Da kyar ta iya mikewa ta soma dafa bango, tana mikewar jini na tsinke mata. Daga nan sai wani duhu ya mamayi ganinta, ganinta ya dauke gaba daya ji ka ke yif! Ta fada a kan Fahimah da ke jan minshari sabida dadin A.C. A firgice ta farka, ta janye Amrah daga kan kafafunta tana salati. Ta mike jiki na rawa ta kunna kwan lantarki. Nan ta ga jini na fita a jikin Amrah, kuma ko motsi ba ta yi. Fahimah saboda gigicewa a guje ta fita dakin Ammi tana kwala mata kira tun daga falo. Hatta Baba Talatu da ke baskwata sai da ta jiyo kiran Ammi da Fahimah ke yi. Babban tsoronta kada a ce ta kashe matar Uwais. Cikin barci Ammi ke jiyo ihun Fahimah yana doso dakinta, don haka a bakin kofa suka ci karo. Fahimah ta hada hannayenta waje guda kasan habarta kamar mai roko. Ta ce, “Ki taimaka Ammi, Amrah za ta mutu a dakina, wallahi ban mata komai ba. Kawai tashi nayi na ganta a kaina jini na zuba. Na shiga uku Ammi…”. Ammi ta ce, “Ke da Allah can shashasha, haihuwa ce”. Ta ture ta ta wuce dakin nata. Daidai lokacin da Baba Talatu ma ta karaso. A tare suka shiga dakin suna ganin halin da Amrah ke ciki suka gane wannan haihuwa ta zo da tangarda. Ammi ta ce da Talatu maza dauko min wayata da mukullin mota”. Talatu da gudu ta juya ta dauko. Ammi da Talatu suka ciccibi Amrah suka yi waje. Ammi na cewa, Fahimah ta dauko jakar da Amrah ta zo da ita gaba daya ba za a rasa kayan jariri ba. Ta biyo su. Asibitin Standard suka wuce don komai dare ba a rasa likita, suna zuwa aka karbe ta da gaggawa. Dubawa ta farko likita ta ce, “Amrah ba za ta iya haihuwa da kanta ba an samu matsala mai girma, sannan babyn a breach yake, abu mai sauki shine CS kawai don su ceceta ko babyn, amma ita ko babyn dole a rasa guda. Sabida tsananin rudewa Ammi kalmar shahada ta ke ja. Fahimah kuwa sai mazari ta ke daga tsaye. Likita ya ce maza mijinta ko mahaifinta su zo su sanya hannu don lokaci ya kure babu wani taimako da za su iya yi mata bayan CS. Talatu ce mai karfin halin ce da Fahimah, “Ba ni wayar Ammi da ke hannunki bayan kin latso min uban dakina”. Haka Fahima ta yi, ita mantawa shaf ta yi da wayar Ammi na hannunta don a gida ta baro tata. Ta lalubo lambar Uwais hannunta na karkarwa ta bai wa Talatu. Bugu daya Uwais ya dauka don yana can kamar mai nakudar shima, yana jiran abin da zai biyo baya, me ya kawo Amrah gidansu har dakin Fahimah cikin dare haka, kuma ina Fahimar ta ke da ta barta ta daukar mata waya tsakar dare? Ya tabbata sha’ani ya lalace kam, da ya ji shawarar mahaifiyarshi tun farko da haka ba ta faru ba. Yanzu da wane yare zai yi wa Amrah bayanin da za ta fahimce shi? Kuma me za ta dauki Fahimah? Ba za ta kara yarda da ita ba duk son da ta ke mata yau zai koma kiyayyah. Talatu na kira yana dagawa, a nitse ta gaya masa halin da ake ciki da bayanin da likita ya yi. Uwais ji ya yi kamar kwarankwatsa ta fado a kansa, ya ji kamar ya yi fiffike ya ganshi a Nijeriya. Babynsa! Gudan jininsa da ya kwallafa wa rai yau ga kuskurensa zai yi sanadinsa. “Ba ni likitar”. Kawai ya ce cikin tashin hankali. Ya gaya mata ba ya kasar, sannan iyayenta ba sa gari, ya amince a yi mata CS din da duk wani taimako da ya dace. Ya kara da cewa, “Likita ki taimake ni kada in rasa kowanne a cikin su. Don dukkansu ina so, and they mean a lot me. Kuma na yi mata laifi ina so in nemi gafarar ta… idan ta mutu a wannan halin bazan taba yafewa kaina ba.....". Gaba daya muryarsa ta karye kamar ba Uwais ba. Bolded and courageous a komai. Likita bata tsaya doguwar magana dashi ba don ta lura ba'a hayyacin sa yake ba, suka shirya Amrah zuwa dakin tiyata. ****** "It’s a baby boy, amma bai zo da rai ba. The mother is still unconscious, za ta dawo hayyacinta in the next two hours in allurar barci (anaesthesia) ta sake ta, sai ku shiga ku ganta". Siririyar nurse din ta fadawa Ammi, a lokaci guda ta mika mata jaririn nannade cikin farin shawul. Ammi hannu da jiki na rawa ta amshe shi ta bude fuskarsa su duka ukun suka zuba masa ido. Uwais sak! Fari sol bai debo komai a jikin Amrah ba. Hatta farcen yaron irin na Uwais ne. Fahimah jin wata irin soyayyar jaririn ta yi, ko don kamanninsa da Uwais, ta kifa kai jikin Ammi tana kuka. Uwais na ta kira babu wadda ta iya amsa wayar sa. Ammi ta ce, Fahimah ta zauna ita da Talatu za su tafi da jaririn maigadi ya kira makwabta a yi masa sutura. Ba su jima da tafiya ba aka gungura Amrah zuwa aminity. Da sauri Fahimah ta bi bayansu suka kwantar da Amraha kan gado suka yi mata duk abin da ya dace sanan suka fita. Fahimah ta ja kujera daidai kan Amrah ta zauna. Tana karanta addu’a tana tofa mata. Ga karin jini ga na ruwa, tana da son haihuwa matuka, musamman da Uwais ya ce zai so ‘ya’yansu ne fiye da son da yake yi wa kansa.... Amma in haka haihuwar ta ke lala - lala ta hakura. Lallai wannan shi ne kafa daya a duniya, kafa daya a lahira. Ta tuno uban jinin da ta ga Amrah na zubarwa, wani matsanancin tsoro ya kara kamata. Tunda dai Allah ya taimake ta ba ta yi cikin ba, to ba za ta kara yarda ta yi abin yin cikin ba. Ta barwa Amrah Uwais su yi ta haihuwa, tarewar ma ta fasa ba za ta yi ba. Zata cigaba da zama da Ammin ta. Wajejen karfe goma na safe Amrah ta bude idonta a hankali. Kafin idanunta su washe a dakin su sauka a kan jinin da ake kara mata. A lokacin ne ta fahimci a kan gadon asibiti ta ke. To me ya kawo ta asibiti ita da ta kwanta a gadon Fahimah za ta yi barci? “Masha Allah, kin tashi Aunty Amrah? Bari in kira likita”. Ta ji muryar Fahimah a gefenta. Muryar da ta tado mata da ainahin dalilin zuwanta asibiti. Da sauri ta kai hannu kan cikinta ta ji wayam! Da azama ta yunkura za ta mike, daidai lokacin da likitan ya shigo, Fahima na biye da shi. Da sauri ya maida ita kwance, ya ce, “Be careful Madam, akwai aiki a jikinki”. Sannan ya tambaye ta, “Are you alright?” Kai kawai ta gyada masa. Ta runtse ido da Fahimah ta zagayo gefen fuskarta, tana tambayar likita ko za a iya ba ta tea ta sha? Doctor ya ce, ta bari sai an jima, Nurse za ta zo ta ba ta da magani. Tunda Amrah ta rufe ido ba ta kara budewa ba. Don ba ta son ganin Fahimah, ba kuma barci ta ke yi ba. Har zuwa lokacin da su Ammi suka dawo. Ammi bata san Amrah ta farka ba ta tsaya tana gaya wa Fahimah har an binne yaron. Allah ya ba su wani mai albarka, Ya bai wa iyayensa dangana. Shi ma Uwais din yana hanya gobe duk da bai gama abin da ya kai shi ba. Wasu dumammun hawaye suka biyo ta gefen idanun Amrah, Dan ta ya koma, duk wannan wahalar da ta ci akan rainon cikin, duk a dalilin bakin cikin Fahimah da Uwais? Ko Uwaisu ne autan maza ta hakura da shi yau, in ba haka ba bakin cikinsa shi zai yi ajalin ta. Ta soma tunanin hanyar da za ta bi ta tsere kafin Uwais ya zo ya tadda ita. To amma da wanne ido za ta koma wa iyayen ta??? Wannan tunanin ya sa Amrah fashewa kuka wiwi a fili. Su ba su san idonta biyu ba, kuma sun dauka kukan na rashin dan ta ne da ta yi. Su basu san abubuwan sun ma zuciyar ta yawa ba. Da wanne zata ji? Ammi ta karasa ta kama hannunta tana ba ta baki. Ta ce, “Ki yi hakuri Amrah, insha Allahu mai ceton mu ne. Ba ki ganshi ba kamar Uwais ya yi khaki. Allah ya yi wa iyayen da suka rasa ‘ya’yansu suna kanana babban tanadi a ranar gobe. Kada ki yi bakin ciki, ki yi addu’ar Allah ya bada rayayye mai albarka, kin ji”. Amrah ko kallon Ammi ba ta yi ba, ta ci gaba da gunza kukanta. A ranta ta ce, duk abin da Uwais da Fahimah ke yi da sanin Ammi tunda ai a gabanta suke, and she is educated enough da za su yi irin wannan danyen aikin ba da saninta ba. Me kuma za ta ce mata yanzu? Ai ta bar mata danta ke nan har abada ta aura wa farkarsa, ko su ci gaba da watsewar su. Gaba daya sun kasa gane kan Amrah, tunda ta farko ta ki ci ta ki sha, sai kuka, sannan ta ki karbar lallashin Ammi. Har dare suna tsaye a kanta suna lallami, amma ko uffan ba ta ce musu ba. Sai da Ammi ta koma ta kira babban likita ta ce ya bincike ta ko da wani abu da ke damunta daban, kada jininta ya hau. Likita ya shigo, ya ce duk su ba shi wuri zai yi magana da Amrah. Ya ja kujera a gabanta ya zauna, ya ce, “Madam, may I know your problem? Na dauka ke musulma ce, kin san mutuwa tana kan kowa babba da yaro? Na dauka za ki yi tawakkali ki yi masa addu’a, ki roki Allah ya sake ba ki wani cikin gaggawa?” Amrah na kuka ta ce, “Doctor ni farin ciki nake da Dan ya koma. Ko bakomai zai dandani irin bakin cikin da ya kunsa min. Tunda gashi nan a dalilin cin amanar da yayi min shima ya rasa abinda ya kallafawa rai. Damuwata yanzu kawai yadda zan je Abuja. Ka taimaka min ka sallame ni a yau, kuma ka ba ni aron wayarka in kira direbana ya zo ya dauke ni”. Doctor ya ce, “Babbar magana. Ba zan iya sallamarki ba sai jibi, a ka’ida in aka yi wa mutum aiki sai bayan kwana uku ake iya sallamarsa shi ma in an tabbatar babu wata matsala da za ta biyo baya. Advisably ki bar ni in yi wa Mamanki bayani cewa kina son tafiya Abujan da zarar an sallame ki, na tabbata za ta fahimta ta kai ki da kanta…”. Da sauri Amrah ta ce, “Doctor ba abin da ya hada ni da su, kuma in ba za ka taimaka min ba wallahi ko a kan iska sai na tafi". Ta ci gaba da rusa kuka. Doctor ya rasa ya zai yi da ita, da ma kuma yana da lambar Uwais da suke magana wadda waccan likitar data karbi Amrah ta bashi da za su yi handing over, sai ya koma ofis ya kira shi, ya yi masa bayanin halin da matarsa ke ciki. Uwais ya rasa inda zai tsoma ransa ya ji sanyi, ga booking dinsa ma an ce ba zai samu ba a goben sai bayan kwana uku, na goben bai yiwuwa saboda hazo. Da kyar ya iya ce da Doctor ya kula sosai kada ya barta ta fita, har zuwa kwana ukun, wato ranar sallamar ta, zai turo matar Yayanta ta tafi da ita, ya tabbata za ta yarda ta bi ta. Daga nan ya kira Jabeer, a yadda Jabeer ya ji muryar Uwais ya tabbata ba lafiya ba. Ya ce, “Jabeer, I donno from where to start, don ko kai ba za ka yi min uzuri ba balle Amrah. Amma wallahi ka yarda da ni ina da niyyar gaya mata ne da zarar na dawo, don in samu ta haihu lafiya. Sai kaddara ta riga fata. Yau ga kuskurena da rashin jin shawarar mahaifiya sun jawo na yi asarar babyna”. Jabeer ya ce, “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel, me ya faru haka Uwais?” Uwais ya share zufar da ke yankowa daga goshinsa, ya kwashe komai ya gaya wa Jabeer, ya kare zancensa da cewa, “I never take it serious, (auren sa da Fahimah), kuma tunda na mallaki Amrah ban kara waiwayar zancen Fahimah ba. Na yi duk iya kokarina a kan Amrah ta fahimce ni ban iya rayuwa babu macen aure, ta dawo B.U.K mu ci gaba da rayuwarmu. Amrah ta ki fahimtata da gangan, ta sa kafa ta yi tafiyarta Malaysia ta bar ni. As a man like me na san za ka fahimci halin da na kasance kuma na san ina da wata matar. Amma wallahi Jabeer ban taba tunanin auren zai je ko’ina ba shi ya sa na dauki lokaci ban gaya wa Amrah ba, sai kuma ga ciki ta samu mai matsaloli, sai na kara jinkirtawa da niyyar zuwa ta sauka. Ban san ya aka yi Amrah ta zo gidanmu ba, har dakin Fahimah, har wayar Fahimah ta je hannunta. Daga nan komai ya lalace wanda I’m sure shi ne sanadin nakudarta. I’m sorry Jabeer, wallahi ban yi da niyya ba, haka Allah ya nufa. Jabeer babyna da na kallafa wa rai ya zo ba rai, sannan Amrah na can ta tubure musu Abuja za ta koma. Bayan already na yi booking ina tafe in three