THE GOVERNOR'S MATAR GWAMNA Bismillahir Rahmanir Rahim Book one *Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani iko da kuma damar fara rubuta wannan labari. Ina addu'ar Allah ya sa yadda na fara lafiya na ƙare shi lafiya. Amin* *wannan labari zai zo daga kashi na ɗaya zuwa kashi na uku Insha Allah. Na ɗaya zai zo a kyauta yayinda kashi na biyu da na uku zai zo na kuɗi a farashin 400* *wannan labari ƙirƙirarre ne, idan yayi kamaceceniya ta wani fanni da rayuwar wani, wata ko wassu to bisa kuskure ne, ba ayi dan cin zarafin kowa ba* 01 (CONGO STATE is a fictional state in Nigeria. Jahar Congo ƙirƙirrerren Jaha ce a Nigeria) *MAFARI* Da ƙyar kyakykyawar matashiyar budurwa da ke riƙe da hannun Mahaifiyarta ke jan numfashi da dogon hancinta da ya zauna ɗas a tsakiyar fiskarta wanda ya ƙara ƙawata ma ta fiskar sosai. Iskar asibitin wanda ke gauraye da warin magunguna, allurai, jini, fitsari da sauran su shi ya ke yiwa mutum iso a duk lokacin da ya kusancin farfajiyar asibitin. Ansan Asibitoci da wari amma wannan warin na sa ya fita daban. Ko dan Asibitin ta gwamnati ne, oho. Rabonta da zuwa General Hospital Congo tun wani ciwo da Abba yai kusan shekaru biyar da su ka wuce. Ba su jima da zama a wajen reception ba wata mata mai ɗauke da jaririya ta fito daga office ɗin Likita ta ce " wai Zainabu Inusa ta shiga" Budurwar nan ta kama hannun mahaifiyarta su ka shige ofishin Likitan. Lokacin da su ka shigo Likitan yana ta cike-cike a file ɗin su. Ba tareda ya ɗago ba ya ce "Malama Zainabu mi ya ke damunki?" "Ciwon ciki" Da sauri Likitan ya ɗago fiskarsa saboda yadda muryar budurwar ya shige shi, bama wannan ba, a file ɗinsu an rubuta Zainabu Inusa matar aure ce mai shekaru talatin da takwas wannan budurwa kuwa da ƙyar idan ta haura shekaru ashirin da ɗaya. Lokacin da ya haɗa ido da budurwar sai da numfashin sa ya tsaya na ɗan wasu sakanni. Muryar da fiskar ba baƙon sa ba ne amma wannan ne karo na farko da ya ke ganin ta gaba da gaba. "Mu ne wanda Dr Ubaydullah Gidaɗo ya turo" ta faɗa da siririyan muryarta me ratsa zuciyar mazaje. "Masha Allah! ke ce ƙanwar mu kenan. ya jikin Umma?" Sai da ta yi murmushi kafin ta amsa mi shi da cewa jikin Umma da sauƙi. Duban Umma Dr Hassan yai ya ce "Umma tun yaushe kika fara jin ciwon cikin?" Ido kawai Umman ta bishi da shi har ya gama maganar sannan ta maida dubanta ga 'yarta wacce ta fara ma ta bayani da yaren kurame. Dr Hassan ya sake baki yana kallon ikon Allah, sai yanzu ya gane dalilinta na iya sign language na kurame dan watarana a wani rahoto da ta naɗa ta yi amfani da shi wajen yiwa wani kurma tambayoyi. Abin ya burge mutane da dama amma yanzu da ya ke ganinta tana yiwa mahaifiyarta tafintan (interpreting) duk abinda ya ke faɗa sai tausayinta ya kama shi. Bayan ya gama sauraron bayanen ta ya ma ta tambayoyi sai ya rubuta mu su takardar scanning ya ce su je su yi su kawo ma sa ya gani. Ba su suka bar Asibitin ba tun takwas saura minti biyar da su ka shigo har sai ƙarfe shaɗaya da minti biyu. Lokacin da su ka fito daga Asibitin Keke daban-daban su ka hau saboda sauri da budurwar ke yi dan ta je wajen aiki yayinda Ummanta ta wuce gida. Da gudu-gudu sauri-sauri ta shigo cikin ma'aikatar ta su, kai tsaye studio na biyu ta wuce domin yau ne za ta fara gabatar da sabon shiri da za a fara a tashar su. Ƙarfe shaɗaya da rabi saura minti huɗu ta gani lokacin da ta duba agogon hannun ta. Ta ja dogon numfashi kafin ta buɗe studio ta shiga. Zaro ido waje ta yi ganin wanda ke zaune akan kujera tareda baƙon su na mako. Gefen C Y ta tsaya wanda ke ta faman saita Camera dan fara ɗaukan shirin. "C Y mi yake faruwa? ya na ga Iklimah a nan" "Sorry Sweery, Oga ya chanja ki" "Amma..." "We are going live in one, two, three" C Y ya faɗa yana ɗagawa Iklimah hannu. Iklimah ta yi wani fari da ido ta fara bayani kamar haka: ma su kallon mu kuna tareda gidan Talibijin na HILL TV, inda a dai-dai wannan lokaci mu ke gabatar mu ku da sabon shiri mai suna BAƘON MU wanda ni Iklimah Jibril zan gabatar. To a yau dai mun taho mu ku da babban baƙo. Jajirtaccen Ɗan kasuwa wanda duniya ta ke damawa da shi. Baƙon na mu dai shine Alhaji Isa Madara... Juyawa ta yi cike da ɓacin rai ta bar cikin studio ɗin. Wannan wani irin walaƙanci ne Oga ya ma ta haka. Kai tsaye ta wuce sama inda office ɗin Ogan su ya ke. Gaisawa ta yi da Sakatariyar sa wata mata wacce za ta iya kaiwa shekaru Arba'in zuwa Arba'in da biyar. "Madam Deborah Oga na nan?" "Yana ciki" ta amsa tana cigaba da latsa na'urar computer da ke gaban ta. Wucewa ta yi ciki zuciyar ta cike da jin haushin Ogan na su. Office ne da ya fi kowanne girma a cikin kamfanin. Mamallakin office ɗin na zaune kan kujera yana duba wa su takardu. A ɗan ƙaramin katako da aka ajiye a tsakiyar table da ke gaban sa an rubuta *MD Adamu Ribaɗo* "Ina kwana Sir" "Lafiya" "Sir na ga Iklimah ta karɓi shirin BAƘON MU" "Eh" ya faɗa ba tareda ya ɗago ya kalleta ba. "Sir amma ni aka ba wa shirin nan, ranan Jummu'a kai da kan ka ka jaddada mini cewa ni zan fara shirin nan, ni na tsara tambayoyi, ni ne na kira Alhaji Isa Madara..." "Kin zo da wuri?" Yai tambayar yana ɗago ma ta ƙananun idanun sa. "Sir inada uzuri, na yiwa C Y text tun da sassafe, kuma na zo kafin lokaci ya cika" "So?" "Sir wannan ba adalci ba ne, kuma..." "Fita" ya faɗa da ɗan ƙarfi. Ranta a ɓace ta fice daga office ɗin da sauri. MD ya bi bayan ta da kallo yana ƙara yabawa da wannan halitta ta Asiya. Kai tsaye office ɗin su ta wuce wanda su takwas ke amfani da shi. Mutum biyu ta tarar a wajen ta gaishe su kafin ta wuce kan madaidaicin desk ɗinta ta zauna, ta ajiye jaka da wayoyin ta sannan ta kifa kan ta a kan desk ɗin. Idan mutum ya ce yana son ka ka ƙi shi shikenan sai ya zama abin damuwa. Tunda ta fara aiki a wannan waje MD ke takura ma ta. "Da wani ƙaton tumbinsa a wajen" ta furta a fili tareda jan dogon tsaki... Yinin ranan gaba ɗaya a hasale ta ke saboda abinda MD ya ma ta. Ita gani ta ke ma da gangan yai hakan, dama tun asali Iklimar ya ke so ta yi shirin ba ita ba. Dama ƙwalele ya ke son yi ma ta... Kusan ƙarfe biyu na rana su ka fita ɗauko rahoto chan wani ƙauye. Faɗa ne ya ɓarke tsakanin manyan ƙabilu guda biyu da su ke wajen. Sun samu sun tattara bayanai sannan sun yi hira da mutane da dama a ƙauyen kasancewa an ɗaura labarin ne life. Faɗa ne da ya faro daga ƙona gona guda ɗaya sai abin ya zamo rikicin ƙabilanci akayita ƙone-ƙone. *"bayan Gwamnatin Jahar Congo ta turo jami'an tsaro zuwa wannan ƙauye, ƙura ta fara lafawa, yayinda iyayen da aka yi awun gaba da 'ya'yan su su ke cikin Alhini. Na tambayi wani jami'in tsaro wanda ya tabbatar mini da zaran sun gama bincike sun tabbatar babu hannun yaran nan guda biyar a sakawa gonar Malam Bala wuta za su sako su wa iyayen su. Muna fata dai wannan abin da ya faru zai tsaya a iya haka domin zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki. Ta ku ASIYA-SHAHIDA FARUQ BABA, tashar Hill TV"* ta ƙarasa maganar tana murmushinta mai shiga rai. Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da C Y ya ce cut. Ba yau ta fara kawo rahoto ba amma yau tunda ta fara ta ke jin ƙirjinta na mata nauyi. Ko dan ranta a ɓace ya ke oho. Ta ɗan ɗaura hannunta a ƙirji tana jin yadda ya ke bugawa da ƙarfi. Ikon Allah! Ko ranan da ta fara tsayuwa gaban camera ta kawo rahoto shekara ɗaya da ya wuce bata ji irin wannan tsoron ba. Lokacin da ta ke kallon camera ta sani tana fiskantar duniya ne, amma yau ji ta ke kamar mutum ɗaya ta ke fuskanta, kamar wannan mutumin da ke kallonta koma wanene idonsa yana ma ta nauyi, ya saka ma ta tsoro, ya kassara duk wani ƙwarin gwiwa da ta ke da shi. Za ka fahimci halin da ta shiga ne kawai idan har ka tuna yadda ka ke ji idan wani mutum da ka ke tsananin jin kunya ya zuba maka ido. Kana jin idon sa na yawo a ko'ina na jikin ka har hakan ya saka ma ka kasala har ma ka kasa iya aiwatar da komai, idan ma kana wani abu to ka dinga kuskure kenan. To ko dai Ubayd yana kallon news ɗin nan ne? Ta tambayi kanta. "You Ok?" C Y ya fargar da ita daga tunanin da ta ke yi Ta gyaɗa ma sa kai tana murmushi. "Ko dai saboda abinda MD ya miki ne? Yau gaba ɗaya kin yi wani iri. Babu wani spark lokacin da ki ke camera" Yana maganar yana lanƙwasa doguwar tripod da aka ɗaura camera a kai. "Ban san mi ya ke damuna ba, its like kamar mutumin da na ke jin kunya yana kallon program ɗin nan. I'm feeling his eyes all over me" "Ba ma her ba, his eyes. Lallai Aseey, ko kin yi sabon crush ne" C Y ya faɗa yana dariya. Ba yau Ubayd ya fara ganin report ɗinta ba. Infact akwai ranan da ya ke wajen ma ta ke ba da rahoto a gaban camera ɗin kuma bata taɓa jin irin haka ba. Idan ba Ubayd ba waye? Certainly not Umma da Abba saboda su kam tun ma kafin ta fara aikin sun kasance confidante ɗinta. Ta iya tuna ranan da aka ƙara mata matsayi ta zama field reporter sai da ta kira suka boosting confidence ɗinta kafin ta fara aikin. Idan ba Ubayd ba idan ba Abba da Umma ba, to WAYE? Ta faɗa tana kallon motar su da su C Y ke faman saka kayan aikin su ciki... *** GOVERNMENT OFFICE, CONGO STATE, dif...dif...dif... ƙarar da yatsar sa ke bayarwa kenan lokacin da ya ke buga table ɗin gabansa da yatsarsa manuniya. Tunda aka fara rahoton ya ke kallo bai ɗauke idon sa ba sai da mai ba da rahoton ta faɗi sunan ta sannan aka ɗauke wajen zuwa announcer da ya ke chan studio yana ƙara commenting akan abinda ya faru a ƙauyen. Ya bibiyi labarin ne saboda shine abu na farko mai mahimmanci da ya aiwatar a wannan shekara wanda har an kusa cin rabi cikin ta. Mutane dayawa kallon hoto su ke ma sa. It has being a challenge lokacin da aka kira shi da gaggawa aka sanar da shi faɗan daya taso a ƙauyen Kayal ɗin. Gwamna baya ƙasar dan haka shine ya ke da damar ba da umurni a aiwatar da duk abinda ya dace gameda matsalar. Tuni ya rattaba hannu a takarda wajen tura jami'an tsaro ƙauyen domin daidaiton lamurra a wajen. Ya ji daɗi da reporter ɗin ta yabawa Gwamna duk da dai shi da yai aikin ba Gwamna ba ne, da alama ko dai ta manta cewa Gwamna baya gari ko kuma dai ta furta Gwamna ne a matsayinsa na wakilin Gwamna ɗin. Gidan Talabijin na HILL TV ba ta Gwamnati ba ce shiyasa ya damu da ganin rahoton daga tashar maimakon CONGO NEWS wacce ta ke gidan Talabijin na gwamnati ba lallai a yaɓawa Gwamnati baƙin fenti ba idan har ba su yi abinda ya dace ba sai ma ayi ƙoƙarin kare su. Bai ida wannan tunanin ba wayar sa ta hau ringing. Mr Governor ya gani ɓaro-ɓaro a screen ɗin. Da sallama ya amsa wayar cikin muryarsa mai sanyi. Daga ɓangaren Gwamna kuwa ko amsa sallamar bai yi ba ya ce ma sa maganan Albashi da zai sa hannu akai ya bari sai ya dawo tukunna. Deputy Governor ya ce "Mr Governor nan da kwana shida fa kenan " "To mutuwa za su yi kafin kwana shidan?" Bai ce mishi komai ba har ya gama magana ya kashe kiran. Yayi tunanin ya kira ne domin yai ma sa magana akan faɗan da aka yi a ƙauyen Kayal may be ma ya yaba ma sa akan ƙoƙarin da yai wajen daƙile faɗan da wuri amma shi damuwar shi kada ya saka hannu a bawa mutane Albashinsu har sai ya dawo. Yau Albashin ya shigo daga gwamnatin tarayya, kwanan wata ya kama ashirin da bakwai idan aka ƙara kwana shida zai zama uku ga wani watan kenan, mutane za su ji jiki. Minene amfaninsa idan har a matsayinsa na mataimakin Gwamna ba zai iya aiwatar da komai na cigaban al'umma ba idan Gwamna baya nan. Ya tabbata kenan shi hoto ne. *** Lokacin da Asiya su ka koma office har anfara kiraye-kirayen sallar Maghriba. Tana shiga office ɗin su aka sanar da ita saƙon MD da ya ke nemanta. A gajiye ta wuce office ɗinsa, ta sani ƙorafi ne zai yi ba komai ba. Tunda a wajensa kullum ba ta iya aiki ba. "Miye matsalar ki ne Asiya?. Today's report was full of crap, sati biyu Gwamna baya gari amma kina ta faɗin Mai girma Gwamna ya turo jami'ai, Mai girma Gwamna ya damu da talakawansa. Give credit to whom credit belongs. Kina ganin da Gwamna Saminu Bacci ne zai tura jami'an tsaro cikin ƙanƙanin lokaci haka? I'm dissappointed in you" Ita kwata-kwata ta manta da cewa Gwamna baya ƙasar to ko yana nan ai Deputy Governor hoto ne. Ba abinda ta taɓa jin ance yayi sai shegen yin ado kaman mace. Indai SSK ne ko mace sai albarka wajen iya ado. Chief Editor na su da ke zaune a office ɗin ya kalli Asiya ya ce " miya faru na ga rahoton ki na yau ba wani armashi, ba ki da lafiya ne?" "no Sir, Ummata ce ba lafiya" Asiya ta faɗa ranta a ɓace. "Allah ya bata lafiya" Ta amsa ma sa da Amin. Da hannu ya ma ta nuni da ta fita daga office ɗin. Bayan ta fita Chief Editor ya kalli MD ya ce " mutumina ka mata a hankali. The girl is good ba wanda ya fi ƙarfin kuskure" "Idan har bama nunawa jama'a goodness na Mataimakin Gwamna kullum kallon hoto za a dinga ma sa. Wallahi da shine Gwamna da jahar nan ta fi haka cigaba cikin shekaru ukun nan. S S Kachallah mutum ne da ya san darajan ɗan Adam, he's a man of vision and mission" "Ni zan gaya maka halin Prof Kachallah tunda ya koyar dani lokacin ina Masters ..." daga nan su ka buge da hiran mataimakin Gwamnan. Asiya na fita daga office ɗin MD ƙasa ta koma wajen office ɗin su ta ɗau jakarta ta fito. Wani mahaukacin yunwa ke cinta ga gajiya a haka tafito daga farfajiyar gidan Talabijin ɗin. Da Ubayd na gari da shi za ta kira ya zo ya ɗauketa amma yanzu sai dai ta nemi abin hawa. Tana tsaye C Y ya fito da tsohuwar baƙar roba-roba ɗin sa. "Ke kalar mota ce da na miki lift zuwa gida" ga faɗa yana dariya. "Ƙaniyarka C Y, kana nufin tafiya za ka yi ka barni kenan" Ɗan dawowa yai da baya ta hau mashin ɗin sannan ya ja suka tafi. Suna tafiyan suna taɗi saboda Clement Yohanna (C Y) akwai surutu shima kamar Asiyar shiyasa ma tasu ta zo ɗaya. A ƙofar gidan su ya sauketa yana faɗin ta gaida ma sa da Umma. Da sallama ta shiga gidan na su, Inna Yaha na faman jan ruwa a rijiya amma ba ta amsa sallamar ba. Ko ba ta leƙa kitchen ba ta san sai yanzu za'a ɗaura abincin dare ko kuma yanzu aka fara girkin. Sannu da aiki ta mata duk da ta san ba amsawa za ta yi ba. Wucewa ta yi ɗakin Ummanta wadda shine ɗaki na biyu cikin ɗakuna uku da su ke jere waje guda. A kan sallaya ta samu Umman ta idar da sallah tana jan carbi, ta san ba za ta amsa gaisuwarta ba har sai ta gama azkar ɗinta shiyasa ma ta wuce wajen wardrobe ta buɗe ta fito da wata doguwar riga mai laushi, rigar guntun hannu gareta. Kayan jikinta ta cire ta saka doguwar rigan. Lokacin da ta zauna bakin gado tana naɗe wandon jeans ɗin da ta cire ne Umma ta fara mata magana da yaren Kurame inda ta ke tambayarta ya aiki, obviously ta ga rahoton da Asiyan ta kawo ɗazu a TV. Itama Asiyan ya jiki ta mata tareda tambayarta ko ta sha magani. Ƙarfe bakwai da rabi da minti takwas bayan ta idar da sallan Isha Cornflakes ta haɗa da madara ta fara sha tanayi tana danna wayarta. Kiran Ubayd ne ya shigo wayarta amma har ta katse ba ta ɗauka ba saima tsaki da ta yi. Bayan ya jera kira biyu ba a ɗauka ba sai a na ukun ta ɗauka amma ba ta yi magana ba. "My Aseeya" ya faɗa da murya mai sanyi. Tasirin da sunan yai ma ta ne ya sa ta yin guntun murmushi. "Tuba na ke ranki shi daɗe. Na san na yi laifi amma a bani dama na faɗi uzuri na" Still shiru ba ta ce komai ba "Mine kina ji na?" "Mine" Asiya ta ɗan jinginar da kanta jikin gadon Umma sannan ta ce "ni mi zan ce tunda Matan Lagos sun ɗauke mun kai. Yau tun da sassafe da muka yi waya ba ka sake waiwaya na ba sai yanzu. Na san ka kalli report ɗina na yau amma ko ka kira ka tambayi lafiyata, you dont even care ko na dawo lafiya ko ban dawo ba, kawai kai..." haka ta yi ta rantings har sai da ta gaji da kanta ta yi shiru, a lokacin ne kuma Ubayd ya samu damar lallaɓata dan ya san halin kayan sa indai tana kwarwa to ba a katseta har sai ta gama. Bayan ta karɓi haƙurin sa ne suka bige da hiran masoya ba ta ma ji shigowar ƙaninta Aliyu ba sai kawai gani tayi ya ɗauke kofin cornflakes da ke gabanta ya fara sha. Tana ma sa magana da hannu amma inaa bai kulata ba sai ya ma koma gefe ya shanye cornflakes ɗin tas. Bayan ya gama kuwa ya dangwarar mata da kofi a wajen yai gaba. Shigowan Umma ɗakin ne ya sa ta yi sallama da Ubayd akan za ta kirashi anjima. Da hannu Umma ta gaya ma ta cewa ta je ta samu Abbansu a falo yana nemanta. Sanda za ta wuce falon Abban ta kula da Inna Yaha da ke ta kwaran-kwaran a kitchen tana rabon abinci, babu wuta kuma torchlight da ta ke amfani da shi ya dafe ba haske sosai. Ba ta taɓa gajiya da mamakin halin Inna Yaha. Asiya ta yi sallama bakin ƙofar falon Abba. Abba ya ce ta shigo. Abba dattijone da kallo ɗaya zaka ma sa ka san ya doki shekaru sittin da biyu zuwa da biyar. Fari ne sosai a lokacin ƙuruciya amma yanzu ya fara dafewa, fiskarshi da kanshi yana yalwacce da gashi wanda kusan ya riga ya zama fari gaba ɗaya sai tsilli-tsillin baƙi da ba za a rasa ba. Bayan ta gaisheshi ne ya ke tambayarta gameda ƙauyen da su ka je yau ɗauko rahoto. Bayan sun yi alhinin abinda ya faru tare ya sanar da ita musabbabin kiranta da yai. Magana ce akan admission da ƙaninta ya samu a Congo University wanda ya dage akan ba zai zauna a hostel ba sai dai ya dinga jeka ka dawo, shawaran Asiya ya tambaya ko dai ya siya ma sa babur kaman yadda Habib ɗin ya buƙata ne?. Abba ya jima da retire har yanzu kuɗin pension ɗin sa su ke lallaɓawa. Ba dan Allah yayi ita da Umma suna sana'a ba da abubuwan ba za su zo da sauƙi ba. Ubayd ma yana nasa ƙoƙari akan mahaifinsa sosai. Bikinta da na Faty da za ayi Abba ke yiwa taru dan haka maganar siyan Babur bai taso ba. Za ta yiwa Habib magana, gigin samartaka ke ɗibanshi yana ji yanzu ya gama sakandare zai shiga Jami'a. Bayan ta bar wajen Abba ɗakin su ta koma inda Umma ke faman tura tuwon da aka miƙo ma ta. Sau ɗaya ta kalli tuwon ta kauda kai. Ga abinci ba za ayi da wuri ba gashi ba zai taɓa yin daɗi yadda ya kamata ba. Kafin ta kwanta sai da su ka sake yin waya da Ubayd sannan ta kira Queen Bee su ka yi maganar Salon ɗin su... *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 02 *** A chan wani ƙaton gida da ke GRA wasu manyan mutane ne guda huɗu ke zaune a wani katafaren falo daya amsa sunan falo saboda girma da kuma irin kayan alatu da aka zuba a ciki. Ɗaya daga cikin su wanda kusan shi za a kira da babban su ya kalli wani da ke sanye da farar shadda da farin hula ya ce "Kachallah kana ganin za mu samu abunda mu ke buƙata a wajen sa?" Kachallah ya ce "inada yaƙinin haka Yallaɓai. Shi mutum ne mai biyayya" Wani mai baƙin suit ya tari bakin Kachallah da cewa "inada shakka akan wannan" "Mr Paul mi kake so ka ce, ba dai kana nufin za a rusa tsarin wannan gwamnatin ba..." "Mr Paul, Alhaji Kachallah wannan ba abun ɗaga hankali ba ne. Har yanzu akwai sauran lokaci dan haka zamu cigaba da saka mishi ido kafin lokacin ya cika. Ko mi ka ce Yallaɓai?" Yallaɓai ya kalli Mutumin da yai magana sannan ya maida dubansa ga Alhaji Kachallah da Mr Paul. A hankali ya fara shafa gemun sa yana yi yana murmushi. Murmushin Yallaɓai na da ma'anoni daban-daban amma a wannan lokaci dukkan su sun yarda cewa yana nufin su kwantar da hankalin su ne, wato akwai nasara a dukkan tsare-tsaren su. *** LADIES HALAAL SALON & SPA waje ne da ya amsa sunan sa, domin kuwa dukkan abubuwan da ake gudanarwa a wajen suna ƙoƙarin tafiya da tsarin da bai kaucewa tsarin musulunci ba. Waje ne da Asiya-Shahida, Queen Bee da Alhaja Oyiza su ka buɗe saboda samawa mata wajen kula da jikin su. Ma'aikatan wajen dukkan su mata ne. Cikin ayyukan da su ke gudanarwa a wajen akwai wanke gashi, drying da kuma stretching, suna gyaran farce (menicure and pedicure). Ana kitso da kuma ƙunshi sannan watanni biyar da su ka wuce da su ka dawo sabon shagon su da ke anguwar GRA suka fara gyaran jiki da spa treatment a wajen (wanda ya haɗa da body, hair and foot massage, facial treatment da sauran su) Shigowar Shahidah sashen da ake yin gyaran gashi da kitso ya sa wajen yai wani irin tsit. Precious da ke yiwa wata mata kitson wig ta tsaya da kitson tana kallon Shahida jikinta na ɓari. Matar ta ɗan ɗago ta ce "ya ki ka tsaya?" Tunda ba sa saida gashin wig kenan matar ce ta zo da abinta. Shahida ta faɗa a ranta. Precious ba ta san ma Shahida na cikin shagon na su ba da ba za ta yi gigin fara yiwa matar nan kitson wig ba. Ta san dokar shagon su amma wannan matar Comissioner ce, duk da ta hannun Queen Bee ta zo ta tabbata za ta raɓi maiƙo a jikin matar, shiyasa da matar ta nuna kitson wig za a mata ba ta iya yi mata musu ba. Shahida ta ƙaraso gaban matar sannan ta kalli Precious ta ce " ina bawa mutane dama ɗaya tak a rayuwa, na ƙarshe kenan da za ki sake taka mana dokan wannan shago. Ki maida mata kuɗinta ta bar mana waje" "Malama ban gane mi ki ke cewa ba. Da alama ba ki san ko ni wacece ba ce" "Duk wanda ya shigo wannan waje domin a masa wani abu a nan to sunan sa customer. A dalilin an ɓata miki lokaci za a maida miki kuɗin ki dan haka ki wuce wajen da su ke yin irin wannan kitso a ƙarasa miki a chan" "What nonsense" matar ta faɗa a fusace tana miƙewa tsaye. "Idan kin fita ki ɗan ɗaga idon ki sama za ki ga sunan wannan waje. Saka gashin wig baya cikin services na mu" Daga haka Asiya-Shahida ta bar wajen. Tana jin matar tana ta zage-zage amma ko ajikinta. Ta yiwa matar farin sani. Habiba sunanta a ƙasan layinsu ta taso. ta tsula bariki sosai kafin ta auri kwamishinan ilimi shekaru uku da suka wuce. Dole ta yi magana da Queen Bee ta jawa Precious kunne tunda ita ta bata aiki. Idan irin haka ya cigaba da faruwa Salon ɗin su zai zama babu wani banbanci tsakaninsa da sauran gama gari... ** Shahidah na zaune tana zanawa Amarya Layla lalle a hannu ta ji matan da ke wajen sun saka ihu. Basma ta ce "Jennifer ƙara mana volume mu ji mi ya ke cewa" Kafin ta gama maganar ma ta riga ta ƙara volume ɗin. Muryan daya doki kunnen Asiya ne ya sa ta jan dogon tsaki ba shiri. "Yanzu dan Allah saboda wannan wawan ku ke ta ihu" Banza su ka yi da ita suka cigaba da yaba mutumin da ke magana a cikin TV. "Ki ga idon sa dan Allah, ko idon kaɗai Allah ya bashi wallahi an zuba ma sa baiwa" wata daga cikin ƙawayen Amarya da ake wa Lalle ta faɗa. "Allah ya shiryeku gaskiya. Mutum tsohai-tsohai da shi ku dinga wani drooling akan sa kaman wasu ƙwailaye" "Ke dai 'yar baƙin ciki ce Asiya. Allah ya isan ma SSK ɗin mu za ki kirashi tsoho" Kafin ta yi magana kuwa Asabe ta ce "ni kin san Allah yanzu haka idan da za ace na zaɓi tsakanin SSK da kuma Ubayd ɗinki Asiya Wallahi Tallahi SSK zan zaɓa" Asiya ta fusata ta kaiwa Asabe duka Asabe ta kauce tana yi ma ta dariya. Ranan har Asiya ta gama yiwa Amarya Lalle ba ta dena diri ba. Hayaƙi ne kawai bai fito daga bakin Asiya ba saboda yadda ta dinga faɗa akan an haɗa masoyinta Ubayd da SSK... ** "Gashi nan ai ya ƙi biyan albashi ya bar mutane da yunwa. Idan ka yi magana kuma a fara ganin baƙin ka mtsww" "Mine kina da abun dariya Allah. Tunda mu ka zauna a nan ba hiran da mu ka yi sai ta SSK. Ki rage ƙiyayyar ki gareshi please. Abun ya fara yawa" "Amma Ya Ubayd..." "Yanzu dai a ajiye maganar sa a gefe tukunna. Albishirin ki" Asiya ta haɗe rai ta juyar da fiska gefe. "My Aseeya haka zan tafi gida ba tareda kin min murmushinkin nan mai sanyaya min zuciya ba" "Ka je SSK ya maka murmushin tunda ka damu da shi" "Mi zan yi da murmushin ƙato bayan inada kyakykyawar budurwa a kusa da ni" "Dama ina so na miki maganar gida ne amma tunda kinyi fushi shikenan" "Dan Allah an gama gyara kitchen ɗin?" Ta faɗa cike da excitement. "Wagga Bafulatana ba ta da kunya samsam" "Eh ɗin" ta faɗa tana murguɗa ma sa baki. "Kinga ɗan bakin nan da Allah zai kaimu wata biyar da kwana shauku da na jima da maganin sa" Asiya ta yi saurin sunkuyar da kai tana rufe bakinta da tafin hannu tana murmushi cike da jin kunyarsa. "Na rufe bakin ko?, gara ma ki sani a matse na ke wallahi. Abba dai ya cuceni daya saka bikin nan da nisa haka. Tunda Mustafan Faty bai gama shiryawa ba da anyi namu bikin idan ya so sai ayi na su daga baya" "Ya Ubaydu wai ka je inji Abba" muryan ƙaninsa Musa ya doki kunnen sa. "Musa kana so in zaneka ko? Za ka faɗo kanmu ba sallama sai kace wani dabba" Musa ya fece daga wajen da sauri tun kafin Ubayd ya damƙeshi dan ya san halin yayan na sa sarai. "Barin je wajen Abba" "Idan ka je ka kai ma sa ƙorafin ka ƙila ya chanja ra'ayi" "Ahaf ashe ba ni ɗaya na matsu ba kenan" Ba ta amsa ma sa ba ta wuce ɗaki da sauri. Murmushi yai mai daɗi yana addu'ar Allah ya kai shi lokacin da Asiya Shahidah za ta zama mata a gareshi. Asiya na shiga ɗaki ta faɗa kan gado. Murmushi ta ke yi tana jin tsananin shauƙin son Ubayd. Ba za ta ce a matse ta ke ba amma harga Allah ba ta so aka saka bikin su wata shida ba, ta ɗauka wata uku ko huɗu Abba zai sa. Koda yake duk dalilin Mustafah wanda zai auri Faty aka kai bikin da nisa saboda ya ce bai gama shiri ba. Suma ɗin cikin wata shida kam sun gama shirya komai. Ƙaran shigowar notification ta ji a wayarta da ke gefen gado, da sauri ta jawo wayar dan ta san ba zai wuce saƙon favourite poet ɗin ta ba ne wato KaSaSa. Ai kuwa tana buɗewa taga saƙon email ɗin daga KaSaSa ce. Tunda ta subscribing a website ɗin ta koyaushe ta ɗaura sabon poem za ta gani a email ɗinta. Ta karanta poem ɗin ya fi sau biyar kafin ta miƙe ta je ta ɗauko littafinta da ta ke rubuta duk poetry na KaSaSa a ciki, ta rubuta sabon poem ɗin da aka turo. Idan Ubayd ya zo sallama dole ne ta karanta mishi poem ɗin dan ya taɓa zuciyarta sosai. A zuciyarta ta ce Allah ya zubawa KaSaSa baiwar kalamai. *** Motoci guda biyar ne su ka shigo wani katafaren gida, irin gidajen nan ne da ƙusosin gwamnati da manyan 'yan kasuwa kaɗai ke iya mallakan su a wannan ƙasa, shi ɗan talaka sai dai ya gani kawai ya buɗe baki ya cika zuciyar sa da buri sannan ya kaɗa kai yai gaba, amma gidan yafi ƙarfinsa. Motocin sun tsaya ne a farfajiyan gidan. Motar da ke tsakiya wacce ta fi kowanne kyau wani bodyguard ya buɗe ya fito daga gaban motar da sauri sannan ya buɗe ƙofar baya. Ƙafafuwansa da ke sanye da designer sneakers ruwan toka ƙirar Dior ne suka fara sauka ƙasa kafin sauran jikin ya biyo baya. Dogo ne da tsayinsa zai kai kamu ɗaya da ɗigo takwas a ma'unin meter (1.8m) kusan a ido za ka ƙiyasta tsayinsa da ta shahararren ɗan film ɗin ƙasar India (Bollywood) wato Amitabh Bachchan. Baƙi ne sosai irin baƙin da ya fi kama da na larabawan ƙasar Sudan. Sai dai na shi baƙin ya haɗu da hutu da jin daɗi sai ya zama har wani sheƙi ya ke yi yana ɗaukar ido. Idanunsa sun fi ko ina ɗaukar hankali a jikin sa. Fari fat da ɗigon baƙi wanda yai kamar an ɗiga baƙin tawada a cikin ruwan madara. Zara-zaran gashin ido da kuma gira da ke cike da baƙin gashi su suka haɗu suka ƙara ƙawata manyan idanunsa. Baƙin saje da ya haɗe da fiskarsa zuwa gemu da gashin baki suka bawa fiskar kyau da kamala. A zahiri kallon yaro ake ma sa saboda kyaun jikinsa da ke ɓoye shekaru ,da kuma yadda akoda yaushe ya ke shiga irin ta Matasa. A ranakun Jummu'a da lokutan zuwa wajen taro na musamman kawai ya ke shiga irin ta Malam Bahaushe, amma fiye da rabin shigar sa shiga ce ta mutanen ƙasar waje. Ba abun mamaki ba ne ka ga SSK sanye da Tshirt da jeans a office tun ma kafin ya shiga siyasa har zuwa yanzu kuwa da su ke kan Gwamnati. Kasancewar ya samu sa'ar karatu da wuri ya amshi Phd ɗin sa yana shekaru ashirin da bakwai ne yayinda ya kai matsayin Professor a shekarun sa talatin da biyar, kusan shekarun da ake ɗiba ma sa kenan idan an kalleshi wanda a zahiri an zaftare ma sa kusan shekaru goma kenan cikin shekarun sa. Yanzu ma SSK na sanye ne da riga mai dogon hannu kalar sararin samaniya, irin yadda sama ke kasancewa a ƙarshen yammaci kafin dare kamar wajajen ƙarfe biyar da rabi zuwa shida ɗin nan, musamman a lokacin sanyi. Wandon jikin sa ta jeans ce kalar light blue, yana sanye da agogo da kuma zoben azurfa a yatsarsa ta tsakiya da ke hannunsa na dama. Tuni bodyguard ya amshi jakar hannunsa bayan ya sara ma sa yana ƙame jiki tareda faɗin "Excellency" Mataimakin Gwamna kenan *Professor Saifuddeen Sa'ad Kachallah* ingarman namiji mai cikar zati da haiba wanda a yanzu ya ke riƙe da jahar saboda Gwamna baya gari. Kai tsaye cikin gidan sa ya wuce wanda ya gina da halaliyarsa tun ma kafin ya shiga siyasa dan ya ƙi komawa gidan gwamnati. Daga falon farko ba kowa sai dai yana iya jiyo hiran matarsa a ɗaya falon da wasu matan. Ya haura matattakala da zai kai shi sama inda ɗakunan gidan su ke. Ɗakin ƙaramin ɗan sa ya fara leƙawa. Yaron ɗan kimanin shekaru shida na zaune akan gado yana buga game a laptop ɗin sa. Sa'ad Saifuddeen Sa'ad Kachallah kenan wanda kowa ke kiransa da Junior. Ya kissing goshin yaron yana tambayarsa ko yayi homework ɗin sa yaron ya amsa da eh. Ya shafa kan yaron sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin. Bai leƙa sauran ɗakunan yaran na shi ba saboda kwana uku da su ka wuce su ka tafi hutu. Babbar 'yar sa Nana Khadija ta tafi gidan ƙanwar matarsa yayinda Aisha da su ke kira da Mahira ta tafi wajen Dadda wato kakar sa. Wanka SSK yai sannan ya sanya farar jallabiya ya fito saboda kiran sallah da ya ke jiyowa daga masallacin kusa da gidan sa. Hajiya Bilkisu na zaune a falonta tareda wasu mata guda uku. Ɗaya matar Comissioner ce, ɗaya kuma matar wani Senator ce, sai ɗayar kuma tsohuwar comissioner of Health ce wato Dr Madam Helen Audu. "Yanzu dai ina so komai ya tafi dai-dai gobe, kar ya zama saboda first lady ba ta nan sai mu kasa gudanar da taron yadda ya kamata" "Hajiya Bilkisu kar ki ji komai, ai abinda ki ke yi a wannan jaha ko firstlady albarka" inji matar senator Bilkisu ta yi ƙasaitacciyar murmushi ta ce "indai akan cigabar jahar nan ne dole na yi ƙoƙari wajen ganin komai ya tafi dai-dai" Madam Helen ta ce "Hajiya Bilki ni zan wuce" "Nagode Mommy, sai mun haɗu goben" Hajiya Bilki ta faɗa da sigar girmamawa saboda Madam Helen ta girme ta sosai, idan ba ta yi sittin ba to za ta kusa kaiwa hakan. Bayan tafiyar Madam Helen da kusan minti shabiyar sannan sauran matan su ka tafi sai a lokacin Hajiya Bilkisu ta samu damar sauke nannauyan ajiyar zuciya tana tararradin yadda gobe zai kasance. Wannan ne karo na farko da za ta gudanar da babban taro ita kaɗai. Taro ne na matan Gwamnonin Arewa wanda tun kafin tafiyar Firstlady aka tsara shi, ita ne ta kawo shawaran kuma Firstlady ta amince da shi sai dai rashin Firstlady a gari ya sa aka yi tunanin ɗaga taron har sai ta dawo amma Hajiya Bilkisu ta nuna ba sai an ɗaga ba za ta wakilci Firstlady a wajen taron. Bayan tafiyar matan nan ta lalubo wayar ta ta cigaba da bibiyar yadda za a sauki baƙin gobe ba tareda an samu matsala ba. Lokacin da ta samu nitsuwa ta haura sama ɗakinta ta wuce ta yi wanka ta saka kaya sannan ta fara sallah, ta haɗa sallar La'asar, Maghriba da Isha wanda zirga-zirga bai sa ta samu yinsu akan lokaci ba. Ƙarfe goma da kwata ta shiga ɗakin mijinta wanda ke kishingide akan gado yana danna waya yana murmushi. Zuciyar Bilkisu sai da ya kusa bulloƙowa waje saboda tsallen da yai, kamar walƙiya ta zo ta ɗauke wayar hannunsa tana huci tana duba abinda ya sa shi irin wannan murmushi haka. Shafinsa ne da ya ke rubuta poems ya ke dubawa, ba mamaki yana dariya ne saboda yadda mabiya shafin ke alaƙanta shi da mace. Saƙon wani fan ɗin sa ta gani da ya ke cewa shi a duniya ba macen da ya ke so kamar KaSaSa. "Darling har yanzu ba za ka ce mu su kai namiji ba ne ba mace ba" sai kuma ta yi saurin gyara maganarta da cewa "gara su cigaba da yi maka ganin macen, kafin yanzu mata su dinga damunka da waya" Mayar ma sa da wayar ta yi tana murmushi " My Darling ka san ina kishin ka dayawa" Bai ce ma ta komai ba ya cigaba da duba saƙonnin masoyan na sa. "Ka ci abinci?" ta tambaya lokacin da ta kwanta gefen sa. "Na leƙa ɗakin Junior ya riga yayi bacci, i guess tare ku ka ci dinner kenan" Still bai amsa ma ta ba. Ta sani idan SSK yana harkan rubuce-rubucen sa baya taɓa ba da hankali a wani abun daban, shiyasa ta haƙura da maganan ta manna ma sa kiss a kumatu tareda faɗin goodnight ta ja bargo ta kwanta. Gobe babban rana ce a gareta shiyasa dole daren yau ta samu isasshen bacci. A wajen SSK ba komai ya hanashi kula matar ta sa ba sai ganin cewa ɓata lokaci ne a gareshi ya faɗa ma ta kuskurenta. Shi ba ma'abocin yawar magana ba ne hakan ya sa tun farkon auren su ya ke ɗagawa Bilkisu ƙafa, sai dai maimakon abubuwan su ragu sai ya zama ƙaruwa kawai su ke yi. Irin rayuwar da yai buri idan yai aure ba ita ce rayuwar da ya ke yi yanzu ba. A wassu lokutan yakan yi tunanin idan da Misturah ya aurah abubuwa ba za su zo ma sa haka ba. Kafin ya faɗa soyayyar Misturah ta kasance abokiya a gareshi wacce ya ke iya gayawa damuwar sa, wacce ya ke iya neman shawara a gurinta kuma ya samu shawara mai kyau. Duk da sun taso gida ɗaya babu wannan kusancin tsakanin sa da Bilkisu. Har yau da su ka kusan cika shekaru shabakwai da aure ba zai ce ya gama sanin halin Bilkisu ba haka nan itama yanada yaƙinin ba ta san wanene Saifuddeen ba. Suna rayuwa ne tareda shamaki kamar labule a tsakanin su. Tun kafin ya zama Mataimakin Gwamna baya samun kulawar daya dace a wajen Bilkisu sannan daga shiga gwamnati abubuwa suka sake taɓarɓarewa. A lokutan dayake cikin ƙunci ya ke buƙatar nitsuwa daga matar sa. A lokutan da kansa ya ɗau zafi daga harkokin gwamnati ya ke buƙatar samun mafaka a wajen matar sa. A lokutan ne za ka ga Bilkisu ta shagalta da harkokin siyasa ko kasuwanci. Tunda ta sako maganar taron matan Gwamnoni da za ayi baya tunanin ta sake saka shi a lissafinta. Idan har ta tuntuɓeshi to tana neman shawara ne bisa jadawalin da ta tsara na abubuwan da za a gabatar ranan. SSK ya juya ya kalli Bilkisu da ta ke gwarti alamun baccinta yayi nisa kenan. Kafin ka yi aure duk irin waɗannan ƙananan abubuwa ba ka saninsu sai kun zauna tare na wani lokaci. Akwai lokutan da idan zai kwanta sai ya saka auduga ko earbud a kunnensa saboda yadda Gwartin Bilkisu ke hana shi bacci, a hankali har jikinsa ya saba da hakan. Aure sai da haƙuri, abunda ake gayawa sabbin ma'aurata kenan. Alokacin ba sa gane me ake nufi da haƙuri har sai sun kwana biyu da aure. A farkon auren su yayi haƙuri da lokutan da zai shiga banɗaki yaga Bilkisu ta jefa pant mai haɗe da pad cike da jini a loundary basket ɗin su. Ko kuma a lokutan da ta ke fama da mura ka ga tissue papers da ta face majina da shi a kan gadon su. Ba zai taɓa mantawa da ranan da ya shiga banɗaki tsantsin majina da aka fyace a ƙasan tile ya ɗebeshi ya faɗi ƙasa ba. Yayi haƙuri da kasancewarta ba ta girki saboda a gidan su bata yi, duk da kuwa girki na cikin abubuwan da ke taɓa ma sa zuciya. Girkin Misturah na ɗaya daga cikin abubuwan da suka saka shi faɗawa soyayyarta tun bai shirya hakan ba. "Saif wannan pepper soup ɗin yana narka zuciyar namiji yana saka mishi nitsuwa. Inada yaƙinin koma mi yake damunka idan ka ci wannan peppersoup ɗin za ka samu sanyi" abinda ta faɗa kenan lokacin da ta miƙa ma sa ɗan ƙaramin food basket da ta riƙo ma sa. Misturah ta yi gaskiya domin ranan da ya sha wannan peppersoup ɗin ya samu nitsuwa. SSk ya kai hannunsa ya shafa gashin wig da ya ɗan bulloƙo ta gefen hular baccin Bilkisu. Yayi haƙuri da kasancewarta mai saka gashin wig duk da kuwa warin gashin na tada ma sa hankali. Namiji na son mace da za ta fahimceshi, ta saurari maganar sa. Sai dai Bilkisu ba ta ɗaya daga cikin irin matan nan. Sau dubu Bilkisu za ta yi iƙirarin tana tsananin son shi tana kuma kishin sa, hakanan kuma sau dubu ba za tayi abubuwan da zai cire shamakin da ke tsakanin su ba, har ta samu damar mallake zuciyarsa. A lokutan kaɗaici he find solitude in poetry, shiyasa ya ke ɓoye kansa da sunan KaSaSa wanda acronym ne na sunansa. SSK yai murmushi ganin Bilkisu ta maki kanta tareda sosa tsakiyar kan. Duk wani mulki daya ke da shi ya tsaya a bakin ƙofar gidan sa ne, a cikin gida shi mijin Bilkisu ne, Abban Nana, Mahira da kuma Junior. SSK ya muskuta ya jawo Bilkisu jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, rabon daya samu nitsuwar miji da mata daga gareta kusan sati biyu kenan. "Darling na gaji" ta faɗa cikin magagin bacci "Kar ki damu ba abinda zan yi" ya furta a hankali wani abu na sukan ƙirjinsa... *** "Kina jina? zan turo miki kuɗin idan na dawo daga office. Ya jikin Muttaƙa? Tana saƙale da waya a kunnenta yayinda ta ke ƙokarin ɗaura agogo a hannunta. "Sumayya ki tabbatar Ale bai san da kuɗin nan ba. Kuɗin maganin Muttaƙa kuma ki tabbatar an siyi duka magungunan shi" Ajiye wayar ta yi ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta wuce inda Umma ke ƙoƙarin raba abun kari. Kunun gyaɗa ta yi da ƙosai da kuma soyayyen dankalin Hausa. "Umma zan wuce" ta faɗa da yaren kurame Umman ta amsa ma ta da cewa ta tsaya ta ci abinci. "Zan makara Umma, amma ki haɗa min kunun da dankalin in tafi da shi office" Murmushi Umman ta yi sannan ta fara neman inda za ta zubawa Asiya kunun. Minti shida kacal ta ƙara aciki ta fito ɗauke da jakarta da kuma ledan da Umma ta ba ta. Motar Ubayd na jiranta a ƙofar gida dan haka tana shiga ya ja motar da gudu. Gaisawa su ka yi a tsanake ta cigaba da duba wayarta tana bitar report ɗin da ta haɗa jiya. Tafiyar minti shabiyu ya kaisu ma'aikatar su ta yiwa Ubayd sallama ta shige ciki yayinda shima Ubayd ya wuce Asibiti. Tana shiga office ɗin su ta printing report ta wuce da shi office ɗin Editor I. "Weldone Shahida" ya faɗa lokacin da su ka gama duba report ɗin tare wanda kusan gyaran da ke ciki kaɗan ne. Tana komawa office ta samu sauran colleages ɗinta suna hiran taron da za ayi yau a jihar ta su. Da SSK da matar sa Bilkisu duk babu wanda ke burge Asiya a cikinsu. "Shahida kin san wa za'a tura yau?" Shahida ta girgiza kai tana cigaba da latsa laptop ɗinta. Mike ya sake cewa " ina tunanin Abigail za a tura, gashi har yanzu ba ta iso ba" "Mike kar ka dameni dan Allah. Idan ba ta zo ba MD zai iya bawa wani ai, ko kai ko Usman" Ta sani magana ya ke son gaya mata akan kada ma tasa ran MD zai bari ta je ta covering report ɗin wajen taron da za ayi na matan Gwamnoni. Ba ta san mi ta tsarewa Mike ba a wannan office ɗin. Tun tana bautar ƙasa kafin a ɗauketa aiki yake sa mata ido cikin lamurranta. Ta cigaba da aiki tana yi tana shan kununta. CY ya shigo office ɗinsu da sauri. "Aseey ki je office ɗin MD yanzu-yanzu" "Miya faru?" Ya ɗaga mata kafaɗa ya fita da sauri. Ta yi saurin kurɓan sauran kunun daya rage sannan ta goge bakinta da tissue ta fice daga office ɗin da sauri tana lura da yadda Mike ke binta da mugun kallo. Ba ta da ikon yiwa MD musu lokacin daya sanar da ita cewa itace za ta kawo rahoton wajen taron da za ayi yau. Lokacin da za ta tafi ya ce "Asiya bana son shirme" "Ok Sir" Ta sani Abigail yai niyyar tura wa saboda Abigail ta fita gogewa a wajen aiki. Tunda aka buɗe gidan talabijin ɗin ta ke aiki da su kusan shekaru shahuɗu da suka wuce kenan. Rashin Abigail Manji ne ya sa MD ya waiwayeta. A wajen CY ta ke jin labarin wai Abigail tayi tafiya, jiya da daddare mahaifinta ya mutu a chan ƙauyen su. Ba su kaɗai ba ne 'yan jarida da su ka zo ɗaukan rahoto kusan kowanne gidan jarida sun aiko da wakilan su. CY ya fito da kayan aiki ya shiga saita camera ɗin. *** Chief of staff (COS) ne ya shigo ofishin mataimakin Gwamna da sauri hannunsa riƙe da ipad. "Your Excellency za ka so ganin wannan" SSK ya karɓi pad ɗin daga hannun COS ya danna kan video dake screen ɗin. Yar jarida ce a gaban hall ɗin da ake taron matan gwamnoni tana bada rahoto. "Kaman yadda al'umma su ka shaida irin almabazzarancin da akayi a wajen wannan taro wanda ake iƙirarin anyi shine saboda talakawa. Ko ta ina talaka zai anfana da mawaƙan nan Wizkid da Patoranking da aka ɗauko daga Lagos domin matan Gwamnoni su shaƙata da waƙoƙin su?. Yayinda matar mataimakin Gwamna wato Hajiya Bilkisu S Kachallah take magana akan yadda za a gina gidan marayu, talakawa na nan suna alhinin rashin albashi, rashin ruwa ga uwa uba malaman makarantar firamare da ke yajin aiki tun sati uku da suka wuce har yanzu Gwamnati ba ta waiwayesu ba. Na zanta da wasu matasa inda su ka bayyana mini cewa taron da Hajiya Bilkisu ta yi wani farfaganda ce kawai da ke son ɗauke hankalin talakawa daga matsalolin da su ka sha mu su kai..." Tsaida video ɗin yai ya miƙawa COS ipad ɗin "Your excellency kana buƙatar mu tuntuɓi gidan talabijin na Hill TV ne?" "A'a" COS na fita daga office ɗin SSK ya ɗau waya ya kira commisioner of finance... *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 03 "Aseey we are dead" CY ya faɗa lokacin da suka shiga mota za su koma office. "Ni fa ka ganni nan ba na tsoron ta ɓaci wallahi. Gaskiya ce zan faɗa ko da ba za ta yiwa wasu daɗi ba. Idan ban faɗi gaskiya ba miye amfanin aikin jaridan da na ke yi" "Dama kin fi kusa da MD ai" "Kai ka san wannan" Lokacin da su ka isa office Asiya ta ɗauka MD zai ma ta faɗa amma bai ce komai ba. Ta yi mamaki kam dan indai MD da ta sani ne to da tuni ya fara diri akan ta sako maganar albashi a rahoton da ta kawo. Awa ɗaya bayan SSK ya kalli rahoton Asiya, ya saka hannu aka sakewa ma'aikata albashin su, zuwa yammaci kusan fiye da rabin ma'aikata kowa ya ji alert ɗin albashinsa. Mintuna kaɗan bayan SSK ya sake albashi kiran Gwamna Saminu Bacchi ya shigo wayarsa. Duk da Gwamna Saminu ya girme shi da shekarun da ba za su wuce biyar zuwa shida ba, SSK bai chanchanci irin tsawan da Gwamnan ya masa ba akan ya sake albashi kafin ya dawo. Bayan ya ajiye wayar ne ya fara tunanin anya kuwa zai iya cigaba da irin wannan tozarcin.. *** Daf an kusa tashi aka kawowa Asiya Shahida letter daga office ɗin MD. Tana gama karantawa ta wuce office ɗin sa da sauri. "Sir yanzu aka kawo min wannan letter, ban gane ba. Two weeks suspension sannan ka maida ni copy editor" "Kafin ki tafi ki je ki reporting a wajen News Director" "Sir???" "Ba za ki sake airing komai ba har sai kin iya banbanta professional da personal affairs" Sai yanzu ta gane ashe shirunsa ɗazu ba yana nufin cewa ransa bai ɓaci da abinda ta yi ba ne. "Idan kuma ba ki gyara ba, Hill TV za ta iya ɗaukan mataki mai tsauri akan ki" Haƙuri ya ke so ta bashi ta sani kuma ba zata bayarba. "Shikenan Sir, nagode" daga haka ta fice daga office ɗin tana dunƙunƙune takardar da ke hannunta. Ko jira lokacin tashi ba ta yi ba ta ɗau jakarta ta bar station ɗin... Asiya na zaune akan stool a ƙofar ɗakinsu tana yiwa Ummanta kitso Ubayd ya shigo gidan da sallama. Da sauri Umma ta jawo hijabinta da ke gefe ta saka ta bar Shahidah da buɗe baki. Umma ba dai kunya ba. Ta faɗa a zuciyarta. Wai dan ma ba ayi aurenta da Ubayd ba kenan. Ubayd ya tsugunna ya gaishe da Umma. Ya iya gaisuwa kam amma har yanzu bai fahimtar yaren kurame sosai kodan bai taso a gidan ba ne? Ya ajiyewa Umma wata ƙatuwar leda tareda kuɗi acikin envelop. Umma ta shiga yi ma sa godiya, ta zunguri ƙafar Asiya alamar ta tayata yiwa Ubayd godiya. "Ya Ubayd yaushe aka yi albashi?" "Ai inaga ke ce dalilin wannan albashin, da safe da ki ka yi maganan albashin nan zuwa ƙarfe ɗayan rana mutane sun fara ganin alert. Ni nawa ya shigo ƙarfe uku da rabi ne lokacin ina Alwala a masallaci" "Mugu ba. Yana tsoron kar ubangidan sa ya dawo ya samu bai biya albashi ba ya haushi da faɗa" "Ikon Allah, yanzu ya biya albashin ma bai miki ba" "Dama ya so yin kasuwanci da albashin mutane ne, Allah ya kamashi" Ubayd ya girgiza kai kawai ya wuce ɗakin Inna Yaha dan ya kai mata nata kayan. *** Yau Gwamna ya dawo daga tafiyar da yai, kusan ya ƙara kwanaki biyu bisa ranan daya ɗiba zai dawo. A ranan ne kuma abubuwa da dama suka faru. A chan gidan Yallaɓai Alhaji Kachallah ne zaune a falon gidan yana jiran fitowar Yallaɓai. Kusan minti ishirin da biyar yai yana zaman jiran sa kafin ya fito yana dogara sandar ƙarfe wacce ta ke ta ado ba wai dan yanada matsalar ƙafa ba. Minti biyar ya ɗauka yana yiwa Yallaɓai bayanin abinda ke tafe da shi. Ya ƙara da cewa " ina fata idan lokaci yayi ba za a juya min baya ba" Yallaɓai yai murmushi ya ce "Alhaji Kachallah ka sani sarai bana magana biyu. Abu ɗaya ne zai sa na chanja maganata, idan har shi ya karya dokar wannan tafiya" "Ina tsoron kada Mr Paul ya idda mugun nufinsa. Idan har kujerar mataimakin Gwamna ta kuɓuce mani, Yallaɓai za a samu matsala a wannan tafiya" "Ka kwantar da hankalinka ba abinda Mr Paul zai iya yi" Alhaji Kachallah ya miƙe ya ce "ni zan wuce" Bayan tafiyar Alhaji Kachallah Yallaɓai ya dubi kujerar da Alhaji Kachallan ya tashi akai, itace dai kujeran da Mr Paul ya zauna akai jiya yana kawo ƙorafinsa akan a dakatar da tafiyar Alhaji Kachallah saboda akwai giɓi sosai a tafiyar ta sa. "Ba shi da experience ko kaɗan a wannan harka Yallaɓai. Yanada sanyin zuciya idan aka ɗaura shi akan kujera zamu samu matsala da shi. Ya kamata a datse..." Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu. Mr Paul yai tsit yana zazzare idanu. Yallaɓai yai murmushin gefen baki, yana son irin wannan wasan... *** Cikin shiga ta alfarma shiga ta ƙasaitattun mata Hajiya Bilkisu ta fito daga ɗakinta. Wani tsadadden leshi fari ta saka ɗinkin buba da zani, ta saka takalmi mai tsini kalar ja wanda yai dai-dai da kalar clutch bag ɗinta, ɗan kunne da awarwaro da kuma sarƙa, Tana takunta ɗaiɗai har ta sauko ƙasa. "Hajjaju Makkatun, Hajjan Gwamna, Hajjan mu" ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya tana ɗan tafa hannu. "Hansa'u kenan" "Hajja idan na girma ina son zama kaman ki" Wani lokaci takan ɗan tausayawa Hansa'u. Wacce ta kawota ta gaya mata cewa auren wuri aka mata tana shekara goma shauku, ta wahala sosai a wajen Kishiyarta. Tana shekaru shabiyar mijin ya rasu. Ba a jima ba ta haihu ɗan bai zo da rai ba wannan psychological trauma ɗin shine ya taɓa ma ta ƙwaƙwalwa. Anyita magani ana tunanin Aljanu ne ko sammu amma shiru. Bayan shekaru ana jinya shine wata Gwoggonta ta kawota Birni dan ta koyi sana'a tunda ta ƙi auruwa. Hansa'u akwai aiki kam amma akwai shirme da shiririta dan har yanzu hankalin ta kaman na budurwar ƙauye ce 'yar shekaru shabiyar. Kusan ko da Hajiya Bilkisu ta girmeta to abinda za ta bata ba zai wuce shekaru biyu ba. "Hansa'u Malamin Junior ya zo ko?" "Eh Juno yana karatu da malamin sa a waje" "Good, idan ya gama lesson ki tabbatar yayi wanka kafin ya ci abinci. Ni zan fita" "Hajjan mu a kawo mana tsaraba" Hajiya Bilkisu ta ɗan yi dariya sannan ta fita daga gidan ta nufi motarta inda driver ke jiranta. Kai tsaye gidan Gwamnati aka wuce da ita. Ba wannan ne farkon zuwanta gidan ba amma abin mamaki ba a bari ta ƙarisa falon First lady ba kamar yadda ta saba yi idan ta zo. Mai aikin gidan ta ce ma ta First lady na da manyan baƙi dan haka ta jira a falon baƙi kafin su tafi. Da farko abin ya yiwa Hajiya Bilkisu banbaraƙwai saboda irin haka bai taɓa faruwa ba amma daga baya sai ta yi tunanin ko dai first lady na tare da surkuwanta ce. Ba abu ne ɓoyayye ba a wajenta irin takun saƙa da ke tsakanin First lady da Maman Gwamna. Rabuwa su ka yi da matarsa ta farko wacce sun yi kusan shekaru ashirin da biyu tare kafin su ka rabun, hakan kuma ba ƙaramin ƙona ran mahaifiyar Saminu Bacchi yai ba, Murjanatu itace uwar 'ya'yan sa guda shida amma haka ya rufe ido ya shure ya saketa ya auro Hajiya Sha'awanatu. Kusan shekaran su bakwai da aure amma har yanzun tsakaninta da Mahaifiyar Saminu Bacchi ba sa ga maciji. Zaman jiran da ta ke gani ba zai wuce minti ishirin zuwa talatin ba shine ya zamana har ya wuce awa biyu. Sau biyu tana turawa a duba ma ta first lady amma sai a ce tana tareda baƙi. Tun Bilkisu na ɗaukan abun ba komai ba har ya zo ya fara ba ta haushi. Awa uku da zamanta a falon ta miƙe tsaye dan ta wuce gida zuciyarta cike da ƙuna. Barka da dawowa ta zo yiwa First lady ba wai zaman walaƙanci ba. Ko bakin ƙofa ba ta kai ba ta jiyo shewar first lady da wasu mata. Ta juya a fusace dan ganin su waye su ka fita mutunci a wajen first lady ɗin, lokacin da ta juya first lady ce ke saukowa ƙasa biye da ita kuma Hajiya Hadiza matar Senator da Hajiya Kaltume matar Commisioner. Hajiya Bilkisu ta bi su da kallon mamaki. Saboda waɗannan matan First lady ta zaunar da ita na tsawon awa uku. "Ba ki tafi ba?" First lady ta faɗa da mamaki Hajiya Bilkisu ta buɗe baki cikin kaɗuwa. "Bilkisu Kachallah. Ashe ke ce ake ta damun First lady wai tana da baƙuwa" Hajiya Hadiza kenan da wannan magana. "First lady saboda waɗannan kika shanyani kaman kayan wanki" ta yi maganar tana nuna su. "Tabbas saboda su kuwa. Bilkisu na ji duk abinda kika yi tun kafin na dawo amma ki sani ba zan lamunci hakan ba. Taron matan Gwamnoni aka ce za ayi ba na matan mataimakan Gwamnoni ba. This is the last time da za ki sake haɗa taro idan bana gari" "Sai da muka gaya ma ta ta bari ki dawo kafin ayi taron nan amma ta ƙi. Wallahi matar Gwamnan Ekiti sai da ta gasa mana magana a wajen taron nan, kin san yarabawa ai" "Ni! Ni ki ke wa munafurci Hadiza?" Hajiya Hadiza ta juya kai tana tura baki. "Ki tsaya iya matsayinki Bilkisu sai a samu zaman lafiya" First lady ta faɗa a fusace Hajiya Bilkisu ta haɗiyi wani abu daya tokare mata maƙoƙoro. "Nagode First lady. Dama na zo yi miki barka da dawowa ne amma na ga alama ba ki cancanci gaisuwar ba. Mu kwana lafiya" Hajiya Bilkisu ta juya da sauri ta fice daga gidan. A cikin mota danne ƙirjinta ta yi saboda yadda ya ke bugawa yana sukanta. Ba ta iya ɓacin rai ba dan tana farawa zuciyarta ke fara ciwo. Shekarun baya ance tanada hawan jini shiyasa ta ke kaffa-kaffa da duk abinda zai ɓata ma ta rai. Bayan ta koma gida ba wanda ta kula ta wuce ɗakinta ta sa key sannan ta kwanta akan gado har lokacin ba ta cire hannu a ƙirjin ba dan ji take idan ta cire zuciyarta zai iya bugawa. Ƙarshe ta tashi ta ɗauko maganinta ta watsa a baki ta haɗiye zuwa minti shabiyar maganin ya fara aiki dan bugun ƙirjinta ya fara raguwa. Idan ba ƙaddara ba da First lady da Hajiya Hadiza da ita Hajiya Kaltumen dukkan su babu sa'anta cikin su. Idan ba muƙami da mazajen su ke riƙe da shi ba babu wadda a cikin su ta taka ƙafarta wajen gata da daraja. *Bilkisu Sani Kachallah* ce fa. Waye bai san tarihin ahalin gidan Kachallah ba. Familyn Kachallah su ne da Jahar Congo gaba ɗaya. Bilkisu Kachallah ba za ta iya tuna lokacin da bacci ya ɗauketa ba. Ta dai farka tsakar dare ta ganta kwance da kayan jikinta sai alokacin ta tashi ta cire kayan ta saka na bacci sannan ta dawo kan gadon ta zauna dan bacci ya washe a idonta, tunani kala-kala ta zauna yi har Asuba. *** Shahidah na bacci wayarta ya hau ƙara. Ta sa hannu ta jawo wayar da ke gefen gado saura kaɗan ya faɗo ƙasa. "Hello" ta faɗa da muryan bacci "Mine kin tashi kuwa? Na kusa isowa fa" "Ka manta anyi suspending ɗina jiya" "Subhanallahi! Ok ok barin zo in gaida Abba sai na wuce office..." ai bai ƙarisa bama Asiya ta kashe wayar saboda baccin da ke cinta. Da sassafiya Bilkisu ta shirya ta sauko ƙasa. Daga wajen dining room wanda ke haɗe da babban falon ƙasa ɗan ta Junior ya ƙwala ma ta kira "Mommy" ta juya da sauri tana maƙalawa fiskarta murmushin bogi wanda ya ɓoye ɓacin rai da ta ke ciki. "My boy" "A'a Nana yaushe kika dawo. Zunairah ya Maman ki?" Ta jera maganar tun kafin ta iso wajen su "Mommy ina za ki sani kuwa. Jiya ina miki magana haka kika shareni kika wuce sama. Daga baya na je na yita buga ƙofar ki amma shiru ba ki buɗe ba" "Sorry Dear, jiya na gaji ne dayawa" "Miyasa Junior ke cin abinci shi ɗaya ina Hansa'u?" "Hansa'u" ta ƙwala ma ta kira da ƙarfi "Mommy Airah ce ta aiketa ta kawo mata boiled egg" "Ok girls barin fita, idan Daddyn ku ya tashi ku ce ma sa na tafi Kachallah House" Bayan tafiyar Hajiya Bilkisu sai ga Hansa'u ta fito da wani bowl ɗauke da ƙwai guda uku ta ajiye a gaban Zunairah. Zunairah ta zaro ido ganin ƙwai da ɓawonsa a jiki sai tiririn zafi ya ke "And what is this? N Luv kinga shirmen wannan crazy old fool ɗin ko?" Nana ta kalli Hansa'u ta ce " yanzu Hansa'u ita ki ke so ta cire ɓawon ƙwan kenan?" "Ke ce ki ka ce na kawo shi kwili-kwili (quickly-quickly) kuma na ji Hajiya na kira shiyasa na kawo shi haka nan" "Dalla je ki ɓare ƙwan ki kawo" Nana ta faɗa da tsawa. Hansa'u ta ɗauke kwanon ta koma kitchen da sauri. Hajiya Bilkisu da ta fito ba ta wuce ko'ina ba sai Kachallah House. Da ta shiga gidan ba ta wuce sashen kowa ba sai sashen mahaifinsu wanda ya ke gefe da asalin cikin gidan, a nan ya ke karɓan baƙin sa a nan kuma ya ke duk wasu harkokin sa. Sashen ya ƙunshi falo guda ɗaya da dining room sai manyan ɗakuna guda huɗu. Ba kowane ya sani ba amma ita Bilkisu ta san akwai falon sirri a gidan wanda Mahaifinsu ke karɓan baƙi na musamman inda ake yin meeting na tsakar dare a ciki. Shekarunta shabiyar lokacin da ta gano ɗakin, ta je duba wani littafi a library ɗinsa ne hannunta ya danna wani switch a jikin bango sai gashi carpet ɗin wajen ya ɗage. Ba tareda tsoro ba ta leƙa wajen daya buɗe ɗin sai taga matakala ce a wajen. Ta sa ƙafa ta fara taka matakalar har ta nitse ciki dan falon underground ne. Ta san turawa na yin ɗaki ko basement a cikin ƙasa amma ba ta taɓa tunanin sashen mahaifin na su na da irin wannan ba. Falo ne Babba da ya sha kayan alatu fiye da ɗaya falon sai ɗakuna biyu wanda tayi-tayi ya buɗu ya ƙi buɗuwa shiyasa ma ta haƙura ta fito ba tareda ta ga abinda ke ciki ba. Ta ci sa'a Baban na su na nan dan lokacin ne ma ya ke ƙoƙarin karyawa ga tulin abinci kala-kala da aka ajiye ma sa wanda aƙalla mutum shida za su iya cin abincin su ƙoshi sarai. "Bilkisu" ya kira sunanta da mamaki. Ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe bakwai da minti arba'in da bakwai. "Lafiya dai ko?" "Lafiya Baba" Bayan ya tambayi lafiyar mijinta da 'ya'yanta sannan ya tambayi mi ke tafe da ita da sassafen nan dan yasan haka kawai Bilkisu ba za ta nemeshi ba. "Saifu ne zai miki kishiya?" "Baba idan kishiya ce ai da sauƙi. Baba tambaya na zo yi" Alhaji Sani Kachallah ya suɗe romon kan rago da ke shirin gangarowa zuwa gwiwar hannunsa. Wani lokaci idan Mahaifinsu yai wani abun kamar wani faƙiri wanda ba shi da gata ko kaɗan. Yanzu miye na suɗe hannu?. Ta yi saurin kauda wannan tunanin a ranta ta maida hankalinta zuwa abunda ya kawota. "Baba yaushe Saifuddeen zai zama Gwamna?" Alhaji Kachallah ya saka bredi ya dangwali romo zai kai baki ya ji maganar Bilkisu ta ma sa dirar bazata. "Wace tambaya ce kuma wannan?" "Baba dan Allah ka amsa min tambayata" Alhaji Kachallah ya kalli idon 'yarsa da kyau ko zai gano wani abu amma bai karanci komai a fiskarta ba sai tsananin ɓacin rai, ya ce " idan Saminu Bacchi ya ƙarisa tenure ɗin sa guda biyu Jaha za ta koma ta Saifu dan shi za mu tsayar a zaɓe na gaba" "A taƙaice kusan shekaru biyar kenan?" Alhaji Kachallah ya ture kwanon gaban sa gefe ya ɗaura hannu akan table yana zubawa Bilkisu ido. "Babu yadda za'ayi Saifuddeen ya zama Gwamna kafin lokacin?. Baba ku ne da gwamnati, ku kuke juya jahar nan, mi zai hana ka ɗaura Saifuddeen a kujerar Gwamna, shekaru biyar ma su zuwa sun yi nisa sosai" "Bilkisu!" "Baba break the rules, boycott the protocols make Saifuddeen the governor and..." Idan da bai yi tunanin hakan ba to yanzu Bilkisu ta ankarar da shi. Mr Paul da ya ke son haɗa ma sa manaƙisa a wajen Yallaɓai dole ne ya nuna ma sa cewa kafin mutum ya ga biri to biri ya gan shi. Bayan fitar Bilkisu daga falon, Alhaji Kachallah ya faɗa kogin tunani. Ta ina zai fara? Akwai gaskiya a hasashen Bilkisu dole ne ya san yadda zai yi ya shawo kan matsalar tun kafin lokaci ya ƙure a juye ma sa baya. *** "Miyake faruwa naga kwana biyu ba kya fita" SSK yai maganar yana zama gefen gadon Bilkisu tareda kissing goshinta. "Ba na jin fitan ne kawai. Ina buƙatar hutu ne ma" "Nima ina buƙatar hutun nan Allah. Inaga tunda Gwamna ya dawo why not mu je UK hutu ko da na sati biyu ne?" "Its a good idea gaskiya. Muna buƙatan hutun nan sosai" ta yi maganar tana murmushi. SSK bai jima da fita daga ɗakinta ba wayarta ya hau ruri. Madam Bintu ta gani a jikin screen ɗin hakan ya sa ta faɗaɗa murmushinta. Ta yi saurin ɗaukan kiran tana faɗin " mutanen Turkiyya kin shigo kenan" Daga ɓangaren Madam Bintu ta ce "na shigo jiya da dare zan shigo wajen ki anjima" "To sai kin zo" Ƙarfe biyar da rabi sai ga Madam Bintu a gidan ta. Hansa'u ta kira ta kawo musu abin taɓawa. "Har yanzu ba ki rabu da wannan matar ba bayan shirmen da ta yi kwanaki" "Bintu tausayi ta ke bani Allah. Besides yanzu ta iya aiki sosai ba kaman farkon kawota ba sai dai ba a rasata da shirme kam. Most importantly tana sani dariya and that's help alot ga mu ma su hawan jini" "Ok" ta faɗa tana ƙarewa Hansa'u kallo. Gani ta ke kaman idon matar na mata kama da wacce ta sani amma ta rasa gano ko wacece. Bayan Hansa'u ta bar wajen Madam Bintu ta tambayi Bilkisu yadda taron matan Gwamnoni ya kasance dan lokacin da aka yi taron ba ta ƙasar. "Ba abunda zan ce miki Bintu sai dai in ce kawai taro yayi kyau. Kuma za a sake wani taron nan ba da daɗewa ba" Madam Bintu ta kalli Hajiya Bilkisu cikin rashin fahimta, maimakon ta mata ƙarin bayani sai kawai ta fashe da wata ƙasaitacciyar dariya. ** A chan gidan Yallaɓai kuwa Chief of Staff (COS) ɗin Gwamna ne a gaban Yallaɓai yana ma sa bayani mai mahimmanci wanda ya sa Yallaɓai nitsuwa na ban mamaki. Har ya gama bayanin Yallaɓai bai ce komai ba sai ma murza gemunsa da ya fara yi a hankali. Ba kasafai ya ke samun ma su taurin zuciya irin ta KACHALLAH ba. Shekaru da dama an taɓa yunƙurin aikata irin wannan abu sai dai kuma komai ya zo ya chanja a ƙurarren lokaci. "Ka haɗa meeting da Kachallah cikin satin nan" Yallaɓai ya faɗa bayan yayi dogon nazari. COS yai murmushin gefen baki dan ya san yanzu liyafa za ta cigaba. Ya ƙwallafa rai sosai akan Gwamna Saminu Bacchi sai dai cikin shekaru uku da yai a kan mulki sun samu saɓani sosai domin lokacin da idon Gwamna Saminu ya buɗe da kuɗi sai ya zamana yana ƙoƙarin take duk wata hanya da su suke yagan rabon su, yanata wawure komai shi kaɗai da iyalin sa ba dan Yallaɓai ya tsayar ma sa ba wasu abubuwan haka za su dinga wuce shi. Saifuddeen Sa'ad Kachallah daban ya ke da Gwamna Saminu, kuɗi ba za su ruɗe shi ba. SSK ya gaji arziƙi irin arziƙin da ko da ba zai yi wani aiki ba zai isheshi ci da iyalen sa har iya karshen rayuwar su ba tareda sun yi talauci ba. SSK shine mafita a gareshi da shi da KACHALLAH. *** "Wallahi an cuceni Ya Ubayd. MD mugu ne wallahi" Ubayd yai murmushi ya ce " ni kam ya min dai-dai, dama daurewa kawai na ke yi amma kullum aka nunaki a TV sai na ji kamar zuciyata za ta fashe" "To ta Allah ba taka ba. Sai an maidani reporting unit" "Ina kishin ki Asiya na haƙura ne kawai saboda babu yadda zan yi amma Allah idan ki ka shigo gidana ba za ki sake bayyana a TV ba, ko dai ki tsaya aiki a bayan fage ko kuma ki haƙura da aikin" "Ya Ubayd you are joking right" "I'm not Asiya. Gara ma ki saba da inda aka kai ki yanzu" Sati ɗaya da suspension ɗin ta aka kirata akan ta dawo. Yau ta fara fita aiki amma duk ta ji ba daɗi ba ta son ɓangaren da aka kaita ko kaɗan. "Ya Ubayd ba haka mu ka yi da kai ba baka ce za ka rabani da aikina ba" "Ba rabaki zanyi da aikin ki ba na dai ce bayan munyi aure ba ƙaton da zai sake ganin ki a TV yana ƙare miki kallo especially with irin shigan da ki ke yi" yai maganar da ɗan ƙarfi Asiya ta miƙe daga kujeran da ta ke zaune ta ce "ba ka isa ba kuwa" Ta wuce ta barshi a wajen baki buɗe. Washegari ko jiran sa ba ta tsaya yi ba ta hau keke ta wuce office... *** " na gaya miki babu kuɗi a ƙasa, duk wani abu da zamuyi yanzu mutane za su yi magana. We need this year to work on something saboda campaign da za a fara nan da watanni huɗu ma su zuwa" Gwamna Saminu Bacchi kenan yana ƙoƙarin lallashin matar sa. "Kana so ka ce min ba ka da kuɗin da zamu celebrating 8years anniversary na mu?" "Ba wai ba kuɗin bane amma kuɗin campaign ne" "Kar ka gaya min magana dan Allah. Uban me Saifuddeen Kachallah ke da shi da zai iya celebrating 15yrs anniversary na su a tsakiyar teku shekaru biyu da suka wuce. Na je party ɗin fa. Sati biyu aka yi a cikin jirgin ruwa wanda komai da komai da mutanen ciki su ka yi yana wuyan sa" "Sha'awanatu. Saifuddeen Kachallah millionaire ne tun kafin mu hau gwamnati ko mi zai yi ba wanda zai zargeshi amma ni..." "Ba zan yadda ba fa. Dole ne ayi anniversary party namu a Italy. Wallahi kai ka ke sawa ma Bilkisu Kachallah tana raina ni. Ina matar Gwamna amma ko motan da ta ke hawa tafi tawa" "Yanzu kinsan ya za ayi ne? Za mu yi party amma a nan Nigeria. Bamu jima da dawowa daga ƙasar waje ba idan muka sake fita mutane za su yi magana..." "Wai ina ruwanka da mutane ne. Kai fa Gwamna ne. Gwamnar jahar CONGO wancan tafiyar Asibiti ka je wannan tafiyar kuma yana cikin yiwa iyalinka hidima ne" " Amma Sha'awa..." Daga haka Gwamna Saminu Bacchi ya haɗiye sauran maganar sa saboda haɗe bakin su da Sha'awanatu ta yi. Washegari da safe Gwamna ya tashi da wani irin ciwon kai da ciwon ƙirji, ciwon ne ma ya tashe shi daga bacci tun ƙusan ƙarfe huɗun Asuba. Wasa-wasa har ƙarfe shida jikin ba sauƙi duk da kuwa ya sha magungunan sa. "Za mu wuce Asibiti ne ko a kira maka likita?" First lady ta tambaya cike da fargaba. "Ki kira Likita" ya faɗa da ƙyar saboda yadda ƙirjinsa ke takure. Bai kai awa ɗaya ba saiga likitan sa ya iso koda ya duba shi cewa yai jinin sa ne ya hau sosai idan akwai wata damuwa da ke ransa to yai ƙoƙarin kauda ita dan abunda ya sa a ransa ka iya jawo ma sa bugawar zuciya. Shi dai ya sani bai sa komai a ransa ba. Ba a fara campaign ba balle ya ce shine ke ɗaga ma sa hankali. To kodai Barasar daya kwankwaɗa jiya da dare ne? Duk da likitan sa na chan Germany ya hana shi shan barasa. Duk da kuwa ya san ba zai iya dena sha ba, sai dai ya rage sha ba kamar da ba. Allura da Likitan ya ma sa ya taimaka ma sa sosai dan har ya samu yayi bacci. Lokacin da ya farka kusan ƙarfe goma shaɗaya na safe. Sha'awanatu ta taimaka ma sa yai wanka ta kawo ma sa abinci har kan gado amma bai iya ci ba sai shayi kawai ya sha. Ƙishirwar giya ce ta dameshi dan duk da yana jin jiki yayi amanna idan ya ɗan kurɓi kaɗan zai samu sauƙi. Fita yai daga ɗakin Sha'awanatu ya wuce na sa ɗakin a nan ya fito da kwalbar giya ya kwankwaɗa ya girgiza kai ya sake kurɓan kaɗan sannan ya mayar da sauran ma'ajiyar sa. Shiryawa yai ya fita saboda akwai meeting da zai yi da wasu contractors ƙarfe biyu na rana. "Yanzu yadda baka da lafiya haka za ka fita?" "To ya za ayi dole ne mu yiwa talakawa aiki" "To. Amma ka dai yi tunani akan abinda na ce" Dariya Gwamna ya fara yi sai kuma ya dafe ƙirjinsa saboda yadda ya ji ƙirjinsa na suya kaman an saka masa wuta. "Your excellency jikin ne?" Kafin ta ƙarisa maganar Excellency ya kai ƙasa. "Your excellency, miya faru? Ƙirjin ka ne?" "Waye a nan? a kira likita. Excellency... Saminu...Saminu ka tashi" Lokacin da aka garzaya da Gwamna Asibiti ya riga ya cika likita ya ce zuciyar sa ce ta buga (cardiac arrest)... *** Mataimakin Gwamna na zaune a office Chief security officer ya kira shi, kiran da ya ɗaga ma sa hankali sosai dan kuwa a kiɗime ya fice daga office ɗinsa ya wuce Asibiti. Mummunan labarin da aka gaya ma sa a waya shi ya tarar a wajen domin kuwa Allah yayiwa Gwamna Saminu Bacchi rasuwa. A chan Kachallah House kuwa Alhaji Sani Kachallah ne ke waya da mijin 'yar sa wato Saifuddeen wanda ya jaddada ma sa mutuwar Saminu Bacchi. "Mi aka ce ya kashe shi?" "Baba ba zan iya cewa komai ba yanzu" Alhaji Sani Kachallah ya ce "ba komai zan kiraka anjima". Yana kashe wayar ya shiga kiran numbar Yallaɓai. A chan gidan mataimakin Gwamna kuwa Bilkisu Kachallah ce zaune a falo tana cin gasashshiyar kifi da soyayyen dankalin turawa haɗe da lemo mai sanyi. "Hansa'u, Hansa'u " Hansa'u ta fito da gudu. Miƙo min remote ina son kallon news. Hansa'u ta miƙa ma ta remote ɗin Bilkisu ta chanja channel daga Zee world zuwa Congo news... *** Asiya Shahidah na zaune a sabon office ɗinta tana aiki akan computer abokin aikinta Ɗahiru ya shigo office ɗin da sauri. "Shahidah kin san labarin dana ji kuwa daga fitata a office ɗin nan?" "Miya faru?" "Yanzu Abigail ta ke kawo rahoto cewa Gwamna ya rasu" "Wani Gwamnan?" "Gwamnan Congo mana" "Innalillahi! Dan Allah?" "Allah kuwa" Asiya Shahidah ta miƙe ta bar office ɗin da sauri... Kusan awa ɗaya da rasuwan sannan Mataimakin Gwamna kuma acting Gwamna ya bada sanarwan mutuwar Gwamna Saminu Bacchi. *"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun. Haƙiƙa dukkan mai rai mamaci ne. Muna yiwa Jahar Congo ta'aziya bisa rasuwan Mai girma Gwamna Alhaji Saminu Bacchi wanda Allah yai wa rasuwa yau shabakwai ga watan Nowamba. Haƙiƙa wannan jaha ta yi babban Rashi"* hawayen da ya zubo ma sa yai saurin sa hankerchief ya goge sannan ya cigaba da bayani *" Insha Allahu za ayi jana'izar sa a gidan gwamnati da ƙarfe biyar na yamma"* Asiya Shahidah da ke kallon news ɗin a talabijin da ke office ɗin su CY ta ce "Ikon Allah har da kukan munafurci kaman bai ji daɗin abinda ya faru ba, Shege. Ai yanzu kam jahar nan ta shiga uku a hannun wannan Wawan" A ɓangaren Yallaɓai kuwa yana gama kallon bayanan da SSK yai ya danna remote ya kashe T V sannan ya kai duban sa ga Kachallah ya ce "To kyan alƙawari dai cikawa. Ina fata Saifuddeen zai bamu haɗin kai" "An gama Yallaɓai" Yayinda wasu ke cikin baƙin ciki da rasuwan Saminu Bacchi wasu kuma na nan suna planning yadda za a juya Gwamnati. Duniyar kenan. Tunma kafin a sa shi cikin ƙasa har an riga an cire shi daga lissafi. Da 'yan siyasa za su dinga tunawa da cewa akwai ranar da dukiya ko matsayi ba zai amfanesu ba ƙila da za su tausayawa talakawan su. *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 04 "Rayuwa kenan. Yau kam Saminu Bacchi sai kwanciyar kabari" Abba da ya kashe rediyon sa ya faɗa. Ubayd ya ƙara da cewa "Ya tafi ba abunda ya ɗauka kuwa" "Muna addu'ar Allah ya taya Saifuddeen riƙo Amin" Ubayd ya ce Amin. Shiru ne ya biyo bayan haka na ɗan mintuna kafin Abba ya ɗaga kai ya ce " 'yata ta dawo kuwa?" "Ƙila aiki ne ya tsaida ita" "Ka je ka dubo min ita" Bai musa ba ya miƙe yana karkaɗa key ɗin mota. Lokacin da motar sa ta sako kai farfajiyar ma'aikatar su Asiya ya hangota tana shirin hawa babur ɗin CY. Yana ɗaya daga cikin abinda yasa ya ke ƙin aikinta irin yadda ba ta damuwa da irin mutanen da ta ke mu'amala da su. Ya sha hanata mu'amala da wannan camera man ɗin amma kaman ma duk cikin Kamfanin su tafi jituwa da shi. Sarai ta hango shi amma ta kauda kai kamar ba ta ganshi ba. Sai da CY ya tada machine su ka fara tafiya ya kula da motar Ubayd. "Aseey ba motar fiancee ɗin ki ba ne wannan" "To sai me" CY yai saurin taka birki har sai da Asiya ta bugu da bayanshi. "Ya ka tsaya?" "Bebz i no wan trouble, plz ki sauka" "CY ka wuce mu tafi" Lokacin da ya tada machine ɗin a hankali ya ja su har wajen da Ubayd yai parking motar sa Asiya na ta ma sa faɗa akan ya wuce su tafi amma bai saurareta ba. "CY za ka haɗu da ni gobe ai. I will deal with you" Bai kulata ba sai ɗagawa Ubayd hannu da yai yana faɗin "weldone Sir" Ubayd ya sauke glass ƙasa ya ce "Sannu da ƙoƙari fa" "Sannu Sir, a yiwa Amarya haƙuri yau ta gaji dayawa ne" "Nagode" Asiya ta watsawa CY harara kafin ta zaga ta je ta shiga motar Ubayd. Sai da ya ga ta shige motar kafin ya ja machine ɗin sa yai gaba. Ubayd bai ce mata komai ba ya tada motar su ka fara tafiya. Itama ba ta kula shi ba sai ma kwantar da kujera da ta yi ta rufe idonta kamar mai bacci. Traffic ne ya riƙesu saboda ma su dawowa daga maƙabarta. Ƙaran siren ne ya tada Asiya daga baccin daya sace ta. Ta rintse ido ta buɗe da kyau ganin har yanzu suna round about na GRA kenan ko kusa da gida ba su yi ba. Sai da motocin Gwamna su ka wuce kafin aka basu hanya suma suka fara wucewa hakan ya sa Asiya ta ja tsaki. "Asiya" ya dakatar da ita lokacin da ta ke shirin fita daga mota. Ta juyo ta kalleshi ba tareda ta ce komai ba. "Zan kiraki bayan sallar Isha" "Ok" ta faɗa sannan ta fita. Data shiga gida tana jin shewar Abida ƙawar Hindatu mai murya kaman na maza. Ta dawo kenan ta faɗa a ranta sannan ta wuce ɗakin Umma. Bayan ta yi sallar isha tana kwance akan sallaya tana danna waya kiran Ubayd ya shigo. Ta san dalilin kiran shiyasa ba ta ma ɗauka ba ta miƙe ta fice daga ɗakin. "Yau kuma shigar ta malamai ne" Ubayd ya faɗa lokacin da ta ke ƙoƙarin zama akan kujerar roba da ke gefen sa. "Idan ma gatse ne ka san dai daga gidan Malaman na fito" "Shiyasa na ke alfahari da cewa jikar Gwani Baba zan aura. Allah ya jiƙan rai" "Ka huce kenan?" "My Aseeya kenan. Kin riga kin sani bana iya fushi da ke ai. Ki yi haƙuri" Asiya ta ɗan haɗe rai tana tura baki. "Kwantar da hankalinki ba haka nan na zo biko ba, na zo da kayan sulhu" Yana maganar ya jawo ledar da ke gefensa ya ɗaura akan cinyarta. "Whoa! Pringles, chocolates. Ba dan halin ka ba dai kaima ka yi haƙuri" tana maganar tana buɗe robar pringles ɗin. "Ya Ubayd gaskiya yau ka yi abin kirki" tana maganar bakinta yana ƙurmus-ƙurmus. "Ba za a sammini ba?" "In your dreams. Ka san yanzu a zaune sai na cinye wannan bai isheni ba" Ganin ya sakata farin ciki ya sa shi yi mata hiran shirye-shiryen bikin su da tsarin yadda komai zai kasance. Yau baya so ayi maganar kowa sai ta su. Ana taɗi ya tuno mata da ranan da ya fara ganinta a gidan su hakan ya sa Asiya mingirewa da dariya tanayi tana "kai Ya Ubayd" Farkon haɗuwar su tana shekara shaɗaya a duniya ta zo yiwa ummanta hutu. Lokacin 'yar mitsila da ita amma wai tana JSS 2. Ya shigo gidan ya ga tsumma a kan igiyar shanya, bai kawo komai a ransa ba ya cire ya tsoma cikin ruwan Omo ya fara wanke machine ɗin Abba da shi. Kamar daga sama ya ji wata siririwar murya tana salati a bayansa ya juyo a ɗan firgice dan ya ɗauka ba kowa a gidan na su, biki ake a gidan su Addaye ƙanwar Abba, duk 'yan gidan suna chan. "Lahaula... Sallalahu Alaihi wa Sallam. Tsumman abuna!" sai kuma ta riƙe baki tana zaro ido. Ubaydullah yana riƙe da tsumman ya kalleta da mamaki ya ce "tsumman miye? Tukunna ke daga ina?" Bai yi aune ba Siririyar yarinya mai wushirya ta yi wuf ta karɓe tsumman daga hannunsa ta shige ɗakin Umma da gudu, bai ƙare mamaki ba sai daya ji ta bugo ƙofar ɗakin da ƙarfi. Shi kam bai gane mi ya ke faruwa ba. Ya dai ƙarasa wanke machine ɗin hakanan. Har ya gama abunda zai yi ya fita yarinyar ba ta fito ba. Sai bayan magariba daya dawo gidan ya tambayi ƙanwar sa Ummi wace baƙuwa su ka yi a gidan. Ummi ta sanar da shi 'yar Umma Kurma ce itace Asiya Shahidan ta da Abba ya basu labari. Tun daga lokacin kuwa Asiya ke gudunsa har ranan da ya titsiye ta yana tambayarta miye dalilin ta na ƙwace tsumman ranan. Yadda ta dinga inda-inda ne ya sa ya fahimci tsumman miye. Ƙannensa sun wuce nan ai dan tun lokacin da ya taɓa kama ƙanwarsa Ummi tana ɓoye tsumma cikin zani ya ɗaurawa kansa siyawa ƙannensa audugar mata tun ma yana shekaru shabakwai kenan balle yanzu daya ke shatara shigar sa Jami'a ya sake wayewa. A ranan ya je ya siyowa Asiya auduga ya bawa Ummi ya ce ta nunawa Asiya yadda za ta yi amfani da shi. A hankali-A hankali kafin ta ƙare hutun ta dena jin kunyar sa tana ɗan sakewa da shi. Tun tana zuwa hutu gidan har ya zamo lokacin da za ta shiga Jami'a ta dawo gidan su da zama gaba ɗaya. Har yau idan yana son ya tsokali Asiya to kalmomi biyu kacal zai faɗa ya tunzurata *"tsumman abuna"* Bai bar gidan ba sai ƙarfe goma saura minti biyar nan ma dan baya son tsallake dokar Abba ne wato baya son hiran ƙarfe goma. Asiya na komawa ɗaki da ta duba wayarta ta ga saƙon KaSaSa a email ɗinta wanda waƙar da ta rubuta yau akan mutuwa ne, wanda tai wa Marigayi Gwamna Saminu Bacchi. Bayan ta karanta kuwa sai da ta tuno mutuwa biyu da su ka fi girgizata a rayuwarta. Mutuwar Kakanta Gwani da kuma mutuwar ƙaninta ɗan shekaru biyu wanda ya rasu a bayanta. Auri sakin mahaifinsu ne ya je ya auro wata mai juju. Dan idan abu ya haɗata da sauran matansa duka ta ke musu, shima kuwa da ƙyar ya sha a wajenta ranan da ya mareta ta kamashi da kokawa sai da ƙyar aka raba su. Ba dan an raba da wuri bama alamu sun nuna Ale Faruƙ ne zai sha kashi a wajen Indo, dan Indo irin matan nan ne ma su ƙarfi, ga jiki ga tsawo. Ale Faruƙ na sane da dukan miji da akace tanayi wanda ya rabata da sauran mazaje uku da ta aura a baya amma ya rufe ido ya ce Indo-ƙarfi zai aura. Bayan faɗan ne kuwa Ale Faruƙ ya saketa ashe tanada ciki. Da ke ba ta da hankali yaron ko suna ba ayi ba ta zo ta ajiye shi gaban Tabawa mahaifiyar Ale Faruƙ wai ga tsiyar su nan. Haka yaro ya taso ba gata. Tabawa ma da ƙyar ta ke kula da shi dan Ale Faruƙ baya kawo kuɗin madara sai ta tsiya-tsiya. Da yaron ya fara wayo ba shi da wata gata a gidan sai ta Asiya. A haka ya taso a yarjale har Allah ya ɗau ransa lokacin yayi wani zazzaɓi mai zafi Asiya ta goya shi tana jijjigashi a bayanta saboda kuka dayake ta tsalawa har Allah ya karɓi ran sa. Shekarunta tara a lokacin amma har yau ba ta taɓa manta yadda abun ya faru ba. Ya jima da rasuwa a bayanta ba ta sani ba har sai da ta zo kwantar da shi lokacin za ta yi wanki dan ta ɗauka bacci yai sai ta ga idonsa a kafe ta fara jijjigashi amma inaa babu alamun motsi nan ta saka ihu ta fita tana ƙwalawa Tabawa kira... *** "Seriously Justice ina tsoro. Kwana biyun nan bana iya bacci fa. This is so sudden for me" Bayan Justice Yunus ya gama yi ma sa nasiha ta jan hankali ne ya ce "Shikenan na gode. Ka gaida Maman 'yan biyu"... "Kai da waye a waya?" Ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wajensa tana zuba ƙanshi. "Justice" "Oh Galadima. Hope zai zo rantsarwar ka" " i dont think so dan ya ce suna Las Vegas" "Ayya! Allah ya dawo da su lafiya. Muma gashi babu halin tafiya tunda ga yadda lamarin Ubangiji ya kasance. Just like a dream" "Just like a dream kam. Har yanzu ina jimamin mutuwar Gwamna" "Haka Allah ya ke lamarinsa. Idan lokaci yayi babu makawa sai an tafi" "Hakane. Muma duk lokaci mu ke jira" Kallonta yai da kyau sannan ya ɗaga gira sama ya ce " sai ina?" "Zamu je shopping ni da yara. Duk cikin kayan su babu na zuwa swearing in naka a ciki. I think dole a chanja mu su wardrobe kwanan nan" "Hmmm. I trust you Bilkisu" ya faɗa yana ɗan jijjiga kai "Miye?" "Allah ya kiyaye hanya" Kiss ta manna ma sa a baki kafin ta fice daga ɗakin ya bi bayanta da kallo. "Mata kenan, wai duk cikin kayan da ta ke dasu babu na zuwa wajen rantsarwar sa da za ayi ranan Monday". "Seriously Mommy i cant believe yanzu mune first family of the state" Nana ta faɗa tana dariya "Well get used to it, dan yanzu aka fara governor's daughter" Bilkisu ta faɗa tana murmushi. Nana ta saka ihu. Har su ka isa Kachallah House hiran yadda rayuwar su za ta kasance yanzu su ke yi. Sai da su ka fara isa ɓangaren Hajiya Aisha wato mahaifiyar Bilkisu kafin su ka wuce gaida Dadda mahaifiyar Alhaji Sani Kachallah. Ko da su ka gaisa Bilkisu ta tambayi ina Mahira ta ke, Dadda ta ce ta wuce Islamiyya. "Yanzu yarinyar nan abinda za ta min kenan bayan na ce ma ta zamu zo" "Inaga ta manta ne" Dadda ta faɗa tana tauna goro. Ba su jima a gidan ba su ka wuce bayan sun barwa Dadda saƙo akan idan Mahira ta dawo ta je gida Bilkisun na nemanta. *** Farar Shadda ya saka ɗinkin babbar riga haɗe da baƙin hula zanna, ya saka baƙin shoe ƙirar Loius Vitton. Ya duba kan sa a madubi ba ƙarya ya fito sosai. Sai dai a ƙarƙashin wannan kayan zuciyar sa ce ke bugawa da ƙarfi kaman za ta ɓula ƙirjinsa ta fito. Lokacin da aka rantsar da shi a matsayin mataimakin Gwamna bai tsinci kan sa cikin fargaba da tsoro kaman na yau ba kodan yanzu matsayinsa ya chanja ne? Ya fesa turarukan sa ma su ƙanshi guda uku sannan ya fito daga ɗakinsa ya wuce ɗakin Bilkisu. A tunanin sa ta gama shiryawa amma har lokacin ana kan yi mata kwalliya. Tamkar biki za a yi haka Hajiya Bilkisu ta nemo professional make up artist da za ta gyara ma ta fiska yau. "Your excellency" mai kwalliyar ta faɗa tana wani ƙamewa. Bilkisu ta ɗago ido ta ce " Darling ka gama shiryawa, yi haƙuri yanzu zan gama nima" Tun kafin ta ƙarisa maganar ya riga ya fice inda ya wuce ɗakin yaran sa. An gamawa Nana da Airah kwalliya Mahira ake yiwa lokacin daya shigo. Fiskarta tamau alamun ba ta so a dole ake mata. Ya sani ta ɓangaren son ƙyale-ƙyale kam Nana ce ta ɗauko komai na Bilkisu amma Mahira bai dameta ba. "Daddy Governor" Nana ta faɗa tana ƙarasowa wajen sa. "Yi a hankali N Luv kar ki ɓata ma sa farin kaya" Airah ta faɗa daga inda ta ke zaune tana danna waya. " Daddy selfie ɗaya kafin ka tafi please" Bai so ba amma dole haka ya tsaya Nana ta mu su selfie kafin ya wuce ɗakin Junior inda tuni Hansa'u ta shirya shi dan lokacin da ya shiga ɗakin ma yana buga game ne. Ya kama hannunsa su ka fice daga ɗakin... Kotu ya cika maƙil da mutane da kuma 'yan jarida. Bayan Alƙali ya shigo ya tsaya sannan Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah ya shigo biye da bodyguard ɗin sa. Bilkisu kaman ta narke saboda farinciki ganin Mijinta a gaban Alkali wai za a rantsar da shi a matsayin Gwamna. Lokacin da SSK ya dafa alƙur'ani ya maimaita kalmar da Alƙali ya faɗa wato*I...Saifuddeen Sa'ad Kachallah. Do solemly swear...* lumshe ido Bilkisu ta yi sannan ta kai dubanta ga ɓangarenta na dama inda Alhaji Sani Kachallah ke zaune ɗauke da Junior a cinyarsa. Irin yadda fiskarsa ke washe da farin ciki da annashuwa ko ita da ta ke Matar Saifuddeen albarka. Mahaifinta shine musabbabin saka Saifuddeen a harkar siyasa and yanzu ne zai ga alfanun sadaukarwar da yai a rayuwar Saifuddeen domin yanzu shi ɗin Gwamnan Jahar Congo ne.... *** Asiya ba ta yi tsammanin kira daga MD ɗin su ba dan rabonta da shi tun ranan da aka bata suspension letter. Sai da ta ƙarisa aikin da ta ke yi kafin ta wuce office ɗinsa. "Sannu da aiki Sir" "Yawwa Asiya. Ya aikin?" "Alhamdulillah" "Inada assignment da za ki yi. Idan kin carrying out na shi da kyau za ki dawo aikin ki na da" Washe fiska Asiya ta yi ta ce "Sir wani assignment ne?" Wata takarda ya tura gabanta ya ce "muna so ki yiwa Gwamna Interview" Murmushin fiskar Asiya ya ɓace ɓat. Wata na biyu kenan da SSK ya zama Gwamna kuma har yanzu ya ƙi yin interview da kowani gidan jarida. Sau ɗaya yai press conference sati ɗaya bayan an rantsar da shi a matsayin Gwamna. "Sir i think Hill TV ta nemi hira da shi kwanakin baya kuma ya ƙi" "Shiyasa na ce assignment ne. Ko dai yanzu akwai aikin daya gagari Asiya-Shahidah ne?" Asiya ta ƙunshe baki tareda sauke ajiyar zuciya. "Ba komai Sir zan nemi permission daga gidan Gwamnati kafin satin nan ya ƙare Insha Allah" Ko da ta bar ofishin sa office ɗin su CY ta wuce ta sameshi yana editing wani video da za a ɗaura anjima. "Babez ya na ga kin haɗe rai?" "za ka rakani Government office gobe" "Government office? Why?" "Kai dai ka shirya kawai". "Okey dokey" *** Ƙarfe takwas saura suna bakin Gidan Gwamnati. Ba su samu matsalar shiga ba suna nuna ID card ɗin su aka ce su wuce. Wani security ne ya mu su rakiya har ofishin Sakataren Gwamna. Asiya ta yiwa Mr Baffayo Sakataren Gwamna bayanin abinda ke tafe da su. Bayan ta gama ya ce " Malama Asiya na ji daɗin zuwan ku gaskiya sai dai Mai Girma Gwamna ya ce ba zai yi zama da kowani ɗan jarida ba yanzu, sai dai ko gaba" "Ranka shi daɗe, Hill TV zata yi hira da shi ne gameda tarihin rayuwar sa babu maganar siyasa a ciki" "Malama Asiya kenan. Zai fi dai ku haƙura zuwa lokacin da Gwamna zai so yin hiran da kan shi" "Sir da dai ka miƙawa Gwamna letter ɗin mu ƙila a dace" ta faɗa a marairaice Sakatare ya karɓi wasiƙar ya ce zai miƙawa Gwamna. Su ka ma sa godiya su ka tafi. Koda Gwamna ya dawo Sakatare bai ba shi wasiƙar ba, bai ma gaya masa su Asiya sun zo ba. Asiya na nan tana jiran kiran Sakatare amma shiru. Washegari ƙarfe goma ta sake komawa ofishin Gwamna. "Kin ga abinda na faɗa miki ɗin ne dai, Gwamna ya ce ba zai karɓi gayyatar ku ba" "Dan Allah Malam ka sa baki. I really need to take his interview" "Ki yi haƙuri. Zan dai sake yi ma sa magana ince kin sake zuwa. Kin san matsalar ne. Akwai wanda su ka fi ki naci sunyita zuwa Kwanakin baya, ƙarshe Gwamna ya ce kar a sake bari ɗan jarida ya zo ofishin sa amma..." "Oh haka ko?" Asiya ta faɗa a hasale Sakatare ya zuba ido yana kallonta da mamaki. Asiya ta ciro wasiƙar da su ka ajiye ma sa jiya a ƙasan laptop da ya ke aiki da shi. "Zan iya rantsewa wannan bai je hannun Gwamna ba" Sakatare ya fara kame-kame. Allah na gani girman shekarunsa da Asiya ta gani ya sa ta iya controlling kanta ba ta ma sa rashin mutunci ba. "Zan dawo gobe, zan jira ko ƙarfe nawane sai na ga Gwamna da kaina na bashi wasiƙar. Zan haƙura ne kawai idan shi da bakinsa ya ce ba zai yi hira da ni ba" Daga haka ta fice daga office ɗin ta bar Sakatare baki buɗe. Bayan tafiyar Asiya da Sakatare ya shiga wajen Gwamna kai ma sa wasu takardu sai ya haɗa da wasiƙar Asiya. "Wannan fa?" Gwamna ya tambaya yana ɗaga envelope ɗin da wasiƙar ke ciki. "Your excellency gidan talibijin na Hill TV ke son hira da kai" "Malam Baffayo hira da 'yan jarida sai gaba, we have better things to do with our time now" "Yes excellency" Daga haka ya fita bai sake ɗago maganar ba. Washegari kuwa kamar yadda Asiya tayi alƙawari sai gata a ofishin Gwamnati sai dai wannan karan ko ƙarasawa ofishin Sakataren Gwamna ba ta yi ba aka dakatar da ita. "Ban gane in tafi ba. Ina son ganin Gwamna ko akwai dokar da ta hana hakan?" Asiya ta faɗa wa security guard ɗin daya tsareta cikin tsawa. "Gwamna baya office ki je ki dawo wani lokaci" "Ba inda zan je. Gwamna yana nan. I need to have audience with him" " idan ba ki fita ta lallami ba, za a fita da ke ta ƙarfi. So please leave" "Ba inda zan je fa" Asiya ta faɗa tana gyara tsayuwarta. A ofishin Sakatare kuwa Gwamna ne ya zo wucewa zuwa wani exco meeting ya jiyo hayaniyar da ake yi hakan ya sa shi ya ɗan tsaya. COS da ke bayan sa ya kalli Sakatare cikin tsawa yace "wai wacece a wajen nan ne?" "Wata 'yar jarida ce ta dage sai ta ga Gwamna". "Kul ka taɓa ni, wallahi yatsata ka taɓa sai ka san wacece Asiya-Shahida a garin nan. Na san 'yanci na dan haka kar ka kuskura ka min barazana" Wannan karan tana maganar ta zauna a kan kujera da ke Lobby ɗin tareda ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana huci. "Malam Baffayo ka ce ta dawo ranan Monday" Ba da ƙarfi yai maganar ba amma duk sun ji shi. Bai jira mai Sakataren zai ce ba ya wuce abinsa. Asiya ta zauna na kusan minti shabiyar kafin Sakatare ya fito. "Malama Asiya ya da haɗe rai haka" "Ba fa inda zan je" ta faɗa tana girgiza kai Sakatare ya miƙa ma ta wani envelop. Tana gama karanta takardar da ke cikin envelope ɗin ta saka ihu. Sai kuma ta yi saurin rufe bakinta da hannunta. Sakatare yai dariya ya ce " gaskiya kin taki sa'a. Gwamna ya amince ya ganki ranan Monday, best of luck" Fiska a washe Asiya ta ma sa godiya ta tafi. Shi kan sa Sakatare yayi mamaki da amincewar Gwamna cikin sauƙi haka. *** A chan ɗakin da ake taro kuwa dukkan wanda ya ke da alaƙa da wannan taro ya riga ya hallara dama Gwamnan kawai ake jira. COS ne ya ja masa kujera ya zauna yana kallon mutanen da ke wajen ɗaya bayan ɗaya. Kusan minti guda ya ɗauka sannan ya ja dogon numfashi sannan ya ce "gentlemen ina buƙatar report na wannan wata" "Kwamishina Isiaka" Gwamna ya kira yana duban wani ƙaton baƙin mutum sanye da babbar riga kalar light blue. Kwamishinan ilimi yai gyaran murya sannan ya fara bada bayani wanda ya ɗaukeshi tsawon minti huɗu da rabi. "Not impressive Kwamishina Isiaka. Ban ji ka yi maganar Albashin Malaman firamare da za a ƙara ba" "Your excellency mun submitting budget farkon watan nan amma abunda ya iso mana daga hannun Kwamishina of Finance shi mu ka yi amfani da shi" Gwamna SSK ya juya ya zubawa Mr Paul idanunsa ma su kaifi hakan ya sa shi fara wiki-wiki da ido. "Mr Paul!" Gwamna ya faɗa da ɗan ƙarfi. "Excellency saboda akwai basusuka dayawa da tsohon Gwamna ya bari muna so a fara rage wannan kafin a fara maganan ƙara albashi" "Abinda aka fara tunkarana da shi lokacin dana ƙarfi wannan kujera shine maganan ƙarancin albashin Malaman Firamare. If i can remember clearly. Sai da na ce Kwamishina Isiaka ya drafting budget ya nuna maka, kana tunanin da wasa na yi maganar?" "No your excellency" Mr Paul ya faɗa yana sunne kai ƙasa. "Ina Kwamishinan raya karkara" "Your excellency" wani mutum fari dogo ƙyamusashshe ya faɗa yana ɗaga hannu. "Banga report dana buƙata ba tun farkon watan nan" Cikin turancin sa da take nuna asalin harshen bahaushe ya fara bayani. "Na tura memo wa Kwamishina Paul ya kai sau huɗu amma babu wanda ya reply aciki" Wannan karan ma Gwamna ƙurawa Mr Paul ido yai. "Your excellency budget da aka yi da tsohon Gwamna babu buƙatun Kwamishina Ɗanladi a ciki shiyasa babu yadda za ayi yanzu a ƙirƙiro kuɗi a bashi sai yai haƙuri sai wata shekarar" "Oh hakane ko?. Ina buƙatar budget da aka drafting na wannan shekarar da kuma abubuwan da akayi da su haɗe da receipts na komai. Kwamishina Paul zan saurari report ɗinka gobe da safe a office ɗina" Mr Paul ya taƙune fiska kamar wanda ya tauna flagyl yayinda sauran excos da ke wajen kowa ya sha jinin jikinsa. Lokacin da SSK ya ke mataimakin Gwamna bai taɓa ɗaga murya ba, infact