GWARAZAN JIYA Littafi na Biyu ©Haƙƙin mallaka Mansur Usman Sufi Shekarar Rubutu Ramadan 2024 Rubuta labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp number 08137237071 Littattafan Marubucin:- TAFARKIN TSIRA JARUMAN DUNIYA KOGON ANNOBA KANGIN BAUTA FATAUCIN BAYI SARAUTAR MUTUWA TAKOBIN ƊAUKAKA SARKIN SADAUKAI GOGA SHA FAMA KARYA DA GASKIYA ƘARNI UKU ƘARSHEN ZALUNCI KUNDIN AL'AJABI GWARAZAN JIYA BABI NA FARKO A kwana na ashirin da biyar ne jaruma Zulaihat tayi gagarumin shiri ta ɗebi dakarun yaƙi kimanin dubu ɗari domin ci gaba da tafiyar ta. Bana ta kammala ne ta ɗora wani dattijo mai suna Razubal a matsayin sabon sarkin birnin Madinatul-dinar, kasancewar shine ya fi kowa fahimtar addinin Musulunci. Sai da sarki Razubal da jama'a suka yi masu rakiya har izuwa bakin gari sannan suka ɗauki hanya aka fara tafiya babu sassauci. Haƙiƙa Ubangiji shine ke iko akan halittar da canja dukkan al'amura, yanzu dai ga shi waɗannan 'yan fashin daji sun daina sana'arsu sun koma izuwa TAFARKIN TSIRA. Ƙasaitacciyar fada ce da aka cika ta da nau’ikan kayan ƙawa da alatun more rayuwar duniya, duk ƙasaitar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin wannan fada, dole ya raina kanshi ya tabbatar da cewa GABA DA GABANTA. A bangon yamma bisa wani zagayeyyen tudu mai hawa sha biyu aka girke wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana’anta ta da yaƙutu aka yi mata feshi da koren lu’ulu'u. Wani shirgegen mutum ne zaune ya hakimce, sanye yake cikin ƙayatattun tufafi na alfarma, kanshi yana ɗauke da wani KAMBUN MULKI da ya ƙarawa fuskarshi kwarjini. Ba wani ba ne wannan mutum ba face sarki Burzam. A gefe guda ‘yan majalissa na zaune bisa kilishi mai taushi, kawunansu a sunkuiye tamkar masu neman gafara, jama'a sun yi fadar tsinke, kuma shiru ya wanzu tamkar mutuwa ta kawo ziyara. Daga can sai sarki Burzam ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar zira hannunshi a cikin aljihun rigarshi ya ɗauko wani madaidaicin madubin tsafi da girman shi bai huce tafin hannu ba, ya buɗe bakinshi ya karanto waɗansu dalasiman tsafi da shine kaɗai ya ɗan me yake furtawa, yana gama rufe bakin shi, sai ga dukkanin abin da ya wakana tsakanin Jaruma Zulaihat da shugaban ‘yan fashi Ausur da yaranshi ya bayyana akan madubin, tun daga farko har ƙarshe. Koda ganin wannan al'amari sai ya taƙarƙare ya kwara ihu, wanda ya ɗimauta dukkan al’ummar dake fadar, kowanne ya sha jinin jikinshi domin sun san cewa duk sa’adda da ya yi wannan kururuwa ba alheri ba ne zai biyo ba. Tsawon daƙiƙa goma ana cikin wannan hali sai daga bisani ne ya tsuke bakinshi tamkar an aiko mashi da WASIƘAR AJALI, ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki yana mai cewa “haƙiƙa jaruma Zulaihat ta tafka babban kuskure da zuciyarta ta yaudare ta cewa za tayi karo da ni har ta samu nasarar ceton ‘yar uwarta Luzaiba a hannuna. Na rantse da halarar tsafina sai nayi mata kisa mafi muni”; Koda gama faɗin hakan sai ya mayar da madubin tsafin izuwa aljihunshi, sannan ya ɗaga hannunshi yana mai yiwa wani barde inkiya, badakaren