Sanadin Boko 1 01 Posted by Mukhtar Ismail Muhammad On www.arewarulers.com.ng Under: SANADIN BOKO Na Maryam Abdullah K.Mashi Ina sauraren duk hirar da kowaccen su ke yi, motar ta kacame da surutu. Wasu na murnar ganin Iyayensu, wasu kuma suna zancen auren su. Mafi yawa daga ciki kuma suna fadin makarantun da za su ci gaba, wasu su ce poly wasu Jami'a, wasu Nursing school. Sa'adatu da ke kusa da ni ta ce, "Hafsy don Allah kema ki shigo (A.B.U Zariya) mu hadu mana." Nayi dan murmushin takaici. "Samun (A.B.U) fa ba kamar shiga Bakori ba ne, saboda in ma zan samun bani da wani tabbas akan za a barni." Ta zaro ido. "Kada kice min kina cikin wadanda za'a dakile a kai gidan miji? Na sake ajiyar zuciya. "Ke dai Sa'a taya ni da addu'a, Allah Yasa ina da rabo, dan kuwa ina son in ga karshen boko." Jamila ta dube ni, "Hafsy ko yaushe kina bani mamaki in kina cewa za ki ga karshen boko. To bari kiji, sai dai boko yaga karshen ki. Ance miki wannan lokacin yana jira ne? Na ce, "To Malama, ban saka bakin ki ba, ina ruwanki. Ke ba kince aure ba?" Jamila ta ce, "Aure kuwa insha Allahu ba ya hana karatu, zan yi aurena na ci gaba da karatuna. Sa'a ta ce, "Wahala ai daya za ki zaba, don da kin yi ciki za ki watsar da batun karatu. Na ce, "Dubu nawa akayi? Ai ni boko yanzu muka sa dan ba." Ta ce, "Shikenan, Allah Ya taimaki kowa kan niyyarshi ta aikhairi". Na ce, "Ga magana da za ki yi kawai, Amin". Da tafiya tayi tafiya, sai ka ji kowa shiru. Ni kam fargabar Babana nake yi, nasan inba wani ikon Allah ba, da wuya naje wata Makarantar. An sauke *yan zariya, sannan mu *yan Kaduna muka nausa hanya, motar makaranta da ke Bakori Katsina, ita ce ta debo mu zuwa gidajenmu, bayan mun yi bankwana da makarantar wato mun kammala. Gidanmu ya kaure da sowa, yara na ta murna "Ga Hafsat ga Hafsat". Innarmu ta fito da gudu ta rungume ni, ina ta dariya. Almajiran da suka dauko min kaya suka sauke, na ce, "Innarmu ba su hamsin". Ta kwance habar zani ta mika musu. Yaran gida suka taya ni da kaya zuwa cikin daki, matan gidanmu kowa sai sannu da zuwa suke min ina amsawa. Inna ta aje min kwano tare da cewa, "Alalar har ta huce". Ta dire min kofin ruwa na ce, "Har yanzu bata kare ba ne?" Ta ce, "Ta kare mana, ai tun kwanaki da Kawunku Bako yazo ya ce min cikin kwanakin nan za ku kammala, kullum sai na aje alalar sai dai in naga magariba tayi ne sannan in ba yara. Nayi dariya tare da cewa, "Innarmu kenan! Ina Yaya Ummar?" Ta ce, "Tun safe bai dawo ba, kin san nasai mashin da aka yi mana rabon gadon nan, Kawun ku Bako na kawo min kudin na ce a sai mishi mashin wannan yaran, tunda zaman banza yake, aikin gyaran wutar nan ba ko yaushe ake samu ba. Ina fama da kannan shi ina fama da shi. Na ce, "Kinyi dabara Innarmu, in yayi Achabar sai a rufa asiri". Ta ce "Kwarai kuwa. Ummi ta zo ta zauna kusa da ni, na ce "Ummi da ba ina ta kiranki kin ki zuwa ba? Inna ta ce, "Kullum sai ta ce Innarmu ina Auntyna?" Na rungumota a jikina ina cewa, "Gani na dawo". Ta rufe fuskarta, ita dole taji kunya. Cin alalata nake ina jin dadi ga ni ga Innata, ta ce "Kin zo a daidai bikin su Hajara da Sakina ya kusa". Na rike baki, "Inna har da Sakina?" Ta ce, "Eh! Na ce, "Uhm! Ni da so samu ne in ci gaba da karatuna ma". Innarmu ta ce, "Malam ne matsala, amma ko Nas din nan da 'ya'yan Kawunki suke yi ai zan so kiyi." Na ce, "Wane Nurse? Ni fa Jami'a nake so, burina in zama 'yar Media". Ta ce, "Me kenan? Na kafa kofin ruwa na daddaka, sannan na ajiye tare da cewa, " 'yar jarida mana! Sai dai matsalar kudi ne". Kai lomar alala da nayi baki, ta zo daidai da sallamar Baba, nan take naji wani daci tamkar na tauna madaci. Innarmu ta mishi sannu da shigowa, tare da shimfida mishi tabarma. Cikin fargaba na soma gaida shi, ga mamakina yau fuskar shi sake ya amsa, har da ce min "An dawo lafiya?" Na ce, "Lafiya lau". Innarmu ta ce, "Allah cikin ikonSa Malam yau dai su Hafsat karatun Sakandire ya kammala." Ya ce, "To dama tunda da mai sonta sai ta yi masa magana ya fito in hada su da Sakina in huta". Inna ta ce, "Anya kuwa? Ina ga daurewa da zaka sake yi ta tafi makarantar gaba da..." Wani kallo da ya mata shi ne ya dakatar da ita. Ya mike tsaye ransa a bace. "Na gaji da wasa da hankalina da ku ke yi, ba zan iya ganin Hafsa gandandan cikin gidan nan ba, duk wanda ya shigo ba zai bambance ta da matan gida ba, duk wata tana zubar da jini, ta zama Uwar mata. Wannan karon zamu yi tsiya da ku yanda bakwa zato. Wai menene cikin wannan bokon da ku ka nace mawa? Ina ce karatun gidan duniya ne?" Inna ta kufulo itama, ta ce, "To dama ka saba ka min tijara cikin gida gaban kowa akan Hafsa, tun da babu sisinka kasa ido, kuma karatu ba fashi. Ya ce, "To zan ga wanda ke auren wani, tsakanin ni da ke". Ya fita. Na dago ido da hawaye, takaicina ace kullum Iyayena basa rigima sai a kaina, bari Munnir yazo anjima, zan ce masa kawai ya turo manyansa ayi magana, ko ina dakin nasa zanyi karatuna. Ban dai fadi ma Innarmu kudurina ba. Na mike ina tattara kwanukan gabana, Inna kuma sai mita take, na ce "Innarmu ki bar batun haka, kinsan gidan nan da gulma, yanzu kowa ya baza kunnuwa yana sauraro". Ta ce, "Suyi ta sauraro din, ina ruwana. Iyaka dai mace tayi da ni naji mu kwashi 'yan kallo ni da ita". Na idar da sallar isha'i, ina zaune a gurin ina istigfari, wani yaron gidanmu yayi sallama, bai jira amsa ba ya ce "Innarsu Ummi wai ana kiran Hafsa a waje". Ta ce, "To". Na mike, nasan Munnir ne, don na aika masa da letter cewa na dawo. Na bude jakata na ciro turarena forever na fesa, sannan na sabi gyalena na fita. Tun kafin na karaso na jiyo kamshin turarensa. Yana zaune saman motarsa kirar (Toyota camry), baka wuluk, sanye yake da wando jean baki, rigarsa fara. Cikin farin ciki na isa gabansa, nayi masa sallama ya dago da kanshi daga wayar da ke hannunsa yana latsawa. "Babyna". Sunan da yake kirana kenan. Na ce, Na'am". Ya diro "Zo muje cikin mota." Na ce, "A'a mu zauna can". Na nuna mishi dakalin kofar gidanmu. Ya dan gyara tsaiwa, "Kin ce fa baki son Baba ya dinga ganina da kananan kaya, kin san dai in muna can zai ganni dole ko?" Na dan yi jim ina nazari. Hakika Baba na fada cewa Munnir ba dan mutunci ba ne, ya gane haka ne tun daga suturar da yake sakawa. Amma bana son shiga motarsa saboda ya cika son taba jikina.. Ya katsemin tunani da cewa. "Zo muje, na zo da muhimmiyar magana". Na ce masa, "Nima ina da nawa muhimmin zancen". Baya ya bude ya shiga, nima na shiga dayan gefen, sai dai ban rufe ba. Ya ce "Rufo kofar mana". Na ce, "Ka barshi haka ma ya yi. Ya kunna wutar motar, haske ya bayyana, ni da shi muka kalli juna cikin ido. Nayi saurin janye nawa idanun, domin wani abu da na ji yana bin jijiyoyin jikina. Ya ce, "Ina sonki Hafsy, ban san irin son da nake miki ba." Ya kama hannuna na kwace, tare da mai da su baya na ce, "Don Allah Munnir ka daina son taba jikina, haramunne fa". Ya ce, "Zamu fara ko? Haba Hafsy, ni ne fa zan aure ki. Ko yaushe ina son in gwada miki so sai ki yi ta ki, yaya ki ke yi tamkar wacce bata je makaranta ba? Sai ka ce ba *yar boko ba? Ni fa kullum ina fada miki ba zan auri mata muje kina min wani kunshe-kunshen jiki ba. Na bata rai, ya shafi kumatuna. "Small beby, dan yi murmushi. Ba kya yin kyau in kin daure fuska". Shikenan, ban san lokacin da murmushin ya subuce min ba, matsalar ina mutuwar son Munnir. Ya ce, "To fada min maganar kafin kiji tawa, don tawa in kinji saikin bani goron albishir. Na ce, "To ni dai dama ina son ne in ce maka ya dace yanzun muyi aure, don wallahi da kyar Baba ya bari na gama karatun nan. Sam shi ba ruwan shi da da boko, ka dai sani". Ya ce, "Haba Baby, aure fa ki ka ce? Kin manta alkawarin da muka yi ni da ke?" Na ce, "Ban manta ba". Ya ce, "To ki kyale fadan Baba kawai, ba nine ke biyan komai na karatunki ba? Come on aje wannan topic din. Na shirya miki gagarumin party ne saboda murnar gama karatunki, don haka yaushe zamu je kasuwa musai kayan sawa? Takaici ya cika ni, don haka ban tanka ba. Ya sake matsowa in banyi magana ba nasan zai iya cewa zai rungume ni. Da sauri na ce, "Duk lokacin da ka shirya". Ya ce, "Gobe yayi? Dan ranar sati ne party din." Na ce, "Um". Ya ce, "Wai ba ki murna ne angel dina? Kada ki damu, kwanan nan za ki zana (JAMB), sai kin zama *yar media insha Allah. Na dube shi, "Yanzu sai zuwa yaushe zamu yi aure?" Ya ce, "Mun kusa, ai shekara hudu ya rage min na hada master dina, before time din kin zama *yar media ko? Nayi shiru. Ya sake matsowa har muna jin numfashin juna, bakinshi daidai kunnena ya ce, "Kin san ina son aure nima tuntuni damuwa daya Dad dinmu shi ne yaki. Yayyena guda uku suna nan harda mace, kin sani dai ya ce duk sai sunyi master sun fara aiki balle ni. Na ce, "To sai yanda Innarmu ta ce". Ya ce, "Bana jin Inna, zata yarda". Ya sake yin kasa da murya "In dan yi kissing din kunnenki?" Naja baya tare da cwa, "A'a". Ya ce, "To bari na tafi". Yana magana yana kallon agogon hannunshi, "Zan kalli wasan Arsenal yau." Na ce, "Kai kam har yanzu kana nan da kallon kwallon nan." Ya ce, "Kema za ki koya in kinzo gidanmu". Nayi dan murmushi. Ina son Munnir, shi yasa zan jure na jira shi, amma Allah Ya sani ina son aure, don ina zaton ina cikin mata masu bukata.... Ya katse tunanina da cewa, "Ko kada in tafi ne?" na ce, "A'a kaje sai gobe". Ya ce, "Shikenan." Ya miko min wata farar leda. ""Gashi kisha, ice cream ne da fresh milk." Na ce na gode, amma don Allah ka daina yimin irin wannan dawainiyar. Innarmu ta dubi ledar bayan na ciro kayan ciki, ashe har da kayan tea. Ta ce, "Kai yaron nan baya gajiya da dawainiya. Ni da zai fito ayi auren nan tunda yana zon karatun kyayi can a dakin shi. "Inna nayi mishi wannan zancen ya ce min in kara hakuri." Kamar na fadawa Inna zancen party din gobe, sai na fasa don nayi imani ba zata barni ba, duk da tana son abinda nike so. Yau Baba dakinmu yake, don haka dakin Babah kishiyar Innarmu zamu kwana. Ina kwance kan yaloluwar katifata mu da Sakina, can kasa sauran kannena da aka musu shimfida. Ko wannan cakudin na daga cikin abin da yasa nake son in ganni a dakin kaina. Washe gari tun safe muka soma aikin alalar siyarwa da Innarmu ke yi. Misalin uku saura Nazifi ya shigo yana cewa, "Hafsa ga saurayinki a waje. Ko da bai ce na kira ki ba, nasan gurin ki ya zo. Dama tuni nayi wankana, ina sanye da riga da siket na atamfar (Java), gyale na sura na ce "Inna Munnir na kirana." Ta ce, "To." Na nufi waje kai tsaye. Yana sanye da kananan kaya kamar ko yaushe, ina isa ya budemin gaban motar na shiga, sannan shima ya shigo. Na gaida shi ya amsa tare da yiwa motar key, na ce, "Muyi sauri ban ce zamu fita ba." Ya ce, "To". Wani (Boutique) muka je, duk tsinannun kaya ne a gurin, shi dai ya zabi nashi, amma ni nace ban ga wanda ya yi min ba. Nan ya shiga jidar min, na bata rai tare da nuna mishi sunyi yawa. Ya ce, "To zabi wanda ki ke so." Na daga duka babu na arziki, siraran wanduna ne da *yan riguna, sai doguwar riga wadda in nasa da kyar zata wuce gwiwata. Na aje su gefe, na dube shi. "Duk ba su yi min ba". Ya bata rai sosai, "Tashi muje". Na kafa mishi ido. Ya ce, "Tashi mana". Cikin daga sauti na ce, "To, to naji zan amsa, amma ni na gane kamar zasu yimin kadan." Ya dan sassauto "Muje gidanmu ki gwada." Da sauri nace, "A'a zasu yi min." Yayi murmushi, sannan muka je ya biya muka shiga motarshi. Ya ce, "Muje mu dan sha Ice cream". Na ce, "A'a kai ni gida, Innarmu bata san na fita ba, kuma nasan zata sa a leka ni, fada kuma zata yi min". Ya ce, "To naji sarkin tsoro, ke dai kawai kina tsoro ne kada na cinye ki." Gabana yayi muguwar faduwa ganin Baba zaune a dakalin kofar gidanmu, na ce na shiga uku, ga Babana, ya ce "To menene? Ina jin mamakin ki wallahi. Shi yasa Dad din mu yake matukar burge ni, baya takura mana, shi dai in dai zamuyi karatun boko to duk abin da muka ga dama muyi. Kuma zai kashe mana the last kudin shi don muyi karatu. Na ce, "Uhm, don Allah ka tafi da kayan, na karba, amma ka fito ku gaisa. Tare muka fito daga motar, jikina har bari yake. Na nufi cikin gida, Munnir yayi gurinshi. Ina isa Inna ta ce, "Daga ina ki ke Malam ya shigo yana ta fada yaga lokacin da ki ka shiga mota? Na ce, "Um asibiti muka je dubo kanwarshi". Ta ce, "Shi ne ba za ki fada ba? Kin san fadan Malam, don Allah ki rufamin asiri kada ki ja min surutu sanadin bokon nan." Na ce, "Kiyi hakuri Inna." Ina rufe baki Babanmu yana shigowa, tun kafin ya karaso na jiyo muryarshi yana cewa. "Na fada maka kenan, in da gaske ka ke yi ka turo min manyanka. Shekara nawa ina ganinka a kofar gidan nan wai ku *yan boko, zaku ce min sai kun gama boko, to ban laminci wannan ba." Hanyar uwar daka nayi, don nasan yanzun ya make ni, ya ce "Ke *yar boko kinbi saurayi kasuwa ko? Inna ta ce, "A'a Malam asibiti fa suka je." Ya zaburo tamkar zai kai ma Inna duka, ya ce, "In ji wa? Wa ya fada miki?" Inna ta ce, "Ga ta nan." Ya ce, "Makaryaciya, to shi abokin yawon nata ya ce min daga kasuwa suke, duk ya rasa wanda zai ce ya raka shi kasuwa sai ke?" Inna ta tsare ni da ido, "Kasuwa Hafsa?" Nace, "Kuyi hakuri, ba zan kara zuwa ba." Tayi kwafa tare da ci gaba da yin aikinta. Baba ya ce "To wallahi ba zan yarda da gantali ba, wai ku *yan boko." Inna ta dube ni, "Ai gara ki saka min da haka. Tunda ni na jajirce ki samu karatun boko." Na ce, "Don Allah Innarmu kiyi hakuri, wallahi ba zan sake ba". Ta ce, "To me yasa ki ka min karya? Kin san dai na tsani a min karya, duk abin da ya faru nafi son gaskiya ko?" Na ce, "Na sani. Haka nayi ta bata hakuri, kun san Uwa, nan da nan ta sauka. Ta min fadan cewa kada na sake yarda na bi saurayi wani guri. Kwana daya, biyu ban ji daga Munnir ba, lallai Babane ya kore shi letter na rubuta na ba Nasirun gidanmu na ce ya kai masa. Tambayarshi nayi ko lafiya? Na jishi shiru. A bayan takardar ya rubuto cewa Babana ya kore shi, don haka shi ya hakura da ni. Na girgiza da jin wannan zancen, don ina son shi kullum burina na aure shi. Shi kadai nake jin sha'awa. Na rasa yanda zan yi ko satar jiki zan yi na je gidan su? Innarmu ta gane ina cikin damuwa, ta ce "Hafsat ba ki jin dadi ne? Na ce, "Ciwon kai ne yake damuna." Ta bayar da Naira goma a amsomin panadol." Da dare nace Innarmu zan je gidansu wata yarinya *yar makarantar mu, in amso wasu takarduna, ta ce, "Kar ki zauna, maimakon kije tun ido na ganin ido?" Na ce, "Ai dazun ciwon kai ke damuna." Ban yi wata kwalliya ba, kada ta gane, sai kawai na dan fesa turare. Na zari mayafi, gidan su Munnir da dan tafiya tsakanin mu saboda mu muna Rigasa ne Abuja Road ta kasa, su kuma suna Makarfi Road. Tun daga nesa na hango shi su da wani tsaye, ga motarshi gefe, ina zaton fita zasu yi. Sai na kara sauri. Daidai ya bude motar zai shiga na ce, "Munnir" Ya juyo da sauri, ya mai da motar ya rufe. Abokin nasa yana ciki, ya ce, "Beby lafiya?" Na jingina da motar, sannan na sauke ajiyar zuciya, domin na gaji. Sai dai kuma lokacin ne naga rashin hankalina. Yanzun ince mishi me? Na zo in bashi hakuri ko nazo biko? Ya sake cewa, "Me ya faru Baby? Na ce, "Ai ba ka ma sani ba?" Dabara tazo min, na ce "Dama nazo ne na maka godiya akan dawainiyar da kayi da ni, don ko zamu rabu bai dace mu rabu ba zumunci ba." Ya ce, "Baby kenan, don na fada kina ganin zan iya rabuwa daKe? Ni ina sonki, Babanku ne ya tozarta ni" Kafin nayi magana ya ce, "Ina zuwa." Ya leka motar yayi magana, sannan ya ce, "Zo muje ciki kiji." Na ce, "A'a. Ya bata rai, "Bana son yawan gaddamar nan, ki daina kada muyi aure mu zo muna samun matsala. Na ce, "Ina jin kunya ne, saboda Mamanku, Ya ce, "Ba za ta san kin shigo ba, zo muje. Na bishi, ya tura Gate din gidan, muka shiga. Yau ne na soma shiga gidansu, ginin zamani ne ga haske tamkar rana, me gadinsu ya ce, "A'a, ka fasa fita dinne? Ya ce, "A'a Baba, yanzun zan fita. Na gaida maigadin muka tafi ginin farko daga cikin gine-gine ukun da ke harabar gidan, ya ce, "Yau kin zo gidan mu, ba don kunya ba da na kira miki kannena su Nana. Na ce, "Barsu yanzun zan tafi, kuma bai dace su ganni cikin wannan yanayi ba, ina nufin shigar da nayi. Ya ce, "Shikenan. Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya zauna hannun kujerar da nike Mukhtar Ismail Muhammad WhatsApp: 08161892123 Sanadin Boko 1 02 Posted by Mukhtar Ismail Muhammad On www.arewarulers.com.ng Under: SANADIN BOKO Na Maryam Abdullahi K/Mashi Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya zauna hannun kujerar da nike. Ya balle hancin gwangwanin ya cika dan kofin ya mika min, na girgiza kai tare da cewa, "Na gode. Ya ce, "Wasa ki ke yarinya, rike nan ko na dura miki. Da sauri na amsa saboda nasan halin shi sarai, zai iya. Kurbata biyu na aje, ya kama hannuna na kwace tare da mikewa. "Tunda ka huce ni zan tafi. Ya ce, "Dama ni banyi fushi ba. Na kalli fuskarshi muka hada ido, ya kashemin idonshi daya, nayi saurin kauda idona saboda yarr din da tsigar jikina tayi. Na ce, "Yaushe zaka zo? Ya ce, "Zauna to mu tsara in da zamu dinga haduwa, don Babanku ya ce in manyana ba su zo ba kada ya sake ganina. Na ce, "Fada min daidai ina ne zamu dinga tsayawa? Ya dan yi shiru, "To ni bansan yaya zamu yi ba, na ce zan hada miki phone kin ce a gida ba za a barki ba, wai ke ba ki da irin 'yar dabarar ku ta mata ne? Ki saka ta a silent. Na ce, "Barta kawai. Ya dube ni, fatin kuma fa? Na marairaice murya ina kallon shi da idanuna, da na lura yana son su. Mu bar maganar party din nan, wallahi ba Babana ba har Innarmu in ta sani zan bani, ka ji. Ya tsare ni da manyan idanunsa. "Yanzun nayi asara kenan? Ya ci gaba "Ban san me yasa gidanku ake yin haka ba, ni kinga kannena su Nana da Suhaila Mom din mu da Dad din mu sune suka shirya musu party din su last week. Amma ku sai ana hana ku. Wannan duhun kai ne, yanzu fa an waye. Na ce "Ba wani duhun kai, kowa da irin tarbiyar da yake son ya yi ma 'ya'yanshi. Ya ce "Shikenan dai, mu bar maganar, naji nayi asarar kudina, kuma ba wani gida ke ce dai ba ki ga dama ba. Wani friend dina yarinyarshi itama 'yar Geto ce, amma ta jirga Iyayenta da cewa suna biki ne tazo muka yi shagali, amma ke kin kasa. Na ce, "Ni dai kayi hakuri kawai. Ya zuba min ido, sai kin yi min kiss zan hakura. Da sauri na dauki hanyar fita, sai kawai naji ya rungume ni ta baya, jikina ya dauki rawa. Cikin rawar murya na ce, "Munnir la..la....lafiyarka? Don Allah sake ni. Da kyar na kwace, kamanninshi sun canza, da sassarfa na fito na dau hanya. Ya biyo ni da mota shi da abokinshi, wai na shiga su kaini gida, na ce, "A'a don na tsorata, dole suka bar ni. Da na zo barci na jima ina tuno abin da Munir ya min, dama an ce mace da namiji in suka kebe na ukun shaidan ne. Ba don son da nake yiwa Munir ba, da tuni na bar shi. Mun canza gurin hira, bayan layinmu yake tsayawa. Na fada ma Innarmu ta ce saboda me? Na ce, Baba ya hana shi zuwa nan. Inna ta ce, "Mallam ho! Shikenan, ki dinga zuwa da Ummi kin san mutane da sa ido, yanzun sai ace wani abin ne yasa ku ke zuwa can. Fatana ki kama kanki. Na ce, "To, nima zuwa da Ummi zai fi min, duk da Munir ganin Ummi bai hana shi son taba jikina ba. Cikin haka muka soma shirin zana (JAMB), Baba bai sani ba, Munir ne ya sai min form, sai dai tsorona daya randa Baba zai sani. Na zama cikin sa'a kamar ko yaushe, Munir ya tsaya tsayin daka har na samu gurbin karatu a (B.U.K) Kano, sai dai ya zamuyi da Baba? Haka na ce ma Innarmu, ta ce yau na yanke shawarar sanar da shi komai, tunda gobe za ku je yin rijista. Kusan goman dare, lokacin ina kwance muryar Innarmu nake ji tar daga dakin Baba, domin bangonsu daya. Tana sanar da Babanmu komai. Bai katse ta ba har ta kai karshe, ya ce, "To bokon nan ba da yawuna ba, bayan shekara shidan da na hakura tayi yanzu kuma wata zata? Wai lahira take so ko duniya? Inna ta ce, "Duka. Ya ce, "Karya ne, duniya ku ke nema, kuma ga ku gata nan. Jami'ar da aka ce 'ya'ya suna lalacewa? Yarinyar ta fada a gabanki sama da shekaru amma baki damu ba. To magana ta ni uku ce, bata kai hudu ba. Na farko duk abin da ya faru da ita SANADIN BOKO ba ruwana, zai shafe ki ne da ita. Na biyu ba zan yafe hakkina da ku ka tauye ba, matsayina na Ubanta, kuka hana ni in sauke nauyin da Allah Ya dora min. Na uku kuma ta nemi Ubanta ke kuma ki nemi mijinki, duk ranar da wata ashsha ta samu SANADIN BOKO. Ba innarmu ba, ni kaina zancen ya girgiza ni. Baba kishiyar Innarmu ta fito daga uwar dakinta, ta zo kusa dani ta zauna. Tasa hannu ta dan dake ni, "Tashi Hafsatu. Na tashi zaune jikina sharkaf da zufa, ta ce "Nasan kin ji duk zancen da Malam yake yi ko? Na ce, "Eh. Muryar Innarmu ta katse ni, ta ce, "Insha Allahu Malam karatun Hafsa zai zama alkhairi garemu da kai gaba daya. Ya ce "Ruwanku. Cikinsu ba wanda ya sake magana. Babah ta ce, " Hafsatu ki bar Babanki yayi iko da ke, ki ce ma Innarku kin fasa karatu. Kalamanshi ba baki yayi miki ba, amma ina ji miki tsoron alhakinshi kada ya kama ki. Na ce, "Babah wanda zan aura karatu yake yi, ba yanzu zai yi aure ba, kuma Iyayenshi ba za su yarda ya auri mara ilimi ba. Babah ta ce, "Sai shi? Akwai masu sonki da yawa, kuma sun ma Babanki magana. Nayi shiru ina nazari, nasan Babah gaskiya ta fada min, amma ya zan yi da son Munnir? Na dube ta, "Babah ki duba irin hidimar da Munnir yake yi da ni, ba zan mishi adalci ba in na ce ba zan jirashi ba. Ta ce, "To yanda ki ka gani, amma karatun nan tunda ba na Muhammadiyya ba ne, banga dalilin naci ba. Kuma ni sai in ga yaron nan tamkar yaudararki yake yi. Anya auranki zai yi? Na ce, "Allah Babah aurena zai yi, ki dubi dadewar mu da hidimar da yake min. Ta ce, "Ba ta a nan, amma fa shawara ce." Na koma na kwanta, ita kuma ta mike ta nufi cikin dakinta. Zancen Babah ya taba zuciyata, illah magana daya da ban kama ba, wai tana ga Munnir ba zai aure ni ba. Nayi guntun murmushi, me zai sa shi ya yi ta dawainiya da ni ba zai aure ni ba? Yanda na raba dare ban yi bacci ba, na tabbata Mahaifana biyu ma haka ne, duk SANADIN BOKO. Da safe ina zaune da kofin koko sai juya shi nake yi na kasa sha, Innarmu ma sukuku take. Lokacin da ta zauna tana shafa ma gwangwanayan alalarta manja, na ce "Inna ko dai zamu hakura da batun bokon nan ne? Ta dube ni, "Saboda me? Na sunkuyar da kai na ce, "Naji duk yadda ku ka yi da Baba jiya. Tayi shiru, can ta ce, "Abu daya zuwa biyu nike so ki min. Na zuba mata ido, na farko ki tsaremin kanki da mutuncinki, kada ki banzantar da kanki, na biyu kiyi abin da ya kai ki makaranta, wato karatunki wanda nike fata ya zama sanadin alkhairi. Ta haka ne za ki wanke wa Mahaifinki tsanar da ya yi wa boko, har