idan za ayi meeting sau dubu to zaka iya irga iya maganan da yai a meeting ɗin amma wai yanzu roughly wata biyu daga rantsar da shi ya rikiɗe musu ya koma wani Zaki. Magana ta ƙarshe da aka yi shine maganar naɗa sabon mataimakin Gwamna wanda Gwamna ya tabbatar mu su da cewa ranan talatin ga wata za'a rantsar da mataimakin Gwamna wanda har yanzu basusan ko wanene ba. "Babu mamaki idan kuka cigaba da irin wannan sakacin a office ɗin ku zan sake sabon cabinet" Gwamna na gama faɗin haka ya miƙe tsaye yana ɗaukan wayoyinsa guda biyu da ipad yayinda sauran excos ɗin ma suka miƙe tsaye suna faɗin "Excellency"... A ɓangaren Asiya kuwa tana fita daga gidan Gwamnati ta wuce ma'aikatar su. Tun a hanya ta kira CY ta ma sa albishir. Tana isa kuwa Office ɗin MD ta fara wucewa. Tana shiga ta ajiye ma sa takardar hannunta wanda tunda ta cirota daga cikin envelope ba ta iya maidashi ciki ba. "Yaushe zan koma bakin aikina?" Ta faɗa tana kallon MD daya wangame baki saboda ganin seal ɗin Gwamna akan takardar. "That's fantabulous Asiya. Ya kika yi? Kai i'm happy. This means gidan talabijin ɗin mu ne za ta fara hira da Gwamna Saifuddeen. Whoaw!" Asiya ta sa dariya. Farin cikinta ko kaɗan ba shi da alaƙa da kasancewarta 'yar jarida ta farko za ta yi hira da Gwamna SSK tun da ya hau kujerar Gwamna. Farin cikin ta ya zo daga abu biyu ne. Na farko aikinta da za a dawo mata da shi (ta tsani aikin editting ɗin nan). Na biyu kuma cimma burinta da ta yi. Idan za ka lissafo halayen Asiya to dole ka sako cewa ita ɗin mace ce mai son cimma duk wani abu da ta sa a gaba. A cikin dictionary ɗinta babu kalmar impossible. Akoda yaushe slogan ɗinta shine *it's possible but.... HOW* Kafin ta bar office ɗin MD sai da ya ce ta drafting tambayoyin da za ta yiwa Gwamna ta kawo mishi kafin a tashi... *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 05 Tunda Gwamna SSK ya zauna ya ke sauke numfashi akai-akai saboda maganganun Baffan na sa daya saka mishi rashin nitsuwa har ya ji ƙirjinsa ya cunkushe. Ƙarshe hannu ya sa a aljihu ya lalumo inhaler yai saurin jijjigata sannan ya kai bakinsa ya matsa. Alhaji Sani ya sassauta muryansa ya ce "sannu Saifu. Har yanzu yana damunka sosai ne?" "Nagode Baba" abinda ya iya faɗa kenan Alhaji Sani bai matsa da cigaba da maganar da su ke ba ganin SSK yana buƙatar hutu sai dai kafin su rabu ya jaddada ma sa cewa tabbas zai kai ma sa ziyara zuwa office ɗin sa gobe. Bayan Gwamna ya bar Kachallah house kai tsaye gidansa ya wuce dan har yanzu ba su koma gidan Gwamnati ba saboda gyararraki da ake yi. Bayan wannan dogon rana ba abunda ya ke buƙata irin bacci cikin kwanciyar rai amma yana isa falonsa ya iske Bilkisu tana zaman jiran sa. "Excellency Darling" ta faɗa tana manna ma sa kiss a kumatu. "You're just here on time, yanzu na gama parking kayanka. May be mu je ka gani ko akwai abubuwan da za ka buƙata" "Parking?" "Dont tell me ka manta jibi Asabar za mu koma Government house" "An gama gyaran ne?" Gwamna ya faɗa yana zama a kan kujera "Darling yaushe ka fara mantuwa ne. Jiya fa na ke gaya maka an gama gyaran gidan za mu iya shiga yanzu" "Bilkisu ki miƙo min ruwa mai sanyi please" Sai da ta ɗan tsaya kaman mai shirin shawara da zuciyarta kafin ta miƙe. Ya sani da a falon ƙasa su ke sai dai ta kira ma sa Hansa'u ko ɗaya daga cikin ma su yi mu su aiki. Ko da ta kawo ruwan ba ta barshi ya sha da daɗin rai ba ta cigaba da maganar komawar su gidan Gwamnati. "Hansa'u da Uwaji za su bimu, sauran za su zauna a nan tunda dai ba za a bar gidan kango ba" Kallon da ya ke mata kallon ki barni na huta ne amma ita Bilkisu sam ba ta karanci hakan ba. Sai ma cewa da ta yi "ko akwai wanda ka ke so a tafi da su bayan su Hansa'un?" Bai amsa ma ta ba, sai ma kauda zancen da yai da cewa "ina yarana?" "Duk sun yi bacci. Mahira ma ta dawo yau da yamma" Gwamna ya miƙe tsaye yana faɗin "sai da safe"... *** "Ya Ubayd ina tsoro, mafarkin danayi jiya ya tsoratani sosai" "Wani mafarki kenan?" "Na yi mafarki wai..." sai kuma ta yi shiru. Ta ina za ta fara ce ma sa ta yi mafarkin marigayi Kakanta Gwani yana ɗaura aurenta da Gwamna Saifudden Kachallah. This is absurd ai, ba abune da ya ke da daɗin faɗa ba. Balle ta san halin kayanta da shegen kishi. "Ance ba kyau faɗin mummunan mafarki dan haka ka barshi kawai" "Yau kuma?" Ya faɗa yana taɓe baki "Mu bar zancen kawai. Ya maganan aikin kitchen ɗin nan an saka sink ɗin nan kuwa?" "An gama Yallaɓiya. Kin matsu ko? Saura wata huɗu da kwana ɗaya tak" Yana maganan ta ji ƙirjinta ya buga hakan ya sa ta yi saurin faɗin "Insha Allah" shima Ubayd ɗin ya maimaita kalmar. Bayan sun gama hira da Ubayd ta shiga ɗaki ta iske Umma na duba wasu kulolin abinci. Umma na ganinta ta mata magana da hannu akan ta zo ta duba kulolin ko sun yi kyau. Asiya ta zauna tana dubasu tareda faɗin kulolin sun yi kalan 'yan ƙyauye. "Umma ni ban san miyasa kike siyan kaya a wajen Laraba dillaliya ba. Ga kayanta tsada gashi ba wani kyau ne da su ba. Indai ni kika siyawa gara ki mayar mata dan ba su min ba" ta ƙarisa maganar tana turo baki Umma ta taɓe baki tana kallon Asiya. "Allah Umma ko kin saka a kayana kyautar da shi zan yi, dan wannan kulan ba zai zauna a dining table ɗin gidana ba ehe" Umma ta yi murmushi sannan ta mata bayani akan gudummawar da ta ke son bayarwa 'yar maƙotan su da za a aurar ne nan da sati biyu. "Yanzu na ji batu Umma na" ta yi maganar tana rungume Umman ta... Yau ma dai mafarkin data yi ne ya tasheta daga bacci, abin mamaki irin mafarkin jiya ne sai dai wannan karan Gwani ya haɗa hannunta dana Gwamna yana ma ta nasiha akan mahimmancin haƙuri da kuma yarda da juna a rayuwar aure. Ba ta cika yin mafarki ba hakan ya sa a mafiya lokuta idan ta yi mafarki za ka ga abun yanada nasaba da rayuwarta. "Allah ka sa wannan mafarki ba gaskiya ba ne. Ubayd na ke so ya Allah" ta faɗa a hankali tareda sauke ajiyar zuciya sannan ta koma ta kwanta sai dai bacci ya gagareta... *** Asiya ta fito daga kitchen a fusace saboda ruwan wankanta da aka juye. "Wani marar imanin ne ya juye min ruwana?" "Waye a banɗakin nan ne?" Ta faɗa tana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin kaman za ta ɓalla shi. "Mutum ya tashi da Asuba ya saka ruwa azo a juye ma sa, a hakan ba za a saka masa wani ba. Koma waye yau sai ya biyani ruwana" Kusan minti uku sannan Hindatu ta buɗe ƙofa ta fito ɗaure da zani. "Miye ne kike ta buga ƙofa kamar wata sabuwar mahaukaciya" "Ke ce mahaukaciyar ai. Na saka ruwa a heater kin zo kin juye min saboda tsabar iya shege" "Dama akwai wanda ya kafa dokar idan kana gidan ubanka sai ka nemi izinin Agola kafin ka yi amfani da abun gidan ne?" Asiya ta buɗe baki za ta yi magana amma ta fasa saboda ɓata lokaci ne biyewa Hindatu da sassafen nan. Ba ta san mi ta tsarewa wannan Hindatun ba. Ta rasa kishi ta ke da ita ko kuma haka kawai tsantsar ƙiyayya ce. Banɗakin ta shige ba tareda ta tankawa Hindatun ba, ta fito da bokiti ta je ta ɗebo ruwa mai sanyi. Kafin ta ce za ta haɗa wuta ta ɗaura wani ruwan wankan lokaci zai tafi dan haka kawai ta daure ta zo ta yi wanka da ruwan sanyi. Tana fitowa kuwa da gudu ta je ta shige ɗakin su ta kullo ƙofar da ƙarfi Umma ta kalleta ta ce lafiya? da hannu "Sanyi Umma" ta amsa tana ƙarisawa wajen jakar kayan kwalliyarta. Ƙarfe bakwai saura kwata Asiya ta fito daga gidansu sanye da wandon jeans blue, baƙin riga sai farin blazer jacket da ta saka sannan ta yane kanta da light blue gyale. Keke ta nema ta wuce ma'aikatar su. Tana zuwa office ta fara duba tambayoyin da ta tsara wanda jiya da daddare MD ya kirata ya ce ta ƙara da tambaya ɗaya wato miyasa Gwamna ya naɗa tsohon Kwamishinan ayyuka Alhaji Bala Yamai a matsayin mataimakinsa. Kusan komai ya tafi daidai. Zuwa ƙarfe tara Asiya da CY su ka kama hanya zuwa gidan Gwamnati. Lokacin da su ka zo an ajiye su a waje na musamman kafin Gwamna ya fito. A cikin ofishin Gwamna kuwa COS ne ya ke ganawa da Gwamna. "Your excellency ina so ka dai sake tunani akan wannan lamari, yanke wannan allowance ɗin dai dai ya ke da fushin cabinet members ɗinka" "Wani ɓangare ne cikin magana na baka gane ba?. Kana sauraron kanka kuwa?. For God's sake bayan ɗimbin ayyukan da ke gaban mu har kuna da zuciyar da za ku tambayi wani allowance" "Excellency wannan allowance ɗin tun kafin administration ɗinka ake bayarwa idan ka ce ba za ka cigaba da bayarwa ba za a samu matsala" "Look Mr Damana. Ba zansa hannu a wannan ɗimbin kuɗin ba bayan munada abubuwa dayawa a gaban mu. Ka ƙara jaddadawa Mr Paul cewa bazan biya kuɗin nan ba. Now please leave my office" COS ya miƙe jiki a sanyaye. Bayan fitan COS Gwamna ya kira Sakatare "Malam Baffayo ka haɗa meeting da Contractors ɗin nan ƙarfe goma" Sakatare yai saurin cewa "Excellency akwai hiran da za ka yi da 'yar jarida daga Hill TV ƙarfe goma, sun ma iso lokaci su ke jira" Har zai ce a ce su dawo wani lokaci sai kuma ya fasa yace ya maida meeting ɗin sa da Contractors ɗin ƙarfe goma da rabi saboda minti talatin kacal zai yi da su Asiya. Asiya na tsaye tana yiwa CY magana Gwamna da tawagarsa su ka iso. Ganin CY yayi saurin miƙewa ya sata juyawa ba shiri. "Your excellency Sir" CY ya faɗa yana murmushi. SSK ya miƙa ma sa hannu CY yai saurin saka hannu biyu ya damƙi hannun SSK yana faɗin " myself Clement Yohanna" "Welcome Mr Yohanna" sannan ya miƙawa Sunusi hannu dreban daya kawo su Asiya. "Allah ya ja zamanin Gwamna. Allah ya kare ka, Ubangiji ya maka jagora" Sunusi ya dinga sunbatu kamar zai haɗiye Gwamna saboda farin cikin sun yi musabaha da Gwamna SSK. Tunda Asiya ta juya ta ganshi bakinta ya kafe. Yadda kasan an tura mata dunƙulen Auduga a maƙoƙoro haka magananta ya toshe ya ƙi fitowa. Sau ɗaya su ka haɗa ido amma gaba ɗaya ta rasa nitsuwarta. Kaifin idanunsa gareta sun karya ma ta duk wata laka da ke jikinta. Abin mamaki wai ita Asiya-Shahidah da ta ke iƙirarin ba mutumin da ba za ta iya magana a gabansa ba sai gashi kusan minti biyu da zuwan Gwamna wajen ta kasa ko da gyaran murya ne. A baya duk lokacin da aka yi maganar ƙwarjinin SSK ƙaryatawa ta ke yi sai gashi yau ta gani a zahiri. Bayan Gwamna ya gama darawa bisa surutun Sunusi da CY sannan ya maida hankalinsa ga Asiya. *"Asya?"* Ya kira sunanta da sigar tambaya Ji tayi jiri yana shirin kwasarta a wajen saboda irin yadda taji wani abu ya ratsa jijiyoyin jikinta lokaci guda. Taya ma zai iya kiran sunanta da daɗi haka? Ta yi kusan sakan goma kafin ta iya haɗiye koma minene daya toshe mata maƙoƙoro ta ɗan yi ƙaramar gyaran murya sannan ta ce " your excellency, Asiya Shahida Faruƙ Baba" "Of course. The famous Asya ta tashar Hill tv" "Sit" ya faɗa yana nuna mu su kujera. Sai da ya zauna kafin suma su ka zauna "Wannan location yayi ko za a chanja wani?" CY yai caraf ya amsa da cewa "yayi your excellency. Barin saita camera sai a fara ɗaukan hiran" Da rawar jiki CY ya miƙe ya fara saita camera yayinda Asiya ta sunkuyar da kanta ƙasa tanajin kamar idanun Gwamna yana yawo a duk ilahirin jikinta. Sai yanzu ta yi dana sani da hijabi ta saka ba gyale ba. Kusan minti shida kafin CY ya gama saita komai ya ɗagawa Asiya hannu yana faɗin one, two.... "ina zuwa CY" ta faɗa sannan ta yi saurin ɗaukan ruwan da aka kawo mu su ta tsiyaya a kofi ta kafa kai sai da ta shanye. Ta sake tsiyaya wani ta shanye. CY ya ɗaga gira sama yana faɗin "Aseey are you nervous?" Asiya ta yi saurin girgiza kai tareda yin gyaran murya ta ce "muje, na shirya " CY na ɗaga ma ta hannu ta tattaro duk ƙarfin halinta ta fara bayani kamar haka *"ma su kallon mu barkar mu da warhaka, barkan mu da sake saduwa da ku a cikin shirin nan mai suna 'Siyasar mu a yau'. A yau dai za ku ga sauyin tsari, domin shirin namu kwacokam zai kawo muku hira ne da wani shahararren ɗan boko, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wato mai girma Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah inda zai bamu cikakken tarihin rayuwar sa da yadda aka yi har ya kawo wannan matsayi. Ni Asiya-Shahidah Faruƙ Baba zan gabatar da shirin a madadin abokin aikina wato Comrade Faisal Kamaye"* Sakataren Gwamna ne ya ƙariso wajen da sauri ya ɗan rankwafa yai wa Gwamna magana a kunne. Hakan ya sa C Y ya dakatar da ɗaukan shirin. Gwamna ya kalli Asiya ya ce "za'a dakatar da shirin zuwa ƙarfe shaɗaya Insha Allah" Bayan Gwamna ya tafi sannan Asiya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tareda fara yiwa kanta fiffita da hannu dan duk iskar wajen ta mata kaɗan. CY ya matso wajenta yana yi mata dariya tareda tsokanarta kan cika bakin da tayi kafin zuwansu sai gashi ganinta kusa da Gwamna ta ruɗe. Tun suna jiran Gwamna zai dawo ƙarfe shaɗaya har su ka fara sarewa ganin har ƙarfe ɗaya saura. "CY anya ba za mu tafi ba. It seems wannan Gwamnan ya manta da mu fa" Kafin CY ya bata amsa Sunusi driver yai saurin ɗaga murya da cewa ko ƙarfe nawa ne za su jira Gwamna tunda ya ce su jira shi. "Bar Aseey, tana mana baƙin cikin kyautan da Gwamna zai mana ne" CY ya sa baki. "Wannan maƙon ne zai baku kyauta?. Keep dreaming Clement". "Allah idan aka bamu banda ke aciki tunda naga adawa ki ke da Gwamna" Sunusi ya faɗa yana ƙarisa sauran maltinan da Asiya ta rage. Bayan Gwamna ya bar wajen su Asiya kai tsaye office ɗinsa ya wuce inda Alhaji Sani Kachallah ke jiransa. Idan ba shi ɗin bama waye zai shiga office ɗin Gwamna kai tsaye haka bayan Gwamna baya zaune a kujera. "Baba sannu da zuwa" SSK ya faɗa yana faɗaɗa murmushinsa. Bayan sun yi musabaha sannan ya je ya zauna a kujerarsa yana kallon Alhaji Sani. Sun gama maganar naɗa mataimakin Gwamna tunda ya naɗa wanda su ke so bai san kuma mi ya kawo sirikin nasa office ɗinsa ba wannan safiya. Bai yi mamaki ba da Alhaji Sani ya kawo maganar allowance na cabinet members daya riƙe. Sai dai duk da kunyan Alhajin daya ke ji hakan ba zai sa ya aiwatar da wannan baɗala ba. "Baba tunda na hau kujeran nan na ke tsoron haƙƙin mutane da ke kaina. Idan na basu kuɗin nan tamkar na ci amanar wannan Jaha ce. Bayan ɗimbin albashi da sauran allowance da doka ta tanadar a basu miyasa zan sake ɗaukan maƙudan kuɗi na basu bayan akwai tarin ayyuka a gabana" Gwamna yayi maganar ne a sanyaye saboda darajar Alhaji amma idan da zai fidda tiriri da zuciyar sa ke yi to ba ƙaramin amon wuta zai yi ba. "Saifu kenan. Kaga siyasa lamari ne daya ke buƙatan hankali da takatsantsan. Kwata-kwata abun da za ka yi a wannan kujera kafin a sake wani zaɓe bai kai shekara ɗaya ba. Idan kuwa hakane dole ne ka tafi da mutanen nan yadda aka riga aka ɗaura su akai. Idan muna da rai kaci zaɓe sai ka fara naka sabon tsarin" Gwamna yai shiru yana kallon Alhaji Sani. Yadda yai maganar cin zaɓe ya bashi mamaki. Domin zaɓe dai ba ayi ba balle a san ko zai koma kan kujerarsa ko ba ze koma ba. "Baba da kamar wuya. Kuɗin sun yi yawa" "Ka biya kaso 70% na kuɗin" Gwamna ya tauna leɓensa na ƙasa tareda sauke ajiyar zuciya. Yadda Alhaji Sani ya shawo kansa akan maganar naɗa Bala Yamai a matsayin Mataimakin Gwamna baya tunanin wannan karanma zai bar ofishinsa har sai ya samu abinda ya ke nema. "Zan biya su kaso 40%" Alhaji Sani ya ɗan ɗaga ido sama na ɗan daƙiƙu kafin ya sauke akan Gwamna Saifuddeen ya ce "mu rufe shi kaso 50% Saifu". Bayan fitan Alhaji Sani daga office ɗin Sakatare ya shigo ya sanar da shi Contractors da za ayi meeting da su sun iso. Gwamna ya miƙe ya fita. A chan wajen meeting ɗin ma wani ɓacin ran ya tarar domin kusan kaso saba'in da biyar na ayyukan da marigayi Gwamna Saminu Bacchi ya fara duk akan bashi ne. 'Yan Kwangila suna son a biyasu kuɗaɗen su idan ba haka ba sun dakatar da duk wasu ayyuka har sai baba ta gani. Gwamna ya duba COS ɗinsa sannan ya maida dubansa ga Mr Paul. Waɗannan biyun sun fi kowa ɗaga jijiyar wuya akan maganar allowance amma yanzu ana maganar ayyukan cigaba na Jaha amma kowannen su yayi tsit. Kuɗin allowance ɗin nan da su ke buƙata idan da za a haɗa na wata huɗu zai biya gaba ɗaya basussukan da contractors ɗin nan su ke bin Gwamnati. Haƙuri Gwamna ya basu tareda mu su alƙawarin zai biyasu dukkan kuɗaɗen su zuwa wani watan sai dai wannan wata za su fara ne da kaso 25% na kuɗin da zai biya su. Basu ɗau lokaci ba suka amince da maganar Gwamna. A take a lokacin Mr Paul ya miƙa masa wasu takardu tareda check Gwamna ya saka hannu sannan aka miƙawa jagoran contractors ɗin wato Mr Azad Sahib Khan. Gwamna na komawa kan kujerarsa Mr Paul da COS suka biyo bayansa da takardar da suke son ya saka hannu. Gwamna ya duba takardan a walaƙance sannan ya kalli fiskar Mr Paul wanda ƙarara ta nuna bai ji daɗin kaso 50% ɗin da za a basu ba ya ce " Mr Paul ina fata baka manta maganan ƙarin albashin malaman makaratan firamare ba" "Your excellency na sani" "Good". Kusan ƙarfe biyu saura kwata da Gwamna zai fita sallar Azahar Sakatare ya tuna masa da su Asiya da ke jiransa tun ƙarfe goma. Gwamna ya girgiza kai ya ce su dawo gobe dan akwai inda zai je idan yayi sallah. Idon Asiya ɗar akan wayarta lokacin da wani security ya iso ya ce musu Gwamna ya ce su dawo gobe ƙarfe goma. "Kan Uba..." "Mungode zamu dawo gobe ɗin" CY ya faɗa yana hararan Asiya. Har suka isa ma'aikatarsu Asiya bata bar zagin Gwamna ba kan walaƙantasu da yai. Har iƙirari ta yi akan gobe ba za ta koma ba sai dai Comrade Faisal ya je yai tunda dama asali shirinsa ne. Sai dai MD bai bata damar hakan ba dan cewa yai ita ɗin dai yakeso tayi hiran da Gwamna goben. Da dare da Ubayd ya zo hira kaman ta shaƙeshi dan yadda ta ke masifa tamkar shine Gwamnan. "Mine, sunana Ubaydullah ni Likitan Ido ne ba Gwamnan Jahar Congo ba. Ki ajiye fushinki a gefe please" "Dan shi Gwamna ne sai akace ya maidamu Awakai. He treat us like goats fa. Ya shanya mu for good 4 hours munata jiransa" "My Asiya Gwamna fa akace. The first citizen of the state" "And so bloody what!" "Shikenan. Yayi haka a chanja hiran" "Da wani shegen idonsa a wajen..." ta ƙarisa ƙarshen jimlar a hankali saboda wani abu da ya zo ya dabaibayeta. Idon da ta ke zagi shi dai ta gani yau ta birkice, ta rasa nitsuwarta. Idon ne dai da ya ke sukanta kamar kibiya lokacin da ta ke zaune daura da shi kafin CY ya gama haɗa camera. Ba ta gayawa Ubayd wannan ba ƙila shiyasa ta dage kawai akan cin mutuncin da Gwamna ya mu su. Sai da Ubayd ya sako zancen kayan lefenta da yake haɗawa kafin ta ture maganan Gwamna a gefe ta koma ta rayuwar da su ke shirin farawa tare nan da watanni kaɗan. *** Taron gaggawa Mr Paul ya kira a gidan Yallaɓai tunda suka haɗu kuwa aketa cacar baki sai da Yallaɓai ya tsawatar kafin sukayi shiru. "Mr Paul ina sauraronka" Mr Paul ya ɗaga takardar da Gwamna SSK ya sa hannu yace "Yallaɓai tunda Saminu Bacchi ya hau kujera bai taɓa chanja tsarinmu ba amma gashi nan wata biyu da hawan Saifuddeen ya hanamu allowance lokacin da ya ga daman bamu kuwa kaso hamsin ya bayar. Ka gaya min ta ina zamu yarda da wannan cin mutunci. Idan har ba zai iya ba to kuwa yai resigning a ɗaura Bala Yamai" "Ka ci gidanku Eugene Paul. A gabana kake cewa Saifu yai resigning saboda baka da hankali" "Alhaji Kachallah ka kama girmanka, ka san bana yarda da cin mutunci a gidan nan" "Ayi haƙuri Yallaɓai amma Paul ya sani cewa an ɗaura Bala Yamai ne ba dan shi ba sai dan kawai lokacin saka mutumin Agun ne a matsayin mataimakin Gwamna. Ya kamata kuma ya sani cewa ba zan lamunta a ci mutuncin ɗana ba" Bayan duka ɓangare biyu sun gama gabatar da ƙorafinsu sannan Yallaɓai yai magana. "Kowani Gwamna muna bashi wata shida dan ya aiwatar da abinda ya ga dama a farkon tenure da kuma ƙarshen tenure ɗinsa. Lokacin Saifuddeen ne yanzu, Mr Paul ka barshi yai abinda yake so" "Amma..." Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu hakan ya sa shi datse maganarsa. *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 06 Washegari Asiya ba ta shirya da wuri ba dan sai takwas da rabi ma ta fita daga gida. So take MD ya tura Comrade Faisal da CY gidan Gwamna amma kash! MD ya nace sai ita ɗin zata je. Yau kan maimakon riga da wando data saba sakawa Atamfa ta saka riga da skirt da ƙaton mayafi daya kai mata gwiwa. Shikansa MD sai da yai wa Asiya kallon mamaki ganin shigar da ta yi, rabon da Asiya ta yi shigar Atamfa zuwa office har ya manta. Suna tafiya a hanya CY ya dinga tsokalarta wai tayi shigan matan aure. Asiya bata kulashi ba dan gaba ɗaya gabanta faɗuwa yakeyi, ta rasa dalilin hakan kuwa. Koda suka isa gidan Gwamnati ƙarfe goma saura minti shabiyar. Wajen da aka ajiyesu jiyan dai nan aka sake zaunar dasu. Basufi minti goma da zuwa ba fitsari ya kama Asiya, cikin ranta sai dana sanin shayin da ta sha kafin su fito take. Ƙarshe data ga abin zai dameta ta miƙe ta tafi wajen wata mata da ke da office a corridor ɗin lobby ta tambayeta ina ne banɗaki, matar da keta tauna cingam kamar zata haɗa da harshenta tayiwa Asiya kwatance tana haɗe rai, Asiya ta wuce tana mamakin matar da fiskarta ya gama soyewa saboda bleaching. ** "Na san ka san matsayinka a wannan Jaha. Kuma ka san baya daga cikin ayyukan ka abinda ka aikata" "Your excellency..." Gwamna ya ɗaga masa hannu ya cigaba "kar hakan ya ƙara faruwa Mr Lamara Damana. Matsayin Chief of Staff zai iya faɗawa hannun kowa nan gaba. Ina fata ka fahimta" "Yes your excellency. Hakan ba zai sake faruwa ba da yardar Allah" "Good. Now ka duba min ko kwamishinan ayyuka ya fara aikin da aka bashi" Lokacin da COS ya fita Gwamna ya jawo takardar da ya ajiye ya kekketata sannan ya watsar. Ba zai taɓa lamunta da wannan ba. Fitar COS keda wuya Sakatare ya shigo ya sanar da Gwamna cewa 'yan jaridan jiya sun dawo. COS na shiga office ɗinsa ya cillar da file ɗin hannunsa takardun ciki suka watse. Ya dunƙule hannunsa kamar mai shirin dambe, ya kira sunan Gwamna da ƙarfi "Saifuddeen Kachallllaaaaah!" Yana cikin huci ya tuna da wani abu nan da nan yai saurin lalubo wayarsa a aljihu ya shiga danna kira, ba aɗauka ana farko ba sai a kira na biyu. "Akwai matsala Kachallah" abinda ya fara furtawa kenan da kakkausar murya. Bai bari wanda yake maganar ya ƙarisa ba ya katse shi da cewa " har Gwamna zai yi iƙirarin cireni a matsayina. Ya manta ne? Ya manta ne?" Yai shiru yana sauraron bayani daga ɗaya ɓangaren sannnan ya ɗaura da cewa "idan har bai san yadda akayi aka ɗaura shi akan kujera ba to kuwa lallai ƙaddarar da ta hau tsohon Gwamna za ta sameshi. Ta inda aka hau tanan fa ake sauka Kachallah... eh inaji.... sai dai abu ɗaya na sani idan har Saifuddeen ya cireni a matsayina saina gayawa duniya cewa Saifuddeen Sa'ad Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna..." Saura kaɗan recorder da ke hannun Asiya ta faɗo saboda firgita da tayi. Tayi saurin toshe bakinta saboda kar mutumin da take naɗan maganarsa ya jiyo nishinta. Ta fito daga banɗaki kenan za ta koma inda aka ajiyesu ta hango Chief Of Staff ya zo ya shige wani lungu a bircike. Curiosity nata na 'yar jarida ya sa ta bi bayansa. Wani office taga ya shige hakan ya sa ta bi bayansa da zimmar ko za ta iya gano dalilin fushinsa tunda hanyar da ta ga ya fito tanan ne office ɗin Gwamna, koma minene ya ɓata masa rai yanada nasaba da Gwamna ɗin. Ihun da ta jiyo COS yayi yana kiran sunan Gwamna yasa ta laɓe ta fidda ƙaramar recorder ɗinta ta fara naɗan maganar sa. Ganin yayi shiru yana sauraron bayanin da ake masa ya sa tayi saurin jan jiki ta bar bakin ƙofar. Ba ta ji ƙarshen maganar sa ba. "Eh...ina sane amma... shikenan zan kiyaye sai dai gara a nuna masa cewa mune muka buɗa masa hanya har ya samu ya hau kujeran, idan aka cigaba da ninke shi a baibai zai yi abinda zai jawo masa dana sani... to shikenan zamu haɗu idan na tashi a office" Da ƙyar Asiya ta iya komawa wajensu CY dan a tsorace take, abinda ta jiyo ya girgizata matuƙa yayinda tsanar Gwamna Saifuddeen ya dira a zuciyarta, dama ya aka ƙare balle kuma... Ta samu CY na faman saita camera, shi da Sunusi suna taɗi shiyasa hankalinsu bai kai gareta sun lura da chanjawar yanayinta ba. Bayan minti biyar sai ga Gwamna ya iso fiskarsa ɗauke da annuri. Kallon tsana Asiya ta bishi da shi tana ji a ranta kamar ta shaƙeshi ya mutu kawai. Maimakon jiya da za a naɗi shirin sannan a editting na shi kafin a ɗaura a tasharsu yau kam live za a saka shirin a gidan talibijin na su. Yau kam ba kamar jiya ba babu tsoro ko fargaba a tattare da Asiya, cike da nitsuwa ta fara gabatar da shirin. Tambayoyin da aka amince ta masa su takeyi sai da aka kai tsakiyar shirin sannan ta sako zancen tsohon Gwamna wanda ba Gwamna kaɗai ba hatta CY sai da ya sha jinin jikinsa da tambayar "Gwamna Saifuddeen duba da yadda mutuwar tsohon Gwamna ya zo bagtatan ko za ka iya sanar damu yadda mutuwarsa ta zo maka?" Tambayar offscript ne baya cikin jerin tambayoyin da akace za a masa shiyasa ya ɗan ji abin banbaraƙwai amma ya dake ya amsa da cewa. "Kowanni halitta dake doron ƙasa sai ya ɗanɗani mutuwa. Dukkanmu lokaci muke jira. Haƙiƙa mutuwar tsohon Gwamna ta girgizani matuƙa saboda yadda ya zo mana lokaci guda..." "Excellency baka ganin ya kamata a duba mutuwar tasa kodai akwai lauje cikin naɗi duba da cewa Gwamna nada 'yan adawa dayawa" Ba dan shirin kai tsaye aka ɗaura shi ba da CY tuni ya katse ɗaukan shirin saboda yadda Asiya take chanja alaƙar shirin nasu. Gwamna ya kalleta cikin zargi amma bai bari hakan ya bayyana a fiskarsa ba yace " Malama Asya mutuwa koda ciwo ko babu ciwo sai anyita. Likitoci sun tabbatar da cewa hawan jini ne yai ajalin tsohon Gwamna Allah ya jiƙan rai" "Ya yanayin alaƙarka da shi kafin rasuwarsa?" "Munyi zama na amana da shi, Allah ya gafarta masa kurarensa da ma namu gaba ɗaya" "Amin" "Tambayata ta gaba ko miyasa Gwamna ya zaɓi Alhaji Bala Yamai a matsayin mataimakinsa duba da cewa ana zarginsa da cin hanci da rashawa har ma shekarun baya hukumar EFCC sun kama shi?" Kafin Gwamna ya bada amsa daga chan ma'aikatarsu aka katse shirin aka saka talle saboda a samu daman katse ɓaranɓaramar da Asiya ke yi. "Jesus! Aseey lafiyanki kuwa?" CY ya faɗa da ɗan ƙarfi, kafin ta bashi amsa MD ya kirata tana ɗauka ya shiga surfa mata masifa kaman zai zo wajen ya bindigeta. Tana ajiye wayar tareda sauke ajiyar zuciya ta haɗa ido da Gwamna. Duk da tsanar da take masa hakan bai hana tasirin kallon sa gareta ba. "Yaudara na ɗaya daga cikin abubuwan da na ke ƙyama. Miss Asya na yarda da wannan interview ne saboda babu maganar siyasa a cikinta, kar ki manta da wannan" A yadda ransa ya sosu da abinda tayi niyyarsa ya miƙe ya bar wajen saidai idan har yai haka ya sani daga lokacin 'yan jarida zasu murɗa labarin da cewa Gwamna ya ƙi amsa tambaya saboda bashi da gaskiya. Ya sani Alhaji Bala Yamai ba shine candidate ɗin daya so ya zama mataimakinsa ba sai dai kamar yadda Alhaji sani ke yawan faɗa masa cewa a siyasa dolene ka yi abinda bature ke kira compromise. Ba zai manta lokacin da Alhajin ya kirashi ya ce masa mataimakinsa shine Alhaji Yamai ba. Ya faɗi maganar kamar bashi da zaɓi, kamar ba shine mai ikon naɗa duk wanda yakeso ba. "Alhaji Yamai yanada record na rashawa, Baba" ya faɗa da murya mai sanyi. "Ka zo gida muyi magana" Alhaji Sani ya faɗa. Koda ya sameshi a gida bayani ya masa wanda hakan ya birkita shi har sai da asthma ɗinsa ta fara barazanar tashi. Ya sani tun kafin ya kawo wannan matsayi Alhaji Sani Kachallah yana ɗaya daga cikin wanda suke riƙe ko yace suke juya jahar Congo. Tun zamanin mulkin soja ake damawa da shi har aka dawo mulkin farar hula. "Mutane huɗu ne keda alhakin zaɓan Gwamna da Mataimakinsa. Wannan karan ɓangarena ne da Gwamna, ɓangaren Mataimakinsa yana hannun ɓangaren Yellow Group kuma sun zaɓi Alhaji Yamai. Kar ka damu, Alhaji Yamai hoto zai zama kawai" yadda Alhaji Sanin ya faɗi kalmar hoto sai ya tuna da yadda shima watannin baya yake kamar hoto a matsayinsa na mataimakin Gwamna. Ya so yaja da hakan amma bai samu ƙwarin gwiwar yi ba. Tun lokacin da Alhaji Sani ya gabatar da shi a jam'iyyarsu ya sanar dashi ma'anar tutar Jahar Congo. Kalar Baƙi da ta fi yawa a jikin tutar ita ke ɗauke da kaso 45% wanda Yallaɓai ke shugabanta yayinda kalar Blue ke ɗaukan 25%, kalar Red ta ɗauki 18% sai Yellow 12%. kalar blue ta Alhaji Sani Kachallah ne hakan na nufin da shi ake damawa a Gwamnati, hakan na nufin Saifuddeen ba shi da ikon yin komai sai da yardar sa. Yanzu da aka dawo daga tallen da aka saka wanda ta kai kusan minti takwas bai ɓata lokaci ba ya amsa tambayar Asiya da cewa ya zaɓi Alhaji Bala Yamai ne a matsayin mataimakin Gwamna saboda an riga an wanke sunansa daga laifin rashawa da ake tuhumarsa da shi shekarun baya, ya haɗa da cewa Alhaji Yamai yanada experience a harkar siyasa fiye da shi shiyasa ya zaɓe shi. Lokacin da ya gama bayanin lokacin da aka ɗibarwa shirin ya ƙare dan haka Asiya bata sake wata tambayar ba ta ƙarƙare shirin. CY na cewa Cut Gwamna ya miƙe ya tafi yayinda muƙarrabensa suka bi bayansa cikin sauri. "Aseey kin fuck up Wallahi" CY ya faɗa yana girgiza kai yayinda Sunusi yake jimamin yanzu ɗan alkhairin da za a basu ya wuce tunda gashi ran Gwamna a ɓace ya bar wajen su. Lokacin da aka katse shirin aka saka talle COS ya zame jiki ya wuce office ɗinsa. Abu ɗayane ya zo masa wato Asiya taji abinda ya faɗa idan ba haka ba babu yadda za ayi ta kawo maganar mutuwar tsohon Gwamna. Tunda aka bashi matsayin Chief of staff lokacin Gwamna Saminu Bacci ya saka CCTV a office ɗinsa saboda shiga masa office da akayi ba da izininsa ba aka bincika masa wasu takardu. Ya kori sakatariyarsa a lokacin amma ya sani ba da saninta aka yi hakan ba, bai jima ba kuwa ya gano wanda yai hakan. Babu wanda ya san yanada ɓoyayyiyar camera a office ɗin nasa. Kasantuwar Sakatariyarsa Jennifer bata desk ɗinta sanda ya shigo ya ƙara tabbatar masa da cewa Asiya ta ji wayar da yai tun ma kafin ya duba CCTV footage ɗin. Bai sha mamaki ba da yaga Asiya laɓe a bakin ƙofarsa da 'yar ƙaramar na'ura da yake da tabbacin recorder ce lokacin daya kalli footage ɗin. Asiya tana waya da Ubayd wani security ya iso ya ce ta biyo shi. CY da Sunusi suka zaro ido tareda tambayar lafiya. Bai ce musu komai ba yai wa Asiya jagora suka bar wajen. Asiya ta tsorata amma ta dake bata nuna ba saboda kar ta bada kanta, yau duk yadda za ayi sai dai ayi amma bazata taɓa fito da recorder ɗin nan ba. Office ɗin Chief of Staff ya kaita kamar yadda tayi hasashe. Tayi mamaki da taga Sakatariya a office ɗin farko wanda ɗazo da ta zo babu ita. Lokacin da ta shiga office ɗinsa Mr Lamara Damana yana tsaye ya haɗe gira. Jakarta security ɗin ya ce ta miƙo tana miƙa masa ya zazzage kayan ciki a walaƙance. Powder, lipstick, hankerchief, jotter, biro da earpiece ne a ciki. Wayar hannunta security ɗin yace ta kawo ta miƙa masa ba musu tana kallon COS da shima ya zuba mata ido yana mata kallon tsana. Wata na'ura da ke detecting devices security ɗin ya bi ya zagaye jikin Asiya da shi amma bai detecting komai ba. COS yace ya miƙa masa wayar Asiya sannan ya basu waje. Bayan fitan security ɗin COS ya kalli Asiya ya ce "na san ba a waya kika ɗauki maganarba dan haka ki fito da recorder ɗin" "Ikon Allah, ina tunanin ka manta cewa ni 'yar jarida ce, wannan cin zarafi da kake min zai ja maka matsala" Asiya ta faɗa a kausashe. Wani murmushin gefen baki COS yai wanda idan ba lura kayi ba baza ka gane murmushin yai ba saboda yadda gefen bakin ya tattare kamar mai shirin kuka. "Asiya Shahidah Faruƙ Baba. Na san kina sane da haɗarin da ke tattare da wuce gona da iri a cikin aikin ku" "Are you threatening me?" "You know better"... Lokacin da ta isa wajen su CY ko magana ba ta musu ba ta wuce gaba suka bi bayanta suna tambayar miya faru. Sai da suka shiga mota Asiya ta karɓi jakar camera da ke hannun CY ta buɗe wani ƙaramin zip ta ɗauko recorder a ciki ta damƙe shi a hannunta, yadda ta damƙe shi har sai da hannun ya fara rawa. CY kallonta yake yi cike da tambayoyi a harshensa amma ya yi gum da bakinsa tunda tace musu kar wanda ya mata magana. Maimakon office gida tace Sunusi ya sauketa. Tana shiga ɗaki ta samu Umma na wanki a tsakar gida, ganin Ummanta duƙe tana wanki ya tuna mata da washing machine da ta ce zata siya tun watan daya gabata. Rashin lokaci ya sa take bada kaya a wanke mata sai ta haɗa dana Umman amma tunda Umman ta ce ba ta son a fita mata da kayan wanki waje ya sa duk weekend indai tana gida take wanke kayan mahaifiyarta. A tsanake ta gaisheta tace mata ta zo ɗaukan abune dan kar ta firgitata. Tana shiga ɗaki kai tsaye laptop ɗinta ta buɗe ta fara ƙoƙarin tura abinda ta naɗa zuwa Laptop ɗin. Maganganun COS sun ɗan razanata amma idan ta tuna itama tanada abinda zai iya wargaza mulkinsu sai ta tausashi ranta. Kafin ta gama abinda take wayarta ta shiga ruri. MD ne ta sani kuma ba zata kulashi ba sai ta gama abinda takeyi. A ƙalla ta kai awa ɗaya da rabi a gida kafin ta shirya ta koma office. Ta ɗauka MD zai mata faɗa kaman yadda ya yi a waya amma sai ta ji ya tausasa kalmominsa gareta "Asiya ban san mi kika naɗa a gidan Gwamnati ba amma ina so ki sani cewa zaki iya taka Gwamna ki kwana lafiya amma Lamara Damana ba zai barki haka ba" "MD kana so kace..." "Asiya na san kinada ƙoƙari sosai wajen dukkan ayyukanki amma ki sani ana iya barin halak saboda kunya" Za tayi magana ya ɗaga mata hannu sannan ya cigaba " already mutane sun fara reacting wa interview da kikayi amma nan da kwanaki kaɗan komai zai lafa, saidai idan kika sake bijiro da wani abun Asiya ba ke kaɗai fitinar za ta shafa ba idan ba ki ji ta ma'aikatarmu ba to ta iyayenki fa?" Jikinta yai sanyi ta kasa cewa komai. "Asiya you are a field reporter not investigative reporter, kada kiyi aikin da ba naki ba. Faɗa da 'yan siyasa ba abu ne da ake ƙareshi ta daɗi ba" "Sir, kana nufin na watsar da gaskiya na rungumi ƙarya kenan?" "Ban san mi kika sani ba Asiya amma koma minene ki yiwa Allah ki haƙura dashi saboda mutuncin ki. Lamara Damana ba mutumin da za ki iya ja da shi bane" "Shikenan na ji" Bayan Asiya ta bar office ɗin. MD ya sauke ajiyar zuciya. Kashedi Chief of staff ya masa ɗazu daya bugo akan in har aka fitar da wata magana da ta shafeshi Hill TV za ta rasa matsugunni a Jahar Congo. Ba wannan ne matsalar ba. Jin ya ambaci sunan Asiya ya sa shi fahimtar dalilin dayasa Asiya ta yiwa Gwamna tambayoyin da tayi, duk da bai san takamaimai mi Asiyar ta jiyo ba amma yanada yaƙinin abune da ya shafi mutuwar tsohon Gwamna. Duk wanda ya ke bibiyar siyasar jahar ya san cewa Lamara Damana shine shugaban munafukan gidan Gwamnati masu hana ruwa gudu. Mr Damana ya fara aiki daga Sakatare ne a hankali ya dinga shiga cikin manya ya zamana anyita ƙara masa matsayi har ta kai lokacin Gwamna Saminu Bacchi aka bashi muƙamin Chief of Staff. Tunda aka koma mulkin farar hula babu Gwamnan da Mr Damana bai yi aiki da shi ba. "Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta naɗi abinda yafi ƙarfinta, idan ya fito waje bana tunanin za ta sake yin rahoto da bakinta" kashedin COS na ƙarshe kenan. Yana son Asiya tun farkon zuwanta ma'aikatar lokacin da tazo yin bautar ƙasa. Ya nemi soyayyarta ta ƙi shi, wanda yanzu ya riga ya haƙura tunda yaji ance an kawo kuɗin aurenta. Duk da COS bai buɗa ba ya fahimci mi yake nufi sarai dan ba yau ya fara aikin jarida ba. Ba zai taɓa mantawa da wani ogan sa edita Mr Simon da suka fara aiki tare lokacin yana Lagos ba, shima kamar Asiya taurin kai ne da shi, indai a wajen bayyana gaskiya ne to baya jin tsoro. Ranan da gidan jaridarsu ta wallafa shafi akan wani asiri da Mr Simon ɗin ya jiyo na wani fitaccen ɗan siyasa ranan bai kwana duniya ba domin yana hanyar dawowa daga office motarsa tayi bindiga ta kama da wuta. Ba zai manta da wani abokinsa Ja'afar ba. Ja'afar Bello investigative reporter ne daya binciko yadda wata Matar Minister ke safarar 'yan mata karuwanci zuwa ƙasashen waje. Yanada isassun evidence a kanta har an fara shari'a haka kawai aka nemi Ja'afar Bello aka rasa, ko sama ko ƙasa. Yanzu shekaru shatara kenan babu labarinsa. Yana tsoron kada taurin kan Asiya ya jawo mata fitina. Asiya koda ta koma office tunanin maganganun COS da ta MD ta dinga yi, a wani ɓangare kuma tana tunanin bazata taɓa bari Gwamna Saifuddeen yaci bulus ba. Ta sani cewa abinda ta naɗa bai kai evidence da za a iya kama Gwamna ba amma idan har maganan ta fito zai jawo cecekuce har a fara bincike, koda ya sha yanzu lokacin zaɓe abokan adawa za su yi kamfen da maganar su hana mutane zaɓanshi, ko kuma idan har akabi komai da gaskiya to dole ne ayi impeaching ɗinsa. Babu abinda take ganin yanzu zai faranta mata rai a rayuwa sama da taga an tsige Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah ... *** A office Asiya ta dinga jayayya da zuciyarta akan ko ta bi shawaran MD tayi shiru da abinda ta ji ko kuma dai ta fitar da shi ta tada fitinar da zai jawa Gwamna matsala. Shawara ta yanke akan idan Ubayd ya zo hira za ta nemi shawaransa ta ji mi zai ce. Daga baya ta kasa haƙuri har zuwa lokacin ta kira numbarsa tace ya hau whatsapp akwai abinda za ta gaya masa. Sai bayan minti shabiyu ya hau saboda yana duba wani patient ne a lokacin da sukayi waya. A tsanake ta masa bayanin komai da kuma abinda MD ya faɗa mata. Bai tsaida ita ba har sai da ta gama bayani ta ce miye shawaransa gareta. " Asiya Shahidah na roƙe ki da girman Allah ki haƙura da abinda kike shirin yi domin ba zai haifar da ɗa mai ido ba. For God sake! we are getting married soon. Kina so rikicin siyasa ya jawo miki wata fitinar ne? Idan har abinda kika ji gaskiya ne then you are not safe Aseeya ba ke kaɗai ba hatta 'yan uwanki ba su tsira ba. Asiya ina za ki iya rikici da Lamara Damana?, Please ki mayar ma sa da recorder ɗinnan ki nuna masa ba za ki taɓa fitar da maganan da kika ji ba" Tana gama karanta rubutun ta sauka tareda jan dogon tsaki. Wai sunata maganan Lamara Damana, Lamara Damana, shi waye da za ta ji tsoronsa. Idan har ba za a fitar da labarin a ma'aikatarsu ba ai akwai social media. Ringing ɗin wayarta ya dawo da ita daga tunanin da takeyi. Koda ta ɗauki wayar Ubayd cigaba da roƙonta yayi yana cewa ta masa alƙawarin ba abinda za tayi, da ta ga ya dameta tace mishi ta ji za ta yi shiru sai dai chan ƙasan ranta ta san ba haka bane. Lokacin da suka tashi CY ne ya nemi ya kaita gida saboda yana son jin labarin miye dalilin sauya tambayoyi da tayi, sannan miye dalilin da yasa COS ya nemi ganinta. "Na san gulma ne ya kawoka Clement kuma ba za ka ji komai ba" "Ahn-Ahn, Aseey Darling ya zaki fassarani haka, jiya ma fa ni na kai ki gida" "Ahaf, ka gama kame-kamen naka dai ka dawo hanya, magulmaci" CY yai dariya ya wuce gaba. Suna fita daga ma'aikatar Obinze Maigadi ya ɗaga waya jiki na rawa ya kira wata number ya ce yanzu Asiya ta fita daga ma'aikatar tasu ya haɗa da cewa tare take da abokin aikinta akan machine kafin aka katse kiran. CY na tuƙi yana yiwa Asiya taɗin budurwarshi mai suna Evelyn da ta ce masa dole sai ya koma ɗariƙar Katolika (catholic) kafin ta iya auren shi, Asiya tana masa dariya. Ba suyi aune ba dai-dai za suyi kwana wata babbar mota da basusan daga ina ta fito ba ta zo ta mangajesu hakan yasa Asiya tsalle sama ta faɗi gefe yayinda motar tabi ta kan machine da ta danne CY ta wuce da bala'in gudu... *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 07 "Darling" Bilkisu Kachallah ta kira da fake American accent ɗinta wanda kunnen Saifuddeen ya kasa banbance "Dolin" tace ko kuma "Durling". Ya dai ɗago ido ya kalleta ba tareda ya furta komai ba. Ya sani ya kamata ya ce mata tayi kyau ko kuma yace jan lingerie (rigar bacci) data saka ya amshi jikinta sosai amma bai ce komai ba. A mafiya lokuta idan ta yi shiga irin wannan tana buƙatarsa ne, ba kawai buƙata ba domin daga ƙarshe idan ta kwanta gefensa tana shafa gashin ƙirjinshi a hankali za ta bijiro masa da wata buƙatar ne, mafiya yawanci abubuwanda take tunanin ba zai mata su ba idan ta tambayeshi kafin ta shigo turakarsa su take tambaya. Rabonsa da ita tun ranan farko da suka tare a gidan Gwamnati. Ba wai baya buƙatarta bane amma rashin nuna damuwarta gareshi yasa yake haƙuri da ita, ƙila saboda a koyaushe baya son takura mata ne. She's not yet 40 amma kuma lamarin sex life ɗinsu ya lalace tun lokacin da ta haifi Junior. Takardu yake dubawa ta tura takardun gefe ta shiga kissing ɗinsa, farko daga goshinsa, kunnensa kafin ta kai bakinsa. Ba a jima ba ya tureta yace " ki bani minti goma na ƙarisa aikin dana ke" "Haba Darling, ka san yaushe rabonka da ni kuwa? Aiki can wait please" ta faɗa tana zunɓura baki. So yake ya ce mata laifinta ne idan bai nemeta ba tsawon kwanakin nan, saboda duk lokacin daya samu free time yake buƙatar kulawarta baya samu, amma bai faɗi hakan ba sai yayi mata murmushinsa mai shiga rai yace " kar ki damu, ba zan jima ba" Bilkisu ta kwanta gefen gado tana kallon ceiling yayinda ya cigaba da duba takardun da idan bai duba yanzun ba bashida lokacin duba su gobe. Kusan minti talatin da uku kafin ya gama komai lokacin har Bilkisu ta fara gwarti. Ya je ya ajiye takardun acikin wani file ya saka a briefcase. Bai tashi Bilkisu ba saboda ya san a gajiye take yau tace masa ta fita duba gidan marayu bai san details ɗinba kuma bai tambayeta ba. "Shine baka tasheni ba" ta faɗa lokacin da ta tashi da Asuba. "You're tired" "Still" ta faɗa tana haɗe rai. "To barin dawo daga masallaci" Lokacin daya dawo daga sallar Asuba ta riga tayi wanka ta chanja kaya, ba rigar bacci ta sa ba amma shima kamar na jiya guntu ne mai hannun spaghetti, rigan ya kamata sosai, ya bayyana ƙaton tumbinta da yake a taƙune. Kamar yadda yai hasashe yana shirin miƙewa ya je yai wanka ta faɗa masa buƙatarta na son buɗe Bilkisu Kachallah Foundation dan tallafawa marayu. Ajiyar zuciya yai sannan yace "Allah ya sanya alkhairi" ya wuce banɗaki tda sauri... Meeting biyu ya shiga daga zuwansa office, yanzun ma wani meeting ɗin zai shiga nan da minti talatin. Yana duba report ɗin da aka kawo masa. Sakatare ya shigo da wasu takardu a hannunsa. "Your excellency na samu COS ya reschedulling ziyarar da za ka kai ƙaramar hukumar Antu zuwa jibi laraba" "Ok" Gwamna ya faɗa yana cigaba da duba takardun da ke gabansa. "Excellency kafin na manta. 