🕊 *KAINUWA* 🕊 _........Dashen Allah_ *Haske Writer's Association* *Na Ayusher Muhd🤸🏻‍♂* *Bismillahi Rahmani Rahim* _All character and event in these novel are Fiction_ May Allah guide us through the right path (Ameen). _Godiya ta musaman ga masoyana, ina godiya da alfahari daku nagode kwarai da gaske._ Aunty Nah Hafsa Khabeer (Aunty Goggo) Allah ya kara kareki ya biyamiki bukatunki (Ameen) *1* *The year 1970* Gida ya cika taf da mutane duk inda ka duba wasa ake yi, wasu na wasan dokuna wasu na wasan shad'i wasu busa suke yi, wasu waka suke yi, haka wasu wasan kidan kalangu sukeyi. Hidima dai kala kala irin ta wasan ninmu na hausa na da, kowa ka gani fuskar nan tasa a washe take alamar farin ciki. Bayi sai murna sukeyi dan irin wannan sha'ani shi ke sa su su fito haka, maroka sai tasu hidimar suke yi. Gidan sarauta na kasar zazzau kenan wato Zariya. Zazzau na daya daga cikin manyan masarautu a Najeriya. Masarautar taci kasashe da dama da yaki, Girman kasar Zazzau ada ta kai har Suleja a Jahar Niger. Masarautar Zazzau ita ce tafi kowace masarauta a yankin Afrika ta yamma yawan makarantun zamani da na addini, shiya sa ma ake mata taken Zazzau, birnin Ilimi. Zazzau yana d'aya daga cikin Hausa bakwai wanda Bayajidda ya kafa, gari ne na sarauta. A wannan shekara ta Alif dubu d'aya da d'ari tara da saba'in karni ne na sarautar Abdulsamad wanda ya kasance d'a ne ka AbdulJalal wanda ya mulki kasar shima ta gadon mahaifinsa. Abdulsamad yana shekara 20 kacal aka daura shi akan mulki sakamakon rasuwar mahaifinsa, suna da yawa a gun mahaifinsu sai dai shine ya kasance d'an sarauniya Kubra sannan yaro ne mai hankali hakan yasa mahaifinsa ya bada wasiyyar shi yakeso a nad'a. An aura ma Abdulsamad mata a wannan lokacin wace ta kasance 'ya ce ga waziri wato " Safina" wacce ta kasance tun tana yar shekara uku mahaifinta ya bada umarni a koyar da ita tarbiya ta matan sarki, hakan yasa ta taso mace mai tsauri da tsananin jan aji, abinda zai baka mamaki ko Abdulsamad sai ya sara mata a gun ji da kai da mulki. Safina ta auri Abdulsamad tana yar shekara 15, wacce aka nad'a a matsayin sarauniya, ta kuma bada umarnin a dinga kiranta da *Magajiya*. Yayanta Hisham shine ya gaji mahaifinsu, wanda aka nad'a sarautar waziri. Auran Abdulsamad da Safina babu soyayya a ciki sam aurene na umarni, sai dai ita dama Magajiya sam babu soyayya a tsarin rayuwarta abu d'aya aka nuna mata ta auri sarki ta haifar masa d'a wanda zai gajeshi. Wannan shine abinda iyayenta suka daura ta akai. A wannan lokacin shekarar Sarki Abdulsamad da Magajiya 20 da aure sai dai har yanzu Allah bai azurtasu da haihuwa ba. Sarki ya cike mata 4 sannan yana da kwarkwara 9 amma har yanzu ba labarin ko da batan wata. Wannan abu na matukar damun Sarki da Magajiya, tayi magani harta gaji har yanzu babu labari. Sai dai alwashi ne tasha babu mai haifar ma Abdulsamad magaji sai ita in har ba ita ba kuwa to lalai bataga wacce ta isa ba. _Wannan kenan_ Kwatsam Magajiya ta fara abin laulayi haka kuma tace ai likita ya bata umarnin zama a d'aki ba tare da fita ba har sai ta sauka, sannan ya hana mijinta kusantarta saboda mahaifarta batada karfi. Sam wannan bai damu Sarki Abdulsamad ba shidai farin cikinsa shine zai samu magaji. Magajiya sam ta daina fitowa haka ma bayinta sai wadanda ta yarda suzo gunta a haka har watan haihuwa tai, nan tace itakam gidansu takesan komawa. Kasancewar Sarki Abdulsamad bai isa da itaba yasa ta shirya ta tafi. Har ta sauka sannan aka aikomai da cewa ta haifi namiji. Fadar farincikin da Hisham yake ciki ma b'ata lokaci ne, wanda ya kasance yau ne ake hidimar sunan d'an nasa wanda aka samai suna Abdulmajid. Anata hidimar suna a waje sai dai daga kuryar d'akin Magajiya itace zaune akan kasan carpet gewaye da tintin sannan d'akin anyi jere sosai na kayan karfi masu kyau da tsada, tana zaune cikin shigarta ta matar Sarki, gefenta kuma Hisham ne a zaune, su biyu ne kacal a d'akin sakamakon sallamar bayinta datai. Kallan Hisham tai cikin isa da mulki tace " Yaya baka manta da abinda na fad'a ma bako?" Dariya yai yace "in banda abinki Magajiya ai ba wanda zai ji wannan sirri dan kuwa ita kanta Sauda(matarsa) na ja mata kunne akan ma karta kuskura ko da wasa tazo gidan nan inkuwa tazo to lallai karta bari su Hadu da Abdulmajid. Murmusawa tai kadan sannan tace " daga Abdulmajid na rufe haifar wani d'a a gidan nan, babu macen da zata haihu bare ma har a fara tunanin wanda za'a daura akan mulki." Hisham yai murmushin mugunta yace " Magajiya gaskiya kwakwalwarki tana aiki ya akai kika zo da tunanin karyar ciki? Sanda na sanar dake Sauda na da juna biyu?" Wani murmushin kasaita tai sannan ta sa hannu akan lab'anta alamar shiru sannan a hankali tace " Yaya kenan ai na fad'a maka tabbas d'ana shine zai gaji sarautarnan, inhar bazan haihu ba dole ne nai amfani da kai jinina." Wani kallo sukama juna na jin dadin abinda suka kulla, Hisham yace " Nace Sauda ta bari sai nan da wata uku sannan ta dawo." Magajiya ta jinjina kai alamar gamsuwa tace " gwara ta kara zama saboda kar aganta aga kalar haihuwa aga kuma ba ciki, dan ma matar nada hakuri kaga bata mana musu ba sanda muka bata umarni." Hisham ya sosa keya yace " inta kawo wargi ai sai ta amshi takardarta." Murmushin jin dadi Magajiya tai sannan tace " ka sa a kara aikomin da maganin nan dan wanda nake badawa a sa ma matansa a girki ya kare." Ya dan sa dariya yace " gaskiya Magajiya ke karshe ce, shi yasa nake baki girma da darajaki, amma bakya gani ko an daina basu maganin yanzu ba abinda zai faru? Gani nake mahaifar tasu ma ai ta gama aiki." Wani murmushi tai wanda ya fahimci cewa tana nufin ta sani amma a kawo. _Nikam nace Hmmm_ Sarki Abdulsamad kam kana kallansa zakasan yana cikin tsananin farin ciki. Bayan ya dawo daga hawan doki ne ya shigo fada sai ga wani bawansa ya sanar dashi yayi bako. Nan ya bada izini akan bakon ya shigo. Wa zai gani? Amininsa ne wanda suka shaku sai dai dayake shi dan Katsina ne wanda aiki ne ya kawo mahaifinsa garin Zariya, har suka shaku haka kafin daga baya su koma garinsu. Da sauri ya karasa gun sarki saboda tsananin murna, nan Sarki ya kallesu da ido wanda ya nunama dogaran akan yanaso su fita, ba musu kuwa sukai waje. Rungume juna sukai cikin tsananin farin ciki Sarki ya kalli abokinsa yace " Amadu ashe zan ganka?" Wani irin farin ciki sukeji na ganin juna, bayan sun nustu ne suka shiga hirar yaushe gamo. Can Sarki yace " ko ziyara Amadu? Da alama yanzuma ba saboda ni kazo ba." Sarki gani yai Amadu yayi kasa da kansa alamar damuwa, cikin kulawa yace "menene?" Hawaye ne ya ciciko a idan Amadu cikin wata muryar abin tausayi yace " Mai martaba ina cikin wani mugun hali." Mamaki ne ya kama Sarki yace "Name kenan?" Ido Amadu ya runtse yace " kanwata aka ma fyade a kasarmu, wanda hakan yasa dangina da na matata duk hankalin mu ya tashi sakamakon habaici da kyamatar mu da akeyi." Cikin tsananin tashin hankali Sarki yace "kanwar ka badai Basira ba?" Amadu ya jinjina kai cikin takaici sannan yace " ita kuwa shiyasa naga zamanta acan bazai yiwuba dan ko fita bata iyayi shine nace bari inzo in rokeka ko zaka tambayarmin yayarka Aunty Babba ko zata zauna agunta ko da kuwa na wata d'aya ne, bani da wanda na sani bayan kai a kasar nan, gashi duk samarinta sun gujeta." Cikin tausayawa Sarki yace " amma garin yaya?" Amadu yace " da daddare matata ta aiketa siyo maganin zazzabi dan bawa d'ana da bashida lafiya, nikuma bana gari, a hanyarta ta dawowa aka tareta aka mata fyade, duhu yasa batasan waye ba bare ta nunashi." Sarki yai shiru yana nazari, Amadu yacigaba " Mai martaba in kuwa kanada wani dogari ko bawa da kake tunani ka hadata dashi a musu aure dan kuwa babban abin kunya ne a ma mace fyade ka san bazata taba samun miji ba sai dai wani iko na Allah gashi ta girma shi yasa nake tunani ko wanene ma kawai ka bata a daura auren kafin nan sai ta zauna gun Aunty Babba." _da yake a wancan lokacin babban abin tashin hankali da kunya ne a ma mace fyade ko ta je gidan mijinta ba tare da budurcin ta ba_ Sarki yai shiru, tausayin rayuwar Basira yakeyi, yarinya ce wacce ba ruwanta ga hakuri. Bayan dogon nazari ya kalli Amadu yace " kaunar da mahaifinka yakema nawa, da wanda kaima kake min yasa na yanke shawara ni zan aureta sqi dai inaso karka bari zancen fyade a fito a ko ina, mu birne ta a nan inba haka ba kyamatarta za'a dingayi a gidan nan." Tsananin mamaki yasa Amadu ya kasa magana sai dai wani zazzafan kwalla daya gangaro masa, kai ya girgiza yace " nagode dajin haka sai dai bazan yarda ka auri macen da aka taba a waje ba." Sarki yai dan murmushi yace" Amadu kenan menene amfanin abotar? Kana tunanin akwai mai rike ma sirrinka bayan nidin? Yanzu in muka mata aure da wani bawan ko dogarin daga yaje ya ga ba cikakiya bace shikenan sai wulakanci, haka ma in sanar dashi mukai bazai fasa wahalar da ita ba." Amadu yai shiru, Sarki ya dafa shi yace "karka damu a goben nan ma zan aureta sai dai bazan bari a sani ba tukunna har sai 'yan taro sun watse saboda hidimar suna da akeyi." Amadu ya zube yana godiya, Sarki yace " ka koma kasarka gobe da safe zanyi shigar burtu na zo ba tare da sanin kowa ba sai wanda na yarda dashi." Amadu wani dadi ya kamashi ya hau godiya sannan yace " nidai zan jiraka mu tafi tare sabida tsaronka." Sarki yai murmushi yace " idan ka tsaya kuma waye zai sanar dasu maganar auran? Sannan nima banaso asan zanje har can din, sannan ka bari in sa akaika a mota dan nasan a irin a kori kurar nan ka zo." _A waccan lokacin in har kaga mutum da motarsa to fa lalai d'an wani ne sannan motar ma mu a wannan lokacin tsohon yayi muke daukanta irin mai shafaffen booth din nan ce.._ Sun dade suna tattaunawa kafin Amadu ya mike yamai sallama, godiya da jindadi kam yayi ba adadi. Nikam nace hmm wata sabuwa.... *ABUTURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA* 🕊 _........Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *Haske Writer's Association* *Na Ayusher Muhd* *2* Shiru Sarki yai yana nazari bayan fitar abokinsa, baiyi zata ba sai jin muryar Aminin nasa yai a kusa dashi alhalin ya dauka ya tafi. Amadu yace " Amma Mai Martaba ba matanka hud'u ba?" Idanunsa ya bud'e ya saukesu akan Amadu sannan yace " Amadu kaje ka sanar da Barde ya kaika gida, ni kuma gobe zanzo." Jin haka yasa Amadu ya fita jiki a sanyaye, Mai martaba yai shiru tare da maida idanunsa ya rufe, ya dade a haka kafin ya bud'e idanunsa sannan ya kira wani bawansa ya sanar dashi akan ya kira masa kaninsa wanda suke uwa da uba daya. Bai dade da fita ba sai gashi ya dawo shi kuma kanin nasa Kamal na biye dashi a baya. Yana shiga ya saki fuska tare da cewa " Mai Martaba ina can ina hawan doki ka aika a kirani, Allah yasa ba matsala bane." Abdulsamad ya tattara hankalinsa kan kaninsa yace " Kamal yanzu ace na baka mata zaka aura?" Kai ya d'aga mai alamar eh sannan yace "ko ma wace iri ce in har ba mara da'a bace ko wacce ta lalata tarbiyarta da darajarta a waje ba." Sarki yai shiru kafin yace " in kuma d'aya daga cikin wacce ka lissafo baka so ne fa?" Kamal yai murmushi kafin yace " maganar gaskiya zan aureta in har umarnine daga bakin Sarki sai dai in har umarnine daga bakin yayana bazayi ba gaskiya." Ya dade yana kallan Kamal kafin ya daure da murmushi yace " ya kaje gun d'an naka?" Kamal ya washe baki yace " Abdulmalik yana can yana bacci amma yau kam zai yi kwanciyar gajiya, ai yau kowa na cikin farincikin magajin sarki." Sarki ya kara fad'ada murmushinsa yana jin dadin kasancewarsa uba kafin ya sallami Kamal. Bayan fitar kamal ne ya shiru yana tunani ( _a yanda tarihi yake mata guda hudu ne kamar yanda musulunci ya umarta mana sai dai akwai kwarkwara wanda suke zama matan sarki in anci garinsu da yaki ko kuma makamancin haka sannan su wad'an nan basu da gadon sarki in ya mutu_) Lalai yau ya yanke hukunci ba tare da yasan mafita ba sai dai yayi hakan ne saboda tunanin kare mutuncin aminin nasa. Matarsa ta karshe ko ince Amaryarsa wacce ya aura a waccan shekarar ita yake tunanin rabuwa da ita badan komai ba sai dan rashin san auransa da takeyi shi kansa yasan tauye mata hakki mahaifanta sukai gun bashi ita, yarinyace 'yar shekara 12 mahaifinta yayane ga sarkin Daura wanda sunyi hadin auren ne a san ransu, ace shi yana shekara 40 amma an bashi yar shekara 12 ai kowa yasan hakkinta aka tauye shi yasa ko tunanin nemanta bai taba yi ba. Da wannan shawara ya mike tare da ba bayinsa izini akan yanasan a kira Magajiya zuwa turakarsa ********** Magajiya kam tana zaune sai shigowa ake yan suna ana mata barka, ba amsa wa take ba sai kai kawai da take kadawa cikin isa da takama. A ranta wani irin nishad'i takeji tabbas tana cikin tsantsan farin ciki dan saura kiris burinta ya cika, wannan burin nata kuwa bai wuce ace d'anta Abdulmalik ya hau mulkin garin na Zazzau ba. Wata baiwar ta ce ta iso kusa da ita ta rada mata a kunne sakon Sarki, idanu ta juya tare da d'an yin karamin tsaki a ranta, itafa batasan takura akan mai shi baxai zo inda take ba sai dai ace wai taje? Tafi minti talatin kafin ta mike ta fito. Turakarsa ta nufa yana xaune akan kilisar dake shimfid'e a gun, nan ta shiga kanta tsaye. D'agowa yai ya kalleta ta iso ta zauna d'an nesa dashi kadan cikin isa tace " gani ranka ya dade." Kallanta yai yace " Magajiya na tasoki kina cikin taro ko?" Kallansa tai ta danyi murmushi tace " da alama kanada magana mahimmiya ne." Ajiyar zuciya yai sannan yace " ana cikin farin ciki sai dai zan sanar dake wata magana ne." Kallansa tai tare da tattara hankalinta kansa. Yacigaba " so nake in ba Rabi'atu takardarta ina tunanin zallintar da mukema yarinyar nan ya isa haka." Kallansa tai cikin mamaki tace " ban gane ba? Ka taba gani inda sarki ya saki mace?" Yace " yau xa'a fara a kaina." Tace " in ka saketa kana tunanin akwai mai auranta?" Abdulsamad yace " zan saketa ne amma bazan bari tabar gidan nan ba, ni zan rike ta har sai ta samu wanda takeso in aurar da ita." Kallansa tai har zatai magana ta fasa dan itakam yanzu babu wani abu da zai dameta d'a ne ta samu yanzu dan haka komai ma zai faru sai dai ya faru. Ganin tayi shiru yasa ya fahimci ta amince nan ya rubuta takardar saki d'aya ya mika mata yace " ki sanar da ita sai ta koma bangarenki da xama ko bangaren Hajiya Umma (mahaifiyarsa) Jiyai tace " sai dai bangaren Umman dan nikam banasan tarikice." Sarai maganar tad'an kona ransa sai dai bai nuna mata ba, takardar ta amsa sannan ta mike ta fita. Itakam Rabi'a bayan Magajiya ta aika tazo ta sanar da ita halin da ake ciki sam bata damu ba sai ma dadi da taji ta kuma ji dadi kwarai da akace zata zauna anan, dan dama tsoronta mahaifinta. Suna yayi dadi an kashe kud'i, 'yan gari sun sha kalo, anyi hawan doki sosai, jaruman maza sun sha wasa da takubba, masu wasa da kura sun sa mutane nishad'i da sauransu. Da haka kowa ya koma gida, Magajiya ta dauko unguwar zoma mai kula da ita. ********* Washegari Sarki Abdulsamad bayan yayi sallar asuba yakira bawansa wanda ya aminta dashi haka kuma shine dama yake jansa a mota ya sanar dashi zasuyi tafiya, suna sallar asuba ya fadama fadawansa akan zai dan yi zagaye cikin gari dan ganin halin da mutanensa ke ciki. Kasancewar kowa yasan dama al'adarsa ce yasa ba wanda ya kawo komai a ransa, suna fita suka dau hanyar katsina. ******* A can katsina kuwa Amadu ya sanar dasu akan gobe za'a daura ma Basira aure da zarar anyu sallar azahar a masallaci. Basira kam batada bakin magana dan ita tun bayan faruwar wannan lamari sam ko magana ta daina yi, ko tambayar mijin batai ba ta mike ta koma ciki. Matar Amadu ta shigo ta ganta a zaune a bakin irin gadon nan na karfe, ta kalleta tace " Basira bakyaso ne?" Kai basira ta jijiga mata alamar A'a. Numfashi ta ja sannan tace " Basira ya kamata ki cire abin nan aranki yau wata d'aya da sati biyu kenan da faruwar wannan al'amari, daga ni har ke rabon da mu fira waje kenan, sai dai ke ko magana ba yi kike ba sai in ta kamaki dole, bakya gani lokaci yayi da zaki cire wannan a ranki? Murmushin dole tai sannan ta mike, ga mamakin Aunty Karima gani tai ta shiga had'a kayenta a akwati, mikewa tai jiki a sanyaye tai waje, ba shakka tana tausayin yarinyar nan gashi Amadu ya ki fada mata waye mijin itakam tana tsoron kar akai yarinyar nan inda zatasha wahala, dan ma dadinta d'aya ciki bai shiga ba sanda akai fyaden tunda har tayi al'adar ta. Basira kam kayanta kawai take sawa a akwati tana gamawa ta shiga tai wanka tare da kwanciya akan gadon d'akin, ta rasa me yasa ko tunani ma ta kasa yi idanunta kawai ta rufe. Bacci ne ya dauketa mai nauyin gaske. ********** Wajen karfe 12 suka iso dan motar wannan lokacin sam ba gudu ne da ita ba kamar ta yanzu ba, hakan yasa suka dade sosai a hanya. Basu san gidan Amadu ba hakan yasa suka shuga neman kwatance dan ma ya sanar dasu unguwar dan lokacin ba a sa sunan layi. Sun dan sha wahala kafin su gane gidan dan ma abun mutane sai sunce gidan su Basira sannan ake ganewa. Wajen karfe d'aya suka isa gidan lokacin Amadu na waje yana ta leke kudu da yamma ko zai gansu. Yana hangosu ya saki ajiyar zuciya dan da ya dauka ko an samu wata matsalar ne. Abdulsamad ko ciki bai shiga ba yace muje masallaci a ayi abunda za'ai in koma dan barin fada ba tare da kwakwaran uzuri ba matsala ne. Amadu ya jinjina kai sannan suka nufi masallacin kusa dasu dama ya riga ya sanarma liman, bayan sunyi sallah ne aka daura auren Abdulsamad da Basira wanda Liman yama Abdulsalam walici shi kuma Amadu yama Basira an daura aure akan sadaki naira dari 200. Wannan kenan....... *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* _Dan Allah wanda yamin magana ban mai reply ba yai hakuri jiya whatsapp d'ina ya samu matsala sai dana sake downloading sai dai sam yaki backup name messages d'ina_ *Na Ayusher Muhd🤸🏼‍♂* *3* Kafin su fito daga masallaci bayan an daura auren mutane har sun cika gaban masallacin, labari har ya kai musu cewa ga wani gara can da baisan me yakeyi ba ya auri Basira. Sarki na kokarin fitowa wannan Bawan nasa ya sha gabansa ya rusuna tare da sanar dashi halin da ake ciki. Jikin Amadu ne yai mugun sanyi, jiyai Abdulsamad yace " Ku fara fita in yaso ni sai in fito daga baya." Amadu yace " ai Mai martaba bakasan gidan ba." Yace ba komai zan biko a baya ne nima ai. Jin hakan yasa suka fara fita, nan fa mutane suka saki baki suna kallan bawan, kowa da gulmar dake fada aransa, wasu cewa suke ai dole ya nemo ko ma waye ya bata da kuma alama ma fakiri ne, wasu kuma suce da alama sadaka aka bashi yaji banza shi yasa bazai iya bari ba. Haka dai kowa da abinda yake tunani, sudai sukai gaba, Mai Martaba na baya cikin mutane yana kuma jin duk abinda kowa ke fada, jikinsa ne yai mugun sanyi lalai ba shakka yayi babban taimakon na auran yarinyar nan dan kuwa da alama ba mai auranta a garin nan. Sai da mutane sukaga sun isa gida sannan kowa ya watse, shi kuma Sarki Abdulsamad ya shiga ciki. Bayan sun zauna ne matar Amadu ta kawo musu fura mai sanyi tare da dambu na tsakin massara yasha gyada, Abdulsamad ya dan ci kad'an kafin ya kalli Amadu yace " Amadu ba zan kai Basira gidana ba yanzu." Gaban Amadu ne ya fadi yace " kana dana sani ko? Na auranta? Ni kai........" Katseshi Abdulsamad yai yace " ina tsorace mata a bubuwa guda uku shiyasa bazan kaita yanzu ba." Yadan ja numfashi na manyan mutane kafin yace " in har taje gidan nan a haka zatasha bakar wahala ba tare kuma da sanina ba, ko Magajiya bazata barta haka ba, ganin jiya akai sunan d'anta ace yau na kawo mata? Sannan na saki yarinya jiya ashe wani nake san sakeyi? Sannan ban sanar dasu zanyi auren ba ma sam. Kaga wad'annan dalilan sune zai sa su wahalar da Basira, gata ita kuma ko harkar gidan sarauta bata sani ba bare ta nemi kwatar kanta." Shiru Amadu yai kafin yace " Gaskiya ne ni kaga sam banyi wannan nazarin ba nidai dadina Basira ta auri wanda nasan ko bani da rai zai kular min da ita." Sarki ya d'an murmusa kadan kafin yace " Zan baka kwatancen gidana a cikin gari, zan kuma sanar ma ma'aikatan gidan in yaso kai zuwa gobe sai ka taho da ita ka kaita can, zan tura mata bayin da zasu dinga kula da ita da koya mata abubuwan daya dace, in yaso zuwa ko sati biyu ne sai ta dawo." Amadu ya shiga godiya, nan Sarki ya mike yace zai wuce. Amadu ya shiga kwallama Basira kira, da sauri Sarki yace " ya isa haka, bance ka kirata ba ai, ina sauri ne in tazo naje na ganta." Amadu ya amsa da to, sannan yamai sallama yai waje. Yana fita ita kuma matar Amadu wacce ta taso Basira da kyar tanata sharar baccinta suka fito, ganin ba kowa a gun yasa tace " Malam ina mijin?" Basira ya kalla yace " Basira gobe zan kaiki shi yayi gaba." Matar tace " a ina aka tabayin haka? Yaya shine zai kai yarinya?" Amadu yace " ni ai da so nai tabi mijinta ma baki alekum to amma tunda haka yace ni na kaita goben" Zata sake magana yace " kul! Mijin Basira baya magana a canzata dan haka ki kiyayi kanki." Mamaki ya kamata sai dai bata sake magana ba, Basira kam tana jin haka ta koma ciki tai alwala tai azahar. ********* A can gidan Sarauta kam ganin Sarki ya dade bai dawo ba yasa Hisham ya shiga amsar matsaloli da dai sauran abinda Abdulsamad ya kamata yai a ranar,dadi kuwa ya kamashi dan ba shakka yana san mulki sosai. Sai wajen shida sannan suka isa zariya. Kai tsaye wanka yai sannan ya zauna a kilisarsa aka shiga jeramai abinci kala kala da 'ya'yan itatuwa.. Sai da ya koshi sannan yai bincike akan abinda ya faru a ranar. *********** Isar Magajiya da mulkinta yasa ta bada umarni bayan auranta dole ne duk matar sarki da kwarkwarori suzo su gaisheta da safe kafin suci abinci anan ne take sawa a kawo musu wani shayi wand sune suke tunanin shayi ne sai dai a zahiri naganin hana daukar ciki ne. ********* Amadu kam ya kai Basira inda aka umarceshi sannan ya mata sallama akan zai tafi. Kallansa tai idanunta suna neman cikowa tace " yaya ina ne nan? Na tabbata ba mai hankali mai kudin kuma da zai aureni." Amadu ya girgiza mata kai yana murmushi yace " a naki tunanin kenan sai dai Basira inaso ki kasance mai godiya ga Allah dan kuaa ya baki mijin da babu kamarsa wanda baki taba tunanin ko gani ba bare aure ba." Zatai magana taga ya juya baya yana kara kallan falon, daga nan ya kara mata nasiha ya fita zuciyarsa fes da ita. ********* Sarki kam sam ya manta da Basira sakamakon hidimomin dake gabansa, yau ya cika satinta uku kenan da zuwa garin amma ko keyarsa bata gani va, sai wasu abubuwa da ake koya mata. Gashi abin haushi komai sai ace sai dai a mata, magana wannan akwai mai nuna mata yanda zatai, itakam duk ta gaji da wannan sabon al'amarin. Yau watanta d'aya cif, Abdulsamad harya kwanta bacci ya tuno da Basira da sauri ya mike cikin tsananin mamakin kansa da takaici ya fito daga turakarsa, Bayinsa ne suka matso suna tambayaraa ko yana bukatara wani abun ne? Da sauri ya nemi bawansa Mudan ya kuma umarci bayin da wannan fitae ta zama sirri, nan yai waje shida Mudan. Kayan fadawa ya saka sannan ya rufe fuskarsa ya hau doki, ba wanda yai tunanin Sarki ne har ya fita. Gidansa ya nufa, a lokacin ita kuma an sa tayi wanka da wasu turaruka masu kamshi kamar yanda suke sata kullum wai hakane al'adar dole in zatai bacci tai wanka da wad'an nan turarukan sannan ta sha madarar shanu ta kwanta. Ta fito kenan ta zira doguwar riga tana shan madara taji sallama. Gabanta ne ya fad'i jin muryar namiji, a hankali ta amsa kamar mai rad'a, nam shi kuma ya shiga. A zaune ya ganta sai dai idanunwanta sunyi zuruzuru. Dama ya umarci bayin dake waje su tafi makwancin su, nan na cikin d'akin suma suna ganinshi suka zube suna gaidashi, nan suma ya sallamesu. Itakam idanuwanta ne duk suka fito jin suna cewa " Mai Martaba barkada shigowa." Batakai ga nemo amsar tambayar dake mata yawo akai ba taji yace " Basira ba gaisuwa?" Kallansa tai sannan ta zube da sauri kamar taga mala'ika sai dai ta kasa cewa komai sai gabanta kawai dake mugun fad'uwa. Murmushi yai sannan ya matso kusa da ita ya d'agata ya, itakam kafafuwanta rawa suke hakan yasa tsayuwar ta fara neman gaggararta, da sauri ya jawota jikinsa tsoro ne yasa ta zaro idanuwa, shikam Abdulsamad yana mamakin girman yarinyar. Kamshin jikinta ne ya sa ya lumshe ido ba shakka kamshin Magajiya ya ninka nata dadi sosai sai dai baisan meyasa yakijin nata wanu daban ba, ji yake yana ratsa zuciyarsa. Bata taba tunani ba haka kuma batau zato ba taji yace " kinyi al'ada ne?" Da sauri ta matsa daga jikinsa ta kalleshi kadan sannan ta sunkuyar dakai, taya za'ai ya mata wannan tambayar? Ko kunya?" Abdulsamad yace "dole ce ta sani yi miki tambayar." Baya ta juya da sauri sannan ta d'aga kai alamar eh tare da shigewa uwar d'aka. Hamdala yai sannan ya shiga ciki shima. Itakam a bakin gado ta zauna tare da rike hannayenta biyu itakam wacce irin tambaya aka mata yanzu? Mijin da bata taba gani ba taya zai fara mata wannan tambayar?" Shigowarsa ne yasa tai saurin kwanciya tare da rufe ido, murmushi yai sannan ya karasa kusa da ita ya zauna, hannu ya sa a kafadarta cikin maganarsa ta isa da sanyi yace " Basira na tambayeki ne badan komai ba sai saboda gaba." Kallansa tai cikin mamaki yai dan murmushi yace "karki damu ni dama nasan ba matsala sai dai ya zana dole na tambaya." Kasa tai da kanta ta maidashi kan filo, kanta ya shiga shafawa a hankali ya kwanto da kansa jikinta, tsoro ne ya shiga kamata ta tuno abinda ya faru da ita. Da sauri ta mike ta zauna tare da matse kafafuwanta. Hawayene ya shiga zubo mata, tana kuka tana girgiza kai. Sarki ya shiga mata kallan tausayi, Basira cikin kuka tace " tsoro nake." Matsowa yai kusa da ita ya rungumeta ta kara fashewa da wani kukan, nan ya shiga jijigata yana bata hakuri cikin salon soyayya a haka har yasa jikinta ya mutu nan shi kuma ya gabatar da abinda yake so........ Bayan ya nutsu ne ya jawota jikinsa itakam har yanzu kuka take, hakuri ya cigaba da bata, ta dade sosai tana kuka kafin bacci yai gaba da ita. Shiru yai yana kallanta, ya sani sarai dolene gobe bayin dake kula da ita su bincika ko jinin da ya kamata ya fita a gabanta sakamakon farkon kusancin ta da maza ya fito, dan sune zasu zama shaidarta nan gaba. Dubawa yai ya samo reza ya bud'e cinyarsa ya tsaga kad'an sannan ya sa a jikin zanin gadon, sannan ya mike ya fito bayan ya dan sumbaci Basira. *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Na Ayusher Muhd🤸🏼‍♂* *4* Wajen Sallar asuba babbar mai kula da ita a cikin bayi ta shigo dan taimaka mata tai alwala. Basira tana kwance tana bacci matar ta shigo ta tasheta, sam Basira ta manta abinda ya faru hakan yasa da karfinta ta nemi tashi, jin zafi a gabanta ne yasa ta tuna, saboda tasha wahala sosai sanda aka mata fyade dan sai da matar yayanta tai ta saka ta acikin ruwa mai zafi tana gasata tukun na, mikin daya warke ne taji ya motsa, hakan yasa ta dan ce wash. Matar ta kalleta tare da yayi zanin gado da sauri, ganin jini yasa ta saki gud'a, Basira kam kallan jinin tai sam bata kawo ba daga jikinta ya fito ba saboda matan da ba ruwansu da zancen nan, hakan yasa batasan sau d'aya yake fitowa ba, itakam matar ce take bata mamaki ganin yanda take gud'a. Kan kace me? Sai ga ragowar bayin sun taho da sauri, nan suka gani kowa ya fahimta, nan wata ta fita dan d'ora mata ruwan zafi, itakam matar zanin ta yayi ga mamakin Basira gani tai ta ninke ta saka a cikin leda. Bayan ruwa yai zafi ta taimaka mata tai wanka tai sallah sannan aka kawo mata abinci, Basira nasan taji wai menene matsayin wannan mijin nata wanda yazo jiya sai dai tana kunyar tambayar hakan. ********** Sarki ne zaune akan kilisarsa Magajiya na d'an nesa dashi tana cin 'ya'yan itatuwa shi kuma yana d'auke da Abdulmajid a hannunsa yana murmushi, can ya nisa yace " Magajiya nayi aure." Kallansa tai cikin isa tace " aure kamar ya kenan?" Ya dan murmusa yace " kanwar abokina Amadu ce zata tare nan da sati d'aya zuwa biyu." Kallan mamaki tamai sai dai isa da ji da kai yasa batace komai ba, sai dai maganar ta kular da ita sosai tayaya kamar ita za'a mata kishiya ba tare da ta sani ba?lalai Abdulsamad yazo da rainin hankali. Mikewa yaga tayi tare da kiran baiwarta, nan ta shigo da sauri, Magajiya ta kalleta tace "Amso Yarima zan koma." Abdulsamad ya kalleta sai dai shima baice komai ba sai mika ma baiwa 'yar yai suka fita. Tana fita ta tura a kira mata Yayanta Hisham. Zaune take a d'aki ya shigo cikin sauri, ganin yanda fuskarta take a had'e yasa yace "Magajiya lafiya?" Kofin dake hannunta ta jefo da karfi inda yake saura kiris ya jefeshi hakan yasa yasan lalai yayi laifi, da sauri ya matso cikin sanyin murya yace "kanwata........." Wani mugun kallo ta bugamai tace " me kakeyi har Sarki yai aure ban sani ba?" Gabansa ne ya fad'i cikin tsananin mamaki yace "Aure kuma?" Wani kallo ta kara mai tace " ba nace ka dinga kula da duk al'amuransa ba? Yaya wai meke damunka ne? Ko ka manta da wasiyyar Baba yace?akan ka dinga bin duk abinda na fad'a?" Yace "Yahkuri Sarauniya uwar Sarki duk wanda yaja dake shine a wahale, tayaya wata mata can da baki santa ba zata kona miki rai bayan ko ta shigo sahun ragowar matan zata shiga?" Shiru tai tana kallansa, yace " menene naki na kishin wata macen bayan ba haihuwa zatai ba bare musa ran samun matsala nan gaba?" Shiru tai kafin daga bisani tai ajiyar zuciya sannan ta d'an ja tsaki tace " ko menene dalilina na jin haka? Tunda yake aure ban taba jin haushi ba sai yau." Hisham yai dan dariya ganin ya shawo kanta yace "kinada yarima magajin sarki sannan kina da ni waziri menene zai saki damuwa?" Murmushin jin dadi tai sannan tace " zan baka sako ka aikama gidan matarka sannan itama ya kamata ta dawo." Kai ya jinjina alamar gamsuwa yace " yanzu kam bamai gane ta haihu." Sukai murmushin jin dadi. _nikam nace hmmmmm_ Yau ranar kwanan Basira ne a yanda Mai martaba ya tsara sai dai kasancewar bata nan ya kamata ace shi kadai zai kwana, sai dai shikam da daddare ya lalaba ya fita. Tana zaune ita kadai shiru, gefenta bayinta ne suke ta hirarsu, taji sallama. Da sauri suka mike suka shiga kwasar gaisuwa sannan suka fita, ya rage saura su biyu. Zama yai daga gefenta kadan yana shirin magana tai saurin cewa "ina wuni?" Kallanta yai yace " da alama sai na sa an d'aure masu kula dake." Dasauri ta kalleshi idanunta sun bayyanar da tsoro tace " me sukai?" Yace " tunda haryanzu basu koya miki abinda ya dace ba." Da sauri tace "Barka da dare." Sannan ta cigaba "wlh na sha'afa ne ba laifinsu bane." Murmushi yai sannan yace " ke bakya magana dayawa ne?" Shiru tai batace komai ba, yana kallanta yace "kishirya zuwa jibi zaki koma gidana." Kallansa tai batace komai ba itakam tana san jin shi d'in wanene. Jitai yace "Abdulsamad sunana sauran bayani zaki gani inkin isa jibi." Kai ta d'aga ba tare da ta kalleshi ba, hannu yasa ya rikota suka shiga ciki. Duk da itakam tana tsoro sai dai bata isa bijire ma wanda ya taimaki rayuwarta ba. Sai da komai ya lafa sannan bacci yai gaba dashi, itakam shiru tai dan baccin ya bar idanunta ta dade tana tunani kala kala kafin tai bacci. *********** Magajiya da kanta tasa aka gyara b'angaren da zata zauna sannan tasa aka sanar da Sarki akan komai ya kammala, shikuma ya aika a sanar dasu lokacin da za'a daukosu. Da daddare aka sata tai wanka, bayan tasa kaya aka miko mata alkyabba irin masu karfin gaske da nauyi irin na da, aka sa mata, mamaki sam ya hanata magana, sarka ta zinare aka sa mata aka sa mata abin kafa da awarwaro, kasa jurewa tai ta kalli baiwar tata tace " amma wannan shigar batai yawa ba? Ni fa na fara tsoro." Baiwar tai kasa dakai tace " tayaya kaya zaiyi yawa bayan haka al'adar masarautar take? " Cikin tsananin mamaki tace "Masarauta?" Kallanta baiwar tai tace " eh mana duk abinda muke koya miki ai abinda zakiyi ko zaki tarar acan mukeyi." Wani abu ne ya tsaya mata a makogaro, sarauta? Ba shakka ta gane yanzu, wato abokin yaya ne wanda kusan duk labarin yaya baya wuce na Sarki Abdulsamad lalai shine ya aureta kenan, to amma ina ita ina shi? Ta ina? Ita da ba cikakiya ba? Jitai an dafata hakan yasa tai firgigit daga tunanin data tafi. Baiwar tace " Ranki ya dade ana jira." Dakyar ta fara d'aga kafarta suka fita. ******* Haka suka isa gidan tunani duk ya isheta. B'angarenta aka wuce da ita suna tafe ana gaidasu danma bata ganinsu saboda fuskarta a rufe take. Har suka shiga aka ajiye ta a kan bakin gado nan kowa ya fita aka barta da baiwarta guda d'aya. A ka'ida bayan an daura mata aure akwai wasu bukukuwa daya kamata ayi agidan sarautar sai dai Abdulsamad ya turo a sanar da Magajiya akan kar ayi, tayi mamakin jin haka ta aika a tambayeshi dalili ganin al'adar gidance hakan. Abdulsamad yace " Gani yai ba'a dade da yin taron suna ba shi bayasan almabazaranci." Magajiya tayi dariya jin haka dan tasan lalai uzuri kawai yake nema na kar ayi amma wannan ai ba hujja bace, hakan kuma ya nuna mata lalai Sarki ba san auran yake ba da alama akwai wani abu a kasa ne. Basira kam da yake mai san shiru ce zaman bai dameta ba. Yau tana tashi baiwarta Ta sanar da ita zuwa gaida magajiya. Batasan dalili ba sai dai tanajin sunan taji gabanta ya fadi, jiki a sanyaye ta fito suka nufi b'angaren Magajiya. Bayan kowa ya zauna ita da ragowar matar nan ta gaidasu kowa na mata kallan wulakanci kallan wacce ba'aso. Fitowar Magajiya yasa taga kowa ya nutsu, nan ta juya suka had'a ido kwarjini da cikar zati irin na Magajiya da isa da mulkinta yasa Basira tai saurin dauke ido, gabanta kuwa yaki daina faduwa, addu'a kawai ta shiga yi har Magajiya tazo ta zauna. Basira ta d'ago suka kara hada ido, gani tai Magajiya ta mata alama da hannu, jiki a sanyaye ta isa gunta. Magajiya cikib muryar rad'a tace "sau daya zan fada ki tsaya kiji dakyau, yau ya zama rana ta farko kuma ta karshe da zan juyo in ga idanuwanki a kaina banasan kallo." Cikin inina tace "Tuba tuba nake." Kowa ya gaida Magajiya sannan aka kawo abinci itakam dakyar ta ci kadab nan aka kawo musu ruwan zafi anmai had'a had'e, itakam Basira komai ya isheta a gun abincin ma da kyar taci ruwan zafi kam da kyar ta iya yin kurb'a d'aya. Magajiya ta kalleta tace " shanyewa zakiyi ai." Basira tai kasa dakai tace Ranki ya dade bana iyashan ruwan zafi tun ina karama." Magajiya tai wani murmushi tace " inkinsha ya kasheki." Basira gabanta na faduwa da tsoro gashi harga Allah batashan ruwan zafi dan tun tana yarinya datasha tai ta amai haka kuraje suka feso a bakinta tun daga nan aka hanata, an nemar mata magani amma ba'a dace ba sam. Nan ta d'aga kofin ta fara sha kafin ta shanye kuwa sai amai ya feso, nan ta mike da sauri ta fita ta shiga kela amai kan kace me kuraje sun cika bakinta. Tsoro ya kama Magajiya gashi ranar kwanan Basira ne, ya zatai in Mai Martaba ya tambayeta dalilin hakan??????? [truncated by WhatsApp] 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Na Ayusher Muhd🤸🏼‍♂* _Alhamdulila an gama *Nayi Nadama* da *Hamal* Allah ya kara Baseera (Ameen) ni da ragowa 'yan kungiyar Haske na muku bangajiya, Allah ya kare mana ku😍_ *5* Ganin yanda takeyi yasa Magajiya tace a maidata b'angarenta, nan kowa ya mike ya fita sakamakon sallamarsu da tai. Suna fita ta aika a kira mata yayanta Hisham, bai dade ba ya shigo nan ta sanar dashi komai sannan ta d'aura da cewa " yanzu in Mai Martaba ya tambayeta ta fadamai tirsasata nai zaiyi zargin wani abu kasan halinsa sarai." Hisham yai shiru sannan ya ce " bari na kira mai magani ya dubata." Wani mugun kallo ta bugamai wanda yasa yace " tuba nake ashe fa babu namijin da ya isa shiga b'angaren matan sarki ba tare da izini ba ko an sanshi ba." Kanta ta d'auke daga inda yake tace " Ka fad'ama Turaki ya tambayar mana kaninsa ko akwai maganin da zai warkar da ciwon tunda naga kanin nasa yasan kan magani." Nan ya amsa da to sannan ta kara kallansa zatai magana yai saurin cewa "na fahimci komai kinaso kice shi Turakin ya rike maganar a sirri." Murmusawa tai kad'an sannan ta juya kai. Hisham ya mike ya fito yana fita waje yai d'an kwafa tare da kallan inda ya fito sannan yai gaba. Basira kam kwanciya tai ta shiga bargo saboda sanyin dake ratsata itakam batasan gidan nan sam ita duk rayuwarma ba dadi take mata ba inta itace har gwara can inda ta fara zama akan nan dan a kalla a can gidan bayi insuna hira suna sata dariya amma nan kam tanaji tunda ta shigo haryau batai dariya ba. Tana nan kwance aka aiko mata da magani, ko kallan maganin batai ba dan itakam ta sab ciwonta inta kwana washe gari zai baje. Bayan tayi isha'i ne wasu bayi suka shigo suka tsaya a inda take, babbar cikinsu wacce suka zauna da ita a can ne, ta matso kusa da Basira tace "Ranki ya dade wanka zaki tashi kiyi." Basira batai musu ba ta mike saboda a can an sanar da ita yin musu laifi ne kuma yana jawo a rage ganin girmanta. Ban d'aki ta wuce, ruwan zafi ne aka saka a katan baho an saka abubuwan kanshi kala kala, kina shiga b'an d'aki wani dadad'an kamshi ne zai bugeki, nan ta sata a ruwan zafin. Bayan sun gama wankan ne suka bata wasu kaya masu kyaubta saka sannan wannan matar ta miko mata wani ruwa a kofi ba musu ta amsa ta shanyi, maganin ba dadi bata koma san dame akayishi ba sai dai tasan akwai zuma a ciki. Tana gama shiryawa wata mata ta shigo mai d'an jiki haka, tana shigowa suka gaisheta jin suna cewa Jakadiya yasa ta fahimci wacece. Jakadiya ta kalleta sannan ta gaisheta tace "Ranki ya dade muje ko?" Basira batai musu ha tabi bayanta. Sun d'anyi tafiya kad'an kafin su shiga wani b'angare, sosai an tsara b'angaren gashi kato ita da tana tunanin b'angaren Magajiya yafi kyau sai dai yau ta gane wannan yafi, ga girma ga kyau,kofar wani d'aki suka isa sannan Jakadiya ta kwankwasa, daga ciki akace shigo. Jakadiya ta kalli Basira nan Basira ta shiga dan ta gane hakan ake nufi. Katon d'aki ne sosai ganinsa yasa tai saurin maida kanta kasa, murmushi ya saki sannan yace " Amarya karaso mana." A hankali Basira ta karasa inda yake ta tsugunna nesa dashi sannan tace "Barka da dare." Alama ya mata da hannu akan ta matso kusa dashi, idanu ta d'an zaro kad'an tana tsoron kar ta matsa ya kula da bakinta da ya ke ciki da kuraje har kan d'an leb'enta. Ganin yanda yake kallanta yasa ta matsa kadan, hannu ya kara nuna mata akan ta kara matsowa, Basira ta rasa yadda zatai a hankali ta matsa sai dai ta sunkuyar da kanta. Abdulsamad yasa hannu ya jawota kusa dashi yace " bakiga me ke gabana bane?" Sai a lokacin ta kalli gun, abincinsa ne a gun da 'ya'yan itatuwa. Ya kalleta yace "Zubamin." D'agowa tai ta kalleshi wanda hakan yasa ya kalli bakinta, mamaki ne ya kamashi yace "Menene hakan a bakinki?" Da sauri ta rufe bakin, matsowa yai ya fizge hannuta sannan ya ce bud'e bakinki, tsoro ne ya kamata dan Allah ya bashi kwarjini, bud'ewa tai cikin tsoro. Idanunshi taga sun canza cikin fada yace "meye hakan?me ya faru da ke? Ai sanda kike can ba haka kike ba." Bakinta ne ya fara rawa, cikin tsoro tace "banashan ruwan zafi ne sai dazu tsautsayi yasa nasha na dauka na warke." Kallanta yau cikin kokwanto da sauri tace "tun ina karama na daina sha sam na dauka na daina." Ta dauka zaiyi fada sai taji yace " kidinga kula yanzu bari nasa a samo miki magani." Kai ta girgiza tace " ai gobe zai warke." Jakadiya wacce ke makale a kofa ta saka kunne tana jin komai da sauri ta juya ta fara tafiya cikin sauri kamar zata kifa. Shikam Sarki daga wannan matsowa ya shiga wani al'amarin daban ya manta da abinci......Lol! Jakadiya kam bata tsaya ba sai a b'angaren Magajiya tana isa ta nemi izini ta shiga. Zubewa tai a kusa da Magajiya nan ta zayyane mata komai. Murmushi Magajiya tai tace "da alama tanada hankali." Jakadiya tace "nima na kuka da hakan." Magajiya tace " ya ya? Ya kusanceta?" Jakadiya tsoro ya kamata itakam sam ta manta ma aiki biyu aka sata ta ji me zatace da kuma ko Sarki ya nemi Basira. Kallanta Magajiya tai tace " menene?" Yawo Jakadiya ta had'iya tasan halin Magajiya sarai ba tada kyau ko yayanta ba raga mai take ba hatta Sarki in ranta ya b'aci sai ta san yanda tai ta kona mai nasa ran ita kuwa ina ita ina yi mata laifi? Amma itakam tana ganin me zaisa Sarki ya kusanceta bayan ragowar Matan ma sai ya dade bai kusancesu ba? Magajiya ta kafeta da ido. Jakadiya ta saki murmushi tace "ina fa? Yana gama tambayarta yai kwanciyarsa dan ko abinci baicibama. Magajiya ta saki wata bazawarar dariya tace " nikaina jikina yaban haka saboda Basira yarinyace bata wuce 16 zuwa 17 ba shi kuma na sanshi sarai bayasan kusantar yara ko ya auresu yafiso sai sun girma." Jakadiya ta sake dariya tace"Ai Mai Martaba ke kadai ce a gabansa Hajiya Magajiya mahaifiyar Yarima Amdulmajid Magajin Sarki." Kanta ta juya tana murmushin kasaita, nan Jakadiya ta mata sallama tai waje. ******** Magajiya ta yanke shawarar daina ba Basira shayin nan saboda taga abinda ya faru sannan taji Mai Martaba bai fara nemanta ba hakan yasa ta sa Hisham ya samo mata wani wanda ba sai a ruwan zafi ba, dan gwara a samo mata ta ajiye kafin Mai Martaba ya fara tunanin kusantarta. Jakadiya kam bayan ta dawi ta tambayi wata baiwa wacce take ta hannun daman ta ce, ita ta bari a gun dama ta tafi kai gulma akan ko wani abu ya faru. Baiwar ta fada mata ai tana tafiya akai abun. Shiru Jakadiya tai tsoro fal ranta sai can tad'anyi tsaki tace "to ai ba abinda zai faru ma dan inaji Sarki Juya ne inba haka ba matansa nawa haryanzu ba haihuwa? Da ya kwanta dasu da kar ya kwanta duk d'aya ne." Baiwar tace " wani juya kuma bayan Magajiya ta haihu." Jakadiya tai dariya a ranta tace " sai dai a rainawa dolo hankali amma ni da nake zuwa gunta banga wani alamar ciki ba, wanda nake gani kuwa baimin kama da ciki ba sannan menene dalilin turani tafiya zuwa Masarautar Kano a daidai watan haihuwarta? Ni nasan akwai wata a kasa. Murmushi tai a ranta, ganin komai ya zo mata daidai. ********** _Bayan wata hudu_ Basira kam duk ta rasa me ke damunta bata iya cin abinci gashi shiru ba al'adarta sai dai bata kawo komai a ranta ba haka kuma tana kokarin yin komai daya kamata wanda hakan yasa ba wanda yai tunanin komai. Sai dai a 'yan kwanakin nan ta fara zargin ko ciki ne ganin yanda cikinta yai tauri sannan ya dan fara tasawa kad'an. Magajiya kam nasan Basira yanzu tunda taji abinda ya faru, haka zatai ta aika mata da abubuwa, itakam Basira har yanzu ta kasa sakar zuciyarta da matar. Matsala ta fara faruwane daga sanda kanwar mahaifiyar Magajiya tai tattaki na ziyara ta kawoma 'yar yayarta, wanda a lokacin matan sarki duk suna zaune kwasar gaisuwa. Kallo d'aya tama Basira tsoro ya kamata dan ta fada dashewa irin na masu cikin nan. Ido ta kurama Basira wanda har tasan akwai matsala, da sauri Basira ta dauke idanta daga kan matar. *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Na Ayusher Muhd🤸🏼‍♂* _Where are u My Dear BillynAbdul? Here is ur special page, tnx for the care Tawan. Allah ya bar zumunci ya kareki daga sharrin masu sharri (Ameen)_ *6* Suna fita Kanwar Mamanta wato Aunty Lami ta matso kusa da ita tare da cewa " Magajiya nikam waccan wacece?" Ta fad'a tare da nuna inda Basira ta zauna, murmushi Magajiya tai tace "Ahhh Basira? Kema ta burgeki ne? Bansan meyasa ba amma yarinyar ta shiga raina." Aunty Lami tai d'an shiru tana tunanin ta inda zata fara, can tace " amma dai ba matar Sarku bace ba ko?". Had'e rai Magajiya tai tace " wace irin tambaya ce wannan? Baki ga kayan jikinta bane? Ko akwai masu sa kayan Sarki bayan matansa?" Aunty Lami ta dafa kai, kanta na kasa tace "amma dai ba ciki ne da ita ba ko?" Kallanta Magajiya tai cikin halin ko in kula ta girgiza kai cikin takaici sannan tace " da alama tsufa ya fara miki illa." Lami ta d'ago ta kalli Magajiya tace " Magajiya wlh ba haka bane lalai ki binciki 'yar nan, kina me har ciki ya zauna a jikinta haka? Da alama ma cikin nan ya kai wata hudu in bai fi bama." Kanta ta juya ba tare da ta bata amsa ba dan ta kula nema take kawai ta kona mata rai. Lami ta kara matsowa tace " wlh Allah da gaske nake, Magajiya kinsan dai da yanda nake, indai naga mace da ciki ko wata d'aya ne sai na gane." Tasan da wannan sarai sai dai tayaya zatace ciki bayan yarinyar haryanzu Sarki bai fara........ Tunaninta ne ya tsaya ta tuno sanda ita kanta waccan satin taga yanda tai haske har take tsokanarta akan lalai gidan sarauta ya amsheta ganin yanda take kyau haka. Zumbur Magajiya ta mike cikin firgici ta shiga kwallama wata baiwarta kira, nan ta karaso da sauri. Baiwar ta zube a kasa, Magajiya tace " jiku shirya zani b'angaren Basira." Mamaki me ya kama baiwar dan tasan Magajiya bata zuwa b'angaren kowa hatta bangaren Mahaifiyar Sarki sai ta shafa watanni bata ko leka ba. Basira kam tana dawowa daga gun Magajiya ta hau amai dan abincin dataci acan sam kawai dai ta tura ne amma bawai dan ranta yaso ba, kwanciya tai akan gado dan wani irin jiri takeji. Mai kula da ita tana kusa da ita tana tambayarta akan ta kira mata mai magani na gidan? Kai Basira ta jijiga zatai magana sai jin kirarin isowar Magajiya tayi ana yi a kofar ta. Da sauri ta mike ta d'an gyara fuskarta sannan ta fito. Magajiya ta gani a zaune tayi zama irin wanda ta saba, tun da ta taho Magajiya da Lami suka kura mata ido har kafarta ce ta hard'e ta kusa fad'uwa. Da kyar ta karaso, Magajiya ta kalleta cikin dabara tace " ya akai? Bakyajin dadi ne?" Kai ta girgiza alamar a'a, baiwar dake kula da ita ta matso ta zube a kasa tace " Magajiya dan Allah a kira mai bada magani ta duba Uwar gijiyata wlh ba lafiya ce ta isheta ba." Gaban Magajiya ne yai wani wawan fad'uwa amma dayake isashiyace sai ta maze cikin gadara tace " je ki kirata." Da sauri ta mike tai waje, Magajiya ta kalli Basira tace " na d'auke ki kamar kanwata ashe ke ba haka bane?" Basira ta d'ago a hankali itakam tana tsoron matar nan, daurewa tai tace " ba wani abun damuwa bane kawai dai naci abinci dayawa ne a gunki." Magajiya ta kafeta da ido, tsoro da fargaba ya cika mata ciki taf. Suna zaune anan mai bada magani ta shigo. Nan Magajiya ta bata umarnin duba Basira, hannunta ta kama ta bud'e tafin hannunta ta zuba musu ido, ta sake ta sannan ta bud'e idanunta na hago, nan ma ta saki ta sake bude na dama. Tana gamawa ta zube a kasa tare da cewa " ina tayaki farin ciki yake Magajiya, babu wani gabanki ba wani bayanki, kece fitila wacce take haskaka gidan nan......" Katseta Magajiya tai tace " ya isa ni fadamin meke damunta." Mai magani tai murmushi tare da kara dukufar da kanta tace " Yarima Abdulmajid ya kusa samun kani ko kanwa ima tayaki murna Magajiya." Ai ba Magajiya ba kowa na gun sai da ya zaro ido, itakam Basira kasa kawai tai da kanta. Mamakin daya rufeni, gani nai Magajiya ta mata alama da hannu akan ta matso kusa da ita, nan ta taso ta iso, tana zuwa Magajiya ta jawota ta rungumeta tsam tace " Masha Allah! Lalai kinyi abin kwatance a wannan masarauta ba shakka ked'in ta dabance." Basira kam addu'a kawai take dan gabanta sai fad'uwa yakeyi. Magajiya ta saketa ta kalli Mai Magani tace " ki biyoni ki amshi tukwicinki mai tsoka. Nan ta mike ta fito. Abinda zai baka mamaki kan kace me? Labari har ya cika gidan, Jakadiyar Sarki kam tana jin wannan labarin ta garzayo gun Basira sai data tabbatar sannan ta tafi gunsa yana fada ta sa a sanar mai. Magajiya kam tana shiga d'akinta ta dafa kanta wanda ke sarawa, idanunta sunyi jaa sosai lalai dabadan tun tana karama an hanata kuka ba lalai yau da sai tayi, sai dai itakam batasan kuka ba, ko da mahaifinta ya rasu batai ba. Lami ta kalla tace a kira Ya Hisham. Nan Lami tai waje da sauri ta aika a kirashi. Hisham na fada ya samu sakon kanwarsa da sauri ya mike ya nemi izini ya taho, a waje yaga mai magani hakan yasa yai tunanin ko batada lafiya ne. Murmushi yai sannan ya shiga, a tsaye ya ganta ta juya baya. Nan ya canza fuska cikin kalar damuwa ya matso kusa da ita ya zauna yace " Magajiya lafiya?" Juyowa tai cikin takaici ta zauna a gun zamanta sannan ta kalleshi tace " ciki gareta." Cikin rashin fahimta yace " wa kenan?" Lami tai caraf tace " Basira Amaryar Sarki." Tashin hankali Hisham ya mike da sauri cikin tsananin mamaki da tsoro yace " ban gane ba? Magajiya ba kince bai kusanceta ba?" Sosai ya damu dan babban burinsa bai wuce yaga d'ansa akan mulki ba, Magajiya ta runtse ido cikin takaici tace Jakadiya ce ta fadamin. Shiru sukai kafin daga bisani Hisham yace " ya zama dole a zubda cikin kafin yai kwari." Magajiya tai shiru sannan tace a kira mata mai magani. Mai Magani ta shigo cikin farin ciki, gaban Magajiya ta tsugunna. Magajiya ta kalleta yace " shekararki nawa kina aiki a gidan nan?" Cikin zumud'i tace "40." Magajiya tai murmushi tace " muhallin zama fa?" Tace " a wani d'an daki muke takura nida mijina da 'ya'yana." Magajiya ta kalleta tace " Zubar dashi." D'agowa tai da sauri tace " me fa?" Hisham yace " ke kika dubo tana da ciki hakkinki ne kisan yanda kikai kika zubar dashi, in har kinasan ki cigaba da aikinki kuma kinasan muhallin zama mai kyau ke da iyalanki." Cikin tsoro tace " Waziri tuba nake amma tayaya zan zubar da kwan Sarki?" Hisham yace " ruwanki ne ki zubar ruwanki ne ki barshi sai dai 'ya'yanki ina tabbatar miki zasu fuskanci gararin rayuwa dan ko aure basu isa suyi ba in har sun zauna da ransu kenan." Cikin tsananin tashin hankali ta d'ago ta kalli Hisham. Lami tace " kinaso mahaifiyarki dake kwance ba lafiya ta rasa inda zata zauna? Ke kuma ki rasa sana'arki?" Kai ta shiga girgizawa, Lamibta cigaba " in har kinaso bakin ciki ya kashe mahaifiyarki kar kiyi abinda aka saki." Ganin ta rikice tana roko yasa Magajiya tace " kwana bakwai, kwana bakwai kacal na baki ki tabbatar kin kawon magani mai karfin da zai tafi da cikin, kar kuma kiyi tunanin bazan gane ba dan sai nasa ankai gun mai maganni ya tabbatar da hakan." Kanta ta shiga d'agawa nan aka sallameta. Tana fita Lami tace " zatabi umarnin mu?" Magajiya ta juya kai batace komai ba. Magajiya tasa a nemo Jakadiya sai dai sama ko kasa an nemeta an rasa bat ta bata dan bata gidan sam. ********** Sarki kam yana tasowa daga fada yasa a kiramai Basira, dan da shi yaso zuwa ma sai Barde yace in yaje za'ai tunanin yafi san Basira ne wanda hakan zaisa matan su fara tsanarta. Farincikinsa ma yau kwanan ta ne, tunda yai sallah ya kasa tsaye ya kasa zaune sai jeka ka dawo yakeyi, yana nan a tsaye har ta iso. Tana shigowa tun bata karasa ciga cikin d'akin ba ya karaso ya rungume ta tsam wani irin nishadi da jin dadi na ratsashi. Bayan ta zauna ya sa hannunsa akan cikinta cikin tsananin murna, itakam kanta na kasa tana murmushi, cikin tsananin farin ciki yace " in Allah ya saukeki lafiya in har Mace kika haifa zan sa mata suna Fatima Zahra wato 'yar Manzon Allah in har kuma Namiji ne zan sa mai *ABU TURAB*." Cikin muryarta mai sanyi tace " Har ka zabi suna?" Yana murmushi yace " sunayen dana fi so kenan haka kuma fatana in ga na saka wad'an nan sunayen." Murmushi tai sannan tace " meyasa baka sama d'an ka na farko ba?" Yace " ai shi magaji ne shiyasa na samai Abdulmajid, tun daga kan mahaifinmu ake sa ma Magaji Abdul a gaba." Murmushi tai sannan ta kara sadda kanta kasa. Dadi ne ke ratsashi hakan yasa ya kara jawota jikinsa lalai baiji haka ba sanda Magajiya zata haihu, yau jinsa yake daban lalai yana cikin farin ciki. _Hmmm Allah yasa farincikin ya d'ore_ *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Na Ayusher Muhd🤸🏼‍♂* *7* Magajiya tasa Aunty Lami akan duk wani magani datasani ko wani mai bada magani data sani ta je ta amso mata maganin da zai kawar da wannan cikin, babu makawa sai ta sa cikin nan ya bi shada dan itakam bataga wanda ya isa ya haihu ba a gidan, dan kuwa bazata tab'a iya jurar ganin yaro na yawo a gidan ba a matsayin d'an wani ba, ba nata ba. Basira tana kwance a d'aki tun safe ta kasa cin abinci, sallamar baiwar ta ce wato lantana yasa ta mike zaune, Lantana ta karaso ta gaidata sannan tace " Ranki ya dade Magajiya ta aiko miki da magani da kuma abinci." Basira tace " nakoshi Lantana sam banajin cin abinci." Lantana ta matso tace " Kinsan bazataji dadi ba in taji bakici ba kinga na jiya ma data aiko bakici ba sai dataji ba dadi." Basira tace " to ke kici mana?" Idanu Lantana ta zaro tace " so kike a yanken hukunci mai karfi? Magajiya ce fa ba wani ba." Zata sake magana sai ga Aunty Lami ta shigo ba ko neman izini, tana shigowa ta matso kusa da Basira fuskarta a sake aosai tace " haba 'yata tashi ki daure kici mana, ko so kike hankalin Mai Martaba ya tashi?" Da sauri Basira ta jijiga kai alamar a'a, Aunty Lami tasa aka kawo abincin da kanta ta bata sai dataga taci sosai sannan ta bata maganin da aka kirashi da sunan maganin dazaisa taji karfin jikinta." Ta dade a zaune ganin Basira ma baccinta take shara yasa ta fita daga d'akin. ******* Zaune take gaban Magajiya wacce itama shiru tai tana tunani, can Aunty Lami tace " amma Mai maganin nan na kan tudu ya rainamin hankali, sai fa daya tabbatarmin cikin minti 15 zata fara fitsari akai akai in har naga haka inbata kwana d'aya cikin zai zube dan dama nacene ya bada wanda zai dan d'au lokaci kafin cikin ya zube kar a gane." Magajiya tai tsaki tace " mai Yaya yakeyi?" Da sauri Lami tace "ya tafi Daura anso wani maganin." Magajiya tace " itafa matar nan ga gidan nan?" Lami tace " ita kuma tace a bata zuwa gobe." Magajiya tai d'antsaki tace nifa banasan jan abin nan dan ji nake kamar akan bushiya nake a zaune." Lami ta matso tace " karki damu 'yata....." Wani kallo Magajiya ta mata wanda yasa tai shiru, kanta Magajiya ta juya gefe sannan tace "kayan abincin dana aika ya karene?" Lami ta d'aga kai, Magajiya tace " zan aika da wani amma sai hankalina ya dawo jikina." dan dama ta sani da zarar taji Lami ta fara cewa 'yata tasan abu take nema. Basira kam ta fahimci Magajiya ce kawai ke santa a matan sarki dan su kiri kiri suke nuna mata kishin cikin nan, dan haka duk abinda aka aiko mata daga bangaren Magajiya bata wani kokonto take ci. Mahaifiyar Sarki wacce ta tsufa itama bata gazawa gun aikoma Basira kayan marmari. Shikam gogan wato Sarki kullum sai yayi aike sau uku akan a dubo lafiyarta, wannan al'amari ya kara dugunguza hankalin Magajiya dan kuwa an sanar da ita, to ita ke yasa sanda akace tana da ciki baya mata wannan aiken? Tsanar Basira da abinda ke jikinta ya kara tsananta a ran Magajiya. Yayanta ya dawo d'auke da magunguna kala kala nan ya zauna yama Lami bayanin komai, nan ita kuma ta shiga yin hidimominta. A ranar da aka fara bata maganin an saka mata shine a cikin miyar kubewa d'anya, san tuwo da takeyi yasa taci tuwon nan sosai, sai dai me? Tunda ta kwanta bacci ta ke juyi a kan gado, tsananin ciwo da mararta keyi yasa tai ta murkusus, da sauri Lantana ta fita ta karasa b'angaren Sarki nan ta aika a sanar mai. Ranar kwanan matarsa ce ta biyu, ai ko fadamata baiyiba yai waje da sauri, sun iso bangaren Basira lokacin ciwon ya mata yawa dan ta fad'o ma daga kan gado, jini ne ya fara zubo mata wanda hakan yasa hankalinta yai tsananin tashi. Sai dai tsananin ciwon da takeji yasa ta kasa magana, shigowar Sarki ne yasa ta daurw ta fara kokarin mekewa, da sauri ya karaso ya rungumota jikinsa, hawayene kawai ke zubo mata a hankali take cewa "shikenan cikin nan ya tafi shikenan nikam na baka kunya...." Hannu yasa da sauri ya toshe mata bakinta sannan ya kara jawota jikinsa, d'aya daga cikin bayin Basira wacce Magajiya ce ta turota b'angaren dan kai mata rahoto. Da sauri ta zame jikinta tai bangaren Magajiya. Tana shiga ta zayannema Lami halin da ake ciki, da sauri Lami ta shiga ciki ta sanar da ita, ajiyar zuciya Magajiya tai tace " yau da alama zan samu bacci mai dadi." Lami ta saki dariya tace " nikuma gobe za'a sallameni ko?" Kanta ta juya gefe bata amsa mata ba sai murmushin jin dadi data saki. Basira kam tana jikin Sarki ganin ciwon ya lafa yasa ya kira Lantana yace ta taimaka mata ta gyara jikinta. Basira tana mikewa Lantana taga yanda jini ya zuba sosai, salati ta shiga yi, Sarki ya kalli gun dan harshima ya b'atashi, Lantana ya kalla ya mata alama da ido akan tai shiru hakan yasa tai shiru itakam Basira hawaye kawai take yi. Shiru yai bayan sun shiga b'and'aki, ji yai idanunsa na neman canzawa, kallan jinin yai yanajin wani abu na tasomai na bakin ciki, ba shakka yasa rai sosai akan cikin nan, yana nan a zaune Lantana ta fito ta debi kaya ta koma. Can sai gasu sun fito, kuka sosai Basira takeyi wai tana bashi hakuri, mikewa yai yaje kusa da ita ya jawota jikinsa yace " karki damu Allah zai bamu wani." Shiru tai batace komai ba, ya daure yai murmushi yace " kishirya gobe insa a maidake gida gun Amadu inkin warware sai insa azo a d'aukeki. Kallansa tai cikin mamaki tace " akan me?sakata kai?" Dariya yai sannan yace " wani irin saki kuma? Ai ba saki a auranmu cewa nai dai kije inda zaki samu kulawa sosai sannan za'a dinga d'ebe miki kewa, sai ku shirya ku tafi da Lantana." Murmushi tai sannan ta sunkuyar da kanta kasa. Magajiya kam an tabbatar mata ciki ya zube shine ma dalilin tafiyarta gida, nan ta aiko mata da kaya kala kala wai ta kai gida, masu murna nayi masu bakin ciki na yi na tafiyar cikin nan. Sarki ya cika musu mota da kayan abinci ya kuma bata kudi sosai yace " zai zo sai dai bai san yaushe ba." Sun shirya sun kama hanya. ********** Matar Amadu kam bata yarda cikin nan ya tafi ba ita kanta basira ganin cikinta na kara tasowa yasa tasan cikin nanan, sai dai ba yanda zatai ta sanar da Sarki tunda dai ba salula babu kuma wanda zata aika, sai dai ta zauna zuba ido akan sanda zai zo. Matar Amadu dashi Amadun tunda sukaga cikin Basira nanan suka d'aura himma sosai na kula da ita hakama Lantana sosai take kula da Basira. _Wannan kenan_ ( _Dan Allah kuyi hakuri da wannan wlh yau abubuwa ne suka cud'emin da kyar na samu nai wannan, Nagode kwarai_) *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *8* Shiru shiru ba sarki ba labarinsa wanda hakan ya kara d'agama Amadu rai gashi lokacin Basira cikinta yakai wata 9, ganin kar Basira ta haihu ba tare da sarki yasan komai ba yasa Amadu ya shirya tsaf ya nufi garin Zariya a akuri kura. Sai yamma liss suka isa, gidan Sarki ya wuce. A b'angaren Mai Martaba kuwa aiyuwa sun cab'e mai a fada wanda ya rasa yanda zaiyi, yaso ya aika aje q dubo Basira sai dai Barde ya bashi shawara akan ya kara jinkirtawa ganin kar a gane tsananin san da yake mata wanda kan iya jawo mata tsangwama in ta dawo. Yau ma kamar kullum yana zaune a fada ana ta fama kawo kara yana hukunci, wasu kuma neman taimako suka zo yi wasu kuma sulhu da dai sauransu, ganin yamma tayi sosai yasa ya sallami kowa akan a dawo gobe, shigowar bafadansa ne yasa ya kalleshi, bafadan ya sanar dashi zuwan Abokin nasa kuma sirikinsa, nan ya bashi izini da sauri. Amadu ya shigo kansa na kasa sai daya gaidashi tukunna, Sarki ya nemi a basu guri, suna fita ya kalli Amadu yace " Amadu ka jini shiru ko? Wlh al'amura ne suka c'abe min gaba d'aya. Amadu yace bakomai sannan ya d'ura da cewa " dama zuwa nai na sanar dakai Basira ta shiga watan haihuwa." Mamaki ne ya kamashi wanda sai da ya bayanna a kan fuskarsa yace "Haihuwa kamar ya?" Amadu yai murmushi yace "ai cikin bai zube ba." Mikewa yaga Sarki yayi da sauri ya shiga matse hannayensa yama rasa mai zaiyi can ya matso jusa da Amadu ya d'agashi tsaye ya rungumeshi kam yace " Basira ta kusa haihuwa kenan?" Amadu yai murmushi yace "kwarai kuwa dan tama shiga watan, haihuwa yau ko gobe, nima sai da Matata ta sanar dani ta kula Basira ta kusa haihuwa sannan nace to ya zama dole yanzu kam inzo in sanar dakai." Abin mamaki kwalla ne ya taru a idan sarki hannu ya d'aga ya shiga godema Allah. Abin mamaki fadawa da bayinsa dake waje nan a ka fara zamewa kadan kadan an tafi kai gulma (lol.....) Sarki yace "aikam yanzu dakai zamu tafi muje in d'aukota." Amadu yai dariya yace " kai da kake fama da aiki sai dai ka tura kawai a d'aukota." Shiru yai yana tunani can yace " ka kwana anan zuwa gobe zansan yanda za'ai." Magajiya na zaune zance ya zo mata, tashin hankalin da ba'a kwatantashi, ba shakka tashin hankalin data shiga ya wuce duk yanda mai karatu zaiyi tunani tana tsaye jitau jiri ma na neman d'ebanta, Hisham kam ba kanta dan kuwa magana ra baci, tsantsan tashin hankalin da ya shiga ya wuce misali. Gun Magajiya ya taho a sukwane, sunyi jugum jugum su biyu a d'aki, can Magajiya tai d'an ajiyar zuciya sannan ta kalli Hisham tace "duk laifinka ne, kaine ka tabbatarmin maganin nan ba karya ko wasa a ciki." Hisham yai shiru can yace " duk ba wannan bane abinyi yanda zamuyi yanzu shine abinyi." Magajiya tai shiru tana tunani, Hisham yace " bafa zai yiwu mu bari a haifi yaron nan ba in ma mace ce da sauki to amma ina muka sani?" Magajiya cikin kufula tace " aikin gama ai ya riga ya gama kanaji ance ta shiga watan haihuwa?" Da sauri Hisham yace " to sai me? Ai ko haifarsa tai sai mu halakashi." Kura mai ido tai can tace " kisa kake so muyi kenan?" Hisham ya share zufa sannan yace " ai da din ma kisa ne, in kuma kina ganin ba wani abu to shikenan kinfi kowa sanin Abdulsamad haka kawai bazai ba Abdulmajid mulki ba dan yana na fari ko yana d'anki ba." Shiru tai tana tunani kafin tace " banasan irin wannan maganar ka fita ka bani guri in na gama yanke hukunci zan kiraka." Mikewa yai ya fita rai a b'ace. Magajiya ta dade tana tunani kafin daga bisanj ta mike ta fito. B'angaren Sarki ta nufa, yana turakarsa banda farinciki ba abinda yakeyi, neman izini da akai akan isowar Magajiya yasa gyadan had'iye abinda ke fuskarsa. Magajiya ta shigo cikin tafiyarta ta isa,zama tai a inda ta saba zama sannan ta kalleshi tace " ina cikin tsananin farin ciki Mai Martaba, nasan ban kaika ba amma natabbata ina bayanka." Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa na tsantsan farinciki yace " nagode Magajiya." Murmushi itana tai sannan tace " ka gode dame? Abinda za'a haifa kamar d'ana ko 'yata ne zan kula da abinda aka haifa kamar nice na haifesu." Kallanta Sarki yai sai dai yau idanunsa ya rufe har ransa yake jin dadin maganar ta. Magajiya ganin ta kamo lagonsa ta cigaba " shine nake tunanin kai ka zauna saboda hidimar dake gabanka inyaso waziri sai yaje ya taho da ita." Sarki ya kalleta zaiyi magana tace " menene amfanin waziri? Dole ne ya wakilceka ko ya taimaka maka alokacin da kai kake wani abun, banaso mutane su fara tunanin kafinsan matarka a kan talakawa da mutanenka." Shiru yai yana tunani ba shakka hakan data fa'a shine gaskiya, ya kalleta yace "haka ne sai dai bakya tunanin Hishan zaiji ba dadi ganin kishiyarki ce?" Kai ta jinjina tace " zaiji mana, sai dai ai a karkashinka yake, sannan in munaso mu girmama Basira shi din ya kamata a tura." Sosak Sarki ya gamsu haka kuma ya amince da wannan shawara. Bayan Magajiya ta dawo b'angarenta tasa aka kira Hisham, ta kalleshi tace " gobe ka shirya kai zaka taho da Basira sai dai inaso ka sani banaso inga Basira a gidan nan daga ita har abinda zata haifa." Tana gama fadar haka ta sallami Hisham ba tare da ta jira abinda zai ce ba. ********** Washegari kuwa da sassafe Mai Martaba yasa suka kama hanya, mota biyu sukau saboda in an tashi d'aukota yace a taho da Matar Amadu saboda ta kula da ita inta sauka, ganin ita ta gidace ba wai dan baza'a bata kulawa a gidan nasa ba. A can garin Katsina kuwa Basira tun dare take nakuda mai azabar wahala, banda juyi ba abinda takeyi duk sun jigata daga ita har abinda ke cikinta har matar Amadu, sai asuba ta sauka, ta haifi d'anta santalale mai tsananin kama da Mai Martaba, duk da dai ance jariri ba'a gane kamarsa sai dai wannan kam kallo d'aya zakamai ka san ba Basira bace. Tana haihuwa wani nannauyan bacci yai gaba da ita, Matar Amadu ta gyara d'an tas sannan ta gyara gun, ganin yaron ya tafi bacci yasa ta zo ta tashi Basira ta gyara ta, sannan tace ta koma ta kwanta bayan ta d'anci dumame. Shiru Matar Amadu tai tana tunani, ga Amadu bai dawo ba gashi Basira ta sauka, ganin zaman ba shine mafita ba yasa ta mike ta fito tai gidan yayanta dake nan kasan layinsu. Babban d'an yayan ta samu tace maza yaje ya samu motar da zatai Zariya ya hau, ta bashi sako akan yaje gidan Sarki ya nemi Amadu in bai ganshi ba yace a sanar ma Sarki Basira ta sauka ta haifi Namiji. Sai dataga ya hau motar sannan ta juyo gida, kazarta ta kama ta yanka ta shiga gyarawa, Lantana na aikin gida. Rashin sani sam itabatai zaton Amadu na hanya ba. Su Amadu sun iso wajen azahar nan ya tarar da abin farin ciki wanda ya kasance na babban bakin ciki ga Hisham, sai ma da aka miko mai yaron yana bacci ganin katon yaro nau kama da AbdulSamad yasa hankalin Hisham ya kara tashi, jiyai kamar ya shake yaran ya mutu. Matar Amadu ce ta kawo musu ruwa da abinci ganin yanda Hishan yake kallan jaririn ne yasa ta tsorata ba shakka kana gani kasan kallo ne na saka mugun abu a rai. Hisham jin motsin ajiye tire yasa yai saurin kallanta sannan ya canza fuska, itakam tana ajiye wa ta juya tai ciki, zuciyarta fal da tunani. Bayan yaci abinci ne yace zaije ya samu hakimin nan garin ya kwana a gunsa zuwa gobe tunda bai kamata su kama hanya yau ba. ******* A can kuwa Sani ya isa Zariya ya sauka ya gangara masarauta, a bakin kofar shiga dogarai suka tambayeshi inda zashi, nan ya sanar dasu gun Kawu Amadu yazo wato yayan Basira wanda yazo jiya, nan suka sanar dashi ai ya koma katsina yau, jiki a sanyaye ya juya, har ya d'anyi nisa sai kuma ya dawo yace " ku sanar da Mai Martaba dama Yafendo ce ta sauka yau da asuba, an samu d'a namiji." Kallan mamaki dogaran sukamai suka ce Yafendo?wacce kenan?" Sani cikin halin ko in kula yace "Basira." Kallan juna dogaran sukai sannan suka kalleshi sukace " da gaske ta haihu?" Kai ya d'aga alamar eh, gani yai sunyi ciki da sauri ko kulashi basu sake yi ba, tsayawa yai yana mamaki, ganin ba kowa a kofar shikam ya shige ciki. B'angaren Magajiya sukai tana zaune a kilisarta dan ko abinci ta kasa ci, bayan sun nemi izini ne suka shiga ciki suka zube a kasa suka kwashe komai suka sanar da ita, zumbur ta mike cikin tashin hankali sai dai ganin su waye a gabanta yasa ta daure ta saki fara'a tace " Alhamdulila kun sanar da Sarki?" Sukace "munje baya fada shiyasa muka garzayo nan." Tace " dakyau ba sai kun fadamai ba bari ni na sanar dashi da kaina, ko kuma dukanmu kar mu fadamai sai dai kawai mu bari in ta dawo gobe ya ganta da d'a lalai zai sha mamaki." Kai suka jinjina alamar gamsuwa sannan ta basu tukuici ta sallamesu. Shikam Sani ciki kawai yai ta shiga har ya ganshi a wajen wasu mutane, a tsatsaye a waje da alama magana mai nahimmanci suke tattaunawa kuma yaga duk wani mutum akewa maganar. Gun ya karasa ya gaishesu, kallansa sukai cikin mamaki,Barde wanda ke tsaye ya kalleshi yace " Lafiya?" Sani ya kara sanar dashi yanda ya fadama dogaran. Barde cikin zakuwa yace " ka tabbata?" Yace " sosai nidin ai d'an yayar matar Kawo Amadun ne." Barde ya kama hannunsa cikin sauri sukai gaba. Gun Mai Martaba ya kaishe yace ya tsaya a waje shi kuma ya shiga ya sanar da Sarki. Sarki kam wani irin dadi ne yake ziyartarsa ji yake kamar zaiyi me dan dadi, nan ya bada umarni a ba Sani tukuici mai tsoka. Magajiya ta rasa abinda zatai da sauri ta aika a kira mata Inna Lami(sry zamusa Inna Lami tunda a lokacin ba Aunty.) Lami tana shigowa ta tsinci labari a sama yana yawo akan haihuwar Basira. Cikin hanzari ta juya tai waje, gun malaminta ta nufa ta sanar dashi komai. Kallanta yai sannan yace " yanzu me kikeso ayi?" Tace "an riga an haifeshi ni kuma ban taba kisa ba kuma itama Magajiya nasan bazataso muyi kisa ba dan haka so nake a nakasar dashi. Kallanta yai yace" Nakasa wace iri?" Tace waccece zata hana mutum yai tunanin hawa mulki? So nake a nakasar dashi a yau yanda in sukazo gobe za'a dauka a haka aka haifeshi." Dariya yai sannan yace " na baki ko na ido? Sune babban nakasu da zasuma mutum." Lami tai shiru can tace " ido, a hanashi gani yanda ko uwarsa bazai sani ba balle ubansa sai dai muryarsu, tunda munyi iya yinmu akan karyazo duniya amma sai da ya zo." Tana zaune anan ya gama abubuwansa sannan ya bata wani yace ta binne, nan ta bashi sallama ta mike ta fito cikin farin ciki. Sai daya gama komai sannan ta shiga gun Magajiya ta sanar da ita. Magajiya ta kalleta tace "kina ganin zai kama?" Tace kwarai kuwa kuma nina fada miki gobe ba ido zaizo gidan nan. Ajiyar zuciya Magajiya tai cikin damuwa...... _Hmmmmmm_ *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *9* Sosai Barde ya ba Sani tukuici sannan ya kamo hanya. Shikam Hisham tun da suka isa masauki ya kasa zaune ya kasa tsaye can ya gaji ya koma ya zauna tare da bubuga 'yatsarsa a guda d'aya a kasa alamar yana cikin dogon nazari ba shakka dolene ya d'au mataki sai dai ta ina?kuma ta yaya? Ganin yaron ma yasa hankalinsa ya kara tashi matuka, ba shakka in har Mai Martaba yaga yaran nan to fa su tasu ta kare, tunda shi jininsa ne. In mun tafi a hanya in jefar dasu a tsakiyar daji ne? Abinda ya fara fad'o mai kenan a zuciya, kai ya girgiza da sauri yace in nai haka kuma ai zasu koma gidan a hankali tunda da kafarsu kuma zasu iya samun taimako. Insa a je gidan a kashe su yau? Kai ya girgiza yace na tabbata in nai haka sai an zargeni tunda dai ina garin. Idanunsa ne ya kada sosai na bakin ciki, gashi dare yayi bare ya tafo daura gun mai magani. Ko guba zan....... Kai ya kada da sauri alamar rashin gamsuwa, idanunsa ya rufe cikin bakin ciki, jiyai daga wajen d'akin da yake wasu na hira "wlh jiya ai munga abin mamaki, tas fa wutar nan ta cinye gidan daga mata da mijin har yaranta biyu ba wanda ya tsira." Zumbur ya mike yace wuta.....Wani murmushi ya saki na gamsuwa da shawarar data zo mai a yanzu. Turawa yai a kiramai wani bawansa wanda ya sa aka bashi matsayi a gidan sarauta saboda tsabar yardar da yamai, bawa ne wanda baya ko tambayarsa dalili in ya saka shi abu, baya taba musa mai ba kuma ya neman sanin dalilinsa na sashi abun. Yana zuwa ya jashi cikin kuryar d'aki ya sa bakinsa a saitin kunnensa alamar rad'a ya fara mai bayani wanda ni da nake tsaye a gun ma bansan mai ake cewa ba. Itakam Basira da Babynta bayan Magrib suna kwance akan gado Lantana na kasa tana ninke kayan data wanke tana ta shirya musu jaka matar Yayanta ta shigo. Basira na ganinta ta fara kokarin mikewa, da saurin tace " koma ki kwanta." Itakam Basira mikewa tai ta zauna, kallan Lantana matar tai tace "Lantana d'an bamu guri." Da sauri Lantana ta mike tai waje. Kallan Basira tai sannan tace " Basira." Yanda ta kirata yasa Basira ta tattara hankalinta gaba d'aya kanta. Ta cigaba " Wani irin zama kukeyi da Yayar wanda yazo?" Basira tace " zaman mutunci mukeyi." Ido ta kura mata sannan tace " gaskiya nakeso ki fadamin." Basira taja numfashi sannan tace " wlh da gaske nake tana kula dani nidin ce zuciyata taki yarda da ita." Meyasa? Abinda taji ta fada kenan. Basira tai shiru kafin can tace " gabana fad'uwa yakeyi in na ganta." Shiru tai sannan tace " ki nutsu kiji mai zance, tun bayan zuwansu hankalina yaki kwanciya da yanda naga yayanta yana kallan yaron nan, kallo ne na tsana tsantsa." Basira tai murmushi tace " kedai kila baki fahimceshi bane amma......" Katseta tai da cewa " Basira zaman gidan sarauta ko ba'a fada ba kasan ba wai zama bane wanda kowa zai soka, bare ke da kika haihu, ki kasance mai hakuri sannan kar ki bari ko kad'an a cutar miki da d'anki." Murmushi Basira tai tace " ki daina damuwa ba komai insha Allah." Sun dade a d'akin kafin ta mata sai da safe ta fito. Wajen karfe 1 na dare Basira ta farka sakamakon kukan da Jaririn yake mata, kuka yake sosai ta mike tana bashi mamma, Lantana ta amsheshi tace kawoshi na fita dashi na lallabashi ki samu ki kwanta. Nan ta amsheshi tai waje dashi, kamar wasa tana jijashi taga hayaki sosai yana tasowa daga wajen d'akin Amadu. Cikin tsoro ta koma ciki dayakr ta kofar baya ta fito a kuma nan d'akin Basira yake, Basira ta gani tana ta tari cikin bacci. Nan ta fara tashinta, dakyar ta samu ta tasheta, ganin yaron nata tari shima yasa Lantana tasa zani ta goyashi. Basira cikin tsoro tace " menene hakan?" Lantana tace bansani ba nima sai dai hayaki na tasowa daga can. Da sauri Basira ta mike ta nufi ciki, tana bud'e 'yar karamar kofar da zata sadata da wajen su Amadu, da yake gini ne irin namu na da, kowa da inda yake sai dai shi yayi dabarar ginewa tsakanin nasu da inda Basira take sai yar 'yar kofa a gun. Basira na bud'ewa taga wuta sosai tana ci ta b'angaren su Amadu, ihu sosai ta kwalla wanda yasa Lantana tahowa da sauri. Ganin yanda wuta ke cin b'angarensu Amadu har ta fara gangarowa inda suke yasa ta saki ihu itama, daga waje sukaji mutane an fifito, Basira kam neman cusa kai takeyi b'angaren su Amadu, ganin yanda ta fita hayyacinta tana ihu tana kiran yayanta da matarsa yasa Lantana ta fara jan hannunta. Fizgewa tai da karfi ta kara nufar ciki, Lantana ta kara riketa tana ihu akan a kawo musu a gaji, nan wasu maza sukai tunanin bi ta baya, suna shiga sukaga yanda Lantana ta kankame Basira tana ihu, nan fa suka kamo Basira sukai waje da ita, ihu take sosai akan a taimako mata yayanta. Suna kaiwa waje gidan ya kara kamawa sosai ihu sosai Basira take ana ririketa, can ma kawai sai gani akai ta suma. Mahaifin Sani wanda yazo gun yasa aka kaita gidansa, sosai ranar anga tashin hankali a unguwar, daga Amadu har matarsa sun kone a ciki, dan da alama bacci suke wuta ta taresu. _Nace Allah ya jikansu Ameen_ ******* Itakam Basira sai wajen asuba ta fardo, kuka kawai takeyi, sai wajen hantsi bayan anyi jana'iza mahaifin Sani ya kalleta cikin tausayawa yace "Basira ya akai wuta ta kama haka?" Kai ta shiga jijigawa akan bata sani ba, shiru yai sannan yace " da matsala." Kallansa tai cikin mamaki tace name?" Yace " Basira wanda suka zo gidanku jiya masu rawani dan bansan matsayinsu ba." Kai ta gyad'a alamar ta sansu, yace "kinsan ko jana'iza basu zo ba, kawai tambayata yai akan kina raye? na sanar dasu kina raye kina gidana, sai ya tambayan yaron fa? Ni kuma sam banga yaro ba alokacin sai nace mai ban sani ba gaskiya dan nima a rikice nake, abinda yaban mamaki yanda naga idanunsa sunyi alamar bakin ciki na kasa gane bakin cikin namenene a ciki, na rashin mutuwarki ne ko na rashin sanin halin da yaron yake ciki." Zatai Magana Lantana ta zo da sauri tace " Ranki ya dade nima naga Kafilu(wannan bawan na Waziri) a lokacin da muka fito sai dai abinda yaban mamaki daga nesa na ganshi ina kallo ya juya yai gaba ba tare da yazo inda muke ba." Basira ta kalleta tace "ya akai kika san shine bayan dare ne?" Tace " akwai hasken farin wata sannan akwai hasken wuta da take ci." Basira bata sake magana ba ta mike zata fita, jitai yace " ni zan fita gun amsar gaisuwa." Basira ta mike ta koma ciki, kallan Abu Turab tai sannan tai shiru tana tunani, randa ta zubar da jini sosai har ta d'auka tayi b'ari shine ya fara zuwa mata, ba shakka ranar abu d'aya taitacu wato tuwon da Magajiya ta kawo mata, sannan ansha sanar da ita akan ta kiyayi Magajiya da Yayanta dan hatta Mahaifiyarsa sai datace mata tai a hankali da Magajiya. Tuno maganar matar Yayanta tai, zumbur ta mike idanunta duk sun kumbura. Hijab ta zura tai waje, tana gani yanda mutane suka taro a waje amma da yake idanunta sun gama rufewa yasa tai gaba. Gidan Hakimi ta nufa inda Hisham yake, basu tsaya mata wasu tambayoyi ba suka mata izini ta shiga wani ya mata jagora, sai da suka kusa zuwa d'akin da yake sai wanda ya mata jagorar yace " bari na kirashi." Nan yai gaba, daga lungun dake bayanta taji ana magana kasa kasa, jitai ance " ina kallansa ya fita da daddare ni kuma da gulma sai dana bishi wlh a idona ya d'au kalanzir da ashana yai gidan." Nidai tsoro yasa na juyo, ni dama nayi mamaki sosai danaga Waziri kamar bai damu ba da haihuwar nan bayan kuma kowa yasan abokin takara zai zamewa d'an Magajiya nan gaba." Jikin Basira ne ya fara rawa, da sauri ta juya cikin kid'ima, tana shiga gida ta kalli Lantana dake cikin mutane alama ta mata da hannu akan tazo, d'aki suka shiga, Basira cikin rikicewa tace " Lantana ke Baiwa ta ce ko?" Kai ta d'aga, tacigaba " kin yarda da duk abinda zanyi?" Nan ma ta d'aga kai, Basira tace " zan fara fita, zan tsaya a karshen layin nan in nai minti biyar ki biyoni. Ba tare da tambaya ba Lantana ta amsa da to, Basira ta kalli Abu Turab tace "Dolene in kareka, nayi rashin yayana da matarsa akan shirme da rashin wayau na dan haka bazan yarda inyi rashinka ba a wannan halin, hawaye ne suka shiga zubo mata, lalai bazata taba yafema Hisham ba in har da bakin Magajiya itama bazata taba yafe mata ba, sannan zata kare d'anta har zuwa lokacin da zai girma ya daukar mata fansar abinda aka mata. Cewa tai Lantana ta fita, Lantana na fita ta had'e kai da gwiwa ta saki wani irin kuka mai tsananin ban tausayi. ******** Da yake yaran da suna dadewa kafin ma su dinga bud'e idansu sannan ko sun bude ma ba alokacin zasu fara gani ba shi yasa sam Basira batai tunanin an ma d'anta wani mugun abu ba. ********** Yanda suka tsara hakan ce ta faro, ta goya d'anta ta fita, ta dade da fita sannan Lantana tabi bayanta....... _To fa abin babba ne🙊_ *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *10* ( Abu Turab an haifeshi a shekara ta alif dubu d'aya da d'ari tara da saba'in da d'aya, shikuma Abdulmajid an haifeshi a alif dubu d'aya da d'ari yara da saba'in, karku manta farkon labarin a shekara 1970 aka fara wanda ya kasance ranar sunan Abdulmajid, a kuma shekarar ne Sarki ya auri Basira har ta samu ciki.) _Wannan tuni ne_ ******** Hisham ya fito sai dai baiga kowa a waje ba, ciki ya koma cikin halin ko in kula dan shi babbar damuwarsa bai wuce ya d'au mataki a kan Basira da d'anta ba dan tuni aka sanar dashi suna raye, ba shakka inya sake wani yunkuri za'a gano bakin zaren shiyasa yake tunanin in suka tafi a hanya ya zama dole ya san yanda zaiyi kafin su karasa garin. ********* Magajiya tun bayan tafiyar Hisham ta rasa inda zata sa kanta, ya zama dole ta fitoda wata sabuwar hanya ta yanda zatai in har d'an ya dawo, ita ta kasa yarda da komai ma. Mamaki ne ya kamata jin sallamar Jakadiya, ta dade sosai kafin ta bata izini, Jakadiya ta shigo tare da washe baki, ta matso kusa da Magajiya ta zauna a kasa sannan ta kalleta ta mata jinjina tace " Sai ke Sarauniyar da babu irinta, ba aiba kuma baza'ai irinki ba, kinci dubu sai ceto takawarki lafiya matar sarki, takawarki lafiya mamar sarki, takawarki lafiya Haj......." Wani banzan kallo Magajiya ta mata tace " me kike aikatawa yanzun?" Jakadiya ta washe baki tace " wato Ranki ya dade matsala aka samu ai yayatace bataji dadi ba shi......" Wani mugun murmushi Magajiya ta sakar mata tace "Babu ruwan kwai da aski, abinda nakeso naki shine ke din wacece?" Yawo ta had'iya sannan tace "taki ce sai dai......" Magajiya tacigaba " waye ya baki wannan matsayin wanda kike takama dashi?" Jakadiya tai zuruzuru da ido, da kyar tace " kece." Magajiya tai wata 'yar bazawarar dariya tace " kinsan da haka ke har kin kai matsayin da zakiyi tunanin yimin karya?ke d'in wacece da har...." Da sauri Jakadiya ta sa gwiwowinta a kasa tace " Magajita tuba nake, sai dai kafin ki yanke hukunci yakamata ki duba yanda nake miki biyayya, nasani sarai Yarima ba......." Gaban Magajiya ne ya fad'i ta kalli Jakadiya a tsorace, dama Jakadiya tasan wannan ce kadai hanyar dazaisa ta tsira inhar ta nuna mata ta san sirrinta. Jakadiya tai saurin rufe bakinta tana waige waige tace "tuba nake ranki ya dade, wannan sirri ne da zan rikeshi har kabari na, tuba nake da subutar baki." Magajiya ta danyi kifikifi da ido sannan ta daure tace " me kike san cewa?" Jakadiya tace " tuba nake Ranki ya dade ai sirri ki nawa ne, baza'aji wannan zance daga gareni ba." Ganin tabbas Jakadiya tasan wani abu sai dai da alama batasan duka ba yasa ta daure tace " tashi kije ni ina bukar hutu." Nan Jakadiya tai waje da sauri. Tana fita tai dariyar mugunta tace " ni da gidan nan da matsayina mutu ka raba." ********* Sarki ya kasa zaune ya kasa tsaye, yau ya kamata su Hisham su dawo sai dai yajisu shiru hakan yasa da kansa yai tattaki zuwa b'angaren Magajiya. Zagi(wanda yake ma sarki iso sannan yake zama a gaba duk inda zaije ya sanar da isowar Sarki.) Mikewa Magajiya tai cikin mamaki, masu kula da ita ne suka shigo suka kara sanar da ita, nan ta fito dan tarbarsa. Sai daya shiga ya zauna, sannan ya kalleta yace " Hisham fa? Bayau zai dawo bane?" Kallan mamaki tamai wato abinda ya kawoahi b'angarenta kenan?so yake yaji zancen matarsa da d'ansa kenan." Murmushi ta saki duk da bakincikin da take ciki tace " mai zaisa hankalin Mai Martaba ya tashi bayan na tabbata yanzu suna hanya?na tabbata ka matsu kamar yanda nima na matsu inga d'ana." Sarki ya d'an kalleta yace " niba saboda haka nake tambaya ba, akwai abinda nakeso najine daga bakin Waziri." Murmushi tai tace "Angon Karni ai ba sai kayi kara ba, nima d'a na ne." Kallanta yai yana mamaki, sai dai yana jin dadi sosai na yanda takesan d'ansa. Yace " Ina AbdulMajid?" Tace " d'azu Uwar Soro( Mahaifiyar sarki, ko yayarsa ko gwaggonsa. ko uwargidansa, wadda ta wanke shi. wadda ke iya gaya masa duk abin da ake jin nauyin gaya masa, ita ake kira uwar soro.) Amma ita Mahaifiyarsa take nufi dan a lokacin nasu ita ake kira da Uwar Soro. Murmushi yai sannan yace " ni zan koma." Kallansa tai a ranta tace ka gama abinda ya kawoka kenan? Amma a fili tace " ina godiya da wannan ziyarar Ranka ya Dade." Yana fita ta d'anyi kwafa cikin takaici tace " ni zaka wulakanta?" ************ Basira kam tana gaba Lantana na baya ta kasa mata magana ganin kawai tafiya takeyi da alama batama san inda takesa kafarta ba. Abu Turab na bayanta, ko da Lantana tai yunkurin ansarsa Basira taki. Sunyi tafiya mai uban nisa dan Lantana harta gaji, itakam tafiya kawai take dan hankalinta baya jikinta, tunanin yayanta da matarsa sun mata yawa, sai da taji Abu Turab ya sa kuka sannan hankalinta ya dawo jikinta. Kallan inda suke tai daji ne sosai juyowa tai ta kalli Lantana sannan ta nemi guri ta zauna ta kunto shi daga bayanta, Lantana ta zo kusa da ita ta tsuguna sannan tasa hannu ta fara danna mata kafarta dataga ta kumbura. Basira kam shayar dashi kawai take ko magana batayi, idanunta ya kafe kaf ta kasa ko hawaye bare taji sanyi a ranta. Sai da Lantana ta danna mata kafa sosai sannan ta kalleta tace " bakici abinci ba ranki ya dade." Basira kai kawai ta girgiza mata, ganin ya koma barci yasa ya fara neman goyashi, Lantana tai saurin amsarsa ta sashi a bayanta suka cigaba da tafiya. "********** Shikam Hisham da yamma yai tunanin zuwa gaisuwa sannan ya sanar da ita tafiyarsu gobe, dan ya tabbata in bai je ba sai gulmar abin ta bazu a garin killa ma dogarawan da suka zo su kai gulmar har masarautarsu. Bayan sunzo gidan ne, ya nemi a kira masa Basira ya mata gaisuwa, sai a lokacin aka farga da rashin su a gidan. Tashin hankali nan fa aka bazama naimansu, ganin Basira bamai yawo bace sannan ba Lantana ba kuma d'anta, wannan ya kara tadama mutane hankali, tun azahar ake nemansu amma ba labari.... Hisham kam hankalinsa ya kara tashi har ya fara zargin kila ko ta samu mota ne ta tafi Zazzau, wannan al'amari ya kara tada mai hankali sosai da sosai...... ********* Basira kam sai da ta fara hakki sosai sannan ta samu ta zauna, dan tafiya kawai suke sai dai in Abu Turab yayi kuka su tsaya yasha sannan su ci gaba da tafiya. Lantana ta matso tace "Ranki ya dade dan Allah ki samu ki huta?" ita kanta Lantana hakki take sosai ga magrib ta kawo kai dan rana saura kiris ta fad'i. Kallan inda suke tai, wani kauyeni da ba mutane sosai, nan suka karasa kauyen. Wani tsoho suka gani a zaune yana wanke alo da alama rubutu yai, lantana ta gaisheshi tace " Baba dan Allah ka taimaka mana da gun kwana zuwa gobe." Kallansu yai ya kalli Basira wacce ke tsaye kamar zata fadi, yace " ku shiga ciki kafin wannan ta samu ta kwanta. Lantana ta shiga mai godiya, Basira kam jiri ne yake d'ebanta, tsohon yace "kuyi sauri ku shiga." Da kayar Basira ta daure tace "Mun gode." Sannan suka nufi ciki. *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *11* Sun shiga ciki sukaga ba kowa a tsakar gidan, nan suka tsaya suna sallama, Basira kam jingina tai da bango. Wata matace ta fito daga bayan gida rike da buta a hannunta ta amsa sallamar tana kallansu, nan Lantana ta gaisheta ta amsa, Lantana zatai magana sai taji muryar tsohon nan ta bayanta yana cewa " 'yata basu guri su huta sai suyi alwala ki basu abinci." Ba tare da musu ba ta amsa da to, sannan tace " ku shigo." Sun shiga wani d'aki wanda da alama nata ne d'aki ne an sa gadu guda biyu d'aya nai rumfa kato sannan sai d'an karami a gefe, sannan ancika d'akin taf da jere na samiru da 'yan china. Akan tabirma data shimfid'a musu suka zauna, sannan ta zauna itama suka gaisa(wannan shine halin mutanen mu na da basa yarda ayi gaisuwa a tsaye ko me suke yi sunfiso suna daga zaune a gaisa) Nan ta mike tai waje, Abu turab ya d'an fara abin kuka, hakan yasa Lantana ta kuntoshi daga bayanta ta fara jijigashi ganin ita kanta Basira yunwa takeji ina zai sami ruwan nonon da zaisha? Itakam tana tausayin Basira ganin tana tafe da d'anyen jego. Matar ce ta sake shigowa rike da fitilar kwai ta ajiye musu sannan ta mike zata fita, kallan Abu Turab tai cike da sha'awa tace " Tabarkalla masha Allah sai dai da alama ba'a dade da haifarsa ba." Lantana tai murmushi tace " yau fa kwanansu biyu." Cikin tsananin mamaki ta kallesu tace "da jego haka d'anye kukai tafiya?" Lantana tai shiru batace komai ba, kallan Basira tai wanda ganin yanda ta galabaita yasa ta fahimci itace Uwar, waje tai da sauri ta karasa murhu ta kada miyar kuka wanda dama ta saka komai kadawa kawai zatai. Tana gamawa ta kawo musu tuwon dawa miyar kuka tasha manshanu. Nan fa suka fara cin abinci, sosai Basira taci abinci. Sai da suka gama sannan Lantana ta tashi tai sallah tunda Basira tana fashin sallah na jinin haihuwa. Sunyi shiru a d'aki shikam Abu Turab bacci kawai yakeyi. Basira tunani duk ya isheta da bakin cikin yanda rayuwa ta risketa. Daga waje sukaji kamar ana dan fada, Lantana ta kalli Basira, jisukai ancigaba da fada " wlh yau bazan bar gidan nan ba sai Shehu ya biyani kud'ina kaf dan kuwa na gaji da wannan rainin wayan." Hakuri sukaji ana badawa amma kamar zuga matar ake sai kara masifa takeyi da k'ak'aji. Basira ta daure ta mike ta fita wajen, Matar da ta kula dasu ta gani zaune a gefe tana kuka, sai kuma wani mutumi a tsaye kusa da ita, ga matar nan da take ta masifa a tsaye a kansu. Wata matace ta fito daga wani d'aki daga gefensu ta saki wani gud'a cikin farin ciki tace "Allah kasheni saboda farinciki, lalai yau take sallah a gurina, anje anci bashi anyi aure gashi an kasa biyan kudin da aka ranta, yo dama ina za'a iya biya tunda an auro mai farar kafa?" Basira ta kalli matar yanzu ta gane inda abin ya dosa, da alama waccan din uwar gida ce, mijin yaci bashi ya auri wannan gashi kuma ba damar biyan kudin?" Mai kudin ta kara zak'ewa tana ta zabga masifa, Basira ta fito ta zo kusa da matar sannan ta zare sarkar dake d'aure a wuyanta, sarka ce ta azurfa wanda a waccan lokacin kudi ce sosai, cikin mamaki matar ta kalleta sannan ta amsa ta shiga dubawa, tabbas azurface mai kyau da tsada wacce kana gani kasan sai mai hali sosai shine zai sa ta. Shehu ya kalleta cikin mamaki sannan ya kalli matarsa yace " wacece?" Hawayene ya zubo mata, zatai magana matar tace " kina nufin kin bani duka?" Basira tace " ki saidata kid'au kud'inki ki ba matar nan ragowar." Wannan d'ayar matar mai guda ta matso da sauri tace " baiwar Allah ked'in wacece?" Basira ta juya ba tare da ta amsata ba ta koma ciki, Dattijon nan wanda ya kawo kai daidai lokacin da Basira ta mika azurfa ya share kwalla da ta taru masa, ba shakka dama yaji ajikinsa alhere ne su yana kallansu ya kalli yaron. Matar ta kalli Shehu tace " Shehu ina ka samo wannan?wlh ka bincike ta in har ba matar wani hamshakin d'an kasuwan bane to tana da dangantaka da sarauta, inba haka ba a wannan zamanin waye zai baka wannan shamfad'ed'iyar azurfar?" Shehu ya fizge azurfar daga hannunta yace "uwar san banza kud'inki dana ranta ko rabin wannan baikai ba, inyaso gobe kizo muje mu sai data inbaki kud'inki." Haushi ya kamata, haka tanaji tana gani tai waje. Uwargidansa ta matso da sauri tace "Shehu kawo na ajiye ma,kasan na iya ajiya." Harara ya maka mata yace "kingama gud'ar?" Kallansa tai cikin zolaya tace "kai bakasan wasa ba?" Tsaki ya ja sannan ya mikama Amaryarsa azurfar yace " ajiye tukunna sai na nemi shawar Baffa." Yana fad'a yai hanyar waje, a tsaye yaga Mahaifinsa, tsayawa yai kusa dashi kansa a kasa. Mahaifinsa yace "biyoni ciki." Nan yai gaba shima ya biyoshi. A tsakar gida ya tsaya, nan Amaryar tai saurin shimfid'amai tabirma, ya kalleta yace "sannu 'yata, d'an shiga ki kiramin bakin nan." Nan tai ciki da sauri, sun fito sun zauna a kan wata tabirmar, nan ya kalli Shehu yace " Zauna kaima." Nan ya zauna matansa ma duka suka zauna. Shiru ne ya biyo bayan kafin yace " Bismillahi Rahmani Rahim, ita bismillah ana san a fara ta akan duk abinda mutum zai aikata, dan haka yana da amfani mutum ya dinga yinta akai akai." Kai suka jinjina sannan yacigaba " Baiwar Allah ya sunanki?" Basira! Abinda ta fada kawai kenan kanta na kasa, yacigaba " daga ina kuke?" Tace " katsina." Yace " bazan tambayeki rayuwarki ba da yanda kikayi ta da abinda ya fito dake ba sai dai inaso inji abu biyu, na farko wannan yaron ta wani hanya kika sameshi?" Lantana zatai magana Basira ta rike mata hannu sannan tace " Allah shine shaidata aure nai na sameshi." "Alhamdulila!" Abinda ya fada kenan sannan yace " tambayar karshe, Yanzu da kuka fito ina zaku?" Basira tace " ni kaina bansani ba, na rasa yayana wanda shi kadai ya ragemin sannan dole ne in taimaki d'a na." Shiru yai kafin yace "Shehu." Da sauri yace "Naam Baffa." "a guara musu bangaren mahaifiyarka su zauna." Ya amsa da to, sannan yacigaba " ku zauna anan har iya lokacin da kukaji zaku koma, ni limami ne a nan garin kar kusa komai a ranku ku zauna anan kamar kuna gidanku." Godiya suka shiga yi, Shehu ya mika mata azurfarta, yace " karki damu zan...." Kai ta jijiga sannan tace " karka damu nayi ne dan Allah da kuma darajar taimakon da aka mana, nima bani akai dan na bada kuma ba wani abin bane." Da wannan aka tashi. Amarya wato ( Kubra) ta mike tai b'angaren mahaifiyar shehu wacce ta rasu wata 5 da suka wuce, b'angarenta daban ne dan sai ka d'anyi tafiya kadan ka shiga kofa sannan zata sadaka da b'angarensu. ************ Tashin hankalin da Hisham ya shiga baya misaltuwa haka suka isa Zariya duk ya gama rikicewa, suna isa yai fada da sauri, Mai Martaba kam ana cewa Hisham ya iso hankalinsa ya kasa kwanciya saboda tsananin farin ciki, kofa kawai ya kurama ido yana jiran shigowar Hisham. Ganin Hisham ya shigo yasa yai ajiyar zuciya, nan Hisham ya matso duk ya birkice ya gaidashi ya d'auka zai haushi da fada akan yabar matarsa ta taho ita kadai, sai jiyai Sarki yace "Hisham ka dawo lafiya? Sannu da kokari ba shakka ka sha tafiya." Hisham ya share zufa cikin tsoron abinda zai faru, Sarki yace " ka je gida ka huta kasha tafiya." Nan Hisham yai godiya yai waje. Mai martaba yai murmushi, yau zaiga Basira da d'ansa, burinsa na sa wannan suna yayi. Bazai taba mantawa ba tun sanda mahaifinsa ya bashi labarin sunan a lokacin da ya ganshi ya kwanta a kasa, ya sa aransa sai ya sa sunan nan. (_Sunan Abu Turab sunane wanda Manzon Allah ya sawa Sayaddina Ali a yayin da ya ganshi ya kwanta a kasa, yai murmushi yace Abu Turab wato Father of Soil." Murmushi ya sake yi. Shikam Hisham na fita yai gun Magajiya da hanzari. Tana tsaye ya sameta dan itama hankalinta ya tashi jin ance Hisham ya dawo amma shi kadai ne ba tare da Basira ya dawo ba. Yana shigowa ta tareshi da cewa " Yaya meke faruwa?" Hisham ya rikice yace " Magajiya muna cikin matsala." Matsala?tame kenan?" Nan ya kwashe komai ya sanar da ita, kanta ta dafe cikin tashin hankali tace " yanzu kenan bamusan a wani hali take ba daga ita har d'anta?" Yace " tuba nake." Wani tulu dake gefenta ta buga da karfi hakan yasa ya fashe, cikin tsoro Hisham ya kalleta, idanunta sunyi ja cikin fada tace " meyasa baka aiki da hankali? Me kake tunani zamu cema Sarki? Bamusan ta mutu ba ko tana raye, in mukace mai ta mutu ta dawo fa? Muce me? In kuma mukace tana raye to tana ina? Me yasa Hisham sam wani sa'in kanka baya aiki? Ni kaji daga bakina nace ka kona musu gida? Waye ya baka damar aiwatar da abinda ban umarce ka ba?" Hisham takaici ya kamashi, me wannan yarinyar take nufi? Cikin fad'a tace " jeka banasan ganinka sannan kar ka shigo gidan sai nan da kwana biyu ni zan san yanda zanyi." Jiki a sanyaye yai waje, wani dogon tsaki taja ta d'aura hannu akai cikin takaici yanzu ya zatai? Shiru tai ta shiga dogob nazari........ _Hmmmmm_ *ABU TURAB TEAM🤝🏼* .. 