ya tawo gare shi ya zuɓe ƙasa cikin ladabi ya kwashi gaisuwa, Sarki ya dube shi da jajayen idanuwanshi tamkar garwashi ya ce “ya kai dirkar birnina sarkin yaƙi Bazzaru ibnu siyaran kayi sani cewa na kira ka ne domin na shaida maka cewa nan da zuwa mako ɗaya, akwai yaƙi da ya tunkaro mu wanda ba'a taɓa yin tamkar shi ba, domin a wannan karon tare da uwar gidana Luzaiba zamu jagoranci yaƙin, saboda haka ina so dakaru suka kasance cikin shirin ko ta kwana, a tanadi makaman yaƙi, kuma a sake tsananta horo ga zakunan sihiri dake cikin kurkukun KOGON ANNOBA”. Koda jin wannan batu daga bakin sarki sai sarkin yaƙi Bazzaru ya risina ya ce “an gama ya shugaba bin umarnin ka shine ibada ta. Yana gama faɗin hakan ya miƙe tsaye ya nufi wata ƙofa a fadar, take dakarun masu gadin shi suka mara masa baya. Bayan sarki Burzam ya kammala yiwa sarkin yaƙi wannan umarni, sai wani badakare ya ɗauko wani zungureren ƙaho dake rataye a gadon bayanshi ya kafa a baki ya busa da ƙarfi, koda jin sautin busar sai baki ɗaya jama’ar fadar suka miƙe tsaye zumbur! Tamkar waɗanda suka ji BUSAR MUTUWA, bisa al’ada duk sa’adda da aka bisa wannan ƙaho sarki zai koma gidan sarauta an kammala zaman fada. Cikin taƙama gami da BAƘAR IZZA sarki Burzam ya miƙe tsaye daga kan karagarshi ya tako matattakalar fadar ya sauko ƙasa, ya durfafi wata ƙofa ta musamman da zata sada shi izuwa cikin gidan sarauta, cikin hanzari dakarun rakiya gami da fadawa suka rufa mashi baya, sai suka ƙule izuwa cikin ƙofar sannan fadar ta watse kowa ya kama gaban shi. Gaba ɗaya jama'ar birnin ba su jin daɗin mulkin sarki Burzam, domin hatta ‘yan majalissa ba ya ɗagawa ƙafa, sau tari su kan yi sunƙurin kawar da shi amma abu ya ci tira. Ƙwace, fyaɗe da zalunci ya zamo tamkar kurɓar ruwan sha a wajen sarki Burzam. Laifi kaɗan mutum zai aikata, amma sai a yanke mashi hukunci aikin bauta a gidan kaso, bisa wannan BAƘIN ZALUNCI ya sanya sarakunan nahiyar ke yiwa kurkukun laƙabi da KOGON ANNOBA. Domin masu hasashe sun tabbatar da cewa tun da aka yi kurkukun DARUL-HUSUF na sarki Sharhal da zamanin shi ya shuɗe a can baya ba a taɓa yin tamkar kurkukun KOGON ANNOBA ba. BABI NA BIYU Sarki Burzam da tawagarshi suka ci gaba da tafiya a cikin ƙasaitaccen gidan sarautar, suna ƙetare barori, barada gami da bayi, duk inda suka gifta sai dai kaga hadimai na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa cikin girmamawa, haka dai suka ci gaba da kasancewa har suka iso wani wani ɓangare da yafi ko ina tsaruwa da ƙawatuwa a gidan sarautar. Babban abin da ya ƙara fito da kyawun ɓangaren shine waɗansu ƙayatattun korran shuke-shuke. Kai tsaye sarki Burzam ya kunna ciki, dakarunshi suka ja suka tsaya a ƙofa, koda shigar shi sai ya tarar hadimai da kuyangi suna kai komo suna hidima, gaba ɗaya turakar shimfiɗe take da waɗansu irin kilisai masu taushi, a gefe guda gimbiya Luzaiba na kishingiɗe bisa wata ƙasaitacciyar kujera, sanye da tufafi shara-shara irin na hamshaƙan sarakai, kuyangi na yi mata fifita da waɗansu irin mahutai da aka yi masu ado da gashin ɗawisu, wasu