'Yan jaridar da suka zo jiya sun yi hatsari" "Asya!" Gwamna ya ɗago kai da mamaki "Ita da abokin aikinta suna komawa gida wata babbar mota ta afka musu..." "Is she alive?" Ya faɗa da tsananin damuwa a tattare da shi "Na ji labarin dukansu suna raye. Ita Asiya ance nata da sauƙi amma shi ɗayan kam rai a hannun Allah" "Hasbunallah! Keep me posted akan labarinta" ya faɗi labarinta kamar ita ɗaya akace tayi hatsarin. Bayan fitan Sakatare daga office ɗinsa ya ɗaura haɓarsa akan hannunsa yana tuna siririn ushiryar dake tsakanin haƙoranta wanda yake ƙara mata kyau idan tana murmushi. *** Umma ne a gefen gadon da aka kwantar da Asiya lokacin da Ubayd da Abba suka shigo. Abba ya tambayeta ko Asiyan ta tashi tace masa bata tashi ba. Lokacin daya zauna ta tambayeshi jikin abokin aikin Asiya Abba yace ance musu har yanzu bai farfaɗo ba. Ubayd ya ƙurawa Asiya da ke kwance ido bai san lokacin da hawaye ya fara zubo masa ba. Ba dan kariyar Allah ba da ita ne ke halin da CY yake ciki ko kuma ace da yanzu an jima da bisineta. Yai saurin goge hawayensa dan kar Umma ta gani. Alhamdulillah ya furta a ransa kafin ya yiwa su Umma sallama ya fita. Ba a jima ba Asiya ta farka a karo na biyu tun safiyar yau. Da farko data farka kuka ta dinga yi tana faɗin a kaita wajen CY. Yadda ta birkice musu sai da aka mata alluran bacci. Wannan karan ma data farka sunan CY ta kira. "Abba CY ya mutu ko?, sun kashe shi ko?" "Kwantar da hankalinki Shahidah. Yana nan da ransa" Da bata faɗa gefen titi ba, da ba wannan zancen akeyi akanta ba. Gefen goshinta, kunnenta da kafaɗarta sai kuma gwiwarta da ya kurje su kaɗai ne ciwon jikinta, sai dai saboda irin faɗuwar data yi duk jikinta ciwo yake mata. Asiya ta sauke ajiyar zuciya hawaye na zubo mata. "Abba idan CY ya mutu bazan taɓa yafe musu ba. Kuma sai na..." "Asiya!" Ya kira sunanta da ƙarfi har sai da ta tsorata. "Ba abinda zakiyi, kina jina? Nace ba abinda zakiyi. Zan mummunan saɓa miki idan kika sake maganan mutanen nan" "Abba..." "Zamuyi magana idan munje gida" Ta kalli Abba da mamaki, ba yadda za ayi yai wannan maganar sai dai idan har yasan wani abu. Kenan Lamara Damana ya tuntuɓeshi. Da yamma da Ubayd ya dawo ta tambayeshi ina CY yace mata CY na CUTH (Congo University Teaching Hospital ) an ɗaura shi a na'ura saboda ya shiga coma. "Mutuwa zai yi ko?" Ta tambaya murya na rawa "Mine mutuwa a hannun Allah take. Ki masa addu'a amma he's in a very bad shape infact an yanke masa hannu ɗaya" "Ya Allah!" Ta riƙe baƙi. 'Yan wajen aikinsu sun zo sun gaisheta. MD shi kaɗai yazo da yamma lis kuma bai jima ba saboda lokacin ɗakin nata akwai mutane. Lokacin daya fita Abba ya bi bayansa da sauri. Bayan sun samu waje sun keɓe sannan MD ya bashi takardar dakatar da aiki na Asiya. Abban ne ya nemi hakan shiyasa yana karɓa ya masa godiya ya koma cikin Asibitin. MD ya girgiza kai yana fata wannan ya zamowa Asiya mafita saboda ta tsokano tsuliyar dodo. Kwanan Asiya biyar a Asibiti aka sallameta har lokacin kuwa ba suyi maganar abinda ya faru da kowa ba saboda Abba ya hanata. Kamar yadda kowa ya ɗauka cewa tsautsayi ne ya kawo hatsarin da suka yi Asiya ta san ba haka bane kuma ta san Abba da Ubayd ma sun san ba hakan bane. Kafin su wuce gida ta roƙi Ubayd da ke tuƙi akan ya kaita taga CY. Da farko ya ƙi amma data takura sai Umma tace ya kaita itama tana son zuwa dubashi. Lokacin da taga CY kwance an jona masa wasu na'ura a jiki sai kawai ta fashe da kuka. Da Allah yayiwo CY mace da zata iya cewa har abada ba za ta iya samun ƙawa kamarta ba saboda yadda jininsu ya haɗu kuma suka fahimci juna, sai dai CY namiji ne shiyasa abotar tasu take da iyaka. Sun gaisa da mahaifiyarshi inda take jadaddawa Asiya cewa Gwamna ya biya kuɗin aikin da za a masa a ƙasar waje takardunta da ake processing yasa basu tafi ba sai wani sati. Jin Josephine mahaifiyar CY ta ambaci sunan Gwamna yasa zuciyar Asiya ta cunkushe, tsanar mutumin ya sake sauka mata. Munafuki ta faɗa a ranta, shine ya jawo wannan matsalar sannan yake ƙoƙarin rufe bakin mutane da maganar biyan kuɗin aiki. Ita Asiya ba zata yi shiru ba, tayi alkawari. Sanda suka isa gida Abba ya zaunar da ita ya mata bayani. "Abinda ya faru Asiya ki ɗauke shi a matsayin ƙaddara. Ki riƙe bakin ki da zargi domin ba abinda hakan zai jawo sai fitina. Na saka an dakatar dake daga aikin ki, daga yanzu babu ke babu aikin jarida. Ban sani ba idan kin koma ƙarƙashin ikon Ubaydullah ko zai barki kiyi amma iya watannin daya rage miki ƙarƙashin kulawata, na dakatar da aikin ki" Asiya tayi saƙeƙe tana kallonsa "Waɗanda kika samu saɓani da su sun zo sun karɓi laptop ɗinki na gida da wajen aiki dama wayarki amma sun dawo da wayar taki jiya. Sun bayarda saƙo a baki *ki cigaba da rayuwarki kamar komai bai faru ba, hakan zai sa su manta da komai*" "Abba ya zaka min haka?" Ta ma rasa haushin wanne ɗaya za ta ji. Na halin da CY ya shiga saboda ita ne ko kuwa dai na aikin da ya hanata ne ko kuma na ɗauke laptop ɗinta da COS ya sa akayi. Abin takaicin ma a laptop ɗin kawai ta tura recording ɗin ba ta riga ta tura a wani wajen ba. "Asiya ki yiwa Allah ki manta da komai. Bana so ko da Umman ki kiyi wannan maganar saboda kar hankalinta ya tashi" "Abba dafa na mutu yanzu, dafa..." "Ki godewa Allah kawai ki riƙe bakin ki Asiya" Abba bai bata daman magana ba sai kawai ta fashe masa da kuka, da tayi mai isarta ta miƙe ta bar falon. Tuwon shinkafa miyar taushe Umma ta zubo mata bayan tayi sallar Isha, ta haɗa mata da zoɓo mai sanyi. Duk yadda take marmarin ci kafin a girka yanzu ya fita mata aka saboda rasa recorder ɗinta da tayi, koya akayi suka samu recorder ɗin ma oho, dan a ƙasan katifar Umma ta saka bayan ta gama kwafan abinda ke ciki zuwa laptop ɗinta. It means bata da wani evidence kenan. Umma ta katse mata tunani da cewa ta ci abinci "Umma ki bani a baki" ta faɗa da yaren kurame. Umma tayi murmushi ta wanke hannu ta fara bata a baki. Ƙarfe shabiyu na dare tanata juyi a kam gado ta kasa yin bacci. Wayarta da Abba ya bata an share komai na kai kamar sabon waya. Tunanin rashin imani irin na Gwamna ya tsaya mata a rai, ita yanzu ta daina ganin laifin COS ma dan gani take da umurnin Gwamna ya aiwatar da komai. Ƙarshe ta jawo wayarta ta sake downloading twitter da facebook da aka goge. Tana saka gmail da password ɗinta na da ta samu access zuwa ga tsohon account ɗinta nan da nan ta shiga rubuta dogon article a blog website nata, data gama ta kwafa ta kai shi twitter ta jerasu a dogon thread of tweets . Ta kai facebook ma ta posting a wall nata. Tana ganin duka rubutun ya hau tace "Excellency yanzu aka fara wasan" Yadda ake fama da talauci da wasu matsaloli wannan rubutu nata tabbas zai jawo hankalin mutane kan Gwamna and this is good. Kalaman ɗan jarida suna da kaifi, kalaman da ke iya kunna jita-jita tsakanin al'umma ya maida gaskiya ƙarya sannan ƙarya ta koma gaskiya. Kusan minti goma shabiyar kafin ta fara ganin comment na 'yan tsirarun mutanen da suka gani. Tana bin comments ɗin tana murmushi idan taga wanda ya yabi Gwamna kuma sai ta yi tsaki. Asiya bata kwanta ba sai ƙarfe uku da rabi, dake Umma a ɗakin Abba ta kwana yasa bata samu mai tashinta da Asuba ba sai ƙarfe shida saura minti biyar da Umma ta shigo ɗakin ta tasheta sallah... *** Chief of Staff Lamara Damana yana kwance kusa da matarsa ƙarfe huɗu da rabi wayarsa ta shiga ƙara. Bayan ya ɗau wayar miƙewa yai ya bar kan gadon dan wanda ya kira ɗin special agent ɗinsa ne mai kula masa da hidimominsa a yanar gizo. "Ina jinka Felix" ya faɗa lokacin daya zauna a kujeran dake falonsa. "Asiya again?" Ya faɗa yana cizen leɓe. Lokacin da aka tabbatar masa Asiya bata mutu ba sannan bata ji ciwo sosai ba yaso ya sa a ƙarisata a Asibiti amma daga baya ya chanja ra'ayinsa. Beside ita macece dole taji kashedin iyayenta. Yanzu da Felix ke karanto masa abinda ta ɗaura yayi mamakin ƙarfin halinta. "This girl! Yanzu dai kasa a blocking accounts nata, sannan ka controlling duk wata jarida da zata yi sharyi akan abinda ta rubuta" Lokacin da Asiya ta idar da sallan Asuba ko Azkar bata yi ba ta jawo waya ta fara duba twitter account ɗinta sai dai kash! An riga an banning account ɗin tun misalin ƙarfe biyar na Asuba, ta zaro ido waje tareda duba website nata cikin sauri sai dai shima an blocking na shi, facebook ma haka. Tayi ƙoƙarin searching article ɗin a google amma an sauke shi gaba ɗaya babu ko mai kama da shi. "Nooo" ta faɗa tana kaiwa sallayar da ta ke kai duka... Gwamna na zaune a office wayarsa ta shiga ƙara yana dubawa yaga sunan Baba. "Saifu mi yake faruwane? Yanzu nake jin wai Umaru Kwom yayi wata magana a twitter akan abinda wata 'yar jarida ta ɗaura" "Bani da labari Baba amma yanzu zan tabbatar" "Nayi magana da COS amma ka tabbatar da adviser ɗinka ya kashe duk wani hayaniya da za ayi a yanar gizo akan maganar" Gwamna na ajiye waya ya kira mai magana da yawunsa a yanar gizo. Umaru Kwom abokin adawar Saifuddeen Kachallah ne saboda lokacin yana tareda Alhaji Sani Kachallah ya so ya zamo mataimakin tsohon Gwamna Saminu Bacchi amma Alhaji Sani ya ƙi ya tsaida Saifuddeen, tunda aka tsaida shi kuwa ya fice daga jam'iyyarsu ta CDA ya koma Q party. Lokacin da Special adviser Ahmad Tanko ya shigo ko kaɗan Gwamna bai ji daɗin yadda aka ƙi sanar dashi abinda ya faru ba. "Mi Umaru Kwom ya ce?" "Excellency an riga an cire duk wani tweet ko post na 'yar jaridar amma awa biyu da suka wuce Umaru Kwom ya tweeting wasu maganganu daga ƙarshe ya haɗa da screenshot na tweet ɗin 'yar jaridar" "What did he say?" Gwamna ya faɗa da ƙarfi. Ahmad ya fito da wayarsa ya fara karanta tweet ɗin "inada tabbacin 'yar jaridan nan tayi gaskiya duba da yadda Gwamna ya biya kuɗin aikin da za ayi wa Clement Yohanna a ƙasar waje. Idan ba a manta ba Clement da Asiya sune suka je interview ranan, idan har babu lauje a cikin naɗi ba abinda zai sa ayi yunƙurin hallaka 'yar jaridar a ranan da tayi maganar mutuwar Gwamna Saminu Bacchi. Bisa wannan, muna so mu gayawa Gwamnatin SSK cewa duk abinda ya sami Asiya 'yar jarida nan gaba zamu yi ƙaran Gwamnati. #a binciki mutuwar tsohon Gwamna" SSK ya sauke ajiyar zuciya kafin yace Ahmad ya miƙa masa wayar yaga rubutun da Asiya tayi. Bayan ya gama karantawa ya miƙa masa wayar yace ya fita masa daga office ɗinsa. Ba yadda za ayi Asiya tayi wannan iƙirarin idan har ba wai ta ga ko ta ji wani abu ranan da suka zo bane. Dole ne ya gana da 'yar jarida Asiya Shahidah... *** "Shikenan ai tunda kinyi gaban kanki, kin nuna cewa ba nina haifeki ba" "Abba ba haka bane, Wallahi ba haka bane" "Kinyi gaskiya Asiya, ba nina haifeki ba ban kuma manta da hakan ba.Tunda ban isa na baki shawara ki bi ba shikenan Allah ya baki sa'a. Kije kiyi magana da Umaru Kwom daganan ku wuce kotu ku bi wa Marigayi Saminu Bacchi hakkinsa" Asiya ta kalli Abba tana zaro ido. Kenan Ubayd ya gaya masa komai. "Tashi ki tafi" "Abba..." "Tashi ki tafi kawai" Jiki a sanyaye ta fice daga falon. Ɗazu Umaru Kwom da kansa ya kirata yace yana son haɗuwa da ita saboda su tattauna iƙirarin da tayi a yanar gizo. Ya tabbatar mata yana tareda ita ɗari bisa ɗari. Bata ɗauka Abba zai fassara maganar haka ba. Abba bai taɓa faɗin magana makamancin wannan ba hakan na nuna ba ƙaramin fushi yai da ita ba. Ubayd ma tun safe daya kira ya gama balbaleta da masifa bai sake waiwayanta ba, koda ta kirashi dan ta sanar dashi kiran Umaru Kwom ƙin ɗaukar wayarta yai. Lokacin da zata shiga ɗakinsu ta ji Hindatu na mata habaici wai 'karyar 'yan siyasa' bata tanka mata ba ta shige ɗaki. Rasa ma mi zatayi tayi dan yadda ran Abba ya ɓaci bata jin zata iya zuwa wajen Umaru Kwom. Da yamma lis tana kitchen tana haɗawa Umma zoɓonta na siyarwa Ubayd ya shigo da sallama. Kasa amsa sallamar tayi saboda wani tsoro da taji ya taso mata lokaci guda. Umma ba ji take ba bata ma san anyi sallamar ba tana faman tuƙa tuwon Masara. "Inna Yaha ina Asiya?" Ubayd ya faɗa bayan ya leƙa ɗakin Umma bai ga kowa ba. Inna Yaha dake ƙullin gyaɗa ta kauda kai gefe tace "kaban ajiyarta ne?" Bai ma gama jin mi take faɗa ba ya wuce kitchen. Suna haɗa ido da Asiya ta ji gabanta ya faɗi. Idon Ubayd ya kaɗa yayi ja. Sama-sama ya gaishe da Umma yace da Asiya ta biyo shi. "Yaya Ubayd miya faru?" Bai kulata ba ya fice daga kitchen ɗin cikin sauri. "A dai bi a hankali har yanzu ba a shafa Fatihan ba" Inna Yaha ta faɗa tana tauna gyaɗa. Da Asiya da Ubayd ɗin duk babu wanda ya kulata suka shige falon Abba. "I'm disappointed in you Asiya. Ban ma san mizan faɗa ba. Tunda attension kike nema kin samu yanzu. Congratulations! Gwamna zai zo wajenki yau da dare" "Gwamna kuma?" "Abinda kike nema kenan ina, kin samu sai mi ya rage kuma" Zuciyarta ne ya tafaso. Taya zai zargeta da neman suna. "Kar ka gaya min magana, idan baza ka tayani neman hakkina ba baka da ikon zargina" "Asiya kar ki kawo mana rikicin siyasa gidan nan. We are happy the way we are" "Ni ban san mi kake nufi ba. Ni ba harka nake son yi da 'yan siyasa ba i just wanted to..." "A gaban Gwani aka mari Abba" maganarsa ya katseta. "Mari?" "Yes Asiya. Abba bai gaya miki yadda komai ya faru bane saboda baya so ya ɗaga miki hankali, amma ke ba abinda kika sani sai kanki. Ranan da suka zo karɓan Laptop ɗinki Gwani na wajen shi ya faɗa min komai. Asiya yaron da bai kai sa'an Habibu ba ya ɗaga hannu ya mari Abba saboda ke..." "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun" "Ko kin san Lamara Damana yayiwa Abba kashedi da kashe ni da ke da su Habibu? Ko kin san saboda hakane ya je ya samu MD ɗinku akan ya sallameki?. Ofcourse ke ba ruwanki tunda kinada irinsu Umaru Kwom da zasu goya miki baya idan wani abu ya same ki. "Asiya end this thing once and for all Dan Allah. In har da gaske kina sona ki ajiye maganar nan, idan ta kama ma ki rubuta cewa abinda kika faɗa ƙarya kikeyi indai hakan zai kawo maslaha to kiyi. I'm having bad feeling about this Asiya" Bai jira amsarta ba ya fice daga falon ya barta tsaye tana hawaye. Da Abba ya dawo daga sallar Isha ya kirata ya sanar mata Gwamna zai zo wajenta anjima. Bata nuna masa cewa Ubayd ya gaya mata ba saima haƙuri data shiga bashi kan abinda ta jawo masa... *** Daga office bai wuce gidan Gwamnati ba asalin gidansa ya wuce ya chanja kaya daga office suit zuwa riga da wando da face cap duka baƙaƙe ya haɗa da baƙin glass saboda yaiwa fiskarsa kariya dan kar a ganeshi. Daga nan ya ɗauki tsohon drebansa yace ya kaishi layin 'yan dabino. Sakatare ya riga ya kira dreban ya masa bayanin gidansu Asiya dan haka bai tsaya ko'ina ba sai ƙofar gidan. Lokacin da aka tsaya yayi kusan minti biyu kafin Gwamna ya kira numbar Abba ya sanar dashi gashi a ƙofar gida. Ko minti ɗaya bai cika ba Abba ya buɗe ƙofar falonsa dake fiskantar ƙofar gida ya fito jiki na rawa. An riga an kashe wutan ƙofar gidan shiyasa da akwai ɗan duhu. Yana ƙarasowa Gwamna ya buɗe ƙofa ya fito kafin kace me sun shige falon Abba. Sai da Gwamna ya zauna kafin Abba ya zauna yana risinawa duk da zai bawa Gwamnan shekaru kusan goma shatakwas amma girma girma ne. A tsanake suka gaisa kafin Abba yace masa bari ya kira Asiya. Asiya na ɗakin Umma ta takure waje guda Abba ya shigo da sallama. "Yana jiranki" "Abba" ta faɗa a hankali kamar mai ciwon baki Abba ya samu gefen gado ya zauna ko kallon Asiya bai yi ba har ta fice daga ɗakin sanye da dogon hijabin sallarta. Ƙanshin turarensa ya game falon dan tana buɗe ƙofa ƙanshinsa ne ya mata marhaban. Kallon tsana ta bishi da shi har ta zo ta zauna daura da shi. Har lokacin data zauna bai ɗago ya kalleta ba, idonsa na kan wayarsa. Ganin bashida niyyar magana yasa Asiya tace " akwai abinda nake yi kafin na fito, zan koma" Har ta fidda ran zai amsa tana shirin miƙewa ta bar masa falon taji yace "miyasa kike zargina? Mi kika sani?"' Da ita mai ashariya ce da ta ɗura masa ƙazamar ashar a wajen. "Ji wani tambayar rainin hankali a nan. Your excellency na san komai, na san abinda ka aikata amma kuma zan yi shiru ne kawai saboda Abbana. Sannan ka sani akwai Allah " Lokacin daya ɗago ido bataga ƙwayar idonsaba saboda face cap ɗinsa ya tare. Sai dai duk da haka sai da taji bugun ƙirjinta ya chanja. " na yaba da jajircewarki sai dai zargi babu shaida matsalace Asya. Umaru Kwom zai yi amfani dake ne ya yar, you are too young for that "Idan kinada shaida akan abinda kike iƙirari kuma, kina iya gabatar min yanzu" Wani abune yazo ya tokare mata maƙoƙaro dai-dai lokacin da take ƙoƙarin kurma ihu. Ita Gwamna zai rainawa hankali bayan shi ya aiko akazo aka ɗauke recorder da laptop ɗinta. Bata san ya akayi ta samu ƙwarin gwiwa ba, ƙila tsanarsa da tayi ne ya bata wannan ƙwarin gwiwa, ƙila kuma saboda marin da Ubayd yace anyiwa Abba ne. Jug ɗin ruwa da aka ajiye a tsakiyar centre table ta ɗauka ta buɗe ta watsawa Gwamna a fiska. "Wannan shine shaidar ka, Azzalumi" Tana tsaye riƙe da jug ƙirjinta na bugawa da ƙarfi kamar zai ɓallo, ta kasa ko motsawa a wajen. Ya kai sakan arba'in kafin Gwamna ya iya cire hular kansa ya buɗe manyan idanunsa. Loƙacin da ƙwayar idonsa ya shiga cikin na Asiya tsabar tsoro saida fitsari ya tsirto wa Asiya. Yai shirin buɗe baki yai magana amma ya fasa kawai sai ya miƙe tsaye, bai gama miƙewa ba Asiya ta fece da gudu ta bar falon... *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 08 "Jiya na yi bacci da wuri ban san yaushe ka shigo ba" Gwamna bai kulata ba ya cigaba da kurɓan shayin dake hannunsa a hankali "gobe zan wuce China, idan na gama siyayya a chan zan wuce Dubai" "Na ɗauka wata uku uku kike zuwa sari" ya faɗa yana kallonta "Manager yace ana buƙatan sabbin kaya, ka san latest goodies nake shigowa da shi" "Ok" Bai sake cewa komai ba ya cigaba da cin abinci a hankali. Jiya bai shiga gidan da wuri ba sai kusan ƙarfe biyu saura na dare. Baccin awa biyu yai ya sake miƙewa dolene ya je office da wuri saboda wani exco meeting da zasu yi ƙarfe takwas na safe. Har yanzu bai bar mamakin abinda Asiya ta masa ba. Gaskiya yarinyar tanada ƙarfin hali. Jiyan Asiya na fecewa yai murmushi dan abin dariya ya bashi. Yana fita cikin sauri ya je ya shige mota Dreba ya wuce da shi gidansa. A nan ya chanja kaya ya ɗan huta kafin ya shiga rubuta waƙa, kafin ya ankara ƙarfe ɗaya tayi dan haka ya tattara komai ya koma gidan Gwamnati. Sai daya leƙa ɗakunan yaran kafin ya je ya kwanta. Ya lura da cewa Nana da Zunairah sun rugume juna cikin bargo amma bai ɗauke shi komai ba. Mahirah kuma da alama karatu take bacci ya ɗauketa dan ga littafin nan gefen gado yana shirin faɗowa. Ya ɗauki littafin mai suna Americanah ya ajiye a gefen side drawer yai murmushi domin Mahirah ce ta ɗauko son karatunsa, bayan ya kashe wuta sannan ya wuce ɗakinsa inda Bilkisu ke kwance ta jima da barin nahiyar Africa... Ta sani abinda tayi bai dace ba, shiyasa lokacin data fito banɗaki ta shige da gudu. Bata fito ba kuwa sai da Inna Yaha ta fara ƙwanƙwasa ƙofar. Lokacin data isa ɗakin Umma, Abba baya nan dan haka ta fara ƙoƙarin chanja kaya ƙirjinta na wani irin dokawa kamar wanda tayi tsere. Washegari kasa zuwa gaida Abba tayi tana zaune a ɗaki ta kasa leƙa ko ƙofar ɗaki tunda tayi Alwalar Asuba. Ɗumamen da ke gabanta ma turashi gefe tayi dan ba iya ci zatayi ba. Shigowar Abba ɗakin da sallama yasa ta miƙewa a firgice, tun jiya take jimamin shirun Abba. Shiga ta musamman yai, yasa babbar riga kamar mai zuwa ɗaurin aure. "Ina kwana Abba" ta faɗi tana rusunawa "Lafiya Asiya Shahidah" "Abba kayi haƙuri, wallahi ban san ya akayi na watsa masa ruwan ba" "Ba tarbiyyan gidan nan bane. Ba kuma tarbiyyan Gwani bane Allah ya jiƙan rai. Girmama na gaba koda ba Shugaba bane tarbiyyan musulunci kenan, tarbiyyan da nake da yaƙinin mun miki kenan Asiya. To amma..." "Abba ka yafe min" Shi kansa Abba tun jiya ya kasa yarda Asiya ce tayi haka sai yanzu da ta jaddada masa. Jiya ya ji gudun Asiya zuwa banɗaki bai kai minti ɗaya ba kuma ya ji ƙaran tashin mota hakan ya sashi zuwa falon nasa da sauri. Jug ya fara gani a ƙasa, wajen da Gwamna ya zauna kuma akwai alaman ruwa a wajen. Ya duba ƙasan wajen nan ma akwai ruwa a malale. Wajen baiyi kamada kwaɓewar ruwa bisa tsautsayi ba yafi kama da cewa watsashi akayi. Kasa gaskata cewa Asiya ce ta aikata hakan yayi. Ya so kiran Gwamna amma rasa abinda zai faɗa masa ya sa ya fasa kiran. Ya kwana da tunanin mi zai yi, daga baya ya yanke shawaran zuwa wajen Gwamna ya bashi haƙuri. Lokacin daya tura saƙo wa Gwamna da bai ga reply ba tsoro ya shige shi. Bayan kamar minti arba'in Gwamna ya masa reply akan ya zo ƙarfe goma da minti shabiyar. "Zan je na bawa Gwamna haƙuri dan gidana ba gidan da ake walaƙanta baƙo bane balle baƙo kuma shugaba. Kamar yadda na faɗa kiyi duk abinda kika ga dama" Yana juyawa yai kiciɓis da Umma. Allah Sarki ta jima a wajen amma dake bata ji bata san mi suke tattaunawa ba. Ta shiga tambayar Abba miya ke faruwa amma yace mata kar ta damu idan ya dawo zai mata bayani. Bayan fitar sa Umma ta tsare Asiya da tambayoyi. Daga ƙarshe dai sai da Asiyar ta faɗa mata abinda tayi. Umma ta kama baki tana zaro ido... Abba na fita waje Ubayd na ƙoƙarin tsaida motarsa. Bai gaya masa abinda Asiya tayiwa Gwamna ba ya dai ce ya zo ya raka shi wajen Gwamna. Haka suka wuce gidan Gwamnati kowa da abinda ke ransa. Daga waje Ubayd ya nuna ID card ɗinsa amma duk da haka sai da masu gadi suka kira suka tabbatar da ana tsammanin zuwan su kafin aka barsu suka shiga ciki. Wani security ya musu jagora har ofishin Sakataren Gwamna bayan ya sanar da Gwamna zuwansu sannan yace su shiga ciki. Kwarjini Gwamna ya ƙara yiwa Abba. Kunyarsa ta gama cika shi lokacin da Gwamna da kansa ya miƙa masa hannu sukayi musabaha sannan ya jagorance su zuwa wajen kujeru inda yake zama ya tattauna da baƙinsa. "Ranka shi daɗe, ba zan iya bayyana maka yadda raina ya ɓaci jiya ba. Ina roƙon ka dan Allah kayi haƙuri ka yafe mata. Asiya..." "Ba komai Malam Nuhu, ya wuce a wajena. Infact na yaba da ƙarfin gwiwarta. Sai dai ina tausayin mijin da zata aura kar watarana yai laifi ya sha ruwan zafi" yai maganar yana dariya Abba ya dara yayinda Ubayd ya sunkuyar da kai yana kallon fiskar wayarsa wanda hoton Asiya ne a wayar, bai ɗago ba sai da yaji Abba yace " ka ji abinda Gwamna yace ko Ubaydullahi, sai ka zage damtse" Gwamna ya kalli Ubayd sannan ya kalli Abba hakan yasa Abba yai saurin cewa "ɗana kenan Ubaydullahi wanda zai aureta nan da watanni kaɗan masu zuwa" "Allah ya musu jagora" Abba ya amsa da Amin. Ko sakan talatin ba ayi ba Sakatare ya shigo ya ce da Gwamna lokacin tafiya yayi. Gwamna ya miƙe yai wa su Abba sallama dan fita zasuyi da tawagarsa zuwa wani ƙauye da akace za a buɗe firamare school na farko a wajen... Gwamna yana ƙauye Alhaji Sani Kachallah ya kira shi akan yana son ganinsa idan ya dawo. A ofishin Gwamna suka tattauna sabon batun daya ɓullo wai Matar tsohon Gwamna tana son shigar da Gwamna Saifuddeen ƙara. "Umaru Kwom ne da wannan aiki. Shegiya ko idda bata gamaba tana maganar shiga kotu" Alhaji Sani ya faɗa da ƙarfi. "Ko sun shiga kotu Baba ba abinda zasu samu sai baƙin ciki. Saminu Bacchi died a natural dead. Ni da likitan mun tattauna kuma ya gaya min jininsa ne ya hau sosai, stress ya sa shi faɗuwa har..." "Na san wannan Saifu. Abinda nake gujewa shine wannnan maganar zata ɓata maka lokaci. Zaka ɓata ƙarfinka wajen biyewa shirmensu sannan alokacin Kamfen zasu dinga ɓata maka suna da zancen. Mutumin da ke karkara idan aka ce masa Saifuddeen Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna ba zai nemi gaskiyar magana ba. Abinda zai yi shine shi da iyalensa ba zasu zaɓi Saifuddeen Kachallah ba. And kasan ƙarfin ƙuri'un 'yan ƙauye kuwa ?" "Baba inaga gara su shiga kotun a gama maganar kawai sab..." sai yai shiru tunowa da yai yadda Abba ke ƙoƙarin risinawa lokacin da yake bashi haƙuri. Idan aka shigar da maganar nan kotu Asiya za ta shigo ciki kuma za ta iya zuwa kurkuku ko ta biya tara mai yawa idan bata iya kare iƙirarinta da shaidu ba. "Kar ka damu zan yi maganin matsalar. komai zai warware" *** Musababbin zuwanta China ba dan saro kaya bane sai dan ta ga Malamin taurari wato Tsu Zhang. Shekaru ishirin da suka wuce a garin New Haven, Connecticut ta ƙasar America lokacin tana karatu a Jami'ar Yale wata Ƙawarta mai suna Paula ta gayyaceta wani taro da za ayi na mabiya addinin Buddha, inda aka gayyaci Malamin addini wato Monk Tsu Zhang ya zo ya yi mu su Lakca. Bayan an gama lakcan Paula da saurayinta Simon wanda basu jima da shiga addinin Buddhancin ba suka nemi ganawa da Malami Tsu Zhang, ya ba su lokaci da adreshin wajen da zasu sameshi. Bilkisu ba ta bisu ba lokacin da suka je ganinsa amma ga mamakinta da suka dawo Paula tace mata Tsu Zhang ya faɗi saƙo a bata. "Yace kinada ƙaddarar matar babban mutum yace tauraronki zai haska tareda ta mijinki" "Haka yace? Taya ya sani?" Tambayoyinta kenan lokacin da Paula ta sanar da ita saƙon Tsu Zhang. Bata tuna da wannan batu ba sai ranar da aka rantsar da Mijinta a matsayin Gwamna. Godiya take son yiwa Tsu Zhang shiyasa ta nemi ƙawarta Paula wacce take aure a ƙasar Brazil. Paula ita ta bata addreshing Tsu Zhang a China. Bata sha wahalar samun inda Tsu Zhang yake ba sai dai kuma sai da ta booking lokaci saboda yanzu Tsu Zhang ya tsufa baya karɓan baƙi sosai. A wani tafkeken temple (wurin bautan gumaka) Bilkisu ta samu Tsu Zhang. Lokacin da aka kaita wajensa ta jima zaune tana jiransa saboda meditation da yake yi. Lokacin daya buɗe ido bai juyo gareta ba, daga inda yake zaune yana fuskantar ƙaton gunkin Buddha dake ɗakin yace " akwai wani tauraro daya fito a gefen tauraron mijinki. Yadda tauraronki ke haskawa tareda ta mijinki haka wannan tauraro zai dinga haskawa tareda shi har sai tauraron mijinki ya haskaka fiye da tunaninki. Idan kikayi ƙoƙarin disashe wannan tauraro babu makawa da taki tauraron data mijinki haskensu zai dinga disashewa. Ki sani taurari uku a waje ɗaya suna bada haske na ban mamaki " "Ban gane ba..." Hannu ya ɗaga mata hakan ya sa tayi shiru. An riga an gaya mata cewa Tsu Zhang idan yai magana baya ƙarawa sannan baya maimitawa. Har ta bar temple ɗin hankalinta bai kwanta ba. Wani irin tauraro ne ya shiga tsakaninta da ta Saifuddeen?... *** Abba daya dawo bai gayawa Asiya komai ba, ya dai yiwa Umma bayanin komai, tareda faɗa mata yadda Gwamna ya tarbesu da mutunci suka rabu ana raha. Ubayd kam ko gidan bai shigo ba dan har yanzu fishi yake da ita. Umma ta bata shawaran ta je ta bawa Gwamna haƙuri amma har yanzu bata yanke shawaran zuwa ba. Gani take idan ta je kamar ta ƙasƙanta kanta a wajen Gwamna ne. Haka dai ta dinga saƙa da warwara har dare. Ƙarfe takwas da minti Arba'in Ubayd ya kirata yace ta sameshi a waje. Da murna ta fita dan a ganinta ya sauƙo kenan. "Kin ji cewa Sha'awanatu Bacchi zata shigar da ƙara akan kashe mijinta da aka yi?" Ya faɗa yana tsareta da ido. "Na gani a newsline" "Kin shirya shiga kotu dan kare kanki kenan?" "Ya Ubayd..." "Tambaya na miki" " ban so haka ta faru ba" "Abinda kike so kenan Asiya. Ina so ki sani cewa shari'arku ta tsaya a wajen gidan nan. Nothing should happen to my family Asiya, kada abinda ya samu Abba ko wani acikin gidan nan. Rigimarku ta siyasa ta tsaya chan nesa da mu"... Washegari ƙarfe shaɗaya ta shirya ta wuce gidan Gwamnati. Indai baiwa Gwamna haƙuri shi zai sa Umma da Abba da Ubayd suyi farin ciki da ita to za tayi. Wunin jiya ko kallon kirki Abba bai mata ba. A duniyar nan babu Uban da take da shi daya wuce Abba. Ale Faruƙ haihuwarta kawai yai amma Abba shine Ubanta. Tunda ta fito daga keke Napep zuwa shiganta Gate sai ɗaukan hotonta ake ta yi. Ta turawa Sakatare text jiya da dare bayan ta bar wajen Ubayd akan tana son ganin Gwamna kuma shi yace ta zo ƙarfe shaɗaya na safe. Tana isa wajensa yace ta shige ofishin, Gwamna yana jiranta. Gwamna ne zaune tareda Alhaji Sani Kachallah lokacin data shiga ofishin. " 'yar jarida mai ƙwazo" Alhaji Sani ya faɗa yana murmushi. Asiya tayi saƙeƙe tana kallonsa. "Bismillah, zo ki zauna ai wannan zama naki ne" Ɗan ɗosanuwa tayi a bakin kujera ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya yayinda ta sha jinin jikinta saboda kwarjini da suka mata. Alhaji Sani ya ɗauki kofin shayin da ke gabansa ya kurɓi kaɗan kafin ya kalli Asiya yace " akwai saƙon da za ki gani gobe. Tukwici ne daga gareni. Ina fata idan kin ga saƙon zai faranta miki rai sosai" Haƙuri ta zo bawa Gwamna amma kuma ta kasa furta komai. Bata gane inda maganar Alhaji Sani ya dosa ba. Da ƙyar ta iya haɗa kalmomi biyu tace "ban gane..." "Idan kinje gida ki gaishe da mahaifinki" Ba sai ya ƙara magana ba ta sani managarsa na nufin ta tashi ta tafi. Gwamna baishe da ita uffan ba sai ma kauda kansa da yai gefe... Daga gidan Gwamnati shagonsu ta wuce wanda tunda sukayi hatsari rabonta da wajen. Tana wajen Umaru Kwom ya turo mata saƙo akan ya kamata su haɗu su tattauna. Ta tura masa saƙo akan yai haƙuri ba zata iya taimaka masa ba. Saƙon Alhaji Sani Kachallah ya isowa Asiya ƙarfe takwas na safe lokacin tana shirin fita shago tunda yanzu ta bar aiki a Hill TV. Aliyu ne ya shigo ɗakinsu da gudu sanye da uniform ɗin makaranta. "Miya sa baka tafi makaranta ba Ali?" "Anty Shahidah wai kije yanzu-yanzu inji Abba" ya faɗa sannan ya ruga da gudu. Hijab ɗin Umma dake kan gado ta saka sannan ta wuce falon Abba da sauri. Tana zuwa ta ganshi ya ƙurawa TV idanu. Baice komai ba dan haka itama ta maida hankalinta kan talabijin ɗin. Bayan minti uku sannan aka fara karanta labarin daya sakata riƙe kai. Hotonta aka nuna tana magana da wani security a bakin gate ɗin gidan Gwamnati sannan ga tanan tana ƙoƙarin shiga office ɗin Gwamna daga nan kuma sai aka nuna hoton wasiƙa zuwa ga Gwamna wanda sunanta da sa hannunta ke ƙasa. Mai karanta labaran yana karanta wasiƙar hawaye na zubowa a idon Asiya yayinda ilahirin jikinta ya ɗau rawa. Cin mutuncin da za a mata kenan a ɓata mata suna. Abba ya rage volume ɗin TVn sannan ya juyo ya kalli Asiya. "Abba wallahi ban rubuta wata wasiƙa ba" "Wanda bai ji bari ba ai zai ji hoho ko Asiya. Kin dai ji yadda 'yan siyasa suka juya labarinki" "Na shiga uku" "Kiyi addu'a Allah ya sa ya tsaya a iya haka. Idan kuma taurin kai da kika saba za ki yi to Bismillah" Kafin ƙarfe goma na safe ko ina ya ɗauka 'yar jarida Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta yiwa Gwamna tayin soyayyarta ne shiyasa ta yaɓa masa baƙin fenti da bai amince da ita ba. Hatta cikin rahoton data kawo tana aibanta SSK lokacin daya ke mataimakin Gwamna sai da aka nemo aka dinga yaɗawa. Kowa a jahar sai tofa albarkacin bakinsa yake yi akan zancen. Wasu suce Asiya irin matan nan ne masu bibiyar 'yan siyasa amma shi Gwamna SSK babu ruwansa da harkan mata. Wasu kuma suce neman suna take yi saboda ta fitar da labarin da zai yi fice da ita a duniya amma dake Allah ba azzalumin bawa bane shiyasa asirinta ya tonu. Wasu kuma cewa suke akwai lauje a cikin naɗi ƙila an yiwa Asiya barazana ne shiyasa ta rubuta wasiƙar nan. Wasu kuma suna ganin 'yan adawa ne suka biyata dan ta ɓatawa Gwamna suna. Maganganu dai kala-kala. Maganar shigar da ƙara da ake ta raɗe-raɗin Matar tsohon Gwamna za ta yi kuwa sai ya zo ya bi ruwa. Lokacin da Likitan tsohon Gwamna yai bayani a gidan talabijin tareda fitar da report na gwaje-gwajen da akayiwa Gwamna Saminu Bacchi bayan rasuwarsa hatta Umaru Kwom sai da ya ji jikinsa yayi sanyi domin babu yadda za ayi ya samu nasara kan tuggun daya shiryawa SSK duk da kuwa ya yarda koda SSK bai sa an kashe Saminu Bacchi ba to Alhaji Sani Kachallah zai iya aiwatar da hakan. A ranan wani Malamin addini ya fito yai bayani akan yarda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau. Yai maganar cewa yana cikin rashin yarda da ƙaddara mutum ya fara bibiyar dalilin mutuwar wani. Gwamna Saminu Bacchi lokacinsa ne yayi shiyasa Allah ya ɗauki ransa abinda al'umma za su yi shine a cigaba da yi masa addu'a da shi da duk wanda suka riga mutuwa. Ita kuma Asiya Allah ya shiryeta. A rana ɗaya tal sunan Asiya ya chanja zuwa maƙaryaciya. Washe gari da safe wani mawaƙi ya shiga studio ya sake waƙa yana yabon Gwamna yana aibata sunan Asiya. Sai da Asiya ta gama shirya kayanta tsaf kafin ta wuce falon Abba, baya nan dan haka ta tura masa saƙo akan cewa zata koma gidan Baffa Malam. Idonta yayi jaa duk sun kumbura saboda kuka. Umma ta goyi bayan shawaran data yanke data ce zata je ta zauna a gidan Baffanta har sai saura sati biyu bikinta kafin ta dawo... *** "Your excellency inada magana" "Bismillah Malam Baffayo" "Yarinyar nan Asiya rayuwarta na cikin haɗari" Gwamna ya zaro ido cike da mamaki. " na samu labari daga majiya mai ƙarfi cewa mutanen Umaru Kwom suna son kasheta saboda a tada sabuwar fitina tunda wancan ta mutu" "How could they, ina kaji wannan magana?" Sakatare yace " Excellency a bar kaza a cikin gashin ta" Lokacin daya bar office kai tsaye Kachallah house ya wuce wajen Alhaji Sani. Bayan ya yiwa Alhaji Sani bayanin da Sakatarensa ya masa sai kawai ya ga ya ɓigire da dariya har da kakkautawa. Ya sake baki yana kallon Baffan nasa. "Wani lokaci Saifu kaman baka san mi ake nufi da siyasa ba. Ba abin mamaki bane idan sun yi niyyar kasheta saboda wata manufarsu, sai dai duk ta inda suka ɓullo ina nan ina jiransu. Har yaushe ma Umaru ya girma da zai ce zai ja dani" Wani abu ya daki zuciyar Saifuddeen. Ana maganar kashe ran yarinyar da bata ji ba bata gani ba amma yana dariya. Ba zai taɓa bari a hallaka rai a rikicin Gwamnatinsa ba. "Baba ba zan bari su taɓa lafiyarta ba balle ma har su kasheta matuƙar ina raye" Alhaji Sani ya kalli SSK da alamar tambaya a bakinsa amma bai furta ba sai yace " kenan zaka aureta?" "Baba ban gane ba" Gwamna ya faɗa cikin rashin fahimtar manufar Alhaji Sani Kachallah. "Hanya ɗaya da zaka iya kareta kenan Saifu" Alhaji Sani faɗa yana cigaba da dariya. WAIWAYE... *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 09 *WAIWAYE* Abu ne da muka sani cewa Allah zai iya jarrabtar mu ta kowani fanni na rayuwarmu. Zai iya jarrabtarmu ta wajen dukiya, lafiya, 'ya'ya, mata, 'yanuwa, iyaye da sauransu. Asalin iyayen Lukman Fulanin Baroroji ne wanda basa zama waje guda su jima. Lukman yaro ne da aka haifeshi da ƙusumbi (hunchback). Yana shekara uku mahaifiyar sa ta rasu wajen haihuwa. Matar uban sa da ake kira da Gaji ta ce ba za ta iya riƙe shi ba, shiyasa Uban sa ya damƙa shi wajen Yayar mahaifiyarsa mai suna Habbi. Yana cika shekara biyar a wajenta ta ɗauke shi ta kaishi wajen Malam AbdulWahab Falke Almajiranci wanda ya kasance Kawu a wajen mijin ta. Tunda aka damƙa Lukman wajen Malam kuwa Mahaifin sa bai taɓa waiwayan sa ba har Allah ya ɗau ran sa, shekaru biyar bayan rasuwan Asiya mahaifiyar Lukman ɗin. Itama Inna Habbin sau ɗaya ta je ta duba Lukman daga nan ba ta sake zuwa ba har rai yai halin sa. Malam Falke ya zamewa Lukman Uwa da Uba sannan Malami. Duk cikin Almajiran Malam, Lukman ya fi ƙoƙari da hazaƙa. Ya maida hankali sosai wajen karatu. Ɗan sarari da su ke samu da sauran ke watayawa cikin gari shi yana amfani da wannan lokaci ne yai ta ƙoƙarin rubutu a Allon sa. Malam Falke Allah bai bashi 'ya'ya dayawa ba. Yaran sa biyar ne kacal sai kuma 'ya'yan da ya ke riƙewa. Huɗu daga ciki mata ɗaya kuma namiji. Kafin a kawo masa Lukman ɗansa namiji ya jima da rasuwa, dan shekaransa shida ya rasu bayan wata ƙaramar jinya. Dayawa mutane sukan ɗauki Lukman a matsayin ɗan Malam ne saboda irin kulawar da Malam ke bashi. A hankali da ya dinga lura da baiwar karatu da Allah ya bawa Lukman sai ya zamana ya fara ba shi karatu na musamman. Duk wani ilimi da ya ke da shi to yana ƙoƙarin ya ga cewa Lukman ya samu, yana ma sa tanadin zama magajin sa. Koyaushe baya rabuwa da yiwa Lukman Du'a'ul Fahmi. Lukman yana shekara tara yai saukan ƙur'ani (tartil) yana shekaru shahuɗu yai haddar ƙur'ani kuma cikin watanni bakwai ya rubuta ƙur'ani da ka. A hankali ya dinga haddace manya-manyan litattafai na addini. Yana shekara shabakwai Malam ya tura shi Borno wajen wani Babban Malami. Bai dawo ba sai da yai shekaru huɗu a chan. A sanda ya dawo ne kuwa ya tarar da Malam ya aura masa wata 'yarsa. Rumaysa'u wacce aka fi kira da Tabawa ita ce auta cikin 'ya'yan Malam. Ita ce kuma Allah ya jarrabce shi da ita. Saɓanin sauran yayyanta da su ka yi karatu sosai har su ka yi sauka tun ma kafin ya aurar da su ita fir ta ƙi karatun. Bayan nan, ƙiriniya da yawace-yawace da ta tsirfata da tara samari ya sa ya ce zai haɗata aure da wani Almajirin sa. Tabawa ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba za ta auri Almajiri ba. Yayi yayi da ita ta ce ba za ta aure shi ba. Ƙarshe ma ta kai ƙarar sa wajen Maigari. Malam ya haƙura ya aura ma ta wanda ta kawo ta ce tana so. Da ke babu albarkan iyaye auren dudu wata biyar su ka yi ya rabu ta dawo gida ta fara zawarci. Kafin kace me sunan Tabawan Malam ya sake zama tamkar waƙa a wajen samari da bazawarai. Lokacin da Malam ya ce ta fito da miji sai ta nuna Chukudi a matsayin wanda ta ke so. Kasuwanci ya kawo Chukudi garin, ɗan kuɗin da ya ke kashewa Tabawa shine ya tsole ma ta ido har ta zaɓeshi a matsayin wanda za ta aura, duk da addinin su ba ɗaya ba, al'adar su ba ɗaya ba, uwa uba ba asan minene asalin sa ba. Wannan karan da Malam ya hanata auren sai wayan gari aka yi aka ga ta gudu daga gidan. Ita da Chukudi aka neme su a gari aka rasa. Wannan cin mutuncin har kwantar da Malam yai, kamar ma ba zai tashi ba sai kuma bayan ya sha jinyar watanni sai gashi ya samu sauƙi amma baƙin cikin da Tabawa ta ƙunsa ma sa yana nan yana cinsa, kullum addu'ar sa gareta Allah ya shiryar da ita. Ya sha tsayuwar dare akan lamarinta sai dai ita ɗin wata jarrabawa ce da Allah ya ma sa. Shekara ɗaya da rabi kafin Tabawa ta dawo gida. Ranan da ta dawo mutanen gidan da ƙyar su ka ganeta saboda lalacewa da ta yi. Bayan ta bi Chukudi zuwa ƙauyen su ashe niyyansa shine ya tsafeta yai kuɗi da ita. Da ƙyar Allah ya kuɓutar da ita daga kaidinsa, sai dai tunda ta bar ƙauyen ta rasa gane kanta. Ta jima tana garari kafin ta samu ta warke ta dawo wajen Babanta dan ta san nan ne kawai gatan ta. Malam ya karɓeta ne da sharaɗi guda, za ta zauna tsakani da Allah da duk wanda ya aura ma ta. Kaman da gaske ta ce ta amince. A take ya ɗaura ma ta aure da Lukman ya kuma tura wasiƙa akan Lukman ya dawo gida idan Malaminsa ya sallameshi. Bai samu dawowa ba sai bayan wata uku. Kafin ya dawo Malam ya gyara ma sa ɗakuna biyu cikin gidansa inda anan za su zauna da Tabawa. Lokacin da Malam ya sanar da Lukman maganar auren da yai masa ya sha mamaki sosai. Ya san halin Tabawa sarai kuma duk abinda ke faruwa babu wanda ba shi da masaniya akai. Ba wai ba zai karɓi zaɓin Malam ba ne amma yana tunanin anya kuwa Tabawa za ta zauna da shi? Tsoronsa kuwa ya tabbata domin lokacin da Malam ya haɗa su zai mu su nasiha Tabawa ta ƙeƙasa ƙasa akan ba za ta auri Mai ƙusumbi ba. Ita duk zaman nan ta ɗauka ɗaya daga cikin manyan Almajiran Malam aka aura mata, bata san Lukman Maiƙusumbi ba ne. "Baba ba zan zauna da Maiƙusumbi, Miskini, marar asali ba. Duk cikin Almajiranka ba wanda ba sa zuwa wajen 'yan uwan su lokaci zuwa lokaci amma wannan bai taɓa zuwa wajen na shi ba. Ƙila ma ɗan shege ne" "Rumaysa'u!" "Baba zan auri kowa amma banda shi Wallahi" "Na fi ƙarfin Miskini" ta ƙara jadda masa kafin ta fice daga ɗakin Malam ɗin. Duk ƙoƙarin da Lukman ya ke akan kada yai hawaye agaban Malam sai da hawaye su ka zubo ma sa. Dai-dai yana gogewa da gefen hannun rigansa Malam ya ce "Lukman ka tashi ka je za a kawo maka ita yanzu" "Malam ka yi haƙuri Dan Allah, tunda ba ta so a bari na sawwwaƙa ma ta" Ran Malam cike da ƙuna ya ce " ka san Allah idan har Rumaysa'u ba ta karɓi auren ka ba sai na tsine mata" Lukman ya zaro ido waje. "Kai ne aka cuta da na haɗaka aure da mace kamar Rumaysa'u, na yi haka ne dan ko Allah zai shiryar min da ita ta hanyar ka" A chan cikin gida kuwa Tabawa ta dinga faɗa wai a rasa wanda za a aura ma ta sai Maiƙusumbi. Wata Gwoggon ta da ke gidan ta fito ta dinga surfa mata masifa. Yadda ta dinga kiranta da butulu shiyasa jikinta yai sanyi. Duk da tarin laifuffukanta itakam ta ƙwammace ta zauna ba aure da ta auri Lukman Maiƙusumbi. Kusan shekaru biyu kawai Lukman ya ba ta. Tun suna yara ta tsaneshi. Yadda Malam ya ja shi a jiki ya maida shi ɗansa na dole ba ƙaramin ɓata ma ta rai ya ke yi ba. Bayan Gwoggo ta ƙare mata faɗan ita da Kulu yayar Tabawan suka tarkaɗata zuwa sashen da aka gyarawa Lukman. Tabawa ta sa a ranta zata zauna ne zuwa abubuwa su lafa, nan da lokaci kaɗan za ta rabu da shi ko da ta ƙarfi ne. Har ta fara bacci Lukman ya shigo ɗakin jikin sa a sanyaye. Umurnin Malam na ƙarshe kafin ya taho ne ya dagula ma sa lissafi. "Wallahi idan har ba ka tare da matarka daren yau ba. Ban yafe karatun da na koya maka ba" A gigice ya bar wajen saboda bai ga alaman wasa a wajen Malam ɗin ba. Da lallami ya nemi Tabawa amma ta ƙi bashi haɗin kai wannan ya sa shi binta da ƙarfi ya karɓi haƙƙin sa. Ya sha tsinuwa a wajen Tabawa kam kafin ya gama saboda da farko ta rena ma sa kan cewa za ta iya ƙwatan kanta a wajen sa. Ƙaramin ruwa gareshi shiyasa ta ke ma sa kallon ƙashi da rai ba ta san yadda ya ke a bushe haka ya ke da ƙarfi ba. Tun daga ranan kuwa ba abinda ya sake shiga tsakanin su. Iya kyautatawa yana yi ma ta amma itakam kullum cikin zagi da tsinuwar sa ta ke, tareda cewa ya saketa indai shi ɗan halak ne. Awata na biyu da auren ta gane ciki gareta. Ta yi kukan baƙin ciki sosai dan haɗa iri da Lukman mugun abu ne a wajenta. Wasu ƙulle-ƙullen magani ta nema ta sha wai dan cikin ya fita. Ba ta jima da shan maganin ba ta cika gidan da ihu. Iyaji Mahaifiyarta ta zo ta sameta cikin jini. Kwanan ta uku a Asibiti kafin aka sallameta. Sai da su ka dawo gidan ne ma Iyaji ta tabbatar ma ta da cewa cikin jikinta na nan. Ta sake shiga damuwa dan da ƙarfi ba ta son abin cikin ta. Ƙarshe Sheɗan ya kaɗa mata kai ta aiwatar da abinda ya zo ya rabata da Mahaifinta har abada. Guba ta zubawa Lukman a abinci akan idan ya ci ya mutu sai ta yi takabar sa ta huta da auren baƙin ciki. Lukman ya zo ya fara cin abincin kenan ko loma biyar bai yi ba wani jikan gidan ya leƙo akan ya je Malam na kiran sa. Ya wanke hannu ya fita. Yana wajen Malam suna magana cikin sa ya fara murɗawa tun yana daurewa har ya riƙe cikin yana murƙususu a ƙasa. Malam ya ɗauke shi aka yi Asibiti da shi bayan ya bashi zumar daya tofa ayoyin shifa a ciki. A chan ne aka ce mu su maganin ɓera ya ci. Ko tantama Malam bai yi ba ya sawa ransa Tabawa ce da wannan aikin. Sawa yai a kira ma sa ita. Lokacin da ta zo yana tare da Lukman da ke zaune gefen sa yayi wani fayau da shi saboda a yau ɗin ne aka sallameshi daga Asibiti. Ko gaisuwarta Malam bai amsa ba ya umurci Lukman ya saketa. Takardar da Malam ya miƙo ma sa ya karɓa hannunsa na rawa. "Ka rubuta ma ta saki na ce" ya sake maimaita ma sa da ɗan karfi. Alƙalamin da ke gefen Malam ya ɗauka ya rubuta wa Rumaysa'u saki ɗaya da rubutun Ajami. Yana rubutun Tabawa na murmushi. Malam ya dubeta ya ce "Bayan Lukman bana tunanin za ki samu wani namijin ƙware da zai sake neman auren ki Rumaysa'u". Magana ce ya mata amma kasancewarsa Uba gareta sai abin ya zame mata baki. Abin mamaki ko Wata ba'ayi ba da rabuwar su Malam ya aurawa Lukman 'yar uwarta wadda su ke 'ya'yan Baffanu (cousins). Indo budurwace mai ƙarancin shekaru amma ta yi biyayya ga zaɓin Malam ta zauna da Lukman tsakani da Allah. Cikin Tabawa na wata takwas Malam ya rasu mutuwar da ya girgiza su sosai. Sati uku da rasuwan ta haifi ɗa namiji. Sunan Baba ta so sakawa amma saboda jinin Lukman ne sai ta ƙyamaci hakan. Da kanta ta samu Lukman akan sunan ɗanta Faruƙu. Ranan suna kuwa bai chanja ɗin ba aka sawa yaro Faruƙ. Tunaninta ta rabu da auren Lukman za ta buɗe da wani auren mai kyau sai kuma duniya ta juya mata baya. Halayyar ta na baya su suka bayyana wa kowa da ke son zuwa aurenta. Tabawa ce dai da ta gudu da wani Arne na kusan shekaru uku. Tabawa ce dai da ta kai ƙaran mahaifinta wajen Maigari, Tabawa ce dai... Tabawa ce dai... Tun tana zaune ba ta komai, da abubuwa su ka fara kwaɓe ma ta ɗan sauran kuɗin da ta samu na gadon Malam ta fara sana'ar tuyar ƙosai. Wasa-wasa sai da Faruƙ ya shekara shida kafin ta samu miji ta yi aure. Aure ta yi amma ɗan ƙaran wahala take sha a cikinsa ko da wasa Ƙaura Mafarauci bai ɗauketa da daraja ba. Tana zaune da matan sa biyu amma duk ciki ta fi su wahala. Bayan duka da ya ke mata da har ya zame mata jiki 'yan kuɗaɗen sana'arta duk shi ya ke karɓa ya sha giya da su. Ƙarshe jari ya ƙare. Ta yi zagin ta yi faɗan duk dan ya saketa amma ya ƙi. Ga shi shekaru bakwai tare amma ko ɓari ba ta taɓa yi ba, shiyasa ma ta kasa miƙawa Gwani Lukman ɗansa Faruƙ lokacin da ya buƙaci hakan. Duk yadda ba ta son Ubansa haka ta ɗaurawa Faruƙ tsananin so. A shekara ta tara da auren Ƙaura ya rasu. Ta yi farin ciki da mutuwar sa sosai. Tana ƙarisa takaba ta dawo gida lokacin ba wanda zai ganta ya ce zai waiwayeta saboda yadda ta tsofe ta lalace. Bata yi niyyar sake Aure ba amma ganin Indo da Gwani Lukman suna zaune lafiya ya sa ta kasa zaman gidan nasu. Lukman shi ya gaji Malam, tun bayan rasuwan sa Makarantar Malam ba ta watse ba. Wani fili da ke gefen gidan Malam wanda tun Malam na raye ya ba shi kyauta ya samu ya fara ginawa, cikin shekaru biyu kuwa ya kammala shi da Indo su ka tare a gidan da yaransu guda biyu maza AbdulWahab da su ke kira da Malam sai Zakariyya da su ke cewa Zakari. Cikin shekarun nan Allah ya ɗaukaka sunan Gwani Lukman Baba fiyeda ta Malam Falke. Babu wanda ke duba ƙusumbinsa sai tarin Ilimin da Allah ya bashi. Daga garuruwa daban daban ana zuwa ɗaukan karatu wajen sa. Tuni sunan sa ya koma Gwani Baba. 