days”. Jabeer ma ransa ya baci sosai, amma sai ya yi hali na dattaku, ya ce, “Ka yi babban kuskure Uwais, kuma magabatanka ma sun yi kuskure tun a wajen neman auren Amrah ya kamata ku gabatar da wannan maganar, in ya so in yin yin, in barin-barin. Amma yanzu ka bata goma daya ba ta gyaru ba. Don ka san Daddy ba wai yana farin ciki da aurenku ba ne don dai ya ga Amrah na so ne ya hakura. Don haka ni ban isa in rike Amrah a gidana ba tare da iyayen mu sun ji zancen nan ba, don Murjanatu ba ta taba haihuwa ba, ba ta san ya za ta yi da Amrah ba. Don haka in an sallame ta zan je in dauke ta a asibitin mu wuce Abuja”. A sautin muryar jabeer Uwais ya tsinkayi bacin rai sosai, don dai yana kokarin dannewa ne. Babban bacin ran Jabeer wai a ce har shi bai gaya wa yana da wata matar bayan Amrah ba? Duk yadda suke da shi, ai zai iya gaya masa ma tun lokacin auren in ya so ya roke shi ya rufa asiri. Wannan itace abota ta hakika. Amma ina? A lokacin idon Uwais ya rufe da son mallakar Amrah anyhow. Don haka yanzu kam yana bayan kowanne hukunci Amrah za ta yanke wa aurenta da Uwais don tana matukar sonsa, kuma ya yi betraying dinta a magana ta gaskiya. Shi ya sa har kullum mota suke kuka da maza a kan rashin amanar soyayya, da gaske ne su maza ba su da tabbas in dai a kan mace ne. Amma why Uwais? Mutumin da ya ke yi wa kallon wanda ya fi kowa son Amrah? (in kina tunanin namiji na da tabbas a kanki to ki daina- Takori). A yadda suka yi sallama da Jabeer a wayar ma duk da yana kokarin dannewa ya fahimci ransa ya baci sosai a matsayinsa na shakikin Amrah. To ina ga iyayenta da ita kanta? Bai dora neman aurensa a bisa tafarki na gaskiya ba tun farko don haka he must try to be a man, ya yi dammarar facing every challenge da zai biyo baya kawai. Duk maganganun da suke yi a kunnen Murjanatu wadda ke zaune a gefen sa. Bayan sun gama ta dubi mijinta sai huci yake yi. Murjanatu akwai ilmi, hankali da kyakkyawan tunani, don haka ta ce da mijinta Jabeer. “Uwais abokinka ne na gaskiya wanda ya kamata a ce cikin kowanne hali ka tsaya tare da shi. Kada ka bi bayan kanwarka ka manta da darajar abokan taka. A halin yanzu he needs your support most. Kada ka manta mahaifyarsa ce ta yi masa umarnin auren yarinyar nan, kuma ita ke rikonta sannan ta ce in bai aure ta ba, Amran ma ba zai aura ba. I’m sure dalilin shi na amincewa kenan. Wato tsoron rasa auren Amrah. Kamar yadda ya ce din ne if you are in his shoe, ya za ka yi? Za ka yi zina ne tunda ita ta ki zama, ko ko za ka tafi ga ajiyayyen halalinka da ke gefe?” Jabeer bai ce mata komai ba, amma yanayin fuskarsa ya nuna sassauci. “Ki tashi mu je mu ga halin da ta ke ciki, ya ce tana asibitin standard”. Murjanatu ta dauko mayafinta ta bi bayansa, domin tuni shi har ya kai waje. Babbar damuwarsa ya san laifin Uwais shi ma sai ya shafe shi a wurin Daddy, tunda dai komai ma shi ne sila. Da tambayar sunan patient wadda aka kawo jiya, ta haihu dan ba rai Jabeer da Murjanatu suka dangana da dakin da su Fahimah suke. Suna tsaye a kan Amrah ita da Ammi, Fahimah rike da kofin shayi mai kauri, Ammi rike da plate din kwai da dafaffiyar hanta da Talatu ta kawo suna ta aikin lallashinta a kan ta ci, Amrah ko idonta ta ki budewa balle ta dube su, abin da ya soma hassala Ammi don dai ita ba ta san laifin da suka yi mata ba, amma Fahimah ta fara shan jinin jikinta. Sallamar Jabeer da matarsa a dakin ya sa Amrah ware dukkan idanunta. Sannan ta yunkura da karfi za ta tashi, Murjanatu ta yi gaggawar rike ta ta maida ta kwance tana fadin, “Oh no Amrah. Ki bari ki samu lafiya, ga ni na zo. Sannu kin ji? And we’re going to Abuja together”. Amrah ta ji hankalinta ya kwanta, sai ajiyar zuciya ta ke yi, ta kuma daina kukan. Abin da ya daure wa Ammi kai, wato su ne ba ta son gani, to me suka yi mata ban da abun arziki? Ko tana zargin su suka kashe dan Uwais da hannun su? Murjanatu ta juya tana gaida Ammi, kallo daya ta yi wa Fahimah ta gane ita ce matar Uwais. Class din yarinyar ya isa. And her black skin is expensive and radiant a cikin mata. Sai ta ji kwarai itama tana taya Amrah kishi da gaske. Kishi da wannan zukekiyar black beauty ai sai jarumar mace mai karfin zuciya, wanda ta tabbata Amrah ba ta daga cikinsu. Har dare Murjanatu na tare da su, ita ta sa Amrah ta karbi shayi ta sha. Abin da ya kara tayar wa Fahimah hankali shi ne, yadda tunda Amrah ta farka ta ki ko da duban inda ta ke. Wannan ya tabbatar mata da kyar in wani bai lalata al’amarin ba (ya riga Uwais gaya wa Amrah) wanda shi ne sanadin nakudarta da wannan fushin da ta ke musu har Ammi. Duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, don haka ta janye jiki daga inda Amrah ta ke. Daga baya ma ganin Murjanatu na nan ta ce da Ammi za ta koma gida ta yi wanka sai dare za ta dawo ta kwana. Ammi ta ce, Murjanatu ta tambayi Amrah me ta ke so a kawo mata da daddare? Amrah ta tsuke baki ta ki cewa komai. Ammi sai da ta kai zuciyarta nesa, amma da ita ma tafiya ta yi niyyar yi tare da Fahimah, amma ta taushi zuciyarta ta zauna. Ita kanta Murjanatu ba ta ji dadin wannan hali da Amrah ke nuna wa uwar mijinta ba. Amma Ammin tana wajen ba ta tashi ba, don haka ba dama ta yi mata fada. Da Murjanatu ta tashi tafiya bayan magriba da Jabeer ya zo daukarta, Amrah tuburewa ta yi ba ta yarda Murjanatu ta tafi ba, sai dai ta kwana da sassafe su wuce Abuja ko Doctor bai sallame ta ba. Kunya kamar ta kashe Murjanatu, don a gaban Ammi Amrah ta fadi maganarta kanta tsaye. Ita ma Ammin tun daga nan ta sha jinin jikinta cewa, abin da ta ke guje wa Uwais tuntuni ya faru. Wani munafikin ya yi masa riga malam masallaci. Sai ba ta ga laifin Amrah ba, domin laifi guda har da rabi Uwais ya yi mata. To amma ita kam babu ruwanta, wanda ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Ba yadda bata yi da shi ba akan ya fada mata tun farko ya ki. Dole Murjanatu ta kwana, Fahimah kuma da ta koma gida ta dauki wayarta a inda Amrah ta yasar da ita, sai ta duba missed calls dinta. A nan ta ga received call na Uwais da sha biyun dare kamar lokacin da yake kiranta kullum don yin midnight call. Ta tuna a inda ta bar wayar, da kuma barci da ya dauke ta da wuri. May be Uwais ya kira, Amrah ta dauka, shi kuma ya yi barambaramarsa da ya saba. Mutumin da in ya soma sakin romantic zance sai ta rasa inda za ta sanya kanta don kunya. “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel”. Fahimah ta fada a fili, ta zauna gefen gado ta dafe kanta. Wannan ne ya sa ta kasa komawa asibitin da daddare. Ta ma kashe wayar don kar Ammi ta kira ta ce me ya sa ba ta dawo ba. Shi ma Uwais yau ba ta so ya kira ta. Kowa ya je ya ji da damuwarsa shi kadai. Ko barci ta kasa, sai kawai ta dasa nafilfili a tsayin daren baki dayansa. Takamaimai ba ta san me ta ke roka ba. Ko me ye bukatarta? Ban da Allah ya kawo daidaiton zukata cikin al’amarin, domin ba za ta so auren Amrah ya mutu a kan nata ba. Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, ko ita aka yi wa haka duk son da ta ke wa Uwais sai ta hukunta shi, balle Amrah da ta dauki dukkan yardar duniya ta ba shi. Ita da ma a philosophy dinta babu sakankancewa a kan cewa namiji nata ne ita kadai. Ta sa a ranta bayan Amrah, Uwais na da damar da zai karo mata biyu, don haka ba ta taba yaudarar kanta ba kamar yadda Amrah ta dauka. To ina batun da ta ke yi mata a baya na cewa ta auri Uwais? Ashe dama duk a baki ne bai je har zuci ba zafin laulayi ne, lol? Ita kam tun daga wancan lokacin ne ta ji ta kara son Amrah, duk da hakan bai hana ta jin kishinta lokaci zuwa lokaci ba. Washegari da safe bayan ta yi sallar asubah da wuri ta shige kitchen ta shirya abin da ta tabbatar Amrah za ta iya ci, da wanda su Ammi za su ci, sannan ta dauko basket din zuwa waje da zummar zuwa bakin titi ta hau adaidaita zuwa asibiti. Tana fitowa harabar gidan motar Ammi na shigowa. Don haka ta ja tunga ta tsaya har Ammi ta yi parking a inda ta ke ajiye motar kullum. Fahimah ta karasa ta karbi hand bag din hannunta suka rankaya zuwa ciki. Tana fadin, “Da ba ki wahalar da kanki ba sun tafi Abuja tun dazu, kuma kin kama kin kashe waya balle in gaya miki. Ni yau na ga abin da ya ishe ni, kishi hauka ne da za ki sabi hanyar Abuja da sabon CS a jikinki?” “Hasashena ya tabbata!” Fahimah ta fada a ranta. Jiki a sanyaye ta maida basket din kitchen ta koma daki. Ta kunna wayarta kenan kiran Uwais ya shigo, da sauri ta sake kashewa don ba ta da courage na cewa komai. Amma sai ga Ammi ta biyo ta da tata wayar har dakin, “Fahimah, don me za ki ki amsa wayar mijinki saboda wata can ta yi fushi da ku? Maza karbi ki yi masa ta’aziyyar rashin da ya yi, ai shi ya ja wa kansa da ya bi maganata tun farko, da yanzu hankalinsa a kwance. Yana bukatar mai lallashin sa, maza karbi wayar nan kamin ki bata min rai”. Fahimah ta karbi wayar. Ammi ta juya ta fita. “Fah-himah, are you there?” Muryar Yaya Uwais, ta karya zuciyar Fahimah ba ta taba jinsa ya yi magana a wanan yanayin ba. A hankali ta ce, “Ya Uwais, I’m sorry… for all the inconveniences, ka zo ka dauke ni mu je mu yo bikon Aunty Amrah”. Murmushi ya yi mai sauti, ya ce, “Ba tafiyarta ce damuwata ba Fahhimah. Yadda na zama silar rasa baby dina. Fahimah I love babies, and I lost one. Ban san kuma yaushe Allah zai sake ba ni wani ba”. “Soon insha Allah…”. In ji Faheemah, sannan ta sassauta murya ta ce, “Ina maka ta’aziyya Ya Uwais, Allah ya sa mai ceton mu ne”. Ya lumshe ido ya ce, “Na gode Fah-himah, amma ya aka yi wayarki ta je hannun ta?” “I don’t actually know. Kawai na farka na ganta a kaina cikin jini”. Ta fada masa duk yadda aka yi suka ga Amrah ta zo ba zato ba tsammani da yadda ta kai ta dakinta don su kwana tare. Uwais ya yi ajiyar zuciya, ya ce Allah ya riga ya tsara za a yi hakan, amma na yi niyyar gaya mata da zarar na dawo. Ya rage nata ta dawo ko ta yi hukuncin duk da ta ga dama”. “A’ah Ya Uwais ba za a yi haka ba, kai ka yi laifi dole ka zage kwanji wajen bada hakuri har sai ta sauko. Ni ba bakuwar zafi ba ce ko guda uku ne ka karo…......". Muryar Uwais wani iri ya ce, "Sabida ke ba kya kishina ko? Ko sabida ba ki sona Fah-himah?” Dariya ta yi, ta ce, “In ka ji So, to daya kenan. So, so, so i love you so much. Ina son ka sau malala gashin tunkiya…...”