanki ciki da waje, idan nace ciki da waje Ina nufin jikinki da kuma matantakanki.. Gyara ko a musulunci nada kyau dik abinda kika san zaisa mijinki yaji dad’i ya kuma samu gamsuwa dake matuk’a bai kauce ma shari’a ba Sannan baya cutarwa kina iya amfani da abinki dan gyaran gidanki.. Abu na gaba ki girmama iyayensa mahaifiyarsa ‘yanuwansa ki nuna masa suma naki ne. Abokiyar zamanki ki zauna da ita zuciya d’aya da alkhairi..” Sadiya kam sadda kanta k’asa tai tana d’aukan karatun Aunty Larai kaman D’alibi gaban Malami. Aunty Larai da ta kula kunyarta take tace “Ki saki jikinki dani kinji koh.. Ki tambayeni dik abinda ya shige miki duhu kinji koh.. Ni da Allah ya bani d’iya haka zan zama very open da ita, kafin ta sani a wani waje ni zan koyar da ita ta hanyar da ya kamata.. Tinda Allah bai bani d’iya ba gaki nan ya bani.. Ki saki jiki dani kinji koh babu wani kunya yanda zaki inganta rayuwar gidanki da auratayyarki nake k’ok’arin fahimtar dake kinji koh.. Maza tashi kije ki wanke fuskarki anjima zamu ci gaba.” Ta jinjina kai a hankali kafin Ta mik’e ta nufi bathroom. Aunty Larai ta bita da kallo fuskarta d’aukeda murmushi, ta d’au alwashin kafin Mu’azzam ya d’auki matarsa sai ta gyara masa ita tsaf, irin gyararrakin da suka cancanci Ta samu. Kama daga wanda idanu ka iya gani harma wanda idanu bai gani. ** Washe gari aka sallami Assad sannan Mu’azzam ya karb’i takardan gwajin DNA da yai, result d’in bai matching da k’wayar halittar Musaddiq ba. Hakan na nufin hular bata Musaddiq bace.. Sosai hakan yasa zuciyar Mu’azzam yin sanyi.. Saidai ya rasa dalilin da yasa ya gaza samun cikakken natsuwa akan sakamakon gwajin. Baisan dalili ba amma can k’asar zuciyarsa yana jin bai yarda da sakamakon ba. Sauk’e ajiyan zuciya yai a hankali yana mai fuzar da fuci lokaci guda ya saka abin goge allo ya goge dogon arrow da ya zana daga hoton Danger zuwa B.A.T da ya rubuta da question mark. Dai dai lokacin Yusuf da Maleeka suka shigo. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *44* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Marker ya kuma d’auka ya zana allon ya sake rubuta abinda ya goge. Maleeka tai masa K’uri tana dubansa, Toh ko bai yarda da sakamon gwajin bane.? Kodai shakku da kokonto ya fara..? Bata kai ga nemo amsar ba ta sinkayo muryar Yusuf yana fad’in “Sir menene B.A.T yake nufi if I may ask..?” Mu’azzam na fuskantar allon yana karantar hotunan mutanen dake mak’ale jiki yake fad’i da Yusuf “Soon enough zamu gano wanene B.A.T.. But for now it’s classified..” Ya k’arashe yana mai juyowa had’ida tsaresu da idanu. Yusuf ya d’anyi gyaran murya yace “Sir, is there any assignment da zaka bamu akan B.A.T..?” Ya tsare Yusuf da idanu yana karantarsa kafin yace “For now akwai certain people a cikin Department d’in nan who are messing with our case.. And we need to find those people and make them pay..” Yana maganar yana duban Maleeka da tuni zuciyarta kaman bai wajen, kana ganinta zaka fahimci tana cikin tsananin tsoro. Mu’azzam ya tako zuwa gabanta idanunsa tar akanta “You will be the one to take this part..” Ya fad’i yana dubanta. Saida ta d’an firgita kafin ta d’ago tana dubansa “Sir..?” Mu’azzam ya d’an gyara tsayuwarsa kafin yace “Are you alright..?” Saurin saita kanta tai kafin ta jinjina masa kai “I’m good, sir.” Ya jinjina kai yana duban hannunta mai ciwo da aka harba “How is your wound.?” Ta k’ak’aro murmushi cikeda jin dad’in ya tambayi ciwonta. Lokaci guda take duban hannun kafin tace “Na warke Sir, and I’m ready for another assignment..” Ya jinjina kai kafin yace “Kinji abinda nace kenan..?” Tai saurin dubansa sai kuma ta dubi Yusuf dake tsaye gefe yai Folding hannayensa yana dubansu. Saurin girgiza kai tai kafin tace “Pardon me sir, did you say something..?” “About B.A.T..” Ya fad’i yana dubanta wanda ya kuma sanyata razana. “Na zaci kace it’s classified, sir.” Ta fad’i a d’an daburce. “I’ve changed my mind.. B.A.T is someone in our Department who is working hand in hand da criminals d’in da muke nema.. B.A.T is Danger’s Spy a cikin CID.. And If we want to catch Danger once and for all we must catch B.AT first dan shine zai leading namu to Danger..” Ya d’an soma takawa kad’an yana zagaye room d’in kafin ya tsaya jikin wani table da Maleeka ke tsaye gefe. Zuciyarta sai tsinkewa yake.. Lokaci guda Mu’azzam ke dubanta kafin yace “You will be the one to carry out this assignment.. ki nemo mana wanene B.A.T a cikin CID.” Daga haka d’aukan folder d’in dake wajen yai kafin ya fice daga office d’in. Maleeka Ta fuzar da fuci tana duban Yusuf “Goddamn binciken cikin gida..? Ta ina zan fara.. Wa zan fara suspecting..? How am I going to carry out this assignment Yusuf..?” Ta k’arashe tana fuzar da fuci. Yusuf ya d’an girgiza kai yana murmushi kafin yace “Tactics kawai zakiyi amfani da ki zak’ulo mana mai cin amanan K’asa da Al’umman cikinta.. Dan duk jami’in tsaron dake huld’a da ‘Yantadda maciyi amanan K’asa ne da Al’ummarta..” Yusuf ma ficewa yai ya barta nan tsaye a wajen gumi na tsartsafo mata. Maleeka ta fuzar da fuci tana d’aura hannayenta saman table ko shakka babu ta fahimci Mu’azzam so yake ya kamata shiyasa kawai ya bata wann aikin.. Dan idan kana son kama mutum sai ka saka shi ya kamo kansa da kansa.. Yanzu mai zatayi..? Dole ta nemi taimakon Chief Dan idan ba haka ba tayi imani Mu’azzam Sai ya fahimci ita ce take masu zagon k’asa.. Da wann tunanin ta fice daga offishin tana sakin huci duk a dame take. Kai tsaye Office d’in Chief Ta nufa tana yarfe gumi. Chief ya tsareta da idanu yana girgiza kai alamun meke tafe da ita. Fuzar da wani hucin ta kuma yi kafin tace “Ya fara zargina Chief..” Chief ya girgiza kai yace “Waye kuma ya fara zargin ki..?” “Waye kuwa idan ba Mu’azzam Gamji ba.. Can you imagine yayi assigning d’ina cikin team d’inmu na nemo masa wanene mai mana zagon k’asa a entire CID.. Idan ba zargina ya soma ba bazai tab’a assigning d’ina ba..” Ta k’arashe tana kuma shafe goshinta. Chief ya murmusa kafin yace “Then give him what he’s asking for.. Ki kai masa mai yi maku zagon k’asan..” Maleeka ta juyo tana dubansa shaye da mamaki kafin tace “Did you hear yourself..? Ni ce zan kai masa kaina ko kuma kai ne zan kai masa a matsayin wanda yake masa zagon k’asa.. Sanin kanka ne Chief binciken cikin gida yafi komai wahala a aikinmu..” Chief ya murmusa kafin yace “Ku duka yara ne a aikin.. Baku San yanda al’amara suke gudana a wajenmu ba.. Especially Inspector Gamji.. Yaro mai k’waza mai kuma so ya kawo sauyi a al’amran tsaro na k’asar nan.. Saidai kash da irin wann k’wazon nasa ina mai tabbatar miki baza’a barsa yaje ko Ina ba.. Ko ni Jaja banyi eliminating nasa ba akwai manyan k’wari a sama da zasu shafe shi musamman idan suka lura zai kawo ma business d’insu cikas.. Su Waye ‘Yantaddan Maleeka..? Suna nan a cikin mu kuma ana dama hark’an mulki da tsaro dasu.. Kawo gyara ba abu bane mai sauk’i a k’asa irin namu saidai talaka yayita add’ua yana neman d’auki a wajen Allah dan shine kawai zai iya saita al’amran k’asar nan..” Maleeka ta fuzar da fuci tace “Ni duk ba wanna ba Chief.. Ya zanyi da Inspector Gamji..?” Chief ya murmusa ya matso yana shafan fuskarta kafin yace “Abu ne mai sauk’i.. Idan ya gwada yana son kamaki ke kuma sai ki tura makusancinsa cikin ramin.. Abinda nake nufi wannan shine perfect opportunity naki da zaki gwara kansa da abokinsa..” Maleeka tai shiru tana sauraron Chief kafin ta girgiza kai tace “Ban fahimceka ba Sir..” Chief ya kuma murmusawa kafin ya saka makulli ya rufe ofishinsa ya janyo Maleeka yana fad’in barin na fahimtar dake. Sai bayan tsawon d’an lokaci kafin Maleeka ta fito daga ofishin Chief tana kintsa kanta. Mu’azzam da fitowarsa kenan daga wani dept d’in nan ya hangi Maleeka ta fito daga Office d’in Chief.. Sannan Ta fito dik a birkice sai waige waige take tana gyara zaman rigarta. Jinjina kai yai a hankali kafin ya furta “Muje zuwa.. Sannu a hankali zamu kamaku..” Daga haka Sa kai yai ya fice daga ofishin gaba d’aya. ** FUFORE Yau ce Rana ta farko da ta soma shiga d’akin Inne, Inne ta aiketa ta d’auko mata k’aramar jakarta dake gefen bedside zasu fita zata raka Innen gaisuwan haihuwa jikar k’awarta ta haihu a cikin gari.. Nan Ajidde ta tsaya tana duban tsarin d’akin baki hangame tana fad’in “Kaga d’aki saikace ba na tsohuwa ba.. Masu shi dai suna abinda suka so.. An gaisheka d’aki kaci kud’in gidan gona gaskiya..” D’aga kan da zatai Ta hangi k’atoton hoto saman gadon.. Inne ce zaune a tsakiya sai Samaruka guda biyu Sun tsaya gefe da gefe sun sakata a tsakiya dukkansu sun dafa Innen murmushi saman fuskokinsu. Ta gane d’ayan Mu’azzam ne wanda tasan jikan Inne ne saiko d’ayan da ko a mafarki bazatai kuskuren mance kamanninsa ba, Kuran tashe nata ne.. Toh ya akai sukai hoto irin haka kaman wasu ahali, a iyaka saninta Kuran tashe yace mata shi abokin jikan gidan ne.. Toh ma saida taga sunyi hoto haka taga kamanninsu ya fito.. Ikon Allah toh kodai ‘yanuwa ne..? Bata kaiga samo amsar ba Mama Hinde ta shigo tana fad’in “Wai an aikeki Ajidde kaman an aiki Bawa garinsu.. Inne nata jiranki zaku fita..” Mama Hindu ta girgiza kai kurum ganin yanda Ajidde ta kafe tana kallon hoto.. “Ke Ajidde Wai bakiji bane..?” Sai sannan Ajidde ta juyo tana duban Mama Hindu.. Sai kuma ta soma nuna mata hoton ba tareda tace komai ba..” Girgiza kai Mama Hindu tai tace “Toh Sarkin shiririta wanene bak’o cikinsu a wajenki. Inne ce baki sani ba ko kuwa Mu’azzam da Musaddiq ne baki sani ba..?” “Mana Hindu kika ce menene sunan wancan dake tsaye daga b’angaren hagu..?” Mama Hindu Ta girgiza kai tace “Wai duk zuwanki gidan nan baki sansa ba.. Kwanakin baya ya koma can Abuja gidan Babansa amma ya jima a nan ai shi Musaddiq d’in..” Ajidde tace “Kika ce sunansa Musaddiq.. Toh ai shine Kuran tashe.. Na rantse da Allah shine Kuran tashe.. Wllhi bazan tab’a mance kamanninsa ba.. Dama jikan Inne ne..?” Mama Hindu ta girgiza kai tace “Adana tambayoyinki har ku dawo Inne na jiranki yanzu tintini Malam Sadi ya tada mota ke ake jira..” Ta k’arashe tana janyo Ajidden daketa faman waigowa tana kuma duban hoton Musaddiq daketa sakin murmushi. Mamaki fal Zuciyar Ajidde Wai jikan gidan ne.. Shine yace mata shi ba d’an gidan bane babu abinda ya had’asu Sai abota da yake da d’an gidan.. Wato k’arya ya mata kenan.. Toh Maiyasa ya mata k’arya.. Maiyasa ya b’oye mata asalinsa.. Duk sai taji babu dad’i.. Jikinta gaba d’aya sai taji kaman an zare mata laka.. Duk da wauta da shahshashanci irin nata sosai taji zafin abinda Kuran tashe yai mata na b’oye mata kansa da yai, sannan tana son sanin Maiyasa ya mata hakan. Ranan haka Ajidde har Ta koma gida tunanin da take kenan b’oye mata kansa da Musaddiq yai.. Sunansa kuwa ranan kaman biya karatu haka taita nanatawa.. Yanzu Kyallu batada lokacinta sosai dan tana samun majinyata da take kwantar dasu a nan gidanta akai akai.. Idan ta baiwa Ajidde maganin Gidan Gona bata kuma bi takanta.. Hakan sai yafi ma Ajidde dad’i da bata yini a gidan balle taga yanda ake shirka ma Ubangiji da sunan magani. Ko safiyan Washe gari ma da zata fice taga wata mata an kawota bata cikin hayyacinta Kyallu tace a kawo Bak’in zakara da budurwa Baru a masu barbara sannan aka buga kan bak’in zakaran da dutse wanda saida ya mutu jini ya soma zuba Kyallu tace Jinin za’a baiwa matar sannan a shafe jikinta da sauran shine maganin ciwonta.. Ajidde Ta girgiza kai kurum kafin ta fice ta nufi gidan Malama Hafsah. Daga yanda Malama ta ganta Jiki a sanyaye ta fahimci wani abu na damunta. Malama ta tambayeta meke faruwa.? Ajidde tai shiru tana duban Malama bata sanar da ita abinda Musaddiq yai mata ba Sai ta soma sanar da ita abinda taga Kyallu tayi. Malama Ta nusa kad’an tace “Da yawan irin wad’ann bokayen sun ari sunayen masu magani na gargajiya suna fakewa suna yin bokancinsu Ajidde.. Tabbas akwai masu magani na gaskiya na gargajiya wanda ubangiji ya huwace masu ilimin sanin magunguna.. Sannan akwai Malamai masu magani da ayoyin Ubangiji bisa tsari da shari’a.. Sannan akwai wad’anda suke fakewa suke bokanci suna yanka dabbobi bada sunan Allah ba suna bawa mushirikan Aljanu jini.. Sai kiji ana cewa a kawo bak’in jaki za’ayi magani, a’a a kawo faran tinkiya za’ayi magani.. Irin wad’ann masu maganin Ajidde duk sun b’adda kama suna shiga cikin na gari suna bokanci da tsafi.. Suna shirka ma Ubangiji da sunan magani.. Akwai majinyata da ciwo zaik’i ci yak’i cinyewa.. Aita kawo masa sunayen masu magani gari wa gari.. Idan ba’ayi sa’a ba har a fad’a hannun irin wad’ann masu maganin wad’anda bokaye ne masu shirka ma Ubangiji ba wai maganin sukeyi ba wasu ma kawai sai su had’a ‘yanuwa gaba suce wane ne yai maka jifa alhali k’arya ce kawai bokanci ne da tsafi... Abu na farko da majinyaci zai saka a ransa shine jinyar nan Bautan Ubangiji yake.. Kuma jarabawa ce da Allah ya jarabcesa da ita domin yaga zaiyi hak’uri yaci jarabawa kokuwa zai kauce wa rahamarsa.. Duk zafin jinya zunubi ake kankare wa majinyaci.. Sannan suma masu jinyar wann majinyacin jarabawa ce da Allah ya jarabcesu da ita kuma duk d’awainiyar da sukai wa mai jinya lada suke samu wanda Allah shi zai biyasu wanan ladan na hak’uri da kuma d’awainiyarsu.. Hadisi yazo ingantacce Manzon Allah (S.A.W) yace babu wata cuta da Allah ya sauk’ar saida ya sauk’ar mata da maganinta. Ko wata iri ce kuwa... Neman magani ba haramun bane kuma godiyan Ubangiji shine ka saka dukiyanka ka nemi lafiya da Ita, amma saidai kar garin neman magani ka kai kanka ga halak’a.. Kar kaje wajen boka domin ya baka lafiya.. Babu mai warkarwa sai Allah.. Shi yake saka cuta kuma shi yake yayewa.. Idan yaso ko baka sha komai ba Sai ya baka lafiya dan shine mai bayarwan. Idan baiso ka sami lafiya ba ko zaka zaga duniyar nan Sai k’a k’arashi neman maganinka baka samu ba.. Tauhidi itace abu na farko da majinyaci yake buk’ata Ajidde.. Ita ce magani na farko da majinyaci zai sha.. Ya saka a ransa Allah shine mai yi kuma shine mai hanawa.. Idan ya tsira da tauhidinsa ko da Ubangiji ya k’addari wann jinya ba na tashi bane sai yayi fatan ya d’auki ransa yana mai imani ba yana mai kauce ma Ubangijinsa ba.. Sau tari zakiga anje wajen irin wad’ann masu maganin anyi bori anyi yanka ma aljanu sannan an halak’a daga k’arshe ba’a samu biyan buk’atan ba dan basu sukeyi ba Allah shine mai yi.. Ba’a samu biyan buk’ata ba Sannan an mutu ana kauce wa Ubangiji.. Allah ya shiryemu gaba d’aya ya kuma datar damu.. Ya ba ma marassa lafiyanmu lafiya, ya tsare mana imanin mu da tauhidinmu.. Ya d’auki rayuwarmu yana mai farin ciki damu..” A hankali Ajidde ta jinjina kai tana fad’in “Ameen Malama..” Malama Hafsah ta mik’o mata ruwa addu’a da take bata sannan ta had’a mata da garin Habbatussauda tace wannan hayak’insa zaki mata a cikin d’akin da take kwana.. Yana koran shaid’anu.. Sannan yanada kyau mutum ya dinga hayak’in habbatussauda a cikin gidansa lokaci zuwa lokaci domin yana kore shaid’anu daga gida.” Ajidde ta jinjina kai tace “Toh Malama Allah ya saka da alkhairi ni zan wuce..” Malama ta jinjina kai tace “Allah ya nufemu da dacewa ya kuma bawa Nuratu lafiya..” Ajidde ta amsa da Ameen kafin sukai sallama da Malama ta fice. ** ABUJA Yau kusan kwanaki uku kenan bata sanyasa a idanunta ba, tinda ya tafi ranan da dare bata kuma ganinsa ba, gashi harta waya ma bai mata ba.. Haka zatai ta kallon lambarsa taji kaman ta danna kira amma sai ta fasa dan batasan mai zata ce masa ba.. Kasancewar laraba tayi ya sanya take ta jin wani Farin ciki cikin zuciyarta dan tafiyarsu Alhamis ne kaman yanda yace. Harga Allah ba Farin cikin tafiyar take ba amma tasan tana Farin ciki ne sabida zata gansa.. Tai shiru tana tuhumar kanta Maiyasa take jin haka akansa..? A baya zata iya cewa bata tab’a jin irin hakan ga kowa ba harta kuwa Sagir da suka kusan aure.. Ko dan lokacin abin hannayensu take so ba Su d’in ba..? Toh Maiyasa yanzu da bata son abin hannun kowa take jin haka gameda Inspector..? Kar fah maganan Aunty Larai ya tabbata cewa son Inspector take.. Cikin sauri ta d’ago kai tana duban fuskarta cikin dressing mirror.. Ta kuma tambayar zuciyarta.. Sai kuma ta rintse idanunta cikeda tsoron ansar da Zuciyar nata ke bata.. Ta k’ura ma fuskarta idanu cikin mirror kafin tace “Are you messing with my heart now Mr Inspector..?” Cikin sauri ta lumshe idanunta tana jinginuwa jikin gini. Aunty Larai dake lab’e bakin k’ofa tana dubanta murmushi saman fuskarta, a hankali tai knocking da yatsarta guda. Sadiya tai saurin tattara natsuwarta tana kintsa kanta. Aunty Larai ta shigo sallama saman bakinta, hannunta rik’eda had’in Kankana.. “Maza Zo ki shanye wann..” Ta fad’i tana zama gefen gado. Sadiya ta d’anyi rau rau da idanu dan kusan kullum Aunty Larai da irin had’in da take bata. Ta d’an dubeta kafin tace “Bari dai na miki bayanin menene a cikin wanann.. Kinga akwai Kankana K’wallo d’aya sannan sakwai sabuwar tsamiya k’wara hud’u sannan akwai tafarnuwa curi d’aya.. Ita Kankana tanada tasiri jikin ‘ya mace sannan tsamiya magani ce itama.. Tafarnuwa kuwa Antibacterial ne.. Duk wata cuta da ta shafi mara tana maganceta.. Yana da kyau bayan lokaci ki dinga yi ma kanki wannan had’in dan takan bada kariya daga cuta na sanyi da ya addabemu a gidajen aurenmu.. Sannan ita wann had’in ko wanda ke fama da cuta na sanyi zai iya had’awa ya dinga sha da izinin Allah za’a samu waraka. A had’asu waje guda a dafa a dinga sha safe da yamma.. Kinga ba wani abu mai cutarwa na baki ba maza d’auki ki shanye.” Sadiya ta d’auka ta kafa kanta ta shanye. Duk a kwanakin had’e had’e iri daban daban masu inganta lafiya da matantakanta Aunty Larai ta dinga bata.. Wasu Ta mata bayani wasu kaw bata mata bayani saidai ta sanyata cinyewa ko shanyewa.. Ga gyaran fata na musamman da take mata ita har Ta fara tinanin kodai had’a baki Inspector sukai da Aunty Larai shisa ya dena zuwa gidan.. Taga har alhamis Yayi babu Inspector babu batun tafiyarsu.. Abin har dai ya soma damunta gashi Aunty Larai bata fasa mata abu guda da take mata ba.. Fatarta ya kuma murjewa har wani kyalli da shek’i yake.. Jikinta ya kuma cika dan tana iya jin hakan tattare da ita.. A tak’aice ita kanta tana jin kanta Ta kuma canzawa. Idan ka kalleta dole kaso sake kallanta.. Wasa wasa saida akai kusan sati Inspector baizo gidan ba.. Ba abin Ta tambaya ba bama zata iya ba.. Idan ta zauna haka zatai ta kallon lambar wayarsa tana tinani.. Wasu lokutan ta kwab’i kanta tace k’ila ma ya mance da ita.. K’ila ma ya d’auki d’aya matarsa sunyi tafiyar.. Wannan tunanin shi yafi d’aga mata hankali.. Kardai ya d’auki d’aya matar tasa sun tafi ne tinda yace bazai kuma tilasta mata komai ba.. Maganganun Aunty Larai suka shiga zuwa mata cewa namiji baya son taurin Kai da kafiyar masifa da kuma musu, wad’ann abin sosai suke rage darajan mace wajen mijinta.. Sannan Ta bawa mijinta dama ya zamto babban abokinta kuma abokin shawarinta.. Yanzu ita da Mr Inspector Wai har zasu zamto manyan abokai irin yanda Aunty Larai ke fad’i..? Ta kuma duban fuskarta a madubi kafin zancen Aunty Larai ya kuma zuwa mata cewa Great Mission d’inta shine rayuwar aure dake gabanta, dan aure ibadah ne kuma bautan Ubangiji ne. Duk abinda Ta gani cikin gidan aure ibadah take.. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kafin ta isa ta kwanta hoton fuskar mijinta cikin idanunta. A ranan da yammaci Aunty Larai tazo da mai lalle Ta zana mata bak’i da ja hannu da k’afa.. Sosai k’unshi yai kyau ya amshi fatarta musamman da shike fatar tata ta d’auki gyara sosai. Idan ka ganta kaman wata sabuwar Amarya ga wani k’amshi na musamman da take duk yanda Ta gifta.. Habeeb ya dubeta yace “Aunty Sadiya kunyi kyau sosai kaman ana bikinki..” Gaba d’aya suka d’an dara Habeeb na kuma cikasu da sururtu. Kafin dare mai kitso tazo tai mata dan harta wanke kai da drying saida Aunty Larai tai mata. Safiyar Washe gari litinin Aunty Larai ta sanyata ta shirya tsaf cikin wani embroidery atampa mai kyaun gaske ruwan cikin k’wai wanda ya tafi da kalan jikinta, d’inkin riga da skirt ne da ya masifan mata kyau cikin kayyakin da su Aunty Larai suka d’inka mata a nan cikin foundation d’in. Dama tin kwanakin baya Aunty Larai ta d’au measurement d’inta ashe Mu’azzam ne ya bama Aunty Larai tai mata d’inkuna masu kyau na zamani.. Sai gani kawai tai Aunty Larai dasu Farida ‘yanmata masu koyar da sana’ar d’inki a foundation d’in suna shigo da kayayyaki kama daga laces zuwa atmapopi hardai irinsu Dubai materials d’in nan. Aunty Larai tasa Farida tai mata light makeup a fuskarta. Dik yanda Sadiya bataso ba haka dole akai mata mai sauk’i dama ita ba gwanar kwalliya ma fuska bace tin tana amsa sunan Sady pretty.. Kaidai barta da gayu ma jiki sai ka rantse d’iyar wata hamshak’i ne.. Dama bata faye fente fuska ba.. Yau d’in Sai abin ya zama na musamman abinka da wacce bata saba ba. Tayi kyau har ta gaji, Farida ta d’aura mata d’ankwalin daidai da kanta. Sai santin kyaun da ta k’ara suke.. Ita dai batace komai ba sai fad’uwa da gabanta keyi dan ko Aunty larai bata sanar da ita ba tanaji a jikinta Inspector ne zaizo, ga Umma ta kauda kai abinta bama ta saka masu baki cikin al’amaransu.. Toh kodai baiyi tafiyar bane.? Ta tambayi kanta tana duban kanta a mirror bayan an ida shiryata. Tabarakallah Masha Allah shine kawai abinda taji zuciyarta na ambata. Ta fito tsaf da ita kaman wata sabuwar Amarya. Tana tsaka da tinanin wayar ya soma ruri. Ta juya tana duban wayar kan gado gabanta na kuma fad’uwa. Tasan idan bashi d’in ba babu mai kiran wayar Dikda cewa ba da lambar da ya sanya mata ba yake kiran. Ta k’arasa a hankali hannunsa sai k’aran awarwaro yake kafin ta d’auki wayar. Bata furta komai ba daga d’aya b’angaren ta sinkayo muryarsa cikin sallama. Ta lumshe idanunta a hankali tana tinanin yaushe rabon da taji Muryarsa. Sallamar tasa ma a zuciya Ta iya amsawa. Shiru kaman babu mai kuma cewa komai. Nan ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Are you ready for your next mission..?” Murmushi ne taji yazo mata wann karon.. Sai ta d’an murmusa tana rufe fuskarta da hannu guda. Mu’azzam yaji sautin murmushin nata ta cikin waya. Shima murmushin yai kafin yace “Ki fito ina jiranki a parlor.” Daga haka k’it ya katse kiran. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana kuma duban kanta. Mayafinta kalan kayan dake aje saman gado ta d’auka ta yafa kaman mai tsoron ganinsa ko kuma wacce basu tab’a had’uwa ba haka nan taji.. Ta kasa fita saima komawa da baya da tai tana sauk’e ajiyan zuciya a hankali. Kusan minti biyar ta kwashe kafin ta daure ta fito cikin taku a tsanake. Tin daga nesa yake dubanta dan musulmin k’amshin da take ne ma ya soma yima k’ofofin hancinsa sallama. Cak ya daina shafa wayar da yake ya mik’e tsaye yana dubanta sanda take k’arasowa. K’afafunsa ta fara hangowa itama nan ta fahimci yau d’in shigar manyan kaya yayi.. Ta d’ago idanunta a hankali tana dubansa. Jampa ce jikinsa kalan ruwan k’asa sai hularsa Wanda ya dace da shigar tasa.. zata iya cewa wann shine karo na farko da ta gansa da idonta cikin manyan kaya tin bayan hoton aurensu da ta gani shida Safeenah a gidansu. Sosai shigar ya amshesa ita zata iya cewa irin wann shigar ma yafi amsar Sa. Ko kuma dan ta kwana biyu bata gansa bane shiyasa taga hakan bata dai sani ba. Kaman wacce aka tsunkula Ta kuma maida kanta k’asa tana jin kaman bazata iya ci gaba da tafiya ba sabida irin kallon da yake mata. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *45* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kasa k’arasowa tai saima tsayuwa da tai daga can nesa kanta a k’asa. Gabanta na wani irin fad’uwa musamman da ta jiyo sautin footsteps d’insa alamun yana k’arasowa. Saida ya tako kusanta kafin yaja ya tsaya yana kuma k’are mata kallo lokaci guda yana tsarkake mahaliccinta.. Cikin ransa yake fad’in Maiyasa suke kiranta Pretty...? Beauty ta cancanci su kirata ba Pretty ba domin kuwa she’s truly beautiful.. Ya k’arashe zancen zucin nasa yana mai kuma k’arasowa kusanta, dab kusanta ya tsaya yana duban tsakiyar kanta sabida ratan tsawo dake tsakaninsu. K’amshin dake jikinta na kuma tasowa yana bugan k’ofofin hancinsa, hannayensa ya bud’e had’ida rungumeta cikin jikinsa idanunsa a lumshe. Itama d’in lumshe idanunta tai tana jin wani irin salama had’ida nastuwa na ratsa zuciyarta. Sun d’an jima a haka kafin ya rik’o hannunta suka zauna saman kujera. Ta d’an duk’a ta gaishesa kanta a k’asa. Ya tsareta da idanu yana duban Bak’on Al’amari a wajenta. Gaba d’aya shi gani yake ma kaman an canzata. Ya amsa ba tareda ya janye idanunsa daga kanta ba. Suka d’auki lokaci a haka Sai k’are mata kallo yake, har ta soma gundura tana tinanin bazai kuma cewa komai ba, dan tasan mai hali baya fasawa. Nan kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “It seems to me you’re ready.. For your next mission.. Kin shirya komawa GIDAN ARO..” Sai sann ta d’an dubesa kafin ta maida kanta wani b’angaren, d’an juyowa tai tana dubansa murmushi saman fuskarta kafin ta jinjina kai tace “Of course Inspector.. I’m super ready to carry out my next mission.. But only for Inne..” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta. D’an tsimewa yai kafin yace “Aw sabida Inne zaki yarda ki bini ba wai dan kina son bina ba.. Didn’t you miss me at all..?” Sunkuyar da kanta tai tana murmushi. Sai kuma ta girgiza kai alamun a’a. Kafeta da idanu yai sai kuma yace “Idan bakiyi kewata ba bazaki min Duka wad’ann kwalliyan ba..” Dubansa ta kumayi, sai ta murmusa kad’an itama tace “Unfortunately ba sabida kai nai ba Inspector.” “Toh sabida wa kikayi.?” Ya tambaya yana dubanta. “Inne of course..” Ta basa amsa kai tsaye. Mamaki ya cikasa ganin bataji haushi ba, yasan da da ne da yanzu hiran ya k’are yana sako mata zancen mission. Ya jinjina kai kad’an kafin yace “Ki shiga ki masu sallama we are leaving now.. Akwai yanda zamu biya.” Ta d’an d’ago tana dubansa a d’an tsorace wann karon “Da gaske kake yanzu zamu tafi..? To.. To.. Bakaci komai ba.. Should I bring something for you..?” Duk sai ta wani daburce lokaci guda. “Calm down.. I’m not hungry.. I’m ok..” Ya fad’i yana mai kamo hannayenta da zanen k’unshi ya k’ara masu kyau. Jiki a sanyaye take duban yanda ya sakale yatsun hannunta cikin nasa “I thought you said Kin shirya ma mission d’inki na gaba.. Why are you panicking then..?” Ya k’arashe yana mata wani salo cikin tafin hannunta. So take ta cire yatsun hannun nata daga nasa amma ta kasa, ga tsareta da idanunsa da yai. Saida ya tabbata ya kashe mata jiki lak’was kafin ya d’anyi gyaran murya yace “Jeki masu sallama na k’agu a fara wann mission d’in..” Gabanta ya fad’i tai saurin d’agowa tana dubansa, sai gani tai yankashe mata idanu guda “Go now.” Ya fad’i murya a hankali yana mai mata alama da idanu. Jiki a sanyaye ta mik’e ta nufi ciki yayinda Mu’azzam ya d’au wayar salulansa Tana shiga ciki maimakon ta sanar dasu d’aukanta yazo, sai ta soma masu kuka. Ta duk’a saman cinyar Umma tana kuka.. Aunty Larai ta duk’a tana lallashinta had’ida bata baki “Haba Sadiya saikace tafiyar da bazaku dawo ba, dukda duka bazaku shige sati biyu ba.. Tashi abinki kayayyakinki ma an fitar miki tintini.. Tashi kar ki b’atawa mijinki lokaci kinji koh.” Ta d’ago tana duban Umma, kwantattun hawaye ta hango cikin idanun Umman. Basu iya furta komai ba Sai rungume juna da sukai. “Allah shi maku albarka.. Allah ya tsareku daga dukkanin abin k’i ya azurtaku da zuri’a d’ayyiba.. Tashi kije Sadiya na yafeki duniya da lahira.. Allah yajik’an mahaifinki ya miki albarka..” Ta k’arashe suna masu kuma rungume juna cikin hawaye. Haka su Aunty Larai dasu Habeeb suka rakota har waje kaman kar su rabu da juna. Mu’azzam ya bud’e mata front seat ya kuma musu sallama kafin Sadiya ta shige kanta a k’asa. Nan suka d’auki hanya sun Aunty Larai dasu Habeeb suna masu waving. Tana hangosu ta mirror tana jin wasu hawayen na kuma zuwa mata. Yana hankalce da ita saidai bai furta komai ba har sukai nisa da tafiya. Hannunta dake aje saman cinyarta taji masa hannun guda akai d’aya kuma yayi amfani dashi wajen rik’e steering wheel. Zata janye taji ya d’an rik’e da k’arfi still idanunsa naga kwalta ba tareda ya dubeta ba. Babu yanda Ta iya dole haka hannunta guda ya kasance cikin na Mu’azzam dake driving da hannu guda. ** Da k’yar ta iya tashi tana murtsuke idanu, alarm d’in da Ta saka ne ma ya tada Ita dan a ranar take shirin komawa Office. Bathroom ta fad’a Tai wanka kafin ta tana drying kanta, sai lokacin ta zira Doguwar riga da hijab tai sallar asuba. Dan dama tin da Mu’azzam ya tasheta tai Sallah sai ta gudo nata d’akin tai kwanciyarta. Harda kulle k’ofa tai dan karma idan ya dawo ya shigo ya tada ita ya tambaya ko tayi sallan. Ta d’an tsuke baki tace “Haka kawai ba gashi yanzu nayi sallar ba, da ace ina can d’akinsa na tabbata da yanzu ya katse min bacci na yace lallai Lallai dole dole Sai na tashi sallah. Dik San bacci na kusanka my Halal zan iya yafe baccin safe a jikinka..” Ta k’arashe tana mai ci gaba da shirin fitarta. Nan ta duba time taga har 9:30am. A gurguje ta ida shirinta ta nufi nasa d’akin Dikda tasan by then ya tafi office. Kaman yanda tai tunani d’akin nasa tas tas kaman basu kwanta saman gadon ba.. Har Ta juya zata fice Ta dawo da baya tana duban side lamp dake kunne.. K’arasawa tai zata kashe lamp d’in nan taga drawer d’in kaman a bud’e ga wani abu kaman picture ya sako kai. Zuciyar Safeenah yai wani irin yankewa.. A hankali ta ida bud’e drawer d’in zuciyarta naci gaba da bugu.. Bata ida jin tashin hankali ba saida ta ciro hoton gaba d’aya. Halal d’inta ne da wannan ‘yariskar yarinyar a park, saikace wasu masoya fuskokinsu cikeda annashuwa.. Zuciyar Safeenah yaci gaba da tsinkewa tana tinanin kenan Mu’azzam raina mata hankali yai ko me.. Kenan ba auren mission yai da yarinyar nan ba..? Take zuciyarta ya bata amsa da fad’in dama bai tab’a ce miki ga kalan auren da yai da Ita ba.. Takarda kika tsinta wanda yarinyar ta bar masa nan kika fahimci cewa auren mission yai da Ita.. Sassauta ma kanta Ta soma da fad’in “Enough Feenah ke shaida ce Babu abinda ya shiga tsakanin mijinki da wann ‘yariskar.. Kuma ma ta iya yuwa wann dik cikin mission d’in ne.. Da ace yana tare da wann yarinyar da bai zauna dake tsawo satittika har biyu ba tareda ya tab’a miki koda zancenta ba balle ya kawo miki Ita gidanki..” Tsayuwa kuma tai tana duban hoton kafin ta girgiza kai, kaman zatai kuka take furta “Toh amma Maiyasa ya aje hotonsu haka..?” Take taji zuciyarta na bata amsa da fad’in Because he loves her. K’ara Safeenah ta saki ta shiga kekketa hoton tana watsi dashi a tsakiyar d’akin.. Tana tsaka da wann bori wayarta ta soma ruri. Mommy ce mai kiranta, rabon da suyi waya da Mommy tin randa Mommy tazo gidan tace sai Mu’azzam ya saki Safeenar. Ta d’aga wayar tana kuka.. Had’iye kukan tai sakamakon abinda Mommy Ta soma sanar da Ita “Safeenah kina ina ..?” Safeenah tace “Ina gida Mommy..” Mommy ta jinjina kai tace “Ba wannan amsar nake so ki bani ba.. Kina ina Maras mutuncin mijinki ya d’auko kishiyar ki ta bariki zai tafiya da ita..” Zuciyar Safeenah yai wani irin tsinkewa. Lokaci guda Ta shiga girgiza kai tana fad’in “A’a Mommy you must have have got this wrong.. My Halal fah baya tare da ‘yariskar can.. Dama auren mission sukai kuma babu abinda ya tab’a had’asu..” Bata kai aya ba Mommy ta katseta da fad’in “Rufe mun baki shashashar banza..!Toh ki zauna a wajen ke ga mai Halal koh. Aiko zai shayar dake halaliyar mamaki.. Gashi nan ya kawo yarinyar suna jiran Daddynki a side d’insa kuma daga nan Fufore suka nufa tare.. Ki zauna Safeenah kar kizo ki k’watar ma kanki ‘yanci..!” Daga haka Mommy Katse kiran tai tana huci. Safeenah ta soma ganin duniyar na juya mata.. Itace Mu’azzam zai mata haka..? Zai d’auki wata ‘yariska Karuwa yace zai tafiya da ita.. Kuma ma wai all this while dama suna tare..? Ta soma sakin huci tana jin k’irjinta na mata zafi.. A fujajan ta nufi closet d’insa tana dubawa nan kuwa taga alamun ya d’ibi wasu kayan yayi shirin tafiya.. Safeenah taci gaba da sakin huci.. Tasa kai zata fice sai kuma ta tsaya cak, juya ta kumayi a nan closet d’in nasa Ta hangi d’aya drawer da ya mance a bud’e wanda bindiga ce cikin drawer d’in. Cikin sauri ta duk’a ta suri bindigar ta shiga juyata cikin hannunta, lokaci guda take furta “Wllhi yau ko ni ko wann ‘yariskar.. Amma kam Tabbas yau za’ayita Ta k’are.. Ko ni ko tsinanniyar can..!” Tana ida fad’in haka Ta nufi nata d’akin ta d’auko car keys d’inta a fujajan, sai sauri take tana had’e stirs tana sakin huci, office d’in da bata je ba kenan Ta d’auki hanyar gidan Mahaifinta. ** Assad na shirin fitowa kenan yana zaune yana shan tea yaji ana masa knocking a apartment d’insa. Mamaki ya cikasa Toh waye wann mai nemansa da farar safiya. K’arasawa yai yana duba ko wanene. Da mugun mamaki yake duban Maleeka dake tsaye k’ofar apartment d’insa tana hawaye ga akwati gefenta. Ya d’an girgiza kai kad’an yana dubanta “Maleeka.. Lafiya..?” Maleeka ta kuma fashewa da kuka mai ban tausayi. Assad ya lek’a bai ganta da kowa ba, ya kuma dubanta ya dubi akwatin dake gefenta. Ya d’an kuma girgiza kai kafin yace “Maleeka meke faruwa..?” Cikin kuka Maleeka ke fad’in “Assad bani da yanda zanje.. Mai gidan da nake haya ta mun wulak’anci ta koreni.. I’ve no one to run to, savings d’ina na watan nan na tura gida wa Mamana dake jinya.. Assad please help me..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana d’ago hannayenta alamun rok’o kaman zata duk’a a k’asa. Fuzar da fuci yai kad’an kafin ya d’an matsa gefe ya bata hanya. Tin kafin ya mata izinin shiga Maleeka ta shige tana kuka. Zama tai saman kujera tana ci gaba da kuka kaman ranta zai fice. Assad ya zauna d’aya kujeran yana dubanta cikeda tausayawa. Bai hanata kukan ba saida tai mai isarta kafin ya d’anyi gyaran murya yace “Garin yaya haka Ta faru..? Kan mai zata koreki daga gidan.. Ince akwai ‘yanmata da yawa da kuke haya a gidan..?” Maleeka ta jinjina kai tace “So take ta dinga samun kud’i damu.. Maza take kawowa gidan ni kuma nak’i amincewa..” Murmushi yai a tak’aice kafin yace “Kina jami’ar tsaro har za’a miki barazana irin haka.. Haba Maleeka saikace bakisan right d’inki ba.. Ki tashi yanzu mu tafi mu filing case akanta.” Girgiza masa kai tai still tana hawaye “Assad kasan yanda al’amra suke a k’asar nan.. Duk isanka da sanin ‘yancinka idan bakada abin duniya Toh fah kai na kowa bane.. Assad matar nan da manyan k’usoshin gwabnati take huld’a ta Ina zan fara shari’a da Ita.. Ga mayafiyata last week an Aiko mun jikinta ya tsnanta da Wanne zanji da shari’ar da bazan iya ba ko da jinyar mahaifiyata..” Ta k’arashe tana kuma fashewa da kuka. Dama Iyayen Maleeka ba Abuja suke na itama aiki ne ya kawota iyayenta a can garinsu Kwara suke kaman yanda iyayen Assad suke Nasarawa Lafiya. Ya d’anyi jim yana dubanta cikeda tausayawa. Fuzar da fuci yai kafin ya mik’e ya nufi kitchen ya kawo mata mug da flask harda bread yace tasha tea. Tai masa godiya kafin ya zauna ya d’auki tea d’insa yana sha. Lokaci guda yake furta “Zamu San yanda za’ayi ki kwantar da hankalinki.. Amma zamanki a nan bazai yuwu ba, kinga dukanmu musulmai ne kuma a shari’a bai kamata mu zauna haka ba.. D’aki d’aya ke gareni nima sai parlor.. Kinga zamanki a nan bazai yuwu ba amma nasan bazamu rasa yanda za’ai a sama maki wani rent mai sauk’i ba...” Ta jinjina kai tana hawaye..” Wannan gaskiya ne.. Kuma na gode maka, banida abinda zan saka maka dashi..” Ya girgiza kai kad’an yana jin idanunsa na masa nauyi.. Lokaci guda yake furta “Kar ki damu ai yima kai ne.. Ki gama karyawa sai mu fita muga yanda za’ai..” Bai kai aya ba maganarsa ta sark’e.. Kan kace mai ya silale cikin kujerar tamkar wani sumamme. Wani irin jahilar dariya Maleeka Ta fashe dashi dan lokacin da Assad ya tashi yaje kawo mata abin karin kumallo ta zuba masa pills cikin tea d’insa.. Ta kuma murmusawa tana dubansa kafin ta soma fad’in “Da kyau Detective Assad, Sarkin taimako da tausayi.. Yanzu sai muga ta yanda zaka tsere wa makirci na..” Tana ida fad’in haka ta kuma fashewa da dariya kafin Ta isa ta janyosa da k’yar ta shigar dashi d’akinsa.. Kwantar dashi saman gado tai kafin ta shiga b’alle botiran rigarsa.. Tana gama cire masa ta cire nata tufafin itama kafin ta haye saman gadon, ta kwanta cikin jikinsa ta dinga d’aukansu pictures da wayarta.. ** A first parlorn Daddy suka zauna, bai ma soma tunk’aran side d’in Mommy da Ita ba dan yasan abin bazai wanye da kyau ba. Ya mik’e da zummar Fita.. Tai saurin mik’ewa itama tana dubansa idanunta sunyi rau rau “Ina zaka kuma..?” Ta tambaya tana dubansa. Murmushi ya sakar mata kafin yace “Ki kwantar da hankalinki nan gidanmu ne.. Babu wanda zai cutar dake..” Ta d’anyi shiru sai kuma tace “I thought kace garinku zamuje..?” Baikai ga bata amsa ba Musaddiq ya shigo da sallama. Suka gaisa da Mu’azzam yana fad’in yanzu zai shirya jirgin sai 12noon Daddy yace yana zuwa yana rounding meeting d’insa a Company ne.. Mu’azzam ya jinjina kai yace “Sai Kai sauri ka shirya kasan bana San delay.” Musaddiq ya jinjina masa kai yana mai sara masa.. Lokaci guda yakai dubansa ga Sadiya wace ta b’ace kaman bata a wajen. Ya d’an k’araso ya duk’a yana gaisar da Sadiya cikeda barkwanci yana fad’in “I’m Musaddiq Gamji.. Mijinki babban Yayana ne kuma my only confident.. Duk wata matsalata wajensa nake kawowa dukda cewa wasu lokutan yanada wuyan sha’ani.. Nasan Kinsan halin kayanki..” Murmushi kawai Sadiya take tana jinjina barkwancin Musaddiq. Janyosa Mu’azzam yai yana fad’in “Kasan banson b’ata lokaci Ka tashi kaje ka shirya kafin Daddy ya k’araso..” Musaddiq ya sara masa yana fad’in “Yes Officer.. Right away..” Lokaci guda ya shige yana murmushi. Mu’azzam ya d’an girgiza kai kafin ya mik’e da zummar ficewa. Nan itama ta mik’e tana dubansa a d’an tsorace “Are we leaving now..?” Ta tambaya kaman mai shirin yin kuka. Dan harga Allah haka kurum taji sam bata sake a gidan ba. Agogon hannunsa ya d’an duba kafin yace “Daddy zai k’araso in a bit.. Idan kun gaisa zamu wuce in sha Allah.. Ki jirani a nan Ina zuwa..” Daga haka ficewa yai cikin sassarfa. Sadiya Ta koma saman kujeran ta zauna zuciyarta na kuma yankewa yanda Kasan wacce aka kawota gidan yankan kai haka take ji.. Sai rarraba idanu take. Tana nan zaune Meema Ta shigo hannunta rik’eda tray murmushi saman fuskarta, tsaf Sadiya Ta gane Meema sune dai sukaje zasu bugeta kwanaki a GIDAN ARO.. Sannan sune ‘yanmatan da suka kuskure Ummanta da Mota.. A tak’aice dai ta gane Meema k’anwar Matar Mu’azzam ce. Tana ganin Meema ta nufota tai saurin mik’ewa tsaye dan batasan da mai tazo mata ba dukda cewa kayan motsa baki ne ta hango saman parantin dake hannun Meemar. Sannan bata mance last meeting d’insu ba. Meema tace “Kiyi hak’uri ki zauna banida niyyan cutar dake..” Tai maganar murmushi saman fuskarta tana mai dire tray d’in gaban Sadiya. A hankali Sadiya ta koma ta zauna Dikda cewa zuciyarta bai gama aminta da Meema ba. Meema Ta zauna kujeran gefenta, murmushi saman fuskarta take duban Sadiyar “Sunana Meema Gamji.. Ni cousin d’in mijinki ne Ya Mu’azzam.. Kuma k’anwar matarsa Safeenah.. Nasan kin ganeni dan ba yau bane farkon had’uwarmu..” Sadiya ta jinjina kai a hankali tana duban Meemar. Meemar ta kuma gyara zamanta kafin tace “Naga shigowarku Keda Ya Mu’azzam nace barin Zo na rok’eki Gafara akan abinda muka miki nida ‘yaruwata.. Nasan baki sanar da Ya Mu’azzam cewa ga abinda muka miki ba, dan kin sanar dashi na tabbata da mun yabawa aya zak’inta.. Dan Allah ki yafe mana..” Ta k’arashe tana duban Sadiyar. Girgiza kai Sadiya tai a hankali kafin tace “Babu komai.. Kar ki damu Ya wuce ai.. Kuma ko wacece akai mata irin abinda akai ma ‘yar uwarki zatayi fin haka.. Ni ban k’ullaceku da komai ba..” Ta fad’i a tak’ice still ba’a sake ba. Meema Ta murmusa tace “Naji dad’i sosai, kuma mun gode.. Kisha lemo mana..” Ta k’arashe tana k’ok’arin zuba drink d’in. Sadiya Ta saki murmushi kad’an tana girgiza kai “A’a a k’oshe nake.. Na gode..” Meema bata fasa zuba drink d’in ba take fad’in “A’a zaki sha wani abu.. Yau ce fa rana ta farko da kikazo gidan nan.. Kuma gidan nan gidansu Ya Mu’azzam ne..” Tana maganar tana mik’owa Sadiya glass cup d’in. Murmushi kawai Sadiya tai ta amsa tana mata godiya ba tareda ta sha ba. Tuni Meema Ta soma janta da fira. ** Mu’azzam kaw yana ficewa d’akin Musaddiq ya shige yanda Musaddiq d’in ke shirya suitcase d’insa. Yana tsaye daga gefe yana karantar Musaddiq dake ciro kaya yana linkewa yana shiryasu cikin Jaka, lokaci guda Musaddiq d’in ke jefo masa fira yana amsawa jefi jefi. “Damina ake bazaka d’auki kayan sanyi ba..?” Mu’azzam ya fad’i daga nan yanda yake jingine jikin gini hannunsa hard’e a k’irji. Jinjina kai Musaddiq yai yace “Na gode da ka tina min..” Lokaci guda ya soma ciro kayan sanyi harda huluna. Hularsa da yake son sakawa wanda bai gani bane ya sanyasa tsayawa yana tinani yana kuma duba shelf d’in hulunan nasa. Mu’azzam ya tsaresa da idanu kafin yace “Kana neman wani abu ne..?” Musaddiq ya d’anyi shiru sai kuma ya girgiza kai yace “No.. No babu komai..” Jiki a sanyaye ya mik’e yana zipping jakan nasa. Mu’azzam dake ta faman karantarsa yace “Are you sure babu komai..? You look tense of a sudden.” Murmushi Musaddiq yai yace “No babu komai.. Shall we..” Ya k’arashe yana duban Mu’azzam d’in had’ida janyo suitcase d’in nasa. Mu’azzam ya jinjina masa kai kafin suka soma takowa, wayar da ya shigo masa ne yasa Musaddiq yin gaba ya bar Mu’azzam d’in a baya yana amsa waya. ** Safeenah na k’arasowa ta hangi motar Mijinta Mu’azzam a gidan. Watau dai da gaske Mu’azzam na gidan tareda wann ‘yariskar.. Cikin huci Safeenah ta d’auko bindigar ta nufi gidan tana hure huren hanci. K’ofar side d’in Daddy data hango a bud’e ya tabbatar mata suna b’angaren Daddy kenan. Cikin huci Ta nufi sashen Daddy rik’eda bindigar. A tare Sadiya da Meema suka mik’e cikin tsananin firgici ganin Safeenah da sukai kansu rik’eda bindiga. Meema ta tare Sadiya ta shiga girgiza kai tana duban Safeenah “Addah Feenah no.. Please don’t do this.. Mai kike tunanin kinayi..?” Safeenah na huci tana duban Sadiya da takai k’ololuwa wajen razana, lokaci guda take nunata da bindigar tana fad’in “Meema ki kauce min idan ba so kike ki bi sahunta ba..!” Meema ta kuma girgiza kai tana d’ago hannu a hankali tana k’ok’arin nufo Safeenar “Addah Feenah please.. Don’t do this.. You are not a murderer.. Kar kiyi abinda zaki zo kina danasani for the rest of your life.. Please Addah Feenah..” “Komin shiru nace Meema ko na had’a dake.. Dama dukanku munafukai ne bakinku d’aya duk son mijina kuke.. Mijina is mine.. Nawa ne ni kad’ai.. Zan fara daga ita kafin na dawo kanki Mema.!” Ta k’arashe tana kuma nuna Sadiya da bindigar. Daidai lokacin Mommy ta shigo a firgice. Ta shiga girgiza kai tana fad’in “A’a Safeenah.. Mai kikeyi haka..?” Cikin zuban hawaye Safeenah ke fad’in “Wllhi sai na kasheta Mommy.. Bazan bari ta shiga tsakani na da my Halal ba..!” Ta kuma saita Ta da dindigar.. Daidai lokaci Mommy Ta soma takowa a hankali tana yunk’urin k’wace bindigar.. Buge hannun Safeenah da Mommy zatai yai daidai da harba bindigar. Mu’azzam da Musaddiq da fitowarsu kenan daga sashen Musaddiq d’in nan sukaji sautin harbi daga sashen Daddy ga motar Safeenah pake a gefe ko rufe marfin motar batai ba. A tare suka nufi b’angaren Daddy a guje. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *46* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Safeenah bata saki bindigar ba dukda rawa da jikinta keyi. Sadiya da Meema da suka tak’ure waje guda rik’eda juna idanunsu duka biyu a rintse dan basu San wa aka harba cikinsu ba. Su dai kawai sunji sautin fitan harsashi.. Muryar Musaddiq ne ya sanyasu bud’e idanunsu har lokacin suna rik’eda juna. Nan sukaga yanda harsashin ya huda jikin gini. Musaddiq ya nufo Safeenah yana fad’in “Feenah bani bindigar nan..” Nunasa tai da bindigar tana ci gaba da huci take fad’in “Don’t come near me Musaddiq.. Stay back.. Kar ka matso kusana..!” Tai maganar tana nunasa da bindigar. Daidai lokacin Mu’azzam ya nufota yana fad’in “Bai nan.. Bani bindigar nan Safeenah..!” “What if na hanaka..? Mugu kawai.. Macuci.. Maci amana..! Azzalumi.. Mai ha’intar aure... Da kai ya kamata ma na fara kafin na k’araso kan ‘yariskar da kake cin amanata da ita..!” Ta k’arashe tana saita Mu’azzam d’in da bindigar. Da rinannun idanunsa yake dubanta ba tareda yayi ko gizau ba. Shine Safeenah take gaya masa maganganu son ranta irin haka.. Ya jinjina kai still yana dubanta. Ba laifinta bane.. Laifinsa ne da ya bari taga girmansa. Cikin dakewa ya kuma fad’in “Hand me over that gun..!” Ya fad’i yana dubanta. Safeenah ta kuma girgiza kai tana hawaye, lokaci guda take furta “Bazan bada ba.. You choose between ni da wannan ‘Yariskar..” Ta k’arashe tana mai nuna Sadiya da bindigar. Izuwa lokacin zuciyarsa ta gama kai k’ololuwa wajen tafarfasa ya nufota a zafafe yana fad’in Ta basa bindigar. Saitasa tai da bindigar tana huci take fad’in “If you take one more step.. I swear I won’t hesitate to shoot you right in the head..And believe me, I mean it..!” Tai maganar sai sakin huci take tana nunasa da bindigar cikin tsananin zafin kishi wanda ya rufe mata idanu ruf bata ganin komai. Izuwa lokacin kam ya tabbatar ma zuciyarsa k’wak’walwar Safeenah ta samu matsala, ba daidai take aiki ba. Yai mata K’uri yana dubanta da idanunsa da tuni sun kad’a. Cikin huci Safeenah dake pointing nasa da bindiga take fad’in “Ka zaci Allah bazai toni asirinka bane.. Kana can ka ajiye wann karuwar a wani waje without my knowledge.. Toh Allah ya kamaka yanzu sai ka zab’a ko ni ko ita.. Idan ka cika kai Mu’azzam Gamji ne ka zab’a yanzun nan wacece zakai zaman aure da ita.. Ni Safeenah ko wannan ‘Yariskar..!” Ta k’arash still tana nunasa da bindiga. “Haka kika ce..?” Ya fad’i yana dubanta. Safeenah Ta jinjina kai tana fad’in “Eh haka nace.. You choose between us..” Tana maganar zuciyarta na k’arfafa mata gwiwa da fad’in Mu’azzam yana matuk’ar k’aunarki tinda har ya kasa sanar dake yana tare da yarinyar.. Hakan na nufin yana shakkun b’acin ranki ne.. Bazai iya rayuwa babu ke ba. Wannan ya tabbatar miki da irin k’aunar da yake miki.. Bata ida tunanin nata ba ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Na sakeki Safeenah..!” K’ara ta saki tana mai d’aura hannayenta biyu aka dai dai lokacin Musaddiq yai azama ya fincike bindigar daga cikin hannunta. Sadiya ta saki Meema ta nufo mijinta Wanda shid’inma tuni ya nufota. Rungumeta yai tana mai fashewa da wani irin kuka jikinta har lokacin bai daina rawa ba. Safeenah Ta kuma fincika daga rik’onda Musaddiq da Mommy sukai mata tana fad’in “Wllhi Mommy sai na kasheta.. Mommy kina gani My Halal ya zab’i wannan ‘Yariskar sama dani.. Wllhi sai na kasheta..” Sai ihu take tana fincika tana fad’in su saketa.. Daidai lokacin Daddy ya shigo ya tadda wann hatsaniyar. Mommy ta fashe da kuka tana salati tana fad’in “Ehh Lallai Mu’azzam ka tabbata.. Ka cika tabbatacce.. Ko mutuwa na kunyan idon uwa.. Ni tinda nake ban tab’a ji anyi saki gaban uwa ba.. Na shiga uku ni Hajara..” Ta dubi Daddy kafin taci gaba da tafe hannaye tana fad’in “Kazo kaga abinda D’an matarka ya aikata ma d’iyarka.. Ya zab’i bare sama da jininsa..” “Enough please Mommy..!” Musaddiq ya dakatar da Ita cikeda takaici. Lokaci guda yake ci gaba da furta “Aiko bai saketa ba Cikin gida biyu ‘yarki zata kasance a guda d’aya.. Kodai Ta tafi gidan Yari ko ta tafi asibitin mahaukata dan babu hankali tattare da Safeenah. Balle ma ita ta buk’aci hakan da kanta.” Safeenah ta kuma kurma ihu ta tsalle tana fad’in atafau bazata yarda ba babu wanda ya isa ya rabata da halal d’inta.. Meema ta k’araso kusanta sanda zata fice, tana duban Safeenar a yatsine. Murya can k’asa tace “Ai saidai kiyi hak’uri Addah Feenah dan Ya Mu’azzam ya zama haram a gareki yanzu kam..” Safeenah ta zabura zata kamo Meema. Tuni Meema ta fice ta basu waje. Musaddiq ya shiga karanto ma Daddy abinda ya faru yana nuna masa jikin garu yanda Safeenah ta huda da harsashi. Ya k’ara da “Daddy what Safeenah needs is a Dr.. A psychiatrist m.. Likitan mahaukata take buk’ata Daddy.. She’s not well..” Haba nan fah Safeenah ta hayayyak’osa tana fad’in lafiyarta lau sune mahaukata da suke tunanin zata rabu da Halal d’inta. Musaddiq ya girgiza kai yana mai jan gajeren tsaki kafin ya dubi Mu’azzam yace zai jirasu a Mota. Jinjina masa kai kurum Mu’azzam yai kafin Musaddiq d’in ya fice. Daddy ya dubi Mu’azzam da Sadiya wacce ke tsaye gefensa kanta a k’asa kana gani zaka fahimci har lokacin a razane take. Daddy yace “D’auki matarka ku tafi Mu’azzam kar ku rasa flight d’inku.” Safeenah Ta kurma wani irin razannan ihu tana fad’in babu yanda zasu tafi wllhi. Ta tafi a guje tana k’ok’arin rik’o Daddy dake haurawa upstairs tana fad’in “Daddy wllhi sakin k’arya ne.. Wllhi My Halal bai sakeni ba.. Mommy ce ta masa dole..” Haba nan fah Mommy ta hayayyak’ota da fad’in “Ni zaki ma sharri Ina mahaifiyarki..! Allah yasa ba ni kad’ai bace wajen.. Daidai kenan yanzu Kinga ranan zab’en namiji akan mahaifiyarki.. Gashi ya zab’i matar da yai auren bariki da Ita ya barki.. Yanzu zaki dawo cikin hayyacinki Safeenah..” Mu’azzam dai bai kuma bi takansu ba ya janyo hannun matarsa suka fice suka bar Mommy da Safeenah sai rantse rantse suke gaban Daddy.. Safeenah tana fad’in Mommy ce ta zugota tazo Mommy tana fad’in hakkin abinda tai mata ne ya kamata. A guje Safeenah tabi bayansu kaman sabuwar kamun hauka.. Mu’azzam zai shige Mota Safeenah ta rik’o rigarsa tana fad’in “My Halal.. Dan Allah kace sakin wasa ne.. My Halal you know I can’t do without you.. Please Mu’azzam kar ka tafi ka barni..!