kannanki suma su samu dama suyi cikin kwanciyar hankali. Yayanki da bai samu damar ci gaba ba yana jin haushi. Ke tunda kin samu dama kada ki bani kunya. Na hada ki da Allah, ki rufamin asiri. Tausayin Innarmu ya cika ni, na ce, "Insha Allahu zan kula sosai, kuma zan fidda ki kunya, SANADIN BOKOn nan kowa zai huta, Baba zai yi alfahari da ni. Munnir yayi tsayin daka har na zama daliba a jami'ar Bayero da ke Kano, har lokacin da zan tafi Innarmu bata daina rokona in rufa mata asiri in lura da kaina ba. Nan na tafi na barta da surutun 'yan gidanmu, da 'yan unguwarmu. Wasu suce tana so ne ta auri mai kudi, shi yasa muka nace boko, wasu su ce dan kyan nawa bai fi cikin cokali ba, amma mun kuke sai nayi boko. Wasu su ce dan-dan masu hali ke sona, duk dai ta toshe kunne watan kwaram daya ne. Baba har fushi yayi da ita, sun jima kafin ya soma amsa gaisuwarta. Karin haushi yakai kararta ga danginta, maimakon su bata rashin gaskiya suyi mata fada, sai suka ba shi hakuri suka ce wai karatun yana da amfani. Ya ce, shi ba ya ce babu amfani ba ne, a'a tayi shi can gidan mijinta. Aure shi ne sama da karatun ta, sai suka ce ya yi hakuri 'yan kwanaki ne zata gama, don haka sai ya dawo ya zura mana ido ******* ********** ********** *********** ********* Jami'a wata rayuwa ce da ta sha bamban da secondary, banga laifin Baba ba yanzun don ya kyamaci boko, sai dai na sha alwashin kula da kaina, don haka na tsare gida bani da kawa ko aboki. Duk da Munnir na shirin tafiya Dubai karatu don kammala Masters dinshi, haka bai hana shi zuwa duk bayan sati biyu ba. Tafiyar tashi bata yuwu ba har muka samu hutun first semester, sati biyu dai za mu yi amma naji dadi, sai dai wannan hutun ne hutun da ba zan taba mantawa dashi ba a rayuwata. (Kuma shi ne dalilin rubuta labari na "SANADIN BOKO" . Sauran kwana biyar na koma Makaranta duk da inata dokin zuwa gida amma zaman gidan bai mun dadi ba, ko gaisuwata Baba baya amsawa har ta kai da naji muryarshi zan boye. Bello Abokin Munnir shi yayi sallama da ni, na sha mamaki don bai taba zuwa shi daya ba. Ya ce, Munnir ya aiko shi muje tare bashi da lafiya. A rude na je na fadawa Inna, ta ce, "Yana asibiti ne?" Duk da ban sani ba sai na ce mata, "Eh." A zatona yana asibiti ne, sai da yaja mota sannan nace, "Wane asibiti ne." Sai ya ce, "Ai yana gida." Har gefen su Munnir Bello ya raka ni, ina shiga sai yace mun, "Toh yana ciki ni na wuce ki fada masa don ya dameni in kawo ki har ciki. Na ce, "Toh!" Na nufi ciki da tafiya cikin dari-dari. Tsakiyar falon na tsaya na zabga Sallama, ga mamakina sai ga Munnir ya fito daga kitchen sanye da gajeren wando da vest duka farare tas, hannunshi dauke da ruwa (C way) yana sha. Na ce, "Ah! Ka samu sauki ne?" Ya ce, "Eh, A'a." Ya nuna min kujera, "Zauna." Na zauna ina kallon shi tare da son jin karin bayani, "Ban gane eh, a'a ba?" Ya tsugunna a gabana, "Ciwon ya dade yana ci na, ga shi zan iya tafiya Makaranta cikin kowane lokaci ba tare da na samu maganin ba." Na ce, "Wane irin ciwo ne?" Ba tare da shakka ki tunani ba ya ce, "Ciwon sha'awarki....." Gabana ya fadi, na mike tsaye da sauri. Shima ya mike, "Hafsat kin san ina son ki, wallahi na gaji da sha'awarki. Ki so ni kamar yanda nike son ki." Na ce, "Munnir ka san ina son ka." Ya ce, "To ki nuna min." Na ce, "Ban gane ba? Sau nawa nake cwa ina son ka? Ka sani." Ya ja tsaki, "Kin dai gane nufi na, ina son yau daya ki taimaka ki nuna kaunarki gare ni." Na ce, "A'a ba zan iya ba, domin haramun ne." Ya ce, "Ni fa zan aure ki!" Na soma tafiya don fita ina cewa, "Sai ka jira sai ka....." Maganata ta tsaya sakamakon murda kofar da naji nayi ta a rufe gam. Na dube shi yana murmushi ya ce, "Ki bani hadin kai don yau ta karfin tsiya ma zan iya biyan bukata ta." Jikina ya soma bari na ce, "Wallahi Munnir zan maka ihu, ka bude min kofa." Ya zauna, "Ko kin yi ihu ba wanda za ya ji ki. Mom bata nan tana gurin aiki, Dad ma haka, su Nana da Suhaila suna Makaranta." Na zube gwiwoyina biyu a rude ina cewa, "Ka min rai kada ka sa ni cikin matsala, don Allah." Na soma kuka. Ya ce, "Nima ki taimake ni na gaji, wanene za ya gane me muka yi?" Na ce, "Allah ya sani, na tabbata zai kama mu." Amma da yake Shaidan ya hura ma Munnir kaho sam ya ki karban uzirina. Muka yi ta zaga falon har na fada wani daki, sai dai kafin na rufo tuni ya banko, mun yi damben bala'i dashi kafin ya samu nasarar aikata mummunan nufinshi a kaina, bayan ya bi duk wata gaba ta jikina ya bugeta, fuskata kuwa ta sha mari sai na ga kamar ba Munnir dina ba. Kuka iya kuka na yi shi, na mike ina gyara daurin zanina, da kyar nake tafiya na fito falon, ya ce, "Duk kin sa mun wahala, a yanzu wa zau sani in ba kin fada ba?" Na ce, "Bude min kofa kawai ni dai na tafi." Ya nufo ni, "Come on kiyi wanka sai na kai ki." Ban san lokacin dana daka mishi tsawa ba, "Budeni mana" Sabon kuka ya kwace min na ce, "Allah ya isa tsakani na da kai, Insha Allahu sai Allah ya saka min." Ya tashi ya bude tare da cewa, "Sai na zo." Ban kulashi ba na fita, dole na share hawayena saboda Maigadinsu, na fita ko ina a jikina ciwo ya ke. A haka na kai gida, kallo daya Inna ta min tace, "Lafiya?" Jikina ya soma bari, ta ce, "Ba dai jikin nashi ba? Na ga duk kin rude fuska a kumbure." Na ce, "Umm jikin ne." Ta ce, "To shine na kuka? ki masa addu'a." Na ce, "To." Na nufi ciki. Ta ce, "Hafsa zo nan, menene wannan a zaninki?"mummunar faduwar gaba ta ziyarce ni, zufa kuma ta shiga keto min, amma sai na yi saurin cewa, "Fashin Sallah ne." Duk da ban juyo ba kuma ban san mai ta gani jikin zanin ba. A gani na in muka hada ido zata gane, ta ce, "Haka kika ratso titi? Ga ruwa da na daura chan kan wuta na tuwo ki diba ki maida min sai ki dauraye jikinki." Cikin bayi ina wanka ina kuka tausayin Innarmu ya cika zuciyata, na karya alkawarin da na daukar mata, Allah ya isa Munnir. Cikin kwanakin da suka biyo baya ko Munnir ya zo bana fita, ranar da zan koma Makaranta har goman safe ina kwance a tsakar daki, Innarmu ta ce, "Ke da naji kina cewa sammako zaki yi? Har yanzun kin kasa tashi?" Na ja tsaki, yanzun na soma tsanar boko bani da daman in tona asirina... Yaron gidanmu ya shigo ya ce, "Hafsa wai in kin shirya wani mai mota ya ce ki fito yana can saman layi." Na ja tsaki, "Ka ce masa ya tafi na san hanya." Innarmu ta ce ma yaron, "Kai zo, je kace tana zuwa." Yana fita ta fara min fada wai bani da hankali, ta lura kullum zai kirani in 'ki fita, haka ake yi? In ma sabani kuka samu ba sai kiyi hakuri ba tunda shi har ya zo? Na kalli Innarmu a zuciya na ce, "Da kin san abinda ya min sai kin fini tsanar shi." Ban ce komai ba na ci gaba da shiri. Inna ta kwance habar zaninta kudine 'yan hamsin hamsin dubu uku na adashena na kwasa, sannan cikin robar can tumatir ne na tafasa shi ga sabulu can inji Baabarki..... Na ce, "Ki bar kudinki." Ta ce, "A'a na dai baki ne, amma badan zasu ishe ki wani abu ba ne. Yaron nan dake dawainiya da ke Allah ya gwada min aurenku." Yana zaune yana latse-latsen waya ya diro, "Gimbiyata, amaryata har yau fushi kike da ni? Gashi doguwar tafiya za muyi? Don Kano zan kaiki." Ban tanka shi ba ya amshi robar hannuna da leda ya daga but ya sa. Ni dai tamkar na haushi da duka nake ji, ya bude mun gaba na shiga don bani da yadda zan yi. Tunda muka dau hanya yake mun magana amma ban tanka shi ba. Ya ciro waya daga gefen shi ya ce, "Ga wayarki." Sai lokacin na yi magana, "Bana so." Ya daurata kan cinyarshi, "Dole ki so ta Hafsat don in na tafi karatu ta yaya zan dinga jin muryarki? Ki saki ranki, abun da ya faru ba wata matsala bace saboda ni zan aureki..." Na zabga mishi harara tare da cewa, "A ganinka kenan, amma ni addinina bai yadda don zaka aure ni kayi ZINA dani ba." Ya katseni, "Ki daina cewa Zina." Na daga murya na ce, "Ka biya sadaki na ne? Iyayenka sun nemi aurena gun iyayena ne an basu? Ko jama'a sun shaida." Ya ce, "Ba daya." Na ja tsaki ban kara tanka shi ba har muka kai. A dakinmu ba yadda bai yi ba na'ki tankashi, ya aje mun kudi da waya ya tafi. Na saka kuka nayi ma ishi na, tunanina in Allah bai yi aurena da Munnir ba fa? Ya sakani cikin matsala kenan don ban san mai zance ma mijina ba yayin da yace ina nakai budurcina? Dole in dauki hakuri in lallaba Munnir ya aureni. -Yana kiran wayata sosai, tun ina sharewa har na hakura don ban san yadda zan yi ba, sai dai bashi da wata daraja ko kima a ido ba, ko na aureshi gani nake ba zan girmama shi ba, tunda na ga irin nashi rashin Imani. Sai mene? Tun jiya sha hudu ga wata ya dace in ga al'adata amma har yau sha biyar shiru. Wannan ya tilastamin shiga rudani. Dora John dakinmu daya har ta gane ina da matsala ta ce, "Hafsy yaya ne?" Na ce, "Ciwon kai ne." Ta bani panadol da sauri na sha don kuwa kan nawa na ciwo. Kwanaki uku suka biyo baya gashi banji daga Munnir ba cikin 'yan kwanakin, naje na sai kati na kira shi, yana dagawa na soma kuka, ya ce, "Mai ya faru?" Na ce, "Banga period dina ba yau kwana uku." Ga mamaki na sai na ji bai damu ba ya ce, "Zan shigo wannan ba wani abun damuwa ba ne." Washegari sai gashi da wani abokin shi, yana shigowa na soma kuka nan take ya bata rai, "Kukan nan ya soma isata, zan barki ki karata in dai ba zaki daina mun kuka ba." Abokin shi Bello ba karamin tsanarshi nayi ba har da cewa, "Daga sau daya sai ciki?" Munnir ya ce, "Nima dai nayi mamaki bata fa tsaya ba ma, gaskiya in anyi bikin mu juya Mahaifarta za'ayi don bana son yara su wuce biyu tsanani uku." Tsabar bakin ciki ya hana ni tankasu, ni dai burina ya san yadda zai yi dani. Bello ya kira wani abokin shi anan Kano wai shi Nasir, ya zo suka tafi suka yi magana sannan suka ce inzo mu je asibiti. Mun shiga office din Likita mace 'yar kimanin shekara arba'in tana tsaye da farin gilashi, ta tsareni da ido bayan duk mun zauna ta kalli Nasir, "Me ke tafe da ku?" Duk muka yi shiru, Munnir ne mara kunya shine ya ce, "Mun kawota ne bata ga period dinta ba, so muna so a gwada ta." Ta tsareshi da ido, "Kanwarka ce?" Ya ce, "Budurwa ta ce." Bakin ciki ya cika ni, na sunkuyar da kai ina hawaye, "To ku dan bamu wuri." Suka fita. Ta zabga min harara, "Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a sarke na ce, "Wallahi... Mukhtar Ismail Muhammad WhatsApp: 08161892123 Sanadin Boko 1-03 Posted by Mukhtar Ismail Muhammad On www.arewarulers.com.ng Under: SANADIN BOKO NA Maryam Abdullahi K/Mashi To ku dan bamu wuri." Suka fita. Ta zabga min harara, "Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a sarke na ce, "Wallahi Anty fyade yayi mun." Ta ce, "Tun yaushe?" Na ce, "Za'a kai wata daya." Ta bani wata 'yar roba ta nuna min wata kofa, "Shiga toilet ki bani fitsarinki." Ina fitowa naga wata nurse tsaye ta ce, "Don Allah sister ina son result yanzun nan." Ba jimawa ta shigo, Likitar tayi ta juya takardar sannan ta dube ni ta ce, "Kina da cikin wata daya da kwanaki." Nan da nan na soma zufa, zuciyata na kwadayin ina ma mafarki ne? Cikin tsananin kuka da kunan rai na ce, "Ya cuce ni. Mai zance da Innarmu? Abun da Baba yake tsoro ya faru. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Kuka na ya shigo da su, ta mika mishi result ya duba sannan ya kalle ta, "To yanzu doctor ya za'a yi tunda gaskiya ni da ita karatu muke yi, bamu shirya taron Baby yanzun ba." Na dube shi yana magana hankalinshi kwance kamar wanda ya aikata abin arziki. Ta ce, "Baka shirya tarban Baby ba mai ya kaiku aikata haka?" Ya ce, "Tsautsayi ne." Ta ce, "A'a ku ji tsoron Allah, aure shine ya fi dacewa da ku, karatun boko ba zai hanaku aure ba. Amma sai kaga ana wasa da Sunnag kun zabi boko sama da raya sunnar Manzo (S.A.W), to ku sani Manzon Tsira (S.A.W) ya ce aure Sunnar shi ne, duk wanda ya ki sunnarshi baya tare da shi. Kun fi yadda kuyi ZINA fiye da aure." Ta nuna shi da biron hannunta, "Musamman irinku 'ya'yan 'yan boko, Iyayenku sun rike wuta sai kunyi karatu mai zurfi basu damu da halin da zaku shiga ba kasancewarku balagaggu, burin su ku iya turanci tare da kawo musu kyawawan sakamako lokutan jarabawar ku. Ba su damu ku san addininku ba bare kusan illar ZINA."munir yace to doctor, yanzu menene mafita? Don matsala ne cikin nan don Allah a cire shi tayi suru tana tunani. Bello yace in bazaki iyaba muje wani asibiti doctor hindu tayi shuru tana nazari, tace to zan tai makeku sai a lokacin naji sanyi ya ratsa zuciya ta. Ta bani wasu kwayoyi wai kafin nan da sati daya zai fita, suka ce nawa? Tace dubu goma nan take suka biya. Sun saukeni makaranta sanan suka wuce, da alkawarin zaya rinka kira yaji abinda ke tafiya. Yau kwana tara shuru sai laulayin da nasoma gadan- gadan, ga sheka amai nan ga zazzabi na kwasa na koma wajen doctor hindu ana kai mata kati na tace a turo ni duk da yarinyar da naga ta shiga bata fito ba, itama yarinyar duk a firgice take, taci kuka ta gode Allah nace sannu doctor. Tace yauwa ya jiki? Cikin saurin baki nace da sauki amma fa har yanzu bai fita ba. Ta mikye tare da diban wayoyin ta ce ku biyo ni. Muka biyo ta cikin harabar asibitin muka nufi wani gida kirar zamani dan madaidai ci. Ta umurce mu mu zauna kan kujerum da ke kayatacen falon,ta shiga wani daki daga cikin dakunan biyu dake cikin falon. Jim kadan ta fito ta canja shigarta zuwa doguwar riga ta atanfa. Ta shiga kicin yafito da doguwar gorar ruwa (swan) da kofuna guda biyu. Ina takure cikin hijabi na, zazzabi ne ya rufe ni ta tsiyaya ruwan ta miko min, sha ruwa nace a a sanyi nake ji ta koma takawo min paracetamol na sha. Ta zauna ta zuba mana ido, ta dubi dayar tace asabe ko? Yarinyar tace eh, menene labarinki? Yarinyar ta ce, Sunana Zainabu,amma an fi kirana da Asabe.Mu 'yan asalin nan kano ne, a karamar hukumar kunci can wani kauye ana ce masa kurje. Wata mata mai suna Gambo tana zuwa kayaunkan garinmu tana diban yara 'yan aiki, wata rana taxo gidanmu ta ce da Babata su bada ni ana samun kudi sosai, wai can zan samu kudin kayan daki. Sai na ce ni ba zani ba, nafi son nan don ina talla kuma ina zuwa karatun allo. Sai Babata ta ce to abar shi, don Babanmu in ya ji ba zai yarda ba, ta ce can ma ana karatun Muhammadiyya, kuma za su saki ga cima mai kyau za ki canza. Haka dai ta zuga Babata hr ta yarda, sai da suka yi rigima da Babana sannan ya yarda. Gidn Hjy Mairo aka kai ni, ba wani aiki sosai kuma bata da tukara. Ba ta da Matsala in kaga damuwarta to ran danta ya 6aci, don shi ne dan ta kwallin tal. Yawancin aikin nawa duk nashi ne don tana zuwa aiki shi ma yana zuwa makaranta, amma ya fi ta zama gida.Ba mu cika shiri da Yasir ba, don shi yana da fada. Watana 3,ranar wata Litinin ina kicin, ya shigo wai in dafa masa Idomie, nan na bar komi na shiga dafa masa, don Hjy ta ce kome nake yi in yazo da nasa in bari in masa don a zauna lfy. Ba ta so ta ga yana zagina, na ce to. Da na gama na nufi dakinsa, na aje zan fita ya ce in dawo, cikin sauri na dawo don ina matukar tsoronsa, kawai sai ya ce in cire kayana. Na soma zare ido, ya ciro wuka da sauri na cire ya kwantar dani ya aikata alfasha da ni, sannan ya hana ni kuka. Ya kuma ce idan wani ya ji sai ya kashe ni. Naja baki nayi shiru, duk uwar wuyar da na sha tun daga nan muka daina fada, Yasir ya maida ni tamkar matarsa. In Hjy bata nan sai ya kira ni dakinsa, akwai lkcn ma da Hjyn taje Umra ta barmu tare da wata 'yar uwarta don ta lura da mu, da kuma gidan,amma Yasir cikin dare zai zo ya buga in kofa, dakinshi nake kwana. Nan da nan nayi wani girma, kirjina ya cika. Daku abn da ya gani zai sai min,wata rana na tashi ba lafiya,sai amai nake shekawa,Hjy ta kira Likitansu tun kafin ya gwada Ni ya ce yana zaton ina da ciki,ya ce amma bari dai ya gwada. Gwajin Farko ya nuna ina da ciki, nan ta shiga salati da sallallami, ta tsare ni wai in fada mata wanda ya min, na ce Yasir ne. Nan ta hau ni da duka wai na masa sharri, dan shekara ashirin da biyar dinne yaya iya yi min ciki? Da ya dawo ta tambaye shi da har ya musa sai yaga ta watso min kayana, wai na tafi zan yi ma danta sharri, sai ya ce mata shi ne,amma tsautsayi ne. Ga mamakina, bata yi masa wani fada ba, sai dai ce masa tayi kada ya kara, kuma Babanshi zai dawo. Ta kai ni wani asibitu aka cire min shi ta dinga min fada wai ko ya kira ni kada naje. A cewarta, wai bashi da laifi ni ce mai laifi. Sati biyu ina jinya, Sannan na gyagije, ganin ta sa mana ido, sai ya ce in dinga barin dakina a bude zai ringa zuwa. Na ce Hjy ta ce mu daina. Ya sake zare min ido, dole na bi yanda yake so, wai baya so Hjynshi ta sani, don ta ce mishi in ya sake sai ta aura masa ni, shi yasa duk ya tashi hankalinsa yanzun. Doctor ta ce, To shi baya son ya aure ki ne? Asabe ta ce, tab ita ma nasan tana tsorata shi ne, domin ba ta da burin yayi aure yanzun. Burinta shi ne ya yi karatun boko mai zurfi,kuma ya zama wani abu a kasar nan SANADIN BOKO." Na jinjina kai, tuni zazza6ina ya sauka. Labarin Asabe ya ta6a ni, kallo na dinga bn ta da shi, Yarinya ce ba zata wuce Shekara sha uku zuwa sha hudu ba. Wanna ma ai child abuse ne, ya kamata a hukunta su shi da Hajiyar shi. Doctor ta katse min tunani da cewa Hafsat me ya faru da ke kuma, menene labarinki?? Na zuba mata ido, hawaye suna zubowa, ta ce fada min ina so ne in taimake ku, na ce zaki cire min cikin? Ta ce Eh, zan cire miki in har naji labarinka, kin cancanta a cire miki.Ina nufin in ban da son ranki hakan ta faru ba. Na share hawaye,sannan na ce da ita. "Sunana Hafsatu, Mahaifina dan asalin jihar Borno ne, ya fito daga gida tun zamanin yana saurayi, a kano ya yada zango, nan yake 'yar sana"arshi.Sun hadu da Mahaifiyata a can lkcn tazo gidn yarta a Na'ibawa. Babana Shi ne ta tambaya ya yi mata kwantancan gidan Malam Ma'aru me Almajirai mijin yarta kenan.Daga lkcn ya nuna yana sonta, ta amince hr yaje Maliunfashi jihar Katsina, unguwar Fayamasa. Ya samu kar6uwa cikin dangi, don yana da nutsuwa da ilimin addini aka ce ya turo magabatansa.Mahaifanshi sun rasu sai babban wansu Babagana, shi ne ya zo suka hadu da wani uban dakinsa. A nan kano suka zo, sune suka amsar masa auran Innarmu.Ba su jima a kano ba ya soma zuwa kaduna, ya fara sana'ar saida lemo da Ayaba,daga bisani ya nemi gida a hayin rigasa ya dawo da Innarmu,lkcn tayi haihuwar farko wato Yayana Ummar. Gidanmu gidan haya ne, Mai girma gaske a layinmu kaf ba gidan da ya kai namu yawa don gidan yawa ake ce mana. Mata goma sha ne, kowace da 'ya'yanta wasu hudu wasu shida,wasu goma sha. Babana ya sake auro wata matar daga kano, itama nan gidan ya samu daki kusa da na Innarmu., Babah tana da kirki da nutsuwa, shi yasa duk yanda Innarmu taso suyi rigima bata biyewa, dole itama ta saki suka zauna lfy. Yanzun Babah 'ya'yanta 6, Innarmu 8. Ni ce 'ya ta 2, masu bina 3 duk maza ne, sannan mata. Innarmu gidan su 'yan boko ne, ko na ce kowa yasan Katsinawa da boko. Don haka tana da burin mu 'ya'yanta muyi boko, shi ko Baba ba ya da burin mace ta wuce primary. A nashi ra'ayin nayi saukar Alkur'ani mai girma ya min aure. Tun muna kanana Innarmu ta kwadaita mana boko, don haka ni da yayana mun taso muna son karatun boko,Primary 5 Umar yake lkcn da ni ma aka sani. Babanmu bai cika biya mana kudi Makarnta ba, don bai cika samu ba.Amma in yana da shi yana ba mu,ganin haka ne yasa Innarmu ta kama sana'a. Gyada take soya mana ni da Yayana in lkcn dafaffiya ne kuma ta dafa mana da wannan muke samun rufin asiri. Cikin haka Yayana ya gama Primary aka kukata ya shiga Junior. Kwanci tashi nima na gama primary, sai dai lkcn ne Baba ya ce Bokona ya isa haka, izifina ishirin a Islamiya ya ce da na sauke za a min aure. Innarmu ta ce ina, yanzun kai ya waye ko ita tayi makarantar gaba da primary balle 'yarta. Sun yi hatsaniya hr abokinsa makocinmu Baba Garba, ya saka baki kan cewa Baba yayi hakur ko aji 3 in yi wato karamar Sakandire. Baba ya ce, shi kenan,amma fa ba ruwan shi, ko yana taka kudi ba zaya ba ni ko na fensir ba. Abubuwa suka kara yi wa Innarmu yawa, ga Yayana Umar kudin jarabawa yasa makarantar tsaya. Sai dai karen mota ya koma yana yi wa wani mu2m a layinmu,kasuwa-kasuwa.Inna ta zaunar da ni ta ce Hafsatu,kin san yanda zamu yi? Na ce A'a na me? Ta ce, na karatunki, kina so ko? Na ce "Tab so kai ba ki ga su Saliman ajinmu na su suna ta zuwa, ta ce to dagewa za ki yi zan dinga alala da safe ki dan zaga. Sai kuma ki zo ki dauki gyada, na ce Innarmu ni wlh Na gaji da talla,wata rana mu2m ya yi ta yawo a ki sayar ta ce sakarya kin zaga tas za a saye. Asusu zan yi riba ko nawa aka ci sai mu zuba kafin gama zangon farko mun tara kudin da za ki shiga, na ceto,gwangwanayen gyada muka fafe wasu tayi alala.Nan da nan ya kare, Ta dafa min gyada na dauka ta ce maza Hafsatu, Allah ya bada sa'a kin ji, kan lkcn Ismaiyya ki saida. Na ce to, Ta ce bn da wasa fa, don na san ki, na ce to.Wasa kam inadashi,kowa ya sani har na gama primary duk report card dina ba wanda ba a rubuta min na cika wasa ba, a haka kuma nake karatuna. a haka kuma nake karatuna haka kuma na dage da talla na wata ranar litinin ina tafiya nice har baban titi na tsallaka, sai ga wata yarinya tana tallan kwakumeti, tace ke ina kike zuwa? Na ba ko ina yawon talla nake. Tace zomuje (governmeet college) ana cinikin gyada in yan makaranta suka tashi nace, to muje tafiya ce sosai har gidan gwamna ta nuna min. Muna isa agajiye muka zauna gin din bishiyoyi ga yan talla nan kala-kala har da masu gyada babu abin da yafi mun dadi irin yanda naga yara nata wasa saboda yan makaranta basu tashi ba. Masu carafke masu yar gala gala nayi, wasu na tayin ziro-ziro duwatsu na tsinta nima nashiga yin yar carafke, batare da na huta ba koda dalibai suka taso nan kowa yasaki wasa suka shiga saida kayansu, ni ko ban damu ba na cigaba da wasa na sai da takowa ta kare sanan aka shiga siyan nawa. Washe gari nacewa innarmu a kara mai makon mudu hudu a dafa biyar. Yau ma wasa na dora haka nan sai da ta kowa ta kare don su suna zaune, a gaban kayan su niko ina can ina wasa na. Zuwa yanzu na saba da dabar hanya zuwa (government college) wata rana ina zaune kan duntsen da na dasa a matsayin abin zama na, gaban tirena hannuna zarene ina ta wasa dashi na hada injin nikan barira inata yar waka ta. Sai naji magana kusa dani ance ke gyadarki ba ta saida wa bace? Ba tare da na dubeshi ba nace ta saidawa ce mana,ya ce, "Sa min daya a leda sarkin wasa." Na ce, "Zaba." Ya ce, "Zabar min." Sai lokacin na kalle shi na dan kara zare ido saboda kyawun shi. Haka nan ba Uniform a jikin shi, kenan ba dan Makaranta ba ne. Na mika mishi ya ciro wani farin kyalle ya shinfida akan jijiyar bishiya ya zauna ya soma cin gyadar. Ni kam kallonshi nike a