*KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* *FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 1-2* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Cikin sasarfa take saukowa da ga matakalen benen, yayin da fuskarta take cike da matuƙar farin ciki. Kallonsa ta yi daidai lokacin da ta miƙa masa agogon da ke hannunta ta ce, "Please dad help me." Karɓar agogon ya yi yana murmushi, zuwa can kuma ya ɗaure fuska yana kallon ta. "Jannah, na ga ya miki ki daina saukowa benen nan da garaje, kina dai tune da faɗuwar da ki ka yi." "I’m sorry, dad, ka san yau ina cikin farin ciki shi ya sa." Dariya ya ƙara yi jin abin da ta ce tare da duba agogon hannunsa."Anya mom za ta dawo da wuri kuwa? Na fara jin tsoron kar ta ƙi dawowa, ka san halinta. Ga shi friends ɗina sun kusa ƙarasowa." Ɗan yaƙe ya yi, amma shi kansa zuciyarsa ta fara karaya. "She will be back, we still got ten more minutes." Ya ce mata cikin ƙarfafawa. Ƙaramin tsaki ta ja, tare da kallon tanƙamemen falon da ya sha ado da kwalliya sai ɗaukar ido ya ke yi. "Sam bai kamata ta je aiki ba, kasancewar yau rana ce ta musamman, amma abin takaici na san da ƙyar ta dawo kan lokaci." Ƙarasowa ya yi gefenta ya zauna tare da miƙa mata wayarta. "Ungo wayar, kira ta ki tuna mata da muna jiran ta." Ba tare da ta ce masa ƙala ba ta karɓi wayar. Sai dai, har ta yi kira sau biyar ba ta ɗauka ba. Jifa da wayar ta yi daidai lokacin da ta ji alamar buɗe get, wanda da sauri ta ruga tare da buɗe windo a tunaninta ita ce. "Oh my God! Dad, friend dina ne, and she isn’t back yet." Sai ta tsaye cikin ɓacin rai lokaci guda idanunta suka kawo ruwa. "No, please don't cry. Ma za ki je ki tari ƙawayenki." Cikin rashin karsashi ta ƙarasa ƙofar tare da ƙaƙalo murmushin dole. "Wow you look lovely!" Suka haɗa baki gurin faɗi hakan, tare da mai da hankali gurin gaishe da dad, da yake kallon su fuskarsa a sake. Ganin tana shirin yin kuka ya kama hannunta zuwa bedroom. "Ina ga bari na je na ɗauko ta, kin ga kar su yi ta jira." "No dad." Ta furta tare da kama hannunsa cikin damuwa. "Kyale ta ba sai je ba. In har ba za ta iya yiwa rayuwata adalci ba, ta ba ni minti talatin a lokacinta, don na taya ta murnar birthday ɗinta, ba na buƙatar zuwan ka." Ta dasa aya tare da juyawa ta nufi hanyar fita falo. "Bari na je na sallame su." Ta ce ba tare da ƙoƙarin fita. "Alhamdulillahi! Jannah ga hon ɗin motarta can, ma za je ki gani nan zuwa." Ya furta tare da yaye labulen ɗakin yana murmushi. Jin abin da ya faɗa ta saki fuskarta tare da share hawayen fuskarta. Da sauri ta ƙarasa falon tare da yi wa ƙawayenta umurnin su ɓoye ta kashe wutar falon bayan dad ya ɗauko fulawar da ya adana don ba ta kyauta. Mom da ke tafiya cikin tsananin gajiya ya yin da take jin wani irin bacci yana fisgarta. Da sauri ta miƙa wa Moses jakarta burinta bai wuce ta ji ta a kan gado ba. "Ma’am, I’ve collected all the document and I’ve sent them to him, he said that he would email you." "Okay," ta ce tare da karɓar jakarta ta cire wasu files ta miƙa mi shi, wanda ya karɓa cikin girmamawa. "Take this and give it to him." "Okay, Ma’am" Tana ƙoƙarin shiga falon wayarta ta yi ƙara a kasale ta kai hannu za ta kashe, sai dai ganin mai kiran ya sa ta ɗauka da sauri. "Hello, uwa ba da Mama, kina jina?" Daga can bangaren aka ce, bayan ta yi sallama. "Eh, Hajiya turai. Na san tun da kika kira ni bayan ba mu daɗe da gama waya ba akwai matsala, me ya faru?" "Haka ne wallahi, kin ga wani ces aka kawo mana yanzu akan fyaɗe, kuma abin takaici yarinyar shekara uku ne kacal." Da sauri ta rintse idanunta sai ta ji tamkar ta sanya kuka tsabar tausayin yarinyar. "Subuhanallahi! Don Allah ki yi duk abin da za ki yi, yanzu zan yi magana da Barrister Tukur. Don Allah ki yi ƙoƙarin da kika saba." "To shikenan, zan yi ƙoƙarin, amma wallahi lamarin nan yana ci mini tuwo a ƙwarya! Ba mu da wani aiki a Ƙasarmu sai kisa da fyaɗe." "Allah ya kyauta! Ya kawo mana agaji." Ta ce tare da kashe wayarta tana jin yadda zuciyarta ke suya. Ƙoƙarin neman numbar Barrister Tukur ta fara yi. Jannah da ke laɓe a bayan ƙofa zuciya ta ciyo ta, ganin kusan mintin goma da shigowarta amma ba ta shigo ba. Da sauri dad ya kama hannunta yana girgiza kansa da alamun kar ta je. Daurewa ta yi ta koma gurinta idanunta na zubar hawaye. Kimanin mintina ishirin da shigowarta sannan ta murɗa ƙofa ta shigo bayan ta gama waya da Tukur. "Happy birthday too you! Happy Birthday too you! Happy birthday too you!" Gabakiɗaya suka ɗauka suna rera waƙa tare da yin tafi. Mom ta saki nannauyar ajiyar zuciyar sai ta ja ƙaramin tsaƙi. Zama ta yi a kan kujera tana murmushin da ga gani kasan ƙaƙalo shi take yi. "Kai! Wallahi sam na manta yau ranar birthday ɗina ne, sai da aka rinƙa kawo mini gift da wishes na tuna. Na gode sosai Jannah." Miƙa mata flowers ta yi tare da rungume ta amma sai ta janye ta daga jikinta tana faɗin, "Thanks, my baby. Bari na je na kwanta kaina ciwo yake, na gaji matuƙa." Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin yin hanyar ɗakinta. Tsananin baƙin ciki ya rufe ta sai ta ji kamar ta sanya ihu, kallon dad ta yi da ya ji kamar ya rufe mom da duka. "Mom, za ki yanka cake. Please don't say no." "Okay, bari na yi wanka." Ta ba ta amsa a gajarce tare da karɓar flower da dad ya miƙa mata, ba tare da ta ce masa komai ba. Ƙarasa shiga cikin ɗakinta yi tana ƙoƙarin cire kayan jikinta. Idanunta suka kawo ruwa sai ta yi ƙoƙarin sharewa."Da ma na san hakan zai faru, na san cewar ba za ta tana ba ni lokacinta ba." Sai ta miƙe cikin azama ta bi bayanta amma lokacin har ta tuɓe kayanta ta shige bayi. Ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta fito. Ba tare da ta ce mata uffan ba, ta wuce wadrop tana neman kayan da za ta sanya. "Mom, why you behaving like that? Ƙawayena ne na gayyato su, don su taya ki murnar ƙarin shekara, amma you just embarrassed me and dad in front of them!" Shiru ta yi kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta juya ta kalle ta. "Don't stress me, I said I would come." Ta faɗa a gajarce cikin rashin kula. Tsananin takaici ya ƙara kamata ta buɗe baki za ta yi magana daidai lokacin da dad ya shigo."Give her a few minutes, she needs to get dressed." Kama hannunta ya yi suka fita. Tsuka ta yi, tana kulle ƙofar da suka bar ta a buɗe. "Jannah rigima! Sam ba ta tausaya rayuwata." Ta ƙarashe maganar tana warware tawul ɗin da ke jikinta. A maimakon ta shirya ta fito kamar yadda ta ce, sai kwanciya ta yi da nufin ta shingiɗa sai dai baccin ya fi ƙarfinta.Ta fusata iya fusata da sauri ta buɗe ɗakin ga mamakin ta sai ta ganta kwance wanda hakan ya sa ta saka kuka."Mom, please!" "Get out! I got to rest." Ta ce cikin tsawa tare da nuna mata hanyar fita. Kuka ta ƙara saki ta faɗa jikin dad. "Na fara tantamar mom ba ita ta haife ni ba Dad! Anya ba adopting ɗina ta yi ba?" Ta fara magana cikin kuka tare da ƙarashe maganar da tsigar tambaya. "Kar ki ce haka Jannah, mahaifiyarki ne." "To me na yi mata take mini haka? Ka na ganin abin da ta yi mini agaban ƙawayena. Ina ganin yadda iyayensu suka gina na su rayuwar da soyayya." "Ki ba ta lokaci za ta daina." Sai ta ƙara sakin kuka tana ƙoƙarin zama a kan kujera" Jannah, we’ve waited for a long time, I think we should go." Shiru ta yi ba ta amsa musu ba wanda fanin hakan ya sa suka fice daga falon. Sosai ta sanya kuka don ta yi matuƙar muzanta ba ta san da wani ido za ta kalle su ba in ta je makaranta. "Ki yi hakuri mom ɗinki na buƙatar lokaci, kin san wace ce mahaifiyarki" "Kai kaɗai nake so; I hate her. Ka yi mini alƙawarin za ka ci ga ba da ba ni kulawa?" "You don't have absolutely anything to worry about. I’ve got this." Share hawenta ta yi tare da rungume shi. "Ina son ka, dad." Sai ya shafa bayanta cikin sigar rarrashi da tausayawa domin ya fita jin hashin abin da ta yi mata. Watsi da alatun da suka shirya akan taburin ta yi. "Tunda ba ta buƙatar hakan, ba zan ƙara wahalar da kaina gurin girmama ranar haihuwarki ba." Ta ce tana tare da sa ƙafa ta tattaka cake ɗin. Washegari da safe ƙin fitowa ta tare da kulle ƙofarta. Sai misalin sha ɗaya saura miniti biyu ta fito, domin ta san cewar zuwa wannan lokacin ta fice aiki. Wanka ta yi ta shirya cikin riga da wando ash colour tare da yafa gyalenta ta ɗauki makullin mota da fice. A kan hanya ta tsaya ta siyarwa ƙawayenta ƙaton cek da drinks ta kai musu tare da ba su haƙuri. Ba ta dawo gidan ba sai misalin takwas na dare wanda shi ma kiran dad ne ya sanya ta dawo, amma ta yi niyar ta sai ten. "Ki daina zama har dare ba ki dawo ba, kin san ba na son yawon dare." "Okay." Ta ce tare da shigewa ɗakinta. Dad ya shigo ɗakin tare da ije mata tsarabar da ya yi mata kana ya ce, "Mom ɗinki ta tafi Malaysia and she’s gonna stay for two weeks." Shiru ta yi, ta ƙi ce masa komai ba don ba ta ji shi ba: Allah ya sa ta tafi gaba da can, Ta ce a ranta. Cikin dare ta kasa bacci sai juye-juye take ga shi wani irin sanyi da yake shiga jikinta. Da sauri ta miƙe ta ɗauko maganinta, domin tana jin kamar ciwonta ne zai tashi, amma sai dai ko da ta sha maganin ba ta ji sauki ba, sai ƙaruwa da yake yi. Miƙewa ta yi a hanakali ta yi ɗakin dad. "Dad ka buɗe mini ƙofa ba ni da lafiya." Ta ce jin ya ji ƙwaƙwansa ƙofar da ta yi. Da sauri ya buɗe ƙofar ya kamata suka shiga. Maganinta ya ɗauko ya ɓalle mata tasha, sannan a hankali sanyin ya fara ruguwa bacci ya kwasheta. Kamar yadda ta faɗa sai da ta yi sati biyu sannan ta dawo da misalin bakwai na yamma. A ranar ba su gaɗu da Jannah ba, don tana dawowa ta kulle kanta ta fara baccin gajiya. Jannah kuwa da ta dawo daga school ta samu ta dawo, tsaki kawai ta yi ta shige ɗakinta, ko kaɗan ba ta yi murnar dawowarta ba. Dad ne yake da rawar jiki da murna, har take away fita ya yi mata, wanda ba ta ci ba sai dai aka sa a frig sakamakon naunanyar baccin da ya kamata. Washe gari da safe tana zaune tana shan tea Jannah ta fito cikin doguwar riga iya gwiwa. "Hi," ta ce mata tare da neman guri ta zauna tana ƙoƙarin zuba abinci. Sai abin ya ba ta dariya sosai, ta san haushin abin da ya faru take yi."Jannah na dawo kuma.." "Excuse me please, I got to take this call." Ta ce tare da ɗaga mata hannu ta shige ɗakinta. Ganin hakan ita ma ta shirya ta tafi ofis. Tsaƙar dare da misalin biyu saura kwata Jannah ta fito daga ɗakinta cikin rawar sanyi tana kiran sunan dad tunawa jin za ta mutu. "Dad please ka taimaka mini." Ta furta tare da fashewa da kuka. Mom ce ta ji kukan sakamakon ba bacci take yi ba aiki take yi a laptop ɗinta, wanda da sauri ta fito ta kamata." Lafiya Jannah, ciwon ne ya tashi?" Ta tambayeta ba tare da ta jira amsa ba ta ruga ɗakinta don ɗauko magani. Duk da ta ba ta amma sai bai lafa ba, wanda hakan ya ta hankalinsu matuƙa musamman dad da ya ƙe jin kamar ya mai da ciwon a jikinsa. Sai kusan asuba sannan ta samu bacci ganin haka koda gari ya waye mom ba ta tashe ta aba akan su je asibiti sai da ta ba ri don kanta misalin sha ɗaya saura ta tashi. A lokacin dad ya tafi gurin aiki sakamakon kiran gaggawa da ya samu wanda kan dole mom ita za ta kai ta. Bayan sun isa asibitin likita ya yi gwaje-gwajen sannan ya ɗago kansa ya ce, "You should take Jannah back to Nigeria due to her situation. I believe that's the best solution for her illness. The climate in Nigeria is much warmer than in London, which might be beneficial." Ya karashe maganar yana duba files ɗin da ke kan teburinsa. Shiru ya ratsa na wasu ƴan daƙiƙa daga bisani ta katse shirun, bayan ta ɗan dogon nazari tare da kallonta da take ta rawar sanyi haƙoranta suna haɗuwa, ya yin da ta takure guri ɗaya. Duk wanda ya kalle ta ya san tana jin sanyin har cikin bargon ƙashinta ganin yadda ta yi. "I will make a decision, and whatever I decide, I’ll let you know. If going back to Nigeria will cure her illness, then I have no choice but to send her, even though I wanted her to complete her secondary school in London. I’ll be praying for the right solution," Ta ba shi amsa cikin jimamin halin da Jannah ta ke ciki." "Alright, take your time to think it through and come up with a solution," ya furta ya na examining yanayin yadda take rawar sanyi. Ɗaukar jakarta ta yi da kama hannun Jannah ta ce, "Alright, doctor. Let's catch up later. Thanks. Ya mike tare da rataye rigar likitancinsa yana taka mata ya ce, "it's my pleasure to assist someone as generous as yourself. " Murmushin ta yi ba tare da ta ce komai ba ta fice daga ofis, zuciyarta cike da jimamin ciwon 'yar gudaliyarta. Haushi ko tsabar takaici zata kira abin da ta ke ji oho, ganin yadda 'yan jarida suka cika gaban asibitin. Jannah ta kalli 'yan jaridar ta juya tana kallon mom da ta haɗe rai tamkar hadarin da ke shirin zubda ruwa, duk da yanayin fuskarta ya nuna she didn't have the time to give them her full attention, but she needed to do something that would provoke a reaction. After all, those journalists were just so frustrating to deal with. Kamar karamar yarinya ta sake ihu da karfi. "Mum, I'm feeling absolutely frozen. Please do something that'll make you stop talking to those blabbermouths," ta furta cikin shagawaba da rawar sanyi a hakorarta. Cikin sauri ta juya ta kalleta sai kuma ta maida kallonta ga direba Maris. Idanunsa suka firfito ganin tsantsar bacin rai a fuskarta. "I'm so sorry, ma'am. It's not my fault at all, and I had no idea how they managed to track down your whereabouts. I just saw them, just as unexpected as you did." Ya furta muryarsa cike da tsoron ta domin ya san abubuwa guda biyu ta tsana wanda yana fatar kada rana ta kasance ya karya doka. Sai a lokacin ta tuna ta yi waya da sakatarenta, Pedris. It must be him! Ta ayyana hakan cikin ranta dai-dai lokacin da suka karaso gurin ta tare da jefo mata tambayo yi marasa iyaka. Ba tare da ta furta musu kalami ta ja hannunta suka shiga cikin mota, yayin da direbar ya ja motar da karfi, ya bar su jiki a sanyaye suna kallon hanyar da ta wuce. Jannah ta kwantar da kanta a kan saman kujerar ta ja karamin tsuka tare da faɗin, "Bloody cunts." Misalin ƙarfe goma na dare suna zaune a falo yayin Jannah take kwance akan akan doguwar kujera, har zuwa lokacin a takure take duk da cewar sanyin ya ragu ba kamar ɗazu ba. Daddy ya rage ƙarar tibin da yake saureren labarai tare da gyaran murya ya ce, "I was thinking the same as Doctor said Halee. You have to feel sorry for her and go back to Nigeria. It’s time for us to face reality and stop avoiding it. Abin da ya faru ai ya faru. " Shiru ta yi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk cewar ta yi kewar ƙasarta, sai ai tana ganin ba wannan lokacin ya kamata ta koma gida Nigeriya ba, domin a wannan lokacin sam ba zata iya ɗaukar damuwa ba, musamman da take son saka hannun jarinta a kamfanin Badoon. "I'm thinking she should go alone cus I don't have a plan for going back in ya so she can stay at Ya Muhammad’s house kafin na gama abin da zan yi na koma, ka san har yanzu James ya ƙi yarda na yi investing din share guda biyu a cikin kashi goma na hannun jarin." Daddy ya ɗan musƙuta tare da ƙara rage sautin tibin. "Har yanzu kin ƙi fahimta ta Halimatu, a ko da yaushe burin ki ki rinƙa yin lamuranki da kanki, duk cewar kin san ni mijinki ne ya kamata ace ni na ɗauki ragamar komai, bawai ina ƙalubantar lamuranki ba ne, sai dai ni ya kamata na jagoranci duk kan lamuranki, domin ita ‘ya mace has limitation. " Ya ɗan numfasa yana kallonta ganin yadda lokaci guda fuskarta ya canza ta haɗe rai tamkar wacce aka aiko wa da tsaƙon mutuwa. Ta ɗan ja fasali tare da kauda kanta barin kallonsa, bayan wasu ƴan daƙiƙa ta mai da ganinta garesa. "Ina tunanin mun gama wannan maganar kuma mun yi alƙawarin mantawa da ita a tsakaninmu." Ta ce ba tare da ɗauke kanta daga garesa. Ya ije remote ɗin hannunsa tare da takowa a hankali ya ƙaraso in da take zaune, daida lokacin da ta juya masa baya. COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 *KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* *FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 2-3* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Hannunta ya riƙo da sauri. "Ki fahimce ni a ko da yaushe ba kya mini kyakykyawar Fahimta, ya kamata ace tsawon shakarun da muka ɗauka komai ya zama tarihi a tsakaninmu.” Lokaci guda ta sa kuka. "So, are you saying I should be dummy? Me kake son ka ce injiniya? Mene ne ban fahimta? Ka sani tun kafin na gama sanin wace ce ni na fahimci komai dake tsakaninmu. Don Allah ina son ka manta da wannan maganar, ya wuce komai ya wuce kuma kai ma ka san hakan." Ta karashe maganar cikin muryar kuka sosai, daidai lokacin Jannah ta miƙe a hankali ba tare da ta kalle su ba zata bar falon kamar yadda ta saba duk lokacin da suke queralling or dispute. Mom kama hannun ta da sauri ganin za ta fadi, amma sai ta fisge. "Please, mom, I need a break." Ta furta bacin rai tare da barin wurin ba tare da ta ji mai za ta ce ma ta ba. Tana shiga cikin ɗakinta garƙame ƙofar da makulli ta sharce hawayen da suke gangaro mata ba tare da ta ji saukarsu ba. Faɗawa kan makeken gadonta da ya kusa cike ɗakin ta yi, ta cire ribon ɗin kanta ta watsa gashinta. Wani irin kuka ya goce mata ba tare da ta yi shiri ba, daidai lokacin da ta ji suna magana da ƙarfi. "I used to believe that family is a source of happiness, but mine seems different. They’re always in conflict. Could it be personality differences affecting their marriage? Ta tambayi kanta cikin zubar hawaye. Sai ta mirgina gefen gadon tana jin zuciyarta na mata suya, musamman da ta ji muryarta ya fi na shi. "She’s always like that, thinking she’s super-talented just because she is influential, but it’s not true—she’s only deceiving herself." Idanunta ta suka kara kawo ruwa daidai lokacin da ta ji yana ba ta hakurin laifin da take ikirarin ya aikata all the time da ta kasa yafe masa. "Me yake tsakanin iyayena wanda suka kasa manta da shi, sannan suka ƙi sanar mini?" Ta tambayi kanta cikin rashin amsa. Sosai take kuka har da buga kanta a kan gadon."Tabbas lamarin iyayena akwai ruɗu a ciki, na rasa yadda zan fahimci lamarin da ke faruwa. Wataƙila hankalina ba kai mizanin da zan fahimci haƙiƙanin abin da ke faruwa ba." Ajiyan zuciya ta saki mai ƙarfi lokaci guda kanta ya kulle. "I’m feeling lonely. The loneliness is too much to explain, and no one seems to be there for me, even though dad tries his best." Ta karashe maganar tana cizon lebenta, sai kuma ta saki murmushi mai kama da kuka. "I wanna go back to Nigeria." Direction na kwanciyarta ta canza tana kallon hoton 'yar tsohuwar dake manne a bangon daki da suka ɗauka ranar da tazo London lokacin da za'ayi mata aikin ido, wanda ta ci kwalliya ta kafe wai a dole sai ta kama kyanta. Dariya ta kwance mata babu shiri Takowa ta yi a hankali ta ɗauke hoton tana kare masa kallo."Hajiya Baaba kenan! Yar tsohuwa mai ran ƙarfe. Ko yanzu ya kike? Na san wannan rigimar na nan." Ta jima tana kallon hoton daga karshe ta mayar inda yake. A ranta tana jimamin halin mom, a kan na ci don har yanzu maganar take murya a ɗage. Sai ta kwana a kan sofa tare da ɗaukar wayarta, ta kunna waƙa ta saka earpiece tana sauraren waƙar har bacci ya kwashe ta. Da daddare misalin sha ɗaya na dare, mom tana sanye da ash din duguwar rigar bacci. Zaune a gefen gado, da laptop dinta a saman cinyarta, ya yin da kuma wayarta ce saƙale a kunnenta tana amsa calls. Dad da ke juye-juye a gado bacci, ya ƙi zuwa masa ya juya kwanciyarsa, tare da kallon ta da take waya tamkar babu abin da ya dameta. Kimanin mintina talatin ta kammala wayar, ta ije a kan stool ta ɗauki tea ɗin ta da ya fara sanyi tana kurɓa a hankali. "See Halee, I’ve had enough of your negative attitude, especially the way you treat me like your son." Ta kalle shi kamar ba za ta ba shi amsa ba sai kuma jikin ta ya yi sanyi, domin ita kanta ta san abin da take yi, was beyond limitation, amma kuma da ta tuna all the things that she went through, all the agony sai ta ga ai he deserved it, in fact, even more than that. Ta bude Baki za ta yi magana sai ya riga ta ganin babu nadama ko kaɗan a fuskarta. "Forget the fact that you’re more influential than I am—I can't tolerate this nonsense. You need to treat me the way a Hausa wife treats her husband, not like those fake people that surround you. Remember your culture." "You’re a cheater, engineer! You know that, right? You make me look like a fool, acting all innocent and calm, but that ain’t you. You’re just like a chameleon!" Ta karashe maganar cikin zubar hawaye. Ya yi shiru yana kallon ta aransa yana mamakin taurin kanta that she couldn't forgive. Sai ya mike zai fita komai ya tuna ya dawo tare da kamata yana ganin he deserved even more than that, tun da halinta ne, he has to take it. "Fuck off, Engineer! You are a cheater, you cheated on me." Ya hada ta da jikinsa. "It’s okay. Let’s focus on Jannah’s illness; she needs your help. We need to talk discuss her future." Ya karashe maganar cikin tsigar rarrashi. "I’m sorry." Ya ji ta furta wanda ya sa ya kalle ta da sauri duk da cewar ba sabon wani abu bane, domin tana fada mishi fiye da hakan shi ne ya bata rawar shi da tsalle ya kuma yi nadama alokacin da ruwa ya karewa dankaɗa, don haka ya kyale ta akan maganar Jannah, considering that she didn't want to talk about it. Washegari da misalin sha ɗaya saura kwata Jannah ta farka. Miƙa ta yi tare da salati ta ya ye bargon da take luluɓe shi ta zuro ƙafafun ta ƙasa. Figigiyar rigar baccin dake jikin ta, ta cire sannan ta faɗa toilet ta ɓata lokaci tana wanka kafin ta fito ɗaure da sky blue tawu, kanta a jiƙe ya yin da ta ɗora ɗan ƙaramin towel tana tsane kanta. Hand dryer ta ɗauka sannan ta kunna socket ta kunna tana busar da kanta, zuciyar ta ke ɗauke da tsananin damuwa wanda kana kallon face ɗin ta you can tell she’s moody. Bayan ta kammala shiryawa cikin wata rigar pink mai kyau, ta ɗauki ribon tare da ɗaure kanta. Wayarta ta ɗauka tare da janyo ƙofar ta ta rufe. A falo ta zauna kan doguwar kujera tare ta kunna kallo ta ɗauki remote ta koma ta zauna. Ganin labaren ake yi sai ba ta canza tasha ba ta ije remote ɗin a kan stool ta fara danna wayarta. Mom ce ta fito sanye da wata fitinannniyar doguwar riga wace tasha ado sai. Siririn ɗankwalin rigar ta yi rolling ɗin sa a kanta, sannan ga jakarta da takalmin ta mai azababben kyau. Jannah ta yi mata kallon uku tara duk da ta yi mata kyau sosa, domin ita kanta ta san she’s so beautiful and dashing. She looked elegant and so charming. Ga shi tana sa masifar tsafta sam ta tsani ƙazanta. Mace ce da ba ta kula da shekarunta ko ta haifi Jannah in tana abu sai ta ba ka mamaki don jin ta take tamkar 'yar shekaru sha takwas. So, she could categorize herself as mace classical wanda a dalilin hakan ta ɗauka take gara mahaifinta kamar ƙwallo duk da cewar shi ma ba baya ba. Ƙarasowa ta yi cikin tafiyar taƙama tana waya, ta zauna a gefenta tare da ci gaba da wayar, wanda hakan, ta yi matuƙar tsana domin sai ta ɗauki kusan awaya tana yi. Hakan ta faru, don ta ɗauki tsawon lokaci har ta gaji ta ɗan saki siririn tsaki, tare da janye hannun ta da ta rike za ta bar gurin, ganin hakan ya sa ta sallami mutum ba don ta gama ba bayan ta riƙe hannunta, yarda ba zata iya fisgewa ba. "Morning, sweetheart. You look pretty." Ta ce tare da ware hannunta da nufin ta rungume ta, amma sai ta matsa gefe ta ƙi amsa gaisuwar. "Jannah na gaya miki." "Mom you constantly nagging, no matter what you do. Please bana so, you are provoking me." Ta ɗan murmusa jin abin da ta ce sai ta ƙara rungume ta duk da ba ta dake zuɓɓurawa ta ja leɓenta tare da kama hancin. "Shiryaya kawai! kina ba ni mamaki, ban taɓa ganin 'yar da take against ɗin mahaifiyarta ba, but you do..." "You caused it. Kece kika sa nake miki hakan, amma kin san babu wacce na ke ƙauna da so kamar ke, but I don't know why you do that to me and me father." Ta katse ta tana fadin haka. "See, your dad deserves it, and I'm tired of this whimsical attitude of yours sai na dawo. Watch your mouth." Sai ta fusata ganin ba ta da ninyar canzawa daga munanan ɗabi'un da take yi cikin muryar kuka ta furta bayan ta sha gabanta. "I think you should go for a relationship therapy, you need that cos you have no idea ho…" Wasu kyayawan mari ta sauke mata a fuskarta cikin ƙunar rai. "Ki san kalaman da za ki rinƙa gaya mini a matsayina ma mahaifiyarki, from now on I won't take your shit anymore." Jannah ta fusata idanunta suka kawo ruwa sai ta sanya ƙara mai razanar ta tokare ƙofar da za ta wuce. "Ba zan ƙara zama dake ba, ki mai da ni gurin Hajiya Baaba, na san za ta ba ni kulawa fiye dake. Mom, I can't stand your attitude much longer." Sai kuma ta yi shiru tare da jan majina tana ƙara sakin wan kukan ta ɗorawa da ce wa, "Idan kuma ki ka ƙi, kin ji na rantse miki, I will kill meself! I think suicide would be better for me than living in this hell you call a family." Lamarin sai bata matuƙar mamaki, ta yi zuru tana kallon ta yadda take faɗin kalamai mara sa daɗin ji. Idanunta suka kawo ruwa, sai ta fara tunanin tarbiya ce ba ta iya ba, ko injiniya ya yi nasarar raba ta da 'yarta? Ba tare da ta furta mata kalami ta ɗauki jakarta ta ture ta tare da fita daga falon idanunta na zubar hawaye daidai lokacin da take cewa, "I will get a visa, I have money on me." Da sauri Rose da take kicin tana sauraron hayaniyar da suke yi ta fito tare da rungume ta "Please, Jannah, take easy; it’s okay." Sai ta kara sakin kuka tare da ƙara rungume ta. "Ba ta sona! Mace ce mai son dukiya da duniya. Shi ya sa ba ta barina na huta kullum cikin karatu, saboda na yi ilmi na tara dukiya. Tir da dukiya irin na ta, wacce ta sa muka kasa samun kulawarta sai da ta ba wa duniya." "Sorry." Ta kara ce mata duk da ba fahimci mai ta faɗi ba tare da kamata suka shiga ɗaki. Da sauri Rose ta buɗe wardrobe nata ta ɗauko mata pills ta ɓalle tare da mika mata, amma sai ta karɓi na hannunta ta ƙara da guda uku ta watsa a bakinta. Zare idanunta ta yi, sai juma ta kasa cewa komai, tana girgiza kanta kamar ƙadangaren kutu. Sosai take ganin sakarcin mom da ta kasa gane 'yarta tana shan maganin depression and anxiety. Koda yake she would not be surprised domin ba ta ba ta lokacinta ba balantana ta fahimci haka. Ko da mom ta shiga mota kusan minti goma ta kifa kanta a sitiyarin motar hawaye ke zuba a fuskarta, bayan ta ba da umurnin kar a bar ta ta fita ko ƙofar gida. "You are so insolent to me. Why?" Ta furta cikin tsananin ɓacin rai. Da ta dawo aiki ko kofarta ba ta kalla ba, saboda haushin ta da take ji, amma tunaninta yana kanta, musamman da Rose ta gaya mata ta ƙi cin abinci. Dad ne kawai zai iya shawo kanta, don haka ba ta damu kanta da ta je gurin ta ba ta yi kwanciyarta. Haka kuwa aka yi don sai da ya shafe kwana biyu yana rarrashi sannan ta haƙura ta saki kamar babu abin da ya faru, sai zaman na su ya dan yi daɗi babu laifi, duk da damar kowa harkar gaban shi ya ke yi. Kasancewar Jannah suna lokacin hutu na first term inda za ta shiga e.s.s 3. Sai ya kasance gidan da ga ita sai Rose. Kullum tana cikin ɗaki, daga kallo sai bacci da chatting, sai in ta gaji ta fito falo ko ta je gurin Rose, don ko mom ta dawo ba ta kanta take bi ba, dad ne wani lokacin yake dan samun kasancewar da ita. A haka sai suke rayuwarsu yau fari gobe tsumma. Ranar kuma aka yi rashin sa'a bayan kwana biyar ciwon ta ya ƙara tashi. A lokacin duk ba sa nan, sai mai aikin su Kelen da take kicinn tana girki, kasancewar ranar ba duty ɗin Rose ba ne. Kelen yarinya ce domin da kaɗan ta girmi Jannah. Tana bacci misalin shidda da yamma ta rinka jin sanyin na taso mata a hankali, tun tana controlling har ta ji this was more than she could take. Wayarta ta ɗauka ta dialling number dad domin ta san shi ne kawai zai ba ta attention her more than mom. She might have been unlucky to call her phone and find it switched off; she could’ve been in a meeting. Out of that temptation ta kira wayar dad, sai dai to her surprise, he wouldn't be coming due to a specific reason that he mentioned. Jifa da wayar ta yi, tare da rufe fuskata da hannayenta, tana jin yadda sanyin ke ƙara tasowa. Sai da aka kira mangariba ya shigo, cikin sauri ya nufi ɗakinta, duk da cewar ya kira doctor ya duba ta, amma sam hankalinsa na kanta. Tana ganin shi ta samu kuka mai karfi. Hanunsa ta kama sosai. "Please do something about this coldness; if not, it will kill me. Look, my body is shaking. Don Allah, dad, i'm tired.” Sosai ya ji tausayin ta lokaci guda kuma ya zargi kansa, domin shi ne sanadin komai. Don haka ya zama dole ya tilasta wa mata, komawa gida, saboda ko ita was like isolating kan ta ta yi, she wasn't enjoying the environment at all. Given her body language, she was pretending. Da taimakonsa sanyin ya fara raguwa bayan ya haɗa mata tea mai zafi ta sha har yana kona mata Baki, sannan ta yi wanka da ruwan zafi sosai, ya kunna mata room heater, sai ta samu sauki duk da cewar har zuwa lokacin haƙoran ta na kaɗuwa. Ganin ta samu bacci ya kashe mata wuya ya fito falo yana zaune har aka kira sallah, daidai lokacin da ta shigo tana rike da jakarta. Kasancewar ba ta san ciwon ya tashi ba, sai ta wuce ɗakin ta don gabatar da farali, sosai ta dawo da yunwa. Dad ya rufa mata baya. A ɗaki bayan sun idar da sallah suka sakko kasa don cin lunch, sannan ya ke sanar da ita. Abincin ta bari na nufi dakinta, sai dai har zuwa lokacin bacci take yi, duk da alamu ya nuna ba ta enjoying ɗin sa, duba ga yadda ta tsakure kamar mage. Kofa ta kama tare da juyowa ta da dawo wa falo ta zauna hannu biyu ta zuba tagumi. "Mu koma gida Halee, don Allah. Our daughter needs that." Kamar mai tunanin she couldn't say a word. She adjusted and hesitated for a moment. "In har muka koma gida ba zan taɓa manta wa ba duk da cewar na yi maka alƙawarin hakan, sai dai ya zama tabo mara guguwa wanda ya zama silar rashin nagartuwar raguwarmu." Ta karashe maganar cikin sautin kuka tare da juya bayanta. A hankali ya taka har gabanta ya tsaya lokaci guda idanunsa suka canza. Gwiwowinsa a ƙasa ya kama hannunta a sauri ta janye, ba tare da ya damu ba ya fara magana. "Don Allah ki manta komai na roƙe ki a karo na ba adadi, ki taimake ni ba don halina ba. Kin san yadda abubuwa suka kasance, amma na yi miki alƙawarin hakan ba zai taɓa garuwa ba in sha Allahu kuma zan tsaya tsayin daka, domin na ga na kare ki da ƙarfina.” Sosai take kuka ba tare da ta saurare shi ba, wanda dalilin kukan yake ƙoƙarin ɗauke numfashinta, ganin hakan ya sanya shi miƙe wa da sauri ya fice daga gidan domin ya san a wannan lokacin babu wanda zai iya rarrashinta. Shi kansa a zaman auren su ya san yana fama da wasu personlity ɗinta wanda suke unlike to his tunaninsa da hankalinsa. Kai tsaye harabar gidan ya fice yare da buɗe murfin motarsa ya shige tare da bata wuta ya fice daga harabar gidan zuciyarsa na tafasa tamkar garwashin wuta. A hankali ya gangara motarsa zuwa gefen titi tare da kashe motar ya buga kansa da sitiyarin mota a hankali yace. "Prideful woman! Yes absolutely she is." Ya furta yana share fuskarsa da zufar da ta tsatsafo masa. "Why, Halima, mai ya zuciyarki take kamar ta kafuran farko, Allah mun masa laifi ya yafe mana, amma sam ba kya yafiya." Idanunsa suka kaɗa jajur har wani turiri kansa yake yi. Kifa kansa ya yi yana jin ina ma ana mai da hannun agogo baya, da ya gyara lamuran da suka faru a baya waɗanda suka zama mara guguwa suka canza alaƙar dake tsakaninsa da iyalinsa, amma sai sai kash! Bakin alƙalami ya bushe kaddara ta riga fata. Tsawon lokaci ta ɗauka tana durƙushe a gurin zuciyarta tana tafasa ji take tamkar ta mutu ta bar duniya duk da cewar Allah ya wadata da komai na jin daɗin duniya, domin tana cikin matan da suka amsa sunansu kuma suke fantamawa da kuɗaɗensu. Kasacewa mace ce jaruma mai kamar maza a tsaye take. Shahararriyar yar kasuwa wacce ta aje aikin gwannnati domin zagaya ƙasashe don kasuwancinta, don zata iya shiga cikin jerin matan da za'a iya irga kuɗinsu a matan Nigeria. Sai dai duk da irin arzikin da Allah ya yi mata amma akwai tabon da ya raunana zuciyarta wanda take jin tamkar gara ta yi bankwana da rayuwar a take ciki, amma sai dai mutum bai da ikon canza kaddarar rayuwarsa. COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 *KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* *FIRST CLASS WRITER'S ASSO....* *Page 3-4* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Kimanin awa ɗaya tana gurin ba tare da ta motsa ba, duk da irin kiran wayar da ake damunta da shi, amma ko motsi bata yi ba, gyara zama da ta yi tare da lumshe idanunta tana jin wani irin raɗaɗi a cikin zuciyarta wanda yake santa kanta sarawa tamkar zai fashe gida biyu. Nannauyar ajitar zuciya ta saki tare a sharce hawayenta ta miƙe daidai lokacin da Jannah ta fito daga cikin ɗakinta tana kallonta, tare da sun yi wa juna magana ba, ta shige cikin ɗakinta. Duk da cewar Daddy ya kan kwana ba'a gida ba, sai dai wannan karon hankalin Mom ya tashi ƙwarai, domin a tunaninta fushi ya yi, don haka ta shiga kiran layinsa, amma bata shiga. Misalin ƙarfe biyu na dare tana zaune a tangamemen falonta idanunta akan fuskar wayarta har yanzu layin shi take kira amma ta ƙi shiga. Jifa ta yi da wayar kan kujera tare da dafe kanta lokaci guda ta shiga sintiri a falon. Motsi ta ji a bayanta da sauri ta wai ga, daidai lokacin da Jannah ta fito daga kicin hannunta riƙe da kofin madara. Murmushi ta sakar mata amma sai Jannah ta kauda kanta, ba tare da ta ƙara kallonta ba ta shige cikin ɗakinta. Saboda ba tana jin abin da ya faru tsakanin su har fitar dad, sakamakon fitsarin da ya fashe ta ta ji suna hayaniyar. Mom ta saki ajiyar zuciya. Zubbur ta miƙe tare da bin bayanta. Zaune ta same ta da kofin madaran a hannnunta, tana kurɓa idanunta na kafe akan wayarta da take kallon korian film. "Jannah na hana ki kallon dare, amma ba kya ji saboda ban isa na gaya miki magana ba ko?" cikin tsigar tambaya da kashedi. Nauyayyan idanunta ta zuba mata wanda bacci ne a cikinsu sun kaɗa sun yi jajir saboda kukan da ta sha "Oh! Please, Mom, ki bar ni na yi kallo saboda ba na jin bacci."Momi ta buɗe baki zata yi magana Jannah ta katse ta cikin muryar kuka, yayin da wasu zafafen hawaye suka gangaro kan kyakyawar fuskanta. "Please, Mom!" Ta furta yayin da ta rushe da kuka sosai. Jim Mom ta yi yayin da take jin kukanta har cikin ƙahon zuciyarta, sai dai bata da kallmar da zata iya rarrashinta a shi, domin in da zata samu damar kukan da tafi buƙatar hakan, don haka ta jawo mata ƙofar tare da jingina jikinta da ƙofar daidai lokacin da wani guntun hawaye ya siraro mata a ƙuncinta waɗanda suka fi garwashin wuta zafi. "Wayyo Allah na!" Jannah ta furta cikin kuka tare da jifa da kofin dake hannunta ya tarwatse ƙarar fasa ƙofin ya ɗaga hankalin Mom ta rintse idanunta tana jin karar yana kuwwa a kanta. "Wace irin uwa nake da ita, wacce ta ruguza duk farincikin rayuwata? Mom sam ba ki yi adalci a rayuwarmu ba, domin kin mai da rayuwarmu tamkar makabarta. Ko mene ne Dad ya yi miki ta cancanki ki yafe masa." Kuka take sosai tana sumbatu. Lumshe idanunta ta yi take zuciyarta ta ƙara ɓaci. "Ke nan Jannah haushina take ji? Sam bata ganin na mahaifinta." Cikin mamaki ta furta hakan a ranta. Da gudu ta ruga cikin ɗakinta ta kulle. A ranar Dad bai dawo ba, sai washegari da misalin shidda da rabi na safe daidai lokacin da Mom ta fito daga cikin ɗakinta, tana sanye da doguwar rigar bacci fara ƙal. A tare suka kalli junansu na ɗan daƙiƙa sai suk ɗauke kai ba tare da sun furta magana ba. Dad ya mai a kallonsa gareta lokacin da ta zauna akan dining table tana ƙoƙarin kiran waya. A hankali ya ƙaraso gabanta ya yi kamar zai zauna a kujerar gefenta sai kum ya fasa ya tsaya a gabanta tare da ƙura mata ido. Ba tare da ta kalle shi ba duk da cewar ta san ita yake kallo, amma ta yi biris da shi har sai da ta kammala kiran wayar duk da ba dogon magana ta yi ba, domin umurni ta bada a wayar ta kashe. Idanunta ta ɗaga ta yi ɓasa wani irin kallo sai ta miƙe da sauri ya kama hannunta ganin zata bar gurin. "Ina fatan sarauniyar mata ta tashi lafiya." Yace da ita tamkar bata ji abin da yace ba ta fisge hannunta zata wuce. Dad ya yi sororo duk da cewar ya saba da hakan amma ya ji babu daɗi kamar duk lokacin da ta yi masa hakan. Tana ƙoƙarin hayewa sama mai aikinta, Rose, ta fito daga kicin tare da durƙushewa ƙasa tana kwasar gaisuwa. Cikin sakin fuska ta amsa mata tare da yi mata, umurnin abin da take so saɓanin wanda yake a rubuce akan timetable, sannan ta haye sama tare da bugo ƙofa garam! Ya daɗe a gurin tamkar gunki zuciyarsa na suya, sannan ya shige ɗakinsa. Ƙarfe goma daidai mutanen gidan suka hallara akan dining domin karyawa. Sam babu mai magana a tsakaninsu. Ga abinci kala-kala amma sai juya cokulansu suke yi, domin gara Mom da Daddy sun sha titi Jannah kuwa babu abinda ta kurɓa. Dad ya yi gyaran murya ya ce, "Jannah, eat up. I don't want you to starve youself. You know that not eating is dangerous for a person, and you’re going for a check-up today. Remember?” Murmushi ta sakar masa ta ce, "I do. Zan ci, dad. Kai ma ka ci abinci. please Dad." Ya mayar mata da murmushin tare da kai lomar soyayyen ƙwai a bakinsa, ganin haka ya sa ta gutsira bread ta saka a bakinta, suka kalli juna tare da ƙara sakin murmushi a karo na biyu. Mom ta ije wayarta da tun da ta zauna take amsa waya, wanda hakan yana matuƙar ɓatawa Jannah rai, domin kusan kodayushe bata da aiki sai waya. Ita kam bata taɓa ganin uwa wacce bata damu da ƴarta ba, domin in suna labari da ƴan ajinsu suna gaya mata irin yadda iyayensu suke wasa da su tare da basu lokacinsu, amma ban da Mom da bata da lokaci saina tare kuɗi da business ɗinta, wanda a irin kuɗin da take da shi ya kamata ace ta bar komai ta ba su farinciki, duk da cewar ta fahimci mom tana tara kuɗi ne don ta wulaƙanta mahaifinta son ranta duba ga tafi sni kuɗi nesa ba kusa ba. Tuni ta gama fahimtar kuɗin da ta fi shi ya sanya take wulaƙanta sa, domin in dai ba don kuɗin ba, ya kamata ace ta yafe masa akan lifin da take iƙirarin ya yi mata. Tun da suka zauna mom bata ce ƙala ba har suka kammala karyawa ta miƙe cikin sauri tare da sumbatar Jannah a fuska. "Ki kula da kanki na wuce amma ba zan daɗe ba." Ba tare da ta jira amsa ba ta fice. Jannah ta taɓe bakinta tare da rakata da idanu har ta isa gurin escouts ɗinta da suke jiranta ta fice daga falon. Taɓe bakinta kara yi tare da mayar da hankalinta kan Dad ta sakar mishi murmushi sannan ta ci gaba da cin abincinta. Kimanin minti biyu da fitar Mom har zuwa lokacin babu wanda ya yi ko tari, kowa da abin da yake saƙawa a ransa. Mom ta buɗe ƙofa ta shigo. "Jannah ki zo mu fara kaiki asibiti daga nan mu wuce." Jannah ta juya jin abin da ta faɗa, ta gyara jibgegiyar rigar sanyin dake jikinta tace. "No, kar ki samu Dad zai kai ni in ba shi time zan yi driving ko Nups ya kaini." Iya abin da tace mata kenan ta juya tare da ci gaba da cin abinta ba tare da ta kara kallonta ba. Shiru ta yi tare da tsayawa sai kuma ta juya ta fice daga falon. "Dad mu koma gida Najeriya ko da Mom ba zata bika ba, in ta zabi kasuwancinta." Ta furta cikin muryar tausayi tare da kallonsa. "Kiyi haƙuri Jannah in sha Allahu zamu koma gida gabakiɗaya, amma kiyi haƙuri yanzu dole zan tura ki gida ko da Mom ba zata so ba." "Ka bar damuwa da damuwarta, domin ban taɓa ganin mace mai son kanta ba Dad. Laifi ne ka yi ma ta kuma ka nemi yafiyarta, ya kamata a ce ta yafe ma ka." Murmushi ya yi ji abin da ta ce. "Wataƙila da a ce ke ce minjinki ya yi miki hakan, ƙila ba za ki iya masa afuwa." Dariya ta yi jin ya ambaci mijinta. Kunya ta kamata sai ta sunkuyar da kanta tace." Allah ya kyauta, zuciyata ba irin tana bane tuni zan yafe masa." Shima dariyar ya yi jin abin da ta ce. Kama hannunta ya yi. "Har yanzu ina ƙara gargaɗinki da ki daina shiga faɗanmu, ko me ta yi mini na cancanci hakan, kuma ina ƙara gaya miki ita ɗin mutuniyar kirki ce. Fatana watarana zata haƙura mu ci gaba da zamanmu lafiya." Shiru kawai ta yi ba tare da tace masa komai ba, lokaci guda idanunta suka fara zubar hawaye. Tausayinsa take ji sosai domin a tunaninta tsanannin son da yake mata ne ya sanya shi rashin ganin laifinta, amma ita ta auna mom a mizanin hankalinta ta fahimci mace ce mai son zuciya da son kanta wacce ta fifita kuɗi akan komai take yin abin da ta ga dama, wannan dalilin ya sa ta ɗauki alƙawarin ba zata taɓa yarda ta nemi kuɗi fiye da mijinta ba, domin gani take a dalilin hakan ne mom ta raina mahaifinta. Ture plate ɗin gabanta ta yi tare da miƙe wa zuwa ɗakinta don ta ɗauke mayafi su tafi asibiti. Dad ya bi ta da kallo cikin so da ƙaunar ƴa guda ɗaya tal wacce Allah ya ba shi. Bayan ta gama ganin likita direba ya dawo da ita. Kai tsaye ɗakinta ta nufa tare da kwantawa a kan makeken gadonta. Ajiyar zuciya mai nauyi ta saka tana jin babu daɗi a ranta. Rose ta shigo cikin girmama ta ce, "Ma’am, lunch is ready." Yamutsa fuska ta yi tare da ɗan jan tsuka ta ɗauki wayarta tana duba time. "What’s for lunch?" "Supaghetti." Ta ba ta amsa. "May be I will eat later, as I’ve lost me appetite." Ta ce ba tare da ta kalle ta ba, sai ma ɗaukar wayarta da ta yi ta kwanta a kan gado. "Please, you know your condition; you hav.." "I said I will eat later! So please excuse me." Ta daka mata tsawar da ba ta san ta yi ba, domin Rose tamkar uba take a gurin ta don kular da take mata sam ba ta samun sa daga mom. "I’m sorry, Ma’am!" Ta faɗa cikin girmamawa tare da juya wa ta fice da sauri har tana haɗawa da gudu, sai kuma ta ji sam ba ta kyau ta ba. Mikewa ta yi daga inda take ta buɗe wardrobe ɗinta tare da ɓalle Amitriptyline ta watsa a bakinta tare da komawa ta kwanta tana jin yadda kanta yake juyawa tamkar ana murza sitiyarin motar da a ka ƙure mata maleji take shararar gudu a saman titi. A hankali ta fara jin kanta na saituwa zuwan can, maganin ya fara aiki wani irin ɗauyayyar bacci ya ɗauke ta. Rose ba ta ji gargaɗin da ta yi mata ba kamar yadda ta saba, bayan ta ba ta ɗau lokaci ta shigo. Ganin ta kwance rigingine ta ɗora filo a fuskarta, sai ta yi matuƙar ba ta tausayi. A hankali ta isa gare ta tare da gyara mata kwanciya, yayin da ta ji hawayen tausayinta na bin ƙuncinta. Ita kam ba ta taɓa ganin mace wacce ta fifita neman kuɗi da taimakon al'umma a rayuwarta ba. Tsananin tausayinta ya ƙara kamata domin ta san she is depressed. Hannunta ta sa ta janye mata gashinta da ya zubo a fuskarta. Mikewa ta yi da sauri ganin ta juya tuna gargaɗin da ta yi mata, amma sai ta ga ta kama hannunta ta riƙe tare da faɗin, "Momiii." Cikin magagin bacci. Ba ta tashi ba sai bayan kiran magariba sannan ta miƙe. Wanka ta yi ta fita neman abinci ba tare da ta damu da sallah ba don yunwa take ji matuƙa don haka ta bari sai cikin dare in ta tashi karatu ta yi sallah har da isha'i. Sai bakwai saura ta shigo cikin gidan da waya a kunninta tana waya. Dad da ya rigata dawowa ya shiga ɗakin Jannah sai ya ga tana bacci don haka ya zauna a falo bayan ya ci abinci ya kunna news. Ɗaga masa hannu kawai ta yi lokacin da take cire takalminta da gyalenta, wanda Rose ta karasa kan kujerar da sauri ta haɗa da laptop ɗinta da ta karɓa. Ido kawai ya bita da shi har ta shige ɗakinta. Duk yunwar da take ƙwaƙaƙularta kasa cin abincin ta yi, wanka kawai ta yi sallah sai bacci. Ba ta tashi ba sai goma da rabi a lokacin Jannah har ta ci abinci tana zaune da littafi tana karatu wanda ya zamar mata ƙa'ida kafin ta kwanta. “Jannah, ya kike, kin ci abinci?" Sai ta kalle ta sheƙeƙe cikin tsananin mamakin kalaman da ta furta wanda ta tabbata subutar kalami ne. "Oh please, Mom! since when do you care whether I eat or not? Da ma dai karatu kika tambaya as usual." Kauda tambayar ta yi ta hanyar komawa ta zauna a gefen Dad tare da ɗaukar laptop wanda hakan ya ƙara baƙanta ransu matuƙa da sauri Jannah ta miƙe ta yi hanyar ɗakinta dad ya kalle ta da takaici ya ɗauki wayarsa ya nufi nasa ɗakin. Tsayawa ta yi da aikin da take yi, ta raka su da ido har suka shige, sannan ta maida hankalinta kan aikinta tare da ajiyar zuciya mai ƙarfi. __________ NIGERIA A hankali ya ƙarasa gaban madubin dake gabansa, ya ɗauko wani sanyayar tureren da tun kafin ya buɗe wani irin sihirtaccen ƙamshi yake tasowa daga cikin kwabar. Sai da ya kusan daƙiƙa talatin yana riƙe da kwalbar tureren yana shaƙa idanunsa a lumshe, a rayuwarsa babu abin da ya fi so irin turaren apple, shi ya sa ko da ya je ƙasar cairo raka Daddy, babu tsarabar da ya yi wa kansa sai kwalaben turaren. Bayan ya gama shaƙar ƙamshi ba don ya ishe shi ba, sai dakin babu lokacin da zai ta shaƙar ƙamshin, sakamakon fita shi da amininsa Ridwan da zai raka shi gurin buduwarsa. Ɗan ƙaramin tsaki ya ja tare da janye yarfe hannunsa ya zauna akan saman madubin yana ƙarewa ƙawataccen ɗakinsa kallo. Kusan kimanin daƙiƙa bakwai ya ɗauke idanunsa tare da tsuka mai sauti. "Na rasa mai yaran nan suka raina ni." Ya yi maganar tamkar wanda ya ke tambayar kansa da tsabar takaici ƙarara a fuskarsa. A zafafe ya miƙe ba tare da ya ɗauki wayarsa da take kan gado ba zai fice, sai dai kiran da ya shigo cikin wayar ya sanya shi dawowa da sauri ya ɗauki wayar domin ya manta da ita. A tunaninsa amininsa ne ya gaji da kiran sa, amma jin kiran wayar ya tabbatar masa da wannan natacacciyar tsohuwar ce, wacce ta ƙi mutuwa mu ci gumba kamar yadda yake tsokanarta. Ya san uzurin ta ne ya tashi ya sanya ta kira shi, don haka ya ƙi ɗaukar wayar ya juya cikin ɗakinsa don ya rufe sashinsa ya fice ba tare da ta sani ba, ballantana ta ɓata masa lokaci da suruntunta na marasa kan gado. Lokaci guda ya ji ransa ya ɓaci a dalilin kiranta, duk da cewar shashinta ya yi ninyar zuwa domin ya shuka wa yaran gidan rashin mutunci don ya yi ninyar dukannin su sai ya yi musu wanka da ruwar sanyi duk da irin hunturun da ake yi, amma da ya tuna ba kanwar lasa bace domin zai ita cewa a tarihin rayuwarsa bai taɓa ganin mace mafaɗaciya ba irin Hajiya Babaa, in tana faɗa har wani girgiza take kamanninta na canzawa. Don haka ya fasa ɗaukar motarsa ya fice gidan cikin sanɗa ba tare da ya bari kowa ya gan shi, duk da cewar bai sai Ammy ɗinsa na tsaye a gefen windon ɗakinta tana kallon fitarsa, duk da cewar ba za ta yi masa magana ba. Murmushi kawai ta yi tare da sakin labulen tana girgiza kai don ta san dawan garin. Hajiya Babaa da take ta famar kiran Ajmal baya ɗauka, tsaki ta ja ta janyo farin gilashin dake cikin gidansa ta maƙala a yar takurarriyar fuskarta da ta fara nuna tsufa da manyanta, sai dai daular da take ciki ya hana bayyana hakan ƙararar. "Ɗan ƙwal’uba! Ja'iri wanda bai yi gado abin kirki ba sai tsiya da muskilanci irin na wancan mara mutuncin uwar tasa, mai kama da tsinƙe ana bata abinci, amma babu amfani. Dama ina zai ɗaga wayata ya raina ni bani da amfani a gurin sa. Ke Nahlin kike ko Hahl." Ta ja tsuka ta ɗora cikin ɗaga murya. "Ku yi ta saka wa kanku sunaye masu wahala da sunan wayewa, ƙila sunan aljanu aka saka miki, domin tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin irin sunayen nan ba, ko acan karkararmu." Ta ƙarashe maganar tare da ɗauko robar lacasera da take sha, sannan ta ɗauko ɓallin goran da ke kan gefen kujerar da take zaune, ta gutsira tare da jefawa a bakinta. Hakan ya sa Nahlin ta ji cikinta ya yamutse wani irin amai ta ji zaizo mata, tun tana yarinya ta tsana sai dai babu yadda zata yi, domin ko da ta ƙauracewa shashin kan dole ta dawo, saboda ƙorafin da Hajiya Baaba ta kai wa daddy cewar yaran suna ƙyamarta. A dalilin haja Aby ya yi faɗa tamkar zai zane su. Don haka ta kauda kanta tana jin wani irin amai na taso mata. Ba tare da Hajiya Baaba ta damu ba, ta kauda kanta tana tauna goron duk da cewar ta ga yadda take wani yatsina, amma ta riga ta saba musamman Ajmal wanda ya sha amai akan hakan, sai dai babu yadda za su yi da ita, domin ta zaman musu ciwon ido nan gari nan bari. Nahlin ta miƙe da sauri zata bar ɗakin amma sai Hajiya Baaba ta yi kiranta tare da cewar. "Iskancin ya tashi kenan ina kiransa ya ƙi ɗaukar wayata, Allah ya shigo da shi lafiya zai same ni har cikin ɗakina." Ta ƙarashe maganar tare da jefa sauran ɓallin goron a bakinta. Sai kuma ta kalli Nahlin dake riƙe da murfin ƙofar falon zata fice ba tare da tace maka ƙala ba. COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). *KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 4-5* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Ciikin ƙufula ta ce, "ke dalla ja'ira ki karɓi wayar nan kira mini ɗan banzan yaron nan ya siyo mini madarar shanu, yau ba ni da wanda zan sha fura, kuma Faɗuma bata kawo mini ba." "Ni dai Hajiya Baaba in dai ba za ki iya kiran sunana daidai ba, ki faɗi ainihin sunana, haka kawai ki rinƙa ɓata mini suna." Bata amsa tare da juyowa da sauri, sakamakon da har ta saka ƙafarta a waje. "Ungo nan! na ce ungo nan, mutuniyar banza kawai." Ta ja numfashi tare da gyara zaninta sannan ta ci gaba da cewa, "zagi na kike mara mutunci! Ni za ki yi wa rashin mutunci kan na zagi wannan uwar taki mai baƙin hali.” Nahlin ta karɓi wayar cikin ƙunƙunai jin abin da tace. "Daɗin abin Ammy ba liability ba ce tana da abin yi, don haka rashin ƙibarta ba zai saka ya zama aibu ba, kin san ko babu Aby zata iya ɗaukar hidimar gidan nan har da ɗawainiyarki." Ta ce tare da ci gaba da ƙunƙunƙunanta. "Barewa ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe. Ai dama hali gado ne, amma ba ki gado ɗana ba, Allah dai ya raba mu da gadon baƙin hali. Ki gaya mini magana son ranki mahaifinki zai dawo." Shiru ta yi ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta miƙa mata wayar. "Ƙin miƙa mini waya ba ki ce komai ba za ki fice ga jarababba ta fara ko? To maza dawo ki zauna yau sai mahaifinki ya dawo sai na ga in shi ya ɗaure miki gindi." "Wayarsa a kashe yake." Tsaki ta yi tare da galla mata harara da fici-ficin idanunta da suke cike da rigimar tsufa. "Babu komai tun da ba za ki yi mini ba, bari na kira uwarki daɗin abin uwarki ta yi karatun boko kin ga ba za ki yi mini rashin mutunci ba, don ban yi boko ba sai na sanya ita ko mai aiki ta yi mini kiranta ta kira mini mahaifinku." Da sauri ta miƙe jin motar yaran gidan sun dawo daga islamiya ko banza ta huta da rigimarta na ɗan lokaci. Ta ƙarashe ficewa daidai lokacin da take faɗin, "Tunda ba za ki kira mini shi ba, ga su andal take ko dal ya kira mini shi." Ba ta san lokacin da ta bushe da dariya ba tana faɗin, "Kya ji da shi fitininanniyar tsohuwa kawai. Ba ki iya faɗin suna ba, ki yi ta ɓata ma mutane suna kamar ance dole, ke dole sai kin shiga zamani." Hajiya Baaba ta ja tsuka cikin ƙubula ta fara ƙoƙarin miƙewa tana salati, sai wani juyi take tamkar wacce zata yi wani aiki. Kusan minti uku tana ƙoƙarin miƙewa saboda ƙiba da ya yi mata yawa, wanda kullum Abby yake mata magana, akan ta rage cin kayan da zai saka ta ƙiba sakamakon ciwon jiki da take fama da shi, amma ta yi kunnen uwar shegu da shi. Sam bata da wani abinci sai waɗanda zasu sanya ta ƙiba da maiƙo. Tun yana mata faɗa har ya gaji ya ƙyale ta. Gyara ɗaurin zaninta sannan ta shige ƙurya ɗakinta tana faɗin"Bari na kira Musa mai-gadi ya siyo mini da alama Faɗuma jikinta ya tsananta." LONDON A yau safiyar Monday aka tashi da hazo ya rufe gidaje, wanda sakamakon hakan ya ɗaga hankalin mom ƙwarai, domin ta san ba karamin ciwo Jannah za ta yi ba. Duk irin ɗumama ɗakin da room heater da ta yi, amma hakan bai yi wani tasiri ba. Jannah kwance akan makeken gadonta wanda ta koma can gefe ta rukuɓe cikin blanket. Gabakiɗaya jikinta rawa yake haƙoran sai haɗuwa suke yi tamkar za su fasa fatar bakinta. Hannunta mom ta janyo tare da ɗorawa akan cinyarta lokaci guda hawaye suka wanke mata fuska, ganin yadda take yi tamkar zata fasa gadon ta shige. Ta miƙe tare da janyo ledar magani mai ɗauke da tambarin pharmacy ta ciro maganin da ta bata ba da jimawa ta ɗauki ruwa tare da hawa kan gadon. "Please kar ki taɓa ni don Allah kar ki buɗe bargon nan, sanyin nan ba zai bar ni ba, domin kamar numfashina zai ɗauke." Ta faɗa cikin rawar sanyi tare da ƙara ƙuɗunɗune jikinta a cikin bargon, sannan ta riƙe shi sosai yadda ba zata ita janye wa daga jikinta ba. Tsananin tausayin ƴar gudaliyarta ya cika mata zuciya. Miƙewa ta yi tare da jingina kanta da mirrow. "Tabbas ya kamata na kawar mataki akan ciwon nan, ba zan iya ganin 'yata a cikin wannan halin ba, hakazalika ba na jin zan iya komawa Nigeria." Ta ƙarashe maganar tare da sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi. Dad ya yi sallama ya shigo tare da dosan kan gadon da take kwance ba tare da ya kalli in da take ba. Kan gadon ya zauna tare da janyo ta ta kwanta akan jikinshi yana shafa kanta, sai kawai ta fashe da kuka cikin muryar kuka tace. "Daddddddddi." Ta ja fasali tare da cewa, "Sanyi nake ji!" Ta ci gaba da kuka cikin muryar shagwaɓa. Shafa kanta ya yi, ya ɗaga idanunsa ya kalli mom da ta yi kamar ba ta san da shigowarsa ba ya ce, "Jannah za ta koma Nigeria zuwa gobe in sha Allahu yau zan kammala mana visa sai ki fara shiri.Ya karasa maganar cikin ɗaga murya. Wani irin kallon hadarin kaji ta yi ma sa tare da taku biyu ta isa gare shi, idanunta cikin na sa ta fara magana. "Ka san me kake faɗi Jabir?" Ta kira sunan shi ba tare da shakku ba, sannan ta ɗora da cewa, "Umurni kake bani akan rayuwata kuma yata da na haifa wacce ba ni da kamarta?" Dariyar takaici ta yi tare da fara taku ta matsa nesa da shi ta tsaya. "Idan har kana tunanin zan bi umurninka na koma gida, tabbbas ka yaudari kanka, domin hakan ba zai tama faruwa ba. Don haka ka daina wannan mafarki, domin ba zan koma ƙasar da zata zamo maƙabarta a dare ni ba. "Halima!" Ya kira sunanta cikin ɗaga murya tare da daka mata tsawa, sannan ya ci gaba da cewa ba tare da ya bari ta furta komai ba. "Ki sani daga yau ba zan ƙara lamuntar mugayen kalamai daga gare ki ba, ya isa iya wanda kika gaya mini. Ina jin zuciyata zata iya bugawa in har ban ɗauki mataki ba." Ya ɗan jinkirta tare da rage murya ya ƙara matsawa gareta. "Na gaji Halima ki sani mi mijinki ne, uban yarki, ina da ikon na ba ki umurni kuma ki bi, saboda duk matsayinki a ƙarƙashina kike, don haka ki iya kalamanki kar kiyi dana sani!" Wani banzan kallo ta yi mishi lokaci guda idanunta suka fara zubar hawaye."Yanzu kake da bakin faɗa mini waɗannan kalamin, bayan ka ɓata rawarka da tsalle. Na ce ba zan koma ba kuma ba zan bi umurnin ka ba, don haka duk abin da zaka iya ka yi ba ni da haufi a kansa." Girgiza kansa ya yi cikin takaici lokaci guda idanuna suka kaɗa tamkar garwashin wuta. "Do you know that Jannah is dealing with a mental disorder, and she’s in therapy secretly That’s cause of your careleness." Idanunta ta zare tare da Kallon shi cikin tsananin mamaki. "What! Are you crazy? Ka San me kake faɗi Jannah ce in her age take shan waɗannan pills ɗin?" Sai kuma ta girgiza kanta tana faɗin, "Impossible! No way this could ever happen!" "Saboda kin ba ta kulawar da ko wace uwa take ba wa 'ya'yanta? Sam ba ta yi miki komai ba, i dar har ba za ki iya yafe mini laifin da na yi miki ba, to ki hukunta iya ni din kawai." Kuka sosai ta sa tana dukan shi tare da cin kwalarshi. "Anya zan iya yafe maka Injiniya? Ka cutar da rayuwata." Sai kuma ta sake sa da ko gezau bai yi ba ta kai mata mari. "Ashe dama mahaukaciya ce ke ban sani ba? Kin san me kike son jawo ma kan ki, kin san irin side effects din da suke da shi." "Leave me, mom! Do you even care about ne?" Ta ce tare da fisge rigarta tana mata wani irin mugun kallo. "Yes, I know all the side effects.” Ta ja numfashi tana kallon dad cikin tsananin mamaki don ba ta taba tunanin ya san tana sha ba kuma Bai tana muna mata ba ko da wasa, lallai yana matuƙar sonta. "Amitriptyline’s for dealing with depression and anxiety, but it also works as a sleeping aid if you can’t crash. Olanzapine’s mostly for depression too, but it can help with eating disorder and can knock you out for some sleep too." Ta furta cikin rashin shakku sai duma ta ɗora da cewa, "Na sani, amma amfani nake don na samu sauki da bacci. Sam ba na iya bacci da karatu, Kuma kin takura mini da dole sai na yi karatu, bayan kin kasa zama da ni, ki bani farin cikin da zan iya mai da hankalina na yi karatu da shi." Sai ta karashe maganar cikin kuka sosai har tana sheshsheƙa. Dad ne ya ɗora da cewa, "In har ba za ki bi umurnina ba dole na ɗauki mataki domin ba zan yarda na zamo mijin tace ba. Na kashe rayuwar 'yata daya da Allah ya ba ni Ina ji ina gani." Ya karashe cikin ɗaga murya. Dariya ta yi mai sauti sosai har ta tafa hannu kamar ta kalle shi sheƙeƙe, duk da cewar ta yi matukar razana da jin abin da take yi, amma hakan bai sanya ta sauko daga dokin na ki da ta hau ba, sai dai ta dauko aniyar daukar likitar da za ta kula da ita har ta daina. Kallon shi ta yi cikin raini ta ce, "Yanzu ka san da wannan? Yanzu ne ka san akwai matakin da za ka ɗauka. Ai tun tuni kake jiran wannan lokacin, don haka gara ka ɗauki ko wane irin mataki, karka damu da ni na shirya tsaf wannan ranar nake jira." Ransa ya ɓace hankalinsa ya tashi ya dafe kansa yana jin yana sara mishi tamkar zai rabu gida biyu, sau biyu yana ƙoƙarin magana, amma duk lokacin da ya buɗe baki sai ya ji wani irin baƙin ciki mai kama da ƙwallo ya taso ya tokare masa maƙogaro kuma ya ƙi wuce wa. Tabbas a yau ya gane ta gaji a zama da shi nemar hanya take yi. In kuwa hake ne bata yi masa adalci ba, musamman ƴarsa da yake ganin ta fi buƙatarta fiye a shi, sai dai ta yi nisa ba ta jin kira. A hankali ya buɗe bakinsa domin ya furta abin da ya san daga bakinsa ne ko iya leɓensa, amma ba daga cikin zuciyarsa ba sai ya ji ya kasa, musamman da ya juya ya kalli Jannah da take ta kuka tun da suka fara muhawar kamar yadda ta saba kuka duk lokacin da suke sa'in sa, sai ya ji matuƙar tausayinsa. "In har da gaske kike kin shirya karɓar duk matakin da na ɗauka to ki...." "Daddiiiiiii." Ya ji muryar Jannah ta kira sa tare da janye bargon da ke jikinta ta sauko daga gadon ta ƙaraa gurin shi tare da rufe masa baki. "No daddy.” Tace cikin matsananciyar kuka tana yi wa mom wani irin kallo. Sai ta juya ta kalle sa tare da girgiza masa kai, duk da cewar ita kanta a wannan lokacin ta fara tunanin rabuwar iyayenta shine kawai matsalar rikicin da sike samu, domin tana gani auren da babu zaman lafiya rabuwa yafi, tun da har ba zata iya yafe masa ba, amma ba akan dalilin ta ba. Sam bata son iyayenta su rabu saboda ita gara ace akan matsalar da suke samu ne, don haka ta girgiza masa kai a karo na biyu cikin kuka tace. "Idan har a kaina zaka rabu da mom don Allah dad ka haƙura na koma Nigeria ni kaɗai karku damu kuyi zaman ku, amma ina roƙon ka don Allah ka kai ni gidan Abby zan fi samun natsuwa a can tun da akwai sa'oina don Allah." Ta ƙarashe maganar tare da ƙara rushe da kuka. Dukkkannin su jikinsu ya yi sanyi dad ya kama hannunta cikin tausayi tare da shafa kanta. Hannnunsa ta kamata haɗe tare da riƙe su duka. "Please! Dad." Sosai ya ji tausayinta duk da cewar ya so ta zauna a gurin mahaifiyarsa, amma babu yadda zai yi wataƙila amincewar zai iya bata farincikin da suka kasa bata a matsayinsu na iyayenta. Sai ya juya ya kalle ta da ta yi halin ko in kula da su, sai cika take tana batsewa tare da kada kafarta, matukar bacin rai ya kara kama sa. Cikin raunanniyar murya ya ce mata, "Na amince, idan hakan zai ba ki farinciki fatana a ce ki yafe mini don Allah." Ya faɗa cikin muryar da ta ƙara bayyanar d tsananin ɓacin ran da y ke ciki. Murmushi mai kama da yaƙe ta yi. "Thanks." Iya abin da tace kenan ta juya ta koma ba tare da ta kalli in da take ba, yayin da wasu irin zafafafan hawaye suke sauka da ga kuncinta. Tsananin tsanar mahaifiyarta yake kara samun gurbi a zuciyarta. Mom ta yi shiru tamkar gunki ta tsaya tana jin ta zuciyarta kamar zata fashe. Zuciyarta ta gama haƙiƙancewa Dad ya zama azzalimi mai son kansa, domin duk abin da yake faruwa a sanadinsa ne shine ya zamo silar komai kuma ya shafa mata kashin kanji yarta take ganin laifinta. Idan har Jannah zata din ga ganin laifinta akan duk abin da yake faruwa sai ta ce rayuwarta da abin da take nema ba shi da amfani a gurinta, sai dai kuma babu yadda zata yi, ammm akwai Allah shine zai hisabi ya bayyana mai laifi tsakaninsu, don bi yi wa rayuwarta adalci ba. Maganarta ta katse mata duniyar tunanin da ta shiga daidai lokacin da ta ji muryarta tana faɗin, "Dad don Allah ina son na bar gidan nan yau in da hali na samu jirgin da zai tashi yau ko ƙarfe na wa ne!” Ta furta maganar cikin rawar murya da karayar zuciya. Dukkannin su zuciyarsu ta karye idanuwansu suka kawo ruwa gabakiɗaya zargin kansu ya kama su. "Kina ji ko Jannah kiyi..." "Don Allah na ce fa!" Ta katse shi cikin muryar da ba ta san ta yi masa ba, sannan ta ci gaba da cewa. "Ina son na yi nesa da ku sosai yadda zan baku damar zama ku kaɗai kuyi tunanin cewa akwai wata halitta wacce ta damu daku take zubar da hawaye a duk lokacin da, in har ba ku daina faɗa ba na roƙe ku don Allah kar kuzo gare ni ku, zan yi ƙoƙari sake wasu ahalin na san iyalan Abby za su bani ko da kwatankwacin farincikin da na rasa agare k..." "Haba Jannah ya kamata ki natsu don Allah ki fahimce ni." Mom tace tare da kamo hannunta. Da sauri ta fisge hannunta tare da cewa, "Don Allah ki bar ni mom, domin babu abin da za ki gaya mini ya tausasa zuciyata. In har akwai bai wuce ki yafe ma mahaifina ba, sannan ki damu da ni and take your responsibility, na ga kuna farin ciki kamar yadda ko wane ma'aurata suke yi." Mom ta tsaya sagale tana kallonta cikin rashin dibara, sam bata yi tunanin ta yi nisa haka ba. Miƙewa ta yi zumbur tare da isa wadrop ɗinta ta fara haɗa kayanta, bayan ta kammala ta ta janyo trolley ɗinta ba tare da ta kale ta da take tsaye ba cikin rashin dubara. Riƙe trolley ɗin ya yi tare da buɗe baki zai yi magana sai dai kallon da ta yi masa ya tabbatar masa da in har ya ƙi aminta da ƙudirinta to tabbas za ta iya ɗaukar mataki wanda zai iya zamar musu nadama har ƙarshen rayuwarsu, don haka ta bawa zuciyarsa shawara tun kafin tusa ta karewa bodari. "A halin da kike ciki bai kamata ki bar gidan ba, duk da cewar ba zan hana ki tafiya ba tun da hakan kike so, amma kiyi haƙuri ki samu lafiya Jannah." Murmushi mai ciwo ta yi jin abin da tace ta janye troley ɗinta da ta riƙe. "Rayuwa a cikin gidan zai zami tamkar maƙabarta ina jin gara na rayu a cikin a wata duniyar sabanin wacce nake ciki da na rayu a duniyar da ba'a maraba da zuwana." "Wa ya gaya miki wallahi ina matuƙar son ki kamar yada yake matuƙar son ki amma kin ƙi fahimta ta." Mom tace yayin da ta nemi sauran maganar ta rasa domin ita kanta bata da abin da zata ce ta kare kanta. "Idan har kina sona ki yafe masa sannan ki bini mu koma gida cikin iyalanmu." Jim ta yi jin abin da tace can kuma ta furta. "Ba ki san irin girman laifin da ya yi mini ban.." "To ki sanar da ni sai na yanke masa hukuncin idan ya cancanci ki yafe masa idan kuma bai cancanta ni da kaina zan ba ki shawara." Ta ce da ita tare da kafe ta da ido. Wuri-wuri ta yi tana zare ido cikin rashin mafita. Ganin hakan yasa ta girgiza kanta tare da kama hannunsa suka nufi hanyar fita. Har sun kusa fita, ta dawo a baya ta tsa gab da ita da take tsaye ruwan hawaye na shatata tana jin ƙara tsanarsa matuƙa tare da tambayar kansa anya za ta iya yafe masa! Muryarta ta ji tana faɗin, "Don Allah kar ki zo gare ni na roƙe ki, idan kuma ya zama dole sai kin zo ki sanar da ni na bar gidan domin bana buƙatar ganin ki." Da sauri ta fice ta bar mom da take kuka tamkar numfashinta zai fita, sai ta durƙushe a gurin tare da sakin kuka mai ƙarfi. "Haƙiƙa ka cuce ni ka raba ni da 'yata wacce na fi so a duniya kuma na ke neman duk wata dukiyata domin ta.” A lokacin da suka fita Jannnah ta faɗa kan jikin shi tana wani irin kuka kukan da take jin tamkar zai tafi da numfashinta. Tana amatuƙar son mom sosai. Mahaifiyarta mace ce wacce ko wace ƴa zata yi alfaharin samun ta, amma sai dai wasu dalilai zai saka ta nisanta kanta da ita. Ƙunshe kanta ta yi cikin rigar sanyin ta, wani irin raɗaɗin zafi take ji a zuciyar tare da kewar mahaifiyarta tun kafin ta bar ƙasar amma ya zama dole ta rabu da ita wataƙila nesanta da ita da ta yi zai zamo maslaha ya saisaita tsakaninsu. Duk irin rarrashin da yake yi mata amma ta kafe kan dole sai ta bar London a yau. Babu yadda zai yi hakan nan ya ɗauki asara ya nema mata visa na jirgin da zai tashi ƙarfe ukun dare sannan ta daina kuka. Tsura mata ido ya yi yayin da tausayinta ya cika masa zuciya. Yana jin da ace zai iya da ya sanar da ita laifin da ya yi mata su taru su bata haƙuri sai dai sam baya son tuna abin da ya faru ballantana ya ta da zance. Dad ya rako ta filing jirgin. Duk da cewa ba bu mai magana a tsakanin su, amma duk bayan mintina sai ya juyo ya kalleta, hankalinsa a tashe, ganin yadda hawaye yake bin fuskarta ba tare da ta yi kokarin sharewa ba. "Zuciyata tana zargin mu da gazawa a rayuwar ki Jannah. Komawar ki Nigeria kamar mun kasa cike gurbin da ya kamata mu cika ne." Ya dan tsagaita ko za ta ce wani abu, amma sai ya ji ta yi shiru ko tari ba ta yi ba, don haka ya dora da cewa, "Going back to Nigeria don't meanyou will outrun your destiney. No, not at all. Rayuwa cike take da jarrabawa. Domin Allah Madaukakin Sarki ya fada a littafin sa mai tsarki, dole ya jarrabe mu ta ko wane hanya. Life has its inevitable challenges, which means you must face them one way or another. Kin ga dole ki ko yi adapting in any situations you find youself in." Shiru ba magana har yanzu, domin zuciyarta cike take da tunani iri-iri. Ga shi tun kafin ta bar London ta fara jin kewar su, amma babu halin zama da su by all means. Kallon ta ya kara yi, sai bai ce komai ba ya ci gaba da tuka motarsa. Yana faka motar ta fito da sauri ko direba ba ta bari ya dauki trolley dinta ba. Dad ya zura mata idanu lokacin da take hawa matakalen upstairs din jirgin tana hawaye tare da daga masa hannu. Ba tare da ya sani ba, sai ya ji zubar hawayen a fuskarsa. Lokaci guda ya kara tabbatarwa kansa da ya zama mai son zuciyarsa da ya ruguza farin cikin rayuwar ahalinsa. A hankali ta karasa kujerar da aka nuna mata mallakin ta ta zauna. Sai ta rintse idanunta ta ce, "I missed just you, dad, and I will keep you posted on everything." Sai kawai ta fashe da kuka sosai tana jin kamar ta yanke shawara cikin fushi ne, saboda tun ba'a yi ni sa ba, fara kewar iyayensu na ta. “Hi, young and cute lady.” Ta ji muryar namiji ya furta daga gefenta, wanda ya sa ta juya da sauri cikin tsoron. Ya dan sakar mata murmushi tare da lumshe ido. "Wow! You look dashing beautiful and adorable! I must say it. Wallahi ke kyakykyawa ce." Ya furta cikin tautausar murya da salon jan hankalin duk wata 'ya mace. Wani irin kallon uku tara ta yi mishi. Kamar za ta yi mishi rashin kunya akan shiga rayuwarta da ya yi, sai kuma ta ga rashin amfanin hakan. Ta taɓe tare da kara kallon shi ƙasa-ƙasa ta mayar da kanta gefe, ba tare da ta ce masa kala ba. Jim ya yi a tsaye don ya ji ba dadi yadda ta yarfa shi, saboda zai iya cewa this is the first time he got disappointed and humiliated in public. Sai dai kuma the way she looks, he would not let someone to downgrade or humiliate her. Don haka jiki a sanyaye tamkar kazar da kwai ya fashe masa ya koma kujerarsa ya zauna yana kallon ta, dai-dai lokacin da ta sake earpiece a kunninta. "She is such a woman with arrogance! But, anyway, she is my type." Ya furta yana kallon yanayin shigarta, kyawunta, har da haiba. Jannah duk ta bi ta takura domin ta tsani kallo a rayuwarta. Matukar mutum ya ci gaba da kallonmu ta tsam take tashi daga gurin, don haka ganin ya kafeta da idanunsa da ta kira mugaye, don har sai da ta faki idanun sa ta tofa addu'ar. A cewar ta kar ya zo maye ne. Har zuwaa kacin hawaye ba su bar shatata da ga fuskar ta ba, wanda hakan ya daga hankalin sa kwarai. "Life’s full of twists and contradictions." Ya furta ganin wannan zukekiyar budurwar da take kuka wanda zai iya kiran ta da hurul ain. NIGERIYA ƘASARMU TA GADO. Misalin ƙarfe goma na safiya agogon Nigeria jirgin su ya sauka, tun da suka iso garin Kaduna ta rintse idanunta a suka kumbura suka yi girma luhu-luhu, sakamakon kukan da ta sha. A hankali ta yi miƙa da salati tana shaƙar iskar garin Kaduna sai ta ji kaso ishirin a cikin kashi ɗari na damuwarta ya ragu. Karab! Suka haɗa idanu da ƙyaƙyawar suarayin da ya zabga tagumi hannu biyu yana kallonta. Tausayinsa ganin yadda ya damu da halin da take ciki ya kamata ta, duba ga iyayen ta da suka yi silar zuwan ta cikin duniyar ba su damu da halin da take ciki ba. Ba tare da ta sani ba sai ta ga ta salon mi shi murmushi mai kama da yaƙe ta yi masa tare da janyo jakarta ta fara sauka daga cikin jirgi, wanda ganin hakan ɗan saurayin ya rugo da gudu har yana bige ma'aikan jirgi, amma bai kula ba ya nufo in da take. Ba tare da ya cimma ta ba har sai da ta sauƙa ƙasa tana waige waigen Abby domin shi zai ɗauke ta. "Haba yake kyakykyawa mai kama da ɗawisu bai kamata ace kin gudu ba tare da ko gaisuwa, bayan irin damuwar da na shiga duk a dalilin halin ki. Duk da cewar ta ji babu daɗi da ya yi mata magana, amma kuma ta saka wa ranta cewar aga yau zata cire komai ta manta koma kuma ta saka farinciki a cikin rayuwarta. Kallonsa ta yi ba tare da tace komai ba ta fara tafiya. Ganin haka da sauri ya bi bayanta ba tare da ya damu da direba da ke jiran sa ba, amma ya ƙi tafiya sai dai ya miƙa wa direba trolley ɗinsa. "I’m sorry idan na ɓata maka but don Allah ina buƙatar hutu please!" Ta furta cikin ɗan ɗaga murya. Maimakon ta ga ya ɓata rai, amma sai ta ga saɓanin haka domin wani irin ihu ya yi tare da rungume wayarsa ya ce, "Wow! Wow!! Ka ji wata irin murya mai kama da sarewa. Gaskiya da zan iya gaya miki gaskiya sai na ce babu macen da na taɓa jin tana da murya irin na ki, amma don Allah ƴar indiya ce ke ko?" Ba tare da shiri ba ta ji wata irin dariya ta kubce mata sosai. Haka kawai ta ji gayen ya yi mata zata iya ɗaukarsa a matsayin aboki domin shigarsa yanayinsa fuskarsa da kyawunsa ya yi matuƙar ɗaukar hankalinta, musamman gemunsa mai ɗaukar hankali. Ganin irin dariyar da ta saki sai kawai ya ƙara sakin ihu da tsalle."Yes na jefa ƙwallon a raga." Kallonsa ta yi sannan ta ce, "In ban da abin ka ka taba ganin indiya baƙa?" "Haba sam ke ba baƙa bace cemin za ki yi chocolate beauty dai." "Humh." Kawai tace ba tare da tace komai ba. "Please don Allah in ba za ki damu ba ki ba ni numbarki, kin ga yanzu kin gaji haka ni ma. So nake na koma gida mom ɗina ta yi mini tausa, tare da b ni abinci a baki. Wani irin tsau ta ji, jin ya ambaci abin da mom ɗin sa zata yi masa, har bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba, wanda ya ɗaga hanklinsa matuƙa ya shiga tambayarta. "Forgive me if I said something that upset you, eh!" Ya ƙarashe maganar cikin sigar damuwa. "No, no at all. You didn't, buddy." "Buddy?" Ya maimaita kalmar cikin razana da tsigar tambayar domin shi ba haka ya so ba, amma da ya tuna babban yarinya ce dole sai ya sha wahala sai ya kada kan sa ya ce, "All right, like you said. Wai Hausawa suka ce da babu ai gara ba daɗi kuma Ana yi da kai, ya fi ba a yi." Sai ta yi dariya ganin kamar ya faye zolaya kuma like she enjoys it. Dai-dai lokacin da ta hangi Abby a tsaye kusa da motarsa yana ɗaga masa hannu, tare da Nahlin da Hajiya Baaba. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 5-6* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Saboda tsananin farinciki bata san lokacin da ta saki troley ɗinta ta ruga cikin farinciki, domin rabon da ta ganta tun lokacin da ta zo hutu za su koma London shekara takwas kenan. Faɗawa jikinta ta yi tare da saka ihun murna yayin da take shafa bayanta. "Ina kike jikalleta farincikin rayuwata jikalle ɗaya tamkar da dubu ina kike zo rungume ni ki kwashe albarkan shekarun da kika rasa." Hajiya Babaa ta fito daga cikin mota tana taku da takalminta mai tsini sosai, wanda yake barazanar kayar da ita. Wani irin ihu ta ƙara saki tare da sakin Nahlin ta rungume ta tana ihu tana sakin mata kiss ta ko ina. "Na yi kewarki hajjjajuta na yi kewarki sosai, ina matuƙar sonki ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe." Ta furta cikin murna sai juyata take. "Haba ai Halimatuu ni na haife ta, amma ban sa in da ta samo halinta ba, haka kawai ta nisanta ni dake akan wasu dalilanta mara ƙarfi, ina gaya miki yanzu kin dawo babu jirgawa ko ina, ko aure kika yi tare zamu je, don na san gidan ki ne kaɗai zani na huta." Ta ƙarashe maganar tana hararar Nahlin da take tsaya tana kyaɓe baki. "Ai a ko sati ba za ki yi ba za'a koro ki sis, domin tsaf zata kashe miki aure, just imagined mijin ta na karyawa ki haɗa wannan kwacamalar ta ki, goro da lacasera. Oh my goodness. I will really pity him, how nausea and vomiting ɗin da zai yi. " Ta ƙarashe maganar tana yamutsa fuska kamar za ta yi amai. "Wallahi yarinya ta zage ni. Uban baki mai haure zan ci. Kin sam ni ko uwarki ba ta ishe ni ba, balle ke da kike iƙirarin turancin ki da bai wuce rabin cokali ba. Kina zagina da turanci sai kin gaya wa aya sakin ta, don na ji kamar har da imanja kike fadi kome. Kin san ni da gidan ki har abada." "Wo Hajiyata." Jannah ta ce, cikin rike baki duk da ta san hali, lokacin da ta zo za'a yi mata aiki a London an sha dirama, ga ba ido ga masifa. "Wa ke gayyar ki a gidansa, ai never. " cewar Nahlin. Babaa ta buga mata harara tana faɗin. "Allah ya kyauta wa rayuwa ni na je gidanki, domin na san yunwa sai ta kashe ni, an riga na gado baƙin hali. Kama kumatunta tana dariya. "Mai hali baya fasa halinsa ko shekaru nawa za'a ɗauka. Kina nan dai da halin ki kamar yadda na sani. Tace cikin murmushi. "Ya canza taɓ! Ai sai dai abin da ya ƙaru." Nahlin tace tana hararar ta. Nahlin ta kama hannunta tana faɗin. "Maza muje sis in dai Babaa ce sai ta kai mu dare a nan ba tare da mun je gida mun huta ba. Babaa ta wafce hannunta da sauri. "Maza kar a ɓata mini jikalle da baƙin hali. Ma za muje kin ji ɗaya tamkar da dubu, ki huta kin shawo hanya." Ta ƙarashe maganar tare da jan hannunta suka fara tafiya. Saboda dariyar yadda Hajiya Babaa take tafiya ya bawa Nahlin dariya, sosai har tana riƙe ciki. Rigima sosai ta yi kafin a sayo mata irin takalmar, domin Ammy sayo wa irin takalmar daga gani ta saka rigimar yana fifita matarsa, ganin irin takalmar ta kuma kafe akan dole sai ya siyo mata. Tun lokacin da aka siyo takalmar bata taɓa sawa ba, sai yau da zuwan Jannah domin takalmar hill ne, ko da za su shiga cikin motar a hannu ta riƙo su sai da suka ƙaraso filin jirgin ta saka. Sai turguɗewa take yi amma ta nace dole sai ta yi tafiya da su, haka take tafiyar tana turguɗe, tana tafiya ta turguɗe sai gata tana shirin zubewa a ƙasa, ji ta yi wani saurayi ya riƙe ta yana faɗin, "Kiyi a hankali Hajiya. Da sauri Hajiya Babaa ta juya tana kallon saurayin. "Sannu ɗan saurayi Allah ya yi maka albarka." Ya amsa cikin natsuwa yana kallon Jannah da ta ƙaraso da sauri ta rungume ta. Nahlin ko me zata yi in ba dariya ba. Tsabar haushin ta da Babaa take ji ko kallon ta ba ta yi, ta cire takalminta ta riƙe a hannun ta tare da jan hannunta suka fara tafiya zuwa motar su. "Allah ya ƙara muki maganin ki da karambani kin ci lokacin ki kice sai kin ce na wani, in ban da rigima irin taki ina ke ina wani takalmi hill." Ta furta hakan a cikin ranta. Buɗe ƙofar suka yi suka shiga yana tsaye yana kallonsa, duk da Jannah ta so ta yi masa magana, amma kunyar su Dad ya hana ta ko kallonsa. Har sai da suka shiga cikin mota direba ya fara tafiya ta juyo ta kalle shi yana tsaye fuskarsa tamkar zai yi kuka duk sai ta ji bata ji daɗi ba, musammman da ta ga ya yi sororo yana nuna mata bata ba shi numbar wayarta ba. Ajiyar zuciya ta yi mai ƙarfi tare da ji gina kanta saman kujera ta lumshe idanunta. A lokacin da suka isa gida wanka ta shige ta rinka kwararawa kanta ruwan sanyi tana jin sanyin ruwan yana sauka har cikin zuciyarta. Bayan ta ɗauki tsawon lokaci tana watsawa kanta ruwan sannnan ta fito daga cikin bayin ta sanya dogon riga kawai ba tare da ta shafa mai ba ta fito daga cikin ɗakin. Kai tsaye kicin ta wuce in da take jin motsin Hajiya baaba tana kwarafniya da tukane. "Yauwa shalelena kin fito? Yanzu nake son na shiga na yi miki magana jin kin daɗe a bayi. Ko ke ma kin ɗauki halin mahaifiyarki na watsa da ruwa lokacin wanka?" Dariya ta yi mata Jin abin da ta fadi."Wai Hajiya har yanzu ba ki daina rigimar yi wa kanki girki ba?" Ta maida maganar tsigar tambaya. "Ato ni hauka nake na rinƙa bari ina cin abincin da zai cutar da ni. Haka kawai ba za a ci abinci mai kwayu ba, sai kullum a rinka cin wata cimar da aka ɗauko daga wata Kabila can. Shi ya sa nake girki da kaina. Kin ga ma za je ki zauna yanzu zan kawo miki abinci, saboda ke na yi tuwon shinkafa miyar taushe, duk da na san ke ma ba'a iya miki." Jannah ta yamutsa fuska jin abin tace mata."A haba Hajiya na yi duguwar tafiya sai ki rasa abin da za ki ba ni sai tuwon shinkafa. So kike cikina ya yi nauyi na kasa bacci?" Sai ta fice daga kicin din tana faɗin ni ba abinci zan ci ba tea kawai zan sha na kwanta bacci, sai bayan na tashi zan ci abinci, amma ba tuwo ba." Hajiya ta biyo tana tana salati. " Haba Jannatuu so kike su yi mini dariya, tun da mahaifiyarki ta gaya mini za ki zo kwana na yi ban rintsa, don Allah kar ki watsa mini kasa a ido." Dariya kawai ta yi ta kwanta akan doguwar kujera daidai lokacin da Nahlin da mahaifiyarta suka shigo yayin da Nahlin take ɗauke da turen abinci, ganin haka Hajiya Baaba ta harari kwanon tare da ɗauke fuska bayan ta taɓe baki. Murmushi kawai suka yi tare da shigowa. "Sannu da hutawa Hajiya." Mom ta furta da sauri ganin zata shige kicin. "Ba aiki nake yi ba kamar yadda kike gani." Shiru ta yi ba tare da tace komai ba har ta shige kicin ɗin tana bambami. Nahlin ta sauke tiren kwanon abincin tana bin bayanta da harara. Ba ta yi ninyar gaishe ta ba kamar kmar yadda tasan ba zata amsa ba. Da sauri ta sauka daga kan kujera ta durƙusa." Mom barka da fatan na same ku lafiya?" Ta furta cikin jin kunya da girmamawa domin Allah ya sanya mata jin kunyar Ammy da ƙaunar ta. Shafa kanta ta yi cikin so da ƙauna."Lafiya lau ya maihaifiyar ta ki." "Daddy yana lafiya."Ta ce cikin basar da tambaya. Murmushi ta yi kawai sannan ta miƙe tana faɗin."Bari na barki da Nahlin, in kika huta da fatan za ki shigo shashin nawa." "Eh Amym ai a ɗakin Nahlin zan zauna." Ta furta domin ta ɗauki aniyar ba zata zauna a ɗakin Hajiya Baaba ba. Akan me za za ki zauna a ɗakinta bayan tun kafin ki zo na sanya aka gyara mana ɗakinki." Ta ji muryar ta tana mata tambaya. "Gaskiya ba zan zauna a ɗakin ki ba, kiyi ta damun mutane da surutu da labarin sa bai shafe ni ba, har da na matattu fisabilillahi ina wanda zai kwanta bacci za a bashi labarin mattatu salon na yi mafarkin fatalwa." Ta ƙarashe maganar cikin shagwaba. "Jakar uban nan!" Ta furta ai kuwa in har ba za ki kwana a ɗakina kin ɗauko ruwan dafa kanki, domin magen da kike tsoro na ɗaura miki a jiki, jiya kasa bacci na yi ina murnar za ki zo, amma sai ki watsa mini kasa a ido, ai gara ki dawo hankalinki tun kafin ruwa ya kare wa ɗankada." Tana gama maganar ta wuce ɗakinta. Dirama sosai aka yi akan inda za ta zauna ganin ta ki cinyewa da kanta ta zaɓi ta zauna a sashin Hajiya Babaa. "Da dai kin hutar da kan ki. Haka kawai an mallake mini ɗana, kuma wanann 'yar gudaliyar za'a haɗa da ita. Ina wallahi uban kuturu ya yi kaɗan. " Ita dai Ammy ba ta ce komai ba. Ajiyar zuciya ta saki, sannan ta fice daga ɗakin. Nahlin ta yi ƙunƙunai wanda ba za ka gane me take cewa ba zata fice daga ɗakin, wanda hakan ya kubular da Hajiya Baaba ta wawuri mafici ta jefa ta da shi. Nahlin ta ruga da gudu tana dariya. Jannah ta yi shiru duk irin surutun da take ba ta da labarin yadda ta mallake mata ɗanta. Sam ba saurara take yi ba domin hankalinta ya yi nisan kiwon dan saurayin da ta ji ba ta kyauta masa ba, ya kamata ace sun yi exchanging contact if possible su rinƙa gaisawa. "Magana na ke, kike kunnen uwar shegu da ni. Wato ga mahaukaciya ko? Kin ga wallahi zamu saka kafar wando daya dake, ba zan lamunci wannan isgilancin na ku da kuka gado ko a ina ba. " Sai kuma ta sausauta murya ganin halin ko-in-kula da ta yi mata. "Kina ji na shalelensa jikata. Kin san ke kaɗai na fi so, duk cikin jikokina ko? Ya kamata ki tausaya mini, matar nan ta riƙe makogaron ɗana sam ba shi da wani kataɓus. Abynku ya zama mijin-ta-ce." Wani irin takaici ne ya kamata sai ta ki ganin ba'a rabu da bakar bane aka haifi habu. Ita da take ganin za ta zo ta huta da damuwa, sai ga shi ko hutawa ba ta gama yi ba, an dauki mata wani damuwar, wannan dalilin ya sa ta so ta zauna a sashin Ammy, amma ta hana to ga shi ba'a je ko ina ba ta fara dana-sa-ni. "To ni mai zan ce miki Hajiya Baaba? Kin san ni ban san komai ba game da rayuwar da kuke yi. Ki yi hakuri don Allah" Tana gama faɗar haka ta shige cikin ɗakin da ta nuna mallakin ta don kar ta kara ce mata komai. Ajmal bai shigo gidan ba, sai misalin goma da rabi na dare, don ya san a wanann lokacin yar rigimar ta yi bacci. Ko da Hamir ya so ya shigo da shi har ciki, amma sai ya bukaci ya yi parking a waje ya sauka. Cikin sanɗa ya shigo zai ije mata hura da nonon da ya zame ƙa'ida kullum sai ta sha sai ka ce magani. "Munafikin Allah! Ina za ka dawo ma za dawo na ce. Ai na ji karar bude get, labarai nake sauraro na yi ma za na kashe don na san haka zai faru. To dawo dan ubanka. " Takaici da haushi suka cika shi, ji ya yi kamar ya wuya ya shake mata makogaro, domin ta saka shi a gaba. Ko iyayensa ba sa zagin sa, amma sai ita haka take tamkar jikar maguzawa. Kamar ba zai juya ba sai kuma ya jiya ya watsa mata kallo yana ƙoƙarin barin wurin "Ka dawo na ce Adamuuu ka na jima ko? Wallahi in ka tafi sai fushin nan ya shafi kowa, don gobe ba wanda zai karya ta daɗi. Ta shi zan yi tun asuba na fara masifa da bala'i. " "Hajiya Babaa, na ce ki dena ce mini Adamuu! I really hate the way you pronounce it. Tun da kin ka sa kiran Ajmal please call me Adam." Ya ƙarashe maganar cikin ƙunar rai da ɓacin rai. "Umm, aikin bit in ji tusa. Da ba'a san asalin angulu ba, sai ta ce daga Ƙasar misrah ta ke. Inji uban ka da ga ƙauye ya fito ɗan kauye ne na gidi. Wallahi lokacin da ya fito birni komai bai iya ba. "Sai kuma ta sa kuka ta ci gaba da faɗin, "Wallahi Allah ya isa tsakanina da ƙanina Hamisu. Haka kawai ka saka finitina ka gudo mini da yaya birni ga shi nan, zuriyana ba su da maraba da iyalan arna. "Iyalan arna kika ce Babaa! "Ya tambaye cikin tsananin mamakin abin da ta furta. "Ina maraban dabbe da faɗa? Bakiɗaya kun ɗauki ɗabi'ar yahudu da nasara kun ɗora ma kan ku. Ni wannan turancin ma da kuke yi shi ya fi ci mini tuwo a ƙwarya. Ƙiri-ƙiri ina gani ku zage ni ba ni da ta cewa. Ina ji ranar nan cewa ka yi ko myh God. Da ga ji zagi ne. Allah shi zai saka mini, don wallahi uwarka ka zaga na ni ba. Takaici da dariya sun hana ya shi ce mata komai ganin ta yi shiru tana zare ido. "Allah ya ba ki hakuri. Bar na je na kwanta bacci na ke ji. "Ya ce, tare da ƙoƙarin ficewa. "Kan ka ake ji. Mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce "Kan ku ake ji ni wankana nake yi. " "Hmmm. Sai da safe." Ya ce yana ƙoƙarin ficewa. Ƙunƙunai ta yi wanda bai ji me ta fadi ba, don haka ya fara ƙoƙarin ficewa a ransa yana addu'ar Allah ya sa kar ta ƙara ɗago wata maganar kamar yadda ta saba, gamakin sa sai ya ji ta mike da sauri ta nufo gurin sa da yake ƙoƙarin fita. "Ai na manta ni jikar mantau. Dawo maza Adamuu. Zo ga yar'uwar bakuwar turai ma za shiga ku gaisa. " Ajmal ya tsaya da takaicin abin da ta ce. "Haba da tsawon dare nan, zaki ce na gaisa da ita? Dare ya yi ki bari sai gobe. Ba ni da lokacin ta. " "To sannu agogo sarkin ƙa'ida. Ai dama na san ba'a abin arzikin da kai. Yar gidan Anty ka Halimatuu ne fa. Kar ka manta duk da bazarta kuke rawa, shi kan shi uban na ka da wa yake taƙama in ba da ita. Arzikin ta ka ci na daina fadarda nake maka, tana hutun gajiya bana son na tashe ta." Ta dasa aya cikin murya mai raɗa kamar wacce ta shinfiɗar da jaririn goye. Ajmal ya yi tsaye sororo. Tabbas ya saba da gorin Hajiya Baaba, amma na yau da ban ne. Yarinya ƙarama take son ya je ya gaisar? Haba wuce nan. Shine har da yi masa gorin ba. Take ya ji wani tsanar Jannah ya kama shi matuƙa. "Ki san kalaman da za ki furta mini, kuma wallahi kika sa ta raina ni, karya ƙasusuwanta zan yi kin san ban ɗaukar raini." Yana fadin haka ya fice daga ɗakin har yana haɗawa da gudu, yana jin lokacin da take fadin, "To sannu ubana ko mijina. Ai gidan nan duk wanda ya so zaman lafiya dole ya yi wa Jannatuu biyayya." Komawa ta yi ta zauna tana bambamin ta tare da kunna rediyon. "Su kuma waɗannan 'yan rashin mutuncin cigaba da labaren su ka yi ba su jira ni ba."Ta faɗi tare sa kallon agogo, inda ta ga sha ɗaya da rabi. "Oh ni jikar maigishiri! Haka lokaci ya tafi wancan mara mutuncin ya tsare ni da surutu zai ja mini makara gobe, ga shi ina da tashin asuba na badawa shalele girki, koda yar gwadashin ba dole ta ci ba. Miƙewa ta yi tare da kashe wutan falon ta fara tofe-tofen addu'a wanda ya zame mata ƙa'ida. Jannah na kwance cikin bargo tana sharan bacci ba tare da ta san wainar da ake toyawa a falo ba, kasancewar tun takwas da ta shiga yin sallah ta yi mata sallama bacci take ji. Yanayi garin ya yi mata daɗi sosai kasancewar duk da babu room heater a ɗakin amma yanayin ya yi mata dadi don babu irin sanyin London. Ba ta tashi ba sai da aka kira sallah. Shi ma karar ƙwanƙwasa ƙofar Hajiya Baaba ya tashe ta. "Ta shi ki yi sallah. Malalaci shi ne ya ke barin jam'i ta wuce shi."Ta ce tana buga kofar ɗakin da karfi. Miƙa ta yi da salati tare da kunna wayarta. Karar tsakon mom ya shigo da ga kunnawa, wanda dalilin kiran da ta dame ta da shi tun a jirgi ya sa ta kashe wayar. "Na tashi Hajiya Baaba! "Ta furta cikin murya kaukausa ganin kiran sallar farko ne ta tashe ta. "Ma za ki yi nafila ki roki Allah ya ba ki miji na gari. " Tsuka kawai ta yi jin abin da ta faɗa. Ta koma ta kwanta duk da ta san ba lallai ba ne ta koma baccin. "Akan miji kika tashe ni cikin tsakar daren nan, sai kace ba ni da buri da ya wuce na aure. Ko guda nawa nake da za ki yi mini maganar miji oho. " Komawa ta yi ta kwanta sai da ta ji limami ta tada sallah san ta janye bargo ta shige bayi tare da sauro alwala, bayan ta bata lokaci gurin wanka, don a lokacin har an sallame sallah. Tana idar da sallah ba ta yi azkar ba ta ta koma ta yi kwanciyarta, tare da saka earpiece a kunnin ta don kar ta dame ta. Season na Korean film take kallo mai dadi mai suna penthouse. Hajiya Baaba ta yi kiran duniya da ƙwanƙwasa kofa akan ta so ta karya ta ƙi fitowa har sai da ƙarfe goma da rabi ya yi. Ranta ya yi matuƙar ɓaci don ita ta ɗauka bacci take yi. Tun asuba ta gama dama mata koko, kosai kuwa bakwai dai-dai Talatu kai nika an soya, amma sai watsa mata kasa a ido ba ta fito ba yanzu. Tana murɗa kofa ta fito ta kwashe da dariya ganin yadda ta zauna a kan kujera ga abin karya ta tasa a gaba tana kallo. COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 6-7* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Tana murɗa kofa ta fito ta kwashe da dariya ganin yadda ta zauna a kan kujera ga abin karya a gabanta. "Ungo nan! Na ce ugo Jannatu. Uwarki kika yi wa banza ba ni ba." Ƙarasowa ta yi ta zauna kusa da ita tare da rungumeta. "Haba tawan ni kaɗai, kin san bamu faɗa. " Murmushi ta saki tare da kama hannunta. "Ke kaɗai na damu dake, amma kika wulakanta ni. Kusan awa ɗaya ina buga kofarki. " "Hajiya bacci na ke yi fa. "Ta faɗa a sangarce cikin muryar shagwaɓa jin abin da ta ce. "Kai dai rashin zaman Halimatu ya sa ta yi sakaci da koya miki addini? "Ta faɗa cikin razana da mamaki. Sai ta ɗora da cewar, "Ko karatun kur'ani ban ji kin yi ba, kamar yadda muka saba a gidan nan, sai kika koma bacci kika rinka shafa bacci kamar rago. " Haɗe rai ta yi jin abin da tace. A ranta take tunanin ina mom take da lokacin ta ballantana ta koya mata karatu, gara ma dad shine ma yake dan ƙoƙari har ta ita haɗa baki a gurin sa. "Aiko da sake. Yaran gidan nan duk sun sauke kur'ani da hadda ke kina nan. "Sai kuma ta kaɗa kanta tana faɗin, "Halima Allah ya yi mace mai taurin kai, ni da ubanta sam bamu da wannan zuciyar ta rashin yafiya. Haka kawai ki nisanta kan ki da kowa saboda wani kuskure da ya wuce." Jin abin da ta ce hankalin Jannah ya koma kanta. "Yauwa Hajiyata. Don Allah ki gaya mini abin da ya faru tsakanin ta da dad wanda ya sa ta ki yafe masa. " "Kiyi hakuri, sai da na ɗaukar mata alkawarin ba zan gaya miki ba, sannan ta yarda ki zauna a gidan nan, amma na san dole watarana su gaji da kumbiya-kumbiya su sanar miki. " Taɓe bakinta ta yi "To koma dai mene ne su suka sani. Na yi nisa da su ta yarda bazan cigaba da ganin abin da ke faruwa tsakanin su ba. " Janyo plaks din koko ta yi tana faɗin, "Manta da su shalele, can suka sani. Ma za janyo kofi musha koko da ƙosai da na yi mik... " "Koko da ƙosai kuma Hajiya? "Ta tambaya cikin muryar mamaki. "Eh koko da kosai fa wanda ada yake gararan iyayen ki shi na dama miki, a tunanina za ki yi murna da hakan tun da kin gaji da cin abincin nasara." "Ni ban gaya miki na gaji ba. Kuma ruwan tea zan sha da soyayen dankali na fi karyawa sha biyu da rabi." "Umh! Sannu haihuwar turawa. Yanzu nufin ki watsa mini kasa za ki yi kamar na jiya. Aiko in dai ni jikar mai gishiri ce bazan kara miki girki ba, sai dai kije duk inda za ki ci kici, ai dama na lura kin fi son cin na wancan kinibiyar salon a mallake mani ke kamar yadda aka yi wa ɗana. " "Dama kin hutar da ran ki. "Ta furta a ranta a fili kuwa, shiru ta yi tana jin ta na bambami ba ta tanka ba, sai ta kwanta tare da daukar remote zata canza tasha. "A'a, a'a bar mini tashana ina kallon al'adun Hausawa, ki canza mini da wani yaren banza. " Ta fadi tare da wafce remote ɗin a hannunta, yayin da ta yi fici-fici da ido tsabar masifa. Dariya ta yi ta san duka haushin ta ki shan koko ne, sai ta kwanta tare da ɗaukar wayarta ta kunna kallon ta ci gaba da kallo. A falon Ammi tana tsaye a gaban dining tana shirya abin karyawa ita da Nahlin. Yar autar ta Ummita ta fito daga bedroom ɗin su da alama lokacin ta tashi tana goge idanu. Da sauri Nahlin ta ɗauke ta tana dariya tare da nufar bedroom na su don ta yi mata wanka. Bayan ta yi mata wanka ta shirya ta cikin rigar da siket na kanti, kasancewar weekend ne ba school. Ammi ta sumbace ta tare da faɗin, "Maza kije ki kira ƙanwar ki ta karya in Hajiya ta yarda. " Miƙewa ta yi da sauri. "Ba dolen ta ba, ni wallahi ɗakina zan dawo da ita da ƙarfin tsiya don ba za ta ji daɗin zama da ita ba." "Taɓ! Aiko kina da aiki in dai Hajiya ne. "Ta ba ta masa tana ƙoƙarin zama. Nahlin ta fita hannunta riƙe da Ummita. Da sallama ta shiga falon. Jannah ce kawai ta amsa gaisuwar, amma Hajiya ko kallon inda take ba ta yi ba. "Ina kwana Hajiya. "Ta faɗi ba tare da ta ji mai za ta ce ba. Shiru kawai ta yi sai motsi da bakinta da ta yi, wanda ba za ka gane mai tace ba, don kamar motsin sakamakon goron da take tauna ne. "Little sis, watching film? Ta faɗi tana leƙa wayar Jannah dake kwance. Miƙewa ta yi tare da daga mata ido bayan ta kashe kallon tana kallon ta. "Morning sis. " "Morning my sis. Hope you sleep well? You know Nigerian weather doesn't like London and mosquitoes everywhere. " A'a na yi bacci sosai, ai Hajiya ta sa maganin zauri. So I must say I enjoyed it. " "Good. " Ta faɗi tana kallon Hajiya da ta yi fiƙi-fiƙi da ido jin an ambaci sunan ta. Dariya ya so ya ƙwace mata amma ta dake. "Allah ya sa ba yi dani ake ba eh! Don na fi ƙarfin mutum ya san da wanda zan yi. "Hajiya ta ce tare da ƙara ɗaure fuska. Dukkanin su babu wanda ya amsa mata, sai Nahlin ta ɗauki wayar Jannah tare da kunna kallon film da take kallo. "Korian film sis, you do like it? Ni ko they are not cup of my tea. Infact I don't have interest. " "Really"Ta tambaye ta cikin mamaki sai ta ɗaga mata kai. "Kin ga ni kuwa da ga su sai Nigerian film I'm fan of them, kuma sam Korea ba sa film mara ma'ana unlike to Hausa movies I didn't say all sometime they do try. " "Allah ko? Ko na fara kallo ne? Kin ga dama admission na ke jira. " "Gaskiya I recommend you should start, you will enjoy it. "Ta ba ta amsa tana kallon ta. "I will sis, since the recommendation is from you. " "Ok, lemme send penthouse. If you don't have interest discard them." "Sure, why not."Ta karashe maganar tana mika mata tsadaddiyar wayarta. "Here you are little sis. " "You will gonna enjoin it." Dariya suka yi sannan Jannah ta miƙa hannu ta na kiran Ummita da ke kallon ta. Hajiya Baaba ta cika ta batse sai dai ba ta ce komai ba, sakamakon rabin hankalin ta na can gurin tunanin yadda za ta yi ta canza dabi'un Jannah, da ta fahimci akwai ƙaracin kula da ibada kuma ta koyi cin abincin gargajiya. "Mom said you should join us breafask. " "Ok. "Ta miƙe tsunbul dama cikin ta karyawa yake sai dai ba ta ga yadda za ta yi ta sha koko a cikin ta ba. "Ke Jannatuu ina za ki? "Ta tambaya ganin sun miƙe. "Please Hajiyata Jannah. Ki daina ce mini Jannnatuu kamar wata 'yar ƙauye. " "Ikon Allah! Ka kawo mu zamanin da 'ya'ya suke gudun sunayen su, sai ƙalƙalar banza. Da sauri suka fice ba tare da sun damu da kiran da take musu ba. "Hajiya is so dramatic! Kuma haka kuke zama da ita? " Ta tambaye ta cikin dariya. "Tab! You never see anything, sai ta haɗu da Yaya Ajmal. "Ta ce mata dai-dai lokacin da suka shiga cikin falon. "Good morning Dad. "Ta ce mishi tare da zuwa gafen sa ta tsaya. Shafa kanta ya yi cikin murna yana amsawa. "Ya kika kwana da Hajiya da fatan ba ta takura miki ba? Na ɗauka tare da Nahlin za ku zauna. " "No, bata ta kura mini ba. I slept like a baby." "Masha Allah. " Ajmal ne ya yi tsallama ya shigo fuskarsa a ɗaure sai dai ganin iyayen nasa ya sa ya saki fuskar tare da neman kujera ya zauna. "Ina kwana Abby. Ammi mun tashi lafiya."Ya haɗa musu gaisuwar a jere. Abby ya harare shi sannan ya ce, "Jiya Alhaji bashir ya kira ni, ba ka je aiki ba, sai 10 kuma you took few minutes ka fita masallaci. " "Eh Abby, na gaya maka zan je gurin aminina mahaifiyar sa ta dawo daga ummara na je gaishe ta. " Ya giddira masa wannan karyar yana mamakin sa, domin ya san gurin sahibarsa ya wuni. "You have to engaged, committed and be productive. Ka san kaine babba a gurin aiki so kome ya faru the blame will be on you. " "I will Abby. " Ya faɗa a gajarce don ya tsani a yi masa fada a gaban kanninsa. "Oh na manta little sis na ka, na gurin ƙanwata Halimatu, da nace ka ɗauko ta ka ce ba ka da lokaci. She has arrived. " "Ok. " Kawai ya ce tare da ɗaukar filet zai yi saving ɗin kan sa ganin Nahlin ba ta da ninya, kuma ya fi ƙarfin ya yi mata magana, wanda ganin hakan da saurin ta ta shi tare da karbar filet ɗin. Sai ya miƙa mata tare da mayar da hankalinsa kan wayarsa da ake ta kira ta whatsapp duk da ya san mai kiran, ya dai ki ɗauka ne don ta faye nacin kira at many times. Haka kawai tun jiya da Hajiya Baaba ta ce mishi ya ci albarkacin ta ya ji ya tsane ta. Kowa a gidan ba ta dafa masa kafa, amma daga zuwan ta har yaci albarkacin ta, ga shi babu abin da ya tsana face ya ci albarkacin wani. "Jannah ki gaida ɗan'uwan ki mana Ajmal." Cewar Aby yana kallonta. "Ina kwana. "Ta furta cikin muryar da ba su da tabbacin ya ji. Kansa kawai ya ɗaga mata, ya ci gaba da cin abinsa ba tare da ya kalle ta ba. Sai dinning ya yi shiru sai ƙarar cokula. Jannah duk sai ta ji ta muzanta sakamakon rashin sabo. Ta rinƙa juya cokali har Abby ya gaji ya ce, "Ki ci abinci, kar ya yi sanyi. " "Toh. " Kaɗan ta ci abincin ta ture. Ajmal ne ya fara miƙewa daga dinning din Abby, Ammi sai na dawo. Bai jira abin da za su ce ba ya fice. "Ka tabbatar ka gaida Hajiya. " Ya faɗi dai-dai lokacin da yake ƙarashe fita daga falon. Don shi ne kawai sai ya gama dama yake zuwa, amma kowa na gidan yana gama sallar asuba zai je tana amsawa a hamsheƙe tamkar wata sarauniya. Sai dai ko kallon shashinta bai yi ba ya yi wa maigadi umurnin ya buɗe masa get. Hajiya Baaba na jin tashin motarsa ta rugo da gudu har zanin ta na shirin faɗuwa ƙasa, ta yi maza ta rike tana faɗi, "Adamuu! Adamuu!! Wato wuyan ka ya isa yanka har ka isa ka fita gidan nan ba tare da ka zo shashina ba? "Taƙaraso harabar gidan tana faɗin hakan. Ganin ta tsaya a gaban motarsa ya yi kamar zai buge ta aiko ta saka ihu da ƙara ta ce. "Dama ka sha faɗa mini na mutu ka ci gumba ashe da gaske kake. Jama'ar gidan nan, ku yi taimako wallahi kashe ni zai yi." Dariya sosai ya yi ganin yadda ta ruɗe tamkar zata zare har zanin ta sai da ya faɗi saura siket. Sai da ya ga ta firgice ya fice daga gidan dai-dai lokacin da mutanen gidan suka fito a razane. "Fitinanniyar tsohuwa kawai! Ki ci zamanin ki ki ci na wasu." Ya ce yana dariya tare da ƙara wa motarsa wuta. Gabaki ɗaya mutanen gidan suka yi turus! Ganin ta yi zaune tana nishin wahala.Aby ne ya ƙaraso da saurin tare da kama ta ya miƙar da ita tsaye. "Subuhanallahi! Hajiya mai ya faru. " "Wallahi ni da Adamuu a gidan sai dai no koshi. Ai dama na san baya ƙaunar ganina a gidan nan." Ta furta cikin muryar kuka. Sai kuma ta ƙara sakin kukan tana ce wa,"Laifin ka ne ai, ka rasa sunan da za ka sa mishi saina wani can dangin dagiro wai siriki. Ga shi nan ya ɗauko mugun hali da bakin jini. Ya girma har ya fara tsufa, ko maganar aure ba'a yi na sa." Ammy ta yi shiru ba ta ce komai ba, amma ta ji gashin abin da ta faɗa. "Ki yi hakuri Hajiya, mu koma ciki zai dawo ya same ni, sai ya raina kansa. " Wafce zanin ta ta yi da yake miƙa mata. "Ni ka kyale ni haka kawai an haifi mini jaraba 'ya'ya sun mai da ni tamkar maƙiyayar su kuma duk laifin matarka ne da ta ke musu huɗubar tsiya. " Ammy dai ba ta ce ƙala ba sai ta juya ta tafi. "In sha Allahu sai dana ya ƙara aure, a gayawa bokan ya yi kaɗan ina nan ina addu'a. " Ba ta tanka ba ta ƙarasa shiga ciki a ranta tana addu'ar Allah ya sa ta gane. Haka kawai ta ɗauki tsana ta dora mata. Jannah sai ta yi turus tamkar gunki a wurin. mamakin diramar da suke sha ya kamata. Ganin Hajiya ta shige ɗaki ta bita domin laifin ta take ganin saboda ta cika zaƙewa, don ko maigidan baya ikon da take yi. "Kin ga ni da idon ki ko? Kina ganin cin mutuncin da ɗan matar nan ya yi mini. Kuma wallahi tsaya ki gani babu matakin da za su ɗauka. Sam! Matar nan ba ta iya tarbiya ba, domin ita kan ta tsoron yaranta take. Ni kuma na isa da ɗana sai abin da na ce a gidan nan. " "Gaskiya Hajiya abin da kike yi is too bad. Hab, ya.. " "Wayyo Allahna na shiga uku. Shi ya sa na ce wa Muhammad karya gayawa makirar matarsa zuwar jikallena, amma da yake baƙin sa ba shi da rufi, ya sanar mata ga shi tun kafin ta zo an kai sunan ta, ba ta ganin kowa sai su. Kai Muhammadu ka zo wallahi da sake a gidan. " Kuka wiwi ta shiga yi har da share hawaye da fyace majina tana kiran Abby da takaicin Ajmal ya ishe shi yana ta kiran wayarsa ya ki ɗagawa don ya san rigimar nan sai an yi sati ana yi. "Tabbas ga inda mom ta kwaso rigimar ta. Barewa baza ta yi gudu dan ta ya yi rarrafe ba." Ta furta a ranta, amma a fili sai ta zauna a gefen kujera tana kallon ta yadda ta hakince tana neman numba a wayarta sai ka ce ta iya. "Ingo kira mini Yaya Bala, shi zai yi sasanci a gidan. " Ta ce da ita fuska a murtuƙe. Sai lamarin ta ya bawa Jannah mamaki matuƙa. Ta rasa mai za ta ce mata, don haka ta karɓi wayar ba tare da ta ce mata komai ba. "Ki kira mini shi na ce Jannatuu. " Ta faɗa cikin tsawa da ɗaga murwa wanda hakan ya ƙubular da ita, ta ije mata wayar ba tare da ta ce komai ba don ta tsani a yi mata shouting. "Allah ka na gani, daga dawowarta an can za mata tunani. Bari ni ma dole na koma makaranta na iya karatun da, da ake mini rashin mutunci akai. Na san ƙwaƙwalwata ba daƙiƙiya ba ce. " "Tab! Ana wata ga wata. An ya zan iya zama gidan nan kuwa? " Ta tambayi kanta cikin jimami. Lokaci guda nadamar dawowarta ya kamata, don haka ta wayarta don ta kira dad. Kwana uku da dawowarta Nigeria ta yi matukar nadamar hakan, domin Hajiya ta hana ta sukuni. Abin da ya fi damun ta rashin barin ta isasshen bacci da ba ta barin ta yi, domin kiran farko na assalatu za ta ta she ta, wanda hakan ba karamin damunta yake yi ba. Sannan inta tashi ba ta tsira ba domin dole sai ta buɗe ƙofarta sun yi azkar da karatun kur'ani. Anan tasha mamaki domin duk iskancin da Hajiya Baaba take yi da sani, saboda tana da ilmin ta daidai gwargwado. Domin in tana karatun kur'ani babu wanda zai raina mata, sai hakan ya bawa Jannah mamaki sosai. Washegari da safe Hajiya Baaba tana zaune tana karatun kur'ani Jannah ta fito daga ɗakinta, ta zauna a gefenta tare da kunna datana ta hau online. Tsaki Hajiya Baaba ta yi sai kuma ta daina karatun ta juyo tana kallonta ta ce, "Tab! Aiko iyayen ki sun cuce ki. Ai wallahi duk wanda ya aure ki na tausaya mi shi. Ina amfanin mace ba ilmin addini? Ai gara sabar biredi dake, domin ban ga amfanin auren mace da babu ilmi ba. " Ta ce tana kokarin miƙewa tsaye tare da rufe kur'nin ta bayan ta yi addu'ar gama karatun kur'ani. Jannah kuka ta saka sosai ta ji zafin maganar da ta yaba mata. "Hajiya ni kike kike gara sabar biredi da ni? Am illiterate? " Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka. "Ato 'karya na yi? Wannan ilmin nasarar da kike taƙama da shi zai cuce ci ranar lahira ne? Dole na sanya Muhamadu ya sanya ki a makaranta da wuri, don kar ayi zuwan zomo kasuwa, yadda mutuwa take wuf da mutane ta ɗauke ki. Shikenan halam kalam. " Duk da cewar ba ta fahimci ƙarshen maganar ta amma sosai ta ji haushin ce mata gara sabar biredi da ita. "Am not illiterate. I'm educated and am better than you that you can't even read names. " "Dawo na ce dan uwarki dawo nan ja'ira. Zagina kike yi? Ai tun da kika ci bincin ta an gama dake. " Jannah ta fice da gudu shashin Amy don ta yi bacci. "Kyaci kanki haka kawai. Wai gara biredi da ni." Kai tsaye ɗakin Nahlin ta nufa inda ta same ta, tsaye gaban wadrop ɗinta tana jera kayanta, da aka kawo ɗaga gurin wanki. Kwanciya ta yi a kan gado, tare da cire wayarta a key ta shiga yanar gizo. Jannah da ke kallo bacci ne ya kwashe ta, amma duk da hakan, ba ta kashe kallon ba, domin sabon ta ne haka, don sautari ba ta iya bacci ba tare da ta kunna waƙa ba. Ganin an kira sallah ba ta tashi ba, Nahlin ta bubbuga bayanta sannan ta tashi. "It is time of prayer so get up and pray."Ta ce mata tare da nufar hanyar bayi. Alwala ta ɗauro tare da shinfiɗa dadduma ta tayar da sallah. Jannah kuwa sashin Hajiya Baaba ta wuce bayan ta yi alwala ta yi sallah. Tun tana sallar calls ke shigowa, wanda rabin hankalinta yana kan wayar ganin mi kiran. Da sauri ta sallame sallar ta ɗauki wayarta don ta kira shi, amma sai kiran mom ya shigo, wanda saboda ɓacin rai ta yi jifa da wayar kan kujera, ta fasa kiran gabakiɗaya. Hajiya Baaba da ke sallah bayan ta idar ta ji dirin motar Ajmal, tun kafin ya shigo ta fasa yin azkar na sallah ta miƙe tare fita. "Ja'iri ma za fito daga motar nan, yau ni ko kai a gidan nan." Ganin ta tsaye tana jijjiga ya dafe kansa."Kai wannan tsohuwar ta zame mini ƙadangaren bakin tulu." Ya ce, tare da ƙin fitowa daga motar. "Ai wallahi ko kwana za ka yi, sai na jira ka ka fito. Ka gama tozarta ni, ka kwance mini zani a kasuwa. Na tabbata da iyayenka ne, ba za ka yi musu haka ba." Hamdala ta yi jin hon ɗin motar Aby." Yauwa zo nan Muhammadu, gara da Allah ya kawo ka, daidai lokacin da ake buƙatar ka, sai a yi komai a gaban ka." Ta ƙarashe maganar tana isa gurinsa da ko gama parking bai yi." Dube shi mara kunya, ya kasa fitowa. So na ke ka zana mini tsakani da shi, don ko mutuwa na yi kar ya zo kan gawata." "Suhanallahi ashsha! Hajiya mai ya kawo wannan magamar ke da angon naki?" Ya ce, cikin tsigar tambaya. "Allah ya tsare ni da uren miji mai baƙin hali irin na sa, ai da haka uban ku ya ke wallahi ko kaza ba zan haifa da shi ba." Ta ba shi amsa. Ajmal tsaki ya yi, ya galla mata harara ji ya ke kamar ya shaƙe ta. COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K *KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 7-8* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Allah ya kyauta ni ko mutuwa zan yi ba aure ni ma gara na mutu, da na auri mace mai hali irin na ki." Ya furta a a ransa, sai kawai ya yi shahada ya buɗe ƙofar ya fito. "Sannu da dawowa Aby, Hajiya barka da yamma." Ya furta tamkar babu abin da ya faru tsakaninsu. "Riƙe gaisuwarka Adamuu, daga yau ba na so, in dai akanta ne za ka nemi kashe ni na haƙura. Kai ni ko atiti kar ka nuna ka sanni, inda na gode ma Allah, sam ba ka yi kama da ɗana ba, sai dangin dagiro." Shiru kawai ya yi yana kallonta domin shi kansa Aby ya ka sa ce mata komai. "Mu shiga ciki mu sasanta. Sam ba ka gudun fushina Ajmal, kullum ina gaya muku ku rinƙa kiyaye doka don a zauna lafiya, amma kai ne babba babban banza, ka na girma kana cin kashi, saboda kullum da ga gareka fitinar take tasowa." Ya yi shiru ko zai ce wani abu, amma sai ya ƙi cewa komai, yayin da ransa ya ƙara ɓaci sosai, domin ya yi matuƙar wahala so yake ya huta. "Dole na yi wa Hajiya biyayya, don na samu na gama lafiya, sannan duk wanda ke son zaman lafiya, dole ya yi mata biyayya." "Ehe ga ya masa ni dakali ne dole a zauna da ni. Dukannnin ku albarkacina kuke ci, saboda ɗanane, ni na haife shi ba uban wani ba." Ta ƙarashe maganar cikin gadara da iko, har wani hura hanci take yi, sai kuma ta ɗora da cewa, "Ai ni na san da arzikin shi na ke ci, da tuni ya sanya mini guba na mutu." Aby ya kalle sa da ya haɗe rai, burinsa kawai ya ji ya watsa ruwa a jikinsa. "Don haka sai ka kiyaye, karka ƙara yunƙurin kashe mini uwa." Ya ce. "Ka yi mana tsakani kawai." Ta ce tana kallo Ajmal da yake shirin miƙewa. "Haba Hajiya ki bi abin sannu-sannu, kuma kin ga na yi masa faɗa, dukanninmu ikon ki ne." "Humm." Ta ce tare da ƙara tsuke fuskarta sai ta ɗora da cewa, "Da ma dai wasu 'ya'yan ba wannan ba, an riga an gama musu huɗubar tsiya, tare da dasa musu tsanata a zuciyarsu." Karamin tsaki ya ja tare da fara tafiya." Shikenan, zan kiyaye ba ri na shiga ciki." Ya ƙarashe maganar yana ƙoƙarin buɗe ƙofa. "Ka na gani ko, ka na ganin irin wulaƙancin da yake mini? Yanzu inda ace uwarsa ce zai rinƙa magana yana tafiya? Amma da ya ke ba ni da matsayi a gurinsa kalli dai ka gani da idanunka, ai gani, ya kori ji. Kai ni jikar mai gishiri na ga ta kaina, an na san za'a rina tun da ka haɗa jini da dangin jaraba!" Ta dasa aya cikin muryar kuka. "Kai Ajmal ina za ka kan jin abin da take cewa?" Ya tsinci kansa da faɗin hakan, domin shi kansa ya gaji da rigimarta. Tsananin takaici ya sa ya tsaya amma ba tare da ya juyo ba, sai da ya ɗan tsaya jim don ya saita fuskarsa, sannan ya koma ya zauna zuciyarsa kamar za ta fashe. "Ma za duƙa ka ba ta haƙuri, kuma ya this should be last and end." Cikin zafin murya ya ƙarashe maganar. "Ki yi haƙuri." Ya faɗa yana hararta da take masa murmushin tsokana. "To in ban haƙura ba, duka zan rufe shi da shi? A dai guji gaba, mutum ya san kamar yadda ba shi da mutunci ni ma ba kanwar lasa ba ce ehe." Har ya kai bakin kofa sai kuma ta juyo tana kallon Aby, bayan ta ƙwala masa kira. "Wallahi daga gani, yaron nan ko ka mutu ba zai yi zumunci ba. Ƙiri-ƙiri 'yar'uwarsa ta zo, amma ba na jin ya ganta ballantana ya yi mata sannu da zuwa. Ana ci a ƙasar uwarta, ana taƙama da jin kai na banza." Ba shi ba, hatta Aby sai da ya ji kamar zai saka kuka. Ya juyo ya kalle sa da idanunsa suka canza kala. Ajmal kuwa, sororo ya yi, yana kallon Aby da ya kasa cewa komai na ɗan wani lokaci. "Kai anya, sun fa gaisa ko Ajmal? In kuma ba ku gaisa ba, ma za dawo ku gaisa." Sai ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin,"Ma za shi tana ciki 'yar albarka, wacce ta yi gadon mahaifiyarta." A wannan karon ma babu daɗi suka ji, duba ga yadda take tsine ma yaransa, tare da jawo masa jafa'i kala-kala. "Haba Hajiya! Kamata ya yi ki kira ta su gaisa ba wai ya je ba, ko don gudun raini, kin ga yana gabanta ai."Ya ce da ita yana ƙoƙarin cire komai a ransa. Ajmal ya kalle ta fuskarsa cike da mamaki. Wato sune jikokin da ta tsana kenan?" Tunaninsa ya yanke daidai lokacin da Hajiya ta ƙwalawa Jannah kira. Jannah da ke zaune da wayarta akan gado tana hira da ƙawarta 'yar school ɗinsu, wanda kiran ya sanya ta kashe wayar tare fita. "Aby ina wuni?"Ta ce tana ƙoƙarin zama a gefen Hajiya Baaba. "Lafiya lau. Ga ɗan'uwanki ku gaisa, ganin ba ta da ninyar gaishe shi." "Ina wuni?"Ta furta a gajarce. Ko kallon inda take bai yi ya msa da."Lafiya." Ya fice da sauri daidai lokacin da ya ji tana ce mata. "Ma za ki shiga kicin, ki zuba abinci kici, na lura sam ba kya son cin abinci. Shi ya sa gaki nan kamar a hure." Jannah ta shige ciki ba tare da ta amsa ba, kuma ba wai don ba ta ji ta ba. Suna fita ta miƙe cikin tsananin murna ganin yadda ta nuna masa iyakarsa, jin kiran sallah ya sa ta nufi bayi tana faɗin, Ma za ki fito kiyi sallah Jannatuu." Ya jima a tsaye a ƙofar ɗakin yana mamakin halinta sannan ya wuce kai tsaye ɗakinsa, yana jin wani irin tsananin tsanarta na shiga cikin ransa, tare da zagaye duk ilahirin jikinsa. Wayarsa ta yi ƙara ganin sunan Hajiya Baaba, sai ya kashe wayar gabakiɗaya ya kifa kansa yana mai da numfashi a hankali. Miƙewa ya yi, ya zura doguwar riga jallabiya tare sa saka takalminsa zai fita, sai kuma ya fasa don ya gaji matuƙa, Nahlin ya kira tn ɗagawa ya ce, "Ki kawo mini abincina, na gaji ba zan iya zuwa mu ci ba." "To Yaya."Ta amsa ta bangarenta. Ya kashe wayar tare da komawa ya zauna. Idanunsa ya lumshe yana jin yadda kansa ke sarawa. "Adamuu, saboda iskanci ina kiran wayarka ka kashe ko? Ko da yake ba shi ya kawo ni ba, ina nonona?" Zuru ya yi mata yana kallonta aransa kam yana jin Hajiya sai ta sanya masa hawan jini. "Ban siyo ba, kuma mai nonon ba ta zo ba." Tsaki ta saka jin abin da ya ce, "To dole sai ita? Ni wallahi ra'ayinka na riƙau na damuna." Tsananin mamaki ya kama sa, domin ita ce ta hana shi siyen ko wane nono sai na ta. "Haba Hajiya! Wallahi ki fita idanuna, kin san ni ma ba kanwar lasa ba ne..." "Au fitsarar da ka saba za ka yi mini? To ina zuwa." Numbar Aby ta nema wanda ko bacci take yana tunanin za ta iya nuna ta, saboda a rana sai ta kira shi ta kai masa ƙara sau kusan nawa. "Tsaya, ubanka zan kira sai ya siye mini." Bai ce mata koma ya tsaya kamar gunki. "Ma za Muhammadu fito ka siyo mini nono, Adamuu bai siyo mini ba, saboda mugun abu." Aby ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, sai ya rasa haushi wa zai ji tsakaninsu. "Kai Ajmal ma za ka siyo mata hura, ai ka san dole sai ta sha take kwanciya." Ya ce tare da kashe wayarsa cikin ɓacin rai. Juyawa ya yi cikin ɓacin rai ya ɗauki key ɗin motarsa zai fice, wanda ta yi kamar zai bangaje ta. "Ni fa ban yi maka dole ba, ka bari ubanka ya siyo mini, ni kaina hankalina zai fi kwanciya, don kar ka sanya mini guba na mutu." Nahlin dake riƙe da farantin abincinsa tana kallonsa sai tsananin tausayinsa ya kamata, ganin yadda yake layi idanunsa sun canza. Haushin Hajiya ya ƙara kamata, domin ji take wani lokacin kamar ta mutu su huta, gabakiɗaya ta takurawa rayuwansu da fita, don kawai ta haifi ubansu. "Hararata kike don ubanki ko? Kin san halina tamkar zawayi na ke." Ta ce tare da kai mata bugu wanda ta kauce da sauri ta shige ɗakinsa tana harararta. Bai dawo gidan ba sai da ya samo nonon. A lokacin d ya dawo, tana falo tana kallon dabbe a tashar tauraruwa. Kallon sa kawai ta yi, daidai lokacin da ya ije ledar ba tare da ya ce mata komai ba, ta ci gaba da kallonta. Wani kallo ya watsa mata yana jin tamkar ya kai mata irin nushin da aka kai wa mutumin da suke dabbe. Bai shiga sashin iyayensa ba, domin hatta Aby ya fara ba shi haushi, don shi yana ganin da ɗaurin gindinsa take gara rayuwarsu kamar ƙwallo. A hakan yadda take juya rayuwarsa, wai tana shakkarsa wani lokacin. Bayan ya ci abinci sai ya samu ɗan sauki ya kwanta tare da ɗaukar wayarsa ya kira numbar sahibarsa Mushirat, da take ta kiransa tun da ya dawo, wanda tsabar takaicin da yake ciki ya hana shi ɗaukar kiran. Ringing ɗaya ta ɗauka cikin muryar shawaɓa. Sun daɗe suna waya daga bisani ya katse kiran ya shiga bayi tare da ɗauro alwala ya yi sallah sannan ya kwanta bacci LONDON Mom zaune akan kujera a cikin ofis ɗinta da mai tsananin kyau. Juyawa ta yi kan kujerar da take zaune, hannunta riƙe da waya tana magana cikin zafi. A jiyar zuciya ta saki tare da kashe wayar tana huci, sai kuma ta ƙara ɗaukar wayar, tare da kira ta ci gaba da cewa, Look! Your attitude shows me that you are trustworthy, and I trust person once, when he disappointed me I can't go with him any more." Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Daga can ɓangaren aka yi magana, sai ta yi shiru tana saurara, zuwa can kum ta ce, Which evidence do you want me to show you? We cought you read-handed. So refund all the money and I cancelled the contract, in that case, I just give you the rest of today." Tsaki ta yi tare da ije wayar tana huci. "Wayyo Allahna! Mai sa mutane suka zama haka ne? Ni kam na rasa mai na yi wa mutane suke ha'inta ta, a duk lokacin da na aminta da su. Honestly! I really don't know. Wataƙila kuma al'ummanne suka ko ɗauki son zuciya da hamdamar dukiyar mutane." Sai ta miƙe daga inda take tare da fara safa da marwa a ofishin. "Ya Allah ka ƙara ƙarfafa zuciyata akan kyakykyawar ninyata kar mutane su canza ta, don na fara tunanin na daina." Ƙarashe maganar ta cikin ɓacin rai, sai kuma ta yi jida da glass ɗin dake ɗauke da kifaye a ciki suna ta wasannin su. Ƙarar fashewar ya tsoratar da sakatariyarta ta yi ma za ta miƙe tana ƙoƙarin kauda gilashin da ya shafe. "Take easy Ma'am." "Please call James tell him that I want to see him urgently." "Ok ma."Ta ce tare da barin abin da ta ke yi ta fice da sauri. Zama ta yi tana jiran sa, sai kuma ta ji ba za ta iya zamar ba, miƙewa ta yi ta ɗauki jakarta ta fice dag ofishin. A mota wayarta ta yi ƙara alamun shigowar tsako ta Whatsapp, wanda da sauri ta ɗauki wayar. Ganin Madam Ketric ce; shugabar marayu na Ƙasar Yukrain. Ya sa ta buɗe jikinta har kyarma yake. Idanunta suka kawo ruwa, sai take mamakin tsananin mugunta da son zuciya irin na Samuel da yake son ya yi handama da babakere akan kuɗin da zai kai musu. Lokaci guda sai take jin memories da ya faru tsawon shekaru yana ƙoƙarin yin recalling a kwanyarta, wanda ita kanta ba ta son tuna lamarin, domin in ta tuna sai tafi wata ba ta dawo daidai ba. Da sauri ta ije watar cikin tsananin tausayawa halin da suke ciki. Ije wayar ta yi, ba tare da ta tura mata da reply ba. Maigadi na buɗe gidan idanunta suka hango mata dad da yake zaune a swimming fool, hannunsa riƙe da jarida yana karantawa, yayin da idanunsa yake sanye da farin tabarau. Da sauri ta yi ƙoƙarin kauda abin da take ji game da shi, wanda ba ta gane tsana ce ko haushinsa take ji ba, don tana ganin shi ne silar duk abin d ya faru da rayuwarta. Kafin direba ya gama perking ta buɗe murfin ƙofar ta fice cikim hanzari, ba tare da ta ɗauki komai ba, tana wani irin tafiya, wanda hakan ya yi matuƙar tayar da hankalinsa matuƙa, domin tun da ya ganta haka ya san babu lafiya. Tunanin hakan ya sanya ya yarda jaridar ya bi bayanta hankalinsa a tashe, ya yin da zuciyarsa ke fargabar isa gareta don ya san yau sai Allah a tsakaninsu. "What's wrong Halima, are you alright?"Ya ƙarasa maganar yana kamata. Watsa mishi idanunta da suka rine ta yi tana masa mugun kallo wanda ya sanya zuciyarsa ta buga da ƙarfi. Dafe kansa ya yi da sauri ya zauna a kan kujera don ya san yau gidan akwai tremendous problem don ba ya tunanin za ta ba bar shi ya kurɓi ruwa lafiya, dama haka take yi in har ta shiga irin mood ɗin kasancewarta mace mai zafi. "She is in trouble sir. Please try to pacify her." Escort ɗinta ya furta tare da ije mata jakarta da takalmin sauran tarkacenta ya fice. Ya bi ta da kallo daidai lokacin da ta ƙarasa cikin ɗaki tare da buga ƙofar da ƙarfi! Dabas ya zauna a kan two seater, ba tare da ya bi umurnin zuciyarsa da take mishi umurin ya bi ta ba amma tunawa da ya yi, she could hurt herself, sai ya zabura tamkar wanda aka yi wa allura ya bi ta, har yana tuntuɓe da center table, amma bai kula ba. Ilai kuwa domin sanin hali yafi sanin kama. Ya same ta tana ta bubbuga kanta a jikin gado. "Be patient Halee. "Ya furta cikin tautausar murya tare da haɗata da jikinsa. "Haka zan cigaba da rayuwa ina mutane suna ha'inta na? Mai na yi nake fuskantar hakan? Mai ya sa mutane suke son ruguza kyakykyawar ninyar da na ɗaukarwa al'ummata. Ina tsananin tausayin talaka da halin da Ƙasarmu da wasu ƙasashen suke ciki, amma mutane sun son burina ya tashi a tutan ma'aho. Wurgi ta yi da laptop ɗinta. Da sauri ya ƙara rungume ta ganin ɓarnan da take yi. "Calm down. What go up, must come down..." Wani irin kallon ta yi mishi da ya sa sauran maganar ta maƙale a bakinsa, sai ya ji duk kalaman da tattara su don ya rarrashe ta da su sun ɓace. To me yake son ya ce mata, kasancewar she was a victim because of his selfishness. Idanunsa suka canza kala, sai ya ji ya kasa cewa komai. "Hence, I need to quit my good intentions." Ta ce tare da wurgi da ɗankwalinta ta fice daga ɗakin. Tsananin ɓacin rai ya ƙara shigarsa, idanunsa suka kawo ruwa, amma sai ya yi namijin ƙoƙarin mai da su ta hanyar jan ajiyar zuciya mai ƙarfi, yana jin yadda zuciyarsa ke zillo tamkar za ta fito wajen. Kusan minti goma ya na zaune a gurin ba tare da ya motsa ba, tunani barkatai suke damun zuciyarsa, wanda ya kasa samun mafita a cikin su. Kimanin 'yan daƙiƙa, ya yi nasarar miƙewa ya yaye labulen dake jikin windon yana kallon waje, ya yin da yake jin matuƙar haushin kansa akan yadda ya biye zuciyarsa ta yi galaba a kan farin cikin rayuwarsa. Lokaci guda Jannah ta faɗo masa sai ya ji duniyar da abin da ke cikinta na son gimshe buƙatunsa. Idanuwansa sauka hango masa ita da take tsaye a gefen filawowi, tana riƙe da wayarta, wanda ya tabbatar da hoton Jannah take kallo, domin y lura ko shi kansa bai yi kewarta kamar yadda ta yi ba, tana dai dojewa ne. Hawayen da take ƙoƙarin mayarwa suka gangaro a saman kyakykyawar fuskar da yake tunanin ba ta cancanci zubar da hawaye ba. Sai ya ji tsanar kansa da damuwa sun ƙara ninka na da. Sakin labulen ya yi, yana mai jin yadda zuciyarsa ke ƙara zarginsa. Mom ta ɗuke idanunta daga kallon hoton Jannah da take yi, wanda suka yi a lokacin da ta rakata Ƙasar India. Idanunta suka ƙara kawo ruwa, har tana jin yadda zafin su ke toya fuskarta. "Ina matuƙar son Jannah. Why Jannah? Mai ya sa ki k zaɓi cutar da zuciyata ta hanyar nisanta kanki da ni?" Ta furta tana shafa hoton. Sai ta rungume wayarta ta ci gaba da cewa,"Don Allah ki dago gare ni, kamar yadda ba zan iya komawa Nigeria ba, haka kuma ba zan iya rabuwa da ke ba. Allah shi ne shedata a kan irin ƙaunarki da na ke yi, amma sai kika sanya shamaki a tsakaninmu." Tsakon da ta tabbatar ko ta tura ba za ta duba ba, kamar yadda take tura mata, amma ba ta duba wa ta ƙara turawa cikin sanyin jiki, tare da fatam Allah ya sa addu'arta ta karɓu ta duba. Jannah ki dawo gare ni. Mahaifinki da kika fifita kura ne da fatar akuya, amma wallahi na fi shi sonki. Burina na taimaki al'umma, kuma dole saina tara kuɗi zan yi hakan.Tura mata ta yi ta online cikin karayar zuciya. Zama ta yi a gurin tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tana jin wataƙila kukan da ƙarfi zai rage raɗaɗin da zuciyarta take ciki. Wani irin tsawa aka saki mai razanarwa lokaci guda aka fara iska, mom ko motsi ba ta yi ba, ballantana ta nemi tsira da ruwan dake shirin gocewa. Lokaci guda aka fara ruwan tamkar da bakin ƙwarya. Sanyin ruwan da yake dukanta tare da wanke hawayen dake sauka a ƙuncinta ya sanya ta ɗan samu sausaucin da ƙunar da zuciyarta take yi. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 *KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 8-9* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Lokaci guda aka fara ruwan tamkar da bakin ƙwarya. Sanyin ruwan da yake dukanta tare da wanke hawayen dake sauka a ƙuncinta, ya sanya ta ɗan samu sausaucin da ƙunar da zuciyarta take yi, wanda hakan ya sa ta ƙi jirgawa ta ci gaba da kukanta mai amo da gunji, domin tana ganin saukar ruwan wani dama ne da Allah ya ba ta wanda za ta yi kukanta, ba tare da kowa ya ji ta ba, domin kuka rahma ce daga Ubangiji. Haka Allah yake. Duk mulki da tarin dukiya da mutum yake da shi, ba ya rasa abin da Allah zai jarabce shi, domin cikin littafinsa mai tsarki ya na ce wa, "Shin mun halicce ku, tunanin ku ba za mu jarabce ku ba." "Ga misali da ni Hajiya Halimatu, uwa ba da mama, na shahara kuma Allah ya azurta ni da dukiyar da ko ni kaina ba na tunanin na san adadinsu, amma sai ya yi mini jarrabawar da na gwammace gara rashin dukiyar." Ta faɗa cikin ranta. Tana wurin har aka gama ruwan, a lokacin har duhu ya fara yi sannan ta shigo gida, tana jin wani sashi daga cikin damuwarta ya ragu. A falo ta fara ƙoƙarin cire doguwar rigarta har ta ƙarasa shiga cikin ɗakin. Kai tsaye bayi ta wuce ta yi wanka, sannan ta fito cikin rigar wanka. Busar da kanta ta yi tare da shiryawa cikin gajeruwar baƙar riga. Da sauri ta ƙarasa dining jin yadda 'yan hanjinta ke zillo suna neman agaji. Ba wani ci da yawa ba, ta miƙe tare da yin brush, ta canza kayanta zuwa kayan bacci. Ba ta yi bacci ba sai da ta tabbatar da ta samu visa, jirgin zai ɗaga karfe tara na safiyar gobe, sannan hankalinta ya kwanta. Kwanciya ta yi, tare da jan ƙaton bargo ta kwanta idanunta a rufe kanta da shi lokaci guda bacci mai ƙarfi ya kwashe ta. Washe gari kasancewar ta san tana da tafiya sai ba ta yi dogon bacci ba, ta shirya cikin gaggawa. Hankalinta a kwance ba tare da tunanin komai ba, ta isa filin jirgi, wanda cikin ƙanƙanin lokaci jirginsu ya ɗaga zuwa Ukraine A cikin jirgi ta zabga takumi hannu biyu-biyu, domin wannan tafiyar ya tuna mata da tafiyar da suka yi zuwa India da irin shirmen da ta rinƙa mata. Ciro wayarta ta yi tana kallon ta cikin tsananin shaukin soyayya. Dad da yake zaune a katafaren falonsu yana ƙunar rai. Duk da cewar wannan karon ba shi ne karo na farko da ta ke yin tafiya ba tare da izininsa ba ko saninsa. Sai dai, wannan tafiyar ya fi masa ciwo. Ta ke ya yarda kuma ya amince cewar da 'yan'uwansa suke ba shi da kataɓus ya zama mijin-ta-ce, domin shi kansa ya aminta da hakan. Lokaci guda tausayin Jannah ya kama shi na nisanta kanta da su, duk a dalilin su samu zaman lafiya, amma zai iya cewa komai ƙara rikicewa ya yi. Anyway ko ba bu komai, in har tana cikin farin ciki a inda take sai ya yi mata fatan alkhairi. NIGERIA Jannah zaune a cikin falon Hajiya Baaba tana kan doguwar kujera. Ta haɗe fuska sai kubbure-kubbure ta ke yi, sakamakon yau ko baccin kirki Hajiya Baaba ba ta kyale ta ta yi ba, ta bijiro mata da rigima. Yanzu ɗin ma kallon ta yi tare da zabga mata wata uwar harara ta ce, "Kin san Allah ba zan zauna ƙazama ba, dube ki mace har mace amma ko ɗan kamfai ba kya iya wankewa, kuma wai abin takaici kike kiran kanki da mace."Ta ce tana kallon yadda take ta jijjiga tare da ƙara harararta. Sai ta ɗora da cewa, "Ke fa gabakiɗaya rayuwarki matsala ce, domin in za'a sanya ni rubutu akan matsalarki wallahi saina cika littafi. Mace ba addini ba iya iya girki ba tsafta. Kullum sai shan kaɗe-kaɗe da raye-raye. Yarinya sai ka ce dangin dujal. Ke ni da tarihi ya zo cewar a mace dujal zai zo sai na ce ya bayyana a jikokina." "Kin ga Hajiya ki daina ce mini Dujal." "Rufe mini baki ina magana kina magana shashasha kawai!" Ta kai mata bugu da carbin da ke hannunta, wanda ta ji zafi sai ta saka kuka sosai." Kika duke ni? Wallahi saina gaya wa dad, kuma ba zan ƙara kwana a sashinki ba." Ta ce cikin tsigar shagwaɓa. "Au iyye kashe ki na yi ba duka ba, ɗan wannan shauɗar da na kai miki? Taf ai ko kina da aiki, don wallahi gidan kowa ya sanni duka nake yi, ke hatta Ajmal ban raga mishi ba, kuma kifi ruwa gudu." "Ashe ko wallahi za ki dukan ma kanki, domin na san right ɗin.." "Au ramawa za ki yi?" Ta tambaye ta cikin sauri tare da ƙara kai mata bugu. "Ni bance ba, amma kuma ni ban san mai zai faru ba." "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un!" Hajiya ta ce tana salati tare da tafa hannayenta. "Oh ni jikar mai gishiri. Ina ta murna jikallena za ta zo, zan huta da waɗancan marasa mutuncin ashe, lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi za'a kawo mini. Ko da yake ni dama tun da na ga idanunki ya soye na san cewar kura da fatar akuya ce ke." Jannah ta buga kafafunta don ba ta gane karin maganar da ta yi mata ba, sai kawai ta ɗauki wayarta tare da tare sakin kuka. "Dad zan kira na gaya mi shi kirana kike da sunayen sabbobi." "Kira shi don ubanki. Daga shi har uwar ta ki ba su ishe ni na. Yo ni da ake jifana da tsafi amma na kasa taɓuwa, ballantana ke da iyayen na ki da kuke shashashu, ba ku riƙi komai ba sai aƙiddar banza ta yahudu da nasara. Ani na sha tabara na sha yasin tun ina ciki." "Oh ko me kika ce dai ba zan saka atamfar nan mai kama da ruwan tumbuɗi ba. Mom na sanya atamfa amma ba irin wannnan marasa kyau ba, don haka dad zan kira ya turo mini kuɗi na siyo zaɓin raina"Ta ce cikin sangarta da shagwaba tare da dorawa. A haka na taso, Kuma tarbiyar da 'yarki ta ba ni kenan, don haka masu aiki za'a ɗaukar mini. "A'a bayi za'a siyo miki, ba masu aiki ba. kuma wallahi ba ki isa ki rinƙa zama mini a gida tsirarara ba. Ki gode wa Allah, da na ba ki atamfofina da ake siya mini duk sallah." "Ba na so. Na lura "yar dirama ce kuma wallahi na fi ki iya tsiya." Ta ce cikin tsiwa. "Ashe ko za'a kwashi 'yan kallo, ba ki san wace ce Hajiya Baaba. Lokacin ƙuruciyata saɓa ƙato nake na nuna ma Allah na buga da ƙasa, sai da na gagari hatta mai-gari ballatana ke karan kaɗa miya kina ji da kwakwankaso kamar an ɗaurawa tabarya zani" "Ki dai ce komai, islamiyar ma ina dama ba zan je ba." Da sauri ta dawo tana jifan ta da kallo ta ce,'Inda kika yi kaɗan kenan, daƙiƙiyar banza kawai." Haƙura ta yi da neman dad sakamakon layinsa da ya ƙi shiga, sai ta miƙe tana harararta har da su muguɗa baki, wanda hakan ya ƙara ƙular da Hajiya ta bita a guje har zuwa bakin falo. Tuntuɓen da Hajiya ta yi da ƙofa ya sa ta daina gudun tana nishi. "Wayyo Allahna! Wanann sheɗaniyar yarinyar ta ja na fasa ƙafa! Allah ya isa tsakanina da ke." Jannah da har ta shige sasan su Aby ba ta ji me ta ke cewa ba. "Hello dad ka na ji na? Please I need to upgrade my drower." Ta furta cikin shagwaɓa tare da fatar Allah ya sa ya ba ta kuɗi da yawa tana son ta yi sub na data don kuɗinta yawanci a data da chaculate yake ƙarewa. "Ok, I will send you 200k, but please do answer your mom's calls." Jan numfashi ta yi jin abin da ya ce."But dad.." "No kar mu yi haka dake, ki bi umurina. Mahaifiyarki na buƙatar ki. She is in depressed and she needs your acompany. Trust me she really adore you." Wannan karon shiru ta yi na ɗan lokaci domin tunaninta ya ba ta kawai yana faɗin haka ne don ya shirya su, ko kuma ta hura masa wuta da rashin mutuncinta kullum. "Ni gask.." "I said please! For the sake of me." "Shikenan ta ci albarkacinka I will give her a call." "Good girl. I know you will. Sure, why not dad?" Sai ya yi dariya yana jin daɗin abin da ta ce. "But seriously dad, don't put the blame on me. Don har yau ina jin babu daɗi yadda take yi maka. Ka duba yadda ta ɗora ma kanta wahala kula da duniya, amma a gidanta ta kasa bamu farin ciki. Shugabanci a gida ake fara yin sa. I knew tafiyar da ta yi, shi didn't seek your permission. Arrogant woman kawai." "Well, my girl I see you poin, but please na ga ya miki your mom has good intention and she is doing the right things." "Oh please dad! She isn't, you are just depending her as you do always." Dariya ya yi sosai jin me ta ce. "Ni dai ƙara roƙon ki na ke da ki kira ta, support her and encourage her for havean sake, will you?" "Sure I will, za ta ci albarkacin son da na ke maka." Ta ba shi amsa. "Promise?" Ya ce cikin muryar roƙo hakan sai ya ba ta tausayi matuƙa, ta san cewa mahaifinta na matuƙar son ta wanda dalilin da sanya take garasa kamar ƙwallo. "Saboda hakan zan tura miki da 300k sai ki saya harda abayoyin da mom ɗinki take sawa, yauwa ba ri na zaɓa miki colour." Sai ya ɗan numfashi yana tunanin can ya ce,"Uuummmm! Pink, pich, and purple. It will fit you, like it does to your mom. Ba ki ga kalar da ta sanya ba da za ta yi tafiya ash colour, sosai ta yi kyau. Tamkar na sace ta na gudu. Yauwa ki haɗa har da ash." Dariya suka yi sosai yana faɗin." Your mom is really beutiful and she has Charming charisma.." "Dad, kai ma fa wani lokaci ba ka iya controlling kanka a kan soyayyar da kake mata shi ya sa ta yi ta gara ka kamar ƙwallo. Please do pretend you don't, don ita ma pretending kawai take yi, amma ai tana sonka, don babu macen da za ta kalle ka ba ta kware ma ka ba." Sosai ya ji daɗin abin da ta ce."Ya zan yi Jannah? Ba ki san soyayya ba shi ya sa., kuma ke yarinya ce har yanzu..." "Common dad am not under age, am 18years. So am full grow woman." "That is why I keep calling you baby." Ya furta tare da kashe wayarsa yana faɗin,"Bye do take care of youself." Ya faɗa jin abin da ta ce ya yin da zuciyarsa take cike da farin ciki don ya san in har ta kira zai samu sausauci daga gurinta. Rungume wayar ta yi cikin farin ciki matuƙa domin tana matuƙar son mahaifinta. Suna gama wayar sai ga alert ya shigo daga gurinsa. Murmushi ta yi mai sauti. Wayarta ta ciro ta tura mata da tsaƙo hi, wanda ko sakan biyu bai ya ba sai ka kiranta. A gadare ta ɗauki wayar. "Wane ne?" Zuciyar mom ta karye sai ta ji babu daɗi duk da ta san ta yi hakanme don kawai ta ɓata rai, amma ta san cewa ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta manta numbarta ba. "Yanzu kina nufin ba ki da numbata Jannah?" Shiru kawai ta yi ba ta ce mata komai ba sai zuwa can ta ce, "Ina son kuɗi zan je shoping." Ta furta ba cikin rashin ladabi da girmamawa. "Na wa kike so? Faɗa mini na yi miki alƙawari ko nawa Jannah, domin komai da nike nema na ki ne. Ki faɗa mini zan ba ki." "200k." Ta sanar mata. "Ok, iya hakan kwai kike so? Ba ri na tura miko dubu ɗari biyar. In ba su isa ba sai na ƙara, ni dai burina ki damu da ni, ki ƙaunace ni ko da kwatankwacin rabin na mahaifinki ba ne." "Yauwa mom, ki gaya ma wancan rigimammiyar mahaifiyar ta ki, ta kiyaye ni, kuma ki ɗaukar mini aiki don ba zan iya aikin da take saka ni ba. Na ga haka kika koyar da ni, idan da ce babu kyau ba za ki tarbiyartar da ni a haka ba, saboda iƙirarin son da kike cewa kina mini." Sai ta ji kalamanta tamkar saukar aradu a ƙwanyarta. Rintse idanunta ta yi cikin ƙunar rai. Wasu zafafen hawaye suka wanke mata fuska. "Na yi kuskuren da ba zai gyaru ba. Ki yi haƙuri zan yi mata magana." "Humh" Ta ce tare da kashe wayar da sauri tana hararar wayar don duk wayar da suke yi daurewa kawai take yi, amma wani zafin ta take ciki. Mom ta ije wayar cikin tsananin damuwa domin a maimakon ta ji sausaucin kirar sai baƙinciki da ya cika zuciyarta, domin ba haka ta so ba, don ta so ta gaya mata kalamai masu daɗi na tsakanin 'ya da uwa sannan ta tambayeta cikin girmama, amma kiran wani nasara ce. "Watarana za ki fahimci gaskiya ki soni fiye da yadda kike so mahaifinki. Sai dai, ina miki fatan ka da ki yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada. Wataƙila ba ni a raye ko kuma ba ki da halin gyara kuskurenki. Allah ya yi miki albarka." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka. Ƙarar shigowar kuɗin ya sa ta zuba wani irin ihu. "Da ma na san za ta tura mini, ai mom is open handed. Ko da yake kuɗin ta ke samu ba ta san darajar kuɗin ba. Miƙewa ta yi tana mazurai ganin Hajiya Baaba a kanta. "Da ga gani ba ki da gaskiya. fitsararriya kawai." "Tun da ba sata na yi miki ba sai a sha fa mini lafiya." Hajiya ta yi ƙuta tare da kai mata bugu amma sai ta dakata jin wani uban ihu da ta ƙwala har sai da gidan ya amsa. "Na ba ni! Ki ji mini 'ya za ki tara mini mutane. Wallahi in kina cin ƙasa ki kiyayyi ta shuri, ki yi mini biyayya mu zauna lafiya babu mai jin kammu. Ungo maza ki je direba ya kai ki a gwada ki ɗinki, da kayan Ummu Kursumu za'a gwada ki." Turo baki ta yi tana kallon kayanta wulaƙance."Allah ya tsare ni. Ni na lura you are trying to deprive me." "Jannah ina matsayin kakarki na yi miki kyauta ki ce ba kya so? To wallahi uban kuturu ya yi kaɗan." Ta zauna tare da gutsirar goro ta saka a bakinta kana ta ci gaba da cewa, A hannuna a ka bar mini amanarki, ni ce na ke da ikon zaɓa miki abin da na ke so a rayuwarki. Zan fara koya miki girki da kula da kanki komai da komai zan koya miki, kar ki yi aure mijin ya ga mun cuce shi, duk da cewar tare za mu yi zaman auren." "Allah ya ba ki sa'a, na ga wanda za ki koya wa, don na gaya wa 'yarki masu aiki za ta ɗauko mini kuma ta amince." "A ina? Amma ba dai a gidan nan ba, kuma ina raye ko. Ai ni mamakin Halimatuu na ke, wallahi albasa ba ta yi halin ruwa ba." "Rigima kike ji in ban da rigimar ki mai zan yi da kayan tsoffafi ai kalar ki ce kayan, ko ba ki san wace ce mahaifiyata." "Dallah rufe mini baki! Na haifi 'yar da cikina? Ai ni ce mai ƙashin ar'azikin, in da ba ɓan haife ta ba a gidan uban wa za ta haife ki. Ai wallahi na iya haihuwa. Kin ga kuwa ƙauyenmu har gori aka yi mini cewar ni da arziƙi sai dai in a jahannama ana yi, sai ga shi Allah ya nuna musu ishira tun duniya ya fara nuna musu ni 'yar aljannah ce. Mata nawa suka ci arzikin haihuwa da maza a karkarkarramu. Shi ya sa na ke shuka musu barbaɗar rashin mutunci. "Huhm daga ganin ki Hajiya kin shuka rashin mutunci da kuruciyar.." "Ubanki na ce"?! Tantiriya kawai ni kike faɗa ma haka." Ɗakinta ta ruga tana faɗin, "Ashe ke muka gado." Ta shige ɗakin ba tare da ji me ta faɗa ba. Hajiya ta ce." Allah ya kyauta gayyar arna a idi. Waɗancan fitsararrun kenan ni suka gado? Ƙarya kike yi, ga dai waɗanda suka gado ni nan sun zamo jigo ga al'umma. Wanka ta yi sannan ta nufi sashin su Nahlin ta same tana zaune a falo tana tsefe wa Ummita kitso. "Don Allah, Anty Nahlin za ki raka ni shopping? Dad ya tura mini da 3000k" Ta ƙarashe tambayar tana zama a gefenta. Murmushi ta yi tare da ware idanunta."Iyye dad's pet. 3 hundred thousand just like that! Ba ri na kammala mata tsifar, in yi girkin rana sai mu shirya, I hope by 4 pm is ok? kin ga sai ki ta ya ni girkin ko?" "Tab, na dai ta ya ki hira, don ni wallahi I can even remember when last I enter kitchen. Komai na ke buƙata sai dai a kawo mini. And you know what? I enjoin that" Ta ce mata tana ƙoƙarin kunna data, ta kunna tiktok. Sai ta juyo ta kalle ta ta ce, Girgiza kant ta yi a ranta tana tunanin anya mom ba ta yi kuskure ba da sunan gyara? "Anty Nahlin kina ƙoƙari fa, na ga gidan nan masu aiki har biyu, amma kullum kina kicin girki?" Dariya ta yi."Eh, tsarin Ammy ce. Ya Ajmal ba ya cin abincin masu aiki, na su suke girkawa da masu gadi, sai karnika." "To sai na wa kenan? Ya mai da ke baiwarsa kenan? In girkin daɗi ne ya girka da kansa mana. I believe ko ruwan zafi ba ya iya dafawa, amma zai takurawa rayuwarki. Ni da tun zuwan gidan nan, na gane ya ɗauki mace baiwa, saboda ko serving ɗin kansa ba ya iya wa, sai dai ki yi masa, sai ka ce cikinki zai kai bincin. I was like haba!" Dariya ta kwashe da shi sai da ta yi mai isarta ta ce, "Lallai kina da aiki kuwa. So what if kika auri miji irin Ya Ajmal mai son girkin matarsa?" Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 9-10* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Allah ya kyauta! Shi kansa ya san matar da zai aura ta yi masa girki. Kamar ni babban yarinya irina mai aji, kuma he will expect me to cook for him?" Ta ƙarashe maganar tana juya jikinta wanda hakan ya ƙara ba ta dariya sosai. "Kin san Allah Anty Nahlin? Ni ko zan yi aure ba yanzu ba, sai na yi degree, master, and phd. If possible na fara aiki. Haihuwa kuwa, anya zan iya may be one." "A tab! Lallai ko da yake yarinya ce ke, ƙuruciya ke damun ki. Amma dai ina gargaɗin ki da kar ƙi ɗauki ra'ayin riƙau, wato feminism da kuma iƙirarin da bature ya ke yi na. What a man can do, woman can do better. A ko da yaushe namiji shi ne a gaba. Kamar yadda littafin mu mai tsarki ya ce. So please ki cire wannan a ranki." Taɓe baki ta yi ba ta ce mata komai ba tana skipping kallon da take yi. Ganin hakan ya sanya ta ci gaba da cewa, "Ko mom da kika gani, a gidan aurenta ta samu wannan ɗaukakar, don haka ki cire wannan tunanin." "Haba Anty Nahlin! It is just my ideation. Kuma planning to my future kike tada jijiyar wuya haka har da su kawo ya da wa'azi. Mutum fa na da ikon tsara wa kansa abin da yake so. Kum..." "Ki gyara kalamanki domin mutum bai isa ya tsarawa kansa rayuwa ba sai Allah, shi ne ya ke da ikon wannan Mudabbirul amri ne. Kin manta ko shi baturen cewa ya yi man proposed but Allah disposed?" "Huhmm." Ta ce cikin guddurar kalamanta. "It hasn't go to that. I just telling you as far as am concerned ne." "Na lura sam ba kya son gaskiya halin ki ɗaya da Ummu Kursum ita ma ba ta son gaskiya. Ni kuma as World concerned na ke gaya miki." "Anty Nahlin. You know what? Let me go to falo and watch film. Is like you don't need my accompany bye." Dariya ta yi ta kama hannunta ta riƙe."Sorry sis, dawo ki zauna na daina." Ba bu kunya ta zauna tana murmushi sai kuma ta fara zuba tana mata hirar celebrities wasu ko sanin su ba ta yi ba. A haka suka gama girkin bayan sun ci sun yi sallah, Jannah ta yi wanka tare da wucewa sashin Hajiya Baaba don ta canza kaya.Bayan ta gama suka ci abinci suka yi sallah. Ta same ta zaune a falo tana shan fura. Gallah mata harara ta yi, tare da kai ludayin furan bakinta. Dariya ta yi tana faɗin, Allah ya bar mini kakata." Sai da ta kammala shirya cikin riga da wando ta fito tana rolling ɗin ɗan siririn veil ɗinta. "Hajiya zan je shopping me zan siyo miki?" "Kin san an gaya miki, ki daina mini isakancin turancin nan na ki? Tun da ba ji na ke ba, in ba haka ba zan shuka miki rashin mutunci." "Allah ya ba ki haƙuri. Siyayya za ni me kike so." "Ban sani ba, umma ta gai da ashsha." Ta faɗa a ƙubule. "To shikenan, sai mun dawo." A gajarce ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa. Ganin da gaske take sai ta ƙwala mata kira ta ce."Dawo mana shalele, maimakon ki rarrashe ne sai ki tafi? Ni fa tsiyata da ke ba ki da kirki. Abu mai daɗi za ki siyo mini." Dariya kawai ta yi ta fice sai da ta kai ƙofa ta ce. "Sai jarabar faɗa da kwaɗayin tsiya." "Abby ya fita da motarsa. Ammy kuma tana gurin aiki, sannan motar ya Ajmal ko da tana nan ta fi ƙarfinmu, nan ga ni, nan bari. Don haka dole mu shiga motar gida." Kallon wulaƙanci ta yi wa motar tana yatsina fuska. "Kai dole mom ta saya mini mota, ba zan iya wahala ba." "Lallai aiko da wuya Ya Ajmal da Abby su yadda. Za ki shiga aji shida na sakandiri ne za ki rinƙa driving? Ki sani Nigeria ba kamar London ba ce." Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarinn shiga cikin motar ganin Musa direba ya shiga ya kunna. A shopping Mall sai da ta yi wa kanta ƙarƙaf sannan hankalinta ya kwanta don ta jido kaya masu tsananin kyau har Nahlin da Ummita ta siya wa sai Hajiya da ta siya mata ƙwalama. Suna shirin fita daga mall ɗin ta hango wata doguwar riga mai tsananin kyau. "Wow Anty Nahlin! Kalli wannan rigar ta tafi da ni, bari na duba app ɗina na palpay kamar ina da kuɗi na sayi rigar nan. "Kai Jannah, na lura ke money monger ce, duk irin kayan da kika siya, amma ba su ishe ki ba?" "Allah ta yi kyau ne." Ta ba ta amsa. Hankalinta bai kwanta ba sai da ta sayi abayar suka je gurin biya. Tana ƙoƙarin transferring ɗin kuɗin ta ji muryar namiji ta bayanta ya na faɗin, "Yauwa Mufid! Ma za ƙaraso yau Allah ya haɗa ni da ɓarauniyar da ta yi mini sata a filin jirgi." Ya faɗa yana tafa hannunsa cikin tsananin farin ciki tare da kallon abokinsa. Da sauri ta waigo cikin tashin hankali take idanunta suka ciko da ƙwallah. Ba tare da ta san ta yarda rigar dake hannunta ba. Kallonsa ta yi tana tunanin kamar sun taɓa haɗuwa don fuskarsa ya yi mata kama da wanda ta taɓa gani. "Like I knew you before?" Ta furta cikin tantama. Sai ya ɓata rai tare da kai key ɗin motarsa kusa da fuskarta kamar zai taɓa ta da shi. "Ban sa ni ba, kin bar ni da tunaninki babu dare babu rana. Haka ma za ki ce mini? Alamun kin manta da ni." Ya ƙarashe maganar tare da ƙara ɓata fuskarsa. War ta yi da idanunta domin ta gane saurayin da suka haɗu a filimg jirgi wanda yake yawan faɗo mata a ranta. "Haba kyakykyawa understand me. I wanna build and development a health relationship between us. A jiyar zuciya ta yi mai ƙarfi, domin tun haɗuwarsu ta lura da irin kallon da yake mata, amma ina sam ba ta shirya ba. " Na gane ka, buddy ne wanda muka haɗu a airport." "Jannah ki zo mu tafi kin ga dare yana yi, kuma Ammy ta ce kar mu daɗe." Nahlin ta furta tare da kama hannunta suka shiga mota, ganin kamar zaƙewarta na kula shi ta yi yawa, duk da cewar ita ma ta gane shi. "Jannah." Ya furta a hankali yana shafa gemunsa da wani irin tsadadden murmushi a fuskarsa. Ganin direba ya tada motar ya sanya ya rugo da gudu a gefen da take. "Haba Jannah, kar ki zama mace mai son kanta. Tun da kika ga mun yi haɗuwa biyu tabbas a kwai ɓoyayyen lamari a tsakaninmu. Yanzu haka za ki tafi ba tare da na san inda zan gidanku ba?" Ya yi tambayar cikin marairaicewar fuska. Kafin motar ta fara tafiya ta leƙo da kanta ta ce. "Jannah Jabir Ingawa." Ta ɗaga masa hannu tare da mayar masa da ƙayatatten murmushin da yake mata. Zuciyarta cike da tsananin farin cikin sake ganin buddy ɗinta. "Jannah Jabir Ingawa da ma ita 'yar family ɗin ce?