Sanadin Boko 4-01 Posted by ANaM Dorayi on 06:21 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Kalmar ta dake ni tamkar saukar aradu jikina yayi sanyi matuka.Tsam na mike daga gabn madubi na koma gado na zauna cikin matsanancin kunan rai.Sai naji tamkar mazaunan nawa ba zasu iya rike ni ba, don haka sai na kashingida tare da lumshe ido. Duk iya kokarin da nayi don na tsaida hawayen idona abn d yaci tura,sai da suka sulalo ta gefen idona, idon haguna kuma hawayen ya biyo ta karan hancina. Yayi dan murmushi ba shi da burin da ya wuce yaga 6acin ran Hafsat,duk da son da yake mata.In ya tuna yanda ta mike tana fada mishi cewa ita karuwa ce sai ya ji tamkar ya binne kanshi don takaici. Ya dubi ni Ki tashi mana kin wani kwanta. Na sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya na ce. Ban san cewa gasar kyau zamu je ba da ban 6ata lokacina gurin shirin tafiyar ba., Kaje ka bata Award din da ka tanada na mika wuya. Ya dan yi shiru. Kila yana nazarin maganar da na fadane can sai ya fita da cewa in kin gama ina jiranki a mota in har ina da izinin bada umurni. Tamkar kada na tashi,amma bani da damar yin haka,dole na koma gaban mudubi. Jallabiyata na saka baka mai ratsin ja, tana da tsukakken hannu shima ja, na nade kaina da dan mayafin, shima yana da ratsin ja. Takalimi da 'yar post din da na saka duk jajaye ne. Na feshe jikina da turare, da na kalli madubi sai nayi dan murmushi don nayi kyau. Zuciyarta ce dai ba dadi sakamakon maganganun da ya ya6a min. Na isa gefen direba in da yake zaune cikin sanyin murya na ce, bari nayi ma su Gwagwal sallama. Ya dago ya dube ni, muka kalli juna cikin ido. Da sauri na rausayar da kaina gefe tare da harde hannuwana a kirji, ya ce to kije mana kin tsaya min kerere. Na dubi shi, "Ai dama umurninka nake jira. Duk sai da na bi kowa gurinta na ce sai mun dawo,duk sun ji dadin cewa gurin Fadima zani. Abin da na lura shi ne, suna son a girmama 'yar uwarsu.Na dawo na shiga gaba kamar yanda ya bude.Tsararran gida ne mai matukar kyau, ga furanni masu bn sha' awa, ina biye da shi hr kyakkyawon falon. Wani dankareren zanen hotonsu ne yake fuskantarka an jingine shi da bango a kasa. Kallo daya na yi wa hoton na kauda kai, tamkar jinsin Larabawa ko Indiya. Ya dube ni ya ce," zauna, bari in kirata."Ya tafi yana fadin "Sweety.," Tamkar in toshe dodon kunne na don kishi. Na nutse cikin kujerar ledar mai kalar siminti. Na dinga bin ko'ina da kallo. Wasu abubuwan ma bn san su ba, ban ta6a ganinsu ba, daga karshe na maida kaina ga dankareren TV bangon da wasu Indiyawa suke ta rawa. Ba rawarsu ce ta birge ni ba, da har na tsura musu ido,tsabar takaici ne ke cina. Amma na lallashi zuciyata da cewa tayi hakur, na sani wata rana dai labari. Hannuwansu sarke da juna suka fito, kama suke sosai da shi,wani abu yazo ya tokare kirjina tamkar in rufe su da duka. Wata zuciyar ta ce, Tashi ki shaketa. Da sauri na ce, "A'uzubillahi minasshaidaninrrajim" sau 3 sannan na ce, Allah ka yaye min wannan duhun da ke zuciyata, ka bani ikon yin dauriya,kasa nafi karfin zuciyata. Suna isowa na mike tsaye,take naji zuciyata wasai, na saki wata fara'a wadda bn san ma ina da ita ba,tare da mika mata hannu. Na ce, Amincin Allah su tabbata a gare ki da rahamominsa da albarkatunsa. Itama ta miko nata tare da cewa, Amin kema amincin Allah ya tabbata a gare ki. Muka sarke hannu.Sannan muka saki na zauna itama ta zauna, ta ce, kullum ina son ki zo mu gaisa. Na ce"To ai yau gani nazo." Ta mike ta nufi gurin da nafi zaton kicin ne, shi kuma ya dauki remote yana canje-canjen tasha. Ya kuma ajiye ya nufi dakinshi, ta iso da kofin tare da kwalin jus a hannu fara'arta dai ba sosai ba. Ta dora kan stool ta dauko shi ta kawo gabana,sannan ta zauna. Na dauki kofin na jingina da kujerar ina kur6a ina kallon TV.Ta mike ta nufin ciki,dakin da ya shiga nan ta nufa. Dakin shi kenan,suka bar ni nan zaune. Tuni na dire kofin jus din don sai naji ya daina zakin sai daci, don tsabar takaici. Kusan minti 10 sannan ta fito shima haka. Ta shiga dakinta shi kuma ya nufo gurina, na kalli agogon bangon falon wanda hoton sune a jiki. Na ce, Tunda mun gaisa zan tafi gida."Ya dube ni "Nan ma gida ne. "Yar aikinta ta soma jera abnci kan dinning. Ta fito ta iso gurinmu "Honey kuzo muci abnci." Ya dube ni " tashi muci abnci . Na ce Tuni naci abnci. Ta ce, Ai kam ba ki isa ba, dole sai kin ci. Ni da ita muka jeru, shi kuma ya zauna saitinta, ta ce In zuba mana? na ce Ban san cikinku ba, yaja plate ya zuna musu. Ya ce ke kuma zuba naki, Ya kalle ta ya daga mata gira tare da kashe mata ido daya. Ta kai masa dan duka cikin wasa, ya cafe ke hannun ta ya sumbaci tsakiyar hannun. Tayi wata 'yar kara na dauke kaina ga barin kallonsu wayata ta soma ringing a cikin pos dina. Na mike na nufi kujear da na taso don nan ma na bar pos din. Ya dube ni Ina za ki? Na ce Amsa waya zan yi. Na dauka, yaya Umar ne. Nayi kasa da murya muna gaisawa ya ce Dama Inna ce za kuyi sallama, suna gidana yanzun zan je in sha mai in maida su." Na ce To yaya Umar. Ya ba Inna muka gaisa. Na ce Ashe tafiya zaku yi?" ta ce," Eh, mun shirya ma yanzun zamu tafi. Dama ina so ne in sake yi miki nasiha Hafsatu!!kiyi zamanki a dakinki, kiyi ta hkr don Allah na roke ki duk rintsi ko yaji bn amince kiyi ba. Ki rufa ma kanki asiri, kin dai ga gatan da Ubangiji ya miki, ya baki miji dan mutunci, ki rufa min asirin nan da Allah. Na fashe da kuka, na ma manta ko a ina nake, take lkcn baya ya fado min lkcn d Innarmu ke rokona cewa in lura da kaina in tsare mutuncina,amma bn yi hakan ba. koda dai ba son raina ba ne, na ce Inna in sha Allahu mutuwa ce kadai zata raba ni da gidan Abubakar. Na miki alkawarin duk rintsi ba zan ta6a yin yaji ba. A hankali nake maganar cikin Kuka. Abubakar ya tsura mata ido daga in da yake yana fuskantata ne. can ya taso ya nufo ni daidai lkcn da muka yi sallama nayi musu fatan sauka lafiya. Na saka fuskata cikin cinyata ina yin kukan takaici, da me zan ji? Da wulakancin Abubakar ko da kishinsa? Ga furucin da mahaifiyata ta min. Muryarshi naji daf da ni. Me ya faru?" ya tambaye ni . Da sauri na dago kaina tare da share hawayen naki kallon in da yake,amma sai na ce dashi. Ba komai. Ya dauki wayata ya shiga duba lamabr da na gamawa wayar yanzun nan. Ya kira hr lkcn wayar na hannu Innarmu. Ta daga ya ce Salamu alaikum, Umar. Inna ta ce, Ba shi ba ne yaje shan mai, mahaifiyarsa ce, Abubakar ya kara rage murya tare da zama. Inna ina yini? Abubakar ne mijin Hafsat. Ta ce Lafiya lau, kuna lfy ko? Ya ce lafiya lau, dama naga Hafsan ce naga ta gama waya kuma tana kuka shi ne na biyo layin in ji ko lafiya??Inna ta ce, Lafiya lau ban kwana muka yi da ita na kuma yi mata nasiha. Ta dan saurara kadan, sannan ta ci, gaba da magana, kai ma don Allah ina son kayi hakuri da ita. ka kuma yi adalci tsakanin matanka,Allah ya tayaka riko. Ya ce Na gode Inna Kuma in sha Allahu zan kula. Ya dube ni bayan ya kashe wayar. Da yake ba kyason gaskiya shi yasa ki ka hau kuka don kawai an miki nasiha. To kiyi yanda ki ke so tunda nasihar ce ba ki so, ai ba yau ce rana ta farko da tace kiyi kaza ki bar kaza ba ki ka ki. , Don haka kiyi son ranki kamar yanda ki ka saba. Ya aje wayar a kan ciyata ya nufi gurin matarshi. Wadda dama duk hankalinta yana gurinmu. Sai dai bana zaton cewa taji abn da muke tattaunawa, sun gama cin abncin su suna ta hirarsu cikin harshensu na Fulatanci suna dariya. Hakan yasa na tsargu cewa zancewa suke yi don haka na maida kaina baya na dora kan majinginar kujera. Na lumshe ido ina son tuno kowace Amarya ce tayi rahin dace irina a cikin dimbin amaran da suka yi aure a ranar dana yi bana zaton za a samu Allah ka bani hakurin da juriya daure wannan abn. Ina gidan hr lkcn da aka kira Sallar La'asar ya wuce ni ya nufi Masallaci, itama ta nufi dakinta ba tare da ta kalle ni ba,tamkar in fita in tafiyata, duk da cewa bn san hanya ba, amma na cije.Me aikinta ta fito na ce ina ne gurin Alwalarsu? Ta ce Duk a bayikan daki suke yi. Na ce, ba ku da ko famfo a waje? Ta ce, ita ma bakuwa ce, jiya ta zo amma taga can fulawoyin can ana basu ruwa, kila akwai famfo a gurin. Na ko samu famfo nayi alwala nazo nan in da na tashi nayi sallata. Ina zaune ya dawo. Ya kalleni, kamar zai yi magana amma sai ya fasa, ya nufi ciki koda suka dawo falo suka zauna. Sam nayi nisa cikin tunani ban san me suke fada ba, suyi da yaransu suyi da turanci, wani lkcn har da hausarsu kamar ta 'yan koyo. Da Magriba ma da ya fita dakin ta nufa da ya dawo ina azkar ya zauna sannan ya kirata da wayarshi. Ta fito ta sake wanka da sabon ado cikin koren yadi mai ratsin ja, doguwar riga ce, tayi kyau sosai, ga kamshi turaren amarci na tashi. A raina na ce, Lallai wannan sai na dage a gurin kwalliya. Ya zuba mata ido, hakan ne yasa na saki baki, kai Hafsa bata yi sallah ba? ta dube ni.ta ce, Gidan ba bakonta ba ne, ita ce ta ki ta shigo, Ya ce, A"a fadima Fadima gidan nan bakonta ne a yanzun,don bata san in da zata shiga ba sai in ki mata jagora. Nan da nan sai tahade rai ta soma magana cikin Fillanci, shi kuma ya ci gaba da magana da Hausa, yana cewa. Ba wani son kai ko bambancin da na nuna miki, in dai kina son gaskiya. Na ce, don Allah ku bar magana laifina ne, ni ceban bukaci shiga cikin ba. Ya ce, mata,To shi kenan zan nuna mata komai ni. Har zuwa lkcn da muka baro gidan ban sake cewa komai ba. Mun biya gidan su Hashim, matarshi mai kirki, daga nan muka nufi gidan iyayenshi. Ummi tazo da gudu ta rungume ni. Rukayya kam tana ta danna waya ko kallo ban ishe ta ba. Na zube a kasa na gaida Daada, sannan na zauna a gurin .Tayi tayi in hau kujera na ce mata kasan yayi. Ta ce masa daga ina? ya ce Gidan fadi ya kai ta. Ta ce, ya hada mu ya yi mana nasiha? Ya ce, eh, ni dai na sunkayar da kai ina tuna nasihar da ya mana,wai mu zauna lafiya, muyi kishi irin na gidan Annabinmu (S.W.A.) Ya ce wai in bi Fadi don ita ce ya za6a uwargidansa, sannan in girmamata baya son raini, ita kuma wai ta kama girmanta, sannan ta dinga hakuri. Ummi ta katse min tunanina, Anty tashi muje ki gaida Abbanmu yana falon shi. Na mike na bita,shima nayi cikin kunya da girmamawa na gaida shi, yayi mun nasiha da in yi hakuri, in yi biyayya sannan in saba da zuri'arsu. Kada kuma na yi wani abu na 6atanci wanda zai sa zuri'arsu suyi da sun sanin shigowata cikinsu. Nayi godiya tare da yi mishi alkawarin kiyayewa. Da zamu tafi har bakin mota suka raka mu. Daada da Ummi, amma Rukayya sai da ya yi mata magana sannan ta gaida shi. Kafin mu iso gida sai da muka tsaya a wani super store muka yi parking ya shiga. jim kadan ya fito da ledoji kuda biyu ya shiga muka wuce.shine ya ruko ledar har dakina.Na fada bandaki donyin alwalar sallar ishai ina fitowa yacemin shifa xai wuce nace toh,har ya kai da kofar daki nace masa ledar ka manta ya waiwayo sannan yace taki ce.na dauka na duba kaxa ce da kayan lashe lashe na zaki nace ka kara muku ni yayi min yawa tunda kaga ku uku ne duk da yar aikin gidan nikuma ni daya ce.ya juya tare da cewa na fiki sanin mu uku ne ai! ya atfi abinsa na tada salla ta.A randa na cika kwana biyar, misalin tara na dare yace in shiri gobe da taran safe xamu wuce kano ,ina murna harda da dan tsalle na.Allah na gode maka da har nacire rai da karatuna,nan take na soma hada shirgi na.da safe dana gama shiri naje na gaida mutan gida na kuma fada musu xan koma mkrtn yau.duk suka min addu'ar fatar alkairi don doki kasa break din kirki nayi.ya iso sanye da na kalar sararin samaniya.yayi kyau,ni na shirya ya kalli kayana.Uhumm dama duk kin kosa ki koma koh?saboda mu cin namar jikin muke yi koh?na sunkuyar dakai bance komai ba ya dauki babbar jakar niku na dauki karamar da ta ratayawa.duk yan gidna sun min ftan alkairi da sauka lfy usaman kanishi ne yaja motar.shi da hashim suka kaimu filin jirgin sama gabana sai faduwa yake.yau ce rana ta farko da xan fara hawa jirgin sama jikina sai bari yake tayi.ina xaton abubakar ya dagoni sai ya tallafoni xuwa gefen kafadarshi ,na lumshe idanu har muka shiga muka xauna sannnan ya sake ni.jikinsa mai laushi da kamshi wani sonsa ne ya ratsa ni tamkar in kwanta a jikinsa...ckn lkc kankani muka sauka a kanon dabo inda rahma da sagir ke jiran mu.ckn murna na rungeme rahma sukuma suka kama hannu suka gaisha.gidan sagir muka je sai d akarfe uku sannan muka fita. na kosa muje gidan dana ke don inje gidan maman rahma inga shadad. Kai tsaye gidan maman muka wuce muna shiga naga shadad na wasn kwallo.da gudu ya taho sai na bude hannu amma sai yaron nan ya wuce wurin Abubakar ya daga shi sama nikam nayi ciki.mun gaisa da maama inda na amshi dan mukulli sannan nayo gaba.su kuma suka biyo cikin motar sagir daya amsa.mun hadu da wasu makota daidai ku, sun mun murnar aure nayi godia.na bude gidan cikin xakuwar shigarsa.yana nan yadda na barsa.na bude daki xan shiga shikuma yace toh ni xan tafi.nace toh sai ka dawo shi da shadad suka tafi.na gama na sa turaren wuta,shawarar rahma ta fadomin lkcn da muke kulle ckn daki.kafin ya tafi kiyi kokarin janyo shi gare ki ta hanyar ado da sauransu yasan ke mace ce "nace hmm shi da matarshi tamkar india,ga iya ado tamkar dawisu ,har wani burge shi xanyi.tace tabbas xaki birge shi yasn da mai kmr indaiyar yanace sai daya same ki,nace toh hum xan gwada. bayan maghrib suka dawo yana dauke da ledoji suka ajiye suak ce sun tafi yin ishai nima sallar nayi na sake fenta fuskata na sake kaya.riga ce doguwa rahma ta yadi ta bani mai rawa ce sannan ta ilahir jikin duk motsin dana yi sai ya bayyyana.yau ce rana ta farko daya shigo ckn dakin gefen katifa ya xauna shadad ya xauna kusa dashi.ya kalli abubakar yace anty bata ci abinci bah"yace xata ci ya kara cewa uncle in xaku kara tafia ku tafi dani.yace toh xamu atfi da kai.haka suka yi ta hirar su ina ta kallon shi yana satar kallona.na xauna tare da janyo ledar na duba madara mai snayi ce.na dauka na sha.na kalleshi muka hada ido sai ya kauda kai ya ciro waya yana kirar layin matarshi.ya kishingida yana magana cikin fillanci haushi ya kama ni.sai kawai na fita tsakar gida.ya jima sannan ya fito lokacin shadad yayi bacci, yace na kam na tafi masaukina.da suari na dube shi nace masauki?bansan ma ya fito bah yace eh masuakina nace hum!!sai da safe.yace toh takaici ya isheni me yake nufi dani?me yake son mai dani.ina kwance dare ya tsala amma na kasa bacci juyi nake yi kurum a kan katif.ni mutum ce kuma mai lfy ina matukar son ganina kusa da maigidana.naja tsakin takiaci me yasa da ban damu da wani namiji ?wata xuciyar tace lokacin ba kida aure, yanxu kuma kina da miji wanda kuma kina so.daga karshe dai na mike nayo alwala nayi sallah wanda ita kadai ce mai mun magani damuwa. ***** ***** ******** Munnir yashiga gdansu cike da tunanin ta ina zai fara yiwa iyayensa bayani, yace mum, tadubeshi cike da tausayi, don tunda yaci karo da ciwon nan suke tausaya masa, tace lfy munnir meya faru? Yace mom eh....daman...wataran....sai yai shiru, tace kayi mgn mana menene yafaru? Yarike kai, tace ciwo yakeyi? Tazo gabanshi a rude, yace mum wani yaro nagani kuma muna matukar kama, kuma ada maman yaron budurwatace, IYE!!! Mekace? Tazauna gabanshi a kasa, tace yimin bayani yadda zan fahimta, tace inba wani abu yashiga tsakaninkuba toya daga ganin yaro dan yayi kama dakai sai kace abaka? Yace mum shekarun baya zaki tuna wata yarinya datazo gdan nan tace tanada ciki? Tayi shiru tanason tanawa shikuma yayita mata kwatance har saida tagane, yace to itace mum, kuma nasan cikinane tunda nina mata ta karfin tsiya, (oh kuji rashin ta ido) mum tace inane gdansu? yace nan abj road ne, tace to bari dadynku yadawo saina masa bayani. Da dady yazo tafada masa, nan da nan sai yau murna tare da shan alwashin in zai karar da duk abinda ya mallaka saiya amsa jikanshi da namiji, munnir cikin murna yace, dady itace wadda yan yola sukazo daurin auranta yau din nan, cikin mamaki dady yace, kana nufin daurin auren damukaje? Munnir yace eh dady, yayi shiru yana tunani, mom tace, ina ruwanmu don dan abokinka ya aureta? Allah yakaimu gobe, nida kaina zamuje gdan, hakan kuwa ta faru, misalin karfe 10 na safe munnir da dadynshi sukayi sallama kofar gdan baban hafsa. Daman baba yana zaune inda yayi sallar walaha bai tashiba........ Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-02 Posted by ANaM Dorayi on 06:37 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ya daddogara yafito, bayan sun gaisa, sai yace dama yazone da batun yaro, wanda 'yarshi ta haifa, baba yace banganeba? Munnir yace, baba baka ganeniba? Ninefa munnir saurayin hafsa, kuma dan data haifa nawane, shine na ganshi gurin bikin nan. Dady Yace, duk abinda aka kashe zan biya, munzone mu sulhunta abamu yaron,ran baba ya baci,ckn xuciyarsa kuma yaqi yadda da yadda suke so.Tun farko matsalar me yana kawo cuta da cin xali don suna takama da kudi shine xasu daurewa dansu gindi yayi wa yarinya mugunta?Baba yace gaskiya ni bansan da wannan xancen ba "yata kuma ba a nan take ba a kano take sannan dan da kake magana yana da ubanshi.Daddy ya kalli munnir toh kaji?Munnir fa daddy yaron yayi kama dani sosai.baba yace itace hujjark kawai?nan gaba wannan ba hujja bace don nasha ganin masu kama dani da sai in bisu ince yayana ne? Daddy yace to wai yanxu ina yaron yake?baba yace sun tafi gidansu sai anjima.ya nufi gida daddy ya hau munnir da fada wai ya musu karya.suka shiga mota suka tafi ,shidai munnir ya tabbata danshi ne kuma xai ta bin diddigi sai ya amshi dansa.ya lumshe ido ya tuna kyakyawan fuskar yaron mai kama dashi mai cike da wayo da dabara gami da lfy.Mom tayi jigum dajin cewa xancen ba gaske bane.tace ina ce son yara ne yasaka yin haka toh ai shi kenan.Munnir yace nidai nasan dana ne kuma xan ta bin diddigi har sai na samo shi.Daddy yace in kaje ka janyo rigima kaga dan wani kace naka ne kai xaka kwana ci.mom tace kai dai ka barshi ya san nashine ta kalli munnir kabi diddigi xamu dauko lauyoyi.Munnir yace yauwa mom danAllah ki sayamin donko nasan cewa yaron nan nawa ne.tace kada ka damu kaidai kabi komai a sannu.ya mike ya fita daddy na kara jaddda musu cewa shi fa ba ruwansa. Kasan cewar ban samu bacci ba sai ya xamana na makara, nayi sallah tare da shirya shadad. kaxar jiya na bashi da milk din yaci.sai ga yayan su Rahma yayi sallama na saka hijabi na fita muka gaisa,yace shadad ya fito xai kai su makaranta shi da yayan sa dama mama tace min shi ke kaisu,duk da cewa ba makarantar su dayaba.muka gaisa suka tafi na shigo na gama yan gyare gyare na nayi wanka.ankon bikin rahma nasa ya shigo da sallamarshi hannuwansa dauke da ledoji farrera guda biyu.na fito da sauri na amshi tare da cewa sannu xuwa yace yauwa sai ya sake fita dauke da buhun shinkafa ya shigo.haka ya dinga shigo da kaya ina ta masa sannu da xuwa har ya gama.na shimfida mishi tabarma a ciki ya xauna na gaishe shi ya amsa.ya amsa ba yabo ba fallasa nace mai xaka ci in maka ya dubeni ido cikin ido yace am ok.ya kalli agogo yace jirgin karfe goma xan bi xuwa yola,na kalli agogon bango karfe 8.na dubeshi wani sonshi ke fisgata kamar in sa kaina a jikinsa.kamshinsa mai sanyin dadi ya karade ko ina acikin dakin, muryarshi ta kaseni.""ki duba abubuwan dana kawo in akwai abinda kike bukata babu sai ki gayamin.Bansan me yasa muryata ta dishe ba nace ko ban duba nasan abundaka siyo sunyi.Allah ya kara budi nagode.yasa hannu cikin aljihu ya kirga kudi naira dubu 10 ya bani.ki riqe wannan bani no mai adaidaitar da yake kaiku makaranta na dauko wayata na dauki lambar tare da mika mishi harda wayar ya amsa tare da dubawa.ya kirashi ya amsa .ce masa yayi yana jiransa an nan gidana yace toh.na sake cewa kodai indomie xan dafa ma yace a'aah.ya fito da wayarshi daga aljihusa tana ruri tare da karawa a kunne yace sweet honey. gabana das ya fadi tabbas fadi ce na mike na fita raina daure naje in kwashe kayan daya xubamin.dana gama na xauna waje kan kujera ina son in tuno abin da abubakar yayi min me yake nufi dani? tamkar in bar gidan saboda bakin ciki yanda suke hira da daria.duk da cewa yarensu suke yi sai turanci jifa jifa sunkusa minti ashirin sannan suka yi sallama.wayata dana baro a dakin sai ta shiga ruri ya dauka ashe dan mai adaidaita sahun ne ya iso don haka ya mike yace yana xuwa.ta gabana ya fice,kusan mintin 5 sannan yace ni xan wuce.na ce saboda anagutsirrkah dole kace xaka tafi ,ko kuma ince ka kosa xaka tafi daga wurin maqiyarka.yayi dan murmushi hakan ne"ya cigaba da cewa ni xan tafi kamar yanda nace kuma ba xan cemiki ga randa xan dawo bah sai san da na samu sukuni.haka nan kuma bayan mkrnt ban laminta aje ko ina ba sai an nemi ixini in sani.maganarshita fako ta kona mun rai wai hakan ne kenan ni makiyarsa ce,na dago na dubeshi "wai mai nayi maka ne kake son kuntata wa rayuwata?tun daga ranar dana sake ganin kah na rasa sukunina,meye nufinka dani? :kuka ya subuce min yace "au da ke baki san kinyi wani abu ba ?to duk ba wannan ba ni me na miki.kince mkrnt na dawo dake na baki abinci na baki kudin cefane, na daukin nauyin dake a kanki na dawo dake.me kike so bayan haka?ya sake matsowa kusa dani tare da sausauta murya "fadamin in kina da wata mastalar?nayi shiru ina son tuna me xance?sai ince baka sakar min fuska kuma baka saurarena ?kai gaskiya in nayi haka ba da kai ne...ya katseni dake nake nace akwai sauran matsala?na dube shi ka fini sani.ya sake matsowa ya ce kuntatawar da nake miki ?nace da ban hadu da kai ba hankalina a kwance.yace saboda ba ki sona koh?haushi ya sake cika ni ,son shi ya cika ni ya hanani sakat sannan ga abubuwan da suke biyo baya,amma xai ce wani bana son shi.bansan sanda nace eh!ai tuni nace bana sonka mai yasa ka tursasamin har sai da ka aureni.ya xura min ido.nayi laifi dana raba ki da rayuwar kangi da gantalin bin maxan d akike yi?na mike tsaye ni kada kamin sharri baka ganin a dandi ba.yayi yar daria yace yaro yaro ne koh ba da kanki kika fadamin cewa ke karuwace a nan gidan ba a wurin nan bah.kila ma dan gidan baya magana ne daya shaideni,nalumshe ido ckn takaici na ce magan xarar bunu na nufi daki shikuma in jin fitarshi.nayi kuka mai isata sannan nace laifina nake nina kashe kaina.shi kuma a cikin jirgi yayi jugum gani yake ya xalunce ta, bai dace ya ringa jefa mata magana ba in yai la'akari da ya fa aureta. :Saidai har yanxu yana takaicin kasancewarta karuwa ce ada bai san adadin maxan da ta kwana dasu ba.Don haka kyankyaminta yake yi in ya ganta sai ya tuna lkcn da take gayamasa ita karuwa ce.sai yaji haushin ta.sai dai duk wannan bai hana sonta yayi anbaliya a cikin xuciyarsa ba.ni kam haka nayini da takaici,washegari haka na bufi makrnt tare da yi wa Sa'adatu suleiman godia.na samu duk tayi min test dina.nan suka yi tamin tsokana wai daga xuwa daurin aure sai na bi miji yola nabarsu da katin walima.daria kawai nayi tare da basu hkr.sam bana xuwa ko ina sai mkrnt.daidai da gidan su rahma bana shiga sai dai in aika shadad yace in gaishe da maama.in nayi abincin marmari sai in aika mata koh in ina dawowa daga makarnt sai in siya mata goro in aikamata dashi :Rahma ma ta gaji da tambayata yaushe xanxo sai gata rannar wata lahadi.itace ma na ba wa dinkunana na ce taje dasu ayi min, tace inxo muyi mgn da telan, nace rahma Abubakar ya hanani xuwa ko ina inba mkrnt ba.ta ce toh"xamuyi magana ta waya in yaso sai in baki no telan nace toh!!nagode.tunda ya tafi sai daya kwana biyu sannan ya kirani ,gaisawa kawai muka yi yace in bashi shadad su gaisa na bashi suka yi ta surutun su hardai na tashi naje nayi sallar isha'i sannan suka yi sallama.shadad ya dube ni Anty kinsan me?nace a'aa yace Uncle yace wai da ina da ina kike xuwa bayan mkrnt nace babu koh gidan su maman rahma ma kin dena xuwa.sai yace ki ringa xuwa kina gaisheta.wai kuma ince miki sai da safe ,kuma in muna son wani abu ki fada mashi ta txt.nace shadad tashi kasa kayan bacci,ka kwanta "cikin xuciyata kuwa nace koda xaya kirani ba xan cemi shi bamu da komai bah koda ba mu dashi.:Kullum xai kirani daidai wannan lkc wato bayan sallar isha kenan,tsakaninmu gaisuwa.kuma xai ce in bashi shadad suyi mgn a waya ,wani lkcn ma kwanciyata nake yi in sharesu inyi bacci na.kwatsam ranar wata juma'a a lkcn muna tsakiyar jarabawa na dawo a gajiye ga tarin gajiya don kullum karatun dare nakeyi.na watsa ruwan sanyi,bacci nake ji baxan iya girki ba don haka gari na jikawa shadad da madara na rufe gida na kwanta.banyi nisa cikin bacci ba anji shadad yana jijjigani .Anty a buga gida inje in bude?Anty? da kyar na amsa.shadad danAllah ka barni inyi bacci.Anty ana fa buga gida inje in buda.nace jeka shadad.naci gaba da baccina.ya taka kujera yaje ya bude nan take ya dane Uncle dinshi suka shigo tare.nayi dai-dai kan katifa na dura kaina kan filo tsakiyar kafa funa na saka filo a tsakiya.sanya nake da farar singlet sai wani siket dina mai fadi ,tsawon shi daidai gwiwata,ya tsura min ido lallai hafsat nada durin jiki mai kyau ,kuma daga ganin fatarta xaiyi laushi.shadad ya soma girgixa kafata Anty tashi ga Uncle anty,a firgice natshi don har ckn kaina naji kiran.idanuna jajir nake kallon shadad "menene?ba nace ka daina tashi na ba ya nunamin Abubakar dake tsaye ya kafe ni da ido.da sauri naja hijabina na rufe jikina sannan nace sannu daxuwa "ya lumshe ido tare da amsawa a ckn wata sarkarkiyyar murya.naja xani na daura sannan na shimfida mashi tabarma na dauki hulata na saka na nufi kitchen.dama naxo da kankarar pure water saboda xafin kano kullum nakan xo da kankara in saka cikin kula.da dauko nikarkiyar shinkafa ta wanda na samata kayn kamshi,na tace na saka mata flavour mai kamshin kwakwa naje fa kankara ckn jug.na dora kan tire da kofi naxo na dire a gabanshi.:na tsiyaya masa ckn cup na aje masa,sannan nace "me xa'a dafa maka?ya dube ni ki barshi.Ban san dalilli ba, sai kurrum naga hawaye sun cika idona, idanuna suna kallon cikin nashi nace in maka fruit?ya cigaba da kallon idona, nima ban dauke nawa idon ba.hawayen idona suna sauka a hnkl.Shadad ya katse mu Anty kiyi mishi fruit Uncle da dadi nima xan sha.yayi yar ajiyar xuciya, sannan ya dauke idonshi daga kaina ya maida gun shadad, yace xaka sha da gaske? Shadad ckn xumudi yace xan sha nayi murmushi kadan sannan ya dauki kofin jus din kunun shinkafar ya kurba.sai naga ya hade rai, ya hadiye jus din da kyar.sannan yace wannan fa?haka yake ba sugar.kinsan bakina yasa ba da xaki.nan da nan sai na tuna ashe sabar sauri ne yasa ni ban saka sugar,lemon tsami ba,don haka sai na saka tare da suga da na zuba masa sai naga ya hau sha. Na kira Shadad na aike shi siyan fanta gidan Maman Yusra. Na yanka abarba, gwanda da kankana, bayan na wanke su na 6are ayaba sai na yanka dabn saboda kada tayi baki, in taji sanyi. Na matsa lemun zaki,shadad ya kawo min fanta mai sanyi na zuba mishi a plate mai zurfi tare da cokali. Sannan na kawo ayabar na zuba,shadad ma na zuba mishi. Nasha mmk, kafin wani lkc ya gama da shi, Sai naji sanyi a zuciyata, farin ciki ya cika ta, dama haka mace ke ji a duk lkcn da mijinta yaci duk wani abu da ta sarrafa? Lallai kuwa zan dinga kirkirar abubuwa don na birge shi dasu. Ya katse min tunani da cewa, Zan iya shiga bayanki? Ina son yin sallah,don bn sami Jumma'a ba. Na dube shi a raunane, Me zai hana? sai dai ko in kana kyama, don namu na talakawa ne. Ya mike ba tare da ya ce kala ba, ya nufi bayina,duk da cewa bayin na gargajiya ne, amma wanke yake tsaf, ba zarni ko karni ko ko wari. Khamshin sabulun wabka ne kawai sai ko na omon wankin bayi. Ya fito yayi alwala. Tuni na shimfida masa darduma, don haka ya tada sallah, ni kuma na fada wanka ko da na zo ya idar. Shadad ya kwaso masa takardun mkrntrsa yana dubuwa, na dire tsakiyar katifa ban cire hijabin ba na murtsuka mai bayan na basu baya. Da zan sa kaya sai na diba na fita waje ya bini da ido har na fita,sai da na saka kayan na zauna kan kujera ina daura dankwali. Na kalli madubi,masha Allah! Nayi kyau, daya ne daga cikin dinkunan da na bawa Rahma na saka, riga ne da siket na leshi mai ruwan dorawa da ratsin baki. Na koma kan katifar ina saka turare, na kalle shi shima ni yake kallo. A duk lkcn da idanunmu suka sarke basa son daukewa daga barin kallon juna. Yanzun haka mun kasa ko kiftawa,shadad ya kalle ni ya kalle shi, sam bamu sani ba, sai dariyarshi muka ji sannan ya ce...Uncel ashe kuma kun iya kallon kuda?" shine yayi saurin janye idanunshi, ya dubi Shadad. Me ka ce? Shadad ya ce, Irin kallon kudan da yaran ajinmu suke yi, wai kada a kyafta ido.. Ni kam