💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *___________________________________ Labari ne da yake dauke da sabon salo,wanda nasan cewa ba ku taba cin karo da irin sa ba,ba zan ce muku komai game da wannan labari ba,ku dai kawai ku biyoni sannu dan jin me yake dauke dashi,me nazo muku da shi a wannan karon Daga gwanar ku fatima y Adam me dauke da Ƙudurar Allah da kuma kaddarata sanadin haske,yanzu kuma gani nan tafe cikin ɓoyayyar raihan,salon na daban ne faaa.....😄 Pg 1 ,,,,,,,,,,,,,,,,,,Yola ..........Alhaji Muhammad nurr shahararren attajiri ne,wanda yayi shura a cikin kasar mu ta Najeriya,kai harma da wajen kasar, bafulatanin Yola ne,sai dai mahaifiyar shi cikakkiyar bakaniya ce wadda mahaifinsa ya aurota a yawon almajiranci ya kawo ta Yola,ya aureta ne a matsayin bazawarar da miji ya rasu ya barta da yaro guda daya me suna yahya,kasancewar shi me son yara yasa shi karbar Yahya a matsayin ɗa tamkar shi ya haife shi,mahaifiyar su me suna rahma su biyu ta haifa. mahaifinsa me suna Aliyu kuma shi kadai ya haifa kwaya daya tilo a duniya, sai dai ba zaka taba gane hakan ba saboda yadda ya rike dan matar sa Yahya tare da nasa dan tamkar duka shi ya haife su, Alh Muhammad nurr bashi da wani dan uwa na jini sai Yahya,sai dai malam Aliyu wanda suke kira da baffa yana da tarin yan uwa.haka mahaifiyarsu rahma tana da tarin yan uwa a can Kano. Alhaji Muhammad nurr ya ta so cikin so da gata,tare da dimbin kulawa daga iyayen shi,ya samu karatun addini daga mahaifinsa kasancewarsa malamin addini,haka kuma ya samu ilmin boko me zurfi shima duk da taimakon jajircewar mahaifinsa,uba tamkar da dubu,saboda gaba ɗaya kusan dukkan komai ya same shi ne daga mahaifinsa,sakamakon mahaifiyarsu ,bata damu da wasu hakkoki na tarbiyya da suke wajibi akanta ba,saboda ita ɗin wata iriyar macece da baka taba iya gane mata ko gane inda ta fuskanta. Yadda baffa Aliyu ya bawa Muhammad nurr tarbiya da ilmin boko da na addini haka ya jajirce ya bawa dan matar shi Yahaya wanda tsawon rayuwar Muhammad nurr bai taba sanin cewa ba uwar su daya uban su daya ba. Sai dai kuma Yahya shi sam ba shi da ra'ayin karatun boko, shi yasa ya dinga wasa tun lokacin secondary wanda daga karshe ya sanar da mahaifinna su shifa ba zai iya wannan karatun ba,duk da baffa bai so hakan ba saboda ganin Muhammad nurr nashi karatun ya mika harma ya wuce yayan na shi,to amma babu yadda ya iya haka ya rabu da Yahya ,sai kawai ya kai shi kasuwa ya bude masa shagon Saida takalman roba irin wadanda Fulani suka fi amfani da shi a can babbar kasuwa. Ai ko hakan ba karamin dadi ya yiwa Yahya ba,dan haka da kwarin sa ya fara zuwa kasuwa,sai kuma Allah ya sawa abun albarka. Muhammad nuurr ya shahara ne ta hanyar jajircewar mahaifinsa,ta yadda ya tsaya tsayin daka ya samar da ilmi da tarbiyya ga tilon dan nasa,shi yasa shima yahya bai barshi haka ba ya bashi abin da ya nuna yana so wanda kuma yake samu sosai dan harma sun kuma bude wani shagon, wannan jajircewa ta baffa kuwa ba ƙaramin taimako yayiwa rayuwar nurr ba,saboda lokaci ɗaya ya samu nasarar rayuwa. Kasuwanci shine a binda Muhammad nurr yayi karatu akan sa,kamar yadda dan uwansa Yahya shima ya fara suna akan harkar takalma, Yahya ya jima baiyi aure ba dan daga karshe ma baffa ne ya samo masa matar ya aura masa,sai kuma a kayi da ce yaji yana sonta, Ganin baffa shine ya zaɓawa Yahya mata sai kawai Hajiya goggo ta ji kishi akan Muhammad nuurr, dan haka ita ce wadda ta fara zaba masa matar aure me suna murja, wadda ta kasance yar kanwarta,bai iya jayayya da iyayen shi ba,dan haka ya karbi murja da hannu bibbiyu duk da cewa babu so ko daya aranshi. Har zuwa tsawon wannan lokacin Yahya matar shi bata taba yin ko ɓatan wata ba,wanda daga baya Hajiya goggo ta so ya kara aure amma ya furje dole ta hakura ta kyale shi,shi kuma ba komai ne yasa ya ki amincewa ba sai dan tabbacin da likita ya ba shi akan cewa kwayoyin halittar shi na haihuwa ne basu da karfi shi yasa har yanzu bai samu haihuwa ba,amma ba wai ance ba zai haihu ba ne gaba daya. Alhaji Muhammad nurr,tun tasowar shi da kuma mafarkan shi,yake fata da burin samun ya mace a cikin zuri'ar shi, wannan burin na shi yana daga cikin dalilin saurin karbar auren murja da ya yi ba tare da musu ko gardama ba. Lokaci ɗaya Muhammad nurr ya samu daukaka ta ban mamaki da arziki me tarin yawa,hakan ya sa ya dinga dibar iyayen shi da yan uwan su,yana kaisu kasa me tsarki,kafin wani lokaci ya wadata yan uwan mahaifinsa da na mahaifiyar sa, Ba tare da kowa ya sani ba Muhammad nuurr ya sayi hannun jari a wata kamfanin sarrafa takalman roba,sai dai kawai ya dankawa Yahya a matsayin kyautar sa ta musamman, wannan al'amari ya yiwa baffa dadi sosai haka Yahya shima ya dinga zuba godiya harda kuka. A hankali harkoki su ka ci gaba da budewa Muhammad nurr,ya yi suna a kasashen waje da manyan jahohin Nigeria,sai dai kuma har lokacin murja bata taɓa ko da bari ba,bare ta haihu, hakan kuma ba ƙaramin tayar musu da hankali ya yi ba,duk da cewa ba wani dadewa auren yayi ba,tunda yanzu bai wuce shekara biyu ba. A cikin wannan tsukinne aka kammala babban ginin gidan da aka yi shi wanda za mu iya kiran shi da estate ta wani bangaren,sai dai ba shi da yawan bangarori,bangare shida ne kawai aciki,bangaren Yahya ,sai bangaren iyayen su,da kuma nasa bangaren da yakasance me bangarori har hudu bayan nasa da ya zama na Biyar,ragowar kuma an yi sune dan fatan zuri'a a nan gaba.ganin haka yasa Ba tare da sanin kowa ba , goggo rahma ta shiga nemawa Muhammad nurr wani auren,ba tayi dubi da zumuncin dake tsakanin ta da uwar murja ba,ita kawai mafitar danta take nema,acewarta koda murja ta haihu dole ne Muhammad nurr ya kuma yin wani auren saboda dukiyar sa ba ta zaman mace daya ba ce. Daga murja har Muhammad ɗin da mahaifinsa,daga sama suka sami labarin,sai dai a wannan lokacin ma baiyi mata musu ba,ya amince tare da sa hannun mahaifinsa baffa Ali da kuma shakikin dan uwansa da ba shi da kamarsa. Sai dai kuma daga ɓangaren murja da mahaifiyarta ansha artabu dan ba daban dukiyar da suke kwadayi ba,da tuni ko mai ya lalace,daga karshe dai dole suka hakura suna ji suna gani aka kawo amarya hanne,wadda ta kasance yar kawar goggo Rahma. Daga nan, aka fara fafata kishi ,tsakanin murja da hanne,yayin da kuma a gefe ta ciki na ciki tsakanin goggo Rahma da surukarta da kuma yar uwarta,(to bari muje zuwa muga me zai faru). Ko waccen su so take taga ta samu ciki,saboda shine damar farko ta samun mallake gidan,a wannan karon ba hankoron neman samun cikin kawai ake ba,harma da fatan samun jinsin da me gidan ke fata da buri,ko waccen su fatan ta ace yau ta samu diya mace,saboda duk wanda yasan Muhammad nurr yasan me yake bida yake fata da buri. Ba komai ne yasa hankalin matan ya kuma ta shi da neman haihuwar mace ba,sai yadda suka ga duk wata babbar kadara da Alhaji Mohammed nurr ya mallaka ya daga ya rubuta sunan RAIHAN,da niyar mallaka mata su ,ba tare da yasan za a haifa masa RAIHAN ɗin ba,ba tare da yasan wacece zata haifa masa RAIHAN ɗin ba,hankalin su ya matukar ta shi da wannan danyan hukuncin da Alhaji Mohammed nurr ya yanke,dan magana har sai da ta kai gaban Baffan shi,duk da cewa da sanin shi yayi hakan, cikin nutsuwa malam Ali ya dubi dan na shi, kafin cikin muryarshi ta Dattako ta karade falon,ya fara da bude taron da addu a , sannan ya dora maganar shi da cewa, Muhammad nurr kasan rigimar da ka haddasa cikin iyalanka a kan wannan hukunci da ka ke ta zartarwa kuwa? A hankali Alhaji nurr ya numfasa sannan cikin tsantsar ladabi ya dubi mahaifin nashi tare da cewa,kayi hakuri Baffa zuciyata ce ta kasa sarrafuwa akan soyayyar da take yiwa RAIHAN,shi yasa na yanke wannan hukunci" goggo Rahma ta yi zaraf ta ce" to kai kana da tabbacin za a haifa maka RAIHAN dinne da har kake kwasar dukiyarka kana rattaba sunayen ta a matsayin ka mallaka mata su?jin jina kansa yayi sannan ya ce" ban san gaibu ba,dan haka ban sani ba ko Allah ya ƙaddara min samun RAIHAN a duniya,abin da na sani kawai kullum duk sakan da mintuna zuwa awowi addu'a nake Allah ya bani RAIHAN" Baffan shi ya ce" RAIHAN kawai kake bukata ba ka neman Alkhairi? Nan ma jinjina kai yayi tare da cewa a'a Baffa ,na roki Allah idan RAIHAN ba Alkhairi ba ce Allah ya musanya min zuwan ta da Alkhairi,idan kuma hakan ba zai samu ba,to nafi bukatar Alkhairin" murja ta tunzura baki tare da cewa amma kuma kasan Allah zai iya yin duk yadda yaso akan RAIHAN ɗin,kake duk wannan a bun bayan kasan zata iya zuwa maka da akasin alheri idan ma an same tan,balle ma babu tabbacin samun nata" cewar hanne ke nan da sai yanzu ta tsoma baki cikin zancan. Alh nurr ya girgiza kan shi sannan ya ce" nayi addu ar samun RAIHAN kuma addu a ta Alkhairi,shi yasa nake ji ajikina cewar zan samu RAIHAN,a kusa ko a nesa insha Allahu". Goggo ta sa salati tana mai tafa hannayenta,kaifa nuru na fahimci kamar baka cikin tunanin ka,idan ba haka ba waye yake zance da gaibu" Baffa ne ya dakatar da ita daga banbamin da take yi,tare da duban Alhaji nurr ya ce" amma kasan abinda kayi ya haddasa fitina cikin iyalanka? Dan gyara zaman sa yayi kana ya bawa mahaifinshi amsa da cewa ey Baffa Amma Ni banga abin husuma a cikin wannan abun ba,tunda dai dukiya tawa ce kuma Ni nayi niyar bayar da ita ga RAIHAN, sannan kuma dukkan su duk wacce ta haifa min macen gurinta dukiyar zata koma idan kuma dukan su suka haifa to nayi alkawarin bada kyautar ga dayar kamar yadda na bawa ɗaya,dan haka ina ga maganar nan a barta kuma nayi alkawarin ko waccen su zan bata kyauta me tsoka tare da kadara wadda zata ji dadi harma su kawar da idanun su daga kan dukiyar RAIHAN". Baffa ya danja numfashi kafin ya ce" shi ke nan na gamsu da hujjojinka , Allah kuma ya baka abinda kake so ,ya kuma zama me alheri a gareka damu baki daya" Amin suka amsa gaba ɗaya,sai dai goggo sam bata gamsu da Wannan lamari ba,dan aganin ta duk wadda ta haifa masa mace ko kuma suka haifa gaba ɗaya ,to tabbas ita ce zata kwana a ciki,ya ma za ayi ita da haifar dan su da mora ai hakan ma ba abu ne mai yuwuwa ba,amma dai bata ce komai ba dan wannan lamari yana bukatar dogon tunani. Tun daga wannan rana ko wacce ta shiga fafutuka ta neman haihuwa ,haihuwarma ta ya mace,yayin da goggo take gefe ɗaya tana kallon kowaccen su,tana kuma fatan ace basu samu abin da suke neman ba,kai ita fa a yanzu bata ki a ce Muhammad nurr ya ki samun haihuwa ba,don kuwa rashin samun haihuwar tasa shine alheri a gareta,tasan cewa idan ya mutu bai haihu ba,dole ita ce mai gadon sa,(Hajiya goggo an san gawar fari ke nan). Kwatsam abin farinciki ya samu a gidan Alhaji Muhammad nurr, sakamakon cikin da aka wayi gari hanne na da shi,kar ku so kuga yadda Alhaji nurr yayi FARINCIKI,sai dai kuma daga ɓangaren goggo da murja abin ba haka yake ba,murja dai har cuta ta yi saboda tsananin tashin hankali,daga nan sai suka samu damar hade kai ita da goggo barakar da ta shiga tsakanin su suka dinke ta,suka shiga fafutukar zubda cikin,sai dai kuma zakaran da Allah ya nufa da cara dole sai yayi,lafiya ƙalau hanne ta raini cikin ta,har zuwa ranar haife shi. To a lokacin ashe itama maimunan Yahya tana dauke da mata cikin wanda hakan ya kara haifar da fariincikinazan tamkar zasu ci kasa. Baffa dai da Alhaji nurr sunturi suke a raseption,tare da adu ar fatan sauka lafiya ga hanne, goggo da murja kuwa ba wannan fatan su ke yi ba,dan ba su ki a ce daga uwar har dan sun mace ba,kamar daga sama suka tsinkayo kukan jariri tamkar zai tsinka musu dodon kunne,kafin ka ce me sun shiga rige rigen fadawa dakin tsakanin goggo da murja,saboda basa jin zasu iya tsayawa har likita ya fito ya sanar da su abin da aka haifa,ita dai maimuna kallon su kawai take tana mamakin yadda suka.kasa boye damuwarsa akan haihuwar hanne, sai dai kuma ba su kai ga samun nasarar shiga dakin ba,wata nass ta dakatar da su,ba dan ran su yaso ba suka hakura sai dai kana kallon su zaka tabbatar da cewa suna cikin tashin hankali da fargaba me tsanani. Sai da suka kwashe tsawon mintuna talatin sannan aka fito da babyn nannaɗe cikin farin shawel me tsananin taushi da kyau,da sauri goggo ta tari nas ɗin da tambayar me aka samu? Mika musu babyn ta yi fuskarta dauke da murmushi ta na cewa meye tukyici na? Murja taja dogon tsaki tana hararar nas ɗin, Baffa ne ya ce" me muka samu tukun daga nan sai a tafi batun tukyici"dariya tayi sannan ta ce" ina taya ku murna an samu baby boy,me kama da maman shi" wata irin guda goggo ta saki tare da cewa alhdlllh anyi min miji lallai kin cancanci tukuici dan haka ungo nan"ta faɗa tana mika mata sabbin yan dubu guda biyar, cikin sauri nas ta sa hannu ta karba tana zuba Godiya,sosai Alh nurr yay farinciki tare da nuna godiyar shi ga Allah,Yahaya ne ya karbi dan ya yi mishi addu'a ,daga nan ya mikawa Baffa Shima ya jima yana masa addu'a,sai kuma ubangaiya shima dai addu'a'in ya yi masa tare da fatan zamowar shi shiryayye. Murja kuwa zamu iya cewa tasa mu sassauci ,duk da cewa ba wai tayi farinciki ba ne,tunda dai a ganin ta ita bata haihu ba,sai dai a ranta tana jin cewa itama tana kusa dan bata fidda rai da samu ba. A ɓangaren hanne kuwa ,bayan farkawar ta daga doguwar sumar da ta tafi bayan haihuwarta,sai ta nemi da a nuna mata abinda ta haifa,da sauri murja ta mika mata babyn bakinta kamar gonar auduga tana cewa gashi nan,mun samu baby boy me kama dake sak ,sai dai fatan Allah ya raya bisa sunna" take hannun hanne ya fara karkarwa harma tana neman yarda babyn sai da murjar tayi saurin tare shi tana jan a uziya,gani kawai su kayi hanne ta sa kuka kamar wadda aka ce mata uwarta da ubanta sun mutu, goggo ta kama baki tare da cewa yau nake ganin ikon Allah,yanzu ke hanne ba zaki yi murna da samun lafiyar ki ba,Ni dai kam na dade banga abin mamaki da takaici ba irin wannan,yanzu har munzo zamanin da aka daina murnar haifa da namiji? Baffa ne yayi saurin dakatar da goggo da cewa me yasa kike haka ne goggon nuru? Haka ta ce miki ba kukan farinciki take yi ba? Murja ta yi tsalam ta ce" yo Baffa ai abin a bayyane yake"harara Alhaji Mahammad nurr ya watsa mata,wanda hakan yasa ta ja baki ta tsuke ranta fes,maimuna kuwa karasawa ta yi wajen hanne tana bata baki cikin kyakkyawan malami, daidai lokacin ne mahaifiyar hanne da yan uwanta suka ƙaraso ,hakan yasa akabar maganar kowa ya shiga san Barka da yiwa juna Barka. Cikin kuka Hanne ta dubi mahaifiyar ta da Yar uwarta tani, ta ce" inna dole nayi kuka,saboda Muhammad nurr bai barwa ya'yansa maza abun dagawa a faɗa a duniya ba,ya tattara komai da yake da muhimmi duk wata babbar kadararsa ya rattaba sunan gaibu ya bawa yarinyar da bata zo duniya ba,ba kuma a san ran zuwan nata ba,yaya tani ta kama baki cikin al'ajabi ta ce" yanzu kina nufin duk yawan dukiyar Alhaji nurr ya kwashe ya baiwa yar da babu batun samunta a duniya? Jinjina kai ta yi tana sharbar hawaye,inna ta ce Ey gaskiya dole ki yi kuka tunda a yanzu ko da yaushe za a iya cewa abokiyar zaman ki na ɗauke da ciki wannan kadan daga ikon Allah" amma kiyi hakuri mu bari zuwa nan gaba kadan tun da har yanzu ba a samu RAIHAN ɗin ba,amma nayi miki alkawarin cewa indai bake kika haifi RAIHAN ba to babu wata mace da ta isa ta haifawa nurr ita,da wannan alwashin na mahaifiyarta ta samu salama a zuciyarta. Anyi suna lafiya an sa wa yaro suna Aliyu sunan Baffa ke nan,daga nan rayuwa ta ci gaba da turawa ,burika na daduwa a zukatan marasa godiya ga Allah. Maimuna ta sauka itama ta samu namiji,kowa ya yi murna da samun karuwar da aka fara yi a zuriar ta su,yaro ya ci sunan baban maimuna wato Bashir,daga nan maimuna ta ci gaba da raunon danta cikin kwanciyar hankali,tunda dama ita babu wannan burin na son samun raihan, wannan ba hurumin ta ba ne,kai ita gani take ko da ace tana daga cikin matan Muhammad nuurr to kuwa babu abinda zai sa ta yi kokuwar neman duniya ta hanyar samun raihan. Bayan shekara daya da haihuwar Aliyu, da Bashir murja ta samu nata cikin itama,wayyo farincikin ba mai faduwa ba ne,babu wanda ya sani daga ita sai mahaifiyarta a cewar ta kar mahassada su ga bayanta ita da abinda ke cikin nata,to ashe itama hanne alokacin ta kuma samun wani cikin ,itama sai tayi shuru saboda irin tunanin murja,haka nan kowaccen su ta shiga ɓoye cikinta da ririta abinta tare da babban fata akan dacewa da samun RAIHAN. A lokacin da cikin da ake boyewa ya baiyyana ,dukan su sai da suka shiga shock na ganin junan su,sai dai tunda ciki yayi kwari dole ko wacce ta aje komai ta fara shirin tunkarar abinda ke gabanta, goggo kuwa kallon su kawai take babu wanda zai ce ga ainahin abinda ke boye cikin zuciyarta,saboda gaba dayansu tattalinsu ta shiga yi da ririta su,har zuwa lokacin haihuwar murja. Kamar wancan lokacin yauma dukan su suna harabar dakin da murja ke yin lebou,sai dai a maimakon murja da maimuna, yau hanne ce da maimuna,dan duk da tsohon cikinta kasa zama ta yi a gida ta jira haihuwar. To alhdlllh murja dai ta sauka lafiya kuma ta haifo santalelen yaron ta namiji me kama da goggo Rahma,dake murja ta danfi hanne wayo sai bata nuna tashin hankalin ta gaban surukanta da mijinta da kishiyarta harma da faccalarta ba,hannu biyu ta sa ta karbi yaronta tayi masa addu ,haka Alhaji Muhammad nurr shima bai nuna komai ba dama kuma babu komai a zuciyarsa ,yayiwa Allah godiya da ya bashi zuri'a yana kuma fatan su zama shiryayyu a cikin al'umma. Yaro ya ci sunan mahaifin murja ,wato Musa ,suna kiranshi Affan. Bayan wata daya da haihuwar murja ,hanne ta sake santalo yaronta namiji daga nan kuma kowacce ta fara kokarin boye abinda ke ranta,ta rungumi yaranta. Daga nan kuma haihuwa ta buɗe a gidan ,murja ta sake samun namiji ya ci suna idris.... Maimuna ce dai har yanzu shuru tun daga haihuwar Bashir. Bayan shekara hudu, A yanzu ko wacce tana da yara uku,bayan idris murja ta kuma samun rufa i,hanne kuma ta samu jamilu,har yanzu dai kowacce ta ɓoye tashin hankalin ta na rashin samun RAIHAN,sai dai abin da sauki tunda ko wacce tana ganin yar uwarta bata samu ba,dan haka suke tunanin hada kai dan samowa kansu mafita , duk da cewa ba su bude wa junsan su sirrin juna ba, goggo ma dai yanzu hankalinta a kwance yake ,duk da cewa ita macece da baka isa gane gabanta ko bayanta ba. Maimuna da mijinta Yahya suma sun rungumi kaddarar su ta rashin yara masu yawa,yanzu dama bata da matsala da goggo tunda dai ta haifa ko kuma ta ce arzikin Muhammad nuurr da ya taka na mijinta sau babu adadi ya sa ta samu sassauci Ta bangaren Muhammad nurr kuwa tuni ya fauwalawa Allah komai,duk da cewa har yanzu bai cire ransa daga samun RAIHAN ba,dukiyar sa kuwa da yanzu fin rabi ta zama ta RAIHAN tuni take karuwa,kamfanunuwan RAIHAN da sheres dinta sai bunkasa suke ,su dai matansa na ganin ikon Allah,duk da cewa kullum zuciyarsu cike take da fargabar samun RAIHAN. Yara tuni sun tasa sun zama samari,makaranta suke yi masu tsada na yayan manya kamar yadda suma suke ya'yan manya. Kwatsam kuma sai idanun Alhaji nurr ya yi gamo da SOYAYYA,wadda bai taba fadawa cikin ta ba,bai ma san ya ake yinta ba,tunda duk matan shi ba aba shi damar zaba da kanshi ba. A can yawon shi na zaga kamfanin RAIHAN,wanda ke cikin wani kauye dake can gabas da agadex,ya haɗu da Ramlatu ne a wajen kamfanin RAIHAN wanda take kai wa ma'aikatan cukyi suna siya su bata kudinta ta koma cikin kauyen su,ranar da ya fara ganin ta yace shima yana son cukui ta kawo masa da yawa zai siya,haka kuwa akayi ta kawo masa ya siya ya bata kudinta ,harma da kari ,saidai kuma tana irgawa ta cire masa kudinsa ta hade nata tayi gida ba tare da ko waiwaye ba. Tun daga wannan rana Muhammad nurr ya rikice da neman Ramlatu da SOYAYYAr ta ,bai kasa a gwiwa ba har sai da ya samu soyayya daga Ramlatu,har kauyen su ta kai nurr wajen mahaifinta cikakken buzu me matuƙar kirki da dattijon taka ,haka mahaifiyarta mace me kirki da sanin ya kamata wadda kusan duk ɗabi unsu ne hakan,su biyu kacal iyayen su suka haifa daga yayan ta sai ita,wanda shi yanzu yana can cikin garin yamai da matar shi, da ɗan shi guda daya yana aikin gadi a wani gidan babban mutum me suna Alhaji Abubakar matawalle,iyayen Ramla sun yaba da Muhammad nurr,dan haka kai tsaye Baba buzu ya sa yayan Ramla ya bincika mishi asalin Alhaji Muhammad nurr. Tabbas ba ƙaramin tsoro ne ya kama Baba buzu ba,lokacin da ya samu labarin waye Alhaji Muhammad nurr,dan haka ya ce shi sam ba zai ba shi yar sa ba,ba kuma wai dan bai yadda da tarbiyyar sa ba ne ,a'a kawai saboda yana tsoran sharrin kudi da tsoran kai kan su inda Allah bai kai su ba,hankalin Alhaji muhammad nurr ba ƙaramin ta shi yayi ba,ko a gida sai da suka fuskanci cewa yana cikin tsananin tashin hankali,daga abun ya gagare shi ,sai kawai ya sanar da Baffa,kai tsaye Baffa ya ce" da sai musu tiket su tafi can agades ɗin. Cikin ikon Allah Baffa ya shawo kan mahaifin Ramla har ya amince da batun auren,daga nan ba su dawo ba sai da Baffa ya bada sadakin Ramlatu,aka tsaida Ranar daurin Aure. Baffa ne da kansa ya tara su murja ya sanar da su maganar auren ,take fa suka shiga tashin hankali harma da koke_koke,ita dai goggo tasa albarka bayan hakan babu wani abu da ya biyo baya,saima shirye shiryen bikin da ta shiga yi gadan gadan,a cewar ta dole itama ta farantawa nurr kamar yadda ya faranta mata ya auri zabinta ba tare da musu ko gardama ba. Duk yadda su Hanne suka so a fasa auren nan saboda shige shigen bokaye da su kayi hakan bata samu ba, Allah ya rubuta cewa Ramla matar muhammad nurr ce Tofa makaranta ya kuka ji abin ,muje zuwa muji shin za a samu RAIHAN ko dai mafarkin Muhammad nurr ba zai tabbata ba, Idan an same ta wace cakwakiya za a tafka, A cikin matan Alh muhammad nurr guda uku wace zata haifa masa sanyin idaniyar sa RAIHAN? Hmmmm wasan da har