. Uwais ya ce, “Ina nan tafe jibi in gani practically, ban yarda da wannan malalar ba. Da Ammi za ta yarda ma tare za mu koma in karasa sauran satittikan da suka rage min, ko outside masaukin mu sai in kama gida, don cikin mu babu wanda ya zo da mata”. Fahimah ta ce, “Sai ya Uwais?” “Yeah, Uwais daban yake kamar yadda matarshi Fahhimah ta ke daban a cikin mata”. Murmushi Fahimah ta ke from ear to ear duk wani tension ya barta. Ta dauka yana cikin mummunar damuwa MATAR SO ta daka borkono, sai ta ji sabanin hakan. Sun dade suna hira kamar ba kudi Uwais ke narkarwa ba. Ya ce, akwai kyakkyawan albishir da zan muku ke da Ammi, amma sai na dawo. Now, kiss me a little ko na ji dan sanyi a zuciyata”. Tafukan hannunta ta kai ta rufe fuskarta. “Ya Uwais!” Shi ma ya ce, “Yaya Fahhimah, I LOVE YOU”. Fahimah kamar ta narke sabida yadda kalaman Uwais suka ratsa ta, suka tsirga har cikin ruhinta. Da yana kusa, kuma za ta iya, a wannan lokacin ba ta san wace irin runguma za ta yi masa ba. “Zan ba ka babban kiss, amma sai ka dawo”. Fahimah ta samu kanta da fada ba tare da ta shirya ba, tana mai mamakin kanta. “Are you sure?” “Very sure Ya Uwais, Allah ya kawo ka lafya”. Zuciyar kowannensu wasai suka yi sallama. **** ABUJA A cikin mota a kan hanyarsu ta zuwa Abuja ba irin ban baki da lallashin da Aunty Murjanatu ba ta yi wa Amrah ba, amma Amrah ko sauraronta ba ta yi ba, ta yi rantsuwa ta gama auren Uwais ko da shi ne autan maza. Sai karfe biyu suka isa gidan su Amrah a Apo, Mama sai ganinsu ta yi katsahan, Amrah babu katon ciki, sannan babu jariri. Itada ta kama hanya ta tafi ko kwana biyar ba'ayi ba. Mama ta ce, “Lafiya? Kin haihu ne? Ina dan?” Amrah ta fada jikin Mama tana kuka. Wani irin kuka mai cin rai. Daidai lokacin da Aunty Wasila ta shigo da sallama don ita haka ta ke, kullum kafarta tana gidansu, ba ta zama gidan mijinta sam, da ta taso aiki sai ta zo ta rashe sai dare ta koma. “A’ah Amrah kuma? Ke da ki ka tafi jiya ki ka ce ba za ki haihu wajenmu ba kada mu kashe miki da?” Amrah ta kara sautin kukanta kamar za ta tsaga falon, ba ta ce komai ba. Sai Murjanatu ce ta yi wa Mama bayanin duk abin da ake ciki. Shi kuma Jabeer da ma tun shigowarsu falon Daddy ya wuce don ya same shi su tattauna. Mama da Aunty Wasila kwafa suka yi, Aunty Wasila har da dariya, ji kake kyal-kyal-kyal. Suka ce, “Amrah Lailah matar Uwais Majnoon, how market?” Amrah ta kara kuluwa fiye da wadda ta ke ciki, ta ce, “Duk da hakan dai na ji ina sonshi har gobe ya ya ranki? Ni boye min din da ya yi ne tun farko ya bata min rai. Amma yarinyar ba yau na santa ba, ba ta da matsala sam. I just cannot share my husband with anyone shi ya sa na yanke shawarar hakura da shi gaba daya”. Mama ta ce, “Gantalalliya, a haka za ki kare cikin bacin ran namiji kuwa, wai har yanzu tana son kayanta. To don ubanki tashi ki koma inda ki ka fito, ba za ki kwana min a gida ba”. Murjanatu ta ce, “A yi hakuri Mama, yanzu jego ne a gabanmu. Wanka za'ayi mata a gasa mata jiki don Allah a dama mata kunun kanwa a gasa mata nama da dan ruwa-ruwa”. Ta fada cikin lallashin surukarta. Mama duk da haushin Amrah da ya kusa fasa mata zuciya, haka ta daure ta bi umarnin Murjanatu. A can falon Daddy shi da Jabeer, kasancewar ranar lahadi ce yana gida, Daddy ya ce, “Lafiya na ganku haka hajaran-majaran da tsakar rana?” Jabeer ya ce, “Mun kawo Amrah ne". A fusace Alhaji Umar Dikko ya ce, “Uban me ta dawo ta yi mana? Ban ce kar ta sake ta dawo min gida ba? Ta je can wajen Uwaisun ta haihu, tunda ita ba ta san abin da ya kamata ba? Ana mata gata tana ganin ba a sonta". Jabeer ya ce, “A yi hakuri Daddy, ta haihu yau kwana uku dan ya koma”. Jikin Daddy sai kuma ya yi sanyi, don yana son Amrah sosai duk bacin ran da yake yi a kanta, ai don ya ginata ne. A sanyaye ya ce, “Shi ne kuma ta dawo?” Jabeer ya ce, “Akwai wata maganar bayan wannan’. “Ina ji”. Ya fada a kagare. “Eh to Daddy, Uwais ya yi wa Amrah laifi, wanda ya dace ku sani. Ashe tare aka daura auren Amrah da na wata ‘yar uwarsa a lokaci daya mu ba mu sani ba. Sai yanzu Amrah ta gane. And he confessed to me. But please Daddy take it easy na san Uwais is a brave husband zai iya zama dasu su duka kuma yana da halin da zai rike su, kuma daga yadda na fahimta mahaifiyarsa ce ta tursasa shi ya auri waccan din. Na tabbata zai kasance mai adalci a tsakaninsu". Alhaji Umar Dikko bai san sanda ya kwada wa Jabeer ashariya ba, har yana zaburowa daga cikin kujerar sa, ya ce, “kun ci kaza-kazan ku kai da Uwaisun naka ku raba. Ya rike adalcinsa, ni ma in rike ‘ya ta. Ni za a raina wa hankali? Nan wannan Balaraben kawun nasa kamar mutumin arziki da ya zo nema masa auren me ya sa bai gaya min gaskiya ba? Nawa Amrah ta ke da za a hada ta da kishiya ko ashirin fa ba ta kai ba, uwarta sai da ta shekara ashirin tare da ni na yi mata kishiya, balle a yi wa tawa ranar nata auren. Da ma auren ba wai ya gamshe ni ba ne. Na ga amrah na so ne, shiyasa na hakura aka yi. Amma ya yi da Umar Dikko dan Adamawa”. Ya fiddo wayarsa a take ya kira Uwais amma ba ta shiga, ya yi ya yi ya kasa samunsa. Sai ya juya ga Jabeer, “Ba ni shi almuri a lambar da ku ke magana”. Jabeer ya soma bada hakuri, wata tsawa da ya daka masa ba shiri ya latso Uwais ya mika masa. Uwais ya dauka Jabeer ne, don haka with much respect irin na wanda ya san ya yi laifi ya amsa. Sai muryar Babansu ya ji yana magana a matukar hasale. “Kana magana da Umar Dikko Baban Amrah. Ina mai gargadinka da kada ka sake ka tako min gida, ka rubuta takardar sakin ‘yata ka ba wa Jabeer ya kawo min, ka ji na gaya maka. In ba haka ba kuwa kotu ce za ta raba ni da kai, na rantse daga nan har kotun kolin Najeriya”. Ya kashe wayarsa ba tare da ya saurari Uwais ba, shima da ma bai da abin cewa, amma a fili ya sauke wayar sa, ya ce, “Me ya yi zafi???” Don so yana son Amrah har gobe, don she’s his first love. Wadda ya fara mallaka wa ragamar zuciyarsa ya ba ta dukkan so da kauna. Amma duk abun mutuncin da zai hada da cin zarafi, to fa Uwais ba ya daukarsa. Ya yanke shawarar rabuwa da Amrah cikin wani hali na kaka-ni-kayi. Kafin Alh. Dikko ya kai ga taba mutuncin sa. Ya gama gane iyayen Amrah ba su son aurensu kaddara da rabo ne kawai ya kaddara auren. Ita ma Amran fama yake da ita a kan karan-kanta don ba ta dauke shi a bakin komai ba. Hakkokinsa na aure kuwa a gantale suke yawo. Ammi ta yi gaskiya da ta ce, kyal-kyal banza ya daina dibanka. Halin mutum shi ne yake sa wa a so shi ba nasaba ko zubin halitta ba. Amrah ga nasaba ga zubin halitta, amma ta rasa iyaye masu dattaku, nasaba da asali ba ta yi amfani ba anan. ‘FAH-HIMAH!’. Sunanta ya fado a ransa yana daga kwance. Ya wani irin lumshe idanunsa. “Ita ko kara ya saka ya ce kada ta tsallaka ba za ta ko doshi hanyar ba. Ga iya soyayya in stylish. Komai cikin class da sanyin rai hadi da girmamawa. Ba ta da wayewa kamar Amrah, amma ta fi daidai da rayuwarsa. Tunda kuwa idan ya yi umarni za a bi shi, idan ya yi hukunci shi ne abin bi. Me kuma yake nema a diya mace wanda bai samu a Fah-himah ba? Ya yarda Fahimah kyautar mahaifiya ce, kuma kyautar Allah a gare shi. Amrah kuma iznah ce kuma jarrabi a gare shi, duk son da yake mata da ita ma wanda ta ke masa rabuwarsu ita ce mafi alkhairi, domin zukata sun riga sun baci, ko an koma za a yi ta ganin juna da tsohon tabo ne. Sannan upbringing na gidan su Amrah bai yi daidai da wanda yake fata wa ‘ya’yansa ba. Fahimah ita ce daidai da shi, daidai da komai nasa. Sun samu tarbiyyah iri daya, raino da upbringing iri daya, wanda yake fatan ‘ya’yansa ma su taso a cikinsa…... A bisa wadannan dalilan da ma wasu da dama, Uwais ya yanke shawarar rubuta wa Amrah saki ba tare da ya yi shawara da kowa ba, daga Ammi har Fahimah don ya san cikinsu babu wadda za ta goyi bayan haka. Bai baro Switzerland ba sai da rubutacciyar takardar sakin Amrah a cikin takardunsa. **** Yau Uwais zai sauka a Kanon Dabo, don haka Ammi, Fahimah da Talatu kowacce tana tsaye a kan kafafunta tun safe. Yau kwanaki uku ke nan Ammi ba ta komai sai gyaran Fahimah da kayan mata masu inganci wanda a baya ba ta samu damar hakan ba. Musamman ta yi wa Hajiya Asabe waya, ta ce ta kawo gudunmawa, gobe ‘yarta za ta tare. Hajiya Asabe a ranar ta zo da babban shirinta har da dafaffiyar kazarta cikin romon maganinsu na Sokotawan usli. Tun jiya Ammi ke ciyar da Fahimah nau’i-nau’in abin da zai kara ni’imtata, ya bambanta da sauran mata a wurin Uwais ko ya daina yo mata kwashe-kwashen ‘ya’yan masu kudi (ta bakinta), wadanda ba su san mutunci ba. Fahimah ba ta san amfanin abubuwan da Ammi ke ta dirka mata ba, amma tunda dadi gare su a baki ba ta da matsala da su. Sai a daren ranar ana i gobe zai dawo ne da ta shiga toilet don yin wanka kafin ta kwanta, ta ji jikinta gaba daya ya sauya, tafi-tafi ta ji ba wanda ta ke son bude ido ta gani sai Uwais domin gaba daya Ammi da Hajiya Asabe sun rikita hormones dinta. Don haka tana fitowa daga wanka yau tun kafin lokacin hirarsu ya yi ita ta kira shi da kanta, Uwais na dauka ya ce, “Anything special for Uwais?” Ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, ta ce, “Ya Uwais, yaushe za ka dawo ne?” “Gaya min tukunna, mene ne damuwar?” Nan Fahimah ta hau kame-kame, “Ba wani abu fa Uwaisu- Uwaisunmu ni da yayata Amrah… I just want to see you, it is almost 70days ban sanya ka a idanuna”. Uwais ya ce, “Kin ma fadi gaskiya za ki yi bayani dalla-dallah in na iso domin Fahimah na tara da yawa.... only Fahimah can treat my unnamed illness”. Fahimah ta kai tafukanta ta rufe fuska tamkar Uwais yana ganinta. Da sauri ta kashe wayarta bayan ta ce, “Ya Uwais I’m not a doctor”. Ba ta karasa jin me yake cewa ba ta kashe sabida yadda muryarsa ta saukar mata da wata irin kasala. Sallamarsu ta daren jiya ke nan. Kafin su gama aikin abinci ita da Talatu, Ammi ta yi kiranta. Tana zuwa dakinta ta ce, “Bar aikin nan wa Talatu, ki zo ki yi wanka da ruwan turaren nan, in kin fito ki zo ki yi tsugunno a kan wannan turaren, sannan ki saka kayanki”. Fahimah ta bi umarnin Ammi. Da ta gama ita da kanta sunsuna kanta ta hau yi sabida dadin kamshin da jikinta ke mata. Ta rasa ina Ammi ta samo wadannan mayatattun traditional turarukan. Fahimah ta shirya cikin wani pink voyel wanda aka yi wa aikin dutse mai matukar kyau da tsari, babbar riga ce Senegales, Ammi ta ce ita za ta je ta dauko Uwais daga airport anjima, ita ba ta jin dadi, ba za ta iya tuki ba. Duk da hannunta ba wai ya fada da tukin ba ne, wani zubin Ammi tana ba ta sai ta makala mata learner. A shagwabe Fahimah ta ce, “Ammi gaskiya ni ba zan iya zuwa dauko Yaya Uwais ba, wallahi Ammi kunya nake ji”. Ammi ta yi banza da ita ta ci gaba da shan shayinta, daga bisani ta ce, “To a barshi a can, kada a dauko shin, asarar wa? In don ta Safeeyyah-Basudaniyyah ne tana da ‘yarta, wata ce za ta yi asarar miji”. Dariya fahimah ta yi don in Ammi ta so raha kamar kakarta ta ke komawa. Ta dade a gaban madubi (dressing mirrow) tana kalmasa daurin kallabi, ta yi ta kwance ta sake daurawa, ta rasa wanne za ta bar wa Ya Uwais ya gani ya san cewa kwalliyar yau musamman don shi aka yi. Sai da Ammi ta kwala mata kira cewa lokaci ya kure, sannan ta hakura ta fita, bayan ta feshe jikinta da turaren oud midnight ta cakuda da (cerruti) ta yafa yalwataccen gyalen da ya shiga lightly da kayan jikinta, sannan ta fito. “Na fito Ammi sai mun dawo”. “Sai ki hanzarta, it’s almost past 8 now”. Fahimah tuki ta ke a hankali ba ta gudu, sannan ba ta hawa tsakiyar titi da gani dai za ka san ‘yar koyo ce. Tun daga ‘Yankaba har airport sabida lattin da ta yi tuni jirgin su Uwais ya yi landing suna can suna kokarin fitar da kayayyakinsu. Ta tsaya daga can gefe, idanunta a kan kofar fitowarsu, yadda duk mai fitowa sai ta ga fuskarsa. Ba ta yi tsayuwar mintuna ashirin ba ta hango shi yana tahowa sabe da jakarsa. Ya maka bakin glass (GUCCI) a idanunsa. Ba don ta yi masa farin sani ba, sama da shekaru sha takwas da ko kusa ba za ta gane shi ba. Domin kyawun da ilhamar sun ninka na baya, kasar Switzerland ga dukkan alamu ta gama karbarsa. Farar fatar nan ta yi luf! Sassalkar gashi ya kwanta a gefe da gefen fuskar wanda a baya ba ya barinsa bai aske ba. Sai ya koma Balarabensa sak da sirkin rayuwar kasar sanyi. Ta gabanta ya gifta