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamaki domin sai ya ce faɗuwa ta zo daidai da zama don a kwai abokinsa a family ɗin. Sunan da ta faɗa mishi ya san ta faɗa masa ne akan ya yi searching ɗinta a social media don haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ciro wayarsa tare da kunna data ya rubuta sunan wanda take ya fito masa har da ɗauke da hotonta tana riƙe da teddy. Murmushi ya saki tare da rungume wayarsa domin shi kaɗai ya san tsananin farin cikin da yake ciki. A gurin ya tura mata da friend request wanda ko minti ɗaya bai yi ba, ta yi acceptin da tura mishi da stiker masu ɗauke da hoton abota. Sai ya ƙara sakin murmushin jin daɗi ya buɗe motarsa ya shiga tare da tada ta ya ja cikin farin ciki. "Huzaifah." Ta furta sunan kamar yadda ta gani a rubuce. "Huhm! You are so humorous buddy." Ganin murmushin ya ƙi ɓacewa daga fuskarta. Nahlin ta gyara maza tana kallonta. " Kamar shine saurayin da kuka haɗu a filin jirgi, kuma na ga kamar sonki yake? Ina gargaɗinki da karki faɗa tarkon namiji ki fara relationship at this age. Kin ga ko ni sai da na shiga Jami'a sannan ya Ajmal ya barni nake kula samari." "Haba Anty Nahlin! Why all this questions and statements? Kar ki kai ni inda ban kai ba. Babu komai a tsakaninmu, shi ɗin abokina ɗauke shi." "Humh." Ta ce sai kuma ta kalle ta tare da yin dariya. "Idan kin ɗauke shi ba aboki, shi ba'a haka ya ɗauke ki ba. Kin dai san soyayya ba ta ɓuy.." "Then I will make him understand ok? Yawancin abokanan na maza ne. So banga komai ba." "It is just a piece of advice." Cewar Nahlin. "Thanks." Ta ce ta maida hankalinta kan wayarta tana reply ɗin messages ɗin da ya yi mata. Mom zaune a kan kujera ta zabga tagumi yayin da idanunta suke cike da ƙwallah tana sauraren Fedris da take ta yi mata bayanin abubuwan da suke buƙata. Kuɗin Ƙasar ta ciro daga jakarta masu tarin yawa ta ije a kan teburin dake gabanta. "Take this and if there is need of it, please contact me. I wanna leave this country tomorrow." Ta furta cikin muryarta mai sanyi tana gyara ɗaurin gyalenta. "Thank you ma'am and I wish you safe trip." Jinjina mata kanta ta yi sannan ta fice daga ofishin. A ranar da ta dawo, sam ba ta fita ko ina ba tana hutun gajiya, har sai da ta yi kwana biyu. Sosai dad ya ji daɗin yadda ta dawo cikin farin ciki, domin ya samu sausauci a tsakaninsu, har da yi masa hira da ba shi labarin ɗubbin nasarar da ta samu, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba, ya rinƙa ji da ita. Washegari da safe ta shirya zata fita tana ƙoƙarin ɗaukar jakarta ya shigo ganin ta cikin shirin fita, ya sauya fuskarsa daga fara'a zuwa ɗaurewa. "Haba Halima, kamata ya yi ace sai kin yi sati kafin ki fara fita, kina cika wa kanki aiki. Ki tausaya mini ni fa mijinki ne, kuma ina da haƙƙi mai girma akanki." "Please Injiniya! Kar mu fara tun yanzu. Ba rayuwata ba ne? I have ambition and I want to do everything humanly to accomplish my goals." Lokaci guda fuskarta ta canza ta ɗauki jakarta ta fice ta bar shi tsaye sororo. Wayarta ta yi ƙara alamun ana kiranta ta whatsapp. Da sauri ta ɗauko wayar tana dubawa. Ganin Jannah ce ya sa ta ɗauka da sauri tare da kanga wayar a kunninta. "Hello mom, Ina buƙatar kuɗi." "Haba Jannah! What I have done to you to deserved this? Kar ki manta ni fa mahaifiyarki, you should respect me." Cikin muryar son kuka ta ƙarashe maganar. Ƙin amsa mata ta yi sai ta ce a maimakon ta amsa tambayar. "I desperately need money. Ba kin ce saboda ni kika hana kanki hutu kike neman kuɗi ba? So do send me I wanna enjoyed." "Amma ya kamata ki tambaye ni cikin girmamawa da sanin darajat.." "To in har saboda ni ne, ina son ki siya mini braded car. Ki kuma tura mini kuɗi a account. Ki kuma yi wa mahaifiyarki magana, domin ta addabi rayuwata ta hana ni shan iska wai sai ta koya mini aiki. Ki sanar mata a haka kika tarbiyartar da ni, ban taso ina yin chores ba. I think is not bad, don kina gaya mini cewar nice wacce kika fi so, na tabbata ba za ki ɓata ni ba ko?" Ta furta cikin gatsali da rashin kunya. Sai ta ji wani irin ƙululun abu ya toƙare mata ƙirji har sai da ta dafa mota. "Na yi kuskuren da na barki kika girma tamkar sakakken kashi, na kasa tsayawa na ba ki kulawa. In sha Allahu zan gara, zan zamo uwa wacce kowa yake fatan samu." "Kina jina?" Ta tamabayeta jin ta yi shiru. "Eh, shikenan zan yi mata magana, kuma zan siya miki duk motar da kike so. Fatana ki damu da ni, ki so ni ko rabin son da kikewa mahaifinki. Ina matuƙar sonki, wallahi na fi kowa sonki. Sai ta yi ƙasa da wayar tare da fashe wa da kuka. Ɗif! Ta kashe wayar da jan tsaki tana faɗin,"Kyaji da shi, haka kawai ki ɗora wa kanki wahala, sai kin tara kuɗi kin kula da al'umma, bayan gidanki kin kasa kula da shi wai ke joy giver ko." Nahlin da ta yi mutuwar tsaye ta kasa ce mata komai na 'yan daƙiƙa si kaɗa kanta take tamkar ƙadagaren kutu. "Are you high?" Ta yi nasarar tamabayarta cikin tsananin mamaki sannan ta ɗora da cewa,"Waɗannan mugayen kalamai kike jifar mahaifiyarki da shi? Kin kuwa son wace ce ita, kuma wane irin ɗubbin nasara kike da shi da kika zo a 'ya guda ɗaya da ta mallaka." Wani banzan kallo ta yi mata mai kama da raini ta ce, "Na san dole sai kin yi maganar. Haba Anty Nahlin komai na yi sai kin ce ban yi daidai ba." Ta ƙarashe maganar a fusace tare da toshe kunninta ganin ta buɗe baki za ta yi magana. Bin ta da kallo ta yi domin ta gama karamtar ta 'yar rainin wayo ce da rashin kunya. Sai ta sanya a ranta za ta daina mata magana akan duk abin da take yi, domin kamar yadda ta ce mom ce ta ba ta wannan tarbiyar haka ne, don su suka bata gurɓatacciyar tarbiya. Sai ta saka a ranta daga yau ba za ta ƙara mata magana ba don haka ta miƙe za ta fice daga ɗakin, wanda ganin hakan ya sanya ta miƙe da sauri ta riƙe ta. "Am really sorry Antyna. Idan kika yi fushi da ni ya zanyi. Ba za ki gane wace ce mom ba. Sam ba ta girmama mahaifina agaban idanuna take daka mishi tsawa. Ta mai da shi kamar ɗan da ta haifa, sannan ba ta zauna a gida ta ba shi kulawar da aure ya sharanɗa ba." "Yarinya ce ke ba za ki fahimci komai ba. Don't be dummy and think logically. Mahaifiyarki abin alfahari ce ga rayuwarki, ke har da ta al'umma domin ita ɗin jigo ce ga al'umma. Kin san gidan marayu nawa take da shi a Ƙasar nan da ma ƙetare? Don haka ki tausasa kalamanki, kar kiyi nadama a lokacin da ba shi da amfani." "Ok, from now on I will take note." Ta ce sannan ta fice ba tare da ko kalami ɗaya ya yi tasiri a gareta ba ta koma ta zauna. Murmushi ta saki ganin maƙudan da suka shigo akawunta. Sai ta mirgina tana ƙoƙarin kiran dad, daidai lokacin da kiransa ya shigo. Jikinta har rawa yake ta amsa. "Jannah, ke ce kika buƙaci mahaifiyarki ta siya mota? Kin san fa Nigeria ba kamar London bane." "Eh, ina son na tuƙa, kuma siyen shine kwanciyar hankalinta wacce take trending." "Ho yarinyata rigima. To shikenan, in sha Allahu cikin satinnan motarki za ta iso branded kuwa." Wani irin ihu ta sanya tare da kashe wayar ta fice don ta yi wa Nahlin albishir. A hankali shaƙuwa mai tsananin gaske ta shiga tsakainta da Huzaifah wanda take matuƙar daɗin hakan. Domin kaso cikin tamanin na damuwarta ya rage sosai. Maganin da take sha sai ta manta kwana biyu ba ta sha ba, kuma ba tare da ta ji canji ko wani alamu ba. Da fari abota suka fara duk da cewar shi ba haka ya so ba, don ya so kai tsaye ya bayyana mata soyayyarsa. Sai dai, zana masa tarin burikan da take da shi da yadda take son tsarin rayuwarta ya sa ya fasa hakan, saboda burinkanta sun girmi tunanin sa da ƙwaƙwalwarsa. Rashin sanin abin yi ya sa ya haƙura, amma kullum cikin bayyana mata yake a zahirince wanda take pretending akan ba ta fahimta ba. Huzaifah mutum ne wanda ya taso cikin 'yanci da kulawa da kuma gata. Mahaifinsa Janar ne daga baya ya koma shahararen ɗan kasuwa. Sai tsarin rayuwarta bai wani dame shi ba, domin yana son rayuwar yanci da hutu. A haka suka yi ta soyayya da sunan abota kullum suna maƙale da juna. Yana matuƙar tsarinta, zubinta da surarta musamman kalar fatarta da ke tafiyar da hankalinsa. Burinsa kullum Allah ya mallaka masa ita sai ya ce ya fi ko wane ɗa namiji sa'a a duniyar. Kasancewarsa yana matuƙar son mace mara ƙiba, shi ya sa ta dace da tsarinsa. Kasa jurewa ya yi don kar wani ya yi masa ƙafa ko late comer ya yi wuf da ita. Sai ya sanar mata da irin tarin ƙaunarta dake faman ɗawainiya da rayuwarsa, wanda hakan sai da ya sa suka yi faɗa har na tsawon sati ɗaya ta ƙi ɗaukar wayarsa. Sakamakon hakan, hankalinsa ya tashi har rama ya yi. Ita kanta ta wahala, amma tsabar girman kai da son cika burikanta ya sanya ta ƙi nemansa. Ranar da ta ɗauki wayar ya cika da murna sosai ya bata haƙuri suka shirya. Ba bu yadda zan yi don tafi ƙarfinsa, amma she kansa ya san she was interested on him. Sam! Bai yadda akwai wata soyayya tsakanin mace da namiji in dai ba ta aure ba. Sai ya ɗauki hakan a matsayin yarinta becouse she was so young. Sam ba ta da wata magana sai ta maganarsa. Kullum cikin posting ɗin hotunansa take a shafinta. Da ga chatting, video call, and voice, babu wanda ba sa yi. Short video na sa da hotonsa jibge a wayarta. Wanda haka the same with him. Ita kanta ta san ya shallake mizanin buddy ya koma wani bangare mai girma na daban. Jannah ta fara zuwa makarantar boko mai tsadar haske, da islamiyar da su Nahlin suke zuwa har da hadda, amma ba ta mai da hankali. Ko islammiyar ta je hankalinta na kan wayarta tana chatting. Ko ta sanya earpiece ta yi kamar tana jin karatun. Da ta dawo gida ba ta ƙara waiwayan karatun da aka yi mata sai in za ta koma islamiyar. Hajiya Baaba ta yi ta ƙorafi tana magana, amma sam ba ta kula ta domin ta yi mata wani irin raini. Wani lokacin ita ce take shakkarta. Kullum malamai cikin ƙorfi suke yi. Abby da kansa ya yi mata magana, amma ta ƙi ji. Gabakiɗaya ta mai da hankalinta kan boko babu dare babu rana. Wani lokacin ko baccin kirki ba ta iya wa, domin horan da mom ta yi mata na cultivating reading culture ya yi matuƙar tasiri a rayuwarta. Burinta kullum shi ne ta zana jarrabawa ta fito da distinction. Ganin suna barazanar dukarta sai ta dena zuwa wanda kan dole Aby ya je da jansa ya ba da haƙuri. Ita gani take takura mata islamiyar take yi, don a lokacin da ta dawo daga school za ta huta ta yi waya da Buddy, sai kuma a dame ta da maganar islamiya. Sati da lahadin ma ba hutu hadda. Ga Hajiya Baaba da ta addabi rayuwarta kan sai ta yi karatun da aka yi mata a gida. Ranar da ta je islamiyar tana zaune a ciki ajin ana yin karatun hadisi, amma hankalita na kan waya suna chatting. "Ba ni wayar." Ta ji mutum a tsaye akanta ya furta cikin tsananin fushi. Da sauri ta miƙe tana zare ido. "Ni babu abin da nake yi da ita, kawai na riƙe ne." Ta ce cikin shagwaɓa da sangarta wanda hakan ya ƙara baƙanta ran Malam Aliyu sabon malamin da aka ka wo musu, sai kawai ya zula mata bulala da ƙarfi. Wani irin ihu ta yi sai ga ta a ƙasa warwar! Babu numfashi, amma ko kaɗan hankalinsa bai tashi ba, domin ya tsani rashin kunya a rayuwarsa. Gabaki ɗaya 'yan ajin suka dare a tunanin su aljanunta ne suka tashi. Kimanin minti ɗaya ba ta motsa ba, wanda ganin hakan hankalinsa ya tashi. Ruwa aka samo tare da watsa mata. Firgigif ta yi ta miƙe sai ta zura da gudu waje tana zunduma ihu. Tun kafin ta shigo ciki Hajiya Baaba ta jiyo ihunta. Barin tuƙa tuwon shinkafar da take yi ta fito har zaninta na faɗi, amma ba ta kula ba. "Uban wa ya taɓa mini jikalle? Waye shi ya san waye mahaifiyarki?" Ta jera mata tambayoyin tare da kamata tana rarrashin. "Wayyo na shiga uku! Inna ƙara zuwa makarantar nan ba dad ya haife ni ba. Dukana ya rinƙa yi, sai da ya yi mini bulala ɗari." Wani irin razana ta yi tare da dafe ƙirji."Na shiga uku ni jikar mai gishiri! Bulala ɗari? Aiko ya ibo ruwan dafa kansa. Ma za muje na ga uban da ya tsaya masa a duniyar nan. Motar 'yan sanda zan sa Halimatuu ta ɗauko masa makarantar gabaki ɗaya ya shafe su." Daɗi sosai ta ji ganin ƙaryarta ta ƙarbu. Sai ta share majina tare da miƙa mata hannu. "Ina jin ma ya karya ni. Ni kawai a cire ni a makarantar sai a ɗaukar mini malami a gida." Ta fakaici Hajiya ta yi murmushi sai ta ƙasa sakin kuka ta ce, "Mugu azzalumi kawai! Ya san irin kuɗin da nake kashe wa jikina da man da nake shafawa, salon ya ɓata mini jiki. Yana ji da fuskarsa kamar ta biri." "Mu je ki ga abin da zan yi masa, don sai ya yi dana-sanin dukanki. Shalelen jikata zai duka.. Kama hannunta ta yi suka nufi makarantar daga shiga ajin ba ta yi wata-wata ba ta kwaɗa masa mari har biyu. "Uban wa ya tsaya maka za ka duki jikalle ta, ka san waye uwarta da abin da take shirin za ma?" "Faɗa mishi Hajiya. Ƙila ya ɗauka yar gidan talakawa ce, wato ga matsiyaciya ya dake ni ya daki banza, mom zan kira sai ta wulaƙanta kaf zuriyarku." Malam Aliyu da zuciya ta turniƙe shi sai ya tsaya yana kallonta ganin yadda take zuba uban masifa bakinta har kumfa yake yi. Malam Kamal ne ya shigo da sauri jin hayaniyar dake tashi a cikin ajin, wanda ya cika da mamakin ganinta tana faɗa. "Haba Hajiya! in rai ya ɓace bai kamata hankali ya gushe ba. Kiyi haƙuri abi komai a sannu-sannu. Ke Jannah wuce ki shiga aji." "Ta je ina? Allah ya kyauta, sai ka ce ba ta da gata. Ai tabar islamiyar nan kenan." "Faɗa musu." Cewarta tana gyara zama hijabinta tare da kaɗa kanta. Nahlin jin muryarta da ga cikin ajinsu ya sa ta sheƙo a guje cikin ɓacin rai." "Hajiya Baaba, wannan wane irin zubar da ka.." "Rufe mini baki shashashar banza! Saboda ba ki da hali maimakon ki taso ki ceci 'yar'uwarki, amma kina ji an kamata an yi mata bulala har ɗari saboda rashin mutunci." "Ɗari?" Suka haɗa baki gurin tambaya. Majina ta ja tare da sakin kuka "Ƙarya na yi? Haka fa ya rinƙa dukana kamar ya samu jaka." Kama hannunta tayi suka fice ya yin da take yi wa malamin gwalo. " A hanya jawo mishi tsinuwa d jafa'i ta rinƙa yi har suka shig cikin gida. "Hajiya Sanyi na ke ji ba ni da lafiya." Tsaki ta buga tare da kama ta tana faɗin, "Ma za hau gado ki kwanta. Bari na ɗauko ruwan zafi na daddana miki jikinki, haka kawai saboda mugunta ya tashi kashe mini jikata ɗaya tal da na samu." Murmushin jin daɗi ta yi. "Yauwa Alhamdulillahi na huta da fita zuwa islamiya." Sai ta ɗauki wayarta don ta sanar da daddy. Hajiya Baaba kuwa hnakalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, domin tana matuƙar sonta sosai. Gani take kamar Halimatu ce a gabanta. Ajiyar zuciya ta yi mai ƙarfi tare da ƙara janyo mata bargon ta rufe ta, don a tunaninta bacci za ta yi. "Ina sonki fiye da yadda nake yi wa mahaifiyarki, don ma wani lokacin ba ki da mutunci da ko tsinke ba zan bari ya taɓa ki ba." Ta furta a ranta ta ɗauki robar ruwan zafin ta fita bayan ta ja mata ƙofa. Tana fita ta saki dariya tana rawa. Wayarta ta ɗauko ta kunna data. Numbar Hazaifah ta kira suka fara hira, yayin da zuciyarta ke cike fall da farin ciki, domin ita a ganinta karatun takur ne a gareta, don ko lokacin da take London so huɗu a wata ake mata karatu, kuma duk lokacin da malamin yazo sai dai ta ce ba ta iya ba ya biya mata, don haka take jin kamar an cire mata ƙaya. Aby na dawowa ko parking bai gama ba Hajiya ta fito tana bambami tare da rantsuwar ba za ta ƙara komawa makarantar ba. Saboda tsabar takaici kasa ce mata komai ya yi, sai da ya ɗauki tsawon lokaci yana sauraren ta, sannan ya fara ba ta haƙuri cikin ladabi. Girgiza kansa ya yi kawai ya wuce sashinsa. Haka kuwa aka yi. Hajiya ta shafa ma idanunta toka akan ba za ta ƙara zuwa islamiya ba, duk da irin haƙurin da Aby ya ba ta ya kuma sanar mata da ya gargaɗe su akan ba za su ƙara dukanta ba, amma ƙememe ta nuna ba shi da iko da it ta hana zuwa. "Ni ma naga ba jahila ba ce, sai da na sauke kur'ani, kuma ɗan haddar nan da hadisai na sani, don haka zan fara koya mata kafin a samu wata makarantar." Jin abin da ta ce babu yadd zai yi kan dole ya haƙura domin ita ce mai faɗa a ji a gidan. Fatan shi Ubangiji ya ba shi damar yi mata biyayya har ranar da mai rabuwa za ta raba su. Duk wannan wainar da ake toyawa Ajmal ba ya nan, domin ya tafi Ƙasar Cairo zai yi tsawaon watanni uku. A ranar da ake sa ran dawowarsa. Gidan ya kacame da aiki ba matsaƙa tsinke sa toye-toye ake yi, yayin da ƙamshi ya cika gidan. It kanta Hajiya Baaba ba'a barta a baya ba, gurin zama ta shirya masa tuwon shinkafa da miyar ganye har da dabbu masu rai da lafiya sanin cewar yana so. Jannah dake falonta tana kallon Arewa24 wani lokacin kuma tama danna wayarta. Juyo wa ta yi ta kalli Hajiya da take ta safa da marwa a kicin ɗin. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K KURA DA FATAR AKUYA* *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 10-11* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Ita kanta Hajiya Baaba ba'a barta a baya ba, gurin shirya masa tuwon shinkafa da miyar ganye har da dabbu masu rai da lafiya sanin cewar yana so. Jannah dake falonta tana kallon Arewa24 wani lokacin kuma tama danna wayarta. Juyo wa ta yi ta kalli Hajiya da take ta safa da marwa a kicin ɗin. Miƙewa ta yi tabi bayanta ta shiga kicin ɗin tana hamma. "Hajiya ina Binta ta dafa mini indomie yunwa na ke ji." Hararta ta yi ta ci gaba da aikinta kamar ba ta ji me ta ce ba, don tun safe take cike da ita sakamakon ba ta tashi ta yi sallah ba sai bakwai da minti arba'in. Jin ta yi shiru ya sa ta cika sai ta ɗaga murya cikin ɓacin rai. "Kina jina fa Hajiy.." "Ke kin san Allah yanzu zan ƙwaƙƙwala miki ludayin miyar nan a kanki. Na ga mace kike da hannayenki? Don haka ki girka da kanki, ko ki ibi abincin da na yi wa Adamuu." Dariya ta mai shewa jin abin da ta ce. "Ni kamata na yi girki, amma dai wasa kike mini ko? Da kika ce na ci wannan kwacamalar ta ki." Ta ƙarashe cikin tsigar mamaki. Hannun rigarta ta fara naɗe wa kamar za ta yi dabbe. Ganin haka ya sa ta fara dariya tana matsawa. "Na lura kamar 'yar dabbe kike wallahi, bari na kama kaina kafin ki sa mini wannan hannun na ki mai kama da icce. " Hararta ta ƙara tare da ɗaukar muciya za ta tuƙa tuwon. "Da kin tsaya ki ga yadda zan yi miki fitsararriya kawai." Wayarta ta ɗauka tana faɗin, "Wa ni? Ai kin fi ƙarfina 'yar dirama. Allah ya kyauta na ci abincin nan, na lura Ya Ajmal mugun bagidaje ne. Ya yi ta wani iyayi, amma ya je ƙasar waje sai ya ci local food taɓ!" Hajiya Baaba ta ci gaba da tuƙin tuwanta aranta tana matuƙar jin haushinta domin da ba'a ce tana sonta ba, sai ruwa ya gagareta sha a gidannan domin halayarta sam babu wanda ya yi mata. Sashin Ammy ta shige. Kai tsaye kicin ta nufa inda take jin kamshin cake da ake baking ya cika mata hanci har sai da ta shaƙa tare da lumshe ido. "Wow! My Anty. The best cooker in the world. Please can I have a bite?" Ta ce tare da ƙarasawa kicin ɗin ta kai hannu ta ɗauki cake ɗin ta sanya a bakinta tana taunawa tare da lumshe ido. Dariya ta yi cikin jin daɗin abin da ta ce. Tan ajuya kwaɓin cake ɗin ta juyo ta kalle ta. "Kwaɗayayya, bayan wanda kika ci." Ƙara kai hannu ta yi sai ta ɗauke tana faɗin, "A nan kika fi auki, ba ki iya komai ba sai kwaɗayi." Ɓata fuska ta yi. " Haba duk yabon da na yi miki? Don Allah ki zuba mini yunwa na ke ji. Yau kin ƙi yin girki da wuri. I beg you." Miƙa mata robar ta yi tana buɗe oven ɗin ganin alamun ya gasu. " Na bari sai na gama aikina yau girkin dare kawai zan yi. " Allah ya sa kiyi aure a kusa na rinƙa zuwa gidanki" Ta bata amsar tambayarta. Ta ce tare da zama akan stool da yake kicin ɗin. "Huhm! You are indeed amazing cooker. I can give you award for that. Gaskiya ya yi daɗi ba kaɗan ba." "Gaskiya ina son ga na iya all intercontinental dishes sosai. Kiyi dedicating time na koya miki." "Humh!" Ta ce tare da kauda zan can ta hanyar cewa, "Wai Anty, duk wannan girkin is for Ya Ajmal? Hajiya ma fa na ga har kusan kala biyu ta yi mishi. Shi kam wane irin ci ne da shi." Dariya ta yi jin abin da ta ce. "Ke dai kin sama Yaya ido." "A,a ba zan zancen haka ba ne, am just jealous don na ga ko lokacin da na zo ba ki tarbe ni haka ba." Dariya sosai ta yi jin abin da ta ce. "Kar dai ki juya zancen don na yi miki maganar koyon girki. Ya Ajmal mutum ne mai son abinci kala-kala, wannan dalilin ya sanya budurwarsa da zai aura sai da ya sanya ta koyon girki. Tana cikin matan da sunan su ya shahara a yanar gizo suke koya girki, don ya hana saka hotonta da kin santa." "A lailai good for him. Na kosa a yi auren mun rinƙa zuwa kwasar girki ko da na lura sam ba shi da kirki, kullum fuska a ɗaure yana mazurai." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar cinyar kaza ta nufi falo da sauri don kar ta yi mata tsiya. Dariya ta yi ta girgiza kanta ta ci gaba da aikinta. Misalin shidda na yamma jirginsu ya sauka a Nigeria. Ayaan ya ɗauko shi daga filin jirgi sai da ya yi baccin gajiya bayan sallar magariba ya shiga sashin Hajiya wacce ta idar da sallah jin sallamarsa yasa ta shafa addu'ar da take yi. Cikin jin daɗi ta juya tana kallonsa. "A maraba da baƙon turai." Zama ya yi kusa da ita yana gaishe ta. Fura kawai ya sha ya miƙe. "Hajiya Baaba, bari na shiga na gaida su Ammy, aka wo mini tuwon sai anjima zan ci." Fuska ta canza jin abin da ya ce. " Kar ka damu zan ɗumama na ci abincina, Allah ya ƙara mini na dage na yi girki, bayan na san da wuya a barka ka ci." Bai ce mata komai ba ya kam hanyar ficewa. "Sai da safe." Ita ma miƙewa ta yi sannan ta kalle shi rai a ɓace. "Ina tsarabar Jannatuu? Na ga nawa ne kawai." Shi kam har ga Allh ya manta da wata aba wai jannah domin tun da ya tafi kansa ya yi zafi. "Wace kenan?" Tsaki ta yi jin abin da ya ce don ta ɗauka rainin wayonsa ne ya tashi. "Ban sani ba, 'yar babin roba ce da na siyo na ke wasa da ita bayan tafiyarka. In har za ka manta da ita, ai za ka manta da kanka tun da a gidan nan kowa da bazar uwarta yake taka rawa." Ransa ne ya ɓace take jin abin da ta ce amma sai danne don baya son ya saka ma kansa damuwa daga dawowarsa. "Oh! Na gane. Mantawa na yi. Da safe sai na haɗa su duka na ba su." " Da dai yafi." Ta ce tare da shigewa ɗakinta ta bar shi tsaye yana mamakin rayuwarta. Falon Ammy ya nufa ya same su dukan su a falon har da Jannah da tafi zama acan sai dai jn tsiyar Hajiya ya tashi sai ta zo ta wartake ta, amma ba shi zai hana ta dawowa ba. Zama ya yi yana kallon Ammy da farin cikin ya bayyana a fuskarta sosai. " How was the journey?" Abby ya ce bayan ya amsa gaisuwar da ya yi masa. "Great!" Ya ba shi amsa. " Sannu da dawowa ya Ajmal." Suka haɗa baki gurin faɗi har da Janaah da ta bi ayarin gurin yin motsi da bakinta. Ɗaga kansa kawai ya yi yana murmushi. "Ke Nahlin suko masa da abincin ya ci a ƙasa, zai fi masa sauƙi." Cewar Ammy wanda ya sa ta miƙe da zamarta don ta ɗauko. A maimakon ta taimaka mata sai ta yi zamanta tana ta kallonta a wayarta wanda yansa ya yi mata mugun kallo bai ce komai ba. Abincin kaɗan ya ci ya miƙe."Ammy bari na je, ina son zan fita zuwa ten zan dawo." Dariya ta yi." Surukar tawa ta yi kira kenan?" Shafa saman kanshi ya yi cikin jin kunya. "A'a, ni ne na yanke shawarar na je yau, don gobe Abuja zan wuce kuma sai na yi kwana biyu." Ta kalle shi daidai lokacin da ya murɗa ƙofar fita. "To shikenan, a dawo lafiya. My regards to her." Kaɗa kansa ya yi ya fice yana taya Abby dariyar abin da Ammy ta ce da yake tsokanarta ba ta da kunya. Jannah duk sai ta ji wani irin babu daɗi ganin yadda ahalin suke farinciki, da yadda suka ɗauke shi kamar wani waliyinsu. Ga shegen girman kai da nuna isa ko ita da mahaifiyarta take damawa ba ta nuna hakan. Fafffaɗan ƙirjin shi ke ba ta haushi sosai domin sam ba ta ƙaunar namiji mai wannan surar, wannnan na ɗaya daga cikin abin da ya sa take son Huzaifah domin komai na sa daidai ya yi mata. Gemun shi irin na gayu ya aje ba kamar shi ba da ya tara da babu laifi, wai shi sunnah. Ɗakinsa ya wuce ya sheƙa wanka tare da saka shadda ash colour ya fashe jikinsa da turare ya shiga cikin mota ya fice. A lokacin da ya isa ƙofar gidansu Mushiirat ya ɗauki wayarsa ya kirata wanda bugu ɗaya ta ɗauka. "Hello, I'm outside you house?" Ya kashe wayar daidai lokacin da take faɗin, "Oh bab stop teasing me." Dariya ya yi yan kaɗa kafarsa da ma suprised ya so yi mata don tun ana gobe zai dawo take roƙon sa akan ya zo gidansu a ranar da dawo. Ko minti biyu cikakke ba'a yi ba sai gashi ta fito da dogon hijabinta har ƙasa da carbi a hannunta. Ganin motarsa ya sa ta saki murmushi cikin tsigar jan hankali. "Oh my God! Bab, you surprised me." Sai ta koma cikin gidan tare da buɗe masa get ba tare da ta jira direba ba. Da sauri ta isa gare shi daidai lokacin da yake ƙoƙarin buɗe ƙofar motar. Hannunta ta kai ta riga shi buɗewa. "You are welcome Sadaukina. Allah na yi mamakin zuwanka har na fara shirin bacci da na idar da hadda." Sai ya haɗe hannunsa ya ɗora a kirjinsa. "Good girl, ina fatan kin gama wanda na ba ki ko." Ta kashe masa idanu tare da kara matsawa kusa da shi. "Na gaya maka umurni ne kawai naka, cikawa kuma nawa. Har na gama na ƙara ma kaina." Hannunsa ya tafa jin abin da ta ce."Wow! You did great my angel. Ma za muje ki na karɓa duk da dare ya yi, ba daɗewa zan yi ba." A hankali ta raɗa masa."Don Allah ka tafi a hankali, ka san ka dawo duk ka gaji bana son ka wahalar mini da kanka." Murushin jin daɗi ya yi sosai, wannan dalilin yasa yake matuƙar sonta. Mace ce wacce ta iya san duk wani techniques and procedures na iya jan hankalinsa. Da ma tuni tsarin rayuwarsa baya son ƙaramar yarinya, yafi son mace mai shekaru wacce sai dai ta kula da shi, ba ya yi rainonta. Mushiirat nurse ce a asibitin Shika. Ƙofar falon mahaifinta ta buɗe masa tare yane labulen falon ya shiga. "Ka ga yadda Ƙasar ta karɓe ka? Ka yi kyau da fresh." Lumshe idanunta ta yi tana shaƙar ƙamshin turarensa da yake tafiya da imaninta a dul lokacin da ta shaƙe sa. Zama ya yi yana kallonta daidai lokacin da ta ce masa."Ina zuwa." Ta shige sashinsu. Jim kaɗan ta dawo. "Yaya, ban san za ka zo ba ai da na yi maka snaks kala-kala. Wannan na bikin 'yar Alhaji Bello da na yi ne." "Good shi ya sa nake ƙara sonki sosai, you re not liability." Murmushin jin daɗi ta yi har sai da haƙuronta suka bayyana. Ya ɗauki samosa ya kai bakinsa tare da taunawa yana mata wani irin kallo."Is testy. Da gaske ya yi daɗi sosai fa! Anya in na aure ki zan iya cin abinci a waje. Gaskiya I salute you interms of cooking." "Relly.?" Ta ce masa sai ya ɗaga kansa tare da kashe mata ido, wanda hakan ya ba ta kunya ta yi dariya ta yi tare da sanya hijabinta ta rufe fuskarta. Sun sha hira duk da cewar ba ta yi tsawo ba ya karɓi haddar sannan ya yi mata sallama ya tafi. Bayan ya isa gida ya kira ta ya sanar mata da ya isa sannan ya kashe wayar bayan sun yi sallama. LONDON Mom zaune a gaban dressing mirrow tana gyara hodar fuskarta. Wayarta ta ɗauka da ke neman agaji ta kanga a kunninta. "Hello James, have you done with the article?" "Almost ma'am." Ya ba ta amsa. Kashe wayar ta yi ta ci gaba da gyara fuskarta da soson hodar. Bayan ta gama ta ɗauki jakarta tana ƙoƙarin fita dad ya shigo fuskarsa a ɗaure da wayarsa a hannunsa. "Is that real about the rumors Halee?" Ya faɗa cikin tsananin fushi yana nuna mata labaren da yake karantawa ɗauke da hotont ɓaro-ɓaro. Ba tare da tsoro ko fargaba ba ta kalle shi cikin ɗaurewar fuska za ta fice ta ce, "Yes it is." Tare da kama hanyar fita cikin takun isa. Da sauri ya juyo da ita yana zare mata ido."Look Halima, what do you take me for? A ce ina matsayin mijinki za ka shiga politics without my awareness?" Ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya ba tare da ya bari ta furta komai ba ya ɗora da cewa, "Babu yadda ban yi ba dake akan mu koma Nigeria saboda 'yarmu and you didn't, now you wanna go back because of politics?" "By the look on your face you are surprised ko?" Ta ce masa cikin gadara. "Na gaji da wulaƙancin da kike mini, kin maida ni kamar yaron gidanki, kullum ba ni wannan ƙasa duk a dalilin hidimarki, kuma ban isa na juya ki ba. Gabaki ɗaya na zama mijin-ta-ce." "Eh, haka ya kamata na yi kuma nake son rayuwa. Mene ne ba ka sani ba game da ni? Har kana da bakin da za ka iya mini magana akan tsarin rayuwa?" Ta ɗaga murya fiye da ta sa sannan ta ci gaba da cewa,"Ba ni da ra'ayin shiga politics, amma suka ɗora ni saboda ganin na cancanta, don haka I don't have any options than to be Minister." Ganin yadda lokaci guda ta canza sai ya sausauta murya domin shi kansa ya yarda mijin-ta-ce ne a gareta. "You wouldn't understand Halee, ke mace ce. Mutanen nan, they are user they will only use you and dumb you. You shouldn't have accepted it. You better think logically and make the right decision." Wani banzan kallo ta yi mishi na rainin wayo." Na yi addu'a kuma na yi istihara kan lamarin Allah na ke roko, na san zai kare ni. Amfani da ni na nawa? Mutane nawa na aminta da su suka ha'ince ni, sai wannan dalilin ya sanya na ƙi yiwa Ƙasata hidama. Allah shi zai kare ni, domin yanzu zamanin nan na jikinka sai ya cuce ka ba tare da na waje ya yi ba." Ga mamakinta sai ta ga yana hawaye. Bai ce komai ba ya fice daga ɗakin. Ajiyar zuciya ta yi mai ƙarfi ta zauna a gefen gado tare da ciro wayarta a jaka ta da take neman agaji ganin Hajiya Turai ce ya sa ta ɗauka da sauri haɗe da sallama. "Hello, uwa ba da mama." "Na am Hajiya Turai ina jinki." "Yarinyar nan da kika tura ni ƙauyensu na je amma akwai matsala."Kafin ta ce komai ta ci gaba da cewa, "Mijinta ya hau dokin na ƙi, kan babu inda za a kai masa mata, kuma kamar harda goyon bayan iyayenta, don sun kafe maganin gida za su yi. Ga shi yarinyar tana cikin mawuyacin hali, mun kaɗa mun raya amma sun ƙi yarda harfa tsutsa ya fara cin ƙafafunta, da wuya ba yanke ƙafar za a yi ba." Shiru ta yi tana nazari na 'yan daƙiƙa."Kai wai me ke damun mutanenmu na daji, ƙaya aka ce mini ta coke ta har ya ja mata wannan sanadin, amma ba za su hankalta ba su bari a nemar mata magani." Tsaki ta yi." Bari na nemi Umar soja kamar in aka je da shi za mu yi nasara. "To uwa ba da mama, don Allah ki dawo Ƙasarki domin tana buƙatar ki, duk da anan ɗin ma ba ki gaza ba." "Shikenan, in sha Allah zan dawo. Allah ya rufa mana asiri." "Amin, in sha Allahu sai kin ci zaɓen nan." Ƙoƙarin kashe wayar ta yi bayan ta amsa amma sai ta ji ta ce "Yauwa na manta sati uku kenan, wata mata na zuwa ofishin mu nemanki, mun yi munyi da ita ta sanar mana buƙatarta, domin daga gani tana neman temako ne, amma ta ƙi burinta ku haɗu da juna. Kuma mun gaya mata cewar kina Ƙasar waje amma sai ta ce za ta jira ki dawo tun da za ki yi zaɓe ko yaushe ne za ta jira. Ni wallahi na yi tunanin mahaukaciya ce ma." "Mahaukaciya?!" Ta yi tambayar da sigar mamaki. "Eh, ba za ki gane hakan ba sai kin ganta, amma fa da hankalinta don cikin natsuwa take magana. Wahala ce ya mai da ta haka. Sai dai, ta nuna ba ta son taimakonmu ta fi son ganinki." "To shikenan, Allah ya kaimu." Ta faɗa da sauri tare da gitse wayar a ranta tana tunanin wace mata ce da duk da ta san bai wuce taimako ta zo nema kuma ko ba ta nan za a yi mata. Miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin bayan ta ja ƙofar. NIGERIA Anty Nahlin ce ta shigo ɗakin Hajiya Baaba riƙe da waya tana ihun murna. "Oh little sis sleeping, wake up let's celebrate." Tana dariya cikin farin ciki. Miƙewa ta yi tana goge ido domin ta yi nisa sosai a cikin baccin. "For God sake, za ki tashe ni kaina ke ciki ciwo." "Ayya sorry, I can't wait ne. Guess what?" Ta ce cikin tsananin murna. Ganin haka ya sa ta tashi ta zauna tna fuskantarta. "Anty Nahlin what's going on? Please tell me, you know I'm not good in guessing." Ɗage kafaɗa ta yi tare da ɓoye wayar da take ƙoƙarin ƙwace don ta gane albishirin da za ta nuna mata yana wayar."No, sis you most guess." Ɓata fuska ta yi."Ok, to shikenan in ba za ki gaya mini ba, let me give it a try. You are engaged?" Ta ce da sauri cikin tsokana. Binta da gudu ta yi suka fara zagaye dakin, "Common, ya za yi na yi aure ya Ajmal bai yi ba. Duba ki ga abin farin cikin da ya same mu a family dinmu. Your mom za ta fito takarar Minister, and soon she will be back to Nigeria." Da sauri ta saki wayar da take nuna mata hotonta wanda ta yi kyau sosai, ganin haka ya sa ta yi sauri ta rike wayar kafin ta kai kasa tana kallonta cikin tsananin mamaki. "What happened? Why are you frustrated?" Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 11-12* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "I hate her. My mom is so selfishness. Za ta dawo Nigeria saboda she wants to be a politician? Or my God! I can't imagine this. Bayan ta ki dawowa saboda umurinin mijinta da ni. Allah ban taba ganin maiyar kuɗi ba irinta. So take ta kwashi kuɗin gwamna..." "Haba Jannah, duk waɗannan mugayen kalamai ga mahaifiyaki kike furtawa. Wannan fa cigaban ahalinmu baki ɗaya ne, ke da za ki yi murna za ta dawo kusa dake." "No, I won't go. Na fi son na zauna a gidan, amma babu inda za ni don ba ta da lokacina. So am happy here." Hararar sakin mata tare da miƙewa" You know what? I can't deal with your shit right now, and is this attitude of you that annoyed me." "You don't know everything. You don't know her shi ya sa kike faɗin haka. "Then disclose it to me, kinga.." "No I don't have that time, abin da kawai na sani ba ta sona." Ta ƙarashe maganar cikin kuka. Hajiya Baaba ta fito daga ɗakinta ta balla mata harara,"Ke dai wallahi anyi 'yar baƙinciki. Ni ban taɓa ganin yar da take wa uwarta hassada ba sai ke. To ta Allah ba ta ki ba, mahaifin na ki da kike so ya fi ta ba haka Allah ya so ba, sai dai ki mutu. Miƙewa ta yi ta tura baki tare da zabga mata harara kamar idanun za su faɗo ƙasa. Ɗaki ta ruga tare da kulle ƙofa tana kuka sosai. Numbar dad ta kira wanda bugu ɗaya ya ɗauka, "Helle dad, is it true that mom wants to come back to Nigeria because of politics?" Shiru ya yi kamar ba zai amsa tambayar ba har sai da ta kara maimatawa cikin ƙaraji. "Oh yes but understand her." "Haba dad, supporting her all the time, you don't have right in your house. Na tabbata in har ta fara siyasa, sai kayi watanni ba ka ganta ba. Please ka rabu da ita ka dawo Nigeria ka yi aure mu yi zamanmu da matarka, ta haifa mini ƙanni, saboda ita mom neman kuɗi ya sa ta ƙi haihuwa. Ni ɗaya kawai ta haifa kamar mayya." Wani irin abu ya daki kansa mai kama da guduma. Ko kaɗan bai taɓa tunanin za ta yi ƙorafi game da rashin haihuwar mom ba. Idanunsa ya rintse yana jin anya in ta ji shine sanadin hakan za ta yafe masa. Take zufa ya keto masa har yana ɗiga a jikinsa. "Haba Jannah, ya kamata.." Ɗif ta kashe wayar tare da jifa da ita."Na rasa wane irin so yake mata ba wanda ya kasa yin wani abu a gidansa. Anya ba asiri ta yi masa ba, don ta juya shi son ranta." Ta tambayi kanta cikin ruɗu. Har ta danna numbarta za ta kira sai kuma ta ga rashin alfanun hakan, domin tunda ta ce za ta yi babu wanda ya isa ya hana ta. "Rayuwarta ne ta je ta yi kowa yana da ikon zaɓa ma kansa abin da yake so. Kamar yadda take rayuwara son ranta ni ma ba ta isa ta ba ni umurni na bi ba." Ta faɗa a hasale Don haka ta cire abin a ranta tunna shi kansa wanda yake da iko da ita ya kasa komai ballantana ita da ba ta bata mahimmanci a rayuwarta ba. Jannah na kwance wayarta ta fara neman agaji. Ganin numbar mom ya sa ta yi tsaki ta koma ta kwanta. Tunawa da motarta ya sa ta zabura daidai lokacin da wayar ta tsinke. Tana ƙoƙarin kira kiran ya ƙara shigowa. "Hello Jannah, motarki ta iso. In sha Allahu gobe yayanki zai ɗauko miki ita." Ihun murna ta saki sosai tana tsalle. Maganar mom ɗin da take yi yasa murnarta ta koma ciki."Haba mom, kan me za'a hana ni driving? Ni gaskiya ba zan yarda ba." Sauke ajiyar zuciya ta yi tana faɗin,"Kafin ki gama sakandiri ne, amma da zarar kin gama za ki fara tuki, kin san Nigeria ba kamar London ba." Kashe wayar ta yi tana gunaguni. Hajiya Baaba da take ƙoƙarin shiga ɗakinta ta ja ta tsaya jin tana ta magana ciki-ciki."To 'yar gidan fitsara, jikar marasa kunya. Uban wa kike zagi, in dai ba 'yata ba?" Harara ta banka mata ta miƙe ta shige cikin ɗakinta sai kawai ta sa kuka. A mota Aby ke nuna w Ajmal motar da zai ɗauko wa Jannah a Abuja. Tsananin mamakin motar da kyauta da tsadarta yake yi. "Yanzu Aby wancan ficiciyar yarinyar mom za ta siya wa mota, kuma ta yi driving da kanta?" Ya faɗa cikin tsantsar mamaki. "Kar fa ka manta mahaifiyarta wace ce. Kuma ita kaɗai ta mallaka." Jinjina kansa ya yi, bai ce komai ba, wanda ganin hakan Aby ya ci gaba da cewa,"Ka ji maganar an tsayar da ita takarar minister ko?" Kallonsa ya yi sai kuma ya mai da hankalinsa kan tuƙi. "Eh na ji kuma ta amince?" Ya ƙarashe maganar da tambaya. Abby ya ce,"Ta amince da ƙyar, amma dad bai bata goyon baga ba, sai dai ka san in har ta amince babu wanda ya isa ya canza mata. Cikin satinnan zan je India na wakilce ta kan kasuwancinta." Ajmal ya kalle sa yana faɗin,"Tana burge ni mace ce kamar maza, samun ta a ahalinmu abin alkhairi ne. Sai dai 'yarta sam ba ta ɗauko ɗabi'unta ba. She doesn't have table manners and she is so cheeky. Ga shi hajiya ta ƙarashe sangarta ta." Aby da ya ji an tsokano masa inda ke masa ƙaiƙaiyi ya gyara zama yana faɗin, "Yauwa, dama na bari ka dawo ne. Ka san yarinyar nan, ta daina zuwa islamiya? Har makarantar ta je ta mari malamin don ya duke ta." Shiru ya yi, a ransa ya ayyana da zata iya fiye da haka, amma a fili ya ce,"Kai Hajiya sai addu'a. To yanzu bata zuwa kenan?" Aby ya ce, "Eh, ta dage sai dai a canza mata wata makarantar, ko a ɗauko mata malami a gida. Kuma wallahi mahaifiyarta ta roƙe ni akan na bata ilmin addini. Don Allah ka yi wani abu." Ya yi shiro ko zaice wani abu, amma sai ya ga bai ɗauki maganar da mahimmanci ba, sai bin karatun kur'anin da ya kunna yake yi, wanda ganin hakan ya ci gaba da cewa, "Ba zai yiwu na zura mata idanu ba, mahaifiyarta amana ta ba ni. Don haka dole na kula da ilminta kamar yadda zan kula da naku, kuma ko Halimatu ba ta da rai ni me riƙe ta ne. Daga yau na ɗora maka kula da ita." Da sauri ya kalle sa jin aikin da yake son ɗora masa."Ni fa sam bana son shiga lamarin su, kasan Hajiya, ni kaina ba ta barni ba, da na yi magata zata fara mini gori a gabanta salon ta raina ni." "Ya za ka yi, hakanan zaka jure ka yi don Allah, ai wani lokacin tana shakkarka " Jinjina kansa ya yi, don ya san aiki ne a gabansa. Kasancewar ranar Juma'a suka yi maganar, don har ya manta a ranar sati, sai da ya ga Nahlin ta fito da zubbulelen hijabinta za ta tafi hadda ya tuna, har ta wuce shi ya dawo da ita ta hanyar ƙwala mata kira. "Na'am Yaya, barka da hutawa." Ta ce tana ƙoƙarin ƙarasawa inda yake. "Ke Nahlin ma za ki ce wa Jannah ta fito kuje hadda." Ta ɗan yi jin sai kuma ta ce, "To." Ta juya sashin Hajiya Baaba. Ta same ta a ɗakinta ta kunna waƙa sai tiƙar rawa take yi. "Ya Ajmal ya ce ki shirya muje hadda." Wani banzan kallo ta yi mata kamar ba da ita take yi ba. Tsawa ta daka mata wanda ya sa ta miƙe tare da tura baki. "Haddar me? Babu inda zani." Ta ce cikin ƙunƙunai. "Oho, ni dai tsaƙo aka aiko ni." Sai ta fara buga ƙafafunta tana faɗin,"Ni fa Allah ba zan koma islamiyar nan ba, wannan ai salon a raina ni ne, ina babban yarinya." Mugun kallo ta yi mata sannan ta furta. "Ki iya bakinki, wallahi Yaya ba sa'an yinki bane. Don haka ki natsu ki san wanda za ki yi wa, in ba haka ba sai ya canza miki halitta." Ta turo baki."Tun da ga ubana ba." Jinjina kai kawai ta yi ta fice, tana mamakin tsaurin idanunta. Tana isa gurin shi da yake ƙoƙarin shiga mota."Ya ta ce ba za ta je b.." "What?" Ya katseta yana tambayarta da ƙarfi tare da daka mata tsawa wanda ya sa ta matsa cikin tsoro. Fitowa daga cikin motar ya yi ba tare da ya kashe ba."Lallai yrinyar nan ba ta da kunya zan koya mata hankali." Buga ƙofar ya yi da ƙarfi ya shigo ga mamakinsa sai ya ganta a falo da remote a hannunta tana canza tasha, wanda ganinsa ta fara ƙunƙunai tana turo baki. Ajmal ya tsaya cikin mamaki yana kallonta aransa ya ayyana da zaginsa take ganin yadda bakinta ke motsawa. Cikin fusata ya ce, "Ke zagina kike yi don ubanki?" Mari ya kai mata a fuska tauu! Wanda ta ji shi har tsakiyar ƙwaƙwalwarta. Ta takura iya ƙarfinta ta canyara ƙara tare da kiran sunan Hajiya Baaba, wacce ta fito da gudu har tana tuntuɓe. "Na shiga uku! Shalele, maciji ya sare ki, ko kunama?" Turus! Ta yi tana ƙarashe ɗaura zaninnta ganin wanda yake falon. Da gudu ta koma bayanta ta ɓuya. "Hajiya Baaba, ya kashe ni mari hamsin ya yi mini. Wayyo na mutu! Dadddyyy." Hajiya Baaba ita kanta ta san ƙarya take yi domin da haka ne wataƙila da wata maganar ake ba wannan ba, amma saboda rashin son gaskiya ta kurma salati da ihu tana faɗin, "Kan uba, uban me ta yi maka da za ka fara dukanta kamar ka samu jaka?" Ta tamabaye sa cikin tsananin ɓacin rai tana girgiza. "Gaya masa Hajiya Baaba, ko iyayena ba sa duka na ballantana wani ban.." Ransa ne ya ɓace lokaci guda idanunsa suka canza zuwa wani kala, ganin tana shirin zaginsa a gaban Nahlin wacce ko magana yake ba ta iya kallon shi, sai kawai ya zare belt ɗinsa ya shiga zuba mata ta ko ina kuma iya ƙarfinsa. Cikin azama Hajiya ta kai masa cakuma tana faɗin,"Ai ko yau sai na ga uban da ya tsaya maka da za ka duke ta." Ture ta ya yi har ta buge da center table, amma ko kula ta bai yi ba, wanda ganin haka ya sa ta ɗora hannu aka ta yi tsakar gida tana ihu tare da faɗin, "Na shiga uku, na lalace an kwaso mini dangin jaraba! Kai kan Muhammadu sam ba ka yi sa'ar zuriya ba. Jama'a ku kawo mini ɗauki." Ammi da ta fito daga sashinta da makullin mota tana sauri domin ta yi latti ta ji abin da take faɗi wanda ya sa ta yarda makullin tare da rugawa sashin cikin tsanin tashin hankali. Wasu irin zafafan mari ta sauke masa."Ashe ba ka da hankali 'yar'uwarka za ka kama da duka haka saboda ga jaka ko?" Ta ce cikin zafi. "Ai ko yau za'a yi ta a gidanan, wallahi sai ka yi sana-sanin dukanta." Cewar Hajiya. Wani irin ƙululu ya ji ya taso masa cikin tsananin ɓacin rai ya kalli Hajiya Baaba yana faɗin, "Kin yi kuskuren fifitata da kika yi akanmu, ki sani in ban yi ajalinta ba to sai na naƙasata." Ya juya zai fice daidai lokacin da ta ce, "Za ka iya, ai zuciyarka kamar ta fir'auna take." Jannah da ta ji duka rungume ta ta yi."Na shiga uku! Don Allah ki kira mom ta yi mini viser na koma ma London, if not he gonna kill me." "Babu inda za ki, sai dai mu bar musu gidan. Shakuruminki shalele." Ta ba ta masa tana shafa bayanta. Aby da ya shigo cikin falon a lokacin da zai fice wanda hakan ya sa ya fasa yana ajiyar zuciya a kai a kai. "Yauwa, ma za shigo, ai sai da na gaya maka ka ja mana layi a tsakaninmu kaƙi, ga shi yanzu zai kashe mini shalele. Dole mu bar gidan nan, daɗin abin mahaifiyarta za ta iya siya mana duk irin gidan da muke so mu zauna ko a ketare ne." Lamarin sai ya rikita kansa ya rasa ta ina zai fara." Tashin hankalin da kake so ka ja mini kenan Ajmal da sunan gyara? Kana jin mahaifiyata za ta bar gidana saboda kai." Takaici sun na shi magana juya wa ya yi ya fice daga falon ba tare da ya ce komai ba, domin matuƙar ya ci gaba da kallonta, ƙila nan da minti uku, sai dai ayi maganar kai jana'izar gawarta . Zuciyarsa ta ɓace tsananin tsanarta ya ƙara shiga ransa sosai. "Tashin hankali na nawa? Ai aikin gama ya gama. Barin gida ya zamar mini dole, ko kwana ba zan ƙara yi ba a gidannan." Jannnah da ta ji duka ƙwaƙwarar motsi wahla yake mata. Ta kwantar da kanta kafaɗar Hajiyan Baaba da ko zama ta kasa yi, sai famar jijjiga take yi. "Ya zama dole ka ɗauki mataki in ba haka ba, watarana sai ya jawo mana tashin hankalinn da ba mu yi tsammann.." "Rufe mana baki! Munafukar Allah. Ai duk tarbiyarki ce, da kika raini 'ya'yanki sakaka kamar kashi, ba kya iya tsawata musu. Ni da na isa da ɗana, kin ga ina ije kara ya tsallake? Ai ni an haɗa mana jini da jaraba." Ta ƙatse Ammy da take maganar. "Ki yi haƙuri Hajiya maganar ba ta kai haka ba." Cewar Aby. Harara ta gallah masa."Ta ma wuce." Ta ba shi amsa. Kamata ta yi suka nufi ɗaki tana faɗin,"Shakuruminki kin ji shalele, babu inda za ki. Sai na ga uban da ya isa ya kai ki islamiyar." Ganin ta ɗauki waya tana neman numba ya yi saurin shan gabanta."Don Allah, kar ki kira Halima. Ni ma ina da iko a kanta, kar ki manta ciki ɗaya muka fito." "Sai na bari ya kashe ta ina gani ko?" Ta tambaye shi cikin ɓacin rai tare da shigewa ciki ta banko ƙofar da ƙarfi. Dafe kansa ya yi, yana dana-sanin gaya masa, domin gashi yanzu ya ɓata goma biyar ba ta gyaru ba. Juyawa ya yi ya fita ganin kowa ya tafi ya barshi shi kaɗai. Ajmal yana shiga ɗakinsa ya shige bayi. Ba tare da tuɓe kayansa ba, ya buɗe ma kansa shower yana ƙoƙarin tuɓe kayan, ya yin da ransa yake zafi zuciyarsa ke tafarfasa kamar za ta yi tsalle ta fito waje. A maimakom ya yi hushi ya ƙyaleta sai ya saka a ransa sai ya ƙuntata rayuwarta don ya baƙanta mata da Hajiya Baaba da ƙiri-ƙiri take fifita ta akansu. Idon don kuɗi ne, ko kuɗin da yake da shi ba na Aby ba ya isa ta daina yi musu gorin sun ci da arzikinta. Yana fitowa ya saka milk colour na jallabiya tare da ƙarasawa frig ya rinƙa banka ma cikinsa ruwan sanyi ko ya ji salama, amma da ya tuna abin da ya faru sai ya ji komai ya zaman masa sabo. Wayarsa dake ƙara tun da ya shiga wanka ya ɗauka cikin ɓacin rai."Kin dame ni." Ya furta tare da daka mata tsawa. Da sauri ta kashe wayar saboda tsabar tsoro jikinta har rawa yake yi."Na shiga uku! Wa ya taɓa shi?" Ta furta cikin jimamin tsawar da ya daka mata. "Allah ya ba ka haƙuri. Ba ni na kar zomon ba rataya aka ba ni." Ta ce tare da ije wayar ta ci gaba da kwaɓin cincin ɗin da take yi. "Hello Halimatuu, kina jina?" Hajiya Baaba ta furta."Eh in jin ki, Allah ya sa lafiya? Don na ji muryarki ta canza." Ta ce kamar ba ta san abin da ya faru ba, don Aby ya yi mata text ɗin komai kafin ta kira wayar. "Ina lafiya, an saci zanin mahaukaciya. Gida za ki canza mana ni da Janaatuu, wannan azzalimin yaron ya tashi..." "Hajiya Baaba, na ce ki daina ce mini Jannatu. Kowa sai kin ɓata ɓasa suna?" Ta katseta cikin masifa cikin kaukausar murya. Takaici ya kamata matsawa da wayar ta yi tana faɗin,"Ka ga mini ja'irar yarinya fitsarrariya! Ina neman miki mafita, amma sai kin nuna halinki, ai na gaya miki albarkacin 'yata kike ci da na bari ya miki dukan tsiya wallahi, na watsawa karnikan gidan ƙasusuwanki." Murguɗa bakinta ta yi ta gyara kwanciyarta tare da ci gaba da kuka da ƙarfi da sheshsheƙa ta yadda mom za ta ji yo ta. Mom da ke jin faɗan da suke yi sai ta shiga girgiza kanta a ranta tana tunanin za ta canza halinta na fitsara kuwa, ganin ko uwarta ba ta ragawa ba. Tun lokacin da Aby ya sanar mata ta yi matuƙar murna da hamdala, domin ta fahimci tana buƙatar wanda zai gyara mata kuskuren da ta aikata, kasancewar ta gama raina su duka. "Yauwa ki nema mana gida wanda zamu zauna daga ni sai ita." Ajiyar zuciya ta saki tana jin yadda take shiga take fita da zage-zage da jawo masa jifa'i tamkar ba matsayinsu ɗaya ba a gurinta wanda hakan bai yi mata daɗi ba, don ko ita ta ji wani iri ina ga kuma shi da iyayensa. "Kiyi haƙuri Hajiya, su ɗin duka matsayi ɗaya suke a gurinki, kar ki sanya tsana ko rabuwar zumuncin su. Zan yi magana da Aby sai..." "Ban san ke shashasha ba ce Halimatuu! Anya kuwa nonona kika sha? 'Yarki ɗaya tal wacce Allah ya ba ki ake shirin kashewa shi ne sai kin yi shawara da ubansa? To shikenan, ki bari ya kashe ta, inya so kuɗin da kuɗin da kike tarawa, kinga sai ki bar ma duniya su..." Fisge wayar ta yi daga kunninta don tana jin abin da take cewa. "Na san ba kya ƙaunata. So I don't want you to prove it. You know? I'm not under age, and my dad has money so I can handle myself." Ta yanke kiran cikin ɓacin rai. Baki ta buge mata."Ke kam ban san lokacin sa kika zama haka ba! Mahaifiyar taki kike wa tsawa tamkar 'yar cikinki?" "Kyale ni, Hajiya ba ta sona ban taɓa yin abu na burgeta ba." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 12-13* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM A can ɓangaren mom ajiyar zuciya ta yi cikin takaici."Yauwa, Alhamdulillahi! Allah ya kawo mini wanda zai kawo gyara a lamarinta."Dariya dad ya yi jin abin da ta ce. "Lamarinta yana bani mamaki ko Hajiya ba raga ma wa ba ita kanta sonta ne ya rufe mata ido, amma ba ka ji yadda take daka mata tsawa ba. Gaskiya na yi sakaci a rayuwarta. Wayarta ta ɗauka ta yi wa Ajmal transfer kuɗi naira dubu ɗari. Bayan ta tura mishi message akan ya sa kati. "Mu yi mata addu'a watarana zata daina har da kuruciya. Ya faɗa daidai lokacin da kiranta ya shigo wayarsa. "Ga kiran mutuniyar nan, ya shigo." Ya ce yana kallonta da murmushi a fuskarsa. " Ka gaya mata yadda muka tsara." Jinjina mata kai ya yi. "Hello dady, na ba ni na shiga uku! Wallahi dangin mom mugaye ne, ka mai da ni family ɗinku ko ka canza mini gida." Murmushi ya yi jin abin da ta ce." Ba za ki iya zama a family ɗina ba, kiyi haƙuri har mu dawo kin ji." "No" Ta ce da ƙarfi. " Ba zan zauna ba ana cin zalina sai dai ka kama mana haya ni da Hajiya Baaba." Ta ƙarashe maganar tare da sakin ƙara har sai da ya kauda wayar a kunninsa. "Ok, sorry I will." Ya faɗa ba tare da shiri ba. Jin abin da ya ce ya sa ta yi shiru sai shan majina take yi. " Ki bari zan nemi gida mai kyau ku zauna, amma yanzu bari na tambaya ki ba ni zuwa anjima." "Ok dad." Ta ce cikin zallar shagwaɓa tare da kashe wayar. Kafin wani lokaci temperature na ta yi yi high sai rawar sanyi take yi, wanda hakan ya ƙara ɗaga hankalin Hajiya Baaba. Ta yi zagi har da kuka. Su Allah ya isa ya sha babu iyaka. Kowa sai dai ya toshe kunninsa. Ganin yadda jikinta ya rikice Aby ya yi wa likita waya ya zo ya duba ta har sai da ya ɗaura mata drip tasha pain reliever sannan aka samu sausaucin kukan da koshi zai iya ja mata ciwon kai. Ajmal na zaune a falonsa yana ƙoƙarin kiran Mushiirat don ya bata haƙurin tsawar da ya yi mata alert ya shigo. Ya yi matuƙar mamakin ganin kuɗin, wanda har sai da ya yi tunanin ko kuskure ta yi, don ya san Hajiya Baaba ta gaya mata ƙarya da gaskiya. A lokacin da ya ɗaga waya zai kirata sai ya ji kunyar dukanta da ya yi, amma da ya tuna abin da ta yi masa sai ya yi watsi da hakan. Tana ɗaga wayar bayan ya yi sallama ba ta bari ya yi magana ba ta ce," Ajmal, ka ga kuɗi ko?" Amsawa ya yi cikin jin kunya. "Na tura maka ne ka sa kati, ka ga sai ka kira surukata. Aby ya gaya mini har an je jin magana ko?" Cikin jin kunya ya amsa mata. "Allah ya kulla alkhairi ni zan haɗa lefe. Ya yi muku albarka. bye." A hankali ya sauke wayar da ta datse kiran. Ji ya yi gaba ki ɗaya jikinsa ya yi sanyi."Sam ba ta yi halin mahaifiyarta mai kirki da tausayi ba." Sai ya ƙara jin babu daɗi akan dukan da ya yi mata, duk da ya ga alamun hakan daɗi ya yi mata, wataƙila ita kanta ta addabe ta ne shi ya sa. Don haka ya sanya a ransa zai watsi da duniyar hajiya Baaba y taimaki rayuwarta ko don mahaifiyarta har ta zamo ta ƙwarai. Yamma na yi ko jiransa ya kira ba ta yi ba ta rinƙa kwaɗa masa kira ba adadi, wanda bai ɗaga ba sakamakon meeting da suka shiga. Yana fitowa ya ɗauki wayar."Dad, Im under the weather, ƙarin ruwa ake mini." Zare ido ya yi jin abin da ta ce wanda muryarta ta bayyanar da zafin ciwon da take ciki. "Subuhanallahi! Abu ai ya kai ga haka." Sai ta jinjina masa kanta kamar yana ganin ta yayin da take nishi tamkar waccce za ta haihu, sai ya tsinci kansa da jin haushin dukan da ya yi mata ganin har da ciwo. Ya yi ajiyan zuciya mai ƙarfi da ƙoƙarin danne hakan a ransa ya ce,"Mun yi magana da aminina, ya ba ni haƙuri kan kar na kama miki gida ko na saya. Kin san ke ɗin wace ce? Ga shi matsalar Nigeria insecurity. Don haka, a shawarce ya ce na bari ki zana jarrabawarki, in ya so sai ki zauna a hostel, kin ga kafin nan mun dawo lokacin hutu sai ki rinƙa zuwa gida Abuja. What you say?" Sai ta saka mishi kuka tana faɗin,"No dad! I said no, I wanna leave this house as soon as possible. So I won't take excuses." Da ma ya san zai sha jarfa da ita cikin dubura ya ce,"Ok, kina son kidnappers su kama ki ko? Kuma wallahi har raping suke yi wa mace ko su bawa namomin daji gangar jikinki bayan sun kas.." Ƙara ta saka ta kauda wayar a kunninta lokaci guda jikinta ya ɗauki rawa don shegen tsoro ne da ita."Stop saying this, and don't be pessimistic. I'm just curious to leave the house." Murmushin samun nasara ya yi don ya san yadda ta tsorota da wuya ta ƙi amince wa. "Shikenan, zan yi haƙuri ai na kusa fara exam." Ta faɗa a sangarce tana tura baki. Sai ta ga zaman ta gama exam ta samu admission would be better da zama gida ɗaya da Hajiya Baaba don takurawa rayuwarta za ta yi. Duk suna kan wayar take wannan tunanin domin ita ta ɗauka ya katse ganin dogon lokacin da ta ɗauka, but to her suprised he was on the call sai ta ji ya ce, "Ki rinƙa zuwa islamiyar da haddar kin ji. Yanzu zan tura miki kuɗi a account ɗinki." Ba ta san lokacin da guntun murmushi ya suɓuce mata ba." To dad, I will as you suggested." Ya saki dariya."Good." Ya ce sannan ya kashe wayarsa. "You can force a horse to the river, but you can't force it to drink the water. Zan je islamiyar in ya san wata ai bai san wata ba. Ba sai na ga damar yin karatun ba? Tun da ba uban wani zan yi wa ba." Ta ce tare da ije wayar a gefenta. "Yanzu da yake ke shashasha ce kin haƙura za ki zauna ya yi ta dukanki kamar ya samu jaka? A maimakon ki ta da fitina dole sai an canza mana gida muci gashin kammu. Ashe fitinarki ba ta yi miki amfani ba." "Mu ci gashin kammu, ko ki takurawa rayuwata? Hajiya rigimarki kawai ta isa tashin farko a makaranta na ganni under probation. Haka kawai, ki rinƙa kunyata ni a gaban ƙawayena. Matuƙar na amince hawan jini za ki ɗora mini, domin ba na tantama har da rigimarki, ya sa mom ta tsani zaman Nigeria." Tsananin mamaki ya sa ta kasa cewa komai sai zuwa can ta ce,"Ko kaɗan ban yi mamaki ba, ai halinki ne butulci. Abin da za ki saka mini da shi kenan. Oh Allah ka cire mini raina akan wannan banzar yarinyar na huta. Wallahi kin ci sa'ar ƙarin ruwan da ake miki da sai na yi ƙasa-ƙasa da ke."Zuɓɓura ba ki ta yi tana harararta. Ajmal da kanshi ya je har islamiyar ya bada haƙuri tare da yi musu alƙawarin hakan ba zai ƙara faruwa ba. Tare da roƙon su duk abin da ta yi su gaya masa zai yi maganinta. Jannah sai ta ji babu daɗi komawarta islamiyar domin a ganinta ƙasƙanci zai jawo mata amma kasancewar babu yadda za ta yi, kan dole ta shirya cikin doguwar riga da gutun hijabi iya kafaɗarta, ko al'qur'ni ba ta ɗauka ba ta fito. A falo ta samu Hajiya Baaba ita da me aikinta da ke shirin tafiya. Ba ta ce mata komai ta bi ta gabanta ta wuce fuskarta kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa. "Ki kika sani kije kuma wallahi ko namanki gunduwa-gunduwa aka kawo mini ba zan ce komai ba, sai dai ma na yi murnar an raba ni da fitsara da rashin kunya. Tana jin abin da ta furta amma ba ta ce komai ba saboda ba ta da lokacin ta. Tunaninta yadda za ta kalli 'yan islamiyar wataƙila su yi mata dariya, wanda ta ɗauki alwashinnsai ta fasa musu baki. A harabar gidan suka same shi zaune yana jiran ya ga fitowarta ko za ta ƙi. Sam a zuciyarsa bai yi tunanin za ta fito ba, ga mamakinsa sai ya ga ta fito tana kubbure-kubbure, wanda hakan ya ƙarfafa masa gwuiwa, domin tun safe yake tunanin in ba ta fito ba ya zai yi da rigimammiyar tsohuwar da ko gaisuwarsa ba ta amsawa tunda abin ya faru. Ganin za su fita ya daka mata tsawa yana faɗin,"Ke dan ubanki, ina kayan islamiyarki, ko ba'a ba ta bane?" Ya ƙarashe maganar yana kallon Nahlin, wacce ta fara magana cikin tsoro tamkar ita ake tuhuma. "Tun ranar da aka kai ta, na ba ta ta sanya, sai ta ce sun yi mata girma." Cewar Nahlin tana zare ido. Ita kuwa ko a jikinta ta nuna, duk da cewar ta yi matuƙar tsorata da shi, kasancewar har yanzu ba ta manta zafin dukan da ta ji ba. "Yanzu suna ina?" Ya tambaye ta. "Ɗakin Ummu-Kursum." Ta ba shi amsa. "Ma za je ki ɗauko mata ta sanya, kuma gobe in Allah ya kaimu zamu koma karatun asuba, sai ku shirya." Ɗaga masa kai ta yi ta juya cikin sauri, ganin har sun fara latti saboda tsayawa jiran ta da ta yi. Kan dole ba don ta so ba ta juya don ta karɓi kayan ta saka ganin babu fuskar wargi."Jarababbe kawai! Na ga wanda ya isa ya tursasa ni na je." Ta furta tan wurga masa harara a fakaice wanda har ya shige sashinsa. Kayan sun yi matuƙar yi mata kyau tare da amsar fatar jikinta, duk da cewar ita ba ta ga hakan ba sai cika take tana batsewa akan an yi mata dole. Fakan idanunsa ta yi ta zabga masa harara tana turo bakinta wanda kamar zai taɓo gini. " Mugu azzalumi jarabbe kawai!" Ta ce tare da jan tsuka mai ƙarfi. Sai kuma tsananin baƙinciki ya ƙara rufe ta."Mom, duk ke kika ja mini wannan bala'in don da kin dawo babu wanda ya isa ya biyo ni ya duke ni." Ta ce tana jin tsanarta na ƙara shigarta mai tsanani. Ganin yana ƙoƙarin ciro belt ɗinsa ya sa ta ruga da gudu hanyar fita da sauri har tana buge kanta da get wanda ta ji zafi sosai. A islamiyar ma, ba wani mai da hankali ta yi ba, abin da aka hana ta shi ta cigaba wato danna waya, don har aka gama karatun aka tashi, ba ta motsa ko da bakinta da ninyar yin karatu ba. A hanya sun taso za su dawo gida. Nahlin ta kama hannunta tana dariya ganin yadda take shan kunu. "Haba 'yar gidan hajiya Baaba, ki saki ranki mana ko laifin ya shafe ni?" A maimakon ta saki fuskar kamar yadda ta buƙata sai ta ƙara ɗaurewa tana faɗin, "Please Anty, muje gida na tafi ɗakinki, I wanna sleep jiya ban yi bacci ba, ina kallon film ɗin nan da na tura miki Abyss. Kuma na san ba za ta barni ba, ganin magariba za ta ce sai na yi sallah, kawai zan bari inna tashi cikin dare na haɗa." "Humh." Ta ce cikin ranta ba tare da ta san mai za ta faɗi ba, domin lamarinta ya girmi tunaninta. Ƙara gasganta maganar Ammy ta yi da akan tarbiyarta. "Kina da ƙoƙari, kin ga wannan da kika tura mini? I haven't watch episode three." Cikin mamaki take kallonta."Lallai ba kallon za ki yi ba, don ni a kwana biyu na kaga kallon shi. "Ina za ki haɗa kanki da ni Jannah, ke da rayuwarki gabakiɗaya ne, sai dai kici ki kwanta. Sai ta yi dariya jin abin da ta ce tana gyara zaman wuyan hijabinta da take jin ya shaƙe ta."To waye ba ya son hutu Anty Nahlin? Girgiza kanta ta yi alamun babu tan ƙoƙarin buɗe ƙofar get ɗin gidan don su shiga. "Yau am full of excitement. Kin san an kai kuɗin sadakin Yaya?" Ta ce lokacin da suka shiga cikin gidan. "Ni kuwa am neither happy nor sadness." Wa kenan, aka kai kuɗin aurensa? Ta tambaya cikin rashin kula. Duka ta kai mata tana dariya."Ba na son iskanci, wane Yaya muke da shi a gidan, kuma jibi Ummu Kursum za ta dawo?" "Don Allah?" Ta tambaya yayin da fara'arta ya ƙaru."Aiko zan ji daɗi sosa, na yi murnan jin hakan."Sai ta canza maganar zuwa na aurensa."Ai gara ya yi auren ku huta. Ni dai ina gama secandary, na samu admission na huta." "Allah kin yi wa Ya Ajmal, mummunar fahimta amma sam ba shi da matsala kawai dai ba ya son rashin kunya ne." "Haka ma za ki ce Anty Nahlin? For goodness sake, mai na yi masa ya kama ni ya rinƙa duka kamar ya samu jaka, amma kike faɗin haka. Anyway, da ma haka danginku suke, komai babu wanda ya iya sai ku. Ku yi ta criticizing mutane, bayan kune on the wrong part. The same with mom, alway criticizing dad." Dariya ta yi tare da kama hannunta sai kuma ta ɗaure fuska ta ce,"Let's change topic, before I loose my temfer akan abin da kike faɗi." "You better not to do, because I said the truth." Cewar Jannah. A maimakon ta tafi ɗakin Nahlin kamar yadda ta yi shawara, amma sai ta fasa ta wuce sashin Hajiya Baaba ta sanya key a ɗakin tare da kunna waƙa ta ƙure ƙarar ta yadda ko ta dame ta da bugun ƙofar ba za ta ji ba. Washegari da asuba bayan Ajmal sun dawo daga massalaci. Yana shiga ɗakinsa ya zauna azkar ya yi, sannan ya ɗauko alkur'ani yana karanta suratul Tauba cikin muryarsa mai daɗi da fitar da ƙira'a. Yaran gidan suka yi sallama suka shigo a tsanake ya karanta musu karatu sannan suka fice. Tun da Nahlin ta shigo take addu'a a cikin ranta da Allah ya sa kar ya tambayi Jannah, wanda cikin sa'a bai tambaye ta ba har suka kammala karatun. A ƙalla sai da suka yi kwana biyu suna karatun, amma ko da wasa ba ta taɓa maganar ba ballantana da yi ra'ayin zuwa, haka Hajiya Baaba ba ta yi mata maganar ba, don har yanzu hushi take da shi ko gaisuwarsa sai ta cika ta mule take amsawa. Har sai da suka shafe tsawon wata suna karatun, babu wanda ya yi maganarta. Da asuba suna tafe da Aby sun dawo daga masallaci. Aby ya kalle shi ya ce, "Malamin su Jannah, ya yi mini ƙorafin sam ba ta mai da hankali, don bai taɓa ba ta hadda ta kawo masa ba. Sannan ba na tunanin yarinyar nan za ta iya karanta ko izifi biyar, wallahi rayuwarta a kwai gyara." Tsananin mamaki ya kamasa jin abin da ya ke cewa,"Ka ce ƙasurgumar jahila ce? Haba! Da ma ai biri ya yi kama da mutum. Shi ya sa ta ke behaving without moral, because she is not religious. Wallahi duk wanda aka aurawa yarinyar nan an cuce shi." Dariya ya yi jin abin da ya ce."Sam ba na ganin laifin yarinyar sai ta yar'uwata, haba don kawai kin je Ƙasar wasu sai ki manta addininki al'adarki." Ya ƙarashe maganar cikin damuwa. "Jihadi za ka yi Ajmal, domin ita ɗin 'yar uwarka ne, kuma Halima ta gane kuskurenta.Ka ga ko dukan da ka yi mata ba ta ce komai ba. Don haka ka dubi zumunci ka rinƙa koya mata karatu, kamar yadda kake wa su Nahlin." Gajeren tsaki ya yi."Damuwata Hajiya Baaba, kai ma kasan halinta. Bambanci take nuna wa tsakaninmu. Har yau da kyar take amsa gaisuwata, don kawai na yi hukuncin da ya kamata. Ba na son na shiga lamarinta ta ɓata mini rai, kuma ba kyaleta zan yi ba." "A lailai Ajmal, wuyanka ya isa yanka. Uwar tawa kake gaya ma haka." "Haba Aby kai ma ka san ina matuƙar haƙuri da 'yar tsohuwar nan, gabaki ɗaya ta addabi rayuwata." "Haƙuri za mu yi da fatan gamawa da ita lafiya. Ka gode ma Allah ina ka yi aure sai ka zo za ta ganka." "Shikenan, zan yi ƙoƙarin hakan. Ba ri na shig na yi karatu, kafin su zo." "Af na manta ka ga an sanya ranar wata bakwai, sai ka yi ƙoƙari ka gama gininka duk da na ga an kusa. Ginin ne na ga ka iba da yawa. Ko kana da tsarin mata biyu ne?" Ya tambayesa cikin tsigar zolaya. "Allah ya kyauta! Ɗayar ma da za'a iya raba ta gida biyu ina so, domin rigimar mata sai su, ko ita Mushiirat wani lokacin sai a hankali, kuma ni Aby ai gado zan yi mata ɗaya ta ishe ni." "To lallai, ai dama kyan ɗa ya gaji ubansa. Matuƙar mutum ba zai iya adalci ba gara ya yi ɗayan." "Haka ne, Allah ya sa mu dace." Ya ƙarashe maganar yana dariya da sosa kai tare da yin hanyar bangarensa. Bayan ya biya Nahlin karatunta ya kalle ta lokacinnda take ƙoƙarin miƙewa ta tafi."Je ki kira Jannah ta fara karatu." Jim ta yi kamar ba ta so aiken ba, sai kuma ta ije alkur'anin ta tafi sashin Hajiya Baaba. Sallama tare da ƙwanƙwansa kofar ta yi."Uban mene ne za'a dame ni da sassafe?" Hajiya ta tambayeta ko gama wassakewa ban yi ba. "Allah ya ba ki haƙuri, ina kwana." "Da ban kwana ba za ki ganni, kinibibabbiya." Cikin ƙubula ta kalle ta dama kamar ta san hakan zai faru shi ya sa ba ta so aiken ba."Ni fa bana son faɗa, Ya Ajmal ya ce Jannah ta zo ta fara karatu." "Lallai yarinyar nan, kin raina ni. Ki kalli tsabar idanuna kice mini mafaɗaciya? Ko da yake ba laifinki ba ne, na san maganin abun ku..." Maganar ta maƙale tunawa da ƙarshen abin da ta faɗa."Kika ce Ajmal ya ce a kira wa?" Cikin rashin shakku ta furta bayan ta gyara tsayuwarta."Jannah." "Oh, dukan da ya yi mata bai ishe shi ba, sai ya tsiri koya mata karatu don ya kashe saboda ba shi da uwarsa ba su da asara ko? To kije kice babu buƙatar hakan, ai yasan ni ɗin ba jahila ba ce zan koya mata. Wuce ki bani guri shashasha kawai."Juyawa ta yi tana hararta. "Ɗan banza mara ta ido kawai." Ta ce tare da mai da ƙofar ta rufe, amma ba ta sanya key ba. "Ya Ajmal, Hajiya ta ce ba za ta zo ba." Miƙewa ta yi yana faɗin,"Ok." Ya yi sashin na ta. Murɗa ƙofar ya yi ya shiga daidai lokacin da ta fito tana banbami."Ke Hafsatu, wallahi ki fita idanuna kin ji na gaya miki, ƙae dawowa ki ka yi kenan?" Turus ta yi ganin wanda yake ƙoƙarin shigewa ɗakin Jannah."Wata uwar harara ta zabga masa. Ya Ajmal ya ce Jannah ta zo ta fara karatu."Ma za zo ka fita, tun muna sheda juna, kafin muyi uwar watsi da kai." "Ba gurin ki na zo ba, kuma umurnin Aby na ke bi don haka babu ruwanki da ni." Ya ƙarashe maganar yana nufar ɗakinta. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 13-14* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Ba gurin ki na zo ba, kuma umurnin Aby na ke bi don haka babu ruwanki da ni." Ya ƙarashe maganar tare da kai wa ƙofar wata uwar duka. Cikin tsanannin tsoro ta miƙe daga baccin da take yi tare da zabga uban ihu domin ita a tunaninta ɓarayi ne suka zo, jin muryar Hajiya Baaba tana bambami ya sa hankalinta ya kwanta. "Na shiga uku! Ashe gari ya waye ban yi sallah ba." Da sauri ta ƙarasa ƙofar ta buɗe daga ita sai figigiyar rigar bacci. Miƙa ta yi tana faɗin, "Ni wallahi kin takurawa rayuwa kuma, gashi na buɗe bari na yi salla.." Maganar ta maƙale mata ganin mutum tsaye gefen Hajiya yana kallonta da take ta tsiya. Ganin haka sai ta tsaya cikin tsoro tana zare ido, sai kuma ta janyo hijabinta ta sanya daidai lokacin da ta kalleta tare da zabga salati tana tafa hannu. "Oh ni jikar mai gishiri, dama ba ki yi sallah ba, duk tashin da na rinƙa miki, kuma haka kike kwana sirara, so kike aljanu su shiga jikinki?" "Haba Hajiya, ta ya ya za ki ce tsirara ba ki ga rigar bacci a jikina ba" Ta ce cikin ɓacin rai tana tura baki. "Dalla gafara can, ina maraban dabbe da faɗa. Wannan yadin ƙyallen tatar kike kira kaya? " "Ma za ki canza kaya ki fito daga yau karatu za ki fara da asuba, kuma minti goma na baki. Ya ƙarashe maganar zai juya ba tare da ya damu da abin da Hajiya Baaba take faɗi ba. Ɗago idanunta ta yi ta watsa mishi."Karatu kuma da asuba bayan na islamiya? Ni fa wallahi.." "Ke shaye-shaye kike?"Ya tambaya cikin tsananin mamakin ganin yadda idanunta suka yi ja. "iInna lillahi! Shaye-shaye kuma? Allah ba bu abin da na ke sha." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka. "A'a Jannatu, biri ya yi kama da mutum. Kalli idanunki kamar an zuba jar bula, ki faɗi gaskiya tun kafin na sa ya canza miki kammanni don ba zan zauna da yar nanaye a gidan ba." Haushin maganar da ta faɗi ya sa ta saki kukan da take ƙoƙarin mayar wa. "Na gaya miki ba na shan komai, energy drink ne fearless, don na rinƙa kallo da daddare saboda bacci ba ya barina kallo. Kuma ko Adal za'a tambaya don shi yake siyo mini." "Wane irin kallo kike yi da har sai kin sha fearless, ke da kike shirin exam and do you know its side effects at this your age kina shan waɗannan abubuwan?" "Me kenan take sha, ko dai kayan mayen ne? Su Jannah an yi kyan ɗan maciji." "A'a ba kayan shaye-shaye ba ne sai dai wani abu take sha don ya hana bacci, kuma yana da matuƙar illa a jiki. Ma za ki ɗauko wayarki na ga irin kallon da kike yi." Ya daka mata tsawa yana faɗin hakan. "A nan dai, kare ta kawai kake yi amma ka fito fili ka gaya mini tana kodimo. Kuma kallon da take yi na wasu mutane ne, da suke faɗin kucauu-kucauu na rantse ko ita ban jin ta san me suke faɗi. Ta yi ta sheƙa dariya tsakar dare ta hama ni sukuni, don ko hira ba ta yi dani sai dai ta barni kamar mayya." Ta ƙarashe maganar tana addu'ar Allah ya sa ya ƙwace wayar. Juyawa ta yi ta shiga ɗauko wayar tana zabga mata harara sai ta ɗauko wayar ta miƙa masa tana zuɓɓura baki. "Korian films ne, kuma ina fahimta don akwai subtitle da.." "Can't you shut that mouth of yours?" Ya daka mata tsawa yana faɗin hakan." Bai karɓi wayar ba ya juya ya fita yana faɗin, " Ki tabbatar kin goge duk wani afilms dake wayarki. Ma za ki zo." "Taɓ! Sannu ubana. Aikin banza kawai to goge ka yi, ai wallahi saina ɗauko ba kuɗi ba kuɗi ke aiki ba. Wayyo Allah har na ji tsoro kar ya ga chatts ɗina da Bud, yau da na shiga uku. Galla mata Hajiya Baaba harara ta yi wacce take tsaye kamar tana son karanta abin da take faɗi a ranta. " To 'yar zuga to babu abin da ya yi mini, na lura gabaki ɗaya kin daina sona." Ta ce cikin ɓacin rai za ta shige ɗakinta. "A kan me zan so wacce ba ta san ciwon kanta ba? Ko ji dake da na ke albarkacin son da nake wa mahaifiyarki ne ya jawo haka, don gani nake kamar ita ne a gabana." Ba tace mata komai ba ta ruga bayi tuna minutes ɗin da ya bata. Wankan aguje ta yi sallar da ina aka tsareta ba za ta iya faɗin abin da ta karanta ba. "Muje na raka ki, ba zan bari ya cutar mini dake ba amana ka bani." Sai ta ji daɗin jin abin da ta ce don haka ba ce mata komai ba suka fice da ga falon.Guri ta nema ta zauna riƙe da jarbi tan ja. "Ina kur'ninki?" Kallon shi ta yi jin abin da ya ce." "Ba ni da shi, bari na ɗauko app ɗin a wayata." Ta ba shi amsa ciki-ciki. Tsananin mamaki ya kamasa ganin tana musulma amma babu kur'ani ko ɗaya a wayarta. "Anty Jannah, ga kur'anina kiyi karatun da shi." Cewar Adal yana miƙa mata. Ƙarɓa ta yi tare da riƙewa batare da ta buɗe ba. "Ke wai ina wasa dake ne? Za ki buɗe inda kike ki karanta." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka. Ni gaskiya, it been long I recited Kur'an. So I can't, just recite it to me kawai." Ta ce cikin kunkunai "Jannah fa ƙasurgumar jahila ce, bana jin tana karatun sallah daidai, don duk lokacin da na takura mata sai ta yi ta motsa bakinta, wai ba ta iya karatu a bayyane ba." " Please! Ni fa gaskiya ki daina kirana da Jahil.." "Rufe mini baki banza kawai! Ƙarya na yi? Ai ni wallahi na ga sakarcin Halimatuu, da ta yi rainon ki kamar na tunkiyoyi, babu abin da kika sani sai fitsara da rashin kunya." Ta buɗe baki za ta yi magana jin abin da ta ce ya daka mata tsawa ta yi shiru sai ruwan hawaye dake tsiyaya. Ta fakaici idanunshi ta zabga mata harara. "Ban ga ana hararata ba sai idanu sun faɗi ƙasa." Ta ce tana jijjiga ƙafafunta ta ci gaba da jan carbinta. Cikin ɓacin rai ta fara karanta suratul Amma da baƙinta da bai gama zaunawa a bakinta ba. Kwashe da dariya 'yan ɗakin suka yi ban da Hajiya Baaba da Ajmal "Inna lillahi! Anty Jannah, da ma ba ki iya karatun akur'ani ba, ƙatuwa da ke? Ko ni na izifina ishirinnda biyar?" "Kai rufe mini baki banza kawai." Ta ce masa tare da kai masa duka. "Wallahi kika ƙara dukansa sai na haɗa ki da gini ai gaskiya y faɗa. Jahilar banza kawai. Babu abin da kika sani sai iyayi da taƙama." Cewar Hajiya Baaba. "Kin dai gani ko Hajiya, kin ga wacce kike karewa har kika tsaya don kar na bige ta?" Ya faɗa cikin takaici da mamaki. "Tashi zan yi ni kam yanzu. Ka koya mata karatun, in ta ƙi ka yi mata dukan mutuwa ka ga tafiyata." Ta fice daga sashin. "Ke kam kin ji haushi da auren mace irin ki gara zama gwauro. Ke Nahlin ki ɗauko mata bagadadi ki rinƙa koya mata. Na ba ta wata biyu ta gama. Duk ranar da ba ta yi ba, just inform me I will just seize her phone. Kuka sosai ta saka harda su share majina ko tari ba ta yi ba ganin wacce take goyon bayanta ta kware mata. Tsawar da ya daka mata ya sa ta yi shiru ta bi Nahlin da taje ɗauko bagadadi don ta koya mata. Wunin ranar babu wanda ta kalla don ɗakinta ta kulle ta yi zamanta. Ko abincin rana ƙinci ta yi, babu abin da ya fi ƙona mata rai irin dariyar da suka yi mata. Ga shi ko da ta dawo haka ta sata a gaba da habaici da waƙe-waƙe. Ta kira wayar dad ya fi sau nawa amma bai ɗaga ba, don haushi ko kallon numbar mom ba ta yi ba, don tana ganin duk ita ta ja mata wannan tozarcin. Duk irin gargaɗin da ya yi mata ba ta ji. Ko da Nahlin ta fara koya mata ganin hankalinta ba shi gare ta share ta kama aikinta, wanda hakan ya yi mata daɗi ta ci gana da kallonta. Washegari da asuba Nanlin ta zo ta tashe ta ko sallah ba ta yi ba suka tafi cewar inta dawo za ta yi. Ko da ta je babu abin da ta iya sai zare ido wanda hakan ya baƙanta ransa. Bulala biyar ya yi mata sannan ya ce," Ma za ki shiga ɗakina ki gyara mini, it is you funishment." "Ban iya ba." Ta ba shi amsa ba tare da shakku ba tana sosa inda ya duke ta. "Allah ya isa mugu azzalimi, in sha Allahu sai an rama mini akan yaranka." Ta faɗa a hankali yadda ba zai ji ba. "Je ki koya mata sannan ta gyara ɗakin da kyau. Kuma wallahi gobe in ba ki iya ba sai na lahira yafi ki jin daɗi." "Ni fa gyaran ne I can't cus I don't know how to do chores." "Ok." Ya bata amsa yana kallonta domin ya gama fahimtar 'yar rainin wayo ce. "If that is the case then you will collect another cane." Ya ce yana ƙoƙarin ɗaga bulalar. Da gudu ta ruga ta ɓoye bayan Nahlin ta ce,"I will don Allah kar ka ƙara dukana." Sai ta bi bayan hanlin da ta riga ta shiga ɗakin domin tare za su yi. Suna shiga ta tsaya a ƙofar ɗakin tana toshe bakinta."I really hate this guy with my whole being. Had I know I will face this I should have not came back to Nigeria. Sam ba shi da imani, I know he has his intentions for threating me, and very soon zan bar gidan nan." "Haba kar kice haka. Shi ɗin ɗan'uwan ki ne, kuma he is doing all for you onw good, you will enjoy it in the meantime. So please let's bare it ok?" "Oh please don't change the topic. I beg you pardon for saying that. Believe me, he has his reasons. Ni wallahi na ƙosa ya yi auren mu huta." Dariya Nahlin ta yi ta fara kakkabe Saman gadon tare da yaye bargon ganin ba ta da ninyar farawa. Zama ta yi tare da ƙara toshe hancinta."Kai this smelling is awfull. Gaskiya ƙazami ne sosai, wari nake ji, wannan matar shi ta bani da ƙazanta Allah. Ji ɗakin is not well organized." Tsananin mamakinta ya sa ta kasa cewa komai sai da ga baya ta ce," Kai anya na taɓa ganin 'yar rainin wayo kamar ki? Ƙamshin tsadaddan turaren na sa kike cewa wari." "Eh ni dai wari yake mini, daga jin ƙamshin outdated ones ya ke amfani da shi." in gyaran muryarsa kamar zai shigo yasa ta miƙe da sauri ta fara taya Nahlin gyaran. Kusan aikin ita ta yi don babu wani abin kirkin da ta yi. "Na gama." Ta ce mishi tare da marairaice fuska ita a dole ta yi aiki ta gaji. "Sai ki fita gobe in kin ga daɓa kar kiyi kayana na nan sai ki wanke, kin ga kuɗina ya huta. Daƙiƙiyar banza kawai." Fita ta yi cilin ɓacin rai tana ƙunƙunai Tan shiga sashinta ta sa kuka." Wallahi na tsani zaman gidan nan, na ƙosa na gama kama hostel, ni gidan nan kowa haushinsa na ke ji." Tsaki Hajiya Baaba ta yi tana faɗjn,"Ni ma na ƙosa ki tafi na huta da ala ƙaƙai da kunna mini waƙoƙin arna. Ke na fahimci iyayenki gajiya suka yi da jarabar ki suka tattaro ki suka kawo mini wahala." Jin abin da ta ce yasa ta ƙara sakin wani kukan. "Allah duk mom ce ta janyo mini wannan musifar ba zan yafe miki ba." "Kyaji da shi, shashashar banza uwar tanki ma ba ki darajata ba ballantana wani. In kin gama kukan shagwaɓar ga abincin ki can da aka gama barbaɗe shi an kawo miki kwaɗayayya kawai. "Oh dai, ni dai ba zan ci wannan jagwalgwalon na ki ba." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar kwanon abinta ta shige ɗakinta. Da ta tasa abincin kasa ci ta yi babu abin da ke mata yawo aka sai dariyar da suke mata da kalmar jahila da daƙiƙiya da suke ce mata sai maimaita kansu suke yi. "Zan ba su mamaki sai na nuna musu ni ba jahila bace, zan dage na koyi karatu sai muga jahili a tsakaninmu, kamar ni da nake ɗaukar distinction a makaranta za su kira ni jahila." Ɗakin Nahlin ta nufa inda ta same ta tana zaune a kan gadonta tana danna waya. Kaanciya ta yi kan gadon har sai da ta gama wayar sannan ta juyo ta kalle ta. "Anty Najhlin please ki koya mini karatu, so na ke cikin wata ɗaya na iya karatu, zan nuna masa ba nahilci ba ne kawai bana son karatun ne." "Ok, ba ki da matsala zan koya miki, kin ga Ummu ta ci gaba koya miki in ta dawo. You will like her she is outgoing and loquacious" "Really." Ta ce tana murmushi wanda ta ɗaga maka kanta tare da miƙewa. Dariya ta yi jin abin da take faɗi,"You really crack me up. Ni ma zan so hakan." Kin ga direba ya tafi ɗauko Ummu-Kursum, kuma na ji Aby yana faɗin kamar makarantarku zai mayar da ita saboda kidnappers sun kai ma makarantar su hari. Kin ga sai ta rinƙa koya miki. Ki shirya an jim in mun yi lunch ki raka ni makaranta zan je screening. "Wow! I can't wait to see me in to tertiary, it will be like.. Cus I wanna chill. I Phone 15 zan rike." "A lallai ba karatun za ki yi ba, kin san ni Jami'a ba baƙuwa bace a gare ni, saboda sai da na yi diploma, yanzu two hundrent level za ni." "Anty Nahlinnnnn!" Suka ji muryar Ummu da ta sheƙo zuwa ɗakin tana kiran sunan cikin ƙaraji. Nahlin tankama hannun Jannah suka fito tana faɗin,"Oyoyo, yar'uwata." Faɗawa jikinta ta yi suna juya cikin tsananin farin ciki." Am so happy to see you Antyna." Ta furta tare da juyawa tana kallon Jannah da ta sagale hannunta tana kallon su cikin sha'awa. "Jannah kin fi kyau a bayyane, gaskiya kina da kyau sosai." "Don Allah?" Ta ce mata tana murmushi. "Wallahi, kuma irin sosai ɗin nan, please let's take pics." Murmushi ta yi ba tace komai ba daidai lokacin da Ummu ta kama hannunta suka shiga ciki bayan sun gama ɗaukar hoton. Ko cikakken minti goma ba ta yi da dawowar Ummu ba suka ɗinke tamkar irin ƙawayen da suka daɗe ba a haɗu ba, saboda Ummu mutum ce mai shegen surutun tsiya da tsokana. Ga ta da son wayewa da hutu da ƙarya, kusan dai halin su ya kusan zama ɗaya. Abin da ya ƙara sa ta saki jiki da ita yadda ta ga shigar ta yi rolling gyalen abayar da ta saka ba kamar Anty Nahlin da kullum take cikin hijabi kamar matar liman ko ƙonannniya ba. "Please sis, punch me your number. Hope you do Whatsapp, Facebook, Twitter, TikTok and Instagram?" "Dariya ta ji jin abin da ta ce,"Including snap chat and telegram." Sai suka yi dariya mai shewa suka tafa. "Wow! Ki ce kema you are so socialized. Please ki ba ni labarin London, ina ta addu'a Allah ya sa Ya Ajmal ya bar Aby ya kaini Ƙasar waje na yi karatu I like going outside Country." "Kar ki damu sai kin gaji." Ta ce mata tana jin daɗin samun 'yar'uwa mai kalar rayuwarta. A tare suka ci abinci suk yi sallah. Suka yi wanka sannan suka wuce sashin Hajiya Baaba a can suka wuni. Ko rakiyar da Jannah za ta yi wa Nahlin tare aka je da Ummu duk da gajiyar da ta kwaso jin Jannah za ta ta dage sai ta bisu. Ba su kwanta ba sai misalin biyu da rabi. Tare suka yi kallo a wayar Jannah, bayan sun gama suka yi karatu sannan suka kwanta. "Ashe kema ƙwararriyace gurin kallon Korian films?Anty Nahlin da na tura mata ta ƙyar ta kalli season one penthouse" Ta tambayeta cikin mamaki. "Eh ina kallo ina zo hutu, kuma suna da daɗi, amma na fi kallon Nigerian film. Ai Anty Nahlin 'yar islamiya ce kuma matar ustazu, ba ki ji ba ta rasa wanda za ta so sai Malam Amir za ta aura ba" Zare ido ta yi cikin tsananin mamaki."Don Allah da gaske!" "Eh, sun daɗe tun kafin ta kammala diploma, har maganar ta shigo gida kuma naji kamar Aby yana cewa bayan na Ya Ajmal, babu jima wa za a yi maganar na ta, yana son ta ɗan yi nisa da boko ne." "Innalillahi" Ta ce tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi."Amma ta sanya ni a kwana. Ranar ya buge ni a gabanta na gama zage shi tatas, har ina faɗin gemunsa ya yi kama da jikin bushiya." Dariya ta kwashe dashi har tana faɗowa saman gado."To what did she say." "You know what? She just smile and she didn't say a word." "Ai ba za ta ce miki komai ba Anty Nahlin akwai kawaici. Aby ya yaba da shi sosai bokin Ya Ajmal ne tare suka yi koyarwa a islamiyarmu. Yanzu lecturer ne A.B.U department of geology." "Tab! Ai ta ba ni mamaki. Sis mai zai hana ki dawo sashin Hajiya Baaba, mu rinƙa kwana zan sa mom ta gyara mana ɗakin sa mana kayan kiɗa." "Sashin Hajiya Baaba, za ta barni? Ni fa ba na wani shiri da ita don ta cika takura." "Ba dolen ta ba, ni kaina ai ban so zama a gurinta ba, amm ta dage. Na yi mamakin yadda akai ba ta zo ta tasa ƙeya ta ba. Mu gwada inta ƙi saina tattaro kayana na dawo nan." "Ok, shikenan, mu gwada mu gani." Ta bata masa tare kwanci sakamakon jin idanunta sun fara zafi. Jannah ta ɗago ido tana kallonta lokacin da take ƙoƙarin kashe wayarta."I like you sis, you are so easy going and approachable." Sai ta yi dariya kawai ta ije wayarta da ta kashe tana faɗin,"I like you sis too, please sleep like a baby." Murmushi suka yi ma junansu suka kwanta domin ko wannensu ya yaba da junansu. Sosai ta ji daɗin zuwan Ummu sai take jin wani farin ciki na zagaye ta. Ta yi amfani da dawowarta ta dage ta koya mata karatu sai ga shi cikin 'yan kwanaki ta fara ba wa masu yi mata dariya mamaki. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 14-15* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Sosai ta ji daɗin zuwan Ummu sai take jin wani farin ciki na zagaye ta. Ta yi amfani da dawowarta ta dage ta koya mata karatu sai ga shi cikin 'yan kwanaki ta fara ba wa masu yi mata dariya mamaki. Jannah ta dage tare da saka ɗamarar koyon karatun. Kullum cikin dare ba ta bacci sai da ta ga taniya haɗa baƙin sosai ya zauna a kanta. Haddar ne tasha matuƙar wahalansa saboda ko ta fara sai ta ji ta gaji, amma da ta jajirce sai ga shi cikin wata biyu ta basu matuƙar mamaki. Washegari da safe, duk tashin da Hajiya Baaba ta yi musu ba su tashi ba, sai misalin bakwai saura minti goma. Jannah sallah ta yi wana tana sallame wa ta ɗauki bagadadi ta fara karatu, sakamakon ba su da karatun asuba saboda ya yi tafiya. Ummu ta yi sallah bayan ta idar ta yi karatun alkur'ani da azkar sannan ta koma ta kwanta don har yanzu gajiya bai sake ta ba, ga shi ba su yi wani baccin kirki ba. Cikin lokaci ƙalilan ta shayar da kowa ruwan mamaki, domin ta nuna musu sa kai ya fi bauta. Sosai ta iya karatun shi kansa Ajmal mamakinta yake yi, wanda ya gane iskanci ne da rashin mayar da hankali ta sanya wa rayuwarta, wanda ganin hakan ya fara mata harda daga baƙara, kuma tana ƙoƙarin kawo masa daidai iyawarta. Dawowar Ummu sai ya ƙara mata jin daɗin zaman gidan. Kusan halayen su ɗaya, sai dai Ummu tana aiki kuma da don ita take yi wa kanta komai, saɓanin Jannah da sai dai ta ci tasha ta kwanta tana kallo ko ta hau ynar gizo. Sun yi matuƙar shaƙuwa tamkar 'yan tagwaye suke. Ummu ta bata shekara ɗaya amma in ka gansu sai ka ɗauka shekarun sun fi haka, don ita tana da jiki, yayin da Jannah ba ta da wani jiki siririya ce sosai. Tun Hajiya Baaba na kauda ido akansu har aka kai mizanin da ta kasa haƙura ganin shaƙuwarsu, don ba ta ƙaunar hakan wanda ya sanya ta fara ƙorafi. Duk lokacin da Jannah ta tafi sashin su za ta bita ta taso ƙeyarta bayan ta yi ƙorafi da zage-zage, amma kuma ba shi zai hana anjima ta koma ba, wanda har ta gaji ta zura musu ido domin daga baya sashinta suka koma da zama gabakiɗaya. Ranar lahadi bayan sun taso hadda suna har suka iso cikin gidan. Kai tsaye sashin su Ummu suka nufa sakamakon yunwar da suka dawo da ita. Tsaki Ummu ta yi tana faɗin,"Kai na san Anty Nahlin ce, da wannan kinibibin tsiyar ta yi mana gudun kurna. Wallahi na tsani abun nan." Taɓe baki ta yi bayan ta buɗe kular."Taɓ, ni fa ban taɓa ci ba, ranar da Anty Nahlin ta yi sai dai na sha tea." Ta mayar da kular cikin ƙyanƙyani. "Let's go to Hajiya's kitchen to see what she cooked. I'm starving to dead." Ta furta tare da jan hannunta suka kama tafiya sashin ta. "Allah ya kyauta! I can't eat that concoction." "Ok, then let's go and cook." Ta faɗa tana rufe ƙofar kicin ɗin. "Allah ya sa ta yarda Hajiya is so abrasived." Dariya Ummu ta yi ba ta ce komai ba suka nufi sashin, wanda kai tsaye kicin Ummu ta wuce yayin da Jannah ta zauna a kan kujera. Harara Ummu ta sakin mata tana faɗin" What this sis, kamata ya yi ki biyo ni kicin ki gyara kayan miya kiyi blending, ko kuma mu jajjaga zai fi ko?" Ta ƙarashe maganar cikin sigar tambaya. "Allah na tuba! Muje dai na taya ki hira, amma ni har yanzu ban gama sanin kalar kicin ɗin nan ba, ballantana na yi girki don ban iya ba." "Wai da gaske kike?" Ta yi mata tambayar cikin mamaki sosai. Jinjina mata kanta ta yi suka nufi kicin ɗin. "Ban ga laifin ki ba sis, ai duk wanda ya samu rana ya yi shanya. Rayuwar hutu daɗi ne da ita. Ke ɗin babbar yarinyace, Allah ya tarfawa garinki nono." Ta ɗauki tukunya ta ɗauraye sannan ta kunna gas tana kallonta."Lokacin da na ji mom na neman minister I was very happy. Allah ya yi miki tagomashi da ya ba ki uwa irin mom." "No, please stop saying that. A kan mom kike cewa na ji daɗin samun ta a matsayin uwa, kin san wace ce ita? Ai ni mamaki na ji da take neman wannnn kujerar matar da ta kasa kula da gidanta za a ba wannan muƙamin! Initially, I was thinking my dad wasn't aware of this and he won't support her, amma kin san ta Mai da shi rakumi da akala." "You don't support you mom in to politics, do you?" Ummu ta ce cikin tsananin mamaki abin da take fadi. "Absolutely, I do not." "A lallai na raina wayonki, kin san kuwa wace ce ita.." "Oh, please. I don't wanna talk about her now, understand? Kawai na ije ta a matsayin bankina, in ina buƙatar kuɗi ta turo mini. That what she is to m.." Jin abin da ta ce ta kuma canza fuska sai ba ta ce komai ba suka ci gaba da ɗor girkin bayan sun gama suka dawo falo suna kallo. "Innalillahi na shiga uku! Dan ubanku gobara kuke son ku haɗa mini, kashe ni kuke son yi ko? Waton na mutu na bar muku duniyar ku ci ta da tsinke."Hajiya Baaba take faɗi tana fito .daga ɗakinta, wanda jin abin da ta ce suka kwasa da gudu zuwa kicin ɗin domin sun mnta sun ɗora girki. "Mun shiga uku! Ya ƙone." Cewar Ummu da ta kashe gas ɗin ta buɗe murfin tukunyar tana kallon haɗaɗɗiyar tliyar da suka dafa ta ji bashshshen kifi sai ƙauri take yi. "Taɓ! Ai wallahi ba zan yi asara ba haka kawai. Ban ci nanin ba nanin ta ci ne. Na rantse iyayen ku za su biya. Ma za Jannatu ɗauko mini wayata a ɗakina na kira uwarki ta siya mini tukunyata, ke kuwa Kursumu ubanki zai biya ni abincina." "Ki kwanatar da hankalinki daɗin abun mu ɗin ba matsiyata bane da sai kin kira iyayenmu kiyi kuɗin tsiya na biya ki." "To ƙaramar mara kunya fitsararra. Ai dama na san ke za ki fara magana. Fita a kicin ɗin tunkafin na yi ball dake, tund ba ubanki ya saya mini gidan ba. Kin ji da kan ki kamar tsandar rake." "Aby da mom uwa ɗaya uba ɗaya suke, don haka nima ina da iko da gidan." "Ok haka kika ce ko? To ba ri na zo kusa dake zan fi gane maganarki, don kamar ba da yaran da na sani kike magana ba." Ta ƙarasa maganar tare da ɗauko muciya ta yi kanta, wanda gain haka ta kwarma ihu ta yi waje. Kan Ummu ta yi da take tsaye tana mamakin tsaurin idanunt do ko Ya Ajmal ba y gaya mata magana ya kwana lafiya. "Fita daga kicin ɗin nan, kema wallahi na ƙara ganinki sai na canza miki kamanni." "Taɓ! Ai in dai Jannah tana sashin nan, sai dai kiyi haƙuri ko ki barta mu koma sashinmu za mu fi sakewa." ta ƙarashe maganar tare da zurawa da gudu, Jannah ta rufa mata baya tana faɗin, "Muje kin ji ni ma ba zan ƙara dawowa ba, na huta da tashina da asuba da take yi kamar me kashin kwance." "Oh Allah na ga ta kaina! Ni kam an haifa mini jikoki sun zamar mini ƙadangarun bakin tulu. Da na yi magana ɗaya sai sun mayar mini da goma." Jarrabawar makarantarsu yake ta matsowa na fita daga sakandiri. Hnakalinsu gabaki ɗaya yana kai ba kamar jannah da ko abinci ba ta iya ci sosai kullum karatu duk ta bi ta rame. Inda suka ɗan samu natsuwa da ana saura kwana goma su fara za a yi bikin Ajmal sai kuma aka ɗaga sakamakon mahaifin Mushiirat da ba shi da lafiya an fita da shi waje. Cikin nasara suka gama zana jarrabawar wanda har sai da ta kwanta ciwo bayan exam ɗin sai hankalinsu ya koma kan bikin Ajmal da za a yi wanda aka ƙara wata biyar. Tun kafin ya matso suke shiri da murna da tsare-tsaren shagalin da za su yi ranar auren. "Na ɗauki nauyin haɗa paty da ƙawayenmu ranar auren don murnar zai bar mana gida muci karenmu babu babbaka. Wayyo Allah har na ga irin rayuwar da zan yi, ga shi lokacin mun shiga higher institution, kai akwai bidiri." Jannah ta ce wa Ummu da take kwance a kan kujerar da Jannah take zaune. "Habawa ke dai bari. Allah dai ya kai dare ga hawara, ko bai ci ba ya yi birgima.Kin san Allah in yaya ya bar gidan nan, akwai kankaro mutunci. Wani irin shiga zan rinƙa yi na mata masu class ina zuwa makaranta." "Ki dai bari kawai! Duk na ƙosa Jamb ɗinmu ya fito. Dole mu hau mota masu kyau, kuɗin mom zai yi kuka." Dariya suka kwashe da shi tare da tafawa sannan suka fice daga falon zuw ɗakinsu. Suna zaune suna kallo Hajiya Baaba ta shigo da kwanon fura a hannunta ta ce, "Ke Jannatu, maza ki kaiwa yayanki Adamuu hurar nan, yau isasshen ya tuna da hurata mai daɗi." "Ni fa Hajiya kin san ban cika son aike ba, haka kawai ga 'yan aiki sai kin wahalar da ni, kuma kin san halin jarabben mutun nan so kike na je ya ce n yi masa wani abu..." "Ta shi ma za kije, sai kin kai mishi banga damar aiken wani ba sai malalaciya kawai, ke Ummu ta ki rakata." Miƙewa ta yi tana zumɓura baki kamar za ta zubar ta fice. "Ke kin san Allah ba zan raka ki ba, yau ikin da muka yi masa daban ne, ka wo wayarki ki same ni a sashinmu."Ta wuce ba tare da ta tsaya ta ni ƙorafin da take mata. Da siririyar sallama ta shiga cikin falon amma ganin ya juya baya yana waya bai ji ta ba sai ta ja ta tsaya tare da maƙala kunninta sosai yadda za ta jiyo shi jin ya rage murya. Cikin salo da jan hankali duk wata 'ya mace yake waya. Dariya ya saki mai sauti yan lumshe idanu, wnda ya ba ta matuƙar mamakin jin yana da irin muryar. Hankalinsa gabaki ɗaya ya tattara akan wayar don har wani takun ƙasaita yake yi a hankali a tsakiyar falon. Cikin wata irin murya ta ji ya ce,"Buɗe bakinki na yi miki kiss, kuma ki rufe ido." Jin hakan ta hangame baki tana mamaki ta zare ido tare da haɗiyar miyau da ƙyar. Wani irin zazzafar kis ya sakin mata har uku sannan ya ce,"Bye, ki kular mini da kanki." Cikin tsananin razana ta saki kwanon furar domin saboda tsabar gulma kayansa ta ji ya ce ta kula da shi. Ƙarar faɗuwar kwanon ya sanya ya juyo da sauri yana kallonta wacce ta zura a guje ganin aika-aikar da ta yi. Sashin su Ummu ta same ta a falo tana waya da Huzaifah. Da sauri ta ja hannunta zuwa ɗakin Nahlin tana faɗin,"Humh zo na shafa miki labari, yau na ji abin da ya girmi kakata Hajiya Baaba. "Mai ya faru sis, give me the gist." "Sai da na gaya wa Anty Nahlin Ya Ajmal kura ne da fatar akuya, fakewa yake da addini yana cin karensa babu babbaka, wi shi a dole uztasu Ahlulu sunnah, amma ta shafawa idanunta toƙa ta ƙi yarda. Ga shi yanzu na gani da idanuna. Kun san me na ji yana faɗi wa budurwarsa?" Anty Nahlin ta kasa magana sai kaɗa kanta take tana mata nuni da shi da yake tsaye a bayanta, amma gulma na cinta ba ta lura ba. Ummu da ba ta ganshi ba ta ce," Do tell me now." Ta faɗa cikin zaƙuwa da son jin gulma. "Kiss guda uku ya yi mata, kum har yana faɗin ta kula mishi da kayanshi. Oh ni Jannah ko wane kaya yake da shi a gurinta oho? Ashe ya Ajmal gogaggen ɗan duniy..." Maganar ta maƙale mata a maƙoshi sakamon Ummu da ta yi mata alamun yana jin ta. Wani irin tsalle ta yi sai ga ta a tsakiyar gado, domin ko kaɗan ba ta taɓa tunanin zai biyo ta ba. Nahlin ta buɗe baki za ta yi magana ya daka mata tsawa,"Rufe mini baki shashashar banza kawai! Kin tsaya kina jin shirmenta." "Yi haƙuri." Ta ce tare da bin bayan shi ta wuce wanda Ummu ta bita a guje domin tsuntsun da ya ja ruwa. A ranta addu'a take Allah ya taimake ta ganin yadda ransa ya ɓace. "Yau zan yi maganinki, ba ke baki da tarbiya ba. A gidan uban wa kika ji na ce ta kular mini da kayana? Saboda kallon finafinai ya ɓata ki." "Am very sorry. Wallahi ba haka na ce ba, please understand me." Mari ya kai mata yana faɗin," I should understand what? Kin ɓata tarbiyarki kina son ki ɓata na ki, sannan ki sanya suna ganin mutuncina su raina ni. Wato dama you been spying on me?" "No, wallahi I don't, I really respect you. It was mistake please forgive me." Marin da ya ƙara kai mata ya sa ta canyara ƙara daidai lokacin da Ammy ta shigo. "Kai Ajmal, so kake ka ƙara janyo wata rigimar? Ma za yarda bulalar nan." Ta faɗa cikin ɓacin rai. What has she done to you?" "I really disappointed, having you as a sister." Ya ce tare da yarda bulalar ya fice ba tare da ya amsa tambayar Ammy ba. "Ba kya jin maganar Jannah, kina ganin kowa a gidan nan, kaffa-kaffa yake kar ya shiga gonarsa amma ke kullum cikin takalarsa, bayan kin san abin da zai je ya dawo." Wuri-wuri ta yi alamun rashin gaskiya sai jan majina take yi. Ammy ta juya za ta fita daidai lokacin da Ummu ta shigo."Sory sis, I was signalling you, amma ba ki gani ba. Dukanki ya yi?" Ture ta ta yi tana harararta." A, a albarka ya shi mini, tare da ba ni kyautar kuɗi. Ai wallahi na san matsayina da inda na aje ki, you left me in, wato ya kashe ni ba ki da asara." Ta faɗa tana harararta. "Am deeply sorry. Kin san halinsa, ya zan yi? Amma ke ɗin tawa ce." "In ban da neman rigima irin na ki, ina ruwanki da wayarsa ba matarsa ba to be ba ce? Kar ki manta it remains 26 days for their weeding." Zuɓɓura baki ta yi ba ta ce komai ba sai ta kama hannu Ummu."Kin ji muje sashin Hajiya Baaba." Shirye-shiryen biki ya kankama Ajmal babu zama duk da bikin gata ake masa amma shi kansa nuna bajinta yake yi. Kmar yadda mom ta yi alƙawari ita ta haɗa lefe na gani na faɗa wanda samun sa sai 'yar gata mai ƙashin arziki. Events kala-kala aka shirya duk da angon yana nuna ustazu ne amma hakan bai hana tsara bikin yadda zai ƙayatar. Amaryar ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta kawo kanta gidanta ganin irin kayan alatun da ka shirya a ɗakin. Duk da iyyen amaryar sun yi bajinta, amma Ajmal sai da ya sanya kayan furnitures a bangarensa masu kyau. A gefe ba a bar su Jannah ba da suke jin kamar an biya musu kujerar makka, ba ma kamar Jannah za ta huta da tashin asuba karatu. Don haka suka gayyaci 'yan makarantarsu da shirya shagali na musammman. Sun ɗinka kaya masu tsada da kyau. Kowa ya yi tunanin mom za ta dawo kafin bikin amma sai dai ga mamakin su, ƙiri-ƙiri ta ƙi zuwa wanda hakan ba ƙaramin haushi ya bawa Hajiya Baaba. Ita ko Jannah ko a tsummar rigarta don ta san abu ne mai wuya tazo sai dai ra'yin kanta. "Anya ba kurciya aka yi wa Halima ba? Lamarin nan akwai ruɗarwa. Tun yaushe take waƙar za ta dawo, amma shiru kake ji malam ya ci shirwa. Ƙila sai na tashi tsaye." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 15-16* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "A'a Hajiya, karki saka kanki ga bibiyan malamai da babu Allah a zuƙakansu. Halima za ta dawo, wani aiki ne ya taso mata. Kuma kin ga dole ta dawo ko dan takarar da ta tsaya. Lokaci ne kawai bai yi ba." Cewar Aby jin abin da ta faɗa. Dinner da aka shirya suke shiri. Sun shirya cikin wani haɗaɗɗen less kalar milk kallo wanda ya karɓi jikinsu matuƙa don anko mom ta yi musu. Ummu ta shigo da turare a hannunta tan fesawa sai kuma ta fara fesawa Jannah, "Kiyi sauri kar mu yi latti, kuma su Huzaifah suna jira." Ɗaga mata kanta ta yi sannan ta ɗauki agogonta ta ɗaura suka fita suna taku cikin yanga da kwarkwasa. Da suka isa ƙofar gida inda Huzaifah yake sai ta tsinci kanta da jin kunyarsa, musamman gainin yadda ya kafe ta da ido. Wow! You look gorgeous and marvelous. Kin zama tamkar wata tarwaɗa." "You are a such Flatter and you are good in it" Cikin jin kunya ta faɗi haka. Gaban motan ya buɗe mata yana faɗin,"No, gaskiya na faɗa." Ya kalli Ummu da ta tsaya tana murmushin sannan ya juya ya kalle ta da dake ƙoƙarin shiga mota ya ce, "Ummu right?" "Haba Huzaifah, nufin ka ba za ka gane ni ba?" Ummu ta amshi tambayar cikin nuna alamun damuwa. "Sorry, na dai tambaya ne kawai, amma kin san hakan na iya faruwa saboda na tabbata ke din ce, kin san hoto ba zahiri bane, musamman da yanzu mata canza halittar su suke in za su yi hoto." "Amm kuma mun sha yin video calls da kai, remember?" Ta faɗa tana kallonsa. "Oh yes haka ne, am sorry." Ya ce tare da haɗa hannayensa. "Kullum ba a barin kunnawana su samu natsuwa sai dai a cika su da labarinka. Yau dai na ganka kuma duk ka cancanci abin da take faɗa a game da kai." Ta shiga bayan motar ta zauna tare da kulle motar sannan ta ci gaba da cewa, " You know what? I have a ton of embarrassing story about Jannah, and it will be perfectly for marital blackmail." "Ke he is my bud, as I said earlier on." Jannah ta karɓe zancen tana faɗin haka da harararta wanda ya sa suka kwashe da dariya. "Oh pardon me, I forgot, amma kin san soyayya ba ta ɓuya idanuwanku za su bamu amsa ko Mufid." Ta ƙarashe tambayar tana kallon Mufid da tun da suka gaisa bai ƙara tankawa. "Exactly, a dai juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe." Dariya ta yi jin abin da ya faɗa. "Da gaske ina son 'yar'uwarki fiye da yadda nake son kaina, amma tunaninta ba shi a kaina, amatsayin aboki kawai ta ɗauke ni. Don Allah ki karkato mini da hankalinta gare ni, na yi miki alƙawarin kula da ita har ƙarshen rayuwa." Ya faɗa daidai lokacin da ya tashi motar ya fara tafiya kamar baya son tuƙi yayin da fuskarsa ta canza kalar tausayi. "Kyaleta ta gama kauce-kauce da zagaye-zageye amma indai mutum ba makaho bane ko ya kalle ta ai ya sam abin da ke ranta. So exercised patient she has fallen in love with you." Dariyar jin daɗin abin da ta ce ya yi, yana kallonta da ta ɗaure fuska ba ta ce komai ba. Suna tafe suna hira har suka isa. Gurin ya cik ya batse babu masaka tsinke. Ango da amarya sun sha gayu da ƙyale-ƙyali, ba kamar amaryar da angon yake jin kamar ya sace ta ya gudu don ta yi kyau sosai. Sai murmushi mai tsada suke sakin ma junansu. Bayan sun zauna Jannah ta kara kuninta a na Ummu, "Ina ta tunanin matar da za ta aure shi da ƙaton ƙirjinsa, ashe ita ma yar lukuta ce, amma gaskiya ba yarinya bace na ganta da jiki." Dariya Ummu ta yi jin abin da ta ce,"Wato ke a jiki ake gane girma ko? Ba yarinya bace, don ta gama degree har da masters aiki fa take yi." "Oh kice guzuma ya aura kuma sun dace, ba ki ga ita ma bagidajiya ce irinsa ji fa wani shiga da ta yi na rashin wayewa on her weeding day sai ta sanya rigar da Ƙaramin hijabin da zai rufe mata duka jiki. Kai Allah ya kai mu nawa auren." Duka ta kai mata."Ban son iskanci, and stop being dramatic you know they are compatible. Kuma Yayan kike kira bagidaje, don kawai yana ahlul sunnah." "Ke dai bari, wallahi rayuwarshi babu wayewa. Kullum cikin jallabiyoyi da wando baya kai mishi ƙafa. Ji fa ko rawar sun kasa sai wani sunne kai suke." "Ba ki da dama, Allah ya sa yaji kina ce msa bagidaje kin san halinsa. Duk wani events da aka yi ba, da yaƙi amincewa wai walima ya wadatar." Tsaki ta yi cikin jin haushe ba ta ce komai ba ta koma ta zauna tana jin bikin babu wani armashi sosai, duba ga yadda take kallon a social media ana cashewa sosai. "Allah ya kaimu nawa zai ga yadda za a yi hosting event differently, it will be a topic on social media." "Allah ya kaimu. Ni ce amara ƙirjin biki. Ganin an fara manna kuɗi suka tashi wanda dama jira suke su yi amfani da wannan damar.Rawa suka fara tiƙa suna musu manni, wanda ganin haka ya sa Huzaifah ya taso ya shiga zuba mata ruwan kuɗi tana tiƙar rawa. Karab! Suka haɗa ido da Ajmal da ya tsaya cikin takaici da mamaki yana kallonsu yayin da baƙinci ya cika shi wai waɗanann ƙanninsa ne. Ganin kallon da yake musu ya sa suka koma gurin zamansu. "Kai Ya Ajmal bai yi ba, yanzu shikenan ya yi mana baƙin cikin tura shagalin bikinsa a social media. Gabaki ɗaya bikin nan babu daɗi. Ji yadda amaryar take motsa jikinta wai a dole rawa take yi." A haka dai aka yi dinner aka tashi sam bata yi musu daɗi ba don haka suka ɗauki ƙudirin party da za su yi sai sun ƙayatar da shi. Washegarin bikin sai shirye-shiryen paty suke yi. Sashin Hajiya Baaba cike yake da mutane haka Ammy don haka suka yanke shawarar su ƙayata gidan harabar gidan gonar Abby. Duk wani hidima sa suka yi a aljihun mom ya fita wanda ta karɓa babu tausasa lafazi. Ganin gidan a cike yake sai suka yanke shawarar yin party ɗinsu a bangaren gidan gonar Aby. Gabaki ɗaya sun ƙure gidan da waƙar Umar m sharrif take tashi. Ba bu yadda Nahlin da Hajiya Baaba ba su yi ba kan su kashe, amma suka ƙi wanda ta yi fushinta ƙyale su. Ajmal da ya shigo da abokansa su gaisa da Aby wanda suka zo masa daga waje. Hayaniyar mutane da kiɗan da suka sanya ya saukar masa da wani irin azababben ciwon kai. "Yauwa Adamuu, gara da ka shigo waɗannan marasa jin maganar sun hana kunnuwana saƙat da kiɗa, don ko da na yi musu magana taƙadiriya Jannatu jawo ni ta yi cikin fage tana juya ni." Tsaki ya yi ba tare da ya ce komai ba jin abin da ta faɗa. Matuƙar kunyar abokanansa suka kama shi. "Albarkar auren nawa kuke son ku kwashe, saboda ga ku sheɗanu ko?!" Ya furta cikin ɓacin rai daidai lokacin da ya kashe kiɗan. Jannah da ba ta lura da shigowarsa ba ta ibo shoki saura kaɗan ta faɗa jikinsa, Allah ya taimake ta ta ja ta tsaya tana mazurai tare da ɓata fuska. "I just give you rest of two minutes, kowa ta ɓace daga nan kafin na yi ball da ku." "Kai wallahi guy ɗin nan bai yi ba, ga shi dai a ido kamar wayayye." Cewar ƙawarsu Maryam tana ƙuta. "You know what? Ku zo kawai muje mu kama waje, ai tun da muna da kuɗinmu bai isa ya hana mu wataya ba, dole na yi murnar aurensa za mu huta da takura." Cewar Jannah. Haka kuwa aka suka kama guri suka sha rawa sai da su ka gaji don kansu sannan suka dawo gida, bayan sun ci sun sha. Biki ya watse bayan an yi tarin shagulgula aka ɗauki amarya zuwa haɗaɗɗen gidanta tare da yin buɗar kai aka bar ta daga ita sai angonta. Tana zaune akan doguwar kujera ta sha matuƙar kyai sai walwali take yayin da ɗakin yake ƙamshi mai daɗin shaƙa. Sallama ya yi ya shigo fuskarsa ɗauke da annuri domin yana jin babu wanda ya kain shi farinciki. Ya shigo shi kaɗai bai nemi rakiyar kowa daga abokanansa ba, domin tun daga get ya karɓi kayan da suka siyo ya nuna musu baya son rakiyar. Tonan sa suka fara yi wanda ya ji ya shanye har suka gama suka ƙyale shi. Da sauri cikin ladabi ta taso ta karɓi ledar bayan ta durƙusa a ƙasa. Wani irin matuƙar farinciki ya kama shi domin yana ɗaya daga cikin abin da ke ƙara masa sonta tsananin biyaryarta. "Barka da shigowa ranka ya daɗe abin alfaharina, barka da wannan rana da ba zamu taɓa manta wa da ita ba." Ta faɗa cikin murya mai sanyi da son jan hankalinsa. Ajiyar zuciya ya yi mai ƙarfi har tana jin hushin numfashinsa a fuskarta duk da ta mayar da gyalenta ta rufe fuskarta. "Ina matuƙar sonki haskena, ina fatan mu yi rayuwarmu cikin farinciki." "In sha Allahu, za ka same ni mai tsananin biyayya tamkar Sarki da bayinsa. Domin zan yi koyi da matan Annabi Muhammad (S.A.W.). Suka ƙarashe tare sannan suka shafa. Miƙewa ya yi yana faɗin,"Bari na shiga kicin na ɗauko plate na ciyar da sahibata." "Kaicona!" Ta faɗi tare da riƙe hannunsa da sauri. "Ni kuwa mene ne amfanin numfashina matuƙar zan bar zauji da aiki? Kenan babu amfanin hannuwana." Tsananin mamakin abin da ta furta ya kama shi duk da ya san cewa ta iya kalamai na sace zuciya, amma sai ya ji ya ƙara darajata da kimanta ta, domin shi mutum ne mai matuƙar son a nuna mishi girma, don haka ya kama hannunta duka ya riƙe yana faɗin, "Kar ki damu kar kiji komai, ki yi mini alfarmar yau na yi hidima da rayuwarki sai ki ɗora da ga gobe." "To shikenan zauji, yadda kake so haka za a yi sam babu jayayya a tsakaninmu." Ta ce tare da komawa ta zauna zuciyarta fal tamkar gonar addu'a ganin yau Allah y mallaka musu junansu. Bayan ya ɗauko ya juye musu banƙararrun kaji da drinks masu sanyi. Kaɗan suka ci sannan suka je bayi suka yi brush tare da canza kaya. A wannan daren Ajmal ya nuna mata irin sonta da yake yi da dakon jiran ranar da ya yi, domin ya shayar da ita ƙauna mai tsuma zuciya ya sa ka manta komai, wanda ya sa ta farinciki ta san ta wuce zarra. Sosai take ganin wautan 'yan matan da suke faɗin ba sa son auren ustazu domin auren riba biyu ne. Ga soyayya kuma ga sa mace kan tafarkin tsira. Washe gari da safe bayan sun tashi sun yi sallah duk yadda ya so Mushirat ta ƙi barin sa ya kunna wuta a ɗakin sabod wani irin kunyarsa da take ji. Haka dai ya daure ya ja su sallah bayan sun idar sun yi azkar shine kawai ya yi karatun ƙur'ani, amma ita komawa ta yi ta kwanta sakamakon zazzaɓi da ya rufe ta. Bayan ya idar ya yaye bargon da ta lulluɓa da shi yana kallon fuskarta da ta yi saurin rufewa da zanin gado. Dariya ya tare da ƙara janye zanin gado."To kuma mene ne abin ɓoyewa kamar wacce ta yi laifi? Ai yanzu mun zama ɗaya babu kunyar wannan a tsakanimu." Ƙara ɓoye fuskarta ta yi tana dariya ciki-ciki ta ce, "Please ya Sheshk ka bari don Allah." Sakin zanin ya yi tare da ƙarasa wa kan gadon ya haɗata da jikinsa ya rungume yana dariya cikin jin daɗi. "Ina alfahari dake matar kirki Allah ya bamu tsawoncin rayuwa da zuriya ɗayyiba." Ba ta amsa ba saboda da salon tsokana ya yi maganar. "Au kin ganni ko? Abinci na haɗa miki a maimakon na kira ki kici na tsaya ina tsokananki." "Abinci ya Sheshk?" Ta tambaya cikin tsigar mamaki sai kuma ta ɗora da cewa bayan ya amsa mata da gira. "Ai da ka bari na ɗan samu tsauƙi na yi tun da na sha magani saboda bana son ka wahala." "Ai ko da bani da tausayi matar kirki. Kar ki damu watarana lafiyarki lau ma zan hutar dake in yi miki abinci ko na taya ki, domin koyi da rayuwar Annabi zan yi." "Tabbas duk macen da ta samu namiji mai addini da aiki da shi ta dace sosai. Uwa uba ga kyau da hankali har ma da natsuwa." Ta ce tana ƙoƙarin miƙewa. Fuska ya ɓata yana faɗin,"Mene ne haka ina za ki?" "Zan tashi muje dining." "Haba sai kace ba ni da tausayi? Bari ki ga ɗaukarki zan yi don yau babu ke babu tafiya. Ko kin manta daren jiya ai kin cancanci a ɗauke ki." Matsawa ta yi cikin kin kunya tana dariyar abin da ya faɗa." Don Allah karka ɗauke ni zan iya tafiya ka ji." Ta ce ganin ya nufo ta amma bai kula ba y sungume ta ba tare da ya ji nauyinta ba har sai da ya kai ta daining ya ije yana ɗan nishi. Dariya suka kwashe tare ya manna mata kis tare da buɗe soyyayyen ƙwai da tea da ya haɗa sai ƙamshi yake ga bread sai kajinsu da ya yi warming. "Laa! Ashe Zaujina ya iya girki ji wani suyan ƙwai yadda ya yi kyau?" Ta faɗa cikin sigar mamaki da zuba masa idanu. "Au ba ki sani ba? Ai Ammy ba ruwanta da namiji ko mace gabakiɗaya yaranta tana koya musu girki I will give you suprised anjima ina yi mana jallop na rise." "Really?" Ta tambaye shi tare da buɗe baki a hankali cikin jin kunya ganin ya gutsiri ƙwai ya nufo ta da shi wanda ya saka mata yana ɗaga mata kansa.Dariya suka kwashe da shi ya manna mata kis. Amarcinsu suke dirza cikin so da ƙauna domin kunyar da amarya ta nuna duka bai wuce kwana biyu ba, ta fito masa da kalar zahirinta wanda dama abin da yake ƙauna kenan shi ya sa bai kai soyayyar ga ƙwaila ba. Yana son macen da za ta kula da shi ta mai da shi tamkar ƙwai ta nuna masa bajintar ta ta ko wane fanni kuma tsaƙar shi ta yanke a matsaƙa domin ya samu Mushirat ta cika ko wane fanni. Ta fanni gayu da tsafta ba a magana uwa uba tunbinsa sannan fannin auratayya sai ya ce ita kaɗai ta ishe shi. Jannah kuwa hankalinta ya kwanta sosai ganin ta yi kwana biyu babu wanda ya takurawa rayuwarta. In ta kwanta bacci sai Hajiya Baaba ta yi da gaske take tashinta. A lokacin da Nahlin ta sanar da su ya ba ta umurnin ta rinƙa koya musu. Wani banzan kallo suka yi mata ba tare da sun furta kalami ba, sai Jannah da ta turo baki, "Taɓ, amma wasa yake yi ko? Don ni da karatu sai na islamiya, ai yanzu ni ba jahila ba ce." Bayan auren da sati biyu Nahlin ta sanar da su za su fara karatun asuba. Da asuba bagan ta yi sallah ta biya wa sauran yaran gidan amma babu ƙeyarsu, don babu tashin duniyar da Hajiya Baaba ba ta yi musu ba suƙa tashi, don tunda suka yi sallar asuba suka koma, amaimakon su tafi karatu. A ƙalla sai Nahlin ta yi kwana uku tana fama da su, ganin sun fi ƙarfinta ya sa ta sanar da shi, wanda washegari da asuba bayan ya yi salla a masallaci ya wuto gidan. Hajiya Baaba na zaune a falo da carbi a hannunta ya yi sallama ta buɗe masa ƙofa tana faɗin, "Yauwa gara da ka shigo, waɗannan yaran sam ba na tunanin suna sallah cikakkiya. Su hana kansu bacci da daddare sai safiya ta yi suce lokacin za su yi bacci, ai dare shine mahutar bawa. Ƙofar ta tura masa ya shiga tana faɗin,"Ita kanta Ummu da nake ganin ta fi ta hankali, ashe kura ce da fatar akuya. Gabaki ɗaya ta ɗauki ɗabi'unta ta sanya wa kanta." Kai tsaye bayi ya wuce tare da ibo ruwa mai sanyin gaske ya watsa musu, Wanda ya sa ta mike a firgice tare da sakin ajiyar zuciya mai karfi. "Uban wa ya zuba mini ru..?" Maganar ta maƙalewa mata a maƙoshi lokacin da suka yi ido biyu da shi, wanda ya sanya ta tashi da sauri tana zare ido. "Na shiga uku! Na mutu, wallahi na ɗauka Anty Nahlin ce ta turo Adal ya tashe mu, don na san shi ne kawai zai iya watsa mana ruwa. Don Allah ka yi haƙuri." Ta furta cikin rawar murya tana shirin kuka. "Rufe mini baki ja'ira, kin dai ɗauka ni ce marainiyar wayonki." Bulala ya zuga mata wanda yasa ta canyar ƙara tare da miƙewa da sauri tana sosa bayanta va tare da ta damu da kayan da ke jikinta ba. Ummu kuwa har ta fara kuka don ta san yau sai buzunta. Ganin kayan da yake jikinta ya sa ya saki bulalar yana faɗin,"Ma za ku shirya ku same ni a falo, marasa jin magana kawai." Ya fice cikin ɓacin rai. Hajiya Baaba ta bi shi tana ƙara zuga shi, don ita ba haka ta so ba. "Wai yau Allah ya taimake mu kayan bacci sun yi ceto." Cewar Ummu da ta miƙe ta nufi bayi. Da sauri ta sanya key a ɗakin ta dawo ta zauna,"Wannan jarabben ba zai barmu mu huta ba duk da yabar gidan." "Au zama kika yi kin manta yana jiranmu ko?" Da sauri ta miƙe jin abin da ta ce. Cikin ikon Allah results ɗinsu ya fito kum duk sun cinye. Baƙaramin murna Aby ya yi ba ganin sun fito da sakamako mai kyau. Washegari da safe suna Hajiya Babaa ta fito daga kicin tana faɗin,"Ani ma zaku raka ni gidan Adamuu, amaryarsa ta zo har sau biyu ban je ba. "Ni dai ba zani ba, ku dai je ke da ita." "Iko wallahi ba ki isa sai kin je, don haka ku shirya zamu je." Kan dole ta shirya ba don tana so ba. Sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu. "Hajiya bari na karɓo key gurin Musa direba na tuƙa motar." Ta faɗa cikin tsokana. "Ke dakata, tsaya na ce ko!" Ta furata cikin ƙaraji tare da ɗorawa,"Ce miki akai na gaji da duniyar, ko mutuwa nake son na yi? Don haka ki bari na mutu maza su kaini ba mata ba. Ni da nake son ganin har jikokinki." Dariya suka kwashe da shi duka ganin yadda ta firgice. "Su Hajiya akwai dogon buri na kusa da ƙasa ana hangen gaba." Uban tsaki ta yi ba ta ce komai ba ta shiga motar tare da kamewa a gidan gaba. "Wow! gaskiya gidan Ya Ajmal ya tsaru. Ina mishi kallon ɗan ƙauye ashe ya san me yake yi. A rayuwarsa gidansa ne kawai ya burge ni." Ta furta tana kallon gidan cikin mamaki d sha'awa. "A gida kam ya yi sai dai fatan rai ya mora. Adamuu ya yi ƙoƙari sosai, Allah ya yi masa albarka. Da ina shiri da maigidan nan kwana nan wuni." "Taɓ!" Ummu ta ce a ranta domin za ta iya rantse yau ce ranar da ta ji ta sa mishi albarka. Jannah da Ummu suka ciro wayarsu ana ɗaukar hoto da bidiyo za a yi posting, har da yi wa Hajiya Baaba bidiyo da take ta kare fuskarta tana zaginsu wai ta zo kwaɗayi. "Gafara masu gida." Hajiya Baaba ta ce da ƙarfi. Dariya suka kwashe mata da shi."Hajiya wa zai ji maganarki a irin wanann gidan." Hannu ta kai ta danna ring bell wanda ya fargar da Mushiirat da ke tsaye da kaskon wuta a hannunta tana turare falon da shi. Ta ije kaskon tare da nufar ƙofar tana takun yanga ta buɗe. Ganin Hajiya Baaba ce ya sa ta faɗaɗa fara'arta "Barka da zuwa Hajiya ku shigo." Ta ce tana kallon su Jannah. Ba su yi aune ba sai ji suka yi ta saki dariya ƙasa-ƙasa. Da sauri Mushiirat ta kalle ta sai dai ba ta ce komai ba ta rage fara'arta ta basu hanya suka shiga. Jannah ta ci gaba da dariyarta ƙasa-ƙasa Ummu na ta zungurar ta da ƙafa amma ta ƙi, duk da cewar tana yi kamar ba da ita take ba, amma tasha jinin jininta domin ta ɗaure fuskarta. "Don Allah kalli wani shiga da ta yi wai ita a dole amarya, ta yi wani cukus da it ko kyau. Haba ai ƙananan kaya ba su dace da ita ba. Wai 'yar lukuta kenan, dama na gaya miki ƙatuwa ce ki kalli ydda ta ƙara ƙiba. Allah matar Ya Ajmal in ta yi haihuwa ɗaya ba za ta ganu ba." "Baki da kirki sis wannan ai cin fuska ne a gabanta in ta ji ki fa. Please ki bari." Ta furta daidai lokacin da Mushiirat ta shiga kicin don ta kawo musu ruwa. "Ki barta 'yar banzan yarinya mai shegen ɗaukar magana, kin san halin maigidan ubanki zai ci. Muje gida saina farfasa miki baki, ai gara ita da kike kamar muciya." "Ni fa ki daina zagin ubana dama dai uwar kika zaga ko a gyalena, amma dad bai yi miki komai ba." Har ta buɗe baki za ta yi magana sai ta yi shiru ganin Mushiirat ta fito daga kicin ɗauke da ƙaton tire da aka cika shi da abin motsa baki. "Bismillah ban san za ku zo ba, yanzu zan ɗora muku abinci, bari na tashe shi yana bacci." "Sannu ɗiyar albarka mun gode." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 16-17* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Murmushi ta yi idanunta na kan Jannah da sai zagaye falon take tana ɗaukar hoto da bidiyo, sai kuma ta miƙe. "Bari na je na taso Sadauki bacci yake yi." Ta nufi sashinsa ba tare da ta ji mai za su faɗi ba. Dariya ta ƙara kwashewa da shi sai kuma ta gimtse sakamakon wata uwar harara da Hajiya ta sakin mata. "Aifa Sadauki inda babu sadaukan ba ina ruwan farakwas." "Ke ko wallahi watarana bakin ki zai kai ki ga halaka ba kya ji ko?" "Na nawa Hajiya." Cewar Ummu. Harara ta zabga mata sai ta ɗauki filet ta zuba ferfesun kayan ciki."Umh, bari muci girki matar Ya Ajmal ɗan iyayi, Allah ya sa ta iya girkin." "Oho, ko bai yi daɗi ba tafi wata da ko gas ba ta iya kunnawa ba." Hajiya ta amshe maganar. Ba ta ce komai ba ta ibi ferfesun ta kai bakinta a wulaƙance sai kuma ta ƙara kai wa."Wallahi ya yi daɗi sosai." Ba ta saurari hajiya dake mata gori ba ta shiga aikawa cikinta tana lumshe ido. Ya fito cikin farar jallabiya fara tas har ɗaukar ido take."Ah yau su Hajjaju ce a gidan?" Ya tambaya cikin raha da tsokana. "Eh, na gaji da fushi da na yi na zo. Kamata ya yi kaje har gida ka ɗauko ni, na yi ko wata ne, amma da yake ba ka gayyata ba ka yi hakan ba." Kauda zancen ya yi bayan ya amsa gaisuwar su Jannah yana faɗin,"Allah ya huci zuciyar kakata, daga yanzu sai kin gaji da zuwa." "Rufa mini asiri matarka da bata da sakin jiki kamar ba ta murna da zuwana har na kwana?" Da sauri suka kalli juna shi da ita wanda jin abin da tace ta ƙara ɗaure fuska, kuma dariyar da Jannah ta yi mata ne ya sanya hakan don ta fahimci 'yar rainin wayo ce. "Kar ki yi mata mummunar fahimta har da rashin sabo amma ba ta da matsala." "Ba wani nan Adamuu, kai ɗin ma ba wani kirki kake da shi ba, ina ga ka sanar mata da halina ne, ko da tazo gida gaishe ni ta yi ta fice, can sashin uwarka da take da iko da kai." "Duk ba haka bane da kaina zan ɗauko ki sai kin gaji ki koma." "Allah dai ya kaimu lokacin Jannah za ta yi aure, mahaifinku ku sai ya yi kewata can zan tare, kasan da yake ita sangartacciyace babu fus ba as dole ni zan rinka girki wa mijinta da rainon yaran." "Wallahi ba na gayy.." Ta furta da sauri tuna Ajmal na wurin ya sa ta yi shiru tana zare ido. "To rasa kunya ɓeran tanka kiyi magana yanzu in ban naushi bakinki sai na miki giɓi ba, ƙarya na faɗa."Ba ta ce komai ba saboda yana gurin. "Allah ya kyauta! Aiko babu mace anan, ke Ummu ki rinƙa faɗa mata gaskiya, kuma saboda fitsara yarinyar nan saurayi ne da ita." Gwalalo ido ta yi." Ni wallahi ba ni da saurayi." "Ok, ƙarya na yi miki kenan, ranar bikina wane saurayi ne ya rinƙa miki mannin kuɗi?" Ta yi shiru ta kasa cewa komai sai zare ido. Ganin haka ya juya tambayar ga Ummu da ta yi duru-duru. "Huzaifah ne kuma ba soyayya muke yi ba, abokina ne."Ta fada a tsorace. Hannu ta shiga tafawa tana salati."Ni kam yaran nan suna shayar dani ruwan mamaki, yanzu ke Jannatu har saurayi kike da shi?" "Na ce miki ba saurayina bane, shi ɗin a.." "Ke dallah can rufe mini baki! Ana wani abokantaka ne tsakanin mace da namiji." Baki ta tura ba ta ce komai ba don ba ta ga amfanin maganar ba. Miƙewa ya yi bayan ya gallah musu harara."Wallahi ku natsu ku kiyaye ni, kuna ƙanana babu macen da za ta rinƙa kula samari don duk wanda ya ɗauko carry over a makaranta sai na zane masa jiki.Hajiya, bari na shiga wanka zan fita." Ya ce yana tafiya daidai lokacin da ta miƙe tana wani yauƙi tabi bayansa. "Ki koma gurin su. Na gaya miki matuƙar kika ga ƙannina ki daina mini wani salo da kwarkwasa, saboda ni mutum ne mara son raini. Rayuwar aurenmu ya zama sirri a tsakaninmu. Yanzu kayan da kika saka ya dace ki fita da su? Na yi miki maganar ki saka hijabi sai kika biyo ni haka. Ki sani matuƙar za ki saɓa umurnina, ki zama mara biyayya ba zan lamunta ba." Fuska ta ɓata sosai kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce,"Ka yi haƙuri." Ta ɗauki hijabin ta saka. "Amma bab, gaskiya ya kamata mu zauna muyi magana. Ina buƙatar mai aiki wacce za ta rinƙa taya ni aikin gida. Da kuɗina zan biyata. Gidan nan ya yi mini girk.." "Look! Mushiirat, hakan ba zai yiwu ba daga ni sai ke a gidan nan, sai kin ɗauki mai aiki. Ina son sakewa a gidana ba in zan fito ba na rinƙa tunanin wata za ta ganni." Ya yi shiru ko za ta ce wani abu, amma sai bata ce komai ba don haka ya ɗora da cewa, "Tarbiyarki da kamun kanki da son addininki ya sa na aure ki, don hak kici gaba da kula dasu domin kar zubewarsu su janyo miki matsala a gareni." Ya shige bayi ba tare da ya ƙara cewa komai ba. Tsayawa ta yi jim kamar mai nazari sai kuma ta harari ƙofar bayin ta juya ta fita. Bayan ya yi wanka ya shirya zai fita sagale da jakarsa. A lokacin ta gama girkin suna zaune suna ci. Jannah sai surutu take tana zuba santi domin ita kanta ta sara mata. "Hajiya Baaba, zan wuce ofis sai na shigo gidan." "Allah ya kai ka lafiya." Ta ce tana kai loma. Ba su wani jima ba suka miƙe za su tafi domin Mushiirat kicin ta shige tana ta ayyukanta, wanda Hajiya Baaba ta ji haushin hakan ta yi mata sallama suka miƙe za su tafi. Ɗaki ta shiga bayan ta yi musu umurni da su jira ta. Leda biyu ta fito da shi mai ɗauke da turare da sabulai manya ta miƙa wa Hajiya Baaba. Ɗayan kuma mai ɗauke da kayan shafa da turare ta ba su Jannah suka yi mata sallama suka tafi. Su Jannah an fara zuwa makaranta a Jami'ar Ahmadu Bello (A.B.U.). Wanka suke yi iya wanka ga shi sun samu ɗaurin gindi gurin mom, don sai da ta sai wa kowace motar ta da tsadaddiyar waya Iphone 15.Tamkar 'yan biyu haka suke shigarsu, kayansu iri ɗaya komai nasu. Jannah jin kanta take ta zama babba domin yadda take nunawa ya girmi jikinta, duk da cewar ba ta da ƙiba Ummu na da jiki amma ba can ba. Maƙudan kuɗi take kashe ma jikinta tana siyen mayuka na gyaran jiki da sabulai masu kyau. Ba fara ba ce, amma duk wanda ya kalli kalle ta sai ya ƙara yadda take haske da sheƙi da ɗaukar ido. In kansu suke a wata sabuwar rayuwa kuma girma ya zo musu. Sun ɗauki girman kai da jiji da ɗagawa sun ɗorawa kansu. Ba kamar Jannah da a class ɗinsu indai ba ta ga akwai alamun ƙumbar susa ba bata kula ka. A ɗan zamansu kowa ya san ita 'yar wace ce, saboda ji da kanta da taƙama da an yi magana sai ta fara faɗin kasan ni ko yar waye. Sabod girman kanta da nuna bata son hurɗa da marasa class sai ba ta cika ƙawaye ba. Da ga Zainab Zeey, wacce take 'yar Kaduna kuma mahaifinta yana da muƙami a gwamnati, sai Shamsiya suna kiranta da Sham, daga Kano mahaifinta ɗan Kasuwane, sai kuma Aisha ita kuma daga Kebbi take, amma ba ta cika shige musu ba, domin kamar ba su da shi kamar su. Duk jan kunne da Nahlin ta yi musu kan babu ruwansu da kowa karatu ya kai su. Da fari sun ji amma da ga ƙarshe ko sati biyu ba ayi ba aka san su a ajin saboda shegen surutu da girmn kai da taƙama. Ko shigowa za su yi cikin ajin makullin mota riƙe a hannu ana karkaɗawa. Lokaci guda suka yi suna harda yin abokai maza guda uku. Musa wanda suke kiransa da Scietics da Ahmad sai Sulaiman. Duk rashin jin su sai dai ba sa wasa da karatu don suna cikin masu ƙoƙarin ajin. Ranar Talata Ajmal ya kira Ammy ya sanar mata da ta tura Nahlin gidansa Mushiiirat ba ta da lafiya, sai aka yi rashin sa'a Nahlin tana da lecture harda test, don haka ta tura Ummu bayan ta ja musu kunne sosai. "Kin san ni sai dai na yi miki rakiya don ban yi wa kaina aiki ba ballantana wata."Ta ƙarasa maganar tana yafa siririn mayafinta. "Eh, sis tafiyar ce bana son na yi mi kaɗai, amma don Allah babu ruwanki da ita." Ta faɗa cikin marairaice fuska. Ba ta yi magana ba suka fice. Jannah ita take jan motar, suna tafe suna hira har suka isa. "Matar nan 'yar rainin wayo ce, kalle ta fa yadda ta ci uban kwallliya sai danna waya take wai ba ta da lafiya." Cewar Jannah da suka shiga kicin ta ɗane saman drowers na kicin ɗin. "Ƙila jinyar ba sosai bane." Ta bata amsa a gajarce tare da sakale gyalenta a saman ƙofar ta fara tattara wanke-wanken dake kicin ɗin. Ummu ta yi nisa da aiki Mushiirat ta shigo zata ɗauki ruwa. Ganinta a zaune sai kaɗa ƙafa take tana danna waya da drink a hannunta tana kurɓa wanda ta ɗauka a frij sai zuba surutu ya sa ta yi mata kallon uku sauran kwata. "Ke kuma fa da kike zaune tana aiki?" Ta yi tambayar cikin gadara. "Ba komai Anty Mushiirat na kusa gamawa ni na ce ta barshi, girki zan ɗaura." Cewar Ummu cikin sauri gabanta na faɗuwa. "Ok, sannu da aiki. Amma in ba aiki za ta yi ba ban ga amfanin zuwanta ba, don banga uban da ya sa ta zo ba." "Ɗan dakata daga nan! Why are you insulting my father, for what reason? Kuma kin ga na yi kama da 'yar aiki ne da zan zo gidanki na yi miki aiki? 'Yar uwata na rako kuma ni da gidan ɗan'uwana ba zan zo ba sai dab dalili? Ba ki san wace ce uwata ba?" Saukar mari suka ji tas! A fuskar Jannah wanda ta ji matuƙar shigar shi har sai da ta ji ba ta ganin komai na 'yan daƙiƙu. "Na lura baki da kunya zai saita miki tunaninki. Sai me don uwarki za ta zama minister, ni iyayena an gaya miki kwasan kashi suke yi?" "Kika mare ni?" Ta furta cikin tsananinn mamaki tana jinjina kanta. "Na mare ki ko za ki rama ne?" Ta bata masa cikin gadara. "Anty Mushiirat, please stop, act matual. Don Allah karki biye mata." Ta faɗa tana riƙe ta tare da kallon Jannah da take cika tana kubbura. "Ki bari sis, kin san Ya zai ɗauki hukunci mai za fi kar kiyi mata rashin kunya." "Mai zai hana ba sai kin tambaye ni ba, domin bana bin bashi."Ta bawa Mushiirat amsa sannan ta ɗaga hannunta iya ƙarfinta ta kwasa mata mari, ba tare da ta damu da maganar da Ummu take mata ba. Tas ta ji ta saukar mata da nata gigitacccen marin har saida ta ji kanta ya sara. "Ni kika mara?" Ta tambayeta cikin tsananin mamaki. "Ok, a tunaninki kin mari banza kenan?" "Yau zan sauke miki fitsarar da ke damunki don sai na canza miki kamanni." Kamata ta yi ta shaƙe tana kai mata duka ta ko ina. "Wayyo Allah na shig uku! Don Allah ku daina Anty Mushiirat, kar ki yi kisa." Ummu ta faɗa cikin muryar kuka. Kasancewar ƙarfi ba ɗaya ba sai ta ci ƙarfinta. Sosai ta ji ta takura da shaƙar da ta yi mata. Duk ƙoƙarinta na son ta ƙwace amma ya faskara, ganin tana shirin kaita barzahu kawai ta kai hannu ta ɗauki cokali mai yatsu ta caka mata a goshi iya ƙarfinta wanda ya sa ta sake ta da sauri tare da ƙwala razannane ƙara. "Wayyo na shiga uku! Ummu kira mini Bab, wallahi yarinyar nan 'yar daba ce." Ta faɗa cikin ihu. Ganin aika-aikar da ta yi sai jikinta ya ɗauki rawa, domin ita kanta tana tsoron jini. Hanyar fita ta nufa amma sai riƙe ta mau." Ai yau sai na ga uban da ya tsaya miki." Sosai Ummu ta sa kuka tare da ɗora hannu aka don duk yadda take ganin lamarin ya zarce tunaninta. Waje ta ruga don ta kira maigadi sai kuma daidai lokacin motar Ajmal ta sawo kai. Da gudu ta nufe shi tana kuka da kiran sunasu don ta rasa yadda za ta yi masa bayani ya fahimta. "Me ke ya samu Mushiirat ɗin kuma me Jannah ta aikata." Ganin ta kasa mishi bayani sai kuka take ya sanya ya ruga zuwa cikin gidan domin ya ji wani ƙara da ta ƙwala jin motarsa. "Innalilahi! Mai ya same ki? Kanki jini yake zuba." "Wayyo bab, ashe gidanku da 'yar daba ba ka gaya mini ba, ka cuce ni ga shi yanzu ta illata ni." Sai kawai ta faɗi luuu ta suma. Tsananin tashin hankali ya kamasa ya ruɗe iya ruɗewa ya kalle ta da ita kanta ta yi nadamar aikatawa. Ya nufeta yana kiran sunanta tare da girgizata amma ba bu numfashi sai ya ruɗe matuƙar gaske. Da gudu ya cicciɓeta zuwa mota kafin ta yi wani yunƙurin guduwa ya sanya key ya kulleta tare da yi wa ummu umurnin ta shiga mota. Sai ta yi duru-duru tana kallon ƙofar falon da ya rufe ta kamar ba ta son zuwa. Tausayinta ya kamata sai ta ƙara sakin kuka tana tunanin halin da za ta kasance. Wata uwar tsawa da ya daka mata ya sanya ta shiga motar babu shiri. Ganin ya kulle ta sai hankalinta ya yi matuƙar tashi sosai. Wayarta ta ɗauko ta kira dad yana ɗauka ta saka masa kuka tare da zayyana masa abin da ya faru. Hankalinsa ya tashi sosai jin abin da ta aikata. "Hana Jannah, ya za ki je har gidan mata kiyi mata haka? Wannan saɓa doka ce." Kuka ta saka tana faɗin,"Na rasa yadda zan yi ne dad kashe ni ta so ta yi, sam ba ta da imani." "Ok, ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru. Matsalar Abby kin san yana Chaina shi da mom." Shiru ta yi ba ta ce komai ba ganin haka ya datse wayar hankalinsa a tashe. "Wayyo Allahna! Bab, ka yi mana tsakani da yarinyar nan. Tun ranar da ta zo gidana na ga tana mini kallon banza." Ta ƙarashe maganar tana sakin ƙara don harda ƙara zuzuta lamarin take yi. "Kar ki damu za ki ga abin da zan yi mata. Na rantse sai na canza mata kamanni ki jira ni ina zuwa. Ke Ummu tashi na kaiki gida." Miƙewa ta yi cikin rashin dabara. Yana shiga gida ya buɗe falon ya kama dukanta iya ƙarfinsa har sai da ya gaji don kansa ba tare da ya ji tausayinta ba. Tun tana kuka har sai da ta kasa. Can ɓangarensa ya kai ta tare da kaita library ɗinsa ya kullu yadda za ta yi ihu babu wanda zai ji ta. Kayan kwana biyu ya ɗauka ya fice daga gidan. Daga asibiti hotel ya kama musu akan na kwana biyu bayan ya kashe wayarsa. Tsananin tashin hankali ya kama Hajiya Baaba jin abin da ya faru. "Wallahi kin ji na gaya miki ya illata mini jika hukuma za ta raba mu, don da biyu kika tura su gidan." Ranta ya ɓace sosai musamman da ta kira wayarsa a kashe sai ruwan bala'i take yi ta ƙi barin kowa ya huta, don kujera ta ɗauko ta zauna a harabar gidan tana masifa sai kuma tasa kuka. "Allah ya isa tsakanina da kai Adamuu! Akan bare za ka nemi kashe yar uwarka? Wallahi ina yi ido biyu da kai hukuma za ta raba mu." Ta furta cikin kuka ganin har zuwa lokacin ba ta dawo ba ga shi dare ya yi. Sallah ma cikin rashin hayyaci ta yi shi. Kuma ta rantse duk wanda ya yi girki a gidan sai ta hukunta shi, yadda Janaah za ta kwana ba ta ci ba haka kowa zai kwana, wanda babu yadda za su yi sai dai suka sha tea a ɓoye. Ta yi kuka ta yi bala'i ta yi matsifa tun tana kiran wayarsa har sai da caji ya ƙare ta sanya a aji. Ammy ita kanta tasha kuka ta ci alwashin matuƙar ta ganshi sai ta hukunta shi, saboda ya cutar da ita. Tsananin tashin hankali ya ƙara kamata ganin goma har da rabi, babu ita kuma an neme shi ba'a samu ba. A wanann lokacin ta tasa bala'i suka ƙara komawa gidansa, amma sun kaɗa sun juya maigadi ya sanar masa da babu ita a gidan, bisa gargaɗin maigidansa wanda ba zai iya karyawa ba don kar abincinsa ya ƙare, amma shi kansa ta ba shi tausayi don tuna tana kuka har ya daina jin kukanta. Kan dole suka dawo gida suka zauna jugum-gujum. Ganin tashin hankalin da Ummu ta nuna ya sanya Hajiya Baaba ta ji tausayinta suka zauna a falonta suna jimamin lamarin. Cikin dare bacci ya gagare su. Ummu zazzaɓi ya rufe ta tun tana kukan ta kasa sai dai ajiyar zuciya, domin ta san tana cikin mawuyacin hali ga shi Aby ba ya nan. Shi kansa Aby Hajiya Baaba ba ta barshi ya rintsa ba, don ya gode wa Allah da ya sanya na shi a garin abin ya faru da bai san halin da zai shiga ba. Dad ya shiga matuƙar damuwa sosai, musamman da in ya kira wayarta ta gama ringin ba za ta ɗauka ba, wanda ya san dole akwai abinnda ya faru da ita, don ko hushi ta yi da shi duk inda ya yi kira biyu ba ta ɗauka ba to ana uku za ta ɗauka tana mita, amma har kira wanda bai san adadi ba ba ta ɗaga ba. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 17-18* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Ɓai taɓa tunanin yana da ƙarfin da zai iya tunkarar mom ya yi mata masifa ba. Ya kuma rantse in har wani ya samu 'yarsa ba zai ƙyale ba. Shiru ta yi masa don a yanayin da take ciki ba ta da lokacin da za ta kula shi. Ta san Ajmal ba mahaukaci ba ne da zai cutar da ita. Ko kaɗan ba ta ji zafi sosai ba, domin ta tsallake iya ta shiga har gidan mata ta mareta kuma ta nemi kashe ta saboda tsaurin ido da rashin kunya irin nata. Washegari dole Aby ya dawo gida ganin yadda gidan yake ciki hankalinsa ya ƙara tashi sosai, domin da Hajiya Baaba da Ummu sun kwanta ciwo reras. Ko hutawa bai yi ba ya bazama neman Ajmal. Kamar yadda ya rantse sai da ta kwana ta wuni sannan ya suka dawo gidan Yana buɗe ɗakin da ya kaita Mushiirat ta sa ihu." Innalillahi! Na shi uku bab. Kar fa ka jawo mini ƙiyayyar dangin miji, kalli halin da take ciki." Shi kansa ya matuƙar tsorata domin ta ɗauke dif babu numfashi. Kamata ya yi ya sanya a mota sai asibiti. Drips aka ɗaura mata wanda ko minti biyu bai yi da fara shiga ta buɗe ido." Wayyo Allah! Dad, mom, na shiga uku. Wallahi ya Ajmal ba shi da imani." Ta ƙarashe maganar tana sakin gigitccen kuka. "Ke ma za koma ki kwanta. Da ga yau sai ki gane bakin rijiya ba gurin wasan yara bane, don matata ba sa'ar ki ba ce. Mara kunya kawai." Ya daka mata tsawar da sai da ta ji 'yan hanjinta sun kaɗa, wanda ba bu musu ta koma ta kwanta sai ruwan hawaye ta ke. Wani irin mugun tsanarsa ya kamata ji ta yi tamkar ta saka mishi guba ya ci a abinci ya mutu. Sai da ruwan ya ƙare ya siyo mata abinci ta ci wanda ya yi mata dole ta ci. Ganin ramar da ta yi ya sanya ya ƙi mayar da ita gida, domin ya san in har Hajiya ta gan ta sai ta yi bandar namansa. "Hello Ajmal, kana ina wane hali Jannah take?" Ya jera mata tarin tambayinsa. "Muna asibiti ana ƙara mata ruwa." "Ka san Allah in wani abu ya faru da yarinyar nan, sai ranka ya ɓace. Kuna da manya mai ya saka za ka ɗauki hukunci da kanka?" "Aby, ka yi haƙuri yarinyar ba da ta tarbiya, ba ka ga yadda ta fasa mata kai ba, har sai da aka yi ɗinki." Shiru ya yi don ya rasa yadda zai ɓullo ma lamarin don haka ya kashe wayarsa ya miƙe. "Muje asibiti tana can ana ƙara mata ruwa." Ya fice da sauri gurin mota yana jin Hajiya na faɗin,"Mugu azzalimi, idona idon shi sai ya raina kansa." Ko da suka je sibitin ba su same shi ba sai doctor Irfan da ya nuna musu ɗakin da take. Tana gainsu ta sanya kuka." Hajiya Baaba, kashe ni ya so ya yi, ba ki ga dukan da ya yi mini ba." "Ki barshi da ni, daga yau babu ni ba bu har abada. Na tsani matarsa babu ruwana da shi. Dubi yadda kika rame da ke ma jiki ba." Ummu ta rungumeta cikin muryar kuka, amma sai ta ture ta daga jikinta. "Ni ƙyale ni, babu ruwana da ku. ba zan ƙara zama da ku ba, hostel zan koma." "Haba shalele, don Allah kar ki gudu ki bar ni, ki tsaya kika matakin da zan ɗauka." Turo bakinta ta yi ba ta ce komai ba amma daga yau ta gama zaman gidan. "Hello Sham, zan yi squatting a ɗakinki kafin na samu nawa." Cikin murna ta ce,"Are you saying the truth, za ki dawo hostel? Inda gaske ne sai kin zo, kuma akwai wata friend ɗina she is married woman, mijinta ya hana ta zaman hostel ya kama mata gida a gari, don haka zan yi mata magana duk da na san akwai waɗanda suka yi mata magana, amma ba za ta hana ni ba." "Ok, ba ni da lafiya ana ƙara mini ruwa, kije ki tamabayeta sai na tura miki kuɗin." Ta kashe wayar. Sai da ta yi kwana biyu sannan aka ba ta sallama. Duk yadda Hajiya Baaba ke rarrashinta kan ta yi haƙuri, amma ta ƙi ta tattara kayanta. "Yanzu shalele guduwa za ki yi ki barni? Don Allah kiyi haƙuri ki bari kiga matakin da zan ɗauka." "Kyale ni dama na gaji da zaman gidan zuwan Ummu ya sa na fasa, amma yanzu babu wanda ya isa ya hana ni." Hajiya ta fusata ainun ganin tun safe take rarrashinta amma kamar tana tunzurata. "To shikenan kifi ruwa gudu, Allah ya raka taki gona." Ta ce tare da balla mata harara ta wuce ɗakinta.Taɓe bakinta ta yi alamun ko a jikinta. Ganin ta kwashi kaya sai ta fito ta saka kuka."Na shiga uku na banu! Adamuu ya raba ni da 'yar Halimatuu da nake ganinta tamkar uwarta. Allah ba zan yafe masa ba." Ummu ta kama troley ɗinta."Please don't go anyway, you know I can do without you." Balla mata harara ta yi tare da janye troley ɗin. Sosai Hajiya Baaba ta riƙe jakar ta rantse babu inda za ta sai dai su tafi tare. Ganin haka Aby ya ja ta suka shiga cikin ɗaki." Kiyi haƙuri ki kyaleta, inta huce za ta dawo. Kuma kin san zamanta a nan ba zai ɗore ba. Gidan Halima an gama komai, kawai dawowarsu ake jira. Kinga dole gidan iyayenta za ta koma. "Ba bu yadda zan yi ne, amma wanann mara mutuncin ya cuce ni." Kafin ma su fito ta fice wanda hankalin Ummu ya tashi ta saka a ranta ita ma dole ta koma zaman hostel don ba za ta iya rayuwa babu ita ba. Tun da lamarin ya faru ta ƙi ɗaga wayar mom domin gani take duk ita ta ja mata shiga wannan halin. Ta yi kiran duniya amma ta ƙi ɗauka, haka ta tura mata tsako ko kallon numbarta ba ta yi. Sai zaman hostel ɗin ya yi mata daɗi. In suka dawo daga lecture library take wucewa ta yi karatu sai yamma take dawowa. Abinci kuwa ba ta girkawa sai dai ta siya. Ko sati ba ta yi ba Ummu ta haɗa kayanta ta biyo ta, wanda ta yi murnar hakan don ita ma ta san fushin da ta yi da ita na ɗan lokaci ne, amma she could not do without her. Karatu suke yi sosai babu kama hannun yaro domin they have future accomplishment and they want to accomplish it." Zaman hostel ɗin ya sa suka ɗauki wasu ɗabi'u suka ɗora ma kansu. Zuwa party da kitson attach. Hijabi kuwa sai dai in za su yi sallah, don wani lokacin hakanan za su sha gayu su ɗauki littafansu su tafi hostel babu mayafi, don cin kararsu suke babu babu babbaka. Shirye-shiryen jarrabawa da ya tunkarosu suka mai da hankali babu dare babu rana, kullum cikin kratu suna library. Cikin sa'a suka kammala jarrabawar. A tunanin Ummu Jannah za ta biyo ta su je hutu, amma sai ta ji saɓanin hakan. Ta kafe kan Zey za ta bi hutu zuwa gida. Hankalinta ya tashi ƙwarai don haka ta ɗauki wayarta ta sanar da gida abin da ke faruwa. Aby cikin ɓacin rai ya kira wayarta, wanda tana ɗauka ya fara magana cikin ɓacin rai,"Hello Jannah, in har ba kya son ranki ya ɓace, kafin na dawo aiki na ganku a gida ke da Ummu." Ɗif ya kashe wayar ya barta sagale da ita. Kallon Ummu ta yi ta banka mata uwar harara. "Munafuka na san ke kika faɗa masa." Ta ce mata tana jan troley ɗinta. "Haba sis, ke ma kin san bai kamata ace ga gidammu ba kin tafi wata uwa duniya hutu." "Kiyi mini shiru tun da kin haɗa ni da shi sai ki tashi mu tafi burinki ya cika." Dariya ta yi tare da miƙewa ta ja troley ɗinta suka fito. Ba ƙaramin frin ciki Hajiya Baaba ta ji da ta ganta ba. Har da kukan murna ta rungume ta. "Ba ki da kirki kwata-kwata har ciwo na yi amma ba ki zo ba." Ɓata fuska ta yi ba ta ce komai ba don har yanzu hushi ta ke yi. Tun tana bonewa har ta gaji ta saki ta kama harkanta. Hutun ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba musamman yadda take nan nan da ita, kuma tun da ta sawo ba su yi faɗa ba. Suna zaune ana hira Hajiya Baaba na gefenta da goro a hannunta. Ɓalla ta yi ta saka a bakinta, sannan ta ɗauki lakasera ta kurɓa ta ije tana kalloon Jannah da take ɓata fuska tamkar za ta yi amai. "Kai Hajiya Baaba, wallahi na tsani kwacamalar nan da kike yi. Don Allah ki bari, ni kam ban taɓa ganin inda aka haɗa goro da lacasera ba." Ummu ta kwashe da dariya tana faɗin,"Taɓ! Ai sai dai ki gaji ki daina, don dalilin da Ya Ajmal ya sa ya daina zama sashinta kenan." "Eh, ina jin bakina ne, kuma cikina zan kai ba na wani ba? Na san lokacin tsufarku abin da za ku aikata." "Allah ya kyauta na ci goro don ni ban ga amfanin cinsa ba." "Gaya mata dai." Cewar Ummu tana kallon Hajiya da take harararta. "Humh, kan ku ake ji. Kwayi kwa gam, domin wanda ya fi ku ƙyanƙyani haka ya gaji ya barni." "To ku ya kamata ku fara maganar fara zance ko da ke Jannah kin fara. Kun dai san ba za mu tara ku ɗigi-ɗigi muna kallo ba." "Haba Hajiya, wane irin magana kike yi, duka yaushe muka fara karatun da za ki fara maganar aure. By the way ni ba yanzu zan yi aure ba sai na gama karatuna ba ki ɗaya na samu aiki." "Ashe laillai ba ki da hankali kuwa. Kai ni fa wannan bokon da kuke yi ba son shi nake ba, domin da za a biye tawa duk aure zan muku." Harararta suka fara,"Aiko da kin cuce mu Hajiya. Allah ya kyauta don ke an cuce ki am miki aure da wuri sai ki rama akanmu. Ta Allah ba taki ba." "Dallah rufe mini baki.Auren nawa ai shi ya yi muku gata a duniya, don ya yi mini rana ban yi karatun na haifi minister." Dariya Ummu ta yi ganin yadda take doro da ji da kai. "Tab! An ce miki zama minister wasan yarane. Ki tsaya ki gane tun kafin zaɓe za ta sha ƙasa.. Aure ne dai sai na yi degree da master har da phd if possible na fara aiki." "Baƙinki ya sari ɗanyen kashi ta Allah ba ta ki ba." Ta bata amsa tana kai mata dunduni. "Wayyo Allahna! Hannunki kamar icce don Allah ki daina." Ta ce tare da gamtsarewa. "Ba dole ya zama icce ba ya ga jiya ya ji yau." Ummu ce ta karɓi zance da cewa,"Wai da gaske kike har sai kin taka wannan matsayin sannan za ki yi aure? Ni dai if pssible I wanna marry before finish degree don bani da wannnan ra'ayin ina samu wanda nake so zan yi aure, ba zan yadda na tsufa a gida ba, kum kina tunanin Huzaifah zai yarda?" "Mai zai hana shi ma ba yanzu zai yi aure ba, don yanzu haka Maleshiya zai je ƙaro karatu." "Ashe ko wani zai yi wuf da ke don wallahi ana bikin Hafsatuu zan tasa ku agaba. Ko mahafiyarki da ta samu ɗaukaka duk tana gidan aurenta ta samu." Cewar Hajiya. " God forbit over my dead body ayi mini auren wuri, don babu wanda ya isa ya yi mini aure da wuri saboda komai na rayuwata a tsare yake ba zan iya haɗa aure da karatu ba." "Shikenan, lokaci zai nuna ai domin aure lokaci ne. Ni bari na yi walha na gaji da suratun banza." Ta miƙe tare da shigewa ɗakinta. Ranar Juma'a suka shirya da Huzaifah zai zo. Tun ranar Alhamis suka je aka yi musu kitson attach sannnan suka lalli mai kyau. Washegarin ranar Juma'ar bayan an sauko masallaci. Jannah na gaban mirrow da soson hoda a hannunta tana gyara hoton da ta shafa. Ummu na zaune kan gado tana kallon tiktok. "Sis Huzaifah zai zo amma bamu yi mishi komai ba don ni kam sai yanzu na tuna duk ni ma na shiririce. Ko iya drinks da snack za mu ba shi." "Don't worry about that I have ordered food for him. They will bring the food before his arrival." "Ok" Ta ce tare da ci gaba da kallonta, sai kuma ta juyo tana kallonta ta ce, "Na so na ce miki mu yi wa matar ustazu magana ta yi mana girki mai rai da lafiya, amma sai na tuna muna zuwa za ta fara mana wa'azin mu koyi girki." Dariya ta yi jin abin da ta ce,"I was thinking the same, but na so na yi mata maganar, amma na san ɓata mini mood ɗina za ta yi. So, it should be better na yi oder." "Eh hakan yafi ai. Rashin kuɗi su ke janyo maka wulaƙanci. Akwai maƙociyarmu da take snacks ba ri na sanya ta turo mana da samosa ta ita sosai." "Thanks." Ta ce ta zauna gefenta tana murmurshi. Bayan an kawo abinci da samosa. Suka jera a dining ɗin Hajiya Baaba sannan suka sha gayu tare da turare gidan da turare . Ta fito za ta shiga kicin ganin su a falo tamkar waɗanda za su fita. Ta kalli dining ɗinta da yasha kayan daɗi, sai ta juyo ta kalle su da suka ɗaure fuska, babu alamun son amsa tambayar da suka san dole sai ta yi. Ga mamakin su sai suka ta basar tare da taɓe baki, ta shige kicin wanda 'yan mintina kaɗan ta fito za ta shige ɗakinta, sai kuma ta dawo da zauna tana faɗin, "Ban gane ba, an yi yamma da kare. Munafunci da ƙus-ƙus da na ji kuna yi, na san da walaki goro a miya. Uban me kuke shiryawa.Ni da gidana mallakina ba za ku gaya mini Kon baƙi mata za ku yi? Don na lura yamzu kun iya kwashe-kwashe." Kallon junansu suka yi tare da kwashewa da dariya."Gidan Abby dai." Cewar Jannah. "Ai kai da kaya duk mallakar wuya ne." Ta bata amsa. "Daɗina dake akwai son jin ƙwaƙwaf, wato tun ɗazu kin yi kamar ba ki san me muke faɗi ba, ashe kin baza kunne kina jinmu." "Ah to za a hana ni ne da kunnina." Ta katse Jannah da faɗin haka.. "Abokin Jannah ne zai zo yau." Ummu ta ba ta amsa tana kallon Jannah da ta tsinci kanta da jin kunya ta rufe ido. "Aboki ko? Munafukan banza. Kwa fito fili ku gayi gaskiya." Dariya sunne kai da Jannah take yi ya bata mamaki. "Eh, abokinta ne mana. Huzaifah ne, kuma ai kin san shi. Saurayin da ya ya riƙe ki a filin jirgi da za ki faɗi, wanda Ya Ajmal ya ce yazo bikinsa." Sai ta faɗaɗa fara'arta tana kallon abincin da suka shirya a dining. "Allah Sarki! Ce mini za ki yaron kirki, na gane shi. Kuma shi ne don son jiki da sangarta kuka kasa yi masa girki sai dai ku siyo masa? Ai da kun gaya mini da na yi masa girkina mai matuƙar daɗi na tsofaffinnda suka ga jiya suka ga yau akan girki." "Dabbu, fate, tuwo, shishshika, ko caccaka ne sunan abicin ko me oh. Shi ne abinci da kika iya masu daɗi? Allah ya kyauta ya ci. Huzaifah namiji ne wayyayye ba irin Ya Ajmal ba. Sam ba ya cin abincin gargajiy..." "Ai ko dai da yaji haushi kuma basir sai sun yi ajalinsa. Ai duk wanda ya bar gida, gida y barshi. Na fi gwara gurbin buduwar da yake so, wacce ko murhu ba ta iya haɗawa." Ta yi shiru ko za ta ce komai amma sai ba ta ce komai ba sai dai harararta da ta yi domin hankalinta na kan wayarta da take tsammannin jiransa cikin sakannni don ya sanar mata sun iso 'yan mintina ya rage. "Allah Sarki har na fara tausayinsa. Ga shi yaron kirki amma ya yi zaɓen tumun dare. Lallai ya haɗu da jarrabawa." Ta canza fuska zuwan kalar tausayi kamar za ta yi kuka. Wani kallo ta watsa mata dai dai lokacin da ta juya zuwa kicin tan faɗin, "Bari na je na yi masa tuwon shinkafa miyar kuka mai daɗin sai kunnensa ya kusa tsinkewa, na rama alkhairin da ya yi mini dama shi danƙo ne." Da sauri ta kalli Ummu da ta yi zuru tana kallon Hajiya Baaba cikin takaici. "Sis ya iso yana ƙofar gida." Ta ce tana kallon fuskar wayarta da ke ɗauke da numbarsa ɓaro-ɓaro. "To sai ki bar girkin babu buƙata don sun ƙaraso suna ƙofar gida, kuma ko kin yi sai dai ya yi kwantai, kuma wallahi in kika kunyata ni kin san halina" Ta bata amsa da faɗin haka da ƙarfi don ta shige kicin sai ɓarin tukwane take yi. Tabe baki ta yi ba ta ce komai ba ta karasa shigewa kamar ba da ita ta yi maganar ba. Ummu ce ta bita kicin ɗin daidai lokacin da jannah ta buɗe ƙofa ta nufi harabar gidan. "Hajiya Baaba don Allah in suka shigo kar kiyi wani abu da bai dace ba kin ga su ɗin baƙi.." Kamar za ta cinyeta ɗanye ta taso mata."Dallah can shashasha rufe mini baki! Saboda gani ƙaramar yarinya, in suka zo zan je na sa hannu a abincinsu ko na yi rashin kunya ko?" "Allah ya ba ki haƙuri ni ba haka nake nufi ba, kin san me nake nufi." Harararta ta yi ta ɗora tukunya a kan gas ta ce, Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 18-19* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Harararta ta yi ta ɗora tukunya a kan gas ta ce, "Kun san kuna da abin faɗin ne ni dai ina gani ba zan yarda a cuci yaro ba don ba zan yarda na mayar masa da sharri akan alkhairin da ya yi mini." Ba ta ce mata komai ba ta juya ta fita daga kicin ɗin amma zuciyarta sai faɗi take tana addu'ar Allah ya sa kar taba da su don sanin hali ya fi sanin kama. Da murmushi mai tsada ta ƙarasa gurinsu wanda ya kashe mata ido tun da ta taho. Hure masa idon ta yi da ta isa gare shi. A jiyar zuciya ya saki mai ƙarfi. "A koda yaushe muka haɗu gani nake kina ƙara kyau bab, kin kuwa ganki tamkar wata a cikin taurari. Murmushi ta yi jin abin da ya faɗi."Ku shigo ciki Mufid ka ga abokinka sai zuba yake." Dariya ya yi."Ai dole ya yi zuba kamar fanfo samun mace irin ki ai baiwa ne. Tabbas abokina ɗan baiwa ne." Ƙara murmushi ta yi tare da nufar hanyar shiga cikin gidan wanda ganin haka suka bita. "Ƙawarmu, aminiya, kuma 'yar uwarmu."Ya faɗa daidai lokacin da ya buɗe labulen falon bayan ya yi sallama. "Barka da zuwa ku shigo. Huzaifah duk wannan matsayin ni kaɗai?" "Ai kin wuce haka ko bab?" Ya yi maganar yana tambayar Jannah dake gefensa. Ɗaga masa kai ta yi tana murmushi. Bayan sun gaisa da tsokanar juna sai Ummu ta miƙe tana murmushin ta ce, "Bari mu shiga ciki mu barku ku ci abinci." "A don Allah ku tsaya na fi son ina kai loma ina cin abinci mai daɗi da my future wife ta girka. I know it will be very testing" Hajiya Baaba da ta fito da hura da nono a hannunta tana faɗin,"Ina kuke 'yan son jiki? Sai ku karɓi wannan hurar ku dama masa, ko banza ya samu yaci abincin da ya fito daga gidanku tun da ƙila kafin in gama abincin sun tafi." Turus ta yi tana kallonsu don ba ta ji shigowarsu ba saboda bayan fitar Ummu rediyo ta kunna. "A lale marhabin da zaratan maza." Ta ce tana washe baki ta ƙarasa gurinsa. Sai suka yi tsuru-tsuru don a tunainsu sun ji abin da ta faɗa. Duƙawa suka yi suna gaishe ta. Guri ta samu ta zauna taci gaba da cewa,"Haba ku tashi ai kamar Adamuu na ɗauke ku. Ma za ku tashi 'ya'yan albarka." Miƙewa suka yi suka koma mazauninsu suna shafa ƙeya. "Sai na ji kamar ka ce za ka ci girkin Jannah ko?" Ɗaga mata kai ya yi cikin kunya yana sosa kai tare da mamakin tambayar. "Taɓ! Aiko ka bugo don wallahi ko ru.." "Hajiya Baaba kamar kin ɗora abu a wuta kamar yana ƙonewa." Cewar Ummu tama kama hannunta ta miƙe. "Ke dallah kyale ni na faɗi gaskiya ai ita ɗaci ne da ita." Ta ƙarashe maganar tana wafce hannunta da ta tsaya kamar mutum mutumi. "In kana jin sangartacciya na bugawa a jaridan ita ce, ka ga duk wannnan abincin da suka shirya maka, wallahi duk siyo shi suka yi. Ni saboda takaici kasa magana na yi, amma na ce sai na gaya maka kar na cuce ka saboda alkhairin da ka yi mini." "Haba Hajiya Baaba, gaskiya abin da kike yi bai dace ba, kum.." "Kin san Allah in kika ƙara magana sai na kwaɗe ki da maficin nan. So kike na cuce shi? Ai gara na gaya masa idan aka yi auren da ni za a taho don ni zan rinƙa masa girkina mai daɗi da rainon yara. Maganar aure fa ake yi, kuma ai dole sai an faɗi naƙasun kowa." Sai ta gyara zama tana kallon Jannah da takaici ya hana ta cewa komai sai hawaye da kin bin ƙuncinta domin ta ji a jikinta dole sai ta kunyata ta. Harara ta banka mata tare da kallonsa ta saki dariya."Ka na jina ko yaron kirki? Da Ummu takan yi abin kirki amma zuwanta gidan komai ta daina, ba su da aiki sai kallo da hira a waya. Shi ya sa na ce ba zan ɓoye maka komai ba gara na sanar dakai fare zamu taho in an yi bikin." Saboda dariya Mufid har tuntsira ya yi. Shi kuwa Huzaifah dariyar yake ƙoƙarin ɓoyewa, amma har sai da ta ci ƙarfinsa ya dara. "Oh my God! Gaskiya you Grandma is so dramatic, I love her." Ya ƙarashe maganar yana kallon Jannah ta yi shaɓe-shaɓe da hawaye sai kuma ta share tana faɗin, "Ai dama shi kansa ya san bai nemi aure inda matarsa za ta rinƙa masa kirki ba, in kin yi hakanne ki kunyata ni." Ta faɗa a tsiwace tana harararta. "Au iyye a gabansa sai kin nuna halinki?" Ta ce tare da kama bakinta tana kallon ta. Sai ta juya kallonta garesa ta ci gaba da cewa, "Ka gani ko? Allah na gode maka da ta nuna maka halinta. Yanzu da na ce maka fitsararriyace ba ta ganin kowa da gashi sai ka ji haushina, amma gara da ta nuna maka halinta ƙiri-ƙiri ka gani.Ita ɗin kura ce da fatar akuya. A waje kamar mutuniyar kirki." "Oh common bab. Kin san ko wace irin mace kike ina sonki, saboda tsarinki da zubin ki duk sun yi mini." Ya ce mata bayan ya miƙa mata handkerchief ɗinsa, sannan ya juya yana kallon Hajiya Baaba da ta ɗaure fuska jin abin da ya ce don ita ba haka ta so ba, ta so ace ya nuna ba zai iya ba ko ta yi zuciya ta koyi aiki. "Ba ki da matsala Hajiya Baaba, mu house is welcome to you at anytime you wish. Sosai kika burge ne Ina matuƙar son ki dawo gidana gabaki ɗaya da zama." "Humh! Ka ji da gulman turancinka na bogi, ai ni ba na faɗa maka bane don na burge ka, na faɗa maka ne don na gaya maka gaskiya." Ta ce tare da juyawa za ta shiga kicin ganin haƙarta ba ta cimma ruwa ba. Ajmal da ya yi sallama ya shigo don kawo mata maganin da tun safe ta addabe shi da kira ba ta da lafiya, amma ga mamakinsa tun daga ƙofar ɗakin ya fara jiyo muryarta tana zuba. Idanu ya zuba musu bayan ya yi sallama ya shigo. Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fita musu magana ba duk da ganin yadda suka yi razana don sun ɗauka har su tafi ba zai shigo ba. Da sauri Huzaifah miƙe zai bi bayansa amma sai Jannah ta hana shi, "Lemme go and great Babban Yaya." "No you don't have to do that."Ta ce tare da riƙe gefen rigarsa tana girgiza masa kai cikin rashin karsashi domin gabakiɗaya Hajiya Baaba ta ɓata mood ɗinta. Sun daɗe suna hira har sai da suka gaji don kansu suka yi wa Hajiya Baaba sallama suk tafi bayan sun cika lalitarta da bugun Abuja wanda ta rinƙa shi masa albarka kamar a ta goya su. "Wayyo Allah! Tun shigowa Ya Ajmal na rasa sukuni. Ni kam mun bani Allah ya sa karya gayawa Aby." Cewar Jannah tana dafe ƙirjinta ganin motar su ta ɓace daga gurin. "Amin, ni wallahi har sai da cikina ya murɗa. I was thinking that he would embarrassing us in front of him, but thankfully he didn't." "He never try that, cus i won't stay an watch it." Cewar Jannah cikin ɗaure fuska, sai kuma ta juya tana kallon hanyar da suka bi. "Kin san Allah yau ni da Hajiya Baaba a gidan nan about what she did to me I was very devastated." Dariya ta yi ta ce," To me za ki yi mata kamar ba ki santa ba, ki ƙyaleta kawai kar ki ja ma kanki. Allah I was expecting that, infact more than that from her. Kawai dai we don't have any options ne shi ya sa." Ƙuta ta yi ba ta ce komai ba ta buɗe get ɗin suka shiga. Washegari da safe ko breakfast ba su yi ba kiran dad ya riske su. Gwalalo idanu suka a tare. "Kai anya kiran nan ba lafiya ba fa. Ni fa kallon da Ya Ajmal ya yi mana na san dole sai ya kai ƙararmu gurin Aby, don ya cika gulma kamar ba malami ba." Cewar Jannh da ta miƙe cikin tsoro. Ita dai Ummu ba ta ce komai ba ta miƙe har ta murɗa ƙofa sai ta dawo ta kalleta,"Don Allah ki yi sauri kin tsaya sai kuma mun ƙara wani laifin." Ta faɗa ranta a ɓace ganin ƙoƙarin zama take wanda ya sa ta miƙe suka fice da sauri. Ganin Hajiya Baaba zaune a kan kujera tana ta girgiza da kaɗa ƙafa jikinsu ya ba su ba lafiya ba. Da sauri suka durƙusa a tare."Ina kwana Aby." "Rufe mini baki shashashun banza! Ina kallon ku masu hankali har na barku kuke zaman hostel ashe wawaye ne ku ban sani ba?" Aby ya furta murya a zafafe," A'a Muhammadu ka san ba zan ɗauki hakan, wanda na san duk zugin wannan munafukin ne. Ai tun da na ga ya shigo ya ije maganin ba tare da ya ce komai ba na san sai ya haɗa munafunci. In ban da gulma tun yaushe na rinƙa kiransa ya siyo mini, amma da yake isashshe ne bai zo ba sai da gulmarsa ta kawo shi." "Haba Hajiya Baaba, ya muna ƙoƙarin gyara za ki ɓata kuma." Sai ya juya gun su. "Ke Jannah da gaske kun kawo saurayi gidanan?"Ya ƙarsa maganar cikin tsawa. "To laifi ne hakan Muhammadu? Na ga shi mace ya aje a gidansa yana hutawarsa. Ko so yake mu rinƙa ado da su a ƙofar gida? In ban da gulma da sa ido waɗannan tiƙa-tiƙan da 'yan matan da ba bu abin da suke yi, sai warin balaga za a tsaya ana tambyarsu don sun kawo maza gida zance." Zare ido suka yi suna kallonta,"Warin balaga?Kai amma Hajiya ta cuce mu duk irin ƙanshin da muke yi." Jannah ta ce tana hararar ta tare da shinshina jikinta. "Ni fa ba aure zan yi ba kuma abokina ne. Bayan wannan babu abin da ke tsakaninmu." Ta furta cikin rashin shakku da tsoro. "Gabakiɗaya ke kike ɓata yarannan Hajiya. Idan aure za su yi ai babu wanda zai hana su, amma sa bari su yi zurfi a karatunsu. Duka fa yanzu suka zana jarraba na first semester, ko Nahlin sai da ta kai 3 hundrent level za ta yi aure." "Da ma na san kashi da tusa duk nice a gidannan, saboda n bi ta bayan gida an shanye ka. Ni dai auren ƙabila babu abin da ya ja mini sai shata layi a tsakanina da ɗana. Ƙiri-Ƙiri ina ji ina gani an yi mini faƙara'u an raba ni da ɗana. Wallahi sai Allah ya saka mini." Ta ce tare da ƙara saka kuka tana share hawaye sai kuma ta kalle su Jannah da idanunta da kamar ba kuka take yi ba dai dai lokacin da Aby fara cewa, "To yanzu don Allah mene na kawo wannan maganar a gaban yara? Na ɗauka mun riga mun zama ɗaya." Ya ƙarasa cikin jin zafin abin da ta furta yana kallon Amy lokacin da ta miƙe za ta shige ɗakinta hawaye na bin fuskarta. "Dallah kyale ni! Sai a dake ni a hana ni kuka." Ta ƙarashe maganar tana kallon Ajmal da ya yi dana-sanin maganar. Zuciya ta ciyo shi kawai ya ɗaga ƙafarsa ya kai musu ita da nufin ya haure su. "Shikenan, ba ni da damar tsawata musu sai ta shige ta hana hakan? Kalli kansu Aby gabakiɗa atach ne a kansu, saboda iskanci sun tare a hostel babu mai tsawata musu sai sheƙe yarsu suke yi. Malaman islamiya sai magana suke ba sa zuwa islamiya da hadda." Ya fara ƙoƙarin nemo bulala ya co gaba da faɗin,"Saboda iskanci a maimakon Ummu ta yi ƙoƙarin a ƙwato ta daga halaka, amma sai ta biye mata suna iskancin su babu mai kwaɓa musu." Ƙara suka saki tare da ɓoyewa a bayanta. Hajiya Baaba ta juya ta kalle su tare da wafce ɗankwalin Ummu ta girgiza kainta. "Kuma fa in anbi ta ɓarawo, abi ta maji sawu. Ni kaina wannan uban gammo da suka ɗaura a kansu yana damuna, in dai akan wannan ne ba zan haka ba ka yi mini ƙasa-ƙasa da su." "Ma za suje da direba ya kwaso kayansu babu wacce za ta ƙara kwana a hostel, in ba za ku yi karatun a gida ba ku bar shi, tun da aure kuke so sai ku kawo miji." Jin abin da ya ce hankalinsu ya tashi ba kamar jannah da har ta fara kuka. "Kuma awa ɗaya na baku ku kwance wannan gashin in ba haka aski zan yi muku." Ajmal ya ce tare da yarda bulalar ya fice, sai kuma ya dawo lokacin da suke hararar Nahlin da take musu dariya ciki-ciki. "Ke Nahlin da ga yau ƙarki ƙara aiki komai su za su yi, kafin su tafi makaranta ki tabbatar da sun yi aiki gudan nan, sannan a wata uku nake su iya girki." Ya fice daidai lokacin da ta amsa masa. "Ai wallahi gara ya yi musu haka dama ni zaman makarantar nan sam bana son shi domin Jannah ƙara lalacewa za ta yi." Ta fice ba tare da ta damu da yadda take kallonta ba, yayin da zuciyarta fari ƙal tamkar farin takadda, don Allah kawai ya san halin da ta shiga da ta koma makarantar. Suna shiga ɗaki tasa ihu tana didddira har sai da ta faɗi ƙasa. "Duk ke kika ja mini wannan bala'in da yanzu na bi Sham duk wannan tashin hankalin bai same ni ba." Ta gallah mata harara tana faɗin hakan. "Na tsane shi wallahi. He just like thread in my life, threatening me all the time for what reasons?" Tsayawa jikin mirrow ta yi tana kallon yadd kitson ya ƙawata fuskarta, ta yi ƙuta tare da faɗawa kan gado tana girgiza gashin dokin. "Yanzu duk kyan da na yi haka zai sanya na tsefe shi saboda rashin mutunci da shegen sanya ido? Wallahi sai Allah ya saka mini." Sallama Nahlin ta yi ta shigo cikin fuskar dariya ta zauna gefen gado. "Please Anty Nahlin, we are not in the mood and you have to respect yourself. You know respect is reciprocal." "And what?" Ta ce Ummu jin abin da ta fada tare da daure fuska, amma cikin zuciyarta dariya kunshe ganin yadda Jannah ta yi da fuska. "I came to pass a message. Ya ce na gaya mu haddar shafi goma za ku bayar gobe, don haka sai ku fara karatu, sannan gobe zan fara koya muku girki tun da muna hutu sai kuyi amfani da damar ku." Wani uban tsuka suka ja."Ya ce mu sauke kur'anin a gobe mana, in yana ƙaryar malinta. Ni wallahi haushi yake bani, in ya ga damar zai zama ustazu dole sai koya ya zama irinsa. Ai tsoron Allah a zuciya yake." Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta kunna data ba tare da ta ƙara kallonta ba. "Na rantse ko shafi biyu ba zan kawo ba don ban iya ba." Cewar Ummu. "Ki gaya masa gobe menstruation ɗina zai fara kuma kin san wahalar da nake sha don haka ba karatu." Jannah ta furta tare da shigewa bayi. "A lallai wuyanki ya isa yanka ƙaramar mara kunya. Ai sai kije ki gaya masa." Cewar Nahlin. Dariya Ummu ta yi." Ke da ya aiko ke za ki gaya masa, haka kawai duk kin bi kin takurawa rayuwarmu." "Kan ku ake ji." Ta bata amsa tare da harararta ta fice. Taba fita daidai lokacin da ta fito daga bayin."Wai a ƙwato ni daga ɓata, wato na kafurta kenan na shiga ɓata? Gani 'yar jujal jikar sheɗan." Ta ce cikin ɓacin rai. Sai kuma ta sa kuka tana faɗin,"Wallahi Allah ya isa kuɗin da na biya, ni ba ma wannan ba yadda zan ita tsefe gashin nan in just one hour? Imagined." Ummu ba ta ce komai ba ta fara tsifar don ta ga surutun cinye lokacin da ya ba su yake yi. Ganin haka ta ɗauki masilla ta yi tare da ƙwala wa Talatu da Atine kira da su ta ya. "Ya rinƙa wani behaving as if he is the most ethical and the most decent person in the world, bayan yaudaren kansa yake ɗan ƙauye kawai. We are in twenty first century he should have known that." Kan dole babu yadda za su yi suka hau tsifar wanda kamar yadda ya basu awa ɗaya ba ta cika ba sai dai suka gama. Tsabar haushi ko lunch ba ta ci ba sai cika take tana batsewa. Bayan sun gama suka je suka kwaso kayansu duka. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 19-20* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM LONDON Mom zaune akan kujera da wayarta tana waya, oder take bayar wa na kalan furnitures ɗin da za a sanya mata a gidanta. Dad ya fito daga ɗakin cikin shirin fita yayin da jakarsa sagale a kafaɗunsa sai ƙamshi yake yi. Ɗagowa ta yi ta kalle shi tare da mai da kanta ta ci gaba da wayarta. Tsayawa ya yi tamkar gunki har sai da ta kammala ta kashe wayar sannan ta juyi ta kalle shi, bayan ta ije wayar akan kujera. "Ranki ya daɗe na fito zan kai tsaƙon nan airport and daga nan I will heading to office." "Ok, but amh. Mun yi magana da Governor I think we must go back to Nigeria within two weeks, because of the campaign and I can't go may be you will go on behalf of me an.." "No way Halima." Ya ce tare da ɗaure fuska sannan ya ɗora da cewa,"You know I do not support you in to politics ina ganin it should be better ki bar maganar na..." "Oh please stop Injiniya, will you represent me or not?" Ta tambaye shi cikin ɗaga murya. "I will not cus am not you errand boy am you husband." "Ok, fine." Ta kwashi tarkacenta ta shige ɗakinta daidai lokacin da ya saki tsaki ya fice daga gidan zuciyarsa a jagule. NIGERIA Nahlin ta tashi da asuba bayan ta yi wa su Adal karatu ta zauna tana ɗan gyangyaɗi tana jiran shigowarsu, amma har ta gaji ba ta ga ƙeyar su ba. "Kai ni kam waɗannan yaran sun ishe ni, Ya Ajmal ya ɗora mini wahala. Miƙewa ta yi ta nufi sashin Hajiya Baaba. Turus ta yi bayan ta buɗe ɗakin ganin har yanzu babu wacce ta farka da alama ko sallah ba su yi ba. "Lailai yaranan ba su da hankali sun raina Yaya wallahi." Duka ta kai musu tana faɗin,"Ku tashi marasa mutunci ayi ta maimata muku magana ɗaya, sai ka ce wasu kurame haba." "Wallahi an takurawa rayuwarmu wai baccin safen mutum ba shi da ikon yi. Da hostel ne in bamu da lecture sai mu kai ƙarfe sha biyu muna bacci." Cewar Jannah. "Aiko an yi asara." Ta ba su amsa sannan ta ɗora da cewa, "Ba wannan ya kawo ni ba don ina da abin yi. Za ku yi karatun ko na kira shi." "Taɓ! Allah na tuba, ai da wuya na haddace ko aya biyu gara Ummu na ga ta yi karatu kafin ta kwanta, kuma ta tashi da daddare." "Ni ma bai zauna ba Allah." Cewar Ummu tana turo baki. "Allah ya shirye ku wallahi. Yara sai kace kafuran farko, ko kafuran aljanu sun shiga jikinku. Ni kama bari na kira shi kun fi ƙarfina." Riƙe hannunta suka Ummu ta ƙwace wayar tana faɗin,"Haba our unique Anty, it hasn't gotten to that. Yanzu zamu fito. A dai yi ma uren nan na ki mu huta." "Allah ya sa ita ma ba kusa da gida za ta sanya a gina mata gida ba don ta takura mana." Ta furta tana ƙoƙarin tuɓe rigar baccinta. Dariya ta yi ta sa kai za ta wuce tana mamakin halin ƙanninnata da take matuƙar so sosai. Bayan sun yi hadda suka dawo bacci suka koma sai gurin sha biyu suka tashi saboda jiya sai ƙarfe uku suka kwanta. Suna zaune a falo suna kallo Nahlin ta ƙara shigo wa."Kenan kun sa zan rinƙa safa da marwa tsakanin sashin Hajiya da namu. Ku ba kwa tunanin sai an yi muku. Sai ku zo na koya muku abinci. Ina ga kawai mu yi shi a matsayin abincin rana." "Lallai m Anty Nahlin, ɗan abincin da zamu koya wanda bai wuce na gwangwani biyu ba, shi ne za ki wahalar damu. Gaskiya ya haka Yaya ce ba." "To shikenan, marasa son moriya ke Ummu wallahi kin shiga uku, da bakinki kike faɗin hakan. Na ji nice baiwa a gidan nan, mu je na koya muku kaɗan ni sai na yi abincin gidan. Mijina ya huta kuna ganin wahalar da kaina nake yi ko?" "Mu ma na mu ai bai ce miki wahala zai sha ba tun da akwai restaurant Kuma da kuɗi." Jannah ta ce tare da canza tasha zuaa wanda suka ga ana kallo. "Hmm, Allah ya kaimu lokaci zai nuna. Kun ɗauka zaman auren film ne, da daɗin bakin da suke muku ko." Shiru suka yi ba su ce mata komai ba. "Mu je kicin ɗin Hajiya Baaba ba sai mun je sashinku ba." Cewar ganin sun yi hanyar fita Jannah tare da nufar kicin ɗin. "Kin san halin Hajiya Baaba kar ta samu da masifa." "Muje mana ba iyayenmu suka tsiya ba? Ni wallahi ko kaɗan bana tsoronta." Bin bayanta suka yi suka nufi kicin ɗin A kicin ɗin ta dage sai yi musu bayani take yi amma hankalinta ba shi a kanta yana wayarta da take duba chatts da Huzaifah ya yi mata. "Jannah kina jina? Don na lura you mind isn't here." Nahlin ta furta. Ije wayarta ta yi ta ce," Anty Nahlin stop waisting your time for the explanation. Kin san with the advanced of technology everything is easier. So you don't need to explain just give me the recipes."Ta ƙarashe maganar tana ɗora tukunya. Baki Ummu ta buɗe cikin mamakin ƙarfin halinta."Uban me za ki dafa, wallahi kin san kika haɗawa Hajiya gobara ko kika ɓata mata kayan abinci za ki sani. You that when we were in hostel ba ta taɓa girki ba." "Then wait and see, I will search everything on YouTube and watch. Yau za ki ci abincin da baki taɓa ci ba. Believe me sis, you will really enjoy it" Ta ce tare da balla mata harara. Baki ta taɓe tana faɗin,"I see, yau mata za su yi girki. I can wait to see." "To shikenan, if you insist. Bari Ummu sai muje sashinmu ta yi acan." Ta ce tana ƙoƙarin fita don ta ba ta haushi. "Su waye a kicin ɗina ba na hana shiga ba don wallahi ban yadda da ku ba, saboda tun da kuka dawo ake mini satar nama. A da sai na yi sati da miyata cike da nama, amma yanzu ko kwana ɗaya ba ya yi." "Allah ya kyauta mun fi ƙarfin satar naman miya sai dai muci."Ummu ta ba ta amsa lokacin da ta ƙaraso. "Gaya mata sis." Ta ce lokacin da take ƙoƙarin kuna gas. "A keee! Dakata karki haɗa mini gobara. Uban me za ki yi?" "Girkin da kullum kike mini gori zan fara daga yau, saboda bana son na yi aure ki bini gidan mijina ki rinƙa mini tereren ke kike wa mijina abinci." "Au to rasai, amma ba da kayan abincina ba ko?" Ta tambayeta jin abin da ta ce. "Kin ga Hajiya Baaba, ki ƙyale ni karki ki sanya na manta abin da na kalla kuma." "Yau na ga lukutar matsifa, ke da ba ki iya ba shine za ki ce rana tsaka za ki koya? To bari mu gani in tusa na hura wuta, an gaya miki girkin wasan yara ne. Kuma kika ɓata mini kayan abinci aljihun uwarki zai yi kuka." Ta ce tare da juyawa ta koma falo. Bayan fitarsu ta gama ƙarewa gas ɗin kallo amma ba ta ga inda zata kunna ba. "Talatu." Ta yi kiranta cikin raɗa tare da yafito ta da hannu. "Na'am ga ni Hajiya." Ta ce lokacin da ta shigo kicin ɗin bayan Janah ta rufe ƙofar. "Ki kunna mini gas ɗin nan." Ta miƙa mata ashana. "Ai ba da ashana ake kunnawa ba, ashanar na kunna gawayi ne da Hajiya Baaba ke sanya turare." "Oho, kunna mini to." Ta ce ba tare da ta ji kunyar Talatu da take mata wami irin kallo ba. "Kin ga yadda za ki yi nan Hajiya, ya kamata ki koya ko don nan gaba." "Please don't lecture me, cewa kawai na yi ki kunna mini. Ce miki akai kuku nake karanta. Zan nuna ma mutanen gidan nan ni ɗin na iya kawai ba na son na yi ne. Allah na tuba girki har wani wahala yake da shi. Na san is so simple as eating food. Dallah ni in kin kunna fita ki bani guri." Ta daka mata tsawa tana faɗin haka. "Allah ya ba ki haƙuri." Ta ce tare da ficewa da sauri. Ba ta ce komai ba ta ɗaura tukunyar tana 'yan waƙe-waƙenta da rawa. "Umh, kamar na ga fa ta soya kayan miya ko?" Ta yi wa kanta tambayar a bayyane. Gnain ba ta tuna ba ya sa ta ƙara kunna video. "Wayyo Allah ta soya kuma wallahi ni kam ba zan tsaya jira ba saboda am eager to start watching queen of tears, ga wan can jarababben ya sa mu hadda." Sai kawai ta diddila mangyaɗa iya son ranta tare da kayan miyar ta kwara ruwa. "Bari na saka mangyaɗa da magi yawa saboda nawa yafi na Ummu daɗi." Ta ce tana rawa da ƙafarta. Ta zuba magi da yawa gishiri ne ba ta cika ba. Ruwan na tausa ta ibi shinkafar da tafi ƙarfin ruwan ta zuba ta juya ta mayar ta rufe tana shaƙar ƙamshin girki da ya ji uban spices har da wanda tea Hajiya take haɗawa da shi. Mintinan da ta ga wacce ta yi girki a yourtube ta bawa girkinta ta iba sannan ta kira Talatu ta kashe mata gas ɗin ba tare da ta duba girkin ba. "Na shiga uku Hajiya Jannah, kar dai har kin gama." Wata uwar harara ta banka mata."Ni fa na lura dake muguwar munafuka ne, don ina zargin ke kike ƙara haɗa ni da Hajiya Baaba a gidanan, saboda shekaranjiya a gabanki na ibi nama yanka tara." "Innalillahi! Don Allah kiyi haƙuri wallahi ba ruwana. Sam ba na shiga sabgar 'yan gida. Na dai tambaye ki ne saboda na ga ko kifin da kika sa na wanke bai isa dahu ba, ballantana naman kayan ciki masu tauri." "To sannu 'yar iya sai ki koya mini girki ni da na koya a yourtube, kuma awannin da ta yi amfani da shi da shi na yi nima. Ke da kike baƙauyiya dake ji be ki fa, har wani girki za ki koya mini." "To ai gas ɗin kaɗan-kaɗan kika saka yake ci fa." "Dallah ni fita kiban gurin tun da kin gama mini amfani." Ta daka mata tsawa tana faɗin haka. Bayan ta fita kuma sai dawo da ta hankalinta tare ta tuna yadda gas ɗin mi girkin yake ci. Da sauri ta ƙarasa gaban tukunyar ta buɗe tana kallon shinkafar da ta tokare tukunya ta yi cikin shige ga mai shanana. "Na shiga uku." Ta faɗi tare da mayar da murfin tukunyar ta rufe. Leƙawa ta yi za ta kira Talatu daidai lokacin da su Ummu suka shigo kicin ɗin. "By the looked on your face, I guessed you cooked delicious food." Cewar Ummu cikin tsokana tana ƙoƙarin ƙarasawa gurin tukunyar. "I can't wait saboda tun ina waje nake perceiving the aroma ina ta salivating." "Oh yes I do, ki bari I will serve you." "Wai me kika dafa? Na ga ko Ummu da te girka taliya har yanzu ba ta gama ba, mun bar wa Jummala ta kula da shi?" Nahlin ta tambaya cikin mamaki. "Fried rice na yi." Tare suka haɗa baki gurin faɗin,"Fried me?" Ummu ta ƙarasa cikin mamaki ta buɗe tukunyar. "Kan uba, yau ke da Hajiya Baaba wannan abinci da kika tokare tukunya da s.." Maganar ta tsaya mata a maƙoshi sakamakon ɗanɗana shinkafar da ta yi. Da gudu ta ruga sink ta buɗe famfo tana watsa ruwa a bakinta bayan ta furzar da abincin ta wanke bakinta. "Haka ake girki? Aiko da tuni mun mutu. Jakar magi kika juye?" Tsaki ta yi tana faɗin,"Ban sani ba." Ta tureta daga gurin tukunyar. "Taɓ! Duk wanda ya ci abincin nan sai dai ya kwana a cikin bayi." "Jannatu, wane irin girki kike yi? Gida ya cika da ƙarnin nama." "Girki mai daɗi Hajiya Baaba, ma za shigo kar ayi babu ke yau mata sun yi girki, in dai kika ci wannan girkin sai kin suma." Nahlin ta ba ta amsa. " Allah ya tsareni girki ko shiririta dai." Cewarta ta tana buɗe tukunyar. "Innalillahi! Ni jikar maigishiri wannan tsunburen da kike yi fa? Ai wannan albazaranci ne. Ni dama na san babu abin da za ki tsinana shegen kafiya ce dake." "Ni fa ba ni da laifi iya yawan da nake so na shinkafar na zuba, shinkafar ne ta kubburo." Kwashewa da dariya suka yi." Wai yanzu sis kina nufin baki san in aka aka dafa shinkafa kubburowa take yi ba taɓ?!" Cewar Ummu. "Oh ni kam na ga abin da girmi kakata an dai yi zuwan zomo kasuwa." Hajiya ta ce tana salati. Wiƙi-wiƙi ta yi da idanu daga ganin ta kasan ba ta da gaskiya don ko ita ta san girkin bai yi ba duba ga yadda ya yi cikin shega ya tsunbure. Kuka ta saka sosai. "You know what? Let me take pic and send it to him, so that he can give you mark." Da sauri ta ɗauke tukunyar ta ɓoye a bayanta tana zare ido. "Ni wallahi an tsane ni a gidan komai na yi kuce bai yi ba, kum ku ci ba da degrading ɗina, to ba zan ƙara yin girkin ba ya bar ni idan na yi aure aka koro ni ba shi da asara." "Dallah ja can shashasha! Yanzu asara kika yi mini kenan?" "To wa zai ci wannan abincin? Ai wallahi ko su Binbo karnukan gidan nan ba za su iya ci ba." A kwana biyu babu abin da za ta iya rantsewa ta koya domin Hajiya ta rantse ta maya babu uban da zai ƙara shigar mata kicin, dama ita ba buƙatar koyon take yi ba don haka ta shiriritar da zancen. Cikin sa'a kuma Ajmal ya yi tafiya don haka suka watsar da koyon girkin har suka gama hutun makarantar suka koma karatu. Ranar Juma'a lecture na su ƙarfe sha biyu suke gamawa. Bayan sun gama Jannah ta kama hannun Ummu. "Sis, kin san me? Ni kam Allah yau babu abin da zai hana ni yin kitson attach, don ina son na fito sosai bikin Maryam. Kin ga hoton kitson ya yi mini sosai musamman na ɗauko shi." "Yanzu duk maganar da aka yi mana baki ji ba? Ni dai babu ruwana va zan sha dukar banza ba." Ta ce tana gwalalo ido. Tsaki ta yi ta shige motar har ta kunna sai kuma ta kashe ta fito daga motar tana cillawa Ummu makullin da bayan ta zauna a kujerar me zaman banza. Ganin haka ba ta ce komai ba ta fito daga motar don ta san me take nufi. "It is my life, and I will do whatever I like." Ta ƙarashe maganar tana jingina kanta akan jikin motar. "Ok." Ta ce kamar ba za ta ƙara magana ba sai kuma ta buɗe baki za ta yi magana. "Please drive the car, or the you want me to start my madness?" Ta ce tare da kunna waƙa ta ƙure tana rawa da kanta. Ganin haka ta figi motar suka bar harabar makarantar. Cikin Samaru suka ta je aka yi mata kitson mai shegen kyau sai ɗaukar ido yake yi wanda ana gamawa ta biya suka dawo gida. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 20-21* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Tun da aka gama kitson take ta ihun raki da faɗin zafi. Ummu sai dariya take mata ganin yadda ta take ta jin zafin kitson. Tun akan hanya take haɗa gumi duk da AC motar. "Kai wannan matar hannunta akwai zafi kamar zata cire mini ƙwanyar kai." "Allah ya ƙara ai wanda bai ji bari ba ya ji hoho." Cewar Ummu wanda ba ta ce mata komai ba ta ci gaba da danna saman kanta da take jin kamar zai ɗaɗɗake. Suna isa gida maigadi ya buɗe get da sauri ta buɗe mofar ta ito ko jira ta gana parking ba ta yi ba. Kai tsaye sashin Hajiya Baaba ta yi ta shige ɗakinta ba tare da ta damu da dariyar da take mata ba. Wanka ta yi ta jiƙe kan da ruwan sanyi sannan ta ji dama-dama ta saka doguwar riga ta dawo falo ta ƙure fankar sama da ƙasa tana jin yadda iskar ke shiga cikin kanta yana rage raɗaɗi. "Ke don ubanki ba kya jin magana ko?" Kamar daga sama ta ji muryarsa wanda ya sanya ta miƙe tana zare ido don ko kaɗan ba ta yi tunanin shigowar sa ba asalima ta san ya yi tafiya. Mari ya kai mata cikin zafin nama yana faɗin," Dole na ɗauki mataki don ba zan bari ku jawo mana abin magana ba." "Wayyo Hajiya Baaba, don Allah kizo kashe ni zai yi." Ta furta cikin ƙara tana sosa fuskarta don ta ji shigar marin. Da sauri ta fito tana gyara zani."Na shiga uku da wannan mai zuciyar kafuran wai kashe ta za ka yi?" Ta ce lokacin da take ƙarasowa gurin. "Don Allah karki barshi ya ƙara dukana kashe ni zai yi." Kallonta ta yi ba tare da ta tambayi ba a sin dukan ba ganin uban kimin atach a kanta don ko lokacin da suka shigo tana sallah bata ganta ba. "Ba kya jin magana Jannah, kin fi son ya yi ta dukanki kamar ya samu jaka. Kina 'yar gidan malamai kina jawo mana zagi?" "Ki yi mini tsakani da shi don wallahi ba zan fasa yadda nake so da rayuwata ba. Ko iyayena ba su isa su hana ni ba balle shi ya fita daga rayuwata na tsane shi. Mugu kawai azzalimi kuma sai Allah ya saka mini wa.." Wani irin mari da ya ƙara kai mata ya sa ta yi shiru tare da ƙara sakin wani ƙaran ta yi bayan Hajiya, amma idanunsa sun rufe zaginsa da maganganun da ta gaya mishi suka tunzura shi yake jin in har bai cire mata haƙoran rashin kunya ba ba sunan shi Adamu ba. "Kai ni jikar mai gishiri! Jikoki sun zame mini fitina. Kai Adamuu kashe ta za ka yi? Ka bar dukan nan, anya za ku yi zumunci bayan bamu da rai." Ta ce cikin ɓacin rai tare da kai hannu za ta ƙwace wayar wutar da ya fisgo. "Karka ƙara dukana ba ka da wayewa. I have right na yi abon da na ga dama." Bige bakinta ta yi."Ke kam Jannah ba ki da kunya. Shegen bakinki yake ja miki duka, kamar Adamu za ki rinƙa zagi." "Ok, bayansa kike goya ko? Wallahi saina shigar da ƙara inhar ya illantani." Dukanta yake bakinta yaƙi rufuwa yayin da idanunsa ya rufe. Tun yana dukanta da bulala har ya fara haɗawa da hannu. "Kai Adamuu kar fa ka yi kisa tun da bakinta ya ƙi rufuwa ka yi haƙuri ka ƙyale ta ai babba juji ne." Ta ce tare da ƙoƙarin shiga tsakaninsu. "Ki barshi ya kashe ni wallahi sai ya yi dana sanin haka don dad ba zai taɓa ƙyale shi." "Hajiya Baaba, ƙyale ni yau saina sauke mata duk wani iskancin kanta sai ta yi dana-sanin zagina." Hajiya Baaba ta rasa yadda za ta yi dasu shi yana dukanta bakinta ya ƙi rufuwa. Kukan kura ta yi ta shiga tsakaninsu tare ƙoƙarin karɓe bulalar hannunsa. Ajmal da zuciya ta tiƙo shi jin yadda take zaginsa tana yin fitsarincinta son rai. Ya sanya hannu ya ture Hajiya Baaba da ta kawo hannu da nufin ya damƙo Jannah. Cikin rashin sa'a ta bugi center table na glas ɗin falon y fashe ta faɗi kansa wanda ta yi taga-taga za ta faɗi kansa amma sai ta yi ƙoƙarin dojewa sai dai duk ƙoƙarinta sai da ta faɗa wanda ya sanya ta ƙwala ƙara tare da zubewa ƙasa luu ta sume. Ƙarar da ta saki ya sa ya bar dukan ya yi kanta yana girgizata tare da kiran sunanta ganin aika-aikar da ya yi. Jannah da ta sha wuya wani irin jiri ya ibe ta ganin goshin Hajiya Baaba na zubda jini sai kawai ita ma ta bi bayanta ƙasa babu numfashi. Ummu da ta shigo cikin falon domin sashinsu ta wuce don yunwa take ji. Ganin abin da ya faru ta sanya ihu tare da girgiza su sai kuma ta ruga da gudu zuwa ɗakin Ammy da ta fito daga wanka ɗaure da tawul. Saboda tsabar kiɗimewa ta kasa magana sai dai nuna sashin Hajiya take tana ihu. "Na shiga ku don Allah ki gaya mini mutuwa aka yi, mai ya faru da Ajmal ɗin ko hatsari ya yi da zai dawo daga tafiyar?" Ta shiga jero mata tarin tambayoyin amma ta gaza furta komai. Ganin haka sai ta ruga har za ta fice sai ta tuna babu kaya a jikinta ta zura hijabi ta fice zuwa sashin Hajiya Baaba. "Kai Ajmal, mai ya faru mutuwa Hajiyar ta yi?" Ta ce tan kallonsa cikin kiɗima ganin ya ɗauko ta jini na zuba goshinsu. "Ammy Jannah, ita ma ta mutu." Cewar Ummu ganin hankalinsa ba shi gareta don har ya fice da Hajiya ya tada mota. "Innalilahi! Ajmal, ya janyo mini musifa daga dawowarsa." Ta ce cikin muryar kuka don ta fra fahimtar komai. "Ma za ɗauko mota mu kai ta asibiti." Cewar ta tana girgiza ta. "Ba zan iya tuƙi ba sai dai direba Musa ya kaimu." Ummu tace tana kallon 'yar'uwarta cikin tashin hankali. Har Ammy ta shiga mota tunawa daga ita sai tawul ya sa ta ruga da gudu sashinta ta ɗauki doguwar riga ta zura suka wuce asibiti bayan ta kira Aby ta sanar mishi. "Wash Allah, a ina nake nan, duniya ko kiyama? Shikenan, sun kashe ni sun huta dama na san watarana sune ajalina." Ta ce tana kallon doctor Irfan da yake dressing ɗin kanta." "Ki kwantar da hankali ki a asibiti ne kin samu minor injury ne." "Kai dallah ni sake ni sai ku yi ta saka fararen kaya a asibiti, saboda ku tsorata mutane su ɗauka mala'iku ne." Ta ce tana ture hannunsa daga goshinta. Murmushi ya yi jin abin da ta ce." Saura kaɗa a gama miki dressing ki tsaya na gama na ɗaure." Ya ce yana kallon Ajmal da yake ɓoyewa a bayansa. Karab! Idanunta suka hango mata shi."Za ka ci ubanka wallahi kai da jannah sai na muku rashin mutuncin da ba za ku taɓa mantawa da ni ba, don saina sanya muku irin tabon da kuka yi mini gashi nan sai dai na tafi lahira da shi. Zan ga ƙarshen ƙiyayya." Ta ƙarasa maganar tana nuna shi da yatsa. Buɗe ƙofar aka yi aka shigo. Jannah ce sai Ammy da Ummu. "Sannu Hajiya." Cewar Ammy Wata uwar harara ta banka mata bata amsa ba sai girgiza kanta take kamar ƙadangaren kutu Jannah kanta ta yi tana faɗin,"Na gaya miki ya tsane ni baya son ga shi yanzu har ke zai haɗa ya kashe, kuma Allah sai kotu ta ƙwato mana 'yancinmu." Ta ƙarasa maganar lokacin da ta isa gurinta. "Matsa ki ban guri shashashar banza. Dama na gaya miki watarana bakinki sai ya yi ajalinki, saboda ba ki da kunya da ta ido. Jannatuu ban san inda kika gado halinki ba sai dai ƙila gurin ubanki don ni dai 'yata mai tarbiya ce. Shi yasa ake cewa in za a yi aure ki zaɓo abokan zama na kirki wanda kuka san asalinsu amma da yake 'yayana ba sa cin magana sukai kunnen uwar shegu da maganata. Ga shi yanzu har ni ya shafa dama iya kansu ya tsaya da sauki." Turo baki ta yi tare da galla mata harara jin abin da ta ce har ta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa don jikinta mugun ciwo yake mata. "Ba dai ni kuka sa na yi kuka da girmana ba? Za ku sani, sai kun gane duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha. Yuawa kai Muhammadu, gara da ka shigo maza kira mini Halimatuu." Ta bashi umurni fuskarta babu wasa tare da miƙa masa hannu. "Hajiya, na roƙe ki don Allah kar a kirata zan iya maganin matsalar duk ikona ne su." "Za ka kirata ko ban isa ba na sa likita ya kira mini ita." Ta katse shi tana faɗin hakan wanda da sauri ya ciro wayarsa tare da miƙa mata yana faɗin, "Allah ya sanyaya zuciyarki da dai anbi abin hankali." "Ba amin ba in dai akan wannan ne ni ma sai na sanya sun ji azaban da na ji." Bugu uku ta ɗauki wayar." Hello, Ya Muhammad sun amince za su saya a haka ne?" Ta ce bayan ta ɗauki wayar domin sun gama waya kenan babu daɗewa akan wani business. "Ban sani ba. Na ce ban sani ba shashshar banza da wofi. Ke ba ki da aikin yi sai harkar kasuwanci da neɓan kuɗi da fakewa da kina taimako, amma 'yarki ɗaya kin kasa ba ta tarbiya kin kawota ta zame mini ƙadangaren bakin tulu." Sai ta sauke ajiyar zuciya tana huci don ji take kamar ta jawota cikin wayar ta rufeta da duka. "Na shiga uku! Waya taɓa mini ke, mai Jannah ta ƙara yi?" Ta tambayeta tana kallon dad da yake lissafi a laptop ɗinsa jina bin da take faɗi ya sa tsaya da aikin da yake yi. "Ba ma wannan ba don ba shi ta sa na kira ki ba. Halimatu ni na haife ki ko da cikina kuma na yi ɗawainiya dake har kika girma ko?" Tambayar ta yi mata banbarakwai wai namiji fa suna Hajara amma sai ta daure ta ce, "Eh ke kika haife mini kuma ina alfahari da hakan. Lafiya Hajiya Baaba, mai ya faru, me ta aikata? Don Allah ki fahimtar da ni duk kin sanya ni cikin ruɗu kaina ya kulle sosai." "Kuma na isa dake har da mijinki ko?" Sai ta ƙara ba ta mamaki ba ta amsa mata ba ta tsaya tana kallo dad da ya ji tambayar don ya ji mai zaice. Ganin ya ɗaga mata kansa ta bata amsa. "Eh, yana jinki kuma ya tabbatar mini da hakan don Allah ki sanar mana da abin da ta aikata." "Alhamdulillahi! Na gode. Dama auren jannah nake nema wa Ajmal, kune dole na nemi izininku amma Adamuu na isa da shi tun da na haifi ubansa." "Gabakiɗaya ɗakin suka haɗa baki gurin faɗin, "Meee!" Da ƙarfin gaske. Sai mom ta ci gaba da tambayarta tana cewa, "Lafiya mai ya faru da za ki yamke hukuncin nan? Na ga ko shekara bai rufa da aure ba, matar tasa ko mutuwa ta yi? Mai ta aikata miki da za ki yanke wannan ɗanyar shawara na yi mata aure da ƙuriciya." "Ai ina tunanin kunji tun da ku ɗin ba kurame bane, sai ku fara shiri za a yi tare da na Nahlin." Ta kashe wayar ta ije akan gadon ta bar mom cikin tsananin ruɗani. Ganin yadda suka yi cirko-cirko kamar ruwa ya cinye su, doctor Irfan ya kwashi kayan aikinsa ya fice daga ɗakin yana mamakin rigimarta, domin a ganinsa an wuce wannnan zamanin. Ajmal ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye. Ba tunani yake yi ba domin ya rasa mai zai tunani don jin abin da ta furta yake kamar wasa. "Aure kuma wai ni Jannah?" Kai in ba da ni take yi ba wataƙila ban ji abin da ta ce da kyau bane." Ya tambayi kansa cikin shakku tare da bawa kanshi amsa. Idanunsa ya ɗaga yana kallonta da ta yi masa ƙuri sai harararsa take yi. Ya ƙara nazarin fuskarta don ya tambatarwa kansa wasa take, amma sai ya ga sam babu alamar wasa a fuskarta duba ga yadda ta ci magani sai huci take tamkar mesa. Ƙafafuwarsa ya ji suna ƙoƙarin bijirewa ɗawainiyarsu. Idanunsa suka canza daga fari tas zuwa ja tamkar an zuba musu jar bula. "Amma dai wasa kike ko Hajiya Baaba ko kunnuwana ba su ji mini abin da kika faɗa bane? Kai zai fi dai wasa kike domin ba ni da matsalar ji kuma daidai na ji." "Wasa nake yi in dai ina wasa da ubanka, don na wuce na yi wasa da kai sai dai ubanka ga yi nan." Ta ce tare da tamke fuska tana harararshi. "Ina Allah ya kyauta over my dead body. Ni na auri wan can abar? Ji beta ba bu tarbiya tana ji da siranta kamar taɓarya. In ma dai ba wasa dani kike ba to yau kin fara don babu yadda za a yi ni Sheshk na auri 'yar bariki kamar ta." Taso wa ta yi cikin zafi tamkar za ta mare shi sai dai kuma rashin ƙarfin jikinta da ciwonta ya sa ta koma ta zauna tana dafe kai. "Wash Allah! Wallahi Allah sai ya saka mini. Haka kawai ina zaman zamana ku fasa mini goshi, saboda mugunta ai za ku gani a ƙwaryarku." Sai Kuma ta ƙara gallah masa harara tana faɗin, "Idan mazan duniya take raba jikinta wallahi sai ka aureta, in dai ina raye." "No impossible! Ke ma Hajiya kin san babu yadda za a yi ki haɗa auren Jannah da Ya Ajmal, they're not compatible at all, kuma yaushe ya yi aure.." "A gaban iyayenki Hafsatuu, kike kallon tsabar idanuna kina gaya mini ban isa ba, ashe har wuyarki ya isa yanka haka? Ina miki kallon mutuniyar kirki, ashe kura ce da fatar akuya.." Sai ta fashe da kukan da babu hawaye har tana jan majina. Ta juya ta kalli Ajmal tana zare idanu."Kai har kana da bakin cewa ba za ka aure ta ba, saboda ba ta da ƙiba? Ashe babu daɗi aka mannawa ɗana kullum yana wahala a kanta, amma babu amfani. Mene ne banbancin ta da uwarka da duk sati sai ana yanka rago amma kullum kamar ana ibanta ana miya? Kai har kana da bakin yi wa wani gori." "Ka ga ni ko! Ga shi nan saboda baƙin zuciyarka sai da ka je ka rafke ta a ka gashi nan ka taɓa mata ƙwaƙwalwa ta taɓu. Ka ja mana bala'i da masifa, don tana da hankali ya muka ƙare ballantana ta taɓu. Bari na kira likita ga duba mana ƙwaƙwalwarta tun kafin ta fara duka." Ta faɗa tare da nufar ƙofar ita kuma har ga Allah da gaske take yi, saboda in ba hauka ta yi ba babu yadda za a yi ta furta haka. "Ke mara kunya dawo. Ba haukacewa na yi ba sama nake cizo. Ko asibitin mahaukata ne ni. Kar ki kira likita mota za ki ɗauko ku kaini dawanau. Shashashar banza mara kunya. Ki bari nan da wata uku in kin tare a gidansa sai ki gane hauka tuburan nake yi." Cak ta tsaya jim ba ta juyo ba sai kuma ta jiyo tana wani irin murmushi. "To indai da hankalinki wasa kike yi don babu yadda za ayi kamata ni babbar yarinya 'yar uwa ba da mama na auri wannan bagidajen. To wai duka shekaruna nawa da za ki yi mini maganar aure, ki bari karki ɓata ni." Ta ce cikin ɓacin rai. "Bariki zan kai ki mara kunya. Lokacin da kika kira saurayinki kina kashe murya da salo na jan hankalinsa kin san ni na koya miki. Duk kalle-kallen da kike yi na fitsara kin san ni nake turo miki. Ai ni nafi na yi wasa dake sai dai da mai dattin hula." Ta ja nu fashi tare da ɗora TO MASU KARATU KUNA TUNANIN ANYA ABIN DA HAJIYA BAABA TA ƘUDIR DON ƊAUKAR FANSA ZAI YU? DUBA GA BAMBANCIN RA'AYI DA TSARIN RAYUWARSU. KU DAI CI GABA DA BIBIYAN LINTATTFIN "KURA DA FATAR AKUYA" KAR KU BARI A BAKU LABARI. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 21-22* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "To tsaya kiji da kunnin basira auren ku babu fashi sai dai ina mutu." "Abu mai sauki saina saka miki gubar matuƙar kika ce za ki aura mini shi." "Wayyo na shiga uku na mutu ba zan ƙara zama dake ba, kuma dole Halimatuu ta dawo cikin satinnan, ta ɗauke masifa da bala'in da ta kawo mini, don na tabbata za ki iya kashe ni saboda ba imani kike da shi, wanda baya sallah sai ya ga dama ina imani a ransa. Daga can a tattaraki akai ki gidansa kin ga sai ku kashe kanku in kun so." Bilhaƙƙi take kukan tana kallon mutanen ɗaki. "Ai kuka yanzu kika fara matuƙar ba ki janye ƙudurinki ba, kuma ko baki faɗa ba dole na koma gurin iyayena." "Ba ki da wannan hujjar na tursasa ni na aure ki don ba ki da iko da mu." Cewar Ajmal yana mata mugun kallo. "Amma na isa da iyayenku, da suka haife ku ? Ni da ku mu zuba shege ka fasa." Har ya buɗe baki zai yi magana Aby ya daka masa tsawa. "Abin kunyar da za ku yi mana kenan? Kamar ƙananan yara haba Hajiya bai kamata ki biye musu ba saboda yara ne su." "Allah Sarki! Da ma laifina za ka gani, tun da ni ba ni da iyayen da za su kare ni duk sun mutu." Sai kuma ta ƙara saka kuka." Allah ya jikan ku iyayena na san da kuna raye da kun kare ni. Allah ya jiƙan ku da rahma domin yau ga ranarku." "Don Allah mu bar maganar nan mu tafi gida zai fi a sasanta kammu a can." "Sasancin kenan ayi auren tun da na faɗa kai ma ka san babu uban da ya isa ya hana sai dai in Allah bai kaddara ba." Lamarinta sai ya ƙara bawa kowa mammaki. Ammy ta ka sa cewa komai sai jinjina lamarin take yi domin ta san tun da ta furta sai wani ikon Allah, kuma in har ta sanya aka yi auren ba ta yi ma su duka ukun adalci ba. Da wani idon za ta kalli iyayen Mushiirat akan ɗan su zai yi wa 'yarsu kishiya auren da ko shekara ba a rufa ba. Sannan ita kanta Jannah ba da take karatu bai kamata ayi mata aure da wuri ba, uwa uba da ba ta da ra'ayin auren miji irin sa. Ga Amal da ya tsane ta da halayenta sannan ta ya ya zai fuskanci matarsa da maganar. "Kai ina hakan ba zai taɓa yiwuwa ba!" Ta furta cikin tashin hankali tana girgiza kanta. "To amma wa zai hana?" Ta tambayi kanta cikin tsananin ruɗani wanda in dai babu lallain akwai sauran rina a kaba. Hajiya Baaba ta miƙe ta bangaje Ammy dake tsaye a gefenta wanda ya sa ta yi saurin matsawa domin ta yi hakanne don ta tofa albarkacin bakinta ta ƙara baƙin jini a gurin ta. A ranta ta yi alƙawarin ko tari ba za ta yi ba in suna maganar, ita dai na ta kallo da fatan alkhairi. Da sauri ta matsa gefen tana kallonta. Tun da Abby ya tsawatar babu wanda ya ƙara ko tari har suka shiga mota, sai dai Hajiya Baaba da take dafe bandejin da aka lulluɓe mata ciwon da shi, tana musu Allah ya isa don rabonta da ta ji ciwo har ta manta. Ko da suka isa gida Aby ya hana kowa tafiya aka zauna a falon Hajiya Baaba don yin taron gaggawa. Tsaki ta yi ta zauna tana faɗin,"Ko me za ka faɗa a taron oho, bayan na riga na yanke magana kuma babu fashi." Ajmal ya ɗago idanunsa yana kallonta ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu kowa ma ya huta, domin da ya san in ya dawo abin da zai faru kenan, da ya tabbata acan har duniya ta naɗe in ya so matarsa ta bi shi can. Tun yana yaro take shigar masa hanci da ƙudundune ga shi ba ta sake zani ba, rana tsaka tana ƙoƙarin shigo masa da wata aba can, wanda ko a tarihin mafarkinsa bai taɓa tunanin rayuwa da ita ba, ballantana a zahirce, don haka a ransa ya sanya ayi abin da za a yi mahaukaci ya ɗauki rigar kurma, ai maganarta ba ta Allah ba ce. "Kai ina ba za ta taɓa yiwu ba bindiga a ruwa. Da wane ido zan kalli abokanaina da mutane na nuna ta amatsayin matata ina matsayin malami, sai ta nemi aura mini 'yar tasha. Yariyar da ko Kur'ani ba ta sauke ba ballantana aje maganar hadda da manyan littafai." Ya furta a cikin ransa zuciyarsa a dagule. Ummu ta ɗago tana kallon Jannah da ba ta wani damu ba, domin ta ɗauki maganar kamar wasa gani take ba ta da right ɗin da za ta yi mata auren dole. Tausayinta da na Huzaifah suka sanya hawaye taruwa a gefen idanunta, musamman Huzaifah da ya mutu akan sonta, ba shi da buri sai dai maganar aurensu. Kallon tausayi ta ƙara mata lokacin da ta ga sai danna wayarta take ba tare da damuwa ko da yake za ta iya mata uzuri don ba ta san wace ce Hajiya Baaba ba, don in har ba'ayi auren ba za ta iya iƙirarin tsinewa iyayensu wanda ba za su so hakan ba. Ba tare da ta sani ba hawaye suka fara shatata a fuskarta. "Kai this is absolutely impossible! Auren nan ba zai taɓa yiwu ba. Huzaifah shi ya dace da ita kuma yana matuƙar ƙaunarta, don Allah Hajiya Baaba ki tausaya rayuwarsu." Cikin zafin nama ta yi kanta za ta zabga mata mari. "To don uwarki sai ki hana in kin isa ba wai ki tsaya kina zagina da turanci ba don kin ga ban yi boko ba. Akan me gida bai ƙoshi ba za a bawa dawa." Da sauri ta matsa bayan Ajmal ta ɓoye domin ita ba ta san maganar zuci ta fito fili ba. Miƙewa ta yi tana gyara zaninta."Wallahi kun ji na rantse in har ni na haifi Muhammadu sai an yi aure nan, don haka ban ga amfanin taron nan ba, in dai ba so ake na sanya fitinar dole a ɗaura a yau ba." Ta ja numfashi tana girgiza tare da balla ma Jannah harara da ta ɗago ido tana kallonta tana dariya domin har yanzu ba ta ɗauka da gaske take yi ba. Ba tare da ta kula da bidiyon da take mata ba ta ci gaba da cewa, "Idan Jannah ba ta da hali da tarbiya ni ina sonta a haka, kuma in bai rufa mata asiri ya aureta ba wa zai aure ta. Kai Muhammadu a gabana kake nuna ba ka son haɗa zuriya da 'yar ƙanwarka wanda kuka rage mini ku biyu tal a duniya, sai na ce sam ba ka yi wa Halimatuu adalci ba. Ka ƙi aminta da auren 'yarta ɗaya tal aduniya." "Haba hajiya na gaya miki ki daina ce mini bani da tarbiya. Sai wani maganar aure aure kike yi, kin san babu yadda za a yi ni kamata ace wai zan auri ustazu kuma mara wayewa. Wallahi ko driver ba zan iya ɗaukarsa ba domin tuƙi zai rinƙa na rashin wayewa. Abin kunya ne na gaya wa frinds ɗina wai zan yi aure da mijin da zan aura. Wato irin rayuwar gidadancin da matarsa take yi kullum cikin ƙumbiya-ƙumbiya da hijabi da safa da niƙabi kike son na je na yi? I know values, noms, and dignity.." "Rufe mini ba ki banza kawai! Kunyar gareki? Kamar kin ci ƙwadun ɗan akuya haka kike. Ga yi nan tun ba a je ko ina ba kin fara girban abin da kika shuka domin kan idonki ake nuna ba a son rayuwa dake, ko shi Huzaifah da kike cewa yana sonki, ba za ku daɗe ba zai wartakoki ki zama ƙaramar bazawara saboda rashin kunya da mugun hali irin na ki." "Ai gara na yi rayuwar zawarci da rayuwa da wanda kike son haɗa ni da shi, ballantana na san Huzaifah yana mugun sona ba zai yi mini haka ba. Kune dai kuka ɗauki mace baiwa kuna ganin in har ba ta iya girki da kula da miji ba ba za ta iya zaman aure ba, amma shi kansa a waye yake ya san 'yanci da hutu." Ta ce ba tare da shakku ko kunyar wani daga cikinsu ba. "Tsakanina dake fa duka kawai ya rage amma kin daɗe da zageni tatas, domin duk wanda ya ke mayar maka da wannan maganar watarana duka zai kai maka. Ai ni dai wallahi Halimatuu ta haifar mini jaraba." Banza ta yi da ita ba ta ce komai ba sai kaɗa ƙafa take yi cikin tsantsar rashin kunya da fitsara. Ajmal ya yi shiru ya ma ratsa mai zai ce domin rashin kunyar da take yi ji yake kamar ya maƙure ta. Allah ya gani shi mutum ne mai tsananin son girma da kamun kai sam baya ƙaunar rashin kunya. Ko Mushiirat da take matarsa akwai lokacin da baya sakin mata fuska, ballantana ita da Hajiya ke son jawo masa raini ta haɗa su aure. Ai da ya yi rayuwar aure da ita ya gwammace ya mutu ba tare da aure ba. Duk rashin kunyar da take zuba wa sai ya zuba mata idanu kawai, burinsa ta fahimci wacce take son haɗa rayuwarsa da ita. In kuma ta yi gigin haka watarana sai dai a kawo musu gawarta domin bugu ɗaya zai aika ta lahira. Miƙewa ya yi zai fice sai ya tsaya gab da ita ya fara da cewa,"A haka kike faɗin na auri 'yar da ba ta ganin ki da gashi? A haka kike son na kwashe ta na kai gidana Hajiya Baaba? In har kika yi mini haka sam ba ki yi mini adalciba ni da matana da muke zaman lafiya. Ina roƙonki tun wuri ki janye maganar auren nan kafin na canza mafa kammanni na yi wa wanda za ta aura asara don ni ko da gida da mota ba zan karɓa ba, saboda na tsane ta bana son ta ko mai kalarta ba na son gani." "Aikin banza na san dai mugun halinta ka tsana amma ba Jannah da take son kowa ƙin wanda ya rasa ba, don ta fi matarka mai kama da doya. In dai don halinta ne ai hannunka ba ga ruɓewa ka yanke ka yar." Ya buɗe baki zai yi magana sai ya kasa ya girgiza kansa idanunsa suka kawo ruwa ya fice daga cikin gidan. "Na riga na gama magana kowa ya fice mini daga ɗaki kuka yi mini tsuru-tsuru kamar wacce ta yi ƙarya ko sata, in kuma sata na yi sai a gaya mini abin da na sata na biya." Ta daka musu tsawa tana faɗin hakan daidai lokacin da Aby ya miƙe ya bi bayansa amma ina har ya tada motar ya figeta cikin tsananin fushi. Sum-sum suka miƙe suka fice ban Jannah da ta dawo gabanta ta tsaya bayan ta ije wayarta akan kujera. Kallon uku saura kwata ta yi mata tare da miƙe wa. "Bari na je na yi sallah don na ga kamar rigima kike ji ko da yake sallar ba ta dame ki ba sai kin ga dama." "Idan bana yi ma ba damuwarki ba ce Hajiya Baaba, tun da na ga ba tare za a rufe mu ba." Ta bata amsa tana girgiza ƙafa tare da ƙara shan gabanta bayan ta fara tafiya. "Allah ya tsare ni da mutuwa a rufe mu tare, domin wallahi na san duka da suburbuɗa za ki sha a hannun walakiri, kin ga kuwa da a rufe mu ta shafe ni, gara a barwa tsutsotsi naman jikina suyi watanga da shi." "Wannan kuma ke ya shafa ba ni ba ai, in kin so ki barwa Kuraye ko a kwalar rigata." Ta ce mata tana girgiza. "Jannah ki fita idanuna domin kin san Allah in kika cika ni zan iya zane ki da carbin nan yanzu. Kin san ke kaɗai kike mini fitsara a gidan nan na shanye da wata ce da tuni na yi ƙulin kubura da ita, ke ɗin ma albarkacin uwarki kike ci duk da albasa ba ta yi halin ruwa ba." "Ai wallahi fitsara yanzu na fara matuƙar kika ci gaba da haɗani da wancan bagidajen. Ina 'yar minister ki rinƙa haɗani da shi, ai ni sai dai na auri ɗan shugaban ƙasa ko gwamna." "To shikenan, sai mu zuba ni da ake shege ka fasa. Ai da uba ake ado ba uwa ba, sai ki gaya mini me ubanki yake da shi? Shi kansa rakuɓewa ya yi jikin 'yata yana cin arziki, don haka baku da komai." "Allah ya kyauta kuma ya fi ƙarfin ki kira shi makwaɗaicin tun da duk abin da yake samu a jikinta aiki yake mata da guminshi yake." "Jannah ki matsa na yi sallah ga shi can an tada sallah kafin na fasa bakin rashin kunya." Harara ta zabga mata jin me tace sai kuma ta ja gefe ta matsa tana huci. "Ko da yake sam bai kamata na tada hankalina ba, domin dad shi yake da ikon aurar da ni, in kuma na ce bana so babu wanda ya isa ya yi mini dole, ko ita 'yar taki a ƙarƙashinsa take." Ta faɗa tana zauna wa a kan kujera. "Au haka kika ce? To zan nuna miki wannan makwaɗaicin uban na ki ba shi da kataɓus 'yata ta mai da shi mijin-ta-ce ta shanye shi da kuɗinta. "Dama tuntuni nake zargin da saka hannunki mom take yi wa dad wulaƙanci ga shi nan zargina ya tabbata." "Ba dole ta yi mishi ba ai duk wanda ya hau motar kwaɗayi a tashar wahala da ƙasƙanci zai sauka." Ta amshe maganar. Haushin abin da ta faɗa ya sa ta saka kuka tare da ɗaukar wayarta ta fice daga falon ta yi sashin su Ummu tana jan majina. "Wawiya wacce ba ta san me yake mata ciwa ba, har wani ƙarfi uban na ki yake da shi da za ki alfahari da shi. Ma gani Allah ya kaimu su dawo sai ya haɗa auren in zai iya." Ta shige bayi tare da kunna famfo. LONDON "Kai ni fa wallahi kaina ya ɗaure! Wai mai ke faruwa ne, mai ya sanya Hajiya Baaba za ta yanke wannan ɗanyen hukuncin? Gabaki ɗaya na shiga cikin ruɗani!" Ta furta tana jin yadda kanta yake sarawa tamkar ana buga mata guduma, domin ji take kamar ta rufe ido ta ganta a Nigeria. "Rose, please give bottle of water and paracetamol." Ta ƙwalawa Rose kira tana faɗin haka tare da dafe kanta tana kallon dad da ya kasa cewa komai sai karanta wasiƙar jaki yake tun bayan da ta kira wayar. Karɓar maganin ta yi ta ɓalla ta watsa a bakinta ta kora da ruwa tare da shanye ruwan kofin tas, sannan ta ƙara miƙa mata akan ta siyaya mata, wanda sai da ta shanye duka, domin ji take bakinta ya bushe babu ko ɗigon miyau. "Shin wane irin lamari ne take shirin ginginmo mana gabagaɗi babu shawara? Wani abu ta yi mata, ko kamata ta yi tana harkar banza." "Never! Karki ƙara danganta 'yata da wannan." Ta ji muryar dad ya daka mata tsawa yana faɗin hakan. Kallon shi ta yi ba ta ce komai ba ganin yadda yake tada jijiyan wuya. "Na san wace ce 'yata, na san me zata aikata." Ya ƙara faɗi tare da komawa ya zauna. Takowa ta yi zuwa inda yake zaune yana huci ta kama hannunsa tare da zama a gefen kujerar. "Jannah fa 'yarmu duka kuma mafi soyuwa a garemu. Kawai na shiga ruɗu ne ya sa na faɗi hakan. Wataƙila ba ta gana sanin wace ce ita ba shi ya sa take son gingimo abin da zai sanya ta kasa zaman lafiya, domin mundin ta tursasa auren nan sai Jannah ta zamo sanadinyar wargaza zumuncinmu da Ya Muhammadu. Sam jannah ba matar da za a nema wa wani bane, don ko wanda take so ya aure ta sai ya yi matuƙar kai zuciya nesa zai iya zama da ita." Saki ya yi ya kauda kansa bai ce mata komai ba domin duk laifin ta yake gani don ita ce ta ɓata komai kuma ta ruguza komai. "Kai ina jin Hajiya Baaba wasa take mini, ko kuma ta yi hakanne don na dawo da tunna ta kasa ba sanar dani dalilin son aurar da ita. Miƙewa ya yi bai ce mata komai ba zai shige ɗakinsa. "Please injiniya, say something don't go." Ta kama hannunshi tare da marairaice fuska tana faɗin hakan kamar za ta yi kuka, wanda ya sa ya koma ya zauna tamkar umurni ta yi mishi amma bai ce komai ba zuwa can ya ce, "I was very surprised Halima, ace kin iya buɗe baki kina faɗin 'yarmu doesn't has table manners." Kanta ta dafe jin abin da ya ƙara faɗin tare da furta "Ya salam! Please understand me, I didn't mean that." "Even if you mean it, ai duk laifinki ne da kika kasa bata tarbiya, saboda rashin yafiya kika gudo da ita Ƙasar da take da bambanci da addininki da al'darki. I really regreted the day I came to stay with you." Ya ƙarashe maganar yana kallonta cikin ɓacin rai tare da ɗorawa da cewa, " Na san wace ce Hajiya Baaba na san artabun da na sha da ita, in har ta ce za ta yi babu wanda ya isa ya hana ta. Baba Bukar ne kuma ba shi a duniya. Sam ba zan ja da maganar ta ba, domin Jannah ta samu miji kamar Ajmal abin alfahari ne a gare ni, kuma sannan ina son ta auri ɗan ɗan'uwanki saboda za ki fi jin zafin rashin bata tarbiyar da ba k.." "Enough injiniya, saboda na nemi shawarar ka sai ka fara gasa mini maganganu? Kuskure na riga na yi kuma ba zan iya gyarawa ba, don haka ban ga amfanin zama kana gasa mini magana kamar 'yarka ba." Ta nisa tana share zufar da ya keto mata a goshinta tare da faɗawa kan kujera ta rintse idanunta, saɓanin da take tsaye tana magana cikin tsananin fushi. "Har kana da bakin faɗin haka? Bayan kaine sanadin da ya sa na baro Ƙasata nake rayuwa cikin kewa da ƙunci. And now you have the audacity to say that to me?" Ta dasa aya da tambayar haka sai kuma ta ja tsuka ta ɗauki wayarta ta shige ɗaki. "Please am sorry, I exceeded my boundaries. Perdon me, I couldn't do it again, but you know the way we raised her wasn't the right way, we should have inculcated good morals to her." "Is fine ya wuce, amma yanzu bai kamata mu tsaya wannan maganar ba, mun riga mun yi kuskure. Maganar auren ta ya ke damuna, I really don't know what to say." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 22-23* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Ina ga we have to sleep on it. Kin san ta don haka mu yi gaggawar komaw.." Bai ƙarashe maganar ba kiran Jannah ya shigo wayarsa, sai suka kalli juna a tare. Zuciyar mom cike da jin daɗin ba ita ta kira ba, domin ta san sai ta gaya mata maganar da za ta kasa bacci da kuka. "Hajiya Baaba ta kira mana ruwa fa." Ya faɗi daidai lokacin da mom ta yi hanyar ɗakinta da sauri tana faɗin, "Ba ri na shiga ɗakina sai ku ƙarata can ba zan iya da rigimarta ba." Cikin sanyin jiki ya sanya wayar a kunninsa bayan ya yi sallama. wanda ko sallamar ba ta amsa ba ta fara faɗin, "Dad, could you imagined wai ni Hajiya Baaba, said that she will gonna give my hand in marriage to Ya Ajmal, as young as I'm, wallahi I really hate him cus he is not civilized at all." Ta ƙarasa maganar tana ƙuta. Shiru ya yi don ya rasa me ze ce mata sai ya tsinci kansa da faɗin,"Never and impossible! Sam ba zan taɓa miki auren dole ba, kuma ba za ki yi aure yanzu ba sai kin cika burinki." "Haba! I wander, ai dama na san wasa take yi mini domin ba za ka taɓa yadda ba, amma sai ta ce mini wai you are so greedy you most agreed." Ta katse shi tana faɗin haka. Maganar ta soke shi har sai da ya rintse idanunsa, yana jin zafi a ransa ba tun yau ba ya san ta tsane shi ba ta son shi, musamman lokacin da lamarin ya faru abubuwa suka rikice." "Kar ki damu ki kwantar da hankali ki saurari dawowarmu, muna dawowa za mu koma gidammu." "Ai dama ban damu ba, kawai she is pestering me, shi ya sa na ga I have to give you a call, duk da na san shi doesn't has authority on me. Please dad take care you of youself I love you." Ta kashe wayar tana murmushi. Kalmar da ta faɗi suka rinƙa masa kuwwa a kunninsa sai ya dafe kansa cikin jin tausayinta. "Ba ki san wace ce Hajiya Baaba ba, domin ba ki da mafita da ya wuce auren nan." Jannah ta sauke wayar tare da ajiyar zuciya mai ƙarfi ta kalli Nahlin da Ummu da suka yi zugum ta ce,"Da ma na gaya muku wallahi ba ta isa ba. Haba ita ɗin wa, don kawai ta haifi mom sai ta ce za ta juya kowa." Miƙewa suka yi suka kalli junansu sannan suka shige ɗaki ba su ce mata komai ba, wanda ganin haka ya sa ta taɓe bakinta ta nufi sashin Hajiya Baba fuskarta a ɗaure babu ko walwala. A falo tana ƙoƙarin shiga cikin ɗakinta daidai lokacin da ta fito daga bayin falon da abu ƙulle a baƙin leda da ƙatuwar roba a hannunta. "Yauwa Jannahtu zo nan, dama yanzu zan sanya a yi mini kiranki, saboda tun yau zan fara miki wankan lalli saboda babu lokacin, don zamaninmu biki tun yana kusan wata bakwai ake farawa wa, ga shi ke duka ba za a sanya da nisa ba don ba zai wuce wata uku ba, don haka gara mu fara tun yanzu." Har ta murɗa ƙofa za ta shige ɗakinta duk da ta ji kiran amma kuma sai ta fasa jin abin da ta ce. Idanunta ta waro mata cikin ɓacin rai daidai lokacin da ta ƙaraso gabanta tana juya ruwan lallin da hannunta. "Kin ganshi lalli ne mai kyau daga barno aka kawo mini shi ina ƙunsawa, yanzu dole na yi waya a kawo mini buhu don sai ya ƙare kafin bikin." Ta sa aya tare da ibo ruwan lallin za ta goga mata a fuska, wanda ya sanya ta matsa da sauri tana kallon shi kamar kashi tare da toshe hanci. "Kin san Allah Hajiya Baaba, kar ki kuskura ki watsa mini wannnan abu mai kama da kashi a jikina, kuma ki bar maganar auren nan you are hurting my feelings, bana so." "Dukana za ki yi? Ke fa daɗina dake ba a miki abin arziki kina sane da gidan kishiya za ki sai kin sha gyara kar kije ki zama mowa." "Na ga alama kin taɓu sai an kai ki gidan mahaukata, ƙila kuma aure kike son yi sai ki samo bazawari tsoho, na san su mom ba za su hana ki ba." "Kiji mini tsiya ni kike faɗin ma haka? Aure ko a lahira na haƙura da shi in dai ba Aminu masoyina za a ba ni. Ki kalli tsabar idona kice mini na taɓu, bari na nuna miki haukar." Kawai ta ibo ruwan lallin mai yawa ta watsa mata a jiki har da fuska, wanda sanyin ruwan lallin ya shigeta sai ta ƙwala ƙara da ƙarfinta har sai da gidan ya ɗauka, wanda ya sa duka mutanen gidan suka sheƙo. "Mutane za ki tara mini don ubanki daga miki abin arziki?"Ta tambayeta tare da toshe kunninta domin ƙarar ya shige har ƙwaƙwalwarta. "Wallahi sai Allah ya saka mini da kika ɓata mini rigar da Huzaifah ya ce tafi kowane kaya yi mini kyau." Ta ce daidai lokacin da mutanen gidan suka ƙaraso a guje. Lafiya Hajiya Baaba, mai ya faru?" Aby ya tambayeta cikin tsananin razana yana kalon Jannah da ke kuka shaɓe-shaɓe. Ba ta ba shi amsar tambayarsa ba ta buge mata baki tana faɗin, "Da maganar wani a kanki kike kiran wani gardi? To me ya rage tun da na riga na tambaya masa kawai auren ya rage, ga sadaki a hannuna yanzu ma zan iya bayarwa" Sai kuma ta kalle su da suka yi jugum-jugum suna kallonta. "Au kuji mini ja'ira dama kin yi ne da biyu don ki tara mini mutane?" Sai ƙara kallon Aby da yake jin damuwar zuciyarsa ta fi ƙarfin ƙwaƙwalwarsa ta ce, "Ni da wannan da ba a mata abun kirki don kawai zan fara mata wankan lalli, shi ne take ci mini mutunci har tana kirana da mahaukaciya shi ya sa na nuna mata ƙarshen haukar. Da yake ita shashasha ce, ba ta san inda ke mata ciwo ba, ai ban gyarata a kwai matsala, tunna gidan kishiya za ta amma tana mini rashin mutunci, ai dole na fara gyarata ta zama mowa ko?" Ta ƙarashe maganar da sigar tambaya tana kallonsa wanda takaici ya hana shi cewa komai sai dai ya ɗaga mata kansa kawai ya fice yayin da sauran suka rufa masa baya. Jannah ta galla mata harara za ta bi bayansu wanda da sauri ta janyo rigarta ta dawo da gabanta tana faɗin," Da wo nan babu inda za ki aini da ke mutu ka raba don ko auren aka yi, mutane na watsewa zan tattara inawa-inawa na dawo gidan. Hannunta ta fisge ta gallah mata harara ta yi cikin ɗakinta tare da bugo ƙofar kamar za ta ɓalla. "Allah Sarki kofa, ba ita ta kar zomon ba rataya aka ba ta." Ta juya ta shige ɗakinta tana mita. Cikin sanyin jiki yake tuƙa motar tamkar wanda aka zarewa lakka har y isa gida ya yi hon. Maigadi ya taso ya buɗe masa yana jiran ya shigo da motar, amma sai ya fahimci ya yi nisan kiwo, domin bai san ya buɗe ba. Tunani ne barkatai a ranshi wanda ba shi da hanyar ɓullo musu. Rintse idanunsa ya yi yana jin tsananin tsanarta yana ƙara samun matsuguni a jikinsa, don sai yanzu ya gane dalilin tsanarta da ya yi matuƙa, saboda tun da ta zo ya kalle ta kwata-kwata ba ta yi masa ba. Ganin ya yi nisan kiwo ya sanya maigadi ya bubbuga gilashin motar wanda ya sanya ya yi firgigif kamar mai bacci. A hankali ya shigo da motar kamar baya son shiga gidan daidai lokacin da Mushiirat ta fito da dogon hijabinta har ƙasa da carbi a hannunta tana ja. Jim ta ɗan yi tana kallon yanayin fuskarsa kafin ta ƙarasa gurinsa. Kamar yadda suka saba duk lokacin da ya dawo sai ya miƙo mata hannu sun yi sallama suna sakar ma junansu murmushi sannan ya yi hugging ɗinsa. Sai dai, yau ita ta fara miƙa masa tare da kwanciya a jikinsa. "Barka habibina, you took more than the time you said." Ta ce cikin shagwaɓa tana shafa gefensa da ya sha gyara sai ɗaukar ido yake. "Am sorry." Kalmar da ya iya furtawa kenan sai ya matsar da ita daga jikinsa zai shige cikin falon cikin rashin ƙwarin gwuiwa, saboda wani irin tausayi da ta ba shi. Ta bishi da kallo har ya shige wanda hankalinta ya yi matuƙar tashi sosai take ta fara tambayar kanta lafiya, amma rashin masa ya sanya tabi bayansa lokacin da ya shige ɗakinsa. "Bab, what's wrong, are you alright?" Ta tambaye shi lokacin da ta rufe ƙofar tana ƙarasowa gurinsa. "Yes I'm, kamar kaina yake son ya yi ciwo bari na watsa ruwa. May be I will better." Ya ce tare da miƙewa zai shiga bayi ba tare da ya kalle ta. "Oh no please, yaushe muka fara ɓoye abin da ke damunmu a tsakaninmu? Don Allah ka gaya mini na shiga damuwa." Ta ce tare da riƙe hannunsa. "Na ce miki kaina yake ciwo." Ya faɗa murya a kausashe yana ƙoƙarin shigewa. Da sauri ta tari gabansa tana kallon idanunsa."Gaskiya ni ba zan yafe wa kaina ba, matuƙar ban ɗauke maka damu.." "Ke!" Ya daka mata tsawar da ta firgita ta, wanda ya sa ta saki hannunsa da sauri ta matsa gefe tana zare ido don har hawaye ya fara sauka fuskarta, saboda za ta iya rantse wa yau ne farko da ta ji ya daka mata tsawa. "Haba na gaya miki babu komai, amma you keep asking let me be." Ya ce tare da ƙarasa shiga cikin bayin. Sharaf ta zauna a gefen gadon tare da saka kuka, dama tun da take kiran wayarsa bai ɗaga ba ta san akwai abin da ke faruwa. Lokaci guda ta fara tunanin abin da zai iya ɓata masa rai haka ya kauda ɗoki da zaƙuwar da yake ta yi ya dawo sun kasance a tare. Miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin ta nufi na ta tare da mayar da ƙofar ta rufe. Bayi ta shige ta ɗauro alwala ta fito har ta zauna a ɗakin za ta fara karatun kur'ani, sai ta miƙe ta fasa karantawa a ɗaki ta koma falo. Ganinsa zaune da kur'ani amma ya kasa karantawa ya sa ta ji matuƙar haushinsa, domin ya karya alƙawarin da ya yi mata na cewar duk abin da yake damun ɗayansu za su kashe su rufa. Zama ta yi akan kujera maimakon inda yake zaune wanda ya ware don karatu wanda ya ke cike kur'anai da littafan addini. Cikin murya mai sanyi ta shiga rera karatu da ƙira'ar hafsi, yayin da wani lokacin take satar kallonsa da ya riƙe kur'anin ya lula duniyar tunani. Idanunsa suka canza tuna maganar auren da Hajiya Baaba take son ƙababa masa na yarinyar da sam ba ta dace da rayuwarsa ba. Da ya kalleta yadda ta kame tana karatu cikin natsuwa sai ta ba shi tausayi, domin ya san duk inda macen ƙwarai take ta kai saboda duk da kasancewarta nurse bai taɓa mata ƙorafi akan rashin kula da cikinsa ko haƙƙinsa da tsafta ba. Sosai take dagewa gurin faranta masa rai, wanda yake ganin bai kamata ace mar'atussaliha kamarta za a yi mata kishiya ba. A hankali ya fara karatun cikin muryarsa mai daɗin gaske. Mushiirat sai ta ji ta kasa cigaba da karatun domin muryarsa ta tafi da tunaninta da duk wata natsuwa ta shi. A kullum tana godewa Allah Ubangiji da ya ba ta shi a matsayin miji, domin shi ɗin mijine na nuna wa tsara wanda ya iya tattalin mace da ba ta duk wata kula da take buƙata. Babu abin da yafi burgeta a gareshi yadda yake da addini da kamun kai, komai na shi cikin tsari da natsuwa da koyi da Annabi. A kullum burinta Allah ya ba su 'ya'ya masu albarka wanda za su tashi cikin koyi da ɗabi'un mahaifinsu. Ganin ta yi nisa cikin tunani ya sanya shi rufe ku'anin bayan ya yi addu'ar, gama karatun yayin da ya ji dama da sauƙi a zuciyarsa ya ƙarasa gabanta wanda ba ta san ya iso ba. Saukar kiss ta ji a fuskarta wanda ya sa ta saki ajiyar zuciya tana kallon shi. "Am sorry." Ya furta cikin jan hankalinta da wata irin murya. Sai kawai ta tsinci kanta da fashe masa da kuka ta faɗa jikinsa."Please, na roƙe ka da karka rinƙa ɓoye mini abin da ke damunka zauji, in ba haka ba za ka yi sanadin rasa n.." "Shiiiiit!"Ya ce tare da saka ɗan yatsarsa ya toshe mata baki. "Waya gaya miki zan iya rayuwa in babu ke? Har yanzu ba ki yadda da ce miki da na yi kece mace ɗaya wacce na ke jin zan iya rayuwar aure dake ba? Kina girmama ni sam bakya mini rashin kunya sannan mace ce ke wacce ta ma sunanta ta kuma isa ta ɗauke hankalin ko wane ɗa namiji." Murmushi ta yi tare da faɗawa jikinsa tana sunne kai. Kiss ta kai mishi a bakinsa ta ce,"Ina matuƙar son ka ya Sheshk!"Ta kira shi da sunan da in har ta kira za ta gaya mishi abu maimahimmanci ne. Ƙara rungumeta ya yi yana faɗin,"Ni ma haka rayuwata." Sai ta ji wani matuƙar sanyi ya lulluɓeta lokaci guda ta manta komai suka shiga faranta ran junansu. Bayan ya dawo daga sallar isha a masallacin gidansa tana falo cikin riga da siket da ya kamata sosai tana jera masa abinci a dining ya shigo. Da sauri ya ƙarasa gurinta ya karɓi filet ɗin ya zuba abincin, tare da zaunar da ita kan kujera y gama gyara dining ɗin sannan ya zuba musu abincin ya fara ba ta a baki. Sai kallonsa take yi lokacin da yake bata labarin abin fa ya faru a tafiyarsu da nasarar da suka samo. Tuni ya manta da komai domin zuciyarsa ta gaya masa wasa take yi, don haka bai yi ƙasa a gwuiwa gurin watsar da komai ya ci gaba da tarairayar matarsa da ya yi mising ɗinta mara misaltuwa. Washegari da safe bayan Aby ya dawo daga masallaci ya shiga ɗakin Hajiya Baaba don ya gaishe sa. Tana zaune a cikin ɗakinta tana jan carbin da sai gyangyaɗi take yi. Jin muryarsa ya sa ta daina gyangyaɗin tare da gyara zama tana kallonsa. Har suka gama gaisawa zai miƙe ba ta ji ya yi maganar jiya ba, wanda ya sa har ya miƙe ta ce, "Dawo ka zauna ina son magana da kai." Gabansa ya faɗi a ransa yana addu'ar Allah ya sa ba zancan jiya za ta yi masa ba, amma sai addu'arsa ba ta karɓu ba domin tun kafin ya gama zama ta fara masa maganar. "Na ɗauka yanzu za mu yi maganar auren da shirye-shirye, ka san lokaci fa ba ya jira. Ko so kake sai Halimatuu ta dawo sai ayi maganar? Ka ji na rantse maka tun da na faɗa auren babu fashi. Karka manta a lokacin da za ka yi aure ka mini alƙawarin daga wannan lokacin ba za ka taɓa saɓa mini ba." "Eh Hajiya, don Allah ki daina tuna baya ai ba na ƙi auren bane, ina dai hangen abin da zai je ya dawo ne." "Babu abin da zai dawo sai lkhairi. Ɗanka za ka ja ma kunne karya sake ya bugar mini ita, don ba zan lamunta ba." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 23-24* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Allah ya kyauta! Hakan ma ba zai faru ba, saboda yana da sani ba zai tasa matarsa da duka ba." "Oho, jan kunne dai domin rigakafi yafi magani." Zama ya ƙara yi cikin murya mai sanyi ya ce,"Don Allah Hajiya Na ji na amince ayi auren, amma ki bari matarsa ta ɗan ko haihu ɗaya ne, ita kuma Jannah ta yi zurfi a karatunta, kin ga kafin lokacin ma ta ƙara hankali tun da duka guda nawa take." "A summa take ko ba a haife ta ba. Lokacin da na auri ubanka ko irgan dangi ban yi ba, kuma amma haka na rinƙa zaro ku sai da na yi takwas don dai ba su tsaya bane." Ta ja numfashi tana kallonsa ko zai ce wani abu amma sai ta ji ya yi shiru cikin jimami don haka ta ci gaba da cewa, "Kuma da kake cewa matarsa ta mutu in ta so, ai dama shi mijin mace huɗu ne ko alƙawarin ba zai yi mata kishiya ya yi ba. In an yi auren ta gungure ta faɗi ta mutu don kishi." "To shikenan, za a yi duk bin da kike so Allah ya sa mu ƙulla alkhairi." Ya miƙe jiki a sanyaye tamkar kazar ƙwai ya fashe mata a ciki zai fice. "Khairan zan ƙulla in sha Allahu duk wannan iskancin za su gaji su zauna dole, don rabuwarsu sai dai in bana raye." Ta ci gaba da jan carbinta tana gyangyaɗi. "Wayyo Alllah na gode maka! Yau addu'ata ta karɓu Halimatuu za ta dawo gida. Allah na gode maka da ka bani tsawon lokaci na ga wannan lokacin. Ta furta daidai lokacin da ta kashe wayarta da suka gama magana wanda ta sanar mata. "Dole na kira malamai su yi saukar Kur'ani da addu'oi akan Allah ya tsareta da mugun gani da ji." Ta ce tare da ɗaukar wayar tana neman numbar Aby. Jannah da Ummu suka yi sallama suka shigo cikin yanayin na matuƙar gajiya, kasancewar da ga makaranta suke. Turus suka ja suka tsaya ganinta tana rawa a tare suka kalli juna sai suka ɗauke kai. Wucewa ta yi ta zauna ba ta ce mata komai ba, domin tun da ta yi maganar auren ta da Ajmal ta ɗauke mata wuta suke zaman kurame wanda ko a tsummar gyalen Hajiya Baaba. Ummu kuwa gabanta ya shiga dukan tara-tara tsoronta kar a kan maganar auren ne take rawa, domin ta san ba banza ba za ta rinƙa tiƙa rawa haka. Gabaki ɗaya sai ta ji ranta ya ɓace, yunwar da ta shigo da ita ta neme ta ta rasa, domin ta tsani maganar auren. Gani take tamkar takurawa rayuwar Jannah za ta yi, gara Ajmal yana da wata matar. Kallon su ta yi ta watsar sai kuma ta fara magana bayan Aby ya ɗauki kiran da take masa. "Kuna ina ne Muhammadu? Da gaske kake yanzu Halimatuu na gabanka a Nigeria? Oh Allah mahaƙurci mawadaci." A tare suka kalli juna mamaki ya kamata ta jin har ta iso Nigeria, amma dad bai sanar mata da yau za su zo ba, duk da cewa ta san ta yi hakanne don su yi suprising ɗinta. Ummu ta sa ihu da tsallen murna duk da cewar ba ta waye ta sosai ba, amma dole ta yi murna domin tsaƙonta yana tafe garesu ko da yaushe, don haka ya rungume ta cikin matuƙar farinciki. "Wow, I can't wait to see mom." Ta ce cikin matuƙar ɗoki. Tureta ta yi da ga jikinta fuskarta sake tamkar gonar adduga. "Hello dad, is it true that you have came back to Nigeria?"Ta yi masa tambayar cikin zaƙuwa. "Oh yes my baby, I wanna suprised you. Did I?" Ya ƙarasa maganar cikin tsigar tambaya. "Yes you did, I can't wait to see you. Ko muzo mu ɗauko ku?" "A,a kar ki damu yanzu haka muna Jaji mun kusa dawowa Aby ya ɗauko mu." Wani irin ihu ta saki ba tare da ta kashe wayar ba tana juyi da Ummu. "Wallahi am not longer hungry my dad on his way. Allah na gode maka zan huta da fitina." Ta ƙara rungume ta sai kuma ta sake ta tana faɗin," Bari na yi wanka ki raka ni na sayo masa suprised. Saboda tsabar ɓacin rai Hajiya Baaba ta kasa magana sai kallonta take cikin tsananin damuwa. "Anya kina son ki gama da duniya lafiya kuwa, kin san haƙƙin uwa a kanki kuwa? A ce mahaifiyarki ta yi tafiya zuwa wata uwa bangon duniya, amma ba kya murnar dawowarta sai mahaifinki, bayan sai da Allah ya ambaci uwa sau uku. Kai gaskiya dole Halima ta tashi tsaye domin Jabiru ya gama da 'yarta." Tsaki ta yi jin abin da ta ce har ta kama hannu Ummu za su shiga ciki sai kuma ta dawo ta fara magana. "Eh shi kawai na damu da shi saboda na san saboda ni ya dawo, ita kuwa 'yarki siyasa ya dawo da ita ba don ni ba, domin a lokacin da nake tsananin buƙatar mu taho tare ba ta dawo ba, don haka babu ruwana da ita." "Dallah can tafi wawiya kawai! Ni na ga wanda take son mahaifinta ta ƙyale uwa. Ina ga duk yadda aka yi akwai tanbotsai akan ki, amma ba haka kike banza ba." "Zo muje kin ji na siyo mishi kar su dawo." Ta ja hannun Ummu suka fice daga falon ba tare da ta ba ta amsa ba. "Ki fi ruwa gudu ai ni ina murnar dawowarta ɗiyar albarka jinin arziki." Ta ce cikin jin haushinta sai kuma ta ɗora da ce wa, "Kai godiya ga Ubangiji Sarki mai yawa. Ba ri na tashi na je na yi musu girki kafin su dawo, Allah ya so jiya naje kasuwa." Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Sannu a hankali take takowa daga matakalen benen, cikin wani irin yanayin da ba za ka iya tantance farin ciki ko akasin haka take ba. Idanunta suka kawo ruwa daidai lokacin da ta sauko daga matakalen benen, tana shaƙar ƙamshin Ƙasarta wanda ta yi kewarta matuƙa. "Please Halee, don Allah ki manta komai.Na yi miki alƙawarin zama miji adali da kawo farinciki har ƙarshen rayuwarki." Ya ƙarasa maganar cikin rawar murya tare da kama hannunta na hagu ya riƙe. A hankali ta sanya gefen hannunta ta share hawayen da ke gangarowa bisa ƙuncinta, ba tare da ta ce masa ko ba ta ƙarasa gurin motar Aby tana sakar mishi murmushi, sai kawai ta faɗa jikinshi ta saki kuka. "Na yi kewar Ƙasata na san cewa ban yi wa dangina adalci ba, ina fatan su yafe mini na dawo gare su ba zan ƙara nesa da su ba." "Is ok Halima, duk abin da ya faru yana cikin kundin littafin kaddararki." Share hawayenta ta yi tana kallon dad daidai lokacin da ya ƙaraso gurin. "Ina son na ga mahaifiyata don Allah mu wuce Zariya, ka san matuƙar na shiga garin Abuja ba zan samu damar kasancewa da su ba." "Ok ba matsala hakan zai fi domin kowa ya yi kewarki matuƙa." Dariya ta yi mai ciwo ba tace komai ba ta shiga cikin mota escouts na ta suna biye da ita. A lokacin da suka ƙaraso get ɗin gidan sai ta fashe da matsanancin kuka yayin da farinciki ganin Jannah da mahaifiyarta ya cika ta. Babu wanda ya ce mata komai domin sun san kukan murna take yi. Jannah na ji hon ɗin mota ta zura a guje dama tun da suka dawo ta kasa zaune sainsafa da marwa take tsakanin falo da harabar gida. "Oyoyooo daddddd." Ta ce tare da faɗawa jikinshi ta saka kuka. "A really missed you dad." Ta ce tana share hawaye ba tare da ta kula da mom da ta fito daga cikin motar da shiga ta alfarma ta tsaya tana kallonsu yayin da wani abu ya toƙare mata ƙirji. Hajiya Baaba ta fito da sauri tana gudu ta faɗa jikinta. "Allah na gode maka yu Halimatuu ta dawo Ƙasarta, Allah ya ci gaba da kare ki da idon maƙiya." Sai kuma ta saketa tana shafa jikinta da ta koma tamkar balarabiya. "Oh kece kika koma haka? Ai zan tsaya tsayin daka na hana duk wanda zai ƙara sanya ki zubar hawaye har ki gudu ki barni sai inda ƙarfina ya ƙare." Dad ya yi shiru sai ya ji babu daɗi domin ya san magana ta yaɓa masa, amma da yake tsuntsun da ya ja ruwa.. Sai bai nuna damuwarsa ba ya janye Jannah da ta maƙale a jikinsa tana kukan murna. "Ki je ki yi hugging mom she missed you more than me." Ya ce a hankali yana tura ta gurinta ganin yadda gabaki ɗaya hankalinta na kanta sai kallon ta take yi. Ɓata fuska ta yi sai kuma ta nufe ta kan dole ganin yadda ya haɗe rai. "Evening mom, how was you trip?" Kowa a gurin bai ji daɗin yadda ta yi mata gaisuwar ba, domin murya ƙasa-ƙasa ta yi ba tare da walwala. "Evening my daling baby, kin ga yadda kika ƙara girma kika yi kyau Jannah, me Hajiya Baaba take ba ki? Kin yi kyau." Ta faɗa tare da kamota ta rungume duk da ba ta so hakan ba, sai dai hakan kawai zai rage mata raɗaɗin ƙaunarta da ke addabarta a zuciya. Da sauri ta janye jikinta ta koma gurin dad ta riƙe mishi hannu daidai lokacin da Ummu ta faɗa jikin mom tana ihun murna. "Dad, duk da you suprised me, but I got you something." "Ok." Ya ce yana shafa kanta. Gabaki ɗaya suka tattara suka shiga falon Hajiya Baaba da ya sha turare sai ƙamshi yake yi. Ammy ta ba da oder aka fara shigowa da abinci kala-kala da drinks. Mom ba yi ta shiga ta yi wanka haka dad sannan suka fito falo bayan sun ci abinci aka fara hira. "Yauwa, na ƙosa ku dawo ayi maganar auren Jannah tun da yanzu kun dawo sai a fara don wallahi na ƙosa na ga na haɗa wannan aure..." "Haba Hajiya Baaba, kar ki manta yau suka dawo ya kamata su huta don Allah." Hararar shi ta yi kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta fara da cewa," Ai da zafi-zafi akan bugi ƙarfe." Jannah kuwa kallon banza ta yi mata a ranta tana faɗin," Ni ba ni da lokacinki, tun da Allah ya dawo mini da mahaifina na ga wanda za ki aura ma wannan tsohon." A ranar wuni ta yi tana maƙale da dad har aka kira sallar magariba ya nufi masallaci. Ko da ya dawo daga sallar isha sai ta bishi sashin Ajmal da yake nan ya sauka. Hannunta ya kama ya riƙe cikin so da ƙauna."Kinga yadda kika canza kika girma? Gaskiya Hajiya ta iya kula dake, gabakiɗaya kin juye kin koma sak mom ɗinki. Ɓata fuska ta yi jin abin da ya ce," And I hated resambling with her da na yi, inda na gode ma Allah kalar fatarka na ɗauko, ba irin na ta jajakuwa ba." Dariya ya yi sosai jin abin da ta ce ya kama kumatutunta ya ja yana faɗin, "Oh my little girl akwai rigima abin alfaharine kiyi kama da ita." "Oh dad, let change the topic amma ni bana son haka. Ina matuƙar sonka na so ace komai na ka na ɗauko." Dariya ya yi shafa kanta tare da miƙa mata tsarabar da ya siyo."Wow dad, thanks na ji daɗi sosai da ka siyo ma Ummu duk abin da ka siyo mini, cus she is alot to me." Sai ya yi dariya tare da miƙewa ya kama hannunta. "Dad, ka ga yanzu tun da ka zo sai ka tsawatarwa Hajiya Baaba maganar auren da take mini I'm sick of it kullum maganarta kenan." Gabansa ya faɗi sosai har sai da fuskarsa ta bayyana. Gyara zama ya yi sannan ya ce, "Ki kwantar da hankali kin san Hajiya Baaba, suruka take a gareni, so I must speek to her politely kuma duka when I have arrived? At least I have to rest to tomorrow." Ɓata fuska ta yi don ita ba haka ta so ba, saboda ta so daga zuwa ya zare mata ido da nuna iko akan dole ba za a yi auren ba. Miƙewa ta yi. "Ok dad, amma ka san dole sai ka zare mata ido ka nuna isa a kaina, don wallahi ba ta da hali ta cika shiga hanci da ƙudundune. Haka kawai ina zaman zamana ta jawo mini bala'i da musifa." Shiru ya yi ba tare da ya ce mata komai ba duk da cewar kallonta yake yana sauraronta, amma ba shi da abin da zai ce mata domin shi kansa tsoro take ba shi, musamman wani mugun kallo da ya gani kamar tana masa. "Dad, you remember that you promised to me you will stand by my side?" Ta tambaye shi cikin sauri ganin yadda ya canza fuskar tsoro, domin gabakiɗaya tun da ya ga Hajiya Baaba ya firgice, gani yake kamar za ta iya nasarar ra ba shi da Halima a karo na biyu. "How could I forget. I had been counting the days, to come back and be by your side my girl." Murmushi ta yi jin abin da ya faɗa." Amma dole ka nuna ba ka tsoronta wani lokaci. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 24-25* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "How could I forget. I have been counting the days to come back and be by your side my girl." Murmushi ta yi jin abin da ya faɗa." Amma dole ka nuna ba ka tsoronta wani lokacin she is so disgusting." "Ok, I will Jannah, yanzu ya kamata ki je gurin mahaifiyarki ku yi hira domin ta yi kewarki sosai. Miƙewa ta yi." I'm very exhausted I wanna rest, goodnight." Ta ce ba tare da ta ba shi amsar tambayar da ya yi ba. Bin ta da kallo har sai da ta ɓace bayan ya ɗaga mata kansa yana murmushi. Mayar da kansa ya yi ya shiga duniyar tunani. A falon Hajiya Baaba suna zaune suna hira bayan Aby ya yi musu sallama ya fice Hajiya Baaba ta kalli 'yarta cike da so da ƙauna. "Ni kam Halimatu kin yi sakaci a rayuwarki, sam Jannah ba ta damu da ke ba. Tun da kuka zo take naniƙe da mahaifinta, amma kallon banza ba ki ishe ta ba." Kanta ta shafa cikin tsananin baƙincikin hakan. Idanunta suka kawo ruwa sai ta yi maza ta goge da gefen hannunta. "Na san cewa na yi kuskure a rayuwata na rashin kula da 'yar da na haifa, idan da ace ana maida hannun agogo baya ba zan barwa masu aiki alhakin kula da ita ba. Zan ware lokacina na kula da ita sai dai bakin alƙalami ya bushe, domin tamkar maƙiyarta haka ta ɗauke ni wanda hakan na mini ciwo kasancewa ita kaɗai na haifa." "Daga baya kenan halimatu, wane irin jan kunne ne ban yi miki ba, amma ki ka ɗauki ɗabi'un yahudu kika ɗora wa kanki, ba ki da lokacin kanki ballantana na ta. Abin takaici kika gudu da ita duk akan banzan dalili na ƙi wanda kina da ikon kawo ƙarshen matsalar. Ai ni wallahi kin bani mamaki. Haihuwa sai dai kika ana yi ita ɗaya Allah ya ba ki, kuma kin ɓata rawarki da tsalle gurin tarbiyarta." Hawaye ta share waɗanda suka zubo mata ba tare da ta sani ba."Na yi sakacin da babu gyara." "Sakaci babba ma kuwa, domin Jannah ta buwayi kowa. Kin san yadda nake da iko a gidanan ba a isa na shata kara ba a tsallake, amma ina saka ɗauka take ta karya shi, ga shi nan yaran gidan gabaki ɗaya sun raina ni." "Ki yi haƙuri hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yar." "Haƙuri ya zam dole amma kin san ko ku da kuke 'ya'yana kuka yi mini saina ɗau hukunci a kanku. Wannan dalilin ya sa zan haɗa aurenta da Adamuu domin shine kawai maganinta, sannan na rama abin da kuka yi mini na auren waɗanda ba na ra'ayi sai kuji zafi da raɗaɗin da na ji." "Haba Hajiya, sau nawa za mu baki haƙuri akan haka? Don Allah ki manta komai ya wuce. Ina lura da kallon da kika yi wa Injiniya, gabaki ɗaya raina ya ɓace shi ɗin fa mijin.." "Rufe mini baki.. Har yanzu kina nan kina wahalar da kanki a kansa duk abin da ya yi miki? Ke kam soyayya ba ta amfanar dake komai ba. Kin dai rako mata duniya wallahi." Shiru ta yi tana girgiza kanta sao kuma ta buɗe ba ki za ta fara magana ta katseta. "Ke ni ba wannan ba, maganar auren Jannah shine a gabana, ba na son a ja da nisa kafin ki tafi Abuja a sanya rana kawai." "Hajiya Baaba, don Allah karki shiga cikin rayuwar Ajmal da matarsa. Suna rayuwarsu cikin farinciki don Allah karki tarwatsa hakan. Kuma Jannah ba ta son shi, tsarin rayuwar..." "Kin san Allah Halimatuu, in kika ga ba ayi auren ba mutuwa na yi babu fashi, in kuma ba kwa so sai na sha guba na mutu ku huta." "Subuhallahi! Ba ta kai nan ba Allah ya ba ki haƙuri." "Haƙuri kayana ai sai an cuce ka ake ba ka shi." Shiru ta yi ba ta ce komai ba sai Hajiya Baaba ta kalleta ta ce,"A cikin gidansa nake son ta zauna don karya je ya ije mini ita a wani guri can, so nake ta zamo mowa a zuciyarsa. Kallonta ta yi tana mamakin ƙarfi hali irin na ta."Ba komai duk yadda kika ce za a yi. Shi Ajmal ɗin ya nuna yana so.." "Adamun banza shi a suwa da zai ce ba ya so. Na ga lokacin da kuka yi auren ku ina so ne?" Girgiza kanta ta shiga yi ba tare da ta ce komai ba domin lamarinta ya fi ƙarfinta. "To kamar haka yadda kuka yi mini ƙarfa-ƙarfa zan yi musu." "Allah ya sanya alkhairi ya kuma ba su zaman lafiya." Ta ce sai kuma ta gyara zama tana kallonta da ta amsa da amin cikin sauri tana harare-harare. "Zan yi magana kan kayan ɗakin da duk abin da ya shafi biki." Ta faɗa cikin rashin karsashi. "Mom, is what I heard coming from you? The you mean you support her?" Ta ce cikin ƙara domin tun da suke maganar ta ke jinsu sakamakon ɓoyewa a bakin ƙofa da ta yi. "Calm down, you need to understand m.." "Understand what mom? No it shouldn't be happened da bakinki kike maganar aurena as my age. To bari kiji na rantse miki babu wanda ya isa ya yi mini auren dole we have passed that era." "Aikin banza don ihu kike bayan hari aure sai dai ki ɗauki haƙuri da azaman yin biyayya don kin san kalar mijin ya jibge ki ba farau bane a garesa." Ihu ta sa tana girgiza kanta." Kin ga Hajiya Baaba ba dake nake magana ba, domin tun da iyayena suka dawo babu ruwana dake." "Au haka za ki ce, bayan na gama miki amfani ko?" "Dad." Ta furta da ƙarfi tare da yin sashin da yake wanda har bacci ya fara kamasa. "Muje ka gaya mata ba za ka amince da auren nan ba domin she is frustrating me da maganar." Zare ido ya yi sai kuma ya kalli agogo."Please ki je ki kwanta za mu yi maganar sa safe.." "No way." Ta katse shi tare da kama hannunsa tana ja. "You must go and tell her, so that she will not be pestering me." Jikinsa babu ƙwari ya bita har zuwa falon da murya Hajiya Baaba kawai ke ta shi. Wani banzan kallo ta watsa mishi lokacin da ya shigo. "Ai ni na ɗauka 'yan sanda za ki ɗauko mini sai kika tsaya anan, to sai ya ɗauko bulala ya zane ni." "Ki yi haƙuri ba ta kai nan ba, amma don Allah ya kamata abi abun.." "Ya kamata mene? Kai Jabiruu kake ko mene? Wallahi ka fita idona tun kafin na shuka maka rashin mutunci, domin ka san ina da cikinka na tsawon shekaru." "Allah ya ba ki haƙuri." "Oho, ko ma me za ka ce ka faɗi aure dai babu fashi, in kuma za ku nuna mini iyakata bismillah." "Dad, ka na nufin kai ma ba ka isa da kanka ba sai abin da ta ce?" Ta yi mishi tambayar cikin tsananin mamaki. "Ba ki san cewa ni dakali ba ne dole a zauna dani. Ai girman kenan tun da na haife su ai dole abi umurnina." "Ina wallahi ba zan yadda ba ina ji ina gani ayi mini auren dole." Ta ce tare da kai wa tibin bangon falon duka, wanda nan take gilashin ya tarwatse hannunta ya fashe. Sai kuma ta sanya kuka ta na jin yadda zafin raɗaɗin ciwon yake tasowa yana bin duk ilahirin jikinta. "Wallahi ba na son shi. Ko a duniyar mafarkina ban taɓa tunanin auren mutum irin sa ba. I really hate him please dad do something if not I gonna die. How can I marry a such person like him?" Sosai take kuka ta faɗa kansa wanda hakan ya sa ya ji tausayinta ƙwarai to amma ya zai yi. Kamota ya yi a hankali ya miƙar da ita ya zaunar da ita har zuwa lokacin ya rasa kalmar da zai rarrasheta da su, saboda sam baya ƙalubantar auren domin auren miji kamarsa ba ƙaramin tagomashi Allah ya yi mata ba. "Hajiya Baaba, na san na saɓa miki arayuwarki kuma na yi butulci amma don Allah ki bari ta gama karatu kuma su fahimci juna, kin san suna da bambancin ra'ay.." "Au wa'azi za ka fara ai ban sani ba, amma da ka je masallaci ka hau munbari domin an fi buƙatarka. Har kana da bakin da za ka yi wa wasu wa'azi?" Sunkuyar da kanshi ya yi lokaci guda hawaye suka fara turereniya akan fuskarsa da take cike da haiba da kamala, yayin da yake nadamar abubuwan da suka faru a baya. Cikin tsananin tashin hankali ta nufi inda Hajiya Baaba take tana girgiza da huci domin wani mugun haushinsa take yi kamar ta shaƙe shi in ta nuna irin abubuwanda ya aikata ya zama kura da fatar akuya.. "Ban san wane irin mutum ce ba kin takurawa kowa kin hana mu sukuni bayan kin ci lokacinki babu wanda ya takura miki, ba sai muna cikin rayuwarku za ku takura mana ba?" Sai ta kama hannun dad ta riƙe cikin ɓacin rai ganin yadda yake zubar hawaye. "Ka saki mom ka ƙara aure mu yi rayuwarmu cikin farinciki I hate them dad." Gabkiɗayan su suk zaro ido har da su Aby da hayaniyar ya sanya suka shigo. "What! Are you insane? Mahaifiyarki kike gaya wa mahaifinki ya sake ta? Cewar Nahlin kamar ta tsinka mata mari. "Yes I do. Auren su babu abin da yake ƙara mini sai baƙinciki don haka rabuwarsu ya fi, kin ga sai na ga uban da ya isa ya yi mini auren dole." Mom wacce tun da jannah ta ji ciwo take kuka sosai damuwarta jinin da yake zuba a hannunta. Kau ta wanka mata mari."Ki iya bakinki in kika yi mini rashin kunya na ɗauka ba zan lamunta gareta ba." Ta faɗa cikin kaukausar murya. Rintse idanunta ta yi."Ni dai wataƙila ba zan taɓa samun farinciki ba, ga shi na gudu don na yi farinciki amma kuma na dawo an ɗora daga inda aka tsaya." Sai ta ƙara sakin kuka ta nufe ta."Mu tafi asibiti jini kika zubarwa." "Fisge hannunta ta yi cikin kuka."Go away, I hate you." Ta ce tara da riƙe hannun dad. "Taɓɗijan! Lallai kin yi sake Halimatuu. Auren ta da shi shine kawai maganinta domin ya ci mini ƙaniyarta in ya so ya kakkarya mini ita akawo ba su Binbo ƙasusuwa." Wani mugun kallo ta yi mata tare da jan majina daidai lokacin da dad ya kamata hannunta suka fita daga falon. "Kai Jannah an yi fitsarrariya." Cewar Hajiya ta galla wa mom harara ta shige ɗakinta. Faɗawa jikin Aby ta yi ta fashe da kuka."Haƙiƙa Allah ka jarabce ni! 'Yata ɗaya tilo take sanar da mahaifinta ya sake ni ya auri wata? Ni kam mai na yi wa duniya take gara rayuwata kamar ƙwallo." "Ki yi haƙuri Halimatuu, ka da ki yi saɓo." Ya furta tare da kama hannunta suka yi sashinsa. A sashin Ajmal dad ya zaunar da ita cikin ɓacin rai ya kalle ta sai kuma ta ƙara ba shi tausayi, amma da ya tuna kalamanta zucigarsa ta ƙara tafarfasa. "Haba Jannah, I really hate the way you talk to your mom honestly I dislike it you are so insolent to her." Ya juya mata baya yana jin kamar ya mareta daidai lokacin da ta ƙara sakin kuka. " So now, you gonna tell me you wanna side her? Tana jin munanen kalamai da mahaifiyarta take gaya maka amma she sat and looking her becouse ba ta ɗauke ka da mahimmaanci ba." Kama hannunta ya yi ya riƙe yana ya rasa yadda zai yi ta fahimce shi domin ya na ganin aminta da auren shi zai daƙile bankaɗar da Hajiya Baaba take son mishi, wanda in har ta ji ya san daga ranar ba za ta ƙara kallonsa da daraja ba. "I really don understand cus the whole situation is akward." Kuka sosai take yi sai kuma ta faɗa jikin shi ta ci gaba da cewa, "Na tsane shi wallahi ba na sonsa ban taɓa hasashen rayuwa da shi ba, a kwai wanda nake so and we are compatible dad, please do something." Idanunsa ya zaro cikin tsananin mamaki." So you mean you are dating someone without my awareness, how could you?" Cikin jin kunyar abin da ya faɗa ta rufe fuskarta."Am deeply sorry dad, initially he was my best friend, but later I found him very valuable to my life and we fall in love. Mun haɗu ne a faling jirgi a ranar da na dawo Nigeria." Sai ya yi shiru yana saurarenta da mamakin ɓoye masa da ya yi domin bai taɓa tunanin hakan ba. "I said am sorry for hiding it, but ina son shi kuma he is well off haka iyayensa they are prosperous. In har ta nace na yi aure ta aura mini shi." Sai ta yi matuƙar ba shi tausayi matuƙar gaske saboda yadda take maganar ya fahimci tana matuƙar son shi. "But please stop talking to your mom in that manner, you shouldn't talked to her in that tongue." Jin ta yi shiru ba ta ce komai ba ya fora da cewa, "You have to go and sleep we will talk about it kin ji." Ya fada Yana shafa kanta. Dukkan mutanen gidan ba su bacci cikin kwanciyar hankali ba sakamakon ko da abin da yake saƙawa a cikin ransu. Washegari da safe ko da ta farka, babu wanda ta yi wa magana hatta dad domin shi kansa haushi yake bata don ko karyawa ba ta yi ba ta fice. Mom da ta kwana kuka sai bayan kiran sallar asuba bayan ta yi sallah bacci ya ɗauke ta wanda ba ta tashi ba sai tara. Wanka ta yi ta sanya doguwar riga ta fito falo don ta karya. Ta yi sallama ta shigo cikin falon tana kallon dad da yake zaune a gefen Aby suna suna hira. Ido ya raka ta da shi har ta ƙaraso kusa da shi ta zauna a gefen kujear da yake zaune cikin murya mai sanyi ta gaishe shi, ba tare da ta jira ya amsa ba ta fara gaida Aby. "Ina ga yau zan wuce Abuja fa saboda gobe akwai taro da zan halatta." "Aiko ba ki isa ba daga zuwanki ina murna." Cewar Hajiya Baaba da ta fito daga ɗakinta. "Dole na tafi Abuja akwai abubuwan da zan yi, ki yi haƙuri da na kammala zan zo." "To kiyi mini wayon Halimatuu, yau aka fara kefa a koda yaushe ba ki da lokacin kanki ballanatana na ahalinki, in kika na ce za ki tafi sai dai na biki domin dama ba wani daɗi na ke ji a gidan ba." Ta yi ƙuta tana faɗin haka. Dukkanninsu ba su ji daɗin abin da ta ce ba musamman Aby da ya san matarsa na iyakan ƙoƙarinta, kawai tsana ce da ƙiyayyar da ta ke mata. "Amma Hajiy Baaba, in kika..." "Rufe mini baki shanyayye kawai! Da ma kai ai bayanta za ka bi tun da ta wanke ta ba ka ka shanye." Shiru kawai ya yi yana girgiza kansa cikin ɓacin rai idanunsa sun kaɗa sun yi jajir. "To shikenan, zuwa anjima za mu tafi har da kai ko Ya Muhammadu za ka bimu akan maganar nan?" "Eh ya ba ta amsa yana ɗaga masa kansa. "Ina ga a shirya tafiyar duk gida sai suje su ga gida ko?" "Ai kuwa hakan ya yi sosai zan so hakan." Mom ta ba Aby suka faɗa cikin fara'a. "Jannah da Ummu suna school sai a jira su." Cewar Aby. Ɗaga masa kai ta yi ta ci gaba da duba tsaƙonnin wayarta, har ta zo kan tsakon da aka turo anonymous kamar haka "Ina miki murnar dawowa ƙasarki da kika gujeta na tsawon lokaci, sannan ina miki murnar tsayawa takarar minister, amma ki sani burinki ba zai taɓa yiyuwa ba matuƙar ina numfashi domin nine ajalinki." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un." Ta furta cikin kiɗima tare da zazzaro ido. "Subuhanallahi mai ya faru?" Gabaki ɗayansuka haɗa baki gurin faɗin haka tare da miƙewa a razane. Fiffita ta fara yi da hannunta take zufa suka fara karyo mata. Ji ta yi yawun bakinta ya ƙafe. "Halee, lafiya?" Cewar dad da ya kama hannunta cikin kiɗima. Cikin dubara ta fita daga mesages ɗin don kar su gane abin da ya sanya ta razana. "Im ok, rasuwar wata mar lafiyarmu na ga ni ya kiɗani." Ta samu kanta da gindira musu ƙaryar saboda ba ta san me za ta ce musu ba musammman dad da baya supporting ɗinta. "Allah ya jikanta ya gafarta mata ai mutuwa is inevitable price, kowa sai ya ɗanɗani ɗacinta." Cewar Aby. Tun daga lokacin sai ta nemi natsuwarta ta rasa duk bayanin da suka mata ta kasa fahimta ƙarshe miƙewa ta yi ta shige cikin ɗaki ta kulle kanta. "Waye wannan, mai na yi masa kuɓa mai na tsare masa?" Ta furta cikin tashin hankali tana safa da marwa a ɗakin. Ƙara duba text ɗin ta yi tana ƙoƙarin goge komai ta da son mata tsakon kiran Hajiya Turai ya shigo wanda ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba. "Hello, uwa ba da mama." Ta furta bayan ta yi sallama. Amsa sallamar ta yi ba tare da ta ce komai ba ta yi shiru. "Wannan matar ce wanda na gaya miki ta zo neman taimako, amma ta ce dole ke take son gani, yau ma ta ƙara zuwa bayan tsawon lokacin da ta ɗauka ba ta zo ba." "Ok, ki gaya mat gobe ta dawo kamar wannan lokacin za ta same ni." Tana faɗin haka ta kashe wayar yayin da zuciyarta ta karkata tunanin wacce mata ce. Ajmal tsaye a gaban madubi yana gyara gashin kansa da kuma. Mushiirat ta yi sallama ta shigo ɗakin tare da takowa anhankali ta rungeme shi. Kis ta sakar masa a bayansa. "Ina sonka mijina." Ta furta cikin wata irin murya wanda ya sanya shi sakin murmushi ba tare da shiri ba. A hankali ya juyo da ita yana manna na shi kis ɗin a goshi. "Ni ma ina sonki sosai Mushiirat fatana Allah ya barmu tare ki haifo mini kyawawan yara masu kama dake." "Amin." Suka haɗa baki gurin faɗin hakan. "Zan wuce work kuma daga yau zan fara duties na dare." Ɗan ɓata fuska ya yi jin abin da ta ce."Ni fa wannan dutie ɗin yana shiga haƙƙina." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 25-26* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Ɗan ɓata fuska ya yi jin abin da ta ce."Ni fa wannan duties yana matuƙar cutata, domin yana nisanta ni da jikinki mai sanyani bacci cikin jin daɗi." Dariya ta yi jin abin da ya ce." Na fika shiga damuwa sosai, sai dai babu yadda zan yi, domin aikin taimakon al'umma ne." "Haka ne, muje na saukenki. Ina matuƙar alfahari da matata da take taimakon al'umma." Kama kumatunsa ta yi ta ja tana dariya sai kuma ta ɓata fuska." Amma ni wannan kwalliyar ta mini kyau, ko zan fasa zuwa aiki na zauna na ɓatata?" Ta tambaya cikin tsigar shagwaɓa tana kashe mishi ido. "Da ko na ji daɗi in aka yi mini haka sai dai gida zanje, kin san na gaya miki mom ta dawo zan je na gaishe ta ne." Ɓata fuska ta yi ba ta ce komai ba domin 'yarta ta ja mata tsana a gurinta. "Ok, ko zamu tafi tare na gaishe ta?" Ta yi tambayar ba wai don tana son hakan ba sai don ba ta so ya fahimci tsanar da ta yi mata. "Da sauri ya girgiza mata kansa ya bar shafa turaren da yake yi ya juyo yana kallonta. "Ba sai kin je ba ki bari zan kaiki har can Abuja ki gaisheta." Sai ta ji daɗi jin abin da ya ce domin ba wai don tana son zuwa bane, sam ta tsani ganin Hajiya Baaba da kallon banza ba ta ishe ta ba. A ransa sai ya ji daɗi jin ba ta ja da nisa ba domin ya san matuƙar taje gidan nan sai ta ji abin da ke faruwa, yayin da ya fi son har ayi maganar auren a fasa baya son ta ji. Jakarta ya ɗauka tare da kamo hannunta suka fita. A lokacin da ya yi sallama mom na zaune da waya a hannunta suna magana da Hajiya Baaba. Ya shigo ya samu guri ya zauna cikin matuƙar jin kunyarta. Kallon shi ta yi cikin fara'a tana amsa sallamar da ya yi, wanda Hajiya Baaba ta yi kicin-kicin ta ƙi kallonsa ballantana ta amsa. "A sannu da zuwa malamai magada annabawa." Ta yi maganar cikin fara'a. Duƙar da kansa ya yi yana shafawa bayan sun gaisa. "Sannu isasshe shafaffe da mai da ya ji. Saboda na ce zan aura maka Jannah shine ka yi gudun hijira sai yau na ke ganin ka ko? Tunaninka ƙin zuwa gidannan zai sa na fasa aurenne? Ka ci gaba da ɓuya sai randa na kawo maka ita a lulluɓe sai kuma ka bar garin." Shiru ya yi baice komai ba saboda mom amma ita ma ta san sai ya tanka. Gaishe ta ya yi cikin ladabi." "Ba zan amsa ba! Na ce ba na buƙatar gaisuwarka. Ni daga yau ƙarka ƙara zuwa gurin.." "Haba Hajiya Baaba! Don Allah k..." "Ba ruwanki Halimatuu na ce ba ruwanki, ba ki san waye shi ba kina ganin shi kamar mutumin kirki kura ne da fatar akuya, domin in ya yi miki wani abun sai kin ɗauka daga bariki ya fito." Ta furta cikin faɗa. Da sauri ya ɗaga kansa yana kallonta. "Ƙarya na yi?" Ta ce mishi cikin gatsali. Tsananin kunyar mom suka ƙara ka masa sai ya ji kamar ya duƙa ya roƙeta akan ta tursasa ta ta janye auren, amma ba zai iya ba don haka ya miƙe jiki babu ƙwari ya yi mata sallama zai fita. Mom ta raka shi da idanu har ya kai bakin ƙofa sosai ya burge ta kuma take ma Jannah sha'awarsa, sai dai ko ita ta san auren na su ba ɗauko rigima ce babba domin rayuwarsu ba ɗaya ba. "Na ɗauka za a kawo mini surikar tawa ta gaishe ni domin tunanina tare za mu tafi Abuja kuka guri?" "Ya kawota ta ji zai ƙara aure ta yi masa duka. Ai wallahi an dai yi girmar kwabo, ayi ta wa ƙanni mazurai amma a gida a kasa kataɓus." Shi da ita babu wanda ya tanka mata sai ya kalli mom ya ce, "Za mu zo har gida zan kawota ina da aiki sosai." "To shikenan, Allah ya taimaka ya bada sa'a." Ta ce daidai lokacin da ya amsa da "Amin." Ya fice da ga falon yana aika wa Hajiya Baaba mugun kallon da take aika masa daa irin sa. "Munafuki macijin sari ka noƙe." Taace tare da miƙewa. "Don Allah Hajiya Baaba, babu wanda yake daidai a rayuwarki ne? Ban taɓa jin kin yabi wani ba domin kowa a gurinki mai laifi ne da aikata ba daidai ba? Dubi yaronanna bawan Allah ko shigar da ya yi bai kamata ki rinƙa ci masa mutunci. Yaro mai hankali da addini." Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. "Ba ki san halin shi ba shin yasa kike faɗin haka."Ta ce tare da miƙewa ta fice daga falon. Bayan sun dawo sun ci abinci dad yake gaya mata tafiyarsu wanda ya da cikin farinciki ta kalle shi ta ce, "Yauwa dad, zan je kuma ga shi yau Alhamis gobe lecturer da muke da shi ba zai zo ba, ka ga zan yi weekend ɗina acan sai musha hirarmu. Murmushi ya yi jin abin da ta ce yana ɗaga mata kansa. "Bari na je na haɗa kayana." Ta ce tare da ficewa cikin tsananin kewarsa. A lokacin da suka isa garin Abuja mai-gadi ya buɗe musu katafaren get ɗin gidan momi ba ƙaramin razana suka yi ba, domin ko ita mom gidan ya yi masifar burgeta duk da ta ga komai a waya sai dai ba kamar a zahiri ba. Su Jannah iyayen hoto duk cikin damuwar da suke ciki bai hana su ɗaukar hoto ba, musammman garden da ya yi matuƙar burge su. Da suka shiga cikin falon sai kansu ya kwance. Jannah ce kawai ba ta wani ruɗe sosai ba, saboda gidan da suke a London ya fi wannan. Mom ta wuce ɗakinta don ta watsa ruwa. Tsayawa ta yi tana ƙarewa ɗakinna ta kallo da aka danƙara dukiya. Tsarin gidan ya yi mata da komai da komai ba Bayi ta shiga bayan ta tuɓe kayan jikinta ta buɗe shower. A hankalinta sauke ajiyan zuciya tana jin daɗinnruwan da yake rage mata gajiya. Bayan ta yi wankan ɗa ɗaura alwala ta fito tare da sanya kaya ta fara sallah. Da ta idar da sallar ba ta ƙara waiwayar kowa ba ta ɗauki laptop ɗinta ta fara aiki, domin ta san yana nan birjik yana jiranta. "Wai lallai Halimatuu, ta tara dukiya irin wannan gida sai ka ce a Ƙasar waje." Cewar Hajiya tana jinjina kanta. Masu aikin gidan suka fara kawo musu kayan abinci wanda Hajiya ta ba da umurnin a sakko musu ƙasa, sakamakon gajiya da suka yi suna son miƙe ƙafa. Jannah da ce da dad kawai suka cin abinci a dining a filet ɗaya wanda ta ci cikin tsananin murna. Ba su yi wani hira mai tsayi ba suka kwanta saboda gajiya. Washegari da safe misalin ƙarfe tara mutanen gidan suka hallara a falon don karyawa ko wannnen su ya yi wanka ya shirya cikin alfarma. "Kai ina Halimatuu? Ita ce kawai ban ganta ba, ma za Jannatu ki kira ta." Hajiya Baaba ta furta tana kallon ta da ta tura baki alamun ba za ta je ba. " Tun safe ta fita sakamakon aikin gaggawa da ya taso mata ta ce na sanar miki ba ta son ta tashe ku ne." Cewar dad da yake sakkowa daga upstairs "Kai Halimatuu, ba za ta huta wa rayuwarta ba. Haba mutum ya baro wata uwa duniya, amma ba zai iya bawa kansa hutun kwana ɗaya ba." Babu wanda ya ce komai sai Jannah da ta taɓe baki ta ci gaba da cin abinta. "Kai ni fa ba zan iya cin waɗannan abincin ba salon basir ya kama mutum, domin in ban da dankalin turawa babu abin da na gane abincin nan, shi ma sai da aka ɓata shi da wannan abun mai kama da majina." Gabaki ɗaya suka kwashe da dariya jin abin da ta ce. "Yanzu Hajiya Baaba, nufin ki ba ki san ketch-up ba? Gaskiya wannan ai sai ki ba damu." "Ai wallahi Anty Nahlin gabakiɗayanta ba ta waye ba domin Hajiya fa ko custard ba ta iya sha, sai dai ta sha koko. Ai tana ba da su mom." "To haka kawai sai na cuci kaina na yi ta cusawa kaina abin da zai cutar dani ai lafiya uwar jiki, haka kawai na kashe kaina lokacina bai yi ba." Ta ƙarasa faɗin hakan tana miƙewa sai ta ci gaba da cewa," Ni ba zan iya ci ba girki zan je na yi. Ke ungozi kike ko wa za a samu kullu a kicin ɗin nan na dama farau-faru." Dariya suka ƙara kecewa da shi." Taɓ! Kullu a wannan gidan sannu Hajiya Baaba." Cewar Ummu tana gimtse dariya ganin kallon da take mata. Shiga kicin ɗin ta yi tana 'yan dube-dube amma ta rasa gane gas ɗin sai ta fito tana faɗin,"Ke Hafsatuu, ma za zo ki nuna mini yadda ke kunna gas ɗin, wannan mai cinyeyen kan ko na yi magana ba ji na za ta yi ba." Miƙewa ta yi ta nufi kicin ɗin ba tare da ta ce komai ba lokacin da Aby ya ce,"Ki duba ma ta ba za ki rasa na serchet ba." "To." Ta amsa sannan ta shige kicin ɗin. Mom zaune a bayan mota da waya a hannunta tana duba tsaƙonnin da aka turo mata ta twinter. Daina duba tsaƙon ta yi tana kallon tanƙamemen get ɗin da aka rubuta Alcharity Foundation Center da rubutu manya a saman get ɗin. Idanunta suka kawo ruwa ta sanya hannunta ta share daidai lokacin da direba ya yi parking. "Barka da dawowa shugaba." Ma'aikatan gurin suka rinƙa faɗin haka cikin girmamawa. Hannunta take ɗaga musu cikin murmushi har ta ƙarasa cikin ofis ɗin. "Barka da dawowa uwar marayu haƙiƙa ƙungiyarmu ta yi kewarki ƙwarai." Rungume juna suka yi cikin farin sake ganin juna. "Na yi kewarku gabakiɗayanku musamman ke aminiyata." Ta ce tana murmushi. Kujera ta isa gareta ta zauna tana kallon Hajiya Turai da ta ƙaraso ta nemi kujera kusa da ita. "Ba ni da lokaci sosai ina files ɗin da na ce ki aje mini, sannnan kin tura ma wannan matar da za a yi mata aikin ƙoda?" Wayarta ta ciro tare da shiga cikin hotuna tana faɗin,"Tun daren jiya na tura musu domin har anyi aiki, jiran farfaɗowar matar kawai muke jira." "Good! Aikin ki na kyau, Ubangiji ya bamu ladar hakan." "Amin." Ta amsa sai kuma ta mai da hankalin akanta bayan ta karɓi wayarta da ta gama kallon hotunan ta miƙa mata ta mayar cikin al'jihunta. "Wannan matar da ta damu kan tana son ganinki, yanzu haka mun yi waya da ita tana kan hanya ina fatan za ki jira ta, saboda yanayin matar tana cikin tsananin buƙata, amma ta ƙi yadda mu taimaka mata dole ke take son gani." "Eh, zan iya jiranta, amma in har ta ƙara minti biyar ba ta ƙaraso ba sai dai gobe, domin ina da meeting." Ta ƙarashe maganar tana duba agogon hannunta. "In sha Allahu za ta ƙaraso." "Allah ya sa hakan." Ta ci gaba da duba files ɗin da take yi. Wayar Hajiya Turai ta yi ƙara da sauri ta miƙe tana faɗin,"Yauwa ga ta nan ma ta iso." "Ok, ki shigo da ita ciki." Fita ta yi tare da ɗaga mata kanta wanda ba ta cika minti goma ba, sai ga ta sun shigo da wata mata cikin wani yagalelen hijabi da doguwar rigar da ta mutsutsutsuke. Duk yadda mom ta so karta toshe hanci sai da abin ya faskara, domin wani irin wari take jin yana tashi, wanda ba ta san lokacin da ta kai hannu ta toshe hancinta, tana jin yadda kayan cikinta ke hautsinawa ba, inda Allah ya taimaketa ba ta karya ba don babu abin da zai hana ta amayar da kummmalon. "A uwa ba da mama ko dai na fita da ita ne? Na ga yadda kike ɓata fuska kar dai kiyi amai? Sai da na gaya mata ta nemi duk irin taimakon da take so za mu ba ta, amma ta n ce dole sai ta ganki"Hajiya Turai ta furta cikin ɗaga murya tana mamakin matar. "A'a, kar ki damu ƙyaleta." Ta furta tana ƙoƙarin daure warin amma ta kasa. "Wayyo Allah na shiga uku! Yanzu Halee, nufinki ba ki gane ni ba? Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Khamis ka cuce ni kai mai da duniyata mara amfani in har zan yi canzawar da Halee, za ta kasa gane ni. Ni kam mene ne amfanina a rayuwata" "Mujee!" Ta furta cikin tsananin mamaki da tare da sakin wayarta ta ƙaraso gareta ta kama ta, ba tare da ta damu da warin ba." "Na shiga uku! Kece kika koma haka ina gayu da kyawunki, mai ya faru kike wari tamkar kashi? Ta riƙe ta tana girgiza ta tare da kallon mamaki ganin yadda ta joma tmkar mahaukaciyar da ta shekara tana hauka. " Ta jere mata tarin tambayoyin da ta gaza amsa ko ɗaya, sakamakon kukan da ya ci ƙarfinta. "Zuciyata ta kasa yarda kece wannan Mujee, ina iyayenki suka bar ki cikin wannan halin?" Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 26-27* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Na shiga uku! Kece kika koma haka ina gayu da kyawunki, mai ya faru kike wari tamkar kashi?" Ta jere mata tarin tambayoyin da ta gaza amsawa sai sharɓar kuka take. "Don Allah Hajiya ki saketa karki shafa ma jikinki warin da take yi, idan ma kin san ta ne, to ki bari ta daina wannna warin." "Ƙyale ni Hajiya Turai ba ki san wace ce ita a gareni ba, saboda ita ɗin ƙawace a gareni, wanda ƙawancenmu ya rikiɗa ya zama 'yan'uwanta tana daga cikin mutanen da suka ƙarfafa mini kafa wannan ƙungiyar ta kuma taimaka da hannunta har da gudummuwarta, daga baya bayan ta yi aure na neme ta na rasa. Don Allah ki bamu guri." Jin abin da ta faɗi ya sa ta ɗauki wayarta ta fita tana waiwayon matar cikin tsananin mamaki, domin farkon zuwanta sun yi tunanin mahaukaciya ce. "Me ya faru kika dawo haka, ina Kham ɗin ki? Ta ya ya akai ya barki cikin wannan halin duk da irin son da ya nuna miki, domin zan iya cewa soyyarku ita ce na farko da ya fara jawo hankalina na fara soyayya." Kuka ta ƙara fashewa da shi."Me kike so na gaya miki akan Kham domin abubuwa da dama sun faru, wanda tuna su sawa yake na tsani kaina da ranar da na fara saninsa a duniya. Haƙiƙa ya cutar da rayuwata. Halee, labari ne mai tsayi wanda ba zan iya gaya miki a halin yanzu ba, domin yunwa na ke ji rabona da abinci kwana biyu kenan, ni kaina dauɗar jikina ji nake kamar zan amayar da 'yan hanjina." Ƙara kallonta ta yi cikin mamaki tana ƙara mamakin wai Mujee 'yar ƙwalisa ta dawo haka! Lallai rayuwa ba abin taƙama bace, in ta tuna da turare in har bai kai 50k ba duk ƙamshinsa ba ta iya fesawa. "Kai wai me wasu maza suka mai da mata ne? A kodayaushe sun mai da mu wulaƙantartu su yi duk rashin mutuncin da suka ga dama akanmu saboda sun san Allah ya haɗa rayuwarmu, ba za mu iya rayuwa sai da su ba?" Ta tambayi kanta cikin tsananin ɓacin rai tana kallon yadda aminiyarta ta koma saboda tabon ɗa namiji wanda ita ma tana ɗauke da shi." "Mu je gidana ki yi wanka ki canza kaya, sannan ki ci abinci sai mu tuna bayan rabuwa." Ta ce tana kama hannunta cikin rashin ƙyanƙyani. A lokacin da suka fito mutane suka rinƙa kallon su cikin tsananin mamakin ganin tana riƙe da hannun matar da in ta matso su za su iya guduwa domin ba ta da marana da mahaukaciya. A mota babu wanda ya iya magana a tsakaninsu sai Mujee, da take kallon unguwar da suka shigo mai tsananin kyau da gidaje masu kyau na fitar hankali. A lokacin duka mutanen gidan suna zaune a falo suna kallo ban da Jannah da ta ke zaune gefen dad tana ta chatting da Huzaifah yayin da fuskarta ke saukar da wani irin tsadadden murmushi. Da sallama ta shigo cikin falon Mujee na biye a bayanta, wanda ta tsinke da kyawun gidan sai kawai ta fara tasbihi ga Allah Maɗaukakin Sarki, domin wannan gida ya cancanci a kira shi aljannar duniya. Da sauri Jannah ta miƙe cikin zabura ta ɓoye a bayan da wanda shi ma ya miƙe yana kallon matar cikin mamaki da tuna son inda ya taɓa ganin fuskarta. "Mom, who is she? She looks like mad woman." Ta ƙarashe maganar tana toshe hanci don har ta ji amai zai zubo mata. "Watch your mounth, she is friend of mine. We ran off today." "No way! This is absolutely impossible this mad woman to be your friend, mom." Ta ce tare da rugawa cikin bayi ta fara kera amai. "Halima yanzu taimakon ya wuce ki taimaka a waje sai ƙin kawo su gida, ai wannan gidan mahaukata ya kamata ki kaita." Cewar Hajiya Baaba cikin zare ido. Ta kalli dad da fuskarsa take cike da alamun tambagar wace ce, tare da mata kallon sani ta ce, "Na san ba lallai ba ne ku iya gane ta ba, domin duk kusancin da ke tsakaninmu na kasa gane Mujee, 'yar Kaduna wacce muka yi Jami'a har tana zama a gidammu." Ta ƙarashe maganar cikin kuka tana rungume ta. "Innalillahi wa inna ilahir raju'in!Duniya ina za ki damu? Ke Mujidatuu, mai ya same ki ina mahifiyarki Hajiya Maryama da mahaifinki Alhaji Sani." Kuka ta fashe da shi ta nufi Hajiya Baaba za ta rungume amma sai ta matsa tana toshe hanci saboda wani irin ƙarni da ya dumfaro ta. "A'a ki dai bari kiyi wanka wannan wari sai ka ce kin yi kashin kwance." Cewar Hajiya Baaba. Zubewa a ƙasa ta yi tare da sakin wani irin zananen kuka tana faɗin,"Sun mutu ba ni da kowa kowa ya guje ni Hajiya Baaba." Zare idanunsa suka yi cikin jimamin jin mutuwar su da suka zamo kamar 'yan'uwa a baya. "Oh rai baƙon duniya Allah ya jiƙansu da rahma, hatsarin mota suka yi?." Cewar Hajiya Baaba cikin hawaye, wanda ta kasa ba ta amsa sai girgiza kanta da ta yi tana share hawaye. Mom kuwa kuka ta fashe da shi tare da janta cikin ɗakinta, domin ta kasa cewa komai irin ƙauna da kular da suka yi mata yake dawo mata ƙwaƙwalwarta, wanda ba za ta taɓa manta hakan ba. "Ki shiga ki yi wanka ga kaya ki shirya, ba ri na sanya a haɗa miki abinci." A falo sun yi jugum-jugum dad kuwa tsananin mamakin yadda ta koma yake yi, tunawa da lokacin da suna Jami'a ita ce take ke amshe gasar wanka da ɗaukar gayu, amma dubi yadda duniya ta yi mata ɗaurin goro ta wuntsilar da ita cikin duniyar da ta yanke zumunta da su. "Please mom, I can believe that, you brought that mad woman into our house. Haba you should have think, saboda ba zan iya cin abinci ba idan ina ganinta." Ta ƙarashe maganar tana yamutsa fuska. "Jannah, ki iya bakinki ba zan lamunta rashin kunya a gareta ba, wanda in kika ƙi ji zan mummunar saɓa miki." Wani irin kallo ta yi mata sai kuma ta kalli dad da ya kasa mata magana tun da ta fara maganar. "Ki taimaka mata can kamar yadda kika saɓa, amma ba zan lamunta wata ta shigo mana cikin rayuwarmu ba. Don Allah dad ka ce ta bar mana gidammmu." Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba. Mom ta juya za ta shiga kicin don ba da umurnin a shirya mata babinci, sai ganinta ta yi tsaye da brush a hannunta. Turus ta tsaya tana kallonta cikin jin kunya wanda ta tabbatar wa kanta da ta ji duk abin da Jannah take cewa. "Na kasa buɗe shower ne kuma na duba ban ga makilin ba." Ta faɗa cikin sanyin murya yayin da idanunta suka kawo ruwa tana jin babu daɗi akan abin da ta ce. "Ok, mu je na nuna miki." Ta bi bayan ta ba tare da ta ƙara cewa komai ba. Bayan ta gama wankan ta fito falo cikin rashin sakin jiki ganin kallon da Jannah da Jannah take mata wanda daga ƙarshe tsaki ta saki ta shige cikin ɗakinta. Zama ta yi a takure tana cin abincin wanda ganin hakan ya sanya mom ta sa aka kai mata kayan abincin ɗaki daban wanda ta ware mata akan ta zauna acan. Abinci sosai ta ci sannan ta yi sallah ko da ta buƙaci ta sanar da mom labarinta, amma sai ta kalle ta tare da riƙe hannunta ta ce,"Kar ki damu ki kwanta ki huta da safe za mu yi maganar." Jannah a ɗakinta tana zaune da laptop ɗinta tana buga game gefenta Ummu riƙe da wayarta assignment da aka basu take yi wanda ita ma ba ta daɗe da gama wa ba. Bayan ta gama ta gama ta ije a drower sannan ta koma inda take zaune tare da buɗe data. "Subuhanallahi! Yanzu maganar strike ɗin nan ya tabbata!" Ta ce cikin jimami tana nuna wa Jannah abin da aka rubuta a wayarta cikin ɓacin rai. "Kai! Waɗannan mutanen fa ba su damu da future na mu ba, domin they are after money. Yanzu in suna yin strike how many years they want us to obtain degree, they should consider us as their youngers." "Kin san Allah ba haushin da na ji muna gab da fara exam fa, ya kamata su bari mu gama exam bayan mun sha karatu." "I'm hoping that they should call off the strike if not, zan gaya wa dad kawai na koma outside Country na ci gaba da karatuna." Tsaki Ummu ta yi ta kashe datar ta ije wayar domin ganin strike ɗin ya ɓata mata mood ɗinta gabaki ɗaya. Wayar Jannah ya yi ƙara wanda ta ɗauka da sauri ta kanga a kunninta tana sakin wani irin murmushi bayan ta kashe mata ido. "Umh, bari kika na tashi kar ku ƙone ya shafe ni." Ta ce tana kai mata dukan wasa a bayanta. Ba ta ce mata komai ba sai murmushi da ta yi. "Hello, my angel kina lafiya?" Ya furta da salon muryarsa na jan hankali lokacin da ya ƙaraso kan gadonsa ya faɗa yana shafa kansa. "Am good bab and you?" Ta ce murya a hankali. "Ina lafiya lau in dai babbar mace tana lafiya." Murmushi ya yi har sai da sautin murmushin ya bayyana."Ina lafiya sosai, musamman yanzu da na ji muryarka sai na ji wani irin annashuwa bab." Dariya sosai ya yi."Ina sonki Jannah, amma yau na yi mafarkin da bai yi mini daɗi ba, domin wani na gani ya riƙe hannunki zai ƙwace ki daga gare..." "Bab, me ka yi mishi, ina fata ka sare kanshi da takobi?" Ta ce da muryarta da ya bayyana razana da firgici. "A'a, ban samu na yi hakan ba a mafarki, amma na ɗauki ninyar haka a zahirce ga duk wanda ya ɗauki ɗamarar yin hakan." "Hakan ma ba zai faru ba bab." Ta ce mishi cikin taushin murya. "Ki ba ni dama na bayyana kaina a gurin magabatanki Jannah, ina sonki wanda in ban aureki ba zan iya rasa rayuwata. Kin ga tafiya waje zan yi in ya so ayi maganar auren, da na dawo sai aure, kuma auren za a ɗaura muje can muyi karatunmu is ok Jannah, duk abin da iyayenki suka ce daidai ne matuƙar ba za su raba ni da ke ba." "I will bab, in dai hakan zai faranta maka ko da ace gobe za a ɗaura mana aure." Wani irin ihu ya saka tare da rungume wayarsa." Da gaske kike Aljannata, da gaske kin sauko da burinki mu yi aure da da wuri ba sai kin kai matakin da kika da kike so ba." Dariyar jin ce mata da ya yi aljannarsa domin wani lokacin haka yake ce mata wanda yake sanya ta nishiɗani. "Eh, na amince in har hakan zai saka nishaɗi." Ta furta a bayyane a ranta kuwa cewa ta yi, "Ba ka san tashin hankalin da nake ciki ba wanda ya sa na sauke duk wani burina, domin wancan kinibabbiyar tsohuwar na neman kashe ni da raina. "Yaushe za ki ba ni dama na yi intruducing ki gurin iyayena? ba su da matsala kuma duk sun sanki na nuna musu hotonki." "Ni ma zan so haka, amma kafin nan ka shirya haɗuwa da dad ɗina sun dawo Nigeria." "Wow, masha Allah. Na yi miki murna sosai I would like to come to see my dad and mom." Murmushi ta yi suka ci gaba da waya, wanda sai da aka kira sallah sannan suka yi sallama, shi ma ba don sun so ba sai dai don su yi sallah. A ranar mom ba ta samu damar ganawa da Mujee ba, domin tun da ta fita da safe ba ta dawoba sai cikin dare wanda tana dawowa ta shige ɗakinta, ta kulle ƙofa ta fara aiki a laptop ɗinta daga nan bacci ya kwasheta. Da safe misalin goma da rabi Ummu ce da Jannah a dining suna karyawa, sai Hajiya Baaba da ke kallo Ammy da Nahlin suna ɗaki tana haɗa kayansu, domin gobe da safe za su tafi. Mujee ta fito daga ɗakin da ya zama mallakinta, ta yi wanka cikin doguwar rigar da mom ta ba da umurnin aka siyo mata da hijabai har da gyaluluwa, domin kusan akwati guda aka yi mata. Babu laifi ta yi kyau don har yanzu tabonnin fuskarta ba su gama washewa ba, amma ta ɗan ciko ba kamar lokacin da ta zo ba sai ƙamshi take bugawa. Ture abincin da take ci ta yi tare da ɓata fuska. "Kai wannan bagidajiyar mata ta sa na rasa appetite na, saboda am not more interesting. Bayan talauci ma har da mai da ta shafa suka ɓata mata fuska, ni wallahi in na ganta I fell like vomiting." Ta ce tana hararta. "Please Jannah, stop is not good and is disrespectable. She is your mom's friend and old enough to be you mom." "Tir! Never over my dead body, wannan kucakar ta zama mahaifiyata." Mom da ta fito daga ɗakinta ta ji duk abin da take cewa, wanda tsabar baƙinciki ya sanya ta tsaya ta kasa magana domin ta rasa mai za ta ce mata, saboda lamarinta yana ba ta tsoro. Ƙarasowa ta yi da nufin ta tsawatar ma ta daidai lokacin da Mujee, ta ƙarasa kan dining ɗin za ta zauna. "Ke dalla can ki je ƙasa ki ci abinci, ko ba ki ga masu gidan suna karyawa ba ne." Ta daka mata tsawa tana faɗin haka wanda har sai da ta firgita Ummu ta miƙe a razane tana kallonta. Da sauri Mujee ta matsa gefe hawaye na bin fuskarta ba tare da ta ce komai ba. "Ke fa ba ki da kunya uban kowa sai kin tozarta har da ƙawar uwarki ba za ki raga mata ba." Cewar Hajiya Baaba. Tsaki ta yi ta tura bakinta ta miƙe za ta bar gurin wanda daidai lokacin da mom ta ƙaraso gurin ba ta yi wata-wata ba ta ɗauke ta da mari. Wani irin ihu ta sa har sai da gidan ya amsa ta yi watsi da lafiyayyen abincin da aka shirya akan dining ɗin. "Wayyo Allah! Na shiga uku! Wataƙila sai kin kurmantar da ni da wannan ƙarar naki kamar gyare." Cewar Hajiya Baaba tare da toshe kunninta. "Kika mare ni akan wannan matar?"Ta tambayeta tana kallonta ido cikin ido "Na mare ki nan gaba duka zan yi miki matuƙar kika ƙara mata rashin kunya." "Daadd! Ka ga mom ta buge ni akan wannnan matar da na tsane ta haka kawai nake jin kamar na kashe ta, kuma ba zan ɓoye ba dole sai ta bar gidan nan." "Ki yi shiru Jannah, ki daina ɗaga murya ga mahaifiyarki, kin san ita ɗin wace ce." "Ba na buƙatar sani burina ta bar gidan nan kawai, kai kake da iko da gidanka don Allah ka kore ta." "Babu inda za ta je zama za ta yi gidan nan har sai ranar da ta yi ninyar barin gidan." Ta ba ta amsa tana zare mata ido. Sai kuma ta kalli Mujee, da take tsananin mamakin kalaman Jannah gareta, domin ta gane sam ba ta da tarbiya idanu ta zaro daidai lokacin da ta nufi tibin bango za ta kai masa duka wanda fahimtar hakan Ummu ta riƙe ta. "Wallahi sai ta bar gidan nan ko ba zan ƙara zuwa ba. Ki ɗauki duk lokacinki ki kula da rayuwar wasu, amma ba ki isa ki shigo da kowa a cikin rayuwarmu ba, wanda yin hakan zai kawo mummunar saɓawa a tskaninmu." "Aiko ba ki isa ba matuƙar ni na haife ki ko kin ɗauka ba ta da galihu ce? Ita ɗin 'yar babban ɗan kasuwa ce, kuma mace mai aji da ilmi tare muka yi degree muka fara master wanda ta yi aure suka suka koma garin Abuja daga baya na neme ta na rasa har da shafinta na yanar gizo sai yanzu na ganta cikin mawuyacin halin da ke kanki ba ki wuce shiga cikinsa ba. "Let her be whatever but, I don't care about her identity, cus I hate her ba za ta zauna a gidan nan ba." Ta ce tare da zare mata idanu. Kuka mom ta fashe da shi tare da faɗawa jikin Mujee, daidai lokacin Jannah ta ruga da gudu ta shige cikin ɗakinta tana kuka. "Kowa akwai kuskuren da yake yi a rayuwarsa amma na wa ya wuce mizanin hankali. Na raini 'yata cikin rashin tarbiya sam ba ta ganin darajata, tozarta ni take da gaya mini magana son ranta."Sosai take kuka har da sheshsheƙa. "Kiyi haƙuri Halee, ba mu da ikon canza rayuwarmu kamar yadda bamu da ikon koma baya gareta, tabbas kin yi kuskure domin 'ya'yanmu sune sanyin idaniyarmu, da kalamansu da biyayyarsu yake sawa muji mu a duniya sarakai amma kuma kin tafka kuskuren saka mata tsoronki a ranta. Zan bar gidan nan na koma inda nake rayuwa cikin bola, saboda 'yarki ba ta sona sam ba na son na kawo muku rashin zaman lafiya." "Sam hakan ba zai taɓa faruwa sai dai matuƙar ba na numfashi, ba ta da ikon da za ta ɓani zaɓi a rayuwata ni ce mahaifiyarta dole ta bi nawa zaɓin." "Na cuci kaina na aminta da Kham ya cuci rayuwata ya bar mini tabo wanda ba zai taɓa goguwa a gare ni ba. Mai na yi masa ya zaɓi ya saka dafi wanda gubarsa ya fi na macici a gare ni? Na rantse da zan gan shi da hannuna zan kashe shi na miƙa kaina ga hukuma domin ni kaina ba zan yafe wa kaina na aminta da na yi da shi ba har na shigo da shi cikin rayuwata."Ta ƙarashe maganar tana kuka sosai. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 27-28* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Ki yi haƙuri ki ba ni labarin abin da ya faru dake bayan rabuwarmu. "Ba yan aurenmu da Kham, mun yi amarci cikin so da ƙauna, a lokacin da muka kammala masters muna zaune ni da shi babu aiki, ke kuma kun tafi waje za ki yi phd ya zo mini da murna ya samu aiki a Ilori kuma aiki mai girma. Na yi murna sosai saboda kin san ko da muka yi aure mahaifina yake kula da mu. Ba mu ƙara yin sati ba a Kano muka tattara muka tafi Ilori inda ya fara aiki cikin nasara. Lokaci guda ya yi gida ya sai mota arziki ya yawaita sosai muna zaman mu cikin ƙoshin lafiya. Babu yadda ban yi da shi ba akan ya barni na haifa ko yaro ɗaya ne, amma ya ƙin akan bai shirya haihuwa ba. Kin dai san yadda ya tsani haihuwa da irin yadda yake zagin matan ajinmu da ya gani da ciki?" Ta ƙarashe maganar tana kallon mom wanda ta ɗaga mata kai cikin sanyi sai ta ɗora da ce wa, "Ƙwasam ranar wata laraba ba ina zaune Kham ya shigo gida, cikin tashin hankali domin kuka yake yi, inda ya sanar da ni 'yan kidnappers sun kama iyayena. Na shiga cikin tsananin tashin hankali wanda har sai da na yi kwana biyu ba tare da na san inda kai na yake ba. Bayan na farfaɗo ake sanar dani sun kira har sun buƙaci kuɗin da suke son a ba su na ranson. Na shiga tsananin ɗimuwa jin maƙudan da suka yi demanding duk da cewa mahaifina yana da kuɗi, amma kuɗin da suka buƙata ya wuce hakan. Haka muka tattara komai muka siyar da komai aka kai musu kuɗin. A ranar da suka yi za a ɗauke su cikin tashin hankali, muka isa gurin da tsoron guda biyu, wanda sai gawan iyayena aka ɗauko mini har da ƙanwata sun kashe su." Ka sa ci gaba ta yi da maganar tana kuka sosai, domin numfashinta har ɗaukewa ya ke ƙoƙarin yi, wanda sai da mom ta kamata cikin tsananin tausayawa. "Ba za ki iya ƙarasawa ba ki yi shiru ki bar labarin zuwa wani lokaci." Ta ce mata cikin kuka. Girgiza mata kai ta yi ta ci gaba da cewa, "Na yi kuka na yi kuka har na ba uku lada. Na ji duniyar da nake ciki ba na muradinta. Rayuwa ta yi mini ƙunci babu iyaye kuma na rasa duka dukiyar da suka mallaka. Na daɗe ban samu na dawo daidai ba don sai da Kham ya haɗa mini da rubutu na dangana na fara walwala. A hankali kuma sai ya fara canza mini da na yi magana sai ihu da zagi. Idan na tambaye shi kuɗi sai ya taso mini tamkar zai cinye ni watarana har da mari. A wannan lokacin na yi tunanin ko zaman da nake yi bana neman na kaina ya sanyan hakan, wanda na kakkaɓe takadduna na fara neman aiki. Cikin ikon Allah na samu aiki a wata ma'aikata kuma da kuɗi mai tsoka. Na dawo gida cikin murna na sanar masa a tunanina zai yi farincin, amma sai ya shafa ma idanunsa toka ya ƙi nuna farincikinsa ya ƙi amincewa, wanda ta kai mu muka yi faɗa sosai har sai da ya yi mini duka ya fasa mini jikina. Na kafe akan bakana cewar dole sai na yi aiki amma sai ya ce mini dole na zaɓi ɗaya ko aure ko aiki, wanda take na zaɓi aikin domin a bana buƙatar sake zama da shi ganin yadda lokaci guda ya rikiɗe ya zama kura da fatar akuya. Take ya rubuta mini saki babu ko tausaya, sannan ya sanar mini kan cewar shi ya tura aka yi garkuwa da iyayena, don ya kwashe dukiyar mahaifina. Na shiga cikin tsananin tashin hankalin da ban san lokacin da na yi kukan kura na fara kai masa duka, da duk abin da na gani ina zaginsa da ja masa bala'i da alkaba'i iri-iri. Duka ya hau ni da shi har sai da ya fasa mini jikina, ya kuma kwashe komai nawa har da takaddun makaranta, bai barni na ɗauko komai nawa ba ya gudu ya canza gida, wanda na neme shi na rasa. Abin duniya suka yi mini yawa ga shi ba ni da ko sisi ga yunwa ga ciwo. Da taimakon wata maƙociyata na kai ƙararsa ga hukuma, aka ba za nemansa amma ba bu shi, wanda kan dole na haƙura na dawo Kaduna ina zama a gidan Ƙanin mahaifina. Sai zaman namu ya ƙi daɗi da duka mutanen gidan domin da kansa, kawuna yake ƙorafi a lokacin da mahaifina yake raye bai taimaka masa ba, don haka na nemi guri kar na ɗora masa wahala. Ina zaune a gidan ba tare da na yi zuciya na bar gidan ba, domin ban san inda za ni ba, saboda mahaifiyata bafulana ne kuma an tashi garinsu, ba ta da wani na kusa da zan je garesa. Wani irin manyan ƙuraje suka fara fito mini a ƙasana, suna ruwa su fashe su rinƙa fitar da wani irin ruwa mai ƙarni da wani ga azabar wari. Ganin haka matar kawuna ta sa ya kore ni cewarta ba zan shafa musu lalura ba, tare da yi mini ƙazafin cewar a gurin biyan maza na ɗauko cutar, amma sai na ƙi tafiya domin babu inda za ni. Tsana da ƙyara da tsangwama na fuskanta saboda ko kofin da na sha ruwa ba sa ƙara ɗauka. A hankali ciwon yafi ƙarfina har ta kai ga na fara wari da mutane suna guduna. Na ji na tsani kaina domin hatta iskan da nake shaƙa a duniyar ba na jin daɗinta. Sai kawai na yanke shawarar mutuwa kawai na sadu da iyayena, amma da mutum baya mutuwa sai lokacinta ya yi, kan dole na haƙura da jiran mutuwa na ci gaba da rayuwa ina bara ina cin abinci, don ba zan iya kashe kaina ba saboda na san hukuncin wanda ya kashe kansa. Watarana ina cikin tafiya kawai na tsinci jaridar mai ɗauke da hotonki da sunan ƙungiyarki. Take na gane ki duk da cewar kin canza ba sosai amma ba zai hana na gane ki ba. Na yi murna sosai domin ban ɗauka ƙungiyar ta ɗaukaka kuma tana aiki ba, wanda cikin farinciki na yi bara na haɗa kuɗina na taho Abuja, amma kwasam aka sanar mini da cewar ba kya Ƙasar wasu ne suke tafiyar da ƙungiyar. Na yi baƙincikin ba zan iya ganinki ba. Duk irin yadda mahukutan ƙungiyar suka nuna mini za su iya taimaka mini ko da ba kya nan, sai na ƙi na gwammace na rayu a haka in har zan warke na yi rayuwa ni kaɗai babu wanda na sani. Ganin halin da na shiga wani namiji ya sanar mini da akwai yiwuwar dawowarki Ƙasar saboda kin tsaya takarar Minister, wanda na yi matuƙar farincikin hakan na saka a raina zan jira dawowarki, ko har zan mutu ba ki dawo ba."Ta ƙarashe maganar cikin matsanancn kuka. Gabakiɗaya ɗakin suke hawayen tausayinta ba kamar Hajiya Baaba kuka shaɓe-shaɓe har da su majina. "Kin ga rayuwa Mujee, na tausaya rayuwarki haƙiƙa ya cutar dake. Allah sai ya saka miki Allah ya jiƙan iyayenki. Da ace na san kina cikin wannan halin da na dawo Nigeria ko da mutuwa zan yi a cikinsa, saboda ni ma ba daɗi ya sa na bar Ƙasata ba. Abubuwa da dama suka faru wanda ba na son na tuna domin komai ya wuce." Ta ƙarashe maganar tana kallon dad da ya sunkuyar da kansa jin abin da ta ce. "Na yi miki alƙawarin nemo Kham, matuƙar ina raye sai na hukunta shi akan laifin da ya yi miki, sannnan ki zauna a gidana har ƙarshen rayuwarki, domin na san zalincin da ya yi miki abu mai wuya ne, ki ƙara aminta da wani ɗa namijin." "Har abada ni da aure mun yi hannun riga, na gode ai kuwa in har kika kamo shi kika hukunta shi babu abin da za ki yi mini bayan wannan, domin burina na ga an hukuntashi ta girbi abin da ya shuka." "Mene ne amfanin ƙungiyar in har ban share miki hawaye ba? Karki manta da kamar wasa ƙungiyar ta kafu kuma da taimakon ku. 'Yancin mata.." Ta furta da ƙarfi tana ɗaga hannunta. "Shine burinmu." Mujee ta ɗaga hannuntan tana faɗi da ƙarfi. Murmushi mai kama da kuka suka fara tare da rungume juna lokaci guda memerories na shekaru suka fara dawo musu. Ummu ta buɗe ƙofar ɗakin da Jannah take ciki ta shigo a ranta tana jimamin halin rayuwa da Mujee ta shiga. "Jannah, don Allah ki tausaya wannan matar, ba ki ji halin ƙuncin da ta shiga ba." Sai ta fara ba ta labarin cikin tsananin tausayawa. "Leave me alone with that story ni ko kaɗan ba ta burge ni, saboda ta yi ruwan munafukai, na tabbata labarin nan fabrications ne. Miƙewa ta yi a zafafe ta fice ba tare da ta kalli inda take ba domin ta ci ka kafiya da rainin wayo. Sakamakon strike da aka fara mom ta roƙi abar Ummu da Jannah har da Nahlin su ɗan yi mata hutu, wanda Jannah ta ji daɗin hakan domin ba ta gama ganin dad ba. Jin za su zauna Hajiya Baaba ta dire kan ba za ta tafi ba sai lokacin da za su tafi, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ba mom ba. A maimakon ta zauna a gidan ta basu lokacinta, amma sam inta fita tun safe sai dare take dawowa, kasancewar abubuwa sun yi mata yawa. Ga siyasa ga ƙungiyarta wanda dawowarta mutane sai zuwa suke sosai. Duk iya ƙoƙarinta na son ta samu lokacin kanta ta zauna da mutanen gidan, amma abin ya ci tura! Saboda ko da safe ba sa ganinta kafin su tashi ta fice. Ta san cewar hakan zai ƙara bakanta ranta, amma sai dai ba ta da wani zaɓi wanda ya wuce hakan. Ta dawo gida da ciwon kai mai tsananin zafi sakamakon wunin yau a meetings ya ƙare. A maimakon da ta sha maganin ta kwanta, amma sai ta miƙe tana jin yadda kanta yake sarawa tamkar zai rabu gida biyu. Files biyu ta ɗauka ta nufi ɗakin Mujee, amma ba ta nan sai ta nufi kicin don tunaninta tana can. "A Halee, yanzu nake son bada umurnin abin da za a girka na shigo mu na yi miki sai da safe. "Ok, don't worry ni ma na dawo da ciwon kai na so nake na huta, but I have to give you this." Karɓa ta yi ba tare da ta duba takaddun ba."Subuhanallahi! Am sorry Halee, but did you take meds? I know you don't like taking it." "Zan sha saboda ya zamar mini dole, ina jin ciwon kan har kwanyata." Ta ce da fuskar da ke bayyana ba ta da lafiya. "Sorry, wishing you quik recovery." "Amin ta ba ta amsa." Tana cewa,"Ki duba takaddar mana ba ki abu kin riƙe kawai." "Oh! Sorry ciwon kanki ya tada hankalina." "Oh my God! Offer na aiki a ƙungiyarki?" Ta tambayeta cikin tsananin mamaki. "Eh, ai kin cancanta Mujee, ko da can ai ke kika nuna bakya buƙatar zama a Arewa, wannan dalilin ya sa na haƙura. Sannan waɗannan takaddun na shedar karatunki ne, da na ƙoƙarta na samo miki su" "Haka ne, ga shi yanzu rayuwa ta yi mini kamun kazar kuka na dawo." Ta faɗa sai hawaye suka wanke mata fuska sosai ta rungumeta cikin matuƙar farinciki. "Haƙiƙa kin cika uwar marayu! Allah ya ci gaba da buɗa miki da haskaka rayuwarki, ya ba ki nasarar lashe zaɓe." "Allah dai ya shige mana gaba. Bari na je na kwanta sosai kaina yake takura mini, gobe sai ki kasance cikin shiri tare zamu tafi. Ke ce Sakatariyar Hajiya Turai." "Ma sha Allah."Ok, sai da safe Allah ya ƙara sauki." Har ta nufi sashinta sai kuma ta dawo." Wai ni kam Mujee, har yanzu skills na ki na yin turaren wuta yanan?" "Eh, ban manta komai ba, don ko a can na tambayi Kham na ci gaba ya nuna baya so." "In sha Allahu zan yi miki transfer na kuɗi, sai ki je kasuwa ki siyo komai ki fara haɗawa. Zan yi magana a nemo miki shago da waɗanda za su zauna, zama babu sana'a ga 'ya mace akwai matsala. Mu tashi lafiya." Ta ce tare da saurin shigewa don ba ta son godiyar da za ta yi mata, ta barta baki buɗe tana share hawayen farinciki. Washegari da safe bayan ta tashi saboda ciwon kan da har yanzu bai daina ba sai ba ta yi fitan sammako ba. Bayan ta yi wanka ta saka doguwar riga ta fito falo don ta karya saboda tun da ta farka take jin yunwa. Gabakiɗaya mutanen gidan suna falo sai Mujee da take kicin da masu aiki. "Yauwa Halimatuu, ma za ki zo gida zan koma saboda sam ban ga amfanin zamana a gidanki ba. Sam ba ki da lokacin da za ki zauna mu yi hira, kar ki manta wata uwa duniya kika tafi na tsawon shekaru, amma tun da kika dawo bana tunananin mun yi zaman minti talatin dake. Kullum sai dai ki barmu da arnar da kika cika gidanki da su wai masu aiki, su yi ta mana yare." Ƙarasowa ta yi ta zauna gefenta."Kiyi haƙuri Hajiya Baaba, na san ban kyauta ba, amma wallahi rashin lokaci ne. Ga shi ina son na tafi Ingila zan yi sati biyu acan." "Ki bar suya? Allah ya kyauta kin san Allah gobe ina Zariya ba zan iya zaman kurame ba. Kullum gida tsit kamar an yi mutuwa gabaki ɗaya kin sa neman kuɗi a rayuwarki." "Ba ki ga komai ba Hajiya Baaba, in dai mom ce, sam ba ta damu da kowa ba sai neman kuɗi. Ni dama saboda dad ɗina na zauna."Cewar Jannah. "Ni kam tafiyata ya zama dole saboda na gaji da zama shiru, ai sai wata cuta ta kama haka kawai." Ta ce tana harararta sannan ta ci gaba da cewa, "Gobe na gaya miki zan tafi inya so ki tafi gaba da Ingila ba ta shafe ni ba." "To Allah ya kaimu saboda ko na ce miki zan samu lokaci hakan ba zai yiwu ba, domin abubuwa sun sha mini kai, amma sai ki bari nan da kwana biyu, sai ki shiga kasuwa ku sayo komai. Su Jannah kuma in an janye yajin aikin sa dawo." "Su yi ta zama zama ni dai ba zan iya ba. Na gaji da abincin arna, kuma na'urorin da kika sa a kicin tsoro suke bani. Gara na koma na rinƙa cin dabbu da fate da gauda. Ranar nan da na ce a yi mana dabbu wani iskancin dabbu aka yi har da su kayan ciki, gabakiɗaya bai yi kama da dabbu ba." "Hmmm! Su Hajiya an saba da cimar wahala." Cewar Jannah tana dariya. "Eh, na ji a haka na haifo masu kuɗi ba." "Ki yi ta mana gorin 'ya'yanki masu kuɗi an gaya miki a tsiyace za mu rayu." "Oh ban sani ba kuma yarinya ta yi mini rashin kunya yanzu zan huce haushin uwarta akanta." Dariya ta yi sai kuma ta yi shiru ba ta ce koma ba don ta san tana iya sakar mata dundu. "To maganar auren Jannah, ya kamata a saka rana ina komawa zan yi magana da Aby, duk yadda muka yi zan sanar muku." Tsiri-tsiri suka yi da ido suna son amsawa, suna tsoron yadda Jannah ta yi musu wuri-wuri da ido, tana son jin me za su ce, wanda ya sa suka yi shiru sai kallon juna suke yi. "Ikon Allah, ina magana kun yi banza da ni kuna zare ido sai kace kun yi ƙarya. Oh Allah ya kawo mu zamanin da uwa take haihuwar uwar gijiyarta. Tsoronta kuke yi kuka kasa magana? To ni bari na gaya mata don 'ya'yan da na haifa bana shakkarsu ballantana wata jika." Ta ce musu tana kallon Jannah da ta cika ta batse jin maganar har idanunta sun fara kawo ruwa. "Maganar auren ki da Ajmal babu fashi don maganar sa rana muke yi." "Ai wallahi ba ki isa ba don ba zan koma Zariya ba, kayana zan kwaso na sanya dad ya yi mini transfer na dawo Abuja." "To shikenan, ma ji ma gani. In kika ji an sanya rana sai ki kashe kanki." Ta ce tare da shiga cikin ɗakinta. "Dad, did you hear what she is saying? Impossible na ce bana sonsa ana dole ne?" Kama hannunta ya yi tana kuka suka shiga cikin ɗakinsa ya kulle ƙofa tare da dawowa gefen gadon da take ya zauna. "Kin san ya za mu yi ki kauce wa aurenan?" "No dad, amma ko mai zai faru ba zan yadda na da auren nan ba, domin in ta matsa zan gudu." "Subuhanallahi! Hakan ma ba zai faru ba. Kar ki manta in kika gudu ba mu da kowa ke kaɗai Allah ya bam.." "To in kana son zamana ka sa ta janye maganar auren."Ta faɗa a zafaffe. Miƙewa ya yi ya buɗe windo yana kallon waje sai kuma ya dawo ya zauna gefenta tare da kama hannunta. "Kina jina Jannah, magana ta fahimta zamu yi, amma don Allah ki natsu ki yi mata kyakykyawar fahimta, saboda ta wannan hanyar kawai za mu samu mafita." "Ok dad, am all ear." Ta ce cikin zaƙuwar son abin da zai ce. "Na yi wa Hajiya Baaba laifuka da dama wanda bai cancanci ta yafe mini ba. Burina Allah ya kawo abin da zata buƙata na wanke laifin da na yi mata. Ki yi haƙuri ki amince da aurena, amma ba ina n.." "No dad! There is no way, I can't accept that." Ta fisge hannunta tana kuka sai kuma ta faɗa jikinsa. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 28-29* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "No dad! There is now way, I can't accept that." Ta fisge hannunta tana kuka sai kuma ta faɗa jikinsa. "Am sorry Jannah, ki tsaya kiji abin da zan ce miki. Kin ga Ajmal baya son auren kuma yana da matarsa, babu abin da zai haɗaku na aure. Za ki zauna kiyi karatu har ki gama degree kina gama wa ni kuma zan ɗauke ki kije duk Ƙasar da kike so kiyi karatu. Kin ga saina fake akan ya ƙi kula ki ne a matsayin matarsa na raba auren, kuma dama ko addinin ya halasta haka." "No, I don't think this your idea will work. Kuma ni bana son na auresa ko na kwana uku ne, domin yana da takura sam ba zan sake ba kuma Huzaifah ina tausayinsa domin yana sona." "Zan ji da shi zan yi masa bayani yadda zai fahimta, kin ga kince zai tafi ƙaro karatunsa lokacin da kika gama sai ki bishi can kuyi rayuwarku." Kuka ta ƙara fashewa da shi."Ina sonsa ba zan iya nisa da shi ba. Ba zan iya ɗaukar tsawon lokaci ba tare da na ji muryarshi ba. Ka bar wannan maganar dad, kai ka haife ni kuma kai kake da ikon zaɓa mini mijin da nake so ba Hajiya Baaba. Sam haɗa aurenmu ba wai ta yi don alkhairi bane, don kawai an fasa mata kai take son ɗaukar fansa. In har ba ka son ka rasa ni kawai ka hana aurennan." "What can I do Jannnah? Hajiya Baaba ta dake kan aurena nan kuma bamu da zaɓin da ya wuce mu yarda, saboda kin fi sanin kowa halinta." "Na san halinta amma ba zam bari ta cuci rayuwata ba. As I said it earlier on, I can't be as his wife, and I love Huzaifah he is my desired." Shiru ya yi yana kallon ta domin ya rasa yadda zai yi ya shawo kanta ya santa da kafiya, amma dole ya yi duk hanyar da zai yi ya shawo kanta ta amince. Marairaice fuska ya yi ya ƙara kama hannunta." Kina son mu rabu da mahaifiyarki ko? Domin mundin na ƙi amincewa da auren zai zama sai dai na zaɓi aurenki ko nawa." "I don't bloody care! Let it be ko ya ya ne. Ni dai kar a aura mini shi, ai dama ba jin daɗin zama da 'yarta kake yi ba sai me don kun rabu." Idanu ya zare jin abin da ta faɗa a ransa yana mamakin lallai ta yi nisa. "To ni ina sonta kin san wahalar da na sha kafin na aureta.." "Is ok dad, I understand much better." Ta fisge hannunta ta ruga da gudu ɗakinta ba tare da ta damu da kiran da yake mata. Tana shiga ta faɗa kan gado ta ƙara sakin wani kukan ta ɗauko wayarta. Numbobinsa ta danna ta kira wanda bugu ɗaya ana biyu ya ɗauka cikin farinciki, saboda abinci yake ci a dining amma ganin kiran ya miƙe ya ɗan matsa nesa da iyayensa. "He my angel how doing? I call you but you didn't pick I wanna tell you that my family wants to see yours" "Huzaifah na shiga uku Hajiya Baaba, za ta raba ni da kai, auren dole za ta yi mini da Ya Ajmal, wannan bagidajen." "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Aure kika ce Jannah?!" Sai kawai ya ji gwiwowinsa sun gaza ɗaukarsa. Wayar ya saki ta faɗin ƙasa sai ya dafe ƙirjinsa. "No, impossible even in my dreams domin ke tawa ce, babu wanda ya isa raba ni dake!" "Subunallahi! Son what's wrong, are you alright ko mutuwa aka yi?" Ta jera masa tarin tambayoyi ganin lokaci guda ya canza daga kalar farincikin zuwa tashin hankali. "Ka zo ka ɗauke ni mu gudu muje can waje muyi aure." Mom ta ɗauki wayarsa da ya jefar a ƙasa daidai lokacin da take cewa haka. Kashe wayar ta yi tare da kamo hannunsa."Please son, don't hurt yourself. Everthing will go right. Ka san waye mahaifinka babu abin da za ka nema ka rasa a duniyarnan, saboda ko balarabiya ka nuna kana so sai mun aira maka ita. " Tsananin mamakin abin da ta furta yake mamakin domin ko kaɗan Hajiya Baaba ba ta nuna masa rashin so ba, a lokacin da suka je gidan kuma mai ya faru har take shirin yi mata auren wuri bayan tarin burikan da take da shi a rayuwarta. "We have to go to her hause right now, saboda ba zan iya rayuwa ba in har babu ita. Ina sonta irin son da ban taɓa ma kowa ba, domin ita ɗin ta cancanci a sota, za ki gane haka in har kika ganta." Ya ce cikin hawaye tare da rungume dad ɗinsa da ya fito. "Dad, za su raba ni da ita wallahi auren dole za su yi mata. Na shiga uku don in har na rasata ba zan iya aure ba." "Mai ya faru Naja'atu, su wa za su yi mata auren dole?" Ya tambaye ta cikin sauri. "I don't know, she just called him and informed him just now." Ta ba shi amsa tana yarfe hannunta. "Ai ko babu wanda ya isa ya rabata da kai ka ji son ka kwantar da hankalinka. Ma za mu gama karyawa mu tafi gidan na su." "I can't eat now. Ku gama ina jiranku lemme call her and know the address." "Ok ." Suka masa masa tare da zama suka fara cin abincin, wanda kaɗan suka ci suka barshi ba don sun ƙoshi ba sai dai ganin yadda ya tada hankalinsa yana safa da marwa a gafensu, bayan ya kirata ta sanar ta yi masa kwatancen gidan. A wannan lokacin suka ɗauki hanyar Abuja duk da tarin ayyukan dake gabansu, amma ba su kula ba saboda farincikinsa yafi musu komai. Jannah da ta san da zuwansu kicin ta shiga ta ba da umurnin ayi musu abinci kala-kala, wanda ganin haka Hajiya Baaba ta tasata da tambaya, amma ko kallon banza ba ta yi mata ba ballantana ta sa ran za ta masa, wanda daga ƙarshe ta yi fushi ta ƙyaleta. "Dad, going out? Iyayen su Huzaifah za su zo, they are on their way." Ta ce masa fuskarta a ɗaure ganin ya yi shirin fita. Ya buɗe baki zai yi magana sai ta juya da sauri ta nufi ɗakinta ba tare da ta ce masa komai ba. Jakarshi ya ije yana mamakin har ta gaya masa sun yo masa zuga ai shi babu ruwansa. Ba su wani ɗauki tsawon lokaci ba suka iso garin Abuja, saboda shi yake tuƙin kuma ya ƙure maneji. Ba su yi mamakin kyan gidan da tsarinsa ba domin sun san wace ce Halima uwa ba da mama. A falo aka ije su wanda ko ruwa ba su sha ba Huzaifah ya duƙa yana kuka a gaban dad. "Dad Allah dad, kar ku raba ni da ita wallahi ina sonta ban taɓa jin son wata 'ya mace kamar ta ba, and we are compatible, zan barta ta yi duk a abin da take so, ba zan zamo azzalimi ba." Sai ya yi matuƙar ba shi tausayi matuƙar gaske har yana jin ƙwallah na shirin zubo masa, yayin da momeries na tsawon shekaru suka dawo masa wanda ya fuskanci irin wannan ranar da ya sha tozarcin da ba a taɓa masa. Sosai ya yi na'am da shi saboda duk da hutu da waye da gata, da aka ƙawata rayuwarsa bai hana shi zama cikakken namiji wanda kowa ne uba zai yi burin 'yarsa ta aura. Uwa uba ga kyau da tashen ƙuruciya da natsuwa, musamman yadda yake masa maganar yana hawaye, ya san idan ya aureta zai kula masa da ita saboda tsananin sonta da yake. Hannunsa ya kama ya riƙe yana shafa bayansa wanda ganin hakan iyayensa suka fara murna suna ganin alamun nasara... "Calm down, ɗan samari. Matsalar ba daga ni ba saboda da ace ni ne ayau zan aura maka Janah, don n yaba da hankalink..." Mom ce ta katse maganar da yake yi wacce ta yi sallama ta shigo, saboda tun da ta sanar masa ya kira ta. Sosai suka yi gaisuwar mutunci da girmamawa, bayan sun gama gaisuwa irin ta su ta 'yan boko masu ji da kansu da aljihu, sai mahaifin Huzaifah ya yi gyaran murya ya ce, "Huzaifah ya sanar mana da soyayyar da yake yi wa 'yarku. Sai dai, ya gaya mana ita yarinyar tana son ta gama karatunta, kuma shima yanzu haka waje za shi ya yi phd ɗinsa, amma kwasam yau ta kira shi take sanar mishi da za a yi mata auren dole. Wanda ba mu yi ƙasa a gwuiwa ba muka zo neman iri tare da ba wa wancan haƙuri tun da tana son Huzaifah." Shiru suka yi na 'yan sakwanni babu wanda ya ce uffan sai mom ta yi gyaran murya ta ce, "Eh haka ne wallahi da yake ɗan yayana ne za a haɗa auren muna baku haƙuri yaje ya nemi wata." "No mom, don Allah karki ce haka ina sonta ba zan iya auren wata in ba ita ba. Ki bani ita na yi miki alƙawarin zan riƙeta duk yadda kike so, amma don Allah don annabi kar ku raba ni da ita." Ya ƙarshe maganar cikin muryar kuka tare da ƙarasowa kusa da ita ya duƙa ya ɗaga hannunsa yana roƙonta. Babu wansa bai ba shi tausayi ba shiru ta yi tana tuannanin yadda za ta ɓullo ma lamarin, saboda Huzaifah ya yi mata ita kanta za ta so ya aureta. A wancan lokacin da ta kawo wanda take so in har da ba shi aka aura mata shi ba Allah kaɗai ya san halin da za ta shiga. "Yaran ba so suke ba mahaifiyata ta tilasta hakan, bari na kira muku ita in har kuka shawo kanta shikenan." "Za ta amince Hajiya Baaba ba ta da matsala, alokacin da naje gidanta hannu biyu-biyu ta karɓe ni." Ya faɗa cikin murna domin shi tunaninsa har ya mallaki Jannah ya gama duba ga yadda ta yi ta nan nan da shi. Mom kuwa miƙewa ta yi ta shige ciki a ranta tana fatan Allah ya sa ta amince, wataƙila don bai san halinta bane ya sa ya furta haka, amma Hajiya Baaba kura ce da fatar akuya." Ta same ta a cikin ɗakinta tana ta haɗa kayanta tana gungunai. Ganin ta shigo ya sa ta haɗe rai ba ta ce mata komai ba ta ci gaba da haɗa kayanta."Hajiya Baaba shirin tafiyar ake yi?" "Eh to mene ne amfanin zamana a gidan da ba a da buƙata ta? Kullum ba ki da lokacina ai gara na koma gidan Muhammadu in ya so yanka ni matarsa za ta yi inna mutu baki da asara. Da ninyar zama na zo amma ba zai yi ba." "Haba Hajiya, ina iyakan ƙoƙarina fa aiki ne suka sha mini gab.." "Ki je ki kashe kanki akan al'umma ke kika sani." "Ni ba wannan ya kawo ni ba muna da baki a guest room." "Mene ne haka?"Ta tambayeta a ƙubule tana mata mugun kallo. Dafe kanta ta yi sam ta manta ta yi turancin."