Subul da baka 2 page 1 Posted by ANaM Dorayi on 07:10 AM, 21-May-15 Under: Subul da Baka Kwance take rub da ciki da gani tana cikin damuwa mukayi sa'a ba kowa da gani korarsu tayi. Ya jefar dani gefe ya isa bakin gadon tare da tallafota ya tada ta zaune kallon da take masa me dauke da mmiki, sha'awa tare da tambayoyi masu yawa ya durkusa gabanta yace fareda ki gafarci yarinyar nan ta tsorata da fushinki ki yafe mata domin kaunar da muke yiwa juna. Kallo daya zakayi mata kasan ta fara rasa hnklnta don hk tayi saurin kallona tace na yafe miki Humaira dama bakiyi min komai ba, idona shabe-shabe da hawaye saiga murmushi ya subuce min. Ta maida kallonta gareshi dahra tym din bai tashi dg durkusonta da yayi ba saima kallonta da yake yana smiling na tuba nima a gafarce ni amaryata kuma gimbiyata... Ban jira amsar da zata bashi ba nayi waje tare da karayin godiya da goge hawayena kowa ni yake kallo sbd ta gabansu muka wuce, banga su rabi ba don hk na wuce dakin kwanansu don na gyara gashi lokcn ya kusa. Ko rabi banyi ba ya shigo har kewayen na kalleshi tare da banko min harara kinsan Allah yau saina kai kararki ga inna na gaji da irin salon rigimarki wllh. Na mulmula maganar tare da lailayata kafin nace rigima ta wuce irn naka kuma kafin ka kaini kara nizan fara kaika In Shaa Allah. Haka kikace? To bari in riga ki isa gidan mugani. Ya fita yana yar dariya, yau saida muka hadu da amira a hanya ta makara ni kuma nayi rana a gurguje muka gaisa ta wuce a kofar lungunmu na tarar da tankamekiyar motar mmk ya kamani wato da gaske yake zai rigani. Daga bangaren yamma a inuwa yake zaune da wasu jakunkuna manya guda biyar inna kuma na can gefe idanunta jawur da alama kuka tayi. Wata irin faduwar gaba naji wadda ban taba jin irinta ba na karasa gabanta na dafa guiwoyinta nace inna lfy? Me kayi miki naga idanunki sunyi ja? Ta kara fidda kwalla tace dinkuna ne yayo mana kowa akwati guda sai kayan kwalliyarki shima akwati guda tsoro +fargaba ya dabaibayeni da kalamansa tare da cewar kada mu butulcewa rahmar Ubangiji domin shima bayin kansa bane. Taci gaba da kwarar hawaye nima kawai sai naj kukan ya subuce min musmmn da aisha ta fara bude min kayan ina kallo. DonAllah inna kiyi hkr kinga har kin sa itama ta fara abnka da ruwa-ruwa. Ya mike na barku lfy inna danAllah kuyi hkr saina kara zagayowa ya fice. Mun dade muna sharbe kafin mukai kayan daki su aisha har an fara gwadawa da takalma kala 5-5. Inna ta kalleni humaira naso kama yaron nan akan abnd nake zargi amma saina rasa hanyar da zanbi sbd hausawa sunce idan baka iya kama barawo ba shi saiya kamaka. Kuma shirun nawa yayi amfani domin daga nasihar tasa na gane cewar haduwar jinin kawai da kuma tausayinmu da Allah ya dora masa. Tsoro na daya saka kayan nan mu shiga jama'a anya baza'a zarge mu ba? Kafin nayi magana mukaji sallamar baba Alh Sheetu inna ta amsa ta fito da sauri daman da hijabi a kanta. Duk muka fito ya kalli inna me kike nufi da hanamu albashin humaira ko kuwa kina tunanin zaki cinyesu ne ranar aurenta kibarmu da siyan kayan daki kinci bulus? Ya girgiza kai zaki dinga bamu rabi duk wata kuna amfani da rabi wann shine babban adalcin da zamuyi miki idan kuma kin amince zaki aurar da ita ne toh! Inna ta sunkui da kai a'a yaya ai bansan haka tsarin yake ba tuni na aiko bari na dauko maka, ta shigo daki bata ko kalli inda muke ba yace maza dauko tunda kinaso ki koyawa yarki son abun dunia shiyasa kika dage abar miki yayanki don kiyi jari. Inna dai batace komai ba ta mika masa 10k ba kunya karba tare da tusawa yace sun cika dama an fada mana 20 ne nayi ta mmkin ina yaji? Ya mika mata yar leda daga aljihunsa ungo goron sanya auren mansura ne wato yarsa sati 2 masu zuwa. Inna ta shigo tare da wasance maganar makarantar su sumayya. Batayi min zancen ba nima na tsuke bakina sbd munga abnd yafi hk. Da dadaare yaxo na tsinci kaina da faduwar gaba na fita da kwanon fura ba tare da nace ya shigo ciki ba sbd banason hirar ta dade kamr kullum jikin nawan ina jinshi wani iri. Muka gaisa nace ga fura. Ya karba amma yau kadan ya sha na maida sauran gida na dawo. DanAllah ka rage zuwa min dadare kaini ziyarar ma gaba daya kadaina idan baka iya dainawa ba. Sbd baki damu dani ba? Ya fada cikin yanayin takura nace a'a. Da kinsan abnd ya kawoni yau wllh da baki fada ba amma bakomai. Tausayi naji ya bani har saida idona yayi kwalla nace kayi hkri danAllah. Idan banyi hkri dake ba humaira ya zanyi? Damuwata na kawo miki kamr kullum su fareda sun hada min tuggu mai martaba ya kirani wai sati mai zuwa sunan nan tafe za'ayi bikinmu da gimbiya kuma ana gama daurin aure zamu tafi gaba daya zuwa yola. Gaba daya hanjin cikina suka kada take suka bada wani irin kara mai kamar sautin hadari. Ya matso gabana Humaira mutuwa zanyi banason yin nesa dake rabuwarmu zata zame..... Kwallar da nake makalewa ta zuraro kuka bazai yi mana magani ba ki bamu mafita domin nasan kinajin yanda nakeji karancin shekarunki da kuruciya zasu barki ki fahimci wani abu dake bin jininki... Kiyi mgn kada nima kiga nawa kwallar. Allah ya sanya alhairi na fada kamr me koyon mgn, ameen tunda kin ambaci alhairi saidai inaso kimin alkawari zanje nayi shawara da mahaifiyata idan ta amince zanzo in rokeki wani abu zaki bani? Na kalleshi nawa ne? Kwarai kuwa mallakinki ne har abada Nayi murmushi cike da kuruciya ko ince wauta nace ba komai ko menene tun a yau ba sai watarana ba idan mahaifiyarka ta amince ka dawo ka amsa ko kuma tun a yanzu na baka ka tafi dashi idan taki amincewa saika dawon dashi. Yayi murmushin dake kara masa kyau yace what a confidence' kawo hannunki, nayi hamzarin mika masa sai naga ya zura min manyan zobuna na gwal baki bude na kalleshi sai yace na alkawarine saina sadda kai kasa. Gobe zamuje Kd sai jibi zan dawo me zan siyoi miki? Nace bakomai ya watsa hannaye kinyi daidai gobe kizo da wuri don mu kara bankwana 7am zamu wuce nace to. Maza shiga gida banda tsawon hira kada a makara. Bacci da wuri bashi ke sa tashi da wuri ba sbd uwar makarar da nayi yau har tafi ta kullum ko wanka bansamu yiba kwaskwarima kawai nayi inata uban saurin na isa amma ina! Ana kokarin rufe get har sun dau hanya sai kurarsu na gani wani irin zazzabi naji ya rufeni inajin saukar hawaye a idona. Sashen gimbiya yau aka kiramu zamu kammala mata kaya tare da wasu shirye shiryen biki na tsinci kaina cikin rashin jin dadi ni kadai nasan yanda nakeji a zuciyata to meke damuna? Yaushe mukai irin wannan shakuwar da har nakejin haka a raina? Meyasa nakejin haushin gimbiya a yau? Wasa sabon aji sabo kuma tirken wawa bansan cewa na shaku dashi saida dare har kuka nayi acikin mayafina tsoro da fargaba suka rufar min na fara zargin kaina kona kamu da SON SA ne? Bani da yawan magana haka bani da kazar kazar sosai amma duk da hk saida inna ta tambayeni ko banijin dadin jikina ne? Shiru kawai nayi mata duk wanda ya ganmu a yanzu sai yayi mmki sbd sauyin da muka samu musmmn fannin cima da sutura yan unguwa sai gulmarmu suke kowa da abnd yake cewa wasu ma cewa suke sata nakeyi a gidan sarki tuni ftar jikinmu ta fara sauyawa ga cima me kyau ga sabulai masu gyara jiki. Washe gari muka shirya zuwa sunan gidan kawu mande nan mukaga jin zafi da bakin ciki karara babu kuma wanda ya kula. A gida bayan mun dawo inna ke shaida min wai ana gulmar yanzu maza nakebi nayi murmushin takaici. Maimakon yayi 2days saida sukayi 4days sannan suka dawo lokacin gidan ya kacame da hidima duk yan aiki sun hadu ba maganr sauyi gaba 1 muke haduwa sai maghrib muke tafiya ba muna can anata soye- soyenaji ana rade radin ya iso da bataliyar abokansa harda yan'uwansa ina jin ana nemana na boye bayan katuwar tukunyar kaji nida amira muka fito zamu tafi na hangoshi tsaye sai wurga idanu yake nasan ni yake nema saina dan boye. Abayantakwana 4 nan ya kara kyau da girma muka wuce bai ganmu ba amira tace min zakije party? Nace Allah ya tsareni. Amira ta tabe baki nima bazan je ba nace mata meyasa? Tace ina gudn dizgi da wulakanci kinsan halin gimbiya musamman idan ta ga jama'a nayi murmushi kawai a kofar gidansu mukayi sallama ina shiga gida na tarar da inna a tsaye a tsakar gida ko sallama ta bata amsa ba tace ina kikaje? Zuwansa 4 nemanki ba kyanan yace duk an duba gidan sarki ba'a ganki ba? Yar dariya kawai nayi haba inna da kinsan girman gidan sarki da bakice haka ba muna can wani bangare suyar kaji kawai mukeyi. Na mika mata bakar leda me dauke da soyayyun kajin da aka bamu nace inna aiki fa mukeyi shi kuma yana can ga abokansa shiru kawai tayi ta fitar da naman daga ledar na dauki cinya ina ci aka fara kiran sallahr maghrib nayi saurin cinyewa na tashi na gabatar. Na hada goldenmon ina sha kenan naji ana sallama a tsakar gida Aisha ta leka naji tana cewa la yaya sannu da zuwa gabana ya fadi inna ta kalleni nayi saurin tashi sbd nasan ma'anar kallon koda ya ganni sai yayi baya kofar gida ya tsaya inda muka saba. Yace fushi kikeyi dani humaira? Nayi shiru kiyi hkri wllh gida na koma na kammala wasu abubuwan kuma mamana ta amince nazo na amshi alkawarinmu. Kafin nan ina son ki shirya zan aiko a daukeki ko inzo da kaina mu tafi gurin party ko bazaki halarta ba? Gsky ban zuwa, me yasa? Hakanan, wllh baiyuwuwa duk mai hnkli bai wani abu saida dalili. Yace shikenan dauko min tabarma nima ban zuwa na kalleshi da mmki yayi murmushi wllh idan ba zaki ba nima ban zuwa dama tilastani akayi. Na rasa yanda zanyi da rigmarsa kullum da wacce zai bullo nace muje ka tambayi inna, da mmkina inna tace a dawo lfy muka fito yace ki saka leshin nan ja da takalmi silver kinji? Na daga kai, zan tafi saina dawo anjima nace to. Ni kadai nake bidirina a daki inna tana tsakar gida ina kwalliyata harda ta saman gira na feshe turaruka na fito tsakar gida inna ta kalleni ido waje tana mmki wann kwalliya haka humaira anya baki wuce gona da iri ba? Na yi murmushi, nace. " Inna ban yi kyau ba? " " kin yi kyau, amma kmr tayi yawa".Na zumbure baki da fadin. " wlh inna haka ake yayi".Ta harareni, "Ina ruwan ki da yayi? kin ga wlh ki dunga tuna matsayin ki, kada ki janyowa kanki damuwa".Shiru kawai nayi. karfe 9 naji ana sallama, na kalli inna. " zamu tafi, Ina jin shine ya aiko".Ta