Subul da Baka 3 page 1 Posted by ANaM Dorayi on 05:11 PM, 21-May-15 Under: Subul da Baka Inna ta yunkura ta shiga daki suku ma suka yi hanyar waje,Ashe zaman tabarma ne nake ga bai mata ba.A firgice ya shigo babu ko sallama yana fadin inalillahi wa inailaihi raji'un daga ni har inna maka mike tsaye cikin firgici inna take tambayarsa lafiya ibrahim? Sai kawai ya durkushe kasa idanun sa jawur inna ya aka yi haka! cikin rashin fahimtar inda ya dosa tace da akayi me yace inna waye kuma hameed.yarima ne hameed meya faru mutuwa yayi? A'a da ransa shine mijinki yanzu an daura muku aure,inna ta dafe kirji wa! Tirkashi inalillahi wa inailahiraji'un Nayi saurin karasawa kusa da ibrahim na rushe da kuka ina fadin ka rufamin asiri kaje kace kaine zabina zan iya jure ko wace wahala amma banda ta gimbiya da mahaifin yarima wayyo ni humaira na shiga uku ! Ke bana san shashanci da hauka ina ma yazo kasar yaushe yasan abinda ke faruwa. Wannan abun yi Allah ne saboda haka na fawwala masa komai Allah yasa haka shi ya fi alkairi a gare mu baki daya ya mike tsaye yafita muna zaune muka jiyo sallama wa yarima zai shigo kanshin turarensa ne yafara yimin sallama. Daga kurya nake cikin duhu,shi kuma ya zauna daidai inda aka ajiye fitila na qura masa ido,ya qara haske da qiba,yayi kyau har yau kasaitar nan tasa na nan,sai faman basarwa yake yi,yana 'yar yamutse fuska. takaici ya qara kama ni na harareshi,nan ma SARAUTAR zai nuna? Cikin girmamawa ya gaida inna. tun kafin yayi magana inna ta jero masa tambayoyi."Haba yarima? don me zaka yanke hukunci ba tare da shawararmu ba? talauci haukane? yarinyar nan marainiya ce meyasa zaka nemar mata tashin hankali fiye da kwanciyarsa? ya zatayi da mahifinka? humaira na iya kishi da Gimbiya?" Ya dago kai fuskarsa a washe yace"Inna ku kwantar da hankalinku,wallahi. billahi ba ni da niyyar cuta ko yaudararku maganar mahaifina yanzu haka yana kwance rai a hannun Allah kuma ina da yaqinin insha Allahu zanyi amfani da wannan damar mu daidaita dashi,tunda har yana ganin ya hore ni da yin biyayya gareshi,kuma na aikata hakan zan lallabashi ya yafemin,ya janye maganar ko bayan ransa." Yanzu haka ana zargin 'yan uwana ne suka jefa shi cikin wannan halin,domin su gaji sarauta. akwai rikici da muke ciki inna,amma hakan bazai taba shafar Humaira ba da iznin Allah. Kafin inje ga maganar zamanta da Fareeda (Gimbiya),ina son ki sani cewa,mahaifan Humaira suna son ganin cewar sun wulakantaku ko ince suna son ganin kun wulakanta. dalili kuwa,nayi bincike sosai a kansu. yanzu haka da muka je maganar neman aure,ban nuna musu vewar ni din dan sarauta bane,asali ma na kasance mai qasqantar da kaina tare da nuna ni din talaka ne mai neman taimako matuka. Sunyi SUBUL DA BAKA mai tarin yawa a cikin jawabansu a inda suke nuni da lallai basu son Humaira ta fi 'ya'yansu wadatar dace da miji mai rufin asiri. Maganar Ibrahim shima nayi bincike a kansa lallai mutumin kwarai ne kuma ya fito daga gidan manya masu mutunci. Matsalar matarsa inda ake nuni da cewar,tafi karfinsa fiye da tunanin kowa,yana tare da muguwar mata wacce tana iya yin ko wane irin ta'addanci,da mugun abu akan duk abin da ta ga zai kawo mata cikas a rayuwa. Wannan dalilin ya qara tsorata ni,ga shi na ji hirarsu da Amira. Kuma da alama kamar Ibrahim din shi ne wanda yake tsayayye a gareta. Nazo don Allah mu warware matsalar wallahi har ga Allah banzo da niyyar auren Humaira ba,amma sai ta qi saurarena wanda ya nuna min tamkar rike ta ke dani a zuciyarta,tana ganin kamar nine sila ta duk matsalarta. Mahaifiyatace ta bani shawarar nazo wurin magabatanta na kawo kaina,ba tare da mun san cewar za'ayi maganar daurin aure ba. Munyi haka da niyyar daga baya sai ta sami wani ta aura ni kuma na janye. Saboda haka kada muyiwa Allah shishshigi,hakan ya rubuta sai muyi fatan ya zamo alkhairi agaremu inna. Kada hankalinku ya tashi,ni ke cikin rikici,amma duk da haka bana cikin rudani. Na farko yadda zan shawo kan Maimartaba. Na biyu rudanin da muke ciki da 'yan uwana. Na uku ya zanyi da rigimar Gimbiya idan ta sani,bazan sanar da ita ba sai na sasanta da mahaifina,in ba haka ba tabbas zata raba mu har abada!" Na runtse ido cikin radadi ina hango rayuwar da zan shiga saboda na tabbatar auren Yarima ba hutu bane a wurina. "Maganar zamansu da Gimbiya ba matsala bane,domin ni ke iko da gidana duka qarqashina suke,wallahi inna ba zan taba amincewa da takura,zalunci ko tashin hankali a gidana ba." Ya tsagaita da bayanin nasa kamar yadda dakin ya dauki shiru. Na kalli inna,sai naga tana zubar da kwalla. Hankalina ya qara tashi. Ya muskuta da fadin"Inna kuyi hakuri don Allah,gobe a bada mata hudu zuwa shida wadanda zamu tafi da su,domin su ga gidana hankalinki ya kwanta. Idan kuma zaki bi ke ma to mu tafi da ke..." "Kai bana son sakarci!" Sai naga yayi 'yar dariyar nan tasa ta qasaita. Ya mike tsaye"Inna ayi ta hakuri,sai mun zo su shirya gobe da wuri za mu wuce,wajen karfe takwas zuwa tara domin mu isa da wuri,kada muyi dare." Tafiya muke yi, amman idanuna na gefen titi, Sumayya da Aisha sai faman tsalle suke yi. Motar su yarima ke gaba tamu na biye dasu, Babban abinda ke damun zuciyata shine, idan mun isa wace tarba za,ayi mana? Ya za a karbi wannan al'amari? Ina tsoran tashin hankalin Gimbiya, musamman idan mukayi tozali da ita ga cewar na aure Yarima a matsayina na na BAIWARTA. Munyi tafiya mai nisan gaske inda ake dauke hanya muka kutsa cikin daji, nan ma munyi tafiya mai dan nisa wanda su baba har sunfara korafi sannan muka isa wani gidan gona katton gaske. Acikin gidan gonar ma sai da mukayi tafiya mai nisan gaske kafin ya tssaya gaban wani tankamemen gida, Goggo Huraira matar Baba imrana kadai ta biyo daga bangaren babana, itama ganin kwaf yakawo ta. Mata hudu muka tarar gidan, babu abinda babu na more rayuwa a gidan, aka kaini wani daki mai dauke da gado kawai sai mudubinsa, ga kuma wata kofa a rufe wacce nake kyautata zatton bandaki ne. Abinci aka dinga shigowa dashi kala kala cikin wasu manyan kololi, Goggo huraira ta dinga raba idano tana yaken dayafi kuka ciwo. Hannu baka hannu kwarya suka ringayi abinka da sabon shiga ga farfesun kaji dana kifi, suna gamawa wasu maza suka shigo da katon gasasshen rago bisa wani dogon tebir, Goggo Huraira tazare ido, bayan fitar su, takalli su inna karsum wai wane ne wannan yaron? YARIMA!!! Nabata amsa takara fiddo ido tace amma ku munafukai ne, shine baku fada tun wuri ba? Su goggo suka kalleta a mamakance kamar zasuyi wani abu sai sukayi shiru, da dare yarima yashigo yace ko akwai abinda ake bukata? Suka ce a a, dare yamika, gari yayi tsit babu abinda akeji sai minsharin su goggo ciki yacika da kayan dadi, nikuwa nayi lamo ina tinanin yadda wannan aure nawa zai kasance. Washegari aka hado kalaci mai rai da lafiya, abin takaici Gogggo ta cika ledoji wai za ta yi guzuri su masu Inna ganin kayan kamar banza sai da suka diba. Karfe goma yarima yace su fito ga wanda zai mayar dasu. A falo muka tarar da shi zaune Goggo ta wangale baki tana fadin dan nan mun fa gode kaji. Yayi yi murmushi yace babu komai. Ya mika wa kowacce bandir din naira dubu dubu yace su yi ysaraba a hanya sannan ya dora da fadin. Akwai buhunhhunan shinkafa, masara, gero, dawa, sukari, gishiri, kwalin taliya, kuskus, mahamisa, sha'iy, madara. Akwai kuma maggi, jarkokin mai kowacce ta dauki biyu biyu sauran a kai wa Inna kafin muzo, sakon kudinta na ba direba idan kun isa shi zai ba kowace kayanta. Mun gode. Su Sumayya ma suka durkusa saboda kayan da ya basu. Washegari aka hado kalaci mai rai da lafiya, abin takaici Gogggo ta cika ledoji wai za ta yi guzuri su masu Inna ganin kayan kamar banza sai da suka diba. Karfe goma yarima yace su fito ga wanda zai mayar dasu. A falo muka tarar da shi zaune Goggo ta wangale baki tana fadin dan nan mun fa gode kaji. Yayi yi murmushi yace babu komai. Ya mika wa kowacce bandir din naira dubu dubu yace su yi ysaraba a hanya sannan ya dora da fadin. Akwai buhunhhunan shinkafa, masara, gero, dawa, sukari, gishiri, kwalin taliya, kuskus, mahamisa, sha'iy, madara. Akwai kuma maggi, jarkokin mai kowacce ta dauki biyu biyu sauran a kai wa Inna kafin muzo, sakon kudinta na ba direba idan kun isa shi zai ba kowace kayanta. Mun gode. Su Sumayya ma suka durkusa saboda kayan da ya basu. Gaba daya jikinsu ya dauki rawa suka zube suna faman godiya. Ni kuma da yake nasan wannan kadan ne daga cikin aikin yarima abin bai zamo mini sabo ba kamar su. Na fashe da kuka lokacin da na ga cewar, motarsu ta bada wuta zasu tafi. Goggo ta leko kai daga tagar motar tace. "To yar banza mai kashin tsiya kukan me kuma kike yi? Wanna aljannar duniya da Allah ya kawo ki har kina da bakin kuka, marar mutunci ko zaki yiwa Allah butulci ne ya rabo ki daga tsiya. Hannuna naji an kama mun yi baya. Da sauri na kalle shi, Yarima ne fuskarsa a daure da alamar maganganun sunyi masa zafi. Ni kuwa banji komai ba saboda na saba da wadanda ma suka fi wadannan. Bisa kujera muka zauna yanayin zaman yasa nayi wata irin kunya ta kama ni. Na yunkura zan mike ya dawo dani na fada saman jikinsa na rasa inda zan sanya kaina don tsananin kunya. Ya rike hannuna duka biyun tare da tsare ni da wannan mayen kallon nasa mai narkar da duk illahirin jikina. Inason furta ya sake ni amma na kasa sai faman motsa baki nake yi kalmomin sun gaza fita. Yayi yar dariya yace Ba fa zan sake ki ba sai kince I Love You Naku Tabdijan! Ashe zamu shekara a haka kenan! Na fada a raina. Wai mai yasa kike mun rowar maganarki Humaira? Ko don kin ga tana kara kayata zuciyata ne? Na rufe idanuna ko ya za a yi in san haka? Baza kiyi min magana ba? To bari na cije bakin da ke yi min rowar sai...... Nayi saurin bude idona. Yayi murmushi yace Matsoraciya goge wadannan hawayen muyi magana. Nayi saurin kallonsa alamar ya sake ni. Ya kashe min ido daya. Ki goge da jikina mana? Bansan lokacin dana balla masa harara ba, ya kyalkyace da dariya. Wannan irin horo? Ya sake ni, amma yayi saurin sanya hannusa yana goge min fuska. Hankalinka ya kwanta yau hannunka ya taba fuskata. Na fada a zuci. Na yunkura zan tashi ya dakatar dani. Tsaya gimbiya, ai yau sarautar hannunki ta ke. Ya mike tare da zama kasa daidai kafafuna. Wallahi bani son irin wannan abunda yarima keyi mini. Na kara daure fuska tamaubabu alamar fara'a ko kadan. Ya kwantar da murya a nutse yace. Humaira kina da tsoro? Tambayar tasa tazo mini a hagunce kamar ya fahimce ni, sai yace. Ma'ana kina iya kwana gidan nan ke daya? Nayi saurin daga masa kai alamar iyawa. Tsakaninki fa da Allah kina iya? Bana son