yanzu bai soma ba ku dai ku biyo NI. Asannu dan jin salon da wannan labari yake dauke dashi. Fatima y Adam✍🏽 Typing 💕*BOYAYYIYAR *FATIMA Y. ADAM*💕 _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page2 ``` An ɗaura aure ankawo amarya Ramlatu, cikin gidan ta a matsayin mata ta uku ga Alhaji Muhammad nurr. Hannu biyu goggo ta karbi surukarta fuskarta cike da farincikin samun kyakkyawar buzuwa cikin ahalinta,Baffa da Abba yahya ma cike da soyayya suka karbi Ramla,sai dai a ɓangaren su Hanne a bin ba haka yake ba,dan kiri_kiri suka nuna rashin amincewarsu a kan amanar Ramla da aka ba su,to shi dai ango ba ta su yake ba ,dan haka cike da farinciki ya haɗa kan su ya yi musu nasiha daga nan ya ja matar sa suka wuce sashen sa. Ramla macece mai tsananin hakuri da kawar da kai,shi yasa taci ribar zaman gidan aure, saboda duk irin cin kashin da su murja suke mata bata taɓa daga kai ta kalle su ba,bare a kai ga tankawa,da wannan suka gaji su ka rabu da ita ,harma da ganin shekaru kusan biyu ko batan wata bata taɓa yi ba,sai suke ganin kamar bin malaman da suke ne ya ba su wannan nasarar,dan haka suka kwantar da hankulan su acewar su sun dinke bakin matsalar su,sai kuma hankoron neman yadda za suyi dukiyar RAIHAN ta zama ta ya'yan su, wannan ke nan. A bangaren maimuna kuwa sosai take kaunar ramla,dan sai da Abba yahya ya zauna da ita yaja mata kunne ya yi mata nasiha a lokacin da aka kawo ramla,to dake dama ita don ba mai tashin hankali ba ce sai ta karbi nasihun mijinnata da hannu bibbiyu, wannan yana daga cikin abin da yasa su murja kuma tsanar ramla,dan acewar su ba komai suke kullawa ita da maimuna ba sai munafunci. A bangaren goggo ma sam bata da matsala da Ramla ,saboda tana yi mata tsananin biyayya,shi yasa bata taɓa tsangwamarta ba,duk da cewa goggo tana da fada da rashin hakuri a wasu lokutan,amma bata taɓa yiwa Ramla ba,haka Baffa tsakanin sa da ita girmamawa ce,ta ɗauke shi tamkar mahaifinta, Abba yahya ma bashi da wata damuwa da ita tsakanin su girmama ce da mutunta juna. Haka wajen mijinta ta samu kyakkyawar shaidar zama mata ta gari yar aljanna, Alhaji Muhammad nurr yana matukar son Ramla da girmama duk wani abu da yazo daga gareta.... A bangaren burin Alhaji Muhammad nurr kuwa babu abinda ya ragu, sai ma karuwa da yayi , a kullum mutane kallon mahaukaci suke masa akan wannan gaibun burin nasa,dan a halin yanzu duk wasu kamfanunuwa da gidajen mai da shaguna sun koma sunan RAIHAN,duk abinda ka ga Ba a maida shi sunan RAIHAN ba to shine nasa ,amma kafin ka je kamfanin da ba sunan RAIHAN ba guda daya sai ka je wanda sunan ta yake kusan guda biyar, wannan al'amari shine yake kuma tunzura zuciyar matan sa,kai harma da ƴaƴan sa da suka fara zama samari,hudubar iyayen su na tasiri a zukatan su. ********** A hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya ta yadda wasu ke so da kuma sabanin yadda wasu ke so,yau shekarar Ramla uku cur a gidan Alhaji Muhammad nurr,wanda yayi daidai da bayyanar cikin da wbabu wanda yasan da shi harma ita kanta mai cikin,tashin hankali wanda ba a saka masa rana shi ne ya baiyana kan fuskoki da zukatan matan Alhaji Muhammad nurr,lokacin da Alhaji Mohammed nurr ya kai ta a sibiti Dan a duba lafiyar cikin da me cikin,a nan aka tabbatar masa da cewa ciki dai ya kai wata shida harma yana shirin shiga na bakwai,al'amarin da ya kuma gigita su murja ke nan,take suka shiga fadi ta shin neman salwantar da cikin,a bangaren goggo da Baffa kuwa kai harma da maimuna da Abba yahya wata kulawa ta musamman suka shiga bawa Ramla, uban gayya kuwa ai ba a magana ,ji yake tamkar ba a taba haifa masa ɗa ba,ji yake da abinda Ramla zata haifa ko da kuwa ɗa namiji ne,duk da cewa a zuciyar shi da jikin shi ji yake kamar lokacin zuwan RAIHAN ne yayi. Ramla tana sane da burin mijinta akan samun RAIHAN sai dai a kullum nuna masa take yi,ya nemi zabin Allah a dukkan ya'yan da za a haifa masa,bata taɓa kwallafa rai akan haihuwar mace ba,sai dai kuma tana taya mijinta fata da neman zabin Allah akan samun RAIHAN,ko ga ita ko ga abokan zamanta,bata taɓa kwaɗayin dukiyar da ta kasance ta abinda har yau ba asame shi ba. Duk irin abinda su murja suke dan ciki ya zube ,abun ya ci tura dan kuwa ciki dai ya kai lokacin haihuwa ba tare da wata matsala ta faru da shi ba. Wata ranar juma a ,da asuba Ramla ta tashi da azababbiyar nakuda,cikin sauri Alhaji nurr ya taso goggo suka nufi asibiti. Tunda suka je ake abu daya haihuwa taki zuwa,har ta kai ga cewa Ramla ta jigata ko da hannunta bata iya dagawa,tana yi tana tsayawa har zuwa lokacin tafiya masallaci,Baffa da Abba yahya da Alhaji nurr suka tafi masallaci suka bar murja da hanne sai kuma noss ɗin dake kula da Ramla. Kamar daga sama Ramla ta fara jiyo maganganu ta bayan window dakin da take labou,wani irin gumin tashin hankali da wahala ne ya fara tsatstsafo mata,yayin da a wani gefe ta yi tsam da ranta tana son gano Muryar da ke son halaka abinda take shirin haifa ɗin. Ina so ki tsaya agurin, ko da aiki za ayi mata nasan cewa kina gurin dan haka ,da kin tabbatar da cewa mace ta haifa ,ki san yadda zaki ki kashe ta,idan kika ga uwar zata kawo miki matsala ki hada har ita,Ni kuma zan cika miki ragowar kudin ki ,idan kuma namiji ta haifa ki rabu da su kuma na bar miki kuɗin da na baki duniya da lahira,"Muryar noss ɗin ta ɗora da cewa kar ki damu zan yi miki abinda kike so ba tare da an samu wata matsala ba,yauwa maza ki tafi kisa dukan idanun ki a dukan motsin su" daga haka Ramla ta ji ɗif, alamun sun bar wajen dan sun kawo karshen maganar su. Duk da yadda take jin jiki amma saida tayi kokarin tashi ta ɗaga labulen window,wai ko Allah zai sa ta ga fuskar matar da take son raba ta da rayuwarta,sai dai ina kafin tayi wannan zafin naman tuni matar tabar shiyar gaba ɗaya,komawa tayi ragwaf zuciyarta na mai dukan tara_tara,take ta fara addu'a akan Allah ya bata ɗa namiji abinda bata taɓa yi ba arayuwata zabar jinsin da take so Allah ya bata, cikin kankanin lokaci naƙuda ta dawo sabuwa,a daidai lokacin kuma likita ya shigo dakin shi da wannan nass ɗin ,da sauri ya ƙaraso inda take yana balbale nass ɗin da faɗa,ai Ramla bata san sanda ta kamo hannun likitan ba,wanda ya kasance likitan su na family, cikin azabar da take ji ta ce" dan Allah likita Ina son magana da kai"shi kadai ya ji abinda ta ce,duban nass ɗin yayi ya ce" je ki wajen Dr alasan ki karbo min sako" dan jim ta yi saboda tasan wajen Dr alasan ɗin a kwai nisa ,ita kuma awannan lukacin bata son abinda zaiyi nisa da ita daga dakin nan,amma babu yadda ta iya haka ta tafi ba dan ranta ya so ba,likita duba ka tabbatar babu kowa a ta waje da window dakin nan,maganar da zanyi da kai tana da matukar muhimmanci" cewar Ramla ke nan tana mai cije labbanta wanda har sun fara fitar da jini,baiyi mata musu ba ya je ya duba ko ina ya tabbatar babu kowa,kana ya zo ya sanar da ita. Cikin irin azabar da take sha ta dube shi,kana ta fara magana a hankali,ta ce" likita don Allah ka taimake Ni ba danni ba ,dan Allah da kuma halaccin Alhaji nurr a gareka"ina jin ki fadi abin da kike so indai bai fi karfina ba kuma bai sabawa Allah ba zanyi miki shi ko dan halaccin mijinki a gareni kamar yadda kika faɗa",Dr so ake a kashe ni nida abinda zan haifa indai ya kasance mace ne"cikin razana da mamakin maganar ta ya ce" kamar ya? A gurguje kuma yadda zai fahimta ta sanar da shi abin da kunnuwanta suka jiye mata,numfashi yaja me cike da takaici ,duk da cewa yasan komai akan batun RAIHAN da kadarorinta amma bai taba tunanin cewa za a iya kashe rai a kan hakan ba' ya ce" to amma Ramlah me zai hana mu sanar da Alhaji Mohammed nurr tunda kince baki san matar ba likitar ma baki gane ta ba,bare mu neme ta a binciko matar,wanda nasan tabbas daya daga cikin kishiyoyin ki ne" girgiza kanta ta yi idanun ta na zubda hawaye ta ce" Dr alasan kar mu sanar da Alhaji sanar da shi ɗin yana nufin abubuwa da yawa ,da ace ma na gane ko su waye shi ne za mu sanar da shi,to amma yanzu hakan ba ƙaramin hatsari ne a tare da mu b.... Maganar ta tsaya saboda wata irin murdawa da marar ta tayi, subhanallah sannu yanzu muyi kokarin cire abinda yake cikin ki idan yaso sai muyi abinda ya da ce"da sauri ta dakatar da shi da cewa a'a Dr dole a cikin wannan lokaci nake son ka samar min mafita,duk da cewa bani da tabbacin macen zan haifa amma ya kamata na samu mafita" yanzu me ya kamata muyi ke nan? Ya faɗa cike da ɗan zurfafa tunani,Muryar Lamra ta katse shi da cewa, idan na haifi mace ka dauke min ita ka yi nesa da ita na baka amana har zuwa lokacin da zan nemeta",a'a Ramla ba za ayi haka ba mu dai nemi wata mafitar,amma raba ki da abinda kika haifa ba shi zai kawo maslaha ba,dole abinda kika haifa ya ji duminki ki kuma shayar da shi a matsayin ki na uwa ya rayu dake cikin farinciki"to likita ya kake so nayi? Ta faɗa cikin rishin kuka da karaya harma da sallamawa. Idan kika haifi mace zamu ce namiji kika haifa a haka zata yi rayuwa a matsayin namiji ba mace ba, wannan shine kawai dabarar mu dan tseratar da rayuwar RAIHAN"zuba mishi ido Ramla ta yi kafin ta ce" ta yaya za ayi haka? Bayan kasan cewa halitta zata nuna kuma Ni ban isa hana mutane daukar RAIHAN ba, bare na ɓoye ta na hana daukarta,ban isa kuma na ɓoye halittar ta ta ɗiya mace ba"Dr Sabo ya yi dan jim kafin ya numfasa da cewa na sani ba wani lokaci hakan zai dauka ba,za muyi haka ne kawai na iya lokacin da zamu gano wannan mata wanda kuma a yanzu na tabbata cewa ba ita ka dai ce ba,zata iya yiwuwa a kwai wasu a can ta gefe waɗan da ba su bayyana kan su ba" duk da haka Dr Sabo dole a kwai kalubale a cikin wannan shirin" wajen minti ɗaya Dr ya dauka yana dogon tunani kafin ya dubi Ramla ya ce" Ramla akwai mafita akan ɓoye halittar matantaka sai dai ban sani ba ko zaki yadda da hakan? Cike da mamaki Ramla ta ce" ta yaya ne za a iya ɓoye halittar Mutum ba tare da wani ya gane ba? Amsa ya bata da cewa Ramla kin san cewa komai ya samu ci gaba a duniyar nan,barin ma a kasashen mu na waje,a kwai wani Dr eka a kasar Kuwait ya taba sanar da ni cewa an kirkiri wani abu mai siffar jikin namiji wanda manna shi kawai ake kuma na yara jarirai,sai dai kuma su sunyi abun ne ba da wata manufa ba sai dan wata cuta da ta bayyana a ƙasar ta lalacewar gaban yara maza to sai suka kirkiri abin saboda shi ake saka musu dan daidaita gaban na su da yi masa kariya daga daukar cutar harya warke sannan a cire musu,to ina ga muma zamu iya amfani da wannan abun mu siyo shi mu sakawa RAIHAN iya na lokacin da zata fara wayo wanda babu mai iya ganin tsiraicinta saike mahaifiyarta". numfashin wahala Ramla ta ja sannan ta ce" amma Dr Sabo kana ganin ba mu ɓata a cikin wannan lamari ba? Bamu ɓata ba,Ramla saboda kariya ce muka nemarwa abinda zaki haifa indai ya kasance mace"shi fa abin roba ne manna mata kawai zaki yi amma babu wanda zai gane cewa roba ce saboda yanayin jikin abin, kuma zaki iya cire mata duk lokacin da kika so dan wanke ainahin halittarta,Dr yanzu a ina zamu samu sannan zuwa yaushe zamu samu? Kasan cewa fa ko da yaushe zan iya sauka indai Allah ya nufa,amma dan Allah indai banyi rai ba ina so ka ɗauke Abinda na haifa ka dan ƙawa iyayena indai ya kasance RAIHAN ce" kar ki damu insha Allahu ma zaki haihu lafiya, yanzu zanyi magana da Dr eka ko da abin bai ƙaraso yau ba ,zan yi kokari koda kin haihu na toshe hanyar ganin ki da ke da jariri har sai mun aiwatar da shirin mu"na gode Dr Allah ya saka da alheri Allah ya taimake ka kamar yadda kake son taimakon rayuwata, Allah kuma yasa abinda mu kayi ya zama Alkhairi a garemu baki daya"Amin Ya Allah,ya ce" yanzu bari naje na fara wancan shirin daga nan sai mu fara shirin yi miki c s,tunda naga lokacin da muka diba idan baki haihu ba ya kusa" daga nan ya bar dakin dan fara aiwatar da shirin su kamar yadda ya faɗa. Hankalin Alh nurr ba ƙaramin ta shi yayi ba ganin har lokacin da aka diba ya cika ,Ramla bata haihu ba,hakan yana nufin dole sai anyi mata aiki ke nan,da kyar ya iya sa hannu aka shiga da Ramla dakin da za ayi mata cs. Sai dai kuma lokacin da ake ƙoƙarin fara aikin Allah da ikon sa ya bawa Ramla dama da karfin nishin haifuwa, tana sun kuto babyn ta Dr Sabo yayi saurin ɗauka ba tare da ya bari kowa ya gani ba,hamdala yayi wa Ubangiji dan tabbas da anyi cs sai an samu wani ya iya gane abin data haifa ,amma dake Allah ya gama zartar da ikon sa na cewa za a haifi RAIHAN kuma zata yi doguwar rayuwa,sai ya bawa mahaifiyarta ikon haihuwa da kanta dan hakan ya zama kariya daga idanun da suke kokarin cutar da ita. Nass ɗin da aka bawa wannan aiki tuni ta shiga baza idanu dan ganin abinda aka haifa,Dr kawo muga abinda aka samu? Ta faɗa tana murmushi kai ba zaka taba kawo cewa akwai wata mummunar manufa a ranta ba,da sauri Dr Sabo ya ce" wannan babyn namiji ne sai dai amma gaskiya ba shi da lafiya dan haka ku gyara uwar Ni kuma zan tafi da shi can dakin bincike" yana gama fadar haka ya fita ta wata kofa daban ba ta kofar da suke shigowa ba. A hankali labarin haihuwar Ramla ya karade dangi, amma ganin yaro ya gagara har yau kwana ɗaya da haihuwa , saboda likita ya sanar da su cewa yaron bashi da lafiya dan haka babu mai ganin sa sai nan da kwana uku,dole kowa ya hakura da ganin baby,Amma dai da yawa hankulan su ya kwanta da sanin cewa Ramla namiji ta haifa. Bayan kwana uku , babyn Ramla ta baiyana cikin kyakkyawar shiga ta fararen kayan sanyi,Masha Allah kowa yake fadi yau gaɗan buzaye kyau ya hadu da kyau ya bada kyau,tunda Alh nurr ya dauki babyn nan ya zuba masa ido yaji gaban sa na faduwa sai dai ba ya ce ga dalili ba,tabbas har mafarki an nuna masa cewa Ramla ta haifi RAIHAN,to sai dai kuma ga shi Ƙudura ta ubangiji ta sauya al'amarin,haka nan yaji zuciyar shi ta karaya ta kuma hakura da samun RAIHAN,amma kuma wani abun mamaki da shine jin duk wata SOYAYYA da yake yiwa RAIHAN ta juye ta rikida ta koma kan jaririn da Ramla ta haifa,wanda take yayi wa babyn huduba da Abdulrahim,haka goggo ta dauki babyn tana ta juyawa cike da so da kauna. Ana sallamar su gida suka wuce,sai dai kuma suna komawa gidan Ramla ta ji zuciyarta taki gamsuwa da zaman gidan,dan haka kawai ta nemi alfarmar Alh nurr da ya barta ta je gida wanka,ya so ya hana ta to amma kuma baya jin akwai wata alfarma da Ramla zata nema a wajen sa in dai yana da ikon yi mata baiyi ba, goggo ma dai taso Ramlah ta zauna to itan ma bata tauye Ramlah ba,tunda sun san halinta da alkunya da bata bukata da bazata taba tambaya ba. Maimuna ma taso ramla ta yi zamanta ,acewarta ita meye amfanin ta da har tana zaune gata ga goggo sai ramla din ta tafi gida wanka,to amma itama ganin ramla hankalinta ya fi karkata ga son zuwa gidan yasa suka bita da fatan alheri. Da wannan hankalinta ya kuma kwanciya tasan ko a kasi aka samu innar ta ce a kusa da ita ,bayan suna Ramla ta wuce agades ita da goggo da tayi mata rakiya. ........Rayuwar Ramla agades. Cikin taka tsantsan take rayuwarta a sirrance,duk da cewa Nan din iyayen ta ne Kuma marufar asirinta ,to Amma tayi yakinin cewa duk ta sake suka sani tabbas maganar zata iya yaɗuwa har tayi Yaɗon da zata Kai inda take tsoran zuuwanta,tun wankan sati Daya da ta bari goggo ta yi wa baby Bata Kuma bari Wani ya yi mata ba,tunda suka dawo agades tace wa innarta ai goggo ta koya mata wankan baby Kuma likita ya ce" lallai ta dinga yi mata da kanta saboda kiyaye wasu abubuwa Wanda ko ita Bai sanarwa ba.da wannan ta samu ta ke wa babyn ta wanka ba tare da anga rashin kunyarta ba,duk da cewa daga ita sai innarta ne a gidan. Tunda suka dawo agades alhaji Muhammad nurr Baya sati Daya sai yazo yaga sanyin idaniyarsa,wata irin soyayya ce me zafi yakewa Rahim tamkar soyayyar RAIHAN,abun har mamaki yake bashi da Kuma Saka shi shakkun da baisan dalilinsa ba,duk lokacin da yaje ya dauki RAHIM ya tsira mashi idanu yakancewa,Ramla gani nake yi ba a taba haifar kyakykyawa kamar RAHIM ba,Wani lokacin idan na kalle shi sai na ga kamar mace saboda tsananin kyansa"a razane Ramla ta dube shi kafin cikin rawar Baki ta ce"Abban RAHIM lallai Ina tunanin ka fara zautuwa akan son RAIHAN idan ba haka ba ta ya RAHIM zai na juya Maka zuwa mace?murmushi yayi tare da cewa to Ina ga dai hakanne maganarki". Tun daga lokacin ta Kuma daukar aniyar boye RAIHAN dinta,Dan ta tabbatar da cewa idan Bata dauki mataki ba wata rana Abbin ta zai iya ganin abun da suke boyewar wanda Kuma Hakan Yana dai_dai ne da rasa yar ta su GABA Daya. A cikin tsananin taka tsantsan Ramla ta ci GABA da wanka har zuwa ranar da ta yi arba in,duk da cewa alhaji Muhammad nurr ya damu da dawowar su Amma hakan bai hana shi bari su zaga dangi ba,sai da su ka Kara sati ɗaya Sannan yazo ya tattara iyalan sa suka koma Yola,zuciyarsa cike da farinciki na zai kasance da RAHIM din shi a inuwa guda. Wannan shine tushen labarin.muje zuwa yanzu din ma ba a fara komai ba,kamar dai yadda na gaya muku salon nasa na dabanne. Typing Fatima y Adam ✍🏽 Typing 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page3 ``` Da fargabar abun da zai iya faruwa Ramla ta koma Yola,sai dai ta yi kwanaki biyu ta samu nutsuwa ganin babu abinda ya faru,kamar yadda take taka tsantsan a can agades haka Nan ma take yi Harma fiye da can din,kullum goggo sai ta sa an dauko mata RAHIM tun Ramla na fargabar hakan har ta hakura ta Maida hankalinta kan mijinta da alamuran da suka shafi rayuwarsu. Kwanci ta shi yanzu gashi RAHIM yana da shekara biyu har da watanni takwas,tuni Ramla wadda yaran gidan suke kira da anty amarya ta yaye shi daga Shan mama,su mama murja tuni suka dauke hankalinsu daga kan lamuran anty amarya duk da cewa suna sane da irin mugun son da alhaji Muhammad nurr yake wa tilon ɗan da ya fito daga tsatson Ramla anty amarya,sai dai yanzu ba wannan ne a gaban su ba, abinda ke gaban su kawai shine yadda za ayi dukiyar RAIHAN ta dawo ta 'ya'yan su da su kansu. Bayan shekara biyu da haihuwar RAHIM,a yanzu fa komai nema yake ya kuncewa,anty amarya saboda yanzu saura shekara uku abin da take sawa RAIHAN ya daina amfani saboda girma da zai fara zuwa mata,take ta fara neman hanyar ci gaba da ɓoyan RAIHAN dinta har zuwa lokacin da ta tabbatar da cewa babu wani me neman rayuwar 'yarta.babu bata lokaci ta nemi Dr Sabo,ya jima yana nazari kafin ya dan numfasa kana ya ce" Amarya wannan ba wani abun tada hankali ba ne,kawai da zarar RAIHAN ta cika shekara goma za a canja mata kayan da take sawa ya kasance duk kayan da zata saka su kasance masu girma da boye halitta ,saboda na tabbatar da cewa nan da shekara goma alamun girma zasu iya bayyana a jikinta ,idan mu kayi amfani da wannan kayan hakan zai taimaka mana wajen ɓoye halittar ta,idan kuma kan lokacin Allah ya bamu nasarar gane makiyan ta shike nan kin ga mun samu sauki,fatan mu dai Allah ya kaimu da ran mu da lafiyar mu" ajiyar zuciya Anty amarya ta sauke tare da cewa shike nan Dr Sabo na gode sosai da gudunmawarka a garemu kuma insha Allah zan kiyaye da duk abinda ka zana min fatan dai Allah yasa mu ga girman da rai da lafiya"daga nan su kayi sallama ta tuko motar su ka dawo gida. Shekarar RAHIM hudu aka saka shi a makaranta me shegen tsada,Ta ya'yan manya,sai kuma su mama murja da suka fara shiga tashin hankali akan yadda komai na RAHIM ya sha banban da na nasu yaran,(a ganin su fa amma)dan hatta da Hajiya goggo kaunar da take wa RAHIM ta musamman ce,duk da cewa tana jin haushin yadda anty amarya take nuna mata rashin yadda akan RAHIM din tunda bata barin sa ko da wasa ya kwana a bangaren Hajiya goggo,bata san dalilin anty amaryar da yin wannan taka tsantsan din da RAHIM ba,ko wasa ba ta barinsa yi cikin yan uwansa yara,ko da yaushe yana kusa da ita a takure. A haka ya fara zuwa makaranta,to makarantar ma ta ce ita ce zata dinga kaishi tana dauko shi,sam Alhaji nurr bai damu da hakan ba sai ma mota da ya siya musamman dan kai RAHIM din makaranta,hakan ba karamin farinciki ya saka anty amarya ba,sai dai kuma hakan tamkar ƙarawa su momy Hanne da yaran su ƙiyayyar RAHIM tayi,dan su momy sun dade da koyawa 'ya'yan su ƙiyayyar anty amarya da tilon yaronta. Irin yadda anty amarya take takura RAHIM abin har yaso yayi yawa,saboda bashi da dama ya sake cikin yara yan uwansa ,sai kuma wani babban al'amari da yake son daga mata hankali wato yadda RAHIM bashi da aiki sai wasa da mata da duk wani abu da ya danganci mace, tasha kwace ribom a hannun sa,wanda take rasa a ina yake samu,saboda ta hana shi wasa da yaran anguwa da na ajin su,abin da bata sani ba shine RAHIM yana da wata kawa yar ajin su kuma makotan su,duk lokacin da yaga abin da ya burge shi nata kai tsaye yake cewa ta bashi,shakuwar da su kayi da ilham me yawa ce,kuma kullum gaba take yi. Yadda Baffa da Abba yahya suke kaunar Rahim abun har mamaki yake bawa mutanen gidan haka ta bangaren inna maimuna wadda suke dinke ita da aunty amarya tamkar wasu yaya da kanwa,dan duk yadda aunty amarya ta kai ga boyon Raihan bata iya yiwa inna maimuna shamaki da ita. Kwanci ta shi gashi yau saboda tsananin kokari irin na RAHIM har an yi masa tsallake an kai shi primary one,daga free nursery,a kuma shekarar ne ya cika shekara biyar. Wani irin sihirtacce kyau ne da rahim me sanyi ,wanda saboda yawan tanka musu shi da ake yasa Abbin sa sa manyan malamai dinga yi masa addu'a da karatun Alqur'ani,haka Hajiya goggo ta shiga bashi rubutuka da tofi na kariya da tsari,Anty amarya dama bata tsaya ba itama tsaye take kan tarbiyyar yarta da kuma yawan addu o i ,wanda take mata da wanda take koya mata. A cikin islamiyar da Rahim yake zuwa ma duk yawancin kawayen sa mata ne,to amma saboda yana tsoran fadar antyn shi sam baya bari ta sani. Hajiya goggo ta so sanar da Abbin irin takurar da antyn Rahim ke yi masa ,saboda shi bai san komai ba tunda ba yawan zama