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka. Kallanta yai ya kalli yanda Ta rik’e masa riga kafin yace “A hukumance abinda kikayi za’a d’aureki akan hakan, Kinyi attempting murder.. Kin sake cin albarkacin Daddy bazan jefaki a cell ba.. Kaman yanda dama zaman auren da kikayi albarkacinsa kika ci.. Sakar min rigata.. You are not my wife..!” Yana ida fad’in haka ya finciki rigarsa yai shigewarsa Mota. Safeenah tabi motar a guje tana fad’in my Halal.. Inaa tuni motar ta fice daga gidan. Ihu ta kuma zundumawa ta nufi cikin gidan tana kuka tana fad’in wllhi sai ta bisu ta dawo da halal d’inta saidai ai duk abinda za’ayi. Zata shige Mota kenan taga Daddy tsaye gabanta ya kai k’ololuwa wajen had’e rai. “Give me the keys..” Ya fad’i yana mik’a mata hannu. Girgiza kai take tana hawaye “Daddy please ka barni na bi mijina.. Daddy wllhi sharrin shaid’an ne.. Daddy zafin kishi ne bansan abinda nake aikatawa ba.. Daddy na tuba dan Allah ka barni nabi Mu’azzam.. Wllhi mutuwa zanyi Daddy idan har ya rabu dani.. Please Daddy dan Allah ka ceceni.. Daddy I’m your Daughter please..!” Ta k’arashe tana mai duk’awa had’ida rik’e k’afafun Daddy tana kuka sosai. Abinka da d’a da mahaifi, Zuciyar Daddy ta raunana.. A hankali ya mik’a hannu ya kamo Safeenah ya tada ita tsaye.. Safeenah ta kuma fashewa da kuka tana mai fad’awa jikin mahaifinta. Bai hanata kukan ba, saida tai mai isarta kafin ya kamo hannunta suka nufi parlornsa. Zaunar Ta saman kujera yai yana dubanta cikeda tausayawa.. Shi kansa ya fara tsoron kardai Kwanyar Safeenah ya tab’u ne. Ruwa ya mik’o mata yace tasha.. Babu musu ta amsa ta kafa kanta ta shanye still hawaye na gangaro mata. “Safeenah inaso ki nastu ki nitsa hankalinki waje guda.. Safeenah da halayya irin wannan bazaki tab’a samun kwanciyar hankali a gidanki ba.. Bindiga Safeenah.. Kisan kai zakiyi akan wata ta auri mijinki..? Waye yace miki shi mijinki ne ke kad’ai.. Waye ya baki wann guarantee d’in..?!” Ya d’an k’arashe cikin tsawatarwa Safeenah batace komai ba Sai kifa kanta da tai tana hawaye. Daddy ya jinjina kai kafin yaci gaba da fad’in “Mu’azzam yana d’aga miki k’afa, yana duba girman zumunci.. Amma ba don haka ba abinda kika aikata yau da ya kulleki a gidan Yari.. Why Safeenah.. Maiysa kike nema ki haukarta da kanki babu gaira babu dalili.. Kan rayuwar duniya da k’alilance ba tabbata za’ayi ba.. Idan kikayi hak’uri wataran babu ke ko Babu abokiyar zaman taki ko ma Babu mijin da ake ta faman tada jijiyan wuya akansa.. Rayuwar duka batada yawa Safeenah.. Har yaushe zakije ki jefa kanki a halak’a sabida soyayya.. Ai so ba hauka bane Safeenah..!” Ya d’anyi fasali yana dubanta. kafin ya d’ago yatsa yana nunata “Toh ki kula.. Ki sani rayuwar duka batada yawa.. Yau idan mune gobe ba mu bane.. Idan kuma baki natsu kin daina wann haukar naki ba Ina mai tabbatar miki ni da kaina zan d’aukeki na kaiki mental facility kin jini koh..?!” Safeenah ta d’ago tana dubansa “Daddy asibitin mahaukata kuma..? Daddy wllhi da hankali na.. Kawai son mijina nake... Daddy na saba dashi bazan iya rayuwa babu shi ba.. Dan ka barni na bisu Daddy..” Mik’ewa Daddy yai yana dubanta cikin tsananin b’acin rai “Idan kika sa k’afa kika fice daga gidan nan.. Ki nemi wani mahaifin amma bani ba Safeenah..!” Daga haka Sa kai yai ya haura upstairs.. Safeenah tai mutuwar zaune tana duban mahaifinta har ya haye sama.. Wani irin sabon k’unci da kuka ne taji sun taru sun bugi k’irjinta lokaci guda.. Ta mik’e ta fice ta nufi side d’un Mommy tana kuka kaman ranta zai fice.. Saidai tana zuwa Mommy ta haura sama ta k’yaleta ita kad’ai.. Tabi bayan Mommy da sauri tana kiranta.. Ko kallo bata ishi Mommy ba balle ta tankata. Tanaji Mommy ta banko k’ofar d’akinta da k’arfin gaske ta rufe akan fuskar Safeenar. Juyowa tai ta dubi k’ofar d’akin Meema dake bud’e. Nan ta hangi Meema saman gadon tana karatun novel.. Suna had’a idanu Meema ta mik’e ta k’araso ta tura k’ofar d’akinta ta rufe.. Silalewa Safeenah tai a wajen tana kuka mai tsuma zuciya. ** Assad kaw bashi ya farka ba Sai wajajen can bayan azahar, ya mik’e ya gansa kwance a d’aki babu riga jikinsa, daga shi sai shorts.. Mamaki ya cikasa.. Yai saurin janyo rigarsa yana rufawa, yana dafe kansa da yai masa nauyi lokaci guda yana tuno abubuwan da suka faru.. Innanlillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum zuciyarsa ke iya nanatawa.. Meke faruwa..? Mai ya faru dashi. Take ya soma tuna cewa Maleeka tazo tana neman taimakonsa.. Toh ya akai ya k’are a d’aki kuma undressed.. Cikin sauri ya mik’e yana duba lokaci.. Wai meke faruwa ne..? Mai ya faru..? Tambayoyi da dama cikin zuciyarsa da ya gaza samo amsoshinsu. A fujajan ya fice parlor yana dubawa ko zaiga Maleeka a parlorn. Babu Maleeka babu alamarta saidai ga kayan karin kumallon da suka ci nan.. Cikin sauri ya suri wayar salulansa ya soma dialing layin Maleeka. Ringing d’in wayar nata yaji a k’ofar parlorn, Ya tsaya cak yana sauraro. D’ago kan da zai ya hangota ta shigo cikin parlorn muguwar murmushi saman fuskarta, Ta canza shiga wann karon cikin wasu sutura masu bayyana tsaraici. “Wai har ka tashi a baccin..?” Ta tambaya tana fari da idanu had’ida bank’aro k’irji. Shaye da tsananin mamaki kurum yake dubanta kafin yace “What really happened Maleeka..? Tell me mai ya faru..?” Yai tambayar cikin tsananin kad’uwa. Murmusawa ta kumayi tana k’ok’arin matsowa kusansa. Ya dakatar da Ita ta hanyar d’aga hannu “Don’t dare.. Don’t you dare..!” Ya fad’i cikin d’acin rai. Ta murmusa kafin tace “Idan kana son sanin komai.. Bani cell phone d’inka..!” Girgiza kai yai yace “Ke koda wasa don’t try me..” Murmusawa tai kafin tace “Ashe ka mance da wa kake tare.. Ka mance profession d’aya garemu.. I won’t say a word.. I won’t explain anything to you.. Until you hand me over your phone..!” Ta k’arashe tana sakin huci. Yana son yasan mai ya faru.. Baisan wani tuggu ta k’ulla masa ba.. Baida wani zab’i face ya mik’a mata wayar. Ta saka hannu ta fuzge wayar nasa.. Aiko nan taga ya danna record Wato zai recording conversation d’insu ya sami evidence against her. Ta katse recording d’in tana sakin murmushi “Do you think I’m that fool Assad.. You might be my senior at the police academy.. Amma a wajen aiki you are my mate.. Nasan yanda abubuwan suke gudana..” Ta k’arashe muguwar murmushi saman fuskarta. Zuciyarsa taci gaba da tsinkewa sanda Maleeka take nufosa. “Kar kizo kusana najasa kawai..!” Ya fad’i yana sakin huci.. Dariya tai kafin tace “Na yaushe kuma Assad.. Ai mun riga da Munyi Abinda Zamuyi..” Dakatar da ita yai da fad’in “K’arya kike makira fasik’a.. Nayi imani babu abinda nayi dake..!” Dariya ta fashe dashi wann karon kafin Ta dubesa tace “If I were you.. I wouldn’t be so sure..” Cikin tsananin huci Assad ke furta “Na fad’a k’arya kike munafuka..!” Ta kuma darawa kafin tace “What if I have a concrete evidenc that clearly shows ni da kai munyi abinda zamuyi.. Kamar dai haka..!” Ta k’arashe tana nuna masa fuskar wayarta hotonsu su biyu kwance saman gado babu tufafi ya bayyana a fuskar wayar. Zuciyar Assad yai wani irin yankewa.. Ya shiga gani duru duru.. Jiri na neman kaisa k’asa. Hannunsa na rawa haka ma muryarsa yake nuna hoton yana fad’in “Menene wannan.. Menene wannan Maleeka..?!” “This is our photo Darling..Making love..” Ta k’arashe tana mai kashe masa idanu guda. Girgiza kai ya soma cikeda jinjina kaidi irin na mace “What..!” Ya furta yana dubanta. Lokaci guda yaci gaba da girgiza kai yana fad’in “That’s not me in the picture.. Bani bane photoshop ne..!” Ta murmusa kafin tace “Unfortunately kai ne cikin hoton nan.. Kai bama hoto guda d’aya bane ka gansu.. Hotuna ne.. Harda videos..” Ta k’arashe tana sliding pictures d’in.. Tsananin kad’uwa had’ida tashin hankali suka had’u ma Assad. Maleeka taci gaba da fad’in “Kai jami’i ne na bincike.. Kasan hoton da aka had’a ka kuma San hoto na gaskiya kaman dai wann.. Munada na’urar da zai nuna cewa da model d’in wayar nan tawa akai hotunan nan.. Hotunan nan na gaske ne.. Kai kafi kowa sanin haka.. Sannan fuskarka da jikinka sun fito sun bayyana b’oro b’oro.. Babu wanda bazai ganeka ba cikin hoton nan koda kuwa yau ne ya soma ganinka.!” Gumi mai tsananin zafi yaci gaba da tsartsafo ma Assad.. Ya shiga girgiza kai yana nunata da yatsa “How could you.. How could you Maleeka.. Banyi niyyan komai ba face taimaka miki.. Maiyasa zaki mun haka.. Mai kike nema a wajena..?!” Ta dara kad’an kafin tace “Now you are talking detective..” Gyara tsayuwarta tai kafin ta soma fad’in “I know you don’t want this videos and pictures to go viral on social media.. Na tabbata bazakaso sunanka ya b’aci ba.. Na tabbata bazaka so ka rasa aikinka da ahalinka ba.. Harma da d’iyarka wacce take hannun matarka da kaketa fafutukan k’watota daga hannun matar taka a kotu.. Assad idan Kotu sukaga pictures da videos d’in nan Alk’ali bazai baka rik’on d’iyarka ba kaman yanda kake so.. Wait Idan ban mance ba kace mahaifiyarta Wato tsohuwar matarka batada kamun kai batada tarbiya hasalima ka kamata da kwarto ne shiyasa kuka rabu.. Kana son amso d’iyarka daga hannunta sabida zata lalata maka d’iya shiyasa kake so Kotu ta karb’ar maka rik’on d’iyarka ya dawo hannun mahaifiyarka.. Toh ina mai tabbatar maka idan Kotu sukaga wann shaida kaida d’iyarka har abada.. Sannan ita kanta mahaifiyarka zata gujeka.. Kai k’arshe ni kaina zan k’ulla maka sharrin da bazaka iya fidda kanka ba.. Dama NPF kam ka saka ma ranka an koreka an gama bayan tuggun da zan k’ulla maka.. Kai bama kora kad’ai ba zaka k’are a kurkuku..!” Duban Maleeka kurum yake yana mamakin Ta yaya mutum zai zama mugu irin haka.. Mai ya mata da tsanani da zata shirya masa irin wann gadar zare.. Girgiza kai ya soma yana fad’in “Maleeka why.. Mai na miki..?!” Yai maganar cikin rawar murya yana nuni da k’irjinsa. Maleeka ta tsefe idanu tana dubansa “Baka mun komai ba Assad.. Laifinka d’aya shine zama aminin Mu’azzam da kai.. Dole ce ta saka ni na aikata maka haka..” Ya girgiza kai hawaye na gangarowa daga idanunsa guda “Maleeka don’t do this please.. Na rok’eki.. Kar ki aikata mun haka.. Ki dubi girman Allah ki dubi girman sharrin da kike k’ok’arin k’ulla ma ran da bata San hawa ba batasan sauk’a ba.. Kar ki cutar da ran da baki da iko akanta..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya. Maleeka ta murmusa kafin tace “Babu kalaman da zakayi amfani dasu wad’anda zasu sa na fasa k’udirina Assad.. Babu gudu babu jada baya.. Wanna shine kad’ai hanyar da zan wanke kaina daga zargin da abokinka yake mun.. Ka saka ma ranka kalan taka k’addaran kenan..!” Ya girgiza kai yace “Ban fahimceki ba.. Mai hakan yake nufi.. Mai kike so nayi..?” Ta murmusa kafin tace “Inspector Gamji your best friend, your only confidant.. Ya bani Assignment cewa na nemo masa wanda yake masa zagon k’asa a CID.. Nasan kanada masaniya akan binciken da yake gameda B.A.T. Ta yuwu ma tare kukeyi tinda yanzu aikin team d’inma kuna classifying nashi.. Dan haka Ina so ka amsa laifin cewa kai kake wa Mu’azzam zagon k’asa.. Ya bani sati biyu kafin ya dawo daga tafiyar da yai na kawo masa wanene B.A.T... A cewarsa B.A.T shine Spy d’in Danger a cikin CID.. Zaka amsa laifin cewa kai kake aiki da Danger sann duk tsawon lokacin nan kai ne kake masa zagon k’asa.. Wato dai zaka amsa cewa kai ne B.A.T..” Lumshe idanunsa Assad yai hawaye masu zafi suka gangaro masa. “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!” Abinda harshensa ya iya furtawa kenan.. Fatan bakinsa suka bud’e da k’yar.. Muryarta ya kuma sinkayo tana fad’in “Zab’i ya rage Naka Assad.. Kodai ka amsa laifin ka rufawa Kanka da mutuncinka asiri ka tsare mutuncin ahalinka, harma da d’iyarka da mahaifiyarka.. Ko kuma kak’i amsa laifin na yad’a wad’ann hotuna a kafafen sada zumunta mutuncinka ya zube.. Sannan ka rasa Farin cikinka Wato d’iyarka... Sannan ka shafawa zuri’arka harma da d’iyarka bak’in fenti wanda bazai tab’a gogewa ba a tarihin rayuwa..” Daga haka Sa kai tai zata wuce.. Har Ta kai k’ofa ta dawo da baya ta aje masa wayarsa saman kujera, kafin Ta dubesa yanda yai zaune ya k’ura ma waje guda idanu, hab’arsa d’aure saman hannayensa biyu. Maleeka tace “You have 2 good weeks to decide Detective.. Kodai ka zab’i kasancewa da Abokinka ka rasa mutuncinka da d’iyarka harma da ahalinka.. Ko kuma kai confessing wa Mu’azzam cewa kai ne ke masa zagon k’asa ka tsira da mutuncinka.. Zab’i ya rage naka..!” Tana ida fad’in haka tasa kai zata Shige. Kukan kura Assad yai ya fuzgo wayarta yana k’ok’arin goge hotunan. Dariya ta fashe dashi kafin tace “Kayi a banza.. Kana abu kaman kana mance cewa inada tunani irin naka.. Profession d’aya ke garemu.. Assad nayi saving d’insu a multiple files inada su a wajaje daban daban.. Zab’i ya rage Naka... Kar ka mance kana da lokaci kafin Mu’azzam ya dawo..!” Tana ida fad’in haka ta funciki wayarta kafin ta fice zuciyarta Wasai.. Tana ficewa ta kirawo wayan Chief tana sanar dashi yanda abu ya kasance. Chief ya murmusa Cikeda k’asaita “Na fad’a miki.. Ni nasan bazaki bamu kunya ba. Yanzu bamuda sauran damuwa akan Inspector Gamji da Assad.. Shikenan mun tarwatsa abotansu.. Ina mai tabbatar miki yanzu Mu’azzam zai zamto baida tudun dafawa a CID tinda amininsa mafi kusanci dashi zai tafi gidan Kaso... Daga wann lokaci case d’in zai fice daga Zuciyar Mu’azzam idan har abokinsa mafi kusanci dashi zai zamto suspect na gaba.. Kinga cikin Sauk’i za’a k’arasa wanann jarabben case da ya tsaya mana a mak’oshi ya mana banga banga..” Ya kuma murmusawa yana fad’in “Good job Officer.. Kinsan aikinki.. Dole BAT ya baki kyauta na musamman bisa jajircewa da kikai..” Ta murmusa kad’an kafin tace “Na gode da yabo Sir.. Amma Sir Ina son sanin wanene asalin BAT.. Shin menene had’insa da case din nan..?” Murmusawa Chief yai kafin yace “Zai fi miki idan kika tsaya a nan ba tareda Kin kuma kutsawa ciki ba..” Maleeka ta d’an girgiza kai kad’an kafin tace “Har yanzu baku gama yarda dani bane.. Chief ina son sanin Wanene BAT.. Ina son sanin ma wa nake aiki..?” Chief ya murmusa kafin yace “Har yanzu dai zan k’ara shawartanki kar ki nemi sanin wanene Jemage domin kuwa bakinksa baya banbance abu mai kyau da najasa, komai ta baki yake. harta najasa ta baki yake fitarwa.. Jemage baida gaba sai baya..!” Ya k’arashe cikin tsoratarwa. Maleeka ta d’anyi jim kafin tace “Chief kana nufin BAT wai Jemage kake nufi ba abbreviation na sunan wani bane..?” Murmusawa Chief yai kafin yace “You love asking crucial questions Maleeka and you never give up akan bincike.. Ked’in material ce Babba.. Zakiyi amfani ma CID sosai da ace zaki zamto mutumiyar k’warai...” Daga haka katse kiran yai ya barta tana tinani.. Ta fuzar da fuci kad’an tana nanata kalmar Jemage. ** FUFORE.. Su Inne dasu Aunty Shemau gaba d’aya suka fito tarbansu, duk wanda ke cikin gidan ma saida Inne ta sanyasa fitowa domin a tarbi kishiyarta amaryar Mu’azzam d’inta. Ajidde ce kawai bata a wajen amma har su Mama Hindu duk sun fito. Gaban Sadiya Sai fad’uwa yake sanda suka soma fitowa daga motar. Ita da Mu’azzam ne a baya sai ko Musaddiq da driver a gaba. Tana fitowa ta hango Dattijuwar sai sakin murmushi take idanunta tarau akanta sauran mutanen na lale lale. A hankali Sadiya ta sadda idanunta k’asa sanda taji hannun Mu’azzam saman nata. Tai k’ok’arin zame hannunta amma yak’i saki.. Ta d’an d’ago idanunta ta dubesa kaman mai shirin kuka alamun ya sakar mata hannu.. Bai sakar matan ba sai ma d’auke kansa da yai alamun ta daina b’atawa kanta lokaci dan bazai cire hannunta cikin nasa ba. Babu yanda ta iya ta maida kanta k’asa. Musaddiq ya tafi da sauri ya rungume Dattijuwan yana fad’in yayi kewarta wanda Sadiya keda tabbacin cewa itace Inne. Inne ta d’an dunguri k’eyarsa tana fad’in “Toh maza kayar dani sai kaji dad’i.. Fitananne..” Musaddiq ya d’an shafi kansa yace “Haba mana Inne tarban da zaki min kenan..” Ta tsaresa da idanu tana karantar k’wayan idanunsa ko da ya tafi Abuja ya koma shan wasu abubuwan.. “Shige ka jirani zanzo na bincike ka..” Ta fad’i tana turasa kad’an. Daidai lokacin Mu’azzam da Sadiya suka k’araso.. Mu’azzam ya bawa Inne light hug yana fad’in “Nayi kewarki Inne na..” Murmushi itama tai kafin ta d’an turasa tana fad’in “Ka dank’aro mun kishiyoyi dole kace haka.. Bani waje na fara gaisawa da kishiyan tawa kafin kai.” Ta k’arashe tana mai nufo Sadiya. Sadiya tai saurin duk’awa da niyyan gaida Inne.. Saidai Inne bata bari ta isa k’asa ba ta kamota tana fad’in “A’a na yafeki.. Tashi abinki ni k’awarki ce ba kishiya ba..” Tai maganar tana mai rungumar Sadiyar. Ita kaw Sadiya daketa sakin murmushi sanne kanta tai da mayafinta jikin Inne dan kunya.. A haka Inne na rik’eda Ita suka nufi cikin gidan. Shemau ta rakasu da idanu kafin ta jinjina kai tace a cikin zuciyarta. Tirk’ashi Lallai Safeenah kinada jan aiki.. Lokaci guda ta soma dialing layin Mommy tana mai barin wajen. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *47* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A d’akin Inne aka soma mata masauk’i a cewar Inne sai Washe gari su kaita b’angarenta suyi mata rakiya kaman yanda akeyi a al’ada. Ba haka Mu’azzam yaso ba, saidai babu yanda ya iya tinda haka Inne tace. Tai wanka nan band’akin Inne Ta kuma sauya shiga cikin tufafi masu sauk’i.. Sai nan da Ita Inne take, gaba d’aya Sadiya ta gaza sakewa Dikda cewa da Innen take ta saki jikinta gida take. Mama Hindu ce ta shimfid’a mata abin sallah sanda ta ida shirin nata.. Nan Mama Hindu Ta nuna mata gabas, itama sai nan nan da ita take. Sadiya tai mata godiya cikeda risinawa kafin ta tada sallar isha. Ruwan sama na kuma b’arkewa kaman da bakin k’warya. Mama Hindu ta fito ta nufi d’akin Aunty Nuratu tana fad’in yau Ajidde batai mata sallama ba ta tafi.. Kicib’is sukai da Ajidde ta fito daga waje ruwa ya jik’ata shakaf rungume da gwaiba cikin hijabinta. Mama Hindu ta saki baki tana duban Ajidde da tsananin mamaki “Ke Ajidde Wai dama baki tafi gida ba.. Toh ina kika tsaya..? Jibi yanda ruwa ya miki lilis..” Tai shiru tana duban Ajidde dake rawan d’ari.. Sai kuma ta girgiza kai tana duban ‘ya’yan gwaiba data jido. Mama Hindu Ta girgiza kai tace “Yanzu tsayawa tsinkar gwaiba kikayi a ruwan nan ga duhun dare Ajidde.. Kar dai ma bishiya kika d’ale a daren nan..?” Ajidde tana tura ‘ya’yan gwaibanta jaka take fad’in “Yo ai ba tsinka nayi ba a k’asa na gansu sun zurzubo.. Kuma ai Inne tace ko mai nake so na tainka kayana wanda bazan iya ba nace a tsinkar min..” Mama Hindu ta girgiza kai tace “Toh amma kinji ruwan da ake tsulawa kuwa.. Waima ya akai yau kika makara ne..?” Ajidde ta dubeta sai kuma ta lek’a waje tana ganin ruwa na kuma zuwa kaman da bakin k’warya. K’arasawa tai Ta zauna dirshan a wajen ta fara sunbatu kaman na mai kuka “Ni wllhi bansan dare yayi haka ba.. Kuma wllhi gwaiban sunada yawa a k’asa ne shisa na bisu d’aya bayan d’ayan ina tsintarsu.. Wllhi su suka jamin.. Na shiga uku Mama Hindu dan Allah ki kaini gida..” Mama Hindu ta girgiza kai tana jinjina shiriritar Ajidde.. Daidai lokacin Inne ta k’araso an Ta jiyo kaman kukan Ajidden. “A’a Ajidde lafiya.. Ya na ganki haka..? Meke faruwa..?” Cikin kuka take fad’in “Inne ai ke kika ce duk bishiyar da nake so na tsinka.. Shine na kad’o gwaiban nan suka zubo da yawa dama tin da ake hadari suke zubowa a k’asa shine na bisu ina tsintarsu ashe Wai dare yayi kuma anata ruwa...” Ta k’arashe tana goge hawayenta. Inne ta murmusa tace “Daina kukan toh.. Goge hawayenki zan saka Shemau ta kira min Innan taki a waya sai na sanar da ita ruwa ya tare ki zaki Kwana nan..” Ta dubi Mama Hindu tace “Ta canza kayan nan nata ya jik’e gaba d’aya.” Mama Hindu Ta jinjina kai tace “Shirirtar Ajidde nada yawa ai Hajiya.. Yo ni gidan nan ma bansan kayan waye zai mata ba..” Sadiya dake tsaye gefe wacce itama kukan Ajidden ne ya fito da ita nan tace “Kayana zasu mata..” Tai maganar tana duban Ajidde wacce ta dakata da goge fuskarta tana duban Sadiyar. Murmushi saman fuskar Sadiya wacce duba guda tai ma Ajidden taji ta kwanta mata, dukda zancen shiriritar da taji tana yi. Inne tace “‘Yar nan ayi haka daga zuwanki..” Murmusawa Sadiya ta kumayi kafin ta girgiza kai tace “Babu komai Inne bara na d’auko mata.” Inne Ta saki murmushi tana duban Sadiya da ta shige d’aukowa Ajidde kaya kanta a k’asa tana gyara zaman mayafinta. Tana shiga d’akin Inne taji an janyota Ta fad’a jikin mutum. Ware idanunta tai tana shirin kurma ihun itama. Nan ta gansa hasken k’wan wutan lantarki ya Haske masa FUSKA tarau.. Yayi wanka ya sauya shiga shima zuwa wasu tufafin ruwan toka, wando mai Laushi irin na sanyi mai kaman roba a k’asa sai rigar itama ruwan toka mai d’aukeda tambarin Adidas wacce itama ta sanyin ce mai dogon hannu saidai bata cika kauri ba. Sai ni’imtaccen scent d’in Blue De Chanel dake tashi jikinsa. Tai narai narai da idanu tace “Inspector ka razane ni.” Tsareta yai da rikitattun idanunsa yana duban shigar data sauya zuwa wata Maroon Dubai gown marar hayaniya mai laushin gaske wanda ya amshi fatarta, ta yane sumarta da mayafin kayan Wanda shima kalan Maroon ne. Ta masa kyau har ta gaji.. Shi data wanke kwalliyar ma sai yaga tafi masa kyau sosai.. Fatarta data sha gyara Sai k’yalli da sulb’i yake. Janyota yai cikin jikinsa yana fad’in “You look beautiful..” Yai maganar murya a d’an dashe ba tare da ya janye idanunsa daga kanta ba. Gabanta ya d’an fad’i, Ta soma k’ok’arin zame jikinta tana fad’in “In..Inspector.. Inne tana jirana.. Aike na akai..” D’aya hannunsa yai amfani da ya kuma shigar da ita jikinsa kafin yace “Yaushe kika zama ‘yar gida da har aka fara aikenki..?” Ta d’an rausayar da idanunta kafin Ta tab’e baki kad’an tace “Bakada labari Inne ta bani certificate na zama cikakkiyar ‘yar gida..” Ta k’arashe cikin dabara tana mai son zamewa daga rik’on da yai mata.. Wannan karan gajeren murmushi ya saki da gefen bakinsa still idanunsa akanta.. Bata ida zame jikin nata ba taji ya kuma juyar da ita ya rungumeta ta baya.. Bugun zuciyarta ya k’aru.. Ta lumshe idanunta a hankali.. Cikin rawar murya take fad’in “Dan Allah kayi hak’uri.. Aike na fah akai.. Yanzu idan aka shigo aka ganmu haka fah.? Tamkar zata fashe masa da kuka haka tai maganar. Hab’arsa ya d’aura kad’an saman kafad’arta guda yana kuma shak’an daddad’an k’amshin dake tasowa daga cikin jikinta, idanunsa a lumshe yake furta “This is my grandma’s room babu mai shigowa..” “Toh idan Inne ta shigo fah..?” Ta kuma fad’i kaman zatai kuka. Hannunsa taga ya mik’a saman switch na wuta ya kashe wutan d’akin. Cikin tsoro take furta “Na shiga uku.. Inspector what are you doing..? Dan Allah ka barni naje zasu gaji da jirana..” Bai bari takai aya ba ya rufe bakinsa da nata.. Wata rayuwa ce da bata tab’a tsintar kanta ciki ba, tsantsan k’aunarsa yake nuna mata wanda bata tab’a koda hasasho su biyun a irin wannan duniyar ba. Saida ta sakar masa kuka kafin ya k’ok’arta ya saketa. Ya kunna switch d’in wutan yana dubanta yanda take share hawayenta. Hannayenta ya kuma janyowa kafin yace “Ke kikace kar a ganmu shisa na kashe miki wutan.. Kuma na mance you are afraid of the dark..” Ta d’an dubesa kad’an kafin tasa kai zata shige.. Yai saurin kamota yana fad’in “Wait tsaya mana.. Kinyi fushi ne..? Idan kika fita haka Inne zata fahimci mai kika tsaya yi a d’akinta gwara ma ki sake wann fuskar taki..” Ta mak’ale kafad’a ba tare tace komai ba still baki a ture. Ya d’an kauda kai kad’an yana murmushi kafin ya maido da dubansa gareta “Ok tell me meye aikan sai na kaiwa Inne kar Ta ga fuskarki da hawaye..” “Idan ma Ta gani zan fad’a mata abinda kayi ne.. Kuma ma ai ba kai ta aika ba..” Ta basa amsa kai tsaye. Sosai ta basa dariya amma sai ya d’an gimtse yace “Ok shikenan.. D’auki aikan ki kai mata ina jiranki a nan zamu je ki gaisa da Mamy..” Ya k’arashe yana mai fitowa Parlorn Inne. Zama yai nan kan kujera yana jiranta. Yayinda Sadiya ta k’arasa ma’ajiyan kayanta jiki a sanyaye jin yace zasuje ta gaisa da mahaifiyarsa. Har Ta fita ta kaiwa Ajidde kayan yana nan zaune saman kujera yana duba wayarsa. K’afarsa d’aya bisa d’aya. Sarai yaji dawowarta amma yai kaman baiji ba. Tai tsaye gefe tana jiran mai zaice, shiru baice komai ba.. Ta d’an Langab’e kai kad’an cikin zuciyarta tana fad’in mai hali baya canzawa. Bata ida tinanin ba taga ya mik’e yana zira wayarsa a aljihu. Ya d’ago yana dubanta sai ta sadda nata kan k’asa. Hannunta guda ya kamo ba tareda ya furta komai ba, nan ta shiga bin bayansa kaman rak’umi da akala. Tin daga k’ofar d’akin take jin bugun zuciyarta na ninkuwa.. Wani irin yanayi mai kaman tausayi had’ida rauni sun taru sun cika zuciyarta. Tasan mahaifiyarsa batada lafiya amma bata tab’a ganin yaya jikin mahaifiyar tasa yake ba. A hanya suka had’u da Mama Hindu tana fitowa.. Suka gaisa da Mu’azzam yana tambayarsa mahaifiyar tasa. Mama Hindu tace tana ciki yanzu ta ida mata shirin bacci. Ya jinjina kai kafin ya kuma janyo hannun Sadiya suka shige. Fuskar matar ta soma hangowa kwance saman gado, Fuskar tata tayi Haske sosai irin na wanda ya jima yana jinya. K’afafunta a mimmik’e gwanin ban tausayi.. Baka ganin komai a fuskar nata sai dogon hanci da kwarmin idanuwa alamun jinya Yaci rabonsa.. Ya Allah ka azurta majinyatanmu da lafiya ka k’ara mana lafiya da zaman lafiya a cikin al’umman musulmi. Hawaye ne taji sun ciko idanunta tab.. Ta tina cewa wannan matar da take kwance babu abinda take nema face lafiya.. Da za’a ce ta bada komai nata dan ta sami lafiya zata bayar.. Ina kai da kake da arzikin lafiya shin mai ka aikata da wannan lafiya da Ubangijinka ya baka..? Shin ka tab’a tambayar kanka lafiyar nan zuwa wane lokaci aka ara maka..? Shin ka tab’a hisabi ma kanka cewa mai ka aikata da wannan ni’ima na lafiya da Ubangiji ya baka..? Shin kasan mutane nawa ne suke buri da fatan su sami lafiya irin naka domin Su bautawa mahaliccinsu da ita.. Allahu Akbar Tabbas Lafiya itace babbar arziki da Allah zaiyiwa Bawa, kuma babu arzikin da ya kaita.. Ina kake mai kukan Allah bai baka arzikin gidan duniya ba, ka sani idan Allah ya baka arzikin lafiya ya gama baka babban arziki wanda mutane da dama Sun saka arzikinsu domin su sameta kuma basu sameta ba. Ina kake mai burin tara abin duniya ka sani idan babu lafiya arzikin da ka taran ma bazaka ji dad’inta ba..Lafiya uwar jiki aka ce babu mai fushi dake.. Idan an d’auke maka ita jarabawa ne.. Haka idan aka Barka da ita duk cikin jarabawa ne.. Allah ka bamu jarabawar da zamu iya ci a rayuwa Ameen. Muryar Mu’azzam Ta sinkayo yana furta “Queen Mother.. She’s my Mum.. My Mamy.. My sunshine.. My Happiness.. My everything..!” Ya d’an sassauta muryarsa kafin yaci gaba da fad’in “Na rasa jin kalamanta masu taushi da dad’in sauraro sama da Shekaru goma sha biyar.. Kunnuwana sun d’auki lokaci mai tsawo basu jiyo albarkan da take saka ma rayuwata ba..” Ya d’an murmusa kad’an still idanunsa akan mahaifiyarsa kafin yace “Do you know, my Dad used to say she cooks the best food.. Sann tanada kalamai masu taushi da zak’i saman harshenta..” Muryarsa ya d’an sark’afe yana k’ok’arin maida k’wallan dake k’ok’arin ciko idanunsa.. “Nayi kewarta sosai.. In fact nayi kewar ahalinmu sosai.. It seems ni kad’ai nai saura cikinsu.. Babu Daddy babu Ikram.. And Mamy tana nan ne tamkar da bata nan.. tana kwance cikin jinyar da Batasan a yanda take ba shekaru goma shabiyar.. An gwada magunguna da dama amma Allah bai mufa za’a dace ba..But Alhamdulillah ala kulli halin shine abinda zamu ce.!” Ya k’arashe yana mai d’aura hannunsa guda saman na mahaifiyarsa. Sadiya ta saka mayafinta ta goge hawayen da suka zubo mata cikeda tsananin tausayinsa. Tabbas idan kaga mutum kar kayi garajen yi masa hukunci dan baka San mai yake going through a rayuwa ba. Watak’ila matsalar da yake fuskanta bazaka iya d’aukan kwatankwacin sa ba idan aka aza maka. Ji yai hannunta guda ya sauk’a saman nasa hannun dake d’aure kan na mahaifiyarsa.. Ya dubi hannayen nasu d’aya bisa d’aya. Nasa saman na mahaifiyarsa saiko na matarsa sadiya da ta aza saman nasa hannun. Ya d’ago yana duban fuskarta da hawaye ke gangarowa. A hankali ta soma fad’in “Allah baya d’aura ma rai abinda bazata iya ba. In sha Allah zata sami lafiya.. Kar ka yanke tsammani daga rahamar Ubangiji kaji.. Da izinin Allah zata sami lafiya ta zamto Tamkar bata kwanta jinyar nan ba.. Muyi fatan jinya ya zamto mata kaffaran kura kurai kaji..!” Tana maganar hawaye na gangaro mata cikin yanayin muryar mai tsananin rauni. Ya jinjina mata kai a hankali yana mai sakin murmushi “In sha Allah..!” Ya furta yana duban idanunta kafin ya d’ago d’aya hannunsa ya shiga goge mata hawayenta. Yana goge mata hawayen yake fad’in “Kinsan cewa itace sanadiyar had’uwarmu..?” D’an duban fuskarsa tai tana mai son Ganin k’wayar idanunsa. “Kace Itace sanadiyar had’uwarmu.?” Sadiya ta tambaya tana dubansa dikda cewa shid’in ba cikin idanunta yake duba ba fuskarta yanda yatsun hannunsa ke sauk’a yana goge mata hawayen nan yake duba. A hankali ya jinjina mata kai kafin yace “Nayi alk’awari wa Mamy cewa matuk’a Ina aikin D’ansanda zan zak’ulo wanda duk ya kashe mata d’iyarta Ikram da izinin Allah.. A ta dalilin binciken mutuwar Ikram na had’u dake har ta kaimu ga aure.. Kinga Mamy tana cikin sanadi.” Ya k’arashe yana mai sauk’e k’wayar idanunsa cikin nata. Ta janye nata idanunta daga barin duban nasa tana mai sakin murmushi a hankal. Murmushin shima yasaki kafin ya maido da dubansa ga mahaifiyarsa. Ya kuma rik’e hannun mahaifiyar tasa dake bacci cikin nasa kafin ya soma fad’in “Mamy.. Ga d’iyarki na kawo miki ku gaisa..” Sai ya d’anyi fasali ya karkato yana duban Sadiya. Lokaci guda yaci gaba da furta “Although She’s the most stubborn person I’ve ever met.. Ko cikin mutanen da nake gwagwarmaya dasu a interrogation room, ban tab’a cin karo da stubborn person irinta ba..” Ji yai ta mintsili hannunsa dake cikin nata. Ya d’an saki k’ara yana dubanta yanda ta firfito da idanu waje. Lokaci guda take girgiza masa kai kafin tace “That’s not true..” Ta fad’i kaman zatai kuka. “Ok nayi shiru kar na fad’a..? Baki so Mamy taji halin ‘yar nata ne..?” Tai narai narai da idanu had’ida mak’e masa kafad’a alamun a’a. Yai intertwining yatsun hannayensu kafin yace “Bribe me idan baki so na fad’a mata..” Ta zaro ido waje tace “D’an sanda da karb’an cin hanci da rashawa..?” Tai maganar a hankali kaman mai tsoron kar Mamayn ta jita. Ya kashe murya kad’an shima kafin yace “Believe me this one is allowed..” Ya fad’i yana kashe mata ido guda. Hakan yayi daidai da shigowar Inne sallama saman bakinta. Suka amsa mata sallamar Sadiya na cire hannunta daga nasa. Ta gyara zamanta sosai daga nan yanda take zaune gaban gadon Mamy. Inne ta k’araso tana tambayarsu ko Mamyn tayi bacci. Mu’azzam ya bata amsa da fad’in tayi bacci ai. Inne ta jinjina kai kafin ta dubi Sadiya da ta sadda kanta k’asa lullub’e da mayafi sai kuma ta dubi Mu’azzam tace “Zata kwana wajena gobe idan Allah ya kaimu da yammaci a kaita d’akinta kaman yanda aka saba a al’ada.. Ba wani taro za’ai ba duba da yanayin jikin Nuratu.. ‘Yan uwa k’alilan ne zasu mata rakiya zuwa d’akinta kaji koh..” A hankali ya furta “Toh Inne..” Kana jin yanda ya amsa kasan a dole ya amsa hakan. Inne ta dubi Sadiya tace “Tashi maza kije koh.. Idan kina son wani abin ki fad’awa Hindu kinji koh.. Ki saki jikinki nan gida ne kinji koh..” Sadiya ta sadda kanta tana mai amsawa da “Toh Inne..” Tana tafe yana binta da Kallo har ta b’acewa ganinsa. Inne na hankalce dashi. Ganin Inne shi take duba ya d’an sanyashi sosa kai kad’an. “Mu’azzam..” “Na’am Inne..” Ya amsa yana dubanta dan tinda yaji batace Modibbo ba ta kirasa da sunansa kai tsaye yasan magana ce mai girma zata masa. Inne ta juya ta nufi parlor tana fad’in “Biyo ni muyi magana.” Babu musu ya mik’e yabi bayanta. A nan parlorn Aunty Nuratun suka zauna, Inne ta tsaresa da idanu. Ya d’an sadda kansa kad’an ba tareda yace komai ba. “Magana nake so muyi kan Safeenah..” Yanajin ta ambaci Safeenah a ransa yace anzo wajen. Inne taci gaba da fad’in “Safeenah ta kirani tana kuka.. Kasan bana d’aukan shashashancin Safeenah amma abinda ta sanar dani cikin waya ya matuk’ar d’aga mun hankali had’ida bani mamaki.. Mu’azzam kana cikin hankalinka zaka furta kalmar saki wa matarka kuma ‘yaruwarka a cikin gidan Mahaifinta.. Gaban mahaifiyarta da kowa nata dan kawai kayi sabon aure..? Babu wanda zai hanaka aure kuma babu wanda zai hanaka d’aukar matarka ka tafi da Ita yanda kake so.. Amma Safeenah tace mun kan kawai tace itama sai ta biyoka shine ka furta cewa ka saketa saikace wata ‘yar tsana.. Haba Mu’azzam saki fah ba k’aramin abu bane.. Ba’a wasa da saki.. Cikin gidan nan kaf wa kaga ya taso yana haka.. Mu ba’a mana wannan shaida ba. Mata hak’uri ake dasu, sabida Kai namiji ne tinanin ka da nasu ba zaizo d’aya ba. Sannan koda mace ta buk’aci saki bazaka biye mata ba.. Dan idan aka biye na mata sai a sakesu sau d’ari musamman idan akan kishiya ce.. Modibbo kishi nada matuk’ar zafi wanda ba Don Allah ne ya hukunta hakan ba kanajin akwai macen da zata amince mijinta ya zauna da wata ce.. A al’amari irin na aure dole a kula da irin haka musamman duba da yanda Kayowa Safeenar wata mata a tsakanin k’ank’anin lokaci.. Banji dad’in abinda ka aikata ba kuma ban amince ka aikata hakan ba saida nasa Safeenah ta bani Hajara a waya ta sanar dani K’warai anyi haka dan kasan bana yarda da wautan Safeenah..” Ta k’arashe cikin b’acin rai. Tinda ta fara magana kansa ke a k’asa. Saida ya bari ta ida kafin ya d’ago yace “Inne kiyi hak’uri.. Nasan bakiji dad’i ba kuma banso Labarin ya riskeki a irin haka ba.. kiyi hak’uri Inne..” Ya k’arashe cikin kwantar da murya. Lokaci guda yaci gaba da fad’in “Inne basu sanar dake gaskiyar abinda ya faru ba.. Quite alright na saki Safeenah amma basu sanar dake yanda al’amarin ya kasance ba..” Inne ta dubesa a d’an karkace kafin tace “Watau dai da gaske dai kayi sakin..” Mu’azzam ya jinjina kai a hankali kafin yace “Nayi amma ba wancan dalilin da Safeenah ta sanar dake bane ya sanyani yin sakin.. Inne ban saki Safeenah dan nayi wani aure ba sann ban saketa dan zan d’auko Sadiya na taho da ita nan ba..” Inne ta katsesa da fad’in “Kana nufin k’arya sukai maka kenan..?” “Kusan haka Inne..” Inne ta girgiza kai tace “Wai meke faruwa ne Modibbo..?” Mu’azzam ya gyara zamansa kad’an yana fad’in “Ni banso kiji wann labarin ba.. Dan nasan zai tada miki hankali ne kawai.. Amma tinda ita Safeenar ita ta kiraki ta sanar dake, kuma hakan na nufin ita ta zab’i kiji, zan sanar dake duk abinda ya faru Inne..” Inne ta gyara zama tana saurarensa. Tiryan tiryan Mu’azzam ke karanto mata dik abinda ya faru.. Tin daga kulle masa k’ofa da Safeenah tai wanda hakan ya hanasa shiga ya sanar mata tafiyar nasa balle yai mata sallama, har d’auko bindigarsa da tai taima Sadiya barazana da rayuwarta harde da munanan kalaman da ta dinga ambatonsa dashi har dai zuwa harba bindigar jikin garu da Safeenah tai zuwa zab’i data basa tsakaninta da Sadiya.. Ko abu guda bai b’oyewa Inne ba sai zuwan Mommy gidansa da tai tace sai ya saki Safeenah shine kawai bai sanar da Inne ba dan har wannan lokaci Kallon Uwa yakewa Mommy dan yasan ko mai Mommy zata masa bazai tab’a biyan d’awainiyar da sukai masu ba daga ita har Daddy musamman akan mahaifiyarsa. Sam baijin zai iya tozarta Mommy koda mai zata masa. Inne da take jin abun, shaye da mamaki take dubansa “Safeenah tace da bindiga zata harbi mutum..?” Mu’azzam yai shiru baici komai ba dan dama ba’a sanar da Innen ba lokacin da aka kama Safeenah ta zama suspect na mutuwar Ikram. Inne taci gaba da fad’in “Ikon Allah.. Abu kaman a cikin shirin wasan kwaikwayo... Kuma waima duk Ina shi Marwan d’in ake wann rashin hankalin cikin gidansa..?” Mu’azzam ya girgiza kai yace “Daddy baya gida shima dawowa yai ya tadda al’amarin..” Inne ta jinjina kai tace “Yanzu a gidan Marwan ake wannan rashin hankalin.. Ita Safeenah ba’a wauta ta tsaya kawai ba abin nata harda hauka ne..? Wann ai Ba abin yin shiru bane abin a nema mata magani ne dan batada hankali bamu San mai zata aikata gaba ba..” Mu’azzam ya girgiza kai yace “Inne da hankalinta tasan abinda take.. Attention take nema as always.” Inne ta jinjina kai tace “Eh Lallai.. Safeenah da harba bindiga..?” Tai maganar tana kuma jinjina lamarin. Sauk’e ajiyan zuciya yai kafin yace “Inne ki kwantar da hankalinki komai ya shige.. Safeenah bazata sake barazana ma wani da bindiga ba.” Tsegege take dubansa kafin tace “Idan aka barta gaba sakewa zatai, zan kira shi Marwan d’in naji wani mataki ya d’auka kan haukar Safeenah.. Asibitin mahaukata zai kaita ko ajeta zai a gidansa.. Dan idan a gidansa zai barta gwara ya kawo mun ita nan a sakata a mari da turu ehe..!” Girgiza kai Mu’azzam yai yace “A’a Inne kar ki kira Daddy please, nasan yanzu haka bayan abinda Safeenah tai gaba d’aya hankalinsa ba’a kwance bane.. Banso hankalin Daddy ya kuma tashi.” Ta tsaresa da idanu kafin ta murmusa kad’an tace “Kai da Marwan kuna matuk’ar son juna.. Ina Farin ciki da matuk’ar alfahari da hakan.. Badon bansan mai ke rufe cikin zuciya ba da Sai nace kai kafi soyuwa a gareshi sama da nasa yaran.” Musaddiq dake k’ok’arin shigowa parlorn fasa shiga yai sakamakon abinda ya sinkayo Inne na fad’i.. Tabbas gaskiya ne. Daddy yafi son Mu’azzam sama dasu.. Jiki a sanyaye Musaddiq ya koma da baya ya fasa shiga. D’aki Musaddiq ya koma yana duban kansa jikin mirror lokaci guda yake furta “You are a monster Musaddiq.. Dole Daddy yafi son Mu’azzam.. Dole kowa yafi son Mu’azzam.. Sabida kai ba komai bane face Monster.. Monster.. Monster..!” Ya dinga nanatawa yana duban kansa cikin madubi. A hankali ya silale ya zauna saman gado zuciyarsa na masa tsananin k’una. ** Sadiya da Ajidde ne zasu kwana wajen Mamy dan dama Mama Hindu ke kwana da ita, yau da Ajidde zata kwana sann ga Sadiya ma ta nuna kwad’ayin kwana wajen Aunty Nuratun Sai Mama Hindu ta k’yalesu su kwana wajen Aunty Nuratun. Mu’azzam baisan Ajidde na gidan ba, baima San zata kwana gidan ba.. Yadai san matarsa Sadiya zata taya mahaifiyarsa kwana na ranan. Hakan yasa ya saci k’afa ya nufi d’akin Mamy. Da wayarsa ya haska ya ganota kwance gefen k’afafun Mamy idanunta a lumshe. Duk’awa gefenta yai yana hura mata iska kad’an a kunne. Ta Ware idanunta a d’an firgice kaman mai shirin kurma ihu. Saurin rufe mata baki yai da hannunsa guda kafin yace cikin sigan rad’a “Hey it’s just me.” Ta d’an ture hannunsa kafin tai sauri ta kunna side lamp da bai cika Haske ba. Ta saci kallon Mamy kafin tai k’asa da murya tace “What are you doing here..?” “Isn’t it obvious.. D’aukan ki nazo nayi..” Ta girgiza kai kad’an kafin tace “Ka mance yau da Mamy zan kwana tashi ka fice before Mamy opens her eyes..” Tai maganar tana k’ok’arin turasa. “Hey relax bazata tashi ba.. Beside zan dawo dake.. Hira kawai zamuje ki tayani.. I’m bored I couldn’t sleep..” Ta girgiza kai tana fad’in “Nak’i wayon.. Dan Allah ka tashi ka fice kafin wani ya ganka.. What if Inne ta shigo taga bana nan..!” Tana maganar k’asa k’asa tana turasa. D’aukanta yai Cak cikin hannunsa yana fad’in “I promise Zan dawo dake kafin Inne tai noticing baki nan..” Bai Kai aya ba sukaji an bud’e k’ofar bathroom, shaff Sadiya tama mance tare da Ajidde suke a d’akin toilet ta shige kafin Mu’azzam ya shigo d’akin. Wani irin razannan k’ara Ajidde ta saki ganin alamun mutum tsaye sabida hasken dim night lamp dake kunne. Tana iya ganin alamun mutum tsaye. Ajidde ta shiga ihu tana tsalle tana fad’in “Wayyo mun shiga uku b’arawo b’arawo..!” Cak yai tsaye yana dubanta ba tareda ya ije Sadiya dake cikin hannunsa ba yana mamakin mai wann mahaukaciyar yarinyar take d’akin mahaifiyarsa. Ai kuwa kan kace mai Inne dake sallah ta jiyo ihun Ajidde dake neman d’auki.. Mama Hindu ma da baccinta bai nisa ba ta jiyo ihun Ajidde daga d’akin Aunty Nuratu.. Kai kan kace mai Ajidde ta tada gidan da ihunta.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *48* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Inne ce ta soma shigowa Mama Hindu na biye da ita, har lokacin Ajidde bata daina tsalle tana ihun b’arawo ba. Tinda Sadiya taji shigowar su Inne tai saurin zame jikinta ta silale saman gado Ta lumshe idanunta tamkar mai bacci. Babu halin ya fice gasu Inne sun shigo sun tare k’ofa. Inne tace “Lafiya Ajidde meke faruwa..?” Ajidde taci gaba da tsalle tana nuna mata alamun mutum da ta gani tsaye kusan gadon Aunty Nuratu. Tana fad’in “Inne kin gansa can lab’e wllhi b’arawo ne.” Cikin sauri Inne ta danna switch na wuta, Haske ya gauraye cikin d’akin.. Mu’azzam suka hango yasha mur sosai yana aikawa Ajidde wani irin razannan kallo. Ajidde ta zaro idanu waje had’ida kame baki. Tana nanata ta shiga uku cikin zuciyarta. Mama Hindu ta girgiza kai kafin ta janyo Ajidde tana fad’in “Shige muje..” Ai babu musu Ajidde Ta bita kaman rak’umi da akala. Sadiya kaw da idanunta ke lumshe sai danne dariyarta take. Aka bar Mu’azzam da Inne tsaye nan wajen. Inne ta girgiza kai tace “Kar kace min komai.. Zo ka shige..” Ta k’arashe tana nuna masa k’ofa. K’wafa yai kad’an cikin zuciyarsa yana furta sai ya taka yarinyar nan kafin ta daina shiga hidimarsa. Suna fitowa parlor Inne ta tsaresa da idanu, tauna leb’en bakinsa na k’asa yai kad’an kafin ya soma fad’in “Inne yarinyar nan fah ba mai hankali bane.. Kan mai za’a barta Ta kwana da Mamy.. Yaushe ma ta fara kwana gidan nan.. What if haukarta ya tashi taje taiwa Mamy wani abin..” “Rufe mun baki.. Kai mai ya kaika d’akin..?” Inne ta tambaya tana tsaresa da idanu. Shafa kansa yai kad’an kafin yace ya soma ‘yan kame kame. Girgiza kai kad’an Inne tai kafin tace “Zo ka fice Allah ya bamu alkhairi.. Gobe in sha Allah za’a kai maka ita..” Tana ida fad’in haka ta janyosa ta turasa waje had’ida janyo k’ofar ta rufe. A b’angaren Ajidde kaw suna zuwa d’aki Mama Hindu ta sanyata gaba da fad’a “Ke Wai bazaki natsu na sai kin ja ma kanki wahala koh.. Kin masa na farko ya janye idanu bai miki komaiba, baki daddara ba shine yanzu ma kika sake tara masa jama’a a karo na biyu koh..?” Ajidde Ta girgiza kai tace “Wllhi Mama Hindu Allah shine shaidata ban San shi bane tsaye wajen.. Kuma Ai ko kece kiga mutum haka dole ki razana.” Ta k’arashe kaman zatai kuka. Mama Hindu ta girgiza kai tace “Allah dai ya yaye miki wann shiririta naki Ajidde.. Mijinki nada jan aiki.. Maza nemi waje ki kwanta a nan..” Ta k’arashe tana mai nuna mata wajen kwanciya. Jiki a sanyaye Ajidde ta kwanta tana tunanin gamuwarsu da Mu’azzam dan tasan wnn karon irin kallon da taga ya mata Allah ne kawai zai ceceta. ** Washe gari kaw sassafe ta fito zata je gida tazo da magani. Tana tafe tana sand’a kaman b’arauniya sai waige waige take.. Kaman daga sama taji ance “Ke.!” Tai saurin juyowa a razane tana duban yanda ta jiyo muryar. Zuciyarta yai wani irin yankewa sakamakon hangosa da tai tsaye bayanta yana sanye da tracksuit alamun morning jugging ya fito. Jikinta ya d’auki rawa ganin yanda ya had’e rai sosai yasha mur. “Ni sa’anki ne..?” Ya tambaya yana dubanta Tai saurin girgiza kai alamun a’a. Sai kwantar da kai k’asa take tsaban tsoro. Yai mata K’uri yana dubanta, take ya tuna farkon zuwansa da ita ya soma had’uwa har taso masa sata sai yanzu kamanninta na wancan ranan ya bayyana masa.. Wato Ta jima tana shiga huruminsa since day one.. Ya zama dole ya taka mata Burki ta yanda nan gaba hanyar da yabi cikin gidan saidai Ta kaucewa wann hanyar. “D’ago kanki ki fad’a mun ni da ke waye b’arawo..!” Tai saurin d’agowa a zabure jin abinda yace sai kuma ta girgiza kai da sauri alamun a’a. Yace “Kinsan sarai mai nake nufi b’arauniya.!” Ta kuma d’agowa a d’an tsorace tana kuma firfito da idanu. “Daina kallo na da wann idanun naki..!” Ya daka mata tsawa da fad’in haka. Lokaci guda yai mata nuni da bishiyar mangoron da taso bud’e masa jaka a k’ark’ashinta “Kin tuna ko in tuna miki..?” Ya k’arashe yana zaro k’aramar piston cikin rigarsa. Wane irin zabura Ajidde tai zata saki k’ara ya d’aura yatsarsa guda saman labb’ansa yace “Idan kika ce pit sai na fasa kanki da bindigar nan.” Ta rik’e labb’anta Duka biyu da k’arfin gaske tana jin kuka gadan gadan na zuwa mata, lokaci guda take girgiza kai alamun ta tuba. “Dama ni tin da na ganki na fahimci kinada suffar criminals.. Yau kwanakin ki ya k’are a gidan nan.. Shige muje..” Ya k’arashe yana nuna mata hanya. Hawaye na zubo mata take tafe hannayenta duka biyu rik’e da labb’anta sabida tsananin tsoro shi kaw Mu’azzam na biye da ita rik’e da bindiga. D’akin da ake aje manyan shanayen gidan gonar suka shiga. Kana ganin Ajidde zaka fahimci Ta tsunduma cikin tsananin tsoro wanda bata tab’a shiga irinsa ba. Yasha mur sosai yana dubanta rik’eda bindiga. Jikinta sai rawa yake tana rik’eda labb’anta tana zuban hawaye. Drum Babba da ake zuba ma shanu ruwa ya nuna mata yace “Ke danna kanki cikin ruwan nan..!” Ajidde ta zaro idanu waje ta shiga girgiza kai, sai lokacin ta iya bud’e baki da muryarta dake tsananin rawa “Dan Allah na tuba.. Wllhi bazan sake ba.. Dan Allah kamin rai.” Bindiga ya d’ana mata a k’eya yace “Idan baki danna kanki cikin ruwan nan ba sai na fasa kanki da bindigar nan..!” Jiki na rawa Ajidde Ta rintse idanunta had’ida tura kanta cikin ruwan.. Ga Mu’azzam tsaye kanta da bindiga ba abun ta d’ago kanta ba.. Saida ya ta fara fiki fiki kaman kaman an jefa kaza cikin ruwa alamun galabaita kafin ya d’aga bindigar yace “D’ago kanki..” Ajidde ta d’ago kanta tana shak’an numfashin azaba tana fitar da iska daga bakinta alamun ta jigata tana bud’e idanunta da suka jik’e da ruwa da k’yar. Ya kuma danna mata bindigar a k’eya yace “Maida kanki..!” Ta sake masa kuka tana rok’onsa dan Allah yai hak’uri ya k’yaleta. “Ke ina wasa dake ne.. Idan baki maida kanki ba Sai na d’ana miki harsashin nan..!” Ya fad’i cikin kakkausar murya yana firfito da idanunsa. Babu shiri Ajidde tana kuma maida kanta cikin ruwan a jigace.. Haka ya dinga mata saida ya tabbata Ta jigata sosai. Kafin ya nuna mata gefe yace “Tsuguna..!” Babu musu ta tsuguna jiki har na rawa tana kuma matsan hawaye ga kanta da fuskarta sharkaf a jik’e. Ya gyara tsayuwarsa yana maida bindigarsa cikin aljihu “Kinsan sunan wann horon..?” Tai saurin girgiza kai tana hawaye. “Wann horon irinshi ake ma b’arayi irinki a police station.. Tashi muje ki fad’a masu wacece ke kafin a dangana dake ofishin ‘yansanda a kulleki..” Ajidde Ta mik’e tana kuka tana fad’in “Wllhi ni ba b’arauniya bace dan Allah kayi hak’uri.. Na rantse da Allah ni ba b’arauniya bace.” “Shut up..!” Ya daka mata tsawa wanda ya kuma sanyata had’iye kukanta. Ya nuna mata k’ofa yace “Shige muje kafin na fasa idanuwankin nan..!” Cikin sauri had’ida rawan d’ari ta fice sabon kuka na zuwa mata. Ta window Shemau ta hango Ajidde biyeda Mu’azzam sun nufi sashen Inne. Babu shiri ta mik’e ta nufo bayansu. Tin daga hanya Inne ta hango Ajidde Mu’azzam na biye da ita, daga yanayin data hangosu ta fahimci ba lafiya ba. Aiko suna shigowa parlorn Inne ta mik’e tana tambayarsu lafiya. Mu’azzam ya nuna mata k’asa yace “Tsuguna a nan..!” Babu musu Ajidde ta duk’a tana kuka. Inne ta tsaresa da idanu tana jiran ba’asi. Mu’azzam ya dubi Inne yace “Da alama baku San wa kuka kawo gidan nan kuka ajiye ba Inne.. Wannan yarinyar b’arauniya ce ba mai magani ba.. Dama ni tun farko ban yarda da ita ba..” Ya dubi Ajidde dake duk’e wajen tana hawaye ya daka mata tsawa da fad’in “Ke.! bud’e bakinki ki fad’i cewa ke b’arauniya ce.!” Inne ta dakatar dashi da fad’in “Haba Modibbo.. Wane irin abu ne zaka saka ‘yar talikan nan gaba kana tuhumarta da sata.. Awho dan Ta maka ihun b’arawo jiya shine yau kaima bari ka kirata b’arauniya.. Ko dan kaga tufafin matarka jikinta.?” Mu’azzam dake faman aikawa Ajidde mugun kallo daga nan yana take duk’a tana hawaye yace “Inne yarinyar nan b’arauniya ce.. Itace yarinyar da ta tasamma min sata kwanakin baya Ran da nazo gidan nan..” Ya kaikaito ya dubi Ajidde yace “Ke.. Ki fad’a mata cewa ke b’arauniya ce.” Ya daka ma Ajidde tsawa da fad’in haka. Kafin Ajidde takai ga basa amsa suka sinkayo muryar Musaddiq ya doso wajen yana fad’in “Ita ba b’arauniya bace..!” Gaba d’aya suka juyo suna duban Musaddiq dake nufosu cikin tsananin dakewa. Mu’azzam ya d’an tsaresa da idanu kafin yace “You don’t know anything Musaddiq.. Just stay out of this..” Musaddiq dake sakin huci dab kusan Mu’azzam d’in ya tsaya suna fuskantar juna lokaci guda yake furta “I told you she’s not a thief.!” Yanda yake maganar da zafin rai yasa Mu’azzam tsaresa da idanu yana dubansa, ya d’an girgiza kai kad’an kafin yace “Are you alright..?” “Garau nake..! Na fad’a maka ita ba b’arauniya bace.. Or did she steal from you..?!” Yai maganar yana duban cikin idanun Mu’azzam. Mu’azzam ya girgiza kai yace “She didn’t amma tayi kusa.. And for that zata bar gidan nan dan bamu San wace irin criminal bace ita.. Bamu buk’atar maganinta..” Musaddiq ya katsesa da fad’in “Babu yana zataje.. Sabida ita mutumiyar kirki ce.. Kuma Aunty Nuratu tana buk’atar maganinta..!” Aunty Shemau ta zaro idanu waje tana kame k’irji, mai Musaddiq yake nufi da cewa Nuratu tana buk’atar maganin yarinyar.. Kodai Musaddiq yasan shirinsu ne itada mahaifiyarsa..? Muryar Mu’azzam ne ya kaste mata tunanin nata. Ganin yanda yake amsa masa magana yasa ya kuma karkatowa yana duban Musaddiq d’in “Are you high..?” Mu’azzam ya tambaya yana tsare Musaddiq d’in da idanu. Tambayar da Mu’azzam yai masa na k’arshe ya mugun tunzirasa, lokaci guda ya soma fad’in “Kana tunanin kai kad’ai ne mutumin Kirki a nan.. Well let me remind you.. You are not a saint Mu’azzam Gamji.. And you need to learn that you can’t control the lives of the people around you.. And yes like it or not Babu yanda Ajidde zataje.. Tana nan a gidan nan..!” Wann karon cikin tsananin mamaki Mu’azzam ya girgiza kai kad’an yana duban Musaddiq d’in “Have you lost your mind.?” Ya furta a hankali yana duban Musaddiq d’in. Inne tai saurin rik’o Musaddiq tana k’ok’arin janyosa baya yayinda Mama Hindu ta janye Ajidde suka fice daga wajen. Shemau kuwa gyara tsayuwarta tai tana kallon show d’in dake wakana. Inne tana janye Musaddiq take fad’in “Ya isa haka abi komai a sannu..” Musaddiq cikin d’aga murya yace “No Inne.. who does he think he is da dole kowa Sai ya bi abinda yake so.. Ajidde bazata bar gidan nan ba.. Kuma zata dawo zama cikin gidan nan na har abada..!” Yaci gaba da sakin huci yana nufo Mu’azzam d’in, saida ya tsaya kaman k’irjinsa zai bangaji na Mu’azzam kafin yaci gaba da fad’in “And do you know Why is that Mu’azzam Gamji..? Because I love her..! Yes I love her.. And I’m going to marry her.. Kai baka isa ka koreta ba Mu’azzam Gamji..!” K’iris ya rage Shemau bata kifa k’asa ba.. Daga Inne har Mu’azzam Cak suka tsaya suna duban Musaddiq dake ci gaba da sakin huci kaman zai kaiwa Mu’azzam d’in naushi. Mu’azzam yai k’ok’arin calming kansa dan ya lura kaman Musaddiq d’in a sama yake.. K’ila yasha wani kayan mayen nasa. Inne zatai magana Mu’azzam ya dakatar da ita yana fad’in “Kar ki damu Inne I’ll take care of this..” Lokaci guda ya mik’a hannunsa yana k’ok’arin kamo Musaddiq d’in yake fad’in “Brother calm down.” Fuzga Musaddiq yai yana ci gaba da sakin huci yake nuna Mu’azzam d’un da yatsa “Don’t you dare.. Don’t you dare come near me.!” Yana ida fad’in haka yasa kai zai shige cikin huci. Inne tai saurin taresa cikin tsananin b’acin rai take fad’in “Baka da hankali ne kake d’agawa D’anuwanka murya haka.. Kodai ka koma shan kayan mayen Naka ne..?!” Bai daina sakin huci ba yake duban Inne “Go ahead and take his side.. Dama abinda kuka iya kenan.. Baya laifi a idonku.. Bani ya kamata ki tambaya ko na koma shan kayan maye ba.. Shi ya kamata ki tambaya tinda har zai tare k’aramar yarinyar nan yace ta masa sata bayan bata sata masa komai ba.. Idan bai gode wa d’awainiyar da takeda mahaifiyarsa wanda bazai iya biyanta kwatankwacin abinda tai ba bazai k’ala mata sharrin sata har yace zai koreta a gidan nan ba.. Kuma kunji abinda na fad’a I love that girl.. Ina sonta.. Ina sonta sosai kuma zan aureta.. Idan zaku koreta a gidan nan sabida shalele Mu’azzam yace a koreta Toh definitely zaku had’a dani dan nima zan tafi kuma bazaku sake ganina ba..!” Daga haka ya fice fuu yana sakin huci. Inne tai mutuwar tsaye tana duban Musaddiq har ya fice. Aunty Shemau dake lab’e bayan parlorn itama kallo tabi Musaddiq d’in dashi tana jinjina lamarin cikin zuciyarta har yazo ya shigeta ya fice a parlorn. Mu’azzam ya k’araso ya rik’e Inne ya zaunarta a hankali saman kujera. Duban Mu’azzam tai tace “Kaga yanda yake d’aga mana murya..? Anya yana cikin hankalinsa..?” Mu’azzam ya fuzar da fuci kad’an yace “Zan same shi Inne.. Zan mishi magana.. Zanji meke damunsa.. Tabbas akwai abinda ke damun D’anuwana.. Koda ya sha abubuwansa ba haka yake ba.. Something is off with him..” Inne dai shiru tai tana jinjina abubuwan dake faruwa da ahalinsu. Safeenah tayi harbi da bindiga. Auren Mu’azzam da Safeenar ya k’are yanzu ga Musaddiq ya bijiro da wani irin hali da basu saba ganinsa ciki ba dukda ya kasance mai gagara. A hankali Ta maida kanta cikin kujera tana ambaton Allah tareda rok’onsa ya tsare mata ahalinta. Basu kuma ganin Musaddiq a gidan ba har dare. Sannan a daren Inne da tsiraru cikin dangi sukaima Sadiya rakiya zuwa b’angaren da tin kwanaki Innen Tasa aka gyarawa Mu’azzam da Safeenah. ** Bugu biyu Mommy ta d’aga wayan Shemau, ko gaisawa basuyi ba tace “Ina sauraronki Shemau, fad’a mun meke faruwa.. Kun raka Karuwar Mu’azzam d’akinta ko k’ak’a..?” Aunty Shemau ta nusa tace “Idan nice ke Aunty Hajara ba wann zan tambaya ba..” Shaye da mamaki Mommy tace “Yo mai zan tambaya..? Ko Nuratu ce ta mutu kike shirin bani albishir..?” Aunty Shemau ta nusa tace “Wann ai ba albishir zan miki ba.. Abin tashin hankali zan sanar dake.” Wann karon mik’ewa tsaye Mommy tai tana girgiza kai take fad’in “A’a Shemau.. Na gaji da jin labarai marassa dad’i.. Kar dai kice mun nakasashiyar matar Marwan warkewa tayi..?!” Aunty Shemau tace “Duk ba’a kansu bane..” Cikeda k’osawa Mommy tace “Shemau ki daina tsinkar min da gaba ki sanar dani meke faruwa.. Marwan ne ya sake yo mun kishiya kokuwa..?” Shemau tace “Duk ba’a kansu bane. Kan d’anki Musaddiq ne..” Mommy Ta dafe k’irji tace “Na shiga uku ni Hajara mai ya sami Musaddiq..” Aunty Shemau Ta murmusa tace “Babu abinda ya sami Musaddiq amma kiyi shirin biki dan Musaddiq ya sami mata a nan..” Mommy ta girgiza kai tace “Ban fahimceki ba Shemau.” Aunty Shemau tace fillanci kike so na miki sai kifi fahimta da kyau. Toh d’anki Musaddiq ya fad’a soyayya da mahaukaciyar yarinyar dake kawowa Nuratu magani..” Mommy ta dafe k’irji tace “Na shiga uku ni Hajara.. Kiyi istigifari Shemau domin kuwa Ina raye Musaddiq bazai auri dangin bokaye da ‘yan bori ba.. Toh banda bak’in jaraba mai ya gani tattare da ita ya tsallake duk matan dake sonsa a nan Abuja.” Shemau ta tab’e baki tace “Yo ina na sani.. Shawarin da zan baki Aunty Hajara tun wuri ki d’auke Musaddiq daga garin nan ya daina ganin yarinyar ta haka ne kawai za’a iya rabasu.” Mommy na safa da marwa cikin d’aki take fad’in “Ta yaya zanyi haka Shemau bayan Kinsan halin wannan jarababbiyar tsohuwa..” Aunty Shemau tace “Tun wuri ki nemowa kanki hanya, kiyi duk yanda zakiyi ki tabbata kin rabasu.. Dan ni duk bama wann ba muddin Musaddiq zai soyayya da yarinyar nan asirinmu tonuwa zai.. Ni babban tashin hankali na kenan..” Mommy tace “Yo da na had’a iri da zuri’ar bokaye da bori ai gwara asirinmu ya tonu..” Shemau tace “Lallai baki San abinda kike fad’i ba Hajara.. Wllhi wllhi bazan bari asirina ya tonu Mu’azzam ya jefani kurkuku ba.. Koda wasa kar d’anki ya mun sanadi.. Ni ba damuwata bace idan ma Jikanyar ifiritu zai aura.. Ni damuwata shine kar asirina ya tonu ehe.. Tun wuri kisan yanda zakiyi ki d’auke d’anki daga garin nan Ni zanji da yarinyar..!” Daga haka Shemau ta katse wayar a fusace. Mommy tana kiran sunan Shemau ko tsayawa sauraronta batai ba ta datse kiran. Hannu biyu Mommy Ta d’aura aka tana fad’in “Na shiga uku ni Hajara Musaddiq zai karni a tsaye.!” Cikin sauri ta shiga neman layin Musaddiq saidai bata shiga. ** A b’angaren Sadiya kaw tinda akai mata rakiya zuwa b’angaren bata sanya angon nata a idanunta ba, har dare ya soma ja, Ta mik’e ta gabatar da sallar isha da batayi ba. Tana nan zaune saman darduma taji alamun shigowarsa dan taji kaman tab’a k’ofar parlorn. Gabanta ya fad’i, bugun zuciyarta na k’aruwa. Bata tashi saman darduman ba saima tsintar kanta da tai tana kuma gyara zaman tahiyar nata kaman dai bata sallame sallar ba. Tanajin alamun bud’e d’aya k’ofar d’akin da yayi dan dama d’akuna biyu ne sai parlor da kitchen a section d’in. Ya b’ata lokaci a d’aya d’akin tana nan zaune tamkar wacce aka dasata. Jim kad’an taji alamun ana tab’a handle d’in d’ajin da take, bugun zuciyarta ya k’aru.. Sai k’irga yatsun hannunta take kai kace tasbihi take a zahiri alhali ita kanta bazatace ga tak’amaimen abinda take ba. K’amshinsa shi ya rigayi muryarsa mata sallama. Ta lumshe idanunta a hankali tana mai amsar sallamar nasa can k’asa dan ba lallai bane ma idan yaji. K’arasowa yai ya zauna bayanta yana jira Ta sallame. Ita kaw tinda taji alamun ya zauna sai ta k’asa katab’us taci gaba da motsa ‘yan yatsunta da take. Sosai suka d’auki lokaci haka, k’arshe gyaran murya yai kad’an yace “Madam a rage sauran addu’an mana muma mu samu..” Ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana murmusawa. Shima d’in murmushin ne saman fuskara ya mik’e ya k’araso gabanta, ya zauna ya nad’e k’afafunsa irin zaman cin abinci. Lokaci guda ya mik’a hannayensa ya janye nata hannayen da ta rufe fuskarta dasu. Da k’yar ta iya d’ago k’wayan idanunta tana dubansa. Yana sanye cikin jallabiya fara k’al irinta Larabawa. Shid’inma ita yake duba kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Sai kuma ta dad’a Murmusawa tana maida nata idanun k’asa. “Mrs Mu’azzam Gamji.!” Ya fad’i yana dubanta still murmushin ne saman fuskarsa. Bata amsa ba sann bata d’ago ta dubesa ba saima sakin kyakkyawan murmushi da take. “D’ago ki kalleni. Ba wani bane ni ne nan Mr Inspector.. And we are going to push through with our mission right this moment..!” Ya d’an k’arashe a dake. Ai bata San sanda ta d’ago tana dubansa a d’an tsorace jin yanda Yai maganar. Taga ya tsime yana dubanta, ya koma mata Mr Inspector data soma sani. Take tsoro ya wanzu saman fuskarta. Ganin haka ya sanyashi sakin murmushi kad’an dan dama reaction d’inta yake son gani. “Kar ki damu I promise you.. This will be the best mission ever.” Ya fad’i yana rik’o hannayenta cikin nasa. “Tashi muyi sallah..” Ya k’arashe yana mai mik’ar dasu tsaye gaba d’aya. Ta d’an d’ago ta dubesa kad’an a d’an shagwab’e tace “Ni fah nayi sallah..” Ya jinjina kai yace “I know.. Zamu sake wani ne..” Ta sadda kanta kad’an sanda ya shige gaba dan yi masu limanci. A natse ya daidaita tsayuwarsa ya tada kabbaran harama dan sallar nafila ba’a mata ik’ama kaman sallar farilla. Cikin natsuwa ya jasu sallar suka sallaci raka’a biyu kaman yanda yazo a sunnah. Bayan sun ida ya d’aura hannunsa na dama saman goshinta ya karanto addu’an neman alkhairi da tsari daga sharri. Ya d’anyi gyaran murya kafin ya ambato sunanta cikin wane irin siga wanda ya kuma kashe mata jiki had’ida haifar mata da rauni. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “I have a lot to tell you wanda ba lallai daren nan ya ishemu ba.. Amma kafin nan Ina so kije wancan d’aki mai kallon wann akwai abinda zaki d’auko min cikin d’akin..” Ta d’an dubesa kaman tana son rambayarsa mai zata d’auko masa sai kuma ta tuna jawabin Aunty Larai cewa kar Ta tab’a masa gardama kan abinda bai sab’awa shari’a ba. Ta yuwu wann assignment ya bata ba tareda ya fayyace mata ga abinda zata d’auko masa ba. Idan tana son cin assignment d’in Toh tayi abinda yace d’in without asking questions.. Kai tsaye ta jinina masa kai kafin ta nufi k’ofa kanta a k’asa. Zuciyarta sai tsinkewa yake tana tinanin mai zataje d’aukowa ba tareda ance ga abinda zaki d’auko ba.. Wann wane irin aike ne. Sanda ta iso k’ofar d’akin tai k’ok’arin saita kanta kafin ta kama handle d’in ta murd’a da bassamalla. Saida tayi sallama kafin ta tura k’ofan d’akin. Ga tsananin mamakinta takarda ta soma tuntub’e dashi an linke. Saman takardan an rubuta mission number 1. A hankali ta duk’a ta d’auki takardan ta warware “I’m sorry.. Please forgive me.!” Murmushi tai kafin ta girgiza kai kad’an tana lumshe idanu. Ta d’an k’ara gaba kad’an taji Ta taka wani takardan, Ta duk’a kad’an ta d’auka an rubuta mission no2 “Look up there.” A hankali ta d’aga kanta tana duban center cikin d’akin. Nan taga an zagaye ginin da red roses k’anana tsakiya an rubuta I LOVE YOU. Hannayenta ta d’aura saman bakinta tana karanta kalaman a hankali cikin zuciyarta da kwanyarta. Tana nan tsaye tana kallon kalaman tana sakin murmushi siraran hawaye na gangaro mata taji sauk’an hannayensa saman kunkuminta zuwa cikinta. Ya rank’wafo da kansa saitin b’angaren kunnenta na dama kafin ya furta a hankali “Do you like my surprise..? Are you ready for mission number3..?” Yai maganar yana mai karkatota suka fuskanci juna. Sai lokacin ta kula da sauran abubuwan da ya shirya cikin d’akin. Saman gadon an jera red roses an zana tambarin heart dasu. Gefe kuma kujeru ne guda biyu k’aramar table a tsakiya kaman d’ai coffee chairs. Saman table d’in harda candles maimakon champagne kwalin fresh milk ne sai glass cups guda biyu saiko faranti mai d’aukeda gasasshiyar kaza. Ta saki murmushi kad’an kafin ta saci kallonsa tace “You did all this..?” Ya jinjina mata kai yana mai dubanta “For my Beautiful Queen.” Ya bata amsa yana mai kuma rik’o hannayenta cikin nasa. Ta d’an rausayar da idanunta kafin tace “Inspector.. Are we on a date..?” Janyota yai cikin jikinsa idanunsa tar akanta “We are on a mission..” Yai maganar yana mata wasu salo masu kashe mata gabb’an jikinta. Ta soma k’ok’arin zamewa daga nasa jikin. Ya saki murmushi a hankali yana dubanta kafin ya rage hasken d’akin sai hasken candles dake saman table d’in kake iya gani. Ta d’an zaro idanu waje alamun tsoro. K’arasowa yai ya kuma kamota kafin ya rad’a mata “I’m with you Babu abinda zai sameki.. Nasan kina tsoron duhu..” Ta saki murmushi a hankali kalan k’aunarsa na kasheta. Ta mance komai bata gani komai sann bata ganin kowa a duniyar sai su biyu. Hannunta ya kamo suka k’araso wajen table d’in. Yai saurin janyo mata kujera yana fad’in “Allow me..” Ta saki murmushi kad’an tana kashesa da wane irin kallo kafin ta k’arasa ta zauna. Zama shima yai ba tareda ya janye idanunsa daga kanta ba. Ya soma zuba mata fresh milk d’in a cup yana fad’in “Allow me to take care of you tonight.” Ya k’arashe yana mai mik’o mata cup d’in kusan bakinta. D’an rau rau tai da idanu had’ida langab’e kai “Inspector nifa na k’oshi..” Ya tsareta da idanu yace “Do you want to fail this mission tin kafin ki fara..?” Ta kuma marairaice masa fuska. Cikin sigan lallashi ya d’aura hannunsa guda saman nata yana kuma kai cup d’in kusan bakinta yana fad’in “Yi hak’uri kad’an zaki sha.. You know you can’t go to bed without eating anything... Oya drink it now..!” Ya k’arashe yana shafa tafin hannunta a hankali alamun lallashi. Nan ko tasha ya kuma bata naman ma Ta d’anci kad’an. Zallan k’aunarsa yake nuna mata. Daga bisani ya mik’e tsaye ya mik’a mata hannu guda yace “May I have this dance.?” Yai maganar yana mai d’an rank’wafowa kad’an. Ta d’an marairaice idanu kad’an tana dubansa “But I don’t know how to dance Inspector.” Ya saki miskilin murmushi kafin yace “I don’t know either.. I guess I just want to have my first dance in history with you..” Ta murmusa kad’an kafin ta mik’a masa hannunta ya d’agota. Hannunta guda cikin nasa ya kuma kamo d’aya hannun nata ya d’aura saman chest d’insa yanda heart d’insa yake kafin ya sakalo kunkuminta da d’aya hannun nasa. A hankali yake motsasu yana kallon fuskarta yayinda Sadiya ke duban k’irjinsa yanda hannunta guda ke bisa. Tana iya jin bugun zuciyarsa na ratsa tafin hannunta zuwa jijiyoyin jikinta. Gaba d’aya ji tai Ta gaza sakewa, a hankali ta kwantar da kanta saman k’irjinsa had’ida lumshe idanunta. Muryarsa Ta sinkayo yana fad’in “Something is missing..” Bata iya d’agowa ba bata iya furta koda kalma ba sabida yanda tai Lami cikin k’irjinsa tamkar wacce aka zare ma laka. Ya d’an kwanto da kansa saitin kunnenta yace “Sing a song for us..” Kaman wacce aka mintsila Ta bud’e idanunta, sai kuma ta girgiza kai tace “Ban iya ba fah.” “Gashi nima ban iya ba, ya kenan za’ayi..? Wait kece yarinya.. Ke kika iya wak’ok’in zamani. Oya sing one for us.” Ta marairaice fuska tace “Da gaske ban iya ba, saidai kai kayi..” Ya d’an murmusa kad’an yana mai kuma kwantarta cikin jikinsa “Ai ban iya na zamani ba.. Saidai outdated ones na zamaninmu..” Ta murmusa kad’an kafin tace “Inaso naji na zamaninka..” Ya kuma murmusawa kafin yace “Come here..” Ya kwantar da kanta saman k’irjinsa, suka d’ibi lokaci a haka kafin can ya soma furta _”If our love was a fairy tale I would charge in and rescue you On a yacht, Baby, we would sail To an island where we’d say I do_ -And if we had babies they would look like you It would be so beautiful if that came true You don’t even know how very special you are_ Muryarta ya sinkayo daga nan yanda kanta ke bisa k’irjinsa tana furta _You leave me Breathless You’re everything good in my life You leave me Breathless_ Ya saka hannunsa guda ya d’ago hab’arta kafin ya furta _I still can’t believe that you are mine._ lokaci guda ya manna mata light kiss saman lips d’inta. Ya tsareta da idanu yace “Ina kika iya wak’ar..?” Ta murmusa kad’an cikeda kunya tana tura kanta cikin k’irjinsa. Shauk’in k’aunarta na fuzgansa ya kuma kamo hab’arta ya tsareta da idanu yace “Did you mean what you said.. That I’m everything good in your life..?” Ta d’ago a hankali tana dubansa kafin ta jinjina masa kai alamun eh. Rungumeta yai cikin jikinsa yana fad’in “Allow me to show you how much you mean to me please Saady..” Yai maganar yana kuma rikitata. Daga yanda yake jin yanayinta ya fahimci tsananin tsoron yanayin da ta tsinta kanta ciki. Murya can k’asa yake furta “I promise I’ll be gentle.. And this mission will be the best of my all missions..” Yana ida fad’in haka ya rufe bakinta da nasa cikin nuna shauk’I na k’auna. Tabbas wann mission d’in yasha banban da ko wanne, kaman yanda yace he’d be gentle bashi ya hanata jin jiki hannunsa ba.. Inspector bai farga da aika aikan da yai cikin mission d’in nasa ba saida ya maida stubborn head d’insa cikakkiyar mace. Kuka da raki kam yashasa wann daren. Haka ya dinga aikin lallama da lallashi kaman ya d’auketa ya goyata bayansa haka yakeji. Duk wani gyara da Aunty Larai tai mata saida Inspector ya b’ata wann gyaran. Hamdala kurum yake cikin zuciyarsa yana kuma godewa Ubangijinsa da wann baiwa da yai masa na mallaka masa mace kaman Sadiya da yai. Soyayyarta da k’aunarta sun kuma ninkuwa cikin zuciyarsa. Wani irin k’imanta ne mai girma had’ida daraja suka k’aru a idanunsa. Tabbas yasha kunya a wnn dare dan zaton da yai mata ba haka take ba. Cikakkiyar budurwa ce wacce ya zamto mutum na farko da ya soma saninta d’iya mace. Tausayinta gauraye da k’aunarta na kuma mamaye masa zuciya. Da kansa ya kaita bathroom har lokacin bata daina masa kuka ba. Ganin Wai so yake ya mata wankan ya sanyata sakin wani sabon kuka tana fad’in “Ni ka fice mun.. Kuma na fasa mission d’in... Kuma zan koma wajen Inne bazan sake dawowa wajenka ba har mu tafi..” Ga tausayinta yanaji ga dariya, lallashinta ya kumayi yace “Ayi mun afuwa kar ki gudu wajen Inne.. Kinga ficewata ma..” Ya fice yana kuma k’unshe dariyarsa. Yana ficewa kuka ta kuma saki cikin zuciyarta tana fad’in dik Aunty Larai ne Ta cuceta, ga Inspector ya tasamma kasheta cikin mission. Da kansa ya kuma gyara masu shimfid’ar tasu ya cire ya canza wani. Tai lamo tana baccin galabaita. Bayan ya ida nafilfili zaune yai gaban gadon yana dubanta cikeda tausayawa had’ida k’aunarta, kai da ganin yanda ta tak’ure kasan baccin wahala take. Ya matso kusanta ya kamo yatsun hannayenta cikin nasa yana tuna munanan kalaman da ya dinga jifanta dasu a baya. Sumbatan yatsun hannun nata yai yana mai lumshe idanu “Thank you for making me the most happiest Man on earth.. Na gode miki da kika adana mun kanki har zuwa wannan lokaci.. Na gode da kika martaba mun kanki.. Na gode da baki watsar min da kanki ba... Dikda irin shaidar da mutane suka miki Kinyi k’ok’ari kin killace min kanki.. Believe me, I’ll love and respect you til my last breath..” Ya d’anyi fasali had’ida manna hannun nata gefen fuskarsa. Lokaci guda yaci gaba da furta “I .. I’m sorry.. I’m sorry for judging you.. It was truly wrong for me to do what I did.. I’m genuinely sorry for my actions.. Please forgive me.” ya k’arashe siririyar hawaye na gangaro masa daga idanu guda. Lokaci guda ya d’aura kansa saman hannun nata, tana jin d’umin hawayensa cikin tafin hannunta, hawaye suka gangaro mata itama. Cikin zuciyarta take furta “Baka mun komai ba Sai Alkhairi Inspector.. Kai d’in alkhairi ne a gareni.” Tana jin sanda ya taso ya kwanta saman gadon ya sanyata cikin jikinsa ya rik’eta sosai kaman zai bud’e k’irjinsa ya sakata ciki. Bacci mai dad’i had’ida shauk’i yai gaba da su. Da niyyan Allah ya tadasu asuba. ** Washe gari kasa fitowa tai sabida kunyarsa da ya dabaibayeta. Idan ta tina abubuwan da yaita mata a daren jiyan sai taga kaman dai ba Mr Inspector bane da ta sani. Wani irin mutum ne da b’angarensa guda Keda zafi d’aya b’angaren kuma Keda matuk’ar taushi. Ta lumshe idanunta a hankali tana jin k’aunarsa na bin b’argo da jijiyoyin jikinta. Tana jin shiga da fitan shi tai kaman mai bacci. Can taji yana waya taji kuma kaman ya fice daga parlorn. Da k’yar ta iya mik’ewa kaman zata kifa k’Asa tana jin jijiyoyin jikinta kaman an d’add’aure, ko ina ciwo yake a jikinta. K’afarta kuwa da k’yar take iya d’agawa. A haka da bin garu ta samu ta zame daga nasa d’akin ta nufi nata d’akin. Wanka ta kumayi ta shirya cikin wani red embellished mai kyaun da taushi, d’inkin riga da skirt da ya mugun amsarta. Ta kuma hayewa saman gado Ta kwanta sabida yanda take jin gaba d’aya jikinta kaman ba nata ba. Sallama da taji a k’ofar parlor ya sanyata dole Ta k’ok’arta ta fito. Aunty Shemau ce sai dubanta take tana karantarta musamman yanayin tafiyarta. Sadiya duk sai taji kunya ya danaibayeta, tanata k’ok’arin b’oye yanayin nata amma tuni Shemau ta d’ago jirgin, ta zauna tana mata sannu. Sadiya Ta k’ok’arta kaman zata duk’a k’asa Don gaida Shemau’un. Tuni Shemau ta kamota tana fad’in “A’a Haba Amarya ai durk’uso ba naki bane. Na yafe wllhi.” Ta k’arashe tana mai zaunar da Sadiyar saman sofa a hankali. Shemau ta zauna gefenta tana sakin murmushi yayinda Sadiya ta sadda kai kad’an ta gaisheta. Gyara zama sosai Shemau tai tana ‘yan waige waige. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDA ARO* *49* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A d’aki ya tadda Musaddiq d’in yana shirin fita. Fuska babu walwala yake dubansa “Can we talk now..?” Ya tambaya yana duban Musaddiq. A d’an karkarce Musaddiq d’in ke dubansa lokaci guda yana manna batten d’in hannun long sleeve d’insa “Say what you want say quickly.. As you can see fita zanyi..” Da tsananin mamaki Mu’azzam ke dubansa. Sosai Musaddiq ya canza abubuwan da baya yinsu a baya. “Really Musaddiq.? What has gotten into you.. what exactly is wrong with you..?” Ya fad’i yana duban Musaddiq din. Karkartowa yai sosai yana dubansa “I should be the one asking you that question.. What exactly is wrong with you.. Why can’t you mind your own business and leave me alone, Mr Officer.!” Ya fad’i kai tsaye. “Musaddiq ni kakema magana haka..?” Murmusawa Musaddiq yai kafin yace “I forgot you are Mu’azzam Gamji.. Wanda ba’a fad’a masa magana.. Wanda yake yin abinda duk yaga dama ba tareda kowa ya taka masa Burki ba..” “Enough Musaddiq..! You know that’s not true..” Ya dakatar dashi da fad’in haka cikin kakkausar murya. Musaddiq ya matso kusansa yana murmusawa kafin yace “Gaskiyar kenan.. You are their favorite.. Kana yin duk abinda kaga dama a lokacin da kaga dama ba tareda Sun taka maka birki ba sabida suna tsoron b’acin ranka..” Ya d’an jinjina kai kafin yaci gaba da fad’in “What..? K’arya nayi.. Ba haka bane..?” Ya d’anyi fasali yana duban Mu’azzam d’in wanda ke kan dubansa. Lokaci guda yaci gaba da fad’in “Ko kuma matar da na zab’o ne batayi ma Mu’azzam Gamji ba yake so ya sauya mun tinda shi a koda yaushe abinda yake ra’ayi shi yake so mutane su bi.. Well idan wann ne ka saka ma ranka na auri Ajidde an gama, and from now I’ll make decisions on my own.. Bana buk’atan tunanin kowa especially kai..” “And you will leave Ajidde alone, sabida ita d’in zata zamto matata nan gaba kad’an.. I don’t care idan kanada matsala da hakan..” Ya d’anyi fasali kafin yaci gaba da fad’in “Koda yake idan har ina d’an ahalin nan zan auri Ajidde wacce ba kowa ba, a wajenka na koyi hakan.. After all, idan har za’a janye ido kan auren Sirrin da kai dukda cewa babu wanda yasan dangin wacce ka auro da asalinta banga dalilin da zaisa a hanani auren Ajidde ba..” Wann karon cikin tsananin k’unan rai yake duban Musaddiq d’in.. Lokaci guda ya d’ago yatsa yana nunasa cikeda gargad’i “Don’t you dare..! Don’t you dare talk about my wife.. Kar ka kuskura ka sake ambato matata.. Much less ka had’ata da wann mahaukaciyar..!” Yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “It’s your life Musaddiq.. Do what you want to do with it.. I just hope you won’t have any regrets..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice ba tareda ya kuma bi takan Musaddiq d’in ba. Mu’azzam yana ficewa Musaddiq ya zauna saman gado yana kame kansa had’ida tamke idanunsa. Ya jima yana zaune haka a wajen kafin ya mik’e ya nufi waje. Yana fitowa ya hangota tana tahowa. Yai tsaye yana dubanta bugun zuciyarsa na k’aruwa. Cak itama ta tsaya sanda ta hangosa. Tinani kala daban daban cikin zuciyarta. Na farko k’watan ta da yai jiya wanda ba Don Allah ya ceceta ba da asirinta ya tonu domin kuwa Tabbas abinda Mu’azzam ya fad’i gaskiya ne amma Musaddiq ya ceceta gaban Inne.. Da ace an koreta a jiyan Tabbas da hallak’ata kurum Kyallu zatai. Tinani na biyu kaw b’oye mata kansa da yai wanda shi yafi komai tsayuwa a zuciyarta. A hankali ta kifa kanta tana mai k’ok’arin canza hanya. Musaddiq yai saurin cimmata yana kiran sunanta yana fad’in ta tsaya suyi magana. Cak taja Ta tsaya ba tareda ta juyo ta dubesa ba. Ya k’araso gabanta yana dubanta. Suka d’ibi lokaci a haka kaman babu mai cewa komai cikinsu. Can ya d’anyi gyaran murya yace “I know by now kin San ko ni wanene..” Sai sann ta d’ago ta d’an dubesa, sai kuma ta kauda kanta gefe ba tareda tace komai ba. Shafa kansa ya d’anyi dan yama rasa mai zai kuma fad’i mata. “Kiyi hak’uri kan abinda ya faru jiya..” Abinda yaji bakinsa ya iya fad’i kenan. Da mamaki ta kuma dubansa kafin ta girgiza kai tace “Maiyasa kake bani hak’uri kan laifin da baka aikata ba.? Maiyasa kake bani hak’uri kan laifin da gaskiya ne na aikata.. Da ni da kai munsan cewa D’anuwanka gaskiya ya fad’i akaina.. Ni b’arauniya ce kuma na tasamma masa sata, ba karo d’aya ba har sau biyu... Tabbas baiyi k’arya ba.. Ni da kai duk munsan haka.. Amma abinda ban fahimta ba shine Maiyasa kake kareni.. Bayan baka bani yarda da amincewarka ba..?” Kauda kansa gefe yai kad’an yana fuzar da huci a hankali hannayensa saman kunkuminsa, lokaci guda ya juyo yana duban idanunta da tuni sun ciko da k’walla. A hankali ya soma girgiza kai kafin yace “No that’s not true.. Ke ba b’arauniya bace.. Inna K’yallu ce ke umartanki da ki d’auki kayan mutane.. Amma ke d’in ba b’arauniya bace.. Kar ki sake kiran kanki da wann sunan domin ke mutuniyar kirki ce..?” Katsesa tai da fad’in “Kaji abinda ka fad’i kuwa..? Mutumiyar kirki..? Ta ya kasan ni mutumiyar kirki ce idan har kana shakkun ka sanar dani asalinka da wanene kai..?” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata. K’ok’arin saita kansa yai kafin yace “Bazaki fahimci komai ba Ajidde koda zan miki bayani.. Amma abinda nake so ki sani shine ban b’oye miki kaina dan rashin yarda dake ba ko wani abu makamancin haka.. Ki yarda dani bana nufinki da sharri face alkhairi..” Shiru tai tana juya kalamansa cikin zuciyarta kafin ta d’ago ta dubesa kad’an. Sai kuma ta goge hawayenta ta murmusa kad’an tace “Banida hurumin jin haushi dan baka sanar dani asalinka ba.. Saidai naji zafi sosai bayan na aminta da kai, na sanar dakai sirrin maganin Innata.. Wanda Sirri ne Babba na zab’i sanar dakai.. Amma kai ka b’oye mun wani abu, dukda cewa munyi tarayya wajen watsar da maganin Inna Kyallu da kuma amsar maganin Malama Hafsah..” Fasali tai tana kuma maida kukan dake k’ok’arin zuwa mata.. Kafin Ta murmusa tace “Tabbas ka taimakeni kuma na gode.. Watak’ila badon kai ba da yanzu nayi abinda Inna Kyallu ke umartana na aikata a cikin gidan nan.. Ina nufin sata.. Na gode maka matuk’a.. Ubangiji ya biyaka..” Tana ida fad’in haka tasa kai ta shige. Musaddiq yabi bayanta da kallo yana jin wani abu can k’asar zuciyarsa. A haka Jume da k’arasowarsa kenan ya hangesa. Har ya iso wajen Musaddiq baisan ya iso ba. Jume ya dubesa ya kuma duban yanda Musaddiq d’in ke kallo kafin ya k’ara sautin muryarsa yace “Wai lafiya kake..? Bakina na uku fah kenan Ina maka sallama..” D’an sauk’e ajiyan zuciya Musaddiq yai had’ida jan gajeren tsaki yace “Kar ka raina mun wayo mana, mai ka d’aukeni da zakata buga sallama banji ba..” Jume ya murmusa yace “Malam naga yanda idanunka ke Kallo.. Fad’a mun mai ya faru.. Ka riga ka sanar da ita yanda kake ji ne tinda har ka sanar da Inne ko so kake taji batun daga cikin gida..?” A d’an karkace ya dubi Jume kafin ya girgiza kansa kad’an ya k’arasa saman karyayyen bishiya ya zauna. Jume ya k’araso ya zauna gefensa. Yai gyaran murya kad’an kafin yace “Wai bazaka iya fad’a mata bane..?” A dak’ile ya dubesa kafin yace “Mai zan fad’a mata..?” “Kace mata kana sonta..” Jume ya basa amsa kai tsaye. Gimtsewa yai kad’an kafin yace “Ni nace maka ina sonta..?” Jume ya saki baki yana kallonsa “Ikon Allah.. Jiya jiya ka d’aga jijiyan wuya cikin gidan nan cewa kana sonta zaka aureta.. Toh ina courage d’in ya tafi..?” “Kai yanzu idan nace maka ina son Ajidde sai ka yarda..?” Ya tambaya yana duban Jemen. Jume ya girgiza kai yace “Ban gane ba.. Mai zai hanani yarda. K’warai ma kuwa da gaske zan yarda.. Maiyasa bazaka sota ba.. Sabida wayewarku ba iri d’aya bane kokuwa status d’inku ba d’aya ba..?” A dak’ile yake dubansa kafin yace “Kaima kasan bazan tab’a fifita kaina sama da wani sabida wani ni’ima da Allah ya bani wanda bai bama wancan d’in ba.. Kawai ni ba sonta nake ba.. Na fad’i haka ne to save her.. But I don’t love her.. In fact ban tab’a kawo Ajidde a irin jerin matan da nake son aura ba.. Kawai dai nasan tana saka ni nishad’i.” Jume ya girgiza kai kad’an had’ida murmusawa kafin yace “Idan kace haka ni bazan ce komai ba.. Allah ya ara mana kwana muga k’arshen taimako.. Ni zan wuce kafin Sarkin gida yace nayi latti..” Daga haka shigewa yai ya bar Musaddiq zaune nan wajen yana tinanin rayuwa. ** A b’angaren Ajidde kaw tana shiga gidan ta tadda Mama Hindu na had’a breakfast. Mama Hindu ta dubeta tace “A’a mutuniyar yau babu shigowa da wak’en da kika saba ne..?” Tana maganar tana murmushi. Ajidde ta turo baki gaba kad’an tace “Ai wllhi Mama Hindu da k’yar ma na shigo saida nayita jero addu’a cikin zuciyata Ina fad’in Allah Sa kar naga Kofur Zalimu a hanya..” Mama Hindu ta saki baki tana dubanta kafin tace “Waye kuma Kofur Zalimu a gidan nan ni Hindatu..” Ajidde ta aje Jakarta tana fad’in “Ahtoh.. Yanzu baki San Kofur Zalimu ba.. Chaabb ga gidansa ta can..!” Tai nuni da section d’in su Mu’azzam. Dariya ce ta kufcewa Mama Hindu kafin tace “Kice shi ya saita mun ke kika shigo a natse salin alin Babu hayaniya.. Fad’a min wace kalan wa’azi ya miki da ya shiga kanki tinda nidai babu kalan wacce ban jaraba ba..” Ajidde ta kuma k’wafa tana danna harara ma rufin kwanon b’angaren Mu’azzam kafin tace “Muguntarsu ta ‘yansanda mana.. Dama ance sunfi Soja iya makirci.. Yanda tufafinsu yake bak’i haka zuciyarsu ma.. Kai shiyasa ma duk suke bak’ak’e da k’yar kaga fari.” Mama Hindu tace “Toh ai shi Baban Inne nada haske idan baki saka sa layin farare ba ai bazaki saka sa layin bak’ak’e ba..” Har yanzu bakinta a ture yake “Ahap ai Farin fata ne kawai amma Zuciyar babu annuri.. Shiyasa kullum fuskarsa kaman an masa mutuwa..” Mama Hindu ta kuma murmusawa kafin tace “Aiko kinzo a daidai dan yanzu nake cewa bara na kirawo Ummilo tazo Ta kai masu abin kari kinga shikenan sai ki kai masu..” Ajidde ta zaro idanu tana aza hannaye saman k’irji “Ni wa..! Mama Hindu ki rufa mun asiri.. Ni wllhi kinga hanyar can ko cikin maye nake bazan yi gigin bi ba.. Bana fata wani abu ya had’ani da Kohur Zalimu.. Ko a k’iyama bana fata mu had’u..” Tai maganar tana nuna hanyar sashen Mu’azzam tana tofi da bakinta. Mama Hindu tace “Haba Ajidde Musulmi d’anuwanki kice baki fata ku had’u a k’iyama.. Kika sani ko ku shiga Aljannah lokaci guda..” Tai maganar cikeda barkwanci. Ajidde tace “Wa Tabb. Ai wllhi dan dai Malama Hafsah tace Babu kyau kai wa d’anuwanka musulmi mummunan addu’a bane da na masa addu’a..” Mama Hindu ta katseta da fad’in “Da kin masa addu’a kar ya shiga aljannah.. Haba Ajidde ko mai ya miki ai dai yaci albarkacin makusantarsa dake k’aunarki.” Ajidde ta jinjina kai tace “Ai sabida su ne ban masa addu’a ba.. Kinga matarsa ai Tanada kirki ni bansan mai ta gani wajen mugun nan ba k’ila tsawon da fankam fankam d’in ta gani dan dai naga itama farar ce tas kyakkyawa tama fisa kyau.. Sai Inne sai Mamy.. Sai...” Musaddiq tai niyyan ambata sai kuma bata ambata ba tai shiru. Mama Hindu ta girgiza kai tace “Banida lokacin shirirtarki Ajidde lek’a baya ki kira mun Ummilo..” Ta kuma rataya Jakarta kafin ta amsa ma Mama Hindu ta fice kiran Ummilo, tana tafe tana sand’a tana addu’an Allah Sa kar tayi mugun gani. ** Aunty Shemau ta mik’e tana fad’in “Toh Amarya.. Bara na barki ki huta dan nasan kina buk’atar hutun.. Kindai ji abinda na fad’a miki.. Ki d’aukeni tamkar uwa.. Dik abinda ya shige miki duhu a gidan nan ki sameni ki sanar dani.. Ni babu wata surkunta kinji koh..” Sadiya dai kanta a k’asa kurum take murmushi har Shemau ta ida bayanan ta. Saida takai k’ofa kafin Ta juyo tace “Allah ya kawo mana k’azantar d’aki da wuri..” Tai maganar tana duban Sadiyar kafin ta fice. Wulk’awarta Mu’azzam ya hango dan fitowarta kenan daga sashen Inne ya tsaya wajen Mamynsa. Ya k’araso ya tadda Sadiya na k’ok’arin mik’ewa. Tana ganinsa kaman wata marar gaskiya ta koma ta zauna da d’an k’arfi wanda har cikin kanta saida taji zafin zaman. Ta tamke idanunta tana sakin k’ara a hankali. Lokaci guda ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta. K’arasowa yai ya zauna gefenta kad’an. Ya d’an shigar da ita jikinsa ba tareda yace mata komai ba. “Kin mance ke patient ce zakiyi irin wann zaman..?” Ya fad’i mata cikin sigan rad’a saitin kunnenta. Ta kuma danne fuskarta da tafukan hannayenta cikeda kunya. Murmusawa yai kafin yace “Wai yaushe kika fara kunyata har haka ne.?” Ya d’anyi fasali kafin yace “Oya toh bud’e idon mu gaisa..” Ta mak’e masa kafad’a alamun a’a. Ya kuma sakin miskilin murmushi kafin ya sakalo hannayensa daga bayanta zuwa cikinta ya manneta jikinsa kad’an yace “Idan baza’a gaisheni ba Na yafe gaisuwan amma a bud’e mun kwalliyata na gani..” Ya k’arashe yana mata wasu salon da hannayensa wanda ya soma birkitata gaba d’aya. A tsorace ta sake masa kuka cikeda shagwab’a tana fad’in yai hak’uri ya k’yaleta. “Toh a bud’e mun kwalliyata a zauna lafiya..” Ya fad’i yana d’ago hab’arta kad’an. Ya jima yana dubanta kafin yace “Kin san wani abu..?” Ta girgiza masa kai a hankali. Yaci gaba da fad’in “At times sai yana mun kaman na tab’a sanin ki can da dad’ewa.. Like mun tab’a had’uwa a wani waje.. But I can’t remember when and where.” Tai masa tsuru tana dubansa itama yanda ya tsareta da idanu. Sai kuma ya murmusa yace “Kema kinji haka koh..?” Ta girgiza masa kai a hankali tana kuma duban kyakkyawan fuskarsa. Su duka biyun duban juna suke cikeda shauk’i. Murmushi taga ya saki mata kafin ya kashe mata idanu guda yace “See.. Nasa kin bud’e idanunki.. I worn..” Ya k’arashe yana sakin murmushi mai bayyana hak’wara. Pillow dake gefenta ta d’auka ta kai masa dukan wasa tana fad’in “That was cheating Inspector..” Ya kuma murmusawa kafin ya janyota jikinsa yace “Inada tactics da dama da zansa kiyi abinda baki shirya ba yarinya..” Ta kuma nitsar da kanta cikin k’irjinsa tana shak’an ni’imtaccen k’amahinsa, ta lumshe idanunta a hankali kafin tace “Because you are a detective right..?” Murmusawa yai tana nan cikin k’irjinsa, ya fashi gefen fuskarta kad’an kafin yace “Because you are my wife and I can read your mind..” Murmusawa tai wanda saida jikkunansu suka d’an motsa ba tareda tace komai ba. Ya saka duka hannayensa biyu yana mai kuma manneta cikin jikinsa had’ida lumshe nasa idanun shima. Dik wani zafin kan da ya kwaso daga wajen Musaddiq sai yaji ya yaye.. Ya nema ya rasa, sai wani sanyi da annashuwa dake ratsa duk wani mahudar gashi na jikinsa. Yanayi da zaice bai tab’a tsammanin zai riske sa a rayuwarsa ta duniya ba. Tabbas yana da damuwoyinsa da kuma abubuwan da yake ya cimma na rayuwa, amma zai iya cewa shigowar Sadiya cikin rayuwarsa ya sanyashi ji kaman ya cimma wani buri na rayuwa. Sannan ta cike wani gurbi da ya jima da gib’i cikin k’irjinsa. Bai tab’a koda hasasho kansa cikin irin wann rayuwar nan kusa ba ko ba don k’alubale da matsalolin rayuwa da yake fuskanta ba.. A’a kawai dan soyayya ba abar shi bace.. Kuma baida lokacinta. Hasalima kullum fad’ansu da Assad kenan.. Sai yana ji kaman rayuwa ta basa dama ne yai experiencing abinda ya jima yana k’aryatata yana kuma gudunta Wato soyayya.. na wani d’an k’ank’anin lokaci k’ayyadadde.. Yanaji kaman rayuwar bazatayi k’argo a haka ba domin kuwa Ita duniya ba komai bace face GIDAN ARO. Bai yarda akwai Farin ciki mai d’aurewa a GIDAN ARO ba kaman dai yanda nasa ahalin basu sami irin wann Farin cikin ba. Sun d’an d’auki lokaci a haka kafin ya ware idanunsa yana duban b’angaren dining area. “Have you eaten..?” Ya tambaya tana nan mak’ale cikin jikinsa. A hankali ta girgiza masa kai alamun a’a. “Oya tashi muje kici abinci you know you are a patient..” Ya k’arashe yana mik’ar da ita tsaye a hankali kaman mai tsoron kar Ta subce cikin hannunsa. “Can you walk..? Or should I carry you to the dining table..?” Ya tambaya still yana tallafe da ita. Marairaice fuska tai tace “Kai Inspector zan iya fah..” Ya d’an ja hancinta kad’an kafin yace “Alright just because you insist.. Ba wai dan inaso na barki kiyi tafiya da k’afarki ba..” “Come here zan tsaya daga bayanki dan kar ki fad’i..” Ya k’arashe yana kamota ya rik’eta a haka suka nufi dining table d’in kaman mai koya mata tafiya. A haka har suka isa sukai kalaci mai cikeda Farin ciki. Haka yinin ranan riritata ya dingayi kaman wata jaririya d’anyar goyo, itakam abin har mamaki yake bata dan bata tab’a zaton ko a mafarki ita dashi zasu kasance haka ba.. Bata tab’a zaton he can be as sweet as yanda yake tarairayata haka ba. Abu ne da a baya ko mafarki tai yanayi zata bud’e ido tace bazai faru ba.. Allah kenan mai gudanar da al’amari yanda yaso ba tareda shawarin kowa ba. A b’angaren Shemau kuwa waya Safeenah tai mata tana tambayarta abinda ke faruwa Fufore. Shemau taci gaba da fad’in “Meye ma bai faru ba Safeenah.. Ai komai ya faru..” Safeenah ta dafe k’irjinta tana fad’in “Aunty na shiga uku komai fah kikace..?” Shemau ta yab’e baki tace “Yo komai kai.. Duk wanda yake cikin gidan gonar nan a kunnensa komai ya faru jiya da dare.. Yau na shiga da sassafe domin na tabbatar da aukuwan hakan.. Yanzu haka maganar da nake miki yini Mu’azzam yai zubur yana tarairayar yarinyar nan. Keda kin gansa yau kinga sabon ango sharr har wani annuri goshinsa yake..” K’ara Safeenah ta saki tana fad’in “Na shiga uku na mutu na lalace..!” Ta kuma kurma wani ihun tana jifa da wayar. Shemau tai k’wafa tace “Bakiyi ihu ba ma sai kin ganta da tumbi d’ol.” Tana ida fad’in haka ta kuma k’wafa tana mai shigewa d’aki yanda ta tadda mijin nata kaman jiran shigowarta yake. “Da wa kika gama waya.?” Ya tambaya yana dubanta. “Banda shahshashar d’iyar D’anuwanka Safeenah.. Wai waya tayo tana tambayata mai Mu’azzam ke ciki.. Kasan ita akan Mu’azzam Sai ta iya halak’a.. Na k’unsa mata bak’in ciki kaman yanda uwarta ta k’unsa mana ta kasa mana amfani ta samo mana documents d’in nan..” Shiru Uncle Salman yai kaman mai nazari kafin ya murmusa ya kad’a ‘yar yatsarsa “Ahaan..! I have an idea..” Shemau Ta dubesa da mamaki kafin ta girgiza kai tace “Ban fahimceka ba mai kake nufi..?” Gyara zama yai yana duban Shemau kafin yace “Idan uwar bata mana amfani ba ‘yar zata mana..!” Ta kuma girgiza kai cikeda mamaki kafin tace “Hajara bata mana amfani ba sai Safeenah da kowa ya mata shaidan shashanci..” Uncle Salman yai wata muguwar murmushi kafin yace “Ki bar mace akan kishi duk dolancinta.. Tabbas Safeenah zata mana amfani fiyeda mahaifiyarta.. Tsaya kiji..” Shemau ta gyara zama sosai tana dubansa. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *50* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* “Dama muka samu Shemau da Zamuyi amfani da ita, Kinga na farko Safeenah d’iyar Marwan ce. Kuma ni nasan D’anuwana kaf cikin ‘ya’yansa babu wacce yake matuk’ar so babu wacce ta shiga zuciyarsa irin Safeenah.. Soyayyar da yake ma Safeenah yasa ya aura mata Mu’azzam dan haka itace key d’in mu idan munaso Documents d’in nan su dawo hannunmu.. Sannan bugu da k’ari Marwan ya jima yana preparing Safeenah dan itace zata gajesa a kasuwanci ba wann mahaukacin D’an nasa ba wanda baisan ina ya saka gaba ba... Saidai dukda shirya Safeenah da ya jima yana yi shashasha ce batada wayo.. Amma kuma mu yanzu zata mana amfani dan ita Keda access da Company.. Kuma tana matuk’ar son Mu’azzam wanda zata iya aikata komai domin Ta mallakesa.” Aunty Shemau ta d’anyi jim kafin ta girgiza kai tace “Mai kake so ayi yanzu..?” Ya murmusa kad’an kafin yace “Zata samo miki wann takardun daga wajen Mahaifinta ke kuma zaki mata alk’awarin mallaka mata Mu’azzam..” Da mamaki take dubansa kafin ta girgiza kai tace “Ka kuwa ji abinda kace.. Ta ina nakeda ikon mallaka mata Mu’azzam..?” “Wani sa’in kina abu kaman marar basira Shemau.. Shin baki samu yarda da amincewar mahaifiyarta ba a lokacin da kika zab’i zaki taimaka mata Nuratu ta bar gidanta..?” Shemau ta jinjina kai a hankali.. Ya kuma murmusawa kafin yace “Everything in life has a price. Zaki san yanda zakiyi ki raba wann yarinyar da Mu’azzam domin ya koma ga Safeenah... Ke kuma sai ta nemo miki wad’ann documents d’in in exchange.” Shiru Aunty Shemau tai kafin tace “Wann aiki ne mai matuk’ar wahala.. Farin cikin Mu’azzam kake cewa mu tarwatsa fah.. Sann mai zance ma Safeenah yanda bazata zargi D’an uwan mahaifinta ba.. Ina nufin kai kenan..” “I don’t give a damn idan zata zargeni muddin wad’ann takardun zasu dawo hannu na.. Kina magana kaman baki San mai duniya ke ciki ba.. Idan ta tona mana asiri kaman ta tona ma kanta ne tinda dole Mu’azzam zai San tareda ita aka had’u aka cutar da matarsa.. In fact mu sai mu jefata a ramin ma ta rufza ciki ita da mahaifiyarta da ta cutar da tasa Uwar.. Kinga Safeenah ta halak’a matarsa Hajara ta halak’a uwarsa shikenan mun zame kanmu cikin sauk’i... Just trust me Shemau wann shine kad’ai hanyar da zamu bi mu mallaki takardun nan..” Shemau tai shiru kaman mai nazari sai kuma ta jinjina kai tace “ Wai shin yaya wann Document d’in yake.. Ya kamanninsa yake..?!” Mik’ewa yai tsaye yana mai rungume hannayensa ta baya, saida ya bata baya kafin yace “Takarda ce doguwa cikin envelope mai ruwan k’asa.. Jikin takardan an rubuta wasu harrufa daga sama *BAT*.”. Lokaci guda ya juyo yana duban Shemau kafin yace “Ina so ta samo mun wann takardan mai d’auke da wad’ann harrufan.. Inaso Safeenah Ta samo mun BAT..!” Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai kafin ta jinjina kafin tace “Mai harrufan BAT ke nufi..? Kana nufin Jemage.?” Juyowa yai yana dubanta sai kuma ya saki murmushi yace “Kalmar BAT ba Jemage yake nufi ba, yanada ma’anarsa mai zaman kansa, kawai ki saka Safeenah ta nemo mana yanda mahaifinta ya adana BAT.. Ni kad’ai nasan mai haruffan BAT ke nufi dan ko Marwan baisan mai haruffan BAT ke nufi ba. .. Saidai watak’ila yanada masaniyar had’arin dake tattareda BAT idan har ya shiga hannu na, shiyasa ya mishi ajiya mai nisa ta yanda bazan cimmasa ba.. Amma yayi kuskure dan idan har ina numfashi sai na mallaki takardan BAT.” Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai kafin tace “Don Allah ka fayyace mun mai BAT yake nufi..?” Ta fad’i a d’an dame. Juyowa yai yana dubanta, murmushi saman fuskarsa, hannayensa hard’e ta baya. Lokaci guda yake furta “B for Bet, A for Agreement, T for Transaction..” Ya k’arashe yana sakin murmushi. Cikin rashin fahimta Aunty Shemau tace “Bet Agreement Transaction..” Ta girgiza kai kad’an kafin tace “Mai hakan yake nufi..?” Ya kuma murmusawa kafin yace “Bet yana nufin rantsuwar da Yayanmu Abubakar yai cewa baya buk’atar komai na daga inheritance d’in da mahaifinmu ya bari. Agreement yana nufin yarjejeniyar da mukayi nida shi cewa idan ina son nasa shares d’in zan iya had’awa da nawa kason duka na cinye. Transaction yana nufin transferring Assets d’insa kaf da yayi daga nasa sunan zuwa nawa sunan..!” Ya kuma karkatowa yana duban Shemau kafin yace “Shemau I badly need that document.. Kafin BAT ya isa hannun Mu’azzam hannuna ya kamata ya fara isowa.. You must help me find BAT..!” Ya k’arashe cikeda zak’uwa. Sauk’e ajiyan zuciya Shemau tai kafin tace “Shikenan zan saka Safeenah ta nemo mana takarda mai d’auke da kalmar BAT.. Toh amma idan ta tambaya na menene mai zance mata..?” “Bazata tambayeki ba muddin zata sami abinda take so Wato Mu’azzam..” Ya bata amsa kai tsaye yana dubanta. Lokaci guda yaci gaba da furta “Aiki zaki bata Ta nemo miki BAT idan har tana so ki taimaketa Mijinta Mu’azzam ya koma gareta..!” Yana ida fad’in haka ya zauna a mazauninsa. Shemau tai masa K’uri tana dubansa. Tunani fal zuciyarta, Anya mijinta bai zauce kan son abin duniya ba.? Bata gama warware qullin da suka had’awa mahaifiyar Mu’azzam ba itada Mommy yanzu gashi Uncle Salman ya kuma ingizata Ta k’ulla wa matar Mu’azzam d’in itada Safeenah.. Ga mahaifiyarsa ga matarsa Anya basu d’ebo da zafi ba..? Tinanin da ta dinga yi kenan har Uncle Salman d’in ya fice yana amsa waya. A hankali ta furta kalman BAT tana mai mik’ewa tsaye. ** Kwanci tashi babu wuya wajen Allah saida su Mu’azzam suka kwashe sati garin yana tarairayar matarsa had’ida bata wani irin kula na musamman, wata rayuwa ce da suke addu’an inama su tabbata cikinta babu yankewa. Dukda tsananin son sake kusantarta da yake bai bari yayi hakan ba, dan gani yake sam kaman bata warke ba. Saidai kusan koda yaushe suna nan mak’ale da juna tana zuba masa shagwab’a san ranta yana tarairayarta. Sannan su Umma kusan kullum sai sunyi waya taji lafiyarsu. Wayar Aunty Larai take kira dan bata faye samun na Umman ba. Tasan yanzu haka Umman ce bata son suke wayar tinda tarewarta kenan. Ta murmusa a hankali tana jinjina lamarin Ummanta. Yau tinda ta shiga sahen Inne bata fito ba, nan ta tadda Ajidde wajen Mamy, ta taimaka ma Ajidde suka bawa Mamy magani tare. Mama Hindu ta shigo tana tambayar idan sun gama bata maganin zata shiryata. Sadiya ta dubi Mama Hindu tace “Mama Hindu zan so na taimaka miki da shirya Mamy koda da gyaran sumarta ne.” Tai maganar cikin tsananin son ta taimaka. Mama Hindu ‘yaruwarsu ce sann tun auren farko da tayi mijin ya rasu nata sake aure ba take zaune nan gidan Inne hakan yasa take kulada Aunty Nuratun. Murmusawa Mama Hindu tai tace “Allah Sarki sai kika tuna min da marigayiya Ikram.. So tari kikan tuna mun ita.. Kunada wani yanayi mai shigen kama.. Itama haka nan idan naje can Abuja gidansu Ina kula da mahaifiyar tata musamman lokutan da take makaranta bata samun lokacin kula da mahaifiyar sai ta ce mun Mama Hindu ki barni na sami albarkan Mamy koda da gyaran sumarta ne.. Sosai kika tuna mun Ikram a yau..” Ta k’arashe k’walla na ciko idanunta. Murmusawa kad’an Sadiya tai k’walla na ciko idanunta itama, a hankali Ta furta “Allah sarki.. Allah yasa tana Aljannah.. Ubangiji yasa ladar jinyar mahaifiyarta da tayi ya risketa har cikin makwancinta..” Mama Hindu ta amsa da Ameen tana duban Mamyn. Lokaci guda take ci gaba da furta “Bata sani ba.. Bata San cewa d’iyarta ta rasu ba.. Zata farka ne ta tadda babu Ikram idan Allah ya nufa jinyar bana tafiya bane..” Ta k’arashe tana goge hawayenta. Sadiya daketa duban Mamyn itama goge nata hawayen tai kafin Ta jinjina kai tace “In sha Allah Mamy zata sami lafiya.. Kuma Allah zai d’agata... Allah zai sanya mata hak’uri da dangana cikin zuciyarta.. Zataima Ikram addu’a wanda zai bita har makwancinta.” Ta k’arashe tana mai dafa hannun Mamyn. Mama Hindu ta murmusa kad’an kafin tace “Allahu yashaa Sadiya.. A lokacin da Aunty Nuratu zata farka zata tadda babu d’iyarta Ikram amma zata tadda sabuwar d’iya Allah ya bata bayan ya amshe Ikram daga gareta.. Shi d’in shine mafi kyawun kyauta da kuma jin k’ai..” Sadiya ta murmusa tana dubanta daidai sanda Ajidde ta k’araso da ruwa da towel Sadiya na warware dogon gashin Aunty Nuratu da yake bak’ik’irin mai sulb’i da shek’i.. Wani ikon Allah duk tsawon lokacin nan da tai tana jinya sam sumarta bai cinye ba, yana nan da tsawonsa saidai abinda baza’a rasa ba. A tare suke gyara mata sumar itada Ajidde gwanin ban sha’awa Sadiya na nuna ma Ajidde abinda zata taimaka mata dashi, Yai tsaye daga bakin k’ofa yana dubansu yanda suke gyara mahaifiyarsa. Sai yaji wani abu can k’asar zuciyarsa na tsargar masa.. For the first time da yaji tsanar da yake ma Ajidde cikin zuciyarsa ya ragu.. Bai shiga ba haka nan bai tankasu ba sai gudanar da al’amaransu suke kaman wani Sun jima da sanin juna. Ya tuna kalaman Musaddiq cewa Wai yana son yarinyar kuma zai aureta.. A hankali ya janye idanunsa yana jin wayarsa dake aljihu tana vibrating. Abokinsa Assad ne mai kira. Saidai kafin ya d’aga kiran yaji Ta katse.. Yai tunanin ko network hakan yasa ya kuma danna kiran layin Assad d’in. Har saida wayar ta kusan tsinkewa kaman bazai d’aga ba sai kuma ya d’aga cikin yanayi na rashin kuzari. Daga yanayin da Mu’azzam ya jisa ciki ya fahimci akwai matsala, snn a ‘yan kwanakin ya kula Assad yana avoiding wayarsa, dan tinda yazo garin zai iya k’irga sau nawa sukai waya ba kaman da ba da ko yaushe suna nan suna waya da juna yana bawa Mu’azzam d’in updates.. Toh amma wnn karon gaba d’aya abokin nasa ya canza amma sai ya alak’anta hakan da cewar Assad d’in space yake basa yaci angwancinsa da kyau..Yasan tsiyar Assad yanzu haka wnn dalilin na iya Sa ya d’an janye masa k’afa har ya gama kwanakinsa a garin. “Ina jinka Wai meke damunka ne..?” Mu’azzam d’in ya tambaya yana ficewa waje. Assad ya d’an tamke idanunsa yana k’ok’arin daidaita bugun zuciyarsa. Lokaci guda ya d’an kuma fuzar da fuci kad’an kafin yace “It’s nothing.. Kayi enjoying hutunka kuma ka kula da Amarya.. Zan kashe wayar banjin dad’i ne..” Girgiza kai Mu’azzam yai yace “Wait Assad don’t hang up.. Wai meye ne ke faruwa.. Meke damunka ne..?” “I told you Babu komai... Stress ne kawai, zamuyi magana later ka gaida Amarya..” Yana ida fad’in haka ya datse wayar yana shafe goshinsa had’ida tattaro naman goshin. Wallet d’insa ya bud’e hoton d’iyarsa mai shekaru biyu a duniya ya bayyana. Take yaji wasu irin k‘walla na ciko idanunsa. Ya lumshe idanu ya sumbaci hoton, lokaci guda yake furta “Zaki girma cikin mutunci da muntatawa.. Bazan tab’a shafawa rayuwarki bak’in fenti ba bayan wanda mahaifiyarki ta Shafa miki.. Nayi alk’awarin b’oye miki dalilin rabuwata da mahaifiyarki cewa na kamata ne da wani.. Maiyasa zan bari wad’ann hotunan su watsu a duniya wanda za’a ajiye miki har girmanki.. Tarihi Ta kuma nuna miki cewa ga abinda mahaifinki ya aikata.. Tabbas ka girma ka tadda iyayenka mutanen kirki ne Dattawan K’warai ba k’aramin rahama bane da Allah zaiwa Bawa. Ban taso na tadda d’aya daga cikin iyayena mutumin banza ba bazanso ke ki taso ana nunaki ana fad’in ga abinda mahaifinki ya aikata ba. Idan har zan rufe miki abinda mahaifiyarki ta aikata Tabbas zan rufe miki wann.. Sweetheart inada zab’i ne guda biyu.. Kodai ki girma ki tadda mahaifinki na kurkuku kan laifin da bai aikata ba.. Ko kuma ki girma ki riski bak’in labari da zai shafi martabarki da sunan ki kan kuskuren da mahaifinki sam shima bai aikata ba..” Muryarsa yaci gaba da rawa yana jinjina kai yake duban hoton d’iyar tasa “Tsakani biyu dole na zab’i d’aya.. Dole na zab’i d’aya..!” Ya k’arashe yana kuma lumshe idanu a hankali. ** A b’angaren Mu’azzam kaw koda yai ta kiran Assad d’in bai d’aga ba yasan dole akwai abinda ke faruwa. Sann yanayin da ya masa magana ciki ya kuma tabbatar masa akwai abinda ke damun Assad d’in. Fuzar da fuci yai kad’an yana tunanin kiran layin Yusuf ya tambayesa abinda ke faruwa. Bai ida tinanin ba wayar Assad ya kuma shigo masa. Cikin sauri ya d’aga cikeda zak’uwa yana son jin meke wakana da Assad d’in. Daga d’aya b’angaren Assad yace “Mu’azzam.. There’s something I need to tell you..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Ehen go ahead ina sauraronka..” Assad ya kuma shafe fuskarsa yana mai fuzar da fuci a hankali “You see.. Bana so na b’ata maka wann lokaci mai mahimmanci na rayuwarka.. But I guess banida zab’i Mu’azzam..!” Ya kuma fuzar da fuci a hankali. Mu’azzam da yai shiru yana sauraronsa ya girgiza kai yace “Tell me Brother.. Meke faruwa, kar ka damu you can just tell me..” Ya d’an rintse idanunsa kad’an kafin ya bud’e yace “It’s... You see maganar bata waya bace.. I think zaifi kyau idan muka had’u.. But kar ka katse tafiyarka.. Idan ka dawo sai mu tattauna..” Girgiza kai Mu’azzam yai yace “No.. You sound serious Assad.. Zan dawo sai muyi maganar.” Assad yai k’ok’arin dakatar dashi amma Mu’azzam d’in bai saurari hakan ba, Assad d’in yasan bazai saurari hakan tinda yace zai dawo zai dawo d’in.. Zama Assad yai yana mai fad’awa cikin kujera k’irjinsa na masa nauyi. Ya dafe kansa yana fad’in “What have you done Assad..?” Lumshe idanunsa ya kuma yi kansa na masa wani irin nauyi. A hankali ya jinjina kai yana furta “Our job however, required us to put our minds over our fears. I must do this.. I have to do this..!” ** Misalin k’arfe 9:00pm suna zaune parlor, kanta saman cinyarsa tayi matashi da cinyar nasa hannunsa saman sumarta yana shafawa a hankali yayinda Sadiyar ke ci gaba da labarta masa barkwancin Ajidde da yanda take jin dad’in labarunta. Nan dai taga kaman hankalinsa baya wajen. Ta d’an mirgino tana dubansa “Are you alright..?” Ta tambaya tana dubansa. Ya saki miskilin murmushi a hankali yana mai jan hancinta kad’an da yatsun hannunsa “Why wouldn’t I bayan kina taredani.. Ga kuma Mamy na a nan ga Inne.. Mataye guda uku da sukeda matuk’ar mahimmanci a rayuwata..” Ta murmusa kad’an jikinta na kuma yin sanyi jin bai ambato Safeenah ba, ko maganarta bai tab’a yi ba tinda sukazo garin. Ta d’an gyara kwanciyarta sosai tana kuma dubansa “Safeenah fah..? Dan Allah bazakayi hak’uri haka nan ka maidata ba.. Kaga fah babu abinda ya faru babu wanda ta harba.. Dan Allah ka mata afuwa haka nan..” K’uri yai mata yana dubanta, sai kuma ya d’auke kansa kad’an “Kar ki sake mun zancen Safeenah..!” Abinda ya fad’i kawai kenan cikin tsananin tsimewa wanda har saida ya koma mata tamkar Mu’azzam d’in da ta soma sani. Jikinta ya d’anyi sanyi, ta maida kanta Ta kwantar, sai kuma ta dubesa kad’an ganin yanda ransa ya b’aci sosai. A hankali ta furta “Kai hak’uri bazan sake ba.” Bai ce mata komai ba Sai k’urama waje guda idanu da yai, al’amarin Musaddiq da Assad na kuma Yawo a kwanyarsa. Tun bayan data masa maganar Safeenah ta lura walwalarsa ya d’auke.. A nata zaton kan maganar Safeenah da tai ne ya maidasa haka saidai batasan cewa abubuwa ne da dama k’unshe cikin zuciyar mijin nata ba. Har wajajen k’arfe 11pm bai shigo ya kwanta ba, tana nan kwance k’walla tab idanunta tana tinanin kodai fushi ne yayi da ita..? Maiyasa bai shigo ba..? Can taji shigowarsa yana waya wanda takeda tabbacin da mutanesa na wajen aiki ne. “Alright Yusuf.. Eh gobe in sha Allah ina nan tafe.. Thanks for the update, Sai munyi magana..” Daga haka katse kiran yai ya k’araso saman gadon ya zauna yana kuma shafa wayar tasa. Sadiya tana jin haka ta rintse idanunta a hankali hawaye na gangaro mata, kar dai tafiya zaiyi.? Kardai fushin da yai da ita har ya kai wann matakin kan kawai Ta masa maganar Safeenah.. Kukan da take ta k’ok’arin dannewa ya soma fin k’arfinta. Ya daina abinda yake ya karkato kad’an yana dubanta. A hankali ya migrino kusanta nan saman gadon. Tana jin alamun k’arasowarsa kukanta ya k’aru. Bai furta komai ba Sai janyota dai cikin jikinsa, kaman wanda yace ta k’ara. Tana nan cikin jikinsa bai hanata kukan ba har dai kukan nata ya soma lafawa a hankali. Ya d’an d’ago fuskarta yana duba had’ida saka tafin hannunsa guda yana share mata hawayen “Tell me.. What happened why are you crying..?” Ya tambaya yana share mata hawayen. Ta d’an dubesa sai kuma ta girgiza masa kai. Ya gyara zamansa cikin gadon yana mai mata matashi da b’angaren jikinsa. Ya kamo yatsun hannunta guda yana murzasu cikin tafin hannunsa a hankali. “Tafiya zakayi ka barni..?” Ta tambaya cikeda rauni. Ya d’aura hannunsa guda saman sumarta yana shafasu a hankali “Kan wann kike kuka kike mu nasaran hawayenki masu tsada..? Kiyi hak’uri tafiyar ne ta taso min babu shiri. Naso na zauna mu k’arashi hutun mu tare but babu yanda na iya akwai ayyuka da suka taso mun.. And akwai wasu adjustments da nakeson yi kafin ki koma.. As soon as everything is done zan turo a d’aukeki..” Ta d’an dubesa kafin ta jinjina kai a hankali “Bakayi fushi dani ba..?” Murmusawa yai yana dubanta kafin ya d’an ja hancinta kad’an Sai ya kuma janyota jikinsa yana fad’in “Come here.” Ya mak’aleta cikin jikinsa ya matseta sosai yana shak’an k’amshinta. Idanunsa a lumshe yake fad’in “I’ll miss you Beautiful..” Tai kwance cikin jikinsa yana narkar da ita da kalolin k’aunarsa. Jin zancen ya soma canzawa ne ya sanyata saki masa kuka. Cikeda tsoron yanda tasha wahala first time. Kansa na nan saman k’irjinta, idanunsa a lumshe yake furta “It’s almost a week fah.. Nayi k’ok’ari ai.. Please ki barni muyi sallama..” Kuka ta kuma fashe masa dashi tana fad’in ita dai tsoro take. “Babu abinda zai faru I promise..” Ya fad’i yana kuma rikitata. Ta d’an turasa kad’an cikin dabara tace “Nifa bana sallah ma ashe.” Tai maganar duk a tsorace. Ya d’ago yana dubanta da mamaki kafin ya murmusa yace “Haba yarinya ma wa zakiyi wann wayon.. Ance miki bansan date d’inki bane..” Ta d’an waro idanu tace “Yaushe ka sani..?” Ya murmusa yana mai kuma janyota jikinsa “The very first time dana soma had’uwa dake.. A ranan kika sanar dani date d’inki..” Ya k’arashe yana mai kashe mata ido guda. Ta murmusa tana rufe fuskarta da tafukan hannunta, sai kuma ta d’an Ware idanun ta narkar da murya kad’an tace “Kai Inspector ni dai gaskiya bansan yaushe akai hakan ba..” Ya d’an janyota yana fad’in “Kin mance da mai kika jifeni first had’uwarmu..” Sai lokacin take recalling abubuwan da suka faru. Ta zaro idanu cikeda kunya sai kuma ta kifa kanta saman cinyarsa cikeda kunya tana fad’in “Na shiga uku Wai dama a kai nai jifan nan.. Innalillahi..!” Ta kuma danne kanta cikeda kunya tana maganar tamkar zata sakar masa kuka. Shiko sai k’ok’arin d’agota yake yana murmusawa. Sai wann lokacin take tuna abinda Safeenah tai mata data tura mata sanitary napkin a baki tace sai ta cinye.. Wato ashe Inspector ta jifa dashi ya tafi gida da abin har Safeenah watak’ila Ta gani..Kunya ya kuma dabaibayeta. “Dama nasan bakisan Kinyi haka ba. But ni tun a lokacin na rik’e date d’in nasan bazaki shige wann range d’in ba.. So you don’t have any excuse idan kuma ba rowa zaki min ba..” Ta marairaice fuska kaman zata saki kuka “Nidai tsoro nakeji..” Shima marairaice mata fuskar yai yace “Matar Inspector bata tsoron mission.. I promise you bazai kai wancan ba.. Trust me..” Ya k’arashe cikin nuna mata salon k’aunarsa. Iya juriya da dauriya kam tayi shi, saidai kaman yanda yace d’in bai Kai karon farko ba saima k’ok’arin maida masa Martanin k’aunar nasa gareta da take. Albarka ya dinga saka mata ya matseta tsam cikin jikinsa yana fad’in irin kewarta da zaiyi. Komai tare sukai itada Inspector d’in nata.. Kama daga wanka zuwa shiryawa dukda cewa da k’yar ta bari hakan ta kasance sabida kunya. Zallan k’auna mai tsafta had’ida tsayawa a rai yake nuna mata. Tabbas sunyi sallama mai tsayawa a rai da zai sakasu kewar juna matuk’a. Kafin Mu’azzam ya tafi saida ya bar mata amanan kanta da kuma Mamynsa. Sann ya sake dank’awa Inne amanar Sadiyar tasa. Kuka da shagwab’a kaw haka ta dinga narka masa da k’yar ya samu sukai sallama da k’udirin zata biyosa nan bada jimawa ba cikin yardar Ubangiji. Dan ba don aikin dake gabansa ba da k’afarsa k’afarta bazai tafi ya barta ba Amma babu yanda ya iya abubuwa suna neman fita out of hand tinda ya taho. Mu’azzam ya tafi ya barta da tarin kewa. ** Tinda Shemau ta sanar da Safeenah dawowar Mu’azzam d’in ta k’udiri niyyan komawa gidanta, sann wancan ‘yariskar Wato Sadiya kenan ta fita da fitar ta kaman yanda Aunty Nuratu ta fice daga gidan mahaifinta. Koda wasa bazata bari ‘yariskar can ta dawo mata cikin gida ba dan dama ta k’udiri alwashin gidanta tamkar dai GIDAN ARO yake a wajenta sai ta fice ta bar mata gida. Da wann tinanin Safeenah ta shirya tsaf ta nufi gidan. Saidai tana isa ta tadda kayan tashin hankali domin kaw kaf kayan gidan Mu’azzam yasa anata fito dasu, daga gani ma’aikatan company ne masu aikin interior design. Sai zuba sabbin furniture ake ana sealing nata cikin manyan cartons ana shiryasu a cikin wata k’atuwar mota. K’irjin Safeenah yai wani irin tsinkewa. A fujajan Ta nufi cikin gidan tana tambayan mutanen wanda ko kallo bata ishesu ba. “Ina zaku kai mun kaya..? This is my house.. Who ordered you to do this..? Kai magana nake maku..!” Bata kai aya ba taji sauk’an k’aton abu kusan k’afarta. Tai tsaye tana duban hoton aurensu da ya fad’o kusan k’afarta wanda ko shakka babu jefosa akai. Da mamaki ta d’ago tana duban Mu’azzam dake tsaye yana dubanta. Ta duk’a a hankali tana Shafa hoton auren nasu hawaye na gangaro mata. Lokaci guda ta mik’e tana girgiza kai tana hawaye. Ta isa wajen Mu’azzam a guje tana kamosa “My Halal.. Zaka canza mana tsarin gidan ne.. Please kar ka cire hotonmu ko sabon hoto kake so muyi a manna.” Tana maganar tana murmushi hawaye na zubo mata. “Safeenah, I’m not changing anything for you.. it’s over between us.. Kin fahimta..” Kuka ta fashe dashi gadan gadan tana girgiza kai tana hawaye “No it’s not over.. You are mine Mu’azzam..! You are my Halal bazan tab’a k’yaleka ba.. Kai nawa ne ni kad’ai.. My Halal please don’t leave me kaji. Wllhi ina maka son da banayi ma kaina..” Ta k’arashe tana kamo arms d’insa had’ida jijjigasa. “Enough Safeenah..!” Ya fad’i yana cire hannayenta daga jikinsa, yaci gaba da furta “This is not love Safeenah.. You don’t love me, you are just obsessed with me.. And.. And this is just a crazy feeling not love.. If you can point a gun at me mai kike tunani Safeenah.. zaki kira wann abun love.. Ba love bane it’s just an obsession.. Please Safeenah you need to accept this.. Kafin Azo ana danasani gwara ya tsaya a nan.. You are like a sister to me and I don’t want to hurt your feelings.. I don’t love you as a woman please..” Ya k’arashe cikin sigan kwantar da hankali. Zabura tai tana mai kuma fashewa da kuka ta ciccib’i hoton nasu tana k’ok’arin maidasa Majinginansa “You are just lying.. I know you love me kawai wancan ‘yar iska karuwarce Ta karkatar maka da tunani.. Tambad’add’iya wacce ta gama watsewa a layi.. Ba dole ka mance kanka ba taje tana maka abubuwan da karuwai matan layi keyi Wanda ni bana maka irinsu koh..!” Fincikar hoton yai ya kuma jifa dashi. Yana nunata da ‘yar yatsa cikin sakin huci “Don’t make me lose my mind Safeenah..! Kar ki sake kiran matata Karuwa.. Sabida matata sabuwa ce, first grade ce, fresh ce.. Sann ni ne mutum na farko da ya mallaki darajarta.. Idan akwai wacce za’a kira tambad’add’iya a nan wacce ta gama watsewarta a club da parties ba kowa bace face ke, kin zaci na yarda da labarin da kika bani ne cewa an miki fyad’e wajen party..?” Ya girgiza kai kafin yaci gaba da fad’in “I didn’t believe you one bit Safeenah.. Kar ki mance I’m a Detective na sani if someone is not telling the truth.. Na miki uziri ne na kauda kai sabida girman zumunci.. Amma kinata pushing d’ina, kinata yin wasu abubuwa baya albarka kike ci.. Zaman bazai yuwu ba Safeenah ya riga ya k’are.. Sann da Mommy take cewa kar na shafa miki cuta.. Ni ya kamata na guje ki dan kar ki Shafa min cutan da kike d’ebo wajen yawon parties da samaruka..!” Ya k’arashe idanunsa tar a kanta yayinda Safeenar tai tsaye tamkar wacce ruwa ya shanye tana zuban hawaye. “Zo ki fice mun a gida..!” Ya k’arashe yana nuna mata k’ofa. Cikin tsananin sanyin jiki ta nufo k’ofar tamkar wacce ruwa ya shanye. Saida ta kai k’ofa ya dakatar da ita. Hoton ya jifa mata bayan ya yage b’angaren nasa fuskar yace “You forgot this..” Safeenah na hawaye Ta dubi hoton sai kuma ta d’aga ido ta hangi ma’aikatan daga can sun ciro wani sabon hoto cikin frame suna k’ok’arin mannawa a wajen. Kuka bai kuma zuwa mata ba saida ta hangi hoton Mu’azzam d’inta da wancan tsinanniyar ce da suka d’auka a park irin Wanda Ta k’eta kwanakin baya shine aka lik’a a wajen anyi enlargement an saka cikin k’atoton frame kaman ka kirasu su Zo. A guje Ta fice daga gidan tana cazgan wane irin kuka tanaji kaman harda zuciyarta ne zai fito waje dan k’unci.. Banda tsanar Sadiya babu abinda ke ruruwa cikin zuciyarta. Bata da burin da ya wuce Sadiya Ta b’ace b’at daga rayuwarsu itada Halal d’inta. Ta shirya yin komai domin ta cire Sadiya daga cikin rayuwarsu. Ko menene kuwa matuk’a Sadiya zata zamto tarihi a garesu. ** Washe gari yake shirin shiga Office, saida ya kirata suka sha firan soyayyarsu kafin ya nufi office d’in. Tin daga nesa Maleeka ta tsaresa da idanu tamkar Zata lashesa. D’an kwana biyu da yai baya nan sai taga ya k’ara mata gizo da wani kyau na musamman. K’warjininsa ya kuma bayyana, ya sake zama wani cikakken namiji mai cikeda Charisma. Wutan k’aunarsa Sai ya kuma ruruwa cikin zuciyarta. Hardai zata dinga ganin Inspector Gamji Tabbas k’aunarsa bazai ragu cikin zuciyarta ba. Take kuma zuciyarta yai wani irin yankewa tana tinanin kar ya tambayeta progress kan Assignment d’in da ya bata. Tana jin sanda suke gaisawa da Yusuf, Yusuf na basa wasu updates d’in. Ta kifa kanta a k’asa zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Bak’ak’en covers d’insa ne idanunta suka sauk’a bisa alamun ya k’araso gabanta. Ta d’ago da k’yar ta dubesa. Sai kuma ta sara masa tace “Sir, welcome back.!” Ya tsareta da idanu ba tareda yace komai ba alamun yana examining nata. Zufa ne kurum ke karyo wa Maleeka dan gani take Inspector Gamji ya ganeta an gama. “Have you found the mole..?” Ya tambaya a d’an tsare. Zuciyar Maleeka ya kuma tsinkewa. Ta kasa furta koda kalma. Ya kafeta da idanunsa masu rikitata had’ida bata tsoro. Cikin k’ok’arin had’o kalamai take furta “I.. I.. I’m still working on it.. Sir..” “You know the mole.. Juts admit it..!” Ya fad’i cikin dakewa tareda k’ok’arin tsoratar da ita dan ya fito da gaskiya daga bakinta. Ta shiga girgiza kai tana fad’in “Sir.. Sir I.. I swear I don’t know what you are talking about.!” “You are their accomplice. You are the traitor here in our team.. You are the one betraying the CID...You are working with those criminals.. You are the one giving them information.. Just admit it now..!” Ya k’arashe cikin tsananin daka tsawa yana dunk’ule hannayensa tamkar zai damk’ota. Irin yanda sukeyi idan suna son tilasta mutum yai magana. Maleeka Ta fashe da kuka tana girgiza kai. Jikinta na tsananin rawa sabida tsoro da tashin hankali. Daidai lokacin Assad ya turo k’ofa ya shigo. “Mu’azzam we need to talk now. There is something you need to know..!” Assad ya fad’I daga nan yanda yake tsaye. Mu’azzam ya d’ago yana duban Assad d’in da yanayinsa. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *51* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cak Mu’azzam ya mik’e yana duban Assad dake shigowa cikin room d’in. Ya tsaresa da idanu sosai yana jiran yaji abinda zaice. Suma Maleeka da Yusuf kallo suka bisa dashi suna jiran jin meke tafe dashi babu kaman Maleeka wacce tai masa K’uri zuciyarta na tsinkewa. Assad yai tsaye gaban Mu’azzam su duka biyun suna duban juna. Idanun Assad suka sauk’a kan handcuff dake aje saman table.. Lokaci guda ya mik’a hannunsa ya d’auko handcuffs d’in kana ya d’aga sama yana nunawa daidai fuskar Mu’azzam. Mu’azzam ya girgiza kai kad’an cikin rashin fahimtar abokin nasa. Assad ya jinjina kai kafin yace “Handcuff me..” Yai maganar yana mik’awa Mu’azzam handcuffs d’in. D’an murmusawa Mu’azzam yai irin murmushin da yake idan Assad yana wasu shirirtarsa a cewarsa. “Yau kuma da irin wann wasan kazo...?” Girgiza kai Assad yai cikin tsananin dakewa “I’m serious Mu’azzam.. You need to arrest me.. I’m here to confess.. I’m here to turn myself in..!” Ya k’arashe yana mik’o hannayensa duka biyu wa Mu’azzam d’in. Maleeka da Yusuf suka dubi juna cikeda mamaki yayinda Mu’azzam d’in ya kasa janye idanunsa daga duban Assad. A hankali yaji fatan bakinsa yana furta “What are you doing Assad..? What is all this..?” Assad ya bud’e murya yace “This is nothing but the truth, Mu’azzam.. Arrest me now.. Just do it..!” Ya k’arashe yana kuma d’ago hannayensa yana mik’awa Mu’azzam d’in. “Have you gone mad.? Ka kuwa San abinda kake fad’I? Maiyasa Zanyi arresting d’inka .. What’s wrong with you Assad.. Wannan ba wasa bane kafi kowa sanin hakan..!” Cikin fad’a fad’a Shima Assad d’in ke fad’in “Na sani.. K’warai na sani.. Kuma nima ba k’arya nake maka ba.. Ba wasa nake ba.. Gaskiyar kenan Mu’azzam.. I’m the rat in our group.. I’m working with Danger.. I’m his accomplice.. Ni ne nan nake cin dunduniyarka Mu’azzam..! Ni nake maka zagon k’asa.. Arrest me now..!” Ya k’arashe hawaye na fitowa daga idanunsa. Girgiza kai kurum Mu’azzam yake yana jin bugun zuciyarsa na ninkuwa cikin dak’ik’a.. Lokaci guda yake girgiza kai alamun a’a ba haka bane. A hankali bakinsa ke furta “No.. That’s not true.. It can never be true.. You are just joking around kaman dai yanda ka saba..” Ya k’arashe murmushi mai ciwo saman fuskarsa. Duban Yusuf Assad yai kafin yace “Takedown my statement now.. Take it down..!” Yusuf yai pause yana duban ikon Allah.. Yayinda Mu’azzam wanda ya koma tamkar ruwa ya shanye yaci gaba da duban Assad d’in cikin rashin yarda. Kafin Yusuf ya soma rubutu Mu’azzam ya dakatar dashi da fad’in “Don’t write anything down Yusuf.. He’s gone crazy.. Ina ganin hakan daga k’wayar idanunsa.. He’s just lying.. Baya aiki da Danger.. I know my brother can never do such a thing..!” Murmushi mai ciwo Assad ya saki yana jinjina kai yake duban Mu’azzam d’in kafin yace “You don’t want to believe me right.. Then zan tafi wajen Chief and confess everything to him..!” Yana ida fad’in haka ya fice gumi gauraye da hawaye saman fuskarsa. Cikin tsananin tashin hankali Mu’azzam yabi bayansa yayinda Yusuf ya take masu baya shima hankali tashe. Suna ficewa Maleeka Ta goge hawayen idanunta, tana mai sakin murmushi ta zauna saman kujera tana juyi a hankali zuciyarta wasai “Good.. Good job Detective Assad.. Lallai kayi tunani mai kyau.” Kafin su Mu’azzam su cimmasa ya isa Ofishin Chief ya soma confessing cewa shine spy d’in Su Danger. Mu’azzam yaja ya tsaya Cak yana duban Assad da Chief. Chief ya girgiza kai irin yana mamaki d’in nan kafin yace “Shattima are you aware of what you’re saying.?” Assad ya had’iyi throat d’insa ya jinjina kai “Yes Chief.. I’m their accomplice.. Ni nake masu aiki a nan CID..” D’agowa Chief yai ya dubi Mu’azzam dake tsaye “Inspector Gamji.. Did you hear that..?” Mu’azzam bai cewa komai ba sai duban Assad kurum da yake cikin rashin yarda. Chief ya k’ara kiran sunan Mu’azzam “Inspector Gamji, are you going to interrogate him..?” Nan ma Mu’azzam bai iya furta komai ba Sai duban Assad d’in kurum da yake. Chief ya dubi Yusuf yace “Take him away.. Jail him Yusuf ya jinjina kai da k’yar had’ida sarawa Chief kafin ya janyo Assad. Mu’azzam kam tamkar wanda ruwa ya shanye haka ya koma har aka shige da Assad. Muryar Chief ya sinkayo bayan ofishin ya rage saura su biyu. Chief yana tsiyaya ruwan a gora cikin cup yake fad’in “So unfortunate mutumin da ka aminta dashi yaci amanarka. Who would’ve ever thought Shattima zai zamto traitor..” Ya k’arashe yana kurb’e ruwansa dake cikin cup. Mu’azzam ya tako gabansa yana dubansa, ya jinjina kansa a hankali yana murmushi, lokaci guda yake waina d’an k’aramin metal clock da aka k’awata table d’in da yatsun hannunsa “My friend is not a rat.. He’s not a criminal.. I’m pretty certain wani ne ya tilasta masa yin hakan because I know exactly how things work here.. And believe me, who so ever did this to my friend.. that person is going to pay.. Zan kama shi ko shi wanene.. And I’ll clear my friend’s name.. Ka rubuta hakan ka ajiye, Chief.!” Yana ida fad’in haka ya fice yana shafe fuskarsa cikin tsananin damuwa da tashin hankali. Da mugun kallo Chief ya rakasa yanaji kaman ya damk’o wuyarsa ya gama dashi once and for all. Wani kujera dake waje ya samu ya zauna, ya kifa kansa a k’asa yana jin k’irjinsa na masa nauyi. Statement d’in Assad kurum yake saurarowa. Ya fuzar da fuci kad’an yana shafe fuskarsa.. Maleeka data hangosa zaune shi kad’ai cikin sauri ta k’arasa garesa, tana isowa ta kifa kanta kad’an kafin ta k’arasa d’aya kujeran ta zauna. Lokaci guda tai gyaran murya kad’an “It so painful.. I never thought mole d’in nan zai kasance daga cikin team d’inmu.. Na kasa gano wanene ke mana zagon k’asa Ina can inata cincike cikin Department d’inmu ashe yana nan kusa damu... Detective Assad of all people.. Kai hak’uri idan ban ida assignment d’in da ka bani on time ba.. Kamo mutum irin Assad abu ne mai matuk’ar wahala idan ba shi yai confessing d’in ba.” D’agowa Mu’azzam yai yana dubanta na d’an lokaci kafin yace “Get out of my sight.!” Maleeka tai rau rau da idanu tana dubansa. Ya kuma furta “Ki b’ace mun daga gani before I lose control..” Zumbur ta mik’e ganin yanayin da Yai maganar ta bar wajen tana waigowa tana dubansa. Mik’ewa yai shima yana kiran wayan Yusuf. Yusuf ya k’araso suka keb’e. Lokaci guda Yusuf ke girgiza kai “Ban yarda ba nima akwai wata a k’asa.. From the way he talks zaka fahimci akwai wata a k’asa.. Wann abun shiryawa akai.” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Na sani Yusuf.. Shiryawa sukai don su b’atar da Assad sabida wata manufa nasu.. But bazamu bari hakan ya kasance ba.. Among the three of us Assad yafi saurin yarda da mutane.. I’m quite certain taking advantage kindness d’insa sukai..” Yusuf ya girgiza kai yace “But Maiyasa zasu sa Assad ya D’auki laifin nan.. What could be their motive.” “It’s pretty obvious so suke su rabamu sai suka b’ullo ta wann hanyar.. But believe me bazan tab’a bari hakan Ta kasance ba.” “Kana tunanin Jaja ne yai haka..?” Duban Yusuf yai kad’an kafin yace “Not only Jaja.. Ai sabida Nasan akwai wanda ke ratting information a team d’inmu shiyasa nai assigning Maleeka Ta kamo mana Rat d’in.. Wann yarinyar inada tabbacin tana aiki dasu Jaja.. Kasancewar banida cikakken shaida a hannuna shiyasa nai assigning nata ta zamto cat d’in sann tayo mana farautan Rat d’in.. You know banida ikon da zanyi accusing nasu koda inada tabbaci akansu har sai inada tangible evidence. That’s why I assigned her to catch that rat. idan ta rufta ciki ni kuma sai nai amfani da damar na kamata redhanded daga nan kaga zata fito da accomplices d’inta.” Yusuf ya jinjina kai yace “Yanzu miye abin yi..?” Mu’azzam ya nusa kad’an yace “We need to clear his name Kafin a gabatar dashi gabansu DIG, kafin a gudanar da wani zama akansa we have to make sure yayi retracting statement d’insa.” Yusuf ya jinjina kai yace “Fad’a mun nawa part d’in zan kula dashi..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Akwai wani asibiti da Nayi DNA test na B.A.T ban yarda da sakamakon gwajin ba. Ina so kaje wann asibitin ka gudanar da bincike na sirri ka gano idan anyi tempering wann result d’in ne..” Ya k’arashe yana mai ciro wayarsa ya nuna masa asibitin. Yusuf ya jinjina kai yace “I’ll investigate kar ka samu damuwa..” Jinjina kai Mu’azzam yai kafin ya dafa kafad’an Yusuf yace “Thank you.” Yusuf ya jinjina masa kai suka nufo building d’in a tare. Cell d’in da aka aje Assad ya nufa. Yai tsaye yana duban Assad d’in daga can nesa yanda yai zaune ya had’e k’afafunsa waje guda kansa kife a k’asa. Cikin tsanaki ya tako ya k’araso k’ofan cell d’in. Assad ya d’ago ya dubesa kad’an yana jin zuciyarsa na masa nauyi. Sai kuma ya kauda kansa kad’an. “Did they threaten you..? Did they force you to take the blame..?” Mu’azzam ya tambaya yana duban Assad d’in. Murmushi mai ciwo Assad yai kafin yace “I don’t know what you are talking about Inspector.. Na riga da na bada statement d’ina.. Mai kuma kake nema..?” “Tell me mai sukai amfani dashi sukai threatening naka..?” Mu’azzam ya kuma jefo masa tambayar. Idanun Assad naga wani b’angaren yake fad’in “Is that how you interrogate a criminal Inspector..?” Mu’azzam ya tsaresa da idanu yana fuzar da fuci kad’an. Lokaci guda yake jinjina kai still yana duban Assad d’in “Ka mance cewa We might have different personalities but we have the same profession.. We both know ba gaskiya kake fad’i ba Assad.. Dani da kai duk munsan haka.. Zaifi kyau idan ka sanar dani gaskiyar komai.” Wann karon mik’ewa Assad yai yana sakin huci ya k’araso jikin k’arafunan cell d’in. Ya rik’esu suna duban juna shida Mu’azzam d’in. Lokaci guda yake jinjina kai idanunsa akan Mu’azzam d’in “Idan har ka yarda munada profession d’aya then you are abusing your profession.. Baka San aikin ka ba.. Idan har kana tunanin akwai yarda mai k’arfi tsakaninmu wanda zaisa bazan iya cutar dakai ba.!” “Shut up Assad.!” Ya katsesa da fad’in haka kafin yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “You’ll retract your statement Tun kafin ya isa sama.. Did you hear me..” Murmushi mai zafi Assad yai kafin yace “Who do you think you are Mu’azzam Gamji. Kai dole kowa Sai ya yarda dakai yabi abinda kake so.. Well you are mistaken wann karon bazanbi ra’ayinka ba.. Wnn shine gaskiyar ka yarda ko kar ka yarda.. Ni ne nan B.A.T d’in da kake nema..!” Ya k’arashe idanunsa na kad’awa. Mu’azzam bai kuma cewa komai ba Sai duban Assad d’in da yakeyi.. Ya jima yana dubansa Assad d’in wanda tuni ya koma mazauninsa ya zauna. Bai kuma cewa komai ba Sai ficewa da yai cikin tsananin sanyin jiki lokaci guda yana tuna sa’insansu da Musaddiq wanda yai shige da na Assad d’in.. His two best friends sun juya masa baya.. Maiyasa bazasuga abinda yake gani ba..? Maiyasa suke basa mummunan fassara.. He wants nothing but the best ma dukansu biyun.. Shin laifi ne hakan..? Ya dafe kansa kad’an yana zama saman kujera. A hankali ya maida bayansa ya kwantar zuciyarsa na fad’i masa cikin tattausar Murya “Kyakkyawan aiki shine aikin da baka neman yarda ko amincewar wani sai na Allah.. Keep being you koda hakan zai masu zafi.. Da sannu zasu fahimci komai daki daki..” Ya k’arashe zancen zucin nasa yana mai sakin murmushi.. Tinanin da yai yanzu da lumshe idanun da yai ji yai tamkar kalamanta ne yakeji cikin kunnuwarsa cikin yanayin sautin ta mai dad’in sauraro.. A halin yanzu babu abinda yake so face ya kasance da ita.. A fili ya furta “My beautiful stubborn head.. I miss you so much.. And I need you so badly..” Ya k’arashe yana mai lumshe idanunsa. Mik’ewa yai. Daga nan bai zarce ko Ina ba sai Company wajen Daddy. ** Assad kaw Mu’azzam na ficewa silalelewa yai ya zauna yana jin rauni na kuma taso masa. Ya lumshe idanunsa kad’an yana furtawa a hankali “I’m sorry Mu’azzam.. Kai hak’uri abokina.. Na fad’a tarkon mace.. Bazan iya Barin wann kayan tashin hankali ya riski d’iyata ba.. Idan Annabin Allah Annabi Yusuf (AS) zai tafi Kurkuku ya shafe shekaru sabida kaidin mace kan laifin da baiji ba Bai gani ba Toh ni wanene da bazan zab’i zaman kurkuku ba.. Kai hak’uri Mu’azzam nima na zab’i na tafi kurkuku akan mutuncina da na ahalina harma da d’iyata.. Kai hak’uri Abokina.. Na tabbata idan har banida laifi akwai ranan da Allah zai wanke ni kaman yanda ya wanke bayinsa na K’warai da aka masu k’age bayan tsawon shekarun da suka kwashe a kurkuku.!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa. ** FUFORE Zaune take gefen Aunty Nuratu tana yanke mata faratunta. Bayan Ajidde ta gama bata ruwan addu’a an shafe mata sauran a goshinta. Sadiya ta k’ura ma fuskarta ido tana kallon kaman tasan mai yanayin kamanninta saidai sabida rama na jinya da fuskar tai sai kuma tana Ganin k’ila dai ta tab’a ganin wata mai kamanninta ne. Ta kuma d’ago nails d’insa da fingers d’in tana dubawa tana juyasu a hankali.. Itakam tanajin wani irin Al’amari gameda Mamy.. Kaman ta tab’a saninta a wani wajen na daban.. Sann tanajin comfort da wani natsuwa na musamman idan tana tareda ita.. Ta murmusa kad’an tana mai aje mata hannun nata cikin zuciyarta tana fad’in dole ma taji natsuwa a kusanta ko Dan kasancewarta mahaifiya ga mijinta abun k’aunarta. Mutumin data farà sanin menene so akansa.. Sai yanzu take yarda da zancen Sabeera cewa duk samarukan da tai a baya babu wanda ta tab’a so.. Kuma dan dai abin hannunsu take so shiyasa take ganin kaman babu wani kalma mai suna soyayya sai idan zaka sami abun Duniya.. Yanzu da Ta had’u da Mr Inspector ta yarda akwai soyayya sosyya irin wanda zaka so mutum kaji shid’in kake so koda bai mallaki wani abu na k’yale k’yalen duniya ba.. Sannan zaka iya kasancewa dashi a duk yanayin da ya tsinci kansa.. Irin wann soyayyar take ma Inspector. Ta murmusa kad’an tana mai gyarawa Mamy kwanciyarta. Aunty Shemau dake tsaye bakin k’ofa tana karantarta jinjina kai tai a hankali kafin tasa kai ta shige. D’aki ta koma ta soma tunanin ya kamata ta binciki Sadiya taji inane asalinsu.. Garinsu da danginsu muddin tana so hak’arsu ya cimma ruwa.. Batasan dalili ba amma ganinta tareda Nuratu yasa taga zubi da yanayin Ikram a tattareda yarinyar.. Idan har Nuratu zata sami wacce zata maye mata gurbin Ikram Tabbas hak’ar mijinta na mallakan dukiyar nan bazai cimma ruwa ba. Toh amma a halin yanzu ba Nuratu ce damuwar ba, yarinyar itace damuwar tinda da Safeenah zasuyi amfani ba da Mommy ba. Da wann tunanin ta mik’e tana zagaye d’akin tana tinanin Ta yanda Zata b’ullowa al’amarin. Zama tai saman gado wani b’angare na zuciyarta na tuhumarta “Shin mecece ribar ganin bayan wani..? Shin wace riba zaki samu a nan duniyar idan kika cutar da wani..? Duniyar da ba komai bace face GIDAN ARO..” K’ok’arin kauda tinanin tai da fad’in “Zan sami yarda da amincewar miji na..” Da wann tinanin ta soma neman layin Safeenah saidai sam ba’a d’agawa.. Kiran duniya Aunty Shemau tayi baa d’aga wayar ba. Tai gajeren tsaki tana aje wayar gefe. ** Mu’azzam na shigowa Company ya hangi Daddy ya nufo parking lot Sai sab’a babbar riga yake yana fad’in gashi nan tafe. Ko sauraron driver baiba ya shige motar da kansa ya soma driving. Kai da ganin yanayin da Daddy ke ciki kasan babu lafia. Cikin sauri shima Mu’azzam d’in ya karya kan mota yabi bayansu. A hankali ya dinga bin bayan motar Daddy.. Saidai baisan ya akai ya nemi motar Daddy ya rasa a holdup ba. Ya fuzar da fuci yana tunanin ina Daddy ya nufa. Ya shafi goshinsa kad’an yana jin motar bayansa na masa horn. Daidai lokacin wayar Inne ya shigo masa. Gaisawa sukai kafin daga d’aya b’angaren Inne tace “Shin bazaka turo ka d’auki matarka ba Modibbo.. Zaman ai ya isa haka nan.” Ya d’an rage girman idanunsa kad’an kafin yace “Shigowata Company kenan ma, Zanyi magana da Daddy inaso a bani driver.. Idan yaso ko zuwa gobe sai ya taho jibi su dawo in sha Allah..” Inne Ta jinjina kai tace “Hakan yayi, zan nemi ‘yar tayin zaman Mota a nan cikin ‘yanuwa sai ta mata rakiya..” Ya jinjina kansa a hankali yace “Shikenan Inne gobe in sha Allah Adnan zai taho gobe in sha Allah.. Daddy ya fice van samu nayi magana dashi ba amma zan sameshi a gida ko zuwa dare.” Inne Ta jinjina kai tace “Yayi.. Allah shi maku albarka..” Daga haka katse sallama suka kafin Inne ta katse kiran. Haka dole ya canza hanya Fuzar da fuci ya kumayi kafin ya soma tunanin tunanin zuwa gidan Daddy. A k’ofar gidan ya had’u da Meema da Kiki na zaune gefenta an bud’e masu gate suna fitowa. Suka taho zasu shige Meema ta sauk’e glass suna gaishesa. “Ina zaku..?” Ya tambaya yana dubansu. “Asibiti zamuje wajen Addah Feenah..” Meema Ta basa amsa da fad’in haka. “Safeenah kuma..? Mai ya sameta..?” Meema da Kiki suka dubi juna. Mu’azzam ya katsesu da fad’in “Bakuji tambayar da na maku bane. mai ya sameta..?” “Tasha poison ne Wai zata kashe kanta shine Mommy ta tsinceta a d’aki tana aman kumfa.” Cewar Kiki. Yai shiru yana jinjina maganar kafin yace “Wani asibiti take.?” Meema Ta fad’a masa asibitin. JInjina kansa yai kafin ya basu hanya suka shige. Kai tsaye shima hanyar asibitin ya d’auka. Tare tare suka iso asibitin dasu Meema. Daidai lokacin motar Daddy ma ta shigo asibitin. A fujajan Daddy ya nufi cikin asibitin bayan su Kiki sun Shige, hankulansu duk a tashe. A natse ya fito daga nasa motar ya nufi cikin asibitin yanda ya hangosu carko carko k’ofar Emergency. Mommy tana hangosa ta nufosa tana fad’in uban mai ya kawosa bayan shine silan shiga tashin hankalin da d’iyarta ke ciki. Ta rufe idanu ko tunanin asibiti ne batayi Ta yanda take shiga bata nan take fita ba saidai Mu’azzam ya fice daga asibitin. Da k’yar Mommy ta daina borin da take saida Daddy ya kusan fice mata a giya. Mommy na hawaye take duban Mu’azzam lokaci guda take dubansa tana fad’in “Idan na rasa Safeenah bazan tab’a yafe maka ba..” Tana kuka take ci gaba da fad’in “Bayan duk abinda nai ma mahaifiyarka a rayuwa abinda zaka saka min dashi kenan Mu’azzam.. I spent half of my marriage life ina d’awaniya da jinyar mahaifiyarka.. Wllhi nayi imani da Allah idan na rasa Safeenah bazan tab’a yafe maka ba..” Ta k’arashe cikin kuka. Daidai lokacin Dr ya k’araso yana fad’in Safeenah tayi regaining consciousness.. Gaba d’aya suka bi bayan Likitan idan ka d’auke Kiki da Meema wanda dama basa tsaye wajen. Suna K’arasowa k’ofa Mommy tace atafau Mu’azzam bazai shiga ba. Bai forcing ba, ya dubi Daddy yaima Safeenah fatan samun lafiya kafin ya fice daga asibitin. Suna shiga cikin d’akin da kuka Safeenah Ta fara masu tana ambato her Halal. Mommy takaici kaman ta shak’o Safeenah dake saman gado tana kuka tana fad’in Ina her Halal yake. Daddy ya k’arasa ya rungume kan Safeenah dake zaune saman gado cikin jikinsa. Lallashinta ya dinga yana k’ok’arin calming nata kafin ya zauna gefenta. Cikin kuka Safeenah ke ci gaba da fad’in “Daddy I love him.. I can’t live without my Halal..” Mommy dake gefe tsawa ta darara mata da fad’in “Kika sake ambato wani my Halal a nan sai na halarta ma tafin hanuna fuskarki.. Sai na shata miki mari Safeenah. Shashasha kawai wacce bata San yanda ke mata ciwo ba.” Safeenah Ta kuma fashewa da kuka yayinda Daddy ya aikawa Mommy mugun kallo “Fita ki bamu waje Hajara.” Ya fad’I yana duban Mommyn. Cika kurum Mommy take tana fuci kafin tai k’wafa tasa kai fuu ta fice. A k’ofa Ta had’u da Dr rik’eda file d’in Safeenar.. Ta dubesa tace “Yaya..?” Likita yace “Report d’in Safeenah ne..” Mommy Ta nuna masa hanya tace “Muje ka sanar dani ni ce nan mahaifiyarta.” Dr ya d’an dubeta sai yace “Mijinta fah.?” Mommy tace “Sun rabu basa tare. Zaka iya sanar dani komai..” Ya d’an jinjina kansa kad’an kafin ya nuna mata hanya yana fad’in “After you.” Mommy tasa kai Dr ya take mata baya. A cikin d’aki kaw yanda Safeenah ke kwance Daddy yaci gaba da mata nasiha da fad’in “What were you thinking Safeenah.. Shin Kinsan matsayin wanda duk ya kashe kansa a addini.. Kafuri fah ya mutu Safeenah.. Shij kinaso ki mutu kafura..? Mai zai sa ki hallak’a kanki kan soyayya. Kwanakin baya kin tasamma halak’a matar Mu’azzam yanzu kuma kina yunk’urin halak’a kanki.. Kan wani dalili Safeenah..!” Cikin kuka take fad’in “Daddy tambayata kake kan wani dalili bayan kasan dalilin son Mu’azzam ne.. Ni dai Daddy gwara na mutu kan na rasasa..” Daddy ya girgiza kai yace “Mu’azzam doesn’t love you Safeenah. Learn to accept this.” Safeenah Ta kuma girgiza kai tana hawaye “My Halal loves me Daddy.. He loves me.. I know he does.. Kawai dai wancan muguwar ce ta rabamu.. Daddy you need to help me please.. Dan Allah ka masa magana Daddy.. Yana jin maganar ka.. Dan Allah Daddy kace ya maidani..” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka. Daddy ya lumshe idanunsa a hankali yana mai tura hularsa baya kad’an. Harga Allah ya soma gajiya da halin Safeenah akan Mu’azzam. Ya kula tana ma Mu’azzam son da bazata iya yakicesa cikin zuciyarta ba. Daga wnn sai wancan. A can office d’in Dr kuwa da tsananin mamaki Mommy ke dubansa, ta d’an girgiza kai tace “Kace she’s 4 weeks pregnant.?” Dr ya jinjina kai yace “Gwaji ne na jini wanda ko cikin Kwana guda ne jikinta zai nuna. Mommy tai shiru tana jinjina kai tana tuna tarewar Safeenah gidan Mu’azzam wata guda kenan harda kwanaki. Muryar Dr ta sinkayo yana ci gaba da fad’in “Luckily cikin bai fice ba amma yana iya zuwa da tangard’a sai a kula da ita sosai kar irin abinda ya faru da ita yanzu ya kuma faruwa.. Dan komai ka iya faruwa.” Mommy Jiki babu kuzari ta jinjina kai tace “Za’a kula da ita Dr. Kuma haka bazai sake faruwa ba.. Amma Likita inaso maganar nan ya tsaya tsakaninmu kar kowa yaji harda ita Safeenar duba da yanayin halinda take ciki.. Nafi so na sanar da Ita a naste.” Dr ya jinjina kai yace babu komai dik yanda tace. Lokaci guda ya mik’awa Mommy result d’in. Ta cukukuye ta tura cikin jaka kafin ta fice daga Office d’in tana sakin huci tana muzurai. Cikin zuciyarta take fad’in “Lokacin ramuwa yayi Mu’azzam zaka d’and’ani k’unci wanda baka d’and’ana a baya ba. Idan sunana Hajara sai na sauk’e maka wann d’anyen kan naka.. Sai na nuna maka kai k’aramin maras kunya ne.” Ta kuma yin k’wafa kafin tasa kai ta shige. ** A can Fufore kuwa tun bayan tafiyar Mu’azzam Ta dawo d’akin Mamy da kwana. Tare tare suke gudanar da komai itada Mama Hindu da Ajidde.. Yau ma ruwan addu’a data kawo Malama ta bata zamzam ce tace ta Bawa makusancinta ya karanta mata ayatul Shifaa a ciki a bata Ta sha.. Saidai babu Mu’azzam wanda yake d’anta sann babu Daddy da yake mijinta. Sadiya ta amsa tace zata karanta mata Ta bata tasha tinda damuwar shine a karanto ayoyin da yak’inin Allah ya bata lafiya. Nan kuwa ta karanto ta tofa mata ta bata tasha saura ta shafe mata a fuskarta. A ranar da dare suna kwance suna bacci taji kaman gadon Aunty Nuratu na motsi. Ta mik’e a hankali daga saman katifar da take kwance.. Kaman wasa motsin na kuma yawa matar da ko hannunta bata iya motsawa. Sadiya ta mik’e tana karanto addu’o’i saman harshenta. Nan ta hangi kaman Mamy d’in ce ta mik’e zaune. Zuciyarta yai wani irin yankewa.. Ta soma lalumar haske zata kunna wutar d’akin.. Tana kunna wutan sai kuma taga tana nan kwance harta abun rufauwarta na nan kaman bata motsa ba. Tai k’ok’ari tai k’arfin hali ta matso kusanta ta karanto mata amanarrasulu da ayatul kursiy da kuma k’ul’au’zai.. Ta tofa mata kafin tai zaune gefenta tana dubanta dan gaba d’aya ji tai baccin ya tafi daga idanunta.. Washe gari da safe haka ta dinga mamakin abinda ya faru daren jiya wanda kaman mafarki ne tai haka take gani. Koda Ajidde tazo Sadiya ta sanar da ita abinda ya faru amma tafi tunanin watak’ila mafarki ne tai. Ajidde ta jinjina kai tace “Ince baki sanar da kowa ba..?” Sadiya ta gyad’a mata kai alamun eh. Jinjina kai Ajidde tai tace “Yauwa Malama tace idan anga wani canji kar ayi Saurin fad’a wa mutane.. Yanzu yau in sha Allah zan sanar da ita abinda kika fad’a mun.. Allah yasa a dace matar nan ta sami lafiya.. Al’amarinta akwai ban tausayi.” Sadiya ta karkato tana duban Aunty Nuratu. Sai kuma ta furta Ameen a hankali. Ta maidoda dubanta ga Ajidde dake saka tsakin habbaussauda cikin gaushi tace “Idan ana buk’atar wani abu ki fad’a mun kinji.. Ajidde ta murmusa tace “Kar ki damu zan sanar dake in sha Allah..” Sadiya ta sakar mata murmushi tace “Barin duba Inne..” Jinjina mata kai Ajidde tai tace “A dawo lafiya.” Suka sakar ma juna murmushi kafin Sadiyar ta fice. ** Bugu biyu a na uku Shemau ta d’aga dan Safeenah ce mai kiranta. “Ina jnki Safeenah tin shekaran jiya nake neman layin ki.. Sai yau kika samu sararin kiran wayata.” Safeenah Ta fuzar da fuci kad’an tana duban hannunta da aka saka mata drip tace “Aunty banida lafiya ne.. Ko Kinsan Jiya a asibiti na yini Ina shan drip..” Aunty Shemau Ta zaro idanu tace “Mai ya faru..?” Safeenah tace “Mommy bata baki labarin abinda Mu’azzam ya mun ba..? Aunty na tsani matar Mu’azzam zanyi komai Dan Ta fice daga rayuwarsa.” Shemau ta jinjina kai tace “Wann sadaka yallar ai ba banza ta bar Mu’azzam ba.. Zan taimaka miki Safeenah.. Zata fice daga rayuwar Mu’azzam na miki alk’awari..” Musaddiq yai tsaye Cak yana sauraron wayar Aunty Shemau da Safeenah. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *52* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Shemau Ta numfasa tace “Kina jina, naji Inne na maganan za’a turo Driver ya d’auketa, kuma naji tana magana da Mama Hindu ko za’a sama mata yarinya ‘yar tayin zaman Mota cikin ‘yanuwa. Nasan duk tsiya cikin satin nan za’a turo direban..” Safeenah ta katseta da fad’in “Aunty ai bazamu bari ta dawo ba.. Ni kawai ki taimakeni kar ta dawo Gidana Dan girman Allah Aunty Shema.. Ayi mai yuwa kar Ta kuma tako mun k’afa cikin gida Ta fita da fitar Ta kenan..” Ta k’arashe tana fito da idanu waje kai kace Shemaun na dubanta. Shemau tai shiru tana nazari Ta tuna exactly abinda Mommy Ta fad’i mata kenan lokacin da za’a kawo Aunty Nuratu jinya cewa Ta fice kenan daga gidanta fita ta har abada. Ta nusa kad’an tace “Yanzu meye abinyi Safeenah..? Mai kike so ayi Kinsan dai tafiya ya zama dole babu fashi tinda har Inne ta amince da hakan..” “Ni kawai kiyi duk abinda zakiyi dan kar ta dawo..” Da Mamaki Shemau tace “Toh kasheta kike so ayi..?” Cikin sauri Safeenah har tana girgiza kai take fad’in “A’a ni bance ki kasheta ba Aunty.. Kawai ki illata shegiya yanda bazata samu damar dawowa ba yanda ma bazata kuma amfanarsa ba. Ki karya mun k’afar munafuka ko ki lak’a mata wani babban sharri.. Ki tura namiji d’akinta kiyi kururuwa ki had’a mata jama’a nayi imani idan Mu’azzam yaji haka ya rabu da Ita kenan rabuwa ta har abada..” Shemau ta numfasa kad’an cikin zuciyarta tana ayyana cewa Wato anama Safeenah kallon shashasha idan akan D’ansandan nan ne tsaf zatai tunanin makirci iri daban daban dan burinta ya cika. Ta d’an nusa tace “Feenah Kinsan had’arin abinda kike fad’i kuwa.. Idan plan d’in yai backfiring fah ba ke kad’ai ba harta ni zan sami matsala bada Uncle d’inku kawai ba harta da Inne sai na sami matsala dan na tabbata ko Mu’azzam bai kulle ni a cell ba Inne zata koreni.. Ta inama zan gayyato mata kwarto cikin gidan gonar nan..? Bayan Kinsan kalan tsaron dake cikin gidan gonar. Safeenah ta d’an rausayar da idanunta cikeda k’osawa tace “Aunty bamuda wani zab’i kawai kisan yanda zakiyi ki lak’a mata wann sharrin shi kad’ai ne zaisa Mu’azzam yaji ya washeta bai ko k’aunar jin mai irin sunanta balle ya ganta.. Haba Aunty Shema ki tausaya min na karkato da akalar hankalin mijina gareni..” Aunty Shemau ta nusa tace “But Safeenah kinsan fah komai a rayuwar nan yanada price..” Safeenah Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa na sani Aunty.. Wllhi idan kika mun haka.. Idan kika taimakeni tsinanniyar nan Ta fice daga rayuwar Mu’azzam ni kuma zan miki komai ko mai kika umarceni na miki zan miki shi without giving it a thought.. I’ll do whatever it takes dan na tabbata Karuwar nan Ta b’ace b’at daga rayuwar my Halal.. Please Aunty Shemau ki taimakeni Kimin wann..” Aunty Shemau ta jinjina kai dan ta tabbata yanda Safeenah tace d’in zatayi komai “Toh shikenan Safeenah.. Zan taimakeki zan gayyato mata kwarto har cikin d’akinta yazo mana da sauk’i tinda a d’akin uwar Mu’azzam take kwana, Kinga idan Ta fice sai mu turosa ya shiga da safe tana dawowa a kamata dashi a d’akin. Ni kuma zan tara mata jama’a.. Kinga tun kafin labari ya isa ga Mu’azzam jarabebbiyar Kakarku zata kori shegiya dangin mayu..” Safeenah ta sauk’e ajiyan zuciya cikeda jin dad’i tana mai sakin murmushi “Aunty kin gama mun komai nan gidan duniya idan har kika mun wann.. Ki fad’a ko me kike so daga wajena kin same shi babu tantama.” Shemau ta murmusa cikeda jin dad’i tace “Zan fad’a miki abinda nake so ki mun.. But for now bari mu cire Sadiya cikin hoton..” Suka shek’e da dariya a tare kafin sukai sallama. Cikin sand’a Musaddiq ya bar wajen yana nanata iyaka abubuwan da yaji suna fita daga Bakin Aunty Shemau. Ya fahimci sunaso Su k’ulla wa matar Mu’azzam sharri ne itada ‘yar uwarsa Safeenah. Ya girgiza kai kad’an ba tareda yace komai ba. Zama yai saman kujera ya d’aura hab’arsa saman hannayensa da ya dunk’ulesu waje guda tinani fal zuciyarsa. Aunty Shemau kaw suna ida waya da Safeenah ta nufi sashen Sadiya. A k’ofa suka had’u da Sadiya zata shashen Inne. Ta sakar mata murmushi tana dubanta “A’a Amarya kar dai fita zakiyi..?” Sadiya ta murmusa kad’an kafin ta d’an risina ta gaida Aunty Shemau. “Dama sashen Inne na nufa Aunty..” Aunty Shemau ta murmusa kafin tace “Koda yake ma ina kika sani a garin nan balle ki fita.. Kuma dai ya kamata ki d’an fita kiga gari kafin ki gama hutunki ko yaya Kikace..?” Murmusawa ta d’anyi kad’an tana gyara zaman mayafinta ba tareda tace komai ba. Sai kuma tace “Aunty Mu shiga ciki ki sha ruwa na barki tsaye.” Aunty Shemau ta murmusa tace “Aiko ba a k’in tayin shan ruwan gidan Amarya.. Ruwan gidan Amarya zak’i ne dashi..” Ta k’arashe cikeda barkwanci. Sadiya dai sai murmushi kurum take. Lokaci guda ta juya ta bud’e masu k’ofa suka shige Parlorn. Aunty Shemau Ta soma bin parlorn da kallo sai kace ranan ta soma shiga. Tai zaune saman kujera k’afafu d’aya bisa d’aya ta d’aga kai sama tana ‘yan kalle kalle “Wai! Dank’ari lallai an kashe Kud’i a parlorn nan.. Kaga kaya kaman order d’insu akai daga waje.. Gidan Amarya dai dik yanda yake akwai santi. Sai ya tuna min lokacin da na raka Aunty Hajara mukai sayayyan kayan auren Safeenah a Dubai da Qatar.. Ni wasu abubuwan ma sunmin kama da na Safeenah..” Ta k’arashe tana kuma dube dube. Jikin Sadiya ya d’anyi sanyi dai dai lokacin da take aje drinks gaban Aunty Shemau. Shemau taci gaba da fad’in “Ai iyaye gaskiya suna k’ok’arin kashe Kud’i wajen aurar da yaransu mata. Duk dukiyar nan da ake kashewa wani sa’in sai kiga aure bai kya ba.. Shiyasa ni bana goyon bayan kashe kud’i da gidan mata suke a aure.. Ka gama kashe kud’i ka sai ma d’iyarka kayan d’aki na gani a fad’i ba shi zai hana namiji ya faskara mata rashin mutunci ba. Dai dai da warmers na zuba masa abinci sai an saya.. Yana cin abincin yana danna wa ubanta ashar.. Namiji kenan k’anin ajali..” Ta k’arashe tana kurb’an drink d’in. Ta d’anyi gyaran murya kad’an kafin tace “Ai ke kinada sa’a da naki iyayen basu wahala kan namiji ba.. Duk wann kayan alatun danginsa suka zuba abinsu.. Ai naga tulin kud’ad’en da Inne tasa aka fitar sanda za’a gyarawa Mu’azzam wann b’angaren da shike lokacin da sunan Safeenah aka gyara sashen nan.. Da yanzu komai nata ne a nan.. Saidai kana Naka ne Allah na nashi.. Na Allah shine daidai dama ya tsaga rabonki ne.. Yo ba dole ma a shak’e gidan nan da kaya masu kyau da tsada ba sabida ansan Safeenah da son k’yale k’yale da gayu..” Tai maganar tana kurb’ar drink. Jikin Sadiya yai matuk’ar yin sanyi da jin irin abubuwan da Aunty Shemaubke fad’i.. Ta sadda kanta k’asa d’ago sai tanaji kaman ita d’in ta tauye hakkokin Safeenah da yawa. Na farko Ta soma tarewa gidan Safeenar tin a can Abuja kafin Safeenah Ta shiga gidan yanzu gashi gidan da aka gina ma da sunar Safeenar ya zama nata.. Anya wann ba rashin adalci bane..? Bata kaiga nemo amsa ba ta sinkayo muryar Aunty Shemau naci gaba da fad’in “Kinga randa ya tasamma maki halin nasu na maza abin bazai ma iyayenki ciwo sosai ba..” Gaba d’aya jikin Sadiya a sanyaye yake, kanta a k’asa tana sakin murmushin da daga gani kasan na yak’e ne. Aunty Shemau taci gaba da fad’in “K’ila al’adarku ce maza ke yin kayan d’aki..?” Sadiya ta d’an girgiza kai cikin rashin sakewa tace “A’a Aunty Al’ada iri guda mukeda shi.. Gidan mata keyin kayan d’aki.. Nawa iyayen ne basu da hali..Kuma ni marainiya ce banida kowa sai mahaifiyata da k’annena..” Aunty Shemau tai rau rau da idanu ta taso da sauri ta dafa Sadiya tana fad’in “Allah sarki ‘yar nan.. Kiyi hak’uri Bansan haka abin yake ba.. Kiyi hak’uri kinji.. Allah sarki ashe dai ked’in marainiya ce.. Allah sarki bansan haka ba..” Sadiya ta murmusa kad’an Wanda yafi kama da yak’e tace “Babu komai Aunty.. Ki daina bani hak’uri dan Allah..” Aunty Shemau tace “Yo dole na baki hak’uri Amarya am.. Bansan ke marainiya bace.. Amma a halin yanzu ke ba marainiya bace dan tinda kika shigo ahali irin wann maraici ya k’are miki..” Ta murmusa kad’an tana sadda kai. Aunty Shemau ta tsareta da idanu cikin zuciyarta tana fad’in ‘kaji munafuka yanda take wane sanne kai’ A fili kuwa gyaran murya ta kumayi tana d’an dafa Sadiyar “Amma naji kince Bakida kowa..Sai mahaifiyarki da ‘yanuwanki. Toh ina ahalinki suke.. Dangin mahaifiya ko na mahaifi..?” Zuciyar Sadiya yai wani irin yankewa dan batasan Ta yanda zata soma sanar da Aunty Shemau Dangin mahaifinta sun gujesu tun kafin a haifeta sabida zab’an mahaifiyarta da yayi a matsayin wacce zata zamto abokiyar rayuwarsa. ko kuma dangin mahaifiyarta da batasan duniyar da suke ba.. Bata kai ga bata amsa ba sallamar Mama Hindu ya katse su. Hamdala tai cikin zuciyarta dan zuwan Hindu ya ceceta daga amsa tambayar Aunty Shemau. Mama Hindu Ta sanar da Ita Inne ke kiranta. Cikin sauri kaman wacce take jira Ta mik’e tana amsawa. Aunty Shemau ta d’auki sauran drink d’in da Sadiya ta had’a ta kawo mata tana sha tana fad’in zata Zo a koya mata irin wann drink d’in dan ta lurar hannun amaryar tasu nada albarka. Sai santin drink d’in take. Sadiya tace “Aunty bari akai miki dama na had’a maku ne dasu Inne.. An kai na Inne tintinin dama na k’ofarki ne ban kai ba nace sai zuwa anjima zan kai..” Aunty Shemau ta d’auka tana fad’in “Allah Sarki Amarya mai ruwan zak’i.. Toh bara na hutasarki na tafi dashi, ai kaw Uncle Salman na son irin wad’ann fresh drinks d’in da babu wani chemicals ciki babu preservatives..” Mama Hindu ta amsa jug d’in daga hannun Aunty Shemau tana fad’in bari ta kai mata. A tare suka jera suka nufo sashen Inne da Shemau da Sadiyar. Suka gaida Inne gaba d’ayansu dan a parlor suka taddata. Inne Ta dubi Shemau tace “Wai har yanzu ‘Yan biyu basu ida hutun nasu bane bazasu dawo haka nan ba.” Shemau ta murmusa cikeda jin dad’in Inne na kewar jikokinta “Dama satin dama za’a d’aukosu Inne..” Jinjina Kai Inne tai tace “Allah ya kaimu.. Ai gwara su dawo haka nan.. Da k’iriniyar tasu a waje yafi.. K’aramin k’afa a waje da dad’i..” Shemau sai murmusawa take cikeda jin dad’i tana fad’in “Za’a d’auko Su Inne..” Inne Ta dubi Sadiya tace “Kinyi magana da mijin naki ne..?” Sadiya ta girgiza kai kad’an tana sadda kai k’asa “A’a Inne bamuyi magana yau ba..” Inne Ta jinjina kai tace “Taw, nasan zai kiraki ya sanar dake... Adnan yana hanya yau.. Zuwa gobe in sha Allah zai d’aukeki zaku koma.. Sai ki fara shiri ko..” Ba zata Sadiya taji batun.. Sai bata ce komai ba ta amsa ma Inne da fad’in “Toh Inne.. Can k’asan zuciyarta kaw dikda tana son kasancewa da mijinta dan tayi kewarsa amma wani b’angare na zuciyarta sam bai son rabuwa da Mamy.. Ta saba sosai da ita d’an zaman da sukai tare dan tare suke kwana sann kusan rabin d’awainiyar da Mama Hindu ke mata Sadiyar ke mata su yanzu. Shemau kaw ji tai kaman an dab’a mata mashi.. Abin yayi kusa bazata samu Ta cimma Alk’awarin da taima Safeenah cikin gaggawa ba.. Ya zama dole Ta b’ullo da dabara.. Ya zama dole kafin wayewar gari tai executing plan d’inta. D’an murmusawa tai tana fad’in “Allah Sarki Amarya zata tafi Ta barmu da kewa.. Gashi bata zaga taga dangi ba.. Dama Mu’azzam ya kamata ya zaga da ita toh gashi baya nan.. Har lokacin tafiyarta tayi..” Inne ta d’anyi shiru sai kuma ta jinjina kai tace “Haka ne.. Ya kamata ta d’an zaga ta gaida dangi ta masu sallama.. Shemau sai ki mata rakiya zuwa yamma..” Shemau ta jinjina kai cikeda jin dad’i “Tau Inne zan zaga da ita In sha Allah..” Inne Ta dubi Sadiya tace “Tinda gobe zaku juya da yamma idan rana tai sanyi sai ki shirya Shemau ta rakaki gari kiga dangi koh..” Sadiya Ta jinjina kai tana amsa dama Inne da “Toh Inne.” Lokaci guda Ta mik’e tana fad’in bari ta duba Mamy. Inne ta jinjina mata kai tana mata izinin tafiya. Suka bi bayanta a kallo daga Innen har Shemau. Murmushi saman fuskar Inne take fad’in “Yarinyar a natse take.. Modibbo yai sa’an iyali.. Allah ya nuna min d’iyoyinsu kafin ya amshi rayuwata.” Shemau Ta murmusa tace “Zaki ga d’iyoyinsu in sha Allah Inne..” Inne ta murmusa tace “Allahu yashaa.” Shemau Ta amsa da Ameen kafin Ta mik’e tace bara ta duba taci kaman shigowar motar Uncle Salman k’ila ya dawo. Inne ta jinjina mata kai tana mai gyara zaman k’afarta dake d’an mata ciwo. Ta bud’e murya tace “Ki fad’a wa Salman d’in Ina nemansa.” Shemau Ta amsa da “Tau Inne.” ** ABUJA _National Police Headquarters (Force Criminal Investigation and Intelligence Department FCID)_ Carko carko sukai shida Yusuf bayan sun fito daga Babban meeting d’in da ya k’unshi manyan ‘yansanda daga cikinsu. An kuma d’aukan statement d’in Assad an basu kwanaki k’alilan su zak’ulo Danger yanda ya shiga ya fita. Mu’azzam ya fuzar da fuci a karo na babu adadi yana shafan sumarsa, dole yai interrogating Assad koda bai yarda cewa Assad d’in mai laifi bane dan a halin yanzu abin ya fi nasa k’arfin ya isa yanda baiso ya isa ba.. Idan yana son wanke Assad dole sai ya kamo asalin b’eran dake cikin Department d’in. Jikin Farin allo da hotunan mutane da case d’in ya shafa ya k’arasa ya manna hoton Assad jikinsa a matuk’ar mace.. Ya janyo arrow yai linking hoton Assad dana Danger yana jin kaman hannunsa na shaking.. Abotansu da abubuwan da sukai going through a rayuwa kawai yake tunawa kama daga lokacin da police academy har zuwa nasarori da k’alubale da suka fuskanta a aikin na D’ansanda. Yusuf ya dubesa cikeda tausayawa kafin ya k’araso yana basa k’warin gwiwa. “Komai zai shige.. Zamu wanke Assad, bazai losing aikinsa ba saidai ma ya samu k’arin yarda da matsayi.. In sha Allah zamu fitar da gaskiya daga cikin k’arya.. Nasan zaka iya Mu’azzam.. Kar ka karaya.. Kar ka nunama Azzalumai gazawarka.. Zaka kawar dasu da yardar Allah.” Duban Yusuf kurum yai da idanunsa da suka kad’a sosai kafin ya maida dubansa fa hoton Assad da aka had’a da na Danger. Ya d’an shafi sumarsa kad’an kafin yace “Kaje wann asibitin.. Mai ka samo so far.?” Yusuf ya d’an ware idanunsa yana mai fuzar da fuci kad’an yace “I couldn’t find anything until now.. Na sa an min playing CCTV footage tin daga ranan da ka kai samples d’in asibitin amma wann ranan da ka kai samples d’in security Cameras d’in asibitin sun sami matsala..” Mu’azzam ya dubesa yace “Kenan ba’a sami footage d’in wann ranar ba.?” Yusuf ya jinjina kai alamun Eh.. Murmusawa yai da gefen bakinsa yana jinina kai kad’an “Na wann ranan ne kawai ya zama missing.. Why..? Maiyasa sai a ranan zai sami matsala..? Don’t you think this is too much of a coincidence..?” Yai maganar yana d’an bubbuga table d’in da marker dake hannunsa. Yusuf ya jinjina kai yace “I thought as much.. Nayi tunanin haka nima..” Mu’azzam ya d’an sosa hancinsa kad’an kafin ya dubi Yusuf yace “K’arya suka maka.. Wann footage d’in na nan kawai basu maka playing d’insa bane.. Wani wasa suke so su buga, but believe me we’ll turn the table on them.. Wann Rat d’in da muke nema shi ya shiga wann asibitin Yayi Sabotaging DAN Samples.. Idan muna so mu kamo b’eran nan sai mun fitar da wann footage d’in daga hannun securities d’in. I’m pretty certain footage d’in na nan biyansu akai dan Su b’oye dan na tabbata by now b’erayen sun san muna hunting d’insu.” Yusuf yace “What if sunyi deleting..?” Mu’azzam yai shiru yana nazarin Yusuf sai kuma yace “Ai asibiti ne bazasu goge record haka kawai ba.. Sannan sunsan test d’in is somehow related to police case. Dole akwai abinda sukai.. Nafi tunanin biyansu akai.. Amma kar ka damu zamu buga wasan sai mun samo wann footage d’in.” Dai dai lokacin Maleeka ta shigo Office d’in. Mu’azzam ya mik’e daga saman table d’in da yai zaune bisa ya dubi Yusuf yace “I’ll interrogate Assad..” Yusuf ya jinjina masa kai kafin ya shige.. Maleeka kaw sai dubansa take k’asa k’asa zuciyarta ba wane irin yankewa sabida taga irin firgitaccen duban da Mu’azzam d’in ke mata. Yana ficewa Ta dubi Yusuf tace “Bansan mai naima Inspector Gamji ba. Ko kallo ban ishesa ba.. Na rasa shi wane irin mutum ne sam da yakeda tsananin ra’ayi.. Ba hurumin kowa yake shiga ba koda aiki tare ya had’aku idan ba dole ba Sai yaga dama yai involving naka.” Ta k’arashe tana zuba files d’in hannunta saman table. Yusuf yaci gaba da tattara reports d’in dake saman table d’insa yace “I don’t blame him idan ya zab’i yai minding business d’insa.. Nowadays mutane ba abin yarda bane.. Kana tare da mutum ne bakasan yana cin dunduniyarka ba.. Excuse me..” Ya fad’i yana d’aukan folder d’in. Tabi bayansa da kallo cikeda takaici dan Ta kula magana ya fad’a mata a dunk’ule.. Zuciyar Maleeka yai wani irin tsinkewa sanda wani tunani ya d’arsu mata cikin zuciyarta. Yanzu idan teburin ya juya fah..? Idan aka fahimci Assad baida laifi kenan fah itace zata tafi kurkuku alhali babu abinda ya had’ata da Danger tinda Ita dai masu Chief take aiki.. Toh amma babu Ta yanda za’ayi a wanke Assad dan sun rufe duk wata k’ofa da za’a ratsa a wanke sunan Assad bugu da k’ari Assad da bakinsa ya bada statement d’insa bama wani ne ya bayar ba. A sabida wann Assad Baida k’ofar ficewa.. Dole ya tafi prison. Ta murmusa kad’an tana duban hoton Assad da akai linking da na Danger. ** A can Fufore kuwa yamma lis kusan goshin magrib suka dawo daga gaishe gaishen nasu, gaba d’aya a gajjiye take dan saida Aunty Shemau tasa driver ya d’an zagaya dasu Sadiyar taga gari. Hakan yasa tana dawowa gida Ta fad’a wanka kafin Ta fito Ta shirya tsaf cikin doguwar riga cotton mai Laushi da fad’i, Ta zira hijab d’inta ta gabatar da sallar magrib dan already anyi kira kafin Ta fito ta nufi sashen Inne wajen Sirkarta.. Shemau na ganin ficewarta Ta d’ago wayarta ta soma dialing wata number.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *53* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Shemau taci gaba da fad’in “Yauwa kana jina koh.. Kana isowa ka kirani a waya ni zanzo na shigar dakai.. Karfa kazo Ta main gate.. Eh ta k’aramar k’ofar baya... Yauwa kana zuwa kawai ka kira wayata ni sai na taho na bud’e maka na shigo dakai.. Toh sai ka iso sai na jika..” Tana katse wayar Ta soma murmushi Ta kusa cika burin mijinta, Ta tabbata idan taima Safeenah wann aikin shikenan Safeenar ta sami abinda take so sann zata nemo masu BAT cikin gaggawa. Hakan na nufin abinda mijinta ya jima yana nema zai tabbata nasa.. Ta murmusa tana juya idanu lokaci guda tasa kai ta nufi nata b’angaren. Shigarta da kad’an Ummilo ta shigo ta sanar da ita Inne na nemanta.. Bataso zuwa ba dan tana tsaka da mission ne bata fatan abinda zai b’ata mata wann mission d’in nata. Gashi babu abinda yafi bata takaici kaman da kiran ya kasance Wai hidiman Nuratu ya shafa.. Takaicin duniya kaman ya kar Shemau ba abin ta silale ta gudu ba kafin bak’onta ya k’araso. Hankalinta gaba d’aya kan wayarta yake tana jira taji kiransa.. Gaba d’aya kana ganin Shemau zaka fahimci ba cikin hayyacinta take ba. Can after like 1hr mutumin ya k’araso location d’in da Shemau ta sanar dashi. Ya k’araso Bakin k’ofar yana ‘yan dube dube. Ya soma k’ok’arin ciro waya kenan zai kirata sai hangota yai tana tahowa cikin shiga bak’in hijabi harda mayanin rufe FUSKA mai kaman nik’abi. Ya murmusa yace “Rankidad’e harda nikabi kika rufa a daren nan..” Ta jinjina masa kai tana masa alama da hannu kan ya k’araso cikin sauri. Ya d’an ci gaba da waige waige yana fad’in “Dole ki b’adda kama dukda dare ne sabida tsaro..” Shemau dai bata ce komai ba tana gaba yana biye da Ita har suka k’araso b’angaren. Ta bud’e masa k’ofofi suka isa har bedroom. Ya haye saman gado ya zauna yana d’an tsalle daga zaune kad’an nan saman katifar yana fad’in “TJ yau zakai bacci mai rai, bacci maiji da lafiya saman tattausar katifar nan.. Dad’i ya maka yawa... Ga kud’i an tura maka account ga bacci saman katifa mai taushi.. Safiya nayi idan an maka ihun kwarto Sai ka arce a guje kafin a capkeka..” Ya k’arashe yana zame rigarsa ya rage daga shi sai singlet ya maida kansa ya kwanta saman pillow harda lumshe idanu yana jijjiga k’afafunsa kad’an yana shak’an k’amshin ‘yan gayun dake cikin d’akin ga taushin katifar da yake jinsa har cikin b’argonsa. Yana jin sanda Shemau ta janyo k’ofa ta rufe. Still idanunsa a lumshe yake furta “Godiya nake Hajjaju yau bacci ko 5star hotel nake albarka.” Musaddiq ya zame nik’ab d’in da ya rufe fuskarsa dashi had’ida yaye hijab d’in.. Cikin sauri ya k’arasa igiyan shanyan Su Mama Hindu yanda ya d’auki Hijab d’in da nik’ab d’in ya maida masu. Haraban gidan ya koma ya zauna yana jin zuciyarsa na masa zafi.. Maiyasa Safeenah da Shemau zasuyi tarayya wajen ruguza auren Mu’azzam.. Maiyasa ahalinsa suka zama mugaye irin haka..? Maiyasa ya fito cikin irin wann ahalin..? Ya k’arashe yana lumshe idanunsa had’ida girgiza kai. A fili yake furta “Monster.! Monster.! Monster.!!” Lokaci guda ya kame kansa yana jin zuciyarsa na masa tsananin k’una. Daidai lokacin motar Uncle Salman ya shigo Gidan gonar. Ya isa yanda yake parking ya ajiye motar, Musaddiq na nan zaune a mazauninsa har Uncle Salman ya ida parking.. Ya k’ura masa idanu yana tuna tsttaunawarsu da Daddy da ya sinkaya gameda sa’insan da Uncle Salman d’in sukai da Baban Mu’azzam kafin ya rasu.. Wani irin tsanar Uncle Salman na kuma taso masa.. Ya jinjina kai yana dubansa sanda ya nufi b’angarensa. A fili Musaddiq yake furta “I’m sure this will ruin you Uncle.. Kaida matarka baku da banbanci.. You both are monsters shiyasa kuka auri juna.. Na tabbata yau d’in abin da matarka tai niyyan yi zai tarwastaku gaba d’aya..!” Ya k’arashe yana ci gaba da dannawa Uncle Salman d’in mugun kallo.. Shigan Uncle Salman da kad’an Musaddiq ya soma jiyo ihun mutumin Uncle Salman na bugunsa.. Har waje suka fito Uncle Salman na bugunsa.. Yana ihu yana fad’in ya masa rai kar ya kashesa.. Musaddiq da securities suka nufo wajen babu shiri yayinda Uncle Salman yaci gaba da tokarinsa yana masa bugun zazzab’en dawa.. Ya mik’e zai arce a guje Uncle Salman na sakin huci yake fad’in kar Su barsa ya gudu.. Wann hayaniyar shi ya tashi hankalin illahirin mutanen dake cikin gidan gonar. Musaddiq yai amfani da wann damar ya bawa Tj hanya, TJ ya arce a guje.. Uncle Salman na fad’in securities su bisa su kamasa. Saidai ina TJ gudun mutuwa yake dan tuni ya arce daga cikin gidan gonar. Shemau jikinta na wane irin rawa ganin Uncle Salman cikin yanayin da bata tab’a ganinsa ciki ba.. Su Inne ma duk hankalinsu a tashe.. Kan kace mai ya kaiwa Shemau wata irin jahilar naushi.. Inne tai k’ok’arin dakatar dashi tana tambayarsa lafiya meke faruwa. Bai amsa Inne ba ya kuma kaima Shemau wata tokarin.. Janyota ya shiga yi a k’asa tana ihu tana kururuwa. Banda sakin huci baya komai “Dan Ubanki yau sai kin bar gidan nan.. Ni zaki kawo ma kwarto har cikin Gida.. Wllhi yau sai kin tafi Shemau.. Babu ni babu ke aurena da ke ya k’are matsiyaciya.. Wato dama dalilin da yasa kika tura yaranmu hutu kenan dan ki dinga kawo min maza cikin gida koh.. Toh yau Allah ya toni asirinki.. Kuma shima shegen da kike kawo mun d’in sai na bincikosa naci Ubansa..!” Shemau na kuka take fad’in “Wllhi wllhi ba halina bane.. Wllhi bansan komai ba..!” Uncle Salman ya rufe mata baki da wani naushin a tsananin hasale ganin tana k’aryata abinda da idanunsa ya ga hakan. Sallalami da salati kawai su Inne suke, yayinda Mama Hindu da Sadiya suka koma cikin gida jiki duk babu k’wari. Shemau taci gaba da kuka tana rantse rantse tana fad’in wllhi batasan komai ba.. Ita bata biye biyen maza.. Kaman dad’a tunzurasa take ya kuma harzuk’a ya yo kanta. Inne tai saurin dakatar dashi tana fad’in “Kai Salman ka natsu nace abi komai a sannu.. Cikin hayyacinka kake jifan matarka uwar yaranka da wann mummunan k’azafi..?!” Uncle Salman na sakin huci yana aikawa Shemau dake duk’e a wajen wulak’antaccen kallo yake fad’in “Inne k’azafi kike cewa bayan bani kad’ai naga d’an iskan da Ta kawo ba.. Harta masu gadi sunga hakan.. Inne d’akin bacci na fah naga wann D’aniskan saman gado na.. Wllhi yau idan ban kasheki ba Shemau sai na miki mummunan rauni.. Matsiyaciya zuriyar mastiyata.. Dama an fad’a mun gidanku ba gidan mutunci bane na toshe kunnuwana na aureki a haka na tsamoki daga yunwa da talauci shine bari ki saka mun da rashin arziki koh.. Toh dan Ubanki kin gama zama a Gidana.. Kuma babu ke babu ‘ya’yana..!” Shemau dake duk’e wajen hannu aka take kururuwa tana fad’in “Na shiga uku.. Dan girman Allah ka mun rai wllhi rugar mu ko service d’in waya babu.. Na shiga uku ni Shemau.. Dan Allah ka mun rai kar ka sallame ni.. Wllhi ba kwarto na bane.. Bansan ya akai ya shigo ba.. Dan Allah ka tsaya na maka bayani..!” Bata kai aya ba Uncle Salman ya cire takalminsa ya shiga kai mata bugu dashi, ya rarumo katakon da ya daki TJ dashi ya shiga rapza ma Shemau kaman wanda aka Aiko Sa.. har saida Inne Ta kare Shemau.. Ya nufi cikin gidan yana huci ya soma firfito da kayayyakin Shemau yana watsi dasu yake fad’in “Yau zaki bar gidan nan Karuwar banza.. ‘Yar iska maras mutunci.. Yau bazaki kwana a gidan nan ba.. Maza a k’ara gaba aje aci gaba da tallan fura da nono.. Kayan ma a gidan nan kika samu.. Zo ki fita matsiyaciya.!” Ya shiga janyota a k’asa tana ihu tana fad’in Ita bazataje ko ina ba.. Ko sauraron Inne bai tsaya yi ba haka ya dinga janyo Shemau a k’asa har saida ya fitar da Ita har k’ofan gidan yai instructing masu gadin da cewa duk wanda ya bar Shemau Ta shigo gidan a bakin aikinsa. Ko mai kaman ta ne kuwa..” Haka Shemau tana kuka tana rok’onsa ya k’yaleta ko sutura ne ta d’auka amma ko sauraronta bai ba saida ya fiddata har waje. Hannu biyu Ta saka aka tana kuka tana fad’in “Na shiga uku ni Shemau yanzu ya zanyi ina zanje.!” Ta mik’e da k’yar k’afafunta babu ko takalmi ta soma tafiya cikin d’ingishi dan da k’yar idan Uncle Salman bai ji mata rauni cikin k’ashi ba. Tana tafe tana kuka ba tareda sanin yanda ta dosa ba. Uncle Salman yana komowa cikin gida zama yai a parlor zuciyarsa na tafarfasa.. Shine Shemau zataci amanarsa ta kawo masa kwarto har cikin gidan Mahaifinsa tsaban Ta maidashi D’an iska.. Shi abinda ya mata kawai ma bai ishesa ba ai taci banza ma kenan.. Idan sunansa Salman sai ta biya abinda ta masa.. Wane irin kishi na kuma turnuk’esa idan ya tuna ganin TJ da yai kwance saman gadonsa. D’ago kai yai yaga Inne tsaye kansa tana dubansa, a hankali ta k’arasa saman kujera ta zauna. Ta d’an girgiza kai kad’an tace “Kai yanzu abinda kai ba asirin kanka ka tona ba. Da Kayi komai cikin natsuwa ba cikin hauka da tashin hankali kaman yanda kayi ba.. Yau kaf fad’in gidan gonar nan kowa yasan abinda matarka ta aikata.. Haba Salman.. Wann ai kaman ka kwance ma kanka zani ne a Kasuwa..” Uncle Salman ya katseta da fad’in “Inne mai zanyi idan banyi haka ba.. Cikin d’akin baccina fah na iske D’aniskan yaron nan.. Wllhi na mata da kyau da ban illatata ba..!” Ya k’arashe yana sakin huci. Inne tai shiru kafin ta girgiza kai a hankali tace “Allah ya rufa asiri.. Ka natsu ka natsa hankalinka waje guda.. Har kullum tashin hankali baya kawo maslaha..” Tana ida fad’in haka ta mik’e ta nufi nata b’angaren zuciyarta gaba d’aya babu dad’i.. Godiyar Allah ma da ya kasance yaran Shemaun basa nan abin bai faru gaban idanunsu ba. Dikda cewa jininsu dama sam baizo d’aya da Shemau ba sam bataji dad’in yanda al’amarin ya kasance ba. Ko Babu komai Shemau sirkarta ce kuma uwar jikokinta an riga an zama ahali.. Sam abu dai baiyi dad’i ba. Tana isa parlor tasa Musaddiq ya mata kiran kaf mutanen da abun ya faru gabansu. Ta had’a assembly tace dan Allah abinda ya faru daren yau ya tsaya a iyaka nan.. Dik wanda ya rufa asirin d’an uwansa musulmi Allah zai rufa nasa ranan gobe k’iyama. Kowa yai mata Na’am da cewa in sha Allah babu mai d’ago zancen. Saidai maganar duniya dama ba mai b’uya bace. Gaba d’aya gidan ranan wane irin bacci akai, abu ne da sam babu dad’in gani balle dad’in labari. Washe gari jikkunansu duk a kace musamman Sadiya da Ta d’auki Shemau Tamkar sirkarta, sai taji sam babu dad’i, sauk’in abun sassafe dama suma zasu d’aga zuwa Abuja. Ta rik’e hannun Mamy suna sallama. Fuskarta Sai Haske da shek’i yake, Ta shafi goshinta kad’an tace “Mamy yau zan tafi.. Amma na miki alk’awarin in sha Allahu zan kuma dawowa.. Ina fata had’uwar da zamuyi na gaba mu tarbi juna akan k’afafunki Mamy.” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta. A hankali Sadiya Ta saka yatsun hannunta ta goge k’wallan da suka ciko idanunta.. Tana k’ok’arin mik’ewa taji Mamy ta rik’e yatsun hannunta.. Zuciyarta yaci gaba da harbawa da sauri da sauri.. Ta waigo domin tabbatarwa. Ai kuwa nan taga yatsun hannunta cikin tafin hannun Mamyn dukda cewa idanunta a lumshe suke. Sadiya ta kuma duk’awa a hankali tana kallon yanda hannayensu ya had’e waje guda sai taji wani k’wallan na kuma ciko idanunta. Ta jima tana duban hannayen nasu.. A hankali kuma taga hannayen Mamyn na k’afewa har dai ya koma a bud’e kaman yanda yake ko yaushe. Sai taga abin kaman imagination d’inta ne kaman mafarki kaman kuma gaskiya. Addu’an samun lafiya ta kuma mata sanda taji muryar Mama Hindu na fad’in ta fito su tafi. Ta saka bayan hannunta ta share k’wallan kafi ta shafi kan Mamy tace “Zaki samu lafiya da k’udirar Ubangiji.” Lokaci guda tasa kai ta fice, bata samu sunyi sallama da Ajidde ba dan fitar sassafe sukai, harda Musaddiq suka komo hakan yasa Inne bata sama mata ‘yar rakiyar ba dan Musaddiq yace yana so yaje ya duba gida shima.. Alhali kaw zaman nasa ne a garin sam baya masa dad’i dan tinda ya dawo ya kula Ajidde ta janye masa jiki sann Ta daina duk wad’ann barkwancin nata da yake sanyasa nishad’i a zaman sa a garin.. Sam sai yaji garin bata masa dad’i gwara ya koma ya taka ma Safeenah birki kan haukar da take dan sosai abin da Ta tassama Yi wa matar Mu’azzam ya d’aga masa hankali. ** Yamma lis suka iso birnin tarayya. Sadiya data sha baccinta a mota, ta bud’e idanu ta gansu a cikin Abuja. Adnan da Musaddiq Sai labarinsu suke, tana ganin an d’auki hanyar foundation zuciyarta ya cika da annashuwa, kenan wajen Su Umma za’a fara kaita. Ko ya akai Adnan yai tunanin hakan bata sani ba.. zuciyarta ya bata amsa da fad’in k’ila Mu’azzam ne yace su fara kaita nan tinda itakam baccinta tasha a mota. Suna isowa Farin ciki ya cika Sadiya. A farfajiyan apartment d’in ta hangi su Habeeb sai wasa suke.. Suna ida parking kaw Habeeb da Ashir sukai tsaye suna duban motar. Aiko suna ganin Sadiya ta fito ciki suka nufeta a guje suna kiran sunanta suna mata oyoyo.. Musaddiq yai tsaye yana dubansu murmushi saman fuskarsa. Nan Aunty larai da ta jiyo hayaniyarsu ta fito itama.. Aka soma Sabon oyoyo. Musaddiq ya k’araso ya gaida Aunty Larai tana masa tsiyan shine ya girma ya zank’ale haka.. Sai murmushi yake yana Shafa kai.. Aunty Larai ta shigar dashi ta masa iso Suka gaisa da Umman Sadiya. Adnan yaita sauk’e masu tsaraba wanda takeda tabbacin Mu’azzam ne ya umarcesa yai hakan dan lokacin da suka tsaya a Jos yin sallah taga sanda Adnan d’in ke sayen tsaraban. Aunty Larai sukai masu godiya kafin sukai sallama Sadiyar ma na masu godiya da fatan sauk’a lafia. Aunty Larai ta kamo hannunta tana tsareta da idanu “Iyye irin wann haske da shek’i da kike.. Aah lallai mission yayi kyau. Tubarkallah Masha Allah.” Sadiya ta murmusa cikeda kunya tana rufe fuskarta da mayafi. Sosai taji dad’in ganin ahalinta cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali. Idan ka gansu duk sun canza ba kaman lokacin da suke cikin tashin hankali ba, Sai godiyar Allah. Tana ida sallar magrib Aunty Larai ta tarbeta da wasu had’e had’en ta tasa ta gaba sai ta cinye ta shanye. Sadiya kaman zatai kuka babu yanda ta iya haka Aunty Larai ta tasa gaba da had’en had’en nan. Harda wasu turaruka na musamman ta had’a mata da shike gidanta zata tafi. Kafin isha Aunty Larai ta sakata ta tsala wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga bak’ar abaya mai kyaun gaske wanda ya kuma bayyana kyaun fatarta. Sai zuba k’amshi take. Ta tada sallar isha kenan ta sinkayo muryarsa da Umma suna gaisawa daga parlor. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *54* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Habeeb ya k’araso sukai handshake ya zaunar dashi gefensa saman kujeran kafin yace “Hello little Cop.. Kaje lesson d’in kuwa..? Fad’a mun mai aka koya maku..” Yai maganar yana duban Habeeb d’in dake wasa da wani silver metal shatin kwabo. Habeeb ya girgiza kai yace “Nace masu ni Cop ne.. Chasing bad guys nake so na koya..” Ya murmusa yana duban Metal d’in wanda ya mugun d’aukan hankalinsa. Take yaji zuciyarsa yai wani irin yankewa sanda ya soma tuna Ina yasan irin wann metal d’in.. Take yarintarsa ya soma dawo masa yana wasa da irin wann metal yana mannasa da magnet. Karb’an metal d’in yai yana juyawa, exactly babu abinda ya raba da irin wanda yake wasa dashi yana yaro. Ya dubi Habeeb yace “Where did you get this from.?” Habeeb dake ‘yan tsalle tsallensa yace “I don’t know.. Kawai nima na samu ne a gidanmu kafin mu dawo wann gidan..” Mu’azzam yaci gaba da juya metal d’in.. Sai wann lokacin yake karanta abun da aka rubuta tsakiyan shatin kwabon cikin yanayin rubutu mai tsananin k’ank’anta wanda sai ka saka idanunka sosai kafin ka iya karantawa _Balck African Team_. Shine abin da aka rubuta tsakiyar metal d’in cikin rubutu mai style. Zuciyarsa ya yanke sanda ya karanta rubutun. Ya nanata a fili Black African Team...!” Ya nanata a hankali yana mai kuma juya coin d’in cikin hannunsa. Hayaniyar Habeeb dake kallon cartoon d’in spider man yana kwaikwayonsa shi ya dawo da hankalin Mu’azzam ya d’an dubesa yace “Hey little Cop.. Can you borrow me this.” Ya k’arashe yana nuna masa Coin d’in. “Sure Mr Cop. Na baka kyauta idan kana so.” Murmusawa yai kad’an kafin yace “Kar ka damu aro zaka bani.. Idan na gama amfani dashi zan dawo maka dashi kaji.” Habeeb ya jinjina kansa daidai lokacin da Aunty Larai ta kirasa ciki. Mu’azzam yaci gaba da juya coin d’in yana nanata word d’in dake jiki wanda a yarintarsa bai kula da wann word d’in ba sai yanzu.. Balck African Team” Ya kuma fad’i yana juya coin d’in. K’amshinta ne ya soma masa sallama, Cak ya tsaya da abinda yake ya soma janye idanuns daga duban coin d’in. Tin daga k’asa ya soma dubanta har zuwa kyakkyawan fuskarta da yai kewa. Ya mik’e yana mai jefa coin d’in cikin aljihunsa. A hankali yake takowa har zuwa kusanta. Suka jima a haka suna duban juna cikeda shauk’i. Hannayensa ya d’ago duka biyu ya tallafi fuskarta, kafin ya matso da nasa fuskar kusan nata. Ya manne goshinsu waje guda su duka biyun idanunsu a lumshe “I’ve missed you.. I’ve missed you so much Beautiful.!” Ya fad’i cikin murya mai tsananin sanyi. Bata iya furta komai ba Sai wane irin sanyi da illahirin jikinta yai. Tana jin sanda ya rungumeta cikin jikinsa. Ta lumshe idanunta a hankali tana shak’an k’amshinsa da tai kewa. Hannunta ya kamo suka zauna saman kujera ya tsareta da idanu kaman ranan ya soma ganinta. Ta d’an muskuta tace “Ina yini..” Bai amsa ba saima ci gaba da kallonta da yake harda yin tagumi still idanunsa akanta. Gaba d’aya sai ta jita a tsarge. Ta sadda kanta kad’an ko zai daina duban nata ya amsa mata gaisuwarta amma inaa kaman ma ba dashi take ba. D’agowa Ta kumayi suka dubi juna still bai daina kallonta ba bai kuma canza position d’in taguminsa ba. Ta d’an tsime kad’an tace “What.. Why are you staring at me like that.. Wait is there something on my face..?” Ta shiga shafe fuskarta tana turo baki gaba. Jinjina mata kai yai yace “Umhum.” Taci gaba da Shafa Fuskar nata tana neman mai yake kallo tana yi tana fad’in “Where ina yake..?” “There.” Ya bata amsa yana d’aga mata gira da idanu alamun yana mata nuni da abinda ke bisa fuskar nata. Ta marairaice fuska tana fad’in “Inspector Nidai banji komai ba.” “Come here.. Zo na nuna miki..” Ya k’arashe yana janyota kusansa kad’an. Dik ta sakankance zai cire mata abinda ke fuskar nata ne saiji tai ya manne bakinsa da nata. Daskarewa tai tanajin yanda yake sarrafa harshenta cikin bakinsa. Tai ta maza ganin yana neman fice mata daga giya ta turasa da iyaka k’arfinta. Tallafo fuskarta yai yana dubanta da idanunsa da tuni sun k’ank’ance “Didn’t you miss me..?” Ya tambaya cikin kasaliyar murya. Kaman zata fashe masa da kuka take fad’in “Of course I did miss you.. But.. Ba irin wann kewar ba.. And besides baka San yanda muke bane.. What if..What if..” Bai bari Takai aya ba ya katse Ta da fad’in “Fine.. Tashi mu tafi gidanmu.. Ince kin masu sallama..” Ta mak’e masa kafad’a tace “Ni dai dan Allah ka barni na Kwana..” D’an shan mur yai had’ida matsawa baya kad’an “Shiga ki masu sallama ki fito mu tafi..” Ya fad’i yana duba writs watching d’insa ba tareda ya dubeta ba fuskar nan babu walwala. Ta kuma yin narai narai da idanu tana dubansa yanda ya canza lokaci guda. Tasan tinda ya fad’i haka bazai canza ba. Jiki babu laka Ta mik’e ta nufi ciki. Daga yanda Aunty Larai ta ganta tasan akwai wani abu “Ya na ganki haka.. Har zaku wuce ne..?” Sadiya ta d’an turo baki gaba kad’an tace “Aunty Cewa yai Wai bazan kwana ba.” Aunty Larai ta saki baki had’ida kame hab’a tace “Au Wai dama saida kika ce masa kwana kike son yi.. Ai ban zanci zaki fad’i haka ba da tun kafin ya zauna na koraki Kun tafi.. Au ashe da yace a fara kawoki nan bai maki ba saida kikace masa kwana kike son yi.. Toh bazaki kwanan ba.. Ko ya k’yaleki ma mu dai kam bamuda masauk’inki a nan.. Kar ma kiyi Umma taji wann batun dan Kinsan Sauran. Ungo amshi nan..” Ta k’arashe tana bata sauran had’e had’en kayan gyaran da ta mata.. Saura idan kinje kar kisha kiyi flushing nasu a toilet nida ke ne.. Natural Herbs ne duka a nan masu kyau ga lafiyar d’anadam da honey ake sha kaman tea zaki had’a maku instead of sugar ki zuba honey har shima idan yana so zai sha kinji koh.. Ta d’an turo bakinta gaba kad’an tana jinjina kai. Tana iya jiyo k’amshin cloves daga cikin jakan da yake da tabbacin dangin itace ne masu inganci da kuma kyau ga lafiya. Jiki a sanyaye ta isa taima Umma sallama ta fito ta taddashi. Sanda ta iso waya ne manne kunnensa yana amsa kira. Yana mik’ewa taga bayan navy blue polo d’in dake jikinsa an rubuta FCID da manyan haruffa.. Ko ba’a ce ba kasan rigar Office ne. Ta d’an tab’e baki kad’an a ranta tace k’ila daga Office ko gida baije ba kenan.. Watak’la ya tsaya wani wajen ne. Har suka shige Mota waya yake, ita har mamaki take shin kunnensa bai gajiya ne. Har suka kusan isa gida waya yake wanda zata ce bata fahimci komai ba dan aikinsa ya shafa.. Yo itakam ma window take ta duba abinta tana kallon tangama tangaman titunan birnin tarayya da aka k’awatasu da security lights ta ko Ina. Koda ya gama wayan bai ce mata komai ba, ta saci kallonsa taga hankalinsa kacaukam naga tuk’a mota. Sai itama ta maida nata kan b’angarenta. Ta kuma jingina kanta tana kallan gari. Har suka iso gida bai ce mata komai ba, dik sai taji jikinta yayi sanyi saikace ba shine ya gama cewa yayi kewarta ba ya wani k’i kulata yanata minding business d’insa. Tai k’wafa cikin zuciyarta. Har dai Patrick ya k’araso yana musu sannu da zuwa welcome sir, welcome ma..” Still Mu’azzam bai kulata ba saima umartan Patrick da yake ya k’arasa da suitcase d’in nata k’ofar parlor. Ko zarafin amsa Patrick dake gaisheta bata samu ba. Toh kardai fushi yai da ita.. Shin meye laifin dan tace ya barta ta kwana d’aya wajen Ummanta da ‘yanuwanta.. Kawai dai mai hali ne da bai fasawa amma itakam bataga wani abu cikin hakan ba. Baibi takanta ba yai shigewarsa, tai k’wafa cikin zuciyarta tana jin zafin yanda yake ta wani basarwa yana shareta saikace ba yau ta dawo ba.. Dama k’ila babu wani missing d’inta da yai.. Da yayi kewarta bazai banza da ita haka ba. Ta K’araso parlorn jikinta dik a mace. D’ago kan da zatai taga gidan an canza masa tsari gaba d’aya. Kaf kayan dake cikin gidan an canza an zuba sabbi.. Taci gaba da takowa a hankali tana kallon tsarin gidan.. Gidan da tai zaton bazata kuma dawowa cikinsa ba. Gidan da tai masa lak’abi da GIDAN ARO. Zuciyarta ne ya yanke sanda ta tuna tangamemen hotonsa da Safeenah da ake soma hangowa idan ka nufi staircase. Ta d’ago idanu tana duban spot d’in da hoton yake.. K’irjinta ya kuma bugawa sakamakon ganin nasu hoton da tai.. Hoton da aka masu suna zaune a park farkon fitarsu mission da sukai tare. Ya matso da bakinsa kusan kennenta yana fad’a mata dik abinda suke acting ne cikin mission ne Ita kuma Ta saki murmushi wanda tasan yak’e ne kawai amma sai gashi a hoton baiyi kama da acting ba. Komai looks real kaman dai soyayya ce ta gaskiya. Ta saki murmushi a hankali still idanunta na kan hoton. Juyowar da zatai ta gansa tsaye bayanta fuskarsa babu yabo babu fallasa. Sai ta d’an sha jinin jikinta ta sadda idanunta kad’an. Ta soma takowa a hankali ta K’araso gaba gareshi. Still idanunta a k’asa take furta “Fushi kake dani.?” Bai ce mata komai ba Sai dubanta da yake. “I’m sorry.. Bansan maganar zai b’ata maka rai ba.. Kai hak’uri kaji..” Ta k’arashe muryarta na rawa kaman zatayi kuka. D’an takowa yai ya matso dab da ita sosai kafin ya kamo hannayenta, ta d’ago idanunta kwantattun k’walla tab cikinsu tana dubansa. Murmushi ta hango saman fuskarsa wanda ba lallai ka fahimci hakan ba sai idan domin kai akayi. Ya juyar da ita had’ida rungumarta ta baya ya d’aura hannayensa saman cikinta, su duka biyun suna fuskantar hoton nasu. “Did you like my surprise..? Tsarin gidan ya miki..?” Ya tambaya yana rank’wafo da kansa kad’an zuwa wuyanta. Mr Inspector kenan komai nasa burgeta yake. Wato bazai amsa mata ba saidai ya nuna mata a aikace. Ta lumshe idanunta kad’an kafin ta jinjina masa kai ba tareda Ta iya furta koda kalma ba. Ya murmusa kafin yaci gaba da fad’in “Nan gidanki ne.. Everything here is yours.. Komai da komai dake cikin gidan naki ne.. Including me..” Ya k’arashe cikin wane irin siga mai kashe mata jiki. Hawayen da suka jima mak’ale cikin idanunta suka gangaro.. Ba komai ta tuna ba face farkon zuwanta gidan da ya jaddada mata cewa gidan tamkar dai GIDAN ARO yake a wajenta wanda za’a iya sallamanta ko yaushe.. ta zauna cikin shiri sann kar ta baje kolinta dan ga duk mai hankali da hangen nesa ba’a baje koli a GIDAN ARO. Sannan dik abinda aka ce maka na aro ne akwai ranan da za’a karb’i wann abun. Hausawa sunce Kayan aro baya rufe katara.. Sann dik daren dad’ewa zaka mayar da abinda aka ara maka.. Juyo da ita yai suna fuskantar juna, ya saka yatsarsa guda yana goge mata hawayen dake gangaro mata. “Baki son gidan ne.. Ko tsarin ne bai miki ba..?” Ta Ware idanunta tana dubansa “Komai yayi mun... Thank you for this wonderful surprise.. But do you know something..” Ya tsareta da idanu, yayinda taci gaba da fad’in “Kaid’in kafi mun duk abinda ka zuba cikin gidan nan.. Soyayyarka da k’aunarka a gareni sun isheni..” Ta jinjina kai kad’an hawaye naci gaba da gangaro mata “A baya wad’ann k’yale k’yaleni sune mafarki na kuma sune burin Sadiya.. Nayi zaton Sune kad’ai suke haifar da soyayya.. Nayi zaton idan babu su babu wata kalma da ake kira So.. Saidai bayan had’uwata da kai na yarda akwai wann kalma da ake kira So koda babu k’yale k’yale na rayuwar duniya wacce za’a tafi a barta a nan duniya.. Ba kaman mutane guda biyu da suka rayu domin Allah suka so juna dan Allah.. A ranan k’iyama Allah ya tadasu tare.. Shin akwai soyayyar da tafi wann..?” Murmushi da hawaye gauraye saman fuskarta. Yayinda Mu’azzam ya k’ura mata idanu yana jin kalaman nata har cikin b’argo da tsokarsa. Ta kuma murmusawa kafin taci gaba da fad’in “Akwai abubuwa da dama da Allah zai baka a duniyar nan kasan cewa ya gama maka arziki.. Kaman dai arziki na lafiya wacce babu arzikin da ya kaita bayan kaancewarka musulmi mai kad’aita Ubangiji.. Bayan naga Mamy da halin da ta tsinci kanta ciki na jarabawa Tabbas na yarda k’yale k’yale na duniya ba komai bane face rud’i ne na d’an wani lokaci da yake k’ayadadde.. Mafarki na ne a baya na kasance cikin daula da tarin arziki... Amma a halin yanzu na shafe wann mafarkin.. Kaine mafarki na.. Kuma kaine cikan burina Mr Inspector... Ina fata na rayu dakai a nan gidan Duniya wanda yake GIDAN ARO ne.. Sannan a rayuwa na gaba Ina fata Allah ya kuma tadani da kai k’ark’ashin Inuwa guda a gidan Gaskiya.. I love you so much my Detective..” Ta k’arashe tana mai rungumarsa. Rungumeta yai yana mai lumshe idanunsa shid’inma siririyar Hawaye ta gangaro masa “I love you.. I love you more my Beautiful Stubborn head.” Ya k’arashe yana mai kuma matseta jikinsa. Soyayya suka dinga nuna ma junansu wanda ya tabbatar masu cewa sud’in sunyi kewan juna sosai da sosai. Babu kaman Mu’azzam wanda har saida Sadiyar Ta tausaya masa taga wautanta da tace zata kwana gida bayan shafe kusan sati da yai baya tare da ita. ** Coin d’in ya dinga juyawa yana tuna lokacin da yake k’arami cikin stuff d’in mahaifinsa ya sami exactly irin wann coin d’in wanda tsakiya an rubuta _Black African Team_ mai hakan yake nufi.. Ya akai ya sami exactly irin wann coin d’in a wajen Habeeb k’anin Sadiya..? Kodai su Danger ne suka yasar da Coin d’in a gidansu Sadiya Habeeb ya tsinta..? Toh kenan wann coin d’in ta iya yuwa nada alak’a da su Danger kenan..? Toh amma idan wann coin d’in nada alak’a dasu Danger ya akai ya sami irinta a cikin kayan mahaifinsa..? Gaba d’aya kansa ya k’ulle.. Anya coin d’in iri guda ne..? Babu abinda zai had’a mahaifinsa dasu Danger.. Ya dafe kansa kad’an kafin ya furta a fili “Su waye su Danger.?” Ya bama kansa amsa da fad’in “Sune mutanen da suka kashe mun k’anwa Ikram..” “Toh idan wann coin d’in nada alak’a da mutuwar Ikram kenan ta iya yuwa mutuwar mahaifinsa ba accident bane..? What if shiryawa akai..? What if su Danger Sun jima suna bibiyan ahalinsa..? What if mutuwar Daddynsa shiryayya ne..? Zuciyarsa yai wani irin yankewa. Ya shiga girgiza kai yana dafe kansa wanda gaba d’aya ya masa nauyi komai ya cunkushe masa. Tunanin yanda ya aje wancan coin d’in ya soma.. Ya zama dole yai comparing coins d’in ya tabbata idan sunada kamanceceniya. Da wann tinanin ya aje coin d’in gefen bedside ya janyo sadiya dake bacci zuwa cikin jikinsa, ya lumshe idanu yana shak’an k’anshinta mai sanyi wanda ya sauk’ar masa da natsuwa cikin zuciyarsa. ** A can Fufore kaw Shemau k’arfe shad’aya na dare ta soma bugun k’ofar gidan k’awarta Baddo. Da k’yar Baddo ta k’araso ta bud’e k’ofa cikeda tsoro dan dama mijinta baya nan yayi tafiya ga yanda duniyar ta zama kowa kaffa kaffa yake da rayuwarsa. A razane Baddo take k’ok’arin tura k’ofa tana karanto addu’o’i dan Ta zaci mahaukaciya ce ko gamo tai cikin daren. “Baddo nice Shemau dan Allah kar ki rufe k’ofar.. Ki ceceni Baddo banida yanda zanje. A cikin uku nake..!” Baddo ta dafe k’irji tana duban Shemau cikeda tsoro dan bata ma ganeta ba saida Shemaun tai magana “Shemau kece haka..? Mai zan gani ni Baddo..” Kuka Shemau Ta fashe mata dashi tana fad’in “Baddo ki taimakeni.. Wllhi cikin tara nake bama uku ba..” Baddo ta shiga salallami tana tafe hannaye tana duban Shemau cikeda tsoron duniya.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *55* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Baddo ta canza position d’in taguminta yafi sau abinda yafi “Ni babu abu guda dana fahimta Shemau. Kinaso kice mun tin jiya da dare abin ya faru.. Toh a ina kika kwana..?” Gajeren tsuka Shemau tai “Duk wann ba lallai kiji ba Baddo tinda Allah ya taimaka na wayi gari.. Da ace jiya kika ganni nayi imani Bazaki ganeni ba.” Baddo tace “Yanzun ma da k’yar na ganeki wllhi saida kikai magana.” Ta ida maganar tana aje mata plate d’in indomie da ta dafa mata. Shemau ta janyo plate d’in ta soma nad’an abincin hannu baka hannu k’warya. Baddo ta rapka uban tagumi tai zaune gefe tana kallon Shemau matar Alhaji Salman Gamji yanda ta fice a hayyacinta cikin lokaci k’ank’ani. Ta gyara zama tana kuma canza position d’in taguminta “Wai ni mi ya faru dake ne.. Mai ya jefaki cikin wann ukun..?” Shemau ta dubeta sai kuma tace “Safeenah ce ta jefani cikin wann bala’in.” Baddo ta girgiza kai tace “Safeenah kuma..?” Shemau ta janyo ledar pure water ta huda tana zuk’a saida ta shanye tas kafin ta dubi Baddo tace “Yo Safeenah Ta jazamin da na d’auki shawarinta..” “Kika d’auki shawarinta kaman yaya..?” “Kinga Baddo ke k’awata ce kuma rugarmu d’aya tare muka taso.. Kin sanni na sanki babu wata ‘yar b’oyo a tsakaninmu dan haka zan fayyace miki dik abinda ya faru.” Ta gyara zamanta tana karanto ma Baddo duk abinda ya faru tin daga kan plan d’insu da mijinta na amfani da Safeenah da sukaso suyi har kawo yanda teburin ya juye zuwa kan Shemaun. Dik Ta sanar da Baddo saidai bata sanar da ita duk abubuwan da sukai da Mommy ba. Baddo Ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Toh meye laifin Safeenah a nan..? Ai idan akwai mai laifi kece number one sai ko mijinki.. Shi da kikai abin sabida shi gashi bai gani ba ya cazga maki rashin mutunci ya kwance miki zani a kasuwa.. Ki gode ma Allah ma da ba kan idanun yaranki abin ya faru ba.. Dama shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ginata gajeriya mai yuwa kaine zaka rufta ciki.. Yanzu ina ribar abinda kika so aikatawa ma wacce bataji ba bata gani ba.. Gashi ke kin kwan ciki kin rufta ciki wanda kikayi domin shi bai gani ba saima tozartaki da yayi a bainar duniya..” Shemau ta katseta da fad’in “Salman baida laifi shawarin shashashar nan ne Safeenah da na d’auka ya kaini ya baro ni.. Banda ma b’atan baseera irin nawa mai zai kaini d’aukan shawarin da ya fito daga bakin Safeenah wacce batada ta cewa sai abinda aka tsara mata.. Zafin kishi ne kawai ya d’ibi Salman kuma nasan idan ya sauk’o zai fahimci cewa bani kawo masa maza cikin gida.. Tsaf zan wanke kaina a idon mijina dan har abada bazamu rabu ba..” Baki sake Baddo ke dubanta kafin tace “Aw bayan wann mummunan wulak’anci da ya miki kina tunanin komawa gidansa.” Da tsananin Mamaki Shemau ke duban Baddo “Toh ina zan koma..? Inada wajen komawa ne..? Ruga kike so na koma a titi kike so na k’arashi gantali na.. Nan gidan duniya bayan Salman da ‘ya’yana su waye nake dashi..?” Baddo ta jinjina kai tace “Haka ne.. Dan ko kin koma ruga bana jin Inna Fini zata amsheki.. Kin wahala hannun matar K’anin mahaifinki.. Kin taso marainiya babu mahaifa.. Allah ya rufa miki asiri ya yaye miki wahalarki da k’uncinki kikai aure gidan masu arziki..” Shemau ta jinjina kai tace “K’warai kaw Salman shine Gata na dan haka ko meye ya umarcen na masa zan masa matuk’a zan iya aiwatar da wann abin. Ina tsaka da shan wuya hannun Inna Fini ina kawo mata tallan Fura da nono cikin gari Salman ya hangoni daga cikin motarsa ya saye abinda nake saidawa ya kuma bini har rugarmu ya auroni dukda mahaifiyarsa bata so auren ba. Da shike yana k’aunata ya auroni ya tsame ni daga k’angin bautan gidan Inna Fini da Baffa. Akasi yanzun ma aka samu da rashin fahimta na tabbata zai fahimceni dan wllhi bazan koma hannun Inna Fini ba.. Ina nan cikin gari har ya hak’ura ya maidani kan ‘ya’yana.. Babu kalan bak’antani da Inna Fini da Baffah basuyi ba a idanunsa amma ya toshe kunne yace yaji ya gani zai aureni.. Har cewa sukai ni mayyace ni na cinye uwata zan lashe masa dangi amma dukda haka bai fasa k’udirinsa na aurena ba.. Toh ina kike tunanin zan koma Baddo bayan ma na riga na saba da rayuwar jin dad’i.” Baddo ta girgiza kai tana murmusawa kad’an kafin tace “Tabbas Duniya karatu ta biya miki Shemau, bayan duk wann uk’uba da kika sha a rayuwa har zakiyi tunanin ki cutar da wani D’anadam bayan ke Allah ya cireki daga cikin wahalan..? Haba Shemau.. Ai idan wani zai mugunta wllhi ke bazakiyi ba sabida Kinsan abin Kinsan ya akeji idan aka cutar dakai.. Nayi matuk’ar mamaki da kikaso cutar da wata..” Shemau tace “Baddo ya kike so nayi bayan wa mijina nake hakan.. Mutumin da ya zamto Gata da sutura a gareni.. So kike na juya masa baya ko me.?” Baddo ta katse ta da fad’in “K’warai kuwa babu biyayya ma wani abin halitta wajen sab’awa Ubangiji koda miji ne ko mahaifa.. Zalunci haramun ne Allah ya haramta ma kansa zalunci sann ya sanya shi ya zamto haramun a tsakanin Al’umma.. Idan mijinki yace sai Kun cutar da wani sai ki nusar dashi idan yak’i ganewa ke dai kar ki aikata duk hukuncin da ya d’auka akanki sai ki bar wa Allah lamuranki da sannu zai samar miki mafita amma ba wai ki bisa duk ku zama mugaye ba dan ya taimakeki a baya.” Shemau ta d’anyi shiru sai kuma tace “Mijina fah ba mugu bane Baddo shi hakkinsa kawai yake nema wajen Yayansa Marwan wanda yayi kane kane akan hakkin nasa.. Yayansu yayi yarjejeniya a rubuce cewa ya mallaka ma Salman assets d’insa da dukiyarsa toh Marwan bai baiwa Mu’azzam ba sann bai baiwa Salman ba mai yake nufi idan ba handamewa yai ba.. Kinga kuwa mijina fad’a kawai yake akan abinda yake nasa ne.. Mahaukaciyar d’iyarsa ce da muka saka cikin plan d’in Ita Ta b’ata komai. Bansan wani b’atan baseera ne yakaini amfani da shawarin Safeenah ba..” Baddo Ta sauk’e ajiyan zuciya tace “Koma dai menene sharrinku ne Allah ya maida maku kanku.. Ke kanki kince baki San wani b’atan baseera ne yakaiki d’aukan shawarin Safeenah ba.. Hakan kad’ai ya isheki ki gane ishara Allah ya nuna miki idan kinada rabon gyarawa amma idan kuma Bakida niyyan gyarawa wann ke ya ragema.” Shemau ta dubeta had’ida tab’e baki kad’an kafin tace “Kinga ni bacci ma nake ji, kar ki damu ko a nan parlor zan kwana dan nasan gidan naki d’akuna biyu ne d’aya naku d’aya na yara.. Yo gidan ma babu AC bansan ya zanyi nayi bacci ba..” Baddo ta tab’e baki tace “Ke kika San wann.. Ni mijina ma baya nan.. Bara na kawo miki abin shimfid’a.” Ta k’arashe tana mai mik’ewa. Shemau tace “Yama fi da baya nan.. Kafin ya dawo zan koma gidana.. Ina zan iya wann rayuwa..” Ta k’arashe tana mai gyara kwanciyarta. Baddo dai girgiza kai kurum tai ta shige abinta ta bar Shemau nan kwance tana lissafi. ** ABUJA Musaddiq na shirin kwanciya Safeenah ta turo d’akin ta shigo sai sakin huci take. Da mugun mamaki yake dubanta kafin ya jinjina kai kad’an yace “Kin dai San ni ba k’aramin yaro bane da zakike shigo min d’aki kai tsaye.” “Bafa zan k’yaleka ba Musaddiq sai ka amsa min tambayata.. Ka fad’a min Idan tareda shegiyar matar Mu’azzam kuka dawo.?” A tsananin kufule yake dubanta, yana tuna sharrin da suka tasamma d’aura ma Sadiya itada Shemau. Yai k’wafa kad’an kafin yace “Ki fice mun a d’aki Feenah..” “Bazan fice d’in ba ank‘I a fice Ai dama gaskiyar Mommy ne tare kuke k’ulle k’ullenku kaida Mu’azzam.. Shiyasa kullum bayansa kake bi baka ganin laifinsa kaima.. A gaban idonka ya zab’i wancan Karuwar ya k’yaleni ina’yaruwarka harda wani binsu ka take masu baya kuyi tafiya.. Kai a dole ga mai rik’e masu jaka ko..” A kufule wann karon yayo kanta yana nunata da d’an yatsa “Be thankful.. Ki gode ma Allah ban sanar da Mu’azzam abinda kuka tasamma yima matarsa ba Keda Aunty Shemau.. Kuma wllhi idan baki daina shiga hidiman gidan Mu’azzam ba zan miki abinda baki tab’a tsammani ba Safeenah.!” Baki sake Safeenah ke dubansa “Eh lallai Musaddiq na yarda k’wayan Naka basa fad’a maka daidai.. Ni kake nuna ma yatsa kaman zaka daka.. Kawai ka dakeni sai nasan ka cika masoyin Mu’azzam.. Laifin Mommy ne da tuntuni bata jefa ka a Rehabilitation centre ba..” “Nida ke waye yafi buk’atan tafiya Rehab.. Dalla Malama fice min a d’aki..” Ya k’arashe yana mai janyota ya turata waje. Har zai maida k’ofar ya rufe ya dakata kad’an yace “Sai Ki kira Ally d’in naki ki mata jaje..!” Yana ida fad’in haka ya maida k’ofar ya rufe akan fuskar Safeenah. Huci kurum take tana murza tafin hannunta.. Kardai plan d’insu backfired.. Taiyita kiran layin Aunty Shemau bai shiga.. Toh meye ne ya faru..? Wato kenan Sadiya ta dawo gidanta.. Ai kuwa sassafe zata tafi gidan ta gane ma idanunta hakan. Tai k’wafa kafin tasa kai ta wuce cikin tsananin b’acin rai. ** Ni’imtaccen k’amshi ne mai gauraye da natsuwa ya tadashi daga baccin nasa. Ya mik’e yana karanto addu’an tashi a bacci fuskarsa d’aukeda murmushi. Cikin zuciyarsa banda hamdala da gode ma Ubangijinsa baya komai. A haka ya mik’e ya nufi bathroom yayo wanka ya fito ya soma shirin fita Office. Tin daga staircase yana sauk’owa yasan matar gidan gwana ce wajen tsafta, ko ina need Sai k’amshi dake tashi ga na room fresh gana turaren k’una dake tashi a natse cikin electric burner, ga na abinci na bada nasa kalan shima.. Gidan sai ya bada wani kalan k’amshi na musamman. Can ya hangota cikin kitchen tana tsaye jikin working base tana chopping onions saman chopping board. Tana sanye ne cikin maroon top da ya kama jikinta d’amas Sai black three quarter wanda shima yai fitting d’inta. Sumar kanta ta tupkesa waje guda tayi ponytail style dashi. Tayi kyau sosai har kaman bazai iya janye idanunsa daga barin dubanta ba, just like a berbie. Ya soma takowa a hankali ba tareda ya bari tai noticing d’insa ba, abinka da yankan albasa bama ta lura na zuwa ba hankalinta kacaukam naga abinda take. Chapp taji hannun mutum saman cikinta. Ta d’an saki k’ara a razane. “Good morning Beautiful..!” Ya fad’i still tana nan rik’e cikin jikinsa. “You scared me... I almost chopped my fingers.” Ta fad’i kaman zatai kuka. Murmusawa yai yana kuma shigar da kansa cikin wuyarta “Every little thing scares you..” Ya k’arashe yana juyo da ita suna fuskantar juna. Hannayensa saman k’ugunta yayinda Sadiyar ta d’ingile k’afafunta ta zuba nata hannayen saman shoulders d’insa dan kar ta b’ata masa jiki da onions. “You look fantastic.. I love you..” Ya fad’i yana bata light kiss. Murmusawa tai kad’an kafin tace “Thank you... Handsome.” Ya murmusa yana mai lakatan hancinta kad’an “K’amshi ya cika mun ciki tin daga upstairs.. Mai ake dafa mana ne..?” Ta d’an marairaice fuska tace “Kai Handsome nothing special fah.. Kawai chicken Sandwitch ne served with black tea..” “Sounds delicious.. But I think I’ll just have the tea.. Sauri nake suna jirana a office..” Tai rau rau da idanu tace “Kai dan Allah Bazaka tsaya ka karya ba.. Kaga fah I’m almost done, onions d’in nan kawai zan zuba..Oh no no I’m sorry.. Bansan da wuri zaka fita ba.. I should have waken up earlier..” Tana maganar tana k’ok’arin rounding up. Hannayenta ya kamo yana fad’in “Relax Beautiful.. It’s okay.. Na gode da kika tashi as early as you can bayan gajiyan hanya da kika kwaso.. You don’t need to stress yourself.. Badon Ina sauri ba zan tsaya naci, na riga na makara ne.. Ban saba makara ba suna can suna jirana..” Ya d’an kashe mata idanu guda kafin yace “But I guess ke kika sa na makara..” Ta zaro idanu waje tace “Ni kuma..! How am I at fault.?” Ya janyota jikinsa kad’an yana mata wasu salon kafin yace “Because last night I slept beside you shiyasa na makara..” Ta rufe fuskarta kad’an cikeda kunya. Daidai nan wayarsa ta soma ruri.. Yusuf ne mai kira yai saurin cirota a aljihu yana fad’in “See, suna jirana.. I’ve to go now.. Take care I love you.” Ya fad’i yana manna mata peck a cheek d’inta. Ta biyosa tana fad’in “Toh tea d’in fah bazaka sha ba..” “Kiyi hak’uri na makara I’ll make it up to you next time..” Ya k’arashe yana mai shigewa Mota. Ta d’ago masa hannu tana masa waving. Ya sakar mata murmushi yana d’an kashe mata ido guda lokaci guda ya juya kan motar ya fice. Ta juyo ta komo cikin gidan tana fad’in “May Allah always be with you my Inspector..” Haka ta k’arasa cikin gidan taci gaba da abinda take. Dik Sai ta kasa cin breakfast d’in itama. Kusan duka ta juye ma Patrick. Ruwan tea d’in da Aunty Larai ta bata kawai taita sha. ** _Police Headquarters_ Motar prison ne ta k’araso aka fito da Assad hannayensa rufe cikin handcuffs. Hajiyarsa ta fashe da wani irin kuka Shaheed k’aninsa na rik’e da ita kaman zata duk’a k’asa sabida kuka. Shaheed sai tausan ta yake cikin k’arfin hali. Ya rik’ota Ta zauna saman wasu kujeru dake a k’ofar wajen. Mu’azzam ya hangosu daga nesa tausayin mahaifiyar Assad fal zuciyarsa, da k’yar ya k’araso wajensu yana jin zuciyarsa na masa wani irin rauni. Baima san mai zai soma fad’i ba, baisan da wasu irin kalamai zai lallashi mahaifiyar Assad ba. Cikin kuka take duban Mu’azzam tana fad’in “Ya fad’a da bakinsa.. Ya amsa cewa yaci amanar aikinsa.. Maiyasa zai aikata haka.. Maiyasa Mu’azzam..Mai yake nema da tsanani a duniyar nan.. Bai duba maraicinsa ba bai duba d’iyarsa da yake fafutukan amsowa daga hannun matar can a Kotu ba..” Kuka ya hanata ci gaba da magana. “Hajiya Assad baida laifi.. K’age aka masa.. Baici amanar k’asa ba.. Baici amanar aikinsa ba.. Inada tabbacin abokina ba D’antadda bane.. Kuma zan tabbatar ma kowa hakan da izinin Allah. Ki kwantar da hankalinki kinji.. In sha Allah komai zai wuce.. Allah zai fidda Assad daga wann bak’in k’ulli da aka masa..” Hajiya bata iya amsa sa ba sai kuka da take. Ya dubi Shaheed yace “Take her home.. And make sure ta sami hutu.. Zan kula da case d’in Assad..” Shaheed ya jinjina kansa yana mai amsa ma Mu’azzam d’in. A tare shida Shaheed suka kai Hajiya Mota Shaheed na rik’eda Ita tana cazgan kuka tana kama k’irjinta. Kai da gani kasan ba lafiya take ba. Shaheed ya dubi Mu’azzam yace “Mun gode K’warai Inspector da d’awaniyarka.. Allah ya saka maka da alkahiri.” Mu’azzam ya dafa hannun Shaheed yace “Kar ka mun godiya.. Banyi rabin abubuwan da Assad ya mun a rayuwa ba.. Nida Assad are practically brothers so dan na masa wani abu ba favor bane dole akaina nayi.. Ka kula da mahaifiyarku na maka alk’awari in sha Allah D’anuwanka zai fito.” Shaheed ya jinjina kai a hankali yana kuma godiya wa Mu’azzam d’in kafin ya shige ya tada Mota. Maleeka dake tsaye daga can gefe akan idanunta komai ya faru. Babu abinda ya d’aga mata hankali kaman ganin mahaifiyar Assad da tai cikin yanayi na tashin hankali.. Sai ta tuna nata mahaifiyar dake kwance gida tana jinya wanda duk kud’ad’en da take samu daga wajen su Chief ma ita take turawa. Hawaye guda d’aya ya gangaro mata.. Meye laifinta dan ta amshi kud’ad’e ta tura ayima mahaifiyarta dake tsananin jinya aiki.. Shin kowa bazai komai domin ya ceci mahaifiyarsa ba.. Tai saurin juyawa ta shige building d’in. Restroom ta shige tana cazgan kuka. A fili take furta “Meye laifina.. Meye laifina dan naso taimakon mahaifiyata..?” Zuciyarta ya soma tuhumarta “Idan wanda kika d’aura ma sharri ya rasa nasa mahaifiyar fah ke taki ta rayu shin wane riba kika samu a cikin hakan.. Shin kin mance duk kalan abubuwan alkahiri da Assad ya miki..? Shin kin mance gwagwarmayar da kuka sha tare.? Shin kin mance barkwancinsa musamman a lokutan da kike tsananin son ganin Inspector Gamji ya kula ki.. Assad was there for you.. Yana k’ok’arin kwantar miki da hankali dukda yasan Abokinsa baki ishesa kallo ba balle ki shiga cikin jerin matan da yake so.. Shin duk kin mance abubuwan da Assad ya miki Maleeka.? Why Assad..? Why him.. He’s a good guy.. A kindhearted wanda a koda yaushe baida burin da ya wuce ya kyautata ma mutane.. Assad bai cancanci haka ba. Ta rintse idanunta hawaye na gangaro mata. Daidai lokacin wayarta ya soma ruri.. Ta saka hannu ta d’auka k’aninta ne yake kira daga gida.. Daga yanda taji muryarsa tasan babu lafia. Cikin kuka take tambayarsa meke faruwa.. Nan take ya sanar da ita Mahaifiyarsu ta mutu ana k’ok’arin shiga da ita tiyata... Wani irin kuka Maleeka ta fashe dashi tana mai silalewa k’asa. Taci kukanta ma’ishi tana kiran Mamanta. Saida tai ma isanta kafin kukan nata ya lafa.. Jiki babu k’wari Ta mik’e Ta fito. Chief ta hanga k’ofar Office d’insa, alama kawai yai mata da ido ta gane mai yake nufi. Jiki babu k’wari ta nufi Office d’insa. ** Mu’azzam kaw yana isa asibitin ya shiga har office d’in securities d’in, mutum guda ya samu a cikin Office d’in wanda yake kula da na’urar cameras d’in. Suka gaisa kafin ya nuna masa ID d’insa yace “FCID, inaso ka min playing cctv footage na cikin asibitin nan for the last 2weeks..” Mutumin ya d’an sosa kai sai kuma yace “Sir.. Baka tunanin yayi tsayi zai d’auke mi some hours..” Murmusawa Mu’azzam yai kafin yace “Barin fad’a maka exact date d’in da nake so kamun playing..” Ya k’arashe yana mai fad’a masa exact date d’in. Security d’in ya d’an fara ‘yan kame kame. Gefen suit d’insa Mu’azzam ya d’aga bindiga ya bayyana. Lokaci guda ya dafa security d’in dake zaune saman kujera gaban Computer ya d’an rank’wafo kad’an, cikin kwantar da murya yace “Zaifi maka kyau idan kayi abinda nace.. I can kill you right here and burry your body ba tareda wani ya gane hakan ba.. Just do what I ask you to do.” Ya k’arashe yana mai manna bakin bindiga a k’eyar mutumin. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *56* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Chief ya girgiza kai kad’an yana dubanta “Meke faruwa..? Ya na ganki haka..?” Kuka Maleeka ta kuma fashewa dashi, cikin muryar kuka take fad’in “I just... I... I just lost my Mom..!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana mai zama saman kujera. Chief ya dubeta da fuskar tausayi yana girgiza kai “Kiyi hak’uri Maleeka.. Sorry for your loss.. My condolences..” Maleeka dai bata iya cewa komai ba Sai cazagan kukanta take tana kiran mahaifiyarta. Chief ya k’araso ya mik’a mata ruwa yace tasha. Babu musu ta amsa tana sha tana kuka. Saida tai mai isarta kafin kukan nata ya tsagaita. Chief ya jingina jikin tabel yana dubanta “Maleeka..” Ta d’ago watery eyes d’inta tana dubansa. Yayinda Chief yaci gaba da fad’in “Naga irin kallon da kike wa mahaifiyar Assad lokacin da za’a fita dashi.. Na hango nadama da tarin danasani cikin k’wayar idanunki.. Na hango tausayi da son jada baya a tattare dake... Maleeka if you dare think of double crossing me, wllhi wllhi I won’t hesitate to execute you.. Shawari nake baki.. Don’t you ever think of ratting us out.!” Da tsananin mamaki take dubansa, Ta girgiza kai kad’an tace “Yanzu nace maka Mahaifiyata Ta mutu.. Ko ganinta banyi ba.. Mahaifiyata ta rasu ko cikakken 1hr batayi ba amma har kanada guts d’in da zaka dubi cikin idona kace zakai threatening d’ina Chief..? Shin kai wane irin mutum ne da babu d’and’anin imani cikin zuciyarsa..!” Murmusawa yai kafin yace “I don’t give a damn dan kin rasa mahaifiyarki.. Kafin ki rasa naki mahaifan na rasa nawa.. Rashin mahaifiyarki bazai sa a fasa komai a duniyar nan ba dan haka shawari na baki ki iya takunki. Idan kunne yaji toh fah jiki ya tsira.. Dismiss now..!” Ya k’arashe yana mai nuna mata k’ofa. Dubansa kurum Maleeka take da rinannun idanunta, zuciyarta na mata tsananin k’una. Jinjina kai tai kafin ta sara masa lokaci guda tasa kai ta fice daga ofishin k’irjinta na tsananin k’una. Tana fitowa bata ko tsaya ba ta fice ta d’auki Cab ta nufi apartment d’inta. Tana isa ta soma shirya kayanta, tanayi tana tuno mahaifiyarta tana zuban hawaye. Meye amfanin aikin da take idan mahaifiyarta bazata Mora ba.. Ta rasa mahaifiyarta wacce tasha d’awainiya akanta tun tana yarinya.. Bata mance lokuta da dama da mahaifiyarta ta kwana babu ci babu sha dan kawai ta biya mata kud’in makaranta.. Mahaifiyarta ta wahala da ita da k’annenta a rayuwa..Taci burin ta biya mahaifiyarta duk wahalhalun da tai akansu itada ‘yanuwanta musamman ma ita.. Ta kuma share hawayenta tana mai jefa kayanta cikin jaka. A fili take furta “I need to make things right.. Kafin na tafi zan gyara komai.. I promise zan gyara duk abinda na b’ata.. Zan wanke ka Officer Assad.. I’ll confess.. I’ll confess everything.. Dik abinda na sani zan fad’a wa Inspector Gamji.. I’m ready to accept my punishment.. And Chief lokaci yayi da zaka bar NPF. Mugaye irinku basu cancanci aikin D’ansanda ba.. Zan bada shaida akan abin da sani.” Tana ida fad’in haka Ta soma neman layin Yusuf. ** Mu’azzam kaw tuni security d’in ya hasko masa wann footage d’in. Tin daga parking lot har zuwa cikin asibitin. Aiko saiga Maleeka cikin shiga irinta ma’aikatan asibiti ta shige lab.. Jim kad’an ta fito ta shige wani store ta canza kayan jikinta fuskarta ya bayyana. Mu’azzam yace “Stop.. Zoom..” Security d’in cikeda tsoro yai yanda Mu’azzam yace. Ana zooming saiga fuskar Maleeka ya fito b’aro b’aro.. Table d’in ya daka yana fad’in “I knew it.. My hunch was right about you Maleeka.. Believe me you’ll pay.. Zaki biya abinda kika aikatawa Abokina.!” Yana ida fad’in haka ya mik’e cikin sassarfa ya fito daga asibitin. ** Yusuf yace daga d’aya b’angaren “I’m sorry for your loss.. Allah ya mata rahama.. Kina nan headquarters ne..?” Maleeka ta girgiza kai kad’an tace “No na tafi gida ina shiryawa.. Zan tafi.. But before na tafi Ina so na fad’i gaskiya Yusuf.. Kana tare da Inspector Gamji ne..?” Yusuf ya girgiza kai yace “Wane irin gaskiya..” Maleeka tace gaskiyar abinda na sani gaba d’aya akan case d’in Officer Assad.. I’ll confess Yusuf.. Zan fad’i komai.. I’m ready to accept my punishment..” muryarta ya soma rawa alamun kuka sanda taci gaba da fad’in “Ku yafe mun team.. Ku yafe mun.. Naci amanarku.. Na yaudareku.. Naci amanan k’asata.. Na wulak’anta aikina.. Nid’in babbar mai laifi ce.. Dan Allah Yusuf ka rok’armun Assad gafara.. Kace masa ya yafe mun.. Nayi komai ne to save my ailing mother.. But at the end dik abinda nai bai hanata mutuwa ba.. Dan Allah kace ya yafe mun.. Ka fad’a ma Inspector Gamji I’m ready to confess.. Kuzo gidana na baku statement d’ina dan nasan idan na fice kuraye zasu iya farauta na..” Yusuf yana waya da Maleeka Mu’azzam yana tafe cikin Mota yana kiran layin Yusuf d’in. Nan Yusuf yake ganin wayar Mu’azzam na shigo masa. Yai saurin jinjina kai kafin yace da Maleeka “Kinaji.. Don’t go anywhere Maleeka.. Zamu taho yanzu.!” D’if Yusuf ya katse kiran ya d’aga na Mu’azzam. Kaman jira Mu’azzam yake ya soma magana cikin sauri “Yusuf na kamo b’eran.. My hunch was right about that girl.. Itace mai mana zagon k’asa.. Yusuf make sure baka barta ta fice ba.. Gani nan Ina tafe na nufo headquarters.” Yusuf ya sanar da Mu’azzam duk yanda sukai da Maleeka. Take yace ya turo masa address d’in gidan Maleekan sai su had’u a can d’in. Yana kashe wayar kuwa sak’on ya shigo wayarsa Yusuf ya turo masa address d’in gidan Maleeka. Sai sauri yake yana fuzgan mota yana ganin kaman bazai isa ba. ** Tana kwance Sun ida waya da Inne kenan ta soma jiyo hayaniya daga gate. Tai saurin mik’ewa zaune tana jin hayaniyar na k’ara yawa. Babu shiri ta mik’e ta nufi upstairs ta zira doguwar riga a jikinta had’ida tura sumarta cikin hula. Sauri sauri ta sauk’o k’asa ta bud’e k’ofar parlorn tana hangen abinda ke faruwa. Tuni Safeenah ta bangaje Patrick tana fad’in shi bai isa ya hanata shiga gidanta ba. Ko Boss d’in nasa ne bai isa ya mata iyaka da wann gidan ba.. Gidanta ne da sunanta aka gina bataga mahaluk’in da yakai ya mata iyaka da wann gidan ba. Ta nufo cikin gidan tana huci Patrick na biye da ita yana rok’onta tazo ta fice abinda takeyi na iya shafan aikinsa. Sadiya kaw tana hangosu Ta maida k’ofa ta rufe tai zamanta. Safeenah na k’arasowa ta shiga bugun k’ofar tana fad’in “Munafuka kizo ki bud’e mana.. Da kika ganni shine kika shige kika b’uya.. K’aramar maras kunya.. Kinyi sa’a wancan karon harsashin bai sameki ba.. Ki bar murna dan kin tsallake tuggun da na had’a miki.. Idan sunana Safeenah Gamji wllhi sai kin bar gidan nan.. Gidan nan nawa ne, mai gidan shima nawa ne ke Kinyi kad’an to come between us nida my Halal.. Kizo ki bud’e nace.!” Ta k’arashe tana mai waige waige tana neman abinda zata daki glass d’in window dashi.. Bata sami komai ba ta cire dogon talakalmin dake k’affunta.. Ta shiga bugun glass d’in window da tsinin takalminta “Zan shigo na taddaki na fitar dake daga cikin gidan da k’arfi.. Come out now.. Ki fito nace..!” Tanayi tana dukan glass da tsinin talkalminta. Idan Patrick ya nufota tayo kansa da takalmin nata tana fad’in sai ta rapza masa. Ana haka Sadiya ta bud’e k’ofar. Patrick ya k’araso da sauri yana fad’in “Ma’am Maiyasa kika bud’e k’ofar gashi nan ina kiran Oga amma baya d’agawa.. But I think I’ll just call the cops..” Safeenah tace “Go ahead and call them.. Ka kirasu nida kai sai muga waye za’a tafi dashi.” Sadiya ta dubi Patrick tace “K’yaleta Patrick. Jeka abinka I can handle her.” But yace “But Ma’am wann fah ba mai lafiya bace.. What if Ta miki wani abun..?” “Uwarka ce batada lafiya..” Safeenah ta basa amsa da fad’in haka. Patrick yace “Ma’am kinaji koh.” Sadiya ta jinjina kai tace “Naji Patrick.. Ni kam Karnukan nan yai ka fita dasu morning exercise.?” Patrick ya girgiza kai yace “A’a Ma’am tun jiya baa fita dasu ba.” Ta jinjina kai tace “Ka bud’esu susha iska zasu buk’aci hakan..” Tana ida fad’in haka ta maida k’ofa ta rufe. Safeenah ta shiga tura k’ofar tana fad’in ta bud’e mata. Patrick kaw tuni ya shige bud’e Karnuka. Safeenah sai kururuwa take tana fad’in Sadiya ta bud’e mata k’ofa.. Ganin bazata bud’e ba ga Karnuka Patrick na shirin kwance su babu shiri Safeenah ta rik’o takalamanta a hannu ta nufi gate a guje tana kuma tsinema Sadiya. Ta window Sadiya ke lek’en gudun Safeenah sai dariya take har Safeenar ta fice tattare da rigarta takalma a hannu. Patrick ma dariya ya dingayi yana fad’in lallai Ma’am ta basa satan amsa wann mahaukaciyar tana zuwa nan gaba abinda zai mata kenan ya k’yaleta Ta shiga ya kwance mata Karnuka tinda tana tsoronsu. ** Maleeka tai zaune a parlor sai murza tafin hannunta take tana jin zuciyarta na wane irin tsinkewa, tasan abinda take k’ok’arin yi abu ne mai matuk’ar had’ari amma nata da wani zab’in da ya shige ta fad’i gaskiya koda za’ayi arresting d’inta ne.. Ji tai bazata iya tafiya da hakkin kowa ba ba tareda ta sanar dasu gaskiyar Al’amari ba. Tana nan zaune tana aikin tunani taji ana knocking daga k’ofa. Ta mik’e tsaye tana tinanin su Mu’azzam ne suka iso.. Batai wata wata ba ta bud’e k’ofar.. Saidai tuni tai wani irin Daskarewa ganin ba Mu’azzam bane ba Yusuf bane.. Wani mutumi ne sanye da bak’ak’en tufafi ya rufe fuskarsa da bak’in mask. Bata iya ganin komai na jikinsa. Take ya soma nunata da k’aramar bindigarsa irin wacce sam ko anyi harbi da ita bazakaji sautin harbinba. Ta soma jada baya tana fad’in “Please don’t kill me.. Dan Allah kar ka kasheni..” Tana maganar tana k’ok’arin k’arasawa yanda makaminta yake. Mutumin da yake all in black na kuma nufota.. Baka ganin komai nasa sanye yake cikin bak’aken tufafi fuskarsa rufe da bak’ar mask hannayensa rufe cikin bak’ak’en black hand gloves. Abinka da wacce tasha training itama tsalle tai cikin k’warewa ta naushi hannun mutumin bindigar ya fad’i.. Take mutumin suka soma fad’a da Maleeka. Dukansu biyun cikin k’warewa suke attacking juna. Kai da gani kasan fad’an wad’anda suka sha training ne. Take Maleeka ta soma kokawan yaye hular mask d’in dake kan mutumin yana k’ok’arin hana faruwar hakan. Maleeka bata gajiya ba taci gaba da kokawan zame hular tana fad’in “Who are you.. Just show yourself.. You coward.. Jaja ne ya turoka ko.. Toh zan kashe ka na kuma kai masa gawarka.. Asirinku ya tonu.!” Ta k’arashe tana mai funcuke hular fuskar mutumin ya bayyana.. Cikin tsananin shock Maleeka ke jada baya.. Ta shiga nunasa da yatsanta dake tsananin rawa tana fad’in “You..you..!!” Su duka biyun suka tsaya suna duban juna. Maleeka na nunasa cikin tsananin rawar jiki yayinda mutumin yai tsalle ya d’auki bindigar. Aiko nan Maleeka tayo tsalle ta fad’o kansa itama tana kokawan k’wace bindigar.. A haka bindigar na tsakaninsu kowa na kokawar k’wacewa cikinsu.. Tau.! Harsashi ya tashi. Zasu iya cewa basusan waye harsashin ta d’ana ba cikin su biyun dan bindigar a tsakaninsu take. Maleeka takai dubanta zuwaga cikinta yanda harsashin ya sameta. A hankali take duk’awa saman gwiwoyinta har ta isa k’asa tana dafe da cikinta yanda ya harbeta jini na zubowa. Ta d’ago a galabaice tana dubansa. Take ya k’ara mata harsashi guda. Kan kace mai Maleeka ta zube tana fidda numfashi da k’yar. Ba tareda ya bar wani trace ba yai gaggawan ficewa daga wajen abinka da k’wararre. Mu’azzam sai sauri yake yana kuma kiran layin Yusuf. Yusuf d’in ma nan ya sanar dashi ya kusan isa holdup ne ya rik’es. Kusan tare tare Yusuf da Mu’azzam suka iso gidan. Gidan babu kowa da shike duk ma’aikata ne duk sun tafi aiki.. A bud’e suka sami k’ofa, suka dubi juna kafin suka k’arasa cikin gidan sauri sauri. Kwance suka hangi Maleeka cikin jini ta gama galabaita tana bud’e idanu da k’yar.. Yusuf bai k’arasa kanta ba sai Mu’azzam da ya isa cikin sauri yana ambato sunanta. Girgiza kai take tana dubansa... Tana so Tai magana ta kasa sabida ta gama jigata gab take da amsa kiran mahaliccinta “B..! BA.!! BA.. You...You....” Kalman da ta iya fad’i kenan cikin rarrabewar harrufa a hankali idanunta suka rufe.. Tana kwance cikin jini... Yusuf ya k’araso yana dubanta sai kuma ya girgiza kai yana duban Mu’azzam “I think she’s gone..” Ya fad’i daga nan yanda yake duk’e. Mu’azzam ya dafe kansa had’ida shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Ya lumshe idanunsa a hankali. Take Yusuf ya mik’e yana fad’in “Zan kira backup.” Mu’azzam bai iya furta komai ba, Sai duban Maleeka da yake. Yasan zai matuk’ar wahala su bar Maleeka a raye tinda yasan yanda Al’amara ke gudana a wajensu. Allah ya wanke Assad ya kuma kub’utar dashi. Saidai kuma Maleeka ta tafi bayan taso tayi abinda ya kamata a k’urarren lokaci. Yusuf ya dubesa sanda aka kewaye gawan Maleeka da igiya ana ana d’aukan bayanai. Yusuf ya k’urawa gawan Maleeka da ake bincike akai idanu. A fili yake furta “She was ready to confess.. Tayi nadama.. Taso ta bayyana gaskiya.. But unfortunately sun kasheta. Basu bata dama ta fad’i abinda ta sani ba.” Mu’azzam ya kaikaito kad’an had’ida k’ura masa idanu. Baice komai ba sai maida idanunsa kan gawan Maleeka da yai zuciyarsa fal tinani. Duk wanda su Jaja sukai amfani dashi wajen kashe Maleeka wani ne wanda ya sansu in and out.. Sann yasan dik yanda zai bi yayi ta’addanci ba tareda ya bar wani trace ba. Wani ne da yake da ilimin abun.. But who could that person be.? Tambayar da yai ma kansa kenan. He needs to solve this puzzle.. Kalman da Maleeka taso fad’i shi ya tsaya masa a rai BA.. Ya Tsuguna a hankali yana duban yanda harsashi ya huda a jikinta. Lokaci guda yana karantar irin harbin da aka mata da kuma yanayin da gangan jikin nata yake a kwance. Wani abu k’arami mai kaman toci mai tsananin Haske ya Ciro cikin aljihunsa yana haska k’asan wajen kaman yana neman wani abu. Dik wani abu mai kama da trace baiga alamunsa ba. Yai shiru yana examining wajen. A hankali ya mik’e yana zira hannayensa cikin aljihu. Wanene makashin Maleeka..? Shine tambayar da ya tsaya masa a rai. ** A k’ofan prison d’in suka tsaya jingine jikin mota shida Yusuf suna jiran fitowar Assad. Can suka hangosa yana nufosu kwantattun k’walla cikin idanunsa. Yana k’arasowa ya shige tsakankaninsu Yusuf da Mu’azzam sai kuma ya rungumesu yana jin hawaye na zuwa masa. Sameena Aleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *56* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Chief ya girgiza kai kad’an yana dubanta “Meke faruwa..? Ya na ganki haka..?” Kuka Maleeka ta kuma fashewa dashi, cikin muryar kuka take fad’in “I just... I... I just lost my Mom..!