Subul da baka 1 page 1 Posted by ANaM Dorayi on 08:41 AM, 20-May-15 Under: Subul da Baka Lungu ne mai dauke da komatsen duwatsu, robobi, leda da kuma fasassun kwalabe, kana ketare Wadannan zaka yi karo da katuwar bola mai dankaren wari, musamman a lkc irin wnn wato damuna. Gefe da bolar daga hnn dama Wani kwarmatsattsen gidan kasane mai ' yar guntuwar katanga yana dauke da daki daya tak! sai makewayin langa-langa, daga bayan dakin. Tsakar gidan murhun kasane da ' yar guntuwar katanga yana dauke da daki daya tak! sai makewayin langa- langa, daga bayan dakin. Tsakar gidan murhun kasane da. ' yar randar ruwa, sai igiyar shanya data raba gidan biyu. Daga nesa kana hango gwangwanayen alwala a jikin langa-langar makewayin. Karamin gadon kara ne a dakin, mai dauke da katifar Rimi, sai jikunan kaya na gana ( Ghana must go ). Daga bakin kofar akwai ' yar kujerar katako ta zama, Kasa kuma an shimfida tabarma. Gida ne na mabukata wnd rashi yayi wa ka tutu. katutu. Na yi saurin maida kwallar da ke zubo min, tare da kara gyara fuskata. mahaifina Allah ya karbi rayuwarsa tun muna kanana kwarai, danginsa kuma sun yi fatali da al'amuran mu, nice babba sai kannena biyu Aisha da Sumayya. Allah ya jarrabi mahaifiyar mu da ciwon asthma, shi yasa duk talaucin mu baka ganin kura a gidan mu, musamman kura. Kr2 na ya tsaya tun shkr 2 da suka wuce, wato lkcn da na gama aji uku. Da farko na fara talla sai muka Ga cewa, hakan ba zai fisshe mu ba, shi ne Wani aminin mahaifinmu ya samo min aiki a gidan sari a matsayin BAIWA cikin bayin da aka dauka sabbi. Insha Allahu kuma gobe nake sa ran farawa. karfe 9 na dare muna shan garin rogo da kuli a matsayin abincin darenmu kamar kullum, Ina ta kalle ni tare da fadin. "Abinda nake son ce miki shi ne, ki yi addu'a Allah ya tabbatar miki da alherin wnn aiki, sannan ya kawar miki da sharrinsa kmr ydd na dage da tawa addu'a ba dare ba rana. Kuma a dk inda kika shiga ki sanya tsoron Allah a zuciyarki, ki tuna matsayin ki dana iyayenki, banda daukar abinda ba a baki ba, wlh ki guji abin hnn mutane ki zauna Lfy. Ban yafe miki ba matukar ba a baki abu ba kika dauka, ko kika roka. Aiki ya Kai ki, shi za ki maida hnkl ki yi, banda yawan surutun banza idan ba tmbyr ki aka yi ba, do min yawan magana na haddasa karya. kada ki manta ko ke wace ce, lkcn da kike ckn gidan SARAUTA, to ki ringa hango yanayin gidanku. Yi na yi bari ya rabaki da kowa, wlh dk wulakancin mutum dk izgilancinsa, matukar zai ce ka yi ko ka bari kuma ka aikata hakan, to lallai sai dai Wani abun,amma ka wuce wulakancinsa. Da fatan kin ji abinda na fada miki? " Na daga kaina Ina fadin, " lnsha Allah inna zan kiyaye ". Tayi murmushi, " Allah ya yi miki albarka, je ki sha ruwa ki zo ki kwanta kada gobe ki makara. Na ji shi mal. barau yace karfe 7 ake son ganinku a fada. ". Na mike Ina fadin, " ko 6 ne inna Insha Allahu akan lkc zamu je".Ta yi 'yar dariya, " ja'ira na sanki da sammako, amma ai dole ki zo ki kwanta din. WASHEGARI A GIDANSARAUTA Muka bi layi ana bamu kayan sawa, wdnd zamu ringa amfani da su a cikin gidan a matsayin " uniform". Yadi ne mai Dan Karen kyau, Ga taushi ruwan sararin samaniya (sky blue) dinkin riga da siket mai kyau iri daya kuma kowacce za a bata dai- dai ita, kowa kala bibiyu ya samu har aka yi saura, don mu 26 ne sabbin dauka amma duka babu wdd ta hour a shkr 22. Mafi akasari sauran iyayensu a nan suke aiki gidan sarauta, sai mu uku ne kawai wdnd muka shigo ta hanyar ALFARMA! Abin mamaki har 'yan kunne da sarkar wuya da ta kafa tare da awarwaronsu aka rarraba mana, irin kalar kayan, amman na duwatsu mai haske. Musamman Wani fankacecen daki aka bamu domin shiga, wai mu sanya kayan da aka bamu yanzu. Duk wnn bidirin a Wani bangare muke cikin gidan ba mu isa inda ake son mu isan ba hr ynz. "Allahumma arzukuna" kawai nake nanatawa lkcn da nake zura kayan a jikina, dk na rude sai kyarma nake yi. Mutum kusan 6 suka hada baki wajen fadamin cewa, NA YI KYAU!! Ni kaina nasan kayan dole su yi min kyau, sbd klr ita ce wdd na Fi so ckn kaloli, ba don komai ba sai don kyan da kalar ke yiwa fatar jikina dk lkc da ta rabu da ni. Muka biyo layi, dogarai sun saka mu a tsakiya wasu gaba, wasu gefenmu, wasu kuma a bayanmu. Inda dk muka wuce bayi ne ke kara-kaina mana da mata, haka na dinga raba ido Ina kallon aljannar duniya a wnn masarauta, wuce wnn tsuntsu, ruwa, filawowi babu abinda ba mu gani ba har Allah ya Kai mu Wani katafaren muhalli. A nan ne naga abin mamaki, mata ce kyakkyawa kishingide bisa Wani hadadden gado, bayi kusan 12 gewaye da ita, wasu na firfita, wasu matsar kafa, wasu na ba ta lbr mai dadi don 'NISHADI' banda wdnd ke bakin kofa da tsakar dakin suna kara- kaina. Aka gaba tar da mu cikin wani irin yanayi na girmamawa dk Ina lura da ydd suke yi. Ta kalle mu ckn Dan murmushi kadan, ta ce. "karasa da su wurin GIMBIYAR " Nan da nan al'amarin ya daina bani mamaki da fargaba gami da tsoro. Wani bangare muka nufa, sashen da ya firgitani fiye da ckn inda muka shiga, naji tmkr ba a duniya nake ba. Can ma wasu bayin ne bila adadin suna bauta. Mun fi mintuna 20 a tsaye ba tare da wani ya kula da mu ba, dogarawan na tsaye su ma kmr gani suka ba ni tausayi (neman halak da wuya). Zuwa can muka hng ' yanmata biyu da ' yan kwanduna a hnn cake da filawoyi masu kyau ga kamshi suna zubdawa a Kasa. Mamakina ya karu ganin wasu nayin shara, wasu na ba tawa. Ai ban karasa mamakin ba na hng hadaddiyar budurwa ta biyo sawun filawoyin ta sha kaya irin na alfarma, Ga wata hadaddiyar alkyabba tana faman jan Kasa, kanta cikin hular alkyabbar wdd bazar kwaliyar ta boye rabin fuskarta, amma kana iya hango kyallin zinaren da ke falauniya a wuyanta da kunnenta. Har ta zauna saman wata rantsattsiyar kujera ba a bar zubda filawar nan ba. "GIMBIYA! !" Na maimaita sunanan ta a ckn raina, Ina kara yi mata kallo. kusan mintuna 15 da zamanta amman ko kallon inda muke ba ta yi ba. Tuni kuguna ya soma rikewa sbd ni kam Allah ya sani ba ni da jimirin tsayuwa. kafin na Kai ga sarewa Allah ya taimakeni ta dago Kai a hnkl kmr mai fama da ciwon sankarau, ta wurgawa dogarawan nan wani mugun kallo, nan da nan naga suna durkusawa suna godiya tare da ficewa da sauri. Ta kalle mu, tare da fadin. "ku zauna". Nan da nan muka ciki umarni. " kafin na raba muku aiki zan barku anan ku taimakawa sauran domin ku ga ydd ake ya cikin kwana uku, daga safe zuwa kr2 6 na marece. Jidda! " Ta kwada kira a hnkl. Da gudu ta karaso dattijuwa ta yi kusan kanwa ta 4 da ita, ko kallonta ba ta yi ba, ta ce. "A kaisu ciki suna bukatar horo na kwana 3 kafin a raba musu aiki". Ta rusuna tare da fadin. "An gama Gimbiya. Ku taso ku biyo ni". Da sauri muka bita riii. .. ****"Inna mutane na wahala a duniyar nan, kuma mutane na jin dadi. Na ga mulki ni HUMAIRA inna, a zage ka, a ci maka mutunci snn kayi gdy, Kai SARAUTA wata aba ce! Wlh inna kwana 2 nan ba ki ji ydd jikina ke yi min ciwo ba." Tayi murmushi tace dama ai sai a hankali zaki saba kuma ai gobe ne kawai ya rage da an raba muku aikin bashi ke nan ba tunda kince akwai na safe akwai kuma na rana dana dare kinga idan na safe Allah yaci da ke karfe 7 kina can 2 kin dawo gida idan na rana ne kuma 2 kina can 6 kin dawo idan kuwa na dare ne 7 idan kika tafi sai safe bashi ke nan ba? Ke dai ki sanya tsoran Allah a duk inda kike ki kuma tuna yana ganinki a kowanne hali kika sami kanki aikin nan mi wahala ne mutuka domin shi ba wani share share ko goge goge ke gajiyar da bayi agidan sarauta ba aa cin fuska da izgilanci ke ba kowa wahala don haka sai an daure mai nema yana tare da samu ki tuna idan baki daure kika hakura ba ina zamu samu abincin da zamu ci?ruwan sha har gagararmu yake yi a gidan nan sai mu roko a makota ga karatun 'yan uwanki tundda ke baki samu halin yiba sannan uwa uba aurenki idan ya tasi wazai bamu?daga dangina har na mahaifinki kin dai san yadda ake saboda haka kiyi hakuri wata rana sai lbari" Baku Murmushi kawai nayi domin a ganina kamar nafi inna sanin wadannan abubuwan kamar kullum muka isa gidan cikin lokaci ni da Amira wacce muke tafiya tare kwana 2 sakamakon gidansu na bayan namu babu nisa kuma nice ke biya mata safiya idan muka dawo zata rako ni har kofar gida kafin ta koma nasu muna cikin wankin gimbiya misalin karfe 12 na rana ina ta alajabin wai har da wandunanta da rigunan nono shin ita bata jin kunya mata bada wadannan wurin wanki nawan haukan nake ganin kamar wani sirrinta ne wanda ya kamata ace ita ke kula da abinta kai wani abin sai gidan sarauta HUMAIRA nayi saurin waigawa na'am bar musu wankin kizo gimbiya na son ganinku ina kyarma na dauraye hannaye na cikin gudu gudu sauri sauri na karasa saboda na lura latti na saurin hasala gimbiya duk abinda ta umarta lallai tana son ayi mata shi da sauri acikin gaggawa ,Na iske su Amira a layi kamar ranar farko ni mana bi sahu ta yatsina fuska tana kallonmu daya bayan daya kamar mai kallon tsohon ciwo a jikin kazamin mutum ku kasu gida 3 ta fada a wahale ciki 'yan mintuna da basu wuce 2 ba muka rabu kamar hanya abin haushi Amira bata kusa dani don haka ya kasance bata cikin namu gungun ma'ana nasu daban ta nuna su Amira da baki daga yau zaku shiga cikin 'yan aikin rana gabana ya fadi nan da nan na hau addu'ar zuci kada Allah ya hadani da aikin dare saboda inna bana tunanin zan iya barinta ta ringa kwana ita kadai sai su sumayya saboda cikin dare asmarta na iya tashi ta juyo garemu cikina ya bada wani kugi kulululu kune masu aikin safe wadannan kuma su shiga cikin masu kwana. A hankali na furta alhamdulillah saboda haka ku nadare kuna iya tafiya sai shida kwazo tare da yan kwana na safe kuma kuyi sauri ku karasa na ku 'yan rana su kar6a xa'a dinga biyan kowacce dubu ashirin awata tana gama fadan haka ta kalli masu bata abinci akawo mun kalaci na anan mukai ta tsalle nida amira,saboda kwanan aikin ne daman muke gudu,ga kuma makudan kudin da muka ji ta ambata fan ni ko rabunsusu wllhy bansa rai ba.ina ta faman sauri babu ko waiwaye shiga wancan lungun kurda wancan hanyar saboda muna da dan nisa da gidan sarkin ban ta6a kawo wa raina abin hawa ba saboda rashin kudin biya.da zafina na isa gida ina dokin yiwa inna albishir,tunda ga tsakar gida na fara jiwo nishinta da kakari alamar ciwanta ya tashi na wancakalar da takalman na karasa a guje tare da tallabo ta a rude nake fadin ina kika ajiye inhelar? Sai neman san karewa take ta faman yi na ga wawtata dana tsaya tambayarta,alhalin nadade da sanin cewa ta kare. ,Haba a guje na fice gidan kamar mahaukaciya,nayi hayin kwalta kyamis din dayyabu ,sai zufa nakeyi na fada shagon ina ta haki, nace."Dayyabu ka dubi girman Allah kaba ni bashin inhela,wallahi na sami aiki gidan sarki da an biyamu zan kawo maka kudinka, bazan sa6a ba insha Allah" kin tabbbatar?yafada yana gargadina da hannu.na durkusa, wallahi dayyabu zan kawo kaji na zantse"yadda ya miko min maganin nace na gode"sai na kwasa a guje. Da zuwa na isketa ta kai kasa warwas na shiga shaka mata ina dan fesawa cikin mintuna 3 zuwa 4 komai ya tsaya.nayi ajiyar zuciya, Allah mai yadda yaso yanzu da aikin rana nake fa? Nadaga hannu sama nace, Allah na gode maka,Ubangiji ka kara rufa mana asiri". A hankali naji tace Ameen na kalleta nace sannu inna"tace yauwa Ahankali,ya aka yi kika dawo da wuri haka?na labarta mata yadda aka tsara sai na ga tana murmushi, ni kuma na mike zuwa tsakar gida na ga wacce dabara zan yi mana a matsayin abincin rana. **** Ina mamakin mutane,gabanka faram faram,amma bayan idonka arinka zaginka ana gulmarka.su yanzu idan gimbiya tajisu yazasuyi ko basu tunanin cewa tunda naji zan iya kwarmata mata?naci gaba da sauraransu "kinsan duk abin nan wlh ganin ita ce bababba kuma sarki duk yafi ji da ita,sannan kowa gidan tarairayarta yake yi ana lallashinta".kware kuwa saboda ko wani abu ake son mai martaba yayi,idan ta kife ciki wlh ba yayi sai da ra'ayinta". "mts! Ni ina ganin harda