yake yi a kasar ba,wani lokacin ma saboda Rahim din yake takura kansa ya yanke wasu abubuwan ya dawo ya danyi kwana biyu ya koma,sai kuma ta bari saboda bata son manufar ramla akan hakan ba. A yanzu gaba daya yaran tun daga kan Affan da bashir har zuwa kan jamilu Abbin su ya tura su karatu,dan haka yanzu babu kowa a gidan sai Rahim.ganin haka ya sa Hajiya goggo dauko jikar, kanwarta me suna jiddo,saboda ta dinga jin motsin yara a gidan tunda Rahim ya zama ɗan kurkuku,sam dauko yarinyar nan baiwa Anty amarya dadi ba saboda kusan sa'ar Rahim ce,dole zasu dinga wasa tare wanda ita kuma haka ne bata so, wannan dalilin yasa ta gwammace Rahim ya koma makaranta da yini,dan haka ta cire shi daga islamiyar da yake zuwa ya koma yini a makaranta,hakan sai yayi wa Rahim dadi saboda kawar sa ilham ma ta yini take yi,sharudda kuwa malaman makaranta sun sha shi ,sai dai kawai sun ji ta ne,dan babu yadda za ayi su hana yaro walwala cikin yan uwansa yara,tun da antyn su ta fahimci irin rayuwar da Rahim yake yi a gida ke nan,shike nan ta bashi damar wata yawa a makaranta,hakan ya mishi dadi kuwa har sai ya zama na yafi son zaman makaranta akan na gidan su,kasancewar yana da matukar kokari kamar wani aljan sai hakan ya da da jawo masa farin jini wajen malamai harma da daliban da suka girme masa,a hankali aka dinga yi masa tsallaken aji saboda basirar sa ta girmi ajinsa. Shekara Goma daidai wanda yayi daidai da fara zuwan shi makarantar gaba da primary,a lokacin ne Abbin shi ya haɗa masa kwarya kwaryar walima ta cika shekaru goma da kuma murnar kammala primary school,a lokacin ne hankalin Anty amarya ya kuma dagawa saboda yadda taga duk taron kawayen Rahim mata ne,mazan ba su da wani yawa, hankalin ta ya matukar tashi saboda gani take kamar yin mu'amalarsa da mata ita zai sa ya tona asirin da take ta ɓoye wa saboda shi,tana matukar son RAIHAN bata jin akwai wani abu da take wa son da take wa RAIHAN,shi yasa take matukar tsoran rasa ta,har hakan yana neman taba mata ƙwaƙwalwa saboda matsawa kanta da tunani,yanzu kam tafara tunanin ko dai bodin school zata maida RAIHAN din , to amma da tayi shawara da Dr Sabo sai ya nuna mata cewa ta bari zuwa lokacin da zata gama jiniyo su ga abinda Allah zai yi,idan har lokacin ba su gane komai ba kawai sai su Kaita bodin school ɗin,da wannan ta samu ta hakura ,sai dai kuma ta kara kaimi da tsaurara matakan tsaronta akan RAIHAN din. A hankali RAHIM (RAIHAN) ya fara fuskantar wasu abubuwa a tare da shi ,dole fa Rahim a matsayin shi na mace kuma musulmi wanda yake zuwa makarantar islamiya yana sanin addini yasan Meye jinsi,haka dole ne idan yana wayo yana shiga cikin mutane yasan komai dangane da banbancin jinsin mace da namiji, wannan dalilin ne yasa take kokarin nesanta shi da mutane ba iya mata ba har ma mazan,abu daya ta manta cewa Rahim yana zuwa islamiya kuma haziki ne shi din wajen karatu,da maida hankali akan duk wani abu mai muhimmanci. Mamaki ne ya fara shiga kwakwalwarsa sai kuma tunanin sa ya fara kai kawo,ya za ayi yana matsayin namiji halittun jikin sa su dinga kamanceceniya da na mata,wayo da ilimin addini da ya ratsashi ne ya sa shi fara wannan tunanin. Da fari so ya yi ya tambayi inna maimuna sai kuma ya fasa sakamakon tuna huɗubar Aunty da Ali da yaushe take gaya mishi duk abin da ya same shi ko ya kulle masa kai kar ya sake ya tunkari kowa sai ita,sam aunty bata ba shi damar fedewa wani samuwar shi ba bayan ita wannan ne yasa ya fasa tunkarar innar Bashir da maganar. Wata ranar Litinin Anty amarya ta shiga makarantar su Rahim dan dauko shi,tana zuwa ta tarar da shi tsakiyar kawayen shi su ilham,yana ganin antyn na shi duk sai ya ruɗe yasan zata yi masa fada sosai tunda ta hana shi shiga cikin mutane irin haka,cikin sanyin jiki ya karaso bakin motar ya buɗe ya shiga yana yin ƙasa da kansa saboda mugun kallon da ya ga antyn na auna masa,ƙwafa tayi bayan ya shigo ya rufe motar,da gudu taja motar ranta a matukar ɓace,suna zuwa gida ko kallon shi ba ta yi ba ta wuce warta bedroom dinta,idanun sa ne suka kawo ruwa yana jin rashin daɗin kinjin maganar antyn da yake, sai dai kuma baya jin zai iya ci gaba da takurawa kansa ta hanyar hana rayuwarsa sakewa a cikin mutane akan dalilin da baisan shi ba,dakin sa ya nufa ya cire kayan sa kana ya shiga bathroom dan kimtsa jikinsa,tsayawa yayi jikin madubin da yayiwa bangon kawanya yana mai kallon kanshi,to Me yasa Ni nakasance a haka? Taba gashin kansa yayi wanda kullum ake cikin aske shi ,dan yau baifi kwana biyar da yi masa askin ba amma gashi har ya fara fitowa,me yasa komai nashi yake kama da na mata? Ya kuma yi wa kanshi tambayar da baisan amsar ta ba,da sanyin jiki yayi wanka tare da daura alwalar magriba,yana fitowa yayi saurin kimtsa wa cikin kayan sanyin shi na ko yaushe masu dan kauri da ɓoye halitta,fita yayi kai tsaye ya nufi dininng room da sauri saude me aiki ta zo ta fara zuba mishi abinci. Abincin yake ci amma gaba daya hankalin shi na kan kofar bedroom din auntyn shi,haka dai cikin sanyin jiki ya gama cin abincin ,dai dai lokacin ne aka kira sallah magriba hakan ya sa shi miƙewa tare da ƙarasawa dinning sink ya kuskure bakin shi ,kana ya nufi ɗaki dan sauke farali,dan babu zancan zuwa Masallaci a gurin sa tunda auntyn bata bari,da dai Abbin shi na nan ne yasan dole zasu tafi tare. Yana idarwa yayi azkar dinsa na marece tare da karanta wasu ayoyi daga cikin suratul Mu'uminin,daga nan ya tashi ya dauko jakarshi ta makaranta,zama yayi dirshen cikin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa a kan kyakkyawar fuskarsa, ribom ya fara ɗaukowa daga nan sai sarƙa da zobe awarwaro,kai duk wasu abu na sha'awa na adon mata haka ya cika gaban sa da su,ya fara wasan sa cikin nishadi da walwala. Innalillahiwa'inna ilaihi raji'un,abun da ya zaburar dashi ke nan ,ya kuma yanke masa nishaɗin da ya tsunduma a sanadin wasan da yake da abin da suke matuƙar burge shi a rayuwa,da sauri ya mike jikin shi babu inda baya rawa saboda tsoran ganin yanayin antyn nashi,wadda ke ta rafsa salati da inna lillahi kamar wadda taga wani mugun abin tsoran,wani irin kallon tashin hankali take bin Rahim da shi kamar zata haɗiye shi ɗanye,gadon shi ya haye tare da ƙudundune kan shi cikin tattausan dovet,yana mai rufe idanun shi da kunnuwan shi dan gujewa tsawar auntyn shi da kuma hargitsewar fuskarta,sai dai abin da Rahim bai sani ba shine yau ran maman shi ya ɓaci fiye da kullum zuciyarta ta shiga fargaba fiye da na kullum,dan haka hukuncin da take jin zata yi masa ya zarta na tsawa,da muzurai,dan a ganinta ya raina hukuncin tsawar shi yasa kullum yake ƙirƙirar sabuwar fitinar da zata iya yin sanadiyar karar da guntun farincikinta. Da wani irin ɓacin rai ta karasa bakin gadon,ba tare da tunanin komai ba,ta janyo shi daga cikin bargon tare da dauke shi da wani irin mahaukacin mari,wanda ya ji saukarsa babu zato,ya kuma yi masa shigar da har sai da jin sa da ganin sa suka dauke,ba tare da ta kula da halin da yake ciki ba,ta shiga banbami da masifar baya jin maganar ta,a hankali kunnen shi ya dawo daidai sai dai kuma idanun sunƙi dawowa daidai,sosai yake ganin duhu saboda jinin da ya taru a gefen idanun nasa,kuka ya saka me karfi yana kiran Abbin shi,cikin siririyar muryar da ake yawan kira masa ita da muryar mata,ya ce"aunty idanuna bana ganin komai zafi suke min a ciki kika buge ni"cak ta dakata daga niyar kwashe tarkacen kayan wasan nasa,ɗagowa ta yi zuciyarta na wani irin bugu ,kafin ta watsar da kayan da ta fara diba ta nufo gun tilon yar da take jin zata iya bada rayuwarta dan fansar rayuwarta, za kuma ta iya mutuwa a duk lokacin da aka ce yau babu RAIHAN din a duniya,Wanda hakanne yasa take yin duk wani abu domin tsira da rayuwar tilon yar tata. Kama shi tayi cikin tashin hankali tana kiran sunan sa, RAHIM bude idanun mu gani me ya same ka a idon?ta tambaye shi cikin son kwarara kanta,aunty bana gani ido na ya rufe"innalillahiwa'inna ilaihi raji'un ta shiga maimaitawa tare da sunkutar shi,su kayi waje tana mai kiran sale driver domin bata jin zata iya tuki a cikin wannan yanayin na tashin hankali da take ciki. Suna tafiya tana kiran Dr Sabo da kyar ta samu kiran ya shiga,yana dagawa ta sanar da shi cewa ga su nan ita da Rahim yayi kokarin shirya musu ganin likitan ido,amsa mata yayi ba tare da ya tambaye ta dalili ba,tunda dai yasan nan din zasu karaso. Suna zuwa babu ɓata lokaci ya kai su office din Dr salamon,ganin yadda duk aunty amarya ta ruɗe yasa Dr Sabo ya ce" plz amarya ki nutsu ki yi mana bayanin da zamu fahimta domin yin solven din matsalar"duban shi ta yi cikin hawaye ta fara bashi labarin abinda ya faru,jinjina kai kawai yayi tunda shi yasan musabbabin komai,da sauri Dr salamon ya shiga aikin sa,ai ko cikin kankanin lokaci ya gano matsalar ,duban Dr Sabo ya yi bayan ya gama binciken sa ya ce"marin da tayi masa ne ya kawo taruwar jini a gefen idon wanda hakan ne yayi affecting din ganin sa ,amma dai ba wata babbar matsala ba ce,dan a halin yanzu ma idanun sun buɗe sai dai magunguna da za a bashi da kuma kiyaye wata matsala da zata kara shafar idanun"ajiyar zuciya me karfi aunty amarya ta sake tana mai rungume Rahim ,ta ce" sorry my son ba zan kuma ba kasan ban taba dukan ka ba ko da tsintsiya ne wannan ma tsautsayi ne"yanzu ka na ganin komai? Ta tambaye shi tana shafa lallausar sumar kansa da ta fara yawa,jinjina kai yayi tare da kara lafewa ajikinta,Godiya ta yiwa Dr Sabo daga nan taja hannun Rahim suka wuce permacy,suna zuwa aka hada magungunan aka basu. Ko a mota ci gaba tayi da rarrashin sa,tare da yi masa nasiha akan ya dinga jin maganar ta,a haka suka zo gida,bangaren Hajiya goggo suka nufa,nan fa ta shiga tarairayar Rahim da nuna masa gata,hakan yasa Anty amarya zama a bangaren saboda baza ta iya tafiya ta bar Rahim ba,kuma bazata iya daukewa Hajiya goggo dan farincikin da ta samu na ganin Rahim din ba,hakan yasa sai wajen sha biyu na dare su kabar sashen,a lokacin ma tuni Rahim yayi bacci. Kwanaki na ja suna zama sati ,sati na komawa watanni watanni na komawa shekaru,abun dadi da akasin sa na faruwa,burukan mutane wasu na raguwa wasu na karuwa,ana haihuwa ana mutuwa,to kamar haka ne ya faru akan Rahim rayuwa na gangarawa halittun shi na canjawa kalubalen rayuwar shi na karuwa, kullum yanzu sai ya duba kan shi a madubi ya karewa matashiyar halittar sa kallo,yayin da zuciyar shi take da ɗa cika da ɗimbin mamaki na yadda Allah ya halicce shi a sunan namiji halittun shi kuma kaf irin na mata,sosai abin yake bashi tsoro dan a yanzu yana matakin shiga shekaru goma sha biyar,ya gama secondary school tare da saukar alkur ani da kuma litattafan addini, kamar su hadisi piqhu sira bulugu akbari ishmawi da dai sauran littafan addini,saboda Rahim hazikine a kowanne bangare shi yasa ya samu karatu wanda ya fi shekarun sa yawa,tun da ya gama secondary school aunty amarya ta tare gaba ta tare baya bata barin sa fita ko ina sai tare da ita,bata barin kowa yazo wajen sa ko a cikin gidan na su ba ko ina yake zuwa ba sai tare da ita, wannan rayuwa da yake ta kunci ya sa babu walwala a tare da shi bai san wani abu wai shi farinciki ba,saboda an riga an gina rayuwar shi da kaɗaici,duk da gatan da yake samu ta bangaren iyayen shi da kakannin hakan bai sa ya rage kadai ci ba,a gurin baffa Ali ne kawai yake dan yin walwala duk da shima baffan fama yake da jinyar da ta tarar da tsufa,Abbin shima kullum burinsa ya ga farin ciki da walwalar RAHIM,haka inna maimuna da Abba yahya wanda shike kula da duk lamarin su na cikin gidan tun da Abbin ba zama ya fi ya yi ba. Haka ta bangaren aunty amarya ma,sai dai duk abin da aunty amarya zata yi masa dan faranta masa hakan baya burge shi ,saboda ya riƙe ta a matsayin wadda ta yanke farinciki da walwalarsa ta hanyar raba shi da mutane masu muhimmanci a rayuwarsa,Abbin shi ya sha tambayar shi damuwar shi da musabbabin juyawar yanayin shi,to amma baya jin zai iya kai korafin auntyn nashi wanda yasan hakan zai iya jawo matsala babba tsakanin iyayen nashi,duk kuwa da cewa ta wani bangaren yana mai jin haushin auntyn a kan yadda ta ke juya rayuwar shi,sai dai so da yawa yana tunani irin na manya kuma da ilmi na sanin darajar iyaye baram ma mahaifiya,dan haka yake kokarin kawo tunanin cewa lallai akwai wani babban dalilin da yasa auntyn take abin da take yin.duk dan kawar da rikon da yake jin zuciyar shi na son yi mata wanda yasan hakan bai da ce ba a matsayin ta na mahaifiyar shi. Haka kuma kulawar da yake samu daga wajen inna maimuna da Abba yahya yana rage masa kadaici,dan sosai suke kulawa da shi wanda hakan ya ke jawo kace nace tsakanin kishiyoyin aunty amarya dan gani suke kawai tsabagen munafunci ne da neman wajen zama a gurin Alh Muhammad nuurr yasa suke yin hakan,duk da cewa har yanzu babu wanda yasan ba Uba daya suke ba. .........✍🏽 typing 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page4 ``` Abu daya ne yake sawa kaga walwalar Rahim da dariya harma siririyar wushiryar shi ta bayyana ,shine sauraron daddaɗar Muryar matashin saurayin nan me gabatar da shirin labarin masoya a tashar nan da tayi ƙaurin suna take kuma kan tashe wato CHIBAƊO FM,a duniya babu abinda Rahim ke kauna sama da sauraron labarin masoya daga Muryar AHMAD WAZIR CHIBAƊO,lokacin gabatar da shirin yana gabatowa zai janyo tap din shi ya yi joinin gidan Radion ya fara zaman jiran cikkar lokacin,ya yadda ya jira amma bai yadda ya wuce shi ba,aunty amarya dai wannan karon bata hana Rahim farincikin shi ba,sai ma dadi da hakan yayi mata,harma da kanta take zama tana taya shi jin shirin dan kawai ta kawata farincikin nasa,ai kuwa hakan ba karamin dadi yake wa Rahim ba,dan haka cikin kaso dari na damuwar sa kaso tamanin ya gushe saboda samuwar shirin labarin masoya daga Muryar matashi Ahmad wazir chibado. A hankali aunty amarya ta karaso kusa da Rahim din hannun ta dauke da wasu tablet sai ruwa a cop din tangaran me garai_garai,ajiye littafin dake hannun shi yayi yana ya mutsa fuska saboda yasan me auntyn tazo bashi,zama tayi a kusa da shi tana cewa meye kake wani haɗe rai sai kasha maganin nan idan ba haka ba yau na hana jin shirin labarin masoya" kuma ko ka kaje bangaren goggo ko inna maimuna su ma ba za su Barka ba tun da suna so ka samu lafiya",da sauri ya bude bakin ta watsa masa maganin tare da kafa masa kofin a bakinsa ,haɗiyewa yayi badan ransa na so ba, cikin sanyin sa da ya riga ya zamar masa jiki ya ce da auntyn Please aunty wannan maganin da kike bani na miye? Na mutuwa ne ta bashi amsa tana haɗe fuska tare da barin wajen dan kar ma tambayar tayi tsaurin da zata janyo tayiwa Rahim din faɗa,(azahirin gaskiya ba ko wane magani take bawa RAIHAN ba illa maganin tsaida jinin al'ada saboda duk wannan yana daga cikin tashin hankalin ta saboda shine abu na farko da RAIHAN zata fara yi ta gama tabbatarwa Ita din fa macece ba namiji ba)bin auntyn yayi da kallo yana dan tura baki irin na shi bai ji dadin nan ba,ko ta bani ba zan kuma hadiyewa ba tunda Ni dai na san lafiya ta kalau". Duk fuskar wanda ka kalla a zahiri za kaga farincikine kwance a kanta,kasancewar yau suna tare baki dayan su family guda su Affan ne kawai ba sa nan,amma hatta da Baffa Ali da Abba yahya da inna maimuna duk suna gurin,duk da cewa dama a sashen su a kayi wannan haɗuwar wadda ta kasance suna yin ta duk bayan wata uku,ba dan komai ba sai dan zumunci da kuma jin matsalar kowa daga cikin su sai kuma hirar da take gudana a tsakanin su duk dan kara son karfafa zumunci da hadin kai da Baffa Ali Yake so ya karu a zuriyar tasa. A bangaren aunty Amarya kuwa wannan zama sam baya yi mata dad'i hasali ma fargabar zuwan sa take yi,a ganinta wata rana za a iya Ankara da sirrin da take faman ɓoyewa tsawan shekaru goma sha biyar ,sai dai ta wani bangaren zaman yana mata amfani ta wajen son gano maƙiyansu a cikin fuskokin da suke zagaye da su,duk kuwa da cewa har yau din bata gano komai ba,kuma hakan shi yake kara cusa mata wata irin fargaba,tunanin ta har tsawon wani lokaci zata kai tana ɓoyan RAIHAN?bayan kuma ita ta sani Dr ya sani sanin mutanen shi kadai ne hanyar bude sirrin RAIHAN, shin RAIHAN zata yi ta zama a matsayin Rahim ne? Ko kuwa zata hakura da rayuwar RAIHAN ta bangakada sirrin ɓoye?,su kuma makiya su farma rayuwar RAIHAN,daga karshe kuma ita ce da asarar ,tunda har yau bata kuma yin ko ɓatan wata ba bare saran samun wani ɗan,wanda kuma bata jin koda ta haifi wasu yaran zata iya hakura ta fansar da rayuwar RAIHAN sanyin idaniyarta,wata ƙwayar halitta da take jin tana mata son da bata yiwa kanta da rayuwarta,share zufar da ta fara tsatstsafo mata tayi tana jin kamar zata yi aman zuciyarta saboda tashin hankali da rudani. Maganar Abban Bashir ce ta dawo da ita daga zuzzurfan tunanin tashin hankalin da rayuwar su take ciki,gyaran murya ya yi tare da fara wa da addu'a kamar yadda suka saba,bayan sun shafa sai ya fara jin damuwar kowanne,shi kuma Abbie yana rubutawa,idan wata kuma matsalar bata shafi kudi bace sai su tattauna har a samo mafita dan gyarata,daga nan kuma a ka ci abinci ,sai kuma zaman hira wanda shine aunty amarya bata so,a ƙage take da ta bar wajen saboda yadda kanta ya dau zafi dan anzo lokacin da ya kamata ta nemowa kanta mafita tun kan abin ya zama daga neman gira. Da kyar ta iya daidaita kanta a ka kammala hirar,amma fa duk tunanin ta ba ya gun ,Dan ba abinda ta fahimta bare ta rike akan abinda aka tattauna,jan hannun Rahim dake jingine jikin Abban Bashir tayi suka wuce sashen ta tare da rakiyar Abbie ,kasancewar girkin momy ne yau. **** WAZIRI CHIBADO HOUSE A hankali kuma cikin nutsuwarsa wadda take haɗe da tsananin kamewarsa,wanda shine yake ƙara fidda zahirin kyau da haibarsa tare da tsananin kwarjinin sa,yake saukowa daga saman Benen da yake ɓarin hagu ta cikin hamshaƙin main falon nasu,a hankali ya sunkuya daga gefen hamshaƙiyar matar da take zaune cikin wadatacciyar kujerar da tafi kowacce girma da kyau a cikin saitin kujerum falon,tare da kai mata sumbata a gefen fuskar Tata,a lokaci daya kuma yana gaida ta cikin yaran fillanci,murmushi ne ya ƙawata kyakkyawar fuskarta wadda take kama da tasa tamkar an tsaga kara,kamo hannun sa tayi tana cewa zo nan wazirin gida yau a gabana zaka yi karin kumallo saboda na gaji da ganin kana fita da yunwa bayan idan ka fita ɓaɓatu kake yi kana karawa kanka yunwa"Ni wallahi har mamakin ka nake ta yadda kake iya zaro zance bayan kuma ba haka ɗabi ar ka take ba"a hankali ya kai hannu ya shafa tattausar suman kansa wadda take kwance lamban ta ainahin Fulani tana ta sheƙi,kafin ya samu damar tanka mata tuni ta daga murya tare da kwala kiran lantana,cikin ƙananan lokaci lantana ta bayyana da abinda ta tabbata shine makasudin kiran,tana cewa gani Hajiya inna wuro,ran wazirin gida ya daɗe" cikin kamewar shi ya ce" yauwa lantana ya aiki? Alhamdulillah sai godiya"ta faɗa tana jera kwandunan da ta fito da su daga kiching. Inna wuro da kanta ta zuba masa kayan karin tasa ka shi a gaba har sai da ta tabbatar ta gamsu da irin cin da yayi,tun. Da dama ba wai cin abincin ne ba ya yi ba,kawai dai ba zai zauna ya ci ba ne,kullum cikin sauri yake ,kuma idan ya fita ba ci yake ba saboda baya iya cin abincin waje indai ba ya yadda da ingancin sa ba kuma ya zamar masa dole ba. Yana gamawa ya mike tare da goge bakin shi da tisue,kana cikin nutsuwarsa din ya ce"inna wuro zan shiga wajen su Abba daga nan zan wuce office" to wazir Allah ya taimaka ya bada sa a, Allah ya kare min kai a duk inda kake"cikin jin dadin addu ar da kakar shi ke mishi a kullum ya amsa kyakkyawar fuskarsa na bayyana ƙaunar da yake yi mata,har ya fita cikin takun shi na cikakkun maza masu kwarjini da haiba tana bin shi da kallon ƙauna me tarin yawa wadda bata ɓoyuwa ko da taso ɓoyewar,numfashi taja tare da kiran lantana ta kwashe kwanukan ita kuma ta kuma maida kai ta kashingida idanun ta akan gidan tv tashar chibado FM. Cikin dan gaggawar da ta nuna a tare da shi ya gaida ,Ammi da Abbu na shi ,cikin kaunar da suke nuna masa suka amsa ,kafin haihuwar kannen shi ta biyo baya,ba tare da ya dubi kowannen su ba ya masa yana mai kokarin ficewa daga falon,Ammi ta ce" Allah ya sa dai wannan shegen saurin naka ya Barka ka karya a nutse? Abbu ya ce" ke ma kin san innawuro ba zata bar shi haka ba" da wannan amsar da abbu ya bawa Ammi ya samu ya kufce ya fita daga falon cikin kakkarfan takun shi me cike da wata izzar nutsuwa. Alhaji WAZIR CHIBADO bafulatanin Yola ne cikakke,dan boko ne ko nace tsohon dan jarida ,wanda yayi suna a cikin jahar ta Yola,hakan ne ma yasa ya bude katafaren gidan tv da rediyo wadan da suka yi suna a cikin birnin Yola da Adamawa,harma da wasu jahohin ,mahaifin sa chibado ya dade da rasuwa kuma su uku kawai iyayen su suka haifa,daga yayar su inna batula sai shi sai kanin sa Mustapha, mahaifiyar sa me suna innawuro,ita kadai ta rage musu,a yanzu haka kuma suna tare a tamfatsetsen gidan sa,matar sa ɗaya Hajiya Binta wadda suke kira da Ammi,sai ya'yan su biyar ,bababban shine Ahmad wazir chibado,sai kalil wazir chibado sai umma rumana wazir chibado,sai kuma Nasiru WAZIR CHIBADO,da kuma auta me sunan innawuro wato Khadijah suna ce da ita shukrah, Kowannen su yayi karatun boko da addini me kyau da na garta,sun samu tarbiyya da soyayya daga gurin iyayen su,anyi auren umma rumana ba da jimawa ba ita da babban dan kawun su,safiyulla,kkhalil yana Amurika bai karasa karatunsa ba, Nasiru ne yazo hutu wanda yake kasar ƙatar wajen yayan Ammin su a wajen sa yake nasa karatun,auta kuma yanzu take shirin shiga jami a ,an zama yanmata, Ahmad kuwa dawowarsa ke nan,daga syprus a can ya yi karatun sa na jarida dake shekara uku ne sai ya ɗora da business account,burin sa ya yi aiki irin na mahaifin