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *12* Ana Magrib Magajiya ta kintsa tsaf sannan ta aikama da Sarki zuwanta, alokacin hankalin Mai Martaba ya gama tashi dan yana tasowa daga fada ya aika wani bafaden sa akan ya dubo masa lafiyar matarsa da d'ansa kafin yazo sai dai abin mamaki dawowa akai aka sanar dashi rashin isowarsu gidan. Magajiya ta iso a lokacin shi kansa ya matso ya ganta dan yana san jin abinda ke faruwa. Bayan ta shigo ne ta zauna a inda ta saba zama wato d'an nesa dashi kadan, sannan ta numfasa cikin isa da kuma nuna alamar damuwa tace " Ranka ya dade muna cikin matsala fa?" Kallanta yai cikin mamaki sai dai bai amsa ba, itama ta kalleshi sannan tace " Basira bata dawo ba." Kallanta ya sakeyi nan ma bai tanka ba, idanu ta runtse cikin alamar kunar zuci na tausayi tace " gobara ce ta kama da gidansu a daren jiya." Lalai wannan kalma ta d'agamai hankali wanda bai san sanda ya mike tsaye ba, Magajiya ta kalleshi cikin kulawa tace " Yayanta da matarsa sun rigamu gidan gaskiya." Sarki a tsaye yake kawai dan hankalinsa ya kai koluluwar tashi, ta cigaba tare da share idanu kamar irin mai kwallar nan, tace Basira da d'anta dai ba abinda ya samesu sai dai firgita datai da abin yasa ta fita da gudu wanda har safiyar yau ba wanda ya ganta. Hankalin Sarki ya kara tashi ya koma Ya zauna dabas kamar ba sarki ba. A hankali ta taso tazo inda yake tasa hannu ta kamo nasa hannun tace " nasani sarai hankalinka ya tashi sosai kamar yanda nawa ya tashi, shiyasa na rasa mai zance maka, Hisham tun safe yake nemanta amma ba labari wanda hakan ne yaga dole yazo ya sanar dakai asan abinyi." Kallanta yai ji yake kamar ya saki wani irin ihu na bakin ciki, Magajiya cikin murya taban tausayi tace " Basira ba yarinya bace na tabbata zata dawo hankalinta ne ya tashi har yasa tai wani hannu sai dai fatan Allah yasa ta fad'a hannu na gari." Sarki ya d'ago cikin tashin hankali wanda tunda Magajiya take bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba, kallanta yai cikin kakkausar murya yace " inasan kad'ai cewa." Kai ta jinjina alamar to, sannan ta mike ba tare da tace komai ba tai waje. Tana fita ta kalli kofar d'akin tai wani murmushi tace " kai da Basira sai a lahira dan duk yanda kaso ko ita taso baku isa ku kara zama tare ba bare har kaga d'anka ka fahimci menene d'a na jini." Juyawa tai tacigaba da tafiya ana take mata baya cikin kasaita da tak'ama. ************ Shikam tana fita ya runtse idanunsa kam jiyai hawaye ya gangaro mai sau d'aya, mikewa yai yaje jikin tagar d'akin ya bud'e ya kurama taurari ido,jiyake kamar zuciyarsa zata fashe ga zuciyarsa ta fara masa sake sake mara amfani, yana tsaye yana kallan taurari sai dai a zahiri tunani ne fal ransa, nan ya shiga tunanin rayuwarsu da abokinsa da kuma matarsa ga kuma bai taba ma ganin d'ansa ba,kasa jure abinda ke ransa yai ya tsugunna a gun tare da dafe kansa wanda ya fara sara mai.... A wannan ranar Mai Martaba ko gadonsa bai hau ba bare ya samu danar rintsawa. ************ Basira ma bataga bacci ba a wannan ranar, tunani ne kawai ke mata yawo a ranta, ido ta kurama d'anta tana ji wani abu na taso mata, ya zatayi? Zama zatai tayi anan saboda tsoron kar wani abu ya samu d'anta? In tai hakan kenan ta raba d'anta da mahaifinsa, sannan auranta fa?" Wad'annan tunanukan sun mata yawa fal aranta wanda sukasa idanunta suka kafe kaf. *********** Magajiya ta sanar da Hisham yanda sukai da Sarki sannan ta sashi yaje ya nema ayima Basira magani akan karta waiwayi gida, a mata maganin da zaisa taji sam batasan gida." ******** Tun bayan tasowar Abu Turab suka kula da rashin ganinsa, da farko sun d'auka lokacin ganin nasa ne baiyi ba sai dai ganin ya kai wata 4 yasa suka fahimci akwai matsala da idanunsa, haka ya taso ba idanu sai dai Allah ya bashi hazaka wanda ko zama kai dashi na awanni sai ka fahimci hakan, yanada baiwa sosai ta fahimta da rike abu. A duk sanda Basira tai tunanin komawa gida sai taji zuciyarta ta kuntata, hakan yasa ko maganar batasan a mata, Lantana kam ko da wasa bata taba tambayarta ba, haka mutanen gidan. Abu Turab har yakai shekara 5, Baffa shi yake koya masa karatu, yana tsananin san yaron saboda san karatunsa da hazakarsa, Basira ta d'aurashi a kan tarbiyya mai tsananin gaske, ko laifi ya mata wanda bai kai ya kawo ba haka zatasa shi a tsakiyar rana gashi bashida ido sai yayi kusan awa uku a tsaye, gashi bai isa yai kuka ba, dan kuwa in ya kuskura yai to fa lalai zai gamu da hukunci mai tsananin gaske, a haka in ka kalleshi bazaka taba cewa baya gani ba dan kuwa idanunsa garau suke, bata bari a taimaka mai har sai intaga yana neman faduwa ko yana neman taimakon sosai, komai da kansa yake yi, zakasha Mamaki in har kaga yanda Basira take tsananta tarbiyar d'an nata. Abu Turab ya taso mai tsananin jarumta gashi dama magana bata wani dameshi ba dan ko abokai bashida shi sannan yaro ne wanda in yana abu dole ka kalleshi domin jinin sarauta na yawo a jikinsa yana da jinkai sannan ko magana yakeyi zakasha mamaki. Shigarsa Shekara bakwai ga tsufa ya kara kama Baffa, yanzu ko fita zaiyi sai an taimaka masa, a yau ya tashi da zazzab'i wanda yasashi zama a d'aki, Abu turab na zaune kusa dashi yana mai karatu kamar yanda Baffa ya sashi. Bayan ya gama ne Baffa yace " D'ana(haka yake cemai.) kiramin Mahaifyarka." Abu Turab ya mike rike da karamar sandar da yake tafiya da ita ya isa b'angarensu, A waje yaji muryarta hakan yasa ya matsa kusa ya sanar da ita sakon baffa. Mikewa tai ta zura hijabinta ta fita, Lantana na zaune tana sana'ar mangyad'a wanda dashi suke rayuwa, ya matsa kusa da ita dan yanajin sautin aikin datake, zaiyi magana yaji tace " Ka zauna." Tai maganar tare da tashi a kan kujerar ta ta nuna masa gun zama. Shiru yai hakan yasa ta rike hannunsa ta zaunar dashi. Murmushi yai yace " Lantana baki tab'a kiran sunana ba tunda nake dake." Kasa tai da kai a ranta tace " ina na isa?" Murmushi ya sakeyi yace " Kujerar da kike kai kika bani ko?" Batai magana ba sai dai a ranta tace " dole na ne ai." Mikewa yai ya nufi hanyar cikin d'aki." ********* Basira zaune kusa da Baffa wanda ya ke a kwance, Baffa ya kalleta yace "Banso na miki magana da kaina ba sai dai inaji a jikina lokaci na ya kusa hakan yasa dole na kiraki." Kallansa tai sannan ta maida kanta kasa, Baffa ya cigaba" Basira ya kamata ki koma gidanki inhar akwai aure akanki to fa lalai kina d'aukan zunubi ne." Kallansa tai idanunta suka kad'a sosai ga mamakinsa hawaye yaga tana zubarwa. Kallanta yai cikin tausayawa yace " ba tillasta miki nake ba sai dai shawara nake baki, in har da aure akanki nace nima ba wani abu ba." Hawayenta ta share sannan tace "Sunana Basira.........." Kaf abinda ya faru da ita ta sanar dashi. Baffa hawaye ne ya gangaromai saboda tausayi, shiru ne ya biyo baya a d'akin domin kuka sosai takeyi miken dake binne a zuciyarta ya tashi. Sun dade a haka kafin Baffa yahau addu'a, sannan yace" nayi zargin wani abu sai dai rashin sanin labarinki yasa ban tab'a sanar dake ba, sai dai yanzu zargin da nakeyi inaji ajikina hakan ne." Kallansa tai cikin rashin fahimta, Baffa ya cigaba " D'ana, wato Abu Turab banaji a haka Allah ya halliceshi." cikin mamaki tace " kamar yaya?" Yace " sihiri baya taba zama daidai da kaddarar Allah." Idanu ta zaro tace " kana nufin....." "kwarai da gaske, bazan rantse ba kuma bazan miki alkawari ba sai dai kafin Allah yad'au numfashina in dai har sihirine to ni zan karyashi da yardar Allah, sannan inaso kimin Alkawari In har d'anki ya warke zaki koma gun mijinki, Allah ne kadai yasan halin da yake ciki na rashin ku." Basira tace " Nagode kwarai sai dai Baffa na rasa dalili sam banasan ai zancen komawata gidan." Hannayensa ya had'e ya shafi fuskarsa yace " dole ki cire tsoro a ranki ki taimaki d'anki, ba wai dan ya hau mulki ba a'a sai dan tsira da rayuwarsa, kina tunanin taimakonsa kikai na kawoshi dajin nan? Ko kina tunanin zaki iya canza abinda Allah ya kaddara a kansa ne?" Kai ta girgiza alamar A'a. Baffa ya cigaba " Abu Turab inaji a jikina yaro ne wanda za'ayi alfahari dashi nan gaba, kada ki kuskura ki rabashi da mahaifinsa, ki zamanto mai yarda da kaddara mai kyau da mara kyau." Hawaye ta share sannan tace " na maka alkawari inhar sihirine yana warkewa zamu koma in kuma ba shi bane ma zan maidashi gun Mahaifinsa." "Alhamdulila, nagode da amfani da shawarata da kikai sannan inkinje ki turomin d'ana sannan ki bashi kaya kala uku a guna zai dinga kwana, yaro ne mai hazaka da ilimi wanda a shekara 7 ya haddace izu 30 wanda tunda nake ban taba ganin yaro mai wannan baiwar ba, ni dashi zamuyi yakin ganin mun warware komai." Godiya sosai Basira ta shiga yi. *ABU TURAB TEAM🤝🏼* ẞ 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *13* Haka Baffa da Abu Turab suke wuni karatu da addu'oi kala kala sannan daga dare yashiga kashi uku Baffa yake tashinsa su shiga saloli da addu'oi, ko waje baya fita, a kwanansu na hud'u Abu Turab ya fara wasu mafarkai cikin dare yake farkawa wani sa'in da kuka sai dai daga ya tashi yake manta mafarkin. Sun dage sosai da addu'oi, karatun qur'ani da saloli. Yau satinsu d'aya kenan Abu Turab na kwance yana bacci hankalinsa a kwance, yau baccib dadi yake masa gashi ko mafarki baiyi ba, Baffa ya sa hannu ya tabashi yace "D'ana tashi lokaci yayi." Mamaki abin yaba Baffa ganin bai tashi ba, kallan fuskarsa yai sai dai kana kallansa zakasan yana cikin kwanciyar hankali, Baffa yai murmushi sannan yai bismillah ya kara taba shi, addu'ar tashi daga bacci ya fara karantowa bayan ya gama ne ya bud'e ido a hankali duk da yasan duhu kawai zai gani sai dai me? Dishi dishi ya fara gani, cikin tsananin mamaki yace " Baffa ido na." Baffa ya dafashi yace " menene? Me idan naka yai?" Murza idan ya shiga yi, Baffa ya shiga karanto addu'oi yana tofa mai, Abu Turab ma yanayi. Cikin tsananin mamaki da al'ajabi Abu Turab yaga tsohon dake kusa dashi, a hankali yakai hannu inda Baffa yake yace "Baffa!" Kallansa Baffa yai shima ya kasa magana sai addu'a yakeyi Allah ya taimakesu. Abu Turab ya tsugunna kusa dashi ya rungumeshi sai ya saka kuka. Baffa ma hawaye ne ya zubomai dan ya fahimci ya ganshi. Abu Turab cikin kuka yace " Baffa na ganka, Ina ganin komai ga katifarka, ga kayanka nan a lank'aye, ga kwanan abinci nan ga leda nan a tsakar d'akin, Baffa ina ganin komai." Idanu Baffa ya lumshe yace " Alhamdulila lalai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah." Tashi muyi alwala muyima Allah sujjada. Mikewa yai cikin wani jin dadi mara misaltuwa yai waje. Bayan sunyi addu'ar godiya ga mahallici ne ya kalli tsohon yace " inje gun Ummana?" Baffa yace " ka barta ta samu bacci zuwa asuba." Nan ya zauna cikin zakuwa, sai kallan abubuwa yakeyi...... Ana asuba yai b'angaren da gudu jin kofar a bud'e ya shiga bugawa, Basira ta mike a d'an tsorace ta matso tace "waye?" Cikin jin dadi Abu Turab yace " nine Umma." Mamaki ne ya kamata da sauri ta bud'e, ya matso da gudu ya rungumeta yana kuka yace " yau Allah yayi na ganki." Idanunta ne suka ciciko da kwalla, ya saketa sannan ya kura mata Ido yace " Umma na ganki, Umma naganki." Rungumeshi tai itama tace Alhamdulila. *********** Satinsa d'aya da warkewa Baffa ya kara kiranta ya mata maganar tafiya nan, tace nan zuwa kwana uku zasu tafi. Zaune take a d'aki tana kan gado Lantana na kasa haka shima D'an nata. Kallansu tai tace "inaso duk ku bani hankalinku, akwai abinda nakesan sanar daku masu mahimmanci guda biyu." Tai d'an ajiyar zuciya sannan tacigaba" na farko zuwa jibi zamu tafi Zariya." Da sauri Lantana ta kalleta shikam baisan me hakan yake nufi ba shiyasa bai wani damu ba. Tacigaba " abu na biyu wanda yafi komai mahimmanci shine inaso Lantana kada ki kuskura ko da wasa ki nuna Abu Turab na gani." Cikin mamaki ta kalleta, Basira tace "wannan umarni ne ba shawara ba." Da sauru Lantana tace " angama Ranki ya dade." Basira ta kalli Lantana tace " d'an bamu guri." Da sauri tai waje. Basira ta kalli d'anta ta mikamai hannu hakan yasa ya mike tare da zuwa inda take. Basira ta zaunar dashi kusa da ita sannan ta rike hannayensa biyu tace " nagode kwarai da baka tab'a tambayata mahaifinka ba." Kallanta yai sannan yai murmushi, ta cigaba " ka nutsu sosai da abinda zance maka." Kai ya d'aga alamar to sannan ya kada nutsuwa, tace " zamu koma gidan da mahaifinka yake wato gidanku sai dai ina tsananin tausaya maka, da farko inaso kada ka nunama kowa kana gani, hatta mahaifinka ka zama makaho a gaban kowa, ka zama mai ido agabana kad'ai." Cikin mamaki yace " me....." Kallan datai mai yasa yai shiru, tacigaba " banaso ka tambayeni dalilin hakan dan kuwa inka mallaki hankalin kanka na tabbata dakanka zaka sanar dani komai, domin zaka samu cikaken amsar tambayarka." Kai ya d'aga alamar to,tace " Abu Turab!" Yanda ta kira sunansa da kakkausan murya yasa ya kalleta jiki a sanyaye, tace "kamin alkawarin zakai wannan abin?nasan kasan me alkawari yake nufi a muslunci ka kuma san hukuncin wanda ya karya." A hankali yace "na miki alkawari ko mai zai saman bazan nuna ina gani ba." Ajiyar zuciya tai na jin dadin baiwar da Allah ya mata wato na azurtata da wannan yaron, tacigaba " gidanku ba kamar gidajan daka sani bane, dolene ka nutsu kaji me zance, da farko duk yanda ranka yaso da b'acci banaso ka nuna, sannan abu na biyu banaso ka zama ragon yaro." Kallanta yai baice komai ba, ta riga tasan wannan sai dai ya zama tuni amma tun yana karami ta horar dashi akan haka, ita dama matsalarta shine taurin kansa dan inbaiyi niyyar abu ba ko za'amai dukan dazai kasa tashi tofa bazaiyi ba, wannan hali nasa shi take jiye masa. Ta riga ta d'au alwashin sadaukar da komai nata dan ta kare d'anta. Sun dade rike da hannu juna tana mai fada a karshe tace " in muka koma gun Mahaifinka banaso ka yawaita cewa komai sai ni, dolene ka rage nuna damuwarka akaina, kallan mamaki ya mata a ranta tace (in aka fahimci nice komai naka to lalai za'a nemi yin amfani dakai da sunana wanda nikuma ba lalai in iya kwatarka ba daga hannun makirai." Abu Turab zaune kusa da Baffa yana jin nasiharsa sun dade suna hira kafin Shehu yazo su zauna, Abu Turab yanajin hirar tasu har bacci ya d'aukeshi. Sukam sunyi hira sosai, da shehu ya mike zai tafi sai yasa hannu zai d'auki Abu Turab akan kaishi b'angarensu. Baffa yace " barshi anan so nake na kwana dashi." Nan Shehu ya ajiye shi ya tafi, Baffa ya d'auko rubutun daya wanke ya tashi abu turab yace ya wanke fuskarsa har zuwa kansa, yana magagin bacci ya wanke sannan ya kwanta, Baffa ya dinga mai addu'a sannan ya kwanta. Jin kiran Sallah yasa Abu Turab ya mike, mamaki ne ya kamashi ganin Baffa a kwance yana bacci, kusa dashi ya matsa ya shiga tashinsa, hankalinsa ya tashi ganin ko motsi bayayi. Da gudu yau cikin gida b'angaren Shehu, a waje ya sameshi yana alwala matarsa na tsaye kusa dashi. Abu Turab ya kalli Shehu yace " Kawu kazo Baffa yaki tashi daga bacci." Inalilahi wa ina ilaihi Raji'un wannan kalma ita Shehu yai ta ambata, dan ko ba'a fada ba ko bai gani ba yasan me hakan yake nufi..... Allah ya jikan Baffa da Rahama Ameen........ ********* A ranar da akai uku su kuma suka shirya tafiyar tasu. _Wannan kenan_ *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* _'Yan grp na Kainuwa Dashen Allah ga naku shafin, tnx 4 d love....._ *14* Sun shirya tsaf ba kaya suka d'auka ba dan komai nasu anan tabarma matan gidan saboda tasan inda zasuje. Shehu shi ya kawosu inda zasu hau mota dan a wannan shekara wato ta 1978 (shekarar Abu Turab 7 sannan shekararta takwas da aure.) a wannan lokacin an sanu cigaban wata yar kurkurar mota bayan akuri kura da motar itace, sai da suka shiga sannan Shehu ya musu sallama ya juya ya tafi, matansa sunsha kuka dan kuwa Basira ce silar zaman lafiyansu. A hanya Basira sai kara jaddadama d'anta takeyi akan abinda takesan yayi. Daga baya bacci yai awun gaba dashi, Lantana ta kalleta sannan tace " Ranki ya dade inasan tambaya duk da dai ba hurumi na bane." Basira ta kalleta alamar tana ji, Lantana tai ajiyar zuciya sannan tace " me zakice ya hanaki komawa? Dan ina tsoron kar a miki wani sharrin." Basira tai murmushi tace " Lantana kenan, a da na yarda ni sukuwa ce wacce bata tunanin abinda zai faru, sai dai yanzu inada abinda nakesan karewa dolene in canza daga sukuwa zuwa nai dabara, karki damu." ta karasa maganar tare da dafata. Sun dade suna tafiya kafin a d'an tsaya saboda wasu yaran na mota najin fitsari, nan fa aka fifita hardasu Abu Turab, bayan an dawo ne aka ci gaba da tafiya. Sai yamma lis suka isa garin na Zariya. Basira bayan sun sauka ta kalli Lantana tace "zaki iya gane gidan da na fara zama?" Kai ta kada mata alamar eh, ta d'aura da cewa "sosai kuwa." "Can zamu wuce." Ba tare da tambaya ba Lantana ta amsa da to, Abu Turab ya rike sandarsa kamar yanda mahaifiyarsa ta umarceshi, dayake dama idanta a bud'e yake tarau a da d'in ma sai ance miki baya gani tukunna dan in kika ganshi haka bazakiyi tunanin rashin ganinsa ba. Haka sukai ta tafiya har suka isa gidan, dan ma ba nisa sosai. Suna isa suka karasa bakin kofar da fadawa biyu ke gadinta, Lantana ta kallesu sannan ta musu gaisuwar da take nuna alamar a masarauta take, sannan ta d'aura da cewa " Matar Mai Martaba ce Gimbiya Basira." Kallan juna sukai alamar basu fahimta ba, dan kuwa su basu santa ba, ba'a dade da kawosu nan ba, sannan ko da ace ma sun santa ai shekarun dayawa dan kuwa mutane dayawa sun manta da ita, wasu sai da insun tunata susa dariya, wasu kuwa suyi tunani ko tana raye? Basira ce ta kallesu tace " bud'e mana, shiga zamuyi sannan d'aya ya zauna dan ya tabbatar da mudin ba da wani nufi mukazo ba, sannan d'aya yaje Fada ya sanar da Mai Martaba yayi baki na sirri anan." Kallan mamaki suka mata, Basira ta kalli na hannun dama tace " naga kamar kai bazaka iya mana komai ba in ma munzo da wani nufi ne, ganin yanayinka, dan haka so nake kaje ka samu sarki in ba hali ka samu Barde kace ya sanar da Sarki a kwai bakin sirri a gidansa na cikin gari." Kallanta yai yana kokonto, Basira tace " kada ka kuskura ka sanarma kowa sai mutanen nan biyu, ganin kafin kaga Sarki abin zai zama mai wuya ina shawartarka ka sanarda Barde, kada ka fadama kowa inba shi ba." To, ya fada yanzu kam ya fara yarda da sunsan mai Martaba duk da dai bai yarda matarshi bace sai dai gani kamanni iri na Abu Turab yasa ya san tabbas akwai hadin jini na sarki a jikinsa. Nan yaja d'ayan yace "ka kula dasu kafin naje na dawo." Nan ya fara tafiya, sukuma suka shiga ciki. Suna shiga Basira tasa d'anta yai wanka sannan ta bashi rigar data taho mai da ita kala d'aya. Itama wankan tai Lantana ta d'auko mata kaya tasa, dan kuwa dana akwai ajiyayun kayayyakin datai amfani dasu. Nan Lantana ta shiga kitchen dan sama musu abin ci. ********** Bafaden nan ya dade kafin ya samu ganin Barde nan ya sanar dashi sakon, mamaki ya kamashi bakon sirri? Ya kalleshi yace "sanar dani abinda ya faru tundaga farko." Nan ya kwashe komai ya fad'amai sai dai ya manta sunanta shidai yasan ance matar sarki ce sannan yaganta da yaro." Barde mamaki ya kamashi yace "shikenan koma gidan zan sanar dashi." Har Bafaden ya juya Barde ya kirashi, ya karaso da sauri, Barde yace " yaron shekararsa nawa?" Kai ya girgiza alamar rashin sani sannan ya dora da cewa "bazai wuce dai shida ko bakwai ba." Gaban Barde ne ya fadi sai dai yai saurin girgiza kai a fili yace " bazai kasance ita bace kar na tadama Mai Martaba hankali." Bafaden na tafiya shima ya koma fada, ko minti goma baiyi ba magrib tai, nan mai Martaba ya mike aka shiga takamai baya fadawansa. Turakarsa ya shiga, yana kokarin shiga makewayi dan kama ruwa da alwala jakadiya ta fara sallama. Amsawa yai tare da cewa " ya akai?" Ta kalli Zagi sannan ta kalli Barde tai kasa dakai tace "Barde ne ke neman iso Ranka ya dade, a gafarceni." Mamaki ya kama Sarki ganin Barde baya biyoshi, nan yai gyaran muryar dayake nuna alamar ya shigo. Nan tace "Godiya yakd Takawa." Nan ta kalli Barde tace " bismillah." Barde ya bud'e kofar ya shiga, a zaune yaganshi nan ya karasa ya zauna a kasa kansa na kasa yace "Tuba nake Takawa na katsema lokacin al'amuranka." Mai Martaba ya kalleshi yace "ya akai?" Barde yai dan huci yace "wai baki ne na sirri suke jiranka a gidanka na ciki gari." Cikin mamakin zancen yace " na sirri kuma? Me kake san cewa?" Barde ya kwashe komai shima ya sanar dashi, a zabure ya mike yace " Barde Basira ce! Basira ce." Barde yace "Mai Martaba kayi a hankali kasan bangon gidan sarauta akwai ji (azancin magana yai - yana nufin ya kula akwai masu lab'e.)" Sai alokacin hankalin Sarki ya dawo dan jin ance Basira ba karamin tadamai hankali akai ba, cikin murya kasa kasa yace " ka shirya ka fara zuwa gidan ni zansan yanda zanyi na fito." Barde yace "an gama Takawa." Su Jakaddiya kuwa an baje kunne ana san jigo gulma ko dayake ba ita kadai ba wasu fadawan ma hankalinsu duk yana d'akin, sai dai ba wanda yaji me akace sai dai sunji kamar an ce Basira kamar kuma Barira kamar dai wai suna ake fada da ya fara da Bas, abinda yasa ba wanda yai tunanin Basira saboda ganin tsawon shekarun, na farko shikansa sarki ba kiran sunanta yake ba bare suyi tunanin wani abun. ********** Mai Martaba kam wasu kayan yasa a jikinsa ana sallah ya samu ya wuce tare da bafadensa na kusa, sannan ya umarci d'ayan akan yace ya koma turakarsa ya kwanta sakamakon kansa dake sarawa. Sun samu sun isa gidan tun a hanya yaketa add'ua akan Allah yasa sune. Bayan ya shiga cikin gidan ya nufi kofar ya sa hannu kamar zai murd'a sai kuma ya fasa, karatun qur'anin dake tashi ya tsaya ji, can ya daure yai sallama, Basira tana zaune akan sallaya tanata addu'a akan Allah ya bata ikon shanye komai ya kuma sa komai yazo da sauki. Abu Turab na gefenta yana karanto suratul Rahman cikin kira'arsa mai dadi. Shiru Mai Martaba yai yana sauraron karatun. Gaban Basira ne ya fad'i jin sallamar muryar da ta kasa b'ace ma kunnuwanta, mikewa tai a hankali tazo bakin kofar ta bud'e gabanta nata fad'uwa. Kallan juna suka shiga yi cikin tsananin kewa da tausayama juna, a hankali hawaye ya zuboma Basira, Mai Martaba ya sa hannu ya riko nata hannu jin yake kamar a mafarki, ba shakka muryar d'ansa ne kenan yake karatu? Hakan yasa ya kamo hannunta ya shigo inda take a tsaye. Cak ya tsaya yana kallan yaron dake zaune kan sallaya yana karanto Suratul Rahman cikin kira'arsa mai dadin gaske, zuciyarsa ce ta karye ya juyo ya kalli Basira sannan ya nuna yaron da hannu ya kuma nuna kanshi da hannu alamar ( wannan nawa ne?)" Hawayenta ne ya gangaro sosai ta kada mai kai tana zubo dasu kamar ana zugo kukan. Sakar hannunta yai ya karasa inda yaron yake a hankali dan jikinsa duk ya gama mutuwa, Zama yai a gaban yaron kan sallaya, Abu Turab ya kura mai ido amma bai daina karatunsa ba, yana kallansa. Hannayensa Sarki ya kamo,hakan yasa yai sadakallahul azim. Sarki yace "ya sunan ka?" Ko kifta ido baiyi ba haryanzu yace "Abu Turab." Kalla. basira yai cikin jin dadi. Sannan ya nuna kansa yace "ka gane ni?ah ba haka zance ba, kasan ko ni waye?" Tunowa da alkawarin dayama Mahaifiyarsa yasa yad'an kalli gefe kad'an ya girgiza mai kai alamar a'a. Sarki yace "ina dama zaka sanni? Ni kaina sai yau na tab'a ganinka." Kai Abu Turab ya sake girgizawa yace " ba haka nake nufi ba, ba na gani ta ina zan ganeka?" Basira wacce ke tsaye tsoro duk ya kamata ganin yanda d'an nata ya kurama mahaifinsa ido ta d'auka ya manta alkawarinsu sai dai jin abinda yace yasa tau ajiyar zuciya. A zabure ya kalli Basira, ganin yanda idanunsa sukai yasa ta daure ta d'agamai kai tana hawaye tace " tun yana jariri idanunsa basa gani." Zuciyar Sarki ta kara karaya jiyake kamar ya sa kuka, da sauri ya jawo d'an nasa jikinsa ya kankameshi kam. Sundade a haka kafin ya sakeshi. Shiru ne ya biyo baya a d'akin, yana zaune kan kujera rike da hannun matarsa ya d'aura d'an nasa kan cinyarsa. Basira ta kalleshi tace "in wani ya ganka fa?" Murmushin yake yai ya shafa kan d'an nasa yace " duk laifinane, da bance kije gida ba d......." Kai tai saurin girgiza mai tace " ko kad'an ba kaifinka bane." Kallanta yai sai dai baice komai ba.. Sun d'anyi shiru kafin Basira ta kalli d'anta tace "koma can ka zauna zamuyi magana da mahaifinka." Nan ya mike ya koma can gun 'yan tumtum ya zauna sai dai hankalinsa na kansu. Jiyai Mahaifin nasa yace " basira ina kuka shiga?hankali na yayi matukar tashi." Murmushi tai tace " ka yafeni nasani nayi babban laifi sai dai ba komai bane ya hanani dawowa sai d'ana, ina tsoron rayuwar da zaiyi a gidan sarauta ba ido, ina tsoron wulakanci da gulma da habaici da zai fuskanta, nafarko ni ba wata mai matsayi ba sannan ga d'ana ba ido, tsoron wulakancin da za'amai yasa na kasa dawowa, sai dai tunanin raba d'a da mahaifi da kuma raba kaina da kai yasa na dawo." Tunda ta fara magana yake kallanta yauce rana ta farko da ta saki jiki take mai magana haka, murmushi yai sannan yace " na fahimcike na kuma gode da kika dawo gareni baki bari na mutu banga d'ana ba." Shiru suka d'anyi kafin yace " ku zauna anan in har kina ganin zaman can zai ma d'ana wahala." A ranta tace da kenan, yanzu in har na zauna anan wayasan me zasumin a bayan idanka?ai in kana tsoron kura ba inda yafi maka saukin zama irin raminta, domin duk abinta bazata taba kawo akwai wanda ya isa shigar mata rami ba bare tai farauta a ramin nata. Murmushi tamai sannan tace " a'a nafisan zamana kusa da kai sannan in na zauna anan yaushe Abu Turab zai dinga ganinka? Sannan in akaji labarin zamana anan baka gani xai jawo ma da ni kaina matsala? Kallanta yai yana kara mamakin yanda ta canza......... *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *15* Mai Martaba ya juya ya kara kallan d'an nasa zuciyarsa a raunane, ba shakka kam d'ansa na bukatar kulawa ji yake kamar laifinsa ne yasa yaron ya makance. Basira ganin yanda yake kallan d'an nasa yasa tace " Ba laifinka bane, kaddararsa ce babu makawa sai hakan ya faru ko da kuwa a gunka muke." Kai ya jinjina cikin tausayawa, tai murmushi tace " ka koma tun kafin mutane su farga da rashinka." Yace " haka ne, kiyi hakuri zuwa wasu 'yan kwanaki zan san yanda zanyi ku dawo ba tare da mutane sunyi zargin komai ba." Ta lumshe ido sannan ta murmusa tace " na yarda dakai." Mikewa yai a hankali yaje kusa da d'ansa ya rungumeshi kam sannan yace "sai da safe d'ana." Abu Turab ya d'aga kai. Haka ya fito tana bayansa, a tsakar gida taga Barde nan ya gaidata sannan ta juya ciki, su kuma suka tafi. Abu Turab ya matso inda take idanunsa fal kwalla sai dai ya rasa mai zaice, ya kuma rasa dalilin jin yana san yai kuka, kallansa tai tace " me kake shirin yi?" Yad'iye kukan yai sannan yace " bakomai." Ta mike ta wuceshi ta nufi cikin d'aki, zama yai dabas yanzu yana ganin mahaifinsa ba dama yace ya ganshi? Shikam ya kasa gane mai mahaifiyarsa take nufi da hakan. ********* Sarki ya kasa bacci sam sai juyi yake akan gadonsa, tayaya zai b'ulowa mutane da matansa? Mai zai fada wanda mutane bazasuyi zargi da korafi ba akan matarsa da d'ansa? Sam ya rasa amsar tambayarsa sai juyi kawai yakeyi. ********* Washegari da sassafe sarki yasa bafaden nan nasa ya tuko mota ya kawo musu kayan abinci sosai, duk wani abun bukata ya kawo musu sannan ya aiko da kudi akan a siyoma Abu Turab kaya da wasu abubuwan bukata. Wajen karfe 10 suka shirya itada Lantana da Abu Turab suka fito dan zuwa kasuwa siyo kaya. Suna tafe suna 'yar hira itada Lantana jikin wani shago ya tsaya dan shi sam bayasan shiga mutane da alama hakan ya faru ne saboda inda ya taso. Yana wajen shagon su kuma sun shiga ciki, kallan wata kantanga yake wacce akai mata zane da wasu rubutu wanda bai taba gani ba, ido ya kurama rubutun yanasan sanin namenene? Wasu yara ne su uku suka fito daga ciki sanye da fararen kaya riga da wando da hijabi, basu wuce shekara 5 ba, su biyu ne mata d'ayan kuma namiji ne. An tashi tara. Suna tafe kamar masifa biyun babbar macen da namijin, d'ayar wace take karama itakuma da alama kuka takeyi, kura musu ido yai yana neman amsar tambayarsa, daga ina suke hakan? Wata ce yaga ta fito da gudu 'yar karama bata wuce shekara hud'u ba, daga inda suka fito tazo ta d'akama babbar cikinsu duka ta kara zurawa da gudu, inda yake tsaye take yowa mamaki ya kamashi ya tsaya yana kallan ikon Allah, yana nan tsaye yaga tana nufoshi shi dai bai matsa ba sai kallan ikon Allah yake. Da gudunta kuwa ta cigaba, kai ya girgiza ya juya ya kalli inda Mahaifiyarsa take, yana juyawa yaji an wani irin hankad'eshi iya karfinta, dukansu suka fad'i a kasa tim, shikam ya fita jinjiki dan sar da hannunsa na hagu ya kurje, cikin fad'a ya d'ago dan ya mata magana, mamaki ne ya kamashi ganin ko a jikinta kad'e jikinta tai tana shirin kara sa wani gudun. Da karfi yasa hannu ya fizgo hijab d'inta ya dawo da ita inda yake. Kallansa tai sannan ta kalli wacce ta daka tace " dan Allah yahkuri ka sakeni karta kamani." A ransa yace wasa kike yarinya, saurin kauda kansa yai daga kallanta sannan yace " malama bakya gani ne?" Kallansa tai taga yasa hannu yana neman gefenta yana jujuyawa kamar irin neman inda fuskarta take yakeyi. Kusa da fuskarsa ta matsa ta kalleshi sannan ta mai gwallo, ganin baice komai ba yasa tasa hannu ta toshe baki tana dariya wato da alama baya gani. Hannu tasa ta fara kokarin zare hijab dinta alamar zata cire hijab din ta gudu ta barshi, jitai ance " me ya faru Abu Turab?" Kallan matar datai magana tai ta ciji leb'e cikin takaici ga waccan ta karaso daf, ganin yana neman sanar da matar yasa ta fizge hijab dinta iya karfinta, ta sakar mai gwalo tace "makaho kaje ka nemo sanda." ta kara falawa da gudu kamar zata kifa. Juyawa yai yana kallanta cikin takaici, yanaji d'ayar tana binta tana cewa " Mariya wlh ko me zakiyi sai na rama gwarama ki tsaya." Daga can itama ta juyo ta jefo mata dutse tace " ki kamani in kinada karfi." Yaja tsaki yace " Umma amma waccan batada hankali, bigeni fa tai kiga yanda naji ciwo amma ko hakuri bataban ba." yakarasa maganar yana nuna hannunsa. Basira ta matso ta duba hannunsa tace " da alama daga makarantar boko suke amma wannan yarinyar kwai fitinaniya, kaga yanda taketa gudu ko ajikinta?" Abu turab yai kwafa ahankali yace " Allah yasa inganta watarana." Basira tace " me kace?" Kai ya girgiza yace bakomai. Lantana tace " inba dan yanayi ba inama ta isa ta ganka a haka? Bare har ta tureka?" Basira tace " muje nikam." Sun gama siyayarsu sannan suka koma gida, Abu Turab sai dayaga sunyi salla sunci abinci sannan yace " Umma menene boko?" Tace " makarantace da ake koya karatu, menene?" Kai ya girgiza alamar ba komai. Kallansa ta sakeyi tai murmushin dan ta fahimci abinda yake nufi. A waccan lokacin ba kowa bane ya damu da karatun, yawanci zakaga yara ba zuwa suke ba, wasu kuwa iyayensu ne malaman makarantar, wasu kuma turasu ake bawai dan sai sunyi karatun ba. ********* Magajiya zaune a kilisarta tanacin inibi, gefenta d'antane Yarima yana zaune kusa da ita shima yanacin ayaba, ta kalleshi sannan ta kalli Jakadiya dake zaune tace " jiya ina Mai Martaba yaje?" Jakadiya tace " ba inda yaje." Wani kallo Magajiya ta mata tace " me kikeso kice?karya na miki ko me?" Dasauri ta rusunnar da kai tace " tuba nake Magajiya ni kaina bansani ba daga gun sallah ne bai dawo ba." Ta bud'e baki zatai magana wata yarinya yar shekara hud'u ce ta shigo da gudu ta zo ta fad'a jikin Magajiya. Fara'a ce ta karfafa a fuskarta ta d'agota tace "wa nake gani haka kamar uwata?" Yarinyar ta d'ago tana murmushi tace " nice Aunty." Kallan d'an Auntyn nata tai wanda ke zaune ko kallanta baiyi ba, ta taboshi tace " Yaya bakaganni bane?" Kallanta yai yace " Yaushe zaki girma ne Khadija? Sai ki dinga gudu kamar wata....." Magajiya ce ta katseshi tace " a mata afuwa Yarima yarinya ce, sannan na tabbata inta ganni ne take haka ko Uwata?" Baki ta turo sannan ta d'aga kai. Magajiya na tsananin san Khadija wacce take 'yace ga Hisham, wanda yanzu 'ya'yansa hud'u itace ta uku, duk da dai 'ya'yansa a matsayin uku suke tunda ba wanda yasan Abdulmajid d'ansa ne. Har mamaki mutane suke yanda ta sakar ma yarinyar fuska, ko dan sunan mahaifiyarsu ne? Haka ta sa Khadija a kusa da ita tana tambayarta 'yan gida da karatun ta. Jakadiya kam ganin haka yasa ta samu ta sulale dan itakam taji dadin ganin Khadija. ************ *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *16* Yau da sassafe kafin Mai Martaba ya tafi bada a aika a kira masa Magajiya. Zama tai irin yanda ta saba sannan ta kalleshi, ba sai an fada mata ba ta fahimci magana yakesan yi mai mahimmanci. Ya dade baice komai ba kafin ya ja numfashi yace " Magana nakeso muyi, ko ince abu nakesan fada miki." Kallansa tai sannan ta maida kanta inda take kallo da. Sarki ya nisa yace " akwai abinda na b'oye miki ko ince akwai abinda ya kasance sirri na ne da ba wanda ya sani." Bata juyo ba dan bata taba kawo wani abu ne babba ba, Sarki yacigaba " Matata da d'ana zan maido gidan nan zuwa gobe." Da sauri ta juyo ta kalleshi tana mamakin kalamansa dan sam bata fahimci ina ya dosa bama. Sarki ya cigaba da cewa "Matata da ke zaune a cikin gari d'aya daga cikin gidajena, uzuri ne yasa take zaune acan saboda d'an data haifa ya kasance yanada lalura, wanda hakan yasa ta naimi zama acan dan ta kula dashi, ba wai dan tana tunanin nan din bazai samu kulawa ba a'a sai dan lalurar tasa babbace wacce take bukatar kulawa." Tunda ya fara maganar take bin bakinsa da kallo dan ta kasa aminta da abinda kunnenta ke ji. Daurewa tai tace " aure kai bamu sani ko me? Nifa na kasa fahimtar inda ka dosa." Kallanta yai yace " Basira nake nufi da d'ana Abu Turab wanda suke gidana shekara bakwai kenan." "me kace? Basira da d'anta?sannan suna zaune a gidanka shekara bakwai? Takawa mai kake san cewa ne?" Mikewa yai yace " ana jira na a fada, sannan na tabbata zakiji abin banbarakwai sai dai gaskiyar kenan." kasa magana tai saboda tsananin mamaki, tana kallo ya juya ya fita. Shikam ya sani in har ya mata lago lago tabbas sai ta bulomai da wani abun. Ta dade a zaune kafin Ta mike tai bangarenta. D'aki ta shiga ta rufe, tafiya ta dinga yi a d'akin cikin tashin hankali, me ke faruwa? Meke faruwa? Ta dade kafin ta aika a kira mata Hisham. Hisham kam ya taho ko a jikinsa dan dama yanasan ya mata magana akan a nad'a dansa matsayin Yarima mai jiran gado sai kuma ta aika a kirashi. B'angaren d'ansa ya fara zuwa, yana shiga yaji alamar fasa abu, da sauri ya shiga ciki hankali a tashe. Abdulmajid ya gani a zaune ga bayinsa sunsa gwiwowunsu a kasa suna bashi hakuri, a hasale Abdulmajid ya kallesu yace " ba nace banasan a kawomin ruwa a irin wannan kopin ba?" Hakuri suke bashi hankalinsu a tashe, ya wani juya kai irin ba saukin nan yace " bazai yiwu ba Ummana zan sanarwa ta d'au mataki a kanku." Nan suka shiga rokonsa, Hisham yai dariya ya juya ya fita yana jinjina kai, murmushi ya saki yace " haka akeso ai, gwara ya nuna musu a kasan sa suke hakan zaisa inya zama Sarki a dinga tsoronsa." A zaune ya tadda Magajiya sai dai kana kallanta kasan tana cikin tashin hankali, nan Hisham ya d'an tabe baki kadan yace "wa ya tabo wannan zakanyar?" Kusa da ita ya karasa ya zauna yace " Magajiya menene?" Ta kalleshi cikin tashin hankali sannan ta bada umarni a basu guri, kallanta yai sannan yai dan dariya yace " menene? Khadija tace a gaisheki." Hucci ta saki tace "ina amsawa amma ba wannan bane a gaba yanzu, kasan Basira ta dawo kuwa? Ko ince wai ashe tana nan?" Kallanta yai yace "Basira? Wa ke........" ido ya zari sakamakom tunowa dayai yace " Basira dai?" Ido ta runtse tace " ita mana, ba ita kadai ba ma harda danta." Mikewa Hisham yai da sauri yace " ban gane ba? Basira tana nan a ina?" Magajiya ta kwashe komai ta fada mai, shiru yai sannan ya zauna a kasa dabas ya dafe kai cikin tashin hankali. Magajiya ta kalleshi tace " naji maganar Mai Martaba sai dai ban yarda da duk abinda ya fada ba." Hisham yace "ban......" Tace " kana tunanin Basira tana garin nan shekara bakwai amma sarki bai nuna alama ta zargin haka ba? Ko na fita? Ko na aika abinci ko wani sako?" Hisham ya kalleta yace " haka ne kuma." Magajiya tai wani murmushin takaici tace " kwanan nan ta dawo." "kwanan nan?" Tace " haka zuciya ta da kwakwalwata ke sanar dani, nasan hali Takawa, nasan yanda yakesan Basira da abin cikinta, na tabbata bazai taba kyalesu ba batare da ya dinga binsu ba." Hisham yace " gaskiya ne,to yanzu meye nafita?" Tace "nayi tunani sosai bayan naji abinda yace sai dai nasan babu abinda zamu iya yi, na farko bazamu sa ta koma ba sannan ba zamu kashe danta ba, sai dai akwai kafita." Hisham ya kara matsowa, Magajiya tace " da farko mu nuna masa ba komai, sai dai ni zan sanar dashi akan in har yanaso in nuna dawowar matarsa ba komai bane har sai ya amince da bukatata." Hisham yace "kina ganin zai yarda?" Tai wani murmushi tace " yafi kowa sanin in na tsani matarsa zaman gidan nan gagararta zaiyi hakan zaisa ya yarda." Hisham ya kata jinjina yace " haka ne, amma meye bukatar taki?" Tace " ya rubutamin alkawari akan ba mai gadar sarautarsa sai Abdulmajin wato d'ana." Hisham ya washe baki yace "kai Magajiya da ke namiji ce tabbas da kin taimaki kasar nan da kwakwalwarki." Kai ta juya tace " sannan basai na damu da d'anta ba tunda yace min yanada lalura duk da banmasan lalurar menene ba." Hisham yace "lalura?" Ta tabe baki tace "oho musu sai dai dolene muyi amfani da dawowar yarinyar nan mu amshi takarda a hannun sarki. Murmushi sukai na farincikin ganin sun warware matsalarsu.... _Nikam nace hmm ba giringirin ba dai........_ ********** Mai Martaba ya sanar a fada akan dawowar matarsa da kuma zamansu a can, mutane dayawa sunyi mamakin wannan al'amari da kuma san suji lalurar d'an nasa. Sannan ya aikama Basira akan su shirya dan kuwa gobe ne ranar komawarsu. ********* Basira yau tace Abu Turab yazo su kwanta tare a kan gado, sun kwanta shiru, ta kamo hannunsa tace " yauce rana ta karshe da zamu kwanta tare duk dadai mun dade bamu kwana tare ba." "dolene ka zamanto mai kauda kai sannan mai gudun rigima in ka koma gidan mahaifinka, zakaga mutane kala kala masu hali daban daban sai dai fatana ka nutsu ka karanci ko wani hali na d'an adam din daka gani." Kai ya d'aga mata alamar to, tai mumushi tace " kada ka kuskura ka nuna ma mutane kana gani, wannan alkawarinmu ne wanda nakeso ka rike har sai sanda nace ma ka nuna musu." Ya kara d'aga kai, tace " zan zamo mai zafi a gareka, zan ki bin bayanka, zan ki nuna ma kulawa, sannan zan nuna rashin damuwata akanka sai dai inaso kasani hakan gata ne wanda zanma, a yanzu bazaka fahimta ba sai dai nan gaba kai da kanka zaka fahimci dalilina nayin hakan." Abi Turab ya kalleta idanunsa sunyi raurau, ba komai yake fahimta ba a kalamanta saboda yarinta sai dai ya san abu d'aya tana nufin akwai dalili dazaisa ta daina nuna mai kulawa. Kallansa tai, batai magana ba yai saurin had'iye kukansa, daurewa yai yace " nikam banasan gidan." Kansa ta shafa tace " Allah ya albarkaci rayuwarka ya karemin kai, wannan itace addu'ata a ko da yaushe." Shirun da sukai ne yasa bacci yai gaba dashi, ta dade tana kallansa zuciyarta na tsananin tausayama rayuwarsa. _nikaina tausaya d'an yaron nan nake cewar Kanwata Yar Fara(Meema White)....Lol_😅 *#TEAM ABUTURAB 🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🤸🏼* *17* Itama Magajiya a daren ta shirya taje ta samu mai martaba da nata sharad'in, yayi mamaki kwarai dajin wannan zancen, ya kalleta harzaiyi magana sai ya fasa yace " shikenan ya amince, hakan datai ya nuna masa lalai ba zaman amana take dashi ba haka kuma ta nuna d'ansa ba nata bane." Magajiya ta juya kai bata ce komai ba dan itakam a yanzu abu d'aya kawai ta sani wato ta tabbatar ta d'aura d'anta a mulki ba komai ba. Haka mai martaba ya rubuta mata a takarda ya kalleta cikin takaici sannan yace "na dauka na sanar dake d'ana yana da lalura?" Bata amsa mai ba ta dai amshi takardar hannunsa sannan tai murmushi tace " ba wai rashin yarda ne ko rashin san d'anka bane yasani yin haka sai dai nayi haka ne saboda kauda matsala dazata iya afkuwa nan gaba, me zai faru idan nan gaba ka tara 'ya'ya anzo ana takara da kishi akan mulki? Amma kaga in har mun riga mun tsaida babban d'a a matsayin magajinka banaji wata babbar matsala zata faru." Kallan yai cikin mamaki duk da dai maganarta ba karya bane sai dai yana ganin sankai da san mulkinta ne yasata yin haka, yafi kowa saninta ya san abinda take tunani, tana tsoro kar nan gaba yaron ya warke in fara tunanin sashi a mulki. Sallama tamai ta fita. ************ Washegari wajen sha biyun rana aka turo da mota dazata daukesu. Kofar gidan sarauta aka bud'e, Abu Turab ya kurama kofar ido yana kallo, gannin tsari da girman gidan yasa ya shiga kalle kalle, mamaki yakeyi duk wannan katan gidan na mahaifinsa ne? Basira ce ta tabashi, ya juyo ya kalleta hararar sa tai sannan ta nuna mai sandarsa, da sauri yai kasa da kansa sannan ya d'auki sandar. Sun sauka Lantana ta kama hannunsa suka nufi b'angaren da wata baiwa tazo dan nuna musu. Ba b'angaren ta na da bane wannan yafi girma saboda an warema Abu Turab nasa bangaren. Haka akai ta zuwa ana gaidasu wasu gaisuwa sukazo, wasu kuwa gulma sukazo, wasu kuwa so suke suga lalurar da yaron ke dashi. Kafin kace me? Zance ya baza gidan akan Abu Turab makaho ne. Abdulmajid kam yana gun Magajiya tana kara huremai kunne akan karya kuskura ya bari yaron nan ya rainashi, dan nan gaba baisan mai zai zamar masa ba. Sun dade a d'akin kafin tace ya tashi ya koma bangarensa. Abdulmajid nada tsananin kishi, jin akwai wani d'a bayanshi a gun Mai Martaba yasa ransa ya bace, kallan masu kula dashi yai yace " muje in ga kanin nawa." Haka ya taho dan ya matso yaga kanin nasa da sam baya farin cikin kasancewarsa, sannan yanasan yagani in da gaske baya ganin. ******* Abu Turab na xaune aka dinga shigowa da kaya, sai dai ba dama ya nuna yana gani, kansa ya kawar gefe yana wasa da hannunsa, sun ajiye kaya dayawa daga na sawa, takalma da sauransu, sannan suka gaidashi. Juyowa yai inda suke ya amsa tare da cewa "su waye?" "Mai Martaba ne ya aikomu mukawoma kayan sawa, sannan ga abinci kala kala ya sa a girkama, yace a sanar dakai xai turo anjima a kaika gunsa." Abdulmajid wanda ke tsaye dan ya shigo kenan yaga ana shiga da kaya yasa ya bisu, wani mugun kishi da tsanar yaron ne ya turnukeshi. Abi Turab ya saki fuska yace " nagode kwarai." Wasu kaya aka ajiye a kusa dashi, sannan wanda ya ajiye yace "wannan zaka sa in zakaje gunsa dan a fada yakesan nunaka." Kai ya daga alamar to, sannan suka juya suka fita. Abdulmajid ya juya ya juya ya kalli bawansa yace " akwai almakashi?" Mamaki ya kamashi sai dai batare da ya tambaya ba yace "akwai amma sai gun soro." Yace " yi gudu maza ka amson." Nan ya fita da gudu. Shiga ciki yai ya tsaya a gaban Abu Turab, Lantana ta gaisheshi. Kallanta yai sannan yace " bamu guri." Hanyar waje ta nufa gabanta na faduwa, shi kuma Abu Turab ya mike ya mika mai hannu dan su gaisa duk da ba saitinshi ya mika ba, sannan yace " sunana Abu Turab." Dariya Abdulmajid yai yace " ta ina zamu gaisa bayan ba gani kake ba? Sannan ni yayanka ne baka gani rusunawa ya kamata kayi?" Abu Turab ya dan kalleshi kad'an sannan ya juya kai baice komai ba. Shigowar bawansa ne yasa ya juyo ya mikamai hannu yasamai almakashin, rigar da aka kawo dan ya saka ya dago ya sa almakashin ya yanka bayanta takai har wajen wuya sannan ya ajiye ya kalli Abu Turab yace " ungo kayanka saka ni ne wanda zan rakaka gun Mai martaba." Abu Turab yana kalan mai yai sai dai ba yanda zaiyi, ya kalli Abdulmajid yace "amma karar me naji?" Kallansa yai a wulakance yace "abu na cire a rigata." Abu Turab ya runtse ido, yana tunanin yanda zaiyi, in ya nuna ya sani alama ce ta yana gani kenan. Haka ya amshi kayan ya kankama a jikinsa bayan yasan duk bayansa a waje yake. Abu Turab ya kalleshi yace " Amma ance turowa za'ai inje ai." Abdulmajid ya kalli Bawansa yace "ga wanda aka aiko nan, sannan cewa akai in kaika." Fitowa yai rike da sandarsa, Abdulmajid na gaba shikuma yana baya, masu kula da Abdulmajid na bayansu. Tunda suka fito ake kallansa ana dariya, lalai wannan ba makanta bane kadai a kansa akwai alama ta hauka. Shikanshi Abdulmajid sai dariya yakeyi sam baisan abin zai kayatar dashi haka ba, shidai kawai yayi ne saboda yasa amai dariya a fada bai dauka tun a hanua za'a fara ba. Sai da sukaje kofar shiga fadar, ya kalleshi yace "shiga." Abu Turab idanunsa suka kada sukai jaa, jiyake kamar ya sa ihu, mahaifiyarsa ya tuno da kuma kashaidinta akan idanunsa. Haryaje shiga ya tsaya Shi mamakinsa mai ya mai? Daga zuwansa ko awa biyu cikakke baiyiba ace harzai mai haka? To shi mai yayi? Daga bakin kofa akace " Bawan Allah ya akai?" Abu Turab ya juya zai bargun da gudu, nan fa akaga bayansa. Barde cikin mamaki dan dashi akaje daukosu yasan yaran ya kalleshi yace "Ba......." Shiru yai ganin yanda rigarsa ta baya take. Dariya aka shiga guntsewa ganin kayansa kowa ya tabbatar d'an sarki ne. Abu Turab duk ya rikice garin gudu ya fadi a kasa, hannayensa ne suka kurje, jiyai idanunsa sun ciciko, fadan mahaifiyarsa na ragonta ya tuna hakan yasa ya hadiye kukan ya mike jiki a sanyaye ya daina gudu, sandarsa ya rike kam yana tafe. Yana fitowa daga fadar, Lantana ta taho da gudu dan labari ya kaimusu ga Abdulmajid can da Abu Turab suna tafe zuwa fada amma shi Abu Turab rigarsa ta baya a yage take sosai. Lantana tunda ta ganshi hawaye yake zubo mata, yaron daya taso a kauyen kayau hankalinsa a kwance yau gashi daga dawowarsa gidan mahaifinsa an maidashi shashasha. Hannunsa ta kama ta rufa mata babban kyallen data d'auko tana hawaye. Kallanta yai sai dai jiyake kamar taimaka mai tai wajen yin kukan dashi yakesan yi. Basira kam tun da aka fada mata take zaune ko motsi ta kasa yi, hannayenta kawai ta matse kam. Abu Turab na shigowa ta shige d'aki da sauri, bayan ta ya kalla ya bita da gudu. Yana kokarin shiga yaga ta rufo kofa. Zama yai a bakin kofar. Hakoransa ne suka shiga kadawa, sanyi ya fara kamashi. Yana nan a zaune bacci ya daukeshi, wani zazzafan zazzabi ne ya kamashi. ******* Magajiya kam jin abinda ya faru yasa ta cikin wani farinciki ba shakka lalai d'a dole ya gaji ubansa, bayan Hisham ga ta ai dolene Abdulmajid yai gadon makirci Da kissa. Dadi ne ya kamata sai murmushi take. Jin wannan labari yasa Hisham cikin farin ciki, shida Magajiya sunyi dariya sosai sun kuma yaba kwazon d'an nasu da alama in ya girma abinda zaiyi ba wanda zai iya tunani. Hisham sai kara wasa Magajiya yake yanacewa "ai kwakwalwa da kwazonta ne ya gado yo dama kaza bazatai gudu d'anta yai rarrafe ba...." Dadi sai kara kamata yake. Da alama basai ta taimaki d'an nata ba, komawa zatai ta zauna ta dinga ganin yanda Abu Turab zai kasance gun Abdulmajid........ nαcє hmmmmmmmm.... *ⓐⓑⓤ ⓣⓤⓡⓐⓑ ⓣⓔⓐⓜ🤝🏼* ************ 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *18* Lantana ce ta zo ta daukeshi tai b'angarenshi dashi, akan gado ta kwantar dashi har lokacin bata daina zubar da hawaye ba, bargo yaja ya luluba ita kuma ta mike ta fito. A tsaye ta taradda Basira, kusa da ita taje ta tsaya ba tare da tace komai ba. Basira ta juyo tace " yana ina?" "nakaishi d'aki." ta fad'a tare da kara share kwalla, Basira ta had'iyi wani yawo na takaici sannan tace " ki amso mai magani yasha." Tace to, sannan ta juya ta fita. ********* Mai Martaba kam ana la'asar ya kalli Barde yace " a aika a kira Abu Turab." Barde ya kalleshi jiki a sanyaye yace " Takawa kayi min afuwa amma ina ganin ka bari sai zuwa wata rana sannan a nunashi a fada." a hankali yai maganar. Mai Martaba yasan halin Barde tunda ya fadi haka da alama akwai wani kwakwaran dalili, hakan yasa bai sake magana ba. Ana tashi daga fada ya tambayi Barde abinda ke faruwa. Barde ya nisa yace " bansan nikaina takamaimai menene ba sai dai naganshi ya taho gunka sai kuma ya juya." Cikin mamaki Mai Martaba yace " ban gane ba?" Nan Barde ya sanar dashi abinda ya gani. Hankalin Mai Martaba ne ya tashi sosai nan ya juya afusace yai bangaren d'an nasa. Bai jira Zagi ya isar da zuwansa ba ya fada ciki da sauri. D'akinsa ya nufa ya bud'e, a dukunkune ya ganshi cikin bargo, da sauri ya karasa gunsa ya d'agoshi. Jikinsa zafi rau wanda hakan ya kara tadamai hankali, ya kalli Abu Turab wanda idanunsa sai lumshewa suke, yace " Menene? Waye ya tabaminkai? Har yajama zazzabi?" Kai Abu turab ya girgiza alamar bakowa. Fuskarsa yace " bayin dana aiko da kayanka sune suka baka yagagge ko akwai wani abun?" Abu Turab jiyai wani kuka yazo mai, baisan sanda yasa kuka ba, kuka ya shigayi sosai. Mai Martaba ya rungumeshi tsam a jikinsa hankalinsa a tashe. Abu Turab ya dade yana kukan sannan ya share hawayensa cikin murya mai raunin gaske yace " kayi hakuri na tadama hankali daga zuwana." D'ago dashi yai ya kalleshi yace " ni zan baka hakuri na rashin kula da abinda ke faruwa dakai." Abu Turab ya share kwalla baice komai ba. Yana zaune kusa dashi har bacci ya dauke d'an nasa sannan ya mike ya fito. Bangaren Basira ya shiga, zaune ya ganta tana cin abinci. Sai daya zauna sannan ya kalleta yace " Abu Turab yaci abinci ne?" Murmushi tai tace "in bashida lafiya bayacin abinci dan ko yaci zai dawo dashi." Ya kalleta ya kalli yanda takecin abinci yace " Basira mai ya sameshi? Ance ya sa kaya bayan rigar a yage." Abincin hannunta ta ajiye dan dama ci kawai takeyi, ta kalleshi tace " bansan me ya faru ba nima na dai san bashida lafiya." Ido ya kura mata, tai saurin kauda kanta gefe, yace " wanene yamai haka? Na tabbata kinsani." Ta dan kalleshi kadan tace " shi bai fadama ba?" Yace "yace bakowa." Murmushi tai najin dadin yanda dan nata yace bakowa, tace " tunda yacema bakowa hakan ne, koma ba hakan bane alama ce ta bayasan kasani." Shiru yai, sannan ya kalleta yace " komai yayi daidai? Na gida nake nufi." Kai ta d'aga tace " komai yayi daidai sai dai inaso ka bani dama na wani abu." . Ya kalleta bai ce komai ba. Tacigaba da cewa " so nake Lantana ta koma gun Abu Turab sannan inaso ka taimaken akan barinta ita kadai ta kula dashi banasan abashi bayi dayawa." Mamaki ya kamashi yace " me kike fada haka! D'an nawa da bashida lafiya kikeso invar lantana kadai ta kula dashi?" Tace" rokon ka nake akan hakan inya tasa lokacin sai ta dawo nan, ya saba da ita da ita kadai yakejin dadin zama." Shiru yai baice komai ba, ita kuwa tana tsoron kar a turamai mutane ya zama harda mutanen Magajiya kada kuma tsautsayi yasa ya nuna yana gani tunda dai yaro ne. Ta kalleshi tace " sannan yana san karatun boko." Mai Martaba yai murmushi yace " akwai mai koyama Abdulmajid da 'ya'yan kanina da na galadima karatu a cikin gida, inyaso sai ya dinga zuwa." Tai murmushi tace " nagode Takawa." Kallanta ya sakeyi yace "amma kina ganin zai iya karatu cikin yara masu gani shida yake makaho?" Tace " zai iya, kuma hakan zaisa su fuskanci juna da 'yan uwansa." Kai ya jinjina alamar gamsuwa. ******** Washegari. Da gudu ta shigo bangaren Magajiya, tana zuwa cikin zumudi tace " Umma ina kanin Ya Abdulmajid d'in?" Abdulmajid ya maka mata harara yace " khadija me yasa bakida hankali ne? Ba na hanaki yima mutane gudu ba? Kina mace?" Baki ta murguda kadan sannan ta kalli Magajiya ta shagwabe fuska tana neman yin kuka. Tace "Umma kinga Ya Abdulmajid ko?" Abdulmajid haushi ya kara kamashi, yace "banace karki kara cemin Ya Abdulmajid ba?" Kuka ta saka sosai, Magajiya ta janyota jikinta tana lalashi. Abdulmajid ya kalli Magajiya yace "Umma duk ke kika b'ata yarinyarnan." Khadija ta d'ago daga jikin magajiya tace "Umma ina kanin ya....." Sai kuma tai shiru. Magajiya tai dariya yace "Abdulmajid kadaina zafafa mata." Itakam ganin anki fada mata yasa tai waje da sauri. Baiwar bangaren Magajiya ta samu tace "kaini gun yaron dayazo jiya." Nan ta dauketa tai bangaren Basira da ita. Ta nuna mata bangaren yaron. Da sauri tai ciki, Lantana ta gani a zaune tana ninke kaya, cikin zumudi tace " sannu, ina yayan da aka kawo jiya?" Lantana ta mata kallan mamaki ganin bata santa ba. Abu Turab ne ya fito daga d'aki bai kula da wani a gun ba yace " Lantana dan bani ruwa." Jiyai anzo an rungumeshi kam. A tsorace ya kalli kasansa. Yarinya ce karama ya gani, cikin mamaki ya tureta yace " waye hakan?" ya fada kamar bai ganta ba. Khadija tai dariya tace " nice nan 'yar gidan waziri, kaine yayan dayazo jiya ko?" Kallanta yai kadan ya kauda kai yace " ni bansanki ba." Dariya tai batace komai ba, itakam tun jiya ta matso ta ganshi. Hannunsa ta kama tace "ai kai zaka dinga wasa dani ko? Bakaman ya Abdulmajid ba ko?" Shiru yai baice mata komai ba, ta kara rike hannunsa tace " sunan ka Ya Turab ko?" A hankali yace eh. Dadi ya kamata tace " zanje gun karatu sai nazo gobe. Nan tai waje da sauri. Baisan sanda yadanyi murmushi ba. Lantana ta kalleshi tana dariya tace " tunda kazo gidan nan sai yanzu naga fara'arka." Ya kalleta yace " bani ruwa kishi nakeji." Tai dariya ta mike, jikinsa ba karfi hakan yasa ya zauna. ********** Jin labarin fara karatunsa agun Mai Martaba yasa Barde shima ya gurfana gaban Mai Martaba yace " Takawa nima inasan abani izini in dawo da yarinyata cikin gida dan daukar darasi." Mai Martaba yace "ba da kace tanayi a waje ba?" Barde yace " wlh Takawa yarinyar tawa ce kasan na fadama bataji sam, kullum ta fita makaranta sai an kawo kararta, ina ganin in anan take zatafi samun nutsuwa tunda ba wanda ta isa tsokana ganin darajar mutanen da zatai karatun dasu." Mai Martaba yadan murmusa yace " shikenan ka kawota, Mairo sunanta ko?" Barde yace "eh Takawa, ina godiya Allah yaja kwana." ********* *ⓐⓑⓤ ⓣⓤⓡⓐⓑ ⓣⓔⓐⓜ*🤝🏼 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🤸🏼* *19* Da yamma suka shirya ita da d'anta dan zuwa gaida Magajiya. Duk inda sukai kallansu ake ana 'yan gulmace gulmace har suka isa b'angaren Magajiya. Tana kilisarta itada d'anta, bayan an neman musu izini nan suka shiga,ta kama hannun Abu Turab sakamakon sakeshi da Lantana tai da zasi shiga. Abu Turab ya sauke idansa akan hamshakiyar matar dake zaune ta kafe kofar da sazu shigo da ido. Kallanta yai sannan ya kalli d'an nata dake gefe sai kuma yai kasa dakai. Magajiya kam ta kafeshi da ido tunda suka shigo har suka isa suka zauna. Ta rasa me yasa tana ganinshi taji gabanta yayi wani wawan fad'uwa, Basira ta kalla sai dai yanzu taga alamar ba tsoro da gidadanci a idanunta kamar waccan zuwan nata na da. Zama sukai,Magajiya ta kara kallan yaron a ranta tace " sak Mai Martaba lalai naji dadi da Yakumbo ta taimaka wajen nakasa idan nan." Gaisheta Basira tai, i Bata amsa ba ta maida idanta gun yaron, ya d'ago suka hada ido da sauri ya kalli gefe yace "Barka da Yamma." Tabbas tasan sun hada ido sai dai dayake zuciyarta na farin ciki da kasancewarsa makaho yasa ta kasa dogon nazari akan haka. Abdulmajid kam ya had'e rai da alama bashida niyyar gaida Basira. Sai da Magajiya tace "Yarima baka gansu bane?" "Barka." Abinda ya fada ma Basira kenan. Murmushi tai ta kalli Abu Turab tace " Yarima bakaga yayanka bane?" Wannan kalma ta ba Magajiya da Abdulmajid mamaki, yarima? Haryaushe yazo?kuma ma a gabansu?" Abi Turab bai kalleshi ba yace "Barkanka dai Yarima." Magajiya zatai magana, Basira tai saurin cewa " haba Abu Turab sai kace ba yayanka ba? Ai kai basai ka kirashi Yarima ba ko Magajiya?" Ta karasa maganar tana kallan Magajiya. Magajiya ta juya ido a ranta tace " lalai wai so kike ki nunamin kin kile ko me?" Murmushi ta saki sannan tace " hakane abinda kika fada sai dai kinsan tsintaciyar mage bata mage." Basira cikin mamaki tace "bangane ba?" Magajiya tai wani nishi na kasaita tace " Dafatan muhallinku an sa komai da komai? Dan ina nan ina fama da al'amuran cikin gida ban samu naje ba." Basira ta daure tace " komai yayi." Shiru suka d'anyi Magajiya na kallan yaran, can tace " naji ance ka fita riga a yage jiya? Meke faruwa? Ko dayake laifinki ne kinsan yaran makaho ne bai kamata ki barshi shi kadai ba." Basira ta kalleta kadan batai magana ba,BU turab yai saurin cewa " Laifinane dan batasan ma nafita ba." Magajiya a hasale tace " kada ka kuskura in inamagana da mahaifiyarka kasamin baki, ko kaga Abdulmajid na haka? Wannan alama kake nunawa na kataso a wani gun daba Gidan sarauta ba." Basira ta kalleshi tace " kada ka sake, sannan yi maza ka bata hakuri." Shiru Abu Turab yai wanda hakan yasa Basira tai dana sanin cewa ya bada hakuri, tasan halin d'anta sarai inhar tace yai abu ya tsuke baki to fa lalai bazaiyi ba. Magajiya ta kalleshi tana jiran ya bata hakuri sai dai jitai yayi gum. Abdulmajid ya kalleshi yace "bakaji me aka ceba?cewa akai ka bada hakuri." Abu Turab aya dan juyar dakai saitin Abdulmajid yace " bansan laifin me nai ba." Wannan kalma tasa ta basu mamaki sosai, a zuciye Abdulmajid yace "bakasan me kai ba? To me ya damemu? Kayi laifi dan haka bada hakuri ya zama dole." Kasa ya maida kansa yai shiru, Basira tadan tabo hannunshi nan ma shiru, Magajiya tai wata dariya kadan ta takaici tace " kai? Nice magajiya gimbiyar sarki, sannan nice a matsayin mahaifiyarka babba dole ne kabi abinda nakeso ka kuma guji abinda banaso." Abu Turab baiyi magana ba, Basira ta kwallama lantana kira tace " Lantana samo bulala." Lantana ta kalli Uban gidan nata cikin tausayawa sai dai ya zatayi? Haka ta fita ta samu bulala na bishiyar maina. Basira ta kalleshi yace mike, Abu Turab ba musu ya mike, ya d'aga kasan wandonsa dan yasa nan zata daka, zata fara dukansa Magajiya tace " Basira meye hakan? Dan d'ana yamin laifi ai hakkinane in hukuntashi bake ba." Basira ta tsaya sai dai a ranta tana addu'a Allah yasa kar tace ita zata hukuntashi. Magajiya ta kalli Abu Turab tace "yi zamanka kaji d'ana." tai maganar fuskarta a sake. Gani tai Abu Turab yaki komawa ya zauna, kallan mamaki tamai gani tai kansa na kasa kusa da mahaifiyarsa. Ya saba da hakan inyai laifi sai tace dakanta ya zauna. Basira ta kalleshi tace " zauna mana." nan ya koma ya zauna, ba shakka wannan abun ya kuna ran Magajiya ya kuma kona ran d'anta, sai dai bata nuna ba har suka tafi, tana tunanin lalai dole ta saita d'an nan. ********** Yau satinsu biyu a gidan, sam Abu Turab baya fita saboda gudun kar wani abu ya faru a gane idansa na gani, sam bayasan gidan, sai dai jefi jefi Khadija na zuwa gunsa tai tamai zuba, shi mamakinsa ma ko mahaifinsa baya gani dan tun daga wannan ranar bai sake sashi a ido ba. Yau ce ranar dazai fara zuwa makaranta da safe yai wanka yasa kaya, Lantana ta kawomai abinci yaci sannan suka fita, Basira ta mai fada sosai kafin su wuce makarantar. Sun kusa isa makarantar sukaji ance Lantana, nan ta juya jin muryar kawarta. Kallan Abu Turab tai tace " dan Allah bari in mata magana." Murmushi yai yace " jeki, ba can bane?" Tace nan ne. Sandarsa yasa a gaba ya fara tafiya yana d'an kale kale kadan kadan. Yaje zai shiga yaji an bangajeshi dakarfi wanda sai daya sashi ya fad'i. Hannunsa ya kalla yaga ya kurje, ya d'ago dan ganin waye, sai dai ga mamakinsa gani yai ta mike tana neman kara mai. Hannu yasa da karfi ya fizgota. Mairo ta juyo suka had'a ido, da sauri ya kauda kansa wato yarinyar nan ce ta rannan? Itama ido ta kuramai tace "la kaine makahon nan ko?" Abu Turab yace " meyasa bakida hankali? Bakiga bigeni kikai ba? Kike neman gudu baki ban hakuri ba?" Dariya tazo mata ta toshe baki, jakar buhun dake hannunta wanda ya rike gam ta zare ta rike da hannunta, yana kallanta a ransa yace " wannan ba karamar fitinaniya bace." Waige waige ta shiga yi nan taga khadija ta nufosu. Alama ta mata da hannu akan tayi sauri, itakam ganin yayanta ne agun yasa takara sa sauri, tana zuwa kusa dagun zatai magana Mairo ta mata alama datai shiru. Mamaki ya kamata ta karaso, alama ta mata da hannu akan ta rike mata jakarta, nan khadija ta rike tana san ganin me zatai. Duk wannan abun da suke Abu Turab na kallansu shi dariya ma abin yake bashi lalai yarinta da ciwo, inba haka ba ko baya gani tana san tacemai bazai fahimci me takeyi ba? Khadija na amsa ta shige ciki da gudu. Da kallo ta bita, can tace " Ya Turab haka zamuyi ta zama anan?" Murmushi yama Khadija yace "cilar da jakar ki shiga muje." Nan ta yarda jakar sukai ciki. Suna shiga suka zauna gu d'aya dayake lokacin da ne, akan tabirma suka zauna, can gefe kuma Abdulmajid ne zaune akan wata daduma mai kyau ya hard'e kafafu. Khadija na zaune kusa da Abu Turab. Mairo tazo ta baya ta tab'ata tace " jakata fa?" Tace tana waje. Waje kuma?yarmin kikai? Khadija tace eh yayane yace in yar. Baki ta murgud'ama Abu Turab tace "yayan naki da ba gani yake ba?" Abu Turab ya kalli inda Khadija take, Mairo ta kalleshi tace " ni anya baka gani kuwa?" Abu Turab ya juya kansa bai tanka ta ba, ta harareshi tare da murgud'a baki ta mike tai waje. ********* Sosai yaji dadin yanda yake fahimtar karatun, dan daga anyi tambaya sai yaga yasan amsar, sai dai ba damar ya fada indai ba tambayarsa akai ba, saboda umarnine na mahaifiyarsa. Abdulmajid in yaji ya bada amsa daidai sai yai dariya a ransa yace duk kokarinka dai baka isa yin rubutu ba saboda rashin ido, yana tsananin jin haushi yanda Khadija ke zama inda yake, sam ma tadaina kulashi iyakacinta dashi gaisuwa. Wata shakuwa mai karfi ce ta shiga tsakanin Khadija da Abu Turab ko makaranta zata ita take zuwa ta rike hannunsa su tafi, in an tashi kuma sai ta rakashi sannan take tafiya. Mairo kuwa da Abu Turab banda fada ba abinda ke had'asu, rigimarta tayi yawa da sam ko kusa dashi bayasan tazo, haka kawai indai taganshi azaune sai ta tsokaneshi. Abdulmajid kam na tsananin kishin Abu Turab ganin yanda ko Mahaifinsu ke nuna mai kulawa da kuma yanda mutane ke sanshi, yasa san ya tsaneshi farincikinsa yaga yamai sharri, sai dai duk sharrin da yakemai cikin ikon Allah sai komai ya warware. _Wannan kenan_ Haka rayuwa ta kasance musu sosai Abu Turab ke kokarin ganin ba wanda yasan yana gani, sannan baya shiga gun mutane saboda tsaro, Mahaifiyarsa tana kara tarbiyantar dashi da nunamai abinda ya dace da wanda bai dace ba. Baya zuwa gun Magajiya akai akai, sannan in yaje gaisheta ma yana zuwa yake cewa zai tafi in kuwa ta hanashi tahowa haka zai zauna gum, sosai ya fahimci matar fuska biyu gareta. Haka ya taso cikin tarbiyya mai tsauri, haka ya taso cikin sanin halayen mutanen gidan, ya kuma fahimci lalai mahaifiyarsa gata tamai, ko daga yanda mutane suke mai kallan tsana sun dauka baya gani, sharrin da ake mai da kuma nuna halin ko in kula akansa. Mutum d'ayace yake zama da ita yaji dadi, daga mahaifiyarsa da Lantana sai kuwa Khadija. *TEAM ABU TURAB🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *_Gaisuwa Gareki Fatity, Meela Adeel, Rasheeda, Zaliha, Safeena, wannan shafin sadaukarwace gareku._* *20* Ganin irin tsananin shakuwar da ta shiga tsakanin Turab da Khadija yasa hankalin Magajiya ya fara tashi, ga yanda take tsananin san yarinyar, Hisham tasa aka kira ta umarceshi akan ya maida Khadija kano gun 'yan uwan mahaifiyarta, a lokacin Khadija nada shekara 10, sai tazo gidan sau nawa amma ko b'angaren Magajiya wani sa'in harta fita bazata ba, Hisham ma ya aminta da hakan dan kuwa shikansa abin ya fara damunsa jin komai a gida zancenta kenan Ya Turab. A ranar da za'a tafi da ita ma tazo gun yayan nata tana ta sashi magana, dan dama kaf gidan ita kadai ce mai sashi yai ta magana, suna cikin hirarsu aka turo tazo Mamanta na nemanta, mikewa tai cikin sauri dan ko d'ankwalinta bata d'aura ba kawai ta sa hijab dinta ta fita, hartaje kofa Turab yace " Khadija." Juyowa tai cikin fara'a, murmushi ya mata ya kalleta yace " karfa kiyi gudu ki tafi a hankali kije ki dawo." Itama murmushi tamai tace " yanzu zan dawo Yaya, in na dawo zan cigaba da baka labarin." Kai ya d'aga mata alamar to, kusa da shi ta dawo da sauri ta kura mai ido, kallanta yai tare da saurin d'auke ido, tace "wani sa'in sai inga kamar kana gani." Fuska ya d'an hade yace " zaki fara ko?" Dariya tai tace "karka damu yaya a kullum in nai sallah addu'ar da nakeyi kad'ai kenan 'Allah ya baka lafiya ka dinga gani.' Fuska ya saki yace "dafatan ba ita kadai kikeyi ba? Addu'ar nake nufi." Mikewa tai da sauri ta fara tafiya, hannu yasa ya riko hijab dinta ta fizge da karfi sai dataje kofa tace " ita kadai nakeyi." Tai saurin tai waje. Dariya yad'anyi tare da girgiza kai, ba shakka Khadija itace take d'ebe mai kewan zaman kad'aici, dan ko sharri akamai ko aka b'atamai rai inyazo ya zauna a d'aki shiru ita ce ke zuwa gunsa, bazatace komai ba sai dai zata zauna kusa dashi harsai taji ya fara mata magana, ya rasa menene dalilin dayasa mahaifiyarsa ma zancenta kenan akan ya rage kula Khadija, ko Lantana ma wani sa'in sai yaji tace " Uban gidana ka rage sa Khadija a ranka." Bai tab'a tambayar dalili ba dan kuwa yasan ba mai fadamai, kuma yana tunanin dan tana 'yar yayan Magajiya ne yasa ake fadamai haka. A can kuwa Khadija na zuwa aka sa ta amota, mamaki ya kamata ta kalli Mamanta tace " ima zamu?" Rufo kofar motar Hisham yai sannan ya kalleta ta yace " ki koma kano gun kanwar Mamanki ki zauna acan, kiyi karatu, inkinyi hankali nida kaina zanzo d'aukanki." Ihu ta saka tace "itakam bataso abarta anan, gub Ya Turab." Tana ihu tana kuka aka ja mota akai gaba, kuka take sosai harda shesheka, sai dai Mahaifiyarta kawai ta jawota jikinta ta kwantar. Tana kuka har bacci ya d'auketa, bata farka ba sai da akai parking a kofar gidan. Da kuka ta shiga gidan. ******* Haka rayuwa ta kasance tun Turab na jiran Khadija kwana d'aya, biyu ba labari, nan ya fara tunanin ko batada lafiya ne. Satar jiki yai ranar datai kwana hud'u ya fito, tunani ya fara ta inane ma inda zaije shidai ba yawo yake ba, ga gidan katon gaske, yana tsaye yana tunani yaji anzo tabayansa ance woo da karfi akai wanda sai daya d'an tsoratashi ya juyo da sauri ganin Mairo ce ya had'e rai tare da dauke ido daga kanta, hannu takai kamar zata dakeshi ta makamai harara tace a hankali " nima ba farincikin ganinka nake ba." Fuskarsa a had'e yace " kinga Khadija?" Bakibta tab'e tace " khadija?" Sai kuma tasamai dariya tace " niban ganta ba." Kallanta yad'anyi kamar ya tambayeta inda zaije yaganta sai kuma ya fasa, Mairo tace "la ga Yayanta nan zuwa ka tambayeshi." Juyawa yai da sandarsa zai koma, jiyai Abdulmajid yace " Abu Turab." Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba, Abdulmajid ya karaso inda yake, ya mai wani kallo na sama da kasa yace " kana d'an sarki menene dalilin fitowarka kai kadai?" Abu Turab ya kalli gefensa baice komai ba, Abdulmajid yacigaba" in har kanada ido ma ba wani abin amma kana makaho ka dinga yawo kai kadai?" Ba kalmar daya tsana irin a dinga cemai makahon nan, Mairo dake tsaye ta kalli Abdulmajid dan dama ba kunya gareta ba tace " yau naga ikon Allah, wani inyaji kana fadar haka daukama zaiyi ka damu dashi." Abdulmajid ya maka mata wani mugun kallo yace " ke kuma uban waye ya sa bakinki?" Tab'e baki tai tace " wai da...." A hankali tai maganar, sai dai yajita, juyowa yai ya kalleta yace " wlh kika batamin rai bakeba har ubanki sai na sa an hukunta." Baki ta murguda kadan tace "badai nawa uba...." Abu Turab yai saurin daka mata tsawa yace "ke Mairo!" Idanu ta zaro dan sosau ta tsorata, yace wuce ki tafi gida. Kallansa tai batace komai ba tai gaba, yauce rana ta farko da taji bazata iya maida murtani ba akan fadan da aka mata. Tana tafiya Abu Turab ya juya zai tafi, kafa Abdulmajid yasa mai ya kifa kuwa tim. Kasa duk ta shiga bakinsa, Abdulmajid ya matso da sauri ya kama hannunsa yace " tashi sannu, kaga irinta ko? Yanzu dan Allah yasa ina nan ne da bamai d'agaka." Mamaki ya kama Abu Turab, sai dai ya daure ya mike ya kade jikinsa baice komai ba ya juya zai tafi. Abdulmajid yace " Khadija fa? Badai cemin zakai ita ka fito nema ba." Abu Turab baice komai ba. Abdulmajid yasa dariya ya dawo gabansa yace " duk amintar ku bata fadama zatai tafiya ba?" Abu Turab yad'an juyo inda yake, Abdulmajid ya dan dafashi yace "yaro man kaza." Baijira mai zaice ba ya juya ya tafi. Jikin Turab ne yai wani mugun sanyi a hankali ya dinga tafiya har ya isa b'angarensa dan yanzu an fitomai da kofa daga b'angaren Basira. Yana shiga yaga Mahaifiyarsa a tsaye a tsakar gida, ga bayinta da nashi duk a tsatsaye. Da alama fada take musu, jin bude kofa da shigowarsa yasa duk suka kuramai ido. Wani mugun kallo tamai ta kallesu tace " ku bamu gu." Nan kowa ya juya ya fita, Lantana kam jiki a sanyaye ta fita dan tasan Ubangidanta yayi laifi. Basira tana matsowa ta wanka mai mari. Hannu yasa a gun bai d'agoba kansa na kasa, cikin kuluwa tace " gidan ubanwa kaje? Sau nawa ina cema karka fita kai kadai?" Kansa na kasa yai gum da baki. Ta kalleshi dan tasan bazai magana ba, ita kanta tayi dana sanin marin nasa sai dai itakam tana tsoron abinda za'amai in aka ganshi shi kadai, balle yanzu dataga gefen kuncinsa kasa ta tabbata wani abun ne ya faru. Juyawa tai a harzuke tai waje. Abu Turab ya tsugunna a gun idanunsa suka ciciko, ga jin khadija tayi tafiya, ga bakincikin Abdulmajid, gashi ya b'atawa mahaifiyarsa rai. Lantana ce ta dawo ta d'agashi ta shiga dashi ciki, a wannan ranar kam Abu Turab sai daya zubda hawaye. *********** Tundaga wannan rana komai na rayuwarsa ya canza, magana wannan sai ya zamarmai dole yake yi, kullum yana b'angarensa, rayuwarsa ta koma ta da, sai dai ko makarantarsu ko kuwa inya fita gaida Mai Martaba ko Magajiya. A makaranta ne dai Mairo take dan mai magana bayan ita kuwa kaf ajin daga gaisuwa ba abinda ke hadasu da kowa. Tun randa ya ma Mairo tsawa kuwa ta rage rainashi, sai tausayinsa ma data darayi, gashi yanzu ya canza kullum fuskarnan tasa ba fara'a. A kwana a tashi ba yuwa yau gashi Abu Turab ya cika shekara 22. Yau an tashi a gidan Sarki anata shirye shirye sakamakon hawan Sallah na karama da za'ai. Zaune yake a d'aki ya saka kayan da aka aikomai inji Magajiya wai ya saka, tunda ake hawan sallah Abdulmajid ne kadai yakeyi, amma wannan sallar wai ta aikomai da kaya akan shima zaije hawa. Murmushi ya saki sannan ya d'aga kayan sama ya tabbata akwai wani makirci da aka shirya mai. Yana nan azaune yaji ana kwankwasa mai kofa. Mikewa yai ya tako yazo ya bud'e. Mahaifiyarsa ce hakan yasa ya matsa mata ta shiga ciki. Zama tai a bakin gado sannan tace " akacemin an aikoma da kayan hawa?" Kai ya d'an jinjina yace " gasu can." Kallan kayan tai sannan tace " Turab amma dai....." Murmushi ya mata yace " zanje." Kallan mamaki tamai tace " baka tunanin so take a mutanen gari su fahimcu baka gani? Ko kuma wani abun sukama dokin kaje ya yarda kai mutane su gane baka iya doki ba? Sannan su fahimci makantarka?" Idanunsa ya d'an rufe kadan sannan yace " Umma." D'agowa tai ta kalleshi yace " har sai zuwa yaushe ne zan nunama mutane ina gani?" Kallansa tai tace " Abu Turab!" Yacigaba " Wani irin tsoro ne damu da haryanzu bamu cireshi a ranmu ba? Kina tunanin wannan tsoron namu akwai inda zai kaimu?" bai jira amsarta ba ya cigaba "a'a, wannan tsoron haka zai cigaba da dawammar damu a inda muke ba tare da mun tsinana komai ba? Na sha wahala tun ina yaro har zuwa wannan lokacin, har sai yaushe ne zamu kwaci 'yan cinmu? Har sai yaushene zaki bari d'an da kika sha wahala akansa zai sama miki farin ciki?" Kallansa take yi cikin tausayawa da tsananin kauna. Hannayenta ya kama yace " na gaji da wannan tsoron, nifa namiji ne, jinin mahaifina haka kuma d'a gareki, haka kikeso incigaba da zama? Ana nuna ked'in ba kowa bace balle ni? Bayan kuma ni nasan ked'in mace ce wacce kaf duniya a gurina banga kamarta ba?" Idanunta ne suka dan tara ruwa kadan, kai ya girgiza mata yace " tun ina d'an yaro kika haneni da ragonta da kuka, Umma kina tunanin Mai Martaba shine zai kwatar mana 'yancin mu?" Kallan mamaki tamai, kai ya girgiza yace " ko kad'an in har kina tunanin wannan ki cire a ranki, Mai Martaba sarki ne, sarkin mutane masu dumbun yawa wanda yake mulkarsu sai dai ba sarki bane a tsakanin matansa, Magajiya bazata taba barinsa yai yanda yakeso ba akan matansa, yaci ace a shekaru goman nan kin fahimci haka." Murmushi tai sannan tace "nasan da haka Abu Turab sai dai ina tsoron karmu lakutowa kanmu abinda gaba bazamu iya magani ba." Dariya yai sai dai mai dan sanyi, wanda rabon dayai dariya haka ya dade yace " ina Umma na ne wacce take tsaidani in nai laifi? Ina Umma nane wacce take hanani kuka? Ina Umma nane wacce ke marina duk sanda na b'ata mata rai?" Harara ta makamai tace " da alama girma ya fara kama wannan Umman taka." _Nikaina sai da na saki wata bazawarar dariya....Lol_ *TEAM ABU TURAB🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *21* Shiru tai tana tunani, kayan da aka aikomai dashi wanda ke kan gado ya d'an kura ma ido alamar tunani kafin ya dawo da kallansa kan mahaifiyarsa yace " Umma zan shirya." Kai ta d'aga sannan ta mike ta dafa kafadarsa d'aya tace " duk hukuncin da ka yanke ina tare da kai dan kuwa na tabbata d'ana bazai bani kunya ba." Bata jira amsarsa ba tai waje. Abu Turab ya shirya tsaf ya fito daga d'akinsa, inda yake zama ya wuce dan bayin sa su nad'amai rawani. Tunda ya shigo suke kallansa dayake sunsan baya gani yasa suka kura mai ido kowa da abinda ke ransa nan fa suka dan fara gulma da ido wanda duk yana ganinsu. Rawanin dayake so ya basu nan suka nad'amai, ya sa takalmi yace su tafi. A kofar gida yaga wani bawa rike da doki yasha ado, bawan na ganin Abu Turab ya taho da gudu ya dan rusuna yace " Ranka ya dade ha doki nan inji magajiya." Murmushi yai sannan yace " ayya? Ya za'ayi? Gashi na riga na aikama Barga akan ya aikomin doki sai dai ma maida wannan gun Bargan gudub kar a maka fada akan rashin isar da sakonka da wuri. Bawan yai saurin sunkuyawa yace "Tuba nake D'an Sarki." Abu Turab yai murmushi sannan yace " ba haushi naji ba ina dai gujema fada ne." Kallan d'aya daga cikin bayinsa yai yace " sanar da Barga ya baka dokina." Cikin mamaki yace " Ranka ya dade ai ba'a mai....." Katseshi yai da cewa " hakan nakesansa." To, abinda ya fada kenan yai saurin fara tafiya. Bai dade ba sai gashi da rike da dokin Abu Turab ya hau. Sai daya bari Sarki zai fita hawa sannan ya shiga cikinsu, bai bari sun ganshi a gida ba. Tunda ya shiga cikinsu kuwa ake kallansa, kowa mamaki wannan wanene haka? Dama tawagar Abdulmajid ya shiga, dan kara gudun dokin yai ya matsa bayan Abdulmajid kadan. Nan fa kowa ya fara kallansa, mutand sai juyowa suke ana nunashi da hannu, ganin yanda ake nunuwashi yasa Abdulmajid ya tsargu ganin saitinsa ne. Kallan na kusa dashi yai yace " menene?" Juyawa yai shima, cikin mamaki ya kalli Abu Turab sannan ya matso inda Abdulmajid yake yace " Yarima ai kaninka ne yake bayanmu." Murmushi yai dan dama yasan da zuwan nashi, sunyi shiri sosai dan kuwa d'inki Magajiya tasa aka mai irin wanda zai saka a wannan ranar, wanda hakan sab'awa ne ga al'adarsu ace anyi anko da Sarki balle kuma bai sani ba. Ya sake murmushi tunawa dayai dokin ma kwalliyar irinta Sarki sukasa akamai. Sai yanzu ya fahimci dalilin dayasa ake nuna Abu Turab. Sai da sukaje inda Sarki zai d'an tsaya kafin ya juyo alokacin ne Abdulmajid yaga yanda ake ta nuna Abu Turab, dariya ya kunshe ya juyo dan ganin yanda ma kayan yamai. Sai dai me???? Idanu ya zaro sosai cikin tsananin mamakin abinda idanunsa suka ganemai, me ke faruwa? Menene hakan? Shi kansa Sarki ya fahimci yanda mutane suke nune nune, hakan yasa ya tambayi Galadima yace " meke faruwa?" Nan Galadima yasa aka bincika. Matsowa yai wajen kunnen Sarki ya rad'amai. Ransa ya b'aci sosai nan ya bada alama akan su juya. Haka sukabi har suka koma gida. Abdulmajid kam sukuku ya karasa wannan hawan zuciyarsa tana ta san taga wani irin hukunci Mai Martaba zai yankema d'an lelen nasa. Suna isa akazo aka sanar ma Abu Turab akan Mai Martaba na nemansa a fada. Yasan za'ai haka shiyasa ya sauka zuciya d'aya ya bada dokinsa ya nufi fadar. Dayaje zai shiga sai ya ajiye sandarsa sannan ya shiga ciki. Zama yai irin zaman gurfana d'in nan, Mai Martaba ya kalli dumbun manyan mutane masu mukamin sarauta dake gun, sai dai wannan karan yazamarmai dole duk san da yakema d'an nasa ya mai tambaya a nan Saboda yau a matsayin Sarki yake ba uba ba. Abu Turab ya kalla fuskarsa a had'e sosai yace " Me zaka fad'a game da wannan shigar ta cin zarafi dakai?" Nan fa aka kara kallansa, Abdulmajid wanda ya shigo yanzu yai murmushin jin dadi tare da zama. Abu Turab yai shiru baice komai ba, kallansa Mai Martaba yai yace " in har bakada amsa akan hakan to lalai ne ka fuskanci hukuncin masarauta." Ya fad'a tare da kauda kai. Abu Turab kansa na kasa yace " Tuba nake in har shigar danai laifice a tsarin masarautarmu." Nan fa kowa ya kara kallansa, rigace ta shadda wacce ta tsufa kana ganinta kasan tsohuwace, sannan na babbar riga a jikinsa ya maka wani tsohon rawani, wannan shigar ko a cikin gida ba yinta yake ba balle a gun hawa cikin jama'a. Hisham ya kalleshi yace " kanasan kace shigarka batada laifi kake nufi ko me?" Abu Turab ya kalleshi fuakarsa a sake yace" kuskure nane sai dai ina fatan amin afuwa." Cikin takaici Mai Martaba yace " Abu Turab! Nasan ba gani kakeyi ba dan haka laifin bayinka ne zasu amshi hukuncin barinka kayi wannan shigar dolene su fuskanci hukunci mai tsauri." Abu Turab ya kara kasa dakai cikin kalar tausayi yace " ko wani hukunci ne amin domin kuwa sun bani kayan da ya kamata insaka sai dai daga laushin kayan da yanayin su yasa nasan ba nine na dace da kayan ba, sai dai hakan baisa na musa ba na saka kayan dan kuwa bansan ya suke ba da idona, ka gafarceni Mai Martaba ina fitowa aka sanar dani kayan irin naka ne sak, sannan dokinma irin kwalliyarka ne dashi, wannan yasa na hanzarta na janyo kayan dabansan ya suke ba na saka sannan na aika Barga ya bani dokina nasa amaida mai waccan." Jin kalamansa lalai sun ba kowa mamaki, Abdulmajid kam cikin tsoron kar asirinsu ya tuno yai saurin cewa " menene shaidarka ta fadar haka? Kana tunanin ko me kace yarda zamuyi?" Abu Turab wanda ana cemai Mai Martaba na kiransa ya tura Salau(mai kula dashi wanda suka fi shiri) akan ya d'aukomai kayan nan,sannan ya aika Barga yazo. Nan yace " Salau!" Daga waje Salau ya amsa da karfi. Nan ya shigo rike da kaya. Abu Turab yaba shi kuna ya ware kayan anan kowa ya gani, to fa! Nan aka fara magana kasa kasa. Abu Turab yace " ka gafarceni Ranka ya dade ba gani nake ba bare nasan da haka." Barga! Nan ya amsa shima daga waje sannan ya shigo. Abu Turab yace " wani irin kwalliya ne da dokin danasa a dawom dashi?" Nan Barga ya musu bayani. Mai Martaba cikin tsananin mamaki yace " wanene ya aikoma da kayan da kuma dokin?" Abu Turab yad'an sadda kai tunowa yai da yanda suka karashe da mahaifiyarsa. Harta fita ta dawo tace " Abu Turab! Me kake san yi dan hankalina bazaj kwanta ba sai naji." Ya kalleta yace " bazansa kayan ba haka kuma bazan hau dokin ba, na tabbata akwai wani makirci akasan wannan kayan da dokin zanje inga wani irin makircine sannan insan abinyi." Muryar Galadima ne ya katseshi da cewa " kayi shiru." Cikin Abdulmajid da Waziri ne ya d'ebi ruwa, tsoro da fargaba ya kamasu, duk suka runtse ido saboda tsoron abinda zai ce. Abu Turab ya d'ago yace " ina wannan wanda baya ganin zai sani? Tuba nake ranka ya dade sai dai nikaina bansani ba andai aiko ne ance ga kayan dazansa." Mai Martaba ransa a b'ace yace "dolene abinciko wanda yai wannan laifi dan kuwa bazan laminci irin haka ba." Abdulmajid ya kurama Abu Turab ido lalai ba shakka yaran nan da saninsa. Suna fitowa ya bi Abu Turab zaimai magana, ya tsaya kusa dashi yace " kai!" Abu Turab ya kalli gefensa sannan yad'an matso kadan yace " karka damu nikaina bansan waye ya kawo kayan ba." Yana fadar haka ya juya suka tafi. Mamaki ya kama Abdulmajid ya bishi da kallo, kallan na kusa dashi yai yace " na fadamai dalilin kiran danamai?" A'a sunansa kawai ka kira. Abdulmajid yai dan murmushi yace " wasa farin girki." *#ABU TURAB🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* _Kuyi hakuri jina shiru da kukai jiya da shekaran kiya, hakan ya faru ne saboda wani dalili nawa, 👏🏼 nagode kwarai_ *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *22* Abdulmajid da sauri ya karasa bangaren Magajiya, ko salama baiyi ba ya fad'a, tana zaune tana duba wasu kaya da tasa aka kawo mata, kayan mata ne aka d'inko kala kala. Jin shigowar mutum yasa ta d'ago dan ganin wanene. Abdulmajid ne ya karaso inda take ya zauna ransa a b'ace. Kallansa tai yace " Yarona lafiya ko sallama babu." Ya kalleta yace " Umma da alama mun sakema yaran can dayawa." Ta kalleshi tace "bangane ba? Ni na dauka zakazo cikin murna kamin bayanin abinda ya faru da yaran can, shiyasa naki yardama kowa ya sanar dani nafisan inji daga bakinka." Abdulmajid yai dan ajiyar xuciya yace " Ai baisa kayan ba, da alama mun sakema yaran nan dan yana makaho shiyasa har yake ganin zai iya takara damu." Magajiya tamai kallan bata gane ba, nan ya kwashe komai ya gaya mata, wani sansanyan murmushi ne yaga ta saki ta kalleshi cikin murmushin tace " shine kake wannan fushin?" Kallanta yai cikin mamaki, ta sake wani murmusawa tace " yaro man kaza, karka badani mana Yarimana." Kallanta yai baice komai ba, tace " yaushe ma aka auri uwarsa, yaushe shima aka haifeshi, yaushe aka daina mai tsarki da wanka? Yaushe ya san kansa?" Ta sake wani murmusawa tace " ko kamanta haryanzu baisan kalar fuskarsa ba bare yasan na uwarsa bare kuma tamu?" Abdulmajid ya fahimceta, dariya yai sannan yace "a maida anin kan uwarsa?" Magajiya tace " in har Mai Martaba ya nemi jin ba'asi to ka tabbatar komai ya koma kan Uwarsa." Dariya ya saki yace "Allah yabarmin ke Umma Magajiya." Murmushi tai tace " yaune isowar Khadija fa." Ya kalli kayan yace " au shiyasa naga kaya kala kala a gabanki? Ashe 'yar d'akinki ce zata dawo." Cikin jin dadi tace " daurewa kawai nake na rashinta, amma kaga yanzu tunda Inna Lami take akwance sannan ga shi ina tunanin turawa takarda had'in aure zuwa masarautar Kano shiyasa nakesan ta dawo." Kallanta yai yace " auren wa?" Tace "auranka mana dolene in nemi masarauta mai karfi in had'a auranka saboda nan gaba ko menene ba wanda ya isa tunanin saukeka daga matsayinka ko kwace ma mulkin ka." Kallanta yai yanasan magana amma ina bazai iya ba, dan bai taba mata musu ba, kayanta tacigaba da dubawa. Jiki a sanyaye ya mike yai waje, shikam bai shirya wani aure yanzu ba amma bai isa cewa komai ba, a tsarinsa yafisan yai auren farinsa auren soyayya tunda dai yasan dama shi dolene yai mata dayawa, yana tunanin ina shi ina soyayya da wani bayan an riga an mai aure? ****** Washegari. Yana fitowa daga d'an nesa ya hangota tana tafiya, tsaki yaja yace " sai na takama yarinyarnan birki." Kallan na bayan sa yai yace " kiramin yarjnyarcan, ina bangarena." Ya juya zuwa bangarensa. Yana shiga yaga an kawo mai abinci ga bayin da suka kawo nan a tsatsaye suna jiran isowarsa. Zama yai baice musu komai ba, umarni ne ya basu dolene in suka kawo mai abinci sai yaci yaji yamai kafin su tafi. Da sallama ta shigo fuskarnan tata a d'aure tamau, shima fuskarsa ya had'e bai amsa mata ba ya d'ago ya kalleta. Kanta na gefe, jitai yace " duk ku fita kubarni da yarinyarnan inasan magana da ita." Nan sukai waje, itakam haryanzu kanta na gefe. Kallanta yai yace " ke baki iya gaisuwa ba?" Bata tanka mai ba. Ya kalleta yace " zo ki zubamin abinci, tunda naga alama uwarki bata isa dake ba, kullum kina hanyar gantali." Wani mugun kallo ta bugamai sannan tace " ko karuwanci nakeyi meye naka a ciki?" Hannu taga ya had'a ya fara tafi sannan ya mike ya tako zuwa kusa da ita, idanunta ta kawar tace " malam lafiya?" Ganin yanda ya matso daf da ita yasa ta fara matsawa, haka ya dinga matsowa har takai jikin bango. Hannu yasa a jikin bangon ya tareta yace " abinda kukeyi kenan da makahon?" Kallansa tai ta had'iyi yawu sannan ta daure tace " yaushe raban ma daka ganni a gidan? Wai ni mena tsolema ne?" Dariya yai yace " na tsani duk wanda yake san makahon can, balle ke harda dadin rashin kunya." Sauri tai ta sulale ta kasa ta juya da sauri zata fita, hannunta ya fizgo da karfi, ya dawo da ita gabansa yace " me? Bakyasan kwalliyar da kikai ta goge ne ba tare da kinje gunsa ba?" D'agowa tai takalleshi cikin takaici. Ya saki murmusawa yace " ahh ya zakiyi? Gashi kuma baya gani bare ya yaba." Hannunta tashiga kwacewa, ganin yaki saketa yasa tace " wlh zansama ihu, kasani sarai kuma zan iya." Kafad'a ya d'aga mata alamar ko a jikinsa yace " Go ahead." Lab'anta tad'an ciza sannan ta kalleshi ta kara hade rai tace " malam sakeni ko?" Kallanta yai ba alamar yana da niyyar hakan. Ta kara cewa Malam sakeni ko?" Yace "Mairo kenan, inhar kinasan in kyaleki dolene ki daina zuwa gun waccan yaran ki dinga zuwa guna duk da nidin bawai sanki nake ba ko burgeni kike ba sai dai inasan yanayin fuskarki da shape na jikinki." Iska ya hura kad'an a bakinta tace " hakan kadai kakeso." Gira ya d'aga mata alamar eh, yamai murmushi sannan tace " sakeni to, indai wannan ne kacal. Nan ya saketa yana kallanta, tace " nagode sai anjima." Zai sake magana yaga tayi waje. Hakoransa yad'an had'e yace " na tsani yarinyar nan, bawanda ya rainani kamarta." ******** Mairo kam tana fita ta gyara mayafinta tafiya kawai take amma gabanta sai fad'uwa yakeyi, haka ta isa b'angaren Basira. Bayan sun gaisa ne, Basira ta kalleta tace "Mairo yanzu sam kin daina zuwa, yauma sai dana aika kizo sannan kika zo." Kanta na kasa batace komai ba, kai kadauka irin salahan nan ce. Basira tace " dama so nake ku fita da Abu Turab gari, na tabbata yau yana bukatar iskar cikin gari bawai ta gidan nan ba." D'agowa tai tanasan tambayarta abinda ya faru, sai dai bazata iyaba. Tace " To." Basira ta kalleta cikin kauna tace " bari a kirashi." Ta kara cewa to. Abu Turab yana d'aki a zaune yana karatun alqur'ani, nan aka sanar dashi sakon Basira. Mikewa yai ya bud'e drawer din da kayansa ke ciki dan canzawa. Kurama d'ankwalim dake ajiye a gaban kayan ido yai, baice komai ba sai dai ya dade a tsaye yana kallan d'ankwalin. Kafin ya jawo wani kaya,har ya rufe kofar ya bud'e ya janyo d'ankwalin yardashi yai a kasa sannan ya sura kayansa, ya kara kallan kasa sannan yai waje. Ya rasa dalilin dayasa yakejin zuciyarsa ba dadi bayan ya yarda dankwalin, sai dai menene dalilinsa na ajiye kayan yarinyar da tunda ta tafi ko sakon gaisuwa bai kara samu ba? Wata zuciyar tacemai wa zata aika? Bayan duk ba sanka suke ba? Shikam ya rasa me yasa yakejin zafinta bayan ya tabbatar ba laifinta bane. Haryakai kofa ya koma d'aki ya d'au d'ankwallin ya maida cikin drawer din sannan yai waje. Yana shiga yaga Mairo a zaune, karasa wa yai ya kara gaida mahaifiyarsa. Mairo ta gaisheshi ya amsa. Basira tace " tunani nake ko zaka fita gari yawo." Kallan gefenta yai yace " gari kuma?" Tace " eh, kullum kana gida a zaune shiyasa nai tunani ko zaka zaga gari dukda ba gani zakai ba amma ina ganin zakaji dadin hakan." Kai ya jinjina alamar gamsuwa yace " bari na sanar ma....." Da sauri tace " ku fita kai da Garzali da Mairo kawai." Kallanta yai yasan me take nufi, dan dama ya dade da sanin so take wata alaka ta shiga tsakaninsu da Mairo. To. Abinda yace kenan ya mike. Mairo itama ta mike ta musu sallama. Garzali na bayansa ita kuma tana d'an kusa dashi kadan, shikuma yana tafe rike da sanda. Sun shiga gari ta gefen ido yana ta kallan yanda mutane suke haba haba, ba shakka wannan shine burinsa ya zauna cikin mutane kamar yanda kowa yakr yi bawai gidan sarauta ba. Jitai yace " Mairo yanzu anbar rigima dai da alama." Kallansa tai tace " lalai Yaya sai kace wata yarinya?" Yace " ah lalai ashefa kin girma." Baki tad'an turo tace " shekarata fa 1." Yace "16? Amma bakiyi aure ba?" Fuska ta d'an had'e tace " ba mijin ne." Ya d'an juyo kadan yace " wanda rannan ya biyoki fa?" Tsaki tadan yi tace "rashin aikinyi ne yamai yawa." Yace " da alama dai akwai wanda kikeso ne shiyasa." Kallansa tai a ranta tace "sosai ma." Ta d'auka a zuciyarta ta fada sai jitai yace " da gaske?" Kallansa tai tace " wasa nake." Murmushi yadanyi yace " kar ki tsaya ruwan ido ki samu saurayin da yake sanki ki aura, bawai wanda ke kike so ba." Kallansa tai zuciyarta ba dadi tace " kamar yanda haryanzu baka manta da Khadija ba?" Tsayawa yai cak, ba tare da ya juyo ba, matsowa tai inda yake tace " karka damu Ya Turab ba wanda yasan hakan, ko ince ba wanda zan fadawa." Bai san sanda ya kalleta ba, yace " me kike nufi? Ko kin tabaji da bakina na fada miki haka?" Murmushi tamai tace " wani sa'in sai inga kamar kana kallona." Fuska ya had'e ya juya kai yace " amsarki nake jira." Daurewa tai tace" a lokacin da Khadija ta tafi bafa yarinya bace ni yaya, ban manta abinda ya faru a lokacin ba, sannan duk sanda muka zauna dakai zancenka kenan khadija tace kaza, ko khadija tayi kaza, a lokacin bansan me hakan yake nufi ba, sai dai daga baya na fahimci meke faruwa." Abu Turab ya juya yace " banasan wannan maganar, sannan ni khadija banaji ko ganinta ma in nai zan iya ganeta." Yana kaiwa nan ya cigaba da tafiya." ********** Tunda suka taho a hanya take kwance kamar mai bacci sai dai zuciyarta fal take da tunani kala kala, Ya Turab! Abinda zuciyarta take fada kawai kenan, anya zata iya ganeshi? Dan ita kamanninsa ma harsun fara bace mata. Ba shakka tasha wuya sosai bayan komawarta kano, sai datai sati biyu tana zazzabi zancen ta kenan a maida ta gun Ya Turab kai kace shine ya haifeta. Yaran gidan har tsokanarta sukeyi suke cemata Aunty Turab. Duk sanda zatai addu'a kafin ta fara rokon komai sai tamai addu'a, ita har mamaki ma take da haryau bata taba mantawa da addu'ar ba in har tai sallah. Ko zai ganeta? Dan wani zuwa da Abdulmajid yai shekarar data wuce data tambayeshi Abu Turab cemata yai wai soyayya suke da Mairo, sannan gwara ma ta cire wani lamarinsa, dan shi kam ya ma manta da ita. A da bata taba tunanin wai san shi take ba, itadai a matsayin yaya ta d'aukeshi sai dai ganin ta kasa cireshi a ranta yasa Aunty Nana wato babbar yarinyar gidan ta fada mata soyayyace bawai 'yan uwantaka ba." Kanta ta kara kwantarwa jikin motar, ya zatayi in har yama kasa ganeta? Dama gashi iyayenta nema suke su had'ata da wani yaron babban d'an siyasa a garin kano yake. Ajiyar zuciya tai sannan ta kara lumshe idanta. *ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *23* A hanyarsu ta dawowa ne wani ya biyo Mairo da gudu, yana kwalla mata kira. Abu Turab yanaji ganin taki tsayawa bare amsawa yasa shima bai tanka mata ba, sai dayazo daf dasu yanata haki na gudu yace "Mairo kina jina?" Kallansa tai tace " nibanji ka ba, lafiya?" Ta fad'a tana kallan Abu Turab daya cigaba da tafiyarsa. Leda ya miko mata yace " gashi." Cikin fada tace " nameye shi kuma?" Kai ya sosa yana shirin yi mata magana, yana d'agowa yaga bata gun, kallanta yai yanda take dan sauri. Da sauri itakam ta karasa gun Abu Turab tace " Yaya ba jira?" Yace " har kin gama zancen?" Tace "zance kuma?" "ki koma dan muma gida zamu wuce, sai da safe." Abinda ya fada kenan ya cigaba da tafiyarsa. Turus tai agun idanunta suka d'an ciciko, meyasa Abu Turab baya ganin yanda ta damu dashi? Shikam ko a jikinsa har suka isa gidan. Yana shiga daga bakin gate yaji ankira sunansa. Yasan muryar waye, fuskarsa yad'an saki kadan ya juyo saitin inda yaji kiran. Sabi'u d'an gidan galadima ne ya karaso gunsa, cikin farin ciki yace "Ranka ya dade daga ina haka?" Abu Turab ya d'an murmusa kadan yace " naje ganin gari." Sabi'u ya kalli Garzali yace "dafatan ba abinda ya faru?" Garzali zaiyi magana Abu Turab yai saurin cewa " ba abinda ya faru, sannan inhar ka damu da ni nan gaba inzan fita kazo ka d'aukeni." Dariya Sabi'u yasa yace " Angama Ranka ya dade, nima daga gun Mai Martaba nake akan maganar binciken abinda ya faru yau." Fuska Abu Turab ya had'e yace "kai akaba aikin binciken?" Fuskarsa d'auke da mamakin ganin yanda Abu Turab yai yace " eh, da wani abun ne?" Abu Turab ya girgiza kai alamar a'a sannan yace " ka koma gida ka kwanta kace bakada lafiya, inyaso zuwa gobe sai ka turo fada a sanar da rashin lafiyarka." Sabi'u yace " saboda me? Ni ai ina ganin nine na dace da binciken saboda sanar ma Mai Martaba gaskiya abin." Abu Turab yace " shine dalilin dayasa ai banasan ka amshi wannan aikin." Kallan Mamaki Sabi'u yamai, Abu Turab ya sa hannu alamar yana nemansa, da sauri Sabi'u ya rike hannunsa yace "ganinan" Hannunsa ya rike yace " Sabi'u ka manta wacece Magajiya ne? Ina tsoron karkaje daga bincike ta juyo da rashe kanka, dan na tabbata bazata taba bari a gane itace ba, saboda haka ka barni da ita ni zansan wanda ya kamata yai binciken." Sabi'u ya fahimceshi kwarai hakan yasa bai musa ba yace " shikenan zanyi yadda kace." Nagode. Abinda Abu Turab ya fad'a kenan. ******** Tare suka shiga cikin gidan suna tafe suna 'yar hirarsu. Yazo yin kwana inda zai shiga b'angarensa, wata budurwa ya hango a tsaye a jikin katangarsa, kanta na kasa da alama ba shiga zatai ba kuma da alama basan barin gun takeba. Harya dauke idanunsa ya kuma maidasu kanta, baiga fuskarta ba sai dai kallo d'aya zaka mata kasan 'yar wani ce. Sabi'u ne shima idanunsa suka kai kanta, daidainan ita ma ta d'ago, suka had'a ido. Da sauri ta juya ta shige ta baya. Sabi'u yai murmushi yace " yau kuma wa na samu?" "kai da wa?" Kansa yad'an shafa yace " wata ce da alama biyoni tai sai sai kunya ta hanata tsayuwa." Kai ya girgiza yace " kana fama." Tana tsaye ta lungun ta zuro kanta kad'an, idanunta ne suka ciciko da kwalla a hankali wani zazzafan hawaye ya taho mata, kallansa kawai takeyi tana mamakin yanda zuciyarta ta kasa mantawa dashi, har yanzu baya gani? Abinda zuciyarta ta fada kenan. Hawaye ne suka cigaba da zubowa sosai sai dai sam ta kasa tsayar dasu. Har suka shiga tanannan a gun ta dade sosai kafin ta juyo ta fara tafiya. B'angaren Magajiya ta shiga. Da sallama ta shiga. Magajiya ta mike cikin tsananin farinciki ta rungume ta. "lale lale da zuwan Khadija ga, Uwata barka da zuwa." Mamaki sosai bayinta suka shiga yi, hatta Abdulmajid yayi mamakin ganin Uwarsa ta mike tsaye saboda taro wani ba sarki ba. Khadija cikin farinciki tace " Nasameku lafiya Umma?" Magajiya ta saketa ta jawota suka zauna, kallan bayinta tai tace " ku kawo mata abinci." Tsugunawa tai tagaida Magajiya sannan ta kalli Abudulmajid ta gaisheshi. Kallan ta yai shima cikin farinciki ya amsa sannan ya d'ora da cewa "inakika tsaya bayan tun dazu aka aiko akan kin shigo?" Kanta ta sunkuyar batace komak ba, Abdulmajid ya hade rai cikin kuluwa yace "badai Gun......" D'agowa tai fuska a had'e itama tace " bangane ba?" Zaiyi magana Magajiya ta katseshi da cewa " Yarima banasan haka, akan me zaka takurawa Uwata daga zuwanta? Na tabbata nan ta fara zuwa." Khadija ta d'auke idanta daga kanshi, shikam ido ya kura mata yana zargin anya kuwa ba gun waccan yaran taje ba? Abinci kala kala aka shiga jerawa, Magajiya tasata a gaba tana ci suna hira, bayan ta gama ta sa aka d'auko mata jakar kayan datasa akadinka mata, Khadija cikin jin dadi tace " nagode sosai Umma." Magajiya ta kalleta tace " yaushe zakije duba Inna Lamin?" Khadija tace " zuwa gobe, amma ya jikin nata?" Abdulmajid yai dan kasa da kai yace " jiki fa ba sauki tana nan dan ko fitsari a kwance take, 'ya'yanta duk sun kama gabansu ba mai kula da ita, hmmita kam wannan gwara ma ta mutu ta huta." Magajiya ta d'an tabe baki, khadija ta kalleshi tace " ko ma menene Yaya bai kamata ka fadi haka ba, addu'a kawai zaka mata, amma nikam Umma bakya ganin Baba ne yakamata ya d'aukota ta zauna a gunsa, ta yaya za'abar ta ita kadai a gida?" Magajiya ta kalleta tare da canza fuska tace " kin fadama Hisham din haka?" Tace " yanzu abin ya fad'omin." " Tun kafin ya hauki da fada karma kimai wannan zancen, ke dai kije ki dubata gobe." Khadija zata sake magana Magajiya tace " Khadija bansanki da musu ba." Shiru tai batace komai ba, sai dai tana ganin hakan bai dace ba, yaza'ayi ace 'yan uwanta da 'ya'yanta duk sun watsar da ita?" ******* Bayan anyi sallar isha'i ne Jakadiya tazo ta sanarmai da sakon Mai Martaba akan yana san ganinsa. Shida Garzali suka fito, bayan ya shiga ya zauna ne Mai Martaba ya kalleshi yace " Nayi dogon naxari akan abinda ya faru sannan na sanar ma Sabi'u akan yai bincike akan abinda ya faru, tunda naga shine na hannun damanka." Abu Turab kansa na kasa yace " Abba!" Kallansa Mai Martaba yai ba tare da ya amsa ba, dan raban dayaji ya kirashi da Abba tunda ya mallaki hankalin kansa. Abu Turab ya cigaba " wani hukunci zaka d'auka akan wanda ya aikata hakan?" Sarki yace " dole ne ya fuskanci hukunci mai karfi." Murmushi ya saki sannan yace " ko da kuwa Magajiya ce?" Kallansa yai yace " me kake nufi?" Abu Turab yace " a matsayin d'a nazo gunka inaso d'a da mahaifinsa suyi magana bawai sarki da d'ansa ba." Sarki ya kalleshi yace " shine nace mai kake nufi?" Abu Turab ya d'anyi shiru kafin yace " zaka iya hukunta Matar da take da mukami fiye da kowa?matarda yayanta yake waziri?matar da d'anta yake magajinka?matar da duk yawancin masu mukamin nan suke a kasanta?" Sarki ya kalleshi ranshi a b'ace yace " Turab!" Abu Turab ya d'an sunkuyar da kai yace " tuba nake ranka ya dade bawai da wanj abin na fadi hakan ba sannan ba wai nace itad'in ce tai ba sai dai ina tunanin mu binne maganarnan inhar hukunta mai laifin zai iya zama wani abu." Sosai ran Mai Martaba ya b'aci mai Abu Turab yake nufi? " bance itace tai ba sannan ban san wanda ya aikata hakan ba, ina tsoron kar ka kasa yanke hukunci ne in laifi ya fada hannun manya." Sarki ya kalleshi jiki a sanyaye yace " kaima kanasan kacemin baka yarda dani ba? Kaima kana ganin nid'in ragon sarki ne wanda bazai kya hukunta Matarsa ba?" Kai Abu turab ya girgiza jikinsa shima yai sanyi yace " bawai hakan nake nufi ba sai dai banasan na zama sanadiyar saka cikin tsaka mai wuya." Murmushin takaici yai yace " na sani ban kula da ku ba kaida mahaifiyarka lokacin kana yaro sannan na sani laifinane da bana shiga duk wani harka data shafeku sai dai na sani bazaka taba gane dalili na nayin hakan ba." "so kake ka karemu, bakasan a gane damuwarka a kanmu bare a mana illa." jin wannan zance daga bakin Abu Turab yasa ya kuramai ido. D'agowa Abu Turab yai ya kalleshi, jiyai zuciyarsa ba dadi, ko dai ya dau abin da zafi ne?" Ga mamakinsa gani yai Sarki ya saki wani sansanyan murmushi sannan yace " Alhamdulila d'ana ya girma." Baisan sanda ya kalleshi ba cikin mamaki. Sarki yamai alama da hannu akan ya matso. Da sauri yad'auke idanunsa, Mai Martaba ya kara mai alama da hannu sannan yace " na sank kana gani Turab." Idanu Abu Turab ya zaro Sarki ya mike da kansa yazo inda yake, kansa ya d'ago saitin sa yace " na sani da dadewa, na janye idona ne daga nuna maka saboda banasan ruguza abinda mahaifiyarka ta shirya ya ruguje." Idanunsa ne suka ciciko, kai ya girgiza mai yace " ka manta mai kace? A matsayin Uba kakeso muyi magana? Yau a matsayin uba nake, daga kabar nan zan koma sarki in kuma manta da abinda ya faru tsakanin mu." Idanu ya runtse yama kasa magana sam, Sarki yad'an had'e fuska kadan yace " ina Abu Turab dina wanda baya shakka ta? Jarumin da nake farincikin samun d'a kamar sa?" Baisan sanda yad'an murmusa ba. Sarki ya kalleshi yace " me ka shirga game da abinda Magajiya ta maka?" Abu Turab ya kalleshi yace " bazan iya fadama Sarki ba, sai dai ina neman alfarma akan kaba Abdulmajid umarnin yin binciken abinda ya faru." Bai kara tambayarsa va yace " shikenan, sai me kuma?" Yace "inaso ka taimaka ka cigaba da nuna rashin damuwa dani da kuma hukuntani sosai in nai ba daidai ba." Yace "shikenan, sai kuma me?" Kai ya girgiza yace " su kenan." Murmushi sukama junansu. Abu Turab ya mike zai tafi, jiyai mahaifinsa yace " yanzu mun zama d'aya kenan ko?" Ba tare da ya juyo ba yace " dama can d'aya muke." Yana kaiwa nan ya bud'e kofa. Yana fita ya had'e fuska sannan ya tsaya a waje kamar irin an mai fadan nan sosai, ya dade a tsaye kafin jiki a sanyaye ya fara tafiya, tuntube yai saura kiris ya fadi da sauri Garzali ya taimaka mai sukai gaba. Jakadiya ta tabe baki sannan tace " da alama ansha fada, ai naso a nan akai ba a kuryar d'aki ba." Nace hmmmm *ABU TURAB TEAM 🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *24* Abu Turab yana shiga d'akinsa ya rufe tare da jingina a jikin kofar, tausayin Mahaifinsa ne yake ratsa jikinsa ace kana san abu amma saboda kana mulki baka isa ka nuna ba? Lalai shikam wannan mulkin sam baya kansa. Haka ya kwanta bacci zuciyarsa fal da tunani kala kala. ******** Washegari a fada Mai Martaba ya umarci Abdulmajid akan ya d'aurashi akan aikin binciken abinda ya samu kaninsa. Ba Abdulmajid ba kowa na fadar sai da yai mamakin wannan al'amari, ai ko ba'a fada ba kowa yasan ba wata soyayya ko mutunci a tsakaninsu, amma ace shine zaiyi binciken? Andulmajid ya kalli Mai Martaba cikin tsananin mamaki, kafin ya daure yace " insha Allah zanyi binciken abin in sanar maka." Yana fitowa Hisham ya biyoshi, Hisham ya kalleshi yace " me ke faruwa?" Abdulmajid ya dan kurama kasa ido sannan yace " abinda ke faruwa?" Umm yad'anyi ajiyar zuciya yace " wannan shine tambayar da zan fara nemanma amsa." Hisham yace " muje gun Magajiya nikaina inasan ganinta." Bayan sun isa gunta ne sun gaisheta, Abdulmajid ya sanar da ita abinda ke faruwa, murmushi ne mai sanyi ya bayyana a fuskarta ta kalli d'an nata tace " hmm lalai Turab ya girma sai dai Tsohon doki yafi sabon takalmi." Abdulmajid ya mata kallan rashin fahimta, "Tsi tsi tsi tsi" abinda tai da bakinta kenan tana jijiga kai tace " karka badani mana Abdulmajid, ba shakka Turab abinda ya nema mahaifinsa yamai kenan jiya. Hisham yace " nima naji labarin zuwansa sai dai naji ance fada aka mai?" Baki ta tabe tace " ko da wasa ni nasan ba fada aka mai ba in har fada ne mezaisa ya shiga kuryar d'aki? Sannan da yamma ya riga ya umarci Sabi'u akan yai bincike sannan yau da safe ya maidashi kan Turab ne hakan yake nufi?" Hisham ya kalleta yace "amma hauka yake da zai umarci Abdulmajid? Bayan yasan ba sanshi yake ba." Abdulmajid ya kalli Magajiya yace " Umma kina nufin yayi hakan ne saboda karmu d'aurama mahaifiyarsa laifi? Tunda yasan ai ni ban isa ince mahaifiyarsa bace hakan zaisa a zargeni." Magajiya ta mai alamar jinjina da hannu tace " kwarai kuwa Yarima na ashe ka harbo jirgin." Dariya Abdulmajid yai yace " lalai yaran nan, yana makaho har......" Katseshi tai tace " munyi sakaci da muka ragamai muna tunanin makaho ai baya ganin komai, masarauta fa muke?sannan jinin mahaifinsa da kakansa suna yawo fa ajikinsa." Hisham ya kalleta yace " yanzu meye abinyi?" "Hmm farko dai tunda ya maida wasan kanmu dole ne mu buga wasan, ai hakorin dariya shi yakanyi cizo." Kallan mamaki suka mata, tai kalli Abdulmajid tace " ka nutsu sosai kaga yanda zan buga wasan." Shiru yad'an biyo baya kafin Hisham yace " ni kuma wani abu d'aya ne yake damuna, me yasa haryanzu sarki ya kasa neman ma Abu Turab magani?tunfarkon zuwan sa da yadanyi na shekaru kad'an yanzu sam baya turo masu magani, ko ya hakura ne da makantar yaron....." Magajiya ta d'an kankance ido tace "ko kuma ya warke ba." Idanu suka zaro suka kalleta, shiru tai tana tunani kafin ta mike da sauri tace " me yasa