kuma na shayar da ita taceccen ruwan inibi, sa’adda da kuyangin suka yi arba da sarki sai suka risina gare shi suka miƙe tsaye suka fice daga cikin turakar. Kawai sai gimbiya Luzaiba ta miƙe tsaye ta durfafi inda sarki yake tana rangwaɗa fuskarta cike da annuri ta tare shi suna haɗuwa suka rungume juna, sun ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali, sannan daga bisani Luzaiba ta janye jikinta daga na sarki suka fuskanci juna, sannan taja hannunshi har izuwa bisa kan ƙasaitacciyar kujera suka zauna tare. Luzaiba ta duba shi cikin alamun matuƙar damuwa ta ce “ya abin alfaharina shin ina dalilin wannan fushi naka? Koda jin wannan tambaya sai Burzam ya sa ki guntun murmushi a gare ta kai kama da yaƙe da ya ƙara tona asirin munin fuskarshi. Sannan ya yi gyaran murya ya dube ta ya ce ”ya muradin ruhina kiyi sani cewa ba komai ne ya ɓata min rai ba, sai domin a ɗazu ina zaune a fada ina gudanar da bincike, kwatsam! Sai gano cewa ‘yar uwarki Zulaihat ta tunkaro gare mu domin ta yaƙe ni da ƙwance ki daga gare ni, wani abu da yafi yi min takaici a hanyar ta ta zuwa nan ta kashe min babban yaro a ɓangaren fashi da makami wato sadauki Ausur, kuma ta musuluntar da ba ki ɗaya jam'ar birin Madinatul-dinar”; Koda jin wannan batu daga bakin sarki Burzam sai Luzaiba ta taƙarƙare ta bushe da dariya. Al’amarin da ya yi matuƙar bawa Burzam mamaki kenan ya ƙura mata idanu. Lokaci guda ta turɓune fuska sannan ta ce “haba ya uban ‘ya’yana ai bai kamata ba ace ka yi fargaba domin yin GABA DA GABA da ‘yar uwata Zulaihat ba, kai fa GWARZON MAYAƘI ne kuma GAWUTACCEN SARKI mai ɗauke da tarin rundunar mayaƙa, ai kawai ka ƙaddara cewa zuwan Zulaihat alheri ne a gare mu. Koda jin wannan batu daga bakin Luzaiba sai Burzam ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, bai san sa’adda ya janyo ta a ƙirjinshi ba ya rungume ta, yana mai cewa “ke ce abin alfaharina, ke ce farin cikin rayuwata. Wannan shi ne abin da ya faru ga sarki Burzam da uwar gidanshi Luzaiba. BABI NA UKU Al’amarin jaruma Zulaihat da dakarunta kuwa, tun sa’adda suka baro birnin Madinatul-dinar, sai suka suna tafiya babu ƙaƙƙauta, suna ratsa sarƙaƙiyar duhuwar dazuka da birane, har ya zamana sun shafe tsawon kwanaki uku, ba tare sun haɗu da wani abu mai cutarwa ba, a wasu lokutan idan ‘yan fashi daji da muggan namun daji suka hango, sai kaga sun bazama daji suna neman maɓuya. Al’amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa wannan saurayi wato Zamran da sauran dakarun kai kenan kuma ya basu mamaki, abin da ba su sani ba shine iko da ƙudirar ubangijin musulunci yake ɗawainiya da su. A iya tsawon wannan tafiya jaruma Zulaihat bata yarda ta bayyana fuskarta ga kowa ba, kodayaushe tana rufe cikin rawani, duk da kasancewar ta lura cewa a kowanne lokaci barde Zamran yana satar kallon ta a fakaice, kasancewar cikin dakarun babu wanda ta shaƙu da shi tamkar shi, domin wasu lokutan idan ba su yi arba da fusakun juna ba, ba su samum kwanciyar hankali. Wannan shi ne abin da ya wakana da jaruma Zulaihat da tawagarta. Kamar