ki kwari kanki idan baki iyawa na samo maki yar kwana. Ina iyawa, na fada da kyar. Abinci fa kin iya dafawa ko a kwao mai koya miki? Kamar zance na iya amma kuma wata zuciyar ta gargade ni dana ce a kawo., saboda yanayin abincinsu da namu lallai akwai bambanci mai girman tazara. Na ce Aa. Ya kalle ni da fadin. Ban gane ba? A kawo na fada a hankali. Da kyau ya fada yana murmushi. Kina son mai share share ko za ki iya da kanki? Allah sarki Inna ita mai lalura yanzu wa zaiyi mata share sharen? Na girgiza kai, zanyi da kaina. Lokacin idonuwana suka ciko da kwalla. Ya matso kusa dani, kiyi hakuri. Yarima ya ishe ki da tambayoyi, ke kuma ba kyason tambaya ko? Na dai yi shiru kawai. Wadda zata koya miki abinci ita zata nuna miki komai na gidan nan. Koda wasa karki nuna mata ke matatace. A firgice na kalle shi. Ya kawar da fuska yace Zan sanar da ita ke matar abokina ce Haka sauran wadanda ke nan shiyyar saboda gudun matsala kafin Allah yasa mu daidaita da maimartaba. Wayyo ni Humaira na shiga uku! Kwallan da nake kokarin mayarwa suka fito day bayan daya. Kiyi hakuri Humaira, wallahi duk saboda kwanciyar hankalinki zanyi haka Kada ki damu Allah na bayan mai gaskiya kinji ? Yau zan wuce mu tafi da maimartaba Eygpt idan an dace muyi kwana hudu zuwa biyar Idan kuma an sami akasin haka to sai yadda Allah yayi. Take kwalla suka karu ni kuma haka Allah ya tsaro min tawa rayuwar?? Ya kalle ni, Don Allah Humaira kada ki sanya wa kanki damuwa kinji? Da na dawo zamu je Kano ki gano su Inna kiyi kokari ki kwantar da hankalinki yadda za su ga cewar ba ki cikin matsala. Kuma insha Allah idan komai ya daidaita ina son dawo dasu kusa damu Saboda Inna na bukatar kulawa. Naji wani sanyi a raina tare da goge kwallan da ke fuskata Ya miko mini sabuwar waya yana cewa Akwai lambata da ta Inna a ciki Kada ki saka lambar kowa sai da izinina kinji? Nace to Wayarsa tayi kara ya dauka Hello!..........ok Ina kan hanya gani nan isowa Ya dawo da dubansa gare ni Ya shiga wani daki kusan mintuna hudu Ya fito rike da wata leda Ina kallonsa ya bude wata dirowa ua dauko wani dan kwali karami ya gama yar diminiyar sa ya fita. Na kwanta dabas kan kujera. Allah gamu gare ka Har kusan karfe daya ina nan zaune. Kofa naji ana kwankwasawa na leka sai ga wata katuwar mata tsaye. Na bude mata sai fara'a take yi. Yanayin gaisuwar da muka yi da yadda ta ke magana na gane cewar ba cikakkiyar ba hausa bace. Tace nice wace zan koya miki abunci. Ta fada tana mai fata'a sosai. Nima cikin sakin fuska nace mata. Ba matsala. Na kawao mata lemu a firij din da ke falon mai sanyi da ruwa Sanana na kalle ta Don Allah ki bani mintuna kadan zan yi sallah. Ta risina cikin girmamawa har mammaki ya kama ni. Tace As u said Madam no problem Toh ai kinji fa ni fa bana son turanci yayi yawa a magan Ko kuma ayi shi cikin sauri domin karatun nawa yanayinsa akwai da rauni. Lokacin dana fito nayi mamakin ganinta dana yi a bakin wata kofa. Tayi hanzarin karasowa kusa da ni. Yauwa madam muje. Na bi bayanta sai na ga ashe kicin dinne To ya akayi ta sani?? Ban sami damar samu amsa ba Ta katse ni da cewa Yallabai kwana biyar ya bamu Saboda haka ki dauko biro da takarda ki ringa rubutawa Saboda gaba rana daya kina iya mantawa da wani abun Na kalle ta sosai nace Bani da biro gashi ni bakuwa ce a gidan Tayi murmushi tace Ayya bari na baki Ni ina dasu. Nafisa A. Mamawa Tabude jaka ta fiddo wani dan book da biro tamiko min, A kullum zamu ringayin abubuwa uku zuwa hudu, ko fin haka idan akwai time, tabude wani katon firij dake kicin din, shakare yake da kayan lambu da naman kaji dana dabbobi, wani kuryar daki dake kicin din shima cike yake da kayan abinci na buhunhuna dana kwalaye, ga doya, dankali, kwai, da sauran tarkacen, ta debo dankali tace hajiya zan ringa yimiki bayani kina rubuta wa, nikuma inayi a aikace kina gani, na ce to. GIMA POTATOES ABUBUWAN DA AKE BUKATA, dankalin turawa, tattasai, Attarugu, Tumatur, albasa, gishiri, curry, thyme, karas, pies, green beans, green pepper, alayyahu, kwai. A fere dankalin turawa kar a yanka, a barshi haka da girmansa sai ki daka tattasai, attarugu, tumatur da albasa, kisoya sai kisa ruwa kizuba dankalin, kisa su maggi, gishiri, curry, da thyme, ki yanka kayan lambumki irin carrot, pies, green beans, green pepper, alayyahu. Sannan ki fasa kwai kamar biyar ko fin haka kisama masa curry da albasa da maggi kisoya shi. Kiduba dankalin inya dauko Dahuwa sai kijuye soyayyen kwan da sauran kayan lambun. Banda alayyahu, shi ki samasa ruwan zafi ki tsane shi, saiki sa namanki ko kifi ko kibarshi haka, kibar kayan lambun suyi laushi ruwan kuma yayi kauri, sai kisa albasa da alayyahu kirage wuta, tayi dariya tace yanzu zakiji shi a bakinki, a time din data gama yawuna har tsinkewa yakeyi domin yunwa nakeji nakuma na cika flet na kuma gefe, gaskiya yayi dadi wannan gima potatoes din, tayi dariya tace to kidai rage wuri ga abinci na biyu mai suna, KABBANI RUS RICE, abinda ake bukata nama, albasa, maggi, kayan lambu, tafarnuwa, Cinamon, Cadamon, mint, Attarugu, Yogot, basmati rice, ki yanka nama kanana sai ki tafasa, kidan soyashi sama sama, kiraba shi biyu, kidauko basmati rice ko kuma wadda kike amfani da ita kidafata ruwan naman sama sama sai ki yanka karas, garlic, pies, albasa, ki hada su guri daya, sai ki daka attaruhu banda tattasai kisoya kizuba su karas, nama, garlic, maggi, da dai sauran su, ga wanda bai shan yaji ana iya amfani da tattasai zalla cinamon, cadamon, mint, sai ki zuba yogot cokali uku ko hudu, in kina son zaki dayawa, idan kuma bakiso sai ki zuba kadan, to your taste. Idan kin gaggauraya sai ki juje guntun ruwan silale a ciki idan yatafasa sai ki sa albasa kirufe ta, kirage wutar har ya tsose yadahu, zaki iya mata sos din albasa da garlic da attarugu ko sos din tumatir kawai ko kici haka. Idan kikayi wannan sai ki sami mangwaro tunda gaki gidansa akwai manya manya nan sai bare bayan saiki yanyanka shi kicire kwallon, sai kizuba tsokar mangwaron atukunya kisa citta, kanunfari, kuzuba ruwa kidora a wuta yadahu sosai yafara fashewa sai ki burge shi kikara ruwa kitace kisa sugar da fulawa kisa firij. Ta koya mata abinci da dama( na tsalake ne saboda nasan dayawanku kun iya musamman...inma da wadanda basu iyaba bazasu wauce abokanainaba su kuma insunaso sai suyimin magana prvt loz). Bayan ta koya mata komai. Tayi mata rakiya har bakin kofa, nace Don Allah kiyi hakuri bai bar min komai ba....gurin is not clear. Tayi dariya tace wallahi ya biya ni har da doriya, ni ke da godiya Madam. Naji dadin samunki mai far'a da son jama'a wallahi domin hausawa na cewa shimfidar fuska tafi ta tabarma. Sorry not clear.Amma gobe kizo da wuri don Allah Na fada ina murmushi. Insha Allah da wuri zan zo yau ma akasi aka samu Na gode sai goben. Nace Allah ya nuna mana lafiya. A kujera na bar wayata na dauko ina latsawa na ga an kira har sau goma sha uku (13 missed calls). Na fido ido, ina dubawa na ga Hameed wato Yarima. Na zauna tare da kura wa wayar idanu saboda a gaskiya bana iya kiransa. Na latso lambar Inna, bugu daya ta shiga. Tayi sallama murya a washe. Wa ke magana? Inna Humaira ce. Sai naji tayi yar dariya. Humaira kuna lafiya? Kalau Inna, su Aisha su iso lafiya? Tace lafiya lau, ya suka barku? Nace kalau. To Allah yayi muku albarka Kiyi mana godiya mai tarin yawa wurin yarima don Allah. Ya kira ni dazun yace zasu yi tafiya , don haka ki kula da kanki, ki kuma kular masa da gida Allah yayi muku albarka. Nace Ameen. Mun dade muna hira inda na lura Inna kamar ba cikin damuwa, sannan muka yi sallam hankalina ya kwanta. Kamar abin jira, kiransa ya kara shigowa. Gabana ya fadi ba wai kiran ke bani so ba, a'a tambayoyi na tsana a rayuwata. Na kara wayar a kunne tare da fadin. Assalamu alaikum. Ya amsa cikin zakuwa tare da ci gaba da fadin. Ina kika shiga ne tun dazun ina ta kira shiru, ni duk kin tada min hankali. "Kicin" na bashi amsa. Me ki ka yi a kicin da zai dauke ki wannan lokacin Humaira? Kinsan kuwa yadda kika sa min damuwa? " koyan abinci". Na kara fada. Yayi ajiyar zuciya tare da waji murmushi mai fidda sauti. To idan za a tafi kicin ba a tafiya da waya ne? Haushi ya kama ni, wai shi ba ya magana kai tsaye sai ya hada da tambaya? Kin ji? Ya bukata. Na ce, na mantata ne kan kujera. Yayi yar dariya, yace Don Allah ni da a ringa makale wata ko'ina za ki shiga kada ki dora min hawan jini, Ko ba a sin kiran nawa ne? Aifa, na fada a zuci. Kinji ba kya son na kira ne? Nayi masa shiru. Yanzu me da me kika koya?? Allah ka raba wannan bawa da tamabay, na fada a zuci. Yayi kasa da murya Don Allah ki fada min irin abin d kika koaya. Ai suna da yawa. Nace da shi. Suna da yawa har guda nawa kika iya? Duka na iya, ai basu da wuya. To ji ma koya kin. Wai ina marar lafiya ka tsaya kana faman tsokana? Wallahi duk tunanina a zuci nayi wannan maganar, sai kawai na ji ya tuntsire da dariya. Ga shi nan kusa da ni, ko na bashi ne?? Nayi shiru, gabana yana faduwa. Hajiya Humaira Gimbiya, wannan kasaitar taki ke kara ruda ni wallahi, Toh ko milk and coconut balls din ne a koya mun. Wai ko Yarima yana dubiya ne? Nayi murmushi na ce. Hmmmm Yace meye humm? Gashi zamu yi tafiyar dare ballantana na taya ki hirar dare. Ba komai. Na fada da sauri. Ke a wurinki yake ba komai, ni kuwa akwai wani abu.... ga su nan sun fito za mu tafi, kar ki kashe wayarki fa. Na ce to. Sai na kira. Ya fada. Allah ya kiyaye hanya, Allah ya bashi lafiya. Cikin jindadi yace, Ameen. Ban jira ya kara magana ba na latse wayar. Na kalli wayar ko me ya sa yake yi min wannan surutun alhalin ba haka yake wa sauran mutane ba? Ban fama tunanin ba na ji karam! Ina dubawa na fa sako. Ina rokonki da ki ringa sakin jiki muna magana ko a wayar ne tunda a fili kin kasa. Ina cikin wani hali Humaira na rashin sukuni da kwanciyar hankali, ga matsalar ciwon maimartaba, ga ta Fareeda. Sannan ga ta jama'a, wurinki kadai nake jin zan samu kwanciyar hankali, ba komai zai haifar da hakan ba sai kin yi responding da duk wata magana da zan yi miki, don Allah ki saki jiki da ni ina rokonki. Murmushi kawai nayi. Ga tsayuwar kicin ' yan share sharen da na yi da magriba, don haka gajiya ta taso mini, ina gama wanka waje karfe tara na kwanta ban kara sannin abin da ake yi ba sai da na bude ido na fa karfe shidda da kwata na safe. Na hanzarta yin alwala na gabatar da sallah Sannan na koma kan gado na kwanta kafin na kara hutawa zuwa billowar rana. Da wuri kamar yadda tayi min alkawari ta zo, don tare da ita muka yi kalaci. Kamar yarda Yarima ya umurce ta cewa kwana biyar, to hakan