hakan baizo min ba?" Da sauri ta kalli Hisham tace " Hisham aika a kiramin yaron nan." Abdulmajid shima ya mike hankalinsa a tashe yace "Ya zamuyi in har yana gani? Kenan za'a iya bashi mulkina!" Magajiya ta bugamai wani kallo tace " so kake ka zama rago akan wani makahon daya warke?" Hisham ne yai waje da sauri ya tura baiwar Magajiya akan ta aika a kira Abu Turab. Shiru tai tana tunani kafin tace " aika a dafomin ruwa mai zafi sannan a zubo a roba, a kuma zubo ruwa mai sanyi shima a roba." Shiru tai tana tunani kafin ta fita da kanta, ba shakka hankalinta ya tashi, ya zatai in har yana gani? Kenan tunda raina musu hankali yakeyi kenan. ******** Zaune yake yanashan ruwan zafi wanda yasa aka dafa mai da kayan kamshi, zafin cittar yasa yake d'an lumshe idanunsa, shigowar Garzali ce tasa ya bud'e idanunsa. Zubewa yai a kasa ya sanar dashi sakon nemansa da Magajiya takeyi yanzu. Bai amsa ba ya cigaba da shan shayinsa. Sai daya gama sannan ya mike ya shirya ya fito, Garzali ya taso da sauri yazo kusa dashi. Tafe suke yana rike da sandarsa, idanunsa ne suka kai gun jiya inda yarinyarnan ta b'uya, ya rasa me yasa yakeji kamar ana kallansa. Yana kallan gun kuwa suka had'a ido. Da sauri ta b'oye tare da dafa kirjinta dayake bugawa da sauri, a tsorace tace " ya ganni?" Kai ta girgiza tace " ta ina zai ganni?" Shikansa jikinsa ne yai sanyi yana tunanin abinda ya gani, kawar da abin yai a ransa har suka karasa b'angaren Magajiya. Tana zaune a kilisarta, Abdulmajid na gefenta, Hisham ma na d'aya gefen nata ya shigo. Sai daya zauna sannan Garzali ya fita. Gaisheta Abu Turab yai ta amsa tana karema idanunsa kallo kansa na kasa, kallan zargi takema a haka tace " Me ya faru ne sam ka daina zuwa gaisheni." Murmushi ya d'anyi yace " Da alama Umma Babba san ganina ne yasa kika manta nazo kwanan nan." Kallansa tai tace "haba? Amma ya akai nakeji kamar na dade banga d'ana ba?" Yace " zan dinga zuwa akai akai in har kinasan ganina." Tai dan murmushi sannan tace " bari a kawo ma abinci kaci, yau takanas nasa a ma d'ana abinci, dan na kula bana baka kulawa yanda ya dace." Ya jita sai dai bai tanka mata ba, nan tasa aka jera mai a binci tace " bismillah." Hannu ya saka yana shashafa kwanukan alamar baya gani, kwarai yaga ruwan zafin dake daf dashi, tunani ya fara yi me ya kawo ruwa wanda yake turiri kusa dashi? Kana kallan ruwan kasan yanzu aka juyeshi, ba shakka zargin ganinsa takeyi, bazai taba ba mahaifiyarsa kunya ba dan kawai ya faranta ransa ba, hannunsa yakai kan ruwan zafi da saninsa ya sa hannunsa zuciya d'aya. Azabar dayaji ne yasa ya zare hannun da sauri ya rike hannun cikin jin zafin zugi da radadin da yakemai. Kallan juna sukayi suka saki murmushi ba shakka baya gani. Da gudu ta karaso ciki tashin hankali, hannunsa ta kama da sauri ta saka cikin ruwan sanyi. Kuka kawai takeyi hankalinta yayi tsananin tashi. Magajiya ta mike itama tace " lafiya Abu Turab?" Ta fada tare da nunama Abdulmajid ya d'auke ruwan zafin. Nan ya d'auke ruwan. Kallansa tai tace " garin yaya? Ina lilahi wa ina ilaihi raji'un, me ya faru? Badai ruwan wanke hannu danace su kawomin bane suka kawo na zafi, inaji sun d'auka kafata zan gasa wacce ma bige jiya." Ba wanda ya kulata tsakanin Abu Turab da Khadija. Shikam yama kasa komai zafin hannunsa da kuma ganin Khadija sun sa sam yama kasa cewa komai. Kuka take sosai ta mike da gudu ta fita, dawowa tai d'auke da zuma a kofi ta shafamai, Magajiya duk ta rikice. Abu Turab ya daure ya kwace hannunsa sannan ya mike yace " bakomai Umma Babba ba laifinki bane na sani, ke mai zaisa kisa a kawoma d'anki makaho ruwan zafi haka? In har dama ba neman halakashi kike ba, wanda nasan ke kuma ba hakan bane a gunki." Ta bud'e baki zatai magana yai waje. Ba shakka ta tabbata magana cikin magana ya fada mata. Khadija ta kallesu dukansu cikin kunar rai sannan tai waje da gudu. Binsa tai inda yake ta rike hannun daya kone ta sama tace " yaya muje a baka magani." Fuska ya d'aure tamau sannan ya kalli Garzali yace " wacece wannan d'in take tabani?" Garzali ya kalleta, zaiyi magana tai saurin cewa " Yaya Khadija ce, nice kasani ba cutar dakai zanyi ba." Hannunsa ya fizge yace " ta ina kenan na san ba cutar dani zakiyi ba? Ko na sanki ne da harzan iya miki shaida?" Sakeshi tai idanunta suka ciciko a hankali tadanyi baya kadan tana mai kallan tsananin mamaki. Garzali wuce muje. Tana tsaye anan har suka kule sam tama rasa abinda zatai tunani. Jiki a sanyaye ta koma b'angaren Magajiya. Taje shiga taji suna dariya, Hisham yace " da alama dai idannan bam yake baya ganin komai." Dariya Abdulmajid yai yace " tab amma fa ya daure dan ruwan zafi ba wasa bane." Bud'e kofar tai da karfi cikin tsananin mamaki ta kallesu. Tace " da saninku?" Dif sukai kowa ya kura mata ido. Hawaye ne suka shiga zubo mata ta girgiza kai tace " kuna 'yan uwa, ko ba 'yan uwantaka ai akwai na musulunci, tayaya zaku samu mutum wanda Allah ya d'auke ganinsa ku samai ruwa ya kone? Nazo da niyyar muku magana akan barin Inna Lami a halin da take bayan na dawo daga gunta, sai in tarar da wanda yafi nata?" Kuka ne yaci karfinta tace " anya akwai tausayin imani a zuciyoy......" Wani wawan mari Hisham ya mata wanda batai zatan jinsa ba. Kuncinta ta rike ta kalleshi, kasa magana tai, waje tai da gudu taba kuka. *#ABU TURAB TEAM🤝🏼* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* _ina baku hakuri jina da kukai shiru, wayatace tad'an samu matsala nagode kwarai da kulawarku, naga sakwaninku na kuma gode, plz wanda yamin magana baiga namai reply ba yai hakuri whatsapp dina baiyi restoring old messages dina ba, nagode._ *25* Turab yana shiga ya bud'e kofar d'akinsa yasa kai zai shiga kenan yaji muryar Garzali yace "Ranka ya dade ana nemanka." Juyowa yai yace " wa?" Garzali yai kasa dakai, Abu Turab ya kalleshi yace "Umma ce?" "Tuba nake ranka ya dade." Idanu Turab ya rufe, Garzali ya tsugunna da sauri yace " Tuba nakeyi." Abu Turab ya juya har yakai kofa sannan ya tsaya yace " ka fada mata komai?" Garzali yace " a'a bansan waye ya sanar da ita xuwan mu can ba, ina shigowa ta turo inxo, tambayata tai me ya faru a inda mukaje....." Katsetshi yai yace " tambayar da maka itace ka fada mata komai?" Garzali yace " nadai sanar da ita kunan dakai amma bansanar da ita wani abu ba daga wannan." Takawa yai ya cigaba da tafiyarsa fuskarsa a d'aure. Xama yai irin zaman daya sabayi a gaban ta, wato lankwashe kafa, kansa na kasa kallansa tai cikin kulawa tace " muga hannun." D'agowa yai ya mata murmushi yace " Umma karfa ki damu ba wani abu bane nine bansani ba na taba ruwan zafi sannan a lokacin aka samun zuma a gun." Ido ta kuramai cikin kulawa da tausayi tace " Turab ba sai ka dage ba wajen b'oyemin gaskiya ba dan hankalina ya kwanta, banaji ko yaro ne yaji xancen nan naka zai yarda." Kallanta yai yace " Umma." Yanda ya kirata yasa bata amsa ba sai kallesa datai. Ajiyar zuciya yai yace " Umma ina neman alfarma a gunki." Idanunta na kansa bata dauke ba haka kuma batace komai ba ya cigaba " abu d'aya nakeso kimin, dan Allah Umma ki rage damuwa dani." Cikin tsananin mamaki ta kalleshi sai dai yanayin yanda yai maganar yasa ta kasa magana. Idanunsa yadan rufe kadan sannan yace " gidan sarauta muke, sarautar ma inda makiyanmu sukai yawa, na tabbata a gidan nan kaf daga ciki har waje in har mukace muna neman wanda yake kaunarmu dari bisa dari banaji zamu samu mutane goma cikaku, in muka dauke bayin dake karkashin mu, yanayin yanda muke rayuwarmu ni dake dole ne sai mun sadaukar da rayuwarmu dolene mu sha wahala in har munasan zama cikin kwanciyar hankali, sa damuwata a ranki da kuma shiga wani hali in har abu ya sameni ina ganin babbar matsala ce, saboda dole wani sa'in zan nemi b'oye miki wani abun saboda gudun shiga wani yanayi da kikeyi." Kallansa tai jikinta yayi mugun sanyi, tanasan sanar dashi abinda ya samu yayanta sai dai a yanda tasan Turab tana ganin in har yasan abinda ya faru dasu to fa lalai tana ganin xai cire wani farinciki a ransa ne ya juya rayuwarsa zuwa d'aukan fansa wanda ita kuma tana san farincikin danta dukda kuwa tasha alwashin hukunta wanda yama yayanta hakan. Kallanta yai ganin yanayin datake ciki yasa ya runste idanunsa da karfi sannan ya mike yai hanyar fita. Jiyai tace " shikenan Abu Turab." Tsayawa yai sannan a hankali ya juyo ya kalleta, ta mai murmushin yake sannan tace " hankalinka ya kwanta?" Kallanta yai cikin wani yanayi, sannan a hankali ya taka inda take zaune ya tsugunna gabanta yace "Umma do u trust me?" Kallansa tai tace " me kenan?" Dariya yad'anyi kadan yace " nufina kin yarda dani?" Kai ta d'aga mai, ya dan murmusa yace " shikadai nake bukata, yardarki gareni, in har kin yarda dani inaso ki yarda xan kula dake bazan bari wani abu kuma ya samen ba sai dai abinda Allah ya kaddara." Kai ta jinjina mai tace " nagode Abu Turab, sannan insha Allah ba abinda zai sameka." Mikewa yai ya mata sallama zai fita. Mairo wacce ta kawoma Basira gwaza wacce mahaifiyarta ta dafata ta fere ta sa ma kula, taxo shiga taji yana cema Basira do u trust me? Wanda hakan yasa ta koma ta tsaya. Jin alamun fitowarsa yasa ta juya da sauri zatai waje garin sauri kafafunta suka harde, baya tai luu kamar zata fadi. Cikin hanzari ya karaso ya tareta. Idanunta ne suka sauka akan nasa, kallansa tai cikin tsananin mamaki, da sauri ya saketa dan sam ya manta ashefa batasan yana gani ba. Jikake tim ta fadi a kasa, sosai taji xafin faduwar saboda sam bata zaci zai saketa ba, kallansa tai kamar tai kuka dan bakin ciki. Hannu yasa yace " sannu faduwa kikai?kina ina?" Haushi ya kamata ta mike ta matso inda yake tace " yaya fadamin gaskiya, da saninka ka sakeni ko?" Gefen inda take ya kalla yace " me kike nufi?" Sake baki tai cikin salon shagwaba tace " inba haka ba tayaya ka taimaken kuma zaka sakeni?" Murmushi yai dan tabbas yaga faduwar datai yasan taji zafi yace " au so kike in rike ki?" Kallansa tai tace " yaushe nace haka?" Iska yadan furzar yace" lalai Mairo da alama aure kikeso." Ya juya da sandarsa ya fara tafiya. Takaici ma ya hanata magana, aure takeso? Me yake nufi da hakan? Kallansa tai ta baya a hankali tace " na tabbata mun fa hada ido dashi." Tana neman amsar tambayarta taji muryar. Lantana taji tana cewa " Mairo? Me kike anan a tsaye?" Juyowa tai ta kalleta idanunta sun dan ciciko, kusa da ita taxo ta ajiye kula tace " kiba Umma." Ta juya da sauri tai waje. Abu Turab kam b'angarensa ya nufa yana bud'e gate, bayinsa suka taho da sauri suka karasa bud'e mai kofa. Ciki ya shiga, yana zama Garzali ya mikomai abu a bakar leda. Yace "Ranka ya dade gashi an aiko a kawoma." Yace "Magajiya?" Garzali yace " a'a wlh bansan waye ba kawai kawowa akai, dana tambaya inji waye sai wacce ta kawo ta juya da gudu." Ya gane Khadija ce, bai sa hannu ya amsa ba yace " ajiye anan kwanciya nake sanyi." Ajiye wa yai ya mike a hankali yai waje. Yana fita ya kalli ledar, shiru yai yana tuno fuskarta, fuskar daya dade yana san gani duk yanda yaso ya yage ta a ransa ya kasa, dan karamin tsaki yaja sannan ya sa hannayensa kan goshinsa. Khadija kam bayan ta aikamai da magani gida ta tafi ta shige dakinsu ta fada gado ta kwanta, kuka kawai takeyi tana jin xafin abinda akama Turab. Duk yanda mahaifiyarta tai akan ta bude kofar taki, ko abinci kinci tai. ********* Yau kwanan Basira ne, ta shirya tsaf ta nufi bangaren Mai Martaba. Bayan sun kwanta ne ya kalleta yace " Basira." Kallansa tai ba tare da ta amsa ba, yacigaba " me kike tunani game da auren Turab?" Kallan mamaki tamai tace "aure? Takawa ka manta Abdulmajid baiyi aure ba?" Kallanta yai yace " na sani sarai sai dai inatunanin auran sa zai sa matsayinsa da kimarsa ta karu a gun mutane sannan inasan nemarmasa matar da zata taimakeshi yanda ko ansan yana gani ba wani wanda ya isa ya nemi cutar dashi." Kallansa tai tace "ban gane ba?" Yace " me kike tunani game da hadin aure da 'yar sarkin kano?" Kallansa tai tace " Bilkisu?" Kai ya daga mata alamar eh. Kallansa tai jiki a sanyaye tace " amma kana ganin za'a bashi? Na farko shi makaho ne a idan duniya sannan Bilkisu ita kadaice mace a gun Sarki Muktar wato sarkin kano, ni nafi mai sha'awar mairo 'yar gidan Barde." Kallanta yai yace " Na fahimceki sai dai ina so ki sani Abu Turab ba mijin mace d'aya bane sannan yana bukatar mace kamar Bilkisu saboda taimakamai wajen hawa mulki." Da sauri ta mike zaune cikin tsananin tashin hankali tace " me? Mulki?" Kallanta yai ya daga mata kai. Idanu ta zaro cikin tsananin mamaki, yace " Bilkisu ita Magajiya takesan aurama Abdulmajid in har ya aureta ba makawa sai ya hau mulki, bakya tunanin abinda zai faru da rayuwar ku ke da Abu Turab kn har Abdulmajid ya hau mulki?" Kallansa tai duk tama rasa ta cewa dan ta tsorata da zancen. Ya kalleta yace " Abu Turab shi kadai ne wanda ko bayan raina na tabbata bazai wulakanta ahalina ba, bazai wulakanta mutanena ba, bazai rushe rayuwar dana gina a kasa ta ba." Kai kawai tashiga girgizawa tana tsoron abinda zai faru da wannan sabon lamarin....... *ABU TURAB TEAM*🤝🏻 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *26* Kallansa tai cikin tashin hankali tace " mai kake nufi da kalamanka? Nasani ka fini iko da Abu Turab sai dai ina rokonka kabar maganar nan a kan gadon nan, ni zan manta munyi wannan maganar dakai." Jitai yace " kin taba jin inda akai magana bayan wanda aka fadama maganar yaji sannan yace zai manta maganar? Ai magana ana manta tane in batada mahimmanci." Kallansa tai tace " dan Allah kabar maganar nan, nafisan Turab ya auri Mairo ya bar gidan nan dan samun farincikin rayuwarsa." "In kuma kaddararsa ce mulkin fa?" Jin maganar tai batai zata ba, Kallansa tai batace komai ba. Shima bai tanka mata ba ya kwanta tare da juya bayansa. Ta dade a zaune tana kallansa kafin ta kwanta. Idanunsa a bud'e suke tunani yakeyi " bazai iya sanar da ita su Magajiya sune sanadiyyar makantar Abu Turab ba saboda bayasan ya sanya mata damuwa da kuma shiga wani yanayi najin wannan zancen. Ba shakka shikanshi jin wannan zance ya daga mai hankali matuka, kamar wasa d'azu da rana Khadija yar gidan Hisham ta samu barde da sakon Lami akan dan Allah tanasan Mai Martaba ya ziyarceta dan akwai magana mai mahimmanci da takesan sanar dashi. Ganin yanayin aikin dake gabansa yasa ya aika Barde akan yaje yaji menene. Zuwan Barde ya taradda ita cikin mugun hali, tana kwance ko mikewa bata iyayi, ba kowa a gunta d'akin banda wari ma ba abinda yakeyi wai a hakan ma zuwan Khadija ne ta gyara mata d'azu. Barde ya kalleta tare da dubata, ya d'ora da cewa "amma ya akai ke kad'ai anan?" Tana kwance sai numfarfashi takeyi tace " Barde." Kallanta yai cikin tausayawa yace " Mai Martaba wani uzuri ya rikeshi shine yace inzo inji menene, bai san jikin naki haka yakoma ba." Hawayene suka gangaro mata tace " Barde ni tawa ta kare dan banaji ko gobe zan kai a duniya, dan Allah ka nemarmin yafiya agun Abu Turab, Basira da Mai Martaba." Kallan mamaki ya mata yace " ban gane ba." Hawayene suka kara kwaranyu mata tace " nice sanadiyyar makantar Abu Turab dan kuwa nice na je gun malami aka makantar dashi, kwanakin nan ko bacci na fara ganin yaro nakeyi ba ido yana tsaye a gabana, na tabbata laifin danai ne yake bibiyata, na sani alhakinsa ne ma ya kwantar dani haka, 'ya'yana da 'yan uwana da nake komai dan faran ta musu rai duk sun gujeni....." Kuka ne yaci karfinta wanda yasa ta kasa karasawa, jikin Barde ne ya mutu mamaki da tsoron wannan al'amari yasa ya taho daga gidanta ba tare da ya gamajin kalamanta ba. Idanu mai martaba yadan runtse a ransa yace " bazan taba yafe musu ba." Babban bakin cikinsa shine a matsayinsa na sarki bashida hujjar hukuntasu, na farko bashida kwakwarar shaida sannan inma yana tunanin Lami zata zamarmai shaida ya tabbata Magajiya juya abin zatai kanta ko za'ai me bazata taba cewa itace sila ba. Ba shakka sanya Abu Turab a mukamin Sarki ita kadai ce hanyar da zai sa ya hukuntasu ta ruwan sanyi wanda yafi na zafi kuna. Dolene Abu Turab ya auri Bilkisu dan kuwa wannan shine mataki na farko na cinma burinsa. Basira ma bacci ya gagareta ta rasa abinda ke mata dadi, itakam ba wata 'yar sarki datake so Mairo takeso ta bashi ko dan farincikin sa na nan gaba. *********** Washegari da safe Abu Turab ya tafi garden din mahaifinsa wanda a yanzu shike zama agun dan kebencewa daga hayaniya, yana zuwa gun ne a duk lokacin da yake bukatar yin dogon nazari game da wani abu. A zaune yake akan kujera ta karfe dake gun, shukoki kala kala ne a gun, wanda ya kayata gun, kansa ya kwantar a kan saman kujerar ya lumshe idanuwansa tare da dora hannunsa daya kone akan goshinsa. Kana ganinsa kaga mai bacci, shigowa tai a hankali gun, tafiyarta takeyi mai sanyi tana tafe tana duba inda yake, cak ta tsaya a yayin data han goshi akan kujera, tunda ya fito ta biyoshi, sannan matsayinta yasa fadawan dake gadin kofar shiga gun basu hanata shiga ba. Murmushi ne ya bayyana a fuskarta ganin yanda ya ke, ta dauka bacci yakeyi hakan yasa ta tako a hankali tazo inda yake. Ta bayan kujerar ta tsaya ya zamana tana tsaye saman inda ya kwantar da kansa. Hannunsa ta kalla gun yayi jaa har yanzu amma bai duri ruwa ba. Kallansa takeyi tanajin wani sanyi na ratsa dukkan sansan jikinta. Jin kamar mutum na kusa dashi yasa ya bud'e idanunsa a hankali. A hankali ya kara maida idanunsa ya lumshe dan ya tabbata mafarki yakeyi, ba wanda ya taba biyoshi gun sannan in ma ana biyoshi mai zai kawo Khadija nan? Idanunta ne suka ciciko a hankali tace " yanzu fa bazai ganni ba ko?" Idanunsa ya kara budewa ya daurasu a kanta, itama kallansa tai. Da sauri ya mike zaune ya dan maze yace "akwai mutum anan ne?" Khadija batace komai ba, jin yayi shiru yasa a ranta tace " da alama bai san dani ba." Dawowa tai ta gabansa ta tsugunna tare da tagumi kallansa kawai takeyi, ba shakka su Magajiya da Mahaifinta sun bata mata rai sosai wannan wace irin muguntace? Abu Turab yana ganinta amma sai yai kamar bai ganta ba. Sunfi minti talatin a haka kafin daga bisani ya mike rike da sandarsa. Yace " na dauka nayi magana akan wanene anan ko? Ko dan bana gani an dauka bana jin motsi da numfashin mutum?" Idanu Khadija ta zaro itama ta mike tsaye, juyawa taga yayi zai tafi da sauri ta sa hannu ta rike rigarshi ta baya. Tsayawa yai va tare da ya juyo ba, yace " wanene?" Shiru tai batace komai ba, rigarsa ya fizge ya fara tafiya da sauri ta sa hannu batasani ba ta riko hannunsa. Tsayawa yai sai dai wannan karan ya juyo. Hannunta ta kalla da sauri ta sakeshi tace " Yaya nice." Fuskarsa a d'aure yace "kece wa?" A hankali tace " Khadija ce." Gani tai ya sake juyawa zai tafi. Gabansa tasha da sauri, shikuma yai kamar bai ganta ba ya taho ya dauka in ya taho zata matsa ita kuma bata taba tunanin zai zo daf haka ba. Jikinsu ne ya hadu da juna wanda tsoro yasa ta rike rigarsa tai baya da sauri, shi kuma rike rigarsa datai yasa ya fada kanta suka fadi tare? Idanunta ta rufe saboda tsananin kunya, shikam kallanta yai sosai dan bai taba kallanta daf da daf ba sai yau. Idanunta a rufe tace " Ya ka d'agani!" Cikin shagwaba tai maganar kallanta yai yace " da wayace ki yarda ni?" Tace " ni kuma? Yaushe?" Mikewa yai tare da sa hannu ya d'agota hannu tasa ta rufe fuskarta. Juyawa taga yayi zai tafi sai alokacin ma abin yazo mata to ma in taji kunyarsa inama ya gani? Daurewa tai tace "Yaya kayi hakuri." Yace "game da me kenan?" Tana tsaye a bayansa tace "game da komai ma." " niban fahimci hakurin da kike bani ba ai." Hawaye ne suka fara zubo mata, cikin kuka tace " na konewar da kai wanda su Umma Babba suka ja ma." Fuskarsa a had'e yace " wannan kuma menene naki a ciki? Meye naki na bada hakuri?" Kallansa tai ta baya tace " taya zaka ce haka Yaya?" Cikin bacin rai ya Juyo ya kalleta yace " kukan me kike kuma?" Cikin kuka tace " ni kaina so nake hawayen su tsaya." Dan karamin tsaki yaja yace " abinda ya kamata kuma nakesan naji kin ban hakuri akai da alama ma bakisan shi ba, bana bukatar kukan ki ba kuma na neman ban hakurin ki." Juyawa yai kamar zai tafi. Rigarsa ta sake rikesa amma hanzu hannun rigar ta rike, a hankali ta furta "Yaya kayi hakuri tafiyar danai ba tare da nama sallama ba." Jikinsa ne yai sanyi, bai juyo ba, ta kara share hawayenta zatai magana ya juyo cikin bacin rai yace " kinsan kwana nawa nai ina jiranki? Awanni nawa nai ina nemanki? Lokuta nawa na bata ina tunanin dawowarki? Zaki tafi menene inkincemin zaki tafi? Hanaki zanyi? Ko dan Kinga na dogara da zuwanki a koda yaushe? Sai dai inaso ki sani na dade da mantawa da ke da jiranki." Juyawa yai ya fara tafiya, tsugunnawa tai kawai tasa kuka. "Ba laifina bane yaya, ba laifina bane nikaina banso tafiya ba, ba laifina bane." Abinda kawai take fada kenan. Yana jinta yai waje shikanshi kukanta har jikinsa yake ji. Yana fita ya jingina da jikin kofa ya dade a haka kafin ya sa sandarsa ya fara tafiya. ******** Mairo ce zaune tana wanke wanke tanayi tana 'yar karamar mita dan itakam ta tsani abinda ake mata, mahaifiyarta su biyu ne, kishiyar babarta sam bata sa nata 'ya'yan aiki amma ita kullum ita ake sawa aiki kuma tanayi ba a gode mata sai tai magana mahaifiyarta tace batada hakuri. Sa'arta ta gani ta gun kishiyar mahaifiyarta ta kalleta tace " nikam Karima wai nikam sai yaushe zaku biyani kudin wata?" Karima ta kalleta tace " kudin wani watan kuma?" Mairo ta harareta tace " na albashin aiki da kuka daukoni mana." Karima tace " ban gane ba" Mairo cikin masifa tace " nifa bazan laminci wannan rainin hankalin ba ehe, sai kace wata 'yar aikinku?" Muryar maman Karima taji a bayanta tace " to bazasuyi ba kedin meye aikinki? Tunda kinki aure?" Mairo tai dariya tace " dan ma dai bani kadai bace banyi auran ba." Karima tace " da wa kike?" Mairo tace " wanda ya tsargu, haka kawai tunda mai taya mu aiki tai tafiya kullum ni nake aiki ni ba 'yar aiki ba bakuma baiwa ba?" Jitai an dada mata duka a bayanta ta juyo da nufin masifa, mahaifiyarta ta tagani, ta kalleta tace " Mairo bana hanaki ba?" Turo baki tai batace komai. *ABU TURAB TEAM 🤝🏻* .🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *27* Garzali ne ya biyoshi suka nufi fada dan yanzu aka aiko akan yaje saboda Abdulmajid zai sanar da binciken dayai. Bayan sun zauna ne Abdulmajid ya dawo tsakiya sannan yace " Ranka ya dade na gama bincike." Galadima ne yace " to munajinka." Abdulmajid yai d'an gyaran murya sannan yace " bincike ya nuna mana cewa ba kowa bane ya jawo wannan abin ba sai mahaifiyarsa." Jin wannan zance yasa mutane suka fara kananan magan magan, Abu Turab kam wani murmushi ya saki kansa na kasa a ransa yace " they take the bait." Kallan Abdulmajid kowa yai, Mai Martaba ya kalleshi yace " meye hujjarka na fadar haka?" Abdulmajid ya gyara zama yace " Mahaifiyarsa tanasan asan shi wanene, ma'ana asan shidin d'an sarki ne, sannan tayi hakan ne dan mutane su farga susan akwai wani magajin sarkin bayan ni." Mai Martaba yace " wannan ita kadai ce hujjarka?" Kai ya girgiza alamar a'a yace " tayi abu kala biyu, na farko in har yasa mutane zasu sanshi saboda kayansa da kuma yanayin dokinsa, na biyu kuma ba wanda zaiyi zarginta sai dai kowa yai zargin Magajiya, kunga ta jefi tsintsu biyu da dutse d'aya." AbuTurab ya d'ago kai yace " Bravo! Ba shakka wannan ma abin dubawa ne." Mamaki hakan yaba Abdulmajid ya dauka abin zai tadamai hankali. Barde ne ya katse mai tunaninsa da cewa " shaidu fa?" Abdulmajid ya juya yace " shigo." Nan wani bawa ya shigo wanda kowa ya sani bawa ne wanda ke kula da al'amuran Magajiya na waje bana ciki ba. Daga can bakin kofa ya zube ya gaidasu, Abdulmajid yace " wannan bawan bawa ne ga Magajiya shi Mahaifiyar Abu Turab tai amfani gun aika mai da kaya dan gudun kar a gane itace." To fa? Nan kowa yad'an fara magana kasa kasa. Abdulmajid ya kalleshi yace " sanar damu abinda ka sani." Muryarsa na rawa alamar tsoro da dana sani yace " tuba nake ranka ya dade amma abinda Yarima mai jiran gado ya fada haka yake, ranar nazo wucewa Baiwarta wato Lantana ta mikon kaya tace " dan Allah sauri nake dan mikama Abu Turab, basai ka shiga ba kawai ka bada a kofar shiga ka wuce." Salati mutane suka fara dayawa sun gamsu dan sunsan ba yanda za'ai bawa yazo gaban mai martaba ya gilla karya haka. Abu Turab yai murmushi sannan yace " Ammm ina Mai bada shaidar nan?" Bawan yace ganinan Yarima." Abu Turab yace " ka tabbata duk abinda ka fada gaskiya ne?" Yace " hakan yake Ranka ya dade, ina ni ina karya gaban Takawa." Abu Turab yace " haka ne, sai dai nima ina rokon a bani dama namai tambaya." Mai Martaba yace " inajinka." Abu Turab yace " inaso ka bani amsar tambaya ta cikin sauri ba tare da kaja min lokaci ba, inaso daga na tambayeka ka sanar dani amsa." Kai ya daga. Abu Turab yace " A ina kuka had'u?" "Gaban Turakar Magajiya." "Hmm kenan can ta bika saboda tana san ta aikeka?" Muryarsa ce tadan sarke yace " banida masaniya akan wannan." Yace " me yasa daka kawo kayan baka ce inji Lantana ba bayan a iya sanina wanda ya kawo kayan ance ya sanar da wanda ya aikosho?" Inin na ya fara cikin tsoro yace " hmm hmm nima sauri nake hmm shi yasa....." Abu Turab ya karseshi da cewa " ok na gane, saurin da kakeyi ne ya hanaka sanarwa ko?" Da sauri yace haka ne. Abu Turab yace " kenan bayi nane sukai karya tunda sun sanar dani an fada musu wanda ya aiko da kayan?" Bawan yai shiru, Abu Turab yace " na fahimceka, yanzu tambaya d'aya zan maka, dakai da Lantana wanene yafi wani matsayi a gidan nan?" Cikin rashin fahimtar zancensa yace " na fita." Abu Turab yace " Good! Ka fita matsayi meya saka ka yarda ta aikeka?" Gaban Bawan ne ya fadi ya fara inda inda "hmm dama...." Katseshi Abu Turab yai yace " dama me?" Shiru yai dan ya rasa bakin magana, Abu Turab yace " bari na aika a kira Lantana da alama kunada wata ala'aka da ita wanda ba wanda ya sani, dan hakan ne kadai zai sa mu fahimci dalilinka na zuwa aikenta." Hankalinsa ne ya tashi da sauri yace " wlh ba haka bane ni banma taba magana da ita ba, ina dai gani suna zuwa gun Magajiya amma wlh ko sau d'aya bamu taba magana da ita ba....." Shiru yai jin ya kauce hanya a zancen sa. Abu Turab yace " to fa yanzu wace maganar zamu yadda da ita?" Galadima a harzuke yace " wannan shaidar bamu yarda da ita ba dan ta nuna itadin bakin ganga ce." Idanu Abdulmajid ya runtse dan bakin ciki. Wani mugun kallo ya bugama Abu Turab, nan mutane suka fara kananan maganganu, lalai dama ance makaho yanada tasa baiwar da alama Abu Turab akwai kwakwalwa, ganin ne dai da Allah ya d'auke mai. Kallansa Mai Martaba yai cikin jin dadi, Abdulmajid yace " inada wata shaidar." Mai Martaba yace " muna jinka." Wanda ya kawoma Abu Turab doki ne ya shigo, bayan yayi gaisuwa Abdulmajid ya kalleshi yace " sanar damu abinda ya faru." Nan yace shidai an aikeshi ne yakai doki bangaren Abu Turab. Abu Turab ne ya katse Abdulmajid wanda ke shirin magana yace " tabbas muryarka ce naji a lokacin, sai dai tunda ba gani nake ba bazan san kaidin bawan wanene ba." Kansa na kasa yace " bawan Magajiya ne." Murmushi Abu Turab yai yace " kenan duk bayin Magajiya ta nemo?" Abdulmajid ya bugamai kallo baice komai ba, Abu Turab yace " amma ni mai ka sanar dani a lokacin? Wa kacemin ya aiko ka?" D'agowa yai yad'an kalli Abu Turab, gabansa ne ya fadi, duk da yasan baya gani amma baisan me yasa ba sai yaga kamar yana kallansa, kwarjini Turab yamai dama gashi duk cikinshi ya gama rud'ewa a waje dan kuwa yaji duk abinda ya faru da d'aya bawan. Shiru yai baice komai ba, Barde yace " zancen banza kenan, tayaya ana tambayarsa ya kasa bada amsa." Mai Martaba ne yai gyaran murya yace " Kana da wata shaidar? Dan wannan shaidar naga farar kura ce." Abdulmajid kasa yai dakai a hankali yace " tuba nake ranka ya dade banida wata." Mai Martaba ya kalli Abu Turab yace " kaifa? Kanada ta cewa?" Abu Turab yace " ina neman alfarma akan mai martaba ya yafema wanda ya aikata wannan laifin gudun samun babbar matsala garin bincike, dan na tabbata duk wanda ya aikata hakan tabbas bazai yarda a gane shi bane." Mai Martaba yace " zanyi tunani, amma wad'an nan bayin da sukai shaidar karya inaso a kullemin su." Da wannan fada ta tashi, kowa yana yaba kwazon Abu Turab. Hisham kam da Abdulmajid a cike suka isa gun Magajiya, bayan taji komai ta kalli Abdulmajid bai yi auni ba yaji ta wanka mai mari. Tashin hankali, d'agowa yai cikin tashin hankali dan tunda aka haifeshi ba'a taba dukansa ba sai yau, Magajiya ta kalleshi tace " wannan shine shirmanka na cewa in barma zaka d'au mataki da kanka? Wannan shine abinda kwakwalwarka kawai zata iya karantama?" Hisham wanda yaji dukan kamar a fuskarsa ya daure yace " kiyi hakuri Magajiya." Kallan Abdulmajid tai tace " ku bani guri." Nan suka mike jiki a sanyaye, Hisham na fita yai 'yar karamar kwafa a ransa yace " wlh wannan marin bashinshi kika co kikira d'ana ya hau mulki zakisan kin mareshi." ********** Bayan sati d'aya. Abu Turab zaune a gun mahaifiyarsa yanacin abinci sai dai zuciyarsa nata tunanin tun randa yaga khadija bai sake ganinta ba har yau, ko dai ta koma inda ta tafi da ne? Yana neman amsar tambayarsa yaji sallamar Mairo. Amsawa yai va tareda ya juyo ba. Gefensa ta karasa ta gaisheshi sannan tace " Yaya ina Umma?" Yace "Mairo tana ciki, kwana biyu?" Murmushi tai tace " na da'uka ko daina zuwa nai bazaka nemanba bare ka tambayen dalili." Juyowa yai yace " tanan kika b'ulo?" Tace "Ba haka bane yaya gaskiya ce ai na fada." Yace " hmm, ina saurayin naki? Ki fada mai fa in har yanasan in ba da ke sai yazo ya kwashi gaisuws." Fuska ta had'e tace "ni bansanshi ba." Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa wanda har hakwaransa suka fito, daidai nan Basira ta fito, kallansa tai cikin jin dadi tana ganin yanda yake tsokanar Mairo, kana ganinsu kasan suna cikin farin ciki, lalai dolene ta tilastamai auren Mairo. Yana gama cin abinci yanashan ruwa Garzali ya sanar dashi nemansa da Sabi'u yake. Mikewa yai ya sa hannu zai dauki sandarsa, da sauri Mairo ta d'auke sandar ta b'oye tana dariya. Yace " Mairo nasan kece, mikomin in fita, in kuma baki ban ba zan fita a haka duk abinda ya samen kece." Da sauri ta mikomai tace " yahkuri yaya." Amsa yai ya fita baice komai ba. Kallo ta bishi dashi tanajin wani abu na ratsa ta. ********* A waje yaga Sabi'u yiyai kamar zai wuceshi, Sabi'u yace " ganinan mutumina." Ya karasa maganar tare da dafashi. Abu Turab yace " Badai aiko ka akai ba ko?" Yace " Mai Martaba ne yace inzo dakai." Fuskarsa a hade yace " dama nasan bazaka kazo dan radin kanka ba." Sabi'u yace " Abu turab kaikasan dalilina, kana gani yanda nake sha fada agun Mahaifina na bayasan in ware ga wanda nakeso saboda gudun nan gaba." Abu Turab yai murmushi yace " da gaskiyarsa, tunda yasan Abdulmajid ne next emperor kaga kuwa yana tsoron kar Abdulmajid ya hukuntaka na shakuwa dani." Sabi'u yai tsaki yace " in kuma kaine fa?" Tsaki Abu Turab yai yace " zaka fara ko?" Sabi'u yace "Allah sau dubu kafi Abdulmajid matsalar ido ce kadai kuma......." Abu Turab ya katseshi yace " muje dan Allah." ********* Sun isa gun hutawar Mai Martaba inda yake zaune rike da wasu takardu yana dubawa, bayan sun gaisheshi ne Mai Martaba ya kalli sabi'u hakan yasa ya mike yai baya dasu. Shiru ne ya biyo baya kafin Mai martaba ya kalli Turab yace " Abu Turab!" Yanda ya kira sunansa ne yasa Abu turab kallan mahaifin nasa. Cigaba yai da cewa "Inaso gobe Asabar dakai da Sabi'u ku ziyarci masarautar Kano." Kallansa yai cikin mamaki, sai dai baice komai ba. Mai Martaba yace " Zakuje Masarautar ne da nufin ziyara sai dai inaso ka samu keb'ewa da Bilkisu 'yar Sarkin garin." Cikin mamaki yace " ban gane ba Abba." Mai Martaba yace " Inaso duk yanda zakai kayi dumin sace zuciyarta." Mamaki ne yasa Abu Turab ya kasa magana. Mai Martaba yace " Umarnine na baka ba shawara ba, inaso ka kwana a garin kamar kwana biyu, a wannan lokacin ka tabbatar Bilkisu ta aminta dakai." Kansa na kasa yace " bazan tambayi dalili ba dan nasan ba kirana kai a matsayi uba ba, ka kira ni ne a matsayin Sarki, zanyi abinda kace sai dai inada tambaya, a makaho xan je mata?" Sarki yace " wannan na bar maka hukuncin domin ni Sarki ne wanda baisan d'ansa yana gani ba." Nagode, kawai abinda yace kenan ya mike. Suna fita daga gun ya tsaya cak, jiyake kamar zuciyarsa zata fashe. Sabi'u ka dafashi yace "me yasa baka musa mai ba?" Yace " ta ina zan musamai bayan Umarnin Sarki ne bana uba ba?" Sabi'u ya kalleshi cikin tausayi yace " amma nifa hadin auren ya birgeni, Bilkisu itakadai ce gun Sarkin kano aurenka da ita zai karama matsayi da kuma daraja agun mutane." Abu Turab murmusawa kawai yai baice komai ba, Sabi'u ya kalleshi yace "yanzu ya zakai?" Juyowa yai saitinsa yace " Sabi'u nasan bazan samu abinda zuciya ta takeso ba dan haka banga wani damuwa ba akan auren wata, ban dauki auren nan wani abun ba banda biyayya da kuma raba gado da wata ba." Dariya ce ta kama Sabi'u yace " raba gado?lalai Turab bakada kyau, taya zaka dauki auren 'yar sarki akan raba gado?" Tsaki yad'an ja yace " to fadamim, soyayya ce?aminta ce?yan uwan taka ce? Ko kuwa shakuwa ce?" Dariya Sabi'u ya sakeyi baice komai ba. ******** Acan gidan Waziri kuwa Hisham kuwa tunda Khadija ta dawo zazzabi ya rufe ta yau sati d'aya kenan tana fama da zazzabi da ciwon kai. Wannan kenan *ABU TURAB TEAM 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *28* B'angaren Mahaifiyarsa ya nufa, tana zaune gefenta kuma Lantana ce, daga bayanta kuma a tsaye Mairo ce take mata kitso, jiki a sanyaye yai sallama. Dukansu suka amsa nan ya karasa ya zauna a kasa tare da lankwashe kafafunsa. Basira ta kalleshi sai dai batace komai ba, d'agowa yai yace " Umma gobe zani Kano." Gabanta ne ya fadi dan kuwa tasan me zaije yi kanon. Sam ta manta da Mairo dan kuwa hankalinta ya tashi, ta kalleshi tace " ka amince da ganin yarinyar ne ko kuwa har auren?" Idanu Mairo ta zaro cikin tsananin tashin hankali, kallan Abu Turab kawai tayi, shima jin kalaman Basira yasa ya d'ago ya kalli Mairo. Ganin yanda idanunta sukai yasa ya kalli Basira kansa na kasa yace "Mairo bamu guri." Jin haka yasa Basira ta juyo da sauri ta kalleta, ganin yanda kwallq ta ciciko mata yasa tace " Lantana shiga da ita d'aki " Mikewa Lantana tai ta ja ta ciki, suna shiga ta zube a kasa tare da hade kanta da gwiwarta, ba kuka take ba sai dai yanda takeji a ranta tabbas taso ace ma kukan takeyi. Tana iya jiyo muryar Basira sama sama tana cewa " Abu Turab nifa wannan hadin auren bai kwantamin ba, nafisan ka auri Mairo ko dan samun nutsuwarka da kuma kwanciyar hankalinka." Dan murmusawa yai yace " Umma kinaso ne na karya umarnin Sarki ko me? Abba ya kiranine a matsayin Sarki bawai a matsayin Uba ba, sannan maganar Mairo nicewa tai tana sona ko kuwa nice nace ina santa?" Shikam yasan tana sansa sai dai yayi hakan ne dan sa Umma ta saduda, ya cigaba da cewa " itama ta kanon xan dai jene kawai inbi Umarnin da aka bani amma tana 'yar sarki guda d'aya tilo mai zatai dani? Makaho?" Basira cikin bacin rai tace " Da farko amsarka xan ba, na tabbata kai kanka kasan Mairo tana sanka, sannan kaima nasan haka, sannan na biyu shi mai martaba cewa yai kaje a Makaho?" Gaban Mairo ne ya fadi, Lantana jin haka ta taso fa sauri daga inda take a d'akin tace " tashi ki shiga can ciki." Mairo ta kalleta tama kasa magana mikewa tai a hankali ganin yanda ta tsaya kamar me shirin faduwa yasa Lantana ta riketa, ji sukai Abu Turab yace " yace inje a duk yanda naso, nima haryanzu ban tantance a me zanje mata ba." Jitai kanta yayi wani irin sarawa, cikin rawar murya ta kalli Lantana tace " meke faruwa?" Lantana ta kamata suka fara tafiya, sai data kaita canciki sannan ta kalleta tace " ba abinda ya faru nikaina bansan me suke nufi ba." Mairo ta kalleta tace " amma dai ba kina nufin in yarda da kalamanki ba ko?" A makaho xakaje mata? Ta maimaita maganar da Basira tai sannan tacigaba da cewa " me hakan yake nufi? Duk wanda qwaqwalwarsa take aiki na tabbata xai gane magana ce aka yita mai ma'ana biyu, a makaho zakaje mata?ko da ido?" Lantana ta kalleta cikin tsoro, Mairo ta mike ta tsaya gaban Lantana tace " zan gyara tambayar dana miki d'azu, Yaya yana gani?" Idanu Lantana ta runtse batace komai ba, Mairo tace " zan kara gyara tambaya ta, Lantana meyasa yake pretending din baya gani?" Lantana ta girgiza kai tace " nima bansan komai ba, da sauri tabar d'akin tare da janyo kofa." Mairo tai shiru tana tunani, me yasa yaya yana gani yake nuna baya gani? Wani irin abu ne yau takeji haka? Abubuwan da sukai ta faruwa dashi yana yari ta tuna, kai ta girgiza tace bazai yiwu ace pretending yakeyi tun da ba sai dai in warkewa yai." A can bangarensu Basira kuwa, kallansa tai tace " Abu Turab harga Allah zaka cemin baka san Mairo tana sanka ba?" Kallanta yai yace " Umma!" Tace " ni mahaifiyarka ce nasan abinda zai taimakeka gun samun farincikinka, Mairo zata kula dakai, zata taimakeka ni aguna ita kadaice zata dawoma da farincikinka." Idanu ya runste yace " nifa Mairo kanwa tace ban taba tunanin zaman aure da ita ba." Jiyai tace " sai ka fara yanzu." Mamaki ne ya kamashi yace " Umma nawa nake? Shekarata kwatakwata nawa? Taya zakumin zancen auren mata ba d'aya ba har biyu a rana d'aya wanda kuma duk cikinsu ba alakar soyayya dake tsakaninmu?" Basira tace " Ba takura maka zanyi ba sai dai inaso ka duba ra'ayina ka kuma ba shawarata lokaci mai yawa." Sunyi shiru kafin tace " tashi kaje." Mikewa yai ya fita, d'akinsa ya shiga ya kwanta akan gado yana kallan sama. Mairo ce ta fito kana ganinta kasan tana cikin wani yanayi, Basira ta kalleta tace " Mairo jeki gida zansa a karasa min kitson." Kai ta girgiza alamar a'a tace " a'a Umma bari na karasa miki." Basira tace " jike Mairo, ninace kije ai." Jakarta kawai ta d'auka ta mata sallama tai waje. Tafiya kawai takeyi amma zuciyarta fal take da tunani kala kala tama rasa ta inda zata samo amsoshin tambayoyin. Jitai an fizgo hannunta, a tsorace ta juyo, janta kawai taga yayi soron kusa da gun ya sata a ciki. Hannunta ta shiga fizgewa ta hada cewa " Malam meye hakan? Sakarmin hannu ko?" Baisake ta ba ya d'ora da cewa " da dan rashin mutunci kina ganina kika wuce ni?" Kallansa tai cikin takaici tace " Malam sakeni dan Allah, ni ba muharamarka ba zaka wani dinga rikeni? In magana zakamin kamin da baki." Murmushi taga ya saki yace " Karki damu saura kiris ki zama matata dan na kula shi kadai ne yanya mafi sauki da zan daidaita miki sahu." Kallansa tai cikin takaici tace " in zama matarka? To ko nidin baiwa ce banaji kamada damar yanke hukunci akaina bare kuma....." Katseta yai tare da sakin hannunta yace " kin dai san nidin waye kin kuma san matsayina a garin nan, ko Mahaifinki bai isa in yanke hukunci ya canza min ba." Dan karamin tsaki taja sannan ta kalleshi ido cikin ido tace " Abdulmajid kake ko wa?" Idanu ya zaro ya kafeta dasu, tacigaba " Zan maka kashaidi xa gargadi na farko kuma na karshe, in har zamuyi magana dakai ka kiyayi min abubuwa guda biyu, na farko kada ka kuskura ka kara rikeni ko ka taba ni ko da kuwa hijab din jikina ne, na biyu kuma kada ka kuskura ka dinga sako iyayena in muna magana, ni yanzu banda lokacin ka abinda ke gabana yafi karfin na tsaya ina bata lokacina." Matsawa tai da nufin wucewa, fizgota yai da karfi ya bugata jikin bango yace " ke harkin isa ina magana kina magana, har kina da matsayin da zaki kira sunana gatse gatse har kice zakimin gargadi?" Ajiyar zuciya tai tace " in kaji haushi inji sammaci." Tana gama fadar haka ta ture hannunsa tai waje. Kallan bayanta yai cikin kuluwa yace " mu zuba mu gani, ina tausaya miki in kika shigo hannuna, auranki kuma ya zama dole a gareni." Yanajin haushin yanda baya iya yanke mata hukunci duk wulakanci da zatamai. Itakam ranta a bace tai gaba, tana kokarin fita taga wata kamar Khadija ta wuce, binta tai da kallo cikin mamaki da san tabbatar da abinda zuciyarta ke zargi. Khadija kam bata kula da ita ba dan ba lafiya ce ta isheta ba yanzun ma daliline ya shigo da ita. *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *29* Khadija bangaren Magajiya ta isa, tana shiga ta taddata a zaune, karasawa tai ta gaisheta, Magajiya ta kalleta cikin kulawa tace " Khadija sannu, ina nan hankalina a tashe ina tunanin yanda jikinki yake, Khadija ya akai haka? Duk kin rame." Khadija ta d'ago ta kalleta bata bata amsar tambayarta ba sai jitai tace " Umma an tura wani ya dubo Inna Lami?" Magajiya tad'an tabe baki kadan sannan ta kalleta tace " na tura, sunce jikin da sauki." Hawaye ne ya zuboma Khadija tace " Umma me yasa bakwasa tausayi a ranku?" Hade rai Magajiya tai tace " KHADIJA!" Khadija tana kuka tace " makociyar Inna Lami ba ta aiko a sanar daku jikinta yayi tsanani ba?" Magajiya tace " a yaushe akai hakan?" Khadija tace " amma tace ai ta sanar da Yaya, Umma Allah ya d'auki ran Inna Lami, ita kanta bata sani ba tunda ita tasan ta sanar da Yaya ta dauka anje an dauketa, ita kuma a ranar tai tafiya, sai jiya da ta dawo ta shiga gidan ta ganta duk ta kumbura da alama ma ta dade da rasuwa, nan tasa aka kira mutane aka mata sallah aka kaita, d'azu da naje take sanar dani......" Kukanta ne ya tsananta sanda tazo karshe. Tace "Umma Inna Lami fa kanwar Mahaifiyar ku ce, tayaya zaku..." Ya isa haka! Abinda Magajiya tace kenan, d'agowa Khadija tai ta kalleta, dan tayi maganar ne da kakkausar murya. Magajiya tacigaba " Ya isa haka Khadija, Inna Lami ta rasu Allah ya jikanta, zansa aje gidan, ke kuma jan maganar ya isa, ba kuma na san ki kara tada maganar nan." Kallanta Khadija ta shiga yi cikin tsananin mamaki, Magajiya ta kalleta tace " ki tashi ki koma gida zan aiko miki da magani da abubuwan bukata, banasan ki dinga kwanciya ciwo akan abinda bai kai ya kawo ba." Sam ma ta rasa me zatace sai kallan mamaki kawai datake binta dashi. Ganin batada niyyar kara magana yasa Khadija ta mike ta fito daga d'akin. Ba shakka yau taga abin mamaki ace d'an uwanka na jini? Sannan harda wani wai batasan taga tana kwanciya akan abinda bai kai ya kawo ba? Kenan abinda sukama Turab da wannan rashin kula da Inna Lamin da sukai ba wani abin bane a gunsu? Samun kanta tai kawai da bin hanyar da zata kaita gun Abu Turab. Sai dataje kofar shiga ta tsaya tana tunani me zatace mai? Tabbas ganinsa ne kadai zaisa taji saukin wannan abin. Tura kofar tai a hankali, Mai kula da gun ne ya taso ya gaisheta, a hankali ta furta Ya Turab nanan? Yace " eh yana ciki, a sanar mai da zuwanki?" Tace " bari na shiga ai kasan ni ko?" Kallanta yai yace " na sani amma taya....." Gani yai kawai tayi gaba batama san yanayi ba. Falo ta duba ganin bayanan yasa ta tsaya taba kallan falon, idanunta ne suka kara zubo da wasu kwallar sannan a hankali ta nufi kofar d'akinsa kwankwasa wa tai daga ciki yace " waye?" Shiru tai sai kuma ta kara kwankwasawa. Mikewa yai ya bud'e kofar. Kallanta yai sannan yai saurin kauda kai ya kara cewa " waye?" Kallansa ta shiga yi hawaye na zubo mata, a zuciyarta tace "Yaya ina cikin wani hali, su Umma Magajiya, Yaya, da Abbana sun fara bani tsoro, banaji suna da digon tausayi a zuciyoyinsu, Yaya ya zanyi in canza su? Ya zanyi in nuna musu hanyar gaskiya?" Hawayenta ta shiga sharewa, jiyai zuciyarsa na kuna ya tsani yaganta tana kuka, gashi yaga ta rame sosai da alama rashin lafiya tai, daurewa yai ya juya da nufin komawa ciki, jiyai tace " nice Yaya." Juyowa yai yace " Khadija? Me kike a nan?" Ta daure tace " ganinka kawai nazoyi, ya hannun naka?" Fuska ya had'e yace " me zaisa ki damu da ciwon da baikai ya kawo ba, bayan kece kike bukatar kulawa?" Daurewa tai tace " yaya ya warke?" Labansa yadan ciza yace " Khadija meke damunki? Me yasa bakya fahimtar abinda nake nufi? Kina tunanin in kika nuna damuwarki akan ciwona kika wulakanta naki lafiyar zanji dadi? Me yasa kike san ki dinga sani cikin damuwa?" Kallansa tai fuskarta cike da mamakin kalamansa, tace " Yaya." Idanu ya d'an runtse yace " please in har kinasan ki nuna kulawarki a kaina to ki kula da lafiyarki." Juyawa yai ya koma ciki, ya rufo kofar. Shiru tai sai hawaye da suke zubowa daga idanunta, jingina tai da jikin kofar, shikansa yana shiga ya jingina da jikin kofar. Idanunta a lumshe tace " Yaya." Bai amsa mata ba sai dai yana jinta, tacigaba " Kayi hakuri yaya, kayi hakuri da rashin sanar dakai tafiyata fa banyi ba, kasan ina zaune a gunka lokacin da aka aiko inje, ina zuwa aka sani a mota ko gida ban shiga ba, kayi hakuri da rashin nemanka dabanyi ba, tunda naje garin ba'a kara barina na zo ba sai wannan dawowar." Iska tadan furzar sannan tace " Yya kayi hakuri na abinda su Umma Babba sukama, sannan kayi hakuri na rashin baka hakuri da sukai." Ransane ya bace ya bud'e kofar da karfi, hakan yasa tai saurin gyarawa ganin ta kusa faduwa, a fusace yace " meyasa kike bada hakuri? Me kikai? Me yasa kike bada hakuri a koda yaushe? Bayan wadanda ya kamata su bada hakurin basusan ma sunyi laifi ba? Me yasa Khadija? Meyasa kike neman tadamin hankali?" Kai ta shiga girgizawa har ya gama fadan sannan tace " Yaya na san....." Katseta yai yace " Khadija meyasa bazaki fahimceni ba? Banasan kina yawan bani hakuri hakan na sa inji kamar nine nake miki laifi." Daurewa tai tace " Nadaina yaya." Yace " Khadija please....." Murmushi ta kakaro tace " na daina Yaya, nazo ne dan ina cikin wani hali zuciyata bata kawo min kowa ba sai kai, shiyasa nazo." Kallanta yai yace " me ya sameki?" Murmushi tai tace " hmm inama Yaya kana gani? Da kaganni ina ma murmushi." Shiru yai baice komai ba, tace " Haryanzu addu'ata kenan, Allah ya bud'ema idanunka." Murmushi taga yayi, itama murmushin tai sannan tace " Ahh da alama zuciyata tayi sanyi,duk da hankalina haryanzu bai kwanta ba." Yace " me ya faru kuma?" Tace " Inna Lami ta rasu." Yace " yaushe?" Kallansa yai tace " ba'a san yaushe bane." Kallan mamaki ya mata, ganin zata d'ago yasa ya kauda kai yace " ban gane ba." Zama tai a kasa a jikin bango, ta kama rigarsa tace " Yaya zauna plz." Zama yai dan ya kula tana bukatar mai lalashi." Zayannemai komai tai. Hankalinsa ya tashi, lalai mutanen nan basuda imani, wato abin ma harda jininsu? Khadija ta d'ora da cewa " Yaya in kaine me zakayi?" "Hmmm in nine ba abinda zanyi." Tace " ba abinda zakai?" Kai ya d'aga alamar eh yace " me zanyi to? Abin nan dai ya riga ya faru, sannan mutanen na basu nuna tausayawa ko dana sani ba, ni da nake d'a me kike tunanin zanyi? Sai dai...." Shiru yai hakan yasa tace " sai dai me?" Yai ajiyar zuciya yace "sai dai dole girma da darajarsu zai ragu a idona." Tace " na fahimceka Yaya na kuma gode." Mikewa tai tace " yau naji dadin dana dade banji ba duk da wata zuciyar tana tausayawa Inna Lami, sai dai wata zuciyar tana farin cikin zama tare da kai danai wanda na dade ban samu ba." Baice komai ba, tace " nagode yaya." Ta fada tare da tafiya. Kallo ya bita dashi sannan ya mike a hankali ya koma ciki. Ya zaiyi? Ya zaiyi? Ba shakka yanasan Khadija sai dai yana ganin auransa da ita ba mai yiwuwa bane, tsanar Magajiya da ahalinta ne suka kara shigarsa jin labarin da khadija ta bashi. Kansa ya dan shafa yace " Ya zanyi?" *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *30* Wajen karfe sha biyu na rana ya fito daga bangarensa sanye da shadda mai kyau da tsada da yake kayan mu na da masu kyau ne da quality kai ka dauka sabuwa ce, yayi kyau sosai sannan ya zuba wasu kayan a cikin yar karamar jaka tunda Mai Martaba yace kwana biyu zasuyi a can din. Sabi'u ne ya zo kusa dashi yana dan tafi yace " Yayai Ango ai da alama Bilkisu takace, ta ina zatai wasa wannan saurayin ya wuce ta?" Fuska ya d'aure tamau yace " zaka fara ko?" Sabi'u yazo gefensa yace " Nadaina Ango." Abu Turab yace " matsalarka ce wannan, mikam mu tafi." Su biyu suka fito dan ko Garzali bai dauka ba, dan Mai Martaba yace zuwan nasu kano ya zama sirri. Bangaren Mahaifiyarsa yaje ya mata sallama, duk da ranta baiso sai dai tamai fatan alkairi, ta kudura a ranta in har Bilkisu ta aminta dashi to fa yana aurenta zatasa ya auri Mairo, in kuma bata amince ba to dama ita hakan take so. Ya fito suka shiga motar da Mai Martaba ya umarcesu suje, suna fita daga kofar gidan ya ga Mairo jikin katangar gidan a tsaye, sun hada ido sai dai da sauri ya dauke na sa idan, ya tabbata fitowa tai dan taga tafiyarsa, shikam tausayinta yake, yana kuma mata fatan samun miji na gari. Sunyi da nisa, jefi jefi suna dan taba hira, sun danyi shiru kafin Sabi'u yace " Abokina!" Turab yace " ya akai kuma? Dan nasanka sarai wannan Kiran kira ne na tambaya." Sabi'u yace " tun jiya nakeso nai ma tambayar sai dai na rasa ta inda zan fara, ba kuma nasan mu samu sabani saboda ita." " ina jinka." Sabi'u yai shiru kafin ya dan kalli titi sannan yace " me kake nufi da a makaho zanje mata?" Abu Turab bai ko kalleshi ba bare yaga alamar mamaki a tambayarsa, Sabi'u yana tukinsa yace " ba wai naso naji maganarku bane da mai martaba sai dai jin maganar nai daga inda nake tsaye." " Ina gani." Abinda Abu Turab ya fada kenan, cikin tsananin mamaki Sabi'u ya gangara gefen titi yai parking, Abu Turab ya kalleshi yace "meye abin tsorata? Harda tsayawa?" Sabi'u yace " ban gane kana gani ba?" Murmushi Abu Turab yai yace " Kaya ruwan toka ne a jikinka ka sa hula baka, sannan kaidin fatsi ne, kanaso in cigaba?" Sabi'u idanunsa a waje yace " Yaushe ka warke?" Abu Turab yai murmushi yace " that's not important, ka wuce muje." Jiki a sanyaye Sabi'u ya tada mota, da kyar ya iya furta amma me yasaka pretending? Shiru Abu Turab yamai, jin haka yasa yasan bazai amsa mai ba, sun dade a haka kafin Abu Turab yace " sanar dani halayenta da akace ka binciko." Sabi'u yace " Bilkisu ita kadai ce mace a gun Sarkin Kano, yarinyace mai kyan gaske, dan kowa yana fadan irin kyan datake dashi, mace ce mai tausayi ayanda aka fada tanada saukin kai, ko kadan batasan a tozarta wani." Shiru yai hakan yasa Abu Turabya kalleshi yace " shi kenan?" Kallansa Sabi'u yadanyi yace sai dai tanada matsala d'aya. Abu Turab ya kalleshi yace " na me kenan?" Sabi'u yace " batasan a komenene a hadata da wani, wannan dalilin ne yasa taki aminta da duk mazan da suke kawo mata hari, a yanda naji ita kishi ko na menene batasan tayi dan tanada zafin kishi." Tsaki Abu Turab yai yace " zancen banza takeyi kuma kenan baya yarda da kanta ba, in har tanaji da kanta tana ganin komai nata yayi 💯 banaji ya kamata ta dinga wannan shirman, wannan alamace na akwai abinda take lacking." Sabi'u ya girgiza kai yana dariya yace " lalai Turab bakada kyau, yanzu kishin ma sai ka fassarashi? To ita kishin in hallitarta ce fa?" Baki yadan tabe yace " sai ta danne shi tunda ba ita tai kanta ba." Sosai yaba Sabi'u dariya, haka sukai ta zancen Sabi'u na kara dariya, sun isa kano da la'asar gidan Sarki suka wuce direct, Mai Martaba sarkin Zariya ya riga ya sanar da Sarkin kano akan zuwan nasu, suna zuwa aka wuce dasu ma saukin su, aka kuma turo musu bayi guda uku masu kula dasu. Sunyi wanka sunyi Sallah sannan aka kawo musu abinci. Abu Turab ya kwanta akan gado tare da daure hannunsa kan goshinsa kamar yanda ya saba, Sabi'u ya kalleshi yace " Malam Makaho sauko muci abinci." Murmushi yadan mai yace " fara ci." Sabi'u ya matso kusa dashi yace " kodai ka kosa ka ganta ne? Dan na kula tunaninta kake yi." Abu Turab ya juya mai baya yace " kasan ni din ai ba kai bane." Saida Sabi'u ya kusan gana cin abincin sannan shima ya sauko dan kadan yaci ya mike ya fito wajen harabar gidan. Wata yarinya ya gani wacce batafi shekara 12 ba tana leko shi. Alama ya mata da hannu akan tazo, tsayawa tai tana wasa da yatsun hannunta, Abu Turab ya tako har inda take ya dan rusuno yace " yan mata me kike anan?" Kallansa tai tace " Kaine Yarima Turab?" Cikin mamaki ya kalleta yace " kin san ni ne?" Kai ta girgiza tace " Aunty na ce ta aikon inganka." UmmaBilkisu?kina nufin Gimbiya Bilkisu?" Kai ta daga alamar eh, sannan tace " amma karka fada mata kaji." Murmushi yai yace " naji kedin wacece to?" Tace " babana shine Yarima Nazir magajin sarki." Kai ya jinjina zaiyi magana yaga ta juya da gudu, mamaki ne ya kamashi ya juya bayansa, ganin Sabi'u yasa ya fahimci ganinsa ne yasa ta gudu, murmushi yai sannan ya juyo. Sabi'u ya karaso yace " Kai da waye?" Abu Turab ya juya yace " bakowa." Sabi'u ya matso yace " an turo wai bayan Magrib zamuje." Harararsa yai yace " Zamuje ina?" Sabi'u ya matso wajen kunnensa yace " Zance mana." Abu Turab yace " dakai zanje zancen?" "Eh mana, da kai da wa?" "Sry Malam ni kadai zanje." Sabi'u yace "Mai Martaba cewa fa yai in bika." Kafadarsa ya dafa yace "sry mutumina amma ni kadai zani." ******* A can kuwa Bilkisu ce xaune a d'aki, Munnira tana shigowa ta kalleta tare da mata alama da hannu akan ta matso, sannan ta sallami masu kula da ita, kallan Munira tai tace " Munnira ya?" Munnira tace " Nikam Yamin UmmaBilkisu dama kibarmin shi." Harararta Bilkisu tai tace " abinda na aikeki kiyi kenan?" Munnira ta turo baki tace " Nidai shi zan aura." Bilkisu ta harareta tace " ni tashi kiban gu bansan kayan haushi." Bayan Magrib bayinta suka kara shigowa aka gyarata sosai,wasu kaya ta saka sun mata kyau sosai, karan miski ne an mata doguwar riga, dashi an sanye wasu duwatsu faga tsakiyar rigar, tayi kyau sosai, alkyaba aka sa mata a saman kayan. Abu Turab kam ya hade rai sosai ganin Sabi'u ya nace akan sai ya bishi, haka Sabi'u ya hakuri shi kuma ya fito bayin da zasu sadashi da inda zasu hadu suna gaba. Sai da sukaga ya shiga ya zauna sannan suka fito. Bilkisu kam Jakadiya ce ta kawota, ta kwashi gaisuwa agun Turab sannan ta fita. Kan Bilkisu na kasa bayan ta zauna, Abu Turab ya d'an kalleta kadan, tabbas tanada kyau sai dai shi wannan bai dakeshi ba. Bayi ne suka shigo da tire dauke da kayan marmari suka jere a gaban Turab. Har suka fita ba wanda yace ufan a cikinsu, ta gefen ido take kokarin san ganinsa sai dai ta rasa me yasa takejin wata irin kunya. Kallanta yai yace " bako iya gaisuwa bane?" D'agowa taita kalleshi, maganar da zatai ne ta tsaya mata sakamakon hada idon da sukai. Kasa tai da kanta batace komai ba. Shima shiru yai, sun dan dade a haka kafin yace " da alama bacci ne ya kamaceni." Kallansa tai tace " da wuri haka?" Yace " to me zan miki? Kinyi shiru, nima nayi shiru to me zamu jira?" Baki ta d'an turo kadan tace " Barka da isowa." A hankali tai maganar Yace " ni banji me ma kikace ba." Dan Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace " Da alama kanada mita." " ni ba mace ba mai zai hadani da mita?" Tad'an tabe baki tace " mata ne kadai ke mita?" " ban sani ba, wannan kuma ke za'a tambaya ai." Kallansa tad'anyi zatai magana ta d'aga girar sa duka biyun yace " baki gama kallan nawa bane?" Idanta ta d'auke da sauri tace "wa yace ma kallanka nake?" "Yarinyar da kika aiko na d'auka ta sanar dake kamannina da yanda nake." Kanta ta juyar gefe, cikin kunya tace " wace yarinyar kenan?" Kafada yadan daga yace " bansanta ba." Shiru tai a ranta tace " Shi wannan haka ake zancen? Neman fada? Ita ta saba duk wanda yazo gunta tofa wasa ta zaiyi tayi itakuma tana dauke kai. Jitai yace " kina tunanin wani irin zance nakeyi haka ko?" Kallansa tai batace komai ba, yace " baki sanni ba, nima bansanki ba yauce ranar da muka fara ganin juna, bazan yabeki akan abinda ba haka ba, ba kuma zan kusheki ba akan abinda ban sani ba, banida tabbas zamu kara haduwa da juna kinga kuwa bazanso in bar tarihin karya ko dadin baki agunki ba." Kallansa tai ta kasan ido, ba shakka kalamansa sun mata dadi. Kanta na kasa tace " Amma ai ina gani ya kamata ka nunamin ko na maka alamar so ko aminta da hadin da akai." Murmushi yadanyi kadan yace " Bana sanki!" Cikin tsananin tashin hankalin jin wannan kalmar yasa ta d'ago ta kafeshi da ido, iska yadan furzar yace " kina sa ran daga ganinki sai in fara sanki?" Idanunta tai kasa dasu batace komai ba, yace " Bilkisu!" Kallansa ta karayi, yace " kina da kyau na tabbata kowa na fada miki haka, kinada mulki wanda ke kanki kinsan haka, sai dai inaso ki sani karkiyi tunanin hakan zai na soki, ba wai dan abinda kike dasu baimin ba sai dai dan ni ban yarda da wadannan sune abinda ya cancanta ba a so, sannan ban yarda da love at first sight ba." Jiyai tace " sai me ka yarda dashi?" Murmushi ya mata yace " sirri ne." Shiru ne ya ratsa na 'yan dakiko. Jiyai tace "Nagode." Kallanta yai cikin mamaki yace " name fa?" Tace " Na gaskiya daka fadamin." Yace " Ina miki fatan alkairi a rayuwarki, ana tabbata ba lalai mu kara haduwa ba." Mikewa yai zai tafi, jiyai tace " in kuma na bukaci hakan fa?" Juyowa yai cikin mamaki ya kalleta bai amsa mata ba. Wani sansanyar murmushi tamai tace " Ban taba had'uwa da mutumin daya fadamin gaskiya ba sai kai, da fari na fara jin haushi sai dai a hankali na fahimci gaskiya dama d'aci gareta." Kallanta kawai yake baice mata komai ba. D'agowa ta kara yi ta sakar mai murmushi tace " Da alama kai zaka gaji masarautar Zariya." Cikin mamaki ya kalleta sannan yace " me kike nufi?" Tace "sani ne bakai ba ko kuma bakasan ne na fahimceka? Na tabbata ka san cewa bazan auri wanda bashine zai gaji sarauta ba, sannan tunda mahaifinka ya turoka nan alamace ta kai yakeso ka mulki masarautar sa." Gabansa ne ya fadi cikin mamaki yace " aurenki haka yake nufi?" " Da farko ance mana baka gani sai dai daga baya aka kara aikowa akan ka samu sauki." Idanunsa ne suka dan rage girma ya matso kusa da ita yace " waye ya sanar daku hakan?" Murmushi tamai tace " na sani sirri ne dan nima ni kadai Mahaifina ya sanar ma hakan, da farko abin yaban haushi dan a gaskiya wannan dalilin ne yasa na tura Munnira ta ganka, sai dai yanzu na fahimci kanada dalilinka nacemin baka gani da alama da bakaso zuwa ba." Wato da bayan sunyi bincike sunji labarin baya gani, amma mai martaba ya aiko da sakon yana gani. Mikewa yai daga tsugunnan dayai a gabanta, baice komai ba yai waje ransa a b'ace. Kenan saboda dalilin nan aka turoshi? Shikuma harda kokarin yi mata sauki dan bin umarni? Ba shakka ransa ya bace na biyomai ta bayan gida da akai... *TEAM ABU TURAB🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *31* Yana fita Jakadiya ta matsu gunsa da sauri tace " Ranka ya dade Mai Martaba nasan ganinka." Kallanta yai yace " Yana ina?" Nan ta nuna mai hanya, tana gaba yana binta a baya zuciyarsa fal take da tunani kala kala. Wani katon d'aki ne ba komai a cikinsa, capet ne a shimfid'e sai 'yan tum tum. Sallama yai ya shiga kamar yanda Jakadiya tace ya shiga. Zama yai nesa da Mai Martaba sannan ya tankwashe kafofinsa, sannan ya gaisheshi. Tunda ya shigo shikuwa Mai Martaba yake kallansa, cikin yaban nutsuwa da zatinsa. Cikin mulki ya amsa sannan yace " Abu Turab Barka da zuwa Masarautarmu, ina fatan komai ka sameshi yanda ya kamata." Kansa na kasa yace " ina kara godiya da karamcin da muka samu." Shiru ne ya d'an ratsa kafin Mai Martaba yace " Ammm Abu Turab" Abu Turab ya nutsu, Mai Martaba yacigaba " Kaga Bilkisu?" "Naganta Ranka ya dade." Me kake tunani game da ita? Abu Turab ya d'ago sannan yace " Ina kara jinjina ma na tarbiyantar da ita dakai da sai dai fatan Allah ya kyautata rayuwarta." Murmushi Mai Martaba yai yace " Ba shakka kai din jinin Sarauta ne ko daga yanda kake bani amsa cikin fasaha ba tare da na zargi wani abu ba." Abu Turab yai kasa dakai yace " ina godiya da yabon da kamin." Shiru suka kara yi kafin Mai Martaba yace " bari na gyara tambaya ta to, mai kake gani game da auranka da Bilkisu?" Sarai yasan abinda yakesan ji kenan sai dai shi bashida ansar wannan tambayar dan kuwa shi dai ba santa yake ba, ba kuma zai iya kallan idan mahaifinta yace baya santa ba, sannan a xahiri gaskiya bai kuma tsaneta ba. Kansa na kasa yace " Ranka ya dade ai wannan tambayar tana hannun Bilkisu, duk abinda ta yanke shine daidai." Kallansa yai cikin yabawa da nutsuwa da kaifin tunaninsa yace " duk da haka inasan ji xaga gareka, Bilkisu ita kadaice 'yata, duk da ina sha'awar ta auri mai mulki sai dai abin da nafiso shine inga ta auri wanda zai kularmin da ita." Abu Turab ya nisa sannan yace " Ran ya dade ka gafarceni amma mune muka nemi had'in auran nan hakan ai yana nuna muna so ne." Cikin jin dadi yace " nagode da jin amsoshinka, Allah yamana jagora." Ameem ya fada. Shiru sukai kafin Abu Turab yace " Zan koma gobe in sha Allah, in munji daga gareku xamu damu dawo da yardar Allah." Duk da baiso tafiyarsu gobe ba saboda yana san yaga sun kara fahimtar juna, sai dai bazai iya hanashi ba. Yace " Allah ya kaimu." Sallama yamai sannan ya mike ya fito, a falo ya tadda Sabi'u yana zaune sallama kawai yai ya wuce shi ya shiga ciki, Sabi'u cikin mamaki ya kalleshi zaiyi magana yana fuskarsa a had'e yasan ko yamai magana ma ba lalai ya amsa mai ba. D'aki ya shiga ya yazauna a bakin gado tare da dafa kansa. Tunanin maganar da Bilkisu ta fadamai yakeyi, me mahaifinsa yake tunani? Anya kuwa abinda take tunani haka ne? Shiru yai yama rasa ta inda zai fara ba ma kansa amsa. Washe gari kuwa da safe yace ma Sabi'u ya shirya zasu koma, Sabi'u bai musa ba dan yaga yanda yake tun daren jiya. Sun sanar da tafiyarsu haka aka kawo kayan tsaraba kala kala daga bangaren Fulani wato maman Bilkisu da kuma bangaren Mai Martaba aka basu. Sunje shiga mota Munnira ta taho da gudu, ganin zai shiga yasa tai sauri cewa " Uncle Turab!" Abu Turab ya tsaya sannan ya waiga, ganin Munnira yai ta karaso da gudu, ya kalleta yace " Munnira ya da gudu?" Tana haki tace " UmmaBilkisu ce ta aikoni naga kuma zaku tafi." Kallanta yai yace " aiken me kenan?" Wata yar karamar jaka ta mikomai tace " Gashi." Amsar jakar yai sannan yace " ki mata godiya." Tace to. Mota ya shiga Sabi'u yaja. Suna hawa kan titi Sabi'u yace " da na dauka itace ta bata maka rai, amma ganin sakonta yasa nasan ba ita bace, me ta kawo mana ne?" Abu Turab ya bud'e jakar, wani kwalbar turarene mai kyau yana bud'e kwalbar wani kanshi ne ya bud'e motar, rufe turaren yai ya ajiye shi sannan ya jinginar da kansa kan kujera tare da rufe idanunsa. Ganin haka yasa Sabi'u yai gum.... ********* A can kuwa Zariya yau da sassafe aka kawo musu gulmar zuwan abu Turab can. Tashin hankalin da Magajiya ta shiga baya misaltuwa, cikin sauri ta aika a kira mata Hisham ko wanka lokacin baiyiba haka ya fito dan ancemai kiran na gaggawa ne. Sun shiga can kuryar d'aki ta kalleshi cikin yanayinta na isa da san boye damuwarta tace " Hisham mai martaba ya biyomana ta bayan gida." Kamar ya kenan? "Ya tura d'ansa ganin 'yar sarkin kano." Hisham yace " ita zai aura?" Ranta ya b'aci tace " kai ni meyasa kwakwalwarka kamar ta kifi take?" Kallanta yai cikin tsananin kunar rai sai dai tsoro yasa yace " Magajiya ban fahimceki bane." Kallansa tai tace " 'yar sarkin kano fa na fada maka, wacce nafadama xamu hadata da Abdulmajid kai bakasan me auranta yake nufi ba?" Hisham yace " Au matar da kikace za'a tura?" Tak tsaki tace " Bakasan halin Mai Martaba ba kenan, ba kuma kasan me yake tunani ba." Hisham ya kalleta da nufin san karin bayani. Tace " ya fara shiri akan d'aura Abu Turab mulki." Idanu Hisham ya zaro yace "Mulki kuma? Makahon?" Idanu tadan kanne na bacin rai tace " shine abinda na kasa fahimta, me zai sa Sarkin Kano ya aminta da makaho a matsayin siriki? Me yake tunani akan aura ma yarsa kwaya d'aya makaho?" Hisham yace "au ya amince ne?" Tace " majiyata ta sanar min da alamar amincewa dan kuwa ancemin har kiransa yai daga baya sai dai ba wanda yasan me sukai a ciki." Cikin tashin hankali Hisham yace " ai kam bazai taba yiwuwa ba, mulki na Abdulmajid ne haka kuma yarinyar dole ne mu san yanda zamuyi." Magajiya tace " tashi zakai yanzu ka je Masarautar kano, ka samu Hajiya Karama kawata wato Amaryar sarki ka tambayeta komai, sannan ka san yanda zakai su tsani Abu Turab ni zan shiryama duk abinda zaka fada." "Hakan yayi Ranki ya dade, yaushe ya kamata in tafi?" Tace " a yau zakaje dan da zafi zafi akan bugi kirji." Hisham yace " na fahimceki amma in suna can fa?" Shiru tai sannan tace " sai yafi ma, yanda za'a katse auren a basu sallama." Dariya yai yace " ko banza naga idan d'an jakar uba." Murmushi tai sannan tace " ai shi mugunta wani sa'in alheri yake sama, in har shi yana tunanin mugunta yamana dole ne mu maidashi abinda zai amfanemu in yaso sai muga yanda xaiyi, kuma Wallahi zaisan niyama haka, zai kuma san Makaho da mai gani ba karfin su d'aya ba, da MAGAJIYA yake zance." Hisham yasa dariya yace " wa ya isa dama yaja dake?" Tai d'an tsaki tace " Abdulmajid inyaso yazo ko zuwa jibi ne." Yace " Hakan yayi." Sallama ya mata akan zaije ya kimtsa. ************* Khadija tayi kwalliya ta fito da nufin zuwa gidan wata 'yar uwarsu a cikin gari, tana tafe cikin sanyinta dan dama mai sanyi ce. Ita kuma a tsaye take a jikin wani shago tana amsar sakon da aka aikota ta amsa, juyowa tai cak idanunta suka hango Khadija wacce take nufo gunta. Kura mata ido tai cikin waswasi dan kuwa an dade rabon data ganta, ta kusa da ita taxo wucewa, cikin rashin yarda da abinda take tunani tace " Khadija!" Kallo gun Khadija tai tare da tsayawa, Mairo ta kalleta tace " Khadija!" Khadija ta matso gunta fuskarta d'auke da murmushi tace " Naam." Mairo ta matso tace " Khadija ce ta gidan Waziri?" Khadija tai dan dariya tace " nice dai Mairo, da ban ganeki ba sai da kika matso daf." Gaban Mairo ne yadan fadi dan itakam tasan ita Abu Turab yake so, daurewa tai tace " yaushe kika dawo?" Khadija tai murmushi tace " Ban dade ba, Allah dai bai had'amu bane." Mairo tace " ikon Allah! Kuma kina shiga gidan Sarki?" Tace sosai ma, ko shekaran jiya ma naje." Mairo ta daure tace " Ya Turab fa? Kun had'u?" Gani tai Khadija tayi kasa dakai tana murmusawa, sannan tace "mun had'u sosai ma." Mairo tai dariyar yake tace " bari naje aike na akai kar aga na dade." Khadija tace " to, sai mun sake haduwa." Juyawa yai ta amshi sakonta ta juya da sauri ta fara tafiya, jitai gaba daya jikinta yai sanyi, ba shakka Abu Turab zai mata wuyar samu yanzu a da tana tunanin kila tanada chance amma yanzu kam ta tabbatar ya mata nisa, balle ga Bilkisu, ina ita 'yar gidan wani Barde ina takara da manya? Haka ta isa gida jikinta duk ya gama yin sanyi, tana shiga ta ajiye sakon ta shiga d'aki ta kwanta, a hankali taji wani zazzafan hawaye yana zubo mata ta kuryar idanunta.... *TEAM ABU TURAB🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *32* Magajiya ce xaune a kilisar Mai Martaba, ta umarci kowa ya bargun, sun dade a zaune kafin cikin kasaitarta tace " Ranka ya dade ashe Abu Turab yana kano?" "Eh." Abinda yace kenan yai mata shiru. Kallansa tai fuskarta dauke da murmushi tace " Daren jiya na aika yazo mu gaisa sannan yaci abincin dare a guna akacemin ai yayi tafiya." "Ha ka." Nan ma daga fadar haka taji bai ce komai ba, sosai ranta ya b'aci ammabta daure tace " Dama zuwa nai in fadama wata magana." "Inajinki." Ta nisa sannan tace " tunanin hada auran Abdulmajid da Gimbiya Bilkisu nakeyi." Yace " hmm shawarace mai kyau hakan sai ki aika musu da takarda." Kallansa tai cikin mamaki tace " ai kai ya kamata ka aika Ranka ya dade." Kallanta yai sannan yadan murmusa yace " fadamin kikai ai ba shawara kika zo nema ba, kinga kuwa banida abin cewa." Kallansa tai sannan tace " Ranka ya dade ka taba nuna cikakiyar kulawarka ga Abdulmajid? Kana sane lokacin auransa yayi amma sam banga kana nema masa wacce ya kamata ba." Kallanta yai yace " kin taba bani girmana na uba a kan al'amuransa?" "Me kake nufi da kalamanka?" "Inkin gama inaso in runtsa kafin na fita fada." Ya fada tare da dan lumshe idanunsa. Ba shakka ranta yayi tsananin baci ace kamar ita Magajiya ita mai martaba zai wulakanta? Kallansa tai rai a bace, mikewa tai ta tako a hankali har inda yake ta tsugunno inda yake ta sakar mai wani sansanyan murmushi tace " Takawa kardai ka manta da Abu Turab idanunsa basa aiki, Abdulmajid shine kadai wanda zai kula dashi, ina ganin ya kamata ka kara karfafa zumuncin dake tsakanin 'yan uwan biyu, ganin Abdulmajid shine babba kuma magajinka." Kallanta yai kawai, itakuma ta mike cikin salan tafiyarta, babu wanda ya isa ya juyata ko kuma ya nemi wulakantata, dolene abi abinda takeso inhar ana bukatar zaman lafiya a wannan gidan. Mai Martaba kam bayanta yabi da kallo sannan ya girgiza kai har ta fita yana kallanta, a fili yace " nine sarki ba ke ba, sannan da Abdulmajid da Turab karkashin ikona suke da ke kanki, tabbas zan nuna miki kashin namiji da mace ba d'aya bane." ********* Abu Turab kam suna isowa ya wuce b'angaren Mahaifiyarsa, mamaki ne ya kamata da Lantana tace mata ta fito ga Abu Turab nan ya dawo. Zama tai a saman kujera, shi kuma yana zaune a kasa ya lankwashe kafafunsa. Bayan ya gaisheta ne ya nemi a basu guri, nan su Lantana suka fita. Kallanta yai yace " Umma me mai Martaba yake nufi da auran Bilkisu?" Kallansa tai sai dai babu mamaki a idanunta tace " Mahaifinka yana san ka gaje shi." Yace "in gajeshi? Ban fahimta ba." Basira tadan yi yake tace " Ni kaina bansan me yake nufi ba." Mikewa yai waje. Yana fita Lantana ta shigo da sauri, tace " Tuba nake ranki ya dade, banyi da nufin jin abinda kuke cewa ba sai dai na taho kawoma Uban gidana ruwa naji abinda yake cewa." Basira tace " ba komai Lantana." Lantana ta ce "Amma Bakya ganin hakan shine ya dace? Ko kin yafe musu abinda suka aika tama Yayanki?" Abu Turab wanda ya dawo domin sanar da ita kartama Mai Martaba maganar tukunna yana tsaye jikin kofar yaji wannan kalaman na Lantana. Ji sukai yace " Me kike nufi da kalamanki?" Basira ta kalleshi a d'an razane,itakam Lantana jikinta rawa ya shiga yi. Takowa yai har inda suke, Lantana ta mike da sauri ta koma ciki. Zama yai daf da mahaifiyarsa gwiwowinsa na kasa yace " Umma meke faruwa? Dama ni nasan akwai abinda kika dade kina b'oyemin sai dai nayi alkawari bazan taba fara miki magana ba." Jiki a sanyaye cikin sanyin murya tace " Tabbas akwai abinda nake b'oyema, a koda yaushe in nai yunkurin sanar dakai sai inji bazan iya ba saboda tsoron kar in sa ma d'aukan fansa a ranka." Yace " Umma dan Allah ki sanar dani tun daga farkon rayuwarki." Basira ta numfasa sannan tace " Sunana Basira........................................................................" Haka Basira ta zayyanemai kaf abinda ya faru da ita tundaga fyaden da aka mata zuwa auranta da Mai Martaba ba da sanin matansa ba, har zamanta a can gidan da kuma zaman da tai anan gidan, da matsalolin data samu bayan ta samu ciki har zuwa haihuwar tashin hankalin da ta fuskanta na zuwan Hisham da jin maganganunsu. Tana kuka tace " Kaji dalilin dayasa muka taso a gidan Malam" Idanun Abu Turab sun kada sunyi wani mugun jaa, ita kanta bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba, fuskarta ta canza bakinsa kawai yake motsawa ta ciki, sai dai kaga alamu ta waje. Handkerchief ya zaro daga aljihunsa ya mika mata baice komai ba ya juya ya fita. Tabbas tasan ya shiga cikin tashin hankali, sai dai ita kanta mikin daya fara dishashewa a xuciyarta ne ya tashi. Sam ko sandar ma bai d'auko ba, yana kokarin shiga b'angarensa yaji muryar Abdulmajid "Kai Blind man." Wani mugun kallo ya juyo ya wurgamai sannan ya bud'e kofa ya shiga ciki. Abdulmajid ya juya ya kalli masu kula dashi cikin tsananin mamakin abinda ya gani yace " kunga idanun Abu Turab? Ba kallona yai ba kuwa?" Sukam basu gani ba sukace " Tuba muke ranka ya dade amma bamu gani ba." Cikin fada yace " karya kuke munafukai, xakuce baku gani ba, anya kuwa idanun makaho ne wannan?" Abu Turab kam yana shiga d'aki ya kule ya zauna a kan gado, sai dai ba wanda yasan me yake tunani yake kuma sakawa a ransa, daga shi sai mahallicinsa. ********** A kano kuwa Bilkisu da kanta ta sanar ma Mahaifinta tana kaunar Abu Turab hakan yamai dadi dan shi kansa ya mai. Shi kuwa Hisham ya isa kano bayan azahar, bangaren Gimbiya Sadiya wato Amarya ga mai martaba, bayan an masa iso. Bayan sun gaisa ne kansa na kasa yace " Gimbiya nazone dauke da sakon Gimbiya." Murmushi tai tace " Magajiya ikon Allah wani sakon ta aikoka dashi?" Yace " Maganar auren Gimbiya Bilkisu da Yarima Abdulmajid" Kallan mamaki tamai tace "Me kake nufi? Na da'uka ai an bar wannan maganar ganin yau d'innan Abu Turab yabar gidan nan, kuma inada labarin Bilkisu ta amince dashi." A razane ya d'ago yace " Gimbiya ta yaya Yar sarki guda zata amince da Makaho? Na tabbata asiri suka mata." Kallan rashin fahimta tamai tace " waye makahon kenan?" "ABU TURAB mana." Ya fada kansa tsaye. Tace " ban fahimta ba, a iya dai sanina banji ancemin yaran nan makaho bane." Murmushin jin dadi yai yace " kisa a tambayo miki gimbiya." Tace " in kuwa hakane na tabbata Mai Martaba bazai aminceba." Nan ta aika a kira mata Jakadiya. Bayan Jakadiya ta gaisheta ne Gimbiya Sadiya ta kalleta tace " Nikam ya Abu Turab yake ne? Yanada wani nakasu ko abin kushewa a tattare dashi?" Jakadiya tace " ban fahimceki ba Gimbiya." Gimbiya Sadiya tace " hakkinane a matsayina na matar Sarki intambayi wanda Bilkisu zata aura." Jakadiya tace " Tuba nake ranki ya dade, amma Yarima Turab bashida wani nakasu a jikinsa." Da sauri Hisham yace " idanunsa fa?" Tace " idanunsa kuma? A iya sanina bashida wata matsala na gani da idanunsa." Hisham ya kalleta yace " Jakadiya ki tuna da kyau, baki ganshi da sanda ba?" Kallan mamaki tamai tace " Na kasa fahimtar wannan tambayar taka, ni dai a iya sanina bashida wata sanda kuma sunyi magana ta fahimta da Gimbiya, ya kuma shiga gun Takawa." Gimbiya Sadiya ta kalleta tace " tashi kije Jakadiya." Zufa ne ya shiga ketoma Hisham tsananin tashin hankali, kasa yarda yai da wannan zancen ya mike yace " bari naje gun Mai Martaba mu gaisa." A ransa kuwa so yake yaje ya dan tambayeshi a dabara. Yana mikewa yaji kafafunsa sun mai nauyi, da kyar ya iya d'agasu. Haka ya garzaya fadar sarki. Bayan ya shiga ne suka gaisa da Mai Martaba. Sarki ya kalleshi yace " Waziri ba dai biyu Abu Turab kai ba?" Hisham ya dan yi yake yace " a'a na dai shigo garin ne naga ya dace inzo mu gaisa." Sarki yace " hakan yayi, Abu Turab sun tafi yau." Hisham yace " ai na d'auka ma sai zuwa gobe zasu taho, ko dai abin bai yiwu bane?" Sarki yai murmusa yace " zamu aiko da amsa cikin wani satin." Hisham ya rasa ta inda zaiyi tambayar ganin yanayin Sarki alama ce ta gamsuwa da yai da Abu Turab. Sallama yamai sannan ya mike ya fito. Sai da ya kara tambayar wasu fadawa kowa ya tabbatar mai ba sanda a hannun Abu Turab sannan ya juya ya shiga mota. Jiyai kansa ya dau wani zafi yana rasa ta inda zai fara tunani. Me ke faruwa? Kenan kallansu kawai yake? Tabbas lalai yau yanada mumunan labari, suna mai kallan dan tsako ashe kura ne????? Nace Daga Baya kenan Hisham....😝 *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *33* Hisham ya iso Zariya cikin tashin hankali, ana magrib yana shiga bangaren Magajiya. Zaune take gefenta kuma Khadija ce tana duba mata wasu kayayyaki, Abdulmajid kuma na gefenta na hago. Hira sukeyi da Abdulmajid sama sama, itakam Khadija bata sa musu baki a zaune kawai take tana aikin da aka sata. Can cikin hirar tasu ne Abdulmajid ya kalli Khadija yace " ke dama inada magana dake." Kallansa tai batace komai ba. Fuskarsa a had'e yace " haryanzu baki daina zuwa b'angaren Abu Turab ba ko? Kina mace ko kunya." Magajiya ce ta kalleta tace " Khadija me kenan?" Kanta ta maida kan kayan tace " meye amfanin ma in naje tunda ba kulani yake ba?" Dariya Abdulmajid yasa yace " kinji kunya wlh, kina mace kina bin namijin da baya sanki." Zatai magana Hisham ya banko kofa cikin hanzari. Jin yanda a ka bugo kofar yasa duk su ukun suka maida ha kalinsu kan kofar. Hisham na shigowa ya kalli Khadija yace " bamu guri." Mikewa tai tsam dan dama ba san zaman takeyi ba sai dai jikinta ya bata ba maganar arziki zasuyi ba. Tana fita ta tsaya a jikin kofar d'akin. Hisham ya kalli Magajiya cikin tashin hankali yace " Magajiya!" Ita kanta hankalinta ya tashi ganin ita data aikashi maganar aure kano? Ya dawo mata a haka?" Kallansa tai tare da tattara hankalinta kansa. Yawo ya had'iya sannan yace " yaran nan yana gani Magajiya." "Yaro? Wani yaro kake nufi kenan?" Yace " yaron nan mana da baya gani." Idanu tad'an juya tace "wai wani yaran kake nufi? Nibansan wani yaro ba." Abdulmajid ma yace " wani yaro kake nufi Kawu?" Hisham yace " Yarancan Abu Turab." Dariya Magajiya tai tace " Waziri? Ko dai gajiya ta fara ratsaka ne? Me kake san fada takamaimai?" Hisham ya kallesu cikin wani yanayi yace " Wlh da gaske nakeyi, yarancan Abu Turab idanunsa garau suke." Abdulmajid ya mike tsaye yace " ni wlh na dauka maganar arziki zaka fada ashe tsokana kazo da ita, ni nayi masallaci." Hisham ya kalli Magajiya yace " Magajiya na taba miki karya akan harkar dana san bazata amfanemu ba?" Wannan lokacin kam ta kalleshi kallan nutsuwa, Abdulmajid ma ya ja ya tsaya. Khadija kam da baya da baya ta juya tai waje cikin tashin hankali, me kenan? Hisham ya kalli Magajiya sannan ya kalli Abdulmajid yace " dayaje kano a garau yaje musu." Magajiya ta kanne idanuwanta tace " ban fahimta ba." Nan Hisham ya zayane mata kaf abinda ya faru na zuwansa. Tashin hankali karara ne ya bayyana a idanun Magajiya, kallansu tai cikin tashin hankali tace " ku bani guri." Nan suka mike suka fita. Abdulmajid ma bangarensa ya wuce cikin d'emuwa da rashin sanin abinda zaiyi. Shi kuma Hisham yai waje. Magajiya ta kasa zaune ta kasa tsaye ba shakka in har hakan ne lalai kaf duniya ba wanda ya taba rainamin hankali irin yaran nan. Kwallawa wata mai kula da ita tai, cikin hanzari ta iso. Bata ko juyo ta kalleta ba tace " kiramin Abu Turab." To tace kawai tai waje itama. Abu turab yana zaune kan sallaya tilawa yakeyi cikin daddadan muryarsa, yau ko masallaci bai je ba dan bayasan ganin kowa. Garzali ya mai sallama, sai daya kai aya sannan ya amsa mai. Garzali ya matso ya tsugunna sannan ya sanar dashi sakon Magajiya. Ya dade kafin yace " ace mata ina zuwa." Nan yai waje. Sai dayai sallar isha'i sannan ya mike ya fito, Garzali ya mikamai Sandarsa wacce Lantana ta kawo. Amsa yai sannan yai gaba Garzali yabi bayansa. Bayan an mai iso ya zauna a kilisarta sannan ta shigo cikin takamarta. Idanu ta kafa mai har ta zauna shikam fuskarsa a had'e take yana zaune kansa a kasa. Bayan ta zauna ne ta kalleshi tace " Abu Turab ka iso?" "Barkanki da warhaka Umma Babba." Murmushi ta sakarmai sannan bata amsa ba tace " kiranka nai in baka wani labari." Shima bai amsa mata ba dan lalai ji yake bazai iya kallanta ba saboda tsananin tsana. Magajiya tacigaba " Wani dan tsakone kurma ya taso karkashin kulawar kura, ita kurar dama tanada nata d'an hakan yasa ta had'asu duka ta rike, a kwana a tashi sai kurar nan ta tsufa, ta fahimci dole tana bukatar barma d'anta mukaminta a daji. Kasan abin mamaki?" Abu Turab ya d'ago suka had'a ido, bai d'auke idanunsa daga cikin nata ba yace " bazai wuce wannan d'an tsakon kurma yace shi yake san aba wannan mukamin ba." Ta kuramai ido itama tace "Haka! Ashe ka harbo jirgin, sai dai kasan wani abun tsoro a labarin?" Kallan ban fahimceki ba ya mata tace " Tun daga sanda Kurar nan ta fahimci kudurin wannan d'an tsakon har yau ba wanda yasan inda wannan d'an tsakon yake." Wani lalausan murmushi ne ya bayyana a fuskar Abu Turab yace " sai dai ban fahimci abu d'aya ba a labarin, d'an tsakon dama can kurma ne ko kuwa yayi hakan ne da saninsa ya noke bakinsa?" Idanun Magajiya ne suka d'an canza sai dai da sauri ta maida fuskarta cikin yanayin hankali a kwance tace " hmm wannan shine abinda ya sa kurar nan dana sani." Gani tai ya saki wata yar karamar dariya har hakwaransa suka bayyana ya kalleta yace " Tuba nake Umma Magajiya, na saki a duhu danai na nuna miki nidin bana gani." Wannan karan kam duk yanda taso ta b'oye bacin ranta ta kasa, karara ya nuna a fuskarta. Abu Turab ya rangwadar da kai yace " umm ya zamuyi yanzu?" Tace da me kenan? Yace " dan banaji zan iya yafemiki." Kallo tamai cikin mamaki tace " bakaji xaka iya yafemin kamar ya kenan?" Fuskarsa ce ta canza idanunsa sukai jaa, ya kalleta yace " bazan taba yafe miki ba daga ke har yayanki, abinda yama yayan mahaifiyata da matarsa da ke da kika umarceshi a sanadiyar kokarin rabani da duniya da kukai kuka jamusu mutuwa, ni Abu Turab in har Basira da Abdussamad sune suka haifeni sai na sa an muku hukunci daidai da laifinku." Wata muguwar dariya ta saki, wanda ya sashi tsayawa yana kallanta tace " kai a suwa kenan?" Yace " a wanda yake da damar zama Sarki." Ta ja tsaki tace " Shekaruna d'aya da mahaifinka, hakan na nuna nid'in batayau bace, ba kai ba hatta mahaifinka bai isa yaja dani ba." Abu Turab ya d'an juya bakinsa sannan ya had'a lab'ansa yace " well, shi daban nid'in daban, mu zuba mu gani." Tace " shikenan mu zuba mu gani, na baka sati biyu kacal, ina zaune anan zakazo gwiwowinka biyu ka nemi gafarata." Yace " ina fatan hakan ta kasance." Kallan juna sukai, kansa ya saukar kasa ya juya kansa gefe tare da d'aukan sandarsa yace " Umma Babba nagode ni zan wuce, ki huta lafiya." Kallan mamaki tamai, gani tai ya sa sanda a gaba kamar makaho. Idanu ta kuramai har ya fita, ta murmusa tace " hmm a kashi 100 na baka 40, ba laifi ka iya b'oye fuskarka da abinda ke ranka, ko dayake d'an Abdussamad ne." Fuskarta ta kuma had'ewa tace " kai har ka isa? Kamar ni? Kamar ni Magajiya ka rainan hankali?" Kwafa ta saki. Abu Turab kam na fita ya juyo ya kalli bangarenta sannan ya juya ransa a b'ace. ********* Itakam Khadija ta shige d'aki ta kwanta akan gado, me ke faruwa? Ya Turab yana gani? Anya kuwa? Ta yaya? Yaushe? Itakam ta kasa yarda da abinda taji, ba dai wani sharrin zasu kullama bawan Allah ba? Da sauri ta mike zaune tace " dole in fadama Yaya gobe akan abinda sukace." *TEAM ABU TURAB🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *34* Washegari. Da safe zaune yake a gaban Mai Martaba a cikin Turakarsa. Mahaifinsa ya kalleshi cikin kulawa yace "Turab me yasa ka dawo tun jiya? Sannan tundaka dawo baka zo ba." Fuskarsa a d'aure take dan sam ba fara'a a cikinta kallansa yai yace " Dama zuwa nai na sanar dakai zan auri Bilkisu yar gidan Sarkin kano." " Alhamdulilah nagode kwarai na kuma ji dadi daka fahimceni." "Bayan umarnin auranta daka bani a yanzu auranta yana tattare da amintata, a da auranta zanyi saboda umarninka, sai dai yanzu zan aureta ne dan kaina." Fuskar mai martaba ta kara fadada da farinciki yace "naji dadi yanda kuka fahimci juna." Kallan Mahaifinsa yai yanajin wani radadin takaici a ransa, yace " zan koma." "Abu Turab!" Komawa yai ya zauna sannan ya kalli Mahaifinsa dan yanda yaji ya kira sunansa yasan yana bukatar nutsuwarsa. Mai Martaba ka kalleshi cikin kulawa yace " Abu Turab me yasa kake so ka b'oyemin abinda ke ranka? Me yasa bakasan mudinga raba damuwar dake zuciyoyinmu?" Shiru yai sai dai zuciyarsa tadan raunana. Sarki yace " Meke damunka?" Shiru ya kuma yi sai dai a wannan karan ya d'ago ya kalli mahaifinsa da idanunsa da suka canza launi. Sarki ya cigaba" Shikenan mubar maganar inhar zuciyarka bata san inji." Abu Turab yace " zan koma Abba." Mai Martaba ya murmusa yace " to Turab." Mikewa yai ya fito daga bangaren mahaifinsa, ba shakka yanasan ya sanar dashi damuwarsa da kuma neman shawararsa sai dai ba yanda zaiyi domin kafin ya kasance mahaifinsa sarki ne shi a wannan garin dole kuma yai abinda ya dace a matsayinsa na sarkin garin. Bangarensa ya nufa rike da sandarsa yana gana Garzali da wani na gefensa. Sunsha kwanar da zata kaisu bangarensa yaji muryar Khadija tace " Ya Turab." Haka kawai ta samu kansa da kin tsayawa dan abinda Mahaifinta sukamai bayaji ko ganin Khadija yana kaunar yi a wannan lokacin. Ganin bai tsaya ba yasa ta kara sauri, har tazo inda suke, tace "Ya Turab." Tsayawa yai sai dai bai juyo ba. Gabansa ta dawo ta kalli Garzali tace " dan Allah kudan matsa kadan zanma Ya Turab magana." Nan suka gaisheta suka matsa. Kallansa tai tace " Yaya." Bai kalleta ba sai dai yace " ya akai?" Tace " yaya kana ganina?" "Me kike nufi da hakan?" Ta kara matsows tace " Yaya ninasan baka ganina, sai dai na rasa dalilin Abba na na zuwa ya fadama Magajiya wai kana gani." Kallanta yai, ta kalleshi hakan yasa ya kauda idanunsa, tace " Yaya Please ka kula da su wlh sam hankalina ya kasa kwanciya dasu, na tabbata da abinda suke shiryama." Jitai yace " yanzu kinaso ki cemin zuwa kikai kiban shawara akan kula da Mahaifinki? Ko kuwa zuwa kikai ki sanar dani Mahaifinki zai cutar dani?" Cikin rashin fahimtar kalamansa tace " Ban fahimceka ba.. .." " in mahaifinki zai cutar dani tayaya nake da tabbas din ke bazaki cutar dani ba?" Kallansa tai a zabure cikin tsananin mamaki tace " Yaya." Yace " da mahaifinki da ni wanene mafi kusanci dake? Wanene wanda yake jininki? Tayaya zan yarda zaki juya ma mahaifinki baya akan wani makaho wanda bakuda hadi dashi?" Gaba daya ta ma kasa magana dan batada amsar da zata bashi, tana neman amsar da zata bashi taga ya fara tafiya. Idanunta ne suka ciciko a hankali wasu zafaffan hawaye suka xubo mata, me yaya yake nufi? Gani tai ya tsaya a jikin kofar bangaren Mahaifiyarsa da alama magana yake da wani, gani tai ya saki fuska ba kamar yanda ya cukule mata ba. A hankali ta tako har gefen da suke. Mairo ta gani a tsaye a gun rike da kula suna magana, juyawa tai zuciyarta sam ba dadi. A bangaren sa kuwa, bayan ya taho daga gun Khadija zai wuce yaji tace " Ya Ina Kwana?" Juyowa yai ya kalleta yace " Mairo kece?" Tace " nice, Umma ce ta sani in kawo mata abu yau da safe." Murmushi yai yace " Mairo kinaji da Umman nan." Ta kalleshi tace " Da cemaka akai Ummanka ce kai kadai?" Kallanta yai yace " Yar gidan Umma ce ke dama ai." Zatai magana yace " ki gaisheta." Tace " bazaka shiga ba?" Kallanta yai fuska a sake yace " Later." Daga nan yai gaba. Kallansa tai cikin mamaki dan taga ba haka suka saba ba. ************ Abdulmajid ne zaune gun Magajiya yace " Umma ya kukai Jiyan? An bincika yana ganin?" Magajiya ta kalleshi tace " Abdulmajid, ka nutsu sosai kaji abinda zan fada ma." Kallanta yai sannan yace " inaji." " Ka shiga hankalin sosai da Abu Turab ka daina masa kallan wanda bashida wayau ko bai san komai ba, wlh wnnan yaran hmmmm" Tai shiru sannan tacigaba " kadai bi a hankali karka kuskura ka fada tarkwansa." Abdulmajid ya dan tabe baki yace " ni Umma har wannan yaran ya kai in shiga hankalina a kansa?" Ta kalleshi cikin isarta sannan ta ce " Abdulmajid kenan." Kara tabe baki yai yace " ni Umma dama maganar aurena nazo muyi, nace tunda dai Bilkisu an riga an hadata da Turab mai zai hana mu juya akalar auran kan Mairo." Ya karasa maganar yana dan sosai keya. Kallansa tai tace " Mairo? Wacece hakan?" Yadanyi kasa dakai yace " Mairo 'yar gidan Barde." Barde?bakada hankali ne?" Yace " Umma to...." Katseshi tai cikin fada tace " nimeyasa baka tunani ne a al'amuranka? Abu Turab zai auri Gimbiya Bilkisu kai kuma dan hauka kacemin wata Mairo? Me yasa ne bazaka dinga abu da tunani ba?" Fuska ya hade dan maganar ta batamai rai, Magajiya ta cigaba " kada ka kuskura ka karamin wannan banzan zancen." Tana kaiwa nan ta maike tai ciki. Kallo ya bita dashi da alama zai je gun Sarki ya fadamai kuwa dan shi kam Mairo yakesan aura ko ta wani haline kuwa, dan kwanan nan har mafarkinta yake wai sunyi aure. 