raina ina cewa, "Dama 'yan gayu suna cin gyada?" Ya dube ni, "Ki yi wasanki mana kada ki sa na kware." Na dauke idona daga bisani na tashi, na soma 'yar gala- gala ta. Yana lura da yadda kowa ke tsaye kan kayansa banda ni, da ya mi'ke zaya tafi ya ce, "To sarkin wasa ga kudinki." Sabuwar naira biyar ya bani a mike, a rayuwa ta babu abinda ke burgeni irin sabon kudi, na ce, "Amma na gode, kalleta kar-kar bazan kashe ta ba." Ya ce, "Mai zaki yi da ita?" Na ce, "Ajiyewa zanyi ba zan sashi cikin asusu ba bare har na lankwasa ta." Murmushi yayi sannan ya ce na bashi daya. Ba bashi ya ci rabi ya bar saura, na ce, "Ji fa baka cinye ba." Ya ce, "Na koshi." Da zai tafi ya kuma bani sabuwar naira goma wai in bashi canji na ce, "Wai don Allah kai kuwa a ina kake samun sababbin kudi?" Bai amsa ba yana ta kallona. Na ciro tsohuwar biyar na mika mishi. Ya girgiza kai, "Ba na amfani da Tsohon kudi." Na ce, "Saboda mene?" Bai amsa ba ya ce, "Gobe zan amshi gyada." Na ce, "Toh"Ku san kwana 2 ban ga mu2min ba, sai ranar 3. Yau ma shigar shi ta 'yan gayu kamar kullum. Ya amshi gyada zai tafi ya kuma bani sabuwar 10. Na ce a, ka manta ne kana bi na canji? Ya ce haka ne, to rike wannan don ni in na ciro kudi bana maida su. Na ce ko? Tab, amma dai sun maka yawa ne ko? Ya dube ni ba alamar wasa, ya ce "Mu ne ai muke kera su. Na zaro ido ina kallon shi, cikin matukar mmk "Kana nufin ku ke buga kudi? Ya sake dubana, kwarai kuwa, na Maida hankalina duk a gare shi. Ka ce kana da su lodi? Ya saka hannu cikin aljihu shi ya ciro sabababn dal 'yan naira ashirin da goma-goma na zaro idanu. Tabbas yanzun na yarda na ce kai ko kaji dadinka, ina ma ni ce. Ya ce da me za ki siya? Na ce na farko zan biya kudin makarantana, kuma na dinga sai mana kayan dadi da su nama da mota, su mashin.Kai komai sai na sai mana. Ban lura ba, ashe shi kam dariya na ba shi, ya ce to ai ni kin ga duk na siya abubuwan da ki ka ce, na yarda kam, shi yasa gaka nan dan gayu da kai, ka ta6a zuwa kasar waje? Ya sake darawa, sannan ya ce eh, da yawa ma. Ya tafi ina ta kallon shi. Sa'a da Zaituna wadanda muke tafiya tare dasu, da na basu labarin dan gayun nan na ce ashe sune suka buga kudi kin yarda suka yi. Suka ce to in shi ne me zai kawo shi nan yana karyawa? Na ce shi ne ya fadamuku karyawa yake yi? Suka ce min tun yaushe suka san shi a nan Makarantar. Na ce ko dai yana koyarwa ni na yarda su ke buga kudi, Ga sabbin kudi nan dami a gunsa, Lura da su Sa'a suka yu cewa ba zan yarda da su ba sai suka bar ni. Sau dai suka ce min ni wawiya ce, sai ka ce bn yi zaman aji ba, sunan na gama aji 6 bn san komai ba, na ce naji din. Su Innarmu a da Baba na kuke ina ba su labarin dan gayu mai buga kudi, amma wai sai suka ce zolayata yake yi, nayi duk wani kokari na wai don su yarda da ni cewa gaske ne,amma sun ki. Sai dai na dauki alwashin zan masa tambayoyin da zai gamsar da su. washegari jumma‘a ba mu cika jimawa ba, saboda ana sallah juma‘a a masallacin da ke kallon makarantar amma kin bin su Sa‘a nayi na fake da cewa sai gyada ta ta kare. In tashi yan makaranta tuni sun watse ina ina zaune gaban gyada yar ragowa ce ma, sai kalke kakle nake. Can na hangoshi zai shiga makarantar, ya sanye da wani ubansun yadi fari kar hatta takalminshi da hular kanshi. Duk da yau ce na soma ganin shi da manyan kaya ban kasa ganeshi ba. Da gudu na bishi ina cewa tsaya tsaya ban san sunan shi ba bare na kira. Shiko bai san dashi nake ba a haka mukayi nisa cikin makaran tar sai dai wani ya lura shi nake bi sai ya tai maka ya tsai da mun shi. Na lura yaji mama kin ganina yace, sarkin wasa ina zaki haka? Na tsaya ina haki saboda gudun da nasha yace sannu na ce yauwa, dama kai nake ta jira zan tam bayeka ne. Yace na me? Nace wai dan Allah da takarda kuke yin kudi? Yayi dariya har hakoranshi farare suka fito yace eh, da takarda ne to in na baka zaka iya yi min saboda mutane sun kiyarda ne dani in nace naga masu buga kudi sai ace karya ne zolayata kake yi. Yace zanyi maki in kina so nace innaso kai, to da wace irin takarda kuke yi? Yace ta rubutu nace gobe zan duba jaka ta da in dauko. Yace ba ayi fa da tsohon littafi ko kina son tsohon kudi ne? Nace a a taf na fison sabo yace to shike nan ki kawo sabo nawa za abuga maki yawan kudin? Nace zaka iya min dubu malala gashin tunkiya? Ga mamaki na sai naga yana dariya har da rike ciki nima na soma dariyar ya numfasa ya ce,in ban da abin ki sarkin wasa wane ne ya san yawan malala gashin tinkiya, Na ce to ko dai nawa ne ina so yanda dai ishe ni na gama karatuna. Ya ce,wai dama nan kin yi karatu? Na dube shi, ba na fada maka ba cewa na gama primary? ya ce ban ji ba lokacin da ki ka fada,yanzun JS1 za ki shiga? "Eh tallar da nake ai kudin rijista muke nema, kaga in ka bugo min kudin na daina talla, ina gama secondry har ta gaba in je in fara aiki. Ya ce "Wane aiki ki ke son yi,? Ina nufin me ki ke son ki zama? na daga kaina sama ina nazarin ya ma ake ce musu? Ya ce ba ki san me ki ke so ki zama ba? Na ce, "Ya ma mutanen da ke yin labarai a Talabijin ko Rediyo? Ya ce, " Media ki ke so? na ce yawwa, haka zan zama 'yar media,yayi murmushi, to ni zan wuce, ina kayanki? Sai lokacn na tuna da tirena da kudina cikin ledar gwangwani, na ce to sai gobe. Na tafi ina waiwayanshi, ina cewa kai,wannan mu2min dan gayu ne,ga kamshin turare yana yi. Ranar Litinin tsawo naga ta min,yau kam d murna na iso,na nutsu ban yi wasa ba,saboda wata zuciyar da ke ce min in ya ki zuwa fa, ga shi na zo da sabon littafina, ba karamin damuwa nayi ba da na ga lkcn tafiyarmu yayi ban gan shi ba. Ina kulle gwangwanaye sai gashi, na ce hr na cire rai, ya ce ai zan zo, na ciro littafi na ba shi, tare da cewa wannan takardar ta isa? Ya ce eh, na ce na gode, na mika mishi gyada tare da cewa na rage mishi ne. Ya ce ya gode ya tafi. kai, kuruci dangin hauka, nifa tsakanina da Allah na yarda suke buga kudi. Daga ranar ban kuma ganin shi ba, Kusan sati 2 hr na soma tunanin ya gudune da kudina kun ji shirme. Wata ranar Jumma'a ranar za a yi wa dalibai hutu hr cikin Makaranta muka shiga muna ta ciniki,mun saida mun fito sai na hango shi tsaye gurin zaman mu. Da sauri na isa gurin shi, me bugakudi...... Mukhtar Ismail Muhammad WhatsApp: 08161892123 Sanadin Boko 1-04 Posted by Mukhtar Ismail Muhammad On www.arewarulers.com.ng Under: SANADIN BOKO @* NA Maryam Abdullahi K/Mashi "Da sauri na isa gurin shi, me buga kudi ina ka tafi na daina ganinka? Ya ce aikin kudin ki ne ya 6oye ni, na ce Allahu! Har ina cewa ka gudu. Ya yi dry, na gudu da kudin ki ki ke zato Na ce eh, nima ina dry. Ya ce kai kina da bn dry, to ga kudinki,amma muje gidan ku na bawa iyayenki kada wani ya bi ki ya kwace. Cikin murna na ce to daga nan ma in sun gan ka sun fi yarda. Na kama hanya a kafa ya ce ga mota can zo muje, in kin san hanya direbn mu sai ya kai mu, ba tare da wata shakka ba na ce to. Sam na manta da su Sa'a, sai da zamu shiga motar naji muryarsu,suna cewa ke Hafsatu ki ka sani ko dan yankan kai ne? Na dube shi, shima ya ji amma sai yayi tamkar bai ji ba, na ce ba wani dan yankan kai na shiga motar da dan tirena, shima ya shiga ya ce kawarki fa,shawara suka baki nace tame? Yace kin san ni ko dan yankan kai ne? Duk da gabana ya fadi amma sai na dake nace, bakayi kama dasu ba yace suna da kama ne? Nace oho amma kai bashi bane yace, dama sunanki hafsatu? Nace eh abakin su sa‘a kaji ko da suka kirani dazu ko? Yace eh nace yan bakin ciki ne, dan fa nace masu kana buga kudi sai suka ce mun karya ne, kai malamin makaran tane. Yace gaske ne ni malamin makaranta ne, amma daga yau na gama nace, duk da kudin da kuke bugawa basu ishe ka ba sai kayi koyarwa? Yayi dariya yace bautar kasa aka turoni daga jahar mu. Nace bautar kasa kuma? Yace kema watarana zakiyi in dai kikayi karatun da kike fadi, gwamnati zakiyi wa aiki na wata tara ko shekara. Ban gane nufinshi ba amma nace Allah yasa naga lokacin. Da gudu na shiga cikin gidan mu ina cewa inna fito kiga mai buga kudi ya bugo min inna ta saka hijab ta fito tana cewa ni ban gane wanan shirmen naki ba, ina mai buga kudin? Wannan yarinya da wautar tsiya kike inna tayi turus lokacin da tayi arba da rantsatsiyar motar tace hafsatu aina kika jajibo wadan nan...? Cak! Maganar ta tsaya lokacin da saurayin ya bude motar ya fito kyawunshi yasa inna tunain ko aljani na janyo, ta soma karanta (ayatul kursiyu) zata juya gida na rike mata hannu. Inna dan Allah ki tsaya mana zo muje gurin su tace a a hafsatu muje ciki bana tsamanin wadannan bil‘adama ne nifa nasan banda aljan ke ina kika isa kiga mai buga kudi, sai dai in jabun kudi. Saurayin yatako har gaban inna ya dan rusuna ya gaishe ta, ta amsa tana dan dari dari, nace to wanan ce inna ta sai ka bata kudina inna tayi ta maza tace samari daga ina? Ni fa ban fahimci surkulen da yarinyar nan take yi min ba? Yayi mur mushi ya dube ni jeki kawo min ruwa nasha, da gudu nayi ciki ban saurari inna ba da takecewa in dibi na baba yafi sanyi ina tafiya ya dubi inna yace mama zolayarta nake yi, ni dan bautar kasa ne an turo ni daga Adamawa state, ina koyarwa a makaranantar da take zuwa talla. Yawan wasanta ke burgeni har na shiga sabagarta, sai kuma na fiskanci cewa tana son karatu amma rashin hali ya hana hakan. Dan ta fada mun tana talla ne dan kawai ta tara kudin makaranta. To ni nazo ne in ba damuwa zan taimaka mata don ni daga yau in sha Allahu na bar kaduna kenan, don na gama abin da ya kawo ni, dai dai nan na taho da ruwa na ce masa gashi. Inna tace mika mashi yace a a dama basha zanyi ba bakiga na sha ruwa a mota ba? Nace eh yace to maida. Yaci gaba da cewa dama nawa ne kudin nata? Tace ni ban tambayi nata ba amma lokacin na wanta inaga dubu uku muka kashe? Ina ga ba zai wuce hakan ba. Ya ciro yan daurin nera goma gama guda uku sababbi fil ya mika mata ga wanan mama dan Allah ku biya mata kudin makaranta, ku cika burinta har tazama abin alfahari nan gaba. Allah ne kadai ya san al‘ummar da zasu anfaneta. Innarmu jiki yana bari ta amshi kudi tana ta zubo mashi godiya ma, sai daka tsale nake tamkar yarinya karama, ina cewa shi kenan na huta talla. Innarmu ta harareni tana cewa to kiyi mashi godiya mana, nace na gode yayi murmushi ya tafi yana daga mun hannu nima haka. Sai dai kash nayi mantuwa ban tambayi sunan shi ba, a lokacin ban damu in san sunan shi ba muka nufi cikin gida da murna innarmu bata da rufi, don haka a tsakar gida ta fada musu cewa wani bawan Allah ya taimaka min da kudin makaranta. Wasu suka taya mu murna ciki harda babarmu, wasu kuwa sun nuna bakin cikinsu a fili don Ade ina bayi naji tana cewa, maman abba yau kinji matar nan mu zata rainamawa hankali ta dai tura yarinyar ta maula. Maman abba tace ai shegen son kudi irin na maman hafsatu ya isa, ace mata sai rashin godiya Allah duk fa kokarin mujinta ta raina. Daga can asabe ta sako baki shi wannan mujin nata ai tuni ta gama dashi katsinawa kuma da shegen asiri? Dubi fa fada irin na mutumin nan sai da tasha karfin shi ga kishiya kuma sai yan da akayi da ita Ade ta ce, ayi dai mu gani, kina nan yarinyar zata janyo mata abin kunya, Maman Abba ta ce ta dage sai yarinya tayi boko, za su ga boko ai. Na fito cikin takaici ina kallon su, sai nan da nan suka canza mgn. Asabe ce suna ta zagin ki,wai kina asiri ke Bakatsina,wai zan ja miki abin kunya. Inna tana da fada, balle in an ta6o ta, ta fita da sauri Yayana Umar ya hau ni da fada,wai don ubana ni mahaukaciya ce da zan fada mata, na ce ka ji gulmar da suke yi ne? Hayaniyarsu ce ta fito da mu, Umar ya je yana cewa, Inna ta bari ta dawo daki, nan dai haka gidan kan rikice wani lkcn. Musamman in ana fada kan yara, ko gulma. Innarmu tana da fada kowa a gidan yana shakkar ta6o ta. Bayan komai ya lafa, muna daki ta ce "Hafsatu kin dai ji da kunanki, ina so ki baiwa mara da kunya, ki kare min mutuncinki, kiyi karatunki ki zama abn sha'awa da kwatance na ce to Inna. Cikin kwazo na soma karatuna, kudin dan gayu mai buha kudi ya bugo min sun taimaka min kwarai. Inna tayi musu kyakykyawan adani,sun ishe ni har zuwa lkcn da na gama JS 3, lkcn shekaruna 14 girma ya soma zuwa min 'yan alamu sun bayyana. Na kan ji mutane suna cewa, wai ban cika kyau a fuska ba, sai dai jiki. Yawan fadin ina da diri shi ne ya sani jin cewa ni mace ce musamman in nayi kwalliya. Wata safiyar Jumma' naje fitsari sai naga jini, cikin fargaba nazo har da hawaye nake fada wa Inna. Ta ce, Hafsatu girma ne ya kama ki yau nawa ga watan bature? Na ce 7. Ta ce to duk 7 ga wata za ki ga wannan jinin. Ta iya yiwuwa yazo kafin 7, ko bayan 7, amma duk wata dai za ki gan shi. In kuma ba ki gan shi ba hakan na nufin kina da ciki. "Na zaro ido ta ce ai ba a samun ciki haka sai in kin kasance me wasan banza da MazaNa sauke ajiyan zuciya,don nasan bana yi. Na ce ni dama ba ruwana da maza, ta ce na sani, amma ki kara.sannan ki kara sa tsoron Allahn ki cikin zcyrki. Daga yau din nan an bude miki fayil dinki, duk aikin alkairi ki ko akasin haka za a rubuta miki, don haka sai ki kula, ki kuma san me ki ke ciki. Tun daga wannan lkcn nasa ma raina tsoron maza, nake kuma duba duk wani aiki da zan yi zunubi zai ja min ko lada. Marubuciyar tace'Yan uwa mata zan dan mana wani tuni nan gurin, mu nutsur da 'ya'yanmu muyi musu bayani mai kyau tare da nutsa tsoron Allah cikn zukatansu, lkcn da suka samy kan su a irin wannan yanayin na balaga.....Allah yayimana jagora Ba zan manta da Jumma'ar ba, misalin 4 da mintina na yamma gari yayi sanyi La'asar, nayi kwalliyata da riga da wandon pakistan da Inna ta sai min a gurin wata mai gwanjo. Kore ne kalar lemun tsami da gyalanshi, Sakina kanwata yarinyar Baba kishiyar Innarmu ta ce " Yaya Hafsatu zan biki." Na ce, zo muje gidan kanwar Innarmu zan je Hayin Malam Bello na kai mata kudin dashin sabulu da suke yi. Ko can gidan matan gidan suna ta yaba yanda kayan suka yi min kyau.Dai-dai kan layin Biliya wasu matasan samari suna tsaye jikin mashin, kallo daya na musu na dauke kaina ban kuma kawo komai a raina game da su ba. Sai naji takun tafiya, ana cewa 'yanmata ji mana,maza sun sha yi min haka bana tsayawa, don Innarmu ta fada min karatu basa haduwa da soyayya, kada na sake na kula kowa. Ya zagayo ta gabana Beby saurare ni mana. Na' kalli fuskarshi,sai zcyta ta buga, ina son mu2m mai kyau, daga ganin shi dan gidan 'yan gayu ne. Na harde hannuwana a kirjina, ya sake dubana daga sama kuwa gsa kasa, "Wow! Ya sunanki?" na ce "Hafsatu." Ya ce "Nice name, Hafsy ina ne gidanku?" Kawai sai na samu kaina da yi masa kwantance, can kasa muke Abuja Road, layi na shida marar kwalta, kana zuwa layin ka ce ina ne gidan yawa za a nuna maka. Ya dan yi shiru don ya fahamice a geto take amma sai yace zan zo anjima ko gobe zan samu ganinki? Nace eh yace to sai kin ganni na tafi ina wai wayanshi sakina tace yaya hafsat mijinki ne? Cikin yar dariya nace eh mijinane wasa ne ya ruda ni na kasa sukuni, tare da boyiwa innarmu don kada ta hanani fita, sai dai har tara banji ance ana kiran hafsa ba,har fita nayi gurin bakin titi ina tunanin wai ko yazo bai gane layin ba na dawo daf da zan shiga gida na ganshi tsaye kofar gidan mu. Wani sanyi naji acikin zuciyata, sai na soma tunanin zan jene na ce mashi gani ko ko ce mashi zanyi ni kake nema? Sai na yanke shawarar na bi ta gabanshi, har na daga labulen buhun da yake kofar gidadanmu zan shiga, sai naji yace hafsy sai na tsaya tare da sauke a jiyar zuciya, sannan na wai wayo na tako cikin irin tafiyar da ban taba sanin na iyata ba. Duk da yake dare ne a kwai kwan lantarki a kofar gidan, yace nafi minti 5 ina jiranki nace ina yini? Yace lfy da farko dai sunana munnir jafar dalibi ne a (A B U) zariya ina shekara ta 2. Sanan muna zaune ne a nan makarfi road son munnir ya kara shiga ta, don a rayuwa ta inaso in auri miji dan boko nace ni kuma na gama js3, yace me ya hanaki cigaba? yanayin garin ne. Haka muka ta fira sam bansan dare yayi ba har 10 ta gota ba sai da naji karan raidiyon baban mu ya nufo gida. Ya tsaya tare da cewa wacece nan? Ke hafsatu me kikeyi haryanzu? Na dubi munir nace ga baba na. Ya cire hular kansa hana sallah yace ina yini baba? Ya dubeshi lfy lau zo ki shige muje, nace to sai anjuma yace zan zo gobe nace to. Tun kafin mushiga daki baba yake min fada tare da tambayata wanene wannan yaron ya dame kugu? Nace dazum ne muka hadu dashi. Hayaniyar shi ne ta tashi inna daga dan baccin da ta soma, tana tam bayarshi lfy malam kake fada da tsohon daran? Yace amma dai ke sakaryar uwace, 10 ta wuce yarinyarki tana can tana zance da wani kato ke kuma kin hamgame baki kina bacci Inna tace hafstu na can tayi baci tuni dakin babarsu, ba ita kagani ba ita da bata fita zance ma yace to ga tanan ma bare ki karyata ni. Inna tace hafsa zance kika fita? Ya mukayi da ke? Baba yace ni dai tashi ya turo mun iyayensa dama ni burina in aurar da ita. Inma shi bayi zaiyi ba akwai mutane da dama sun min magana. Inna tace je ki kwanta itama ta maida kai ta kwanta alamun zancen baba bai shigeta ba. Da safe ta tsareni da son jin wajen wa na fita? Nace inna wlh jiya ne fa da kika aikeni ya ganni shine yazo. Tace amma nace maki ki fita hanyar samari ko? Kin san babanki matsawar zaki rinka tsayawa zance kina son karatun nan zaki barshi ko nace inna naga shi wannan yana son karatun, don su gidansu yan boko ne. Maman shi da baban shi duka aikin gwamnati sukeyi yace min jami‘a yake yi (A B U) zariya tace to ni dai banaso kurinka tsayawa nace yama ce zai bani kudi nacigaba da karatu na. Inna tace to indai ko haka ne sai dai kitafi makarantar kwana, saboda kin san babanku sarai. Koda munnir yazo washegari, haka na zauna na fada mashi komai dangane da ma haifina game da kin boko. Yace taf kice cutarki zaiyi? Tun kina karama zai kasheki da aure ai gaskiyar innarki ne kada ki yarda. Nace kudine matsalar mu sai dai in shiga ta kwana yace haka ne, yace zan baki kudi bari dad dinmu zai bani kudi in yadawo tafiya. Nayi ta masa godiya yace a a shidai abinda zanyi mishi kada in saurari kowa kuma na saki jikina dashi, nace kada yaji komai cikin sati 1 na gama yarda munir na sona, nima kara sonsa nake duk zuwa yakan zo min da wani abu, turare ko dan zobe ko dan wani abun kwalama. Bana manta ranar lahadin da yazo min sallama zai koma makaranta ya kuma bani kudi naira dubu 20 har kuka nayi mashi dan bana so rabuwa dashi. Ranar shida abokin sa sukazo wai shi faisal, kawai sai naji munnir ya rumgume ni, wani abu naji tun daga tafin kafata har tsakiyar kaina,shiko sai cewa yake inyi shuru in daina kuka hannun shi kuma na zaga sassan jiki na, fadan inna ya fado min cikin rai inda take cewa. In kula da kaina wasan banza da namiji zai iya sawa in sami ciki, nayi sauri na janye jiki na daga gareshi, yasa hannu yana share min hawaye muka yi ban kwana na shiga gida. Suna tafiya faisal yace munir dagaske kana son yarinyar an? Munir yace da dai nazo na dan kwashi rabo nane, sai kuma na gane yariyar ba yar hannu bace. Sannan kuma nasamu kaina da sonta na gaske faisal yace ka dai san dadinka ba zai barka ka auri yar geto ba ko? Yace kai nif zan zaba da kaina ba zan yarda ace min naje ga yar wani ba. Nikam ina shiga gida muka soma murna da inna, nan muka shiga tsara yanda zamuyi wa baba bayanin munir. Washegari inajin inna tana cewa baba wai kananta da yayansu sunce ta kaini zasu nemmar min makarantar kwana. Baba yace a a shifa bai yarda ba, tace yayi hakuri kwana nawane zan gama? Baba yace nifa ba kin karatun nake ba, nafiso tayishi a can dakinta inaso kisani har in yarinya ta soma tsayawa da saurayi mafi kyawu shine ayi mata aure. Inna tace za ayimata malam, wannan yaro da ka ganta dashi shene yake son auranta na lura itama tana sonshi yace to ba sai ya turo magabatan shi ba muyi zancen manya! Inna tace yo shima ai karatun yake sai ya gama itama ta gama kafin nan. Shuru yayi bai sake tankawa ba shurun ba yana nufin ya yarda bane, shurunsa yana nufin mukarata can shi ba ruwansa. Kwana 2 tsakani muka shirya ni da inna muka nufi manunfashi kananta kawu sha‘iabu da kawu bashir harda wanta kawu kabiru sun sunji dadi sun kuma tsaya har saida nasamu shiga ss1. Haka baba ya hakura ya zuba muna ido, na cigaba da karatu cikin nasara da kwazo, yan gidanmu kam da makota sai gulma da tsegumi, ba mu damu ba. Fatan inna shine inzama abin kwatance nan gaba. A duk lokacin da nazo hutu munnir nazuwa, haka duk lokacin ziyarar dalibai in yana da sarari yakan zo. Hidimar karatuna shi yake yinta haka nan duk wani kaya na yan mata shi ne yake siyan min, wanan shine yasa na kara sake wa dashi. Matsalata dashi son taba jiki na, kawai lokacin da wani hawaye yayi min wai in bishi muje dakin wani abokin shi, niko nace a a muji tsoron Allah ba don son da nake yiwa munnir ba a tuni na hakura dashi. Cikin haka na gama karatuna na secondary. Na dubi likitar idanuna suna zubar da hawaye nace, anty ko lokacin da na gama karatu na baba ko gai suwa nayi baya amsawa, kannena yaran kishiyar mama na guda 2 ya musu aure. Sannan karatuna kafin na tahoshi sai da ta kai yace in har wani abu ya biyo baya abakin auran innata, sannan in nemi uba..... Kuka ya kwace min mai karfi, ina fadin na shiga ukuna zan kashe auran iyaye da kaina. Munir ya cuceni fyade yayi min anty ki taimaka ki cere cikin nan. Yan gidanmu da yan unguwarmu duk dariya zasuyi mana. Kalo kawai likitar keyi cikin tausayi har nayi kukana mai isata na gama ba wanda ya bani hakuri. Daga ita har asabe tace to, ke hafsat ki koma makaranta gobe kizo, keko asabe ki kwana nan nace anty don Allah nima zan kwana nan din, ko naje makarantar ba zan iya komai ba, tace shikenan. Ta mike sannan ta nuna mana wani daki, ku shiga nan kuyi sallah da komai a ciki. Ba tare da ta jira amsa ba ta nufi dakin ta, kaiwa da kawowa kurum take yi. Ta ina zata bullowa wayanan yara? Sam bazata cire cikin ba, bazata kuma bari suje su cire su zubar ba. Ta lura Asabe tafi saukin kai don haka da ita zata fara. Yanda naga rana haka na ga dare, alwaula kawai nayi na yi nafila. Daga bisani na koma istigifari, washegari bayan ta lalabemu mun karya, sai ta bamu wasu magun guna tace kada in damu in koma makaranta insha, suna da karfi na sati 3 ne, ta tabata cikin zai fita nayita godiya na komo. Sai da daktar hindu ta sami shugabar kungiyar kare hakkin bil adama. Tayi mata bayanin komai game da halin da asabe ke ciki, Shugabar Hjy Adama ta ce, to za su samu Hjyr Yasir su fara neman sulhu, in ta ki kuma to za a maka Yasir a kotu. Doctor Hindu taji dadin haka, don haka ta tambayi Asabe yaushe aka fi samun Hjy Mairo a gida? Asabe ta ce Lahadi da rana, sauran ranakun sai dare ake samunta. Sun same ta cikin Kasaitaccen falonta tana shan kayan Marmari, suka sanar da ita dalilin zuwansu. Ta ce, sam ita dai ba danta ba, ai ta ja mata kunne, nan suka nuna mata cewa zata amsa kira a kotu gobe Litinin. Yasir na dawowa ta hau shi da fada, ya ce tayi hakuri sharrin shaidan ne, ta daka mishi tsawa ta ce, yi min shiru,wawa kawai. Ta tausasa murya a bin da nake so da kai, za su shigar da mu kara, saura in mun je ka saki baki ka nuna kai ne, ina so ka bata rai ka hade fuska ka nuna sam ba ka sam ba ka san zancen ba. Ni kuma zan tsaya maka, Babanka zai tsaya maka, domin duk Alkalin garin nan ba wanda zai ketare bukata mahaifinka. Yasir cikin murna ya ce, "To Hjyta. A daran ranar ta kira mahaifin Yasir ta shaida mishi abn da ya faru, wai me aikinta tayo ciki tazo ta ce Yasir ne, yanzun haka kungiyar kare hakkin dan adam ta shigo cikin lamarin sun ce za su shigar da kara,Ni kuma na ce su shigar, ya ce amma ba ki da hankali, kina fa da masaniyar ina da burin tsayawa takara a siyasa mai zuwa, ko kin manta? Kin san cewa abokan gaba za su iya fakewa da wannan su ci zarafina har suyi nasarar kada ni? Ta ce to yanzun yaya za'ayi? Ya ce bani Yasir din a waya, ko ba ya kusa? ta ce ba ya kusa, ka kira layinsa. Yasir ya daga kiran wayar Mahaifinsa, ko gaisawa ba su yi ba ya jeho masa tambaya, gaya min gaskiya kai ne kayi cikin? Yayi shiru, fada min na ce kai ne ka min shiru? Uban ya fada cikin daga murya. Yasir ya ce "Dad ba zan kara ba, Mahaifina ya ce, Ok kai ne kenan? Ya ce Tsautsayi ne. Alhjn yayi shiru yana nazarin abn yi. Can yaja tsaki, in ka kuma ranka zai 6aci fiye da zatonka. Abn da zan maka sha mmki, kila ma kayi zaton ko ba ni ne na haife ka ba. Ya ci gaba da fada. In ma ba iskanci ba duk nawa ka ke 25 years amma ka iya jarabar mata? Yasir ya dinga ba wa Mahaifin shi hakuri, Alhjn ya ce shi kenan, ya kira Hjy Mairo ya ce, kada su shiga kotu, su nemi sulhu duk yanda aka yi su fada mishi. Washegari da kanta taje ofishin shugabar kungiyar don neman sulhu. An kira Dakta Hindu sun zo tare da Asabe, sharadin 2 suka gindaya wa Hjy Mairo, aka c ta za6i daya.Na farko ko dai dan nata ya auri yarinyar bayan ta haihu, na 2 kuma in ba zai aure ta ba, to zai dauki nauyin cikin tun daga yanzu hr zuwa lkcn da za a haife shi a yaye shi. Daga bisani su dauke shi. Hjy Mairo ta nemi saukin Asabe ta rike danta za su ci gaba da mishi komai,amma shugaba ta ce a'a ba za su yarda ba, domin Asabe in ta samu miji aure zata yi. Ba zai yiwu ta tafi da dan wani gidn wani ba. Nan ta take ta kira mijinta ta mishi bayanin komai, ya ce su dauki za6i na biyun in yaso zasu yi shawara in ya dawo. Ta ce to. Nan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa hannu Daga nan ta tafi........ Mukhtar Ismail Muhammad WhatsApp: 08161892123 SANADIN BOKO 1-5 Posted by Mukhtar Ismail Muhammad On www.arewarulers.com.ng Under: SANADIN BOKO Nan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa hannu Daga nan ta tafi. Likita ta dubi shugaba ta ce, " Amma ko da Asaben zata ba su dan su sai an sake zama, don kada suje su halaka shi, kin san mutane ba imani. Shugaba ta ce, wannan ka'ida ne, yanzun ki dauki yarinyar nan ki koma da ita gidanku,gobe zamu je mu samu iyayenta. "Doctor ta ce, Insha Allahu." Washigare suka nufi kauyen kurje, iyayen Asabe sunyi murna da zuwanta, amma da suka ji dalilin zuwan nan suka soma kuka tare da yiwa Asabe Allah ya isa. Asabe na ta kuka, Doctor suka yi ta bai wa iyayen baki tana rokon su yafe ma Asabe. Da kyar suka shawo kan su, sannan suka yi musu bayanin komai game da yanda suka yi da Yasir. Mamanta ta ce, to ni dai ba za ta zauna min a nan va, kauyen nan suyi ta zagina suna yada ni 'yata tayo ciki. Ta sake rushewa da kuka, Likita Hinda ta ce zan tafi da ita in zauna da ita hr ta haihu, in ta yaye sun dauki dansu sai ta samu miji tayi aurenta, ko a nan ne. Maman Asabe tana ta gdy, shi ko Babn tunda yayi waje hr suka tafi bai dawo ba, suka dauko hanya bayan sun ba uwar Asabe sha tara ta arziki. ***** ***** ***** Sati 3 daidai babu alamun cewa cikin jikina zai zube,duk da cewa kusan kullum sai na je gun Likitar, ita kuma sai tayi ta kwantar min da hnkl, wai in jira sati 3n su cika,don ba za ta iya bani wani magani ba tunda aikin wannan bai kare ba. Sam lkcn bn san yaya Asabe take ciki ba, don nima ina cikin nawa tashin hankalin, gara ma Asabe. Bana iya cin abnci,yunwar ma ba jin ta nake ba,karatu kuma ina mantawa cewar shi na zo yi, don ko na shiga aji ba na fahimtar komai, ga laulayi mai tsanani. Munir kuma bai kuma zuwa ba,wayar ma sau 2 ya kira ni, cikin sati 3 da likita ta bani yau kam ko sisin mashin bani da shi, a kafa na sabi hanyar zuwa gidan Doctor. Asabe tare da me yiwa Likita aiki wata gyatuma ana kiranta Yalwa, su na samu. Asabe ta ce min Likita tana cikin asibiti zama nayi don jiranta. Sai uku da rabi muna sallar La'asar ta shigo, da fara'ar ta tare ni tana cewa? na dai san bukata ta biya tunda ban gan ki ofishina ba. Kamar ko yaushe,sai hawaye suka soma zuraro min, na ce wlh Likita ya ki fita, ni dai a kwakule min shi. Ganin tashin hankalin da na shiga, sai ta lallashe ni da cewa, nayi hakuri bari ta dan huta. Na koma na zauna ina kuka,wanda ya zama abn yina koda yaushe, tun da Asabe ta bani lbrn yanda aka kwashe da tata rigima hankalina ya kara tashi. Addu'ata Allah yasa nima kada Likitar ta ce haka za a yi, domin zancen cikin ne sam bana kaunar Innarmu taji bare Babana. Sai shida saura ta fito, na dora sabon kuka Nan ta hau ni da fada,wai in tashi ni tafi kukana ya min magani. Na share hawayena, tare da bata hakuri,ta ce "Hafsatu! Ina son ki bani aron hankalinki, ki saurare ni, na ce to. Ta ci gaba da magana. Cikin nan naki ba zaya fita ba, domin na baki duk wani magani mai karfi,amma a banza. In ko ki ka ce a kwakule shi akwai yiwuwar ki rasa ranki. Da sauri na ce gwara na mutu zan fi son akai gawata ga iyayena fiye a kai ni gaban su da ciki. Ta ce, To naji amma kin shirya abn da za ki fada wa Mahalccinki? Kin mutu gurin kisan kai ko in ce ma kin kashe kanki? Kin fi son kunyar lahira fiye da ta duniya? kada ki manta, kin ce fyade ya miki ko? Na daga kai cikin kuka, ta ce to ki dauki wannan abn a matsayin kaddara. Kada ki manta, Ubangiji ya kan jarabci bayinsa don ya gwada Imaninsu, ke me zai hana ki rungumi kaddara? Allah ba ya dora ma wata rai abn da ba zata iya ba, Zufa ta rufe ni, na ce Likita ba za ki gane ba ne.Innata da Babana auran zai mutu SANADIN BOKONA. Alhakin Babana ne kash! Hakika da na san haka zata faru gare ni da na yarda Babana ya aurar dani, in yaso sai in ci gaba da karatun acan gidan mijina. Likita ta ce, Yanzun dai shawar da zan baki ita ce, kije ki samu shi saurayin ki tunda yana sonki, ku sulhunta, in kin haihu a daura muku aure. In kuma kina son sako hukuma kamar na Asabe to in sako, za su tsaya miki a kwatar miki 'yanci. In ta kama hr kotu kuma ko su waye iyayenshi. Na ce A'a zan fi son in same shi muyi magana don bana son asirina ya tonu a unguwarmu. Likita ta ce, yauwa, in kun sasanta ni kuma zan fahimtar da iyayenki, na rike kai, Boko! Boko!! Na jajirce sai nayi boko,yanzun kuma gashi tun ban je ko ina ba bokon na tsane ta. Likita ta ce, "Hafsaty duk wanda ya dauki boko sama da aure a karshe sai yayi nadama, saboda halin da ki ka shiga ina son ki kwana a gidannan anjima zan baku lbrna, don ki san kinyi kuskure kema." Tara na dare da 'yan mintina Likitar ta shigo sanye da kayan bacci masu kauri riga da wando, tire ne a hannunta dan karami mai dauke da kayan marmari, lemo da ayaba da abarba. Ina zaune zugum kan sallaya Asabe na kwance a tsakar daki ta dubi Asaben "Tashi! "Tashi!! Tun yanzy kin soma bin sanyin kasa? kada na kuma ganinki.Asabe ta tashi, Likitar ta ce In bacci ne ki hau gado mana. Ta zauna bakin gado ta turo mana plate din kayan marmarin bayan ta dauki abarba guda daya dama ina jin bakina babu dadi sai shiga bayi nake ina zubar da miyau Na dauki lemu guda daya ina dan lasa, Asabe ma ta dauka. Likitar ta dube ni Tun ranar da naji lbrnki naji ina son in fada miki nawa. lbrn. Amma kafin na fada miki ina son ki sanar da ni daga ranar da ki ka fara ganina zuwa yau me ya birge ki a tare da ni? Na gyara zama, Na farko iliminki,sai kyan halinki,ga shi kina da kyau,ke ba kya tare da matsala kina da kudi. Tayi guntun murmushi,sannanta dubi Asabe ta ce, Asabe ban yi kama da mai matsala ba ko? Asabe tayi murmushi. Anty ai ke ba ki hada hanya da damuwa ba, bare matsala. ke kam kin ji dadinki. Likita tayi shiru na dan lkc sannan ta ce. "Sunana Hindu, mahaifiyata Bafullatana ce, mahaifina yana da kudi sosai,don lkcn da aka haife ni ma yana matsayin Sakataren Gwamnati. Mun taso cikin daula da gata, haka nan muna da kyau 'yan gidanmu tamkar mu ne muka hallice kanmu. Yayyena 2 maza,sai kuma kannena guda 5. Mu 8 ne gurin mahaifinmu, amma a gurin Mamanmu mu 5 ne, Kishiyar ta ke da 3. Tun da na taso nake da tsananin son BOKO burina kullum in zama Likita,wannan yasa mahaifina ke matukar sona,don shima dan bokon rikau ne. Shi irin matanan nan ne wadanda za su iya hana cikinsu su ba ma boko,takarda komai tsadarta in dai ta boko ce zai siya. Wannan tasa nake zaton dama an halicce ni don nayi Boko. Lokacin da na gama secondary ina da shekara 18, kyawuna ya kara fitowa Nan fa samari suka min ca 'ya'yan manyan mutane,masu kudi da sarakuna.Ni kam lkcn wani faifai na bude na walakanta samari, don in fito in zage saurayi ko dan wanenr baya damuwata.Bana manta wani saurayi Nasir,Babanshi shi ne Gwamnan jiharmu wancan lkcn tamkar zai yi hauka don sona, kullum sai ya zo gidanmu ya min kuka,amma na ce ni fa sai na zama Doctor. Babana ya daure min gindi, ina ta tsulawa samari tsiya. Yayuna maza sukan suna son aure,mma Babanmu ya ce suma ba yanzu ba. Amma shi a wannan lkcn ya sake dallo wata amaryar wadda bata wuce sa'a ta ba.Sam ban damu ba, Su Hjy kam ransu ya 6aci,haka yayuna. Babban sai ya shiga dibn mata yana kawo su wai don Babanmu ya gani ko zaya mishi aure,amma sai Baba ya kira shi yana zagin shi. Abn da in na tuna yake bani mmk lkcn Baba hr d cewa in zya nemi matan shi yaje can ya nema,amma ya daina kawo masa gida. Na ce Alhj fada zaka masa ya daina,ya ce kyale shi Hindu, yaje yayi ta yi,wata rana kan shi zaya bari. Ni dai har na tafi Jami'ar Ahamadu Bello,ba suyi auran ba.Karatu gurina ba sauki,sam bana wasa da BOKO. Shekarata 3 a Jami'a sannan aka yi wa yayuna aure, shima da kyar suna ta hada Babanmu da mutanen da yake jin kunya. Kwanci tashi na kammala karatuna,tsawonshekara 7. Lokacin ina da shekara 25. Saboda kwazona, na samu damar zuwa wani kwas kasar Germany na tsawon shekara 2. Hjyta hr d kuka,don bata son tafiyar burinta in yi aure,amma na kekasa kasa na ce ko na gama karatu sai na fara aiki. Haka kuwa, ina gamawa ban jimaba na soma aiki a babban asibitinmu a matsayin babbar Likita. A lokacin Shekarata 30 babu kadan,sai a wannan lkcn ne hankalina ya dawo jikina. Nayi boko na zama Likita,yau gani inna aiki. Nan fa maza suka sake min ca! amma duk wanda na ta6a babu na aure,sai dai in zan yarda a lalace,daga wanda zai ce in zo in raka shi Abuja,sai me cewa in zo in raka shi Dubai. Da na nuna ba haka nake ba, sai na dinga nemansu daya-bayan-dayaina rasawa,daga karshe duk suka gudu. Lokacin ne kuma idona ya raina fata,wasu suka dan soma zuwa amma fa ba yaro,don ko wani ma zaya girmi Babana, na ce tab, ni kan ai saurayi sabon jini. Kafin shekara na nemi suma tsofaffin na rasa.Bana manta wani dattijo da ya soni na ki, sai gashi ya kawo min wata 'yar yarinya ba za ta fi sha takwas ba, ba ta da lfy tana laulayin ciki. Ya ce min, Matarsa ce. Sai na soma tunanin cewa in nemo samarina na da mana,duk wanda na bncika sai in samu lbrn cewa yayi aure. Hankalina ya tashi matuka, yanzun gurin mu2m daya nake sa rai,wato Nasir wanda ya soni tamkar ransa, duk in da zan samu lbrn Nasir naje amma bn samu lbrnshi ba. Wata safiyar Asabar, misalin karfe goma na safe,na nufi supre markte don siyan kayan shafa, domin nawa sun kare. Ina sa kafa daya kan na dago dayar,wata 'yar kyakkyawan yarinya 'yar kimanin shekara sha biyo ko sha daya ta rugo da gudu daga ciki sai ko ta rungume kafata tana cewa . Anty 6oye ni Fadil za ya kwace min (Teddy)na. Na daga ta sama,daidai lokacn da yaron ya iso, daga gani kaninta ne yana da kiba. Ya ce, Anty nima ki ce ta bani boll dina. Na dube ta, ina boll dinsa? Tana dry ta ce, Anty boll dinsa fa tana mota. Na ce to dauko masa, zan sauke ta ta sake kankame ni. Anty Fadil yana da karfi zaya ture ni ya kwace (Teddy) na. Dry na ke t musu, ga shi sai naga sun shiga raina, na ce to muje in sai maka wata boll a ciki. Muna isa daidai gurin kwallaye na ce za6i wadda ka ke so, yarinyar ta ce Anty nima zan kara (Teddy) daya. Muryar Babnsu naji ya ce, sannu da kokari sun dame ki ko? Ina daga ido na sauke kan Nasir, da sauri na ce Nasir! Da alama sai lkcn ya gane ni, ya ce a'a Hjy Hindu BOKO uwaka ubanka ya karatu? Sai naji tankar ya min habaici ne, na ce Alhmdulillah, mun gama hr na soma aiki,ya ce lallai kam buri ya cika, na ce yaranka ne wadandan? Ya ce, eh Fadil da Fadila,sai kanwarsu Yasmeen. Na karkata kai tare da cewa, Allah ya raya su. Ya ce Amin. Na ce, yanzun kana ina ne? yace muna Abuja ne mun zo hutu ne, ke fa? kafin nayi magana wata mata kyakkyawa ina ga zan girmeta ta iso tana sanye da after dress me shegen kyau. Ta ce Beby ka gan su? Ya ce ga su nan sweet heart, ta dube ni ta yatsina baki tare da cewa, wannab fa? Ga mmkina sai na ji ya ce,Ina tsohuwar budurwata Hindu,? To ita ce wannan. Nan take ta watso min wani mummunan kallo, sannan ta figi yaranta gami da cewa, mijin mace daya zo muje. Yayi murmushi tare da daga min yatsu 2 gami da cewa bye. Ban iya tsayawa siyan komai ba na fita. A gida ma ina shiga kai tsaye dakina na nufa,na fada kan gadona ina kuka. Tambayar kaina nake, wai dama gaske ne da Bature ya ce dama sau daya take zuwa ma mu2m a rayuwa? In ko haka ne na cuci kaina na bar damata ta wuce. A ranar ne na soma tsanar BOKO akida, tun daga nan na koma ga Allah, ko yaushe nayi sallah addu'ata ita ce Allah ya ban miji. Kawayena, sa'annina duk sunyi aure da yaransu,kuma bn tsere musu a karatu ba,tunda aina aiki suma suna aiki. Amma sun tsere min don suna da aure ga kuma 'ya'yansu. Doctor Hindu ta dube ni, Hafsatu kin ganni nan da kama aikina yau shekara goma sha biyu kenan,amma babu miji. Har Malamai na shiga don kawai in samu miji. Daga wanda zai ce Aljani ya aure ni, sai wanda zai ce asiri aka mini,suka yi ta cin kudina suna min karya, daga karshe naga babu wani ci gaba na watsar da su. Yanzu na rumgumi kaddarar da nawa kaina, mahaifina ya rasu shekaru hudu da suka wuce abin da yasa nabar gida katsina na dawo nayi asibitin kaina shine, kannena yaran amaryar babanmu duk sun raina ni gashi ba mu cika shiri da hajiyata ba. Shiyasa da aka raba muna gado na yo nan na gina asibiti da gidana, sai dai ina zuwa gida kan lokaci in duba su hajiya ta. Share hawayenta nima sharar kwalla na ke tayi, dan murmushi me kika fahimta ko nace wane darasi kika samu cikin labari na? Nace na farko ba kyau wulakanci, sannan mu daina sanya boko ya zama gaba da aure kamar yanda nima nayi. Tace hafsatu naki mai saukine dan ke kin kama saurayi shi ne dai wanda kika kaman ya cuce ki. Amma ni abinda nayi saboda boko! Ta jin jina kai sanna tace ko rabi ban fada maki ba kuma halin da nake ciki yanzun nima na kirashi SANADIN BOKI, nace auty haryanzu baki wuce aure ba. Tace to in ban wuce ba hafsat ina mijin? Kwata kwata na daina burge maza, sam ba sa jin sha‘awa ta sai yan yara wanda da nayi aure kan ka ida na rantse miki hafsa da yanzu inada kamarki koma wanda yafiki don haka sha warata dake ki daure ki haifa dan cikinki baki saniba ko shi kenan kwanki a duniya. Sannan kiyi aure tun da kuruciya, aure ba zai hanaki boko ba kamar yanda mahaifinki yace. Magana daya zan fada maki, kada ki sake yarda saurayi ya taimaka miki game da komai na kudi, zai iya anfani da hakan ya cutar da ke, duk da nasan akwai masuyi don Allah. Asabe da ke gefe cikin tagumi sai yanzu ta tsoma baki, anty wallahi ban taba zaton kina da matsala ba, duk kalon da nake maki mijinki da yaranki suna kasar waje. Maganarta sai ta dan bamu dariya. Har likitar ta barmu ta koma dakin ta ban daina mamakin lbr ta ba, duk kyanta duk kudinsu duk bokonta ta kasa samun miji lalle kuwa boko yaja mata. Wata zuciyar ta ce min ba boko bane wulakancinta ne ya jamata, koma mene yanzu na fiskanci aure yana sama da komai. Washe gari gida na shirya wucewa kaduna, sai dai kudin mota bani dashi amma ba zan iya fada mata ba. Dan haka nayi shuru dari biyar ta bani wai nasha ruwa a hanya. Makaranta na koma na canja kaya na dauki kwalin wayata na nufi kasuwar masu waya ni dai ban tsaya ciniki ba, dan ba a cikin nutsuwa nake ba, yace dubu 6 inji mai siyan wayanr, bani kudin kawai nace don na kosa insami munir inji yadda zamuyi. Kai tsaye gidansu na dosa ko unguwarmu ban sauka ba, koda mai gadinsu yace min sun fita da maman shi sai nasami can gefen gidan na zauna. Ko shekara zasuyi sun dawo su same ni, na fada cikin raina. Kusan awa 3 sanan motarsu ta dawo tayi hon, mai gadinsu ya bude ban bata lokaci ba na mike na rufa musu baya. Daga inda nake tsaye ina hango kannanshi mata suna sanye da gajerun wanduna, kai ba dan kwali suna ta shiga da kaya. Dayarce ta hangoni sai naji tace mom ga wata can ko mai aiki ce? Matar ta waiwayo, kamanninta sak da munir haka ma kannanshi. Ta nufoni lafiya? Warin munir yayana ya aikoni, tace wai me? Nace abokinsa ne zan amsar masa sako ne, sunyi magana da munir din. Tace ok ta nufi ciki tana kwala mashi kira. Yafito daga cikin gida yana cewa yes mom.... ganina yasa shi yin wani turus! Tace gawata can wai yayanta ya aiko ta." Da sauri ya ce, "Oh na gane sako zan bata." Ya iso gurina fuska daure, "Lafiya Hafsatu kika biyo ni gidanmu?" Na ce, "To ciki fa bai fita ba." Da sauri ya dora yatsanshi a lebe tare da cewa, shishsh. Ya nufi gefensu gami da cew Zo. Muna shiga ya ce, "Kina nufin cikin bai fita ba?" Na ce, "Wallahi." Ya ce, "To ki koma gida zan zo anjima da dare in kaiki wani asibitin a fitar da shi, wannan bata san aikinta ba." Na ce, "A gaskiya ba zanje a kasheni ba, don Likitar tayi duk wani kokari don ganin ya fita amma abin ya ci tura. Ta kuma fada min in na matsa cewa sai an cire to zan iya rasa raina. In je in cema Ubangiji na me?" Ya ja tsaki, "To me kike nufi?" Na ce, "Shine na zo mu san abin yi." Ya ce, "To me kike ganin za'a yi?" Sanyi na ji cikin raina, Allah ya sa ya yarda na ce, "Ina ga mu hakura in zauna can gidan Likitar, ko Inna ba zan fadawa ba in na haihu sai muyi aure." Ga mamakina sai na ga yana dariya, a zato na zancen ya masa dadi, kuma shawara ta ta shige shi. Amma sai naji ya katse tunani na da cewa, "Amma ban taba sanin baki da hankali ba sai yau. Kina zaton ko aure na yi yanzun nan da shekara goma zan haihu?" Ya girgiza kai, "Ba zan haihu ba, saboda haka dole ne a cire wannan cikin, in kuma kin dage to kije can ki nemi Uban danki." Da sauri na dube shi, "Munnir ka san me kake fada?" Ya ce, "Eh, ina da ja kan wannan cikin, cewa nawa ne. Daga sau 1 shima ba cikin kwanciyar hankali ba amma shine ciki zai shiga?" Bakin ciki ya hana ni magana, idanu kawai na tsura mishi, shima ni yake kallo cikin harara gami da daure fuska. Na ce, "Allah ya sani ni ba mazinaciya ba ce,,,,,,,,," Kuka ya kwace min, "Kai ne ka soma keta min mutuncina, ka raba ni da 'yan matanci na, yanzun kuma ka bini da sharri. Allah ya isa tsakani na da kai." Ya matso kusa da ni, "Zan mare ki in kika zage ni, banza butulu. Duk taimakon da nayi miki da kokarin da nayi miki amma kin kasa gode min, shashasha, Kin zata zan kashe miki kudi a banza ne tsawon shekaru? Ki sani in kin ga kare yana shinshina takalmi to dauka zai yi, ni ba ajinki bane don ki sani." Kuka mai karfi ya kwace min, "Allah ya isa Munnir, dama yaudarata kake yi kace zaka aureni?" Ya yi 'yar dariyar mugunta, "Kin dai yaudari kanki, to ai ni ne ma zanyi Allah ya isa tsawon shekara 3 zuwa 4 ina miki bauta ke da me kika taba saka min?" Ban san lokacin da nayi kukan kura na shako wuyanshi ba ina kuka ina cewa, "Allah ya isa." Shi kanshi yayi mamakin yadda ya so kwacewa daga jikinshi ya kasa.Muryar Mom dinsu muka ji tana cewa, "Lafiya? Ke, ke sake shi mana me ya faru?" Na kasa magana sai wani irin kuka nake yi ina fadin, "Ya cuce ni." Ta dubi Munnir, "Me kayi mata?" Ya ce, "Ban fa ko sanya ba daga aiko ta gurina ta shakeni wai na mata ciki." Wani kallo Mahaifiyarsa ta watso min sannan ta nuna ni da yatsa gami da cewa, "Ke! Shiga taitayinki, tafi can ki nemi wanda ya miki ciki." Cikin tsananin kuka na ce, "Wallahi shine ya min fyade. Kuma da shi muka je asibiti Likita ya ce ina da ciki." "Ke!" Ta kara daka min tsawa, "Fita a nan." Na ce, "Nifa ba inda zani sai dai ya san yanda zayayi da ni......." Saukar mari na ji, sannan ta ce, "Fita ko in kirama Iyayenki 'yan sanda." Ta fita da sauri tana kiran Baba megadi, ya iso ta nuna mishi ni, "Baba fita da wannan bana son in kuma jin ko labarin an ganta a layin nan, in haka ta faru har da kai zan hukunta." Ya dubeni ya cem "Mu je." Na tsaya ya ce, "Shige mu je mana ina magana kina kallona." Na dago jajayen idanuna na kalli Munnir, wani murmushi ya saki na mugunta sannan na ce, "Akwai Allah." Na fita megadin yana biye da ni sai da muka fito ya ce, "Yarinya kin yi kuskure, koda ban san abinda ya faru ba, amma na san yana da nasaba da abinda yayi ta faruwa da wasu 'yan mata a gidan nan." Na dube shi, "Baba me ya faru da wasu 'yan matan?" Ya ce, "Samarin gidan nan da abokansu suna kawo 'yan mata ta hanyar yaudararsu da kudi, su yi lalata da su." Na dube shi bayan mun fito wajen gidan, "Baba ni nawa salon yaudarar ya bambanta da na sauraNan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa hannu Daga nan ta tafi. Likita ta dubi shugaba ta ce, " Amma ko da Asaben zata ba su dan su sai an sake zama, don kada suje su halaka shi, kin san mutane ba imani. Shugaba ta ce, wannan ka'ida ne, yanzun ki dauki yarinyar nan ki koma da ita gidanku,gobe zamu je mu samu iyayenta. "Doctor ta ce, Insha Allahu." Washigare suka nufi kauyen kurje, iyayen Asabe sunyi murna da zuwanta, amma da suka ji dalilin zuwan nan suka soma kuka tare da yiwa Asabe Allah ya isa. Asabe na ta kuka, Doctor suka yi ta bai wa iyayen baki tana rokon su yafe ma Asabe. Da kyar suka shawo kan su, sannan suka yi musu bayanin komai game da yanda suka yi