'Ya'yan sa Malam da Zakari kuwa sun zama abun kwatance cikin gari. Ga tarbiyya ga karatu. Kukan Lukman kullum akan Faruƙ ne wanda Tabawa ta janye shi daga jikinsa. Tun yana yaro idan ya sa shi ya zo wajen sa karatu yake guduwa. Da ya fara masa duka sai ya dena zuwa kwata-kwata, Tabawa ta ɗaure ma sa gindi har da samun Lukman akan ya bar ma ta ɗa ba lallai ne sai ɗanta ya zama Malami kamar sa ba. "Ba a chanjawa tuwo suna Ruma. Duk lokacin da ki ka kalli Faruƙ na san fiskata kike gani a tasa. Ki bani ɗana Allah ya taimakeni na ɗaura shi akan tarbiyya mai kyau" Ruma ta ce ba ta san zance ba. Lokacin da ta koma gida haka ta titsiye Faruƙ a gaba tana kallo wani abu na sukanta a zuciya. Kallo ɗaya za ka yiwa Faruƙ ka san jinin Gwani Lukman ne. Idan ka cire ƙusumbi da bashi da shi komai na Gwani ya ɗauko, hatta da murmushi idan yai sai ka ɗauka Gwani ke yi. Ta sani Lukman kyakyawane sosai, Ƙusumbin da ke bayansa da kuma ƙaramin jiki da Allah ya bashi shine kawai naƙasu da Allah ya mishi. Bayan ta gama takaba da shekara ɗaya ta auri Saleh. Ganin Saleh babban mutum ne dan ya ɗara shekaru hamsin alokacin kuma shine sarkin noman Doka wani garin da ke maƙotaka da su ta yi tunanin samun lamuni a auren. Da Faruƙ ta tare duk da kuwa alokacin yana kusan shekaru shashida a duniya ya ƙi karatun Arabi ya ki ta Boko. Ko Primary bai gama ba ya dena zuwa. Ta ɗan samu zaman lafiya na ɗan wasu watanni kafin asalin halin Sarkin noma ya bayyana ma ta. A gidan Sarkin noma ne ta ƙwammaci tun asali da ba ta rabu da Lukman ba. Bayan munanan halinsa kuma ga uƙubar kishiyoyi. Lokacin da ta fara Sana'a tana ɗan samu abun rufawa kanta asiri ɗaya daga cikin kishoyinta ta je aka mata surkulle kasuwan ƙosai da ɗanwake da ta keyi ya lalace ga uwa uba ciwo da aka sa ma ta. Ko shekara Faruƙ bai yi da ita ba ya tafi Birni neman aiki, bai sake waiwayanta ba. Haka ta zauna cikin ƙunci ita kaɗai. Dama tunda ta rabu da Lukman zumuncinta da 'yan uwanta ya yi rauni. Lokacin da ta koma Doka da zama da abubuwa ke mata daɗi ba wanda ta waiwaya a cikin su. A shekara na uku da rashin Faruƙ wata rana da Adda Karime ta kawo ma ta ziyara. Ashe Allah yayiwa mahaifiyar su Iyaji rasuwa kusan wata biyar da su ka wuce ba ta sani ba. An aikawa Saleh lokacin mutuwar amma bai gaya ma ta ba. Tabawa ta yi kuka sosai. Lokacin da Adda Karime za ta tafi ta roƙeta da Allah akan ta faɗawa Gwani ya nemo ma ta Faruƙ tunda Karimen ta faɗa ma ta suma rabon su da Faruƙ ɗin tun bayan tarewar ta. Addu'a sosai Gwani ya sa gaba akan Allah ya dawo ma sa da Faruƙ gida tunda Tabawan da ya ke tunanin yana wajenta ma tace ba ta san inda ya shiga ba. Allah maji roƙon bawa a cikin wata na huɗu sai ga Faruƙ ya shigo gari. Idan ka ganshi ba za ka ce ɗan Malam kuma jikan Malami bane. Ya tara uban gashi yana sanye da wando na yayi wanda ta matse daga sama daga ƙasa kuma ta buɗe. Cikin ikon Allah da Gwani yai ma sa maganar aure sai ya amince. Ɗan kuɗi da ya zo da shi da kuma abinda Malam ya haɗa mi shi da shi yai jari ya fara kasuwanci. A hankali kuma Allah ya sa ma sa albarka a ciki, cikin lokaci kaɗan ya samu rumfar kan sa a kasuwa. *** A wani madaidaicin gida kuwa wata budurwa ce ke aikin wanke-wanke. Kwanukan yawa garesu, kuma yawancin su robobi ne madaidaita hakan zai sa ka kira su da kwanukan saida abinci. Daga yadda budurwar ta duƙa tana wanke-wanken wani yaro wanda ba zai wuce shekaru goma ba ya ɗira ma ta dundu a baya. Budurwar ta juyo a zabure tana zare ido. "Kurma ki je inji Mama" ya faɗa yana nuna mata dai dai barandar da ɗakuna uku su ke jere reras. Maimakon ta ɓata rai da abinda ya mata sai ta masa murmushi. Ta goge hannunta ajikin zaninta ta wuce ɗakin Mama Asabe. Tana ɗaga labulen ɗakin sai da ƙirjin Mama Asabe ya buga saboda ta ɗauka mijinta Malam ne. Ganin Kurma ce ya sa ta ɗan sauke ajiyar zuciya. Cinikin da su ka yi da safe da kuma na rana ta ke irgawa. "Yawwa Kurma zo ki je ki auno min shinkafar gobe wanda ya rage ba zai kai ba" Ta ƙarisa maganar tana miƙa mata wani dunƙulen kuɗi da ta ajiye a gefe. Bayan da Kurma ta karɓi kuɗin a hannunta ta cigaba da yi ma ta bayani da hannu ta yadda za ta gane. Tun tana shekara huɗu aka kawo mata ita kuma cikin shekaru goma ba abinda ba ta iya ba a yaren kurame. Yadda ta jaddada ma ta cewa a rumfar Ale Faruƙ ta ke so ta siyo ma ta shinkafar hakan ya sa ta yi saurin zuwa ta ƙarisa wanke wanken da ta ke yi dan daga gidan su zuwa rumfar Ale Faruƙ aƙalla sai ta yi tafiyar minti shabiyar zuwa ishirin. Lokacin da za ta fita daga gidan ne ta ci karo da Malam a zaure. Ta ɗan risina ta gaida shi kafin ta wuce. Malam Sabo Yayan Mahaifinta ne. Bayan rasuwan mahaifiyarta lokacin tana watanni bakwai da haihuwa Mahaifinta Malam Inusa bai ƙara aure ba har Allah ya ɗauki ran sa shekaru uku bayan rasuwan matar sa. A wajen Inna Talatu Zainab kurma take tun rasuwan mahaifiyarta amma bayan rasuwan Malam Inusa, Yayansa Sabo ya karɓota ya kawota wa matar sa Asabe. Da niyyar zai ɗauki nauyin marainiyya ya karɓeta amma ba wannan ne gaban sa ba irin gadon gona da gida da ƙanin sa ya bari. Ba ayi shekaru biyar ba ya cinye komai, ya siyar da gida ya siyar da gonan duka sun bi ruwa babu ko ɗaya yanzu. 'Ya'yan Mama Asabe Maza huɗu ne shiyasa ta ke moran Zainab Kurma son ranta tun tana ƙarancin shekaru. Yau rumfar Ale Faruƙ a cike ta ke da mutane magidanta da zawarai. Benchi uku aka jera kuma duk sun cika da mutane. Yankan farce akewa Ale Faruƙ lokacin da ya ɗaga ido yaga Kurma na tahowa rumfarsa kanta a ƙasa saboda kunya. Yana ganin yaron shagonsa Iro ya miƙe yai saurin miƙewa ya ƙariso wajen. Da hannu ta ke nunawa Iro daron shinkafar da ke kan teburi tana nuna ma sa yatsunta biyar alamun mudu biyar zai auna ma ta. Ba yau ta fara zuwa ba shiyasa Iro ya fahimci bayanin ta. Zai fara aunawa kenan Ale Faruƙ ya dafa kafaɗan sa ya ce ya koma ya zauna zai auna ma ta. Mudu biyar ta ke so, Iro ya faɗa kafin ya bar wajen dan ya san halin Uban gidansa indai ya ga mace to hankalinsa ya tashi kenan. Sai da Ale Faruƙ ya auna mudu biyar zai zuba na shida Kurma ta yi saurin kai hannunta dan ta dakatar da shi aka ci sa'a hannunta ya taɓa nashi. Dama tuni kyakyawan fiskanta ya riga ya zautar da shi balle kuma yanzu da ya ji sanyin hannunta akan na shi. Ta yi saurin ɗage hannun tana yi ma sa bayani akan mudu biyar ta ke son siya. Ya san biyar ɗin ne yana so ya ƙara ma ta mudu ɗaya ne saboda neman guri a wajenta. " 'yan mata ai ba a hana Ihsani. Idan na kyautata miki na san Allah..." "Maigida kurma ce fa" Muryan Iro ya katse shi. Ale Faruƙ ya wangale baki yana kallon Iro da mamaki. Yana kallo Iro ya karɓi kuɗin hannun Kurma ya miƙa ma ta ledar da aka zuba shinkafan bai iya cewa komai ba. Sai da Kurma ta yi nisa ya samu daman tambayar ko ita ɗin 'yar gidan waye?. Wani cikin abokansa ya ce " shege mutumina, yanzu kuma kan Kurma za ka koma kenan" yana maganan yana dariya. Kafin a tashi a kasuwa Ale Faruƙ ya samu duk wani bayanai da ya ke so gameda Kurma. Ya san marigayi Malam Inusa, balle uwa uba Baffanta wanda abokin karawan sa ne, yanzu haka yana bin Malam Sabo bashin kuɗi ma su yawa. Ya so haƙura zuwa washegari kafin ya je ya samu Malam Sabon amma kuma zuciyar sa ta kasa nitsuwa, kyakykyawar fiskar Kurma ce ke ta ma sa gizau. Kusan ƙarfe tara da rabi ya nemi babban riga ya saka ya wuce gidan Malam Sabo. Tun a daren suka gama magana. Tunda Ale Faruƙ ya ce ya yafewa Malam Sabo bashin da ya ke binsa ya fara washe baki saboda ya san ba haka kawai Ale Faruƙ zai yafe ma sa kuɗi ba sai dai idan akwai wani abu na shi da ya ke so ne. Da farko dai ya sa a ransa indai maganan Injin niƙan Asabe ne to kuwa za ayita dan ya san halin Asabe sarai. Sai kuma ya ji zancen akan 'yar wajensa ce Zainabu Kurma, indai ita ce ba shi da matsala da wannan. *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 10 Lokacin da Ale Faruƙ ya auri Zainab Kurma matan sa uku ne, dan bai jima da sakin ta huɗun ba. Da ganinta da auren duka-duka sati huɗu ne. Mama Asabe har ga Allah bata so aka yi auren ba, ba kuwa saboda halin Ale Faruƙ ɗin bane na auri saki sai dan saboda ayyukan da Kurma ke mata. Duk wani ƙarfin sana'arta to Kurma ce. Ita da Malam Sabo dai sun yi ƙarfa-ƙarfa sun mata gado da tabarma da buta daga nan kuma kowa ya tsuke Aljihun sa. Duk da kuwa irin kuɗin da Malam Sabon ya yaga a wajen Ale Faruƙ ɗin. Inna Talatu wacce ta reneta lokacin tana yarinya da kuma wasu cikin 'yan uwan mamanta su suka haɗu suka mata sauran kayan ɗakin. Lokacin da aka kawo Kurma gidan ɗakin Iyani aka fara kaita wacce ta ke Uwargida sannan aka wuce da ita ɗakin Fulani wacce ta ke matarsa ta biyu a gidan, matar da ta zame masa ƙarfen ƙafa ita bata haihu ba amma ta ƙi tafiya duk da kuwa rashin mutuncin da take shukawa a gidan. Sai ɗakin Halime matarsa ta uku wacce shekaransu uku kenan da aure. Lokacin da aka kaita ɗakin Tabawa ko kallon kirki bata yi musu ba, ta ɓantari goro tana taunawa tace "Faruƙu kenan. Abin nasa yanzu ya koma kan Miskinai. Allah rufa asiri" Inna Talatu ta harzuƙa zatayi masifa wata yayarta ta hanata. Kafin su fita kuwa Inna Talatun ta kirata da tsohuwar banza. Tabawa ta biyosu tana zagi tana tsinuwa amma babu wanda ya kulata. Rayuwar Zainab a gidan Ale Faruƙ tamkar 'yar aiki ce a gidan iyayen gidanta. Sati ɗaya da Ale Faruƙ yai yana kwasar amarci ya dinga tattalin Zainab, shi yake siyo mata abinci daga waje: nama, bredi, ƙwai da madara sune cimarta. Baiwar Allah har ta fara sake jiki tana godewa Allah tunda rayuwar da take ciki yanzu akwai daɗi ba kamar gidan Mama Asabe ba. Lokacin da aka fara rabon girki nan ne ta ƙwammaci kiɗa da karatu. Gidan Ale Faruƙ babban gidane wadatacce dan kowacce mata ciki da falo gareta, shima sashensa ciki da falo ne, sai ɗakuna huɗu na yara sai ɗakin mahaifiyarsa Tabawa, sannan akwai ɗakuna uku a zaure na saukan baƙi. A lokacin daya auri Zainab 'ya'yansa goma shabiyar ciki kuwa bakwai ne da iyayensu. 'Ya'yan Iyani su guda shida, maza biyu,mata huɗu sai Halime dake da 'ya ɗaya. Da farko Fulani ce ta fara ɗaurawa Zainabu nauyin girkinta daga baya Iyani da Halime suka biyo baya. Kafin kace me gaba ɗaya ranakun girkinsu ita ke yi. Fulani kam hatta Sana'arta na shinkafa da wake da take da rana sai da ya zamo Zainabu ce ke yin komai , ita dai sai kawai idan ta gama ta zauna ta dinga siyarwa. A hankali Yaran gidan da suka ga iyayensu na saka Zainab aiki sai suka fara taɓawa suma. Lokaci lokaci sai su bar mata wanke-wanken gidan ko kuma su jiƙa kayan wanki su ƙi wankewa saboda idan Kurma ta zo ta gani tana son amfani da baho ko bokiti dole sai dai ta wanke musu kayan tunda bata da mugun zuciyar da zata bar musu kayan a ƙasa. Ranan da ta fara zuwa ta ga sunyi haka, ɗakin yaran ta je tana musu bayani akan za tayi amfani da bahon wanki. Haka suka manna mata hauka akan basu san mi take faɗa ba, abin takaicin yawanci bahon nata ne dan Fulani da Halime basa taɓa barin nasu a waje. Ita kuwa Kurma ko bata fito da su ba yaran sukan shiga ɗakinta su ɗauka babu yadda ta iya. Cikin zalunci da ake yiwa Zainabu ba abar Tabawa a baya ba. Itama ba ta taɓa ragawa Zainabun ba, dama duk cikin matan Ale Faruƙ babu wanda ta ɗauki mahaifiyarsa da daraja haka ma jikokinta. Kafin zuwan Zainabu gidan Tabawa ke wanki da kanta, haka ma abinci sai abinda aka zuba mata amma Zainabu Kurma bata taɓa mata rowan abinci ba haka nan wankinta da gyaran ɗaki duk ita ke yi. Kafin shekara ɗaya Zainab ta zabge ta koɗe. Aikin da take a gidan Ale ko rabinsa bata taɓa yi ba a gidan Mama Asabe. Ale Faruƙ ya san mi yake faruwa a gidan tunda shi ba makaho bane amma halinsa dama shine idan mace ta shigo gidansa komai ta tarar ruwanta ne, sai dai ta ƙwaci kanta daga sharrin sauran matansa amma shi ba zai tanka ba. Akwai lokacin da Zainab tayi ɓarin cikin sati uku bata sani ba bata ma san cikine ba dan jinin al'ada ta ɗauka. Tana zaune ne a gidan amma gaba ɗaya komai na gidan ya fita mata aka. Akwai lokutan da take tunanin gara kawai Ale Faruƙ ya saketa. Sai dai dokar sa ce baya sakin mace kafin ta cika shekara biyu. A cewarsa lokacin bai gama morar kuɗinsa ba. A cikin shekara na biyu da auren Zainabu da Ale Faruƙ ta sake samun ciki. Cikin yazo mata da laulayi mai tsanani amma babu wanda yake tausaya mata a gidan. Ba ta son warin abinci, bata cin abinci sai ƙanzo da kunun tsamiya. Idan za ta yi girki sai dai ta sa tsumma ta rufe hancinta saboda kar ta ji ƙanshin. Ranan da ta ƙi yiwa Fulani girki ta nuna cewa sai dai tayi tunda ranan girkinta ne haka ta mata chaa har da mata kashedin indai bata yi girkin ba za ta mata duka a gidan. Ranan da Ale Faruƙ ya dawo ɗakinta, tace masa ya gayawa matansa cewa ba zata sake yiwa kowacce girki ba. Abin mamaki sai cewa yai tunda ta riga ta fara sai dai ta cigaba da hakan har zuwa lokacin da zasu ce ta dena. Abin ya ƙona mata rai. Bata taɓa tunanin kai ƙaran Ale ko matansa ba, koda wasu cikin 'yan uwanta sun kawo mata ziyara nunawa take bata cikin matsala. Washegari ta saka hijabi ta wuce gidan mahaifinsa. Ɗan karatun allo da tayi kafin aurenta da shi ta iya rubuta bayaninta da rubutun ajami a takarda ta miƙawa Mama Indo matar Gwani. Mama tana karantawa sai ga hawaye ya cika mata fiska. Tana tambaya ne akan ko addini ya bayarwa namiji daman ya yi rashin adalci tsakanin matansa. Sannan idan ta ƙi yiwa matan mijinta aiki akwai zunubi awajen Allah? Mama bata bari Gwani ya gama karatu da almajiransa ba ta aika akan ya zo akwai matsala. Koda ta bayyanawa Gwani abinda Zainab ta faɗa ransa ya ɓaci sosai. A kullum tsakaninsa da Faruƙ shawara da addu'a domin muguwar tarbiyar da Tabawa ta bashi da kuma jahilci da ke damunsa shiyasa yake tafiyar da rayuwansa bisa ra'ayin kansa. Arziƙi dai Allah ya bashi amma ni'imar ilimi da kakansa Malam Falke keda shi, da Gwani keda shi da ƙannensa Malam da Zakari keda shi ya barranta masa. Bai nemi ilimi yana ƙuruciya ba kuma har yanzu da yake da damar neman ilimi kuɗi da mata sune a gabansa. Gwani ya fayyace mata hakkin mace akan mijinta da hakkin miji akan matarsa hakan yasa zuciyar Zainab ya ɗan yi sanyi. Mama da kanta taje gidan ta tara matan Ale Faruƙ ta gaya musu saƙon Gwani akan duk wacce ta sake takurawa Zainab zai mugun saɓa mata. Yadda basa shakkan Tabawa haka suke tsananin shakkan Gwani. Tabawa na zaune ƙofar ɗaki tana tauna goro ta fara faɗin "su matar Malam manya. Duk tsiyar ki dai Faruƙ ɗana ne. Idan Allah bai bashi ilimi ba ai ya bashi arziƙi" ... Daga ranan kowacce mata ta karɓi girkinta. Cikin Zainabu na wata bakwai Gambo wata maƙociyarsu ta fita daga takaba hakan ya sa Ale Faruƙ ya fito nemanta. Kamar kowacce mace arziƙinsa, kyaun surarsa da kuma gulmar ƙarfinsa da matan daya saka suke, shi ya kwaɗaita wa Gambo shiga gidansa, sai dai ta san mata huɗu gareshi. Halime, Ale Faruƙ yai niyyan saka saboda ta kwana biyu a gidansa amma tunda ta masa rantsuwar duk ranan da ya saketa sai ta yanke masa gaba sai ya chanja tunani. Ba zai saki Iyani ba saboda itace uwar manyan 'ya'yansa sannan Fulani kuma ya rasa dalilin da yasa ya kasa sakinta. Kurma ce kawai zai iya saka a halin daya samu kansa sai dai kuma gaskiya bai shirya rabuwa da ita yanzu ba, har yanzu akwai ƙuruciya a tareda ita. Kuma ita kaɗaice macen da idan yace tayi abu za tayi idan yace ta bari ma zata bari. Da dai yaga Alhaji Mato na ƙoƙarin kauda shi a wajen Gambo sai ya yanke ɗanyen shawaran sakin Zainabu. Da sassafiya ya shiga ɗakinta ya miƙa mata takarda ya mata bayanin zata iya zama a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan har ta haihu. Ba tayi boko ba shiyasa ko karanta hausar daya rubuta bata iya yi ba. Zuwa tayi wajen Jamilah ɗaya daga cikin yaransa wacce take da ɗan hankali tace ta rubuta mata abinda Ale ya rubuta da ajami. Jamilah ta rubuta mata kamar yadda ya rubuta da Hausa *na saki Zainabu saki ɗaya* bayan ta karanta rubuntun da Jamilar tayi a ƙasan na Ale, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗauki takardar ta koma ɗakinta ta shiga haɗa kayanta. Zuwa ƙarfe sha biyu na rana ta gama tattara kayanta ta wuce gidan Inna Talatu. Ba zata iya komawa wajen Mama Asabe ba saboda a halin da take ciki wajen da zata samu kwanciyar hankali take nema. A wajen Inna Talatu yar mahaifiyarta ce kaɗai zata iya samun wannan. Haka kwanaki suka dinga tafiya har wata ranan Jumma'a ranan da cikin Zainabu ya shiga wata tara da kwana biyar ta haifi kyakykyawar 'yarta. Suna dawowa daga Asibiti da ɗanyan haihuwa haka ta ɗauki 'yarta ta wuce gidan Gwani da ita haɗe da takardar da ta rubuta ranan da Ale Faruƙ ya saketa. Gwani na alwalar sallar la'asar Zainab ta shigo ɗauke da jaririya a hannunta. Tana zuwa gabansa ta ɗan rusuna sannan ta miƙa masa takardar hannunta. Gwani da hankalinsa ya tashi da ganinta haka ya karɓi takardar yana ƙwalawa Mama kira. Lokacin daya karanta takardar hawaye ya taru a idonsa. Tausayin ɗansa Faruƙ ya fi kamashi akan na Zainabu. Mama ta fito daga ɗakinta tana tambayar Zainabu yaushe ta sauka amma Zainabu bata kulata ba. Gwani ya ajiye takardar ya ƙarisa alwalarsa sannan yai wa Zainabu alamar ta miƙo masa jaririyar. Zainabu ta miƙa masa 'yar. Gwani yai wa yarinyar kiran sallah a kunnenta na dama sannan yai mata iƙama a kunnenta na hagu kafin ya gama Mama ta shiga ɗakinta ta ɗauko masa dabino, dake cimar Gwani ne ba a rasawa a ɗakinta. Huɗuba yaiwa 'yar da suna Asiya Shahidah sannan ya shiga tofa mata duka addu'o'in da Zainabu ta rubuta a takardar data kawo. Yai addu'ar kada Allah ya sa ta ɗauko ko ɗaya daga cikin halayen mahaifinta da ta kakarta Tabawa. Yai addu'ar ta zamo mai ilimi, mai tausayi, mai imani da riƙon amana. Yai addu'ar kada ta zamo azzaluma mai tauye hakkin mutane, yai addu'ar yadda mahaifiyarta bata ji bata magana Allah ya sa ta ji ta kuma yi magana. Yai addu'ar ta zama jaruma marar tsoro wacce akoda yaushe neman gaskiya da aiwatar da gaskiya shine halinta, yai addu'ar Allah ya kareta daga sharrin Mutane, Aljanu, Dabbobi da kuma Shaiɗan la'ananne. Yai addu'ar ta zamo abin alfahari ga iyayenta dama al'ummar musulmai gaba ɗaya. Ya ƙara da cewa yana addu'ar ta samu tabarakkin mai sunanta wato Nana Asiyah. Bayan ya gama addu'o'in sannan ya karɓi dabino a hannun matarsa ya gutsura ya tauna sannan ya sakawa Asiya a baki. Sai alokacin Zainabu ta fara murmushi. Ita da Mama ne suka koma gidan Inna Talatu wacce ta birkice saboda rasa Zainabun da akayi a gidan... A gidan Gwani aka yi suna dan kwana huɗu da haihuwan ya nemi Zainabun ta dawo gidansa. Kunyar Baban tsohon mijinta ya sa bata iya musawa ba. Ale Faruƙ ma dai nauyin Gwani daya ji ya sa shi kawo rago da kuɗi dan a yi suna da shi. *** Tun kafin Asiya ta cika shekara biyu Inna Talatu ke yiwa babban ɗanta mai suna Nuhu kwaɗayin ya auri Zainabu. Matarsa ta farko ta rasu sannan Yahanasu da ya aura wacce ita ɗin 'yar dangin mahaifinsa ce sai ta kasance fitinanniyar mace. Shekarar Asiya uku aka yi auren Malam Nuhu Principal da Zainabu Kurma. Lokacin da Ale Faruƙ ya ji labarin auren baƙinciki kamar ya kashe shi, duk cikin matan daya rabu da su babu wacce yake jin rabuwar da ciwo kamar rabuwarsa da Zainabu. Ya rabu da Halime ita kuma Gambo data shigo gidansa tama fi Fulani fitina. Malam Nuhu Gidaɗo Malamin makaranta ne da ya kai matsayin Principal inda yanzu yake shugaban makarantar Special School Congo. Matarsa ta farko Hassana sati biyar da haihuwa ta rasu hakan ya sa rainon ɗansa Ubaydullah ya koma wajen 'ya uwarta Hussaina. Shekaru uku da rasuwan matarsa kafin Mahaifinsa ya haɗa shi aure da Yahanasu wacce take marainiya a lokacin. Lokacin daya auri Zainabu yaran Yaha uku ne duka mata. Aisha da suke kira da Ummi sai Fatima sai kuma Hindatu daga baya ne ta haifi Musa bayan ita Zainabun ta haifi ɗanta na fari wato Muhammad Habibu sai Lukman da suke kira da Gwani sai autanta Aliyu. Sanda Zainabu ta tare ko wata huɗu batayi ba Malam Nuhu ya sata a makarantar kurame inda ake koya musu rubutu da karatu da kuma sana'o'i. A nan ne ta koyi ɗinki da saƙa. Asiya Shahidah ta taso ne tsakanin gidan Gwani da Inna Talatu bata zuwa gidan Mahaifinta sai dai idan shine yazo ya ɗauketa dan Allah ya saka masa ƙaunar Asiya. Saboda ita ne ma ya dage da zuwa gidan Gwani duk bayan kwana biyu maimakon da da sai yai sati biyu uku bai leƙa mahaifin nasa ba. A duk lokacin da ya zo idan yaji Gwani yana yabon kwanyar Asiya akan tana ɗaukan karatu sai ya dinga jin wani nishaɗi a tattare da shi. Duk yaransa a wajen Gwani suke zuwa ɗaukan karatu tun suna shekara biyu da rabi yake sawa a tisa ƙeyarsu wajen Mahaifinsa. Kuma duk cikinsu idan ka cire babban ɗansa Nafi'u daya rasu babu wanda ya taɓa ji Gwani ya yabi kaifin ƙwaƙwalwarsa kaman yadda yake yabon Asiya. Wani lokaci idan yazo sai ya ce Asiya ta ɗauko Allonta ta biya masa karatu ya ji. Duk da idan ka cire karatun sallah shi kam Jahilin Ƙur'ani ne hakan bai hana shi jin daɗin karatun Asiya ba. Allah ya buɗa masa arziƙi amma hakan bai hana wani lokacin ya ji kishin ƙannensa Malam da Zakari ba, wanda suma Malamai ne yanzu domin sunyi karatu mai zurfi. Dake idan Asiya tazo gidan Ale Faruƙ damunsu take da rigima shiyasa basa ma son zuwanta gidan musamman Fulani da Tabawa. Bata taɓa yin shiru idan aka gaya mata magana. Bayan Gambo tayi yayinta ta ƙare, lokacin maganinta ya dena ci, a lokacin ne kuma Ale Faruƙ ya lalubo musu wata mata mai suna Yawo. Daga chan wani ƙauye ta fito wanda ake yawan cewa ƙauyen akwai mayu a wajen. Ba budurwa bace dan aurenta bakwai amma tacewa Ale Faruƙ aurenta biyu. A rumfarsa suka haɗu ta zo siyayya, farar fatarta ya ja hankalinsa. Sati biyu da tarewarta Ale Faruƙ ya fara ciwo. Idan ya tashi da safe sai yaji duk jikinsa na masa ciwo musamman hannu da ƙafafuwansa. Tun yana iya fita kasuwa har ya koma zaman gida saboda ko bai fita ba haka kawai jikinsa sai ya dinga ciwo. Ya je Asibiti an bashi maganin ciwon jiki amma duk da haka abun ba sauƙi. Ana hakane kuwa biyu daga cikin 'ya'yansa suka rasu mace da namiji dukkansu 'yan ƙasa da shekaru goma. Abin duniya yabi ya isheshi, rashin fita kasuwa kamar yadda ya saba duk ya saka shi damuwa dan gani yake baza a kula masa da dukiyarsa kamar yadda ya kamata ba... A gindin wata bishiyar giginya wasu mata guda uku suka haɗu a talatainin dare. Cikon ta huɗunsu ta taho tana basu haƙuri akan dalilin rashin zuwanta taron nasu da wuri. "Ni kam Yawo keda kike da nisa ya akayi kika rigani zuwa?" Wacce ta zo yanzu tayi tambayar tana kallon farar cikinsu wacce duk da kasancewar dare ne sosai farin fiskarta na haskawa. Yawo tayi dariya tace "ai dokina shegen gudu gareshi. Gashi chan na ɗaure shi a wancan bishiyar" Matar ta juya ta kalli inda Yawo ta nuna mata sannan ta ƙyaƙyale da dariya tace "ashe zaki bani aronsa idan zan je taron mutanenmu da za ayi na ƙasa" "A ina za ayi taron?" Wata tsohuwa tukuf a cikinsu ta tambaya. "Wancan shekaran anyi a Kaduna ne amma wannnan shekaran a Ogbomosho za ayi" "Kai yayi nisa ba zan je ba" tsohuwar ta faɗa tana lashe baki ganin naman da aka kawo musu wacce jaririyar Gambo ce da ko wata bata cika ba. "Kai! Yawo gaskiya aurenki da Ale Faruƙ akwai daɗi. Kullum cikin ƙoshi muke" Yawo ta baza haƙora tana dariya tace " nan gaba naman wancan 'yarsa daya fi so zan kawo, nasan ba ƙaramin daɗi za ta yi ba" Dukkansu huɗun suka bushe da dariya marar daɗin ji. Washegari Asma'u 'yar Gambo ta rasu. 'Yarta ta biyu kenan a gidan Ale. Da yamma Mama da Asiya da matar Baffa Malam suka zo ta'aziyya gidan. Suna falon Gambo Yawo ta shigo gaishe da Mama. Suna haɗa ido da Asiya ta fara mata murmushi. Asiya ta ce " Maman Rabi'u ga wadda ta cinye miki Asma'u" gaba ɗaya sai suka maida dubansu ga Yawo da Asiyar ke nunawa. Yawo ta kama salati tana salallami harda fashewa da kuka. Mama ta kwaɓi bakin Asiya tace "bana son shegen surutu Asiya. A ina kika ji wannan banzar maganar?" Asiya ta tura baki tace "in ta cinye duka 'ya'yan Baba ai shikenan, nikam bazata iya cinyeni ba" Mama ta ranƙwasheta tace ta rufe musu baki. Sannan ta shiga bawa Yawo haƙuri. Maganar ta tsaya a ran Mama shiyasa da suka koma gida tace zata faɗawa Gwani idan ya dawo daga tafiya. Ranan da dokin Yawo ya je Ogbomosho washegari Ale Faruƙ ya tashi ko yatsarsa baya iya ɗagawa. Yadda ka san wanda jikinsa ya shanye haka yake kwance a sanƙare ko'ina yana masa ciwo kamar anyita dukansa da taɓarya. Bayan kwana huɗu da rasuwan Asma'u Gwani ya dawo. Da ya huta Mama ta gaya masa abinda Asiya ta faɗa, tareda faɗa masa cewa ranan da suka dawo, da dare Asiya ta dinga sunbatu cikin baccinta tana cewa babu wanda zai iya cin namanta. Gwani ya ɗau Allo ya rubuta ayoyin shifa ya wanke da ruwan zamzam ya zuba a gora ya miƙe da kansa ya wuce gidan ɗansa. Lokacin daya isa gidan kai tsaye sashin Ale ya shiga inda Ale Faruƙ ke shimfiɗe a kan tabarma a tsakiyar falonsa. Fulani da ɗansa Bello wanda shine babban ɗansa namiji ya gani a kusa dashi suna ƙoƙarin bashi kunu. "Ya jikin nasa?" "Yau kam Malam ko hannunsa ya kasa ɗagawa" Fulani ta amsa cike da tausayawa mijinta wanda duk yadda yake tana sonsa a haka. Bello ya taimakawa Gwani wajen bawa Ale ruwan rubutu. Bayan ya sha, Gwani ya karanto addu'o'i ya tofa a hannunsa ya shafa masa a goshi, hannu da ƙafafuwansa. Da yamma ma yazo yai masa haka, washegari ma ya sake zuwa yai masa haka safe da yamma. A rana ta uku kuwa da Yawo ta tashi hawa doki zata je majalisansu doki ya ƙi tashi, tayi tayi amma inaa ya ƙi ko matsawa gefe hakan ya sa ta haƙura da ɗaukansa. Da ta isa majalisa ta kai ƙorafin abinda ya faru wajen shugabarsu tsohuwa Ayya. Ayya tace ai mahaifin Ale Faruƙ ne ke shirin ɓata musu aiki kada ta bari ya sake zuwa wajensa. Naman Asiya ma da suke son ɗauka shima abin ya gagara shiyasa suka koma kan ƙanwarta Farida 'yar Halime wacce nan da kwana uku zasuyi abincin dare da ita. Washegari ya kama kwanan Yawo dan haka ita ce ta kasa ta tsare a gefen Ale Faruƙ. Ƙarfe tara na safe sai ga Gwani ya zo yiwa Ale addu'a. Yawo ta garƙame falon da kwaɗo ta zauna a dakalin ƙofar shiga falon, yana zuwa tace masa Ale na barci yace kar a tashe shi. Gwani yace ta buɗe masa ƙofa ya shiga ya dubashi ba zai tashe shi ba. Yawo ta tura baki tace sai dai ya dawo wani lokacin. Yadda ta dage ba zai shiga ba ya sa ya juya ya tafi, cikin ransa yana tunanin tabbas maganar Asiya gaskiya ce. Da yamma tareda ɗansa Malam suka zo, nan ma a ƙofar falon suka tarar da Yawo tana zaune daram kamar da safe. Wannan karan sai da Iyani da Fulani suka leƙo suna cewa Yawo ta buɗewa Gwani ƙofa domin tunda ya fara yiwa Ale addu'a suka fara ganin sauƙi. Tana cikin magana Malam ya fito da wata dorina ya tsura mata a jiki yana faɗin "ƙarya kike la'ananniya, ƙarya kike Mayya" Yawo ta saka ihu tana kuka. "Kin cinye masa 'ya'ya za ki cinyeshi ko? Asirinki ya tonu" ya cigaba da zaneta. Ƙoƙarin gudu take amma Gwani da sauran Matan da yaran Ale kusan biyar sun tare wajen sun hanata gudu. Bello ma daya shigo bada jimawa ba itace ya sunkuco ya shiga taya Baffan nasa dukan Yawo. Sai da Gwani ya tsaida su kafin suka dena dukanta. Ya tambayeta ta faɗa musu gaskiya. Yawo baki da hanci duk jini ta fara cewa ta tuba a yafeta. Baffa Malam ya daka mata tsawa hakan yasa ta fara faɗan abinda tayi tace da gaske ne ita ta cinye yara uku a gidan amma Ale Faruƙ doki take da shi bawai cinyeshi zata yi ba. Tabawa da ke gefe tayo kan Yawo da gudu ta fara dukanta tana yaguni. "Shegiya ɗan nawa shine doki, ɗan nawa kika mayar doki" Da ƙyar Baffa Malam da Bello suka janyeta akan Yawo. Gwani yace su ɗaureta kar wanda ya sake taɓata amma ina, samarin anguwa sukace basu yarda ba aka fita da Yawo ana bugu. Lokacin data suma aka fara ƙoƙarin ƙonata saiga wata tsohuwa ta ratsa cikin mutane ta zo ta taɓa Yawo shikenan ita da Yawo suka ɓace. Mutane kowa yai ta kansa sai 'yan tsiraru da suke da ƙarfin zuciya suka tsaya suna ihu suna faɗin duk ranan da suka kama Yawo ko wani maye ko mayya a garin ƙonashi za suyi. Kwana uku da aka cigaba da yiwa Ale Faruƙ addu'a ya warke sarai kamar ba shi ba. Lokacin da yaji labarin cewa Asiya ce ta fara gane cewa Yawo Mayya ce hakan ya sa shi dagewa Gwani akan sai dai Asiya ta dawo gidansa da zama. Gwani bai musa ba tunda dai 'yarsa ce ya dai jaddada masa akan koyaushe Asiya ta dinga zuwa karatu. Bayan Yawo sai da Ale Faruƙ yai shekaru huɗu kafin ya ƙara wani auren. *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 11 Dr Saifuddeen Sa'ad Kachallah saurayi ne mai kimanin shekaru ashirin da bakwai a duniya. A rana ta farko daya shigo jami'ar Congo a matsayin malami a ranan ƙaddararsa ta haɗu da ta Misturah Sulayman Adeyemi. Da ya gama duk abinda zaiyi a ranan sai ya tattara kayansa ya wuce wajen motarsa. Ishirwa yake ji hakan ya sa shi wucewa wani kiosk da ake saida kayan masarufi da ke kusa da shi. Yace da yarinyar da ke tsaye a shagon ta bashi ruwa mai sanyi na gora, yarinyar tace babu sai dai na leda. Saifddeen ya ɗan gyatsine fiska sannan ya ce "ok kawo" Yarinyar ta miƙa masa ruwa guda biyu a leda, lokacin ne kuma wata budurwa baƙa ta iso kiosk ɗin ta ajiye litattafanta akan kantan wajen tana huci tace "Abeg Bisi give me cold water" Ya kalli budurwar da tayi maganar. Baƙa ce amma ba sosai ba tana da ɗan jiki amma ba zaka kirata ƙatuwa ba. Ɗan ƙaramin mayafin data yafa ta cire ta fara fiffita dashi saboda yadda take haɗa uban zufa, da gani ta sha tafiya cikin rana. "Sista Mistura e take ye easy" "Omo iya ko easy oo, Professor Badmus fe pawa, wahala re ti po" Saifuddeen ya kauda kansa daga kallon budurwar ya miƙawa mai shagon naira ɗari biyu. "Ha! Oga i no get change oo" Ta kalli budurwar tace " abi Sista Misturah e ni change ke bami se?" "E lo?" "200" "Haa! Kilo ra?" "Omi meji" Saifuddeen ya katse hiransu da cewa " i'll come back for it tomorrow" "Ok Sir" Har ya juya ya fara tafiya sai ya dawo. Ba lallai ya tuna da chanjin ba gara kawai ya sayi wani abin ya bar mata sauran. Bayan ta miƙa masa coke mai sanyi daya buƙata yace ya yafe mata sauran chanjin. "Ode ni Bobo yi" Budurwar ta furta a fili. Suna haɗa ido da Saifuddeen tayi saurin kauda kai dan gani tayi kaman ya ji abinda tace. Bayan tafiyar Saifuddeen ita da mai shagon suka yi gulmar shi inda Baƙar budurwar ke cewa Saifuddeen irin sabbin ɗaliban nan ne masu rawan kai da burga. Kwanansa biyu da fara aiki inda ya ke ɗaukan ɗalibai 'yan aji uku da 'yan aji huɗu sai kuma masu yin masters. Bai saba cin abinci a waje ba amma takanas Dr Hassan da office ɗinsu ke kusa yazo ya ja shi akan suje cin abinci. Canteen ɗin da suka je na wasu yarabawa ne, daga bakin wajen an rubuta *Iya Bola's Food* Ba laifi wajen ya haɗu akwai tsafta amma duk da haka dan ta Saifuddeen ne ba zai ci abinci a wajen ba. Bayan an serving ɗinsu abinci suna ci ya hango baƙar yarinyar ranan tana serving wasu abinci. Dr Hassan ne ya fara cinyewa inda ya ce da Saifuddeen zai wuce aji yanada ajin ƙarfe biyu. A lokacin bai san halin Dr Hassan bane ya jawoka cin abinci yatashi ya bar ka ka biya masa. Saifuddeen ya cigaba da cin abinci ahankali, lokacin daya gama ya zauna saboda wajen da ake biyan kuɗin a cike yake da ɗalibai, gaskiya wajen ana ciniki. Yana zaune baƙar yarinyar tazo kwashe masa kwanuka. "How much?" Ya faɗa a hankali "400" Arhan abincin da ya ji ya sashi ce mata na duka biyu yake nufi. Ta kalli ƙwayar idonsa sannan ta kauda kai tace " still 400" Chanjin naira ɗari zata bashi amma yace ya yafe mata ya miƙe ya bar wajen ya bar Mistura da buɗe baki. A ranan daya sake zuwa wajen shi ɗaya ya zo Mistura na ganinsa ta zo wajen da sauri "Mr keep the change what can i serve you?" " jolof rice and fish" "With Dodo abi with chips?" "What's Dodo?" Ya faɗa bil haƙƙi saboda bai sani ba. Baƙar yarinyar ta ƙyalƙyale da dariya harda kama baki. "Oga Ajebo, dodo is fried plaintain" " Ok with Doodoo" ya ja sunan kamar dodon tatsuniya. Lokacin da ta kawo abincin ta tambayeshi ko a aji ɗaya yake sannan a wani faculty. Jin yace shi ba ɗan aji ɗaya bane ya sa ta tambayi ajinshi. Yai shiru yana kallonta saboda kamar kowa itama tunanin ɗalibi take masa. Ko ranan daya fara shiga aji ma ɗalibansa kallon raini suka masa sai da suka ji yace shi zai ɗaukesu darasi sannan jikinsu yai sanyi. Lokacin da ta kawo masa abinci ta tambayeshi sunansa. Ya amsa da cewa "Saifuddeen" "Misturah, 400 lvl Economics. Tunda ka ƙi faɗamin wani aji kake, i can bet cewa ba zaka wuce 100lvl zuwa 200lvl ba" "Miyasa kika ce haka?" "Kana yi kaman wani JJC" Saifuddeen yai murmushi ga mamakinsa sai ya ji tace " kana da kyau and i love your smile" "Misturah...Misturah..." "Maaa" ta amsa tana barin wajensa da sauri. Cikin sati biyu da yai yana zuwa wajen sai gashi ya san komai nata. Shi kansa ya rasa dalilin daya sa ya zama regular a wajen kuma in har bata wajen ba zai ci abinci ba sai ya tabbatar tana nan kuma ita tayi serving ɗinsa. Iya Bola mai saida abincin Ƙanwar Mahaifin Misturah ce kuma a wajenta ta taso tun tana shekara takwas. Ita ce ta ɗauki ɗauyin karatunta har yanzu da take final year. Bai sanar da ita ko shi waye ba saboda ya sani yadda ta sake jiki da shi idan har ta san lecturer ne ba zata kula shi ba. Da bakinta tace masa bata mu'amala da malamai. A sati na biyar da fara koyarwarsa aka bashi ajinsu Misturah. Farfesan daya ke ɗaukansu ya tafi wani conference na sati uku a ƙasar America. Dr Kachallah ɗalibai da Malamai ke kiransa kuma sunan ba baƙo bane a wajen Misturah dan taji labarin tsaurinsa a wajen ɗalibai 'yan Pol science. Lokacin da course rep ɗinsu ya gaya musu cewa Dr Kachallah ne zai ɗauki darasin Prof Badmus ta ji daɗi saboda ta tsani Prof Badmus, kowa ma a ajin ya tsaneshi domin yadda fiskarsa ke da muni haka zuciyarsa take. Yanada tsauri, baya sassautawa ɗalibai ko kaɗan gashi ba wai ya iya koyarwa bane dan ba a gane darasinsa. Abinda Misturah ta sani gameda Dr Kachallah shine shi ɗin sabon Lecturer ne kuma yaro, dan sun ji ƙishin-ƙishin ɗin ko shekaru talatin bai kai ba sai dai akwai kwanya. Lokacin daya shigo tana ƙoƙarin karanta wani journal ne da ya ke da nasaba da project topic ɗinta. Nitsuwar da ajin yai ya sa ta ɗago idonta car acikin na Saifuddeen da ke tsaye a wajen podium na ajin. Da muryarsa mai sanyi yai bayani akan shi zai cigaba da ɗaukansu darasin Prof Badmus kafin ya dawo. Sunan daya rubuta akan allo ta ƙurawa ido, da manyan baƙi ya rubuta *SAIFUDDEEN SA'AD KACHALLAH* Sun gane darasin da yai musu sosai, sai dai matsalarsa ɗaya wato yawan jefo tambaya idan yana bayani. Haka kawai sai ya nunaka ya tambayeka wani abu sannan baka isa kace baka sani ba dan shi a ajinsa babu kalmar i don't know. Ya fi so ko baka sani ba ka yi abinda bature ke cewa attempt, dole sai ka faɗi amsar a naka fahimtar. Misturah kam kasa nitsuwa tayi dan gani take idonsa na kanta ko kuma idan yai tambaya ya nuna mutum yace YOU gaba ɗaya sai ta ji ƙirjinta ya buga dan gani take kamar ita zaice. Basu taɓa fahimtar darasin Prof Badmus irin na yau ba. Daga su 'yan Economics har 'yan Political science da suke yin darasin tare kowa ya yarda akwai banbanci a koyarwar Dr Kachallah data Prof Badmus nesa ba kusa ba. Daya gama darasi ya bada damar ayi tambaya yawanci matan ajin suka dinga ɗaga hannu suna masa tambayar shirme dan dai kawai ya kulasu. Kamar kullum bayan yayi sallar Azahar Iya Bola's food ya wuce ya samu waje ya zauna yana jiran Misturah sai dai ko mai kama da ita bai gani ba. Kwana uku ya jera yana zuwa wajen baya ganinta. A rana ta huɗu sai ya zo da wuri ya kuwa ci sa'a tana nan. "Sir mi za a kawo maka?" Tayi tambayar kamar a yau ɗin ne ta fara ganinsa. "Misturah ya kamata muyi magana..." "Munada Semo, sakwara, Amala, Eba, white rice, jollof rice..." Miƙewa yai ya bar mata wajen, ta bi bayansa da kallo cike da mamaki. Daga ranan bata sake ganinsa ba dama gudunsa ta fara yanzu kuma sai ta fara dakon zuwansa amma shiru. Idan yazo ajinsu kuwa ko gefen da take baya kallo hakan yai matuƙar damunta. Wasa wasa gaba ɗaya ta rasa nitsuwarta. Bayan sati ɗaya da yin hakan ta kasa ɗaukan shirunsa, ta kasa ɗaukan sharewar da ya ke mata. Ta nemi inda office ɗinsa yake ta je ta sameshi dai dai zai fita ya tafi gida. "Sir kayi haƙuri ranan..." "No no no, ba laifin ki bane. I should have told you the truth tun ranan da kika tambayeni a wani aji nake" "Kenan baka fushi dani?" Sai da ya ɗau jakarsa sannan ya ce " na baki space ne saboda kince bakya son kowacce mu'amala da malaminki. A da ni ba malaminki bane amma yanzu..." Sai bayan sati huɗu daf za a fara exams da Prof Badmus ya dawo ya karɓi ajinsa tukunna Misturah ta sake jiki da Dr S S Kachallah. A lokacin da su kayi hutu lokaci zuwa lokaci ya kan je gidansu. Tun Iya Bola na mata faɗa akan mu'amalarta da Saifuddeen har tazo ta haƙura tunda ta nuna mata cewa ba soyayya suke ba sannan kamalar Saifuddeen ya sa Iya Bola ta fara yarda da shi. Gaba ɗaya kasancewarsa ɗan babban gida bai sa mishi girman kai ba. A wajen Misturah ne Saifuddeen ke iya sakewa ya faɗi son ransa yai abinda ya ga dama. A wajenta ya koyi cin abincin da yake da nasaba da ƙabilun kudancin ƙasar. A wajenta yake iya sakewa ya fayyace mata damuwar ransa, a wajenta ya samu ƙwarin gwiwar fitar da rubutunsa na waƙoƙi wanda ada sai dai ya rubuta ya zuba su a wardrobe. Dalilinta ya wallafa littafin rubutattun waƙoƙi da pen name Jabir Al Jabir yayi amfani da sunan na shekaru biyu kafin daga baya da suka rabu da Mistura ya koma amfani da suna KaSaSa. Sai da Misturah ta gama aji huɗu tana jiran sakamako kafin Saifuddeen ya bayyana mata cewa yana sonta. Faɗuwa ne tazo dai dai da zama dan a wajen Misturah kam tun kafin ta san shi malami ne soyayyar Saifuddeen ya shiga zuciyarta. Duk da ya san ba lallai bane a amince masa ya aureta kasancewa shi ba Bayarabe bane amma kuma ya ɗaura aniyar sai inda ƙarfinsa ya ƙare akan neman auren Misturah. Lokacin daya faɗawa Sikiru mijin Iya Bola cewa yana son ya turo magabatansa bai yi mamaki ba da yace masa sai ya nemi izinin 'yanuwansa a chan gida. Letter Sikiru ya fara turawa chan garinsu ya musu bayanin waye Saifuddeen amma da aka dawo da amsa sai ya ga cewa wai basu amince Misturah ta auri bahaushe ba. Mamaki ya kamashi dan da alama basu fahimci wani Kachallan yake nufi ba. Haka ya shirya ya wuce garin Akure. Lokacin daya fayyace musu asalin wanene Saifuddeen Kachallah mantawa sukayi da batun kudu da arewa suka ringa kiran ai Nigeria ɗaya ce kuma ya kamata a daina nuna banbance-banbancen ƙabila ko yanki. Cikin kashi ɗari na danginsu kashi tamanin da biyar sun amince da auren bayan sun ji kuɗi da mulkin gidan da Saifuddeen Kachallah ya fito. Bayan Saifuddeen ya samu amsar daya ke so daga wajen Sikiru sai ya gabatar da buƙatarsa na son auren Misturah wajen Alhaji Sani. Ga mamakinsa sai yace masa ko zai auri wata mace to bayan ya auri Bilkisu ne, dama jira yake ta ƙarisa jarrabawarta na ƙarshe ta dawo ya haɗasu aure. Ba zai taɓa iya yiwa Baba musu ba shiyasa ya amince da hakan. Sun taso da Bilkisu kuma tsakaninsu akwai jituwa sai dai bai taɓa sawa ransa zai iya auren mai irin halayen Bilkisu ba. Girman kai, Shagwaɓa, kasala, zafin rai da ma ra'ayin ƙin talaka sune halayenta da suka sha banban da tashi. A matsayin 'yar uwa yana sonta amma a matsayin matar aure gaskiya... Lokacin daya faɗawa Misturah hukuncin da aka yanke masa ranta ya ɓaci sosai har take ce masa dama halinsu kenan 'yan arewa, gashi tun bai aureta ba yana mata maganar kishiya. Sai dai soyayyar Saifuddeen ta rufe mata ido shiyasa ta amince zata zo gidansa a matarsa ta biyu. Wata ɗaya da rabi Bilkisu ta shigo Nigeria, tazo ta tarar da tsarin da aka shirya mata. Za ayi bikinta da Saifuddeen nan da watanni biyu sannan za ayi na Misturah da Saifuddeen wata bakwai bayan aurensu lokacin Misturah ta gama bautan ƙasa. Da soyayyar Saifuddeen ta taso kuma tun kafin ta tafi jami'a ta riga ta sanar da mahaifinta cewa idan ya haɗa aurenta da wani ba Saifuddeen ba bazata aure shi ba. Lokacin data tsara rayuwar aurenta bata tsara cewa za tayi tareda wata bare ba. Ita da Saifuddeen za su gina rayuwarsu kuma babu wacce ta isa ta shiga tsakaninsu. Sati biyu bayan ta iso Nigeria tasa aka fara yiwa Misturah transfer daga inda take bautar ƙasa kusa da Jahar Congo zuwa chan kudu. Bata taɓa ganin Misturah ba sai ranan data je gidansu ta kai mata letan relocation ɗinta tareda kashedin duk ranan data sake shigowa Congo saita sa an yankata sannan idan har bata sa an kashe maganar aurensu da Saifuddeen ba zata sa a kashe Iya Bola da iyalenta, ba nan ta tsaya ba har Akure tace za ta je tasa a ƙona family house ɗinsu da duk wanda ke ciki. Dama anacewa Yarabawa da tsoro. Tuni Iya Bola da Sikiru suka shiga bata haƙuri yayinda Misturah ta riƙe takardan da aka miƙa mata tana furzar da numfashi mai zafi... Ƙila Saifuddeen ba zai taɓa sanin dalilin tafiyar Misturah ba domin ranan daya je hira gidansu wasiƙarta Iya Bola ta bashi inda a wasiƙar Misturah ta bayyana masa cewa ba zata iya zuwa gidansa a ta biyu ba. Daren ranan duk yadda ya daure sai da yai hawaye saboda Misturah itace macen daya fara so a rayuwarsa. Bai nemeta ba kuma har bayan ya auri Bilkisu bai nemi inda Misturah take ba saboda shi mutum ne da baya son takurawa ɗanuwansa. Duk da yana sonta sosai amma hakan ba zai sa shi tursasa mata ba. Sai da shekaru suka ja kafin watarana daya haɗu da wata ƙawar Misturah ta gaya masa cewa Misturah tayi aure a Lagos. *** Tarihin gidan Kachallah ya samo asali daga ainihin wanɗanda suka kafa garin Congo. Lokacin yaƙe-yaƙe da Jihadi duka sunan gidan na nan. Sunada alaƙa mai ƙarfi da gidan Sarauta dan ko yau wani ya fito daga tsatson Kachallah yace zai zama Sarki babu wanda zai ja dashi dan kusan shekaru ɗari uku da suka wuce anyi Sarki Kachallah a garin wanda yai mulki na shekaru shabakwai. Alhaji Habu Kachallah tareda matarsa Khadija wacce yanzu 'ya'ya da jikoki ke kiranta da Hajiya Dadda sun haifi 'ya'ya shida tare. Mariya Kachallah itace ta farko wacce yanzu ita da mijinta da 'ya'yanta suke zaune a Saudiyya, dan aƙalla yanzu zata kai shekaru arba'in a Saudiyya. Na biyun shine Sani Kachallah sannan Fatima Kachallah wacce ta jima da rasuwa amma ta bar 'ya'ya uku a duniya. Aminatu Kachallah wacce kowa ke kira da Hajiya Umma ta shekara arba'in da biyu da mijinta kafin rasuwarsa kuma Allah bai bata haihuwa ba sai dai ita ta raini 'ya'yan Yayarta Fatima wato Aisha, Abdullahi da Umar. Na biyar ɗinsu shine Sa'ad Kachallah sannan Hauwa Kachallah. Alhaji Sani Kachallah ya auri mata biyu. Ta farkon Hajiya Maryam ta rasu ta barshi da 'ya'ya biyu Fatima Batula da Aminatu. Yayinda matarsa ta yanzu Hajiya Aisha ta haifa masa Rufaidah, Bilkisu, Saudah, Khadija da kuma Halima. Sa'ad Kachallah a jami'ar Dares Salaam ta ƙasar Tanzania ya haɗu da Aysha Ali Jallow lokacin yaje wani conference ita kuma tana ajin ƙarshe a jami'ar. A wajen conference ɗin sau uku tana ɗaga hannu tayi tambaya hakan ne ya saka ya shaida fiskarta har yaji ta burgeshi. Daga baya da aka gama taron ya nemi sanin ko ita wacece kuma bai sha wahala ba saboda ita ɗin ɗaliba ce mai ƙwazo da tayi suna a jami'ar. Kaman wasa ya mata tayin soyayyarsa ranan farko daya je wajenta, amsar da zai fito daga bakinta shine " I love Nigeria" daga haka bata ƙara da cewa komai ba hakan ya sashi tunanin ko bai mata bane. Wata ɗaya da komawarsa London ya samu wasiƙarta inda take cewa 'yar fulanin Gambia zata je gida idan da gaske yake ya je ya samu mahaifinta amma ya shirya yaƙi da danginta duk da ma ta san 'yan Nigeria jarumai ne. Ousmana Jallow babban mutum ne a ƙasar Gambia, Shanu da Raƙuma da Allah ya azurta masa shi kansa ba zai iya lissafta adadinsu ba. Bafulatani ne mai riƙo da al'ada fiyema da addini wani lokaci. 