🤣 ************** Kwana biyar da dawowarsu kuwa Mai Martaba Sarki Shu'aib mahaifin Bilkisu ya aiko mutane daga Masarauta akan amincewa da aure da sukai. Wannan labari ya tadama Khadija hankali, sai dai duk yanda taso ganin Abu Turab abin ya faskara, itadai ba dama ta shiga bangarensa dan ya bada umarnin hana kowa shiga bayan Mahaifiyarsa, sannan ko a waje tadaina ganinsa. Mairo ma wannan labarin ya d'aga mata hankali, sai dai ba yanda zatai dan dama ta riga tasan komai. Yau ta gama aikin gida kenan tana 'yan kukuninta na takaicin abinda ake sata yi, wani yaro ne yazo ya sanar da ita ana san ganinta a waje. Hijab dinta ta ja ta saka dan bata kawo saurayi bane ko wani na kunya ba. Mamaki ya kamata kwarai ganin Abdulmajid a tsaye a jikin soron gidansu. Kallansa tai cikin mamaki sannan ta karasa gunsa tace " Malam lafiya?" Abdulmajid ya kallesta kalleta yace" Mairo ina kika shiga ne? Sam na daina ganinki dole kika sani na zaro jiki na fito." Kallan sa tai tace " ban fahimci inda ka dosa ba." Yace " Kin manta me nacemiki ne? Na dauka na sanar dake kedin matata ce." Dariya ta saki tace " Matarka? A yaushe kenan akai hakan? A iya tunanina ban amshi sadakin ka ba." Idanu yadan rage yace " An kusa ai indai wannan ne, inkuma kinaso in baki yanzu to." Ka bani yanzu? Da alama tunanin ka ya fara tafiya ko? Matsowa yai a zuciye hakan yasa ta matsa da sauri sannan ta nunashi da hannu tace " Stop Malam! Tsaya anan karka kuskura ka tabani." Kallanta yai rai a bace yace " Mairo." Tace " kwarai kuwa sunana Maryam wacce ake cewa Mairo yar gidan Barde kanada magana ne?" Kwafa yai sannan yai murmushin mugunta yace " ina tausaya miki yarinya randa kika zo hannu." Baki ta murguda tace kafa zanzo ba hannu ba. Ta juya tai ciki ranta a bace. Murmushi ya sakeyi sannan ya juya. *TEAM ABU TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *35* Wata yarinyace wacce bata wuce shekara goma sha hudu ba ta, kana ganinta kasan yarinyace da take aiki a gidan duba da yanayin kayan jikinta. kwankwasa kofar tai mai kula da kofarsa ya bude tare da tambayar ta me ya kawo ta. Yarinyar mai sanyi ce kana ganinta kuma kaga shiru shiru, kanta a sunkuye tace " Yarima Turab ne ya umarceni da inzo." Yace " to, shiga." Nan ta wuce ta shiga, yanata mamakin abinda ya kawota da magrib din nan. Ka idar rayuwar Abu Turab in yai sallar Magrib to sai yayi Isha'i yake tashi, sannan kwanan nan saboda bayasan haduwa da kowa yasa ko masallaci ma ba zuwa yake ba, sai dai yai sallah a gida yai tilawarsa. Yarinyar nan tana shiga ta zauna a cikin falon da ba kowa sai shi dake zaune daga can gefe kan sallaya yana karatu. Falon ba wani haske gareshi ba, in ba gabansa dake d'auke da fitila kusa da al_qur'anin sa ba, ya kashe fitilun ne saboda kar a fahimci idanunsa yana gani, sannan karatun ma bada karfi yake yi ba. Yarinyar tana zaune a bakin kofa har sai dataji kiraye kirayen sallar isha'i sannan ta mike ta fito, sam Abu Turab bai ma san da zuwanta ba, balle fitarta. Haka yarinyarnan ta d'au kwana hud'u tana wannan zuwan, kullum kuwa ana magrib take zuwa. Mai gadi kofar kam kullum yana mamakin wannan abu, sai dai bashida ta cewa dan da Abu Turab bai yarda da zuwanta ba tabbas da ya haneshi da barinta ta shigo sannan da ita kanta ya koro ta. Yau ne kwanan ta na hud'u da fara zuwan, kamar yanda tasaba zama a kofar yau ma haka tai, sai dataga an dade da sallar magrib sai ta tsiri rage kayayyakin jikinta. Ta rage daga ita sai wata yar bes sai zanin dake jikinta, kara ta saka tare da fad'uwa kasa. Abu Turab dake karatu ya mike da sauri tare da tahowa inda yaji karar, ganin mace yai a kwance tanamurkususu sam bai kula da jikinta ba ganin yanayin da take ciki, da sauri ya karaso ya d'agota yana tambayarta abinda ke damunta, juyi kawai take tana wash wash. Masu kula da bangarensa kuwa suna zaune suna hira sukaji wannan karar nan suka taso da sauri. Shigowa sukai ganin duhu yasa Garzali ya kuna fitila dan sun dauka wata matsalarce ta faru jin yanda Abu Turab ke cewa lafiya? Ita kuma tana kiran wash. Haske ne ya bayyana a d'akin me zasu gani? Abu Turab ne rike da yarinya, gashi cikin duhun nan yarinyar tai amfani da damar ta ballemai botira guda biyu na saman rigarsa. Gaba d'aya turus suka tsaya cikin tashin hankali me zasu gani? Meke faruwa? Abu Turab ne ya kallesu sannan ya kalli yarinyar dan sai a lokacin ya kare mata kallo. Sai kuma a lokacin ya fahimci sharri ne akazo a kula mai. Mikewa yai tare da hankad'e yarinyar, ita kuma ta hade kafafuwanta tasa kanta a ciki tasa wani irin kuka. Zaiyi magana sukaga an bud'o kofa. Abdulmajid ne, gefensa kuma Galadima. Kallan sa Galadima ya shiga yi cikin mamaki da tsana yace " ashe dama abinda ake fadamin da gaske ne? Lalai ka zubar da mutuncin masarautarmu." Abu Turab ya kalli Abdulmajid wanda yad'an juya yana dan murmushin mugunta. Galadima ne yacigaba da cewa " Yanzu Ka kyautama mahaifinka da mahaifiyarka? Kana makaho? Ace har da neman mata? Wa'iyazubillah, dolene gobe a zauna saboda kai, ko kuma yanzu ka wuce muje gun Mai Martaba tun kafin magana ta fita." Abu Turab ya jujuya sannan yace " Galadima?" Inajinka. Abu Turab yace " ina neman alfarma." Tame kenan? "Inaso ka taimaka muje gun Mai Martaba a wannan lokacin, sannan mu tafi da yarinyarnan, a kuma taimaka a kira mahaifiyata da kuma Umma Magajiya dan su zama shaidar abinda zai faru." Galadima yace " dama ai canzamu yanzu, ya kalli Garzali yace " jeka kira Magajiya da Mamansa." Nan yai waje. Galadima yace " muje." Haka suka isa gun Mai Martaba lokacin yana zaune bayan ya dawo daga masallaci. Bayan Zagi ya nemarmusu uzuri sun shiga. Mai Martaba ya kalli galadima yace " Galadima lafiya?" Kallan Abu Turab yai sannan yace " ba lafiya ba sai dai muna jiran isowar shaidu kafin a fara shari'a." Sun dan dade a zaune kafin Basira ta fara isowa sannan Magajiya wacce hankalinta kwance ta iso dan dama jiran kiran take in kuma ba'a kirata ba tana jiran labarin korar Abu Turab ko kuma killaceshi da hanashi fita daga bangarensa, a kuma hana kowa ganinsa. Bayan kowa ya hallara Galadima ya sanar da duk abinda ya faru ga Mai Martaba. Tashin hankali ne karara ya bayyana a fuskar Basira. Magajiya ta kalli Galadima tace " Galadima me kake san kafad'a? Kana tunanin Abu Turab keta mata hadi yai ko me? Na san halin Turab bazai yiwu ba abinda ka fada sannan ta ina ma zai fara yin lalata bayan idanunsa ba gani suke ba?" Abu Turab ya saki wani murmushi yace " Haka ne Umma Babba ba gani nake ba tayaya zan kama yarinya ta karfi in keta mata hadi?" Abdulmajid ya kalleshi yace " bayan kamaka da mukai?" Abu Turab yace " ina yarinyar?" Nan Galadima ya kirata. A jikin bango ta takure kana ganinta a ido kaga salaha. Abu Turab yace " ba gani nake ba sai dai ina fatan yarinyar tana nan?" Sarki yace " tananan me zaka ce mata? " Abu Turab yai kasa dakai yace " Tuba nake ranka ya dade sai dai ina bukatar yi mata tambayoyi." Nan Sarki ya bashi dama. Abu Turab yace " baiwar Allah ya sunan ki?" Tace " Zulaika." Yace " Zulaika kin san ni?" "Eh yarima Turab sunanka." " Me yake kawoki bangarena?" Kuka ta saka tace "kaine ka ce indinga zuwa duk bayan magrib." Abu Turab yace " gaskiya ne, amma a ina muka hadu na fada miki haka?" Tace " a waje ranar ka fito." Allah sarki me nake miki in kinzo? Kuka ta saka hakan yasa Sarki yace " karki damu sanar dani duk abinda yake miki. Tana kuka tace " tatabani yakeyi ya cire min.... ."kuka ne yaci karfinta hakan yasa tai shiru. Abu Turab yace "Galadima a ina kaga yarinyar nan da ni?" Galadima yace " a falon ka mana." Abu Turab yace " waya taba neman mata na lalata a sarari? To ko mata tace ya kamata a ganni da ita a falo?" Galadima yai shiru, Sarki ya katseshi da cewa " in idanun ka ya rufe da alfasha fa?" Kai ya jinjina yace " haka ne sai dai inada tambaya ga yarinyar, ni ba gani nake ba wanda kowa yasan da haka, ta ina zan iya janyota? Ko ince ta ina zan iya mata karfi?" Sarki ya kalli yarinyar yace " bashi amsa." Tana kuka tace " kirana yake yi." Abu Turab ya ce " Umma babba yi mana shari'a aa nan an ganmu a farko farko gaba da kofa kadan sannan tace kiranta nakeyi me zakice?" Magajiya wacce tunda ya fara tambayoyinan ranta yake a b'ace tsananin mamakin rainin hankalin dayake musu yasa tama kasa magana, makaho? Wanda kowa yasan da hakan? Kallansa tai jin tambayar daya mata tace " gaskiya ne wannan abin dubawa ne galadima." Abu Turab yace " Umma babba dan Allah inada tambaya, in har yarinyar nan ta karfi nake mata me yasa ba'a taba jin kararta ba sai yau?" Magajiya ta kalleshi zuciyarta fal bakin ciki amma a fili tai murmushi tace " Gaskiya ne Turab wannan ma abin dubawa ne." A ransa yace "Hajiyar Poker Face." Abu Turab yace "Galadima in har lalata nake da yarinyar nan ta yaya za'a ganta a nuste ina nufin kayanta da kuma d'an kwalinta, banda rigarta data cire, inasan in tambayeta wani irin lalata ne wannan." Galadima ya kalli yarinyar yace " ke dan kwal uba........sanar damu gaskiya ko kuma wlh daga nan sai dai ki sameki a gidan horo." Idanunta ta zaro a rikice, Abu Turab yace " ke na taba lalata dake? Wannan shine tambayata ta karshe dake in baki fadamin gaskiya ba......" Sarki ya karasa " ni kadai nasan hukuncin da zan mata." Da sauri ta zube a kasa tace " tuba nake ranka ya dade." "Tuba? Name kenan?" Magajiya ta saki wani lalausan murmushi tace " yaro yaci galaba a dokan farko, bari muga na biyu." Dan tasan ko za'a kashe yarinyar nan batasan wanene ya umarceta da wannan aikin ba, kudi da kaya aka kaimata sai umarnin aikin dazatai da wata ta fada mata, wacce ta fada mata kuwa bama a gidan take ba. Kuka take sosai yarinyar tana neman gafara. Abu Turab ya kalli Magajiya yace " Umma Babba na gode da aminta dani da kikai." Daga nan aka wuce da yarinyar dan mata hukunci da tambayoyi akan laifin data aikata. Abu Turab suna fita ya karasa da saurin gun Magajiya wacce take tafe Abdulmajid na bayanta. Yana isa ya sha gaban ta yace "Umma ina kara godiya fa." Kallansa tai tace " karka damu d'ana ina laifi in uwa ta taimaki d'anta?" Ya kalli Abdulmajid yace " ba dai anyimin wannan wasan kwaikwayon bane dan labari yakai masarautar kano?" Abdulmajid ya makamai harara yace " Wa kake tambaya?" Abu Turab yace " ba tambaya nake ba, shawara dai nazo badawa, in har za'a hanani auren Gimbiya Bilkisu ko kuma a sani in nemi gafara da gwiwowina bana tunanin wannan wasan yaran zaici galaba a kaina maganar gaskiya na fahimci ashe Babbar tamu ba iya babban game tai ba." Yana kainan yai gaba. Magajiya ta kalleshi tai dariya tace " Abu Turab! Nayi laifin farawa da mafi kankanta daga cikin shiri na." Abdulmajid ya kalleta yace " Umma kefa yake nufi ko?" Tace " kwarai zamu gani ai." *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *36* Jakadiya dake tsaye tana kallan abinda akeyi ta sheke da dariya tace " Magajiya kin hadu da daidai ke, na kosa inga idanunki a lokacin da yaran nan ya fahimci shi kadai ne jinin sarauta Abdulmajid ba d'an Sarki bane." Takara sa dariya sannan ta juya cikin farin cikin ganin an wulakanta Magajiya. Magajiya na shiga d'aki ta rufo kofar sannan ta zauna tare da kurama kasa ido, ranta yau inyayi dubu ya b'aci. Abdulmajid kuwa bangaren Abu Turab ya nufa, daidai lokacin shima yana kokarim shiga cikin nasa gidan. Turab. Abinda Abdulmajid ya fada kenan. Abu Turab ya tsaya sannan ya juyo ya kalleshi, matsowa yai inda yake yace " Kana tunanin kaci riba ko?" Abu Turab yace " a wasan yara ba." Abdulmajid ya matso daf dashi sosai yace " Karkai tunanin kaci riba, karkuma kai tunanin nidin soko ne, ba damuwa nai da auranka da Bilkisu ba,dan ni Mairo nakeso kuma zan aura, mulki kuma wallahi kaji na rantsema baka isa kahau kujerata ba in har kuwa kaga ka hau to wlh sai dai in mutuwa nai." Abu Turab ya saki wani murmushi har hakoransa suka fito yace " Malam Yarima, ita d'in Mairon sanka take?" "So? Wannan kuma ai kai kasanshi, in dai harni ina santa?" Abu Turab yamai wani kalo shekeke yace " Indai har kana santa? Me kake tunani?" "Me kuwa nake tuna? Nine magajin sarki auranta kuma dole ne a garine." Mamaki ya kama Abu Turab yace " banda neman matan da kakeyi, bayin gidan nan, haka kakeso ta kunshi bakin cikinka?" Yace " Neman mata ai iyawa ne sannan bakin ciki kuma wannan damuwarta ne in har ina zaune da ita ni ba ruwana, gargadi na a gareka karka kuskura kai tunanin shiga tsakanina da yarinyar nan." Juyawa yai zai tafi, da sauri Abu Turab yasa hannu ya fizgo hannun Abdulmajid sannan yace mai " in kuma na aureta fa?" Wani irin mugun kallo Abdulmajid ya bugamai, kishi ne karara ya bayyana a idanunsa, Abu Turab yace " ni ina mamaki, na d'auka ma Khadija zakace kanaso ganin kunfi kusanci da ita sann......" Dunkule hannunsa yai ya naushi kuncin Abu Turab wanda baiyi zato ba, hakan yasa bai karasa maganarsa ba. Abu Turab sai daya kusa kaiwa kasa, gefen lebensa ne a fashe kadan, Abu Turab ya kalleshi zaiyi magana, Abdulmajid ya nunashi da yatsa yace " Gargadi zan maka, wlh kar insake ji kace zaka auri Mairo ta wannan shine kashedi na na karshe dakai." Ya juya a fusace yai gaba, Abu Turab ya kalleshi sannan yace " ayya Malam kace Mairo ce weakness dinka." Juyawa yai ya dan furzar da iska. Basira kam sosai hankalinta ya kwanta ba shakka ta samu d'a, tana kuma kara godema Allah da kuma rokonshi ya kare mata shi. ************* Washegari na sassafe ya nufi bangaren mahaifinsa bayan ya gaisheshi ne ya d'ago yace " Abba zuwa nai nuyi wata magana. " Sarki ya kalleshi yace "Ina jinka." "Me zai hana a kaini asibiti a matsayin an kaini amin aikin ido inyaso ko zuwa sati d'aya inyaso sai ace na warke." Sarki ya jinjina kai yace " hakan yayi, ko dan saboda maganarka da Gimbiya Bilkisu dole ne mutane su gane kana gani, to gwara kafin abu yai nisa a fahimci kana gani, ko dan ka kwaci kanka." Abu Turab ya kalleshi sannan ya sunkuyar da kansa yace " Tuba nake nasan jiya....." Kayi daidai Abu Turab, naji dadi abinda kai, hakan ya nunamin ko a wani hali kake zaka kqaci kanka, yanzu yaushe zaka tafi asibitin?" Abu Turab yace " yau ko gobe, dan gwara mu hanzarta kafin a samu matsala." "Ka yi tunani, a asibitin Ahmadu Bello akwai wani tsohon abokina na sirri director ne a asibitin in ka sanar dashi komai zai san abinda ya dace." Abu Turab yace " nagode Abba." Sun dade a zaune shiru kafin Abu Turab yace "Nasan ban kyauta ba abinda nai jiya, kamar rainuwa ce nama Umma Magajiya, nasan zakai tunanin haka." Sarki yai murmushi yace " ko kadan Abu Turab, nasan Magajiya sosai da sosai nasan kuma sharrin ta da izzar ta, sai dai fatana ka kula da kanka kar su maka illa, ni nasan abinda nakeyi, bawai banasan Abdulmajid bane ko ina fifitaka akanshi sai dai dolene in kare masarautata da garina, inhar Abdulmajid yahau mulki tabbas mulki ya koma gun Magajiya da Hisham da ahalinsu." Abu Turab yace " nifa....." Basai ka ce komai ba, na sani na kuma fahimci me zakace, bawai san mulki kake ba, sai dai nasan akwai lokaci da zakaso mulkin, shiyasa nake rokonka daka bar komai a ranka harzuwa lokacin." Haka ya taso ya fito, Jakadiya tana ganinsa ta taho da sauri ta gaisheshi amsawa yai ba tare da ya kalleta ba. Ta bishi da kallo tace " inama kana gani ai sai kunfi fafatawar da Magajiya, mu kuma 'yan kallo mu kwashi namu rabon." ************* Washegari Basira da Lantana suka rakashi asibiti, nan magana ta fito akan antafi yimasa aiki saboda isowar wani kwararen likitan ido a asibin na Abu. Magajiya kam tayi dariya sosai dajin wannan rainin hankali, sanda akazo mata da maganar kuwa tana zaune Khadija na cire mata jan lalen data mata, mai kula da ita ta shigo da sauri tace "Ranki ya dade yanzu naji labari akan Yarima Turab ya tafi asibiti." A zabure Khadija ta mike tace " meya sameshi?bashida lafiya ne?" Kallan mamaki matar ta mata sannan tace " a'a aikin ido za'amai." Magajiya ce tasa dariya tace " aiki? Lalai yaran nan." Gani tai da gudu Khadija tayi waje. Sauri take sosai daga can gun shiga mota ta hangosu, sauri take sosai sai data kusa isa daf sai ta hango Mairo a gefen wajen boot din motar rike da kula. Turus tai ta tsaya tana kallanta. Gani tai Abu Turab din ya matsa kusa da Mairon batasan me suke cewa ba. Shikuwa gunta ya karasa yace " Ke kuma waya fadamiki?" Tace " Umma na mana ko kamanta nidin 'yar gidanta ce?" Kai ya jinjina yana murmushi yace " na d'an manta kadan." Kula ta nuna mai tace " gashi kaci inkaje can, Goggo ce tace in kawoma, nasan in mace zan bika hanani zakai." Kallanta yai yace " akwai maganar ma danakeso muyu dake, kizo mu tafi tare, in kuma da abinda zakiyi kizo ko zuwa gobe ne." Kallansa tai cikin mamaki tace " yaya? Wai da gaske kake?" "Me kika gani?" Zatai magana ta hango Khadija a kusa dasu kad'an ta kura musu ido. Mairo ta kalleshi tace " yaya anzo gunka." Juyawa yai ya kalli gun, sannan ya juyo yace " zamu tafi sai na ganki." Mota ya bud'e ya shiga. Dama su Basira sun shiga tasu motar. Nan aka jasu shi da Garzali, Basira kuma da Lantana. Yana kallan Khadija ta glass har suka wuce. Ba shakka har zuciyarsa yanajinta, balle yanda yaganta a tsaye tana kallansu ya tabbata taji ba dadi na ganinsu tare. Motarsu na wucewa Khadija ta karaso gun Mairo ta kalleta jiki a sanyaye tace " wani asibitin zasu?" "Me yasa baki tambayeshi ba?" Khadija ta kalli Mairo tace " Mairo menene tsakaninki da ya Turab?" Mairo ta kalleta cikin mamaki, ita ya kamata ta mata wannan tambayar, zatai magana taji ta kara cewa " ko da yake bake ya kamata in tambaya ba." Juyawa tai zata tafi, Mairo ta kalleta tace " wani abu ya hadaku da Yaya ne?" Khadija ta juyo sai dai batace komai ba. Mairo tacigaba " Kinaso kicemin bakisan wa yaya yake so ba?" Khadija ta kwakwalo murmushin takaici tace " na sani yanzu, nasani ni kadai nake bilayi na." Mairo zata sake magana taga Khadija tayi gaba. Kallan mamaki ta mata tace " Wai batasan ita yaya yake so ba?" Juyawa tai itama ta fita.... *TEAM ABU TURAB🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *37* Sun isa asibiti Doctor Jamil wanda ya kasance director ne a wannan asibiti, matsayi da girmansa yasa mutane suke karramashi dayawa, sannan ga kokarin yin aiki da kyautatama wanda bashi dashi. Kafin su isa dama Sarki ya sanar dashi komai hakan yasa suna isa wani yaransa yazo ya kaisu wani d'aki, wanda yasa aka kamashi domin su. D'aki ne babba gani matsayi da mukamin wanda zai zauna a d'akin, Dr Jamil da kansa yazo, bayan sun gaisane ya nemi keb'ewa da Abu Turab, hakan yasa Basira da Lantana suka koma gida tunda akwai masu kula dashi. Dr Jamil ne ya kalli Abu Turab yace " Yarima ni kaina nayi mamakin jin abinda ya faru, dan mun taba had'uwa dakai lokacin bakafi shekara 13 ba, sosai na d'auka baka gani." Abu Turab ya d'an murmusa yace " ya fad'ama komai kenan?" Murmushi yai sannan ya matso tare da nad'o wani abu kamar kyale yace " sry fa zaka zama makaho na kwana biyu." Ban fahimta ba? " zamu kula da kai zuwa gobe, sai muce an maka aikin gobe, sannan mu rufe idanuwanka na zummar mun maka aiki, zamu jira zuwa awa 24 sannan mu duba muga ko an samu cigaba, kaga a kalla xamu kai zuwa kwana biyu saboda kar mutane su fahimta, in mun since sai kuma ka jira ko da kwana 3 zuwa hudu ne sannan mu sallameka." Abu Turab ya jinjina kai sannan yace "Na fahimta na kuma gode sosai, Allah ya saka da alkairi." Kafadarsa ya dafa sannan yace " Karka damu, d'a kake a gurina abinda zan maka banaji ma zan wa nawa 'ya'yan domin Abdussamad ya taimakeni dan shine silar zamana duk abinda na zama a yanzu." Abu Turab ya kalleshi sai dai baice komai ba. Dr Jamil yace " duk abinda kake bukata ka fito ka sanar dani, kaji?" Abu Turab yai murmushi sannan ya d'aga kai alamar to. Zarya kawai take a cikin d'akinsu, hankalinta ya gaza kwanciya sam, ganin ba haza ga yamma tayi ta jawo hijab dinta ta fito da sauri. Tana kokarin fita Mahaifiyarta na kawo kai. Tsayawa tai, Ummanta ta kalleta tace " Khadija ina kuma zaki?" Bakinta ta d'an motsa kamar zatai magana sai dai bata ce komai ba. Kallanta ta karayi tace " dama fad'amiki xanyi yanzu mahaifinki ya dawo yace in sanar dake Saifullahi yazo yana gun Magajiya, nan kuma bayan Magrib zai shigo." Gabanta ne ya fadi dan ita sam ta manta da wani Saif da ake san bata. Ta kalli Umma tace " Umma nifa na d'auka an bar maganar nan." Ambar maganar kamar ya kenan? Khadija wai me kika d'auki maganar mahaifinki ne? Kasa tai dakai sannan tace " naji Umma kiyi hakuri amma dan Allah yanxo zan d'an fita kadan ba dadewa zanyi ba." Ina zaki? Yanzu zan dawo nan kasan layi zani. Umma tace " kinga dai magrib ta kawo kai karki dade. Da sauri ta wuce ta a tafe tana amsa wa da to. ******* A bakin asibitin ta sauka ta fito ta shiga ciki, tsayawa tai tana tunani inda zata nufa, Allah ne ya taimaketa ta hango Garzali. Da sauri ta karasa gunsa, shikuma lokacin yana kokarin komawa ne dan yaje gida d'auko wani sako da Abu Turab ya aikeshi. Sai data kusa isa tad'an kwalla mai kira, juyowa yai yana ganin itace ya karaso da sauri sannan ya gaisheta. Amsawa tai sannan ta d'ora da cewa " ina akwma kwantar da Yaya? Muje ka nunamin." Garzali yace " to ranki ya dade." Nan yai gaba ita kuma tana binshi . Sunyi tafiya mai d'an tsawo kafin su isa d'akin. Nan yai sallama ya shiga tare da ajiye mai ledar aiken, Abu Turab ya kalleshi zaiyi magana ya hangota tsaye a jikin kofa. D'auke kansa yai daga inda take yace "Garzali kai ne? Har ka dawo?" " Nadawo Ranka ya dade, sai dai bani kadai bace." Zai sake magana Abu Turab yace " karka damu jeka." Garzali ya fita daga d'akin. Tana tsaye a kofar, gani tai ya koma ya kwanta. A hankali tasa kafarta cikin d'akin, sai dataje kusa dashi ta bayansa ta kuramai ido cikin sanyin murya tace " Yaya ina wuni?" Shiru yai baice komai ba, zama tai a kujerar dake jikin gadon da alama wani ne ya jawota ya zauna agun, kallansa tai bayan ta zauna ta sa hannunyenta kan gadon tana wasa da hannu a hankali ta ce " Yaya ina cikin wani hali, duk duniya kai kadai ne nakejin zan iya sanar mawa, na rasa yanda zanyi, ina tsoro abubuwa guda uku." Shiru tai kafin tai ajiyar xuciya ta cigaba " ina tsoron Abbana da Umma Magajiya dan na tabbata ba tun yanzu ba suke aikata laifi, na biyu ina tsoron kar a cutar dakai." Shiru tad'an sakeyi tad'an furzar da iska sannan tace " yaya, bansan ya zanyi ba da alama maganar Saif tananan, ni kuma......" Kasa karasawa tai saboda zuciyarta dataji tayi rauni. Abu Turab yana jinta har kuma zuciyarsa yakejin kalamanta. Hawayen dayad'an ziraro mata ta goge, tai murmushi sannan tace " Yaya sai dai akwai wani abu da yake sani farin ciki, inajin dadi sosai da wannan aikin da za'ama, na rasa meyasa inaji a jikina lokacin ganinka yayi, sannan inhar kana gani ina ganin ba yanda su Abba zasuyi." Murmushin yake ta sake yi tace " Kayi hakuri na takurama da nakeyi, na sani yanzu bakasan kula ni." Ta mike jiki a sanyaye tace " Yaya inaso kasa abu d'aya a ranka, wlh wlh ni bazan taba cutar dakai ba bama kaiba, bana fata in cutar da kowani mutum a duniya, ko da kuwa a rashin sani ne." Juyawa tai xata tafi, dan dama wannan amsar itace wacce ta dade tanasan ta bashi, tayaya yaya zai dubeta yace mata wai itama tana da tabbas din bazata cuce shi ba?" Sai datakai kofa ta juyo tace " Allah ya baka lafiya Yaya." Nan ta juya tai gaba, juyowa yai da sauri ya kalleta, bayanta ya kalla lokacin data rufe kofar. Idanunsa ya runtse sannan yad'an had'a lab'ansa. Ba shakka sai ya jure sosai, dan a lokacin datake magana jiyai kamar ya juyo ya lalasheta, Saif? Saifullahi? Wa kenan?" Tunowa yai da abinda Mahaifinta ya musu, kwafa yai sannan ya juya. Itakam tana fita ana kiran sallar magrib. A can gida kuwa sai nemanta akeyi dan kuwa Saif kafin ai sallah ya iso,anan sukai sallar Magriba, sai dai shiru ba Khadija. Hankalin Waziri da Mahaifiyarta ya tashi sosai. Nan yasa aka fito dan nemanta. Saifullahi yaro ne ga Senate Kassim, 'yan siyasa ne sannan bayan siyasa sun gaji kudi. ******,* Mairo kuwa da yamma itama ta shirya fes dan zuwa gun Abu Turab saboda shi yace mata tazo akwai maganar da zasuyi. Ta fito zata fito ta gami dashi a zaune a ciki motarsa a kofar gidansu. Yi tai kamar bata ganshi ba xata wuce, Abdulmajid ya fito daga motar xai nufota, da sauri ta koma ciki. Komawa yai ya xauna a saman mota dan jiranta, Mairo kam tana shiga ciki ta dafa kirjinta tace " nikam wannan akwai dan masifa, na tabbata kuma tsabar rainin hankali ne ke damunsa wlh ba so ba, wannan wani irin rainin hankali ne. Itakam tsoronta d'aya shine karta fita tana mai magana Mahaifinta ko wani ya gansu a sanar mai. Dole ta koma ciki fitar da batai ba kenan. *ABU TURAB TEAM🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* _Gaisuwa Gareki Kawar Arziki *Faizah* nagode kwarai da kauna, Allah yabar zumunci Ameen suma Ameen_ *38* A kwanar gidansu ta tsaya, tana tsaye tana kallan gidansu daga d'an nesa, ita a rayuwarta bataji zata iyama wani saurayi kara, Abu Turab take so ba taji zata iya zance da wani. Juyawa tai, sai dai ina zata? Idanunta ta d'an runtse kadan sannan ta cije lab'anta, a hankali take takawa harta kusa isa gidan. A waje taga mahaifinta shida masu musu hidima na gida, sunyu carko carko. Tsoro yasa tad'an hanzarta dan ta d'auka ko wani abun ne ya faru. Tana zuwa kusa dagun fitilar dake kofar gidan ta hasko ta. Wani daga cikinsu yace " Yallabai gatannan." Nan kowa ya juyo ya kalleta, Waziri ya kalleta cikin takaici sai dai alama ya mata akan ta wuce ciki. Nan ta shiga gida, ko d'aki bata shiga ba ya shigo ransa a b'ace yace " Khadija ke ba....." Kallan idanunta yai yaga sunyi jaa sosai da alama har kuka ma tayi. Yana san yarinyar jiyai bazai iya mata fada ba, yace " jeki kintsa kizo ku gaisa da Saifullahi, tun dazu yake jiranki." "To, amma banyi sallah ba." Kiyi sauri kiyi kizo yana jiranki. Tace to. Juyawa tai ta shiga d'aki. Ummanta tana kitchen tana duba kayayyakin abincin da za'a kaimai. Sallah tai sannan ta gyara fuskarta, ta jawo hijabinta ta zura. Mahaifiyarta ce ta shigo kallanta tai tace " Khadija ina kika je?" Shiru tai hakan yasa tace "ki canza kaya kisa sabo." Tana kainan tai waje. Labanta ta ciza na takaigi sannan ta kwabe kaya tasa wani. Fitowa tai ta nufi inda Umma ta nuna mata. Sallama tai sannan ta shiga. Saifullahi ya amsa sallamar tare da kurama kofar ido. Tunda ta shigo yake zuba mata murmushinsa na yaudara har sai dataji kafafunta suna neman hard'ewa. Zama tai daga can nesa dashi, sannan a hankali ta motsa baki tace " Ina wuni?" Gani tai ya mike ya dawo gabanta inda take zaune, kanta na kasa sai gani tai ya sunkuyo inda kanta yake cikin salonsa na soyayya yace " Gimbiyata sai yau Allah yai." D'agowa tai tare da d'an jan jikinta baya tace " Saif meye hakan?" Ajiyar zuciya yai yace " tun randa na ganki a kano sai yau Allah yai na sake ganinki, nikadai nasan dadin danake ji." Baki ta tabe ba tace komai ba. Gani tai ya sake matsowa ta d'ago da sauri tana kallansa tana zazzare ido. Dariya taga yayi yace " Sry mikewa zanyi so nake in kara ganinki sosai." Mikewa yai ya koma gefenta kadan ya zauna yace " Khadija dan Allah ki saki jiki dani, sam banasan inga mace tana wannan kunyar." Kallansa tai tace " Ai kuwa mace da kunya aka santa tayaya za'ace ta daina?" "Oh God c'mon my Khadija." Yanda yaga tana kallansa alamar tsananin mamaki yasa ya saki dariya yace " Khadija wannan kalan fa? Gaskiya xanji dadi in mukai aure dan inasan wannan kalan dayawa." "In mukai aure kamar ya kenan?" Gani tai ya canza fuska yace " bangane ba, kinaso kice bakisan wani watan iyayena zasuzo gaisuwa ba? Daga nan kuma sai me?" Tsananin mamaki da fargabar kalamansa ne yasata yin shiru, nan fa ta tuno da abin begenta Turab. Jitai idanunta sun ciciko. Saif ya kalleta yace " Deejah na menene?" Kaina ke ciwo, tun d'azu. Ya kalleta kalar tausaya yace " sannu." Mikewa tai tace "Saif i am sry amma dan Allah zan je na kwanta, kaina saramin yakeyi." Kai ya jinjina yace " sannu, jeki kwanta nima gidan kawuna zani gobe da safe zan wuce kano." Tace " Nagode Allah ya kiyaye hanya." Tana kai nan tai waje. Shiru yai sannan ya mike tare da murmusawa. Tana fita tai hanyar d'akinta jitai Ummanta tace " Khadija? Ya tafi ne?" "Eh." Ta wuce ciki. Kwanciya tai ta shiga yin juyi akan gado. ********** Magajiya zaune ta a lissafi da hannunta wanda nikaina bansan me take lissafawa ba, Abdulmajid ne ya shigo rai a b'ace, yana shiga ya zauna dabas. Harararsa tai tace " kai kuma meye hakan? Zaka shigo ba wani tafiyar takama da isa irin na magajin Sarki?" Kallanta yai yace " Umma ki taimaken ki auramin Mairo, in ban koyama yarinyar nan hankali ba ta hanyar auranta ba, banaji hankalina zai kwanta." Wani mugun kallo ta bugamai tace " in har koya mata hankalin kake san yi da gaske ai basai ka aureta ba, kawai ka sa a hukuntata." Kai yad'an sosa yace " Ai Umma.." Katseshi tai cikin fada tace " badai auren Mairo bakam, nasan sarai me kake nufi, kai maza ka cireta a ranka, na fadama " Mikewa yai cikin takaici yai waje.... Ita kuwa Mairo yau bakin ciki duk ya hanata sukuni gashi ta ma Abu Turab girki da kanta, haushi da takaici duk ya gama isarta tana kallo kishiyar babarta da 'ya'yanta suka cinye abincin. *********** Washegari an rufe idan Abu Turab, mutane sai zuwa dubashi akeyi kowa na kawo abubuwa na kayan dubiya. Bayan azahar yana zaune yad'an samu ya zare abin da aka d'aure idanun nasa dan hutawa, Garzali ya shigo yace "Ranka ya dade Mairo ce." Bai maida ba yace "ta shigo." Shigowa tai fuskarta d'auke da murmushi. Ta karasa kusa dashi inda kujera take ta zauna, sannan ta kalleshi tace " Inna wuni yaya." Bai amsa ba yace " Hajiya Maryam na d'auka jiya zan ganki?" Baki tad'an turo tace " wani bunsuru ne ya tare mana kofar gida ya hana ni fita." Bunsuru? Tace eh, amma karka damu ya gaji ya tafi. Yace " ce miki nai na damu?" Fuska ta d'an tsuke kad'an tad'an juya kai tace "ba kara?" Cikin rashin zato taji yace " meye tsakaninki da Abdulmajid?" Kallansa tai cikin mamaki, zatai magana sukaji an bud'e kofar da karfi. Abdulmajid ne, Garzali na bayansa yana kokarin mai magana akan karya bud'e. Abu Turab ya kalleshi sannan ya kalli Garzali yamai alama daya koma. Abdulmajid me ya karaso ransa a b'ace ya kalli Mairo sannan ya kalli Abu Turab yace " Tsakaninmu kake tambay?" Abu Turab yamai wani kallo sannan yace " banaji dai acikin kalamaina na sako ka,sannan bakasan laifi bane shigowa mutum guri ba tare da neman izini ba?" Abdulmajid ya matso saitin Mairo ya tsaya yace " ke harkin isa jiya inzauna jiranki amma kiki fitowa? Shine yau dan kin rainamin hankali in ganki anan?" Abu Turab a ransa yace " Au kaine Bunsurun?" Baisan sanda yai dariya ba. Hakan ya kular da Abdulmajid matuka. A zuciye ya kalleshi yace " kai kuma me kakema dariya?" Abu Turab yace " wani bunsuru na tuna, sannan inka gama abinda kake plz kai waje dan na tabbata ba dubani kazo ba." Kallan Mairo yai yace " wuce muje." Harararsa tai tace " inje ina? " Wuce muje nace ko? Tace " yau naga ikon Allah a matsayinka na wa?" "Mene?" Tace " ban fahimta bane ina zaune kawai kace in tashi muje." Ransa yakai kololuwar baci dn dama Magajiya ce tasashi wannan zuwa dubiyar anma da yasan abinda zaigani kenan ko abinda zata mai kenan a gaban yaran nan da baizo ba... Kwafa yai sannan yai waje a zuciye. Yana fita taja tsaki. *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *39* Yana fita Abu Turab ya kalleta tare da daure fuska yace " Mairo, Abdulmajid d'in ne Bunsuru?" Tace "laa yaushe nace haka yaya? Nifa zancen da nake daban." Girman idanunsa ya rage yace " fad'amin tsakaninki dashi." Tace " ni meye tsakanina dashi kuwa? Nema kawai yake ya takuramin da kuma san ya wulakantani." Shiru yai sannan can yace " amma kamar yana sanki." Dariya tad'anyi, sannan tace " kai ka yarda yaya? Wannan ne yake so na? Banaji yasan ma menene soyayya abu d'aya ya sani shi...." Sai kuma tai shiru, kallanta yai yace " me ya sani?" A ranta tace " neman mata mana, amma a fili tace bakomai." Ganin batasan fada yasa yace " ki dai bishi a hankali kinsan halinsa sarai." Baki ta tabe batace komai ba. Ta dade sosai a asibitin dan sai da su Basira sukazo sannan suka tafi tare da ita, Zuciyar Basira fal da farincikin ganin yanda Mairo take kula da Abu Turab. ************* Magajiya ce ta shirya tsaf tasa aka mata girke girke kala kala, kwalliya sosai tai tasa aka jera mata kaya a cikin mota, tana kokarin fitowa Khadija ta shigo. Bayan sun gaisa Khadija tace " Umma Babba bacci ne ya d'aukeni sai dana tashi Umma tacemin kina kirana." Magajiya ta kalleta tace " fita zanyi ki jirani inje asibiti in dawo." Tanajin zancen asibiti tai saurin cewa " zanje Umma Babba inyaso mayi maganar a hanya." Kallanta tai tace " ba dai san ganin Abu Turab d'in ne yasa kikesan zuwa ba ko?" Dasauri tace "a'a Umma." Muje. Nan suka fito tare. Masu kula da bangarenta ta kalla tace ku sanar da mutane tafiyata duba Turab kunsan me nake nufi ai, sukace mun gane ranki ya dade. Tayi hakan ne dan asan abinda takaimai da kuma nunama jama'a tana san yaran. Sun shiga mota, Magajiya ta kalli Khadija cikin yanayin bugat ciki tace " Ashe Saifullahi yazo?" Khadija tace " eh yazo jiya." "Yace zai dawo?" Khadija tai shiru dan batasan me zatace ba, Magajiya ta tsuke fuska tace " Badai wulakantashi kikai ba ko?" Khadija ta kalleta jiki a sanyaye tace " Umma ni na kasa gane dalilin had'in auran nan....." Wani mugun kallo ta mata wanda yasa tai shiru bata iya karasa fadar abinda zata fada ba. Magajiya tace " Khadija kina tunanin zamu cutar dake ne? Yaran nan d'an gidan manya ne sannan shi kad'ai ne namiji agun iyayensa, ga kudi ga matsayi auranku dashi zai taimaka ma Yayanki Abdulmajid zai kuma taimakeki." Mamaki ma ya hanata magana, au wad'an nan sune dalilin dayakesa ayi aure? Matsayi?kudi?" Magajiya ta dafata tace " na yarda dake dan haka karki bani kunya, kinfi kowa sanin Abu Turab bazai taba auranki ba ko matan duniya sun kare dan ko shi ya yarda ni da mahaifinki bazamu taba yarda ba, in ma kina tunanin wani shirme a ranki to kiyi maza ki cire wannan ki maida hankalinki kan Abu Turab." Khadija tai kasa dakai kawai batace komai ba. Sun isa asibiti nan aka kwashi kaya aka fara shiga dasu. Abu Turab na kwance lokacin bacci ne ya fara d'aukansa, Garzali ne ya shigo ya sanar dashi isowar su Magajiya. Idanunsa na rufe dama saboda dazu Galadima da Barde suka tafi. Tashi yai ya zauna, ta shigo cikin isarta da yanayin tafiyarta, tana kallansa ta saki wani murmushi, ba shakka yaran nan dan rainin hankali ne harda wani rufe ido? Shiga tai ta zauna, khadija tana tsaye a jikin kofa bata karaso ba. Magajiya ta kalleta tace " dan bamu guri Khadija d'a da uwa zasuyi magana, in na gama sai ki dubashi." To kawai tace tai waje. Magajiya ta kalleshi tace " Turab bazaka kunce daurin ka gaida mahaifiyarka da kyau ba?" Abu Turab yace " ai na gaidake ,sannan nida banda lafiya an min aikin ido ta ina zan ganki?" Murmusa wa tai tace "ahhh na tuna ashe fa makaho ne wanda akamai gyaran ido." Abu Turab yace " naji dadi da kika tuna." Shiru sukai kafin can tace "Mahaifinka ya tura mutane yau sunkai kayan godiya da amsawar da masarautar kano ta basu na auranka." Batajira amsarsa ba tacigaba " Kaifa kana tunanin kaci galaba ko?za kuma ka auri Bilkisu ko?" Tad'an juya kai sannan tace " sai dai kuma inaso ka sani sai har in an gama shafa fatiha na d'aura auranku sannan zan yarda kaci galaba akan Bilkisu, abinda nazo in fadama kenan." Murmushi ya saki yace " na d'auka kinzo ne akan mutane susan kinzo duba d'anki? Ashe zuwa kikai kimin kashedi." Kallansa tai tace " ai dole ne uwa tazo duba danta." Yace " hmm gaskiya kam " Mikewa tai tace " zan koma, ina fatan makaho ya dawo gida a matsayin cikaken ido hakan ne zaisa wasan yafi dadi, muga tsohub hannu da sabon hannu." Kai ya jinjina yace " kuma fa hakane." Juyawa tai tai waje. Khadija ce ta ke kokarin shigowa yanaji Magajiya na ce mata wuce muje ba sai kin shiga ba. Khadija tace " Umma ba dade wa zanyi ba dan Allah." Wuce muje ko? Ko kin taba gani an duba mai lafiya? Zata sake magana ta mata wani kalli, juyawa tai idanunta sun ciciko. Komawa yai shima ya kwanta, tunda ta tafi jiya duk yanda yaso ya cire zancen Saif a ransa ya kasa, waye shi? Menene matsayinsa a gunta? Sai dayai yaki sosai da tunanin kafin ya samu ya kawar da shi a ransa. Khadija kam harta shiga mota bata ce komai ba, Magajiya duk da ganin Khadija a haka yasa taji ba dadi sai dai inaaa, bazata yarda da yanda Khadija ke nuna tsantsar damuwarta akan yaron ba. ********** Yau ya cika sati d'aya kenan da zuwan Turab Asibiti, yau ne kuma ranar da zai koma, tsaf suka shirya komai, Mai Martaba da kansa yazo dan tafiya da dansa, su Hisham da su Barde duk sunyo rakiya. Mairo kam kusan kullum sai tazo dan Basira ma wani sa'in ita take aike, Khadija kam ba damar zuwa, tun randa suka tafi, sai dai kome take Abu Turab na ranta, kullum sai ta tashi tamai addu'a da daddare. *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *40* Magajiya ce kicinged'e a kilisarta da alama tunani takeyi duba da yanayin da take ciki. Jin muryar Hisham ne yasa ta katse tunaninta tare da bashi izinin shigowa. Hisham ya shigo sannan ya zauna kusa da ita, ya gaidata. Magajiya tad'an ja numfashi bayan sun gama gaisawa tace " Hisham dole ne sai mun kawar da Abu Turab daga gabanmu, domin na kula in bamuyi wasa ba Mai Martaba zai biyo mana ta bayan gida, da farko ya had'a Turab da 'yar sarkin kano sannan mun fahimci yana gani, sannan gashi zamansa a asibiti manyan masu mukamai sunje dubashi sun kuma dawo da yaban d'abi'arsa." Hisham ya kalleta yace " Magajiya nikaina abin nan ya damen, me zai hana mu raba shi da du......" Wani mugun kallo ta bugamai tace " so kake ka lalata mana shiri irin sanda yana jariri? Duk badadan kaje kayi shirman kona musu gida ba me zaisa Basira tabar gidan nan? Da cikin ruwan sanyi zamu turashi barzahu ba tare da an fahimci komai ba, dan haka karka kuskura ka kara gigin daukan hukunci ba tare da ni na sani ba." Ba shakka yaji haushin kalamanta a ransa, sai dai a fili cewa yai " shikenan." Tace " nayi tunani sosai na fahimci Basira itace lagwan yaran nan, in har muka sata a tsaka mai yuwa to fa Turab zai zamar mana tamkar akala." Hisham yace " Na d'auka Turab muke hari ba wata Basira ba." Tsaki tai tace " kai matsalata dakai kenan, kwakwalwarka gaba d'aya bata ja, kai kana tunanin yaran nan ba wani abu bane?" Hisham yace " to nawa yaran yake?" " nawa yake amma har ya nemi ja min masifa nida Abdulmajid? To bari kaji in fada ma, wlh wannan yaran in ba munyi da gaske ba reshe ne xai juyi da mujiya." Tacigaba " so nake kasa a samomin guba amma mara karfi." Cikin mamaki yace " guba kuma? Wace iri?badai Basira zaki kashe fa ita ba? A fusace tace " wai meyasa in na fadi abu ne yaya sai kace sai na fadama dalili? Kasa a samo abinda na fadama, sannan ka tabbatar kasa anba wannan yarinyar da muka saka a bangaren basira data saka a cikin abincin da za' a kawo min?" Idanunsa ne suka firfito yace " bangane abincin da za'a kawo miki ba? Kina nufin kece zakici gubar?" Tace " wannan ba damuwarka bace in har kanaso mu d'aura Abdulmajid akan mulki to kawai ka dinga bin abinda na umarceka ba tare da tambaya ba." Daurewa yaiyace "to." Tace " gobe zasuzo gaisuwa, dan haka ayau zaka samo gubar ka kuma aika da ita a daren nan." Yace to, mikewa yai ya fito yana mamakin me take shirin yi. Yana fita ta mike, sannan tai murmushin mugunta. ********** Shikam Abu Turab bayan ya iso yana gun Mahaifinsa sun dade suna tattaunawa game da bikinsa da kuma wasu al'amura na sarauta da mahaifinsa ya nemi shawarar d'an nasa akai. Sun yanke shawarar komawarsa garin kano a wannan sati, in ya dawo kuma sai a tura kayan gaisuwa da na lefe a saka rana. Bayan ya fito ne ya nufi gun mahaifiyarsa, duk inda ya wuce mutane sai tayashi murnar warkewa sukeyi har ya isa. Basira tasa an mai girke kala kala kana ganinta zakaga tsantsan farinciki a fuskarta. Bayan sun gaisa ne tasa aka jera mai abimci kala kala, Abu Turab yai murmushi yace "Umma kenan sai kace wanda na bar garin?" Lantaba Tace "ai Uban gidana inaji da kai mace ne in kai aure binka zatai." Dariya suka saka, nan ya fara zuba abinci. Basira tace " Magajiya ta shirya walima na kusa da zamuje gobe na murnar warkewarka." Kallanta yai sannan ya baida kansa kan abincin yace " she is trying hard." Basira tace " magana kai?" A'a, amma su waye zasu gun? Tace "hmm daga dai mu matan Takawa da shi Mai Martaban sai kai da Abdulmajid, amma bansan ko da wasu ba." Yace "hmm." Basira tace " tace insa ayi abinci daga nan, nafi san kowa in mai abincin danasan yafi so, saboda taro ne akayishi saboda d'ana." Zuciyarsa d'aya dan bai kawo komai a ransa ba yace " to, amma karki wahalar da kanki Umma." Tace " wace wahala bayan ba ni zanyi girkin ba?" Murmushi yai ya cigaba da cin abincinsa. Sai daya gama ya mike ya fito, bangaren kakarsa ya nufa wacce ta tsufa sosai gashi batada lafiya, yana tafe su Garzali na bayansa. Sam bai kula da ita ba wacce ta shigo gidan na sarauta dan kawo ma Abdulmajid sakon da mahaifiyarta ta aikota ta kawo. Sai da suka kusan junan su sannan suka ankara da juna. Kallanta yai sannan ya d'auke idanunsa ya cigaba da tafiya. Wani sanyin dadi ne ya kamata ta karaso da sauri tace " Yaya." Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalleta fuskarnan a d'aure. Murmushi ta saki tace " Yaya baka taba ganina ba ko? Nice Khadija, ahhh nasan kasan muryata, hmm Alhamdulila yau Allah ya amshi addu'a ta." Kallanta yakeyi kawai sai dai zuciyarsa ta karaya sosai, Khadija ta share kwallarta data taho tace " Yaya Allah ne kadai yasan farincikin danakeyi ganin idanunka sun bud'u da izinin Allah bud'ar idanunka zai kawoma alheri masu yawa a rayuwarka." Ta karasa maganar cikin rawar murya dan kuka na neman kufce mata. Sama ya d'an kallan kadan yana neman dake zuciyarsa dan tabbas kalamanta sun ratsashi. Kallanta yai yace " nagode, sai dai inaso ko a hanya muka hadu ki daina nuna kin sanni, banasan inzama mai jawo miki bakin ciki shiyasa nake fatan ki cireni daga ranki ki kuma daina damuwa dani." Kai ta jinjina ta na kokarin share hawayenta da hannu tace " naji yaya, zanyi abinda kace." Kallan mamaki ya mata dan bai yi tunanin abinda zatace kenan ba. Khadija ta kara share hawayenta tace " kasan meyasa zan rabu dakai yaya?" Kallan ta yai baice komai ba. Ta cigaba " saboda ka daina murmushi in kana tare dani, ka daina fara'a, ko farin ciki kakeyi daga kaji muryata sai inga farincikin nan ya tafi daga fuskarka." Hawayenta ta kara sharewa tace " kaine mutum na farko dana taba so, banaji zan kara san wani haka, ba kuma naji zan daina ma fatan alkairi da yima addu'a a rayuwarka sai dai bazan taba yarda inzama nice sillar bakin cikinka ba, bansan dalilinka na canzamin hala ba, sai dai ba yanda z........" Hawaye ne suka taho sosai wanda ta kasa karasawa, jiyai gaba daya daga tsakiyar kansa har zuwa 'yan yatsun kafafunsa sun amsa, shikansa sai dayaji idanunsa suna neman canzawa na yanayin kawo ruwa. Kallansa tai sannan ta kakaro murmushi tamai sannan ta juya ta fara tafiya. Kasa motsawa tai daga inda yake, su Garzali na gefe duk da basusan me tacemai ba amma sun fahimci yana bukatar keb'ewa. Abu Turab kallanta yakeyi har sai da ya dena hangota sam ya kasa motsawa, yafi minti 20 a haka kafin ya taka kamar wanda aka tsuma a ruwa ya karasa bangaren kakar. Jikinta kam ba sauki duba da yanayin tsufan datai, bai dade ba ya taso. D'akinsa ya nufa ya shige ya kwanta rigingine, rayuwarsu da Khadija ya shiga tunowa, wasu kananan hawayene suka zubo ta gangaren idanunsa, mirginawa yai ya kwanta ganin tunaninta na neman addabarsa ya mike zaune da sauri ya bud'e cikin drawer dinsa ya dauko d'ankwalinta har yayi kamar zai yadda sai kuma ya fasa ya d'aga can kasan kayansa ya saka shi. Ya koma kan gado ya kwanta........ Khadija kam tana fita ta wuce gida dan kuka kawai takeyi, sam bata kula da Hisham ba dayake tsaye gefen kofar shiga gidan shi da su Galadima. Hisham ya kula da kukan da takeyi sai dai ba damar magana saboda bayasan a ganta tana kuka. *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* .🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *_Wannan Shafin sadaukarwa ce gareku Aminan arziki, BillynAbdul, Billy Badaru da Ummu Basheer Allah yabar zumunci da aminta (Ameen)_* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *41* Yau tun safe ake hidimar yin walimar da Magajiya ta shirya, barin ma bangaren Basira wanda aketa hada hadar girke girke, katon d'akin da suke taro na lokaci zuwa lokaci tasa aka gyara, an mai kwalliya sosai, kowa an waremai gurin zamansa. Abu Turab kam yana can gun hutawar mai martaba wanda ya saba zama, yarasa meyasa yakejin hankalinsa bai kwanta da wannan walimar ba sai dai ya rasa ta ina matsalar take, kalaman Magajiya ne suke ta mai yawo a zuciyarsa, ya tabbata akwai abinda ta shirya a wannan taron. Ganin bashida amsa da hujjar dazai kama yasa ya mike, ya nufi bangaren Mahaifiyarsa. Tana tsaye a kitchen tana kula da abincin da ake tayi, Mairo ma aiki take tukuru, murmushi yai na jin dadin yanda take taimakon mahaifiyarsa. Basira ce ta juyo ta kalleshi sannan ta kalli Mairo tace " Mairo bari na shiga ciki." Tace " To Umma" kallan Abu Turab tai tace " Yaya Ina Wuni? " Yace " Mairo sannu da aiki." Bata amsa ba sai murmusawa datai. Bayan Basira yabi, Suna shiga ciki ta kalleshi tace " Dazu na tura a kiramin Mairo, sai datazo hankalina ya kwanta har nake shigowa ciki." Kallanta yai yace " Umma kinaji da Mairo, itama haka." Tace " Abu Turab in fadama gaskiya babban burina a duniyarnan a wannan lokacin bai wuce in ganka cikin farinciki ba, sannan banaji akwai mai saka wannan farin cikin daya wuce ta." Kasa yai da kansa baice komai ba, ta kalleshi tace " komai da lafiya ko?" D'agowa yai ya kalleta cikin wani yanayi yace " Umma sam hankalina ya kasa kwanciya, inaji a jikina akwai abinda zai faru a gun taron nan sai dai na rasa menene." Kallansa tai cikin kulawa tace " Turab nasan me kake tsoro sai dai inaso ka sa aranka ba abinda zai faru in shaAllah, dana menene abin jin? Bai wuce ta zuba mana wani abun a abincin mu ba, to ninake yin abincin kaga ba wani abu da zata iya yi." Jitai yace " shine abinda ke damuna Umma, yin girki a nan bangaren." Kai ta girgiza tace " Abu Turab kenan, insha Allah ba abinda zai faru." Shiru yai baice komai ba, sai dai shikam abin na damunsa menene dalilin barin mahaifiyarsa ta d'au nauyin girke girke?" Basira ce ta katseshi tace " ka tashi kaje ka shirya nima shirya wa zanyi tunda ankusa kamala komai, sannan Mairo da Lantana suna gun." Mikewa yai ya fito jiki a sanyaye. Sai dayazo saitin kitchen sannan ya kalli kitchen din aiki kawai akeyi, Mairo ce ta fito tazo jikin kofa tace " Yaya lafiya?" Yace " Mairo dan zo." Takowa tai har zuwa inda yake, ya kalleta kamar zaiyi magana sai kuma taji yace " shikenan." Kallan mamaki tamai sai dai batace komai ba, juyawa yai zai wuce sai kuma taga ya tsaya ya kalleta yace " Nagode Mairo." Nan ma kallan mamaki tamai, sai dai bata iya cewa komai ba. Abu Turab ya fita zuwa bangarensa. Wanka yai sannan ya shirya cikin wata had'adan yadinsa d'inkin yamai kyau sosai, yasa hula sannan yai sallar la'asar. Ya dade yana addu'oi kafin ya mike ya fito. Su Garzali dama suna tsaye suna jiransa. ************* Magajiya ta sha ado na gani na fada, tayi kyau sosai kamar batakai yawan shekarunta ba, kallan kanta tai a madubi ta saki murmushi a ranta tace " nayi kuskure babba na bawa kishiyoyina maganin hana haihuwa, kaine ka nunamin kuskurena Turab, ba su ya kamata in ba wa magani ba mijina ya kamata inba, sai dai ganin an haifeka ina zaune kamar wawiya yasa na dawo hayyacina, tun kuwa daga lokacin nasa aka amsomin magani akesama Mai Martaba a abinci, ba'a ja dani, ka jirani zan nunamaka wacece Magajiya a ranar yau, zan nuna maka bakasan komai ba a harkar wasa. Takalmi ta saka ta zura alkyabbarta kyanta da kwarjininta suka kara fitowa. A falonta ta tadda ragowar matan kannan mai martaba da kuma kishiyoyinta. Nan suka gaisheta, tana gaba suna bayanta haka har suka isa. A zaune suka tadda Basira, a mazauninta, sai matar Galadima da Mamar Khadija. Tana shigowa ta mike sai data zauna sannan kowa ya samu gu ya zauna, wannan tsarin ita tafito dashi, duk sanda za'ai taro dolene sai ta zauna kafin kowa ya zauna. Sun d'anyi gaishe gaishe kafin a sanar da isowar Abdulmajid. Nan ya shigo ya gaida Magajiya da matan mahaifinsa sannan yaja ya zauna, a gun zamansa. Can aka sanar da Zagi ya sanar da isowar Mai martaba. "Lafiya Sarkin yakin Sarkin musulmi Lafiya maida garin wani kango Lafiya Barden mahadi Lafiya Sukukun bakaka Lafiya Darzaza amalen sarakuna Lafiya ba hau da wani ba sauke wani Lafiya hana kangara Lafiya Sakaka babban bako Lafiya Bango madafar bayi Lafiya hadarin kasa maganin mai kabido........." Mai Martaba ne ya shigo Abu turab na bayansa. Yana shiga kowa yagaidashi. Sai da ya zauna a gun zamansa. Gyaran murya yai sannan yace " Nagode kwarai da zuwanku taron nan na taya murnar samun saukin Abu Turab, Allah ya saka da alkairi." Nan sukace Ameen. Abu Turab na zaune gefen hagunsa sai tunsu d'aya da Abdulmajid wanda ke zaune a bangaren dama. Sai daya gaishesu shima kamar yanda Abdulmajid yai sai dai shi sai daya gaida kowa. An d'anyi shiru kafin Magajiya tace " D'ana Abu Turab fatan alkairi gareka da kuma rayuwarka, yanda idanunka suka bud'e ina maka fatan kyakyawar rayuwa mai d'orewa." Nan kowa yace "amin." Abu Turab kallanta yai sannan yai kasa dakai yace " ina godiya Umma Babba na kuma gode da addu'arki." Murmushi tamai wanda hakan ya d'ansa shi kara kallanta. D'auke idanunta tai daga kansa ta kalli basira sa nan ta kalli sarki tace " Haikawa Basira ce tace abar mata harkar girke girke." Murmushi ya saki sannan ya kalli Basira yace " ai ba laifi, hakan yayi." Mamaki abin yad'an ba Basira dan kuwa ba ita ta nema ba, itace ta ba ta, to meye na fadama ma Sarki?" An d'anyi hira kad'an kafin Lantana ta shigo ta fara jera abinci, wanda masu kula da bangaren Basira ke rike da tire manya manya. Da yake abin a tsare yake ,Lantana ta ajiye ma kowa nasa a gabansa. Nan Mai Martaba ya bada izinin aci abinci. Sai daya fara ci kafin kowa ya bud'e nasa. Abu Turab kam ko bud'e nasa bai yiba sai kallan kowa yakeyi yana san yaga inda wani shiri da takesan tadawa. Kallansa tai ta saki murmushi dan ta fahimceshi. Nan ta bud'e nata itama hankalinta a kwance. Kafin ta faraci sai data kalli Turab tace " D'ana ya naga ko bud'ewa bakai ba?" Kallanta yai tare da d'an rage girman idanunsa, sannan yace " yanzu zanci." Bud'e nashi yai, kallanta ya sakeyi, gani yai tana tacin abincinta hankalunta a kwance, kowa ya kalla yaga kowa yana ci ciki kuwa harda Basira. Yana kokarin kaiwa bakinsa sukaga Magajiya ta fara wani abu, da sauri Abdulmajid ya mike cikin tashin hankali. Nan fa kowa ya yo kanta, kumfa ne ke fita ne daga bakinta, idanunta sai farfari suke. Abu Turab ya runtse idanunsa da karfin gaske, sanna ya bud'esu sun kada sunyi ja, hannayensa ya saka duka biyun ya shafi fuskarsa abinda ta shiya kenan? Mai Martaba ne cikin tashin hankali ya kalli Abu Turab sannan ya ce " Turab yi sauri kasa a kira mai magani, ya sameta a bangarenta, bari a maidata can." Nan akai waje da ita, sai amai kawai takeyi. Basira kam gaba d'aya ta gama rikice wa sai yanzu itama ta fahimci dalilin dayasa tace tai girki. Abu Turab ya kira mai magani suka isa bangaren Magajiya. Nan aka shiga mata magani, amai take har yanzu, mai maganin ta d'ago ta kalli mutanen gun tace " guba ce, guba taci." Hankalin kowa a tashe aka kalli Basira. Abu Turab yana rasa mai zaice. Abdulmajid ne ya shigo da gudu cikin dabara ya tura mata wani abu a bakinta. Aman ya tsaya sai dai da alama hankalinta baya jikinta dan a sume take. Abu Turab ya kalleta cikin tsananin mamaki, yau abin harya kai ta nemi halaka kanta? Akan mulki? Akan ta hanashi auren Bilkisu? Ya tabbata yanzu basuda mafita, in zance ya yado zaije har masarautar kano, wani sarkin ne ko wani uban ne zai bashi aure? Fitowa yai waje dakyar yake sa kafarsa. Khadija ce ta karaso da sauri, itada Mahaifiyarta. Yana kallanta ta shiga ciki kamar bata ganshi ba. Kallan waje yai mutane sun cika gun sosai, sai gulmar Basira akeyi, kowa na fadan albarkacin bakinsa, shikansa yana fitowa ya fahimci gulmar hardashi. Wato Basira dan taga d'anta ya warke shine take kokarin halaka Magajiya, sannan ta halaka Abdulmajid ta d'aura nata akan mulki. Inka ganta kamar bazatai haka ba. Gulma dai kala kala... Basira kam tana zaune a falo cikin tashin hankali, ta tambayi masu aikinta kowa yace baisan meya faru ba. Mairo duk ta rukice itama ta shiga kitchen sai dube dube takeyi cikin tashin hankali. Kan kace me? Zance har ya fita daga gidan ya shiga cikin gari...... *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *_Wannan shafin naku ne 'yan Zauren BieBie Isa, tnx alot 4 ur support....Much luv_* *42* Abu Turab ya shiga bangaren mahaifiyarsa, ba kowa a falon sai Lantana dake zaune jugum. Tana ganinsa ta mike ta gaisheshi, kallanta yai yace " Umma fa?" A hankali tace "tana d'aki." Juyawa yai ya fita, dayake magrib ta duso massalaci ya nufa. Ana idar da sallar wasu dan gulma tun a cikin massalacin suke yan gulmace gulmacen maganar, mikewa yai ya fito. Bangaren Mahaifinsa ya nufa. Jakadiya tana ganinsa ta iso gunsa ta gaidashi. Kallanta yai yace " Mai Martaba fa?" Tace " Yana ciki, a ma iso?" Kai ya d'aga mata alamar eh, har ta fara tafiya sai ta dawo gunsa tace " Hmm nikam Yarima naji abinda ya faru, sai dai kuma hmm tuba nake ranka ya dade amma ni nasan akwai alamar tambaya a al'amarin nan." Gefe da gefe ta kalla tace " Sai dai neman Allah ya fitar da ku lafiya." Kauda kansa yai daga kanta dan shi sam bayasan harkar gulma tunda kuwa yaga yanda take wani juye juye yaji ransa ya baci. Juyawa tai, bata dade ba sai gashi ta dawo tace ya shiga. Abu Turab ya shiga. A zaune ya tadda mahaifinsa sanye da tabarau, rike da wata takarda da alama karantawa yakeyi. Abu Turab ya shiga sannan ya kara gaidashi. Sarki ya zare tabarau din ya kalleshi yace " Turab ya akai?" Abu Turab ya kalleshi yace " Abba, na tabbata kasan Umma bazata aikata wannan laifin ba." Murmushi yai sannan yace " bansan komai ba Turab, bansan ko zata aikata ba ko bazata aikata ba." Kallan mamaki Abu Turab yamai yace " Abba." Sarki ya kalleshi kallo wanda bazaka tana fahimtar yanayin da mutun yake ciki ba yace " Abu Turab ba dai so kake kacemin in yarda da Basira ba, bayan a gabana Magajiya ta fadi?" Abu Turab cikin mamaki ya kalleshi yace " Amma......" Katseshi yai yace " In har kanaso in yarda da Mahaifiyarka to inga evidence wannan shine kadai abinda zan fadama." Abu Turab yai shiru" nagode." Kawai abinda yace kenan yai waje. Mai Martaba ya bi bayansa da kallo cikin tausayawa a fili yace " Abu Turab dolene sai ka yaki weakness dinka, Magajiya ta riga tasan Basira tace lagwanka, tunda nake bantaba ganinka cikin damuwa kamar tayau ba. Abu Turab yana fita ya nufi bangarensa, sam ya rasa dalili zuciyarsa ta kasa bashi wata mafita, kwakwaran tunani ma ya kasayi, mahaifiyarsa kawai yake hangowa lokacin da ta kalleshi cikin wani yanayi, kallo d'aya yamata ya fahimci tsantsan tashin hankali karara a idanunta. Wannan rana ta zame musu ranar tashin hankali, Abu Turab da Basira. Magajiya kuwa ta daina amai sai dai har alokacin bata bude idanunta ba a haka a ka kwana, khadija ce ta zauna a gunta. Washe gari da safe yana zaune a d'aki Garzali ya kwankwasa mai kofa. Mikewa yai ya bud'e, kallansa yai yace " Garzali ya akai?" Garzali yace " Sabi'u ne ya zo Ranka ya dade." Bai koma ciki ba kawai ya jawo kofar d'akin ya fito falo. Garzali yabi bayansa. A zaune yaga Sabi'u. Kusa dashi ya karasa ya mikamai hannu sukai musabaha. Sabi'u ya kalleshi cikin kulawa yace " Mutumina are u okay?" Murmushin yake ya masa yace " ya akai da safen nan?" Sabi'u ya kalleshi yace " maganar Gimbiya Bilkisu ce." Kallansa Abu Turab yai yace " ta fasa aurena?" Murmushi yai yace " nasan haka zata faru ai." Sabi'u yace "no ba haka bane." Ya fada yana girgiza kai. Abu Turab ya kalleshi sai dai baice komai ba. Sabi'u yace " nemanka takeyi." Cikin mamaki Abu Turab ya kalleshi yace " nema kamar ya?" Sabi'u yace " bansani ba ni kaina, bansan me ya faru ba d'azu da safe wambai ya kira gida a landline ya ce abani, ina amsa ya sanar dani, kasan Wamban kano shike auren kanwar Mamana." Abu Turab yace " shikenan a satin nan naje." Sabi'u da sauri yace " da alama neman na gaggawa ne fa, kasan ana asuba aka kira wayar? Bansan meke faruwa ba amma tabbas yanda aka sanar dani da alama neman gaggawa ne." Mikewa yai yace " Kana tunanin zan tafi inbar Umma na da take cikin wannan halin?" Sabi'u yace "haka ne sai dai ina ganin ka nemi shawararta, ita kanta nasan cewa zatai kaje." Abu Turab yace "zan nemeka duk yanda mukai da ita." Daga nan ya wuce ciki. Tun dare yake tunanin mafita, sau biyo yana komawa bangaren mahaifiyarsa amma har a lokacin bata fito ba wannan dalilin shi ya kara d'agamai hankali sosai. Har ya zauna sai kuma ya mike ya fito bangaren mahaifiyarsa. Lantana tana ganinsa ta taso ta gaidashi. Kallanta yai cikin damuwa yace " ta fito?" Lantana ta girgiza mai kai alamar a'a sannan tai kasa da kanta alamar damuwa. Kofar d'akin ya nufa, ya kwankwasa, shiru yaji ya kara kwankwasawa. Jin ba alamar motsi yasa ya murd'a kofar d'akin. A kan gado ya hangota a kwance lulube da bargo. Da sauri ya karasa ciki. Bacci takeyi sai dai kana kallanta da yanda take futar da numfashinta zakasan ba tada lafiya. A hankali yakai hannunsa kan goshinta. Zafin dayaji ne yasa hankalinsa ya tashi. Da karfi ya kwallawa Lantana kira. Da gudu ta shigo dan yanda ya kirata tasan da matsala, Lantana ta kalleshu cikin tashin hankali ta kalli basira. Cikin fada yace " Lanata me kike yi jikin Umma yakai haka?" Lantana ta kalli Basira cikin yanayin na ban tausayi tace " Uban gidana jiya da zata shiga tace kar inbar kowa ya shigo mata ciki kuwa harda ni, sannan ko abinci in na kwankwasa mata sai tace min kar na sake shiyasa ban kara dawowa ba." Idanu ya runtse cikin tashin hankali yace " kira mai magani." Hannu Basira tasa ta rike hannun Turab cikin a hankali tace " a'a Turab inba so kake magana ta kara karfafa ba ka bar zancen mai maganin nan " Kallanta yai cikin tausayawa idanunsa duk sun rine yace " Umma?" A hankali tace " Lantana kisa a kira Mairo kice ta tahomin da magani, hakan ya isheni Turab " Rasa abin cewa yai, jiyai tace " Ya jikin Magajiyan?" Kallanta yai cikin wani yanayi, yace " wake zancen wannan? Matar da ita tajama kanta ciwo dan ganin bayana? Meyasa in zatai sharrin bazai tsaya iya kaina ba? Menene dalilinta na had'awa dake?" Kallansa tai, jiyai zuciyarsa ta kara karaya, mikewa yai da sauri ya fito daga d'akin, bakin ciki ya addabeshi. Bangaren Magajiya ya nufa rai a bace. Tana kwance, Khadija ce kawai a gunta tana zaune tana matsa mata kafa. Kallo d'aya yama khadija ya maida dubansa kan Magajiya, yana kallanta yace " Ta farfado?" Khadija ta kalleshi ba shakka tafi kowa sanin yana cikin wani hali sai dai ita kam ta rasa inda matsalar take, ta tabbata Umman Turab bazata taba yin haka ba, to meya faru? Daga ina aka samu matsalar? "A hankali ta amsa mai baya farka ba yaya." Idanunsa nakan Magajiya yace " d'an bamu guri." Mikewa tai jiki a sanyeye tai waje, zuciyarta a karye, ba shakka tasan jiya ya turab ko bacci bai samu ba. Juyowa tai ta kurama kofar d'akin ido, ya zatai da ya Turab?ya zatai ta taimaki mahaifiyarsa?" Abu Turab bayan ta fita ya kalli Magajiya yace " Kina kokari, na kuma jinjina miki a salo na makirci da iya tugu, kinfi mahaifiyata girma amma saboda kinasan ganin bayana kika ajiye girmanki." Gani yai ta bud'e idanunta. Kallan mamaki ya mata yace " Idanki biyu?" Murmushi ta saki ma tsantsar mugunta tace " Turab naji da ka fahimci na girmi uwarka, kaga alama ce ta ko ita bata isa taja dani ba, duk sanda ka nemi izinin durkusawa da bani hakuri lokacin zan saurareka." Tana gama fad'ar haka ta maida idanunta ta rufe, tsananin mamaki ya hanashi magana, kallanta yai cikin takaici yace " zan baki mamaki, wlh wahalar da mahaifiyata da kikai, zagin da kikasa a ka mata......" Kasa karasawa yai jin an turo kofa. Abdulmajid ne, yana shigowa ya ce " malam yi waje ko? Tayaya ma Khadija zata barka kai kadai a ciki? In ka karasata fa?" Abu Turab ya kalleshi kamar zaiyi magana sai kuma yai waje. Khadija tana tsaye taga ya fito, kallansa tai cikin tausayawa, ko kallanta baiyi ba yai gaba. Kansa ya dafe cikin tsananin takaici. Sabi'u ne ya nufoshi cikin hanzari. Yana karasowa gun Abu Turab ya kalleshi, kafin yai magana Sabi'u yace " Yarima ko zuwa zamuyi kuyi magana da Gimbiya? Na d'auko number data kira da ita muje dan Allah ka kirata, yanzun nan ta sa aka sake kirana tace ko magana ne a hadaku kuyi." Abu Turab yace muje to. Da yake akwai landline a bangaren Basira nan suka nufa. Sabi'u ya danna numbobin, bayan sun gaisa da wace ta d'aga yace " Gimbiya suke nema ga Yarima Turab din." Nan tace to. Ba'a dade ba Bilkisu ta amshi wayar. Nan ya mikama Abu Turab bayan ya gaidata. Abu Turab ya amsa, Sabi'u kuma ya fita. Shiru ne ya d'an ratsa kafin Abu Turab yace " kuna lafiya?" A hankali tace " naji abinda ya faru, ya Umman taka?" Mamaki ne ya kamashi dan baiyi zatan abinda zaiji daga gareta ba kenan. Bata jira amsarsa ba tace " ance bazaka samu damar zuwa ba." Yace " Bilkisu kinsan halin da ake ciki sannan Umma batajin dadi." Kai ta jinjina tace " na fahimta, Abbana yace zai sake tunani akan auranmu." Yasan hakan zai faru sai dai baiyi tunanin ji daga bakinta ba. Murmushi yai yace " Nasani dole ne hakan ya faru, duba da yanayin da muka shiga, ko nine mahaifinki dole ne na sake tunani akan auran." Jiyai tace " abinda yasa na kiraka shine inaso in tunama abu 2, kada ka bari wannan abun ya kwantar dakai, bansan meke faruwa a masarautarku ba sai dai nasan abu d'aya in har ka bari akaci galabarka a kan wannan abun banaji zaka farfado daga kuncin abin, zan duba ingani zan kuma sanar da Abbana akan mujira mugani in zaka iya warware matsalar nan daka shiga, na san zuciyarka dakakiya ce, zuciyace kuma ta 'ya'yan da suka kasance jarumai dan wannan dalilin ne yasa na aminta dakai, sai dai jin muryarka yanzu ya nunamin Mahaifiyarka itace lagwanka, inhar aka biyo ta bangaren Mahaifiyarka alamace ta angama cutar ka, an kuma rufema tunaninka da jarumtarka." Idanunsa ne suka canza daga kalar tausayawar da suke dazu, Murmushi ya saki yace " Nagode Bilkisu jin kalamanki yasa na fahimci dalilin dayasa aka biyo ta bayan mahaifiyata, dan ansan bazan iya yin komai ba, zuciyata zata raunana ta hanani tunani komai, ta sani cikin rudo da tausayawa." Zai sake magana yaji ta katse wayar. Ajiye wayar yai yabita da murmushi lalai Bilkisu jinin sarautace ta asali, har daga jin muryarsa ta fahimci abinda ya kamata ta fadamai? Mikewa yai ya nufi waje. Mairo wacce ta taho da magani ta ganshi. Ta d'auka xata ganshi cikin yanayi na tashin hankali. Kallanta yai yace " Mairo kin iso?" *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* _Tuba nake plz na jina shiru da kukai ✌🏻dayz_ *43* Mairo ta tsaya kawai tana binsa da kallo, kai yad'an lank'wasar kadan yace " Lafiya?wannan kalan fa?" Cikin mamaki ta amsa mai " Yaya Umma ta warke ne?" Kai ya girgiza alamar a'a yace " baki taho mata da ganin bane? Ko samu ne ba'ai ba?" Tace " to ko an gano gaskiya ne?" Kallan rashin fahimta ya mata yace " menene?" Tace " naganka ne kamar abin ya daina damunka, sannan idanunka suna d'auke da confidence." Murmushi taga ya sakar mata yace " ni kaina bansan ya akai ba bayan nayi wata 'yar karamar waya na samu kaina cikin wannan yanayin." Tana kokarin tambayarsa wace irin waya yai jitai yace " shiga ciki, inada abinyi." Kafin tai kokarin magaa ma yayi gaba. Komawa yai b'angarensa yai wanka ya d'auko kaya had'ad'u ya saka, shadda ce bugagiya light brown, yayi kyau sosai da sosai. In har ka ganshi to fa lalai zaka d'auka wani taro na mahimmanci zaije. Haka ya fito hankalinsa kwance, Garzali na ganinsa ya mike ya biyoshi yana tambayarsa inda zasu. Turab yace " Bangaren Umma Babba zamu." Bayan ya shiga ne yaga ragowar matan sarki da kuma matan kannansa a zazzaune suna gulmar abin, da alama dubiya sukazo suka bige da gulma. Ganinsa yasa kowa ya ja bakinsa ya tsuke, Abu Turab fuskarsa d'auke da murmushi mai sanyi ya gaishesu, haka kowa ya dinga amsa gaisuwar a kunyace dan sun tabbata yaji me sukace. Kowa sai dayai mamakin ganin yanda ya d'au kwalliya duba da yanayi da suke ciki. Kwankwasa kofa yai, Khadija ta taso. Tana tura kofar tai ido hudu da Abu Turab, tana rike da kofar take binsa da kallo, kallanta yai kallo na bege sai dai bayanda zaiyi, da sauri ta katse kallon da takemai tace " Barkanka da Zuwa." Ta karasa maganar tare da matsamai ta bashi guri. Magajiya ce a kwance kamar d'azu sai dai Abdulmajid na zaune a kasa yana cin abinci. Murmushi ya saki sannan ya kalli Khadija yace " nima zanci abincin." Da sauri Abdulmajid ya kalleshi dan da ya dauke kai dayaji muryarsa. Khadija ta kalleshi itakanta tayi mamaki sai dai amsa mai tai dato, tai waje. Abu Turab ya kara tura kofar ya shiga bakinsa d'auke da sallama. Abdulmajid ko amsa mai baiyi ba sai kallan mamaki da yake binsa dashi, wannam kwalliyar fa? Abu Turab ya karaso ciki ya zauna gaban Abdulmajid yace " Abdulmajid Barka da war haka." Bai amsa mai ba sai kallan mamaki da yake mai. Shima bai nemi amsar tasa ba Kallan Magajiya yai yace " Har yanzu Umman tamu bata farfad'o ba? Inata tsoro kar muje ta wuce ta can kasan matsalar guba akwai illa ta gaske." Yanda yake maganar kai kace irin Abokinsa ne Abdulmajid d'in. Abu Turab ya kalleshi yace " kayi shiru ko baka neman mata sauki ne?" Abdulmajid ya saki wata dariya ta takaici yace " duk duniya inda wanda zai fi damuwa da ciwon ta ai banaji ya kaini ko?" Jinjina kai ya shiga yi yana cewa " gaskiya ne kuma kayi magana anan, sai dai ni kaina ina mata fatan samun waraka, dan ciwonta duk ya hanani sukuni." Mamaki da takaici ma sam ya hana Abdulmajid magana. Abu Turab ya d'an furzar da wata iska yace " ta ina zanso Ummanmu ta gangara bayan ko bikina da Gimbiya Bilkisu bata gani ba? Sannan Bata ga d'anta akan mulki ba?" Ba shakka wannan kalma ta hawa mulki ta konama Abdulmajid rai, cikin zafin rai ya mike a zuciye ya kaima Turab naushi a kunci, wamda hakan yazo da daidai Khadija ta shigo d'auke da abinci. Tana ganin Abu Turab ya fadi ta saki abincin tai gunsa da gudu. Kallansa tai cikin tsananin kulawa tace " Yaya sannu." Sannan ta d'ago ta kalli Abdulmajid cikin takaicin abinda ya aikata tace " Yaya kana hauka ne? Ta yaya zaka nausheshi?" Idanu Abdulmajid ya zaro yace" Khadija? Ni kike fadawa haka?" Idanunta ya rufe gaba d'aya cikin masifa tace " an fadama, tayaya zaku dinga abu sam ba tunani? Me ya Turab ya maka? Dan yazo duba Umma? Ko dan ana zargin Mahaifiyarsa?" Wannan kururuwar tasa mata dake zaune a falo leko d'akin dan dama Khadija bata ko rufe kofar ba. Abu Turab ne ya sauye fuska zuwa yanayin tausayi yace " Khadija ki bari menene hakan kike yi?Laifine in yaya ya hukunta kaninsa?" Kallansa tai cikin tsananin tausayawa idanunta sun ciciko da kwalla, tace yaya kalli gefen bakinka fa? Ya fashe." Magajiya dake kwance tana jin duk abinda ke faruwa jitai zuciyarsa kamar zata fashe ba shakka sai taci mutuncin yaran nan. Abdulmajid ganin yanda Khadija take ma AbuTurab hawaye yasa ma ya kasa magana, tsawa ya buga mata yace " ke dam gidanku fita daga nan." Kallansa tai fuskarta a turbune cikin tsananin bacin rai, Abu Turab yace " fita mana." Juyawa tai cikin takaici ta nufi kofa, ta na fita tai gida, tana tafe tana hawaye. Magajiya data d'auka Khadija ta fita sannan ba kowa a d'akin kenan sai Abu Turab da Abdulmajid ta mike cikin kunar rai zatai magana. Idanunta ne ya sauka akan matan dake labe jikin kofar d'aki, suma kallanta suke cikin mamaki. " Laaa Magajiya ta farfado." Nan suka shigo ciki, Abdulmajid ya runste ido na takaici sannan ya kalli Abu Turab. Gani yai Abu Turab ya sakar masa murmushin rainin hankali. Mikewa yai yace " Umma kin farfado? Kin ganeni?" Wani irin kallan tsana da takaici takaima Abu Turab dan gaba d'aya ya wargaza mata shirinta ita dataso sai an ma Basira hukunci mai tsanani kafin ta nuna musu ta farfado? Sai an d'auka ta kusa mutuwa tukunna? Kowa murna ne ya bayyana a fuskarsa, Abu Turab ya sosa keya yace " Lalai na yadda Mai maganin nan ya iya bada magani daga bata yanzu har ta warke?" Kallansa sukai cikin mamaki sukace " Yanzu ka kawo mata?" Kai ya d'aga alamar eh sannan ya kalli Abdulmajid yace "ko yaya?" Abdulmajid bakim ciki yasa kawai ya d'aga kai , nan suka fito cikin tsananin farin ciki. Suna fita Magajiya ta kalli Turab kallan Takaici tace " kai bazaka tafi ba? Uban me kake jira kuma?" Fuska ya canza yace " Umma ina kikeso inje bayan yanzu kika farfado ke kanki ai bazaki so d'anki ya barnan ba." Kallansa tai tace " mene?" Yace " abinda kikaji nace, ni ai yanzu tunanin dawowa kusa dake nake yu saboda na kula bakyasan nai nesa dake." A zuciye Abdulmajid ya fizgoshi yace " kai wai kanka ko ya zare ne?" Hannu Abu Turab yasa ya tureshi da karfinsa sannan ya nunashi da yatsa yace " Gargadi ne zan maka shi ka tsaya kajini dakyau, yau inaso ya zama rana ta karshe da zaka kara gigin tabani, wlh duk randa ka sake ina sanarma da duk abinda ya biyo baya kai kuka da kanka." Sannan ya kalli Magajiya yace " Umma ya kike jinki? Kina farin ciki da dawowa duniya da na taimaka miki kikai da wuri?kinga yanzu kafin na fita d'aga nan zance zai kaiwa mutane na maganin dana baki kika warke da kuma wulakantani da Abdulmajid yai dan nazo baki magani." Ya d'an langwab'e kai yace " ya kika gani Umma? Puzzle din ya shiryo ko?" Ta cika taf dan kawai wani kallo takemai, Abdulmajid ma ya gama cika, juyawa yai ya fara tafiya har ya kusa isa kofa sai kuma ya juyo yace " ahhhh ina tayaki murna Umma dan Gimbiya Bilkisu bata yadani ba akan wannan al'amarin, na gode da kara bani karfin gwiwa da kikai na auranta." Yana kai nan yai waje. Magajiya yana fita ta juyo ta kalli Abdulmajid cikin tsawa tace " fita." Waje yai yana fita ta ta kama bargon da aka lulubeta dashi ta matse da karfi kai kace juyemai bakin cikin takeyi. Bangaren Mai Martaba ya nufa. A hanya yaga Jakadiya tana ganinsa ta iso da sauri tace " ikon Allah ashe yarima kaine ka samu mata magani? " Bai tanka mata ba saidai yana tsaye. Tace " hmm gaskiya ne amma nikam yarima banso ka cece ta ba Kana ganin halin datasaka mahaifiyarka a........." Katseta yai yace " Jakadiya, in zaki fadi abu ki fada amma banasan zancen gulma." Ya juya yai gaba. Zance ya yad'o a masarauta akan Abu Turab shine ya nemi mata magani, ba shakka in har mahaifiyarsa ce take neman kasheta bazata taba yarda d'anta ya nemo mata magani ba, wannan labari yasa mutane dayawa sun canza zargin su na cewa Basira ce ta bata gubar nan. Zaune yake a gaban Mai Martaba, Sarki yace " Ka kawomin shaida ne?" Abu Turab yace " a'a sai dai na rage zargin da akema Ummana." Yace " kana tunanin wannan ya isa?" Kai ya girgiza alamar a'a yace " sai dai zai rage zagi da gulmar da ake mata, gaskiya kuma zan bayyanata ko ba yanzu, na kula in nace zan nemi gaskiya yanzu bazan taba samun komai ba dan na tabbata Magajiya ta riga ta gyara komai." Sarki ya jinjina kai yace " na fahimceka." Abu Turab yace " sannan maganar Gimbiya Bilkisu." Ya karasa fadar sunan yana susa keya. Sarki yace " inajinka." " Dama ina ganin zan shiga gunta karshen satin nan." Murmushi mai Martaba ya saki yace " Naji dadi da fahimtarka da kuma amincewarka Allah ya kaimu karshen satin lafiya." Abu Turab yace Ameen. *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *44* Mikewa Magajiya tai daga kan gado cikin tsananin takaicin abinda Turab ya mata, abin haushi jitai baiwarta tana sanar da ita isowar baki dan tayata murnar warkewarta. Haka ta bada umarni suka shigo, kan gado ta koma ta zauna, kowa yazo tayata murna sai ya jinjinama Turab da kokarinsa wannan abu yafi kular da ita, wasu dan gulma ma so suke suji me ya had'a Abu Turab da Abdulmajid. In taji haka sai dai kawai tace " zancen mutane ne kawai amma su ba abinda ya had'a su." Sai wajen Magrib ta samu sauki tai wanka ta sa kaya sannan ta aika a kira mata Hisham. ******* Mairo kuwa bayan ta ba Umma magani nan ta dafa mata abinci ta bata taci, suna zaune labarin abinda ya faru ya isomusu, wannan labari yasa Umma dan jin dama dama. Mairo kuwa jitai Abu Turab ya kara birgeta, ba shakka jinin sarauta ma yawo a jikinsa, ba shakka kwakwalwarsa da basirarsa tana aiki. Sai wajen Magrib ta baro bangaren, Basira nata mata godiya, tana tafe tana murmushi dan ba shakka hankalinta ya kwanta da abinda ya faru. Sam bata kula da shi ba tadai san ta wuce wasu daga gefenta sai dai bata san su waye ba. Tana tafiya kawai taji an cafko hannunta ta baya. A tsorace ta juyo, dan sai da gabanta ya fadi lokacin daya rikota. Kallan mamaki da takaici ta sakar masa, sannan ta kalli hannunta tace " Malam sakeni ko" Yace " ina san magana dake." Tace " To dan kanasan magana dani sai akace ka rike min hannu? Sakeni tun kafin mutane su gamu." Ga mamakita gani tai ya kara kankame hannunta yace " kina tsoron aganmu ne?" Kokarin kwace hannunta ta shiga yi tana cewa " meye hakan?" Abdulmajid ya matso daf da ita kamar zai rungumeta tsoro yasa tai baya, karfi yasa ya rikota, cikin murya mai kama da rad'a yace " zaki biyoni ko sai na rungumeki anan?" Idanu ta zaro ta cigaba da kokarin kwace hannunta. Murmushi ya sakar mata yace " Gimbiyata muje ko?" Ya karasa maganar tare da sakar mata hannu sannan ya nuna mata hanya. Harara ta makamai sannan tai hanyar daya nuna mata. Bangarensa ta nufa da ita a tsakar gida taja ta tsaya tare da hard'e hannayenta. Kallanta yai yace " muje mana." Tace " muje ina kenan?" Da kai ya mata alama da ciki. Harara ta kara makamai tace " d'ad'in abin ni d'in da hankalina bawai a bola ka ganni ina tsince tsince ba." Dariya yai sannan yama masu kula dashi alama da su fita. Suna fita ya fara matsowa inda take, hannu ta d'agamai tace " dakata daga nan Malam ko kuma wlh insama ihu." Yace " Wayyo da naji dadi, ni ai so nake kisamin ma ihun kinga duk abinda za'ayi na riga na mallakeki kenan dan Sarki zai sani auranki saboda rufin asirin mahaifinki." Kallansa tai kallan tsana tace " wai dan Allah in tambayeka? Ana so dole ne?" Sai kuma ta girgiza kai tace " bama haka ya kamata ince ba, dan ba so na kake ba." Yace " Mairo abinda zakice kenan? Wlh tunda nake a duniya kece mace ta farko da zuciyata take so, inaji a raina in har ban aureki ba to tabbas zan shiga wani hali." Baki ta tabe tace " da alama bada gidan sarauta ka dace ba da d'an siyasa ka dace, to ni ko soyayyar ce nace banayi, ko anayi dole?" Kallanta yai sai dai yanzu fuskarsa ta nuna alamun jin haushin kalamanta. Mairo tacigaba " Akwai wanda nake so, banaji akwai wani karin bayani dakake nema daga bakina." Tana fad'ar haka ta juya zata fita. Da karfi ya jawo hijab dinta, jikin bango ya sata, idanunta ne suka firfito. ya kalleta ransa a bace yace " badai wanda kike so d'in a gidan nan yake ba?" Kai ta juyamai bata bashi amsa ba, cikin takaici ya kara cewa " badai wanda kike so sunansa Abu Turab ba?" Juyowa tai ta kalleshi tace " koma wanene wanda nake so d'in banaji yazama dole na sanar dakai." Hannu yakai kamar zai kifa mata mari dan har ta rintse idanunta, sai kuma taji shiru, a hankali ta bud'e idanunta. Kallansa tai, hannunsa ya ajiye sannan yace "Mairo ko duk duniya zasu had'u dan ganin ban aureki ba wlh sai dai kowa yayi ya gaji, amma wlh nine mijinki, inkuma harni Abdulmajid ban aureki ba to wlh duk duniya ba namijin daya isa auranki sai dai in bana dorar kasa." Kafin ta nemo amsar da zata bashi gani tai yayi ciki. Da kallo ta bishi tama rasa me zatace. Haka ta fito jiki a sanyaye. Jakadiya wacce tazo wucewa dan ta dawo daga duba magajiya ta hango Mairo ta fito daga bangaren Abdulmajid, kai ta gyad'a tace " abin harya kai haka?" Dan dama an sha kawo mata gulmar an gansu. ************ Hisham zaune a kilisar Magajiya shi kadai, sai dai kana ganinsa kasan tunani yakeyi. Magajiya ce ta shigo cikin takunta. Ta karaso ta zauna sannan ta kalleshi tace " Yaya na d'auka na sanar dakai umarnin mikewa in har zam shigo guri ko?" Kallanta yai yace " tuba nake Magajiya hankalina ne ya tafi." Girarta ta d'aga sama tace " a kiyaye." A ransa yace " ki jira hawan Abdulmajid mulki, lokacin ne zan kiyaye." Kallansa tai tace " Abu Turab ya wargaza mana shirinmu na hukunta uwarsa." Hisham yace " ni kaina abinnan ya kona mun rai." Murmushi tai tace " Abu Turab! Abu Turab! Lalai na yadda jinin Abdussamad na yawo a jininsa, dole ne in zamuyi shiri na gaba sai mun shirya yanda ya kamata." Kallanta yai sannan yace " ni Magajiya ina ganin kawai mu mikashi kabarinsa." Wani kallo ta bugamai tace " na d'auka na fadama ba kisa ko?" Yace " haka kikeso to muyi ta yin shiri yana wargaza mana?har sai yaushene zamu d'aura Abdulmajid akan mulki? Sai mun tsufa? Ko......" Tsawa ta daka mai tace " YAYA! Kallanta yai tare da yin shiru, tace " kana tunanin ni Magajiya? Ni Gimbiya Magajiya wacce mulki da takama da isa suka bi jinina, kanaso kace ni wannan Magajiyar har wani yaro wanda na girmi uwarsa, wanda aka haifa kwanan nan zaici galaba akaina?" Kasa yai dakai yace " Tuba nake ranki ya dade, ni din wa? Ina na isa ince haka? Kawai dai gani nai mutuwarsa tafi sauki." Idanu ta juya tace" to nace banda kisa, sannan ina tunanin ya kamata Saifullahi ya kawo kudin gaisuwa, in har bamu isa raba Turab da Bilkisu ba dolene mu nemi wanda yakeda mukami a gomnati saboda kudi dan neman taimako nan gaba " Hisham yace " to Ranki ya dade angama." Mikewa yai ya fito, yana fita yabi d'akin da harara yace " wlh zakisan ni kikema tsawa, duk 'ya'yan da kike takama dasu na waye? Daga khadijan har Abdulmajid d'in? Kiyi ki gama wlh sai nima na gasa miki aya a hannu, wa kike dashi? Wa kike dashi da zai taimakeki? Harni zaki dingama tsawa? Harni zaki ce in mike dan zaki shigo?" Kwafa yai sannan yai gaba. ************** Magana ta lafa a gidan Sarauta, yau take juma'a yau kuma Abu Turab ya shirya shida Sabi'u dan zuwa garin na Kano. Mai Martaba yasa ankawo kaya sosai wanda zasu kai gidan. *TEAM ABU TURAB 🤝🏻* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *45* Sabi'u kamar jira yakeyi su shiga mota, suna shiga ya kalli Turab yace " Mutumina wai ta yaya basirar taimakon Magajiya yazo maka? Gaskiya ka birgeni da ka nuna musu kai dasu d'aya ne." Abu Turab ya dafa kafad'arsa yace " baka kawo komai a ranka ba da akacema nine na kawo mata magani?" Cikin rashin damuwa yace " sosai ma, abu d'aya ne yazomin na tabbas kai ba ruwanka." Murmushi Abu Turab Yai yace " then it's okay." Sabi'u yamai kallan mamaki yace " ban gane ba? Ba kai kakai mata magani ba?" Nine mana. Sabi'u yace "yauwa sannan dan Allah inada tambaya, wai wannan yarinyar menene tsakaninku?" "Yarinya? Wacce kenan?" Fara tuki yai yana cewa " yarinyar gidan Waziru wacce da na d'auka ni take kallo, sai daga baya na fahimci kai take kallo tun kafin idanun ka su dawo gari." Kallansa Abu Turab yai sai dai ya kasa cewa komai dan tabbas kasan zuciyarsa begen Khadija yakeyi, dan ranar ya tabbata da b'acin rai ta tafi. Duk yanda yaso ya tsani yarinyar abin yaci tura. Sabi'u ne ya kalleshi, gani yai Abu Turab yai saurin maida kallansa jikin window. Sabi'u yace " yauwa Khadija, na tuno sunan dai sai dana tambaya saboda gulma dake cina." Abu Turab ya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanunsa yace a hankali yace " wacce ya kamata in tsana, sai dai a duk lokacin dana b'ata mata rai nakejin zuciyata na zafi." A hankali yai maganar wanda Sabi'u sam baiji ba yadai san magana yake sai dai bai san jeyake cewa ba, hakan ne yasa yace " me kace?" Abu Turab bai bud'e idanunsa ba yace " bakomai." A zuciyarsa yace " Allah ka cire mata sona, bazan taba addu'a ko dana sani akan san da nake mata ba, dan ko da ace za'a maida hannun agoggo baya na tabbata i will fell for her, i will always pray for her happiness." Sabi'u ganin kamar bayasan magana yasa yad'an yi shiru, can yace " Mutumina ni daga waya ne kuka dinke da Gimbiya Bilkisu ne?" Abu Turab ya bud'e idanunsa yace " kaidai kanasan kaji gulma, koma me mukai menene damuwarka?" Sabi'u yai dariya yace " wlh kayi babban tunani, kun bala'in dacewa da Bilkisu, tun randa na ganta na san ....." "To malamin had'aka na sanjin gulmar soyayyar da bata shafeka ba, wai ni Sabi'u kai yaushe zakai aurene?" Turab ya katse shi daga maganarsa. Sabi'u yai d'an ajiyar zuciya yace " lafinka ne da ka rufe kofa, ai da ka bari an ma kanwa da ba haka ba." Turab ya girgiza kai kawai baice komai ba, sai murmushi kawai dayai. Sun d'anyi niss ba tare da kowa yace komai ba, can kuma Sabi'u ya d'an cigaba da jansa da hira haka jefi jefi. Bayan sun isa garin kano, Mai Martaba Sarkin kano yasa an gyara musu b'angaren da suka zauna waccan karan. Shamaki yazo ya musu iso, sai daya tabbatar an kawo musu komai na bukata sannan ya tafi. ********** A zariya kuwa Magajiya zaune a d'aki, Abdulmajid na kasanta. Cikin muryar takaici take cewa " Abdulmajid wato kai bakada kishi ko? Bakasan darajar kanka ba ko? Kana kallo Abu Turab ya tafi kano gun Gimbiya Bilkisu amma kai ko a jikinka, wai me yasa ne sam kwanan nan baka abinda zai amfaneka?" Fuskar Abdulmajid a had'e yace " Umma to ya kikeso nayi? Kina gani dai Mai Martaba ya fifitashi a kaina, in ba haka ba ta yaya banyi aure ba ya nema ma kanina aure?" Magajiya ta mai wani kallon takaici tace " wannan matsalarsa ce, duk da inada takardar da take na shaidar amincewa da yardarsa akan kaine zaka gajeshi sai dai a koda yaushe zuciyata da hankalina sun kasa kwanciya, nasan Abdussamad sarai zai iya yin yanda takardar zata zama bata da amfani nan gaba, dan haka dole ne mu nemo ma mata kaima wacce take 'yar mulki." Abdulmajid ya d'ago da sauri yace " Umma ki taimaken ki bar zancen wannan auren na 'yar mulki, ni Mairo nake so 'yar gid. ...." Kamin shiru ko sai na kifa ma mari? Kana tunanin na sha guba saboda inji wannan shirman naka ne? Shiru Abdulmajid yai kansa na kasa. Ta cigaba " inasane da duk fa abinda kakeyi a gidan nan, kar in kuskura in kara ji ancemin ma anganka da wannan yarinyar." Abdulmajid ya d'ago ya kalleta idanunsa yai ja yace " amma Umma bakya gani auran Mairo zai taimakeni? Kinfa san yanda Mai Martaba yakesan Barde bakya tunanin zaiji takaicin rabasu?" Kallansa tai sannan tai murmushi tace " Lalai Abdulmajid da gaske san Mairo kakeyi, tunda har tsarani kakeyi, to ni nace banaso." Fuska ya had'e sannan yai kasa da kansa. Wani kallo tamai tace " tashi kaban guri." Mikewa yai ca sauri kamar dama can jira yakeyi. ************* Gimbiya Bilkisu tana zaune b'angaren Fulani, lale aka sa mata tana jiran yaci. Munnira ta shigo da gudu tacemata "UmmaBilkisu ya iso." Sam bata kula da Fulani ba bata kuma kula da Bilkisu dake ta mata alama datai shiru ba. Tana gama fadar haka ta kalli Fulani da sauri ta tsuke bakinta tace "Inna Barka da warhaka." Ta karasa maganar tana zama a gefen Bilkisu. Bilkisu ta harareta sannan tace " Munnira Muhsin d'in ya iso?" Sunan kanin Munnira ne, Munnira ta kalleta alamar rashin fahimta. Bilkisu ta harareta hakan yasa tai saurin cewa " ya iso." Fulani ta saki murmushi tace " Bilkisu ayi maza a cire lale aje a kimtsa kafin Muhsin ya iso, yo dama ai nasan domin Muhsin akai lalan nan." Ta karasa maganar tare da mikewa tai ciki. Bilkisu ta rufe fuska da bayan hannunta dan tasan Mahaifiyar tata ta fahimci me suke nufi. Tana shigewa, Bilkisu ta harari Munnira tace " Ba wakafi ba alamar tsayawa, baki kalkalkal ya iya wassafa zance, wai ke in kina magana bakya kula da mutanen dake zaune ne?" Baki Munnira ta turo tace " Ni murna ne yasa wlh sam ban kula ba." Bilkisu ta kara harararta tace " murna? Dan kina murna sai kisa a gane komai?" Munnira ta turo baki tare da kumburo fuska, Bilkisu tace " na daina ma had'awa dake." Munnira tai kamar zatai kuka, Bilkisu tace " jeki ki duba to kiga ko akwai wani abu da suke bukata." Munnira cikin zakwad'i ta mike tai waje. Bilkisu tai murmushi tare da yin kasa da kanta. ************** Abu Turab yai wanka sunyi sallah sannan suka zauna cin abinci, Sabi'u ne yace " Turab jiya ai munsha hira da Babanmu, na tausaya ma Mahaifinka wlh." Turab ya mai kallan tambaya, sannan yace "name?" Sabi'u yace " ya dade bai samu haihuwa ba, har fa ya fitar da rai da samun haihuwa." Abu Turab ya kalleshi sai dai baice komai ba. Sabi'u ya cigaba " Magajiya fa har kasashen waje ta fita saboda neman magani amma ba labari, sai daga baya kawai akace ciki gareta, kumafa inaji sai da cikin yakai wata 3 sannan inaji itama ta sani." Kallan sa yai cikin rashin kulawa yace " lalai." Sabi'u yace " kasan abin dariya?" Abu Turab ya kalleshi. " duk fa farko wai mutane dayawa basu yarda da cikin ba, harshi Mai Martaban." Abu Turab ya kalleshi yace " ban gane ba." Sabi'u yace " kasan Magajiya kowa yasan yanda takesan ta haihu shi yasa mutane sukai ta zargin ko ta fadane ba wai gaskiya bane." Abu Turab ya mike yace " Lalai, kace sai da ta haihu suka yarda." Yai maganar cikin salon rashin damuwa da kuma gamsuwa da labarin. Sabi'u yasa dariya yace " shiyasa randa aka haifi Abdulmajid ai anyi murna wai kamar ba gobe." Baki Turab ya tabe a ransa yace " ni kuwa sanda aka haifen mutane fiye da rabi bakin ciki sukai, wasu ma tunani hallaka jaririn yaron sukai." Ciki ya shiga dan zuciyarsa ta karaya da tunowa da wahalar da mahaifiyarsa tasha. Kwafa yai daya tuna sharrin da suka ma Mahaifiyarsa, tabbas dole ne ya sa tun a duniya a hukuntashi. Mikewa yai ya d'auko turare ya fesa ya sa hularsa ya d'auko takalmi ya saka, yayi kyau sosai da sosai. Yana fitowa Sabi'u yace " kai Ango, gaskiya yau inaji sai na rufe kofa dan banaji Gimbiya zata barka ka taho, ko dai in aikama da bargonka can ne? Dan banaji ana san rakiya ta." Turab ya kalleshi yace " ba sai ka aikp da bargo ba itama ai tana dashi, d'an rainin hankali, ni taso muje karakani." Sabi'u ya mike yana dariya........ *********** A can gidan Waziri kuwa Khadija tun ranar ko waje bata sake yi ba, kullum tana d'aki, abin duniya ya daneta, takaicinta d'aya yanda zuciyarta ta matso dasan ganin Abu Turab. .. 🤝🏻 *TEAM ABU TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* _Ina 'yan group na fans d'in kungiyar Haske Writer's? Ina kuke 'yan group d'in The Queen Bee? Ga taku sadaukarwar, wannan shafin sadaukarwace gareku....🤝🏻_ *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *46* Jakadiya ce tazo dan kaisu inda aka tanada dan ganawarsu, an kayata gurin sosai, gun kamar rumfa yake, salo da kayata gun da akai duk yanda kaso da karka nuna sai gun ya burgeka. Gashi sai hayaki na turaren wuta ne ke tashi. Sabi'u cikin mamaki yake kallan gun ya kalli Turab wanda shikansa abin ya kayatar dashi yace " Kai gun nan ya burgeni, amma dai ba dan kai aka shirya gun nan ba ko?" Abu Turab ya kalleshi yace " kai kuma sarkin zuga zugi, to kardai ka wuce makad'i da rawa." Sabi'u ya kara shan mamaki ne a sanda yaga yanda aka saka irin carpet da 'yan tumtum a gun sannan aka jera kayan ciye ciye kala kala, ya jinjina kai yace " Turab da alama gaisawa kawai zamuyi da Bilkisu banaji anyi wannan shirin dan mu biyu." Cikin gatse Turab yace " Gaisuwar ma sai ka hakura." Sabi'u yace " ahh lalai Turab abin ba kara? To bari inje waje in tsaya in yaso in kungama ganawar na shigo daga baya mu gaisa." Turab kai kawai ya girgiza, ya juyo da niyyar mai magana yaga bayanan. D'an tsaki yaja kad'an yace " Sabi'u kenan." Zama yai a gun da aka shirya dominsa, irin zama na manyan 'ya'yan Sarki. Sai dayai minti 15 da zama sannan wani dadadan kamshin turare ya bugi hancinsa. Cikin isa da takama take takowa, tafiya takeyi irin ta kasaitatun mata masu mulki. Bai d'ago ya kalleta ba haka itama ko data shigo kallo d'aya ta masa ta cigaba da takunta. Har sai da ta iso gun da zata zauna sannan ya d'ago ya kalleta, itama a lokacin ta kalleshi. Tabbas yarinyar tana da kyau, balle yau datai shiga mai kyau sosai sannan tai kwalliya haka, wani sansanyan murmushi ta sakar masa, shima murmushin ya maida mata, a hankali ta zauna sannan ta umarci bayinta dasu fita. Shiru ne ya ratsa gun kafin cikin muryarta mai dadi tace "Barka da isowa Yarima Turab." Kallanta yai cikin yarda da amincewa yace " Barkanki da isowa Gimbiya Bilkisu." Murmushi tai sannan tace " ka dade a zaune ko?" " Ya zama dole ai in jiraki tunda haka tsarin yake, sannan ba wani dadewa nai ba." Bata ce komai ba sai shiru da suka sakeyi. Kanta na kasa, batai zato ba sai jitai yace " Bilkisu." Yanda ya kira sunanta sai dayasa taji wani yarr a jikinta. D'agowa tai a hankali ta kalleshi idanunta sun canza zuwa salon soyayya, murmushi yai yace " Naji dadi da yanda kika amince da ni." Idanunta ta lumshe sannan ta bud'esu. Yacigaba " ban taba zatan zaki yarda dani ba haka, duba da rashin sani na da kikai, tunda haduwarmu d'aya dake." Nan ma idanunta ta kara lumshewa ta bud'e, yace " A wannan lokacin na sa ma raina tabbas zaki zama mace ta gari a gun duk wanda kika aura, sannan na yaba sosai da yanda kike da tunani." Murmushi ta saki sannan ta maida kanta kasa, hannayenta ta had'e gu d'aya tana murza zoben hannunta da d'aya hannun. Harya d'auka bazatai magana ba sai jiyai tace " I can feel the pain that hide behind ur smile Turab." D'agowa yai ya kalleta sai dai jikinsa yai sanyi, kallansa tai tana murmushi tace " me zakace game da ni?" Kallanta yai kallo mai alamar tambaya. Kanta ta d'an karkatar tace " ka taba sanin Fulani ba ita ta haifen ba?" Idanunsa ne suka fifito alamar mamaki, Tace " bansan ta ba, bansan ya kamanninta suke ba, tana haifata a gun Allah ya mata cikawa." Tausayinta ne yaji ya kamashi. Idanunta ne suka d'an ciciko tace " karka kallan da fuskar tausayi Turab, i am okay, tunda dadewa na cire san ganinta a raina, sannan ina ganin in har na nuna damuwata akan mahaifiyar data haifen ya Fulani wato mahaifiyata ta yanzu zataji?" Turab ya kura mata ido yana nazarin kalamanta. Can yace " U are indeed a good woman, sai dai jin zancen nan naki yasa na fara tunani ban kai qualification na aurenki ba, kin cancanci saurayin da zai soki kamar ransa wanda zai kula dake har rabuwa ta rai ta zo." Hannu tasa ta goge hawayen daya d'an gangaro ta kwarmin idanunta tana murmushi tace " kai bakada confidence na sona kamar haka?" Jitai yayi shiru sai dai yanayin kallan da yake mata ya canza, kallansa tai tace " Me kake nufi?" Yace " Bilkisu inada abubuwa da dama a gabana wanda sai na ga sun kammala ne hankalina zai kwanta, banida lokacin soyayya ko farin ciki sai na ga mutanen nan an musu hukunci." Shiru yai dan tuno abinda aka ma Mahaifiyarsa. Baiyi tsamani ba bai kuma ji alamun tasowarta ba sai gani yai ta mikomai kofi. Kallanta yai idanunsa sunyi ja, sannan ya kalli kofin ruwa ne a ciki alama tamai da kai akan ya amsa. Hannu yasa ya amsa yana murmushi, yace " sry......" Katseshi tai tace " naji dadi." Fuskarta d'auke da murmushi tace " naji dadin yanda ka nunamin, yarda harka ke sanar dani hakan." Kofin ya ajiye bayan ya shanye ruwa ciki yace " Bilkisu i....." Kara katseshi tai tace " is okay, na fahimceka, na kuma san tabbas akwai wahalhalu da kasha ko fansar wani abu da kake san d'auka, sai dai inaso in taimakeka gurin d'aukar wannan fansar, bazan nemi soyayyarka ba har sai ka kammala abinda zakai, sai dai kaima bazan yarda kaso wata ba har zuwa wannan lokacin, in kuwa har da wacce kakeso yanzu inaso ka ajiye soyayyar a iya kacin zuciyarka harsai ka gama aiwatar da abinda zakai, a wannan lokacin ne nakeso ka tambayeni abu d'aya." Idanunsa na kanta tacigaba " inaso ka tambayeni in har banyi dana sanin auranka ba, in har nace ma banyi dana sani ba to inaso ka tirsasa zuciyarka ta soni in har aka kai wannan lokacin baka sona, in kuma har nace nayi dana sani inaso ka tambayeni abinda nakeso a wannan lokacin." Tana gama fad'ar haka ta koma ta zauna sannan ta d'ago ta kalleshi tace " Deal?" Bai san sanda wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba yana murmushi yace " Deal! sannan naji dadi da kalamanki, ba saki a tsarin aure na ko da shi kike tunani a karshe sannan yanda kika amince dani ba tare da kinji abinda nakesan aikatawa ba, zanyi kokari wajen ganin bakiyi dana sanin aurena ba." A tare sukama juna murmushi nan tamai alama da hannu akan yaci abinda aka kawo masa. Tabbas tana bala'in san yaran nan, ko da kuwa zatai dana sani akan auransa bataji zata iya rabuwa dashi a wannan lokacin, sai dai ta d'au alwashin taimaka mai da tayashi d'aukan fansa akan duk wani wanda ya cutar dashi ko da kuwa zatai amfani da karfin mulki na mahaifinta ne. Kamar yasan me take tunani jitai yace " for using you, dole ne ma nemi yafiyarki, sai dai zan nemane in na gama komai, is that okay?" Kai ta jinjina mai alamar eh, ta bishi da kallo na so tsantsa. Bayan sun gama hira ne ya mata sallama sannan ya mike, har ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya tako a hankali zuwa inda take. Awarwaro ya ajiye mata wanda suke cikin gidansu sannan cikin magana mai kama da rad'a yace " da kunyar badawa nakeyi, sai dai bani na siya ba Sabi'u ne ya siyo" Mikewa yai ya fara tafiya, kallansa tai tana murmushi tace " nagode." Bai kara magana ba yai gama yana murmushi. Tabbas Bilkisu ta samu daraja a idanunsa, yanaji zai iya zama da ita a rayuwar aure dan dama ya ma cire burin ganinsa da Khadija daga sanda yaji abinda mahaifinta ya musu ko da santa zai zama ajalinsa bazai taba yarda ya bakanta ran mahaifiyarsa akan 'ya mace ba. *🤝🏻TEAM TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *47* Duk yanda taso ta danne zuciyarta ta kwanta ta kasa, mikewa tai ta zura alkyabbarta sannan ta kalli Mai kula da ita tace " yau kwanan waye?" Kasa tai dakai tace " naki ne ranki ya dade." Magajiya ta d'an d'aga gira sama sannan tace muje inasan ganin me martaba. Tayi mamaki sosai dan rabon da Magajiya taje turakar mai martaba da niyar kwana har ta manta. Haka suka fito suka nufi b'angaren Mai Martaba. Sunje shiga soro bangaren nasa sukaji ana gulmar Abdulmajid da Mairo, d'ayar tace " wlh jakadiya ce ta gansu da idanta yar gidan Barden ta fito daga b'angaren Yariman." Magajiya ta cusa kai suna ganinta suka rude a tsorace suka tsugunna sukace " Barkanki da zuwa Magajiya." Kallansu tai fuskarta dauke da iza tace " ina san dukanku kuje bangarena ku jirani, kada kuma ku manta a tsaye nakeso kuntsaya har na iso." Kara runkufawa sukai suna neman bada hakuri, wani kallo ta musu da ya sa sukaja bakinsu sukai dif. Nan suka karasa ciki. Jakadiya ce ta fito da sauri kana kallanta zaka gane abinci takeci ta taso. Wani banzan kallo Magajiya ta mata, da sauri tai rusuna tana gaisheta. Magajiya bata amsa ba sai alamu da ta mata na ta mata iso. Mikewa tai ta nufi b'angaren Sarki. Rubuce rubuce yake tayi, yana jin sallamar Jakadiya yai saurin had'e takardun nan ya sa a kasan carfet din da yake kai. Jakadiya ta shigo ta gaisheshi sannan ta sanar mai da zuwan Magajiya, alama kawai ya mata da kai akan ta shigo. Magajiya ta shigo ta zauna a inda ta saba zama, sannan ta kalleshi tace " Barka da dare Haikawa." Sarki ya amsa sannan yace " lafiya dai da daddaren nan?" Tace " ina tunanin yau kwanana ne? Banaji na cancanci inji wannan kalmar daga bakinka." "Kwana? A tun wani karnin kenan?" Murmushi tai sannan tace " Turab na garin Kano ko?" Kallan ta yai sai dai bai amsa mata ba, a ransa yace abinda ya kawoki kenan?" Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace " na yaba da d'ana Turab ba shakka yanada hazaka da tunani, ina kuma kara godemai da maganin da ya bani." Sarki ya jinjina kai yace " ai dama hakkin d'a ne ya kula da uwarsa, in har ita uwar tana neman cutar dashi to shi ya kamata ya nuna mata yana santa." Kura mai ido tai dan tasab magana yake gwab'a mata. Isakar ta d'an firzar kadan tace " haka ne, sai dai inaso uban d'an ya cigaba da nunama d'an nan hanyar dazai kula da mahaifiyar tasa." Murmushi Mai Martaba ya saki tare da d'an juya kai kad'an harzaiyi magana sai kuma ya fasa. Kallansa tai dan fuskarta cikin fara'a tace " yaushe zaka yima babban d'anka mata? Dan na tabbatar kanada babban buri akansa shiyasa ka kasa yimai cikin gaggawa " Ya fahimci me takesan cewa hakan yasa yace " ni ai danayake na d'aura buri akansa shiyasa nai tunanin barinki ki nemomai mata." Fuskarta ta tsuke dan tabbas taji haushin maganarsa. Takarda ta d'auko ta taso a hankali tazo ta ajiye mai agabansa. Kallan takardar yai yace " na menene?" Tace " tuni nake maka akan rubutu dakai na cewa Abdulmajid ne zai gajeka." Fuskar shi ya d'aure yace " sai akai yaya kuma?" Kallansa tai tace " ba abinda akai Takawa kawai dai ina tunatar dakai ne, saboda tsaru." "Tsaro? Kina tunanin wannan takardar kad'ai zata iya canza abinda ke zuciyata?" Idanunta ne suka canza ta kalleshi, yace " eh, kina tunanin ita zata canza min ra'ayi? In na ce bani nayi ba fa?" Kallan tsananin mamaki tamai sam tama kasa magana, murmushi ya sakar mata sannan ya kamo hannayenta yana shafa samansu yace " kin tab'a ji nace miki inaso in d'aura Turab akan mulki? Banaso kidinga zargin abinda bakiji daga bakina ba, ko warkewa bakiyi ba kin sa abinda bashida tabbas a ranki." Wani kallo tamai dan tabbas tasan bakar magana yake gaya mata a cukurkud'e, kai ta d'an rankwfo sai tin kuncinsa kamar mai shirin sumbatar sa sannan tace " ina fatan Takawa zai tsaya kan maganarsa." Juyowa yai inda bakinta yake hakan yasa bakinsu suka kusa sumbatar juna, wani lalausan murmushi ya mata yace " banaji na d'auraki akan mai bani shawara." Fuskarta ce ta canza hakan yasa ta mike tsaye, tace " Ranka ya dade zan koma." Alama ya mata da ido akan ga fili ga mai doki. Duk yanda kaso ka gane ranta a b'ace yake bazaka taba ganewa ba saboda fuskarta d'auke take da annashuwa. Jakadiya tana ganinta ta taho da sauri, Magajiya ta kalleta tace " biyoni." Haka kawai ta fada tai gaba. Haka jakadiya ta bita har suka isa b'angarenta ta wuce cikin d'akinta nan ma Jakadiya ta bita. Bayan sun shiga ta juyo tace " rufe kofar." Gaban Jakadiya ne ya fad'i ta tura kofar a hankali ya rage daga ita sai Magajiya. A jikin kofar Jakadiya ta tsaya tana tunanin abin cewa. A hankali Magajiya ta tako har inda take, fuskarta tayi bala'in canzawa zuwa tsananin b'acin rai. Tana zuwa kusa da ita ta d'aga hannu ta zubawa Jakadiya mari. Da yake sam batai zatan hakan ba jin marin yasa hankalinta yayi tsananin tashi. Kanta na kasa sai dai hankalinta ya tashi sannan takaici ya cikata, kamar ta?duk girmanta? A kalla ta tabbata taba Magajiya shekara 4 amma ko kunya ta sharara mata mari? Magajiya ta kalleta sannan ta ce " d'ago." Jakadiya ta d'ago sai dai yanzu ta dake tace " Mai na miki? Banaji nayi wani abu daya cancanci duka." Magajiya ta kanne ido tace " ke harkin isa kidinga yad'a gulma akan Abdulmajid? D'an nawa? Da alama kin gaji da aikinki. " Ran Jakadiya ya kara tunzura jitai tsoron da ke zuciyarta yakau ta kalleta tace " Magajiya d'anki fa kikace?" Gaban Magajiya ne ya fad'i ta juyo da sauri ta kalleta. Jakadiya ta daure tace " sharri na masa? Ki tambayeshi da kanki kiji wannan karan ya fara jan hannun Mairo zuwa b'angaren sa? Sannan maganar aiki da kikeyi ni da kaina zan sauka in lokaci na yayi, ina sanar dake hakan ne domin kar akaini bango dan zan iya sanarma Yarima Turab komai." Tana kai nan ta rusuna tace " Tuba nake Ranki ya dade in bakisa wani sakon zan koma kar Mai Martaba ya nemi ni." Gaba d'aya ma Magajiya ta kasa magana tana tsaye sororo har Jakadiya ta fita. Tana fita Magajiya ta saki wani kara na takaici tace " me yasa komai baya tafiya daidai? Dole ne na saita komai su koma yanda suke." ************* D'agowa Barde yai hankali a tashe ya kalli Abdulmajid yace " Yarima me kake nufi? Abdulmajid yace " Mairo nakeso, kuma zan aura dan gobe nake shirin sanar ma Mai Martaba shiyasa naga ya dace in sanar maka a matsayinka na mahaifinta." Barde cikin rawar murya yace " na kasa fahimtarka ne ai, ta yaya kamar kai zakace kanasan Mairo? Ta yaya? Dan Allah Yarima kabar maganarnan anan." Abdulmajid ya mike tsaye yace " zan jira a waje inaso ka turomin Mairo in ganta kafin na koma." Barde sam ya kasa yin komai tsaya wa yai sororo har Abdulmajid ya fita. Mairo kuwa da yanzun nan Ummanta ta sanar da ita zuwan Abdulmajid ya sa ta shigo falon da gudu ko sallama babu tana shiga ta tsaya ganin Babanta. Jiki a sanyaye tace " Baba!" Kallanta yai a sanyaye yace " me nake ji Mairo?" Kai ta girgiza dasauri tace " wlh Baba ba haka bane, shi kad'ai yake kid'ansa yake rawarsa, kaima kasani Baba wlh ni......" Katseta yai da cewa " Me yasa baki sanar dani ba?" Hawaye na fara zubo mata tana girgiza kai tace " wlh na d'auka shirmansa ne, na kuma d'auka zai hakura tunda nace mai banaso." Mikewa yai yace " kije yana jiranki a waje, mayi magana daga baya, kije in har kinaso komai ya rabu lafiya." Yana kai nan yai waje. Dabas ta zauna a kasa, sai kuma ta mike a zuciye tai waje. ************ Hisham zaune a falo, gefensa matarsa ce sai kuma kasansu Khadija ce zaune kanta na kasa. Hisham ya kalli Khaduja yace " Khadija ba zaki fad'amin me ke damunki ba? Sam kin daina ko magana a gidan nan, na tambayekinko bakida lafiya ne kince ba haka ba, Bazaki sanar dani halin da kike ciki ba? Saifullahin ne bakya so?" Kai ta girgiza tace "bakomai Abba " Ran Hisham ya baci yace " to uban me aka miki kika fito daga gidan Sarki kina kuka?" Khadija ta kalleshi da sauri, sannan ta maida kanta kasa. Ganin batada niyyar magana yasa ya mike cikin takaici ya kalli Mahaifiyar Khadija yace " duk laifin ki ne da bakya kula da 'yar da kika haifa." Ya juya yai waje. 🤝🏻 *TEAM ABU TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *48* Mairo ta dade a tsaye kafin tai waje cikin tsananin b'acin rai. A tsaye ta ganshi yana tsaye ya juya baya a jikin motarsa, hannunsa sanye cikin aljihun rigarsa. Tama rasa dame zata karasa mai. Tsayawa tai kawai tana tunanin wacce kalma ce mai tsananin muni da ya kamata ta fad'amai?" Juyowa yai dan jikinsa ya bashi ana kallansa, a hankali ya tako har inda take, tana tsaye kawai tana kallanshi. Yana zuwa inda take yace " Amince Agareki Matar Abdulmajid ko ince Gimbiya Maryam wacce zata gaji Magajiya." Wani kallo kawai tamai dan ta ma kasa magana, murmushi yai sannan ya d'an kara matsowa yace " Kin rasa bakin magana ko? Na tabbata dama zaki fahimceni, zaki kuma amince da soyayyata." Kallansa tai cikin takaici sai kawai ta tsartar da yawo ta gefensa ta juya zatai ciki. Ransa yakai kololuwa gun baci da sauri ya sha gabanta yace " me kike nufi da abinda kikai? Kyama ta kike?" Fuskarta a had'e tace "Kyamar hallayanka nake, ta yaya zakazo ka samu mahaifina bayan kasan ba sanka nake ba? Ko kana tunanin hakan dakai shine zaisa a auramin kai?" Lab'ansa ya d'an ciza yace "me kika d'auken? Kina tunanin sanar ma mahaifinki danai nayi ne dan in aureki?" Mairo tamai kallan ba haka bane? Gira ya d'aga mata ya na kad'a yatsunsa yace " kin makaro Mairo dan kuwa bazaki taba jin shirina a kan aurenki ba, sai dai na d'au alkawari a zuwa daren yau zakisan matsayina a garin nan zakuma kisan nid'in yaro ne ga Sarki Abdussamad." Yana kaiwa nan ya juya ya shiga mota yai gaba. Da harara ta bishi tace " ba zuwa dare ba inji an shafa fatiha a nan da awa d'aya." Tai ciki. ************ Sabi'e ne ya mike daga kan kujerar daya kwanta ya kalli Sabi'u yace " Me kake tunanin Mai Martaba zai tambayeka?" Abu Turab dake rike da littafin Riyadul Salihin yana dubawa yace " ina na sani? Sannan meye naka na damuwa da abinda bai shafeka ba?" Sabi'u ya d'an yi ajiyar zuciya yace "yau ma tafiya zakai kenan ka barni anan ni kadai? Da alama dai ba amfani a rakiyar nan dana maka." Tsaki yai yace " Kai dai wlh akwai sanjin gulma ni na shiga ciki." Ya mike ya shiga d'aki, Sabi'u ya shafa kansa yace " ahhh Sabi'u ka zama d'an d'aki, ni ba mace ba." Abu Turab kam yana shiga ya kwanta yana tunani. Ta yaya zai warware matsala da kuma hukunta wad'anda suka wulakanta mahaifiyarsa? Suka kuma halaka masa kawunsa? Ina ma bai tab'a sanin Khadija ba a rayuwarsa, ina ma itama muguwace irin iyayenta? Hakan shine zaisa yaji dadin hukuntasu, idanunsa ya runtse da karfi, baisan meyasa ba bayasan Khadija taga wulakantar iyayenta, kuma ya zamana shine silar wulakantarsu wanda takeso tun tana karama. A da auran Bilkisu zaiyi ne saboda ya kuntatawa Magajiya da kuma umarni na sarki, sai dai a yanzu ya cire wannan a ransa zai auri Bilkisu ne saboda rad'in kansa, tunda wacce yakeso bazai taba samu ba to gwara ma ya aminta da wacce ta fahimceshi wacce kuma ya yarda da ita, Mairo fa? Idanunsa ya bud'e daya tuno da ita, wata zazzafar iska ya furzar tabbas dama shi yasan a rayuwarsa ba auran soyayya ba kuma farinciki mai d'orewa ya yanke wannan hukuncin ne tun a sanda Mahaifiyarsa ta sanar dashi komai. Wajen Azahar yai kwalliya sosai dan babbar riga ma ya saka ya saka hula akan sumarsa, yayi kyau sosai da sosai ya saka takalminsa irin mai lankwasan nan na sarauta. A falo ya tada Sabi'u yanata baccinsa, fita yai. A waje yaga dogarawa guda biyu a tsaye da alama sun d'an dade suna jiransa. Suna ganinsa suka matso suka gaidashi. Yace " tun yaushe kuke nan?" D'ayan yai kasa dakai yace " tun d'azu muka zo, Mai Martaba ne yace mu tsaya a waje mu jira har sai ka fito karmu takura maka." Kai ya jinjina kawai yace " muje." Bilkisu ce ta shigo b'angaren Fulani, ta zauna kusa da ita sannan tace " Umma da gaske Baba ne yace miki zasu fita da Turab?" Fulani ta kalli Bilkisu sannan ta kalli Munnira tace " Uwar gulma har kin kai mata rahoto?" Munnira ta b'oye bayan Bilkisu tana dariya. Fulani ta kalli Bilkisu tace " me? Kina tsoron kar a wahalar dashi?" Da sauri Bilkisu tai kasa dakai cikin kunya tace " Umma wlh ba haka nake nufi ba kawai dai abin ya ban mamaki ne ganin baya fita da kowa, dan kosu Yaya ban tab'a ji ance ya fita da wani daga cikinsu ba." Fulani ta murmusa tace " nima d'azu ya aiko a fad'amin sannan bai fad'i inda zasu ba." Bilkisu tai kasa dakai tare da wasa da hannayenta tana murmushin kunya. *************** Su biyu ne zaune a cikin mota a baya sai mai tukasu da dogari d'aya a gabansu. Sai da suka fara tafiya sannan Sarki ya kalli Turab yace " baka tambayi ina zamu ba?" Abu Turab yai kasa dakai yace " tuba nake ranka ya dade amma ina ni ina tambaya?" Sarki yai murmushi yace " a kowani karshen wata ina fitowa inga yanayi da halin da 'yan gari na suke hakan na karamin karfin gwiwa wajen kula da basu hakkinsu." Abu Turab ya kalleshi cikin jin dadi. Sarki ya kamo wannunsa hakan yasa ya kalleshi cikin mamaki, Sarki ya mai murmushi yace " bansan dalili ba ina ganinka naji gamsuwa da yabawa da kai danai, duk da nasan hakan yasamu karfi ne daga mukamin mahaifinka sai dai dukda hakan matsayi da yardar da nake maka dabance." Turab yai kasa dakai yace " Godiya nake." Haka sukai ta shiga gari guri guri kafin daga karshe suje wani katon gida wanda kana ganinsa kasan gida ne na sarauta duba da zanen da ke jiki. Sai da suka shiga ciki, Bafaden nan ya sa makulli ya bud'e gidan, nan suka shiga ciki. Abinci ne kala kala an shirya musu an kuma ajiye da alama dama ajiye wa akai kawai dominsu. Bayan sun zauna Sarki ya kalli Turab yace " Abu Turab!" Kallansa yai sannan yai saurin maida kansa kasa yace " Ganinan Ranka ya dade." Mai Martaba yace " Bilkisu 'yatace wacce duk cikin 'ya'yana nafi kauna, bawai dan wani abu ba sai dan maraicin ta, batasan mahaifiyarta ba, ita kanta mahaifiyarta ko riketa batayi ba Allah ya amshi ranta, hakan yasa nake tsoron auran da ita saboda banasan ta auri wanda bazai kularmin da ita ba, sai dai duk yanda naso ba yanda zanyi tunda mace ce ita." Abu Turab yai kasa dakai, Mai Martaba ya kalleshi yace " Turab ka kularmin da Bilkisu wannan rokone daga bakin mahaifi zuwa wanda zai kasance abokin rayuwa ga 'yarsa ba wai roko bane daga bakin sarki ba." Da sauri Abu Turab ya mike ya d'ora gwiwowinsa a kasa yace " ni ne ya kamata inyi roko inkuma yi godiya, sannan bazan ma alkawarin bata kulawa wanda take samu anan ba, dan in na fad'i haka to tabbas nayi karya sai dai ina zanyi iya kokarina wajen ganin na bata kulawar da ya dace sannan zanyi kokari wajen ganin bakai dana sanin auramin ita ba." Kallo d'aya zakama Sarkin ka tabbatar ya gamsu ya kuma ji dadin kalamansa. Mikewa yai yazo inda Turab yake ya d'agashi sannan ya rike hannayensa yace " Nagode Turab." Nine da godiya. Sarki ya zaunar dashi kusa dashi yace"muci abinci." Cikin kunya haka Turab yake cin abincin. ************ Magajiya ce ta d'au kofin dake hannunta wanda take shan ruwa dashi ta shilo inda Abdulmajid yake, da sauri ya kauce. Idanunta karara suke nuna b'acin rai tace " me? Auran Mairo?" Abdulmajid ya daure yace " Umma kitaimaka ki amince dani inhar kika yarda da hakan nikuma na miki alkawarin hawa mulkin garin nan." Cikin b'acin rai tace " Abdulmajid fita ka bani guri, sannan kar in sake jin maganar nan." Mikewa yai ya fito cikin b'acin rai. Kofar d'akinta ya kalla bayan ya rufe yace " Kiyi hakuri Umma wannan karan zan saba miki, dan auran Mairo shine kadai zai sa in rama yawun da ta tofa a kusa dani." Yai gaba. Zaune ake a fada a cike taf, Abdulmajid ya shigo a zauna a gun zamansa sannan ya gaida Sarki. Tunda ya shigo Barde gabansa ke fad'uwa. Bayan Sarki ya amsa gaisuwarsa sannan Abdulmajid yace " inada magana Ranka ya dade." Nan aka bashi izinin magana. Durkusawa yai alamar roko yace "Ina neman alfarma gun Mai Martaba . Sarki cikin mamaki ya kalleshi yace " ina jinka." Abdulmajid ya kalli Barde wanda yake had'a zufa sannan ya kalli Hisham wanda shi kansa ya kosa yaji da wace magana Abdulmajid yazo. Abdulmajid yai kasa dakai yace " Mairo 'yar gidan Barde nakeso a auramin." Tsananin mamaki ne ya bayyana a idanun Mai Martaba, tashin hankalin dake idanun Hisham kuwa ba'a magana. Sarki ya kalleshi cikin mamaki sannan ya kalli Barde. Galadima ne yai caraf yace " Masha Allah wannan had'in yayi kuwa ranka ya dade, ba shakka wannan had'in zai karfafa zumuncin sarauta." Nan kowa ya fara fad'in gaskiya kam. Sarki ya kalli barde yace " me kace?" Barde ya daure yace " Ai 'ya'yana da ni kaina umarnin ka ne, duk abinda ka yanke shi za'ayi............ Sarki ya d'ago ya kalli Abdulmajid. 🤝🏻 *TEAM ABU TURAB* .🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* _Gareku 'Yan Ayusher Fan Club, wannan Shafin naku ne kacokal...Allah ya bar zumunci_ *49* Sarki ya kalli Abdulmajid sannan ya kara kallan Barde wanda duk jikinsa ya gama mutuwa. Gyaran murya Sarki yai yace " Zan duba maganarka, sannan bana jin hakan dakai ya kamata, Mahaifinta ya kamata ka sanarmawa sannan nima ka samen ka fad'amin hakan ne zai sa musan abinda ya kamata, bawai dan kana d'ana ba zakai tunanin dole namaka duk abinda kake so." Abdulmajid yai kasa dakai yace " Tuba nakeyi." Bayan ya fito, Hisham ya taho shima da sauri. Tsayar dashi yai ta hanyar kiran sunansa. Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalli Hisham. Hisham cikin sauri ya karaso yace " Abdulmajid menene hakan? Wace irin Mairo? Wacece ita da har zaka zo cikin fada kace kanaso a baka?" Abdulmajid ya kalleshi cikin rashin kulawa da abinda ya fad'a yace " wacce nakeso kuma zan aura." Hisham yace " Abdulmajid yar gidan barde ce fa, me kake tunani?" Yace " D'an 'yar gidan Barde ce sai me? Ni wai kawu me yasa kai da Umma bakwa duba halin da nake ciki ne? Me yasa bakwa tausayawa soyayyar da nake mata?" Mamaki ma sam ya hana Hisham magana, Abdulmajid bai jira jin wani abu ba kawai yai gaba. Yana kokarin shiga b'angarensa, wata baiwa daga b'angaren Magajiya ta karaso da gudu tace "Yarima ana kiranka." Nan ya juya zuwa b'angaren Magajiya. A tsaye ya ganta a cikin d'aki yana shiga ya rufe kofa, matsowa tai inda yake ta zuba mai wani mari, jikinsa sai daya amsa, tsoro karara ne ya bayyana a idanunsa dan yanda yaga bacin rai karara a idanunta. A hankali ya zauna a inda ya fara zama kansa na, juyowa tai cikin tsananin takaici tace "Abdulmajid kai harka isa har ka isa ince karkai abu kayi? In haifeka a cikina kace kana neman kafi karfina? To bari kaji tunda nake a duniya duk wani buri nawa ba wanda ban cikashi ba sai abu d'aya wanda shikad'ai ne nake danasanin gangancin danai, daga shi kuma bana bukatar wani danasani a rayuwata, baka isa kai ka sani bakin ciki ba....." Katseta yai yace " Umma yanzu menene aibun auren Mairo?" "Aibu? Shi kake san ji? Idan har ba so kakeyi rayuwarta ta shiga cikin kunci ba kai gaggawar janye maganar nan." Yace " indai har a kusa dani zatai kuncin nikam banajin zai damen." Kallansa tai cikin tsananin mamaki tace " Abdulmajid." Kasa yai da kansa kawai baice komai ba. Khadija ce tai sallama bata jira ba ta shigo da sauri ciki. Magajiya ta kalleta, gaban Abdulmajid tazo ta tsuguna tace " yaya yanzun nan Umma ta aikoni in kawo sako naji ana zancen kana san auran Mairo, Yaya Meke faruwa?" Kansa ya kawar gefe, hawaye ne ya fara zubo mata ta shiga girgiza kai tana cewa " yaya please kabar maganarnan, Mairo itace Ya Turab yake so ta yaya zaku zama kune sanadiyyar kuntata masa rayuwa, na sani ba santa kakeyi ba, in har ni bazan zauna kusa dashi ba dan Allah yaya kabar ta ta zauna gun Ya Turab......." Kuka ne yaci karfin ta mamaki ne karara ya bayyana a idanun su duka su biyun, Magajiya ta juyo tace " Turab ne yake san wa? Mairo?" Khadija kuka kawai takeyi tanacewa "Dan Allah yaya ka janye maganarnan." Abdulmajid ya buga mata wani harara yace " Khadija kina nufin saboda farincikin Turab kinaso ni in kuntata? Farincikinsa ya fiye miki?" Kallansa tai tana girgiza kai tace " ba haka bane yaya, inka duba rayuwarsa zakaga abin tausayi ne shi, yaushe ya fara gani? Sannan waye gareshi a kusa dashi?" Jitai an fincikota a tsorace ta d'ago Mahaifinta ta gani, Magajiya na tsaya tana mamakin abinda takeji. Hisham yace " Akan wa kike kuka?" Kallansa tai sai dai batace komai ba, cikin fad'a ya kara cewa " Waccan karan ma akansa kike kuka? Akansa kika daina magana? Akansa ne kike neman ture auran Saifullahi?" Hawaye ne kawai ke zubo mata sai kai kawai da take girgizawa. Hannu ya d'aga kamar zai daketa sai kuma ya fasa, ya kalleta cikin takaici yace " Kin bani kunya Khadija......" "Ya isa hakanan, Khadija wuce ki shiga cikin d'akina maganar ta isa haka." Magajiya tai maganar cikin kakkausar murya. Khadija a hankali ta shiga ciki jikinta duk yai sanyi, Hisham kam bakin ciki yasa ko motsi ya kasa, yana bala'in san yarinyar. Magajiya ta kalli Hisham da Abdulmajid tace " ku bani guri zan nemeku anjima." Nan kowa ya mike. Zama tai tare da had'e hannayenta guri d'aya ta matse su tai shiru. " Turab nasan Mairo? Abdulmajid na san Mairo? Sannan Khadija nasan Turab?" Dolene ta fito da hanyar dazaisa komai ya warwarw mata. *********** Mairo ta fito daga wanka tana shafa mai, mahaifiyarta ta shigo tace " kiyi sauri kisa kaya mahaifinki na nemanki." Nan ta zura bakar doguwar riga bayan ta gama kintsawa. Mayafin rigar ta yana a kanta ta fito zuwa falonsa. A zaune ta ganshi yayi shiru, jin sallamarta ne yasa ya dawo daga tunanin dayake yi. Zama tai sannan ta kara gaidashi. Kallanta yai, idanunsa duk sun canza yace " Mairo, Abdulmajid ya sanar ma Sarki yana san auranki." Idanunta ta zaro cikin tsananin tashin hankali tace " aure? Ni da shi?" Barde ya kakaro murmushi yace " Kinfi kowa sanin kuma ban isa bijirewa umarnin sarki ba." Ya mike yai cikin d'aki, da alama ya shiga ne dan kar yaji tausayin 'yar tasa. Mairo tai shiru a zaune dan tama rasa ta inda zata fara. Mikewa naga tayi da sauri ta zura takalminta tayi waje. Tafiya take zuwa gidan Sarki, tana tafe tana cewa " Ya Turab ya zanyi? Menene mafita?" Tunda ta shigo gidan ake gulmarta. B'angarensa ta nufa a waje taga Garzali, da sauri tace " Ya Turab fa?" Garzali yace " Yana kano." Taku biyu tai zuwa baya dan ji tai kamar an kwad'a mata abu, cikin rikicewa ta nufi b'angaren Basira. A zaune ta ganta tana shan fura ita kanta yau bata samu cin abinciba sai yanzu da yamman nan. Basira tana ganinta tausayinta ya kamata, Mairo ta karaso da sauri ta zube gabanta tace " Umma ki taimaken." Basira ta kalleta cikin tsananin kulawa tace " Mairo." Mairo idanunta suka ciciko tace " ba sona yake ba, Umma haka ake so? Ta karfi? Umma kinsan halayen mutumin nan, ni na hakura da Ya Turab dan da alama dama naso kaina dayawa ne, Umma amma ba Abdulmajid ba, dan Allah Umma ki tai......." Idanu ta runtse dan ji take kamar ta kwalla kara na bakin ciki. Basira ta matso da ita ta rungumeta tana lallashinta, kuka sosai Mairo takeyi tana cewa " Umma ba Abdulmajid dan Allah, naji aban kowanenen amma bandashi." *************** A can garin kano kuwa bayan sun dawo a kofar shiga Mai Martaba ya kalli Turab yace " Inka koma wannan karan kasa a turo domin sa rana dan ba'asan masarauta da jan magana ba." Turab yace " Godiya nake Mai Martaba." Bayan mai tuka motar yai parking, wani bafade ne yazo da gudu ya bud'e sannan ya rad'a mai magana a kunne." Murmushi naga yayi sannan ya kalli Abu Turab yace " Turab muje kaima kwa gaisa da Minister." Abu Turab ya kalleshi sai dai baiyi magana ba yabi bayansa. Wani bangare aka kaisu, bangaren ya tsaru sosai wasu maza ne guda biyu a zaune kana ganinsu kaga uba da d'a duba da yanayin kamar su. Suna ganin Mai Martaba suka mike, uban na ta murmushin jin dadi. Sarki ma cikin fara'a ya kalleshi yace "Malam Haruna yau kaine da kanka?" Wanda ya kira da Haruna ya karaso suka gaisa, yace " Tuba nake Ranka ya dade da alama fishi ake dani." Zama Sarki yai sannan suka kara gaisawa. Yaran nasa ne ya matso ya gaisheshi. Shima Abu Turab ya gaida mutum. Haruna ya kalli Sarki yace " Ga d'ana Saifullahi, kullum ina cewa zan kawoshi ya gaidakai sai yau Allah yai." Saifullahi ya kara gaidashi. Sarki yace " naji dadi, ni kuma wannan sirikina ne." Mamaki ya kama Haruna ya kara kallan Turab. Sarki yace " d'an Sarkin Zazzau ne, Abu Turab." Fara'a ce ta kara bayana a fuskar Haruna, Saifullahi ya kalli Abu Turab." Haruna ya kalli Turab yace " Kace na ganka kai tun yanzu kafin mu had'a zuri'a." Turab yamai kallan mamaki da rashin fahimta. Haruna ya kalli sarki yace " ai Saifullahi shine zai auri yar gidan Waziri sunanta Khadija." Wani mugun fad'uwa gabasa yai da sauri ya d'ago ya kalli Saifullahi, wanda shima kallansa yakeyi. Idanu suka kafema juna. Sarki shikam bai kula dasu ba ya kalli Haruna yace " lalai Minister na tayaka murna Allah ya sanya alkairi." Yanayin kallan da Abu Turab yakema Saif yasa Saifullahi yace " Lafiya?" Turab yai saurin kauda kai yace " ba komai." Kallan mamaki Saif ya bishi dashi, dan ya kasa fahimtar ma'anar kallan da yake mai. 🤝🏻 *TEAM ABU TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *50* Mikewa Turab yai ya kalli Mai Martaba sannan yai kasa da Kansas yace " bari na baku guri." Ya fad'a kansa na kasa. Sarki ya jinjina kai yana murmusawa yace " To Turab kaje ka huta." Gaida Mahaifin Saif yai sannan ya musu sallama yai waje. Jiyai ance Ina magana. Tsayawa yai tare da juyowa dan duba mai magana. Saif ya gani ya ya tsaye daga kan baranda, saukwa yai ya nufoshi. Tunda ya taho Turab yake binsa da kallo ni kaina bansan me yake aiyanawa a ransa na. Saif ya karaso sannan ya saki fuska yace " Naga kamar bai dace mu rabuba ba tare da sanin junan mu ba, duba da yanayin nan gaba zamu zama dangin juna?" "Dangi?" Abu Turab yai fad'a sannan ya murmusa yace " Yama kace sunan?" Saif. Turab ya jinjina kai yace "Saifullahi, am sai dai kayi mantuwa Abdulmajid zaka fadawa haka bani ba." Saif ya kalli Turab tabbas yaji haushin maganarsa yace " Amma na d'auka......" Turab ya katseshi yace "Allah ya sanya alkairi." ya juya ya tafi, dangin juna? Ya kara maimaita Kalmar tare da jan tsaki yace " kama rainamin hankali." Yana shiga masaukinsu Sabi'u ya taso saga zaunen da yake yace " Ka dawu? Sirikin mu." Turab ya bugamai wani kallo yace " wai ni har wani d'an rainin hankali zai kalla yace wai mun kusa zama dangin juna? Ha ha amma ya gama rainamin hankali ya karasa maganar tare da zama. Sabi'u cikin mamaki ya kalleshi yace " Nikam kai da waye?" Turab yaja tsaki yace " wai wani Saif, ko Khadija yakeso ko Khadija zai aura ni ban ma sani ba." Sabi'u ya tuntsure da dariya yace " Turab? Kaine?" Kallansa Turab yai baice komai ba sai dai takaicin dariyar yakeyi. Sabi'u ya matso kusa dashi yace " Khadijan ka?" "Eh ma......." Sai kuma yai shiru sannan yai saurin mikewa tsaye yace " wace irin banzar tambaya ce wannan, ban gane Khadija ta ba? Wai kai Sabi'u me yasa ka iya abin haushi ne?" Sabi'u yace "ohhh abin haushi? Sai naga kamar kishi ne ya ciwoka kake bukatar tausa." Turab ya bugamai wani banzan kallo yace " kishi?" Mtsw kai fa sai a hankali wlh. Ya fad'a tare da shigewa d'aki yanaji Sabi'u na cewa " karka manta anjima zakaje gaida Fulani mijin Gimbiya " Yana shiga d'aki ya zauna a bakin gado yace " me ya sameni? Why am i acting like this?" Sai kuma ya nuna kansa cikin mamaki yace " don't tell me kishi nake?" Kai ya girgiza da sauri yace " inaa tayaya ma zanyi kishi akan wacce take zuri'ar makiyana?" Yin baya yai ya kwanta akan gado, yana takaicin wannan abu, inama shikam baisan Khadija ba a rayuwarsa?" ********* A can Zariya kuwa Magajiya ta rasa abinda ya kamata tai ta dade tana tunani kafin daga baya ta wuce cikin d'akinta. A zaune a kasa ta taradda Khadija kana ganinta kasan tana cikin wani hali. Magajiya ta karaso kusa da ita tace "Mamana mike." Ta fad'a tare da miko mata hannu. A hankali Khadija ta tashi sannan ta zaunar da ita a bakin gado itama ta zauna a kusa da ita. Hannayenta ta riko tace " Khadija san Abu Turab kike?" D'agowa tai da sauri ta zubama Magajiya idanunta wad'anda suka cika fal da hawaye, sai dai bata iya bata amsa ba. Magajiya tai murmushi sannan tace " kin san waye Abu Turab?" Kallan mamaki ta mata dan bata fahimci me take nufi ba. Magajiya ta d'anyi ajiyar zuciya tace " Khadija baki san waye yaran nan ba, wannan maciji ne wanda dafinsa keda tsananin zafi, kinsan yaron nan idanunsa biyu amma yake nuna makaho ne? Kinsan ya tsaneni da mahaifinki amma yake nuna miki so dan kawai yai amfani da ke? Mune jininke, mu kad'ai ne muka san darajarki bazamu taba cutar dake ba." Ganin Khadija ta zare hannunsa daga cikin nata yasa ta tsaya da maganar tana binta da kallo. Sai kuma ta mike sannan tai murmushi tace " Umma Babba bazan ce nasan Ya Turab ba tunda ba tare mukai rayuwa dashi ba sai dai namanta ban fad'a miki kalma d'aya ba, nice nakesan Ya Turab ba shine yakeso na ba." Ta juya tana tafe kamar wacce zata fad'i dan ba shakka kalaman Magajiya sun so kawo mata rud'u cikin kwakwalwarta, maciji?yana gani?amfani da ita? Ba shakka ba dan tayi saurin katseta ba da alama da sai ta canza mata ra'ayi a xuciyarta. Kallan kofar data rufo ta Magajiya tai a ranta tace " Umma Babba please don't disappoint me anymore." Abdulmajid ta gani a tsaye a waje da alama ma jiranta yakeyi. Yi tai kamar bata ganshi ba ta fara tafiya. Da karfi ya finciko hijab dinta yace " Wato ke Abu Turab ya fi miki ni ko? In taimaka in barma Turab Mairo? Ke meyasa bakida hankali ne?" Khadija ta kalleshi idanunta sunyi raurau tace " Yaya me ka nema ka rasa a duniyan nan?" Kallanta yai baice komai ba. Tace " kanada komai na rayuwa, matsayi,iyaye, lafiya, girmamawa, me ka nema ka rasa?" Ta share hawayenta tacigaba " Ya Turab na san yarinyar nan, kai ko tausayin sa bakayi?" Kallanta kawai yake yama kasa magana, ta share hawayenta sannan tace " ku kanku kunki kyale bawan Allahn nan, bakin cikin abinda kuke mai shine na tabbata dalilin dayasa ko ganina baisan yi....." Hawaye ne suka nemi fin karfinta, da sauri ta juya ta fara tafiya. Abdulmajid baki kawai ya saki yake kallan mamaki. Shi Khadija takema wannan banzan sharhin? ********* Mairo kuwa baya ta gama fad'an kalamanta Baseera ta jawota jikinta tana lalashi. Tace " Mairo dama kina san Turab? Na dade ina hasashen haka sai dai wani sa'in ina tunanin rad'in kainane yasa nake ganin haka ba wai kece kike sanshi ba, ki kwantar da hankalinki ki koma gida, tunda har nasan abinda ke ranki ni kuma xanyi iya kokarina naga komai ya dawo daidai." Mairo ta d'ago sai dai batace komai ba. Hisham na fita ya wuce gida ransa a b'ace a tsakar gida yaga mahaifiyar Khadija a zaune. Rufeta kawai yai da fad'a. " Aikin banza ace tarbiya wannan kin kasama 'yarki, inba rashin tsaro ba har yaushe ma kika bari yarinyar nan ta sakankance da wani can sokon yaro, yaron da zuwansa doron kasa shine abu mafi muni da ya taba faruwa a rayuwata, to wlh inma zaki sa Khadija ta cire wannan shirman a ranta kiyi dan wlh in har na sake kamata tana kuka akan yaron can wlh abinda zan miki sai kinsha mamaki." Bai jira ta tofa komai ba yai gaba fuuuu....... 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *51* Zaune yake a cikin wani had'ad'an gun hutawa, a hankali yana cin inibin dake gabansa sannan yana duba littafin hannunsa, lumshe ido yake yi saboda yanda yakejin dadin rayuwa, cikinsa ne yaji ya murd'a nan fa wani azababben ciwo mai tada hankali ya rutsashi, baisan sanda ya durkuso kasa ba yana murkususu saboda azaba, idannan nasa yayi jaa kamar garwashi, tsananin tashin hankali da rad'adin da ya ke ciki. Jiyai an sakar masa wata irin dariya na keta da sauri ya d'ago dan ganin wani mugun ne wannan ba taimako sai dariya? Magajiya ce cikin wani had'ad'an shiga tayi kwalliya sosai, dariya take sosai. Abdulmajid ne ya fito daga bayanta shima yana dariya harda kyakya tawa. D'ayan gefen kuma Hisham ne ya fito shima dariya yakeyi sosai, nuna shi suka shiga yi suna dariya. Basira ya gani a kasansu a kwance wanda baisan ko tana raye ba ko ta mutu. Sannan Abdulmajid yana rike da igiya yana jan wata yarinya a kasa, kallan yarinyar yai ga mamakinsa sai yaga Mairo. Kirjinsa ne ya d'au zafi, Khadija ce ta taho da gudu gunsa tana kuka kamar ranta zai fita, da sauri Hisham yasa hannu ya fizgota. Jiyai gaba d'aya ya kasa numfashi da sauri ya bud'e idanunsa. Cikin tashin hankali yake kallan d'akin, ga zufa da yai sharkaf. Zama yai cikin tashin hankali yana addu'oi, ba shakka wannan mafarkin ya tsoratashi, shi yasa baccin yamma bashida kyau. Mikewa yai ya sauko daga kan gadon, sai dai jiyai kafafunsa na rawa. Gado ya dafa tare da runtse idanunsa. Ya dade a haka kafin ya daure ya shiga ban d'aki. Bayan ya fito ne ya zauna a bakin gado, ba shakka mafarkin ya bayyana karara kamar gaske. Ga kansa na mai wani azababben ciwo. Sabi'u ne ya leko yace " Ranka ya dade ka tashi? Wai daga shigowa sai in tadda kai kana bacci?" Turab ya kalleshi kawai baice komai ba. Sabi'u yacigaba " dama aiko wa akai in anyi magrib zakaje ku gaisa da Fulani." "Gobe da sassafe zamu koma gida." Abinda Sabi'u yaji ya fad'a kenan. Mamaki ya kama Sabi'u da sauri ya karaso cikin d'akin yace " Mutumina lafiya?" Turab ya kalleshi, ganin yanda idanunsa sukai ja ya matso da sauri yace " Yarima Lafiya?" Turab ya mike yazo kusa dashi kawai ya dafa kafad'arsa sannan ya wuce. Waje ya fito ya tsaya yana kallan sararin samaniya, me yasa yakejinsa haka? Bayan Magrib jakadiya tazo ta raja Abu Turab gun Fulani, sosai ta karbeshi sannan itama ta rokeshi akan rikon Bilkisu, irin amsar dayaba Mai Martaba ita ya bata. Haka ya taso cikin gamsuwa da yanda sukesan 'yar tasu. Munnira ce ta biyoshi da sauri ta mikamau wata takarda. Amsar takardar yai ya kalleta yace " ta menene?" Munnira tai dariya tace " UmmaBilkisu ce tace in baka." Amsa yai yana cewa " Yau Umman taki rowar ganinta take min?" Munnira tace " zaka ganta gobe ai." Bud'e takardar yai yana cewa "Gobe zan tafi da safe." Kallan mamaki tamai tace " Amma UmmaBilkisu vata sani ba?" Kai ya d'aga yace " nima dazun na yanke shawarar haka, amma zan dawo ko zuwa sati biyu ne." Duba takardar yai, number waya ce ta landline a jiki a kasa tasa, inka samu time ka nemin a layin nan." Murmushi yai ya kalli Munnira yace "kice mata nagode, dama nayi tunanin tambayarta." Ya juya yai gaba *********** Washegari. A zariya Basira tayi shiru tana tunanin mafita, ba shakka ko d'anta bazai auri Mairo ba bazata taba bari Abdulmajid ya aureta ba. Mikewa tai ta kali Lantana tace "Lantana muje in duba Hajiya sannan muje gun Magajiya." Mamaki ne ya kama Lantana sai dai bata ce komai ba. Sunje gun Hajiya jikinta kam kamar kullum ba sauki sam, dan ko maganarta dama ba ganewa akeyi ba. Yau kam jikin ya d'anyi sauki. Mai kula da ita suka tarar tana bata magani, sai dai tana ganinsu ta daina bada maganin ta mike da sauri ta rufe maganin ta d'auka. Basira ta kalleta tace " ta gama shan maganin ne?" Dan yanayin yanda yarinyar tai yasa ta kasa fahimtar hakan. Cikin rawar murya tace " ta gama." Ta karasa magana tare da fita. Basira ta zauna kusa da ita sannan ta gaisheta. Kai ta d'aga mata, Basira tai murmushi tace " yau kam naga jikin da sauki." Basira gani tai ta miko mata hannu alamar ta riketa. Nan ta riketa tace " Hajiya." Kokarin magana takeyi sai dai ta kasa da alama akwai abinda takesan fad'a. Kunnenta ta matso dashi tace " Hajiya menene? Akwai abinda kike so ne?" Ma ma ma ga....... Basira tace " maga me?" Hajiya ta kara daurewa tace " Abbbbb......" Da sauri wannan yarinyar ta shigo tace " Hajiya a kawo miki ruwa?" Yunkuri takeyi da alama akwai abinda takesan ta fad'a. Basira ganin yanda taketa keta zufa tace " Hajiya ki barshi sanda kika ji dama in har abun daya kamata ne sai ki fad'amin." Idanu ta runtse na takaicin kasa magana da take, gashi dama ko zama bata iyayi. Sun dade kafin su fito, Hajiya tai shiru tana tunanin abinda ya faru shekaru hud'u da suka wuce. Taya zatai ta sanar da d'anta abinda ke faruwa? Tundaga ranar da ta mata magana akan abin a ranar ta fara rashin lafiya wanda har yau ciwo sai gaba yake baya raguwa. Kowa ya d'auka tsufa ce ta sata wannan rashin lafiyar sai dai ita tasan ba haka bane. B'angaren Magajiya suka nufa. Bayan ta zauna a kilisarta ne, aka shiga ciki dan sanar da Magajiya zuwan Basira. Ta dade dan takai akalla minti 20 kafin ta fito. Tafiyarta take cikin takama, tazo ta zauna cikin isa sannan ta kalli Basira a wulakance. Basira ta gaisheta sannan tace " Zuwa nai muyi wata magana." Magajiya ta kalleta tace " inajinki, sannan inaso ki hanzarta saboda inada abinyi." Basira tai shiru tana tunani kafin tace " Me kike tunani game da auran Abdulmajid da Mairo?" Magajiya ta zuba mata ido sai dai batace komai ba. Basira tacigaba " Zuwa nai inji ra'ayinki akan auran......." " nikam a iya sanin kwakwalwata ban ji ance kin sake haihuwa ba, ko ince banji ance kina d'auke da cikin wata yarinya Mairo ba, dan haka banaji kina da hakki akan auranta." Basira ta d'ago cikin mamaki tace " ai ba sai ka haifi mutum ba kake da hakki akansa ba Ranki ya dade." Magajiya tai wani banzan murmushi tace " ko? To in haka ne nima bari nai iko da Abu Turab wanda ban haifa ba, inaso kice ya dawo daga garin kano sannan ya janye auren Bilkisu ya auri Mairo wacce kike so." Tsananin mamaki ya hana Basira yin magana, ta kalleta tace " ban gane......" "Kurma ce ke? Ko kuwa fahimtace baki dashi?" Sai kuma tai wani lalausan murmushi tace " ko dayake wacce akai rufa rufa agun auranta saboda rashin matsayinta da abinda ta aikata a baya banaji tanada inda zatai tunani a kwakwalwarta." Gaban Basira ne ya fad'i tama rasa me zatace. " kin kyauta da kika zo, dama ko bakizo ba zan aika kizo, inhar kinaso in rufe sirrin da aka fad'amin ki tabbatar kin sa d'anki ya janye auran Bilkisu dan d'an sarki sai 'yar sarki, Abdulmajid zai auri Bilkisu shikuma d'anki Turab ya auri Mairo kinga in akai hakan komai yazo da sauki kenan, kema kinsamu abinda kikeso kamar ni." Basira tai dauriya tace " me kikaji akaina? Banaji inada wani abu da zan......" "Hmmm kin manta ba'a cikakiya aka aureki ba?" Tashin hankali ne karara ya bayyana a idanun Basira, ta daure tace " ban....." Wata irin dariya Magajiya ta saki ta kalleta tace " Basira sunana Magajiya." Basira tai shiru sai jikinta dake tsuma. Magajiya ta mike ta zo inda take ta tsugunna tare da dafata tace " Me yasa banyi tunanin komai ba da? Sai dai karki damu sirrinki zan tayaki ajiyewa in har kika sa d'anki ya janye maganar auran Gimbiya, dan ko za'a mutu bazan taba bari ya aureta ba." Ta karkad'e mata kafada tai gaba. Magajiya tana shiga d'aki tai wani mugun murmushi tace " lalai da gaske ne." Tunowa tai jiya bayan ta rasa mafita kawai ta kira Hisham tace ya kira abokinsa dake garin Daura, yasa yamai bincike akan Basira, ba shakka sai yanzu ta fara tunanin tabbas haka kawai sarki bazai auri Basira a b'oyeba, duk da batai tunanin wannan matsalar ba tadai san akwai wani abun. Basira kam da kyar ta mike jikinta na rawa ta fito. 🤝🏻 *ABU TURAB TEAM* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* _AyI hakuri da Jina shiru da kukai kwana biyu, azumi nakeyi_🙈 *52* Abu Turab dama ya sanar da Fulani zancen tafiyarsa, nan sukai sallama da mai martaba cikin jin dadi dan bai tambayeshi dalilin tafiyarsa ba. Sai da suka gama shiryawa tsaf sannan ya nemi ganin Bilkisu dan yin sallama. Itakam Bilkisu tunda Munnira ta sanar da ita take tsaye tana zagaye d'akin, meke faruwa? abinda ke mata yawo kenan har mai kula da ita ta sanar da ita neman da Turab yake mata. Cikin sauri ta duba fuskarta a jikin madubi sannan ta nemi fita, harta kai kofa sai kuma ta tsaya, taja wani dogon numfashi sannan ta kara neman nutsuwarta kafin ta fito. Yana zaune yayi shiru ta shigo da sallama, dagowa yai tare da amsawa yana kallanta. Sai data zauna sannan ta gaisheshi tare da cewa " Lafiya dai ko?" kallanta yai yace " nikaina abinda nake san sani kenan." Kallan mamaki tamai sannan ta d'ora da cewa " badai wani abu mara kyau bane ya faru ko?" Hannunsa ya sa yad'an shafi saman goshinsa sannan yace " Ina ji nane ba dadi, inajin kamar da wata babbar matsala datake faruwa a gida." Kallansa tai sannan ta d'anyi murmushi tace " Insha Allah ba abinda ya faru sai alkairi, sannan in har wani abu mara kyau ya faru ko ka fuskanci kana cikin tsaka mai wuya ina rokonka da karka yanke hukuncin da nan gaba zakai dana sani, ka jinkirta yanke hukunci har sai zuciyarka ta aminta da wannan hukuncin." Murmushi ya sakar mata yace " Nagode." Itama murmushi tamai sannan ta sunkuyar da kanta kasa. Mikewa yai yace " zan wuce." D'agowa tai ta kuramai ido sai dai batace komai ba, a hankali ya tako zuwa inda take sannan ya tsuguna a gabanta tare da zaro abu a aljihu, ya nuna mata takardar databa Munnira na layin waya, yana murmushi yace " na gani na kuma gode." Kallansa tai sannan ta saki wani lalausan murmushi. Mikewa yai yace " kafin in dawo maybe an tsaida rana." Da sauri ta maida kanta kasa, wata yar karamar dariya yai wacce batada sauti yace " wannan d'in kunya ce?" D'agowa tai ta harareshi tace " dama haka ake yi? da kanka ya kamata ka fad'amin zancen?" Dariya ya sakeyi yace "au haka ne? to goge abinda na fad'a a zuciyarki inyaso sai a sake sabon la le." Murmushi tamai tare da juya kanta gefe tace " na goge." cikin zolaya yace " nikam me ma nace?" Hararar sa ta sakeyi sannan ta maida kanta kasa tana murmushi, ashe yanada side na zolaya, farkon ganinsa ta d'auka mutum ne wanda bayasan wasa sam, sai dai yanzu ta fara tunanin tsauri da jinin mulki ne ya sashi haka. Dagowa tai ta kalleshi sai dai batace komai ba. Murmushi ya mata sannan yace " zan kira." kai ta d'agamai, yace " zan wuce" nan ma kai ta d'agamai. Lab'ansa ya d'an hade sannan yace " nagode." Murmushi tamai, nan ya juya yai hanayar fita. Sai dayaje kofa yaji muryarta a hankali tace " Allah ya kiyaye hanya." Juyowa yai yana murmushi yace " Ameen." Nan ya juya ya fita, yana zuwa ya tadda Sabi'u ya sa an fita da komai, nan suka kama hanyar gida. Basira kam abin duniya duk ya gama damunta tama rasa ina zata saka kanta, da farko tayi tunanin fad'ama Sarki sai dai tace me? wad'annan tunanin sun hanata sakat, fatanta kawai d'anta ya dawo, ta sanar dashi hukuncin magajiya. Magajiya kam tana zaune a kilisarta tana kurb'an shayi wanda yaji kayan kamshi, tana sha tana lumshe ido, kana ganinga kaga wacce take cikin nishad'i da jin dadi. ********** Da rana su Abu Turab iso, Sabi'u yana ajiyeshi ya sauka daga motar yace " ni nayi gida mutumina." Turab kai kawai ya d'aga mai, fadawa ne suka taho da sauri suka shiga kwashe kaya. Kallansu yai yace"ku kai kayan b'angaren Umma ni zan shiga fada na gaida Sarki." nan suka amsa da to, shi kuma yai gaba. Bayan ya shiga fada ne ya kwashi gaisuwa, Sarki cikin mamaki yace " me ya dawo dakai yau? bayan sai gobe kace?" Shiru yai na wasu dakiku kafin ya d'an sosa keya yace " zuwa nai na sanar da Sarkin Kano mahaifin Gimbiya yace ya na jiran lokacin sa rana." ya karasa maganar tare da maida kansa kasa. Galadima yace " Alhamdulila abu yayi kyau, nikam Takawa mai zai hana ka had'a auran yarima Abdulmajid da na Yarima Turab kawai ayi a rana d'aya?ko har yanzu ba'a tsaida maganar ba?" D'agowa Turab yai cikin mamaki sannan ya kalli Galadima, cikin neman karin bayani yace " Abdulmajid ya samu mata ne?" Galadima yana murmushi ya kalli Barde wanda yai shiru kamar wanda aka daka haka yake jinsa, sannan ya kalli Wambai yace " au ashe fa bakanan? ai 'yar gidan Barde yakeso yama sunan ta?" Wambai yace " Mairo." Idanu Turab ya zaro cikin tsananin mamaki yace " Mairo? ya fad'a yana kallan Barde, sannan ya kalli Hisham wanda shima yaci magani." Murmushi ya kakaro sannan yace " Bari na shiga ciki Ranka ya dade." Sarki wanda shima ya rasa ta cewa yace " Ya kamata kam, kaje ka huta." Turab ya kara gaidasu sanan yai waje. Cikin hanzari yake tafiya Mairo? lalai ma yaran nan ba karamin mahaukaci bane, an tab'a aure dole? Hangoshi yai a gabansa kamar irin yasan maganarsa d'in nan yakeyi. Tsayawa Turab yai ya kafeshi da ido, shima Abdulmajid wanda ke hanyar Fada dan jin hukuncin da aka yanke ya tsaya tare da kafe Turab shima da ido. Cikin kasaita kowannen su ya fara takowa, idanunsu na kallan juna har zukazo daf da juna. Abdulmajid ya kalleshi yace " Sirikin sarkin kano ka iso?" Wani murmushi na gefe Turab ya saki yace " Sai ina?" Abdulmajid ya tab'e baki sannan yace " ya zanyi? kasan na kusa zama ango dole ba zama." Turab baisan sanda yai wani banzan murmushi ba har hakwaransa suka fito ba yace " Ango? Are u kidding me?" Abdulmajid ya had'e rai sannan ya kara takowa jikin Turab daf yace " Kana tunanin zaka hanani? to ka bud'e kunnuwanka da kyau kajini, yanzu ba lokacin damuwa da abinda bai shafeka bane na aurena da matata Mairo ba kaje ka duba lafiyar tsohuwarka dan naji Umma tace ta saita komai akanta" sannan ya murmusa yace " ka kuma san Umma in tace abu to da abun ne." Sosai Turab ya harzuka da kalamansa, ya juyo ya kalleshi sannan ya sa hannu ya kade mai kafadarsa kamar irin abu ya hau kai d'in nan yace " Ya za'ayi? dan nasan in Magajiya tace abu tofa abun ne sai dai ni kuma in nace abun nan ya isa to fa dolene ya dakata." Ya karasa hannu ya kad'emai d'aya bangaren yace " Ka tabbatar ka sanarwa Ummanmu kalamai na sannan auran Mairo?" yai dariya yace " ko a mafarki kama daina dan baka isa kasa baiwar Allah cikin kunci da bakin cikin auranka ba." ya juya yai gaba ransa a b'ace, da alama an ma Ummansa wani abun, Idanu ya d'an rufe kad'an yashiga fad'in _Innalilahi Wa Ina Ilaihi Raji'un_ ********** Har yaje sai shiga bangaren Umma sai kuma ya fasa yai b'angaren Magajiya. Batai mamaki ba sam da aka sanar mata da zuwansa dan dama tasan in har ya iso to da dole ta ganshi. Kara gyara fuskarta tai ta kalli wacce ta sanar da ita zuwan nasa tace " Muna bukatar abu mai sanyi." Nan ta amsa da to sannan ta juya. Magajiya ta zura takalminta mai kyau sannan ta kalli kanta a madubi kawai sai gani nai tayi wani murmushi, sannan tad'an cije lab'anta ta kara murmusawa. A hankali ta tako cikin izarta ta iso kilisarta. Abu Turab na zaune ya had'e hannayensa guri d'aya. shigowa tai cikin takama ta zauna, sannan ta kalleshi tace " Bakaga shigowar mahaifiyarka bane?" Kallanta yai sannan ya d'aga gira yace " Au banji shigowarki ba, sannan yai kasa dakai ya gaidata." "Me ya kawo ka?" Kallanta yai yace " zuwa nai na gaidake na kuma sanar dake abubuwa biyu a matsayinki na Uwata." Kallansa tai batace komai ba. Yace " Sarkin kano yace yana jira daga bangaren mu, na tabbata kin san me yake nufi, sannan abu na biyu ki fadama d'anki ya janye auren......" Wata dariya ta saka sannan tace " Turab? da alama bakaje ka gaida wacce ta haifeka ba ko?" Kallanta yai cikin shakka yace " Na'am?" Dariya ta kara sawa tace " me yasa ne nikam na girma amma haryanzu nakejina kamar yarinya? fatata bata canza ba sam." Ta karasa maganar tana kallan hannunta, kallanta yai cikin tashin hankali idanunsa suka kada sosai, yace " me kikana Umma na?" Baiwar nan ce ta shigo d'auke da tire da jug da kofuna ta ajiye sannan ta zubama Turab ta kuma zuba ma Magajiya. Magajiya ta amsa sannan ta kurba tace " sha akwai sanyi dan ka d'auko rana." Kallanta yai sannan ya kalli kofin, yarinyar ta fita. yace " me kikama Ummana?" Yai maganar cikin kakkausar murya. Kara kub'a tai sannan tace " ta yaya zan sani?" A harzuke ya mike yai waje cikin tashin hankali. Me tama Umma haka? da yake ganin tsantsar confidence a idanunta??? 🤝🏻 *TEAM TURAB* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *53* Har ya murd'a kofa sai yaji tace " Ahh na manta ashe akwai wacce kake so?" Tsayawa yai cak sai dai a hankali ya juyo zuwa kallanta. Murmushi ta saki tace " Hmm na kula da gaske ne, dama Khadija ce ta sanar dani akwai wacce kake so, nayi mamaki da naji haka da alama san mulki ne yasa ka ture wacce kakeso zuwa auran Gimbiya." Idanunsa ne suka kad'a sosai Khadija? Da karfi ya bud'e kofar ya fita cikin b'acin rai. Magajiya ta bishi da harara tace " Mairon yakeso da gaske? Ko kuma akwai wata a kasa? Dama hakan ne yasa batace Mairo ba kai tsaye saboda tanaso taga yanda zaiyi, sai dai ta kasa ganewa." Abu Turab tsaya wa yai a waje yai shiru, wata zazzafar iska ya fitar daha bakinsa yana kokarin juyawa ya ga Khadija ta taho. Kallanta yai sau d'aya ya d'auke kansa, kalaman Magajiya ya maimaita na game da wacce yakeso, kenan kila na Khadijan har fada musu tai ita yake so? Wato gaba gaba amfani zasuyi da san da yake mata su cutar dashi? A da yana tunanin Khadija bazata tab'a cin amanarsa ba amma a yanzu ya cire wannan abun a ransa, bai san ta iso inda yake ba. Sai jiyai cikin muryar tausayi tace "Yaya." Kallanta yai fuskarnan tasa a d'aure tamau, ta d'auka jin abinda ya faru ne yasa shi cikin wannan hali, a hankali tace " Yaya kayi hak........" Katseta yai da cewa " Alhamdulila banaji a yanzu zanyi kokwanto akan hukuncin da zuciyata zata yankemin, a da ina tunanin halin da zan sakaki, nagode kwarai da kika nunamin ke jinin Magajiya ce." Yana kaiwa nan ya wuceta. Sam ta kasa ma magana saboda ta kasa fahimtar abinda yake fad'a. Ita datazo dan yima Abdulmajid magana da kara bashi baki akan ya janye maganar nan, me Turab yake nufi? *********** B'angaren Mahaifiyarsa ya nufa, a zaune ya ganta ganin yanayin datake yasa yaji idanunsa sun ciciko, shiga yai ciki ya zauna sannan ya gaisheta. Fuskarta d'auke da murmushin data kakaro tace "Turab akacemin ka dawo, nayi mamaki sosai ganin ba yau ne kace zaka dawo ba." Mikewa yai jiki a sanyaye ya karaso inda take a hankali ya kwantar da kansa a kan gwiwarta idanunsa sun ciciko yace " Ba sai kin b'oye damuwarki ba a gabana Umma, na sani akwai babban matsala data kunno miki kai, ki sanar dani Umma ko na nemanr mana mafita." Jitai hawaye na neman zubo mata da sauri ta mike tsaye ta juya mai baya tace " Ba komai Turab kawai dai jiya na d'anyi zazzab'ine shi yasa ka ganni haka." Mikewa yai shima ya kalleta sannan yace " Me Magajiya take nufi da inzo ki sanar dani?" Basira ta juyo tace " Haka tace ma?" Kai ya d'aga alamar eh sannan tace "Maganar Abdulmajid ne da Mairo bayanshi banaji akwai wani abu." Kallanta yai sai dai bai gamsu ba ya dai fahimci batasan yasan ko menene. Juyawa yai yace "bari na koma ita ta sanar dani." Cikin tsawa tace " Turab dakata." Juyowa yai ya kalleta cikin yanayi na tausaywa yace " Umma kin manta wahalar da mukasha a rayuwa ni da ke? Kin manta matsala da tashin hankalin da kika fuskanta? Ta yaya zakiso ki b'oyemin wani abu?" Idanu ta runste tace "Turab muna cikin tashin hankali, in har abinda Magajiya ta sani ya bayyana banaji zamu kara samun kwanciyar hankali a gidan nan." Cikin shakkun kalamanta yace "Umma badai tasan maganar lahanin da aka miki ba?" Kallansa tai hawayen dataketa dannewa suka zubo tace "Turab ya zamuyi? In har maganar nan ta fito ban san yanda mutane zasu kallemu ba, ba kuma naji za'a yadda da kai." Idanunsa ne suka kad'a sosai lalai Magajiya bala'i ce yanzu mikin da ke b'oye a zuciyar matarnan sai data taso mata dashi hankalinta ya kwanta, lalai yaji dadi da mahaifiyarsa ta sanar dashi komai kafin rana irin ta yau, da bai san yanda zaiji maganar nan ba. Murmushi ya sakar mata ko ince yake ya mata yace " Sai me Ummana? Iya kace mutane su gujemu to sai me?" Kallansa tai cikin kunar zuci tace "kanaso kacemin baka fahimci me take nufi ba? In har magana ta fito zargin tsatson ka za'a shiga yi, in kuma ba haka ba sai dai kabi umarninta ka auri Mairo shikuma Abdulmajid ya auri Gimbiya." Gani tai yasa dariya mara sauti yace " ohh wannan shine dalilinta?" Basira ta kallshi tace " Kana tunanin Sarki zak taimakemu ko? Ka cire wannan a ranka in har kana wannan tunanin, Sarki ne shi kafin mahaifinka ko ince kafin ya zama mijina.' Turab yace " Umma kin taba gani nace Sarki ya ya shiga ko ya taimakamin a yayin da matsala ta kunno min kai? Sai dai inje gun Abba na dan neman shawara, sannan maganar auran Bilkisu da Mairo duk wannan lamari ne na ubangiji Allah shine yasan matar da Abu Turab zai aura, Allah shine yasan ko dukansu zai aura, Allah ne yasab ko duk cikinsu ma ba wanda zan aura, sai dai nasan abu d'aya duk yanda zanyi bazan bar Abdulmajid ya auri Mairo ba saboda kamar kanwa take a gurina, sannan bazan bari ya auri Bilkisu ba saboda yarinya ce wacce bata cancanci miji kamar Abdulmajid ba." Yana kaiwa nan ya juya zuciyarsa fal da bakin ciki. Sam ya rasa ma ta ina zai fara. Har bayan Magrib ya rasa mafita kawai ya nufi b'angaren Mahaifinsa. Jakadiya ta matso ta gaisheshi sannan tace "Ranka ya dade Magajiya tana ciki." Magajiya? Ya maimaita yana kallan Jakadiya. Jakadiya tai gyad'a kai tace "Sai dai ka dawo gobe inkuma kanaso in sanar masa." Turab ya girgiza kai sannan yace "Barshi, sannan karki sanar mai da zuwana ko daga bayane." Tace "to." Harya juya ta biyoshi da sauri tace "Yarima." Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalleta yace"Lafiya?" Daurewa tai tace "naji abinda ya faru, sai dai abu d'aya na isa fad'ama wannan abinda ta shirya reshe zai iya juyawa da mujiya, dan kuwa Magajiya tanada babban sirri duk abinda ake tunanin nata ne ba nata bane." Turab ya kalleta cikin mamaki yace "Jakadiya ni fa......" "Na barka lafiya Ranka ya dade, kai mutum ne mai zurfin tunani da kaifin basira zaka gano abinda nake nufi in har Allah ya nufeka da ganowa." Ta juya tai gaba. Da kallo ya bita sannan ya juya yai gaba. ************* Abdulmajid wanda bayan shigarsa fada yana neman yin magana mahaifinsa ya mai wani kalli wanda kwarjini yasa ya kasa karasawa. Ana magrib kuwa ya zari mota yai gidansu Mairo. Tana xaune a waje ta kurama sararin samaniya ido tana kallan yanda yanayin duhun gari yake, yaro ne ya shigo yai sallama sannan yace " wai ana kiran Mairo." Mairo ta kalleshi tace "inji wa?" Yace "wai mijinki." Kwafa tai sannan ta ciji lab'anta ta kuma mike da sauri, mayafita kawai ta zura tai waje dan ko Mamanta bata sani ba. Yana cikin mota yana ganinta a tsaye a soro ya fito da sauri yana murmushin jin dadi. Itama murmushin ta maida mai hakan yasa yaji kansa ya fasu. Ya karaso gunta yace "Mairo na." Tace "Yarima na." Kallan mamaki ya mata sannan yasa dariya sosai yace "Mairo kece kuwa?" Tace nice, kana mamaki ne? Fuskarsa ya shafa cikin jin dadi sannan yace " Sosai ma " Wani banzan kallo tamai tace "Kana tunanin haka zan ma in ka min ta karfi?" Kallan tai yai yace "me kik....." Katseshi tai tace " please Abdulmajid ka tashi daga wannan wawan baccin da kakeyi, wlh wlh in har ka kuskura ka dage da aurena har aka yi wlh ina tausaya maka da ni kaina dan a yanda nakejin tsanarka komai zai iya faruwa, dan wlh dana aureka gwara na auri talaka wanda bashida komai." Jiyai zuciyarsa ta d'au zafi yace "Mairo how can u?" Tace "me? Kana tunanin sunyi kadan kalaman nawa Busuru kawai, ka lalata 'yan mata sannan ka nemi auren wacce batasanka? Ko kana tunanin nima so na kake?" Ta kalleshi cikin takaici tace "Aurena? Hmm please go ahead, a kaini gidanka inga ko zaka samu abinda kakeso." Taja dogon tsaki zata juya. Hannunta ya rike da sauri yace "Mairo taya zaki fadamin bakaken maganganun nan ki tafi?" Ta makamai harara sannan ta kalli hannunta daya rike tace " sakeni ko?" Kallanta yai sai taga ya sa dariya yace " Mairona in baki shawara? Ki bala'in kwantar da hankalinki ki aureni cikin farinciki dan wlh duk duniya ba wanda ya isa ya aureki sai ni nan Abdulmajid d'an Magajiya da Abdussamad." Hannunta ta fizge tai cikin gida. 🤝🏻 *SASSANIN KUNGIYA TA ABU TURAB SADAUKI🏇🏻* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *54* D'agowa yai cikin tashin hankali ya kalleta yace" me?" Idanu tad'an juya tace " Na yaba da kokarinka wajen ganin ka kare hakkin matar so, sai dai duk yamda kaso ka b'oye sirrin nan matar ki ta gano komai." Tambayar ki nakeyi me kike nufi? Ta sakar mai lalausan murmusji sannan tace " Ya zamuyi ai dolene mu cigaba da b'oye sirrin nan, gaskiya na tausayawa kanwata Basira fyad'e ai mugun abu ne." Tai tagumi kamar wacce take cikin halin tausayawa tace " Ya zamuyi in zancen nan ya fito? Sannan wace dabara kai nikam dan a sanda ka kawo Basira gidan nan tabbas ankawomin zanin gadon dake d'auke da budurcin ta." Tai ajiyar zuciya tace " Hmm ni yanzu tsorona ma kar a maida zancen daga fyad'e ya koma karuwanci kasan mutanen mu akwai matsala." Tsananin tashin hankali je ta gani karara ya bayyana a idanun Abdussamad. Mikewa tai ta tako a hankali zuwa gabansa sannan ta tsugunna tace " Tuba nake ranka ya dade dan bakina yayi kuskure dan tuni na tura mata d'anta akan yaji meke faruwa." Zuciyata ta turnukoshi ya kalleta wani irin kallo na tsana da kiyayya, kai ta juya sannan ta kalleshi idanunta sun canza kala tace " Ba sai ka min kallan tsana ba, na dade da sani tsana da kyamar da kakemin, kana tunanin banajin haushi? Ko kana tunanin nid'in ba mace bace? Tunda ka auro Basira zan iya kirgama sau nawa ka kusanceni." Ta mike tsaye tace " Baka min kara a harkar abinda kakeso, nima bazanyi kara akan zartarda abinda naga yayi daidai da zuciyata ba." Da karfi yasa hannu ya fincikota sai gata a gabansa, idanunsa sun kada sosai da sosai yace " Kara? Ke har kinsan kalmar nan ta kara? Duk karar danake miki? Kina tunanin shakkarki ce tasa nake shanye duk laifin da kike min?" Kallansa kawai take saidai tsoro da shakka sun d'arsu a zuciyarta dan tunda take yauce rana ta farko dataga Abdussamad cikin irin wannan b'acin rai. Daurewa tai tace " Kadaifi kowa sanin hukuncin matar da take ba cikakiya ba a matsayin matar Sarki..." Hannu ya d'aga kamar zai kifa mata mari wanda hakan ya tsoratar da ita sosai, sauke hannunsa yai sannan ya runtse ido cikin takaici yace " ke ba mace bace? Tayaya rashin imaninki zaisa ki taso da mikin daya riga ya warke a cikin zuciyar marainiyar Allah, Magajiya wani irin rashin tausayi da imani gareki?" Bakinta ta d'an rufe dan magana take san yi taji yana rawa, kallansa tai bayan ta cije tace " inhar ka damu da ita ba kuma kasan mutane su san kazantar data aikata kasa d'anka ya janye auren Gimbiya sannan ya auri Mairo, sannan kayi murabus ka barwa Abdulmajid kujerarka." "mene?" ya fad'a sannan ya d'anyi dariyar datake kunshe da tsantsan takaici yace " kinaso kicemin akan auran Bilkisu kike neman halaka rayuwar Basira?Ko kuma tsoron Turab ne yasaki b'ulo da wannan makircin?" Kallansa tai cikin tsananin takaici tace "mene?" Sarki yace "Ahhh yanzu na fahimta, tsoron kar Turab ya samu power ne ta b'angaren auransa yasaki haka, kina tsoron abinda zai miki inhar daga baya yaji abinda kika aikata masa." Idanunta ne suka firfito tace "mena aikata masa?" Sarki yace "kin dauka bansan kece silar nakashewar idanunsa ba? Ke har zakiyi maganar kara da matar so? Ko kina tunanin tsoronki ne yasa na kasa miki hukunci?" Da sauri ta juya mai baya tace "bansan wannan zancen ba, meye nawa na nakasa mai ido?" Sarki yace " fita." Juyowa tai ta kalleshi tace " koma waye ya fada maka haka karya yamin sannan kace ya kawo shaida, sannan maganar aure da Murabus ina jiran amsarka inba haka ba Basira da d'anta subar gidan nan." Ta juya da sauri tai waje. Hannunsa dake kan cinyarsa ya dunkule tamau saboda bakin ciki da takaici. *********** Abu Turab jeka ka dawo ya shigayi a tsakar falonsa. Da sauri naga ya fito ya yi waje. Bangaren Basira ya nufa, lokacin tana bandaki, sai daya jira ta fito sannan ya mike yazo inda take ya tsugunna yace " Umma akwai wani laifi da Magajiya ta tab'ayi ko kuma wani Makirci da kikasan ta tab'ayi?" Kallansa tai alamar tana nazari sannan ta girgiza kai tace "kasan halinta duk makircin da takeyi bata taba yarda tabar wata shaida da zata sa a ganeta." Shiru yai kafin can yace " ki sake tunani Umma ko wani abu ne wanda kikasan baki yarda dashi ba sai dai bakida tabbas akanshi, abu d'aya ne zaisa muci galabarta wato yanda tasan weakness d'inmu muma musan nata." Basira ta girgiza kai bayan dogon nazari tace "ban tuno komai ba Turab." Mikewa yai jiki a sanyaye yace "shikenan Umma, inkin tuno ko daga bayane." Har ya fara tafiya tace Turab. Juyowa yai da sauri. Tace " Akwai wani abu da take bamu kamar shayi a farkon zuwana gidan nan, to ni dayake banashan ruwan zafi na sanar da ita, sai dai abinda yaban mamaki tursasamun tai sai dana sha, sai dataga abinda nai sannan ta daina bani." Tai ajiyar zuciya tace "nasan ba wani abun zargi bane amma na kasa cireshi a raina, sannan Turab mai zai hana ma hakura da auran Bilkisu?" Kallanta yai yace " Umma kina tunanin saboda hana aurena ne kawai yasa tai wannan maganar? Sannan in ma haka ne kina tunanin nan gaba bazata sake amfani da wannan kalmar ta kara samu abinda tai ra'ayi ba?" Basira tai shiru, murmushi ya kakaro yace " Na tafi." Yana shiga d'akinsa ya rufe kofa yai shiru yana tunanin kalaman Ummansa, tabbas akwai abinda ake sawa a cikin ruwan zafin nan, to amma menene? Kalaman Jakadiya ne suka kara fad'omai, da sauri ya girgiza kai yace " inhar na tambayeta ta fad'amin gulma ina da tabbas gaskiya zata fad'amin?matar da sam bai yarda da ita ba? Sannan tayaya ma zata bi bayansa ta ajiye Magajiya? ******** A kano kuwa Bilkisu kwance a makeken gadonta ta kwantar da kanta a kan matashi ta lumshe idanunta ta shiga zazarfan tunani, tunanin da ni kaina bansan wani iri takeyi ba. Murmushi ne d'auke a fuskarta kai kace wani albishir aka mata wanda yasa ta fara'a har a cikin bacci. A hankali ta bud'e idanunta, da sahri ta mike tai baya tare da d'an zabura tace "Munnira meye hakan?zakizo ki sani a gaba, wlh na tsorata." Munnira tace " Gani nai kinata murmushi shine nakesan ganin abinda ke saki murmushin." Harara ta maka mafa tace " an kirani a waya?" Munnira ta girgiza kai alamar a'a, baki Bilkisu ta turo tace " Lalai ma Turab ai ka kira kacemin ka isa ko wani abun." tai maganar cikin d'an kukuni. Kallan Munnira tai rai bace tace "Fitarmin daga d'aki." Munnira tai waje tana mamakin abinda ya samu UmmaBilkisun ta. ************ Duk wani tunani yayi amma ya rasa mafita mai karfi, cir ya kwana bai runtsa ba yana neman mafita sai dai bai samu ba. Yanayin sallar asuba Mahaifinsa ya aika a kirashi. Sun zauna shiru a d'akin bayan sun gaisa, Sarki ya kalleshi yace " Naji ance kazo jiya." Kallansa yai baice komai ba, Sarki yace "naji kuma ance kace kar a fad'amin kazo." Turab yai kasa da kansa. Murmushi Sarki yai yace " To ya? Ka nemo mafita?" Kallan Mai Martaba yai sannan cikin sanyin jiki ya girgiza kai alamar a'a. Ajiyar zuciya Sarki yai yace " Murabus takeso nayi." D'agowa Turab yai cikin tsananin mamaki yace "Murabus?" Sarki ya murmusa yace " ya ya? Kana mamaki ne? Ko so kake kacemin bakasan Magajiya ba?" Idanu Turab ya zaro yace " amma....." "Hakura zakai da auran?" katseshi yai da wannan tambayar. Kallansa Turab yai sai dai bai iya cewa komai ba. Sarki yace " Hakura zakai saboda mahaifiyarka ko saboda ni?" Kallansa TURAB yai yama rasa me zaice, kai ya girgiza yace "bansani ba Abba, kwakwalwata ta rufe, Magajiya ta fara sani shakkar makircinta, how can she ask u..How c...." Dariya Sarki yai mara sauti yace " baka taba tunanin zatai haka ba?" Abu Turab idanunsa suka ciciko yace "Abba ta yaya zaka cigaba da zama da matar da bata ganin girma da darajarka? Ta yaya zaka cigaba da zama da matar da take neman muzguna maka?" Sarki ya kalleshi cikin wani yanayi yace "Kasan me yafi komai wuya a harkar sarauta? When u have something to protect." Turab ya mai kallan rashin fahimta, murmushi sarki yamai yace " me kake tunanin zai faru in na rabu da ita ba tare da babban dalili ba?" Turab yace "matarka ce fa ka kuma rabu da ita, me zai faru?" Kai Sarki ya girgiza mai yace " Turab kenan, Magajiya zata iya sa a kwace mulki daga hannuna duk da kuwa sarautar tawa ce." Me kake nufi? Sarki yai murmushin yake yace " shiyasa na ke san ka auri Bilkisu wacce tasan kanta ta kuma san darajar sarauta wacce mulkin a jininta yake ba koyarsa tai ba." Turab ya kalleshi yace " is she that powerful? Magajiya nake nufi" Sarki ya kalleshi yace " Tasan hanyar makirci kala kala, ta kuma san manyan mutane kala kala, ta kuma san yanda zatai ta samu duk wani abu da takeso ko ta wani hali ne kuwa ko da hakan zai zama silar halakar nata ne." Turab ya kalleshi yana kokarin magana Sarki yace " Turab kasan kai kad'aine zaka iya sa Magajiya ta amshi hukuncinta? Ni bazan taba iya cin galaba a kanta ba ko dan saboda zuri'ar dake tsakaninmu, bazan taba san d'ana ya shiga halin tashin hankali ba saboda wani buri daya ke nawa, zan kula da Basira in ta kama ma zan iya d'auketa daga gidan nan kn maidata inda ta fara zama, kada ka kuskura Magajiya tasan wani lago naka, kada ka kuskura ka bari ta nemi cin galaba akanka, na sani zaka iya, a duk lokacin dana tuna da kai inaji a raina komai zaizo da sauki da yardar Allah." Turab duk yanda yaso ya daure sai da kwalla ta gangaro masa kad'an. Ashe haka mahaifinsa yake zaune cikin takaici? Jiyai Mahaifinsa yace " Kuka ba wai ana yinsa bane saboda bakin ciki, sannan dariya bawai ana yinsa bane saboda farinciki, a koda yaushe zuciya tanayin abinda tasan hankalinta zaifi kwanciya dashi ne." Idanunsa ya runtse yai kasa dakai, mai yasa yakejin kansa yayi nauyi sosai yakeji kamar an d'auramai wani babban nauyi na kare mahaifansa da kuma duk wani abinda yake so? "Idanunka itace silar lahantasu, banso sanar dakai ba sai dai a yanzu na fahimci dolene na fada maka, ni dakai dolene mu had'u dan ganin mun kawar da masifar dake nanad'e damu, bazan taba bari Abdulmajid ya gajeni ba dan kamar naba Magajiya kujerata hakan zai kasance, ita kuma nasan bazata taba bari na baka kujerata ba." Turab ya daure kansa na kasa ya d'ago ya jinjina kai yace " Na fahimci me kake nufi, sannan ni kaina na dade da zargin itace silar matsalar idona sai dai ganin ba wanda ya taba zancen ba kuma wanda ya nuna yasa ban taba maganar ba." Sarki ya mai murmushin tausayawa yace " Kayi hakuri Turab da samun Mahaifin da bashida karfin hukunta wad'anda suke da laifi." Turab ya girgiza kai yace "Ba haka bane Abba, a koda yaushe ina alfaharin kasancewarka uba a gareni." *ABU TURAB TEAM* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *55* Turab na fitowa daga b'angaren sarki ya hau tafiya, Garzali ya biyoshi da sauri yace "Ranka ya dade ina zamu?" Juyowa yai ya kalli Garzali yace " akwai makullin mota a hannunka?" Kai ya girgiza alamar a'a. Turab yace "d'an hanzarta ka d'auko fita nakesan yi." Garzali ya juya da sauri. Turab ya shafi fuskarsa zuwa kansa sam jiyake gidan ya mai zafi, duk hirman masarautar jiyai kamar a takure yake. Inama ya iya mota? Da dakansa zai d'auka yai waje, sai dai matsalar idanunsa yasa bai tab'a koya ba gudun kar asiri ya tuno. Bai dade ba sosai sai ga Garzali nan ya bud'emai gidan baya ya shiga shikuma ya shiga gaba sukai waje. Tafiya kawai sukeyi, ganin baice komai ba yasa Garzali yace "ina zamuyi Ranka ya dade?" Turab yana kallan window yace " ka cigaba da tafiya kawai, ni kaina bansan inda zamu ba." Jin haka yasa Garzali ya cigaba da jan mota. Komar da kansa yai jikin kujera ya rufe idanunsa kamar maiyin bacci. Sai da sukai tafiyar a kalla awa d'aya sannan yace mu juya. Nan Garzali ya juya da kan mota, kasancewar safe ne dan lokacin karfe 10 ne na safe, gashi lokacin damuna ne yasa garin yai luf abin sha'awa ba kuma rana. Sai da suka shiga garin Zariya sannan ya kalli Garzali yace " kasan gidan Barde?" Garzali ya murmusa sannan yace "eh." Turab ya d'anyi karamin tsaki yace "Garzali a idanuna dana mutane ina ganin kamar nid'in mutumin kirkine sai dai a zahirin gaskiya banida kirki ko kad'an." Garzali yace "Ranka ya dade ta yaya zaka ce haka?" Turab ya jingina kansa jikin kujera ya hard'e hannayensa tare da maida idanunsa ya rufe yace " Duk yanda yarinyar nan ke kula da Mahaifiyata da nikaina ace ko gidansu ban sani ba, sai dai ita tazo inda muke." Ya karasa maganar tare da juyar da kansa gefe. Garzali yai shiru kafin can yace " Ai kai kaga baka fiya fita ba, sannan yaushe ma ka warke Ranka ya dade?" Turab bai ce komai ba, sai da suka isa gidan Garzali yai parking sannan ya kalli Turab wanda ya bud'e ido jin tsayawar motar yace " mun isa, a kira maka ita?" Turab ya kalleshi yace " Cema akai zance nazo ko me? Ka sanarma Barde da zuwana." Garzali yace to, sannan ya fita. Yana fita Turab ya kalli waje, unguwar ya shiga kallo. Garzali ne ya dawo da sauri yace " Kunye sab'ani ance d'azun nan ya tafi fada." Turab yace "ayya, Mairo fa?" Garzali yace "Ban tambaya ba dan nima dama bance kai bane kazo." Turab yace " kira min ita, tunda nazo harnan mu gaisa." Nan ya juya, yaron d'azu wanda da alama a gidan yake ya kara turawa yace "ya kida masa Mairo." yaran yace ince inji wa? Garzali yace kace inji Yarima Turab. Nan yaran yai ciki da gudu. Mairo ta gama cin abinci kenan tana tattare kwanuka yaran dayake d'an babbar yayarsu ce da aka kawoshi hutu ya shigo da gudu ya rike mata riga yace " Ana kiranki a waje." Tace " Khalid meye hakan? Waye yake kirana?" Yace " Wai kije inji Yarima Turab." Hararar sa tai sannan ta kwace rigarta tai kitchen tana cewa "Lalai Abdulmajid ma Ya raina mata hankali, taje inji Turab?"tai tsaki tace ko kunyar karya ma mutum bai iya ba. Hannunta ta wanke sannan ta fito tai d'aki, kan gadonta ta kwanta, can kuma ta mike zaune tace karfa inje da gaske ya Turab ne. Hijab dinta ta jawo tai waje. Lekowa ta fara yi ganin duk suna cikin mota yasa ta kasa ganewa. Ta kara lekowa, Abu turab ne ya zuge glass d'in window dinsa sai daya tabbatar itace sannan ya bud'e motar ya fito. Mamaki ne ya kamata ganin shi d'in ne ya fito, kallansa kawai take d'auke da tsananin mamaki har ha iso soron. Bayan kofa ta shige fa sauri tare da bin jikinta da kallo, ko kwalliya batai ba, jitai kamar ta ruga ciki. Turab ya tura kofar yace " ko dai in juya ne?" Tana bayyan kofar tace " Ya Tutab." Takowa yai zuwa ciki yana cewa " Ba dai Abdulmajid har ya fara hanaki kula yayan naki ba." Fito tai tare da had'e fuska tace " waye shi kuma?ni ai banaji a list d'in yayuna inada mai irin sunan." Yace " To ko a kirashi sai a tambayeshi? Inga ko zaki iya tambayarsa." Dariya tai mara sauti tace "Yaya kana tunanin bazan iya ba?" Hannunsa yasa ya rufe bakinsa yace " Tab ai na manta ashe fa Mairo ce. mairon data yardani sau biyu." Juyawa tai da sauri cikin shagwab'a tace "Haba yaya" Murmushi yai yace " Barde nazo nema ashe bayanan." Juyowa tai tace " ya tafi fada." Turab ya kalleta yace "Are u okay?" Yanayin fuskarta ne ya canza tace " akan me?" Kallanta yai sai dai baice komai ba, murmushi ta masa tace " I am okay yaya." Kara kallanta yai idanunsa d'auke da alamar kokonto, jitai idanunta na neman cicikowa, kanta ta d'aga sama tana neman maidasu, sannan ta kalleshi tare da girgiza kai tace " Yaya i am not okay, na rasa yanda zanyi, Abba yace bashida yanda zaiyi, kai baka nan, kunya nakeji in koma gun Umma sannan yaya bazan iya auren mutumin dana san ba sona yake ba, wlh yaya da ace Abdulmajid san tsakani da Allah yakemin ko da banasan sa zan jure na aureshi ko dan neman gyara halayensa." hawaue ne ya zubo mata ta girgiza kai tace "Sai dai yaya ni nasan Abdulmajid nasan irin kallan da yakemin, na tsani kallan da yakemin, na rasa ya....." Kasa karasawa tai ganin tana neman yin kuka, gashi batasan Turab yaganta cikin wannan halin. Tsananin tausayinta ne ya kamashi, kallanta yai sannan ya zaro handkerchief daga aljihunsa ya mika mata. Ansa tai ta goge hawayenta sannan ta kakaro murmushi ta kalleshi tace " Ya yayar tamu? Ka barota lafiya?" Murmushi ya mata yace " Bilkisu ce yayarki?" Tace "eh mana, a yanzu dai ba yaha ta bace amma inta aureka ai ta zama yayata." Kallan tsananin tausayawa ya mata dan tabbas yasan yanda take sanshi, yace " Tana garinsu, sannan Mairo ba kya ganin ya......." Gabanta ne ya fad'i tana tsoron kar yace ya kamata ta daure ta auri Abdulmajid, da sauri ta katatshi tace " Yaya kasan me? Khadija fa ta d'auka ni kake so, tun kwanaki nakesan fadama sai in manta." Kallan mamaki ya mata yace " mene?" Daurewa tai tace " nima bansan ya akai tai wannan tunanin ba." Iska ya d'an furzar yace " share wannan zancen sannan ni in tambayeki kinji na cemiki Khadija nakeso da bakina?" Tace " Au sai ka furta? Banda abinda idanunka suka nuna?" Handkerchief dinsa dake hannunta ya fizga sannan ya kwad'a mata akai, hannu tasa agun da ya daketa tace " Yaya da zafi fa." Murmushi sukayi a tare, sannan ya saki wani hucci na tunowa da matsalar dake gabansa. Kallanta yai yace " Karki damu, ke dai kicigaba da addu'a In Allah ya yarda komai zaizo da sauki." Kai ta d'agamai tace "Nagode Yaya." Juyawa yai ya fita, kallan bayansa tai har sai da ya shiga mota. ********** A gidan Waziri kuwa, Khadija ce tsugunne gaban mahaifinta. Hisham ya kalleta fuskar nan tasa ba wasa yace " Khadija mun riga mun yanke hukunci akan aurenki, dan Magajiya harta sa an sanar ma iyayen Saifullahi akan maganar sa rana, dan haka ki shirya, bazan tab'a yadda da wani zancen banza ba...." Kallan mahaifinta tau idanunta fal hawaye tace " Abba tunda akai maganar Saifullahi ban tab'a cewa a'a ba ko wani abu, ni dai naji zan aureshi amma yaya Abdulmajid dan Allah ya janye auren nan na dole da yake neman yima baiwar Allah." Kallanta yai ransa ya kara tun zura, mahaifiyarsa ya kalla da take zaune shiru, dan ko baki bata sa musu ba. Yace " biyoni ke kuma." Ya fad'a tare da yin ciki, Khadija na ganin haka tasan shikenan ta jama mahaifiyarta, da sauri tace " Abba...." bata soma fad'in komai ba Mahaifiyarta ta kalleta tare da girgiza mata kai alamar kartace komai. Suna shiga d'aki ya kalleta yace " wai wani irin tarbiyya kikama Khadija? A da na d'auka duk gidan nan tafi kowa jin maganata da hankali amma yanzu na fara tunanin zugata kikai inba haka ba yarinyar da nasan komai nacemata tanayi akan me yanzu akan wani can sokon yaro ta nemi bijiremin, kece kike zigata kome?" Kallansa tai ranta ya tunzuro dan itakam ta tsani yanda suke neman yima Khadija auren wanda bataso tace "Tunda nake dakai na tab'a musa ma? Ko a sanda ka d'auki d'an dana haifa ka kaima yar uwarka magajiya na hanaka? Ko har izuwa wannan ranar na tab'a kaucewa akan sharad'in daka gindaya min?ko kuwa kana tunanin banajin zafin ganin d'an dana haifa na fari agun kanwarka? Yaro bai san matsayin ba, ko suna uwa bai taba kirana dashi ba." Hawaye take sosai, kallanta yai rai a b'ace yace " Bazakiyi shiru ba?" Cikin b'acin rai tace" kana tunanin tsoronka nake daga kai har Magajiya? Sannan yanzu ni kun gama min abinda kukaga dama 'yar tawa ma haka kuke san juya mata rayuwa? Ko kana tunanin duk wani abu na makirci da kuke kai da Ma" Da baya da baya ta fara ja tana girgiza kai, sam ta ma rasa me take ji, tahowa tai dan taba mahaifinta hakuri sai dai me? Juyawa tai da gudu ko takalmi bata sa ba tai waje, ko mayafi babu a jikinta. Tafiya kawai take bata ma san knda takesa kafar ta. Sam bata kula da motar da take mata horn ba, jan burki yai da sauri ganin taki kaucewa, duk da haka sai da motar ta d'an bigeta kadan. Turab ya kalleshi da sauri yace " lafiya?" Garzali yace " bansan wacece ba, inajina bigeta. " ya karasa maganar tare da bude motar. Kusa da ita yaje yana tambayarta lafiya? D'agowa tai ta kalleshi ganin bibiyi take, mikewa tai kawai tana neman cigaba da tafiyarta. Da sauri ya kalli Turab wanda ya bud'e motar ya fito yana tsaye rike da kofa, yace " Ranka ya dade Khadija ce." Da sauri Turab ya kalli inda yarinyar take, ganin Khadija yasa ya taho da sauri yace "Khadija?" Kallansa tai sai tai baya luu kamar zata fad'i da sauri yasa hannu ya tareta, suka tsugunna, kallanta yai cikin tsananin tashin hankali yace "Khadija?" Kallansa tai sannan ta shiga girgiza kai tana cewa " Abba meke faruwa? Wani d'ane umma ta ba kanwarka? Abba...." Jijigata yai yace " Khadija? Meke faruwa?" Kai ta shiga girgizawa, ta shiga kankame jikinta alamar tsoro. Turab ya rasa abinda zaiyi d'aukanta yai cak ya sakata a mota, ya rufe ya koma gaba sannan ya kalli Garzali yace " mu tafi mu kaita gida, da alama bata cikin hayyacinta." Sun isa gidan ya rikota ya kalli Garzali ba sai ya tambaya ba dan kana kalla tsari da fentin gidan kasan gidan mai mukami babba ne na sarauta. Nan ya nufi gidan da ita. Hisham wanda ya fito ransa a b'ace da rainin hankalin da matarsa ta masa yai kicibis da su. Mamaki da takaici ne ya kamashi yace " Malam wani irin iskanci ne haka zaka rikomin 'ya......." Bayan Turab ta b'oye ta rikemai riga tana cewa " wayyo Allah, dan Allah tafi dani daga nan, wad'an nan......" Tsawa Hisham ya daka mata yace " Khadija bakida hankali ne?meye hakan?" Turab ya juyo ya kalleta yace "Khadija menene?meke faruwa haka?" Kallan Turab tai sai yanzu ta gane shine, hannunsa ta kamo da sauri tace " Yaya Abba da Umma Magajiya..." Hisham ya fahimci akwai wani sirri da take san fad'a, da sauri yasa hannu ya fizgota. Tace " Kanwar Abba? magajiya kenan, kenan Ya Abdulmajid......" Toshe bakinta yai ya sa hannu ya finciketa da karfi yai ciki da ita. Turab ya kalli inda suka shiga yace " me ke faruwa?" *ABU TURAB* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *56* Turab na zaune a cikin mota yai shiru yana tunani, me ya samu Khadija? A can kuwa Hisham na shiga da ita cikin gida ya rike hannayenta duka biyu yace "Khadija, menene? Me kikaji?" Kallansa tai tsananin tsoronsa taji ya shigeta, kai ta girgiza batace komai ba, kara jijiga ta yai yace " wanene ni?" A hankali tace " Abba ne." Yace " me kike kokarin sanar ma Abu Turab?" Kai ta girgiza da sauri tace "bakomai." Idanu ya kankance yana san gano abunda take b'oyewa, mahaifiyarta ce tazo gun tace " Khadija? Lafiya inata kiranki shiru?" Kwace hannunta tai ta tafi gun Uwarta da gudu. Hisham cikin zargi ya ke kallanta, Ummanta ta riketa tace "lafiya Khadija?" Tattaro nutsuwarta tai sannan ta samun kanta da cewa " Bakomai Umma faduwa nai a waje." Umma ta kama hannunta cikin kulawa sukai ciki. Hisham ya bisu da kallon zargi sai dai bashida tabbas akan abinda yake zargi, sannan yasan Khadija da ace taji maganar da sukai da matarsa dazu da ciki zata shigo taji me suke nufi bawai waje zatai ba. ***** Sun isa gida, Turab ya fito sannan ya nufi hanyar b'angarensa. Abdulmajid ya hango yana tahowa shima da alama shima fita zaiyi, tsaya wai cak yana kallansa sannan yana maimaita kalamun Jakadiya, da kuma Khadija, da alama duk maganarsu a karkashinta dai maganace wacce ta shafi Abdulmajid, to amma me suke nufi? Sam hankalinsa bai kawo ba d'an sarki bane dan shi a ganinsa duk mugunta da makircin magajiya bazata taba tunanin yin wani abu mai kama da haka ba. Abdulmajid ne ya iso inda yake kallan banza yamai yai gaba abinsa. Turab ya bishi da kallo sannan yai gaba. Har ya je zai shiga b'angarensa sai ya juya ya nufi bangaren Hajiya. Yaje shiga yai kicibis damai kula da ita, sam bata san ya taho ba haka shima. Bigetan dayai ne kufin dake hannunta ya fad'i kasa. Turab ya kalleta yace " sannu....." Ganin yanda ta shiga saurin dauke kofin da tayar sam tama manta da bigeta akai, tana d'aukewa tai hanhar fita, kasa ya tsuguna ya d'au yar karamar ledar data fad'o daga jikinta yana kokarin mata magana akan ta yarda abu sai gani yai ba kowa agun. Mamaki ya kamashi ina tai? Kallan maganin yai sannan ya shinshina maganin, a aljihunsa ya saka sannan ya shiga ciki. Sam jikinta ba sauki sai ma karuwa da yakeyi, kusa da ita yaje sannan ya riko hannunta yace " Hajiya nine Abu Turab." A hankali ta bud'e idanunta ta kalleshi cikin karfin hali ta sakarmai murmushi. Cikin kulawa da tausayawa yace" Hajiya kinganni shiru ko? Tafiya nai sannan abubuwa sunyi yawa dana dawo, ya jikin?" Idanu ta lumshe sannan ta bud'e, kallan d'aki yai sannan yace " kin gaji da kwanciya ko?." Tunani tai yanzu ne lokacin daya kamata ta yunkura ta fadama Turab abinda ta sani. Bakinta ta shiga motsawa tana kokarin yin magana, kallanta yai yace " akwai abinda kikesan fad'amin?" Kai ta d'aga da sauri alamar eh. Matsowa yai da kansa kusa da bakinta yace "menene Hajiya?abu kikeso?" Daurewa take sosai da kyar ta iya cewa "Maga...." Yace "magani?" Kai ta girgiza alamar a'a yace "Magajiya?" Kai ta d'aga da sauri alamar eh. Cikin mamaki ya kalleta yace " wani abun ta miki?" Da kyar ta kara daurewa tace "Abb duu........" Yace " Abdulmajid?" Kai ta jijiga alamar a'a yai shiru yana tunani can a ransa yace Abdussamad? Kallanta yai yace " Abba?" Kai ta girgiza da sauri yace " me ya faru?" Kokarin magana take sai dai ina ta kasa, ganin yanda take shan wahala yasa yace " Hajiya daina magana." Yawo ne yashiga zubowa mai kumfa, cikin tausayawa ya mike da sauri yana neman mai kula da ita. Yarinyar nan ya gani a waje tana ta dube dube cikin b'acin rai yace "bakiji ina kiranki ba?" Tahowa tai gunsa, yace " Hajiya jikinta ya motsa nemo mai magani." Ya fada tare da komawa ciki ya d'agata yana goge mata, sai far fari take da idanunta, mai bada magani tana zuwa ta shiga mata jike jike tana bata, sai dayaga ta samu bacci sannan ya mike cikin tausaya mata. Dakinsa ya shiga ya kwanta akan gado kansa na kallan sama ya d'aura hannunsa akan goshinsa, me Hajiya takesan fada mai? Ya tabbatar yanzu kuma abu ne tsakanin Magajiya da Mahaifinsa. Hannu yasa a aljihunsa ya d'auko wannan maganin, mikewa yai ya fito waje. Garzali ya taso da sauri yazo gunsa, Turab ya kalleshi yace " ka kiramib jakadiya kace ta sameni a gun shakatawar Takawa." Garzali ya amsa da to, juyawa yai ya fita. A kan kujera ya zauna, bai dade ba sai ga Jakadiya. Tana zuwa ta zube a gabansa ta shiga gaidashi, Turab ya amsa sannan ya kalleta yace " tambaya zan miki, banasan gulma ba kuma nasan had'i sannan kada ki kuskura kimin karya abinda na tambayeki shi kadai zaki amsa min bana bukatar wasu kalamai na daban." Kanta na kasa tace " To ranka ya dade" a gaskiya tana ganin girma da kimar yaron tunda yake bata taba ji ance ya nemi jin magana daga bakin wani ba a masarautar, sannan ga kwarjini da izza ta sarauta da yake da ita. Turab ne ya katseta da cewa " Menene tsakanin Magajiya da Abdulmajid da kuma Hisham? Wani sirri ne a tsakaninsu?" Gabanta ne ya fadi ta kalleshi tace " Ranka ya dade." Kallanta yai yace " jiranki nake." Yawo ta hadiya sannan tace " Amsar d'an kaninta da juyawa a matsayin nata." Idanu Turab ya zaro cikin tsananin tashin hankali, mikewa yai tsaye gabansa na wani irin fad'uwa gabansa yai, idanunsa ne suka kada sosai kallanta yai cikin kokonto yace " meye naki na sanar dani wannan babban sirrin? Sannan ta yaya ke kika san haka?" Jakadiya ta kalleshi cikin tsoro tace " Tuba nake ranka ya dade amma wannan magana haka take sannan sanar dakai danai bawai da wata manufa na fadama ba......" " Badai kina tunanin kin sanar dani hakan bane dan kar asiri ya tuno kiyi tunanin zan taimaka miki? Sannan meye dalilinki na b'oye wannan siriin bayan ked'in jakadiyar sarki ce?" Tsoro ne ya kama Jakadiya jikinta ne ya hau rawa ta kalleshi tace " Ranka ya dade........." Kallanta yai cikin takaici yace " ba dai dake aka shirya b......" Tsugunawa tai cikin tsoro tace "wlh ba dani bane Ranka ya dade, wlh ba dani bane." Komawa yai ya zauna sannan yace " jeki zan nemiki in nayi tunani." Fita tai cikin tsananin fargaba. Jiyai hannunsa na rawa, da sauri ya had'e hannayensa guri daya sannan ya bud'e idanunsa da sukai jawur. Mikewa yai cikin takaici yai bangaren Magajiya. Tana zaune a kilisarta aka sanar mata da zuwansa. Murmushin jin dadi tai tace ace ya shigo dan ta tabbata yau dolene ya nemi ya fiyarta. Turab ne ya shigo, tsayawa yai yana kallanta cikin tsananin mamaki. D'agowa tai ta kalleshi tace " meye hakan? " Murmushi yai sannan ya matso ya zauna tare da gaisheta. Amsawa tai cikin isa sannan tace " kun yanke shawarar?" Turab yace " sosai ma Umma shiyasa nazo miki da umarni." Kallansa tai shekeke tace " Umarni? Kai zaka ban?" Kai ya d'aga mata tare da yin murmushin gefe yace " inaso a satin nan ki fara shirya lefe na daga nan zuwa sati biyu ki gama hada komau dan zuwa kaiwa Masarautar kano, sannan in zaki saka lokacin biki banasan kijashi da nisa." Kallan mamaki ta mai batasan sanda tasa wata dariya ba tace " me da me?" Yace "kamar yanda kikaji na baki umarni hakan nakeso ki aiwatar min, sannan sirrin ki da nake rike dashi a hannuna zan aunashi a ma'auni, da namu sirrin da kike rike dashi zan duba inga da ni dake wanene nashi sirrin yafi nauyi, inhar naki yafi nauyi dole ne kiyi tabin umarnin d'anki Abu Turab har sai sirrinki ya kai daidai d'aya da namu inyaso sai kowa ya tona nashi sirrin a lokacin ne zamuga wanda zai ci galaba." Gabanta ne ya shiga fad'uwa dan yanda idanunsa suke nunawa tasan tabbas akwai wani babban sirrinta daya sani, menene? Wanene daga ciki?" Daurewa tai tace " kana tunanin zan yarda da wannan shirman naka?" Kallanta yai cikin tsana yace " to ko in sanar ma Abdulmajid?" Gabanta ne yai wani wawan faduwa cikin rawar murya tace " Abu Turab." Murmushi ya sakar mata sannan ya mike ya kalleta yace " kiyi gaggawar sa d'anki ya janye auren Mairo, ahh ba......" sai kuma yasa yatsa a baki alamar yin shiru yace " sry" ya fada tare da nuna alamar zip a bakinsa. Juyawa yai yai waje. Yana fita ta shiga kakkarwa, mikewa tai da sauri cikin tsoro me ya jiyo? Me ke faruwa? Turab na fita ya kalli bangarenta cikin takaici sannan yace " kin cuci Abba yanda kika ci amanar sa da cutar da mutane sai na nuna miki abinda kika aikata babbam kuskurene, babu babban yaki sai wanda kika yarda dashi yaci amanarki, kijira juya miki baya da zansa Hisham yai, sai kinyi dana sanin abinda kika aikata." Darajar mahaifinsa kawai taci amma da....Yai kwafa ya tuna yanda aka bashi labari dadin da mahaifinsa yaji a lokacin da aka haifi Abdulmajid. Kallan bangarenta ya karayi cikin tsananin takaici sannan yai gaba. *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *57* Turab na fita Magajiya ta d'auki kofin da ke gabanta ta jefi madubin dake manne a kilisar. Mikewa tai cikin tsananin tsoro da fargaba tai cikin d'akinta. Me ya sani? Me ya sani? Me ya sani? Wannan kalmar ita kawai take mata yawo a kwakwalwarta gaba daya ta rasa inda zatasa kansa, fitowa tai ta bada umarnin a kira mata Jakadiya cikin gaggawa. Jakadiya na zaune tasa kwanan abinci agaba sam ta kasa ci akazo aka sanar da ita kiran Magajiya. Zufa ce ta shiga karyo mata, mikewa tai ta fito. Haka ta karasa tana ta tsoron abinda zai faru. Magajiya na zaune a kan gadonta yayi shiru tare da kurama kasa ido. Ko sallamar Jakadiya bata amsa ba, har Jakadiyar ta zauna tare da gaisheta. Magajiya bata amsa ba sai dai ta kalleta cikin wani yanayi na zargi, sai kuma ta murmusa tace " Jakadiya ba tin yau ba nasan tabbas sai gulna da tsautsau bakinki yasa kin sanar ma Turab sirrin Abdulmajid." Jakadiya ta zaro ido sannan ta tuno kalaman Turab a yayin da ya mike zai fita bayan ya gama mata fada " Kada ki kuskura ki nunama Magajiya munyi maganar nan dake, duk yanda taso ta bugi cikinki ki tabbatar baki bar wata hanya ba dazai sa ta fahimta, nagode da sanar dani da kikai." Ya juya ya fita, tunowa datai da kalamansa yasa tai saurin zubewa tace " Gimbiya Magajiya ta yaya zakimin wannan shaidar? Bayan shekaru sama da ashirin ina rike da wannan sirrin? Sai yanzu ne zan tona? Inci ribar me?" Magajiya ta kalleta tace " Amma ai kwanaki kin min birga akan sirrina da kike rike dashi sannan banida tabbas ke d'in yanzu a bangarena kike duba da abinda kikamin." Magajiya ta daure tace " Gimbiya bani bace, me nene ma zaisa in fadamai?" Ganin yanda Jakadiya tai yasa ta gamsu akan ba ita bace, ta kalleta tace " bani guri." Fita Jakadiya tai, tana zuwa waje ta saki wani ajiyar zuciya. Magajiya kam tana fita ta dafa kanga cikin tashin hankalu tace " ba wannan bane, tunda duk gidan Jakadiya ce kawai tasan wannan sirrin, tunowa tai da Hajiya, ba dai Hajiya ce ta fad'i dayan sirrin ba?" Mikewa tai da sauri ta fito, ta sanar ma Bayinta akan zuwa bangaren Hajiya. Tana shiga wannan baiwar ta taho gunta da gudu ta gaisheta. Magajiya ta kalleta bata amsa mata ba tai ciki. Mai kuka da ita wacce tafi kusanci da Magajiya ce ta kalli Baiwar tace " kina zubawa?" Cikin tsoro tace eh, dan bazata iya cewa ta batar da maganin ba dan ta tabbata inhar ta fada to lalai kwananta ya kare. Magajiya na shiga ciki ta rufe kofa. Kallan d'akin tai a wulakance sannan ta toshe haccinta wai wari. Zama tai daga nesa da Hajiya sannan ta kalleta cikin jin dadin yanda take shan jiki ba damar magana tace " Hajiya? Kin ganeni?" Kallanta Hajiya tai, tana ganin Magajiya ta shiga yunkuri tanasan magana ta kuma kasa, Magajiya tace " Lalai Hajiya kiji da jikinki har kike wani yunkurin magana? Da nadauka ko kinsamu sauki ne harkinyi tsautsayin yin magana amma yanzu naga ba haka ba, bakya tunanin ya kamata ki sallama komai na duniya ki jira mutuwa tazo ta daukeki?" Hajiya yunkuri take sosai, ganin ba dama yasa tai shiru sai hawaye da yake ziraro mata ta gefen ido, tunowa tai da abinda ta gani. { " Wasika aka ba da akawo mata tashin safiyar yau, amsar wasikar tai ta bud'e, kana kallan rubutun kaga rubutu ne na 'yan koyo, sai dai da yake bata iya karantawa ba yasa ta ajiye wasikar a tunaninta ba mai amfani bace. Sai dai me? Kwana hudu kenan ana aiko mata da wannan wasikar sannan yaro ne yake kawowa kuma daga ya bada yake sa gudu yai waje, yau abin ya fara damunga dan da alama magana mai mahimmanci ake san sanar da ita. Sawa tai a kira mata Rabi'a, bayan tazo sun gama gaisawa ta d'auko wasikar ta bata tace " Karantamin." Rabi'a ta amsa tare da bud'e wa. Na farko an rubuta "Hajiya d'anki na cikin matsala." Na biyu " Hajiya ki yafemin sai dai ba yanda zanyi dolene na cigaba da zuba maganin nan inba haka ba Magajiya halakani zatai." Na uku "Hajiya ki taimaken ki d'au mataki ko na samu zunubina ya tsaya anan." Na hudu " Hajiya kiyi wani abu dan Allah." Hajiya ta amshi takardar a taorace tace "Rabi'a kin tabbatar da abinda aka rubuta kenan?" Rabi'a tace "Hajiya wlh abinda akace kenan amma me hakan yake nufi? Magajiya tana ba sarki magani? Akan me?" Hajiya tace " jeki gida sannan maganar nan ta zama sirri tsakaninmu koda wani abu zai sameni kimin alkawarin bazaki taba fadan wata kalma ba." Rabi'a tace "Na miki alkawari, nan ta mata sallama ta fita da tsananin mamaki, bazata taba iya ma Hajiya musu ba." Tana fita Hajiya ta kona takardar sannan tai shiru tana tunani, ba wanda ta yarda dashi bare suyi maganar dashi, sannan batasan wacece tayo mata wasikar ba, gashi ita ta tsufa ba wani abu da zata iya yi. Abu d'aya ne ya dace tai shine taje gun Magajiya dan nuna mata ba tsoronta ake ba sannan ga fadamata inhar bata daina ba zata sanarma Sarki. Yau da safe tasa aka kira mata Magajiya, tun safe aka sanar da ita amma sai yamma liss sannan tazo. Hajiya na zaune da charbi, zama tai akan kujera sannan tace" Hajiya kim wuni lafiya?" Hajiya cikin takaici ta kalleta tace " me kike bawa d'ana?" Magajiya ta kalleta cikin mamaki tace "me nake ba d'anki kamar ya kenan?" Hajiya tace "Kamar yanda kikaji haka yake, wani tuggun kike dubgawa Abdussamad, nasan dai ba maganin mutuwa kike bashi ba tunda zamansa a mulki shine zamanki kema a mulki, sanar dani me kike masa?" Dama Magajiya na tsananin jin haushin Hajiya dan tunda aka aureta tasan ba santa takeyi ba, fuska ta canza ta d'aure fuska tace " koma me nake bashi ai mijinane sannan bakida ikon shiga tsakanin mata da miji." Ta mike zata fita, Hajiga abin ya bata mamaki tace " waye ya haifa miki har kika aura? Sannan ni dama tunda na fara ganinki wlh nasan ke ba alheri bace a gareshi ba kuma matar zama bace ta amana, ko kiyi gaggawar daina abinda kike bashi ko kuma wlh in sanar dashi, zakiyi mamaki inkika ganki a gidan yayanki da takardar saki, ba'a saki a gidan sarauta bari sakin uwargida wacce take sarauniya sai dai ina sanar miki za'a fara akanki." Wata banzan dariya Magajiya tai tace " Me? Ni za'a saka?" Hajiya ta kalleta sai dai yanda taga Magajiya tayi yasa tsoro ya d'arsu mata dana sani ya kamata me yasa bata fadama d'anta ba ta sanar ma Magajiya?" Magajiya tazo kusa da ita ta sakar mata murmushi tace " ina jiran lokacin da za'a bani takarda, ki kuma tabbatar an bani, sannan maganar magani maganin hana d'aukan ciki ne ki tabbatar kin sanar dashi haka." Ta juya ta fita, tana kallan Hajiya duk ta rikice jikinta ya d'auki rawa. Bayan Magrib tanashan ruwa shikenan ta kasance ba lafiya tun daga wannan rana har yau ba baki ba zama bare tafiya." } Magajiya ta mike tazo saitin kunnen Hajiya tace " Kijira d'ana ya hau mulki in har kinada rai ni zan taimaka a fitar dake daga gidanan akaiki can bayan gari ki zauna kyafi jin dadin zaman duniyar, in kuma kinaso in hada da jikanki da kuma uwarsa Basira ku zauna tare acan." Ta mike tai waje. Tsayuwa tai a wajen gidan, me turab ya sani? Bataji akwai wanni babban sirri dazai tsoratata da ya wuce wad'an nan biyu, sauran duk sai dai tasa a aikata amma badai ita dakanta ba, inma zancen kashe yayan Basira ne ai ba ita bace tai Hisham ne. Dolene ta nemi Turab ta kuma bihi cikinsa da jin sirrin da ya sani. Turab zauna akan kujera yana d'an kada dan yatsansa d'aya tunani yakeyi wace hanya ce mafi sauki da kuma bakin ciki da zai sa Magajiya ta fita hayyacinta in taji Yayanta Hisham yaci amanar ta? Ya tabbata Hisham da Magajiya kowa amfani yake da dan uwansa. Ita tana amfani dashi dan cikar burinta, shi kuma yana amfani da ita dan samun matsayin da zai wuceta nan gaba, murmushi yai yace " Badai tana tunanin in Abdulmajid ya hau mulki komai na burinta ya cika ba?" Mikewa yai ya fito waje. Hango Abdulmajid yai a zaune yana shan iska jiyai tausayinsa ya dan darsu mai, ya zaiji in yaji wannan sirrin? Yauce rana ta farko dayaji tausayin Abdulmajid ya kamashi. Ya zaiyi ya sa Magajiya da Hisham su tunama junansu asiri da kansu? Khadija! Shiru yai jin sunan daya zo mai, tabbas itace a tsakanin mutanen biyu, ita da Abdulmajid, sai dai me? Zuciyarsa zata iya jure amfani da ita? Juyawa yai ya koma ciki tare da furzar da iska mai zafi....... *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *58* Duk yanda Magajiya tai akan samun mafita ta kasa, da sassafe kuwa ta aika akan a kira mata Hisham. Ko gaisuwarsa bata amsa ba tace " Yaya inaji fa yaran can yasan wani abu namu." Gabansa ne ya fad'i kallanta yai sannan ya tuna kawo Khadija gida da yai, ba dai wani abu ta fada mai ba? Daurewa yai yace " bangane ba? Me ya sani?" Ta girgiza kai tace ban sani ba sai dai daga yanda yazomin da kuma yanayin kalamansa inada tabbacin yasan wani abu wanda yafi fyaden da akama Basira." Hisham ya sauke ajiyar zuciya jin da alama ba Khadija bace yace " amma kinsan yaran nan shegen yaro ne anya ba dan karkiyima Mahaifiyarsa wani abu bane?" Magajiya ta girgiza kai cikin yanayin tunani tace " Yaya bakaga idanun yaran nan ba alokacin, sannan cemin fa yai in fara hada kayan lefensa yaban zuwa sati biyu, kamar ni dan karamin yaron da ko uwarsa na girma yazomin da zancen rainin hankali irin wannan?" Hisham shi kansa yayi mamakin jin haka yace " da kuma bakinsa ya fad'a miki hakan?" Tace " anan gun kuwa, sannan harda cemin in sa Abdulmajid ya janye auren Mairo, umarni fa yazo ya bani wanda ko ubansa bai taba ban umarni akan abinda yasan ina duk wani abu na ganin na hana wannan abun." Hisham yace " da alama yasan wani abun to amma ta yaya?" Magajiya ta juya kai tace " wannan shine abinda ke damuna." Shiru sukai kafin can ta kalleshi tace " Yaya" Kallanta yai yace " ya zakiyi?" Murmushi ta saki tace " kamar ni? Abinda yafi damuna kenan dan jiya ko baccin kirki ban samu ba, kamar ni Magajiya ace wannan yaran zai kalla ya bani umarni?" Hisham a ransa yace " an tabo Masifa." Magajiya ta kalleshi cikin iza tace " zanyi abinda yace bayan na tabbatar da akwai sirri na a hannunsa, zanyi lefe zan kuma sa a sa rana, zan nuna ma jama'a Turab ma d'anane." Hisham cikin tsananin tsoro ya kalleta dan ya tabbata wank mugun abun zata fada daga karshen abin arzikin datai, dan yasanta haka take in har aka bata mata rai sai ta nuna bakomai Sai kuma tayi abinda baki bazai fadu ba. Magajiya ta kara wani murmushin jin dadi tace "Aure? Auren Bilkisu?" sai kuma ta sa dariya tace " lalai nayi gangancin barinka da rai." Hisham ya kalleta yace " me kike tunanin yi?" Kallansa tai sannan ta wani juya ido tace " sai muga ranar auransa waye zai je gun, mai makon kaga ai aure da shi a d'aura da Abdulmajid sannan su gama d'aura aure suzo su tadda angon da aka shirya za'ai dashi a kwance ba numfashi." Hisham ya kalleta yace " ban fahimceki ba....." Tace "Zaka fahimceni, dan kuwa kaine zakasa a kamashi a hanyarsa ta zuwa d'aurin auran, sannan musa abokinsa dole ya sanar akan bazai samu zuwa ba dan shi ba auran yake so ba, kaga ran Sarki zai b'aci matuka ya aura ma Abdulmajid Bilkisu sannan mai makon mu sakeshi lafiya sai mu juya abin a matsayin 'yan fashi ko kuma hatsarin mota, kaga mun jefi tsuntsu biyo da dutse d'aya." Mamaki ya hana Hisham magana kawai kallanta yakeyi. Kallansa tai tace " ya? Wasan nawa ya had'u?" Idanunta ya kalla yace " Magajiya kenan, duk duniya Allah bai taba hadani da mai kaifin basira irinki ba, da ace Basirarki a abu mai kyau kike sa ta lalai da ancigaba a gidan nan." Harara ta makamai tace " mai kake nufi?" Jinjina ya mata da hannu yace " komai yayi nake nufi." Tace " Uwata fa?" Sai daya had'iyi yawo yace " tana gida ba lafiya." Cikin kulawa tace " da alama sam yaya baka kula da Khadija, inaji zan dawo da ita gabana har tai aure, munyi magana da Mahaifin Saifullahi yace tunda yara sun daidaita zasu kawo kudi." Hisham yai murmushi yace "Allah ya kaimu." Kallansa ta kuma yi tace " Ya ake ciki a fada akan maganar auran Abdulmajid da wannan sakaryar?" Hisham yai tsaki yace " kwana biyu dai anyi shiru da maganar dama Galadima ne uban san kawo maganar da Turaki." Magajiya tai shiru kafin tace " Gun Abu Turab zani yanzun nan dan in tabbatar da abinda yake dashi." Hisham ya kalleta yace " da kanki zaki? Ba gwara ki aika yazo ba?" Murmushun jin dadi tai tace " ai tun yanzu za'a kulla abotar d'a da uwa saboda gudun zargi da zai biyu baya." Kallanta yai sannan yai kasa dakai. Mikewa tai ta fita sannan shima ya fito. B'angaren Turab suka nufa, mai kula da kofarsa ne ya bud'e tsananin mamaki ya kamashi na ganin Magajiya. Su kansu mutane duk wanda yazo wucewa alokacin sai dayai mamakin ganinsu. Bud'e mata kofa yai tare da gaisheta. Magajiya ta shiga tana kanta tsaye. Garzali ne ga taho da sauri tare da gaishesu. Magajiya ta kalleshi tace " Turab fa?" Yace " yana d'aki." Nan ya nuna mata hanyar falo ta shiga. Tsayawa tai tana kallan bangaren, abinda ko bangaren Abdulmajid tunda ya tasa bata zuwa. Garzali yai ciki dan kiran Turab. Abu Turab ya gama sa kaya kenan yaji ana kwankwasawa, yace waye? Garzali yace "nine kayi baki ne." Bai tambayi waye ba sai huka da ya saka ya sa turare ya fito. A zaune ya ganta tayi zamanta na isa akan kujera. Mamaki ne yasa ya ja ya tsaya tare da jingina kansa da bango, yace " Umma Magajiya da kanta?" Alama tama bayin da su fita daga falon,saj da suka fita sannan ta kalleshi tace " tsayuwar anan ta menene? Abun mamaki ne in uwa tazo ganin d'anta?" Kallanta yai sannan ya tako a hankali yana cewa " inafa abin mamaki, dama ai hakkinta ne na ta kula da d'anta." Ya karasa maganar tare da zama. Kallansa tai tace " nayi tunani akan maganar ka sai dai banaji kai ka isa ka bani umarni sai dai In zaka canza yanda kamin magana daga umarni zuwa roko." Kallanta yakeyi har saida tazo karshe, gani tai ya sakar mata wani bazawarin murmushi yace " ko?" Ranta ne ya d'an soso ta kalleshi. Yace " kin fara had'a kayan? Ko dayake jiya mukai maganar bazai yiwu ace kin fara ba, amma ina sanar miki sati biyu na baki kacal in har kika wuce ina tausayin halin da zaki shiga dan banaji Sarki zai barki da ranki, in kuwa har ya barki to lalai a kurkuku zaki karasa rayuwa daga ke har yayanki." Gabanta ne ya fadi, ta daure tare da kakaro dariya tace " inji wa kenan? Kai kana tunanin duk duniya akwai wanda ya isa ya hukuntani? Sarki? Hahah lalai yaro yaro ne." Turab kallanta kawai yake, jin kalamanta yasa ya mike tsaye yace " Ba sarki bane zai hukuntaki Umma mantawa nai, nine nan d'anki wanda zai hukuntaki, ya kuma hukunta duk masu hannu a abinda kuka aikata." "Ahhh, bansan me yasa nake tausayin mutanen da kukai amfani dasu gun cimma burinku ba, sai dai ina tunani anya zasu yafe muku? Sannan Hisham da kike takama dashi...." Sai kuma yai shiru tare da yin kasa da kai yana dariya yace " ke kina tunanin zai cigaba da bin umarnin ki har sai sanda kika jefashi halaka?" Kallansa tai cikin mamaki tace " mene?" Kafada ya d'aga mata ya girgiza kai yace " Bansan komai ba." Juyawa yai yace " in kin gama ganin gidan d'an naki kya rufomai kofa." Ya juya yai ciki ransa a b'ace, wato bata d'auki Sarki da wani matsayi ba? Gani take tafi karfinsa. Ba shakka ran Magajiga yakai gurin tunzura, lalai dole taga karshen yaron nan ita ganin sa ma ta tsani yi yanzu. Haka ta fito rai a b'ace. ************ Abdulmajid kam yana tsaye a kofar gidansu Mairo sai data dade sosai dan sai da mahaifiyarsa ta tsawatar mata sannan ta fito. Yana ganinta ya sauko yana washe baki. Tsayawa tai tare da hard'e hannayenta ta juya mai baya a cikin soron. Abdulmajid ya karaso ya kalleta ta baya sannan yace " Gimbiya irin wannan tsayuwa haka kamar mai shirin yin hoto?" Juyowa tai ta kalleshi tace " Abdulmajid." Da sauri yace " Naam." Tace " dan Allah dan Annabi ka kyaleni, wlh wlh ni kam na gaji da wannam abun, ka sanni sarai banaso raina ya bace dan wlh xanyi abinda kaima sai kai dana sani." Kalamanra ko a jikinsa yace " eh wlh, dan Allah Mairo kiyi abinda zanji jiki ni wlh so nake yi." Wani banzan kallo tamai na takaici tace " wai kana d'an sarki me yasa kake abu kamar karamin yaro?" Hannunta ya kamo, da sauri ta fizge tace " Wai Abdulmajid meke damunka ne? Na d'auka na sanar dakai banasan ka dinga tabani ko? Kaje can kun karuwan......." Batai auni ba taji yasa hannu ya rufe bakinta. Matsowa yai da sauri ta matsa jikin bango tana zare ido tace " meye hakan?" Kallanta yai yace " Mairo me yasa kike tunani ni din dan iska ne?" Harararsa tai batace komai ba. Yace " nasan bazaki yarda da abinda zance ba amma wlh kinji na rantse ban taba sanin wata 'ya mace ba, ma sani sarai ina shafa bayin gidan mu dan jin dadi na sai dai ban taba bari abin yakai nan ba." Kallansa tai tace " kana tunanin zina sai ka sadu da mace kawai take a matsayin zina?" Kallanta yai yace " Mairo ni duk wannan ba sune a gabana ba, in kikace in daina taba mata zan daina nidak dan Allah ki auren, ko na aureki in kikaga dama kice sai kin amince zan kusanceki Wlh zam yarda ni dai dan Allah ki yarda ki auren, ina san......." Katseshi tai tace " Ni dai dan Allah ka kyaleni na rokeka da Allah." Murmushi ya sakar mata sannan yace" ma tafi yau, sai na dawo zuwa jibi." Kafin tai magana har ya tafi, juyawa tai ta wuce gida. ******* *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *59* Magajiya sam ta rasa yanda zatai, ganin ba mafita yasa ta nufi gun Sarki. Yayi mamakin jin zuwanta bayan ta shigo ta zauna sannan ta gaidashi. Kallanta yai tare da amsawa yace " Lafiya dai ko?" ya fada tare da d'aukan ruwan dake gabansa a kofi dan sha. Fuskarta a sake kai kace cikin farin ciki take tace " dama maganar auren Turab ne, ina tunanin ya kamata in fara had'a lefe....." Furzo da ruwan bakinsa yai tare da kwarewa, kallanta yai cikin tsananin mamaki yace " me? Me kika ce?" Dariya tai na salo tace " me? Kana tunanin lokaci baiyi ba?" Ido ya kura kura mata yace "Magajiya!" Kallansa tai bata amsa ba, yace " kinsan me kike anan kuwa? Kin tabbatar a hankalinki kike ko kuwa wani tugun muguntar kika shiryo?" Sansanyan murmushi ta sakar mai tace " ko d'aya na dai fahimci cewa aikinane wannan, sannan waye Turab? D'anka ne fa wanda daga shi baka kara samun wani ba, ta ya za'ai yara kwaya biyu ace mun kasa kula dasu? A wata masarautar sai kaga 'ya'yan sarki sunfi 30 amma mu a namu haryanzu biyu Allah ya bamu, me zaisa mu zauna muna samun sab'ani akan su?" Wata banzar dariya yai dan ko magajiya zata dafa Al-qur'ani bayajin zai yadda da wad'annan kalaman nata, ya tabbatar da abinda take shiryawa. Kallanta yai yace " yanzu me ake bukata?" Nan ta fara mai bayani, yace zai bada kudi ayi komai cikin girmamawa da matsayi. Tana fitowa yabi bayanta da kallo yana tunani, me ke faruwa? Ya tabbata Turab ko mai zai ce mata bazata taba yarda da zancen nan ba balle ma tasan sirrin mahaifiyarsa, me zai sa ta amince? Ya tabbatar akwai wani shirri da take yi. ********* Turab zaune agun hutawar daya saba zama ya saka ledar maganin nan a gaba a hannunsa yana kallo cilla maganin yai sama kad'an sannan ya cafe yace " kai kuma aikin me kakeyi?" Mikewa yai dan dole ne ya binciko maganin menene wannan. Bangarensa ya nufa, yana shiga Garzali ya taso ya gaidashi sannan ya sanar dashi nemansa da mahaifiyarsa takeyi. Mikamai maganin yai yace " so nake ka bincikomin maganin menene wannan yanzu, sannan ya zama sirri kar ka tambaya a gidan nan, kaje wajen gari" Garzali yace " to" sannan yai waje. Bangaren Mahaifiyarsa ya nufa, ta sa an shiryamai abinci, Turab ya zauna sannan ya gaisheta. Kallansa tai cikin kulawa daga dawowarsa daga kano har ya d'an fada, Lantana ta kalla tace " Lantana zubamai abincin." Turab ya kalli Lantana sannan yace " barshi zan zuba da kaina." Nan ya jawo plate ya d'ebi fankaso guda biyu ya zuba miyar taushe wanda yaji kaza. Hannunsa ya wanke sannan ya fara ci, sai da ya gama yasha zubo sannan ta kalleshi tace " ya kukai da Magajiyan?" Murmushi yai mata sannan yace " karki damu Umma, sirrin nan sai dai ta tafi dashi har kabarinta badai ta sanarma wani ba." Basira tace "me kake nufi? Kasan halin Magajiya fa?" Yace " Nasani Umma sanin ne ma ya sani fad'in haka, sirrinki datake tunanin amfani dashi wajen hanani auren Bilkisu da kuma sa Mai Martaba yin murabus wannan sirrin ba wani abu bane akan sirrinta da nake rike dashi, ke dai kawai ki kula da lafiyar wannan shine kadai abinda nake nema daga gareki." Kallansa tai cikin jin dadi da gamsuwa tace " maganar Mairo fa?" Yana murmushi yace " Umman Mairo, wai ni Umma daga ni da alama ba wanda kikeso sai Mairo ko?" Tace " Turab kenan, kasan yarinyar nan itace ta taimakeni har nakejin zaman gidan nan bai zaman min takura ba?itace ke d'ebe mana kewa daga ni har lantana, jinta nake kamar 'yata." Turab ya jinjina kai yace " haka ne, shi yasa akoda yaushe nake godiya gareta, na sani ta kula dake wanda ni da nake d'anki ban baki wannan kulawar ba." Basira ta kalleshi sai dai batai magana ba, sai dai yanayin kalamansa da yanda yake fitowa tasan magana ce wacce ke kwance a kasan zuciyarsa. Turab ya d'ago sannan yace " karki damu Umma, Insha Allah ba abinda zai faru sai alheri." Tace " Allah yasa." Zama sukai shi da Lantana da Basira sukai hira sosai sai da yaji la'asar tayi sannan ya fito. Yana shiga Garzali ya shigo falon, tare da mikamai maganin nan. Turab ya kalleshi yace "Maganin menene?" Garzali yai kasa dakai sannan yace " magani ne wanda zai halaka gab'obin jiki, ya hana mutum yin komai, ya kuma shanye mai b'arin jiki, a takaice dai guba ce mai illar gaske wanda samunta yake da matukar wahala." Turab idanunsa ya runtse da karfin gaske dan ji yake gaba daya kamar an kwara mai ruwa. Idanunsa a runtse yace " Ka yarda da sanin mai maganin daka tambaya?" Garzali yace " kaf garin nan an san dashi dan nima kaini gunsa akai, shikansa yayi mamakin ganina da maganin, sannan ya sanar dani maganin a hankali yake lahanta mutum ba wai tashi d'aya ba." Turab yace " jeka na gode." Garzali ya mike yai waje. Yafi minti goma idanunsa na runtse, wace irin matace wannan? Dan ya tabbatar itace tasa a ba Hajiya maganin nan, amma mahaifiyar mijinta? Wannan wace irin masifa ce?" Jiyai kansa ya sara, ya mike yai sallah ya dade yana addu'oi kafin ya shiga bandaki ya sakar ma kansa ruwa. Ruwa ne ke zuba a jikinsa hayi shiru yana tunani, ya dade sosai kafin ya fito. Shiryawa yai sosai cikin wata dakakiyar shaddarsa ruwan madara, hula da takalmi ya saka sannan ua saka agoggo. D'ankwalin khadija ya kalla ya dade yana kallan d'ankwalin kafin ya rufe kofar da karfi, takardar daya ajiye a gefen gado. B'angaren Magajiya ya nufa yana tafe cikin isa. Yayi sa'a Abdulmajid na zaune a gunta. Tana jin ance yazo sai dataji gabanta ya fad'i, yauce rana ta farko data taba jin shakkar zuwan wani d'an adam gunta ba sai yau. Ba shakka wannan abu ya kona mata rai. Abdulmajid yace " ya shigo." Turab ya shigo tare da sallama. Abdulmajid ya bugamai banzan kallo yace "ina zakaje haka?" Turab ya kalli Magajiya sannan ya kalli Abdulmajid yace " zance zanje." Abdulmajid ya tab'e baki sai kuma ya zabura yace"badai gun Mairo ta ba ko?" Turab ya kalleshi sannan ya maida idanunsa kan Magajiya datake kallansa yace" yau ba gunta zanje ba, gun Khadija zani." Tashin hankalin daya bayyana a idanuwan Magajiya ba'a magana, Kallansa tai tace " me? Khadija? Ba dai Khadija wacce take 'ya ga yayana ba?" Turab ya d'aga mata gira sannan yace " ya? Kin sanar ma Sarki akan maganar lefe na?" Abdulmajid ya sheke da dariya yace "Lalai Turab amma kai ba karamin had'amamen mutum bane, kana tunanin soyayya da aure wata a lokaci d'aya?" Turab yai murmushi yace " ba'ayi ne? Da farko dai ni d'in mijin mata hud'u ne banda kwarkwarori." Abdulmajid yace " wannan damuwarka ce sai dai ka fita hanyar kanwata dan badai yar uwata ba kai ko kunya ma damu zaka had'a zuri'a?" Magajiga kam kallansa take cikin idanunta da suka canza kala wanda bakin ciki ne karara ne d'auke a idanun. Turab ya kalli Abdulmajid sannan ya kalli Magajiya tare da ciro ledar maganin nan. Ruwan dake gaban Andulmajid ya jawo ya zuba a kofi sannan ya zuba maganin nan. Magajiya ta kalleshi tace " meye hakan kuma?" Mika mata kofin yai yace " Umma sha." Wani banzan kallo tamai tace " a gabana ka zuba magani kace insha? Nasan ko maganin halaka ne?" Kai ya d'an langwab'e yace " kuma fa haka ne, kar in baki maganin dazai kwantar dake ya kashe miki gab'obin jiki sannan ya hanaki magana, ya kuma hana kwakwalwarki aiki yanda ya kamata." Gabanta ne ya shiga fad'uwa, daurewa tai ta saki murmushi zatai magana Abdulmajid yace" ansha karya, yanzu kai kana tunanin akwau irin wannan maganin a duniya? Sannan in akwai ma mai zai sa ka saku?" Turab ya kalli Abdulmajid yace " shine ai abin tambayar, Umma ya akai kika samu wannan maganin?" Kallansa tai tare da fito da idanuwanta, daurewa tai tai wani dariya tace " Turab kenan, kanasan zolaya, yanzu ka shigo da magani kace ni na baka?" Turab yace " kin manta? Ke kika bani a sanda muka had'u a b'angaren Hajiya?" Magajiya tace " ni bansan wannan zancen ba, sannan mai zai sani in baka?" Yace " shine abin tambayar? Mai zaisa ki bani? Sannan me na tare miki da zaki bani irin wannan abin? Karfa ki manta nid'in d'a ne a gunki." Idanu suka kafama juna dan magana ce suke yinta a juye wanda su biyu ne suka san me suke nufi, ita tasan Turab sanar da ita yake abinda ta sa akeba Hajiya, shi kuma so yake yaji menene dalilinta na neman halaka kakarsa? Wacce take uwa a gareta? Abdulmajid ne ya kallesu, kana kallan yanda suke kallan juna kasan kallo ne mai tatare da ma'anoni kala kala, hannu yasa ya daki kafadar Abu Turab yace " Turab bakada hankalu ne? Umma kakema wannan kallan?" Magajiya ta juya kai sannan ta kalleshi tace " bansan me kake cewa ba Turab." Yace " wasa nake yi nima, ya maganar lefen?" Tace " na d'auka mungama wannan maganar hakki nane a matsayina na mahaifiyarka ai inyima lefe." Yace " haka ne, yauwa bari na kira Gimbiya na tabbata ta damu da jina shiru tunda na dawo, bari nai amfani da wayar b'angarenki." Magajiya ta gama cika fal, Abdulmajid mamaki ma ya hanashi magana, kallan sa yai harya mike yai falonta, sannan ya kalli kofin ya d'auka yana kallan ruwan ciki, yace "Umma me wannan yaran yake cewa?" Sam bataji ma me yake cewa ba dan ta tafi dogon tunani. Kallanta yai ganin yanda ta tafi tunani ya sa jikinsa yai sanyi, bai taba ganin ta haka ba, me ke faruwa? Me zaisa Ummansa tama Turab lefe bayan tasan yanda ta tsani auren nan? *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *60* Abdulmajid ya kara kallan Magajiya yace " Umma wai meke faruwa?" Tsawa yaji ta dakamai tace " Fita ka bani guri." Tsananin mamaki ne ma ya hanashi d'auke ido daga kanta, me yai? Yauce ranar daya tabaji tamai tsawa haka balle ma akan wani Abu Turab? Mikewa yai rai a b'ace yai waje. Ko bi ta kansa batai ba ta sa kafa tayi ball da wannan kofin, mikewa tai ta nufi falonta. Turab kam number Bilkisu ya danna, ta dade kafin a d'aga, gaisheshi akai sannan akace wanene?" Turab yace " Ina Gimbiya?" Daga can akace bari a sanar mata, waz'ace?" yace "Abu Turab." Da sauri mai maganar ta gaisheshi sannan ta ajiye kan wayar a gefe tai