akayi, amma fa na koya abubuwa domin sai dana cika littafina mai farka arba'in. Kwana biyu kenan ba mu yi waya da Yarima ba, kuma na kasa nemansa. Sai na dauko kamar zan kira sai kuma na fasa. Zaune nake ina gyaran kumbar hannuna naji motoci sun shigo, na mike tare da lekawa ta taga ba hango zungura zunguran motoci nan na sarauta masu kofofi hudu. Budewar farko na hango Yarima ya yi saurin fitowa daga nan na ga an kamo maimartaba sun nufi babbab gida dake bayan inda nake. Gabana ya fadi, na dafe kirji tare da koma kan kujera nayi laggwab. Har bayan isha'i ban ga Yarima ya shigo ba, nan jikina ya kara mutuwa. Haka na kwanta ba don bacci ba, Can wajen karfe sha daya naji motsin mukulli ana bude kofa. Na runtse idona kamar mai bacci. Kamshin turarensa ya fara ziyarata kafin na ji ya shigo Na kara yin lami. Ya gama yan hidindimunsa duk cikin dakin ko wanka a nan yayi, sannnan naji yana kokarin hawa kan gadon inda nake. Na tamke idona. Ya hawo tare da yaye bargo dana lullube Shirun da na ji ya yi ya bani tabbacin kallona yake yi. Na tsargu saura kadan na bude idona sai kawai na yu saurin juyawa kamar cikin bacci ai sai naji ya janyo ni jikinsa tare da maida bargo ya rufe mu. Ai sai na fara kokarin zame jikina Ya kuwa rike ni tamau! Ya karkato bakinsa daidai kunnena yana magana a hankali. Ke ni ne ki kwanta ban yi niyyar tadaki ba. Amma sai da na zame jikina. Mene ne haka Humaira? Kina fa wahalar da ni da yawa Kin yi min rowar muryarki kwana da yawa Kuma yanzu sai ki hana ni jin dumin jikinki? Kin ji? Da ke fa nake magana? To me zance masa dan Allag? Ba ki magana? Ya tashi zaune. Wallahi ko ki matso konkuwa na hau kanki. Ba shiri na matsa. Yayi yar dariya. Matsoraciya duk kya gama Yan kauce kaucen naki ki dawo hanya......mun dawo me zan samu na sannu da zuwa? Ya rada min a kunne, na ji wani yarr!! Kamar na shakare shi duk na takura Wannan salon kuma ya dawo da shi? Lallai bone ta ci ni kuwa. Ba fa zan lamunci shirun nan ba wallahi. Humaira na gaji da wahalar nan Ko ba kiji ina magana ba? Ya jikin Baba?? Na fada kamar mai koyon magana. Da sauki yana nan gidan ma zai huta na wani lokaci Don haka kada ki sake ki nuna ina da alaka da ke. Gabana ya fadi ras! Lallai akwai babbar matsala. Yanzu me zan samu? Me fa! Duk tunanina a zuci na yi Sai da na ji yace Me fa ? Hmmmm. Yayi shiru sai na ga kamar ban kyauta ba Na daure na ce. Ka fadi me kake so sai in girka maka Bana burin abinci ya kwana Kuma ban san yau zaka dawo ba. Ni ba abinci nake so ba. Ban san lokacin dana ce To me kake so Ya dan kara kasa da murya kamar wani zai ji Ko dan kiss Ko motsi ban kara yi ba Kin ji? Zan samu? Humaira da ke nake Wallahi da Yarima zai gane da ya daina yi min wadannan tambayoyi nasa. Shi ne kika kyale ni? Kin ji? Na kara kulewa sai kace bakinsa aka yi kalmar kinji Don girman Allah ki taimaka mini Wallahi na kawo wa raina. Ya kusa bani ma dariya har da magiya. To tunda kin yi min bukulu juyo ki fuakance ni Ko hakan ma ba zan samu ba? Na dai yi masa shiru. Kinji? Wai don Allah kai ba ka san ina jin kunyarka ba?? Na fada kamar shirin yin kuka. Sai kawai naji ya kyalkyace da dariya. Ni ban sani ba. Ashe kunya ta ake ji? Wannan kunyar bata yi min adalci ba wallahi. Juyo na rage miki ita Don na lura ke ma ta takura ki Kin san Allah sai kin zaba Ko ki juyo ko kuma kiss. Sai me? Bakinsa naji ya hada da nawa Zan kwace yayi min wani riko. Na rasa inda zan sa raina don kunya. Ya dauki mintuna kusan talatin har jikina yayi lakwas. Yana zame bakinsa na yi saurin cusa kaina jikinsa kamar in bude kasa in shige abin da dama ya ke so kenan Ya kara gyara ni tare da rufe mu da bargo. Sama sama na fara jin nufashinsa alamar ya sami barci, amma da na motsa sai ya yi firgigi tare da matse ni. A haka har na hakura ni ma ban san kokacin da barawon ya sace ni ba. Ko da na farka ban ganshi ba, lokacin bakwai har ta wuce. Ban yi mamakin wannan muguwar makara fa na yi ba, na hanzarta gabatar da sallah ban tsaya gyaran dakin ba na fada kicin. Na soya dankali, sannan na dafa tsokar nama da albasa da kayan kamshi, sannan na jajjaga tattasai da dan tumatir tare da albasa duk na ajiye gefe, na dauko albasa ba yankata faken falen sannan na daka wannan dafaffiyar tsokar. Na zuba mai a tukunya na kawo yankakkar albasar nan na zuba cikin man ta dauka dahuwa sannan na zuba cijin man ta dauko dahuwa sannan na zuba jajjagena da dakakken nama na ci gaba da motsawa kafin na dauko baked beans shi ma na zuba ciki tare da kabeji dana yanka, sannan na zuba su maggi da sauran kayan kanshi. Wannan itace miyar cin dankali. Bayan na gama na soya kwai, sannan na hada kunun kuskus. Madara na zuba a tukunya kofi daya ta gari da ruwa rabin kofi suka tafaso sannan na zuba kuskus tare da kara dan ruwa na bar shi ya dahu lugub ba sanya maburki na burke ba juye a kwano na kawo flavour mai kamshin madara na zuba da madarar ruwa peak sai sukari. Na hada wadannan kaya na shirya wasu a tire na rufe da dan kyalle na rufe abinci, gyalena navdauka tare da fita wajen gidan Cikin sa'a sai ga wani zai wuce na kira shi muka gaisa yana min kallon rashin sani ban damu ba nace. Don Allah ka taimaka ka kai wa maimartaba kace daga gidan abokin Yarima. Yana ji na ambaci Yarima ya fara kyarma tare da karba cikin hanzari yayi gaba. Ni kuma na kima ciki don hada wa yArima nasa. Sannan na shiga gyaran gidan da yan share share cikin yan mintuna kamshin freshner da turaren wuta ya gauraye ko'ina. Na fada bandaki na yi wanka, abin mamaki ina fitowa na tarar an ajiye min wata doguwar riga mai dankaren kyau. Motsin kwanukan da na ji a falo ya ba ni tabbacin shi ne ya shigo. Nayi saurin shiryawa, amma kunya ta hana ni fita, yadda riga ta kame ni kam kamar daman an auna da jikina na kalli kaina na kara kallo. Kai duniya komai na son gyara. Ni kaina na yaba da kyan da nayi. Ganin lokaci zai kure har sha daya na niyyar yi yasa na daure nafito, saboda gabatar da abincin rana. Zaune yake yana faman latsa waya na dan karasa nesa da shi kaina kasa ban yarda mun hada idi ba nace Barka da sfiya, ya karfin jikin maimartaba? Gaisuwar tayi masa dadi a yadda na fahimta, yace. Alhamdulillahi da sauki wallahi, na je ma gida amso masa karin kumallo ne. Ina dawowa na tarar har ya gama cin wani abinci ta baiinsa mai dadin gaske, wai an kawao masa daga gidan abokina shi ne nakr neman wannan dan iskan in ji ko shi Abdul amma ba wanda na samu. Shiru na yi tare da mijewa na kwashe kayan, ga mamaki ya cinye komai. Ya kalle ni yana murmushi. Kr ni fa na lashe abincin, kin dai ci naki ki? Nayi yar dariya, Eh Dariya na baki? Ya fada cikin wata irin siga mai nuna matsanancin farin ciki. Ni dai na yi gaba abina in murmushi. Abin da na fara yi shine gyara kaza na wanke na jajjaga dan tarugu da albasa sannan na daka thyme da citta da tafarnuwa na hade wuri guda na kawi mai na zuba ciki, sannan na zuba maggi da gishiri na motse na shafe kazar nan da su ciki da waje, na saka gefe na dauko albasa davtumatir na yanka fyalen fyalen, na yanka kabeji kanana na ajiye gefe. Na dauki kazar na sa a oven tare da timing mintuna arba'in da biyar. Na wanke shinkafa da ma na dora ruwan zafi sun tafasa na zuba, sannan na barta ta dan dahu, sannan na sauke na wanke na tsane. Na yanka wani kabeji, karas, kokumba, koren wake da peas na tafasa hanta na yankata kanana da yar albasa. Na zuba mai a tukunya kadan yana yin zafi na juye vegetables dina da hanta sannan na zuba zuwa kadan na kawo shinkafar na zuba tare da motsawa, ruwan suka hau kanta kadan yadda zan ida dafata na rufe. Ina cikin gyara kayan miya Yarima ya shigo ya sha uban ado da irin kayansu na sarauta nan da nan jikina ya dauki rawa na kasa ci gaba da yankawa. Ya matso tare da shishige min. Me kike dafawa haka gida ya rikice da kamshi?? Zaka fara ko? Na fada a zuci, amma a fili na ce Abinci. Zan sami kamar na mutum hudu zuwa biyar? Insha Allah. Na bashi amsa. Ya rungume ni very good my princess. Zamu zo around 2:30 mu ci , kaya na nan su za ki canja kinji? Nace To. Duk na kagara ya tafi. Ya kai hancinsa a wuyana. Inason wannan turaren very sexy. Na dai yi shiru saboda na riga na yi mutuwar tsaye, ko me ye sexy kuma? Na tambayi kaina. Gobe dani za ayi girkin nan gaskiya, yau ma don am busy shi ya sa. Ya sake ni, sai mun zo cin abincin. Yana fita na saki wata ajiyar zuciya jikina gaba daya ya bige da kamshi turarensa. Da hanzari na kara gyara wasu kajin uku tunda wankewa ce kawai, akwai a firij na yi musu hadin ta farkon na kunna dayan oven din nasa su a ciki. Daidai shinkafar ta dahu na kwashe a katuwar kula kafin na gama na san ina zan zuzzuba. Muna da lemuka kala kala don haka ban wahalar da kaina wajen hada wani juice ba gani har biyu da mintuna biyar. Na sami babban kwando na zuba abinci na shirya wa maimaryaba komai na ajiye gefe, sannan na je na shirya wa su Yarima nasu a fako a kan table abin mamaki naji ana buga kofa. Na san ba Yarima ba ne sabida yana da makulli, na hanzarta isa sai na ga wani dogari da kwanonina, na bude ya durkusa. Maimartaba ya ce a yi godiya sosai. Na ce yauwa tsaya ka tafi da wannan. Na hanzarta na dauko lemuka kansa na sanya masa kusan kala takwas. Na kwashi nawa na yi daki na tarar ya ajiye min wata danyar shaddda galila ta sha aiki sosai, na yo alwala na saka, sannan na fara gabatar da sallah. Ina kabbarawa na ji motsin shigowarsu, wani dadi ya baibaye ni. Ya leko Au sallah kike yi? Ya fice. Koda na gama naci gaba da cin abincina a tsanake tunda su ma na ji suna cin nasu ne. Na gama nayi lamo ina jin hirarsu sai faman santi suke yi, sunabyi wa Yarima sharri. Wai da man don ya kwashi girki yasa ya haukace kaina. Na yafa gyalena na leka muka gaisa, za su fara tsokanata nayi saurim komawa ciki. Muryar wani na ji yana cewa, shege ina ka samo wannan shuwa arab din? Dole Gimbiya ta haulace bala'in nan alkur'an yarinyar tsoro ta bani......amma da ita zaka tafi jibi ko? Dadi ya ziyarce ni, ashe tafiya zai yi jibi? Ni dama gobe ko yau ne. Baka jin maganar Yarimaan saboda kasaita da jan girma wannan mutumin akwai isa. Yaushe ne ta ke haihuwa Gimbiyar? Ciki gare ta ashe? Na fada a bayyanr. Suka dai gama hirarsu ina ji suna amarya mun gode amma na yi shiru. Tunanina da shi aka fita sai kawai na ga mutum ya shigo alkyabba a hannu. Ya miko min. Ungo ki kai min daki. Na mike na isa tare da mika hannu sai kawai naji mutum ya rungume ni. Haba irin wannan delicious ai sai da tukwicin hug. Wallahi kwakwalwarki na ja, na san ko ita malamar taki da ta koya miki girkin yanzu ba zata hada kanta da ke ba. God bless u my princesss. Ya sake ni, zan