ce a dawo lfy, Allah ya tsare".Na ce "Ameen". Har na Kai bakin kofa, tace."kada ki wuce 11 dk abinki"."INA". na ce tare da ficewa. Sbd tsinin tklm ga rashin sabo sai na dinga takawa a hnkl kada na fadi, ckn direbobin gidan sarki na gani da alama bai ganeni ba. Motoci 4 na tarar a jefe, ya bude min Wacce tafi ko Wacce kyau da girma, na shiga Ina addu'ar neman tsari kmr Klum idan na baro gida hk ya zame min tamkar sallah. Yana rufewa naji an janyo ni a tsorace na kalli gefena, sai kawai naga Yrm. Kunya ta kamani, na ce, " Ba ni na gyara".Ya sakeni na matsa nesa da shi Ina fadin. " Ban son haka, don Allah ka daina".Ya yi murmushi, sai ya matso na kara takurewa ya ce. " kin yi kyau kmr ruwa. Cire 'yan kunnen na baki sarka".Ya fada yana laluben aljihunsa. A ciro bakaken 'yan kunnena dk sun yi baki sbd tsufa. Ya miko min wata dankareriyar sarkar zinare da 'yan kunnen ta.Na make hnn, "kayi hkr bazan karba ba, sbd wdnn zobunan ma inna tayi mini fada sosai"."sanya aro na baki ba kyauta ba, zan karba idan mun dawo".Jin haka na Sanya. " Ina alkawarin mu?"Na yi murmushi, " ya na nan"."Zaki bani ynz? ""Idan kana ganin Ina da shi a nan din".yayi 'yar dry, " Ai ko Yaushe kina tare da shi".Na ce, " Bisimillah".Ya yi Kasa da murya, "kada ki manta kin fa mallakamin tun kafin ki san ko menene".Na yi shiru kawai. Ya kama hnnyna duka biyun. "Humaira Ina barar soyayyarki, don Allah". A firgice na kalle shi daidai lkcn mota ta tsaya. Harabar wurin dankam da jama'a duk hankalinsu kuma ya dawo ga motocin da suka tsaya lkc guda. Dogarawa suka rugo suna bude mini kofa, ta kowane bangare barori kuma na watsa filawoyi. Abokansa suka rufa mana baya, naja tunga da sauri na tsaya, suka yi gaba. Wuri na nema na tsaya kusa da wata mota zufa kawai ke tsatsagomini ta ko'ina. Na kasa fassara yanayin da nake ciki.A hnkl naji an dafa kafadata, kafin na dago naga an zagaye ni. Na kalli sauran abokansa, nayi Kasa da kaina. " she is pretty".Na ji wani ya fada. Na kusa da shi ya ce."Akwai class I see".A hnkl yace, "Humaira mu je ki bani kwarin gwiwa, wlh bana son partyn nan ". wani ya matso, "kada ki biyewa zcy Humaira, ki tallafawa mai kaunar ki kada ki jefa shi...""kan uban can". Na ji saukar uban zagi kmr daga sama, ckn karaji Gimbiya ce tsaye tana hura hanci gefenta kawaye da sauran barori na kewaye da ita. Na zaro ido Ina yin baya- baya ckn matsanancin tsoro da firgita. " Ni Zaka ciwa mutunci? Ni zaka kunya ta a gaban jama'a ka rasa Wacce zaka hada sonta da nawa sai BAIWATA? Dama duk zame-zamenka a nan ka sauke? Haba biri yayi kama da mutum, ban manta abubuwan da suka ringa faruwaba, sai dai ka haddasa mata fitina, bala'i da tashin hkl ita da iyayenta a garin KANO!" ji kake tas! tas!! mari na wanke fuskarta ko ta Ina. " shut up! Idiot! " Ya bita da wdnn kalmomin, "kin isa ki yi abinda Allah bai nufa ba ne? ko kina ganin za ki iya hana abinda Allah ya hukunta?" To bude kunuwanki kmr ydd na sha fada miki, ba ki daga ckn tsarin matan da nake muradin aure.Bacin hadin iyaye babu abinda zan yi da ke a AURAKA! snn ki sanya wa ranki cewar Zaki yi kishi da baiwar da kika raina a kirata da GIMBIYA kmr ydd kike takama da sunan".Ta fashe da kuka, abokansa suka janye ta suna bata baki, amma har lkcn bata bar fadin, " ita ka cusawa wnn bakin cikin, wnn zan bambance muku MULKI da TALAKA sai an batar da su a kasar nan! !" Yunkurin cafkota yake yi ana rike shi, sauran abokan suka yi min zobe ganin Ina da niyar kwasa a guje. Tashin hnkln ya hana ni kuka, zcyta ta daskare kmr dutse, na kalli wnd ke bangaren damana ckn wani irin yanayi na ce. " ka taimakeni ka maidani wurin inna".Ya juyo da sauri jin muryata, hnn ya kama zamu bar wurin. wdnda suka janye Gimbiya suka tare mu da sauri. "Haba, Ina kuma zaka je kana ganin mun shawo kan Gimbiya? sauran 'yan korenta mun ja musu kunne su yi shiru da bakinsu".Ya kalle su, "Ba zan attending ba..." Suka rufar masa kowane da abinda yake fada, da kyar suka shawo kansa. wnd naji ya kira da suna sahabi ya karbi mukullin hnnsa zai mayar da ni gida, har mota ya Kai ni, snn ya saki hnn yana fadin "komai dare zan zo, kada ki yi bacci kin ji?" kmr na wawuro fuskar in cije don takaici, me kuma zai yi mini? wane bacci gare ni Ina ckn wnn tashin hnkln? A daidai Lungu ya tsaya na fita da sauri Ina jin yana cewa. " Mu kwana lfy ". Amma na yi kmr ban ji shi ba, zaman da na yi dabas ya sanya ta kalle ni da sauri, "Lfy? ""Da sauki inna ". Na fada ina rike kaina."Me ya faru? "Ta bukata a rude. Na zayyana mata komai. Ga Mamakina sai na ga ba ta wani razana ba, ta ce. " Ni dama na yi zargin haka tun farko, ganin cewar bai furta da bakinsa ba ya sanya na yi shiru, sbd maganar Hausawa idan baka iya kama barawo ba shi sai ya kama ka. Ba zan yi saurin cewa ba zai yiwu ba, sbd ba mu san hkncin Allah a kan lamarin ba, kada mu yi masa shishshi har mu saba masa. Amma da kmr wuya BAIWA ta auri DAN SARKI, kina karkashin mulkin gimbiyarsa". Na rike kaina da ke fizgawa tmkr zai bar wuyana tare da runtse ido, ba wai son shine ba ni yi ba, a'a ina hangar wa kaina tashin hnkln da ke gaba. Kmr inna ta karanci zcyta ta ce. " ynz kam dole runtse idanunmu, mu kuma toshe kunnuwanmu akan abinda zai biyo baya. A gaskiya zan roki yaron nan da ya janye bukatarsa abu ne mai whl ya rufa mana asiri, ya dubi maraicinmu". sai ynz kuka ya zo mini. Ta kalle ni. " ynz kika fara hawayenki su kare a banza, ko ki janyowa kanki wata matsala" "Ban katse ka ba, ina son ka gane abu guda. Yrnyr nan marainiyace, ka ga kuma ydd muke ba Wani boye-boye ynz, don hk son da ka ce kana yi mata to ka nema mata kwanciyar hnkl a rayuwarta. Gsky kayi hkr, wlh ba zan baka Humaira ba, sbd ka fi karfinta, ba km daya kukeba kai ni Ina shakkar son da kake yi mata da mamaki".Ga mamakin inna ta ga ya zube gwiwa bibiyu yana kwalla. " Haba inna, kada ki yi jayayya da ikon Allah mana, akwai wnd ya fi wani ga Allah ba ya ga mai tsoronSa? shin ya tsoron Allah ya ke? yin tawakkali da yrd akan dk abinda ya hukunta".Tausay insa ya far mata, sai kawai ta sunkuyar da kai. " Na amince, Allah ya yi mana jagora".sauran kwalln sk shatato masa."Nagode inna, Allah ya kara girma, ya kuma bani ikon rike Humaira bisa yrd da aminci". Yace ameen ya mike Zan koma sbd nabar gida kamr sansani yanzu abokaina basu sami runtsawa ba tace Allah yai mana jagora yace ameen. Har ya kai bakin kofa ya waigo donAllah Inna ku toshe kunnuwanku da duk maganganun da za'a zo muku dasu tace ISA ta fada tana mikewa shi kuma ya fice yana fadin zan dawo anjima idan humaira ta tashi. Kwalla ta zubo min burinsa ya cika ya rabani da aikina, motsin inna naji ta sassauta murya ki tashi wann kwanciyar bata da wani amfani a gareki. Ba'aja da ikon Allah sbd har abada bazan mance alhairin yaron nan ba sanadiyarsa ina neman rasa cutar tun shekaru masu yawa nake fama da ita tun magungunan da alluran da yayi min bai kara tashi ba. Na fahimci Allah ya dasa masa kaunarki matsayinsa yafi gaban ya zubda kwalla akanki ko yaudara yazoyi zan iya mallaka masa ke sbd yaudarar tazo cikin tsafta sai gashi ya tsugunna a gabanki ni mahaifiyarki yana kuka yana rokon amincewata kina tunanin Allah bazai kamani ba da alhakinsa? Ko kuwa mun yaba kyautarsa kenan? Ta girgiza kai tunda fahimci kyautar da yake mana wllh zan jure duk wani wulakanci da cin mutunci kema sai kin jure sbd bayan wuya sai dadi. A matsayina na mahaifiyarki humaira yanda nasanki da rashin sun magana tashin hankali da sauransu ina jiye miki kishi da gimbiya. Sai a lokacin kuka kuka yazo min da karfi na dinga sharbe harda majina Ta girgiza kai yanzu kika fara kuka dama kin daina wahalar da hawayenki a banza sbd yanzu aka fara bamusan abnd gaba zata haifar ba. Mutane muka hango a tsakar gida ai bansan yanda akayi na ganni a kofar daki ba hanjin cikina suka kada waya nunawa gimbiya gidanmu? Na fita daga kofar dakin ganina ya kara mata bacin rai. Don ubanki ina kazamar uwarki? Yanda tayi zagin gabana ya kara faduwa anya zan iya dauke cin mutuncin iyaye? Yana iya dama inna tace saina jure. Motsin inna naji a bayana tana cewa ganinan... Ta nunata da yatsa ba asiri ba wllh ko tsafi kike da bakar jaba yarki bazata auru ba munafuka. Tsautsayi yasa inna ta matso tana bata hakuri ta kuwa kundumo mata wani mugun zagi ba tare data girmamata ba. Zan nuna miki cewar sarki da talaka akwai bambanci sai kun raina kanku a garin nan shegu MATSAFA! Maganr ta daki zuciata anya zan iya shanye wulakancin su? Magnr ta tunzuro hrt dina tsanarsa ta bijiro min don shine musababbin karar marurrukan dake sauka kuncin inna yasa ta tangal- tangal nayi saurin riketa gabana yana faduwa kada ciwonta ya tashi aiko nan da nan ta fara shessheka ina kokarin zuwa dauko mata magani naji gimbiya na cewa a dakemu. Kota ina duka mukeji maza da mata su Aisha sai kuka sukeyi ganin an hada mana jini daga ni har inna niba dukan ke damuna ba ciwon inna kada ya galabaitar da ita amma rashin imani da tausayi baisa sun kyalemu ba saida muka matukar galabaita tuni inna ta sume rai yana kokarin fita ganin haka suka fita daga gidan jini yana fita a hannuna da goshina Na rarrafa na dauko mata maganin su sumayya suna watsa mata ruwa ina shaka mata maganin. Cikin ikon Allah ta farfado amma hannunta yaki motsawa, ihun su Aisha ya tara jamaa lokacn su gimbiya sun tafi abinka ga safiya ba kowa ya fito ba mal bala ya kalli hannun yace kamr karaya? Inna ta rintse ido mike cikin radadi suka kamata hannun yayi baya sai kawai ta zube tare da yin wata kara nima na kurma ihu na tallabeta jamaar gurin suka rude wasu suka ruga kiran mai dori kafinsu dawo mukaga bataliyar abokansa tun daga waje suka gidan dankam da mutane suka karaso a kidime basu jira komai ba suka dauki inna sukai asibiti da ita tuni ya tasa keyar su Aisha dama ni tun shigowata ya rike hannuna ya cika da tambayoyi. Bani iya masa fitsara dana gwada masa yau, kafinmu isa zazzabi ya rufeni ruf. Ni asibitin ma tsoro ya bani sbd kyaunsa nan da nan aka shiga da ita tiyata ni kuma aka bani daki da gado allura 2 akayi min sai magunguna da nasha shiys dressn din da akayi min banji zafi ba ita kuwa inna gurin kare dukan ne suka karyata kai Allah ya isa! Bacci ya daukeni wasan