yadda sarki Burzam ya faɗa haka al'amarin ya kasance, a kwana na biyar ne kafin hudowar rana aka hango rundunar jaruma Zulaihat daga can nesa. Koda ganin hakan sai sarkin ƙofa ya umarni wani barde dake can saman ganuwar birnin ya busa ƙahon yaƙi, koda busawar sai ƙofar birnin ta yi ƙara alamun zare sakata, sai ga dakaru masu tarin yawa sun tururuwar fitowa, wasu akan dawakai, wasu raƙuma da toron giwa wasu a ƙafa, makaman yaƙin su kuwa ga su nan birjik. Lokacin da aka matso daf da juna, runduna ta fuskanci runduna, sai aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu, daga can sai dakarun abokan gaba suka dare gida biyu suka buɗe hanya mai faɗi da dawakai biyar za su iya jeruwa waje guda, sannan a hankali tawagar sawaye da gurnani ya fara bayyana, daga can sai ga sarki Burzam tare da gimbiya Luzaiba, tare da sarkin yaƙi Bazzaru, dakaru Kimanin ɗari biyu na take masu baya ɗauke da waɗansu girɗa-girɗan zakunan sihiri, shigar da su sarki Burzam suka yi ta baƙaƙen sulke ce mai matuƙar kwarjini da ban, kuma suna zaune bisa ingarmun dawakai jajaye. Lokacin da rage saura taku goma tsakanin su da Zulaihat suka suka linzamin dawakan su suka tsaya can! Aka shiga yin kallon-kallo. Sa’adda dakarun Zulaihat suka yi arba da tsananin yawan dakarun sarki Burzam sai suka ɗimauce suka ji tamkar su ja da baya, domin sun san cewa ko ba a gwada ba, linzami yafi ƙarfin bakin kaza. kuma haƙiƙa SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI. Lokaci guda Zulaihat ta katse shirun da ya wanzu a tsakaninsu ta hanyar buɗar baki ta ce “ya ke ‘yar uwata Luzaiba ki yi sani cewa ba na zo nan domin na yaƙe ki ba ne kamar yadda ke kike tunani, abin da ya kawo ni kawai shine na janyo hankalin ki izuwa TAFARKIN TSIRA, ki tuba ga Allah SWT ki dawo zuwa musulunci, domin ki samu rabauta a nan duniya da gobe ƙiyama”. Koda jin wannan jawabi daga bakin Zulaihat sai Luzaiba ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta tamkar ba zata daina ba, daga bisani ta turɓune fuska sannan ta dube ta cikin kallo na ƙasƙanci ta ce “ya ke Zulaihat ki yi sani cewa ke ba 'yar uwata ba ce kamar yadda kika furta, ina mai yi miki albishir da cewa ni da maigidana zamu ƙarar da dukkanin waɗanann rafkanannun mayaƙa na k, Kuma nayi miki kisa mafi muni, daga nan kuma nayi shirye-shiryen zuwa birninmu domin karɓar karagar mulkin mahaifinmu”. Koda jin wannan batu daga bakin Luzaiba sai hawayen baƙin ciki suka zubowa daga idanun Zulaihat. Daga bisani ta share hawayen dake kan kuncinta, sannan ta ce “yake ‘yar uwata yanzu saboda abin duniya kin zaɓi mai gidanki a kaina, shin kin manta cewa ni da ke jini ɗaya ne”; Sa’adda Zulaihat yazo dai-dai a zancen ta sai hawaye suka sake kwaranya daga kurmin idanuwanta. Al'amarin da ya sanya jarumi Zamran dake tsaye a gefen ta ya ji ya kamu da matuƙar tausayin ta, kuma ya ji ya tsani Luzaiba da maigidanta sarki Burzam. Kafin Zulaihat ta sake buɗar baki ta furta wani abu, sarki Burzam da Luzaiba sun zare waɗansu kaifafan takubba a damtsensu, suka sakarwa dawakansu linzami suka durfafi inda take suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a FAGEN GUMURZU. Koda ganin hakan sai Zulaihat ta zare takobinta, cikin zafin nama jarumi Zamran ya yi koyi da ita ya zare tashi takobin, ya tari sarki Burzam, ita kuma ta tari ‘yar uwarta suka rugumtsume da azababben yaƙi, mai matuƙar kwarjini, muni da ban tsoro. Gwarazan huɗu suka wanzu suna kaiwa suna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Lokacin da ɓangarorin biyu suka ga shuwagabannin su suna bawa hammata iska, sai kowannensu ya ɗaga makaminshi ya yi ɗauki kan abokin gabar shi, ana haɗuwa aka yi KARON MAZA, in da a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin tawagar biyu suka haɗu da juna aka yamutse da yaƙi dole ne ya ɗimauce, saboda yadda ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, ƙarar karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne. Kafirai na ihu da hargowar banza, musulmi na kabbara da tsarkake Allah (SWT). Lokacin da aka kwance waɗannan zakunan sihiri suka afka cikin dakarun musulunci, sai suka hau su da cizo da yakushi, nan fa jini ya dinga kwaranya yana tsartuwa yana kwaranya a ƙasa. A ɓangaren sarkin yaƙi Bazzaru kuwa, duk inda ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun musulunci na zube ƙasa matattu, waɗansu magashiyan suna kabbara da ƙarfi. A ɓangaren arna kuwa ba ƙaramar ɓarna musulmi suka yi masu ba, domin duk irin matuƙar yawansu ya zamto a banza, musulmi sun zame masu alaƙaƙai kuma ƙadangaren bakin tulu. Abin da kafiran ba su sani ba shine addu’o’in da musulmin ke yi ne ke basu ƙarfi da juriya, tamkar na’ura ce ke sarrafa su, jikkunnan su ba su kasance na jini da tsoka ba. Wohoho! Haƙiƙa yaƙi abun tsoro ne da tashin hankali, wanda bai san shi ba shine yake fatan zuwan shi. A ɓangaren mayan GWARAZAN JIYA kuwa wato Zulaihat da gimbiya Luzaiba, sarki Burzam da barde Zamran kuwa tuni labari ya sha bamban. sai da GWARAZAN JARUMAN suka shafe tsawon sa’a ɗaya suna ɗauki ba daɗi, ba tare ɗayan su ya yiwa abokin gwamin shi koda ƙwarzane ba. Al'amarin da ya fusata su kenan, suka sake zage damtse gami da canja salon faɗan su. Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canja dole ne rawa ma ta canja. Faruwar hakan ke da wuya sai yaƙin ya canja salo. Ana cikin wannan artabu ne sarki Burzam ya kaiwa jarumi Zamran wani wawan sara da nufin tsinke mashi wuya, cikin baƙin zafin nama Zamran ya wurƙila ya zillewa sara, kafin ya mayar da martani Burzam ya kai mashi wani saran, koda ya sanya gatarinshi ya kare saran, sai da ya durƙushe ƙasa da dokinshi, saboda ƙarfin saran, kafin ya yu yunƙuri sarki Burzam ya lafta mashi wani wawan sara a hannu, take inda ya sara ya dare jini ya yi tsartuwa ya zuba a ƙasa, Zamran ya ƙwalla kabbara da ƙarfi, ya sulale ƙasa daga kan dokinshi. Cikin wani irin baƙin zafin nama sarki Burzam ya dako tsalle daga kan dokinshi tamkar an janye shi da ƙugiya, ya cafki wuyan Zamran kafin ya kai ƙasan ya gabza mashi wawan naushi a fuska, saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da Zamran ya yi katantanwa a sama sau uku