da Yasir. Mamanta ta ce, to ni dai ba za ta zauna min a nan va, kauyen nan suyi ta zagina suna yada ni 'yata tayo ciki. Ta sake rushewa da kuka, Likita Hinda ta ce zan tafi da ita in zauna da ita hr ta haihu, in ta yaye sun dauki dansu sai ta samu miji tayi aurenta, ko a nan ne. Maman Asabe tana ta gdy, shi ko Babn tunda yayi waje hr suka tafi bai dawo ba, suka dauko hanya bayan sun ba uwar Asabe sha tara ta arziki. ***** ***** ***** Sati 3 daidai babu alamun cewa cikin jikina zai zube,duk da cewa kusan kullum sai na je gun Likitar, ita kuma sai tayi ta kwantar min da hnkl, wai in jira sati 3n su cika,don ba za ta iya bani wani magani ba tunda aikin wannan bai kare ba. Sam lkcn bn san yaya Asabe take ciki ba, don nima ina cikin nawa tashin hankalin, gara ma Asabe. Bana iya cin abnci,yunwar ma ba jin ta nake ba,karatu kuma ina mantawa cewar shi na zo yi, don ko na shiga aji ba na fahimtar komai, ga laulayi mai tsanani. Munir kuma bai kuma zuwa ba,wayar ma sau 2 ya kira ni, cikin sati 3 da likita ta bani yau kam ko sisin mashin bani da shi, a kafa na sabi hanyar zuwa gidan Doctor. Asabe tare da me yiwa Likita aiki wata gyatuma ana kiranta Yalwa, su na samu. Asabe ta ce min Likita tana cikin asibiti zama nayi don jiranta. Sai uku da rabi muna sallar La'asar ta shigo, da fara'ar ta tare ni tana cewa? na dai san bukata ta biya tunda ban gan ki ofishina ba. Kamar ko yaushe,sai hawaye suka soma zuraro min, na ce wlh Likita ya ki fita, ni dai a kwakule min shi. Ganin tashin hankalin da na shiga, sai ta lallashe ni da cewa, nayi hakuri bari ta dan huta. Na koma na zauna ina kuka,wanda ya zama abn yina koda yaushe, tun da Asabe ta bani lbrn yanda aka kwashe da tata rigima hankalina ya kara tashi. Addu'ata Allah yasa nima kada Likitar ta ce haka za a yi, domin zancen cikin ne sam bana kaunar Innarmu taji bare Babana. Sai shida saura ta fito, na dora sabon kuka Nan ta hau ni da fada,wai in tashi ni tafi kukana ya min magani. Na share hawayena, tare da bata hakuri,ta ce "Hafsatu! Ina son ki bani aron hankalinki, ki saurare ni, na ce to. Ta ci gaba da magana. Cikin nan naki ba zaya fita ba, domin na baki duk wani magani mai karfi,amma a banza. In ko ki ka ce a kwakule shi akwai yiwuwar ki rasa ranki. Da sauri na ce gwara na mutu zan fi son akai gawata ga iyayena fiye a kai ni gaban su da ciki. Ta ce, To naji amma kin shirya abn da za ki fada wa Mahalccinki? Kin mutu gurin kisan kai ko in ce ma kin kashe kanki? Kin fi son kunyar lahira fiye da ta duniya? kada ki manta, kin ce fyade ya miki ko? Na daga kai cikin kuka, ta ce to ki dauki wannan abn a matsayin kaddara. Kada ki manta, Ubangiji ya kan jarabci bayinsa don ya gwada Imaninsu, ke me zai hana ki rungumi kaddara? Allah ba ya dora ma wata rai abn da ba zata iya ba, Zufa ta rufe ni, na ce Likita ba za ki gane ba ne.Innata da Babana auran zai mutu SANADIN BOKONA. Alhakin Babana ne kash! Hakika da na san haka zata faru gare ni da na yarda Babana ya aurar dani, in yaso sai in ci gaba da karatun acan gidan mijina. Likita ta ce, Yanzun dai shawar da zan baki ita ce, kije ki samu shi saurayin ki tunda yana sonki, ku sulhunta, in kin haihu a daura muku aure. In kuma kina son sako hukuma kamar na Asabe to in sako, za su tsaya miki a kwatar miki 'yanci. In ta kama hr kotu kuma ko su waye iyayenshi. Na ce A'a zan fi son in same shi muyi magana don bana son asirina ya tonu a unguwarmu. Likita ta ce, yauwa, in kun sasanta ni kuma zan fahimtar da iyayenki, na rike kai, Boko! Boko!! Na jajirce sai nayi boko,yanzun kuma gashi tun ban je ko ina ba bokon na tsane ta. Likita ta ce, "Hafsaty duk wanda ya dauki boko sama da aure a karshe sai yayi nadama, saboda halin da ki ka shiga ina son ki kwana a gidannan anjima zan baku lbrna, don ki san kinyi kuskure kema." Tara na dare da 'yan mintina Likitar ta shigo sanye da kayan bacci masu kauri riga da wando, tire ne a hannunta dan karami mai dauke da kayan marmari, lemo da ayaba da abarba. Ina zaune zugum kan sallaya Asabe na kwance a tsakar daki ta dubi Asaben "Tashi! "Tashi!! Tun yanzy kin soma bin sanyin kasa? kada na kuma ganinki.Asabe ta tashi, Likitar ta ce In bacci ne ki hau gado mana. Ta zauna bakin gado ta turo mana plate din kayan marmarin bayan ta dauki abarba guda daya dama ina jin bakina babu dadi sai shiga bayi nake ina zubar da miyau Na dauki lemu guda daya ina dan lasa, Asabe ma ta dauka. Likitar ta dube ni Tun ranar da naji lbrnki naji ina son in fada miki nawa. lbrn. Amma kafin na fada miki ina son ki sanar da ni daga ranar da ki ka fara ganina zuwa yau me ya birge ki a tare da ni? Na gyara zama, Na farko iliminki,sai kyan halinki,ga shi kina da kyau,ke ba kya tare da matsala kina da kudi. Tayi guntun murmushi,sannanta dubi Asabe ta ce, Asabe ban yi kama da mai matsala ba ko? Asabe tayi murmushi. Anty ai ke ba ki hada hanya da damuwa ba, bare matsala. ke kam kin ji dadinki. Likita tayi shiru na dan lkc sannan ta ce. "Sunana Hindu, mahaifiyata Bafullatana ce, mahaifina yana da kudi sosai,don lkcn da aka haife ni ma yana matsayin Sakataren Gwamnati. Mun taso cikin daula da gata, haka nan muna da kyau 'yan gidanmu tamkar mu ne muka hallice kanmu. Yayyena 2 maza,sai kuma kannena guda 5. Mu 8 ne gurin mahaifinmu, amma a gurin Mamanmu mu 5 ne, Kishiyar ta ke da 3. Tun da na taso nake da tsananin son BOKO burina kullum in zama Likita,wannan yasa mahaifina ke matukar sona,don shima dan bokon rikau ne. Shi irin matanan nan ne wadanda za su iya hana cikinsu su ba ma boko,takarda komai tsadarta in dai ta boko ce zai siya. Wannan tasa nake zaton dama an halicce ni don nayi Boko. Lokacin da na gama secondary ina da shekara 18, kyawuna ya kara fitowa Nan fa samari suka min ca 'ya'yan manyan mutane,masu kudi da sarakuna.Ni kam lkcn wani faifai na bude na walakanta samari, don in fito in zage saurayi ko dan wanenr baya damuwata.Bana manta wani saurayi Nasir,Babanshi shi ne Gwamnan jiharmu wancan lkcn tamkar zai yi hauka don sona, kullum sai ya zo gidanmu ya min kuka,amma na ce ni fa sai na zama Doctor. Babana ya daure min gindi, ina ta tsulawa samari tsiya. Yayuna maza sukan suna son aure,mma Babanmu ya ce suma ba yanzu ba. Amma shi a wannan lkcn ya sake dallo wata amaryar wadda bata wuce sa'a ta ba.Sam ban damu ba, Su Hjy kam ransu ya 6aci,haka yayuna. Babban sai ya shiga dibn mata yana kawo su wai don Babanmu ya gani ko zaya mishi aure,amma sai Baba ya kira shi yana zagin shi. Abn da in na tuna yake bani mmk lkcn Baba hr d cewa in zya nemi matan shi yaje can ya nema,amma ya daina kawo masa gida. Na ce Alhj fada zaka masa ya daina,ya ce kyale shi Hindu, yaje yayi ta yi,wata rana kan shi zaya bari. Ni dai har na tafi Jami'ar Ahamadu Bello,ba suyi auran ba.Karatu gurina ba sauki,sam bana wasa da BOKO. Shekarata 3 a Jami'a sannan aka yi wa yayuna aure, shima da kyar suna ta hada Babanmu da mutanen da yake jin kunya. Kwanci tashi na kammala karatuna,tsawonshekara 7. Lokacin ina da shekara 25. Saboda kwazona, na samu damar zuwa wani kwas kasar Germany na tsawon shekara 2. Hjyta hr d kuka,don bata son tafiyar burinta in yi aure,amma na kekasa kasa na ce ko na gama karatu sai na fara aiki. Haka kuwa, ina gamawa ban jimaba na soma aiki a babban asibitinmu a matsayin babbar Likita. A lokacin Shekarata 30 babu kadan,sai a wannan lkcn ne hankalina ya dawo jikina. Nayi boko na zama Likita,yau gani inna aiki. Nan fa maza suka sake min ca! amma duk wanda na ta6a babu na aure,sai dai in zan yarda a lalace,daga wanda zai ce in zo in raka shi Abuja,sai me cewa in zo in raka shi Dubai. Da na nuna ba haka nake ba, sai na dinga nemansu daya-bayan-dayaina rasawa,daga karshe duk suka gudu. Lokacin ne kuma idona ya raina fata,wasu suka dan soma zuwa amma fa ba yaro,don ko wani ma zaya girmi Babana, na ce tab, ni kan ai saurayi sabon jini. Kafin shekara na nemi suma tsofaffin na rasa.Bana manta wani dattijo da ya soni na ki, sai gashi ya kawo min wata 'yar yarinya ba za ta fi sha takwas ba, ba ta da lfy tana laulayin ciki. Ya ce min, Matarsa ce. Sai na soma tunanin cewa in nemo samarina na da mana,duk wanda na bncika sai in samu lbrn cewa yayi aure. Hankalina ya tashi matuka, yanzun gurin mu2m daya nake sa rai,wato Nasir wanda ya soni tamkar ransa, duk in da zan samu lbrn Nasir naje amma bn samu lbrnshi ba. Wata safiyar Asabar, misalin karfe goma na safe,na nufi supre markte don siyan kayan shafa, domin nawa sun kare. Ina sa kafa daya kan na dago dayar,wata 'yar kyakkyawan yarinya 'yar kimanin shekara sha biyo ko sha daya ta rugo da gudu daga ciki sai ko ta rungume kafata tana cewa . Anty 6oye ni Fadil za ya kwace min (Teddy)na. Na daga ta sama,daidai lokacn da yaron ya iso, daga gani kaninta ne yana da kiba. Ya ce, Anty nima ki ce ta bani boll dina. Na dube ta, ina boll dinsa? Tana dry ta ce, Anty boll dinsa fa tana mota. Na ce to dauko masa, zan sauke ta ta sake kankame ni. Anty Fadil yana da karfi zaya ture ni ya kwace (Teddy) na. Dry na ke t musu, ga shi sai naga sun shiga raina, na ce to muje in sai maka wata boll a ciki. Muna isa daidai gurin kwallaye na ce za6i wadda ka ke so, yarinyar ta ce Anty nima zan kara (Teddy) daya. Muryar Babnsu naji ya ce, sannu da kokari sun dame ki ko? Ina daga ido na sauke kan Nasir, da sauri na ce Nasir! Da alama sai lkcn ya gane ni, ya ce a'a Hjy Hindu BOKO uwaka ubanka ya karatu? Sai naji tankar ya min habaici ne, na ce Alhmdulillah, mun gama hr na soma aiki,ya ce lallai kam buri ya cika, na ce yaranka ne wadandan? Ya ce, eh Fadil da Fadila,sai kanwarsu Yasmeen. Na karkata kai tare da cewa, Allah ya raya su. Ya ce Amin. Na ce, yanzun kana ina ne? yace muna Abuja ne mun zo hutu ne, ke fa? kafin nayi magana wata mata kyakkyawa ina ga zan girmeta ta iso tana sanye da after dress me shegen kyau. Ta ce Beby ka gan su? Ya ce ga su nan sweet heart, ta dube ni ta yatsina baki tare da cewa, wannab fa? Ga mmkina sai na ji ya ce,Ina tsohuwar budurwata Hindu,? To ita ce wannan. Nan take ta watso min wani mummunan kallo, sannan ta figi yaranta gami da cewa, mijin mace daya zo muje. Yayi murmushi tare da daga min yatsu 2 gami da cewa bye. Ban iya tsayawa siyan komai ba na fita. A gida ma ina shiga kai tsaye dakina na nufa,na fada kan gadona ina kuka. Tambayar kaina nake, wai dama gaske ne da Bature ya ce dama sau daya take zuwa ma mu2m a rayuwa? In ko haka ne na cuci kaina na bar damata ta wuce. A ranar ne na soma tsanar BOKO akida, tun daga nan na koma ga Allah, ko yaushe nayi sallah addu'ata ita ce Allah ya ban miji. Kawayena, sa'annina duk sunyi aure da yaransu,kuma bn tsere musu a karatu ba,tunda aina aiki suma suna aiki. Amma sun tsere min don suna da aure ga kuma 'ya'yansu. Doctor Hindu ta dube ni, Hafsatu kin ganni nan da kama aikina yau shekara goma sha biyu kenan,amma babu miji. Har Malamai na shiga don kawai in samu miji. Daga wanda zai ce Aljani ya aure ni, sai wanda zai ce asiri aka mini,suka yi ta cin kudina suna min karya, daga karshe naga babu wani ci gaba na watsar da su. Yanzu na rumgumi kaddarar da nawa kaina, mahaifina ya rasu shekaru hudu da suka wuce abin da yasa nabar gida katsina na dawo nayi asibitin kaina shine, kannena yaran amaryar babanmu duk sun raina ni gashi ba mu cika shiri da hajiyata ba. Shiyasa da aka raba muna gado na yo nan na gina asibiti da gidana, sai dai ina zuwa gida kan lokaci in duba su hajiya ta. Share hawayenta nima sharar kwalla na ke tayi, dan murmushi me kika fahimta ko nace wane darasi kika samu cikin labari na? Nace na farko ba kyau wulakanci, sannan mu daina sanya boko ya zama gaba da aure kamar yanda nima nayi. Tace hafsatu naki mai saukine dan ke kin kama saurayi shi ne dai wanda kika kaman ya cuce ki. Amma ni abinda nayi saboda boko! Ta jin jina kai sanna tace ko rabi ban fada maki ba kuma halin da nake ciki yanzun nima na kirashi SANADIN BOKI, nace auty haryanzu baki wuce aure ba. Tace to in ban wuce ba hafsat ina mijin? Kwata kwata na daina burge maza, sam ba sa jin sha‘awa ta sai yan yara wanda da nayi aure kan ka ida na rantse miki hafsa da yanzu inada kamarki koma wanda yafiki don haka sha warata dake ki daure ki haifa dan cikinki baki saniba ko shi kenan kwanki a duniya. Sannan kiyi aure tun da kuruciya, aure ba zai hanaki boko ba kamar yanda mahaifinki yace. Magana daya zan fada maki, kada ki sake yarda saurayi ya taimaka miki game da komai na kudi, zai iya anfani da hakan ya cutar da ke, duk da nasan akwai masuyi don Allah. Asabe da ke gefe cikin tagumi sai yanzu ta tsoma baki, anty wallahi ban taba zaton kina da matsala ba, duk kalon da nake maki mijinki da yaranki suna kasar waje. Maganarta sai ta dan bamu dariya. Har likitar ta barmu ta koma dakin ta ban daina mamakin lbr ta ba, duk kyanta duk kudinsu duk bokonta ta kasa samun miji lalle kuwa boko yaja mata. Wata zuciyar ta ce min ba boko bane wulakancinta ne ya jamata, koma mene yanzu na fiskanci aure yana sama da komai. Washe gari gida na shirya wucewa kaduna, sai dai kudin mota bani dashi amma ba zan iya fada mata ba. Dan haka nayi shuru dari biyar ta bani wai nasha ruwa a hanya. Makaranta na koma na canja kaya na dauki kwalin wayata na nufi kasuwar masu waya ni dai ban tsaya ciniki ba, dan ba a cikin nutsuwa nake ba, yace dubu 6 inji mai siyan wayanr, bani kudin kawai nace don na kosa insami munir inji yadda zamuyi. Kai tsaye gidansu na dosa ko unguwarmu ban sauka ba, koda mai gadinsu yace min sun fita da maman shi sai nasami can gefen gidan na zauna. Ko shekara zasuyi sun dawo su same ni, na fada cikin raina. Kusan awa 3 sanan motarsu ta dawo tayi hon, mai gadinsu ya bude ban bata lokaci ba na mike na rufa musu baya. Daga inda nake tsaye ina hango kannanshi mata suna sanye da gajerun wanduna, kai ba dan kwali suna ta shiga da kaya. Dayarce ta hangoni sai naji tace mom ga wata can ko mai aiki ce? Matar ta waiwayo, kamanninta sak da munir haka ma kannanshi. Ta nufoni lafiya? Warin munir yayana ya aikoni, tace wai me? Nace abokinsa ne zan amsar masa sako ne, sunyi magana da munir din. Tace ok ta nufi ciki tana kwala mashi kira. Yafito daga cikin gida yana cewa yes mom.... ganina yasa shi yin wani turus! Tace gawata can wai yayanta ya aiko ta." Da sauri ya ce, "Oh na gane sako zan bata." Ya iso gurina fuska daure, "Lafiya Hafsatu kika biyo ni gidanmu?" Na ce, "To ciki fa bai fita ba." Da sauri ya dora yatsanshi a lebe tare da cewa, shishsh. Ya nufi gefensu gami da cew Zo. Muna shiga ya ce, "Kina nufin cikin bai fita ba?" Na ce, "Wallahi." Ya ce, "To ki koma gida zan zo anjima da dare in kaiki wani asibitin a fitar da shi, wannan bata san aikinta ba." Na ce, "A gaskiya ba zanje a kasheni ba, don Likitar tayi duk wani kokari don ganin ya fita amma abin ya ci tura. Ta kuma fada min in na matsa cewa sai an cire to zan iya rasa raina. In je in cema Ubangiji na me?" Ya ja tsaki, "To me kike nufi?" Na ce, "Shine na zo mu san abin yi." Ya ce, "To me kike ganin za'a yi?" Sanyi na ji cikin raina, Allah ya sa ya yarda na ce, "Ina ga mu hakura in zauna can gidan Likitar, ko Inna ba zan fadawa ba in na haihu sai muyi aure." Ga mamakina sai na ga yana dariya, a zato na zancen ya masa dadi, kuma shawara ta ta shige shi. Amma sai naji ya katse tunani na da cewa, "Amma ban taba sanin baki da hankali ba sai yau. Kina zaton ko aure na yi yanzun nan da shekara goma zan haihu?" Ya girgiza kai, "Ba zan haihu ba, saboda haka dole ne a cire wannan cikin, in kuma kin dage to kije can ki nemi Uban danki." Da sauri na dube shi, "Munnir ka san me kake fada?" Ya ce, "Eh, ina da ja kan wannan cikin, cewa nawa ne. Daga sau 1 shima ba cikin kwanciyar hankali ba amma shine ciki zai shiga?" Bakin ciki ya hana ni magana, idanu kawai na tsura mishi, shima ni yake kallo cikin harara gami da daure fuska. Na ce, "Allah ya sani ni ba mazinaciya ba ce,,,,,,,,," Kuka ya kwace min, "Kai ne ka soma keta min mutuncina, ka raba ni da 'yan matanci na, yanzun kuma ka bini da sharri. Allah ya isa tsakani na da kai." Ya matso kusa da ni, "Zan mare ki in kika zage ni, banza butulu. Duk taimakon da nayi miki da kokarin da nayi miki amma kin kasa gode min, shashasha, Kin zata zan kashe miki kudi a banza ne tsawon shekaru? Ki sani in kin ga kare yana shinshina takalmi to dauka zai yi, ni ba ajinki bane don ki sani." Kuka mai karfi ya kwace min, "Allah ya isa Munnir, dama yaudarata kake yi kace zaka aureni?" Ya yi 'yar dariyar mugunta, "Kin dai yaudari kanki, to ai ni ne ma zanyi Allah ya isa tsawon shekara 3 zuwa 4 ina miki bauta ke da me kika taba saka min?" Ban san lokacin da nayi kukan kura na shako wuyanshi ba ina kuka ina cewa, "Allah ya isa." Shi kanshi yayi mamakin yadda ya so kwacewa daga jikinshi ya kasa.Muryar Mom dinsu muka ji tana cewa, "Lafiya? Ke, ke sake shi mana me ya faru?" Na kasa magana sai wani irin kuka nake yi ina fadin, "Ya cuce ni." Ta dubi Munnir, "Me kayi mata?" Ya ce, "Ban fa ko sanya ba daga aiko ta gurina ta shakeni wai na mata ciki." Wani kallo Mahaifiyarsa ta watso min sannan ta nuna ni da yatsa gami da cewa, "Ke! Shiga taitayinki, tafi can ki nemi wanda ya miki ciki." Cikin tsananin kuka na ce, "Wallahi shine ya min fyade. Kuma da shi muka je asibiti Likita ya ce ina da ciki." "Ke!" Ta kara daka min tsawa, "Fita a nan." Na ce, "Nifa ba inda zani sai dai ya san yanda zayayi da ni......." Saukar mari na ji, sannan ta ce, "Fita ko in kirama Iyayenki 'yan sanda." Ta fita da sauri tana kiran Baba megadi, ya iso ta nuna mishi ni, "Baba fita da wannan bana son in kuma jin ko labarin an ganta a layin nan, in haka ta faru har da kai zan hukunta." Ya dubeni ya cem "Mu je." Na tsaya ya ce, "Shige mu je mana ina magana kina kallona." Na dago jajayen idanuna na kalli Munnir, wani murmushi ya saki na mugunta sannan na ce, "Akwai Allah." Na fita megadin yana biye da ni sai da muka fito ya ce, "Yarinya kin yi kuskure, koda ban san abinda ya faru ba, amma na san yana da nasaba da abinda yayi ta faruwa da wasu 'yan mata a gidan nan." Na dube shi, "Baba me ya faru da wasu 'yan matan?" Ya ce, "Samarin gidan nan da abokansu suna kawo 'yan mata ta hanyar yaudararsu da kudi, su yi lalata da su." Na dube shi bayan mun fito wajen gidan, "Baba ni nawa salon yaudarar ya bambanta da na saura Zaharaddeen Shomar whatsapp. 08168575100 Sanadin Boko 1-6 Posted by ANaM Dorayi on 12:26 PM, 12-Sep-15 Under: SANADIN BOKO ." Kuka ya sake sarkeni, na ci gaba da cewa, "Shekara 3 da doriya yana min dawainiya da sunan zai aureni, kuma Wallahi Baba fyade ya min." Megadi ya ce, "Kuskurenki shine zuwan da kika yi gidan nan, ki kiyaye zuwa gidan samari ko dakin samari. Yanzun kije ki yi hakuri, in ba haka ba zaki jawa Iyayenki matsala. Kin san masu kudin nan ba duka bane suke da tsoron Allah, 'ya'yansu su ne 'ya'ya na wasu tamkar dabba suka dauke su. Shi Munnir sau nawa yana samuna yana rokona shi da abokansa wai in kai musu kudin gaisuwa gidajen 'yan matansu a matsayin nine Ubansu." Na ce, "Baba ka je?" Ya ce, "A'a ni nasiha na musu dan nima inada yara da jikoki. Tunda haka samarin yanzu suke yi, su kai kudin gaisuwa don su bata yarinya. In ta'ki su ce aurenta zasu yi. Na san koda ban kai musu ba sun je sun samu wani, kuma ya kai musu, kila ma sun cimma burinsu, don haka ki je kiyi hakuri ki kuma kiyaye gaba." Na ce, "Na gode." Ko da wasa ba zan ce maigadin nan ina da ciki ba. Tahowa na yi ina mamakin kalaman Munnir, wai ya taimakeni ne don bukatarshi, dama haka halin maza ya ke? Dama Munnir mayaudarin 'yan mata ne? Tafiya nake amma sam ban dauki hanyar gida ba ko cikin mafarki ai ba zanje gida ba. Zuciyata ta bushe na share hawaye na na nufi Babban titi. Kwatsam! Sai ga Yayana Umar ya sauke wani a mashin, cak na tsaya don mun riga mun hada ido. Cikin mamaki ya ce, "Hafsa daga ina haka?" Gabana ya fadi matuka, amma sai na kanne banda wata damuwa na ce, "Na zo ne yau ko gidama ban karasa ba, gidan su wata na zo." Ya ce, "Wacce watan?" Na 'kirkiro 'yar dariya, "Yar ajinmu ce ta yo mana gaba da kaya to na zo kuma bata karaso ba." A take karyar tazo min, ya ce, "Hau na kaiki gida." Muna cikin tafiya ina tunanin ban so na hadu da Yaya Umar ba, sai ya jeho min tambaya, "Hafsa sai na ganki duk a hargitse, fuska a kumbure kamar kin sha kuka." Gabana ya yi mummunar faduwa amma don kada ya ganoni na ce, "Kukan lafiya? Ka sam zaman mota, kuma baccina na sha har na gaji." Ya ce, "Irinku ne ake sace wa, nan da Kano kin hangame baki kina bacci,." Na ce, "Cikin kwanakin nan ne bamu samu bacci ba saboda karatu." Ko Inna abinda ta soma tambaya ta shine lafiya? Cikin dariyar da bata kai zuci ba na ce, "Lafiya Innarmu." Na shige daki na kwanta kan gado.Jim kadan Ummi kanwata ta shigo da kwanon alala ta ce, "Anty gashi." Na amsa na aje. Ummi ta tsaya tana kallona, ina zaton dan wasan da na saba yi mata ne taga ban mata ba. Inna ta shigo, "Wai Hafsa lafiya na ganki kwatsam! Kuma kina zuwa kin zube a gado?" Ban san yadda aka yi maganar ta zo min ba, sai dai kawai naji ina bata amsa, "Innarmu gajiyar mota ce, kuma dama bani da lafiya ne. Can ma muna ta sintirin asibiti shine aka ce in zo gida in nemi na hausa." Cikin fargaba da Tausayi ta ce, "Ashsha, me ke damunki?" Sai kurum na ji bakina ya ce, "Shawara da Basiri." Ta jinjina kai, "Sannu, Allah ya sauwake, jiki da jini haka ne. Ta ce ci alalar." Ta daga murya, "Ummi! Ummi!!" Yarinyar ta shigo da gudu. Inna ta ce, "Kira min Baban gida in aike sh dattawa ya hadowa Hafsa maganin basir da shawara." Ta kwance habar zaninta ta ciro kudi naira dari 3 da ashirin ta ce, "Ungo ka hau mota ka je layin dattawa gurin masu magungunan gargajiya ka siyo mata maganin shawara da na basir." Ya ce, "To." Ya amsa ya fita. Bani da damar in ki sha domin Inna tsareni take, a cewarta tun ina karama bana son magani. Duk lokacin da zan sha ina sha da niyyar cewar Allah ya sa cikin nan ya fita amma shiru, sai ma tsananin amai da ya karu gareni da kuma kasala. Tausayin Inna yana sani kuka, in naga irin fadi-tashin da take yi gurin neman min magani.Wata rana ina kwance dakin Baabah amai ya sarkeni na tashi da sauri kafin na bude kofa na soma sheka shi. Baabah ita ce ta taimaka min na gyara jikina ta kuma kwashe aman. Har na kwanta ta ce, "Hafsa!" Na ce, "Na'am." Na tashi zaune, ta ce, "Zo nan." Na mike na bita can kuryar daki ta ce, "Hafsa ki fada min tsakaninki da Allah me ke damunku?" Gabana ya yi mummunar faduwa, zufa ta keto min na ce, "Me,,,,,me kika gani?" Ta ce, "Hafsa na ga wasu alamu da suke nuna kina da ciki, menene gaskiyar hasashena?" "A'a bani da komai." Tayi-tayi da ni in fada mata gaskiya