cikin d'aki da sauri. Gimbiya na Kwance rike da wani littafi tana karantawa. Bayan yarinyar ta nemi izini ta shigo ta tsugunna sannan tace "Gimbiya, yarima ne ya kira waya." Mikewa tai zaune da sauri tace " Turab?" Yarinyar tace " eh Gimbiya." Da sauri ta juya zata sauko, sai kuma ta koma ta zauna tace jekinkice ina zuwa. Yarinyar ta amsa da to sannan ta mike. Bilkisu sai da ta d'an dade a zaune sannan ta sauko a hankali ta fito. Sallamar duk masu kula da ita wad'anda ke falon tai sannan ta d'auki wayar, cikin kasalaliyar murya tace " Barkanka da Warhaka." Turab wanda yasan dolene ya jira saboda mulki, yai murmushi sannan yace " na d'au lokaci kafin na kira Gimbiya, ina fatan za'amin afuwa." "Hmmm za'a duba uzurunka sai a maka." Turab ya kalli kofa dan yasan tabbas Magagiya zata leko dan ganin me yake yi. Gefen fuskarsa ya d'am shafa sannan yace " Abubuwa ne wad'anda nikaina banyi tsamanni ba suka dinga bulbulowa wad'anda suka rike tunanina." Tace " Hmm yanzu fa? Ka warware komai?" Yai shiru, hakan yasa tace " Karka damu nasan zaka iya, koma menene, kardai kacemin baka yarda da kanka ba?" Turab ya kalle gefen kofa inda ya hango inuwar Magajiya, yiyai kamar bai ganta ba, murmushi yai sannan ya gyara zamansa irin mai jin shaukin nan yace " Kuma fa haka ne, ya kamata in zama mutum na farko mai yadda da kansa." Tace " A koda yaushe ka dinga tunawa ina tare da kai akan komai, duk da ayanzu bazan iya taimaka maka ba, bazan kuma iya kula da kai ba sai dai inaso kasa a ranka akwai wacce take tare da kai a koda yaushe." Har zuwarshi sai da yaji wani sanyi ba shakka Bilkisu macece wacce ta san kanta ya tabbata zasu zauna lafiya, sannan yana ji a jikinsa ita alheri ce a gareshi. Jiyai tace " kayi shiru? Ba dai kalamai na......" Katseta yai da sauri yace " wannan layin nawa ne bance ki fada ba." Tace " layin me?" Yace " Kalamanki sun ratsani na kuma ji dadi, ba haka zaki ce ba?" Bata san sanda tai dariya ba, tace " mene? Haka nace ma?" Yace " sosai ma." Gani inuwar Magajiya yai ta juya. Fuska ta rufe kamar yana ganinta, Turab yace " zan kiraki zuwa ko zuwa anjima ko zuwa gobe." Tace " Karka damu dani, yanzu ma da mukai magana ya isa, duk sanda ka samu sarari ka kirani." Yace " Nagode, ki gaida Munnira." Bai jira ta amsa da to ba ma ya ajiye kan wayar sannan ya mike. Magajiya kam ta gama kuluwa da alama ma soyayya suke da yarinyar, itakam duk duniya ba wanda ta tsana yanzu irin wannan dan banzan yaran, ko ganinsa batasan yi, wai kamar ita ace ta zauna yaro yana raina mata hankali? Dolene ta nemi abinda zatai amfani dashi ko da yake ai ta shirya da auransa hmmm tai kwafa tace a ranar aure ka zai kasance jana'izar ka. Ta na kokarin shiga d'akinta yace " Umma me kike anan?" Juyowa tai fuskarta a had'e sai kuma ta saki fuska tace " Na d'auka ka tafi ai, ashe kana ciki?" Turab yace " na d'auka zakizo ku gaisa da sirikarki, ko zaki koma in kira miki ita?" Idanunta ne suka canza har fuskarta sai data nuna bacin ranta, daurewa tai ta saki yake tace " Meye abin azarbabi bayan nice shugabar kai lefe?" Kai ya jinjina sannan ya dawo gabanta, fuskarsa a hade tare da kallanta. Kallansa tai tace " ya akai kuma?" Wani banzan murmushi yai yace " maganinki da kika sa a dinga sama Hajiya ina tunanin sai kinsa a nemo wani." Idanunta ne sukai rawa alamar mara gaskiya tace " me kake fada?" Yace " ba abinda nake fada ina dai sanar dakeni duk wanda ya maida Hajiya haka wallahi wannan rantsuwa ce nai bazan taba kyaleshi ba, sai na sa anmai hukunci daidai da abinda ya aikata, ko da kuwa Umma tace Basira ta aikata hakan, duk da nasan bazata taba zalintar d'an adam ba kamar wasu." Magajiya ta kalleshi sannan ta saki wanj banzan murmushi na rainin hankali tace " Ko nima zan tayaka d'aukan hukuncin, sai dai ka tabbatar kana da karfi na hukunta mai laifin? Ba wai karfi na jiki nake nufi ba." Turab ya kalli kwayar idanunta yace " Ahhh to wa ya sani?" sannan ya murmusa yace " kece kika sa aka fara game d'in, sai dai ni nake da ikon tsayar dashi, sannan inaso ki tabbatar idanunki na nan a bud'e har sanda zan tsayar da wasan, zakiga inda mara karfi yake kaskantar da masu karfi." Magajiya tama kasa magana kallansa kawai takeyi. Turab ya juya ya fara tafiya, har yayi nisa ya juyo yace " Ahh ki gaida Khadija banaji zan iya zuwa yau ba, ko da yake bata sani ba." Kallansa tai cikin takaici tace " Kana tunanin ita Khadijan yarda zatai dakai?" Wata dariya ya saki yace " Khadijan? Kin tabbatar Khadijan da kika sani kike fad'a? Ahh Umma ya zakiyi? Dan Khadija ba sai na tambayeta ba dan nasan abinda ke ranta." Ya juya. Jiyai tace " Lalai na yarda yarinta na damunka kanka kuma na rawa, ya zakayi to? Dan kuwa an kusa sa ranarta da Saifullahi." Bai san me yasa ba amma sai dayaji wani abu ya taba zuciyarsa. Sai da ya daure ya juyo fuskarsa d'auke da murmushin da yake iya lab'ansa yace " ai mace sai anyi aurenta an shafa fatiha ake tabbatar da mijinta." Ya juya ya fita. Agogon dake manne a bangon gun tasa hannu ta fizgo sannan ta bugashi a kasa, kanta ta dafe sannan ta shiga d'akinta, da karfi ta bugo kofar. Ji take kamar ta saki kara. ********** Turab na fita ya dafe kansa, ba shakka matarnan bala'ice, wacce mutum zai dinga neman tsari da ita (irinsu sai a karshe zakaji suna cewa sharrin shaid'an ne) Khadija ya hango daga nesa, tafe take kamar mara laka a jiki, da alama batajin dadi. Me ya sameta? Juyawa yai da sauri dan bama yasan zuciyarsa ta nemi yin rawa saboda ita. Ganin ya juya zai wuce yasa ta tsaya cak, idanunta ne suka ciciko dan taga da alama goje mata yake sanyi, ita kanta bataso shigowa ba sai dai dolene ta fadama Magajiya akan bazata auri Saif ba, ita dai su barta ta karashi rayuwarta a haka, inta tunan mumunan abunda suka aikata ji take baxata iya kallan wata zuri'ar da sunan mutum na gari ba. Ko me ya tuna sai kuma ya juyo, kallan kallo sukayi daga nesa. Juyawa yai a hankali ya fara tafiya. Bata san tana binsa ta baya ba, ji take ganinsa kamar yanasa taji abinda ke tokare a ranta na raguwa. Yasan tana binsa sai dai ya rasa dalilinsa na nuna mata bai sani ba, sannan ya rasa dalilinsa nayin tafiya a hankali cikin saibi. Har ya isa bangaren Hajiya. Yarinyar nan ya gani tana shara, kallanta yai yace " ajiye tsintsiyar ki kuma biyoni." Gabanta ne ya fadi ta kalleshi tace "Yarima laifi nai?" Wani mugun kallo ya mata, da sauri tai kasa da kai tace "Tuba nake Yarima." Ajiye tsintsiyar tai tabi bayansa. B'angaren sa ya nufa da ita, suna shiga cikin falo ya d'aga hannu cikin zafin rai zai kai mata mari, idanunta ta runtse dan ta gama sadaukarwa. Saura kiris ya mareta sai kuma ya tsaya cikin tsananin b'acin rai. A hankali ta bud'e idanunta ta tsugunna da sauri tace " Tuba nake ranka ya dade." *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *61* Jin bataji saukan mari ba yasa ta bud'e ido a hankali, kallansa tai sannan tai saurin zubewa a kasa ta saki wani irin kuka. Turab idanunsa ne suka canza, kallo d'aya zakamai ka tabbatar da tsantsar b'acin rai, maganin nan ya cilla mata. A tsorace ta d'ago jiginta ya hau karkarwa. Cikin kakkausar murya yace " Waye ya saki?" ba wai dan baisan amsar bane, a'a yanaso yasan ko tana danasanin abinda takeyi. Kasa ta karayi tana kuka sosai tace " Ranka ya dade ka yafe min wlh in na fad'a kasheni za'ai, sannan mahaifina karshensa yazo." Magajiya? D'agowa tai da sauri jin abinda yace, yanayin kallan da tai yasan dama abinda yake zargi haka ne, kusa da kafaffunsa ta matso tace " Ranka ya dade wlh nima ba'a san raina nakeyi ba, mahaifina na bukatar aiki na gaggawa a asibiti shine akace in ina sa maganin nan za'a biyamai kud'in aiki, sannan komai ua faru in sanar da ita. Fuskarsa ya shafa da hannayensa biyu a ransa yace Inalilahi wa ina ilaihi raji'un. Zama yai a kan kujera sannan yace " me ya faru tsakanin Hajiya da Magajiya?gaskiya nakeso ki fadamin, ni zan taimakeki, zan kuma bayar da kudin aikin." Tana kuka ta girgiza kai tace " wlh ban sani ba, nadai san a ranar da Umma Rabi tazo a ranar ta aika a kira Magajiya, sannan daga ranar aka fara sani aikin." Turab ya kalleta yace " naji, zan sa Lantana ta koma dake bangaren Hajiya da kula da ita, zan gani ko kinyi dana sanin abinda kika aikata, sannan ki jira hukuncin da zansa a yanke miki, mahaifinki ni zan taimaka mai sai dai ke dole ki fuskanci hukunci." Kuka take sosai tace " na sani Ranka ya dade, na gode kwarai da cetoni da kai daga cikin masifa." Turab yace ta tashi ta tafi. Fitowa yai, ya nufi can cikin gida bangaren kannen mahaifinsa dan zuwa gun Umma Rabi. Ko Garzali baya yarda ya biyoshi duk da kuwa ya yarda da shi. ********* Khadija kuwa ganin Turab ya shiga bangaren Hajiya yasa ta juya. Har zata wuce bangaren Abdulmajid sai kuma ta karkata ta shiga. Bayan an sanar da zuwanta, Abdulmajid dake zaune abin duniya ya dameshi yace ta shigo. Khadija ta shiga, kallan bangarensa tai sannan a ranta tace " yafi na ya Turab kyau sosai, da ban kula da hakan ba amma yanzu na gani, ya zakai in kaji kai ba toshen gidan nan bane?" Idanu ta kura mai tana wannan tunanin, ji tai tsananin tausayinsa ya kamata. Batasan ma ya miko yazo kusa da ita ba, sai jitai yasa kafa ya d'an harbota. Kallansa tai tace " Yaya." Abdulmajid ya hard'e hannayensa ya shiga zagayeta yana kallanta yace " me ya kawoki? Ba dai zuwa kikai akan rabamu da Mairo ba?" Hannu tasa ta riko rigarsa tace " Yaya wannan zagayen fa? Ai sai jiri ya kamani." Murmushi yai sannan ya koma ya zauna. Kallansa ta karayi a ranta tace " ya ya zanyi? in har kaji abinda suka maka wace rayuwa zaka shiga? Alokacin ba ka da wanda zaka gani kaji dadi, komai da kake tunanin naka ne a lokacin xakaga babu abu ko d'aya daya kasance naka, dama ace Mairo na sanshi ne....." Khadija meye hakan? Abinda ya fadane ya dawo da ita daga tunaninta. Fara'a ta saki sannan tazo ta zauna kusa dashi tace " Yaya." Ya kalleta yace " menene? Nifa na fara shakkar me kikazo dashi naga sai wani kafeni da ido kikeyi." Murmushi tai tace " yanzu ace kai ba dan sarki bane wace rayuwa kake tunanin zakai?" Dariya ya saki sosai yace " ban taba wannan tunanin ba, dan tun ina d'an shekara uku Umma ta fara horar dani akan magajin sarki, kinga kuwa banda wannan lokacin." Khadija ta jinjina kai tace " Haka ne, amma ka taba tunanin rasa mulki?" Wani kallo ya mata yace "Khadija meke damunki? Kinsan tun ina dan shekara uku Umma take sanar dani ni kadai ne magajin sarki, shi kanshi Abba a lokacin nunamin yake nine magajinsa, a haka na taso har sai bayan zuwan Turab sannan na fahimci canji daga gun Mahaifina wanda hakan na kona min rai, sam ya daina wasa dani gaisuwa ce kawai ke had'amu, bayan da shi dakanshi yake aikawa a kirani." Yai wani murmushin takaici yace " Khadija duk wani abu na rayuwata a da ina yinsa ne dan faranta ran mahaifina, burina naga ya dubeni yacemin Abdulmajid kayi daidai, sai dai inaa duk wani abu dazanyi bana birgeshi, ko jarabawa ta na kawomai banaji ma yana bud'ewa...." Wani abu ya had'iya sannan ya kalleta, hawaye ne yaga ya zubo mata. Harararta yai yace " tausayi na kike?" Shiru tai batace komai ba. Yai murmushi yace " tundaga lokacin na tsani Abu Turab tsana mai yawa sannan akoda yaushe Umma na sanar dani shi din fa makiyinane, kar na kuskura ba barshi." Yai ajiyar zuciya yace " kinsan me?" Kai ta girgiza alamar a'a Ya matso alamar rad'a yace " ko kiran mata da nakeyi bangarena yi nakeyi dan in batama Sarki yai ko naki dadin rashin damuwa dani dayakeyi." Idanu ta rufe a hankali wasu zafaffan hawaye suka biyo mata, kallanta yai yace " Karki damu Khadija, na saba da rayuwa, kinsan tunda nake a gidan nan ba wanda ya taba tambayata ya nake? Tambaya ta kulawa, ina nufin Umma na ko Abba na, ita burinta shine in zama abinda takeso, shikuma dama bana cikin shafinsa." Hawayenta ta share tace " Yaya me yasa baka taba fad'amin ba?" Dariya yai sannan ya mike yace " na fizan na zama bad guy, hakan ne zaisa in rage takaicin abinda ke raina, sai dai Khadija kiyi hakuri amma bazan taba ba Abu Turab Mairo ba, ya kwacemin uba, mutane, na bar masa amma banda wannan." Jitai tama kasa magana, me yasa itama a koda yaushe takejin zafinsa? Gani take baya kyautawa sannan shidin mutumin banza ne? Ashe bakincikin dake ransa ne yake amfani dashi dan kuntatawa na kusa dashi? Ya zaiyi in yaji sirrin nan? Daurewa tai tace " Yaya kana tunanin Mairo zata soka? Bayan kai din mutum ne wanda yake had'uwa da Magajiya su aikata abinda bai daceba na zalunci?" Yace "Ahhh zalunci? Hmmm Khadija kenan bana tunanin kinsan Umma." Kallansa tai tace " bansan ta ba sannan bana bukatar Saninta, sannan kaima Yaya zuciyarka na neman riked'ewa gaba d'aya ta koma ta Umma, ka gaggauta kaucewa daga sharrinta." Murmushi yai sai dai baice komai ba, a ransa yace "hakan na nufin in bijiremata ita kuma ta yarda ni, ita kadan da nake sa rai tana sona itama ta juyamin baya." Khadija ta mike tare da kallansa tace " Yaya zanje gurin Umma Magajiya ne, akan maganar aurena da Saif." Yace " Ya ya? Maganar auren an kusa ne?" Kai ta girgiza tace " a'a." Juyawa tai ta fita, aranta tana mai fatan kub'uta daga sharrin Magajiya da Mahaifinsu." ******** Falon yai tsit kamar ba kowa a ciki, Umma Rabi tai shiru kamar ruwa ya cinyeta sannan ta d'ago ta kalleshi. Abu Turab yace " Umma ki taimaka ki sanar dani, Hajiya na cikin wani hali." Tace " Turab sirri ne...." Yace "wa ke zancen Sirri rayuwar Hajiya na cikin had'ari?" Umma Rabi tai shiru kafin can ta d'ago ta kalleshi. Nan ta sanar da shi abinda ta sani. Shiru yai kafin yace "ita waccan d'in wacece? Wacce ta aiko da wasikar?" Umma Rabi tace " ban santa ba sai dai kafin Hajiya ta fara rashin lafiya da yamma na koma gunta, a lokacin ne ta sanar dani wani sirri wanda ahi nake tsoron sanar dakai." Yace " na menene?" Ta dade batace komai ba, yace Umma dan Allah ki fadamin. Tace " ka tabbatar zaka iya ja da Magajiya?" Yace " kwarai kuwa." Yanda yai maganar ya bata kwarin gwiwa tace " Maganin da ake zubawa sarki na hana d'aukan ciki ne." Tashin hankali. Bakinsa ne ya shiga rawa yama rasa mai zaice. Umma Rabi ta kalleshi sai dai itama batasan me zatace mai ba, a hankalu tace " ni kaina ina zargin ciwon Hajiya da Magajiya, sai dai banida shaida sannan bansan wa zan tara da maganar ba." Turab mikewa yai kamar wanda bashida laka a jikinsa. Tafiya kawai ya keyi yana tunanin wannan al'amari. Jiyai kansa ya d'au wani zafi, tsayawa yai a jikin wata bishiya ya dafata, addu'a kawai yakeyi Dan neman sauki a zuciyarsa. Ya dade sosai kafin ya nufi bangaren Hajiya. Hajiya kam babu, dan jikinta ba dadi to abune da anriga an gama halakata, ba shakka bai taba ganin mutum irin Magajiya ba, kenan duk wanda yasan sirrita ajali shine zai biyoshi? Kallo d'aya zakama Hajiya kasan inaa sai dai wani ikon Allah. *********** Magajiya na kwance a d'aki dan tun tafiyar Turab takejinta haka, a kwance take taji sallamar Khadija. Daurewa tai ta mike zaune, Khadija ta shigo. Bayan ta gaisheta, Magajiya tace " Khadijata ina kika shiga? Kwana biyu sam ban ganki ba." Khadija fuskarta a had'e tace "Ina gida." Magajiya ta kalleta cikin kulawa ganin duk ta rame, tace " Khadija mai kike tunani akan dawowa nan da zama kafin lokacin aurenki?" Khadija ta kalleta duk da gabanta na fad'uwa saboda tsananin kwarjini da Allah yaba Magajiya ta daure tace " Dama zuwa nai in fadamiki akan bazan auri Saifullahi ba." Magajiya ta zaro ido tace " mene? Wace irin banzar magana ce hakan?" Khadija tace " dama abinda nazo fadamiki kenan." Magajiya ranta ya b'aci tace " Akan Abu Turab?" D'agowa Khadija tai ta kalleta, Magajiya tace " ke kina tunanin zan baki Abu Turab?" Jitai zuciyarta ta dake tace " ina fa zance Ya Turab zan aura? In ba so nake ku halakashi ba?" Magajiya ta kalleta cikin tsananin takaici tace " in kin san da haka to kiyi gaggawar cireshi a ranki." Khadija jitai ranta ya b'aci wato duk abinda sukeyi baya damunsu? Tace zasu halakashi amma ko a jikinta. Sun biyu suna neman ruguza rayuwar mutane dayawa, na farko sun gama cin amanar sarki, sun jefa Abdulmajid cikin halaka, suna neman jefata sannan sun takurawa wanda yake jinin gidan, suna neman halakashi. Ita kanta batasan tace " To ko Ya Abdulmajid zan aura." Jitai gabanta yayi wani fad'uwa, mikewa tai tace " wani irin hauka kike fad'a, bakida hankali ne? Ko kanki me ya zare?" Khadija tace " in har ba Ya Abdulmajid ko Ya Turab zan auraba inaso ku barni, banaji zan yi aure har karshen rayuwata dan bazan iya auren wani da hali irin na mahaifina ba." Magajiya tace " Khadija? Me kike cewa?" Mikewa tai saboda ta fara jin dakewar tata na neman gazawa tace " na barki lafiya." Magajiya mamaki ma ya hanata magana sam, anya Khadija ce? Ba waccan tsinanen yaran bane ya zigata kuwa? Yace tace a aura mata Abdulmajid? Jitai idanunta sun daina ganin komai sai duhu, baya tai lyuuu kamat zata fadi sai kuma tai saurin rike gadon tana maida numfashi. Cikin wata sarkakiyar murha tace " *ABU TURABBBBBBBBB*" Nima na tayata fada *ABU TURAB😂* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *62* Khadija tana fita ta samu guri a waje ta xauna, jitai jikinta duk ya kaure da rawa, ba shakka wannan ce rana ta farko da tai tafa kukewa tai ma wanda ya girmeta magana irin haka, balle Magajiya mace mai tsananin kwarjini da mulki. Mikewa tai a hankali, so take ta samu Abu Turab taji a wani mataki na aure ya d'auka tsakaninsa da Mairo? Dan ba shakka tana san d'an uwanta ya aureta ko dan ranar da wannan sirri ya bayyana ya zama akwai wanda zai gani yaji dadi, ta tabbata in tai magana gani za'ai kamar kishi ne ke damunta sai dai ko d'aya, tasan akwai kishi na wanda take tsananin so shikuma ba ita yake so ba, sai dai a yanzu burinta tai kokarin ganin ta gyara wani abu ko yaya ne na daga cikin laifukan da aka aikata. Bangarensa ta nufa, har takai hannu zata kwankwasa ta fasa saboda batasan da wace kalmar zata fara masa magana ba, a hankali ta juya cikin damuwa. Idanu ta zaro, kallanta yai sannan ya kalli kofar, miyau ta had'iya sannan tace " Ya Turab." Kallanta ya sakeyi sannan yace "Lafiya?" daga bangaren Hajiya yake sam bayasan magana. Khadija tai shiru tana wasa da hannayenta, tunanin abinda zata cemai takeyi. Ta gefenta ya wuce zai shiga ciki ganin batada niyyar magana. Itama ganin haka yasa tai saurin cewa "Magana nakeso muyi." Juyowa yai ya kalleta sannan ya kauda kai yace "Banaji akwai wata magana da zamuyi." Kasa tai da kai tare da jinjina kai cikin rashin jin dadin abinda ya fada tace " haka ne, na tabbatar ba wata magana datai saura tsakaninmu, sai dai inaso ka bani ko minti goma ne." Harshensa ya zaro kadan ya d'an lashi lab'ansa da suka bushe yace muje. Mai makon yai ciki sai taga ya juya ya fara tafiya. Bata tambayi inda zasuba itama binsa kawai tai a baya. A hankali suke tafiya yana gaba daga gefen dama, ita kuma tana bayansa daga gefen hagu, tafiya kawai yakeyi. Yana kara tattaro duk wani tugu da ya sani wanda Magajiya ta aikata ita da yayanta wanda ya kasance mahaifin yarinyar dayafiso a rayuwa. Ta yaya zai iya zaman aure da ita ko bayan komai ya kamala? In har ya sa akama mahaifinta da Magajiya hukunci ta yaya zai iya kallanta da sunan soyayya? Itama ta yaya zata iya kallan wanda ya ruguza rayuwar gidansu da sunan soyayya? Ai duk san da takemai bai kai na iyayenta ba, shima haka, duk sanda yake mata bazai taba kwatanta shi da wanda yakema mahaifiyarsa ba. Juyowa yai ya kalleta, ganin irin kallan da yake mata yasa jikinta yai wani irin sanyi. Baice mata komai ba sai nuna mata inda zasu shiga dayai. Kallan gurin tai, inda ya ke hutawa ne, sai daya shiga ta bi bayansa. Can yaje ya zauna akan kujerar dake gun. Rasa inda zata zauna tai dan kujerar gud'a d'aya ce a gun doguwa. Kallanta yai sannan ya mata alama da kai akan ta zauna daga gefe. Nan ta zauna, ta d'an kalli sararin samaniya, kasancewar yamma ce garin yayi luf abin sha'awa, bare lokacin na zafi ne, iska tana kad'awa a hankali. Jitai yace " ina jinki." Khadija ta kalleshi kallo na tsananin kauna, inama lokacin da suke yara ya dawo? Lokacin da suke kullum tare, cikin tsananin bege da kulawa. Kin kafeni da ido bakice komai ba. Khadija ta kakaro murmushi tace " Ba fara'a yanzu a tsakaninmu." Kallanta yai sai dai baice komai ba ya maida kansa inda yake kallo da. Murmushi ta sake yi na tausayin kanta cikin wani yanayi ta fara cewa " sa dayawa ina tunanin ina ma, ina ma ban sanka ba? Ina ma banida had'i da wannan gidan? Inama da naje kano ina karama ban dawo ba." Tacigaba bayan ta d'an had'a hannayenta gu d'aya. "Yaya na rasa wace irin mummunan kaddara ce tsakaninmu? Banida abinda xancema na abubuwan da mahaifana suka aikata, bani kuma da bakin baka hakuri akanshi, sai dai zam baka hakuri akan abubuwa gudan biyu." Hawayene suka zubo mata ta sa hannu ta sharesu tace " Yaya kayi hakuri akan abinda Ya Abdulmajid ya maka, ba wai ina baka hakuri bane dan ka yafemai a'a ina baka ne saboda neman sassauci akansa, ina tsananin tausayinka sai dai ina tausayin Ya Abdulmajid." Juyowa yai ya kalleta, da alama tasan komai, dama ranad da ta fad'o musu gaban mota tai wannan firucin ya tabbata akwai wani abu da ya sani." Idanunsa na kanta yace " kin san komai kenan da alama." Hawayenta ta sake sharewa tace " Yaya wancan sokon yayan nawa baisan komai ba, baisan abinda suka aikata mai ba, tunda yake bai taba keran wacce ta d'au cikinsa na wata tara da sunan uwa ba, bai taba yi mata wani abu ba wanda d'a ya kamata yama uwarsa ba, ko magana tamai gani yake matsayinsa ya wuce a nemi bashi shawara, wancan soko yaya baisan matsayin da yake takama dashiba ba nashi bane, matar da yake kokarin faran tawa rai a koda yaushe baisan amfani take dashi dan cikar burinta bawai dan so ba, Yaya Turab sannan wancan sokon ya gama mutuwa akan san wacce bata sansa, tunda yake a rayuwarsa banaji akwai mutum d'aya wanda ya kasance yana kaunarsa kauna ta yanda yake bawai dan tushensa ba ko dan halayensa ba,yaya wancan sokon d'an uwa nane jini nane wanda ni kaina......." Kuka ne ya ci karfinta wanta take yinshi daga cikin zuciyarta kuka mai taba zuciyar mai sauraro. Duk yanda yaso ya jure ya kasa dan kukan sosai yake taba ransa ba shakka shi kansa yana tausayin Abdulmajid, mikewa yai ya nemi hanyar fita. Cak ya tsaya dan jiyai bazai iya fita ba tana irin wannan kukan. Handkerchief ya zaro daga cikin aljihunsa na wando ya nufo inda take. " Ungo." abinda ya fada kenan yana mika mata. A hankali ta d'ago sannan tasa hannu ta amsa. Juyawa yai zai fita, da sauri tasa hannu ta riko rigarsa. Turab ya tsaya sai dai bai juyo ba. Saukowa tai kasa ba tare da saninsa ba ta sanya gwiwowinta biyu a kasa. Tace " Ya Turab." Juyowa yai kallan mamaki ya mata gani gwiwowinta biyu a kasa. Yace " meye hakan?" Tace " kasa ama duk wani laifi a cikinsu hukunci sai dai dan Allah yaya ka hakura kaima da abu d'aya, kana da komai a rayuwarnan. Mulki, uwa ta kwarai, mata, sannan dukiya da ilimi da kuma masoya, dan Allah ka sadaukarwa Ya Abdulmajid da abu d'aya na daga cikin wad'an nan abubuwan da Allah ya azurtaka dashi ka bar masa Mairo kad'ai, ita kadai, in tana tare dashi gani nake ko wani abu ne zai sameshi zai jure sannan ko wani hukunci aka mai zai yi kokarin jureshi." A hankali ya furzo da wata iska sannan yasa hannayensa biyu ya d'agota, kallanta yai ido cikin ido, yace" bazan yi miki dogon bayani ba, ba kuma zanyi duk wani abu da kikeso ba, abu d'aya na sani shine duk wani mai laifi zan sa a hukuntashi indai da raina, akan ganin bayan Magajiya even u i will have to use u." Ba tare da wani tunani ba tace " use me ya Turab, kayi amfani dani ta kowace hanya da kakeso, bazai damen ba, me kake tunanin zanyi?." Wani murmushi wanda ni kaina bansan ma'anarsa ba yai sannan yace " even if i hurt u?" Kallansa tai sannan ta ce " please yaya hurt me." Shiru yai yana kallanta dan tabbas kalmar data fada har zuciyarsa ya jita. Murmushi ta mai sannan tace " Yaya a koda yaushe zam kasance mai ma addu'a." Wuceshi tai ya fara tafiya, tana tafe hawaye na zubo mata, ji take kamar yau shine rana ta karshe da zasuyi magana irin haka, itakam tasan farinciki? Bataji zata sameshi a duniya. Idanu ya runtse dan tabbas yana bala'in san Khadija, ya tabbatar yauce rana ta karshe da zasu zauna kamar haka, Allah ka bani ikon yin abinda ya dace, abinda ya fada kenan sannan ya juya. ********* Duk yanda taso tai bacci ta kasa, juyi kawai take a kan gado tana tunanin abinda ya cancanta. Tabbas dolene ta gajarta rayuwar Abu Turab, a ranar auransa dolene ta kaudashi ko ta samu salama, duk sanda bacci ya d'auketa sai taga Abu Turab a gabanta ya sa hannu ya shake mata wuya, dole ta tashi daga barcin. Wannan abu ya dameta. Da safe ta shirya tsaf dan ta gama yanke hukuncin yin komai da Abu Turab zai umarta na lefensa har ta samu a zo bikinshi ita kuma ta sa Hisham ya aiwatar da abinda ya dace. Sai yamma ta samu nutsuwa dan tana ta yin aike. Ta zuba abinci zataci kenan aka sanar da ita zuwan Abu Turab. Ta rasa dalili duk sanda taji zuwansa kwanan nan sai taji gabanta na fad'uwa. Mikewa tai ta gyara jikinta dan batasan ya fahimci wani abun. Zama tai irin zaman data saba. Turab ya shigo sannan ya gaisheta. Amsawa tai cikin isa sannan tace " ya akai?" Murmushi ya sakar mata yace " na d'auka farin ciki zakiyi da ganina? Banji dadi ba ganin ba kiyi farincikin zuwana ba." Tace " ina fa? Ka taba ganin inda uwa tayi bakin ciki da zuwan d'anta?" Yace " haka ne fa kuma, ya an fara had'a lefen?" Ta kalleshi sai dai batace komai ba. Yace " Jiya naga Khadija ai, nan tazo ko ganina tazo yi kadai?" Magajiya wani abu ne yazo mata ta kalleshi tace " gunka ta fara zuwa kafin tazo nan ko?" Turab ya kalleta dan bai fahimceta ba, tace " ai na sani, dama ni nasan yarinyar nan da ba ruwanta ba yanda za'ai tazo min da wannan banzan zancen." Turab ya fahimcu Khadija magana tai da Magajiga wanda da alama abin ya sosa ranta. Yace " hmmm ai banyi tunanin wannan abin zai b'ata miki rai ba......" Magajiya tai dariya kadan tace " kana tunanin in ka zugata karta auri saif zan amince dakai ne? Meye manufarka da neman had'a auran ta da Abdulmajid?" Sai yanzu ya fahimta baisan sanda yai wata dariya ba, Khadija? He can't believe that naive girl can...... Magajiya ce ta katseshi da cewa " In har kanasan Sirrin mahaifiyarka da kuma auranka ya yiwu karka kuskura ka kara sa Khadija cikin al'amuran mu." Turab ya kara murmusawa yace " me? Akwai wani dalili ne dazai hana auransu?" Idanu ta zaro tace " baka da hankali ne?" Ya dan tabe baki yace " ban fahimta ba? Akwai dalili ne?" Magajiya ta kalleshi tace " ba wani dalili kana san ka hadasu aure bayan ba san juna suke ba?" "Ooooo soyayya? Banaji dama a aure irin namu ana neman soyayya, kinsan da haka kike neman had'a Abdulmajid da Gimbiya? Hmm banaji kema auran so kikai." Mikewa tai da sauri tai wani murmushi wanda yake iya lab'anta tace " in ma hakan ne ina tunanin bakada hakki akan auransu, Khadija da Abdulmajid ina tunanin duk 'ya'yanmu ne basuda had'i dakai." Turab ya jinjina kai yace " kuma haka ne fa." Tace " ba sai ka kara zuwa bangarena ba, in na gama had'a lefenka zan aika ma uwarka ta gani." Ta juya tai ciki. Turab ya bita da kallo......... *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *63* Kallansa tai tare da yin ajiyar zuciya tace " wai ni Abdulmajid mai na tsare maka ne?" Kallanta yai sai dai baice komai ba, tace " saboda kai yanzu ko gaida Umma Basira ba na iya yi, na fadama banaso dan Allah ko ana so dole ne?" Kai ya rangwada gefe ya sakar mata wani lallausan murmushi yace " Mairo inaso inga kina fada, kyau yake miki." Rasa ma mai zatace tai ta saki baki cikin takaici tace " Dan Allah nidai na rokeka ka kyaleni." Abdulmajid ya matso hakan yasa tai baya da sauri dan ta san halinsa. Sai da takai jikin bango sannan tace " matsa menene hakan?" Abdulmajid fuskarsa a had'e ya sako fuskarsa saicin kuncinta. Tsoro yasa tasa hannu biyu a kirjinsa ta turashi. Hannayenta ya rike yace " Mairo sai yaushene zaki daina wahalar dani?" Gabanta ne ya tsananta fad'uwa, ga dare ne soron ba haske, tace " ban fahimceka ba, wahalar dakai name?" Jawota yai saura kiris ta had'u da jikinsa gashi ya rike mata hannaye duka, yakai bakinsa saicin kuncinta kamar wanda zai sumbata, da sauri ta runtse idonta cikin tsananin fargaba tare da sa kafa ta taka mai kafarsa. Ko gezau baiyi ba sai dayai bakisa daf da kuncinta sai kuma ya saki dariya yace " Mairo kinganki kuwa?" Gabanta sai wani irin fad'uwa yake ta kalleshi, hannayenta ya saki yana cigaba da dariya yace " sry, wlh ba abinda zan miki kawai so nake naga yanda zakiyi." Lab'enta na kasa ta ciza sannan ta sa kafarta ta kara taka kafarsa da karfi. Kara ya saki sannan yai baya da sauri yace " Mairo amma dai ke wlh da a india kike da film zakiyi, boss zaki zama." Harararsa tai tace " Allah Abdulmajid ka kiyayeni." Kansa ya shafa yace " ba laifi ai in namiji ya kiyayi matarsa." Ta makamai wata hararar tace " mijin tace kawai." Ta fada tare da juyawa zatai gaba. Gabanta yasha da sauri yace " Sai da safe, gobe zan sake magana a fada dan na gaji da jira." Tana kokarin bashi amsa yai gaba, tsaki taja sannan tai gaba, haushinta ma da mahaifiyarta ta sata ta fito da ai ta ce ko yazo bazata sake fitowa ba. Tana shiga ta wuce d'akinsu ta fada kan gado. Ummanta ce ta leko tace " kin dawo?" Mairo tace " Umma ni dai ko yaran nan ya dawo dan Allah karki kara cewa in fita, ni wlh bana so." Tace " Mairo shifa aure da kike gani ba wai mutum ne yake zab'awa kansa ba, babu yanda za'ai wani ya auri matar wani, haka kuma babu yanda za'ai wata ta auri mijin wani, duk wanda kika ga sunyi aure to fa dama akwai aure a rubuce a kaddarar rayuwarsu, inhar yaran nan ba mijinki bane cikin ruwan sanyi sai kiga kun rabu bawai fadanki bane zai sa ku rabu." Mairo ta turo baki, tana san magana taga Umma tayi waje, kara komawa tai ta kwanta a fili tace " Ya Allah!" ************ Magajiya kuwa a daren yau ta tsaya sosai tayi tunanin al'amarin dake faruwa, yanzu ta fahimci Abu Turab bai san sirrinta na Abdulmajid ba, tunda a tunaninta da hankalinsa bazai yi tunanin had'a auren Abdulmajid da Khadija ba in har yasan wannan sirrin, tunda yasan ba abu bane mai yiwuwa. To wanne ya sani? Maganin nan ta tuno da abinda ya fad'a mata a lokacin, mikewa tai zaune tace " yasan sirrin ba Hajiya magani." da alama wannan shine sirrin da ya sani. Washegari da sassafe tasa aka kira mata wannan yarinyar, yarinyar ta shigo jikinta sai tsuma yakeyi, ta shiga ta zauna a falon da ba kowa. Magajiya ta shigo sanye da rigar bacci dan ko wanka batai ba, karfe 6 ne na safe. Magajiya ta kalleta tace " ina abinda aka baki?" Da sauri tasa hannu a lalitarta ta d'auko maganin. Magajiya ta kalleta tace " akwai wanda ya kamaki da wannan maganin?" Kai ta girgiza alamar a'a tace "ba kowa, ina kuma zuba mata kullum." Magajiya ta kalleta tace " kin tabbatar? Kinsan dai mahaifinki na cikin wani hali, kuskurenku d'aya zai jawo masa ajali." Da sauri ta sunkuya tace " tuba nake rankiya dade amma ba wanda yasan maganar nan." Magajiya ta amshi maganin sannan tace" jeki." Mikewa tai tare da karayin godiya. Tana fita tai ajiyar zuciya, kalan Abu Turab ta tuna sanda ya ce karta kuskura ta nuna yasan komai, sannan ya bata maganin saboda gudun zargi." Magajiya tai shiru bayan ta fita, tace " to me yake nufi? Ta tabbatar akwai wani sirri da ya sani, sannan ko baisan maganin nan ta hannun yarinyar nan ba ta tabbatar yasan da zancen maganin, dan tabbas irin wannan ne a hannunsa. Ajiyar zuciya tai tace " mai ya sani yaran nan?" Tun kafin asiri ya tuno gwara ta salwantar da maganin, sannan yarinyar nan ta turata wani garin ita da mahaifinta. ********* Abu Turab zaune kusa da Hajiya wannan yarinyar tanamai bayanin komai, ya jinjina kai yace " hakan yayi, sannan ki shirya zan canza ma mahaifinki asibiti sannan ke kuma ki koma ki kula dashi, kafin lokacin da zaki bada shaida yayi." Tace " to." Turab ya kalli Lantana yace " Lantana akwai wacce kika yarda da ita a gidan nan?" Tace " eh akwai wata yaruwata da aka kawo." Turab yace " ki dawo da ita nan sannan ke ki koma gun Umma dan kar Magajiga ta fahimci wani abin, ina tsoron kar ta ma Hajiya illa ta wani gun." Lantana tace "to." Mikewa yai ya wuce bangarensa, yana shiva Garzali ya sanar dashi kiran da Mahaifiyarsa take masa. Turab ya juya. Sai da ya gaisheta sannan yace " Umma gani." Ta kalleshi tace " Abu Turab me yasa baka zuwa gub Mahaifinka?" Kansa na kasa bai d'ago ba baikuma ce komai ba. Basira tace " Mahaifinka na nemanka, yana san ganinka." To, kawai yace, sannan ya kalleta yai murmushi yace "zanje Umma, shikenan?" Fuska ta saku tace " ko kaifa?" Kansa ya sunkuyar yana murmushi, tace " Ya maganar Mairo?" Kallanta yai sannan yace " Hmmm Umma yanzu ba wannan bane matsala, sai dai insha Allah shima ba wani matsala." Tace " to, amma Turab nidai kayi a hankali da Magajiya dan wlh wannan matar bala'i ce." Yace " Nasani Umma, bala'in gaske ma kuwa, sharrinta ya wuce duk yanda kike tunani, zan sanar dake komai sai dai ba yanzu ba." Tace "shikenan." Sai yamma sannan ya nufi gun mahaifinsa, sai daya gaisheshi sannan Sarki ya kalleshi yace " Turab ina ka shiga ne haka?" Turab yace " ina nan, abubuwan ne sukai yawa." kansa na kasa yai maganar nan. Sarki ya kalleshu yace " kasan tunda ka shigo baka kalleni ba?" Turab a ransa yace " ina na isa? Nima ai mai laifine tunda nima na b'oyema sirrin nan " Katsemai Tunaninsa yai da cewa " na aika abin bukatu na lefen." Kansa na kasa yace "to, angode." Mamaki ya kama mai martaba yace " Umarni sarki zai baka ka d'ago ka kalleshi." Turab ya d'an runtse ido kad'an sannan ya d'ago a hankalu ya kalli Mai Martaba. Sarki yace " Turab menene?" Abu Turab ya kakaro murmushi yai sannan ya girgiza kai yace " ba komai, sai dai jikin Hajiya da ba dadi, ne yasa baza'a kaita asibiti ba a kwantar da ita?" Ajiyar zuciya yai sannan yace " Hajiya mace ce mai masifar kishin al'adarta, ko sanda za'a kaika asibiti sai datai ta fada wai akan me za'abar maganin hausa a koma maganin bature? Ita ko mutuwa zatai bata yarda a kaita wani asibiti ba." Turab yai shiru sannan yace " Amma Abba yanayin jikinta ne ba dadi." Yace "haka ne ni kaina har banasan zuwa dubota." Turab yad'anyi shiru kafin yace " Ko za'a maidata cikin gari? Sai a tafi nata da masu kula da ita?" Mai Martaba yace " Turab kenan, nan d'in ba'a kula da ita?" Kai ya girgiza alamar a'a yace "ba haka bane kawai dai gani nake zatafi jin dadi in tana can." Sarki ya kura mai ido ya tabbata akwai dalilinsa ma fad'ar haka, sai dai baisan menene ba, yace " shikenan, zansa a maidata a satin nan." Turab yai saurin cewa " a maidata gobe, dan Allah." Sarki ya kalleshi yace " Akwai abinda kake b'oyemin ko?" Turab yai kasa dakai, Sarki yace " na sanka da taurin kai tun kana yaro, jn har bakaso fad'ar abu ba to fa bazaka tab'a fada ba, zanyi yadda kace sai dai ka tabbatar ka sanar dani abinda ke faruwa nan kusa ba da dadewa ba." Yace "godiya nake, sannan insha Allah zan sanar dakai." Nan ya mike ya fito. Hakan kuwa akai washegari da safe a ka d'auke hajiya, wanda ba wanda ya sani sai Turab sai Sarki da masu d'aukan, Jakadiya kuwa sai dariyar mugunta take kasa kasa dan ta tabbata akwai wani abu da Turab yake shiryama Magajiya tunda taga ta zake tana shirya mai lefen auren da tace ko zata mutu bazata bari ayishi ba. *"******* A duk bayan kwana biyu Turab suna waya da Bilkisu, shakuwa ce a hankali take shiga tsakaninsu, duba da yanayin gidan da suka taso da kuma aminta ta yarda dake tsakaninsu. Magajiya ta shiga tashin hankali, ta rasa wannan yarinyar wato Zakiyya sannan an d'auke Hajiya wanda ba wanda yasan inda aka kaita, da farko ta aika gidan cikin gari sai dai bata nan, shikansa Turab baisan inda Mai Martaba ya kai ta ba. Sai dai yasan Sarki ya fahimci Uwarsa na cikin wani halin ga tsufa, ya san hakan ne yasa ya d'auketa. Magajiya ta gama had'a lefe wanda ta yishi na gani na fada dan ita d'in yar kwallisa ce ta gaske, an kashe kudi kam, hankalin Magajiya a kwance take had'a kayan nan, dan itada Hisham sun gama tsara yanda zasu shirya komai. A b'angaren Turab kuwa jira yakeyi a tsaida rana dan shima ya fara aiwatar da nasa shirin kamar yanda suma suke nasu shirin, Magajiya ta gama yanke hukunci akan Halaka Turab dan wannan ita kadai ce hanya, ganinsa ma batasanyi sam. An tsaida lokacin biki nan da wata d'aya. Magajiya ta sa Hisham ya hana Khadija fita, yanzu ko nan da nan ba a barinta fita. Wannan kenan. *Turab* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *64* Abdulmajid yau tun safe yai wanka tsaf ya shirya ya nufi bangaren Sarki, Mai Martaba ya bashi izinin shiga. Ya dade rabon da ya keb'e da mahaifinsa irin haka, shiga yai a hankali kamar ba shi ba sannan ya gaisheshi. Sarki ya kalleshi yace " Ya akai?" Ba shakka har cikin ransa sai dayaji ba dadi, ya akai? Abinda uba ya kamata ya fara tambayar d'ansa kennan sannan kuma fuska a d'aure? D'agowa yai jiki a sanyaye yace"dama maganar Mairo ne....." Katsehi Mai Martaba yai yace " maganar Mairo a me kenan? Kana tunanin kayi daidai a zuwa cikin tsakiyar fada kace kana san auran Mairo? Bayan ni naka sameni ba?" Abdumajid yai shiru, Sarki yacigaba " Na rasa wani irin hali ga reka, gani kake komai naka ne kamar Magajiya ko?" Abdulmajid ya d'ago idanunsa sun ciciko sosai da kwalla yana tsananin ganin kwarjinin mahaifinsa amma ya daure yace " menene laifina? Abba ni ba d'anka bane? Me yasa komai sai dai Abu Turab? Ka samomai mata yar mulki, gashi yanzu har an tsaida rana ana ta shirye shirye, nine fa babba ba shiba, amma bance komai ba, sannan nace ga wacce nakeso itama an kasa bani, ko itama Abu Turab din za'a ba?" Sarki ya kalleshi yace " Kana tunanin duk abinda kukeyi kai da mahaifiyarka sani ne banyi ba ko ka d'auka karfina tafi? Sanda kukama Turab sharri kana tunanin bansan ku kuka aikata ba?" Abdulmajid yai shiru, sai dai zuciyarsa na tafasa da tsanar Abu Turab tsantsa. Sarki yace " Maganar auren Mairo ni har yanzu ban yanke hukunci ba, zamu zauna da mahaifinta muga wanda ya dace da ita." Abdulmajid ya d'ago sai dai baice komai ba amma kana kalla idanunsa zakaga tsantsar b'acin rai. Mikewa yai yama mahaifinsa sallama ya fita. Cikin tsananin takaici ya nufi bangaren Magajiya. Tana zaune tana shan madarar shanu, wanda takesha duk safiya dan gyara mata fatarta. Ko sallama baiyi ba ya afka ciki. Magajiya ta kalleshi har ya zauna, baigaisheta ba yace " Umma nikam na gaji da abinda Abba yakemin, wlh zan d'au mataki a kaina." Magajiya bata daina shan madarar ta ba ta kurb'a sannan tace " me ya faru?" Abdulmajid ya kalleta yace " Umma ni kam na tsani yaran can, me yasa ne komai nake so a rayuwa sai ya kwacemin?" Tace " karka damu ka kara hakuri na wasu 'yan lokuta, sannan ka shirya nan da wani satin dan zuwa ganin yar sarkin daura." Kallanta yai yace " inganta in mata me?" Kallansa tai tace " tambaya kake?" Kansa ya maida kasa sannan yace " Amma Umma kinsan ai ni M......." Kallan data masa ne yasa yai shiru, ajiye kofin tai sannan ta juyo ta kalleshi tace " me yasa kake neman canzawa? Da baka tambayata akan abinda na sharadda maka amma yanzu naga alama yar iskar yarinyar nan tana neman canza maka hali, a kanta ka fara neman canzamin." Kansa na kasa yace " Amma Umma." Mikewa tai tsaye tazo kusa dashi ta sa hannu a kafadarsa tace " Abdulmajid ka zama mai bin duk abinda na sharadda maka, komai da kakeso a rayuwa ni zan baka, in nace komai ina nufin komai d'in, kai dai kabi ni." Shiru yai, ita kuma tana gama magana ta juya tai ciki, ya dade a zaune kafin ya mike ya fita. ******** Turab yau da kansa yaje fada ya dade a can sai dayaga fitowar Waziri sannan shima ya mike ya fito. Yana kallan Hisham ya shiga mota ya wuce gida, shima ya shiga tasa motar wanda dama ya sa Garzali ya jirashi ya bi bayansa. Hisham na kokarin shiga gida, Turab ya fito da sauri ya biyoshi. Hisham na shiga aka cemai wai yayi bako, yayi mamaki sai dai bai yi tunanin Turab bane yace " ace ya shigo." Turab ya shiga cikin falo ya zauna, sannan Hisham ya shigo. Mamaki ne ya kamashi na ganin Abu Turab. Karasawa yai ya zauna yace "Yarima lafiya?" Turab ya gaisheshi sannan yace " biyoka nai ai daga fada." Hisham yace " wani abin ne ya faru da baka sanar dani a can ba sai da ka biyoni gida?" Turab yai kasa dakai yace "ai yanzu a matsayin siriki mai neman 'yarka nazo." A zabure ya kalli Turab cikin raahin fahimta yace " me kake nufi?" Turab ya d'ago idanunsa yace " zuwa nai maka da abinda zai taimakeka ya kuma taimakeni." Hisham ya bishi da kallo, Turab yace " khadija zaka auramin kaga nan gaba ko da komai naka ya kare a kalla 'yarka tana da matsayin da zata kwace ka." Ran Hisham ya b'aci yace " Ta karemin kamar ya?" Turab ya d'an furzar da iska irin damuwar nan yace " Badai kana tunanin in Abdulmajid ya hau mulki Magajiya zata barka da matsayinka ba ko ta barka kayi yanda kakeso da d'anta ba?" Hisham yace " wannan banaji yana daga cikin damuwarka." Turab yace " Hake ne sai dai inaso kayi tunani sosai kaga mafakar da zata bul'ema, ka fini sanin kanwarka ka kuma san halinta, kana tunanin zata barka ko shawara ne kaba Abdulmajid? Inka bada ma shawarar kana tunanin zata bari yai aiki dashi?" Hisham ya mike tsaye cikin takaici yace " koma menene damuwatace ba taka ba, sannan kana tunanin ni zan kai 'yata a ta biyu gidan wani? Sannan ni ban taba tunanin had'a zuri'a dakai ba kuma bazan yi ba har abada." Turab yace "kumafa gaskiya ka fada, ni kaina bansan me yasa nazo ma da zancen ba, inaso ka sanar da 'yarka hukuncinka saboda mu hakura da juna." Ya mike yamai sallama ya fito daga falon. Yana fita yai wani murmushin gefe yace " nazo neman iri ne na auran 'yarka? Inji wa? Kai dai na tabbatar abinda na saka a kwakwalwarka ya shiga zai kuma fara aiki." Ya juya, Karo suka kusa yi da Khadija wacce ta taho da tirw daga kitchen rike da tire wanda yake d'auke da juice. Kaucewa tai saboda ganin zata bugeshi, garin kaucewa bata kula da kafarsa ba ta taka ta tafi kamar zata fadi, da sauri ya rikota ta baya. Ajiyar zuciya tai da karfi dan tabbas ta d'auka fad'uwa zatai. Juyowa tai a hankali, nan taga wanene idanunsu ne suka had'u da juna. Sai da 'yan wasu dakiku suka wuce a haka kafin Turab ya daure yace " Baki bige ba?" Gyara tsayuwarta tai sannan ta kalleshi, a hankali ta d'aga kai, kallanta ya sakeyi yaga ta rame, ita kuma tana san tambayarsa abinda ya kawoshi, a tare sukace "Nace me......" Ganin yanda sukai maganar a tare basu san sanda sukai dariya ba, Turab yace " fara magana." Kallansa tai tace " a'a ka fara." yana kokarin tambayarta yaji murya ance " Khadija me kikeyi anan baki kai ba?" Juyowa tai ta kalli Ummanta tace " yanzu zan kai." Kallan gun yai, mahaifiyarta ya gani, suna tsananin kama da Khadija sosai, da ace itace Abdulmajid to fa yasan tabbas zargi zai bayyana. Gaisheta yai sannan ya fita, Hisham kam Turab na fita ya kumburo baki yana tunani, tabbas dolene ya fara jan d'ansa a jikinsa dan sai yanzu ya farga ya san Magajiya sarai tabbas gaba ma neman ma hanashi zuwa gidan zatai. Ko tabin bayan Khadija data shigo baiyi ba ya shiga cikin d'aki. ********** A can kano kuwa shiri sosai akeyi na auren Gimbiya, auren da babu kamarsa agunsu domin ita kadai ce 'yar sarki mace, shiri ake sosai wanda yasa kishiyoyin Fulani jin kishi dan komai ita keyi, Bilkisu kuwa an shiga gyara, dama ba zancen zance dan in suka fara gyaran jiki to ango bazai ga amarya ba saboda so ake inya tashi ganinta yaga kamar ba ita ba. Turab kam na kiranta sosai suna waya. Hisham ya gama tsarawa dan yau yana tashi daga fada ya nufi bangaren Abdulmajid........ *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* _Sakon ta'aziyya gareki kawar arziki BillynAbdul Allah ubangiji ya jikan Mahaifinmu yasa Aljanna ce makomarsa.....(Ameen)_ *Na Ayusher Muhd🤸🏼* _Masu san karanta Matar Fayrouz na AsyKhaleel da sauran litattafanta su duba ta a wattpad @asykhaleel.😘😘_ *65* Hisham yana fita yai bangaren Abdulmajid, baya nan ma sai ya zauna a falo ya aika a nemoshi, yace " in an ganshi kar acemai shine yake nemansa. Abdulmajid ya fito daga bangaren Magajiya kenan aka sanar dashi yanada bako. Yana shiga yaga Hisham, ya karasa ya zauna sannan ya gaidashi, Hisham ya washe baki yace " Abdulmajid sai ka ganni ko?" Kallansa yai yace " Kawu me ya kawoka? Naga baka taba zuwa bangarena ba." Hisham yai murmushi tare da kallansa yace " yauma wucewa nazoyi sai na fahimci ban taba shigowa ba." Kai ya d'aga kawai baice komai ba, yau ce rana ta farko da suka kebe su biyu haka shiyasa yakejin abin wani banbarakwai kamar ba kawunsa ba. Hisham ya kalleshi yace " ya maganar auren naka da Mairo? Har yanzu Magajiya bata sauko ba?" Hisham ya kalleshi kallan mamaki, cikin rashin fahimta yace " eh kasan halin Umma ai " Hisham yace " karka damu inaso kome ke damunka ka dinga sanar dani, ni zan yi iya kokarina wajen ganin na taimaka maka, Magajiya bazata taba bari ka auri yarinyar ba, sai dai ni zan san yanda zanyi in har kanasanta." Ya kasa fahimtarsa, mamaki yake na yanda yake mai, Abdulmajid yace "Nagode, amma kana tunanin Umma zata yarda?" Hisham yace " karka damu, kai daj ka yarda dani, duk wata matsala taka ka dinga zuwa kana sanar dani, ni zan taimakeka akan komenene, kawai dai ka dage kar ka taba bari Turab ya kwacema mulkinka." Abdulmajid kallansa kawai yakeyi, Hisham ya matso yace " inaso a sati ka dinga zuwa gidana cikin gari, zansa Maman Khadija ta dinga shiryama duk abincin da kakeso, kaga sai kazo ayi hira, hakan zai ragema kewa ya kuma kara mana zumunci." Shekarata nawa da haihuwa? Da can ba'ai zumuncin ba sai yanzu? Abinda ya fada kenan a ransa, sai dai a fili kallan Hisham yai kawai baice komai ba. Hisham ganin yanda Abdulmajid yake yi yasa ya mike yace " ni zan koma sai mun ganka ko ran Juma'a ko asabar,sannan karka fadama Magajiya zuwana da zancen da mukai, ka santa." Uhm hmm, kawai yace. Hisham yai waje. Kallansa Abdulmajid yai sannan ya mike yai ciki. Hisham kuwa na fita ya jinjina kai yace " a hankali zan jawoka jikina, ai tsakanin Uba da d'a sai Allah." Yana fitowa yai wuf yai kwana ya wuce, Abu Turab wanda yana shiga bangaren aka sanar dashi zuwansa ya fito dama yana jiran fitowarsa. Yana hangoshi ya taho kamar irin bai ganshi ba d'in nan, Hisham na hangoshi ya tsaya tare da neman inda zai b'uya, dan dai girma ya kamashi ne amma da gudu zai saka, juyawa yai da sauri dama abinda yasa ya bi ta baya saboda bangaren Magajiya ne ta gaba, yana tsoron kar aganshi. Abu Turab yana kallan ya juya yai wani murmushin jin dadi. Hisham ya shiga bangaren Magajiya. Tana kishingide ta bashi izinin shigowa. Hisham ya shiga yana dariya yace " Magajiya ikon Allah hutawa kikeyi ne?" Wani banzan kallo tamai hakan yasa yai shiru sannan yace " Magajiya barka da yamma." Idanu ta d'an juya bata amsa ba, zama yai sannan yace " na lekone mu gaisa." Tace " ka sandai muna da abinda ya kamata mu shirya na ranar auren yaran nan ko? Ga lokaci yana matsowa amma sam ka ki shigowa ayi magana." Yace " haka ne, nima ai ba mantawa nai ba, yanzu ya kikeso ayi?" Ta bud'e baki zatai magana aka sanar da ita zuwan Abu Turab. Fuska ta canza tare da yin wata karamar kwafa, ba shakka itakam ta gaji da jin ko sunan yaran nan. Shigowa yai ganin batada niyyar bashi izini. Yana shigowa yace " Umma bakiji isowar d'anki bane?" Murmushi ta saki sannan ta koma ta gyara zamanta tace " banyi tsamannin zuwan ka bane." Zama yai sannan ya kalli Hisham yace " da alama sirri kukeyi da Kawun namu au ko ince Babana." Magajiya ta had'e fuska, shima Hisham yaci mazu, Turab ya d'aga hannayensa yace " Tuba nake Babana kar in bata ma sirikin nawa rai kafin abani Khadija." Magajiya ta kalleshi cikin takaici tace " kai dai ka nutsu akan auranka da Bilkisu ka daina wata banzan magana wacce bazata amfaneka ba." Turab yace "Haka ne Umma, nayi..." yai alamar zip a bakinsa. Kallan Hisham yai yace "Amma waziri kamar daga bangaren Abdulmajid na ganka ko?" Hisham ya zaro ido, da sauri ya kauda kai gefe irin mara gaskiyar nan yace " a'a wucewa nai ba shiga nai ba." Turab ya jinjina kai yace " kayi kokari sai naga kamar tacan yafi nisa." Hisham yace "Hmm." da sauri ya kuma cewa " bari nikam na koma." ya fada dan kawar da zancen. Turab yace " a'a bari ni na tafi da alama Umma akwai abinda zata cema, da na d'auka ma d'anka kazo ba gun Umma ba shiyasa na shigo." A tare gabansu ya amsa da rass, Magajiya cikin tsananin tsoro tace " D'ansa?" Hisham kam har zufa ta fara afko masa, Turab yasa dariya yace " menene hakan? Da ba d'ansa bane?" Ai tuni Hisham kansa zuwa wuyansa ya cika da zufa, Magajiya kam a ranta tace "shikenan ta faru ta kare." Turab ya karayin dariya yace " lalai Umma ba kara? Na d'auka d'anki a ka'ida d'an Waziri ne saboda jininku d'aya." Bakin Hisham har rawa yake gurin cewa " sosai ma haka ne." Magajiya kam idanu ta bud'e ta kurama Turab tana kokarin ganu abinda ke b'oye a ransa da gaske abinda yake nufi kenan?" Turab ya kalleta yace " Umma lafiya? Naga kinata kallo na." Idanu ta d'auke tare da cewa " ba komai, ya shirye shiryen biki?" Yace "Thanks to you, komai na tafiya daidai." Kai ta d'aga tace " yayi kyau." Turab yace " Ayi hira lafiya." Ya juya ya fita, yana fita ya kara kallan kofarsu ta gefe, "Haka ne nima ba mantawa nai ba, yanzu ya kikeso ayi?" kalaman Hisham da yaji sanda ya iso gun ne ya kara dawo mai, tabbas akwai wani mugun abu da suke kara shiryawa, ya tabbatar. Juyawa yai ya fita. Yana fita Hisham ya saki wata ajiyar zuciya ya kalli Basira yace " kinji hanjin cikina?" Magajiya ta kurama kasa ido kafin tace " Inaji ya kamata mu maida Khadija kano." Yace " Kano? Kamar ya?" Tace "kasan Mahaifiyar Saifullahi ta kirani jiya da daddare tace wai Khadija tace ma Saif akwai wanda takeso, dolene mu maidata kano in taga bata gani yarancan sai ai auren, inba haka ba intaga mutuwarsa abin zai baci, ka san dagar da akai da ita sanda tana karama ma bare yanzu." A ransa yace " ni da 'ya'yana sai dai a dinga sharada min abu, da girmana amma a dinga kaskantar dani" A fili yace " hakan yayi." Nan suka cigaba da tsarinsu..... ********* Basira zaune a falonta, gabanta kuma leda ce irin mai karfin nan, da alama kaya ne a ciki. Amsa sallamar Turab tai sannan ta kalli kofar da ganin shigowarsa. Turab ha shigo sannan ya zauna yace "Umma gani." Kallansa tai tace " Dama aikenka zanyi." Kallanta yai sannan ya kalli ledar gabanta, sai kuma yar murmushi yace "Gun 'yarki?" Tace " eh, Mairo zaka kaimawa, sa wa nai a d'inka mata na bikinka." Murmushi yai yace "Umma kenan." Kallansa tai tace " Amma baka tunanin hakan yazo da kamar wulakanci ko?" Turab yace "wulakancin me?" Tace " Na kaimata kayan da zata sa a bikinka bayan akwai wata a kasa." Turab yace " Lalai Umma, ni bansan wannan ba ki tambayi Lanta....." Da sauri yai shiru tare da kallanta, Kallansa tai itama tace " Turab har yanzu ba labarin inda Hajiya take? Bare Lantana?" Kai ya d'aga alamar eh. shiru sukai ganin haka yasa ya jawo ledar yace " Zanje in anyi Magrib." ********* Garzali ne ya kaishi, yana cikin mota Garzali ya fito ya aika a kirata. Ta gama kunce lale kenan wanda tayi a hannunta, aka sanar da ita zuwan Turab. Wankewa tai dama ba sallah zatai ba ta saka hijab ta dan murza hoda sannan ta fito. Tanaji 'yayan kishiyar babarsu na mata habaici, ko ta kansu bata biba tai waje. A jikin soro ta tsaya dan bata fita waje zance, ka'idar gidansu ne haka. Turab sai da ya hangota sannan ya bud'e motar ya fito, rike da ledar. Tundaga nesa take murmushi har ya iso, Kallanta yai sannan ya karasa cikin soro yace " Hajiya Maryam an fito?" Kallansa tai tace " Yaya ina wuni?" Bai amsa ba sai cewa dayai " kwana dayawa?kin bata bat." Fuska ta d'an rufe tace " wlh inasan zuwa gaida Umma magana ce banaso." Leda ya mika mata yace " ga sakonki inji Ummanki." Amsa tai tana murmushi tace " oh ni, me na samu?" Yace " kayan bikin yayanki ta d'inka miki." Gani yai ta d'ago da sauri, sannan yanayinta ya canza, yace " Badai Umma tayi lefi ba?" Ya ke tai tace " a'a." Kallanta yai zai yi magana aka dallesu da fitilar mota. A tare suka kalli motar, Turab ya sa hannu ya rufe idanunsa dan sam bayasan a haskashi irin haka saboda idanunsa. Mairo ta juya kai tare da jan tsaki. Turab ta kalla ganin yanda ya rufe idanunsa yasa ta taho dan nufo mai motar. Har ta iso sannan ya kashe, tare da fitowa daga motar. Kallansa tai tace " Abdulmajid me ke nan?" Kallanta yai fuskarsa a d'aure yace "me kike a can?" Tace " ko ma me nakeyi banaji ya shafeka amma wannan dallenin da kai da fitila fa?" Kallan inda Turab yake yai bai amsa mata ba taga ya nufi inda Turab yake. Abdulmajid na zuwa ya d'aga hannu zai naushi Turab, Abu Turab ya sa hannu ya tareshi. Kallo kallo sukai kafin turab ya sakar mai hannu sannan yace " ka kiyayi kanka da san duka, sannan ka kiyayi kanka da saurin hawa Da kuma kishi " Abdulmajid yace " Kai waye da zaka bani shawara?" Turab ya kalleshi ba shakka yana tausayamai alokacin da yasan sirrinsa shiyasa baya neman fada dashi a wannan lokacin. Mairo ce ta karaso ta kalli Abdulmajid, zatai magana Turab yace " Bari na wuce." Ya karasa maganar tare da wucewa ta gaban Abdulmajid. Biyoshi tai tace"Yaya kama Umma godiya." Juyowa yai ya kalleta sannan ya kalli Abdulmajid dake tsaye yace " Mairo." Kallansa tai bata amsa ba, yace " karki dinga zafaffama Abdulmajid." Tace " Yaya na fadamai ba so nake ba, na rasa dalilin takurar." Shiru yai tare da cigaba da kallan Abdulmajid yace " ba yanda za'ai?" Kallan mamaki tamai tace " yanda za'ai me?" Kai ya girgiza da sauri yace "ba komai." Ya karasa mota ya shiga. Shiru tai tana kallansa har sukai gaba, ba yanda za'ai? Me yake nufi?" Karasawa tai inda Abdulmajid yake. Kallanta yai yace " Mairo mai ya kawoshi?" Ledarta ta nuna mai tace " abu ya kawomin, ko da wani abun?" Abdulmajid yai murmushi yace " Mairo lalen ki yayi kyau sai kika fito kamar amarya." Harararsa tai tace " kamar Ango ne ba amarya ba." Dariya yai yace " in kika zama kamar ni Angon ki ai ba wani abin bane." Baki ta d'an murguda tace " Ka manta." ********* Turab kam kansa ya kama a cikin mota wanda yaji yana sarawa, yace " Ya Allah! Ka kawo komai da sauki, kada ka bani ikon cutar da wanda bashida hakki akan al'amarin nan, ka bani ikon aiwatar da komai yanda ya kamata. Nace Ameen *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* _Haly(Mom Farhan) Allah ya kara lafiya yasa kaffara ne....Wish u quick recovery_ *66* Abu Turab idanunsa ya bud'e a hankali ya shiga kallan d'akinsa kafin a hankali ya furzar da wata yar karamar iska daga bakinsa. Sannan yasa hannu ya dafa gadon ya mike ya zauna, idanunsa ya rufe ya shiga karanto addu'oin safiya, kafin ya sauko daga kan gado. Yau saura sati 3 bikinsa, dayake gidan maza ne ba wani abu special ake aikatawa ba, an dai kammala ginin bangaren da zasu zauna da gimbiya. Saukowa yai daga kan gadon sannan ya nufi bandaki dan kama ruwa da yin alwala. Bayan ya dawo daga masallaci ya zauna yai ta tilawar al-qur'ani har sai da gari yai haske, wannan al'adar haka yake yinta dan koyar wace ta ma'aiki S.A.W. Sai wajen karfe goma yaci abincin safe sannan ya fito. B'angaren Mahaifiyarsa yaje sukai 'yar hira kafin ya fito. Yana kokarin komawa bangarensa ya hango Baiwar da take kula da bangaren Abdulmajid wanda ya shine ya sakata a bangaren dan kawomai rahoto akan Hisham. Karasowa tai cikin hanzari sannan ta gaisheshi, tana yi tana kalle kalle. Turab ya kalleta yace " lafiya da safen nan?" Tace "banga d'an aike bane, dama Waziri ne ya zo yanzun nan, sannan rike yake da lefa katuwa, da ya shiga ciki na amshi laidar sai naga kula ce sannan ga kamshin abinci nan." Turab yace " yayi kyau, koma bakin aikin ki." Tace "Yarima Abdulmajid ya......" Dakatar da ita yai yace " na tambayeki rayuwar Abdulmajid? Ko kuwa a sanda na baki aikin nan nace ki dinga kawon zancensa? A iya sanina ce miki nai kawai in Waziri yazo ki sanar dani." Tace " Tuba nake ranka ya dade." Turab ya sallameta sannan shikuma ya shiga ciki. A bakin kofa ya tadda Garzali da alama fita zaiyi. Turab ya kalleshi yace " in zaka fita ka biya bangaren Sarki gub Jakadiya." Garzali ya kalleshi yace " Jakadiya?" Turab yace " ka sanar da ita Hisham na bangaren Abdulmajid." Garzali cikin rashin fahimta yace " to." dan bazai iya tambayarsa dakili ba. Garzali ya garzaya yaba Jakadiya sako. Ita kanta kallab Garzalin tai tace " abinda yace kawai ka fadamin kenan?" "iya kacinsa kenan." Ya juya. Jakadiya tai shiru tana kara maimaita kalmar kafin daga baya ta fito. Bangaren Magajiya ta nufa, Magajiya na karyawa ta shigo. Sama sama ta amsa gaisuwarta tanayi kamar bataso. Sannan tace " me ya kawoki?" Jakadiya ta miko mata leda tace " maganine aka kawo na gyaran fata." Magajiya ta kalli maganin dake cikin farar leda sannan ta kalleta tace " ni ce miki akai ko wani kare da doki ya bani magani amsa nake?" Jakadiya tace "badai haryanzu baki hakura ba?haba Hajiya Magajiya, matar sarki, uwar sarki, kakar sarki." Magajiya ta wani juya kai sannan tace " Me ya kawo ki? Dan na tabbata ba wannan bane kadai abinda ya kawoki." Jakadiya ta dan shafi fuska sannan ta matso tace " hmm dama na kasa fahimtar wani abu ne, Na rasa me yasa nake ganin Waziri yanzu yana zirya bangaren yarima Abdulmajid." Magajiya ta kalleta tace " ban gane ba.." Jakadiya tace " Tuba nake Ranki ya dade amma nifa hankali ya kasa kwanciya da zuwansa." Ruwan da ta gama sha ragowar cikin kofun tai kamar zata zubo mata har ta rufe idonta ta d'auka ita zata zuba ma. Magajiya ta ajiye cup din sannan ta kalleta tace " najiki inaso kuma ki fita." Jakadiya ta had'iyi yawu sannan ta mike tai waje. Magajiya tai shiru tana tunani, dama kwanaki Turab ya sanar da ita ya ganshi amma shi ha musa, sannan an fada mata rannan an ganshi, sannan yau Jakadiya ta fada mata, me Hisham yake tunani? Tamai magana akan kai Khadija Kano ma ya mata burus sannan yanzu ya fara kewayewa yana zuwa gun D'anta? Turab kam zama yai a falo yai zama cin abinci sannan ya rufe idanunsa, yana kada 'yan yatsun hannunsa, Magajiya! Ki jira juyawar bayan duk wani na kusa dake, a hankali zan ruguza miki duk wani abu da kike takama dashi....Slowly ya saki murmushi sannan ya bud'e idanunsa, ta ya zakuyi kisa ku cigaba da zama kamar wad'anda basuyi komai ba? Kun halaka rayuwar mutane dayawa amma ko tunawa bakwayi. Hannunsa ya dunkuke sannan ya kalli bakin kofa cikin tsananin kunar rai. ******** Abdulmajid na mikewa daga kan gado aka sanar dashi zuwan Hisham, baiyi mamaki ba dan ya kula yanzu wata gulma ce take damunsa, inba haka ba da can me yasa bai mai haka? Sai dayai wanka sannan ya fito. Hisham ya sa an jeramai abincin dayasa matarsa tai, ita kuwa tanayi tana farinciki dan yauce rana ta farko da zatai abinci domin d'anta Shikadai. Kallan abincin yai sannan ya karasa ya zauna, ya gaisheshi. Hisham ya amsa fuskarsa a washe yace "Ashe bacci kake?" Abdulmajid yace " eh wlh, kayi hakuri na barka kai kadai kawu." Hisham yace ba komai, zauna kaci abinci, goggonka ce ta dafa ma. Abdulmajid ya kalleshi sannan ya kalli abinci yace "Kawu me kakeso?" Hisham yace " name kenan?" "na tabbatar abu kakeso a gareni shiyasa kake nunamin kulawar da baka nunamin da, badai so kake in auri Khadija ba ko wani abun ba?" Da sauri Hisham ya zaro ido yace "ka auri khadija kuma? Wannan wani irin shirmene? Auzubillah." Abdulmajid yayi mamaki yanda yaga yayi, sai dai bai kawo wani abu ba yace " to inba shiba menene? Na tabbata akwai dalilinka na yin haka balle ma kace kar na dinga sanar da Umma zuwanka." Hisham yai shiru yana tunani kafin yace " ko d'aya kawai dai ina ganin ya kamata mu saba da juna ne, na ga ko aboki baka dashi." Abdulmajid ya kalleshi baice komai ba ya fara cin abincin. ******* Magajiya kam Jakadiya na fita hankalinta ya kasa kwanciya, mikewa tai ta shirya ta fito ta nufi bangaren Abdulmajid. Da yake ta baya ne bata wani dadeba ta isa. Ana kokarin sanar da isowarta tace ayi shiru. Kai tasa tare da tura kofar a hankali. Hisham taji yana cewa " Na d'auka wancan sati zaka zo, sai naga baka zo ba." Abdulmajid wanda ya gama cin abinci ya kalleshi tare da wanke hannu yace " ya su Umman da Khadija?" Hisham yace " suna lafiya, zakazo ran juma'ar?" "Yaje ina?" abinda sukaji kenan da ga bayansu. A tsorace suka mike, Abdulmajid ya kalleta yace " Umma." Kallansa tai sannan ta kalli abincin da ya gama ci tana gani tasan Hisham ne ya kawo dan ga kuka nan a gabasa, sannan ita ba irin abincin da aka kawo mata ba kenan. Ba shakka ranta ya baci sosai, dan idanunsa sun canza fuskar nan tata ta had'e ta tamau. Kallan Hisham tai tace " Yaje ina?" Hisham ya kalleta sannan ya kallu Abdulmajid, kallan Abdulmajid tai tace " ina zaka?" Abdulmajid yace " Umma." Kallan abincin tai sannan ta kallu Hisham tace " me kenan? Waye ya baka ikon kawomai abinci?" Hisham ya kalleta yace " dan na kawo mai abinci wani abin ne?" Cikin d'aga murya wanda ni kaina sak dana razana tace " wani abin ne babba ma kuwa, yaya me ke damunka?" Abdulmajid wanda ransa ya dan sosu ya daure yace " Umma dan ya kawomin abinci wani abun ne? Kawu nane fa na tabbata bazai cutar dani ba." Kallan Abdulmajid tai tace " ta ya kasan bazai cutar dakai ba? Dan yana kawunka kawai?" Hisham yace " mene? Kina nufin ni zan cutar dashi?" Cikin bacin rai tace " yaya biyoni inasan magana dakai." Tai gaba. Abdulmajid ya dafa kai, sannan ya kalli Hisham wanda yama rasa mai zaiyi. Yana kallan Hisham yai waje. Komawa yai ya zauna jiki a sanyaye. Ita kuma suna shiga d'akinta ta juyo cikin tsananin bacin rai zatai magana. Hisham ne yai saurin cewa me kike nufi da zan cutar da abinda na haifa? Wata irin dariya ta saki mai razanarwa, sannan ta tsuke bakinta lokacin d'aya ta matso kusa dashi tace " me? Abinda ka haifa? Inji wa kenan?" Hisham yace " mene?" Tace " ahhh dalilin kenan da yasa kake neman kula dashi yanzu? Saboda d'anka ne? Ko saboda kanasan amfani dashi nan gaba?" Hisham yai kasa dakai. Tace " idan har kana san kanka da arziki ka fita harkar d'ana, shine magajin sarki banasan wani abu ya faru har sai ya hau mulki, in kuma har kana tunanin wani abu kama daina dan zan iya sa Abdulmajid ya daina ko gaidaka ne kai kasani." Kallanta kawai yake yama rasa mai zaice. Hannu tasa ta shafi fuskarta sannan Tace " Yaya banaso muna fada akan abinda bai kai ya kawoba, ban hanaka kula Abdulmajid ba amma bance ka shishigemai ba, d'ana ne banasan wani abu na shakuwa ko sama da haka ya shiga tsakaninku." Sam yama kasa magana, sai mamaki kawai da yake na kalamanta. Magajiya tace " Yaya na aika da kayayyakin bikin Abdulmajid gida, sannan karka manta da shirin mu na ranar d'aurin aure, wannan shine abinda ya kamata muyi ba fada ba." Ta karasa maganar tana murmushi kamar ba abinda ya faru. Hisham " to." kawai yace ya mata sallama ya fita. Tabbas daga Abu Turab sai ke zakisan ni kikama haka, ba uwa d'aya uba d'aya ba ko 'yatace ke wlh sai kinsan nikikama haka. *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* _I sincerely apologize to u 😌_ *67* Basira ce ta kalli mai martaba tace " Barden ya amince ne?" Takawa yai shiru alamar tunani sannan ya kalleta yace " Basira kiyi hakuri, nasan yanda kika d'auki Mairo na kuma san halin Abdulmajid, yanda Magajiya ta raineshi a haka yake, yaro ne wanda bai yarda da babu ba, sannan duk abinda yakeso gani yake dolene sai ya samu, hakan ne yasa nake nunamai ba haka ba, nake kuma janyeshi daga jikina saboda banaso yai tunanin komai nasa ne kamar yanda Uwarsa ke koyar dashi, sai dai nayi tunani dakyau yaran yanasan yarinyar sannan Mahaifiyarsa ba so take ba, ko dan Magajiya taji ciwon bijire mata da d'anta yai ina tunanin Amincewa." Basira tace " ba wai naki aminta da kai bane sai dai meyasa nakeji kamar kanasan had'a auren ne bawai dan farincikin d'anka ba ko dan karfafa zumunta da Barde ba, ya nakeji kamar dan cikar burinka na kuntatama Magajiya kake san had'a su?" Sarki ya kalleta yace " wannan tunanin shine babban dalilin dayasa na dage akan auren Turab da Bilkisu." Tace " bangane ba." Yace " a masarauta dolene ka sadaukar da wani abu dan samun wani abun, bazai yiwu ka samu komai ba, inhar inaso Turab ya zama Sarkin da naso na zama dolene na samarmai mace jinin sarauta wacce tasan sadaukarwa." Basira ta kalleshi tai murmushi dan ta fahimcu a fakaice magana ya gwab'a mata, tace " Allah ya baka hakuri." Hannunta ya kamo duka biyun yace " inaso ki zama mai karfafamin gwiwa akan al'amurana, bawai dan Magajiya ba kawai nake san had'asu, inaji a jikina zata zama mata ta gari agareshi." Shiru tai dan batasan me ma zatace ba, amma itakam dan ba yanda zatai ne, bataso Magajiya ta zama sirika a gun Mairo. ************ Yau kwanan Abdulmajid biyu kenan Magajiya bata kulashi, gaisuwarsa kawai take amsawa. Yau dai abin ya dameshi bayan ya gaisheta yaki tashi. Ya dade a zaune kafin yace "Umma nikam sai yaushe zaki huce ne?" Bata kalleshi ba bare yasa ran amsawa, yace " kema kinsan ba ji nace ya kawomin abinci ba, sannan gani nai Kawu Hisham yaya yake a gunki kinga kuwa Uba yake a gurina......" A gun wa yake uba?" Kallan mamaki ya mata yace " Umma kinsan kwanan nan kin canza kuwa?" Kallansa tai tace " na canza ko ka canza?" Yace " Umma yanzu na kula kamar akwai abinda ke damunki, abinda bai kai ya kawoba sai inga kinji haushi, a da kuwa kina dadewa kafin inga b'acin ranki." Shiru tai ita kanta tasan haka ta rasa me yasa takejin ta akoda yaushe kamar intai sake Abu Turab zai ruguza mata rayuwa. Abdulmajid ya taso yazo gabanta yace " Umma meke damunki?" Murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace " Abdulmajid." Naam Umma. "inaso kamin alkawari a koda yaushe cikin ko wani hali zaka zama a bayana, bazaka taba juyamun baya ba." Murmushi yai wanda sainda hakoransa suka bayyana yace " bakyasan indinga shiga jikin Kawu?" Kai ta girgiza alamar a'a tace " kawai dai banasan inga wani yana neman janye min kai ne." Yace " Umma kenan, wa ya isa ya janye miki d'anki? Nifa d'anki ne ba kuma wanda ya fimin ke duk duniyar nan." Tace"ka tabbatar ka ajiye wannan kalmar a kasan zuciyarka." Kallanta yai yace " Umma na kasa fahimtar dalilinki na yin hidimar bikin Turab, akan me wacce ta haifeshi bazatai ba sai ke?" Magajiya tai shiru a ranta tace" kwalliya zata biya ai kud'in sabulu." Amma a fili tace " karka damu nice uwargidan Sarki, hakkinane na kula da hidimar bikin 'ya'yansa." Abdulmajid ya dai kalleta ne kawai amma zuciyarshi bata gamsu da wannan sharhin nata ba. Haka ya taso ya fito. Da yake juma'a ce massalaci ya wuce, bayan an idar da sallah Abu Turab na cikin mutane suna ta gaigaisawa ana tsokanarsa akan ya kusa zama ango. Abdulmajid na zaune yana hangoshi, shi kansa Abu Turab baya minti biyu sai ya kalli inda Abdulmajid yake saboda yanasan ganin Hisham kusa dashi. Abdulmajid ya miko yazo shima aka fara gaisawa dashi. Hisham ne ya karaso gun, yana zuwa Abdulmajid na gaisheshi ya juya zai yi tafiyarsa. Hisham ganin haka yabishi da sauri tare da kiransa, tsayawa yai tare da juyowa, Hisham ya iso yace " gida zaka?" Abdulmajid ya kalleshi yace " eh, da wani abun ne?" Zaiyi magana Abu Turab ya karaso yace " Abba barka da juma'a." A tare suka juya suka kalleshi, Hisham yace " ni?" Turab yace " Kai Abba, zumunci akeyi shine kuka taho gefe?" Abdulmajid yace " a yaushe ya zama Abbanka?" Turab ya kalli Hisham irin jin kunyar nan yace " Waziri baka sanae dashi ba?" Hisham ya had'e rai yace " me zan sanar dashi?" Turab yai murmushi yace " Abdulmajid ai munkusa zama surukai." Kallan Hisham yai cikin mamaki, yace " me? Sirikai? Badai Khadija ba?" Turab yai kasa dakai yace " da alama kuna bukatar keb'ewa ko kwa zanta na maganar, ko gun Khadijan zaka kaji komai?" Abdulmajid ya cika yai fam, yace " Kawu me kenan?" Hisham ya kasa magana. Turab ya kalli Abdulmajid yace " ka tambayi kanwarka." Ya juya yai gaba, sai dai hankalinsa na kansu. Baisan me sukace ba sai dai yaga sun juya a tare sunyi hanyar fita. Turab ya kalli Garzali yace " dubamin ko gida sukai." Yace to. Bai dade ba ya dawo yace " ya gansu sum shiga mota a tare." Murmushi Turab yai yace " Bari muje muga Hajiya Umma Magajiya." Yai gaba. Tanaji an sanar da ita zuwan Turab sai da gabanta ya sake fad'uwa. Mike wa tai ta shiga cikin d'aki, gyara kanta tai sosai, sannan ta fito. A zaune ta ganshi yana cin ayaba. Karasowa tai ta zauna, Turab ya kalleta yace " Umma barka da rana." Ta amsa cikin izzarta sannan tace " banyi tsammanin ganinka ba." Yace " nima bansan zanzo ba sai dai kinsan Juma'a dole ne d'a ya kwashi gaisuwar iyaye." Baki tad'an tabe, jujuyawa yai kamar yana neman wani abu yace " Banga Abdulmajid da Waziri ba, na d'auka nan sukazo." Kallansa tai tace " baka gansu ba anan kuma ka d'auka nan suka zo? Wace irim tambaya da amsa ce wannan?" Turab yace " naga sun fita tare da aka idar da Sallah shiyasa na garzayo saboda ingaida Baban namu." Shiru tai sun fita tare? Me kenan? Badai Hisham baiji fadanta ba? Turab yace " Hala sun shiga garine zumunci, abinka da d'a da mahaifi." A hankali ya karasa maganar. Kallansa tai tace " me kace?" Turab yace " me nace? Nikaina na manta." Idanu ta kafa mai tace "kamar zance d'a da mahaifi kai...." Dariya yasa yace " d'a da mahaifi kuma? Wa? Abdulmajid da Waziri? Ta yaya?" Kallansa tai tsoro ya gama kamata, duk yanda taso ta b'oye sai da Turab ya gano hakan, yace " Umma?" Kallansa tai tace " wani shirme kake fad'a, kai da Sarki nake magana ai." Yace "Ahhh ni da Abba? Ko Abba da Abdulmajid?" Magajiya ta makamai harara, yace "Au ashefa ni Abban nawa sun zama biyu tunda akwai Waziri." Magajiya tai murmushi tace " Wai kana shirye shiryen bikin kuwa? Ko kuwa kana nan kana neman auren wacce ba baka za'ai ba? Turab ya mike yace " Umma ki tabbatar komai na bikina ya tafi lafiya yanda ake so, in har kinaso bakina yai shiru kenan, sannan auran Khadija sai dai in ni ince bazanyi ba badai ku ba, daga ke har Wazirin saboda......." Sai kuma yai wani murmushi yace " a bar dai maganar ko Umma? Banasan ciwo ya kamamin ke kafin bikin d'an naki." Kallansa tai idanunta sun kasa d'aukewa daga kallansa tace " ko? Zamu gani ai." Gira ya d'aga yace " ya kamata mu gani kam." Ya juya yai waje. Yana fita ta fara maimaita kalamansa, ta rasa me suke nufi, tabbas dole ne tasan me dan iskan yaran nan ya sani. Mikewa tai tace "Hisham dani zakaja?" A can gidan kuwa, sun isa gidan Waziri, khadija ta fito daga wanka kenan, mai kawai ta shafa ta saka doguwad riga ta zauna a bakin gado, ita yanzu komai ma baya mata dadi, in har ta tuno da kazanta da kuna rashin imanin da suka aikata. Muryar Umma taji tana kiranta, fitowa tai tare da amsawa, ganin Umma tai bakinta yaki rufuwa saboda tsantan farinciki. Umma tace mata " Khadija yarima ne yazo, yana nemanki." Sam bata kawi Abdulmajid ba dan bai taba zuwa gidansu ba, ta d'auka masoyin ranta ne. Da sauri ta koma d'aki ta shafa hoda da turare sannan ta yafa mayafi ta fito. Sallama tai a falon, muryar data amsa ne yasa tasan ba muryar masoyin nata bane, bud'e labulen tai tare da cewa "Yaya?" Abdulmajid ya kalleta sannan ya kallu Umma wacce ta taho rike da tire. Matsa mata khadija tai Umma ta mikama Khadija tire mai dauke da lemon zobo, sannan tace " a kawo abinci?" Khadija ta kalli Abdulmajid tace " Yaya wai a kawo abinci?" Murmushi yai dan shi ya rasa me yasa Goggo take kunyarsa, sam Bata iya tsayawa suyi magana ko zuwa can tai, yace " na koshi khadija, zobon ya isa." Umma ta juya, kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin tsantsar farin ciki. *Turab* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *68* Khadija ce ta karasa ciki ta zauna sannan ta gaisheshi. Kallanta yai yace " Khadija meye tsakaninku da yaran can?" Kallansa tai sannan tai kasa da kai. Yace " Khadija me kike tunani? Kinaso kicemin yaran da na tsana shi kike so? A ma bar maganar so tunda nasan dama Kina sanshi amma me kike nufi da aurensa?" Khadija a ranta tace " abinda nasan bazai taba yiwuwa ba kenan." Amma a fili tace " Ya Abdulmajid." Cikin fada yace " kinaso ki je gidan sarauta a matsayin kishiyar Gimbiya? Sannan a matsayin matar wancan yaran?" Khadija ta kalleshi tace " Yaya wai me yasa ka tsaneshi da ya wa haka?bayan bai taba yima komai ba?" Abdulmajid ya kalleta cikin b'acin rai yace " na tsaneshi, kallansa ma ba san yi nake ba, duk duniya shine mutum na farko dana tsana." Khadija batasan sanda tace " bayan shine ya kamata ya maka wannan tsanar?" Yace " mene?" khadija ta kalleshi tace "Yaya please ka dinga sa ruwan sanyi a ranka, in har wannan karamar maganar ta b'ata ma rai ya zakayi in babbar magana ta doki kunenka?" Yace " babbar magana? Wacce iri kenan?" Juya kai tai da sauri tace " ina dai fada ne saboda ni banga abin jin haushi a maganar ba." Abdulmajid ya mike a zuciye yai waje ko zobon baisha ba. Kanta ta dafe tare da rufe idanunta. Hisham kam yana d'aki yana cire Babbar riga Umma ta shigo bakin nan nata a washe, tace "wai ya akai ya biyoka?" Yace " sai ki rufe bakin ai, kin wani baje baki kamar yau kika taba ganinsa. Kasa tai da kai tana murmushi. Hisham ya shiga band'aku dan kama ruwa, yana fitowa yai falo inda Abdulmajid yake. Me zai gani?" Ba kowa a falon, da sauri ya fito yana kiran Khadija. Fitowa tai daga d'aki tace " gani." Cikin tsawa yace " ina Abdulmajid?" Tace ya tafi. Yace " ban gane ba?" Shiru tai dan batasan me zata ce ba. Waje yai da sauri cikin tashin hankali. Umma ce ta karaso gunta tace " Me kika ce masa da har zai tafi ba ko sallama? Yanzu khadija bawan Allahn nan bai taba zuwa fa gidan nan ba sai yau, amma ki koreshi? Ta ya ya zaki......" Kasa karasawa tai, Khadija cikin tausaya mata tace "kiyi hakuri Umma amma ba korarsa nai ba." Umma tai shiru kafin tai ciki. Khadija ta bita da kallo cikin tausayawa. Abdulmajid yana fita yai gida. Har zaiyi bangarensa aka sanar dashi kiran Magajiya. Yana shiga ya taddata a tsaye da alama yawo take a tsakar falon. Shiga yai ya kalleta yace "Umma ga......" Wani wawan mari da ta sakar mai ne yasa ya kasa karasawa, tace " Uban me kaje yi gidan Waziri?" Kasa magana yai sai kuncinsa kawai daya rike yana kallanta. Magajiya ta kara hasala tace " wato bakajin maganata ko? Na d'auka na sanar dakai ba kai ba keb'ewa da yaya? Wato shine har da zuwa gidansa ko? Ka nunamin yafini matsayi a gunka ko?" Abdulmajid yai shiru, tace " fitarmin daga falo, sannan wlh karka kuskura inkarama magana akan wannan zancen, na fadama." Abdulmajid yai waje jiki a sanyaye, mota ya fada ya ja ta da gudu yai waje. Abu Turab na kallan sanda ya fita, ba shakka yasan Magajiya ta haushi da fada ne, a fili yace " am sry, sai dai kaima kayi abubuwa marasa dacewa wanda dolene kaima kaji ba dadi." Juyawa yai ya koma b'angaren sa. Har zai zauna ya fito ya nufi bangaren Umma. Tana zaune tana ta raba cingam ya shiga. Yace " Umma amma dai harda 'yan katsina zaki aikama ko?" Tace " kanaso kenan bikinka ya lalace daga biki zuwa gulma, gulmar da zata zama silar rugujewar komai." Turab ya kalleta yace " Kina tunanin zasuyi zancen anan?" Tace " Abu Turab kenan, bakasan mutane ba, kai a ido ne zaka ga kamar 'yan uwa ne amma a zahiri ba haka bane." Kallanta yai sai dai baice komai ba, a kasan ransa shikansa yana san yaga 'yan uwansa. Basira ta cigaba, kun had'u da Mai Martaba? Yace " a'a." Tace shikenan. Kallanta yai cikin kulawa yace " lafiya dai ko?" Tace bakomai. ******** Abdulmajid kam bai tsayar da motarsa ba sai a kofar gidansu Mairo, kallan kansa yai a madubi yace " baka da inda zaka sai nan?" Kofar gidansu ya kalla sannan ya kwantar da kansa jikin sityarin motar ya dade a haka kafin ya tada motar yai gaba. Yayanta ne ya shigo lokacin taba tsinke alayahu. Yace " Yauma kin fita kikai?" Mairo tace " infita zuwa ina?" Harararta yai yace " wlh ki kiyayi kanki da wulakanta mutum, mutum ma irin Yarima wanda kalma d'aya zai iya sa rayuwar gidan nan ta ruguje, tun dazu bawan Allahn nan yake waje har ya gaji yai gaba." Baki ta tabe tace " ni bai aikomin ba dan bansan yazo ba." Ciki yai tare da yin kwafa. Mairo ta cigaba da tsinke alayahunta, can tace " me ya kawoshi da ranar nan? Sannan bai aiko ba?" tsaki tai tace " damuwarsa ce." ************ Washegari kuwa Magajiya tasa aka kira mata Hisham, yana shiga ta rufeshi da fada kai kace itace uwarsa ba ma yayarsa ba balle kuma kanwa. Ganin abin ya zo mai wuya yasa yace " Wai Magajiya inada tambaya." Yaran nan da kike fada akansa na waye?" Tashin hankalin da ba'a misaltawa. Idanunta kadai sun isa su nuna maka tsantsan tashin hankalin da take ciki, tace " Yaya?" Yace " kwarai ni yayanki ne, sai dai abun ya isa haka, akan yaran nan yaje gidana zaki sani a gaba da fada haka? Cinyeshi nai a gidan nawa ko me?" Kallan mamaki takemai yanzu, yauce rana ta farko da Hisham yake maida mata murtani. Tace " yaya ni kake fadawa magana?" Yace " an fada miki d'in, duk yanda naso in kyautata miki na kula bakya gani, yanzu kwata kwata kin zama sai a hankali komai fada, ina Magajiyar da na sani wacce tsoro baya cikin zuciyarta?" Tace " nikaina bansan meke damuna ba Yaya, sai dai tundaga sanda yaran can ya ce yasan sirrina nakejin kamar komai na rayuwata xai ruguje, yaya ka taimakeni ka kashe yaran nan da uwarsa, ni har itama banasan gani ba shi ba." Hisham yace " in taimakeki? Duk abinda kike min?" Tace " amma ai kai kasab burina ko? Dolene mu kawar da duk wata matsala da zata kawo mana kai akan nad'a yaran nan mulki." Hisham ya kalleta a ransa yace "Magajiya kenan, zanyi duk abinda kikeso saboda d'ana, sai ya hau mulki in shekaki kema barzaho." Hannu ya saka zai murd'a kofar shiga, abinda yaji ne yasa ya tsaya cak sai jikinsa da hau tsuma saboda tsananin tsoro da razana. Magajiya ce ta katseshi tare da cewa " yaya." Kallanta yai bai amsa ba. Tace " na fasa kashe basira, mai kake gani in muka haukatata?" Hisham yace " hauka?" Tace kwarai " idan muka halaka Turab a ranar auransa ita kuma sai musa a haukatata kaga sai ace rashin d'anta ne yasata yin haukar." Hisham ya sheke da dariya yace " gaskiya Magajiya ba digon imani a ranki, duk duniya kece mutum ta farko danasan yasan salan mugunta, ko shed'an sai dai ya sara miki." Murmushi tai tace " ni dai yaya ka taimaken ka kyalemun yarona, wannan shi kadai ne abinda nakeson ka dashi, mu samu komai ya kammala, banasan wani abu ya tare mai hawa mulki." Kafafunsa ne suka kasa d'aukansa da sauri ya dafa bango, dan gaba d'aya jikinsa kaurewa yake da rawa...... *Turab* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *69* D'aki ya koma da sauri ya shige cikin d'aki shi kadai, labulayen d'akin ya rufe duka, ya shige lungun gado ya kankame kafafunsa. Kalaman dayaji ne suke dawo masa, a haukata Basira? A kashe Turab ranar auransa? Me ke faruwa? Me kunensa yakeji haka? Tsoro da fargaba sun hanashi fita, adaren ranar kuwa da zazzabi ya kwana. Cikin dare kuwa yayi mafarkin wannan abu yakai sau nawa. A zabure ya mike ya shiga cikin bargo, me Umma da kawu suke shirin yi? Kisa? Duk yanda yaso ya daure ko fitowa yai ya kasa. Kwanan Abdulmajid biyu ko kofar gidansa bai fita ba, ya rasa menene abinyi dan abin duniya ya dameshi. ***** Biki na ta matsowa, Gimbiya ansha gyara, gyaran da fadarsa ma bata lokaci ne, kullum Abu Turab na kiranta su gaisa. Yau ma tsokanarta yai tayi a waya wai bata gajiya da killaceta da akai? Ba dama ko fita tai? Sai dai tai murmushi tace " itakam bata ga wani abu ba." Suna gama waya ya ajiye kan wayar sannan ya kalli Sabi'u yace " ya ya irin wannan sa ido haka? Ko kishi kake ne?" Sabi'u yace " Gaskiya Turab da alama kanasan Gimbiya." Turab yai murmushi yace " bai kamata in so ta ba?" Sabi'u yace " ina na isa? Kawai dai da na d'auka kamar tursasa ma akai, amma yanzu naga kamar san ranka ne." Turab yai murmushi tare da mikewa tsaye yace " Sabi'u kasan menene abinda ke halaka rayuwar zaman aure?" "a'a." Turab yace " nunama mace kiyayya." Sabi'u ya kwashe da dariya yace " lalai Ango da alama ka fara shirye shiryen canza rayuwa." Turab a ransa yace ina zaka gane abinda hakan ya jawo? Jiya da daddare ya dade yana tunanin wani abu, idan ya duba menene ya sa Magajiya ta zama tsantsar muguwa ba shakka rashin nuna mata damuwa da Sarki yai ne tun farko, wannan shine yasa take neman ta kwatarma kanta 'yanci na samun duk abinda takeso, tare da sashi ya so ta ya kuma kaskanta a gunta, wanda hakan ne ya jawo tai ta tafka kura kurai tare da kauce hanya, gashi yanzu tayi nisa wanda ta manta ma da dalilin dayasa ta cikin wannan halin tun farko. Ajiyar zuciya yai tare da kallansa yace " Sabi'u kenan." ************ Gobe ne ake sa ran tafiya kano dan d'aurin auren Abu Turab, shirye shirye ake sosai da sosai, dan ma masu shirin suna Kano, masarautar kano kam ta cika ta batse da 'yan uwa na jini, na mulki da kuna na siyasa, Sarkin kano sosai yake cikin farinciki. Dan ana sauran kwana hudu daurin aure yasa aka kiramai Turab ya kara bashi amanar 'yar tilon 'yar tasa da yake ji da ita kamar nama d'aya a cikin miya, yayyinta ma haka sukai ta bashi amanar ta, ba shakka ya fahimci tsantsar gata da ji da Gimbiya Bilkisu da akeyi, sai dai ko ina kalma d'aya yake fad'a _Baiyi alkawarin santa ba kamar yanda suke santa ba, sai dai ya musu alkawarin kula da ita, da kuma kaucema duk abinda zai sata dana sanin auransa._ Magajiya kuwa da Hisham sun gama shirinsu tsaf, ta rasa gane kan Abdulmajid dan sai yai kwana biyu kafin yazo gaisheta, inyazo kuwa gaisheta kawai yakeyi ya mike ya tafi, sai dai batasa wannan a ranta ba dan tana ta faman shirin yanda zasuyi gun halala Turab. A ranar d'aurin auransa ne Abdulmajid sai zarya yake a d'aki, mai ya kamata yai? Duk yanda yaso ya cire abin a ransa ya kasa, shi gani yake menene nashi a ciki? Sannan shima ai ba san Turab yake ba, sai dai gani yake kamar duk saboda shi Magajiya da Hisham suke neman halaka Turab, dan ya hau mulki ya kuma auri gimbiya, sannan su salwantar da mahaifiyarsa wanda take tushensa. Har wajen karfe takwas yana ta zarya, gashi a lokacin mutane duk sun shirya ma sunyi gaba. Magajiya ce ta aiko akan yai wanka yai shiri sosai na gani na fada. Bai musa ba kuwa ya je yai wanka, kayan data aiko mai ya saka, kaya ne masu tsananin kyau da tsada, wanda ya tabbata ankashe kudi sosai a kansu. Harya fita ya koma ciki tare da yanko yar takarda ya rubuta kamar haka _Ka tabbatar ka sanar ma mahaifiyarka kar taci komai yau, in har ba ita tai da kanta ba, kar kuma tasha komai._ Fitowa yai ya samu wata baiwarsa wacce take kurmiya, ya mika mata yace taje waje ta ba yaro ya kaima Abu Turab, sannan ta tabbatar bata fadama kowa ba wanda ya aikota sannan karta bari a ganta. Hakan tayi kuwa, dan kurma Allah ya bashi iya rike sirri da kuma alkawari. Turab yana zaune, Sabi'u na ta wani fesa mai turare kamar zai juyemai kulbar a jikinsa. Turab yayi kyau na ban mamaki, Magajiya ta aikomai had'adun kaya sai dai bai sa ba, dan wannan Mahaifinsa ne ya aikomai. Dole ne in ya wuce sai ka kalleshi saboda tsantsar kyan da yai, kwarjininsa da zatinsa kadai xai sa ka kalleshi ta baya. Turab ya fizge turaren dake hannun Sabi'u yace " Ka bari in akazo naka auren sai ka fesa turare har a cikin bakinka ma, ba damuna zaiyi ba, amma ba ni ba." Sabi'u yai dariya. Shigowar Garzali ne yasa Turab ya kalleshi yace " Garzali ba na baka kaya nace ka saka ba?" Kansa ya sunkuyar yace " Ranka ya dade kayan ai sunfi karfina." Sabi'u ne yace " Gaskiya Turab ka d'au mataki da alama Garzali ya fara daina jin maganarka." Da sauri Garzali yai kasa yace " Tuba nake ranka ya dade, yanzu zan saka." Mikamai takarda yai yace " gashi inji wani yaro." Turab ya amsa tare da bud'ewa. Abinda ya ganine yatada masa hankali, yace " Garzali ina yaran yake?" Yace " ya tafi." Turab da sauri yai hanyar waje, dafashi Sabi'u yai yace " Lafiya?" Turab yace " ina zuwa." Waje yai da sauri sai dau ba yaran ba kuma alamunsa. Fitowa yai ya nufi bangaren Mahaifiyarsa tana zaune kasanta mutane ne suna ta kukula Kayan robobi da su dubulan da zasu raba. Mairo ya gani a gefenta, alama ya mata da hannu akan tazo. Mairo ta mike ta fito. Waje suka fita sannan ya kalleta yace " Mairo kina nan ai yau cir anan ko?" Tace " a'a anjima nakesan tafiya." Tai maganar fuskarta a had'e, irin wai kishin nan, balle yanda taga yasha kyau, haka kawai tana sanshi ba tun yanzu ba amma wata can a sama tazo zata aureshi...