je na amso wa maimartaba abinci, Umma har ta kai ga yi min waya. Nace to kawai. Har ya juya ya dawo Zo ki yi min rakiya. Ya fizgo ni muna zuwa bakin kofa ya mamayeni ya kai bakinsa ga nawa, sannan ya saki ji tare da yi min gwalo, sai kawai abin ya bani dariya sosai. Shi ma da dariyar ya bar gidan, na gaya shiga wani farin ciki mara misaltuwa, Yarima Hameed kenan. Karfe shidda na marece naji ana kwankwasa kofa, na hanzarta tare da tambayar waye? Yace kwanoni ne aka kawo na abinci. Na hanzarta budewa da man da hijabi a jikina. Kamar jiya ya risina. Maimartaba yace, ayi masa godiya mai tarin yawa, Allah ya albarkace ku ya azurtaku, ya rufa muku asiru duniya da lahira. Nayi murmushi cike da jin dadin wadannan addu'oin nace. Amin ya rabbi. Na karbi kayan ina shirin juyawa gida, sai ga Yarima kamar daga sama. Gabana ya fadi jikina yayi sanyi, ya kalli dan sakon da tuni ya zube kasa yana. Allah ya taimaki Yarima! Ya daure fuska, ya ya dai? Na maido wa matar abokinka kwanoni ne, kuma maimartaba na dada godiya, Allah ya bar aminci. Tashi ka tafi. Ya fada a hanzarce. Ni kuma nayi ciki da sauri. Ya biyo ni har kicin. Dama Humaira ke ce ke aikawa da abincin da maimartaba ke faman yabawa? Ke ce matar abokina da yake faman fada wa duk wanda ya ziyarce shi? Waye ya baki wannan shawarar? "ba kya tsoron hakan xai iya janyo a yi saurin fahimtar tsakaninmu 2nda kin nemi wannan kusancin har an san da ke? Kin ji?". Ba tare da na kalle shi ba, na ce. "ka yi haquri". Ya matso kusa dani "ba laifi na ce kin yi ba, shin kina ganin ba wata matsala ko ba kiyi 2nani ba kafin ki yanke hukunci?" a qagare na ce da shi "ba wata matsala in sha Allah". "kin tabbata?" "eh". Na fada ina shirin gifta shi na fita. Ya janyo ni jikinsa. "Allah ya yi miki albarka humaira". Bai qara fita ba, ya ce muje na taya shi harhada kayansa, sai wajen 9 muka gama, saboda mun yi sallar magariba da isha'i sannan tambayoyi da yawan maganarsa suka ringa bata mana lokaci. "wai humaira don Allah sai yaushe xaki saki jikinki da nawa?" murmushi kawai na yi "kin san shawarar da na ke yi yanxu?". Na ce "a'a". Ya ce "so nake yi idan na dawo na san yadda xan maida ki makaranta, ko ba ki so?". Na fadada murmushin kusan xuwa 'yar dariya "wallahi ina so saboda ma 2ranci". Ya kalle ni sosai "2ranci kuma?". "eh wallahi, ina son iya 2ranci sosai". Ya qyalqyale da dariya "to ko london xan kai ki qasar 2rawan?". Cikin 'yar dariya na ce "da ko ka kyauta". Wasa- wasa hira ta barke tsakaninmu, nan da nan ya fahimci lallai ina son ilimi 2nda ga shi ina hira da shi cikin sakin jiki, abin da ba taba ba. Da yake hirar ta yi min dadi ban damu da yadda muka kwanta gado 1 ba, muna ci gaba da hirar har sai da na lura da irin shige min da ya yi tare da yadda salon maganarsa ke... sauyawa nan da nan tsoro da kunya suka kama ni, amma ina lokacin da na farga na makaro, 2ni yarima ya kasa sarrafa kansa, yana faman salo... Ya rasa ta inda xai billo min nayi shiru, ni kaina na san kukan ba wai na ciwo ba ne, tsabar kunya ce ya sa na kasa tsaida shi, saboda ina 2nanin ta inda xan tashi, ga shi a dakin ya kasa ya tsare. "don Allah humaira ki yi haquri". Kalmar da yake ta nanatawa kenan 2n tashinsa. Ganin ba wani sauyi sai kawai ya dauke ni cak xuwa bandaki ya hada min ruwan dumi da komai sannan ya fito. Na sami damar dago kaina daga qasa ina raba idanu kamar wacce ta yi qarya. Na ma ba kaina dariya na samu na yi wanka amma fitowar ta gagareni. Sai na jiyo motsinsa can bayan daki, ai ko na yi hanxarin fitowa. Ga mamakina ya gyara dakin tsaf! Ya sauya xanin gado sai qamshi ke tashi. Ta taga na hango shi yana shanya xanin gadon da ya kware, wato wankewa ya yi. Ina cikin saka kaya ya shigo, ai ko na yi cikin wardrope din sai kawai na ji yana dariya. "xan je gurin maimartaba, ki hada abincin da ni don sai xuwa jibi xan wuce, na fasa tafia yau". Gabana ya fadi, ni kam na so ya tafi yau din kamar yadda ya tsara. Kamar kullum na hada abinci kala-kala, na shirya masa nasa na aika wa maimartaba sauran. Na sallame shi sallah kenan na ji shigowarsa da baqi. Har suka gama ban fita ba, shi ma bai shigo ba, da suka tashi kuma suka fita tare. Ina xaune falo ya dawo da qa2war leda. "sorry humaira, kadaici ya dame ki ko?". Ya qaraso inda nake. "wallahi 2n fitarmu ina kasuwa don samo miki abin kore kadaici". Yana maganar yana bude ledar tare da fiddo littatafan hausa da fina-finan hausa sabbi, masu kyau. Dadi ya kama ni, da ma in taba kara2n hausa ko a gida, musamman littattafan jamila ibrahim kankia, naja'atu haruna 'najnoor nasimat', da kuma na xainab dahiru wauwo 'xeedee'. Ya miqo min littattafan kusan guda 20, a sama wani sabon littafin mu2niyar ne, wato xeedee wai shi 'INA XA MU JE?' daga jin sunan littafin nasan dole ya yi dadi. Na yi murmushi "na gode qwarai". "ga kuma hausa films xo in koya miki hada kayan kallon yadda xa ki ringa sauyawa daga DVD xuwa satelite wataqila ba xa ki iya gane connection din ba duk da a hade suke ko da remote sai ki sauya". Nace "to". Tare da matsawa cikin doki da murna, saboda gaskiya xaman kadaici ya ishe ni kam. "abin ma ba wuya". Na fada ina yar dariya. Ya yi murmushi. Gare ki mai saurin fahimta ba...... Akwai sairan abinci? Wallahi yunwa nake ji. Eh na dafa wancan babu na ga ba ku rage komai ba. Yauwa bari na watsa ruwa, hada min kafin na fito Na shirya masa hadadden farfesun 'yan ciki da fried taliya, sai kemon kuskus mai madara da kwakwa a ciki. Ya kwashi girkin nan da kyau, da ma kadan na yi daidai ni da shi, ya cinye nasa duka. Na yi yar dariya tare da kallon empty kwanonin da farantin, sai ya kyalkyace da dariya. Me kike son cewa? Na kwashe kawai na wuce kicin. Ya ci gaba da cewa. Ko fiddo maganarki yarinya, so kike kice ina da ci ko? Kin manta garinku kenan lokacin da kike ba ji abinci halan? Daren ranar mun yi hira da kallon wani fim na Hausa mai ban dariya na dan Ibro. Washegari kuwa tunda ya fita da safe sai yamma ya dawo, sai ga shi da uwar tsaraba kayan daddawa, kuka,kubewa sauran tarkace wai in ji Inna. Na yi ta murna, tamkar Inna ce gabana. Goma na safen washegari ya bar gari da alkawarin bai wuce sati daya ko biyu. Nanji dadin tafiyarsa saboda na sami damar sakewa in yi karatun littattafan da ya sawo mini da fina finai. Maimartaba ya bada kayan itatuwa kwando kwando aka kawo tare da dumbin godiyar dawainiyar da ake da shi. Kullum idan Yarima bai kirani sau hudu biyar ba, ya kira ni sau uku karanci. Kamar daga sama ranar wata asabar, sai ga mahaifiyarsa da wasu barorinta guda biyu. Na ji dadin zuwanta sosai, saboda itace wadda ta fara kawo m8n ziyara daga bangarensa. Na zubo mata abonci dankayan makulashe, abin mamaki ta ci komai tana yi tana mini nasihar na rike mijina, kuma na dage da addu'a. Da za ta tafi na zubo mata dambun naman kaji cikin wata katuwar samira, sannan na kunso mata snack na ba daya daga cikin barorin na ce ta rike mata. Ta dinga yi min addu'a sannan ta tafi. Kwanan Yarima goma da tafiya ya yo mini waya ga shi nan zai hau jirgi yau zai dawo. Nan da nan na fara shirye shiryen tarbarsa. Ga mamakina har kusan karfe biyun dare ban yi bacci ba ina sauraron zuwansa, amma shiru! Na kira wayarsa sau wajen uku a kashe, hankalina yayi matukar tashi. Baccin da ban sami yinsa ba kenan har garin Allah ya waye. Da safen ma har kusan karfe sha biyu ba wani labari. Haka na ci gaba da aiki kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Ina cikin harhada kayan abincin maimartaba na jiyo alamun budewar kofa, da hanzari na fito. Ya shigo a hargitse kamar ba shi ba, gabana ya fadi, kada dai ace maimartaba ya rasu? Ya kamo hannuna idanunsa jawur, muka zauna bisa kujera. Humaira tare muka zo da Zarina, kuma yau maimartaba zai koma fada. Na saki ajiyar zuciya a hankali. To mene ne abin damuwar a nan? Na fada a zuci. Ya karkace kai kamar mai shirin yin kuka, ya ci gaba da cewa. A dalilin kyautatawarki da abin da kike aika masa tun zuwansa yanzu haka ya ce zai zo a yi miki godiya, kuma har da Zarina yanzu haka... Na dafe kirji tare da zaro ido ina shirin yin magana muka jiyo bugun kofa. Da sauri ya mike tare da lekawa, ya dawo da gudu. Wallahi su ne! Take na ce Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma laa sahlan illa maa ja'aktahu salan, wa'anta tij'alik hazna iza'shi'ta sahlan. Na je na bude ina kara karanta adduo'in neman sauki a kan duk wani tsanani a zuciyata. Su Umma ne a gaba kafin wasu dattawan mata gudu biyu, sannan shi maimartaba wasu manyan mutane hudu na bin bayansa. Sannan dogarawa, a bakin kofa dogarawan suka tsaya. Rakube nake jikin oofa, ban da kyarma babu abin da nake yi kaina kas. Kutumar uba! Aka biga wannan zagi da karfi, a firgicr na dago kaina. Ganin Gimbiya na yi kusa da ni da alama ita ce karshe wajen shigowa. Munafuka! Algunguma!! Kowa yayi cirko cirko tare da kura mata ido, amma ban da Umma da ta sami kujera ta yi zamanta. Da ma ke ce matar abokin Yarima yar iska? Makircin da kuka hada ke nan ke da uwarki? To wallahi ba ku isa ba, ina Yarima? Na rantse da Allah yau sai ya sake ki..... Ke wai lafiyarki kalau kuwa Zarina? Duk wannan cin zarafin da kike wa yar mutane na mene ne? Shin ko kin san dalillin zuwanmu wurinta kuwa? Cikin dattawan matan nan daya ta katse ta da fadin haka. Ta hankado keyata na yi taga taga zan fadi, kawai na ga mutum ya tare ni na fada jikinsa. Da sauri na kalle shi sai kawai muka ga maimartaba ya zauna a duke. Ganina jikin Yarima ya kara harzuka Gimbiya, ta fara zubda ruwan rashin mutunci ba tare da ta yi la'akari da wadanda ke wurin ba, tana fada wa dattawan kobji wace ce, saboda suna da masaniya kan maimartaba ya haramta aurena da Yarima ko bayan ransa. Sau biyu tana kawo harin za ta dake ni yana tarewa, ni kuwa banda kuka babu abin da nake yi, saboda tashin hankali. Ni ba na Gimbiyar ya fi damuna ba, irin hukuncin da maimartaba zai yanke a kaina kawai na ke ji. Wuri ya harmutse, fada tsakanin Yarima da Gimbiya su kuma dattawan wasu na goyon bayan Gimbiya su kuma dattawan wasu na goyon bayan Gimbiya, wasu na nuna cewa ba ta kyauta ba ta yi rashin kunya sosai, tunda ta aibanta Yarima gaban iyayensa. Duk wannan hargitsin su Momy da Maimartaba ba su ce komai ba Ganin abin ya ki ci ya ki cinyewa yasa maimartaba daka musu wata irin tsawa da kowa da ya yi mamaki. Nan da nan kowa ya na'abba. Wannan ai hauka ne! Ya fada, sannan ya ci gaba da cewa. Ba ku da bambanci da dabbobi, musamman kai. Ya nuna Yarima. Gabana ya yi wani mummunan faduwa, ya kira dansa DABBA ni kuma mai zan koma. A matsayinka na namiji yausha zaka biye wa mace musamman lokacin da