kusan 3 na farka gadon da ke kallon naga inna kwance itama tana ta sharar bacci. Su Aisha da abokansa suna zaune shi kuma yana tsaye ya jingina da bango ya harde hannuwa. Gaba 1 suka taso zuwa gaban gadon nayi saurin rufe idona sbd wani abu danaji yana harbin zuciata. A hnkl naji ana mgn kusa da fuskata kiyi hkri ki tashi kiyi sallah tym yana wucewa komai yayi zafi mgninsa Allah! Da sauri na bude ido jin muryar sadauki ya kada min kai ya kalli yarima ya maido kallonsa gareni muna tausaya muku anci zarafinku kuma zamuyi saurin daukar mataki wannan cin mutnci yayi yawa they have crossed their limit! Ga maganarsa ga kuma sannun da sahabi yake min narasa wanne zan saurara yarima kuwa har tym din ya kasa cewa komai da alamu ni yake kallo amma na kasa bude idona na ganshi Bayan nayi sallah suka fitineni saina ci abnc saida na cusa kadan. Sahabi ya kalli sadauki yace muje ko? Yace su Aisha muje waje muyi kallon haraba...... Turo kofar da akayi ne yasa maganr ta makale saura kadan na kwasa da gudu wata shamkiyar mata ce ta shiGo da dogarawa 4 a bayanta kallo 1 zaka mata kagane fuskarce bambancin tana mace yana namiji. Sadauki da sahabi suka zube a kasa suna barka da yamma Mama. Nayi saurin sunkui da kaina inajinta amsa kasa-kasa a tym din ya taho daga tsayuuwar da yake sai kawai ya fada jikinta baice komai ba ita kuma tasa hannu tana dan bugun bayansa alamar rarrashi, ta janyo hannunsa zuwa bakin gadona ga mmkina saita zauna kusa dani shi kuma ya zauna muka sata a tsakiya. Nayi saurin sauka kasa na zauna kusa da kafafunta. Sai naga dogarawan sun fice da alama umarni ta basu. tace dawo ki zauna nan ta nuna inda na tashi na girgiza kai kawai ina mmkn zuwanta a wnn tym din. Tayi shiru kamr yanda dakin ya dauki shiru cikin dabara sahabi ya fiddasu sumayya sanna ya dawo ayi komai a gabansa. Ta gyara murya toni yanzu mezanyi mk Hameed? Kamr yana jiran tambayar ne ya kalleta ido jajur cikin damuwa yace Mama duk duniar nan baya ga Allah banida wani gata saike ki dubi girman Allah zucita tana cikin tsananini ki rabani da wann auren na gimbiya bani kaunarta da duk wanda ya shafeta... Ta katseshi Bazan iyayi maka wann alkawarin ba sbd mai martaba ya bar wasicci ko bayan ransa idan baka auri farida ba bai yafe ba. Ya sassauta murya mama yarinyr nan bata da hnkl ki dubi inna... Sun karyata sannan dubi raunukan da sukaji mata ita da humaira shin Sarauta hauka ce mama? Ni nace inason yarnyr nan wllh har yanzu ban sami wata amsa dg gareta akan abnd tayi musu shin meyasa zucoyata bazata buga ba? Kina ganin wanda yayi wann aika-aikan bazai iya kisan kai ba? Kafiya gareka Hameed ina jiye maka fushin mahaifinka kana sane da cewa bazai amince maka ka auri wacce ba jinin sarauta ba gaba na ya buga da karfi taci gaba da cewa... Zuwan nan kadai ya fahimtar dani wani abu wllh na yaba da kunya nutsuwa da kuma hnkl kana da tabbacin kai sarki yabar wasiccin ka gajeshi idan ka tsaya akan wann ra'ayin lallai sarauta zata bar hannunka har abada. Wani abu naji ya tsikareni jikina yayi sanyi lakwas. Mama ya kira sunanta cikin wani ayanayi ta amsa ta kalleshi cikin jimami, duk dunia ba wanda yasan damuwata halina da kuma al*amurana kamar ke sbd ko tari nayi ko a bayan idonki saina sanar dake dn hk nakeso kibani mafita ayau wllh mamana zuciyata tana min zafi. Ina kallon sadauki ya matso kusa dashi ya dafa kafadarsa daidai tym din inna ta farka na mike zuwa gareta amma saiya rigani. A hnkli mama ta iso inna ta kallemu sai tayi smiling. Sannu ya karfin jikin ne? Mama Ta fada tana kallon hannu daya karye, da sauki ta fada tana kokarin tashi muka kamata har maman ta zauna saman gadon ganin hk yasa na koma na zauna yana ta koakrin mu hada ido amma naki. Mama ta dafa hannunta sannu inna, murmushi kawai tayi. Ganin hk ta fara magana donAllah kuyi hkri an zalinceku an shiga hhakinku amma danAllah kuyi hkri. Inna tayi shiru ta kauda kai, bazan gaji da baku hkri ba wllh inajinku har cikin raina domin duk abnd Hameed zai so ina son shi kamr yanda nake kin abinda bayaso. Nayi farin cikin ganin Hameed ya sami wacce tayi masa kuma ya furta yana kaunarta da bakinsa. Abnd na dade ina mafarkin gani yau gashi Allah ya tabbtr min dashi sbd kowa yana tunanin ko bashi da lfy ne baligi kamr sa ace baisan SO ba kullum sai yace bai sami wacce tayi masa ba don har dariya mukeyi masa tare da yan'uwansa idan yana suffanta yanayinta. A gsky na gasganta halayen Humaira dan zuwan nan da nayi nasan Hameed nice mahaifyarsa nasan kuma wayeshi wllh bazan taba jayayya da kaunar da yake mata ba nasan na gsky ne daga Allah. Kamr yanda nayi farin ciki ta wani fannin kuma ina bakin ciki sbd lokacin daya tsinci kansa cikin kaunar wacce yake mafarkin samu a lokacin ne mahaifinsa yasha alwashi akansa. Nasan halin mahaifinsa da tsatstsauran raayinsa akan duk abnd ya zartar mutum ne me zafin gaske me kishin sarautarsa baya kaunar talaka ya shigo masarautarsa da sunan haduwar jini duk kaunar da yake wa dansa zai iya yafeshi akan wann. Bani ba har inna saida ta razana da wann maganar a hnkli na zame na sulale kasa jikina ya dauki zafi sosai. Taci gaba da cewa shiyasa ayau abun ya daga min hnkl sosai jin kalaman da yake fada min a waya nasan zai aikata abnd yake fada. Ta kalli inna kaunar da yakewa Humaira ya zarta tunani amma ina da wata shawara guda, mu duka mu dage wajen fadawa Allah yanda ya hada wannan soyayya da yardarsa zai warware komi cikin sauki idan abun zaiyuwu yafimu sanin tsarin yanda zaiyi haka idan bazai yiwu ba. Ta dafa kafadar inna danAllah muyi hkri wata rana sai lbr. Kada muyi shisshigi na tabbata mai kudi da talaka da mai sarauta duk Allah guda suke bautawa. Kuma ba wanda yafi wani a gurin Allah sai wanda yafi tsoronsa. Zan tafi dashi don ya halarci bikin gudun faruwar wani abun zamansa anan zai iya zama wani tashin hnkln nizan bar wanda zai kula da kamar... Inna ta kalleta ISA bazamu kara kwana a nan ba yau zamu tafi gida. Da sauri ya dago kai gsky mama ba inda zanje gobe idan an kai amaryar da daddare na taho washe gari ayi budar kai amma dole in tsaya in kula da lfyrsu inna don nine musabbabin faruwar komai. Inna ta girgiza kai ko kadan bazakyi wann danyen aikin ba wllh mun yafe duniya da..... Ni inna ban yafe ba. Dakata to yanzu me kakeso ayi? Wane irin so ne mama ke masa batason bacin ransa kokari take tayi masa yanda yakeso. Ya bata fuska yace a kyaleni na zauna da inna gashi tfyta tasa zasu koma gida suma... Inna tayi murmushi na rantse da Allah ba wann ne yasa zamu tafi ba asibitin ne kawai bana son zama . Sadauki yace to ai ba'a gama dubaku ba ko inna? Tayi shiru bata tanka ba. Tace to zuwa yaushe za'a sallamemu? Ya langwabar da kai nan da kwana 4 da an kwance daurin. Ta kauda kai tace Allah ya kaimu suka amsa ameen. Mama ta mike zan bar mace 2 ta dinga kula daku zuwa sanda za'a sallameku zasu dinga siyo muku abnci da duk abnda kuke bukata, ta dora bandiran kudi akan gadon inna ga wann ko zaku bukaci wani abu, Allah ya bada lfy Har ta fito bai motsa ba Inna ta kalleshi tace tashi ka bita Allah ya bada sa'a. Saura kadan kwalla ta zubo masa ya kalleta yace inna banida lfy zuciyata na min zafi ga humaira tana fushi dani bata kaunar kallona tun jiya bata min maggana. Ya kara langwabar da kai inna laifi na ne? Cikin tausayawa tare da mmkin soyayyarr da yake min tace ba laifinka bane humaira kuma kada ka damu wann halinta ne nima tana min irin wann. Yace inna in bata waya? Tace a'a bazan taba amincewa ka bata waya ba kayi hkri kamr yanda nasha fada maka to yau ma kalmae ce. Ya sauka kasa ya durkusa. DonAllah inna ki taimakeni kinga gobe nisa zanyi daku. Tace kayi hkri wann sharadin mahaifinta ne idan ka aureta saika bata. Jin wann batun yasa ya mike kamr me koyon tfy haka yabar dakin. Wani dunkulallen abu ya tokare min wuyana shi bai wuce ba shi ba fito ba na runtse ido a cikin raina ina fadin Innalillahi wa'innalihirraji'uan. Motsin su Aisha yasa na bude idona na dauka ko shine ya dawo da sauri na maidasu na rufe ruf a yau na tabbatar yayi min nisa. Anya zai dawo gareni? Na dafe kaina cikin ikon Allah sai kwalla suka zuraromin makar famfo inna ta kauda kanta. na fara rokon Allah ya cire min tunanin yarima kuma Alhmdllh na fara ragewa sosai. Da marece bayan mun gama awara ina zaune inna taje gidan kawu auwalu su Aisha sunje islamiyya kamr daga sama naji sallamar amira da gudu na tarota muka rike juna cike da murna na kalleta a lokacn data zauna Inna bata fada miki inata zuwa ban iskeki ba? Ta dan bata fuska wllh humaira inajin sakonki matsalar bana zama kullum nayi dariya sannu agogo. Ta kai min duka na kauce ta mike dama lbr nazo na baki sannan nayi miki albishir kiyi min murnar abnd ya sameni safiyar nan kuma muyi bankwana amma tunda....... Haba kawata yi hkr, da kinjawa kanki yarnya ta kara gyara zama humaira yanayi miki wani irin so wanda bazan iya fassara shi ba domin abnd ya faru lokcn da za'a tafi da gimbiya motar mu daban amma ni ya hanani nabi cikinsi ya sanyani a motarsu. Nida shi ne a baya tunda muka tafi kansa yake a duke har muka bar garin nan zuwa can ya dago ido jajur don saida na tsorata. Inason kawarki amma son bayada amfani gareni. Na sunkuyar da kaina kawai ina wasa da yatsuna wanda ke tukin motar ya juyo kaidai akwai dan iska yaushe muna kan layin raka matarka gida amma kana zancen wata? Shiru yayi kamr bada shi yake ba kinsna miskilancin mutumin naki. Yaja guntun tsaki daga nan bai kara mgn ba har muka isa. Humaira naje karshen mulki a sarauta naga inda ake takama da sarauta ashe su gimbiya basu iya komai ba? Motarmu na tsayawa wasu gardawan sarki suka zo wani ya kwanta saman shi ya sauka biyun kuma sukayi sama dashi bisa wani dan gaka suka daukeshi sukayi ciki dashi daga nan ban kara ganinshi ba sai washe gari. Kwana akayi shagali washe gari da misalin 12 akazo nemana na gane hakan ta yadda akayi kwatancen wacce suka shigo mota 1 da yarima cikina ya dinga kadawa sbd tsoro kada ace ko cigiya sukeyi. Munyi tafiya sosai kafin muje inda suke ya nuna wata kofa ki shiga ba tare da bata tym ba na shiga mazane shakare a falon duk gimansa sun cikashi na duba amma nakasa gane kowa a cikinsu da alama basu damu da shigowata