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana mai zama saman kujera. Chief ya dubeta da fuskar tausayi yana girgiza kai “Kiyi hak’uri Maleeka.. Sorry for your loss.. My condolences..” Maleeka dai bata iya cewa komai ba Sai cazagan kukanta take tana kiran mahaifiyarta. Chief ya k’araso ya mik’a mata ruwa yace tasha. Babu musu ta amsa tana sha tana kuka. Saida tai mai isarta kafin kukan nata ya tsagaita. Chief ya jingina jikin tabel yana dubanta “Maleeka..” Ta d’ago watery eyes d’inta tana dubansa. Yayinda Chief yaci gaba da fad’in “Naga irin kallon da kike wa mahaifiyar Assad lokacin da za’a fita dashi.. Na hango nadama da tarin danasani cikin k’wayar idanunki.. Na hango tausayi da son jada baya a tattare dake... Maleeka if you dare think of double crossing me, wllhi wllhi I won’t hesitate to execute you.. Shawari nake baki.. Don’t you ever think of ratting us out.!” Da tsananin mamaki take dubansa, Ta girgiza kai kad’an tace “Yanzu nace maka Mahaifiyata Ta mutu.. Ko ganinta banyi ba.. Mahaifiyata ta rasu ko cikakken 1hr batayi ba amma har kanada guts d’in da zaka dubi cikin idona kace zakai threatening d’ina Chief..? Shin kai wane irin mutum ne da babu d’and’anin imani cikin zuciyarsa..!” Murmusawa yai kafin yace “I don’t give a damn dan kin rasa mahaifiyarki.. Kafin ki rasa naki mahaifan na rasa nawa.. Rashin mahaifiyarki bazai sa a fasa komai a duniyar nan ba dan haka shawari na baki ki iya takunki. Idan kunne yaji toh fah jiki ya tsira.. Dismiss now..!” Ya k’arashe yana mai nuna mata k’ofa. Dubansa kurum Maleeka take da rinannun idanunta, zuciyarta na mata tsananin k’una. Jinjina kai tai kafin ta sara masa lokaci guda tasa kai ta fice daga ofishin k’irjinta na tsananin k’una. Tana fitowa bata ko tsaya ba ta fice ta d’auki Cab ta nufi apartment d’inta. Tana isa ta soma shirya kayanta, tanayi tana tuno mahaifiyarta tana zuban hawaye. Meye amfanin aikin da take idan mahaifiyarta bazata Mora ba.. Ta rasa mahaifiyarta wacce tasha d’awainiya akanta tun tana yarinya.. Bata mance lokuta da dama da mahaifiyarta ta kwana babu ci babu sha dan kawai ta biya mata kud’in makaranta.. Mahaifiyarta ta wahala da ita da k’annenta a rayuwa..Taci burin ta biya mahaifiyarta duk wahalhalun da tai akansu itada ‘yanuwanta musamman ma ita.. Ta kuma share hawayenta tana mai jefa kayanta cikin jaka. A fili take furta “I need to make things right.. Kafin na tafi zan gyara komai.. I promise zan gyara duk abinda na b’ata.. Zan wanke ka Officer Assad.. I’ll confess.. I’ll confess everything.. Dik abinda na sani zan fad’a wa Inspector Gamji.. I’m ready to accept my punishment.. And Chief lokaci yayi da zaka bar NPF. Mugaye irinku basu cancanci aikin D’ansanda ba.. Zan bada shaida akan abin da sani.” Tana ida fad’in haka Ta soma neman layin Yusuf. ** Mu’azzam kaw tuni security d’in ya hasko masa wann footage d’in. Tin daga parking lot har zuwa cikin asibitin. Aiko saiga Maleeka cikin shiga irinta ma’aikatan asibiti ta shige lab.. Jim kad’an ta fito ta shige wani store ta canza kayan jikinta fuskarta ya bayyana. Mu’azzam yace “Stop.. Zoom..” Security d’in cikeda tsoro yai yanda Mu’azzam yace. Ana zooming saiga fuskar Maleeka ya fito b’aro b’aro.. Table d’in ya daka yana fad’in “I knew it.. My hunch was right about you Maleeka.. Believe me you’ll pay.. Zaki biya abinda kika aikatawa Abokina.!” Yana ida fad’in haka ya mik’e cikin sassarfa ya fito daga asibitin. ** Yusuf yace daga d’aya b’angaren “I’m sorry for your loss.. Allah ya mata rahama.. Kina nan headquarters ne..?” Maleeka ta girgiza kai kad’an tace “No na tafi gida ina shiryawa.. Zan tafi.. But before na tafi Ina so na fad’i gaskiya Yusuf.. Kana tare da Inspector Gamji ne..?” Yusuf ya girgiza kai yace “Wane irin gaskiya..” Maleeka tace gaskiyar abinda na sani gaba d’aya akan case d’in Officer Assad.. I’ll confess Yusuf.. Zan fad’i komai.. I’m ready to accept my punishment..” muryarta ya soma rawa alamun kuka sanda taci gaba da fad’in “Ku yafe mun team.. Ku yafe mun.. Naci amanarku.. Na yaudareku.. Naci amanan k’asata.. Na wulak’anta aikina.. Nid’in babbar mai laifi ce.. Dan Allah Yusuf ka rok’armun Assad gafara.. Kace masa ya yafe mun.. Nayi komai ne to save my ailing mother.. But at the end dik abinda nai bai hanata mutuwa ba.. Dan Allah kace ya yafe mun.. Ka fad’a ma Inspector Gamji I’m ready to confess.. Kuzo gidana na baku statement d’ina dan nasan idan na fice kuraye zasu iya farauta na..” Yusuf yana waya da Maleeka Mu’azzam yana tafe cikin Mota yana kiran layin Yusuf d’in. Nan Yusuf yake ganin wayar Mu’azzam na shigo masa. Yai saurin jinjina kai kafin yace da Maleeka “Kinaji.. Don’t go anywhere Maleeka.. Zamu taho yanzu.!” D’if Yusuf ya katse kiran ya d’aga na Mu’azzam. Kaman jira Mu’azzam yake ya soma magana cikin sauri “Yusuf na kamo b’eran.. My hunch was right about that girl.. Itace mai mana zagon k’asa.. Yusuf make sure baka barta ta fice ba.. Gani nan Ina tafe na nufo headquarters.” Yusuf ya sanar da Mu’azzam duk yanda sukai da Maleeka. Take yace ya turo masa address d’in gidan Maleekan sai su had’u a can d’in. Yana kashe wayar kuwa sak’on ya shigo wayarsa Yusuf ya turo masa address d’in gidan Maleeka. Sai sauri yake yana fuzgan mota yana ganin kaman bazai isa ba. ** Tana kwance Sun ida waya da Inne kenan ta soma jiyo hayaniya daga gate. Tai saurin mik’ewa zaune tana jin hayaniyar na k’ara yawa. Babu shiri ta mik’e ta nufi upstairs ta zira doguwar riga a jikinta had’ida tura sumarta cikin hula. Sauri sauri ta sauk’o k’asa ta bud’e k’ofar parlorn tana hangen abinda ke faruwa. Tuni Safeenah ta bangaje Patrick tana fad’in shi bai isa ya hanata shiga gidanta ba. Ko Boss d’in nasa ne bai isa ya mata iyaka da wann gidan ba.. Gidanta ne da sunanta aka gina bataga mahaluk’in da yakai ya mata iyaka da wann gidan ba. Ta nufo cikin gidan tana huci Patrick na biye da ita yana rok’onta tazo ta fice abinda takeyi na iya shafan aikinsa. Sadiya kaw tana hangosu Ta maida k’ofa ta rufe tai zamanta. Safeenah na k’arasowa ta shiga bugun k’ofar tana fad’in “Munafuka kizo ki bud’e mana.. Da kika ganni shine kika shige kika b’uya.. K’aramar maras kunya.. Kinyi sa’a wancan karon harsashin bai sameki ba.. Ki bar murna dan kin tsallake tuggun da na had’a miki.. Idan sunana Safeenah Gamji wllhi sai kin bar gidan nan.. Gidan nan nawa ne, mai gidan shima nawa ne ke Kinyi kad’an to come between us nida my Halal.. Kizo ki bud’e nace.!” Ta k’arashe tana mai waige waige tana neman abinda zata daki glass d’in window dashi.. Bata sami komai ba ta cire dogon talakalmin dake k’affunta.. Ta shiga bugun glass d’in window da tsinin takalminta “Zan shigo na taddaki na fitar dake daga cikin gidan da k’arfi.. Come out now.. Ki fito nace..!” Tanayi tana dukan glass da tsinin talkalminta. Idan Patrick ya nufota tayo kansa da takalmin nata tana fad’in sai ta rapza masa. Ana haka Sadiya ta bud’e k’ofar. Patrick ya k’araso da sauri yana fad’in “Ma’am Maiyasa kika bud’e k’ofar gashi nan ina kiran Oga amma baya d’agawa.. But I think I’ll just call the cops..” Safeenah tace “Go ahead and call them.. Ka kirasu nida kai sai muga waye za’a tafi dashi.” Sadiya ta dubi Patrick tace “K’yaleta Patrick. Jeka abinka I can handle her.” But yace “But Ma’am wann fah ba mai lafiya bace.. What if Ta miki wani abun..?” “Uwarka ce batada lafiya..” Safeenah ta basa amsa da fad’in haka. Patrick yace “Ma’am kinaji koh.” Sadiya ta jinjina kai tace “Naji Patrick.. Ni kam Karnukan nan yai ka fita dasu morning exercise.?” Patrick ya girgiza kai yace “A’a Ma’am tun jiya baa fita dasu ba.” Ta jinjina kai tace “Ka bud’esu susha iska zasu buk’aci hakan..” Tana ida fad’in haka ta maida k’ofa ta rufe. Safeenah ta shiga tura k’ofar tana fad’in ta bud’e mata. Patrick kaw tuni ya shige bud’e Karnuka. Safeenah sai kururuwa take tana fad’in Sadiya ta bud’e mata k’ofa.. Ganin bazata bud’e ba ga Karnuka Patrick na shirin kwance su babu shiri Safeenah ta rik’o takalamanta a hannu ta nufi gate a guje tana kuma tsinema Sadiya. Ta window Sadiya ke lek’en gudun Safeenah sai dariya take har Safeenar ta fice tattare da rigarta takalma a hannu. Patrick ma dariya ya dingayi yana fad’in lallai Ma’am ta basa satan amsa wann mahaukaciyar tana zuwa nan gaba abinda zai mata kenan ya k’yaleta Ta shiga ya kwance mata Karnuka tinda tana tsoronsu. ** Maleeka tai zaune a parlor sai murza tafin hannunta take tana jin zuciyarta na wane irin tsinkewa, tasan abinda take k’ok’arin yi abu ne mai matuk’ar had’ari amma nata da wani zab’in da ya shige ta fad’i gaskiya koda za’ayi arresting d’inta ne.. Ji tai bazata iya tafiya da hakkin kowa ba ba tareda ta sanar dasu gaskiyar Al’amari ba. Tana nan zaune tana aikin tunani taji ana knocking daga k’ofa. Ta mik’e tsaye tana tinanin su Mu’azzam ne suka iso.. Batai wata wata ba ta bud’e k’ofar.. Saidai tuni tai wani irin Daskarewa ganin ba Mu’azzam bane ba Yusuf bane.. Wani mutumi ne sanye da bak’ak’en tufafi ya rufe fuskarsa da bak’in mask. Bata iya ganin komai na jikinsa. Take ya soma nunata da k’aramar bindigarsa irin wacce sam ko anyi harbi da ita bazakaji sautin harbinba. Ta soma jada baya tana fad’in “Please don’t kill me.. Dan Allah kar ka kasheni..” Tana maganar tana k’ok’arin k’arasawa yanda makaminta yake. Mutumin da yake all in black na kuma nufota.. Baka ganin komai nasa sanye yake cikin bak’aken tufafi fuskarsa rufe da bak’ar mask hannayensa rufe cikin bak’ak’en black hand gloves. Abinka da wacce tasha training itama tsalle tai cikin k’warewa ta naushi hannun mutumin bindigar ya fad’i.. Take mutumin suka soma fad’a da Maleeka. Dukansu biyun cikin k’warewa suke attacking juna. Kai da gani kasan fad’an wad’anda suka sha training ne. Take Maleeka ta soma kokawan yaye hular mask d’in dake kan mutumin yana k’ok’arin hana faruwar hakan. Maleeka bata gajiya ba taci gaba da kokawan zame hular tana fad’in “Who are you.. Just show yourself.. You coward.. Jaja ne ya turoka ko.. Toh zan kashe ka na kuma kai masa gawarka.. Asirinku ya tonu.!” Ta k’arashe tana mai funcuke hular fuskar mutumin ya bayyana.. Cikin tsananin shock Maleeka ke jada baya.. Ta shiga nunasa da yatsanta dake tsananin rawa tana fad’in “You..you..!!” Su duka biyun suka tsaya suna duban juna. Maleeka na nunasa cikin tsananin rawar jiki yayinda mutumin yai tsalle ya d’auki bindigar. Aiko nan Maleeka tayo tsalle ta fad’o kansa itama tana kokawan k’wace bindigar.. A haka bindigar na tsakaninsu kowa na kokawar k’wacewa cikinsu.. Tau.! Harsashi ya tashi. Zasu iya cewa basusan waye harsashin ta d’ana ba cikin su biyun dan bindigar a tsakaninsu take. Maleeka takai dubanta zuwaga cikinta yanda harsashin ya sameta. A hankali take duk’awa saman gwiwoyinta har ta isa k’asa tana dafe da cikinta yanda ya harbeta jini na zubowa. Ta d’ago a galabaice tana dubansa. Take ya k’ara mata harsashi guda. Kan kace mai Maleeka ta zube tana fidda numfashi da k’yar. Ba tareda ya bar wani trace ba yai gaggawan ficewa daga wajen abinka da k’wararre. Mu’azzam sai sauri yake yana kuma kiran layin Yusuf. Yusuf d’in ma nan ya sanar dashi ya kusan isa holdup ne ya rik’es. Kusan tare tare Yusuf da Mu’azzam suka iso gidan. Gidan babu kowa da shike duk ma’aikata ne duk sun tafi aiki.. A bud’e suka sami k’ofa, suka dubi juna kafin suka k’arasa cikin gidan sauri sauri. Kwance suka hangi Maleeka cikin jini ta gama galabaita tana bud’e idanu da k’yar.. Yusuf bai k’arasa kanta ba sai Mu’azzam da ya isa cikin sauri yana ambato sunanta. Girgiza kai take tana dubansa... Tana so Tai magana ta kasa sabida ta gama jigata gab take da amsa kiran mahaliccinta “B..! BA.!! BA.. You...You....” Kalman da ta iya fad’i kenan cikin rarrabewar harrufa a hankali idanunta suka rufe.. Tana kwance cikin jini... Yusuf ya k’araso yana dubanta sai kuma ya girgiza kai yana duban Mu’azzam “I think she’s gone..” Ya fad’i daga nan yanda yake duk’e. Mu’azzam ya dafe kansa had’ida shafe fuskarsa da tafukan hannayensa. Ya lumshe idanunsa a hankali. Take Yusuf ya mik’e yana fad’in “Zan kira backup.” Mu’azzam bai iya furta komai ba, Sai duban Maleeka da yake. Yasan zai matuk’ar wahala su bar Maleeka a raye tinda yasan yanda Al’amara ke gudana a wajensu. Allah ya wanke Assad ya kuma kub’utar dashi. Saidai kuma Maleeka ta tafi bayan taso tayi abinda ya kamata a k’urarren lokaci. Yusuf ya dubesa sanda aka kewaye gawan Maleeka da igiya ana ana d’aukan bayanai. Yusuf ya k’urawa gawan Maleeka da ake bincike akai idanu. A fili yake furta “She was ready to confess.. Tayi nadama.. Taso ta bayyana gaskiya.. But unfortunately sun kasheta. Basu bata dama ta fad’i abinda ta sani ba.” Mu’azzam ya kaikaito kad’an had’ida k’ura masa idanu. Baice komai ba sai maida idanunsa kan gawan Maleeka da yai zuciyarsa fal tinani. Duk wanda su Jaja sukai amfani dashi wajen kashe Maleeka wani ne wanda ya sansu in and out.. Sann yasan dik yanda zai bi yayi ta’addanci ba tareda ya bar wani trace ba. Wani ne da yake da ilimin abun.. But who could that person be.? Tambayar da yai ma kansa kenan. He needs to solve this puzzle.. Kalman da Maleeka taso fad’i shi ya tsaya masa a rai BA.. Ya Tsuguna a hankali yana duban yanda harsashi ya huda a jikinta. Lokaci guda yana karantar irin harbin da aka mata da kuma yanayin da gangan jikin nata yake a kwance. Wani abu k’arami mai kaman toci mai tsananin Haske ya Ciro cikin aljihunsa yana haska k’asan wajen kaman yana neman wani abu. Dik wani abu mai kama da trace baiga alamunsa ba. Yai shiru yana examining wajen. A hankali ya mik’e yana zira hannayensa cikin aljihu. Wanene makashin Maleeka..? Shine tambayar da ya tsaya masa a rai. ** A k’ofan prison d’in suka tsaya jingine jikin mota shida Yusuf suna jiran fitowar Assad. Can suka hangosa yana nufosu kwantattun k’walla cikin idanunsa. Yana k’arasowa ya shige tsakankaninsu Yusuf da Mu’azzam sai kuma ya rungumesu yana jin hawaye na zuwa masa. Sameena Aleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *57* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Murmushi yake yana dubansu, su d’inma murmushi ne saman fuskokinsu. “Thank you both for not giving up on me.. Thank you for believing in me.. Na gode K’warai..” Assad yace yana dubansu. Yusuf ya dafasa kad’an yace “You don’t need to thank us.. This is what brothers are for.. Na maka murna” Ya k’arashe yana d’an buga kafad’arsa murmushi saman fuskarsa. Mu’azzam baice masu komai ba har lokacin, kaman baya wajen haka ya b’ace shiru. Yusuf yai gyaran murya kad’an ya dubi Mu’azzam d’in yace “I’ll be heading to the headquarters.. Suna jirana akwai report d’in da zan basu.” Mu’azzam ya jinjina masa kai kurum yana dubansa. Assad ya masa fatan sauk’a lafia. Wajen ya rage saura Mu’azzam da Assad. Assad ya d’an dube mutumin nasa cikin ransa yana ayyana yanda zasu kwashe. Abubuwan da sukaita faruwa shi yake zuwa zuciyarsa. Yai gyaran murya kad’an “Na yarda ka fini gaskiya a akasarin lokuta.. Kuma kaid’in ka fini sanin makamar aikinka.. A akasarin lokuta nakan yi zaton ka tsaurara.. Nakan yi k’ok’arin dakatar dakai.. Like you said, we have same profession but our personalities differ.. Mu’azzam aikin da kayi zan iya cewa kaid’in k’aararre ne a sanin makamar aikinka.. You proved me wrong.. Tabbas ba ko yaushe ake yarda da mutane ba.. Na d’auki darasin rayuwa bayan abinda ya faru dani.” Mu’azzam ya d’an kauda kansa gefe kad’an yana zira hannayensa cikin aljihu “Ka zama mai bud’edd’en zuciya.. Ka yarda da mutanen da suka baka yarda.. It’s not a crime don ka zama mai sauk’in fahimta.. But it can be a crime idan ka zama wanda kowa zai d’ebo sharansa ya zuba..” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Kowa zai iya zama mai laifi.. Ban cire maka kowa ba.. Harta ni da kai zamu iya zama masu laifi.. People change, zuciya batada k’ashi.. Tsokace zalla da takeda tsananin rauni lokaci guda kuma takeda power a gangan jikin D’anadam.. Idan ka bata wann power d’in nan ne zata kaika Ta baro ka.. Amma idan ka barta da rauninta.. Sannu a hankali zata kasance a haka.. Sai ka samu power da zaka sarrafata..” Ya k’arashe yana juya coin d’in Black African Team dake rik’e cikin hannunsa.” Assad ya kafe abokin nasa da idanu yana dubansa yana murmushi. Zuciyarsa fal jinjina ga abokin nasa. Jinjina kai yai a hankali kafin ya gyara tsayuwarsa yace “Na gode da kalamanka... Na gode da bakai watsi dani ba.” Kauda kansa gefe ya kumayi yana rage girman idanunsa kad’an. Dan bayan yaji statement d’in Assad a gaban Prosecutor yaji kalan tuggun da Maleeka taso k’ulla masa sam baiga laifin Assad na amsa laifin da bai aikata ba. Yayi ne to protect his reputation. Ko a shari’a idan aka maka barazana da b’ata suna bakai laifi ba don ka amsa laifin da ba Naka ba ka zab’i tafiya gidan kaso. “Let’s get going Detective. Akwai aiki sosai gabanmu.” Mu’azzam ya fad’i yana bud’e marfin mota. Assad ya d’an tsaresa da idanu kad’an yana duban Mu’azzam d’in, gajeren murmushi yai kafin ya jinjina kai yace “Yes Inspector.!” Yai maganar yana sara masa. Girgiza kai kurum Mu’azzam yai kafin yaja motar suka shige bayan Assad ya shige cikin motar. Suna tafe labarin mutuwar Maleeka ya kuma zuwa ma Assad “Dukda ta mun laifi naji zafin yanda mutuwarta ya kasance. Hak’ik’a ta zab’i turba maras d’aurewa.. Tanada k’wazo da sanin kan aikinta.. But still ta zab’i tabi hanya wanda babu komai cikinta face k’arya da tsananin duhuwa. I’m quite sure silencing nata sukai..” Shiru Mu’azzam baice masa komai ba saima ci gaba da tuk’a motar da yake, idanunsa naga kwalta. Assad yaci gaba da fad’in “So sad.. Sun kasheta bayan ta zab’i tai abinda ya kamata.. Na yafeki Maleeka..! Kuma ina fata ki samu rangwame wajen Ubangiji.. Allah yasa masu hali irin naki su hankalta su gyara.” Sai lokacin Mu’azzam ya amsa da Ameen yana mai duban window d’in dake side d’insa. Suna tafe Assad yaga ya d’auki hanyar Lafiya. Da mamaki yake duban Mu’azzam d’in kafin yace “I thought kace aiki na jiranmu.” Mu’azzam bai amsa sa ba yaci gaba da driving. Assad ya d’an murmusa kad’an had’ida girgiza kai, yasan bazai amsa shin bane. Suna isowa k’ofar gidansu Assad yaja yai parking. “Hajiya ce tafi cancanta ta soma ganinka fiyeda Chief Jaja..” Yai maganar cikeda barkwanci wanda zaka iya cewa kaman ma ba daga bakinsa ya fito ba. Assad ya kuma murmusawa yana girgiza kai yana duban abokin nasa lokaci guda yana bud’e marfin motar. A tare suka jera suka nufi cikin gidan yayinda suka soma had’uwa da Shamsu zai fice shago dan dama yanada shago a d’an k’asa dasu kad’an. Cikin sauri Shamsu ya k’araso ya rungume D’anuwansa cikeda jin dad’in ganinsa yana masa Barka da fitowa. Ya k’araso yana gaisawa da Mu’azzam had’ida sake masa godiya kan d’awainiyar Assad d’in da yai. Assad kam tuni ya shige ciki yana ambato Hajiyarsa. Hajiya harda hawayen murnan sake ganin D’an nata tai. Allah sarki D’ah da mahaifiya kenan. Yanda Assad da Hajiya suka rungume juna suna hawaye ya karya Zuciyar Mu’azzam. Tausayin kansa ya rufesa.. Allah sarki, rabonsa da yayi haka da tasa mahaifiyar shekaru ak’alla goma sha biyar. Ina ma shida Mamynsa zasu rungume juna wata Rana suna hawayen Farin ciki irin haka. Ya d’an sadda kansa k’asa yana k’ok’arin barin wajen. Hajiya ta dakatar dashi tana kuma masa godiya. Ya murmusa kad’an yace “Babu komai Hajiya.. Nida Assad ‘yanuwan juna ne.” Hajiya ta murmusa tana goge k’wallanta “Allah yasa amincinku ya d’aure har Aljannah.. Allah ya rabaku da sharrin mak’iya na b’oye da na zahiri a dik yanda kuka kasance. Allah shi maku albarka.” Daga Assad d’in har Mu’azzam Ameen suketa amsawa dashi cikeda jin dad’in addu’o’in Hajiyar a garesu. Assad yace bari yai ma Mu’azzam rakiya. Har mota ya rakosa. Ya saluting nasa yana fad’in “Idan Inspector yace kar nai reporting back to work Sai nan da sati ma bazance komai ba.” Gajeren murmushi yai da gefen bakinsa kafin yace “I thought prison did change you..” Yana maganar yana shigewa mota. “Sai munyi magana.” Mu’azzam ya k’ara da fad’in haka. Assad na murmushi yake jinjina kai “Alright shikenan.. Da Allah ka bani update fah.” Bai amsa sa ba sai key da yaima motar. Yasan ba lallai ya amsa d’in ba. “Zan kira Yusuf kawai naji komai.. Drive safe.” Ya k’arashe yana d’an saluting nasa kad’an wanda kaman d’abi’ar aikinsu ne. Mu’azzam ya jinjina masa kai yana mai masa horn alamun sallama. Yana tafe saman kwalta yana tuna kalaman Maleeka na k’arshe “BA.. You..” Ya furta a hankali kafin ya fuzar da huci kad’an. Kai tsaye gidan Maleeka ya kuma komawa yaci gaba da examining gidan yanda abun ya faru. Tin daga k’ofa yake karanta. Ya d’aga kai yana duban yanda wasu frames irin mai guda biyar d’in nan Babba da k’ana... Nan yaga babu guda d’aya.. Ga wajen da yake makal’e harda alamun k’usa amma babu.. Take ya soma tinanin Maiyasa babu guda d’aya. “Garin kokawa ya fad’i glass d’in ya fashe.. Wanda yai kisan sai share komai kaman dai Babu abinda ya fashe.. Kenan Maleeka tayi fad’a da mutumin da ya kasheta kafin ya cimma kashetan.” Zuciyarsa ce take wann zancen. Yanayi yana kamanta yanda Maleeka sukai bata kashi da makashin nata. Hoton abubuwan na zuwa cikin k’wayan idanunsa. K’aramar torchlight d’in ya ciro cikin suit pocket d’insa ya shiga haska k’asan wajen. A hankali ya duk’a yana kuma haska wajen nan ya hango k’anan broken glass alamun dai tinaninsa ka iya zama gaskiya, akwai k’aramar frame d’in a wajen garin kokawa Ta fad’i ta fashe. Yai shiru kaman mai nazari. Gefe kad’an ya haska nan ya hango shatin alamun k’asan takalmi saman farar tile d’in. Cikin tsanaki ya zaro Balck marker dake cikin aljihunsa. Take ya soma tracing shatin k’afan takalmin cikin tsanaki da k’warewa. Saida ya zana tsaf suffar shatin k’asan takalmin ya bayyana. Ya jinjina kai a hankali yake duban zanen tracing k’asar takalmin da yai. Wayarsa ya ciro yai hoton zanen k’asan takalmin da yai kafin ya mik’e yana kuma k’are ma gidan kallo yana karantar ko Ina a tsanake. Dik iya binciken da yai gidan bai samu abinda zai linking Maleeka da Chief ba. Koda shike yasan hakan abu ne mai matuk’ar wahala, bazasu yarda su bar wani abu da zai nuna sunada wata alak’a ba. A fili yake furta “Sannu sannu bata hana zuwa Chief Jaja.. Da sannu zaka iso hannu.” Daga nan ficewa yai daga gidan ya nufi gidan Daddy. ** Umma tai zaune tana tinanin ina ta yar da sisin kobon. Wann sisin kwabon shi kad’ai ne abinda yake tuna mata bayanta. Bazataso ta rasa sa ba. Mik’ewa tai ta janyo akwatin da suka tara kayayyakinsu na wancan gidan. Addu’a kurum take Allah yasa yana ciki. Ta shiga bincikawa tana duba cikin akwatin.. Babu wann sisin kwabon babu alamunsa. Tai zaune tana tinani.. Watak’ila a Suleja ta yasar shi.. Shikenan Ta rasa abinda yai mata saura na bayanta. A hankali ta koma ta zauna tana girgiza kai hawaye na k’ok’arin ciko idanunta “A’a a’a bazan rasa wann sisin kwabon ba.. Shine kad’ai saura mun.. Zanci gaba da nemansa cikin kaya har Allah yasa na samu.. Nasan yana nan mak’ale wani wajen.. Zanci gaba da dubawa sannu a hankali har na sameshi..” Ta lumshe idanunta hawaye masu zafi suka gangaro mata. ** Ta yanda Mommy take shiga bata nan take fita ba “Sabida bakida hankali ke shahshasha ce wacce ta rako mata duniya koh.. Shine kika d’ibi k’afafu kika tafi gidansa kikaje kina haukar nan naki da bazaki daina ba koh.?!” Safeenah ta turo baki tana jin zuciyarta na tashi kaman zata amayo da cikinta. Yamutsa fuska tai tace “Mommy dan girman Allah ki barni naji da abinda ke damuna.. Ni wllhi ganin matar Mu’azzam da nai ya haifar mun da tashin zuciya.. I already have headache dan Allah ki k’yaleni haka nan Mommy, Please..!” Ta k’arashe tana mai d’ago wa mahaifiyar nata hannu. Cikeda takaici Mommy tace “Ai idan baki cire wann jarababben cikin zuciyarki ba haka nan zaki k’are da wahala.. Jarababbiyar banza ‘yar wahala.” “Mommy idan dai akan my Halal ne ki kirani da sunan da kikaga dama wllhi wllhi babu abinda zai rabani da mijina.. Ko shi Mu’azzam d’in bai isa ya raba aurenmu ba.. So ki daina bama kanki wahala kan My Halal.” Throw pillow dake gefenta ta jifawa Safeenar dan takaici “Kinci ubanki keda Halal d’in.!” Hakan yai daidai da mik’ewar Safeenah a guje ta nufi guest toilet tana k’waza amai.. Mommy ta bita da kallo baki sake ita ta ma mance Safeenah ciki gareta. Sallaman Mu’azzam ya dawo da hankalin Mommy.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *58* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Zabura Mommy tai babu shiri ta nufo k’ofar tana k’ok’arin taresa take fad’in “Mai ya kawoka gidan nan.. Kai yanzu idan kanada kunya sai ka kuma tako k’afarka cikin gidan nan bayan dik kalan rashin mutuncin da ka fesa mana.. Idan gaisuwa ce ya kawoka ni Hajara na yafe bani buk’ata a k’ara gaba ehe.. Idan kuma k’anina mahaifinka kazo gaidawa shima kasan yanda zaka samesa.. Kaje can company ka samesa amma ba gidana ba.. Sann Idan tak’amarka shine nan d’in gidan mijin mahaifiyarka ne Toh itama bata a nan gidan balle kace zakake shigowa kanka tsaye duk sanda kaga dama.!” Ta k’arashe tana huci tayi famkam famkam Ta cike k’ofar gaba d’aya. Mu’azzam baice mata komai ba Sai dubanta da yake cikeda mamaki. Wai Mommy ke masa duka wad’ann abubuwan. Matar da a baya bata nuna masu komai ba face zallan k’auna.. Abubuwan da take masa shi gani yake yayi yawa ace duk kawai kan laifinsa k’wara d’aya take hukuntasa haka. Ya fara shakkun k’aunar da Ta nuna masu a baya shida ‘yaruwarsa da mahaifiyarsu. Musaddiq ya k’araso yana girgiza kai ganin ko damuwa da cewa gidan akwai ma’aikata sann ga k’annensa Mommy batayi.. Ita kawai damuwarta ta tozarta Mu’azzam. “Mommy dan girman Allah wann wane irin abu ne.. Mommy will you please..” Dakatar dashi Mu’azzam yai ta hanyar d’aga hannu kafin ya dubi Mommy na d’an lokaci kaman mai karantarta. Sai jijjiga take nan bakin k’ofar tana addu’a cikin zuciyarta Allah hana Safeenah fitowa daga band’akin nan a yanayin da take. Ya d’an d’ibi dak’ik’ai a haka kafin ya jefa hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ba tareda ya furta komai ba ya juya ya fice daga parlorn. Musaddiq ya dubi Mommy kawai had’ida girgiza kai kafin yasa kai ya shige. Tabi bayansu da kallo tana jinjina kai “Ba yanzu ba Mu’azzam.. Bazan bari kasan cewa akwai gudan jininka kwance cikin Safeenah ba sai zuwa lokacin da na tsara.. Shiri na musamman nake maka my dear stepson or should I call you my dear Son-in-law.” Tana gama fad’i Ta murmusa a hankali kafin Ta juyo tana duban k’ofan bathroom d’in da Safeenah ta turo ta fito dik a galabaice. Fuskarta ya kuma yin haske na musamman, kana ganinta kaga mai k’aramin ciki. Dikda jiwa dake k’ok’arin d’aukanta bai hanata nufan k’ofa tana fad’in “My Halal.. Mommy kaman naga My Halal yazo..!” Janyota Mommy tai a fusace ta zaunar saman kujera “Zauna dan Ubanki babu yanda zakije.. Mahaukaciyar banza.” Safeenah ta turo baki tana duban Mommy “Mommy Nifa bazaki min wann fir’aunanci na d’auka ba ehe.. 21st century fah muke.. Da a k’asashen waje ne nayi imani da na makaki kotu.. Saidai kawai kiga sammaci..” Mommy ta saki baki “Ni kike ce zaki maka Kotu kan wancan watsettsen.? Eh lallai Safeenah yayi.. Wato Ina karb’ar miki ‘yanci baki gani.. Toh maza tashi tashi ki bisa d’in kiji bak’ak’e.. Matarsa ta kwance miki Karnuka shi kuma saidai ya kwance maki mari masuji da lafiya.. Idan ke shashasha ce ki tashi kije..!” D’an lumshe idanunta Safeenah tai tana dafe kanta dake d’an sara mata. Ga k’amshin turaren wutan dake tashi a parlorn sam bai mata dad’i ba. Batabi takan Mommy ba ta shiga kiran ma’aikatan gidan tana tambayarsu wane irin turare suka saka yau a gidan. Dik suka ce wanda aka saba sakawa ne. Tsaki tai ta shiga masu masifa tana fad’in kar su sake saka wann turare mai warin a gidan. Ma’aikatan wann ya dubi wann wancan ya dubi wancan. Da gani zaka fahimci akwai zance a bakunansu. Mommy tai masu izinin tafiya tana fad’in su canza turaren. Haka suka wuce suna ‘yar k’us k’us anya ba ciki ne da Safeenah ba. ‘Yar dattijuwar cikinsu tana fad’in ai da ganinta kaga mai ciki, d’ayar fad’i take da safe ta kai mata tea d’in data saba sha dik safiya Ta watsar tace is too concentrated kar Ta sake kawo mata. Dattijuwar ta murmusa tace “Allah yasa wann rabo yasa a maida Safeenah d’akinta.” ‘Yanmatan tab’e baki sukai ba tareda sun amsa da Ameen ba dan dama haushi take basu. Suna tsaka da zancen sai ganin Mommy sukai k’ofan kitchen d’in tana aika masu firgitaccen kallo. Gaba d’aya suka natsu suka shige taitayinsu. Mommy ta tako cikin kitchen d’in cikeda isa da mulki tana dubansu d’add’aya “Naji duk abubuwan da kuke cewa munafukai.. Aikin da kuka iya kenan dama. Toh wllhi kunji na rantse maku idan kuka kuskura naji zancen nan ya fita kaf zan koreku na canza ma’aikata.. Ko Safeenah ce ban yarda ku sanar da ita abinda gulmanku ya raya maku ba balle wani cikin gidan nan.. Dik abinda take so ku girka ku bata bakinku alekum.. Idan kuka sake naji zancen nan wani waje kunsan sauran.!” Ta k’arashe tana mai gyad’a kanta alamun jaddada kalamanta kafin tasa kai ta fice. ** Mu’azzam kaw suna ficewa shida Musaddiq ‘yar nasiha yaima Musaddiq d’in kan hak’uri da iyaye especially Mommy. Musaddiq ya d’an fuzar da fuci yace “Wai baka ganin Mommy Ta tsira abubuwan da batai ba a baya ba. Batayi wad’ann abubuwan zamanin k’uruciya ba sai yanzu da girmanta muma da girmanmu.. Haba Mu’azzam wann ai rashin dacewa ne.” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Na Sani Musaddiq. But still Mommy mahaifiyarka ce.. Kar kace zaka d’aga mata murya ko zaka mata tsawa.. Iyaye ko ba musulmai bane ba’a d’aga masu murya Musaddiq.. AlQura’ani mai girmama wajaje da dama yayi umarni da cewa a kyautata ma iyaye. Wann zai tabbatar maka iyaye ba abun wasa bane.. Girman hakkinsu ya shige abinda za’ayi wasa dashi.. Musamman uwa wacce takeda girman hakki akan D’anta kaso uku kafin uba wanda yake da guda d’aya kaman yanda yazo a hadisin Annabin rahama (S.A.W).” Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Ko nasiha zakai ma iyaye kwantar da kai ake da lallami da kwantar da murya da lallashi.. Ba’a yima iyaye ihu Musaddiq.. Sai Mommy ta d’aga maka k’afa ka shiga Aljannah.. Kaje ka bata hak’uri anjima kuma ka lallasheta.. Ni nasan ba halinta bane kawai zafin abinda naima d’iyarta Safeenah ne yasa take duk wad’ann abubuwan.. But I believe Mommy tanada zuciya mai kyau tinda ta rik’emu bisa gaskiya da amana ta kuma d’auki tsawon shekaru tana jinyar mahaifiyata. Wacce duk zatai haka akwai goodness a cikin zuciyarta.” Musaddiq ya d’an jinjina kai kad’an yana had’e fatun bakinsa “Shikenan zanyi yanda kace.. Zan bata hak’uri..” Mu’azzam ya murmusa yana dubansa, Sai ya tuna sab’anin da suka samu a Gidan Gona. Ya kuma murmusawa yana jin dad’in yanda al’amra suka soma daidaituwa tsakaninsa da D’an uwan nasa. Ya d’an bubbuga kafad’ar Musaddiq d’in guda kafin suka soma tafiya suka nufi b’angaren Musaddiq d’in Mu’azzam na fad’in “muje mu buga PS mana na d’an lallasa maka kad’an.” Video game din suka d’anyi tare wanda suka jima basuyi ba, Musaddiq d’in sosai yaji dad’in samun time da D’anuwansa da yayi wanda suka kwana biyu basuyi hakan ba. Haka Musaddiq ya lallasa wa Mu’azzam a game d’in. Mu’azzam ya aje control pad d’in yana d’ago hannayesa biyu alamun surrender. Musaddiq ya dara kad’an yana fad’in “Haba Officer ka bada gari kenan..?” Mu’azzam ya tab’e baki kad’an yana d’aga kafad’unsa “Ni yanzu bayan bincike I guess babu abinda na iya.” Yai maganar yana mai mik’ewa tsaye. Musaddiq na nan rik’e da control pad d’in yana ci gaba da darawa idanunsa kan TV. Mu’azzam ya d’an matsa gefe yana duban D’anuwan nasa. Take tunanin B.A.T ya fad’o masa. D’an kauda fuska yai yana k’ok’arin kauda tunanin. Kaman ance ya dubi saman kujerar dake bayansu ya hango hular Musaddiq mai d’aukeda B.A.T ya k’arasa a hankali ya d’auki hular yana juyata. Musaddiq dake ci gaba da buga game d’insa d’an juyowa yai yana duban Mu’azzam rik’eda hularsa ya k’ura mata idanu. Murmushi yai yana furta “Duk wanda ya sanni ya sanni da son wann hular.. Idan baka mance ba a wani Kanti muka saya a London nida kai wani rakiya da mukayi wa Aunty Nuratu.” Tin a shagon na d’auki hular sanyin na gwada akaina.. Kuma na kasa rabuwa da ita har yanzu.. Kwanaki da ban ganta ba har na soma tunanin ko na rasata ne ashe a laundry na saka.” Mu’azzam ya murmusa kad’an yana mai jinjina kai kafin ya aje masa hular. Lokaci guda zuciyarsa tana tuhumarsa Maiyasa zai tunanin Musaddiq nada wata alak’a da Danger bayan hula ce kawai ya gani mai kamanceceniya data Musaddiq d’in.. Company zata iya yin dubanninsa. Aje hular yai yana fad’in bari ya shiga nasa d’akin yana zuwa. Musaddiq ya jinjina masa kai yana mai bin bayansa da kallo.. Aje control pad d’in shima yai kafin ya k’arasa ya d’auki hular yana juyata. Cikin sauri ya nufi d’aki hular tana nan dunk’ule cikin hannunsa. Wardrobe ya bud’e ya turata can ciki yana mai shafe fusakrsa da duka tafukan hannayensa. D’akinsa na samartaka ya shige abubuwa cunkushe cikin zuciyarsa, ya rasa Wanne tunani zaiyi. Drawers ya soma k’ok’arin dubawa ko zaiga yanda ya aje wann coin mai kamanceceniya da wanda ya samu hannun k’anin Sadiya wanda yakeda tabbacin su Danger sunada alak’a da wann coin d’in. Sann idan haka d’in ne zasu iya zama sunada alak’a da mutuwar mahaifinsa. Toh amma tin mahaifinsa nada rai ya tab’a samun coin d’in cikin stuff d’in mahaifin nasa.. Toh kodai akwai abinda wad’ann kalaman na jikin coin d’in suke nufi ne..? Ko maybe wata K’ungiya ce da ta shafi su Danger.. Mahaifinsa was a successful business man. Watak’ila su Danger da Association d’insu sun jima suna bibiyan ahalinsa.. Watak’ila akwai dalilin da yasa suka sace Ikram.. Yai shiru hab’arsa saman hannayensa da ya dunk’ulesu waje guda yana tunani. A hankali ya mik’e had’ida tura hannayensa cikin aljihu yana taka d’akin yana nazari. Mai Maleeka take son sanar dashi.? Take zuciyarsa ta basa amsa da fad’in “So take ta sanar dakai ga makashinka.” Ya k’ara jefo tambaya ma kansa “Wanene Makashin Maleekar.?” Zuciyarsa ta kuma basa amsa “Ka bud’e kalaman da Maleeka ta sanar dakai a dunk’ule zaka iya fahimta.” Ya d’an shafe hab’arsa kad’an kafin yana mai k’arasawa jikin window. Sai yaji kaman mostin mutum ya fice daga bayansa. Ya d’an waigo yana dubawa baiga kowa ba. Shafe fuskarsa ya kumayi yana jin duk tunaninsa ya k’are. Bai samu coin d’in ba hakan yasa ya fito yai sallama da Musaddiq. Bai tsaya jiran Daddy ba ya nufi gida dan yanada abubuwan yi da yawa. Bincike ne da yake so yayi kan mutuwar Maleeka wanda baya so yai involving kowa ciki harda abokan aikinsa. ** Ta gama jera komai saman dining table tana jiran zuwansa. Saida ta k’ara tsala wanka ta shirya cikin wata riga off neck ruwan d’aurawa wanda ta tsaya daidai cinyarta. Tayi kyau sosai kaman ka sure ka gudu. Ta k’araso kan kujera tai kwanciyarta tana bud’e shafukan zumunta dake cikin wayar nata. Facebook taje ta duba account d’in k’awarta Sabeera ko zataga ta amsa mata sak’on da ta tura mata tun kwanaki amma shiru bata amsa ba ga wayar Sabeeran sam ya daina shiga. Ta lumshe idanunta tana addu’an Allah yasa da rabon su sake had’uwa da Sabeera. Tana nan a kwance taji k’aran bud’e masa k’ofa. Ta mik’e da sauri ta k’arasa jikin window tana lek’ensa. Murmushi saman fuskarsa take dubansa. Har ya ida rufe motar nasa waya mak’ale kunnensa na hagu. A ranta tace sarkin waya ba, shi ko gajjiya bayayi.. Gashi a zahiri baida hayaniya baida yawan magana amma idan abinda ya shafi aiki ne tana tsammanin zai iya kwana yana waya. Ya turo k’ofar ya shigo yana mai k’are mata kallo dan Ta masa kyau sosai. Sauri sauri yai rounding wayar nasa kafin ya bud’e mata hannaye alamun ta taho. Aiko nan ta taho a guje Ta haye cikin jikinsa. Cak ya d’agata kaman wata baby yana juyi da ita. Ya mak’aleta tsam cikin jikinsa yana fad’in tayi kyau. Ta d’an rufe idanunta da tafukan hannayenta tana murmushi. Hannayensa yasa ya cire nata hannayen daga saman fuskarta yana kuma tsareta da rikitattun idanunsa. Hannayenta cikin nasa suna fuskantar juna yake fad’in “Beautiful bazaki daina rikirkita mun lissafi a gidan nan ba. Naga alama yanzu ke kike bani Assignments d’in ba ni nake baki ba.. Duka missions d’in naki ne yanzu kam.” Ta d’anyi fari da idanu kaman zatai kuka tace “Kai Handsome, ni kuma mai nayi yanzu..? Kaga muje ka fara yin wanka sai ka sauk’o kaci abinci.” Tana maganar tana warware masa necktie d’insa. Yayinda ya kasa janye idanu daga barin dubanta. Ya d’an janyota cikin jikinsa yana kwanto da fuskarsa kusan nata yake furtawa a hankali “I think I’ll start with you first before abinci..” Ya fad’i yana kashe mata idanu guda. Kafin tai wani aune ya sureta cikin hannunsa ya nufi upstairs da ita yana nuna mata kalolin k’aunarsa. Itama dai saida ya b’ata mata nata wankan suka kuma shiryowa tare suka nufo downstairs mak’ale da juna. Haka yaita santin abincin Su duka biyu suna cike da nishad’i kaman rayuwa ta dawamma masu a haka ba tareda wani iftila’i ko tashin hankali ya ratsa tsakani ba. Suka k’arashe yininsu suna nuna ma juna zallan k’auna. Sallah ce kawai ke fitar dashi. Kafin su kwanta bacci ma saida sukai shafa’i da wutiri tare sukai addu’o’insu suka kai koke kokensu wa Rabbil Izza wanda shine majib’icin lamuransu. Kallo ya saka masu a laptop d’insa, yai mata matashi da k’irjinsa, ya rage wutan d’akin yabar dim-night popcorn gabansu suna kishingid’e saman gadon suna kallon wanda da gani zaka fahimci sabida ita kawai ya saka kallon ba wai dan yanada lokacin kallon ba. Babu ma film cikin computer d’in, downloading yai a Netflix kawai sabida ita, dan ya bata lokacinta a matsayinta na matarsa tinda yasan yanda yanayin aikinsa yake, shi kansa gani yake kaman lokacin na kasa masa. Kasancewar horror film ne haka yasa duk abin tsoro da aka nuno sai ta cukukuye cikin jikinsa. Shiko da biyu ya saka horror film d’in. Dan idan taji tsoro idanunta suka firfito waje cikeda shagwab’a mugun kyau take masa. Yaita sakin murmushi yana kallonta har bacci yai awon gaba da ita nan cikin k’irjinsa. Ya gyara mata kwanciyarta a hankali ya rufa mata bedcover d’in, ya shafa mata addu’a had’ida manna mata peck a cheek d’inta kafin ya kashe kallon. Cak ya d’auki computer d’in ya sauk’o parlor. Dining area ya zauna yana nazarin abinda ke gabansa wato binciken mutuwar Maleeka. Cikin laptop d’in nasa ya soma binciken abinda ke rubuce jikin coin d’in nan Wato Black African Team. Results da dama ne suka bayyana masa wanda baiga wani tak’aimammen abu guda da zaice yayi kamanni da ta’addanci ba. Hasalima results d’in akasari associations na bak’ak’en fata ya dinga nuno masa wasu na schools a k’asashen waje wasu ma a nahiyoyin Africa d’in amma bai samu tak’aimammen abinda zaice gashi ya had’a Su Danger ko nasa ahalin da wad’ann kalmomi ba. Yai shiru yana kuma duba net. Babu abinda ya samu hakan yasa ya d’an tura computer d’in gefe yana dafe kansa kad’an. Mik’ewa yai ya d’auko paper da pen ya dawo ya zauna yana k’ok’arin rubuta kalaman da Maleeka taso sanar dashi. BA.. You... Ya rubuta saman takardan. Kafin ya sauk’o k’asa kad’an ya rubuta Black African Team. B zai iya zama yana nufin Black. A zai iya zama yana nufin Africa.. To kodai BAT taso sanar dashi..? Kodai taso tai abbreviating kalmomin ne. Sai su zamto BAT a sauk’ak’e.. Kenan BAT d’in da Ta so sanar dashi sunan k’ungyar su Danger ne? Maybe You d’in da tace taso tace “BAT.. You need to find BAT..” Maybe kenan haka Maleeka taso fad’a masa “BAT.. You need to find BAT..” Ya nanata a hankali yana bubbuga pen d’in saman takardan. Tagumi yai kad’an yana kuma wani tunanin. What if Maleeka BAD taso ambata tinda an masa text kwanaki da sunan BAD..who could be BAD.. Take ya bama ma kansa amsa da fad’in “Barrister Ameer Dikko..” Ya kuma canza position d’in taguminsa yana fad’i a fili “What if Ba da tace Barrister Ameer take son fad’i.?” Ya kuma nanatawa kaman haka “Ba.. You need to find Barrister Ameer..” What if BA d’in da Maleeka take nufi kenan..?” Ya d’an shafe bakinsa a hankali yana fuzar da huci. Amma makashin Maleeka k’wararre ne kuma yayi fad’a da Maleeka kafin ya samu galaban kasheta.. And Ameer is not that well trained da zaiyi fad’a da Maleeka irin haka.. Could it be Danger ne ya kashe Maleeka..?’ Ya kuma gyara zamansa yana ci gaba da tunanin yanda zai solving wann puzzle d’in. ‘Amma Maleeka tasan Danger.. Da da yazo kai tsaye instead of BA da DA tace dashi wanda yake nufin Danger kai tsaye. Dole wanda ya kashe Maleeka wani ne da ya k’oshi da raining ko dai na ta’addanci ko kuma na aikin tsaro.. Toh wanene wann mutumin.?’ Ya mik’e tsaye ya soma zagaye parlorn. Wayar salularsa ya bud’e yana duba hoton sketch d’in k’asan takalmin da yake da tabbacin na makashin Maleeka ne.. Ta yaya zai samo wann mutumin..? Tambayar da yai karan tsaye a zuciyarsa.. A hankali ya saki murmushi shi kad’ansa yana jinjina kai kama wanda ya tina wani abin. Lokaci guda ya saita garu da pen d’in hannunsa ya jefa. Ai kuwa bai missing target ba. Murmusawa ya kumayi kafin ya furta a fili “Allah ya kaimu gobe zamu buga wasan Naka Chief Jaja..!” Ya k’arashe yana sakin murmushi mai bayyana hak’wara. ** D’akin taron yayi shiru. Yayinda Deputy Director General (DIG) ke zaune daga center. Manyan ‘yansanda kusan guda biyu suna zaune gefe da gefensa. Chief Jaja yana gefe guda. Sai sauran Team Members d’insu Assad da kuma Yusuf suna zaune gefe guda suma. Duk saman doguwar teburin dake kewaye da kujeru suke. Mu’azzam yai tsaye yana masu nuni da Farin allon da yai rubutu bisa. Solution d’in da yai saman takarda a daren jiya shi yake rubuta masu saman allon yana kwararo bayanai. Yayinda DIG da sauran ‘Yansandan ke jefo masa tambayoyi sahu sahu yana amsa masu. Gaba d’aya sun bada hankulansu suna sauraron yanda Inspector Gamji zai zak’ulo makashin Maleeka. Kallo guda za kaima Chief ka fahimci cikin tsananin tashin hankali yake. Dikda sanyin AC dake busawa cikin d’akin taro Chief Jaja gumi ne ke tsartsafowa cikin jikinsa. Mu’azzam ya k’arasa jikin allon yana k’are masu kallo gaba d’aya. Ya murmusa kad’an yana duban position d’in da kowa ke zaune cikinsu yana jinjina kansa yake furta “True failure isn’t missing the target.. True failure is never taking a shot..” Yaci gaba da takowa still murmushi saman fuskarsa yana d’an kewayesu kad’an yana ci gaba da examining nasu “BA could be either BAD or BAT.. And YOU could be you..!” Ya k’arashe yana jefa pen d’in dake rik’e hannunsa. A firgice Chief ya d’ago yana duban Mu’azzam dake sakin murmushi yana sarawa DIG, lokaci guda yake furta “puzzle solved, Sir.” Lokaci guda ya d’ago hoton k’asan takalmin dake cikin wayarsa yana nunawa a fuskokinsu.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *59* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin sakanni Zuciyar Yusuf da Mu’azzam ya jifa da alk’ami yake bugu. Ya ware idanu yana duban mutanen dake kewaye wajen suma suna dubansa, babu kaman Deputy Inspector General. Ko gizau Yusuf ya kasa har saida Mu’azzam ya tako zuwa gabansa yayi folding hannayensa ta baya. Chief Jaja ya kasa d’ago kai ya dubi Yusuf dan baya so su had’a idanu balle a fahimci wani abu. Shiko Assad cikin tsananin shock yake duban Yusuf da Mu’azzam d’in. Mutanen da sukayi dik yanda zasuyi har Allah ya fiddashi daga k’agen da aka masa.. Ta yaya Mu’azzam zai nuni da Yusuf yace shine ya kashe Maleeka.. Wann abu ne da bazai tab’a yuwa ba.. Sud’in abokan juna ne wanda tinda aka soma binciken nan tare suke komai.. No. no it can’t be Yusuf.. Not Yusuf.. Yusuf bazai tab’a zama Traitor ba.. He is a good person.. Shi ya tabbatar da hakan. Muryar DIG ne ya katse Assad sanda yake jefowa Mu’azzam tambaya. “Mai hakan yake nufi Inspector Gamji.. Ka nuna mana hoton zanen k’asan takalmi sann kayi nuni da Detective Yusuf.. Akwai wani abinda hakan yake nufi ne.?” Mu’azzam ya jinjina kansa yace “K’warai kuwa Sir. Hakan yana nufin Detective Yusuf shine makashin Maleeka.. Wann hoton zanen k’asar takalmansa ne.. Idan ka bani dama Sir.. Inaso na umarci Yusuf da ya ciro k’afan takalminsa na hagu kaman dai yanda na zana wann ni kuma zan tabbatar maku cewa shine makashin sann zan fayyace maku yanda ya buga wasan nasa.” Tinda ya soma magana Yusuf baice komai ba Sai dubansa yake da idanunsa da suka gama kad’awa yana dunk’ule hannunsa cikin alamun rashin gaskiya. Shiko Chief addu’a kurum yake Allah yasa kar wann binciken tonon sililin da Inspector Gamji yakeyi ya k’araso kansa. Mu’azzam ya k’arasa gaban Yusuf yai tsaye kansa su duka biyun suna aika ma juna wani irin duba. Fuskar Mu’azzam a matuk’ar tsume. Girgiza kai Yusuf yai yana duban Mu’azzam wanda ko gizau bai ba “How could you..? How could you accuse me of serious crime Inspector.!” Yana maganar ne daga nan yanda yake zaune. Mu’azzam ya jinjina kai yace “Ka ciro k’afar takalminka na hagu.” Zuciyar Yusuf bai daina bugawa ba. Bai daina aikawa Mu’azzam kallon tsana ba. Lokaci guda ya zame takalmin ya mik’a masa. Mu’azzam ya murmusa yana juya k’asan takalmin dan tinda ya hango k’afar Yusuf ya fahimci cewa wann takalmin ne sanye a k’afarsa sanda yai committing crime d’in. D’ago takalmin yai ya had’e da hoton dake cikin wayarsa yana nuna masu, exactly babu abinda ya raba da zanen dake k’asar takalmin Yusuf, harta lambar takalmin iri d’aya ne Wato size 43. Yusuf ya soma girgiza kai yana furta “This is rubbish.. Wann zai iya zama takalmin kowa don ba ni kad’ai Company ta k’era takalmi ba.” Mu’azzam ya jinjina kai yace “K’warai ba ma kai kad’ai Company ta k’era takalmi ba amma wann hoton k’asar takalminka ne..” Ya d’an gyara tsayuwarsa yana duban cikin idanun Yusuf “Ka zaci ka iya buga wasan ne.. Saidai ka mance a ko wani wasa akwai coach.” Ya murmusa kad’an kafin ya juyo yana dubansu yaci gaba da fad’in “Na kira layin Yusuf a lokacin da na d’auki hanyar headquarters daga can asibitin yanda na gano cewa Maleeka ita ke cin amanarmu.. Amma sai naji wayarsa bata shiga, can kuma Sai naji ana sanar dani line busy.. Kenan Yusuf yana waya a daidai wann lokacin.. After some seconds still wayar bata yanke ba.. Yusuf ya d’aga kirana alamun ya gama wayar da yakeyi kenan..” Nusawa ya d’anyi kafin yaci gaba da fad’in “Ya sanar dani cewa Officer Maleeka was ready to confess.. Zata bada statement d’inta, zata fad’i duk abinda Ta sani kan wad’anda take ma aiki, mu sameta a apartment d’inta. A cikin team d’inmu ni kad’ai ne bansan location d’in gidan Maleeka yake ba. Abokan aikina sun sani.. So Yusuf yasan gidan Maleeka kenan. Hakan yasa ya turo mun sak’on adireshin gidan immediately bayan mun gama waya.” Ya d’an ci gaba da takawa yana fad’in “Tsakanin lokacin da mukayi waya yaci ace Yusuf yaje gidan Maleeka ya dawo daga yanda yake fiye da yanda nake.. Yusuf yaje location d’in domin ya kashe Maleeka, saidai abinka da k’wararru koda Yusuf ya soma attacking d’inta tayi retaliating. Sukai fad’a irin na well trained police officers.. Har Allah ya bama Maleeka nasaran bud’e fuskar Yusuf wanda probably yake rufe da mask.. Ga dukkan alamu She was shocked sanda taga fuskar Yusuf yazo a matsayin wanda zai kasheta. Sunyi kokawan k’wace bindiga a tsakaninsu kwatsam harsashin ta huda Maleeka a cikinta. Domin kuwa a binciken da akai na gawan Maleeka harsashi na farko a kwance ya huda cikinta ba a tsaye ba, wanda hakan ka iya zama kokawa suke bindigar tana kwance tsakankanin jikkunansu ko wanne cikinsu na son k’wace bindigar kwatsam harbi ya same Maleeka. Sai Yusuf ya k’ara mata harsashi guda dan ya tabbatar ta mutu gaba d’aya, wann yana iya zama dalilin da yasa Yusuf ya harba mata second bullet.. Yayi saurin kawar da duk wata shaida ko alama.. Abinka da k’wararre yayi k’ok’ari yaga bai bar wani trace da zai bayyanasa a matsayin makashin Maleeka ba. Saidai kuma na samu burbud’in glass na frame da ya fad’o ya fashe a lokacin da suke kokawa da Maleeka.. Sann akwai alamun footprint d’insa wanda ya manne jikin tile ba tareda ya kula ba.. Yayi komai ne cikin gaggawa Sai ya nufi mab’oyarsa wanda ga dukkan alamu baida nisa da gidan Maleeka ya canza shigarsa ya k’ona duk wasu abubuwa da yai amfani dasu wajen kashe Maleeka.. Amma fah ya mance bai k’one wann takalmin tasa ba harma yaci gaba da sakata.. Watak’ila takalmin tanada mahimmanci ne a wajensa sosai.. Kaman dai yanda yau ya sakota a k’afafunsa.” Gaba d’aya suka zuba masa idanun jin yanda yake aiki da tunani da iliminsa na bincike yana fayyace masu hanyar da Yusuf yabi ya kashe Maleeka tamkar yana a wajen. Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Na kira Yusuf naji ko ya isa location amma sai yace mun bai isa ba holdup ya rik’esa.. A yanda akai advancing hanyoyin garin nan babu irin wann holdup d’in da zai hana Yusuf isa wajen Maleeka.. Nayi amfani da lokaci nayi calculating time d’in da ya d’auka kafin ya isa gidan Maleeka.. Kaman yanda nace maku daga yanda yake zuwa gidan Maleeka yaci ace yaje gidan Maleeka ya dawo amma sai yace mun holdup ne ya rik’esa wanda hakan yasa muka isa gidan Maleeka tare tare bayan ya sauya shiga yayi destroying duk abubuwan da yayi amfani dasu wajen kashe Maleeka.. Sanda muka Zo gidan Maleeka mun taddata kwance cikin jini numfashinta yana gab da barin gangar jikinta.” Ya duk’ar da fuskarsa yana duban Yusuf “Yusuf bai k’arasa kan gawar Maleeka ba Sai ya tsaya daga baya dan kar tai pointing d’insa da hannunta. Har saida Maleeka ta cika kafin ya k’araso kanta..” Ya d’ago yana duban su DIG kafin yaci gaba da fad’in “Sir, bayan binciken da nayi a daren Jiya, a safiyar yau sai nayi tunanin komawa wancan asibitin domin na binciki security da alhakin kula da na’urar ke wuyansa naji wanene ya sayesa ya b’oye wann Footage d’in da muke nema daga farko.. Na nuna masa hoton Maleeka na tambayesa ko itace ta sayesa ta rufe bakinsa da kud’i amma Sai ya girgiza mun kai yace ba ita bace.. Daga nan na soma tunanin hunch d’ina ka iya zama daidai.. Sai na nuna masa hotunan sauran abokan aikina.. A daidai hoton Yusuf ya tsaya yana kuma duba kafin yai pointing nasa yace mun shine mutumin da ya sayesa..” Ya d’anyi taking excuse kafin ya nufi k’ofa ya tura wani police ya taho da mutumi security d’in asibitin da Mu’azzam ya nemo Footage d’in da yaga Maleeka ciki. Da tsananin mamaki Yusuf ke dubansa dan baiyi tsammanin Mu’azzam zai iya kamosa haka ba. Mu’azzam yai nuni da mutumin wanda kansa ke duk’e yace “Wann shine security d’in da Yusuf ya saya da kud’i ya rufe bakinsa dan kar ya fitar da CCTV footage na wann asibitin dana gudanar da binciken DNA test a can. Abun mamaki na tura Yusuf ya gudanar mun da bincike a wann asibitin domin mu kub’utar da abokin aikinmu Assad ba tareda nasan cewa Babban b’eran na tura ya kamo k’aramar B’era ba.. Koda yaje sai ya buga wann wasan.” Ya k’arashe yana sakin murmushi. Yusuf ya kifa kansa kurum a k’asa dan tuni mutumin ya kuma nuna Yusuf d’in a matsayin wanda ya saye bakinsa da kud’i. Bayan ya gama bada statement d’insa Mu’azzam yai alama ma D’ansandan da ya shigo dashi cewa ya fita dashi security d’in. D’ansandan ya jinjina kai yana mai furta “Yes sir.” Lokaci guda ya janye security d’in suka fice. Assad mamaki da tsoron mutanen duniya ya kuma cikasa yayinda Chief keta raba idanu tsoron Mu’azzam fal zuciyarsa ganin ya kama duka yaransa Yusuf da Maleeka. Wanda ita kanta Maleekar batasan Yusuf d’in yaron Chief bane har Sai randa zata bar duniya.. Idan kuwa Mu’azzam zai iya kamo Yusuf haka Tabbas ya kusa cimmasa kenan.. Ji yai kaman ya cire kakin dake jikinsa yai jifa da ita sabida tururin zafi dake kuma fito masa daga can k’asa. Tafin DIG ne ya dawo da hankalin Chief.. DIG da sauran ‘yansanda suka mik’e suna tafasa Inspector Gamji bisa wann k’ok’ari da yayi na kamo mai cin amanan aikin D’ansanda da kuma k’asa. DIG yana tafawa yake fad’in “Impressive..! Gamji Mazan fama.. Well done Inspector Gamji.!” Ai Chief ma tuni ya soma tafawa dan kar a zargesa. Yanayi yana Washe baki yana fad’in wann ba ci gaban Mu’azzam bane kawai ci gaban Team d’insu ne gaba d’aya tinda shine rahamar case d’in ke hannunsa. Mu’azzam Sai duban Chief yake cikin zuciyarsa yana ayyana cewa saura kai Chief Jaja.. Sannu a hankali zamu iso Kanka Babban B’eran B’eraye.. Bayan mun gama da muk’arabbanka zamu iso kanka ne da izinin Allah.. B’eran banza sai na capko wuyanka In sha Allahu kafin na bar aikin D’ansanda.” Ya k’arashe zancen zucin nasa yana mai mik’awa DIG daketa faman mik’o masa hannu sukai masabaha. Yana kuma masa jinjina had’ida tabbatar masa samun goyon bayansa har a isa k’arshen wann case d’in. Mu’azzam ya sara masa yana mai masa godiya “Wann nasaran mu ne gaba d’aya NPF Sir, dukda cewa ban kai yanda kake tunanin na kai ba amma na gode da kalaman yabo Sir.” Ya k’arashe yana sara masa dan yasan ba iyawarsa bane ko k’warewarsa ya kaisa wann matakin. A’a taimakon Allah ne da fawalla masa lamuransa da yayi.. Amma ko d’aya bai yarda akwai iyawarsa ko k’warewarsa a ciki ba. Bayan sun fito daga Zauren taron kai tsaye cell d’in da akai detaining Yusuf nan cikin Headquarters d’in suka nufa shida Assad. Hannayen Mu’azzam dafe da belt d’insa yake duban Yusuf yana tuna tsawon lokacin da ya kwashe yana cin amanarsu. Bai iya cewa komai ba sabida zafi da zuciyarsa ke masa. Ya tsani a raina masa hankali a ha’incesa.. Sun d’auki Yusuf d’aya daga cikinsu amma daga k’arshe yaci amanarsu.. Assad ne ya iya furta “Why did you do it.. Maiyasa ka aikata..?” Yusuf ya mik’e ya k’araso gaba garesu yana sakin murmushi “I was only following orders.. Dear Team mate.” Ya k’arashe murmushin saman fuskarsa. Assad ya girgiza kai yace “Waye yake baka umarni.. Was it Danger..?” Murmusawa Yusuf ya kumayi “Ka bar shi wanda yake tunanin yanada brain d’in yayi tambayoyin amma ba kai ba wanda mace tai outsmarting naka.” Izuwa lokacin ran maza ya b’aci, wani irin finciko wuyansa Mu’azzam dake aika masa mugun kallo yai.. Ta cikin kmarafunan cell d’in ya tura hannu ya capko Yusuf ya matsesa sosai kai kace zai fiddosa ta cikin matsin k’arfen ne. Dan wani irin damk’a ya masa ya shak’esa kaman mai shirin aikasa lahira har saida Assad ya k’waci Yusuf d’in da k’yar. Yusuf ya zube nan wajen yana fidda numfashi da k’yar. Mu’azzam kam sabida b’acin ran abinda Yusuf yai kasa cewa komai yai saima ficewa da yai daga cikin ofishin gaba d’aya. Assad ya dubi Yusuf ya girgiza kai disappointedly kafin yasa kai yabi bayan abokinsa Mu’azzam. Saida Chief ya tabbata sun bar Ofishin kafin ya nufi wajen Yusuf. “Kar ka damu zamu kula da iyalanka.. Sann zan samo maka hanyar da zakai escaping daga prison.. Kawai don’t rat us out.. Ka iya takunka ni kuma na maka alk’awarin zan maka komai..” Yusuf ya tsaresa da idanu kafin ya murmusa da gefen baki yace “Kana tunanin yanda Inspector Gamji yai rantsuwa Sai ya kai k’arshen case d’in nan bazai kai bane.. Kana tunanin zaka iya dakatar dashi ne.. Idan ni da kai bamu b’ata ji da gani ba.. Inspector Gamji ya riga yasan da zaman Boss At the Top ko ince maka Babbanmu A Tushe..” Murmusawa Chief yai kafin yace “Yasan abinda ya sani dai amma bazai tab’a sanin wanene Jemage ba. Yusuf ka iya takunka mu kuma zamu kub’utar dakai.” Yusuf ya tsare Chief da idanu kafin ya soma jinjina kai yana fad’in “You better keep your words domin idan kai failing d’ina Chief believe me I won’t go down alone.. Ni ba kamar Maleeka bane.. You know I also have my own ways of doing things.. Zan baka mamaki idan ka zab’i juya mun baya.” Chief ya kafesa da idanu kafin ya saki gajeriyar murmushi.. Lokaci guda yasa kai ya bar wajen. Yusuf yai zaune yana tunanin makomar rayuwarsa data ahalinsa. A haka har aka kwashe kusan sati biyu suna gudanar da bincike kan Yusuf. Dik yanda Mu’azzam yaso ya fitar da wani abu daga bakin Yusuf abu yaci tura.. Duk kalan horon da za’aiwa mai laifi dan yayi magana anyi ma Yusuf amma yak’i sanar dasu komai.. Saima raina masu hankali da yai da fad’in Danger ne Boss d’insa. Shi kaw Mu’azzam Chief yake so ya kama dan yasan Chief shine Babban b’era a Department d’in nasu saidai haka kurum ba tareda hujja ba baida ikon kamasa. A wajen matarsa Sadiya kurum yake samun sauk’in abubuwan wajen aiki, saiko abokinsa Assad wanda Allah ya nufa ya tsallake tuggun azzalumai. A b’angaren Sadiyar ma takan ziyarci Su Ummanta, saidai Umma ta hanata zuwa wajensu akai akai. A cewarta ba birgewa bane ace kullum matar aure tana gantali saman kwalta. Kamata yai ta killace kanta a gida ba taita fita barkatai ba hakan ba birgewa bane. Haka Sadiya zatai Ta ture turen bakinta babu dai yanda ta iya ne. K’arshe ma Umma wa Mu’azzam d’in tai magana tace ya daina biye Sadiya Wai idan zai fice aiki Sai ya kawota gida ya aje. Umma tace ya dinga barinta can gidanta idan abokan gira take nema za’a ke kawo mata su Ashir tinda ta kula kaman harda kad’aici ke damun Sadiyar. Dan a ‘yan kwanakin Mu’azzam na yawan jimawa wajen aiki ga fita bincike da suke shida Assad wasu lokutan ma har sukanyi dare sosai. Umma tace da ita ko wace mace haka tai hak’urin zaman gidan miji itama tai hakan tinda tasan ga yanayin aikin mijinta. A b’angaren Safeenah da Mommy kaw, Mommy sai rainon cikin Safeenah take ba tareda Safeenar ta kula ba. Saidai yawan zazzab’i da k’anan ciwon kai dake damunta yasa Ta soma shakku.. Sai wann lokacin ma take tunanin Ta wuce kwanakin al’adarta tuntuni.. Calendar d’inta Ta duba tana mai kuma mamakin yanda abun ya canza da yawa.. Anya kuwa lafiya take.. Ta soma tinanin kwanaki biyu da suka shige taso zuwa asibiti amma sai Mommy ta hanata tace Malaria ce kawai no need taje a mata test zata bata anti Malaria tasha.. Ita dai cikin Magagin bacci ma ta amshi maganin tasha. Zata iya cewa batasan kalan maganin da Mommy ta bata tasha ba.. Anya bazata tafi asibiti ba.. Ta mik’e tana tunani.. Daidai lokacin Dattijuwar mai aikinsu ta shigo mata da farfesun kayan ciki da tace tana son ci. Dubanta Safeenah tai tace “Iya nikam na tambayeki.” Iya ta jinjina kai tace “Ina sauraronki.” “Wai dan Allah meye alamomin mace mai ciki..?” Iya ta zaro idanu waje tana tuna kashedin da Mommy ta masu. Ta kasa furta komai sai girgiza kai da take. A kufule Safeenah tace “Bakiji tambayar da na miki bane..?!” Daidai lokacin Mommy ta shigo. Ta dubi Iya tace ta fice abinta.. Kana ta maidoda dubanta ga Safeenah “Mai kike son sani..?” Safeenah ta kafe Mommy da idanu kafin ta girgiza kai tace “Kin sani Mommy.. Kinsan komai Kika zab’i ki b’oye mun.. Maiyasa Mommy..?” Ta k’arashe tana duban mahaifiyar tata. Mommy Ta girgiza kai tace “Ban fahimci mai kike nufi ba..” Safeenah ta mik’e zaune sosai tana kuma jinjina kai “Don’t play dump Mommy.. Kinsan komai.. Kinsan ina d’aukeda cikin Mu’azzam amma kika zab’i kiyi shiru kik’i sanar dani.. Mommy kina ganin yanda naketa faman shan wahala kan na karkato da akalar hankalinsa gareni.. Kina ganin yanda nake masifar son komawa gidan mijina amma duk kika zab’i kiyi biris sabida wani dalili naki.. Mommy shashanci nan ai bai kai yanda kike tunani ba.. Kina tunanin bana jin changes ne a jikina.. Kina tunanin bazan fahimci cewa inada ciki nan kusa bane.. Mommy abinda ban gane ba shine kan wane dalili zaki b’oye mun wann Babban makamin da zanyi amfani dashi wajen winning mijina back.. Haba Mommy Maiyasa zaki min haka.. Kinsan sarai Mu’azzam shine rayuwata shine cikar burina.. Maiyasa zaki hanani komawa gidansa..” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka. Mommy ta matso kusanta ta kamo hannayenta cikin nata, lallashinta ta somayi tana fad’in “Ba nak’i ki koma bane Safeenah.. Kuma ba nak’i sanar dake bane sabida wani manufa nawa.. Shin baki ganin yanda nake kulawa dake ne..? Irin tarairayar da ake wa mata masu ciki shi nake miki Safeenah..” Cikin kuka Safeenah Ta fincike hannayenta daga cikin na Mommy tana fad’in “Ba ke kikeda alhakin kula dani da D’an ciki na ba Mommy.. Mijina shine zai tarairayeni ya kula dani.. Nayi imani da Mu’azzam yasan cewa inada ciki minti talatin bazan k’ara a gidan nan ba.. Haba Mommy wllhi ni kin cuceni.. Kinyi depriving mana right d’inmu nida d’ah na wajen kasancewa da mahaifinsa.” Mommy ta girgiza kai “Safeenah ba haka bane.. Banda rashin wayo irin naki yanzu ai zai zaci k’Arya kawai kike masa babu wani ciki tattareda ke. Zaiyi tunanin so kike ya maidaki d’akinki sai kika b’ullo ta wann hanyar.. Kina tunanin zai yarda Kina da ciki ne.. Na bari cikin ya fito ne ya bayyana kowa ya shaida sai ki fi samun kulawar mijinki..” Safeenah na hawaye take girgiza kai “Haba Mommy civilized world fah muke.. Kan wani dalili zaisa yak’i amincewa akwai gidan jininsa cikin jikina bayan ga prove na asibiti.. Mommy Mu’azzam needs to know.. He needs to know I’m carrying his child.. Kin fahimta..!” Ta k’arashe tana zaro idanunta dake jik’e da hawaye waje. Ba tareda ta jira cewar Mommy ba ta janyo wayar salulanta ta soma dialing layin Mu’azzam.. Taita ruri ba’a d’aga ba. Ta soma k’ok’arin tura sak’o kenan Mommy ta kamo hannayenta tana fad’in “Mai kikeyi..?” A d’an dak’ile take duban Mommyn “Text zan tura masa yasan da zaman D’ansa cikin jikina.” Mommy Ta girgiza kai tace “Haba ke kaw Safeenah. Yanzu fah Mu’azzam a tafin hannnunki yake sai yanda kikaga damar juyasa. Yanzu lokaci ne da zaki d’aga darajarki a idanunsa ba wai kiyita lik’e masa kaman wata ‘yar anace ba. Ai idan kinaso ya yarda ya amince ciki gareki ba ke ya kamata ki kirasa ba. Ni ce nan zan kirasa na kuma sanar dashi halinda kike ciki.. Na tabbata idan yaga kirana bazai tsallake ba zai d’aga.” Safeenah tai shiru tana duban Mommy kafin Mommyn ta jinjina kai a hankali, tai kiran mai aiki ta d’auko mata wayarta a uwar d’aki. Ana kawo wayar Mommy Ta danna kiran Mu’azzam yayinda Safeenah Ta kafeta da idanu. ** Mu’azzam kaw suna tafe saman kwalta shida Assad wayar Mommy ya kuma shigo masa bayan kiran Safeenah ya k’araci ruri bai d’aga ba. Assad ya dubesa ya girgiza kai kad’an yace “Wai bazaka d’aga kiran nan ba.. Zai iya zama wani abu ne mai mahimmanci.” Ba tareda ya dubi Assad d’in ba, idanunsa da hankalinsa naga tuk’in mota da yake yace “Mommy ce mai kira nasan duk bazai wuce kan fitinar Safeenah bane.” “Haba Mu’azzam Mommy Ta wuce kaga kiranta kai biris da ita.. Ka daure ka d’aga kaji ko menene.. Tinda har kaga Safeenah ta kira sann ga Mommy na kira na tabbata it might be something serious.. Ko ba komai Mommy uwa ce ka d’aga wayarta dan Allah.” Gajeren fuci ya fuzar kafin ya d’aga wayar ba tareda yace uffan ba tinda yasan shidai a idanun Mommy Sarkin laifi ne. Daga d’aya b’angaren Mommy na jijjiga kaman wani Mu’azzam d’in na ganinta take fad’in “Ka rik’e gaisuwar ka dama bana so..” Saida tai fasali kafin tace “Mu’azzam, kazo ka d’auki matarka Safeenah ko dan ajiyan da kayi cikin cikinta.” Out of the blue yaji maganar wanda har saida yasa ya kusan gwaran motar gabansa dan baima kula traffic light ya tsaida su ba. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *60* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* D’if yaji Mommy Ta katse kiran ba tareda Ta saurari abinda zaice ba. Ya dinga nanata maganar Mommy a kwanyarsa yana ji kaman sautin maganar cikin kunnensa. Dik maganan da Assad ke masa yana fad’in an basu koren wuta baiji mai Assad d’in ke fad’i ba har saida ya soma jiyo horn daga motocin dake bayansa sahu sahu. A hankali ya soma jan motar yana kuma jin maganar Mommy har wann lokacin. “Are you alright..?” Assad ya tambaya daga yanda yake zaune gefensa. Bai amsa Assad ba sai canza hanya da yai ya d’auki hanyar gidan Daddy dan dama kusan layin gidan suke. Assad ya zuba masa idanu dan yasan tinda Yai shiru bai amsa ba idan zai kwana a wajen yana tambayarsa ba lallai ya amsa d’in ba. Suna isowa Assad ya dubesa kad’an yace “Daddy fah yana ciki ne..? Naga kusan duka motocinsa gasu nan a gida.” Girgiza kai Mu’azzam d’in yai jikinsa duk ba kuzari “No yana Adamawa..” Gyara zamansa cikin kujera Assad yai yana fad’in “Tinda baya nan no need na shiga ka shiga kai Bikon matarka kai kad’ai dama da Daddy na nan ne da Sai na shiga na tayaka biko.. A fito lafiya.” Ya fad’I yana mai tura kai cikin kujera cikeda zolaya. Mu’azzam bai ce masa komai ba sai dubansa da yai kad’an kafin yasa kai ya nufi cikin gidan. Zaune ya hango Safeenah a parlor fruit salad bowl ajiye gabanta. Aiko Safeenah tana jin alamun shigowarsa tai saurin ture kwanon fruit salad d’in ta soma yunk’urin amai kai kace da gaske aman ne ke taso mata. Cikin sauri ya k’araso parlorn yana ambato sunanta “Feenah are you alright.? Do you need help..?” Yana maganan yana k’ok’arin duk’awa kanta. Safeenah bata amsa sa ba sai k’ok’arin k’wak’ulo amai take tana rik’e cikinta tana kiran Mommy. Babu shiri Mommy ta k’araso tana raba tsakanin Mu’azzam da Safeenah take fad’in “Safeenah sannu koh.. Cikin ne.. Tashi muje na rakaki bathroom.. K’ok’arta ki tashi..” Kuka Safeenah ta fashe dashi tana kuma narkewa take fad’in “Mommy cikina it hurts.. Mommy bazan iya tashi ba.. Wayyo Mommy..” Mu’azzam ya d’an kuma matsowa kaman mai son taimaka wa Safeenar. “Kar ka kuskura ka tab’a mun ‘ya kauce ka bamu waje..” Mommy tace tana rik’o Safeenah, Mu’azzam ya d’an matsa gefe kad’an ya zuba masu idanu har suka nufi toilet. Furzar da huci yai kad’an yana mai daidaita tsayuwarsa, nan idanunsa suka sauk’a kan takarda dake gefen Safeenah. Ya k’arasa ya d’auki takardan yana karantawa. Sakamakon gwajin cikin da aka mata ne wanda yai daidai da lokacin data sha poison har aka bata gado a asibiti.. Safeenah nada ciki har poison take sha duk a sabida shi.. What if wani abu yaje ya sami d’an.. Koma cikin ya fice gaba d’aya.. Baya fata rashin hankalin Safeenah yasa ya rasa D’ansa ko ‘yarsa dake cikinta. Yaita juya takardan yana kuma nanatawa cikin zuciyarsa, Wai shi Mu’azzam zaiyi D’ah.. Allah mai iko.. Sai kuma yaji murmushi from no where na zuwa masa. Yana nan zaune saman kujera har su Mommy da Safeenah suka fito, Mommy na tallafe da ita. Yanda Mommy ke riritata Kai kace kanta aka soma yin ciki. “Sannu ko.. Kina buk’atan wani abu ne..?” Idanunta a lumshe tace “No Mommy.. I just need to rest.” Ta fad’i daga nan yanda take kishingid’e. Mommy ta dubi Mu’azzam da ya tsare Safeenar da idanu, har lokacin takardan na nan cikin hannunsa “Toh likita yace kar a dinga d’aga mata hankali.. High risk pregnancy ne da ita.. Matuk’a tana shiga damuwa komai ka iya faruwa..” Daga haka bata saurari mai zaice ba ta juya ta fice. Mu’azzam baice komai ba, kansa na duk’e har Mommy ta gama maganganunta. Tana ficewa ya taso daga kujeran da yake ya dawo kusan na Safeenah. Safeenah tana jin alamun dawowarsa kusan kujeranta, tsaban kewarsa da tai sai taji kaman ta rungumosa ta sanar dashi irin missing d’insa da tai.. Amma sai Tai k’ok’arin rik’e kanta sabida ta d’auki shawarin Mommy na cewa Ta nuna masa itama mace ce kuma tanada aji da matsayi musamman yanzu da zata bashi abunda babu wata mace da Ta tab’a basa wato D’an cikinta. Muryarsa ta sinkayo Wanda Ta jima bataji ba, muryar da duk duniya babu muryar da take jin dad’in sauraro sama dashi. “Why didn’t you tell me.. Maiyasa baki sanar dani tuntuni ba.?” Idanunta a lumshe still tana nan kishingid’e take fad’in “Ka damu ka sani ne.. Yanzu ma ba don ina cikin mawuyacin hali ba da bazan bari Mommy ta kiraka ba..” Muryarta ya soma rawa irinta mai kuka “Kayi neglecting d’inmu nida abinda ke cikina.. Baka damu kasan wani hali nake ciki ba.. Yanzu idan aka haifo D’an nan yaji ga abinda Dad d’insa yaiwa Mom d’insa lokacin da nake d’aukeda cikinsa kana tunanin yaron zai tab’a yafe maka ne..?” Ta bud’e idanunta masu zuban hawaye “Every single night cikin pain nake bacci sabida high risk pregnancy da nake d’auke dashi.. Dr ya bani bed rest ko toilet wasu lokutan bana iya zuwa sai Mommy ta taimaka mun.. Duk baka San wann wahalan da nake sha ba bayan cewa D’an nan ba nawa ni kad’ai bane harda kai.. And idan na haifesa har sai ka fini gadara dashi.. Sabida ku maza haka kuke.. Mace zata d’auki ciki na tsawon watanni tara.. Ta raini kayanta tayi enduring duk wani pain amma sabida son zuciya irin naku na maza ku amshe yaron nan ku rabasa da uwarsa yayi tashin maraici.” Ta gyara zamanta tana ci gaba da fad’in “Irin haka ne kake so ya faru da d’anmu..? Do you really want our child to grow up without a complete family... Do you really think your decision won’t affect our child..?!” Tinda Ta soma magana yake tattara naman goshinsa yana furzar da iska a hankali. D’agowa yai had’ida dakatar da ita da fad’in “Enough Safeenah.!” Tai Burki tana dubansa da idanunta masu zuban hawaye. Daga nan yanda yake zaune ya d’an rank’wafo hannayensa saman gwiwoyinsa yake jinjina kai yana fad’in “My child won’t grow up without a complete family in sha Allah.” Yana maganar yana jinjina kai alamun tabbatarwa. Wani irin sanyi Safeenah taji ya ratsa zuciyarta tana jira taji yace ya maidata d’akinta sai sinkayo muryarsa tai yana fad’in “Have you forgotten.. Inada mata, and I’m hundred percent sure zata kular mun da d’ah na ina raye ko bana raye..” Yaci gaba da jinjina kai still yana duban Safeenah wacce ta daskare tana dubansa “I’ll be a parent to my child.. Koda ban zama miji ga mahaifiyarsa ba.” Baikai aya ba ya hango Safeenah tana sauk’owa daga saman kujera cikin hawaye. Lokaci guda ta duk’a gabansa ta had’e hannayenta biyu waje guda alamun rok’o.. Girgiza kai ya shigayi yana furta “What are you doing Safeenah.. Please get up..” Bata tashin ba, taci gaba da hawaye tana fad’in “Nasan ni mai laifi ce.. Nasan nayi kurakurai da dama a baya.. But please kar ka bari kurakuraina ya shafi innocent soul d’in dake cikina... Ko banci darajan kasancewa ‘yaruwarta ba.. Naci darajan gudan jininka dake cikina.. Dan Allah kar ka bari D’anmu ya fito duniya ya tadda iyayensa basa tare.. Punish me all you want.. But please don’t punish our child..!” Ta k’arashe tana shafe cikinta still tana nan duk’e gabansa tana hawaye. Tinda yake a rayuwarsa bai tab’a jin tausayin Safeenah irin na yau ba.. Allah ya gani baya sonta matsayin mace face ‘yaruwa.. Allah shine shaidar shi yana ma Sadiya soyayyar da bazai iya had’ata da wata mace ba.. Yana tsoron yai rashin adalci a tsakaninsu Ubangijinsa ya tuhumesa.. Amma yau yaji tausayin Safeenah.. Irin tausayinta da bai tab’a ji ba.. Shin yanzu idan Sadiya ta gujeshi zaiji irin ciwon da Safeenah ke ji cikin zuciyarsa..? Tambayar da ya kuma kashe masa gwiwa lak’was. Cikin kwantar da murya yake fad’in “Safeenah.. Feenah.. Tashi ki zauna..” Girgiza masa kai tai still tana duk’e gabansa tana hawaye “No.. Sai kace ka maidani..” Ya furzar da huci kad’an yana shafe fuskarsa kafin ya duk’a nan gabanta suna fuskantar juna. Cikin yanayin kwantar da murya yake fad’in “Feenah ki nastu ki daina wann obsession d’in.. Ki tuna you are carrying a child in your womb now.. Abinda kikeyi can affect the child.. Look if you need a therapist zan nemo miki..” Katsesa tai da fad’in “Aw bayan obsession da kake fad’i yanzu kuma mahaukaciya ka d’aukeni.. Well idan akan soyayyarka ne kana iya kirana komai.. Har abinda yafi mahaukaciya.” Ya kuma furzar da huci kad’an yana mai duban wani b’angaren dan yanzu abin Safeenah ya daina basa mamaki, yafi danganta abin da rashin lafiya.. Idan bai bita a hankali ba za’a iya rasa abinda ke cikinta. “Ba mahaukaciya na d’aukeki ba.. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Idan na dawo zamuyi magana a natse. Kinga Dr yace high risk pregnancy kike d’auke dashi.. And shiga damuwa ko tashin hankali won’t do any good for the Baby.. Kuma kema Nasan baki son abinda zai samu Babyn right.?” Yanda yake maganar tamkar mai lallashin k’aramin yaro maras cikakken hankali haka yake mata. Ta saki murmushi a hankali tana jinjina masa kai hannunta guda dafe da cikin nata. Murmushi ya sakar mata shima kafin yace “Good.. Yanzu ki kwanta ki huta.. And idan kina son wani just tell me right away kinji koh..” Ta jinjina masa kai a hankali kafin tace “Idan ka tafi zaka dawo ka dubamu..?I mean nida Babynmu..” Tana maganar tana shafa cikinta murmushi gauraye da hawaye saman fuskarta. Jinjina mata kai yai yace “Of course zan dawo.. Just get some rest now kinji koh..” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye ya isa ya gyara mata pillow da tai matashi dashi yace “Zo ki kwanta ki huta..” Ta mike tana murmushi ta iso ta zauna a kujeran. Ya sakar mata murmushi kad’an kafin yace “I’ll be goin now..” Ta sakar masa murmushi tace “Ka sayo min roasted corn.” Ya jinjina kai yace “Akwai wani abinda kike so kuma.?” Ta girgiza kai kad’an “No gasashiyar masarar yayi.” Ya jinjina kai kafin ya sakar mata murmushi kad’an ya fice zuciyarsa fal tausayinta. Safeenah tabi bayansa da kallo tana murmushi “Sannu a hankali Mu’azzam.. Zaka mai dani gidana kafin na haife abinda ke cikina..” Ta k’arashe zancen zucin nata tana mai gyara kwanciyar ta. Mommy dake lab’e taji dik yanda sukai. Murmushi ta saki kafin ta furta a fili “Greatest weakness d’inka shine wann cikin Mu’azzam.. Na maka alk’awari ni kuma sai nayi amfani da wann cikin na tarwatsa ka.. Ba’a cin bashi na a wanye lafiya ni Hajara.!” Tana ida fad’in haka ta juya ta bar wajen. Tana shiga d’aki ta tadda wayarta na ruri. Lamba ce Babu suna.. Ta yatsina fuska kafin ta d’aga kiran tana fad’in “Hello hello wake magana.. Hello ba service.. Wrong number... Shuuuuuu..!” Mommy tace tana Yawo da wayar a iska. Muryar Shemau ta sinkayo daga d’aya b’angaren tana fad’in “Kar ki kuskura Hajara..!” Mommy tai tsaye tana sauraronta yayinda Shemau taci gaba da fad’in “Wllhi idan kika kashe mun waya yau kam sai na tona miki asiri. Na Sani sarai mijinki na nan Fufore yazo duba matarsa.. Yau kusan sati kenan Ina kiranki da different lines kina raina mun hankali, da kin d’aga ki wani fara hello hello ba network.. Toh ko uban Network ne Babu yau kam kika katse mun waya wllhi sai na kwance miki zani a kasuwa. Naji labarin Alhaji Marwan Gamji na gari tin shekaran jiya.. I can go straight to him na sanar dashi komai duk abinda kika aikata wa matarsa.” Mommy tai ‘yar bazawarar dariya kafin tace “Shemau kenan.. Yo ce maki akai barazanarki zai bani tsoro.. Ince atata kice mun had’a baki nida ke mun d’auko wa Nuratu mai gani na bogi..” Ta mik’e tsaye tana zagaye d’akin, still waya manne kunnenta. Muguwar murmushi saman fuskarta take fad’in “Barin tambayeki Shemau, tsakanin ni da ke wacece Kyallu ta sani..?” Shemau tai shiru batace komai ba jin Mommy zata juya teburin zuwa kanta. Mommy tai murmushin cin nasara kafin taci gaba da fad’in “Ko nuna ni akaima Kyallu nayi imani bata sanni ba, bata tab’a gani na ba.. Wa ta sani..? Wacece Ta d’auko ta matsayin mai magani..? Kece Shemau.. Ke kikai kid’anki kuma kikai rawarki.. Ke da kanki zaki kama kanki.. Kuma na miki imani da Allah yanda yanzu baki tareda Salman Gamji tsaf Mu’azzam zai turaku kurkuku ne keda Kyallu..” Ta murmusa kad’an kafin tace “Kin zata bani da hankali ne..? Kin zata ni shahshasha ce.. Shemau nasan yanda nake buga wasanni na.. Ce miki akai bansan amfani kike so kiyi dani ba.? Nasan dole Kema akwai abinda kike nema wajena Watak’ila nan gaba kad’an ki bijiro min da abinda kike nema shisa kike taimakona.. Toh ni ba mahaukaciya bace Shemau.. Nasan sarai mai nakeyi.. Bakida wata dalili ko hujja akaina.. Idan kuwa kikai gangancin sanar da Marwan Gamji kin d’auko wa matarsa ‘Yar damfara matsayin mai magani ba ke kad’ai ba harta mijinki sai Mu’azzam ya bincika.. Kinga kuwa a banza Salman zai kuma tsananki..” Shemau ta saki baki da hanci tana jin tuggun da Mommy ke fad’i, Wato ashe itace babban Shashahsha da tai komai ita kad’ai ba tareda tayi involving Mommy ba tinda Mommy tana Abuja ne.. Ita dai Shemaun ita ake aike. Cikin tsananin k’unan rai Shemau ke fad’in “Amma Hajara Bakida kirki.. Bakida imani.. Juya min baya zakiyi..?” Mommy ta dara tace “Iya ruwa ke fidda kai.. Kowa ya biya allonsa sai ya wanke.” “Ban gama dake ba Hajara. Akwai last card d’ina da zanyi amfani dashi akanki.. ‘Yarki Safeenah..!” Mommy ta tsaya Cak tana sauraron Shemau. Yayinda Shemaun taci gaba da fad’in “Zan tona mata asiri wajen Mu’azzam cewa itace Ta bani umarni na kawo wa matarsa Sadiya kwarto.” Katseta Mommy tai cikin k’yalk’yalewa da dariya “Amma kin tabbata shashasha Shemau. Yo a d’akin waye aka kama Kwarto. D’akin Mijinki ne ko kuwa D’akin matar Mu’azzam.?” Shiru Shemau bata bata amsa ba sai hawaye dake k’ok’arin ciko idanunta. Mommy ta kuma murmusawa kafin tace “Bakida wata hujja akanmu daga ni har ‘yata.. Babu wanda zai yarda dake Shemau b’ata ma kanki lokaci kawai kike..” Ta kuma murmusawa kafin tace “Sai ki tattari k’wararen da aka kawoki dasu maza a koma ruga.. Dan idan ban mance ba da k’waraye uku kawai aka kawoki, na wayar dake na gogar dake na nuna miki duniya shine bari ki min tijara har ni kike ma barazana.. Go ahead Shemau.. Kije ki fad’a ma duk wanda zaki fad’i kiga ko akwai mai yarda dake..” Daga haka D’if Mommy ta kashe wayar. Aka bar Shemau rik’e da waya tana jinjina lamarin duniya. Wato duk tarayyar da ba’a ginata dan Allah ba da tsiya take watsewa.. Wasu irin k’walla ne na nadama Shemau taji suna ciko idanunta.. Shin dama ita rayuwar duniya haka take..? Shin dama da gaske ne hausar nan da ake cewa idan ka so wa mutane alkhairi kaima ka tsammaci alkhairi a matsayin tukwicin duniya.. Haka idan Kaso wa mutane sharri kaima sai ka tsammaci sharri a matsayin tukwicin duniya.. Bata ida tunanin nata na ta sinkayo muryar mijin Boddo daga parlor yana ci gaba da sababi “Ni gaskiya ta fice ta bar mun gida.. Ba yanda za’a yi matar nan ta k’ara kwana a gidan nan.. Wllhi kinji na rantse miki idan baki sallami bak’uwarki a gidan nan ba zan had’a harda ke na sallameku dan ni babu masauk’inta a gidana.. Matar da labari ya gama karad’e gari cewa maza take kaiwa cikin gidan mijinta.. Ke barin fad’a miki.. Daga yau.. Daga rana mai kamar ta yau na yanke alak’arki da ita.. Babu ita Babu ke kinji na fad’a miki.” Boddo ta marairaice fuska tace “Haba Abban Huzaifa Shemau batada majingini ne dan Allah ka tausaya mata.. Wllhi akasi aka samu amma ba halinta bane biye biyen maza.. Ni zanyi wann shaidar.” Banda uwar harara baya aikata mata komai “Wann kuma matsalarku ce can abinda naji a gari dashi zanyi amfani. Ko mutuwa kai shaidar da aka maka shi zai bika dan haka wann watsattsiyar batada masauk’i gidana.. Toh ma Wai batada iyaye ne.. Ubanta ne ni da za’a koreta Ta kwaso k’afa tazo mun gida.. Ki fice a idanuna fah Boddo..” Ya k’arashe yana nunata da yatsa. Boddo ya sauk’e ajiyan zuciya Ta mik’e Jiki babu k’wari. Shemau dake rakub’e d’aki tana sauraron tattaunawar mijin Boddo da Boddon sai taji wasu k’wallan na kuma ciko idanunta “Na shiga uku ni Shemau Ina zan saka kaina..!” Ta k’arashe tana d’aura hannayenta biyu aka. A haka Boddo ta shigo ta taddata. Shemau na hawaye take fad’in “Baddo naji komai. Kuma wllhi nasan Kinyi iya k’ok’arinki.. Na gode matuk’a K’awata... Zan tafi dan bazanso Kema na lalata miki naki auren ba.. Kaman yanda na lalata nawa..” Boddo ta k’araso ta dafa Shemau tace “Kiyi hak’uri Shemau wllhi babu yanda na iya ne.. Tinda Abban Huzaifa yace haka nasan bazai kuma sauk’owa ba.. Amma da ace zaiyi hak’uri ya barki ki zauna a nan wllhi da bazan bari ki tafi ba.. Kiyi hak’uri k’awata.” Rungumeta Shemau tai tana kuka tana girgiza kai “Dole na tafi Boddo dan kar Kema na jaza miki.. Abinda na shuka ne Tabbas nake girba.. Duniya makaranta ce dama.. Yau ta kuma biya mun wani karatu.. Mutanen da nayi tarayya dasu wajen aikata muggan laifuka duk sun juya mun baya.. Sun barni a rana tsaka babu rumfa babu majingini.. Ga Salman har umarni yai ma securities na Companyn su cewa ko mai kamannina suka sake gani k’ofar wajen Su koreta..” Ta saka bayan hannunta tana goge hawayenta kafin taci gaba da jinjina kai tana fad’in “Banida zab’i da ya wuce na koma ruga can wajen su Inna Fini da Baffah.. Boddo zan koma rayuwar da na baro a baya.. Rayuwar da Allah ya cireni a ciki ni kuma nayi butulci... Na butulce wa Rahamar Ubangijina... Bani da zab’i da ya wuce na fuskanci wann rayuwar a halin yanzu..” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka. Tausayinta ya cika Boddo. Tabbas Shemau ta bata tausayi dukda cewa kuskure Ta riga da Ta tapka.. Tana rok’on Allah yasa wann karatu da duniya ta biya mata ya shiga kanta.. Sann masu d’abi’a irin na Shemau su hankalta su gane.. Boddo Ta k’arasa Ta d’auki ‘yar jakanta Ta ciro ‘yan kud’ad’e riban Kunun ayanta Ta bawa Shemau tace tai kud’in mota.. Harda ‘yan tufafi Ta had’awa Shemau. Shemau na hawaye Boddo na hawaye haka sukai sallama. Rayuwa kenan. Idan Allah yayi maka baiwa da wani rahama toh ka gode masa sai ya k’ara maka da wani.. Idan ka zab’i butulce masa Toh ka sani shine mai jujjuya al’amara a lokacin da yaso.. Cikin k’ank’anin lokaci zai canza labarin rayuwarka ka koma tamkar baka tab’a jin wann dad’in ba. Ka ribaci abu uku a GIDAN ARO kafin a amsheta daga wajenka. Ka ribaci lafiya tun kafin rashin lafiya ya sameka, ka ribaci K’uruciya tun kafin tsufa ya taddaka, ka ribaci rayuwa kafin mutuwa ya taddaka.. Allah kasa mu dace duniya da lahira Ameen.! ** Zaune suke su biyu shida Assad a parlorn laptop aje gabansu suna gudanar da bincike. Kana ganinsa zaka fahimci gaba d’aya ma hankalinsa bayaga abinda suke. Har Sadiya tai sallama ta aje masu ruwan shayi bai kula da hakan ba.. Yadai ki gaisuwan da suke itada Assad har Assad na jefo mata ‘yan zolaya. Ita kanta Sadiyar ta kula yau d’in mijin nata ba k’alau yake ba. Ta k’agu su keb’e taji meke damunsa. Bayan Ta koma ciki Assad ya dubesa cikeda kulawa, ya d’an gyara zamansa kafin yace “Wai har yanzu tunanin abin kake ne..?” Mu’azzam ya furzar da huci kad’an yace “Assad it’s Safeenah we are talking about... She’s not mentally stable sann ga gudan jinina a cikinta.. Ta yaya abin bazai dameni ba..” Assad ya d’an murmusa kad’an kafin yace “Tanada hankalinta sann Tana son D’anta, bazata yi abinda cikin zai sami wani matsala ba..Ko mahaukaci yasan abinda yake nasa Mu’azzam..” Ya d’an girgiza kai kad’an yace “Kana magana kaman bakasan wacece Safeenah ba.” Assa ya d’an Ka kwantar da hankalinka in sha Allah babu abinda zai sami D’anka... Toh amma ni a nawa tunanin mai zai hana ka maida Safeenah tunda gashi har rabo ya tsaga..” D’an duban Assad yai kad’an ba tareda yace komai ba. Ya kuma d’aura hab’arsa saman hannayensa da ya dunk’ule waje guda “I’m still not sure idan Safeenah tanada gurbi cikin rayuwa na.. Amma abinda na sani shine D’ah na ko ‘Yata bazan bari su girma gaban wani ba ni ba matuk’a Ina raye.” Assad ya d’anyi jim sai kuma yace “Ko wane d’ah zaiso ya girma tareda iyayensa guda biyu musamman idan dukansu suna raye.. But unfortunately wasu lokutan akan dole iyaye suke rabuwa. Kaman yanda na rabu da Hanifa.. And hakan affects the children..” Ya k’arashe murya a hankali. Mu’azzam ya dubesa kad’an sai kuma ya jinjina kai yace “Haka rayuwa ta gada.. Unfortunately we don’t choose our Destiny.” Ya k’arashe yana kurb’an shayin da Sadiya ta aje masu. Assad ya jinjina kai yana furta “Haka ne, Allah yasa mu dace..” Ya k’arashe yana mai janyo computer d’in lokaci guda yana danna keyboard d’in alamun yana typing. Black African Team shine kalaman da ya rubuta ya kuma danna search. Jim kad’an results suka bayyana masa. A tsanake ya dinga bi d’aya bayan d’aya yana karantawa yayinda Mu’azzam ya b’ace duniyar tunani kaman bashi a wajen. Tinanin juna biyu da Safeenah ke d’auke dashi sam ya hanasa sukuni.. Gani yake kaman Safeenah bazata iya kula da cikin jikinta ba, dan bata kula da kanta ba balle abinda ke cikinta. Tinda yasan wacece Safeenah da kuma kalar haukarta. Muryar Assad ya sinkayo yana fad’in “Look.. Duba nan kaga.” Mu’azzam yai saurin karkatowa yana duban abinda Assad ke nuna masa. A tare suka soma karanta shafin da Assad d’in ya bud’e. Black African Team wata K’ungiya ce da shekarun baya suke fataucin mutane daga nahiyoyin Africa wato k’asashen bak’ak’en fata zuwa Nahiyar turai. Tun a wad’ancan shekarun akayi nasaran murk’ushe wann K’ungiyar a port na jirgin ruwa dake can jihar Lagos. Black African Team sukan d’auki mutane daga Nahiyoyin Africa sai su yaudaresu da cewa da anje Turai za’a sama masu rayuwa mai inganci sann zasu samu Dukiya da abunyi.. Alhali kuwa ba haka bane. Idan an kwashesu daga nan zuwa Turai tamkar bayi haka ake maidasu. Za’a basu wahala wasu ma a sayar da sassan jikinsu masu amfani irinsu K’oda da sauransu. Idan akwai ‘yanmata kyawawa sai a tilasta masu yin Karuwanci na dole domin su sama ma iyayen gidansu kud’i.. A tak’aice dai Wann K’ungiyar Human Trafficking Syndicate ne Wato K’ungiyar ‘yantadda ne da suke fataucin mutane a wancan lokacin kafin ayi nasaran murk’ushesu. A tare Assad da Mu’azzam suka dubi juna bayan sun gama karancewa. Assad ya girgiza kai yace “Human Trafficking Syndicate ne..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Kenan Danger nada alak’a da wann Syndicate d’in.” Assad ya d’anyi jim yace “Zai iya yuwa.. But shekarun sunada yawa, how’s this possible..?” Mu’azzam yai shiru kaman mai nazari sai kuma yace “Maiyasa na samu shaidar wann Syndicate d’in cikin kayan mahaifina..?” Yai maganar fuskarsa fal damuwa kafin ya kuma duban Assad yace “Babu abinda ya had’a mahaifina da wann Syndicate d’in right Assad.?” Yanda Yai maganar dole ya baka tausayi. Assad ya jinjina kai yace “Don’t think like that Mu’azzam.. Babu abinda ya had’a Mahaifinka da wann Syndicate d’in..” Ya katse Assad da fad’in “Toh Maiyasa na sami shaidar k’ungiyar cikin kayansa.. And why does it seem ahalina su Danger suke bibiya.. Maiyasa zasu kashe Ikram bayan sunyi kidnapping d’inta basu nemi Ransom ba.. Assad Wai meke faruwa ne.. I’m lost Assad.. I don’t know what to think anymore.. What is all this..?” Ya k’arashe cikin tsananin damuwa. Assad ya d’an Dafasa kad’an yace “Kar damu Mu’azzam.. Zamu samo duka amsoshinmu sannu a hankali..” Muryar Mu’azzam ya sinkayo yana fad’in “I need to catch Danger once and for all.. Yanada tambayoyi da dama da zai amsa min.” SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *61* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Sallama sukai da Assad bayan sun sami matsayar yanda zasu b’ullowa Al’amarin. Bayan Assad ya fice komawa yai cikin kujera yana jingina kansa tunanin wann Syndicate d’in bai k’yalesa ba wanda. Ba komai yafi tsaya masa a rai ba kaman shaidar K’ungiyar da ya samu cikin kayan mahaifinsa.. ‘What if mahaifinsa nada wata alak’a ne da wann K’ungiyar.?’ Cikin sauri ya shiga girgiza kai yana mai k’aryata zuciyarsa. Mahaifinsa bazai tab’a samun wata alak’a da wann K’ungiyar ‘Yantaddan ba. Yafi k’arfafa zaton Su Danger dai Sun jima suna bibiyan ahalinsa ne. A b’angare guda kuwa ga tinanin juna biyu da Safeenah ke d’auke dashi ya kasa barinsa. Jiki babu wani kuzari ya mik’e ya kashe duk wani abinda ya danganci wutan lantarki dake parlorn kafin ya nufi upstairs. Kai tsaye d’akinta ya nufa. Ya hangeta tsaye gaban dressing mirror d’aure da towel alamun fitowarta kenan daga wanka, hair dryer rik’e hannunta tana aikin busar da sumarta. Sautin k’arar dryer d’in ya hanata sauraron shigowarsa. Yaci gaba da takowa a hankali har ya isa ya d’aura hannunsa saman dryer d’in. Ta juyo tana murmushi tana dubansa. Shid’inma kasaltacciyar murmushin ne saman fuskarsa. Babu musu Ta sakar masa dryer d’in ya amsa cikin hannunsa, a nata zaton taimaka mata zai ya busar mata da sumar amma Sai gani tai ya kashe ya ajiye gefe. Ta baya ya rungumota yana shak’an k’amshin shower jell da shampoo da tai amfani dasu, idanunsa a lumshe yake fad’in “Why didn’t you wait for me bayan Kinsan tare muke shirin bacci.. And Meye ma na wahalan busar da suma bayan yanzu zaki sake jik’a shi..” Ta gane mai yake nufi, tuni ta marairaice masa tana fad’in “Kai Mr Inspector yau fah akwai sanyi anyi ruwan sama fah.. Nidai sanyi nakeji..” Ya d’an kuma shigar da ita jikinsa kad’an, fuskarsa saman wuyanta idanunsa a lumshe yake fad’in “Yeah I know.. Shiyasa nake so nai warming naki ..” Yana maganar yana rikitata da salon k’aunarsa. K’ok’arin zillewa take kaman zata sakar masa kuka take fad’in “Nak’i wayon..” Amma sai taji ya fuzgota sun fad’a saman gado, yai mata rumfa suna duban juna. Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yake fad’in “It’s been a while since I heard you call me Mr Inspector.. You know a bakinki kawai nake jin sunan nan ya mun dad’i..” Ta murmusa kad’an tana fad’in “Who would’ve ever thought That Tyrant Mr Inspector zai zama wann Prince Charming d’in da yayi rescuing Princess d’insa..” Tana maganar cikin dabaran zillewa daga jikinsa saiji tai ya mirginota Ta dawo samansa, ya saka hannayensa ya tallafi bayanta, still su duka biyun suna fuskantar juna. Saida suka kwashi d’an lokaci a haka yana dubanta cikeda kulawa, d’an Sauran ruwan dake cikin sumarta ya d’igo zuwa nasa goshin, ya lumshe idanunsa a hankali kafin ya furta “I love you.” Ya k’arashe yana mai ware idanun nasa a fuskarta. Yanda yai maganar ya tabbatar mata tin daga zuciyarsa ya furta hakan ba wai a fatar baki bane kawai. K’wayar idanunsa da sautin fitar kalmar sun tabbatar da haka. Ta murmusa kad’an tana share masa ruwan cikin sumarta da ya d’igo saman fuskarta da yatsarta guda “I know.. And I love you too.” Ya kafeta da idanu sosai kafin yace “Don’t ever leave me.!” Wann karon ma da gani kasan zuciyarsa ne ke furta hakan. Tai masa K’uri tana dubansa kafin tace “I won’t leave you.. I’ll never leave you.. Zan rayu dakai kuma zan mutu da kai.” Dubanta yake ba tareda yace komai ba cikin shauk’in k’aunarta, a hankali ya janyota ya had’e bakunansu waje guda.. Sunyi nisa sosai cikin wata duniya da basu gani kowa face su biyun wayar Mu’azzam dake gefensu ta soma ruri. Da k’yar ya iya mik’a hannunsa ya janyo wayar. Safeenah ce mai kira. Babu shiri ya mik’e zaune yana k’ara wayar a kunnensa. Shafa kansa yai kad’an yace “Ina Musaddiq..? Ba kowa a gidan ne..?” Ya d’anyi jim alamun yana sauraro daga d’aya b’angaren. Jiki babu kuzari ya mik’e ya soma had’a botiran rigarsa still wayar manne kunnensa yana fad’in “Ya isa haka, gani nan tahowa.. Kar ki kuskura kice zakiyi driving.. Gani nan zuwa..” Ya k’arashe yana duban Sadiya data tsaresa da idanu alamun bata gane meke faruwa ba. Peck ya manna mata a gefen kumatu yana mai matsar da bakinsa saitin kunnenta, cikin sigan rad’a ya furta “Wait for me right here kinji koh.” Yai maganar murya a dashe. Ya mik’e yana duba agogon dake d’aure hannunsa ya nuna 10:30pm. Lokaci guda yake furta “Safeenah needs me now.. Zamuyi magana idan na dawo kinji koh.” Bata iya amsa sa ba sai nanata abinda yace cikin zuciyarta take. Wai Safeenah ke buk’atarsa.. A cikin daren nan.? toh meke faruwa kenan.? Ji tai jikinta yayi mugun sanyi. A hankali ta kuma nitsewa cikin gadon tana janyo bargo Ta rufa akanta. Har lokacin zuciyarta bai daina tsinkewa ba. Safeenah tana buk’atarsa cikin daren nan? Abinda fah ya fad’a mata kenan.. Sai nanata kalmar take cikin zuciyarta . Ta lumshe idanunta a hankali tana k’ok’arin nitsa zuciyarta. Har lokacin ta Kasa ficewa daga cikin gadon. ** Yana isowa gidan ya tadda Safeenah ita kad’ai a parlor sai kuka take tana fad’in mararta da bayanta ciwo suke mata. Aiko tana ganin Mu’azzam ta kuma fashewa da wani irin kuka tana ciza labb’anta. Sai yarfe hannu take alamun tana jin jiki. Ya k’araso cikin sauri ganin ita kad’aice a parlorn. Ya duk’o cikeda kulawa yana dubanta “Tun yaushe ne Bakida lafiya.. Kuma duk gidan nan a rasa mai kaiki asibiti.?” Cikin yanayi na kuka take fad’in “Musaddiq Bai dawo gida ba.. Ba driver ko d’aya dake kwana a gidan nan yanzu. Meema kuma tun last week ta tafi sch a hostel take zama. (Meema ta samu gurbin karatu a Nile University dake birnin tarayya). Safeenah taci gaba da kuka tana fad’in “And Mommy yanzu bata iya tuk’i musamman da dare.. Kuma Mommyn da Kiki duk sunyi bacci.. Ni kad’ai aka bari a nan, na tashi zan tafi d’aki naci marata da bayana sun rik’e ko tafiya bazan iya ba.” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya. Ya d’an girgiza kansa kad’an yace “Tashi muje.. Zaki iya tashi..?” Ta kuma fashe masa da kuka tana girgiza kai lokaci guda take furta “Bazan iya tashi ba.. Ciwo yake mun..” D’an sunkuyowa yai yana k’ok’arin kai hannunsa jikinta, sai kuma yaji tana kuma sakin k’ara babu shiri ya tallafota yana fad’in suje. Safeenah ta Kasa tafiya sai Sabon kukan da ta sakar masa tana kuma d’ingile k’afarta alamun bazata iya tafiya ba. D’aukanta yai cak ya nufo downstairs da ita. Bai wata wata ba ya sakata a mota yana mata sannu ganin yanda taketa ciza baki tana dafe bayanta da cikinta. Asibitin da Ta soma ganin Dr tai masa umarni suje.. Suna zuwa kaw Dr d’in yai attending nasu.. Ya duba Safeenah ya bata magunguna.. Mu’azzam ya tambayi ko Babyn na lafiya.. Dr yace yana lafiya amma a dinga kulawa, dama dole zata dinga jin irin wad’ann pains d’in lokaci zuwa lokaci musamman dake cikin k’arami ne ga kuma yanayin da yazo dashi na had’arin ficewa ko wani lokaci.. Abu k’ank’ani zai iya sa cikin ya salwanta.. Saidai a dinga kula. Mu’azzam yai masa godiya yana jinjina kai ”Za’a kula in sha Allah Dr..” Sukai masabaha had’ida sallama, Mu’azzam yai masa godiya. Da k’yar Safeenah ta mik’e tana jan k’afarta, Mu’azzam na biye da ita dan gani yake kaman zata iya fad’uwa k’asa tsaban yanda take taka k’afarta da k’yar. A haka suka isa mota, Safeenah sai raki take tana kuma narke masa. Suna tafe saman kwalta sukazo Shige DownTown Take away. Safeenah tace Shawarma take son ci. Parking yai yana tambayarta ko akwai abinda take so bayan Shawarma. Ta girgiza masa kai kad’an alamun a’a. Wallet d’insa kurum ya d’auka ya fice, ya mance wayarsa nan cikin motar. Safeenah ta dubi wayar tana tab’e baki kad’an, hannunta Takai saman wayar ta d’an Shafa hasken wayar ya bayyana. Ta murmusa cikeda jin dad’in yanda time ya tafi, har kusan k’arfe 12:30pm. Bata janye idanunta daga barin duban wayar ba taji wayar na vibrating. Ta duba mai kira taga an rubuta _Beautiful_ Dogon tsaki Safeenah taja dan tasan shegiyar can ce mai kira. Katse kiran tai. Nan kiran ya kuma shigowa Safeenah ta kuma katsewa tana murmushi take furta “Wann lokaci na ne yarinya.. Sai lokacin da naga dama ya koma miki.. Yanzu ne zakiyi danasanin shiga tsakanina da My Halal har kiyi gangancin baje Koli a Gidana.” Ta murmusa kafin Ta jefa wayar nasa k’asan seat yanda zai kaman wayar ta fad’a wajen bai sani bane. Ta hangosa yana rik’e da takeaway d’in. Nan ta kuma shigewa cikin kujera tana lumshe idanunta kaman mai bacci. Duba d’aya Mu’azzam yai mata ya janye idanunsa, sai kuma ya k’ara dubanta yaga kaman bacci take gashi ta tak’ura cikin seat d’in.. D’an rank’wafowa yai yana k’ok’arin kwantar mata da kujeran dan taji dad’in kishingid’an nata.. Safeenah tana jin ya rank’wafo Sai ta fad’o jikinsa da gangan kaman batasan tayi hakan ba. Ya tsaya cak ya daina abinda yake k’ok’arin yi.. Cikin dabara ya janye Safeenah daga jikinsa kafin ya kwantar mata da kujeran. A hankali ya daidaita nasa zaman cikin kujeransa kafin ya soma driving. Cikin Zuciyar Safeenah fal annashuwa, ta kula yanda yake driving d’in ma cikeda kulawa ne dan kar wani abu ya samu Babynsu. A haka har suka iso gida. Ya d’an bubbuga kujeran da take zaune bisa “Feenah wake up now.. We are here.” Ta bud’e idanunta da k’yar kaman mai baccin gaske. Ta yunk’ura Zata tashi ta d’an saki k’ara kad’an tana fad’in “My back still hurts..” Sannu ya dinga mata yana fad’in ta k’ok’arta ta fito. Haka Safeenah ta fito daga cikin motar kaman mai koyon tafiya. Mu’azzam ya rik’o sauran tarkacan, danginsu maganinta da takeaway d’in. Iya dake jiransu dan sanda zasu fice sun had’u da ita Mu’azzam d’in ya sanar da ita zai kai Safeenah asibiti. Nan take masu sannu da dawowa tana tambayar jikin Safeenah. Har d’aki Mu’azzam ya rakata, ya d’auko ruwa ya bata maganin yace tasha. Babu musu Ta amsa tasha tana kuma narke masa. Saida ya tabbata tasha maganin kafin ya mik’e yana zira hannayensa cikin aljihun jeans d’insa. D’an shafa aljihun yai yana duba wayarsa yaji bata nan. Nan yai tunanin k’ila a mota ya barta. Safeenah na hankalce dashi Ta fahimci wayarsa yake nema. Ta marairaice fuska tana fad’in “Yanzu tafiya zakayi..?” Ya d’an dubeta sai kuma yace “Is there something you need..?” Tai rau rau da idanu tace “Yanzu idan naji ciwo cikin dare fah..? You heard what the Dr said ai.” Cikin shagwab’a take maganar. D’an shafa fuskarsa yai yana fuzar da fuci kad’an “Feenah bazai yuwu kiyi amfani da cikin jikinki ki zaunar dani a nan ba.. Kar wann tunanin ya shiga kanki kin fahimta.” Ya k’arashe yana d’an bud’e idanunsa. Cikin yanayi mai ban tausai ta jinjina kai tace “Na Sani.. I know my place.. You don’t need to remind me.. Nima dan Ina cikin ciwo ne shiyasa na kiraka kuma dan babu wanda zan kira ne..” Ta k’arashe kaman zata saki kuka. Ya d’an furzar da huci kad’an yace “Ki kwanta ki huta haka nan.. Ni zan wuce.. Allah ya baki lafiya.. And please ki kula..” A hankali ta jinjina masa kai tana mai binsa da kallo har ya fice.. Ji tai kaman ta nufesa a guje ta rungume bayansa sabida tsananin kewar kasancewa tare dashi da tai. Ta lumshe idanunta hawaye masu zafi suka gangaro mata. Shiko Mu’azzam agogon dake manne Parlorn k’asa yake duba har kusan k’arfe 12:am Wato shabiyu na dare. Duban Iya dake rakub’e gefe yai tana gyangyad’awa alamun fitowarsa take jira. Mu’azzam yai mata sallama cikeda kulawa kafin ya fice. Mommy tana jin fitarsa ta mik’e ta nufi d’akin Safeenah. ** A b’angaren Sadiya kaw katse kiranta da yai har sau biyu shine babban abinda yafi d’aga mata hankali gashi har shabiyun dare ta gauta bai dawo ba. Wasu irin k’walla ne taji suna ciko idanunta. Maike shirin faruwa da ita da aurenta..? Tambayar da ya tsaya mata kenan a zuciyarta wanda yasa tuni taji k’walla sun ciko idanunta. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *62* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ta jima sosai zaune a parlorn ko zataji zuwansa amma shiru bai K’araso ba. Jiki a sanyaye ta koma d’aki tai zaune bakin gado had’ida rapka uban tagumi. Wata zuciya tana tuhumarta ‘Kika sani ko ya maida auren Safeenah ne..? Toh amma Maiyasa zaiyi rejecting call d’inta.?’ Tai saurin lumshe idanunta tana San yakice tunanin koma menene cikin zuciyarta. Tashi tai ta d’auro alwala tai sallah raka’a biyu tana addu’an Allah ya sassauta ma zuciyarta. Duk k’alubalen da jarabawa da zata fuskanta a gidan aurenta Allah ya bata juriya da hak’urin cinye wann jarabawar. Tinda aure dama ibada ne. Kuma dik abinda akace ibada ne Toh kuwa dole a fuskanci k’alubale cikinsa. Ta ida addu’o’inta ta mik’e ta haye Gado idanunta kan agogo tana sauraren ko zataji an bud’e gate. Can taji shigowarsa, maimakon ta mik’e ta nufo parlor sai ta kuma nitsewa cikin gado tana jin wasu hawayen suna zuwa mata. Ita ba jimawan da yai a waje bane damuwarta, abinda bai tab’a yi ba shine katse kiranta.. Kuma har sau biyu ya katse balle tace kuskure ne, gashi bai kuma kiranta back ba.. Wann abin duk yafi sanyar mata da jiki. Tai lamo cikin Gadon tana jiran taji shigowarsa. Ya turo k’ofan d’ankin nata a hankali, nan ya hangeta kwance saman gado. A nasa tunanin bacci take sai bai shiga d’akin ba Bai tasheta ba ya wuce nasa d’akin. Sadiya kaw tana jin ya juya bai shigo ba taji kuka na zuwa mata gadan gadan, tana jin sanda ya bud’e d’akinsa ya shige. A yanda tasan shi ko bacci tai a nata d’akin baya tab’a yarda su raba shimfid’a, koda ace bacci ya d’auketa a d’akinta wasu lokutan farkawa take ta tsinci kanta a nasa d’akin ya sureta ya kaita can, wasu lokutan kuma shima kwanciyar yake a nata d’akin ta kula baya tab’a yarda suyi bacci ba cikin jikin juna ba.. Itama d’in zata iya cewa ta riga ta saba da hakan bacci cikin jikin mijinta, ya sabar mata da hakan yabi jikinta..Ta kuma jin wani rauni na taso mata can k’asar zuciyarta. Yanzu idan Safeenah ta dawo dole komai rabawa zasuyi.. Wai dama haka kishi yake.. Haka matan da mazajensu sukeji idan mazan suka kuma kawo wata mace.. Lallai duk macen da mijinta ya k’aro mata aure ta kumayi tawakkali ta amshi k’addararta a yanda yazo mata wann matar ta cika a kirata jarumar mata.. Kuma ta cika a nad’a mata Kambi na sarautar mata.. Tabbas zuciya rauni ne da ita mai juriya da tsoron Allah ne kawai Zata iya jure wann rad’ad’i na kishin.. Allah ka iyar mana abinda bazamu iya ba ka bamu abokan zama na k’warai idan ka k’addara hakan a garemu. Ta kuma lumshe idanunta a hankali siraran hawaye suka gangaro mata. Mu’azzam kaw koda ya shigo ya hangeta tana bacci sai bai tasheta ba dan dama ba kwanciya zaiyi ba, research yake so ya d’an gudanar kan K’ungiya masu safaran mutane da yaci karo dashi cikin bincikensa. Dan haka tuni ya bud’e computer d’insa bayan ya ida shirinsa na bacci ya shiga bincike yana duba ko zai sami wani abu da zai nuna cewa an capke ‘yanta’addan a wancan lokacin maybe suna wani prison serving their sentences. Saidai duk iyakan binciken da zai bai samu labari mai kama da hakan ba.. Bacci b’arawo ne yai gaba da shi nan wajen. ** A can b’angaren Safeenah kaw koda Mommy ta shigo ta taddata kafeta da idanu tai tana fad’in “Kar ki raina mun hankali Safeenah. Na Sani k’alau kike salon makirci ne kawai ya sanyaki kiran Mu’azzam...” Safeenah Ta turo baki tace “Toh Mommy ya zanyi Ina son kasancewa da Uban D’a na.. Sai na zuba ido yana can yana cin soyayyarsa ni an barni da dakon yaro cikin jikina.. Mommy meye laifina Dan naso kasancewa da Uban d’a na..” Mommy tace “Ke tafi can ki rufe mun baki.. Toh a haka ne zaki samu kulawarsa.? Aima saidai ki hau masa kai har kisa yaji baya marmarin cikin naki.. Ke barin Fad’a miki da wann hanyar da kika d’auko sam ba mai b’ullewa bace, bazaki samu kansa ba a haka.” Safeenah tace “Tab ai wllhi Mommy yanzu na fara babu gudu babu jada baya sai na k’wato abinda yake nawa ne.. Kuma wann D’an cikin nawa shi zai taimaka min mu yak’i wancan shu’umar mu k’wato Babansa daga wajenta.. Idan kuma nai duk abinda zanyi bai working ba sai na sanar da Inne da Daddy nasan matuk’a suka San inada ciki dole a maida aurenmu da Mu’azzam.” Mommy ta katseta da fad’in “Ashe ke shashasha ce lamba d’aya.. Banda Rashin wayo wayace miki ana sanar da samuwar k’aramin ciki haka gatse..? Idan kika sanar dasu yanzu sam bazasuyi d’okin cikin ba.. Amma idan kika bari suka fahimci haka sai kifi samun goyon bayansu da kulawarsu.. Koda wasa kar kiyi wann kuskuren..” Feenah ta saki baki tana duban Mommy dan ita bataga mai zai hanasu farin ciki idan ta sanar dasu ba. Mommy ta katseta da fad’in “Kina jina bazaki sanar dasu yanzu ba.. Ki bari akwai lokacin da na tanadar ma hakan.. Amma idan kika zab’i kiyi abinki ke kad’ai ni bazance komai ba Sai na zuba miki idanu kiyi duk yanda kike so.. Idan kikaje garin shashashancinki da haukarki kika salwantar da cikin kinga ai shikenan kin huta..” Safeenah tai shiru tana sauraron Mommy.. Sai kuma ta jinjina kai tace “Shikenan Mommy bazan sanar dasu ba zan jira lokacin da Kikace d’in..” “Yauwa yanzu naji batu.. Tashi muje ki kwanta ki huta..” Babu musu Safeenah ta mik’e tabi bayan Mommy. ** Washe gari ma sassafe ya fice Dan ko sallama bai samu sunyi ba Assad na jiransa akwai yanda zasuje sann yana so ya soma biyawa Prison wajen Yusuf kafin suje yanda zasuje da Assad d’in. Koda Sadiya ta farka taga har ya fice Sabon tashin hankali ta shiga, ba d’abi’arsa bace fita bai mata sallama ba.. Ko sauri yake zai shigo ya manna mata kiss ya kuma mata sallama ya sanar da ita aiki na gaggawa ya taso masa.. Amma sai gashi yau ya fita kuma sam ita dai bataji alamun shigowarsa ba.. Mai hakan yake nufi..? Tai jigum abin na neman ya d’aga mata hankali cikin k’ank’anin lokaci. Taji kanta na wani irin sara mata ga daren jiya ba wani samun isasshen bacci tai ba, haka tai kusan kwana tana juyi. Kewan gida ne ya isheta.. Taji tana son taje taga Umma da ‘yanuwanta. Tai tunanin kiran layinsa sai kuma ta tuna jiya fah rejecting yai sann bai ko bi takanta ba har wann lokacin.. Jiki a sanyaye ta aje wayar nata ba tareda ta kirasa ba. Tai zaune a parlor kaman marainiya tana tinanin rayuwa da irin k’alubalen data fuskanta a rayuwa.. Shin wann ma wani sabon karatun ne..? Tambayar da zuciyarta tai mata. Kwanciya tai lak’was cikin kujera tana jin ko kitchen kaman bazata iya shiga ba a nan bacci b’arawo ya d’auketa abinka da wacce bata wani sami bacci daren da ya gabata ba. ** Mu’azzam yai zaune yana jiran fitowar Yusuf a wajen da aka tanada domin ganawa sa prisoners.. Can ya hangosa ya nufo yanda yake wani ganduroba biye dashi. Mu’azzam ya tsaresa da idanu yana dubansa yanda yake nufosa, a maimakon kayan ‘yansanda kayan prisoners ne jikinsa.. Ya d’an kauda fuskarsa kad’an yana jin wani abu na tokarin zuciyarsa.. Maiyasa abokinsa zaici amanarsa.. Maiyasa Yusuf..? Daidai lokacin Yusuf ya k’araso gajeriyar murmushi saman fuskarsa, ya zauna a kujera mai kallon na Mu’azzam teburi ya raba tsakaninsu. “Inspector, what brought you here this early..?” Yusuf ya tambaya yana d’an shafa hab’arsa kad’an idanunsa akan Mu’azzam d’in. Mu’azzam ya kafesa da idanu yana dubansa, saida ya kwashi tsawon lokaci a haka har Yusuf ya soma gudura, ya saki murmushi yana ‘yan waige waige lokaci guda yana rage girman idanunsa kad’an “You shouldn’t been seen here Inspector.. You know this could be dangerous for me... Kar ka mance they have eyes everywhere.. Suna karantar duk wani movement d’ina..” Ya kuma duban Mu’azzam d’in yana sakin murmushi a hankali “I don’t want to get killed Inspector.. Nida munsan ya criminals suke gudanar da al’amaransu musamman a Prison.. They can easily eliminate me here.” “Kayi magana idan baka so su kashe ka.. Ka fad’i duk abinda ka sani.. Na tabbata sentences d’inka bazai kai nasu ba.. Yusuf Maiyasa kake karesu.. Maiyasa ka zab’i ka biya laifinsu alhali su suna can suna ci gaba da b’arna.. Yusuf idan ka tab’a valuing aikin ka a matsayinka na jami’in tsaro zaka Fad’i gaskiya.. Yusuf wad’anda kake karewa bazasu tab’a k’yaleka ba koda kayi abinda suke so..” Ya d’anyi fasali yana dubansa Yusuf.. Su duka biyun duban juna suke, kafin Mu’azzam ya kuma daidaita zamansa yana fad’in “If you once valued our friendship zaka sanar dani abinda ka sani..” Yasa hannu a aljihunsa ya ciro coin d’in Black African Team ya nunawa Yusuf yace “Tell me... What do you know about this..?” Yusuf ya k’ura masa idanu yana kuma duban coin d’in kafin ya murmusa yace “Mai wann yake nufi..? Wann ai sisin kwabo ne..” Mu’azzam ya jinjina kai yace “Black Africa Team.. Mai ka sani gameda wann Syndicate d’in..?” Yusuf ya murmusa kad’an yana shafa hab’arsa sai kuma yace “I don’t know.. Ban Sani ba Mu’azzam.. Bansan wani Syndicate mai wann sunan ba.” Mu’azzam ya kuma jinjina kai yace “Human Trafficking Syndicate.. But it’s been long destroyed.. Danger is somehow connected to that Syndicate.. Idan har kana aiki ma Danger, I’m quite certain zaka iya sanin wani abu gameda Balck African Team..” Yusuf ya d’an sosa kunnensa kad’an yana Murmusawa. Mu’azzam ya kuma tsaresa da idanu yana fad’in “For all time sake Yusuf.. Please do what is right..” Ya k’arashe yana duban Yusuf d’in cikin yanayi na ban tausayi. Jikin Yusuf ya d’anyi sanyi, Dan shi kansa cin amanan abokansa da yayi sosai abin ke masa ciwo.. Ya d’ago yana duban Mu’azzam ga lokacin komawansa ciki yayi Dan har ganduroba d’in ya k’araso yana jira suyi rounding up. Yusuf ya mik’e Mu’azzam ma ya mik’e yana girgiza kai “Please Yusuf, do this for our friendship.” Yusuf na murmushi yake duban Mu’azzam d’in, cikin k’arfin hali yake danne hawayen dake k’ok’arin ciko idanunsa “What Friendship are talking about Mu’azzam.. Abotan da na lalata.. Abotan da bai mana rana ba..? Abotan da ya rikid’a ya koma k’iyayya.. Wann abotan kake magana akai..?” Mu’azzam ya girgiza kai yace “Bansan dalilinka na cin amananmu ba Yusuf amma na sani you are not like them.. Kai ba kaman su bane.. You still have good in you.. Kar kabi abinda zuciyarka ke fad’a maka.. Kabi abinda mind d’inka yake sanar dakai.. Expose them Yusuf.. Kar ka bari suyi amfani dakai..” Yusuf ya murmusa kad’an kafin yace “I guess circumstance na rayuwa yakan iya jefa bawa cikin k’addaran da bai tab’a tsammanin zai tsinci kansa ciki ba.. It’s too late Mu’azzam.. Na riga da na makara.. Kaje Mu’azzam, I’ve faith in you.. I know you’ll bring them down.. Nasan zaka kamasu zaka cimmasu watarana.. Sabida ka d’auko hanya..” Ya d’anyi fasali yana rok’on Ganduroban ya k’ara masa mintoci kafin ya dubi Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Zan fad’a maka wani abu guda d’aya.. Kaje ka nemo wanene BAT.. Idan ka cimma BAT ka samu kan K’umurcin da kaketa farauta..” Ya juya zai wuce Mu’azzam ya dakatar dashi da fad’in “Kana nufin Black African Team.. Shine BAT d’in..?” Yusuf ya murmusa kad’an sai kuma ya girgiza kai yace “Bansan komai gameda wann Syndicate d’in ba.. BAT yana nufin Babbanmu A Tushe.. Ko kuma nace maka Boss At the Top.. Kaje ka nemo shi Mu’azzam.. Ka nemi BAT duk yanda ya shiga ya fita.. Idan ka kamo shi ka gama cin nasara.. May God be with you, Dear Friend..” Daga haka Sa kai yai ya shige Mu’azzam yabi bayansa da kallo. Furzar da huci yai a hankali yana kuma juya coin d’in cikin hannunsa. A fili ya furta “BAT.!” ‘Is this another mission.?’ Zuciyarsa tai masa wann tambayar. A fili ya kuma furta “Where are you Danger..? Ni da kai ya kamata mu sake had’uwa..!” Ya k’arashe yana kuma juya coin d’in cikin hannunsa. Lokaci guda ya zira coin d’in cikin aljihunsa kafin yasa kai ya fice yana jin wayarsa na ruri. Ya d’aga yana amsa kiran Assad. ** A sace Safeenah ta d’auki car keys Ta fice daga gidan dan dama Mommy ta mata kashedi Ta hanata fita ko k’ofa sann ta k’wace mabud’an motar ta. Saida ta tabbata Mommy ta Shige wanka kafin ta saci k’afa ta fice. Bata zarce ko ina ba sai gidan Mu’azzam. Patrick ya ganeta saidai da mamakinsa wann karon bata masa hauka ba. A mutunce ta masa magana harda cewa ba shiga zatayi ba sak’o tazo badawa ya shiga yai mata iso da uwar D’akinsa. Patrick ya amsa mata kafin ya nufi cikin gidan. Sadiya na tsaka da bacci taji ana knocking.. Ta mik’e tana mutsuka idanu lokaci guda tana duban agogon dake manne Parlorn, tana Mamakin yanda bacci ya saceta nan da nan gashi har ta jima tana bacci nan wajen. Gashi baccin ba wani mai dad’i tai ba, bacci ne da babu komai cikinsa face wasu irin mafarkai sarara marassa kan gado.. Gashi ta farka da wani irin azabebben ciwon kai. Nan ta sinkayo Muryar Patrick yana kuma knocking. Da k’yar ta mik’e tana jin duk jikinta ya mata nauyi.. Ita sai lokacin ma take tuna yau ko azkar na bayan sallan Asuba bata samu tayi ba, duk hankalinta baya jikinta. Ta mik’e tana fad’in gata nan zuwa. Haurawa sama tai Ta d’auko mayafi ta rufa kafin ta k’araso ta bud’e k’ofar.. Nan Patrick ke sanar da ita ana sallama da ita waje. Ta d’an rage girman idanunta tana dubansa cikeda mamaki “Ni kuma sallama Patrick.. Ni kaw wa na sani a nan..?” Patrick yace “Matar Oga ce da take gidan nan da..” Yanzu kam ta fahimci Safeenah ce tazo. Ta d’an lumshe idanunta kad’an tana k’ok’arin saita kanta dan saida taji gabanta ya fad’i da Patrick yace Safeenah ce mai sallama da ita, ta shiga tuna jiya Mu’azzam wajen Safeenar ya tafi bai kuma waiwayanta ba har safiyar yau d’in. “Ma’am should I go and tell her you are not available..?” Patrick ya tambaya cikeda risinawa. Sadiya ta girgiza kai tace “Maiyasa bata shigo ba tace ka mata sallama dani..?” Patrick ya d’an girgiza kai kad’an yace “Nima ban Sani ba Ta dai ce na miki magana bazata shigo ba.” Ta jinjina kai kad’an tana fad’i cikin zuciyarta ‘K’ila ta tuna arangamarta da Karnuka ne kwanakin baya Shiyasa ta zab’i kar ta shigo d’in.. Da wann tunani Sadiya ta nufi waje da zummar ganin Safeenah..” Safeenah tana hangota ta bud’e motar ta fito muguwar murmushi saman fuskarta. Sai faman k’are ma Sadiyar Kallo take yanda ta wani k’ara cika da kyau an samu duniya an baje Koli a Gidanta.. Saima rage girman idanunta Sadiyar take tana kare fuskarta da hannayenta sabida hasken rana irin mai zafin nan da ya bayyana. Kana ganinta kasan ba fitan take ba, hutu da jin dad’i sun zauna a wajen. Fatarta kad’ai ka kalla zai tabbatar maka da hakan. Safeenah taci gaba da tab’e baki tana dubanta. Yayinda Sadiyar ta sakar mata murmushi tace “Ya kika tsaya daga waje.. Mu k’arasa ciki mana.. Allah yasa da alkhairi kika Zo..” Safeenah taci gaba da k’are mata kallo tin daga sama zuwa k’asa kafin ta murmusa tace “Ba shiga nazo yi ba. Zuwa nai na baki sak’o..” Sadiya ta murmusa kad’an tace “Toh banda abinki nan fah gidan Yayanki ne kinga ai bazan hanaki shiga ba matuk’a ba da tashin hankali kika Zo ba..” Safeenah ta murmusa mai sauti tace “Kar ki nuna mun bariki yarinya.. Tar nake kallonki.. Ki gama duk wani iskancin da kutungwilarki na d’an lokaci ne.. Naji dad’i da kika San cewa ni da shi tushe guda ne.. Kece bare a tsakaninmu.. Har abada mu zamu tab’a rabuwa ba.. Domin kuwa akwai jini mai k’arfi da ya had’amu..” Ta saki murmushi tana mai d’aura hannunta saman flat tummy d’inta da kaman babu komai ciki.. Lokaci guda take ci gaba da fad’in “Shin kin tambayi mijinki jiya da wa yake tare a daren jiya..?” Ta wani rausayar da idanu kafin taci gaba da shafa cikin nata tana fad’in “Koda yake naga kinata kiransa amma yanata katse kiran naki.. Toh Maiyasa ma bazai katse ba alhali yana tsaka da jin dad’insa..” Izuwa lokacin k’wallan da Sadiya keta k’ok’arin dannewa Sun gama ciko idanunta.. Safeenah tai murmushin cin nasara ganin yanayin Sadiyar ya sauya gaba d’aya. Lokaci guda taci gaba da fad’in “My Halal bazai tab’a rabuwa dani ba.. Ni da shi are one.. Haka kikazo kika samemu kuma haka zaki fice daga rayuwarmu ki barmu tare kaman dai yanda kika samemu tare.. Kinsan Maiyasa..?” Ta k’arashe tana kuma matsowa kusan Sadiyar kafin ta janyo hannun Sadiya guda ta d’aura saman cikinta.. Murmushi bai bar saman fuskarta ba take duban Sadiyar wacce ta daskare tana kallon hannunta da Safeenah ta aza kan cikin ita Safeenar “Akwai ajiyar shi a cikin nan.. Zan bashi abinda babu wata mace da ta tab’a bashi a duniyar nan.. Product na soyayyarmu ne a cikin nan.. Tab’a kiji da kyau ki tabbatar da hakan... Kar kiga laifinsa , Kinsan mace mai juna tana buk’atar kulawa na musamman sann jariri na buk’atan d’umin mahaifinsa dole ya katse kiranki..” Sadiya tai azaman fincike hannunta daga saman cikin Safeenah tana goge hawayen da suka shiga gangaro mata. Safeenah Ta kuma murmusawa kafin taci gaba da fad’in “ Dama na fad’a miki gidana tamkar GIDAN ARO yake a wajenki.. Mijina nawa ne.. Ni kad’ai.. Ki fara k’irga kwanakin ki a gidan nan domin kuwa kwanakin ki a gidan nan K’ayaddadu ne.. Zaki fice ki bar mun Gida kaman dai yanda na miki alk’awari.. Bari dai muga mai zai faru yanzu..” Ta k’arashe a daidai sanda ta hangi motar Mu’azzam ya karyo layin.. Safeenah Ta silale nan wajen, tai saurin jifa da takalmanta gefe.. Ta kama k’asan rigarta ta keta.. Ta d’aura hannunta guda akai d’aya kuma ta aza saman kwamkwasonta daga nan ya da take duk’e gaban Sadiya. Ta shiga zunduma ihu tana kame cikinta tana kuka “Wayyo sun kwance mun karnuka.. Wayyo cikina.. Wayyo zan mutu.. My baby.. I don’t want to lose my Baby.. Wayyo Allah na..!” Sadiya tai tsaye Cak cikeda mamaki tana kallon wani irin makirci da bata tab’a arangama da irinsa ba.. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:36 AM] My mom: *GIDAN ARO* *63* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Hango Safeenah zaune darshan a k’asa da yai ya sanyasa saurin taka birki. Babu shiri ya bud’e marfin motar ya fito ya nufosu cikin sassarfa, ga Sadiya tsaye gabanta tamkar wacce aka dasa. “Feenah.. Ke Safeenah lafiya.. What’s going on here..?” Ya tambaya yana k’arasowa. Safeenah ta kuma kame bayanta tana nishi da k’yar “Wayyo.. Wayyo Allah na.. Karnuka Ta sakar mun.. Wayyo na shiga uku.. Wayyo zan mutu.. Bayana.. Marata..” Cikin kuka taci gaba da nuna Sadiya tana fad’in “Gata nan.. Itace tasa mai gadinka ya kwance mun Karnuka.. Ni banyi niyyan zuwa gidanka ba amma dashike inada appointment da Dr tau shine na taho muje tare tinda kaima Kanada iko akan D’anka kuma ka canci kasan dik abinda ake ciki... Shine wann matar taka tasa security man ya kwance mun Karnuka.. Dama ba yau bane kawai Ta tab’a mun haka.. Ranan ma ta mun haka harda cewa ni mayya ce Ina bibiyanka bayan ka sakeni.. Ai ko da ace Babu aure tsakaninmu nan fah gidan D’anuwana ne zan iya zuwa gidan nan..Amma shine ta kwance mun Karnuka saikace wata b’arauniya, wllhi da k’yar nasha.. Wayyo cikina..!” Ta kuma kurma wani ihun daidai sanda Patrick ya fito da Karnuka.. A nasa tinanin Safeenah ta tare Sadiya ne da fad’a shine ya fito da Karnukan dan ya mata barazana kaman yanda suka mata wancan ranan. Patrick ya turo gate yana rik’eda Karnukan yake fad’in “Ma’am Ta tafi ko na sakar mata su Danny su tayata shawagi..” Yai birki wa kalamansa sakamakon hango Mu’azzam da yai. Safeenah ta kuma sakin ihu tana rarrafawa Ta isa bayan Mu’azzam Ta rik’e k’afafunsa tana b’uya tana fad’in “Ka gani ko.. Kaga abinda nake fad’a maka koh.” Wani irin tsawa ya dararawa Patrick wanda saida yasa Patrick sakin chain d’in wuyan Karnukan dan tsoro dan shi sam baisan Mu’azzam d’in ya iso ba.. “Are you stupid.. Ashe kai mahaukaci ne..!” Cikin fad’a fad’a yake maganar wanda zai tabbatar maka ransa a b’ace yake. Patrick fad’i yake “Sorry Sir.. I.. I didn’t know.. You..” “Shut up.. Just shut up.!” Mu’azzam ya kuma daka masa wani Tabawan. Sadiya dake Hawaye bud’e baki tai da niyyan magana ya dakatar da ita ta hanyar d’aga mata hannu “Banson jin komai, ki shige gida yanzun nan.!” Ta saki baki tana kallon ikon Allah. Ta girgiza kai tace “Amma...” “Bakiji mai nace bane..? Ko kurma ce ke..? Kina iya adana bayanan ki har na dawo..Please.” Ya k’arashe yana mai janye idanu daga barin dubanta. Take taji hawayen na zuwa mata gadan gadan, Jiki babu laka Ta nufi cikin gidan, yayinda Patrick keta k’ok’arin basa hak’uri yana janyo igiyan wuyan Karnukan. Ta jikin gate Sadiya Ta mak’ale tana hange Safeenah dake kuka Mu’azzam na tambayarta ko zata iya tashi.. Wani sabon kuka ne taji yazo bakinta. Safeenah ta girgiza masa kai tana hawaye “I can’t.. I can’t walk.. Wllhi bazan iya ba.. Ni da nasan Karnuka za’a kwance mun a gidanka wllhi da bazanzo ba in the first place..” Kuka ya hanata ci gaba da magana, tana hawaye tana shafa cikin take fad’in “Our Baby Mu’azzam.. I don’t want to lose our child.” “Ya isa haka Kimin shiru..” Ya fad’i yana d’aukanta Cak cikin hannunsa. Sadiya Ta kuma fashewa da kuka ta nufin cikin gidan a guje kukan na fin k’arfinta. Patrick ya bita da kallo cikeda tausayawa dan shi kanshi yasha mamakin tuggun da Safeenah ta k’ulla. Motar Safeenar Mu’azzam ya shigar da ita gefen mai zaman banza kafin ya zagayo ya zauna a mazaunin driver. Sai matse ido take kaman da gaske tana jin jiki, tana yi tana satan kallonsa yanda ya kai matuk’a wajen tsimewa. Ya daidaita zamansa saman kujeran ya soma driving. Safeenah na kuma sakin sabon kuka tana fad’in cikinta. Birki ya taka wanda saida ya sanyata had’iye kukan nata cak, ta d’ago tana dubansa a tsorace. “Safeenah..!” Ya fad’i a hankali idanunsa naga kwalta. Ta saci kallonsa kad’an. Lokaci guda yaci gaba da furta “If something bad happens to your pregnancy.. Believe me, you will regret it..!” Ya d’ago yana dubanta yana jinjina kai alamun tabbatarwa, hannayensa saman steering wheel yake ci gaba da fad’in “Idan kika kashe mun d’a da ganganciniki ki yarda dani, bazan sassauta miki ba har sai kin biya abinda kika aikata... Ki rubuta hakan ki ajiye..” Yana maganar yana jinjina kai alamun tabbatar da kalamansa. Baki sake Safeenah ke dubansa, sai kuma ta soma sakin huci tana fad’in “Matarka tayi niyyan kashe min d’a shine zaka tasa ni gaba da fad’a kana gani Ina cikin sever pain amma dikda haka bayan wancan makirar kake bi.” “Ke kar ki maidani D’aniska.. Nasan abinda nake.. Mai ya kaiki gidan in the first place.. Ni ne zaki raina ma hankali, wani Wai kinada appointment da Dr.. Inace jiya da dare mukaje kikaga likitan.. A yaushe kukayi setting appointment din..” Ta turo baki ranta a jagule. Ya kuma gyara zamansa yana fuskantar ta sosai “Kina jina.. Kar ki kuskura Safeenah.. Kar ki kuskura.. I am warning you.!” Ya k’arashe cikeda gargad’i, daidai sanda wayarsa Ta soma ruri. Mommy ce mai kiran nasa. Ya d’an harari Safeenar dake ci gaba da ture turen baki kafin ya d’aga wayar. Yana d’agawa Mommy Ta soma fad’in “Mu’azzam idan kana tare da Safeenah bata wayar muyi magana, ga wayarta ta bari a gida sann ta d’auki car keys ta fice ban Sani ba..” Duban Safeenar ya kumayi kafin ya mik’a mata wayan ba tareda yace komai ba. Ta amsa tana k’arawa a kunnenta dan ta fahimci Mommy ce. D’add’aya Mommy tai mata sann tace tasa aniya ta dawo gida. ** Sadiya kaw tana shigewa gida wani sabon kuka Ta fashe dashi, Ta soma tinanin abubuwan da suka faru daki daki, tin daga k’in d’aga kiranta da yai yaita rejecting, sann da ya dawo baibi takanta ba, yanzu ga abinda ya mata, bai saurara daga b’angarenta ba amma ya hau kan abinda Safeenah tace.. Ta kuma tina yanda ya d’auki Safeenar cikin hannunsa ya shigar da ita mota.. Take taji wasu sabbin k’walla suna ciko idanunta. Cikin kuka Ta nufi upstairs ta d’auko handbag da mayafinta. Tana fitowa Patrick ya tareta yana tambayarta Ina zata ganin har lokacin bata daina matsan idanunta da suka kod’e sabida kuka ba. “Ma’am please don’t leave.. Laifina ne da na fitar da Karnunkan, Believe me bansan Oga ya iso ba.. Kuma bansan abun zai juya ya zama haka ba.. Dan Allah Ma’am kiyi hak’uri ki dawo.. It’s all my fault.. But I’m sure Oga zai fahimci matar can makirci kawai ta k’ulla.” K’ok’arin saita kanta tai tace “Kar ka damu Patrick. Ka daina d’ora ma kanka laifi kaji koh.. Bazai ce komai ba dan na tafi..” “But M’am last time da kika tafi na samu matsala sosai da oga, kar na kuma shiga wani matsalan.” Ta girgiza kai kad’an tace “Wancan karon da wann akwai banbanci..” Tai maganar tana mai ficewa. Patrick ya biyo bayanta yana fad’in “Ma’am toh ki bari a kirawo miki Cab..” Bata sami zarafin sauraron Patrick ba dan tuni ta fice daga gidan. Patrick yai tsaye yana kallonta yana tunanin yanda zasu kuma kwashewa da Mu’azzam. ** Haka Safeenah ta kumbura ta cika tai fam cikeda jin haushin plan d’inta bai mata aiki yanda taso ba.. Wllhi dole ta sanar dasu Daddy ciki ne da ita tasan zasu sa Mu’azzam ya maidata. Da wann tunanin suka iso gida. Ya tasata gaba yana biye da ita, har lokacin a kumbure take kaman zata fashe. Suna haurawa sama suka tadda Mommy tana jiran shigowarsu. Aiko suna shiga Safeenah ta duk’a tana kame cikinta tana sakin k’ara kad’an. Mommy dake cike fam da niyyan tsefe mata masifa nan tayo kanta tana ambaton sunanta. Mu’azzam ma ya k’araso yana ambato sunan Safeenar. Mommy ta nufi d’aki babu shiri Ta d’auko mata wasu pills ta mik’a mata had’ida glass of water tace maza tasha. Babu musu Safeenah Ta amsa Ta had’iyi pills d’in har guda biyu Mu’azzam na mata sannu. Ikon Allah maimakon ciwo ya lafa amma tana shan wad’ann pills d’in da Mommy ta bata sai ciwo ya k’aru babu k’akk’autawa. Mommy tai tsaye tana dubanta yayinda Mu’azzam ya d’an kuma duk’awa yana ambato sunan Safeenar wacce da gaske take murk’usoso yanzu kam. “Feenah can you hear me.. Safeenah do you need a Dr..?” Dik a d’an birkice yake maganar. Muryar Mommy ne ya katsesa “Babu yanda zataje.. Ba kuma Likitan da za’a kira..” Da tsananin mamaki ya d’ago yana duban Mommy dake wann maganar ga d’iyarta cikin pain. Ya girgiza kai kad’an yace “Mommy kin kuwa ji mai kike cewa..?” “K’warai kuwa naji kuma nasan mai nake cewa.. Duba nan kaga..” Tai masa nuni da k’afar Safeenah da tuni siririn Jini ya soma gangarowa. Mommy Ta kafesa da idanu tana murmushi ga Safeenah kwance k’asa tana murk’usoso tana rik’e mararta. “Gashi nan.. Ga D’an Naka yana fita... Sai ka duk’a ka tattara d’anka.. Na fad’a maka sai na d’au fansar duk k’uncin da ka jefa mu ciki.. Ba’a cin bashin Hajara a wanye lafiya Mu’azzam.. Wann shine sakamakon duk rashin darajan da ka jaza mana.. A tunaninka zan bari cikin nan ya fice garin sakarcin Safeenah da wautan ta ne.. A’a ai idan na bari D’an ya fice garin haukar Safeenah ai na cutu.. Ban k’untata maka ba kenan.. Naci alwashin ni zan salwantar da wann shegen cikin naka Mu’azzam.. Kaman yanda ka k’untata mun lokuta da dama... Kaman yanda ka k’untatawa d’iyata Safeenah.. Toh D’ah baifi D’ah na kaima kaji dik irin k’uncin da naji.. Gashi nan ga gudan jininka na bin k’asa.. Ka tsuguna ka kwashe gudan jinin naka..” Ta k’arashe tana masa nuni da jinin dake d’iga daga k’afafun Safeenah wacce keta ihu tana neman d’auki tana kame mararta. A daidai lokacin Musaddiq da ihun Safeenah ya tadashi daga bacci ya shigo parlorn. Cak ya tsaya yana sauraren Mommy dake ci gaba da fad’iwa Mu’azzam ya duk’a ya kwashe gudan jininsa. Wani irin zufa ne ke tsartsafo masa.. Duban Mommy yake cikin wane irin yanayi.. Ko a labarai bai tab’a ji ko ganin mai hali irin na Mommy ba.. Sabida mugun zuciya Ta zab’i Ta salwantar da jikanta dan kawai ta k’untata masa.. Shin mai yayi wa Mommy da tsanani..? Shin wann wane irin tsana ne.. Shin Sakin Safeenah da yayi a gabanta ne har yakai tai masa irin wann hukuncin kokuwa dai auren da yayi ba da saninsu bane sann ya tare da matar a gidan Safeenah kafin akai Safeenah shine dalilinta na yi masa wann hukuncin..? Shin cikin abubuwan da yai har akwai wanda yakai tai masa irin wann tsartsauran hukunci..? Gumi bai daina karyowa daga cikin sumarsa zuwa goshinsa ba, yaci gaba da takowa yana duban Mommy cikin wane irin yanayi.. Jinjina kai ya shiga yi still yana duban Mommy “You.. You’ve gone too far..! Kin tafi da nisa wann karon.. Kin tafi da nisa.!” Ya k’arashe numfashinsa na fita a hankali yana kuma jinjina kai yana duban Mommy da idanunsa da suka gama kad’awa. Juyawa yai zai fice Musaddiq yai saurin bin bayansa yana kiran sunansa saidai Inaa bai cimma Mu’azzam ba. Musaddiq ya dawo da sauri ya k’arasa kan Safeenah yana k’ok’arin taimaka mata yana mata sannu, lokaci guda yake aikawa Mommy dake tsaye tana dubansu mugun kallo. Safeenah kuka take tana fad’iwa Musaddiq “My Baby.. My baby Musaddiq.. My Baby.. I don’t wanna lose my Baby.. Tell me Musaddiq.. Please tell me nothing bad is goin to happen to my child.. Please tell me..!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka mai ban tausayi tana kukan tana kame cikinta. Musaddiq yai saurin rungume Safeenah daga nan yanda take duk’e tana cazgan kuka mai tab’a zuciya. Hawaye ne yaji suna gangaro masa, tausayi da k’aunar ‘yaruwarsa fal zuciyarsa. Sosai ya rungume kan Safeenah cikin k’irjinsa yana k’ok’arin lallashinta. Iya ce ta shigo Musaddiq yai mata umarni ta taimakawa Safeenah. Iya ma hankali tashe take k’ok’arin d’ago Safeenar. Tana mata sannu suka nufi d’aki har lokacin Safeenah kuka take cikin tsananin sanyin jiki tana kame da cikinta. Kallo guda zakai mata ka fahimci batama a cikin hayyacinta. Suna shigewa d’aki Musaddiq ya d’ago yana duban Mommy yana jinjina kai, lokaci guda yake furta “Kin gama mugunta Mommy.. Kin gama cutar da kowa da muguwar zuciyarki..!” Mommy Ta daka masa tsawa da fad’in “Musaddiq.!” Mommy taci gaba da huci tana fad’in “Ko ban cire wann tsinannen cikin ba Safeenah zata ciresa da haukarta.!” Hawaye na zubo masa yaci gaba da jinjina kai yana fad’in “Kiyi shiru Mommy.. Kin riga da kin b’ata komai..!” Mommy Ta soma hawaye tana fad’in “Bazan tab’a yarda na had’a iri da Nuratu ba.. Never Musaddiq..!” Cikin kuka yake furta “Don’t call my name.. Don’t you dare call my name Mommy.. You are not going to stop Mommy.. Right..? Ke d’in Bazaki tab’a dakatawa ba..!” Yaci gaba da jinjina kai alamun tabbatarwa “Zan sanar da Mu’azzam da Daddy komai.. Duk abinda na sani akanki Mommy.. Zan sanar dasu komai.. Bazan kuma rufa miki asiri ba Mommy..!” Cikin rashin fahimta Mommy ke girgiza kai tana fad’in “Mai kake nufi Musaddiq..? What are you talking about.. Mai ka sani akaina..?” Cikin zuban hawaye yake fad’in “Zan sanar dasu yanda kuka had’a baki keda Aunty Shemau kuka d’aukowa Aunty Nuratu mai magani na bogi dan kawai Aunty Nuratu ta fice daga gidanki da kuma rayuwar mijinki.. Naji wayar da kukai keda Aunty Shemau Tun kafin mu tafi Fufore.. Na riga nasan shirinki Mommy..” Muryarsa ya soma rawa sosai yana ci gaba da hawaye yake fad’in “Kin San Maiyasa ban tona miki asiri ba Mommy..? Because you are my mother.. And I love you so much.. Kuma nayi zaton zaki tub’a... But then... Yau d’in nan na yarda cewa Ke baki cancanci a kiraki uwa ba..!” Mommy da duniyar ya soma juya mata, hawaye Ta soma tana rok’on Musaddiq “Musaddiq don’t please.. You are my son Musaddiq..Don’t do this to your Mom.. Musaddiq Kurku fah za’a jefa mahaifiyarka..!” Cikin tsananin daka tsawa hawaye na tsartsafowa daga idanunsa yake fad’in “No..! I’m not your son Mommy.. Kin kashe D’an Safeenah da kanki Mommy.. Wace irin uwa ce zatai ma d’iyarta haka.. Idan zaki iya kashe D’an Safeenah wanda yake jininki ne Mommy Tabbas zaki iya kashe kowa sabida bak’in zuciya irin naki..!” Hawaye yaci gaba da gangaro masa ana ci gaba da fad’in “You don’t deserve to be a mother.. Baki canci zama uwa ba Mommy.. Babu uwan da zatai abinda kika aikata yau, son zuciyarki yakai mak’ura..!” Ya k’arashe yana mai kuma girgiza kai hawaye basu daina ambaliya a fuskarsa ba.. Lokaci guda yasa kai ya fice cikin sassarfa. Mommy ta biyo bayansa a guje tana kuka tana k’walla masa kira amma inaa tuni ya fice. Zubewa Mommy tai a wajen ta d’aura hannayenta biyu aka tana k’walla wani irin ihu had’ida kiran sunan Musaddiq da tuni ya fice. A d’ari Mommy Ta mik’e Ta nufi d’aki ko takan Safeenah dake murk’usoso a d’aki batabi ba Ta suri mayafinta da jaka ta fice daga gidan hankali tashe. ** Mu’azzam kaw tinda ya fice daga gidan da k’afafunsa kurum yake tafiyar yanaji kaman ba’a saman k’afafun nasa yake tafiyar ba, maganganun Mommy sai Yawo suke a kwanyarsa, hannayensa sakale cikin aljihunsa. Mommy ta kashe masa d’ah a gaban idanunsa. Matar da ya d’auketa uwa Itace tai masa hakan.. Shi duk tunanin duniyar nan ma ya rasa wane dalili ne zaisa Mommy ta aikata abinda ta aikata Wai kawai dan Ta rama abubuwan da yai mata.. Toh ma Wai shi mai yai mata da tsanani da zata d’auki wann d’anyen hukuncin.? Ya k’arashe tunanin nasa yana zama saman wasu kujerun shak’atawa dake d’an k’asa da layin masu kad’an. Mu’azzam yai zaune yana tunanin lamarin nan ya hango Musaddiq na tahowa. D’an kauda fuskarsa gefe yai kad’an har lokacin yana jin zuciyarsa na masa zogi. Musaddiq ya k’araso jikina sanyaye ya zauna a gefensa ba tareda yace komai ba. Sun b’ata lokaci a haka babu mai cewa komai kafin Musaddiq ya soma fad’in “I’m sorry.. I’m sorry Mu’azzam.. Please forgive me..!” Kansa a k’asa yake maganar. Da mamaki Mu’azzam ya d’ago yana dubansa, Maiyasa yake basa hak’uri bayan bashi yai masa laifi ba. Hannun Musaddiq dake aje gefen Mu’azzam d’in saman kujeran da suke zaune bisa Mu’azzam ya dafa, Musaddiq ya d’ago idanunsa masu zuban ruwa yana duban Mu’azzam d’in. D’an girgiza kai Mu’azzam yai yace “Maiyasa kake bani hak’uri Musaddiq.. Baka aikata mun komai ba.. Mommy ita ta aikata laifin ba kai ba..” Kuka sosai yazo wa Musaddiq ya rungume Mu’azzam yana kuka yake ci gaba da fad’in “Nayi shiru ne sabida ita d’in Mahaifiyata ce.. Mu’azzam ka yafe mun.. Ka yafe mun it I kept this from you..” B’anb’aresa daga rik’on da yai masa Mu’azzam yai yana binsa da kallon mamaki yake girgiza kai “What do you mean Musaddiq..? What are you trying to say..?” Ya tambaya cikin rud’ani. Cikin zuban hawaye Musaddiq ke fad’in “Mommy ‘yar damfara ta d’aukawa mahaifiyarka a matsayin mai magani Mu’azzam.. Ba don komai ba Sai dan ya fice mata daga gida da kuma rayuwar mijinta gaba d’aya..” Bibbiyu Mu’azzam ke ganin Musaddiq zuciyarsa na wani irin harbawa. SameenaAleeyou📚 [9/3, 8:39 AM] My mom: *GIDAN ARO* *64* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kauda kansa gefe yai yana d’an shafa sumarsa kad’an cikin rashin yarda da abinda Musaddiq d’in ke fad’i “Kamin magana da yaren da zan fahimta Musaddiq..” Ya fad’i cikin rarrabewar kalamai. Musaddiq da har lokacin bai daina zuban hawaye ba, yaci gaba da jinjina kai “I’m sorry Mu’azzam.. I really I’m sorry brother.. Dan Allah ka yafe mun.. Ban zaci Mommy zata kawo wann lokacin bata hankalta ba.. Had I known abubuwa zasu kasance haka da nayi magana tuntuni koda ta kasance mahaifiyata.. Inajin laifina ne daka rasa D’anka, Watak’ila da nayi magana tuntuni da an d’auki mataki kan Mommy.. Watak’ila da baka rasa D’anka ba..!” Kuka ya hanasa ci gaba da magana yayinda Mu’azzam yai zaune yana ganin duniyar na jujjuya masa. Ya k’ura ma waje guda idanu, cikin wane irin yanayi da zai iya cewa bai tab’a kasancewa ciki ba, a hankali cikin kwantacciyar murya yake fad’in “Tell me everything Musaddiq.. Ka sanar dani duk abinda ka sani..” Musaddiq dake duk’e wajen tafukan hannayensa yasa ya shafe fuskarsa dasu, kafin ya shiga jinjina nasa kan shima.. Lokaci guda ya shiga karanto wa Mu’azzam duk abinda suka faru harda yanda suka juya maganin Kyallu shida Ajidde da k’udirin Kyallu na turo Ajidde gidan dan tai mata sata.. Musaddiq na labarta masa abubuwan da suka faru Mu’azzam d’in na tuna komai daki daki harda lokacin da Ajidde taso masa sata farkon zuwansa gidan.. Allah sarki ashe ba b’arauniya bace kaman yanda ya zata.. Ashe tilasta mata yin satan akayi.. Shin wace irin duniya muke rayuwa ciki..? Haka Musaddiq ya dinga karanto wa Mu’azzam duk abubuwan da suka faru gameda jinyar Aunty Nuratu da rawar da Ajidde ta taka wajen watsi da maganin Kyallu tana kuma karb’o mata ayoyin Allah daga wajen Malama Hafsah.. Yarinyar da yake ma kallon shashasha mahaukaciya, yarinyar da yake ma kallon bata cancanci kasancewa kusan mahaifiyarsa ba balle tai mata jinya.. Yarinyar da yai mata lak’abi da Mahaukaciya.. Ya kuma lumshe idanunsa a hankali yana jin zuciyarsa na wani irin harbawa.. Muryar Musaddiq ya sinkayo yana ci gaba da fad’in “Shisa a lokacin da ka dage sai Ajidde ta bar gidan nima na dage cewa bazata tafi ba.. Shisa nima nai duk yanda zanyi nabi duk hanyar da zanbi domin na tabbatar Ajidde bata bar gidan ba..Nida Ajidde tuni mun had’a Team wajen ganin munyi watsi da maganin dasu Mommy suka so d’aura Aunty Nuratu akai..” Muryar Musaddiq yaci gaba da rawa “This is the least I can do bayan cutar da Aunty Nuratu da mahaifiyata taso yi..” Musaddiq ya had’a hannayensa biyu alamun rok’o ya duk’a saman gwiwoyinsa yana fuskantar Mu’azzam still hawaye ne saman fuskarsa “Mu’azzam dan Allah kai rangwame wa Mahaifiyata.. Dan Allah ka mata rangwame..!” Cikin sauri Mu’azzam ya kamo Musaddiq ya rungumesa yana jin wasu k’walla masu zafi suna ciko idanunsa yayinda kukan Musaddiq ya k’aru. Cikin wane irin yanayi Mu’azzam ke furta “Mommy ta tafi da nisa Musaddiq.. Ka sani, banyi niyyan d’aukan mataki akan Mommy ba sabida kisan d’ah na da tai akan idona..” Ya d’anyi fasali yana duban Musaddiq d’in kafin yaci gaba da fad’in “Kasan Maiyasa..? Sabida Sadaukarwa mai girma da tayi na jinyar mahaifiyata tsawon shekaru.. Amma bayan labarin da ka bani yau Ina shakkun idan Mommy tsakani da Allah ta shafe shekarun nan tana jinyar mahaifiyata.. Musaddiq kai hak’uri, bazan tab’a sassauta ma duk wanda ya cutar da mahaifiyata ba.. Ina buk’atar ganin Mommy.. Akwai tambayoyi da dole zata amsa mun.. Idan ta aikata wani abu domin ta cutar da mahaifiyata, I’m sorry Musaddiq.. But I won’t spare her..!” Ya k’arashe hawaye mai zafi na gangarowa daga idanunsa guda zuwa k’uncinsa. Daga haka Sa kai yai ya nufi hanyar da zai kaisa gidan. Musaddiq yai saurin take masa baya suka nufi gidan a tare. Saidai suna shiga gidan suka tadda wani tashin hankalin Safeenah suka hango saman k’arafan dake balcony d’inta Ta kama ginin Ta d’ale zata fad’o k’asa ga ma’aikatan gidan sunyi cincirindo Sai rok’onta suke tai hak’uri Ta sauk’o. Shigowarsu Mu’azzam yai daidai da shigowar Kiki itama ta dawo daga makaranta kenan ta tadda wann badak’ala dake tashi cikin gidansu. Musaddiq fad’i yake “Feenah don’t.. Don’t jump please..” Safeenah na kuka take fad’in “Mutuwa zanyi Musaddiq.. Meye amfanin rayuwar.. Bata da sauran amfani.. Ka barni na mutu nima..!” Tana maganar tana kuka tana kuma yunk’urowa kaman zata duro k’asa. Ko kulawa da Mu’azzam da tuni ya haye sama basuyi ba.. Dukan k’ofan d’akin Safeenah dake kulle ya dinga ti da k’arfasa har saida ya bud’e d’akin.. Yai azaman shigowa balcony d’in yanda Safeenah ke tsaye tana fad’in zata fad’o k’asa Musaddiq na bata hak’uri, Kiki kam ma school bag d’inta Ta d’ora aka cikin tsananin daburcewa tana kuka. A daidai sanda Mu’azzam ya shigo Safeenah har ta saki k’arafan ta nufo k’asa, ya daka firgitaccen tsalle daga yanda yake ya tallafo Safeenah had’ida janyosa ta dawo cikin jikinsa. Ganinsa da tai sai ta kuma fashewa da wani sabon kukan ta fad’a cikin jikinsa tana fad’in “Our Baby.. Our baby Mu’azzam.. Mommy killed our child.. Ta kashe mana D’a.. Mommy ce ta kashe mana D’a Mu’azzam.. Bazan tab’a yafe mata ba..” Sosai ya rik’eta cikin tsananin tausayi yana furta “Ya isa Safeenah.. Kiyi shiru haka nan.. Ya isa..” Safeenah ta kuma fashewa da wani kuka daidai sanda Musaddiq da Kiki suka k’araso wajen. ‘Yanuwan suka k’arasa a guje suka rungume Safeenah babu kaman Kiki wacce Ta mak’alk’aleta sosai tana fad’in “Addah Feenah don’t please.. Don’t ever try that again.. Wllhi muna sonki..” Fincika Safeenah tai daga rik’on da Kiki tai mata, tana kuma jada baya bata daina hawaye ba take fad’in “Baku nake so ku soni ba.. The only person da nake so shine wann..!” Tai nuni da Mu’azzam dake tsaye gefe yana dubanta. Safeenah taci gaba da jada baya tana kame cikinta tana fad’in “Daga shi sai D’anmu.. Su kad’ai nake so su soni a Duniyar nan.. Ban damu wani ya soni ko ya k’ini ba idan har zasu soni, idan har zan kasance tare dasu.. Kuma d’ah na yana nan I’m sure Mommy batai nasaran ciresa ba kaman yanda tai niyya.. Zo ki tab’a kiji Kiki.. Ina iya jin motsinsa..” Tana maganar hawaye saman fuskarta amma murmushi take tana kuma shafa cikinta.. “Ga D’ah na nan.. D’ah na yana nan.” Tai Saurin K’arasowa wajen Mu’azzam tana fad’in “Kaji D’anmu na motsi.. Gashi nan yana motsi.. He’s a fighter.. Bai yarda Mommy ta datse masa rayuwarsa ba..” Ana haka d’aya daga cikin ma’aikatan gidan ta shigo da package ta mik’awa Kiki tana fad’in delivery man ne ya kawo Wai a shigo ma Safeenah dashi. Kiki ta amsa ta nufo d’akin, Safeenah tana hangota da package d’in ta mik’e tana fad’in “Look my Halal.. Ga kayan Babynmu da nai order jiya online ya iso.. First gift d’insa daga wajen Mamansa.” Tana maganar tana warware package d’in ta shiga fito da kayyayakin wanda duka kayan yara ne.. Kama daga kayan sakawa na early born baby zuwa takalmi harda toys.. Sai fito da kayan take tana sunbatu Tamkar dai mai tab’in hankali. Kiki tai lamo tana duban ‘yaruwarta cikin tsananin tausayawa yayinda Mu’azzam ya shafi fuskarsa kad’an ya janyo Musaddiq suka fice. “Ina Mommy..? Na tabbata bata gidan nan..” Mu’azzam yace yana duban Musaddiq. Girgiza kai Musaddiq yai “I have no idea.. Bansan yanda taje ba..” Mu’azzam ya kafesa da idanunsa da suka gama kad’awa zuwa ja “Musaddiq zan sake tambayarka a karo na biyu, Ina Mommy take..?” Girgiza kai Musaddiq yai yace “Wllhi ban Sani ba.. Tare da kai muka shigo..” “I know, nasan tare muka shigo.. But maybe zaka iya sanin yanda taje.. Gidan ‘yar uwa, Abokiya ko wata Confidante haka..?” Ya k’arashe yana tsare Musaddiq d’in da idanu kaman dai yana interrogating nasa. Musaddiq ya kuma girgiza kai “Ban sani ba Mu’azzam.. Kuma idan na sani zan fad’a maka..” Jinjina kai Mu’azzam yake yana duban Musaddiq d’in “Zan nemo Mommy.. Zan nemota duk yanda ta shiga.” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice cikin sassarfa. Musaddiq yana komawa cikin gidan ya tadda Safeenah sai tsalle take tsakiyar d’akin tana juyi tana rungume kayan baby cikin jikinta.. Sai sunbatu take Kiki na gefenta tana kuka. Kuka ne yaji yazo masa, cikin sauri ya fice daga d’akin yana kame kansa dake tsananin sara masa.. Kiki ma cikin kuka ta kulle Safeenah a d’aki kafin ta shiga dialing Daddy. Daddy dake zaune gefen Aunty Nuratu sai ganin kiran Kiki yai na shigo masa, koda Daddy ya d’aga wayar Kiki kuka ta fashe masa dashi tana fad’in “Daddy... Daddy dan Allah kazo.. Daddy komai ba lafiya a nan.. Daddy Mommy Ta gudu.. And Safeenah is gone crazy..” Ta k’arashe cikin tsananin kuka tana mai duk’awa k’asa. Alhaji Marwan ya soma karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un a hankali kafin yace “Karimatu lafiya.. Ki nastu ki sanar dani meke faruwa..” Cikin kuka Kiki ke fad’in “Daddy kawai ka dawo kafin Adda Feenah ta rasa ranta.. Daddy bazamu iya ba dan Allah ka dawo..” Ta k’arashe cikin kuka sosai. Daddy ya lumshe idanunsa a hankali kafin yace “Ina Hajara..? Wai me yake faruwa a gidan ne..?” Cikin kuka take fad’in “Daddy kawai ka dawo dan Allah Daddy..!” Kuka ya hanata ci gaba da magana. K’ok’arin natsa kansa Daddy yai kafin yace “Shikenan, ki natsu kinji.. Ina nan tafe.. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Ina Yayanki Musaddiq..?” Kiki ta d’an waigo saidai bataga Musaddiq ba “I don’t know Daddy.. Maybe sun fice da Ya Mu’azzam..” Daddy ya jinjina kai yace “Take care of your sister kinji koh.. Don’t leave her alone.. Zan kira yayun naki..” Daga haka katse kiran Daddy yai yana neman layin Musaddiq, saidai wayar Musaddiq bata shiga.. Ya kira na Mu’azzam ma bai samu ba.. Tanata rantse ringing ba’a d’agawa. Juyowa Daddy yai yana duban Aunty Nuratu. A hankali ya d’aura hannunsa guda saman nata dake aje gefensa. Ya k’ura mata idanu kafin ya d’ago hannun nata ya sumbata. Lokaci guda yake furta “Kin tuna.. Kin tuna lokacin da ni d’in na tsinceki.. Kina cikin yanayi ne irin wann.. Ko ince yanayi mai kama da wanda kike ciki yanzu.. Baki san kanki ba a lokacin.. Kinyi losing memory... Bakisan komai ba, baki kuma san daga wata duniyar kika Zo ba.. A lokacin ina makaranta ne a can jihar Lagos birnin Ikko, dani da Yayana Abubakar.. Ranar sa ce ta k’arshe a makaranta..” Daddy yai shiru a daidai lokacin da ya soma tuno wani b’angare na rayuwarsu a baya. _WAIWAYE_ Samaruka ne guda biyu suke zaune a k’ofar University of Lagos. K’aramin wanda duka duka babban bazai tsere masa da shekaru biyu zuwa uku ba ya dubi D’anuwan nasa wanda kallo guda zaka masu ka fahimci akwai shak’uwa da k’aunar juna irinta ‘yanuwantaka mai k’arfi tsakaninsu “Hamma zanyi kewarka sosai a makarantar nan.” Wana aka kira da Hamma ya dubi D’anuwan nasa murmushi saman fuskarsa, Ya d’an shafi sumarsa kaman yanda yake masa a ak’asarin lokuta. Sai yace “Nima zanyi kewarka Marwan.. Amma kar ka damu zan dinga kawo maka ziyara.. Lagos ai ya zama mana gida.. Sann ga Salman kwanan nan shima zai taho ya soma nasa karatun.. Bazakai kad’aici ba..” Marwan ya d’an b’ata fuska yace “Jami’a ba kaman sakandare ba balle kace zaka ke kawo mun ziyara.. Nasan Salman zai taho kwanan nan amma da kai nafi sabawa D’anuwana.. Zanso nima na koma kusa da Baffah da Inne na k’arasa karatu na a can.. Gaskiya na gaji da zaman kudu.. Balle yanzu da baka nan banjin zan iya..” Abubakar wanda shine Hamman Marwan ya kuma murmusawa yace “Zaka iya Marwan... Wayasani ko matarka a nan Kudu take. Kaga sai ka samo mana sirka a nan.” Yai maganar Cikeda barkwanci. Marwan ya zaro ido waje kad’an ya girgiza kai yace “Aure a kudu.. Kaima kasan Baffa da Inne bazasu tab’a amincewa da hakan ba.. Musamman Inne..” Abubakar ya murmusa kad’an yace “Kasan menene..? Tashi muje..” Ya k’arashe yana mik’ar dashi tsaye. “Ina zamuje..?” “Gari zamu zaga kafin na tafi..” Marwan ya murmusa kafin yace “Toh ina zamuje..?” “To the Port.. Muje muga jiragen ruwa muyi nishad’i bakin Teku..” Abubakar ya basa amsa kai tsaye. Marwan ya murmusa yace “Zanji dad’in hakan kuwa.” Suka murmusa a tare yayinda Abubakar ya janyo D’anuwansa suka soma tafiya. Sanda sukazo tashan jirgin Ruwa sun tadda tashan wayam babu kowa kaman anyi yak’i an cinye.. Sukaita Yawo tsakankanun jiragen ruwa suna kallon wasu jirage da suka k’one. Marwan ya tsaya jikin wata babbar jirgi da ta lalace yana kallon cikin jigin, nan ya hango kaman k’afar mutum daga kwance. Baiyi wata wata ba ya haye ya shige cikin jirgin yayinda Abubakar ya soma kiransa yana fad’in yazo su tafi kafin wani abun ya samesu. Marwan ya girgiza kai yace “Ka jirani a nan Brother ina zuwa..” Bai tsaya sauraron D’anuwan nasa ba ya shige cikin jirgin yana kuma mamakin abinda ya hango. Saida ya k’araso sosai ya kuma tabbatarwa k’afar mutum ne ke reto.. Cikin sauri ya soma k’ok’arin janye katakon da ya rufe fuskarta zuwa gangar jikinta. Gabansa ya yanke ya Fad’i sakamakon bayyanar kyakkyawan fuskarta. A hankali Marwan ya furta”Nooor..” Yai fasali yana kuma dubanta kafin ya duk’a a hankali “Mai kikeyi a nan baiwar Allah.. Wacece ke...?” Yanayin suturan dake jikinta da wani irin kitso dake kanta wanda akai kaman gammo da sumarta ya tabbatar masa watak’ila daga wata nahiyar ta taho nan.. Ya duk’a a hankali yana kuma k’are mata kallo.. Kyakkyawar budurwa ce wacce bazata gaza shekaru 15 ba a wancan lokacin. Marwan yai zaune ya tasata gaba yana kallonta yama mance tareda D’anuwansa yake. Har saida Abubakar d’in yaji shiru ya shigo cikin jirgin yana neman D’anuwansa, can ya hangosa zaune gaban mutum. Ya k’araso a hankali yana dubansa. “Marwan wacece wann..?” Abubakar ya tambaya. Marwan ya girgiza kai alamun bai sani ba, Abubakar yai saurin k’arasowa ya kamo hannunsa “Tashi mu tafi.. Tashi mu bar wajen nan..” Marwan ya girgiza kai “No.. Bazamu tafi mu barta a nan ba.. She needs our help..” “But we don’t know her Marwan.. Ina zamuje da ita... Kaga Zo mu tafi kafin wani ya ganmu.. Ban yarda da wajen nan ba..” Abubakar ya k’arashe yana k’ok’arin janyo D’a uwansa Marwan. Tarjewa Marwan yai yana fad’in “No bazan tafi na barta ba.. I’m staying right here with her.. Dan Allah ka taimaka min mu d’auketa mu kaita asibiti..” Abubakar yai shiru yana duban D’anuwan nasa yana kuma duban budurwar dake kwance idanunta a lumshe “Marwan bamu santa ba, bamu San daga wace duniya take ba.. Bamu San wacece ita ba.. Maybe ‘yanuwanta suzo nemanta.. Kaga kazo mu tafi bana so ka saka kanka a matsala..” “Hamma bazan tafiba ba tareda ita ba.. Idan kuma kai zaka tafi fine kaje..” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin d’agota. Abubakar yai tsaye yana dubansa sai kuma ya girgiza kai yace “You are so stubborn Marwan.. Yanzu ya zamuyi da yarinyar nan.. Ko asibiti muka kaita mai zamuce.. Babu police report.? Yarinyar da ko sunanta bamu sani ba.. Balle musan daga wace Nahiyar ta fito..” Yana maganar yana k’ok’arin taimakawa Marwan suka rik’eta su biyun. “I don’t know Yaya.. Amma Iyakacin abinda na sani shine bazamu tafi ba tareda ita ba..” Abubakar ya jinjina kai yace “Shikenan muje.. Allah Sa kar ‘yansanda su ganmu da mutum haka su tuhumemu..” Marwan ya amsa da “Babu ma abinda zai faru in sha Allah.. Allah yaga niyya mu na taimako.. Muje..”Ya k’arashe suna masu ficewa tallafe da Budurwar. Kasancewar yamma ne lis yasa kowa nasa sauri sauri yake ya yada zango.. Babu wanda ya kula dasu da tsintuwarsu abinka da birni mai yawan Al’umma.. Wani asibtin kud’i suka kaita kasancewarsu yaran attajiri tuni Likita ya amsheta.. Sai kuma likitan ya tambayesu mai ya sameta sann wacece ita.. Suka dubi juna a tare cikin rashin sanin mai zasuce.. Marwan yai saurin cewa “‘Yaruwarmu ce had’arin mota ta samu..” Likitan ya dubesu da mamaki yana kuma dubanta dan ga alamun bruises kad’an jikinta alamun dai had’arin tai. “Toh ina iyayenku kuka kawota ku kad’ai..” Likitan ya kuma tambaya. Wann karon Abubakar yai saurin cewa “Makaranta muke a nan gaba d’ayamu iyayenmu basa nan.. Dr please save our sister.” Dr ya jinjina kai kafin aka soma attending ‘yar uwar tasu. Likitan ya kuma tambaya “Ya sunata..?” Cikin rashin sanin mai zasuce suka dubi juna, sai kuma Marwan yai saurin fad’in “Nur.. Sunanta Nuratu..” Abubakar ya dubesa sai kuma ya dubi likitan ya jinjina kansa. Daga nan aka soma kula da ita, barin garin da Abubakar baiyi ba a ranan, koda Ta farfad’o Likita ya tabbatar masu cewa ‘yar uwarsu Ta samu matsalan shafewar tunani.. Bazata iya tuna komai ba, bata kuma San ita wacece ba.. Watak’ila sai gaba tunaninta ya iya dawowa.. Saida Abubakar ya kuma shafe Sati a garin yana dubata a asibti kafin aka sallameta. Marwan da Abubakar sukai zaune suna dubanta daga yanda take zaune, Abubakar ya girgiza kai yace “Yanzu ya zamuyi da ita.. Mai zamu sanar da Inne da kuma Baffah..? Kasan yanda Baffah yakeda tsauri.” Marwan yace “Tsintar ta mukai, batasan kowa a nan ba, batada kowa.. Na tabbata Inne da Baffah zasu rik’eta amana, Nidai kawai kasan mai zaka sanar da iyayenmu tinda suna jin maganarka..” Yana maganar yana dubanta kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Lokaci guda ya kuma kamo hannayen Abubakar yana fad’in “Kamin wann taimakon Yaya.. Ka kaita wa Inne da Baffah.. Su rik’e mun Ita har na ida karatuna na dawo..” Abubakar ya tsaresa da idanu sai kuma ya murmusa yace “Da alama addu’ana ya kama D’anuwana ka samo masu Inne sirka a Lagos..” Murmushi Shima Marwan d’in yai had’ida sadda kansa kad’an “Kallo d’aya nai mata hasken fuskarta ya haskaka zuciyata... Shiyasa na ambaceta da suna Nuratu.. Noor... Haske..” Abubakar ya murmusa kad’an kafin ya dafa D’anuwan nasa yace “Zanyi duk abinda kace, zan kuma kaita ma Inne da Baffah.. Zan tabbatar nayi convincing d’insu, Zasu rik’e maka Nuratu har dai ka dawo.. D’anuwana..” Suka rungume juna kyakkyawan murmushi saman fuskokinsu.. Marwan yace “Allah ya kiyaye maku hanya.. Ka kula D’anuwa.” Abubakar ya jinjina masa kai suna waiving ma juna kafin ya k’araso yanda Nuratu take. Bata um bata um um tinda ta farfad’o, dama Likita yace zata d’auki lokaci mai d’an tsawo kafin Ta soma magana. A haka suka d’auki hanyar Adamawa Abubakar da kuma Nuratu. Koda suka iso gida Inne da Baffah sunsha mamakin ganin D’an nasu da bak’uwar fuska.. Baffah ya tsaresa da tambayar Ina ya samo yarinya budurwa gashi bata um bata um um.. Abubakar ya sanar da Iyayen nasa komai cewa tsintarta sukai batada kowa kuma batasan daga yanda take ba. Hasalima tinaninta ya shafe magana ma bata fara ba tukuna. Tausayinta ya lullub’e Inne da Baffah, saidai da fari Baffah ya dage kan a bincika ko za’a sami iyayenta, amma yin hakan ba abu bane mai sauk’i musamman a wancan lokacin da akeda k’arancin ci gaba. ga k’aunar Yarinyar da ya shige zuciyar Inne lokaci guda kasancewar basu tab’a haihuwar d’iya mace ba. Ji take Allah ne ya azurtasu da samun d’iya mace bayan yara maza har guda uku da Allah ya albarkacesu dasu. Tuni Nuratu ta zamto d’iyar Inne, k’aunarta ya dabaibaye Zuciyar Inne, Ta samu d’iyar da bata tab’a samu ba, ga biyayya ga saurin shiga zuciya.. Sannu a hankali ta soma magana saidai har lokacin bata iya tuna ko ita wacece da kuma yanda ta fito.. Nuratu ta shiga Zuciyar su Inne harma da Baffa musamman duba da yanda takeda biyayya da kuma hankali, yarinya ce natsatsiya wacce kowa zai alfaharin ace ita d’in d’iyarsa ce. A haka take zaune da Iyayen Abubakar da kuma Marwan suna nuna tsananin k’aunarsu gareta yayinda ita kuma take nuna biyayya garesu. Ta d’auki Abubakar tamkar babban Yaya, takan kirasa Hammana shi kuma ya kirata Nurie ‘yar k’aramar k’anwata, Yakan koya mata karatu boko da Islama har ya zamto tamkar malaminta, akasarin lokuta suna tare musamman da shike ya kammala karatun Jami’arsa, ya kuma fara kula da Gidan Gonarsu, abu kaman wasa iyayen suka kula kaman soyayya ce take neman k’ulluwa tsakanin Abubakar da Nuratu.. Sukam hakan yayi masu domin kuwa koda basu haifi Nuratu ba sunyi Na’am da hankalinta da kuma Tarbiyarta. Baffah shi ya yanke shawarin had’a auren Nuratu da kuma Abubakar wanda Inne ma ta goyi bayan hakan dan sosai take k’aunar Nuratu kaman ita ta haifeta. Koda Baffah ya sanar da Abubakar da Nuratu k’udirinsu na had’a aurensu Nuratu sanne kai tai cikeda kunya dan Allah ya gani sosai take k’aunar Hamman nata koda bata furta ba. Sabo da shak’uwarsu shi ya haifar da Soyayya tsakaninsu, saidai a b’angaren Abubakar zuciyarsa ta raunana, Tabbas bai tab’a tsintar kansa cikin soyayya da wata mace ba face Nuratu budurwar da yaima D’anuwansa Alk’awarin zai dawo ya isketa.. Bazai iya musu wa Baffah ba dan bai tab’a bijire ma umarnin mahaifansa ba.. Hakan yasa koda Baffah ya sanar dashi ga k’udirinsu bai masa musu ba bai kuma ce a’a ba.. Saidai ya shiga rud’ani na rashin sanin wanne abu zai aiwatar.. A zuciyarsa yana matuk’ar son Nuratu sann wani b’angare na Zuciyar ya kasa natsuwa, gani yake kaman amanan D’anuwansa zaici idan har ya amince da auren Nuratu.. Tuni an soma shirye shiryen biki har lokacin Abubakar baisan mai zai aiwatar ba. A ranan d’aurin aurensu da Nuratu Marwan ya dawo daga makaranta. Yaga cincirindon mutane a k’ofar gidansu, koda ya tambaya sai sanar dashi akai auren Yayansa Abubakar da kuma Nuratu ake. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.! Shine abinda Marwan ke iya nanatawa cikin zuciyarsa. Ya saki jakansa a hankali ya silale k’asa. Ya dawo da burin ya auri Nuratu.. Ya dawo da burin ya kasance da hasken zuciyarsa.. Saidai tuni ya iske wann labari na cewa Yayansa ya aure Nuratu.. Sukai tsaye suna duban juna shida Abubakar. Abubakar ya sadda kansa k’asa ba tareda ya iya duban Marwan dake tsaye yana zuban hawaye ba. “Maiyasa..? Ka sanar dani maiyasa..?”Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka. Abubakar na hawaye ya k’araso da zummar kamo hannun D’anuwan nasa. Marwan ya kuma jada baya yana girgiza kai “I thought we were brothers..” Yaci gaba da jinjina kai yana hawaye “Kace zaka rik’e amana.. But what did you do.. You did the total opposite Hamma.. Kaci amana.. Ka yaudareni.. Ka rud’eni Yaya.. Ka rabani da Nuurr.. Ka rabani da hasken zuciyata.. How could you do this to your own brother..?” Ya k’arashe dafe da k’irjinsa yana hawaye. Cikin kuka Abubakar ke Fad’in “Bayina bane Marwan.. Banso hakan Ta kasance ba D’anuwana.. Dan Allah ka yarda dani banci amanarka ba D’anuwana..” Marwan na hawaye yake girgiza kai yana hawaye “Kaine D’anuwa mafi soyuwa a gareni amma ka zab’I kaci amanata.. Bansan mai zance maka ba.. Amma ka sani ka dab’awa zuciyata tabo da bazai tab’a warkewa ba.. Ka sani Nuratu zata rayu a gidanka ne tamkar tana a GIDAN ARO.. Ko ba dad’e ko ba jima zata dawo gareni..!” Har ya soma tafiya ya juyo ya kuma dubansa da idanunsa masu zuban ruwa “From now on.. You are not my brother m.!” Daga haka Sa kai yai ya shige d’aki yayinda Abubakar ya lumshe idanunsa hawaye suka gangaro masa. ‘Yanuwa masu k’aunan juna suka samu rashin jituwa, saidai Abubakar baiyi k’asa a gwiwa ba, bai bari iyayensu sun fahimci wann sab’ani da suka samu ba. Kullum cikin k’ok’ari yake yaga sun koma like before shida D’anuwansa. Saidai tun ba’aje ko ina ba Marwan yai sadaukarwa mai girma, ya sadaukar da soyayyar Nuratu ga D’anuwansa Abubakar, sabida yaga yanda su biyun suke matuk’ar k’aunar juna. Sann idan Nuratu zata kasance cikin Farin ciki da D’anuwansa shima zaiyi Farin ciki da hakan, zaiyi k’ok’ari ya mance da Noor har abada.. Marwan ya karb’i k’addararsa... Ya samu mata Hajara a cikin garin Yola akai aurensu dikda ba wani sonta yake ba Sai dan yana so yai moving on ya kuma daina rayuwa in the past. Bai yarda ya sanar da kowa labarin ba, ya binne hakan a zuciyarsa dan Farin cikin Nuratu da kuma D’anuwansa Abubakar. A haka rayuwa taci gaba da tafiya, Ko wannensu ya maida hankali kan ahalinsa da kuma kasuwancin ahalinsu dan tuni sun soma hayayyafa daga Duka b’angarori biyun. A haka suka bud’e dairy company bayan meat factory d’insu dake nan Fufore.. Daddy Sai ya rik’e ragamar Dairy Company ya koma Abuja da zama sann hakan yafi masa, yayinda Abubakar mahaifin Mu’azzam yake kula da Meat Factory da kuma gidan Gona, a haka Salman na makaranta yana tasowa shima. Saidai tinda Salman ya gama karatu sai ya d’aura idanunsa kan Meat Factory Kampanin da mahaifin Mu’azzam ke kula dashi, baida buri da ya wuce ya zamto shine mai kula da wajen dikda cewa an sama masa gurbin aiki a ma’aikatan bayan kammala karatunsa, saida fah shi hakan bai masa ba, yafi so ya zama shine shugaba a wann Ma’aikatan, musamman da yaga yanda mahaifinsu ke matuk’ar son Abubakar sabida k’wazonsa wajen aiki da kuma tabbatar da had’in kan ahalinsu. hakan yasa sam Salman bai jituwa da D’anuwansa Abubakar.. A haka kasuwancin ahalinsu na bunk’asa har Allah ya amshe rayuwar mahaifinsu Jauro Gamji suka ci gaba da kula da kasuwancin ahalin kaman yanda mahaifinsu ya d’aurasu akai. Wannan kenan. _CI GABAN LABARI_ A hankali Daddy ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya, ya sumbaci hannun Nuratu guda yana hawaye “Bansan furucin da nayi zai zamto gaskiya ba, bansan cewa D’anuwana zai tafi ya barki ba.. Ko da wasa ban tab’a kawowa zaki zamto matata a duniyar nan ba.. Nuratu na jima da cireki cikin zuciyata.. Ban zaci zan rasa D’anuwana har mu kasance tare ba nida ke...” Muryarsa yaci gaba da rawa sosai yana kuma kifa kansa gefenta, cikin rawar murya yaci gaba da furt “Noor ke kad’ai ce macen da na tab’a so a rayuwata.. Kuma Ked’in ke kad’ai ce.. Har abada ke kad’ai zaki kasance babu wacce zata maye gurbinki..” Ya k’arashe wasu hawayen na gangaro masa. Ya d’an b’ata lokaci kafin ya manna mata kiss a goshi yana dubanta, murmushi gauraye da hawaye saman fuskarsa yake furta “Mu’azzam ya girma ya zama babban mutum harda iyali, sann yana kan bincike dan gano makashin Ikram, bazai huta ba har Sai ya gano azzalumin da ya rabamu da Ikram.. And justice will be served..” Ya k’arashe yana jinjina kansa alamun tabbatarwa. Hannunta ya kuma rik’owa cikin nasa ya sumbata kafin yace “Zan tafi gobe Noorie, but next time in sha Allah tare zamu tafi.. Akan k’afafunki.. Zaki koma gidanki da kika baro akan k’afafunki da yardar Ubangiji... Kaman yanda nai alk’awari ma D’anuwana.. Zan kula da bayansa.. Zan kular masa daku..!” Ya k’arashe hannunta cikin nasa yana murzasu a hankali, kyakkyawan murmushi saman fuskarsa mai gauraye da hawaye. A hankali ya gyara mata kwanciyarta kafin ya kuma sumbatar goshinta ya sa kai ya fice. Yana ficewa hawaye suka gangaro daga lumsassun idanunta. ** ABUJA... Tinda Ta shigo gidan gaisuwa kawai sukai ta k’ule a d’aki tana aikin kuka. A haka Aunty Larai ta shigo ta sameta, juyin duniya Aunty Larai tayi ta fad’i meke damunta meke faruwa tak’i fad’i sai kuka take. Aunty Larai ta kuma lek’a waje ko zata hango motar Mu’azzam amma shiru bataga kowa ba. Ta dawo d’akin ta dafa Sadiyar. “Sadiya.. Wai meke faruwa ne..? Wani abu ne ya sami Mu’azzam d’in.. Kinzo kin kulle kanki a nan Kina kuka.. Idan Umma ta ganki haka ai sai ki d’aga mata hankali.” Maimakon ta amsa mata sai kuka da kuma fashewa dashi mai d’an sauri wann karon. Aunty Larai ta girgiza kai kafin ta dubi Ashiru da shigowarsa kenan d’akin tace “Kai Asheer d’auko min wayata a parlor, idan bazaki fad’i ba shi Mu’azzam d’in ai zai fad’i ai..” Wani kuka Ta kuma fashewa dashi ta rik’o Aunty Larai tana girgiza kai take fad’in “A’a Aunty nidai kar ki kirasa dan Allah.. Kawai nayi kewarku ne shine nazo..” Ta k’arashe tana goge hawayenta.. Aunty Larai Ta dawo da baya ta zauna “Ina sauraronki.. Meke faruwa..?” SameenaAleeyou📚