sa,to gashi yanzu daga dawowarsa ya fara aiki da sabon gidan rediyon da mahaifin sa ya gina musamman saboda shi,ɓangare biyu yake dauka,yana daukar bangaren binciken yan siyasa da zakulo manyan matsaltsalin da muke fama da su musamman akan siyasar manyan mu da yadda ake gudanar da ita,sai kuma ɓangaren nishaɗin masoya da yake gabatar wa a kowa ce ranar juma a da misalin karfe takwas na dare. Duk da matsayin da yake kai bai hana shi gabatar da shirin ba,a cewar sa bai samu wanda zai iya gabatar da shirin yadda ya kamata ba. Jajircewa da kamanta gaskiya yasa matsayin sa dagawa yaje har inda bai zata ba,sunan da mahaifinsa ya yi sai ya zamana ba komai ba ne akan yadda nasa ya yi,daukaka dai daga Allah ne to su dai Allah ya basu dan babu in da sunan AHMAD WAZIR CHIBADO bai kewaya ba. Innawuro macece fasifaffiya sai dai tana da mutunci ga san kyauta,amma fa idan ta ce bata son abu sai dai ka bita da yadda take so,sai abin da ta faɗa ta kuma tsara ,saboda ya'yan ta suna matukar yi mata biyayya ,shi yasa hatta da jikokinta suke mata biyayya bata daukar wargi ko kadan,tana matukar son Ahmad Wazir tamkar tayi masa numfashi haka shima yake sonta da son faranta mata,sosai yake mata biyayya kamar ita ce ta tsuguna ta haife shi,shi yasa ma gaba daya ya yi kaura zuwa sashen ta ,ko mai yake so tana yi masa,shi yasa shima yake faranta mata akan duk abinda take so. Wannan ke nan. Ahmad wazir chibado nutsutstsan matashi ne ,wanda yake cike da haiba da kwarjini irin na matasan samarin da suka san ciwon kansu, kyakkyawan bafulatani ne dogo me cike da kwanji irin na asalin barebari,kasancewar mahaifiyar su yar asalin meduguri ce babarbariyar Usul,miskili ne a ɗabi a da halayyar sa,amma a bangaren aikin sa yana kawar da wannan ɗabia tasa,amma duk da haka cikin zancan sa da yadda kalaman sa suke fita dallah_dallah zaka fahimci shi ɗin mutum ne kamamme mara son hayaniya,fatar shi ba fara ba ce ,sai dai tana da wata irin kala mai matukar kyau da ƙyalli ,wadda zamu iya kiranta da sama da ruwan tarwada,saboda ruwan tarwada ce amma kasancewar ta haɗu da hutu da gogewa yasa ta koma kala me tsada a cikin al'umma,bai da zafi ko saurin fushi amma yana da wahalar saukowa idan yayi mummunan fushi,yana da tausayi sosai shi yasa tun yanzu talakawa da kananan yara wadan da suka sanshi na kusa suke matuƙar kaunar shi da mutuntashi,hannun sa a bude yake ga duk wanda yayi katarin mikawa hannun,shirin da yake gabatarwa ya kara masa farin jini da daukaka a idanun matasa da kuma yanmata masu haukar sonsa da bai ma san da su ba.kadan ke nan daga dabiun AHMAD WAZIR CHIBADO,sai gaba zamu kara fahimtar wasu daga cikin halayyar sa. A ɗan kure ya shiga office ,ko sauraron staff din shi dake ta miko gaisuwa baiyi ba,saboda yau yaso yayi abin da tun da ya fara aiki baiyi shi ba,wato latty, sai da ya ji shi a cikin lafiyayyan officer din shi me kama da fadar shugaban kasa,kana ya samu nutsuwa, cikin kan kanin lokaci ya fara karbar bakuncin manyan mutane yan siyasa da manyan yan kasuwa,duk wadan da suke son a saka musu talla,saboda duk wanda yayi dace Ahmad wazir chibado ya karbi tallan sa,to tamkar ya fara kasuwanci ko siyasa a Sa'a ne, wannan farinjinin nasa shi yake taka rawar gani a duniyar 'yan siyasa da 'yan kasuwa,wanda mutum ko ba yaso sai yabi abin da ya tallata ya kuma bi shi har inda yake,hakanne yasa yan siyasa da manyan 'yan kasuwa suke rubububin mika tallarsu ga tashar me farinjin yaro matashi wato AHMAD WAZIR CHIBADO. Kamar yanzun dai ,da ya samu bakuncin babba kuma shahararren ɗan kasuwa kuma ɗan siyasar da zai fara damawa acikin wannan shekarar ta dubu biyu da ashirin da uku,kamar yadda kuka sani ne duk wani dan siyasa ko ɗan kasuwa yana son a talla shi domin samun kaiwa ga cimma nasara a kan burin su da kuma kudirin su, shahararren ɗan kasuwa wanda a yanzu ya juya ya koma dan siyasa ,wato Alh Garba me fata,da kan shi ya tako ba sako ba wanda shi yanbarwa kan shi dalilin zuwa kafa da kafa. Bayan ya samu ison shiga office din ,ya bar gerd din sa a wajen kofar kamar wasu status, sallama ya yi cikin kamilalliyar Muryar sa,wadda a cikin Muryar zaka fahimci tsananin dattijantaka da kamala, cikin girmamawa A Wazir ya amsa yana miƙewa tsaye dan girmamawa ga mutumin da ya yi sa a da mahaifin sa ba ,wai dan yana me kudi kuma dan siyasa ba,musabaha su kayi cikin mutunta juna, sannan A. WAZIR,ya nuna mishi wajen zama,duban shi ya yi bayan ya zauna tare da haɗe hannayen shi guri guda ,cikin kammammiyar muryarshi irin ta matasan da suka san ciwon kansu,ya ce"Alhaji Garba muna yi maka Barka da zuwa da kuma ban hakuri akan rashin ganawar mu da wuri sakamakon kasa amsa kira da nayi", Alh Garba ya gyara zaman babbar rigar shi tare da yin gyaran murya duk a lokaci guda, sannan ya ce" babu komai mune da godiya ai mun san yadda abin yake dole sai ana daga muku ƙafa,dan haka kar Ka damu muna godiya abisa karramawa",jinjina kai A, Wazir ya yi daga nan suka hau kan ainahin abin da ya tara su,a wazir ya karbi tallan Alh Garba na siyasa,duk da cewa baya karbar talla sai yasa anyi masa bincike a bisa sahihancin abin da yake tallatawar,a cewar sa ba zai taba karbar tallan gurbataccen abu ba,saboda hakan zai iya ruguza duk wata kima ta su,amma a wannan gabar sai yake yiwa Alh Garba kyakkyawan zato saboda kowa yasan shi yasan halinsa da kuma nagartarsa,duk kuwa da cewa sanin zuciyar mutum sai Allah,kuma shi ma ba ya karba haka nan bane ,ya karba ne kafin yayi bincike da tabbacin zai samu kyakkyawan sakamako daga Alhaji Garba,sallama su kayi cikin mutunci daga nan Alhaji Garba ya bar office din cike da farinciki. Yana shiga mota babban Aminin shi Alh Muhammad nuurr ya fara kira ya bashi albishir,saboda yana daya daga cikin masu karfafa masa gwiwa akan shugabancin jahar ta su,saboda yadda da aminci da kuma sanin halin Dattaku Da amana irin na Alh Garba,kai tsaye Alh Muhammad nuurr ya sanar da shi ya same shi a gida su tattauna batun. ******** Rahim lafiyar ka kuwa ka zauna ka haɗa tagumi kamar wanda uwarsa ta mutu,cewar jiddo ke nan(jikar ƙanwar Hajiya goggo da ta dauko ta tun shekarun baya)zame hannun shi ya yi,tare da kirkiro murmushi kan kyakkyawar fuskarsa har gefan kumatunshi daya tana lotsadawa,ya ce" babu komai kawai dai ina tunanin yaushe zan fara zuwa school ne kamar yadda Anty amarya ta faɗa"jiddo ta zauna gefan shi tana cewa kai ma dai dan uwa Rahim ai kasan zaka je school,me ye na wahalar da kanka da tunani? Ɗan yatsuna fuska ya yi sannan ya ce" tsoro nake ji kar Anty amarya ta hana Ni zuwa,bayan Ni kuma burina bai wuce nayi karatu ba,ko dan na zama ɗan jarida kamar A Wazir chibado"dariya jiddo ta yi kana ta ce" dalla ka share Ni nasan cewa Anty amarya zata Barka kayi karatu kamar yadda kowa na gidan nan ya yi"Allah yasa ya fada cike da alamun karaya,daga nan ya ware su ka ci gaba da hirar su. Cikin dare Rahim ya tashi da wani matsananciin ciwan mara,shi kadai yadinga birgima saman katon gadon sa. Farkawar ta ke nan ,ta shiga bathroom,bayan fitowar ta ,sai ta kasa komawa ta kwanta ,duk da cewa bata jima da duba Rahim din ba,Anty amarya na kula da Rahim sosai ,saboda duk tashin da ta yi sai taje ɗakinsa ta duba shi ,sam bata sake a bangaren kula da sanyin idaniyarta,a hankali ta tura kofar dakin bayan ta saka safaya key dinta,,da wani irin hanzari ta karasa bakin gadon da Rahim ke kokarin faɗowa saboda juyin ciwon da yake yi,ɗago shi ta yi tana cewa lafiya Rahim me ya same ka haka? Dakyar ya yi mata nuni da cikin sa saitin mararsa,da gudu ta koma dakinta,ta dauko waya,hannun ta har rawa yake wajen danno lambar Dr Sabo,sai da kira wajen sau biyar sannan ya dauka a na shidan ,cikin alamun bacci yayi sallama,ba tare da ta tsaya gaisuwa da amsa sallamarsa ba,ta shiga koro masa bayani,tashi zaune ya yi yana ture matar shi dake bacci a jikin shi,ya ce" ok Amarya ki nutsu yanzu zanyi miki bayanin yadda zaki bashi taimako kafin gobe ku karaso asibiti"ok Dr Amma kasan fa Abbie shi yana gari ina tsoro ko wata matsalar ce,saboda nasan dole shi zai ce zai kawo shi ,tun da yanzu da asuba tayi zaka ga yazo ta dashi suje masallaci kaga kuwa dole sai yasan halin da ake ciki"calm down karki damu da wannan ko da tare kuka zo kin san ba zanyi abinda zai kawo matsala ba,zan bashi wasu bayanan daga baya ke sai nayi miki bayani,saboda Nima naga alamun ciwan kamar ya danganci sirrin mu"shike nan Dr Sabo"ta faɗa tana shafa kan Rahim da ya dan fara samun nutsuwa saboda ɗumin jikin uwa,kamar yadda yayi mata bayani haka ta yi masa ,cikin ikon Allah kuwa Rahim din ya samu bacci,a jikinta,jingina ta yi da makarin gadon tana sauke ajiyar zuciya,a duniya babu abinda yake saurin firgita Anty amarya da saka ta cikin mummunan damuwa kamar abinda zai taba Rahim ko wane iri ne. Har asuba bata samu kara rintsawa ba,Rahim na jikinta tana tattalin lafiyar sa,a hankali ta janye shi taje ta dauro alwala,tana fitowa taji knock din Abbi yana kiran Rahim cikin taushin murya,da sauri ta fita tana cewa Abbien Rahim kayi hakuri ka tafi masallaci Rahim baya jin dadi tun jiya da dare"da sauri ya nufi dakin yana kiran subhanallah amma shine baki sanar dani ba,antyn Rahim?kar ka damu cikin dare ne kuma na kira Dr Sabo ya gwada min dabarun da zanyi masa kafin mu karasa asibiti shi yasa ma har ya samu yayi bacci" ajiyar zuciya Abbin ya yi tare da shafa kan Rahim din yana cewa shike nan bari naje kar na makara idan na dawo sai ku kimtsa muje muga likita" Tom shike nan sai ka dawo" fita yayi ya dan waigen Rahim din kamar ance masa idan ya dawo ba zai ganshi ba. Ajiyar zuciya Anty amarya ta sauke ,kafin ta kabbara sallah,sai da ta idar sannan ta tashi Rahim din ,ta raka shi ya dauro alwala,bayan yayi Sallah ya koma jikinta ya lafe yana sauke ajiyar zuciya,shafa kanshi ta yi cikin taushin murya ta ce" Sweet ya cikin ya rage maka ciwon? Ɗaga kanshi yayi kafin ya bude baki a hankali ya ce" Anty ya daina amma ba duka ba" ok my boy kar ka damu yanzu Abbin ka zai dawo muje Dr Sabo ya duba ka"jinjina kai ya yi yana mai lumshe idanun sa. Yau ko zaman da ya saba yi a masallaci bai yi ba,Baffa da Abba yahya ne suka lura da dakuwar shi har suka takbaye ko lafiya,Rahim ne ya ke ciwon ciki tun daren jiya, subhanalla cewar Baffa shima da damuwa ta kwanta saman kyakkyawar fuskarsa, Abba yahya ya ce",ya kamata muje Asibitin a duba shi ciwon yaro kamar Rahim ba shi da dad'i", ganin yadda suka shiga damuwa yasa abbie ya ce kar ku damu ya yi sauki yanzu zamu je idan da wata damuwa sai na sanar da ku",to Allah ya bashi lafiya Baffa da Abba suka hada baki wajen fada,daga nan ya shige bangaren aunty amarya da damuwar rashin lafiyar Rahim din,kai tsaye dakin Rahim din ta wuce, ya same su Rahim kwance jikin Anty amarya,da alamun san komawa bacci a tare da shi,zama yayi gefan su yana shafa kan Rahim din cikin wata irin soyayya da kauna ,ya ce" Rahim ya jikin naka? Jin Muryar Abbien shi yasa shi saurin bude ido,take fuskarshi ta yalwata da murmushi ,a hankali ya zame daga jikin Anty amarya ya koma jikin Abbin shi ya lafe, sannan ya ce" Abbie Barka da safiya? Barka dai my Love yajikin naka? Alhamdulillah Abbie da sauki" zuba musu ido Anty amarya ta yi zuciyarta cike da sake saken da kullum suke saka ta neman zaucewa,hannu yasa yaja dogon hancin ta yana cewa ya dai da tunani haka,antyn Rahim? murmushi ta kirkiro saman fuskarta tare da cewa kawai ina kallon wata ƙauna ne tsakanin ɗa da uba" dariya Abbie yayi cike da farincikin kasancewar Rahim a tsatson sa,ya ce" tashi ku shirya mu wuce asibitin kin san bana wasa da lafiyar Rahim". Lokacin da Abba yahya ya ke sanarwa da inna maimuna rudewa ta yi Sosai,sai da ya kwantar mata da hankali ya nuna mata cewa ba wani abu ne babba ba,duk da haka dai bata gamsu ba, ta hakura ne dan ba yadda ta iya. Abba yahyan ma hali yake, dan suna matukar son Rahim kamar su suka haife shi. Fateema y Adam..........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page5 ``` Ɗan jim Dr Sabo ya yi bayan ya gama bincike harma da scainin akan ciwan cikin Rahim din,wanda bayan ya gama binciken ya tabbatar da cewa ba ciwan ciki bane,tsananin ciwan mara ne ya kamu da shi a sakamakon magungunan da Anty amarya take bashi na hana yin jinin al'ada,duban ta yayi fuskarshi cike da tuhuma da tambayoyi na me yasa ta yi hakan bayan tun tuni ya ce ta daina bashi sakamakon binciken sa da ya nuna masa cewa hakan zai iya zama babbar illa a tare da lafiyar mahaifar RAIHAN ɗin,likita kayi shuru baka ce komai ba ina fata dai ba wata babbar matsala ba ce"Alhaji Muhammad nurr ya tambaya fuskar shi na nuna tsananin damuwa da fargabar da ya samu kanshi a cikinta. da sauri Dr Sabo ya daidaita kanshi cikin jawo jarumta,ya ce" a'a Alh kar ka damu ba wata matsala ba ce,ɗan ciwan ciki ne kawai wanda ya yi shi sakamakon yawan cin kayan zaƙi da yake,amma ga magunguna na rubuta insha Allah ba wata matsala sai dai a kiyaye da irin zakin da zai dinga sha"ajiyar zuciya Abbie ya yi tare da duban Anty amarya da tayi tsumu_tsumu zuciyarta cike da fargaba dan tasan ma anar kallon da Dr Sabo ya yi mata,ya ce" kinji dai antyn Rahim sai ki dinga kulawa tun da ke ce kike tare da shi ko da yaushe idan kuma ba zaki iya kiyayewa da kulawa min da lafiyar Rahim ba,sai na dauke shi na ta fi da shi can kalfoniya ,idan yana kusa da Ni sai na fi samun nutsuwa,tun da ke nayi nayi ki bini can din kin ƙi"ya karashe maganar idanun sa akan Rahim dake lafe a jikin sa. Gaban Anty amarya yayi mummunan faduwa ,cikin sauri ta ce" a'a Abbie wallahi zan kula sosai ,insha Allah ba zaka samu damuwa akan haka ba"jinjina kai ya yi yana mai mamakin yadda bata son su zauna kusa da shi ita da Rahim ko kuma shi Rahim din yayi nesa da ita,baya son zurfafa bincike akan abin da yake ganin ba shi da wata hujja ko makama ,dan a ganin shi har yanzu Anty amarya bata waye ba,kasancewar rayuwar da tayi me tsawo har girmanta a cikin jeji,duk kuwa da cewa yanzu tayi ilimi kuma tayi cuɗanya da manyan mutane matan abokanan sa,da kawayen ta yan makaranta. Maganar Dr Sabo ce ta dawo da shi duniyar mutane,Dr Sabo ya ci gaba da cewa shike nan, Alh zaku iya tafiya"musabaha su kayi da juna kana suka bar office din ,zuciyar Anty amarya cike da tunanin matsalar da Dr Sabo ya gani tare da RAIHAN. Suna fitowa wayar Abba yahya ta kuma shigowa wayar sa ,dan tun zuwan su asibitin yake kira dan jin halin halin da ake ciki, wannan kauna da Abba yahya da matarshi suke nunawa Rahim na daya daga cikin abin da yake kara musu zumunci da kaunar juna,ɗaga wayar ya yi ya kwantar masa da hankali,ya ƙara da cewa ga su nan ma zuwa gidan yanzu,da wannan ne duka suka samu nustuwa har su goggo Rahman da Baffa. Har bayan kwana biyu lokacin Abbie ya dawo ɓangaren Anty amarya,bata ji komai daga Dr Sabo ba,hakan kuwa ba karamin tayar mata da hankali ya yi ba,ji tayi ta ƙagu Abbie ya bar ƙasar,zaman shi a wata ƙasar shine kwanciyar hankalin ta,duk irin son da takewa mijin nata sam bata son ya ce zai zo kasar ,saboda gudun samun matsala akan sirrinta,da kyar ta iya daidai ta kanta ta dawo da walwalarta,har zuwa ranar da ya bar ƙasar,ranar kuwa daga filin jirgi asibiti ta wuce kasancewar a dakin ta ya tafi ita ce ta kaishi filin jirgi ita da Rahim. Zugum ta yi tana duban Dr Sabo,idanun ta cike taf da hawayen tashin hankali,Dr Sabo ya ci gaba da cewa ,gaskiya amarya idan ba muyi gaggawar samun mafita ba,zamu cutar da rayuwar RAIHAN,karshe ma muyi abinda zai iya sanadin rayuwar da muke yin komai saboda ita"cikin kuka Anty amarya ta ce" dan Allah Dr Sabo ka taimaka min kamar yadda ka saba idan na rasa RAIHAN nima mutuwa zanyi"amarya yanzu fa duk wata dabarar mu ta kare,abu daya ne ya rage mana shine sanar da RAIHAN ita din ko wacece,tun da ko ba mu sanar da ita ba dole ne ta sani,saboda kullum girma take yi matakan budurci na hawa kanta,yanzu wannan abin da ya faru ina tabbatar miki da cewa shine matakin farko da RAIHAN zata gama tabbatar da jinsin ta,saboda watan da zai zo dole sai ta yi al'ada,kuma RAIHAN ba jahila ba ce,da ilmin ta,dan ko a yanzu na tabbatar hakuri kawai take take kawar da kai amma tabbas zuciyarta na cike da tunani da rudani iri_iri wanda kuma idan ba muyi hanzarin kawar mata da wannan tunani ba shima zai iya zama babbar illa ga lafiyar ta"ajiyar zuciya Anty amarya tayi ,kana cikin damuwa ta ce"to yanzu Dr ya zanyi da wadan da suke neman rayuwar RAIHAN,dole ta sa nake BOYE RAIHAN saboda gudun kar a cutar min da ita kuma kaima kafi kowa sanin hakan,yanzu idan na gaya mata ta ina zan ci gaba da ɓoye ta dan kare rayuwarta? Amarya rayuwar RAIHAN a hannun Allah ta ke ba a hannun mu ba kuma ba a hannun wanda yake son kashe ta ba,mu dai namu shine mu zama sanadin rayuwar tun da Allah bai kawo karshen ta ba,kuma ko a yanzu muka bayyana RAIHAN ina ga ba muyi aikin banza ba tun da ta yi girma ta yi wayo ta kuma fara sanin ciwon kanta,,,,katse shi Anty amarya ta yi da sauri tare da cewa a'a Dr Sabo har yanzu RAIHAN yarinya ce bata isa kare kanta ba,na yadda da maganar ka kuma Nima nasan haka,Amma kasan da cewa Allah da kansa ya ce ta shi in taimake ka,babu ta yadda za ayi kana zaune a inuwa Allah ya yi maka abu dole sai da sanadi,to rayuwar raihan tana hannun Allah amma mune sanadin dorewar rayuwar tata" jin jina kai Dr Sabo ya yi kafin ya dan numfasa ya ce"na fahimce ki amarya kuma nayi miki uzuri na kasancewar ki uwar da take matukar so da kaunar ɗan ta da kuma son ganin yayi rayuwa me tsayi,na fahimce ki a matsayin ki na uwar da bata da kowa sai wannan tilon dan da ake son ganin bayan sa,dan haka nayi alkawari zan ci gaba da taimaka miki har zuwa inda numfashi na ya tsaya da kuma bayyanar makiyan ɓoye"na gode Dr Sabo Allah Ubangiji ya sa ka maka da alheri Allah ya raya maka zuri'a Allah yasa ka gama da duniya lafiya"Amin ya Allah ya fada cike da jin dadin addua daga bakin wadda yake gani kamar y'ar uwar shi ta jini. Cikin fesar da iskar da take bakin shi ya ce"amarya amma duk da haka bamu da wata hanyar bayan wadda na fada miki,dole sai dai mu sanar da RAIHAN ko mai,amma ba ina nufin Mu bude sirrin ɓoye ba,dole RAIHAN sai ta bamu hadin kai a wannan gaɓar"kamar ya ke nan Dr ? Anty amarya ta tambaye shi cike da zakuwar san jin manufar hakan,ɗan cizon bakin biron da ke hannun shi ya yi,kafin ya ce" dole RAIHAN zata ci gaba da zama a matsayin namiji bayan ta san ko ita din wacece" shi yasa nace miki dole sai mun samu hadin kanta, wannan ita kadaice hanya ,kin ga mun jefi tsuntsaye biyu da dutse guda daya,wato mun kawar da damuwar RAIHAN ta hanyar sanar da ita ko wacece,idan yaso sai muji da fara binciken makiyan RAIHAN " Dr Sabo ta yaya zamu gane wadan nan mutanen? Murmushi Dr Sabo ya yi sannan ya ce" amarya ba zamu iya gano makiyan RAIHAN ba dole sai ta hanyar ta" kamar ya ke nan,ta tambaye shi cike da mamaki,muskutawa ya danyi Sannan ya dube ta ,ya ce" amarya gane makiyi sai Allah,idan har ba bayyana RAIHAN wa duniya mu kayi ba to tabbas ina mai tabbatar miki da cewa sai dai muyi ta bulayi wato lalube a duhu,mu bar Raihan a ɓoye zuwa nan da wani lokaci wato lokacin da zata san kanta lokacin da ta zama cikakkar budurwa me shekaru goma sha tara zuwa ashirin,to mu kuma alokacin ne zamu bayyanar da ita ga kowa ,dan mu janyo hankalin masu san ganin bayanta,a yanzu raihan bata da wayo ko hankalin da zata fahimce mu da manufar mu,dan haka mu bar wa lokaci komai ,yanzu dai mu yi wannan matakin na gaba,amma shima kar ki sanar da ita kai tsaye sai nazo akwai hanyoyin da zamu bi mu sanar da ita ba tare da ta shiga tashin hankali da rudani ba,fata na dai kawai mu sanar da ita da kanmu,idan muka bari ta fahimta da kanta baza mu shawo kan ta har ta bamu hadin kai ba"ajiyar zuciya Anty amarya ta saki ,sai alokacin wani dan takaitaccen murmushi ya sibuce mata,tare da samun kwanciyar hankali,ta ce" to shike nan Dr Sabo na gode Allah ya nuna mana lokacin ya bamu a ran rai da lafiya,Amin ya Allah"ta shi ta yi tana cewa bari naje nasan yana can mota ya kumbura dan fushi ,saboda dakyar na lallaba shi ya zauna"ok tom shike nan amarya sai kin jini"daga nan ta fita daga office din tana mai jin yar nutsuwa a ranta. Ko da ta samu Rahim a mota ya cika taf din kamar yadda ta faɗa,shafa kanshi ta yi tana murmushin samun nutsuwa, cikin tausaya wa ta ce,"sorry my friend na jima ko? Ɗan karamin bakin sa ya tura kana ya dubi a gogon dake daure a siririyar tsintsiyar hannun shi,sannan ya sube ta a shagawabe ya ce" Anty amarya kin san tun dazu akayi sanarwa A Wazir zai yi hira da Alh Ibrahim mangal shahararren ɗan kasuwar nan kuma fitaccen dan siyasa ,akan dalilin sa na komawa jam'iyar adawa wato jam'iyar su Alhaji Garba Me fata" rike baki Anty amarya ta yi cike da mamakin yadda Rahim ya iya zaiyano wannan lissafin,kafin ta ce" to Rahim kai meye damuwarka da siyasa da ka damu sai kaji hirar?ta tambaye shi Daidai lokacin da take harba motar bisa kwalta bayan fitowa daga harabar asibitin,karyar da wuya Rahim ya yi cike da sangartar da ke nuni da tsananin gatan sa,ya ce" Anty ke ma kin san ba wannan nake son ji ba,A Wazir chibado kawai nake son gani" to shike nan my Love kar ka damu kayi hakuri zaka samu ji tun da har yanzu da sauran awa daya a gaba" da wannan hirar su ka karasa gida,sai da Anty amarya ta tabbatar ta bawa Rahim magungunan sa sannan ta shiga sabgar gida, ta bar Rahim da jiran lokaci. Ba Rahim kadai ba,zan iya cewa gaba daya kusan daukakin mutane jiran wannan hira suke,wadda ita ce damar su ta farko da suka samu dan ganin fuskar wazir chibado,a zahirin gaskiya da yawan mutane ba ta hirar suke ba ,ta yadda kawai zasu ga fuskar WAZIR CHIBADO ne,dan da yawa basu san ainahin fuskarsa ba,sai daddaɗar muryasa da ta gewaya birni da ƙauyuka harma da wasu kananan jahohi,ƙalilan ɗin mutane