'Ya'yansa uku ne maza Aodullahe Jallow, muhammadou Jallow da kuma Ali Jallow. Gidansa ba a auren bare hakan ya sa yisu-yisu fulanin yankin kawai suke aure. Fulanin Senegal, Cameroon, Niger ko Nigeria duk bare ne a wajensa. ya riga ya shirya haɗa auren jikarsa Aysha da kuma Boubacar ɗan Aodullahe Jallow, jira kawai yake ta ƙarisa bokon da ubanta ya sakata dole tayi sannan ayi biki. Fiqhu da psychology take karanta amma Fiqhun kawai aka gayawa Alhaji Ousmana shiyasa ya amince da karatun ba dan ya so ba sai dan yana son Ali sosai. Yaƙi ne kawai bai tashi ba lokacin da magabatan Sa'ad Kachallah suka zo neman auren Aysha Jallow. Sannan ita Ayshar ta nuna Sa'ad take so Mahaifinta kuma ya goya mata baya tunda a cewarsa bai san da maganar za a haɗa 'yarsa da Boubacar ba. Cikin 'ya'yan Ousmana Jallow Ali ne yai boko mai zurfi dan alokacin ma ya haɗa Phd ɗinsa a ɓangaren Economics. Abu dai ta kai ta kawo saida Ousmana Jallow yace ya cire hannunsa a lamarin Ali da iyalinsa, yayi duk abinda ya so. Ali Jallow riƙaƙƙen ɗan boko ne da ko kaɗan baya so a tauye hakkin wani, shiyasa ma da ya nuna sai tilon 'yarsa tayi boko bai ji shayin ko mahaifinsa zai yarda ko ba zai yarda ba. 'Ya'ya biyu ya haifa, namijin ƙanin Aysha ya rasu tun yana watanni kaɗan da haihuwa. Ali bai damu ba da 'yan uwansa suka ja baya da shi. Sanda magabatan Sa'ad suka dawo ya sa bikinsu nanda watanni huɗu lokacin Aysha ta gama karatunta. Lokacin da akayi bikin abokanansa da 'yanuwan matarsa ne kawai suka shaida amma nashi 'yanuwan ba wanda yazo. Ousmana Jallow ya yi alƙawarin fishi da duk wanda yaje bikin. Haka akayi biki Amarya da angonta suka wuce Nigeria. Bikin nasu da watanni shida Ali Jallow da matarsa sukayi hatsarin jirgin sama lokacin zasu koma ƙasar America saboda aiki da aka bashi a United Nation (majalisar ɗinke duniya). Labarin yazo wa Aysha daidai tana laulayi mai tsanani hakan yasa ta birkice sosai dan soyayyar uba da 'ya dake tsakaninta da mahaifinta ba kaman na sauran 'yanuwan mahaifinta Fulani bane. Mahaifinta zai zauna da ita suyi taɗi, ya saurari matsalarta ya bata shawara ba wai ya tursasa ta ba. Mahaifinta tamkar babban abokinta ne dan shaƙuwarsu da shi ta fi ta mahaifiyarta. Kaman baki wata biyu bayan mutuwar Ali Jallow da matarsa Sa'ad Kachallah yai hatsari ya rasu yana hanyarsa ta zuwa airport zai je London. Wannan mutuwar ta girgiza Aysha matuƙa dan sai data koma tamkar wata zararriya. Cikinta na wata shida alokacin amma har ranan data haihu cikin ciwo take. Lokacin da ake nema mata magani ne wani malami yace ko kaɗan kar a bari ta bar gidan dan sammu ne a kanta, idan suka bari ta fita ba zasu sake ganinta ba. Kullum cikin tsaronta ake kuma Alhamdulillahi maganin da ake bata ya sa bata samu ta gudun ba. Ba ayi sunan Saifuddeen ba ta rasu hakan yasa Saifuddeen Kachallah bai san iyayensa ba sai a hoto da kuma bidiyon da akayi na biki dana wasu tarurruka da mahaifinsa ya halarta lokacin yana raye. Sunyi mamaki matuƙa da babu ko ɗaya cikin 'yanuwan Aysha da ya zo bayan an aika musu rasuwarta, infact sharesu suka yi kamar ba alaƙar dake tsakaninsu. A ɓangaren Boubacar Jallow kuma ya kaɗu matuƙa da ya ji mutuwar Aysha. Shi ya saka a kashe Sa'ad sannan a hana Aysha zaman Nigeria, sannan shi ya sanar da Ousmana Jallow cewa Aysha da ɗan data haifa sun mutu dan shine ya karɓo wasiƙar da aka rubuto. Kasancewar suna zargin sammun da aka yiwa Aysha daga 'yanuwanta ne shiyasa tun Alhaji Habu Kachallah na da rai ya hana a kai Saifudden wajen 'yanuwan mahaifiyarsa. Rashin haihuwar ɗa namiji ya saka Alhaji Sani Kachallah ya ɗaura duk wata soyayyarsa akan Saifuddeen. Shi ya zaɓa mishi makarantar da zai je da abinda zai karanta wato political science inda bayan Saifuddeen yaje chan ne ya ɗauki major biyu wato Communication and Political Science a postgrad kuma yai History and International relation. Saifuddeen ya fara koyarwa a jami'ar Congo har ya kai matsayin Professor yana shekaru talatin da biyar a duniya. Yayi Rector na Congo Polytechnic na shekara ɗaya da rabi har lokacin kuma yana koyarwa a Jami'a kafin Alhaji Sani yasa a bashi Kwamishinan ayyuka na jahar daga nan kuma ya jawo shi cikin siyasa tsundum inda rana tsaka yace masa "congratulations Saifu, kaine mataimakin Gwamna na jihar nan" ya yi maganar tun ma ba a fara maganar zaɓe ba sai gashi watanni kaɗan bayan haka Saifuddeen Kachallah ya tsinci kansa wajen yawon kamfen har kuma a kwana a tashi ya tsinci kansa a mataimakin Gwamna, sannan yanzu alƙalamin ƙaddararsa ta juya, ya wayi gari shine Gwamnan jihar Congo... *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 12 *GUZURIN TAFIYA* "Asiya....Asiya" Juyowa tayi ta kalli Mama ba tareda ta amsa mata ba. "Ba za ki je ki gaida Baban naki ba. Sau biyu yana aikowa wai kije" "Mama zan je gobe, na gaji" "Ba abinda kika yi tunda kika zo gidan nan sai kuka. An gaya miki kuka na maganin matsala ne. Tashi maza ki shirya ki je ki gaishe shi kafin Magariba ta ƙariso" "Mama ba zan iya fita yanzu ba. Dan Allah ki bari sai gobe" "To ki kirashi ki gaya masa zaki je goben" Hannu data ɗaga zata jawo jakarta sai data rintse ido saboda yadda zuciyarta ke sukan ƙirjinta. Missed calls ta gani dayawa a wayar wanda na Ubayd ne yafi yawa. Tun isowarta ta turawa Umma text ta sa wayar a silent ta jefata cikin jaka. Numbar Ale ta kira taji shi a kashe, hakan ya mata daidai dan ba son magana da shi take ba. "Numbarsa a kashe take" ta faɗa da muryar da yafi kama da raɗa. "Ki tashi kiyi wanka kizo ki ci abinci. Haka kawai ki hana kanki sakewa saboda a kanki aka fara yaɗa jita-jita" "Tashi maza kin ji. Barin cewa Ladi ta ɗeba miki ruwan zafi" "Toh" *** "Sumayye, Sumayye" "Na'am Baba" "Uban me kike a ɗakin ne. Ki fito mu tafi ko na barki a nan" "Gani zuwa Baba" Minti ɗaya sai ga Sumayya ta fito daga ɗaki sanye da hijabi ruwan toka wanda saboda akwai duhu zaka ɗauka baƙi ne. Babu wuta shiyasa gidan ya ɗau duhu, wata da taurari kuma a daren kaman sunyi ƙaura. Wayar latsawa ce a hannunsa amma yana dannata da ƙarfi kaman wanda idan bai yi hakan ba ba za tayi aiki ba. "Baba gani" Ya ɗan yi murmushi saboda bazawararsa da suke chatting tace tana jiransa ya zo ya ga kwalliya. "Baba gani fa" "To fasa mun kunne Sumayye." Sumayya ta fara tura baki wanda ba dan dare bane kuma hankalin Ale na kan bazawararsa da ya gani. "Kin ɗauko kazar?" "Na ɗauka" Ficewa sukayi daga gidan dan yana sauri daga wajen Asiya zai wuce wajen masoyiyarsa Lubabatu. Cikin motarsa ƙirar peugeot 406 fara wacce aƙalla ta bawa shekaru shatakwas baya ya ɗau Sumayya suka wuce gidan Gwani wanda yanzu ƙannensa da iyalensu ke zaune a ciki. Masallaci ya fara tsayawa ya gaisa da Baffa Malam wanda ke koyarda ɗalibai karatu sannan ya wuce cikin gida ɗakin Mama. "Gashinan Anty Asiya Ale yace a kawo miki Kaza. Ni na soyata da kaina" "Ki ajiyeta Summy ba zan iya ci ba" "Dan Allah ki tashi ki ci" "Salamu Alaikum" "Amin Alaikas Salam. Bismillah" "Ina wuninku dai" "Lafiya, Sannu da zuwa Ale Faruƙ" Mama ta miƙe daga kujera ta koma bakin gado gefen Sumayya. Bayan sun gaisa da Mama sannan ya maida dubansa ga Asiya ya tambayeta ya hanya. Daga inda Asiya ke kwance ta amsa masa da lafiya. "Mama bata da lafiya ne? Ko za a kira Malam ya mata rubutu ko Asibiti zamu wuce?" yai maganar ba tareda ya tsaya ya ja numfashi ba. "Taƙi cin abinci ne fa tunda ta iso" "Wai haka Asiyata? Ke Sumayye baki bata kazarta bane?" "Baba gashi nan ita tace ba zata ci yanzu ba" "Ki daure dai ki ci kinji Asiya" Kaman gaisuwar ce kawai ta kawoshi sai kuma bayan shirun minti biyu ya fitar da abinda ke ransa. "Ke Sumayye ki bamu waje" Bayan Sumayya ta fita daga ɗakin, Mama ta fara ƙoƙarin miƙewa Ale yace ta zauna. "Asiyata ya jikin dai" bai jira amsarta ba ya cigaba. "Wai asalin kuɗin da akace 'yan adawan sun baki nawa ne? Tun da safe Malam Yusha'u da Alhaji Ɗansabo suke musu akan kuɗin nan, ni dai nace duk kuɗin Umaru Kwom ai ba zai baki ƙasa da Miliyan biyar ba ko?" Kaman wanda aka tsikara haka Asiya ta miƙe zaune tana yiwa mahaifinta kallon ƙurilla kamar yau ta fara ganinsa. "Ba sai kowa ya san asalin kuɗin ba Asiya. Kinga bikin ki ya kusa idan kika bani miliyan biyu ko uku a ciki zan juya miki shi kafin lokacin biki" Magana take son yi amma kukane ya ƙwace mata. Abin nata ya kai har mahaifinta ya tsaya musu da wasu akan kuɗin da ba ta san da su ba. Ba ma wannan ba, ashe har sunanta ya ɓaci a garin da take iƙirarin cewa nan ne asalinta. "Lah! Daga tambaya sai kuka. To kiyi haƙuri" "Ale Faruƙ inaga dai gara ka barta ta huta zuwa gobe sai kuyi maganar" Bai musawa Mama ba ya miƙe ya musu sai da safe ya fice daga ɗakin. Sumayya dake zaune a balbalin Baaba Ladi matar Baffa Malam tana ganin Ale ya fito daga ɗakin Mama tayi saurin miƙewa ta wuce ɗakin da sauri. Lokacin da ta shiga ɗakin kuka ta samu Asiya ke yi. Tayi saurin ƙarisawa wajenta ta shiga jijjigata tana bata haƙuri. *** "Shi Malam Nuhu mijin uwarta ne, shi kuma Ale Faruƙ Uban daya haifeta kenan. Inaga dai chan garin nasu kawai zamu je saboda ayi komai daga tushe" "Kana jina kuwa Saifu?" "Baba, Bilkisu..." Gwamna ya faɗa cikeda damuwa "Idan ta dawo ka turo min ita, za muyi magana" Daga haka bai sake cewa komai ba. Shima Gwamnan ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da taraddadin abinda zai faru idan Bilkisu ta dawo taji maganar auren daya ke shirin yi... A daren ranan Gwamna ya wuce gidan Abba. Tunda ya fara yiwa Abba bayani Abban bai ce uffan ba, kansa na ƙasa ya kasa ɗaga ido ya kalli Gwamna. Magana ne yayi a taƙaice amma nauyinta zai iya kaiwa nauyin treloli goma. Ba wai bai yarda da maganar Gwamna bane daya ce zai auri Asiya ne saboda ya kare rayuwarta. Girmansa ya wuce ya zo har gida ya masa ƙarya. Gaskiyarsa ya faɗa sai dai gaskiyar nauyi gareta. Idan har zai yi tunanin cewa auren Asiya shi zai sama mata lafiya to kuwa tabbas abinda ke bibiyan Asiya abune mai girma. Asiya 'yarsa ce kuma lafiyarta shine abu na farko da zai fara dubawa sama da komai. Ƙila ƙaddarar Asiya kenan, ƙila tsakaninta da Ubaydullahi sai dai alaƙar Ya da ƙanwa. Ya kai minti biyu bai iya cewa komai ba. Ya sani, indai su Alhaji Sani Kachallah suka je gaban Ale Faruƙ gobe to an riga an gama dan maganar aurenta da Ubayd ta tashi kenan. Ya ji daɗi da Gwamna ya girmama shi bai manta cewa Ubaydullahi shine saurayin da zai auri Asiya ba. "Ba a kai sadaki ba. Mun tambaya ne kuma an bamu kuma har an saka lokaci. Shi Ubayd akwai kuɗin sadakinta daya ajiye a wajena zuwa idan lokaci ya ƙarato sai na baiwa magabatanta, amma tunda Allah ya rubuta ba matarsa bace zan maida masa kuɗin gobe da safe idan Allah ya kaimu" "Malam Nuhu..." "Your Excellency nagode daka karramani, ka bani girma har kazo da kanka ka sanar dani komai. Ina addu'ar Allah yasa wannan haɗi ya zamo alkhairi a rayuwar Asiya" Gwamna ya so yai wata maganar amma bashi da bakin yi. Duk abinda zai faɗa ba zai chanja abinda Abba zaiyi tunani akansa ba. *** Kwanaki biyar kenan da zuwan Asiya gida. Kwana biyun farko zazzaɓi mai zafi ya sata a gaba. A kwana na uku ne ta samu ta fara warwarewa saboda ta rage tunani da kuka. Umma ta kan turo mata saƙo na ƙarfafa gwiwa kullum sannan Mama ma kullum tana cikin yi mata nasiha akan haƙuri da kuma yarda da ƙaddara. A wannan lokaci ta so ace Gwani na da rai. Yadda duk lokacin data shiga damuwa yake karanto mata tarihin Nana Asiya dan ya nuna mata mai sunanta jaruma ce da bata taɓa karaya ba. *"Kina tunanin Allah ba zai jarrabce ki bane?"* Kalamansa kenan ranan da tazo ta sameshi tana kuka saboda Ale Faruƙ ya gaya mata cewa ya karɓi kuɗin aurenta a hannun Alhaji Talba. Tana shekaru shabiyar alokacin, Alhaji Talba kuma zai iya kaiwa shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar. Da kuka wiwi ta iso zauren Gwani inda yake koyarda wasu manyan Almajirai dama wasu ɗalibai magidanta dake ɗaukan karatu a wajensa. Bayan sun keɓe ta fara bayani "Shi Baba komai kuɗi komai kuɗi. Ni gaskiya ba zan yarda ya sayar dani ba, ai bance masa aure nake so ba. Ni gaskiya karatu zan yi" tayi maganar cikin kuka. "Ishiru Uwata, faɗa mini mi aka miki?" Asiya ta goge hawaye ta zayyane masa duk abinda ya faru kan cewa Ale ne da safe ya gayawa Iyani da Fulani cewa su shirya karɓan baƙi gobe za a kawo kayan gaisuwar Asiya. Ta haɗa da cewa " shi Baba rayuwarsa ta ƙare a kuɗi da mata. Abin kunya kwanakin baya daya saki Delu ina Bibalo ya auro. Bibalo fa, yarinyar da tun tana ƙarama take fama da taɓin hankali. Tsofai tsofai da shi ya ɓata mata rayuwa gashi Aljanunta sun hanata zama a gidansa" Jin irin maganganun nan na fitowa daga bakin jikarsa zuciyarsa ta shiga ƙunci. Yai saurin karanto Isti'aza a zuciyarsa sannan ya riƙo hannun Asiya yace *"Kina tunanin Allah ba zai jarrabce ki bane?"* Tayi shiru tana kallonsa. Ya cigaba da yi mata nasiha tareda cewa ba abinda zata iya yiwa Ale sai dai ta rinƙa masa addu'ar Allah ya shirya shi, domin shi ɗin Uba ne gareta hakan kuma ba zai chanja ba har abada. Bayan wannan abinda ya faru Gwani ya kira Ale Faruƙ ya masa faɗa yace bai hanashi aurar da 'yarsa ba idan ya ga hakane mafi alkhairi amma matuƙar yana raye ba zai taɓa bari ya mata auren dole ba kuma ko yayi bai yafe masa ba. Saboda fasa auren da akayi Alhaji Talba ba ƙaramin rigima sukayi da Ale ba dan sai da suka yi kaca-kaca da shi. Wannan dalilin ne kuma yasa Asiya ta dawo gidan Gwani da zama permanently har lokacin data samu admission a Congo University ta koma gidan Ummanta da zama. Ale Faruƙ na kasuwa aka zo aka sameshi da zancen daya saka shi shiga mota ba takalmi dan har sai daya fita daga motar ya tunkari motocin Alhaji Sani Kachallah daya taka wani ƙaramin kara mai tsini ya lura cewa ashe babu takalmi a ƙafarsa. Wannan bai karya masa gwiwa ba yai saurin cire karan a ƙafarsa sannan ya ƙarisa motar daya ke tsakiya wacce yake tunanin a nan babban baƙonsa yake. Samun buɗi ya sa Ale Faruƙ ya gyara ƙofar gidansa dama sashensa, wanda yanzu falo biyu gareshi ta farko ta karɓan baƙi ta biyu kuma wanda yake kallo ya ci abinci sannan anan yake zama da 'yan uwansa da abokansa na kusa lokaci zuwa lokaci. Lokacin da Alhaji Sani ya fito daga mota har ƙasa Ale ya durƙusa yana kwasan gaisuwa fiskarsa washe kaman an masa albishir da Aljannah. Jiki na rawa ya masa jagora da tawagarsa ta mutum uku zuwa falonsa. Sai da suka zazzauna ya sake risinawa ya gaida su. Alhaji Sani da wani tsoho da yake tunanin zai kai shekaru casa'in sun girmeshi sosai amma sauran biyun ɗaga cikinsu zai kai sa'an Bellonsa sai ɗayan kuma dai zaiyi sa'an ƙaninsa Zakari. Ƙokarin fita ya nemo musu ruwa yai amma Alhaji Sani ya dakatar da shi yace idan akwai wanda zai kira ya kira domin sun zo neman auren 'yarsa ce. Ale Faruƙ ya ɗau waya ya fara kiran Baffa Malam yace ya zo maza-maza akwai manyan baƙi na jiransa. Bai san wacce cikin 'ya'yansa ake so ba amma cikin 'ya'yan dake gabansa mata da suka kai aure ba suyi aure ba, su biyar ne. Asiya data haura ishirin, Nafisatu da Ɗayyiba da suke shatakwas sai Sumayya data ke shabakwai sannan Baraka dake shashida. Koma waccece a cikinsu Alhaji Sani na nunawa to ya bashi ita ne kawai, babu mahalukin daya isa ya hana. Gwani ne ya isa ya dakatar da shi akan lamurran 'ya'yansa kuma Allah ya jiƙan rai ya jima acikin ƙasa. Malam Audu maƙocin Ale ne ya fara isowa kafin Baffa Malam da Baffa Zakari wanda dama jiran baƙin suke dan tun jiya da dare Abba ya kira Baffa Malam ya sanar dashi abinda Gwamna yace da kuma matakin da shi ya ɗauka na janye neman da ɗansa ke yiwa Asiya. Baffa Malam da Baffa Zakari sun tattauna tsakaninsu kuma sun zuba ido ne tun jiyan suga yadda komai zai wakana tunda magana irin wannan Ale ne zai yanke hukunci ba su ba. Minti bakwai da zuwan Malam Audu suma suka iso, dake kujerun sunyi kaɗan A ƙasa suka zauna tunda uban gayyarma a ƙasa suka sameshi. Duk da Alhaji Mustafah Kachallah Baffa a wajen Alhaji Sani ya nemi su Baffa Malam su zauna a kujera, Baffa Malam da Malam Audu ne kawai suka zauna a kujera. "Na bayar" Ale Faruƙ ya faɗa tun kan Alhaji Mustafah ya ƙarisa bayaninsa. "Idan hakane zamu ajiye sadakin yarinyar da kuɗin mun gani muna so idan yaso a hankali sai a kawo sauran abubuwan. Sannan kuma idan babu matsala muna so nan da sati biyu ko uku a ɗaura auren" "Wallahi ko yanzun nan kuka ce a ɗaura mun shirya" Baffa Malam ya bi Ale da ido. Kuɗi ai ba hauka bane. Tunda ya shigo falon ya lura da yadda Yayan nasa ke yi kaman wani wawa a gaban waɗannan mutane. Ya yarda suna da kuɗi sunada matsayi, suna da daraja a idon al'umma. Amma ba wannan bane zai sa kuma su basu wuƙa da nama a lamarin auren 'yar su. Sunada 'yanci ai. Ya dai yi shiru ne kawai saboda sanin halin Yayansa da yai, abune mai sauƙi a wajensa idan yai magana ya fara masa gori cewa ai shine Uban Asiya. Miliyan ɗaya cash aka ajiye musu. Sadaki dubu ɗari biyar sauran dubu ɗari biyar kuma kuɗin na gani ina so kamar yadda suka faɗa. Su Baffa Malam ne suka raka baƙin waje yayinda Ale ya shige ƙuryar ɗakinsa yana neman wajen yiwa kuɗin mafaka. Sanda ya fito zai bisu ya ci karo da kayan da aka jibge a ƙofar falon, tarkacen kayan gaisuwane su buhun gishiri, buhun suga, kwalin sabulai, kwalin minti da cingam, damin goro kusan kashi goma da kuma ƙwaryan Zuma guda uku. Ya haɗiyi yawu ya yi waje da sauri lokacin har motocin baƙin sun riga sun juya... *** "Ba zaku maidani mahaukaciya ba Baffa. Ta ina za'a karɓi kuɗin aurena bayan akwai maganar aurena da Ya Ubayd. Baffa kaima ka koma son abin duniya ne kaman Baba?" "Zauna Asiya" "Noo Baffa. Ka gayamin gaskiya, kuɗi da mulki sun fara tsole muku ido kuma?" "Ki zauna aka ce miki ko" Baffa Zakari ya daka mata tsawa. "Wannan abin yafi ƙarfinmu. Amma duk abinda kika gani ya faru da bawa to rubutacce ne daga Allah. Ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara. Insha Allah zamu cigaba da yi miki addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi a rayuwarki" "Shikenan dan kunga Gwani baya raye sai ku yanke hukunci bisa son zuciya. Baffa wannan son zuciya ne, da ku da Baba duk dukiya ce ta tsole muku ido. Ba zan auri kowa ba sai Ya Ubayd" Daga haka ta bar musu ɗakin da gudu. Ranan ƙarfe bakwai na yamma a gidan Abba ya mata. Tayi ta kiran nambobin Ubayd amma duka a kashe su ke. Hankalinta ba zai iya ɗaukan wannan abin ba. Ta yarda da ƙaddarar data faɗa mata na abubuwan da suka faru da ita cikin kwanakin nan. Yanzu ma maganarta ya ja baya a duniyar yanar gizo an koma gulmar wani ɗan film da aka ce yana luwaɗi. Umma ma kamar kowacce Uwa ta damu da halin da 'yarta ta shiga musamman data ganta a fige kamar kazar sadaka. Ta yi iya baƙin ƙoƙarinta wajen nuna mata cewa hukuncin da aka yanke mata ana mata zaton alkhairi ne ba sharri ba. " Addu'a shine abinda ya rage miki yanzu Asiya ba kuka ba" Maganar Mama kenan lokacin da ta riƙe mata ƙafa tana kuka akan ta tayata roƙon Baba da Baffaninta. Itama Umman sunan addu'a take kira mata. Addu'a, Addu'a, Addu'a. Ta fa gaji da jin wannan suna. Lokacin da tace zata fita, Umma cewa tayi sai dai dole su tafi da Gwani ko Aliyu. Dake Aliyun ne ke kusa shine ya rakata gidan su Umma Hussaina. Rabonta da gidan ma zai iya kaiwa shekara. Ta tsammanci samun Ubayd a gidan amma aka ce mata yayi tafiya. Ta jima tana zaune a ɗakin Umma Hussainan kafin daga baya ta haƙura ta miƙe ta tafi ko sallama bata yiwa Umma Hussaina ba. Damuwa kan chanja tunanin mutum matuƙa. Wasu lokutan Asiya sai ta shirya zata gudu sai ta fasa, wani lokaci kuma tayi tunanin ta kashe kanta ma kawai ta huta. A wasu lokutan kuma tayi tunanin samun bindiga ta je ofishin Gwamna ta bindige shege kowa ma ya huta. Wani lokacin kuma tayi tunanin ta haukace kawai saboda a dakatar da komai. Wasu lokutan ma zuciyarta na riya mata cewa ƙila ba Ale Faruƙ bane ubanta. Abin da ya fi riƙe mata rai ma bai fi yadda Ubayd ya ɓace mata ba, ga numbarsa da har yanzu bata shiga. Ta fara tunanin ƙila Gwamna ne ya sa aka ɗauke shi, an ƙi faɗa mata ne kawai. Sati ɗaya tayi a gidan bata san inda kanta yake ba. Abba da Umma kullum suna nuna mata ta saki ranta komai zai zo ya wuce amma zuciyarta bai shirya ma yarda da zancensu ba balle har ya amince da shi. Ubaydullah shine masoyinta na farko kuma na ƙarshe, ita tunda ta taso ma bata taɓa son wani ba, ko crush na primary ko secondary school bata taɓa ba. Ubayd ta fara so tun lokacin da ya ɗauka mata tsumman abunta, tun lokacin bata san so ba. Saboda Ubayd bata taɓa bawa wani damar shiga rayuwarta ba. Ko lokacin da take Jami'a da tayi tashe, samari ke mata chaa babu wanda ta taɓa buɗewa ƙofa. It has always being Ubayd and will always be. Yayinda Asiya ke fama da damuwa, a chan gida kuwa Ale Faruƙ ya kasa ya tsare wajen ganin wannan biki ya tafi yadda ya kamata. Sati ukun nan gani yake kaman ba za su iso ba. Tun yanzu ya fara kiran kansa sirikin Gwamna har tambayar siriki yai da turanci aka ce masa Inlaw amma idan shi ya faɗa sai kaji kamar 'yanlo yace. Yi masa kirari da sirikin Gwamna kaga ya ɗau kyautan dubu ya baka mutumin da ɗarinsa idan ba a mace ba baya iya bayarwa. Tuni yasa aka yiwa gidansa sabon fenti. Matansa da sauran yaransa duk ya musu ɗinkin biki kala biyar biyar hatta yayyen Asiya da ke gidajen mazajensu ya aika musu da nasu kayan. Wannan kashe kuɗi ko a sallah albarka. Shi dai yanada abu ɗaya gidansa ana cima mai kyau amma wani siyan kayan sawa ko na ado to ko a sallah sai anyi da gaske, yawanci ma iyayen 'ya'yan ke musu. Haka batun makarantar boko idan ka wuce sakandare sai fa ka tallafawa kanka. Mace ɗaya ce tayi karatu a 'ya'yansa mata bayan Asiya, itama kuma a gidan mijinta tayi. Adda Hadiza kenan da ta karanci ɓangaren midwifery. *** "It was for political reasons Bilkisu" "Shine sai dai naji a bakin Babana" "Sanda kika dawo bana gari kuma wannan magana bata waya bace" "Saifuddeen ka rasa wacce zaka aura sai 'yar Kurma jikar maiƙusumbi" ta tintsire da dariya. "I'm sure ba wai zaka nemi haihuwa da ita bane ko? dan ba zan juri ganin 'ya'yan guragu, kutare da makafi a gidan nan ba" Gwamna yai seƙeƙe yana kallonta. Ita ce dai da take zuwa gidan marayu tana ɗaukan hotuna da naƙasassun yara. "Na ɗauka baka ƙyamar nakasassu Bilkisu" "Oh please Saifuddeen. Ka sani sarai campaign nake yi" Ido ya zuba mata ya rasa ma mi zai ce. She never seizes to amaze him. "And Darling, ka sani zan haƙura ne kawai saboda lokacin campaign ya kusa, bana son abinda zai ɓata maka ƙuri'u. Abu na ƙarshe kuma shine ka nema mata wani gidan dan a nan" ta juya yatsarta manuniya "ni kaɗaice Matar Gwamna"... 2g Novels Home / THE GOVERNOR'S WIFE / THE GOVERNOR'S WIFE 13 THE GOVERNOR'S WIFE 13 2g novels THE GOVERNOR'S WIFE *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one *Assalamu Alaikum* *Barkanmu da warhaka. Babu kalmar da zan iya baku haƙuri da shi daya wuce na haɗa ku da Allah. Dan Allah kuyi haƙuri.* *Ban so na kai waɗannan ranaku babu update babu bayani ba. Amma akwai dalilin daya sa na yi haka.* *Kwanan baya nayi rubutu ina son na yi copy and paste sai nayi deleting nashi. I was blocked, for days na kasa sake typing. Daga baya nace ni da update sai na kammala typing part 1. Na dena hawa online ne saboda bana son distraction.* *Wanda suka min magana ta whatsapp ko wattpad ban amsa ba, ina baku haƙuri. Wanda suka kirani numba na a kashe suma ina basu haƙuri. Ya kamata ace nayi muku bayani amma banyi ba. Ina neman afuwa akan haka.* *Insha Allah part 2 zai fara zuwa daga ranan Asabat idan Allah ya kaimu.* *Nagode da haƙuri da ni...* 13 Matar Gwamna. Ayyiriri Amarya" "Queen Bee bana so, ki bari. Tukunna ma ya akayi kika sani? " Queen Bee ta ɗaga mata waya tana faɗin Umma. "Haba Asiya! So kike a kaiki gidan Gwamna kamar wata ƙwarangal. Look at you" "Idan wannan ya kawoki, tashi ki tafi" "Baki isa ba, Wallahi baki isa ki ja mana kunya ba. Dole sai anyi miki gyaran nan" "Zaki yi ki barni dan ba abinda zanyi" Duk yadda Queen Bee ta so su fara gyara Asiya bata ba da haɗin kai ba. Duk da Umma ta sa baki hakan baisa ta chanja ra'ayinta ba. Ana saura kwana bakwai a ɗaura aure, da safe irin ƙarfe goma shaɗaya aka kawo lefen Asiya. Lokacin bata gida, ta raka Sumayya makaranta, za ta fara registration dan ta samu admission a Jami'ar Congo. Lokacin da Asiya da Sumayya suka shigo gidan, a cike suka samu da mutane, yawanci maƙota ne sai kuma 'yan tsirarun 'yanuwansu dake zaune a Congo. Faty 'yar Inna Yaha ce ta jata suka shige falon Abba saboda ɗakin Umma a cike yake da baƙi. "Ban gane mi yake faruwa ba, wani taro ake yi a gidan?" " 'yaruwa kinga lefenki kuwa?" Ƙoƙarin buɗe ɗakin Abba ta shiga yi Asiya ta katseta. Bata buƙatar ganin koma minene aka kawo. Ashe shiyasa jiya da yamma Umma da Fatyn suka wuni suyan kaji a kitchen. "Ki barshi Faty, ba sai na gani ba" Faty bata bari ta ƙarisa ba ta jata suka shige ɗakin. Akwatuna ne akan gado gefen gado da duk wajen da akwai sarari. Wasu baƙaƙe, wasu ja, wasu blue, wasu brown, wasu lemon green da kalan silver. "Ashirin da huɗu cif" Faty ta faɗa tana wage haƙora. "Yanzu Anty Faty an buɗe dukkansu?" Sumayya ta tambaya cike da farin ciki. "Guda shabiyu aka buɗe, Hajiya Adda tace a barsu haka, wai da ana maida kayan an rasa zannuwa uku a ciki" Asiya juyawa tayi ta bar musu ɗakin dan ba zata juri ganin kayan takaicin nan ba. Ubayd ya kammala haɗa kayanta kawowa ne kawai ba ayi ba. Akwatuna biyar ne kuma ta riga ta san minene a ciki saboda fiye da rabin kayan kuɗi ya bata ta siya, wasu kuma sukan je siya tare. Lefen da Ubayd ya haɗa shi take so, ba wannan kayan ƙaryar ba. Fita tayi daga gidan gaba ɗay ta wuce shagonsu. Tana cikin keke text ɗin Umma ya shigo, ta maida mata amsa da cewa shago zata je. Saura kwana huɗu ɗaurin aure sai ga text ɗin Ubayd a wayarta, yace ta zo ta sameshi a office ɗinsa da ƙarfe biyar na yamma. Ƙarfe uku text ɗin ya shigo, dan haka tana sallar La'asar ta ce da Umma zata fita, Umma tace ba inda za ta je. Hakan ya sa ta mata ƙarya akan gidansu Queen Bee za su je karɓan saƙo ita da Sumayya. Umma tace su je amma lallai su dawo kafin ƙarfe shida na yamma. *** "Daddy da gaske aure zaka ƙara?" Nana tayi magana tana tsare mahaifinta da idanu. Gwamna yai shiru bai ce komai ba. "Ka bata amsa mana Mijin 'yar Kurma" Gwamna ya maida dubansa ga Hansa'u da ke bawa Junior abinci a baki yace "Kada ki sake bashi abinci a baki. Kada wanda ya sake bashi abinci a baki" "Tuba nake ranka ya daɗe" Hansa'u ta faɗa tana ajiye cokalin da ke hannunta "Kar ka saukar da fushinka akan ɗana. Kai ka sawa kanka auren jikar maiƙusumbi" Nana da Zunnairah suka fara dariya ƙasa-ƙasa. Ko kallon Bilkisu bai yi ba ya miƙe ya bar dining room ɗin. A irin wannan ranaku da yake samun daman zama da iyalinsa ba abinda yake so sama da soyayyarsu. Sai dai yanzu kam Bilkisu ta gaza bashi wannan soyayyar. Dolene ya takawa Bilkisu birki. Juniour ba yaro bane da sai an bashi abinci a baki. Nana ta yi girman da bai kamata ta masa magana karangatsau haka ba, sai dai koma minene shi ya jawo wa kansa. A ƙaramin falo Bilkisu ta zauna ita da babbar ƙawarta Madam Bintu suna tattaunawa kan kasuwancinsu. Bayan Hansa'u ta kawo musu abin taɓawa sai kawai suka ga ta zauna a tsakiyar falon ta ƙurawa TV ido. "Hansa'u lafiya? Baki da aikin yi ne?" "Shirin su Aarti da Yash zan kalla" "A duk faɗin gidan nan sai a nan zaki yi kallo. Tashi maza ki bani waje" Bilkisu ta daka mata tsawa. "Kema dai Bilkisu miyasa zaki kawota nan. A chan gidanku ma tana shirme balle a nan" "Akwai ƙauyanci a tattare da ita amma ta iya aiki ne Bintu. Kuma gaskiya ban sake da ma'aikatan gidan nan ba duba da cewa sun yiwa Sha'awanatu aiki a baya. In fact, chief cook ɗin ma sai dana sa aka chanja shi" "Wai baza ki tashin bane?" Hansa'u ta miƙe tana susa kai ta bar wajen. *** Da sauri-sauri take tafiya zuciyarta na tsalle a cikin ƙirjinta. Ita kaɗai ta san ya take ji a ranta. Tana son shi, tana fushi da shi, tana kuma tausayinshi. Sai da ta ja dogon numfashi kafin ta buɗe ƙofar office ɗinsa a hankali. Ubayd na zaune a madaidaicin office ɗinsa da ke ɗauke da wata na'ura da ake duba idon mutane. Akwai kujeru biyu na zaman masu jinya. Akwai manyan hotonan ido da akayi rubutu ajiki a bangon office ɗin. Farar riga da likitoci ke sanyawa ya ɗaura akan jamfar da ya saka kalar toka. Fiskarsa ɗauke da baƙin gilashi daya ɓoye idanunsa. Sautin karatun ƙur'ani ke fitowa daga laptop ɗinsa, shigowarsu ya sa shi katse karatun. "Ina wuni Yaya" Sumayya ta gaisheshi idonta na kallon ƙasa, duk da yana sanye da gilashi ba zata iya kallon idonsa ba. Duk cikin 'ya'yan Ale, Asiya ta fi jituwa da Sumayya shiyasa ya mata farin sani. Tun kafin ta ƙare Sakandare ta sha zuwa hutu wajen Asiya. "Lafiya Sumayya, yaushe a gari?" "Na ɗan kwana biyu" "Bismillah, ga kujera" "Barin baku guri" bata ji ma mi yake faɗa ba ta fice daga office ɗin da sauri har lokacin Asiya na tsaye ta zubawa Ubayd ido. "Ki zauna Asiya" Kafin ta zo ta tanadi maganganun da za ta faɗa masa amma ganin fiskarsa ya share komai na kwanyarta. "Asiya ..." "Kai na ke so Ya Ubayd, fight for me, fight for us" ta faɗa lokacin da ta zauna "Asiya muyi haƙuri" "Zamu iya guduwa Ya Ubayd, there's still time. Mu je Kano gidan..." "Ba inda zamu je Asiya" "Saboda ka dena sona? Saboda kana tsoro, Saboda..." "Saboda na karɓi ƙaddarata da hannu bibbiyu. Saboda nayi alƙawarin yiwa mahaifina biyayya matuƙar ba abune daya saɓawa addini ba" "Oh! Ni ce ban san mi nake ba ko. Ni ce bana girmama iyayena ko?" "Ina sonki Asiya Shahidah. Bana tunanin zan so wata kamar yadda nake son ki. Amma in har aurenki da Gwamna zai kawo..." "Ya isa!" Miƙewa Asiya tayi tsaye, ta sa hannu ta goge fiskarta fes babu ko ɗigon hawaye. "Ya Ubayd ka ci amanata, ka ci amanar soyayyarmu. Zan auri Gwamna, but mark my words Ya Ubayd, Ni Asiya sai na ga ƙarshen Gwamnatinsa, Ka huta lafiya" "Mine... Asiya... Asiya... Asiya" Ciro hankerchief yai daga aljihun labcoat ɗinsa ya shiga goge gumin goshinsa, Shikenan daga yau bashida ikon kiranta Mine. Lokacin daya cire gilashin idonsa sakanni kaɗan bayan fitan Asiya, hawaye ne masu ɗumi suka fara gangaro masa. Chan cikin zuciyarsa kuma yana yiwa Asiya addu'ar Allah ya sassauta zuciyarta kar taje tayi abinda za tayi dana sani daga baya... ** Kwana uku saura ɗaurin aure gari ya ɗauka cewa Gwamna zai ƙara aure. Ba kuma kowa zai aura ba sai 'yar jaridan nan da ta so ɓata masa suna kwanakin baya. Mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu akan batun, wasu na ganin kwata-kwata bai dace ba, wasu kuma suka fara cewa ai dama chan karuwarsa ce, maganganu dai kala-kala. Bilkisu Kachallah ce ta juya akalar maganar inda ta fito ta bayyana cewa tausayin mahaifin Asiya yasa Gwamna ke son auren Asiya Faruƙ Baba. Ta bayyana cewa, sun samu labarin saurayin da zai aureta ya fasa saboda abinda ta aikata, kuma yadda duniya ta riga ta san abinda Asiya ta yi babu namijin da zai so aurenta. Yadda iyayenta sukayi ta roƙon Gwamna shiyasa ya ji tausayinsu, ya musu wannan alfarmar akan zai auri Asiya dan ya rufa mata asiri... An gama zanawa Asiya lalle tana jira ya bushe a cire Queen Bee ta gaya mata abinda ta gani yana yawo a social media. "Baby kar ki damu, idan kika shiga gidan ki yi maganin shegiya" Queen Bee ta faɗa dan ta kwantar ma Asiya hankali "Yanzu Ya Ubayd ma sai da aka ɓata masa suna" "Shahidah dan Allah kar ki saka wannan a ranki. Bari kiga a ɗaura auren nan, wallahi sai abinda kika ce a faɗa za'a faɗa" Tunda ta bar office ɗin Ubayd ta sawa ranta indai ta shiga gidan Gwamna Saifuddeen Kachallah to sai inda ƙarfinta ya ƙare amma yadda ya rabata da masoyinta itama sai ta rabashi da kujerarsa. Tun daga lokacin ta sake jikinta duk abinda akace tayi, tanayi. *** Minti arba'in kenan da kiran Bilkisu da yai amma har yanzu bai ga idonta ba. "Darling" ta faɗa lokacin da ta shigo ɗakinsa fiskarta ɗauke da murmushi. "Sorry na jima, maganar aurenka ne ya riƙeni. Ka san cewa Hajiyan Saudiyya zata shigo gobe, yaushe rabonta da Nigeria. Ni inaga ma kamar jira dama take a min kishiya ta zo taron biki" "Bilkisu please!" "Idan akan abinda na faɗa ne to ka sani duk abinda zai ɗaga darajarka a idon mutane zan yi, saboda an kusa zaɓe" "Ba sai kin ci zarafin iyayenta ba Bilkisu. Ya kamata ki san..." "Idan akan wannan ka kirani, then excuse me, inada aikin yi" "Ba wannan kaɗai bane" ya faɗa ƙasa-ƙasa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa. "Asiya zata zauna a gidanmu na da..." "Asiya zata zauna a Kachallah House" Bilkisu ta ƙatse shi tun kafin ya dasa aya. "Na riga nayi magana da Hajiya Umma akan za'a..." "Matarka zata zauna a Kachallah house. Idan kuma chan bai isheta ba ka iya siya mata wani gidan daban amma wancan gidan Bilkisu ne" tana gama maganar ta fice masa daga ɗaki. Dunƙule hannunsa yai yana huci. A waje shi Gwamna ne, a cikin gida kuma shi mijin Bilkisu ne. Ba yau ta fara fita daga ɗaki idan suna tsaka da magana mai mahimmanci ba amma yau abin ya taɓa shi sosai. *** *Takawarki lafiya Asiya Matar Gwamna.... Ayyiriri yiriri yiriri* Guɗa da kirari ke tashi ta ko'ina, masu watsa filawowi nayi, masu yawo da turaren wuta nayi, haka aka shigo da Amarya Asiya ɓangaren Hajiya Dadda kakar Gwamna. Hajiya Dadda na zaune da wasu manyan mata aka zaunar da Asiya gabanta, Asiya na sanye da alkyabba ruwan Gwal ko fiskanta ba a gani saboda hular alkyabban ya rufe. Dadda ta riƙo hannun Asiya ta dinga zuba mata addu'a. Bayan an gama da wajen Hajiya Dadda aka kai Asiya wajen Hajiya Aisha mahaifiyar Bilkisu. Hajiya Umma ce ke gaba akan komai, tunda Gwamna ya kirata ya gaya mata cewa a Kachallah House Asiya zata zauna ta shiga faɗa, wai sam ba zai yiwu ba. Bilkisu ba zata ja musu magana ba. Yadda aka riga aka tsara hakan za ayi. Za a fara kawo Asiya Kachallah House tayi kwana ɗaya, washegari a wuce da ita gidan Saifuddeen. Duk cikin ƙannen Alhaji Sani, Hajiya Umma ce macen da ko shi Alhaji Sanin ba ƙaramin shakkanta yake ba. Tanada faɗa sosai kuma bata ragewa kowa. Bai san ya suka ƙare da Bilkisu ba, da dare daya shigo gida Bilkisu ta sameshi akan cewa ya sani bata yadda a saka Asiya a sama ba. Indai wannan ne da sauƙi dan dama a ƙasan aka shiryawa Asiya kayanta. Bayan sun bar sashen Hajiya Aisha sai aka wuce da Asiya ɓangaren Saifuddeen lokacin yana saurayi. Ƙaramin falo ne da ɗaki a ciki haɗe da banɗaki. Anata shigowa gaishe da Amarya sai ƙarfe shaɗaya da rabi Hajiya Umma ta kori mutane aka bar Asiya da ƙanwarta Sumayya, Faty da kuma ƙawarta Queen Bee. Gobe da safe za'ayi wuni da yamma kuma ayi dinner wanda Bilkisu Kachallah ta shirya. Bayan an watse ne Asiya ta samu ta cire kaya ta shiga banɗaki dake cikin ɗakin ta fara wanka. Kuka ta saka lokacin da ruwan shower ya fara sauka mata. Kukan da bata yi ba lokacin da za'a kawota, kukan da bata yi ba lokacin da aka kaita gaban Abba yai mata nasiha. " an ɗauraaaa, Anty Asiya kin zama matar Gwamna" maganan Sumayya kenan tana tsaye dai dai ƙofar ɗakin Umma. Live aka nuna ɗaurin auren a gidajen talabijin. Hakan ya sa 'yan biki suka cika falon Abba da ɗakin Inna Yaha sai kuma masu kallo a waya. Umma kam dama babu TV a ɗakinta shiyasa Asiya ta samu salama, ta kwanta tana ayyana abubuwa da dama a ranta. Su uku ne a ɗakin sanda Sumayya ta leƙo tana faɗa mata munanan kalamai. Umma da ba jin mi ta faɗa tayi ba ta cigaba da ninke kaya. Wata Goggon Asiyan da ke kwance saboda ciwon kai ta miƙe zaune tana doka kabbara lokacin da taji abinda Sumayya ta faɗa. "Anty kinga fiskar Ale kuwa ? da aka nunoshi kaman mai tallen Makilin..." "bar nan Sumayya!" Sumayya ta sake labule ta sa gudu. Buga ƙofar da Queen Bee ke yi ya sa ta yi firgigit ta dawo hayyacinta. "Governor's wife, fata zaki chanja a banɗakin ne wai? Muma zamu watsa ruwan fa" Bata kulata ba sai kawai ta matsi shower gel ta fara shafawa a dogon gashinta wanda ruwa data bari ya zuba mata akai ya sa ruwan mai ya mamaye ilahirin jikinta. Ba ƙaramin gyara gashin ya sha ba a hannun Queen Bee saboda harkanta kenan. Bayan ta gama wanke kan ya dena fitar da mai sannan ta yi wanka ta ɗaura towel ta fito. "Queen Bee akwai hand dryer a kayanki?" "Yanzu wanke kai kikayi tun Ango bai gani ba" Queen Bee ta faɗa tana taɓe baki. "Kin zo da shi, e ko a'a?" Tayi maganar da ɗan ƙarfi dan ruwan kanta ya fara sauka ƙasa saboda bata goge kan ba. "Barin ɗauko miki" Faty na zaune bakin gado tana kallon ikon Allah. Babu walwala ko kaɗan tattare da Asiya irin na Amaren nan. Lokacin da aka kira mai hoto cikin gida ana ɗaukan hotuna ko sau ɗaya bata murmusa ba, ƙarshe ma cewa tayi kanta na ciwo ba zata iya tsayuwa ba. Anya Asiya ba zata yi wani mugun abu ba kuwa wajen dinner ɗin da za ayi? Ko kuma ma idan an kaita tayi ƙoƙarin illata Gwamna. Tayi saurin kauda tunanin a ranta da cewa Asiya na da ilimi ba zata yi wannan haukan ba. Asiya ta kunna hand dryer ta fara busar da gashinta, Faty ta miƙe daga inda take kishingiɗe ta ce " kawo na miki" Lokacin da Queen Bee ta fito daga banɗaki suka rutsa Asiya da ke shirin bacci da nasiha. Faty a matsayinta na ƙanwar Ubayd kuma ƙawa ga Asiya tunda duk cikin 'ya'yan Inna Yaha itace suka shaƙu ƙwarai, shiyasa ma aka saka aurensu lokaci guda ita da Asiya kafin lamari ya chanja. Faty ta bata shawaran ta manta da Ubayd ta rungumi mijin da Allah ya bata. Queen Bee ma a matsayinta na babbar ƙawa wacce suka yi Jami'a tare, sannan suka haɗa business tare, ta bawa Asiya shawaran haƙuri da hukuncin Allah. Asiya jinsu kawai take amma ba abinda ta ɗauka cikin maganganunsu. Tun kafin Queen Bee ta ida maganarta Asiya tace ta gaji, bacci za ta yi. Asiya ta samu gefen Sumayya da ta jima da bacci ta kwanta zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. *** Zurmemiyar wuƙa Asiya ta ɗauko a kitchen ta wuce ɗakin Gwamna da shi. Yana tsaye sanye da farar jallabiya yana waya ya bata baya, a hankali ta ƙariso ta zurma masa wuƙa a gefen cikinsa. Gwamna ya saki ƙara, ya juyo a hankali yai taga-taga kamar zai faɗi ƙasa Asiya ta riƙo shi "I hate you Saifuddeen Kachallah" ta faɗa tareda ƙara danna wuƙar ciki sosai. Buɗe idon da Asiya tayi ta hango ceiling ɗin ɗakin. Dogon numfashi ta ja kafin ta ce a ranta " ba zan kashe ka ba sai dai..." *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 14 *** Tunda su Asiya suka ci abinci suka koma sashen Dadda. Daga safe zuwa yammaci baƙi ne ke ta shigowa ganin Amarya. Matan manya da kuma manyan manyan Mata da su kayi suna a ƙasar. Wasu kallon ƙwaƙwaf ne ya kawosu saboda a samu latest gist da za a tattauna idan an haɗe a wajen shaƙatawa, wasu