kishi ya turniki zuciyarta? To kowa ya zauna zan yi magana biyu zuwa uku, amma kafin nan zan fara da abin da ya kawo mu. Ya kalli Yarima, Ya sunanta? Kansa duke ya ce, Humaira. Humaira zo daga nan. Ya nuna min kusa da shi daga kasa, tsoro ya kama ni saboda na san kaina kawai zai sare da adda shi ne sakamakona. Ina kyarma na karasa har lokacin kukan nake. Godiyar da na zo yi miki ba zan fasa ba. Na gode, Allah ya yi miki albarka. Wane ne mijinki kuma?.saboda har da wannan tambayar na zo yi miki, domin kullum Yarima ce min yake yi matar abokinsa. Wayyo duniya! Wayyo Iñna! Wani sab9n kuka ya zo na ji kamar na zura a guje. Ko ba kya iya magana? Na ce wane ne mijinki? Wane ne fa banda Yarima. Gimbiya ta fada a hasale daga inda ta ke zaune. Cikin tsananin bacin rai maimartaba ya kalle ta.. Kada ki yarda na gane ba ki da da'a domin za mu bata, batawa mai tsanani. Ta zumburi baki ta kauda kai tana gunguni, abinda ya ba wa kowa mamaki. Ya kalle ni, Humaira ko zan san wane ne mijinki? Na dukar da kai ina wani irin kuka, da kyar na iya furta. YARIMA NE! Amma don Allah ka yi hakuri, wallahi ba laifina ba ne, ni ma ba da son.......Dakata! Bari kukan kada ki sarke. Yanayin yadda ya fadi maganar cikin tausayi ya sa ni da Yarima saurin kallon juna. Ya mike tsaye, sai kowa ma ya mike, ni ma dole na mike saboda an bar ni ni kadai a zaune. Sakamakon abin arzikin da kika yi kin na yafe wa Yarima, kuma na aminta da aurenku ko lahira wani yana cin arzikin wani, to shi ma ya ci arzikinki, domin tunda ya yi auren farko ban taba shan riwan gidansa ba sai a nan. Sai ka tattara matanka ka hada su wuri guda, shi zai hada kan iyalanka. Yana fadar haka ya yi hanyar waje, saura kuma suka mara masa baya. Wani yayan Yarima ya banko mini harara wacce ta sa dole na yi kasa da kaina. Karaf! A kan idon Yarima, ashe hankalinsa na gurinmu da ma. Gimbiya ta fara zazzaga masifa, tana fadar maganganu har tana ikirarin plan ne aka shirya da ma don a ci mutuncinta. Yan baya suka ji abin da ta ke fada, amma shi maimartaba tuni ya fice, har ya kai a mota. Ta yunkura tare da shako wuyana ta makare ni jikin bango, Yarima ya taso lokacin har ta kwada min abin fulawa ta fasa min goshi. Da kyara ya kwace ni tana faman dukana da harbi, ni kuwa sai kuka nake. Hayaniyarta ta dawo da su Momy, da kyar suka fidda Zarina gidan tana ta hauka. Jikina sai rawa yake yi saboda tsoro duk na firgice sai bari nake. Da kansa ya wanke min jinin ya sa auduga ya daure da bandeji. Wayarsa ta fara kara ya dauka tun bayan da ya yi sallama, ban da kalmar TO babu abinda yake fada har ya ajiye. Ya kalle ni asanyaye. Maimartaba ne ya ce kar k8 sake ki kara kwana nan gidan, na maida ki can gidana inda Zarina ta ke ku..... Wallahi Kano zan tafi, ba ni kara kwana nan garin, ban iya masifar Gimbiya ko kadan nan din ma kana ganin ga manya ba ta j8 kunyar raunata ni ba, ina ga nan ware daga ni sai ita? Aure ne na yi na Allah, amma ba zan kuma ba. Idan ita ba ta da hankali ke ma....... Kwarai ni ma haukan nake a kan komawa gidanka kam, kai auren gaba daya ke bana yi, ko dole ne? Na fashe da kuka. Da ma tun farko ni wannan masifar nake gudy wallahu. Ya langwabe kai. Allah ya baki hakuri. Na hayyako masa. Eh da man duk wanda ka ji ana ba hakuri ai an gama cutarsa. Haba Humaira 8na hankalin ki ne yau? Daga turu na fito karewar hauka. Na mike ina faman hada kaya a jaka. Ya karaso murya a raunane ya ce. Don Allah ki yi hakuri, mu gode wa Allah da matsalar ta tsaya gurin Zarina kadai, kin ga alherinki ne ya sanya mahaifina ya yafe mini kan rashin bin maganarsa, shu ya sa aka ce YADA ALHERI BAYA ka tsince shi gaba. Wallahi.na tabbatar da lallai ya ji dadi sosai a kan abinda kika aikata, domin ni ina tunanin fushi da wulakanci wanda zan fuskanta a lokacin da ya gano abin da nake boyewa, don ko mahaifiyata ba za ta tsira ba. Shi ya sa na nace wa aurenki don na san ke alheri ce a wurina. Wallahi ba ki ji yadda hankalina ya kwanta ba..... Dole ka sami kwanciyar hankali mana, ni tunda ka ti silar tada nawa. Xaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Subul da baka 3 page 2 Posted by ANaM Dorayi on 05:17 PM, 21-May-15 Under: Subul da Baka Ya yi murmushi, "ya xa a yi na yi silar tada hankalinki?" "ban sani ba". Na fada lokacin da nake qoqarin rufe jakar. "Allah ya ba ki haquri, kin ga maimartaba ya yaba hankalinki kada ki yi abinda xai sanya ke ma ki fita ransa kamar xarina". "dole kuwa in yi, domin na tsira da raina da lafiata.. A gabanka ta fasa min jiki, to ina ga ba ka nan?". "nima ai bayan idonta gashi kina mini tsiwa mai ya hana ki rama? Ko kin san xarina ta gane kin tsorata da ita? To wallahi ni ba xan tare miki fada ba, domin akwai lokacin da dole ba na nan kinga kuwa dole ta ringa ba ki wahala, amma idan ta ga cewar ke din ba ki tsoronta, to lallai xa ta shafa miki lafia, don Xarina ba ta fi qarfinki ba ni a ganina. Abin mamaki kishiya...". "ka ga malam ni ba fitina na xo yi ba...". "nima bana son ki yi fitinar, amma ya kamata ki amsar wa kanki 'yanci, ki nuna ke ma fa MATA ce ba baiwa ba. Maganar gida kuma wallahi babu inda xa ki tafi yau a gidana xa ki kwana ke da axara'ilunki xarina ta qarasa ki". Na fashe da kuka, sai kawai ya shige bandaki. ***** ***** *****Tashin hankali ba a sa masa rana, kwana 2 da komawata gidan aka kawo mini dattawa guda 2 wadanda xa su ringa tayani aiki, sabanin gimbiya da nata yara-yara ne majiya qarfi, kuma aqalla xa su kai su 9 ko 10. Qaton gida ne da babban 'gate' sannan kowace bangarenta guda. Yau xan amshi girki don haka magariba na yi na fara kimtse-kimtse, 2n 6:pm na sallami su dagwayye ana gama sallar isha ya shigo. Na kawo masa abinci ya kalleni. "yo ina en aikin?". Ba tare da na yarda mun hada ido ba na ce, "sun tafi sashensu na sallame su". Murmushi ya yi, "to dauko abincin mu tafi sashena". Gabana ya fadi, amma ban yarda ya fahimta ba. A falonshi muka xauna mai tattare da kayan more rayuwa, kujerun kansu sun ishi mu2m kallo, ban iya tsayuwa fasalta falon amma ina iya cewa komai ya ji na more rayuwa, hmmm! Jin dadi sabo na fada a xuci. (kun ji mu2niyarku an kile an fara 2nanin jin dadi). Allah sarki su inna qwalla suka kwanta suka kwanta a idona da na tuno inda na baro su. Na duqa xan fara xuba masa abincin kenan naji an ingijeni nayi baya- baya na fada qasa da qarfi, kafin na yi wani motsi ta biyo ni da qafa tana harbi, a rude ya taso tare da ture ta wuri guda ita ma. "ke wace irin dabba marar 2nani ce fareeda?". "wallahi wannan munafukar sai na hallakata a gidannan, don uban...". fas! fas!! tasst!!! ya wanka mata kyawawan mari guda 3 a jere. "kar ki dauke ni sakarai, shashasha mana, ke me ya sa kike da fitina da rashin son xaman lafia ne? ko don kin ga ina tausaya miki saboda abinda ke jikinki?". ta harxuqo masa kamar ta rama marin da ya yi mata. "mene kai din in ba sakarai shashashan ba?". ya qara wanka mata wani marin guda 2 qwarara, ya juya xai dauko kebul (cable) ta ko dauki wani abin fulawa ta kwada min a goshi. "bari in kashe ta don ubanta in ga abin da xa ka yi". Tana qoqarin qara rusa min shi ya riqe da sauri. 2ni jini ya balle yana son dauko tsumma yana tsoron kada ta qara min wani dukan. Ya fige ta ya 2ra waje kafin ya rufe qofa ta banko da qarfi. Ganin idan ya biye mata ni kuma xan rasa jini da yawa ya sanya shi qyale ta, ya nufo gurina da sauri. Cak! Ya dauke ni xuwa bandaki sai kyarma nake ina kuka, tsoro da fargaba sun fi yawa a gabana. Muka fito, ya janyo wani akwati sai ga kayan dressing ya ci gaba da gyarawa. Ta xo kanmu, "aikin banxa aikin wofi, an asirce ka, an magance ka er talakaka ke wa wannan kyarmar kuma don ubanki yau na ga yadda xa ki kwana dakinnan. Na rantse da Allah ko gawarki ba a yi mata wanka nan dakin domin ba na hada daki da ke, banxa talaka". Ya kalleta a wulaqance saboda yau da fareeda ba ta da ciki, da Allah kadai ya san illar da xai mata, ya ce "ga ki nan talaka wacce ba gaji arxiki ba, maimartaba da ya tilasta ya sa na aure ki Yau saboda munanan dabi'unki na tsiya yana dana sanin aurena da ke, 'yar talakar da ki ke qyama ki ka raina kuma a yau ita ake alfahari da ita a matsayin suruka". Bai rufe baki ba ta hargitso masa qa2war talabijin da ke manne a bango, ta fado bisa sauran tarkacen kallon da abubuwar glass ji kake ratsatsatsa!!! Ya dauki waya kamar mahaukaci. "hello sahabi kana ina? Don Allah idan kana iya fitowa yi sauri ka xo gidana yanxu". Ni kam ina can rakube jikin bango kaina kamar ya bare, ga wata masassara da ta taso mini, ko tashin hankali ne ya hana ya yi min allura, ko ya bani magani? Oho! Shi ya fada ita ta fada, da ya matsa kusa da ita ta nuno shi da kwalbar glass ya rasa inda xai billowa tashin hankalin, iyakar qarshe ya kai. Sallamar sahabi ya sa duk suka yi shiru daga ita har shi din "Subhanallahi, innalillahi, Hameed mene haka ya faru? "mtsew! Shigo idanunka su gane maka barna da asarar da yarinyar nan tayi min, duk goshin er mutane, marainiyar Allah...". "shegiya dai! Domin mun dade da sanin shegiya ce ba ubanta ya mutu ba..." "haba gimbiya don...". "yi min shiru munafuki, ina ce da kai aka hada baki duk abin da aka qulla. Ni xa a yi wa makirci? ayi wa plan? xa a qirqira dafa abinci ana kaiwa sarki don munafunci, wallahi yau sai dai ayi wacce xa a yi". "Me fa xa a yi bayan na shirge ki kamar jaka, don ba xan tausaya miki ba 2nda na ga abin naki ya wuce 2nani...". "haba yarima har sau nawa xan fada maka ka daina biye wa mace?". "ka san Allah na dauka wa raina sai dai yau na kwana prison, amma lallai gab na ke da na lalata rayuwar wannan...". In taqaice muku, haka muka kwana a tsaye ana abu guda 1, ko sallar asuba sai da yarima ya fara yo wa sannan sahabi ya tafi gudun kada ta qara ji min wani raunin. Suka dauke ni muka bar gidan, amma sai da yarima ya tare ta sannan sahabi ya fidda ni dakin, saboda yunquran da take yi sai ta caka min gilashi a ciki. Iyakar firgita da kaduwa nayi, 2n ina kuka har na koma xare idanu, ni kadai na fige kamar wacce tayi ciwon shekara. Gidan sahabi muka je, na yi wanka na yi sallah, na nemi ciwon kai da masassara na rasa, har qara kan da ya yi min wani jummm! Allah ka raba bawa da tashin hankali da fitina. Da qyar na sha rabin kofin tea shi ma don Hafsat ta matsa min matar sahabi. Ina kwallonta tana goge qwalla, ta tausaya min. Xuwa can wajen 12 sai ga su sun dawo. Ban san me suka tattauna ba, tayi juyin duniya ta fita na qi fita, saboda sam bana son ganin yarima, don a ganina shine musabbabin haddasa min wannan fitinar, 2n farko da bai dawo rayuwata ba kamar yadda muka haqura da juna da farko, da