sannan ya baje a ƙasa magashiyan yana mai kiran sunan Allah (SWT). Kawai sai sarki Burzam ya zare wata takobin daban a damtsenshi ya taka da ƙafafuwanshi har zuwa inda Zamran ke kwance, ya ɗora KAIFIN TAKOBIN akan wuyan shi yana mai bushewa da dariyar mugunta. A ɓangaren su jaruma Zulaihat kuwa sai da suka shafe tsawon sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari suna bawa hammata iska, har ta kai dukkanin makaman yaƙin su sun lale ce, sun koma gwada ‘yar ƙashi suna naushi da bugun juna hannu da ƙafa, ya zamana sun haɗa junansu jini da majina, sun faɗi ƙasa magashiyan, suna fitar da numfashi da ƙyar. Wohoho! Haƙiƙa faɗan gwani da gwani daɗin kallo gare shi. Nan fa filin yaƙin ya ƙara yamutsewa, duk inda mutum ta kai duban shi gawarwakin dakaru ne kwance fulu-fulu cikin jini babu ƙyan gani, dawakai kuwa suka dinga haniniya suna zubar da mahayan su suna nausawa cikin daji. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai sarki Burzam ya yi an soka mashi waɗansu zaratan takubba biyu a gadon bayanshi, saboda kaifin su sai suka fasa ƙirjinshi suka ɓillo ta gaba, cikin ƙarfin zuciya Burzam ya waiga bayanshi domin ya ga wanda ya soke shin, a dai-dai lokacin da jini ya fara kwaranya a ƙirjinshi tamkar an ɓalle kan fanfo, koda waigawar ta shi ai kuwa sai ya yi arba da waɗansu ƙananan yara ‘yan kimanin shekaru sha uku mace da namiji. Nan fa ya ƙura masu idanu ko ƙiftawa ba ya yi, a lokacin da zafafan hawayen baƙin ciki suka fara kwaranya daga idanuwanshi. Kuma ya durƙushe ƙasa bisa gwiwoyinshi yana kakarin mutuwa, kafin shuɗewar daƙiƙa goma ya komai na jikinshi ya sandare ya daina motsi, alamun rai ya yi halin shi. Su dai waɗannan yara da suka kashe sarki Burzam sun kasance ‘ya’yan wani attajiri, sarki Burzam ne ya kashe mahaifinsu ya mayar da mahaifiyarsu farkarshi, fiye da shekaru goma sarki Burzam ya gani a cikin halarar tsafin shi cewa, waɗansu ƙananan yara ne za su zamo ajalinshi, sai dai ya kasa gano inda yaran suke ballantana ya hallaka su. Sa’adda dakarun kafirai suka ga irin mutuwar wulakanci da shugaban su ya yi, sai suka zubar da makamansu suka durƙusa ƙasa bisa gwiwoyinsu tare da yin mubaya'a ga Zulaihat. A dai-dai wannan lokaci ne Zulaihat ta samu nasarar hawa kan ruwan cikin Luzaiba a lokacin da take numfashi da ƙyar! Ta dube ta ta ce “ya ke Luzaiba yanzu kin ga yadda Ubangiji ya nuna ikon shi a wannan yaƙi, shin yanzu ba za ki yi nadamar abin da kika yi ba ki dawo zuwa ga Musulunci, ki tuna zumuntar dake tsakaninmu da kuma soyayyar da abbanmu ke yi mana”. Koda Zulaihat ta zo nan a zancenta sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta. Al’amarin da ya karya zuciyar Luzaiba kenan, ta ji nadama ta kama ta kawai ta buɗi baki ta ce “ina mai bayar da gaskiya ga Ubangijin musulunci”. Koda jin wannan batu cikin matuƙar farin ciki Zulaihat ta rungume ‘yar uwarta a ƙirji, suna masu fashewa da kukan farin ciki. A wannan rana aka ɗunguma izuwa cikin birnin Baitul-Shamas, aka kafa tutar Musulunci aka rushe gumaka, bayan mako guda kuma aka turawa sarki Abu Huzaifa