lumshe ido nayi, bn so shadad ya katse mu ba, domin ina karanta abubuwa da dama a cikin yalwatattun idanunshi., Jikana a mace naja filo na sulale na kwanta, Jim kadan na jiwo wayata sbd jin shigowar text. Na kalle shi, sbd ganin lambr shi ce mai dauke da sakon,shima ya dan kalle ni sannan ya maida kanshi ga Shadad. Na bude sakon,cewa ya yi "KIN YI KYAU." Murmushi ya su6uce min,dadi mara misltuwa ya rufe ni. A hankali na dago kai na kalle shi, shima ya dan saci kallona, sannan ya dauke kai tamkar ba shi ba. Na dinga kallon kyakkyawar fuskarshi, Shadad na ta krt, bana zaton ma Uncel din yana tare da shi, don waya yake dannanwa. Wani sakon ya shigo wai "KALLON FA NA NAWA NE? na kuma dubn shi, sannan na rubuta cewa. KALLON SO NE.na tura mishi,ya dago muka hada ido. Nayi saurin sunkuyar dakai. Ya mike tare da cewa, "Shadad zo muje." Na dube shi, Ina za ku?" ya ce, Tadi gurin budurwata." Na tsuke fuska,ya ce "Shadad zaka gurin Antyn nan me baka ice ream?" Da gudu yasa takalmi "Za ni Uncel, zata bani da wannan biskt din mai dadi?" Gabana ya fadi, ko dai gaske ne? nayi shiru raina 6ace . Abubakar yayi murmushi mai sauti, cikin jin dadi ya ce Zata baka. Suka fice. Na rasa me ke min dadi, Rahma ta kira ni tana min tsiya,wai miji ya dawo in dai kokarta in shawo kanshi. Cikin yanayin tausayi na ce, "Uhm! Wane shawo kai? Mu2min da ke nemn wani auran? Rahma ta ce, Daina fada min wannan zancen,tsokanarki kawai yake yi, duka-duka yaushe aka yi abin? Amma kada in katse ki, menene dalilin da yasa kika fadi haka?" Na ce, "Tun kafin yace yana sona ina jin shi yana cewa za shi tadi, su fita shi da Shadad. To yau ma yana ce ma Shadad za shi gurin Aunty yaro ya hau murna, har da cewa za'a bashi irin wannan biskit din mai dadi!" Rahma ta ce, "Kika sani ko wata mai sai da kayan kanti ce da suke sayayya yake ce mata AUNTY?" Ta ci gaba, "Ke ko bama haka ba Abubakar ba zai tarki wani aure yamzun ba, kiyi aiki da hankali mana. Kishi ya rufe miki ido, baki ga ko ke baki soma cin amarcin ba?" Na yi murmushi na ce, "Ni ko da har naji haushi." Ta ce, "Don Allah kiyi amfani da matantakarki ki fizgi mijinki." Na ce, "To Rahma duk na kasa gane mishi ne, amma yau da sauki tun da har yaba kwalliyata ya yi." Rahma ta ce, "Ki yi wadda tafi ta kafin ya dawo, ki ajiye duk wani taurin kai ko shariya da jan aji, ki zuba basirarki ki samu ki kwato shi gare ki." Na ce, to na gode. Dambun shinkafa na mishi wanda na cuda shi da nama, karas da kabeji gami da koren wake. Gida ya dime da kamshi, na hada mishi jus din kokumba da abarba da kwakwa, na nike su a blender na tace, na saka kankara da flavour. Bayan na kammala na je na tsala wanka tare da yin Sallar Magriba, nayi shafa, wata jar atamfa (java) na saka mai fulawa blue, na gyare gidan tsaf na yi shimfida a tsakar gida na jera masa, na kunna masa turaren wuta ko ina ya dauki kamshi.Shi da Shadad kawai suke 'yan zantukansu, ko nace yake taya shi shirme. Kusan goma saura ta ce, "To Madam ni zan tafi na kwanta." Muka yi masa rakiya, na yi Sallar Isha'i tare da Shafa'i da wutiri na kwanta, zan soma addu'a sai naji shigowar sako, wanda na zata shine wato Abubakar. Na bude, cewa yayi, "Ban taba cika ciki irin na yau ba, abincinki yayi dadi, zan zo in miki kyauta kuma ina son ki zabi abin da zan baki." Na yi murmushi na lumshe ido, zuciyata tana wassafo burina, na rubuta cewa, "Duk abin da ka zaba min da zaka barni ma sai in ce yaba min din da kayi ma kyaute ce a gurina." Da ya karanta sai ya ji dadin lafazin, don haka sai ya sake rubuto cewa, "In sai miki turare? Ko in canza miki waya? Ko kin fi son in canza miki wani gida kafo mai tsarin zamani? Don lafazinki yasa naji cewa dole ne ma in miki kyauta." Na yi shiru ina nazari, wato Abubakar yana so na dinga nuna kulawa gare shi, in ko haka ne zan yi ta nuna kulawata a gurinsa, sai na rubuta cewa, "Duk wannan basu yi min ba, tunda kace in zaba aba abu daya nake so, ka yarje min in fada?" Da sauri amsarsa ta shigo ya ce, "Eh, fadi." "Son ka da kulawarka kurum nake so, in zan samu sun fi duk wani abu na kawa ko na dadi da zaka bani." Ya yi shiru yana maimaita zantukan, sai kurun na ji kira, na daga tare da yin sallama kasa yanda ko wani na kusa da ni ba zaya ji ba, ya amsa min sallama shima cikin wani sauti mai nuna cewa muryata ta ratsa shi ya ce, "Hafsah!" Cikin wani irin sauti ya kirani, har yatsana naji nima nace, "Sadiq!" Ya ci gaba, "Ni naki ne, sona ke kadai yake naci, kuma zan kula dake, wannan kawai kike so?" Na saki ajiyar zuciya, "Wannan kawai shine burina, na gode." Ya ce, "Nima na gode. Ki yi bacci.......... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-03 Posted by ANaM Dorayi on 06:39 PM, 28-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ki yi bacci mai dadi tare da yin mafarkina." Na ce, "Kullum cikin yin mafarkina ni ke, ina sonka sosai." Na kashe wayar don jin nauyin furucina, na dauki filo na rungume na lumshe ido ina tuno fuskarshi. Shima a nashe gefen ma filon ya manna a kirji yana jin dadi. Nan take kuma sai wata zuciyar ta ce masa, "Yanzu kai saboda yarinyar da ta tabbatar maka da cewa ita karuwa ce ka ke wannan?" Nan take kuma sai ya saki tsaki tare da yin jifa da filon, zuciyarshi ta ci gaba da wassafo mishi cewa, "Ba wani son da take maka, wanda take so shi daya ne, tunda har ta bashi kanta. Kila ma da zai dawo yanzun da ta nemi ka barta ta koma gurinshi." Take ya nemi farin cikinsa ya rasa. Lokuta da dama wannan tunanin ke sa shi jin haushin Hafsah....... A zato na zai shigo da wuri, don haka na shirya masa abin kari, sai ga sakon shi ya shigo, "Madam ki yi hakuri, kila ki zaci zan shigo, zan duba ma Dada wasu daga cikin (super market) dinta. Idan mun gama da wuri zan zo da wuri, in bamu gama ba ki dubi hanyata da rana. Ina fata kina cikin koshin lafiya?" Lallai Abubakar zai cika alkawarinsa na kula da ni, to nima Insha Allah zan kula da shi. Na bashi amsa da cewa, "Lafiya lau (Hayate) rayuwata, Allah ya sa ka gama abubuwan da zaka yi lafiya, ya kawo min kai cikin kwanciyar hankali.".. Duk da cewa har Abubakar ya bar Kano babu wata mu'amala ta auratayya da ta hada mu, ban damu ba saboda ya nuna kulawarsa gare ni. Ya bani kudi, ya canza min waya zuwa (BB), ya kara min abinci. Haka nan ko da ya tafi ya kan kira ni sau 3 a kullum, nima kullum na ke kiran Mahaifanshi da safe in gaishe su, haka nan Lamido da Matanshi kullum sai na kira su cikin girmamawa na gaishe su har muka kammala Jarabawa. Lokacin yayi tafiya zuwa India akan harkokinsa, na ce mishi, "Tunda muna hutu har da Shadad ina son inje Kaduna da Funtuwa da Malumfashi." Ya ce shi kam bai yarda in je Kaduna ba, amma in je Funtuwa gurin Inna in kwana 2, Malumfashi kwana 2. Sagir zai sani jirgi in wuce Yola. Na ce masa, "To na gode." Don na lura baya son gayya. Washegari Sagir ya zo ya bani kudi dubu talatin, wai inyi tsaraba in ji mijina. Na yi godiya shima na tura masa da sakon godiya, sannan na ce, "Ko zan iya zuwa kasuwa mu yo musu tsaraba?" Ya ce, "Ki je amma ga sharudda na, ki saka katon hijabi, sannan ki kausasa murya yayin cinikayya da maza." Dariya sosai na yi, sannan na tura masa cewa, "Zan kiyaye Insha Allahu." Innarmu ta yi murna sosai da ganina, mun yi hira sosai mijinta da 'Ya'yanshi ma sun nuna jin dadinsu da zuwana tamkar sun sanni. Na bata tsarabar ta, kwanana biyu na wuce Malumfashi, daga can na dawo Kano. Sagir da Rahma suka sani a jirgi sai Yola. Hashim ne na samu yana jirana ni da Shadad, masu aiki ne suka taya ni gyaran sashen. Daga nan na fitar ma da 'yan gida tsarabarsu. Washegari da muka yi waya na ce masa, "Zan je gidan su Dada." Suma na kai musu tsarabar su Sabulai, turarurruka da 'yan kunnaye. Ummi kuma na sai mata wata doguwar riga mai kyau, tayi ta tsalle tana rungumeni, Rukayya kam sai fushi da harare-harare. Ban so jikina ba na amshi Dada da girki, dama ita da Rukayya ne, da kyar ta barni, Rukayya na ganin Daada ta fita itama sai ta bita, ta ce, "Koma mana ku gama." Ta ce, "Toh!" Da ta dawo sai ta samu guri tayi zamanta tana latse-latsen wayarta. Ummi ta shigo, "Aunty yaronki yayi bacci." Na ce to. Ta ga ina yanka albasa ta amsa. Shinkafa ce fara da miya, kuma ba mai yawa bace tunda basu da yawa a gidan, nan da nan muka kammala. Lallai girki hannu ne ba cika kayan miya ba ne, to duk abin da suke sawa suka bani amma sai gashi suna ta santi, illa Rukayya da takici wai ita sai dai ta dafa Indomie. Daada kuma ta ce bata isa ba. Na kai har bayan la'asar sannan na shirya muka koma. Daada da Abba sunata shimin albarka. Ai hutun nan na saki jiki cikin dangin mijina don jan su nake jikina, na kuma saki hannuna, kyauta tana sa dangin miji su soka.Wata rana matar wani wansu ta haihu,ya kaira ni na fada mishi, yace duk abin da ya faru nan ckn danginsa to inje.ummi ce taxo muka je barka,ranar suna ma ita ce taxo kafin na shirya na bata kudi ta siyo min kayan baby na hada da turmin xani na shirya muka je.Mai jego tana ta godia,duk wanda yaxo sai a ce ga kayan barka da Amaryar hamma ta nbata,sai godiay ake min.can muna shirin tafia sai ga Fadima ta shigo cikin isa da jin kai,da muka hada ido sai na fadada fara'ata,duk da cewa gabana ya fadi.Itama nata gaban ya fad, in anyi la'akari da aynda nan da nan ta canxa.ta zauna can kusa da yan'uwansu,huk da haka na bita na gaisheta,da kyar ta amsa ba tare da ta kalle ni ba kuma ciki-ciki.Sai yatsina taka tana harare-harare,ni dai sai mana mike nayi musu sallama na fita na kira Ummi muka tafi.Duk wata kulawa Abubakar yana bani,ko da ya dawo gidana ya sauka,gadona ne kurum baya kwana.Ni kuma ban taba nuna mishi ba,du da cewa hakan yana damuna,hutuna ya kare ya maida ni Kano.Ya siya min gado da sauran abubuwan bukata,ya kuma yimin alkwarin cewa in yaxo xaya dinga koya min mota saboda ya saya min don xuwa mkrtn.duk da cewa karatun nawa karashe ne kowa ya ganni sai yace nayi kyau Wata rana Umar ya kira ni yace jikin Baba ya tashi, yanxu haka suna asibitin Dutse.A rude an kira Abubakar a ways, yace in jira shi yaxo gobe muje, sai nasa masa kuka tare da cewa yayi hkr in je yau.Ina ta rokonshi yace shi dama baya son motar haya ne, amma in tafi in kuma kula da kaina,tare da shadad muka tafi,Baba yana jin jiki,na yi ta kuka su Babasuna ta bani hkr,wai ai jkn ma da sauki.WashegariAbubakar ya iso,nan take ya kira liktansu don suna da asibiti nan kaduna.Cikin awa guda aka canza masa asibiti.Masha Allah, zuwa washegari jiki yayi kyau. ABUBAKAR YA XUBE MIN KUDI MASU dama sannan,ya tafi.baba dasu Baabah sai godia. Na zo na zuna ina tunanin dame xan saka ma Abubakar, abubuwan da yake min? gashi yaki ya bani dama in nuna masa irin dumbin son da nake masa. na fito dga asibitin ina rike da hannu shadad muna jiran mashin don xuwa gidan Umar. Wata dirkekiyar mota ta tsaya gabana, nan nan na hade rai tare da cewa yan'iskan mutane ba dama suga mutum su kyale. kofofin motar suka bude a lkcn guda,sai kawai naga Munnir. nan take wani irin bacin rai ya xiyarce ni. Yace"Hafsy manya" nace cikin ihu kai!kai! mallam kada ka akra kiran sunana. naja hannun shadad muka yi gaba, ya biyo ni. Ki tsaya ina so ne muyi mgnr dana? Cak!na tsaya tare dayi mishi wani mugun kallo."Ba ka da daa gurina, ka fita hanyata in ko ba haka ba xaka hadu da nadama. Na tare dan mashin muka hau ba tare da an fada masa in da xanje ba. Dare muna gidansu baaba sai gashi da Mom dinsa da dadynsa,muna cin abinci da sakina itama taxo tana jiran mijinta xai xo ya dauke ta da mashin... Raina ya baci,suka gaisa da mutan gida. Mom tace "Don Allah Hafsa nake nema, nace gani. Sakina ta bata kujera Ta kure shadad da ido,da kyar na amsa gaisuwar da take min,tace "ikon Allah!! Lallai wannan yaron Munnir ne,kamannin har ya baci."Ta dube ni"yar nan nazo ne mu daidaita, wannan yaron dai jikana ne, "cikn daga murya na ce "Dana ba jikanki ba ne. na fasa kuka nan mutanen gida suka taru nace "ki fitar mana daga gida.na daga waya na kira yaya umar, sai ga shi ban taba ganin fadansa ba irin na ranar.ya ce sun san dansu ne can da ba su xo ba sai yanxu?nan fa itama Mom ta shiga masifa har waje,Munnir wai shi sai ya shigo gidanmu ya dauki dansa. Umar ya ce, shigo mu rusa maka kai, dan iska mara kunya"kai, ranar naga tashin hnkl shi kanshi shadad din ma kuka yake, ganin ina yi.Na kira Abubakar ina kuka na fada masa cewa sun xo wai xasu dauke shadad. Yace "xa suyi me?to kan me?na ce nima ban sani ba, yayi shiru can yace "xan shigo gobe. Washegari ko asibiti na kasa xuwa, sai kusan sha biyu Abubakar ya iso.lkcn kuwa Munnir suna waje tare da Umar,wai ko a ba su yaro ku su kai kara kotu,kuma su dauki lauya.Abubakar ya kalli Munnir tsaf,nan take ya ji ya tsane shi.ko shakka babu wannan shine Baban shadad.Ya ce " kan wane dalili kake son a baka yaro?"yayi mishi wani duba,sannan kai tsaye yace, Dana ne"Abubakar yace "ka taba aurenta ne?ya ce ai kowa yasan cewa budurwata ce a da. Ran abubakar ya sake baci,ya ce"don kawai tana budurwarka a da yanxun sai kazo kce danta naka ne?yace ita tasan komai ai.Umar yace to sai dai in ku ku kai karan mu amma babu wanda xai baku yaro.Abubakar yace ina Hafsat din? Umar yace tana ciki.ya shiga gidan ranshi a bace,ya same ni dakin baabah. Cikin fushi yace"wannan kadan kika gani kin xabi son xuciyarki kin bar tafarkin Allah, dole kiga kaico.Sai ma wani ya sake xuwa yace shima dansa ne tunda kin xama bola mai dibar sharar kowa, ba ki san adadin maxan daki ka bi ba a rayuwarki."Namike tare da fashewa da kuka na ce,"sam ni babu wani namiji dana taba bi a rayuwata, ko shima fyade ya min ai shi ya sani."Ya ce to da bakinki kika sanar dani cewa ke karuwa ce kuma a yawonki ne na karuwanci kika yin ciki,ko ba haka kika ce ba? Na ce "Ni fana fadi haka ne saboda kawai saboda ina son ka barni.Ya ce"ke dai kika sani,wanda bai ji maganar iyayen shi ba ai dole ne yayi nadama in ko ba haba ba ni ba da aure na ba xa'a je kotu,sai ki tattara dansu ki basu.Na xube gwiwa biyu a gaban shi tare da rike kafafunshi na ce"Don Allah ka taimake ni,in na bashi yarona ya cuce ni,ya toxarta ni a baya. Abubakar xan yarda in ka rabu dani saboda ya xama ajalina akan in ba da yarona. Ya fita fuu a fusace ,kamar minti 15 ya dawo ya dauki shadad ya fita. Na bi shi da gudu har gurin motar Yaya