da rashin 'ya'ya dayawa ga sarkin,kinga fasu duka shiddane a gidan ita kadai ce wurin uwargida su ta sallah kowa na da biyu biyu,sai Amarya da ke da daya namiji shi yasa duk suka tsane ta sai kace ba Allah ne ya bata ba"ke kuwa sun tabbatar ta haifo MAGAJI.duk suka kyalkyale dariya harda tafawa."Wai ni ya maganar auren gimbiya?"Uhum!shu'umin mijin ne yaki zuwa har yau,kin san idan sarauta ta hadu da sarauta dole a baza MULKI.Amma naji an ce ya kusa zuwa nan gidan zai yi wata 2 sannan iyayen su zo maganar sanya rana"wannan wace irin al'ada ce haka? "Ke ma kin gani,gidan nan ai sun yi bin da yafi haka kawai tsabar ISA ce".kinsan abinda yafi bani mamaki tace A'a". ,Wallahi kullum idan muna tare da gimbiya ita ce mai nemansa a waya,bai ta6a bugo mata ba".suka kara dariya tace,"YARIMA!!! Wlh yarima na wahalar da gimbiya,ina tunanin sarautarsu tafi wannan zafi".ko? Kware kuwa,ki ga fa mulki irin na gimbiya da giman kai,amma wlh cikin kunnena naji tana kwantar da murya tana rokonsa kada ya ajiye mata waya". To ko bai sonta? Cikin sauri ta kai mata duka."Yi shiru ban ce ba,domin ba a jimutuwar sarki a bakina ba".yaushe zai zo? "An ce talatar nan".kin san da maimartaba da babanshi wasu irin abokai ne na kud-da-kud,kara tu ma tare suka yi a kasar waje". ,ke a Ina kika ji?""ya za ki tambaye ni bayan kakar innarmu a nan ta yi aiki?""Uhm lallai, tashi ki tayani kwaso wnk guga zan yi na zannuwan gado".Na biyu da kallo a kaikaice Ina kara luliya hirarsu ckn kwakwalwata, kafin daga bisani na wancakalar da shi. Na dage ckn bada himma Ina aiki na baji ba gani kmr daga sama naga Gimbiya da tawagarta sun zagaye ni. ' Yarbaba Wacce ke hnn damanta ta ce. " Allah ya ja da ran Gimbiya, shin ko wnn kike magana? " Kafin ta yi yunkurin magana tuni ' yan ' yan cikina sun kada, nan da nan gudawa ta kusa kubuce min ckn wando, tunani na ko laifi na yi. Ta kalle ni sama da Kasa kafin tace, " a zo da ita daki ". suka juya. ' Yarbaba ta daka mini tsawa. " Saki wnn aikin maza ki zo Kiran Gimbiya ". kwalla suka cika min idona, muna tafe Ina addu'ar Allah ya tserar da ni. Da shigarmu ta sallami kowa suka fice aka barni da ita.Ta kalle ni a yatsune, "Me ye sunanki? " Na ce,"Humaira".Ta rausayar da Kai, "Na yaba da hnkl lki, Nutsuwa da kuma kawaicinki. Kina da kyakkyawar trby kwarai da gaske, sbd hk na daukeki a matsayin Wacce Zata dinga kula da yarima idan yazo da safe kawai, ckn masu aikin rana ma zan sami guda domin ba zai so 'yan aikin dare ba sai dai wadanda ba a rasa ba. In son da safe da kin zo ki Kai masa ruwa a tasa kmr ydd al'adar gidan nan take, zai wanke kafarsa kafin ya sakko daga gado ma'ana bayan sallar asuba. Ke ce Zaki dinga wnke masa kewaye da gyaran dakinsa tare da bashi kalaci., sa sauran kulawa har zuwa karfe 2 rana, kafin ta ranar ta karba".Dadi ya kume ni na rusuna ckn girmamawa na ce."Godiya nake Gimbiya". Ta kawar da Kai, "Na sallame ki" ,Ta fada ba tare da ta kallo inda nake din ba. Na kara russunawa karo na 2 tare da fadin, "Godiya nake Gimbiya ". snn na mike tsaye shima kafin na Kai ga tafiya sai da na dan rusuna mata alamar girmamawa. Snn nayi gaba abina. Washegari mun dukufa gyaran sashen da yarima zai sauka, an kawata wurin komai an saka sabo wai har da sutura aka saka zuba mishi ckn sif, shin dama tsinken raginsa zai zo? Kai! wnn al'ada da wnn mulki da tsauri suke. Shi mulki, ita mulki, na ga wnn so yayya. Gulmar mutanena ta kara katsen tunani da hasashen da nake yi."Gimbiya na whlr da kowa a gidan nan".Inji Rabi Mamman. Ayyo ta amshe tana murmushi, "Baki ji abinda sarki ya fada wa matan gidan nan ba?" "Don yace ita ce sarautar sai a yi ta amfani da ra'ayinta, ga wuri a ce babu mai ra'ayin kansa sai abinda ta zartar? ""Mulki ke nan! ""Ni abinda ya fi damuna wlh da aka bar mu a haraba na so ace muna 'yan cki-cki don m u ga kwakwaf! Duk fa sabbin daukar nan ne ta raba a nan din, ashe daman sbd zuwansa ya sanya aka karo BAYI, ana yi da Kai ya fi ace ba a yi da kai".Ta yi dry,"wnn hk yake. sai mu jira jibin mu yi kallo, Allah ya taimake mu ya zo da irin na su bayin, watakila mu sami mazaje ciki ko kuwa?""In sami miji dai malama ke Ina sama'ila Tasawan? "Ta buga tsaki, wnn fa mayaudarine ba aurena zai yi ba sai shegen wayo kllm idan an bamu albashi sai ya kalallame ni ya amshi rabi ko da dada ba na fadawa, kllm ckn matsala yake kin ji fa wayo, ko ke kin ga mijin aure a nan?" "Ina! Wlh da sake ku yi mishi korar kare mai wayon tsiya". Ni dai a nan na barsu sbd na gama nawa aikin na nan bangaren, na koma bangaren Gimbiya, can ma na karasa wnd na baro. Idan kana duniya zaka ga abin mamaki kala-kala. Duk inda ka gitta kamshi ne, Gimbiya an ci kwalliya ta kin karawa. Motocinta ne a jere wdnd ke dauke da sunanta, GIMBIYA 1, GIMBIYA 2 har zuwa GIMBIYA 10, rantsattsun motoci na zama ni, ,Mu ne ckn sahun gaba zamu je taro Yrm, magana ba aiki na bace, don hk na tsuke bakina Ina kara mamakin wnn shagali. Lallai Gimbiya na matukar kaunar Yrm, hatta sarki da matansa ba a bar su a baya ba wajen tsara ydd za a tarbi wnn gagarumin baki. Inda za a hadu kmr ydd aka tsara nan muka tarar da su, don haka ba tare da bata lkc ba aka dungumo zuwa fadar Mai martaba don Kai gaisuwa. Mu kam tuni kowa ya kama tsagin da aka bashi don fara gudanar da aiki, ni kuwa inda Allah ya taimakeni a dai-dai wnn lkc na gama nawa a takaice 'yan rana Zasu karba, don hk tuni na harhada yanawa-yanawa na yi gida kafin kuma gobe da safe. Yau ma lbrn ya sha bambam da na klm, Inna ta dinga kyalkyala dariya, tana fadin, " lbrn gidan sarki bai karewa Humaira, ni dai hr na fara gajiya sbd tun da kika fara aikin nan klm da sabon lbr ake zo mini, babu maimaitawa. Kinga ni na manta wlh inhelar ta kusa karewa ki koma wurin Dayyabu ko Allah zai sanya ya kara baki wata kafin biyan ki" . Na ce, "to Inna, bari na yi sallar la'asar na je mu gani in zai bayar". Ckn yardar Ubangiji kuwa muka yi sa'a ya bayar, amman ckn kashedin lallai da an biyani na Kai masa kudinsa. Washegari na isa kan ka'ida kmr Klum, sashen Yrm na yiwa tsinke masu tsaron kofofin ko'ina na wuce suna tsaye ana gudanar da aikin tsaron. Masu dafa abinci na kicin sun dukufa. Na hanzarta zuwa falonshi na hau gyara ba tare da an sami wani wani kuskureba, snn na shiga dakin kwananshi. Abinka da rashin sabo, sai kawai na tsinci kaina da faduwar gaba, nan take na karanto, 'Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un". Barci yake sosai, daga shi sai gajeren wnd, ya kure na'urar sanyaya daki (A/C), dakin yayi karara don tsabar sanyi. Na kalle shi sosai, jin dadi sabo duk wnn uban sanyin amma bai rufa ba, na yi saurin fadawa makewayi na ci gaba da wankewa, tunanina ne ya tayar da shi, sbd lkcn da na gama na fito sai na tarar da shi zaune saman gadon. Da ma tuni na gama hada mishi ruwan wnk, da sassarfa na karaso wurinshi tare da durkusawa. "Barka da tashi Yrm, da fatan ka wayi gari ckn koshin lfy". Na fada kaina na Kasa. "Lfy, mai ya kawo ki dakina da sassafe kin hanani brc? "Na kara yin Kasa da kai."Allah ya huci zuciyar Yrm, tuba nake yi , wlh ban zo dakinka don na takura maka ba...""Ke!!"Ya daka min tsawar da sai da hanjin cikina suka kada."Ba ni amsar da na bukata".Ya fada ckn fada-fada kmr zai bugeni. Na yi sunkui da kai Ina fadin. "Ni ce mai kula da nan bangaren. .. Budewar kofar da aka yi ne ya sa nayi shiru. Gimbiya na gani ckn doguwar riga irin ta brc mai Karamin hnn. ya dalla mata wani rainannen kallo kafin ya ce da ita. "wnn yrnyr me Zata yi mini?" Maimakon ta ba shi amsa, sai ta dubeni. me ya rageGyaran gado da sharar nan". Na fada Ina nuna tsakar dakin."sai kuma kawo karin kumallo"."Da kyau,je ki hado kalacin ki kawo mishi, idan yayi wnk a gyara dakin".Inji ta. Na yi saurin cewa "an gama Gimbiya".snn na yi waje, ban San ydd suka kare ba. Tafe nake Ina al'ajabin wnn tsayayyen Yrm, shin ko gaskiyar 'yan gulma ne ba son Gimbiya yake yi ba? idan kuwa hkn ne lallai akwai MATSALA! Bisa kaina na doro tiren sbd ba ni iya dauka da hnn, akwai nauyi. Gimbiya ta tafi, amma shi yana inda ya ke, jallabiya kawai na ga ya saka. Na zuzzuba mishi komai, snn na hada mishi ruwan shayi (tea) kafin na zuba sukari na dube shi kadan. "wane adadi ne kake bukata? " "Au! Ni kike hadawa? "tmbyr tasa taso ta bani mamaki amma sai na sunkuyar da kai ckn girmamawa na ce. "Allah ya taimaka, duk kai nake hadawa karin kumallo"."To na koshi, dauke kayan ki ba na ce, ki ce wa Wacce ta aiko kin ba zan ci ba".A rasa new na dago Kai. "Allah ya taimakeka ba gardama zan yi maka ba, sai dai Ina rokonka don Allah ka rufa mini asiri ka amshi kalacin nan, lallai rashin amsarsa na iya haifar min da barin aikina a gidan nan". "So what? (sai me?)".Ya fada yana yarfe hannaye. Idona ya cika da kwalla na yi Kasa da murya. "Don Allah yallabai ka yi hkr kada ka yiwa kanka horon yunwa, ni matsalar Zata shafa". "Me Zata yi miki? "Ya tmby ni ."komai ma, ni dai kayi hkr ko na yi maka laifi? " Yanayin ydd na yi mishi tmbyr yasa na ga kmr ya dan tausayamin, sai yace. "Ba ni na hada Da kai na". Na yi saurin mika mishi kafin. Zaune nake har ya gama, sannan na kwashe kayan na fita. Lkcn da na dawo har ya shiga wnk, na yi hanzarin gyara gadon snn na share dakin. Na koma waje na ba shi mintuna 30, snn na koma. Har ya gama shiryawa, na yi turus! Jeans da T-shirt ya saka, maimakon Alkyabbar da na ga Gimbiya ta kawo mas. Na durkusa a gabansa. "Allah ya taimaki Yrm, kake bukata? "Ba tare da ya kalle ni ba yace."Ina bukatar a kyale ni na huta". Na dan sunkuya,"a yi hutu lfy". Snn na juya na fita. A bakin kofa muka yi kicibus da Gimbiya, na kwashi gaisuwa kafin ta shiga. Tuni yan rakiya suka tunga a bakin kofa. Ina can nesa zaune saman dakalin filawowi na hango ta fito rai bace. watakila wata maganar ya yabo mata marar dadi. Zuwa can shima ya fito, tuni 'yan rakiya suka fara zubda filawowi irin wdnd ake zubarwa Gimbiya masu kyau da kamshi. Ya daka musu tsawa,"kai mene ne haka?" Suka russuna, "Gimbiya ce ta aiko mu, wnn shine aikin mu"."ku bace mini da gani, bana so!"Tuni suka tsorata, "Don Allah yallabai ka yi hkr, Gimbiya ba Zata ji dadi ba matukar muka je mata da wnn sakon".Ya nuna su da yatsa, ku bace min da gani tun kafin ran ku ya baci, na ce bana so ku cewa Gimbiyar na ce bana so!"Da sauri suka bar wajen. Ya nufi wurin jimina yana bata abinci a baki suna wasa. sai fata rai a bace, Ina dai hng su da juyo abinda suke fada. Zuwa can shima ya fito, tuni 'yan rakiya suka fara zubda filawowi irin wdnd ake zubarwa Gimbiya masu kyau da kamshi. Ya daka musu tsawa,"kai mene ne haka?" Suka russuna, "Gimbiya ce ta aiko mu, wnn shine aikin mu"."ku bace mini da gani, bana so!"Tuni suka tsorata, "Don Allah yallabai ka yi hkr, Gimbiya ba Zata ji dadi ba matukar muka je mata da wnn sakon".Ya nuna su da yatsa, ku bace min da gani tun kafin ran ku ya baci, na ce bana so ku cewa Gimbiyar na ce bana so!"Da sauri suka bar wajen. Ya nufi wurin jimina yana bata abinci a baki suna wasa. sai fata rai a bace, Ina dai hng su da juyo abinda suke fada. "ka ce ba ka son abinda na sanya?" Ba tare da ya kalle ta ba yace. " kwarai kuwa".""sbd me?""Ba na bukata". Ya bata amsa kai tsaye. "Wai Yrm mai yasa kake son bata mini rakiya? " Ya ci gaba da wasa da jiminar kafin ya ce. "Kike batawa kanki dai, kin san ni ko wane ne mu, tsarin mulkinmu ba haka yake ba". "Mts! Ta buga tsaki, fuuu! Ta yi ckn gida. Na yi kadake Ina jimamin wnn al'amarin ko don yana ganin ya fita kyau shi yasa? Ni dai har lkcn tfyt yayi bai koma daki ba, yana ga waccan tsuntsu ba ya ga waccan, na yi tfyt. Rana ta 2 na iso da karin gwiwar aikina, sai da na gama da falon snn na shiga ciki, sabanin jiya yau idonsa 2 yana zaune a bakin gado, hnnsa rike da waya. Na karasa da sauri don Kai gaisuwa, ya amsa fuskarsa babu yabo babu fallasa. Na mike don zuwa kewaye na wanke ya dakatar da ni. "zauna, ynz me Zaki yi ne?" Na ce, "zan wnk kewaye ne kafin a gama hada kalaci