hakan ba ta faru a gare ni ba. Ganin ba ni da niyyar fita ya sa ta ce, ya shigo dakinta ya same ni. Baqin cikin shigowarsa ya sanya ni kuka. Ya yi shiru kusan mintuna aqalla 8-10, kafin ya fara magana cikin sarqewar numfashi. "kiyi haquri humaira, na san cewa ke ba mai son magana ba ce, ballantana tashin hankali irin wannan, amma komai ya xo qarshe, mai martaba ya amince da na raba muku gida. Yanxu haka har ya bamu wani a lowcost cikin estate din da ya yi. Don haka ya sa kika ga mun dade sai da muka kammala komai, yanxu haka ana can ana sauran gyare- gyaren da ba a qarasa ba". Ke dai da ke kara2 idan na tanka kin tanka, ya matso kusa da ni, "ko sai xuwa dare idan kin qara hutawa nan? Na ga can din ma ba hayaniya, sannan babu aikin da xa ki yi, saboda su malama dagwayye na can 2n daxun". Ko motsi ban yi ba. Ya matso tare da xama bakin gadon. .....Farko da kuma kullum lallai tana kan hanya, 2nda a duk lokacin da muka hadu sai ta nemi xubda jinina. Ka sallame ni na tafi gida don girman Allah, bana sha'awar xama da kai ko da da qwayar xarra ne, domin wannan fitinar somin tabi ce yanxu aka tsoma hannu, ma2qar ina tare da kai". "kar ki so kanki mana humaira! Yanxu wannan baraxanar ce xa ta sanya ki bijire min? Ki iya 2na cewa, so da qaunar da nake yi miki ya sa na take dokar mahaifina na aure ki saboda Allah, na xabe ki fiye da tsinuwar mahaifina da fushinsa. Duk wannan baraxanar fareeda ta sami qwarin gwiwa ne daga wurinki, don ta fahimci kin kamu da matsanancin tsoronta. Ina qara fada miki, ki tashi tsaye ki qwatar wa kanki 'yanci, na tabbatar fareeda ba ta fi qarfinki ba, kawai kin sa wa ranki tsoro ne. Ga babban takaici ni din da take yi domin ni, saboda ta fahimci irin son da nake yi miki baki nuna damuwa a gare ni ba, babu wata kulawa. Ki nutsu ki kwantar da hankalinki ke ma ki nuna mata lallai ke ma mace ce, saboda duk wannan haukan da cin mu2ncinta ni ba xan sake ta ba domin al'adata ba ce sakin mace, duk da ba ni sonta, kuma ba xan sake ta ba ballantana ga dana ko diyata da ke jikinta". Ya miqe "xan jira ki a waje ki kimtsa mu tafi". Yana fita na koma na kwanta wajen mintuna 5 sai ga hafsat ta shigo, salati ta kama yi tana tafa hannaye. "kai jama'a, wai humaira kwanciya ki kayi? To wallahi tashi ki bi mijinki". Na miqe ganin ta dauki abin da xafi. Ta biyo tana fadin "wallahi ba ki da wayo yadda kika dace da mai qaunarki haka, duk wannan fitinar bai girgixa shi ba, amma kike ja baya da shi? Wallahi da ni ce wani sabon salon shafin soyayyar xan bude, kuma sai a gaban gimbiya xan nuna don ta ji haushi". Nayi mata banxa saboda na fahimci bata gane irin salon masifar gimbiya ba. Xaune yake cikin motarsa anaconda sahabi na tsaye jikin taga ban san abinda suke tattaunawa ba. Yana ajiye ni ya juya wai xai je gida, umma na son ganinsa. Kai daure har lokacin da bandeji a goshina, su dagwayye suka tarbe ni suna masu jajantawa, tausayina fal a fuskarsu. Nayi murmushi lokacin da na sami kujera na xauna. "ashe duk kuna jin wannan fitinar?". "qwarai kuwa ranki ya dade, wannan tashin hankalin ai babu dadi yau kam na kusa da ita ya shiga 3 saboda yarinyar nan ba ta da kirki ko alama, rashin ragowa a ba ya da dadi a rayuwa". "hmmm" kawai na ce. Wayata ce ta dauki kuka, nayi saurin dubawa don idan yarima ne wallahi ba xan dauka ba. Sunan inna na gani, wani irin dadi na ji har cikin raina, na kalli dagwayye. "ina ne dakina?". Ta nuna min da hannu. "ga shi can". Na miqe tare da daga wayar saboda bana son maganar gabansu duk da sun santa. "Assalamu alaikum, inna kashe in bugo miki kar a cinye miki kudi". "a'a barshi ina da isassun kudi, yarima ya turo min kati sosai, da ma wancan bai ko yi rabi ba... Duk kuna lafia ko?" "da sauqi dai inna". Na fada a hankali cikin muryar damuwa. Hankali tashe ta ce "me ya faru ne? Ko mahaifin nasa ya gano matsalar ne?". "a'a inna ko daya, shi mun daidaita". Na fada mata duk yadda aka yi "to me aka yi yanxu kuma?". "gimbiya ce inna wallahi bana iya masifar wannan matar". "haquri xakiyi, watarana sai labari". "inna ita fa har gabansa yi min take yi, ga shi tana iqirarin sai ta hallaka ni". "duk kishi ne babu abinda xata yi miki wanda Allah bai miki ba". Kamar in yi kuka, wai me yasa inna ba ta ganewa kullum idan ina kwatanta mata, ga shi ba na son fada mata raunin da ta ji min kada hankalinta har asmarta ta taso. "xata daina kiyi haquri dama xama ya qunshi haka ga masu sabon aure, kuma na hore ki da kai qararta ma2qar abinda ya faru tsakaninku bayanan. Yana fada miki baya sonta a baki, wallahi ba ki san xuciyarsa ba musamman yanxu da take dauke da ajiyarsa, duk yadda yake sonki yake kuma dokinki da kin kai masa qorafin matarsa xai ji kin fara sure masa. Ko 2nkararsa kika yi da muhimmiyar magana ba xai wani baki kyakkyawar kulawa ba, domin xai yi 2nanin qorafinta xa ki kawo masa. Rayuwar aure humaira haquri ake yi, kowace mace baki san irin xaman da take yi ba nata abokan xaman, amma tayi xamanta... Haka ki rike sirrin mijinki kuma ki kyautata zamantakewar zamanki da mijinki.munanan lafia kalau muke kuma muna cikin kwanciyar hankali dajin dadi alhmdllh kiyita godewa Allah ga mansura can yar uwarki mijin dukanta yake watanni nawa da aure amnan hr ya saketa saki 3 wanda Allah ya haramta..yarima ne tsaye bakin kofa ya kuramin ido cikib tuhuma na da dauke fuska..Allah ya kyauta inna zan kiyayae insha Allah inyi yadda kikace..yawwa toh Allah yayi miki Albarka ki dage da addu'a kada yi sanya da ibadarki,nace toh a gaushe da mutanan gidan nace zasuji a gaida su sumayya..ke kika buga mata ko ita ta bugo miki ya tambayeni lokacin da na ajiye wayar idonsa kyam a kaina wallahi na tsani kallo, na fada a zuciya amma a fili sai nace ita ce ta kira ni, wai me? kokwanto na me ni da uwata? ni ma ai uwata ce ko? na zaro ido ashe ba a zuciya nayi maganar ba,na lura ta yi masa zafi sai na hau kame- kame yayi saurin tarata cikin kunar rai "don me zaki fada mata rikicin da ake ciki,ko duk salon rashin kwanciyar hankalinta ne kike bukata? rainin hankali duk duniya akwai wanda ya kaini tattalin kwanciyar hankalin inna. "mst" ya buga tsaki wallahi humaira kina da matsala yasa kai ya fice rai a bace mamaki ya kamani ni na bishi da ido. kamar abin jira wayata ta kara kuka nayi saurin ridota na ga sunan amira a hanzarce na daga domin ina da bukatar nemanta ni kaina. hello kira ni don allah kiran gwandala daya ce ba kudi tuni ta mutu alamar kwandala dayar data ambata an cinye ta babu bata lokaci na kira ta. kaji manya ta yarima bada kanki a sare. nayi murmushi nace ke ni bana son iya shege da man wallahi ni ma ina da niyar kiranki a yau dinnan. dan allah? nima tun dazu nake neman ki bata shiga ba daman na fada maki an sanya rana nan da wata shida bikin yayi. a'a toh allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna mana lokacin lafiya. safwan kuma ya sami addmission saudi arabia zai cigaba da karatu yace shi da nigeria har a bada . nace allah sarki, amira baki tambayata ya zamana ba ? nayi mata tambayar dan na kau da wanchan zancen. hmm ai ko ranar juma'ar nan da abin ya tuko ni har zan kira ki sai na ga cewa ke fa har yau baki ce min komai ba toh ni kuma binciken me zanyi? nayi murmushi, hmmm ke dai bari na kwashe duk labarin kaf na fada mata sanna na cigaba da cewa "wai amma duk wanna fitinar ni yarima yake gani da laifi shin amira ina ni in fada da gimbiya lillahi warasuluhu? "tabdi" ta fada da karfi. nace maccen da kemin wannan illar har yaushe zan biye mata ranar da ta kunso wuka ta luma min fa? lallai kam ta kara fada "yanzu haka fushi yake yi da ni,wai na ki sakin jikina da shi yana ganina da wani gaggarumin laifi."ikon allah ta fada tana kara jinjina maganar. "ba ma kisan ina cikin matsala ba sai na fada maki cewa ,yanzu ya gama min fadan don me zan sanar wa inna,kuma wallahi amira ni ban ma fada mata gimbiya ta ji min rauni ba shine yayi fushi ya fita, kiji faa? "ke kam bone ta ciki humaira. wallahi kuwa na fada a marairaice. to iya gimbiya ta san inda ka maida ke ni yanzu? ni ban sani ba amma kema kin tabbata komai daren dadewa sai ta gano ni matukar ba baruwa nayi da yarima ba. ta ja dogon tsaki tace " ke wallahi bnaza ce saboda wata banza sai ki rabu da mijinki maimkaunar ki haka humaira? wannan furuncin naki fa zai sanya matsala ta afku tsakaninki da yarima. wai inna ta baki labarin yadda ya mayar da gidan ku? gabana ya fadi nace " kamar ya fa? tace "wai baki sani ba? ko daya ni dai na rabe da kullum mukan yi waya da inna sai ta ce kada na gaji da yiwa yarima godia" "lallai to wallahi kin san gidan honorable? na hanga nace kwarai, saboda duk shiyyar unguwarmu babu gidan daya kama kafar gidan honorable nura nasimat." to ko kofar gidan ku be kai ba a yanzu wurin kyau da tsari ke yan aikin inna biyu fa da me mata abinci da me mata shara da goge goge. " tsakanin ki da allah amira"? " na rantse da allah ta fada tana yar dariya. shiyasa nace maki wlh ki daina wannan furucin , yarima baya taba iya rabuwa da ke. da yayi maki fada yanzu har yai fushi ai da sai kiyi tunanin cewa inna fa mahaifiyarki ce amma ya nuna damuma fiye da taki, ke bama abin alfaharinki ne ma kina in a wanna zamanin akeyin fito na fito da surakai? to wallahi ki gaggauta zuwa ki bada hakuri sannan kada matsalar gimbiya ta sanya kiyi watsi da masoyinki, baraka ta shiga a sami rauni wannann shine babban burinta. nayi kasa da murya " amira nagode allah ya bar zumunci". Amin amin, na gode sai munyi magna. na dafe kaina tsananin tausayin yarinma ya mamaye zuciyata kmr kaina zai bare. a hankali na mike ,rabi na goge wasu zannuwan gado nace "ina yarima ne ko ya fita?" "A'a yana dakin chan" ta nuna min da hannu na bi sirdaden da ta nuna na sa hannu na murda gaa mamakina naji ta bude. na shiga sai na ga tankamemen falo ne daa yaji kayan gayu irin na zamani. na hango kofa daga yamma alama nan dakin yake na hanzarta isa tare da budewa. jin an bude kofar yasa shi dagowa da sauri na lura da idanunsa sun yi ja matuka, shi dai kam bacin rai na haddasa masa jan idanun, na fada a zuci saboda yadda na san idanunsa farare tar har wasu ruwa kake gani kwance saboda haske. ganin nice sai kawai ya maida kansa ya kifa kamar yadda yake kwance ruf da ciki.tausayinsa ya kamani ,naji kamar na dago shi na rumgume a yadda naji sonsa ya karu a raina. sai dai miskilancina bazai barni aikata hakan ba, na zauna bakin gadon gab da kafafuwansa ko motsawa bai yi ba. na rasa inda zan fara, toh me zan ce masa? daraba ta fado min. "amma yarima wannan kwanciyar ce fa aka haramta saboda ta yan wuta ce babu kyau yin ta" a hankali ya juya amma sai ya bani baya ya kalli can. raina ya bani fushi yake yi." allah ya baka hakuri" na fada a hankali. bai dai ce komai ba bai kuma motsa ba, nan da nan kunya ta baibaye ni naji duk na tsani kaina. na tuna irin dizgi da wulakanci sa da gimbiya ta sha, ba shi da wuyar dizgi ai sai na raina kaina. Na yunkura zan tashi gwiwa sake ina nadamar kawo kaina, sai kawai naji an ruko ni ta baya."ina zaki je kuma? haka ake lallashin maigida idan yayi fushi?" na sunkuyar da kaina, ya buga tsaki "ni di wanna kunyar wallahi tana kwarata....zo na koya maki yadda ake bawa maigida hakuri" ya shiga yimin cakullulo tun ina zillewa har na hau kyalkyata dariya sai kawai ya kura min ido, nayi saurin rufe idona shi kuma ya kai bakinsa ga nawa nan da nan yaren ya sauya.