(😂nace Mairo ai dama haka rayuwa take, Matar mutum...Lol) dan itakam dan Basira ma ta aika tazone amma da bazata zo ba. Turab ya mika mafa takardar nan, tana karantawa ta d'ago cikin tsananin tsoro tace "Yaya mekenan?" Yace " ban san meke faruwa ba, sai dai na tabbatar akwai abinda ake shirin yi, ki tabbatar Umma bataci komai na gidan nan ba, ko ruwa in zatasha ki sa a kawo kara daga gidanku." Tace " ko ruwa?" Yace " bazai yiwu haka ba, yanzu bari nasa amaida ta kawai gidan Abba dake cikin gari, inaji hakan zaifi sauki." Tace " mutanen da zasu nemeta fa?" Kai ya dafa sannan yace " ko waye ma yazo nemanta ace batada lafiya tana asibiti." Mairo tace "to." Yace " ta fito yanzu ba sai kin fada mata ba, kawai kice wani guri nace a rakata ta gani, zan turo garzali, in yaso in kukaje gidan kya fada mata." Tace to Nan tai ciki, sai dayaga fitar Mahaifiyarsa sannan hankalinsa ya kwanta. Haka suka kammala komai suka fito, sai dai jikinsa gaba daya yayi sanyi, inhar Magajiya zata cutar da Mahaifiyarsa ya tabbata ta kanshi zata fara, ya tabbatar akwai abinda take shirin yi masa. Kansa ya dafe, da alama yayi sakaki da sharrin Magajiya, ya yi sake dayai tunanin bata isa yi masa komai yanzu ba. Abdulmajid yana kallansa a tsaye, cikin mutane suna ta gaigaisawa, sai dai ya tabbatar shima abin na damunsa, dan murmushin da yakeyi inka kula da kyau iya l'abansa suke basu kai har zuciyarsa ba. Ya tsani yaran can, amma me yasa yakeji bazai iya bari a kashe shi ba? Kai ya girgiza yace " ba wai saboda shi bane, ni raine bazan iya gani a d'auka ba, Allah ne kadai ya isa yin wannan." Cikin isa yazo ya wuce ta gun Abu Turab ko kallansa baiyi ba, shima Abu Turab ganin haka ya juya mai baya, Abdulmajid na zuwa ya bud'e had'adiyar motar Sarki wanda ya bada dan tafiyar Ango ya shiga. Sannan ya kallu mai tukawar yace " mu tafi." Kallansa yai yace " Ranka ya dade amma ai....." Katseshi yai cikin fada yace " ina sasa dakai? Ko kanasan yanzu insa a kulleka?" Da sauri ya shiga motar ya tada. Yai gaba, Turab yana kallan sanda Abdulmajid ya shiga sai dai bai d'auka tafiya zaiyi ba. Ganin sunyi gaba ya bi motar da kallo, lalai Abdulmajid, wannan kuma wani sabon wulakanci ne?" Sabi'u ne ya kalleshi yace " kaga mai ya faru?" Turab yamai alama da hannu yace " yai shiru kar aji, ba komai shi ya tafi a motar sa." Sabi'u yai kwafa yace " amma wancan anyi mara mutunci wallahi." Turab ya wuce ya shiga motarsa sukai gaba. Tafiya suke sai dai gaba d'aya hankalinsa ya kasa kwanciya. Me Magajiya take shirin yi? Yayi niyyar zuwa gunta kafin ya fito sai dai bangarenta taf yake da mutane. Abdulmajid kam tafiya kawai sukeyi su biyu a mota, ya tabbatar duk wani abu da zatayi daga kan hanya zata yishi. Sunyi nisa da tafiya wajen jeji kawai sukaga an tare gabansu....... *TURAB😌* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *70* Motar suka kalla da kyau da yanda aka nuna musu suka tabbatar itace, tsaida motar sukai ta hanyar tsayawa agaban titin tare da manyan sanduna da makamai. Tsoro ne ya shiga jikin Abdulmajid l, shikansa driver din ya tsorata sosai. Katon cikinsu ne ya bud'e motar ya cillo da driver din waje shikuma ya shige ciki. Nan yaja motar sukai gaba, can cikin wani daji suka shiga dashi. Abdulmajid ya kasa magana sai tsantsar fargaba dake damunsa, me ya kaishi? Amma dagaske su Umma abinda sukai shirin yima Abu Turab kenan? Lalai shikam yasan kwanansa ya kare, ashe bazasuyi sallama da Maironsa ba zai tafi kabari, dan tunda yaji wannan maganar a d'akin magajiya bai ko kara zuwa yaga Mairo ba. Sai da sukai tafiya mai nisa sosai, wani gida ne kwaya d'aya a tsakiyar dajin, gida ne karami, mutumin ya tsaida mota ya bud'e bayar motar ya fizgo Abdulmajid. Yana shiga ya cillashi ciki da karfi, jikake gum, ya buge, jikinsa ne ya shiga rawa ganin ba imani ko kadan a idan wannan mutumin, jawo kofa yai ya rufe, bai dade da fita ba yaji karar wata mota da alama ragowar ne suka iso dan ihu yaji sunayi kamar tab'abu. Tsoro ne ya kara shigarsa, idanunsa sun firfito da tsananin tsoro. Jiyai an banko kofa da karfi suka shigo. Ogan cikinsu ne yazo inda yaje ya d'aga sanda ya makamai a kafa da karfinsa. Wani mugun kara Abdulmajid ya saka wanda sai da dajin yai kara, tsananin azabar dayaji je yasa yasan anma kafarsa illa babba. Zufa ta ko ina take ketomai, hawaye ne ke zubomai sosai saboda rad'adi so yake ma yace musu su kira wanda yasasu aikin dan ba shi bane amma ina...Azaba ta hanashi magana sam. Murkususu yakeyi, ogan yasa dariya yace " ance mu wahalar dakai kafin mu shekaka bar zaho." Suka tuntsire da dariya...... ********** A motar Abu Turab kuwa tafiya suke amma gaba d'aya hankalinsa ya kasa kwanciya, sai dayaga sun isa kano sannan yaji ya d'an samu sauki kadan a ransa. Yana isa ya tadda masallacin masarautar nan taf take da jama'a, sai kiranshi ake suna gaisawa da mutane. Har Saif ya gani a gun taron, sai dai kallo d'aya yamai ya d'auke kai yai kamar bai ganshi ba. Yanda Hisham yai a sanda yaganshi yasa yasan da wani abu, kusa da Hisham ya karasa yace " Waziri lafiya?" Shidai Hisham yana bayan motar sarki kadan, saboda dama anyi daga zarar motar ta fito tayi gaba sai ya bisu a baya, yana kallan aka cilar da driver din sannan wanj ya shiga yaja motar, sannan yayo gaba. Kallan Turab yai a razane yace " motar Sarki ba a ciki ya kamata kazo ba?" Turab yace " a ciki ne amma Abdulmajid.........." Yanda yaga idanun Waziri sunyi ne yasa ma ya kasa karasawa, kallansa yai yace " ya akai kasan a motar sarki zanzo?" Hisham kam baimasan me yake cewa ba shidai juyawa yai da sauri zai fita. Turab yasa hannu da sauri ya riko rigarsa yace " ina Abdulmajid?" Hisham ya gama rikicewa kai kawai yake girgizawa. Turab yace " ina Abdulmajid?" Hisham ya fizge rigarsa yai waje da gudu. Sabi'u ya taba yace " yi sauri kabi Waziri kaga ina zaije." nan sabi'u yai waje. Turab nan ya dunga kutsawa cikin mutane yana neman Abdulmajid sai dai bashi ba labarinsa. An d'auran Auren Gimbiya Bilkisu da Yarima Abu Turab a ranar Asabar da misalin karfe goma sha d'aya na safe, a massalacin dake gidan sarki na kano. Abu Turab kawai dai yake yakeyi amma gaba d'aya hankalinsa baya jikinsa, meke faruwa? Hisham kam mota ya shiga ya dinga zabga gudu, sabi'u na bayansa yana ta binsa, a ransa yace " ko dai zariya zai koma?" Har yai tunanin juyowa ganin suna ta tafiya ba tsayawa, gani yai ya gangara ya sauka daga kan titi ya nufi wani lungu cikin daji. Tsayawa yai yana tunani kafin ya ajiye motar ya fito yabi bayansa cikin dajin, dan ya tabbatar inyashiga da mota hisham zai ganshi. Hisham na isa wannan d'an gidan ko kofar motar bai rufe ba ya fito cikin hanzari. Buga musu kofa yai tayi da karfi sai dai ba alamar kowa a ciki. Ya gama rikicewa gaba d'aya dan ya gama sadaukarwa an gama kashe mishi d'a, zama yai a waje kawai yasa wani irin kuka. Sabi'u ne ya karaso duk ya gama gajiya, hango gidan dayai ne yasa ya tsaya, Hisham ya gani a zaune yana baza wani irin kuka. Boyewa yai jin shewar mutane, Hisham na jinsu ya taso a zabure ya cakumi wuyan ogan cikin su yace " ka kasheshi ko? Ka kashemin d'ana ko?" Ogan ya kwace rigarsa yace " Malam me kenan? Kai kabamu kwangila sannan yanzu meye na zuwa mana da wannan zancen?" Hisham cikin karaji yace " Abdulmajid kuka kama ba Abu Turab ba." Kallansa sukai sukace " anma ai shine a cikin motar." Hisham a rikice yace " bud'e min kofar, kun kasheshi ko?" Bud'e kofar sukai, da sauri ya shiga ciki, yanda yaga Abdulmajid a yashe yasa ya gama rikicewa, cikin tsoro ya karasa gunsa, durkushewa yai a gub yana kuka sosai yace " najama kaina masifa, na kashe d'ana na cikina da kaina saboda wani buri nawa na shirme, nikam na shiga uku na...." Oga ne ya matso yace " tab amma Allah ne ya kiyaye dan har naso mazgemai wuya nai tunanin barinsa zuwa anjima, ba shakka da anyi tsiya." Hisham ya kalleshi a tsorace yace "kana nufin yanada rai" Sosai ma sai dai kafarsa d'aya banaji zatai aiki. Abdulmajid dake kwance yana fitar da numfashi sama sama kalaman Hisham suka daki kunuwansu, d'ansa?na cikinsa? Sai dai ba wani abu da zai iya yi dan ko magana ya kasa yi saboda dukan da sukai tamai da kafa. Hisham ya d'ago Abdulmajid ganin yana numfashi yasa yace su taimaka mai ya sashi a mota. Nan suka fito. Ogan yace " Kayi hakuri yallabai, yanzu ya za'ai mu kama d'ayan?" Hisham ya buga musu kallo yace " ku tabbatar kun bar garin nan kafin wani abu ya faru, ai dama na gama biyanku kudinku. Nan ya shiga mota. Sabi'u na kallansu, Abu Turab sukaso kamawa kenan su halaka? To ya akai Abdulmajid ya shiga motar? Da alama yasan da shirinsu kenan? Lalai mutanen nan basuda imani. Sai da Hisham yai gaba sannan shima ya fito, ya fita ya shiga mota, har zaiyi Zariya sai ya koma Kano. Abu Turab yana cikin jama'a bayan an gama aka shiga cikin gida dan yin walima wacce yayun amarya suka shirya musu. Suna gamawa ya fito kenan sai ga Sabi'u. Da sauri ya matsa gunsa yace " ya ya?" Sabi'u yace " Abdulmajid suka kama sun d'auka kaine, da alama Waziri ne yasa a kamaka." Turab ya shaka fuskarsa da hannu biyu, ji yai idanunsa sun ciciko, mai yai wa mutanen nan, mai ya tsole musu a duniyar nan, duk abinda yaji game dasu, mahaifin Khadija? Magajiya? He will never forgive them, kallan Sabi'u yai yace " ya jikin Abdulmajid din?" Sabi'u ya girgiza kai yace " da alama ba dadi abin dan naga kaishi mota akai." Turab ya d'aga kansa sama saboda hawaye dake neman zubomai, sannan ya kalli Sabi'u yace " Da alama yasan abinda suke neman aikatawa, how can i forgive those people?" Duk yanda yaso ya kore abin saj da hawaye ya zubomai ta kwaryar idanunsa, Sabi'u ya dafashi yace "Amma dama haka kake rayuwa cikinsu?" Turab yai wani murmushin takaici sannan ya cije lab'ansa, wato su sukai su kasheshi sai su ba Basira magani suce hauka take saboda na mutu? Tabbas sai yanzu ya had'e puzzle din. Hannunsa ya dunkule kai kace wani zai kaima naushi........... Nikam ina ganin haka nai waje da gudu dan na d'auka ni za a make dan yanda naga idanun turab? Ba sauki...... *Turab* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *71* Magajiya kam tana zaune cikin mutane anata hidima, sai dai ta rasa gane kan dalilin dayasa akace mata wai Basira bata gidan, aikenta uku amma duk maganar d'ayace wai bata nan, ba haka taso ba lalai d'an iskan yaran can ne ya d'auke ta, to menene dalili? Inta tuna haka sai tai dariya tace " bakasan gani na karshe zaka mata ba. Kowa yazo sai ya yaba kyan datai, saboda tsananin kyan datai, ga wani annashuwa da jin dadi dake fita daga fuskarta, tasha kwalliya, tasha lalle,hmmm abin ba a magana farinciki biyu take jira a kawo mata, na mutuwar Turab dana auran Abdulmajid da Gimbiya, taga uban da zai nemi kwace mulkin d'anta. Aikowa akai akan Waziri nasan magana da ita, tace " a sanar dashi ina cikin taro, dan itakam ta san me zai sanar mata. Dama kuma abinda take jira kenan." Sau biyu yana aikowa akan yana nemanta daga karshe tace " wai akan me tana cikin taron mutane zai dinga aikawa tazo?" Murmushi tai a ranta tace " nafisan in zan fita anjima infita da kukan mutuwar d'ana Turab. Jin haka ne yasa Waziri yaga in ya biyema jiran Magajiya d'ansa zai karasa, fitowa yai ya ja mota ya wuce asibitin ABU Gun abokin Mai Martaba. Cikin tashin hankali da tausayawa aka shiga dashi cikin emergency. ********* Tana zaune akan kujerarta Sai da sukai ta sallama da mutane sannan aka barshi ya taho. A hanya addu'a kawai yake akan Allah yasa ciwon Abdulmajid ba mai lahani bane, motar tasu tsit har suka isa kamar ba motar Ango. Suna isa ya fito bai bi takan masu mai busa ba yai bangaren Magajiya. Yana shiga aka fara gaisheshi, ganin gidan a cike taf yasa ya rasa yanda zaiyi, ga shi mata ne fal, juyawa yai ya fita tare da dafe kansa. Kallan Sabi'u yai yace " muje gidansa, da alama ba nan yayo ba, dan ba alamar sun san wani abu." Nan yai waje, sunje gidan Waziri tare da sanar da masu kula da kofa akan neman sa da suke yi, nan suka sanar dasu ai baizo ba. Turab yace " muje gun Umma in sanar da ita sai mu shiga duba asibiti, dan na tabbatar tunda aka kaita wannan gidan a tsorace take." Nan sukai gidan Mai martaba na cikin gari. Mairo tana cire mata lalen data mata suna yar hirarsu sama sama, sukaji sallamar Turab. Wani lallausan murmushi ne ya bayyana a fuskar Umma dan ba shakka zuciyarta a d'arare take, Mairo ma ta mike tare da d'auke robar lalen. Turab ne ya shigo ya kalli Mairo cikin jin dadi yace " kanwata ina godiya sosai." Murmushi tai tare da sunkuyar da kai. Umma ta kalleshi tace " Alhamdulila, sai yanzu hankalina ya kwanta." Turab ya zauna tare da cewa " umma ke sai yanzu kikai lalen bikin?" ya fada yana kallan Mairo ta gefe. Fuska ta hade tace " itadai Umma lalle tai ba wai na biki ba, ko Umma?" Basira ta d'aga kai tace " ina na isa yin lalle abikin Turab ai ni bikinki ne kadai zanyi Lalle Mairo." Mairo tace " yauwa Umma." ta juya tai waje. Turab ya kalli Umma yace " Umma kin tsorata ko?" Kai ta girgiza alamar a'a tace " Turab taya zan tsorata akan abinda nasan kana da dalili na aikata shi?" Murmushi yai sannan yace " Umma da matsala Amma." Tace " tame kenan?" Mairo ce ta d'auko mai lemon zubo da tai tare da abinci, tana kokarin shiga taji yana cewa " Abdulmajid inaji yana asibiti." Basira tace " mene?" Turab ya kwashe komai ya sanar da ita. Idanu ta runtse tashiga fadin Inalilahi wa ina ilaihi raji'un. Mairo kam jikinta ne ya shiga kakkarwa, daurewa tai tai sallama. Turab ya amsa tare da juyowa. Ajiye tiren tai ta mike zata fita. Turab ya kalleta, yana kallanta ya fahimci taji me yace, nan yace mata "Abdulmajid na asibiti." Kanta na kasa tace " Me ya dameni Yaya? Fatan sauki ne namai Allah ya bashi lafiya." Mikewa tai ta fita. Turab ya mike ya biyota tana kokarin shiga kitchen yace " kin tabbatar bai dameki ba?" Kai ta d'aga mai sannan ta shiga ciki. Kallan Umma yai wacce gaba d'aya komai ya mata zafi yace " Umma karki damu yanzu zanje mu duba inda yake." Basira tace " ka cire babbar rigar." Nan ya zareta sannan yasa akan kujera." Tace " abincin fa?" Kai ya girgiza yai waje. A kofar kitchen din ya tsaya, Mairo ya kalla tana tsaye ta juya baya, ba abinda take a kitchen din, da alama tunani take. Yace " Mairo zo ki rakani." Kallansa tai tace " ina?" Yace " neman Abdulmajid." Tace "ni kuma meye nawa?" Turab yai murmushi yace " wai dole ne sai an nunamin akwai dakakkiyar zuciya? Bayan ni ina ganin rauninta?" Mairo ta juya kai, yace "wuce muje." Fitowa tai tasa takalmi suka fita. Sabi'u na cikin motar turab ya shiga gaba. Ita kuma ta bud'e baya ta shiga. Sabi'u ya kalli Turab ya kuma kalli Mairo ta madubi sai dai baice komai ba. Turab yace " mu fara da asibiti babba ko?" Sabi'u yace " ni nasan ma yana ABU dan shikadai ne asibitin da zasu(😂nace da wannan lokacin ne da bakace haka ba, yanda asibitoci sukai yawa.)" Turab ya jinjina kai. Sun isa asibitin ABU, suka nufi emergency, Mairo tana tsaye bakin kofar shiga, gabanta ne kawai ke faduwa, wanda ita kanta batasan dalili ba. Can suka hango Hisham, Sabi'u ya taba Turab tare da nunamai Hisham. Nan suka nufi gun. A kwance yake kamar mai baccu sai kafarsa da aka gewaye da katako, kallo d'aya zaka ma gun ka fahimci karayace a gwiwarsa sannan ga bandage da aka nad'e kasan gwiwar dashi alamar ciwo, duk fuskarsa ma an masa dressing guri guri. Hisham kam kallan Abdulmajid kawai yake ya baza tagumi. Turab na isa gun ya kalli Hisham cikin b'acin rai. Baimai magana ba ya kalli wani nurse dake gun yace " ya jikin shi?" Yace "duk an gyara ciwokan da kuma karayar yanzu ma d'aki za'a maidashi dan neman samun sauki, saboda Director yace kar a barshi anan." Turab yace " to." Nan suka turo gadon. Ta gabanta sukazo suka wuce, gaba d'aya jitai komai na jikinta ya dena aiki, kana kallansa kasan yana jin jiki sosai. Binsu kawai take har suka isa d'akin, a baya ta tsaya ganin d'akin da suka shiga. Hisham na kokarin shiga turab ya tare kofa tare da kallansa. Yace " Waziri mai kake anan?" Hisham ya bishi da kallan mamaki, wannan wace irin tambaya ce? Ya kawo yaro asibiti amma a tambayeshi me yakeyi anan?" Turab ya kara cewa " waziri mai kake yi anan?" Hisham yace " bam gane ba?" Turab yace " saboda tsaro da kuma yin bincike na ke sanar dakai abu d'aya in har kanasan kaga Abdulmajid sai ka bi abinda nace." Mamaki ya hana Hisham magana, Turab yai wani murmushi yace " ko kana tunanin bansan ni kukaso a ma illa ba?" Gaban Hisham ya yanke ya fadi. Turab yace " kaje gidanka yanzu, ka jirani zuwa gobe." Hisham samun kansa yai da cewa to, ya juya yai gaba jikinsa a sanyaye, yanayi yana waiwayen kofar. Kallan Abdulmajid Turab yai, ya dade yana kallansa, tsananin tausayinsa ne ke ratsashi gashi duk jikinsa ciwuka banda karaya, kamar ba shiba sam. Turab ya kalli Sabi'u yace " zo muje gun likitan." Sabi'u yace " karkuma abarshi shi kadai." Kallan Mairo Turab yai da take rakube a gefe yace " akwai wanda ahi kansa mara lafiyar yafisan ya gani." Bai fahimta ba sai dai ya gane akwai wanda zai zauna har suje su dawo. Sai da sukazo inda taks Turab yace "ki shiga ki duba shi." Sukai gaba. Mairo a hankali ta tura kofar d'akin ta shiga. Jikin gadon ta karasa sannan ta kalli fuskarsa, gaba d'aya an mata faci. Fuskar ta kurama ido tana tuno abubuwan da suka dinga shiga tsakaninsu. Sam bata san sanda hawaye suka ciciko a idanunta ba, a hankali wasu siraren hawaye suka gangaro kan fuskarsa. Jin ruwa a fuskarsa ne yasa ya dan motsa idanunsa kadan, a hankali ya bud'e idanunsa da suka kumbura idanunta a rufe suke, yana kallanta ya maida idanunsa ya rufe. Ina ya isa ya kalleta a cikin wannan halin? Ba ma wannan halin ba, ina ya isa yi mata magana bayan bai gama sanin wanene shi ba? Menene matsayinsa? Idanunta ta bud'e a hankali sannan ta juya baya, tare da zama akan kujera, itadai so take ta karyata zuciyarta akan kukan nan tayine saboda tausayin d'an Adam ba wai saboda wani Abdulmajid ba. Shikam ji yake inama ba wani babban sirri agabsa yaga Mairo tana nuna damuwa haka a gabansa? Meke shirin faruwa dashi? Wasu zafafan hawayene suka gangaro ta gefe idanunsa. ******** A can kuwa Magajiya takaici ya isheta, har yanzu busa takeji da wasanni a gidan sarauta bata fara jin koke koke ba. _TURAB_ 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *72* Turab ne ya kalli likitan sannan yace " kana nufin kafarsa bazata dawo dai dai ba?" Kansa ya girgiza alamar a'a yace " ba wai bazata dawo daidai gaba d'aya ba, sai dai dawowarta daidai din abu ne mai wahala, a yanzu inya warke zamu had'ashi da sanduna dan taimaka masa gun tafiya, idan har Allah yayi sai kaga a hankali kafar ta warke in yana samun kulawa." Turab yai godiya suka mike, kallan Sabi'u yai bayan sun fito yace " Sabi'u muje ka kaini gida, sai ka d'auko Khadija ka kawo asibitin ta zauna jinyarsa, ni akwai abinda zanyi." Sabi'u yace " wacce muka kaifa?" Turab yai murmushi yace " kana tunanin zai sake a gun yarinyar da yake so?" Gaba yai daga fadar haka, mota suka shiga ya kaishi gida, akan inya d'auko Khadija sai ya maida Mairo. Magajiya kam ana zaune a waje dan an fito waje wajen wani had'aden kwalliya ta sarauta da aka zagayen gun dashi, matane manya ke ta kid'an kwarya na ruwa, sai gaishe gaishe akeyi. Turab yana shiga ya wuce bangarensa wanda yanzu komai nashi an kwashe daga bangaren, wanka yai sannan ya bud'e drawer da ya ajiye wata shadda a ciki dan dama ya ajiye ne saboda zuwa bangaren Amarya da ita, jawota yai tare da kallan d'ankwalin daya biyo bayan shaddar. D'ankwalin Khadija ne, sawa yai a aljihunsa dan yau zai maida mata d'ankwalinta, inhar ya maida mata kuwa to yana nufin komai na alakar dake tsakaninsu ta tsaya kenan. Fitowa yai daga bangaren, rawani yasa akamai, sannan yasa a d'aukomai dokin da Sarki ya bashi. Had'aden dokin da mai martaba ya bashi ya hau, yasha ado na ban mamaki, Turab ya hau kai sannan ya nufi inda ake ta mai hawan dawakai. Yana Isa masu busa suka canza salan busarsu aka saki wani kiraki. Magajiya tana zaune labari ya iso mata na hawan da Ango yake yi. Kallan yan aiken tai tace " Turab ne?" Sukace sosai ma, duk da dai rawanun dayai bazai bari mu tabbatar shi bane amma ai kowa yasan Ango ne. Tsaki tai a ranta tace " zancen banza kenan, Ango? Ai Abdulmajid ne angon." Yana gama hawa dan ba dadewa yai ba ya nufi inda Magajiya take. Aiko mata akai akan d'anta yazo kwasar gaisuwa. Murmushi ta saki tace " ace ya shiga ciki ina shigowa." Nan aka sanar ma Turab. Ciki ya shiga ya samu guri ya zauna. Magajiya ta mike cikin yauki ta nufi ciki. Murd'a kofar tai ba tare da ta kula ba saboda bayansa ya juya tace " Ango kasha kamshi, dafatan yanzu ka hakura da aura........." Juyowar da Turab yai tare da cuge rawanin ne yasa ta tsaya cak da maganar, jitai wani abu tundaga tsakiyar kanta har kafarta. Turab ya tako cikin isa ya karaso inda take, hannu yasa ya tura kofar d'akin data rike da karfi bai cire hannunsa daga kai ba yace " Kina mamakin ganin wanda ya kamata ya mutu ne a tsaye a gabanki?" Magajiya ta kakaro murmushi tace " me kake nufi? Kaine Angon mana, ko akwai wani aure da akai da ban sani ba?" Turab ya girgiza kai yace " ina fa? Ai ni kadai ne a gidan nan aka d'aurama aure yau sannan aka Wani asibiti." Magajiya tace "asibiti kuma? Me kake nufi?" Turab idanunsa ne suka canza kala ya juyo ya kalleta yace " sa mayafi mu fita." Tace " mene?" Yace " abinda kikaji shi zakiyi." Wata muguwar dariya ta saki tace " mene?kai harka isa ka sani nayi abinda banyi ra'ayi ba?" Murmushi ya mata yace " daya wannan lokacin kuwa duk wani abu danai ra'ayi shi xakiyi." Ranta ne ya baci matuka ta d'aga hannu zata wanka mai mari. Jitai yace " Ya Abdulmajid zai ji in yasan kece kika sa aka kusa kashe shi?" Hannunta ta tsayar kusa da fuskarsa, tace " Abdulmajid? Me ya sameshi?" Turab yace " me ya sameshi? Yana kan gadon asibiti numfashi ma banaji yanayi, ko kin manta ke kika sa a kasheni? " A rikice tace " to meya kawo Abdulmajid ciki?" Turab yace " wannan kuma ke zan tambaya, ya zakiyi? D'an da kike gwagwarmaya a kansa gashican nufashinsa na neman d'aukewa." Wani irin ihu ta saka ta kama kwalar rigar Turab tace " kana nufin d'an nawa ba ma tabbas ko yana da rai?" Turab yace " ke nake jira muje ki ganshi kafin mu mikashi gidansa." Wani irin ihu ta kara sakawa tace " kai har ka isa? Waye ya baka damar cewa d'ana numfashinsa na neman yankewa? Amma ban taba ganin mutum mara imani irinka ba, d'an nawa ka tura a ka kusa kashewa?" Turab yai dariya yace " mara imani? Na tura? Magajiya na kasa fahimtar wa kikema inkiya a wannan maganar, ko kinaso kicemin Waziri shi kadai yai abin ba tare da kin sani ba?" Magajiya ta kalleshi tace " Hisham? Eh shine yasa akai komai, ni meye nawa na neman ganin bayan rayuwarka?" Turab yai wata dariya yace " dama ta ina zaki yadda kece sila bayan ni nasan wacce ke? Duk abinda Hisham ya miki kenan kanki kawai kika sani?" Fuska ta had'e tace " bugar cikina kazoyi kenan?" Turab ya bi kwayar idanunta da kallo, tace " me? Akwai wasu daka b'oye a d'akin nan? So kake kaji me zan fada?" Turab yace " me kike san kice?" Tafin hannunfa ta d'aga tace " ka san me yasa muke da zane kala kala a hannun mu?" Yace " kwarai, kissa ta biyo akan mata ne lokacin Annabi Yusuf......" Ta matso kusa dashi sosai yanda shikadai zai iya jin ke take cewa tace " mata ko? Amma tunda kasan wannan kissar kasan me matar da ta sasu tai ko?" Kallanta kawai Turab yake, tace " mace aka ce, ni kuma a matan ma dabamce. Sharri na da sanin duniya da nai ko rabinta bakai ba, kai baka isa ka shiryamin ramin da zan afka ba." Hannu tasa ta ture hannunsa ta bud'e kofa tai waje. Turab ya ciji lab'anbansa. Mahaifinsa dake jikin d'ayan d'akin ne ya fito. Bazaka taba cewa sarki bane dan Shadda ya saka ba rawani a kansa sai hula, shida Sabi'u ne. Abdussamad ya matso ya dan daku kafadar Turab yace " ya kafadar jarumin d'ana zata yi kasa?kana tunanin daga bugun farko zakasa magajya tai kasa? Da daddare naje naga jikin nasa, sannan mayi maganar abinda ke faruwa a hankali, yanzu in aka kula na dade bama fada za'ai zargin wani abu." Turab yace " Tuba nake." Sarki yai murmushi yace sannan yai waje. Turab ya tuno plan dinsa. Sanda Sabi'u zai tafi d'auko Khadija ya sanar dashi akan in har yanasan ganin d'ansa to yaje ya sanar da Sarki akan Magajiya na san ganinsa ganin gaggawa dan da matsala, saboda shi a ka'ida bai isa yaje fada yasa mahaifinsa tasowa. Idan mahaifinsa yaji haka ya tabbatar ransa zai baci, sai dai bai isa nunawa ba saboda girmama matarsa kuma uwar gida. To in ya fito sai Jakadiya ta sanar dashi shigar burtu. To yasan mahaifinsa inyaji haka yasan Turab ne ya shirya wani abu. Ita Jakadiya zatazo bangaren magajiya ta tabbatar ta sa mutane sun fita gun kida da wayau, shikuma Sabi'u yana dawowa sai ya taho raka sarki yanda ganinsu tare bazai sa mutane susan sarki bane. Turab ya kalli Sabi'u yace " da alama nayi gaggawa akan yin plan dina, bazata taba yarda ta a sake fooling dinta twice ba." Sabi'u ya girgiza kai yace " wacce kake yi da ita ne tafi karfin plan din bawai kayu gaggawa ba." Turab ya shafi kansa yace " ka kai khadijan?" Yace " eh, na kuma maida Mairo gun Umma." Turab yace " nagode." Sabi'u yace " gobe fa Amarya zatazo haka zaka tarbeta jiki a sanyaye?" Turab yai murmushi yai waje. ********* Magajiya na fita tai bangaren Abdulmajid tasa a kira mata Hisham. Gabanta sai faduwa yake ba kakkautawa, inka kula da hannunta ma rawa suke yi. Yana shigowa ta taso a rikice tace " Me ya samu Abdulmajid?" Hisham yace " tun yaushe nake aikawa kizo?" Tace " meya sameshi?" Hisham yace " yana asibiti gun Turab." A rikice tace "wani irin hauka nakeji haka?" Ganin baiyi magana ba cikin tsawa tace " uban waye ya dakarmib d'a? A kuma wani dalili ne zai kasance gun Turab??" *Turab* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *73* Ta gabansa ta wuce a zuciye tai waje. B'angaren Turab ta nufa, ba kowa a bangaren sai mai kula da kofa, gaisheta yai ya sanar da ita ai ba kowa a nan. Juyawa tai hankalinta a tashe, ina ya kaimata d'anta? Itakam mai makon wannan ranar ta zama ranar farin ciki yau kam wannan ranar ta gama zame mata ranar bakin ciki. Ga magrib ta kawo kai..... *********** Duk yanda Khadija taso da ya bud'e ido amma inaaa, ya kasa,yana kwance idanunsa a rufe, itakam gani take kamar baya haccinsa, sai dai shikam bayaji zai iya bud'e idanunsa yaga maike faruwa a wannan duniyar, bayasan ya bud'e idanunsa yaji abinda kwakwalwarsa bazata iya d'auka ba. Khadija zama tai a gabansa duk ta rame a 'yan kwanakin nan dan itakam sam yanzu rayuwar bata mata dadi, tace " Yaya ka taimaka ka farka." A can gidan Barde kuwa kwance take a kan gado banda juyi ba abinda takeyi, ta rasa menene ya hanata bacci, ta dade tanata juyi ta gaji ta mike zaune tare dayin dogon tsaki tace " Allah ya isa? Wannan wace irin muguntace? Haka kawai ku samu mutum ku hau dukansa ba gaira ba dalili?" Ahh ashe fa akwai dalili tunda Ya Turab akaje daka shi kuma ya shiga motar? Hannu tasa akan kirjinta tare da turo baki gaba tace " Allah sarki, ashe mutumin nan nada tausayi, sannan zuciyarsa ba wai mara kyau bace duka, me yasa muka kasa gani?" Ajiyar zuciya tai ta tuno sanda take mai rashin mutunci shi kuma yake nuna ba komai, batasan sanda ta sa murmushi ba, tunowa datai yanda ta ganshi a kan gado yasa jikinta yai sanyi. Idanunta ne taji ya ciciko, da sauri ta kwanta taja bargo ta rufe duka har kanta. *********** Mai Martaba ne ya kalli Turab yace " ya akai Abdulmajid ya kasance cikin wannan halin?" Turab ya kalli Abdulmajid da ke kwance yana bacci, karfe shida da rabi ne na safe dan ana sallar asuba suka taho shida Mai Martaba. Khadija na kwance akan sallaya rike da karamin kur'ani izu biyu da alama tana karatu bacci yai gaba da ita. Yace " Tuba nake ranka ya dade amma ni akaso halakawa." Sarki ya kalleshi yace "Shi kuma yaji kenan?" Turab ya d'aga mai kyai. Idansa ya runtse kadan sannan ya juya. Turab yace " Abba bazaka shiga ba?" Kai ya girgiza yace " kana tunanin zaiso gani na? Ko kana tunanin zai so ganin kowa? Bayan yaji da kunnensa mahaifiyarsa na neman yin kisan kai? Me kake tunanin yana ayyana wa a kwancen nan da yake?" Turab ya kalli Andulmajid cikin tausayawa. Sarki ya kamo hannun Turab yace " Abu Turab!" Turab ya kalleshi sai dai bai amsa ba. Sarki cikin wata irin murya yace " na girma, sannan ko ban girma ba haka na taso a rayuwar auranmu da barin Magajiya taci galaba akan dukkan lamuranta, saboda bata taba barin evidence dazai nuna tabbas itace ta aikata abu, sannan inba wanda ya san halinta ba ba wanda zai yanda akan abin da zata iya aikatawa, ina rokonka daka taimakama wannan mahaifin naka ya aiwatar da babban harkar shari'a ta gaskiya na karshe akan gadon mulkinsa, ka kawomin hujjojin da zasusa Magajiya ta fuskanci hukunci akan mayyan laifukan da ta aikata, wannan shine babban burina da ya ragemin a duniya in hakan ta faru inaso inyi murabus in baka mulkin nan, in d'auki mahaifiyata da matata mu ziyarci ka'aba dan ziyarar d'akin ma'aiki sannan mu jira sanda in karasa rayuwata cikin al'umma ina kallan yanda kake tafiyar da naka mulkin wanda shine abinda nafisan gani." Turab yai shiru yanajin kalaman mahaifinsa,can ya d'ago yace " Abba insha Allah wannan d'an naka bazai baka kunya ba, sai dai maganar murabus mayi daga baya in komai ya kamalla." Sarki yai murmushi sannan ya kara kallan Abdulmajid cikin tausayawa sannan yai waje. Turab ne ya murd'a d'akin jinshi a kulle ya kai hannu zai kwankwasa. Yanda yaga khadija tana bacci ne yasa ya sauke hannu tare da fasawa, ya tabbatar tana bukatar hutu. Maida kayan mota yai ya zauna a cikin motar tare da kwantar da kansa jikin kujera. Garzali ya saukemai glass, a hankali shima bacci ya zareshi. ********* Magajiya kam wannan rana a zaune digirgir ta mata, babban tashib hankalinta duk inda ta aika a nemomata Turab sai ace baya nan, a wani hali Abdulmajid yake ciki? Dan itakam batasan wani abu ya sameshi, yanzu in matsala ta sameshi ta tabbatar shikenan ba shi ba hawa mulki, in hakan ta faru kuwa to wallahi sai dai kowa ya mutu dan Abu Turab bai isa hawa mulki ba sai dai su mutu tare. Karfe bakwai tai wanka tai kwalliya tsaf kai kace ba matsalar dake damunta ta kintsa ta fito. Masu kula da ita mutum biyu tace " su biyota." Wajen karfe takwas tasa driver dinta akan ya wuce da ita ABU, manta wa ma tai ta tsaya tunanin ina aka kaishi. Suna isa asibitin cikin sa'a ta hango motar Turab a waje. Driver dinta ta kalla tace " je ka kiramin Garzali." Nan yai waje, bai dade ba sai gasunan tare, Magajiya ta kalli Garzali tace " me kuke a waje haka?" Yace " Yallabai ne ya samu bacci." Tace " ayya, gashi shi yace inzo asibitin mu shiga tare gun Abdulmajid, kuma ba dadi yana bacci a tasheshi, ga ba wanda yasan gun, da alama sai dai ka taso shi din ko?" Garzali yace "gun Yarima zaku?" Tace " eh, kasan jiya ina cikin taro ban samu nazo ba sai yanzu." Sunkuyawa yai yace " nasan d'akin in ba damuwa sai na kaiku kafin ya tashi." Tace " shikenan." Ta fada tare da fitowa. Sun isa har d'akin, ta sa aka kwankwasa kofar. Khadija dake kwance ta mike tare da zuwa bakin kofar tace waye?" Magajiya tace " Bud'e." Kallan masu kula da ita tai a Garzali tace "su juya." Gaban Khadija ne ya fadi dan Turab ko Ummansu bai bari tazo ba, a hankali ta bud'e kofar Suna juyawa ta d'aga hannu ta wankama Khadija wani gigitacen mari. Kuncinta ta rike saboda azabar da taji, shikanshi Abdulmajid sai daya farka daga baccin, dukda dai bai bud'e ido ba amma yana jinsu. Magajiya tace " Wato ke kin zama rikakiya ko? D'ana bashida lafiya dan tsabar rashin mutinci baki aikomin ba, bare insa ran zaki sanar dani inda yake." A yanzu ji take zata iya yin komai dan kare d'anta, duk kuwa da yanda takesan Khadija. Wucewa tai ta kusa da ita ta nufi gadon da Abdulmajid ke kwance. Kallansa ta shiga yi sannan ta sa hannu kan kafarsa tace " wa ya saka? Wayace ka shiga motar da ba taka ba? Da kai nake magana, ka bud'e ido ka bani amsa ko sai ranka ya b'aci?" Gaban Abdulmajid ne ke ta faduwa. Muryar Khadija taji tace " Haka Uwar kirki ya kamata ta fada ma d'anta dake kwance ba lafiya?" Magajiya ta juyo ta kalleta tace "mene?" Khadija tace " girma ana bawa wanda yasan darajarsa ne sai dai wanda baisan darajar ba banaji ya cancanceshi, bansan me kike nufi ba da cewa Wayace ya shiga mota ba amma banaji haka ya kamata uwar da danta ke kwance ta fadama d'anta." Magajiya cikin gadara ta fara takowa inda Khadija take, ba shakka yarinyar nan Turab ya gama lalatata. Kusa da ita tazo ta d'aga hannu zata kara wanka mata mari. Har Khadija ta runtse ido jin bataji saukar mari ba yasa ta bud'e idanunta a hankali. Magajiya ce ta kalleshi tace " me kakeyi hakan?" Turab ya kalli Khadija yace " bamu guri ko?" Khadija tai waje. Turab ya sauke mata hannunta yace " me kike anan?" Tace " kaine kasa d'ana a cikin motar daya kamata ka tafi ko?" Turab yace " mene?" D'anki? Hannu yasa akasan hancinsa yace " a da banso kisan abinda na sani ba sai dai kunnuwana sun gaji dajin muryarki tana cewa d'an da batasan zafinsa ba da sunan d'anta." Idanu Magajiya ta zaro, a tsorace tad'anyi taku biyu baya. Turab yace " me? Kina mamaki ne? Wato kinaso ki halaka asalin d'an sarki ki saka d'an d'anuwanki akan mulki shiyasa kika sa a kasheni?" Magajiya bakinta ya fara rawa tace " bansan me kake cewa ba, sannan zance kasheka bansan wannan maganar ba, sai dai ka tambayi Hisham." Turab ya kalleta yace " banyi mamaki ba, dan dama nasan cewa zakiyi shine ya aikata hakan." Shiyasa ana sanar dani zuwanki nasa Garzali ya kirashi, bari yazo sai muji wanene yasa a kasheni, daga nan sai mu nufi turakar Sarki." Magajiya tsoro da fargaba ne suka dinga ratsata, inza'asan komai nata bazai dameta ba amma banda sirrin Abdulmajid, komai zata iya kwatar kanta inhar d'anta nada matsayinsa. Abdulmajid dake kwance a kan gado a hankali wasu zafafan hawaye suka gangaro mai. Turab ne ya kalli kan gadon, ko tunanin me yai sai ya kalli Magajiya yace "ahhh yau Gimbiya zatazo banaji ya kamata in zauna anan, ina tunanin maganar a gida ya kamata muyi." Ya juya da sauri yai waje. A can gefe ya hango Khadija, gunta ya nufa fuskarnan a d'aure yace " Abdulmajid ya farka bayan na tafi? Tace "a'a." Bai jira mai zata kara cew ba yai gaba. Dawowa yai inda take, kallansa tai, hannu yasa a aljihunsa ya ciro d'ankwalinta ya mika mata. Ya juya yai gaba, bakinta ta saki tana kallansa. Kallan bayansa tai har sai da ya bace mata, kwallar data zubo mata ta share. Sannan ta kurama d'ankwalin ido, ita kanta dan dai ya bata d'ankwalin ne yasa tasan nata ne, amma ita kanta ta manta dashi. Hawaye ne suka shiga zubo mata, in har Turab zai ajiye abinda ita kanta ta manta dashi to ba shakka yana santa. Amma meye amfanin san da bata tashi sani ba sai lokacin da bazai mata amfani ba, ko da yaks da can ma ko ta sani ma ba zai musu amfani ba. Jingina tai da bango tanajin zuciyarta na mata wani irin rad'ad'i na azaba........ ******* Magajiya kuwa Turab na fita ta rufe kofa da makulli ta zauna kusa da Abdulmajid tace " Uban waye ya isa ya ce ba ni na haifeka ba?" Inhar kana tare dani ba abinda ba zan iya ba, dan haka ka gaggauta mikewa, Mairo kake so ko? Ka farka zan baka ita, mulki? wannan dama dole ne, sai me? Turab? Karka damu ko me zai faru sai naga bayansa, bazan taba bari yafadama wani sirrin nan nawa ba. Ko mai zai faru banaso kasan komai, ni dai kawai ka tashi. Sam hankalinta ya kasa kwanciya ganin Abdulmajid ko motsi baya yi. Shi kuwa Abdulmajid samun kansa yai da Addu'a mara amfani, baisan sanda yace " Allah ka d'auki raina......" ******* A can kano kuwa anata shirin zuwa kawo amarya, dan wasu ma yau da wuri suka taho dan kara gyara gidan Amarya da kara duba jeren da akai, Amarya Gimbiya Bilkisu kuwa yau tun safe ake ta gyarata, gyara mai sunan gyara na gargajiya bawai irin na xamani ba...... *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *74* Turab gidan Umma ya wuce inda take, yana isa ya tadda ta shiryamai abinci, nan yaci sannan ya kwanta akan kujerar falo. Fitowa tai daga d'aki ta kalleshi tace " Turab meye hakan? Ta ya zakaci abinci ka kwanta?" Mikewa zaune yai yace "Wlh Umma kaina kemin ciwo." Zama tai gefensa tace " Ba dole kanka yai ciwo ba, tun da ka tafi d'aurin aure har yanzu banaji ka samu isasshen hutu na awa biyu cikake, ni na kasa gane me kake tayi a waje haka, gashi ni kace in zauna anan." Turab ya kalli falon sannan yace "Umma ni dama ki dawo nan da zama." Kallansa tai tace "akwai abinda kake b'oyemin ko?" Turab yai kasa dakai yace " Ni Umma haryanzu Abba bai fad'amiki inda Hajiya dasu Lantana suke ba?" Umma tace " Bai fad'amin ba, sai dai inaji kamar fa har yanzu jikin Hajiya ba sauki." Turab yace "dama nayi tunanin haka, dan da ta warke da ta sanar dashi wani abu." Basira ta kalleshi tace " me kenan?" Kai Turab ya girgiza sannan yace " In kawo miki masu aiki daga can? Naga waccan kamar aikin zai mata yawa." Tace " karka damu, ni ma zaman haka kawai damuna yakeyi, yanzu kai haka zaka zauna har a kawo Amaryar?" Turab yace " name?" Tace " ko ma dai menene, ka samu ka huta sosai kafin suzo, kar suzo suganka a haka." Murmushi yai yace " a haka kamar ya?" Tace " oho dai nidai na fad'ama in ba so kake su juya da ita suce dama Ashe Angon ba shida jini a jika." Dariya ya saka sosai, yace " lalai Umma, kawai kice kinaso in huta amma wannan sharhin babu shi." Tace " haka kace?" Yace " hmm, ni kam Umma akwai abinda nakesan sanar dake." Tace " name kenan?" Yace " Umma so nake idan komai ya kammala in d'aukeki da Bilkisu muje kauyen da na taso." Umma ta kalleshi cikin jin dadi, tace " Ni kaina inasan zuwa sai dai ina tunanin me zance ma Sarki." Yace " ki jira in gama abinda nakeyi, sannan ki kara min addu'a akan Allah ya bani ikon gurfanar da masu laifi, ya kuma kareni daga sharrinsu, sannan karya bani ikon cutar da wasu saboda wani buri nawa." Basira cikin kulawa take kallansa tace " Insha Allahu Allah na tare dakai, sannan muma bazamu daina maka addu'a ba." Haka sukai ta dan hira sama sama kafin daga baya ya kwanta. Bacci sosai ne ya d'aukeshi wanda shi kansa bai san jikinshi ya gaji haka ba. Bai tashi ba sai karfe biyu na rana. ********* A can gida kuwa Magajiya ce zaune a kuryar d'aki ita da Hisham ta kalleshi tace " Yaya Yaran can yasan komai." Hisham yace " name kenan?" Magajiya tace " yasan Abdulmajid ba d'ana bane." Hisham yai kasa dakai wato shiyasa ya ce mai haka? Sanda ya koreshi daga asibiti?" Magajiya ta kalli Hisham tace " yaya duk yanda za'ai inaso ka tabbatar baka bari an san nice na sa a kama Turab ba, inaso ka yarda akan kaine kai komai, ni zan san yanda zanyi karyai magana akan Abdulmajid." Tsananin mamaki ne ya kama Hisham ya kalleta yace " ban gane ba?" Tace " inaso ka ce kaine kasa a kama Turab in Sarki ya tambayeka, ni zansan yanda zanyi kar a hukuntaka." Tsananin mamaki yama hanashi magana sai kallanta kawaj da yakeyi. Magajiya tace " Sannan inaso a maida Khadija Kano, duk sauran matsalar daga baya ni zan san yanda zanyi, kai dai kai wannan abun guda biyu." Ta mike ba tare da ta jira amsarsa ba tace " bari naje na kara shiryawa asibiti zan koma, dan bazan iya barin D'ana a can ba." Hisham yabi bayanta kawai da kallo Baki a bud'e. Ya dade a zaune kafin ya mike yai waje cikin tsananin takaici. Gida ya wuce, ya shiga d'aki ya baza uban tagumi. *********** Mairo kuwa tana gama aikin gida da takeyi tai wanka ta shirya ta cema Ummanta zataje gun Umma Basira, nan ta fito, sai dai me? Asibiti ta fara wucewa. A jikin windown d'akin ta tsaya, ba kowa a d'akin, batai niyyar shiga ba dama, gani tai yana kokarin motsi da hannunsa da alama idanunsa a bud'e yake kuma abu yakesan d'auka. Da sauri ta shiga ciki, yana jin motsi ya koma ya kwanta tare da rufe ido. Mairo ta karasa gunsa da sauri tace " me kakesan d'auka?" Ta fad'a tana kallan gefe, ruwa ta gani a jarka da alama shi yakesan d'auka. Tace "Ruwa zaka sha?" Jin shiru yasa ta matsa daf dashi tace " nice bakasan gani?" Ganin bashida niyyar bud'e ido yasa haushi ya kamata ta juya zata tafi, jitai an riko hannunta. Tsayawa tai ba tare da ta juya ba, Abdulmajid a hankali yace "Karki fad'awa kowa na farfado, na rokeki." Cikin mamaki ta juyo ta kalleshi, gani tai yayi wani mugun fadawa, tace " bakasan asan ka farfado?" Kai ya d'aga mata, tace "ban gane ba? Abinci fa? Ruwa fa? Kashe kanka kake sanyi?" Maimakon taga ya bata amsa gani tai yana murmushi, tace " murmushi ma kake?" Yace "in kina fada kyau kikeyi." Kallan mamaki tamai, sannan ta d'auko ruwa a cup ta mikamai tace ungo. Sam ya ma manta abinda ke gabansa ganin Mairo, yace " bazan iya tashi ba." Harararsa tai sannan tace " ta ya ya ma zaka sha ruwa? Ai kullema ciki zaiyi." Ta karasa tare da ajiye ruwan. Inda kayayyakinsu yake ta shiga dubawa, kular abinci ta bude ta zubo shinkafa miya wacce taji naman kaji. Abdulmajid yace " so kike inaci wani ya shigo?" Tace " wai me ke faruwa?" Idanunsa nd suka kada yace " ban cancanci cin abinci ba, magana ma bancancanci yimiki ba, Mairo." Mairo ta kalleshi tace " nima ce maka akai ina san yi maka magana?" Yace " haka ne, amma yanzu in wani ya shigo fa? Dan Khadija ma fita tai taje ta dawo." Bata amsa mai ba kawai yaga ta kukule window ta sa sakata a kofa, sannan tazo ta taimaka mai ya zauna ta mikamai abinci. Hannunsa ya nuna mata tace " to me kakeso ai?" Yace " shiyasa nace bazan ci........" Abincin data samai a baki ne ya hanashi karasa abinda zai fada. Haka ta shiga bashi abinci, tana bashi ruwa, daga zaiyi magana zata ballamai harara. ********** Turab na farkawa yaga Sabi'u a kujerar gabansa. Kallansa yai yace " kai kuma fa?" Sabi'u yace "gaskiya ban taba ganin ango irinka ba, ana can ana ta hidima a gidan sarauta amma kai baka nan, Ummanka bata nan, yayanka bayanan, nikam yau an ka wahalar dani." Turab yai murmushi yace " dama ko muna nan ai jama'a ne masu hidimar ba mu ba." Sabi'u yace " ka tashi ka shirya mu tafi, 'yan uwan Amarya sun fara zuwa. Yace" to ni mai kake nufi inje?" Sabi'u yace " au bazaka ku gaisa ba?" Turab yace "amma lalai kafi kowa, a ina aka taba haka?" Sabi'u yace " haba? Ba haka ake ba?" Turab ya girgiza kai yace " kai in anzo naka kayi, yanzu ina Umma?" Ya fada tare da mikewa. Sabi'u yace "ta tafi gun 'yan uwan Amarya, tace in fadama inka tashi, insun watse ta taho." Turab ya d'aga kai alamar gamsuwa. Sabi'u ya kalleshi yace " dazu waziri ya aiko inje." Turab yace " me yace?" "yace zaiyi tunani akan abinda kace mai." Turab yai murmushi a ransa yace " ko kayi tunani dolene ka amince da abinda nace dan nasan halin magajiya maida komai kanka zatai, in har kanasan taimakon d'anka da kuma kanka dolene kabi abinda nace." Sabi'u ne ya kalleshi yace "me kace mai wai?" Turab yace " ba komai." Yai ciki. Wanka yai ya saka kayan da Sarki ya aikomai. Yadi ne mai masifar kyau, kallo d'aya zaka mata kasan tsadarsa. Farin yadi ne, ya saka aikin babbar rigar kayan, yasa hula da takalmi ya fito. Tafi Sabi'u ya saka yana ganinsa yace "kai Ango, yaufa ba dama, da alama Gimbiya yau sai an tausaya mata." Turab ya kalleshi yace " yo ai dole a tausaya mata tunda Amaryar Sabi'u aka kai." Sabi'u yace "anma kafadamin magana." Haka suka taso suka fito. ""******** Zaune take a cikin mota, sai kuka takeyi, kanwar Fulani na gefenta da kishiyar Fulani. Wani had'ad'an leshi na da mai nauyi da tsada, ta sanya, tayi kyau sosai da sosai sai dai kukan da takeyi yasa duk kwalliyar fuskar tata ta tafi. Haka har suka isa garin na zazzagawa. Suna isa gidan aka saki wani busa na sarauta. Su Magajiya dama sun shirya dan tarbar ta, tana isowa suma suka fito suka zo inda suka tsaya. Magajiya ta dafa ta saboda fuskarta a lulube take ruf. Nan suka shiga har bangarenta, ana tafe ana zabga guda. Magajiya na ajiyesu ta tabbatar komai ya kammala ta fito. Tana san ganin fuskar Amarya amma hankalinta na gun Abdulmajid. ******** A asibiti kuwa Mairo tana gama bashi abinci, tana bashi ruwa aka fara kwankwasawa. Nan ta tattare kwanukan ta ajiye a kasa, shikuma ya kwanta. Kofar ta bude tana addu'a Allah yasa ba Magajiya bace. Ajiyar zuciya tai ganin Hisham ne da Khadija. Khadija ta kalleta tace " saukar yaushe?" Mairo tace " d'azu, har abinci ma naci, dan sanda ma taho ban tsaya naci abinci ba." Hisham ta gaida, jiki a sanyaye ya amsa ya shiga ciki ya duba Abdulmajid sannan yai waje. Mairo ta kalli Khadija tace " are u okay?" Khadija tace " name kenan?" Mairo tai murmushi tace " yau ake tariyar ya Turab." Khadija kanta ta sunkuyar sannan ta d'ago tace " ke zan tambaya ai duba da yanayin dake tsakaninku na shakuwa, ni dama mun dade a haka." Mairo ta kamo hannunta cikin tausayawa ganin yanda idanun Khadija suka ciciko, tace " Khadija ya Turab na bala'in sanki, in nace so tofa so d'in gaske nake nufi, tun kina karama yake sanki sai dai da alama har zuwa wannan lokacin bai bayyana miki ba." Kallanta khadija kawai takeyi, idanunta na zubo da kwalla. Mairo tace " Ya Turab a matsayin kanwa ya d'aukeni, kece zabin ransa ban san me yasa soyayyar ku ta koma haka ba." Khadija ta runtse ido tare da share kwallar ta tace " Mairo inaji dama can Allah baiyi akwai wata rayuwar jin dadi ta soyayya ba a tsakaninmu, soyayya ta zamantakewa bazata taba shiga tsakanina da yaya ba, mahaifina da Kanwarsa sun zalunceshi sunmai abinda na tabbatar bazai iya mantawa ba (nace wanda ma kika sani kenan), ta ina kuwa zamu iya zaman aure dashi?" Mairo tace " to amma ai ba ke bace kikai, kuma laifin wani ai baha shafar wani." Khadija tai murmushi tace " haka ne sai dai........." Kallan Abdulmajid dake kwance tai, a lokacin ta tuno da kalaman Turab, a sanda take juyawa zata tafi d'azu daya ce ta fita. Kamar Magajiya yake tambaya akan ciwon yaya. Mikewa tai da sauri tai waje da gudu, Mairo cikin mamaki ta kalleta. Abdulmajid na kwance duk yana jinsu, hawayen tausayin kansa dana kanwarsa ne ya ziraro mai ta gefe. Khadija can ta hango mahaifinta da karfi ta kwalla mai kira, ko takalmi babu a kafarta. Tsayawa yai yana kallanta, da gudu ta karaso tana hakki tace " Baba kai da Umma Magajiya kuna da hannu a ciwon Yaya?" Kallanta yai sai dai baisan me zaicw ba, tace " Ya Turab kukaso ama haka, amma Ya Abdulmajid ya tare?" Hisham ya kalleta yace " Khadija..." ya fada tare da kokarin kai hannu ya riko ta, da sauri tai baya tana zare ido tare da girgiza kai, dan yanda ya kira sunanta ta ya bata amsar tambayarta..... *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *75* D'akin da Abdulmajid yake ta koma, tana shiga ta taradda Mairo dake tsaye tana jikin kofa da alama nemanta take. Yanda ta ganta yasa tasan ba a hayyacinta take ba, Mairo ta ja hannunta ta shiga da ita ciki sannan ta zubo ruwa a kofi ta mika mata, tace " naga kina bukatar kad'aicewa ni bari na wuce." Khadija bata tanka mata ba haka kuma bata sha ruwan ba sai daj yana rike a hannunta. Tashi tai taje kusa da Abdulmajid tana kallansa, hawayene kawai yake zubo mata, ganin kukan na neman kamata tai ban d'aki da gudu. Tana gama kukanta ta fara wanke fuskarta, taje zata bud'e kofa ta fito taji muryar Hisham na cewa Khadija? Da alama shigowa yai nemanta, bayan kofar bandakin ta labe da sauri, shi kuma jin shiru yasa ya d'an bud'e ban daki, da yake a rikice yake bai yi tunanin zata iya b'oyewa ba, kawai sai yai tunanin bata ciki. Juyowa yai zai fita, Magajiya ce ta shigo, ko ta kanta baiyi ba ya fara kokarin wucewa, ba abinda ta tsana irin a ganta ai kamar ba'a ganta ba, a xuciye tace " Waziri meye hakan?baka ganni bane?" Yace "na ganki, sai dai abinda ke gabana yasa idanuna suka rufe." Ganin yana neman fita a xuciye tace " Yaya Tsaya!" Tsayawa yai sannan ya kalleta yace " bakiji nace idanuna sun rufe ba? Alama ce ta ba lafiya ai." Tace " wannan ba damuwa ta bace, damuwar ka ce, sai dai inaso in sanar ma inma ka nuna baka ganni bane saboda abinda na fadama na cewa ka tabbatar kace kaine sanadin komai, kake neman yadda ni to kada ma ka soma, ka fi kowa sanin nice yar uwarka kadai a duniya nice sirrinka kuma nice reshenka." Ran Hisham yakai makura yace " reshen da bai dade ni da komai ba sai wahala? Sanar dani me wannan reshen yamin a rayuwa?" Magajiya tace "mene? Ni kake fadama haka yaya? Ni kake tambaya me na maka? Duk daula da jin dadin da kake zaune a ciki waye sanadi? Kana tunanin karfinka da matsayinka ne yasa?" Cikin takaici yace " daular banza daular wofi, daular data sa 'ya'yana suka tarwatse? Daular da ta ke rinjayata nake aikata abinda bashi bane? Daular da tasani kisan kai?" Jikin Khadija ne ya kaure da rawa, batasan sanda ta tsugunna a bandaki ba, kisan kai? Abdulmajid kam gaba d'aya jiyai gab'obin jikinsa sun daina aiki. Magajiya ce ta sa dariya tace " ashe kasan da wannan, na d'auka ka manta da mumuman abinda ka aikata." Hisham fuskarsa ta canza sosai yace " kina tunanin duk abinda nake miki kyaleki nake ko dan ina tsoranki? Dama ina jurewa ne saboda d'ana, yanzu kuwa abinda nake jurewa dominsa na kwance ba lafiya, kina tunanin akwai abinda zai tsayar dani?" Kallansa tai tace " me zaka iya yi in baka jure ba? Sanar da abinda muka aikata? In haka ne kaine a ruwa dan kai kasan ni da kaina ban taba kaahe mutum ba haka kuma bantaba sawa da bakina a kashe wani ba." Hisham kallan tsananin mamaki kawai yake mata, yace " mene?" Tace " ni na saka kaje kashe Turab sanda aka haifeshi?ko nice na saka ka sama gidansu wuta ka kashe yayan mahaifiyarsa da matarsa?" Abdulmajid ji yai kansa na wani irin juyawa, yanasan yai kara yace musu khadija na bandaki sai dai inaa, wani irin juyawa kansa yakeyi wanda gaba d'aya bakinsa ma ya kasa bud'uwa. Hisham ya sa hannayensa biyu ya shake ma Magajiya wuya, kallansa tai tace "wani kisan kake san yi? A gaban d'an ka?" Kallan Abdulmajid yai sannan ya saketa, nuna ta yai da yatsa sai dai baice komai ba sai idanunsa da fuskarsa da suka canza sosai. Magajiya ta kalleshi shekeke tace " yaya baka isa ka gudu daga tarkona ba." Kallan Abdulmajid tai sannan ta juya dan tambayar Likita halin da yake ciki. Abdulmajid mutsu mutsu kawai yake akan gado. Mairo kuwa harta hau kan mashin ta tuna tabar ledar kayan da zata canza in zata gidan bikin daga gun Umma. Saukowa tai ta nufi ciki. Tana shiga ta taradda Abdulmajid na kokarin faduwa, da sauri ta shiga ciki ta rikeshi tace " Abdulmajid!" Jin muryar Mairo yasa ya bud'e idanunsa wanda suka canza kala sosai, hijab dinta ya riko bakinsa ya shiga rawa yana san magana. Mairo duk ta gama rikicewa, kallansa take tana cewa " menene?" Ganin ya kasa magana ta gyara mai kwanciya sannan ta zare d'ankwalinta ta shiga fifitashi, dan gumi yake kamar ba fanka a d'akin. Wani irin ajiyar zuciya yai wanda duk wanda yake kusa sai ya juyo, Mairo ta kalleshi tace " Abdulmajid!" Yace " Toilet, Mairo Toilet." Toilet? Ta maimaita tare da yin hanyar, A kwance taga khadija shame shame a cikin bandaki, duk ta gama rikicewa nan ta shiga kokarin fito da ita, da kyar da jawota duk yanda ta jijigata ta kasa tashi, ga kayanta duk ya soma jikewa, a rikice ta shiga kokarin cire mata kaya, ta d'auko nata wanda ta manta, ta zare zanin ta sa mata siket dinta. Ganin rigar bata jike sosai ba yasa fito da sauri dan neman nurse. Wani ta gani da farar riga irin ta likita, tace " Dr wata ta fadi." Likitan ya kalleta yace "a ina ne?" Nuna mai d'akintai suka shiga. Khadija na kwance, ya shiga da sauri inda take ya gyara ta zuwa rigingine. Ya dade a kanta kafin ta farfado, kallan sa kawai takeyi, tana kuma bin d'akin da kallo. Mairo na zaune ta baza tagumi Magajiya ta shigo. Kallanta tai tace " ke kuma fa?" Mairo tace " Khadija......." Fita! Abinda kawai tace mata kenan tare da nuna mata hanyar kofa. Mairo ta kalli Abdulmajid wanda ke kwance idanunsa a rufe, kawai tai waje duk tsiwar mutum kwarjinin Magajiya daban ne. Gidan Sarki kawai ta wuce, ga yamma tayi. *********** 'yan kawo Amarya kam sun sha hidima, dan ba shakka an musu tarba sosai, sai yamma suma sukai ma Bilkisu sallama suka kama hanyarsu. Mairo ta iso sai dai bata samu ko ganin Turab ba dan yana cikin mutane, umma kuma tana ta fama da mutane, balle dama batama san me zatacema Basira ba. Turab kam bai samu ya shigo ba sai bayan isha'i, shima tare yake da 'yan rakiya, yasha kwalliya sosai. Bangaren Umma kawai lekowa yai ya mika kaya ya wuce, Mairo tana sallar isha'i ya shigo, tana idarwa ta tambaya akace ai ya tafi bangarensa. Haka tai sallama da Umma ta fito dan tasan in aka rakashi shida fitowa sai gobe. Gimbiya na zaune a d'aki, tasha had'adiyar alkyabbarta kayan jikinta masu tayi kyau sosai da sosai, sai dai an saka hular alkyabbar sannan an kawo mayafi an rufe fuskarta. Jeren da aka mata kuwa, ko ban fadaba kowa yasan an kashe kudi dan ma dai lokacin ba kamar yanzu bane da kudinmu bashida daraja. Da masu kula da ita wanda daga can kano aka raho mata dasu guda biyu saboda rashin sabo da batai da na nan ba. Su Sabi'u manyan yan tsokana, haka sukai ta tsokanar shi kafin daga baya su bada kudin siyan baki, wanda rashin kawaye yasa sai ajiyewa sukai anan, da yake haka ta taso ba kawa sannan cikin maza ta taso bare tai abokantaka da yayunta, haka suka fita suka bar Ango da Amaryar sa. Turab ne ya zauna kusa da ita sannan ya yaye mata mayafin dake yafe a fuskarta sannan ya kalleta yace " Gimbiya Bilkisu barkanki da shigowa gidan auranki, barkanki da sauka cikin wannan gida." D'agowa tai ta kalleshi sannan ta maida kanta kasa, rabonshi da ita ya dade, haka itama, ba shakka yayi mamakin tsananin kyan da ta kara, itama a ranta taga yayi kyau sai dai kallo d'aya datamai ta ga ya fada. A hankali tace "Barkanka dai Yarima Turab." Murmushi yai yace "kinyi sallar isha'i?" Tace " a'a." Yace " ki tashi kiyi alwala sai muyi tare." Kanta ta sunkuyar tana wasa da hannunta wanda yasha lale. Jikinsa ne ya bashi da alama bata salla, sai yace " bari nai sallah ni tukunna, ga abinci nan ki fara ci." Ya fada tare da shiga ban d'aki, sai dayai sallah yai shafa'i da wuturi sannan ya dawo inda take. Ledar na gabanta sai dai ko bud'ewa batai ba. Zama yai yace " Tunanin gida?" Kallansa tai tace " kawai inajin abin ne kamar wasa." Ledar ya bud'e tare da ciro ledar naman ya sauka kasa kan karamib carpet din tsakar d'akin ya zauna, sannan ya ciro ledar juice masu sanyi ya ajiye. Alama ya mata da hannu akan ta sauko ta zauna, ya fada yana nuna mata kusa dashi kadan. Murmushi tai sannan ta sauko ya tura mata gabanta sannan ya mike ya d'auko cup ya tsiyaya mata juice d'in yace " Bismillah." Kallansa tai tace "banajin yunwa, ni kai naga ma kamar kaine bakaci abinci ba." Fuskarsa ya taba yace " na rame ko?bayan amare aka sani da rama." Tace " ka rame mana, badai matsalar bace har yanzu bata warware ba?" Iska ya furzar yace " Abin ai ba karami bane." Tace " Da alama an tsorataka?" Dariya yai wanda harsaida hakwaransa suka fito yace " Tsoro? kuma fa kin fadi gaskiya an tsoratani." Tace " an ba da ni." Yace " ahh ya zakiyi yanzu? Gashi na riga na kwaceki bare a kasa ni?" Kanta ta sunkuyar tace " Ni dai nace an badani, banaji ni akwai abinda zai tsorata ni." Yace " hmm a hakan? Ke har zaki iya wani abun ma? Ni da na d'auka zan taddake irin ba wasan nan sai naganki mai saukin kai." Wayau yake mata yaga inyana sata magana tana kara sakar jikinta dan gashi yanzu har naman ta fara dan ci. Kallansa tai tace " a haka ne ka ganni mai sauki, amma in na rikid'e? Hmm ba wasa." Ohhhh kice akwai wadi side ban sani ba, ko za'a gwadamin? Murmushi tai tare da yin kasa da kai tace " Ka fadamin wanene yake baka matsala kaga abinda zan iya yi." Yace " kice sai dai in koma baya in kallo?" Tace " Magajiya ce?" Kallan mamaki ya mata yace " me kika gani?" Murmushi tai tace " Ka manta a inda na taso ne? Na kuma san d'anta taso ta had'a dani, sannan d'anta takesan tasa a kan mulki." Turab yace " hmm lalai, na sha mamaki." Kallansa tai sannan ta sunkuyar da kai tare da zare hannunta daga ledar, ya tabbata gida ta tuno, matsowa yai ya jawo ta jikinsa ya rungume ta tsam. Yana shafa bayanta a hankali alamar lalashi, yace " i will try my best not to make u lonely, sannan ban manta da alkawarina dana miki ba, bazan nemi wani abu ba a tsakaninmu harsai na kammala abinda ke gabana, a lokacin ne zan nemi yardar na zamantakewa, a lokacin ne zaki yanke hukunci in zaki iya zama dani." Luf tai a jikinsa, sun dade a haka kafin ya d'agota a hankali sannan ya shiga bata naman da kansa. Da kunya ta ke amsa sai dai wata shakuwa na kara shiga tsakaninsu a hankali. Yanajinta kamar kawarsa dan abinda zai gaya mata bayaji akwai wanda yake iya fadawa kai tsaye, bai san me yasa yakejin yardarta har zuciyarsa ba........ *********** *TURAB* ************ 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *76* Washegari. Da asuba ya farka a kan kasan carpet din daya kwanta, salati yai sannan ya mike tare da kallan kan gadon da Gimbiya ke kwance, karasawa yai inda take ya gyara mata bargon data luluba dashi, sannan ya juya zai fita. Jiyai ta kamo hannunsa, juyowa yai ya kalleta yace " idanki biyu?" A hankali ta bud'e idanunta tace " yanzu dai na farka? Masallaci?" Yace " eh, sai na dawo." Sakeshi tai sannan tace " adawo lafiya." Murmushi yai sannan ya juya yai gaba. Alwala yai sannan ya fita, sun idar da sallah ya fito, jiyai ance " Yarima Turab!" Yanda aka kirashi cikin rad'a yasa ya juya ba tare da ya amsa ba dan ganin me kiran. Daga lungu ya hangoshi a tsaye jikin bango. Turab ya karasa sannan ya kalleshi cikin mamaki yace " Waziri lafiya?" Hisham ya kalleshi duk ya canza yace " Kaga Khadija?" Turab yace " bangane naga khadija ba? Wannan wace irin tambaya ce?" Hisham a rikice yace " Turab?" Ya fada tare da riko hannayensa yace " ka taimakeni dan Allah bansan inda Khadija tai ba, tun jiya nake nemanta wlh ko barcin arziki ban samu ba." Turab kallan mamaku yake masa yace " Ni fa nakasa fahimtarka, b'ata tai ko me?" Hisham yace " da kanta ta tafi, sai dai bansan inda tai ba." Turab ya kwace hannunsa yace " da kanta ta tafi? Kuma ko kunya kazo kana tambaya ta?" Hisham yace " Turab na rasa inda zansa kaina, in ta fada hannun mutanen banza fa?" "wannan damuwarka ce ba tawa ba, kaine ka lalata mata rayuwa ko menene ya sameta, sannan karkaga kaine ka haifesu kayi tunanin duk wani abu da ka aikata musu ba laifi bane, haifarsu kai ba hallitarsu kai ba." Ya juya yai gaba. Hisham idanunsa suka ciciko dan shikam yana cikin garari. Turab tafiya kawai yake sai dai abin zirya yake tamai a zuciyarsa, ina taje? Menene kuma dalilin tafiyarta?" Har yaje zai shiga bangarensu sai kuma ya juya, Garzali ya kira suka wuce asibiti. Abdulmajid na kwance yana bacci, sai wata baiwa da Magajiya ta sata zama a gunsa, d'ayan gadon ya kalla wanda da ba kowa, amma yanzu yaga Khadija kwance. Mamaki ya kamashi yaje kusa da ita, sannan ya dawo inda Abdulmajid yake yad'an tabashi. Sannan yace " d'an tashi." Abdulmajid bai bud'e ido ba sai dai yana jinsa. Turab ya kalli wannan mai kula da su din da aka bari yace " bamu guri ko?" Tace " to ranka ya dade." tai waje Turab ya kalli Abdulmajid yace " magana zamuyi." Abdulmajid a hankali ya bud'e idanunsa ya kalli Turab. Turab ya zauna kusa dashi yace " ya jikin naka?" Baice komai ba sai dai ya kawar dakansa. Turab cikin wata irin murya yace " Nagode Abdulmajid." Cikin tsananin mamaki Abdulmajid ya kalleshi, sannan yace " karkamin godiya dan ba saboda kai nai ba." Turab yai murmushi yace " saboda ba saboda ni kai ba shi yasa nake ma godiya." Abdulmajid yace " mene?" Turab ya ce " Mu bar wannan maganar, me ya samu Khadija?" "kana tunanin zan fadama?" Turab yace " sosai, dan duk duniya yanzu ni kadai ne zaka iya fadama wannan sirin naka." Wata dariya yai yace " bakai tunanin na gwammace na had'iye matsala ta ba?" Turab yace " wannan tsarinka ne, zaka iya yadda zakuma ka iya kin yadda, sai dai in har kanaso ka ceto rayuwar mutanen dake kewaye dakai dolene mu had'a kai." Abdulmajid ya kalleshi sai dai baice komai ba, Turab ya cigaba " haka zakabar matar da ta rikeka ta cigaba da tafka laifufuka? Haka zaka bar mahaifin daya haifeka ya cigaba da aiwatar da laifufuka? Ko kuwa rayuwar kanwarka dake neman tarwatsewa?" Abdulmajid ya juya kai idanunsa suka ciciko, Turab yace " tunda ka zabi yin shiru, ni zan aiwatar da abinda naga shine daidai." Ya mike zai fita, Abdulmajid a hankali yace " inajin kunyar hada idanu dakai, bansan abinda iyaye na suka aikata maka ba kenan, duk abinda sukai how can i face u?" Turab ya juyo ya dawo kusa dashi ya zauna sannan ya kalleshi yace " bazance kaima bakada laifi ba dan kaima kayi abubuwa marasa kyau a baya, sai dai yanzu kana biyan laifin daka aitaka." ya fada tare da kallan kafarsa wacce ba hope din zata mike. Turab ya cigaba " dole ne ka cire tsoron Magajiya in har kanasan ka taimaketa, kaine kadai wanda inka juya mata baya zataji gaba d'aya duniyar ta mata zafi domin dakai ta dogara sannan saboda kaine take ganin komai zatai ba zai zamar mata wani abu ba." Abdulmajid ya share kwallarsa yace " haka ne, sai dai banaji ko ni Umma zata saurarawa, sannan Waziri ba tun yanzu yake kisa a kaina ba, na kula duk abinda ke faruwa saboda ni ne...." Ya kasa karasawa saboda wani kuka daya taho mai. Turab wani tausayinsa ne ya kamashi, daurewa yai yace " yanzu ba lokacin kuka bane, inhar ka yadda kana da hakki akan laifufukan da suke aikata wa to dolene ka nuna musu kuskurensu gun aikata abinda auka aikata." Abdulmajid yace " hakane, yanzu me zanyi?" Turab ya kalli Khadija sannan yace " da farko kasa Waziri ya maida yarinyar nan kano." Abdulmajid yace " Khadija?" Turab yace "eh, zuciyarta mai rauni ce duk da tasan mahaifinta da kanwarsa sun tafka kuskure intaga ana wahalar dasu zuciyarta bazata d'auka ba." Abdulmajid yace " haka ne, zansa gobe amaida ita." Turab yace " sannan ka nuna ma kowa ka farfado." Yace " sai me?" Turab ya matso daf da kunnensa ya rad'a masa wani abu wanda duk yanda nakai kunnena gun banji me yace mai ba, sai da ya gama sannan na kalli Abdulmajid naga yana kallan Turab. Turab yace " me? Bazaka iya ba?" Kai ya girgiza yace " ko d'aya kawai dai ina mamaki ne wanda yanzu na fahimci komai, a da ina kishin ko mai na rayuwarka, daga yanda Abba ke sanka zuwa yanda kuke hira da Mahaifiyarka cikin kulawa, zuwa yanda Kanwata da Wacce nakeso ke sanka bani ba, sannan zuwa yanda mutanen fada ke girmamaka, saj dai yanzu na fahimci dalili." Turab yace " menene dalilin?" Abdulmajid yai murmushin yake sannan yace " zuciyarka itace dalili." Turab ya kalleshi ya murmusa, Abdulmajid yace " yanzu me yasa ka yarda dani? Baka tunanin zanci amanarka tunda abu ne na mahaifana?" Turab yace " ko kadan, saboda yanzu idanunka sun canza, a da ambition da kuma kishi nake gani karara a idanunka sai dai yanzu ina ganin tsantsan guilty da kuma dana sani a idanunka." Abdulmajid yai kasa dakai. Turab yace " u have to do it right, karka bari kwarjini da tsoron magajiya yasa ka kasa." Abdulmajid ya d'aga kai yace " nagode Turab." Turab ya kalleshi ya dafa shi sannan ya juya. Kallan Khadija yai ya juya ya fita. Abdulmajid ya bishi da kallo idanunsa na zubda kwalla. ********* Magajiya yau cikin baccinta ta tashi yakai sau uku, kalaman Hisham ne ke mata yawo, da kuma Turab, yau kam ta tabbatar Turab yasan Abdulmajid ba d'anta bane. Ana sallar asuba kuwa ta aika a kira mata Jakadiya. Tun 6 take zaune tana jiranta sai dai ba labari, har wajen karfe 8 abin ya gama damunta ta mike a zuciye ta fito. Karfe 7:30 kuwa Turab ya iso gidan, yana sauka a mota Jakadiya ta taho da sauri. Kallanta yai yace " Jakadiya lafiya?" Jakadiya a rikice tace " Yarima tun dazu nake jiranka, Magajita ce ta aiko naje." Turab yai murmushi yace " ai na d'auka tun jiya ta kiraki, ashe zata iya bari sai yau?" Jakadiya ta mai kallan mamaki tace " Bam gane ba?" Turab ya kalleta yace " kije in ta kiraki sannan ki sanar da ita abinda kika sani." Jakadiya tace " abinda na sani? Ban gane ba?" Turab yace " ba kiranki nai nace zan hukuntaki ba? Ki sanar ita duk abinda ya faru." Kallansa tai tace " amma baka ganin zata iya lahantani?" Turab yace " in ta lahantaki ma tsakaninku ne, ai kema kinyi laifi bawai wannan ne kawai abinda kika aikata ba, banaji inada damuwa akan abinda zai faru tsakaninku." Hankalin Jakadiya ya tashi da sauri ta tsungunna a gabansa tace " Ranka ya dade kasan Magajiya." Turab yai murmushi yace " na sani, saninta da kuma saninki ne yasa na fadi haka, ki kwaci kanki tunda kema da wayanki kuma ba ta yau bace." Ya juya yai gaba yana murmushi. Bangarensa ya nufa, yana shiga ya wuce d'akinsu, sallama yai yaji shiru hakan ne yasa yai tunanin ko bata ciki ko bacci taje har a lokacin. Kofar ya tura tare da shiga da sallama, yana shiga ita kuma tana fitowa daga band'aki d'aure da towel, wani kamshin dadi ne ke fitowa daga ban d'akin wanda hakan yasa nasan lalai anyi wanka da kayayaki masu kamshi. Da sauri ta juya baya, baisan sanda idanunsa suka shiga kallanta ba tundaga kafarta har zuwa kanta ba, abinda da zuciya ga Bilkisu mace ce mai tsananin kyau da kira. Juyowa tai ta kalleshi da sauri ta sake juyawa tace " Ba ka fita ba?" Turab yai murmushi sannan ya tako a hankali har zuwa inda take daf da ita yazo zuciyarsa na rayamai abubuwa, ita kuwa gabanta ne ke faduwa dan ma tasan ba sallah take ba. Harta runtse idanunta tana tunanin zatajishi kusa da ita ko wani abu. Toilet ya shiga sannan yace " A shirya lafiya." Ya karasa maganar tare da tura kofar. Kallan kofar tai sannan ta saki wani ajiyar zuciya kafin tai wata yar siririyar dariya. Turab shima yana rufe kofar ya saki wani ajiyar zuciya, yana mamakin me ke damunsa? Bayan bai tabajin haka ba,yaji wai zuciyarsa na kwadaitamasa taba mace? ********* *TURAB* ********** .🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *77* Tana shiga kilisarta Magajiya dake zaune ta mike tsaye sannan tace " biyoni. Sai da suka shiga cikin d'akinta Magajiya ta zauna akan kujerarta sannan tama Jakadiya alama da hannu akan ta matso inda take. Jakadiya ta karasa gun ta zauna sannan tace " Barkanki da Safiya...." Magajiya ta kalleta tace " Me kuka kulla ke da Turab?" Gabanta ne ya fad'i tace " ban fahimt......" Kinaso in sake maimaitawa? Jakadiya tace "Ai ban fahimceki bane Magajiya." Magajiya tace " ba sai kin fahimceni ba, sannan nayi kuskure ma dana tambayeki, abinda ya dace shine ki jira kiga yanda wanda ya ci amanata yake kasancewa, dan wlh sai na baki mamaki." Jakadiya tai kasa dakai tare da fashewa da wani irin kuka tace " Magajiya ni na isa naci amanarki?bansan komai a abinda kike fadaba, ni dama wata magana nazo sanar dake banyi tunanin neman da kikemin da biyo kike min ba." Magajiya ta kalleta tace " magana?" Jakadiya ta juya ta kalli kofa sannan tace " naji wani abu wanda ya tsoratani." Magajiya ta kalli kwayar idanunta. Jakadiya ta dan had'iyi yawo tace " Jinai Abu Turab yana magana wacce ta tsoratani tsantsa, ta yaya akai kika bari yaran nan yasan sirrin nan namu?" Magajiya ta kalleta tace " me kike nufi?" Jakadiya ta matso tace " Jinai yana cema Basira wai Abdulmajid d'an Waziri ne, wannan labarin ya tadamin hankali tsantsa, ta ina yaji? Garin kuma yaya?sirrin da mukai alkawarin rikeshi har bayan ranmu?" Magajiya jitai hannunta na rawa, ta daure ta kalli Jakadiya tace " bani guri." Nan Jakadiya tai wuf tai waje kai kace dama jira take ace ta fita. Tana fita Magajiya ta dafa kanta, tabbas yasan sirrin nan, garin yaya? Dolene ta b'olo da hanyar da zatasa ya kasa fadan komai, amma Basira ta sani ai, tabbas sai tayi dogon nazari. ********** Sai daya cire kaya ya gama wankan sannan ya tuna ba towel a cikin toilet din. Tsayawa yai, yai shiru yana tunanin mafita. Ita kuwa Bilkisu ta shirya tsaf cikin wani had'ad'en leshi mai kyau, peach colour tayi kyau sosai, tana kokarin kame kanta da ribbon ne taji alamar kwankwasa kofa, kallan band'akin tai tana mamaki, sannan ta mike tazo kusa da toilet din tace " Daga nan ne?" Turab yai gyaran murya, tace " wani abu kake so?" Iska ya furzar sannan a ransa yace sai ince bani towel? Itace ta katseshi da cewa " Yarima?" Turab yace " towel zaki d'an bani." Idanu ta zaro sannan tace " to." BJuyawa tai ta d'auko sabon towel ta kwamkwasa a hankali ya d'an bud'e kofar tare da zuro hannu, ita kuma ta juya kanta tana ta mikamai, yana kokarin kamo towel ya kamo hannunta, shiru ne ya biyu baya batare da ya sake ta ba, a hankali ya shafa zuwa kasan hannunta ya ja towel din. Itakam gaba d'aya jikinta yayi sanyi tanaji ya turo kofar band'akin ya rufe. Juyowa tai ta kalli toilet din sannan ta murmusa. Turab kam shima a ciki yana rufewa yai murmushi sannan ya sa towel din, tana jin alamun zai fito ta fita falo. Sai da ya shirya tsaf sannan ya fito falon, tana zaune kan kujera, kasan carpet din an jera musu kayan abinci kala kala, kamshin turarensa ne yasa tasan ya fito. A hankali ta lumshe idanunta. Kallanta yai yace " Amarya kin tashi lafiya?" Murmushi tai tace " ina kwana? Kaga ka sa ban gaisheka ba sai daka fara tambaya ta ya na tashi?" Yace " daga masallaci na biya wani guri ne." Tace " ayya! Kaci abincin sai muje gaisuwa." Gaisuwa? Tace " eh, zaka kaini in gaida matan Sarki." Yace " ohh lalai, to sauka muci abincin." Tace "nasha madarar shanu ni sai anjima zanci." Bai ce komai ba ya zauna a kasan carpet din, yana kokarin bud'e kula ta sauko tare da d'aukan plate ta zuba mai. Kallanta yai fuskarsa d'auke da murmushi yace " masu aiki nawa kikeso a turo nan bangaren?" Tace " amin uzuri da masu aikin nan, tun ina karama komai sai dai amin banasan a gidan mijina ya zamana komai sai dai amin, ni ba abinci na iya ba ba shara na iya ba balle wanke wanke, banaso akawo mutanen da zasusa ya zamana kula da kaina da mijina sai dai amin." Kallanta yai cikin jin dadi yace " Kina tunanin zaki iya?" Tace "ummm" Yace " shikenan zan sanar ma Umma." Ya gama cin abinci sannan suka nufi bangaren Matar sarki ta biyu, sai da suka gaisa sannan sukaje gun ta uku, duk inda sukaje sai kowa yai mamakin tsananin kyau irin na Gimbiya, sannan suka nufi bangaren Magajiya. Tasa an had'a abincin sha da kayan marmari an jera a falon ta dan dama tasan da zuwansu, taci kwalliya na gani na fada kai kace wani had'ad'en taro zata hallarta. Sai da suka zauna sannan ta fito cikin isa da izzarta. Gimbiya tayi zama irin na 'ya'yan mulki a gaban iyayensu Kanta na kasa ta shigo. Magajiya ta zauna tare da kallansu, Turab yace "Umma Magajiya Barka da Safiya." Tace " Ango na d'auka zaka bari sai zuwa jibi, irin wannan wahalar da amarya haka?" Ta fada tana kallan Bilkisu. A hankali ta d'ago ta kalli Magajiya, idanunsu ne suka had'u, Bilkisu ta sakar mata wani sansanyan murmushi tace " Barka da Safiya." Magajiya idanunta na kanta tace " Amarya barka da shigowa masarautar Zazzau, dafatan zaki samu kwanciyar hankali kamar yanda kike samu a can." Tace " Karki damu indai farin ciki ne Umma dan na tabbata d'anki zai kula da ni sosai." Ta rasa meyasa taji zafin kalamanta, bayan ba wani abun ta fada ba, amma me yasa takeji kamar magana ta fada mata? Daurewa tai tace " Haka akeso, ai Turab yaro ne na gari." Bilkisu tace "Godiya muke, dan yabonki yana nuna hakan take a gun al'uma." Magajiya ta kara kallanta, me yasa yanzuma taji maganar ta bata mata rai? Turab kam murmushi yai yace " na d'auka kina gun Abdulmajid." Tace " dama ku nake jira mu gaisa sai in fita." Yace " ohh amma da sai naji kamar kince da mun bari sai nan da kwana uku." Ta kalli Bilkisu tace " hmm ai da dai ka barta ta huta d'in." Bilkisu tace "godiya nake da kulawa, amma Umma duk wani hakkina ina ganin gwara nayishi lokacin daya dace." Tace "haka ne." Turab kallan Magajiya yake yana mamakin yanda take amsawa Bilkisu duk da dai yasan da bakunta amma yasan dukda haka wannan ba style dinta bane. Basu wani dade ba suka fito, har ya kai falo tace " Turab." Dawowa yai ya shigo d'akin, kallansa tai tace "Magana nakesan muyi." Yace " banaji akwai wata magana data rage a tsakaninmu a wannan lokacin, sannan asibiti nakeso na tafi dan kuwa naji labarin Abdulmajid ya farfado inada bukatar jin wanene a kuma garin ya ya aka aikata mai hakan." Magajiya zatai magana yai gaba. Yana fita ta mike tare da matse hannayenta, Abdulmajid? Yana fita itama ta mike ta sanar da masu kula da ita akan zuwa asibiti. ******** Hisham ya gama galabaita gaba d'aya ya wuce asibiti dan ganin Abdulmajid da jikinsa, yana zuwa ya tadda khadija a zaune ta had'a gwiwarta da kanta a kan sallaya. Yana shiga ya tafi da sauri inda take ya rike hannayenta ya d'agota yace " Khadija!" D'agowa tai sannan ta kura mai idanunta da suka kumbura, wanda har fuskarta itama ta kumbura. Muryar Abdulmajid yaji yace " Khadija zaki iya komawa gida da kanki?" Kallansa tai batace komai ba, yace " kije gida ki jira Waziri, ko kuma kije waje ki jirashi yazo kuje gida, magana zamuyi." Mikewa tai kamar wacce ba tada laka a jiki tai waje ko kara kallan Mahaifinta batai ba. Tana fita Hisham ya matso yace " Abdulmajid yaushe ta dawo....?" "Ba wannan bane abinda yasa nace zamuyi magana, tambayarka nakesanyi." Hisham ya kalleshi gabansa na faduwa. Abdulmajid yace " menene tsakanina dakai?" Hisham ya had'iyi yawo yace " naam?" Abdulmajid yace " ni d'anka ne?" Hisham kallansa kawai yake dan bashida amsar da zai bashi. Abdulmajid yace " inaso daga rana irinta yau ka cire batun nan a ranka dan bazanci amanar Umma ba, ban damu da wanene ya haifeni ba wacce ta raineni itace Uwa a gareni, akan Umma zan iya juya ma baya zan kuma iya tozartaka, kaine ka d'aukeni ka bata dan haka babu damuwata akan duk wani abu da zai shafeka." Hisham bai taba tunanin abinda zaiji daga gareshi ba kenan, yace " Abdulmajid kanaso kace ni dana haifeka banida matsayi a gunka?" Yace " matsayi? Kai kasan wannan, sannan ka gaggauta maida Khadija kano inhar kanasan rayuwarta ta daidaita, sannan in har kanaso in d'inga ganin kimarka da darajarka a matsayin wanda ya haifeni ti ka tabbatar ka fita hanyar Umma ta, sannan ko da wasa naji labarin ka aikata abu irin kwatankwacin abinda ka min banaji zan iya yafe maka." Hisham da sauri ya d'ago ya kalleshi yace " naji bazan aikata ba ko kadan amma laifin dana aikata a baya fa?" Abdulmajid ya ce " au akwai abinda ka aikata irin wannan a baya? To a wannan d'akin inaso ku warware a lakar dake tsakaninmu." Hisham ya matso da sauri yace " Abdulmajid kayi hakuri wlh....." Idanu ya runtse sannan yace " naji amma kada ka kuskura abinda ka aikata ya fito fili dan bazan iya kallan mutane ba in har abinda ka aikata ya fito fili, ciki kuwa harda abinda kamin." Hisham da sauri yace " naji, naji." Abdulmajid yace "kaje gun Khadija, ba dadi take ji ba." Nan yai waje. Yana fita ya kalli kofa sannan yai ajiyar zuciya, yace " anya Turab wannan hanyar zata bule?" Tunowa yai da kadan daga cikin kalaman Turab dayace " ka tabbatar ka nunama Waziri kai a bayan Magajiya kake sannan ka nuna masa in har ya amsa laifinsa to lalai kai dashi har abada........" Tunowa da ragowar kalaman yai a ransa sannan yace a fili " Turab kenan, wato in Waziri ya ki amincewa da laifinsa sannan ya fahimci ni a bayan Magajiya nake lokacin ne kishi zai afko a tsakani, ita zataji haushin kin amsa laifinsa wanda za'ai ta bincike gun gano gaskiya, sannan shi kuma zaiji takaicin bijerewata zuwa gun magajiya, idan ya raba tsakaninsu sai ya sani nasa Umma ta fadi laifukanta da kanta cikin ruwan sanyi ba tare da tasan abinda takeyi ba, saboda yardarta gareni ganin na ki mahaifina saboda mulki............" Murmushi yake yai ganin ya fara hada kan puzzle din da Turab ya bashi, a fili yace " daidai nake aikatawa??????" Nikam da sauri nace " Kwarai😄😂" *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *78* Hankalin Hisham yayi tsananin tashi yana fita jiyai jiri na neman d'aukansa sai daya dafa bango. Daga nesa ya hango Khadija a zaune a jikin bango tana bin mutane da kallo, tsananin tausayinta ne ya kara ratsashi, shi dai bai ga ranar da wannan buri nasa ya masa ba, ina amfani gaba d'aya ya tarwatsa rayuwar 'ya'yansa? Kusa da ita yaje yace "Khadija " Kallansa tai sai dai ba magana, yace " tashi muje." Mikewa tajeyi da yake batada karfi tai kamar zata fadi, da sauri yasa hannu ya rikota yace "yi a hankali." Hannunta ta fizge sannan tai gaba. Kallabta yai jiki a sanyaye suka shiga mota, ya ja sukai gida. Har suka isa ba wanda yai magana a cikin motar, tana shiga gida ta wuce d'aki ta sauko da akwatinta ta shiga had'a kayanta. Umma ce ta shigo cikin kulawa tace "Khadija ya jikin Yari......" Ganin tana had'a kaya yasa maganarta ta tsaya, kallanta tai tace " Khadija me kenan?" D'agowa tai ta kalleta sai dai bazata iya cewa komai ba dan ta tabbata tana magana kuka ne zai zo mata, kurama Umma ido tai a ranta tace " me yasa kikai haka Umma? Me yasa baki hana Abba aikata munanan aiyukan nan ba?" Kallanta Umma tai tace " Khadija lafiya?" Khadija ta maida kanta kan kayan ta cigaba da shiryawa, ganin batada niyyar magana yasa ta fito. Hisham ta tarar a d'aki ya baza uban tagumi, ko sallamar da tai bai amsa ba, tace " Baban Khadija me ke faruwa?" Kallanta yai shima sororo, tace " ba shiru zakai ba me ke faruwa naga Khadija duk ta canza sannan tana ta faman hada kaya? Sannan ni bakacemin komai game da ciwon Yarima ba kadai cemib kawai bayajin dadi ne......" Ya isheni haka nan, ki barni da abinda ke damuna dan Allah, haba! Kinsan ya nakeji a zuciyata a wannan lokacin? Komai na neman rugujewa a rayuwata, d'an da nake tunkaho zai ramamin rashin mutunci da cin zarafin da Magajiya tamib yanzu ya rikide yace shi ba wani abu tsakanina dashi, itace uwarsa, sannan Khadija ko kallona basan yi take ba ke kuma zakizo ki sani a gaba kamar wanda ya amshi bashinki?" Umma tace " ban gane me kake nuf......" "ba sai kin gane ba, dama ina kanki zai yi aiki? Kwakwalwace dama kamar ta kifi?" Umma ta juya jiki a sanyaye tai waje, dakin Khadija ta koma ta tsaya kawai tana kallan ikon Allah. Khadija kam dama tun jiya idanunta biyu taji sanda Turab yace ta koma kano, sannan dama itama bataji zata iya cigaba da zama a wannan garin, Umma ta kalla tanasan mata magana sai dai ta kasa. Umma idanunta duk sun ciko dan itakam kalaman Hisham sun kona mata rai, inda sabi yaci ace ta saba amma duk sanda ya mata sai ta dingajin ba dadi. Hanyar band'aki ta nufa bayan ta dau zanin wanka, ta daure tace " kano zan koma." Ta shige ban d'akin, kallan kofar Umma tai jiki a sanyaye sannan ta mike hartaje zata shiga d'akinsu kuma ta fasa saboda takaici, juyawa tai ta koma d'akin khadija ta zauna. ********** A bangaren Basira kuwa su Gimbiya anata kunyar suruka, Umma sosai ta yaba da hankalinta, nan tasa aka kawo mata abincin safe jin Turab yace bataci abinci ba, duk da bataso ci ba sai da Umma tasata taci, sun dade kafin Garzali ya turo a sanar da Turab akan zata fita. Abinda kawai aka ce kenan shiyasa Basira bata fahimcesu ba, Gimbiya kuwa kallansa tai sai dai bata tambayeshi ba, ya kalleta yace " in barki anan ko in maidake can kafin in dawo?" Tace " ina nan." Yace " ok, ba dadewa zanyi ba." Umma ta kallesu tai murmushin jin dadi. Turab ya juya ya fita, Garzali ya tarar a waje yace " ta fito?" Yace " yanzun nan." Turab yace " muje, ka tura a sanar mai?" Garzali yace " eh Ranka ya dade." Mota suka shiga suka tafi asibitin, suna kallan motarta daga gaba su kuma suna baya, har suka isa. Magajiya ta fito ta nufi d'akin da aka kwantar da Abdulmajid. Turab yana kallanta ta shiga shikuma ya tsaya a bakin kofa. Tana shiga aka ajiye kayayyakin data kawo, kallan danta tai cikin jin dadi ta matso tace " Abdulmajid? Idanunka biyu?" Kallanta yai sai dai baice komai ba. Magajiya ta zauna kusa dashi cikin jin dadi tace " na sani ai, nasan d'ana ta ina magajin sarki zai kwanta kamar bara numfashi?" Abdulmajid ya murmusa yace " Umma kiyi hakuri na saki damuwa." Kanta ta girgiza tace " wa ke wannan zancen? Ai farfad'owarka shine komai nawa." Kallanta yai sannan yace " Umma kinsan Kawu yanada hannu akan abinda aka min?" Idanu ta zaro sannan tasa hannu a kirji tace " mene?kanaso kace shiya ja maka wannan abun?" Turab ya murmusa yace " GOOD JOB ABDUL" Abdulmajid yai kasa dakai cikin rashin jin dadi, Magajiya tace " karka damu ba yayana ba ko Sarki ne ya kuskura ya tab'amin kai bazan taba yafemai ba." Abdulmajid ya kalleta yace " na sani dama........" Turo kofar da akai ne yasa shi yin shiru, Turab ne ya shigo tare da sallama. Bata juyaba amma tanajin sallamarsa sai da gabanta ya fadi, me ya kawoshi? Turab ya matso yana cewa "Umma ashe kin garzayo." Juyowa tai ta kalleshi tace " Au Turab kaine?" Yace "ni ne, kinsan dolene nazo duba Abdulmajid tunda ni aka je halakawa tsautsayi.........." Katsesh tai da sauri cikin tsoro tace " ina amaryar? Badai barinta kai ba?" Yace " ya zanyi? Dolece ta sani zuwa ai, naje gunki akan zamu gun Mai Martaba dan yin wata magana ashe ke kina nan?" Idanunta ne suka fito, duk yanda taso b'oye tsoronta sai da ya nuna tace " ban gane ba?" Turab ya matso yace " magana ce wacce ya dace ayi gani gaki ga Abdulmajid sannan ga Waziri." A rikice ta d'ago ta kalleshi sannan ta kalli Abdulmajid tace "Turab wai kwanan nan meke damunka ne? Wuce muje gida mayi maganar a can." Murmushi yai sannan yace " Bakyaso muyi a nan?" Hararsa tai tace " muje ko?" Ta na kokarin mikewa Zagi ya sanar da isowar Mai Martaba. Kallan Turab tai dan tabbas tasan yasan da zuwansa, murmushi ya mata sannan ya d'an d'aga gira kadan ya juya kai. Sarki ne ya fara shigowa bayansa kuma Waziri ne ya shigo. Abdulmajid ya kalli Turab dan baisan me yake shirin aikatawa Ba. Sarki ya nemi fadawa daau fita dan zai duba d'ansa. Nan kowa yai waje, kallan Abdulmajid yai cikin tausayawa yace " Ya jikin naka?" Abdulmajid ya dan sunkuyar dakai yace"Barka da war haka Takawa." Kallansa sarki yai sannan ya kalli Turab wanda ya rusuna tare da gaidashi, Magajiya ma tace " Barkanka da war haka." Sarki ya kalli Turab bayan ya zauna yace " me kakeyi anan kabar yar mutane ita kadai, ba kayi dubiyar ba?" Yace " yanzu nake kokarin tafiya dama inasan zuwa gunka ne nida Umma." Magajiya ta kalleshi sai dai kafin tai magana yace " Dama wani abu nake san......" Katseshi magajiya tai da sauri tace "Ya kamata ka koma gida ko? Ba dadi ango daga aure ace yana waje." Turab ya kalleta sannan ya kalli Hisham wanda yai tsuru tsuru yace " Magana ce akan Abdulmajid." Yanda gaban Magajiya ya ke faduwa zata iya cewa wannan shine rana ta farko da takejin faduwar gaba haka ba kakkautawa dan tabbas tasan so yake ya sanar da tsakaninta da Abdulmajid...... Meye mafita? Kafin kwakwalwarta tai aiki muryar Turab taji yace "Umma maganar da mukace zamuyi da Abba akan abinda ya samu Abdulmajid, ina ganin dolene ga Waziri anan wanda nake tunanin yafi kowa sanin abinda ke faruwa." Wata irin ajiyar zuciya ta saki wanda sai da kowa ya kalleta. Kallan Hisham tai sannan ta kalli Turab a ranta tace " tanan ka b'ulo?" Hisham kam gaba d'aya ya rasa abinda ke mai dadi, ga Abdulmajid yace karya kuskura ya aminta akan shine sila. Magajiya ta kalli Turab sannan ta kalli Sarki tace " haka ne Turab sai dai ina ganin abari yaji sauki tukunna kafin ai wannan maganar." Turab ya kalleta yace " haka ne amma bakya tunanin kafin nan wanda ya aikata laifi ya kamata shima ya fuskanci, ba dai saboda zargin da akema yayanki bane yasa kike......" Wani mugun murmushi tai tace " Kana tunanin in har Waziri nada hannu a ciki zan nemi birne laifinsa?" Turab zaiyi magana sarki yace " ya isa haka, ina kuma tunanin tunda naji maganar na kuma sam mai ya faru yanzu dolene ayi bincike a fada, gunda alkalai suke." Hisham! Kaine ka aikata?" Hisham ya kalli Abdulmajid sannan ya kalli Magajiya tunowa yai da Khadija wacce ta fito da akwatinta a gida tana jira ta tafi aka aiko yazo shine yace ta jira ya dawo. Ina zai sa kansa? Magajiya tsoro take kar magana ta shiga fada dan tabbas in ta shiga daga bincike sai ance meye dalilinsa na aikata hakan, daga nan kuma tana tsoron kalaman da zasu fito daga bakin Hisham in yaji ana tsananta bincike a kansa. *********** Turab ne ya kalli Magajiya wacce fuskarta yau ta bayyana da shakka karara, murmushi taga ya sakar mata a ransa yace " are u scared?" "In kika tsorata tun yanzu the game will not be fun." Idanun Turab kawai take kallo.......... *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *79* Mikewa tai tace " Turab me yasa kuke san bud'e abu cikin bainar jama'a? Me zai hana........"ganin irin kallan da Turab, Sarki da Abdulmajid suke mata ne yasa ta fahimci tana neman kauce hanya, daurewa tai sannan tai wani murmushi tare da komawa ta zauna tace " Yaya! Abu d'aya zan tambayeka kafin in cigaba da magana, da gaske kaine ka nemi halaka Abdulmajid?" Hisham ya kalleta cikin mamaki dan shi gaba d'aya ya rasa ma mai zaice, Abdulmajid ya kalla wanda shima kallanaa yakeyi. Turab ya kallesu sannan yace " Abba da alama ya kamata kaba Umma lawyer cikin gida." Kallansa tai tace " mene?" Turab yai dan dariya yace " menene na tada hankali Umma? Naga kamar kina neman d'aurama Waziri laifin da ba lalai shine ya aikata ba." Bakinta ta dan motsa sannan tace " me kakeso kace a takaice?" Sarki ya kalleshi sannan ya kalli Hisham yace " Waziri!" Hisham ya rusuna da sauri, takawa yana kallansa yace " me zaka iya cewa game da abinda ke faruwa a d'akin nan?" Hisham yai kasa dakai cikin tashin hankali, Sarki yace " jeka jirani a fada in har bakada abin cewa anan, to lalai zaka samu abin cewa a can, saboda dolene ka sanar damu dalilin dayasa ake zarginka." Hisham yace "Tuba nake ranka ya dade amma ni kaina bansan dalilin dayasa akemin wannan zargin ba." Turab yace " gaskiya ne, nima kaina ban fahimci me yasa ake ma wannan zargin ba, me ka aikata takamaima? Shi yasa nake ganin gwara aje fada yanda za'a tabbatar da zargin da akema ba gaskiya bane." Abdulmajid yace " Haka ne, nima ina tunanin hakan yafi Umma." Magajiya ta kalleshi gabanta na faduwa sai dai jin wata dabara ta fad'o mata yasa ta murmusa tace " hakan yayi, sai yaushe yanzu za'ai zaman?" Turab ya kalleta, kamar wanda ya shiga ranta sai jitai yace " Abba gani nake yanzu in har ba abinda zakai gwara ai shari'ar nan yanzu, in ba haka ba shi kansa Waziri banaji zai samu kwanciyar hankali." Takawa yai gyaran murya sannan yace " hakan yayi, ina neman Waziri da Turab a fada nan da minti talatin." Abdulmajid yace "Abba nima ina neman alfarma dan hallarta." Sarki ya kalleshi yace " karka damu, kai dai ka kula da kanka." Abdulmajid kasa yai da kai dan shi kam yafisan yasan kome ke faruwa a idanunsa. Turab ya fahimci haka sai yace " Abba zaman asibiti ba dadi mai zai hana mu nemi sallama, in yaso saboda kafarsa sai a dinga turashi a kujera?" Sarki yace " a'a ku barshi anan dan samun lafiyarsa." Magajiya kam kamar wanda aka nausa a ciki haka taji ta, tsananin tashin hankalin data shiga, dolene a cikin minti talatin d'in nan tai tunanin abinda zata tsarama Hisham dan fad'a a fada dan in batai da gaske ba lalai asirinta zai tuno, ita tsoronta ma wannan munafikin yaran dazai kasance a gun. Sarki ne ya mike sannan yai waje. Yana fita Turab ya mike shima yai waje dan ya tabbatar Magajiya tana bukatar kadaicewa da yayanta. Abdulmajid ta kalla sannan tace " Abdulmajid bari in raka Yaya tunda fada zai wuce." Kai kawai ya d'aga. Suna fita ta mai alama daya biyota, sai da sukai tafiya sosai gun da ba mutane sosai, yau ko tafiyar kasaitar ma batai ba, suna shiga gun daba mutane ta juyo tace "Yaya ya zamuyi?" Hisham yace "game da me kenan?" Tace " ina tsoron kar muje akwai wata shaida da wannan yaran yake dashi na kana da hannu akai, dan yanda yake magana na tabbata akwai wani abu a kasa." Hisham ya kalleta yace "ni ba wannan ne a gabana ba Khadija na gida tana jirana." Kallansa tai tace " Waziri!" Kallanta yai dan yanda ta kira sunan alamace ta ranta ya baci, Magajiya ta had'e rai tace " me kake san kace? Ba damuwarka bane ko me ya faru?" Ya kalleta yace " ba haka nake nu......" Tace " ko ma menene ba damuwa ta bace, abu d'aya na sani idan har ka kuskura ka bari sunana ko alamun sunana ya fito daga cikin wannan abu to ba shakka zan iya yada kai, kafi kowa sanin wacece ni, akan kaina ba abinda bazan iya aikatawa ba." Ta juya ta fara tafiya, idanu ya runtse dan yama rasa ya zaiyi, da girmansa da komai amma yana cikin halin tsoro na jin kunyar duniya, juyowa tai ta kalleshi tace " ahhhh na manta ka kiyayi bakinka tun kafin 'ya'yanka susan kisan kan daka aikata." Ta juya tai gaba. Hannayensa yasa ya shafi fuskarsa sannan ya kalli sama, a hankali ya juya yai waje. Gida ya nufa. Khadija na kwance akan gado kalaman da taji tsakanin Magajiya da Hisham ne suke mata yawo a kwakwalwar, kalaman da bata taba jin mugayen kalamai irinsu ba, filo tasaka ta rufe kanta wasu zafaffan hawayene suka shiga zubo mata. Mahaifiyarta ce ta shigo ta kalleta, jikinta ne yai mugun sanyi ta karasa gunta tare da d'aga filon, Khadija ta gani tana hawaye hannunta ta rike tare da cewa tashi khadija. Khadija ta mike a hankali ta zauna, hannu tasa kan goshinta saboda taji zafi sosai sanda ta rike hannunta. Jin yanda kanta ya d'au zafi yasa ta kalleta tace " Khadija meke damunki? Meke damunki da kike san tafiya ki bar mahaifanki?" Khadija a hankali ta kwantar da kanta kan cinyar mahaifiyarta wasu zafaffan hawayene suka zubo mata a hankali tace " Umma mecece rayuwar nan? Me cece a ciki da har mutane ke jefa kansu akan san zuciya wacce ba komai bane a ciki sai tsantsar buri da halaka dake cikinta?" Umma ta kalleta tace " Haka rayuwar ta maidamu Khadija, ni kaina ina dana sanin abinda zuciya ta sani na aikata, a koda yaushe ina takaicin abinda na aikata." Khadija ta d'ago ta kalleta tace " Umma!" Kallanta mahaifiyar ta tai tare da maida hankalinta kanta. Khadija tace " me yasa kike yadda akan duk abinda Abba yace? Mai kyau ko mara kyau? Haram ko halal?" Umma idanunta ne suka canza kala tana kallan Khadija, tace " ban taba yimai musu ba haka kuma ban taba bijerima abinda yake so ba, shine ginshikin yan uwana, da abin hannunsa suka zama abinda suka zama yanzu." Khadija tace " saboda abin duniya? Saboda 'yan uwanki suji dadi kike yarda da duk hukuncinsa? Ba kya tunanin kema kinada kamasho na laifufukan da ya aikata?" Umma ta mike tare da kokarin maida kwallarta tace " Khadija! Kada ki kuskura kiyi rayuwa irin tawa, kada kisa 'yan uwa da iyayenki gaba da maganar Allah, wannan shine babban kuskuren da muke tafkawa idan Mahaifanmu,mijinmu ko 'yan uwanmu suka samu abu, bama tunanin dacewarsa ko kaucewarsa a addininmu sai muyi kokarin aikatashi dan musu biyayya da faranta musu." Ta kalli Khadija wacce ke hawaye tace " khadija me kika sani? Me kika ji wanda ya tada hankalinki haka, kin canza, kin rame tunda kikazo ko abinci baki ci ba sannan neman barin gari kike yi, menene kikaji da yasa ko kallan iyayenki bakyasan yi?" Khadija ta runtse ido wasu hawaue suka fito tace " menene ribarku akan kai Ya Abdulmajid gun Umma Magajiya?" Gaban Umma ne ya fadi ta kalleta a tsorace, Waziri da tun dazu yake tsaye yana jinsu duk gab'obin jikinsa sunyi sanyi, jin wannan magana ta khadija yasa ya kalli kofar d'akin da sauri, cikin tsananin tsoro. Khadija tace " kuna tunanin wannan sirri bazai taba fitowa ba? Idan Abba yayi hakan dan samun karfin mulki da juyowar mulki daga zuri'ar jinin sarauta zuwa nashi, kefa?" Umma kallan Khadija kawai take batasan hawaye na zubo mata ba. Hisham juyawa yai jiki a sanyaye yai waje zuwa masarauta, dan bazai iya jin naganganunsu haka ba. Umma ta tsugunna a inda take tare da dafa kanta, Khadija kuka take dan bazata iya fadar dayan abinda taji ba dan ta tabbata Umma batasani ba, sai yanzu ta fahimci tsantsar dalilin dayasa Turab ya canza mata, ba shakka ba yanda za'ai sanda yake mata yai tasiri in har yasan sirri nan, bayan ita din jinin Hisham ce bawai rikonta akai a gidan ba..... ************ A cikin fada kuwa Sarki na zaune akan kujerarsa ta mulki cikin nad'i na sarauta, Galadima da Barde su kadai aka kira sai alkalin cikin gida. Sai dogarawa dake tsaye a gefe, Turab ne ya shigo ya zauna a inda ya kamata, shiru sukai suna jiran Hisham dan isowarsa. Galadima ne ya kalli agogo yace "Ranka ya dade minti 15 ya wuce daga lokacin daka bashi." Sarki yace " a kara mai minti biyar." Minti biyar ce tai, Barde yace " minti biyar tayi ranka ya dade." Sarki ya kalli Alkali yace " wannan alama ce ta ya aikata abinda ake tunanin ya aikata ko?" Turab kam addu'a kawai yake akan Allah yasa ya zo. Alkalin zaiyi magana aka sanar da isowar Waziri. Wani irin dogon numfashi Turab yaja na jin dadi. Wannam shine shafin farko na d'aukan mataki akan abinda Magajiya ta aikata musu, shi, mahaifiyarsa, Sarki, Abdulmajid da Khadija. Bazai so wani abu ya jawo rashin zuwan Hisham ba. ********** Mairo kam duk ta rasa me ke damunta, ba shakka tunanin halin da Abdulmajid yake ciki shine ya dameta, yaci abinci? Ya sha ruwa? Karfa tun abincin data bashi har yanzu bai sa komai a cikin sa ba? Mikewa tai zaune daga tsintar wanken da bata san ma me takeyi ba. Tace a fili, zanje in dubashi ne bawai dan na damu da halin da yake ciki ba, sai dan zuciyar muslunci da tausayi. Kai ta d'aga tace " ai duba mara lafiya ma babban aikin samun lada ne, dan haka dubiya zanje bawai dubiya zani saboda Abdulmajid ba....." 😄😄😄😂Nace anya kuwa Maryama???? *Turab* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *80* Kowa da ke cikin gurin ne ya zuboma Hisham ido, jiki a mace ya shigo ya zauna. Galadima ya kalleshi sheke ke ya tuno abinda dansa ya sanar dashi, ba shakka ko waye ya ji dolene yasan da hannun Hisham a wannan lamarin inba haka ba ta yaya ya san inda aka kai Abdulmajid? Gyaran murya da sarki yai ne yasa kowa ya nutsu, Takawa ya kalli Hisham sannan ya kalli Alkalin yace " a fara." Nan alkalin ya ciro takardar ya fara karantawa kamar haka. " A jiya ranar lahadi ne aka kawo karar Hisham wanda akace ya nemi da a kama Abdulmajid wanda hakan ya jawo masa karaya a kafarsa da kuna manyan ciwuka a gab'obin jikinsa." Kallan Hisham yai yace " Hisham kana da abin cewa a game da laifin da akace ka aikata?" Kalaman Abdulmajid ne suka fad'omai ya kalleshi yace " ta yaya zan so wani abu ya samu d'an kanwata? Ni fa na kasa fahimtar takamaimai me na aikata" Galadima yace " ina muka san manufarka?" Turab ne ya d'ago sannan ya kalli Hisham ya juya ya kalli Alkali yace " Gaskiya ni kaina na kasa gane takamaimai me ka aikata, zuwa gun d'aurin aurena dakai ka tambayeni a inda na taho? Ko kuwa jin Abdulmajid ya taho a motar daya kamata in taho da kaji hankalinka ya tashi? Ko kuma ganin da Sabi'u yama ka je ka d'auko Abdulmajid? Ni kaina Mai Martaba na Kasa gane mai Waziri ya aikata." Hisham yace " dan na tambayeka in da ka taho gani nake ai ba laifi bane." Turab ya jinjina kai yace " haka ne, sai Dai ya akai kasan inda Abdulmajid yake farat d'aya? Ba tare da bincike ba?" Hisham ya d'ago ya kalli Sarki. Sarki ya kalleshi yace " amsarka nake san ji." Hisham ya daure yace " nima ba sani nai ba bincike nai har Allah ya kaini gun." Galadima yace " gaskiya kam, ai hakan zata iya faruwa, amma ni a sanina Sabi'u baiga alamar bincike a tattare da kai ba." Hisham ya kalli Galadima cikin takaici sai dai bai amsa ba. Turab ya mike ya dawo gefen da Hisham ke zaune ya kalli sarki yace "Ranka ya dade menene dalilin daya sa Abdulmajid ya shiga motar da ta kasance mota ce wanda Ango zai shiga?" Kallan Hisham yai yace " Waziri mai kake tunani?" Hisham ya kalleshi dan bai fahimcu me yake nufi ba. Turab yace "baka tunanin yaji wani abu game da abinda zai faru?" Idanu Hisham ya zaro yace " kanaso kacemin Abdulmajid yasan abinda zai faru a ranar?" Turab yace " ranar? Wace rana kenan?" Hisham kallansa yai sannan yace " bansan me kake so kace ba." Turab yace " zata iya yiwuwa, sai dai da alama bakwa tunanin abinda Abdulmajid yakeji a wannan lokacin, ace yayan mahaifiyarsa shine ya nemi halaka mai rayuwa, ko meye ribarka........" Cikin zafi Hisham yace " kai yaro, ya isheka haka, har yaushe aka haifeka da zaka zo ka dinga d'aure magana? Hauka nakeyi da zan nemi halaka Abdulmajid? Tsautsayi ne dai ya afka ya shiga motar da bai kamata ya shiga ba, amma ni ban yarda ya ji ba, ni ina tunanin kai ne ka sashi ya shiga motar ma." Kallan Turab sukai, Shikam bai san sanda ya sa dariya ba, yana dariya ya sunkuyar dakai yace " tuba nake ranka ya dade, bansan sanda dariya ta kwacemin ba, ni? Meye ribata in nayi hakan?" Hisham yace " ka hau mulki ba tare da matsala ba mana." Turab yace " kana so kace in har d'aya ya kauda d'an uwansa a tsakaninmu d'ayan zai hau mulki ba tare da matsala ba kenan?" Hisham yace " Sai ka tambaya?" Turab yace "ahhh na gane, amma in na kusa damu ne suka neman taimaka mana gun rage mana iri fa?" Hisham yace " ban fahimceka ba." Turab ya kalli Alkali yace " ina so a duba maganar Hisham kamar haka, na farko yace Tsautsayi ne dai ya afka ma Abdulmajid ya shiga motar, na biyu zuciyarsa tana tunanin halaka junanmu shine hanyar da ya fi cancanta d'ayan mu ya hau mulki, sannan bai musa ba akan shi da wani sun aikata wani abun tunda sanda na cemai Abdulmajid yaji bai musa ba akan bai san me yaji ba sai cewa dayai wai bai yarda yaji ba." Ji sukai " Abu Turab kuka so ya shiga motar?" rq Gaba d'aya kallan mai martaba sukai wanda idanunsa ke kan Hisham, ya cigaba " motata dana bada ta ango ce, menene dalilin dayasa ba'a tare ko wace mota ba sai ta Ango?" Turab Murmushi yai dan dama shi bai isa yai tambayar nan ba, fatansa d'aya mahaifinsa yai. Hisham ya rikice ga tsananjn kwarjini na idob Sarki, kalaman Khadija ne kawai suke mai yawo, meye ribarsu?meye ribarsu? Duniyar ma nawa take? Sarki a zafafe yace " Dakai nake magana Hisham." Hisham ya kalli Sarki a tsorace sannan ya kallu Alkali. Turab ya kalleshi, Hisham duk ya rikice. Turab ganin ya gama rikicewa yai sauri yace " Waziri nine bakasan gani a duniyar? Me na tare ma?" Kallan Turab yai yana huci yace " tambaya kake? Zuwanka duniya shine abu na farko da mukai dana saninsa." Sarki yace " mene?" Hisham ne ya kalli Sarki a tsorace sannan yai saurin sukunyawa duk jikinsa rawa yake, ina zai sa kansa?me zaice wanda bazai taba rayuwar Abdulmajid ba. Turab jiki a sanyaye yace " kai da wa kukai dana sanin zuwana duniya?" Hisham ya kallu Turab sannan ya kalli Alkali dasu Galadima da Barde wansa suka saki baki dab tsananin mamaki. Hisham ya gama sadaukarwa yau kam tashi ta kare. Idanu ya runtse yace " nine na aikata, ni ne nasa a kamaka, tsautsayi ya fada kan Abdulmajid." Dolene ya fadi haka ba wai dan Magajiya ta sashi ba sai dan yasan yau kam tashi ta kare, ko ma menene dolene ya kare rayuwar Abdulmajid. Inalilahi wa ina ilaihi raji'un..... Abinda kowa ya shiga fada kenan a fadar. Turab yace " kana so kacemin kai kadai ne ka shirya wannan abin?" Hisham yace " ni kadai ne, da dani dawa nake yanke shawara ta?" Turab yace " ni na kasa fahimtar menene ribarka a ciki in Abdulmajid ya hau mulki, dan yana d'an kanwarka? Ko kuwa da wani abun?" Gaban Hisham ne ya fadi ya kalli Turab, tsananin tsoro ne karara a idanunsa. Sarki a kufule yace " kai da wa kuka aikata? Magajiya?" Kasa yau da kansa da sauri yace " ko d'aya bata ma san da wannan zancen ba, ni kadai na aikata bawai kuma saboda mulki na aikata ba sai dan ina bakincikin yanda Khadija ke san yarima Turab shi kuma yana murnar auransa." Turab ya kalleshi a ransa yace taban ka biyo? wato so kake har karshw kar ka nuna dana sani ko? Zuciyarka ta gama kekashewa wanda ko kayi dana sanin bazaka taba sanarwa mutane da ka yi ba? Kunyar duniya ce bakasan kaji? Ran Sarki ya baci yace " Alkali inaso a kewa Hisham daga wannan lokacin sannan ayi bincike sosai akan kaf laifufukan daya aikata inaso a sanar dani nan zuwa kwana uku." *********** Magajiya kam ta rasa ina zata sa ranta, a zaune dai take kusa da Abdulmajid amma sam hankalinta baya gun, tashi hankalinta bai wuce sanda ta tuna abinda Abu Turab ya mata ba bayan sun rabu da Hisham. Tana kokarin shiga d'akin taji muryarsa a bayanta yace " kin gama tsaramai?" Juyowa tai ta kalleshi batace komai ba, sai wani kallo da take mai wanda ni kaina bansan manufarta ba. Turab yace "shawara nazo baki, kiyi gaggawar zuwa ki sanar da laifufukan da kika aikata, dan wannan karan bazan taba bari kici galaba akaina ba." Murmushi tamai tace "bari? Kana nufin kai kake bari nake yin nasara akan al'amurana? Sai dai ya zakayi Turab? Har karshen rayuwarka baka isa kai nasara akai na ba, ka sa wannan a ranka." Ta shige d'akin, idanunta ta runtse sannan ta mike da sauri, bataga ta zama ba. Kallan Abdulmajid tai wanda shi kansa a kwance kawai yake tace " zan je gida." Bata jira amsarsa ba tai gaba. Da kallo ya bita. Baga dade da fita ba yaji an turo kofar, idanunsa ya maida ya rufe dan ya d'auka itace, sam baiji sallamara datai ba. Kusa da gadon taje a hankali tace " Malam kaci abinci?" Idanunsa ya bud'e da sauri sannan ya kalleta, ji yai wani sanyin dadi ya ratsashi sai dai yana tunanin ko ita taji sirrinsa kila kallonsa ma bazata sake ba. Had'e rai tai tare da cewa " karma kai tunanin damuwa nai dakai nazo dubaka, asibitin nazo shine na karaso inga Khadija." Murmushi ya sakar mata yace " ko ma menene dalili naji dadin ganinki." Baki tad'an tabe tace " ya jikin Khadija?" Yace " ta koma gida." Tace " yayi, kai fa? Ka daina pretending d'in baka farfado ba?" Murmushi yai yace " me? Kin damu ne akan rashin cin abincin da nake? Kullum ina kwance?" Kai ta kawar da sauri tace " inji wa kenan? Tab!" Dariya ya d'anyi ganin yanda tai saurin bashi amsa........... ************** A can bangaren Turab kuwa, Gimbiya na zaune a kan gado ita kadai a cikin d'aki, ba shakka ya dade bai dawo ba, dan ita ma bata dade da dawowa daga bangaren Umma ba. Jitai an kwankwasa kofar tare da yin sallama. Amsawa tai sannan ta mike jin muryar Turab. Kallan kofar tai a hankali taga ya shigo. Tana ganin yanayinsa tai saurin karasowa inda yake tace " lafiya?" Jitai ya jawota jikinsa ya rungume ta tsam. Mamaki ne ya kamata, sai dai bata nuna ba, a hankali takai hannunta bayansa. Ajiyar zuciya yai a hankali...... *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* *Na Ayusher Muhd🤸🏼* *81* Ya dade a jikinta kafin ya d'ago ya kalleta yace " i'm sry." Abinda ya fada kenan yai fara takawa zaiyi waje. Takunsa biyu yaji ta riko rigarsa, tsayawa yai ba tare da ya juya ba, a hankali ta tako zuwa inda yake itama ta sake rigarsa sannan ta kwantar da kanta a bayansa. Yayi mamakin jin ta a bayansa dan shi har yanzu gani yake auren had'i ne tsakaninsu shi kuma bazai taba shiga hakkinta ba. Cikin wata murya mai sanyin gaske tace " Thanks alot for showing me ur weaknesses." Jiyai wani abu ya tsirgamai, murmushi tai mai sanyi sannan tace " ban san me ke zuciyarka ba game dani, sai dai at least nasan abu d'aya wanda inaji shikadai ya isheni zama dakai cikin farin ciki." " menene shi?" Kanta ta d'aga daga bayansa tana murmushi tace " nasan u are comfortable in kana tare dani." Murmushi yai sannan ya juyo ya kalleta yace "Hmm abinda kika ce......" Kallansa tai cikin mamakin dan yanda yai maganar alama ce ta zai musa abinda take tunani, da sauri ta juya bayanta tace " ba sai ka fad.. .." Kansa ya sako ta bayanta saitin kunnenta yace " abinda kikace hakan yake." Sam ta manta da kanta na gefen kunnenta ta juyo da sauri jin amsarsa. Numfashinsu ne ya sarke dan fuskarsu tayi daf da juna, a hankali ya saukar da idanuwansa ya kalli bakinta wanda yake dan karami mai kyau, gashi tasa jan baki jaa amma bai turo ba. Wani abu ne yaji yana tsirgamai, dif sukai kamar an d'auke wutar nefa sai shi da yake dan kokarin kara karkatar da kansa wanda ita kuma tai kasa da idanunta saboda kunya. (mai kake shirin yi Turab? Me zuciyarka take neman saka? Ina alkawarin?) Jisukai an kwankwasa kofa, juyasa yai da sauri ya nufi kofar ya bud'e. D'aya daga cikin masu kula da Gimbiya ne, ta gaisheshi sannan tace "Yarima an turo Mai Martaba na banana. " To kawai, yace yai waje. Yana fita ya furzar da wata iska sannan ya d'anyi fifita da hannunsa yace " why am i feeling hot?" Itama yana fita ta fada kan gado ta kwanta tare da saukar da ajiyar zuciya itama. Bangaren Mai Martaba ya nufa, a waje yana jiran kafin a sanar ma Mai Martaba zuwansa ya kalli wani yace " Jakadiya fa?" yace " ai yau da safe tace wai yarta ba lafiya, shine aka dawo da wannan nan, ita kuma ta tafi." ya karasa maganar yana nuna mai wata. Murmushi yai dan ya tabbatar guduwa tai, nan ya shiga bangaren Sarki. Yana zaune ga abincin nan a gabansa da alama yanzun nan ya gama ci. Sai da ya kara gaisheshi sannan ya zauna tare da lankwashe kafafunsa yace " gani." Sarki ya kalleshi yace " me kake tunani game da Waziri?" Turab yace " ban fahimceka ba..." " na rasa me yasa nake ganin kamar akwai abubuwa da dama da kake b'oyemin." Turab yace " me yasa kake tunanin haka? Ni kam ba abinda nake b'oyema." Takawa ya kalleshi sannan yace " Turab? Kana tunanin zaka iya kama Magajiya da kanka?" Turab ya d'ago ya kalli Sarki sannan yace " Abba me yasa ka ke kokonto a kaina?" Sarki ya girgiza kai yace " Abu Turab!" Kallansa Turab yai jiki a sanyaye, yace " Hajiya ta farfado, sannan naji abinda ya ke faruwa." Idanunsa ne suka canza yana kallan Mahaifinsa saboda tausayawa. Sarki yai murmushi yace " alokacin da naji abinda ya faru lokacin ne na tabbatar da Magajiya tafi karfina sannan babu ko dan d'igon imani a zuciyarta, a da nayi tunanin rashin nuna mata kulawa ne yasa ta rikid'e ta koma haka, sai dai abinda naji sam ya hanani bacci, hankalina ya tashi. Ban taba tunanin a duniya akwai wanda rashin imani zai sa ya aikata hakan ba, sannan bayan abinda ta aikatamin har ta nemi halakamin mahaifiya, a wannan rana nayu dana sani sosai na zamantowata Sarki dan da ace ni ba Sarki bane banaji duk wad'an nan abubuwan zasu faru dani." Turab yace " Kaddarar ka kenan Abba, sai dai fatan Allah yasa kaci jarabawar da ya maka." Sarki ya kalleshi yace " wato ita daga d'anta bata san in sake haihuwa kenan?" A ran Turab yace " Abba shima ba naka bane." Sarki ne ya cigaba, Turab kai Kainuwa ne dashen Allah, shi yasa duk wani makirci da kiyayya bata hanaka takawa duniya ba, bata kuma haka bud'e ido ba a duniya, wannan itama Baiwa ce da Allah ya bani wanda nake gode masa." Turab ya d'ago ya kalli Mahaifinsa yanajin wani tsananin tausayinsa na ratsashi, cikin takaici yace "Abba wai kana sarki ke zai hana ka hukuntata daidai da laifukanta, barinta fa da akeyi shi yasa ma take abubuwan dataga dama." Sarki ya dade kafin ya murmusa yace " Turab kenan, bakasan me nene nauyin dake d'aure akan kujerar nan ba, sannan abu ko ya shafeni dole sai na fitar da shaida sannan nai hukunci cikin jama'ar fada, sai dai matsalar itace Magajiya bata barin abinda zaisa a gane tayi abu, sannan duk wani wanda yake da hannu akan abun to fa sai ta san yanda tai ta kawar dashi." "Hajiya fa?" Sarki yace " wa zai yadda da shaidar tsohuwa? Sannan suruka?" Turab yace " haka ne na tabbatar zata iya juya laifin kanta." Sun dade suna tattaunawa kafin su rabu. Turab na fitowa ya bi d'akin mahaifin nasa da kallon tausayi, tabbas dolene ya hanzarta sanin abinda ya kamata yai da Magajiya. Magajiya kam tana dawowa taji labarin killace Hisham da akai, wannan abu ya tabata sosai ya kuma kara tada mata hankali domin ta tabbata Turab sai tayi da gaske akansa, wannan shine karo ma farko da aka kada ita da dan uwanta akoda yaushe sukecin riba bawai su a ci riba akansu ba. Bayan La'asar ta aika a kira mata Basira. Basira kam ta gama had'a kayanta kenan da Turab yace ta koma can ko sati d'aya zuwa biyu ne tayi, sannan Sarki yace za'a maida Hajiyarsa can gidan. Jin wannan sakon yasa tai shiru kafin ta fito, dan a ka'idar mulki Magajiya ce Sarauniya wacce duk matan sarki ke karkashinta dolene ta amsa kiran data mata. Magajiya na zaune kan kilisarta kai kace ba wani abu dake damunta sai dai zuciyarta fal take da tsoro da shakkar abinda ke faruwa. Basira ta gaisheta sannan ta zauna. Magajiya ta kalleta cikin izzarta tace " Basira kin san ko ni wacece ko?" Basira ta kalleta cikin mamaki da rashin fahimtar abinda take nufi, Magajiya ta murmusa sannan tace " ba wai wani abun nace ba, tuna miki dai kawai nakeyi, ni d'in macece wacce banida yafiya akan duk wanda ya nemi tozartani, inaso kisa hakan a ranki sannan ki sanarma na kusa dake abinda na fada, daga ke har abinda kika haifa banaji kunyi kaurin wuyan da zai sani na tsugunna muku, tunani yakeyi shine yake cin galaba akaina shiyasa na kiraki ke wacce kika haifeshi in sanar dake hakan." Basira ta kalleta sannan tace " Magajiya ni na kasa fahimtarki, Turab ne ya tozartaki kike sanar dani in gargad'eshi ko me?" Ran Magajiya ya b'aci sai ta saki dariya tace " me? Tozartawa?au har an hallici d'an dazai tozartani a duniyar nan?" Basira ta murmusa sannan tace "nima abinda na gani kenan, shi yasa nake mamaki danaga kin kirani kika neman sanarmin in jaa ma Turab kunne, bayan yaran nan naki ne." Magajiya ta kalleta a ranta tace " wato kema kin rika ko?" Basira tace " zan koma in ba wani abun." Bakin ciki baisa Magajiya ta kara tanka mata ba. Tana fita Magajiya tasa kafa ta ture tiren inibin dake gabanta cikin b'acin rai, sannan tai wani dan karamin kara ma takaici, me yasa yanzu sam bata iya shanye bakin ciki? Mikewa tai cikin takaici tace " ke aika a kiramin Waziri." Baiwar ta sunkuyo tace "Ranki ya dade kin manta an........." Matsowa tai ta kifama yarinyar mari sannan tai ciki ranta na soyuwa. Tafiya ta kamayi a d'akin cikin b'acin rai, yanzu ba Hisham wanda sai dai tana daga zaune tasashi aiwatar mata da duk abinda take so, sannan ba Abdulmajid wanda take tunkaho dashi Yana can a kwance. Kanta ta dafe sannan ta d'ago idanunta cikin tsananin bacin rai, tace "Abu Turab!!! Ka jirani, zan shayar dakai abinda har karshen rayuwarka bazaka manta dani ba, wannan shine zai zama fad'anmu na karshe dakai, in har nai kuskuren halaka rayuwarka to tabbas nasan tawa rayuwar zatai rawa." Kurama kasa ido tai cikin tsananin takaici, rabon datasamu bacci mai dadi ta manta, kullum sai tai mafarkin Turab na neman illatata, tabbas dolene suyi fito na fito yakin karshe a tsakaninsu..... (😂😂😂😂nace Allah yaba mai rabo sa'a) Khadija kam ta gaji da jiran Mahaifinta tana zaune a waje akwatinta na gefenta, ganin yamma tayi yasa ta mike ta fito waje. Tsayawa tai ta kira mai kula da kofar su, ta tambayeshi " ina Abba wai yaje?" Yace "wlh ban sani ba na dai san ya fita." Juyawa tai ta koma ciki kawai, Umma na kwance a d'aki tunda sukai maganar nan da Khadija ta shiga d'aki bata fito ba, tanaji kannan Khadija da yayyinta na shigowa su fita amma ta kasa tashi, saboda tsananin dana sani dake damunta. Wannan kenan.......... *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *82* Bayan tayi sallar magrib ta yafa mayafinta katon gaske, lulubi tai sosai da sosai, wanda inba kaga fuskarta ba bazaka taba cewa Magajiya bace, ta fito, tara bayinta tai ta sanar dasu zata fita sai dai batasan kowa yasan ta fita sannan ko anzo nemanta a tabbatar ance tana bacci. Ita kadai ta fito ta nufi inda aka killace Hisham. Tana zuwa ta sauke mayafinta sannan ta kalli masu tsaron gun tace "yana ciki?" Kallanta sukai bayan sun gaisheta sukace " Ranki ya dade Sarki ya umarcemu akan kar kowa......." Wani kallo data buga musu shine ya hana su karasa maganar, tace " nice kowa?" Da sauri sukace " ba haka bane......" "ya isheni, bud'e." Jikinsa na rawa ya bud'e kofar ta shiga." Hisham na zaune ya had'a kai da gwiwa saboda abin duniya da duk ya taru yamai yawa, ba shakka yana cikin tsaka mai wuya. Ta window ta