ba tare da ya gane ta ba. Sai kawai ta bi shi a baya. Har suka fita daga reception. Ya duba agogon (swatch - blustery) da ke daure a damtsen hannunsa yana kallon hanyar da jama’a ke bi. Kamar daga sama ya ji muryar Fahimah a bayansa. “Maraba, lale, Ya Uwais! Na kara baki ko akan nawa, shi ya sa ba ka gane ni ba?” Da sauri ya juyo cikin wani irin yanayi, “Fah-himah, ke ce da kanki ki ka zo daukana? Wow! Lucky me’. Ya sa hanun damansa ya janyo ta barin damansa, daya hannun rike da bakar jakarsa. Kunya ta kama Fahimah, ta soma kokarin zamewa don ga mutane nan birjik suna wucewa, wasu suna shigowa. Ya ki ba ta damar hakan, domin kuwa ya rike ta gam-gam, suka zama kamar madara da bombita (black & white) suna taku tamkar ba su so, zuwa inda ta ajiye motar Ammi. Ya bude booth ya sanya jakar hannunsa, sannan ya ce, “Ba ni makullin, ban shirya mutuwa yanzu ba da zan hau tukin ki. Ban dauki bakaken ‘ya’yana ba masu yi min addu’a? Ammi wane ganganci ya sa ta ba ki mota? Anyway, ni ta taimake ni cikin dimbin alfarmominta da ba sa karewa a gare ni”. Ya karbi mukullin daga hannun Fahimah, ya bude mata gidan gaba ta fara shiga, sannan ya zagaya ya shiga ya zauna. Yadda yake treating dinta like a queen wajen shiga motar kadai abun ka tsaya ka kalla ne. Maimakon ta ga sun dauki hanyar ‘Yankaba sai ta ga Uwais ya karkata kan motar ya dauki hanyar Sultan Road. Suna tafe a motar yana satar kallonta yana fadin, “Fah-himah kin kara yin baki, amma kin kara yin fresh, in ji dai ba aikin wahala ki ke yi ba? Kodayake ko zirga-zirgar makaranta cikin ranar kasar Nigeria ya isa ya sa dalibi duhu”. Fahimah ta ce, “Umh, ina muka nufa ne Ya Uwais?” Ya ce, “Inda ya kamata masoya kuma ma’aurata su samu privacy, kafin mu je ana kulle min mata ana saka min ka’idodi”. Fahimah ta gintse fuska ta ce, “Da wa ka ke kenan? Ammin?” Ya ce, “Akwai mai rike min mata ne bayan ita da zan kyale shi yana abin da ya ga dama idan ba ita ba?” Fahimah ta marairaice fuska tace, “Ni dai babu ruwana Ya Uwais, mu wuce gida don Allah. Ammi na can na jira, ta tanadar maka abinci, in ta ga mun dade me za mu ce mata?” Uwais ya wani irin juyo ya dube ta yana shigar da sexy eyes dinsa can ciki, ya ce, “Akwai abincin da ya kai black wife dina dadi ne? Ki bar ni in mori kuruciyata kafin furfura ta zo ‘ya’ya su cika gida su hana ni sakewa”. Ya karasa fada ta hanyar sanya hannun damansa ya rungumo ta gaba daya, saura kadan sitiyarin motar ya kufce masa. Fahimah ta zaro ido tana fadin. “Ya Uwais kada ka zubar da mu ba mu ajiye wa Ammi ‘ya’yan da ta ke buri ba”. Maganar Fahimah ba karamin dadi ta yi wa Uwais ba. Ya kara kankame ta da hannu guda yana tuki da dayan cikin gwaninta har suka zo gidan sa. Maigadi yana nan don Uwais ba ya wasa da hakkinsa da extra ihsani. Suna zuwa ya zo da gudu ya bude musu yana ta faman sannu da zuwa wa Uwais, Fahimah ta yi gingirin a cikin mota ta ki ko motsi bayan Uwais ya kashe motar ya bude mata kofa. “Fito mana my sweet 16? Ko sai an ja min ajin ne yadda aka saba? Kiyi a hankali kada ya tsinke don na kusa hango ta uku” Fahimah ta tsuke baki ta tattare gira ta ce, “Ya Uwais! Ba zan shigar wa Amrah gida don ba ta nan ba, Ammi ta ce kowa da gidanta, ta ya ya za ka kawo ni gidanta?” Uwais ya kankance ido cikin mamaki. “Gidanta ko gidana? Nawa muka hada ni da ita muka sayi gidan? Tun muna shaidar juna ki fito, ko ki ga abun mamaki a cikin motar nan”. Amon muryarsa kadai Fahimah ta ji ta gane asalin Uwais dinta ne rigimamme, mara karbar uzuri kuma mara ragowa ta wannan bangaren. He will go far beyond abin da ya ce din in ta sake ta ki bin umarninsa, to kuwa maigadi zai sha kallo daga inda yake zaune. Motar Ammi farin gilashi kal gare ta. Kafa a mace ta zuro ta kasa ta sauko tana turo baki tana kunkuni, “Haka kawai daga zuwanka sai rigima? Ba za ka bari mu gama gaisawa ba?” Uwais ya sanya mukulli yana bude falon gidansa, ya ce. “Akwai gaisuwar da ta fi wannan ma’ana ne?” Ya karasa fadi ta hanyar janyo ta cikin falon da wata irin azama. Kamar yadda ta yi tsammani farkon love making din Uwais hot and deep kisses ne a kullum, amma na yau ya fi na kullum domin a urunce yake sumabatarta a ko’ina, kusfa-kusfa yana yi yana kiran sunanta. Abin har sai da ya koma ba ta tsoro, domin ba ta taba ganinsa a cikin kwatankwacin irin wannan bukatuwar ba. Tamkar bai taba kusantarta ba sai yau… ya ba ta dukkan soyayyarsa, ya ba ta dukkan amanarsa da sirrikansa wanda daga ita sai Ubangijinta sai shi suka sani. Wani hidden side ne na Uwais da ko Amrah ba ta taba gani ba don ba ya jin tsananin urge din da yake ji akan Amrah kamar a kan Fahimah.... wadda ta zo cikin takaitaccen lokaci ta gigita duniyarsa, ta canza ta, ta fahimtar da shi a baya ba soyayya yake ba, sha’awa ce ta kyawun halitta. Duk da haka har gobe yana son Amrah, amma yana ganin rabuwar tasu ita ce mafi alkhairi a gare su baki daya. He will miss Amrah, amma yana da yakinin yanzu zai iya rayuwa ko babu ita. Infatuation dinsa a kanta kullum kara raguwa yake yi, anya haka Ammi ta barshi? Wane irin sirri ne haka tattare da Fahimarta? Uwais ya kasa shiru, a bisa doguwar kujerar falonshi suke yana kanannade jikin Fahimah domin ta yi rantsuwa ba za ta hau gadon Amrah ba, dakinsa ma ba za ta shiga ba tunda kuwa Ammi ta raba tuntuni, duk wani hali na Ammi na tsayuwa a kan magana daya ya lura Fahimah ta dauke shi tsaf. Don haka ne ya sa shi ma ya hakura ya kyale ta suka sha soyayyarsu anan falon shi kamar babu gobe… a karshe Uwais bai yi mamaki ba da ya ji damshi a idanunsa, ‘Hawaye yake yi ba tare da ya sani ba'. Fahimah ko a aljannah yana fatan a bar masa ita kadai a matsayin hurul eeninsa. Ya yafe 'yammatan aljannah. “Ki yafe min Fahimah, hakika na yi kuskure a baya wanda yake hunting dina har gobe. Da zan iya da na maida bara-bana, na gyara all those inconveniences da na wanzar a tsakaninmu. Dana hadiye kalamai na na baya marasa dadi akan ki. Watakila har in koma ga Ubangijina ba zan daina nadamar abin da na yi miki a baya ba. Ni dai na san a halin yanzu hukunta ni Ubangiji ke yi da hakkin ki, soyayyar ki nema ta ke ta kashe ni…”. Fahimah ta kai tausasan yatsunta ta toshe masa bakitana girgiza kai, cikin wata irin tattausar murya ta ke magana. “Tashi mu tafi wajen Ammi haka Ya Uwais, ko ta ganka ta ji dadi a ranta itama. Na ga Uwais after 70days, na kasance cikin alfarmar Uwais after 70days ....in a way and manner da na tabbata wata diya mace ‘yar uwata ba ta taba samu ba. Idan na rike Uwais a raina bayan duka wannan ni’imar da Allah ya yi min ta mallaka min shi matsayin mijina uban 'ya'ya na, na zama mara godiyar Ubangiji. Besides, an ce so hana ganin laifi Ya Uwais, ni fa ban taba jin haushinka ba, karewa ma komai ka ke yi burge ni ka ke yi. Rana daya ce na ji haushinka a rayuwata, ranar nan a Sudan…”. Da sauri shi ma ya toshe mata baki yana girgiza kai, "Kada ki tono abin da ya riga ya wuce, domin na tabbata alhakin wannan ranar ba nawa ba ne, naki ne. And i sincerely repented, so ni da ke duka masu laifi ne kuma tare za mu ke istigfari”. Let’s go for another ......…” Ya rada mata sauran maganar cikin kunnuwanta. “Umh…” Fahimah ta iya cewa domin dadin bakin Uwais in yana son abin da yake so yawa gare shi, ba ta da ikon musantawa don bai ba ta damar hakan ba ma. Ammi ba ta gansu ba sai karfe sha daya na dare. Fahimah sai baya-baya ta ke yi daga bayan Uwais da ganin ta ka ga mara gaskiya. Shi ko Uwais ko a jikinsa, karasawa ya yi da sassarfa ya rungume Ammi ya sumbaci goshinta. Da wannan damar Fahimah ta yi amfani ta gudu dakinta, ta barsu suna tasu soyayyar ta da da mahaifi. Har wata ajiyar zuciya ce ta kwace mata da ta ganta a dakinta. Ba tare da ta karbi query daga Ammi ba. Ammi kuwa ba ta bi ta kan wannan ba, farin cikin ganin Uwais ya ishe ta. Sun gaisa sun sake gaisawa har da musabaha irin ta larabawa. Ta ce, “Uwais kamar ba kai ba, Switzerland ta amshe ka, ina fatan an yi nasarar duk abin da aka je nema?” Uwais ya ce, “Nasara kam an same ta Ammi alhamdu lillah, ga sabon albishir da nake son yi muku, World Bank da muka je yin course dasu sun ba ni aiki tare da su a yanzu haka, na bar GT idan na dawo. Yanzun ban karasa ba saura sati 3 mu gama gabadaya, na ga cewa ya zama dole in zo in saita al’amuran gidana”. Ammi ta ce, “Ina yi maka ta’aziyya Uwais, Allah ya sanyaya, Allah ya ba mu rayayye. Sannan sai ka kai zuciya nesa ka yi hakuri da Amrah, don kuwa laifi kan laifi ka yi mata. Don haka ka jure duk abin da za ka gani ko za ka ji daga gare ta ko iyayenta, tunda kai ne mai laifi”. Uwais ya yi murmushi kawai ya mike, bai gaya wa Ammi abin da Alhaji Umar Dikko ya ce ba, na cewa in bai sako masa Amrah ba zai kai shi kotun koli. Da kuma hukuncin da zuciya ta kwashe shi ya yanke tun a lokacin ta sakin Ammi, yanzu haka takardar tana cikin kayansa, jira yake zuwa jibi in ya kara hutawa ya runtse ido ya kai wa Jabeer. Yana addu’ar Allah ya sa kada rabuwarshi da Amrah ta yanke kyakkyawar alakar da ke tsakaninshi da Jabeer Dikko. Wanka ya sake yi sannan ya sa farar shirt (Hilfiger) da wandon jeans dark blue ya fito falon jaye da akwatuna guda biyu. Ya samu Ammi tana marking takardun dalibanta da medical glass a idanunta. Ta daga kyawawan idanunta ta dube shi tana murmushi. “Sai ina kuma? Na ganka ka dau wanka ka janyo akwatuna? Ko bikon za a tafi cikin daren nan?” Murmushi Uwais ya yi ya zauna a gefenta yana bude akwatunan, ya ce, “Ammi bikon lafiya? Laifin me na yi da zan je biko? Na dauka bayan Amrah da Fahimah ina da damar kara guda biyu ba tare da na yi wa Ubangijina laifi ba?” Ammi ta ce, “Haka ne, amma a al’adance ka yi laifi ba a addinance ba. Ni dai ban yi wa kowa cikinku laifi ba daga kai har Amrah domin kuwa auren Fahimah na sa aka fara daurawa, ban kuma ce wani cikinku ya boye zancen ba, don haka can ta matse muku kai da Amrahn. Amma ina so ka yi hakuri ka dauki girma ka amsa laifinka, sannan ka bada hakuri ta dawo dakinta. Kowa ta zauna a gidanta, ban yarda da hada muhalli ba”. Uwais bai ce komai ba, ya rika fidda tsala-tsalan atamfofi, shaddodi da lesuka yana tulewa a gaban Ammi, ya ce, “Ammi ga tsarabarku. Sai ki zaba wa Fahhimah wanda zai dace da ita, I don’t know her favourite colours yet, kuma ban yi azancin tambayarta ba”. Ammi farin cikinta ya fi gaban misali, “Allah ya albarkaci rayuwa Uwais. Amma ni tsohuwa me zan yi da wadannan kayan gayun? Na bar wa Fahimah bakidaya tunda tarewa za ta yi, ta je ta yi ta yi maka kwalliya da su’. Murmushi ya yi ta sake cewa, “Ina na Amrah?” Kamar ya ce mata, “She’s no longer Mrs Shagari now”. Ya tuno halin Ammi na dattaku ba za ta bar shi ya bada takardar nan ba ko da za su kai shi kotun. “Zan kai mata jibi in za ni, don gobe tun safe har dare in na fita ba zan dawo ba, zan maida hankali a kammala komai na gidan Fahhimah ta tare jibi, don tare za mu koma Switzerland tunda sun yi hutu, wata daya ne na gama gaba daya don a reshensu na Najeriya za'a ajiye mu. Kuma a garin Abuja ne, don haka zan nema wa Fahimah transfer zuwa (BAZE) tunda ta gama year 1”. Ammi ta ce, “Hakan shi ne daidai, ni bana bayan miji na wani gari matarsa tana wani saboda kananan dalilai. Duk abin da zai zama dole ba a barshi a nemi alternative a zauna tare a nemi lahira. Tunda duk wani buri