Umar, nace "Ina xaku dashi?Yaya Umar bai tanka ni ba,sai Abubakar da yace ckn fushi.koma ciki ki jira,duk ranar da kika koyi magana sai ki kira wayata,yaron kuma xan kai shi gurin uban nashi,in yaso kije ki dauko shi.Umar yaja mota suka tafi.Kai tsaye kano suka nufa,gidan Raham suka kai shi,sannan Umar ya dawo ,ni ko ina nan sai kuka nike mutanen suna bani hkr,wasu na cewa,in hkr mana,muna huta lkc da abin ya faru baabah taje gurin Babah a asibiti. Da ta dawo kuma sai ta same ni ckn kuka da tashin hnkl,nace"Umar da Abubakar mijina sun dauki Shadad sun kai ma Munnir. Baabah tace kiyi hkr,ki kuma gode ma Allah,dmn wannan wata mafita ce ya baki. kin san hatsarin ba yanxun bane,sai nan gaba yaro yayi girma sai ya tsare ki ina babanshi,me xa ki ce mashi? Don haka kiyi hkr,wannan ma wanke ki ne Allah yayi.Na nisa."ni kam baabah ba xan fa yarda ba,ni kadai nasan halin da na shiga tun daga lkcn da Munnir yayi min fyade har xuwa yanxun,in na bashi yarona yaci bulus. Ta ce "to me xa kiyi?kina ganin kin fisu tunani ne?kada ki manta mijinki ne fa da wanki."na hada kai da gwiwa ina kuka tace."bana son ki sake yin wani abu da za a ce baki kyauta ba,ko yan'uwanki suyi fushi dake..."Yanxun ya ya xanyi"Na katse ta, ta ce "ki nutsu ki bisu,duk yanda suke so.Na ce, shi kenan" Na kira Innarmu na fada mata komai game da abin dake faruwa,har xuwa abin da Baabah ta ce.Innarmu ta ce."Ki kwantar da hnklinki shawarar da Baabarki ta bada ita ce ya kamata ki bi,sannan ki tuna cewa mahiafinki yana kwance a gadon asibiti kada ki kara masa wata damuwar."Na ce "to shi kenan,na hakura.Da dare kuma guraren 9pm,na kira Rahma ashe lkcn suna tare dasu Abubakar shadad kuwa yayi bacci. Tace, gata ta kira, yace kada ki nuna mata cewa mun xo.Bayan mun gaisa ta ce"Ya jikin baba?na ce da suki sosai.Ta ce "ya ya naji muryarki wat iri? "na ce Um! sai kuka tace lfy?nace Munnir yana son kashe ni da raina.Kinsan yanxun ya kunna min wuta wai in ba shi dan shi? su kuma Umar da Abubakr dina suka dauke shi suk kai shi.Ta ce " To yanxun yaya xa kiyi?na ce "Rahma ba ni da abin yi daya wuce addu'a in xura musu ido.Tace "hakn in kika yi shine abin da yafi dacewa."na ce "Um,wai Abubakar ha da cewa ban iya magana ba.Wai in xauna a gida in na koyi magana in kira shi a waya,wai da gaske ne Rahma don Allah ban iya magana ba?Ta ce "to kila shi ne kika sakr ma magana son ranki "na ce "Rahma xan iya rantse miki cewa ban taba sa'in sa d ashi ba tunda na aure shi. Ta ce. To ki lallaba shi sai ya fada miki maganr da kika fada masa mara dadi.Na sauke ajiyar xuciya."shi kenan na gode.Na koma na kwanta.Bayan na yanke ma kaina hukuncin cewa ba xan kira wayarshi ba har sai lkcn daya neme ni.Sam daren ban runtsa ba,washegari jkn Babah yayi sauki,aka sallamo shi ya dawo.Can kusan karfe 4 aka yi sallama,mun xata masu duba baba ne,ashe wai kara iyayen munnir suka kai kotu.Tirkashi!Sai lkcn baba yaji komai, na kira Yaya Umar na ce "To gashi sun yi kararmu to ta me bayan kun basu dansu?ya Umar ya ce kara kuma?na ce kwarai kuwa,ga magatakardar babban kotu yaxo.Ya ce"Ina xuwa ya kira Abubakar lkcn ya koma Yola,bai ko hutu ba don saukar shi kenan,ya ce to yanxun ranar yaushe ne shiga kotun?Umar yace "Monday"Abubakrya ce . to xan xo jibi da lauyana."Umar ne ya fada wa Innarmu komai,itama tace tana xuwa.Inna wanka najiyo muryar Abubakar suna gaisawa da mutan gida.Sannan ya shiga gurin Babanmu , na tashi na dan kintsa jikina,ya ce ya shigo suka gaisa da Baba sannan ya koma gurin Baaba suna tattauna batun rikicin.N ashigo na xauna gaida shi,ba tare da na dube shi ba,ya amsa sannan ya tambayi jkn baba, na ce yaji sauki.Daga nan yace ,to nazo da lauyana xumu kwana nan tunda ance gobe ne shari'ar ko/na ce eh!ya ce ki shirya yanxun muje yayi miki tambayoyi.Ya dubi baba ya ce,Baba ayi mata fada ta fada mishi gaskiya,dmn da ita ce xa'a yanke miki duk wani hukunci.Baba yace."kwarai kuwa in kin fadi gaskiya to kin hutar da kanki,kin hutar da kowa,Allah ya ba da sa'a.Muka fita xuwa mota,lauyan ba xai wuce sa'anshi ba,baki mai yar'kiba kadan,yana amsa suna Barista murtala.In da suka yi masauki nan muka je, amma gurin shakatawar muka zauna.lauya Murtala yace in fada mishi sunana,na fada mishi.Daga nan ya tambaye ni tarihina,Abubakar na xaune na xayyana ma lauyan komai,tun daga haduwata da Munir har xuwa yau.Lauya Murtala yace "kin tabbata haka ne?Na ce ko ckn bacci ka tashe ni xan maimaita maka wannan don ba xan manta da wannan bakin tarihin nawa bah.Abubakar ya ce?Kada dai ki fada man karya,don ke baki iya magana ba.ya ci gaba da cewa."yaya batun xagawa duniya da kika yi?Na ce,"banje ko ina ba,kuma ban da shi da ya min fydae ban taba hulda da kowane namiji ba.Ya ce "in har hak ne fyade yayi mata barista sai in ga kamr shari'ar xata yi sauki ko?Murtala yace "inshaAllau in an gam matsalar yaron sai tayi karan cewa fyden da ya mata,tana son abi mata hakkinta,tunda nasan dole xai amsa laifinsa.Bayan gama gabatar da shari'ar a ranar litinin din da muka gurfana a gaban kotu lauyoyi suka fito,lauyan shi ne yafi bani mamaki, yanda ya kuke kan cewa a ba shi danshi xai biya duk abin da aka kashe.ni dama koda aka tambaye ni dans ne?na ce dan shi ne,ban bata lokaci ba.Lauyana ya bukaci in ba da labarin dangantakata da munir,mijina ne?na vce a'a saurayina ne ,ya ce to saurayinki ya ya aka yi kuka haihu har ma ki ka hana shi danshi?ya dubi Alkalin ya amince nan na xayyano komai har xuwa yau.Jama'a da dama sun xubar da hawaye don tausayin min aka tamabyi munir shima bai bata lokaci ba ya amsa da cewa tabbas fyade ne yayi min.kuma duk abin da na fada haaka ne,sai dai shi bai san cewa na shiga wani hali ba,sannan ko nawa na kashe wa dan xai biya ni.nan dai lauyoyi suka yi ta kafsawa,daga bisani na ce ina son a bi min hakkina na fyaden da yayi min .nan Alkali ya daga kara xuwa sati biyu masu xuwa,kuma ranar ne za'a yanke hukunci,haka muma Alakli ya bukaci a xo da yaron.Muka fito ,Abubakar sai kallona yake yi tamakr yau ya soma ganina,ya ce Umar ya wuce da su Innarmu saboda shi xai tafi tare da lauyan,don in sake mishi karin bayani.Tunda muka xo daidai dakunan su Barista Murtala ya shige nashi,ya rike hannuna xuwa ckn nashi masaukin.tsakiyar dakin ya tsayar dani ya rike hannuwana tare da kallon fuskata ckn matsanancin tausayi ya ce min."Hafsat me ya hana ki sanar dani ainahin abin da ya faru ki ka sa ni ckn kunci nima ni dinga kuntata miki? Na tsura ma fuskarshi ido."Abubakar a lkcn na furta maka haka ne don kawai ka rabu da ni,sam ban san xa ka zama makusancina ba,lkcn bana bukatar wanda xai kusanto ni da gida,ban san lamura xasu xo da sauki haka ba,ya manna ni a kirjinsa, lokaci guda muka sauke ajiyar zuciya, ya ce ki yafe ni, na nisance kine saboda in ina tuna cewa bansan adadin mazan da kika yi hulda dasu ba, ga kuma kishin ki mai wahalar dani...... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-04 Posted by ANaM Dorayi on 05:15 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na soma kukan farin ciki. "Na yafe maka, dama kuma ni ko kusa ban rike ka da komai ba, saboda ba duka namiji ne ne zaiji furucin da nayi ma kaina lakabi da shi ba, sannan ya saurare ni, sai sadauki, jarumi irinka mai taimako don Allah." Na sake kwantar da kaina a kirjinsa, na ce "Nima ka yafe min bata maka ran da nayi." Ya dago fuskata, ya sumbaci goshi na, sannan ya tsurawa kwayar idona nasa idon. "Na yafe maki, sannan ya sake maida ni kirjinsa da wani kalar salon nuna soyayya. Wayar shi ce ta katse ni, sanda muka yi nisa cikin wata duniya muka sake ajiyar zuciya, sannan yasa hannu ya zaro wayar a aljihu. Ni kuma na zauna, zuciyata kuwa farin ciki ne maras misaltuwa. Ya daga wayar, mahaifinshi ne suka yi magana cikin fillanci na tsahon minti goma sannan suka yi sallama. Ya zo ya zauna kusa dani, sannan ya kira Sagir ya bashi labarin yadda shari'a ta kaya, sannan ya ce zama na gaba ya zo da Shadad. Suka yi sallama, ya ce "To mu fa zamu wuce ne, yanzun haka Abba na jira na saboda tafiyar dake gaban mu zuwa Pakistan." Na ce "To ni in zauna a nan?" Ya ce "Kano za ki koma, ki kwantar da hankalinki, In Shaa Allahu za a bi maki hakkinki, domin na kula Alkalin yana da kokarin kamanta gaskiya." Ya ce, "Amma fa ki barshi gurin sagir kada a zo a dauke shi, na ce to" ya soma hada kayan shi ina taya shi har muka gama. Ya rike hannuwana, "Ko in raka ki Kanon ne?" Na ce "A'a, ka ta fi kiran Abba din." Sai da suka kaini gida, ya cika ni da kudi, sannan ya roki Umar da cewa ya kaini gida baya son na shiga motar haya. Su Baba ma yayi masu alkhairi, sannan ya tafi. Abinda yayi wa zuciyata dadi, yanda na samu mutan gida suna tattaunawa akan shari'armu. Wasu sunje kenan ku yau sunji da kunnan su cewa Munir fyade yayi min. Ade ta dube ni, "Hafsat ina maki murna, Allah ya dora ki a kan shi." Na ce "Ai dama gaskiya tana halinta komai daren dadewa. Sannan masu zagina da masu cewa nayo ciki SANADIN BOKO duk na barsu da Allah." Asabe ta ce "Ba a yi haka ba Hafsat, zance na gaskiya ko mu gidan nan ba wanda bai yi da ke ba, sai dai ki yafe mana, Allah ya baki hakuri." Ni dai nayi daki. Na koma Kano naci gaba da zuwa Makaranta, wata uku jal ya rage min in kammala HND dina, tun tafiyar abubakar bamuyi waya ba sai dai text yake turo min. Cewar inyi hakuri wai abubuwa sunyi masa yawa shi yasa, amma zai kira ni ina ranshi. Cikin bacci naji karar wayata da faduwar gaba na tashi, sai da na kalli agogo karfe 2 da minti 40 sannan na dauki wayar na duba sadeek dina na furta a hankali sannan na daga wayar a hankali na furta "Amincin Allah a gareka" ya amsa da cewa " Ameen kema amincin a tare dake, na tashe ki a bacci ko? Nayi rigingine tare da matse filon a kirjina, nace ka isa kayi fiye da hakan" Ina jiyo sautin mumurshinsa ya ce tunaninki ya hana ni bacci,kewar muryarki ta dame ni shi yasa na yanke shawarar kiranki. Na ce Nima kewar ganinka nake yi yaushe za ka dawo? ya ce, da gaske kin kosa ki ganni? na ce um, ai ganinka ya fiye min komai a rayuwa Sadeek dina. Ya numfasa"Me ki ka tanadar min kafin nazo? Me ka ke so mijina? Ya ce, ke kadai nake so. Na sake tausasa murya,Ni taka ce mijina,zan zama mai binka a kowane lkc. Ya ce Na gode Hafsat,zan nuna miki kalar soyayyata,za ki sha mamakina. Na katse shi,"Wace iri ce ka fada min. ya ce a"a sai in nazo za ki ga zahiri,yanzun zan sunbace ki in kin amince. Na ce Bismillah. Sai kawai naji sumbarshi a cikin dodon kunnena har cikin karamin yatsana, ya ce kiyi bacci da mafarkina mai dadi. Na ce ba zan iya ci gaba da bacci ba, zan tashe ne in nuna murnata ga Allah,tare da yin addu'a ya tsare min kai, ya baka duk abn da kaje nema,ya kuma dawo min da kai lfy. Da sauri ya ce, Amin-amn sweet heart . Na ce Wannan Sunan Fadima ne, zan fi so nima kasa min nawa. Ya ce, To shi kenan. Kusan sakon hudu sannan ya ce, ki kashe wayar,na ce kai ne babba kai ya kamata ka kashe,ya ce na gode. Abin tamkar cikin mafarki, wai ni ce matsalolina ke ta kwakkwancewa a hankali. Na tashi cikin farin ciki nayo alwala nazo na zube gabn Ubangijina, addu'o'i nake tare da nuna godiyata ga Allah. Na kuma yi wa mijina shima, Allah ya dawo da shi lfy,ya biya mishi dukkan bukatarshi na alkhairi,tare da dukkan Musulmi baki daya. Ta gidan Rahma na biya na ce Lissafo min abubuwan nan da ki ka ce ya dace in yi amfani dasu. Ta dubi ne, Wane abu kenan? na ce, Na Amare.. -Ta sheke da dariya, sannan ta ce, "Dadina da gobe saurin zuwa, yau ke ce kika zo neman abin da nayi ta binki da shi kina gwasale ni?" Nima 'yar dariya nayi sannan na ce, "Fada min." Na fito da memo da kuma biro daga jakata. Ta ce, "Da gaske ki ke yi? To ai gara kam ki rubuta don ba zan baki hadadde ba, zan fada miki abubuwan da ya kamata ki dinga ci." Na ce to. (Fruits ne ta yi mata listing including Nono, zuma, madarar shanu, nonon rakum, kokumba da gurji) Ta ce, "Kin rubuta?" Na ce, "Eh! Amma zan ta cin su ne haka ko yaya abin ya ke?" Rahma ta ce, "Kina iya cin su ko ki hada wannan da wancan. Na barki kije ki gwada basirarki." Na natsu ina kara kallon abubuwan, sannan na mike tare da cewa, "Bari in tafi kada Shadad ya dawo ya same ni, amma zan baki mamaki. Sai kin zo gurina rokon in fada miki irin nawa sirrin." Ta ce, "Zamu gani." Na tafi ina dariya. Na cema dan adaidaita don Allah ya kaini kasuwa. Ya ce, Ba komai." Duk abin da na rubuta sai da na siyo su. Ta kan kankana na fara na fere bayan na markade ta har 'ya'yanta cikin blender, na dauko kwakwar da na yanka kanana itama na nika, na daka raken da na yanka kanana. Na fidda ruwan shi na hada su guri daya ban ko tace ba na fasa madara peak na zuba zuma na fasa kankara na jefa, ranar shi ne abincin dare na. Da safe kuma ina da garin alkama, na dama shi da madara na zuba zuma, bayan na dama shi ya zama kunu na sha. Da na dawo makaranta na dafa zogale na yanka gurji a ciki kanana, na kwada da kuli na zuba tumatir. Nan na zauna na ci na koshi, sannan na kora da kunun aya da dabino da kwakwa da madara da zuma yayi kauri na sha na yi kat. Da daren ranar kuma farfesun kaza na yi ruwa-ruwa na lankwashe na sha romon sosai. na yi kat, na zauna ina cin apple (Hhhhhh, lallai Hafsa da gaske take yi 'yan uwa, shan romo har da lankwashe kafa? Washegari hadin kazar amare na yi ta tamkar yanda na taba ji. Tun daga ranar ruwan 'ya'yan itace shi ne ruwan sha na, dukkan abubuwan da Rahma ta lissafo min na maidasu abincina, abin sha na. Kafin sati daya ni da kaina na yarda cewa na hadu, kai ina mamakin kaina idan na tuno irin kalaman da nayi ma Abubakar idan ya kira ni. Shi kan shi Abubakar din baya iya daukar awa 3 ba tare da ya kira ni ba, lallai na amince iya yin lafazi mai kyau ga miji yana sa mace ta mallake mijinta, nuna damuwa ga damuwar miji tana sa miji ya kara son ki. Ana gobe za su dawo na shiga kasuwa na yo cefane, duk da bani da tabbacin cewa Kano zai sauka, Na damu ya zo don shirina da nayi ya soma damuna. Ina kwance bayan la'asar na kira layinshi ya daga, cikin sauri ya ce, "D only! Yaya ne?" Na ce, "Hayate don Allah ta nan zaka biyo?" Na yi maganar cikin sigar shagwaba. Ya ce, "Muna tare da Abba yanzun, zan kira ki in mun rabu dashi kin ji?" Na ce, "Toh." Ba'a fi koh minti 10 ba ya sake kirana. "D only kina jina?" Na ce, "Eh!" Ya ce, "Muna