ba. Keni sai tsoro ya kamani nayi saurin juyawa kamar daga sama naji ya kira sunana ashe yana kishingide cikin kujera yana kallona Hmmm miskilanci da kasaitarsa yana ba mutane tsoro, a tsorace na karasa inda yake ko kallona bayyi ba ya miko min wata rantsattsiyar wayarsa, ungo kisamin lamabr da kike gani zan iya magana da kawarki nakasa karba sbd kinga banida lamabar kowa a kaina wllh kota sadan gidanmu ban rike ba. Murya na rawa nace wllh banida lambar kowa akaina Allah ya taimakeka. Kallon da yayi min na rantse saida guntun fitsari ya zubo min idanunsa sukayi wani irin ja har wani ruwa ruwa ya kwanta. Tunda ya dauke kao bai sake kallon inda nake ba saida na kusan 1hr a haka nagaji iyakar gajiya har kafafuna sukayi sanyi, dogarawan dake tsaye suna masa firfita sai kallona suke na raina kaina a wurin ranar naji na tsani abotarmu dake. Da Allah ya taimakeni saiga wani abokinsa ya kalleni yace wann fa? Naga bakuwar fuska, ya kalleni da wann yatsinar tasa yace ki tafi mana. Simi-simi nabar gun kamar na bude kasa na shige don kunya. Bansan wace amsa ya bashi ba. An gama shagulgula amarya ta tare a gidanta wann sashe daya kirani gida yasha kayan kwalliya dukiya tasha kuka. Abnd ya bani mmk har yanzu basu bar al'adar nuna kwanan amarya ba. Sbd washe gari gida ya rude da gimbiya bata cika budurwa ba Abun kunyar gimbiya ya nemi komawa fitina da tashin hnkl. Ga yarima an nemeshi an rasa tun safe gimbiya ko sai kuka take sharbawa kamr ranta zai fita tana rantsuwa tana sharbewa wai bai kwanta aure da ita ba. Magana har gaban sarki gida ya sake rudewa duk inda ake zatonsa an aika amma ba'a tadda shi ba, hnkln gimbiya ya kara tashi mai martaba ya kara fusata ita kuwa mahaifiyarsa ko gezau saima fada data kamayi ita bata ga amfanin auren dole ba shin tunda yace bayaso bayaso a kyaleshi ya auri wacce yakeso mana. Aiko magana ta komawa sarki, ta kalleni Humaira munga tashin hnkl bana fatan sake ganin fushin babba idan haka yake. Maganar na zuwa wajen sarki kuma sai aka sami wayar sarki yace duk inda yake wllh ya bashi 3mins ya gurfana agabansa sannan ya aika aka kira sauran matan gidan cikin yan dakikai falon me martaba ya cika da ahalin gidan gimbiya na tsakiya har lokacn bata daina kuka ba zuwansa kawai ake jira. Shigowarsa ke da wuya ga mmkin kowa sai mai martaba ya mike ya dinga kwada masa mari har sau uku hancinsa kuwa ya balle da jini amma wllh ko gezau baiyi ba. Ni zaka kawowa raini? Ni zaka tozarta ka kunyata a idon dunia? Ka kwanta da matarka ko kuwa? Jinin dake zuba a hancinsa har ya fara bata gaban rigarsa fara, ya sunkuyar da kai a'a ban kwanta da ita ba. Ya fusata kayi hakane don ka nuna ban isa dakai ba? Ya kalli jakadiya saikije ki fada mutane yarinya bata kwanta aure ba Allah kuma zai saka mata bacin sunan dakayi mata. idan kuma nina haifeka wllh babu kai ba talaka komai ya dawo kunnena yau kuma na tabbtr da daurin gindin daka samu daga uwarka. Duk ranar da naji baka rabu da ita ba to wllh na yafeka dunia da lahira shashasha sakarai! Wann furucin na sarki ya haifar da zazzafar tsana da kiyayya tsakanin gimbiya da mahaifiyar yarima shima cin zarafin da akayi masa gaban jamaa ya kara sashi jin tsanarta fiye da baya. Sarki yayi musu kaca-kaca shida mahaifiyar sbd ina zargin ita ke goya masa baya. Sann yace da gimbiya dataga wani abu wanda baiyi daidai da tsarinta ba ta sanar dashi zaiyi maganin abun cikin gaggawa. Ana barin fada yaje ya zuba kankana akan habon jinin ya tsaya muna harabar gidan mukaji karar gimbiya sau daya. Muka razana kar dai ace shaketa yayi muka nemi shiga amma ya kulle kofar Ganin ya kullo kofar tsoro ya kamamu don munga shigarsa cikin tsananin fushi, karima ta kalleni gsky amira guduwa zanyi bana iya wan bala'in da gimbiya...uhm uhm wllh duk abnd yayi mata ita taja auren nan hadin iyayene, tun farko ya nuna mata bayaso shin idan ita mai wayo ce basaita lallabashi ba? Ga rashin so ga izgilanci da tsageranci mekike tunanin zai haifar? Kinga kuwa abnd tayiwa mahaifiyar humaira da ita kanta humairan? Wllh na tabbt gimbiya zata iyakisan kai, amma ke bakiga yanda ya shiga da fushi ba? Shin koma menene aiya riga ya faru ko kina iya balle kofar ki shiga? Ko dukansa yake kofa bude kina iya karbar gimbiya hannunsa ne? (Wannan rawar kan sai SIYYA) to wai humaira na sonsa da gaske? Kwarai saidai tsoro ya rinjayi son shiyasa ba kowa ke ganewa ba amma wllh humaira na sonsa matuka. Nayi saurin kai mata duka ni nace miki ina son sa? Kai-kai-kai ni kika doka? Baki sonsa kenan? To bari na tafi gida dama na dauka kina sonsa shiyasa na tsaya bata tym dina ina baki lbrnsa. Na marairaice yi hkri kawata dan karasa min wasa nake miki sorry, kina sonsa? Sosai ni kuwa ke sonsa zauna ki karsa min dukanta yayi? Wace irin fitina ce ya kara janyowa kansa? Na fakaiceta na mata gwalo, ta zauna idanunta sunyi ja kwalla ta taro mata taci gaba d acewa muna cikin wann magana humaira sai gashi ya fito ya sha kananan kaya yana ta uban kamshi hhar tym din acikin fushi yake. Dogarai suka rufa masa baya yayi hanyar shakatawa. Yana bacewa mukayi hanyar daki dake kallon nasa muna jiyo gunjin kukanta. A hamzarce muka nufeshi kwallan da take kokarin maidawa suka zubo gabana ya fadi na kosa naji abnd yayi mata ta kalleni kwallar na zuba wllh humaira duk irin isgilancinta saida ta bani tausayi, kwance take bisa gado yarima yayi mata kaca- kaca jini duk ya bata zanin gadon (wayyo Allah yarima ashe dai mugu ne kai?) Kukanta kawai kakeji har muryarta ta dashe amma bata iya ko motsawa hannu karima ta dora aka ta kurma ihu ni kuma na hau kyarma kukan yaki zuwa min hnklina ya bala'in tashi don ko a lbri wllh ban taba jin irin haka ba da gudu na fita zuwa sashen mama na sanar da ita abnd yake faruwa. Cikin halin ko in kula tace aje a sanar da jakadiya. Zuciata ta tsaya cak guri guda naji ya fita a raina sam, na sunkuyar da kaina na kassara abnd ke zuciaya wanda ya bakunceni yanzun nan. Abin haushi wai jakadiya na zuwa saita rangada guda wllh nan da nan mata suka cika dakin a ka ciccibi gimbiya wasu sukayi toilet da ita tana uban ihun zafi wasu kuma suka yaye zanin gadon sukayi fada dashi. In takaice kiki har dinki akayi mata yaji mata ciwo sosai saida tayi jinyar sati w tun daga ranar ina kula ko kallon arziki bata samu daga gurinsa. Bayan 2wks yana zaune falo mun kawo masa b/ fast yana rike da waya a hannunsa kullum haka yakeyi a she pic dinki ne ajiki yake kallo kwatsam saiga gimbiya wllh humaira idan ni yayiwa wann wulakancin ko shine autan maza na hakura dashi. Amma don rashin zuciya irin na gimbiya daga fitowarta ko kunyar mu bata ji ta ta haye kan cinyarsa tana wani kissa aiko karaf idon ta ya kai akan wayar shi tayi sama da wayar tana surfa uwar ashar tana zazzaga bala'I wai me kake nufi dani ne ko an gaya maka abinci kawai nazo ci? Kin ji fa wato ita bata ji haushin abunda ya mata ba har wani neman shi take yi Wannan yar iskan kenan bata kyale ka ba har yanzu. To wlh ga mai marta ba zan kai ka kuma shi zan ba wayar ai bata karasa ba yayi kukan kura ya amshe wayar shi ta harziko sai kawai ta fara zagin sa banza dan talaka wanda bai gaji arziki ba wanda suka yiwa sarauta haye ai da bamu san asalin angulu ba duk abunda kayi babu mamaki tunda sarautar BORE ce kuma hakkina da kake tauye man Allah ya isa..... Bata karasa ba ya juyo ya kalle mu yace duk mu fita wlh a. Falo ya. Kara yi mata wani wulakancin ya barta nan kwance yayi tafiyan shi ranar nida karima muka taimaka mata ta gasa jikin ta kamarna bata shawarar ita ma ta kyale shi mana sai kuma nayyi shuru a tunani na a tunda an kara na 2 bata bari a kara na 3 ba Bayan kwana 2 ya kira ni yace na kawo mashi tea ba madara da dankali. Na ttafi zan kai masa na ga gimbiya tace na bata wannan na hada mai wani (kiji neman. Dalili da rashin zuciya) ina cikin hada masa kashi na 2 ya shigo kicin din ganin ina aikin yasa bai yi magana ba amma da ganin shi ranshi ya baci kinsan halin mutumen naki. Da KASAITA Har ya juya zai tafi na yi sauri na duka nace *llah ya taimaka kayi mini gafara na hada maka zan kawo gimbiya ta amsa tace na hada maka wani ya yatsina fuska kamar yadda ya saba kafin yayi magana Kina iya bari na fasa maza kije ki shirya zamu je garin ku ki raka ni wurin kawar ki watakila dalilim zuwa dake ta saurareni wlh wlj humaira daga ni har shi bamu san gimbiya ta fito ba ashe jakadiya ta aika aka kira mata ta tura ta gun sarki a shaida masa abinda yake shirin yi Tayi shigewarta daki na fiti a shirye yana zaune a falo yana shirin mikewa kenan aka turo kiransa a fada nazauna a saman kujera dogari ya kalle ni ya ce harda ke ma yar rakiyan yake kira gabana ya fadi ashe tunmi ya fahimci abunda ke faruwa Muna isa mai marta ba ya fara bala'I inda yake shiga bata nan yake fita ba duk yaddake sin kare kansa amma abu ya faskara ya dinga yi masa muna nan kalamai wadanda zasu bi shi matukar bai rabu da ke ba in takaice maki magana mafarin ya ce zasu bar kasar kenan da zama don ya manta dake shi da sarki ya mutu ya zo a bashi sarauta idan kuma ya saba ko da gigi yazo naija to babu shi har abada duk wanda yake son gani yayo waya zaa tura mashi shi ni kuma aka gargade ni akan duk randana sake biye masa muka aikata hakkan to zanyi zaman bursuna na shekara 20 a gidan sarauta kwalla suka zubo mata ina kallon ta ta ce humaira wlh muna fitowa fada wuri ya smau ya zauna kawai naga ya fashe da kuka nima sai na taya shi ya kalle ni bani da saa dunia ni kuma kaddarar da Allah ya nufe ni da ita kenan to shine fa aka bamu butu kafin cikin mu a zabi wacce zaa tafi da ita a matsayyin mai aiki ranar da zamu taho ya bani takardar nan ya ce na kawo maki amma dom Allah kada kiyi kuka sbd haka zai tafi ki kawo rply na kai masa kuma zamu rinka waya da yaya zan ce ya rinka kawo maki muna gaisawa nace to tayi juyin duniya nace wlh bani da wata amsa ta gaida shi dole ta kyale. Ni Lbrn da amira tazo man dashi shi ya sa komai ta koma mini sabo nayi kuka har kaina yafara ciwo Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Subul da baka 2 page 2 Posted by ANaM Dorayi on 07:12 AM, 21-May-15 Under: Subul da Baka kuma akace damu za a tafi wallahi yau yau dinnan na dawo wanka kawai nayi don na