Ɗakin baƙi nake nufi" "To shine sai an nuna mini iyaka na rashin turanci?" Tsaki ta yi ta ci gaba da haɗa kayanta ba tare da ta kalle ta ba. "Hajiya jiranki fa suke yi." Ta faɗa cikin ƙosawa wanda ta taso mata a harzuƙe. "Su waye ne? Wa na sani a garin Abuja da za su zo mini? Ki fita idanuna ki barni na haɗa kayana, na koma Zariya tun kafin na taɓa miki halina." "Ni dai don Allah ki zo ki gannin ma idanunki." Ta ce tana ƙoƙarin ficewa. Tsaki ta ƙara saki kamar ba za ta je ba komai ta tuna sai ta ije jakar da take shiryawa ta fice. Jannah dake laɓe a bayan labule don tun da suka shigo ta zo gurin ta laɓe, tana addu'ar Allah ya sanya kunnuwanta su ji mata Hajiya Baaba ta amince, wanda za ta sa a sanya rana a gurin don kar ta canza shawara. Hajiya Baaba da ta so za ta shige ɗakin sai ta hangi ƙafafunta a basu shige ba. Yaye labulen ta yi tana kallonta wanda ta fara mazurai. "Uban me kike yi a gurinan? Yaushe kika zama munafuka kike laɓe?" "Ban sani ba kuma ba ruwanki da ni." Ta ce a hankali kuma cikin tsiwa. Jikinta ya bata bakin na ta ne ko iyayen Huzaifah. Wani rashin mutunci ta saka a ranta don ko maka fa madina za su ba ta ba za ta fasa auren nan ba. "Iyayen Huzaifah kika ɗauko mini ko? To ko shugaban Ƙasa kika kawo bai isa yasa na janye ƙudirna ba. Shashasha kawai." Ta saki labulen tana mata mugun kallo wanda ba ta ce komai ba saboda da ƙarfi take maganar, kuma ta san tana yi ne don mutane suji. Da sallama ta shiga falon yayin da ta yi fiƙi-fiƙi da ido sannan ta haɗe rai tamkar an aiko mata da mala'ikan mutuwa. Zama ta yi a hamshaƙe tana masa gaisiwar da iyayen Huzaifah suka yi mata a gajarce do ko na Huzaifah da lafiya kawai ta masa ta sha kunu. Jikinsu ne ya yi sanyi ganin yadda ta karɓe su. "Hajiya Baaba don Allah ki taimaka kar ki raba ni da Jannah wallahi ina sonta zan iya mutuwa in ban sa.." "Kai ko Huzaifah kake ko wa? Wane irin rashin kunya kake da shi? A gaban manya kake maganar son da kake ma mace? To ai ni ban ga amfanin zuwan iyayenka ba matuƙar kai za ka yi magana." Ta faɗa tana salati da tafa hannu sai ka ce wanda ya aikata mugun zunubi Huzaifah sai ya cika da matuƙar mamaki, take ya gane ita ɗin kura ce da fara kauya, domin lokacin da ya je gidanta ba haka ta karɓe shi ba. Jikinsa a sanyaye ya koma ya zauna lokaci guda hawayen da yake ƙoƙarin mayarwa suka wanke masa fuska. Ganin hakan, sai jikinsu ya ƙara matuƙar sanyi jin abin da ta ce, don ba su ga abin aibu ba mahaifinsa ne ya yi gyaran murya. "Ki yi haƙuri kin san sha'anin yara da abin da suke so. Ki taimaka mana ki bamu auren Jannah za ki yi alfahari da hakan." "Haka ne, ai dama ban ce ba zan yi ba, amma gida bai ƙoshi ba ina za a bawa dawa? Adamun da zan haɗa shi aure da ita shine kawai zai iya zama da ita domin kura ce da fatar akuya. Kuma tunani juya Adamun ya aura in har ba aure na yi masa ba, yadda matarsa ta mallake shi ba zai iya ƙara aure ba ni kuma ina son kafin na mutu na aurar da yarsa." "Hajiya magamar da ya kawo shi daban da wanda kike masa. Yaran suna son junansu don Allah karki raba so.." "Sannu Laila da Majnun! Na gaya maka Jabiruu in ima magana kana saka mini baki wallahi sai na yi maka tonon silili, saboda ba ka da ta ido har baki kake da shi." "Allah ya ba ki haƙuri." Ya ce tare da kama bakinsa bai ƙara cewa komai ba yana kallon mom, da ta dafe kai tana dana-sanin kiranta, yayin da kunya ta kamata kamar za ta nitse, jin ta ɗauko magana daban. "Da haƙurin ta mutu sadakar nawa ka bani?" Bai tanka mata ba ya yi shiru. Juyawa ta yi ta kalli iyayen Huzaifah aure da na ƙulla babu uban da ya isa ya sa a fasa ko da iyayensu. "Ɗanku ya je ya nema a waje ga matanan birjik sai wanda ya zaɓa, don ma bai san halinta bane har yake asarar hawayensa da kun san ita ɗin kura ce da fatar akuya ba za ku nema wa ɗanku ba. Ai Jannah sai Adamuu shine daidai da ita." Jin abin da ta furta Jannah dake kuka abayan labule ba ta san lokacin da ta banko cikin falon da ƙarfi ba. "Ina sonsa kuma shine wanda nake jin zan iya rayuwa da shi. Na rantse babu wanda ya isa ya raba ni da shi, in ba haka ba zan kashe kaina "Shashasha! Wa ya damu don kon mutu. Kafin ke mutane nawa suka mutu akan soyayya kuma har yau ba a daina raba masoya. Ni da kaina iya siyo miki gubar kici ki mutu kuma ba zan fasa aura miki shi ba sai ku yi rayuwar auren a kiyama." Ta ce tare da juya ta kallo iyayensa ta ci gaba da cewa, Kun ga ku tashi ku fice mini daga gidan 'ya kuka wani zauna ɗika-ɗika daku kun cika kujera." Wani irin gigicecen ƙara ya saki ta nufi Huzaifah ta faɗa jikinsa. "Ina son shi don Allah karku bari ta raba ni da shi don Allah dad, do something I love him." Ta ƙarashe maganar tana gurmusheshen kuka. "A lallai fitsararki ta kai intiha a gaban iyayenki kike rungume ƙato? Ai ko ba ki ji kunyar ta da kika raina ba ka ji kunyar iyayenki. Mara kunyar banza kawai." Huzaifah ya kama ta ya riƙe sosai shima kukan yake yi. "Don Allah dad, ka yi wani abu ka sanya kuɗi ka aura mini ita I really love her and I can't do without her." "Au ya sanya kuɗi an gaya muku mu ɗin matsiyata ne? Ko tirelal kuɗi za ku kawo ba zan aminta da auran na ba." Dad ne ya ɓanɓare Jannah daga jikin shinya riƙe tana kuka sosai yayin da hawaye ya cik masa zuciya. Wani irin haushin Hajiya Baaba ya ke ji kamar ya shaƙeta ta mutu kowa ya huta. Sai yake ji a ransa kamar yabi maganarta kan ya rabu da mom ya ƙara aure in har hakan zai sa ta auri wanda take so, amma da ya tuna halin da mom take ciki da siyasar da ta faɗa, wanda dole tana buƙatar wanda zai ba ta kariya, don ko ita ba ta san ta sa kanta cikin tashin hankali ba. Sai ya ji ba zai iya ƙyale ta ba domin yana sonta yana jin ransa fansa ne a kanta. Yana son ta manta baƙincikin da ya sanyata na wasu tsawon shekaru. "Ku ɗauki ɗanku kubar mini gida kar ya ƙara kiran sunan Jannah domin ina komawa gida za a sanya ranar aurenta." Ta faɗa a zafafe tananmusu kallon banza. "Na shiga uku shikenan ta raba ni da shi Jannah ina sonki! Rabamu tamkar raba rai da gangar jiki ne ba zan iya rayuwa in babu ke ba." Sai kawai ya yanke jiki y faɗi a sume. Ganin haka Jannah ta ruga ta faɗa jikinshi tana kiran sunan shi amma babu numfashi. "Huzaifaaah!" Ta ja sunan tare da zubewa a kansa ta sume wanda ganin haka suka yo kansu da ruwa aka watsa musu. "Kai amma 'ya'yannan sun iya shirin film ku gama shirin film ɗin aure babu fashi." Ta ce tana dariyar takaici, ta fice ba tare da ta damu da halin da suke ciki ba. Tsananin mamaki ya kama su na rashin imaninta. Take dad ya fara tunanin anya ta san zafi da raɗaɗin soyayya? Ruwa suka wasa musu wanda sika farfaɗo kusan a tare. "Dad, ta amince kuwa?" Cewar Huzaifah. Jannah kuwa kuka ta saka tare da faɗawa jikin dad. "Ban san girman laifin da na yi mata ba take son aura mini shi." "Ku yi haƙuri don Allah! Domin bamu da zaɓi wanda ya wuce mu bi umurninta. Ku kanku shedane akan rarrashinta da muke yi." "Zo muje son na ga jikar na ta ba gwal ba ce da in ba ka aureta ba za ka mutu. Ka zaɓi wata macen ko 'yar gidan uban wane ne zan aura maka." Mahaifiyarsa ta furta cikin tsananin zafi tana hucin ganin ƙasƙancin da Hajiya ta yi musu. "Duk abin bai kai haka ba kuyi haƙuri zan yi iyakan ƙoƙarina kan abin." Cewar dad cikin tausaya. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 29-30* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Mom kuwa ta kasa cewa komai tsananin tausayinsu ya cika zuciyarta. A ranta dana-sani take yi akan bijirewa umurninta na ƙin auren zaɓinta, wanda ba ta taɓa tunanin ko a duniyar mafarki za ta ɗauki fansa a kan 'yarta ba. Ga shi wanda ya isa ya yi mata dole babu shi ƙasa ta rufe idanunshi. Ta ɗago idanunta tana kallon Huzaifah da ya kama ƙafafunta yana kuka ya ce, Please help me, ina sonta ba zan iya rayuwa babu ita ba." Sai ta kasa ce masa komai idanunta suka kawo ruwa. Tana ganin mahaifiyarsa, ta ja hannunsa za su fice, wanda ganin haka Jannah ta bi bayanshi da gudu tana kiran sunan shi. Da sauri dad ya kamata ya riƙe sosai yana rarrashi har sai da ya ji fitar motarsu. Kuka ta ƙara saki ta duƙa ƙasa. "Yanzu shikenan, ta raba ni da shi? Kai ina ba zai yiwu ba!" Ta tambayi kanta tare da bawa kanta, amsa sai kuma ta ruga fa gudu zuwa ɗakin Hajiya. Tibin dake bangonta sauke ta danƙarashi da ƙasa tare da watsi, da kwalaben turare da na kwalliyar show glass da suke ciki. "Na ce bana son shi ko an aure dole? I dan laifi iyayena suka yi miki, ki yi musu hukunci, amma ba wai ki raba ni da wanda nake so ba!" "Aikin banza in kin so ki fashe kayan gidan nan ko ki rushe gidan, ko a kwalar rigata don iyayenki kika yi wa hasara." "Hajiya Baaba, ba kya sona kin tsane, kuma wallahi kin ji na gaya miki ko mutuwa za ki yi, ba zan aure shi ba." Ta ce cikin fusata jin abin da ta faɗa. "Aikin banza kike don banga abin da za ki faɗa ya sani baƙiciki ba, saboda kin faɗi wanda ya fi wannan, kaffara dai ki shirya bayan bikin na rantsuwar da kika yi, ko da yake ina kika damu da addinin ballantana ki rama." "To shikenan, tun da haka kika ce." "Jannah ki iya bakinki mahaifi.." "Please ki ƙyale ni don tana mahaifiyarki sai ta shiga rayuwata, ai duk ke kika ja mini inda kin tsaya kin kula da ni, da ban je gidanta ba har ta maƙala mini wannan auren." Sai ta sa kuka tare da zaman 'yan bori tana faɗin, "Saboda ina gurin ki ne shi ya sa za ki yi mini auren dole. Na rantse ba zan dawo Zariya ba, domin na tsani zaman Zariya gara dad ya yi mini transfer na dawo Abuja da karatu." "Au Allah ko? To ki sani ko London kika koma wallahi sai an ɗaura auren nan." Tamkar wata ƙaramar yarinya ta ci gaba da ihu tana birgima a ƙasa. Sai suka rasa yadda za su yi da ita, suka zuba mata idanu domin hatta shi kansa dad, da ya matsota kuka ta ƙara saki tana matsawa ta ce, "No! I said don't come closer to me, in har ba za ka iya hana auren nan." Kamar umurni ta ba shi ya juya ya fita kanshi na sarawa domin shi kansa lamarin ya ishe shi. Yana ƙoƙarin shiga cikin motarsa ya ji muryar maigadi yana magana da ƙarfi, wanda ya sa ya juya da sauri yana kallon gurin. "Na ce maka ka ƙyale ni na shiga cikin gidannan, saboda ɗan'uwana Mudi yana cikin gidannan." "Waye wani Mudi? Ma za ka ɓace domin bamu san wani Mudi ba." Cewa Hamisu mai-gadi yana tura shi. Da sauri ya ƙaraso gurin har yana tuntuɓe wanda saura kaɗan ya faɗi ƙasa. "Kai Hamisu ƙyale shi ya shigo ɗan'uwana ne." Ya furta daidai lokacin da ya ƙarasa gurin yana kallonsa wani iri. "Innalillahi! Mudi, ashe da gaske ne kun dawo Nigeriya? Sannu da mantawa da mu." "Shigo ciki Yaya Bala." Abin da ya ce kenan ya matsa ya basu hanya zuciyarsa cike da baƙincikin zuwarsu. "Oh ni Jummai! Ka ga wallahi bai yi farincikin zuwanmu ba. Anya Mudi za ka wuce siraɗi kuwa." "Haba Yaya! Na ce ku shigo kun tsaya kuna zuba kamar kaɗanya. In ke kike sa mutum ya wuce sai ki hana ni, ina zo wucewa." Ya ƙarashe maganar yana ba ta amsa. "A mai da wuƙar ai ban isa ba, amma ka san duk wanda ba ya zumunci ba ya samun rahamar Ubangiji. Kawai saboda mace ka gudu ka barmu don ka ga babu idanun Inna da Baba." "Ki ƙyale shi ai baƙin kwaɗayinsa sai ya ja masa wahala, domin na tabbata matar nan, yankan kan mutane take yi. Dubi daga zuwa Ƙasar waje, sun gina gida tamkar aljanna." Bala ya furta yana shafa get ɗin gidan. "Za ku shigo ne ko na kulle ƙofar, ko sai kun gama tozarta ni kuna gaya mini asalina?" Ya furta cikin ɓacin ganin duk abin da suke faɗi maigadi na jinsu. "Kai amma aradu wannan mata ta nemi duniya Allah ya ba ta, dubi irin wannan gida. Ni fa tun da uwata ta haife ni ban taɓa ganin bango da tayas ba." Jummai ta ce bayan ta tsaya cikin tsananin mamaki tana ƙarewa gidan kallo, sai kuma ta sa hannu tana shafawa tsantsin na mata daɗi, tana washe bakinta da ko wankin kirki baya samu. "Ke dallah banza! Na taɓa gani a lokacin da naje neman kuɗi a birnin Legos. To ogana gidansa irin wannan ne haka na yi ta shafa tayas ɗin." "Kai 'yan birni suna jin daɗinsu. Allah ya kai damo ga harawa, ko bai ci ya yi birgima." "Yanzu don Allah abin da kuke mini ya dace, haka za mu shiga ku kunyata ni? Maganar gaskiya ku zo na sallame ku, ku koma gida." "Wallahi ba ka isa ba Mudi! Ka gudu ka barmu ka bi mace tsawon shekaru, kuma yanzu Allah ya sa mun gano ka kace mu koma ƙauye. Ai nan zama nan kwana." Tsananin baƙincikin abin da ya furta ya ishe ya buɗe baki zai yi magana sai Jummai ta maƙale jakar buhunta ta riga shi da cewa, "To in ban da ya raina mana hankali, mu shigo irin wannan gidan ya ce mu koma ko shiga, ai ni ko kayana ba zan ɗauko ba, domin yadda maiƙo da zaƙi ya sa ya maƙale a jikin mace haka muma zamu zauna muci arziki." "Ƙwarai kuwa Jummai, domin ƙauye zan koma na kaso matata da 'yayana." Zare idanunsa ya yi yana faɗin,"Ku zauna a ina, wai ni wa ya gaya muku inda nake?" Wani irin ranƙwashi ta kai ma kanta har sai da ya ce ƙas tana dariya ta maƙale a bango tare da ɗaga ƙafa. "Wallahi abokinka Shafi'u, shi ya gaya mini za ka dawo birni, ni kuma da na ji haka na dame shi da ƙyar ya bani adireshin gidan, kuma ba shi na ciyo muka taho." Ƙuta ya yi bai ce komai ba ya fara tafiya wanda suka bi bayan shi da gudu suna murna "In isasshiyar matarka ba za ta yarda ba to ta ɗauke ni 'yar aikin zan yi, amma na rantse ba zan koma ƙauye ba." "Ni kuma gadi amma babu maganar komawa, ai sai a yi mana dariya." Be tanka musu ba ya ƙarasa shiga cikin falo cikin jin kunya, sosai domin bai san wani irin tarba za su samu da ga Hajiya Baaba da kuma Mom da Jannah. "Kai dakata! Dakata!! Ku kuma daga ina? Idan bara kuke yi ai sai ku tsaya daga ƙofa ba, wai ka shigo mana da su ba Jabiruu." Hajiya Baaba ta ce tana kallonsu cikin ƙyanƙyani. Shiru ya yi yana sosa kanshi sai kuma ya ce," 'Yan'uwana ne suka zo daga ƙauye." "Gaya mata Mudi, mu ɗin ba mabarata bane muma 'yan gidane."Cewar Bala. Da sauri Jannah da ta fito daga cikin ɗakinta jin muryar dad ta tsaya tana kallonsu. Yadda take kallonsu zai bayyana maka mamakin da take yi. "Dad, waɗannan ne 'yan'uwanka." Ta tamabaye sa cikin tsananin mamaki tana wani yatsina fuska tamkar ta ga kashi. " 'Yan'uwansa na jini kuwa, domin Yaya Bala shi ne farko sai Ya Mudi ni ce 'yar auta Jummai." Ta faɗi tana washe baki tare da riƙe gefen rigar dad tana yamutsa gugar da tasha. "Waye kuma Mudi?" Ta ce da sauri tana watsa mata kallon ƙyanƙyani. "Jannah da gaske 'yan'uwana ne domin babu ƙaryar abin da ta faɗa." "Laah! Wai kana nufin Murjanatu ne ta girma haka? Ikon Allah girma ba wuya. Ke Murjanatu ta ho 'yata." Ta ƙarashe maganar za ta rungumeta. "Please don Allah dakata! Dad, na kasa yadda waɗananne 'yan'uwanka? Please do explain, saboda fitowar da na yi akan ka ɗauke ni ka kaini gurinsu." Ta faɗa cikin muryar kuka. "Hehe, nananye, to ai ko yanzu ba ta ɓace ba, domin za ki iya bin su a koma ƙauye ayi daka da surfe. Kin dai gani ga dangin uban na ki nan da kike ta mana ɗagoshi da su." Cewar Hajiya Baaba tana dariya cikin tsokana. "Don Allah ka fahimtar da ni domin na kasa yadda waɗannan kucakan sune 'yan'uwanki." "Tabbas ba ni da waɗanda suka fisu, kamar yadda sune gatanki." "No dad!" Sai ta sa kuka sosai tana faɗin,"Su ba 'yan'uwana bane I have nothing to do with them." "To sai kije ki zaɓo waɗanda kike so su zama 'yan'uwanki, domin a lokacin da nake gaya miki uban na ki ba kown kowa bane kasa yadda kika yi, saboda yana cikin arzikin 'yata. Kin ga yanzu dole aure tun da ba ki da dangin zuwa, sai ki gane gata zan yi miki." Ta ƙarashe maganar tare da juyawa za ta bar falon Mom da jin hayaniya ya sa ta farka daga baccin da take yi ta fito tana zuba hamma. Turus ta yi ganin waɗanda suke falon tana kallonsu cikin tsananin mamakin yadda kai suka san ta dawo Nigeriya da inda take. Tsuru-tsuru suka yi domin a tunaninsu za ta yi musu rashin mutunci ko ta kore su, amma sai suka ga akasin hakan duk da abin da suka yi mata ya dawo mata tamkar sabo. "Barkanku da zuwa, baƙi muka yi?" Ta furta cikin sakin fuska tana ƙarasowa gurinsu. "Sannu da zuwa Ya Bala, sannu da zuwa Anty Jummai." Ta furta a tare lokacin da ta ƙarasa gurinsu, wanda ganin sakin fuskar da ta yi musu yasa suka rage tsoro suna ƙaƙalo murmushi. Tsananin mamaki ya kama Jannah matuƙa take ta gasganta maganarsa cewar 'yan'uwansa ne, sai ta rinƙa kallonsu cikin tana yamutsa fuska. Da sauri ta juya ta shige cikin ɗakinta, daidai lokacin da Hajiya Baaba wanda fitowar mom, ya sa ta tsaya taga wani irin tarba za ta yi musu. "Ba za ki kawo wa 'yan'uwanki ruwa ba." Ta ce tana dariyar mugunta. Mom ta ba da umurnin a kawo musu abinci wanda suma ci har da dabbe. Bayan sun gama ta nuna musu ɗaki akan suje su yi wanka. Falo suka dawo suka haye kujera suna ta kallo da ihu da shewa. Jannah ta fito daga ɗakinta za ta shiga kicin domin matuƙar yunwa take ji, idanunta ya kumbura ya yi luhu-luhu saboda kukan da ta ji. Wayarta a hannunta tana ta neman phone ɗin Huzaifah da iyayensa suka karɓe wayarsa. Tsayawa ta yi cikin tsananin takaici da baƙinciki tana kallon su Bala da Jummai da suke zaune kan kujer suna ihu akan kallon da suke yi. "Kai ka ga mini shegen mutum da mugunta ya kama mutum da duka ji yadda ya ji masa rauni." Jummai ta furta tare da miƙewa da sauri za ta je gaban tibin. "Wallahi rama masa na kai, ni kam na tsani mugunta." Ta ƙarashe mganar cikin muryar kuka hawaye shaɓe-shaɓe daidai lokacin da mutum ya coka masa wuƙa a ciki, sai ta fashe da kuka da saka ƙara za ta nufi gaban tibin. "Wallahi ya sokai, wannan sam ba shi da imani." "Ke banza, shashasha fim ne fa, ke duk shiri ne bai mutu ba. Da yake ba ki shigowa birni ya sa ba ki sani ba, amma ni nasha kallon irin finafinan nan, duk da ni ma da fari na ɗauka mutuwa zai yi." "Ai Bala, yanzu kana nufin tashi ya kai?" Ta tambayeshi cikin tsananin mamaki. "Me zai hana ke jar bula suka shafa masa kamar jini." "Yau ga lalalattun banza, wanga him ai ba abin kallo na bane, a kahe mana hi." "A ke, barmu mu kalla ai shine birnancin kuma. Ke dai zauna muga abin mamaki." Suka zauna suka cigaba da kallo ba tare da sun damu da yadda 'yan falon suke kallon su ba. Wani banzan kallo Hajiya Baaba ta yi mata tana mata dariyar ƙeta da ta ke tsaye tana kallonsu tamkar ta shaƙe su su mutu. "Kin ga fa danginki na kallo da yake ke ba ɗiyar mutunci bane, kamata ya yi kizo ki taya su." Wani banzan kallo ta yi mata domin ta san duk takalarta take wanda ta ci alwashin ba za ta ƙara mata magaba ba. Wucewa kicin ta yi tana harararta da su Bala ba tare da ta ce mata komai ba, wanda Hajiya Baaba ta ci gaba da gyara hularta tana dariya ƙasa-ƙasa. A ƙofar kicin ɗin suka ci karo da mujee, wanda da gangar ta sanya kafaɗa ta bangajeta har abincin da ta ibo a flate ɗin ya zube. "Ka ga mini yarinya mara mutunci, wallahi Maijidda ki tsinka mata mari har sai hannunki ya kwanta tun ba ba ta da kunya." "Ƙyale ta Hajiya Baaba, ƙuruciyace za ta bari." Ta ce tana ƙoƙarin tattara abincin da ta zubar. "In ba da duke ni ba sai ki zo ki duke ni. Na gaya miki ki fita idanuna domin yanzu mun yi hannun riga dake." "Au ni ma fitsarar za ki yi mini bari na taso ki gani don ba zan ɗauka ba." Ta ce tare da miƙewa cikin fushi. Hannu ta ɗaga za ta wanka mata mari amma sai Mujee ta tare ta. "Don Allah ki yi haƙuri karki biye mata." "Ki barni da ita ta san halina sarai, domin wallahi sai na sanya kiyi amarci da kubburerren fuska mara mutunci kawai." "Ki kashe ni shi zai fi mini domin auren nan da kike so ki ƙaƙaba mini is more than beaten Hajiya Baaba, you are killing me!" "Kin ci albarkacin Maijidda da kin yaba wa aya zaƙinta mara kunya kawai." Ta koma ta zauna taci gaba da gyara hularta ba ta ƙara tanka mata ba. "Haba Jannah, ki yi shiru mana muje na zuba miki abinci..." "Dallah! Malama ƙyale ni!" Ta ce cikin tsawa tare da juya ta koma cikin ɗaki ta ci gaba da kuka, abincin da ba ta ci ba ke nan duk da yunwar da take ji. Bayan dad ya dawo ya yi wanka ya ci abinci. Ɗakinta ya fara shiga amma sai ya ga tana kwance tana baccin da ga gani da tsiya aka yi shi, domin ko kwanciyar daɗi ba ta yi ba. Gyara mata kanta ya yi yana kallonta cikin tsananin tausayi domin ya san Hajiya Baaba ta shiga rayuwarta na raba ta da masoyinta. Wayarta da take waƙa ya ɗauka ya kashe tare da jona wayar a caji ganin ba bu caji da yawa. Ƙofar ya ja mata ya rufe sannan ya fita. Ɗakin su Bala ya shiga suna zaune suna ta aika ma cikinsu abinci. "Ya Mudi ka dawo?" Jummai ta ce masa tana yagar cinyar kaza. "Eh, na dawo." Ya ba amsa a gajarce. "Kai wallahi gidannan akwai daɗin zama ka na cin daɗin ka. Irin waɗannan girki shi ya sa ka yi kyau ka zama tamkar balarabe. Sam yanzu bana ganin laifin ka ba, domin ko ni da zan samu wata Hajiya ta yi wuf da ni, da gudu zan amince aradu." "Ga gurin cin abinci mai ya sa za ku shigo ɗaki? Yanzu kalli yadda kika ɓata gurin da miya kamar me yoyon baki" Ya ce cikin ɓacin rai. "Ba zamu iya cin abinci a gurin nan ba, saboda mutanen gidan kallon ƙasƙanci suke mana kuma harda yarka mara mutunci. Duk dai wulaƙancinta babu wanda take da shi da ya wuce mu." Tsaki ya yi jin me suka ce. "Ita wannan tsohuwar sirikata ce, kuma ba za ta yarda ku zauna a gidanan ba. Jannah kuwa maganar aurenta ake yi." "Yanzu Mudi, sai ka aurar da 'yarka ba tare da mun sani ba?" Jummai ta tambaye shi cikin mamaki ta riƙe da bakinta, sai kuma ta ɗora da cewa, "Talauci bai yi ba domin na san saboda bamu da komai ne ya sa ka ɗauke mu wulaƙantantu." "Na gaya muku tun da Inna da Baba suka mutu babu ruwana da ƙauyen nan, domin ba zan zo ku ƙara sani a keken ɓara ba, ku yi mini sakiyar da babu ruwa." Tsuka suka yi jin abin da ya ce."Shikenan, tun da kai ba za ka zo ba, muna da ƙafa za mu zo ai. Ko ince mun zo sai dai mu kwaso 'ya'yanmu." "Ku zauna a ina? Ku san Allah in kun daɗe ku yi sati biyu, amma ba za ku kashe mini aure ba." "Ai dama mun san an wanke gaba an baka ta ina za ka yarda mu zauna." Cewar Bala cin ɓacin rai tare da ture abincin da yake ci. "Ko ma me za ku ce sati ɗaya za kuyi zan haɗa muku abin arziki ku koma da jari." Ɗan sakin ransu suka yi jin zai ba su kuɗi. "Za a yi auren Lantana 'yata nan da wata uku..." "Kar ki ji komai zan yi mata kayan ɗaki, amma dole ku bar gidan." Ya ɗan tsaya ya ji me za su ce, ganin sun yi shuru sai cika suke suna ɓatsewa ya sa ya fice tare da ja musu ƙofa, a zuciyarsa yana jin daɗin ganin ba su yi masa gardama sosai ba. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 30-31* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Mom zaune a ɗakinta dad ya shigo ba ta ɗago kanta ba har sai da ya ƙaraso gefenta ta zauna. "Injiniya, I was about to go to your room and inform you that wannan contracts ɗin sun yi approving so you will go to Paris within this week." "Really! and when? Kin san Allah na ɗauka ba za su amince a haka ba, more especially da na ga how strict he is." "Common, is like you don't know how bussiness is? Duk techniques na business ne." Sai ya yi dariya yana duba takaddun dake gabanta."Haka ne fa, shi ya sa we have to be verry wise in all aspect." Ɗaga masa kai ta yi tana murmushi tare da ci gaba da aikinta. "Tafiyar it should be bayan su Ya Mudi sun wuce ko?" "Eh, dole sai sun wuce. Ni ma ina son na yi magana da kai akan su, domin ya kamata a basu jari da tallafawa rayuwarsu." Kallonta ya yi cikin mamakin kirkinta." Yanzu Halee, kin manta duk abin da suka yi miki za ki taimake su? I will not have the face to came, if ware them." Dariya ta yi"Haba komai ya wuce. Na taimaka wa wasu ballantana dangin mijina, kuma tun da suka tako zuwa inda nake ai na san sun yi nadama." "Haka ne, tun da kika manta da bin da ya faru kika karɓe ni a karo na biyu, tabbas za ki yi fiye da haka. You are so generous." Ya furta cikin muryar dake bayyana rauninsa. Barin aikin da take yi ta yi tare da kama hannunsa ta riƙe tana kallon ƙwayar idanunsa. "Ina sonka Injiniya, kai ma sheda ne domin ka san na yi maka soyayyar da ban taba yi wa wani ɗa namiji ba, son da nake maka dole ya sa na manta komai duk da cewar har yanzu akwai abin da ba zai taɓa goguwa a gare ni ba." "Haka ne, na sani amma ki gafarce ni. In sha Allah ba za ki ƙara dana sanin zama da ni ba." Rungumeta ya yi yana shafa bayanta cikin tsigar soyayya. "Tabbas rayuwa da masoyi akwai daɗi! Ina matuƙar tausayin Jannah na raba ta da Huzaifah da Hajiya Baaba za ta yi. Kina ganin babu abin da za mu yi wanda zai hana hakan?" Ya tambayeta cikin murya mai sanyi. "Ba na tunanin haka domin ka san in ta faɗa ya zauna ko lokacinmu, Allah ya kaddara zamu yi aure ne kuma da albarkacin kawu da yake raye, amma yanzu sai in ba ta numfashi. Mu yi wa Jannah fatan alkhairi a auren ta, domin zaɓin da ta yi mata ba tumin dare ba ne. Ajmal miji ne da ko wane iyaye zai yi fatan 'yarsu ta samu. Yaron yana burge ni karka manta shine malamin da ake ji da shi, wanda ya haɗa kyau da ƙuriciya uwa uba addinin boko da islamiya." Ta yi shiru ko zai ce wani abu amma sai ba ta ji ya ce komai ba sai jinjina kansa da yake alamun abin da take faɗi yana shigarsa. "Na sheda Huzaifah na matuƙar sonta, amma ka san ko sun yi auren matsaloli zai ta tasowa, saboda yanzu soyayya ke rufe musu ido, zama da Jannah sai mai tsauri." "Haka ne, ni ma na kan yi m hakan, amma kin san..." "Karka damu muyi mata addu'a domin jikina yana bani alkhairi zata haɗa, watarana sai mun yi alfahari da hakan. Tana jin maganarka ka samu ka shawo kanta." "Kamar ba ki san Jannah ba, tana da kafiya ba ta da sausauci akan abin da take so." "Duk da haka ka gwada nasararka za ka iya cin nasara wataƙila, tun da ni kallon banza ban ishe ta ba." Fuskanta ya ciko da gawaye tausayin kanta da damuwar da take ɓoyewa suka bayyana. Janyota jikinsa ya yi tare da haɗa hancinsu. "Ina gaya miki watarana Jannah, sai ta nuna ba ta da wacce take so fiye da ke. Ki yarda ki jira lokaci domin ko yanzu tsananin kishinki na fifita aiki da rashin ba ta lokacinki yake damunta." "Ina fatan hakan ina kuma jiran lokacin, ina addu'ar kar hakan ta faru a lokacin da ba shi da amfani." Ta ce tare da maida hankalinta kan aikinta tana jin hawaye na zubo mata. Hannunta ya riƙe da take ƙoƙarin operating ɗin laptop ɗin. "Hakan ba zai faru a lokacin da abu amfani ba domin da zarar ta yi aure hankali zai shige ta." Ya ce tare da sanya hannunshi yana ɗauke mata hawaye. "Am hoping for that injiniya." "Ni fa kwana nan ina fushi dake sam ɗan lokacin da kike bani, yanzu bana sanu, domin kwanan nan tamkar wani Zaki dake ɗauke da yunwar sati ɗaya nake." Dariya ta yi sosai tana kallon ƙwayar idanunsa domin yadda ya yi maganar ya sata cikin nishaɗi sosai, wanda hakan ya tuna mata da rayuwarsu na da wanda cike take da so da ƙauna. "Please Injiniya ka bari bana so. Can't you see that am working and they need the details before tomorrow." Ta ce jin abin da yake mata. Dariya ya yi sosai yana faɗin,"Haba, na ƙi wayon Allah kwana biyun nan, sai haƙƙina ya kama ki domin kina ƙwarata. Kullum aiki tamkar agogo." Haɗata da jikinsa ya yi tare da manna mata kis a leɓenta wanda ya sa suka yi shiru suna jin bugun numfashinsu yadda yake sauka a hankali kuma a tare. "I adore you." Ya ce tare da janta suka faɗa gado. Ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi ita kanta tasan tana kewar mijinta wansa ya iya ƙauna da tarairayar mace. Sai dai, abubuwan da suke sha mata kai su ke sanya ta manta ƙaunarsa mai kashe zuciya, amma ta san ta yi missing alot. A hankali ya kai bakinsa kan nata wanda ta rufe idanu tana murmushin da ya ƙara ƙawata kyawun fuskarta. "Ni ma ina sonka Injininiya." Sai suka runtse idanunsu suna jiran saukar laɓɓarsu akan na juna. Wani irin ƙara suka ji Jannah ta ƙwala wanda ya sa ya janye jikinsa daga gareta. "Tom lafiya mai ya kuma faru da wancan 'yar rigimar?" Mom ta ce cikin damuwa. Dad da jikinsa ya mutu da ƙyar ya miƙe. "Ba ya wuce rigimarta kin san yanzu kamar jaririyar goye take, in kika ga birgimar da ta yi sai kin yi mamaki." Ya ce tare da miƙa mata hannu da alamun ta zo, wanda ta noƙe. "My dougher is crying I most go and check on her." Ta ce tare da gyara zaman rigarta. Tsaki ya yi yana sakkowa daga kan gadon. "A taƙaice ta hana mu samun lada?" Gwalo mom ta yi masa ta fice tana dariya wanda ya biyo ta cikin kasala murmushi ɗauke a fuskarshi. "Keeeeee! Ba na son iskanci, ina karatuna za ki sa uban ƙara sai ka ce wacce ka tsire, wallahi sai da na firgita. Uban mene ne?" Ba ta ko kalli Hajiya Baaba da take faɗin haka ba ta ci gaba da kukanta. Dad da ya sauko ya kamata ya riƙe. "What happen? Kin ci abinci wa ya taɓa mini ke?" Ya ce cikin tsigar rarrashi wanda ya sa Hajiya Baaba ta yi tsaye cikin baƙinciki ta na jin kamar ta kifa masa mari. "No, I wanna go and take my food in the kicin, shi ne na zo wucewa Anty Nahlin ta mini dariya, kuma dama na ji suna mini dariyar za a aura mini tsoho." Da sauri su Nahlin da Ummu suka zare idanunsu cikin tsananin mamakin jin sharrin da ta yi musu. "To don ubanki da ta harare ki ciwo kika ji, ko ina hararar ta maƙale miki za ki haukata mutane da ƙarar ki kamar gyare?" Hajiya Baaba ta furta cikin ɓacin rai wanda ko kallon arziki ba ta samu ba ballantana ta yi tunanin za ta amsa mata. Mom kuwa da dad kallon junansu suka yi suna baƙincikin ɓata musu yanayin da suke ciki. "Tsoho, Ajmal ɗin ne tsoho? Ke Nahlin kika ce mata Ajmal tsoho?" Cewar mom cikin mamaki. Nahlin da mamakin sharrin da ta yi mata ya cika ta sai tafa hannu take tana salati ta kasa cewa komai, domin ta daina shiga sabgarta tun jiya da ta kalleta ta zabga mata harara har da murguɗe ya sa ta kama kanta don ba ta son rashin kunya. "Ƙarya ne ba tsohon bane? Mutumin da har ya yi aure da mata ai tsoho ne." Ta ce tana jan majina cikin zallar sanagarta. "Ko da sanda yake tafiya da ita sai kin aure shi ja'irar banza kawai." Hajiya Baaba ta furta tare da tsakin tsaki ta koma kujera ta zauna. "Ki yi shiru muje ki zauna zan yi mata faɗa." Mom ta ce tare da kama hannunta wanda ta wafce ta riƙe dad tana faɗin, "Dad, am sterving." Kama hannunta ya yi yana faɗin, "Ok, lets go and eat." Abincin ya zuba mata da kan shi ya ɗauko tana biye da shi a bayansa tamkar jela. Ya ije abincin akan dining tare da fara ba ta a baki tana ci tana danna wayarta duk wanda ya yi nasarar kallonta sai ta balla masa harara. "Kai innalillahi wa inna ilahir raju'un! Ni kam ina ganin taɓara da sangarta. Wai shin arziki hauka ne da kuka mai da yarinyar nan kamar wata 'yar goye? Irin tarbiyar da na ba ki kenan Halimatuu? Wallahi da irin ta ne tuni Jabiru ya sake ki. Kun ɓata yarinya kun sagartata kun mayar da ita taɓararriya. Kun san Allah ku kiyaye ni domin in kuka ci gaba da haka, tsaf zan sheme ku har da Jannah." Ta ja tsaki za ta shige ɗaki tana faɗin,"Adamuu, ka yafe mini domin na haɗaka da masifa da bala'i." Mom da dad babu wanda ya yi magana sun san gaskiya ta faɗa, amma ba za ta gane ba ne, domin ita ce 'ya ɗaya tal wanda Allah ya mallaka musu in ba su kula da ita ba wa za su kula da shi. Ɓata rai ta yi tana kallon ƙofar da Hajiya ta wuce bayan ta rakata da harara. "Dad," "Do eat your food don't nagging." Ya ce da sauri tare da kai saka mata loma yana tunanin mood ɗin da ta ɓata mishi, sai ta ci gabada tauna abincin kamar an mata dole. Washegari da safe mom ta shirya ta sauko ƙasa za ta wuce aiki ta tsaya turus tana kallon Hajiya Baaba da ta tsaye da jaka riƙe da kwankwaso. "Lafiya Hajiya Baaba, na ɗauka tafiyar jibi ce?" "Ban sani ba, yau na ga damar komawa gida." Ta ɓata masa cikin ɗaure fuskar da babu hanyar da za ta gani ta yi musu. "Amma Hajiya Baaba, da kin bari sai gobe saboda jirginku na jibi na yi reserving." "Kin san Allah? Yau in kika ga na ƙara kwana a gidan nan sai dai ba ni iya tafiya, amma ko a ƙafa sai na koma gida." "Hakan ba zai taɓa fauruwa ba dole na san yadda zan yi." Ta ce tana ƙoƙarin kira a wayarta daidai lokacin da ta ce, "Haka kawai, sai na zauna baƙinciki ya kashe ni. Ba ki da lokacin da za ki yi hira da mutane, sai dai wuni mutum ya yi ta kallon tibi, salon idanun su makance da wuri. Ga yar banzar yarinyarku da ku ka sangartata ba ta kallon kowa da gashi ta hana mutum saƙat da koke-koke. Gara na koma gidana zaman can yafi mini, in lokacin bikin ya yi kwazo ayi akai masa tsiyarsa." Mom dai ba ta ce komai ba har aka ɗaga wayar da take kira ta yi magana sannan ta kashe. "Ki ɗan jira zuwa rana sai ku wuce bari na sa a haɗa muku tsarabarki. Su Nahlin su bari sai an janye strike sai su dawo har da su Janna..." "Jann me? Kin san Allah ko aljannah take karki sake ta dawo mini gida, domin ni da ita mun yi hannun riga mara mutunci kawai. Ai na yi muku tsawon shekarun da na yi tana gaza mini gyaɗa a hannu ya isa. Ku da kuka ɓatata can muku na gaji a sakin mini mara na yi fitsari." "Ni ma ba dawowa zan yi ba, ni da gidan ki ko a ƙiyama in ana ziyara ba zan zo ba." Jannah da ta fito da waya a hannunta ta ce ba tare da ta kalle ta ba ta wanda ita ba ba ta tanka mata ba domin ba ta da lokacinta. Da misalin ƙarfe huɗu jirgin Hajiya Baaba ya ɗaga wanda Jannah tafi kowa murna a gidan domin gani take kamar babu wanda ya isa ya biyo ta har gida ya yi mata auren dole. Karatun ta ne kawai ta ke jin babu daɗi na transfer da za a yi mata saboda ƙawayenta da sabon da ta yi da su. Ummu kuwa dama ba wani harkanta take shiga sosai ba, tun da ta yi mafarkin ta yi mata dariya wai za ta riga ta aure ta ɗauke mata wuta. Zaman na su sai ya yi babu daɗi ko kaɗan domin kowa harkar gaban shi yake yi. Su kansu su Ummun ba wani daɗin hutun suke yi ba duk da cewar ga komai nan sai dai cuci su sha su yi kallo, amma fa mom ba ta da lokacin su har gara dad ya kan yi ƙoƙari ya gansu kafin ya tafi aiki, da in ya dawo, amma mom sai ta yi kwanaki ba su sanya ta a idanunsu ba, domin da wuri take fita har gara Nahlin da take ɗan tashin wuri. Su Bala da Mudi tuni suka kama kansu cikin murna suka tafi ganin yadda mom ta cika su fa abin arziki da jari mai nauyi, wanda suka yi matuƙar jin daɗi da alƙawarin wa kansu dawowa bayan wani lokacin, domin sun ga gurin zuwa. Washegari da safe suna zaune a falo kowa na harkar gabanshi. Dukanninsu waya ce a hannunsu wani ni lokacin su duba wayarsu wani lokacin su yi kallo, amma babu mai ko tari a tsakaninsu. Mom ce ta fito tana janye da troley cikin maroon ɗon abaya ta yi kyau sosai tamkar ka saceta ka gudu. Murmushi ta yi lokacin da suka ji ƙarar saukkowarta suka kalli saman benen "Nahlin, Ummu, Jannah, tafiya ta kamani zuwa cameroon kuma I think I will stay long, akwai komai da kuke buƙata duk abin da kuke so babu ku kira ni ko ku yi wa masu aiki magana. Da fatan za ku kula da kanku?" Ta yi musu tambayar yana nazarin fuskokinsu. Ummu da Nahlin suka ɗaga kansu amma Jannah ko alamun da ita take magana ba ta yi ba ta ci gaba da danna wayarta. "Jannah, I w.." "Oh please mom! I heard you. If you like go to heaven I don't bloody care, since my dad is around." Ta ce cikin ɗaga murya ta ci gaba da abin da take yi. Shiru ta yi tana kallonta sai kuma ta miƙe tana hamdala da ta riga shi tafiya domin ba ta san wainar da za a su toya ba, matuƙar ta ji zai yi tafiya kuma sai ya daɗe sosai donnsai gabda zaɓe zai dawo. "To na tafi, Allah ya yi muku albarka." "Amin." Ummu da Nahlin suka amsa ita kuwa miƙewa ta yi tana faɗin, "This house is so boring." Ta haye sama kallon mamaki suka bi ta da shi. "Wannan yarinyar fa ba ta da mutunci lokaci guda ta canza mini fuska, saboda mun zo gidansu. Na lura kallon banza take mana ba, wallahi zan mata mata ni ma ɗin ba kanwar lasa bane, kuma ta san gidan ubana ba abin rainawa bane." Cewar Ummu cikin ƙubula domin haushin shareta da ta yi take ji, tana ganin she didn't deserved that duba ga how very closely they are. "Wallahi kuwa, ni kallon mamakin sharrin da ta yi mini nake kuma tai mursisi duk da na san kurace da fatar akuya ban yi tunanin ta kai haka ba.' "Ƙyale mara mutuncin kawai! Ki barta maganinta zan yi. Ni Yaya nake tausayi yana zaman lafiya da matarsa za a kai masa fitina." "Yayan za ki tausayawa ko ita? Ke ma kin san halin shi daidai yake da ita ba zai ƙyale ta ba, ƙaniyarta zai ci shi ma ba ƙyaleta zai yi ba. Kin san halin shi." "Duka za ta ci kamar jaka wallahi ba ta da kunya ga kafiya da raina na gaba da ita, shi kuma zuciya da son girma." "Humh, na ga yadda wannan aure da Hajiya Baaba ta haɗa zai yi wu kuma a zauna lafiya? Ita ma ta iya rigima." "Ki barta sai sun kai ta lahira lokacinta bai yi ba, domin ta san ba alkhairi ta haɗa ba, dama ta ƙyale shi da matarshi mai hankali." "To munafukai, duk na ji abin da kuka ce. Na ce kuna gulmata kun ƙaryata, yanzu mai za ku ce da na kama ku da kunnuwana." Da sauri suka waiga suna mamakin ganinta a jingine da ƙarfen bene tana karkaɗa wayarta cikin isa da gadara. "Ban sani ba, ai duk abin da muka faɗa haskiyane saboda mun zo gidanku kin gama raina mu har ki kalli idanun Anty Nahlin kice mata munafuka." Ummu ta ce. "To malama kike so na kirata? Kuna ta wani gulma ba ku tausaya mini halin da nake ciki ba, ai duk na gane halinku kuma zan yi maganinku. Don kawai ina da wanda nake so ne da sai na yadda an yi auren kuga yadda zan wahalar da ɗan'uwanku na mai da shi tamkar almajirina na shishshuka masa rashin mutunci son raina sai na ga uban abin da za ku yi ku masu ɗan'uwa." "Jannah, Anty Nahlin kike gaya ma haka?" "Ki barta saman zan hauro na zane ta kuma ta san babu wanda zai ce mini komai." "To mai ya hana ki ai gani a gabanki bismillah." Ta ce cikin tsiwa wanda ya tunzura ta ta fara hawa benen da sauri. Ganin haka ta yi maza ta ruga ɗaki ta kulle ƙofa tana haki! Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 31-32* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Ganin haka ta yi maza ta ruga ɗaki ta kulle ƙofa tana haki." A tunaninki bari zan yi ki duke ni? Muguwa kawai." Ta ce cikin tsoro. "Matsoraciya ai da kin tsaya ki ga yadda zan yi ƙasa-ƙasa dake." Cewar Nahlin cikin ɓacin rai. "Ga rashin kunya sai shegen tsoron tsiya, ai ni addu'a zan yi Allah ya sa auren nan ya ƙullu, ko don ya koya mata hankali ta rinƙa girmama mom." Ummu ta ce suka ci gaba da kallo. Tun da ta san tsiyar da ta shuka ba ta sakko ƙasa ba ko da ta ji yunwa frij ɗin dad ta buɗe ta yi ɓarnarta son ranta. Tana kwance akan gadonsa gabakiɗaya ji take rayuwarta komai ya tsaya mata cak. Ko sallah ba ta tashi ta yi ba har sai da dad ya dawo sannan ta buɗe ƙofar ta faɗa jikinshi tana hawaye. A tunaninsu wani ƙaryar za ta yi musu sai ta ba su mamaki don ba ta yi masa ƙorafin komai ba sai cewa da ta yi, "Dad, I miss you." Ta furta tana riƙe da hannunta. Ledar tsarabar da ya yi musu ya miƙawa kowa na ta sannan ya ije na Jannah yana ƙoƙarin buɗe mata robar ice cream. Da kanshi ya fara ba ta sai kuma ya miƙa mata ya shige bayi don ya yi wanka. Washegari da safe bai sakko ƙasa ba har sai sha ɗaya lokacin duk suna zaune a falo suna kallo. Kwana biyu da tafiyar Hajiya Baaba, da mom duk sai gidan ya zama babu daɗi, domin tsoro yake ba su. Ko bacci za su yi sai tsoro ya kama su saboda girman gidan. Zaman gidan sai ya yi musu babu daɗi domin shi kansa dad, sai dare yake dawowa, in bai fita da wuri bane ya fita takwas na safiya. Ranar da ya cika sati ɗaya da tafiyar mom wanda ta gaya musu saura kwana tara ta dawo, suka cika da murna ganin an janye strike don haka suka fara shirin komawa Zariya cikin farinciki, ban da Jannah da take contemplating whether to stay or not, saboda ita kanta ba daɗin zaman gidan take yi ba. Haka dai a ranar da aka yi call off ta wuni cikin tunanin ba tare da ta samu mafita ba, saboda hankalinta ya fi karkata da ta koma, amma in ta tuna auren sai ta ga gara zamanta a Abuja. In ta hanga a wata mahangar ta ga zaman kaɗaicin da take yi sai ta yanke shawarar gara ta koma Zariya duk abin da zai faru ya faru, saboda ko sun yi mata auren ita ce mai zaman ta ga yadda za a yi ta zauna. Cikin wanann halin na tsaka mai wuya wanda take ganin rayuwarta yana gaba kura baya siyaki. Ta kwanta ba tare da ta samu mafita ba, tana ganin su Ummu suka haɗa kayansu cikin farinciki don har sun kira mom, sai dai rashin sa a wayarta ba ya shiga amma sun bar mata tsaƙon kar ta kwana na shirin tafiyarsu. Cikin fargaba yake sakkowa da troley ɗinsa yana ja zuciyarsa cike da tsoron yadda zai tunkareta ya sanar masa da tafiyarsa. Ilai kuwa ganinsa da jaka ya sa ta miƙe a zabure. "Dad, traveling?" Ta ce tana kallon shi da idanunta har sun fara kawo ruwa. Bai amsa mata ba har sai da ya sauko ƙasa ya riƙe hannunta suka zauna kan kujera. "Eh Jannah, tafiya ta kama ni ban san da tafiyar ba, and I must go it is an important." "No, you will no go anyway I know it is mom that send you." "Haba Jannah, na gaya miki tafiya zan yi and I will stay a bit long." Ya ƙarashe maganar cikin tsawa domin ya san in ba haka ya yi mata ba zai sha fama da ita. A maimakon ta saduda sai ta sanya kuka. "Babu ind za ka dad, ita ba ta zauna ba kai ma ba ta barka ba, gabakiɗaya ta takurawa rayuwarka. Ga shi su Ummu za su koma Zariya sai a barni ni kaɗai a wannan ƙatoton gidan, ni wallahi ba zan iya zama ba, saboda yanzu I can't stay in loneliness, na saba za ma cikin mutane." Dafe kansa ya yi cikin rashin dubara."So what do yo want Jannah? You know I must go cus na yi reserving flight ko so kike mom ta yi asara." "Eh, Let her do. Ban damu ba in dai za ka kasance dani don ba zan iya zama daga ni sai masu aiki a wannan gidan ba." "Am sorry but I have to go. nan da awaya ɗaya zai tashi I have to be hurry." "I said you are not going anyway." Ta ce tare da riƙe rigarshi tana kuka. Ransa ya ɓaci ya juyo ya kalli su Ummu da suka yi tsuru-tsuru suna kallonta. "Nahlin, gobe za ku wuce ko? Mom told me that.I wished you safe trip and ku kula da karatu. Ga wannan mom ta ce a baku ku riƙe za ta yi booking flight na ku, sannan anjima direba zai kai ku shooping. Choose whatever you like it is on her." "Ok, thanks dad, mun gode Allah ya ƙara buɗi." Kallonta ya yi sai ya fisge rigarsa." Ba kya jin magana, karki manta ni mahaifinki ne, in na gaya miki magana you must obey haba you have to give me that respect I earned." Ya ƙarashe maganar cikin tsawar da ya firgita ta matsa gefe tana zare ido. "Na gaya miki planning ɗina akan auren ki, amma you didn't agreed. Hajiya has power and authority that I can do anything than tha..." "Leave me alone!" Ta ce tare da ƙara matsawa da fisge hannunta da ya yi. "Na gane kai ma mom ta zuge ka da kuɗi, I understand that you were living in object puverty that's why mom manipulating you with money and make you like her errands boy. Your family are poor that is why you married mom to be rich. Saboda money sai ka kasa bani farinciki dad, ka na gani za a yi mini auren dole da wanda ba na so! Why did you marry mom becouse of money why dad?" Sai ta fashe da kuka tare da durƙushewa. "I love Huzaifah like crazy I want him to be my wedded husband, please do something." "I'm sorry that I can't help, but you have to understand that my love to your mom is genuine." "Isn't dad!" "To shikenan, tun da ba kya jin magana you always do as you wish, sai ki je kiyi abin da za ki yi, kuma daga yau na cire hannuna akan maganar aurenki." Ya ce cikin fushi tare da ɗaukar jakarsa. "Nahlin, ku gida gida zan kira in ji kun sauka lafiya." Ya kama hanya zai fita yana jin yadda kukanta ke ƙona masa zuciya. "Ni ma zan bi su do the viser with me I can't stay alone." Ta ce cikin muryar kuka. Jiyowa ya yi ya kalleta sai kuma ta ba shi tausayi ya kasa ce mata komai domin ya sani suna cutarta da yawa, ya yi tunanin dawowarsu zai ba ta farinciki, sai ga shi maganar aurenta ya taso wanda shi ne sanadin dagula komai, ba shi da zaɓi wanda ya fi ta koma gidan Aby ta amince da auren, domin zaman ta da rayuwarta acan sai ya fi mata fiye da nan da ba su da lokacinta. "Shikenan, I will do the viser." Ya ce tare da ficewa ransa na ƙuna. Nahlin da Ummu sai ta ba su tausayi sun sani duk wani abin da take yi da ɗaurin gindin iyayenta da suka yi sakaci da rayuwarta. Kuka take sosai kamar ranta zai shiɗe tana ganin sam iyayenta ba su da buƙatar haihuwarta, wannan dalilin ya sanya da suka haifeta suka tsaida haihuwar gabakiɗaya, domin rashin lokacin da za su kula da yayan, duba ga ita kaɗai da suka haifa sun yi wa rayuwarta riƙon sakainar kashi tana watangaririya cikin duniyar rayuwarta, saboda da sun tsaya sun kula da ita har yaushe za a laƙa mata wannan ƙaddarerrren auren Ganin kukan ya ƙi ƙarewa ya sa Ummu ta ƙarasa gurin ta kama tana matuƙar jin haushin Hajiya Baaba da ta kafe sai anyi auren domin duk ita ta jagula komai, suna rayuwarsu cikin farinciki da annashuwa. "Please sis, stop crying. Kina sa na ji kamar na yi. Kyakkyawar fahimta ya kamata ku yi tsakaninki da iyayenki." Faɗawa jikinta ta yi. "Me zan fahimta ba sa sona kawai, dad ne kuma shi ma gashi za ta yi nasarar raba mu, honestly dad, is after money ba ya son ya bi zaɓina mom ta rabu da shi ya yi rayuwar talauci." "No, don't say dad." Cewar Nahlin ta riƙe hannunta. "Anty Nahlin mu bar gidannn yanzu zuciyata tana mini zafi, na tsane su ba na son zama a gidansu." "Ki yi haƙuri mu bari zuwa goben." Ta ce tare da kama hannunta suka zauna. Lallaɓata suka yi ta ci abinci Ummu ta shirya mata kayanta wanda dama duk iskancin da take yi da ya ji ba za ta koma Zariya ba sai da ta ci babu daɗi tana tunanin yadda za ta saba da tashinta. Duk kiran da mom take mata ta ƙi ɗagawa sai dai suka yi waya da Nahlin da Ummu. Ta tura musu maƙudai suka je shoping, wanda ko tsinke ba ta ɗauka ba sai Ummu da in ta ɗauki abu, ta ke siya biyu tun da dama komai iri ɗaya suke sanyawa. Washegari suka koma Zariya wanda Jannah tun da suka hau jirgin ba ta ce ƙala ba, tana ganin kiran dad da ya dame ta da text har da hotonsa ya turo masa da ya isa amma ba ta kalla ba. Adal da Ummita suka rugo da suka rungume su suna faɗin,"Oyoyo Anty Nahlin, Ummu da Jannah." Wani irin zabura Hajiya Baaba ta yi domin duk da ta san cewar su Nahlin za su dawo ba ta san da ita za a dawo va, sai Aby da Ammy kawai suka sani. "Kamar su nan Jannah na ji an ambata a gidannan?" Ta ce tana kallon su Adal da suka ruga da gudu suna rungume su da suke fitowa daga cikin mota. "Ke! Uban me ya dawo sake daga gidan?" Ta ce mta cikin tsawa. Jannah da ta fito daga motar fuska kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa kallonta ta yi ba ta ce komai da troley ɗinta za ta nufi sashinta. "Tsaya na ce, ina za ki ai ba dai sashina ba?" Ta yi mata tambayar cikin ɓacin rai tana girgiza. "Kin ga Hajiya Baaba, ki matsa mini na shiga babu ruwanki da ni." "Akan me saboda ina jin tsoronki ko? Ko gidan iyayenki ne da kika raina kowa ba kya ganin kowa da gashi?" Ba ta ce mata komai ba ta matsa ta gefenta za ta wuce. "Kin san Allah in kika ga kin shiga cikin ɗakin nan, sai dai in bani a gurin nan. Daga zuwa gidanku kika rinƙa suka mini rashin mutunci kala-kala ke mai iyaye. Shi ne yanzu kun ɓata kin sassaɓo jiki kin dawo gani tsohuwar banza na karɓe ki ko? To ba za ki zauna a ɗakina ba, sai in ki nemi wani gurin ko ki zauna da su Bimbo, ai dama idanu na zuba miki saboda iyayen na ki har wasu iyaye ne da za a yi togiya da su. Mutanen da basu da buri sai kuɗi. Ki ji da kyau auren da zan yi miki da Adamuu wallahi gata na yi miki, domin ba ki da kowa sai shi don haka ki yi masa biyayya." Tsaki ta yi ta ƙara matsawa za ta shige. "Au kin ɗauka wasa nake miki, bari ki gani."Ta ce tare da janyo ƙofarta ta rufe. "Ƙyale ta Jannah, kin ji zo mu koma shashinmu da zama." "Eh, can gasu gada, zomo ya ji kiɗan farauta. Ba dai ɗakina ba fitsararriya kawai." Ta ce jin abin da Ummu ta ce. Tafiya suka yi ba tare da ta ce mata uffan ba domin a mood ɗin da take ba za ta ji kalmomi ma su daɗi ba in ta ce za ta kula ta. Suna shiga sashin Ammmy ta rushe da kuka wanda Ammy ita ta zauna ta rinƙa rarrashi har ta yi shiru ta ci abinci. Hutun kwana biyu suka yi na gajiyar dadowa suka koma makaranta da ake karatu babu kama hannu yaro don exam suke shirin farawa har ana ƙara fito musu da sabon time table. Tun da suka dawo ba ta nufi shashin Hajiya ba kamar yadda ita ma babu ruwanta da ita domin da gaske fashin take da ita, amma ko muryarta ta ji sai ta leƙa ta ganta. Bayan sun dawo da sati ɗaya suka fara exam wanda hankalinsu ya koma kan jarrabawar gabakiɗaya ba su da lokacin kansu. Zaman su ya yi daɗi sosai duk wani rashin kunya da iskanci da ta ke musu ba ta yi wanda kuma ba su nuna mata komai ba suka cigaba da zamansu lafiya. Nahlin ce wani lokacin ba ta shiga sabgarta don kar ta ƙara raina na. Ranar laraba dukanninsu suna zaune a falo suna hira bayan sun kulle kansu a ɗaki sun sha karatu na exam ɗin gobe. Ajmal ne ya yi sallama ya shigo fuskarsa a sake ganin Ammy zaune a tsakiyarsu ana hira da ita. Jannah dake zaune kusa da Ammy kamar za ta shige jikinta ta ɗago daga kallon wayarta da take daddananwa ta kalle shi ta watsar. Shigowarsa ya sa suka daina hirar da suke yi suna gaishe shi ban da ita da ta yi kamar ba ta san wata halitta ya shigo ba kuma yana lura da ita. Zama ya yi gefen Ammy." Kwana biyu shiru har zan fara cigiyarka." Ta ce tana murmushi ganinsa. "Eh wallahi Ammy, am on the go. Abubuwa sun cuɗemini ba ofis ba karatutttukan da nake da shi." "Allah Sarki Ubangiji ya dafa ya yi albarka." "Amin." Ya amsa cikin farinciki yana kallon 'yan ƙanninnasa da suka rame saboda exam. "Ya exam kun ga yadda kuka rame kuwa?" Ya ce daidai lokacin da idanunsa suka sauka akan Jannah, wanda sai da ya ɗan saki dariya ganin yadda ta rame sai idanu zuru-zuru, domin abu abubuwa da dama suka ramar da ita, wanda rashin magana da dad shi yafi komai ƙara ramar da ita, amma saboda kafiya ta ƙi amsa calls ɗinsa duk lokacin da ya kira. Sai ya tsinci kansa da kallonsa yana mamakin irin ƙarfin hali na Hajiya da ta danganta ta da shi, wai a matsayin matarsa, saboda in banda rashin mutunci mai zai yi da ita kamar sanda wanda ko ƙirjinsa ya ɗora mata sai ya karairayata. Shi ya ma manta da ita da maganar aurensu soyyayyarsa kawai yake sha da amaryarsa, don sai ya yanzu da ya ganta. Wani uban harara ta zabga mishi har da sakin siririn tsaki domin wani mugun haushinsa take ji. Ransa ne ya ɓace ya buɗe baki zai yi magana amm so Ammy ta yi mishi nuni da kar ya kulata da idanunta, wanda ya sa kan dole ya yi shiru ba tare da ya ce komai ba, amma zuciyarsa na tafarfasa. Jin duk 'yan ɗakin sun ji tsaki da hararar da ta gi masa sai ta miƙe ta shige ɗakinsu domin t ji kunya da suka gani musamman Ammy da take biye mata tana taɓararta yadda ta ga dama, don har kwanciya a jikinta take yi. "Ammy, kina ganin abin da yarinyar nan ta yi mini, amma kika yi mini nuni da na ƙyale ta." "To kasheta za ka yi Ajmal? na ganta amma dole haƙuri za ka yi, domin karka manta shiga sabgarta da kake yi duk ya janyo aka maƙala maka aurenta." "To ina gani sai ta yi ta zuba rashin kunya da fitsara, yanzu ki gani kamar ni za ta harara ta yi mini tsaki. Wallahi in ta ƙara saina tattaka ta sai dai duk abin da zai faru ya faru, ita kanta Hajiyar yanzu saboda fitsararta korenta fa ta yi, amma saboda ni ba ni da gata za ta laƙa mini, ina zaman lafiya da mamata ta kawo mini jaraba, ita kanta ta san bamu dace ba." "Ba ka da abin yi ban da wanda ya wuce addu' da fatan Allah ya zaɓa abin da yafi alkhairi, domin tun da ta furta sai wani ikon Allah." "Kin san Allah Ammy ina ji ina gani ba zan yarda ta kawo mini jaraba da matsifa gidana ba, in kuma ta tilasta aka ɗaura auren da kanta in ta gaji da zamanta za ta zo ta kwashi tsiyarta, saboda kallon banza ba za ta ishe ni ba." "Akan me tana matsayin matarka kana malami haƙƙinta za ka ɗauka?" Cewar ta cikin ɓacin rai. "Ba ni nace ina son auren ba dole za a yi mini." Ya ba ta amsa tare da miƙewa domin hirar ta gimshe shi. "Ka dai yi abu da hankali ka rinƙa aunawa da mizanin hankalinka. Jannah yar'uwarka ce, ko babu aure akwai zumunci tsaka.." "Ammy, zan wuce gida dama na zo kiyi mini addu'a akwai tafiyar da zan yi kuma khairan in sha Allah." Ya katseta yana faɗin hakan domin ya gaji da hirar. "Ok, masha Allahu. Ina maka addu'a da neman buɗi da ɗaukaka a dukkan rayuwarka. Ko akan wananan maganar ce?" Ta ƙarashe maganar da tambaya. "A,a ita ma tana kan hanya aci gaba da mana addu'a." "Kullum babu dare babu rana muna yi fatan nasara." "Amin." Ya amsa tare da ciro damin kuɗi ya ije kusa da ita. "Ba ri na wuce anjima zan turo Kamal ya kawo muku kifi, saboda yau za a kwashe ba ki ga girman da suka yi ba, Mushiirat na ta mamaki don ba ta ɗauka za su yi wannan girman ba." "Masha Allah muna jira, duk da wanda aka kawo mana ma bamu gaba amfani da su basuna frij, ai gaskiya hannunka na da kyan kiwo ji kajin da aka kwashe wancan satin." "Sun yi girman mamaki, ai albarkan da kuka sa mana ne." Ya ce tare da fara tafiya. "Ai ko zamu ci gaba ka gaida Mushirat, ka ce na gode da tsaƙo Allah ya yi mata albarka, karka manta ka shiga ka gaida Hajiya Baaba." "To." Ya ce tare da ficewa amma kuma bai shiga ba wanda tana ganin motarsa, da shigarsa tashinta har ya gama abin da yake yi, ya fito ya fita har leƙensa ta yi yana ta hararar shashin ya fice. "Ni kake ma wannan wulaƙancin saboda zanyi maka aure, za ku ci ƙaniyarku da ga kai har ita." Ta ce tare da ɗaga waya ta kira wayar Aby wanda cikin rashin sa a ba ta same shi ba. Fita ta yi ta bawa Musa Direba kuɗi ta ce,"Ka je ka siyo mini goro da tabarmai masu kyau da tsada ko nawa ne karka damu." "To Hajiya, yanzu kuwa." Ya karɓi kiɗin yana mamakin me za ta yi dasu. Bai jima ba ya dawo wanda ta karɓa ta adana su tana ta maganganu da habaici a sashinta wanda babu wanda ya jita don Ammy kwanciya ta yi. Da daddare Aby ya dawo Hajiya Baaba ta yi kiransa wanda duk ciwon kan da yake fama da shi dole yazo. Ganin uban goro da tabarmi sai da gabansa ya faɗi. "Ah, Hajiya Baaba, waɗannan kayan fa? Na san na gaya miki iyayen manemin Nahlin sun roƙi abar maganar aurenta zuwa yaron ya dawon London ƙaro karatu da gurin aikinsa suka tura shi." "Ba na son iskanci Muhammadu, nufinka Nahlin ce kawai mace budurwa a gidannan sauran ƙwailoli ka ɗauke su?" "A'a Hajiya, na ga dai ita ce da muka san da maganar ta wani yana nemanta." Harararsa ta yi. "Ka manta da maganar auren Jannnatuu da Adamuu, ko ka ɗauka wasa nake?" Ji ya yi gabansa ya ƙara faɗi."Na dai ɗauka kin yarda sai ita jannar ta yi nisa da karatunta shi kuma matarsa ta haihu ko ɗaya ne." Ya ce cikin rawr murya. "Matarsa ta haihu aka ce maka haihuwar za ta yi, saboda inda haihuwar za ta yi da ko wata ɗaya ba za ta yi ba yi ba za ta fara laulaluyi, tun da yanzu amaren yanzu kamar da cikin suke shiga, sai ka ga aure bai yi shekara ba an haihu hu. Matarsa juya ce ba haihuwa za ta yi ba." Ya kasa magana sai kallonta yake yana mamakin ƙarfin halinta da maganar da take faɗi sai ka ce ta san gaibu, wanda ganin hakan ya sa ta ci gaba da cewa, "To ban amince ba ta zane shi ko ta kashe shi in za ta so." Kansa ya dafe ya duƙa ƙasa da gwuiwowinsa."Hajiya Baaba, ki wa girman Allah ki bar maganar nan zuwa wani lokac.." "Ka fita idanuna Muhammadu, ka daina dawo mini da hannun agogo baya domin uren nan babu fashi. Ga ka kayan sa ranar nan, ka san na gaya maka ni zan yi komai, ko ƙwandalarku ba na son ku kashe, dama kuɗin da nake tarawa ban san me zan yi dasu ba, gara na yi aikin lada na samu lada, na sani ƙila ma shi ne zai sa na shiga al'jannah." Shiru ya yi yana kallon kayan don ya rasa me zai ce. "Za ka yi magana ne Muhammadu, ko ka mai da ni taɓaɓɓiya. Ka gaya mini nawa ne sadakin sai na biya." "Na yi tunanin sai an zauna da yaran da kuma iyayen Jannah, musamman mahaifinta don bai kamata mu yi abu gabagaɗi ba, saboda yana da haƙƙi, kin ga dole ya gaya mana wanda zai naɗa waliyin Jnanh mu ne mu aurenta." "To sannu tsarau da iya tsara zance, amma tun da haka haka." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 32-33* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "To sannu tsarau da iya tsara zance, amma tun da haka kace ina zuwa." Waya ta ɗauka ta danna numbobin dad wanda yake zaune yana cin abinci. "Hello Jabiru, maganar auren Jannah da Adamuu ne, waliyin da za ka na ɗa nake tambaya saboda ina son asa rana." Shiru ya yi ya rasa me zai ce a ransa yana tunanin ta dai na ce sai an yi auren nan. "Ka yi shiru ko ba ka jina ne?" "Abby ya zama waliyinta na ba shi wannan damar."Ya ce tare da kashe wayar yana mamakinta. "Saboda iskanci ya kashe mini wayaa ina sirikarsa ya manta lokacin da ya yi mini ƙarfa-ƙarfa aka ɗaura masa aure da Halimatuu, ashe babu daɗi ramuwar gayya." Ta ƙarashe maganar tana kallon Aby da ya rasa bakin magana. "Ai ka ji abin da ya ce ko sai na ƙra maimaita maka." "A, a na ji ina son na kira abokina ya nema wa Ajmal auren." "Shikenan, kira shi yanzu don ba zan tashi ba sai an saka rana ga sadaki da komai ayi mini kuɗin tsiya na biya, duk da mara kunyar ba tsada za ta yi ba saboda fitsararta, don duk wanda aka ba shi cutarsa ma aka yi, Adamun da yake ɗan gidane shi ya sa, saboda hannunka baya ruɓewa, ka yanke ka yar." Shi dai baice komai ya ɗaga waya ya kira shi sannan ya kalle ta bayan ya kashe waya. "Hajiya Baaba, ya ce ga shi nan zuwa, bari na je na sha magani na ci abinci kaina ke ciwo." "Ka je ina? In kaga ka jirka an sanya ranar nan ne, bari na ɗauko maka maganin ciwon kan da abinci in da su. Yau abin da kafi so na girka gudun kurna, na gane wayon ka salon ka tafi a zuge ka ba." Bai ce mata komai ya zauna har ta kawo masa abincin wanda ya kasa ci duk sonsa da gudun kurna sai dai ya sha maganin y koma ya zauna ya na tunanin lamarin. Bai ɗauki tsawon lokaci ba Alhaji Umar ya shigo ya same su, zaune jugum-jugum babu mai magana sai Hajiya Baaba, da take kaɗa ƙafa fuskarnan babu ɗigon rahma, domin kamar ta fuskanci Aby ya yi masa text kan ya zo ya ba ta hakuri. Jiki a saɓule ya samu guri zauna yana kallon Aby, da yake ƙyafta masa idon akan ya gwada sa arsa ganin yadda jikinsa ya yi sanyi. Hajiya Baaba, ƙuta ta yi tana kallonsu ta gefen ido a ranta take faɗin,"Munafukai ku gama ina kallonku." "Barka Hajiya Baaba, mun same ku lafiya." "Alhamdulillahi, lafiya lau kamar yadda ka ganni, sai abokin na ka yake ciwon kai." Ta ce a daƙile ba tare da ta kalli inda yake ba. "Ashsha! Allah ya kawo afuwa." "Amin" Suka amsa da shi sai ta gyara zama ganin yana gyara baki da tunanin ind zai fara. "Abokin na ka ya gaya maka komai ko. Maganar auren duk bana son ya wuce wata uku, saboda ni da za a yi cikin satin nan zanfi murna." "Ki yi haƙuri dai abi sannu tun da ba sauri ake kuma, kuma Hajiya da kin ƙara duba lamarin." "Dakata, na ce ka dakata wato kun haɗa baki ko? To babu ruwanka da shiga harkan zumunci, za ka sanya ranar ko ni na saka da kaina tun da uban 'ya ya amince." "A'a ba za ayi haka ba, kai Umar sanya ranar kawai, amma don Allah ki yi haƙuri asa ta yadda Jannah za ta kai aji uku a makaranta." "Wata uku na ke so kuma haka za a sa. Na ga kuɗaɗena za su yi ciwo ba na ka ba, don haka ina ruwanka don an saka ko gobe ne." "To shikenan, Allah ya ba su zaman lafiya." Ya ce tare da kama hannun abokinsa suka fita daidai lokacin da Hajiya Baaba ta amsa da. "Amin." Sai ta ci gaba da cewa,"In ma ba su zauna lafiya ba, za su gaji su zauna domin auren nan mutu ka raba... Sai dai, ina mutu ku raba su, kuma ina sha Allah ina duniya har sai na ga jikokinsu." Ta ƙarashe maganar tana hararar ƙofar da suka fita. Wayarta ta ɗauka wanda bugu ɗaya Halima ta ɗauka saboda tun da ta tafi ba ta kirata ba, kuma ko ta kirata sai ta mula ta mulmule take amsawa shi ma iya gaisuwa ta katse wayarta "Hello, uwata ta kaina macen da ta fi ko wace mace a duniya." Ta amsa tana mata wannan kirarin "Ba kiranki na yi ki mini kirari da ƙarya da ƙarerayin da kuka saba na 'yan siyasa ba, wanda sai mun zaɓe ku ku fito da manufofinku na zalunci da yaudara." Shiru ta yi tana jinjina abin da ta ce sai kuma ta gyara murya ta ce,"Amma kya yi mini fatan alkhairi na zamo ta ƙwarai na kuma banbanta da saur.." "Ke kika sani Halima, ai ni kin gama sire mini tun da kika yi mini haka. Maganar auren Jannah, an saka rana wata uku sai ki fara shiri." Ta ce tare da gimtse wayarta ba tare da ta jira abin da za ta ce ba. "Ka ji wai har ansa rana wata uku fa? Kai Hajiya ta ɗauki lamarin nan da girma." Ta ce tana jinjina lamarin da tunanin halin da Jannah take. "Humh, a rigimarta in ba an yi bikin nan ba ba za ta taɓa samun sukuni ba." "Ina fatan ta ƙulla alkhairi." "Amin, in sha Allahu." Cewar dad sai kuma ya ɗora da cewa," Ki ce zuwa Zariya rarrashi ya kama ni." "Aiko dole don yanzu Allah kaɗai ya san halin da take ciku, kuma ga shi ko na kira wayarta ba za ta ɗaga ba. Ka ƙara gwadawa ko za ta ɗauka." "Humh, kamar ba ki santa ba sai ta huce." Ya ce yana ɗaukar wayar sa kira amma har ta gama ringing ba ta ɗaga ba. "Ni kam na rasa wane irin kaya zan yi mata domin so nake gidanta ya banbanta da sauran 'yayan duniya dole na kashe mata kuɗi." Dariya ya yi jin abin da ta ce."Gaskiya ita ce ya ɗaya tilo wanda Allah ya bamu. Yanzu fa shikenan, girma ya kama ki za ki ɗauki suruki." "Hararsa ta yi cikin wasa tana faɗin,"Ban gane ba ko ka barwa Ya Bala surukutan ne." "A'a ni ai yanzu nake tashen kuriciyata, kin san zan iya aura mace budurwa ke kuma kwanannan za a fara ce miki kaka." Dariya sosai ta yi jin abim da ya ce wanda har ya sa ta tashi da sauri zata kai mishi duka sai ya ruga ta bishi da filo yana maka masa. "Allah ba ka da kirki, wato tsufata kawai kake hangowa ko injinjiya? Ko dayake in dai 'ya'yan Ajmal ne ina fatan ta haifa mini su da yawa domin zan yi alfahari da su, ban haihu da yawa ba ina son ta haifa harda nawa. Sai dai, kuma ganin yadda auren na su yake hakan zai faru?" Ta ce cikin murya sanyi wanda ya sa ya rungumeta yana faɗin," In sha Allahu za su zauna lafiya auren nan sai mun yi alfahari da shi." "Ina fatan hakan." Ta ce tare da ɗaukar wayarta tana faɗin,"Bari na fara kira na gayi sa ranar na kuma fara shiri." "Ah amara kirjin biki. Akwai lokaci ba." "A'a barni Injiniya mai zurfin ido da wuri yake fara kuka." Ta fara kiran ƙawayenta. Aby na fita bayan sun ɗan tautauna da Alhaji Umar wanda ya ba shi baki, da ƙara tausasashi kan su ci gaba da neman zaɓin Allah, sannan ya yi masa sallama ya rakashi har ya shiga motarsa ya tafi. Ɗakinsa ya koma ya kwanta sharf! Yana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. "Abby, jikin ne? Ko za mu je asibiti ko da yake bari na kira doctor Irfan." "Karki kira shi na ji sauƙi don na sha magani a sahshin Hajiya." "To me ya faru you look worry?" Ta ƙarashe maganar tara da dafa shi tana taɓa goshinsa. "Akan maganar auren yaran yanzu Hajiya ta tursasa aka sanya rana wata uku." "Sa rana?" Ta tambaya cikin tsananin mamaki da ruɗani. "Eh, dad ya naɗa ni waliyin Jannah, Alhaji Umar da ya ƙara tsayawa a waliyinsa." "Ikon Allah!" Ta ce tare da nisawa. Sai kuma ta saki numfashi ta ci gaba da cewa, "Ajmal ɗin ya sani?" "A'a da shi da ita babu wanda ya sani yanzu dai zan kira shi na sanar masa, Jannah ce ban san yadda zan yi ba you know how rude she is." "You have to hurry, kafin ta kira su ta hargiza su ta yadda zamu kasa shawo kansu, domin ka san ba za ta gaya musu da dadi ba" Wayarsa ya ciro da sauri don ya kamata tun tuni ya kira shi kafin ta kira don da biyu za ta gaya masa don ya harzuƙa. "Hello Ajmal, where are you?" "At home dad, ai na zo gidan you were in ofis." "Ok, can you come? We need to talk." "Lafiya Aby?" Ya tambaya jin murya sa wani iri. "Lafiya lau sai ka zo." Ya kashe wayarsa yana tausayinsa. Ajmal ya juya yana kalon Mushiirat da ta fito daga ɗaki cikin riga da wando iya gwuiwa rigar kamar singeleti. "Zauji, ya ka gani? I told you it would fit me sosai." Tsayuwar da ta yi masa ya tafi da imaninsa domin cikin jan hankali ta yi da gantsarewa. "Wow you look amazing and nice in that outfit, ashe na iya zaɓe." Dariya ta yi tare da rungume shi tana faɗin,"I told you." Juyo da ita ya yi yace,"Kin yi kyau sosai ɗin nan fa matar kirki, musamman hibs da waist ɗinki sun ɗauki kayan." "Allah ko?" Ta ce tana canza tsayuwarta har sai da ya ɗauke ta hoto da yawa. "Eh, Aby ya kira ni yanzu, I'm thinking is urgently lemme go, I will be back soon, na ɓata gayun nan don ya tsokale ni." Dariya ta yi ta kashe masa ido."Ok, waiting don Allah ko na biyo ka." "No, za a yawo ko?" Ya ce tare da ficewa don kar ta ƙara ce masa komai domin baya son ta san da maganar auren Jannah sai komai ya warware. Tsayawa ta yi a bakin ƙofa tana kallon shi har ya fita ta ƙara sakin murmushi ta koma ta zauna tana begen sa. Ajmal kuwa, a hanya yana ta tunanin kiran sai ya ji gabansa ya faɗi tunawa da bai gaishe da 'yar mulki ba, wanda zuciyarsa ta zargi akan shi ne. Ko da ya shigo bai leƙa sashinta ba kai tsaye shashin iyayensa ya shige. "Abby, ga ni ina ta tunanin lafiya." Ya ce tare da zama a gefen kujerar da yake. "Lafiya lau, kuma ni da ɗana don ya yi auren ya yi nisa dani ba zan kira in na so na ga ganshi ba?" Dariya ya yi yana shafa kansa jin tsokanar da ya yi masa."Ba haka bane Abby, I was thinking something differently." "To zauna ka natsu na so na ganka kuma a kwai maganar da za mu yi." "Ok."Ya ce tare da ije wayarsa da take hannunsa ya tattara dukkan hankalinsa, ya mai da ga mahaifinsa ganin yadda shi ma ya yi serious ya san dama dole akwai wani abu, sai yana addu'ar Allah ya sa alkhairi. "Ya maganar da muka yi shekaranjiya akwai update?" "No, Abby amma har yanzu ina addu'a ban cire rai ba." Ya ce tare da zaƙuwar ya je direct to streat point ba ya tsaya kwana-kwana ba. "Ok, Allah ya sa mu ji alkhairi." "Amin." Ya amsa zuciyarsa cike da zaƙuwar jin musambabin kiran. "Da ma na kira ka akan maganar auren ka da Jannah, an saka rana wata uku." Ya yi ƙarfin faɗin hakan domin tsoro da rawar murya ya ji. "What Aby! Ni Jannah aure na ga gaya muku ba na sonta kuma ba zan aure ta ba." "Calm down, and be matual Ajmal." Cewar Ammy da ta daga shi ganin yadda ya miƙe a razane jijiyoyin jikinsa suka tashi. "No Ammy! Na gaya mata bana sonta, lafiya nake zama da matata, ban ga dalilin da zai sanya na ƙara second wife ba. Besides that ,am not interested in her so there is no way." Ya ce cikin ɗaga murya wanda har ya sanya su Jannah da suke ɗakinsu suka ji. Zubbur ta miƙe kamar wacce aka tsikara."Rana ni da Ya Ajmal, aka sa? Ai dama wannan fitinanniyar tsohuwar ba ta bar maganar auren nan ba?" Ta ce tare da fara hawaye sai ta ruga sashin Hajiya Baaba tare da ta damu da kiran da su Ummu suke mata ba. "Mene ne haka? Muna magana cikin sirri za ka ɗaga murya kowa ya ji.Tabbas yanzu aka sanya ranar da Jannah, kuma yadda ta nuna aure babu fashi, domin ko ƙwandala ba ta bari na biya ba." "Ba zan amince ba, tun da bana so ai ba a aure dole, don haka sai ta janye sa ranar nan." Ya ce tare da ficewa daga ɗakin ya yi sashinta ba tare da ya damu da kiran da suke masa, wanda suka rufa masa baya. "Kin san Allah saimkin janye sa ranar nan, saboda na fita harkanki ko kallonko ba na yi don me kuma za ki dage sai an yi bikin." "Don ubanki to za ki buge ni, ko ki tsare ni a fasa. A tunaninki shiru da banzan da na yi muku na ƙyale ku ne? Habawa yara sai ka ce ba ku san wace ce ni ba." Ta ce tare da wafce rigarta da ta riƙe wanda ta sa kuka da faɗuwa ƙasa tana birgima. "Ki fasa aurenan, na ce bana son shi in ba haka ba, saina sha guba na mutu." "Kisha gubar bera in kin so, iyayenki kika yi wa asara ba ni ba." Ta ce daidai lokacin da Ajmal ya buga kofa da ƙarfi Yana huci ya shigo. "Hajiya Baaba, tun ina miki mutunci ki janye maganar aurennan, domin ina da matata mai tarbiya babu yadda zan yi na auri jikarki fitsararriya." "Au haba mai hurul ain, ai ba ka gaya mini matar taka daga sama aka sauko maka da ita ba saboda malinta, da ban damu kaina na aura maka wannan mara mutuncin ba, amma ka ga yanzu ka makaro sai dai a guji gaba. " Ta ce cikin gatsali sai kuma ta ɗora da cewa, "Kana maganar ita mara tarbiya ce, kai kana da tarbiyarne kake tarar gabana ka gaya mini abin d ka ga dama. Idan iyayenka ne suke magana za ka musa musu? Kai Adamuu, inda zan fayyace wa duniya abin da kake yi wallahi in ka hau mumbari za yi wa'azi da dutsuna za a wartako ka. Shashashu kawai marasa mutunci a tunaninku tabon da kuka yinmini ƙyale ku zan yi? Ai duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha." "Oho, koma me za ki ce ki faɗi amma ba zam auri wannann bagidajen ba, domin ina da saurayina ɗan gayu ba irinsa da ya tara gemu kamar na buntsu..." Wani wawan mari ya zabga mata."Ke wallahi saina yi ajalinki yanzu nan, mara mutunci kawai ba duk abin da yake faruwa ke kika ja ba, saboda rashin tarbiyarki da fitsara." Ya ce cikin zafi tare da ƙoƙarin neman bulala domin wani irin haushinta yake ji yana dana-sanin dawowrta gidansu. "Ka kasheta in ka so kaso ka ga sai kaima a kasheka, ka na huta da jarabarku amma aure babu fashi." Ta ce tana karkaɗa ƙafafunta ba tare da ta damu da dukan da ya ke mata ba, wanda ta canyara ƙara ta ci gaba da birgima, domin ta san ya yi haka ne don ta fasa auren. "Kai Ajmal, in ka ƙara kai hannu gareta saina tsinka maka mari."Cewar Ammy da ta ke bayan Aby ta ƙarasa gurinta ta miƙar da ita tare da riƙe ta tana rarrashi. Aby kuwa ƙarasa gurin shi ya yi ya ɗaga hannu zai tsinka masa mari sai ya ga rashin dacewar hakan ya fasa tare da sauke hannunsa. "Ba ka da hankali ko? Dukanta za ka fara ka nuna mana abin da za ka yi in an kai ta ko, kana malami aana dukan matar da za ka aura?" Sai ya juya gurin Hajiya Baaba da ke tsaye ko a kwalar rigarta."Hajiya, kin ga abin da za ki haɗa ko?" "Ka bar shi ya kashe ta sai ya ƙara rayuwarsa a zaman kurkuku." Ta ce tare da shigewa ɗakinta ta barsu tsaye tamkar haƙora. Aby ya kama hannunsa suka nufi sashinsa yayin da Ammy ta kama hannun Jannah da take kukan mari da saka rana suka tafi. A ɗaki ya sashi ya nuna masa ɓacin ransa sai kum ya yi masa nasiha ya kuma koma rarrashi. "Abby, wallahi bana sonta na tsaneta, ban taɓa tunanin ko mafarkin na yi rayuwar aure da ita ba, in kuma aka ƙulla auren nan akwai cutarwa, domin ƙyamarta nake saboda na tsani macen da za ta saka attach ko sau ɗaya ne, kuma ka san yadda nake nuna wa abu tsana in na tsane shi." Ya ce yana kallonsa ko zai ce wani abu sai ya numfasa ya ɗora da cewar ganin bai ce komai b. "Ina matuƙar zaman lafiya da matata, an shiga haƙƙinta da tozartata na sanya ni na ƙara aure ko shekara bamu rufa ba. Tana matuƙar darajani amma ita zagina take a gaban kowa za ta sanya matata ta raina ni. Don Allah Aby, ka yi wani bu akan auren na, in ta nace sai na yi aure zan iya ƙarawa da mata masu mutunci da tarbiya, amma ba Jannah ba." Ya ƙarashe maganar hawaye suna zubowa a kan fuskarsa. "To shikenan, zan ƙar mata magana da turo wasu mu gani ko za ta yarda ta janye ta shi ka tafi gida, amma kar ka ƙar kuskuren kai mata duka hakan ya saɓawa addininmu. Kuma duk wanda ya ji haka mutincinka zai zube." "Ka yi haƙur zafin zuciya ne, ni kaina ban san lokacin da nake kai mata duka ba. Ina girmama mata bana son wani ya ci musu mutunci." "Allah ya yi maka albarka maza tashi ka tafi gida." "To." Ya miƙe kamar wani ƙaramin yaro ya fice zuciyarsa na suya. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 33-34* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "To." Ya miƙe kamar wani ƙaramin yaro ya fice zuciyarsa na suya. Jannah kuwa duk irin rarrashin da Ammy take mata ta ƙi yin shiru sai zunduma ihu take yi. Da ƙyar da siɗin goshi Aby ya samu ya shawo kanta bayan ya yi mata ƙaryar ba za a yi bikin ba, wanda ta yadda ta sha paracetamol ta kwanta sai bacci. "Auren nan na su babu fashi sai dai su yi haƙuri, yanzu dai bari ita Jannah ta gama jarabawa ka da maganar auren ya sa ta samu matsala, kuma kin san ta da kafiya tana iya cewa ba za ta yi jarabawar ba." Bayan ta gama jarabawar mahaifinta za ka sa yazo shine kawai ƙila ya ci ƙarfinta, saboda ka san yanzu ko wayarsa ba ta ɗauka kuma duk akan maganar auren ne. "Kai Hajiya Baaba, haƙiƙa ta ɓullo da inda za ta rama abin da muka yi mata cikin ruwan sanyi. Wallahi ba ki gani ba Ajmal hawaye yake mini akan a fasa auren nan, ya ba ni matuƙar tausayi, domin hakan ya nuna mini yan zaman lafiya da matarsa ba ya son ya kawo ruɗani." "Aiko sai dai ya yi haƙuri, domin Hajiya Baaba ta yi nisa ba ta jin kira.