tare da Abba ne kin ga ba dama mu rabu ko? Kuma Fadina tana sa ran zuwana." Na ce, "Kai Hayate (cikin shagwaba nake maganar) Ba fa nan ka tashi ba, don Allah ka min adalci in ganka kawai ka wuce, ko ba ka zauna ba." Zai yi magana na ce, "Please Mr Cool, bana jin zan iya kwana 2 ban ganka ba, sorry pls." Sai naji yayi ajiyar zuciya tare da cewa, "To yanzu yaya zan yi da Abba?" Na ce, "Ya san kana da ni fa a Kano, in kace zaka zo ai bana zaton cewa zai yi fada." Ya ce, "Bana son ayi zargin cewa nafi sonki amma zan dan yi dabara in zo din ko ban kwana ba, muka ga juna sai na wuce." Na ce, "To na gode Mr cool. Sai na ganka." Hmm! Ranar da zai dawo ko Makaranta ban je ba, tun safe na ke hada mishi sinasir da miyar alayyahu, simmer fish, meat bolls, meat into potatoe da peppered chicken. Na yi fruit salad na yi coslow, jus din cocumber, sai kuma na yi masa coconut drink. Nan na shiga jera masa duk abubuwan da na tanadar masa. Jus din na soma zuba masa ya sha sannan na bude masa dukkan abubuwan da na girka na ce, "Wanne zan soma zubawa?" Sai da ya hadiyi miyau sannan ya ce, "Kowanne kadan." Tun da ya soma yake fadin, "Alhamdulillah Masha Allah, na yi dace kam." Dadi nake ji tamkar in yi tsalle sai sake zuba mishi na ke, ya ce, "Bar shi kada in kasa bacci." Na sirka mashi ruwan wanka, ya ce da na sanyi zai yi na ce, "A gajiye ka ke zaka fi jin dadin wanka da na dumi." Ya ce, "To." Daki ya shiga ina daga waje ya bude jakarshi ya canza kaya, sannan ya ce, "Zo ki raka ni in kama masauki." Na ce, "Nan gidan ba za'a iya bacci ba?" Ya yi dan murmushi, "Zo dai mu je mu dawo." Shahararren masaukin bakin nan muka je ya kama daki, na bata rai. Bayan mun zauna bakin gado ya ce, "Yi min dan murmushin nan mana." Na dan harare shi da wasa, "Ba ka 'ki kwana gidana ba." Ya ce, "To ni nan zaki taya ni kwana." Na zaro ido, "In taya ka me? Tab! Tunda dai na rako ka maidani gidana." Ya ce, "Tsoro nike ji, dakin yayi min girma." Na harare shi tare da cewa, "Da can ba kai daya kake kwana ba?" Ya ce, "To ai yau na soma jin tsoron, ba kin ce kin min tanadi ba?" Na ce, "To ba na baka ka ci ba?" Ya ce, "Daman wai tanadin abinci ne?" Na ce, "Eh mana." Ya ce, "Ammafa ba haka muka yi da ke ba." Na ce, "To yaya muka yi?" Ya mike ya dauko jakarshi, "Zo ki gani." Ya fitar da duk kayan jakar, can kasa ya fito da wasu kaya, kayan baccine 'yan India masu shegen kyau, baki da pink ne. Ya fito da pink din ya ce, "Gwada wannan in gani." Na amsa na daga ina kallo, akwai kyau amma zai fi dacewa da sunan Fandarinki tsirara. Na yi tsaye ina kallonshi yana mai da kayan, ya mike, "Kawo in gwada miki." Na ce, "Zan iya." Na fada toilet na saka, na dubi kai na, zan iya fita kuwa? Na yi ta maza na kama kofa zan bude, sai kurum na ga ya bude ya shigo. Na runtse idona shi kuma ya ce, "Kai cancadi! Zo mu je in miki hoto." Ya rikeni muka fito. Ya zauna bakin gado tare da dorani kan cinyarshi, Kai Subhanallah!!! Abubakar ya fara shafani tun daga wuyana har ya sauko kirjina wanda ba kace na shayar da Shadad ba, ya rude ya shiga kissing dina, anan dai ya dinga yaba min irin goyon bayan da na bashi tare da tanadin da nayi masa, ya dinga min surutai wanda bana gane mai yake cewa, sai dai numfashinsa kawai nake ji, kai ba zan manta da wannan rana ba, son Abubakar da kaunarshi gami da kishinsa sun karu gareni, kai na so in cuci kaina, kuma na yarda cewar soyayyarshi mai tsada ce, amma na kula shima ya yaba da ni matuka. Nan muka yi Magriba da Isha'i munata tarairayar juna, ian kallonshi ya kashe dukkan wayoyinshi, a takaice dai nan muka kwana muna faranta ran juna cikin farin ciki, ko kuda baya son yaji a jikina. Misalin Goma na safe muka dawo don 12 zai nufi Yola, amma sai muka bude sabon shafin soyayya anan gida na, ya dinga lugwiguita ni yana zantuka iri-iri masu wuyar ambato, Abubakar ya dinga santi tare da yabon Hafsa cikin kalamai masu dadi, nan muka kwashe lokuta da dama dan bamu san lokaci ya tafi ba, har ya so ya makara. Ni kam da zai tafi har da kukana, ya lallashe ni da cewa jibi zai zo mu wuce Kaduna don karkare shari'ar nan, da kyar ya lallasheni sannan ya tafi. Kwana daya jal da muka yi ya sani na manta duk wata damuwa da ke raina, lallai Abubakar shine irin mijin da mata ke so, wanda zai shagwabaka, ya so ka kuma ya riritaka, har ka mance a duniyar da kake. (Ohh! Su Hafsah sai sambatu ake) Ya san so yasan sirrin so, ya san yanda ake zama da mace. Haka ya tafi ya barni da kewarsa duk na rikice. Da dare ina kwance tamkar in kirashi amma sai na tuno can mafa yana tare da matarshi, kishi ya isheni, yanzun duk irin kulawar nan da ya bani haka zai bata? Sai hawaye masu dumi suka soma sakko min, can dai na dauko wayata ina kallon hotunan da muka dauka ni da shi cikin soyayya da kauna irinta masoya, lokacin muna cin abinci cikin soyayya da tsokanar juna a masaukinsa, kawai sai na samu kaina da rubuta masa I LOVE U na tura masa. Can har na fara rubuta dogon text na soyayya, sai kuma na fasa na ce abinda baka so a maka kai ma kada kayi ma wani, don haka sai na danne. Kusan 12 sai ga kiranshi, da sauri na daga, a hankali yake magana ina zaton ko Matarshi ta yi bacci ko kuma ta dan fita oho, ya ce, "The only kina jina?" Na ce, "Eh." Ya ce, "Na ga sakonki, ina sonki sosai, ba zan manta irin kaunar da na sha a gareki ba, kin jiyar da ni dadi matuka, inata tunanin kasancewa tare da ke, kiyi bacci kinji?" Cikin Marairaita na ce, "Ba zan iya ba Cool, yaushe zaka zo?" Ya ce, "Zan kira ki anjima kin ji?" Na ce to. Ya ce, "To in kin kasa bacci tashi kiyi mana addu'a Allah yasa mun samu Baby." Na ce, "To Cool, miss U." (Hhhhhh, Su Hafsah an hau duniyar sama an gaza saukowa) Hakan kuwa na yi, da nayi alwala na dauki Al-kur'ani na soma karatu, sai na samu nutsuwa. Kusan 2 na dare ya kirani, "Me ya hana ki bacci d only?" Na ce, "Tunaninka mana." Ya ce, "Nima kina raina Hafsah, da ban same ki ba da nayi asara." Na ce, "Wai! Ni ce zan ce da nayi asara don irinka akwai wuyar samu." Ya ce, "Maza da yawa ba zasu gane ba sun fi kallon kyan fuska, Hakika suna zaban tumun dare." Na yi dariya sannan na ce, "Ka kwanta don Aunty Fadima ma baza ta so muna yin doguwar hira lokutan kwanan ta ba. Sai da safe." Ya ce, "To." Na sake alwala na zo ina Nafila dan wannan sallar tana da Muhimmanci gurinmu, in har zaki yarfe bacci ki tashi daidai wannan lokacin ki fadama Allah, to kuwa duk wata matsala taki zata yaye. Ubangiji da kanshi yake cewa da mai bukata ya tambaye shi Shi kuma ya biya mana, wannan kadai na tsare, ba boka ba mallam ga matsalolina a hankali duk sun warware. Allah ka yaye mana dukkan matsalolinmu Ameen. Ranar Lahadi kuwa ranar da zai zo cewa yayi in masa tuwon semo, sai kuma in masa jus din Shinkafa din nan. Miyar danyar kubewa na yi masa, ta ji bushashshen kifi da nama, na masa jus din shinkafa, sai irin kunun ayan da nike sha mai dabino da kwakwa da zuma. Wando da riga na ci sabbi ne na siyo su, da ina zaton ba zan iya saka wando ba amma daga baya sai na ce kiji kana cewa baka iya kukan mutuwa ba Uwarka ce mata mutu ba. Da kadan ya wuce gwiwata, rigar ma ta dame ni. Kallona yayi ta yi tunda ya shigo na masa oyoyo, da kyar na bambare daga jikinsa don yi masa shimfida, ya ce, "Ya ya aka yi kika san ina son shigar English wears?" Na ce, "Duk abinda ka ke so a kwayar idonka nake karanta, ai ba kallon kawai nake maka ba." Ranar dai mun ciyar da juna abinci, sannan muka shiga wani shafin, daga baya muka yi wanka muka dunguma gidan su Rahma. Shadad kuwa sai tsalle da ya ganmu, da zamu tafi ya so binmu, har zan ce mu tafi da shi sai Abubakar ya ce, "Shadad unguwa zamu, amma gobe zaku taho da Uncle dinka na nan gidan." Ya ce, "To." Muka dawo nan gidan muka kwana. Gaskiya duk macen da ta samu miji kwatankwacin Abubakar, to ta gode ma Allah, mamaki na daya, yanda ya iya kula da mace ta kowanne fanni...... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-05 Posted by ANaM Dorayi on 05:17 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Asubanci muka yi tare da su Sagir, Sagir ke tuki shi da Abubakar, ni da Rahma da Shadad muna baya. Sagir na zuba mana hira don shi Abubakar mutum ne bame yawan surutu ba, sai dai mun ta hada ido da shi ta madubi sai ya kashe min ido daya mu yi murmushi, har Rahma ta gane mu ta ce, "Kai ku dai wanna soyayya ko ina sai kun nuna ta?" Na ce, "Kuma ku nuna mana." Kotu ta cika lokacin hankalina na tashe, gani nake shi kenan za'a kwace min da. Bayan gabatarwa Alkali ya bukace mu muka fito ya ce, "Ina yaro?" Aka fito da shi ya ce, "To a musulunce za'a yanke hukunci tunda mu Musulmi ne." Duk muka amince. Alkali ya yanke cewa, "Duk da cewa fyade aka yi mata ta samu ciki, to dan ba dan Sunna ba ne, ma'ana ba ta hanyar aure aka haife shi ba. Don haka in ma ace tayi cikin shege dan nata ne ba a danganta shi da namijin saboda sai da yardarta, don haka wannan ma nata ne, sai dai shawarar da zamu iya bata ita ce ta bawa wannan mutum dan saboda zata fi mutunci, haka nan shi dan ko kuma a ba yaron zabi zai bi Uban nasa shikenan. Sannan hukuncin fyade tunda an ce bai taba aure ba, to za a yi masa bulala dari." Nan fa suka soma kuka, Mom ta zo tana kuka tana rokona wai in basu shi, na ce "Gaskiya ba zan iya bada dana ba." Shi kuma Dad dinsu ya samu alkalin suka kiramu suna ta rokonmu wai tunda gashi shi za'a dake shi, gashi bashi da koshin lafiya. Abubakar ya ce, "In dai yayi hutu za'a ringa kawo shi saboda ya san Ubanshi da danginshi." Suka yi ta godiya muka kame kanmu. Kano muka wuce bayan mun je gidanmu kowa na taya ni murnar cin nasara, daga nan muka koma Kano. Na gama jarabawata ta fita, murna ba a magana yanzun saura service Washegari da gaggawa Abubakar ya zo ya tafi dani Yola. Shadad kuma dama Sagir ya kai shi Kaduna gidan Babanshi suna ta murna. Shi kam da kyar ya lallasu daga kukan da yake sai da Sagir din ya kira ni ya ce in mishi magana. Na ce, "Shadad." Ya ce, "An'am Aunty, ni zan dawo ne ki fada ma Uncle ya dawo da ni." Tausayinshi ya kama ni na ce, "Gidanku ne ai, gidan Babanka da kake ta damuna da zancenshi." Ya ce, "Aunty ban san su ba." Na ce, "Zaka san su kayi hakuri kaji ko?" Ya ce, "To." Munir ya ce ma Mom ta amshi lambata in ya so sai su dinga kira mishi ni. Sagir ya bada lambar sannan ya tafi. Ikon Allah Shadad na ganin gata, tamkar a cinye shi don tarairaya, har an sai mishi waya don ya dinga kirana, ni kam cewa na yi kada su bata min tarbiyyar yaro, saboda su ba su da tarbiyya. Mahaifin Munir ya yiwa Shadad kyautar gidanshi da ke Kabalar road, tunda wai an ce bashi da gadon Ubanshi. Suka bude mishi account ni kam ina can Yola gidan mijina mai sona da gaske. Yau gidan Fadima yake, amma ya kira ni wai zaya zo cin abinci da rana. Na ce, "A'a, sai dai na yarda ka aiko a karba maka, don kada mu shiga hakkinta, Don nima ba zan so amin ba." Ya ce, "To naji." Na yi masa french dish rice serve with grill chicken, sai kuma na masa dan waken rogo da dawa, dama ina da garin, sannan na masa jus din karas, duk san da zanyi girki na kan yi da dan dama saboda mutan gidanmu suna son abinci na. Hakan nan na kan kirkira girki inyi ma Abba da Lamido da kalokin Jus na kan zauna ina kallon tashar girke- girke ina rubutawa na Chanis ko Italia ko Senegal da dai sauransu. Saboda kawai in samo girki wanda ba a saba da shi ba. Fadima ta dube shi, "Ban gane nufinka da amsa abinci gidan Hafsa ba?" Ya dube ta bayan ya dire kofin hannunsa ya cea, "Ta iya girki ga kokarin yi, bata da kuiyar dafa abincin ko kala nawa ne." Ta hade rai, "Ni ban iya ba kenan?" Ya ce, "To ke ko kin iya din ma yaushe kyuya zata bar ki? Ballantana kure girkinki shi ne shinkafa da miya ko taliya. Da zaki daure da kin je kin koyo kafin ta tafi CAMP." Ta harare shi sannan ta ce, "God Forbid in je gurinta koyon girki ka cuce ni, kuma wallahi ba zan yarda ba. A ranar girkina ace abincin ta zaka ci? In an sake kawo min nan zan zubar dashi." Ya ce, "To shi kenan, zan so ki zubar din." Cikin fushi ta shige daki. Duk ranar da yake gidana akwai wasu jus na kankana, Apple, ayaba, madarar ruwa, zuma da kuma garin ridi, in sa kayan itacen a blender in nika in zuba madarar da zumar da kuma garin ridin in sha, in kuma zuba masa ya sha, har dai wata rana ya tambayeni me nake sawa cikin wannan jus din? Don shi kan shi yana jin shi kullum yana kara lafiya da kuzari, yakan kuma ji yanayi daban da in bai sha ba. Na ce 'ya'yan itace ne. Har ma watarana a gabanshi nake hadawa. Wataran kuma in hada rake, zuma, madara peak, garin ridi. Kafin wani lokaci sai gashi na zama Malama ta hada kayan gyaran jiki, in mun yi waya da Rahma in na fada mata wasu sai tayi ta mamaki, na ce, "Dama na fada miki." Abin da yafi bani mamaki, da zan tafi CAMP a Kaduna aka tura ni har da kukan shi da hawaye don damuwa. Shi ya kai ni sannan ya biya ya taho da Shadad ya kai shi gidan Rahma a Kano. zaman sati 2 a camp ko ni na san na yi missing din gwarzon masoya, Abubakar Sadiq. Fadima ta dubi Rukayya, "Kin san Allah ni zan kai karar Hamma gurin Abba, sam baya cin abincina sai na Hafsa. Don gulma har nan zaki ga ta yo ta aiko mishi da shi, kenan ya fada mata cewa ban iya girki ba." Rukayya ta ce, "Ai Hamma ta riga ta gama da shi, ke har su Daada ma in kinji yanda suke yabonta? In ta yo abinci ta kawo ma Abba kiga su Ummi har ma Daada din sai suyi ta yabonta." Ta ce, "To gurin Lamido zanje." Rukayya ta ce, "Kin ji ma inda zaki fi jin dadin kai karanki, kuma zaya ci musu daga shi har ita. Dama ai ba son auren yake ba, kila ma yana kushe auren." Cikin zumudi Fadima ta ce, "Anjuma zan je." Ta shigo gidan da sallamarta suka gaisa da mutan gidan, tsoffin suna mata tsiyar cewa sun kwace miji. Ta shiga gurin Lamido, bayan sun gaisa ta ce dama ta kawo karan Hamma ne. Lamido ya gyara zama ya ce, "Tun kafin aje ko'ina har an soma matsala? To me ya faru?" Ta ce, "Baya cin abincina, ranar da yake gidana sai ya aika nan a karba mishi abinci fa, kuma in nayi magana sai ya ce ta fini iya girki. Shi ne ni na gaji da wannan maganar." Can ya ce, "Shikenan?" Ta ce, "Eh." Ya ce, "To yanzun ina Baban nawa?" Ta ce, "Yana cikin gari." Lamido ya kira shi a waya ya ce ya zo yana nemanshi. Kusan minti 30 sannan ya iso Lamido ya ce masa, "Daga ina?" Bai ji mamakin