cika alkawarin dana daukarwa.. Da sauri na kalleta' se kuma na sunkuyar da kaina kasa. Ta fiddo doguwar takarda tace: "Gashi yace dan Allah kada kiyi kuka' kiyi masa wannan alkawarin" Murmushi kawai nayi idona ya ciko da kwallo' tayi saurin kawar da fuskarta'sannan ta kara mikomin takarda ambulan doguwa. Ta mike' zan tafi akwai labari' amma se zuwa jibi idan na dawo' gobe zanje Karkasara shi yasa. Nayi murmushi tare da mikewa na rakata' rakiya mai nisa har kusan lungun gidansu sannan na koma. inna nacan tana wanke waken awarar gobe' su Aisha na taya ta na shiga dakia kagare inji takardar abinda ta kunsa' haka kawai jikina ya ba ni maganace mai dauke da kwanciyar hankali domin na tabbatar yana sane da halin da na shiga. Tun kafin na fara karantawa na qurawa rubutun ido, yadda yayi shi wara wara yaddazan fahimta, nace "Bismillla" "Gimbiya Humaira" Na runtse ido ina sauraton yanayin furtakalmar acan baya da yayi' wanda ya kasancemasa tamkar" SUBUL DA BAKA" "ina roqonki da girman Allah ki daure ki cije kada kiyi ma rubutunnan kuka, kiyi mini wannan alfarmar please! Humaira ba se na fada miki ba na tabbata kin fahinci kaunar da nake miki, na da de ina mafarkin samun macen da nake muradi kafin Allah ya hadani dake, amma rashin sa'a se muka sami banbancin ra'ayi damahaifina. Nayi duk iya kokarina in tallabomatsalar amma abu ya faskaradomin yayimini FURUCIN dana tsorata da shi, furucin daya tsoratani kuma ya firgitani. Don haka ina rokonki kiyi hakuri mu dauki abin nan kaddara duk da na fahimci cewa ni ban kwanta maki arai ba humaira bana son farida bana kaunarta wannan cutar kadai xata galabaitar dani soyayyarki kuma takaini lahira mu yafewa juna domin gobe xamu bar kasar nan xuwa australia a can xamu xauna dindindin inji sarki harsai bayan ransa in dawo in karbi sarauta ga cheque dina nan na banki duk nayi signing ki rinka fidda kudi kuma ki koma makaranta idan xakiyi aure ayi miki kayan daki insha Allahu xan kawo maki xiyara anytime. Kuka y hananani karasawa nayi nayi kamar raina xai fita inna ta shigo da sauri tana salati dakyar na bayyana mata wani abun shiru tayi tare da ficewa waje amma a zihiri na ga ranta ya baci bata yi mini maganar ba sai da daddare ina zaune saman abin sallah na hade kaina da guiwa cikin wani yanayi idanuna ina jin su tamkar garwashin wuta kirjina kuwa kamar an dora man dutsen dala Humaira inna ta kira sunana Na amsa naam murya ta kasa kasa Yanzu kinfi son ganin tunon asirin rayuwan mu akan rufuwan sa Nayi shuru ban amsa ba Ashe ba zaki hkr ba? Kwalla suka zubo mani nace wlh inna ba wannan ne damuwa ta Na bata lbrn takardar da aka kawo mun da abunda amira tazo man dashi ta harzuka to ina abunda ya dame ki dasu bance ki manta ba kuma nima ba zan taba mantawa dashi ba amma wlh ki cire maganar soyayya Yafi karifin ki humaira ba mijinki bane kiyi nesa da soyayyar wahala idan kika kuskure sai gimbiya tafiki kwanciyar hankali nayi saurin kai kaina kasa ina sujjada "Ya Allah kana ji Allah ka yi mini maganin matsala ta Allah kai ka haifar soyayya a zukatan mu Allah kayi magana maganin ta bayan kwana 2 inna tace gaskiya nima na goyi bayan ki koma makaranta amma baxamu taba kudinsa ba Sbd haka saimu shirya gobe muje Govt college muji idan zasu mai daki. Hakan kuw akayi ga mmkina aka sakani SS3 kuma saura 3mnths suyi exams na dage da karatu wanda rabinsa tunani ne. Dr ibrhm kuwa tun ina shareshi harna fara sakin jiki dashi sbd fadan inna kada nayi saki na dafe a dinga nunani nayi kwantai har an fara min shaidar me kudi nakeso, Inna ta buga tsaki sannan kiyi kaffa kaffa da masu zuwa wurin ki domin iyayen ki sunyi mugun kudiri akan ki maganar karatu kuma sun ce basu amince ba matukar kika ci. Gaba da zuwa wlh komai suka yi miki don kanki Ko don ina cikin damuwa? Sai maganar bata wani dame ni ba idan Allah ya nufe ni da ilimin bokon nan na tabbatar da kudin da ya bamu zasu ishe mu har zuwa wani lokaci ko da bamu sanaa balle ma muna awara ga cek bayan sati 2 na dayaye dr ibrahim yaci gaba da zuwa kusan kullun kwatsam rannan yazo ya ce zai tafi karo karatu an tura shi singapore kuma shekaru 4 zai yi inna ta nisa ta ce to Allah ya tabbatar da alkhairi amin ya fidda sabuwan waya mai kyau da tsada ya bani yace inna ga wannan zamu rinka gaisawa kusan kullun don Allah tace to bata angode kawai raina ya baci watau ya tabbata inna bata son tunda kiri kiri ta hana ya bani waya ya miko mani dalleliyar blackberry sabuwa dal na amsa fuskata babu yabo ba fallasa, Inna ta hararoni nayi kmr ban gani ba yana fiata ta jefoni da murfin kwano zaki bishi kuyi bankwana ko kuwa? Na mike idanuna cike da kwalla na bishi yana tsaye jikin katanga ya hada kaida bango mostina kawai yaji da alama ni din yake bukatar gani yayi saurin dagowa idanunsa sun dan yi ja abnd ban taba gani ba nayi saurin kauda kaina sbd wani abu da naji yana bakuntar zuciata ya dubeni yace humaira zan tafi amma bakin cikina bansami wata kwakkwarar amsa daga wurinki ba. Jikina yayi sanyi zuciata tayi kunci haka kawai nakasa fahimtar abnd ke damuna. Ya kara kwantar da murya na kasance ma'abocin son zama da mace kwaya 1 a rayuwata amma burina ya rushe lokacin da nayi katari da matar da muka sami babbancin akida. Wllh humaira ba don ina kaunarki nake kushe matata ba na rantse miki banajin dadinta ko alama. Kadan daga cikin abnd tayi min kuma shine mafi karanci data mari mahaifiyata agabana...... Da sauri na kalleshi yayi murmushi irin na takaici yace kuma ta hanani na saketa, ki taimakeni ki sanar dani matsayina a wurinki wllh humaira bazan taba wulakantaki ba magnrki taje ko ina a danginmu mamana kullum sai tayi zancenki babana kuma ya rasu. Kuma nayi promise bazan hadaku gida 1 ko unguwa 1 ba believe me humaira pls. Tunani yazo min idan nayiwa ibrhm wulakanci koban amsa masa ba banyiwa kaina ba kuwa? Wa nake jira wa kuma nake dashi a hannu? Idan har abnd yake fada gsky ne ai nayi dace amma matsalr nayita jira har 4yrs? Kamr ya karanci zuciata naji yace kada kiji nace 4yrs ki dauka ko zaki ta zaman zuwana ne a'a ISA duk year zan dinga zuwa inaso ki tabbtr min da mgnta ne ni kuma a yau din nan zan gabatar da maganata zan bar komai in yaso da nazo hutu ayi biki idan da hali mu tafi tare if nt saina barwa broda na komai daga baya sai ki bini idan kuma kina ganin akwai matsala donAllah ki sanar dani. Nayi shiru ina nazari shin idan nace baiyi min ba wa zai min a dunia? Ko haka zan zauna ba wan ba kanin? Kirjina yayi min nauyi idanuna suka ciko da kwalla har yaushe zan manta da yarima a rayuwata? Ko in baki tym muyi magana a waya? Nayi saurin daga kai na alamar eh. Yayi murmushi to shikenn sai munyi magana. Na daure nace Allah ya kiyaye ya bada sa'a. Yanayinsa ya nuna min yaji dadi nagode humaira thank U so much for ur prayers, na yi murmushi na juya na shiga gida. Ko zama banyi ba inna ta hau fada wllh humaira banajin dadin halayenki da kika tsira har yaushe zaki daina tunanin yarima a rayuwarki? Wllh inna ni..... Zaki kaffara don kin isa yinta kibar rantsuawa. Wannan kunge-kungen da kikeyiwa wann bawan Allahn na menene? Kwata kwata kin daina sauraron kowa, wallahi kiyi nesa da kanki, iyayenki sun hanaki karatu saboda wata manufa tasu daban, shin auren kuma sai kihana kanki wanda shine mutumcin kowace ya mace? Humaira asirinmu kike son tonawa? Kin mance abinda mahaifinki ya fada akan soyayyarku? Gabana ya fadi saboda yanayin yadda naji inna tayi maganar kamar zatayi kuka. Kinyi dai dai, kuma Allah yabaki sa'ar kin sauraron ibrahim, yaron arziki bna ki tunanin Allah ne yakawo miki madadin....? Tunda shima gwargwado yanada kyawunsa? Ilimin nan yana dashi, sannan ga arzikinsa na rufin asiri? Anya ba maganar mutane bane Humaira kwadayi ke fizgarki ba? Haba inna..... Rufe mini baki mara kunya to me kike nufi in ba kwadayin SARAUTA ba? Ga babanki Auwalu can yadauki alwashin sai ya cusa mana bakin ciki ni da ke, bansan abinda yake nufi ba, yana korafin jin zafin yayansa na auren masu kudi, shiyasa kike wannan sakarcin, to yasan maganinmu. Ko dan wannan ma bakya yiwa kanki fada ba? Kiyi fatan Allah ya baki nagari mai kaunarki da danginki.. Ta kawar da fuska amma ba komai kije kiyi abinda kika ga dama.. Na sauko kasa, Inna kiyi hakuri, in sha Allah zan sanar da Ibrahim cewa na amince da shi... Da sauri ta kalleni to shikenan ya wuce Allah yamana jagora nace amin... Kwalla suka zubo min narasa na menene ni kuma haka Allah ya taaro mini rayuwa?? Baniga karaty baniga aure tunda shi Ibrahim......koda yake yace idan nayarda zai dawo a yi biki. Sallamar yaro muka ji inna tace ya shigo. Wai humaira ta zo anbugo mata waya daga kasar waje Ina jin haka na miqe zumbur na . gane ameera ce. Ya miqo man lokacin da muka isa nida aisha. Na koma gefen shagon kusada bedi na kanga a kunne 'Hello' amira kun isa lafia? Lafia qalau, baki lafia ne naji muranki kamar kinyi kuka? Na girgiza kaina kamar tana kallona, lafiata lau ina fama da mura ne. Nima kuwa nayi waya. Don Allah? Ta fada tana murna. Walhi kuwa zan sanya a turo maki lambar se mu dinga magana da tawa. Yauwa to yayi kyau nagode.nace nima nagode qawata se na kiraki. Haba yaya me ya hanaka qarasawa gdan? Yayi murmushi hakanan. Na miqa masa wayata turamata lambata nima ka sakaman tata. Yace to humaira manya wannan irin babbar waya? Nayi murmushi 'Ni don Allah gobema idan kanada lokaci zan zo gdan kadan gwagwada mani yadda take kasan sabon shiga, kuma ka turamani qur'ani da adu'o'i. Yayi dariya yayi ustaziya karfe nawa zaki shgo? Lokacin da kake nan, ni gobe ba inda zan je. Nace to zan shgo wajan goma zuwa sha daya. Muna bin hanya zamu koma gda wayar ta hau kuka nayi saurin latsawa na dauka a tunanina amira ce dan ko suna ban duba ba Assalamu Alaikun kinga lambar ta shigo? Yayi murmushi wacece har an fara rabawa qawaye lamba? Nayi jim, to me tafiya ne ya bugo yace maki gashi a cikin jirgi, nace au walhi ban duba bane kayi hakuri, Allah ya saukeku lafia. Amin ya Allah humaira zan kiraki idan na sauka. Na bawa qanena lambarki duk sati zaya dinga sako maki kati kinji? Ban san lokacin da nace haba harda wahala kuma? Yayi murmushi 'a wurinki yake wahala' hmmm to na gode. Zan kashe wayata sena kiraki idan