amma na dage kan cewa bani da komai, don haka ta kyaleni tare da cewa, "Shike nan. Dama ke nake tunanin zaki bani hadin kai domin Innarku ba zata fahimce ni ba na sani shi yasa na miki magana." Na ce, "Ni fa kalau na nake." Don haka sai ta rabu da ni. Kafin sati 2 duk 'yan gidanmu sun gane halin da ake ciki, amma banda Innarmu sam bata lura ba bata zata ba, ba kuma ta tsammanin haka zata faru ba, 'yan tsegumi har cewa suke mata, "Yaya 'yar boko da jiki?" Haka ta ce, "Da sauki." Tana washe baki ita a dole an gaishe ni. Sannu a hankali zance ya soma fita makota sai gashi ana shigowa dubani, niko ko yaushe ina cikin Hijabi. Baabah Maimuna ita ce ta shigo dubani yau kawar Innarmu ce kut da kut ta kalli Innarmu, "Kin san zancen da yake yawo unguwar nan?" Ta ce, "A'a." "To 'yan gidanku sun fita suna yada cewa Hafsa ciki ta yo." Inna ta mike cikin tsananin tashin hankali, "Wane dan sharrin ne? Wallahi zan iya maka mutum a kotu." Maimuna ta ce, "Saurara kiji, kafin ki fita kiyi wata magana soma tuhumar ta tukunna." Innarmu ta ce, "Haba Maimuna, sanin kanki ne Hafsa bata da rawar kai irin na 'yan iska, sharrine kawai za'a mata. Kin san bani da hakuril dole sai ba ni ba'asni wanda ya mata wannan sharrin." Maimuna ta ce, "Don Allah ki bar zancen nan." Amma Inna bata saurareta ba ta fita tana fada, wai yaya za'a yi ta bar wannan zancen ana kallon 'yarta a matsayin 'yar iska! Kai tsaye sashen su Asabe ta nufa tana fadin, "To munafukai magulmata masu zuwa lahira da kokon dambu! Za kuce 'yata cikine da ita, to aniyarku ta biku. Kuma Insha Allahu 'ya'yanku ne zasu yi ba tawa ba. Kanta aka fara ciwo da za'a mata sharri?"Kuma in sha Allahu yayanku ne zasuyi ba tawa ba kanta aka fara ciwo za a mata shairi? Asabe tace aina kika ji? Mu nan dai ba wanda ya san haka inna tace rufe min baki munafukai, to nazone in muku gar gadi zan maka mutun a kotu, sai ta fito mun da wanda ya fada mata. Ade tace maganar gaskiya ki bin ciki yarki dan muma a makota mukaji. Inna tace ahaf na san duk inda aka zaga aka zago kune zaku fadi wanan maganar, kuma zaku amsa kiran alkali,gida ya hautsine baba ya shugo yana tambayan ba asi, babah tace a a yar rigimar yara ce ba sai kaji ba. Nufinta kada yaji don tasan in yaji sai yabi duddugi amma jin zantukan sun cika gidan har makota sun soma zagayowa, ya fito dan jin ba‘asin tun bai karasaba ya soma jin muryarsu Ade na cewa an dai fada maki kije ki tuhimi yarki, ba kizo ki tasamu kina zagi ba. Ki dau mataki tun kafin lokaci ya kure miki, in shairi a ka mata sai kiji dadin kaiwa kotun. Asabe ta kara da cewa, inko kin tafi yanzun kya iya zuwa kiji kunya. Ya iso gurin yace zo, babah ta malam na kiranki don Allah kiyi hakuri ki bar zancen nan, wanda ya fada ba don kansa ba. Ta nufo daki inda baba ke kiranta, ina kuryar gado tare da fatan Allah ya dauki raina yanzunnan. Baba ya dubeta, to in kin gama fadan kira min yar bokon yar taki inna tace saboda Allah malam daga ciwo sai ayi mata sharri? Ca wa fa sukayi tana da ciki yace ai ba abin mamaki bane kira min ita. Hafsa zonan, na fito kishirya mutafi asibiti inna tace malam asibiti suna bada maganin basir ne? Acan makarantarsu fa sunyi na asibitin sun gaji shinefa sukace ta taho gida ayi na hausa. Yace to ai ba matsala bace wanan, matsalata in tabatar da zargin da ake yi mata inna tace ai! Malam kaima ka yarda za ta iya? Yace kwarai kuwa, yace ita ba mutum bace? Ya ba kanshi amsa yacemutum ce kuma baliga mai lafiya, don haka yanzu da bayanin likita zan yarda da duk abinda zakuce. Nan take tsoro ya kamani hankalina yafi da tashi. Inna tace je kushirya kutafi asibitin inma har har danine sai muje. Yafita tare da cewa ina jiranku waje. Nace inna kice masa don Allah mu bar zuwa asibitin nan kinji? Tace a a ki shirya kindai san halin babanki, in ba‘aje likita ya wankekiba bamu da zaman lafiya, nace inna mudai mu hakura ba sai mu barsu da Allah ba, masu cewa inada cikin? Tace shin hafsat kodai kina da cikin ne?nazaro ido nace a a ni bani da komai tace to shirya muje, garuwa ki daureye jiki nace to a ban daki tamkar in haure yar gajeruwar katangar mu in gudu, domin na san yau idan mukaje asibiti asiri na yagama tonuwa. Yau auren iyayena zai rabu na shiga 3! Nan wata zuciyar ta fada mun ba laifina bane, in bisu inje asibitin inyaso duk yanda Allah yaga daman zai faru dani shikenan, sai in rungimi kaddara. Afili nace Allah ya isa munnir asibitin dutse muka je, baba shine ya yankar min kati suka tura mu gurin da zamu ga likitan mata. Duk da halin da nake ceki sai da nayi Allah wadai da shugabannin da muke dasu. Asibiti ka mar wannan ace likitoci mata basufi uku ba, ga mata nan sun kusa 100, wata mata dake kusa dani tace min tun asubahi suka zo nan tayi sallah. Amma har yanzu ba‘a zo kanta ba. Ina ganin rashin kula da ba ayi da likitocin shine dalili da yasa basu zuwa aiki. Haka muka yini a gurin, amma baba ya dage sai munga likita. Muna shiga ya bashi kati likita ya tambayi meke damuna?Kafin nayi magana baba yace yata ce, munzo ne ayi mata gwaji kotana da juna biyu. Likita yace bari yaji ta bakina, ya tambayeni meke damuna? Nace basir da shawara, yace yaya kikeji a jikinki? Nace amai da zazzabi. Kama hannuna yayi ya duba, nan take ya bamu wata takarda wai muje amin gwaji nayi fitsari na kawo. Nan take sakamako ya fito baro baro ina da ciki nurse bata fada muna ba, ta dai bamu sakamakon mu kaiwa likita. Lokacin zuciyata ta gama bushewa, na mekawa Allah komai. Mun shiga yana rubuta muna wani magani, sai da ya gama sanan ya duba. Ya kali baba, tana da miji? Baba yace a a likita yasake kalona, amma ke kinsan kina da ciki? Wata muguwar faduwar gaba naji, tamkar yau nasoma jin cewa inada cikin. Baba yace tanada ciki ko? Yacigaba da rubuta wata ta karda yana cigaba da cewa tana dauke da ciki. Abinda sakamako ya nuna kenan. Amma kuje ayimata (scan) don kusan ko wata nawa ne inna kawai na kallah wada ta kafa min idanu sun kada sunyi jajajir,Baba ya ce a"a bama bukatar sai tayi hoto,dama tabbacin cewa akwai cikin muke son sani, tunda akwai shi kenan. Ya kalli Innarmu,bana bukatar sai na sake tuna miki komai daga ke har ita. Ya fita abinshi. Inna cikin kuka ta ce, Hafsa haka zaki min? Hafsa na dace da wannan sakamakon? kin min adalci kenan? cikin kuka nima na ce kiyi hakuri Inna, wlh fyade Munnir ya min. Ta ce, karya ne, ki min shiru. Ta dubi Likitan da ya zuba musu ido,don Allah Likita ka taimake ni ka cire mata cikin nan. Da saurin Likitan ya mike tsaye cikin murya mai karfi, fita anan domin nan ba asibitin zubar da ciki ba ne. Muka fito muka nufo gida, Inna na fadin Hafsa kin cuce ni kin kuma cuci kanki. kafin mu isa gida tuni Baba yaje yayi fadan shi a tsakar gida kamar yanda ya saba, muna isowa kowa sai kallonmu yake yi. Muna shiga yazo ya ce ya va mu zuwa da safe mu fice, yanzun ma don dare ne. Mutane na ta bashi hakuri,amma ya ce to wane hakuri zai yi? Dan ya ce mata in haka ta faru a bakin aurenta, kuma ta yarda. Ranar inna kasa fadan nata tayi, duk da matan gidan da suka cika a kofar dakinmu. Ni kaina kasa min fada tayi sai kuka da take shara6awa. Mun kule can daki, can cikin sulusun dare na tashi dan bacci taya dauki Inna na fice. Bayan na kwashe duk wani abuna mai mahimmanci, Baban titi na mika ina tafiya ba tare da tsoro ba. Daf! da Asubahi naji wata mota suna cewa kano ne? na tsaida su na shiga duk da cewa ba ni da ko sisi,saboda ragowar kudina na mikawa Inna tun zuwa na, wato kudin wayata. Sai da muka dau hanya suka ce dari biyar zan ba da, bn yi mng ba, don haka sai suka zata na yarda ne. bakwai da 'yan mintuna muka isa Gyadi-Gyadi, suka ce kudina, na ce bani da kudi,don Allah su taimaka min. Nan kwandastan ya hau ni da zagi, ni dai kallon shi nake yi. Direbn ya ce, in je amma nan gaba in banda kudi in dinga magana tun kafin na hau mota, don ba kowa zai iya kyale ni ba. Na ce na gode.Sai lokacn kuma na soma tunanin ina zan je? Wata zuciyar ta ce bakina karanta littattafan su Anty Fauziya D. Sulaiman da su Anty Sadiya ba? Ai suna fadin cewa in yara sun gudu su kan je wani gidan a rike su a taimake su. To suma ai sa rike ki in kin je ki zauna da sy za su fahimce matsalarki don suna rubutu kan haka. Amma sai wata zuciyar tace, ki je gurin Likita nan, ban san lkcn da na tsaida dan mashin ba, na masa kwantace muka tafi. Ta fito kenan zata ofis sai gani, ta ce a'a Hafsa ce .da safen nan? Na ce eh, Anty ga shi ma bani da kudin da zan ba mai mashin din. Ta zuge jakarta tana cewa, nawa ne? na ce,daga Gyadi- Gyadu ne ba muyi ciniki ba, ta bashi dari biyu,naga dai ya bata canji, amma bn san ko nawa ba ne, ta ce daga ganin ki ba wata nasara amma shiga ciki. Sai da ta huta bayan ta dawo sannan na fada mata komai, tace to ke yanzun menene burinki? Na ce ni da zan samu wani dan aiki in dauki nauyin kaina ba tare da na sake neman taimakon kowane da naminji ba, zan so haka,amma da wuya tunda takardun sakandire kawai gare ni, ta ce amma bn san hikimar guje ma iyayenki da ki ka yi ba, musamman mahaifiyarki wadda ta gwada miki kauna. Da kin bita kun gudu tare ko kwa tsira tare. Na ce Aunty ina tsananin jin kunyar mahaifiyata. Ba zan iya zama da ita ba. A halin yanzun itama nasan ta dauki hanyar gidansu, da wane ido zan kalle su? Ta ce to yanzu ina son ki zauna nan mu ga yanda za"ayi. Ni da Asabe mun zama 'yan gidan Doctor Hindu, ita ke mana awo da komai, magunguna duk ita ke ba mu. Cikin haka hr muka shiga watan Haihuwarmu ko na ce haihuwar Asabe. Ta kawo min kaya jarirai yayin da Asabe aka kawo mata daga gidan su Yasir. Doctor ta ce, Kin gani kin hana mu dauki mataki da kema yanzun dole su ringa yi miki komai. Na ce, Bar su kawai Anty, Ni yanzun ba n da burin da ya wuce in haihu lafiya, ina so in tsaya da kafafuna ko Allah zai taimake ni in dawo da iyayena farin cikin su. Ina tuna kannena, musamman Ummi, Nasan Baba kishiyar Innarmu bata da mugunta, zata rike su amma nasan ba za su yafe min ba, Matsawar suka ji cewa ni ce na kashe auren uwarsu da ubansu. Doctor ta ce kada ki damu, Insha Allahu za ki dawo musu da komai. Asabe ta haihu'ya mace, kyakykyawa. Duk da 'yan gidan su Yasir da shi kan shi ba su zo ba, amma sun aiko da komai hatta ragon suna. Sannan suka ce ta sa ma 'yarta sunan da take so. Doctor ce ta bada shawar a saka sunan mahaifiya Yasir wato Maryam.A cewar Likitar, zai fi girmama yarinyar duk lkcn data koma gare su. ... A ganina matsalar Asabe mai sauki ce, don mahaifiyarta har duba ta tazo sa6anin ni da ban san halin da nike ciki ba? suma ba su san in da nike ba, Mai aikin Doctor ita ce ke mata wanka., Kwanci tashi ni ma(E .D. D) na ya cika har ya gota, amma shiru ba batun nakuda bare haihuwa, Ranar Litinin tana min gwaji ko na ce awo, ta ce yaran nan naki fa yayi girma da yawa ga shi kin kasa kwantar da hankalinki jininki kullum kara hawa ya ke yi. , Yanzun ya wuce ka'ida ina miki tsoron afkawa cikin matsala, kin kasa daukan kaddara. Kuka ya kwace min Anty zan so in mutu a gurin haihuwa nan, shi ne kawai burin zcyta. Likitar ta ce dama mun saba fada, duk lkcn d zan miki awo,mugaye fatan d ki ke yiwa knki kuwa da kina da kambun baka da yanzun kin lalace., Na ce Allah isa tsakanina da Munnir Ta ce " Ameen. Amma yanzun na fi so ki kwantar d hnklnk kin ji? Na ce to. Wasa- wasa gani na kara sati 3 ta ce in na kara kwana 3 za a yi min akin. Talata Doctor ta tafi wani taro a brnin Tarayya, ranar ce kuma na soma nakudar Haihuwa. Haka na kwna na yini, mai aiki tana kula dani, bayan magriba ta shigo fada ta hau mu da shi me yasa b muje asibiti ba? Ni kam na galabaita matuka,gado aka turo aka dauke ni, zuwa cikin asibiti, amma haka na sake kwana dole ayi min aiki. dn hk Likitar tasa a min shiri a sani a dakin tiyata.Tare da taimakon wani Likitan suka yi nasarar ciro min katon yaro namiji. Hakika na matukar shan wahala, kusan kwana 3 ban sami kaina ba., Sai a rana na 4, din ranar har na tashi an jingina min filo. Likitar ta kawo min yaron. kai na kauda domin a ganina shi ne silan raba ni da iyayena. Ban ta6a ganin fushin Likitar ba a iya zamana a gidanta sai yau. Ta ce, Dauke shi ki ciro nono ki bashi . Na fashe da kuka Anty ban yi aure ba kada ki sa in ba shi nonona su fadi, ba zan ba shi ba. Ya ya za'ayi ya raba ni da iyayena, na ci gaba da kuka, ta ce ke rike shi kafin in zabga miki mari. Shi ina ruwan shi? Shi ya samar da kan shi ko samar da shi ku ka yi? Don me za ki ga laifin shi ? Da ba ku aikata abin da ku ka aikta ba da Allah bai samar da shi cikin mahaifarki ba, ganin irin kukan da nike yi yasa ta koma lallashina, bayan na dauke shi. Babansa ya juya masa bya, kada kema ki zama kin juya masa, Kina nufin ba za ki rungumi kaddara ba? da lallashi ta shawo kaina na ciro nono yana sha ina kuka. Satina daya na gargije, muka koma gida., Ba a yanka ragon suna ba, sai dai na ce ma Anty duk sunan da ya dace ta sa mishi ta ce a sa mishi SHADDAD. sunan wai yana mata dadi. Har ta kara da cewa da Allah ya nufe ta da aure ya bata da sunan da zata sa masa kenan, don haka yaro ya ci suna Shaddad. A hankali na rinka jin kaunar yaron tana shigata, sai dai kullum kamanninshi da Munnir kara bayyana take, ban ta6a ganin da mai tsanabin kama da ubansa ba irin haka. Zuwa yanzun zcyt ta dake,watanmun 3, Wata rana Doctor Hindu ta zo mana da lbr mai dadi, wai ta samu miji, tsohon ministan ilimi na kasa. Muka yi ta murna, ita kam har da Azumi 2 don nuna godiya ga Ubangiji. Sati 4 aka sa bikinta, mu ne har Katsina gidansu. 'Yan uwanta da take bamu lbr duk mun gansu,ita ce ta dinka mana ankon dinner. Ranar daurin aure da dare aka yu dinner. Sam na kasa sakewa,saboda kallon da maza ke min, duk da yaron da ke kafadata. Ni kuwa yanzu duk namiji da zai kalle ni ko da bisa rashin sani ne ai bn da makiyi kamar su. Mun sha biki,sannan muka dawo,mun samu gidan yasha gyara,an zuba komai sabo,shi yana zaune a Abuja da Iyalansa, amma ita zata zauna a gidanta saboda aiki. Ada na cika wasa da tsokana ga son raha, amma yanzu na koma miskila,masifaffiya, mara fara'a.Bugu da kari yanzu ba ni da tsoro, musamman akan namiji. Kwanci tashi hr Asabe ta yaye 'yarta, kuma tuni an kaita gidan su Yasir. Bayan hukuma ta shiga batun don kare lafiyar yarinyar. Sannan ta samu miji a can kauyensu, mun je har can bikinta garin da aka kaita ya dan fi kauyensu zama birni. Ni kam kullum cikin yiwa Likita naci nake, ta samar min aiki ko na gida ne, ta ce an gudu ba a tsira ba, dubi abin da ya faru da Asabe sanadin aikin gida. Cikin satin da muka yi wannan maganar tazo min da lbrn cewa ta samo min aiki a wani Super market, amma da nisa tsakaninsu da unguwarmu. Mukhtar Ismail Muhammad WhatsApp: 08161892123 Sanadin Boko 1-7 Posted by Mukhtar Ismail Muhammad On www.arewarulers.com.ng Under: SANADIN BOKO Cikin satin da muka yi wannan maganar tazo min da lbrn cewa ta samo min aiki a wani Super market, amma da nisa tsakaninsu da unguwarmu.Na ce ba komai zan iya, ba d jimawa ba na yaye Shadad, na ci gaba da zuwa aikina, a wata dubu goma ake biyana. Shawara ta bani, wai in bude (account) tunda bn rasa komau ba, hatta sutura tana bani nata. Dan Adaidaita ta samo min duk wata sai dai in biya shi, sauran na kai banki, Nayi-nayi ta dinga cire wani abu a cikin albashina, amma sai ta ki ta ce ita don Allah take zaune da ni,matsala daya a gurin aikinmu ita ce manajanmu ba shi da mutunci.Farkon zuwana ya yi ta shige min shi yana sona, ganin yanda na birkice mishi sai ya sama min lfy, amma akwai zuga rashin mutunci. In minti daya ka kara bisa karfe 8, to zaya iya korarka, ban ta6a kai takwas ba tare da naje ba, sbd ina matukar son aikina. Shadad yana da hkr yana zaman shi gurin mai aiki. Cikin haka muka wayi gari cikin farin ciki, Doctor ta samu juna biyu, Mijinta mu2m mai mutunci da sanin ya kamata. Yayi murna, sai dai cikin yazo mata da matsaloli masu dama, ko dn ta manyanta ne? oho. Kwanci tashi ta shiga watan haihuwarta, mijin ya ce ta shirya su tafi Abuja ta haihu a can, wani asibiti na musamman. Sun tafi ko yaushe muna waya da ita, maganarta daya kullum ita ce mu sa ta addu'a, sannan ta ce min " Hafsa koda bn dawo ba kiyi kokari ke nemi mahaifanki tare da neman yafiyarsu. Mummunan lbrn da ba zamu ta6a mantawa da shi ba, musamman ni, shi ne na rasuwar Doctor Hindu, nayi kuka tamkar raina zai fita. Ta rasu bayan awa daya da haihuwarta, ta samu 'yan tagwaye mace d namiji, Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, ko dangin Doctor basu kai ni jin mutuwarta ba, domin ni ita ce dangina uwata kuma ubana. Can Abuja a kayi jana'izarta, amma gidanmu ake zamn makoki, in da dangin ta da na shi suka zo. Tun kafin bakwai na soma tunanin gurin zuwa, don kan yanzun asirina ya tonu, gatana ya fadi., A zaton danginta ni 'yar aiki ce, amma dangin mijinta sun zaci ni 'yar uwarta ce, yaranta tubarkalla, lafiyyu ana ta ji da su. Ranar 7 kuwa subahanallah,tunda aka ce mu hada kayanmu za su rufe gidan hankalina ya tashi, mai aiki kuwa dama daga kauye take, bata samu matsala ba don ta riga ni tafiya. Ga shi gobe zan koma aiki hutun da gurin aikina suka bani a matsayin uwata ta rasu, kamar yanda na fada musu. Rahma ce ta fado min a rai, yarinyar da muke aiki shago daya da ita.Rahma tana da mutunci, bari in nemi taimakonta. Na kira lmbrta t daga, na ce Rahma don Allah ina nema wani agaji, ta ce na me? muryata ta sarke, Rahma ina son dakin haya a unguwarku, zan samu? Ta ce yau-yau din nan? Na ce eh, ta ce gskiya ba za a samu ba, sai dai in an bincika a hnkl. Na ce na shiga uku! Ta ce wai me yake faruwa? Na ce ba ni da gurin kwana, ta ce, gidanku fa,? Na ce ba gidanmu ba ne, kuma yau masu gidan zasu rufe gidansu, Ina da matsala. Ta ce ok, yanzun kina ina? Na ce ina gidan ina hada kayana, ta ce to za ki gane gidanmu? Na ce eh, ba Tukuntawa ba? Ta ce eh, Mama tana nan sai kiyi mata bayani kafin na dawo, na ce to na gode. Sun bani kayan sawa nata da yawa, na nemo dan tasi ya dauke ni zuwa Tukuntawa unguwar su Rahma, Mama da matar Yayan Rahma ne kadai a gidan. Muka gaisa, Mama ta ce daga ina? Sobada ganina da ta yi da kaya riki-riki na ce sunana Hafsat gurin aikinmu daya Rahma. Ta ce oho, yarinya da ku ka zo duba ni kwanaki ko? Na ce eh, ta ce ba Rahma ta ce min Mamanki ta rasu ba? Na ce eh ba Mamana ba ce, ta rike ni ne kuma yanzun 'yan uwanta sun zo zasu rufe gidan saboda ya zama na 'ya'yanta. To shi ne nake son ko zan samu dakin haya nan kusa da ku? Ta ce to za a cigita, sauke yaron ki shiga da kayan ki can dakin Rahma. Ina jin dadin zama da su Rahma don ina yin biyayya gare su, matar wan Rahma ce ka dai ke son min tambayar kurilla,tana yawan cewa to wai ina iyayenki? Ban ta6a amsamata ba, don ko Rahma bata san komai a kaina ba, bata san Matsayin Shadad a gurina ba, duk da ta cancanta in fada mata. Matsawar da nayi da son samun dakin shi yasa su Mama suka sa ne man dakin, amma d ta ce in yi zamana a nan gidan tun da ba ni da matsala, haka dana. Na ce, a'a ni dai na fi sobn na samu daki gidan mutunci gidan Hjy Iya aka samu dakin sai dai sun ce min sai nayi hakur, don tana da fada. Na ce, ba komai, in dai sai an tsokane ta ne zata yi to ba za ta ta6a yin fada da ni ba. Matsalar in da zan dinga kai yarona kafin ya isa shiga makaranta, ko da rainon kudi ne. Ta ce, ki dinga kawo shi nan mana tunda shi ba mai haya niya ba ne, Mun je naga dakin, karami ne ta ce dubu shida shekara, dari biyar kenan dk wata, na ce ba komai, zan biya. Naje banki na ciro dubu ashirin cikin kudina nazo na bata shida, naje kasuwa na siyo kayan abnci da yar tukunuya da dan risho na dawo. Zaman mu da Hjy Iya ba matsala, don ina bn ta sau da kafa,daga ni sai ita a gidan tun Asubahi in na tashi zan wanke mana bandaki, in share tsakar gidan, komai na dafa zan bata. In ko zan yi wanki na kan ce kawo naki Hjy, kullum sai dai ka ji tana shi min albarka, Shadad kuwa dama tuni ta ce in dinga bar mata shi tunda in bana nan ba shi da matsala, musamman in ya gane cewa gidan muke kwana. In ko unguwa na fita dashi kiwa ce dashi, sannan ya yi ta 'yan rigime-rigime. Mun zauna yanzu albashina da kyar nike kai dubu biyar banki a wata, saboda hidimomin gida wanda a da ban san suba, kai ko kan wannan ba zan manta da Doctor ba, domin ita ce ke yi min komai. Burina na gaba shi ne, in koma makaranta, amma yaya zan yi da aikina wanda shi na dogara da shi? Wata rana da dare na shiga gurin Rahma muna hira, na ce mata ina son na koma makaranta, ta ce aikin fa? Na ce shi ne matsala, amma ina son in samu ko 'yar Diploma ba sai nayi jami'a ba, ta ce hakan ma yana da kyau. Aikina daga karfe takwas din safe ne zuwa hudu na yamma, sannan wasu su zo masu kaiwa dare, na ce Rahma ko in koma aikin dare ne. Ta ce albashinsu fa bai kai namu ba kuma yawan cinsu duk maza ne, na ce to ya zanyi? Haka nan zan hakura in dai manaja zai yarda ta ce matsayaci ba, sai shegen iko sai ka ce gurin shi. Na ce ai dama ba shi ne da gurin ba? Ta ce ba shi ba ne, na wata Hjy ce mai kudi, ina zaton ma ba a kano din nan ta ke ba. Na ce to Allah dai yasa in dace zan tare shi in masa mgn, Rahma ta ce to in ya ki fa? Na ce ki taya ni addu'a ya yarda, Rahma ta ce to Allah yasa a dace, in za ki masa magana sai muje tare .Haka ce kuwa ta faru, domin washegari muna tashi daga aiki sai muka nufi ofishin manaja, yana zaune gabn shi laptop ce. Muka gaishe shi, cikin daurewa ya amsa, na ce "Yalla6ai nazo neman uziri ne. Ya harare ni,wannan karon ko me kika zo nema kuma kowa ya mutu ba zan ba ki wasu kwanaki ba, sai dai in ki nemo wadda zata zauna madadinki. Rahma ta ce, Sir, ba mutuwa akayi ba, tana son koma mkrnt ne. ya ce, to sai ta bar aikin. " Ya ci gaba da abn da yake yi. Muka kalli juna ni da Rahma, na ce ko zan iya komwa akin dare? ko kuma in zo duk lkcn d nike free hr dare? Ya ce wace makaranta? Na ce poly zan shiga, ya kalle ni dama ba ki riga kin shiga ba? Na ce eh, ya ce to in kin shiga sai muyi magana. Ni da Rahma muka yi godiya, bai amsa mu ba, mu dai muka fita muna mamakin yanda ya saurare mu. Ina jin an fara saida form na garzaya na sayo. Rahma tana ta min dariya wai na cika zumudi, Allah shi ne mai shirya ma ba wa al'amuran shi. Yau gani na samu gurbin karatu a poly, daga karfe daya zuwa biyu nake tashi, uku in zo shago, bn damu da rage min dubu biyun da aka yi cikin Albashina ba, saboda na samu shiga makaranta. Kuma na samu irin course din da nake so, wato (Mass comm) Rahma da murnarta take shaida min saurayinta Sagir zai turo magabatan shi, na ta6a baki tare da cew. "Yau an yo odar kaya a shop din nan, kin lura? Tace eh na lura mana. Amma me yasa kullum na dauko batun