ganin Fadi ba. Lamido ya karanta mishi laifukan da ta fada, sannan ya tambaye shi ko haka ne? Abubakar ya ce, "Haka ne." Lamido ya ce, "Don me to baka son cin abincin nata?" Abubakar ya ce, "Don bata iya ba, kuma don na amso a gurin Hafsat wadda ta iya bana zaton na yi laifi. Saboda Manzon Rahma (S.A.W) yana amso abinci a gurin Nana Safiyya ya ci in yana dakin kowacce daga cikin matanshi. Don haka ni Sunna na yi." Ta ce, "Amma shi bai yi wulakanci ba." Lamido ya ce, "To naji yanzun dai sai kiyi kokari ki gyara." Abubakar ya ce, "Abin da in riga ta dawo wa kullum sai na fa jira ta ta dawo sannan ta min abincin. Ita kuma Hafsah ko ina zata sai tayi min abincin ta bari in dai tana gari, amma ita wannan sai son jiki." Lamido ya ce, "Ka yi hakuri tashi ka je abinka.Bayan fitar Abubakar Lamido ya ce, "Ke Fadima abin da zan fada miki, kin ga bakuwar yarinyar nan? To ta fiki hankali. Tun yaushe rabonki da gidan nan da sunan ki zo gaishe mu? Ita kuwa ko bata garin nan ta kira mu ta gaishe mu a waya. Girkinmu daban ga girmama mutane, don haka ki nutsu ki zauna lafiya. Ba zan 'kita ba don tana bare, dama ai mugun iri ake tsoro." Fadima dai ta tashi jiki babu kwari ta tafi gida, zuciyarta cike da haushin Hafsah, wato ta zo zata siye dangi? Ta ja wani Uban tsaki. Allah cikin ikonsa mun gama CAMP sai dai Abubakar ya ce zai yi duk yanda zai yi a barni a Yola, ba zan kara nisa da shi ba. Daga baya ma ya ce in na gama bazan yi aiki ba, ni dai ina jin shi ban ce komai ba. Allah ya taimaka da ya shiga ya fita sai ko aka barni a Yola, ni kaina nayi murna don bana son inyi nisa da mijina, Shadad ya dawo Yola shima Abubakar ya canza masa Makaranta mai kyau, duk da cewa Iyayenshi suna ta turo kudi wai na karatunshi. Dad har Yola ya zo kuma ya sanar da abokinshi Mai Martaba Baban su Hashim cewa Shadad jikan shi ne, don haka yaron bai da matsala ko cikin gida, gashi da farin jini. Cikin haka ne FADIMA TA SOMA LAULAYIN NAN, naga rawar kai wurin Abubakar da 'yan uwansa, ganin haka nima na soma zuwa kullum ina dubata, sai ta tsiri cewa wai turarena na sata amai, in daina zuwa. Abubakar ya ce, "Fadima ta ce bata son turarenki ki daina zuwa kawai." Allah yasan na ji haushi, amma sai na share saboda sanin halin Abubakar shi mutum ne sak babu kwane-kwane a tsarin shi, baya rufa-rufa ko kara zance, yanda aka fade ta haka yake daukenta, shi yasa na sha wahala lokacin da na ce mishi ni karuwa ce, har sai da ya zo ya ji komai da kunnanshi na samu sukuni. To yanda Fadima ta ce haka zai fada gaskiya tsagwaronta yake yi ba ruwanshi, don haka na ce, "Shi kenan, na ringa kiranta a waya muna gaisawa." Ya ce, "Hakan zai fi." Daga baya sai ta tsiro cewa ita ba zata iya bacci ba sai in yana gurinta, Ya ce to bari ya same ni. Ina kwance na dawo daga gurin aiki wata makaranta aka turani ta 'yan mata nake koyarwa. Na yi abinci na gama nayi wanka na kwanta, ya zauna na tashi na mishi sannu da zuwa, na dire mishi abinci. Yana ci ya ce, "The only, ina son ki yiwa Fadima taimako daya." Na ce, "Na me?" Ya ce, "Bata samun bacci don Rukayya ta fada min cewa zaune suke kwana. To tana son in dinga kwana gurinta har ta dan murmure."Zancen ya bani mamaki, sannan na fahimci cewa makirci ne, amma sai na ce, "Ba komai." Ya ce, "Dama na san ki baki da matsala." Da dare kuwa ya tafi, haka-haka har sati uku. Sai dai fa in yana da matsala ya yi min sammako ko kuma in ina gurin aiki ya zo ya dauko ni daga baya ya dawo da ni. Ban taba nuna mishi damuwata ba. Lamido ya kira shi ya ce, "Ubana an fada min baka kwana a gidan nan ko?" Ya ce, "Eh, saboda bata samun bacci ne in bana na." Lamido ya yi murmushi sannan ya ce, "An fada min kuma tana zuwa hurin aiki ko?" Abubakar ya ce, "Eh, ai matsalar tata da dare ne." Lamido ya ce, "To, daga yau na hana, kowacce ka dinga kwana gidanta a ranar kwananta, kanta aka soma ciki? An ce ta samu sauki ba shike nan ba?" Abubakar ya ce, "Shi kenan." Har na soma bacci na ji kwankwasa kofa, na zo na ce, "Wane ne?" Ya ce, "Ki bude." Na bude na ganshi na ce, "A'a baka tafi ba?" Ya ce, "Ke ce kika fada ma Lamido cewa Fadima ta ji sauki amma ban daina zuwa ba ko?" Na ce, "A'a bani ba ce." Ya ce, "To wanene?" Na ce, "Ka tambaye shi." Ya ce, "To ni bana son kai kara, don ban soma zuwa ba sai da izininki." Na ce, "To gaskiya ba ni bace." Ya ce, "In ma ke ce din ai yana zuwa kanki, tunda an ce ai haka ciki ke yi muku." Na yi masa shiru don haushi. Abinda bai sani ba nima lokacin ina manne da nawa cikin wata biyu, ina kuma laulayina sai dai bai yarda ni ba, sai dai amai kuma nafi yin shi da rana, kuma ban fasa komai ba. Azumi ya kusanto ya zo ya same ni wai in zo muje gidan Fadi, zai yi wata shawara, na ce to.......... Cikinta ya fito, amma yanda take tike kugu gami da turo cikin ko watan haihuwarta ne sai haka, tana yi da kyar take daga kafa, a dole ga mai ciki shi kuma kallonta yake yana murmushi, ni sai suka ma bani dariya. Ya kamata ta zauna yana yi mata sannu, ita ko sai faman cije-cijen lebe take, na yi 'yar dariya nace, "Maman twins an fito?" Ta ce, "Umm na fito." Muka gaisa ya ce, "Dama saboda zuwan azumi ne ina son in bada sadaka wa kuke ga ya dace in ba?" Fadima ta dube shi, "Kawai honey ka bamu mana, ni ga ma sayayyar da ke gabana na kayan baby." Ya dubeni, "Ke fa?" Na ce, "Ka kai Masallaci ko ka samu mabukata ka basu tunda Alhamdulillah mu muna cikin wadata." Ya yi murmushi, "To dama nima tunanina kenan, don haka zan bai wa masu bukata Zakka, sadaka kuma zan baku ku bada, ko cikin family dinku ko nawa."ta zobaro baki, "Kenan shawarata bata yi ba?" Ya ce, "Eh." Ta yunkura, "To ai da ba'a kirani ba." Ya ce, "Hakkinki na baki da ba sai na zo ba din, don nasan ita zata iya bani shawara ta masu ilmi." Kudi ya zube min dubu dari uku da dari biyar, wai in raba ma masu bukata. A zatonshi zan tafi da shi gidanmu ne in raba ma dangina, sai na tambayeshi zuwa kasuwa ya yarda. Ni da Ummi muka je. Shinkafa kawai na lodo da taliya sai kuma zannuwa, Ummi ta ce, "Aunty me zaki yi da shi?" Na ce, "Sadaka." Ta ce, "Don Allah akwai wasu dangin su Daada dake can wata ruga talakawa ne, jiya ma Abba ya aika musu da gero da sugar na kunun azumin." Na ce, "To." Daada din naje na samu na ce, "Sadaka zan raba ta abinci saboda neman falalar wannan wata, to ina so in cire na dangi na can Ruga shine nake so ki cire musu nasu sai na ba makota sauran." Ta ji dadi sosai, tayi ta shi min albarka, duk da ta san cewa shi ne ya bamu kudin, ta ce min ya shawarceta, ita ce ma tace yayi shawara da mu, ta ce ya ban kai dangina ba? Na ce, "Da ku da dangina Daada ai duk daya ne ba wani bambanci." Ta ce, "Allah ya shi min albarka. Ta cire musu sannan na saka 'yan samarin gida mua yi ta mika wa makotanmu wadanda ke da karamin karfi. Dama kananan buhuna ne. Lamido har kofata ya zo yayi min godiya tare da shi min albarka. Abubakar kuwa da ya dawo ya ga makota na ta mai godiya tare da addu'a sai kuwa kanshi ya daure, da yai zaton geron da Lamido ya raba ne, sai da ya je gurin Lamidon shi ne ya bashi labarin abin da nayi sannan ya ce, "Ka rike matarka hannu 2, don ka samu macen da babu irinta cikin yaranmu, Allah ya azurta ku da Yara masu albarka." Abubakar rungume ni yayi tare da min godiya na ce, "Allah shi ne abin godiya." Ashe zakkar shi can ya kai ma su Babana bayan ya dibar ma Innarmu. Shima bai fada min ba sai da Ya Umar ya kira ni ya fada min wai mijina ya kawo wa Baba zakkar kudi naira miliyan 2, Inna dubu dari biyar, in masa godiya sannan yana son mu yi shawarar abinda za'a siya. Na ce, "Yaya Umar ku nemi dan madaidaicin gida ka sai ma Baba kawai." Ya ce, "Nima haka na ce, kuma shima Baba zai so hakan. Allah ya saka masa da alheri." Na ce, "Amin. Kuka na saka da muka gama wayar, ban san ko kukan me nake yi ba, na farin ciki ne? na son mijina ne? na barin iyayena baya ne? Oho. Inna ma ta kirani ta ce in masa godiya na ce to. Da ya dawo kuka na sa tare da rungume shi, ya rude ya firgice yana tambayata, "Me ya faru D Only? Wa ya taba ki?" Na ce, "Ba kowa, na gode da taimakon da ka yiwa Iyayena, Allah ya saka makada alkhairi, Allah ya kara budi, ya tsare ka daga dukkan sharrin abin ki, ya kuma bani ikon binka sau da kafa." Ya shafa kaina, "Amin Masoyiyata, game da batun Zakka kuwa ba sai kin min godiya ba hakki ne na Allah na cire." Na ce, "To da ka cire din da kaga dama ai wani zaaka ba." Ya ce, "To shike nan." Da dare muna kwance ya ce, "Wai ya za'ayi da sayan kayan Sallanku? Kudin zan baku kuje kasuwa ku siyo?" Na ce, "A'a da kai zamu je saboda ka zaba mana son ranka." Ya ce, "Bari sai na ji ra'ayin Fadima." Ya janyo wayarsa ya kirata, "Sweet heart." Ta amsa da, "Na'am Sweet honey." Ina jin muryarta, don ina jikinsa ya ce, "Gobe zaku shirya ne mu shiga kasuwa tunda bani da aiki?" Ta ce, "To, daga nan sai mu siyo kayan Babys din tunda an ce mace da namiji ne?" Ya ce, "To sai ki shirya zamu shigo wuraren 11am saboda kada ki sha rana ko?" Ta ce, "To Honey sai kun zo." Ya ce, "Yauwa, ki shafa min Babys." Suna yin sallama na kankame shi, "Yan biyu zamu samu?" Ya ce, "Eh, dazun da ta dawo asibiti take fada min wai an ce 'yan biyu ne mace da namiji." Na ce, "Kai na yi farin ciki, ina son twins shi ne baka min albishir ba?" Ya ce, "Na same ki kina kuka yaya zan tuna da maganar 'yan biyu?" Na ce, "Allah ya sauke mana ita lafiya." Ya ce, "Amin, kema Allah ya baki ina son in ga kin haihu, duk wannan dina har yanzun ba ciki, ko dai zamu je asibiti ne?" Na ce, "Haba dai, duka yaushe aka yi abin? Ko fa shekara banyi ba." Ya ce, "Don Allah ki daina zancan nan, yara nake so sosai, yanzun kin ga zan fara da biyu na zo daidai da Kanina Usman, in kin haihu ko da daya ne kin ga na fishi ko? Balle ma kema biyun zan baki." Na ce, "Oh! Kai ne ma kake badawa?" Ya ce, "Allah ne zai bani ni kuma in baki." Na ce, "Dama kun gaji 'yan biyu ne?" Ya ce, "A family ni zan fara, shi yasa kowa ke doki, jiya kinga yanda 'yan uwa ke murna?" Na ce, "Ai abin so ne, Allah ya bamu masu albarka." Har zuciyata na taya shi murnna. Katon super market muka shiga, gefen zannuwa, lesuka da shaddoji zuwa yaduka, ya ce mu zaba, na ce, "A'a ka zabo mana." Sai cewa Fadima ta yi, "Ni zan zabi abina." Na ce, "To ni ka zabo min." Duk wanda ya miko min ko bata kamfanin ba amsa nake in ce yayi kyau. Ya ce, "To dama atamfa ce nake da irin wadda nike so, amma sauran zabi." Da muka gama sai na zabar wa Ummi atamfa da Shadda da leshi Rukayya ma haka. Daada kuwa yawan namu na daukar mata, ya bini da kallo itama haka ya ce, "Wannan fa?" Na ce, "Na su Daada ne, ta ce, "Su Daada ne za'a sai ma kaya?" Ya ce, "Shi ne ai, su Daada da ke da super market zuwa fa zasu yi kawai su zaba..........."....... Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sanadin Boko 4-06 Posted by ANaM Dorayi on 05:20 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na ce, "Za ka biya ko in biya?" Na fada cikin daure fuska, ya ce, "A'a zan biya in basu amsa ba sai kin san yanda zaki yi da su." Fadima ta ce, "Neman gindin zama." Ban ko kalle ta ba shima bai ce komai ba. Da muka isa gurin da ta sai Shaddoji da Yaduka sai na dibar ma Abba, ya ce, "Dama kin daina wahala na fa san ba zasu amsa ba." Don haushi ban kuma tanka su ba, don Fadi sai dariya take yi, ban fasa dibar musu ba, har turaruka na dibarma Abba, su kuma kayan shafa. Ita kuma muna zuwa gurin kayan Babys nan tayi ta jida, kowanne bibbiyu ni ko nayi ta taya ta. Da muka je gurin takalma da jaka na zaba musu. Da zai sai nashi na zaba ma Abba har huluna ya ce, "Ke baki san lambar takalma ka kina ta diba har da hula." Na ce, "Ido ba mudu ba ya san kima." Ita kuma ta ce, "In da rabon ka tafka asarar kudi ai shi kena." Ni sai na sharesu kawai na ci gaba da lamurana.Mun dawo gida cike da lodin kaya, but din mota shake, kujerar baya shake, da kyar na dan samu gurin rabawa. Dama hakima ta gaje gidan gaba, ita muka soma saukewa sannan muka wuce gida. Muka yi ta jidar kaya zuwa ciki, har lokacin fuskata daure saboda yanda yayi ta gwasale ni, don kawai na ce ya sayawa Iyayenshi kaya. Ba gidan zai sha ruwa ba yau, don haka ina yin sallah na kwanta sai bacci, ban san lokacin da ya tafi ba ma ni. Sai da ya dawo Asham sannan ya biyo gurina, ya samu ina sallar Asham din nima, ya zauna yana kallona. Na idar na gama addu'a ya taya ni shafawa na dube shi, "Sannu da zuwa." Ya ce, "Yauwa, na zo ne inga ko kin huce, naga yau an yi bacci an share ni." Na ce, "Ai bani fushi da kai Mr Cool." Ya yi murmushi na ce, "To yanzun dai sai na dauko maka ka kai musu." Ya ce, "Sai dai ki zo muje tare, dan kuwa ba za'a sace min gwiwa ni daya ba.Na mike na dauko hijabi zan sa ya ce, "Zo nan." Na zo ya dubeni sama da kasa, "Wai wanna kibar fa? Sama da kasa duk kin cika?" Na shafi kumatunshi na ce, "Ka iya kiwo ne." Na mika mishi ledar dan in bagarar da maganar, "Ga wannan mu je." Ni kaina na san cewa na yi kiba, cikina a kirji da hips ya tsaya, marata ba me cewa ina da cikin wata biyar da 'yan kwanaki. Duk a falo muka same su suna kallon Tafsir din Sheikh Amin Daurawa, na zube na gaishe da Daada da Abba, Ummi da murna ta hawo jikina, Daada na mata fada da fillanci. Rukayya ta tabe baki ta gaisheni a dakile. Abba ya ce, "Daga gida ku ke?" Na ce, Eh! Ya ce, "To sai ki basu." Na ciro ledar Daada na yunkura naje gabanta na ce, "Gashi in ji shi." Dama bana iya kiran sunanshi a gaban Iyayenshi. Ta ce, "Me muka samu?" Na ce, "Kayan sallah ne ba yawa." Na mika ma Ummi da na Rukayya sai suka hau murna, Rukayya ta daga kai ta ce, "Hamma ya aka yi kasan kalolin da muke so? Ni komai ja Ummi komai pink." Ya kalleni, Daada ma sai murna take yi tana fadin, "Allah ya shi maka albarka ya baka zuri'a ta gari wadanda suma zasu fita hakkinka." Ya dube ni na kauda kai ina fadin, "Amin Daada." Na mika ma Abba nashi wanda ke kallonmu yana dariya tare da fadin, "Masha Allah." Ya ce, "Har da ni? Ikon Allah Abubakar an yi hankali." Muka sa dariya. Bayan an nutsu ya ce, "Wato Hamma abin da yasa kaji na ce ashe kayi hankali shi ne, ka sani duk kudinmu muna da hakki a kanka, kuma na gode Allah ya kara budi." Muka ce Amin. Ya ce, "Ni fa da har ba zan sai muku ba naga kuna saidawa." Daada ta ce, "Don muna saidawa shi kenan bazaka fita hakkinmu ba?" Ya kalle