na duniya an gama samunshi, ilmi, career da aure na hakikah. Yanzu sai shirin tarbar abokai da kawayen Ammi. Sannan Uwais na aika takardar murabus daga aiki, idan kun dawo daga Switzerland kun nabba’a a permanent sabon muhallinku, ni kuma zan koma SUDAN gaba daya, a can zan karasa rayuwata. In kun haifa ku kai min Khartoum zan rike muku”. A firgice Uwais ya ce, “Kada ki yi mana haka Ammi, Fahimah ba ta da kowa a kasar nan sai ke, ni ma ba ni da kowa sai ke Ammi, we need you behind us, burina shi ne in mun koma Abujan ki dawo gidanmu ki zauna tare da mu Ammi”. Ammi ta shafo lallausar sumar kansa, ta ce, “No Uwais, ku yi hakuri ba zan bi ku ba, I’m going back to Khartoum. Dukkanku kun kai munzalin da za ku tsaya da kafafunku ku tara iyali ku yi musu tarbiyya irin wadda ku ka samu. Ku yi hakuri ina Sudan ina Najeriya tunda kullum akwai jirage masu zuwa? Sannan ga waya, ko tari ku ka yi zan jiyo ku ta cikin waya”. Ammi ba ta san yaushe Fahimah ta fito ba, ta kuma tsinkayi karshen maganganunta na komawa Sudan. Ai sai ta dora hannuwa biyu a ka ta saka kuka wiwi. Ta fada jikin Ammi tana ta yi, Ammi na lallashinta tana fadin, “Ai da saran lokaci ba gobe ba zan tafi ba, na ce sai kun nabba’a a waje guda tukunna”. Fahimah ta ce, “Ammi lallai sai na amsa sunan marainiyar da gaske? Idan ina ganinki kullum manta ko ni wace ce nake, idan ki ka tafi ki ka bar mu zan tabbata marainiya, rayuwata ba za ta taba zama cikakka kuma mai dadi ba kamar da”. Ammi Safeeyyah na murmushi, ta ce, ‘Bayan ga ki ga Uwaisun naki? Uwaisu sarkin soyayya, baban soyayyah?” Kunya sosai Fahimah ta ji, ta sunne kanta a jikin Ammi tana cewa, “Kai Ammi". Uwais waya yake amsawa don haka bai san me suke cewa ba”. Ammi ta ce ta kwashe kayan nan duka ta tafi da su dakinta tsarabarta ne in ji Uwais. Fahimah ta ce, “Ammi ai ban ga naki ba”. Ammi ta ce, “Na tsufa da lesussuka Fahimah, don haka na bar miki”. Ta sanya hannu ta dauki atamfa Vlisco guda biyu ta aje a gefe, ta ce, “Ga shi na dau wannan Allah ya yi muku albarka”. “Ammi zan je na kwanta. Na gaji sosai”. Ammi ta ce, “Fahimah kin gyara misni dakin in ce ko?” “Na gyara Ammi, har maganin sauro na fesa kada sauro ya ciji dan kasar sanyi daga dawowarsa”. Dariya Uwais ya yi ya wuce yana kada kai, ya ce, “Kin ci bashi kuma za ki biya”. Ammi ta ce, “Kayya da ba ki fesa ba, da kin barshi ya gane cewa ya dawo kasar haihuwarsa, kowa ya bar gida ai gida ya bar shi”. Fahima tana dariya ta ce, “Kai Ammi”. Ya wuce ya barsu suna ta barkwancinsu kamar jika da kaka. Da wuri ya kwanta don da gaske yake ya gajin. Da asubah da ya dawo sallah daga masallacn kusa da su ya ce, bari ya tada Fahimah ta yi sallah. Don wasu lokutan tana da nauyin barci. Ilai kuwa ya same ta ta yi dai-dai tana barci da wata ‘yar kyakkyawar nighty a jikinta wadda ita da babu duk daya. Uwais ya runtse ido a hankali amma sai ya ce bari ya mata mugunta tunda ta gota lokacin sallah. Toilet ya je ya debo ruwa a kofi mai sanyi da shi ya zo ya yayyafa mata. Ai kuwa ba shiri ta mike a razane. Ganin shi ne ta shagwargwabe fuska, “Kai Yaya Uwais, wannan ai mugunta ce”. Ya ce, “Yanzu wannan barcin da ki ka ware minshari kina yi kin yi sallah ne?” Da sauri ta mike tana fadin, “Ya salam”. Ta yi toilet, shi kuma ya fita zuwa dakin Ammi. Bisa sujjadah ya same ta tana lazimi, ta jima da idar da sallah. Ta ce, “Uwais har ka dawo masjid?” Ya ce, “Na dwo Ammi sabahul khair”. Suka yi gaisuwa cikin harshen larabci tana fadin, “Bari in je in tashi Fahimah ban ganta ta shigo ba”. “Na tashe ta yanzu tana sallah. Ammi da na yi breakfast zan tafi can UDB (inda yake ginin Fahimah) in tsaya a kan ma’aikatan nan sai komai ya kammala. Sannan Ammi na tura kudi a wayarki da za a yi mata kayan daki, duk da ba zama za mu yi sosai ba a sayi komai ya dace a zuba, don duk sanda muka zo Kano a nan za mu zauna. Sai maganar komawarki Sudan, don Allah Ammi ki barta”. Ammi ta girgiza kai zuciyarta cike da jin dadin abin da ya yi kuma yake kan yi a kan Fahimah, mai nuna a karshe ya gama maraba da ita cikin rayuwarsa, ya ba ta matsayi mai girma kamar ko ma fiye da na Amrah. Don tun saukarsa ba ta ji sunan Amrah a bakinsa ba, Fahhimah… Fahhimah dai kamar shi ya rada mata sunan. "Kada ku bata ranku a banza, kai ma ka san bana magana biyu, Sudan na koma ta na gama insha Allahu. Fahimah na godiyar kayan daki daga Yayanta, wannan ya nuna min Uwais ko babu raina za ka rike min Fahimah da amana. Kuma da ma ko ba kai Fahimah ta aura ba hakkin kayan dakinta yana wuyanka. Sai ka yi amai ka lashe abinka”. Ta karasa cikin zolaya. Cikin murmushi Uwais ya dukar da kai ya ce, “Ammi for the first time ina bada hakurin duk abin da na yi a baya cikin ajizanci irin na dan Adam. Ammi kin ce watarana zan zo in gode miki ba ki yi karya ba, yau ga ni gurfane a gabanki ina miko kwandon godiya ta. Kin ce da kaina zan zo in gaya miki wace ce Fahimah, kuwa ba ki yi karya ba. She’s a darling (ita din abar so ce, kuma sai mai tsananin rabo zai yi sa’ar samunta a matsayin matar sa. Sai namijin da Allah ke so da rahma. Ammi na I remain loyal, grateful, and I remain regretful’. Ammi ba ta san lokacin da ta kama tausasan hannuwan Uwais ta rike cikin nata ba, tana murmushi ta ce. “Ban rike ka da komai ba Uwais sai tarin fatan alkhairi, ko babu komai ka yi gaggawar gane gaskiya kafin lokaci ya kure maka, ka zo ka yi nadamar da ba ta da amfani. Yanzu kuwa repentence dinka bai makara ba, ka yi shi a lokacin da ya dace. Nasiha ta da kai Uwais ita ce, in za ka so abu ka so shi sawwa-sawwa, haka in za ka ki shi, kada ka zurfafa kiyayyar. Domin Allah shi ne kadai masnain gobe da abin da ya boye cikin rayuwarmu”. Uwais ajiyar zuciya ya sauke yana mai AMANNA da kowacce kalma da ke fita daga bakin Ammi. Fatansa Allah ya bar masa Ammi. Ya tsawaita rayuwarta, Ya inganta lafiyarta har sai ta yi wa ‘ya’yansa da Fahimah aure. Wayewar gari ke da wuya ya nufi gidansa na UDB Road, a wannan tafiyar Uwais ba kananan kudi ya samu ba, don haka akalar ginin ta sauya gabadaya, gini ake sosai na gani a fada. Kafin ya dawo dama sun kammala komai, yau ya zo ya tsaya ne don a karasa kananan abubuwan da ba a karasa ba. Ammi da Fahimah kuma suka tafi zaben kayan daki. Ba yadda Ammi ba ta yi ba Fahimah ta zabi abin da ta ke so ta ki, ta ce, “Ammi, duk abin da ya yi miki ni ma ya yi min. kin sani kullum ra’ayinmu yana zuwa daya, don haka ko me ki ka dauka zan so shi”. (Me ya fi danka ya auri matar da ta san mutuncinka ta ke girmamaka fiye da mijin kansa?) Ammi Safeeyah ta fada a zuciyarta. Don haka ita kuma ta zage ta yi wa Fahimah kayan daki na gani na fada, wadanda sai ‘ya’yan gata kadai ke samunsa. Bayan kudin da Uwais ya bayar, Ammi ta zuba nata har ba adadi. In ka ga gidan Uwais da Fahimah komai ya yi acan-acan na masu ilmi da iya tsari, babu almubazzaranci ko kadan, komai da ke dakin Fahimah da kicin dinta mai amfani ne. Inda Uwais ya sa aka yi mata english kitchen duk wata na’urar saukaka girki ta zamani Ammi ta saka wa Fahimah. Don haka a washegari ma bai samu zuwa Abuja ba, kuma ba su samu komawa a ranar da aka gama komai ba sai washegarin ranar. Washegarin kuma da asubah Ammi ta ce su tafi, don an fi so a shiga sabon gida da asubahi. Da daren ranar Fahimah na gaban Ammi kuka kawai ta ke yi, Ammi na hada mata sitturunta da ke dakin da duk wani abin amfaninta, ita ma dauriya kawai ta ke yi, amma ta gama karaya. Shekaru kusan goma sha tara ban da zuwansu Lagos da Sudan ita da Fahima ba su taba kwana ba gida daya ba. Lallai aure ya ci sunansa yakin mata. Ban da shi din, wa ya isa ya raba ta da Fahimarta? To amma me? Uwais ne mijin. Uwais dinta kwalli daya, don haka Fahimah sauyin muhalli kawai ta samu, amma tana nan cikin gidanta. Wannan tunanin ya sa Ammi Safeeyyah ta rage wa kanta damuwa, ta koma tsokanar Fahimah wai ai yanzu 'yammata sun daina kukan aure. Ita mai auren gata ma auren gida, auren cikin daki, auren da babu mai raba ta da Amminta. Washegarin ranar da karfe 5:30am Ammi da Talatu suka raka Fahima har motar Uwais. Tunda ya dawo masallaci bai koma gidan ba ya yi zamansa cikin mota don ba ya son ganin rabuwar Ammi da Fahimah. Ko shi da yake namiji ya ji barin gidan a ransa kamar wannan ne karo na farko da ya fara yin aure. Yanzu ne yake jin barin gidan sosai a ransa, ko don Ammi ta dage ita ma barin gidan za ta yi oho! Gida ne da ya kunshi tarihin duk wata dabdala ta kuruciyarsu. Ya sabbaba aure mai dimbin tarihi tsakaninsa da Fah-himah, Fah-himar da ta juya duniyarsa da tunanin sa baki daya. Talatu ce ta rufe mata kofa don Ammi ba ta iya tsayawa ganin tashinsu ba. Kukan Fahimah ya karya zuciyarta sosai. Ta koma cikin gida cike da kewar Fahimah amma tana mai hamdala a zuciyarta. Yau ta sauke babban nauyin da burin kowacce UWA ta sauke shi, sai ta koma binsu da addua kala-kala. Uwais ya kashe motar a harabar flat dinsu, wanda aka yi wa rufi da dark blue roofings. Bai cika girma sosai ba, amma ya tsaru iyakar tsaruwa daidai bukatar kowanne mai rufin asiri. Duk abin da Uwais ya samo a course dinsa na World Bank a gidan Fahimah ya kare. Amma ji yake inda yana da abin da ya fi hakan zai yi, don Fahimah da yayanta masu zuwa a gaba. Ya kashe motar a inda aka tanada don adanata, sannan ya mika wa Fahimah kamsassan hanky dinsa, If you are done with the cry sai ki goge hawayen mu shiga da kafafun dama, Im sleepy. Farin cikin yau zan mallaki Fah-himah by my side a matsayin uwargida a duniya da lahira, bai barni na runtsa jiya ba. Burina da fatana kawai gari ya waye in shaida wannan rana mai nisan zuwa kamar eternity. Ki shigo gidanki cikin aminci, so da kauna da yardar mijinki. Na yarda da ke Fahimah na amince da ke matsayin uwar yayana. Ki yi hakuri da ni a inda na kuskure don yanzu ne rayuwarmu ta hakika za ta fara. Rayuwar da duk son da ake wa juna sai an yi hakuri da 'flaws' din juna. Sabida yanzu ne zan koma Uwaisu ki koma Fah-himatu, not Uwais and Fahimah sarauyi da budurwa". Maganarsa ta karshe ta ba ta dariya duk da hawayen da ke fuskarta sai da ta murmusa tana share su da hanky din da ya ba ta, Uwais ya bude suka fita, sai ya zagayo ya sakalo hannunsa a kugunta, a haka suka shiga falon farko na gidan. Fahimah ta ga cewa in ta tsaya kallon gidanta wanda ko a mafarki ba ta taba yin na mallakar kwatankwacinsa ba, to kuwa Uwais zai ce 'yar kauye futuk ya aura. Gara ta adana kallon zuwa sanda ba sa tare. Soyayyar yau daban ta ke, domin ta zarce ta birnin Ikko wannan ta nutsuwar zukata ce. Mai licence, sannan ba hobbasar Uwais shi kadai ba, Fahimah ta agaza ta taimaka fiye da zatonsa. Shi da kansa ya yi mamaki domin ta sakar masa komai fiye da koyaushe. Ya ce, "My wife today deserves an accolade!" Kwana uku kenan suna barzar amarci kamar ba za su gaji ba. Takardar sakin ma bai san inda ya jefa ta ba. Tsabar yadda Fahimah ta tafi da dukkan nutsuwarsa, ta zamo silar wani irin 'life contentment' ga rayuwar Uwais. Gabadaya ya mance da Amrah. Da yammacin yau yana daga can bayan gidan inda shuke-shuke suke yana motsa jiki kamar yadda yake yi a kowanne yammacin Allah iya dawo gida da kowacce safiya. Fahimah ta karaso inda yake da kofi mai zurfi (jug) a hannunta mai dauke da sassanyan kunun aya da kwakwa da ta matse da kanta. Ta zauna bisa fararen