wasikar nasarar yaƙi, don haka yayo na musamman zuwa birnin, ya ɗaura auren jaruma Zulaihat da jarumi Zamran ashe dama sun daɗe suna son juna a ɓoye, gimbiya Luzaiba kuwa ta auri wani jarumi mai suna Khalid bin Sudeis. Ango Zamran ya zamo sabon sarkin birnin Baitul-Shamas, Khalid ibn Sudeis ya zamo wazirinshi. Daga wannan rana farin ciki ya mamaye birnin da nahiyar ba ki ɗaya saboda hasken Musulunci. ALHAMDLILLAH Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071 ƊANƊANO DAGA LITTAFIN KUNDIN AL'AJABI Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 Ƙasaitaccen keken doki ne da aka ƙawata shi da nau'ikan kayan ado na sarauta. Kuma dokin dake janye da keken yakasance ingarmar doki fari sol!. Dokin na janye da keken ne cikin matsanancin gudu na keta sa'a a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin kwarjini daban tsoro, haɗe da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi, duwatsu da ƙoramu. Abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure masa kai shi ne, Duk da irin ƙawatuwa da kayan alatun da keken dokin ke tare da shi amma babu bil'adama a kanshi face wata akwatu ta baƙin karfe guda daya jal ajiye a cikin shi. Sai da ingarmar dokin ya shafe tsawon sa'a ɗaya yana falfala azababban gudu a dajin ya wanzu yana ratsa ƙoramu, duwatsu, sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, gami da ƙwazazzabai babu alamun gajiya a tattare dashi, Babu abin da zai burge mutum face yadda dokin yake gudu cikin gwanin ta da ƙwarewa, Duk da irin duhun daren da ya mamaye dajin tamkar akwai wani bil'adama dake sarrafa shi, Sa'adda yazamana dokin ya shafe tsawon zango biyu yana tafiya sai karfin gudun sa yafara raguwa. Ana Cikin wannan hali ne bisa kuskure wasu saiwar bishiya ya harɗe ƙafafuwan dokin na gaba, Take ya hantsila yayi adungure wannan akwatu dake cikin keken ta faɗi can gefe guda. Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu ashe inda dokin ya faɗi gangare ne wanda a ƙarshen shi wani rami ne mai zurfin gaske, Ai kuwa sai keken dokin ya dunga gangarawa har ya faɗa izuwa ƙarshen ramin. A dai-dai wannan lokaci ne wani mafaraucin ya rugo izuwa wajen sakamakon haniniya gami da kukan dokin ya cika cika dajin baki ɗaya, Ko da isowar shi sai ya kai duban shi inda ramin da keken dokin ya faɗa, Nan take takaici ya turnuƙe shi bisa ganin cewa bai samu nasarar ceto rayuwar keken dokin da mutanen dake kanshi ba. Yana cikin wannan hali ne idanuwanshi suka kai kan wannan akwatin baƙin karfe da ta faɗo daga cikin keken dokin, Cikin matukar farin ciki ya taka da ƙafafuwanshu zuwa wajen da akwatun take ya tsugunna ƙasa ya sanya hannunshu ya buɗe murfin akwatun sa'dda ya yi arba da abin da ke cikin ta sai ya miƙe tsaye zumbur cikin matukar kaɗuwa. Bakomai ne ya firgita shi ba face arba da yayi da wata tsaleliyar jariiriya, Wacce tunda yazo duniya bai taɓa gani ko jin labarin mai tsananin kyawun ta ba. Ita dai jaririyar an lullluɓeta da mayafi na alhariri a gefen ta kuma an ajiye wani kambu na damtse da aka yi shi zallar zinariya da jauhari, Mafaraucin ya