kuwa sun zo ganin Asiya Shahidan da ake kururutawa ne saboda ba su santa a Talabijin ba. Wasu kuma sun zo ne domin samun gindi a wajen Asiya dan basa shiri da Bilkisu Kachallah. Asiya bata bada fiskar da zai sa a gane tana cikin matsala ba. Ko Faty da Queen Bee sun yi mamakin yadda ta sake tana dariya cikin mutane kamar auren soyayya akayi. Kusan ƙarfe biyar da rabi na yamma Anty Saudah ƙanwar Bilkisu ta kawo musu wata jaka tace kayan da Amarya zata saka ne a wajen dinner. Basu waiwayi kayan ba saboda suna cikin jama'a. Ƙarfe bakwai da minti Arba'in bayan Asiya ta idar da sallar Isha ta shiga banɗaki ta watsa ruwa. Suna ɓangaren da suka kwana jiya, su huɗu ne a ɗakin a chan falo kuma ƙawayen Asiya na makaranta ne da abokanan aikinta da suka samu pass ake wa kwalliya. Queen Bee ce ta karɓo pass ɗin dan haka Asiya bata san iya mutanenta da zasu zo wajen dinner ba. Tunda Queen Bee ta fito da kaya Asiya ke girgiza kai, amma bata ƙi ta su Faty ba da suka ce ta dai gwada ta gani. Abu ɗaya ta sa aranta shine ko ta sha giyan wake ba za ta sa wannan kayan ta fita waje ba. Gown ɗin yayi ba ƙarya, ya amshi jikinta, duk wani tudu na jikinta ya fito sosai, sai dai rigar offshoulder ce rabin ƙirjinta a waje yake sai net da aka rufe wajen da shi wanda ko makaho ya shafa ya san ba abinda net ɗin ya tare. Cikinta ma net ɗin aka saka saboda an fafe lace ɗin wajen ne aka saka net. Ɗinkin yayi kamar bra ta saka da skirt sai aka rufe sauran wajen da ke bayyane da net. "Inaga za mu nemi shawl da zai je da kayan kawai sai..." "Baki da hankali Bahijja" ta kira sunan Queen Bee na asali. "Gaskiya dai wannan kayan sai a hankali" Faty ta faɗa tana girgiza kai, sai yanzu da Asiya ta sa kayan ta gano akwai matsala. "Bilkisu Kachallah ta riga ta rubuta headline da zai fito gobe a labarai idan na sa kayan nan. Beside, ni ba mahaukaciya bace na san darajan gidan dana fito" "Anty dan Allah barin ɗauke ki a hoto, wallahi kin yi kyau" Sumayya ce da wannan maganar. "Ban yadda ba... ki bari" sai kawai ta haƙura ta tsaya saboda Sumayyan ta riga ta fara ɗaukanta hoto. Ɗaya kayan dake cikin jakar ma babu kanta, atampa ce da aka yiwa fitanniyar ɗinki. Ko gwadawa batayi ba ta tura gefe. Ba abinda ya rage sai dai su saka abinda suke da shi. "Ko na yiwa Hajiya Umma magana ne? tunda dama tace za a kawo mana kaya na ce an riga an kawo" Queen Bee ta faɗa tana kallon Asiya da ke zaune a gefen gado daga ita sai zani. "Akwai wani gown a jakar da nace ki tahomin da shi Sumy, ɗauko min" Tayi maganar kaman mai shirin yin kuka. Malaysian gown ne data gani a Amazon watanni kaɗan da suka wuce. Simple gown ce ruwan madara da aka yiwa design da duwatsu ruwan gwal. Model ɗin data saka kayan ta yi rolling da gyalen kayan ta saka crown a kanta kamar sarauniya. Asiya alokacin data ga kayan hango kanta ta yi sanye da irin kayan tana zaune kusa da Ubayd a ranan da za ayi kamunsu. Su Queen Bee sun yaba da gown ɗin, sai dai kamar yai kaɗan ace Matar Gwamna guda ta sanya gown irin wannan da kuɗinsa ba zai wuce dubu hamsin ba. Kuɗin shipping dana kayan duka-duka dubu arba'in da huɗu Asiya ta siya a kuɗin Nigeria. Lokacin da Queen Bee ke mata rolling gyale wasu mata suka shigo wai suyi sauri motoci sun fara isowa, Gwamna ya kusa ƙarisowa. Asiya tace ba make up, amma duk da haka sai da Queen Bee ta shafa mata powder, ta sa mata mascara ya ƙara fito da dogon gashin idonta, sai kwalli da man leɓe, shikenan. Ɗankunne da sarƙan diamond da aka haɗo a cikin kayan duk ba wanda Asiya ta saka. Hannunta dai zoben Azurfa ne da Ubayd ya siya mata sai kuma awarwaro na Azurfa shima da Maama ta bata da jimawa. Takalmi flat ta saka ruwan gwal sai Queen Bee ta bata wani purse ruwan gwal shima. Ba su yi amfani da ko ɗaya daga cikin kayan da Bilkisu Kachallah ta aiko musu ba. Hajiya Umma ce da kanta ta shigo yanzu dan duba shirin na su tunda Gwamna yace mata zasu iso nan da minti uku zuwa biyar. Asiya tayi kyau sai dai ga wanda ya gaji arziƙi zai ga kamar shigar bata dace da irin wannan taro ba. "Hajiya kayan da aka kawo bai d..." "Kar ki damu, Bilkisu ai da gayya ta aiko miki kaya. Kinyi kyau sosai, ni dai roƙona kar ki bata dama akan ki domin yau ranan ki ne" Asiya tayi murmushi. Ba wai dan taji daɗin abinda Hajiya Umman ta faɗa ba sai dan kawai dama abinda tayi niyyar yi kenan. Yau zata fara haɗuwa da Bilkisu Kachallah kuma sai ta nuna mata cewa ita ɗin ba hajar Kamfen ba ce. Tana cike da ita da abinda ta fitar na cin zarafi data mata, iyayenta da kuma Ubayd. Da sannu zata bata kashinta a hannu. *** Gwamna ne da matarsa Bilkisu zaune a bayan lemosine wanda motar Alhaji Sani Kachallah ce aka fito da ita takanas saboda tafiyarsu wajen dinner. Gwamna bai shirya yin hidima ba bayan reception da aka yi jiya suna dawowa daga wajen ɗaurin aure. Akwai abubuwa dayawa a ƙasa da suka fi hidiman bikinsa mahimmanci. Bilkisu ta riga ta shirya komai ba tareda ta tuntuɓeshi ba, abokinsa kuma ɗanuwansa Abdullahi ya takura masa akan sai yaje dinner ɗin sannan a ƙarshe kuma Alhaji Sani ya kirashi ya faɗa masa manyan mutanen da zasu halarci dinner ɗin. Ya sani sarai Bilkisu neman suna take da abinda ta shirya, fatansa kawai ayi taro a watse lafiya. A dai dai sashen Alhaji Sani Kachallah motarsu ta tsaya. "Here's the plan, zaka zo tareda ita, ni kuma zan tareku a bakin ƙofa daga nan sai mu wuce wajen zamanmu. And, ka gayawa 'yar kurma ta yi murmushi saboda hotunan da za a ɗauka" Bai amsa mata ba sai kawai ya shiga kiran numban Hajiya Umma. Ana buɗewa Bilkisu Kachallah mota ta fita tana murmushi ta wuce inda jerin wasu motoci ke jiranta, Saudah Kachallah na bakin wata mota tana zuba mata murmushi na jinjina. Hajiya Umma da Queen Bee ne suka fito da Asiya daga cikin gida, dake daga ɓangaren da suke zuwa inda motar Gwamna ke jiransu akwai tazara ko ina suka wuce sai guɗa da kirari ake mata ana taka musu baya. Sanda aka kai wajen motan Gwamna mutanen da suka rako Asiya sunyi Ishirin. Wani security ya buɗewa Asiya mota Hajiya Umma ta yi kane-kane a wajen saboda masu ribibin son ganin Gwamna. Sai da ta tabbatar Asiya ta zauna da kyau kafin ta rufe ƙofar tun ma kafin security ɗin yayi. Kallo ɗaya ta masa ta kauda kai gefe. Yana sanye da farin babbar riga. Fari na ƙarawa baƙinsa haske, yana ƙara fito da kyaunsa. A kallo ɗaya data masa wanda hankalinsa ma na kan waya sai taga ya mata kwarjini, duk wani haushinsa da take ji sai taji wani nitsuwa ya sauka mata. Ba ta san dalilin da ya sa ta ɗago dan sake dubansa ba, sai dai rashin sa'a lokaci ɗaya suka kalli juna. Ƙirjinta ya shiga lugude musamman da zuciyarta ya ankarar da ita cewa ita ɗin matarsa ce. "Ina fata babu ruwan zafi a purse ɗinki?" Yai maganar yana nuna purse ɗin data riƙe. Bakinta ya kafe na wasu sakanni, ta kasa bashi amsa har sai da ya sake cewa "Abubuwa sun faru a ƙurarren lokaci Asya. Amma a hankali zaki fahimci banyi komai dan na cutar da ke ba" Maganar da ya faɗa ya tunzurata. Tace "Mai girma Gwamna, a sannu zaka fahimci cewa bana barin sai ta kwana" Daga haka ba wanda ya ƙara furta komai. Suna isa hotel ɗin da aka shirya taron kafin a buɗe ƙofa Gwamna ya kalli Asiya yace "banda rawa" kafin Asiya ta bashi amsa aka buɗe masa ƙofa. Tana jira a buɗe sashinta ta fita sai taga Gwamna ya ɗan rankwafa ya miƙa mata hannunsa. Ta so ta buge hannun amma ta sani idon mutane akansu yake, duk abinda za tayi dole tayi takatsantsan. Ba mamaki akwai 'yan jaridar ƙwaƙwaf da ke ankare da samun hoto mai jan hankali. Bata sani ba ko tunaninta ne, ko kuma dai gaske ne amma taji wani shock ya ratsa ilahirin jikinta sanda tafin hannunta ya shiga cikin nashi. Ko kaɗan hannunsa babu taushi da aka sani da hannun maza. To ina zai yi taushi kullum cikin AC. Lokacin da ta fito maimakon ya sake hannun sai ya ƙara damƙe shi da kyau, a haka suka shige cikin hotel ɗin, Securities sun saka su a tsakiya suna basu kariya. *to yanzu dai zamu dakonci shigowar Mai girma Gwamna Alhaji Professor Saifuddeen Kachallah da Amaryar sa Hajiya Asiya Kachallah. Dan haka kowa ya tashi tsaye a nuna musu soyayya* MC kenan da wannan magana. Daga inda suke tsaye suna jira a buɗe ƙofa Asiya ta ja tsaki jin sunan da MC ya kirata, kwana ɗaya da ɗaura aure amma har an fara laƙa mata Asiya Kachallah. Daga bakin hall ɗin 'yan mata da maza ne masu ji da kansu suna tsaye daura da juna kowa ɗauke da ƙaramin kwando na alfarma da aka cika da flowers. Security biyu da suke gabansu Asiya suka juyo garesu suka sara musu sannan suka koma gefe dan basu waje. Bismillah Asiya ta furta a bayyane hakan ya sa Gwamna ya juyo ya kalleta kan kace me an musu hoto yayi goma. Hannunsu sarƙe cikin na juna Suka fara takawa a hankali. Waƙa na tashi yayinda 'yan mata da samarin nan ke barbaɗa musu flowers a duk inda zasu taka. Daga inda Bilkisu Kachallah ke zaune wani abu mai tsini ta ji ya soki zuciyarta. Abu biyu ne ya zo mata lokacin da ta kalli Asiya da Saifuddeen suna takowa fiskarsu ɗauke da murmushi. Na farko dacewa na ban mamaki da suka yi wanda tamkar an halicci Asiya dan Saifuddeen ne dama. Shi baƙi dogo, ita fara doguwa. Ita ga ushirya daya ƙara hasko da kyaunta, shi kuma dimple ɗinsa daya bawa fiskarsa kyau da kwarjini na ban mamaki. Asiya bata saka kayan data aika mata ba, hakan na nufin babu abin yaɗawa gobe kenan, asalima kayan da ta saka da kuma kwalliyar da ba ta yi ba zai ja a yabeta a kafafen yaɗa labarai. Na biyu kalaman malamin taurari Tsu Zhang ne ya sake dawo mata. *akwai wani tauraro daya fito a gefen tauraron mijinki. Yadda tauraronki ke haskawa tareda ta mijinki, haka wannan tauraro zai dinga haskawa tareda shi har sai tauraron mijinki ya haskaka fiye da tunaninki. Idan kikayi ƙoƙarin disashe wannan tauraro babu makawa da taki tauraron data mijinki haskensu zai dinga disashewa. Ki sani taurari uku a waje ɗaya suna bada haske na ban mamaki* Murmushin yaƙe tayi a ranta ta furta "in dai ni Bilkisu Kachallah ina raye sai na juya ƙaddararki, tauraronki ba zai taɓa haskawaba. Saifuddeen nawa ne ni kaɗai, idan na gama dake har Saifuddeen ya shige cikin ƙasa babu macen da zata sake karambanin shiga rayuwarsa" Kamar wacce aka tsikara sai ta miƙe da sauri tana faɗaɗa murshinta kamar bakinta zai taɓa kunnenta. Tana isa gabansu Asiya ta buɗe hannu ta rungumesu duka biyu nan da nan mutane aka sa tafi, hasken camera ta ko'ina sai wawal-wawal kake gani a hall ɗin. Lokacin da ta sake su ta kama hannun Gwamna, ɗaya hannun kuma ta sa yatsa tana ƙoƙarin taro ƙwalla. "Ikon Allah" Asiya ta faɗa a zuciyarta. Dukkansu uku sai da suka zauna a mazaunin da aka tanada musu sannan mutane suka zazzauna banda ɗaiɗaikun manyan mutane irinsu Alhaji Sani, Umaru Kwom da Yallaɓai da basu tashi ba tun farko. Kujerar Gwamna ce a tsakiya, gefensa na dama ta Bilkisu, gefensa na hagu kuma Asiya. Bilkisu Kachallah ta kalmashe ƙafa sai wani bushashatul wajahi take yi kamar itace Amaryar. MC ya shiga yabon Bilkisu na yadda ta ajiye kishi gefe ta rungumi Amaryar mijinta. MC da azarɓaɓi harda cewa Bilkisu Kachallah tana koyi ne da matan Manzon Allah wanda suke kishi da ilimi. Asiya da jin haka ta ja tsaki. Babu wanda zai ce Amarya bata fito ba. Babu kwalliya na hauka, babu takalmi mai tsini, babu sarƙa na Gwal ko Diamond, babu babu babu. Amma duk da haka Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta burge kowa, shigarta mai sanyi ne daya fito da sahiihin kyaunta, babu ƙyalƙyalin shirme. Queen Bee ce ta bada tarihin Asiya yayinda Alhaji Abdullahi babban abokin Gwamna ya bada tarihin Gwamna. Lokacin da aka zo yanka cake su duka ukun suka haɗa hannu suka yanka. Gwamna ya fara bawa Bilkisu cake ɗin a baki, zai kuma yankawa ta karɓi wuƙan ta yanka ta kai cake ɗin saitin bakin Asiya tana murmushi... Asiya bata yi mamakin ganin 'yan adawa a wajen ba saboda dama haka siyasa ta gada. Umaru Kwom sai washe haƙora yakeyi kace bikin ɗansa ko 'yarsa ake. Haka yazo yai musabaha da Gwamna aka ɗau hoto. Da aka fara ɗaukan hotuna har sai da Asiya ta fara jin hajijiya, sai lokacin ta ankara ma ashe tun karyawar safe bata sake saka komai a bakinta ba. Hoto za'a ɗauka tareda 'ya'yan Gwamna, Asiya tayi baya kamar zata faɗi sai jinta tayi jikin mutum, idonta na rufe dan haka bata san ƙirjin wa ta faɗa ba. Ba ta ma san duk abinda ke faruwa ɗaukansu kawai ake a hoto ba. Bata ma samu kanta ba sai da mutumin da take ƙirjinsa ya jata ya zaunar da ita a kujera mafi kusa da su. Ya miƙa mata ruwa a baki, ta kafa kai ta shanye ruwan tas. Dai dai kunnenta ya furta "are you alright?" Sai lokacin ta ankara da mutumin da take tare da shi shine mutumin data fi tsana a duniya. Gwamna ya murza hannunta yace "kar ki damu hoton ya isa haka" Bai ƙarisa maganar ba Bilkisu ta iso wajen ta saka hannunta a kafaɗar Asiya ta raɗa mata magana a kunne. "What's the meaning of this, na san ba zaki so gobe a rubuta ciki gareki ba ko" "Idan an rubuta, zan faɗa musu cewa cikin Gwamna ne" Babu wanda ya san mi suke faɗa. Ko Gwamna da ke wajen bai ji mi suka faɗa ba. Mutanen da ke wajen sun ɗauka Asiya na yiwa Bilkisu bayanin abinda ke damunta ne. Dinner yayi kyau kowa ya samu abun gulma idan anje gida. 'Yan jarida kuma gobe zasuyi rububin bada bayanin abubuwan da suka faru a wajen taron dinner. Bilkisu ce ta yiwa mutane bayanin cewa Amarya na tare da gajiya dan haka za'a ƙarƙare taron da wuri. Ƙarfe goma da kwata na dare Hajiya Umma da Hajiya Batula suka wuce da Asiya Kachallah house inda aka sa tayi wanka ta shirya cikin wani haɗaɗɗen lifaya kalar baby pink mai zanen flowers ja, fari, purple da kuma yellow. Dake daga wajen dinner kowa gida zai wuce shiyasa babu ko ɗaya cikin 'yanuwan Asiya lokacin da aka kaita ɗakin mijinta. Hajiya Umma da Hajiya Batula kawai ta sani cikin waɗanda suka rakota amma akwai wasu matan kusan su shida da bata taɓa ganinsu ba. Addu'a suka mata da 'yar nasiha sannan suka mata sai da safe. Bayan kowa ya tafi Asiya ta ɗau wayarta ta turawa Umma text. Allah Sarki UWA ko minti biyu bai cika ba Umma ta turo reply tana yiwa Asiya addu'ar Allah ya bata zaman lafiya sannan ta kwantar da hankalinta ta yiwa mijinta biyayya. Asiya na gama karanta saƙon ta fashe da kuka. Kukan taka umurnin Umma da zata yi, kukan hukuncin data yankewa kanta ta ke, wanda shi kaɗai take ganin zai kawo mata kwanciyar hankali a rayuwarta. Bayan ta sha kuka ta ƙoshi ta kwanta akan gadon tana tunanin inama inama. Inama wannan dare tasu ce ita da Ubayd... *** "Mutumina irin wannan soyayya haka. Ka ganka a wajen nan kuwa, kaman wani super man tamkar ƙyaftawar ido har ka tarota jikinka, ni na ɗauka ma ɗaukarta zaka yi sai na tuna akwai sauran burbuɗin kunya a tattare da kai" Gwamna ya harareshi yace "ban san yaushe zaka girma ba" Alhaji Abdullahi ya sa dariya. Bayan sunyi sallama da Abdullahi Gwamna ya haura sama yana takawa a hankali kamar mai tsoron wani abu a saman. Cire kayansa yai ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya cikin riga da wandon bacci masu tsantsi kalar navy blue. A hankali ya sauko ƙasa ya shige sashen da aka gyarawa Asiya. Falo da ɗakuna biyu. A da wajen an ginashi ne saboda Juniour idan ya kai kaman shekaru shabiyar sai ya koma wajen amma yanzu wajen ya zama ɓangaren amaryarsa. Saifuddeen Kachallah bai taɓa tunanin ƙara aure ba tunda ya auri Bilkisu. Bayan ya rasa Misturah bai taɓa sawa ransa zai auri mata biyu ba. Asiya ta zo gareshi ne saboda akwai ƙaddararta a cikin rayuwarsa. Sai dai yayi alƙawarin idan har aka gama ribibin zaɓe komai ya lafa zai sawwaƙa mata ta je ta auri wanda take so, alokacin babu wanda zai yi farautar Kamfen da ita. Bai faɗawa kowa hakan ba amma shawaran daya yanke a zuciyarsa kenan, kuma ya sani hakan ne daidai... Da sallama ya shiga ɗakin Asiya. Tana kwance a tsakiyar gado tana sheshsheƙar kuka. Tausayinta ya ji ya shigeshi. Shi mutum ne da bayaso ya takurawa kowa balle kuma mace. Bata ankara da shigowarsa ba sai da taji ya ɗan taɓa hannunta. Ta yi saurin tashi zaune tana faɗin "lafiya?" Lifayarta da ya saɓule ya bashi damar ganin dogon baƙin gashinta mai tsantsi. Ya ƙurawa gashin ido yana tantamar gashinta ne ko kuma wig. "Na ce lafiya?" "Ahm. Na zo ne na..." lura yai da hannunta na rawa alamar ta tsorata da shi hakan ya sa shi matsawa gefe, sannan ya cigaba. "Kin sani daga jiya matsayinki ya tashi daga Asya 'yar jarida a jihar nan. Hakan na nufin akwai nauyi a kanki. Play your part a matsayinki na Matar Gwamna ni kuma zan sawwaƙa miki a lokacin da komai ya lafa" "Lallai kam, to barin gaya maka idan ma wani abun kake nema ba zaka samu a wajena ba. Gangar jikina, zuciyata, ruhi na duka mallakin Ya Ubayd ne" Magananta na ƙarshe ya shigeshi fiye da zato "Ki faɗi koma minene, hakan ba zai chanja cewa daga yau gangar jikin, zuciyar da ruhin duka Allah ya mallaka min ba" "Babu wanda na tsana irin ka, babu wanda na ke Allah wadarai da rayuwar sa irin ka, sannan ba ni da maƙiyi a duniya da ya wuce ka Your Excellency Governor Saifuddeen Sa'ad Kachallah. Ba za ka taɓa maye gurbin Ya Ubayd ba ko mi zaka yi kuwa" Ta ƙare maganar tana huci. Ta ɗauka zai fusata, ta ɗauka zai nemeta ta ƙarfi amma sai gani tayi ya tashi ya fice daga ɗakin ba tareda ya furta komai ba. 2g Novels Home / THE GOVERNOR'S WIFE / THE GOVERNOR'S WIFE 15 THE GOVERNOR'S WIFE 15 2g novels THE GOVERNOR'S WIFE *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 15 Washegari da Asiya tayi sallar Asuba komawa bacci ta yi sai ƙarfe goma aka fara buga mata ƙofa. Jiya bayan Gwamna ya fita daga ɗakin kullewa tayi dan bata yarda da shi ba. Lokacin da ta buɗe ƙofa wata mata ta gani sanye da uniform riga da wando da ƙaramin hijabi kalar ruwan ƙasa. "Ranki shi daɗe fatan kin tashi lafiya. Na zo tambaya ne shin abin karinki a kawo shi falonki ne ko a barshi a dinning room?" "Ki kawo min ɗaki" "Shikenan, barin kawo" Bayan ta karya kiran Faty da Sumayya ta yi ta musu ban gajiyar biki. Da ta kira Queen Bee tsiya ta dinga mata wai ƙila an samu ɗan Gwamna jiya da dare. Asiya tace Allah ya sawwaƙa. Duk da ta yiwa Ummanta text da Asuba sai da ta sake yi mata wani text ɗin tana tambayarta ko 'yan biki sun gama tafiya. Ƙarfe shaɗaya da rabi, Uwani matar data kawo wa Asiya abinci ɗazu ta zo ta sanar da ita cewa tayi baƙi. Asiya ta zura hijabi ta fito babban falo inda baƙin ke jiranta. Wasu mata ne guda huɗu dukkansu babu wanda ta sani a ciki. Jagorarsu ta mata bayanin ko su ɗin su waye, sannan suka faɗi abinda ya kawosu wai sun zo gaisheda Amarya. Women leader ce ta jam'iyya da kuma shugaban ƙungiyan Mata 'yan kasuwa da Sakatarorinsu. saura kaɗan Asiya ta ce musu ko uban mi zuwansu zai ƙara mata sai kuma ta dakatar da harshenta. Ta musu godiya bayan sun ajiye mata kyauta, ta haɗa da cewa da basu yi wahalar kawo komai ba. Asiya ba tayi minti shabiyar da shiga ɗaki ba aka sake zuwa kiranta wai tana da baƙi. Wannan karan su Hajiya Batula ne da wasu 'yanuwan Gwamna suka zo mata sallama dan zasu wuce garuruwansu. Haka baƙi suka dinga zuwa mata gaisuwa har dare. Ƙarfe bakwai na yamma ta ce da Uwani duk wanda ya sake zuwa ace ya dawo gobe. Bayan ta bada umurnin sai kuma chan ƙasan ranta ta fara tunanin tun yanzu har ta fara bada umurni, ita ɗin fa ba kowa bace. *** "Mommy zan je gidan mu, akwai wasu kayana da na ke son ɗebowa" "Nana duk kayan da suke nan basu isheki ba" "Kai Mommyyy, kin san dai ba komai muka ɗauko ba da zamu dawo nan" "Naji, je ki amma ki dawo da wuri, sannan ba ruwanki da jikar maiƙusumbi" "Yes Mom" Daurewa kawai take amma tun safe take neman hanyar da zata zo ta ga Asiya. Airah data kasa ta tsare ne ta hanata zuwa. Asiya na sallah Nana ta faɗo mata ɗaki babu ko sallama. Sai da Asiya ta sallame ta juya ta ga Nana zaune a kujera tana murmushi. Ta ganeta saboda kamannin Gwamna gareta har dimple ɗinsa. "Lafiya za ki shigo min ɗaki babu sallama?" "Haba Amaryarmu, nan ma fa gidanmu ne" "Idan gidan ku ne, ai ba ɗakin ki bane. Tashi ki fita " "Haba Anty nah" ta faɗa tana bubbuga ƙafa tana tura baki Lallai yarinyar nan sangartacciya ce. Asiya ta faɗa a ranta. "Anty dan na zo gaishe ki shine zaki kore ni" "Ya sunan ki ma?" "Nana Khadijah" "Fita min daga ɗaki Khadija. Nagode da gaisuwa" Nana ta miƙa mata hannu tace " please be my friend" "Kin san Allah idan baki fita ba zan wanka miki mari" "Ok, goodnight Sweet Anty" Asiya ta bi bayanta da kallo tana taɓe baki... Washegari ƙarfe tara na dare Gwamna ya shigo gida. Asiya na jin shigowarsa ta fito da sauri tabi bayansa suka haura sama tare. Da safe ya bata key ɗin mota wai kyauta daga Alhaji Sani Kachallah sannan yace duk lokacin da zata fita akwai Dreba da zai fita da ita Zai buɗe ƙofar falonsa tace " inada magana" Bai amsa mata ba ya kutsa kai ciki. Sai da ya zauna ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya sannan yace " ina ji" "Ina so ƙanwata ta zo ta tayani zama. Sannan ina son kawo Driver nawa na kaina" "Mi ya samu Dreban da aka baki?" Yai maganar yana tsareta da idanu. "Na fi son wanda zan yarda dashi ɗari bisa ɗari" "I see. Ki submitting CV ɗinsa a duba" " Yayana ne, Ubanmu ɗaya, akwai wani CV daya wuce wannan?" "Ta ya zan yarda cewa wanda ki ka faɗa shi ɗin za ki kawo?" Ta ji zafin maganansa amma ta dake tace " ka iya sawa a mana DNA test da ni da shi" Yai murmushin gefen baki yace " abu ne mai sauƙi ai" "Sannan abu na gaba. Bana son kuɗin jini, kuɗin talakawa. Kasan yadda za ka yi ka cire kuɗin da ka zuba a account ɗina yau da rana, bana buƙatarsu" Miƙewa yai yace " gudummawa ce da Ahalin Kachallah suka miki, idan ba kya buƙata ki tuntuɓi Hajiya Umma ki mata bayani" "Zan iya kawo Sumayyan? ko itama sai da DNA test" "Zasu iya zuwa" ya furta sannan ya wuce wani hanya wanda take ganin a nan ɗakunan sashen suke. Tana shiga ɗaki ta kira numbar Yaya Bello. Yana nan teburin mai shayi ana rikici da shi akan kuɗi ta kira. Daga wajen da yake yana ɗaukan kira ya fara cewa "gashi nan ai ƙanwata Matar Gwamna ke kira" "Yaya Bello" "Hello Asiya, Hello esselenci. Esselenci kina jina" "Ina ji Yaya, ya kuke" "Lafiya lau muke. Ya Gwamna?" Asiya ta katse zancen da cewa "Yaya inada aiki da zan baka, idan babu matsala" "Wallahi zan yi" Lokacin data faɗa masa direbanta take so ya zama wani tsalle ya daka yana ihu. Yaya Bello ya girmeta da kusan shekaru shahuɗu amma bai damu da cewa ƙanwar bayansa zai dinga tuƙawa ba. Shine babban ɗa namiji acikin 'ya'yan Ale Faruƙ amma kuma shine marar aikin yi walaƙantacce. Shaye-shaye ya lalata masa rayuwa. Lokacinda yake yaro shekara goma shabiyu zuwa shabiyar haka, ya taɓa halin ɓera, da abin ya ishi Ale sai ya kaishi wajen Gwani. Gwani ya dinga masa addu'a yana bashi ruwan rubutu har ya zo ya rabu da abun. Daga baya daya bi wasu abokai suka tafi chan kudu leburanci shikenan ya lalace da shaye-shaye. Baya bin mata, dan akoda yaushe addu'ar Gwani Allah ya raba shi da sata da kuma zina. A shekarar da Gwani ya rasu a shekaran ya dawo gida. Bai dawo da komai ba saboda komai ya tafi a shan abubuwan maye. Ale ya masa aure ya buɗe masa shago ko zai nitsu amma inaa. Kafin wata shida komai ya ƙare a shagon, ita kuwa Amarya shekara ɗaya tayi da 'yan kwanaki iyayenta suka sa ya saketa saboda tunda aka kawota ko hannunta bai taɓa riƙewa ba. Ale ya kaishi wajen wani abokinsa mai maganin gargajiya a duba shi ko bashida lafiya ne, amma akace lafiyarsa lau. Ƙannensa maza biyu sun yi aure harda 'ya'ya, sannan suma kasuwancinsu ya fara bunƙasa tun lokacin da Ale ya yaye su daga kasuwancinsa, amma Yaya Bello kam sai zaman daba... *** Asiya na aiki a laptop ɗinta Sumayya ta shigo ɗakin da sallama. "Kai Anty na gaji" ta ajiye jaka ta faɗa kan gado "Tun yanzu? Shekara huɗu zaki yi, idan kuma aka shiga yajin aiki ƙila kiyi biyar ko shida" "Kai! Allah ya sawwaƙa" "Welcome to the game sister, haka muma muka yita cika bakin nan, daga ƙarshe sai da muka ƙara wata biyar akan shekaru huɗun daya kamata muyi" "Anty kin san me, wata a ajinmu tace tana son ƙawance dani, ta nuna min hoton da mukayi a wajen dinner ashe nima na zama celebrity" "Ban yadda ba" "Iye?" "Ban yadda da ƙawancen nan ba. Duk wacce za ta shiga jikinki saboda ke ƙanwar Matar Gwamna ce ba ƙawa ce da zata ɗore ba. Sannan ina so ki sani cewa matsayina na Matar Gwamna na lokaci kaɗan ne" Sumayya tayi saurin miƙewa zaune. "Anty dan Allah kada kice min za ki bar gidan nan. Kwana biyu dana yi a gidan nan ban taɓa gani kin shiga sashen Gwamna ba, idan ya dawo ko..." "Bana son gulma. Kada ki bari wani matsayi ya ruɗe ki dan ba mai ɗorewa bane" Sumayya ta riƙe baƙi tana kallon Asiya da hankalinta ke kan abinda take ta rubutawa a laptop ɗinta. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, Sumayya ta je ta buɗe. Da ta dawo ta miƙawa Asiya wani envelop tace Uwani ce ta kawo. Asiya ta karɓi envelop ɗin ta yaga ta fito da wasiƙar ciki. "Shegiyar mata wai office of the first lady, ko uban wa ya bata office oho" "Anty minene?" "Bilkisu Kachallah ke gayyatata taron gajiyayyu da naƙasassu da za ayi gobe Asabat a foundation ɗinta" "Anty zaki je?" "Idan ban je ba ai ta ci nasara a kaina"... Tunda aka kawota bata taɓa fita ba, a ranan da ta yiwa Yaya Bello maganan zama Direbanta washegari ya niƙo garinsa ya taho. Kiran Yaya Bello tayi a waya tace masa gobe za su fita za ta aiko Sumayya da key ɗin mota ya duba lafiyar motar. Washegari kuwa ƙarfe shaɗaya Asiya da Sumayya suka wuce wajen taro. Lokacin da suka je an tanada mata waje na musamman kusa da Bilkisu Kachallah. Tana zama Bilkisu tace "ƙarfe goma aka fara taro, nan gaba ki duba agogonki da kyau" "Ohh sorry! Kin san yau Excellency zai bar gidana, dole na kimtsa shi kafin na fito. Kin san ai yana jimawa a banɗaki idan zai yi wanka, da muka shiga tare kuwa na yi ƙoƙarin na dirzashi da kyau amma dana taɓa shi sai jikinsa ya ɗau mazari..." "Shut up!" Bilkisu ta faɗa a fusace, bata san ma maganar ta fito da ƙarfi ba sai da ta ga wanda suke kusa da su na kallonta. Sai ta bige da kama hannun Asiya tana dariya kamar irin wasan nan take. Asiya ta yi murmushin nasara, yau duk ta inda Bilkisu Kachallah za ta fito tana nan dai dai da ita. Kiran Bilkisu Kachallah da aka yi ta zo tayi bayani nan take naƙasassun wajen suka fara tafi suna kiran sunanta. Ko da za su shigo hall ɗin abin daya fara ba wa Asiya haushi shine UWAR MARAYU da aka rubuta a saman hoton Bilkisu Kachallah. Bilkisu ba ta yi kama da macen da za ta so talaka ba balle maraya amma da sannu za ta karya mata fiffiken da take furkawa da shi. Maganan minti shabiyar tayi sannan ta ce zata kira 'yaruwa, ƙanwa, kuma abokiyar zamanta ta zo ta faɗi abu ɗaya ko biyu a wajen duba da cewa ita ɗin ma ta fito daga tsatson naƙasassu. Asiya ta cizi leɓenta lokacin da Bilkisu Kachallah ta kirata da 'yar Kurma jikar maiƙusumbi. " Hajiya Asiya Kachallah" MC ɗin wata mata wacce bleaching ya gama koɗar mata da fiska ta sake kiran Asiya a karo na biyu bayan Bilkisu ta koma ta zauna. Dai dai zata tashi taji Bilkisu tace "maza aje a gaya musu yadda ake kula da naƙasassu" Sallama Asiya tayi lokacin data karɓi mic a hannun MC. Jin an amsa ƙasa-ƙasa ya sa ta ƙara maimaita sallamar da muryarta mai kaifi, wannan karan suka amsa da ƙarfinsu. "Barin baku wasu labarai masu daaaaɗiiiii" ta ja ƙarshen maganar tana juya hannunta. Nan da nan aka saka dariya "Akwai wani yaro da aka haifeshi da ƙusumbi shekaru tamanin da biyar da suka wuce. Aka damƙa shi wajen wani malami dan yai karatu tun yana shekara shida haka. Wannan yaro yai karatu sosai a wajen Malaminsa dama wasu Malaman daban. Yai aure Allah ya azurta shi da 'ya'ya uku Maza. Wannan yaro mai ƙusumbi ɗinkin hula yake yana ciyar da iyalinsa da gumin hannunsa har Allah ya ɗau ransa. Sai dai kun san me? Kafin ya rasu yayi karatun ƙur'ani, ya ji haddan Ƙur'ani har mutane su ka rinƙa kiransa da Gwani. Wasu daga cikin ɗalibansa sun ce kafin Gwani ya rasu ya rubuta ƙur'ani daga farko har ƙarshe da ka sau ashirin da ɗaya wasu ma su kance sau talatin ne. Lokacin da Gwani ke ciwon ajali kafin a bashi abinci ya ci sai ya yi ƙoƙari ya rubuta ayoyin ƙur'ani a Allonsa kafin ya ɗanɗani abincin. Har ya koma ga Allah bai taɓa roƙo ba, bai taɓa zuwa maula wajen Attajirai ba. "Akwai wata mace dana sani da aka haifa da lalurar kurmanta, aka mata aure, suka rabu da mijinta da 'ya ɗaya tsakaninsu. Wannan mata ta sake aure mijinta ya taimaka mata ta fara karatun yaƙi da jahilci. Ta koyi sana'ar ɗinki da saƙa, yanzu haka matar nan Allah ya rufa mata asiri tana ɗinki tana kuma saida kayan sanyi irinsu, Zoɓo, kunun Aya da sauransu. "Akwai wani gurgu a ƙasan layinmu kullum idan zan wuce Islamiyya yana zaune a ƙofar gidansa yana gyaran takalmi , da Allah ya yassara masa har takalma ya saro na maza da mata yana saidawa, duka a ƙofar gidansa. "Lokacin da nake bautar ƙasa a wani gidan talabijin akwai wata mata makauniya wacce ke gabatar da shiri na musamman dan wayae da kan al'umma akan mahimmancin ilimi wa naƙasassu. Inaga za ku tuna da Dr Hajiya Laraba Bakatsine wacce ta rasu farkon shekaran nan, ga wanda basu sani ba degree uku ta yi kuma duka da lalurar makanta. "Abu na ƙarshe da zan faɗa shine, naƙasa ba lasisi bane na yin barace-barace ko maula. Ina so ku sani Naƙasassu na da damar yin kasuwanci ko sana'a, sannan su nemi ilimi kamar kowa. Ina fata Gwamnati za ta bawa naƙasassu damar yin kasuwanci d neman ilimi kamar kowa. Mu tashi lafiya" Kafin ta kai kujerarta wani gurgu ya turo kekensa ya sha gabanta, idonsa fal da hawaye ya haɗe hannunsa biyu ya fara mata godiya, kan kace me, naƙasassu sun yanyameta suna mata godiya. Maganganunta sun taɓa naƙasassu da dama a wajen, wanda zuciyarsu ta kafe kuwa, sun sawa ransu cewa bara sana'a ce kuma ko me za a musu sai sun je Kudu sun yi sana'ar su. Yadda ka san sassaƙa Bilkisu akayi haka ta daskare akan kujera ta kasa motsawa. Ba ta hango wannan ba, ba haka ta shirya ba. Da ƙyar ta iya tashi lokacin da aka kirata ta zo ta rufe taro da addu'a. Asiya ta yi murmushi lokacin da taji Bilkisu tace ayi salati wa Annabi amma ba ta buɗe baki anji salatin ba, sai ta rufe ido tana muimui da baki kaman Akuya na cin ciyawa... *** A wani ƙaramin ɗaki kuma wata mace ce sanye da riga da zani da ɗankwali dukkansu daban-daban. Kallo ɗaya zaka mata ka kirata 'yar ƙauye, sai dai yanzu da take gaban wata na'ura tana magana da harshen faransanci dole ka kirata gogaggiyar 'yar boko, yadda take magana da harshen ka ce a birnin Paris aka haife ta. Cikin bayaninta take bayyana cewa har yanzu bata samu ƙwaƙwƙwaran hujjar da take nema ba, amma kuma tanada yaƙinin za ta samu nan bada jimawa ba. Babu tantama matar da take bincike akanta tana kasuwancin miyagun ƙwayoyi, amma saboda matsayinta ba za a kamata ba sai da hujja mai ƙarfi. Hujjar take nema sama da shekara ɗaya da take aiki da ita. "Ba matsalata Bilkisu Kachallah ba, matsalata Madam Bintu ce ka sani. Dan haka ba ruwana da matar da Gwamna ya aura, that's his business" Mutumin da take magana da shi yace "akwai jami'ar DEA da zata zo daga America kan batun safarar miyagun ƙwayoyi, idan ta iso zan haɗaki da ita. Agent Dahlia tanada interest sosai akan case ɗin nan, kuma na san za ta taimaka sosai" "Yes Sir" daga haka ta rufe na'urar ta ɓoye shi a ma'ajiyarsa... "Hansa'u...Hansa'u...Hansa'u" Masu aiki uku ne a gaban Bilkisu Kachallah amma ba su take nema ba. Hansa'u ta iso da gudu tana faɗin "Hajjaju nah ki gafarceni, sallah nake" Bilkisu ta ce " Sallan Uwarki, matso nan" Hansa'u ta matsa kusa da ita kafin ta gama matsawa ma Bilkisu ta ɗauketa da mari tana faɗin " dan Ubanki kashe min ɗa zaki yi? " "Hajiya wane Ubana" Hansa'u tayi maganar tana sosa kumatu "Uban me ya hana ki sawa junior inhaler a aljihunsa?" Ta sani lokacin data shirya Junior ta saka masa inhaler a aljihun wandonsa sai dai in cirewa yai, amma a yadda Bilkisu Kachallah ke tiriri ba zata saurari bayaninta ba sai dai kawai ta bada haƙuri. "Tuba nake Hajjaju, mantawa nayi" Bilkisu ta sake kai mata duka tana faɗin "idan haka ya sake faruwa sai na yanka ki a gidan nan" Abu biyu ne ya haɗuwa Bilkisu, na farko ta ƙumso baƙin ciƙin Asiya, na biyu kuma ta shigo falo ta samu ɗanta na kokawa da numfashi babu kowa kusa da shi. Saboda mijinta da ɗanta na da lalurar Asthma ba a rasa inhaler a jakarta. Hakan ya sa ta ciro ta jakarta ta matsa masa a baki. Hansa'un dai aka saka ta goyi Junior ta wuce da shi ɗaki. Da dare da Gwamna ya dawo gidan Gwamnati saboda kwanan Bilkisu ne. Bilkisu ta same shi ta fara sauke masa fushinta. "Saifuddeen sati ɗaya da zuwanta amma har ka fara nuna banbanci. Ta ya zaka siya mata sabon mota bayan akwai mota a gidan da za ta yi amfani da shi. I thought you said you married her for political reason, miyasa kake wanka tare da ita? Have you slept with her?" Gwamna ya fara rage kayan jikinsa ya manta da ita a ɗakin. A gajiye yake baya son abinda zai ɗaga masa hankali. "Saifuddeen ka gaya min gaskiya, ka..." "Wanda suka kawo miki gulmar za ki tambaya bani ba" "Ita da bakinta ta faɗa min yau kun yi wanka tare" Har ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa yai murmushi ya wuce banɗaki. Kafin ya kulle ƙofa Bilkisu ta faɗo ciki tana faɗin da ita zai yi wanka. Lokacin da Sakatare ya nuna masa video na abinda ya faru a wajen taron da Bilkisu ta shirya ya jinjinawa Asiya saboda tarko Bilkisu ta ɗana mata lokacin da ta kirata da 'yar Kurma jikar maiƙusumbi. Ya sani ta so Asiya ta harzuƙa ne ta faɗi baƙaƙen maganganu a wajen ko ma ta zagi Bilkisun da wani abu, sai kuma Asiya ta nuna mata cewa ita ɗin 'yar jarida ce. *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 16 Asiya da Sumayya na cin abincin dare Sha'awanatu Bacchi ta kirata. Jinjina ta mata kan abinda ya faru a wajen taro, ta bata shawaran kada ta taɓa bari Bilkisu Kachallah ta taka ta sannan idan tana son samun matsayi sama da Bilkisu dole ne ta koma gidan Gwamnati. Asiya ta mata godiya ta ajiye wayar tana murmushi. "Anty Ale ya kira wayarki ɗazu da kika shiga banɗaki" "Kin ɗauka?" "A'a" "Good" "Anty, har yanzu fishi kike da shi?" Asiya ta ajiye cokalin hannunta tace "taya ba zan yi fushi ba Sumy. Bayan kuɗin da Mutumin nan yake da shi, bayan kuɗin daya karɓa a wajen 'yanuwan Gwamna, kwanana huɗu da aure ya kirani yana cewa na nema masa kwangila a wajen Gwamna. Wani uban ƙwarai zai yiwa 'yarsa haka. Dan ba a chanja Uba ne da tuni na chanja shi" Sumayya ta sa dariya. Basu gama cin abincin ba Nana ta kira Asiya. Ko a ina ta samu numbarta oho. "Antyna ina gayyatarki birthday na da za'ayi ranan Friday. Dan Allah ki zo" "Wai ni yarinyar nan mi kika ɗaukeni ne?" "Please Sweet Anty" Asiya ta yi shiru na 'yan sakanni kafin ta ce "zan zo" Tana ajiye wayar tace "inaga Gwamna mahaukata ya ajiye a gidansa" Sumayya ta kwashe da dariya ta ce "Anty ai harda ke" "Zan saɓa miki Sumy. Ni sa'ar ki ce" "Anty ke fa kika faɗa da bakinki" "Da matarsa da 'yarsa duk basu da kai, ranan da ta zo nan kinga yadda take girgiza kai kaman notinan kanta sun kunce, ni cewa ma nayi kan roba gareta" "Kai! Anty" Asiya ta sa dariya. *** "Babu birthday wannan karan. In fact har na bar kujeran nan babu birthday, babu anniversary, babu wani celebration da za ayi sai dai biki ko suna" "Wasa kake Saifuddeen. Mun yiwa Junior nashi farkon shekara ita kuna Nana sai kace ba za a mata ba. Ina ruwana da abinda mutane za su faɗa. Mu fa ba matsiyata bane, babu abinda muka rasa kafin ka hau kujeran nan dan haka dole ne mu kashe kuɗi wajen taya first born ɗinmu murnan cika shekara shabiyar a duniya" " lokacin da Mahira tace ba ta son birthday ta gudu wajen Dadda, wani abu ya sameta da ranan ya zo ya wuce ba tareda anyi komai ba" "Darling Mahira daban Nana daban" "Dukkansu 'ya'yana ne Bilkisu. Kuma yadda ba ayi na Mahira wannan shekaran ba, ba za ayi na Nana ba" Bilkisu ta matso kusa da shi, ta riƙe hannunsa tana murzawa a hankali, ta sassauta murya tace " na san baka son abinda zai jawo maka magana a gari, nima bana son haka. Ka yi haƙuri muyi mata small get together birthday party, acikin gidan nan, daga ƙawayenta sai 'yanuwa. I promise babu, 'yan jarida da za su zo. Na yarda Mahira ba ai mata birthday ba wannan shekaran, amma kasan itace tace bata so, Nana kuma tana so. Ba kuɗin Gwamnati zamu yi amfani da shi ba ka sani. Na maka alkawarin ni zan ɗau nauyin komai daga aljihuna" "Still dai..." Shhhh ta faɗa tana rufe masa baki da yatsunta biyu. Ta sani an gama kenan, Saifuddeen mijinta bai iya dogon jayayya ba... Ranan Alhamis Gwamna Saifuddeen Kachallah ya wuce Birnin tarayya wani taro da za su yi na Gwamnonin Arewa. Ranan Jummu'a kuwa Bilkisu Kachallah ta shiryawa 'yarta bikin birthday. Babu taro sosai saboda taron strictly na wanda aka gayyata ne. Ana tsakiyar taro Asiya ta zo, Nana na ganinta lokacin za ta yanka cake ta je da gudu ta rungumeta. Bilkisu Kachallah ta hangame baki tana mamakin 'yarta. Asiya ta karɓi ɗan ƙaramin akwatin gift da ke hannun Sumayya ta miƙawa Nana ta ce "Happy birthday" Nana ta sake rungumeta tana faɗin "thank you, thank you" An ci, an sha, an bada kuma an karɓi kyaututtuka. Ana daf da za a rufe taro Asiya ta tafi. Da Asiya ta dawo gida, dare ta bi tana tsara labari a laptop ɗinta, da ta gama ta turawa Mr Bassey tareda hotunan data ɗauka. Washegari jaridar Climax ta fito da labarin birthday ɗin 'yar Gwamna. Hoton Nana sanye da wata matsatstsiyar doguwar riga kanta babu ɗankwali shine a shafin farko na jaridar, an rubuta *Gwamna Saifuddeen Kachallah ya zubar da miliyoyi wajen yiwa 'yarsa birthday* A ƙasan labarin kuwa irin ɓarnar kuɗi da akayi aka lissafo, tun daga decoration, abinci, cake, souvenirs dama kayan da Nana da Bilkisu Kachallah suka dinga chanjawa a wajen, duk an bayyana. Daga ƙarshe aka ƙiyasta jimillar kuɗin da aka kashe zasu kai miliyan arba'in. Lokacin da Bilkisu Kachallah ta ga jaridar Climax cilli tayi da wig ɗin kanta tana faɗin koma waye yai rubutun nan sai ta sa an ɗaure shi. Ta kira wani numba tana faɗin a nemo mata wanene ke da jaridar Climax, sannan tana son sannanin ɗan jaridar daya yai rubutun nan. Duk wanda suka zo bikin sai da aka karɓi wayoyinsu saboda ba a son ɗaukan hoto. Mai hoto ɗaya ne ta yadda ya ɗau hotuna a wajen, cousin ɗin Nana ne ɗan Anty Rufaidah, babu yadda za ayi ya siyar da hotunan Nana wa 'yan jarida. Koma waye ya fitar da hotunan nan sai ta sa an hukunta shi. Gwamna Saifuddeen na ɗakin hotel da suka sauka Chief of Staff ya nuna masa jaridar Climax a wayarsa. Gwamna ya haɗiyi yawu da ƙyar. Ba abinda aka rubuta ne ya dameshi ba sai ganin duk cikin hotunan Nana da aka ɗaura babu wanda tayi shiga na mutunci aciki. Ya cizi leɓensa na ƙasa yana inama Nana a wajen Dadda ta taso kamar yadda Mahira ta taso a wajenta, ƙila da duk wannan ba zai faru ba. Da farko Bilkisu ya ɗaurawa laifi daga baya kuma ya gane cewa shine silar komai, ya barwa Bilkisu ragaman tarbiyyan 'ya'yansa bayan ya san irin tarbiyar da itama ta taso a kai. "Wa ye keda jaridar Climax?" Ya tambayi COS bayan wasu mintoci daya ɗauka bai yi magana ba. "Da dai wani ne Mr Emmanuel Bassey amma na ji ance wani ɗan siyasa ya siyi jaridar watanni biyu da suka wuce" "Ka bincika min waya siya" "An gama excellency" *** Asiya kuwa tsaf ta shirya dan fara aiki da investigative reporter mai suna Fou'ad Salisu. Shekaransa uku da fara aiki amma ya fitar da manya-manyan report guda biyu da ya ɗaukaka shi a ƙasar da ma duniya baki ɗaya. Fou'ad ya yiwa Asiya alƙawarin binciko mata abin da take nema cikin ƙanƙanin lokaci... Asiya na zaune akan kujera ta harɗe ƙafafuwanta, hannunta ɗaya riƙe da waya tana karatu, ɗayan kuma soyayyiyar gyaɗa take ci da shi. Lokaci lokaci ta kan yi dariya. Wannan karan da ta fara dariya harda tunkuɗe kwanon gyaɗa da ke gefenta. Sumayya da ke rubutu a kan carpet ta ɗago ido ta kalli 'yaruwarta tana tambayarta ko lafiya. Sai da Asiya ta yi dariya ta isheta kafin ta ce "wani waƙar KaSaSa nake karantawa wai Attaruhu, kin ji abin dariya. Kai matar nan Allah ya bata baiwar tsara waƙa. Bari ki ji na karanta miki..." Sallamar Uwani ya katseta. "Ranki shi daɗe kinada baƙi a falo" "Su waye?" "Yaya Bello ne da wani tsoho" Asiya ta kalli Sumayya, Sumayya ta kalli Asiya, dukkansu suka haɗa baki wajen faɗin "Ale". Asiya ta sako hijabi ta fito yayinda Sumayya tace fir bazata fito ba. Ale na zaune yana kora lemu Asiya ta shigo falon. "Matar Gwamna" Ale ya faɗa da ƙarfi kaman wani Yaro. Asiya ta haɗe rai ta zauna nesa da su tace "Baba lafiya?" "Haba Asiya Shahidan Baba. Babu gaisuwa sai tambaya" "To ai ni ban taɓa jin inda aka yi aure sati biyu Baban Amarya ya fara bibiyar 'yarsa ba, sai dai idan babu lafiya ne" "Lafiya ƙalau muke, su Baffanki ma sun ce na gaisheki" Yaya Bello ya miƙe yace "barin barku ku tattauna" Asiya ta harareshi dan ta san shine zai yiwa Ale kwatancen gidanta. Sai kuma ta tuna Ale da Yaya Bello basa shiri. "Tunda na miki maganar kwangila kika dena ɗaukan kirana. Haka ake yi, ko kin shigo daula kin manta da iyayenki ne" "Ban manta da iyayen da tunda nayi aure suke aiko mani da addu'a ba. Amma na manta da Uban da ke maula a wajen mijin 'yarsa" "Asiya!" Ale ya faɗa yana miƙewa a fusace. Basu ji shigowar Gwamna falon ba sai da yai sallama. Asiya ta kalleshi ta kauda kai yayinda Ale ya shiga gaishe shi jiki na rawa. "Asya" ya kira a hankali. Ta ɗago ido ta kalleshi "Follow me" A tsakiyar falonsa ya tsaya, ya juyo ya kalleta. Yana tattare da fushin Bilkisu da Nana abinda ma ya hana ya fara wucewa chan gidan kenan, ya biyo nan ne saboda ya ɗan huce kafin ya je gida, kada garin fushi zuciyarsa ta sa shi aikata abinda bai dace ba. To gashi ya zo nan ma itama wannan Attaruhun tana yiwa mahaifinta rashin kunya. "Disrespecting your father Asya. Kin san darajan Uba kuwa, kin san mutane nawa ne a duniya ke kukan rashin Uba. Ba zan lamunci wannan ba, ki je ki bawa mahaifinki haƙuri" "Ba abinda zan yi. Ba a chanja Uba amma ni na chanja ranan da ya sayar maka ni. Idan ba zaka lamunta ba ka sake ni mana, ai kasan yadda nake sarai amma ka nace sai da ka aureni saboda zalin....ci" Numfashinta sai da ya kusa ɗaukewa saboda matsowa da Gwamna yai daf da ita. Kallo ɗaya ta yiwa ƙwayar idonsa ta san babu wasa tattare da shi. "Na gaya miki iya zaman da za mu yi tare dole ne ki riƙe matsayin Matar Gwamna da kyau, which means duk wani rashin kunya, shirme da shiririta za ki ajiye su gefe. Ki je ki bawa mahaifinki haƙuri kafin raina ya ɓaci" Ai da sauri Asiya ta bar falon. Bata manta kashedinsa ba, daren farko da aka kawota gidan. Ya riga ya san abu ɗaya take tsoro, kuma da