kujerun roba da ke gefe da tebiri a tsakiyarsu ta ajiye a kan tebir din ta tsiyaya a tambulan tana sha. Uwais ya dakata da excercise din yana yarfe gumi daga goshinsa ya ce. "Abun naki ba ta yi? You know i'm thirsty". Fahimah ta ce ba tare da ta dube shi ba, "Bari in dauko maka naka (power Horse) wannan na mata ne". Uwais ya karaso wajen ya dauke jug din gaba daya ya kafa kai ya shanye duka. Ya ce, "Ki hada kayanmu yau na kwana biyu, gobe za mu je Abuja a yi miki visa". Ambatar Abuja da ya yi ya sa Amrah ta fado mata a rai, "Ya Subhanallah Ya Uwais, yaushe za ka je ka taho da Aunty Amrah?" Ya dan bude ido yana kallonta bai ce komai ba sai da ta sake maimaitawa. "In muka je goben zan biya". Ya ki yarda su hada ido kada ga gane rashin gaskiyarsa. A cikin kayan da ya dawo da su ta ke cire masa wadanda zai tafi da su. Cikin haka takardunsa suka zubo, wata 'yar farar ambulan ta fado da sunan 'Amrah' a jiki. Ba ta yi niyyar budewa ba amma ta ji gabanta ya fadi, sabida rubutun na Uwais ne. An ce ba abin da ya fi dagawa mace hankali irin miji ya ba ta wasika ba tare da ta san me ta kunsa na, kuma an saka sunan Amrah baro-baro. "Ya Ubangiji in na yi ba daidai ba ka yafe mini, but I must quench my curiosity". ****** Uwais na dakinsa yana fama da aiki cikin macbook sai ganin Fahimah ya yi tsaye a kansa rike da takarda tana hawaye. "Yaya Uwais!". Ta fada cikin rauni. Ya dago lumsassun idanunsa yana dubanta ba tare da ya ce uffan ba. Hawaye suka sake shimfidowa Fahimah, da kyar ta iya cewa, "Me Aunty Amrah ta yi maka ka sake ta? Mene ne hujjar hakan? Yaya Uwais ko don mun daidaita ni da kai ne? Ta ya ya ni ma ba zan yi tunanin in ta uku ta zo, ba za'a sake ni ba? Wannan shi ne ga mari ga tsinka jaka. A yi mata laifi kuma a sake ta Ya Uwais, don Allah na roke ka don darajar Ammi ka janye sakin nan kada ka kai shi don Allah ya Uwais..." Kukan da ta saki har cikin kwakwalwar Uwais, domin ta sanya gwiwarsa ta yi sanyi, jikin sa ya mutu, ya ce. "Fah-himah ba laifina bane, kuma ban daina son Amrah ba. Babanta ne ya ce na sake ta ko ya kai ni kotu". Fahimah ta ce, "Sai ka zage ka lallashe su dukkan su, bacin rai ne yasa shi fadar hakan, i don't think he mean it, amma fushin fari ba naka ba ne Ya Uwais. Amrah ba ta da laifi ko me za ta yi, laifi ne ka yi mata, sai ka karba a wuce wurin kawai". Uwais ya yi shiru bai sake ce mata uffan ba, amma a cikin ransa ya janye sakin da ya yi wa Amrah. Sun kwana da niyyar washegari Uwais zai tafi Abuja bikon Amrah. Don haka Fahimah da wuri ta tashi ta sallame shi da dukkan abin da zai bukata. Karfe takwas na safe Uwais ya kama hanyar Abuja cikin motarsa Elantra. A hanya ne ya kira Jabeer, yana dagawa kafin Jabeer ya ce komai ya ce, "Friend, I'm on my way for biko". Jabeer ya yi ajiyar zuciya, don ya san mawuyaci ne Daddy ya sake sauraron Uwais a kan batun Amrah. Amma bai fada masa hakan ba, don ya sani kullum Uwais mutum ne mai sa'a. Auren Amrah ma da ya yi ba karamar sa'a ya taka ba, don haka yanzun ma ba shi da tabbacin ko Alhajin nasu zai sauko daga fushinsa tunda ya yi tattaki ya zo don ya amsa laifinsa. Ya isa Abuja wajejen azhar sannan ya karkata kan motar sa zuwa Apo. Daga Amrah sai Mama a gidan yau Aunty Wasila ba ta zo ba. Maigadi ne ya shigo ya fadi cewa Uwais mijin Amrah ya zo yana waje. Mama ta dubi Amrah don ganin reaction dinta sai ta ga fuskarta kamar an mata bushara da zuwan mala'ikan daukar ranta. Sosai Mama taji dadin hakan, wannan ya nuna Amrah ta dauki zugar da suke kwana da yini yi mata. Dare da rana ba abinda familyn Amrah ke yi sai zugata akan rabuwa da Uwais, in har tana so rayuwar ta ta gyaru. Yau da gobe aka ce 'zuga' abu ce mai matukar illah, in bata dau wata ba tana daukar wata. Don haka auren Uwais ya fucewa Amrah a ka, tana ganin gara ta hakura ta huta akan taje ta yi zaman kishi da Fahimar da bata san Yaya tsakanin ta da Uwais yake ba har yau, tunda su munafukai ne. Da farko ma cewa tayi da maigadin ya je ya ce bazata zo ba. Mama tace. "Ba za'ayi haka ba Amrah, gara kije ki san matsayin ki, in yin-yin in barin-barin". Sannan ta yi kwafa tace. "Wannan Uwaisun, ya gama rainawa mutane hankali. Har yana da 'guts' din kwaso doguwar kafarsa ya sake kawo mana nan?" A fusace Amrah ta zari mayafi ta fita, a dakin da suka saba zama lokacin da yake zuwa zance acan ta sameshi. Uwais na tsaye har lokacin bai zauna ba, da hannuwa zube cikin aljihu, yana zuba idon ganin ta inda Amrah zata bullo, zuciyar sa cike da waswasi. Ba jimawa Amrah ta bayyana a gaban sa cikin wata fuska da wani yanayi irin na kamar dadai duniya bata taba sanin sa ba. Daga bakin kofa ta tokare ta tsaya, Uwais ba ya son tuna yanayin da ya ga idanun Amrah a wannan lokacin; babu komai cikin su sai tsananin tsanar sa zallah. A hankali yayi tattaki zuwa gaban ta, yana nan har yanzu a Uwaisun sa data sani mai kayatar da zuciyar ta, but he lose his magical appearance of love and trust. Dan burbushin son da ya rage a cikin zuciyar ta yanzu ba zai hana ta komai a rayuwa ba., Suka tsaya cirko cirko suna kallon juna kamar zakaru, kowanne striving yake da zuciyar sa don son gane cewa soyayyar tana nan ko ta ragu? Ko kuwa gabadaya ta kama gaban ta? Ta Uwais tana nan, amma ta ragu 50%. Ta Amrah na nan, amma bacin rai, kishi tsana da tunanin betrayance din da Uwais yayi mata ya kashe shi da 70%. Sauran kashi talatin din da ya rage, Amrah ta sabya shi matsayin sabo da juna, kuma na tunani; zata iya overcoming dinsa da zarar ta koma Malaysia. "Ina fatan ka taho min da takarda ta UWAIS SHAGARI?" Amrah ta fada kai tsaye, da sunan da bata taba kiran sa da shi ba. Murmushi yayi, wanda da gani iyakar sa fatar bakinsa, sannan cikin karfin hali irin na maza gogaggu da suka yarda da kan su, yace. "Amrah ko gaisuwa babu? Na dauka tsakanin mu ya wuce haka?" Wani irin kallo Amrah ta yi masa, tana mai tariyo kalaman data ji yana fadawa wata mace ba ita ba a waya, watan ma da ya ce 'yar aikin gidan su ce. Kalamai masu tsauri da matar ka ta sunnah kadai ya kamata ka iya gayawa. Kuma in a gaban idon ta ne ya nuna ko son zanen yarinyar baya yi. Wanda ke iya fadar wadannan tsauraran kalaman a waya, a fili wace irin soyayya yake aikatawa a gareta? Allah kadai ya sani. "Ban fito nan don kayi min dadin baki ba, na fito ne in karbi takarda ta, domin na yanke shawarar dana ke ganin tafi amfani a gare ni. Itace rabuwar auren mu". Da kyar Uwais ya zuki numfashi ya fesar. "Ko rabuwar kika zaba Amrah, yana da kyau ki saurari kalaman baki ba, kafin ki yanke kowanne irin hukunci, ban ce lallsi ki yarda dasu ba, amma inada hujjojina, tunda dai soyayya ce da yarda suka hada mu ba akasin su ba". Amrah tayi wata irin dariya tace "soyayyah........ Uwais? Really? Does it really exist a duniyar nan kuma a zamanin nan?" Uwais ya shafo lallausar sumar kansa cikin damuwa yace "It really does, and i still love you Amrah. Kamar yadda nake son Fah-himah itama. Amma ki yarda cewa aure na da Fah-himah wata rubutacciyar kaddara ce daga Allah wadda tafi karfin na tsallake ta....". Tiryan-tiryan ya soma bata labarin Fahimah, tun daga lokacin da Ammi ta dauko ta daga 'orphanage', kuruciyar su, yadda ya rayu yana uzzura mata, da goranta mata halitta, zuwa haduwar shi da ita Amrah a gidan Jabeer. Yadda Ammi ta kafe in bazai auri Fahimah ba itama Amrah ba zai aura ba. Artabun da Ammi ta sha da shi akan Fahimah, kafin ya yarda su tafi Ikko tare. Ya takataita zancen sa da cewa. "A wannan tafiya da nayi tare da Fah-himah, a dalilin rashin zaman ki wuri guda, al'amura suka sauya beyond my capability to escape. Kada ki manta ni namiji ne kuma mai cikakkiyar lafiya kamar kowanne dan adam, wanda Allah ya baiwa damar auren abinda yayi masa dadi daga daya-daya, biyu-biyu, uku-uku ko hurhudu. Ko Ammi bata aura min Fahimah ba, a irin rayuwar da kika zaba mana, dole in kara aure. Don haka Amrah bai kamata ki ga laifi naba don na so Fah-himah at this expense tunda aure ne na sunnah a tsakanin mu, kamar yadda yake tsakanina da ke. Laifi daya na san na yi muku Amrah, na rashin gaya muku tun farko, sai na gina neman aure ne a lullube, abinda ya kamata in yi a wancan lokacin shine tun farko in fada, cewa ku biyu za'a aura mini a lokaci guda, da ke zabin rai na da zabin mahaifiyata, in ya so in kin ga zaki iya aure na a haka ayi, in kin ga bazaki iya ba na hakura. To amma Amrah idanuna sun rufe, na kurumce na makance a dalilin son ki, burina kawai na mallake ki. Ina tsoron duk wani abu da zai shiga tsakanina da wannan burin nawa. Na san kuma muddin na fada a wancan lokacin to na rasa ki kenan Amrah...... and i cannot affort to lose you. In kuma nace miki a halin yanzu bana son Fah-himah Amrah na yi miki karya na yaudare ki, wanda hakan zai yi sanadin sake gina rayuwar auren mu akan rashin gaskiya a karo na biyu. Ni dai na san zan kasance jajirtaccen miji mai adalci a gare ku, in kin bani dama kin dawo dakin ki Amrah". Ko kadan maganganun Uwais cikin lallashi da karbar laifi (submissiveness), kwantar dakai da tsage gaskiya da hakikanin asalin Fahimah da ta ji a yau bai wanke zuciyar Amrah ba, daga cin amanar da take ganin Uwais yayi mata. Karewa ma, labarin da ya bata sai ya ninninka mata kishin Fahimah..... the way Uwais yake kiran sunanta kadai cikin shauki zaka fahimci tana da kima da matsayi mai girma a zuciyar sa.... Tunanin Amrah a a wannan lokacin shine; ko ta koma gidan Uwais bazata taba ganin farin sa ba, komai adalcin sa da yake ikirari, ya riga ya munana a idanun ta, zuciyarta ta riga ta gama sallama shi. Sannan ta gama tsanar Fahimah a rayuwar ta. Ba don kuma wai ta daina son sa bane a'ah, sai don hakan take ganin ya fiye mata maslaha. Akan dai ta je ta zauna tsakanin wadanan 'yan gida daya, da suka ruwa a kofi guda, suka rayu gida daya karkashin tarbiyya da soyayyar uwa guda, suka kuma yi aure mai dimbin sarkakiya wanda a karshe ya koma musu auren soyayyah. Daga Baban ta har mamanta da yayyenta babu mai son auren ta da Uwais, ita kadai take son kayan ta, sai ko Yaya Jabeer. Shima yanzu ya ce ya cire hannun sa. Hukuncin komawa gidan Uwais ko akasinsa nata ne babu ruwan kowa. Amrah ta ga cewa duk ne yayi zafi akan soyayya wadda bata zama dole a rayuwa ba? Da ita, da babu, dan adam irin ta mai abun yi bazai kasa rayuwa ba. Tana da tarin abubuwan yi masu yawa da muhimmanci a gaban ta, she's a goal-oriented, dama auren Uwais ya zame mata kamar alaqaqai ga 'goal' din ta, da take ta faman raba hankalin ta a kai, don ganin ta bada lokacin ta da energy din taga kowanne bangare (aure da karatu) wanda haduwar su waje guda abu ne mai wahala ga 'yan hutu irin Amrah. Da wannan tunanin dama wasu hujjojin ta masu yawa da bata ambata ba, Amrah ta runtse ido tace. "Uwais Shagari, na ji dukkan bayanan ka, sannan na fahimce su. Amma abu daya nake so ka gane it's too much for me to bear. And it's too late to cry.....when the head is cut off. Ka riga ka dusasar da tauraruwar ka daga idanuna bazan iya kara yarda da kai ba. Ka zo da bayanin gaskiya a lokacin da bakin alkalami ya riga ya bushe, wani nawa bazai iya sauraron ka ba, including Yaya Jabeer. Don haka aimakon mu cigaba da zaman daukar hakkin juna da wahalar da zukatan juna, mu yi hakuri da juna shi ya fi, wanda aka yi a baya Allah ya bada