mun sauka. Nace to masha Allah. Dai dai lokacin da muka isa dak, 'keda wa kuma ko kin turamata lambar ne? Nace a'a ibrahm ne tayi murmushi yayi kyau, nayi yar daria 'kai inna na lura kina cikin gwamnatin mutumin nan. Ai dole humaira yaron daya so naka ba don wani abu ba sbd Allah kuma dangi da yan'uwansa basu nuna kyama ba dole a soshi Kema harda yarinta ke damunki bazaki abnd nake nufi ba sai nan gaba. Bakina yayi SUBUL DA BAKA nace ina fa? Inna gurin shi daban yake a zuciata wanda yayi sanadiyar rabuwata da ciwona ai alhairnsa bazai gushe ba a zuciyata. Cikin raina nace kema kenan inna ni kuma nace me? Wanda ya cusa min soyayyarsa da karfin tsiya ba tare dana farga ba. Wayyo Allah wayyo sarki ya samu cikin damuwa. Na maida kwallar data zubo min. ** N9,035 muka kirga cinikinmu na awara na yau inna ta kalleni tana yar dariyar jin dadi. Kai Alhmdllh humaira mungode Allah ya taimaki yarima ya rufa masa asiri shine silar wannan rufin asirin da muke samu. Nayi murmushi inna kullum sai kin min fadan na manta dashi gashi ke har yau kinsa mantawa dashi shin kin kasa mantawa dashi inna yaushe nima zai gushe a raina? Ni kuwa kinsan shawarar dana yanke mana? Nace a'a tare da smiling don na kula zancen nawa zata kawar. Kinga muna da yan kudinmu na sana'a da wadanda ke ajiye me zai hana musa a gina mana daki babba daga can gurin tukwanen ruwan can mu koma wann kuma ya koma kicin sbd damuna? Na buga tsalle kwarai inna kin kawo shawara amma a gina mana ciki da falo yafi sirri. Ai kudi na keji humai, inna In Shaa Allah zasu isa har ayi rara dayawa. To shikenan dama inaso mu fara siyan kayan aurenki d an gama kada muji kunya ISA inna bazamu taba jin kunya ba Allah daiya kara rufa mana asiri tace amin. Kullum adduarmu kenan kuma Alhmdllh muna ganin budi. Babansu amira inna taba kudin siminti da yashi washe gari aka fara aikin da misalin 1pm nakaiwa masu ginin abnc kenan mukaji sallama kallo daya nayi mata nagane ta jikina ya mutu murus wani yanayi ya dawo min sabo. Tunda ta shigo idonta yake kaina da sauri na nufi daki inna mun shiga 3 ga innar...... Tsaye tabarni tayi waje da gudu cikin rudu, mashaa Allah jiki yayi kyau, ta fada tana murmushi. Inna tayi ajiyr hrt ta karasa tana yar dariya tace maraba lale sannunku da zuwa. Na fito daga dakin bayan sun zauna narakasa na gaidasu kaina kasa. Humaira ya jikinku ya bayan kwana 2? Nace ya warware Alhmdllh ina sunkuye da kai kasa. Na mike ina kokarin kawo musu ruwa da abnc tace zauna humaira ina zakije? Kaina kasa naceabnc zan kawo muku da ruwa, tayi yardariya tace Allah sarki wllh a koshemuke mungode Allah ya bada ladarniyya. Kowa na dakin yace ameen, nakoma na zauna kamr yanda ta bukata.Hameed ya turoni yace inji lfy kia barkaratun? Banyi mmki ba sbd nasanamira ce ta fada masa, inna ta fahimcihalin da nake shirin shiga don hakatayi saurin gaya mata abnd ya farugaba 1. Tayi jim to Allah yasa haka yafialkhairi a gareki inna tace ameen, tamike mu zamu koma ta fiddo kudimasu yawa ta aje a kusa dani ga wannasai jambaki da hoda. Da kyar naceangode don kunya inna ce tayi musurakiya har kofar gida.Ko zama batayi ba tace kai jamaawadannan mutane suna kaunarmuhumaira. Shiru nayi kawai sbd zuwanya haddasa min abubuwa da dama.Koda inna ta lura saitayi saurin sauyazancen zuwa lbrn ban dariya. Aini datace kisai jambaki ba wacce ta fado minarai sai ummu Ahmad Rufai ta sokotowacce akafi sani da ummu labour ita fahar kamfanin jambaki sunsan da ita ita ke banilbr wai wani mutum yayi sabuwaramarya jawara ranar data tare ya fitasiyo musu kaza daya dawo saiya tararta tasa huluna guda 3 a gaba tanatakuka ya karasa hnkli tashe amarya yaakayi ne ranar farin cikinmu kina kuka? Yace kiyi mgn wadannan hulunan fa?Tace hulun nan da kake gani wannranar da aka daura mana aure ya rasuwann kuma ana shirin kawoni gidansaya rasu shi kuwa wann ranar da akakawoni gidansa ya rasu kaga kuwa dolenayi kuka ta sake rushewa da kuka.Da jin haka sai ya cire hularsa ya jefamata saiki kara kice wann kuma wandaya gudu ne har ya bar miki kaza dagidan shine gaba daya haba! Saiyakwasa a guje! Hahahahahahha bansansanda na kwashe da dariya ba. Innatace tsaya ma kiji wani lbrn wasu barayine su 2 suka sato lemuka basu tsayako ina ba makabarta suna cikin rabosaiga wani mutum yazo wucewa saiyaji ana cewa kai ga naka niga nawa!Haba saiya ruga da gudu ga liman daisarsa sai yace Allah ya gafarta yanzunnan da zan wuce ta makabrta najimala'iku suna rabon yan wuta da yanaljanna, liman da jin haka yace ai saimuje muji wann ilimi ne babbab mefadakarwa, suna zuwa sai sukaji ana toga sauran naka ga nawa sai dayan yaceka manta akwai saura yace wannekenan? Yace wadannan biyun dakewaje fa? Haba! Su liman sai aka dafekeya wann ya wuce wancan wancan yawuce wannan hahahaahhahahaah!Wayyo cikina inna ta sani dariya hardakifawa Inna na jin dadin dama ina kaunar labarukan ban dariya. Ta kara cewa, sai wasu abokai su uku su ka kai matansu haihuwa asbt sai ga nurse tace ina mai aiki a twintower? Yace gani tayi dry tace cngrts matarka ta haifa maka twins. Tana komawa ba da jimawa ba kadan tadawo ina wandake aikin 3 crown? Gani kasami yan 3. Dayan naji najin haka sai yafashe da kuka lfy? Ni ina aiki a 7up ne... Narike cikina wayyo duniya inna shi bazai hakura ma azo kanshi ba yana tsoronkada ace an haifa masa yara 7..nakara kyalkyalewa da dry, cikin dry nace nima tsaya kiji wani inna akwai wani mai arziki yanada matarsa daya da dansa junior da yar aikinsa budurwa kyakkywa merry da kuma yaron gida suna zaune cikin jin dadi komai a wadace wata rana maigida ya kawo giyarsa mai tsada ya ajiye a firij yafita da niyyar in yadawi ya sha.yaron gida yabude firij yanaso yasha ruwa sai yayi ido 4 da giya kawai yakwashi giyar yashanye tas sai yacika kwalbar da yogot.aka duba giya tazama yogot oga ya kwalaqaYaron gida kira bulus ya amsa......(dayake nasan duk kunsan labarannan bari Na tsallakesu ANaM Dorayi) ta kyalkyale dariya haka mukayi ta labarai maau ban dariya. Raina yayi fes namanta da duk wata damuwa. Zuciyar innaZuwar mahaifiyar yama gushe kwatakwata daga raina. Wayar amira ta katseni daga dariyar na kara wayar a kunne lokacin sauran yar dariyar. Turawa sa kwai nafada cikin zolaya tayi murmushi mai fidda sauti to ya son ranki? Bugowa nayi ince don Allag ki aikawa inna wayarki mu yi magana nanemi tata ban samu ba yaya kuma yace baya gida.. Nace bari nakai mata wayar da kaina zan kiraki idan na isa Na sahidawa inna sannan nasaka hijabina na tafi. Zaure na tarar dakofar dakinsa bude nayi mmk da farkoamma da nayi wani tunani sai nagawautata watakila lokacn ya shigo. Daisata ko zama banyi ba ta bugo saidasuka gama sannan muka gaisa ina yardariya nace naga yayan ma ya dawo.Ban rufe baki ba tace na ina? Shi fabaya ma gari bako yayi wllh ko dagamalufashi ne sun daiyi waya yace yanahanya. Wann furar ma shina siyowa.Nace Ayya ta mike bari na kai masanayi saurin karba haba inna kawo nakai masa meye amfanina dama nasanrashin dan aike zaisa kikai da kankitunda gani ai shikenan. Tayi murmushito humaira Allah yai albrk yas amugaaurenku lfy. Nidai nayi gaba kawai.Kishingide yake na kunna kai wanikamshin turare ya dokeni fuskarsa rufeda littafi nayi sallama da sauri ya dagokai mukayi ido 4 domin kuwa idona nakansa. Ya Salam! Naji ya fada a hnkl.Ina wuni ga fura inji inna.ganin bashida alamar motsawa yasa na ajiye masana juya. A hnkl yace donAllah dawo!Cak na tsaya tare da juyowa na kalleshiya daga kai. Karki gujeni ki dawo gareniwayyo ni ashe yaudarata ake baki mutuba HAFSAT!!! Gabana yayi muguwarfaduwa na zaro ido na dafe kirji Ni? Yamike zai nufoni cikin wani irin yanayiidanunsa har sun kwao kwalla sainakwasa a guje nayi wurin inna. Yadda ta ganni yasata firgici ke Humaira menene? Itama duk ta firgice.. Shigowarsa yasa inna yin shiru, nikuma nakara matsawa kusa da ita sosai..durkusawa yayi gwuiwa 2 kamar mai neman gafara, sai kawai yafashe da kuka.. Inna wacece wannan? Don Allah kar kice mini ba Hafsat dita bace, wayyo ni dafwan, Allah ka kaddareni da jin tabbacin Hafsat ditace domin nashiga shakkun wannan sbd ta nuna tsoro a gareni sai yakara fashewa da kuka dai dai kuma lokacin Yaya yai sallama.... Na rikice na rude hankalina ya dunguzuma sai kawai nima nafashe da kuka ganin cewar wani balain ne ka ke neman haye min. Subhanallah inna meke faruwa ne? Inna ta rausayar da kai tonima sun sakani cikin rudu wlh. Cikin kuka nace inna yadai sakamu ni wlh ban san shi ba Yaya, don Allah yimasa bayani fada masa cewar ko ni wacece.. Wani kallo yayi min kafin ya kawar da fuskarsa har lokacin kwalla ke fita a idanunsa kamar anbude famfo. Nadafe kaina, shin kowace mace haka take samun wadannan kalubalen ga maza, kokuwa ni tawa halittar ke da haka? Da kyar Yaya ya shawo kansa abinka ga fari mai idanu fuskar nan tayi jawur, musamman hancinsa, idanun suka rikide suma sannan girmansu yakaru... Yanayi yanda inna fa Yaya ke masa bayanu yasa shi kara nitsuwa, nitsuwa irinta sauraron magana don a fahimta. Suna gamawa ya kalleni wasu siraran hawaye suka biyo baya.. Na yarda Inna sannan na amince amma don Allah ku rokar min ita idan zata maye mani gurbin Hafsat. Da sauri nace an fidda min miji kayi hkr bana.... Inna ta dalle min baki. Yayi murmushi mai nuna daci da kuncin zucia. Humaira sunanki bayyi kama dana marasa tausayi ba ki tausaya min ko don halin dana shiga donAllah.yaya ya dafa kafadarsa wane hali ka shiga safwan? Yayi dan smiling tsaya kaji LABARI na: ina dan 3yrs mahifiyata ta rasu don haka na tashi a hannun kishiyarta. Ni kadai ta haifa ita kuma tana da yara 4, tunda na tashi naga mahaifina yana yawace yawacen kasashen dunia don gudanar da harkar kasuwancinsa wato ba mazauni bane, yana int'l biz. Na tashi cikin wahala da azaba irinta kishiyar uwa sai nayi bara gidaje nake samun abncin da zanci kamar yanda umma ta umarceni duk da arzikin mahaifina kuwa. Sakamakon dangin mahaifiyata ba'a nan suke ba yan asalin yamai ne ta jamhuriyar nijar su kuma dangin mahaifina an rasa wanda zaiyi hobbasa kada tayi zuga ya daina basu abun arziki. Taimako daya da Allah yayi min skul 1 mukeyi da yayanta tayi ta rabamu Abbana yakiya amma fa ko ruwa bana tfy dashi. Tun