ka kimtsa, sai na gyara nan din"."Barshi, bude durowar can ki fiddo duk kayan da ke ciki, ki Kai su falo ki zo ga jaka can ki jera mini wadanda ke ciki". Gabana ya yi mummunan faduwa, tsadaddun kayan da aka yi mishi oda daga kasar ingila zai fitar? Lallai bai nemi zaman lfy shi da Gimbiya ba, wane irin mutum ne shi mai wuyar hali haka? Ckn aikin nake, amma Ina wnn tunanin har na gama, snn na fara jera masa nashi. Ya mike tsaye ya ce."Fiddo mini kala 1 wnd zan sanya kafin na fito wnk". Kmr mai koyan magana, na ce,"To".Na rasa wnd zan fidda masa duk ya daure ni a ydd na fahimce shi mutum ne wnd ba a yi masa gwaninta, sbd salon wulakancinsa ya sha bambam da na Gimbiya, Na ci gaba da karanto addu'o'in samun sauki da kare fitina, domin Ina gujewa wulakancin wnn mutane, musamman shi da na fahimci tsaye yake, ita kanta Gimbiyar shakkarsa ta ke yi. Wani farin boyel ne mara nauyi, ma'abocin taushi da laushi na ware masa cike da fargabar kada ya ce ba ya so, ko ya gwasale ni. Da sauri na kammala shiri tare da ficewa dakin bana son ya fito wnkn Ina ciki haka Ina ganin bai dacewa ba ne. Idan ya gama kintsawa na dawo na gyara sauran wuraren da suka rage. Na fada kicin don hado abin kari, na tarar da su Rabi ita da Murja sun gama kammalawa suna zaune da Rabi'u mai tsaron kofa sai tattaba su yake yi, inda sabo na saba da ganin haka, tun muna bangaren Gimbiya shi yasa har yau na Kasa sakarwa su Rabin fuska, ballantana shi sai sun ji motsi kaga gudu, amma da sun ga cewa ni ce za su dawo suci gaba. Ba ta su nake ba, sun san hakan. Na kwashi kayan na yi falo na sami kujera na zauna don kara bashi lkc. Ina yi Ina kallon agogo har kusan mintuna 15 snn na mike dai-dai lkcn da ya turo kofa zai fito. Na yi saurin durkusa ckn girmamawa, nace ,"Kalacin ne zan kawo maka, wlh tun dazu ya hadu laifi na ne kusan mintuna 15 ke nan Ina zaune don na bari ka kammala shiryawa, bayan ka fito wnk amma a gafarce ni".Shiru naji yayi, ga shi kuma a tsaye. Na dago Kai na sai naga yana murmushi, ya tsuramin ido. Na yi saurin sunkuyar da kai cikin faduwar gaba Ina mamakin kayan da na fiddo masan ne ya saka ba tare da ya sauya. Muna haka Gimbiya ta shigo, ta ci uban gayu sai kamshi ke tashi a jikinta. Ta dube shi, "wdnn kayan fa?""wdnd na tarar a dirowa sun ciken guri shi ne na ce a kwashe a fitar". Da sauri ta fita ba tare da ta yi magana ba. " Ke ba ni ruwan zafi na sha kin ji". Ya ce da ni. Yana ckn kalacin Dogarin sarki ya shigo Ina rakube ina jiran ya gama na kwashe kayan. Ya kwashi gaisuwa kafin ya ce. " Allah ya taimaki Yrm, sarki ne ya turo a yi kiranka da gaggawa"."Ina kalaci da na karasa zan kawo kaina". Ba dogari ba, ni kaina sai da na Kai duba na ga Yrmn. Hnkl sa kwance yana kurbar shayi, na jinjina kai Ina addu'ar Allah ya tserar da mu wnn mutumin ya fi Gimbiya IZGILANCI!!! Dogari ya fita sukuku, ya gama shan shayin ya dubeni, na yi saurin kawar da fuska sbd shi din nake ta kallo tun dazun. ,Ganin haka yasa ya fada fadin abinda zai ce, ya mike kawai ya yi waje. Daman a ka'ida dk abinda Yrm ya ci idan ya rage ni zan juye na tafi da shi gida yau ma kmr jiya na juye uban farfesun kaji da soyayyen kwai da agada ckn kwanona na rufe snn na rufe snn na koma dakinsa na gyara. Na bata lkc sosai wajen gyara dakin, sbd har zanin gado na sauya. Na goge ko'ina byn na gama shara snn na fesa abubuwan kamshi (freshners). Dakin ya yi ydd nake sonsa sosai, sai na fada bandaki na shige can kuryar inda ake wanka na fara wankewa, sai da yayi kal snn na fito.Yrm na gani tsaye ya gama fitsari, Allah ya taimake ni ya maida wandonsa yana kokarin fita ne na fito, shima da alama bai san Ina ciki ba, hnn na jage-jage da kumfa. Na tsorata kwarai da gaske, na zube Kasa ckn kidima da fjrgici, kwalla na shatata a idona, kukan da mutum kan yi a lkcn da ya ga samu rashi kuma ya gitta. "Na tuba na bi Allah na bi ka Yrm. ka taimakeni ka yafe mini, kwarankwatsa dubu ban San ka shigo ba, don Allah kayi mini rai ka yafe mini?" Abin mamaki sai naga yana murmushi tare da fadin. "Tashi tsaye, kewaye kike, mike babu komai ni ne zan baki hkr sbd laifi na ne". Nan take na saki ajiyar zcy tare da goge kwallana na dan rusuna na ce "Nagode kwarai, amma Ina rokonka da kar ka fadawa Gimbiya matukar ta ji karshen aiki na ya zo a gidan nan ". Ya kara murmushi ,ya ce ,"kwantar da hnklki na yi miki alkawarin babu wnd zai ji wnn maganar".Yana fita na fadi Kasa dabas! Ina godewa Allah, ni dai Allah ya dorani saman Yrm wasa-wasa yana daga mini sosai. Lkcn da na fito yana kwance saman gado, kaina Kasa na yi hnyr fita. Can Kasa naji muryarsa yana fadin."Idan kin huta ki kwaso kayan nan da kika fitar". Na rusuna ba tare da na dubi inda ya ke ba na ce, "To".Wane hutu gare ni lkcn da Yrm ya sanya ni aiki ko so yake yi Gimbiya ta shigo ta rafshe ni? Tas! Na kwaso su yace na jera su cikin jakar da ba kwashe kaya a ciki, Ina ckn yi Gimbiya ta shigo. Bakin gadon ta zauna ckn ' yar shagwaba naji tace masa."Ba ka shiryaba? ""Ina zamu je?" Yayi maganar ckn halin ko'in ku "Haba Yrm tun jiya fa da marece na Snr da kai zamu je super market, kuma ynz ma da muka fito fadar sarki na kara tuna maka"."ki maida tfyr zuwa gobe, yau na gaji da yawa". "Aikin me kayi?"Ta bukata. Yace,"Noma". Ta ce,"Humaira taso ki fita". Na yi zubur daman jiran haka Yace ke zauna kici gaba da aikin dana sanya ki. Haba yrm mgn fa mukeyi idan muka gama ta dawo ta karasa, saidai keki tafi idan ta gama kya dawo ki karasa tunda maganr ta zamar miki dole. Ya dubeni cikin fada yace nace kici gaba da aikin gabanki ko zata hanaki ne? Cikin tsananin fushi tabar dakin na juyo ina hawaye kamar famfo sbd na tabbata niya jawowa bala'in, sharben dana keyi yaji amma baice komai ba sai tsaki da yake ta famanyi. Na mike zan fita yace zo nan, na dawo na durkusa har sannan hawayen basu daina zuba ba, me akayi miki? Tambayr tashi ba maraba da rainin hnkli, bakiji ni bane kikai shiru? Na bude baki a hnkli nace bakomi, shagwaba ce? Ya tambaya, wa zanyi wa? Na tmbayi kaina, kina jina na girgiza kaina, dakin san yanda kuka yake maidaki da baki dinga yi ba, tashi ki tafi. Maganrsa ta tsaya min a rai matuka. Karfe 2 na isa gida na tadda inna tayi mana danwake nayi sallama na karasa bakin murhun, sannu da aiki inna yauwa sannu humaira ya aikin.... Maganr ta sarke mata yayin data kalleni cikin kulawa, ya naga kamr kinyi kuka? Hawaye suka zubo min kafin na fara bata lbrn abinda ya faru ta jinjina kai cikin tausayawa ,kiyi hakuri humaira Allah yana tare dake kedai ki sanya tsoronsa a cikin zuciyarki kuma komai zakiyi kisa a ranki yana ganinki. Inna bazaki gane ba... Iyakar ganewar kenan tunda na ambaci Allah kuma komai a duniya idan akace Allah an gama saimu bar lamarin a hannunsa, nayi shiru, tace dauko kwano na zuba miki danwaken da zafinsa nasan kinason me zafi. Nadan bata fuska cikin nuna damuwa nce wllh inna kinason wahalar da kanki yau ma kiga uban abincin danazo dashi ina maganar ina bude kwanon da ledar dankalin yau naman ma yafi na kullum yawa. Tace nasan haka nima kwadayin danwaken yasani yinsa. Inna banason kina wahala kinga hayakin nan matsalane ga lfyrki batace komi ba har muka gamacin danwaken nace yau kam inna gsky bazanje Islamiyya ba kaina ke ciwo, Sumayya tace yaya malam yace mu fada miki wann watan ma an yafe mana kudin wata nayi murmushi Allah ya saka da alhairi inna tace ameen. Da safe kamar kyllum nagama bayan nagama duk aikina yauma idonsa biyu amma ya barbaza takardu akan gado yana rubuce-rubuce akai. Na gaisheshi ya amsa min a takaice sbd aikin yasha kansa. Harna kammala komai yana nan sannan na fita na kawo masa kalaci lokacin yana kwashi takardun na ajiye cikin girmamawa sannan na koma gefe ina jira ya na kwashe. "Kinga nifa nayi wanka ina jiranki ne kizo ki bani kayan da zan saka, gabana ya fadi nayi saurin tashi ina bashi hakuri na nufi gurin kayan, to meyasa gimbiya bata fada min wannan ba ko mantawa tayi sbd ban taba sanin har kaya ni zan zaba masa ba na dade tsaye sai nayi la'akari da ranar na zabo masa jeans brwn kolo da shirt cream kolo mai ratsin layin red nd blue na ajiye akan gado ina karanto Innalillahi...a zuciyata. Abin mmki har ferfesun kan ragon yasha kai gsky yau yaci abnci sosai kwai da plantain ne kawai bai ci ba. Na kwashe kayan nakai kicin na ajiye sannan naje store na samo ledoji ina cikin juyewa kawai naga mutum a tsaye akaina ya kura min ido nayi saurin durkusawa nace ko yana bukatar wani abu? Ya girgiza kai naci gaba da juye abincin na ajiye bread din daban, ya wuce abinsa nagama na koma dakin na gyara wajen daya bata na ninke kayan daya cire na zubasu a kayan wanki. Falo ya dawo ya zauna abnd bai tabayi ba kenan anan gimbiyar ta tarar dashi yau kam yan arzikin suna kansa tunda fitowa 2 sai naga suna dariya.. ,Ganin haka yasa ya fada fadin abinda zai ce, ya mike kawai ya yi waje. Daman a ka'ida dk abinda Yrm ya ci idan ya rage ni zan juye na tafi da shi gida yau ma kmr jiya na juye uban farfesun kaji da soyayyen kwai da agada ckn kwanona na rufe snn na rufe snn na koma dakinsa na gyara. Na bata lkc sosai wajen gyara dakin, sbd har zanin gado na sauya. Na goge ko'ina byn na gama shara snn na fesa abubuwan kamshi (freshners). Dakin ya yi ydd nake sonsa sosai, sai na fada bandaki na shige can kuryar inda ake wanka na fara wankewa, sai da yayi kal snn na fito.Yrm na gani tsaye ya gama fitsari, Allah ya taimake ni ya maida wandonsa yana kokarin fita ne na fito, shima da alama bai san Ina ciki ba, hnn na jage-jage da kumfa. Na tsorata kwarai da gaske, na zube Kasa ckn kidima da fjrgici, kwalla na shatata a idona, kukan da mutum kan yi a lkcn da ya ga samu rashi kuma ya gitta. "Na tuba na bi Allah na bi ka Yrm. ka taimakeni ka yafe mini, kwarankwatsa dubu ban San ka shigo ba, don Allah kayi mini rai ka yafe mini?" Abin mamaki sai naga yana murmushi tare da fadin. "Tashi tsaye, kewaye kike, mike babu komai ni ne zan baki hkr sbd laifi na ne". Nan take na saki ajiyar zcy tare da goge kwallana na dan rusuna na ce "Nagode kwarai, amma Ina rokonka da kar ka fadawa Gimbiya matukar ta ji karshen aiki na ya zo a gidan nan ". Ya kara murmushi ,ya ce ,"kwantar da hnklki na yi miki alkawarin babu wnd zai ji wnn maganar".Yana fita na fadi Kasa dabas! Ina godewa Allah, ni dai Allah ya dorani saman Yrm wasa-wasa yana daga mini sosai. Lkcn da na fito yana kwance saman gado, kaina Kasa na yi hnyr fita. Can Kasa naji muryarsa yana fadin."Idan kin huta ki kwaso kayan nan da kika fitar". Na rusuna ba tare da na dubi inda ya ke ba na ce, "To".Wane hutu gare ni lkcn da Yrm ya sanya ni aiki ko so yake yi Gimbiya ta shigo ta rafshe ni? Tas! Na kwaso su yace na jera su cikin jakar da ba kwashe kaya a ciki, Ina ckn yi Gimbiya ta shigo. Bakin gadon ta zauna ckn ' yar shagwaba naji tace masa."Ba ka shiryaba? ""Ina zamu je?" Yayi maganar ckn halin ko'in ku "Haba Yrm tun jiya fa da marece na Snr da kai zamu je super market, kuma ynz ma da muka fito fadar sarki na kara tuna maka"."ki maida tfyr zuwa gobe, yau na gaji da yawa". "Aikin me kayi?"Ta bukata. Yace,"Noma". Ta ce,"Humaira taso ki fita". Na yi zubur daman jiran haka Yace ke zauna kici gaba da aikin dana sanya ki. Haba yrm mgn fa mukeyi idan muka gama ta dawo ta karasa, saidai keki tafi idan ta gama kya dawo ki karasa tunda maganr ta zamar miki dole. Ya dubeni cikin fada yace nace kici gaba da aikin gabanki ko zata hanaki ne? Cikin tsananin fushi tabar dakin na juyo ina hawaye kamar famfo sbd na tabbata niya jawowa bala'in, sharben dana keyi yaji amma baice komai ba sai tsaki da yake ta famanyi. Na mike zan fita yace zo nan, na dawo na durkusa har sannan hawayen basu daina zuba ba, me akayi miki? Tambayr tashi ba maraba da rainin hnkli, bakiji ni bane kikai shiru? Na bude baki a hnkli nace bakomi, shagwaba ce? Ya tambaya, wa zanyi wa? Na tmbayi kaina, kina jina na girgiza kaina, dakin san yanda kuka yake maidaki da baki