ladansa. Inada yaqinin cewa you've found your true and real love wanda ya zarta nawa........". Amrah ta fada, tareda fitowar wani guntun hawaye daga gefen idanun ta. Ba mutuwa ake wa kuka ba sabo ne. Ta daga kai ta dubi Uwais da murmushi a kyakkyawan bakinta. "I'm wishing you and Fahhimah all the very best in life, so many kids as you are dreaming, masu kama da dukkan ku, don zasu fi yin kyau fiye da nawa da naka a dalilin mixed complexion". Ta karasa cikin zolaya duk da cewa still da kananan hawaye cikin fararen idanun ta. "Uwais, ina taya ka murnar mallakar mace daya da daya a cikin mata, na zauna da ita na san halin ta, na kuma fahimci qualities din ta. Allah ya baku zaman lafiya ya hada hankulan ku da ra'ayoyin ku wuri guda ba kamar ni ba...". Da sauri Uwais ya rungume Amrah, yace cikin rawar murya. "Amrah na yarda mu cigaba da auren mu yadda kuke so ke da iyayenki, i will never complain again, duk sanda kika samu dama sai ki ziyarce ni. Yanzu kam na amince da wannan tsarin since i have an alternative, mun wuce wannan wurin. Sauran matsalolin duk da zasu biyo baya na tabbata zasu kasance kanana ne Amrah, wadanda zamu iya overcoming din su da karfin son da muke wa juna. Tunda zama waje guda shi ke kawo matsaloli zan yi kokari inga cewa kowacce tana muhallin ta daban nesa da na 'yar uwar ta, sai kun so zaku hadu da juna........". Amrah ta girgiza kai ta sanya yatsunta cikin na Uwais ta ce. "Auren ne bana bukata kwata-kwata yanzu, i'm going for my life ambition, i'm done with it, i have to go for my goals. Ban sani ba dai ko a can gaba in bukaci auren? Allah shi ya barwa kansa sani". Uwais ya fahimci ko me zai ce da Amrah ta riga ta yanke hukuncin da take ganin shine dai-dai da rayuwar ta. Zai zamo ihu ne bayan hari. Amrah no longer wants him in her life. Don haka shima ya ce. "Na fahimce ki Amrah, and i will not force you ki yi abinda ba kya ra'ayi, tunda shi aure contract agreement ne na mutane biyu ba mutum daya ba. I wish you good luck in your all endeavours. Kuma ina fatan as you actualize your goals, (bayan cikar burikan naki) zaki yi aure immediately, ko da ba da ni Uwais ba. Ki sani Amrah duniya ba matabbata bace, lahira ita ya kamata a yiwa kyakkyawan tanadi irin wannnan ba zaman duniya mara tabbas ba, wanda mai karewa ne kamar kiftawar ido". ****** Wannan ita ce rabuwar masoyan ta karshe, wadda tazo ta dagula zukatan su a kwanakin da suka biyo baya. Kowannen su ya zama emotional. Bayan Uwais ya kaiwa Jabeer takardar sakin Amrah wadda ya sake rubutawa again. Ya zama saki biyu kenan bayan na farko da ya riga ya rubuta. Fahimah data fahimci Uwais na cikin wani hali bayan dawowar shi daga Abuja sai ta janye jiki daga gare shi, ta daina shige masa, bata takura masa da tambayar me yake ciki shi da matar sa ba, don dai ta bashi dama yayi sulhu shi da zuciyar sa. Ta dai fahimci ba'a yi nasara ba a komen Amrah amma da bakin sa bai ce mata komai ba. Illa iyaka walwalar sa ta ragu, amma hakan bai sa ya daina nuna mata kulawa da soyayya in a gentle way ba. Kwana daya, biyu har uku bata ga Amrah ta dawo ba, abinda bata sani ba already su Wasila kamar jira suke sun zo sun kwashe kayanta kaf daga Sultan Road zuwa Abuja. ***** Uwais yayi sallama a falon Ammi, dawowar ta kenan daga BUK, ta amsa da madaukakiyar far'a tana zolayar sa, "ka ga angon Fahimah da Amrah, mai mata biyu wanda ba aminin gwauro ba". Murmushi yayi kadan, sannan ya zauna a daidai kafafunta. Suka sake gaisuwa, irin tasu ta Sudanese, Ammi ta tambayi Fahimah yace tana barci ya fito. Sannan ya sake tankwashe kafafunsa ya ce. "Ammi mun rabu da Amrah fah, ina nufin auren ya kare". Ammi ta ja wani dogon salati ta sanar da Ubangiji. "Garin yaya Uwais? Me ya kai ka aikata wannan danyen aiki?" Uwais ya sunkuyar da kai sannan ya dago idanun sa da suka rine ya dubi Ammi. "Because this is the best decision agare mu ni da ita. Fahimah ta isheni rayuwar duniya har da ta gidan aljannah mai zuwa anan gaba in Allah ya yarda. Amrah bata bukatata cikin rayuwar ta yanzu Ammi, na fahimci ma kamar dama jira take ta samu hanya ta kubucewa auren. Tana da abubuwan da tasa a gaba da suka fi ni muhimmanci, na dade da sanin wannan ina karyatawa ne da gangan har zuwa yanzu da ta bayyana hakan da bakin ta". Ya kwashe duk yadda suka yi da Alh Umar Dikko a waya ya gaya mata, yadda ya rubuta sakin tun kafin ya dawo, yadda aka yi Fahimah ta gani da takura mishi da ta yi ya maida auren, ya kuma yi tattaki zuwa Abuja don ya dawo da Amrah. Da kuma yadda ta kasance a tsakanin su. Ammi Safeeyah is speechless, ta gamsu da hujjojin sa, yayi iya duk abinda zai iya don ya zauna da ita, ita kuma for now ta ga bazata iya ba, sabida principles din da aka riga aka dora ta akai. Ammi bata ja zancen da nisa ba, dama auren Amrah ai zabin zuciyar sa ne, yaran yanzu ne abinda kake hango musu su ba shi suke hangowa ba, in suka so mallakar mace kamar Da ya so fitowa cikin uwar sa. A kullum kyal-kyal banza da kwadayin dukiyar iyayen yaran ke burge su. Duk da ta san Uwais kam bai kwadayin dukiyar gidan su Amrah amma yana kwadayin kyawun halittar ta. Shi da kansa yanzu ya zo ya gane cewa kyawun halitta does not matters a lot in marriage, sabida shi aure ba abu ne da ake yi don nishadin zuciya kawai ba, a'ah ibada ce mai zaman kanta wadda a cikin ta akwai jarrabawar imani kala-kala ga kowanne dan adam. Don haka ake so a gina shi bisa doro na gaskiya da amana, sannan kauna da soyayya su biyo baya. "Idan wannan shine alkhairi a gare ku kaida ita, Allah ya hakurkurtar da zukatan ku, ya hada kowa da rabon sa na alkhairi". Wannan sune kalaman Ammi a takaice, akan rabuwar Uwais da Amrah, "Amin Ammi, insha Allah shine alkhairin da muke rokon Ubangiji dare da rana, akan kada ya bar mu da iyawar mu, ya zaba mana abinda zai fi zame mana alkhairi". **** UWAIS&FAHHIMAH (When Hatred turned to Extreme Love). "FAH-HIMAH, kin gama ne mu wuce ko har yanzu kina nan kina lakai-lakai din kwalliyar taki sai jirgi ya tashi ya bar mu?" Uwais ya fada daga bakin kofar shigowa bedroom din su, tana zaune gaban mudubi daga ita sai farin towel iya cinyoyin ta, ga cinyoyin nan sambala-sambala a fili suna sparkling suna zagin idon Uwaisu, wanda ya hade cikin shadda getzner deep green. A matsayin sa na farin mutum sharr mai sirkin jaja-jaja! Kada ki so ki ga yadda deep green colour ta amshi fatar jikin sa. Yau din kuma yayi saisaye ya aske duka gashinnan na kansa, don haka bai saka hula ba yau, don ya san ko ya saka bazata zauna daidai ba. Ta lakato lotion din ta (Makari) a tafin hannun ta, ta jefe shi da wani irin lallausar kallo kafin ta shigar da fararen kwayar idanun ta cikin nasa, ta juya su ta sake juya su cikin sigar jan hankalin maigida, ta ce. "Jira na ke ka zo ka shafa min lotion". Uwais yayi murmushi broadly yana karasowa gabanta hannayen sa duka biyu zube cikin aljihun sa kamar yadda yake a al'adar sa. Takun sa gonin kyau kamar yadda komai nasa yake mai kyau a fili da boye. "In shafa miki lotion a nawa? Kin san ni komai nawa DEAL ne!". Dariya ta yi da ta tuno da birnin Ikko, damben Ikko, kisses din Ikko, a lokacin har ya matso lotion din a tafukan hannun sa ya mutstsika ya soma shafa mata a cinyoyin da tun dazu suke zunguro idanun sa. Amma da shafa mai yayi shafa mai, sai ta ji Uwais ya saki layi gabadaya. Ta san haka zata faru, itama kuma dama ta yi ne don ta tsokano shi. Nan suka shiririce cikin farantawa juna, da kyar in jirgin bai tashi ya bar su ba. Sanda suka isa 'terminal' ma an kusa rufe jirgin, wanda zai tashi zuwa Geneva din Switzerland babbar hedkwatar bankin duniya (World Bank). Kusan sune karshen shiga jirgi, suna shiga ana rufe jurgin na Boeing 704. ***** FAHIMAH DA UWAIS A GENEVA Geneva, shine gari na biyu mafi girma da shahara a kasar Switzerland bayan Zurich wato (capital territory) din kasar. Ganeva, shine tabbataccen muhallin majalisar dinkin duniya 'United Nations' (bayan muhallin su na kasar Amurka dake New York). They speak German, Italian, French and Romansh. A shekarar 2017 population na Geneva ya nuna 198,979 (-United Nations). Sabida haka garin is not crowded at all. Birnin Geneva ya shahara akan guraren ziyara guda biyu; wadanda aka sani da 'Lake Geneva' wato kogin Geneva, da kuma 'Jet d’Eau' (Europe’s largest Alpine lake). Wanda sune manyan tourist attraction na garin Geneva. Rayuwar Uwais da Fahimah a wannan birni mai sanya nutsuwa ga zukatan masoya, kwatankwacin rayuwar su ta birnin Ikko ce. Banbancin shine wannan cike take da soyayya, yarda da Amanna da juna. Waccan ta Ikko kuwa cike take da waswasi, rashin tabbas da rashin tsayuwar zukata wuri guda. Ba sa komai sai kula da juna, daga Uwais ya je aiki ya dawo, sai tayi girki su ci a kwana a hantse ana shan soyayya. A wannan lokacin Fahimah da Uwais suka kara dinkewa da juna tamkar Lailah da Majnoon, soyayya suke zubawa kamar a birnin Hindi, Fahimah bata baro Geneva ba, sai da tsarabar yaron ciki dan sati biyu. Shiru tayi da bakin ta bata gayawa Uwais ba alokacin da Pt stripdin ta ya nuna mata, musamman in ta tuno yadda ya kallafa rai akan cikin Amrah, amma a karshe Allah yayi bai rayu ba. Gara ta yi shiru kawai kada ta dugunzuma masa zuciya har sai ya gane don kansa. Inda Allah ya taimake ta cikin mai hakuri ne bai da laulaye-laulaye, in dai zata ci ta koshi to kuwa lafiya-lafiya ita da dan tayin cikin ta. In bata ci abinci bane na kamar awanni biyu don gigicewa kamar ta zauce, kuma zata yi ta ci hannu baka hannu kwarya. Satin su uku Uwais ya kammala course din da ya kai shi kasar Switzerland, dama kuma ba a masaukin su ya sauki Fahimah ba, wani karamin gida daga waje can ya kama musu, don ba'a basu accommodatin na iyali ba, suka tattaro suka dawo gida da sabon cigaba, wato takardar daukar aikin Uwais da World Bank Group. Reshen kasar Najeriya mai muhalli a birnin tarayyah. Hedkwata din su na kasar Nigeria na nan a Yakubu Gowon Crescent. Don haka gidan da Uwais ya kama bai da nisa da ofishin su. Tunda suka dawo gida ba abinda suka sa a gaba sai shirin komawa Abuja, inda Uwais zai shiga sabon ofishin sa matsayin daya daga cikin jami'an World Bank na kasar Najeriya. Yayi sallama da GT kuma. Sun tsara a junan su su biyu shi da Fahimah, tare da Ammi zasu tafi Abuja su yi ta hilatar ta suna mantar da ita komawa Sudan. Ammi kamar ta sam me Uwais da Fahimah suke shirya mata, da suka zo suna fada mata cewa tare da ita zasu koma Abuja in ya so daga can ta wuce Sudan. Dariya ta yi musu tace "ni din ai ba ta yau bace Fahimah&Uwais. Ku bar ganin babu furfura a kai na amma na kwana biyu bazaku yi min wayo ba. Na gaji da kasar Najeriya cikin dangina zan koma, kuyi hakuri bazan biku gidan ku in zauna ba. Amma na amince idan kin haihu zan zo in zauna in yi miki jego na kwanaki arba'in. Na yi wannan alkawarin. Daga nan har ki haihu ai amarci bai kare ba Fahimah, kin ga dacewar Uwa ta zauna a tsakanin ku?". Ba Fahimah kadai ba har Uwais ya ji kunya. Ana i gobe Ammi zata tashi zuwa Khartoum Fahimah da Uwais a gidan suka kwana manne da Ammi, sun kasa matsawa ko nan da can daga jikin Ammi. A wannan ranar Fahimah ta yi kuka har ta gode Allah. Shi kansa Uwais daurewa yake yi a matsayin sa na namiji, kada Fahimah ta ga karayar sa ta kara sarewa. Da asussuba suka