ina kukan yunwa harna daina gashi ba'a tadamu sai karfe 3. Da mun koma ggida sai islamiyya hakan ya zame min jiki abnc baifi na samu sau daya a rana ba shima sai bayan maghrib idan nayi bara. Allah mai tausayin bayi na shiga wani gida a bayan gidanmu naga wata yrny da sharbebiyar wuka cikin dabara na dauketa zuwa cikin gidan. Zaune suke ana rabon wasu kaya kamr tsaraba nayi sallama tare da gaidasu nace wann yrnyr tafita da wukar nan tana wasa ai nan da nan suka dau salati suka rude sukaita samin albrk sukace daga ranar na dinga zuwa karbar abnc. Abin mmki Hafsat kullum bata cin abncinta sai nawa har muka shaku sosai da ita mahaifinta yasan shakuwqrmu har aka sanya mata hafsar safwan. Da yake sunsan ni da lbrn wuyar da nake sha saina koma kamr dan gidan. Lokcn da tafara girma sai muka juye soyayya wacce ita tafara bullo da hakan. Kowa ya fahimcemu har iyaye sun bani ita. Kwatsam muka tafi karatu akayi mana waya bata da lfy ana gobe zan taho ganinta aka karamin waya TA RASU...... Ya fashe da kuka.... Gashi ban taba soyayya da wata ba ban shaku da kowace mace ba sai ita. DonAllah ku taimakeni kuce Hafsat ce wann wllh kamr su daya. Wani takaici ya rufeni bawai na rashin tausayin sa bane a'a kawai yana musulmi zaiyi wasa da imaninsa. Wallh gwara matsalarsa da tawa shifa mutuwa tayi ni fa? Gashi da rai amma yayi min nisa nisan da bani tunanin zai dawo gareni nima saina fashe da kukan. Kamr inna takaranci zuciata saita karyar da murya tace Safwan! Inason ka tuna cewar kai muslmine wanda yayi imani da Allah ko kafirai sunyi imani da mutuwa ballantana kai musulmi ashe kayi imanin wanda ya mutu zai dawo? Ya girgiza kai a'a inna, ta bata fuska wallh kayi mana tunda gashi kana kiran wata da Hafsat. Ina mahaifyarka? Maiyasa ita bata dawo ba sai hafsat? To ahir dinka wllh kaji tsoron Allah kayi imani a mutuwa don akwai ta kuma duk wanda ya muutu baya dawowa har abada. Sai naga yana goge kwalla alamar maganr ta shigeshi. Wann yarnyr sunanta humaira haifaffiyar nan ce kawar amira ce, kusan tare mukai goyonsu da mahaifiyarta gidan su na can gaba da an sha kwana snd haka..... Bakomai inna wllh kamr ce har tayi yawa shiyasa.... Allah yafi da haka bai kamata ka firgice haka ba sbd soyayya har kayi sabo. Ya karkatar da wuya wllh inna bazaki gane ba amma bakomi ni yanzu ki taimakamin da yar taki donAllah... Kafin inna tayi magana ninayi ina mike nace kayi hakuri anyi min miji. Ban jira wata mgn ba nayi waje cikin fushi.ko zaure ban fita ba wayata ta dauki kara kmr abin jira, alamun kira ne ya shigo. sunn Ibrahim ne alamar shi ya kira, na lafe bakin kofa sbd na tsani tfy ina waya kmr wata sabon shiga.sllm nayi kafin ya amsa, sai da yayi wata ajiyar zcy na yi dan murmushi sbd inda sabo na saba da jin hk.A hkl yake maganar kmr mai tsoron furta kalmomin, "Humaira zcyta Zata fashe kaunar ki ta hanani aiwatar da abinda na zo yi, ki taimakeni na turo a daura mana aure ckn satin nan a kawo min ke ko na sami sukuni".ban San lkcn dana kyalkyace da dry ba nima ckn zolaya na ce, "to na taimake ka". Ya yi murmushi mai fidda sauti wani abu ya taso min wnd nake ji kullum idan na kasance ina irin wnn hirar, na runtse ido kawai. Ya kara narkar da murya, "wlh da gsk nake na takura mata nake so kusa dani".Na bude idona ina jin alamar kwalla, amma na daure na maida su tare da kokarin kawar da damuwar da nake neman shiga, na ce. " Ibrahim ka zamo mai adalci, shin mai zai hana ka tafi da matarka don Allah ka yafe mata mana". "Baza ki taba gane abin da nake nufi ba ynz matata ta wuce muguwa, wlh shaidaniyace, ke dai ki dage da addu'a Allah ya tserar da ke daga sharrinta". Gaba daya jikina ya yi sanyi, gaba na ya fadi, tsoro ya kama ni, amma sai ban nuna masa hakan ba, sbd ina son jin tushen mgnr. Ina 'yar dariya nace. " Nima abin ya shafeni kenan?" "ku san haka, sbd wai ta ji ana mgnr neman aure shi ne ta bugo mini waya jiya da daddare cewar wlh sai ta gano ko Wace ce, km sai ta kashe ta ko ta yi sanadiyar nakasata kin ji muguwa". Ckna ya bada wani kululu. Na zaro ido tare da dafe kirji. Ya yi murmushi, " kin san wnn ai haukane, ni dai sai kawai na bi ta da karya ne dona zauna Lfy. Ibrahim da na daure na cije ba don ina sonsa ba, kawai gudun bacin ran inna, shi kuma ga Inda tashi matsalar take. shi kansa yana tsoron sharri da tuggu na matarsa ina ga ni karabiti? shin in fadawa inna ko in yi shiru? Fadar babu abinda zai janyo mata sai tashin hkl da rashin kwanciyar zcy. wayyo ni Humaira ga 'yan uwan ubana sun tasoni a gaba, kr2 ma sun hana mini sbd jin zafi da bakin ciki, Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un. kai dole in sanar da inna, domin itace mai yi mini addu'ar da Allah zai amsa da gaggawa. A kfr gida na tarar da su tsaye kallo 1 nayi musu na gane 1 daga cknsu shine muka hadu wurin biya wa su Aisha kudin makaranta na farkon zango Ni sai da ma na ganshi na tuna ban kai kudi an aka sanyo musu baje ba jikin uniform din. Da fara'ata na karasa sbd ban mance taimakon da yayi mana ba, na cika mana #30 sbd babu canji a lkcn, ya ce mu bari zai bayar. Har Kasa na durkusa don gaida su. Ina murmushi nace, "Mun fa gode ". Ya yi murmushi, " wai ni har ynz gdyr nan bata karewa? "Na yi 'yar dariya kawai. Abokin yace ," Nan muka zo gurin musbahu tun dazu muna nan unguwar sai ga kannenki (su sumayya) za su tafi islamiya, abin mamaki yaran nan suka ganeni. shi ne suka gwada mini gidanku nace bari "Eh wlh nan baya na je kai wani sako ". Abokin yace, " to madallah, mu zamu wuce sai wani lkcn ". Na ce, " to nagode ". Na wuce gida Ina kallo ya Kai masa duka da harbi na yi kmr ban gani ba, na yi ciki abina. " wai lfy kika dade hk? ko lbrn ne naku ya tashi ke da innar taki? " Ta karasa mgnr tana murmushi, na ce. " Humm bari inna na zauna tare da ba ta lbrn duk abinda ya faru hr wayarmu da Ibrahim ". sai na ga tana dry.Na bata fuska." to me zan yi? " "Duk ciki banga abin dry ba sai na kuka kika gani? " " wlh ba komai ke dai ki ci gaba da addu'ar Allah ya warware mana, wlh nasa Allah ma ji rokon bawansane, ba zai ki amsar mu ba, wataran sai lbr, INA lkcn da Zaki tuko zukekiyar mota ki zo kina alfahari da mijinki". Na yi murmushi, " waye inna?" " Allah kadai ya sanshi". Mafarkina suna nuna min mijinki sai dai har yau banga fuskarsa ba, ni na San..." sllmr su Baba Auwalu ne da wasu dattawa guda 4. Ckn ladabi na gaida su tare da yunkurawa zan tashi ya dakatar da ni. Inna ta mika musu tbrm 3 suka zauna, Baba Auwalu zakakke shi ya fara mgn.Abu 1 ya kawo mu nan mgnr Humaira gabana ya fadi. Wani ma'aikacinmu ne yaga Humaira yana so shi ne ya turo abokansa su ji masa mgn, to na fada musu gsky yrnyr ba ta aje kanta nan ba mai kudi take so, ko dan sarauta ko kuma likita mai kwasar albashi da tsoka. wnd ta sami daurin gindi daga uwarta aka maishe da iyayenta maza banza. ko da Allah ya azurta 'ya'yanmu da auran masu kudi ba tallarsu mukai ba, sune suka biyo su har gida, muna kora suna likewa don hk nace gwara mu zo su ji daga bakinku. Tashin hnkl ba'a sa masa rana, wnn cin mutunci da wulakancin ya isa.Na kalli dattawan akalla kowanne zai yi 55-56 yrs wai abokinsu ne ke sona, Yaushe ya ganni, km a Ina? wnn abu daga ji tsarine km salon wulakanci da tozarta ne. " ku nake saurare shin akwai wnd kuka fidda mata ko mu je a amshi sadakin wdnn?" Gabana ya fadi, ni da inna muka yi kallon-kallo sai kawai naji kwalla na bin kumatuna. " Allah kai ne gatana" Abinda kawai nake fada a zcyta Inna ta yi Kasa da murya, " Alh. akwai wnd suka daidaita da shi ynz hk mu yake saurare sbd hk a yi hkr za a turoshi". Nan da nan ya fusata, " kin ji ko? me na fada muku? ku tashi mu tafi idan sun san wata ai basu san wata ba".Ya kalli baba jamilu, " ka zama shaida mun baku nan da kwana 7 idan babu wnd yazo, to wlh mlm Datti zan bawa". Ya kalli dattawan, " ku ce masa ya zauna ckn shiri don baza mu yrd a yi mana abin fada a dangin ba, duk take-takenta ta lalata mana 'ya". Idan da sabo mun saba da jin wnn klm dk muka yi shiru ni da inna. suka bar gidan ckn korafe-korafe, shin me muka tsare wa su Baba? wnn amsa har yau na Kasa samunta. Hnkln ya tashi na dinga risgar kuka shin wa zan fiddo ni Humaira? Abinda kawai nake nanatawa kenan, inna dai tayi shiru abinta. Zaune nake bakin kofa ruwan koko kawai ke cikina, sai 'yar madarar da na sanya masa gaba daya na rasa inda ke yi mini dadi. Ni kadai ce a gidan inna ta tafi gadon kaya barka, Sumayya kuma sun tafi mkrnta. Hnkln ba kwance yake ba domin bani da tudun dafawa, Ibrahim ne hnnna km ynz ba na ko san jin mai sunan, dama a dosane muke gashi km ya billo da matsalar muguwar matarshi har abin na niyar shafata. Ya zan yi? Ban sami amsar tmbyr ba wayata ta yi kara, shi din dai ne naji kmr kar na dauka. Yau ma kmr Klum ya fara rokona da hr zan ki fada masa, amma sai na ga 'kara na sanar da shi wata kila shi yana da dabara tunda inna tayi shiru tun jiya bata ce min kala ba. Na kwantar da murya abinka ga Wacce ta sha kuka, ta kara raunana. Na kira sunansa, gaba daya naji ya kidime sbd ban taba ba. Ina saurarenki Gimbiya ". Ya fada ckn zumudi. Na had iya wasu hawaye da ke shirin zubo mini na fara mgn a hnkl. " A gsky ina cikin matsanancin tashin hnkl, iyayena sun tasoni a gaba akan yin aure shi yasa aka tsaidamini kr2. Yau ya zo mini da tsoho cewar ya bani 7 days na turo wnd zan aura, ko ya aura mini shi, to a gsky Ibrahim a ynz Ina tunanin auren tsohon, domin ba zan boye maka ba, a gsky ban taba jin sonka a raina ba, amma ina tausayinka tare da bin umarnin mahaifiyata don faranta mata rai, wnd har na fara jinka a raina. To sai da da mgnrmu ta jiya tasa na hkr da ki, sbd tsara da raina, da kuma lfy ta.A gsky kmr ydd kake jin tsoron sharrin matarka nima hk nake tsoro. sbd hk ni dai ga ni ga Allah, sai na fashe da kuka a hnkl. Iyakar tashin hnkl shima ya shiga, ya rude."saurara Humaira, dan Allah kiyi hkr, saurare ni mana". Na dan tsagaita, "wlh.. wlh Humaira babu abinda zai same ki ynz hk sbd ke nake neman aiki nan kasar, wlh ba zan zauna da ke ba a Nigeriar ballantana ma wani abu ya faru, amma ki kwantar da hnklki, na rantse da Allah Humaira duk na fadawa dangi da iyaye don a yiwa tufkar hanci. kin san kuwa bazan ta gifta raina