ne wadan da siyasar ke tsakiyar kansu suke daukin jin makasudin abin da yasa Alhaji Ibrahim mangal sauya sheka. Yanmata kuwa bazan iya kirga adadin su ba,ko wacce ka kalli fuskarta sai kaga annuri da farincikin ganin gwarzan matashi me farinjini a duniyar matasa, To a dai-dai wannan lokacin ma Hajiya innawuro ce zaune a hamshaƙin falonta ita da jikarta wadda ta samu bakuncin zuwan ta safiyar yau ɗin,gaba daya sun zubawa ƙatuwar tv flaxuma ido ,tare da ɗan satar kallon a gogo,zuciyar rabi a cike take da dokin yin tozali da fuskar dan uwanta yayanta kuma rabin ranta wanda kullum take mafarkin ya zama angonta,duk da cewa ita din fuskarshi ba bakuwar ta ba ce,to amma sai taji yau ta zamar mata bakuwar kasancewar jimawar da tayi bata ganshi ba,dan lokacin da ya dawo daga karatu ita kuma suna jarrabawar karshe shi yasa bata samu zuwa ba,shi yasa suna kammalawa ta hado kayanta ta yiwa gidan tsinke,axewarta bata barin gidan sai da igiyar auren A Wazir. Karfe biyar dai-dai ƙatuwar tv flaxuma dake girke a bangon falon Anty amarya ta hasko kyakkyawa kuma kamilalliyar fuskar A, Wazir chibado a tashar nan ta su me farinjini wato CHIBAƊO TV. Wata yar zabura Rahim ya yi,yayin da zuciyar shi ta yi wani irin mahaukacin bugu,wanda ba zai iya cewa ga dalilin hakan ba,Anty amarya ma zubawa fuskar a wazir idanu ta yi,haka jiddo da ta gudo nan ta bar Hajiya goggo itama ta zubawa wazir chibado ido zuciyarta na bugu da ganin wani irin kwarjini da haiba tare da kamala a fuskar wazir, a hankali sassanyar Muryar shi me cike da wani irin amo wanda yake tafe da tsananin kamewa ta fara karaɗe kunnuwan masoyan sa da masoyan Alhaji Ibrahim mangal,idan kaga yadda yake fitar da kalaman sa abin zai matukar birgeka ya kuma kayatar da me kallon sa,tabbas mutane sun shaida baiwar da Allah Ubangiji yayi wa wannan bawa nasa,hira ce ta kasance tsakanin sa da baƙon sa cikin hikima da sanin makamar aiki ga kuma iya sarrafa harshe,hirar mintina talatin da yayi da bakonsa ta kuma janyo masa yawan mutane da shi kansa Ibrahim mangal ɗin wanda tun kafin ya bar gidan tv ya fara amsa sakon masoya wanda suke goya masa baya dalilin hirar sa da A Wazir ,hakan kuwa ba karamin farinciki ya sanya shi ba. To bare kuma mai gayya mai aiki ,dan har sai da kansa ya fara daukar ɗumin ciwo saboda amsa sakonnin masoya,da ƙyar ya takaita karbar sakonnin da dalilin gabatowar lokaci wanda hakan ne ya kwace shi ya baro dakin tattaunawar cike da gajiya da kasalar da ta rufe shi. Ko da ya koma gida bai tsaya wajen Innawuro ba bare ya amshi bakuncin rabi a,kai tsaye ya wuce sama inda anan bangaren sa yake,bath ya fada tare da sakarwa kanshi shaya,sai da ya ji dan dama kana ya yi wanka tare da ɗauro alwalar magriba. A masallaci suka ci karo da mahaifin sa,daga nan suka yo sashen innawuro,kasancewar duk dare a nan suke haduwa gaba daya suna yin dinner,a nan suka samu Ammi da shukrah,gaida Ammi ya yi kana ya koma kusa da innawuro ya zauna tare da jingina kansa a kafadar ta,alamun shi ya nuna gajiyar da yake ciki sosai, shukrah ce ta fara gaida shi kafin rabi'a ta dora tata gaisuwar cike da kisisina ko kunyar su Ammi ba ta ji ba,kamar yadda ya amsawa shukrah haka ita ma ya amsa mata,duk sai taji jikin ta ya mutu na rashin nuna halin ko Inkula da ya yi da ita,duk da cewa ta san halinsa amma sai tayi tunanin wannan aikin da yake yi ya canja shi,to ashe har yanzu dai yana nan a miskilin sa,Ammi ce ta fahimci yadda gwiwar rabi a ta saki,hakan ya sa ta danyi gyaran murya tare da cewa babana rabi a dai an gama karatu ya kamata ka taya ta murna"ɗan duban Ammin ya yi idanun shi kamar masu jin bacci kana a hankali ya ce"nayi mata murna, Allah yasa ya amfani al'umma "take kuwa fuskar rabi a ta washe har sai da kowa ya fahimci farincikin ta a fili,kowa ya fara cin abinci cikin nutsuwa, kamar yadda ɗabi a kuma ya kasance koyarwar ma aiki,idan suna cin abinci babu me yin magana har sai sun kammala,to yanzun ma haka ce ta kasance,A Wazir bai ci loma sama da biyar ba wayar shi ta fara haske alamun kira,ɗan zubawa wayar idanu ya yi ,duk da cewa wayar pasinal din shi ce ,hakan bai hana shi mamakin me kiran a wannan lokaci ba,har zai share sai kuma ya yi tunanin ba ko wane yake da wannan layin nasa ba,dan haka ta iya yiwuwa kiran yana da muhimmanci, a hankali ya kai hannu ya dauki wayar tare da danna ok,haka kawai ya samu kanshi da wani irin faduwar gaba har bai san lokacin da ya kwantar da kanshi jikin makarin kujerar dinning din da yake zaune ba,tare da rufe idanun shi duk a lokaci guda, a hankali kuma a nutse sanyin Muryar Rahim ta cigaba da cewa Assalamu alaikum A Wazir ne akan layi? Ta fadi haka saboda jin ba a amsa mata sallamar ta ta farko ba,Muryar shi a ɗan shake ya ce" I'm ,dariya Rahim ya yi wadda ta yi gudun fanfalaki ta shige kunne har da jijiyoyin jikinsa,a wani irin bazata Muryar tazo masa,sai kuma ta saukar masa da wani irin yanayi da kara masa kasala da gajiyar da yake ciki,Rahim ya ce"Ni fand ɗin ka ne kuma masoyinka,sunana Abdul Rahim Muhammad nurr,kuma muna gari daya jaha daya,ina fata zaka karbe Ni a matsayin a boki na musamman kuma ƙani,wani kayataccen murmushi Ahmad ya saki wanda tun shigowar sa gidan babu wanda ya ganshi a saman fuskarsa sai yanzun,shi kuwa ba komai ne ya sashi murmushi ba sai jin yadda Rahim ya dage yana introduced din kansa ,babu kwama bare full stop,duk da cewa bai cika son mutum me surutu ba,amma sai yaji Rahim ya burge shi yanayin yarintar shi ya kayatar da shi,dan haka cikin Muryar shi da a yanzu ta dan saki ya ce" thanks Rahim Nima Ina sonka kuma na karbe ka a matsayin abokina kuma amini dama bani da amini abokin shawara,dan kwabe fuska Rahim ya yi kamar yana gaban shi sannan ya ce" to bandirawo wazir amma fa wannan ba waya ta ba ce wayar Anty amarya ce ,Abbie na ya ce zai sai min waya ita kuma ta hana ,amma yanzu dole a saimin waya tun da nayi aboki". Wazir ya kuma ƙawata fuskarshi da murmushin da yake matukar wuyar samuwa a kan fuskar shi sannan ya ce" na gode Rahim zan ajiye nomber antyn ka,kafin lokacin da zata bari a siya maka",yeee Rahim ya fada yanayin murna wadda ke cike da yarinta,daga nan suka yi sallama kowa ya ajiye wayar, innawuro ta ce"wai har ka koshi ne wazirin gida? Shafa shafaffen cikin sa yayi har yanzu kuma fuskarsa a washe take duk da cewa ba murmushi yake ba,amma kana gani kasan yana cikin nutsuwar zuciya,ya ce" I'm ok granny kar ki damu an jima ki hada min fruet da hannun ki zan sha"yauwa to shike nan yanzu naji zanje,Abbu ya ce" ina zaune kirkiri an kawacemin uwa" gaba daya falon aka sa dariya,wazir kuwa lumshe idanun shi ya yi kawai. Bani wayata Sarkin surutu,kayi sa a ma da ya daga wayar taka,,langabe kai Rahim ya yi tare da cewa dan Allah Anty ki barni nayi waya, komai kin hanani karatu waya da duk wani abu da zai sa na samu farinciki"ya fada idanun shi na cika da hawaye kuma hakan shi yake nuna raunin sa da tsananin damuwar da yake ciki a kan haka,da sauri ta dawo kusa da shi tare da kama shi ta kwantar da kanshi saman kafadunta,cikin damuwa ta ce" No Rahim bana so ka tuhume Ni a matsayin uwar da bata son farincikin danta duk abin da ka nema zan yi maka kuma duk wata walwala da ka rasa zan dawo maka da ita zan sa a kai ka University joda ka karanci media zan cika maka burinka na zama cikakken dan jarida,da wani irin farin ciki ya rungume antyn yana cewa da gaske kike Anty amarya duk abin da kika fada zaki yi min? Zan yi maka Rahim amma da sharaɗi"ta faɗa tana mai ɗago fuskarsa dan tana son ya gano gaskiya a cikin idanun ta,meye sharadin Anty amarya? Sharadin shine zaka ci gaba da ɓoye mana kanka ta yadda babu wanda zai fahimci kaiwaye kuma wane jinsi ne,dole sai kayi mana wannan alkawarin tare da yiwa mahaifiyarka biyayya akan hakan"Dr Sabo ke nan da ya shigo akan gaɓa ya bawa Rahim amsar tambayar sa ,wanda zaman na jiran zuwan sa ne. Fateemah y Adam.......... ✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page6 ``` ....Da sauri Anty amarya ta tashi ta duba waje ta leka ko ina, sannan ta gyara contain ɗin falon ,zuwa ta yi gaban tv ta kara volum,shi dai Rahim kallo yake bin ko wannen su da shi,dan kwakwalwar shi ta kasa hasaso masa komai,iya kacin sa jiran tsammani,zama Anty amarya ta yi a gefan sa yayin da Dr Sabo yake fuskantar sa. Kama hannun sa Anty amarya ta yi idanun ta cike taf da hawaye,ta ce" Rahim nayi maka babban laifi wanda ban sani ba ko har da Ubangiji na nayiwa saboda nayi shishshigi cikin lamarin sa,duk da cewa so ne ya rufe min ido da kuma neman mafita,dan haka nake kyautata zaton cewa idan ma nayi laifi gurin Allah insha Allah zai yafe min,haka kaima ina saran yafiya daga gareka ,duk abin da nayi saboda kaine saboda kar na rasa ka nayi kuma har yanzun ina kan baka na saboda Allah ya ce tashi na taimakeka,kuma ina so na zama uwar da ta zama sanadin kyakkyawar rayuwa me nisa ga danta,dan haka kafin na gaya maka komai kuma na cika maka alkawarin ka, sai Nima kayi alkawarin yi min biyayya akan abin da na umarce ka" duk da cewa Rahim ya shiga ruɗu amma ya aiyana cewa mahaifiyarsa baza ta taɓa cutar da shi ba,dan haka kai tsaye ya ce" Anty amarya nayi miki alkawari ko da baza ki cika naki alkawarin ba,Ni ya zamarwa wajibi da nayi miki biyayya dan haka babu sharadi a tsakanin mu akan abin da kike so nayi miki" da kyau yaron kirki wanda ya samu tarbiyya ta gari,cewar Dr Sabo ke nan da kalaman Rahim su kayi matukar birge shi da bashi mamaki a matsayin sa na yaro karami,sai dai kuma idan ya yi duba da cewa Rahim ɗin ya samu ilmi me zurfi da kuma ingantacciyar tarbiyya ,abin ba wani abin mamaki ba ne,dan haka ya dan yi gyaran murya tare da kara gyara zaman sa,ya ce" Rahim nasan ko baka fada ba akwai tarin tambayoyin da kake da su akan ka da kuma rudani da kake shiga na yanayin halittar ka" da sauri Rahim ya ɗago kansa yana zuba idanunsa masu sheƙi cikin na Dr Sabo,duk da cewa bai ce komai ba amma Dr Sabo ya kuma fahimtar yadda al'amarin yake matukar damun Rahim ɗin,wanda har hakan yake gab da shafar lafiyar sa,ci gaba ya yi da cewa Rahim kayi hakuri ka kuma gafarce mu,kai ba namiji ba ne macece mahaifiyarka ta haifoka kuma sunan ki shine RAIHAN" a wani irin zabure da matukar rikicewa RAIHAN ta mike tsaye tana mai nuna kanta bakin ta na wani irin karkarwa komai ya kasa fita daga bakinta,da sauri Anty amarya ta janyo ta ta rungume ta tare da sakin wani Marayan kuka me cike da ban tausayi,cikin kukan ta shiga bawa RAIHAN labarin asalin su da yadda komai ya faru har da yadda sunan ta ya samo asali da irin kaunar da Alhaji nurr mahaifin ta ke wa mace me suna RAIHAN,komai bata bari ba har zuwa ranar da aka haife ta da kuma gundarin dalilin da yasa suka boye ta,shuru raihan ta yi tana sakin ajiyar zuciya, ya yin da kuma daga wani bangaren na zuciyarta yake son saka mata ganin laifin mahaifiyarta,wani kuma sai kokarin ture hakan yake da maye gurbin laifin da matsananciyar kauna da tausayi na mahaifiyarta harma da mahaifinta,nasihun da Dr Sabo ya shiga yi mata da kuma yi mata bayanin alkawarin da suke son ta yi musu, shi ya katse mata tunani,ya ce" RAIHAN ki daure ki ci gaba da zama a matsayin ki na Rahim a idanun duniya ,ke kadai ce yanzu muke da hope din zaki taimaka mana mu cimma gaci,ki duba halin da mahaifiyar ki take ciki da kuma wahalar da tasha akan boyanki,dan Allah ki bamu hadin kai"a hankali ta zame jikin ta daga na Anty amarya tashi tayi tare da barin falon ba tare da ta ce musu komai ba,dakinta ta Wada ta shiga rafsa kuka,kukan da ta rasa na menene , Da sauri antyy amarya ta bi bayanta ,amma sai taji kofar a rufe ,gashi safayar nata duka suna dakin tun da yanzu tare suke kwana,kuka anty amarya tasa tana cewa Dr Sabo na shiga uku RAIHAN bata fahimce mu ba,ta rufe dakin bana son damuwar ta kar wani abun ya same ta"ta faɗa tana mai sake rashewa da kukan,Dr Sabo ya ce" a'a amarya kar ki saurin yanke hukunci ki bari ta huce ta fita daga alhinin ƙaddararta,ni nasan cewa RAIHAN zata fahimce ki kuma zata bamu hadin kai ,ki yi hakuri ki bata lokaci,kin san dama dole sai haka ta faru"dor bell din da a ka danna ita ta zaburar da anty amarya,cikin sauri ta shiga goge hawayen ta da kokarin dai-dai ta kanta,zuwa ta yi ta bude kofar ,Hajiya goggo ce ita da jiddo,duban antyy amarya ta yi fuska a hade ta ce" ina Rahim ɗin? Cikin bugun zuciya da in ina antyn amarya ta ce",me ya faru goggo? Ai ke zan tambaya me ya faru ,tun dazu jiddo tazo gurin Rahim amma sai ta samu kun rufe kofa kuna azabtar da shi dan ta ce kukan sa kawai take. Jiyowa"Da sauri Dr Sabo ya mike yana gaida goggo bai saurari amsawarta ba ya shiga bata hakuri da cewa kiyi hakuri goggo Ba wani abu ake yi masa ba,kin san dai halinsa akan shan magani da allura,wasu ragowar magani ne da Allurai da ba akammala masa ba shine yake ta rigima wai ana damunsa da allura yanzu ma ya gudu dakin yaki budewa"goggo itama ta juya ta zubawa anty amarya ido kafin ta ce"anya babu abin da kike boye mana akan RAHIM? Cikin jan numfashi da karkarwar baki Anty amarya ta ce" babu komai goggo in da da akwai bazan boye miki ba" ƙwafa goggo ta yi tare da nufar dakin Rahim ɗin ta na cewa ,Ni dai ina gargadinki da babbar murya idan ma da wani abu a ranki"taba kofar ta yi ta ji a rufe kiransa su ka fara yi ita da jiddo,amma babu alamun zai bude kofar bare ya kulasu,haka suka gaji suka bar wajen Hajiya goggo sai masifa take akan anty amarya tana takurawa Rahim ,shi dai Dr Sabo tuni ya bawa kafafun shi iska tun kafin Hajiya goggo ta make shi,itama anty amarya Hakuri kawai take bata duk dan bata so ta zargi komai,a haka ta samu ta bar shashen duk da cewa bakinta bai yi shiru ba. Tun da RAIHAN ta kulle kanta a daki take kukan yadda kaddarar ta tazo, wannan wace irin rayuwa ce? Take tambayar kanta,ke nan haka zan ci gaba da boye kaina?me yasa tun baya ba su gaya min ba?yanzu ne suka ga ya fi da cewa da su sanar dake tun da ko ba su gaya miki ba,dole zaki gane saboda alamun balaga da su ka fara bayyana a jikin ki,da kuma ilmin da kika yi wanda ba dan kuruciya ba tun baya ya kamata ace kin gane ba tare da an gaya miki ba,wani bangare na zuciyar ta ya bata wannan amsar, murmushi ne ya suɓuce a, kan kyakkyawar fuskarta,a hankali ta tashi ta nufi jikin badubin dakin,zubawa kanta idanu ta yi tana mai tsarkake buwayar Ubangiji da kuma ƙara kaɗaita shi akan yadda yayi mata baiwa ta zamowa mace kuma ya bawa mahaifiyarta da Dr Sabo fikira da basirar ɓoye ta a matsayin mace da bayyana ta zuwa namiji. Take ta shiga kai kawo a dakin da tunanin umarnin Anty amarya,idanun ta ne suka kuma cikowa da kwalla tana jin jina yadda zata iya ci gaba da boye kanta tun da ta san dole tabi umarnin aunty amarya a matsayin ta na me son kare rayuwarta da taimakon Ubangiji,tabbas ta yiwa aunty amarya uzuri akan abin da ta yi ,to amma ita ta yaya zata fara fuskantar sabuwar rayuwarta a matsayin namiji?share kwallar ta yi tare da karasawa bakin ƙatuwar sif din kayanta,budewa ta yi tare zubawa sutturunta ido,yar ajiyar zuciya ta saki saboda yadda ta ga kaf kayanta manyan kayan sanyi ne masu wando da hula,mara sa nauyin basu da yawa,rufewa ta yi tare da aiyyana cewa haka nan zata ci gaba da saka su tana boye jikinta dan tsira da rayuwarta da kuma cika alkawarin Anty amarya har ma da son samar da nutsuwa ga mahaifiyarta abar kaunarta. Antyy amarya ta rasa sukuni da nutsuwa ,tun da RAIHAN ta kulle kanta,ko da me aikin su ta dawo daga aika , anan bakin dakin RAIHAN ta samu Anty amarya nazarya da kaiwa da kawowa,ko da larai ta tambaye ta cewa tayi Rahim ne baya jin dadi shine ya rufe kofar dan kar ya sha magani kamar dai yadda suka sanar da Hajiya goggo.da wannan amsa ta kawar da tunanin larai. Ranar dai yinin damuwa aunty amarya ta yi,wanda hakan da raihan ta sani ne yasa ,ta fito daga dakin domin samawa Anty amarya nutsuwa,ai kuwa da sauri antyy amarya ta janyo ta jikinta ba tare da ta ce mata komai ba ta jata suka shige ɗakin RAIHAN ɗin,haba RAIHAN ya zaki min haka ?dan Allah ki yi hakuri ki fahimce Ni kar ki min kallon muguwar uwa wadda bata son farincikin ƴaƴanta "da sauri raihan ta tare antyy amarya da cewa ,haba mamy dan Allah ki daina bani hakuri,Ni ce zan baki hakuri ba na gudu daki dan in bata miki ba,kawai na gudu ne saboda na samu nutsuwa da kuma yin tunani akan sabuwar rayuwar da zan fara na ɓoye kaina tun da yanzu da akwai banbanci da ban sani ba yanzu kuwa na sani dan haka dole nayi tunani a kan hakan"rungume RAIHAN antyy amarya ta yi tana sa mata albarka da fatan rayuwa me kyau a nan gaba. Dalilin hirar da A Wazir chibado ya yi da Alhaji Ibrahim mangal ya sa ta kuma janyowa jam'iyyar su farinjini gurin jama a,harma da abokan adawa wanda suma suka dinga zazzage rigar su suna juyowa jam'iyyar su Alhaji Garba,kafin kace me zan tuka sun fara yaɗuwa masu kyau da marasa kyau. A lokacin ne aka tsaida Alhaji Ibrahim mangal matsayin defity gomner, wanda da bashi aka so bawa ba, Alh garba so ya yi Aminin shi Alhaji Muhammad nuurr ya karbi matemakin,to amma sam ya nuna baida ra ayin siyasa,hakan ya sa ya ce a bawa Alhaji Ibrahim mangal,shi kuma Alh Garba ba dan komai yaso Aminin shi ya karba ba sai dan yadda ya tsaya masa da dukiyarsa wajen takarar,kuma har yanzu yana kanyi tunda ba wai anyi zaben ba ne,to amma ganin baya so dole tasa ya rabu da shi,daga karshe ma har karar sa ya kai gurin Abba yahya da Baffa,to su ma dai ba su goyi bayan shigar sa siyasa ba,amma sunyi na'am da ya ci gaba da bada gudummawar da yake badawa,da wannan aka kashe maganar. .......A bangaren A.Wazir kuwa ,sam shi bai da damuwa da hakan,hasali ma tun da aka yi hirar ya ture batun su ya manta su a babin sa,wanda bai san su a wajen su ba Haka ba ne,ya zamar musu tamkar wani linzamin da zai kai su ga nasarar abin da suke hari,hakan ya sa suke ta kulle kulle a tsakanin su duk akan A Wazir. A bangare daya kuma ya sakawa jam'iyyar adawar su Alhaji Garba tsananin tsanar sa,saboda suna ganin shi ne ya bawa alhaji Garba damar samun nasara akan su,duk da cewa ba ayi zaben ba,kamar su Alhaji ribodo da Alhaji sale me shanu,to shi dai A wazir duk bai san suna yi ba,daga wadan da ya yiwa dalilin nasarar da shi ma bai san ya yi ba,da wadan da ya yiwa dalilin faduwar da shi ma bai san ya yi ba.to bari dai mu bi su a hankali muji yadda abin zai kaya. A sannu a hankali shaƙuwa ta fara shiga tsakanin RAIHAN da A Wazir,duk da cewa ba su taba ganin juna ba, kuma Raihan na hakuri da halin miskilancin sa,sosai ta fahimci cewa shugaban din gwani ne wajen miskilanci da rashin son hayaniya. Abangaren A wazir kuwa shi dai yasan yana grmama yaron da ya dauke shi tamkar yaya,haka kuma yana jin sa a rai da zuciyarsa,duk miskilanci irin na A Wazir bai cika yin sa wajen Rahim da aikin sa ba,a cikin ƙanƙanin lokaci kowa na gidan su ya san da zaman Rahim duk da cewa ba fitowa fili ya yi ya bada labarin sa ba,ta yadda kawai su ka gane shi ta yanayin yadda yake amsa wayar Rahim,ba wani abu yake nunawa kan fuskar sa ba kawai dai yadda baya ignoring din coll Dinsa ta hakan ne suka san shi din mai muhimmaci ne a rayuwar A.wazir,baram ma innawuro da har so take taga Rahim domin taga wane irin kwarjini ne da shi haka da yayi tasiri a rayuwar jikanta A Wazir. Lokaci daya Abbie yaji maganar karatun Rahim daga bakin aunty amarya,kintsaye ta sanar da shi ta amince ya nemawa Rahim din makaranta a kasar da yaga ta da ce da irin karatunta,sosai ya ji mamakin saukowar ta lokaci daya akarankanta kuma,bai zurfafa tunani ba ya shiga neman karantu har ya da ce da samu a kasar syprus,ba su gayawa Rahim ba sunyi niyar yi masa ba zata ne dan hakan ya faranta masa. Lokaci daya RAIHAN ta ji zancen tafiyarta makaranta har kasar syprus,amma duk da yadda take son karatun jarida sai da hankalinta ya tashi ba dan komai ba saboda A Wazir,wanda har yanzu bayan gani na farko da ta yi masa a tv bata kuma ganin sa ba a zahiri ba ko a tv ,sai dai muryarsa da ta hadda ce a ƙwaƙwalwa da zuciyarta,shi kansa A Wazir sai da yaji wani irin sanyin jiki da na zuciya lokacin da abokin shi Rahim yake sanar da shi,(kar ku manta cewa a idon duniya RAIHAN namiji ce )ganin yadda Rahim ya damu sai yayi ƙoƙarin bashi karfin gwiwa tare da nasiha, da haka ya samu ya dawowa da Rahim ɗin farincikin sa na samun cikar burin sa na san zama ɗan jarida me gaskiya. Raihan ta so yin sallama da A Wazir ta hanyar haduwa ido da ido,sai dai hakan bai yiwu ba,babu yadda ta iya haka ta ta fi tare da rakiyar antyn ta da innar ta maimuna zuwa kasar syprus. Karatu Raihan ta shiga yi ka in da na in ,saboda tana son ta fita da kyakkyawan sakamako, ta kuma fita a iya shekaru biyun da zata yi ba tare da ta samu matsalar da zata sa ta kuma maimaitawa ba,lokaci lokaci suna waya da A Wazir yana kara mata karfin gwiwa da wayar mata da kai akan duk abin da bata gane ba,sosai kuwa take gane karatun nasa,wanda yawanci shi yake mata karin bayani akan darussan nasu. Yayin da kuma a tacan bangaren yan siyasa su Alhaji Garba me fata da Alh Ibrahim mangal,ba karamin ci gaba su ka samu sakamakon tallata siyasar su a gidan rediyon CHIBADO FM ba,sosai mutane suke ganin mutuncin Alhaji Garba me fata,tare da girmama shi, ba komai ne yasa A Wazir ya bada himma wajen sawa a tallata siyasar ta Alhaji Garba me fata ba sai dan ganin irin yadda yake da son talakawa da kuma irin yadda yaga yana da burin tallafawa marayu da matasa, ba A Wazir ka dai ba,hatta da jama a sun shaida cewa Alhaji Garba me fata ya cancanta da su zabe shi a matsayin gwamnan su,kuma Alhaji Ibrahim mangal ya cancanta da ya zama matemakinsa,saboda kyakkyawan halayyar shi,dan haka duk inda ka duba a cikin jahar ta Adamawa postan shi ne ,sosai ya samu karɓuwa a wajen talakawa. Anyi zabe lafiya kuma Alhaji Garba me fata ya samu nasarar