kai Ammi da himilin kayan ta filin jirgi, Baba Talatu ta fi bada tausayi da tafiyar Ammi kasancewar tunda sauran kuruciya suke tare. Ammi ta yi mata ihsanin da zata dade bata nemi komai a rayuwarta ba. Kuma ta ce in tana so ta bi Uwais da Fahimah Abuja su zauna tare. Baba Talatu ta ce kwarai zata so hakan amma itama 'ya'yan ta sun matsanta kan ta koma Jahun sabida tsufa ya riga ya cimmata, amma ta yi alkawarin kai musu ziyara lokaci-lokaci. Ammi ma ta yi alkawarin duk sanda ta sake zuwa Nigeria zata kawo mata ziyara har Jahun. A lokacin da jirgin su Ammi 'Air Sudan' ya karci kasa ya daga ya bar Kano, yayi dai-dai da lokacin da Fahimah ta saki wani kakkarfan kuka ta kankame Uwais a bainar jama'a. Ji ta yi kamar ance rayuwar gata da parentship ta yi mata adabo. Ji ta yi kamar su biyu suka rage a fadin duniya daga ita sai Uwais. A wannan lokacin Uwais ya rungume Fahimah cikin lallashi, his words are all supportive, loving and ecouraging cikin daukar mata alkawura da dama, alkawuran cewa zai tsayawa rayuwar ta tamkar Ammi in every aspect. Yayi alkawarin zama mijin marainiya, namiji dan goyo har da daurewa da majanyi koda har su koma ga Mahaliccin su bata ga kowa nata ba. Wanda zai taka rawar IYAYE, MIJI, 'DAN UWA, ABOKI KUMA MASOYI ga matar sa duka a lokaci guda (all at once). Zai zame mata uban 'ya'ya nagari ta yadda bazata taba dana sanin zuwan ta duniya a yadda ta zo ba!!! Alkawuran da Uwais ya daukarwa Fahhimah a yau, har ba su da adadi, wadanda yake fatan Allah ya bashi lafiya, tsawon rai da ikon cika su. ***** Amma har bayan kwanaki uku da tafiyar Ammi Fahimah bata koma daidai ba, she became moody and depressed, haka bai kara ganin fararen hakoranta a waje ba balle a yi zancen kulawa a shimfida. Duk kulawar da yake samu ta zama a gefe she's internally suffering a zuciyar ta..... ya yarda Ammi itace gatan Fahimah amma kuma ai Allah shine gatan bawa. Sannan ko kai kadai Allah ya yi nufin zaka rayu a doron kasa to fa zaka rayu cikin hikima, iko da yardar sa. Yau in aka ce Ammi mutuwa ta yi, shin bazata yi tawakkali ba??? Abinda Uwais yayi ta kokarin nusar da Fahimah kenan a kwanakinnan, yace ko Ammi ta zauna a Nigeria tunda tace bazata bi su Abuja ba to fa duk daya ne da zamanta Sudan cikin 'yan uwanta. Gara mata zama a can din. Yana da yakinin zata fi samun farin ciki da kulawa acan fiye da ta zauna a gidan ita kadai babu Fahimah, tunda shi dama namiji ne, neman abinci bai bari ya tsugunna waje guda. Fahimah dai har kwanaki bakwai she's still moody, don haka a hakan ta Uwais ya tattara ta suka kama hanyar Abuja. Suna tafe a mota ma lallashin ta yake ta yi babu gazawa, har suka zo birnin tarayyar Najeriya da yammaci lis. Gidan nasu yana kan titin Yakubu Gowon Crescent. Uwais ya sa mukulli ya bude suka shiya kayataccen falon. Ya juyo yana riko hannayen Fahhimah a cikin nasa... "This is your humble abode!" Uwais ya fada yana zaunar da Fahimah akan kujerun falon su, wadanda Fahimah bata taba hawa kujera mai laushi da taushin su ba. Su ba fata ba su ba roba ba su ba leather ba. A gidan duniya dai gidannan da bai cika girma ba kuma bai cika kyale-kyale ba ya ishe ta rayuwar duniya. Uwais ya sunkuya yana fadin "lemme give you a welcome kiss Fah-himah my life, my wife, mother of my children, the one i love most (after Ammi). May we live together in prosperity and blessings, die together in love and affection, blessings upon blessings....... May Allah's Rahmah cover us forever......". He then start to kiss her....... tun daga kololuwar zuciyar sa sautin sumbar yake fita tsut-tsut. Daga wannan ranar, wani sabon shafin rayuwa na gangariyar soyayya ya fara........ ***** Sai da cikin Fahimah ya shiga watanni hudu sannan Uwais ya farga. A ranar Uwais sai da ya kusa kuka don farin cikin yafi gaban ya yi masa dariya. Ya goya Fahhimah a gadon bayan sa, yana zagaye makeken falon su da ita a hankali, sannan ya dire ta cautiously akan gadon su. Ya tashi da azumi a washe gari, ya kuma yi sadaqah a gidan marayu na garin Abuja, yana rokon Allah ya sauki Fahhimah lafiya, ya kuma raya duk abinda zata haifa, walau mace walau namiji shi bashi da zabi, kowanne Allah ya bashi yana so kuma ya gode, zai cigaba da godewa da basu ingantacciyar tarbiya har sai gashin kansa ya kode ya zana fari tas, yana rokon Sa yasa Fahimah ta haifi abinda ke cikin ta lafiya cikin tarbiyyyar Islam da koshin lafiya. ***** MURFI Kowanne dan adam yana da burin sa da kalar tunanin sa, wato dai kowanne dan adam da irin perception dinsa. Da irin aqidar sa wadda a ganin sa itace dai-dai da tsarin rayuwar sa. Saidai daga sanda aka bar fadar Allah Ubangiji SWA aka kama ta malam bature zallah, (wanda shi bai san Allah ba, bai yarda da dokokin sa ba, bai san rayuwar duniya aikin banza bace) to baza'a ga yadda ake so ba, wato baza'a ga daidai ba. Ina wannan sharar fagen ne akan Amrah Umar Dikko da ire-iren ta. Bayan wucewar shekaru bakwai, Amrah tayi nasarar zama cikakkar likitar fida (surgeon) ta fito da kwali mai daraja ta biyu, a wannan lokacin ne ta ga ya dace ta komawa masoyin asali; UWAIS SHAGARI, don yanzu ne take da lokacin sa 100%. Kuma yanzu ne ta shirya haifar 'ya'ya don tuni ta samu aiki a National Hospital. A daidai wannan lokacin Uwais Da Fahimah yaran su uku; Abdulkarim, Safiyyah da Little Fahhimah wadda Uwais ya sanyawa sunan Fahimah don ya nuna mata matsayin da take dashi a rayuwar sa. A wannan lokacin promotion na aiki ya maida su kasar Switzerland gabadaya, a babban reshen World Bank, suna zaune a Geneva, inda acan ne Fahima ta haifi Safiyyah (Mami) da (Little Fah) yadda suke kiran ta. Abdulkarim kadai ta haifa a gida sanda suke Abuja. Ammi Safeeyah duk bayan watanni uku take zuwa Geneva daga Sudan, tayi wata daya tare dasu ta koma Khartoum. Lokacin da Abdulkarim da suke kira Baba Shagari ya cika shekaru bakwai a duniya sai Ammi ta dauke shi daga Geneva zuwa Sudan, acan aka kaishi makarantar haddar Al'qurani mai hade da kimiyyah a Oumdurman ta kasar Sudan, Safiyyah (Mami) da Fahima (Little) su suka cigaba da karatun firamare a (La Decouvertè School) Geneva. Karkashin kulawar jajirtacciyar uwa (the great Economist) Fahimah Shagari da uban da babu kamar sa wajen kulawa da nunawa iyali soyayya: Uwais Abdulkarim Shagari. A wannan shekarar Fahimah zata fiddo kwalin P.hD (Dr. Of Philosophy) akan Economics daga University of Geneva. Amrah na can tana neman inda zata hadu da Uwais Shagari helter-skelter. Ta san har gobe Uwais bazai guje ta ba idan sauran mazan dake tare da ita suna bata mata lokaci babu zancen aure sai na holewa sun guje ta. Amma neman duniya Amrah ta yi bata samu Uwais ba a Kano, Abuja da Lagos. Layukan wayar sa data sani tuni ya daina amfani dasu. Har tattaki ta yi zuwa 'Yankaba hopefully ko bata same shi ba za ta samu Ammi, inda ta tadda 'yan haya ne a gidan, suka kuma tabbatar mata masu gidan basa kasar Nigeria dukkansu. Amrah kamar tayi dan karamin hauka, ga Jabeer ma yace shi rabon sa da Uwais tun samun aiki da yayi da World Bank, a karshe Amrah ta yanke shawarar ta nemi Uwais a social media platforms. Tashin farko da ta nemeshi a facebook da IG da Twitter da sauran su bata sameshi ba. Amma cikin ikon Allah sai ta ganshi a LinkedIn tunda shi (professional network) ne, duk wasu manyan ma'aikata da kanana suna cikin sa. Wani lafiyayyen hoton Uwais ya fito karkashin sunansa data rubuta. Inda ta ga cewa yana zaune a birnin Geneva, karkashin bankin World Bank. Gabadaya ya canza completely, girma da ya kara sai ya kara masa ilhama da cikar zati, yayi wani irin fresh kamar bai hada jini da hausawa ba ko kankani. Amrah ta kusa suma don dadi, a take ta rubuta masa personal messege ta tura. A ciki ta bayyana masa dukkan success din ta, duka burika sun samu, shi kadai ya rage mata rayuwa ta koma cikakka. She's now a medical doctor amma bata da aure kuma bata da Da ko daya. Ya zo su koma da auren su, ta yarda ko mata uku gareshi zata zauna a ta hudu. Uwais bai ga sakon Amrah ba sai a daren ranar da ya hau LinkedIn don duba sakonnin ofis. Da ya karanta sakon Amrah bai san sanda yayi murmushi ba, sannan ya saki wani mikkakken tsaki. This woman is sheer LUNATIC, me ta dauki soyayya ne? Gare-gare abin wasan yara ko kuwa me? Shi tunda ya bar Nigeria bai kara tuna Amrah ba, yanada duk abinda yake so a matar sa. Ba Amrah kadai ba, duk wasu matan duniya ma basu kara burgeshi ba. Kowacce kallon wadda ta rako FAH-HIMAH duniya yake mata. Da farko bai yi niyyar bata amsa ba, amma sai ya ga cewa in har akwai abokantaka ta gaskiya to har gobe Jabeer abokinsa ne. Ya rabu da Jabeer ne bai nemeshi ba tun zuwan sa Geneva don baya son wani abu ya kara hada shi da Amrah. A yanzu kuwa tunda duniya ta koya mata darasi ta waiwayi reality ya kamata ya bata amsa wadda zata sa ta kara sanin rayuwa ta kuma san baya bukatar ta arayuwar sa yanzu. Hoton shi da matar shi da kyawawan 'ya'yan su guda uku masu kama da ruwa biyu (halfcaste) shi ya fara saka mata, sannan a kasa yayi rubutu kamar haka; "A ganin ki wannan perfect and loving family suna bukatar wata mace daban a cikin su bayan MAHAIFIYAR SU? Amrah kinyi kuskure da kika dauki soyayya tamkar gare-gare abin wasan yara! Da zaki iya gara tayoyin ta duk sanda kike so, gaba ko baya. Ni a wajena soyayya shuka ce mai rai dake bukatar ban ruwa da taki domin ta cigaba da yin yado. Daga sanda aka bar wannan shuka babu ban ruwa babu taki, to grass-root dinta yake mutuwa tun daga karkashi har zuwa ganyayen ta, su bushe su mutu su zube a kasa..... Wannan typical example ne na baki akan Uwais da Amrah. I already found true love, and all what a man dreamt of in my current WIFE. So i wish you all the best in life. Ina fata wannan ya zama sako na karshe da zaki turomun please and please, don in mata ta ta gani zata rufe min kofa. -Uwais Shagari. Ai kuwa yana gama tura sakon tana fitowa daga toilet kanta yana yararin ruwa, yanzu kam tana dan retouching dinsa ba kamar da ba, don haka kakkarfan gashin ya russuna sosai ya kwanta, wanka ta yi, domin kwanciya barci kuma rigar wanka ta tawul ce kawai a jikin ta. Alamun rashin gaskiya ta gani a tare da shi ta kankance ido "Baban Fah, kai da wa kake waya?" Sosa kai yayi, "ba fa waya nake yi ba, LinkedIn ne. Ko kinji ina magana ne?" "Ban ji kana magana ba, amma ga ka da waya a hannu, lokacin da ya kamata ace already ka kashe, tunda kuwa lokaci na ne yanzu. Wannan lokacin na chatting din dare da 'yammata, ai in ina ganin ka da waya da daddare jini na zai hau ne, inta kissime-kissime koda ba chatting din kake yi ba". Dariya sosai Uwais yayi, ya mike ya isa gareta ya tsaya a gabanta, ya sanya hannu ya rungumota gabadaya yana sumbatar ta ko ta'ina yana fadin; tsofai-tsofai dani at 40 zan tsaya chatting da 'yammata Fahimah? Inada wannan hadaddiyar Babyn a gida? Luscious, succulent and....." sauran maganar makalewa tayi a bakin Uwais sabida yadda Fahimah ta kwace linzamin ragamar rayuwar sa gabadaya. **** NB A karshe Amrah ta auri wani tsohon consultant dinta, yana da mata biyu ita ta uku. Kuma ra'ayi da akida ya zo daya, don haka lafiya suke zaune. Don bai hada ta da matan sa ba. Har ga albarkar ciki a halin yanzu. KARSHE. Masha Allah Laquwwata illa billah. 07030137870 Sumayyah Abdulkadir 20/09/2021.