shi ne kawai zai iya maganinta. Ale na zaune yana jujjuya maganganun Asiya a ransa, Asiya ta shigo falon. "Kayi haƙuri Baba" Asiya ta faɗa ba tareda maganar ya kai zuciyarta ba. Ta tsani halin mahaifinta fiye da soyayyar da take mishi. "Ya zan yi da 'ya'yan zamani. Allah ne ya baki wannan matsayi Asiya, ni ba sayar da ke nayi ba. "Na ji daɗi da kika kawo Bello kusa da ke, ina fata za ki nutsar da shi ya dena shaye-shaye, yai ƙoƙarin ajiye Iyali. Na barki lafiya" "Baba" Asiya ta kira da muryar kuka. Ale ya juyo ya kalleta jikinsa a sanyaye. "Ka yafe min dan Allah" "Na yafe miki, nima ki yafeni in Allah ya so ya yarda ba zan sake yi miki maula ba" "Haba Ale Faruƙu na gidan Tabawa da Gwani Lukman. Ni fa ban ce kana maula ba, inaga dai daga TV ka ji wannan maganar" Ta yi maganar tana kamo hannunsa ta zaunar da shi a kujera. Wani abu ta gani a idonsa lokacin da yai maganarsa ta ƙarshe. Bata taɓa tunanin Ale zai ji kunya ko yai danasanin wani abu ba, amma yau ta ga kunya a idonsa, ya yi danasanin neman alfarma da ya zo yi. "Baba barin shiga kitchen da kaina na maka girki" Ale yai dariya yace "Ina Sumayye? ko ta je makaranta" "Barin kira maka ita". Asiya ta shiga kitchen ta zage ta yiwa Ale girki. Tuwon shinkafa miyar kuka da ya ji naman kaza ta yi, ta haɗa masa da tacaccen juice ɗin Kankana da Abarba. Ale ya ci abincin sosai ya kuma sa albarka. Da zai tafi ya ce ta gaishe masa da Gwamna ya ajiye mata kyautar da ya kawo wa Gwamna na tacacciyar Zuma a cikin jarka 5 liter. Ga mamakin Asiya lokacin da ta shiga falon Gwamna sai ta sameshi a dining table yana cin abincin da ta girka. Ta san dai ta ɗebi abincin Ale sannan ta barwa Sumayya ta kwashe sauran. Yaushe Sumayya ta haura sama ta kawo masa abinci bata sani ba?. Tukunnama dama tuntuni bai fita bane. Ita ba sanin ranakun ta yi ba balle ta gane yau kwananta ne ko ba nata bane. Bata taɓa masa girki ba, idan ya zo gidanta bata san ya yake cin abinci ba, bata ma san su waye ke gyara masa sashensa ba. Gaskiyar Sha'awanatu Bacchi ne da tace dole ta koma gidan Gwamnati. Idan suka cigaba da zama irin haka ba zata rinƙa samun bayanai akansa ba. "Babana ya wuce, ya bayar da wannan a baka" Ta ajiye jarkar kusa da ƙafarsa. Bata san ya akayi ta tsaya kallon ƙafarsa ba, babu takalmi a ƙafarsa, jallabiya ya saka hakan ya sa zaman da yai ya bayyana silangarinsa da ƙafafuwansa. Ta kan ce Ya Ubayd na da marteten ƙafa, mai kauri, mai faɗi. Har tana tsokalarsa idan suka yi aure sai dai ya dinga saka safa saboda ƙafarsa ba ta da kyau. Ta zubawa doguwar ƙafarsa ido, ƙafar a mulmule take da gani zai yi laushi, yanada dogin yatsu cike da baƙin gashi zara-zara da suka ƙarawa ƙafar kyau. "Ƙafar ne yai miki kyau ko neman wajen da zaki ɗaura min jarkar kike?" "Allah sawwaƙa, mi zan yi da baƙin ƙafa kamar na Burgu" Murmushi yai har saida haƙwaransa suka fito. Asiya ta yi saurin ajiye jakar ta juya. "Ki shiga min da shi ɗaki, Please" "Ban san wanne ne ɗakin ka ba" "Kin taɓa tambaya ba a nuna miki ba?" "Zan nema da kaina" Ɗakin farko da ta duba a kulle yake, na biyu ma haka, na ukun da ta shiga ta ajiye masa jarkar kusa da gadonsa. Ɗakin ya mata kyau sosai, tun daga design zuwa furnitures da aka saka. Ta buɗe ƙofa kenan tayi kiciɓis da Gwamna zai shigo. "Har kin gama ganin ɗakin?" "Babu abun kallo ai" "Na ɗauka za ki tsaya muyi wanka tare ai" Yai maganar yana kanne mata ido. Ƙirjinta ya shiga lugude. Iya zaman da za ta yi da shi ba abinda zai shiga tsakaninsu, jikinta da ruhinta duk na Ubayd ne. Ta tsane shi, daga nesa zata gama cika baki akansa amma yana zuwa kusa da ita ƙwaƙwalwarta sai ya juya ya fara kawo mata wasu tunani daban. Matsawa yai ta fice daga ɗakin ba tare da ta iya furta komai ba. *** Umaru Kwom na zaune a guest house ɗinsa tareda wasu mutane guda biyu. Ɗaya member ne na House of Assembly, ɗayan kuma mai bashi shawara ne. "Idan har aka tsige Saifuddeen Kachallah banida matsala da Alhaji Yamai, saboda tamkar na lashe zaɓe ne an gama" "Kana ga za a tsige Saifuddeen Kachallah? Mutumin nan fa ba shida wani aibu, he's totally clean" "Senator Bashari kenan. Ai idan Saifuddeen Kachallah bashida wani datti, mu zamu yaɓa masa dattin, burinmu ai duniya ta ganshi da datti ne" "Da kamar wuya Alhaji Umaru" Senator Bashari ya faɗa. Ya cigaba bayan ya kurɓi giya "Alhaji Sani Kachallah ba zai taɓa bari a tsige ɗansa ba" "Ko ba a tsige Saifuddeen Kachallah ba, na yi alkawarin shi da kansa sai ya yi resigning" Mai bashi shawara yace " ban ƙi taka ba Excellency, amma koma mi zamu yi ya kamata muyi da sauri tunda sati uku masu zuwa za a yi primary election daga nan kuma ba wani lokaci garemu ba, Kamfen za a fara gadan-gadan" "Kar ku damu komai zai zo cikin sauƙi, an riga an fara aiki akai" *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 17 Lokacin da 'yan fensho (pension) suka yi zanga-zanga jaridar Climax ce ta fitar da labari mai jan hankali akan haka. Kusan jaridar Climax ta maida hankali ne wajen nuna gazawar Gwamna Saifuddeen Kachallah. Tunda jaridar ta fitar da labarin birthday ɗin 'yar Gwamna sai mutane suka maida hankalinsu wajen karanta jaridar. Kafin Umaru Kwom ya sayi jaridar Climax, jaridar ta disashe, ba kasuwa. Yanzu kam a Jahar Congo tana ɗaya daga cikin jaridar da mutane ke marmarin karantawa saboda labarai masu zafi da take fitarwa. "Har yanzu ba a san wanda ya sayi Jaridar Climax ba?" Gwamna ya tambayi COS daya kawo masa jaridar. "Umaru Kwom" "Umaru Kwom? Hmmm wannan mutumi dai ya ɗau aniyar ɓata mini suna kafin zaɓe" COS yai shiru yana nazari, ya faɗawa Gwamna waye mai rubuta labaran nan ne ko kuma ya gayawa Kachallah. Idan ya faɗawa Gwamna zai shiga tashin hankali, amma ba abinda zai iya yi akai. Lokacin da ya gayawa Kachallah cewa Asiya ce 'yar jaridar da ta saurari maganansa kwanaki ba abinda aka mata dan haka zai yi shiru ya zubawa dukkansu biyu ido zuwa lokacin da zasu gano da kansu wanda ke ɓata musu suna a jaridar Climax. "Ina son sanin waye ɗan jaridar da ke rubutun nan" "Angama Excellency, za a nemo koma wanene" COS ya faɗa yana murmushin mugunta. *** Asiya tana zaune ta shirya kayanta tsaf tana jira Sumayya ta gama haɗa nata kayan su tafi. "Ni kam Anty Allah bana so mu bar nan, a chan fa takura za mu yi" "Idan ba za ki bini ba, kya iya wucewa hostel daga nan" Asiya ta faɗa tana hararanta. Babban labari take bibiya kuma dole sai tana gidan Gwamnati za ta samu. Irin kira da saƙonnin da Nana ke tura mata ya sa tayi zargin ko yarinyar 'yar maɗigo ce. Har a whatsapp idan tayi hoto sai ta turawa Asiya wai ta gani ko tayi kyau. Yaya Bello ne ya kaisu gidan. Asiya ta shiga gidan tana addu'ar Allah ya sa ta samu ta gama komai cikin ƙanƙanin lokaci. Masu aikin gidan sun ganeta sai dai ganinta da kaya yasa suka tsaya cirko cirko. Babu wanda ya faɗa musu Amaryar Gwamna za ta zo. Gashi Gwamna da Bilkisu ba sa nan balle aje a tambayesu. Hansa'u da ta fito ta kalli Asiya zaune a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, gabanta kuma akwatuna ne guda uku. Hansa'u ta yi murmushin gefen baki dan ta hango drama idan Bilkisu ta dawo. "Hajiya Barka da zuwa, a shiga miki da kayan ciki ne?" "Kira min Nana" Asiya ta faɗa tana danna wayarta Hansa'u ta wuce ɗakin Nana da gudu. Lokacin da ta shiga cacar baki ta samu Nana da Zunnairah na yi. "A wani dalilin za ki ce ta dawo gidan nan idan ba soyayya ku ke ba" " Tana da ikon zama a gidan nan saboda itama matar Daddy ce. Sannan idan ma soyayyar muke ina ruwanki. Ke mata nawa kike da shi. Yes ina sonta" Hansa'u tayi gyaran murya, dukkansu suka juyo suna dubanta. Ta taɓa kamasu suna aikata maɗigo tun farko-farkon fara aikinta a gidan. Sun mata kashedi akan kada ta kuskura ta faɗawa kowa, sai dai ba kashedinsu ne ya sata yin shiru ba. Aikinta bai bata daman tona musu asiri ba sannan ta lura Bilkisu gafalalliyar Uwa ce. Wani lokaci tana gani suna abinda bai dace ba amma sai tayi shiru. "Hajiya Asiya tana neman ki " "Ina zuwa" Nana za ta fita Zunnairah ta riƙe hannunta tace " wallahi duk ranan dana kamaki da ita sai na gayawa Daddy komai" " ni kuma sai na faɗawa kowa cewa ke ɗin 'yar shegiya ce, da cikin ki Mommynki ta yi aure" Zunnairah ta kaiwa Nana duka Nana ta goce ta fice daga ɗakin da gudu. Zunnairah ta dunƙule hannu tana huci. Tun ranan da ta saurari faɗan iyayenta abin ya taɓa mata ƙwaƙwalwa. Tana shekara shaɗaya a lokacin ta buƙaci mahaifinta ya kaita karatu ƙasar waje, lokacin yawanci 'yan ajinsu 'ya'yan manya da suka gama firamare tare iyayensu sun kaisu ƙasar waje. "Ni zan kashewa shegiya kuɗi" amsar daya bata kenan data faɗa mata buƙatarta. Ta wuce ɗakin mahaifiyarta tana kuka. Daren ranan bayan ta kwanta ta jiyo Iyayenta na faɗa inda mahaifinta ke cewa ba lallai bane ace cikinsa ne tunda ba budurwa ya sameta ba, sannan koda suke tare ai tanada wasu samarin. Yayinda mahaifiyarta take cewa idan bai yadda Zunnairah 'yarsa bace ya je ayi gwajin DNA. "Koma minene dai ba zan kashe mata kuɗi ba. Idan ba zata boarding school da aka sama mata ba ta haƙura da karatun" Da wannan aka tura Zunnairah boarding school a nan kuma aka koya mata maɗigo... Nana na zuwa falo ta rungume Asiya tana dariya. Ita ta mata jagora har ɗakin da ke kallon nata tace ta zauna a ɗakin idan Daddy ya dawo sai ta zaɓi ɗakin daya mata. Bilkisu bata shigo gidan ba sai chan yammaci. Tana zuwa kuwa aka ce mata Asiya ta zo, ta haura sama kaman za ta tashi sama. Ɗakin Nana za ta shiga ta ga Zunnairah ta fito daga ciki. "Ina take?" "Wa?" "Shegiyar da ta shigo min gidana" Zunnairah ta nuna mata ɗakin da Asiya take. Bilkisu ta banko ƙofa ta shigo ɗakin tana huci. Nana da Asiya da Sumayya ne ke zaune akan gado suna hira. "Ku bamu waje" "Mommy daga zuwanki" Nana ta faɗa tana tura baki. "Ki fata ko na ci miki mutuncin, wawuya kawai" Kafin ta gama magana ma Sumayya ta fice daga ɗakin, yayinda Nana ta fice tana buga ƙafa. "Ehen, mi ya kawo ki?" Bilkisu ta faɗa bayan su Nana sun fita. "Mi ya kawoni kuma?" "Uban wa ya baki damar zuwa gidan nan?" "Inaga dai kin manta cewa ni da ke matsayinmu ɗaya. Yadda kike da iko da gidan nan haka nake da shi" "Never. I am the first lady of the state, ba ki da matsayi a nan. Ki koma inda kika fito kafin na sa a maida ki ta ƙarfi" Asiya ta miƙa mata wayarta tace "gashi, kira shi ki ce masa ba zaki bi umurninsa ba" "Shi...shi Saifuddeen yace ki tattaro ki dawo nan?" Bilkisu tayi tambayar ta kasa gaskata hakan. Gwamna ba zai taɓa kawo Asiya ba bayan ya san ba ta so. "Ki tattara kayanki ki koma inda kika fito" "Idan kinga na tafi, to Excellency ne da kansa yace na bar gidan nan" "Asiya kike ko wa. Ki fita a gidan nan kafin rayuka su ɓaci" "Bismillah, Bilkisu Kachallah" Asiya ta faɗa tana dariya. Bilkisu na fita daga ɗakin ta shiga kiran Gwamna, bai ɗauka ba hakan ya sake tunzurata. Lokacin daya kira bayan minti talatin ihu ta fara masa a wayar kan a wani dalilin zai cewa Asiya ta dawo gidan Gwamnati. Gwamna yace koma minene ta bari ya dawo. Bilkisu har ƙarfe shaɗayan dare haka ta zauna zaman jiran dawowar Gwamna. Lokacin da ya shigo gida shabiyu saura a falonsa ya samu Bilkisu tana zaman jiransa. "Ina ji, miya kawota gidana?" Da rana bayan sun yi waya da Bilkisu, kiran Asiya yai dan ya ji dalilin dawowarta Gidan Gwamnati amma sai tace tana son zama a gidan ne, tana son sanin ya ake ji idan ana zaune a gidan gwamnati a matsayin Matar Gwamna. "Saifuddeen ina jin ka" "Bilkisu ke ba yarinya bace, ku ba yara bane. Ka da ku ɗaga min hankali dan Allah, akwai abubuwa dayawa a kaina" "Haka ma zaka ce...haka ma zaka ce ko" Gwamna ya wuce ɗaki ya barta a wajen. Da sun san abinda ke damunsa yanzu da ba za su fara faɗa akan gida ba. Ya kasa biyan albashin 'yan fensho da suke bin gwamnati har na wata huɗu, ga kumadu 'yan secretariat da malaman Sakandare duka sai dai ya biya su kaso hamsin na albashinsu wannan watan. Lokacin da yayi wanka ya kwanta, bacci ƙaurace masa yai. Yana so koda kaɗan ne ya samu ya rintsa amma zuciyarsa tana cikin ƙunci nan da kwanaki kaɗan idan bai biya albashi ba mutane zasu fara magana. Ƙarshe dai sai daya sha maganin bacci kafin bacci ya ɗauke shi. *** Da sassafiya kira ya shigo wayar Asiya tana dubawa taga numbar ƙasar waje . Tana ɗauka aka kira sunanta "Aseey" "Ya Allah! C Y?, kana nan, ya kake ya jiki" " lafiya Excellency, jiki da sauƙi" "Gaskiya na ji daɗi C Y, ya hannunka" "An samin na roba" "Sorry ka ji" "Ki tayani yiwa Gwamna godiya, he's a good man Wallahi, na ji daɗi da aka ce kin aure shi" "Tsaya, tsaya, CY kana asibitin ma gulma kake. Waya gaya ma na auri Gwamna?" CY ya ƙyalƙyale da dariya yace " har video ɗin dinner ɗinku na gani" "Magulmaci, yaushe za ka dawo?" " sunce za su sallameni nan da sati biyu haka" "Na missing ɗinka sosai" "Rufa min asiri kar Gwamna ya sa a harbeni" Asiya ta sa dariya. Kaman haɗin baki suna gama waya da CY sai ga kiran Fou'ad Salisu. Kafin ta amsa kiran sai da ta shige banɗaki ta kulle ƙofa. "Ina jinka Fou'ad" Daga ɓangaren Fou'ad ya fara yi mata bayani "akwai wani account mai suna Sa'ad Kachallah, inaga na Gwamna ne. Lokacin da Gwamna ya bayar da takardar shaidar kuɗi da dukiyar daya mallaka kafin a rantsar da shi bai haɗa da wannan account ɗin ba, sannan account ɗin duk wata akwai miliyoyin kuɗi da ake turawa ciki. Zan ƙarisa bincike na tabbatar da gaskiyar komai" Asiya cike da farin ciki tace " idan aka tabbatar account ɗin nashi ne za a iya tsige shi kenan?" "Za'a iya" Asiya ta yi murmushin jin daɗi... *** Sumayya tana gama lectures na ƙarfe shabiyu ta hau keke ta wuce Asibitin da Ubayd ke aiki. Ta samu yana tareda marar lafiya dan haka sai da ta jira kusan minti talatin kafin yace ta shigo. Da suka gaisa Sumayya ta masa bayanin abinda ya kawota. Murya na rawa tace "Yaya Ubaydullah, Ina tsoron abinda zai faru idan Gwamna ya gane Anty Asiya tana cin amanarsa" Ubayd ya jawo kujerarsa gaba ya gyara zama da kyau yace "mi take yi?" "Dan Allah kar ka faɗa mata cewa ni na gaya maka. Anty Asiya tana son ɓatawa Gwamna suna, da bakinta tace min sai ta sa an tsige Gwamna hankalinta zai kwanta" Ubayd ya ɗan jijjiga kai alamar ta cigaba. "Anty Asiya ta san Nana 'yar Gwamna tana shaye-shaye sannan...sannan" Abin yai wa Sumayya nauyin faɗa. "Kar ki ji tsoro ba abinda zai faru" "Nana 'yar lesbian ce, Anty Asiya tace zata wallafa hotonta da ta 'yaruwarta suna kiss tsirara" "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun" "Dan Allah ka hanata, Wallahi Gwamna yanada kirki ba zai taɓa jin daɗi ba idan aka buga hoton 'yarsa tsirara a jarida" Ta ƙarisa maganar kamar za ta yi kuka. Ubayd ya ja dogon numfashi yace " kar ki damu zan kirata" Sai da yai sallar Azahar kafin ya kira numbar Asiya har yanzu sunan da yai saving da shi ne bai chanja ba wato *Mine* yanzu kam dole ya chanja numbar ko dan gudun zargi. Asiya za ta shiga wanka ta ji wayarta na ringing. Tunaninta Mr Bassey ne shiyasa ta koma ta ɗau wayar dan ta gaya masa nan da anjima kaɗan za ta tura masa labarin da ta rubuta. Ta gama rubutun editting ɗinsa kawai za ta yi. Tana duba wayar ta ga sunan Ubayd. "Ya Ubayd kuma?" Ta furta a fili, sai da wayar ya kusa yankewa ta ɗauka tareda sauke ajiyar zuciya. "Asiya ke ce kike rubutu a jaridar Climax ko?" Ya katse shirun na su "Ya Ubayd dan Allah kada kace na dena" "Ai ban isa na hanaki abinda kika yi niyya ba. Ina ce taurin kanki ne ya zamo mafarin komai" "Ya Ubayd..." "Yanzu ba za ki karɓi hukuncin Allah a rayuwarki ba. Yanzu Asiya har zuciyarki ya bushe za ki iya nuna hoton tsiraicin yara ƙanana a jarida" "Za a rufe inda bai kamata ya fito ba, ina dai so a gansu suna aikata maɗigo ne" "Idan har haka kika zamo Asiya, Alhamdulillah da ban aure ki ba. Asiya kin san ya yaran nan za su ƙare rayuwarsu idan kika tona musu asiri haka. Kina kiran Gwamna Azzalumi amma inaga sunan daya kamata ki fara kiran kan ki kenan" "Kar ka zageni Ubayd. Ni miye Gwamna da matarsa ba su min ba, har yau akwai mutane dayawa da suke min kallon karuwa" "Asiya kina da ilimi, da da yanzu ba ɗaya bane. Yanzu Gwamna mijin kine" "Mijin da bana so ba, bana son shi Ya Ubayd, ba zan taɓa son shi ba" "Idan kika wallafa hotunan tsiraicin yaran nan bana tunanin Allah zai yafe miki Asiya" Daga haka ya kashe wayar. Asiya ta fashe da kuka. Da ta yi mai isarta ta shiga banɗaki ta fara wanka. Komai ya zo mata da sauƙi sai gashi Ubayd yana so ya dagula mata lissafi. Kwananta huɗu a gidan ta kama Nana da Zunnairah akan gado, ba tareda sun ankara da ita a ɗakin ba ta ɗauke su hoto ta fita. Ta zo tana editing hoton a laptop Sumayya ta gani hankalinta ya tashi. Asiya tace mata maganin 'yan iska za ta yi. Da farko labari za ta rubuta akan hoton da Mr Bassey ya turo mata, wani hoton Nana ce a wajen party tana shan shisha. Hoton bai jima sosai ba dan ba zai fi wata ɗaya da aka ɗauka ba. Ko a ina ya samo hoton oho ita dai damuwarta ta yi rubutu ta aibata Gwamna sai kuma kwatsam ta samu hoton da ya fi wancan armashi. Tana fitowa daga banɗaki ɗaure da towel ta dafe ƙirji saboda ganin Gwamna da tayi riƙe da wayarta. Idonsa ya kaɗa yayi ja sai ta fara tunanin kodai ya ga hoton Nana ne, to amma kuma wayarta akwai password. Ringing wayar ta fara yi hakan ya sa ya miƙa mata wayar. Jiki a sanyaye ta ƙariso ta karɓi wayan a hannunsa. *Ubayd Luv* ta gani ƙarara a fiskar wayar, ta ɗaga ido ta kalli Gwamna wanda shima kallonta yake yi. "Akwai taron da zamuje gobe da ƙarfe goma na safe" daga haka ya fice daga ɗakin. "Ashe dai bai gani ba" ta faɗa a hankali. Ba ta ɗau wayar ba sai da ta je ta kulle ƙofa kar wani ya sake shigo mata ɗaki bagtatan. Kiran numbar Ubayd tayi bayan ta zauna a gefen gado. Lokacin da ta ɗauka roƙonta ya fara yi akan dan Allah kada ta wallafa hotunan nan. Yadda ya dinga yi mata nasiha yasa dole ta haƙura da abinda tayi niyya, tace masa ba zata wallafa hoton ba. Da suka gama wayar ta saka kaya ta jawo laptop ɗinta ta goge rubutun da tayi da farko ta fara rubuta wani sabo akan hoton da Mr Bassey ya turo mata. *** Washegari aka fitar da labari mai taken *'yar Gwamna tana shaye-shaye* rubutun ya soki Gwamnatin Saifuddeen Kachallah inda aka bayyana cewa yadda Gwamna bai iya kula da tarbiyar 'yarsa ba haka zalika ba zai iya kula da haƙƙin talakawa ba. Duk da jaridar bata fito ta bayyana cewa Nana Kachallah 'yar maɗigo bace amma ta yi ishara da hakan ta hanyar cewa akwai alamun Nana Kachallah za ta iya zama 'yar maɗigo saboda illar shaye-shaye. Gwamna bai samu ganin jaridar da aka wallafa ba sai da ya dawo daga taron buɗe wani Asibiti da suka je a wata ƙaramar hukuma shi da matansa biyu. Lokacin da ya ga hoton 'yarsa tana zuƙan shisha sai dayai ƙwalla Allah ya taimaka ma babu kowa a office ɗin nasa. Gaba ɗaya komai ya fice masa a kai, tunda aka fitar da hoton birthday ɗinta ya ja mata kunne akan irin shigar da take yi sannan ya hanata fita idan ba makaranta ko gidan kakanninta ba. Amma a haka bai tsira ba, mulkin gaba ɗaya ya ishe shi. Lokacin da yake koyarwa yanada lokacin iyalinsa sosai amma tunda ya shiga siyasa yanayin zama da iyalinsa ya ja baya, musamman yanzu da yake kan kujerar Gwamna. Kiran Direban yaransa yai yace ya je ya ɗauko Nana a makaranta ya kaita Kachallah house. Shima ɗin bayan ya samu zuciyarsa ta ɗanyi sanyi Kachallah House ɗin ya wuce. Yana zuwa ya samu Dadda na yi mata faɗa, suma sun ga jaridar. Dadda shigewa ɗakinta tayi ta basu waje. Nana da idonta ya ciko da hawaye ta shiga rantse-rantsen sau ɗaya ne kuma a wajen party aka tirsasata saboda ƙaryar da Bilkisu tace tayi kenan. "Hoton bai yi kama da yarinyar da aka tursasa ba, ya fi kama da yarinyar da ta ƙware wajen shan shisha dama wasu abubuwan" "Daddy I swear..." "Ki gaya min gaskiya yanzu, ko kuma na sa a binciki jininki a duba min traces na kayan maye. Idan aka samu Nana ba za ki so ki sake kirana mahaifinki ba" Nana ta tsorata da yanayinsa, yadda ya ɗau fushi ba abinda ba zai iya yi ba. Ƙarshe da taga gaskiyar ce kawai zata fishsheta sai ta sanar da shi komai. Zunnairah ce ta koya mata shan syrup da shisha. "Wani mummunan abun ta kuma koya miki?" "Babu. Allah babu" Nana ta yi saurin faɗa tana fashewa da kuka. " Khadijah ba zan bar nan ba sai kin gaya min duk abinda Zunnairah ta koya miki. Idan kika min ƙarya zan gane dan nasa a bincika mini CCTV camera da ke cikin gida" duk da sai yanzu yake danasanin ƙin yarda a saka masa CCTV a gida da yai. Tsoro ya ɗarsu a zuciyar Nana, kenan duk abinda suke da Zunnairah Daddy zai gani. Idan haka ne ta kaɗe. "Ina jin ki Khadijah" "Daddy ka yafe min, wallahi ba laifina bane. Airah ce, Airah ce ta kemin wasu abubuwa tun bana so har na zo na fara so. I swear Daddy na dena, cewa tayi zata faɗa maka shiyasa na sake yi" Gwamna ya jingina kansa da kujera yana faɗin "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun" *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 18 Asiya ce ta fara shiga falon. Ta samu Gwamna yana zaune yayi tagumi. Ya mata tsufa, idonsa ya faɗa, ƙasan idonsa ya yi baƙi, ga furfura kaɗan-kaɗan a jikin gemunsa. Asiya ta zuba masa ido ba tareda tace komai ba. Minti uku sai ga Bilkisu ta shigo ɗankwali a hannu. "Saifuddeen koma wanene ya rubuta labarin nan sai na sa an nemoshi an hukunta shi. In fact sai nayi kaca-kaca da jaridar Climax" "Nana tana zama a gidan nan tareda ke amma baki san tana shaye-shaye ba" "Kar ka kawo min wannan Saifuddeen, ka san ina ƙoƙari akan yarana, especially Nana. Zunnairah ce ta koya mata. Na riga na turata wajen uwarta kafin ta ɓata min 'ya" Ta zauna gefensa kafin ta cigaba da magana "Saifuddeen kai ne Gwamna, ya kamata ka ƙwace lasisin gidan jaridar Climax. Ta ya za su ce Nana zata zama 'yar lesbian" "Saboda da gaske ne" Gwamna ya furta a hankali Bilkisu ta zaro ido. "Da gaske kuma? Mi kake nufi?" "Nana ta faɗa min komai. Ita da Zunnairah suna aikata maɗigo a gidan nan kuma babu wanda ya sani cikinmu, saboda mun gaza, mun gaza Bilkisu. Ba jaridar Climax zamu bincika ba, kanmu za mu bincika a matsayinmu na iyaye" Jikin Bilkisu yai sanyi, ta fara yin fifita da ɗankwalin hannunta duk da kuwa sanyin AC ya ratsa falon. Kaman wanda aka tsikari Bilkisu haka ta tashi ta fice daga falon. "Tsanar da kika min har ta kai haka" Asiya ta zaro ido dan a tunaninta ya gano cewa ita ta rubuta labarin ne, sai kuma ta ji ya ƙara da cewa. "Na karɓi wayan Nana, na ga irin saƙonni data dinga tura miki. Lokacin da tace tana sonki miyasa baki faɗa min ba? A matsayina na Uba ba kya ganin ya dace na san 'yata tana yiwa wata mace 'yaruwarta kallon da bai dace ba" In dai ya ga chats ɗinsu to babu halin ta masa ƙarya dan a ƙasan wajen da Nana ta ce mata "I love you" tambayarta tayi wani irin so, Nana ta amsa da cewa " ina son lips ɗinki, ƙirjinki, bayanki, kai komai na halittar ki" "Ko a tunaninki yarinyar shekara shabiyar ya kamata ta dinga faɗin irin wannan maganganu?" Idan ya cigaba da bin diddigi zai iya alaƙantata da jaridar Climax kuma ba yanzu take so ya sani ba. Ta yi saurin cewa " ni ban ɗauki wannan komai ba tunda na ga kamar tarbiyyan gidan kenan. Kana gani 'ya'yanka na yin shiga da bai dace ba a cikin gidan nan bayan akwai ma'aikata maza, baka taɓa musu magana ba, ban taɓa gani suna karatun addini ba, bana ma tunanin suna zuwa Islamiyya. Rayuwar da kuka ɗaurasu irin ta turawa ce, sannan a wajen mahaifiyarsu ni jikar maiƙusumbi ce, a wajenka kuma ni hajar Kamfen ce. Taya zan ƙalubalanci abinda 'yarka ke faɗa mini, ƙila ba matsala bane a wajenku" Tun kafin ta gama bayanin Gwamna ke kokawa da numfashinsa, yana ƙoƙarin ciro inhaler a aljihunsa inhaler ta faɗi ƙasa. Asiya ta yi saurin ɗauko inhaler ta matsa kusa da shi ta jijjiga sannan ta miƙa masa, ya haɗa da hannunta ya matsa inhaler ɗin a bakinsa. Kallonsa ta ke yi yadda lokaci guda ya rikiɗe har jijiyoyinsa sun taso saboda wahala. Matsayinsa ba komai bane a hannun wannan lalura. "Nagode" ya faɗa bayan numfashinsa ya daidaita. Asiya ta girgiza kai sannan ta fita daga falon zuciyarta fal. Ta ji daɗin ganinsa cikin halin tashin hankali, itama haka mahaifiyarta ta shiga damuwa lokacin da aka ɓata mata suna a media. "Yadda Umma ta zubda hawaye saboda abinda kuka min haka kaima sai ka zubda hawaye saboda 'yarka. Ita kuma waccar kucakar matar taka rananda aka koreku a gidan nan zata san cewa ba a dawwama a matsayin Matar Gwamna" Da wannan tunanin Asiya ta shige ɗakinta tana jiran yadda za su ji wata sati idan aka kai masa impeachment notice. Daren ranan Gwamna ya je ya samu Alhaji Sani akan yana son ajiye aikinsa. "Kanada hankali kuwa, Saifu mi kake nufi za ka yi resigning. Saboda abinda wata jaridar ƙarya ta rubuta akan 'yarka. Miye ne a ciki idan duniya ta san Nana na shaye-shaye, kai ne kaɗai Gwamnan da yake da yara masu shaye-shaye. Ban yarda da wannan maganar ba, ta mutu a nan" "Baba ko da ban yi resigning ba, ba zan nemi takarar zaɓen bana ba" "Ba za ka ɓata min shiri ba Saifu, shekara takwas ɗin nan sai kayi Gwamna a jahar nan. Ban yafe ba idan ka yi resigning" "Baba..." "Idan kuma zaka nuna min cewa ba nina haifeka ba to, Bismillah" Gwamna yai shiru bai iya cewa komai ba. Kafin ya bar gidan sai daya leƙa sashen Dadda. Ya samu Mahira tana karatun ƙur'ani a falon Dadda. Zuciyarsa yai sanyi, da zai maida hannun agogo baya da duka yaransa biyun zai ajiyewa Dadda, ƙila da Nana itama halin Mahirah za ta tashi da shi "Ina 'yaruwar ki?" Ya tambaya bayan ta gaisheshi. "Tana bacci" "Dadda fa?" "Tana sashen GrandMa" "Mahirah" "Yes Daddy" ta amsa tana rufe ƙur'anin da ke hannunta "Akwai abinda kike buƙata, ina nufin baki da matsala, ba abinda ke damunki?" Mahirah ta girgiza kai tausayin mahaifinta ya kamata. Yana ƙoƙari sosai a kansu, shi dai kawai sanyinsa ne da yai yawa yasa a mafiya lokuta yake biyewa mahaifiyarsu. "Ehm Daddy, Dan Allah kar a kai Nana ƙasar waje, idan aka barta a nan ma zata warke, zata dena duk abinda take yi" "Allah ya miki Albarka" Mahirah ta amsa da Amin. Shima tunanin da ya zo masa kenan da Alhaji Sani ya ce bai amince ya ajiye muƙaminsa ba. Dama da ya amince ɗin yai niyyar zai tattare iyalinsa ne su koma ƙasar waje, a nan kuma zai kai Nana rehabilitation centre har sinadarin ƙwayoyin da tai ta sha ya bar jininta. Sannan a cire mata sha'awar mata. *** Labarin 'yar Gwamna ya zamo abin hira a kowanne lungu da saƙo na Jahar. Kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake. Wasu na zagin Gwamna wajen rashin bawa 'yarsa tarbiyya wasu kuma na ganin cewa laifin first lady ce saboda ai mace aka sani da tarbiyya domin itace ke tare da 'ya'ya koda yaushe. Mai bawa firstlady shawara ya fito ya ƙaryata maganar maɗigo da jaridar Climax ta soki 'yar Gwamna da shi sannan sun rantse cewa Nana Kachallah bata shaye-shaye, a wajen party ƙawayenta suka tursasata ta sha shisha. Kuma za su shigar da jaridar Climax ƙara. Ko kaɗan Asiya ba ta ji ɗar ba da wannan magana koba komai ta samu abinda take so, yadda aka yi ta yawo da ita a yanar gizo ana gulmanta haka nan itama Nana za ayi ta gulmanta har zuwa wani lokaci, kuma hakan zai ƙona ran Gwamna ita kuma duk abinda zai ɓata masa rai sai ta yi. Yanzu jira kawai take ta rubuta labarin da zai wargaza Gwamnatin Saifuddeen Kachallah. *** Ranan Litinin ƙarfe tara na safe aka kawowa Gwamna notice na impeachment trial. Bai yi mamaki ba saboda tun lokacin daya rage kuɗin allowance da ake bawa members na state house of assembly suka fara nuna ɓacin ransu gareshi. Ba abinda zasu iya tuhumarsa da shi. Record ɗinsa is clean. Sai dai dama tunda yana son ajiye aiki ƙila yanzu Alhaji Sani zai bari yai resigning kafin a fara trial ɗin. Ya kira Alhaji Sani ya sanar da shi gameda takardar da aka kawo, tun a wayan ya bircike yana faɗin ba zai yiwu ba, babu wanda ya isa ya tsige Saifuddeen matuƙar yana raye. Yana gama waya ya kira Mr Paul yana masa kashedi akan indai shine ya haɗa hannu da Umaru Kwom dan a tsige Saifuddeen to ya sani ba su isa ba. Ba a taɓa tsige Gwamna a jahar Congo ba kuma baza a fara akan ɗansa ba. Mr Paul ya saka dariya yana faɗin miye abin tsoro idan har ya san Saifuddeen bashida abin aibu. Ai trial za a fara idan ya kare kansa bisa duk zargin da za ai masa ai shikenan. Alhaji Sani ya kashe wayar ya kira Yallaɓai, nan ma nunawa yai duk wanda yasa aka tsige Saifuddeen sai ya ga bayansa a jihar. Yallaɓai ya kwantar masa da hankali akan indai ya yarda da Saifuddeen to ai babu mai tsige shi a kujerarsa. Da wuri Gwamna ya isa gida yau, ƙarfe huɗu da rabi yana falonsa. Bilkisu ya kira yace ta sameshi a falonsa. Yana zaune ya miƙe ƙafafuwansa akan table wayarsa ta fara ƙara, yana ganin sunan Attaruhu yai murmushi sannan ya ɗauka. "Your Excellency Ummata ba ta da lafiya, na taho gida tun ɗazu. Idan ba matsala ina so na kwana a gidanmu" "Ba matsala" Ƙiit ta kashe wayar. Ba dan Abba da yace bai yadda ta kwana ba ai ba abinda zai sa ta kira Gwamna ta nemi izininsa. Ta kusa ta daina amsa sunan matarsa balle ace komai za tayi sai ta tambayeshi. Minti ishirin yai yana jiran Bilkisu saboda bata gida lokacin da ya kirata. Tana shigowa gidan, Hansa'u da ke kallo a falo ta karɓi jaka da gyalenta ta wuce mata da shi ɗaki. Bilkisu ta ƙarisa sashen Gwamna. Ta riga ta samu tabbaci akan babu wanda ya isa ya tsige mijinta shiyasa ta shigo gidan hankali kwance. "Na san kin ji labarin Impeachment notice da aka kawo" "Wahala kawai za su bawa kansu, ba wanda ya isa ya tsige ka" "Ki fara tattara kayanmu, zamu koma asalin gidanmu" "Wasa kake ko?" "Zan yi resigning Bilkisu. Kin sani tun farko ba wai ina son harkan nan bane, ina yin komai ne saboda Baba. Munada komai Bilkisu kafin wannan matsayin babu abinda muka rasa na rayuwa. Bayan komai ya lafa dukkanmu zamu bar ƙasar nan. Nana, Mahirah, Junior duk zasu samu kulawar mu" Bilkisu ta fara kallon gefe da gefenta sannan tace "akwai abinda ka sha ne kafin na shigo?" "Bilkisu siyasa ba a jinina yake ba, i'm failing the people, i'm failing my family. Ki duba yadda Nana ta lalace a ƙarƙashinmu because we are busy doing other things" "Ba ka hau kujerar nan dan na zamo matar Gwamnan wata shida ba. Shekara takwas zan yi a matsayin nan kuma babu wanda ya isa ya ja da hakan" "Bilkisu" "Idan ka yi resigning gawata za ka zo ka tarar a gidan nan, ba inda zan je, siyasa kuwa yanzu ka fara dan wanda kayi a baya sharar fage ne" Gwamna ya zubawa matarsa ido yana kallon yadda ta ke magana da izza kaman ta san gaibu. "Suma masu son tsigekan muna nan jira muga da wani ƙaryar za su tuhumeka" *** Umma tayi-tayi Asiya ta tafi gidanta ta ƙi. Kunyar 'yarta take ji wai sun je Asibiti tare ance musu ciki gareta. Bata san ciki gareta ba da ba za ta bari su je Asibiti tare ba. Yawan amai da zazzaɓi da take ji ta ɗauka malaria ce, ta ma siyi maganin malaria ta sha na kwana uku amma sauƙin sai a hankali. Ali daya shigo da rana ya samu tana sheƙa amai sai ya ji tsoro ya kira Asiya ya sanar da ita saboda Abba baya nan Inna Yaha ma ta fita. Asiya kam ko ajikinta sai murna take yi za a haifa musu ƙani ko ƙanwa. Ta shiga kitchen ta haɗawa mahaifiyarta dambun couscous da ya ji kayan lambu da hanta. Lokacin da ta kawo tare suka zauna, suna ci tana bata labarin wasu 'yan ƙauye da suka zo kwanakin baya wai su dangin Matar Gwamna ne. Suka zo su kusan takwas da tsummokaransu har da zabi da suka riƙo wai za su bawa Gwamna, da aka hanasu shiga suka ƙi tafiya suka tsaya a bakin gate, ƙarshe aka nemo Yaya Bello ya zo ya gansu yace bai taɓa ganinsu ba. Asiya tace abinda ya fi bata dariya wai su da Yafendon Tabawa uwa ɗaya uba ɗaya suke. Umma ma sai da tayi murmushi. Asiya ta cigaba da gaya mata cewa kusan kullum sai an kirata ana ƙaryar dangi da ita. Akwai wadda tace ƙanwar Ale Faruƙ ce Asiya tace mata Ale ba shi da ƙanwa mace. Bayan Isha Ya Ubayd ya zo gaida Umma. Sama-sama suka gaisa da Asiya kowa da abinda yake ji a zuciyarsa. "Asiya we have to talk" ya faɗa yana nufin ta yiwa Umma bayani. Umma dai ta yiwa Asiya kashedi akan ta sani ita ɗin matar wani ne dan haka ta kama kanta. A ɗakin suka yi maganan nasu wanda ko Umma da bata jin abinda suke faɗa zai da ta zargi akwai matsala. Da ta tambayi Asiya mi suke faɗa Asiya ta mata ƙaryar magana suke akan bikin Faty da za ayi, tace sai anyi Kamu shi kuma yace ba za ayi ba. Umma tace mata ta bari yai abinda ya dace domin ya fita kusa da Faty. Ubayd dai fita yai a ɗakin ransa ba daɗi. *THE GOVERNOR'S WIFE* ...... MATAR GWAMNA.... *©Azizat Hamza* wattpad Azi_zat Bismillahir Rahmanir Rahim Book one 19 Da dare kusan ƙarfe goma COS ya je wajen Yallaɓai, batun tsige Gwamna da ake shirin yi ya kawoshi. Ya sani Umaru Kwom ne da wannan shiri amma kuma yana da yaƙini akwai sa hannun Mr Paul a ciki. "Yallaɓai baka ce komai ba. Kana so a tsige Saifuddeen ne?" Yallaɓai yai dariya yace "Lamara kenan, kana ganin za su iya tsige shi ne?" "Amma tunda suka fara maganar ai sun shirya wa abun ne" " idan sun shiryawa abun ai Alhaji Sani Kachallah ma a shirye yake" "Hakane kam, amma nayi mamaki da kace kada na faɗawa kowa cewa Asiya ta haɗa hannu da Umaru Kwom" "Wannan rikicin cikin gida ne, mu zuba musu ido kawai" "Yarinyar fa abin tsoro ce, kada gaba ta zo tana bamu matsala" "Ina ganin akwai rawar da Asiya zata taka a gwamnati Saifuddeen Kachallah, The girl has Charisma" Yallaɓai yai maganar yana shafa gemunsa. *** Maganar tsige Gwamna da ake yi ya ja hankalin ƙasar kan siyasar jahar Congo. Ko'ina ka shiga maganar ake yi. Mutane da dama sun yarda Saifuddeen Kachallah mutum ne adali, yayinda wasu maganar albashin 'yan fensho da ba a biyaba ya sa suke ganin ya gaza. A ɓangaren Asiya ko ɗar ba ta ji ba da Ubayd ya mata magana akan kada ta aikata abinda tayi niyya. So take ayita ta ƙare, ana tsige shi za ta nemi takardar saki idan ya ƙi bata kuma kotu zata kai shi a musu Khul'i. Ba abinda zai sata farinciki sama da ta ji yau ance mata an tsige Saifuddeen daga muƙaminsa na Gwamna. Ranan ƙila sai ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. A ɓangaren Bilkisu kuwa ta rantse babu wanda ya isa ya tsige mijinta. Idan aka tsige Saifuddeen tamkar an mata tsirara ne a kasuwa. Shima Alhaji Sani Kachallah ya shiga ya fita akan maganar dan har wajen party chairman na ƙasa yaje sun bashi tabbacin indai Saifuddeen bashida laifi ba wanda zai tsigeshi. Wannan magana yasa Alhaji Sani ya gane akwai mutane masu fiska biyu, kai har uku ma a tafiyarsu, kuma da sannu idan ƙura ta lafa zai yi maganin 'yan banza. Sun zaɓi ranan da Gwamna zai je buɗe stadium da aka gyara a matsayin ranan da za a wallafa dalilin daya sa za a tsige Gwamna. Lokacin da Umaru Kwom yace zai sa a jefi Gwamna Asiya tayi na'am da hakan. Duk abinda zai ƙasƙantar da Saifuddeen Kachallah to tana so. Abinda Asiya bata sani ba shine, shirin da take da Umaru Kwom daban, shima shirin da yake da nasa mashawartan daban. Ita burinta ta ɗau fansa akan Gwamna Saifuddeen ne shi kuma burinsa ya hamɓarar da Saifuddeen saboda ya samu ƙarfin gwiwa a zaɓen da za ayi. Idan ya tsaya takara da Saifuddeen to ba makawa zai rasa kujerar amma idan da wani daban ne yana da yaƙinin zai ci zaɓe. *** Ranan Asabat ƙarfe tara da rabi Gwamna ya fita daga gida zai fara zuwa Kachallah house kafin ya wuce Stadium. Asiya ta zauna a ɗaki tana jiran komai ya tafi yadda aka tsara. Ƙarfe goma saura kwata wayarta ya fara ringing, ta ɗauka da sauri ganin Fou'ad Salisu ke kiranta. Bayanin da ya fara mata ne ya sata miƙewa tsaye da sauri dan ta tabbatar dai kunnenta ya ji dai dai. "Hello kina jina? Na ce ba Gwamna ke da wannan account ɗin ba. Alhaji Sani Kachallah ne. Account ɗin Sa'ad Kachallah an buɗeshi lokacin Gwamna yana shekara goma a duniya, bashi da masaniya akan account ɗin. Na gayawa Umaru Kwom amma ina ganin kema ya kamata ki sani" Tabbas ta ji shi a karo na farkon da yai maganar. Ɗimuwa, kiɗima da gigicewa shine ya sa ta daskarewa a wajen. Asiya ta tunɓuke ɗankwalin kanta ta yi cilli da shi lokacin da wayar da ke ɗare a kunnenta ya faɗo ƙasa. "Na shiga uku ni Asiya" ta faɗa tana dafa ƙirjinta *idan labarin nan ya fita, sunana zai kafa tarihi a duniya. Zai kafa tarihin cewa ni ce Matar Gwamna ta farko a tarihin ƙasar nan da na yaƙi mugun Gwamna na kawo ƙarshen sa* Abinda ta faɗawa Ubayd kenan ranan da ya mata magana a kan abinda take shirin yi. Kalamansa suka fara dawo mata filla filla a kwanyarta. "Asiya ki dena abinda kike yi. Babu kyau. Gwamna adalin mutum ne, shi ɗan Adam ne, zai iya yin kuskure kamar kowa, ki masa uzuri. Kar ki manta fa MIJIN KI ne. Ko ban aureki ba Asiya har gobe ke ƙanwata ce, dan haka ba zan taɓa bari kiyi abinda zai jawo miki dana sani ba. Ki riƙe mijin ki da kyau ki dena ƙoƙarin hamɓarar dashi. Ki rungumi mijinki Asiya, we are not meant to be" Ta durƙusa ƙasa ta ɗauki wayarta da sauri. Hannunta ɓari ya ke lokacin da take ƙoƙarin kunna wayar saboda ta mutu lokacin da ta faɗi ƙasa. Wayar na kunnuwa ta shiga lalubo numbar Mr Bassey, tana danna numbar ta ƙara wayar a kunnenta, ga kowanne ringing da ke fita yana dai dai da dokawar da zuciyarta ke yiwa ƙirjinta yana ƙoƙarin barin mazauninsa. "Hello. Mr Bassey. Kar a fitar da labarin nan. A dakatar da komai" ta faɗa da iya ƙarfin muryarta. "Miya faru Hajiya?" Ya faɗa cike da mamaki bayan awa biyu da su ka wuce aka gaya mi shi cewa ya wallafa labarin. "Dan Ubanka na ce a dakatar da komai, komai na ce" Ɗif dodon kunnenta ya buga saboda dena jin komai da ta yi na wasu daƙiƙu. Lokaci guda ta yi fatan inama kaman Umma Allah yayi ta marar ji marar magana. Durƙusawa ta yi ƙasa, ƙafafuwanta da gwiwowinta su ka nitse cikin lallausan Italian carpet da ke ɗakin. A yanzu maimakon laushin carpet ɗin kaushin sa take ji, ji ma take kamar a cikin harawan dabbobin Umma ƙafafuwanta suke. *" Hajiya, ai kusan minti talatin kenan da wallafa labarin a website ɗin mu da shafukan sada zumunta. Yanzu haka an fitar da jaridan kasuwa"* Bata iya cewa Mr Bassey komai ba saboda aikin gama ya gama. Idan labarin nan ya isa ga Gwamna zai yi bincike, ba za a daɗe ba zai gano cewa itace da wannan aikin, ita ce take yiwa jaridar Climax rubutu. Idan aka jefi Gwamna ba lallai ya san akwai hannunta a ciki ba, tunda yana da maƙiya dayawa zai ma ɗauka mutanen Umaru Kwom ne da wannan aikin. Amma idan ya san ta haɗa hannu da Umaru Kwom wajen hamɓarar da shi... Ta sa hannu ta dafe ƙirjinta da tuntuni ya ke ta bugu da ƙarfi. Ɗumi ta ji a kumatunta hakan ya sa ta shafa wajen da sauri. Karo na farko kenan tun zamanta MATAR GWAMNA ta yi hawayen danasanin abubuwan data aikata. Idan komai ya fito fili sunanta a tarihi zai koma Maƙaryaciya, Mayaudariya kuma Munafuka. Kyakykyawan fiskar Gwamna ta hango yana faɗin "Asya WHY?" T V dake ɗakinta ta yi saurin kunnawa ta nemi remote ta lalumo tashar Hill TV dan ta san za su bayyana koma minene dalla dalla. Daga wajen da ake kawo rahoton kai tsaye na buɗe filin wasan ƙwallon ƙafa da aka gyara suka yanke zuwa labari da ɗumi-ɗuminsa. An bayyana dalilin daya sa ake son tsige Gwamna Saifuddeen. Shekaru shabiyar da suka wuce ya ci zarafin wata yarinya lokacin da ya ke koyarwa a Jami'ar Congo. Asiya ta zaro ido ganin abinda aka rubuta da kuma abinda mai karanto labaren ke faɗi wanda bai kama hankali ba. Ba abinda ta rubutawa jaridar Climax kenan ba. Ta yi saurin jawo wayarta ta duba website ɗin jaridar Climax ta ga suma labarin cin zarafin da Prof. Saifuddeen yai wa wata ɗalibarsa Lami Ninja suka wallafa. Kanta ya kulle dan abu daban ta rubuta abu daban aka wallafa. Wacece ma Lami Ninja?. Ta nemo numbar Umaru Kwom ta danna masa kira, ba a ɗauka ba sai a bugu na uku. "Alhaji Umaru ban gane abinda ake faɗa ba. Na ɗauka maganar kuɗi ake" "Kuɗin Alhaji Sani ne ba nashi ba, ba za a tuhumeshi da wannan ba shiyasa muka nemo abinda zai hamɓarar da shi cikin sauƙi" "Miyasa ba a gaya min ba, miyasa ka barni cikin duhu?" "Siyasar kenan Yarinya " daga haka Umaru Kwom ya sa dariya ya kashe wayar. Asiya tayi taga taga kamar zata faɗi. Kenan Ubayd yayi gaskiya da ya ce zai iya yiwuwa duk abinda ake Gwamna bai sani ba, ƙila kisan Saminu Bacchi ma bai san komai akai ba. "Ki yiwa kanki adalci Asiya, a iya zaman da kika yi da Gwamna Saifuddeen kinga alamar zai iya kisa saboda mulki, kinga alamar kuɗi da dukiya za su ruɗe shi?" Tambayar da Ubayd ya mata kenan amma ta bari ƙiyayya da son zuciya suka sa ta amsa da cewa "eh, Saifuddeen Kachallah zai iya duk abubuwan daka lissafo" "Ko kin san saboda ya kuɓutar da ke daga hannun Umaru Kwom ya aure ki. Abba ya faɗa min komai, kuma na yarda cewa saboda ya tseratar da rayuwarki ya aureki. He's protecting you Asiya. Umaru Kwom amfani da ke zai yi ya yar. Idan kika gama masa aiki juya miki baya zai yi..." "Tatsuniya kenan Ya Ubayd, ni yarinya ce da zai kareni, wani irin kariya ne da ba zai iya bani ba har sai ya aureni?" Dana sani ƙeya. Da ta saurari Ubayd ranan da duk wannan bai faru ba. A iya zaman wata biyu da sati ɗaya da ta yi a gidansa ta zalunce shi, ya mata laifi, amma ita laifin data masa ya ninka nasa sau dubu. Ta kai dubanta ga talabejin inda aka nuna Gwamna na buɗe Stadium daya gyara, hannunsa riƙe da Almakashi zai yanka ribbon ɗin da aka sa. Ta ƙura masa ido kaman yau ta fara ganinsa, tabon sallah da ya fito dal a saman goshinsa, dimple ɗinsa da ya ke lotsawa idan yana magana, sajensa da gemu da suka ƙawata fiskarsa. Bata taɓa yarda ba idan mutane na faɗa amma yau zuciyarta da idanunta sun amince Saifuddeen Sa'ad Kachallah yana da kyau. Ta rintse idanunta lokacin da ta tuno cewa Umaru Kwom ya tsara za a jefi Gwamna da zaran ya gama hidimar buɗe Stadium. Ta jawo wayarta ta yi abu na ƙarshe da take ganin zai fishsheta. "Allah Sa'id ni" ta furta a hankali, ta kwanta kan gado ta fashe da kuka mai ɗaci... A nan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya a labarin Matar Gwamna. *Shin za a jefi Gwamna?* *Wani hukunci zai biyo bayan abinda Asiya ta aikata?* *Ya maganar tsige Gwamna?.* *Shin Hansa'u zata samu abinda take nema a wajen Bilkisu Kachallah?, wacece ma Hansa'u* *Shin Umaru Kwom zai yi nasara akan Gwamna Saifuddeen?* *Wacece Lami Ninja da aka ce Gwamna Saifuddeen ya ciwa zarafi lokacin da yake koyarwa?* *Shin Gwamna zai iya yin gaban kansa kuwa? Ko dai Alhaji Sani ne zai cigaba da juya shi* *shin Bilkisu Kachallah zata bari tauraron Asiya ya haska kuwa?* *Yaushe Asiya za ta gane cewa ita ce Attaruhu?* *Akwai yiwuwar soyayya mai daɗi tsakanin Gwamna Saifuddeen da Asiya Shahidah. Kuwa?* *kaɗan kenan daga cikin batutuwan da za ku gani a kashi na biyu* From 2g Hausa Novel Compiled by Hausa Novels Online (Telegram Channel)