dinga yi ba, tashi ki tafi. Maganrsa ta tsaya min a rai matuka. Karfe 2 na isa gida na tadda inna tayi mana danwake nayi sallama na karasa bakin murhun, sannu da aiki inna yauwa sannu humaira ya aikin.... Maganr ta sarke mata yayin data kalleni cikin kulawa, ya naga kamr kinyi kuka? Hawaye suka zubo min kafin na fara bata lbrn abinda ya faru ta jinjina kai cikin tausayawa ,kiyi hakuri humaira Allah yana tare dake kedai ki sanya tsoronsa a cikin zuciyarki kuma komai zakiyi kisa a ranki yana ganinki. Inna bazaki gane ba... Iyakar ganewar kenan tunda na ambaci Allah kuma komai a duniya idan akace Allah an gama saimu bar lamarin a hannunsa, nayi shiru, tace dauko kwano na zuba miki danwaken da zafinsa nasan kinason me zafi. Nadan bata fuska cikin nuna damuwa nce wllh inna kinason wahalar da kanki yau ma kiga uban abincin danazo dashi ina maganar ina bude kwanon da ledar dankalin yau naman ma yafi na kullum yawa. Tace nasan haka nima kwadayin danwaken yasani yinsa. Inna banason kina wahala kinga hayakin nan matsalane ga lfyrki batace komi ba har muka gamacin danwaken nace yau kam inna gsky bazanje Islamiyya ba kaina ke ciwo, Sumayya tace yaya malam yace mu fada miki wann watan ma an yafe mana kudin wata nayi murmushi Allah ya saka da alhairi inna tace ameen. Da safe kamar kyllum nagama bayan nagama duk aikina yauma idonsa biyu amma ya barbaza takardu akan gado yana rubuce-rubuce akai. Na gaisheshi ya amsa min a takaice sbd aikin yasha kansa. Harna kammala komai yana nan sannan na fita na kawo masa kalaci lokacin yana kwashi takardun na ajiye cikin girmamawa sannan na koma gefe ina jira ya karasa na kwashe. "Kinga nifa nayi wanka ina jiranki ne kizo ki bani kayan da zan saka, gabana ya fadi nayi saurin tashi ina bashi hakuri na nufi gurin kayan, to meyasa gimbiya bata fada min wannan ba ko mantawa tayi sbd ban taba sanin har kaya ni zan zaba masa ba na dade tsaye sai nayi la'akari da ranar na zabo masa jeans brwn kolo da shirt cream kolo mai ratsin layin red nd blue na ajiye akan gado ina karanto Innalillahi...a zuciyata. Abin mmki har ferfesun kan ragon yasha kai gsky yau yaci abnci sosai kwai da plantain ne kawai bai ci ba. Na kwashe kayan nakai kicin na ajiye sannan naje store na samo ledoji ina cikin juyewa kawai naga mutum a tsaye akaina ya kura min ido nayi saurin durkusawa nace ko yana bukatar wani abu? Ya girgiza kai naci gaba da juye abincin na ajiye bread din daban, ya wuce abinsa nagama na koma dakin na gyara wajen daya bata na ninke kayan daya cire na zubasu a kayan wanki. Falo ya dawo ya zauna abnd bai tabayi ba kenan anan gimbiyar ta tarar dashi yau kam yan arzikin suna kansa tunda fitowa 2 sai naga suna dariya. Nansuka kusa yini don ni har lokacin tafiyata anan na barsu na harhada kayana nayiwa su Rabi sallama na tafi. Misalin karfe shida saura kwata na dawo islamiyya natarar ciwon inna ya tashi abun yau yafi na kullum hnklina ya tashi na rude na shiga neman maganinta bangani ba kusan 7* ina tambayarta amsa ta gagara duk inda nake zato na duba bangani ba na dinga kuka nan da nan na fyalla shagon dayyabu na fada shagon kamr mahaukaciya ina fadin dayyabu ka taimakeni don girman Allah ciwon inna ya tashi ka bani inhealer wllh an kusa biyanmu a gidan sarki kasa a lissafi..... Ke fitar min a shago bazan bayarba...! Na rushe da sabon kuka na durkusa ina rokonsa amma ko a jikinsa naga cewar babu Sarki sai Allah (dama shi kadai ne Sarkin) sai kawai nabi hanyar gidan a guje watakila su Aisha sun dawo sun san inda ta aje adaidai kwanar lungunmu wata rantsatstsiyar mota tasha gabana neman yanda zanyi ta kaina nake bata ita nake ba abun mmki sai naga amira ta fito daga motar ta taho ta rikeni humaira lfy kika gigice kamar mahaukaciya? Nace wllh Amira ciwon inna ne ya tashi narasa maganinta, SubhnAllah dama tare muke da yarima gashi can a mota yace na rakoshi (chai! Diaris God ooo! Har anzo gurin?) Nayi saurin fiddo da idanu yarima? Lfy? Meya kawoshi gidanmu? Tace kinga yanzu ba wann tym din tambayoyin ta karasa mota cikin sassarfa. Da sauri naga ya fito zo nan! Ya kirani da sauri naje shiga mota! Kamar jira yake ya fizgi mota da gudu ya nufi wani katon shagon magani ya shiga gudu ya siyo magunguna ya kara fitowa da gudu ya kuma fizgar motar har gidanmu na fito guje ya bani inhealer daya na shaka mata na kara shaka mata sbd ta riga ta gama galabaita cikin less dan 20seconds ta sami kanta nnayi ajiyar xuciya sai sanann na farga da yarima dake tsaye na janyo jakar kayana yana kallo na fiddo zaniin shiga taro na shimfida masa akan kujerar katakon na umarce shi da ya zauna, sai kawai ya yane zanin ya mikomin tare da zama akan katakon na sunkuyar da kaina ya kalli inna cikin girmamawa yace sannu ya jikin? Tace da sauki yace Allah ya sawwake, ya miko ledar yace magungunnan nan danAllah a daina bari suna karewa nace inna yarima ne fa mijin gimbiya ta kara kallonsa mungode fa mungode yace bakomi inna zan koma Allah ya kara sauki tace ameen. Nida Ameera muka rufa masa baya har bakin mota na durkusa har kasa nace masa nagode da taimakon da kayi min Allah yasaka da alhairi ya biya da gidan aljannah (nima nace ameen) Yace amin Allah ya bata lfy, Amira tace Allah ya taimaki yarima ni daganna zan karasa gida tym din tashina yayi, yace badamuwa mu kwana lfy ya figi mota yayi gaba nayi ajiyar zuciya na dubi amira nace lfy yarima yazo gidanmu kuma ya akai yasan unguwarmu daya? Ta kalleni sosai tace muna tsaye ni Rawila muna ban ruwa in gaya miki ya fito a hanzarce sai naji yana cewa wasila ke xonan ina wann yarnyr da take gyara min sashena? Tace wa yallabai? Yace yar farar marar jiki zaki ganta magana ma bata dameta ba ya daka mata tsawa ke yar doguwar nan nake nufi wacce bata fiddo gashinta waje. Nan da nan na ganne ke yake nufi na rugo nace ko humaira kake nufi yallabai zaka ganta kullum tana nade da carbi a hannunta? Yayi saurin cewa kwarai ita ce kirawo min ita yanzu tana ina? Ya karasa mgnr yana dube-dube, nace tana gida dama aikin safe takeyi yace kinsan gidan? Tambayr ta bani mmki amma nace eh yace muje ki rakani, wllh gimbiya batasan ya fito ba kuma kinga da kanshi ya tuko motar, na dubi amira nace ko lfy yazo nemana amma wata kila wani abun yake nema bai gani ba shine.....wllh bashi bane na fahimci sonki yake baki lura da kallon da yake miki a dakin inna ba. Na kyalkyale da dry amira baki da hnkli kawai na fahimci yarima mutum ne me tausayi kawai yana tausayawa rayuwarmu ne Yanzu ko daura min shi akayi amira ina zan kai yarima? Zata kara mgn na daga mata hannu kibar maganar nan kin jahilci yarima ba haka yake ba a dole tayi shiru, bayan na rakata na isa gida na tadda inna harta tashi, tace yo ke ashe wann maganin ba irin wanda nake sha bane na amsa na duba sainaga babban ne me tsada ya siyo a kwalinsa me 24 kuma da gani zai dade bai kare ba sbd yafi wancan girma da karfi nayi murmushi nace ai wllh mungode. Ina kuka hadu ne? Nace wllh inna Allah ne ya kawo yarima na bata lbr kamr yanda mukayi da amira har yanda mukayi da dayyabu. Ta girgiza kai kawai tayi ajiyar zuciya hrt har 2* kafin tace Allah kenan buwayi gagara misali donAllah gobe ki kara yi masa godiya, nace wann ai dole ne inna sumayya da Aisha sunyi tsuru-tsuru sun kasa cewa komai na wasance su sbd naga sun kidima, da wuri muka kwanta bacci yau a gidan *****Gimbiya ta kwala min kira na juya da sauri ina mmkin wann sammako tare da adduar Allah ysa bata ji lbrn zuwan yarima gidanmu ba, ta mikomin doguwar takarda kibawa yarima idan kin shiga na karba nayi wata irin ajiyar hrt, harna gama komai bai tashi ba na kawo kalaci na zauna ina jiran tashin shi. Tunani kawai nake in banda rashi da talauci wann aikin bai dace da yar musulmi, katon namiji yana kwance a gado ni ina dakin kuma ba muharramina ba na daga hannu ya Allah ka karemu daga sharrin shaidan. Na mike na dauko masa kayn da zaisa na aje a gadon. Sai 12:30 ya fito ina zaune a gefen kujera daga kasa yazo ya zauna a kujerar dake fuskantata nayi zaman yan makaranta na gaidashi ya amsa ya tambayi jikin inna da sauki na fada ina murmushi na sake satar kallonsa nace gsky naji dadin hallacin dakai min jiya bazan taba mantawa ba inna tace a kara maka godiya ya kalleni yace ba wani abu kije ki kawo kayan kalaci, harna kai bakin kofa yace waya baki takarda kikawo min? Nace gimbiya ce ita gimbiyar tace ki ajemin takarda kibani a hannuna? Da sauri na zube cikin kidima na rantse da wanda raina ke hannunsa babu ruwanta naga cewar kana bacci kuma..... To ki dauki takardar ki mayar mata yanda ta baki na kalleshi idanu jajur kayi hakuri laifinane, Humaira kinada matsala wllh abu kankani saiki tada hnklinki musmmn aka ambaci gimbiya a ciki ba aikoki tayi ba? Na daga masa kai to ni kuma na aikeki. ,Na mike kamr wacce kwai ya fashewa a ciki tana falo ta kalleni cikin kulawa lfy dai ko? Na durkusa na mika mata nace yarima yace na kawo miki ta amsa ta bude sai naga tana murmushi kice masa nagode, na juya cikin kwarin guiwa naje na gaya masa harna fito yace Humaira zo nan, ya nuna mini wuri na durkusa na sunkui da kai ina sauraronsa jiya inaso na tambayeki na mance ina babanku? Ya rasu! Yafi 6mins baiko motsa ba,dama inna ita kadai ce? ,Nace amsa masa uhm ita kadai ce, yayyenki nawa? Nace nice babba, wadannan yanmatan kannenki ne? Nace eh, sunawa ne? Su biyun daka gani, skul fa? Na daina zuwa amma su zasu koma wann hutun idan an koma, kefa? Nayi shiru, kinji? Baki magana ne? Nakasa cewa uffan wllh saina sami bakina da yin nauyi, tashi ki tafi to tunda na bata miki rai kiyi hakuri (wai shema tana kallon daukaka) tsoro ya kamani ni wacece da yarima zai bata wa rai har ya bani hakuri, wann abu kamr asiri nakasa cewa kala, ya dan sassauta murya yanzu ya kikeson ayi kinki magana nace ki tafi kinyi jugum? Magana tana miki wuya ko? Na girgiza kai yayi murmushi yace to tashi ki tafi na mike na nufi kicin na fice ta kofar baya na tarar da mutanen ana sana'ar ko kallonsu banyi ba nace Allah ya ganar daku, wata irin yunwa nakeji na debo kalaci cikin wanda ya rage a bakar leda dankaline da kwai na tafi can baya na zauna inaci kamar daga sama na ganshi wani irin kallo yake min na tausayawa yace donAllah zauna kici kalacin ki na zauna amma na kasa cigaba da ci, a gsky baki kyauta ba dama baki kalaci ba ki hau aiki tun safe sai yanzu kusan karfe daya da kwata? Ya karasa zancen yana duba agogonsa, Nayi dan murmushi wllh na karya tun a gida yanzu ne dai na dan jin yunwa, bai kara mgn ba ya wuce abinsa. Suna zaune shi da gimbiya a saman wasu kujeru na fito da shirina cikin wata kokakkiyar atamfata kafata sanye cikin kodadden silifas da hijabina har kasa na wuce su ina ga yau ce rana ta farko dana taba tafia gida ya bini da kallo harna tsargu, gimbiya ta ware murya ta kirani na taho da sauri na zube gabansu tace yarima yace ku ba'a koya muku bankwana bane? Kafin nayi magana gimbiya ta surfan zagi dama bakice masa zaki tafi ba ko yana bukatar wani abu? Jikina ya dauki rawa yace tayi min bankwana dazu yanzu ne dai batayi min ba (Allah Sarki yarima bai san za'a zageta ba) kana bukatar wani abu ne da zata yi maka? Yace a'a to meye nayi mana wani bankwana keyi tafiyarki, sai naji yana dariya nidai har tuntube nakeyi don sauri ina isa natarar da inna sun shirya cikin kayan da basu da wata nagarta tausayin kanmu ya kamani nace sai ina kuma inna? Tayi murmushi tace ai nayi babban kuskure na manta yau ne ake bikin Harira yar gidan babanku Auwalu raina ya baci amma na kasa nunawa sai nace shine zaku tafi yau baku hakurin gobe? Ta dan harareni suwaye masu aikin abncn idan ba muba? Nace kai Inna har yaushe zaki dinga wahalar da kanki akan wann mutanen da basu san ciwonki ba cinmu da shanmu da suturarmu da uwa uba karatunmu? Ai ba 6angaran dahuwar zan tsaya ba,kinga akwai gyaran kayan miya,yankan albasa,alayahu,fere ka6ewa da sauransu".na ta6e baki kawai.na sauya maganar da cewa,"cikin satin nan naji ana cewa za'a biya mu saboda haka gaskiya inna har dunkuna sai munyi". Kuruci dangin hauka,in ba hamaira ba yaushe ana ta ciki za ai ta tsumma?Allah dai yakawo albashin lfy,biyan bashi dai shine farko idan Allah yaso". Nace,"Amin". Na fiddo abincin da nazo dashi,suka ci suka yi kat,sannan ta mike,"kiyi kokari ki lega gurin 'yanmatan kafin lokacin islamiyyar". Da kai kawai na amsa mata. Ta yi murmushi,"mgn ku,a ta kulle?" Na dai yi shiru."Don Allah kada kije kiyi wannan miskilancin cikin jama'a,ki saki jiki wani abun daurewa ake yi". Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Subul da Baka 1 page 2 Posted by ANaM Dorayi on 06:04 AM, 21-May-15 Under: Subul da Baka * Na dai yi murmushi kawai ta fita tana fadin."Hali zanan dutse".na dan watsa ruwa sannan na fiddo wasu riga da siket a sosassen leshi wanda akalla zai yi shekaru 4,yana 1 daga cikin na ganin sarki wanda nake takama da shi. Na yayyyafa masa ruuwa tare da bigewa saboda cikwikwiyewar ta tashi.farin gyale duk. Ya tashi saboda tsufa na yafa,sannan nasaka takalmin robata na zuwa biki,ko suna ruwan hoda. Na fito tare da jawo kofar gidan nadan sanya tsinken kara da dan icce gurin hancin na kulle kamar yadda muke idan zamu fita tare da kudurtar insha Allah da an biya mu kudi zan sawo mana kwado. Tafe nake kaina a kasa na wuce gungun samari kusan 5,kwanar karshe da zan bita kai ni kofar gidan nayi karo da wata majalisar. Na dan gifta kadan na ji wani yace,"kai yarinya har yarinya amma ba galihu".karaf naji wani ya amshe,irinsu kuma sai shegen girman kai na banza, waccan yarinyar ita ake yiwa kirari da danwake kafi ubanka,a unguwarsu gidansu na dan nesa da na su ibrahim balarabe,an ce girman kan tsiya gareta saboda..." Maganar tayimin nisa,ban karasa jinta ba na shige gidan kawai inda sabo na saba da irin wadannan maganganun bakin samari,shi yasa bana mai da kai.dalili kuwa shine ina yawan yin samari da farko,amma duk wanda zai zo sai ya yi amfani da talaucinmu ya nemi yi mini maganar banza,korar karen da nakeyi musu ne yasa suke yi mini shaidar mai kashin tsiya,kuma girman kan tsiya gareni,sannan danwake ce ni. Na kan yi mamaki,TALAUCI HAUKA NE? Ina ganin tsira da mutumcin 'ya mace shi ne babban arzikin duniya da lahira. A nawa fa tunanin. Kamar duk lokacin da hidima ta tashi a kullum muna raku6e gefe,haka ma wannan lokacin.zaune nake kusa wasu tsofaffin maroka ina kallon kowa yadda ake shagali bare wanda bai hada komai dasu ba,ya fi ni sakewa da gata saboda BABU.... ,Babu wacce ba ta ganni ba,amma ko kallon arziki har aka kira la'asar ko ruwa na shiga nace,"yaya harira sai Allah ya kaimu". Tayi watsi kamar ba taji ba,na kara maimaitawa,ta daka mini tsawa,"naji". Na juya cikin abokanta naji wata ta ce "kin sallame su?" Ta ce,"wa?" Ta nuno ni da yatsa,"ba 'yar marokan can ba ce?" Na dan juyo dan kallon wacce ta yi maganar. Ta yatsina fuska, "wai 'yar uwarmu ce". Dayar na zaune da waya a hannunta tana latsawa tun shigowata ta kyalkyace da dariya,tare da fadin,"shegiya harira,wato wai ma ne?" Gaba daya dakin ya dauki shewarsu,ni dai na yi waje ina mai takaicin irin wannan salon wulakancin,a ce duk sabga da salon irin wanda za ayi mana? Dama waecan karon an kira inna da 'yar aikin gida. A tunanina zan tarar da su inna su ma sun dawo saboda zuwansu Aisha islamiyyar,sai na ga cewa ba su dawo ba. Na dauki littatatfaina da hijabi bayan na gama sallah na fito... Shekara 2 da suka wuce nayi saukar alkur'ani,yanxu ta 2 zanyi,wacce nake hadda,ga shi na gama littattafai da dama kamar su;ZADUl MUSLIM,HAKKUL MUBIN,KHAMSUNA HADITH,HUSNUL MUSLIM,BULUGUL MARAM...kai za su kai 12 yanzu wasu sabbi muka shiga irin su,ma'anar addu'a da fassarorinta,tarihin Annabawa da kissoshinsu,da sauransu. Acan na tarar da su sumayya suka ce daga gidan bikin suka taho,inna sai anjima na kada kai kawai cikin raina nace ba ta gama bautar ba ko? A gida muka tarar da ita bayan mun tashi da nairarmu 300,wacce aka bada sadaka wani bawan Allah ne ya kawo.tun a hanya na siyo mana taliyar leda daya,naira 110.magin 20,gishirin 10 sai mai na 20 kwanti. Na san muna da dan sauran busassen tattasai muka rago 150,su Aisha sai tsalle ake yi gobe za a yi kalacin koko har da kosai. Ba karamin dadi wannan labari ya yiwa inna ba,na ba Aisha ta siyo mini icce na 20 ashanar 5. Nan da nan na dora dafadukat taliya.saboda rashin kamawar iccen ya sanya ana kiran isha'I na sauke. Bayan munyi sallah na zuzzubawa kowa na gyara wurin na kauda duk kayan da na yi amfani da su,sannan ni ma na karasa saman tabarma nan waje farin wata ya haske ko'ina. Lomar farko almajiri yayi sallama da robarsa a hannu nayi saurin hadewa da hanzari don samun damar amsa masa sallamar. "Ance ana magana da humaira". Wani gululu ya taso mini, dama na hango tsayuwar mutum jikin katangarmu tunda karamace,nasan cikin 'yan iskan samarin nan ne saboda yau na wuce majalisa da yawa,shi yasa ban ciki son zuwa gidan baba Auwalu ba,unguwar da hanyarta kamar nan aka tara samarin KANO! Ko motsi nakasa yi har yaron ya fita da amsar inna,wato. Tana zuwa". Na fi minti 5 a haka cikin nuna fushi inna tace. Baki da halin zuwa kika sa nayi karya?.Raina ya kara 6aci,wani abu sai iyaye,shin inna ta manta da cewar abinci nake ci? ko kuwa nice na ce ta byr da amsa? "sai kin gama shawara Zaki tashi?"Ta katse ni tana fada . Na mike kawai ba tare da nace komai ba. "wnn miskilancin? wnn miskilancin?? Allah ya rabaki da shi Humaira, ace duk aikin duniya babu mai miki wuya sai MAGANA? "Na dan yi murmushi lkcn da na sako hijabi, maganar taso bani dariya, Inna kenan. Na fada a raina. Wani kamshi ya doki hancina, kamshi mai kwantar da zcy da tarwatsa tunani zuwa wuri guda . tsaye yake ya jingina da katangar hnnynsa goye a kirji. Na kasa klln fuskar na dan jingina ni ma dan nesa dashi kadan muna fuskantar juna. Ya yi magana shiru! har kusan 25mins a kiyasina. Tun Ina daurewa har tsayuwar ta fara gundurata, km da alama ni kadai yake kallo. Gaba da gabanta, na fada a zuci, Inna da mutanen gari na kirana MISKILA, yau ga wnd ya shafeni. A tunanina shi yazo ba tare da na gayyatoshi ba. Wasa sabon aji hr ana neman kusan 40mins haushi ya turnikeni, wnn wulakanci da yawa yake, amma zan ba shi 20mins nan gaba, matukar bai yi magana ba to zanyi tfyta. "Kai zo nan".Tattausar muryarsa ta katsen lkcn da ya kira wani almajiri.Tsoro, fargaba da kuma razana duk a ckn wdnn 'yan sakanni suka shige ni, na dago Kai tare da kallonshi. Tuni ya maida kallonsa ga yaron, har ya karaso. Ya ce "shiga ciki ka ce YARIMA ya ce yana son shigowa ya gaisa da inna". Na sunkuyar da kai ckn jin kunya, da kyar na kalato klm 3, "wlh ban San kai ne ba..."Yaron ya fito, "Ta ce, ka shiga".Ba tare da ya kalle ni ba, ya gitta ta gabana tare da wucewa ciki, sai a lkcn na lura hnnynsa akwai leda baka. Simi-simi ckn faduwar gaba na rashin kyautatawata na bi bayansa... ,Aisha,sumayya duk sunyi barci anan inda muke zaune inna ta bashi tabarma ita kuma ta dan tsugunna a kofar daki. Na dinga addu'ar Allah ya sanya su sumayya basu zubda taliyar ba,saboda fararen kayansa karsu nadi manja?."Mun same ku lfy? Ya fada a hankali,sai ka ji zaka san irin su magana na basu wuya. Inna tace lfy kalau,ya kuke? Lafiya ya fada a gajarce. Na koma kusa da inna na tsugunna ni ma. Sai dayayi 'yan mintuna 2 kafin ya ce,ya jikin? Tace "Alhmdllh". Ya bude ledar ya fiddo magunguna. Ga wadannan. Ya mika mata 1 wannan kuma 1 ne kwal zaki shanye a daren nan. Sai wadannan sau uku-uku guda 2 kowanne kullum. Mamaki ya kamani,ashe yana bayani?shi kawai nake kallo. Ya fiddo wani abu a gaban aljihunsa. Sai wannan allura ce idan ba zaki damu ba zan yi miki ita yanzu ta kwana 3 ce yau,gobe,sai kuma jibi a hannu akeyi". Na kara yi masa kallo 'likitane ? Na tambayi kaina,dama 'ya'yansarauta na karatu?shin yarima TAUSAYI gare shi ko kuwa KIRKI? "Me zai hana yarima,wlh ayi mini ina so,na kuma gode,Allah ya biya".inna ta fada. Ya taso hr kusa da ita, abn mamaki sai naga ya rage tsawo. Yana gamawa ya dan kalleta ckn murmushi, " Inna da zafi? " Ckn -yar dariya ta girgiza kai. Ya mike tsaye yana fadin. " Don Allah a sha maganin akan ka'ida.Mu kwana lfy".Ya juya abinda. Na yi saurin mikewa na bi bayansa tun kafin inna ta gargadeni. Har ckn Lungu na bishi nufina sai zai shiga mota snn na bashi hkr, amma sai na ga ya dan tsaya are da juyo wa. "Za ki bi ni ne?" Na yi turus! Ba motsi. "Idan Zaki bi ni ne, to mu tafi. idan kuwa ba Zaki bi ni ba ne koma gida".Ya nuna mini hny da yatsa. Na yi wani dummy!!! kunya ta kamani ainun, shin mai zan kira hkn da ya yi mini, dizgi ko wulakanci? Ya dawo baya, "mu je!!"Da sauri na juya hr bakin kofa ya Kai ni ba tare da wani abu ba, ya juya kawai abinsa. "wnn Yaro Humaira Allah ya dasa masa tausayinmu".Maganar da Inna ta tare ni da ita ke nan. Na yi murmushi kawai. "Tunda yazo ashe abin na damunsa, wlh mun gode, Allah ya nuna mana aurensa da Gimbiya".Na ce,"Ameen".Ckn rai. Kasa cin taliyata na yi, na rufewa su Aisha da safe su dumama. Yau na dan makara sbd lkcn da na isa kusan 7.30 hr ta gota. Na tarar da 'yan aikin safe an tara su a falo maza da mata. Gabana ya fadi, ko a gabansu zai koreni? Nima na yi hanzarin shigowa tare da samun wuri na durkusa. Sanye yake cikin shiga ta alfarma,wata rantsatsiyar alkyabba ce ya saka ciki kana hango kayan sakin da ya zuba kansa da hula irin ta sarakai,yau ya fito a matsayinsa na (PRINCE)wato yarima mai jiran gado a kowane lokaci. Gabana ya fadi lokacin da muka hada ido nayi saurin saukar da kaina kasa.yau mulkin yake ji,ya dago hannu,dogarin sa dake tsaye yace. "Yarima na amsa gaisuwarki". Duk muka sunkuyar da kai alamar godiya. Ya dan gyara murya. Dogari ya yi saurin cewa. "Magana ta 2 kowa ya nutsu inji yariman gimbiya". A tausashe yace,Na hana zuwan maza cikin gidan nan iyakarku waje,saboda aikin cikin gida na mata ne. Ina sane da ta6arar da ake aikatawa". Nan da nan mutane na ido ya raina fata. Ya kara da cewa.""ma'aikatan abinci Ina son daga yau a kara yawan abin da ake ba ni, ya na yi min kadan".Duk suka amsa da, "An gama yarima " ya mike tare da shigewa ciki, kowa ya tashi tare da kama tsaginsa. Na gama da ko'ina snn na shiga ciki, yana zaune dirshan saman kafet da takardu baje a Kasa, shigowata wayarsa ta fara kuka. Ganin ya kanga a kunne yasa na shige kewaye kafin na karasa shima ya gama na Kai gaisuwa tare da ban hkr. Aiki nake yi, amma Ina jin hirar tasa wadda na tabbatar da mahaifiyarsa yake yi, sbd jin ya ambaci MAMEE. "kun tashi lfy?"Ya kara narkar da murya yana shagwaba ya ce, "Ni kam Klum Mamee... wlh har yanzu bana jin sonta. ,Don Allah a nemar mini afuwa gurin mai martaba a janye auran nan. Da yake ba na jin abinda ta ke cewa,ya kara shagwa6ewa har ina mamakin kato dashi da shagwa6a. "Mamee HAMEED din ki ne fa,don Allah ki taimaka,wallahi ba ta da kunya.kullum sai ta kai karata ga sarki. Na jinjina kai tare da maimaita sunan 'HAMEED'wato sunansa ke nan. Ni dai mamee kiyi wani abu,bana so!!! What? Ya fada da karfi,wallahi mutuwa zan yi ko na gudu na bar muku kasarku...o.k... O.k,to shi kenan,mom ina jira fa". Yayi murmushi,bye love you!!" Tare da ajiye wayar. Ya koma ta baya ya kwanta tare da rufe idanunsa duka,hannayensa yayi filo da su ba tare da ya motsa ba. Na dawo wurin kansa daga nesa na durkusa. "Brk da asuba". Da sauri ya bude idanunsa, sun yi jawur ga su tubarkalla ya dallo mini su tare da maidawa ya rufe.Na daure na cije sbd ni ce Kasa, na ce." Yrm !!!"Da sauri ya tashi zaune yana mai kara shigar da kallonshi gare ni. Na yi Kasa da kai, na kara yin yaki wajen furta klmr. "Don Allah ka yi hkr jiya..."sai kuma mgnr ta makale ta Kasa fitowa. Ya jinjina kai,"Uhum? "Alamar na ci gaba yana saurare. "Ban San cewar kai ne ba wlh, a tunanina irin samarin unguwarmu ne da ke damuna". Ya daga kafadu tare da watsa hnn yana tabe baki alamar bai damuba. ,Na tashi kawai na fita tare da hado kalaci. Yanayin