lashe zaben wannan shekarar,sai fatan Allah ya taya shi riko. Takanas Alhaji Muhammad nurr da Abba yahya da Baffa suka je yi masa Barka da samun nasara,a lokacin ne kuma ya yiwa Abba yahya tayin matsayin chip accounter idan yana da ra ayin siyasa,dan jim ya yi yana duban Abbie da Baffa,ganin hakan yasa Baffa cewa,idan har kana da ra ayi mu ma su yi maka addu'a ne",shima Abbie kallon sa ya yi cike da bada kwarin gwiwa,hakan yasa ya karba tare da godiya me yawa,gwamna Alhaji Garba ya ce",ai mune da godiya ba zan iya manta alherin Muhammad nuurr a gare Ni ba,duk matsayin da na kai shine sanadi dan haka nine zan ci gaba da kokarin kyautata masa tare da addu'ar gamawa lafiya. Wannan shine sanadin shigar Abba yahya siyasa tare da matsayi me girma. A daidai lokacin kuma Raihan take cin shekara daya da fara karatu a kasar syprus. Raihan bata samu matsala wajen boye kanta ba ,saboda tana zaune ne a ƙasar da kowa yake har kar gaban sa,dan dama yawanci kayanta irin na su ne,tunda su kullum cikin sanyi suke. ........sosai Dr Sabo yake son taimakawa aunty amarya da yarta,dan haka ta wani bangaren za mu iya cewa ya fara nasa yunkurin na son gano me ke a ƙasa. A bangaren gwamnati kuwa ,za mu iya cewa talakawa na jin dadin mulkin Alhaji Garba me fata tare da matemakin sa Alh Ibrahim mangal, yana musu aiki daidai gwargwado,sai dai kuma akwai babbar matsalar da aka kasa gane ta ina take bullowa,daga mutanen gari har zuwa kan gwamnati yanzu gaba daya hankalin su na kan son gano inda matsalar take,mutane suna yawan mutuwa ta hanyar shan magani , sai yawan mutuwar da yara ƙanana suke yi ta hanyar yawaitar fyaɗe,sai daba ta hanyar zubda jinin al'umma,dan haka nan suke tada fituna dan kawai suyi ta kashewa jini na zuba kamar an yanka rago,hankalin mutane a ta she yake da wannan al'amari ,da yawan mutane yanzu sun fara jin tsoron fita ,baram ma da zarar magriba ta yi,saboda kusan kullum sai an samu gawarwaki sama da biyar na kananun yara,gaba daya yanzu iyaye basu da sakewa saboda wannan babbar matsalar da ta Kunno Kai wadda ta zamar musu kamar annoba,gaba daya gwamna bashi da kwanciyar hankali saboda tashin hankalin da talakawan sa suke ciki,kuma wani karin abin mamakin shine, ba iya yaran talakawa ake dauka ba hatta da ya'yan masu hannu da shunin dauka ake wasu idan suka bata sai dai aga gawar su,wasu kuwa ko gawar ta su ba a gani,to yanzu dai akan binciken da gwamnati da hukuma su ke kai ke nan,harma da yan jarida, da duk wani ma aikacin bincike. Yanzu fa gaba daya gari ya dau dumi ,duk gidan rediyon da ka kunna batun da zaka ji ana yi ke nan kafin a saka ko wane shiri,tabbas talakawa suna jin dadin mulkin Alhaji Garba me fata,sai dai kuma rashin kwanciyar hankali ya hana su samun jin dadin yadda ya kamata,wasu daga cikin abokan adawa sun fara korafi a gidajen rediyo kan cewa , wannan abin da yake faruwa ya kamata a binciki gwamnati ,saboda sai da suka hau mulki wannan abun ya fara faruwa,to da yawan mutane basu gamsu da wannan yarfe ba,kowa dai yasan yadda siyasa take, wannan batu da ya fito sai ya sa mutane suka fara dogon tunani,take zance ya juya kan cewa abokan adawa ne suke aikata wannan fasadi dan kawai su ɓata gwamnatin dake ci,ai kuwa abokan adawa sun jawa kansu,kan kace meye an shiga ce ce kuce a Media,har ma jami an tsaro sun fara bincike wasu daga cikin manya wadan da zargin su ya fi yawa,to bari mu tafi muga a inda gizo ke sakar. Jin yadda abin yake son taba kimar gwamnati ne yasa Alhaji Muhammad nurr,zama da gwamna dan tattaunawa akan batun. Duk da cewa Alhaji Muhammad nurr ba dan siyasa ba ne,to amma dole abin da yake faruwa ya shafe shi tun da ya shafi Aminin sa da kuma dan uwansa da a yanzu yake cikin siyasa dumu_dumu. Shi din me kishin talakawa ne kuma me tausayi,sai dai kuma sam bashi da sha'awar siyasa,shine dalilin da yasa ya bawa Aminin shi tallafi da kwarin gwiwa ganin cewa shi yana da sha'awar siyasa,sunan Alhaji Muhammad nurr bai taba fitowa a jerin yan siyasa ba,sai dai a jerin manyan masu kudin da suke tallafawa talakawa da marayu kai da duk wani aikin lada,dan haka yanzu ma ba wai dan kar sunan sa ya ɓaci ba ko kuma sunan Aminin shi da yayan shi ya ɓaci ba,a'a kawai tsabar tausayi da alhinin halin da al'umma suke ciki ne,duk da cewa ba za ku ce baya tsoran wani abu da zaisa mutuncin su ya tabu ba. Wannan ne yasa shi neman zaman tattaunawar da gaggawa dan ganin ko yana da hanyar taimakawa al'umma da suke cikin halin ƙaƙaniƙayi . Cikin fuskar damuwa Alhaji Ibrahim mangal ya dubi Abba yahya ya ce",nifa ina ga kamar dan uwanka shima ya fara zargin da ake mana na cewa muna da sa hannu akan al'amarin da yake faruwa",wani duba gwamnan Adamawa Alh Garba ya yi masa kafin cikin takaicin maganar sa ya ce",tur da wannan kalami naka,ko da yake na maka uzuri akan baka san yadda nake da Muhammad nurr ba,amma dai shi yahya ai kasan cewa dan uwansa ne ciki ɗaya,dan haka ka yi saurin kawar da wannan tunanin daga ranka ,dan idan Muhammad nuurr ya ji ransa zaiyi matukar ɓaci",yana rufe baki Alh Muhammad nuurr ya shigo ɗakin tattaunawar bakin sa dauke da sallama,amsawa su kayi tare da fara yin musabaha da juna,kafin cikin kamalar sa da Dattaku ya zauna idanun shi akan mutane biyu da yake kauna wato dan uwansa da amininsa. Ina ga ba sai muunyi wani dogon surutu ba, dan kuma kun san halin da ake ciki wanda shine makasudin zaman nan namu,gaba daya suka jinjina kai cike da tabbatar da hakan,cikin nutsuwa ya ci gaba da cewa,halin da jahar mu ke ciki kullum sai karuwa lamarin yake,wanda kuma idan har ba mu ta shi tsaye an magance matsalar ba to tabbas za mu iya wayar gari an karar da mu baki daya,dan tun ana taba kananun yara da matasa gaba kan iyaye da kakanni za a koma in dai ba mu dau mataki ba,"wannan magana haka take cewar ur exsellency ya ɗora da cewa kuma duk abin da ya faru lefin mu ne,saboda a karkashin mu jama'a take dole mune muke da hakkin kulawa da ita", Abba yahya ya ce abu na gaba kuma shine yadda mutane suke mana wani kallo kan rashin daukar matakin har sun fara zargin mu akan al'amarin dan duk inda ka je zancen ɗaya ne shi ake ta maimatawa,gaskiya ne wannan cewar defity Alh Ibrahim mangal wanda tun da aka fara tattaunawar sai yanzu ya magantu,ya ci gaba da cewa duk maganar da ku ka yi gaskiya ne,dan haka Ni shawarar da zan bayar ta farko shine ,mu sa jami'an sirri masu amana da gaskiya su yi bincike ta kan duk wani da ake tunanin da sa hannun sa, sannan kuma mu nemi dan jaridar nan AHMAD WAZIR CHIBADO shima ya yi mana aikin binciken ta can karkashin kasa,ina ga Ni dai shawarar da nake da ita ke nan ",jinjina kai su kayi gaba daya cike da gamsuwa da shawarar da defity ya kawo,daga nan suka cigaba da tattaunawa duk akan yadda za a samu sauƙin matsalar. A cikin wannan ruguntsumin Raihan ta kammala karatun ta,cike da tarin nasarori,farincikin da iyayenta da abokinta A Wazir suka shiga ma kadai ya ishe ta farinciki,Abbi ne da kanshi ya bar duk abinda yake ya dauko Rahim suka dawo gida cike da shaukin ganin yan uwan shi. Kwanan ta biyu da dawowa,A Wazir ya dira a gidan su dan yi wa abokin shi Raihan sannu da zuwa ta musamman. A hankali ya danna hon , da sauri,me gadin dake bakin gate din ya leko dan ganin waye, kamilalliyar fuskar A Wazir ba biyayya ba ce ,dan haka take me gadi ya wangale mishi kofa ,shi kuma ya danna hancin motarsa wacce tayi matukar dacewa da yanayin tsarin sa,cikin girmamawa suka gaisa da me gadin kafin ya shiga cikin gidan dan sanar da Rahim zuwan A Wazir chibado. Kamar daga sama RAIHAN dake can cikin kiching ta tsinkayi sakon da taji shi tamkar bushara,cikin sauri ta dauki ƙatuwar rigar sanyin ta ta zura,tare da ƙara gyara dogon gashin da tuni ta daina aske shi dan sanin hukun cin hakan a musulunci,cusa shi tayi cikin hular sanyin dake kanta,kafin ta fito cikin takun ta na nutsuwa wanda ko takun ka duba sai ka fahimci cewa indai wannan namiji ne to tabbas yana da tarin nutsuwa. Kai tsaye ta fita daga falon dan so take ta tabbatar da abin da kunnuwan ta suka ji mata, Zubawa kyakkyawar bakar motar dake fake daga can wajen aje motoci ido ta yi,kafin cikin san gyara takun ta ,ta isa gab da motar Ba tare da ta dauke idanun ta daga kan motar ba. Bude murfin motar ta bangaren driver ta ga anyi,a hankali ya zuro kyakkyawar kafar shi wadda take sanye cikin rufaffun takalma,kafin a hankali ya fito da gangar jikinsa da kuma fuskarsa me cike da kyawu da annuri da wani irin kwarjini me tsuma zuciyar matsoraci, Tuni zuciyar Raihan ta shiga wani irin bugu me karfi,duk da cewa ta taba ganin fuskarsa sau daya a tv,to Amma yanzu ji tayi kamar bata taba ganin sa ba,haka kuma gani take kamar camara ta rage tamanin cikin dari na kyau da kwarjinin sa,wani irin jan numfashi ta yi saboda yadda taga yana kusantota da wani irin murmushin da kana gani kasan ba koda yaushe yake yin sa ba, tare da takun da ke cike da nutsuwa tamkar me tafiya saman gajimare. Jin shi tayi daf da ita ,wanda kafin ta dawowa duniya ,ta kuma tsinkayar tattausan hannayen sa cikin nata hannun,a lokaci daya kuma yana magana cikin muryarshi me fita ɗai-ɗai,ya ce" my friend nayi maka ba zata ko? Shiɗewa ne kawai Raihan ba tayi ba,saboda kafin ta bude baki taji ta cikin jikin A wazir yana mai ɗan bubbuga bayan ta tare da cewa ya kamata ka dawo hayyacin ka, rahim wannan mamakin ya isa haka". Samun kanta tayi da cusa fuskarta cikin jikin shi tana mai kara shaƙar daddaɗan kamshinsa,idan ta ce ba ta yi mamakin zuwansa ba tabbas ta yi karya,ita shaida ce akan halin wazir da tsananin ajinsa,duk da kuwa cewa ita din ta daban ce a gurin sa amma hakan baisa ya kasa gwada mata halin tsumewarsa da yake halittarsa ba. Tabbas A Wazir idan ya ce bai ji wani sauyin yanayi a tare da shi ba yayi karya,sai dai kuma bai kawo komai a zuciyar shi ba,saima korar shaidan da yayi,dan a ganin sa duk sharrin sa ne tun da Rahim namiji ne shi ma namiji ne dan haka bai ga amfanin jin yanayin da yaji lokacin da ya rungume Rahim ba... Fateemah y Adam..........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page7 ``` Ɗago fuskarta da take ta cusawa a jikin shi yayi,tare dage mata gira , ya ce" aboki saukar da za Amin ke nan? Kunya ce ta kama Raihan,hakan ya sa ta yi saurin sakin sa ta wuce gaba da sassarfa tana cewa sorry Hamma wazir taho mu shiga ciki Abbie ma suna shida Abba yahya bai koma ba" bin bayanta cikin takun shi na nutsuwa fuskar shi kadaran kadaran babu Murmushi kuma ba tsumewarsa da ya saba. Sosai A Wazir ya samu karba daga gurin Abbie da Abba yahya, antyy amarya kuwa kamar ta goya shi saboda karramawa,har wajen su momy sai da antyy amarya ta ce suje su gaisa daga nan kuma suka dire bangaren Hajiya goggo,anan kam jiddo da ita ma ta dawo daga school kafin dawowar Raihan ta saki baki da hanci tana kallon A Wazir,wanda har sai da Raihan ta taɓa ta, sannan ta dawo hayyacinta gaishe shi ta yi cikin nutsuwa da son jawo hankalin sa kanta,amsawa ya yi ba tare da ya maida hankalin shi kanta ba,hasali ma hankalin shi na kan Hajiya goggo da suke tattaunawa akan batun halin da ake ciki na binciken masu kashe kashen nan saboda yanzu abin kamar yawa yake yi a maimakon ya ragu,jiddo dai bata so haka ba ,to amma ta sawa ranta cewa ai bata da damuwa akan A Wazir tun da har ya iya zuwa gidan su saboda Rahim to tabbas tasan zata iya cin albarkacin rahim ɗin yaso ta harma ta ya aurenta(tofa su jiddi an fada)akan wannan tunanin ta tsaya kuma take ganin shi zai kawo mata mafitar son A wazir da ya dade da kama zuciyarta. Abbie ya dade da sanin AHMAD WAZIR CHIBADO tare da Rahim dan duk gidan babu wanda bai san yadda Rahim ya dauki A.wazir da muhimmanci ba,Abbie ya ji dadin tarayyar su dan sun jima da sanin juna da mahaifinsa kuma har yanzu ana mutunci da gaisawa harma idan wani abu ya faru da daya suna gaiyatar juna. Lokacin da zai tafi ne suka tattauna da Abbie akan batun aikin Rahim, Abbie ya dubi A Wazir cikin son ya bashi hankalin sa ,ya ce" Ahmad hakika na yaba da hankalinka ,kuma na yaba da amincin da ke tsakanin ka da Rahim,dan haka zan roki alfarma a gurin ka,ina so zan nemawa Rahim aiki a wajen ku,saboda wasu dalilai.bayan wadan da nasanar da kai"murmushi A Wazir ya yi kafin cikin ladabi ya ce" Abbie kar ka damu tuntuni Rahim ya samu gurbin aiki a wajen mu jiran dawowarsa kawai muke,kuma shine babban dalilin da yasa na aje komai nayi tattaki nazo gida saboda nayi muku bayani yadda zaku gamsu" Cikin farinciki Abbi ya ce" to alhamdulillah amma kuma ɗaukar Rahim aiki kai tsaye ba tare da anyi masa interview ba hakan zai yuwu? A wazir ya dan gyara zaman sa ,kana cikin nutsuwarsa ya ce" Abbie na riga da munyiwa Rahim interview kuma ya cancanci aiki tare da mu, Abbie ina tabbatar maka da cewa ba son zuciya na bi na dauki Rahim aiki ba,cancantar sa ce ta kawo shi matsayin da muka bashi,dan haka kar ka damu ko yaushe ya shirya zai iya fara zuwa aiki" Murmushin manya Abbie yayi tare da cewa shike nan Ahmad na gode Allah ya taimaka ya ci gaba da baku ikon zakulo gaskiya a duk inda take" Amin ya Allah A Wazir ya fada cikin jin dadin addu'ar,sallama su kayi da alkawarin Rahim zai shiga office ran Monday,daga nan fitowa ya yi daga falon Abbien inda ya samu Raihan na zaman jiransa,sallama ya yi da aunty amarya,daga nan suka fito shida Raihan. Duban shi ta yi cikin marairaita ta ce", Hamma wazir saura alfarma daya nake so ka yi min, duban ta ya yi kawai ba tare da ya ce",ko mai ba,dan surtun da ya yi har ya sa mishi ciwon kai dauriya kawai yake yi,nuna mishi wani bangare ta yi dake gab da fita babban gate ta ce",ina so ka gaisa da inna maimuna innata tama so na ita ce matar Abba yahya ta karasa maganar cikin hade hannuwa alamar roko,jinjina kai kawai ya yi fuskar shi na dan nuna alamun gajiya,ina ita Raihan sam bata ma lura da yanayin nashi ba tun da ba sabon gani da ido ta yi.da shi ba bare ta fara gane yanayin shi,abu daya ta haddace a muamalar su shine maganar sa ta kurmanci ko da ido ya yi mata magana sai ta gane abin da yake nufi,jan shi ta yi suka fara tafiya ganin baya son Surutu yasa itama nata miskilancin ya motsa dan haka tafiyar kurame su kayi har suka karasa gate din inna maimuna. Ai ko inna maimuna ba karamin farinciki ta yi ba,tarbar ta yi masa itama ta mutunci da nuna muhimmancin mutum a guri,daga nan bai zauna ba ya yi mata sallama tare da kyautar kudi masu yawa,kamar yadda ya zubewa aunty da goggo,godiya sosai inna maimuna ta yi masa, Raihan ma ta ji dadin karamcin da wazir ya yi wa iyayenta. Bayan tafiyar A. wazir aka sanar mata batun aikinta Murnar da Raihan ta yi ba kadan ba ce,burinta ya cika na zama yar jarida, sannan zata yi aiki tare da wadanda suka san mutumcin aikin. Sosai Abbie da Antyy amarya Inna maimuna da Hajiya goggo su kai mata fada tare da nasiha me ratsa zuciya akan riko da gaskiya da amana. Kebantacciyar nasihar antyy amarya ga Raihan kuwa bai wuce ta kula da kanta ba, saboda nan ba kasar waje ba ce ,kuskure kadan za ta yi a gano ko ita din wacece,ba karamin sanyi jikin Raihan ya yi da tunatarwar antyy amarya ba,ita fa gaskiya ta gaji da wannan abin dan dai kawai babu yadda zata yi ne,da tunanin yadda zata fara mu amala da sabbin mutane a matsayin namiji ta fara shirin tunkarar Monday. ********* Tunda driver ya sauke ta cikin gidan jarida ta CHIBADO FM,take bin ko ina da kallon sha awa,hakika ma aikatar ba karamin burge Raihan ta yi ba,musamman yadda taga ko ina an tsara shi da kalar fentin da take matukar so,a hankali ta shiga takawa har zuwa bakin katon reseption din da zai kai ka ko wane office dake sama da kasa,tana nan tsaye tana yan dube_dube da tunanin wanda zata tambaya ya Kaita babban office din A. wazir,daga bayanta ta ji anyi sallama,juyawa ta yi tare da amsawa tana mai duban me sallamar,yauwa ina fata kaine Rahim Muhammad nurr? murmushi me kyau ne ya baiyana akan fuskar Raihan kafin ta ce"ey nine"cikin girmamawa mutumin ya ce"nazo ne nayi maka iso wajen sir wazir"na gode Raihan ta faɗa tana mai bin bayan mutumin. Sama suka hau daga nan suka kuma bin wata doguwar baranda wadda kai tsaye ta sada su da wani katon office me ƙatuwar kofar glass,suna shiga suka tarar da wani dan kebantaccen guri ga dukkan alamu wajen sakatare ko sakatariya ne,ba tare da sun dakata a wajen ba mutumin ya kuma nufar wata kofar glass ɗin me fadi,wani abu ya danna wanda kai tsaye ya bude kofar,shiga ya yi RAIHAN ta bishi a baya. Zaune yake saman kujerar da take ta faman juyi da shi kan shi a kasa yana duban takardun dake gabanshi,zubawa kwantacciyar sumar shi dake ta kyalli ido ta yi,kafin a hankali taji bugun zuciyarta na sauyawa. A hankali kyakkyawan matashin me lunkume da shekarun da basu wuce talatin da daya ba, ya ɗago kanshi dake sunkuye wanda tun shigowar su yaji idanun Rahim din na yawo a kanshi,mutumin nan ne ya katse su da cewa yauwa oga ga baƙon naka"jin jina mishi kai kawai A Wazir ya yi, cikin ladabi mutumin ya juya dan yasan ba amsar baka zai samu ba,nunawa Rahim din wajen zama ya yi fuskar shi na ɗan sassutawa daga kamewar da tayi da wan ba kowa ke samu daga gare shi ba,a hankali Raihan ta matsa tare da zama a wajen da ya nuna mata,cikin sauyin yanayin da ta samu kanta a ciki ta bude baki cikin siririyar muryar ta mai matukar ɗadin saurare ta ce"good morning Hamma wazir? morning dear Rahim"A Wazir ya amsa idanun sa akan Rahim din da ya kula kamar ba a sake yake ba,ɗan gyaran murya ya yi tare da kama hannun Rahim ɗin da yake ta faman ƙasƙas da su, ya ce Rahim what happened? Jujjuya Kai Raihan ta shiga yi saboda bata san me zata ce ba ,itama ba tasan me take ji ba,kuma bata san me ke faruwa da ita ba,abu daya ta sani shine duk sanda ta ganshi ko taji muryarshi sai zuciyarta ta buga da wani irin ƙarfi haka kuma sai ta samu kanta cikin yanayin zazzaɓi me ɓalle ƙasusuwan jiki,to amma kuma ai bata san me ke jawo hakan ba dan haka bata da amsar da zata iya bashi kai tsaye. Murza yatsun ta dake cikin nashi da yayi shine ya dawo da ita hayyacin ta,cikin rashin abinyi ta langabar da kanta se kawai ga ruwan hawaye a cikin kwayar farar idaniyarta,ya Salam A Wazir ya fada tare da ta shi daga gurin zaman sa zagayowa ya yi inda take zaune tare da durkusawa a gabanta ,ya ce" Rahim wai me ke damunka ko wani yayi maka wani abu ne daka shigo?girgiza kanta ta yi saurin yi tare da kirkiro karyar da ya zama dole ta yi "Hamma wazir kawai haka nan na tsinci kaina da shiga fargaba sai nake ji kamar wani abu zai same Ni ta sanadin aikin jarida tunda na riga nayi kudirin rike gaskiya da kamantata a kan aiki na"hannu yasa ya share mata hawayen da suka gangaro tare da tashi tsaye ya koma mazaunin sa wanda hakanne ya ɗan samarwa da Raihan nutsuwa,zama ya yi ya shiga binciken takardu sai da ya ɗibi wasu mintina kana ya ce" Rahim babu abinda zai same ka tunda kaima ka fada ka rike gaskiya kuma zaka ci gaba da rike ta , dan haka ka saki ranka ka fara aiki cikin kwarin gwiwa da karsashi"ya fada yana mai ɗago kansa da sakarwa Raihan murmushin da ya kusa tafiya da dukkan numfashinta,ina fatan ka fahimta A Wazir ya fada idanun shi akan Raihan da ke neman kasa rike kanta,da sauri ta daga kanta tare da share guntun hawayen da itama ba tasan ko na meye ba. Daga nan ya samu hankalinta ya yi mata dukkan bayanin da zata fahimta,da kanshi ya tashi ya fara zagawa da ita cikin ma aikatar ,kafin ya sa sakatariyar sa Ruma ta sanar da kowa ne staff cewa suna da mittin karfe biyu na rana. Saboda sanin muhimmanci na lokaci da A. Wazir ya koyawa ma aikatansa yasa karfe biyu daidai kowa ya halatta a cikin katon dakin taron, ba tare da wani jan lokaci ba ya gabatar musu da makasudin taron wato sabon ma'aikaci Rahim Muhammad nurr wanda zai dinga gudanar da shiri akan siyasar mu a yau da kuma hira da su dan jin manufofin su, sannan zata karbi shirin labarin masoya wanda A.qazir ke gabatarwa. daga nan Raihan ta yi dan takaitaccen bayani da kuma godiya ,sai kuma ko wane ma aikaci ya tashi ya gabatar da kansa da kuma ɓangaren da yake dauka,karfe hudu suka tashi daga taron kowa ya nufi masallaci dan yin sallah mata kuma suka nufi nasu masallacin. Halima ita ce mataimakiyar Raihan,dan haka ko da kowa ya dawo kai tsaye da ita A Wazir ya haɗa Raihan,saboda itama tana da hazaka wajen zakulo gaskiya,ita ce take binciken yan siyasa a sirrance sai dai kuma yanzu dole duk abin da ta gano ko ta binciko sai ta sanar da oganta Rahim, Wannan aikin yana bukatar masu gaskiya shi yasa A Wazir ya dora Rahim a matsayin shugaban halima da ita kanta halimar.wannan ke nan. A hankali Raihan ta fara gudanar da aikin ta cikin tarin nutsuwar da Ubangiji ya bata,cikin kankanin lokaci ta fara tara masoya,saboda yadda ta iya sarrafa harshe gurin tambaya da kuma yadda take bada hankalinta gurin zakulo ra ayin mutane, musamman a bangaren talakawan mu da kuma jin ra ayoyin su. Ta fannoni da dama Raihan wadda duniya ta fi sani da RAHIM,ta kawo ci gaba a gidan rediyon CHIBADO FM,kafin wani lokaci sauran gidajen rediyo sun fara kawowa Rahim kokon baransu na san zamowa daya daga cikin ma'aikatan su, tare da tayin makudan kudade dan kawai tabar aiki da CHIBADO FM ,sai dai kash ba su san cewa Raihan ba dan kudi take aiki ba,dan da yawa basu san ita din ko yar gidan waye ba,sun san dai Rahim Muhammad nurr amma basu taba kawo cewa Muhammad nurr din da suka sani ba ne,dan tunanin su bai basu cewa Muhammad nurr zai bar daya daga cikin yaranshi su yi aiki a karkashin wasu ba,shi yasa kwata kwata hankalin su bai kai kan sa ba,hatta da Aminin mahaifinta gwamnan jihar Adamawa baisan cewa Rahim ya fara aiki tare da su chibaɗo's ba. A gajiye Raihan ta koma gida saboda wasu aikyuka da suka ƙaran mata a office.sai da ta kimtsa sosai ,kana ta fito falo inda ta tarar da Antyy amarya zaune tana duban labarai a tashar ta su ta chibaɗo FM,zama tayi kusa da ita tare da kwantar da kanta a kafadar ta, cikin sanyin murya ta ce"antyy amarya na gaji sosai"shafa kanta antyn ta yi tare da cewa Allah ya baki lada ya kuma ci gaba da kare min ke ,Amma gaskiya Rahim ba zan boye maka ba wlh ban gamsu da wannan bangaren da aka baka ba, ƙasa ta yi da murya sosai ta ci gaba da cewa karfa ki manta da akwai raunin mace a tare da ke Raihan karfa nayi gudun Gara sannan nazo na haye zago,bana so duk tattalin rayuwar ki da nake akan makiyan da bamu san su ba,ya zamana kin karowa kanki wasu makiyan kin san fa harkar jarida jaridar ma irin bangaren da aka baki Raihan yana da haɗari sosai"ta shi zaune Raihan ta yi kafin cikin san kwantar da hankalin antyy amarya ta ce"antyy amarya wlh babu wata matsala Ni kaina naji abinda kika ji lokacin da na fara aikin to amma daga baya sai naga duk ashe ba haka ba ne,ita fa matsala sai ka kai kanka take samun ka,dan haka ki kwantar da hankalin ki ki mikawa Allah komai kamar yadda Abbie ya yi"murmushi antyy amarya ta yi kana ta ce" shike nan Raihan Ni dai kawai farincikin ki nake buƙata amma dai gaski,,,,,da sauri Raihan ta rufe bakin antyy tana cewa dan Allah antyy ki bari ki kwantar min da hankalin ki"dole antyy amarya ta yi shiru suka shiga wani zancen, tare da bawa RAIHAN ɗin abincin da me aikin ta kawo mata. CHIBADO HOUSE Tun daga farkon shigowa falon zaka jiyo fadan innawuro da hargowarta,duk da cewa shi wanda take yi saboda shi din ko kallon inda take baiyi ba,kai kace ma baya falon,ganin yadda yayi shakulatan ɓangaro da ita ya sa ta ɗauki jarkar ruwan dake gabanta ta wulla masa tana ci gaba da cewa, Ni zaka mayar mahaukaciya saboda ba uwar ka ba ce ke maka magana,to wlh na gaya maka na gama baka lokaci idan wata dayan da na ɗeba maka ta cika baka kawo matar da zaka aura ba,wlh sai na aura maka yar uwarka da kaƙi ta, duk da irin son da take maka"dawo da duban ta kan Ammi ta yi tana cewa ai kuna kallon sa yake yin duk abin da yake yi to in ku zaku iya Ni ba zan jura ba ehe"babu wanda ya tanka mata saboda sun san hali babu wanda yake shiga fadan innawuro da Ahmad idan ma ka shiga kai zata bari da jin kunya,dan take a gurin zata kunyata ka,shi yasa daga Abbu har Ammi basu tanka mata ba, shi kuwa gogan ko ajikinsa,karshe ma tashi ya yi ya bar falon ba tare da ya tanka mata ba,da ƙatuwar harara ta bishi tana ci gaba da yan guna_gunin ta. ........ Washe gari saboda kar innawuro ta kuma tada masa zancan aure ko bari ta fito baiyi ba , ya fice daga gidan, duk da cewa kowa yasan shi ɗin me zuwa da wuri ne mutum ne da yake matukar martaba lokaci shi yasa baya wasa da shi Ako wace gaɓa. Tun da ya shiga office ya maida kansa busy dan duk ya cire tunanin da yake neman sarke zuciyarshi,a hankali aka bude kofar tare da shigowa kai tsaye wanda hakan yaja hankalin A Wazir,karaf idanun shi suka shige cikin nata,duk da ranshi ya ɓaci da yadda ta shigo masa kai tsaye amma sai ya dake ya dan saki fuska kadan,tare da kawar da kanshi daga kanta,Asiya Kabir ke nan abokiyar shi ta karatu,tun bayan da suka gama karatu ya rabu da shegen nacinta saboda tafiyar da ta yi wajen kakarta dake can Saudiya,sai kuma yau rana tsaka ya ganta cikin office dinsa. A hankali a ka turo kofar tare da sallama, bayan sanar da shi cewa yana da bakuwa,amsawa ya yi can ƙasan makoshi,waje ta samu ta zauna ba tare da damuwa da yanayin na shi na gizago da ta fuskanci cewa a jinin sa yake,Barka da aiki ta faɗa idanun ta akan shi tamkar zata haɗiye shi,Barka ya kuma fada cikin dakakkiiyar Muryarshi dake fita da sautin rashin sassauci ko wasa,ji ta yi jikin ta ya kuma mutuwa yau din ma dai ba za ta iya fadin abinda ke ranta ba,wai shi wannan wane irin mutum ne haka me tsananin kwarjini)ta tambayi kanta. Meke tafe dake?tambayar da ya yi mata ta katse mata tunani.kame kame ta fara domin ta rasa abin cewa, idan baki da abin cewa za ki iya tafiya?ya kuma fada fuskarshi na kan computer da yake ta latsawa tun shigowarta. Asiya daya daga cikin fans dinsa ce,fasifar son shi take yi,amma babu fuskar nunawa bare sanarwa,baya daukar wayarta,dan bai ma san ita dince ba ko ta kira, ɗan yawan takura mishi da ziyara da take ne ma yasan ya dan shaida fuskarta. Duk sanda zata zo da kwarin gwiwar sanar da shi abin da ke ranta take yi,amma da zarar ta zo gaban sa ko mai sai ya kufce mata,kamar dai yadda yanzun ya faru. Turo kofar aka kuma yi tare da siririyar sallama,wadda lokaci daya Muryar Rahim ɗin ta shiga kunnen sa,asiyar ce ta amsa,shi ko motsawa baiyi daga abin da yake ba,hakan yasa zuciyar Raihan ta sosu,kallon Asiya ta yi idanun ta cike taf da ruwan masifa,sai dai ba tace ko mai ba,ta kuma duban wazir din da har yanzu dai bai ko kalli inda take ba. To yallabai Ni zan wuce sai na dawo",cewar Asiya da ta ɗan samu kwarin gwiwa bayan shigowar Rahim,jin jina mata kai ya yi ba tare da ya ɗago ya kalleta ba. Tana fita daga office din Raihan ta matsa kusa da shi idanunta akansa ta ce",Hamma wazir ina zata dawo?yanzun me tazo yi?kuma wacece ita? Ɗan lumshe idanunsa ya yi saboda yadda Muryar take shiga ko wace kafa ta jikinsa,sai dai kuma sam ya kasa amsa mata tambayoyinta,saboda baisan me zai ce mata ba, Ganin yadda yayin hakan sai ya kuma harzuka zuciyar RAIHAN,sai kawai ta fashe da kukan da yake ta yakushin ranta,tun ganin Asiya a office din nasa wanda ita kanta bata san dalilin jin zafin ganin nata ba.cak ya tsaya da abinda yake yi,babu wani abu da yake saurin karya lagwan A Wazir sai kukan Rahim babu wani abu da yake saurin sashi damuwa irin damuwar Rahim,idan ka cire iyayen sa to Rahim ne na biyun su a matukar muhimmanci a rayuwar A wazir,a hankali ya ajiye keyboard din dake hannun shi yana sarrafa computer,ya juyo inda Rahim din yake tsaye a tagefan shi yana wani irin Kuka me sosa zuciyar me sauraro,kana jin kukan za kasan cewa yana fitowa ne da wata irin damuwar dake can cikin ƙasan zuciya,cikin wata irin sassanyar murya A Wazir ya ce" Rahim me aka yi maka meye damuwarka? Ya fada cikin damuwar da kukan Rahim din ya jefa shi a ciki,dan sai ya ji ma ya manta da duk wata damuwa da ya shigo da ita da kuma wadda tazo ta tarar da shi,janyo hannun RAHIM ɗin ya yi yana ƙoƙarin rarrashinsa cikin yanayinsa n rashin son hayaniya.meye damuwar? Ya kuma tambayarsa cikin kwantar da murya, a hankali Raihan ta ɗago idanunta da suka sauya daga ainahin su na farare masu sirkin zaiba,tambayar da ta yi mishi na amsa ta ba ita ta kuma maimaitawa. wacece waccen da ta fita yanzu?" Nima ban sani ba kawai dai daya daga cikin fans ne“ya bawa Raihan din amsa cike da son jin abinda asiyar ta yiwa Rahim ɗin,jin Rahim din ya yi shiru yasa A wazir ya kuma tambayar sa da cewa wani abu tayi maka"girgiza kai Raihan ta yi tare da barin office din tana cewa lokacin aiki ya fara sai an jima oga" cike da mamaki yabi bayan Rahim din da kallo, zuciyar shi tana mai son gano mishi dalilin Rahim din na damuwa da zuwan Asiya ko kuma tarayyar sa da ita wanda tuntuni ya fahimci ba wai a kan Asiya ne Rahim ya fara wannan ɗabi ar ba,yawanci baya son huldarsa da mata ko abokanan aiki ko kuma waɗanda suke zuwa musamman danshi,dan sau da yawa yana gani Rahim din ne ke yi masa maganin tarin yammatan da suke addabar shi,ajiyar numfashi ya yi tare da komawa ya zauna,ci gaba ya yi da aikin shi dan son kawar da tunanin abun a ranshi............... Fatimah y Adam.......✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page8 ``` Yanzu murja haka zaku zauna ku zuba idanu dukiyar mijin ku kuma uban ya'yan ku tana ta zama ta gaibu,kun zauna sakoko da baki kun kasa tsinana komai,cewar innar murja ke nan kuma kanwar goggo Rahma,cikin takaicin da yake cin ran murja ta buɗe baki ta ce" wallahi inna na fi ki shiga halin bakin ciki da ruɗu akan wannan lamarin,amma ba komai ne yasa nayi shuru ba illa so nake yarana su taso saboda mu hadu mu kwatarwa kan mu yanci,to kuma alhamdulillah tun da yanzu dukkan su sun yi wayo sun mallaki hankalin kansu,jira nake kawai su dawo gaba dayan su ,domin mu ɗora daga inda muka tsaya" tsaki inna ta yi tare da cewa to wane tabbacin ne dake na cewar zasu baki haɗin kai tun da dai kin san mutumin nan mahaifin su ne babu yadda za ayi su yadda a cutar da shi" dariya murja ta yi kafin ta haɗe fuska ta ce" inna tun yarana ba su san komai ba bare wata aba ƙiyayya na riga na cusa musu tsanar yan uwansu da ganin baƙin su karma wannan Rahim din ya ji labari,shi kuwa mahaifin su na riga na saka musu a ransu cewar baya kaunar su,dan haka da wannan damar yanzu zanyi amfani su bani hadin kai domin kwatar dukiyar RAIHAN wadda a yanzu nake kyautata zaton zata iya zama ta Rahim saboda mugun son da na fuskanci nurr na yi masa,duk kuwa da cewa yana kokarin boye hakan a gaban idanun mu da idanun yaran",ajiyar zuciya inna Ta yi fuskarta ɗauke da murmushin samun nasarar karya yar uwarta a ta dalilin muguwar hassadar dake cin ranta ,na iya tsawan lokacin da Allah ya ɗaukaka Muhammad nurr.na gode y'ata kuma nayi miki alkawarin cewa da Ni za ayi wannan yakin dan haka duk lokacin da kuka shirya ki sanar da Ni dan karo makaman yaƙi.da wannan batun suka rufe hirar ta su,inna ta tashi ta koma bangaren yar uwar Tata wadda acewarta ita ta kawowa ziyara. Halima ce tsaye a bakin wani katon shopping moll, sanye take cikin doguwar rigar a baya fuskarta kuma sanye da facemask,fitowa ta yi daga gurin aiki saboda siyayya da take son yi, dan yau sai ta tsaya ta gabatarwa da Rahim rahotanni da suke hannun ta na sirri,shi kuma Rahim din sai ya gama gabatar da shirin siyasarmu a yau.shi yasa ta yi tunanin ta fito ta gabatar da uzurinta,idan yaso tana ta shi gida kawai zata nufa babu batun tsaye tsaye,tun da dama yau bata da fitar aikin sirri. Kamar ance ta kalli saman barandar hotel din dake opposite da shopping moll din da ta ke tsaye a gurin, gani ta yi wani mutum me sanye da cot ya ritsa wani saurayi da bindiga,ga dukkan alamu a boye mutumin ya nunawa saurayin bindigar bai kuma yi tsammanin ta yi fitowar da har za a ganta ba,sai dai kuma kash ido biyu Halima ma'aikaciyar jarida wadda ke aikin sirri a gidan rediyon CHIBADO FM,ta yi da wannan bindiga,zaro idanunta tayi sosai dan tabbatar da abinda idanun nata ke gani,gani tayi mutumin ya boye bindigar sun kuma jero shi da saurayin da ya nunawa bindigar kamar wasu abokanan aiki,har kafadar saurayin mutumin ya dafa suka sauko daga saman barandar hotel din,cikin wani irin hanzari halima ta tare me mashin din a daidaita,kokarin saita kanta ta yi a matsamayinta na sirrintacciyar 'yar jarida tare da ƙara bawa kanta ƙwarin gwiwa,ta ce"da me nafef din malam dan Allah wannan motar da zata tafi yanzu nake so ka bi min cikin nutsuwa bana so su gane cewa muna bin su"to Hajiya kar ki damu wannan aiki na ne" me nafef ɗin ya faɗa yana tada mashin ɗin da sauri saboda yadda motar ta zo ta wuce su da gudu,shi ma me nafef din da gudu ya bi bayan su. Sakon da halima ta turawa Raihan ta sanarwa da wazir shi ya tilasta mata zuwa office din Wazir badan ranta ya so ba,sallama ta yi tana ta faman ciccin magani saboda ganin sakatariya da ta yi tsaye ta zuba masa ido kamar ta samu tele,shi kuwa da alama bai san ta na yi ba,dan gaba daya hankalin shi na kan takardar da yake saka hannu zai bata,harara Raihan ta zubawa saude kafin cikin jin haushin da bata san dalilin sa ba bare kuma wanzuwar sa da sanin muhallin sa,tace to Malama cinye shi zaki yi ne kin wani ƙwalalo masa ido kamar zaki cinye shi ɗanye"ta ƙarasa faɗa tana mai tura karamin bakinta da yiwa Wazir din kallon ƙasa ƙasa,tun da ta fara maganar ya bar abin da yake yi tare da maida hankalin shi kan ta,amma ba zaka taba gane hakan ba,mikawa saude takardar da ya gama sa hannun ya yi tare da yi mata alamun ta fita,babu yadda ta iya haka ta karba ta fita ba tare da ta samu damar tankawa Rahim ba,tunda ko ta girme shi yana matsayin samanta ne,ko ba haka ba ma wazir ba zai taba daukar hakan ba. Rashin abin da zai cewa Rahim ɗin yasa shi ci gaba da wasu aiyukan.tura baki Raihan ta yi idanuwanta na cika da hawayen rashin dalili,jin damuwar Rahim din a cikin jikin shi ya yi ,hakan yasa shi ɗago manyan idanun sa masu saurin kashe jikin duk wata lafiyayyar mace, ɗora Mata su ya yi tare da cewa, Na kasa gane komai akan abin da kake yi,sai dai kuma na fahimci abu daya shine kamar kana kishi da duk wani da yake son tarrayya da Ni,ragowar ne ban fahimta ba dan haka sai ka fahimtar da Ni"ya fada yana ta shi daga saman kujerar sa kai tsaye ya nufi bathroom dan dauraye hannunsa. Haka nan Raihan ta samu kanta da jin bakin cikin kasancewar ta a matsayin namiji,bakin cikin da bata taba riskarsa ba,haka nan take jin matsananciyar damuwa akan ɓoyewa Wazir kanta da ta yi,to amma ya ta iya wannan alkawarin mamanta ta yiwa shi,kuma ya zama dole ta cigaba da riƙe shi,wani irin kuka wanda ke tafe da wata irin damuwa ya kufce mata,wanda ya sa ta fita daga office din ba tare da ta isar da sakon da halima ta turo mata ba,nata kuma bashi amsar tambayar da ya yi mata ba,ba ta tsaya ba kai tsaye office ta nufa ta fara gabatar da shirin siyasarmu a yau. Ko da wazir ya fito yaga bai same Rahim ba,duk sai ya kuma jin damuwa ta lullube shi,bai san me ya sa ba sam baya son abin da zai taba ran Rahim , yana matukar jin shi a zuciya da gangar jikin shi,kai duk wani motsin shi ma sai ya ji Rahim a tare da shi,dan lumshe idanun sa ya yi tare da furzar da huci. Alhaji sale anya kuwa kana ganin wannan hanyar da muka dauka zata bulle inda muke so ta bulle kuwa? Cewar Dr sanate ke nan, ɗan numfashi Alhaji sale me shanu ya furzar kana ya ce"Dr kar ka damu wannan hanyar da muka ɗauko ita ka ɗaice mafita a gare mu dan samun damar tarwatsa gwamna"kafin Dr ya bude baki sai ga mutumin nan da wannan saurayi ya tunkuɗo shi cikin falon kamar wani kayan wanki,oga an kammala wancan aikin saura wannan kawai shima umarnin ku nake jira na isar da sako"kafin su samu bakin bashi amsa wani gurnani ya fara fitowa daga can karshen falon wanda ga dukkan alamu dai daki ne,kuma gurnanin bana komai bane sai na irin alamun ana jin dadin fitar hayyaci,tsit falon ya yi kamar ɗaukewar wuta ,su Dr da mutumin nan dai da alamu sun san me ke faruwa a cikin dakin,sai dai kuma tuni suka bar ƙwaƙwalwa da gangarjikin halima kyarma,domin kuwa tagar da ta samu ta laɓe tana gab da jikin dakin da wannan gurnanin yake fitowa,gyara camarar ta ta kuma yi sosai dan tana son komai ya fito tar. Dr ne ya dubi wannan basamuden mutumin ya ce"kwaro mu dukan mu bamu da damar yin komai har sai shugaba ya fito daga dakin hutu kuma kaima ka sani dan haka sai ka dakata mu jira fitowar sa,yana rufe baki ma sai ga shi nan ya fito shida wani matashin saurayi sai sakin murmushi suke kamar wani saurayi da budurwa, ko da yake kusan hakanne su a wajensu. Zaro ido halima ta yi saboda mamakin mutumin da ta gani da kuma gane dalilin jin gurnanin nan,wa iya zubillah Allah ka tsaremu daga sharrin masu fuska biyu, ta faɗa tana kara dai-daita camarar ta,dan ji take kamar karshen su ya riga yazo tun da har Allah ya tona musu asiri ta hanyar ganin su da ta yi,ba kowa ba ne wannan mutumin da halima ke mamakin ganin sa ba,fa ce,Alhaji rabi'u me kwangila,wanda ya kasance shugaban jam'iyyar su Alhaji Garba me fata,wanda kuma kowa ya san cewa ba jam'iyar su daya da su Alhaji sale me shanu ba,hasali ma abokan adawa ne na bugawa a jarida,kuma a fili kowa yasan basa shiri da shugaban jam'iyyar wato Alhaji Rabi'u kwangila,abu na biyu kuwa kowa yasan wadan nan mutanen basu da wata lamba ko wani hali da zaka bigi kirji ka ce idan ka gansu a wannan yanayi ba zaka yi mamaki ba. Saurin barin wancan tunanin ta yi don fuskantar abin da suke shirya wa,shugaban jam'iya ne ya dubi alhaji sale ya ce" ya dai me kuke jira da wannan baku bazar da shi ba,ai irin su ba su da wani amfani a cikin irin mu,dan haka ya dubi ƙwaro ya ce" ƙwaro maza sashi baccin da ba zai farkaba kuma ka tattara shi ka kai tsohuwar rijiyar a jiya" an gama shugaba" ƙwaro ya fada yana nufar wannan saurayi da aka datsewa baki da salatif,take saurayin ya fara mutsutsu da daga hannayen sa da suke a haɗe wanda tunanin halima ya bata cewa lallai amota bayan yayi masa barazana da bindiga sun shiga ya yi masa wannan daurin,kafin halima ta kai ga dire tunanin ta ,ta tsinkayi karar harbi har cikin tsakiyar kunnen ta,a tunanin ta ma ita aka harba sai da ta bude idanun ta da ta rintse su bayan jin Harbin sai taga ashe saurayin nan ƙwaro ya zubawa bullet har biyu a tsakiyar kirji. Burin mu shine duk abin da muke aikatawa ya koma kan gwamna da wannan dankanzagin nasa Alhaji Yahya,dan naga alamu ya ma fi defity samun guri a gurin sa, Alh sale ya ce",duk ba dan Allah yake yi ba saboda kawai yana yayan Amininsa ne Alh Muhammad nuurr,kasan shine komai nasa kai dukiyar ma da yake takama da ita duk ta Alh Muhammad nuurr ce,a yadda naji ma cewa a kayi ta wata yarshi ce Raihan da ba a haifa ba ya bashi yake juya masa saboda yaddar da ya yi da shi",rike baki shugaban jam'iya ya yi yana cewa kai duk a ina kasan wannan maganar? murmushi kawai ya yi tare da kawar da maganar ta hanyar cewa,ku fita da gawar akai ta ma ajiyar". Bata san lokacin da ta saki wata siririyar ƙara ba,wanda karaf sai a kunnen su shugaba,cikin tashin hankali ta bar jikin window ta fara kurɗawa cikin ciyayi da mugun gudu tana yi tana turawa Rahim sako ta WhatsApp,wani tunani ta yi sai kawai ta yi saurin goge lambar Rahim da sakon video da na test bayan ta tabbatar sun shiga. Ka kira duka yaran ku bita kar ku sake ku dawo ba tare da gawaarta ba,Dr sanate ya fada cikin tashin hankali,shugaba kuwa kaiwa yake da kawowa burin shi da fatan shi bai wuce a ce an kamo wannan tsinanniyar yarinyar ba. Sosai suka bazu dan neman halima,ita kuwa a cikin wannan ciyayi ta samu ta binne camarar,tana gama binnewa ta cigaba da gudu numfashinta har daukewa yake ,amma ta yi yakinin Allah zai bata lada ko bayan ranta tana da tabbacin Rahim zai karasa aikin da ta dauko koma fiye da yadda ta so yi.kamar daga sama taji saukar bullet a tsakiyar bayan ta,take kuwa ta fadi ko shurawa ba ta yi ba.allahu akbar Allahu ya karbi shahadarki halima. Tsugunawa ya yi a gaban gawar yana kallon ta na tsawon lokaci kafin ya ɗago idanun sa da su kayi jajur ya ce" meyesa ƙwaro me yasa baku yi tunanin kawo min ita a raye ba,idanuwa na sun rufe na baku umarnin kashe ta bayan kuma kashe ta ba shi ne mafita ba,kamata ya yi mu fara tambayar ta su waye su ka turo ta kafin mu aiwatar da nufin Mu akan ta" duk shuru su kayi cike da jimamin katoɓarar da su kayi,Dr sanate ne ya ce" shugaba ai ina ganin tun da munyi nasarar karbar wayar ai bamu da matsala da wanda suka turo ta" kai ku dakata" alhaji sale ya fada yana wani dan nazari kafin da sauri ya tashi tsaye yana cewa kai yarinyar nan fa har da camara a hannun ta wannan video ba iya wayarta ya tsaya ba akwai camara a hannun ta tabbas,take hankalin su ya kuma ta shi,Dr ya dakawa yaran tsawa to me kuma kuke jira maza kuje inda kuka harbeta ku lalubo camarar" ko rufe baki bai gama yi ba su ka fita cikin mugun hanzari. Sai dai kuma babu duban da ba suyi ba amma babu camara sama ko kasa ,haka suka haƙura suka dawo, amma sun ji babu dadi a wajen shuqagabannin su,haka su ka tattara gawar su ka fita da ita,shugaban jam'iyya ya ce" ita kar ku Kaita tsohuwar rijiya ku je ku jefar da ita a gefan hanya ta yadda yan uwanta zasu ganta,ina tunanin ta wannan hanyar ce kawai zamu san su waye suka turota" wannan shawarar ta yi cewar Dr. Ganin da Raihan da su salim su kayi halima bata dawo ba ,har aka gama shirin siyasarmu a yau,sai su kayi zaton ta wuce gida,dan haka su ma suka ta shi ,amma ko wannen su kokarin kiranta ya shiga yi dan tabbatar da cewar tana gidan. Cike da gajiya da yar damuwa Raihan ta koma gida,ba tare da ta iya aikata komai ba ta zube akan lafiyayyan gadonta,tana maida numfashin damuwa da gajiya. Koda Anty amarya ta shigo taga Raihan bata yi mamaki ba, sannan bata tsaya tambayar ta damuwarta ba,dan ta san tatsuniyar gizo ba zai wuce ƙoƙi ba,sai dab da magriba RAIHAN ta tashi ta dauro alwala, duk da cewa ba sallar zata yi ba,to amma bata sake ta zauna babu alwala,damuwar dai bata sake ta ba ,to amma yanzu sai take jin wata irin fargaba da faduwar gaba wanda ta rasa daga ina ne,sai kawai ta shiga jan innalillahiwa'inna ilaihi raji'un,da haka ta samu sassaucin fargaba da faduwar gaban da ya same ta gab da magribar. Tun bayan tashin sa daga office,yake gwada nomber ta amma a kashe, bangaren su ya shiga dan ganin yadda komai yake kamar yadda ya saba duk lokacin tashin sa daga aiki,dole zai shiga dan ganin wadan da zasu karbi aikin dare, salim ya tambaya ina halima ko ta tafi? Ishaq ya ce" ai rabona da halima tun karfe hadu saura ta ce" min zata shiga shopping moll ta dawo,ina ga dai wuce wa gida ta yi" ok Wazir ya fada yana kiran nomber halima ,ita ma din dai a kashe ,kawai sai ya hakura amma ya ce da su salim anjima su kuma gwada kiran wayarta saboda su tabbatar da lafiyarta. Haka nan ya kasa bacci ya tasa wayarsa a gaba ,daga ya kira Rahim sai ya kira halima,amma har zuwa wajen goma babu wani labari,dole ya hakura ya danne zuciyarshi. A gidan su halima kuwa ,mahaifinta ya riga ya san irin aikin da take yi shi yasa bai damuwa da yin daren ta,to amma fa duk da haka ya a damu a yau saboda duk yadda aiki ya riski halima bata haura tara na dare,to yau kuma gashi har goma ta gota,mahaifiyarta wadda suke kira da umma ta ce" Ni dai malam ka kira ogan nasu a ji ko lafiya ina ga sai hankalin mu ya fi kwanciya" da shawarar ta ya yi amfani ya danno kiran yayan haliman ya fara sanar da shi,daga nan shi kuma yaya Usman din ya danna kiran A Wazir. Kamar almara haka ya ji batun na yayan halima, cikin