Sagir sai ki daure fuska? Haka nan ranar da na ce kuje ku gaisa kikaki.Shi ko kullum sai ya ce in gaishe ki. Na ce, um, ki dai yi hattara da samarin yanzun. Ta ce, Sagir yana da kirki kuma aurena zaiyi, na kafa mata ido, kada ki ba wa namiji amana fa, in kin yarda kenan. "Ta ce, to zan kula. Wata rana ta ce min za su je gidan Yayar Sagir, zata gaishe ta, wai tayi 6ari, na shirya muje na kalle ta dabadan Rahma ba ce dana zabga mata ashar. Amma Rahma ta wuce in zage ta, kema da zan fada miki ki ji da sai na ce miki kada kije, ta ce ko zan san dalili? na ce yaudarar mazanzamani.Tayi 'yar dariya, "Hafsat me yasa kin matukar tsanar maza ne? Me suka miki har haka?" Murmushin takaici ya subuce min na ce, "Sun min da yawa." Ta ce, "Kada ki manta shekararmu 1 da Sagir kuma kudin gaisuwarshi na gidanmu." Sam ban san lokacin da maganar ta subuce min ba sai ji nayi ina cewa, "Shekaru 3 da watanni muka yi ni da Munnir, amma hakan bai hana shi yaudarata ba."Hawaye suka soma zuba daga idona. "Rahama zan fada miki amanar sirrina, in kin boye min kin kyauta, in kin tona min don kanki ke da Allahn ki." Nan na kwashe komai na labarta mata, ni kuka Rahma kuka, ta rungumeni babu mai ba wani hakuri sai da muka gaji da kanmu. Na ce, "Rahma zan koma boko ne kawai don faranta Ran Mahaifiyata, Insha Allahu zan kawo haske cikin zukatan Iyayena SANADIN BOKON nan." Rahma ta ce, "Ina bayanki, Allah ya shige mana gaba. Lallai zan ja baya da Sagir kuma ba zanje gidan Yar tasa ba." Na ce, "Na kula Sagir dinki kamar bashi da matsala, duk daba anan take ba. Ki ci gaba da mishi yadda kika saba amma ko da wasa kada ki bishi wani guri. Amma ni a kan kaina na gama soyayya, na kuma sha alwashin duk namijin da yayi gangancin cewa yana sona zan ci zarafinsa matuka. Rahma ko kinga laifina?" Ta ce, "A'a."Rahma 'yar amana ce, ko Mahaifiyarta bata fadawa labari na ba, haka na ci gaba da Karatuna tare da aikina, na tsare mutuncina ko a makaranta nasha jin ana zagina wai na cika girman kai, daga ganina ni ba 'yar kowa bace sai shegen Iyayi, ga daure fuska. Sam ban damu ba, sai dai mutum in ya isa ya zo gabana ya fada. Kwanci tashi har na hada Diploma, kuma ina da burin ci gaba da HND,shekara 2 kenan. Cikin shekara 2 har Shadad ya isa shiga Makaranta, kuma na lura zaya dauki Karatu sosai, shekarunshi 4 kenan da 'yan watanni. A hanyar zuwa gurin aikina naga wata Makaranta Al-Iman, boko ce da Islamiyya don haka na je Makarantar na karbar masa form, sun ce yaro ya zo tun 8 na safe sai 6 na yamma. Duk da Islamiya da hadda, sati da lahadi sai karfe 2 zai je. Alhamis da Juma'a karfe 2 zasu tashi. Tsarin makarantar ya min daidai domin zan samu lokacin daukan shi, sati na zagayowa ya soma zuwa, da dare kuma inai masa bita. Tambaya daya ya min wadda ta sa ni kwana kuka, tare da tunanin me zai faru nan gaba? Ko ba komai nasan nan gaba akwai kura, abin da ya faru ranar da ya fara zuwa Makaranta ya dawo muna yin home work ya ce, "Anty." Na dube shi, "Menene?" "Me yasa da kika kaina Makaranta baki sa min sunan Babana ba? Duk 'yan ajinmu ana kiransu da sunan Babansu, ni kuma ana kirana da Shadad H." Gabana ya fadi, amma da yake shi karami ne yanzun ba zai fahimta ba sai na ce, "H din nan farkon sunana ne Hafsat na sa maka ko baka so?" Ya ce, "Anty kowa sunan Babanshi yake sawa, wani yaro yace min wai menene H? Wai Hamza sunan Babana?" Na ce masa, "Ban sani ba, nace ba sunan Babanka ba ne, sunana ne kaji ko?" Ya ce, "To." Can kuma sai naji ya ce, "To shi Babana ya sunan shi?" Gabana ya sake faduwa na daure na ce, "Na manta, amma in na tuna zan fada maka." Na mike don kar ya sake yi min wata tambayar. Shadad karamin yaro ne amma in ya maka magana sai kayi zaton Babbane. Ina tsoron nan gaba kadan ya tsareni don in fito masa da Ubansa, abu 1 na sa a raina, shine zan zama uwarsa kuma ubansa, zan yi masa komai da uba zai ma dansa. Tun da na bar gida har yau ban daina kuka ba, ban daina tunanin iyaye da 'yan uwana ba, kullum sai na zubar da hawayena tare da yin Allah ya isa kwando dubu ga Munnir, ba zan zagi Boko ba sai dai ba zan gaji da cewa itace sanadin shigata matsala ba. Haka kwanaki suka yi ta shurawa Allah ya taimake ni na koma don samun HND sai dai manejin rayuwa nike, albashina yayi karanci ya dauki nauyin karatuna da na Shadad, don ma na tara kudi da farko lokacin Dr. tana nan. Sai dai na dauki alkawarin ko zamu kwana ba mu ci ba bazan taba neman taimakon abokin halitta ba, sai dai in nema a gurin Mahalicci. Cikin wannan halin yarinyar Hajiya Iya wadda ke zaune a Saudi ta zo ta dauke ta tare da barin amanar gidan a hannun Babban Yayan Rahma. Amma ni Hajiya Iya ta ce in yi zamana kyauta har sai lokacin da Allah ya daga, don ta ce ina lura da ita, kuma duk abinda na ci sai na bata koda bata san da shi ba. Na ji dadin samun wannan rangwame duk da cewa kudin ba wasu yawa bane dama, amma sauki yana da dadi. Na dawo ni 1 a cikin gidan, in zan fita na kulle, in sati ne ko lahadi ko dai wane lokacin ne Shadad ba zai je Makaranta ba sai na kai shi gidan su Rahma gurin mama, in ko ba nisa zanyi ba nakan yi kasadar kulle shi ya taka kujera ta ciki ya sa sakata, in na dawo sai na kwankwasa ya bude. ****** ******** ******* A garin Kaduna tun da aka wayi gari Hafsat ta gudu, bakin ciki ya karu ga zuciyar Innarta, don haka ta tattara yanata-yanata ta fice ta bar su Ummi suna ta kuka, Baba tana lallashinsu. Har ta isa Malimfashi idanunta basu kafe da hawaye ba, bata boyewa 'yan uwanta komai ba,sunji bakin ciki suma saidai sun bata shawarar tayi mata addu'a kada ta mata baki.Haka ta ci gaba da zama har zuwa lokaci mai tsawo. Wani abokin wansu Babba ya zo ziyara daga Huntuwa ya ganta ya ce yana sonta, bata da zabi tunda duk yayyinta sunnuna sun amince, kuma aurenta da uban 'ya'yanta ba kome. Alhaji Danlami Matarshi ta rasu wurin haihuwa, amma yana da yara kuma yana zaune tare da su ne, shekarunsa 3 kenan rabonsa da aure, ta tare a gidansa dake Nasarasa Funtuwa, dole ta koyi hakuri domin zama da yara sai hakuri, in ta kalle su sai ta tuna da nata da ke can wani gida. Sai ta kyautata musu ko don a kyautata ma nata, yadda take kula da Yaran sai suma suke son ta. Cikin haka ta samu ciki ba don san ranta ba, amma ba zata butulcewa kyautar Allah ba. Ta haifi danta namiji ya ci sunan Rabi'u. Umar ya kan kawo mata ziyara da 'yan kannanshi, mijinta yanada kara don in zasu tafi yanai musu shatara ta arziki. Shi kuwa Babansu Hafsa har yau yana bakin cikin tafiyar ta duk da shine ya koreta, yana kuma addu'a Allah kada ya bashi mai irin halin Hafsa cikin 'ya'yansa, ganin halinta ne da na Uwarta, ko wani buri suka ci na son abin duniya shiyasa suka dage da boko, boko har taje ta yi abinda taga dama.Ni kuma lokacin rayuwa ta min tsanani, zuwa wannan lokacin kudin da ke cikin account dina sun kare, albashina ya min karanci, karatuna ga na Shadad, ga abinda za mu ci, omon wanki, sabulun wanka har da suturar sawa, duk a dubu 8. Don ma bana biyan haya. Yau na wayi gari ko na karyawa bani da shi, ga shi wannan watan shine zan bada kudin term na Shadad dubu 4, gashi zan yi registration, gashi bamu da komai na abinca ga kudin dan adaidaita sahu. Hakika komai ya tsananta gare ni, kukana ya karu, nadamar barin gidan Iyayena ta sake shigata sai dai ba zan iya komawa gidan yanzu ba, duk da kuncin rayuwar da nake fuskanta. Lallai babu komai cikin barin gida in ba takaici ba, danabi Mahaifiyata na san danginta za su saurareni za kuma su fahimceni, zan samu gata ni da dana kafin Allah ya min sakayya akan Munnir. Bana ba duk wata 'ya mace shawarar barin gaban iyayenta don gudun zubewar mutuncinta. Hawaye na bin kumatuna ban damu da na share su ba, domin da hawaye na karewa da yanzun nawa sun kare. Muryar Shadad ce ta katseni, "Antyna menene yake damunki kullum kike kuka?" Na share hawaye tare da kakaro murmushi, "Babu komai." Ya dafa cinyata, "Kina tunanin Iya ne?" Na ce, "Eh." Ya tambayeni ni don ya san kalmar da zan fada mishi kenan, a duk lokacin da ya tambayeni haka nake ce masa. Ya bata rai, "Anty to muje gurin Iya din, ni bana so kina kuka." Na ce, "Da nisa jirgi ake hawa kuma bani da kudi." Ya ce, "To ina girma zan saya mana jirgi muje ko?" Na ce, "Allah ya sa." Kicin na shiga ina dubawa, ko zan ga dan wani abin na baiwa Shadad, duk da nasan cewa bani da komai. Shiru na yi tare da tunanin abinda zan bashi. Rahma ta yi sallama, na amsa, ta shigo kicin din tana cewa, "Ina Hajiyar gidan nan?" Na yi guntun murmushi tare da cewa, "Rahma kenan, duk tsokana kin santa." Ta ce, "Na zo shan tea din kin nan mai kayan kamshi." Na ce, "Sai dai na baki kayan kamshin ki je ki dafa." Ta zuba min ido cikin sanyin jiki, sannan ta ce, "Hafsa kin 'ki daina kukanki ko?" Na ce, "Ina kika ga ina kuka?" Ta ce, "Haba Malama, ga idonki nan?" Ta shiga bude-bude, bata ce min kala ba ta fita. Ina cewa, "Rahma zo ki ji." Bata juya ba ta wuce. A zuciyata na ce Rahma kenan, ita dai ta tsani ta ganni cikin damuwa, ina son zama da ita don ita kadai ce kan sani murmushi. Jim kadan sai gata da kunshin kosai da jug dauke da koko, bata min magana ba ta zuba ma Shadad. Na ce, "Rahma koko kuka dama?" Ta zabga min harara sannan ta ce, "Ai wallahi Hafsat kina bani haushi, ina lura da ke duk matse-matsen da kike yi cikin satin nan, har ta kai baki da abinda za ki ci amma ba zaki iya tambaya ba? Ni kam ko yaushe gidan ki nake cin abinci, saboda ina daukarki 'yar uwa ta jini." Na ce, "Rahma dama ni dake ai babu wani bambanci duk daya ne." Tsaki Rahma taja, sannan ta dora min dari 5 kan cinya, zan yi magana ta ce, "In kin ce tak Allah ya isa." Da kallo na bita har ta fita sannan na saka dariya, Rahma kenan. Karatuna ya shiga wani hali, har ina ganin in ba wani ikon Allah ba tsayawa zaiyi. Cikin wannan matsatsi aka sa ranar auren Rahma da Sagir, kullum tunani na me zanyi ma Rahma lokacin bikinta? Da dare Rahma tana min kitso muna hira na ce, "Rahma kin san me nake tunani?" Ta ce, "Kudin Registration?" Na ce, "A'a, so nake ki fadi abin da zan miki lokacin biki." Cikin tsokana ta ce, "Italian bed da leader sit." Muka sa dariya, na ce "Allah ya hore, har kayan kicin sai na miki." Ta ce, "Ni dai Hafsat nafi son ki bada hadin kai lokacin bikina kin ga dai bani da wata aminiya sai ke, sauran duk kawaye ne." Na ce, "Tabdijan! Rahma kada ki sani yin abinda ba zan iya ba." Ta saki kaina, "Kin san Allah?" Ta nuna ni da kibiya, "In bikina ya yi kyau ke ce in ya baci ke ce, kuma yanzune zan san matsayina a gurinki." Na ce Zaharaddeen Shomar what's app 08168575100 Sanadin Boko 1-8 Posted by ANaM Dorayi on 12:13 PM, 18-Sep-15 Under: SANADIN BOKO , "Maida wukar, Allah ya kaimu. Yauwa dama ina son in miki batun da ke raina. Ina son in samu manaja ya bani koda rabin albashina ne in sai ma Shadad takardu." Ta ce, "Kin san rashin mutuncin sa, abinda zai fi dai in tambayar miki rance gurin matar Yayana." Na ce, "A'a ki bari zan same shi in yaga dama zai yarda." Rahma ta ce, "Hafsa kenan, ke bakya son bashi sam! Kuma ai naga bashi hanji ne yana cikin kowa." Na yi 'yar dariya. Haka kuwa na yi, na samu manaja da bukata sai ya ce, "Kin cika daure fuska, da ace kina da fara'a har karin albashi zan miki. Banda kyautukan da zaki yi ta samu a kai-a kai." Na sake hade fuska, "Bana bukatar karin ko wata kyauta. Hakkina kawai nake so." Ya ja tsaki, "To sai ki jira lokacin baki hakkin ya yi, ke bazaki taba ganewa ba. Wai me ma zakiyi da kudin?" Ban amsa shi ba har sai da ya sake maimaita tambayar, Na ce, "Zan biya kudin littafan makaranta ne na yaro."Ya yi tsaki, "To sai ki jira lokacin don in kin ga na yiwa mace mutunci itama ta yi min ne." Na mike ba tare da na sake magana, don Manzon Allah ya ce ka fadi alkhairi ko kuma ka yi shiru, amma na so in zabga masa ashar in ya so ya kore ni gaba 1 daga aikin. Cikin kwanakin sai manaja ya soma shige min, duk da dinke fuskar da nayi masa, ya zo ya kawo min albashina wai gashi nayi bukatar da zan yi, na ce ya barsu ai ni na ma hakura. Kwatsam! Rannan sai naji ana buga min gida, lokacin 9 ta gota na dare, don har na soma bacci. Na zo na bude, nayi mamakin ganin manaja a gidanmu na ce, "Lafiya?" Ya ce, "Kalau, na zo ne mu gaisa." Na ce, "Na gode da gaisuwa. Sai da safe." Na juya ya ce, "Kina nufin har mun gaisa? Bai dace ki yi min haka ba." Na ce, "Za a min fada an hanani fita." Na fadi haka da nufin karema kaina mutunci. Ga mamakina sai naji ya ce, "Haba yarinya, ni zaki yi wa karya? An ce miki bansan cewa zaman kanki ki ke yi ba? Ni zaki saki jiki ki ci arziki ki saki, in ba zaki saki ba talauci sai ya yi ajalinki." Jikina ya yi sanyi lakwas, na maimaita kalmar zaman kaina! Na ce, "Ni ce mai zaman kaina?" Ya ce, "Sharri na miki? Kowa ya san ke kadai ce ba kuma a san iyayenki ba." Ya ja tsaki tare da cewa, "Banza mara rabo." Ya tafi. Ranar na yi kukan da ya isheni, wato kowa ya san zaman kaina nake? Wata zuciya ta ce, "To yanzun ai an daina kiwon dabba mutum ake kiwo." Sai dai da mutane zasu min adalci ya kamata su san cewa bana hulda da maza, da ace ina da wani aikin lallai zan bar super market din nan, sai dai bani da zabi. Da safe duk da kirkiro fara'ar da nike yi sai da Rahma ta gane cijewa nake yi saboda damuwar da ke raina. Ta kafa min tambayar me ke damuna? Nanfa na fada mata, na kara da cewa, "Dama duk mutanen unguwar nan kallon da suke min kenan? Ina zaman kaina?" Rahma cikin muryar lallashi ta ce, "Sam, shi dai yabi diddigi ya ji cewa ke 1 ce anan. Amma ba maza kike tarawa ba, kowa yana yabonki a unguwar nan don kin tsare kanki, kuma shi ya fada hakane don takaicin bai samu abinda yake so ba. Ki barshi da Allah." Nace, "To in ban barshi da Allah ba yaya zan masa? Ai bani da yanda zan yi dashi. Da ace ma ina da wani aikin barin musu wurinsu zan yi." Rahma ta ce, "To ai ba gurinshi ba ne shima cin arziki yake yi, don haka ba inda za ki je." Daga wannan lokaci muka sa 'yar tsama da shi, ya bi duk ya tsane ni, nima kuwa ya kara dasa min tsanar maza, yana son ya ga nayi wani dan kuskure ya tozarta ni, niko duk wata hanya da zata ja min cin mutuncin shi na 'ki sakaci da ita, lokacin zuwa aikina baya cika nake isowa, musamman in zuwan safe zan yi. ******** ******** ***** Munnir an kammala karatu an kuma dawo gida. Tuni ya manta da wata Hafsa da labarinta. Ya iso gida cike da soyayyar Mina, yarinyar wani kusa ce a gwamnati, sun kulle ne tun a yanar gizo ta (Facebook), sun jima suna soyayya kafin suga juna, bayan ya zo hutu itama ta dawo daga inda take karatu, suka hadu. Sun yaba da juna, sai dai sanin cewa ba za ayi musu aure da wuri ba suka kazanta soyayyar su ta hanyar biyan bukatar zukatansu. Sam! basu dauki hakan laifi ba, nasu ganin duk cikin soyayya ne a nasarance suke koman su don boko suka sani, shi suka iya, kuma shi suke yi. Sun dai kulla alkawari ga junansu cewa za suyi aure in lokacin yinsa ya zo, Allah ka shirye su shirin Addinin musulunci. (Ameen). ¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Bikin Rahma ya gabato don haka na ciro dubu goman da na makale na ce mata na ba da rabin kudin Registration naje nasai mata sestin kula da jug. Dubu bakwai na kashe, nazo na kai mata gida, batan hakan ya min dadi. Su Mama suna ta gdy, ta ce yanda garin nan babu kudi shi ne zaki ta wannan dawainiya har haka? Na ce Mama ta kama ne. Da dare ina krtn Alkqur'ani,sai gata ta ce, Yayi kyau Hafsa, ina kika samu kudin sayan kayan ban masu tsada?Na ce Daga Sarki Allah. Ta ce, ba dai kudin Registration din ba ne? Na ce in sune fa? Don Allah zo ki zauna muyi batun anko. Ta ce ba zama nazo ba ki zo in ji Sagir da wani abokinshi, ki fada musu kudin abubuwan da zamu yi. Da karfi na ce " What? hum........ hum..... Rahma kada ki sani cikin hulda da maza. kije kawai ki amsa, na yarda zamu je kasuwa siyayyar tare. Zata yi mgn na rantse mata da girman Allah cewa ba zani ba, ta juya ba tare da ta ce kala ba. Nasan tayi fushi, amma sam fushinta bai dame ni ba, in dai akan abin da zai sa nayi hulda da maza ne har nai musu dry. Don ni nasha alwashin namiji ya gama ganin hakorina. Mun je kasuwa, duk abn da zamu bukata gurin walima mun sayi, don Walima kadai zamu yi kayatacciya, sai dai ta ce, Sagir za suyi (Dinner) kuma za su yi (Pink & blue day). Kullum rokona take in je har dai na amsa mata zani. hakan ya tilasta min siyan shadda kamfala (pink) mai ratsin bulu,yayin da Shadad na dinka masa(blue) din shadda, atamfar walima kuwa Rahma da kanta ta sai min., Bikinmu yayi kyau, komai a gidana aka yi duk da cewa ina zuwa gurin aiki da mkrnt, kin yi wa Manaja mgn nayi don ba zan sake yi mishi wani zance ba, ko neman wani abu. Ranar daurin aure kam ban je makarantaba, kuma banje aikin ba, saboda aubuwan sun kwa6e min. Malamai sun halarci walima, sun kuma yi nasiha akan mahimmancin yin aure tare da falalar da ke tare dashi. Sun ja hanklin iyayen yara masu cewa su dole sai 'ya'yansu sunyi boko mai zurfi, ko sai sun kama aikin kafin suyi aure. da cewa wannan ba koyarwa addinin Musulunci ba ce. Suka ce, ita mace babu abinda yafi daraja da mutunci a gare ta irin aure. Sun ce boko ba ya hana aure, kamar yanda aure baya hana boko. In 'ya'yanku suka lalace saboda kun hana su aure sai boko, hakika laifin zai fi ta'allaqa a kanku iyaye., Nasihar da suke yi ta sani shiga dogon tunanin, ni kaina misalice SANADIN BOKO gani yau na zama 'yar kaina, domin da ace ban ce bokoba nabi zancan mahaifina nayi auran da yaso, da yanzun ina tare da dangina da ban kashe auran iyayena ba, da ban haifi shege ba, da maxa ba su dinga latsa ni suna son mu lalace ba. Ban san hawaye na sauka daga idanuna ba, sai dai hannun Rahma naji a kumatuna tana share min tare da yi min rada a kunne. Haba Hafsa cikin fa taro ki ke, ya ya za ki ba mutane damar yin tunanin ke wacece? Please ki share don Allah. Walima ta tashi lfy, na ce da Rahma bari na leka shop, kin san ban dauki uxiri ba, ta ce min ba damuwa. Naje na samu su Ishak, ya ce nasan kuna biki shi yasa ban tashi ba, na fada mawa manaja cewa zan zauna madadin ki har ku gama biki, ya kuma san auran Rahma ne shi yasa bai ce komai ba.Ya kara da cewa, ki koma har sai kun gama ki mata fatan alheri, mun so muzo daurin aure amma kin san Manaja. Na ce na gode, ya ce a'a ba komai, wata rana irin haka zata iya faruwa da mu, na dawo nake fada ma Rahma ta ce, Ishak da Musa suna da kirki sosai, dn dai kin kasa Fahimtarsu ne. Na ce, Ba zai sa don sun kar6ar min aiki in sakar musu fuska ba, gaisuwa kawai ke hada mu ko da, kuma ita zan ci gaba da yi kadai. Anje anyo ma Rahma danki(jere) an zo ana ta lbrn kyan gidan an ce ango ma ya zuba labulaye da kayan wuta, Sai an kai Amarya sannnan za'ayi sauran shagalgulan da ango suka shirya, wai ba a son mutane suyi yawa, sai ka nuna pass sannan zaka shiga. Da muka kai amarya unguwar Sharada, gidan kam ko ni ya min sosai, taso in kwana na ce mata ta min hakur sai gobe in mun hadu gurin (pink & blue day' . Ta ce don girman Allah kada ki ki zuwa, na ce kin sanni Rahma in har na ce zan yi abu bana fasawa, ta ce shi kenan, ki gaida min Shadad. Na tafi ina hawayen rabuwa da Rahma, don ita wani bangare ne na farin cikina. Gidan su Maman Rahma naje na dauko Shadad, jikinshi naji da dumi, ina zuwa gida na bashi (paracetamol) Na kwantar da shi. Sannan na shiga gyaran gida. Ina zuwa na samu ma yayi bacci, nayi Shafa'i da wutiru nima na kwanta. Cikin dare na farka don yin nafila kamar yanda na saba, sai dai kawai naji jikin yaro sharkaf da zazzabi. Na cire masa riga na dunga goge masa jiki da ruwa mai sanyi. Sanna na kara bashi magani, kafin safe Allah ya taimakeni jikin yayi sauki. Sai dai yan rigin gimun da yake yi na shiga gidan su Rahama muka gaisa da su mama, ina zama Kiran Rahama na shugowa, ina ji dama nasan ita ce, dan bani da number kowa a cikin zumu dina na daga ina cewa hajiya kenan, amarsu ta ango. Ta katseni da cewa, ba wata hajiyarki, shine ko ki kirani da safe ko? Nace shi kenan sai na hau doka maki kira da safe kisa angonki ya ji haushi na. Tace wane ango? Kin san Allah ba nan ya kwana ba, tare da su hadiza kawaye na muka kwana, ba ke kinki ba? Nace ai gara da na dawo, dan na sami shadad da zazzabi haka muka kwana. Amma yanzu Alhamdu lilahi. Tace to Allah ya kara sauki. Tace don Allah ina sa ido gurin programme din nan, wlh in baki zoba bikin zai baci, don kina da muhinmanci matuka a gurin. Nace to zan kokarta duk da shadad nata yan rigingimu, kin sanshi in baya jin dadi sai yayi ta rigima, tace yaro kenan Allah dai ya kara sauki,nace amin, yace kizo da wuri dai. Sai da na fara yima shadad wanka, sannan na shiga na fito naga gari ya soma hadari, nayi alawala dan yin sallar la‘asar, haka kawai yau naji ina sha‘awar shafe shafe a fuskata. Na fito da kayan shafa da rahama ta di bar min na lefenta, har da jaka da takalmi da mayafi ta bani duk pink, tun asali ni mai son yin kyale kyale ce, halin da na tsinci kaina ne yasa na daina, nafi minti 30 ina kyalekyale a fiska ta. Na dinga kalon kaina a madubi nasan nayi kyau sosai, har shadad yana kallo na, nace nayi kyau? Ya daga kai ina kulle gida rahama na kira na, na daga tace aminiyata ki tai makeni kada kisa naji kunya, wlh guri yayi guri amma ke kadai muke jira da wani abokin sagir da ya sauka daga adamawa state, anje daukoshi daga filin jirgin don Allah kiyi sauri. Nace to zubaina ganin zuwa amma fa garin akwai hadari, Allah yasa in sami abin hawa da wuri. Tsaye nake a bakin titi duk wani dan a daidaitan da yazo yana dauke da mutane, masu son banza watan yan rage ma mata hanya suna tsayawa Amma ni ko kallon su bana yi. Wata jibgegiyar jeep ta zo ta gifta, sai kuma ta dan dawo.sai tin inda nake ta tsaya, gilashin motar ya sauka a hankali,naga mai tukin saurayine yana sanye da shadda yar gaske blue mai duhu, hularshi itama blue ce, amma kalar sararin samaniya. Ta gefen ido na kaleshi, sannan na dauke kaina. Yace, yan mata ina zaton guri daya zamuje in na lura da shigar da ke jikin ki ko? Na kaleshi nace ba dole hakan ta kasance. Yace, yace ki shugo muje kinga hadari. Nace kuje na gode. Glashin baya ya sauka, naji saukar galas din ne da wani sauti da yayi, amma ban waiga ba, saima na dan kara taku biyu ta baya na. Muryar da naji ne tamkar in waiga, amma sai na dake yace shugo mana ga hadari nason zubo da ruwa gaki da yaro. Na dubeshi dan son in tuna inda na san wanan muryar, kyawunshi yasa nayi saurin kauda kaina, tare da cewa kuje ni ba zan shiga ba.daga cikin motar naji wani yana cewa don Allah mutafi amma za a taimaka mata tana yiwa mutane yanga,da sauri na kallesu cikin bacin rai, idanuna