tsaya tace "Yaya!" D'agowa yai ya kalleta, ba shakka wannan itace wacce ta ruguzamai rayuwa, dan itace ta kawo shawarar d'aura d'ansa akan mulki wanda hakan ne yasa ya bata d'an ba tare da yin wani dogon nazari ba, sannan wannan shine dalilin daya sa sam idanunsa suka gama rufewa yakejin koma meye zai iya zuciyarsa ta zarme indai akan hawan d'ansa mulki ne to tabbas zai iya koma menene. Kallansa tai cikin zafi tace " magana nake." Mikewa yai ya iso inda take, kallanta yai yace "ya akai?" Tace " baka tambayeni jikin d'anka ba?sai kacemin ya akai?" Kallanta yai yace " d'ana? Bayan kece kika hana wannan maganar?" Tace " yaya ai duk hanawar danai jini ai jini ne, sannan karka damu da gida, zan kula dasu kamar yanda zan kula da kaina, kai dai ka kara hakuri." Kallanta ya sake yi yace " me ya kawoki? Dan na tabbata bazaki taso nan ba bayan kinsan abinda ke faruwa kizo nan ba tare da kwakwaran dalili ba." Tace " Yaya ka san kome nakeyi a yanzu saboda Abdulmajid nakeyi ko?" Kallanta yai dan yama kasa magana, tace "yaya karka damu da duk abinda ke faruwa, koda wani abun ya sameka ni ina nan, sannan in har ina duniya tofa kamar kai kana cikinta ne, d'an mu da 'yayanka ni na d'au alkawarin rikesu amana......." Katseta yai da cewa " me kikazo fad'amin." Juyowa tai ta kalli waje, can ta hangoni rakube jikin window rike da takardata da birona, kallo d'aya ta sakarmin na fita a guje kamar wacce aka biyo da wuka, dan tabbas na tsorata, wannan dalilin yasa sam Bansan me tace masa ba. Sai dai tana gama maganarta na kalli Hisham, kallan da Hisham yake mata kadai zaka kalla ka tabbatar da lalai shi kansa yasha mamakin kalamanta. Kallansa tai tace " Yaya bansaka dogon tunani ko dogon nazari ba dan abinda na sanar maka shi za'a aikata indai kana san kanka da lafiya, ni kabarni da waccen yaran, kai dai kayi abinda ya dace." Yama kasa magana sai kallanta da yakeyi, tace "ni na wuce, ina kuma jiran ganin abinda nace." Ta juya ba tare da taji asarsa ba. Tsananin mamaki kawai yake, sai binta da kallo kawai da yai. Tana fitowa ta ciro abu a jikinta ta mikama masu kula da kofar tace "waye ya ziyarci Waziri?" Da sauri sukace " ba kowa ranka ya dade." Juyawatai tai gaba abinta. Tana shiga bangarenta cikin d'aki ta yaye mayafin ta shiga zirya a d'aki, Hisham zaibi abinda tace? A fili tace dole ne ai. Ya zatai in bai bi ba?? Kai take girgizawa da sauri in zuciyarta ta nemi kawo mata wannan tunanin, sai tace innaaaa....." ******* Basira kuwa da yama ta wuce gidan dan Turab dashi da Garzali ne sukazi suka rakata, hmm Umma anga Lantana. Nan suka shiga hirar yaushe gamo bayan ta dan zauna gun hajiya ta dubata da jiki. Turab ya zauna gun Hajiya wanda jikin nata dai to, sai a hankali duba da yanayin tsufan datai, sannan dama in girma ya kama dama ciwo kad'an ke zaunawa a jikin mutum, ita kadaice wacce take da wannan shekaru a cikin masu mukami dake gidan, dayake duk kishiyoyinta basa gidan sai ita wasu matan nasa sun mutu wasu kuwa sun bar gidan. Turab ya kalleta duk ta rame ta kara motsewa, tace " Ina cikin farincikin ganinka, a koda yaushe tambayata d'ayace kana ina? Kana lafiya? Dan gaba d'aya hankalina yana kanka tunda na riga nasan abinda ke faruwa." Yace " me kika sani hajiya?" Tace " kasan komai ko? Wannan shine yasa nake tsoro saboda wannan matar batada imani ko kad'an, na tabbata bazata taba kyaleka ba." Yace " Hajiya karki damu, ba ta isa tamun abinda Allah bai mun ba, in har wani abu kuma ha sameni to tabbas kaddara tace bawai wani abun ba, karkisa wannan a ranki." Tace " Turab kana tunanin taimakawa yarinyar nan da kake hakan shine daidai? Karfa ka manta itace ta dinga zubamin magani " Yace " na sani hajiya hakan ne ma ya sa naji taimakon take bukata, Da ace mun farga ko munsan halin da take ciki mun taimaka mata da wuri banaji Magajiya ta isa ta sa ta wannan abin, sai dai ganin tana cikin hali na bukata yasa takejin zata iya yin komai..... Hajiya kallansa kawai take cikin jin dadi. ******** Yau ma a kasa ya saukar da filonsa ya kwanta, tana kan gado a zaune ta kalleshi tace " ka dawo nan, ni sai in sauka kasa." Kallanta yai yace " so kikeyi gobe in ziyarci asibiti?" Tace " saboda me kenan?" Yace " kin taba kwana a kasa?" Tace " zan fara yau." Murmushi yai yace " ke dai ki kwanta a inda kike kafin ki tada mana hankali da ciwon baya da gab'obi." Kallansa tai tace "kai ma ciwon bayan kakeyi?" Gani tai ya kwanta sannan ya ce wash Allah na, cikin irin muryarnan ta marasa lafiya. Hankalinta ne ya tashi, da sauri ta sauko inda yake ta zo ta sa hanny tad'an d'agoshi tace " Lafiya? Menene?" duk ta rikice." Idanunsa ya bud'e sannan ya mike ya zauna yace " yanzu in ni ina namiji daga kwanana a kasa na fara ciwon baya ai na zama rago." Harararsa tai tace " yanzu nan d'in kenan zolayata akai?" Dariya ya guntse yace " a'a" Hannunta data ririkeshi ta nemi zarewa tare da had'e rai, hannu yasa ya rike hannun yanda ba yanda za'ai ta zare, kallanta yai ita kuma tai saurin juya kanta gefe. Yace " ta ya za'ai ina namiji na barki ki kwana a kasa?" Kallansa tai tace " ni ma tayaya za'ai in dinga barinka kana kwana a kasa?" Murmushi yai yace " ke bakisan wahala ba......" Kallansa tai saurin yi tace " kai sani kai?" Murmushi yai yace " Bilkisu ni a kauyen kayau na taso." Kallansa tai da sauri tace " kauyen ina?" Murmushi yai sannan ya kwanta a kan filo din sannan ya jata itama fa kwanta a kan filon ta gefensa, duk suna kwance a rigingine. yace " kinsan nayi makanta ko?" Kai ta d'aga tace " eh" Yace " da ita aka haifeni." Shiru tai dan jin tausayinsa ya kamata, a hankali ya shiga sanar fa ita rayuwar da yai a kauyen nan. Har zuwa dawowarsu garinan, hawaye ne ya gangaro ta gefen idanunta wanda ita kanta bata farga da zuwanshi ba. Ya karasa zancen tare da juyowa yace " kinga kuwa ni a kasa ma wanda ba carpet zan iya kwana." Kallanta yai yaga hawaye ya zubo mata, komawa yai ya kwanta sannan ya sa hannu ya riko hannunta. Kallansa tai tare da sunkuyar dakai, yace " Kiyi hakuri na barinki kina yini ke kadai." Murmushi tai batace komai ba, shiru ne yad'an ratsa kafin can tace " Umma......" Sai kuma tai shiru, juyowa yai kalleta ta saitin inda take, yace " me ne?" Tace " Na jinjina mata ne a raina." Yace " jinjinar me?" Tace " duk yanda ta shiga cikin wannan halin bai hanata kula da baka tarbiyya ba." Murmushi yai sannan a ransa yace " shiyasa bazan taba yafema wad'anda suka ruguza mata rayuwa ba." ji yai tace " basu cancanci yafiya ba, sannan duk da bansan me suka mata ba na san d'anta zai hukuntasu daidaj laifikansu." Murmushi yake yana kallanta, Sund'an dade suna hira kaffin bacci ya d'auketa, shiru yai yana tunani shikam, a wani hali Khadija take jin abinda ya sami mahaifinta? Dan ya tabbatar bata tafiba tunda ya tambaya. Bilkisu ya kalla sannan ya mike ya d'auketa ya d'aurata a kan gado ya rufeta da bargo dannan ta mike ya zai sauka, jiyai ta riko hannun rigarsa. Idanunta a rufe tace " baka tunanin kaine ya dace ka kwanta akan gadon?bayan kasha wuya kana karami?" Yace " ba bacci kike ba dama?" Bata bud'e idon ba sai kara kasa datai dakai, yace " zan kwanta ta can bayanki, zan kuma sa filo a tsakaninmu, shikenan?" Kai ta d'aga cikin jin dadi. Mikewa yai har ta d'aukama yayi gaba, sai jin muryarsa tai saitin fuskarta yace " in mutum ya hauro inda nake garin bacci, duk abinda ya biyo baya ba ruwana...." Ya juya yai gaba yana murmushi.Filo ta janyo ta rufe fukarta tana murmushin kunya. ********* Khadija kam ana sallar asuba ta fito waje, tana ganin gari ya waye ta taho gidan sarki cikin tashin hankali. B'angaren Magajiya ta nufa. Tana kwance tana bacci taji ana kwankwasawa. Cikin mamaki ta mike a d'an zabure, jitai gefen cikinta yad'an amsa, tai tsaki sannan ta mike ta zo ta bud'e. Khadija ta gani, tace" Khadija?" Masu kula da ita ne suka shiga bada hakuri, tace " kuje." Khadija ta shigo sannan ta kalli Magajiya tace " Umma ina Abba?" Magajiya tace " Yaya? Ina yaje?" Khadiya ta kalleta tace " ke zan tambaya ai, banaji akwai wani dayasan inda yake bayan ke." Magajiya ta kalleta tace " khadija! Ni kike tsarewa da magana?" Khadija ta kalleta tace " wanda ake kasa magana a gabansa wanda yasan girma da darajarsa kenan bawai wanda ya halaka rayuwarsa, ta 'yayansa da kuma ta 'ya'yan yayan nasa ba sannan ya ruguza rayuwar duk wani wanda bai mai ba." Magajiya tace " mene?" Khadija wacce hanayenta da kafafunta duk sun sunyi shakaf sabida tsoro tace " kina tunanin kullum cikin samun nasara kike?" Ba abinda Magajiya ta tsana irin a dinga nuna mata abinda ta ke tunani ba daidai ba. Wani kallo ta mata tace " karki bari raina ya baci, ina raga miki ne saboda san da nake miki da kuma darajar sunan naki." Khadija bata damu ba tace " Ya Turab bazai taba barinki kice nasara ba, domin kuwa Allah na tare dashi sannan gaskiya tana da adalci na yawo a jikinsa, in kinga Abba, ko inya dawo daga aikin sharrin da kika sashi ki sanar dashi ni na wuce." Ta juya ta fita da sauri saboda karkaraa da jikinta keyi.......... *Turab* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *83* Kanta ta dafe a waje tana tunanin abinyi, bazatace bata damu da inda mahaifinta yake ba, sai dai ganin mahaifiyarta yau da asuba ta yabbatar bata samu bacci ba jiya. Ya Turab? Abinda yazo mata kenan, sai dataje bangarensa ta kalla, ganin kofar ba mai kula da ita yasa ta tuna da ashe fa yanzu ya tashi daga nan, tunda yanzu yayi aure. Haka ta juya jiki a mace ta koma gida. Magajiya tai shiru tana tunani, tafi awa d'aya a zaune shiru kafin ta mike sannan ta shiga wanka. Sai data cancad'a kwalliyarta kamar yanda ta saba sannan ta saka alkyaba mai tsananin kyau, wanda ya kara fito da kyanta. B'angaren Sarki ta nufa. Yayi mamakin jin ance itace ke nemansa, kuma wai a kilisarsa bawai a bangarensa ba. Tana zaune, irin zaman data saba na isa da mulki. Mai Martaba ne ya shigo sai daya zauna sannan ta gaisheshi. Abinda ya bashi mamaki, yana zama sai ga Alkali ya nemi izinin shigowa, nan ta bada izini ya shigo. Ko zama baiyi ba sai ga Abu Turab, Sabi'u sun shigo, shikam Turab ya d'auka ma Sarki ke nemansa. Yayi mamakin ganin Gimbiya a zaune, shikansa Sarki kawai kallan kowa yake cikin mamaki, Turab na ganinta yasan akwai abinda ta shirya. Sai da suka gaida Sarki da Magajiya sannan suka zauna. Magajiya ta kalli Sarki tace " Ranka ya dade muna bukatar Hisham a gun nan." Kallanta yai sannan yace " Ba yanzu ba, sanar dani me ke tafe dake sannan inyi tunanin kiransa." Ta numfasa sannan tace " jiya naji duk abinda ke faruwa, dan ni bansan abinda ke faruwa ba, duk yanda na tambayi Abdulmajid bai sanar dani ba." Sarki yace " meke tafe dake yanzu?" Murmushi tai sannan ta kalli Sabi'u t ace " Abinda na kasa fahimta shine na d'auka Sabi'u shikadai ne shaidar abinda ke faruwa?" Turab kallanta kawai yakeyi, haka kawai zuciyarsa take raya masa abinda take shirin yi. Alkali yace " eh shikadai ne." Magaijiya tai murmushi sannan ta kalli Sarki tace " Sabi'u kowa yasan aminin Abu Turab ne, me yasa mutane suka yarda da maganarsa ba tare da bincike ba? Me yasa ba wanda ya kawo Turab shine ya sa a kama Abdulmajid shikuma Sabi'u ya tafi inda aka killaceshi, wanda bai sani ba ashe Waziri ya bishi a baya?" Turab ya kalleta baisan sanda wani murmushi na takaici yazo mai ba, lalai matar nan bala'i ce. Sarki kallan mamaki shikansa yake mata, ita kuwa ta kalli Alkali tace " Turab d'ana ne sai dai ko d'ana ne naga zaiyi abinda bai dace ba dole ne na maidashi kan hanya." Alkali yace 'm" haka ne, kuma sai da kikai magana naga ya kamata kam a sake bincike." Kallan Sarki tai tace " Takawa tuba nake in na b'ata ma rai, sai dai Abdulmajid yaji magana a lokacin da yake kwance agun, kuma tabbas sunan yarima suka kira, banaji kuma akwai wani yarima wanda yake masarautar nan bayan Abdulmajid to Abu Tutab ne." Sarki ya kalli Turab wanda kallan Magajiya kawai yakeyi. Sarki yace " Turab!" Abu Turab ya kalli Magajiya bai d'auke idansa daga kanta ba yace " haka ne, ba shakka Umma kinyi gaskiya, Sabi'u abokinane sannan ni da Abdulmajid bama shiri." Magajiya tace " Banso nai maganar nan ba sai dai ina ganin dolene a sake bincike saboda ina tsoron kar wani kazamin sirri ya fito daga bakina." Turab ya kalleta yace " me kike nufi?" Kallan Sarki tai sannan tace " Banasan ragewa wacce ta haifeka daraja a idon duniya wanda nake ganin shine dalilin....... Sarki ne ya katseta " me kike shirin cewa??" Ta kalleshi tace " ba wai dan Hisham yaya na bane sai dai dan bazan baro a hukunta mara laifi ba." Kallanta Turab yake zuciyarsa na wani irin kuna, ji yake kamar ya tona asirin Abdulmajid a gun nan, sai dai abu biyu ne ke hanashi, na farko yana tsoron yanda Sarki zaiyi inyaji wannan maganar duba da yanayin girmansa, sannan yana tausayawa rayuwar da Abdulmajid zaiyi nan gaba." Alkali ne yace " me zai hana a kira Abdulmajid da Hisham aji abinda ke faruwa daga garesu?" Magajiya tace " Abdulmajid na asibiti amma za'a iya tambayar Hisham." Sabi'u wanda ransa ya gama b'aci yace " wallahi da idona naga Waziri yaje gun, sannan nine na bishi ba shine ya bini ba." Tace " wanene zai yadda da hakan? Bayan ba kada shaidar da zata nuna hakan?" Turab ya sa hannu ya dafa cinyarsa yamai alama dayai shiru. Sarki tsananin mamakin ta ma yasa ya kasa magana. Daurewa yai yace " gobe za'a sake zama saboda wannan maganar, zakuma a sake yin shari'a akan wannan al'amari." Magajiya tai kasa dakai tace " Godiya muke ranka ya dade." Nan ta mike cikin isa tai gaba. Tana fita alkali yai sallama ya fita, Turab ya kalli Sabi'u yace " dan bamu guri." Nan Sabi'u yai waje. Turab ya kalli Sarki wanda gaba d'aya fuskarsa ta canza, tsananin bacin rai ne bayyane a fuskarsa. Kallan Turab yai. Turab ya kakaro murmushi yace "Abba ba wani abu " Sarki yace " Turab ina matsayin mahaifinka? Nasan duk abinda ke faruwa amma banida ikon bin bayanka? Banida ikon kareka? Ina zaune za'a maka sharrin da baka sani ba?" Turab yace "karka damu Abba, muna wani stage ne na wanda ko ni ko ita, wani mataki muke wanda in har bata nakasa rayuwata ba ni zan nakasa tata, dolene dukanmu mu fito da b'oyayen ajiyar da mukama junan mu dan gogawa, karka damu Allah na tare da mai gaskiya." Sarki ya kalleshi cikin kulawa yace "kada ka kuskura kai mulki irin nawa wanda zaka sakarwa matarka komai, ka kuma bari ta dinga cin galaba akanka." Turab ya jinjina kai kafin ya mike ya fito. Yana fita yai waje mai makon ya koma cikin gida. ****** Magajiya kuwa tana shiga bangarenta ta saki wani murmushin jin dadi tace " Takawa ya kaji a zuciyarka? D'an da kake masifar so na cikin halaka?" Turab kam gidan da Umma take ya nufa. Suna zaune a waje suna yar firarsu da Lantana. Ya shiga, sai da suka gaisa sannan ya kallu Lantana yace "ina yarinyar nan?" Tace "wa kenan?" Yace " mai kula da Hajiya." Tace " au Marakisiya? Tana gun Hajiya." Shiga yai ciki kai tsaye tana shara, Hajiya ya kalla wacce ke kwance tana bacci, yace " zo." Tace "to." Falo suka dawo ya zauna kan kujera ita kuma ta nemi kasa ta zauna, kallanta yai yace " baki manta abinda kika cemin ba ko?game da ko a gaban waye zaki fadi gaskiya akan Magajiya?" Tace " eh." Yace " kinsan waye ya saki ba hajiya magani?" Tace " eh wacce tafi zama kusa da Magajiya ce." Yace " Yauwa." Mikewa yai ya fito. Bai ko zauna gunsu Umma ba ya fita. Bayan ya shiga mota ya dade a zaune a bayan mota shiru yana tunani, kafin yacema Garzali su tafi Asibiti. ********** A gida kuwa Mairo ta gama cin abincin safe kenan tai wanka, ta hau kan gado, tunowa tai da abinda Abdulmajid yace mata da zata tafi. Yaushe zaki dawo? Tsaki tai a fili tace " harda wani tambayar yaushe zan dawo ko kunya, ko mai zan koma in mai?" Can kuma tace " ni biki ma zamu tafi gobe zuwa cikin garin kaduna, kaga wacce zata zo." Kara gyara kwanciyarta tai. Abinda yaban dariya shine batafi binti biyu da kwanciya ba naga ta sauko daga kan gadon tace " hmm bari dai inje neman lada kafin mu tafi kaduna." Hijab d'inta ta janyo ta fito. Abdulmajid na kwance akan gado, yana tunanu, wanda kwanan nan aikinsa kenan, gaba d'aya tunani sun kasa barin zuciyarsa, gani yake duk yanda rayuwa zata juyamai bayaji zai taba samun jin dadi wannan rayuwar, bata ubansa ba ba kuma ta uwar data rike shi ba. Sallamarta ce tasa ya kalli kofar. Shigowa tai fuskarnan a had'e tare da kallan d'akin tace " hmm da alama yauma Khadijan bata nan" Abdulmajid kallanta kawai yake yana murmushin jin dadi. Tace "Sannu da jiki, ni na tafi in ta dawo ma had'u." Juyawa tai kamar mai shirin fita. Da sauri yace " Maryam!" Tsayawa tai cak sai dai bata juya ba, yace " Maryam!" Yanda ya kira sunan ta ne yasa taji ta wani iri. Abdulmajid yace " Maryam dan Allah karaso nan." Juyowa tai a hankali ta kalleshi sannan ta karasa inda yake. A jikin gadon ta tsaya tace " gani, menene?" Yana kallanta yace " bazan tambayeki komai ba, ko magana in bakyasan na miki bazan yi ba, so nake kawai na kalleki ko na minti biyu ne, please." A hankali ta d'ago idanunta ta kalleshi, sannan cikin sanyin murya tace " meke damunka kwanan nan?" Yace " ba komai, ko ince ko me ke damuna inaji in har ina ganin fuskarki kullum ko na minti biyar ne zan iya jurewa." Maida idanunta kasa tai batace komai ba. Zaiyi magana Turab ya kwankwasa kofar Tare da sallama. Da sauri ta matsa daga jikin gado tare da kallansa. Yana kallan kofar yace mata "tsoro kike kar yai tunanin ko akwai wani abu tsakanin mu?" Harararsa tai batace komai ba. Turab na shigowa ya kallesu, Mairo ta kalleshi sannan ta d'an matso da sauri ta gaisheshi tace " Ya Turab na shigo asibitin ne shine na leko neman Khadija." Turab ya kalleta yace " au ba dubiya kika zo ba?" Kallan Abdulmajid tai wanda ya juya kai, kasa magana tai. Turab ya kalli Abdulmajid wanda ya kula shima yad'anji ba dadi yace " Mairo kenan, da alama kunyar yayan nan naki kikeyi, me zaisa in miki fada dan kinzo duba shi?" Kallan Turab tai sannan ta sunkuya kai tai gefe da sauri tai waje..... Murmushi Turab yai, duk da dai yana tunani akan wannan lamarin nasu sai dai yana musu addu'a dukansu. *TURAB* .🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *Gaisuwa Gareki Maman Abrar wannan shafin naki ne, Allah yabar zumunci Ameen.......* *84* Ajiyar zuciya yai sannan ya kalli Mairo, kanta ta sadda kasa sannan tai hanyar fita. Abdulmajid ne ya bita da kallo, sai dataje jikin kofar zata fita sannan ta juyo idanunsa na kanta dan Ji yake kamar kartaje ko ina. Murmushi tamai sannan taja kofa tai waje Tare da rufo musu. Tana fita ya maida kallansa gun Turab yace " Waziri fa? Ya aka kare?" dan tun jiya abin nan ke damunshi. Turab yace " yana gida sai dai Sarki yasa an killaceshi kafin a gama shari'a." Mairo taje zata gangara ta hango Magajiya na nufo gun. Gefe ta matsa tare da juya baya har ta wuce, har taje zata sauka ta tafi sai kuma ta fasa. Turab ya kalleshi yace " Magajiya ta bu'lo da wani sabon al'amari." Abdulmajid yace " na me kenan?" Turab zaiyi magana yaji Garzali na sanar da isowarta. Tura kofar tai ba tare da sallama ba, dama tunda taga Garzali tasan Turab na nan. Tana shiga ta kalleshi sannan ta kall Abdulmajid. Murmushi Tai sannan ta karasa ciki. Kallan Turab tai tace " kana nan ashe?" Turab ya kalleta sai dai baiyi magana ba. Girarta ta ja sama sannan ta kallu Abdulmajid tace " zuwa nai in maida kai gida, a kula dakai acan." Kallanta yai yace " gida?" Tace " eh, sannan dama inasan inma wata tambaya agaban kanin nan naka, nikam Abdulmajid tsakanin Waziri da Abu Turab wanene ya nemi halaka maka rayuwa?" Kallan mamaki ya mata yace " ban gane me kike nufi ba?" Tace " tsakanin Turab da yayana wanene yasa aka kamaka?" Yace " ni ai ba........" Katseshi tai da sauri tace "bakaji tambaya ta bace? Tsakanin Turab da Yayana wanene yasa akama ka?" Turab ya kalla wanda daidai lokacin shima ya kalleshi. Turab a hankali yamai wani murmushi. Magajiya tace " kai nake jira." Yace " Turab ne." Wata dariya ta saki tace" kaji ko? Ina fatan kasan yanzu amsar da za'a bada a zaman da za'ai, sannan banasan wanda ya nemi kashe min d'a yazo kuma yana neman shiga jikinsa, dan haka karna kara ganinka da Abdulmajid." Turab ya kalleta idanunsa na kanta ya taku har inda take yana tafa mata, sai dayazo daf da ita yace " Bravo! Kai gaskiya Umma u are indeed a very dangerous woman." Da yake lokacinta ba makaranta tai ba, sai dai tsabar basira datake dashi ta tabbatar magana ce ya fada mata, tunda lokacin karatun mata ba'a wani daukeshi da wani abu ba. Kai ta jinjina mai tace " in fadama wani sirri?" Kallanta yai, tace " abinda kake dashi akaina ba abinda zasumun, kasan dalili? Ta matso daf dashi saitin kunnenaa tace "Saboda kai jinin mahaifinka ne, bazaka taba sanar dashi d'an dayake tunanin nashi ne ba nashi bane." Sannan ta kalleshi tace " kasan dalili?saboda kana tsoron halin da zai shiga." Turab kam jiyake zuciyarsa kamae zata fashe saboda takaici, daurewa yai ya kalleta yace " haka kike tunani?to in har haka kike tunani kin bada ni, domin in har irin wannan d'an karamin abun zai firgitashi to ba shakka bai dace da mulki ba." Ya juya yai waje. Dunkule hannunta tai ta matse a jikin zaninta, ji take kamar ta jawo yaran can ta shake shi. Shikansa yana fita ya saku wata ajiyar zuciya sannan ya dan cije labbansa, yai gaba. Kallan Abdulmajid tai wanda ganin yanda suke magana yasa ya runtse idanunsa saboda takaici, waje tai a zuciye Ta tambayi inda likitansa yake. A hankali ya bud'e idanunsa, hawaye ne suka zubo mai dan ba shakka shikam yasan duk abinda ke faruwa duk saboda shi ne. Tura kofar tai a hankali ta shigo, taba kallan sanda Turab ya fita, Sannan taga yanda Magajiya ta fito rai a bace. A hankalu ta tako inda yake, hannunsa ya rike yana karza babban d'an yatsansa a kan bayan hannunsa sam bai kula ba gun yar ya d'an fashe. Har ta karaso gun baimasan tazo ba, hannunta tasaka akan hannun da yake karzawa, idanunsa ya d'ago ya kalleta, kura mata ido yai, daurewa tai tace " me kakeyi hakan?" Kasa magana yai sai kallanta kawau da yakeyi, tace " ko me ke damunka addu'a zakai bawai karza hannu ba." Ta zare hannunta tace " zan wuce." Ganin yanda fuskarta take a had'e yasa yai saurin riko hijab d'inta. Tsayawa tai ba tare data juyo ba, yace " kiyi hakuri." Kallansa ta juyo tai cikin zafi tace " me yasa kake cutar da kanka? Me yasa in abu baima ba bazaka fadi abinda ke ranka ba? Mahaifiyarka tafi wanda ya halliceka ne? Akan me bazaka dinga nuna mata abinda take aikatama ba daidai bane? Ko zuciyarka ba irinta Turab bace at least kai namiji ne ya kamata in har tai abinda bai dace ba ka nuna mata." Ko mai ta tuna, sai kuma tai shiru taja hijab dinta tai waje. Magajiya na dawowa ta sa aka sashi a keken guragu aka kaishi mota, sykai gida. *********** Juyi tai ta ganshi akan sallaya, agoggo ta kalla taga karfe d'aya saura minti goma. Farkawa ta kara yi , Abu Turab ta gani a zaune a kan kujerar dake d'akin, ya had'e hannayensa alamar dogon tunani, dayake ba haske sosai a d'akin, sai wata yar karamar fitila dake gefen gado ta d'aya bangaren ne a kunne. A hankali ta kalli agoggon d'akin karfe biyu da kwata, mikewa tai ta zauna sannan ta kalleshi. Kallanta yai dan yaji motsi, ganinta a zaune yasa ya mike ya taso yazo inda take. Kusa da ita ya zauna sannan yace " farkawa kikai?" Kallansa tai tace " eh, kai fa? Kasa bacci kai?" Kai ya girgiza, tace " tunanin gobe kake?" Juyowa yai saitin da take kallansa yace " Bilkisu." "Uhmm mm" Shiru yai sai kallanta da yake, tace " inajinka." Hannayenta ya kamo duka biyun ya rike yace "bansan ya zata kaya mana ba gobe, shiyasa nake tunanin wani abu." Kallansa tai tare da tattara hankalinta zuwa kansa. Yace " idan har Magajiya taci galaba akaina, wani abu ya sameni inaso ki koma gida, ba tare da waiwaye ba, kiyi rayuwarki kamar baki san niba, zan aiko da takardarki......." Hannunta ta zare daga cikin nasa sannan ta sa kalleshi tace " me kake sam cewa?" Yace " nama mahaifinki alkawari bazan......." Katseshi tai tace " kana nufin in had'a kayana kenan kafin gobe ko me?" Baice komai ba sai kallanta da yake, mikewa tai ta kunna fitilar d'akin sannan ta bud'e wardrobe dinta cikin kunar rai ta shiga zubo da kayanta kasa. Ganin yanda take zubo da kayan ne yasa ya mike ya karasa inda take, hannu yasa ya riko hannun da take zubo da kayan, yace " Bilkisu!" Juyowa tai ta kalleshi idanunta sun ciciko da kwala tace " na d'auka kai kace in shirya kaya na?" Yace " Na fada amma." Tace " kanaso ka nunamin ni da kau ba d'aya bane? Kanaso ka nunamin matsalarka ba tawa bace?" Bata taba nuna bacin ranta ba a iya zamansu tun kan suyi aure sai yau, hannunta ta shiga kokarin kwacewa. Rungume ta yai a jikinsa, sai da yaji tayi sanyi da kokarin kwace kanta sannan yace " ba haka nake nufi ba, banaso insanyaki cikin damuwar da ni kaina bansan sanda zata kare ba." Idanunta ta lumshe tace " menene tsakanin miji da mata? Na d'auka duk runtsi duk wahala su shanyesu tare, su birne matsalarsu sannan su taimaki junansu? Da wannan buri nai aure, taya zaka cemin inka shiga matsala in tafi gida? Bakasan gwara kace mu rabu saboda baka sona ko saboda akwai wani abu nawa da baka so ba?" Kara rungumeta yai yace " ko d'aya, in fact a kullum nai sallah ina gode ma Allah daya bani ke a matsayin matata, wacce ban taba zato ba, sannan maganar bamu zama d'aya ba ko kad'an ba haka bane." D'agowa tai ta kalleshi tace " me yasa kake tunanin fad'uwa? Baka tunanin kaine zaka kada ta?" Murmushi yai yasa hannunsa d'aya a kan kafadar ta, tace " mai gaskiya baya faduwa, sannan Allah na tare dakai, muma muna ma addu'an samun nassara, inaji a jikina matsalar ka ta kusa warware wa, sannan da yardar Allah ba wanda zai cutar dakai." Murmushi kawai yakeyi yana binta da kallo, tace " me? Baka yarda dani........." Batai zato ba taji bakinsa cikin nata, shikansa bai san sanda zuciyarsa ta sashi hakan ba. Sun dade suna aikama juna sakwan ni, abinka da wanda bai taba yi ba, jinsa ya dinga yi kamar ana angizashi. Sam ya manta da alkawarin da ya d'aukarma kansa. Jin kafafunta suna neman kasa d'aukarta ne yasashi sa hannu ya zareta zuwa kan gado, a hankali ya zare bakinsa daga nata, ya kai fuskarsa zuwa wuyanta tare da sa hannu yana kokarin rabata da kayanta. Cak ya tsaya, tare da saurin mikewa idanunsa sunyi jaa sosai. Kallansa tai ita kanta duk da tana tsoron wannan rana sai dai abinda takeji a yanzu dadi ne muraran. Idanunsu ne suka hadu da juna, dawowa yai ya zauna tare da rungumeta tsam yace " what should i do?" A hankali tace " akan me?" Yace " the promise......" Kanta ta sunkuyar tana murmushi, dan ya bata dariya. A hankali yace " ya zanyi?" Murmushi kawai takeyi, d'agota yai ya kalleta, idanunta a lumshe a hankali ya maida bakinsa cikin nata........... Nace su Turab dai to😂 ************* Washegari da sassafe bawan da Magajiya ta aika ya iso, rabansa da gidan sarki yau sati d'aya kenan. Tanajin shine ta ce ya shigo. Yana gaisheta yace " Magajiya na samoshi." Tace "yana ina?" Yace " yana wajen gidan." Tace yauwa na gode........ *THE LAST BATTLE 😄* *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *Gaisuwa, jinjina gareku Aminan Arziki 'yan Sauyi, Dizzy, Rabes, Faty Shafi'u, Yar Gaya, Salamah, Kozali, Sharubutu, J.B, Rambi, da sauran Yan Sauyi...... *85* A hankali ya bud'e idanunsa, sannan ya kalleta, bacci takeyi akan hannunsa na hagu, haka kawai ya samu kansa da yin murmushi, sannan ya tuno abinda ya faru jiya. Ya akai jiya idanunsa suka rufe? Sam ya kasa controlling din kansa? Har sai da ya maidata mace? Lalai jiya yaci sa'a Bilkisu tayi wankan tsarki, da tabbas yanda yaji jiya in har bata sallah baisan yanda zaiyi ba, abu yaji wanda tunda aka haifeshi bai taba ji ba. Lalai wannan rana ta zamar mai ranar da bazai mantata ba, murmushi yai sannan ya tuno da, a da ko zaiyi tunanin aure sam zuciyarsa bata raya mai farin ciki. Khadija zuciyarsa take kauna kuma ya tabbata in ba dai wani ikon Allah ba bayanda za'ai ya aureta, shikuma bayaji zan iya rayuwa da wata ba ita ba, sai dai a yanzu ya tabbatar abin ba haka bane. In har ka samu mace wacce ta sanka, sani ba wai na suna ba, sannan wacce ta ke sanka, take kokarin farantama rai, zuciyarta da kuma suffarta masu kyau ne, mai addini, to lallai shikam yana gani a hankali zuciyar mutum zata koya ma san wannan yarinyar. Zuciyarsa haryanzu tana so da kaunar Khadija sai dai baxai taba auranta ba, saboda har abada ya tabbata bazai taba manta abinda jininta suka aikata mai ba, sannan inya hukunta iyayenta me zaice da 'ya'yan da suka haifa nan gaba in har sun tambayeshi kakaninsu na bangarenta? Kuma abu ne na sarauta wanda zai bar tarihi, ko da ya b'oye musu ya tabbatar labari zai isa har kunnensu, mai zai ce dasu a lokacin? Iyayenta sune suka........... Motsin da Bilkisu tai da kanta shine ya katsemai wannan tunanin, kiran Sallah ake tayi a massalaci, idanunta ta bud'e cikin bacci ta kalleshi. Ganin idanunsa a bud'e shima ita yake kallo yasa tai saurin maida idanunta ta rufe, sunkuyowa yai ya sumbaci goshinta sannan yace " zanyi alwala." Kai ta daga mai alamar to, yace " zan dan fita daga nan kina ganin ba matsala? Naga........" Da sauri tace " zan iya." dan batasan maganar kunya takeji. Kanta ta zame daga hannunsa a hankali, murmushi yai bayan ya mike. Bandaki ya shiga yai alwala sannan yai waje. Idanunta ta bud'e a hankali bayan taji alamar fitarsa, sannan ta mike zaune, yaye bargon tai, sannan ta mike a hankali. Dama tasa an sanar da ita duk abinda ya dace tai, yanzu zamani yazi ilimin addini ya kara wadata balle a mata tonon silili. Bedsheet din ta yaye tai toilet, a roba ta sashi ta zuba ruwa sannan tai wankan tsarki bayan ta gasa jikinta da ruwan dumi wanda sai data dafa a heater. Kallo d'aya zakama yanayin tafiyarta ka fahimci ba daidai take tafiya ba, bayan tayi sallah ta dade tana ma mijinta addu'a kafin ta mike. Turab kuwa a massalaci, bayan ya gama addu'oinsa ya fito shida Garzali bayan gari yayi haske suka fito wajen gari. ********** Magajiya kam jin an taho dashi yasa taji wani nishad'i ya kamata, gari yana haske tasa aka kira kata matan sarki. Bayan sun zauna ne ta kallesu tace " yau munada zama na shari'a da za'ai, hakan ne yasa nakiraku dan inji ta bakinku, da Abdulmajid da Abu Turab wa kuke ganin zai gaji Sarki?" Kallanta sukai fuskarsu da murmushi sukace "Abdulmajid mana." Tace " ba sai na tsaya bata lokaci na ba tunda kunsan abinda ya kamata, ina fatan zaku bi bayana anjima." Kallan juna sukai kafin su amsa da to, suka taso suka fita, suna fita d'aya tace " matar nan tana neman maidamu yaranta, da izinin Allah d'an datake takama dashi bazai zama sarkin ba." D'ayar tace "Ameen." ************ Gimbiya tayi kwalliya tana zaune a falo wata yarinya ta nemi izinin shigowa. Bayan ta shigo ne ta mika kata wani dan karamin kwali na agoggo tace " daga fadar mai martaba nake, aikoni yai da agoggo wai aba Yarima Turab, sannan yana mai fatan alkairi." Kallanta Bilkisu tai sannan ta amshi agoggon, tana shiga d'aki ta d'aurashi akan madubi dan ita kam bata ji hankalinta ya kwanta da agoggon ba Sai daya gama shiryawa yazo kan madubi yana sa turare yaga kwalin agoggo, yace " wannan fa?" Ta sanar dashi abinda yarinyar tace data kawo sannan tace " ni amma......." Kwankwasa kofar da akai ne ya katse maganar, kofar ya nufa tare da zura agoggon yana tambayar waye. Mai kula da Gimbiya tace itace sannan tace wai lokaci yayi, yce to. Sannan ya kalli Bilkisu yace " Muje?" Tace " ina?" Yace " gun mana." Cikin mamaki tace " harda ni?" Murmushi yai sannan yazo inda take ya tsaya yace " bakyasan kije?" Tace " inaso inje amma......." Kasa tai da kanta alamar kunya. Murmushi yai har hakwaransa suka fito yace " kunya kike?" Ta mike tace " bafa haka bane, tafiya......" Sai kuma tai shiru. Yace " menene a ciki? Indai bazaki bane, bazan takura miki ba." Ya juya, takunsa uku ana hudu tace " zanje." Murmushi yai kafin ya juyo sannan yace " muje." Komawa tai ta d'auko babban mayafinta. ******** Karfe 11 na safe an gyara babban d'akin da za'ai shari'a. Basira itada Lantana sun iso gidan, dan Sarki yace duk a kira na cikin gida tunda shari'ar ta cikin gida ce, sai a kara shaidu. A d'akin taro kuwa, Hisham na gefe a zaune daga gefe, dogarawa biyu na tsaye kansa. Galadima da Barde da mai Shari'a su suka fara zuwa. Sai Matan sarki ne suka fara isowa a mata, sannan Basira. Magajiya ce ta iso cikin shigarta ta isa da jin kai da sanin akwai kudi da matsayi, gefenta Abdulmajid ne aka turoshi a kekensa. Kallo d'aya tama Hisham ta d'auke ido sannan taje gaba ta bangaren Mata ta zauna, bangaren maza kuma akasa Abdulmajid wanda ya zamana yana saitin ta. Ranta ya baci ganib ta riga Abu Turab zuwa. Sanar da isowansu akai, shigowa sukai shida Gimbiya a tare, tayi iya kokarinta na ganin ta saita kafafunta kar a gane, shikansa Turab saboda ita yake tafiya a hankali. Suna shigowa aka zubo musu ido, Abdulmajid sai a wannan lokacin shima ya ganta. Ba shakka ta hadu sosai, Magajiya ce ta dago ta kallesu, takaicinta daya yanda ita kanta sai da kayan jikin Bilkisu suka birgeta, Turab ya samu gu ya zauna kusa da Abdulmajid wanda hakan yasa ta zauna kusa da Magajiya dan Basira ce ta nuna mata gun zama. Bilkisu sai data gaida Basira ta gaida matan sarki sannan ta kalli Magajiya tace " Umma Barka da warhaka." Magajiya ta kalleta, bata amsa ba. Basira tai murmushi tace " Bilkisu da alama bakisan tsarin mu na masarautar zazzauba, a ka'ida sai kin fara gaida Magajiya. Bilkisu wacce dama tasan da hakan, tai murmushi sannan ta kalli Magajiya tace "Umma nayi laifi kenan?" Magajiya tace " karki damu ai bakisan tsarin bane." Bilkisu tace " godiya nake." sannan ta d'auke kanta. Shigowar Sarki ne yasa aka tsaya da gaishe gaishe, mai martaba ya samu guri ya zauna. Sannan akai addu'a aka tunatar da abinda akazo yi. Turab yace "Takawa ina neman izinin shigowar wata bakuwa wacce take da dangantaka akan shari'ar nan." Sarki yace " to bismillansu." Shigowar Matar Hisham ne yasa Magajiya ta kalli Turab, murmushi yai sannan ya d'auke kai daga kanta, kallan juya sukai da sauri shida Abdulmajid ganin wacce ke tafe a bayanta, Khadija? Me ya kawo ta. Khadija kuwa wacce d'an aiken ita ya sanar mawa tace ma Mahaifiyarta ai tare aka ce suzo, ta kalli Turab sannan ta kalli Abdulmajid. D'auke kai tai har suka zauna. Mai shari'a ya kalli Magajiya yace " Magajiya ta kawo nata sharhin a game da shari'ar da akai kwanaki, in akai duba da kalamanta tabbas suma suna da nasu ma'anar, hakan ne yasa aka daga shari'ar zuwa yau." Sarki ya kalli Abdulmajid yace " Abdulmajid sanar dani da bakinka a kuma cikin mutanen nan, wanene yasa a kama ka? Mahaifiyarka tace Turab ne, shi kuka Turab yace Hisham ne ya nemi halakashi kai kuma ka sadaukar da kanka, wanene yake fada mana gaskiya?" Abdulmajid ya kalli Magajiya wacce itama kallanshi kawai take yi, Khadija ya kalla wacce itama shi take kallo. Juyowa yai ya kalli Turab, wanda yake kallan Kasa. Sarki yace " Abdulmajid!" Abdulmajid yana kallan Magajiya yace " ni kaina bansan wanene ya sa aka kamani ba." Magajiya ta kalleshi tace " mene?" Turab kam ko gizau baiyi ba. Magajiya ta kalli Sarki tace " ta yaya Turab bazai nemi halaka Abdulmajid ba? Bayan yasan in akaji sirrin mahaifiyarsa shida sarauta sai dai a lahira? Amma in ya halaka Abdulmajid ko ma menene shi kadai ne jinin sarki dole ne a yafe mai." Galadima ya kalleta yace " sirri? Mai kike nufi kenan?" Kallan Sarki tai wanda idanunsa suka fara canzawa, sannan ta kallu Turab wanda ta tabbatar maganin ta yafara aiki dan yanata lumshe ido kamar mai bacci sannan ta kalli Basira tace " Basira? Me zakice?" Umma kam jikinta duk ya fara rawa, Magajiya tace " ina neman izinin shigowar mai bada shaida." Sarki ba yanda ya iya dole yace " ya bada" Shigowar mutum ne yasa gaba d'aya jikin Basira ya hau rawa, Bilkisi dake kusa da ita tasa hannu ta rike hannunta tana kallanta, kallan Turab tai wanda gaba daya ta rasa meke damunshi dan kamar baya baya cikin hayyacinsa. Basira kam duk ta gama rikicewa. Ganin haka yasa hankalin Sarki ya tashi. Magajiya tai murshi sannan tace " Basira kin gane wannan? Badai zaki mance da wanda ya amshi budircinki ba?" Cikin tashin hankali kowa yaji maganar, nan fa aka fara kananan gulma, Sarki ya runtse ido saboda tsananin takaici. Turab wanda ke kokarin maido da hankalinsa ne ya kalli wanda ake magana, cikin layi. Kallo d'aya zakamai kaga alamar shaye shaye da talauci a jikinsa, tsugunne yake yana dan cicila ido. Kallan Basira yai wacce gaba d'aya jikinta rawa yakeyi. Bilkisu ganin ba wanda yai magana yasa ta kalli Turab da sauri, gani tau kamar baya hayyacinsa. Khadija itama kallan Turab tai dan kowa ya san zaiyi magana, yanda taga yanayi da kansa ne yasata kuramai ido tana san gano meke faruwa. A zuciyar sarki kuwa addu'a kawai yake akan Turab yai magana. Bilkisu ce ta kalli Magajiya wacce ta saki wani murmushin mugunta tare da kallan agoggon hannunsa ta gefe, a tsorace Bilkisu ta kara kallan agoggon tabbas bata karasa sanar dashi ba dazu aka kwankwasa kofa. Matsowa tai gun Basira da sauri ta rada mata abu a kunne. Basira ta kalleta sannan ta kalli Turab wanda idanunsa ke juyewa. Mikewa tai ta zo inda Turab yake, tunda wannan mutumin ya hangota ya taso da sauri ya biyota yana neman rikota yana cewa " kece ko? Kamar kece? Kai na tabbatar ma kece." Da sauri Dogarawa suka rikeshi, nan aka shiga tambayar wanene wannam din? Kowa fuskarsa dauke take da tambaya. Basira ta daure ta karasa inda Turab yake, kowa yana jira yaga mai zatai, da karfinta ta dage ta wanka mai wani wawan mari wanda yasa kowa kallan Turab. Bilkisu da sauri ta mike ta isa inda yake, Turab kallanta yai. Basira tace " bakada hankali ne? Ta ina zaka bari magani ya rinjayi jikinka? Bayan ni ina cikin tashin hankali? Ta ina......." Kuka ne ya nemi kamata, da sauri Bilkisu tasa hannu ta balle agoggon ta zareshi daga hannunsa, sannan ta kalli Turab wanda ya ke kallan Mahaifiyarsa gaba daya idanunsa sun canza. 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *86* Kansa yainta girgizawa saboda gaba d'aya hankalinsa na neman gushewa, Bilkisu idanunta ne suka kada ta taso daga inda suke sannan tazo gaban Mai Martaba ta tsugunna, tare da ajiye agoggon akan tebirin gabansa, tace " Tuba nake Ranka ya dade amma zaka iya gane agoggon nan?" Magajiya ce tai saurin katseta tace " Bilkisu wani irin banzan tarbiyya ce wannan? Bakiga magana muke akan wannan dake gaban mu ba?" ta fada tare da nuna wannan namijin da aka rike. Bilkisu ta kalleta sannan ta sunkuyar dakai bayan ta juyo bangaren Sarki tace " Tuba nake ranka ya dade amma dan Allah ka bani amsar tambayar nan." A kasan ranta kuwa addu'a kawai take akan Allah yasa abin ya sakeshi kafin ta gama maganar nan, dan tana tambayar ne dan neman karin lokaci dan ya wartsake. Magajiya zata sake magana sarki ya katseta tare da kallan agoggon yace " Agoggon menene?" Bilkisu tace " dazu aka aiko ma Yarima akan kaine ka bada a kawo mai." Sarki yace " ni kuma?" Bilkisu tace " haka ne Takawa, yarinyar ta kawo akan kaine ka bada a kawoma Yarima." Sarki ya daga agoggon sannan yace " menene dalilin aika agoggon nan da sunana bayan bani na bada ba?" Bilkisu ta kalli magajiya kadan sannan ta kalli Turab wanda yake ta kokarin bud'e idanunsa da kyar tace " ni kaina shine abinda ban sani ba." Magajiya tace " to yanzu menene? Abinda ya kawomu shine abinda ya kamata muyi ba wai wani zancen agoggo ba wanda bai damemu ba, da a aikamai da agoggo da kar a aika menene namu?" Galadima yace " Takawa ni wannan mutumin nake san sanin wanene? Da matsayinsa." Magajiya ta kalli Bilkisu tace " Gimbiya dawo ki zauna ko?" Bilkisu ta mike tare da kallan Turab. Sam hankalin Khadija ya kasa kwanciya ganin halin da yake ciki, idanunta duk sun ciciko da kwalla. Basira kam gaba d'aya ta rasa ina zata sa kanta, Magajiya ta kalli mutumin tace " kai ka nutsu a gaban Sarki kake, sannan wannan da kake neman yima magana mata ce a gun Sarki ka kiyayi kanka kafin a kamaka." Mutumin yasa dariya yace " mata?" Galadima yace " kai! Meye tsakaninka da matar Sarki?" Kallan Basira yai yace " Basira in sanar dasu?" Kallansa Basira tai idanuwanta sun cika da tsoro, Abdulmajid ne ya kalli Turab ganin har yanzu ba a hayyacinsa yake ba kawai ya fara tari kamar irin ya kware din nan sosai. Da sauri Magajiya tace a kawo ruwa. Nan aka kawomai ruwa, da yake hannunsa ba kwari sai yai kamar irin rikewa ya kasa kawai ya juye ruwan a kan Abu Turab. A firgice Turab ya mike tare da rike kansa. Magajiya tace " meye hakan kuma?" Turab ya kalleta sannan ya kalli mutumin nan, sai a yanzu maganar take kara dawo mai daya bayan d'ayan. Lokacin shi kuma mutumin yana kara cewa " Basira in fada?" Turab ne ya taho da sauri basu ankara ba ya kai mai naushi. Karfinsa ya sake sosai dan har saida gefen leb'ansa ya fashe. Dif d'akin yai da wuta saboda mamaki. Turab ya kalleshi sannan cikin murya mai sauti yace "Ka fad'i me?" A lokaci d'aya mutane biyar sukace Alhamdulila Turab is back (nasan kun sansu....Lol) Magajiya kam takaici ya kamata, Turab ya kallesu sannan ya kalli mai shari'a yace " a shaida da tambaya, mutane nawa ne ba'a yarda da amsarsu?" Kallansa yai yace " da mahaukaci da......" Turab ya katseshi yace " wannan hankali gareshi?" Kowa ya kalli mutumin. Turab ya kalli Sarki yace " Takawa kayan jikinsa kawai nakeso a kalla, wannan mutumin hankali gareshi?" Sarki ya kalleshi sannan yace "da alama babu." Turab ya kalleshi yace " bawan Allah ya sunan ka?" Mutumin ya kalleshi yace " wani rai...." Turab yace " bakasan sunan ka ba ko?" Yace " na sani mana." Turab yace " meye sunanka to?" yace "wannan wani irin tambayar rainin hankali ne?" Turab yao murmushi yace " me kuka gani anan? Zakuce wannan nada hankali? Mutumin da ko sunansa bai sani ba?" A zuciye mutumun ya kwace tare da yowa kan Turab. Nan aka kamashi da sauri, Turab yace " Galadima mai zakuce game da wannan mutumin?" Galadima da Barde suka kalleshi, wanda shikuma takaicin abinda Turab yamai yasa abin ya motsa ya shiga yin gurnanin ihu na manyan 'yan shaye shaye akan lalai sai ya kashe Turab. Ba shiri akai waje dashi. Turab ya kalli Magajiya yace " Umma me zakice ke kuma akan kawomana mahaukaci gun shari'a?" Magajiya ta kalleshi sannan tace " ban gane ba....." Yai dariya yace " baki gane me ba? Kinaso kicemin mahaukacin nan shi ya kawo kansa......" Cikin tsawa tace " kai Turab! Kasan da wa kake magana, ko ka manta wacece ni, ko wacce ta haifeka bata isa ta dinga min magana haka ba." Sarki ne ya kalleshi yace " Turab a daidaita kalamai, kar ka manta mahaifiyarka ce." Turab ya kalleta sannan ya koma ya zauna tare da sunkuyar da kai yace " tuba nake ranka ya dade, zuciyatace take tafasa." Magajiya ta bishi da kallon takaici. Sarki yace " munajiran mai shaida na gaba dan jin asalin meke faruwa." Turab yai gyaran murya sannan ya zubawa Magajiya ido yace " bansan me yasa ake tunanin nine na sa akama Abdulmajid ba, sai dai ni da bakina bazan taba cewa ba ni bane, sai dai kafin a kawo wata shaida da zata nuna nine nai wannan laifin inaso in gabatar da wani laifi wanda yake bukatar bincike, ina fatan za'a bani dama." Mai shari'a ya kalli Sarki yace " mai kake gani?" Sarki ya kalleshi yace " menene?" Magajiya ta kalli Turab cikin takaici da san jin me yake shirin yi." Turab ya d'ago yace " godiya nake, magana ce game da Hajiya." Da sauri Magajiya ta kalleshi. Yai murmushi sannan ya cigaba " Bayan mun kai Hajiya asibiti likita yayi bincike gun warkar da ita, a lokacin ne ya gano cewar guba ce aka bata wacce ta nakasar mata da duk gab'obin jiki." Inalilahi wa ina ilaihi raji'un, abinda yake fitowa daga bakin jama'ar gun kenan, Abdulmajid da sauri ya kalli Magajiya. Turab ya mika ma dogarin dake tsaye akan Sarki takardar yace " ga abinda likitan ya rubuta." Duk da sarki yayi mamakin jin wannan zancen wai likita? Bayan har Hajiya ta warke Turab baisan inda take ba, sai dai bai bari mamakin ya bayana ba a fuskarsa. Amsar takardar yai ya gani sannan ya mika aka bi kowa aka nuna mai. Sarki nuna bacin ransa yai kamar irin baisan komai din nan ba, yace " Guba kenan aka shayar da Hajiya?" Turab yace " sosai, sannan inada shaidar da zata sanar damu hakan." Nan yace shigo. Yarinyar dake waje aka ce waye xai shigo? Nan tace nice, tare da shiga. A tsorace ta shiga, tana shiga ta zube a kasa tare da gaisuwa. Sarki yace " kece shaida akan abinda ke faruwa?" A rikice tace " Tuba nake ranka ya dade na cancanci hukunci mai tsanani." Galadima yace " tashin hankali." Turab yace " sanar damu abinda ke faruwa." Yarinyar ta d'ago tana kallan Turab a tsorace. Turab yace " sanar damu abinda kika sani." Magajiya ta kalleta duk ta rasa me zatace. Hisham kam idanunsa kawai ya runtse dan yasan yau kam sai dai Allah. Yarinyar ta kwashe komai ta sanar dasu. Mai Shari'a yace " yarinyar data baki maganin tana nan?" Kai ta girgiza alamar a'a, dan mai baiwa ce." Sarki yace " wannan alama ce ta kenan wanda ya bada umarnin mutum ne mai mukami." Turab yace " a wani bangaren take aiki?" Magajiya ta kalla sannan ta sunkuyar da kai. Magajiya tace " kanaso kace guba aka ba Hajiya? Wani mara imanin ne zai in aikata hakan?" Turab yace " ina muka sani, ko mara imanin na cikin d'akin nan?" Bai bi takan me zatace ba ya kalli Yarinyar yace " a wani bangare take aiki yarinyar?" Yarinyar ta nuna da yatsa, yatsar kowa yabi sukaga ta tsaya akan Magajiya. Magajiya tai murmushi tace " ba dai ni kike nunawa ba ko?" Kallan Magajiya kowa yai. Yarinyar ta sunkuya sannan tace "a bangareki take aiki sannan tace inhar ban sa maganin ba......." A zuciye ta mike tace " ke dan gudanku sharri zakimin?" Sarkin yace " Magajiya me kikeyi hakan?" Tace " ban gane me nakeyi ba, bayan ina zaune ana neman ace nine nake neman halaka Hajiya, meye dalilin da xai sani halaka mahaifiyarka?" Turab yace " shine yanzu zan sanar." Tace " mene?" Turab ya kalleta sannan ya kalli ragowar matan sarki yace " ko zaku iya tuna shayin da Magajiya ke baku a shekarun baya?" Kallan juna sukai dukansu harda Basira, sannan sukace eh. Turab ya kalli Magajiya sannan yace " Magajiya tana saka magani a ciki wanda zai hanaku d'aukar ciki a wannan shayin, bansan dalili ba wanda yasa daga baya ta canza tunani ta koma shayar da Sarki wannan shayin." Mikewa tai sannan tai wani murmushi tace " mene?" Turab ya kalleta sannan ya kalli Hisham yace " Waziri me zakace game da sharhi na?" Hisham ya kalli Magajiya sannan ya tuna ziyartarsa da Turab yai jiya, ya sanar dashi abinda ke faruwa da Hajiya da abinda ta sani har Magajiya ta mata hakan, Hisham yace tabbas shine ya amso maganin dan akan matan sarki aka fara. Magajiya ta kalli Hisham tace " Yaya me kenan?kana nufin kaine ka sanar dashi wannam kagagen labarin?" Hisham ya kalleta yace "Magajiya sai yaushe ne zaki daina san kanki?" Kallan sarki tai tace " bansan wannan labarin ba, sai dai in shi Hisham din shine ya aikata hakan." Gaba d'aya d'akin kowa kallanta yakeyi. Khadija kuwa gaba d'aya jitai kanta na wani juyawa, Abdulmajid kam idanunsa kawai ya rufe, ita kanta mahaifiyar Khadija ta girgixa da jin wannan muguntar. Bilkisu kam kallan Magajiya tai cikin tsananin mamakin wannan muguwar zuciyar tata. Sarki ya daka mata tsawa yace " ashe bakida imani?" Kallansa tai itama tace " dama abinda kake fata kenan ya faru, ko kana tunanin bansan so kake kaga bayana ba?" Sarki yace " mene?" Tace " da kai da danka kun hada kai kuna neman mun sharri, shine yanzu zakace wai banida imani?" Hisham yace " Magajiya!" Kallansa tai tace " yimun shiru tsohon munafuki, ni zakaci amana?" Khadija tace inada magana. Kallo ne ya dawo kanta, Turab ya zuba mata idanu. Khadija tace "tuba nake ranka ya dade amma Umma Magajiya da Abba sun aikata laifin dayafi wannan." Magajiya ta kalleta sannan tai dariya tace " khadija ke kam wa kike tunanin zai yarda da maganar ki? Bayan kowa yasan yanda kike bala'in san Abu Turab? Banaji akwai abinda zai saki da bazaki aikata ba." Da sauri Bilkisu ta kalli Khadija sannan ta kalli Turab wanda hakan yayi daidai da kallanta dayai. Murmushi ya sakar mata sannan ya d'auke idanunsa da sauri ya kalli Magajiya yace " Umma bakya tsoron incigaba da magana? Ko zaki fad'i sauran laifin da kanki?" Tace " laifi?ni ba laifin dana aikata." Turab yai murmushi yace " idan har zan sanar da laifufukan da kika aikata banaji wannan rana xata ishemu." Magajiya tace " good kun kyauta, sai kuce yau ba ranar bincike bace akan abinda akama d'ana, ranar yimun sharri ne." Turab ya kalli Sarki yanasan tona d'ayan sirrin sai dai inya kalli Abdulmajid ya kuma kalli Sarki sai ya kasa. Kansa ya sunkuyar yana tunanin abinyi. Muryar Andulmajid ce ya katseshi dayace " Umma ya isa haka nan, sao yaushe ne zakiyi nadamar abinda kika aikata?" Tace " mene?" Cikin murya mai sauti yace " Umma please ki tsaya haka nan, a da ina tunanin san da kike mun ne yasa kike aikata abinda kike aikatawa sai dai yanzu jin abinda kikema matan sarki da kuma shi kansa yasa nasan san kaine kawai naki, sai yaushene zuciyarki zata gamsu da abinda take so? Sai na zama sarki? Ko sai kin ganki akan gangarar mutuwa?" Tace " Abdulmajid." Abdulmajid yace " kin rabani da Mahaifana, tunda nake ban taba kiran matar data reni cikina da sunan uwa ba, ban taba kyautata mata ba a matsayin wacce ta d'au cikina na wata tara ba......." Da karfi tace " YA ISA HAKA!" Turab ya runtse ido tare da cewa thanks Abdulmajid. Inalilahi wa ina ilaihi raji'un....... Ba shakka wannan kalaman sunfi tadawa kowa hankali, Hisham kam hawaye ne ya zubo masa, Turab Sarki ya kalla wanda gaba d'aya zuciyarsa tayi wani nauyi, kallan Abdulmajid kawai yake yana nanata kalamansa. Bilkisu ce ta daure ta kalli Abdulmajid cikin mamaki tace " kana nufin ba Umma Magajiya bace Mahaifiyarka? Ba kuma Sarki ne ya haifeka ba?" Gaba d'aya zubama Abdulmajid ido akai cikin mamaki. Khadija kam hawaye ne ke zubo mata, itakam Umman Khadija jitai hawayen ma sun kafe kaf sun kasa ma zubowa........ *TURAB* 🕊 *KAINUWA*🕊 ......... _Dashen Allah_ ( _*A Historical Fiction*_) *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *Wattpad :-AyusherMohd* Gaisuwa da fatan alkairi gareku masoyan littafin nan gabaki d'aya, ina godiya kwarai da kaunar da kuke ma littafin nan, nagode da hakuri dani na rashin posting akai akai da kuke, ni kaina ba hakan naso ba. Always love u....... *86* Wani irin ihu Magajiya ta saka da karfi tace " ABDULMAJID....." Mikewa tai a zuciye ta isa inda yake, ta d'aga hannu zata zabgamai mari, da sauri Turab ya tsaya a gabanta. Kallansa tai idanunta duk sun kada sunyi jaa, kallan juna suka shigayi, tana mai wani irin kallo wanda ba komai a ciki sai tsantsar kiyayya. Mai Martaba idanunsa a rufe kawai suke saboda jin abin yake kawai yana mai yawo akai. D'akin yayi tsit kowa da abinda yake sakawa a ransa, wani dogari ne ya shigo da gudu ya tsugunna, Barde ya kalleshi yace " lafiya kai kuma?" Cikin in in na yace " mai kula da kofar gidan mai martaba ne na cikin gari." Galadima yace " to ya akai?" Bakinsa ya shiga motsawa ya kasa magana, Basira tace " ya akai Hadi?" Da sauri ya ya maida kansa kasa ya sa kuka, Turab ya kalleshi ganin yanda yake kuka yasa Turab ya matsa daga gun magajiya ya taho inda yake yace " Hajiya......" Wani kuka dogarin ya saka, da sauri Sarki ya bud'e idanunsa wanda gaba d'aya sun yi jaa, mikewa yai yana kokarin takawa baya yai da sauri dogarawan dake bayansa suka tareshi, kallansu yai sannan ya kwace jikinsa ya koma ya zauna saboda jirin da yakeji, Dogarin yace " Allah yama Hajiya cikawa yanzun nan......" Inalilahi wa ina ilaihi raji'un......Abinda kowa dake d'akin ya shiga fada kenan, Banda Magajiya wacce take tsaye, sai Sarki wanda gaba d'aya yaji kansa ya kulle ya kasa tunanin komai. Turab ya karasa inda yake da sauri yace " Abba!" Idanunsa ya sauke akan Turab cikin tsananin tausayawa, ba shakka lalai bai cancanci mulkin nan ba, lalai laifinsa ne na kyale Magajiya tun farko ta dinga yin abinda taga dama. A hankali ya fara karanto inalilahi a ransa, kallan Turab yai sannan yace " jeka zauna." Turab ya mike ya koma gun xamansa. Gaba d'aya d'akin yayi tsit kowa ya koma gun zamansa, Sarki ya mike tsaye tare da zare rawanin kansa ya ajiye akan teburin dake gabansa, sannan ya tako a hankali har zuwa inda Magajiya take gaba d'aya kana kallanta kasan a tsorace take, kallan ta Sarki yai ya dade idanunsa na kanta sannan ya kalli Hisham, sannan ya maida dubansa kan Abdulmajid, haka yabi kowa da kallo d'aya bayan d'aya. Akan Barde ya tsaya yace " Barde jeka taho da gawar Hajiya." Nan barde ya mike. Sarki ya kalli Magajiya sannan yace " kafin in sallaci gawar Hajiya inkaita makwancinta inaso in sanar da abu d'aya kafin in yankema Matarnan hukunci, daga wannan lokacin na ajiye mukamin mulkin Masarautar Zazzau, sannan na d'aura d'ana Abu Turab a wannan matsayi, wannan matar a d'aureta da kaca itada d'an uwanta Waziri a rufaffen d'aki, sannan bazan yanke mata hukunci ba d'an da take neman ganin baya, wanda ta makantar dashi bayan neman ajalinsa, wanda ta ke neman halaka masa rayuwa a koda yaushe shine zai yanke mata hukunci da kansa, sannan na umarceshi da yanke mata hukunci mai tsaurin gaske." Ya juya ya fara takawa kallo d'aya zakamai kasan lalai yana cikin tashin hankali. Matan sarki ne suka mike suka bi bayansa. Sunje zasu fita daga kofar Magajiya cikin karaji tace " KAI ABDUSSALAMAD!" Gaba d'aya d'akin kowa juyowa yai ya kalleta tace " mene? Kaba Abu Turab mulki? Inji uban wa? Inji uban wa? Kana tunanin ni Magajiya zan yarda wannan dan tsinaniyar yahau mulki? Mafarki kukeyi daga kai har yan d'akin nan, indai har ni inada.........." Kasa karasawa tai jin muryarta ta sarke, duk yanda tai gun yin magana ta kasa, tsugunnawa tai da sauri tare da rike wuyanta, a hankali kowa na d'akin ya fita wannan abu yafi komau yi mata ciwo, balle tana kallan Abdulmajid Khadija ta turashi a kekensa sunyi gaba, ga magana ta tsaya cak. Masu tsaro ne sukazo inda take rike da kaca, Hisham aka fara sawa kaca, kallan Magajiya yai yace " Allah ya isa tsakanina dake, shawararki itace tasa zuciyata ta rikid'e gaba d'aya, sannan maganarki bazata taba d'aowa ba wannan rana itace rana ta karshe da kikai magana da bakinki, domin kuwa inbaki mantaba da gubar da kikasha danyima Basira sharri, a lokacin dana amshi wannan gubar dama ansanar da sharad'inta, bata fita duka a jiki sannan kar babba wanda ya wuce shekara 45 yasha wannan gubar sannan duk sanda ran wanda yasha gubar nan ya baci sosai to xata cigaba da mai illa ta cikin jikinsa, sannan idan tai nisa xata jawo kurmancewa, sannan zata nakasa gab'obin jiki." Kakari ta shiga yi idanunta kamar zasu fito, kirjinta ta shiga bugawa da karfin gaske, Hisham yace " kina tunanin duk abinda kikemin a banza?" Ya juya yai gaba. Durkushewa tai cikin tashin hankali tana rike da wuya, tana wani irin gurnanin gaske. Bayan sun fita ne daga d'akin Turab ya kalli Bilkisu yace " bari muje mu d'auko Hajiya." Kallansa tai cikin tsananin tausayawa sannan ta daure ta kakaro murmushi tace " to, bari inje gun Umma." Gun Abdulmajid taga ya nufa, ya kalli Khadija yace " kawoshi zamu gun jana'iza tunda anan za'ai." Khadija ta saki hannun kujerar data rike tana kallan Turab, bai ko kara kallanta ba ya tura Abdulmajid. Suna d'an matsawa kadan Abdulmajid dake hawaye yace " Turab ta yaya xan iya zuwa gun jana'izar Hajiya?" Turab yace " me kake nufi? Kai ba d'an Abba bane ko me?" Abdulmajid ya juyo ya kalli Turab idanunsa na kara zubar da hawaye, Turab ya kalleshi yace " meye hakan kuma?" Abdulmajid ya maida kansa kasa. Bilkisu ta kara kallan Khadija wacce ke tsaye kusa da Mahaifiyarta. Karasowa tai kusa dasu tace " ciki zaku shiga gun zaman makoki?" Umma ta kalleta da idanunta da suka kod'e tace " ta yaya zamu iya shiga ciki? Da wani idon zamu kallesu?" Khadija tace " mun gode da kulawa amma....." Bilkisu ta katseta tace " in kuna ganin hakan ne yadace ba matsala." Ta juya ta fara tafiya. Sai datai nisa sannan ta juyo ta kara kallen inda suke, can ta hangosu sunyi nisa. Juyawa tai ta nufi bangaren Umma. An d'auko Hajiya an mata wanka an mata sallah sannan an kaita gidanta. (Allah ya mana kyakyawan karshe Ameen suma Ameen) Ana gama jana'iza Abdulmajid ya kallu bawansa yace " mu fita." Turashi yai sukai waje. Motarsa ya sakashi sukai waje. Sai a sukai nisa akan titi sannan Ya juyo yace "ina zamu?" Idanunsa a rufe yace " ina zani? Ni kaina bansan inda zani ba, banida gun zuwa......" Hawayene suka kara zubomai. Yace kaini can bayan gari iska nake san sha, nan ya kara jan motar sukai gaba. Sunyi tafiya mai nisa kafin su fita can wajen gari. Sai daya gangara gefen titi wajen wata bishiyar darbejiya katuwa yace " nan yayi?" Abdulmajid ya kalli gun yace yayi. Nan ya fito dashi ya d'aurashi kan kekensa. Abdulmajid ya kalleshi yace " barni anan kai tafiyarka." Yace " Yarima....." Abdulmajid yace " ina san kasancewa ni kadai, sannan karka kara kirana da Yarima." Jiki a sanyaye ya kalli Abdulmajid sannan ya hau mota ya koma. Yana komawa gidan sarki gun Abu Turab ya nufa ya sanar dashi abinda ya faru. Turab wanda dama nemab Abdulmajid yake yace " kasan gidan Barde?" Yace "eh" Turab yace " kaje gidan kace Umma na naiman Mairo in ta fito ka kaita gun Abdulmajid a hanya ka ce mata injini nace Abdulmajid na cikin wani yanayi tai kokari ta taimaka ta dawo dashi nan." Yace to, Turab yace " ni ban isa fita ba cikin wannan yanayin." nan ya amsa da to yai waje. Gidan Barde ya nufa yai yanda Turab yace mai, a mota tana shiga ya sanar da ita sakon Turab. Gaba d'aya ta kagu su isa inda yake dan jitai gaba d'aya jikinta yayi sanyi, dan ta tabbata tunda taji Turab ya ce a sanar da ita haka to tabbas babban abu ya faru. Suna isa ta fito da sauri ko motar bata rufe ba ta taho inda yake da sauri. Daga dan nesa kadan ta tsaya tare da kuramai ido, kallanta shima yakeyi idanunsa na zubar da hawaye. Jitai idanunta sun ciciko, a hankali take takawa zuwa inda yake idanunsu nakan juna. Kusa dashi ta tsaya sannan a hankali tace " me kakeyi a nan?" Idanunsa ya rufe tare da kokarin shanye kukansa, tace " me kakeyi anan?" Kallanta yai sannan yace " Maryam ni ba d'an Abba na bane." Tace " mene?" Hawaye na zubomai yana dariyar takaici yace " iyayen da kike tunanin iyaye nane ba sune suka haifeni ba." Yanzu kam ta fahimceshi sai dai ta tabbatar inta nuna karayar ta to lalai batasan wani hali zai shiga ba, ta daure tace " to sai ka canza daga Abdulmajid dan ba sune iyayenka ba?" Ya kara cewa " yariman da nake tunanin ni yarima ne mai jiran gado ashe ni ba kowan kowa bane." Tace " dan kai ba yarima bane sai aka canza ka daga Abdulmajid?" Hawaye suka sake zubomai yace " wacce ta d'auki ciki na ta haifen ko sau d'aya ban taba girmamata ba da sunan uwar data haifeni." Yanzu kam sai da hawaye suka gangaro mata tace " Yanzu lokaci bai kure ba ai..." Yace " Maryam duk wata rayuwa da kika sani nawa ta karyace." Tace " hakan na nufin a karyar harda san da kake min?" Hannu yasa ya share hawayen yana girgiza kai, kara takowa tai wanda takun ya zama ta karasa daf dashi ta tsuguna inda yake sannan tace " then it's okay." Kallanta yai sam ya kasa magana, murmushi ta mai sannan tace " me yasa bakazo guna ba?" Yace " ta yaya zanzo bayan ina tsoron kiji abinda ke faruwa, da wani ido kike tunanin zan kalleki? Ga takurar da namiki a da, wanda nije sanadin hanaki auran wanda kike......" Hararsa tai tace " ka taba ganin wanda ya auri mijin wani? Duk aurab da kaga anyi a duniya to dama wannan auran Allah yayi sai anyishi, duk kuwa kiyayar dake tsakanin masoyan biyu, duk kuma inda kaga aure bai yiwu ba to lalai dama Allah baiyi za'ai wannan auran ba, duk kuwa da irin san da suke ma junansu." Yace " amma ai nasan kinasan Turab, inaji kamar nine sanadi..." Tace " ina sanshi kam, sai dai yanzu a wannan lokacin na tabbatar san da nakemai yana neman zama past tense." Kallanta yai, murmushi tai tace " Turab yace ka koma ai jana'iza dakai." Ta mike dan taji kunyar kalamanta ta rike keken zata tura. Kansa ya juyo saitinta yace " Maryam me kike nufi????" Harararsa tai tace " abinda nake nufi bansan ragon namiji." Kara kallanta yai yace " Maryam kina nufin......" Tace " tambayarka nai? Inka fahimci me nace sai ka had'iye a ranka." Bai san sanda wani lalausan murmushi ya bayyana a fuskarsa ba..... Magajiya kam an rufeta ruf a wani d'aki wanda yake dulum duhu gareshi sosai, an d'aureta cikin kaca, abinci sai dai a turo mata ta karasa ta d'auka taci. Gashi bata saba cin irin wannan abincin ba, ga ta da gardamar tsiya, gani take tafi karfin haka, kin cin abincin tai har dare. Wani irin ciwon ciki ne ya shiga murd'a mata, ga bata isa yin magana ba......... *TURAB* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *Nayi mistake wancan page din zan saka 87 na kara sa 86* *88* Gidan ya cika taf ana ta fama zuwa gaisuwa, Turab jefi jefi yake kallan Mahaifinsa wanda yake ta amsar gaisuwa daga manya manyan mutane, bayan anyi sallar la'asar ne Sarki Ya shiga d'akinsa tare da bada umarnin a kira masa Turab. Ya dade sosai baiyi magana ba kafin yace " wanene mahaifin Abdulmajid?" Turab ya kalleshi a sanyaye yace " Abba!" Sarki yai saurin cewa " su waye iyayensa?" Turab yace " d'an gidan Waziri ne." Kallansa Sarki yai yace " waziri?" Turab yai kasa da kansa. Idanu ya dan runtse kafin yace " Tun yaushe kasan maganar nan?" Turab ya d'ago yace " sanda na fahimci abinda sukama Hajiya, daga nan ne abubuwa dayawa suka fara bayyana." Shiru ne ya ratsa kafin Sarki yace " Allah kana ganin abinda ya sameni, kaine ka bani mulkin nan ba ni na ba kaina ba, saboda mulki an bani d'an da ba nawa ba a Matsayin nawa, sannan an halakamin matan da zasu haifar min, an kuma halakamun nawa jikin dan kar na haifa, sai dai duk da haka bazanyi fishi ba saboda ka bani wannan d'an da ke gabana, Allah ina rokanka daka karemin wannan yaran daga sharrin duk mai sharri ka kuma bashi ikon rike mulki da taimakon talakawa, ka bashi ikon yin hukunci na gaskiya ba san rai ba, ka karemin shi daga had'uwa da wanda zai nufeshi da sharri, Allah ina rokonka wannan yaran............." Kasa karasawa yai saboda muryarsa da yaji ta fara rawa. Duk dauriyar zuciya irin ta Turab sai da hawaye suka zubo masa,kallan Mahaifinsa yake cikin tsananin tausayawa, lalai yau Allah ne kadai yasan yanda bawan Allahn nan yake ji a ransa. Sarki ya kalleshi yace " Abu Turab." Nutsuwa Turab yai tare da tattara hankalinsa kan mahaifinsa dan ya fahimci magana mai mahimmanci yake san yi. Sarki ya cigaba " zan d'auki ragowar mata na uku zamu koma can wajen gari inda nai katan gidana, inaso daga anyi sadakar uku inyi murabus in baka mulkina sannan in tattara inbar gidan nan." Turab yace " Abba akan me zakayi murabus?" Sarki ya girgiza kai yace " kana tunanin bayan faruwar wannan al'amarin zan iya cigaba da zama akan mulkin nan?" " to me kayi? Duk ai laifin ba naka bane na Umma Magajiya ne." Sarki ya girgiza kai yace " Me kakeso ince? A matsayin na sarkin garin zazzau wanda ya kasa kula da matarsa? Ko a matsayina na sarkin garin wanda matarsa tafi karfinsa?" Turab ya motsa baki yana sanyin magana, sarki yace " na gama yanke hukuncina sannan umarnine daga Sarki bawai mahaifinka ba." Turab yai kasa dakai. Sarki yace " sannan Magajiya, Hisham da Matarsa, inaso kowa kamai hukunci dai dai da laifinsa, sannan kada ka kuskura ka sassautama d'aya daga cikinsu, wannan ma umarni ne." Turab ya kalleshi yace " Matar Waziri?" Sarki yace " kwarai, a matsayinta na uwa, akan me zata amince da abinda mijinta da kanwarsa suka tsara?banda itama tana san jininta yahau mulki?" Turab ya had'iyi wani abu tunowa dayai mahaifiyar Khadija ce. Sarki ya cigaba " sannan duk wanda suke da hannu akan al'amarin nan, da al'amarin Hajiya inaso ka hukunta kowa, shima umarni ne." Turab yace " to Ranka ya dade." Sarki yace " Abdulmajid......." Sai kuma yai shiru dan baisan me zai ce ba, Turab ya kalleshi yace " Abba, me zai hana mu bar maganar matsayin Abdulmajid a junan mu?" Kallansa Sarki yai yace " mene?" Turab yace " Abba wace rayuwa Abdulmajid zaiyi in har akasan asalin abinda ya faru dashi?" Sarki yai shiru. Turab yace " Abba idan muka duba wannan lamari wanda akafi cuta ba kowa bane sai Abdulmajid, gaba d'aya shine aka ruguzawa rayuwa, sannan shine wanda za'afi tausayama." Sarki yace " Abdulmajid ni kaina bazanso akan laifin da banasa ba ya shiga garari na rayuwa ba, amma kana tunanin hakan zai yiwu?" Turab yace " a lokacin da akai maganar nan akwai mutane dayawa, sannan shi sirri duk yanda akaso da b'oyeshi in har akwai mutanen da suka sani to fa ba wani abu da za'a iya yi, ina tunanin mai zai hana tunda yanada ilimi sannan yanada babbayar hanya na matsayinsa na d'an Sarki a nemar masa aiki babba na gomnati yabar garin nan, yanda baya kusa ma balle gulma a dameshi, sannan yanada matsayin da ko asiri ya tuno ba abinda zai sameshi." Sarki kallansa kawai yake cikin jin dadi, yace " lalai Kai Kainuwa ne, dashe ne wanda Allah yai, ba shakka kasata xataji dadin mulkin ka." Turab ya sunkuyar da kai cikin jin kunya. Sarki yace " ni kuma zan kwabi duk wanda ke d'akin sannan ni zan sa a bashi aikin ba sai ka wahala ba." Turab yace " Godiya nake, amma Abba mai zai hana ka cigaba da zama anan ko dan shawara da nunamin hanya?" Sarki ya girgiza kai yace " Turab kasan me yasa ake kishi, gaba, tsana, sharri da mugunta akan mulki?" Turab ya gurgiza kai cikin rashin fahimta, Sarki yace " saboda duk wanda ya d'and'ani mulki sai yayi da gaske zai iya yageshi daga ransa. Mulki abu ne mai dadi wanda a hankali yake halaka zuciya, idan na zauna anan to lalai zuciyoyinmu sasu dinga samun sab'ani, wannan dalilin ne yasa kaga ba'a fiya yin murabus a mulki ba, har sai rai yayi halinsa." Turab yai shiru baice komai ba, Sarki yace " ka sa a sanar da matan nawa hukunci na." Turab yace " To Abba." Sarki ya mike ya shiga band'aki. Nan Turab ya taso. ******** A can wajen gari kuwa bayan sun shiga mota ita da Abdulmajid, habu na waje a tsaye ta kalleshi tace " Turab yace amaidakai gun zaman makoki." Yace " Maryam wai ta ina zan iya zama agun?" Tace " Dama shakuwa ta d'a da mahaifi bata shiga sai jini ya ratsa?" Kallanta yai baice komai ba, tace " ka taba ji ance d'a da uba ko d'a da uwa sun hadu amma basu san juna ba?" Yace " eh in rabuwa ta hada iyayensu ko aka tsinci yaran." Tace " Shi shakuwa da kauna tana shiga zuciyoyi ne basai jini ya ratsa ba, na tabbata Sarki a zuciyarsa kana nan a matsayin d'ansa, sannan kaima na san yanda kake kaunar Sarki a matsyin mahaifi bazai canza ba." Murmushi ya mata yace " lalai zuciyata tana cikin kunci sai dai wani bangaren yana cikin tsananin farinciki, dan inaji inhar kina tare dani ba bakin cikin da bazan iya shanyewa ba, sannan duk wani tashin hankali inaji indake to lalai komai zaizomin da sauki." Harararsa tai tace " a hakan? Kana kukan?" Yace " ai samun nutsuwa danai ne ya sani kukan." Ta kara harararsa tace " Gaskiya Abdulmajid kai dan yaudara ne." Yace " ban gane ba." Ta hade rai tace " inba haka ba ya akai kasan kalaman da zasu sa mace tai sanyi?" Dariya yai yace " inhar kalamai nane suka saki yin sanyi lalai ban yarda ba, dan kuwa na tabbatar da tuni kin amince dani." Hade rai tai tace " amma ai kasan nasan tarihinka da ko?" Yace " Maryam wallahi ai na rantse miki ban taba sanin wata 'ya mace ba, na dai yarda da nayi lalata na taba mace wanda nake dana sani sosai, sai dai Allah bai taba bani damar lalata da wata ba." Kallansa tai tace " me yasa to in aka ce kanayi baka musawa?" Yace " Ince me to?" Tace " yanzu fa kana tunanin bazaka sake ba?" Da sauri yace " Maryam baki yarda da irin san da nake miki bane?" Had'e rai ta sake yi tare da gard'e hannayenta tace " inafa nake da tabbas, abu na d'a namiji?" Yace " Maryam wallahi........" Sai kuma ya kalleta yace "Wait...Maryam kina nufin kin amince dani a matsayin abokin rayuwarki kenan?" Baki ta tabe tace " hmmm waya sani?" Wani lallausan murmushi ne ya bayyana a fuskarsa yana mata kallan tsantsar so wanda ba algus a ciki. Mairo ta kalleshi tace " yanzu zan maidakai gida kai zaman makoki." Kai ya d'aga kawai yana murmushi, tace " tambaya biyu zan maka, Waziri shine mahaifinka?" Abdulmajid ya d'aga kai tare da kallan window, tai murmushi yake, tace " Mai zakayi idan Babana ya hanani kai?" Yace " Zanyi iya kokarina wajen ganin ya aminta dani." Tace " shikenan." Murmushi sukama juna, sai da aka fara ajiyeshi ta tabbatar Habu ya kaishi gun zaman makoki sannan ta shiga gun Umma. Tana shiga Gimbiya na kokarin fita, Mairo ta bita da kallo, kafin ma acemata jikinta ya bata itace, saboda yanayin shigarta. Tace " Gimbiya Barka da warhaka." Bilkisu ta juyo ta kalleta tace " Barka da warhaka." Sannan tace " ban gane ba...." Mairo tace " Yar gidan Barde ce." Bilkisu tai murmushi, zatai magana Lantana tace "Mairo kin iso?" Mairo ta gaisheta sannan tace " Umma fa?" Lantana tace " tana ciki." Mairo ta kalli Gimbiya tace " Zan shiga ciki." Bilkisu tace " inkin fito zaki shigo?" Mairo ta kalleta tace " zanzo, dama inatasan inga Matar Ya Turab, sai yanzu Allah yai, amma zanzo." Bilkisu ta murmusa sannan tai gaba, da alama akwai shakuwa tsakaninta da Umma da kuma Turab. Mairo ta bi bayanta da kallo, a ranta tace " Allah mai baiwa, gaskita tanada kyau, dan zata iya cewa tunda Allah ya halliceta bata taba ganin mace mai kyau irin na Bilkisu ba, duk da wani bangaren na zuciyarta na dan kishi saboda shi so ba farat d'aya yake fita gaba d'aya ba indai har san na gaskiya ne." ************** Bayan ta gaida Umma kuwa ta nufi bangaren Gimbiya, Bilkisu har tayi wanka lokacin ta canza kaya, aka sanar da ita zuwan Mairo. Fitowa tai taganta a zaune akan kujera, kusa da ita bilkisu ta zauna. Mairo ta kalleta tace " Da har ina tunanin guduwa, ganin bansan mai zance miki ba in muka hadu." Bilkisu tace " tunda nazo garin nan banida kowa sai mutanen gidan nan, shiyasa ganinki yasa naga kamar na samu wata." Mairo tai murmushi tace " ga Ya Turab ba koda yaushe yake nan ba." Bilkisu tace " sosai." Murmushi sukama Juna. Bilkisu tace " tun yaushe kikasan shi?" "Ya Turab?" Tace " eh." Mairo tace " tun muna yara na dawo daga makaranta da gudu..............." Nan ta bata labarin haduwarsu da abinda ta dingamai na tsokana ganin baya gani..... Sosai Bilkisu take dariya tace " lalai kinyu kiriniya." Mairo tace " hmmm ai a aji shi kullum yana zaune shiru dama Khadija ce..........." Da sauri ta gumtse bakinta sannan ta wayance tace " Abdulmajid ne ma....." Bilkisu ce ta katseta tace " kinsan Khadija ne?" Mairo ta kalleta da sauri tace " Naam?" *TURAB* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* * SECOND TO D LAST PAGE* *89* Bilkisu tace " Mairo menene tsakanin shi da Khadija?" Mairo tace " menene kuwa, zumunci ne na ya da kanwa kamar ni." Bilkisu ta kura mata ido, da sauri Mairo ta mike tace " bari naje gida naga yamma tayi." Kafin Bilkisu tai magana tayi wuf tayi waje. ""*******"""" Gimbiya ta dade a zaune tana tunani kafin ta mike ta shiga d'aki, tana shiga ya turo kofar tare da sallama. Juyowa tai ta kalleshi tare da amsamai. Karasowa yai inda take kawai sai jitai ya rungumeta tsam a jikinsa a hankali yake fitar da wani numfashi, murmushi tai sannan tasa hannu ta shafi bayansa tace " Weldone dear." Sun dade makale da juna kafin ya d'ago tare da rike kafad'unta yana kallanta. Wani sansanyan murmushi tamai tace " ya akai?" Yace " jikinkinfa?" Tace " na ware, sai kadan" Ya kara rungumeta yace " Sannu, yau nasan kinsha wahala." Tace "kaine kasha wahala, ni me nai? Ya hakurin mu? Ni ko ganin Hajiyar ban taba yi ba,Allah bai nufa ba." Yace " Hajiya ta girma sosai wanda kowa yake mata tunanin mutuwa, sannan dan rashin imani matar nan ta nemi halaka mata rayuwa ba tare da tayi duba da tsufanta ba." Bilkisu tai shiru, jiki a sanyaye. D'agowa yai tare da kama hannunta suka zauna a bakin gado, kwanciya yai tare da d'aura kansa akan cinyarta yana kallanta yace " Kinji abubuwa na tashin hankali da mamaki yau ko?" Hannunta tasa akan sumarsa tace " a'a, ni duk abinda ya faru abu d'aya yafi tadamin hankali, ganinka danai cikin wani yanayi kana neman fita hayyacinka." Yace " abinda Magajiya tai fa?" Tace "Magajiya? Hmm ko kad'an ban tsorata da ita ba saboda na tabbatar in har hankalinka da ta nemi gusarwa ya dawo to tabbas komai zai daidaita, sannan zaka juya kan akalar muguntar da ta shirya." Murmushi ya mata sannan yace " Thanks alot for believing in me." Tace " nima Thanka alot." Yace " ke kuma for me?" Tace " bakasan abinda yafi komai min dadi ba?" Yace "a'a" Tace " yanda nima ka yarda dani kake kuma sanar dani damuwarka." Murmushi ya mata yace " ni kaina har yanzu ina mamakin yanda ke kadai zuciyata ke iya bod'ewa damuwarta." Tace " ina rokon zuciyarka da ta kara sanar dani d'amuwa d'aya da na ke san ji." Kallanta yai yace " name kenan?" Kallansa tai sannan tai kasa da idanunta a hankali ta furta Khadija!" Kallanta yai sannan ya mike daga kan cinyarta ya zauna yace " Khadija?" Juyowa tai ta kalli kwayar idanunsa. Mikewa yai hannu tasa ta riko hannunsa da sauri tace " Yarima." Tsayawa yai sai dai bai juyo ba, tace " inada tsananin kishi hakan ne yasa nakesan na auri wanda yake sona sosai, sai dai duba da yanayin gidan dana fito nasan tabbas Mahaifina bazai bada ni ba sai ga wani mai matsayi na sarauta, sannan nasan Sarki bazai taba zama da mace 'aya ba, in har ka b'oyemin tsakaninku shine zai sani jin ba dadi a raina bawai shirunka ba." Turab ya juyo ya kalleta sannan ya sakar mata murmushi yace " Later, zan sanar dake komai amma ba yanzu ba, banasan wani abu ya shiga zuciyarki a wannan lokacin, zan sanar dake in har kika sake tambayata, sai dai ba wannan lokacin ba." Murmushi tai tace " nagode sosai." Kusa da ita ya matso ya rikota jikinta. Sai da sukai sallar isha'i sannanya sanar da ita hukunci sarki da kuma abinda suka yanke akan Abdulmajid sosai ta yaba da shawarar da suka yanke. A ranar uku kuwa Mai Martaba Sarki ya tattara mutane ya sanar dasu hukuncinsa, sannan dama ya riga ya hana mutanen dake d'akin zancen Abdulmajid. A lokacin ne aka nad'a Abu Turab a matsayin Sarkin garin Zazzau. Kasancewar anyi rasuwa a gidan yasa ba'ai wani taro ba na biki a gidan Sarautar ba. Turab na hawa kan mulki Sarki yace " kafin na bar gidan nan inaso ka yankema mutanen da ya kamata su amshi hukuncinsu a hannunsu." Turab yace a fito da masu laifi su gurfana. Abdulmajid na zaune jin ance a fito dasu yasa jikinsa yai wani irin sanyi. Turab yace " a fara shigo da matar nan data mai sharrin fyade, dannan wacce take sama Sarki magani da kuma wacce take sama Hajiya, dan dama a kwanakin nan duk sai da aka kamosu." Turab ya kalli Matar data mai sharri yace " duba da yanayin laifinki an yanke miki hukunci yin aiki a gidan nan, aiki na karfi na jiki na shekara biyu ba tare da an biyata komai ba." Sannan ya kalli Sarki, murmushi mai martaba yai hakan yasa ya gane hukuncin yayi. Turab ya kalli Matar da take sama Sarki magani. Yace " kin aikata babban laifi na sa magani ga Mai Martaba, duk da bakisan maganin menene ba kinyi laifi na sakawa, sai dai rubutama Hajiya da kikai yasa za'a miki sassauci ke kuma zakiyu aiki kema na shekara uku ba tare da biya ba." Sannan ya kalli matar da itace shaida a garesu yace " kema kinyi kuskuren sawa Hajiya magani duk kuwa da anyi amfani da rashin lafiyar kaninki gun umartarki da yin wannan aiki sannan kin kula da Hajiya kin kuma bada shaida akan abinda aka saki kika aikata hakan ne yasa za'a kaiki asibitin Abu inda kaninki yake dan yin aiki acan na karfi na shekara d'aya." (In akacema Mace aikin karfi ina nufin, girki, wanki, wanke wanke, wanke band'aki, surfe, daka, sisika da sauransu.) Shigowa akai da Jakadiya, kallabta yai sannan yace " Jakadiya kinsan laifin ki?" Jakadiya ta sunkuyar da kai. Turab yace " laifin sani tare da takewa, sannan laifin amfani da wannan sanin dan cikar burinki, na cireki daga matsayinki na babbar jakadiya a wannan gida, sannan zaki bar gidan nan batare da kin d'auki komai ba, ki koma kauyenku ki zauna." Jakadiya kam jitai kamar tasa kuka dan tabbas tana cikin garari. Hisham aka shigo da shi. Turab ya kalleta sannan yai shiru, can yace "Waziri da farko dai daga wannan lokacin na cireka daga matsayinka na waziri sannan kai namiji ne wanda yake uba yake kuma da mutane a karkashinsa, sai dai bakai amfani da wannan matsayin da kake dashi ba, ka kashe mutane biyu a daura, wanda shikadai ya isheka karasa rayuwa a gidan yari, ka biyewa Magajiya kunyi ta tafka laififuka wanda bazasu irgu ba, hakan ne yasa za'a maidakai gidan yari ka karasa rayuwarka acan wato d'aurin rai da rai." Hisham ya runtse idanunsa hawaye suka shiga zubomai, mai rayuwar nan ta dada mai? Kallan Abdulmajid yai wanda yai saurin d'auke kansa tare da juya kansa gefe dan yanaji wani abu na ratsashi. Hisham yai murmushi tare da rusunawa yace " ina godiya da alfarmar dakama abinda na haifa, ina kuma rokon ka daka taimaka ka sassautawa matata ko dan kula da zuri'a ta." Turab yace " a d'aukeshi." Nan akai waje dashi yana kallan Abdulmajid. Anje fita dashi ana kokarin shigo da Magajiya. Gaba d'aya ta canza tana ganinshi tahau kakari alamar masifa, duk ta rame, ga wani azababban ciwon ciki da take kwana dashi kullum. Ana shigo da ita aka fara gulmace gulmace. Kalan kallo suka fara da ita, wani irin kakari take tana neman kwacewa ganin Turab akan kujerar mulki, sai wani kakari takeyi Tana girgiza kai ba kakkautawa. Turab ya kalleta duk ta canza, nan aka tad'iye kafarta aka gurfanar da ita, Turab ya kalleta yace " Rashin godiya ga abinda Allah ya maka, rashin sanin darajar mutum, d'aukar rayuwar d'an adam kamar kaice kika bashi, halaka duk wani abu da yake neman kawo miki cikas a rayuwa, san zuciya da tsantsar san kan da kike dashi, laifufukan da kika aikata banaji zasu irgu, wayasan tun wani lokacin kike aikata laifufuka? Ba imani ko kadan a ranki. Sannan a wannan lokacin ma banaji zuciyarki tana dana sanin laifufukan data aikata, na tabbatar da za'a baki wuka to tabbas zaki nemi kawar da abinda bakyasan ganin a fadar nan." Turab ya kalli Sarki wanda kallanta kawai yakeyi, Turab yace " Ina rokon Takawa da ya hukunta wannan matar, dan kuwa kai ta cutar cutarwa ta ruwan sanyi wacce tafi ciwo." Sarki ya kalleshi sannan ya kalleta yace " abinda nake jira kenan, abin kuma da ya tsayar dani kenan, jira nake naga yanda matar nan zatai in zata wanda ta tsana a duniya zai yanke mata hukunci, sai dai inaso tasan abu d'aya a cikin mutanen nan, ni Abdussamad na yanke igiyar aurena da Magajiya, na yanke duk igiya ukun dake kanta." Wani irin gurnani ta shiga yi. Turab ya kalle ta sannan ya kalli Abdulmajid. Magajiya ta shiga kokarin mekewa cikin tsananin tashin hankali, Turab ua runtse ido, a hankali muguntar Magajiya da tsantsar rashin imaninta ya dinga dawomai a zuciyarsa, tabbas ko gidan yari bata cancanta ba, a kalla acan za'a bata abinci zakuma a bata gurin kwana. Gyaran murya yai sannan yace " Magajiya, daga wannan lokacin an saukeki daga matsayinki, sannan zakibar gidan nan ba tare da komau ba sai kayan jikinki, zan sanar a garin nan akan kar wanda ya kuskura ya bata muhallin zama, wannan umarni ne daga gun Sarki, abinda ya dace da ita shine ta shiga gari taga yanda mutane suke, taga yanda marasa muhalli suke rayuwa, yanda mahaukata suke rayuwarsa, su wad'an nan ba wai tsanarsu Allah yai ba ya gusar musu da hankali, a'a wasu kaddara ce ta Allah wasu kuwa irinku ne wad'anda suka haukatasu, kije kiga yanda ake rayuwa, kije kiga yanda abinci yake samuwa da tsananin wuya, wannan shine abinda ya dace dake, kije kiyi rayuwa wacce yan uwanki basu isa sun taimaka miki ba, in kikai irin wannan rayuwar ta shekara biyar daidai lokacin kin manyanta da yawa, sai a dawo dake gidan yari ki karasa rayuwarki acan." Kakari take yi har muryarta ta kakari na neman d'aukewa, wani irin karfi take badawa kamar zata kamo Turab agun nan, yanda kasan mahaukaciya sabuwar kamu. Nan akai waje da ita kakari take kamar zata ciro ranta........ *Turab* *KAINUWA*🕊 ......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_ ( _*A Historical Fiction*_) *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝* *Wattpad :-AyusherMohd* *ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀* *LAST PAGE* *90* Yanda aka fito da Magajiya sai kallanta akeyi, kan kace me an cika ana zuwa kallanta labari duk ya baza akan maganin da take ba Sarki na hana haihuwa, sannan maganin da ta sama Hajiya dan kasheta, nan fa kowa ya fara tofa nashi albarkacin bakin. Ana fitar da ita waje a ka tsaya da ita dan jiran umarnin daga sarki na asaketa. Tahowa yai gadan gadan rike da wani makeken katako yayo kansu, kallo daya zakamai kaga bigegen d'am shaye shaye, dogarawan dake tsaye kanta kuwa suna ganin haka suka fyalla da gudu, yanda taga yayo kanta tasan tabbas sai ya maka mata, da sauri tai kasa ta tsugunna, yana karasowa kuwa ya d'aga katakon nan ya maka mata a gadan bayanta. Ga ba baki bare ta calla kara, wani irin zakwadi na zafi ta shiga yi sai juye juye takeyi dan yauce rana ta farko da zatace a rayuwarta an mata irin wannan dukan, tsugunnowa yai inda take ya nuna ta da yatsa yace " menene damuwarki da Basira? ai na tambayi wanda ya kawoni garin nan bayan na karyamai Kafa akan wanda yasa aka kawoni shine yamin kwatance sannan naji labarin an kamaki, yau za'a yanke miki hukunci, yanzu nan da kika ganni gidan Sarkin nazo shiga kota wani hali ne dan sai naje gunki, sai naji ana cewa Magajiya, dan kut............. Dama amfani kikesan yi dani gun muzguna mata?" Ya kara d'aga katakon zai mazga mata, da sauri ta rike kafafunsa dan ta tabbatar inya kara maka mata to fa lalai sai bayanta ya karye. Da karfi ya fizge kafarfa sai gata a kasa ta fadi yace " kinsan masifar dana shiga bayan na mata fyaden, sam rayuwata lalacewa tai, banda shaye shaye banida aikin yi, kowa nawa ya gujeni, sannan kike kokarin jefani cikin masifa?" Ina Magajiya ba bakin magana ga magana a ranta yana cinta, hannayenta ta hada tana bashi hakuri. Yatsa ya nuna mata sannan yai kwafa. A zuciye ya juya yai gaba, Magajiya sai ji tai hawaye ya zubo mata, da sauri tasa hannunta ta tabo hawayen cikin tsananin mamaki, yau itace take kuka? Ita Magajiya? ************* A can fada kuwa Abu Turab ana fita da ita yace " Bazan maida sarautar Waziri gidan Hisham ba, sai dai zan nba babban dansa namiji wato Salihu wani mukami wanda bai kai Waziri ba." Sannan magana ta karshe inaso kowa ya cigaba da girmama yayana Abdulmajid da bashi matsayinsa, banaso gulma akan Mahaifiyarsa ya shafeshi dan bazan yafema duk wanda aka kawo kararsa ba akan hakan." Kallan juna sukai shida Abdulmajid, da sauri Abdulmajid ya maida kansa kasa yana tuno abubuwan da ya aikatama Turab a baya, lalai duniya abar tsoroce in ka bari santa ya shigeka to lalai kana cikin garari na rayuwa. Sarki yana ganin haka yace " Alhamdulila komai yazo karshe, ina maka fatan alkairi ina fatan ku nacikin d'akin nan zaku bashi had'in kai kamar yanda ya kamata." Galadima yace " Masha Allah, ba shakka komai yayi daidai, sai dai nima ina neman alfarma daga wannan lokacin inaso in ba wa Sabi'u mukamin mulkina na Galadima, ni dakai tare muka fara, haka kuma tare zamu gama, suma sai su fara a tare." Sarki yai murmushi yace " Allah ya tayasu riko ya kuma kare mana su." Nan akace Ameen. Haka taro ya tashi, sai da mutane sukagama fita, Abdulmajid na kokarin fita Abu Turab yasa acemai ya sameshi a cikin falon Sarki wanda yake ta cikin fadar. Nan Habu ya turashi zuwa falon. Abu Turab na zaune a kasa, Sarki na kan kujera aka shigo da Abdulmajid. Shiru ne yad'an ratsa falan kafin Sarki yai gyaran murya yace " Abdulmajid!" Yace " Naam Ab......" Sai kuma yai shiru, Sarki ya kalleshi sannan yace " Abu Turab!" Turab yace " Naam Abba." Sarki kallesu sannan yace "Abdulmajid mun yanke shawara nida Turab akan lamarinka, hakan ne yasa muka nemar maka aiki, Alhamdulila duba da matsayina da iliminka yasa ba'a sha wahala ba, dan an tabbatar min a wannan satin mai shiga komai zai kamala, anan cikin garin kaduna zaka fara aiki ba sai kayi nisa da gida ba." Abdulmajid jiyai idanunsa sun ciciko yace " Na gode Allah ya saka da alkairi." yana karasa maganar hawaye na zubomai. Sarki ya kalleshi yace " yanda kake da na matsayin d'a a gurina yanzu ma baka canza ba, sannan inaso in sanar maka har cikin raina a matsayin d'a kake a gurina har abada kuma bazan yada kai ba, sai dai ina fatan zaka cigaba da rayuwa kamar yanda kakeyi yanzu, rayuwa mai tattare da nutsuwa da kuma girmama mutane, tare da bin dokokin Allah." Abdulmajid yace " insha Allah." Sarki ya kalli Turab yace " inaso ku hada kanku, duk da ba a kusa kuke ba inaso ku rike zumuncin dake tsakaninku, Abu Turab mulki da kake gani yana tattare da jin dadi, samun babban matsayi da farin ciki na dayuwa sai dai wannan duba ne na mutanen da basa kan mulkin, kai da kake kan mulkin a hankali zaka fahimci rashin jin dadinsa, wanda mutane bazasu taba ganin haka ba." Sarki ya numfasa yace " sannan kace akwai abinda zaka fad'amin, menene?" Turab ya kalli Abdulmajid sannan yace " dama Abba maganar auran Yaya Abdulmajid ne." Da sauri Abdulmajid ya kalleshi yace "Yaya?" Sarki ma kallan mamaki yamai sai dai daga baya yai murmushi yace " Yaya? Hakan yayi kyau, ai da dadi mutum ya samu wanda zai kira da yaya." Turab yace " akwai wace yakeso,itama ta sanarmin tana sanshi." Sarki yace "Yar gidan Barde?" Turab yace ya akai ka sani? Sarki yai dariya yace " yanzu Turab kaf gidan nan waye bai san sanda yaran nan yakema Mairo ba? Bayan har fada yazo ya fada saboda rashin kara?" Abdulmajid jiyai kamar kasa ta tsage ya shige saboda tsananin kunya. Sarki yace " Tunda auran d'ana ne nine zanje neman auran, karka damu kaidai ka kula da abubuwan masarauta da kukan mutane, ni zan kula da Abdulmajid." Turab yace " godiya muke." Abdulmajid, kokarin mikewa ya shiga yi daga kan kujera dan taugunnawa, Sarki yace " bari mana karkaji ciwo." Abdulmajid yace " Abba bansan ta ina zan fara bane." Sarki yace " ba sai ka fara ta ko ina ba, ni dai ka zama mutum na gari wannan shine burina." Turab yace " Abdulmajid akwai sauran hukunci d'aya da bansanar a fada ba wato hukunci Matar Waziri." Abdulmajid ya kalleshi. Turab yace " na aika da takardar hukuncin ta gida saboda banasan asan matsayin laifinta." Abdulmajid ya kalleshi sannan yace " ina tayaka murna Turab hakika ba wanda ya dace da wannan mukami na sarautar garin nan sai kai, nayi mamaki kwarai da abubuwan da suka dinga faruwa, lalai kai namiji ne, kaine kadai kuma Magajiya take tsoro a fadin duniyan nan, sannan hukuncin daka yanke ma kowa yayi daidai, Umman Khadija kuna ba sai na tambaya ba dan nasan bazaka yanke mata hukuncin da ya wuce laifinta ba, sai dai kayi mantuwa baka yanke min nawa hukuncin ba, dan kuwa nima na biyewa Magajiya, na kuma wahalar dakai kana yaro." Turab ya kalleshi yace " wani hukunci kake nema banda wanda aka maka? Ka duka nan an maka wanda haryanzu ba ka tafiya? Kamin abubuwa a baya, sannan bazan boyema ba a baya ko had'uwa banasan muyi, sai dai ahankali ka wanke duk laifin da ka aikata mana, sai tausayinka da mukeji yanzu a zuciyoyin mu." Abdulmajid yai shiru.... Turab yace " Umma na yanke mata hukunci na zama a cikin gidanta tare da kula da 'ya'yanta, ban yarda ta fito wajen gidan ta ba sai da kwakwaran dalili, sannan ko da wasa naji ance yaran gidan yayi laifi to fa lalai wannan hukuncin ita zanyimawa, wannan shine hukuncinta." Abdulmajid yace " nagode kwarai Turab, nagode sosai....." Sarki yai murmushi yace "Allah ya kara hada kanku." Nace Amin...... ********* Sarki sun tattara sun koma gidansu, Umma kam ta kara yima Bilkisu nasiha sosai, sannan ta kara bata labarin tashin hankalin da suka fuskanta a baya, tundaga cikinsa, nan ta bata amanar Turab tace " ga Amanar d'an ta nan tanaso ta kukar mata dashi." Bilkisu kam jikinta ya yi sanyi, jin gwagwar mayar wahalar da Turab ya shiga yasa ta kara jin wani sansa da tausayinsa na kara ratsata, ta kuma d'au damarar taimakamai da kula dashi har karshen rayuwarta. Haka aka rakasu mota suka tafi. Kwanasu biyu da tafiya Sarki ya d'auko Galadima sukaje gidan Barde. Yayi mamakin ganinsu, nan aka kawo musu abinsha, aai da sukai hira sannan yace " dama yazo ne akan maganar auran Mairo da dansa Abdulmajid." Barde yace " Abdulmajid?" Sarki yace kwarai, domin kuwa d'ana ne ada sannan d'ana ne a yanzu. Wannan kalma ta sa Barde bai iya cewa komai ba sai cewa yai " ai 'ya'yana 'yayanka ne, kanada hakkin aurar dasu ga duk wanda kaso, ba tare da ka tambayeni ba." Nan aka bada kudin gaisuwa tare da amincewa. Mairo ana d'aki dama tunda taji sunzo tasan mai ya kawosu dan dama Abdulmajid ya sanar da ita yanda sukai da Sarki. *********** *Bayan Shekara D'aya* Idanunsa ya bud'e a hankali tare da kallanta, baccin ta take sosai murmushi yai tare da kokarin zare hannunsa. Sa hannunta tai ta rike hannun tare da kara gyara kanta, a hankali yace " Princess idanki biyu?" Kai ta girgiza alamar a'a. Ya sake murmushi yace " ba idanki biyu ba amma kike magana?" Kai ta d'aga mai alamar eh. Yace " so nake in duba wasu takardu da aka kawomin jiya, sannan kinsan gobe zamuyi baki daga kasar America zasu shigo garin." Idanunta ta bud'e ta kalleshi tace " Kullum fa baka kwanciya da wuri sannan da wuri kake tashi, baka tunanin babyn ka na san jin diminka?" Jawota yai jikinsa sannan yasa hannu kan cikinta yace " in mace ce nasan zatawa mahaifinta uzuri dan tasan ba laifinsa bane, in namiji ne kuwa dama dolene yamin uzuri tunda dai lokaci ne zai juyo kansa." Kallansa tai tare da dan harararsa na wasa, murmushi yai sannan yace " zan duba takardun na awa biyu kafin nan kin kara samun bacci sai muyi hira ta awa biyu, sai in fita fada, hakan ya wanke laifina?" Tace " ya wanke kadan." ta karasa maganar tare da nuna karamin d'an yatsanta. Mikewa yai ita kuma ta gyaamra kwanciyarta tana kallansa, kan carpet ya zauna inda karamin tebirinsa yake ya shiga duba takardu. Tunowa tai da abinda ya faru shekaranjiya. An turoma Turab wasikar hada aure tsakaninsa da masarautar Bauchi, jin hakan ne yasa ta tambaya akan Khadija. Jitai ancemata ai Khadija tana nan agida, saurayin dake santa Saifullahi duk yanda yai taki amincewa dashi, ita tace zama zatai suyi hukuncin mahaifiyarta tare dan laifin iyayenta nata ne, jin wannan maganar ne yasa Bilkisu ta tabbatar da hankalin Khadija kuma tabbas dolene yau ta tuntubeshi da maganar. Tana wannan tunani bacci yai gaba da ita...... Awa biyun na cika ya kalli agoggo sannan ya mike yai wanka, yana fitowa daga toilet ita kuma tana bud'e idanunta. Kallan sa tai sannan ta kalli agoggo a hankali ta sakar mai wani murmushi, sannan ta mike tare da saukowa daga kan gado. Towel ta d'auka ta cire kayan jikinta ta d'aura. Yana tsaye yana kallanta, tana kokarin yin hanyar toilet ya sa hannu ya jawota jikinsa, d'agowa tai ta mai wani murmushi bakinsa ya saka a cikin nata.............. Sai da sukai wanka suna zaune akan kujera tana tayashi duba wasu takardu, ta kalleshi tace " in na tambayi labarin Khadija yanzu za'a sanar dani?" Kallanta yai sannan yace " me kike san ji game da ita?" Tace " ko mai." Murmushi ya mata sannan yace " in kika ji haushi fa?" Tace " hmmm nasan zanji haushi sai dai ba kamar da ba, a da banida hujjar amincewa akan inada wani matsayi a zuciyarka, sai dai yanzu nasan ko ya ya ne akwai ni a ranka, bazan nemi hada matsayin san da kakemin ba da wanda kake mata, sai dai zanyi kokarin fahimtar girma da darajjarta a gunka." Murmushi yai sannan yace " kamar yanda kika sani sunanta Khadija............" haka ya kwashe labarinsu da Khadija da irin rabuwar da sukai. Kallansa tai, gaba d'aya yanayinsa ya canza ba shakka itace First Love dinsa, sannan san da yake mata mai zafi ne, duk da dai yana kokarin b'oyewa sai dai yau ta fahimci dalilun da yasa yake san yarinyar dan tabbas labarinsu mai ban tausayine, ta kuma fahimci dalilin rabuwarsu. Kallansa tai tace " saboda laifin iyayenta ka hakura da auranta? Abdulmajid yana can da matar da yakeso suna rayuwarsu ita akan me bazata samu farin ciki ba?" Yace " me kikeso mu sanar ma 'ya'yan da zamu haifa tsakaninmu?" Tace " Baka ganin bakuyi wa kanku adalci ba? Sannan shi aure rabone in har Khadija matarka ce to tabbas sai ka aureta ko ta wani hali ne." Kura mata ido yai yana kallo kafin yace " Princess." Tace " Kada ka nemi bijerewa ikon Allah, ni zan sanar ma Abba sannan za'a tura neman auranta, sai a d'aura auren tare da kanwar sarkin Bauchi, in har matarka ce zakaga abin ya faru in har ba matarka bace saikaga an warware cikin ruwan sanyi." Turab ya kalleta sannan yai murmushi zaiyi magana tace " Please!" Kasa magana yai sai jawota jikinsa dayai...... ********** Ajiyar zuciya yai cikin sakalci yace " Maryam ni wlh yau na gaji, ba gashi ina iya mikewa ba?" Hararsa tai tare da had'e rai tace " zamuje ko sai nayi fishi na?" Hannu yasa ya kamo kugunta tare da kwanciya akan cikinta yace " Maryam ni....." Tace " sakeni." Yace " naji mu tafi to." Murmushi tai sannan tace " ko kaifa, bakajin rashin dadi in kaje gun aiki kullum sai Habu na kanka?" Yace " haka ne, na dai so yau d'in ne inzauna dake....." Tace " duk zaman da muke tare?" Yace " to muje......" Haka suke rayuwarsu cikin farinciki dan Abdulmajid na tsananin san Mairo so mai tsanani kuwa, ita kanta gaba d'aya ta maida hankalinta gun kula da shi. Har dai wannan lokacin Allah bai bata ciki ba. Dan yanzu wata na 6 kenan da auransu. ************ Yau 'yan America sun zo daga kasarsu, magana ce sukesan suyu da Mai Martaba Sarki Turab, bayan sun gama maganarsu ne suka fito gari dan zagaya wa dasu, akan irin kujerar nan ta doki yake suna tafe mutanen gari an taru ana kallan Sarki. Tahuwa tai da gudu ba tare da an fargaba, dogarawa sam basu kula da ita ba sai gani sukai tana neman karasawa gun Sarki rike da wuka, kayan jikinta duk sun kode wani gun duk a yage yake, kakari take tana neman sukarsa, ana riketa, Turab jin hayaniya yasa ya juyo, Magajiya! Mamaki ne ya kamashi, gaba d'aya in ba ka santa ba sosai, bazaka taba cewa ita bace, ta rame ta gama fita hayyacinta, 'yan gari kam ganin za'a farma sarkinsu yasa suka fara jefanta da dutse. Dogarawa suka hankadeta da karfinsu cikin takaici. Jifanta ake, duk yanda Turab yaso ya hana ai inaa saboda yanda take kara yunkurowa zata kasheshi. A take a gun rai yai halinsa, yana gani suka wuce ba tare da sun kalli gawar ba, sai turawa yai akan a mata sallah A kaita makwancinta. Allah ya mana cikawa mai kyau Amin suma Amin. *********** Bilkisu da kanta ta samu Umma ta sanar da ita sannan ta kara neman shawara, dafarko Umma tayi kokwanton amincewa duba da abinda ya faru, sai dai Bilkisu ta nuna mata shi laifin wani baya shafan wani ko a gun Allah ne, sannan iyayenta laifi sukai aka hukuntasu bawai yin kansa bane. Wad'annan dalilai ne yasa jikinta yai sanyi itama ta duba yanda tasan Turab nasan yarinyar hakan yasa ta sanar da Sarki. ********** Yau yana zaune acikin gun hutawar sa, a gaba da gidan Sarki Abdussamad kadan gun yake, Bilkisu ce ta takura akan sai ya kaita gun, shiyasa suka fito bayan magrib, gashi ta shiga gunsu Umma. kwantar da kansa yai jikin kujera tare da lumshe idanunsa, rayuwa yake tunowa, sannan yau ya tura Sabi'u kauyen garin da suka zauna d'auke da sha tara ta arziki, shi da Lantana suka tafi dan kai musu tare da mika musu sakon gaisuwa da godiya. Lalai rayuwa ba'a bakin komai take ba, karasowa tai gun tare da kallansa, ganin tabbas shi din ne yasa tai saurin juya baya zata juya, jin motsi ne yasa ya bud'e idanunsa. Bayanta kawainya kalla ya gane itace, a hankali yace "Khadija!" Juyowa tai ta kalleshi, kallan juna suka shiga yi dan tabbas raban da suka juna sun dade, daurewa tai tace " Aikowa akai akan inzo inji Umma Basira, sannan akace tana nan......." Kallanta yake kamar bashida niyyar maganar, yawo ta had'iya sannan tace " kayi hakuri inaji ba'a nan take nemana ba." Juyawa tai zata tafi, a hankali taji yace " Guna ta turoki, ganin ni hidimomi sun hanani zuwa sannan bansan me zance miki ba in mun hadu." Juyowa tai ta kalleshi idanunta sun ciciko tace " ni kaina bansan da wace kalma zan fara ma magana ba, abubuwa dayawa sun faru wanda na hana kaina fita saboda hakan, raban da in fita waje ni kaina na dade, sai yau da Umma ta aika inzo." Alama ya mata akan tazo ta zauna gefensa, kallansa tai tace " Ranka ya dade amma...." Yace " haka kike kirana da?" A hankali tace " Ya Turab." Yace " zo ki zauna inji ya bayan rabuwa......" Bata tako ba tace " Ya Turab mai zance?" Hawaye ne taji suna neman zubo mata, da sauri ta juya bayanta. Tausayinta ne ya kamashi dan tabbas taga rayuwa, ba ita tai laifufuka ba amma duk sun shafeta, hakika duk ta rame ta canza ba shakka tana cikin wani hali. Mikewa yai ya dawo gabanta yace " Haryanzu saurin kukan na nan?" Tace " Yaya ni......" sai kuma ta kasa karasawa, yace "ke me?" Kallansa tai cikin kalar shagwaba tana san tai magana, yanda yake kallanta yasa tai murmushi, shima murmushin ya sakar mata........... *ALHAMDULILA* _Dukan Godiya ta tabbata ga Allah Ubanngijin talikai, muna neman tsari daga gareshi, Allah ya mana mai kyau, ya bamu ikon fin karfin zuciyoyin mu, ya sa mu a hanya madaidaiciya, shi ke shiryar da wanda yaso a kuma lokacin da ya so, ya Allah ka mana mai kyau ka kara karemu daga sharrin zuciya ka bamu ikon kyautatama iyayenmu. Yanda zamu fara azumi lafiya Allah kasa muga karshensa lafiya, ya bamu ikon yin ibada yanda ya kamata._ (Ameen suma Ameen) *Godiya ta musamman ga duk masu karanta littafin nan musamman yan Wattpad, da Whatsapp tnz alot, naji dadi kwarai yanda kuka kaunaci littafin nan.....* Abinda nai kuskure a ciki Allah ya yafemin, abinda na fada daidai Allah ya bamu ikon yin amfani dashi. Double thanks to all My Fans, I really appreciate ur love..... *SARKI TURAB*