yadda ya ke cin abincin ya bani dariya a cikin rai,mutum sai ka ce mace,wallahi ko macce ta yi yangar yarima tayi kokari,sai yatsina yake yi abin har ya zamar masa jiki. Ya ture kayan har zan dauka yace,zauna ki ci a nan! Na dafe kaina,wannan mutumin na neman haddasa mini fitinar Gimbiya,ga shi ba a yi masa gardama. Na dan cusa kwan da dankalin tare da satar kallonsa. Na ce, na koshi". Ya kada kai kawai. Har nakai bakin kofa ya ce idan kin juye ki dawo". Nace to. Kawai na fice da sauri. Wata wayar na tarar yanayi sa'adda na dawo,amma yanayin wannan ya tabbatar mini abokinsa ne. Na yi tsaye na jingina da bango kaina a kas har ya gama. Dakin ya dauki shiru na wani lokaci. ,"Humaira".Ya kira sunana a hnkl. Na yi saurin dago kaina.ya shigar da idonsa sosai ckn nawa."Magana tana yi miki wahala ko?"Na girgiza alamar a'a. ya yi murmushi, ckn KASAITA ya ce. "Bata yi miki? Na daga kai alamar, 'eh'.Murmushi ya kara yi ya ce."To bani lbr..."Da sauri na kalleshi ya daga min gira yana bin fuskata da kallo. ana sunkuyar da kaina Kasa Ina wasa da 'yan yatsun hnn. Zuwa can na dago ido, ashe ni din yake kallo.Muka yi arba da juna ya kara saka mini murmushi, nayi saurin dauke kai. "Humaira ". Ya kara kirana a karo na 2.Na dago Kai ban yrd mun hada ido ba.yace,miskilancinki da jan aji har ya fi na 'ya'yan SARAUTA,da ana sauyi yau da kin koma GIMBIYA,ita kuma na mayar da ita BAIWA ta zama barorinki kamar yadda kika zamanto a cikin nata a yanxu. Gabana yafadi matuka. Ba zaki yi mini magana ba?.Nace zan yi. Yanayin yadda na fadi maganar ya sanya shi fahimtar gab nake da yi masa kuka. "Kin takura ko? Ya fada... Nayi shiru ina kallon babban yatsan kafata, Humaira! Gabana ya kara faduwa wai me yakeji idan ya ambaci sunana? Ko kuwa duk salon wulakancin ne zai ta takura min? Jin ya taso yasa nayi saurin dagowa kwalla ta taran min nace yanzu zan baka wllh yallabai lbrn nake hadawa....amma saida ya matso gabana gashi gab dani kamshinsa yana dokar hancina jikina ya dau kyarma addu'a nake Allah ya karemu daga sharrin shaidan ya sunkuya dab da fuskata yace kina da sarauta? Nace a'a to meya sanya kin cika TAKAMA? Nace kayi hakuri.Yace to bani lbr koda tarihinki ne yau sai naga miskilanci irin naki... Yace gaba na fiki rashin son mgn da miskilanci tunda na ajiye girman kai harna tambayeki dole ki gaya min har gidan ku naje amma kika kasa tambayata dalilin zuwana. Ya dalli bakina oyya am waiting.... Na kalleshi idona taf da kwalla nace ai kaga gidanmu ko? Ya kanne ido daya yace ban kula ba sbd duk na gama tsorata dashi... Mu kenan babanmu ya rasu ya barmu 6yrs kenan muna da yan'uwa da yawa a nan garin. Ya kalleni kin gama? Nace umm yace to saura ni na dago da sauri saura kadan mu hada fuska sbd ya dan duko, donAllah ka matsa na fada ina fidda kwalla. Baki so? Ya fada cikin maraitacciyar murya. Na ce,"eh". Sai ya koma saman gado ya zauna. "Ki shiga kowaye ki wanke fuskarki,kada ki fita a haka,ko kuwa ba komai ? Na yi hanyar fita. Zan wanke a kicin. Zaune nake dirshin ina tunani ban ga wurin aiki a nan ba,saboda idan haka halin yarima yake lallai shima yana layin 'yan unguwarmu. Har na tafi gida bai kara sanya ni a ido ba,duk tsanarshi tashiga zuciya ta.Da daddare na yiwa inna karyar barci zan yi da wuri don haka lokacin da ya zo da daddare yiwa inna allura sai ta ce ya shigo kawai. Ina jinsu ya share wuri ya yi zaune inna na yi masa labarai wanda shi ne ke mata tamboyoyin,sun dade kafin ya tafi. Da safe na yi shiri kamar na tafi na zame gidan su Amira na yi mata karyar daga can nake ba ni da lafiya shi ne aka ba ni izini ga shi inna ba ta nan tana gidan yini,ni kuma sai anjima zamu tafi party sai 2 na koma gida. Da daddare yazo,inna ta fada masa muna wurin walima. Washegari na wuce gurin walima abina. Wasa wasa sai da nayi kwanaki 4 banje ba,kullum ba ya tadda ni sai yau. Ina alwalar magriba na ga mutum a tsakar gida yana sallama. Gabana ya yanke ya fadi,tuni inna ta kabbara sallah. "Wurinki na zo. Ya fada tare da juyawa ya fita waje. Na zuro hijabi na kalli inna,na ce "inna yarima ke kirana a waje". Tayi gyaran murya,wanda na gane umarni ne ta bani na je din. Na sameshi waje ya harde hannayensa yana tsaye. Barka da isowa. Na fada a hankali. Ya kalle ni,zuwa na yi bada hakuri da neman afuwa,ina kuma biko don Allah a koma aiki na tuba idan halina ne kuma zan kara. Nayi shiru kawai ina mamakin mutum mai GIRMA matsayi yazo bani hakuri. Allah ya baki hakuri ya kuma huci zuciyarki Humaira, acikin raina nace yana kaunar sunan nan nawa. Kin jahilceni Humaira zuciyarki tana gaya miki karya lalai da kinsan waye yarima da baki shiga rudani haka ba but am sorry pls, shiyasa nakeson ki sami sakewa cos shiru shirun naki is too much kada ki sami wata cutar amma na daina kiyi hakuri 'bakomai' itace kalmar dana fizgo daga bakina na fada yayi murmushi to acikin abnd ya faru meya bata miki rai dani? Nayi shiru donAllah kiyi min magana ko sai munyi sallah? Da sauri na daga kai, to kawo min buta, na tsya ya gama alwalar yaceDako min tabarma nayi ta anan".Na zaro ido Ina murmushi har bakina ya dan bude kadan, sbd ya bani dariya, na ce."Gafa masallaci can".Na nuna masa da yatsa.Ya sosa keya kawai ya wuce yana murmushi.Na rasa abinda zan cewa inna akan zuwan Yrm, abin ka da wnd yasan hali sai kawai ta share ni.Ana karasa sllr isha'i ya dawo, na dakko tbrm a kusa da katangar tana kallon dakin inna, sbd bani son ta ji hirar har ta ganoni. Na leka nace "shigo ciki yallabai". Karshen tbrmr na zauna nesa kadan shi kuma ya zauna bisa daga farko. Ba tare da ya kalle ni ba ya ce, "kin fi sha'awar zama hakane, ko kuwa kina ckn takura?"nayi saurin kai guwoyina Kasa.ma'ana na durkusa. Ya dago Kai.... Ke nake sauraro,ko sai kin gama jan ajin? Na yi shiru saboda na rasa ta inda zan fara masa. Ya kuran ido wataKe nake sauraro... Nayi shiru sbd narasa ta ina zan soma yu kuran ido ga wata me haske kamar lantarki.. Uhm....uhmm...u hmmm..daman... Kai wani kaya sai amale wasu na fama da magana wasu kuma wahala take musu duk maganar nan bata wuce kalma uku ko hudu ba sbd iyakar zancenki kenan idan mutum ya matsa amma kin kasa furtawa, kinga dare yana karayi kada ki jawo min wata masifar bana son yawan korafi, nayi kasa da kai nakara rage murya nace kasan aikina yana da hadari kuma ance inda duk mace da namiji suka kebance na ukun su shedanne kuma gashi naga....... Kinga me? Nayi shiru bakiji? Ya maimaita.Uhm me kikace? Duk daya san ban yi magana ba. Ganin ka taso daga kan gado yasanya na tsorata, nafada kamr zanyi kuka yadan matso kan tabarmar tare da juyowa ya fuskanceni sosai ta hanyar jingina da bango, ya sassauta muryar nan tasa mai taushi "saurara kada kiyi kuka inna zata zargeki kota sani?" Nayi saurin girgiza kai yayi murmushi don Allah ina neman alfarma a dinga ce min e ko a'a tunda basu da tsayi kinji? Nace to da kyar, kiyi hkri bazan kara ba shikenan? Na sunkuyar dakai kawai naji kunya ko bakiyi bane? Nace nayi. Ina jin sautin murmushinsa ya kalleni inaso ki fahimceni zan fada gsky ba don na kare kaina ba wllh Humaira ko Qur'ani kika dauko zan dafa na rantse, duk me ya kawo haka na tambayi kaina, na girgiza kai, zaki amince dani? Na girgiza kai to wllh Humaira ban taba yin zina ba na rantse da Allah a turai nayi karatuna saida nayi 9yrs amma budurwata 1 itama hi hello ne tsakaninmu muna gama karatu muka rabu dama ita take damuna lokcn dana dawo kuma na tarar an hadani da Fareeda wato gimbiya a matsayin wacce zan aura ba don kuma ina sonta ba ganin ina kaukauce wa alamarin yasa aka yi min wannan kofar ragon,ga shi zuwan bai wani amfani ba domin ya kara min tsanarta maimakon na ji sonta. Wallahi ba ta cikin tsarin macen da nake son aure,ko mun dace? Nace,uhm. Ya kalle ni,nayi saurin daukar da kai. Uhm fa kika ce? Nayi murmushi. Magana zaki yi,domin shawara na zo mu yi ko ban isa ba? Kai isa mana,amma kayi hakuri zan yi tunani". Yanayin yadda ya tabbatar min da maganar ba karamin dadi tayi masa ba. Zuwa yaushe?"Jibi. Na fada. Yace, A'a,zan jira ki gobe da safe idan kin zo. Na yi shiru kawai ko ba zakizo ba? Nace ,insha Allah zan zo". ,yayi murmushi wai ke baki iya karrama bako bane humaira ko dan ruwa? Narasa inda zansa kaina kamr na tsaga kasa na shige don kunya, zan mike yace a'a zauna saida na roka Allah ko kin kawo bazan sha ba. Nasan dama barazana ce ba zai iya shan ruwan gidanmu ba kamr ya karanci hrt dina naji yace gobe ki tanadar min fura mai dadi na sha kinji? Nace uhm! Sbd tunanin bazai iya cin abncnmu ba yasa ko ruwa bana bashi. Ya mike zan wuce naga inna ta shiga ciki watakila ma tayi bacci ko bakya bacci da wuri? Inayi fada tare da mikewar nima, yar gayu' kalmar ta tsaya min arai ina ce yan gayu sune masu hira ba bacci da wuri ba? Muna kaiwa bakin motar nace Allah bamu alhair da sauri yace kezonan! Kibari na bashi fitila mana ko kinason fadawa kwata ne? Da rana ma mutum bai tsira ba balle dare wann lungun naku(kai yarima a hakan dai!) Ya mikon wayarsa na zare ido ki haska gobe kya taho min da ita, na juya baka gajiya zo humaira na tsaya batare dana juya ba ya karaso gabana natsani gardama donAllah ki daina ungo wayar nan ko wllh in yarda, jin ya rantse yasa na karba hannuna yana rawa jikina yana kyarma kirjina naci gaba da faduwa, kinji dadi? ,Nace uhm amma cikin raina fal haushi maimakon yabarni na koma sai cewa yayi zomuje mota nai miki kyauta ko bakya so? Maganar gsky idan haka halin yarima yake to banaso sbd banason yawan takura dayawan tambaya (kunji kinibabbiya) ace duk maganar da mukayi saiya nemi na bashi amsa kamr yasan zuciyata saiya dan duko yace kona dameki? Na bata fuska kabarshi kawai bakyaso? Na kalleshi cikin takaici na wuce wajen motar kawai sbd na tabbatar yarima mutum irin mai naci ya biyoni lalala! Ashe kin iya harara haka irin wann harar ai saikisa na kasa bacci a yau. Maganar tashi tayi min tsaye naita luguiguitata cikin kwakwalwata. Abin takaici sai naga ya fiddo da cakulet kwaya 1 ya mikomin harga Allah bansan sanda nayi dariya ba wacce har yaga hakorana shin ko dai yarima auta ne? Shima ya kara kura min ido yana murmushin nan nasa na kasaita mai kunshe da nishadi marar misaltuwa yace. "I can't express my feelings bcos of this beautiful laughing thank U so muc!" Duk cikin wann dogon turancin da yayi thank u din kawai na fahimta, na juya kawai jikina ya bani kallona yake bai tafin ba har na kai karshe layi zansha kwana na juya sai naga ya dago min hannu yana dariya. Inna na zaune na shiga tace yau kam ya dade lfy ko? Na zauna nace inna yarima na bani tsoro, tsoro kamar yaya Humaira? ,Wai inna shawara yazo na bashi akan gimbiya fareeda wai shi baya sonta, inna ta zare ido baya sonta humaira? Haka yace inna. Naci gaba da bata lbr da irin yawan tambayoyin da yake min. Zan baki shawara 1 goben ki gaya masa yayi biyayya da iyayensa shine kawai mafita don bazasu sashi hanyar dasuka san bata da amfani ba ita kuma gimbiya a matsayinsa na namiji shi zai nuna mata yanda yakeson tayi sbd mu mata muna da rauni da karamar kwakwalwa duk zurfin iliminmu kuwa. Nayi murmushi nace amma inna ngd da wann shawarar wllh dama narasa me zance masa. Ki yi wa kanki godiya da kin yi shiru kinga ai ba zan sani ba bare na ba ki shawarar. Shi yasa ake son duk abin da yaro zai yi ya shawarce magabatansa. Na langwa6ar da akai ina fadinada mata irin abubuwan da yake yi min. Ta yi murmushi har sau biyu,sannan ta kalle ni. Kin san abin da ake nufi da HADUWAR JINI? Na girgiza kai ta kara murmusawa. ,Abin da akae nufi shine,kauna ta cikin jini,haka kawai Allah ya hada bayinsa cikin hikima tasa. Ma'ana yarima Allah ya hada jininku ba don komai ba,saboda hakan Allah ya rubuto. Wallahi ina mai tabbatar miki,da yana tausaya mana ne kawai na farko yafi karfinmu nesa ba kusa ba. Tsarinmu da shi ya sha bamban da sa.kuma ya fahimci hakan. Shawara daya zan baki. Kiyi kokarin inga ba shi amsa gamsasshiya a duk