Ɗaukar fansa ne a ranta." "Allah dai ya kyau kawai." Cewar Aby da ya miƙe zai shige bayi jin kiran sallar magariba. Ajmal da ya fita sai ya kifa kansa da sitiyarin motarsa, yana jin ransa na matuƙar ɓaci da dana sani akan bai canza mata kammannin ta ba, na cewa da ta yi gemun shi kamar na buntsuru ba. Sai kuma ya tsinci kanshi da kallon gemun a madubi yana shafawa cikin so da ƙaunar da yake masa, tare da tuna irin maƙudan kuɗi da gyaran da yake sha. Mata nawa suke crushing ɗinsa tamkar za su mutu, na social mediya da 'yan mata masu ilmin addini da boko ba irinta mara tarbiya da kamun kai ba. Ya daɗe a gurin yana jinjina abin da ta gaya masa da jin matsanancin baƙinci kamar ya mutu. A hankali ya tayar da motar yana janta kamar mai jin bacci saboda gabakiɗaya babu karsashi a jikinsa. A ransa yana tunanin abin da zai yi a fasa auren duba ga yadda ya kifa mata marin ko a kwalar rigarta. A bakin gate ɗin gidansa ya yi ƙoƙarin manta komai domin baya son ta fahimci wani abu, a ransa yana addu'ar Allah ya sa Aby ya ɗauko wanda zai sanya ta fasa auren. Da ya shiga gida yana ƙaƙalo murmushin da iya fuskarsa ya tsaya. Faɗawa jikinsa ta yi tana murmushi."Bab, ka daɗe har na fara ƙoƙarin na kira ka." "Eh, Aby ne muka je asibiti baya jin daɗi." Ya tsinci kansa da faɗin haka. "Ayya! Allah ya ba shi lafiya, sai na je na duba sa ko? Ina ganin gobe ina dawo aik..." "No karki je, ki bari zan kai ki da kaina kin san halin Hajiya Baaba, sam bana son ta faɗi abin da zai ɓata miki rai." Ɗan jim ta yi sai kuma ta tuna da halinta wanda in har ta ganta sai ta ji gabanta ya faɗi. "Tom, Allah ya kai mu, amma ya jikinsa." "Yaji sauƙi." Ya ba ta amsa yana ƙoƙarin rage kayan jikin shi, saboda zufan dake keto masa tamkar wanda ya yi ƙarya. "Bari na shiga wanka zafi na ke ji." Ya ce tare da riƙe ƙofar bayin yana kallonta. "Na zo na taya ka, na ga sai gumi kake kamar wanda ya yi gudu." "No karki damu shirya mini abincina." Ya ce tare da shigewa bayin saboda wani irin zafi yake ji sosai. Bayan fitarsu Hajiya Baaba ta ja tsuka tare da garƙame falonta. "Kuje can kuyi ta jarabarku, ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka jarabbbu kawai, da kun ɗauka rashin kunyar da kuke zuba mini iyayenku na gani saboda so basu iya kwaɓa muku, ni kuma na zama juji ku yi shuka mini rashin mutunci babu mai tsawata muku." Kwana biyu da saka ranar sai yaran gidan suka ɗauke mata ɗip! Duk da cewar ba wani shiga harkarta suke yi ba, amma duk safiyar Allah za su shiga su gaisheta Jannah ce kawai ba ta zuwa, amma daga ranar da aka sanya ranar sai suka daina domin matuƙar haushinta suke ji. Ba ta kula su ba kamar yadda suma ta kansu suke yi ba exam har suka gama suka shiga hutu sai zuwa islamiya. Ranar talata da yamma sun fito za su je islamiya suka ga Hajiya Baaba zaune akan farar kujera na roba, tasha kunu da 'yar rediyonta tana ta canza tasha. Babu wanda ya ce mata har suka kusa wuceta sai Nahlin da ta daure ta ce "Sannu." Ta ɗauke kanta. "Zo nan, na ce don ubanki da kika ce mini sannu ciwo nake?" Tura baki ta yi ba ta ce komai ba. Miƙewa ta yi ta tsaya cikin masifa tana kallon Jannah, wacce ta yi kamar ba ta san da mutum ba, domin da za a tambayeta wace ce maƙiyarta da gudu za ta nuna ta, wanda hakan ba ƙaramin zafi yake mata ba, domin har ga Allah tana matuƙar jin sonta da ƙaunarta fiye da sauran jikokinata, Duba ga yadda iyayenta ba su damu da ita ba. Matsalarta ɗaya rashin kunyarta da sangarta wanda ita kuma babu haƙuri take tunzurata. "Saboda kun raina ni bani da mutunci shiyasa kuka daina kula ni don na haɗa auren da ba ku so ko? To wallahi bari kuji na gaya muku sai dai ku mutu. Ke Hafsatuu, ki yi addu'ar saurayinki ba tsotse ƙwallon mangwaro ya yi ya yar don ya huta da ƙuda ba, don yana wuce lokacin da ya iba babu neman shawara sai dai a lulluɓe ki a kaiki gidan duk wanda na aura miki. Ke kuwa Ummu-Kursumu da babu mashinshini, sai aukin iyayi da kininibi ki zuba idanu ki gani kar ki daina biye wa wannan shashashar, da ba ta san inda ke mata ciwo ba, wallahi kin jin rantse miki da Musa direba zan haɗa ki." Wani irin ƙara suka saka saki hadda Jannah da ta ci magani jin abin da ta ce, wanda ya sa suka juya cikin sauri suna kallon Muda direba da yake goge motar Abby da sun bar shi yana shiri zai fita, yana ta washe naki jin abin da Hajiya Baaba ta ce duk da ya san da kamar wuya auren gurguwa nesa, don ya san ta faɗa ne don ta ƙuntata mishi, amma ina shi ga auren wannan zuƙeƙiya zankaɗaziya mai kama da matan aljanna, kuma da hakan zai faru ai sai ya ce tsuntsu daga sama gasshshe. Ummu ta ƙara juwawa ta kalle shi taga yadda yake washe haƙora da suke gantso sai kawai ta sa kuka ta nufi shashin su. Duk damuwar da Jannah take ciki sai da ta kwashe da dariya, a zuciyarta tana tabbatar da Hajiya Baaba, ta ƙai maƙura gurin rashin mutunci tun da ta haɗa ta da Musa direba, domin da ita ne ta tabbata sai ta kwana amai da ƙyanƙyani saboda muninsa. Harara ta zabga mata tare da ɗaure fuska sosai ta bi Nahlin da ta koma rarrashin Ummu ganin tana kallonta, wanda Hajiya ba ta ce mata komai ba sai ido da ta bita da shi tana mamakin ramar da yi, ganin yadada ta koma kamar waccce mayu suka kama. "Innalillahi! Dubi yadda ta koma sai kace ƙashi. Oh ni jikar mai gishiri, wanann rama haka to mai angon zai samu anan dama ba auki ba? Ga shi mara mutunci ne da na haɗa mata abubuwanda za ta cika kafin bikin." Duk ita kaɗai take tunanin zuci har suka fito suka wuce wanda ƙarar buga get ɗin gidan ya fargar da ita. Miƙewa ta yi ta ɗauki kujerarta ta koma ciki ganin ta isar da abin da take son faɗi, domin shi ya sanya ta zauna kawai don ta jira fitowarsu. Ganin da gaske bikin za a yi mom ta kama siyayyan kaya na hauka, domin zuwa lokacin komai an siya hatta kayan furnitures ta siya masu kyau da tsada. Dad, shi ma ya yi nasa bajintar sosai don kuɗi maƙudai ya bawa mom duk da ta nuna bata so, amma ya kafe saboda yana son ya yi mata bajinta. Ta fannin ango kuwa har ya manta da wani maganar biki, domin tun da Aby ya rararshe shi kan cewar zai samo matifa, ya manta komai ya ci gaba da sabgoginsa don haka babu wani shiri da yake yi. Jannah ma ba ta ƙara maganar auren duba ga yadda Hajiya Baaba, ta fita daga sabgarta kan maganar bikin burinta a koma makaranta su ci gaba da karatunta, wanda take ganin a yanzu ba ta da abin da yafi karatun duba ga yadda iyayenta suka yi watsin karan mahaukaciya da ita. Hajiya Baaba, babu zama an saci zanin ɓarawo, saboda kullum ranar duniya sai ta je kasuwa ta yi siyayya, domin kashe kuɗi sosai take kan maganar auren. Maganarta kullum dole ta yi abin bajinta da gyarata saboda gidan kishiya za ta. Sai dai, duk abubuwan da take yi, ta kasa yi wa amaryar maganar ta zo a gyarata sai rara gefe take yi, amma babu fuska wanda ganin haka ya sanya ta bari sai mom ta zo. Lokaci dai baya ƙarya domin a yadda aka sanya ranar ya rage saura wata ɗaya cif. A ranar da ya rage wata Hajiya Baba, ta sa rigima tun da asuba ta fara magana cikin ɓacin rai. "Ai wallahi, Muhammadu, ka bani matuƙar mamaki saboda karka manta Jannatuu, yar Halima ce. Kana bin uwarta a gindi-gindi, amma na bawa ɗanka 'yarta ka ƙi maida hankali akan maganar bikin, saboda ita uwarta samu kake da ita, ita kuwa ɗanka hidima zai yi da yarta." "Ashsha! Don Allah mai ya kawo maganar nan? Na ga an riga an saka rana, to mene ne na ƙorafi akai?" "Babu Muhammdu, mai zai san ya na yi ƙorafi kan maganar auren babu ai ko? Sai dai, in dai ƙorafin da na saba, domin na sani a gidan nan, kowa kirana yake da jarababbiya." Dafe kansa ya yi ya rasa bakin magana saboda shi kansa bai san me zai faɗi ba. Yana matuƙar tsoron wannan haɗin aure da za ta yi, amma ya rasa inda zai ɓullo, saboda hatta Ajmal tsoron yi masa maganar auren yake yi, kuma ga dukkan alamu mom ta yi na'am da auren duba da ba ta taɓa masa ƙorafi ba sai ma kiransa da ta yi kan maganar shirin bikin. "Hajiya Baaba, in kika ce za ki ci gaba da irin waɗannan maganganun za ki iya raba zumuncin dake tsakaninmu musamman ta wurin yaran." "Na lura kamar so kake kace kowa ya kama harkar gabanshi a dalilin auren nan ko Muhammadu?" "Ba haka nake nufi ba ina dai tunatar miki maganganunki zai iya kawo naƙasu a zumunci." "To ina ruwana domin in baku yi ba kwayi shi a ƙiyama." "Yanzu mai kike so game da auren?" Ya tambayeta cikin takaici yana ƙoƙarin ɓoye damuwarshi. "Na ga ai Jannatun ba kaza ba ce da har yanzu ba a fara shirye-shiyen aurenta ba, a lokacin da zai yi wancan uren saura wata ɗaya da kwanaki gidanan ya far kacamewa, amma ita saboda ba kwa sonta babu maganar akwati da hidimar biki, kamar wanda za a aura masa yar baben roba." "Ki yi haƙuri yau za a fara kuma zamu yi maganar da Ajmal yau in sha Allahu." "Ka kira shi yanzu ka gaya masa ko na je har gidansa mu yi maganar a gaban matarsa, kuma ka san halina in yaso sai ta yi tsirensa." Wayarsa ya ɗauko ya danna numbobinsa."Bari na yi masa bayani Hajiya Baaba, don Allah ki bar ni na shiga ciki mu yi magana ta hankali." Y ace cikin marairaice fuska. "Kun dai ba ni wallahi ku haifi yaya da cikinku kuna jin tsoronsu." Ta ce tare da sakin tsuka ta bar gurin wanda ya yi sororo tamkar mutum mutuni. "Hello Aby, mun tashi lafiya?" Ajmal ya furta cikin girmamamawa, bayan ya ɗauki wayar wanda ya tunatar da shi kan kira yake. "Ajmal, in har nina haifeka ka aminta da auren Jannah, kuma ka fara shirye-shiye saura wata ɗaya." Jikinsa ne ya mutu murus ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi yana tunanin abin da zai ce masa, amma sai ya ji ya kashe wayar cikin huci, wanda hankalinsa ya maƙurar tashi domin ya san in Aby ya yi fushi ya gaya masa magana cikin fushi dole ya bi. Zama ya yi cikin motarsa yana jinjina lamarin, yayin da damuwa suka haɗu suka yi masa rubdugu har ya rasa ta inda zai fara saboda ba zai iya kallon Mushirat ya samar mata da auren sa ba, haka zalika ba zai taɓa kallon Jannah a matsayin matar aurensa ba. Wani irin juya ya ji yana ƙoƙarin kamasa wanda ya yi sauri ya zauna tare da dafe kai, domin ya san cewa da ga ranar da aka aura masa ita ya yi bankwana da farinciki a rayuwarsa. Wata dubara ta faɗo masa wanda da sauri ya ɗauki wayarsa da ya sanya caji a cikin mota ya fara ƙoƙarin neman numbar mom, duk da ya san cewar alfarmar da zai tambaya tana da matuƙar tsauri da rashin kirki, domin ko wace uwa ba za ta ji daɗi namiji kamarsa mai haiba ya kira ta ya sanar mata da baya ƙaunar 'yarta tare da roƙon alfarmar a janye auren ba, amma domin farincikinsa dole ya yi hakan don ba shi da zaɓin da ya wuce wannan. Ringin biyu ta ɗauka cikin sakin fuska tana jin wani irin girmarsa da nauyinsa ya kamasa. "Hello Ajmal, kamar ka san ina son kiranka yau ɗin nan fa." Gabansa ya buga jin tana buƙatar kiransa wanda bai san akan mene ne ba. "Barka da safiya Mom." Ya ce cikin rashin karsashi yayin da yake ƙoƙarin nemo kalmomin da zai yi magana da su a bakinsa, amma sai ya ji tamkar bai iya magana ba, domin ji ya yi kalamansa sun ɗauke ɗif." "Ka yi shiru are you on the call?" Ta ce jin shirun ya yi yawa. "Eh mom." "Ok, dama akan maganar auren ku ne da Janaah, ka san lokacin aurenka na farko na yi maka lefe haka na Jannah ma, sannan maganar ɗakin da za a sanya kaya na gama danki kawai ya rage." Wani irin tashin hankali ya ƙara riskan shi jin yadda ta ɗauki auren domin zaƙewarta ya yi yawa sosai. Take ya ji ya kasa iya roƙonta wanda kuma in har ya yi haka ya cutar da kansa, don haka ya yi namijin ƙoƙari ya buɗe bakinsa don kar ya cutar da kansa, wanda kamar ta san abin da yake shirin roƙo ta rigasa ta da cewa, "Yauwa sai magana ta biyu Ajmal, kan aurenku ne, don Allah ku zauna lafiya ban damu da duk abin da za ka yi mata ba, matukar za ta zama na ƙwarai, saboda na san cewar na yi sakaci a rayuwarta, a ka ga abu uwa saɓanin hankalinka ka yi haƙuri la ladabtar da ita, domin zan so hakan ta gane rayuwa ba irin wacce take ciki ba." Ta yi shiru ko zai ce wani abu amma si ta ji ya saki naunayar ajiyar zuciya ba tare da ya ce ƙala, domin ji yake maganar da take kamar ta ɗauki dutsen dala ta ɗora masa. "Ba ka sonta na sani domin duk macen da yake da mace kamar matarka babu abin da zai iy da ita, kuma na san Hajiya Baaba, dole ta yi maka, amma ina roƙon don Allah ka aureta ka nuna mata rayuwa, a cikin rayuwarta babu wansa take tsoro sai kai na san nauyi zan ɗora maka, amma don Allah ka yi wallahi ko duka dunkiya kake so zan baka matukar watarana Jannah za ta fahimci gaskiya ta soni ta zama ta ƙwarai. Ta so ni ta nuna mini ƙauna ta gane nice wacce na fi ƙaunarta fiye da kowa a duniyar nan." Sai ta fashe masa da kuka soasai wanda ya karyar da duk wani karsashi da gabbobin jikinsa har ya ji shima ya na son ya rushe da kuka na ƙarfa-ƙarfa da ake ƙoƙarin yi wa rayuwarsa. Ya kasa cewa komai kuma ya kasa rarrashinta da take kuka, tamkar ranta zai fita wanda jin haka ta kashe wayar tana ji a ranta bahu daɗi domin a yadda ya yi ta san cewa ba ya so kuma baya ƙaunarta. Ya kasa tuƙi sai ya kifa kansa a saman sitiyarin yana jin yadda zuciyarsa take tafarfasa da zillo tamkar za ta fito waje. "Innalilahi wa inna ilahir raju'un! Tabbas Hajiya Baaba, kin shiga rayuwata, domin ban san yadda zan yi na yi adalcin zama da wacce ba na ƙaunarta, bayan ina da macen ƙwarai wacce ta gama siye zuciyata har ma da gangar jikina. Ya Allah ka kawo mini ɗauki." Ya furta a bayyane tare da sakin wawan ajiyar zuciya mai ƙarfi, zuciyarsa cike da tunanin shikenan yanzu ba shi da zaɓin da ya wuce na aminta da auren? "Jannah, daga yau za ta koma sashina domin kin san bikinta ya rage saura kwana talatin cip, ya kamata a fara gyarata ba sai lokaci ya ƙure ba." Hajiya Baaba ta furta ba tare da ta kalli Jannah da take zaune fuskarta a turbuɗe tun sallamar da ta yi. "To shikenan, Hajiya Baaba, sai ta koma Allah ya taimaka." Ammy ta furta cikin muryar sanyi. Harara ta doka mata ba ta ce komai ba tana kallon Jannah da take aika mata da na ta tamkar idanunta tamkar za su faɗo. "Ke, ba na son iskanci ki wuce mu tafi tun kafin na sanya Musa direba ya zo ya yi miki ɗaukar dawa." "Babu inda zani kuma ba zan sha komai ba. Ai ni da ɗakinki ba zan ƙara shig ba." "Shikenan, ba zan yi miki dole ba bari uwarki ta zo in ta kasa saki dole kije kice baƙinciki zai kashe kina ji kina gani a fifita kishiyarki." Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 34-35* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Shi ɗin banza da zan damu don ya so wata fiye da ni, dama an gaya miki na damu da ya so ni ne. In ya so ya haɗiyeta ko a kwalar rigata don da shi da banza duk ɗaya." Ta ce ba tare da ta ji kunyar Ammy ba da take tsaye tana jinta wacce ba ta ce mata komai ba sai kallonta take. Shiri gadan-gadan aka fara yi wanda ya ta da hankalinsu matuƙa, musamman Ajmal da ya rasa yadda zai yi ya sanar mata domin inya kalleta sai ta ba shi tausayi, ga shi bai san yadda za ta ɗauki zancen ba. Tabbas ya san ta mace mai addini da aiki da shi, amma ya san tana da mugun zafin kishi wanda tun da suka haɗu ta sanar masa, kuma ko ba ta da zafin kishi dole abin ya taɓe ta, musamman da ta san halin wacce za a kawo mata a matsayin kishiya na kunya da fitsara. Har bikin ya rage saura sati uku bai samu hanyar sa zai faɗa mata ba. Abin da ya ƙara tada hankalinsa kiran mom ta tambaye shi ranar da za a kawo kaya ya ba su key, wanda ya ji tamkar zai ɗora hannu aka ya yi ta zunduma ihu, domin ta tababata sai ta shigo cikin rayuwarsu da suka tsara daga su sai 'ya'yansu. A ranar da ya rage saura sati biyu da kwana uku wanda ya zama kwan sha bakwai cip! Hankalinsa ya tashi ya sanya a ransa dole ya gaya mata yau, tun da gobe za su zo danki ga shi Hajiya Baaba, ta kafe kan dole sashin Ajmal take so ya tashi ya bawa Jannah, saboda uban kayan da mom ta yi mata. Ya shigo cikin gidan cikin rashin karsashi don da ƙyar ya iya fitowa daga cikin motar, tulin kayan da ya siya mota ya ya ɗauko ya shiga ciki falon da sallama yana mamakin dalilin da ya saka har ya shigo gidan ba ta tare shi ba. Yana buɗe ƙofar da sallama ya ji ta maƙalƙaleshi tana dariya da tsallle. Tsayawa ya yi yana kallonta, ganin yadda ta cika da matsanancin farinciki, har ya rinƙa tunanin dalilin da zai sanya ta shiga cikin farincikin nan. "Ka san me Zauji?" Ta ce tare da kai masa kis bayan ta karɓa ta ije abin da ya siyo. "A'a sai kin faɗa sahibar raina, amma kamar wannan farincikin yana nufin mun kusa zama mu uku a gidan.?" Ɗan canza fuska ta yi jin abin da ya ce." Ba kuma fa hakan ba ne, ai tun da na yi miscarriage, bab ban samu wani ba." "Shikenan, is ok babu komai zai zo na yi tunanin wannan ne, in sha Allah next time in aka samu zan yi ƙoƙari na bi dokar likita kar na cutar da babymu."Ya faɗa ganin ta fara hawaye. Miƙa masa takadda ta yi tana murmushi."Da ga gurin aikinmu aka ba mu zamu je kwas na sati biyu, wanda in sha Allah, in har na ci jararrabawar ina dawowa za a ƙara mini matsayi." Gabansa ya yanke ya faɗi sosai ganin abin da take shirin yi wanda ya zama dole ya kwantar mata da hankali, saboda ba ta iya shiga damuwa ba, don ba ya manta lokacin ciwon mahaifinta da ya yi ciwo kamar za ta zauce haka ta yi. Sai ya fara wasiwasin ya gaya mata ko ya ƙyaleta wanda zai zama in har sai ta dawo ana saura kwana biyu bikin ne, anya kuwa ya yi mata adalci kuwa? Amma kuma ba shi da zaɓin da ya wuce hakan. "Masha Allah! Ina miki murna sosai yaushe ne tafiyarku?" Ya tambaya cikin zullumi da firgici wanda saboda tsabar murnar da take ciki ta kasa gane halin da yake ciki. "Jibi fa bab, wallahi sun ba ni haushi da suka gaya mana a ƙure kuma duk salon munafunci da baƙincikin karmu ci ne, don ya fi son yarensu su ci, ka san halinsa da mugun nuna tribalism, don haka ga zama dole na jajirce na yi karatu tuƙuru." "Allah ya shirye shi dole ki dage sosai, kuma in sha Allahu na san za ki ci domin ba ni da haufi a kanki dear Tabbas my you gonna rock it." Kanta ne ya fasu jin abin da ya ce."Muje na haɗa maka ruwan wanka, ni ma yau zan fara shiri kar na manta da wani abun."Ta ce tare da aama hannunsa suka shiga cikin ɗaki. Tsakar dare Ajmal ya kasa bacci sai tunani yake yi har ya buga filon da take kwance ya yi kundunbalar faɗa mata, wanda da ta miƙe sai ya kalle shi cikin mamagin bacci. "Allah Sarki bab, ka tashe ni ko? Ka ga na manta da zan yi karatu ina ta bacci amma da yake kafi ni damuwa da shi ka kasa bacci." Ta ce tare da miƙewa ta shige bayi wanda ya bi bayanta da kallo. Alwala ta yi sannan ta fito ta yi sallah raka'a biyu ta fara karatu, wanda ganin hakan ya miƙe ya ɗauro na sa alwalar ya fara sallah yana addu'ar Allah ya kawo abin da zai hana auren. Washegari da safe Ajmal ya shirya zai wuce gurin aiki ya bi ta gidansu. Yana ƙoƙarin shiga sashin su suka ci karo da Hajiya Baaba da ta fito daga sashin tana wa Adal bambami. Kallon juna suka yi tamkar wasu abokan gaba sai suka ɗauke kai a tare, wanda hakan ya baƙanta mata rai domin ta so ya kulata ta ba shi na shi kason. Fici-fici ta yi da idanunta tana kallon shi har ya shige sashi. "Jarababbiyar tsohuwa kawai." Ya ce sannan ya ja tsaki saboda matuƙar haushinta yake ji. Hajiya Baaba da ranta ya ɓace matuƙa domin duk tsiyar da take shuka musu ba ƙaramin son jikokin na ta take yi. Haushin rashin kula ta da bai yi ba ya sa ta dage iya ƙarfinta, ta saka kuka wanda ya sanya shi daina ƙoƙarin buɗe ƙofar shiga falon Ammy da yake yi, yana mamakin halinta domin ya san sharri za ta kulla mishi. "Lafiya Hajiya Baaba, mai ya faru?" Aby da Ammy suka furta a razane daidai lokacin da suka ƙaraso gurinta, wanda saboda tashin hankali ba su kula da Ajmal da yake tsaye ko kallon gurin sa take bai yi. "A gidannan, na san an gama mai da ni bolar kowa. Ku yi mini rashin mutunci haka 'ya'yanku, in ban yi kuka ba zuciyata ba za ta taɓa samun sauƙi ba, domin Ajmal ya gama mugun raina ni a gidan nan, kamar ni zai kalla ya yi mini tsaki kamar ma harda zagina ya yi." Zare idanu suka yi."Ajmal, shi da kansa awaya kenan, ko yaushe ya shiga cikin gidanan." "Ai dama na san ƙaryata ni za ka yi ba a waya ba fatalwa ya yi ya zage ni. Ko yaushe ka makance da ba ka ganshi ba ya shigo yanzu don ya yi mini tijira ba." Mamaki ya kama Aby don sai yanzu yaji ƙamshin turrensa wanda ya tabbatar masa yana gida. "Ajmal!" Ya kira sunan shi da ƙarfi cikin tsananin fushi, wanda ya amsa tare da ƙarasowa gurinsu hankalinsa kwance tamkar ba akan shi take masifa. "Na'am Aby ga ni." Ya ce yana nazarin fuskokinsu. "Mahaifiyar tawa za ka zaga, wai mai ya sa ba ka da hankali ne?" "Ni Aby da yaushe, matar da ko ganinta ban yi ba." Ya ce yana kallonta fuskarsa ɗaure don ya lura sai ya fito mata ta inda ba bata tunani. "Au haka kace shikenan, abar maganar wataƙila fatalwarsa ce, ka san ba shi da mutunci a zahiri haka baɗini domin Allah kaɗai ya san irin mugun abin da fatalwarshi take aikatawa, ƙila yau rashin mutuncinta ta kaina ya ƙare, amma dai a bar maganar ba wannan ba." Ta ce tare da ɗan jinkirtawa tana kallon su sai kuma ta ɗora da cewa, "Tun da aka saka rana bai taɓa zuwa ta zance ba, kuma na ga lokacin da yake neman aure, in har ya fita gidannan tun magariba, baya dawowa sai ƙarfe biyun dare yana can yana lalube musu yarinya. To yanzu ita Jannatun nufinsa haka za a kai masa ita a banza babu kuɗin zance?" Mamakin abin da faɗa ya kama su, sai suka kasa magana suna kallonta wanda ya harzuƙata, ta buɗe baki ciki fushi sai Aby ya tari numfashinta da cewar, "To yanzu me kike so ay.." "Magana mai sauƙi ya fara zuwa zance, a yau kuma ba sai gobe ba." "Aby zuciyata ta fara gaza ɗaukar abin da Hajiya Baaba, take mini da jawo mini raini.." "To dukana za ka yi, eyee in za ka iya dukar bismillah, dama dukan ne ya rage fitsararre kawai." Ta tari numfashinsa tana faɗin hakan cikin gatsali. "Mahaifiyar tawa kake gaya ma haka Ajmal? Ma za ka ba ta haƙuri, sannan anjima da daddare ka zo zance gurin Janna.." "Amma Aby ai..." "Umurnin nake ba ka ba shawara ba." Ya ce cikin fushin da yake ji na Hajiya Baaba, amma babu damar sauke mata sai dai shi. Juyowa ya yi ya wuce yana tausayinsa wanda Ammy, ta rufa masa baya tana kallon ɗan na ta da ya yi sororo yana kallonsu ya kasa ko motsi. "Ka yi haƙuri Ajmal, duk laifina ne da soyayya ya sa na biyewa mahaifinku na aure shi a tunanina in muka haifi Hajiya Baaba, za ta so ni da 'ya'yana, ashe ban sani ba tun da ta tsani ni don ina ƙabila ba za ta taɓa ƙaunata ba." Ta ce tare da share hawayen da suka gangaro mata. "Yauwa, ka ji abin da ya ce sai kuma ka taho da toshi, don na lura sai an gaya maka, domin daga ganinka mugun maƙo ne da kai, saboda duk zamana da kai a gidan nan, kyautar ka ta girma ba ta wuce dubu ashirin sai aukin siyo ma mutane littafan addini kamar kai kafi kowa sanin Allah." Ta ce tare da ballama masa harara. "Ba da ni kake yi ba a gidanan, har za ka gani ka yi mini kallon banza ka nemi bangaje ni bayan zagin da na ji kana mini a zuciyarka, za ka sani muje zuwa, ka san kowa ya ci tuwo da ni miya yasha." Ta ƙarashe maganar a gadare tana tafiya tamkar wata sarauniya. Idanunsa suka yi raurau hawaye za su zo saboda takaici, amma sai ya yi bamijin ƙoƙari ya mayar da su yana jin zuciyarsa na ƙara ɓaci. Ya jima a tsaye yana kallon inda ta wuce yayin da ya rasa wane irin tunani zai yi. Juyawa ya yi ya fita gidan gabakiɗaya tare da dana-sanin shigowa. Misalin ƙarfe bakwai bayan an idar da sallah Hajiya Baaba, dake jiran Ajmal ya zo taɗi ta ji shiru har aka yi isha, wanda ranta ya ɓaci sosai, take ta ɗauki waya ta kira Aby da ke zaune a masallaci yana lazimi, wanda ganin kiran sai da gabansa ya buga da ƙarfi, amma ya daure ya ɗaga domin ya san rashin ɗagawar matsala ce. "Na ji shiru bai zo ba, ko ba ka isa da shi bane?" "Ban sani dalilin da ya sanya bai zo ba Hajiya, ƙila wani abun ya riƙe shi." "Muhammadu, in har na isa da kai ma za ka ɗaga waya ka gaya masa ya zo zance. Ai na gaya maka ka yi sakaci da baka ɗauki irin tarbiyar da na ba wanda baka isa na ije kara ka tsallaka ba, amma ka bari wata shashasha can ta ɓata maka tarbiyar 'ya'ya." Ɗif! Ta kashe wayar ta ci gaba da bambami. Ran Aby ya ƙara ɓaci domin har da damunsa da ya san za ta yi, ya sa ya tsaya a matsallacin da nufin sai dare ya yi. Wayarsa ya ɗauka yana neman Ajmal wanda zuwa yanzu ya fara ba shi haushi. "Ajmal, kana son mu saka ƙafar wando ɗaya da kai ko? Na ɗauka idan na yi maka umurni za ka bi, domin a tunanin 'yar Halima ko musaka ce aka ba ka za ka yi mini biyayya ka aura. Ma za ka je zance kamar yadda Hajiya tace." "Ɗip ya kashe wayarsa don kar ya yi masa ƙorafi wanda jira yake ya dasa ya. Tsaki ya yi ganin ya kashe wayar yana jin yadd zuciyarsa ke zafi. Miƙewa ya yi ya ɗauki key ɗin motarsa zuciyarsa cike da mamakin wai za shi zance gurin 'yar fifigiyar yarinyar da baya tunanin ta fara irgar dangi. "To na ce mata me?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamaki, wanda tsabar haushi da rashin amsa ya sa ya ije key ɗin tare da komawa ya zauna ya dafe kansa, amma da ya tuna abin da Aby ya ce sai ya miƙe da sauri ya fice gidan cikin tsananin ɓacin rai. A ƙofar gida ya tsaya sai bai shiga ba saboda kowa haushinsa yake ji. Har zai kira wayar Ummu ta kira masa ita sai ya fasa ya kira numbar Nahlin, domin gani yake girmansa zai zube don wataƙila ta ce su fito tare. "Ke Nahlin kira mini wannan mara kunyar yarinyar, tsaƙo zan bata." Ya ce a gajarce yana mamakin kansa da jin haushin kansa da ƙarfa-ƙarfar da ake masa. "To yaya." Ta ce tare da miƙewa tana kallon Ummu dake kallo a wayarta. "Where is Jannah?" Ta ce mata da sauri. "I don't know, but ɗa zu tana nan." Ta ce tana ƙoƙarin miƙewa. "Kamar tana waje na ga ta sayi sabuwar waya da sim, ina ga numbar Huzaifah take nema. Lemme call her." "A'a ƙyaleta bari na dubo ta." Ta ce tare fa miƙewa wanda ya sa Ummu ta zauna ta ci gab ada kallonta. Ɗan tafiya kaɗan ta yi ta hangeta zaune akan kujera a tsakar gida. Gabakiɗaya hankalinta nakan wayar tana ta kira numbar da baturiya ke sanar mata da akashe take amma ta ƙi daina kiran sai hawaye take yi. Cikin tausayi ta ƙarasa gurinta wanda har sai da ta ɗan tsorata ganinta ya sa ta saki ajiyar zuciya tare da ci gaba da kiran ba tare da ta ce mata komai ba. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 35-36* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Ya is calling ya ce yana gurin aje motoci." Wani banzan kallo ta yi mata kamar ba za ta tanka ba sai kuma ta ji ta ce, "Wa kenan?" Haushin tambayar ya sa ta ji tamkar ta tsinka mata mari duk da tana tausayin halin da take ciki. Sai dai, kuma ba ta son rashin zuwanta ya shafeta don haka ta daure ta cije ta ce, "Ya Ajmal, tun ɗazu ya aiko ni ban ganki ba ina ta neman.." "Ya makance ne da ba zai iya shigowa gidan ba yake nema na na yi masa jagora?" Ta ce a gatsale bayan ta miƙe. "Jannah, ki kama kanki tsaƙo ya bani kuma na isar in kin.." "To kije kice masa na ce ba zan zo ba, Allah ya sa makantar ta tabbata ya dauwama anan har ƙarshen rayuwarsa. In kuma ba makanta ya kama sa ba, to in ya isa ya zo ya jani." "Jannah, ki fita.." Nahlin ta fara magana cikin fushi dai kuma ta kasa ƙarasawa ta juya ta koma domin ta san ko kasheta zai yi ba za ta zo ba, kuma in ta daɗe duk laifin zai iya ko awa kanta, wanda tuna hakan ya sanya ta wuce kamar kububuwa. Tsaki ta yi ta ci gaba da neman layinsa tana hawaye. "Ta ce ba za ta zo ba." "Ok." Ya ce domin ya yi tunanin hakan wanda har zai ɗaga waya ya kira Aby sai ya fasa tare da yanke shawarar ya je da kansa ya yi mata warning wataƙila ta iya sawa a fasa aure. Har Nahlin ta juya ta fara tafiya bayan ta yi masa sai da safe a ranta tana tausayinsa na jawo masa raini da aka yi, amma sai ta ji ya ƙwala mata kira wanda ta juyo ta ƙaraso, tana addu'ar Allah ya sa ba ƙara aikenta zai yi ba, domin ita kanta haushin rainin da baƙaƙen maganganun da take faɗi take ji. "Tana ina ne?" Ya tambayeta ba tare da ya daina danna wayarsa ba. "Tana gurin bishiyar lemo zaune." "Shikenan, je ki sai sa safe." Ya ce tare da zaman shi a mota har sai da ta ɓule sannan ya fito, domin kunya yake ji wai shi zai ta ka ya je gurinta. A lokacin da ta ji alamun tafiya hawaye take yi amma jin ƙamshin da ta tabbata ba na Nahlin ba ne, ya sa ta fara kuka da ƙarfi. "Wayyo Huzaifah masoyina don Allah ka ɗauki wayata, domin kai kaɗai nake so kuma nake ƙauna, saboda bayan kai kaɗai sauran mazan duk losaraye ne." Ta ƙaraso tana faɗin hakan kuma ya ji ta bai tanka mata ba. Hotonsa ta yi zumming tana shafa fuskarsa."Ina matuƙar son gemunka domin na ka baya ka a da irin na bagidajen mazan da suke ajewa kamar na buntsu.." "Ke!" Ya ce cikin tsananin fushi wanda ko gezau ba ta yi. "Saboda iskanci na aika a kira ki kika ki zuwa, na zo shine za ki fara gaya mini magana don kin raina ni ko?" Banza ta yi da shi sai kuma ta ɗago ta kalle shi daidai lokacin da ya leƙa wayar yana kallon hoton Huzaifah. "Shi kan dai murna za a yi masa da rabuwa da jaraba da ya yi, ni kuma a jajanta mini. Sai ya taɓe baki ganin ba ta ce komai ba, wayarsa ya ciro wayarsa tare da nuna mata hoton. "Ki kalli wannan hoton." Kallon banza ta yi kamar ba za ta kalla ba sai kuma ta kalla a wulaƙance. "Na gani gidan kifi ne, ba ka da jari ne kake son na roƙi mom ta ba ka?" Ta ce mishi a gatsale. "A'a." Ya ce tare da dariyar mugunta ya mayar da wayar a aljihunsa. "Na zo na nuna miki na kuma yi miki albishirin da cewar matuƙar kika yadda aka yi auren nan, a daren amarcinki a nan za ki kwanta. Juyowa ta yi da sauri tana kallonsa yayin da take son gasganta abin da ya faɗa. Gira ya ɗaga mata sai kuma ya ɗora da ce, "Matuƙar kika ba yi abin da za a fasa auren nan ba aka kawo ni ki gidana, sai kin gwammace dama guba kika sha kika mutu, domin ina da matar kirki kamila mai kame kanta da alfasha mai zan yi dake ballagaza." Kuka ta saka da ƙarfi sai kuma ta ga babu amfanin haka ta juya ta kalle shi ta saka dariyar takaici. "Ka kwantar da hankalinka domin in har ban sha guba na mutu ba, zan yi sanadin ranmu ni da kai domin ba zan taɓa yarda na jawa kaina abin kunya na auren bagidaje irinka ba." "Ok, haka kika ce." Ya tambayeta cikin mamakin rashin kunyarta. Ɗaga masa kai ta yi tare da balla masa harara za ta wuce sai kawai ransa ya ɓaci ganin kallon da take masa ya sa ƙafarsa a tsakaninta kafafunta wanda ta harɗe ta faɗi ƙasa wayarta ta fashe. Tsabar baƙinciki da zafin faɗuwar ya sa ta canyara ƙara wanda sai ga mutanen gidan a gurin har da Hajiya Baaba. "Lafiya Ajmal? Na lura ba za ku taɓa barinmu mu huta ba." "Da ga na zo zancan shi ne ta yi mini rashin kunya shine na fara koya mata yadda ake yiwa miji magana domin matata, haka take mini ba, ka ga gara na koya mata don kar ta ɓata mini tarbiyar matata." Ya ƙarashe maganar tare da kallonta yana murmushin mugunta. "Ba zan iya ba da kuɗin zance ba Hajiya Baaba, domin ko lokacin da nake zuwa zance gurin Mushirat, in har ta ɓata mini rai bana bada kuɗin zance." Murmushin mugunta ya yi y fice tare da faɗin,"Sai da safe." Hajiya Baaba, ta kalle ta da take kuka sosai ga baƙincikin sabuwar wayar da ta siya ya fasa har ta ƙi kawowa. Kuka ta ƙara rushewa da shi. "Wallahi Allah sai ya saka mini akansa da wacce ta haɗa auren, ba zan taɓa yafe wa ba." Ta ruga da gudu tana kuka. "Fitsararra! Kin dai ji haushi wallahi, saboda ko wace mace in aka zo zance kuɗi ake ba ta, amma ke tsabar rashin kunya ya jawo miki, duka kika samu, to wallahi ba zan takurawa kaina ba, iya abin da ya samu za mu kai miki." Ta wuce tana bambami ba tare da ta kalli su Aby ba. Dad ɗin Huzaifah ya shiga cikin matsanancin tashin hankali, ganin ya ƙi ci ya ƙi sha sai kuka da kiran sunanta wanda ganin haka ya sanya shi yi wa Zariya dirar mikiya, ba tare da shawarar mom da take ta yi masa tsiya ganin zai kashe kansa a banza ba. Bai sha wahalar ganin Aby ba wanda ya karɓe shi cikin mutunci ya yi mishi karɓa ta ban girma duk da ba a san da zuwan shi ba. "Ni ne mahaifin yaronan Huzaifah, wanda yake son Jannah, na san kuna da labarin mun zo lokacin suna Abuja, yanzu ma na ƙara zuwa akaro na biyu, saboda yarona he is in critical condition. Na roƙe ku don Allah.." Ya ce hakan tare duƙawa a ƙasa yana hawaye. "Yarona zai mutu kuma shi kaɗai Allah ya ba ni ɗa namiji, ku taimaka ku bar yaran su yi aure." Aby sai ya ji babu daɗi ganin mutum da girma kamar sa da muƙami yana roƙonsa. Sai dai, ko kuka ya yi baya tunanin za ta amince da idanunta ya rufe na ɗaukar fansa a kan dukanninsu. "Ka yi haƙuri Hajiya Baaba, ba za ta amince ba, domin idanunta ya rufe fansa kawai take so ta ɗauka. Mu ɗin mun yi kuskure wanda ya shafi yaronmu. Ina fatan yaronka ya samu lafiya." "A lokacin da muka je Abuja bamu ji da daɗi ba, amma don Allah ka ƙara kira mini ita na ƙara roƙonta ko za a dace." Jiki a sanyaye ya miƙe bayan ya sanar masa da yana zuwa ya shige sashinta wanda ya same ta da uban tulin kaya a gabanta tana gyarawa ta a za saka a cikin mota a kai gidan Ajmal saura ne wanda ba a kai ba. "Hajiya Baaba, mahaifin yaron nan ne ya ƙara zuwa a karo na biy.." "Kai dakata! Da hankalinka kake ƙoƙarin neman aure cikin aure? Ni ban ga wani abin damuwa don ya rasa Jannah ba, saboda ban taɓa ganin ubanka sai ranar da aka kai ni ɗakina, kuma muka yi zamanmu lafiya lau, har da ya mutu sai da na yi kwanaki ban dawo hayyacina ba, amma su da yake yaran ƙarshen zamani ne wai sun iya soyayya har yake shirin kashe kansa. To kace masa ya mutu kansa don ba ni za a turmuƙa a rami ba." Ta ce tare da cigaba da aikinta. Ganin ba ta da ninyar zuwa ya shigo da shi har cikin sashin na ta wanda tana ganinsa ta ci magani ta ci gaba da aikinta ba tare da ta kalle shi ba. "Barka Hajiya, m..." "Kai dakata! Yi waje ka ba ni guri domin babu kalmar da za ka yi amfani da ita na sa a fasa auren nan, kuma kun san ai haramunne neman aure cikin auren, amma saboda mugun son zuciyarka kake son a fasa don a bawa ɗanka da yake gwal ne." Jannah da take kwance tana kuka cikin bargo haƙoranta na karkarwa don ta bata da gaske auren za a yi mata. Tun ranar da aka yi danki ta kwanta ciwo take kuka da shuka rashin mutunci da ihu amma a banza don tana fanin ba duka ta rufe ta da shi ba babu yadda za a yi ta fasa auren Jin an ambaci mahaifin Huzaifah ya sa ta diro daga gadon daga gadon da take kwance wanda Ummu ke gefenta har hawaye ta yi mata akan ta tashi tasha ko ruwan tea, amma ta ƙi. Ganinta kawai suka yi a gabansu cikin kuka ta kalli mahaifinsa ta ce,"Dad, where is Huzaifah? I miss him. Don Allah ka gaya masa ya zo gare ni domin zuciyata ba za ta iya ɗaukar girman rashinsa ba." "Munafuka dama lafiyarki lau, kike ma mutane iskanci ki kwanta kina numfarfashi, amma yanzu daga ambaton Huzaifah kin sheƙo da gudu kina gudu bamfaleƙe."Cewar Hajiya wanda ba ta bi ta kanta ba. "Ta shi ki wuce ciki domin yanzu ke matar wani ne." Ta ce tare da kamata wanda ta fisge ta kama ƙafafun mahaifinsa da ya fara tafiya domin ya sare ba za ta amince ba ɓata bakinsa kawai yake. "Don Allah karka tafi ka gayawa Huzaifah ya buɗe wayarsa zan kira shi mu gudu muje can mu yi aure." Ta ƙara faɗi cikin kuka. "Au ki gudu ki ban ni da jin kunya ko kina ganin an fara zuwa bikin, to in kika ga kin leƙa waje sai kin gudun wawiya kawai." Ta ce tare da kamata ta riƙe tamau ta shigar da ita ciki wanda ta yi ƙoaƙrin ƙwacewa amma ta kasa. "Haba 'yannan, to ko mahaifinki na riƙe ai bai isa ya ƙwace ba." Ta ce tara da kaita har cikin ɗakinta ta rufe ƙofa. "Ummu!Ummu!! Shikenan, Hajiya Baaba, ta raba ni da masoyina Huzaifah na shiga uku!" Ta ce tare da ƙara rushewa da kuka ta faɗa jikinta. Huzaifah kwance a tanƙamemen falon su yana riƙe da wayarsa da dad ɗinsa ya karma tun ranar da suka je gidan su Jannah. Har yau zuciyarsa ba ta daina tunanin wulaƙancin da Hajiya Baaba ta yi musu ba, wanda ya cika da mamaki ya gasganta kura ce da fatar akuya. "My son, the you mean you will keep thinking about her? Ka na son na rasa ka ne? Ka san cewa ba zan iya rayuwa in har babu kai ba." Mom ɗinsa tace cikin muryar kuka tana share hawaye. "I love her mom, I really love her like crazy. Tun ranar da muka haɗu a filin jirgi na ji a raina da ita kawai zan iya rayuwa. Ita ɗin tamkar maganaɗisu ce a cikin rayuwata, don Allah ku taimaka ku ba ni ita karku sanya zuciyata ta buga." Sai ya riƙe hannun dad ɗinsa yana dannawa a kan ƙirjin shi da ke harbawa fat! Fat!! wanda har sai da mahaifinsa ya cire da sauri saboda irin ƙarfin harbawar da take yi. "Ka ji ko dad, harbawar da zuciyata take yi ƙara mini sonta take a cikin zuciyata wanda in har ban same ta ba zan iya mutuwa. I have to give you my will cus I'm gonna die, I can't make it without her." Kamar ƙaramin yaro ya saka kuka tare da rungume mahaifinsa da yake kallonsa cikin tausaya. "Ya kamata mu koma gidansu Jannah mu ƙara roƙonta saboda in har ɗana ya mutu na rantse sai na yi shari'a da ita." Cewar mom da take zubar hawaye domin ba ta taɓa ganin abin da ya ƙwallafa ransa akai har ya kaishi zubar da hawaye da kwanciya ciwo. "Na nawa saboda, I went to Zariya jiya, amma in vein don ya rage one weeks aurenta da shi." "What!" Ya ce tare da miƙewa tamkar zai zura. "No, it can't be her. Jannah ba za ta bari ayi mata aure ba da ni ba." Ya ƙara faɗi cikin zautuwa sai kuma ya sa kuka ya koma ya kwanta yana suratai kamar ya zare. "Innalillahi! Suma yake yi fa kar ya mutu." Cewar mom ganin idanunsa na ƙyafƙyaftawa. Da sauri dad ya kama shi ya rungume yana kiran sunansa. "Jannnahh." Ya ja sunan tare da yi masa wasali da gunna sai kuma ya yi shiru can ya buɗe idanu ya fara tari sai aman jini, wanda ya ɗaga hankalin iyayensa suka sa ihu tare da kiran direba. Dad ya taitaye shi ya sanya a mota yana girgiza shi da kiran sunan shi amma ina sai aman jini yake yi. A lokacin da suka isa asibitin da ƙyar likitoci suka yi nasarar dawo da shi cikin hayyacinsa ya daina aman jinin, amma bai daina kiran sunan Jannah ba. Doctor ɗin ya fito yana share zufar goshinsa wanda yana buɗe ƙofa suka yi kansa. "How is he likita? Ya farfaɗo ya jikinsa." Suka tambaya cikin tsananin tashin hankali. "Please, do whatever you can to make him to have yarinyar da yake faɗi." Cewar likitan yana kallonsu. "Ba zai iya samunta ba saboda kwana biyu ya rage a ɗaura mata aure doctor, da ace kuɗi na amfani da zan yi na samar mishi yarinyar, amma iyayenta ba sa buƙatar kuɗi, saboda suna da su." Ya ƙarashe maganar cikin rauni yana share zufar goshinsa. "Mafitar ceton rayuwarsa shine a samar masa da abin da yake so." "Hakan ba zai yiwu ba doc na gaya mata babu yadda za a yi na shawo kan iyayenta." "Innalillahi! Yanzu rasa shi zan yi kenan? Don Allah likita ka yi wani abu wallahi shine kawai ɗa namiji da Allah ya ba ni." "To ku yi masa viser ya bar Ƙasar nan, zan haɗa ku da wani doc a India yana da sani sosai akan zuciya in sha Allah zai samu sauƙi saboda ya kamu da ciwon zuciya gab take da ta buga." "Innalilahi!"Suka furta a tare suna hawaye. "Ok, I will give me the doctor's numba." Dad ya ce a firgice tare da ɗaukar wayarsa ya kira akan a fara nema masa viser na su duka ukun. Cikin ƙanƙanin lokaci suka yi viser suka nufin India ba tare da ɓata lokaci ba. A lokacin da suka isa Ƙasar India hankalinsu ya tashi kwatankwacin tashin gwauron zabi! Don babu numfashi suka isa da shi, wanda jinin su ya yi sanyi tamkar ƙarƙarar dake cikin firij. Suna kallon shi ta gilashin ɗakin an sanya masa oxygen yana kwance shememe kamar gawa sai cikinsa da yake ɗan motsi alamun akwai numfashi a jikinshi. "Ke kam wannan tsohuwa sam ba ki yi man adalci ba sai Allah ya sakawa waɗannan yara saboda son zuciyarki ki nemi ki kashe mini ɗana ɗaya tal da na mallaka." Ta ce cikin matsanancin kuka tana jin kamar ta ɗauki bindiga ta harbe ta har lahira. A ranar da mom ta shirya za ta taho sai aka kira ta kan wata mata ta haihu 'ya'ya biyu babu jini babu abincin da za ta ci ballantana kayan da za a sanya wa jariran ga shi mijin ya mutu." "Innalillahi! Kai maza anya wasu suna tausawa mata kuwa? Dole na zo na taimaka mata ina ganin ke Hajiya Turai, ki je garin nan da za ku je ni da Mujee, sai muje cikin shiri daga nan mu wuce Zariya, kin ce sai jibi za ku zo ko?" "Eh, kon san dole na jira baƙinan mu taho." "Ok tom shikenan, don Allah ki karɓo mini kayan mata na SURAIYA D kin san ba kowa ne maganin mata nake iya siye ba, amma sai nata saboda yana da inganci kuma akwai aiki sosai." "Haka ne km SURAIYA D kayan matan ta ingantattu ne, ko ni bana iya amfani da ko wanne sai na ta. Ki ce wannan ango babu ragi tsakaninsu domin Uwa ba da mama kusan na dubu ɗari biyu kika siya." "Eh, so nake ta kama mini shi a hannu kamar yadda na riƙe mijina, sannan surukin nawa tsadadde ne mai aji da ilmin addini, wanda ya san haƙƙin aure da sanin darajar mace, kin ga dole na yi mata gyara." "Allah Sarki! Aiko na tausaya masa domin ya zo hannu don kayan mata na SIRAYYA D ka yi amfani da kaɗan ya ka ƙare ina ga kuma an sha da yawa." Mai buƙar kayan matan SURAYYA D *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* "Eh, haka nake so 'yata ta zamo zinariya a gidan aurenta kamar yadda na zamo, don Allah ki dafa duk sauyoyin nan in za ki zo." "Yauwa na manta na ce zan gaya miki waɗannan magungunan ki fara mata kamar haka: Kyaran jiki Ki samu kokumba ki yi blending a tace a sai ki shafa a jikinki. Sau biyu ya kamata a yi, kin ga ko bayan auren sai ta ci gaba. Maganin warin jiki: Kanumfari lalli a haɗa a jiƙa a shafa a gaba. Siddir A ije mata siddir a gidanta ya fi ƙarfin aljanu. Haɗin ayaba: Ki sayi ayaba ki ɓare ayi blending 7-or 10 ya niƙu sai ki zuba milk the quantity you want then sai ki sugar ki aje a frij in ya yi aanyi kisha. Sannan ki sanya ta kullum bayan asubahi ta rinƙa karanta YA WADUDU ƙafa ɗari hudu yana saka soyayya tsakanin masoya da kawo buɗi. Bari dai na barki da waɗannna in sha Allahu in zan taho zan dubo masu yawa harda addu'oin sace zuciyar miji da zaman lafiya." Ajiyar zuciya mom ta yi mai ƙarfi a ranta tana tunanin yadda za ta iya tunkararta da magungunan. "Na gode sosai Allah ya bar zumunci." "Ba ki da matsala, sai mun zo ki gaishe mini da Hajiya Baaba uwar biki." "In sha Allahu." Ta ce tare da kashe wayarta sannan suka shirya suka kama hanyar ƙauyen. Jannah ta ci kuka har ta bawa uku lada tamkar za ta shiɗe duk ta rame ta fita hayyacinta. Sosai Aby ya tausaya mata sai dai ba shi da abin da zai yi mata sai addu'a. Dad kan dole ya shiryo ana saura kwana biyu biki ya kamo hanya don rarrashi jin taƙi ci ta ƙi sha. Hankalinsa ya tashi ganin yadda ta koma wanda har sai da ya zargi kansa. Ganinsa ta faɗa jikinsa ta yi kuka ta yi kuka tamkar za ta shiɗe wanda ya tausaya mata har sai da ya yi ƙwalla, domin tsananin tsanarsa da take yi ya bayyana a idanunsa. Saboda tsabar kuka ta kasa cewa komai sai ajiyar zuciya take wanda yake barazanar tafiya da numfashi Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 36-37* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM Saboda tsabar kuka ta kasa cewa komai sai ajiyar zuciya take wanda yake barazanar tafiya da numfashinta. "Ina ga ya kamata mu kai ta asibiti she is convulsived." "Eh haka ne na kuma siyo mata magani bari na kira Ajmal ya kaita." Ya ce yana ƙoƙarin kiran wayarsa, wanda bugu ɗaya ya ɗauka don a tunaninsa zai ce amfasa aurensa ne, amma sai ya ji saɓanin haka na kiransa, duk da hakan bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya zo yana addu'ar Allah ya sanya ayi masa albishir da fasa auren. Da sauri ya ɗauki mota ya fice saboda Mushirat ta kira shi nan da awa biyu za ta iso Zariya ya je tasha ya ɗauko ta, wanda yake jin matsanancin tashin hankali saboda dole ya sanar mata don tana zuwa ɗakinsa, za ta nufa ga shi yanzu ya koma ɗakin Jannah an shaƙe shi da kayan da ya shiga sai da ya yi mamaki. Yana isa ya same su a falo Jannah a kwance kan cinyar har lokacin ba ta daina hawaye ba tana ajiyar zuciya. "Yauwa Ajmal, matarka za ka kai asibiti ba ta da lafiya." Cewar Aby fuskarsa a ɗaure. Ganin babu fuska ya ce."Ok, ta tashi mu tafi saboda zan je wani guri ne." Ya faɗa bayan ya gaida dad da ya masa cikin fara'a. "Jannah, ma za tashi ki je ki sanya mayafi ku je asibiti." Cikin tsananin tsoro da rawar murya ya faɗa domin ya sam abu ne mai wuya ta amince. Har ta buɗe naki za ta musa sai kuma ta ba su mamaki, ta miƙe bayan ta fakaici idanunsu ta galla masa harara wanda aka ci sa a ko kallon inda take, bai yi ba ballantana ya yi tunanin akwai wata halitta a gurin. Da ta shiga ɗaki a maimakon ta ɗauki mayafi sai ta saka rigar sanyi kan doguwar rigarta ta saka hula tare da ɗaukar wayarta ta saka a cikin aljihun. 'Dad, na shirya." Ta ce a sangarce tana jan majina, wanda gabakiɗaya suka bi ta da kallo har shi da ya ji kamar ya tashi, ya rinƙa kifa mata mari har sai ta je ta sanya hijabi. "Haba Jannah, ke da kike jin sanyi ba sai ki saka hijabi ba." Cewar Aby yana nazarin fuskarta. Kafin ta ce komai dad ya ce,"Go and wear hijab." "Sun yi datti dama biyu ne duk gyale na ke da su." "To ba sai ki ari na Nahlin ko Ummu ba." "Ai ba na aron kaya." Ta ce ba tare da ta damu da tunzurar da suka yi ba, ganin duk inda suka ɓullo sai ta kauce. Dad ya buɗe baki zai yi magana Aby ya ce,"Ƙyale ta je ki saka gyalen." Babu musu ta juya ta ɗako wani siririn gyale ta yafa iya kafaɗa, wanda shi dai bai ce komai ba ya miƙe yana mata wulaƙantaccen kallo. "Sai kun dawo Allah ya yi muku albarka, ko Ummu ta raka ku?" Ransa ya ƙar ɓaci jin an ambaci ƙanwarsa ta raka su, wanda ya ƙara jin baƙincikin haɗa shi da ita da suka yi, fa yi nan an fara jawo masa raini wai Ummu ta raka su. "A'a babu buƙatar haka, yanzu zamu dawo." "To shikenan, sai kun dawo Allah ya yi muku albarka." Shi kaɗai ya amsa don ita ko kallon su ba ta yi ba ta fice. Tana fita falon ta cire gyalen ta ƙudundune ta saka a aljihun rigar ya rage daga doguwar rigar sanyi. Zuciyarsa ta kawo wuya ya ji tamkar zai yi hauka. Wani irin ƙululun baƙinciki ya taso masa ya zu wuyansa ya tokare shi bai wuce ba, kuma bai faɗa ciki ba. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ya ce yana kallonta ta madubi daidai lokacin da ta buɗe motar cikin isa da taƙama ta zauna a baya ta mai da shi direbanta kenan. Tunanin yadda zai iya kallonta ya gaya wa mutane cewar wai ita matarsa to be ne duba ga shigarta ba ta da maraba da arniya. "Anya iyayena sun san ni ɗin wane ne da matsayina aidanun duniya suke ƙoƙarin zubar mini da mutunci?" Ya tambayi kansa cikin ruɗani. "Tsakanina dake Hajiya Baaba, Allah ya isa." Ya faɗa da ƙarfi tuna tashin hankalin da ke gaban shi. "Dallah ni idan ba za ka yi driving ɗin ba lemme know, ka sa ina ta sweating.." Maganarta cikin tsawa da son kuka suka doki kunninsa wanda bai san lokacin da ya juyo a sukwane yana mata mugun kallo. Motar ya figa a fusace ya bar gidan wanda sai da suka yi nisa ya yi parking ya ɗan jima ko mai ya tuna sai ya figeta a guje har suka shiga cikiin asibiti, wanda ko motsi ba ta yi ba ballantana ta hafimci me yake yi, saboda ta fishi iya gudu a mota. Mushirat, cikin damuwa take kiran wayarsa wanda har ta yi ringing sau tari ba a ɗaga ba, saboda ya manta da ɗayar wayarsa a falon Aby. Adal da ke zaune da Ummita suna kallo a cikin falon hankalinsa ya kai gurin wayar da take ihu da neman agaji, wanda ya ɗauka da sauri ya nufi gurin mom da take kicin ana haɗa abincin su mom da za su zo. Yana gudu zai kai wayar ya haɗu fa Hajiya Baaba, da take sauri za ta shiga sashin Ammy don yin magana da Aby. "Kai Adaluu, zo nan wayar waye a hannunka? Ka wo wayar maza kira mini Aby a waje. Da sauri ya ƙarasa ya miƙa mata wayar."Ga shi ta Ya Ajmal ce, ina ga faɗuwa ta yi a aljihun shi kima ana ta kira." Karɓar wayar ta yi wacce ta ƙara ɗaukar kuwa. "Duba ka ga wane ne ke kiran maza ɗaga ka gaya masa baya nan." Ta ce tana miƙa masa wayar. Ganin an rubuta matar kirki ya sanya jikinsa ya ba shi Mushiirat ce, amma bai ce mata komai ba ya ɗaga wayar da sallama. "Hello Anty Mushiirat, Ya Ajmal ba ya nan ya manta da wayar a gida sun fita da Anty Jannah." Wani irin faɗuwar gaba ta ji har sai da kunnuwanta suka daina aiki na ɗan taƙin lokaci. "Lafiya mai ya faru da Jannah? Kuma mene ne haɗinsa da ita da zai su fita?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin ruɗani wanda ba ta san ta fito waje ba. Karaf sai a kunnin Hajiya Baaba, da har ta juya za ta wuce. "Miƙo mini wayar nufinta ba ta san za a yi auren ba ko me? Oh tsoron da yake mata ya sanya shi kasa gaya mata kenan, ai shikenan bari na hutashshe shi." Ta ce tare da karɓe wayar. "To isashshiya matar gwal! Waton tsoron ki da yake ji ya kasa gaya miki saura kwana biyu ya angwanje da yar'uwarsa Jannah." "Aure, Jannah kuma?" Ta furta cikin tsananin mamaki da ƙarfi. "Mamaki kike yi? Sai ki bari zuwa gobe ki tabbatar idan kin ga an kawo miki ita a gida..." "Haba Hajiya Baaba, wannan ba girmanki bane ki bari ya gaya mata don Allah kar ki ɓata lamarin." Cewar Ammy cikin tsananin ɓacin rai wacce tazo wucewa ta ji tana faɗa mata hakan. "Dallah, kauce ki ba ni guri in yana tsoronta kamar uwarsa ai shi ya sa na hutashshe sh..." "No!" Ta ce da ƙarfi tare da sakin wayar ta toshe kunnuwanta da hannunta jin muryar Ammy tana magana wanda ya tambatar mata tatsuniyar da take gaya mata gaskiya ne. "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Na ba ni na shiga uku Allah ka ɗauki raina na huta. Da gaske zauji zai yi aure ba tare da ya gaya mini ba, wannan ita ce maganar da yake sanar fa ni zai gaya mini. Ashe duk tsauri da jan ido da yake mata soyayya yake da ita a ɓoye? Yarinyar da na tsana fiye da mutuwata." Ta ce tare da nufar titi tana suratai tamkar wata mahaukaciya. "Wallahi haka ba zai taɓa yiwu ba, zan iya danne kishina ya auro ko wace mace amma ban da ita." Kamar wata zautacciya sai ta kuma dawo gurin da ta watsar da wayarta ta ɗauka wace har ta tsage tana neman numbar mahaifiyarta. "Ka cuce ni ka ci amanata Allah ya isa tsakanina da kai tun da har za ka iya haɗa baki da 'yan gidanku ka uri 'yar'uwarka ba tare da na sani ba, saboda mahaifiyarta tana fa kuɗi ko?" Ta yi tambayar kamar yana gabanta. Sai kuma ta dawo inda ta yar da wayar ta ɗauka kamar wata taɓaɓɓiya ta nemi numbar mahaifiyarta wacce ta ɗauki wayar ba tare da mata lokaci ba. "Mama, kin ji Ajmal zai yi aure kuma yar uwarsa wannan fitsararar?" Ta ce cikin tashin hankali tana kuka wanda hakan ya tada hankalin mahaifiyarta ta fara kiran sunanta. "Shi Ajmal ɗin? Yuashe kuma wace ƙanwarsa?"Ta jera mata tambayoyin cikin tsananin ruɗani. "Ba zan iya gaya miki ba domin ban san halin da nake ciki ba, sai dai ina jin rayuwata ta ƙare domin ba ta da amfani sam ban ga amfani samun girman da na yi ba, duba ga cin mutuncin da ya yi mini aure fa zai ƙara aurenmu ko shekara bai rufa ba." "Kina ina ne Mushirat, kin sauka don Allah ko natsu ki kaantar da hankali." "Ajmal ka cuce ni saninka bai yi maka amfani ba rayuwatavta ƙare mama, ki turo Ya Najib ya zo ya ɗauke ni ina tasha ba zan iya tarar abin hawa ba, dama mun yi da shi zai zo ya ɗauke ni amma ya tafi kai ta asibiti." Ta ce ba tare da ta lura titi take nufa tana maganar ba sai kawai ta ji ana faɗin "Ke!Ke!!." Wanda ya sa ta yi sauri ta waigawa tare da ɗora hannu a sama ganin ƙatuwar mota ta tunkarota gadan-gadan. Mom tafiya mai nisa suka yi sannan suka isa ƙauyen. Ɗaukar matar da jarirai suka yi wanda kai tsaye asibiti suka wuce ganin yadda suke cikin mawuyacin hali. Bayan an duba matar da ɗaura mata jini sannan ta biya tare da bada maƙudan kuɗi da za su kula da kansu. Saboda tafiyar da za su yi ba ta wani jima ba suka kama hanyar Zariya. Sun ɗan yi tafiya mai nisa suna tafe suna hira da Mujee. "Inyaa!Inyaa!! Inyaaa." Suka ji kikan jarirai a cikin bayan motarsu wanda ya sanya suka saki salati tare da waigawa. "Innalillahi! Mun shiga uku. Jariran 'ya'yan aljanu muka ɗauko a bayar motar?" Mom ta tambaya cikin tsananin tsoro da tashin hankali. Da sauri direba ya gangara ya yi parking zuciyarsa cike da tsananin tsoro da mamakin yadda aka yi jarirai a cjkin motar, wanda ya tabbatar da 'ya'yan jarirai ne. Cirko-cirko suka yi sun kasa isa gurin boot ɗin motar ballantana su yi ƙoƙarin buɗewa sai zare ido suke yi. Direba ne ya yi namijin ƙoƙari ya ƙarasa jikinsa na kyarma ya buɗe boot ɗin tare da rintse idanunsa kar ya ga aljanu, wanda tun yana yaro ya san cewar duk wanda ya ga aljani kwanan shi ya ƙare. "What!" Mom ta furta cikin tsananin mamaki tana kallon yaran da suke cikin kwali suna canyara kuka. "Mujee, this is absolutely impossible! Waɗannan ba yaran da muka kai wa mahaifiyarsu taimako ba ne." "Mun shiga uku, wallahi sune garin ya akai suka shigo cikin motar nan." Mom da gumi ya jiƙata sharkaf ta share zufar zuciyarta saboda bugawa tamkar za ta sinke, domin ta gane sharri za a ƙulla mata. "Someone is behind this Mujee, sharrin maƙiya ne, kuma da makusancina a ciki. Shikenan, rayuwata ta ƙare na shiga uku." "Tabbas sharrin abokan takara ne Hale.." "A'a duk wanda ga aikata wannan ya san da duk motsina na jikina n..." Ajmal kuwa, suna isa cikin asibitin ya fahimci ya manta da wayarsa wanda ya tabbata a falon Aby ya ciro ta domin ya yi chatt da Mushiirat. Da sauri ta ɓalle motar ta fito da sauri ganin ya fita burinsa ya rigata shiga karsu jera tare, wanda ta gane lagonshi ta haɗa da sauri ta isa gare shi tana kallonsa suna tafiya. Tamkar ya shaƙeta haka ya ji ga kunyar yadda mutane suke kallon shi duk da sun san 'yar'uwarsa. "A'a Ya sheshk, kai ne haka da yammar nan?" Cewar doctor Irfan yana kallon Jannah da ta shigo a bayansa. Ba bu wanda ta kalla a cikinsu ta samu guri ta zauna tare da fito da wayarta tana kallon tiktok duk matsanancin zazzaɓin dake damunta amma burinta ta ƙuntata masa. "Madam ce ba lafiya?" Ya tambaye sa ganin tun da ya ba shi hannu ya kasa ce masa komai domin zuciya ta tuƙo shi. Bai tanka masa ba haka Jannah ba ko kalli inda Irfan yake ba. Ganin haka ya ɗauko abin gwajinsa ya fara duba ta yana kallon yadda take kallonsu a wulaƙance. "Zazzaɓi ne mai zafi ya kamata kuma ta saka damuwa a ranta. Zan ba ta magani sannan za a yi mata allura guda biyu har na tsawon kwana uku." Wani irin zabura ta yi ta miƙe tare da ja baya domin idon akwai abin da ta tsana be wuce allura ba, don ba ta yi tunanin zai ce zai yi mata allura ba da ba ta zo ba. Murmushin mugunta ya kubce masa ganin ya gano lagwanta daidai lokacin da ta ce,"Kai mugu don't inject me, just give me meds." Ta ce tare da bayyana tsoronta a fili. "Ba ki da kunya ko? Irfan ka haɗa mata duka allurar, saboda ka san jibi ne bikinmu cin amarci ba zai bari muzo ba." Ya ce fuskarsa a murtuke wanda ya sanya ta daka tsalle ta miƙe tana mazurai. "Haba, sai ka ce ba ka san yadda ake allura, dole biyun ɗin za a yi mata inyaso na zo gida na arasa mata sauran." "Na rantse babu wanda ya isa ya yi mini allura sainka ce wacce ta zo a sume da ƙafafuna na zo ni na ma daina jin ciwon na warke." Dariya ta so ta kubce wa Irfan ganin yadda ta tsorace tana mazurai. Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093 KURA DA FATAR AKUYA *RUBUTAWA:-* *JAMILA LAWAL ZANGO* (JAMSY) *SADAUKARWA GA:-* *BADAMASI (AUTA)* FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?) Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka. *PAGE 37-38* *BOJUWA HERBAL'S* *KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA* *KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE* *GYARA GASKIYA NE SISTERS* *KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?* *KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN* *A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅 *080327733332* *KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*. *DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*. *NA GODE* *Contact* *Bojuwa HERBAL'S* *For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*. *08032773332 Whatsapp only.* BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM "Ba ke iskanci da taɓara ba, kin ciwon ƙarya kina ta zuba iskanci sun biye miki, zan yi maganinki." "Ma za Irfan haɗa ruwan allurar." Ya ce yana nannaɗe hannun rigarsa. "Wayyo na shiga uku! Dad zan kira na sanar masa don ba zan yarda a yi mini allurar ba." Ta ce tana ƙoƙarin kiran dad wanda ya wafce wayar ya aje kan kujera, ya sanya hannunsa ya damƙota da take ƙoƙarin ficewa da gudu. Wani irin ƙara ta canyawa wanda ya sanya har ya sake ta ya ƙara damƙota da hannunsa ɗaya yana toshe kunninsa tare da ɗaga hannunsa zai mareta. "Ba ki da hankali ne za ki ƙwala kamar mahaukaciya?"Ya ce cikin zafi da tsawa. "No, please karka duƙeta ka ka yi haƙuri, ka san akwai waɗanda suke tsoron allura. "Ƙyale ni Irfan in har ban duketa ba, ba zan ji daɗi ba. Za ayi mata allura kamar za a kasheta. Mushiirat da kanta take yi wa kanta allura, sai ita za ta zauna tana buɗe baki." "Mushiirat, babba ce ita kuwa wannan da ƙuruciya." Tsaki ya yi ya ƙara damƙota da ƙarfi sosai." Caka mata allurar sauri nake yi, in ta ƙi bari ka karya allurar a ciki." Wani irin ihu ta ƙara saki sosai take kuka duk ta cika ofis ɗin da ihu da ƙara. Lokacin da ya tsira mata allurar sai da ta yi wani irin ƙarar da ya fi wancan, wanda haushi ya sa ture ta ta faɗi ƙasa. "Abin da nake gudu kenan, a haɗa ka da yara suyi ta maka hauka. Jibi abin da take yi wannan haukar." "Walllahi Allah ya isa kuma saina gaya wa dad mugaye kawai." Ta ce cikin muryar kuka tana taɓa inda aka yi mata allurar. Da sauri ya ƙarasa guri ta zai ɗauke ta da mari." Haba, don Allah karka biye mata." "Ka na ji fa zaginmu take." "Ka kyaleta ku dubi yadda ta yi har cikin zuciyarta ba ta son allurar." "Allah ya sa ya zama ajalinta."Ya a ransa a fili kuwa ɗaukar wayarsa ya yi suka yi musabuha yana faɗin, "Bari na wuce matar kirki yau za ta dawo." "A masha Allah na ji ance ta samu ƙarin girma Allah ya sanya alhairi." "Ai da yake kwanyarta na ja don ni kaina ban yi tunanin za ta ci jarabawar ba." Ya ce cikin farinciki da murmushi ɗauke a fuskarsa. Haka suka fito suna tafe tana kuka wanda ko kallon inda take bai yi ba, wanda ya haɗa harda gudu ya shige motarsa ya tayar. Ganin haka taƙarasa da sauri ta shiga. Suna tafe tana kuka da jan majina yayin da take jin inda aka yi mara allura yana tsikarinta, wanda in har ba ta sa ƙanƙara ba sam ba za ta ji sauƙi ba. Da takaicin sawa da ya yi aka yi mata allura da zafin allurar suka ishe ta sai ta sanya ƙara ta ci gaba da kuka, wanda ya sanya cikin tsananin ɓacin rai ya gangara titi ya yi parking ɗin motar. "Ke fito daga cikin motar nan domin ba za ki kashe ni da takaici ba " Ya furta cikin ɓacin rai yana watsa mata mugun kallo. "Ba zan fito ba kuma na rantse ka yi ka maida ni gida in ba haka ba sai na ta kwarara maka ihu ince sato ni." "Ok, haka kika ce? To Allah ya ba ki sa a ki fara tun kafin na fasa miki bakin ihun." Ga mamakinsa sai ya ga ta sa fuskarta a saman kujerarsa tana goge ruwan hawayen da ya ƙi tsawa, sai kuma ta fyato majina ta goge, wanda ya sa ya ji tamkar zai yi amai yana kallonta cikin ƙyanƙyani. "Ƙazamiyar banza fito mini daga mota na rantse sai dai ki nemi abin hawa." Ya ce tare da finciko ta ya direta a waje ya shige motarsa. Kuka sosai ta ƙara saki har da su birgima a ƙasa wanda ya ji kamar ya shaƙeta ya mutu motarsa ya shiga ya tada tare da fara tafiya, sai kuna ya tsaya ya leƙo yna faɗin, "Ba na gaya miki ki san yadda za ki yi ki kar ki aure ni ba, amma kin kasa haka to bari kiji na gaya miki, na rantse sai kin gwammace zaman gidan kurkuku fiye da zama a cikin gidana, domin ina zaman lafiya da matata ba ki isa ki rage mana jin daɗi ba." Ya ce yana watsa mata mugun kallo. "Dube ki wata kucaka, ƙazamiya wawiya da ke. Gabakiɗaya ke ko ta ina naƙasa ce a jikinki. Mace babu addini babu tarbiya sannan jikinta kamar an ɗaura wa taɓarya zani gabakiɗaya babu shape kamar sanda haka kike. Tir mai zan yi dake bayan ga mace wacce ta masa sunanta mace take da komai na nake so." Sai ya tofar da miyau yana faɗin, "Ina miki albishirin aurena wanda za ki gwammace gara a kaiki ramin macizai ki rinƙa kwana da su, domin sai na mai da rayuwarki wulaƙantacciya. Dukan safe daban na yamma daban. Kuma sai na sanya rayuwarki ta gimshe ki. Domin zan zamo macijin da zan rinƙa sarar naman jikin ki a kullum, don haka ki aje rashin kunyarki da fitsararki ba yanzu za ki yi mini su ba, domin wataƙila su yi miki amfani a lokacin da babu mai ceton ki a gidana. Marin da kika sa aka yi mini kullum shine zai zama sallama da daddare a tsakaninmu." Ya ƙarashe maganar yana kallonta ganin yadda take mishi wulaƙantaccem kallo kamar ta ga kashi, kuma ko kaɗan kalamansa ba ta nuna sun firgita ta ko sun nuna ta ɗan tsorata ba. "Wayyo Allahna! Ka ce zamu mai da gidanka gidan dabbe da tashin hankali da rikici. Sanin kanka ni ni ɗin ba kanwar lasa ba ce domin hatta wacce ta haɗa auren ba ta bani tsoro ballantana kai. Ka dai na tunanin wannan ɗinbegegen jikin na ka zai sanya na ji tsoronka. Ka ji na rantse a rayuwarka sai na zame muku ƙadangaren bakin tulu! Ruwa sai kun gagara kurɓa a gidan nan. A yadda kake kallona kamar wata fensir "KURA CE NI DA FATAR AKUYA." Domin ina cire fatar akuya rikiɗa harda na wacce ta haɗa auren. Yaga-yaga da namarku na cinye tas kuma na zauna lafiya. Matar da kake kira ta so ko? Watarana sai ta zame maka matar ƙi, domin sai na shafa mata baƙin tabon da kashin kajin da za ka ji ka tsaneta. Bayan na lalata rayuwar zaman auren ku sai na je na auri masoyina ɗan gata mai kyau a tashen kuruciya ba irin ka ba. Wannan abin da zan yi maka sakayya ce ma mayar da ni ƙaramar bazawara da ka yi." "Ok haka kika ce mu zuba shege ka fasa." Ya ce yana mamakin tsaurin idanunta da fitsararta ko da yake bai kamata ya yi mamaki ba domin waɗanda suka kawo ta duniya ba ta shakkarsu. Don haka ya figi motarsa ya tafi ya barta a gurin. Jannah kuwa ba ta matsa ba ta ci gaba da ihu tana kiran sunan dad, domin so take ta kashe shi da baƙinciki gane yadda ya ke ƙuluwa, in ta yi mishi abu kasancewarsa ba ya iya ɓoye baƙinciki. A ranta ta ɗauki aniyar tun da yake kiranta da yarinya, wacce ba ta da abin da zai kalla ƙwaila ita kuma sai ta kashe shi da baƙincikin, abin yarintar da za ta rinƙa masa don sai ta mai da kanta tamkar 'yar wata bakwai. Har ya yi nisa sai kuma ta ga ya fara dawowa da baya har ya ƙaraso gurin ta, sakamakon kirar Aby da ya yi masa kan ya yi sauri ya ga sun daɗe. "Ki zo ki shiga motar nan tun kafin na fito na canza miki kamanni, kuma wallahi ba ki isa ki shi ga baya ba, domin na fi ƙarfin zama direbanki." "Ba zan shiga ba kuma na rantse yau Allah kawai zai ce ce ka kan sharrin da zan yi maka mugu kawai." Ta ce tana ƙoƙarin tarar adaidaita ta hanyar tsayar da shi. Da takaici ya kwashe shi ganin ta tsayar tana ƙoƙarin shiga cikwikwiyeta ya yi ya tura a gaban motar ya kulle tare da zagayawa ta gefen direba ya shiga, ba tare da ya damu da ihun da take yi ba tana neman taimako ɓarawo ne. "Kai malam, lafiy kar.." Direban adaidaitar ya faɗi daidai lokacin da ya buga ƙofar da ƙarfi ya ja motar. Wani irin burki ya ja wanda ya yi ƙara ƙiiiiiy. "Ke na rantse ki kiyaye ni da wanan ihun don za ki iya sawa na zubar damu sam bana son iihu wawiya kawai." "Ba zan dena ba har sai ka saukar da ni kuma in ka zubar damu sai me ai wallahi da aurenka gara na mutu na je lahira, kuma Allah sai ya saka mini na raba ni da masoyina da ka yi." Ajmal da zuciya ta ciyo shi domin tun yana yaro ya tsani kuka da ihu yanzu zai rikice ya fita hankalinsa. "Tun da haka kika ce kuma ƙin ƙi yin shiru bari na watsar damu kin ga duk mu mutu mu huta." Ya ce don ta yi shiru ya fara tagal-tagal da motar, amma sai ya ga ko gezau ta kalle shi ta yi dariyar takaici tace, "Sai me don na mutu, wasiya kawai zan rubutawa masoyina na neman yafiya, amma bayan wannan ba ni buƙatar komai sai mutuwa." "Au haka kika ce yau ni kuma zan nuna miki ƙaryar fitsara." Ya ce tare da sakin sitiyarin sai motar ta yi kamar za ta kife sai kuma ya riƙe. "Na ka wasa ne bari na nuna maka na fi ka son mutuwa." Ta ce tare da saka hannunta iya ƙarfinta ta riƙe shi ta hana shi tuƙin wanda ya sanya iya ƙarfinsa ganin aika aikar da take yi, amma ina ta yi nisa ba ta jin kira don har sai da ya buga kanta da murfin ƙofar ta ƙi saki wanda kafin ya yi wani ƙoƙarin tsayawa ko wanin abun motar ta yi taga-taga da su ta kife, wanda Jannah da fari ko gezau kuka take tana tuna Huzaifah sai ta ke jin ta rasa komai na jin daɗin duniya domin shine ya yi alƙawarin kulawa da rayuwarta ya ba ta duk wani farincikin da iyayenta suka gaza zai zama tamkar mom ya kuma ninka soyayyar da dad yake mata. Amma sai dai kash! Wannan baƙin auren da Hajiya Baaba, ta maƙala mata ya zama cikas da zamowa shamaki a tsakaninsu. Yua ga Huzaifah yana can kwance mutu kwakwi rai kwakai, ba ta da abin da za ta yi ta ceci rayuwarsa, wanda ya sanya ta ƙudiri gara ta mutu da zama da baƙin kumurcin da ta tsana fiye da komai a rayuwarta, domin shine mutum da ya fara mata dukan da iyayenta ba su taɓa mata ba, ya takurawa rayuwarta tare da daƙile duk wani farinkici da na rayuwarta don haka ta gwammace gara mutuwarta. Tunaninta ya katse daidai lokacin da ta ga mutuwa a zahiri raɗaɗin zabarta da tashin hankali da firgici har ma da alhinin da ke cikinta ya sanya ta tsananin razana wanda ya sa ta ƙwarma uban ihu numfashinta ɗauke. Mom ta shiga cikin tsananin tashin hankali! Ji ta yi numfashi na neman gagararta. Ta rintse idanunta tana son gano wanda ya shirya mata wannan tungun, amma mizanin hankalinta ya gaza aiki. Sai ta fara wilƙita ido cikin rashin dubara tana ji tamkar ta yi hauka. "Na shiga uku Allah ka kawo mini ɗauki ka fitar da ni daga cikin wannan sharrin da ake so a ƙulla mini." Ta furta tana share zufan jikinta daidai lokacin da wayarta ta ɗauki ruri, wanda ya ƙara dugunzuma sauran natsuwar da ke jikinta. Ƙarar shigowar wayar ya sa ta yi ma ta maza ta ɗauka, yayin da zuciyarta ta buga da ƙarfi har sai da ta dafa motar, domin a tunaninta anonymous ne ya kira ta gabin sabuwar numba, wanda kamar ba za ta ɗauka ba saboda zuciyarta ya gaya mata ba alkhairi za ta ji ba, amma sai ta ga numbar Jannah, wanda ya sa kan dole ta ɗauka. "Hello muna magana da makusantar me wannan wayar ne?" "Eh ina daga cikin makusantarta domin ni ɗin mahaifiyarta c." Kafin ta ƙarashe maganar ya ci gaba da cewa,"Ok, muna buƙatar kizo da gaggawa domin sun samu accident ita da wani namiji, a daidai 'yan goro yanzu haka an saka su a ambulance za a kai su asibitin koyarwa na shik..." "Innalilahi wa inna ilaihir raju'un." Cewar mom tare da ɗora hannu a ka, wanda ya sanya Mujee, ƙarasowa gurin ta da sauri ta kamata tana faɗin, "Lafiya Halee, mai ya faru." "Jannah sun yi hatsari da Ajmal a hanyarsu ta dawowa daga asibiti suna asibitin shika." Sai ta rushe da kuka tare da durƙushewa a ƙasa ta ci gaba daɗin, "Wane irin musiba yake shirin faruwa da ni? Ba zan iya rayuwa babu ke ba Jannah, domin saboda ke nake samun ƙarfin zama a cikin duniyar da sam bana jin daɗinta. "Subuhanallahi! Yanzu ya za mu yi don dole mu kama hanyar Zariya, kuma waɗannan jarirai fa." "Bari na kira 'yan sanda na yi musu reporting sai na barku a..." Sai ta kasa ƙarasa maganar tana kallon motar 'yan sandar da suka tinkarosu suna jiniya. "Kamar 'yan sanda nake gani, wucewa za su yi ko gaya musu akai akwai jariran a cikin motarmu." Mujee ta furta cikin tsananin firgici tana ɓoye wa a bayan mom da ta sandare ta kasa magana saboda mamaki wanda take ta gana makirci aka haɗa mata. Ba tare da ta ce komai ba ta zuba musu ido har suka ƙaraso suka fito daga cikin motar da bindigu. "Kece Hajiya Halima ko? An sanar mana da kina fakewa da taimako kina sace 'ya'yan mutane don kiyi tsafi da su kici zaɓe." Ido Mujee ta zaro jin abin da ya faɗi. "No, ba halinta bane domin zuciyarta tsarkakarka ce, saboda Allah take yi ba don siyasa ba." Ta ce tana zare ido bayan ta rufe boot ɗin motar. "Ok, tun da kin ce haka bari mu duba boot ɗin in bmu gani ba sai mu yarda." Kare boot ɗin ta yi tana faɗin,"I said there is nothing in ku.." "Matsa Mujee, let them see akwai, amma wallahi ba satarsu na yi ba, kuma ba ni da masaniyar yadda akai suka shiga ciki. Makirci ne kawai na maƙiya." Ta ce cikin muryar kuka tare da ƙarasawa gurin motar ta buɗe. "Rufe mini baki! Dama irinku haka kuke 'yan siyasa ku rinƙa fakewa da taimakon al'umma bayan da jininsu kuke kuɗi." Ya ce tare da ciro ankwa. "You are under arest!" Ya faɗa yana nuna mata ankwa wanda ya sa ta yi mutuwa tsaye, sai kuma ta saka kuka tana faɗin, "Don Allah, ku sake ni 'yata ɗaya kwance na mallaka tana asibiti ta yi hatsari kar ta mutu ban gan ta ba. Akwai rashin fahimta a tsakaninmu in dai banje ba lamarin zai zafafa." "Shout up kin san daɗin 'ya'ya amma kike yin kuɗi da 'ya'yan mutane don ki yi kuɗi da suna." Ya ce cikin zafi tare da fara tafiya za su sanya ta a mota. "Wayyo Allah wai da gaske kamata za ku yi? Don Allah ku saketa wallahi bamu da masaniyar yadda aka yi suka shiga cikin motar. Ni sheda ce akan hakan, Halima mutuniyar kirki ce. Siyasarta tsarkakarka ce." Mujee ta faɗi tana riƙe mom da wata mace ta sanya mata ankwa. Har sun fara tafiya Mujee na kuka tana roƙonsu amma ba su kula ba. "Na shiga uku! I dan Jannah na raye ta farka ba ta ganni ba za ta ƙara nisanta kanta da ni. Mujee, don Allah ki tafi Zariya ki je ki ganin mini ita, domin in har ta mutu ni ma mutuwa zan yi." Ta furta cikin matsanancin kuka a ranta tana tunanin wanda ya ƙulla mata wannan makircin yayin da zuciyarta take sanar mata da makusancinta ne wanda ya san duk motsinta yake tare da ita. "Waye wannan kura da fatar akuyar?" Ta furta cikin tsananin tashin hankali, daidi lokacin da motar ta tashi tana kallon Mujee, da direba da suke kallonta suna kuka cikin tashin hankali. "Oya maza kuma muje police station ɗin da ku a wancan motar don kuma sai mun bincike ku." Ɗada daga cikin Police ɗin ya furta tare da tasa ƙeyarsu. Mom na ji na gani tamkar wacce ta yi kisa aka garƙame da ankwa. Wani irin tuƙuƙi ya turniƙeta. Kukan da take yi ta nemi hawayen ta rasa sai ta fara ajiyar zuciya mai ƙarfi wanda yake barazanar tafiya da numfashinta. "Ni kuma shikenan, ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba?"Ta tambayi kanta cikin tsananin baƙinciki tana jin tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu, yayin da lokaci guda abubuwa da dama waɗanda suka faru suka fara dawo mata a ƙwanyarta tare da mayar mata da abubuwan tamkar lokacin ya faru wanda ya sa ta rinƙe idanunta ta fashe da kukan da ta yi nasarar yin shi tana jin rayuwarta ta zo ƙarshe. Kash! Masu karatu anan na kawo ƙarshen book one na littafin "KURA DA FATAR AKUYA." Sai mun haɗu a kashi na biyu akan kuɗi naira 500 kacal in kuma aka gama 600 a account number nan 8144072423 Jamila Muhammed Lawal Opay. Masu tura katin waya sai ku turo ta nan:07072971093. Ƴan Nigar kuma za su tura ta nan:7 74007457 Isma'il Nita. Littafin ya fi na farkon haɗuwa domin yana ɗauke da tarin tambayoyin amsarku masu karatu kamar haka: Shin wane ne wanda ya zamo "Kura da fatar akuya" Yake kai hari ga rayuwar taurarumarmu kuma uwa ba da mama? Mai dad ya yi wa mom wanda ta kasa mantawa kuma ta gudu ta bar ƙasarta? Shin Jannah ta yi nasarar kashe su domin hutawa da auren? In har suna raye wane irin zama za a yi na aure da Jannah da ba ta gama fahimtar kanta ba ballaantana ta gane aure? Shin Huzaifah zai hakura da soyayarta, ya ya halin da yake ciki? Ya za ta yi ta samu soyayyar Ajmal da yake da matar da yake ji bayan ita duk sauran matan sun rako ta duniya ne, saboda hankali da biyayya da kissa da kisisina? Wane hali Mushiirat take ciki na afakawa titi saboda jin aurensa? Ina kham; mijin Mujee, wace duniyar ya shige ya yi ɓatan damo? Shin Hajiya Baaba, ko za ta janye ƙudirinta na ɗaukar fansa kan iyayen da 'ya'yan ta haƙura da auren ganin in suna raye? Duk tarin amsoshinku yana cikin littafin na biyu ku daure ku biya kar ku bari a baku labari. 'Yar'uwa in kika daure kika biya sai ki karanta hankalinki kwance babu damuwar kin karanta ba tare da kin biya ba.Sai mun haɗu a littafin na biyu. Taku Jamila Lawal Zango (Jamsy) Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy). FOR WHATSAPP: 08144072423 CALL: 07072971093