ƙurawa jaririyar idanu wacce take kwance ta na sharar barcin bata san abin da ke gudana ba, Abin tambaya anan shi ne daga ina wannan jaririya ta fito? Kuma mene ne dalilin da ya sanya aka sakata a cikin wannan akwatu? Amsar tambayoyin da mafaraucin ya kasa bawa kansa kenan. An ya kuwa badan a tseratar da rayuwar wannan jaririya ba ne yasa aka sakata a cikin akwatin? Koda ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya durƙusa ƙasa a karo na biyu ya sanya hannuwanshi ya rufe murfin akwatun sannan ya cicciɓeta ya ɗora akan kafaɗarshi ya juya ya cigaba da tafiya yana mai kunna kai izuwa cikin dajin, Jim kaɗan da tafiyar shi sai ga waɗansu ZARATAN DAKARU sun iso wajen, Dakarun suna ɗauke da miyagun makamai dangin gatari, Sungumi, Takobi, Al'amudi da takobi, adadin su ya kai dubu da ɗoriya wasu akan dawakai wasu a ƙafa, Sai muzurai suke yi suna dube-dube a dajin tamkar zasu ci babu. Ko da bayyanar su sai suka kama kalle-kalle da dube-dube suna nazarin takun sawayen keken dokin, Kaico Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan yayi arna da mayaƙan dole ne ya firgice. A lokaci guda su ka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak, suka shiga haska takun sawayen keken dokin da fitilar ice tsawon waɗansu daƙiƙu. Daga bisani shugaban dakarun ya dawo zuwa inda dokinshi ke tsaye ya dubi sauran dakarun cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce " Ya ku 'yan uwana dakaru kuyi sani cewa binciken da na gudanar a yanzu ya tabbatar msni da cewa keken dokin da ke ɗauke da jaririyar Hunaisat ya faɗa izuwa cikin wannan rami dake gaban mu, Kenan kanan ya nuna cewa jaririyar bata raye a halin yanzu. Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban sai wani saurayi daga cikin dakarun yayi gyaran murya ya dube shi cikin ladabi ya ce " Ya shugabana shin wata shaida ka ke da ita da ya tabbatar da cewa keken dokin da ya faɗa wannan rami shine ke ɗauke da jaririyar Hunaisat? Kasan fa masu iya magana na cewa "kaɗa Mage ba yankawa ba ne". Ko da jin wannan tambaya daga bakin saurayin sai shugaban dakarun ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa ya shafi gemunshi mai tsawon kamu huɗu tamkar an tufka igiyar ya ce " Ya kai Hamsil ka yi sani cewa ai "Komai gudun kare baya ƙure daji" ina da tabbacin cewa jaririyar Hunaisat bazata taɓa kuɓuta daga tarko na ba, kada ka manta cewa fiye da shekaru sha uku nine ke kula da dawakan da ke ɓangaren gimbiya Hunaisat. Koda jin wannan batu daga bakin shugaban sai dakarun suka ƙaure da shewa da ihun murna , muryoyin su su ka amsa kuwwa izuwa cikin dajin su na masu ɗaga makamansu izuwa sama. Tsawon daƙika goma su na cikin wannan hali sai daga bisani ne suka kaɗa linzamin dawakansu suka koma izuwa cikin dajin. Abin tambaya a nan shi ne mene ne ne dalilin da sanya waɗannan dabaru ke farautar jaririyar? Daga ina keken dokin ya ɗauko jaririyar kuma wane ne ya sanya ta a cikin wannan akwati?. Dalilin faruwar hakan kuwa shine Mu haɗu a babi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. Mansur Usman Sufi 08137237071