******** Cikin kwana uku ya bude min ido ya koya min son sa da tarairayarsa muka bude sabon shafin soyayya.na yi nadamar rashin sakin jikina da nayi tun farko na gane cewa lallai ba karamin so yarima ke min ba, ban da shagwaba babu abinda yake zuba min , duk yadda na wasance dole wani abun idan yayi min shi sai naji kunya, shi kuwa banda zagi babu abinda yake yiwa kunya, wai kunya na kwarar sa (mata a rike kunya domin ita ce adon mace, wallahi duk yadda kuka dade da miji ki rika nuna kina jin kunyar sa wasu lokutan musamman lokacin da kuke kebe kudai yana karawa mace martaba da kima a idonsa). Kullum cikin zabga karya yakeyi a asibiti cewar yayi tafiya ne maimartaba ya aike shi. Washe gari ya kama zai koma gidan gimbiya kamr kar ya tafi nice me kwarin gwiwar bashi magana, da kyar ta tafi wajan karfe biyar na yamma. kullum yana zuwa da safe mu gaisa da marece kuma ya dawo yi min sai da safe, ina lura dashi sam walwalarsa ta sauya amma sai kawai na share na san shi da mutuniyar ne ni dai allah ya min alamnashara. Rnar da zai dawo ina ta shiri sai ga shi ya shigo da sauri ina zaune bisa kujerar gaban madubi. Humaira am sorry kano zanje yanzu aka aiko maimartaba baban gimbiya bashi da lafya har zaa fidda shi waje shine zan kai su umma suyi masa allah ya kiyaye hanya yanzu haka gasu chan suna jira na. nan da nan halin namu ya motsa wato KISHI wani kallo na fara jefan sa da shi tukun kafin nace "duk gidan ku a rasa direba sai kai?" abin mamaki sai naga kamr ransa ya baci. "haba humaira ina laifi dana ma zo yi maki bankwana da kiji cewar na tafi ba?" yanzu haka na fada maki ga su maimartaba can a waje suna jira na idan ba ke ba wazan wa haka?" ai naga kana ta faman kyarma ne zaka gdan surukai" kema haka ake kyarma idan zaa gidan naki.... maganar ta maqale daga karshe alamr SUBUL DA BAKA yayi. in shirin maida masa sai kawai ya fice, wani gululu ya taso min. Banyi barcin kirki ba ranar, kagara nake ya dawo na amayar masa ta cikina. haka abinci ko ruwa na kasa sha. har yarima ya is aya wulalantani abinda kawai nake nanatawa araina kenan. kwance nake daki naji shigowar sa na mike tsaye tare da rike kugu yana shigowa ko rufe kofa beyi ba na hau masifa daman ance me shiru-shiru be iya fada ba. "da zaka fada min magana kan wata banza na taba aiken ka zo?" ko kuwa na taba aiken ka wajan uwata....." haba humaira wai maganar bata wuce ba?" toh kiyi hakuri ni da wasa na fada."eh din ai da wasan daren ake fadawa wawa magana. "duk naji kiyi hakuri dan allah wai dole sai ka zuna da ni ne?nace bana yi ko dole ne? ya kyakyale da dariya dama na lura sai gumtseta yake yi. Raina ya kara baci wato ya maida ni mahaukaciya sai naga ya fara rawa yana waka 'ashe ana kishina ana kauna ta, a'a lallai yarima taka-taka' Ban san lokacin da nima na kyalkyale da dariya ba,saboda ko waye sai ya dara idan yaga yadda yarima ya dage yana kwasar rwa. ya daina rawar tare da daure fuskar nan irin ta shagwaba. "gaskia ni dai a cigaba da fadan bana so a daina " ni dai na cigaba da murmushi, yana matso yana yar dariya "muguwa na gane ki ashe haka nan ake wani basar wa kaunar yarima tayi katutu a rai?" nayi murmushi "eh din an ji" ya rungumo ni "me aka ajiye min?" ina shirin bashi amsa wayar sa tayi kara ya zura hannu, sai naga ya sake ni da sauri ya latsa tare da sanya handsfree yayi kasa da murya "Allah ya taimake ka" "zancen banza zancen wofi, yanzu nake jin labarin ka raba gida, wannan ai shirme ne lallai ka hanzarta hade matanka waje guda tun kafin raina ya baci,yaushe zaka iya adalci matukar basa tare? anya kai jarumi ne yrima? ba ka iya daidaita matanka?oh allah wadarai a yau nake so ka maida wacce ka ware maza- maza. yana gama fadin haka ya kshe wayar. Gwaram! na koma na zauna tare da dafe kaina . ya kalle ni "kiyi hakuri sai ki tashi mu tafi kar abin yazo da bacin ran sarki" Wayyo ni humaira Wayyo Allah na. Tunda muka fito gbana yake faduwa ni na tabbatar idan aka auna jinina a yanzu ya kai dari biyu da wani abu. har muka isa ina rike da kaina shi dai bai ce komai ba. Komai yana yadda na barshi su rabi suka shigo min da akwatuna na. Nayi tsaye sai zare ido nake ina kyarma ya shigo da sauri. haba humaira duk kin bi kin tada hankalin kan waccen yar iskar. Bai rufe baki ba sai gata "Don ubanki har kina neman raba ni da shi bayan kin samu kin shigo?" Bata rufe baki ba ya wnka mata mari uku a jere,sannan ya kwale belt ya fara tsula mata ta duke kawai tana kuka tana faman karewa. Na rike shi "dan allah ka kyale ta,wayyo ni humaira" na fada ina kuka. bai saurare ni ba na janye shi baya ta sami halin mikewa tsaye ta nuno ni da yatsa "wallahi sai na rama kanki shegiya" zai kara damko ta tayi waje da gudu. tana fita yaranta suka boye saboda duk sunji abinda ya auku. ya kalle ni a fusace "Haka zaki yi mata duk ranar da ta kara zuwa miki ida yar iska" ni dai a sukurkurce na kwana,washe gari ya fita da wuri saboda zai je tiyata. na kulle kaina a daki har kusan karfe daya saura sai da yunwa taci karfina sannan na fito. "Rabi dan Allah kawo min tea" tace "to" tare da juyawa. ni bana sha'awar wani yayi min aiki amma babu yadda na iya saboda masifar gimbiya. Ganinta nayi kamr an jeho ta, nayi saurin mikewa tsaye ban ankaraba ta rufe ni matsiyacin duka na dinga kokarin rugawa amma ta babbake ta hani ni wucewa. Tun ina motsawa har jikina yayi tsami ni dinga rizgar kuka. Sai da ta barni kwance tukun ta fita. Rabi ta shigo dauke da tire duk jikinsu yayi sanyi "Sannu ranki shi dase,sannu!" Dagwayye ta fada lokacin da ta ke kokain daga ni ta maida bisa gado. Rabi ta kalle ni "Wallahi sai kin tashi tsaye gidan nan lallai gimbiya kwararki za ta ci gaba da yi dan bata fi karfin ki bakawai kin sawa ranki tsoro ne" Shiru kawai nayi masu, fuskata tayi jawur saoda duka ga shi gefe daya ya kumbura . Na samu na kurba ruwan tea din sannan na sallame su. karfe udu yarima ya dawo hankalinshi yayi mugun tashi. "Himaira lafiya me ya same ki haka? na langwabar da kaina sai kuka. "Badai fareeda bace ko?" me tayi maki?" nan ta shigo"?Duk ya kidime ya rude, nayi saurin girgiza kai "Faduwa nayi a bandaki silbi ya kwasheni...." Subhanallahi, Rabi,Rabi!! ya daga murya kamr ba shi ba sai gata da gudu "Don me zaku rika wanke toilet ba ku gogewa? maza je ki tsane duk wata lema da ke ciki". sumi-sumi ta wuce. "kin sha magani?" na girgiza kawai saboda jikina ya gama yin tsami. wannan fitina har ina? cikin wata tara amma be hana gimbiya tashin hankali ba. Da Allah ya tashi taimako na sai gashi washe gari ta haihuwa da karfe uku na rana. A yadda su Rabi ke fada min tunda aka ce mata mace ce take kuka har suka bar asibiti. Nayi murmushi saboda ni farin cikina na samu sauki.Abin karin tashin hankali sarki yace a bar yarinya ba ai an kaita fada ba. ni dai ina bangarena, wanda ya shigo maraba wanda be shigo ba bana neman sa. Hidima aka yi sosai an sha shagali ni ma ba'a barni a baya ba, ko leke ban leka bangaran gimbiya ba. yarinya taci sunan Fadimatu Zahra'u. *** ***** ****** Maryam yar uwar yarima ce, jininmu sai ya hade da ita kwarai dan a daki na ma take kwana ita da wasu yan tawagarta. Bayan suna da kwana biyu na aiki rabi gurun su umma ta kai masu abinci, ita kuma dagwayye na baya tana wanki, sai ka gimbiya a harzuke. "Toh munafuka an fada mana kina tsalle kina murna an haifa mace,to dan ubanki matsiyaciya ke ko haihuwar ma baza kiyi ba" Na zaro ido cikin tsoro da mamaki nace "Wa? Ni? Wallahi billahi karya....Ban rufe baki ba naji saukar wani lafiyayyen mari. "Ni zan maki karya shegiya?" na dafe kunci. "Wallahi ban ce ba,haba ya zaayi?" ta kai min harbi a cinya har sai da na tsugunna. "Dan allah gimbiya kiyi min rai.wannan masifa ta ishe ni, wai ya kike son na yi ne? Me zan miki ki kyale ni?" Ta harzuko min "Ina son ki kyale yarima ki fita rayuwarsa ko kuma wallahi na kashe ki na kashe banza" Na rushe da kuka. "Yace bai sakina,bai kyale ni..." "Daure ki akayi da baza ki tafiba makira?" na baki kwana hudu idan ba ki bar gidan nan ba wallahi sai dai uwari ta sake haifo wata mayya kawai". Tana fadar haka ta fice. "Dole na bar gidan nan" na fada a sarari tare da shiga daki ina laluben waya. Ban ga laifin gimbiya ba saboda gaskia ta fada,ba'a daure ni ba, gidan nan dole in kama gabana kwana lafiya yafi. Na dauki waya na latso number Amira, bugu daya ta shiga,ringin biyu ta dauka."Ta yarima ba da kanki a sare" kirarin da take min kenan a kullum da ta dauki wayata,ko da kuwa ita ce ta kirani ina cewa hello zata fadi haka. "Hmm" Na fada kawai. tace ya akayi mutuniyar, hmmm humaiki kimin magana na sani... AMeera guwa xanyi, saboda me?? Nakwashe duk yadda mukayi da gimbiya nasar daita, kinga tunda har tabani zabi gara kawai... Ta kunduma wani zagi lalle humaira agaisheki, wallahi yau nakara tabbatarwa cewa saunace ke, haka zaki zauna tana cutarki, lallai ki kwatarwa kanki yanci tunda wuri, nayi mata me?? Nafada ahankali, kiwanka mata mari kuma ki tabbatar mata kindaina jin tsoronta.. Hmmmmm.... Nafada kawai, au bazaki iyaba kenan?? TO wallahi karki kara kirana akan matsalaki. Idan azaba ta isheki seki nemawa kanki mafita ameera ina gudun kada aga zakewata kituna matsayina da tushena kada naje na debowa kaina masifar dazatafi karfina. Fada zakiyi ne? Nace fada zakiyine? Bata hudo miki dazuwa miki idan yarima baya nan ba? To kidaki shrgiya kuma kiyi shiru muga idan zata fada. Nasaki ajiyan zuciya, to ameera nagode. Zan jarava, nayi agumi, wannan jarabar dayawa take. Atunanina taga banida halin fitane yasa takara dawowa, wannan karan ma tsautsayi nafito kenan bawa dagwaye zanin gado, tana shigowa tamaida kofar baya ta rufe, gabana yafadi, na fella da gudu zan fita ta kofar baya tarigani isowa tana kokarin kullewa, kafin in ankara, ta shako wuyana, tana neman makogwarona, har ga allah bani niyyar