ni, nayi maza na kauda kai don bana son ya ce nice. Abba ya ce, "Bari Usman ya zo ya kai ma telana su, don da su zan je Idi in Allah yasa mun kai lokacin." Haka suka yi ta shi mishi albarka, tare da yi masa fatan samun zuri'a tagari. Da zamu tafi Rukayya har mota, Rukayya ta ce, "Hamma Allah ya kawo mana 'yan biyu lafiya..." Muka ce Amin. Har lokacin wani gani-gani take min suka juya. Ko nisa ba suyi ba ya wani kankame ni ya rungumeni ya ce, "Na gode D Only, na gode da sani a hanya da kika yi, ni a zatona tunda iyayena suna dashi fiye da ni ba sai nayi musu wata hidima na sai dai in ma danginsu marasa shi daga ciki." Na ce, "Ko sune suke kera kudi wajibi ne ka basu hakkinsu, yi musu biyayya na san kana yi, yi musu alheri kai har abinci ya kamata ace duk wata kana sai musu ko buhu dai-dai ne." Ya ce, "Zan soma daga wannan watan Insha Allah, kai yau naji dadi ashe haka mutum ke samun farin ciki in ya faranta ma Iyayenshi?" Na ce, "Sosai ma kuwa.Ya ce, "Na gode Allah da ya bani mace ta gari, yanzun fada min bayan su ko akwai wadanda ya dace in sai ma kayan Sallar?" Na ce, "Su Lamido da duk kanne da yayin Babanka, ka sai musu kowa wanda ya dace da shi zasu ji dadi."ya ce, "To gobe zamu koma kasuwa kenan." Haka ya kaini gida yana ta shi min albarka, sannan ya tafi gidan Fadima ya kwana. Washegari mun shiga kasuwa harda list din mutanen don kada a manta, lallai kudi sun mutu a ranar, alheri sai bawa ya dage, amma in kayi dadi ka ke ji, shi kuma wanda ka wa yana jin dadi. Ya ce, "To wanene zai kai musu?" Na ce, "Ka samu Hashim ka ware rana kayi ta kai musu." Da suka dawo kuwa Hashim sai labarin yanda Iyayen suka yi ta murna da godiya ya ce Abbanshi, Sarki kenan, har gori ya mishi ya ce, "Hashim kalubalenka, sai ayi koyi da Hamma." Na yi murmushi, na san kowa zai yaba don kaya ne na alfarma da takalma da hula. Hashim ya ce, "Allah ya nufe ni nima." Ranar ma godiya yayi ta min, su Lamido ma suna ta shi masa albarka, wanda ma baya nan in ya dawo gida ya gani sai ya kira waya yana sa albarka. Allah kasa mu dace amin. Saura sati biyu Sallah Abubakar ya ce min yana son ni da shi mu tafi Umara, don haka ma in tashi muje inyi fasfot. Na ce, "A'a da Fadi ya dace kuje." Ya ce, "Ba zata iya zuwa ba." Na ce, "Ina tsoron abin da zai ja min bakin jini cikin zuri'arku, amma ka je ka shawarci Daada." Ya ce, "Shi kenan" Ko da ya samu Daada da batun sai ta ce mishi ya bari mun je aikin Hajji dukkanmu, kada ya zama abin tsegumi ace ya kai bare, amma Hajji kafin lokacin ta haihu. Ya dawo ya ce min bakinku yazo daya da Daada. Na ce, "Ka gani ko? In kaje ka samu a addu'a." Ya ce, "Wannab ba sai kin roka ba. Ni dai na so inje da ke ne saboda mu dan shakata." Na ce, "Wata rana zamu shakata. Koda yanzun ma ai mun sha iska." Ya yi 'yar dariya.da xai tafi ya bar ma kowa komai, na ce xan je kaduna da salla, ya ce a'a in bari ya dawo ma je tare na ce to.su Ummina sun xo min da salla har da Yaya Umar, nayi murna sosai kwanansu 2 suka tafi da Shadad, na ce su bar min Ummi in xamu xo sai mu xo da ita. Bayan sallah da kwana 3 xaya dawo,nasan kuma gidana xaya sauka, domin yana fada min irin yadda yayi missing dina,ko na ce muka yi missing din juna.Tun safe na soma shirya masa girki kala-kala da abin sha, jus nayi mas kusan kala 3 n akuma hada nawa hadin mai kyau nayi ta sha tun safe.misalin 3 ina tsaye gaban madubi nayi adona ckn 1 daga ckn atamfofin daya siya min,sam banji shigowarsa ba,sai dai ji nayi an rungeme ni ta baya kamshin turarensa yasa na gane mijina ne.da sauri na juyo muka makale juna cikn murna, ya sumbaci lebunana, sannan ya ce bari mu isa gidan Fadi, sai in dawo. In na xauna ba xan iya tafiya ba.xamu wuce ne da Hashim daya dauko ni naga ba xan iya wucewa ban ganki ba,na ce to in ka san ba xa ka dawo ba to ka wuce da abinci.Cikin marairaita nayi maganar,ya shafi kumatuna. kada ki damu d only yanxun xan dawo naji gidan na kamshi na ce to "Da sauri ya shige mota suka tafi.kafin ya dawo na kara gyara gidan, na canza kaya doguwar rigar leshi nasa mai kalar sky blue, su hudu suka shigo duk da Hashim.na jera musu abinci da na sha, in adaga daki ina jiyo su suna santi.Hashim ya ce, Hamma gaskiya xan kullo ma Hafsat kawance da Shatu, ina son taxo ta koyi kalolin girkin nan, Dayan ya ce na riga ka a xuci ka riga ni a baki, shi ko dayn ba shi da mata, cewa yayi xaya kawo budurwanchi ta yi hadda.shi kuma Abubakar sai murna da cika baki. fadi ya ke "Matata yar baiwa ce, duk abubuwanta cikin ilimi ne da daraja girkin Hafsat daban ce.Amma fa ba xa ku takura min mata ba, da Ummi taxo tana kwashe kayan bayan sun gama,Hashim ya ce ko dai xan tsaya nan ne Hamma ka tsaya min a bani wannan in kiwatat?Abubakar ya ce "Katon banxa wa xai baka?suka sa daria.Misalin karfe tara saura muna ta shirin kwanciya, Fadi ta kira shi ya daga ta ce"sweet hrt ba nan ka ke ba?ya ce "In ji wa?ta ce Eh!! mana yi lassafi.Ni dai wlhy kada ma ka ce xaka kwana can, don ba xan yafe ba.Duk ina jin su, kuma ba gidanta xai sauka ba, saboda randa xai dawo gidana ya tafi.Na ce to koma can din , ya ce ba xan koma ba, tana xaton ban san me nake yi ba?ya share ta muka ci soyayyarmu, dama mun yi rashin juna.Wata juma'a misalin 3 muna cikin bacci wayarsa ta soma kuka, ni ce na farka na daga.Sweet hrt na gnai a jiki na daga, Muryar Goggo Jami naji tace, "Ina Hamma din?N ace "yana bacci "Ta ce to tashe shi Fadi bata da lfy shi bacci ma yake?a raina nace kada yayi? Namatsa kusa dashi na shafa fuskarshi, ya rike hannuna zuwa kirjinshi, nayi masa rada cikin kunne. Mr Cool ka tashi yau twins zasu fito, Fadi zata haihu." Firgigit! Ya mike ya zura jallabiyya ya dauki key din mota. Na ce yanzun zaka fita?" Ka bari a kira Sallah." Ya ce ba komai kada ki damu, na ce to Allah ya raba su lafiya." Ya ce "Ameen the only." Takwas na safe na kira shi, ya ce har yanzu dai shiru, na ce gani nan. Na isa gurin na samu 'yan gidan su, sai su Rukayya. Shi kuma can na hange shi tare da su Hashim da Usman kaninshi. Na gaida su Goggo Jamin, sannan na nufi gurinshi. Rukayya harda cewa 'yan biyun nan suna ba mamansu wahala, Allah yasa kada zuwan wasu yasa abin ya sake rikicewa. Wata da ban san ko wacece ba, ta ce ai mun rike Allah, kuma sai ta sauka lafiya da izininshi. Ban da lokacinsu bare amsarsu, don nasan dani suke, gurin mijina ma ni na nufa. na dube shi har yanzu ko? Na yi maganar ne cikin nuna tausayawa da tausasa murya. Ya ce, wallahi, na matso na kama hannunshi na dama na matsa kadan. Ka da ka damu samu ruwa a tofa mata addu'a, In shaa Allah zata sauka lafiya. Goran Ruwa ya kawo na karanta mata, YA HAYYU YA KAYYUM, YA ZULJALALU WAL IKRAM, BIRAHMATIKA ASTAGISU, sau bakwai na ce ya bata tasha. Da kanshi ya kaimata tasha, ya fito, ko minti ashirin ba a yi ba Nurse ta fito da murna tana fadawa su Goggo Jami ta sauka. Kawai sai naji mutum ya rungume ni a bainar jama'a yana fadin "Alhamdulillah." Usman ya ce "Aunty na Allah ya amshi Addu'armu, sai dai kuma me? Maimakon biyu sai aka fito mana da yarinya katuwa mai kyau. Sai kace mamanta tayi kaki, aka amsa da murna ana cewa ina dayan? Wannan ce Hassana kenan.Nurse ta ce ai daya ce, ita kenan aka haifa. Yanzun haka mai jegon ana gyara mata jiki. Gaba daya sai naga jikinsu yayai sanyi, har shi kanshi angon karnin. Usman ya ce amma 'yan asibitin nan sun cika shegiyar karya, shine suka ce biyu? Doctor ya fito, su Hashim suka bishi suna tambayarshi, "dama daya ne? Ya eh ai dama daya ce duk scanning dinta bai taba nuna biyu ba, wa ya ce biyu ne? Abubakar ya ce "ita ce" likita yayi tsaki ya ce "haka wasu matan suke yi ban san amfanin hakan ba, alhalin sun san cewa akwai ranar irin wannan da za a kure su. Ya dafa kafadar Abubakar "kada ka damu, ka yiwa 'yarka addu'a Allah yasa mai albarka ce." Duka suka ce "Ameen" Masu habaici da rawar kai kowa dai baki tsuu, shiru kake ji. Kullum nake zuwa gidan mai jego har ana jibi suna. Ranar da ya kawo mata zannuwan fitar suna ta ce basu yi mata ba, ranar ce ya amayar mata da takaicinshi a gaban 'yan koran nata. Ya ce "ki bini a sannu, banza makaryaciya, zan maganinki, kuma in na dawo baki dauki kayan nan ba sun zama ba rabonki ba. Ki sani ko bari kika yi zan so shi, bare dan mutum. To meye ribar karyar da kika yi kika sa muma muka yi? Mutuncin ki ya zube a gurina da sauran mutane. Sannan baki isa ki juya ni ba, kinfi kowa sanina. Zata yi magana ta rike kugu, ya ce yi min shiru, in kin furta wata magana zan bata maki yanzun nan. Ta yi tsit, ya fice. Nan ta shiga kuka suna bata hakuri, Rukayya tana cewa sai ta fadawa Dada da Abba. Yarinya taci suna Nana Fiddausi, in da ni kuma na shiryawa Abubakar kalolin girki kusan bakwai da kayan drinks. Suka yi walima, Ummi da kanwata Ummi sune yan taya aiki. Bayan suna da sati daya muka je Kaduna don maida Ummi tare da dauko Shadad daga gurin babanshi. Har da Umminsu ta mana rakiya don sun kulla kawance da Umminmu,saboda xaman mota sai kafafuna suka kumbura,sannan nayi ta shar amai,duk Abubakr ya rude hankalinsa ya tashi.kafin kace haka na kwana shrkaf.muna isa kaduna asibitin Garkuwa ya wuce dani, da gudu-gudu aka kawo gadon tura mara lafiya aka yi ciki dani,likitan yana duba ni yana mishi tambayoyi,tana da ciki ne?ya ce kai bana xatao, sai dai ko in yanxun. likitan ya maida allurar da yayi niyar yi min ya aje,yasa aka tura ni xuwa dakin scanning, kusan min 30 aka fito dani yaxo ya dauko ruwa aka yi wasu allurai a ciki, sannan aka dora ni ,ana da nan bacci yayi gaba dani,likitan ya kalle shi"matarka tana da ciki kusan wata 5 ko ma fi,sai in ta farka nayi mata wasu tambayoyi tukunna. Abubakr ya tsura mishi ido,kace tana da ciki wata 5? likitan ya ce kila ma ya fi. Abubakar dai yayi shiru,amma ba don ya yarda ba, ya kira Umar ya fada masa kusan minti 30 suka iso dasu Baabah.Sannan ban tashi ba, ya ce don Allah yaya umar ya kai su Ummi gida don suna ta kuka,kujera Abubakr yaja ya xauna ya rike min hannu su Baabah sai waje suka fita don kunyar yanda ya tasa ni gaba kamr xai cinye ni.ya kira su Hashim ya fada mishi su Daada ma ya sanar da su,kusan wa daya na farka.Da sauri ya tashi yasa hannunshi a kuskata, yana cewa "Sannu Hafsat sannu.Na ce yauwa Na yunkura xan tashi ya kama ni na xauna ya xauna gefen gado. Ina ne ke miki ciwo yanxun?nace "Ba ko ina yunwa nike ji, bakina ya cika da miyau,na ce xan xubar "ya miko min wata yar tasa sannan yace bari in kira likitan.Da sauri ya fita ya ce ma su Baabah na farka, suk shigo suna min sannu, na amsa na ce ni babu gurin da ke min ciwo,yunwa kawai nake ji (dama cin abinci a gurina tun dana samu cikin nan kmr gara)suka shigo da likitan aka ce su fita Abubakar kuwa xama yayi kusa dani likitan ya ce "Madam cikinki wata nawa ne?Da sauri na kalli Abubakar sannan na sunkuyar da kai.Ya ce "Fada min mana "Na ce na zaton cewa xai kai shidaa."Abubakrya dago idona ina da yaro dan wata shida a gurinki, ina me ban sani ba?likitan yayi daria,'kila tana son ta baka mamaki ne ko?na ce"Ina son in ci abincin. Da sauri likitan ya ce me xa ki ci?na ce "Tea xan sha.Nan da nan yayi waya a kawo min tea.Abubakr kuwa cikin rigata ya xura hannu yana shafa cikina yana min magana a kunne."d only me yasa kika rufe min?na ce To kana fama da mara lfy sai nima in kwanta mu taru mu daga maka hnkl?Ni ba xan iya ba, bana son in ganka ckn damuwa,shi yasa na daure. ya ce "Allah yi miki albarka, dama nasan kece mai son kwanciyar hankalina. bayanna huta ya sallame mu muka nufi gida sai yau naga gidan da aka sai masu Baba a nan dai Abuja Road din ne amma can kasa gurin sabon guri ne kuma gida mai kyau flat. .. Abubakar kam da ya fita sai ya je ya kama masauki, sai dare ya dawo. Ya ce na zo muje, bansan ko ina bane na cewa su Baba ina zuwa. Sai kurum ya kaini masauki, wai nan zamu kwana, na ce "Haba Mr Cool, ka maida ni gida mana su Baba zasu ga rashin kunyata." Ya ce, "Bazan iya barinki ba, bakiji Likita ya ce na kula dake sosai ba?" Sai waya nayi wa su Baba na ce munje gidan wani abokinsa can zamu kwana. Suka ce to, kwanan mu uku, kullum da safe zai kawo ni amma da dare zai zo ya tafi dani. Wata sabuwar soyayya da tarairaya Abubakar ya soma yi min, da zamu koma gida jirgi muka bi. Muna isa ya fara yadawa ina da ciki, dama Likita yace in mun dawo na soma yin awo. Shine ya kaini asibitin ya yankar min kati, a dakin scanning Likita ya ce "Madam kin san cewa 'yan biyu ne?" Na zaro ido "'yam biyu?" Ya ce "kwarai kuma kin gansu duk maza" Na ce ba a fi sati daya ba da akayi min scanning a Kaduna ba a fada min haka ba." Ya ce to yanzun dai gashi nan" na ce to don Allah ka taimake ni kada ka rubuta a cikin sakamakon" Ya ce "don me?" Na ce "Don haka ta faru ga kishiyata, a karshe sai ta haifi mace guda daya."............ Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sabadin BOKO 4-07 Posted by ANaM Dorayi on 05:21 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Ya ce to shike nan, ya rubuta komai lafiya amma bai rubuta mace ko namiji ba, bare ya saka 'yan biyu.haka naci gaba da samun kula, yanzun da asiri ya tonu sai cikin ya fito yayi rum. Da da ba a sani ba kuwa lakwam, har cikina ya kai wata takwas ban taba yi masa batun kayan haihuwa ba. Shi ne da kashi ya ce "wai the only baza mu sayo kayan haihuwa ba? Na ce to, sannan muka je ni da shi da Ummi. Wata safiya na tashi da matsanancin ciwon ciki da mara, gashi ya je Lagos amma ranar zai dawo. Da ya kira duk da koakrin da na ke na nuna masa bani da wata matsala sai da ya gane. Ya kira Dada ya ce a zo a duba ni lafiya? Ummi ce ta zo har ta tafi ban bari ta fahimci wani abu ba, tunda ciwon yana yi ne yana lafawa. Kafin dare na jigata, lokacin da ya shigo fayata ta fashe haka suka kwashe ni zuwa asibiti. Da Lamido na fadan me ya sa naki fadin banda lafiya, sai su Gwogwal suka ce ai kunya ce. Lallai ni yar mutunci ce, ni ba fulani ba amma ina da kunya. A raina na ce kunya ai ta dan sunna ce bata Fulani ba. Don haka duk Musulmi mai Imani zai zama yana da kunya. Da kaina na haihu, dana kato zuwa can kuma sai sabuwar nakuda, sai kuma ga wani dan. 