akan kry ba don Allah ki taimaka mini". Na dan ji sanyi, amma duk da haka na ce. "To shikenan ba komai ke nan zamu yi mgn zuwa jibi idan mun gama shawara da inna ". Ya ce, " Ba matsala ". Ya dinga lallashina yana ba ni 'yar dry snn muka yi sallama. Har lkcn dai kaina bai warware ba yana daure ckn rudani na yi shiru. Rayuwa mai daci, wayyo maraici yau da mahaifina yana da rai, wa zaiyi min wnn musgunawar? Na dinga sharara kuka ba kakkautawa, sai da na yi mai isa ta snn na yi shiru. Na zaro wayata na latsa lambar Amira, bugu 1 ta shiga. Tana dauka tace."'yar halak ynz kuwa nake batunki".Na ce " ko?" " wlh kuwa ya gida ya kano? " "Kano gatanan Amira tayi mini kunci". "kuncin me Humaira?" Ta fada ckn damuwa. " Amira zaman gida ya janyo mini matsala". Na zayyane mata abinda da faru, ta fara salati, snn na fada mata kuma ydd muka yi da Ibrahim. Na ci gaba da zubda hawaye. " sbd hk ni ynz gsky Amira zan amince da dattijon da in kai kaina halaka". "A'a Humaira, amma yaya ya fadamin akwai wani abokinsa safwan, kinga shi Yaro ne bashi da matsala..." " wlh Amira baki ji ydd na tsane shi ba, Sam bana kaunarsa don bai kwanta mini a rai ba".Ta ce, " Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un. Ynz me ye mafita?" Na ce, " Dalilin kiranki kenan, dan ki nema mini ita?" Ta yi shiru, har sai da na ce, " Hello".Tace "ina jinki Humaira, wai nazari nake yi, amma ki bari zuwa gobe gobe zan kira ki". Na ce, "Ba matsala ". kafin inna ta dawo har na daura sanwar awara, duk da jikin nawa ba dadi. Ina shirin fara tuya ta shigo, " sannu Humaira ". Abinda tace dani kenan. Na ce, " sannunku inna da hny". Ta matso, " kin kuwa ci abinci? ko ba ki ga tsakanin jiya kawai zuwa yau ydd kika yi zuru-zuru ba? "Na dai yi shiru. " kada ki sanya damuwa ga al'amuranki, ki fauwalawa Allah, shi ne mai maganin damuwa". Na ce, " to". Ta fiddo kullin nama har da zafinsa da lemon kwali ta miko mini, na samu na cunkusa da kyar kada ranta ya baci.Aiko sai gashi naji dan karfi-karfi. Da daddare muna zaune aka aiko sllm dani. Na sami kallon inna naga ni take kallo, na cewa yaron. " ka ce ina zuwa". Ya na fita na kalli inna ckn muryar kuka, " shin inna me fitar nan zata yi mini? Wlh yaron nan banda shirme babu..." " kwarai kuwa gara ki zauna a cigaba da zarginmu tunda yara ne ba masu mota ba ko? " mikewa kawai nayi ba tare da na kara cewa komai ba, idona Taf da kwalla. Raina kmr ya fita, zcyta sai zafi take yi sbd kuna, wayyo ni Humaira. Ina fita na kalleshi, sai naga safwan ne wnd muka hadu gidan su Amira. Da ban yi niyar gaida shi ba, amma sai na daure muka gaisa. Idanuna suka suka zubo da hawaye na kalleshi, " Don Allah ka yi hkr zan koma gida akwai aikin da nake yi". Yayi murmushi, " To naji, amma kukan fa na mene ne? ko duk aikin ne? " Na runtse ido mgnrshi ko na ce tmbyr ta soke ni kmr mashi. " Humaira ban boye miki damuwataba, don me Zaki boye mini taki?" Na kalle shi, " Ba ni da damuwa sai Wacce kake neman saka ni ciki, don Allah ka rabu dani na koma gida ". Na rushe da kuka tare da durkushewa. Shi ma durkushewar yayi, tare da sassauta murya. " Haba Humaira ynz Amira ta kirawo yayanta muna tare, ta sanar da shi wayar da kuka yi. Don me zaki damu kanki? ki share hawayenki gani na zo zan je na gabatar da kaina wurin iyayenki, wlh Zaki same ni mijin da kowace mace ke mafarkin samu, zaki yi alfahari da aurena". A tsiwace na kalleshi ina girgiza kai, yayi Kasa da murya. "Ki yi hkr, nasan baki sona, to wlh zan yi hkr har zuwa lkcn da Zaki so ni, ni ma marayane Humaira, matsalar mu daya ynz haka nima irin auren da za a yi miki ake son yi mini a gidanmu". A langabar da kai ckn zubar hawaye, " safwan wlh ba zan iya amsa maka ba..." "sbd me? " Na kwantar da fuska, " Baza ka gane ba ". Ya yi murmushi, " zan gane Humaira, fada mini shin zaki cutune?" Na yi masa shiru. "kiyi mgn ko kina ganin wancan auren zaki amince da shi, na dattijo? Kinsan halinsa? su waye matansa? ko kina tunanin tsufan ne kawai ba matsalar iyali? shin yaransa nawa? ko kina da labari mafi yawa kishin ynz da 'ya'ya ake yi bada iyayeba? " Na mike, " wayyo ni Humaira,safwan zan rungumi kaddara, sbd kai din ma bansan wane ne ba? shin ya 'yan uwanka da kishiyar mahaifiyarka Zasu dauke ni? cewar baka da matsala ne zai tabbatar mini hkn? Na girgiza kai, " safwan kada ka ya bi kanka, shi yabon kai jahilcine". " Humaira kiyi tunani, zan dawo jibi komi kenan, pls kada ki so kanki da gobe zan koma, amma zan jira hr naji amsarki. Allah yayi mana jagoranci, zan wuce ki je ki kwanta, amma kiyi kokarin tashi ckn dare kiyi nafila, domin neman zabin Allah". Ban ce komai ba na wuce ciki, amma ko bai fada ba dama ina da wnn niyar. kwance nake na rasa abinda ya ke yi mini dadi, sbd lallai mgnr safwan shi su waye iyalan dattijon? Da farko ina tunanin auren sa shine mafita, amma ynz km hnklna ya tashi. " Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un ". Har karfe 2 idona 2, na mike nayo alwala na dinga salloli ina addu'o'i ckn sujjada, snn ban tashi wurin ba sai da aka yi sallar asuba. Na tashi da matsanancin ciwon kai, na samu na kwanta bayan na sha (Boska). Idona rufe wayata ta fara ruri, na duba Amira ce. " ya naji muryarki haka Humaira?" Na fada mata ydd muka yi da safwan, ta yi shiru kafin tace . "Turkashi, Humaira ki dage da addu'a nima ina yi miki nawa kokarin Insha Allah matsalar ki ta zo karshe". Na yi murmushin takaici. " Hm Haba Amira, wai har su baba Auwalu ke cewa, ba zan taba auren mai rufin asiri ba, don bana fin yaransu, Yaushe na taba zabin irin wnd nake son aure Amira? " Ta yi ajiyar zcy, " wlh hassada ce kawai suke yi miki, don hk kedai ki fauwalawa Allah komai. Bari ina ina zuwa ga Gimbiya can tana kirana". Ta kashe. Kmr abin jira, Kiran Ibrahim ya shigo, naja wani dogon tsaki, wnn waya tana neman jawomin matsala, sbd ko motsin tsintsiya ba a son ji wlh. Ina dauka bai jira mun gaisa ba yace, " INA yau zan baro kasar nan ki saurare ni zuwa gobe da yamma". Na bude baki, amma sai na ji ya kashe. Da sauri na tashi zaune daidai lkcn da inna ta shigo, na ce. " kin ji wai Ibrahim yana hanya". Ta zaro ido, " zuwa ina? " "Nan zai taho, wai na saurare shi zuwa gobe da yamma". " Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un, ni kam a gaskiya ni kaina mgnr Ibrahim ina fa tangarda da ita, sbd hatsabibiyar matarsa tnd har ta furta kisa ko na kasa..." Kiran Amira ne ya shigo, na dauka, ta cigaba da lallashina tana bani hkr, nace ba komai, muka yi sallama. Jin wnn mgn yasa na fada mata mgnr safwan, ta girgiza kai. " Haba Humaira, kawai daga ya zo sai a amince da shi mun san halinsa? " " Nima hk na gani inna. shi baba bai gaya miki wane dattijon ba? Tayi dry, " bai fada ba, wlh jiya hr gidan naje ki kyale wdnn mutanen, Allah ya fi su". Washegari ya kama sauran kwana 2 tnd safe safwan yazo, na fita. Ya kalle ni, " yau ma kukan ne? " " A'a.Na fada a gajarce. " To gani ina mgn ta kwana? " " Na fidda wani" " wane ne? " " wani ne na fada kaina a Kasa. "Bashi da suna? " " yana da shi". "To fada". Na yi masa shiru. " Haba Humaira, me yasa ki ke son koyon karya, km da alama kmr ba halin ki bane". "Ya za a yi na yi maka karya? " "wlh karya kike yi, sbd hk ni zan je na gabatar da kaina". Na yi saurin dago Kai. " A'a wlh kada kaje, ban turaka ba". Ya kyalkyale da dry. " kin kama kanki, ni zan tafi sai kin ji daga gareni, sbd na lura baki da tunanin kanki, baki da shawarar kanki, haka baki da zabi".Yana gama fadin haka yayi tfyrsa. kmr na kirashi ya dawo muci gaba da tattaunawa har ya fahimce ni, amma na kasa. Na koma gida rai jagule. Ina ckn damuwar abinci Ibrahim yayi sllm hr ckn raina gaba na ya fadi, ya bada kululu. Da inna suka yi mgn snn ta ba mu wuri. Ya kalle ni ckn tausayawa, " wayyo Humaira dk kin rame, sannu ko wane tsanani tafe yake da sauki. Inna ta yi min bayani, na kuma gamsu, km nima ta fahimce ni, sbd hk zan tafi gida jibin itace ranar karshe, zamu zo da iyayena a yi komai, yau kinga yaushe na zagaya dangi har aka yi mgn? Gobe kuwa sai na sanar jibi tunda safe mu taho". Na dai yi shiru kawai, rayuwata ta kara jagulewa. " zan wuce, ki ci gaba da addu'a, zan aiko Yaro da kayan ki, suna waje ckn mota".Ya ajiye min bandir din kudi ya mike. Inna ta karaso, " yaronan ya bani tausayi Humaira, ki yi hkr da shi dk ya Snr da ni komai, kuma na amince da shi". Shiru kawai nayi mata. Da magariba ina zaune ina lazimi, yaro ya shigo ana sallama da Humaira. saura kadan in kurma ihu. Na kalle shi, " kace ta daina fita, sbd an yi mata miji, mata aure ce ynz". Inna da ke sallah ta yi gyaran murya. Takaicina ya karu, wai inna me ke damuta? Na fita raina kmr garwashi, zcyta sai zafi take yi. kamshin da ba ni taba mantawa ya daki hancina, nayi saurin kallonsa. Tsaye yake ya harde hnny a kirji, ni yake kallo, na durkushe sai kuka. Ya sunkuyo, " ki yi hkr Humaira, nasan kin yi fushi dani, wlh Humaira ba laifi na bane. ki daina kuka don Allah, menene damuwarki zuwa nayi muyi maganinta tare, Amira ta sanar dani komai". kuka nake, me ya kawo ka a wnn lkcn, me yasa kazo ka famamin ciwon da yaki wankewa? " Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un, don Allah ki saurare ni..." Na mike, " Don Allah ka tafi, wlh bani son ganinka a rayuwata, ba don na tsanekaba, a'a sai don na tsira da mutuncina, kai kuma ka gama da iyayenka lfy..." " saurara..." Nayi gida da gudu. Abin mamaki na kasa sanar da inna ko waye, ita kuma bata tmby ba. Zaune na kwana, duk wnd ya sani a da ynz ya ganni sai na bashi tausayi, nayi muguwar rama ga baki. Tashin hnkl sai ranar da adadi ya cika da safe, misalin karfe 10.30 na safe sai ga baba Auwalu su uku da buhun goro. jikina ya dauki rawa da yake zaune muke ni da inna a bakin kofa. Ya kalle mu a wulakance, sannan ya nefo ni da 20k. " To barkanki, wlh da na ba tsoho ha goran daurin aure nan mun dauki 2, Kuyi amfani da wnn, Na daura miki aure da wnd kika turo yau da safe karfe 9.30. Don haka ki shirya gobe zaku wuce babu mgnr taro". Na kalli inna itama ta kalle ni. kash!!! Nima ku nake kallo masu kr2, da wane ne aka daura auren da shi? safwan ko Ibrahim? Me ya kawo? mu tara a ltf na 3 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100