har kan kancewa sukayi don ta kaici, cikin kalon hadarin kaji nace taimako? Ce muku nayi ina neman taimako? Na dan duka tare da leka motar, kai me fadin taimakon nan kasani bana neman taimakon wani abin halita sai ma halincci, ni ban tsai da ku ba. Na kara rike hannun shadad da kyau, na soma tafiya dai dai da ruwan ya kece, kamar da bakin kwarya, ba tsanmani sai naga kofar ta wangale na bakin kofar ya sauko kafa tare da sauko hannu ya dauki shadad zuwa cikin motar, a gigice na dubesu yace ki shigo in kuma ba zaki shigoba ki samemu a can. Amma shi kam ruwa ba zai dake shi ba. Bani da zabi, tunda sun daukar min yaro dole na shiga. Gashi bana son dukan ruwan, don haka sai na shiga. Shadad na ciyar mutimin da muryarshi ke sani faduwar gaba, kamar na taba jinta ada innaso in tuna inda nasan muryar ko mai irinta. Muryar ta sake katseni da tunanin da nake yi, yace ma shadad boy ya sunanka? A zatona shadad ba zai yi masa magana ba, saboda shi yaro ne mara son ma gana, musanman in bai san mutun ba, sai naji yace shadad. Mutumin ya mai maita sunan shadad, sunanka yayi dadi, to wanan fa? Ya nunani ya sunanta? Shadad ya kalle ni, na zabga mashi harara, amma ga al‘ajabi na sai yaron nan ya kauda kai yace anty. Mutumin yace to kana zuwa makaranta? Yace eh al‘iman sunan makarantar mu, kuma muna yin (A B C D) har da(1234). Na rike baki inata al‘ajabin yaron nan, tunda nake dashi ban taba jin yana rarata surutu haka ba, harda kin kalona shida ko abu aka bashi da ya kali fuskata zai gane, in ina nufin ya karba ko karya karba amma sam ya ki kallona tunda ya gane ina hararan shi. Mutumin yace gud, kana yin kokari? Yace eh mana, har ma naci number one, aka min kyautar books. Anty na kullun tana koya min karatu, da su home work harda ma islamiyya, ban san sanda nace shut up stupit boy! Mutumin ya kalle ni, shikuma shadad ya kwanta lakwas a jikin mutumin. Ya tsorata dan bana mashi tsawa, ko yawan zaginsa. Na daga can gefen yace. Ke! Wai wane irin hayaki kanki ya keyi? Ko kuwa ance maki wani kyau ne dake? Ko ance miki sonki ake yi? Ko kuwa burgewa ce wannan masife masifen da kike yi. Nace kai saurareni bana son shishshigi da katsalandan cikin lamari na, nayi magana da kai? Ko nace ka kalle ni ne bare ka tan tance kyauna?gani na kayi a filin gasar kyau? Balle kace nace ina da kyau ne? Masifa kuma dole ku jita tunda ku ka nace sai kun dauko ni, haka nan bana bukatar burge kowa cikinku na fison in burge kaina. Don haka yi ta kanka dan dukanku bakwa gaba na, zaiyi magana mai dauke da shadad ya daga masa hannu alamun yayi shuru. Shi kuma yaci gaba da shafa kan shadad wanda yayi kwance a jikinsa. Wayata ta shiga ruri, ban ko kula ba dan nasan rahama ce, sai yi take tana katsewa, ana 5 din na daga a kufule, don itama haushinta nakeji ba don bukin ta bane wa za ya hadani da wayanan gardawan. Mukhtar Ismail Muhammad WhatsApp: 08161892123 Sanadin Boko 1-09 Posted by Mukhtar Ismail Muhammad On www.arewarulers.com.ng Under: SANADIN BOKO Don itama haushinta nakeji ba don bukin ta bane wa za ya hadani da wayanan gardawan. Cikin fada nace wai meye ne kika dame ni da kira, ina hanya in kuma zaki matsa min sai na juya gida abina. Tace mai da wukar Allah ya baki hakuri, da ma ruwan da ake shekawa ne nace bari naji ko kin koma gida ne saboda ruwan sai direban su sagir yazo ya daukeki. Nace na hutar dashi, gani nan zuwa na kashe wayata tare da tsaki.Harabar hotal dam yake da jama‘a, ko ince motoci jama‘a sun cika holl din suna tsayawa na kama kofar zan buduwa. Ashe daga gaba ne direbab zai bude mu. Yana budewa na fita, sanan na nufi ciki mai surutun tsiya nan shadad ba tare da na kalesu ba na nufi wata yar baranda ina ta yi mashi fadan irin surutun da ya dinga tsugawa acikin motar, sai ya bale mun da kuka yana fadin.uncle! Uncle!! Nace yi min shuru ko in mareka, sarkin shishigi, bai daina kukan ba, na na ciro wayata na kira rahama gani nan fa ba zan iya shiga ba, mutane sunyi yawa. Ta ce mun ganki kin tsaya ga Aisha nan tazo zata taho dakegurin mu tare zamu shiga. Nice a gefen amarya sauran kawaye suna bayan mu,haka nan ango da abokan shi suna biye da mu, ina reke da hanum shadad, wanda har lokacin bai daina gunjin kuka ba, muka shiga. Kidan da ke tashi kamar zai fasa kwanya yasa naji tamkar in bar gurin kai tsaye. Wani mai dauke da abin magana yace, ango da amarya sun shigo, kowa da amininshi zai zauna, sagir ya zauna gefen shi wanan mutumin, ni kuma ina gefen Rahama tare da shadad ta dube ni, mutuniyata wa ya taba ki ne, naga fuskarki ta kasa boye fushinki, nace uhm! Ke dai bari, abokanan muijinki ne wlh, sai kuma shadad yaron nan ya kular dani yau. Tace to dan saki fuskar mana saboda guri ya kayatu, kisan fushinki zaisa gurin ya dishe. Na harareta tare da dan murmushi, tace ko kefa. Sagir yace ranki yadade, ya gajiya? Na nace tana gurinku ya jama‘a? Yace gasu muna tare nace Allah yasa alheri, da ganan na maida hankalina gun mai abin magana, yace za mu kira baban bako kuma baban abokin ango don yayi mana jawabin maraba tare da dan fada mana wanene sagir. Sai dai kafin nan babar kawar amarya hajiya hafsat sai ta bude mana taro da adu‘a, na kali rahama tace please, tashi kawai. Na mike cikin natsuwa na isa gurin na amshi abin maganar. Shadad yazo ya rikeni yana kuka, sai wai abokin ango ya taso ya daukeshi. Bayan n gama adu‘a na dora da karanbanin nawa, ina bawa jama‘ar da ke gurin nan shawar kada suyi liki, almubazaranci ne ga duk mai sha‘awar ya burge ango da amarya su dan ka musu a hanun su, amma ba dole bane kuyi yanda nace,sha wara ce. Na koma na zauna, bayan sun bini da tafi. Shiko da zaije yin jawabin maraba tare da shadad yaje yana rike da hanunshi. Cikin jawabin ne naji yana jaddada maganata cewa abinda na fada yayi kyau, don haka ba‘a son liki, duk wanda zai lika yazo ya ba ango ko amarya a hannusu. Wanan ma yasa aka kashe rawa da za‘ayi, rahama ta dinga yi min dariya wai a gaisheni da karfin hali har ta sanima na dinga dariyar. Sagir cewa yayi nazo na hanasu rawa, to wane rawa zasuyi ba liki? Nace tai makonku nayi ai rawa haramun ce ko? Haka aka ta gabatar da abubuwan da za ayi har lokacin da akayi sanarwar ango da amarya tare da da masu tayasu zama dan dibar abinda suke son ci da kansu, kasancewar dibi da kanka ne za ayi a gurin. Muka hadu muka jeru amarya tana biye da ango yayinda ni kuma nake biye da abokin nashi, shi kuma yana dauke da shadad a kafada tamkar wani danshi. Ango yasa abida yake so sai fruit ya ce ko zaki tai maka min? Inji abokin ango tamkar ince a'a amma sai nace me zan sa maka? Ganin yana sabe da shadad yace ki samin ko menene, zan ci. A raina nace kaji dashi, ba tare da tsayawa tunani ba ko mai hanu na yakai shi nake zuba masa, sai da na shake plate din sannan na bi bayanshi da plate 2. A gabanshi na dire tare da samashi cokali, na koma ma zaunina. Sai kurum naji sarkin surutun nan wato mai rike da abin magana yana cewa, kai gaskiya ango da amarya kun burge ni, kun zauna da aminan ku kuma mata da miji har da dansu, to yace ke amarya yaya bakiyi koyi da kawarki ba kema ki zuba ma ango da kanki? Kai abokin angon nafa yi maka murna, matar kada kayi mata kishiya, dubi yanda ta cika maka plate da kaji da kifi kila abinda ka fi so kenan, wanan ya nuna ko a gida ba a barinka da yunwa. Sai kurum naji gurin ya dau tafi. Da sauri na dubi plate din, lallai kam kaji ne da kifi, sai dan cosilo a gefe, na dubi fuskarshi yana dan murmushi. Rahama da sagir kuma dariya naga suna ta shekawa nan take na hade rai tare da kin kai komai bakina. Shiko shadad sai uban cin naman nan yake yi, shi da mutimin tuni gurin ya rikice da ciye ciye kowa na diba da kansaRahama tace to kici mana,nace mata ke ni nama koshi, ba yan haka ma ni ba zan iya cin komai a taron nan ba, kowa yana kallona. Haka nan bayan an tashi duk na matsu naje gida domin magariba ta yi, ina so inyi sallah sai dai tun da muka fito banga shadad ba, ban ga mutumin nan ba. Nace rahama ina suke? Tace suna cikin jama‘a in dan jira. Can nesa na hango wani shago naje na siyo ruwan naira 10 nayi alwala, nasami gefe dama da hijabina a jaka, nayi sallah ta. Rahama tazo tana ce min sun dawo? Nace ke zan tam baya, ina mijinki? Kune kuka sanshi ku zaku nemo shi. Takira sagir tace sun ko dawo? Hafsat tana son zuwa gida. Yace a'a na kira wayarshi kuma a kashe, tace a a to ina ya shiga? Kai kana inane? Yace gani nan kusa da shago ina kallon ku ai. Muka nufi girin ango, hankalina ya tashi da rahama take fada min wai wayanshi a kashe.rahama ta dubi angon ta tace, ba kace min bako ne ba? Yace eh amma kano ba bakuwa bace a gurinshi. Ki kwantar da hankalinki, yauwa gasu nan zuwa ma, duk muka kai duban mu gurin shi. Yana rike da hanunshi, shi kuma yana reke da leda. Suna tafe suna yan zan tukansu har suka isko mu, nace kai ka cika shegen yawo, ina kaje? Na finciko shi yace anty munje masalaci ne da uncle, ba kin ce mun wai in dinga sallah a farkon lokacinta ba? Nace naji ni dan Allah wuce muje na dubi rahama sai watarana, tace dinner din fa, anjuma karfe 10 naja tsaki ke kinsan ba zan iya wanan galafirin ba, gara ke sai dai nazoo. Sagir yace ki bari a kaiki don Allah, gari yayi sanyi ga duhu, nace nagode, sai anjima nayi gaba.Wani daga cikin abokan da suke tsaye wanda har dashi muka shigo motar nan da zamu zo, ya dubi rahama yace kai wanan kawar taki ta cika masifa, ita ba kyau ba rahama tace a a kada ka zagar mun kawa masa‘udu, hafsat bata da masifa,tana da kirki sosai na jima banga mace mai saukin kan hafsat ba, ita dai abu 3 ta tsana a rayuwarta, inko mutun ya kiyaye ba mai jin su. Ni da ita bamu taba yin fada ba koda munyi sai dai ni ni na ta sababi na amma bata biye min. abubakar lamido yace yanzu kai kaga masifarta? Ya dubi masa‘udu masa‘udu yace au yanzu duk abinda take maka baka gani ba? Yace ni kam me tamin? Bata min komai ba, duk abubuwan da takeyi sun matukar burgeni. Ya dubi rahama, ni kam in tambaye ki? Rahama tace ina jin ka, yace amma dai ba matar aure bace ko? Rahma tace a a daga nan bai sake magana ba. Duk abubuwan da Abubakar Lamido ke gani daga hafsat bai taba ganin wani aibunta ba, tunani 1 ya dameshi, ina ya santa? Shi dai yasan cewa koda a hanya ne ya taba ganin ta. Anashi ganin Hafsat ta san mutuncin kanta shiyasa take wanan dabi‘un. Acikin masauki ya kasa zaune da tsaye, baisan meyasa ya damu kanshi da dabi‘un hafsat ba, bai taba ganin mace da ta burge shi irin ta. Yasan daga ganin halayenta za asha wuya kafin a samu soyayyar ta, duk da bashi da tabacin sonta yake ko burgeshi take. Ya dai san ko ma dai menene ya damu da ita. Kafin kwana 3 ya damu da son sanin wacece ita? Alwashi ya sha ma kansa ba zai bar kano ba har sai yasamu cikaken labarinta, wanda yasan gurin rahama ne kadai zai san haka, haka a rana ta 4 ya kira sagir yace gashi nan zuwa, zaya ci dinner tare dasu. Duk da tulin kayan da aka tara a gaban shi na lashe-lashe da tande-tande, sam basu dameshi ba, ya dubi sagir cikin hausarshi na fulanin yola ya ce, nikam ka bani dama inyiwa amaryarka wasu tanbayoyi game da kawarta nan sagir yace wace ba dai hafsatba? Bai san da lilin fadiwar gaban da yaji ba, haka nan bai san lokacin da kalma ta fito daga bakinshi ba, tana da miji ko? Ya tsare sagir da idanun shi masu kama da na mata.Sagir ya ce bata da miji, amma fandarrarun halayenta ne zasu gundire ka, yace bana zaton haka, yanzu dai nafi so ka min izinin zantawa da matarka, yace to ya kirata tazo ta zauna tare da cewa ba dai har ka gama cin abincin ba?Yace ai kafin abincin ya samu shiga nikam sai naji batun kawarkinnan hafsa. Rahama ta dubeshi da sauri tace me kake son sani game da ita? Yace unguwarsu da kuma dan lbr ta haka rahama tace unguwarmu daya, sannan ita daliba ce a Poly yanzu haka tana HND dinta ne. Iyayanta fa mutanen kirki ne? Rahama ta danyi din sanan tace eh yace ta taba aure ne? Kuma shadad dan tane? Nan take zufa ta karyo mata, amma bata da amsar da ta wuce eh ya jijiga kai, dama nayi zaton danta ne duk da batayi kama dashi ba sun rabu da mijinta ne ko ya rasu ne? Nanma tace eh, yace Allah sarki inaga shiyasa bata son hulda da maza, dama ance mace in mujinta ya rasu kafin ta manta da wuya. Iyayan ta din sunan layinku? Rahama tace eh, a a karatu tazo suna kaduna. Gurin aikinmu daya ne super market ne, yace to zan iya samun number dinta? Rahama tace wai gaskiya yallabai sai dai kayi hakuri, in na baka number ta zai iya zama sanadin rabuwar mu kwata-kwata. Ya dan yi shuru yana nazari, Rahama tace duk yanda kake tunanin hafsat ta wuce nan. Yace amma ina zaton bakinki naji yana fadin tana da saukin kai da dadin zama, kuma bata da fada? Rahma tace gurinmu mata ba, amma game da maza sam bata da sauki, ta tsani namiji ta kijinin ace anason ta sanan bata son taimako daga namiji, ko wannen abu 3nnan ba taso. Yace to me tafi so? Rahama tace abinda tafi so shine kada kashiga harkarta, in kuma kashiga kayi tsananin dace ta kula ka to kada ka tam bayeta ko wace irin tanbaya, sannan kada kace kana sonta, ban san me zakayi ba ta saki jiki da kai ba, don naga maza da yawa wanda suka sota amma dole suka hakura rashin sakin fuskarta yasa maza suna tsoranta. Da zaka hakura da ya fi maka lada don ko taji hau shin abinda MC yace mata a gurin bikinmu inda yace ku miji da mata ne. Abubakar yace niko sai naso ace gaske naji dadi maganarsa. Rahama ba zan iya hakura da hafsat ba don ina jin wani abu game da ita wanda ban taba jinshi a wata yarinya ba ina zaton shine so. Su Rahma suka sa dariya sagir ya nisa yace lalle sonka din nan ya iya jan rigima ya fada inda zaku sha wahala Abubakar yace sona yayi daidai don yasan bama ra‘ayin mata marasa aji wadanda ke bin maza da kansu suce suna so zanje in gwada sa‘a ta kafin na bar kano zanga yada zamuyi. Sukace Allah ya taimaka yace kasan ban sami daurin aure ba so bansan gidansu rahama ba bare insan nasu hafsa din. Yace bari inje in nuna maka daga nesa suka fita suna dariya ba tare da yace komai ba shi tuni ya manta da menene a gabanshi ko da sagir ya nuna mashi sai yace ba yanzu zanje ba sai gobe da safe. Ni kam tuna ranar da muka dawo daga bikin rahama kulin shadad bashi da magana sai ta uncle dinshi tun ina jin haushin shi ina mai fada har na dawo lallashinsa, saboda har lokacin yana fama da zazzabi nakan lallabashi da cewa kayi hakuri zai zo ya daukeka ranar cikin dare har da cewa to anty kirashi a waya nace to ka bari sai da safe yanzu yayi bacci, cikin kwana ukun nan da kyar na samu ya manta da maganar uncle sai jifa-jifa. Da safe yana sanye da kayan makaranta ni kuma nayi shirin gurin aiki. Yau bani da lecture da safe don haka gurin aiki zanje dama ka‘idar da manaja ya bani kenan dan a daidaitanmu yana jira, shadad ya fita da gudu ni kuma na kule dakin na fita. Ina rufe gida naji muryar shadad yana cewa anty ga unclena anty na wai wayo baya na datse kwado, ilai kuwa yana tsaye jikin wata yar kyakyawar motar blue kiran kanfanin (toyota) sanye da t-shirt da wando jeans baki, riga baka da ratsin ja. Ta kalmin kafarshi baki ne sauciki. Na dauke fuskata daga kalonshi bacin nayi fuskar shanu shadad wanda tuni ya daneshi, murna yake yana cewa unclue kazone? Da ma anty tace indaina kuka zakazo, takaici ya kamani. Shi kuma sai ya dubeni anty antashi lfy? Ba tare da na kaleshi ba nace kalau na daga labuln dan a daidaita na shige. Sai naji yana cema dan a dai daitan, ungo nan malam kaje sai bayan kwana 2 ka dawo tun da nazo ni zan rinka kaisu kafin in tafi. Ya mika mushi yan dubu dubu sababi fil guda 3 ya amsa yana cewa na gode yalabai to sai zuwa yau she zan dawo yace nan da kwana hudu haka nace sannu da karfin hali menene gamina da kai? Da har zakaso ka min iko? Bai ce kala ba ya juya. Na cema dan a daidaita sahu muje na leka nacewa shadad zo mutafi ko nayi tafiyata. Mutumin ya kaleni shima fuska a kame ki fito muje ban san sanda nace to ubana! Sai kazo ka jani ya kara matsowa saitin dan a daidaita yace ka sauketa katafi abinka. Sai kawai mai a daidaita yace kiyi hakuri yar uwata, ki sauka ban tankashi ba bankuma sauka ba,gani nayi zamuyi latti nace yanxu kai malam haka zamuyi da kai? Duk tsawon lokacin da muka dauka yau kace bazaka kaini ba? Yace to Alhaji ne yace ki sauka ai, kuma ni bansan dangantakarku ba kada in shiga hurumin da banawa ba. Nace to bawata dan gantaka a tsakanin mu, asalima ni ban sanshi ba da muna da alaka da baka gan shi ba ko sau daya? Yace ki sauka mana nasan duk yanda akayi kunsan juna. Ganin zai bata min lokaci sai na sauka na dauki jakata nace shadad ya wuce muje, a mota yasaka shi amma ya tada mota sukayi gaba. Na tare mai mashi muna ciniki yazo yace mai mashi tafi abinka, in ka dauketa zaka gamu da hukunci... kafin ya rufe baki yaja mashin ya kara gaba. Na kaleshi nace me kake nufi dani? Yace gurin aiki zan kaiki kawai,nace banaso dan Allah kai mayene? Yace a'a ni ba maye bane, to bin me kake min? Nifa ba yar iska bace. Yace nasani ai, to dan Allah kafita hanyata, in kanawa darajar mahaifinka. Yace don girman Allah ki shiga motar nan mu tafi, kada shadad yayi latti, sannan inaso ki bani lokaci nazo mu dan tautauna, nace bani da lokacin da zan iya baka, ka fita harkata please, nacigaba da tafiya. Ranar dai a kasa na tafi gurin aiki, shikuma sukayi wani guri shida shadad, nasan sai dai suyi tambaya amma shadad ba zai iya gane makarantar ba, ganin nakusa bansha wahalar hawa abin hawa ba na karasa, takwas ta gota ina shiga ishak yace yau bamakaranta kenan? Nace eh, gashi ma nayi latti, musa yace manaja kuwa yazo yananan ya zagaya ciki nasan sai yayi maki surutu, nace uhum sai dai yayi tunda dai latti na riga nayi shi.Ina zama yana isowa, ban ko kalleshi ba na jawo takarda dake kan teburina zan fara duba abubuwan da suka fita da safen nan, sai ya ce, "Kin san zaki zo da safe me yasa zakiyi latti?" Na ce, "Abin hawa ne ban samu ba." Ya ce, "Amma ai ba'a wahalar mai ko?" Na ce, "Kamar yaya?" Ya ce, "Ballantana ki ce ana wuyar abin hawa." Na ce, "Akwai abin hawa mana." Ya ce, "Baki da kudi ne?" A kagare na ce, "Ina da shi." Ya ce, "Ok kin soma gajiya da aikin kenan?" Na san shi sarai zai iya cewa ya koreni, kuma dai Allah ya sani da aikin na dogara, don haka nace, "Tunda ba halina bane lattin amin uzuri." Ishak yace ayi mata hakuri Sir. Ya ce, "Kune kuka iya bada hakuri ita bata iya ba ko? To ba zan mata uzuri ba, sai dai in taimaka mata." Cikin sauri na ce, "Bana son taimakon kowa sai na Allah, nace dai amin azuri." Ya ce, "To ki je gida ki huta na sati 2 don ki koyi yadda zaki dinga zuwa aiki." Muryarshi muka ji ya ce, "Uzuri za'a yi mata manaja." Ya dubeni har na mike, "Koma ki zauna. Manaja akwai uzuri a rayuwa, ko tana latti?" Ya ce, "A'a ranka ya dade bata dai da mutuncine, in banda rainin hankali tana fada min akwai abin hawa kuma tana da kudi amma ta zo latti?" Ya ce, "Duk da haka ka mata azuri da tace baka san dalilin ta ba, so tayi zamanta." Na dube shi ina mamakin karfin halinsa, sai naga ya nufi Ofishin manaja na ce kila ya san shi ne. Ni dai na zauna na ci gaba da aikina. Ina jin Musa da Ishak suna mitar rashin mutuncin shi.Abubakar ya dubi Manaja ya ce, "Ka daina yiwa mutane haka, musamman na kasa da kai, a rayuwa dole ne mutum ya dinga hakuri, yanzun kasan uzurin da ya tare ta?" Manaja ya ce, "Yallabai yarinyar nan bata da mutunci sam!" Ya ce, "Ko zan iya sanin halayen ta marasa kyau?" Ya ce, "Na 1 bata da fara'a ga kallon banza, kuma ta fi karfin kace zaka taimaka mata sai ta hau bala'i, ina ce sakin fuska ma abu ne?" "Ni kuma hakan ya birgeni." Abubakar ya katseshi, "Ban ga laifinta ba, don ta kare mutuncin ta. Shi kenan sai ya zama zubar da mutunci don bata saki fuska ba?" Manaja ya yi 'yar dariya, "Yallabai yarinyar nan fa in ma sonta kake ka hakura don ba zata baka hadin kai ba, in mata kake so 'yan gayu isassu na debe kewa sai in kawo maka su. A ina ka sauka?" Abubakar ya ce, "Na fada maka ina son ta ne? Ko na fada maka ina son mata ne? Inma matan nake so ai baka fini saninsu inda zan same su ba, ina maka nasiha ne ka daina wulakanta na kasa da kai, in dai suna yin abinda ya dace." Ya ce, "To zan kula Yallabai -ya ci gaba da cewa- Ya hajiya? Ai mun yi waya da ita jiya tace matake fada min kana Kano zaka shigo ka duba abubuwan dake tafiya." Abubakar ya ce, "Kwarai kuwa, bari in duba takardun. Fito min da su." Ya jima sannan ya kammala ya fito, Manaja yana biye da shi ya tsaya kusa da ni, "Ki yi hakuri kin ji ko?" Sannan ya fita.Ni kam ban ko kallesu ba. Tunanina 1 ina ya kai min yarona? Lokacin tashina nayi na nufi Makarantar su Shadad na dauke shi muka nufi gida. Tun akan hanya ya isheni da labarin Uncle, Anty Uncle ya sai min ice-cream ya kai min da muka yi break da su sweat, kuma ya tambayi Auntynmu wai ina karatu? Ta ce mishi inayi sosai, kuma ana lura dani wurin yin home work, yana ta jin dadi. Na yi tsaki tare da cewa, "Yi min shiru." Da dare ina Sallar Isha'i naji bugun gida, sai da na idar sannan na nufi zauren nace wanene? Ba'ayi magana ba har zan juya aka sake bugawa nace wanene wai? Yace Abubakar ne. Na gane muryarshi amma sai nace, "Wa kake nema?" Ya ce, "Shadad." Na yi shiru ina nazari, hausawa sunce mai Da wawa, inna bar wannan mutumin zaya fake da dana ya cutar da ni, gara in masa rashin mutunci ko ya fita daga harkata. Na bude kofar sannan na dogare bakin kofar, "Kai Malam! Ka fita idona, ina ganin kimarka bana son ta kaimu ga rabuwa fata-fata ni da kai, ina nufin in zabga maks rashin mutunci, ka ja tsumman rayuwarka ka yi gaba, ka fita harkar yarona, anzo za'a fake da yaro a cuceni." Na ja tsaki tare da maida kofar garam na barshi tsaye da leda shake da kaya. Daga ranar ban kuma ganinshi ba, hakan ya min dadi don haka na godewa Allah. Sai dai damuna da Shadad keyi na kiran Uncle har da kuka. Kwana 8 bayan haka ina ta kici-kicin girkin rana, yau lahadi sai da yamma zan fita aiki. Tuwon shinkafa miyar alayyahu nake son mana na gama kwashe tuwon cikin leda na zuba a kula na samu Shadad yana home-work na ce, "Yauwa ka zauna zanje kasuwa in dawo." Daman nakan barshi. Ya ce, "To Anty." Ya tashi ya dauko kujerar da yake takawa yasa sakata ta ciki. Na nufi kasuwar don ba nisa sosai. Ban fi minti 30 ba na dawo, sai dai me? Kofar gidan a bude, haka na nufin Shadad ya cire sakata, a hanzarce na shiga. Takardun shi suna gurin, takalminshi suna gurin. Kaf babu inda ban dyba ba cikin gidan amma ban ganshi ba, da hanzari na nufi makota duk da na san baya zuwa,,,,, Me ke shirin faruwa da nine? End of 1 Mukhtar Ismail Muhammad WhatsApp: 08161892123 www.arewarulers.com.ng