lokacin da yayi miki tambaya,hakan zai sanya ya daina damunki tunda halinsa ne.Yarima ba yaro bane don akalla zaiyi 38yrs ke kuwa duka fa yanzu kike 15 kawai daiya dauke a kanwarsa ko yar cikinsa a tunani. Jin tayi shiru nace to inna yace gobe zai dawo na dama masa fura, fura? Ta tambaya tana kallona nace uhm tayi tagumi to bamusan abnd Allah zaiyi goben ba na mika mata wayarsa daya bani aro ta karba itama hannunta yana kyarma don kyaunta ga wani kamshi da yake fita ta juyata ta kara juyata Allah sarki humaira yaron nan tausayi gareshi adana masa zuwa safiya na amsa ita kuma ta juya ta fara bacci ni kuma yau baccin sama-sama ne sbd kamshin yarima daya addabeni (kuji mayya lol) kamshin da yake a jikin wayarsa harta hanneyana ma kamshin sukeyi. Saina tsinci kaina cikin faduwar gaba ina tunanin irin halayensa. Tun daga kofar shiga falon na fara fahimtar yau gidan babu lfy kowa ka gani yayi tsuru-tsuru yana zare idanuwa ba mazan ba ba matan ba kowa yana cikin fargaba. Jikina ya dauki rawa don bana kaunar tashin hnkli a dunia. Takun farko dazan shiga cikin falon najiyo muryar gimbiya tana balbala masifa abnd kunnena ya jiyemin saura kadan fitsari ya zubo min nayi saurin komawa ta kicin tare da lafewa a jkin bango ina saurare. Duk abnd kake takama dashi nima ina takama dashi yanda kake dan sarauta haka nima ubana yake sarki na gaji da wann cin kashin da kake min tun zuwanka! Kullum da irin salon wulakanci da rainin wayon da zaka 6illo min da su kana kunyata ni a gaban BARORI nah! Ya zama dole ka amsa min tambayar nan INA KAKE ZUWA KULLUM CIKIN DARE? Na tambaye ka jiya bayan ka dawo kace min bacci ka ke ji. Yo yanzu kuma fa? Da kai nake kayi banza dani,ko za kayimin izgilanci ne da kasaitar da ake yi maka kirari da shi? To ka tuna cewa,nan ba masarautarku bace,don'yan magana na cewa,sarki a gidan wani sarkin sunansa BAWA....Ba za kayi magana ba? Lallai zaka amsa kira a fada yanzun nan,idan ka raina ni ina ganin sarki yafi karfin raini a wurinka. Ta banko kofa,tuni kowa ya kama aikin karya kada ta gane ana sauraronta. Na makale wayar a siket dina,kada ma wani ya gani. Kallo daya zaka yi min ka gane ina cikin tashin hankali. Aiki kawai nake amma Allah Allah nake ta dawo a aiko kiran yarima fada nayi amfani da wann damar na hamzarta kammala tare da ajiye masa wayarsa koda a karkashen carpet ne tunda ba mai shiga dakin saini amma shiru kakeji. Rabi ta kalleni na tsaye kawai ta matso. Gimbiya fa batasan baki zoba kwana 2 sbd haka kadaki bari ta gane kiyi hamzarin kammala aikinki kinga yau za'a bamu albashinmu tana cikin fushi kada a kiramu baki kammala ba. Gaba kawai nayi zuwa daki dama can kadai ya rage da bandaki ina tura kofar na ganshi kwance idanunsa jawur kamar wuta. Kamar dama ni yake jira yayi saurin tashi zaune ya tura kofar tare da kullewa da mukulli nayi saurin kallonsa har lokacin idanunsa jawur suke fuskarsa murtuk kamar zai fashi... ya karaso gabana ya kalleni kamar zai fashe da kuka idanun sun kara ja na sunkuyar da kaina ya kankantar da murya kamar zaiyi kuka. Humaira banason gimbiya na tsaneta wllh... Nayi saurin kallonsa ya bude min idanu sun kara rikicewa cikin matsanancin bakin ciki yaci gaba da cewa ni fareeda zata kira BAWA sbd nazo gidansu na zauna? DonAllah ki taimakeni menene shawara? Kwankwasa kofa mukaji na kalleshi cikin tashin hankali tare da saurin fiddo da wayarsa na mika masa ya karba sannan ya dan ware murya yace waye? Dogari ne Allah ya taimakeka, lfy? Ya bukata a fusace yace Allah ya taimaki yarima. Sarki ke nemanka fada karfe 12 na rana.ya kalle ni cikin wani yanayi sannan yace. Allah ya nuna mana. Hannuna ya kamo muka zauna bakin gado. Na kyale shi ganin kamar hankalinsa ya dan gushe saboda 6acin rai. Ya kalle ni,ni kuma na dan zame hannuna. Humaira ya zan yi da fareeda?kayi hakuri kuma kayi biyayya ga mahaifinka, Allah yana nan. Ya tallabo fuskata ya kara yi min kallo sosai,na dauke kaina. Ya kara yin kasa da murya. Nayi hakuri shine tunaninki? Nayi dan murmushi,bayan wuya sai dadi yarima,sannan ka daina fitar daren tunda bata so,dole ka rinka gujewa 6acin ranta matukar kana son kwanciyar hankali. Kinga kalle ni". Ya fada... ,Na kalleshi a kaikace ya nuna min saitin zuciyarsa,wani abu ya tasayan nan kamar dutse gaskiya guduwa zan yi,bana zama a kashe... Na kyalkyalce da dariya,sai kawai naga ya sakko kasa ya zauna gabana tare da tsire ni da ido. Dariya mana baki ko?ya fada kamar zai yi kuka. Nace,to don Allah ko ni yarinya yanzu nace zan gudu? Baki sani ba ne wallahi da gaske nake. Na zaro ido,don Allah kayi hakuri kada ka 6ata ran mahaifinka. Yayi shiru,sai kawai ya ba ni tausayi to shi wa ya ke so?na dube shi a tsanake tare da ambaton sunansa.yayi saurin dubana. Na ba ka shawara? Ya daga kai yanayin yadda ya yi kamar yaron goye, sai ya bani dariya. Nayi murmushi. Idan kun je fada ka kama bakinka,kada kace zaka maida magana saboda gudun yin SUBUL DA BAKA,ka fadi abin da zai janyo wata matsalar da tashin hankali. Murmushi kawai yayi. Tashi ki kawo min karin kumallo na. Na mike na tarar lokacin suka gamasaukewa,don haka sai da na jira tukunna.... Kafin na kai masa ya wanke kewaye tare da gyara dakin. Na rasa abin da zance masa,amma faduwar gabana ta karu. Ina ajiye farantin wayar nayin kara. Dariya na ga yana yi kafin ya kara wayar a kunne. Haba Alhaji nayi fushi,ka jira dawowata zaka kwana yau don ubanka! Hakan ya fahintar dani abokinsa ne. Ya ce,kana ta wannnan albishirinka?...ina ganin Allah ya amshi addu'ata...I FOUND A LITTLE BABY THAT I DREAMT ALWAYS TO BECOME MY BELOVED" ya kyalkyale da dariya kamar bashine ya gama fushi yanzu ba yace. "AM TELLING YOU. Ya dan saci kallona. Uhm! I CAN'T EXPRESS BUT JUST EXACTLY I DESCRIBED. Bana fahimatar turancin,amma sai kawai naji cewar na tsargu da hirar. Ya kara cewa. Wlh abokina HUNDRED PERCENT. Na mike zan bar dakin,yayi saurin nuna min hannu alamar na zauna ya na fadin. DO YOU KNOW WHAT? Na gama kamuwa billahillazi saboda JUST 3 DAYS bamu hadu ba sai ga zazza6i...ka dai bari zan kira ka anjima,akwai STORIES A LOT. Yana gama fadin haka ya ajiye wayar. Ya kalle ni yana murmushi idanunsa sun washe sauran dan jan kadan. Taho 'yar kanwata muyi karin kumallo kin ji? Ko baki gode da aikin da na yi miki ba? Na yai murmushi, Na gode,amma...maganar ta makale saboda sauyin da na gani a fuskarsa... Haka na dinga cusa wainar kwan sbd kallon daya tsareni dashi yana karin kumallon duk ya samu nutsuwa, baki son kallo ko? Na daga kai Eh wllh, yayi murmushi kiyi hakuri zaki saba dashi bansan sanda nace kallon? Ya kurbi ruwan zafi kawai bai bani amsa ba wai ke ya maganar karatunki? Babu nace babu fa kikace ke bakison ilimine? Nayi murmushi kusan hakan. sbd me? Ina ganin bacan alhairin yake ba, istihara kikayi ne? Nayi murmushi ina mmkin yanda baya gajiya da tambaya. Gimbiya Humaira ya fada yana murmushi idanunsa kyar akaina nayi saurin kallonsa. Sbd yanda naji sunan banbarakwai. Aka buga kofa waye? Rabi tace Humaira tazo muje karbar albashinmu idan ta gama. Nayi saurin mikewa ya kalleni da Allah zauna na karyar da wuya na kalleshi yayi murmushi a dawo lfy jeki. Kayan fa? Idan kin dawo kya kwashe ko baza'a bamu salala ba? Nayi murnushi duk na dauka wasa yake zan baka mana nawa? Ya tambaya duk yanda kake so yayi murmushi rabi zaki bani harda aikin da nayi miki yau. Nace to. ,Duk zatona Gimbiya ce za ta raba kudin ashe wasu ne daban. Muka bi layi nice ta 2n karshe,ga shi biyan baya sauri shi yasa muka dauki lokaci mai tsawo,har ku san karfe 1 saura. Ban tarar da shiba,amma na tarar da 'yar guntuwar takarda gefen faranti wanda ya rubuta da manyan baki cewar 'KIN AMSO? TO KI AJIYE MIN NAWA KARKASHIN FILO. hakan kuma aka yi,na ajiye na fito. Da dubu 7200 na isa gida,saboda na biya basussuka sauran kudin icce da maggi kawai ya rage,su kuma ko su Aisha na aika. Inna tayi murmushi da na gama yi mata bayani tace. Gwadaki yayi kawai yaga cewa,kina da rowa? yanxu bada 50 a sawo masa furar sai nonon ma na 50 ko yagot zaa sanya?"Yadda ki ka ka gani inna. Na fada. Tace. A hada masa duka,kin san maza akwai son din dadi. Yau kam har balangu muka ci da lemon kwalba. Ana gama sallar isha'I ya iso,yace na yi masa iso wurin inna. Bayan sun gaisa yace, don Allah inna ina son Aisha da sumayya da kuma humaira suyi min rakiya wani wuri. Jin an ambaci su Aisha yasa inna cewa Allah ya kiyaye yarima,mun fa gode. Ni kuwa saura kadan na kurma ihu don takaici. Ba wai rakiyar nake ji ba tambayoyinsa da son maganarsa ke damuna. Muka fito fuskata a daure su Aisha sai tsalle suke yi don rashin sanin ciwan kai. Muka shiga motar nan naji wani tsam!karo na 2 dana ta6a shiga karamar mota,ranar da ya sawo wa inna magani sai yau... Wani daddadan kamshi (not clear)na dai daure duk wurin sai kallona suke yi,ban san me suke cewa ba kamar suna wani yare. Ana cikin sharcewa ana gyarawa suka shigo,naji takaici. Shi kuwa kamr mutuwar tsaye yayi bakin kofa zuwa can ya tako kusa dani,tare da sunkuyowa yace. Masha Allah. A hankali. Abin dariya abin haushi,sai naga mata na faman barbaza gashi nayi hakuri ta gama kawai tana sakar min kai na hade shi wuri guda,na cushe kamar yadda nake yi. Tayi saurin cewa. OH SORRY YOU NEED HOSE WIFE? Ko kallon sakarai ban yi ba, nayi gaba kawai abina. Su sumayya kuwa kowacce hannu cike da kayan zaki ana washe baki. Maimakon muyi gida,sai naga ya karya kwan,shagon da muka shiga sai dana tsorata don ganin duniyar dake ciki. Ya sami kujera 2 ya zauna tare da miko min dayar na zauna. Ya dubi sumayya da Aisha dake tsaye yacekunga kekunan can? Sukace eh yace to kowacce ta turo guda 1 ku zagaya duk abnd kukeso ku dauko ku zuba aciki. Yaro! Yaro! Wani takaicin sai yaro wllh bai ida rufe baki ba su ka kwasa da gudu sukayi gaba na dubeshi nace mekake nufi? Yace shopping zanyi musu, danAllah meyasa kakemin haka? Kinason sanin dalili? Nayi shiru cike da takaicin na tambayeshi ya tambayeni yayi murmushi konayi miki bayani a yanzu bazaki gane ba. Kamr nace masa sbd mahaukaciya ya daukeni ko? Amma sai nace kaga kai kake haddasawa kanka fitina da rashin kwanciyar hankalin gimbiya. Yayi dariya ba wani abu lokaci ne zanyi magana yace waike baki kunshi ne? Shiru kawai nayi sbd bani da amsar bashi. Samarinki nawa Humaira? Ashirin na fada, ya kyalkyale da dariya har nayi mmki yace ashe kin iya gatse? Wllh idan muna tare sai naji kamar na saceki na gudu. Nace eyeh? Ya dubeni da sauri nan da nan na fahimci SUBUL DA BAKA yayi idanuna jajur nace me nayi maka zaka sace ni ka gudu? Yanzu kai.... Ke! Ya matso da kujerarsa wllh wasa nake nan da nan ya hau yan kame-kamen furta kalmar. Daga nesa na hango lodin kaya na yo kanmu ba ka hango masu tura kayan saboda tsoran da suke yi. Ni tsorata manayi,tunanina kayan ne suka turo kansu. Sai kawai na ga su Aisha na mike tare da salati. Me ke damunku su.. Ya taso babu ruwanki. Waje na fita na tsaya bakin mota ina jiransu kawai. Maza 4 suka rako su kowanne hannunsa da kartin ledoji. Har muka isa gida bance komai ba,nayi gaba abina,shi ya jido kayan kafin ya shiga. Na gama fadawa inna komai. A tsakar gida ta ta fito tana salatin wadannan himilin kaya,yana tsaye shi kuma ya goya hannayensa duka a kirji. haba yarima har yaushe zaka biye haukan yaro? Inna kada ke maki ga laifinsu,wlh ni na sanya su ko humaira? Shiru kawai nayi. Ya kara yin kasa da murya... Amma inna ayi hakuri. Nan da nan inna ta gaza cewa komai,sai kawai ta shiga daki tana yi masa godiya. Ya kalleni ni,dauko min furar ko baki dama ba? Na wuce kawai na kyale shi. Zaune yake saman tabarma. Kofar daki na ajiye kwanon na yi tsaye. Ya dube ni kawai,sannan ya fara shan furar. Ga mamakina sai na ga uya shanye duka ya mike tar da matsawa kofar daki. Inna na bar ku lfy. Tayi saurin cewa. Allah yabamu alheri yarima an fa gode. Su Aisha murya zauu!Aka ce yaya yarima sai gobe. Yace Allah ya huta gajiya kunji? Yaya dube ni,yace. Mu