fada da gimbiya amma danaga tana neman rabanida raina, bansan sanda na wancajar daita ba abinka dame hakuri nayi zuru!! inna kawai nake tunawa idan gimbiya bata tashiba, nafashe da kuka nashiga uku! ashe surabi da yaran gimbiya suna tsaye kaina bansani ba seda naji daya tace..hakanan zaki tada hankalinki dimin ko kotu akaje bakda lefi, saboda taddaki tayi har gidanki, nayi saurin daga kai. Wallahi nibansan naiya fada haka ba hasalima nibanida abokin fada aduniya. HAba gimbiya munsani aim duka danaji banbarakwai sena daure nace gashi yanxu tajanyomin batacciya, ina fadin haka wayata tafara kuka inadubawa naga yarima, bugun zuciyata ta karu batare dabace kimai ba nakara akunne na hello humaira.. Hum nafada,, kina gidane, huum nafada ahankali. Lafiyarki kalau koh ko akwai abinda farida tamiki? Babu nace atakaice, kin tabbata? Um. To me kika wa mata tayi irin wannab dogon sumar? Sena fashe da kuka ina fadin tsautsayine wlh, itace ta hayemin da fitina taki ta kyakeni, bace mata vanason fada tunda namata alkawarin zan barmata kai kamar yadda ta gargadeni, mtschw, sekuma ya ajiye wayar. Haba ranki yadade dan me zaki tada hankalinki tunda kunfara kwatarwa kanki yanci, walh kidage kiyi maganin gimbiya, aikinmayi kokari. Sannan duk abinda kikewa yarima na kyautatawa karki fa, dole ki rashi ki kwatan wa kanki yanci, Allah ne yabaki babu me kwace miki, mutunciki yasuya miki duk wannan darajar. Shiru kawai nayi ina saurarinsu idan wannan takai aya se wannan ta cabe. Karfe 4 yashigo da kasaitarsa, ina falo yashigo duk nayi firi firi. Kallo 1 yamin yakawar dakai. BAn ruwa insha yafada batareda ya kara kallona ba. Ina bashi yahada da hannayena yajanyoni jikinsa. Wai lafiyarki haka, duk kin wani firgice, meya hadaki da farida amma babason kuka yafada saboda ya lura idanuna sun cika da kwalla. Batareda na boye masa komaiba na zayyana masa jomai daga farko har karshe, yaja dogon tsaki, aidama seda kowa yayi zaton haka. Musamman da sahabi yabada shaidar nan ya kwashe tashi yasa ran maimartaba ya baci yayi min fadan da babu gaira, wai bani adalcine shiyasa, har yau yakasa gane rashin tarbiyyar yarinyar ne, har yana barazanar babu wacce zan rabu da ita cikinku. Dle indaidaita kuzauna lfy, bansan lokacinda nace tabdi ina!! Yayi dariya, kina ganin dawuya ko, nasunkuyar da kai, ai ina hango matsalar ne. Kuma wlh me sauki ce, kinsan meye saukin? Na girgiza ka, kece zaki bi min daita, Allah yaga zuciyata ba nayi miki haka bane da niyyar ina tsoronki kema, nandai baa kano bane balle in nuna miki karfin mulkin sarauta, ita ma a karkashin wata masaraurar take dole tayi biyayya. Nace to. Bani abinci inci, zankoma asibiti. Seda nabari yagama sannan nace ko inzo muje nima indubota. Yayi murumshi, ai harta dawo bazakije ba, kuma ina gargadinki da wannan tausayin kiboye shi koda tadawo kada ki nuna mata dan zata kara samun wata barakar. Amma idan kika shareta lalle zata fara tsorata da alamuranki. Shiru kawai nayi ina mamakin irin wannan zuga ta yarimam shi baze kashe wuta ba sedai ya rura? Nifa anawa tunanin kenan, kullum sauraron dawowarta nake, sgikuma innatanbayeshi yaushe zata dawo seyace min tana can dai, nama amira waya danneman shawarta ga mamakina duk magabar dayace irinta yarima. Haka na santawa sarautar Allah ido ina sauraron dawowarta. kwana2 natashi banajin dadin jikina raina yata baci zuciyata tana zafi, tun bandsmu ba har abin yafara bani tsoro, inyita neman fada dashi amma baya yarda yabiyemin, ina zune afalo naji hayaniyar dawowar gimbiya, banji faduwar gaba ba kamar baya, shuru bata shigo gidana ba kamar yadda nayi tsammani har kwana 4. Ranar jumaa yakama agidanta yake bayan yadawo masallaci yakawo min huduba wadda yake tagomin daita duk sati. Lokacinda yashigo ina wanka seda yajira nafito sannan. Ashe tayi zargin wani abu, bayan yafita nakoma daki ina gyaran wadrobe kawai naga mata, waike dan ubanki me kike nufi ne? Dane kike takama banza talaka? Bansan lokacinda nacire dankwalina nadaure kugu na daura hannu duka2 abinda kike nufi nima shinake nufi kema dan ubanki, tazaro ido cikin mamaki, nikike zagi? Anzageki koda abinda kike ganin zaki iya? To bari infada miki bani tsoronki, ko kifitarmin gida koyauma kiy kwana asibiti, koki bakunci lahira don lallai cikin 2 nan se anyi 1. Sakarai wadda batasan abinda takeyi ba, ke baki zauna lfy ba baki bar wani yazauna lfy ba, a sarautar da kike takama dashi raini da rashin tarbiya ne salon mulkin naku? Ke ko kunya bakiji, agaban baroron dakike mulka mijinki ke dizgaki saboda dakikacinki har dukanki yakeyi amma kinkasa yiwa kanki karatun tanutsu? Ni diyar talakawan dakika raina gashi nazo nakwace fadarki awurin iyayen mijinki dakike taka suna sonki? Kingani riba 2 goma da ashirin, dan haka kirika addua Allah maji rokon bayinsa ne. Nizaki fadawa Allah?? anfada miki farida ko da yadda zakiyi dani ne? Na matsa kusa daita, ina jiranki! Ta girgiza kai, lallai zaki raina kanki ta juya tafita. Na fincikota ta baya kedin banza aisedai ji raina kanki a gidan nan, kuma daga yau zaki gane shirun da nakeyi a baya ba tsoro bane, zaman lfy ne nake neman amma tunda kinkasa ganewa shege kafasa. Sakar min riga tafada tana hararata. Na ingizata baya tareda rufe kofa ta. Nadafe kirhi, oh waini yauke zazzagawa gumbiya masifa tayi shiru? Lalle yau na gano abinda amira da yarima ke nufi, ban fada masa yadda mukayi daita ba danko nuna masa tazo gdan banyi ba. Da marece muna kwance kan gado abinka da lahadi na langabe ina shagwaba. nidai yau sonake muje baya musha iska, zaune yatashi zumbur me? Namaimata ya watsa hannu ok lets go. Cikin raina nace aikaji shi komai turanci idan zaa kashe ni ban iya fassara abinda yake nufi, amma dai nafahimci abinda yake nufi, na umarci abimu dakayan marmari, ni nariga nabashi abaki musamman dana lura tagan gimbiya abude. Shikuwa yana mamaki amma isa da miskilanci yahana ya nuna min. Yana gamawa nace to yagoyani yayi yawo dani cikin lambu, zauyi gardama nafara dira dira ina shagwaba irin na yara idan akaki musu abu. DUK ya rude ya diririce koda ya sureni yayi zagaye 2 dani se yayi cikin gda da gudu, ALlah yatemakeni su rabi duk suna sashensu. SEya kasance duk ranar aikin a lambu muke wuni gashi bayan dakin Gimbiya ne duk abinda yake faruwa tana ji wannan abu yana kona mata zuciya. Da wani yammaci ne su Rabi suka kawo min 'Yar gidan Gimbiya raino in ji Yarima dan na saba da 'yar shi, naji tsoron karba ma saboda kada wani abu ya faru a zarge ni, su Rabi suka ce dani dawani abu yafaru muzamu zama shaida agareki. jn haka yasa na mi,a hannu na amsheta, tun daga ranar kullum se ankawo min ita nima haka nake aikowa daita idan har tayi kuka ban taba yarda naje gidanta ba. ranar da yarima yacemin zeyi tafiya be fada mun inda zeje ba ranar baa kawo hauwau ba na tura rabi wurin yar aikowan karta bari gimbiya taganta taji ko lfy? DUK naji babu dadi musamman daaka kwana 2 ana na 3 ne ina dakin yarima ina gyarawa dayake ranar zan amshi girki, senaji ana kwankwasa kofa, atunanina cikinsu rabine senace shigo mana menene. Ahankali tabude kofan gavana yafadi yau kuma dame tazo don Allah kifita ke bakijin komai kullum masifa ke kawoji gidana amatsayinki na babba?? Ta girgiza kai senaga kwalla sharr duk se jikina yayi sanyi. AHAnkali tafara magana, zuwa nayi inbaki hakuri akan abibda yafaru abaya sannan inmiki bankwana domin nafahimci lalle yarima kaunatace bayayi. Tunkafin na aureshi nake shan wahalarsa gashi har yau ban taba jin wani dadi daga gareshi ... Kai dena fadan haka halinki shiya janyo miki wannar tsanar kuma laifinki ne, tun farko kinfahimci baya sonki kamar yadda ake tilasta aurenki gareshi, memajon kidage da biyayya da kyawawan dabiu se kika nuna ke YAR SARAUTA ce alhalin shima haka gaba da baya yanzu haka dazaki gyara halinki yarima me saukin kaine aidakyarne, domin nitunda ya aureki be karayin kwanciyar aure dani ba, setayi shiru da alamun SUBUL DA BAKA tayi seta bani tausayi saboda yadda duk ta sukurkurce akan nadamar datayi, setaci haba dacewa rashin iya zancena da yadda nake magana cikin gadara yasa yarima yakara tsanata iyayena danake samun sauki awurinsu sun tsanenu, kedin danakeyiwa kinkai karshe. Seta fashe da kuka hakika shaidan ya rivace ni laananne, Allag shiyasa shiyasa na yanke shawarar hakura da yarima dan baze taba sona ba. Injiwa? Nafada, walh inda dagaske kinyi nadama gumbiya yarima ze kaunaceki, nikuma zanyafe miki duniya da lahira nima kiyafe min, tashare hawaye, ga mamakina sebaga ra tashi ta tayani gyaran dakin, dakanki kikeyi ina masu aikin?? nayi murmushi aini da dakin mijina da abincinsa bame tayani, nike gyarawa nayi masa girki da kaina. DAgas? Nace Allah. Lalle zan dunga zuwa daukan course. SAi magariva takoma gidanta. Kamar inva yarima lbr sebati shiru dan ze iya gwasalebi koya karya mata tsari. Washe gari wajen 11 segata da hauwau muna falo muna karin kumallo. Kida tashigo setayi turus shikuma ya daure fuska. Alanar sarautar ta motsa, nati kamar ban lura dasu ba namike ina yar dariya oyoyo hauwau. Nakarbeta tamiko min ita dama ita nakawi miki. Tajuya zata kima sena kamo hannunta Ai tunda kinzo sai munyi karin kumallon zaki tafi. Da alama taji dadin hakan saboda batayi gardama ba shi kuwa wani irin kallo yake yi mana cikin tuhuma da zargi. "Ya akayi, mene ne haka?" Cikin zolaya na kalleshi. "Yo mun shirya da Yayata..." "Mtsss" kawai ya buga tsaki tare da mikewa zai bar wurin. Na sha gabansa "haba Yarima, mutum yayi laifi har ya gane ya tuba amma..." "Kin tabbatar da gaske take, ko sharrin wannan ce kika manta?" Kafin na kara magana ta zube kasa tana rokonsa har da kuka, ni ma sai na kama kukan saboda tausayi. Kai rayuwa abin tsoro ce, Allah ka sa mu dace, amin! Ganin munyi masa rubdugu yasa yace, "shikenan komai ya wuce". Yana fadar haka yayi ficewarsa babu wacce ya tsaya ya lallasa. kusan kwana uku bai dayaye ba, sai da na ringa lallashin sa da ban magana, sannan yake zama muna hira saboda ko girkinta ne kullum da marece tana gidana, har hakan ya zame mana tamkar zaman majalisa. Maimartaba kuwa har kyaututtuka ya aiko mana da su. Da muka tashi zuwa kano tare mukaje da ita har gida ta roki Inna gafara. Zama ya koma mana gwanin dadi, ashe duk neman fadan da nakeyi ciki gareni, mukaje Yarima yayi min scanning sai ga namiji, kullum addu'a ta Allah ya sauke ni lafiya. TAMMAT BI HAMDULILLAHI. nanmuka kawo karshen littafin subul da haka 1,2&3 amadadin Zainab dahiru wauwo ( zeedee)***naku ANaM Dorayi kemuku fat an alkhairi saimunhadu a Novel nagaba Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100