'Yan biyu masu kama da juna, sannan duk wanda ya kalle su yasan 'ya'yan Abubakar ne. Tunda Nurse ta kawo na farko Abubakar ya ke ta murna da su Hashim, sai ta ce zaka bani goron albishir ina zuwa. Da tazo da dayan sai suka kama murna, kafin ka ce haka, dangi sun cika asibitin harda su Rukayya. Ni dai na ga lele, Fadi ko leke don ko da ta sami labrin ina da ciki bata zo ba. Lamido har asibiti ya zo, kwanana daya aka sallamoni zuwa gida. Tun a ranar Lamido yasa aka kada Sa aka yanka, nima yan uwana washe gari suka zo tare da su Rahma. Abubakar tamkar ya goya ni don kauna. Ranar suna kuwa fadar shagalin da akayi bata baki ne. Kyauta dai mun samu Masha Allahu, nayi kyau mai zane fulawa ta yarfa min nayi kyau har na gaji. Mun sha hotuna, Abubakar kuwa da abokansa tare akayi suna dasu. Na cii gaba da shayar da yarana kuma ana basu madarar M.S.A, suka yi tubarkallah. Mijina kullum kara son mu yake. Fadi kuwa na sama kanta damuwa, kullum ita kenan fada da miji ko a gaban waye sai tayi ta karta masa rashin mutunci. Yanzun ma sun raba jiha da Rukayya, dangin mijina tamkar su cinye ni don so. Tunda na gama service na samu aiki a gidan TV na Yola, amma Abubakar ya ce sai yara sunyi kwari. Ban ja musu ba, watansu shida na soma zuwa aiki na, bayan ya mallaka mana mota ni da Fadi kowa da tashi. Bani da matsalar rainon yarana don rubibinsu ake yi. Account na bude ina zuba albashi na. Domin akwai burin da naci dasu, tunda ba abindana nema na rasa. Daidai da katin waya sai Abubakar ya zuba min dubu biyar dubu goma, nayi kyau da ka ganni kaga matar so. Gyaran jiki kuwa da sabbin girki ba a magana. Shi kanshi mijina duk wanda ya kalle shi yasan matarsa tana son shi. Kusan in mutun yana cikin kwanciyar hankali daka kalle shi zaka gane, musamman namiji. In kaga namiji a hargitse a rame ton ba halittarsa kenan ba to kila bai dace da mata ba. Duk ranar da babu aiki na kan ce ya kawo min Nana Fiddausi, ina son yarinyar don ina son mace. Fadi bata son ya kawo mata 'yarta gurina. Amma bayanda zata yi, tunda baza ta iya hana shi daukar 'yarshi ya fita da ita ba. Sannu a hankali rayuwa tana tafiya kwanukan mu suna karewa, lamurra suna canzawa. A hankali na rika dora mijina kan hanyar taimako dukda cewa yana yi dama. Lokacin da ya gina sabongida Lamido yace ya saka ni a ciki saboda ya yarda ni na zama daya daga cikin zuri'arsu. Na cancanci in sakata in wala a zuri'arsu, komai sabo ya saka min, gado dan italiya, kujeru na alfarma, kayan kicin na gani na fada. Itama ya sa aka mata fenti ya canza mata kayan daki.Nayi walima ta alfarma har su Rahma sai da suka zo, gidan ya tsaru harda gurin wasan yarana. A ranar farko da zamu kwana a gidan yana zaune yana waya a bakin gadon dakinsa na alfarma. Na shigo sanye da kayan bacci, da hannunshi ya nuna min cinyarshi in zauna, ya ce "Alhamdulillahi, gida ya dace dake." Na ce yanzu saura ka gina dakin Allah (Masallacin Juma'ar) ungwar nan ka sabunta shi. Sannan ka gina wanda za a dinga kamsus-salawati, a wannan layin da muka dawo. Ya ce "an gama gimbiya, yanzun sai ki zabi wanda za a ba kwangilar ginin." Na ce duk wanda ranka ya kwanta dashi. Mai amana." Ya ce "To zan duba." Hakan ce kuwa ta faru nan da nan aka soma gini. Taimako marasa lafiya, gajiyayyu da marayu duk na kwadaita masa yasan zakinsu. Yana mutunta iyayena tare da taimaka masu. ********** Shekarar yarana daya da wata biyu, naji ban gane kaina ba. Hankalina ya tashi matuka. Ranar Abubakar yana gidan Fadima, na mashi text cewa zanje asibiti, ya ce Hassan ne ko Hussaini ba lafiya? Na ce "Ni ce" ya ce sai ga kiran shi, ya ce meke damunki the only? Sai kawai na saka kuka na kashe wayar.Minti ashirin sai gashi ya zo. Kayan bacci ne ma a jikinsa, me aiki na ya samu tana kara goge kicin. Ya ce "ina take?" Ta ce ina ciki sai gashi na tasa 'ya'yan idanuwana jajir, ya ce wai lafiya? Na soma sabon kuka, ya zauna ya jawoni jikinsa yana lallashi na, wai in fada masa meke damuna? Na ce nifa banga al'adata ba, ya ce ban gane ba? Na ce ina da ciki ne fa gashi kuma ban yaye su Hussaini ba. Sai naji ya hau fadin Alhamdulillah, Allah ya amshi addu'ata, don Allah wannan karon ma don Allah twins, na harare shi banfa yaye yarana ba. Ya ce goben nan za a yaye su, na ce tab! Wata ashin da uku fa zasu yi. Ya ce "in basu yi kani ba ba?" Na ce ni dai zanje a bani magani." Ya fita ya ce "Me kika ce?" Nan take ya hada girar sama da ta kasa. "To shike nan kije ki cire" ya fita washe gari na tsi da amai, na sheka shi har na gaji. Nayi ta kuka karshe na kira Rahma na fada mata, ta ce lallai Hafsat samun guri, ni yanzun dakyar na samu Allah ya bani kinsan dai yawon asibitin da nayi. Amma yanzun don Allah yayi maki kyauta shen zaki butulce? To kiyi kokari ki batawa mijinki rai. Sai ta kashe wayarta. Ina kwance jikina zazzabi yaran nata kuka ko wanka ban masu ba. Ranar shine yayi masu wanka ya shrya su, sannan ya zuba su cikin mota da abincin su, sai gidan Dada ya ce mamansu bata da lafiya ina ga ma yaye su za a yi, ta ce me yake damunta? Kai tsaye ya ce ciki ne, tana can tana tana ta kuka ma. Ni dai na kawo su zan kawo kayansu. Dada ta ce to Allah ya bata lafiya. Gidana ya dawo yayi ta lallashi na. "Haba Hafsat, ke da nike kallonki mai ilimi da sanin yakamata? Bai dace kiyi irin wannan tunanin na jahilai ba. Kinsan matsayinki a gurina? Duk yanda kike tunanin matsayinki ya wuce haka a gurina. Kada ki zubar da kimar ki a idona, ina alfahari dake, kuma yayin da kike haifa min 'ya'ya lokacin ne nake kara so da kaunarki." Kunya ta kamani, lallai naso nayi wauta. Yanda mijina ke nuna min baikamata inyi masa haka ba. Ni da na kasance mai bada shawara ba girmana bane in yi haka, don haka sai nace kayi hakuri Mr Cool. Tausayin yaran ne." Ya ce "yanzun ma kayansu zaki hada suna gurin Daada, mu kuma sai muyi rainon wannan ko? Na ce ya zaka kaima Daada aiki, kasan fa barna suke dashi." Ya rike tafin hannu na ya ce "ni suka biyo Dada ta ce lokacin da ina yaro nayi barna, ai kin san kuma ga Ummi ga Rukayya ina kaisu kowacce ta zabi nata, na ce Allah ya raya su." Fadi taji cewa an yaye twins sai ta zargo ko ciki ne dani, don haka hankalinta ya tashi. Har gida sai gata da yake bata taba zuwa ba, tayi ta bin ko ina da kallo, sannan daga bisani muka gaisa. Na ce "Maman Nana yaune kika taba zuwa gidana." Ta ce "to bama zama ko nazo kina gurin aiki, nima haka." Na ce "Amma koda dare?" Ta ce "da dare kowa ya gaji, yanzun dai ba gashi nazo ba." Na ce to na gode" ta ce "can naga su husaini a gidan Daada, wai an yaye su, na ce me ya jawo maki yaye yanzu?" Na ce Abban su ne ya kwashe su ya kaisu. Ta tabe baki lallai sweet heart shine lokacin da zan yaye Nana ya hau yayi ta fada. Na ce to ai kinga ita mace ce, dole ya tausaya mata, ta ce kodai kin sake kunsar wani cikin ne? Na ce to inma hakan ne meye aibu tunda mijina na so? Ta ce kedai fadi gaskiya, kina son kiyi ki cika gida da yara saboda kiyi gado." Ta mike tsaye, "kiyi haihuwarki a sannu dan mu mungaji kudi, so kinga banda matsalar su. Na ce gaskiya ne baki da matsalar kudi, shi yasa na ganki zaune a gida bakya zuwa aiki, sannan suna nan cike da daki a gidanki sai dai ki bude ki diba. Ta ce "inma kina yi min ba'a ne nasan dai na fiki." Ta fita fuuu, na ce "sauka lafiya." Tare muka je asibiti dashi, inda likita ya gwada ni ya tabbatar cikina wata uku. Kuma lfy lau, sai murna gurin mijina. Munje Umara tare harda ita, haka nan aikin hajji lokacin cikina ya tsufa. Mun dawo bada jimawa ba ba haihu, 'yar budurwa mai kyau, tamkar inyi tsalle don murna. Ina son 'yar budurwa, itama anyi sha'ani, don lokacin Abubakar ya kara zama (Don). Yarinya taci sunan Daada, Abubakar yace ya yarda in kana taimako Allah yana taimakonka. Budi ta ko ina, sai yanzun na binciki kudin account dina, lallai kudi wawaye ne, in da zaka tara su zasu taru, don haka na kuduri niyar yin abinda zanyi dasu. Kaduna naje yawon arba'in, na dauki babana na kaishi aka yi masa hoton fita, wato international passport. Lokacin aikin hajji kuma na biya masa. Abubakar ya fara min fada wai yana cikin lissafinshi a bana zai biya masu. Na ce yayi hakuri alkawari na dauka, SANADIN BOKO sai na kaishi makkah. Ya ce "Allah ya biya ki" shi kuwa baba da na fada masa na biya masa kujera da kudin aikina sai ya sa kuka. Ya ce gashi SANADIN BOKON nan da nayi ta tsana zanje daki Allah, inda ban taba zaton zuwa ba. Ki yafe ni Hafsa, tuni na gane boko ba dukka ta ba ce illah, tana da amfani." Ya ci gaba da cewa Hafsa na gane hakan ne ta hanyar taimako da wata likita mace tayi ta mun lokacin da na kwanta a asibiti. In shaa Allah su Ummi zasu yi karatun boko, dama dai na addini wajibi ne, zan bisu da addu'a Allah ya tsare su yasa su sami ilimi mai amfani. Ya raba su da sharrin ko hadarin da ke cikin boko, na ce ameen Baba. Ya ce in da zaki yi adalci Innar ki ya dace da wannan kujerar, don ita ce tasha wuyar iliminki." Na ce "ita ma Abubakar ya bata kujerarta da Yayana Umar, kai nidai na gode Allah da nasha wahala yanzu kuma ina cikin gata. Wata rana na matsawa Abubakar muje katsina ina son in sami labrn yaron dr Hindu da yake munsha zuwa gidan nasu lokacin tana raye. Sai ban sha wahalar gano gidan sosai ba. Cikin sa'a ma yaron an kawo shi hutu. Duk sunyi girma, naji dadin ganin su, na karbi adireshin dinsu na Abuja. Nasha alwashin zuwan sannan nayi masu kyauta mai tsoka. A kwana na biyu na nemo Asabe tayi aure da yaranta biyar. Sai dai gaskiya basu dashi, na taimaka mata sosai. Ta ce min tana son zuwa gurin yarta tana tsoro, na ce zanje mata. Wata rana munje Kano Rahma ce tayi haihuwa ta biyu muka je, daga nan ta tambayi inda zan sami hajiya Mairo, Da dare naje gidan bayan isha'I cikin shiga ta alfarma da dankareriyar motar mijina. Da kima ta marabce ni domin tasan daga ganina taga matar gwaska, falon alfarma ta kaini muka gaisa bayan an cika teburin gabana da kayan shaye shaye. Ta ce ban gane ki ba, na eh baza ki gane ni ba daga Yola nake, ni 'yar uwar Asabe ce wadda ta taba maki aiki kuma take da da tare da danki mai sunanki, shine nazo na ganta." Ta ce Allah sarki sai ta soma kuka, na ce "lfy? Ta ce ai dan tilon dan nawa tuni ya mutu, tunda ya dawo daga kasar waje ba lfy inda yaje karatun boko." Na zaro ido "shima sanadin bokon ya rasa ransa?" Ta ce wallahi yar nan can abokai suka bashi wata kwaya mai karfi yasha. Tunda ya kwanta tashin da bai yi ba kenan sai a kiyama." Na ce tabdijam, yanzu ina ita takwarar taki? Ta daga waya ta kira wata tace jeki ki kira min Ummi, ta dube ni yanzu ita nake gani naji dadi. Kinga da na salwantar da yarinyar nan da nafi haka bakin ciki."yarinyar ta shigo cikin kayan bacci, mai kyau da ita, girmanta bai wuce na shadad ba, na rungume ta ina murna. Na ce Allah ya albarkace ki. Hajiya ta ce ameen, na dubi haji kada a barta ba ilimin addini, domin inda addini, boko bazai batar da bawa ba sai wanda ya batar da kansa. Ta ce haka ne 'yar nan ai naga darasi, in sha Allah yarinyar nan zan mata tarbiya irin ta addini,na ce Allah ya sa. Na kawo kudi na bata na ce ki sayi sweet sannan na amshi lambobin wayar su na ce zan ba mamanta. Nima zan dinga kira muna gaisawa, ta ce don Allah ki kaima uwar tata don ta zo ta ganta. Na ce in shaa Allahu ***************** Rayuwata ta zama abin sha'awa a idon wadanda zuka kyamace ni da. Duk wanda na sani taimakonsa nake yi. Mun sami daukaka ta fannoni da dama, 'yan uwana suna hutawa a dalilina. Abubakar yasa na bar aiki na koma makarantar jami'ar Yola, hatta kishiyar mamana sai da Abubakar ya bata kujera. Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100 Sabadin BOKO 4-08 Posted by ANaM Dorayi on 05:28 AM, 29-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Taimako kuwa a danginsa duk me son wani abu da ya same ni an gama. Fadi ta sakar min ragamar uwar gidanci, kuma na rike, 'yan uwanshi tamkar nawa na rike su. Iyayenshi kuwa tamkar su suka haife ni. Bikin Rukayya ya taso, ta zo ta same ni, ta ce "Aunty dan Allah ki ce ma Hamma kayan kicin dina ina son a sayo min a Dubai." Na ce "an gama" ta ce "Na gode" guri aunty Fadi ta soma zuwa, ta ce duk kayan kicin din kasar nan zan ce sai waje?" Na ce kada ki damu zamu je" Da asuba ni da shi muna kwance cikin bargo ranar asabar ce bashi da aiki, nima ba makaranta. Na ce "Ga biki na zuwa Mr Cool me muka shirya ne? Ya ce to ya za a yi?" Na ce zamu je Dubai sayen kayan kicin" ya ce keda wa?" Tunda kinga aiki yamin yawa yanzun?" Na ce "zamu da Rukayya da Ummi" ya ce "To yaushe?" Na ce zamu shrya" Na yaye baby na gurin Daada na bar su muka tafi Dubai.Mun yo sayayya ta gani ta fada Daada sai shimin albarka take, biki kuwa nice uwar biki, hatta Daada dani take shawara, matan Usman da umar ma suna bina a matsayin matar wan mijinsu. Fadi sai ta koma baya a wajen bikin. Mun kaita Abuja, dan Baffa na abuja ta aura, Ummi kuma Kabir take so kanin Hashim, Umminmu tazo bikin Aliyun su abubakar ya ce yaga mata. Su Daada suka ce koba 'yar uwata ba indan na santa to sukam sun amince. Nidai murmushi nayi tare da godewa Allah. Ina kicin ina hada Zuma ta amfanin kaina Abubakar ya shigo, the only yaufa zamu fita ne. Zuwa ina? na tambaye shi. Hutu na samu na wata daya zmu tafi Abuja, daga nan mu wuce England" Na ce "kana dai sane bani kadai ba ce ko? Ya rke kugu, to nidai dake zani, na ce a'a kayi kuri'a kuma in tafiya ta fado kaina saudiyya zamu. Ya ce "to shike nan, yanzun ya zanyi da maganar kuri'ar? Kayi rubutu a cikin takarda guda daya sauran kuma ba rubutu ka bamu mu zaba, wanda ya dau mai rubutu tafi dashi zaa yi. Kuma kayi tskani da Allah, da ya samu Fadi sai ta ce ita ba inda zata tabar aikinta. Saudiyya muka yada zango, muyi soyayya muje ka'aba munyi addu'a. Nidai yanzu duk abinda nake so a duniya na samu, saura lahira kawai nake rokon Allah ya bamu, kasa Aljanna ita ce makomarmu gaba daya da dukkan musulmi. Ameeen TAMMAT BI-HAMDULLAH! Taku har kullum Halima Abdullahi K/Mashi. ******************************** Alhamdulillahi dukkan gogiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da ya bamu ikon kammala wannan littafi SANADIN BOKO, tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Shugabamu Annabi Muhammad SAW, Allah yasa mu amfana da darasin da yake ciki. Godiya ta musamman ga marubuciyar wannan littafi Halima Abdullahi K/Mashi Inna godiya ga dunbin mabiyana ta blog,pls kidinga kokarin yin comment ta yanda lallai zanfagimci muna tare Zaharaddeen Shomar whatsapp 08168575100