je!!! Kamar kada nabi shi,haka na daure muka isa bakin motar. Ya jingina bayansa a motar tare da fuskanto ni yana kallona. Ya zura hannu a aljihu ya fiddo ambulan ruwan kasa mai fadi,ga tudu yace. Ungo kudinki ni wasa nake yi miki. Na sunkuyar da kai kawai. Kin ji? Nadai yi shiru. Ki kar6a nace dare na kara yi kin san halin Gimbiya,ana can an dake lamba... Allah ka dauka. Nace dashi. Wallahi wasa nake yi,kar6i kudin babu inda zan je dasu. Jin ya rantse yasa na mika hannu,sai kawai ya fizgo ni na fada kirjinsa,nan da nan na ji wani irin abin duniya mai wuyar fassarawa. Ya rikr ni gam!nayi kwance a saman kirjinsa. Wai fushin na mene ne? Ya fada tare da sunkuyowa saitin fuskata.... ,Sai kawai na tsinci kaina da sunne kai a jikinsa. Ya dago ni yana kallona fuskata. Na runtse idona ni kaina na rasa kunyar ta mecece. Kunya ta kuma ake ji? WONDERFULL ya fada. Ni dai ka sake ni ban so. Na fada murya na rawa. Cewa zaki yi na kyale ki ba wai na sake ki ba,wannan kalmar bata har abada tsakaninmu. Idan kina son na kyale ki kuma sai kin fada min fushin da kike yi tun fitarmu. Ba fushi nake ba. To mene ne? Yadda yayi maganar ya kara jefa ni cikin yanayi. Gida zani. Na fada da kyar. Zan raka ki yau,kada ki damu. Ya fada tare da kara riko ni. Wannan abu yayi min yawa. Na fada a zuci. Ga shi sam haka kawai na kasa kallonsa,da kyar nace. Wannan fa haramunne. To naji,amma idan na sake ki kada ki matsa kin ji? Na ce to. Yana sakina na yunkura zan kwasa da gudu,yayi saurin maida ni jikinsa yana fadin. Ashe kina da wayo? To ai ni... Nayi shiru. Sai kawai na sanya kuka. Yayi shiru,zuwa can ya sake ni yana fadin. Kina rugawa zan biki. Na tsaya cak! Goge hawayen,goge su. Sai kuma yayi shiru. Baki so ko? Nace uhm. To na bari muje na raka ki gida. Zan je kawai. Ke dai mu tafi,ai ba roko ki ka yiba,ni na sa kaina. ,Har tuntu6e nake yi don sauri,jikina ya yi min wani iri. Zuciyata ta tsaya wuri 1 cak!yayi saurin shan gabana. Kin kagara ki rabu dani ne? Nayi shiru kawai. Wai wannan snkui sunkui da kan na mene ne? Muryarsa na kara dagula min lissafi,na ce. Ba komai. Humaira kenan,wlh miskilancinki na burgeni. Da akwai namiji gidan nnan yau da a nan zan kwana a dakinsa. Tsoro ya kamani,anya yarima baya da ta6in hankali?kamar wanda ya shiga zuciyata,sai ji nayi yace. Ke ni idan muna tare rasa hankalina nake yi. Abin nan yafi karfin kwalkwalwata,sai kawai na hau addu'o'in tsari a zuciyata da kyar ya kyale ni kamar zai bi ni cikin gidan. Hakan ya kara lalata kwalkwalwata tare da tunzura zuciyata zuwa wani babin tunani. Labule kawai na daga na fara ce da inna. Inna!inna! Yarima yana bani tsoro. Tsaye ta mike. Abin tsoro ne humaira,domin na karanto inda ya dosa. Na mika mata ambulan. Kudin dana bashi ne ya maido. Tace daman na fada miki jaraba ki yayi. Ta hankada filo kawai ta ajiye. Kinga kaya?nayi shiru,tace gaba da cewa. Kaya ne wani abun ma ban san ko mene ne ba. Na kwanta kawai. Inna kyale su sa cinye tunda su suka debo. Idan akwai wanda ba'a ci ciki fa? Nace A'a to ,Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Ina ta fada. Shiru nayi maganganun nadawomin cikin wani irin yanayi tare da kwanciya danayi a jikinsa. Nan da nan tsikar jikina ta tashi. Fasalinsa ya fado min,na lumshe ido,sai gefin asuba bacci ya sace ni,kiran sallar farko na farka. Na tsinci kaina da kosawa gari ya waye na tafo aiki. Karfe 6 saura muka fiddo kayan nan don kara dubawa ni da inna,bayan mun karasa lazimi. Ko madara tafi guda 10,wasu abubuwan kam mun kasa gane su balantana mu san yadda ake amfani dasu. Ta dube ni,idan yazo kya tambayar mana shi yadda suke,idan muna iya amfani dasu toh!idan kuma ba ma iyawa lillahi warasulihi gara ya mayar a bashi kudinsa da yayi asaraa,ko yakika gani? Nace gaskiya kam,sannan da alam dinki zai mana tunda har ga teloli muka je fa. Tace,su Aisaha sun fadan. Kinga kudinmu sun kara auki ke kadai zaki yi sauran musha shagali. Na karasa maganar ina murmushi. Sai mu yi sana'a kada mu ajiye haka nan,kinsan zara bata barin dami. dauko mana su nan in tisa ko naji sanyi,hadi da sauran suna cikinjakar filo. Sai da na hure kyandir din kafin na tashi,saboda hasken daya gauraye ko'ina wato gari ya waye. Na fara mika mata na ciki ambulan din ni kuma ina tisa canjin da suka kwana. Humaira!!! Inna ta kira ni da karfi,wanda yayi sanadiyar tashin Aisha da sumayya. Tsaye na mike ganin bandir din 'yan dubu- dubu a hannunta ina zare idanu cikin tsoro. Karkarwa da hannuna ke yi ya taimaka wa bandir din faduwa kasa. Munfi mintuna 10 muna musayar kalllo kafin tace. ,Akwai abin da yaron nan ke nufi humaira,lallai kudin nan koma masa zasu yi,domin sun fi karfinmu. Idan kin je ki ce inna na son ganinsa a yau din nan,wannan alamari yafi karfin tunainmu. Kasa ce mata komai nayi,na shiga shiryawa domin na ji an yi sanarwar karfe 7 saura mintuna 13 a rediyon inna. Har na bar gidan inna ba ta daina sambatu ba,tana faman mita. Na isa kan lokaci kamar kullum,na shiga gyaran falo,amma cikin yau ya fi na kullum saboda sauya tsarin da nayi. Wanda yana 1 daga cikin gargadin da Gimbiya ta yi min,cewar duk. Bayan sati 1 sai na yi hakan. Su kuma 'yan aikin rana duk bayan sati 2. Lokacin dana kammala ina goge 10 har da ku san kwata,motsin fitowarsa naji tare da kamshin turarensa da ke fadar min gaba a duk lokacin dana shaka. Kamar kullum hadin baki,sai ga Gimbiya ta shigo da irin nata kamshin nan da nan falon ya hade ya gauraye da wani irin daddadan kamshi. Na bada gaisuwa ga kowannnesu ba tare daba kalli 1 daga ciki ba,sannan na ci gaba da aikina. Ina jiyo sautin murmushinta,lokacin da tace. Barka da safiya. Ban ji ya amsa ba,amma wata kila yayi mata da fuska,nasan kasaitarsa. "Na zo yin karin kumallo da yarima,tunda ni an ankasa zuwa har yau ayi dani, nayi gayyatar cin abninci har na gaji. Kai kuma ka. Kasa gayya tatat,shine yau ni nazo. Bai dai yi mgn ba,ta kara cewa. Da za'a taimakamin yau kadai da na fita da kai unguwa. Lokacin ne yayi mgn da wata 'yar shakakkar murya. Yau bani da lokaci,sai dai wani. Dama nasan haka zakace,wai yarima wannan halin ko inkulan da kake nuna min na menene?ta katse shi da fadar hakan cikin nuna tsananin 6acin rai. "Humaira zoki bani kalaci. Ya sauya mgnr yana mai kara kallona.nayi saurin dauke kaina saboda ganin irin kallon da yake yi min. Na ajiye kayan,ta kalle ni cikin fushi. Je ki kawai,zan yi SERVING dinsa. Ya dube ni,zauna ki bani abinci humaira. Hankalina ya tashi saboda ganin yana neman haddasa min fitina da tashin hankali,wanda zai haifar min da rashin zaman lfy. Rai a 6ace ta kalle shi,tuni ya maida hankalinsa gare ni. Haba yarima,me yasa kake neman gwasale ni a duk lokacin dana ke kokarin nuna gwaninta a wurinka? Shekeke ya kalle ta cikin izgili yacekarya ki ke,dan da baki baza borori a kaina ba... Ni kake karyatawa a gaban BAIWATA? Shin zuwa kika yi neman tashin hankali da neman rigima,ko kuwa gaisuwa ce kika kawomin da gaske? Ya fada yana mai kare mata kallon raini. Ta sassauta murya,tace. Zuwa nayi in faranta maka rai saboda... To ki bi abinda nakeso,bana son shisshigi,nan sashena ne ina da ikon yin duk abin da naga dama a harkokkin gidan,sai ki bari ranar da naje inda kike irin duk yadda kike so shi zan bar kiki aiwatar. Ya na gama fadin haka yace. Zo ki bani BREAK humaira. Jin Gimbiya tayi shiru yasa na dukusa ina zuzzuba masa,sanan ita ma na hada mata tayi min wani mugun kallo,kafin tace. ,Sanya ki nayi? Shi kenan ya janyo min abinda nake gudu! wammamn mgn ita kawai nake maimaitawa a raina,kamar nayi ta kurma ihu. Ta daka min tsawa. Ki kayi wa mutane tsaye munafukla,wuce ko na harfe ki da kafa,mai kama da aljannu!!! Wannan kalma tayi min zafi,sai kawai naji kwalla sahr! Shi ma ya fusata yayi mata tsawa. Tsawar danaji har cikin raina,saboda na san fitina kawai zai kara janyo min,yace. Kiranki nayi,ko na aika miki da katin gayyata?don me zaki zo ki haddasa min fitina? A hanzarce ta dube shi daidai lokacin na bar falon,amma duk da haka ban daina jin amon muryarsa ba,yana balbala mata masifa. Daga jin muryar kasan kuka take son yi. Yarima zan hadddasa maka fitina da BAIWA? Mene alakarka da ita?shi yasa na lura kana yi mata wani kallo na daban? Ke!kada ki kullan sharri... Ta mike tsaye tana fadin. Lallai zan dauki mataki a kan wannan,domin bazan ta6a daukar rai ni ba. Na juyo karar buga kofa alamar ta fita na rushe da wani irin kuka. Ba motsin dana ji kawai ba,turarensa maya ganar dani cewe shine ya shigo. Kukan na mene ne?saura kadan na dauko ta6arya na kwada masa don takaicin wannan tambayar ta rainin hankali da ya wurgo min. Zaki yi WASTING hawayinki a wofi, domin ita ba Allah bace da zaki damu kanki daon tana ganin kin yi mata laifi.saboda hauka da tsabar son kai ta mance ni ne mai laifin,ko kuwa fib karfi take son nunawa?kizo muje muyi kalacin kada yunwa... Na dora hannu saman kai na kurma ihu,ina fadin. Ni kam kana neman haddasa min fitina alhalin ni din ba wata bace,iyayena ba wasu bane dazu su kare min. Da sauri ya bar kicin din ganin alamar su Rabi na da niyyar zagayowa ta baya. A rude suke,kuma a kaidime gaba daya har da mutuminsu suka hada baki. Lafiya 'yar fulani?sai a yau na san wannan suna ashe haka suke fadamin idan bana nan,ko suna kwatancena. Na dago kaina jage- jage da hawaye. Don Allah rabi ku yafe min abinda nayi muku iya zaman da muka yi,karshin zaman gidan nan yayi. Ta dube ni kamar ita ma zata yi kuka tace. Wallahi muba kiyi mana komai ba yaushe ma mgn ta hada mu ballantana ki 6ata mana rai?laifin me kikayi wa yariman? Zanyi mgn ya shigo duk suka tsorata tare da ja baya suna kame-kame. Humaira zo ina son ganinki. Ya na fadin haka ya juya. Rabi ta matso tace tashi kije watakila yafe miki zai yinaga kamar yana tausaya miki. Ni ba zan jeba. Duk suka zabura da fadin. Kin yafe aikin ne? Nace,Ai yazama dole,saboda wacece ma keyi domin ta ita ya hada min gwarmai(rigima) a wurinta. Bamu gane ba. Inji harira. Na fada musu badakalar da ka yi yanzu a falo,duk suka hada baki suna INALILLAHi. Yau ke kin bani. Allah ya tsare ki da shiga wakafi don da wuya idan baki yi yariba. Na rushe da kuka cikin wata irin kidima. Zubairu yayi dan tsaki tare dayin kasa da murya. Ba zata yi tari ba,domin yarima SON HUMAIRA yake yi!!! Duk muka kwalala masa idanu cikin firgita abinka ga dan duniya sai yayi murmushi yace ,Wallahi na fahimmace haka tun ba yau ba. Saboda haka kada kiyi wa kanki salalar tsiya,arziki ne ke binki. Ya kara yin kasa da murya. Don Allah humaira kin san ya mu cikin barorinki?mu kam daman Gimbiya...tishe kunnuwa na nayi tare da fasa wata irin kara. Yarima muka gani tare da dka musu wata irin tsawa yana mai korarsu,wai sune ke kara tsoratani. Ina kallonsu ta bayan taga sun la6e. Shi kuma ya fara magana a hankali. Rigimar Gimbiya humaira yawa gareta kullum da abin da zata tsiri. Fitar nan da nayi wurin mahaifinta ta kai ni kara,wai na fifita ki a kanta,kin ga duk ta zubar da kimata wurin iyayenta. Yanzu hak na baro tana mgn da mahaifina,ban san abin da zatace masa ba,ta 6ata ni gurin nawa. Ta durkuso,sannan yaci gaba kiyi min mgn na sami saukin abin da nake ji azuciyar ann koda kuwa ba mai bdadi bane. Kada kiyi fushi dani a lokacin da nake bukatar taimakonki. Lokacin ne daba ni da wani gata sai wanda kika bani a matasayina na marayan Allah. Kamar na shake yarima nake ji,sai kawai na kara fashewa da kuka. Yau ni HAMEED na gata kaina! Sai kawai ya fice. Na duke ina shawarar na tafi yanzu ko kuwa na bari loacin ya cika? Ban karasa yanke hukunciba naji an fizge ni. Na dago kai sai kawai naga yarima ya rike hannuna. Dukewa kawai nayi ban dagi ba,sai da naga mun shiga sashen Gimbiya kawai sai na kara maida kaina kasa. Shin dukanta zai yi?cin mutunci ko kuwa? Ganin mun doshi dakin kwananta ya samya nayi hanzarin kallon shi. Naku ANaM Dorayi Amadadin Zainab Dahiru Wauw nakecewa muhadu a kashi na 2 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100