hanzari ya tashi ya fito yana sanar da shi duk abin da ya faru kamar yadda Ishaq ya sanar da shi. Kafin wani lokaci su Ishaq da salim ma sun fito an baza neman halima 'yan sanda kuwa ko wane lungu da sako bi suke dan binciko inda Halima take,har lokacin wayar Rahim a kashe take ,kuma koda a kunne take ya sanar da kowa kar wanda ya gaya masa, saboda yasan halin sa haka yake kamar mace nan da nan sai ya ruɗe ya fara koke koke,duk kuwa da jarumtar da yake da ita. Misalin karfe goma sha biyu na dare a ka tsinto gawar Halima a can bakin wani katon kwalbati in da mafi aksari a can aka fi tsintar gawarwakin da ake yawan kashewa. Tashin hankali an shige shi a wannan dare, dan ma ba kowa ya san Halima a matsayin yar jarida ba,kasancewarta yar jaridar da take aiki a sirrince,to Halima dai ta yi shahada Allah ya jikanta da Rahma. A ranar nan sam bacci bai ga idanun Ahmad wazir chibado ba, innawuro babu lallashin da bata yi masa ba amma ko duban inda take baiyi ba,zuciyarsa a cinkushe take da tunani iri daban daban ,shin meye silar mutuwar Halima ? Su waye suka kashe ta? Me ta yi musu ? Wadan nan tambayoyin su suka hana shi rintsawa, tare da wata irin fargaba da hangen rayuwar Rahim da ya ɗauka ya saka a cikin irin wannan aiki mai matukar haɗari. Sai karfe bakwai Raihan ta farka,a gurguje ta shiga bathroom ta yi wanka tare da brush,sai da ta shirya tsaf sannan ta fito dan ta karya ta wuce office,tun da ta fito take latsa kiran Halima amma sai taji wayar a kashe,dole ta ajiye wayar ta fara karyawa, daidai lokacin taga antyy amarya ta fito cikin shigar dogon hijab har kasa,antyy amarya Barka da safiya" Barka dai Raihan ta faɗa ba tare da ta dubeta ba,antyy amarya ina zuwa haka da sassafe? Zan raka Hajiya goggo ganin likita ne,inna maimuna ma zata ga likita dan haka ki zauna mu dawo sai ki tafi aikin"ok shike nan sai kun dawo"har antyy amarya ta bude kofar fita , Raihan ta jefo mata tambaya da cewa antyy me yake faruwa ne kamar kina cikin damuwa? Ba tare da ta juyo ba ta ce" babu abin da yake faruwa ke dai ki zauna muje mu dawo" Tom sai kun dawo ta faɗa tana kara gwada lambar halima,kafin ta ɗago har antyy amarya ta fice, tana fita wazir ya kirata ,dagawa ta yi bayan sun gaisa tare da yi masa gaisuwa ,ta ɗora da cewa zaka iya karasowa gidan yanzu. Mu mun tafi gidan gaisuwar" ok antyy amarya ganinan amma dai kin hana shi kunna tv ko dan yanzu haka a na kan baza labaran tare da hotunan gawar Halima da kuma wanda take raye"wallahi wazir ban hana shi ba kawai dai kayi sauri nasan ba Lallai ne ya kunna ba tun da nace mishi yanzu zamu dawo" daga nan su kayi sallama. Mintina goma da fitar antyy amarya Raihan ta shige dakinta,ganin ba kowa yasa ba ta rufe dakin ba sai kawai ta cire kayan da suke matuƙar takura mata ta dawo Raihan dinta ta asali,Masha Allah abin da zamu iya cewa ke nan,ban taba kallon surar Raihan ba sai yanzu saboda bata bada damar hakan, Raihan gata dai yarinya karama wadda har yanzu ko shekaru sha tara bata cika ba,amma sai kira,ko da ike zamu iya cewa Allah ne ya nuna ikon sa ta hanyar ƙawata budurcin Raihan,wanda ko antyy amarya ta na da niyar ci gaba da boye Raihan to kuwa nan gaba kadan tabbas ba zata boyu ba,dan ba kankanuwar sura Ubangiji ya yi mata ba,kai hatta da booms din Raihan abin kallo ne domin kuwa a cike suke kuma masu kyau wadan da baza su taba lalacewa ba,sai dai muce tubarakallah. Zama ta yi kawai sai hankalinta ya kai kan tv,daukar rimot ta yi tana jin Gara ta kunna taragewa kanta damuwa,tana kunna wa ta dauki wayarta dan sake gwada kiran Halima wanda har yanzu mamakin kashe wayar na Halima take yi. Fatima y Adam ✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page9 ``` Ɗan tsaki ta yi tare da maida wayar ta ajiye,tunanin buɗe chat din ta yazo kanta hakan yasa ta maida hannu dan daukar wayar,sai kuma labaran da ake watsowa a tashar c nn tv yasa ta fasa daukar wayar tare da zubawa tv din ido zuciyarta na wani irin bugu da sauri kamar wadda ake doka guduma,zaraf ta mike tsaye ganin an nuno hotan Halima lokacin da tana raye da wanda take a mace , jikinta duk jini da alamun harbi,wata irin kara ta saka wanda yayi daidai da shigowar wazir falon ,kuma karar tata ce ta alamta masa inda dakin nata yake,dan haka kai tsaye ya saka kansa zuwa ainahin dakin Rahim wadda a daidai wannan lokaci tuni ta koma asalin RAIHAN dinta. ..................... Abba yahya da defity gomner tuni suka sanarwa da gwamna abinda ke faruwa,alokacin ma tuni ya riga ya gani a labarai,hankalin su ya yi matukar ta shi ,wanda hakan ya sa suka hada tarin gaggawa,duk wannan abin da yake faruwa sun san cewa daga makiya ne so kawai ake a yi musu sarƙa. RAIHAN....... Kuka take yi tun karfin ta tana kuma yin watsi da duk abinda taci karo da shi,cak wazir ya tsaya zuciyar shi na wani irin bugu,zubawa Raihan ido ya yi cike da mamakin kammannin da su kayi da Rahim dan sam zuciyar shi ba ta bashi Rahim din ne ba,kawai dai ya yi tunanin yar uwar antyy amarya ce wadda su ke kama ta sosai da Rahim,ko kuma su din 'yan biyu ne,sai dai bai gama tunanin da yake kan yi ba,su kayi ido hudu da Raihan wadda har ta fara fita a hayyacinta,da wani mugun gudu ta nufoshi tsayawa ta yi a gabanshi tare da kama hannunshi, da gaske Halima ta tafi ta barni da gaske mutuwa ta yi? Da gaske ne wasu ne marasa imani suka kashe mana ita?jin shuru yasa ta fara dawowa hayyacinta wanda take ta fahimci halin shock din da wazir ya shiga,sakin hannunshi ta yi tana mai saurin tattare gashinta da yake ta faman lilo a gadan bayanta,to me yay saura kuma ya riga ya ganta to me zata ƁOYE mai? Cikin sarkewar harshe ya yi dauriyar bude baki ya yi mata tambaya da cewa ina Rahim shi nake NEMA? Matsowa ta yi kusa da shi idanunta na sake cikowa da hawayen dalili biyu,ta ce" Hamma wazir babu Rahim Rahim gaibu ne RAIHAN ita ce gaskiya,duba yake mata me cike da tashin hankali da ruɗu duk da cewa ba zaka taba gane hakan ba,domin kuwa wazir jarumi ne kuma dakakken namiji me cike da tarin nutsuwa da ilhama,dan haka da wuya ka gane rudewar shi,cikin yanayin nasa na kamewa ya ce"ban fahimta ba?ey abin da nake nufi shine Rahim din da kake tunanin akwai shi to babu shi sai dai RAIHAN, Raihan ce kake tare da ita a matsayin RAHIM" . Jin kamar kafafun shi zasu kasa daukar shi su kuma fallasa halin da yake ciki yasa shi takawa a hankali ya isa bakin gadon ta ya zauna yana mai ci gaba da bin RAIHAN da kallon tuhuma da mamaki,itama cikin sanyin jiki da mutuwar Halima ta saukar mata ta karaso gaban sa tare da durkushewa a gaban sa,ba tare da ta saurare shi ba ta fara bashi labari kamar yadda antyy amarya da Dr suka sanar mata ko mai bata ƁOYE masa ba har zuwa yau da ta riski ta shin hankalin mutuwar Halima. Zuba mata ido ya yi zuciyar shi cike da mamakin dama Rahim namiji ne tsawan lokacin da yasan shi ,amma bai taba ganewa ba? Ko da yake a kwai wasu lokuta da dama da yake yin wasu abubuwan da yake sawa ya fada zuzzurfan tunani,to amma bai taba kawo cewa ai Rahim din ba namiji ba ne. Kukan RAIHAN dinne ya dawo da shi tunanin sa, da Allah Hamma wazir kar ka gayawa kowa wlh kai ma na gaya maka ne saboda babu yadda zanyi ka riga ka ganni,kuma nayiwa antyna alkawarin cigaba da boye kaina"cikin tarin nutsuwar shi ya dube ta kana ya ce" kar ki damu Raihan Nima nayi miki alkawarin zan ci gaba da boye sirrin ki ,zan ci gaba da kallon ki a matsayin Rahim har zuwa lokacin da kaddarar ki zata sauya"na gode Wazir su kaji Muryar antyy ta ratso kunnuwan su,gaba daya suka maida hankalin su kan kofar shigowa inda anan antyy amarya take tsaye duk da cewa a lamu sun nuna bata jima da shigowa ba, karasowa tsakiyar dakin ta yi tare da jan Stoll din madubi ta zauna ,kana cikin damuwa ta ce" wazir ka riga kasan sirrin mu,sirrin da babu wani abin yarda ta da ya taba sanin sa,da muna mu biyu muka dawo mu uku gashi yanzu mun dawo mu hudu,ban san kuma waye zai zama cikon na biyar din ba,ina matukar jin tsoran fitowar sirrin nan ba tare da mun shirya ba,nasan cewa Raihan bazata taba dauwama a matsayin da take kai a yanzu ba,to amma ba yanzu nake bukatar hakan ba,wazir ina son RAIHAN,,,,ta faɗa Muryar ta na rawa zuciyarta kuma na son karyewa,da kyar ta daidaita kanta ta ci gaba da cewa ,ji nake kamar zan rasa Raihan wannan abin da ya faru da Halima ya kuma tayar min da hankali matuka da gaske,ina ji kamar ko nets target din mugayen nan Raihan ce"da sauri wazir ya dakatar da ita cikin nutsuwa da son kwantar mata da hankali ya ce"antyy ki dai na wannan batun dan Allah,Ni nayi miki alkawarin cewa babu wanda zai san wacece Raihan a bakina ko a bangarena ,kuma nayi miki alkawarin babu abin da zan bari ya samu Raihan insha Allah bazata wahala ba,zan yi iya yina da taimakon Ubangiji dan ganin na bata kariya,dan haka ki sawa zuciyarki nutsuwa RAIHAN tana tare da ke insha Allah,kuma ki sa aranki cewa babu wanda ya isa yiwa RAIHAN ko mai face da izinin Allah, Allah zai kare ta da ga dukkan me Binta da sharri". Ajiyar zuciya antyy amarya ta yi kafin cikin samun nutsuwa da maganar wazir ta ce"na gode wazir kuma ina nan ina ci gaba da addu'a har malamai nasa suke taya mu da addu'a da karatun Alqur'ani ko mai zai zo mana da sauki,idan kuma kaddarar mu ta kasance wata iri babu yadda zanyi dan ban isa yin kokawa da ƙaddara ba."ita dai RAIHAN duban su kawai take amma gaba daya tunanin ta yana kan Halima shi yasa ma sam bata tsaya ta fuskanci inda maganganun nasu suka dosa ba,ko ta tsaya ma ba lallai ne ta fuskanta ba tun da har yanzu tunanin ta karami ne, RAIHAN"ta kuma maimaita kiran sunanta ganin duk hankalinta baya kansu,,,ɗago idanunta da suke cike taf da hawaye ta yi tana duban antyn,kimtsatstsiyar Muryar WAZIR ce ta ratsa kunnuwan ta har zuwa can wani sashe na zuciyarta wanda kai tsaye ba zata iya cewa ga wane sashe ba ne,da kuma manufarsa ta karbar sakon ba.kiyi hakuri ya fada yana mai yi mata wani irin lallashi da idanun sa da kuma dukkan zuciyarsa ,wanda take Tata zuciyar ta karbi sakon lallashin nasa harma tasa hannu ta yi saurin goge hawayen da suke ta tsere saman kyakkyawar fuskarta. Ganin haka yasa ya saki wani dan tattausan murmushi wanda ko da can ita ka dai take iya ganin sa,yauwa ki nutsu gobe zan dawo muje gaisuwa gidan su Halima ,amma idan antyy ta sanar da Ni kin kuma yin kuka ba zaki ganni ba har nan da kwana haka"ya fada yana nuna mata yatsun shi biyar,zaro yalwataccen idanun ta tayi tare da cewa bazan yi ba"kinyi alkawari? Jin jina mishi kai ta yi tana murmushi irin na tsantsar yarinta,ok by sai kin ganni"daga haka ya fita da sassarfar takun shi wanda ya cude da nutsuwa da kamalar shi,bin bayan shi ta yi da kallo tana. Jin wani irin kewa na mamaye ta tare da wani irin nauyi da ya karu a kirjinta. Antyy amarya ta tashi tabi bayan sa tana yiwa RAIHAN gargadin ta tashi ta kimtsa kanta ,dan ta samu nutsuwa yanzu zata dawo. _______________ Duk inda zaku nemo camarar nan sai kun nemota,haba ace yarinya ta Shammace mu irin haka ba tare da mun sani ba"shugaban jam'iya ke nan da yake magana cikin yanayin tashin hankali,Dr ya ce"Ni abin da ya bani mamaki shine yadda aka yi Wazir ya mamaye mu har yasa yar jaridar su ta bibiye mu"Alhaji sale ya ce"kar ka yi saurin yanke hukuncin cewa wazir ne ya sata Ni nafi kyautata zaton cewa shige_shigenta ne ya kawo ta inda muke tun da binciken da mu kayi ya tabbatar mana da cewa yar jaridar sirri ce shi yasa ma bamu sanya ba", shugaban jam'iya ya ce"to amma lallai ta turawa wani video nan idan kuma ba haka ba ta turawa wani a cikin su sakon inda ta ajiye camarar kuma tabbas camarar tana cikin dajin nan da ƙwaro ya harbeta,yanzu abin da ya kamata mu yi shine ,bincike zamu yi mu gano wanda su ka fi kusa da ita a wajen aiki ko irin nasamanta din nan ko dai kawarta ko abokin da sukafi shakuwa,ina ga wannan ita ce hanya mafi sauki da za mu yi saurin gano wanda ta turawa sako"Dr ya yi saurin tarar nufashin shugaban jam'iya da cewa a'a zamu yi hakan amma fa Ni ina ga kawai wayarta za mu kai jago ya yi mana bincike nasan take zai gano wanda ta turawa sakon,ina ga bamu da lokacin da za mu tsaya yin wannan dogon binciken"Alh sale ya ce"tabbas wannan ita ce shawarar dauka mu duk mun ruɗe sam mun ma manta da saukakakkiyar hanya"jin jina kai kawai shugaban jam'iya yake saboda anzo gabar da zai iya yin komai dan samun rufuwar asirin sa da kuma dorewa kan mulkin da suke ta son hayewa a zaben da yake tun karo su. A nan ne kuma ya samu sakon taron gaggawa da gwamna ya nema yan majalisar ta su da sauran membobin da abin ya shafa,dole ya katse tattaunawar da suke da su Dr sanate ya yi shirin tafiya. ______ Tun da Wazir ya tafi tunanika suka cika kwakwalwarshi,tausayin RAIHAN ne fal a ranshi ta yadda ƙaddarar ta tazama haka,to amma babu tsimi babu dabara abin da Ubangiji ya rubuta zai faru dole sai ya faru,yaji tausayin antyy amarya matuka ta yadda ya yi duba da matsanan cin son da takewa gudan jinin ta RAIHAN,tsoran kar ta rasa ta yasa ta kuma kawowa rayuwarta matsala wanda ita antyy amarya duk bata ganin hakan saboda idon ta ya rufe da SOYAYYAR tilon yarta,to yanzu ta yaya zata bayyanawa duniya RAHIM a matsayin RAIHAN,anya kuwa hakan ba zai zama wani babban kalubale ga Raihan din ba,tabbas ya kamata ya zauna da Anty amarya akan wannan batun,dan ya riga ya dauki alkawarin kare Raihan da taimakon zuljalalu Wal Ikram,da wannan tunanin ya karasa gidan makoki,inda yana zuwa jiniyar gwamna Alhaji Garba me fata ta karade baki daya anguwar ta su marigayiya Halima,take mutane suka fara turereniyar ganewa idon su asalin gwamna me zuwa gaisuwar talakawansa da aka zalunta,tuni mata suka fara leke ta soraye masu yi ta katanga na yi,kai harda wadanda suke fitowa waje ,ba don komai ba sai dan zuwan adalin gwamnan su. Cikin mutunci da kamala su ka fara miƙa gaisuwa, abin mamaki a cikin tawagar gwamna har da shugaban jam'iya,shine ma kan gaba wajen mika ta'aziya da bada umarnin yin addu'a ,sosai gwamna ya yiwa WAZIR gaisuwa tare da jaje,daga nan aka fara shiga da manyan buhunan shinkafa da katon katon din ruwa , da kudi masu yawa da ya bawa iyayen Halima, wannan abu da gwamna ya yi ba karamin kayatar da mutane ya yi ba,tabbas ya yi abin da sauran gwamnoni basu taba yi ba,shi yasa baka jin komai sai addu'a da talakawa suke shararo masa tare da yi masa fatan sake komawa gwamnati kai harda masu fatan shugaban kasa,daga nan su kayi sallama, Wazir yana zaune inda yake bai motsa ba bare ya nuna wata alama na son yiwa gwamna rakiya,gaisuwar ma ya yi musu ita ne saboda Abba yahya da yake matsayin uba ga Raihan,ganin haka ne yasa gwamna Alhaji Garba me fata ya ya fito shi ,ba dan yaso ba ya ta shi ya karasa kusa da shi ,Wazir idan ba zaka damu ba ina son ganin ka idan ka samu lokaci dan ina son tattaunawa da kai akan kisan yarinyar nan duk da cewa har yanzu muna kan binciken nemo yan ta Addan da suke son ganin bayan mu"dan sassauta fuska Wazir ya yi kana ya ce"shike nan insha Allah zan samu na zo"idan zaka zo kayi min waya da fasinal layina saboda bana son ka biyo ta kan p.a dan maganar tana bukatar sirri"cewar gwamna ke nan da yake yin gaba dan tarar da mutanen da su kayi cincirindon a bakin motocin su,dan ma 'yan sanda suna yi suna korar su. Shima wazir din bai dade ba ya yi sallama su ka wuce shida su Ishaq. Sosai zuwa wannan jana isa ta kuma samowa Alhaji Garba me fata farinjini,kowa. Ya budi baki sai san Barka da fatan alkhairi yake yi masa (to muma Allah ya bamu shuwagabanni na gari Amin ya Allah) . Da sauri rabi a dake zaune a falon ita da innawuro tana tausa mata kafa,ta mike saboda shigowar da Wazir ya yi,duk da cewa yanayin shi ya nuna a matukar gajiye yake hakan baisa Rabi'ah ta hakura da kokarin tarrar shi da take yi ba,sai dai kafin ta kai ga inda yake har ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu,shigewa yake kokarin yi innawuro ta dakatar da shi cikin nuna kulawa ta ce"wazirin gida ya kamata ka zauna ka huta ka dan saka wani abu a bakin ka,tun shekaran jiya fa in dai ban ɓata lissafi ba rabon ka da saka abinci acikin ka,a gajiye ya dube ta da lumsassun idanunsa da suka kuma lumshewa har rufewa suke saboda gajiya da damuwa kai harma da yunwar da bai kula da ita ba, a hankali ya bude baki kamar me ciwon baki ya ce"innawuro zan bari na kimtsa tukun amma bana son abu me nauyi ki hada min Koda salad ne"to shike nan Allah dai ya jikan wannan yarinya ya kuma tona asirin masu yi mana wannan aika_aika"Amin ya Allah ya fada a saman harshen sa,da sauri rabi a ta ce" bari na hada maka salad din kafin ka fito" bai ko kalli inda take ba ya haye sashen sa. Sai da ya sakarwa kansa shaya ya wanke jikinsa,tare da ɗauro alwalar magriba sannan ya ji nutsuwar sa ta fara dawowa,doguwar blue din jallabiya ya saka tare da fesa turarukan sa masu sanyin kamshi.daga nan ya zura tattausan silifas dinsa ya dauki wayoyin sa ya fita. Kusa da innawuro yaje ya zauna tare da dora kansa a kafadar ta ,shafa kanshi ta yi tana cewa rabi a kawo masa salad din nan zai fi ci a.gabana". Ba dan yaso ba sai dan rabuwa.da mitar innawuro ya karba ya fara ci a hankali,yana yi yana duba sakonnin da suka.tarun masa,bai wani ci da yawa ba duk dan saboda ba innawuro ce ta haɗa masa da kanta ba,dan haka a darare ya ci wannan din ma,ta shi ya yi tare da duban innawuro ya ce"zan shiga gurin Ammi sai anjima zan dawo"Tom shike nan sai ka dawo,rabi a najin haka ta mike tsaye,ganin tana kokarin fita , Wazir ya kara haɗe fuska kafin cikin miskilalliyar Muryar shi ya ce"ki zauna da innawuro"daga haka yasa kai ya fita,babu yadda ta iya dole ta hakura da bin nasa, innawuro ta dube ta tare da zabga mata harara ta ce"wannan rawar kan da kike shi zai hana ya yi miki duban Rahma bare na soyayya ,dan haka idan zaki nutsu ki kama kanki to ki nutsu kin dai san halin sa sarai bai san hayaniya"tura baki gaba ta yi ta koma ta zauna tana saƙa yadda za ayi ta cusa kanta cikin zuciyar Wazir . ________ Tsaf antyy amarya ta dawo ta samu Raihan,dan haka sai ta koma ta debo mata abinci ta zo ta zauna kusa da ita,cikin rarrashi ta shiga yi mata nasiha har ta samu ta fara karbar abincin.koda ta gama bata abincin bata barta ita kadai ba,zama ta yi tare da ita tana ɗebe mata kewa, cikin hakan da kuma dabara ta dinga jin damuwar RAIHAN har taso ta dan fuskanci wani abu akan mu amalarta da A Wazir,sosai antyy amarya ta bawa Raihan lokacinta ,wanda dama tana yin hakan lokaci lokaci tun can farkon tashin Raihan din ,ko dan ganin yadda ta kuntata rayuwar ta ta hanyar hanata mu'amala da mutane,yanzu kuwa da ta fara girma tana zama da ita ne saboda bata son kusancin yarta da kowa idan ba ita ba,bata son yarta ta yadda da kowa idan ba ita ba,bata son 'yarta ta kaiwa wani damuwarta idan ba ita ba,haka ba ta so 'yarta ta zama me yi mata nuku_nuku akan lamarinta. Aiko dai aunty amarya ta yi nasara dan kuwa ta yiwa RAIHAN ja a jikin da bata iya boye mata damuwarta. RAIHAN aunty ta fada tana shafa kan Raihan din dake kan cinyarta,na am aunty Raihan ta amsa cikin siririyar muryar ta me cike da yarinta,ki daina damuwa akan mutanen da suke son mu amala da Wazir saboda idan kina yin haka zai dinga jin haushin ki,musamman ma akan kokarin ki na raba shi da duk wata budurwa"tura karamin bakinta ta yi, sannan ta ce"auntyy nifa ba hana shi na yi ba,kawai dai bana son suna kula shi ne sai na dinga jin wani irin bugu a kirjina,aunty nifa ko tunawa nayi sai naji damuwa ta lullube Ni"ta karasa maganar tana jin damuwar tunawar da gaske tana lullubeta,shuru aunty amarya ta yi tana nazarin maganar Raihan din,dama ta yi haka ne dan ta san dalilin da yasa Raihan din ke korar yammatan ko dan ta yi tunani me zurfi akan hakan, shafa kan Raihan din ta ci gaba da yi tana cewa ki dai dinga daurewa bana so yazo yana jin haushin ki kinji ko"gyada kai Raihan din ta yi daga haka suka tashi dan yin alwalar magriba,duk da cewa Raihan din ba yin sallar zata yi ba. Wazir yana shiga falon Ammi aka kira sallar magriba,hakan yasa ya gaidata a gaggauce su ka fita sallah shida Abbu. Koda suka dawo daga masallaci bayan sallar Isha, wajen Ammin ya koma ,sun jima tare Ammi da Abbu na yi masa nasiha akan abinda ya faru,daga nan Ammi ta tilas ta masa cin abinci ,yana ci suna yi masa hira har ya ci da dan yawa bai sani ba, sosai yaji nutsuwa atare da shi, cikin murmushin da bayan su da innawuro da Raihan ba kowa ne yake samun sa akai akai ba,ya ce"Ammi kunyi min wayo dai kamar wani karamin yaro"dariya Abbu ya yi tare da cewa to ai dama mu kullum kamar jariri kake a wajen mu,kaima kuma nasan haka kake ji ko? Sassanyar dariya ya yi tare da ƙara lumshe idanun shi da dama suke kamar na me jin bacci,haka nan ya dinga jin nishaɗin kasancewa tare da iyayen nasa ,haka nan sai kuma RAIHAN da damuwarta suka fado masa,tashi ya yi yana duban agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa,ya ce"Abbu dare ya fara yi ni bari na wuce na kwanta na huta,ga kuma sammakon zuwa sadaka"to shike nan Allah ya tashe mu lafiya,Abbu ya fada ,har zai fita sai kuma ya dakata tare da juyowa ya ce"Abbu tare zaku tafi da innawuro saboda Ni zan bi ta gidan su Rahim na dauko shi"fadar sunan Rahim da ya yi sai yaji kamar ya yi sabo,Abbu ne ya katse shi da cewa Tom shike nan idan ka shiga sai ka sanar da ita"jinjina kai ya yi ya fita yana ci gaba da sauraren addu ar da Amminsa ke yi masa, da haka har ya fice gaba daya daga falon yana mai jin kaunar iyayen sa na kuma nunkuwa a zuciyarsa da dukkan rayuwarsa. _______________ A bangaren gwamna kuwa sai da suka dawo daga ta aziya, sannan su shiga dakin taro, Alh Garba ya so ace Amininsa na wajen ,to amma duk da haka bata ɓaci ba,dan yasa Abba yahya joining din shi ta video call.sosai suka tattauna akan matsalar karancin tsaro wanda kuma duk wannan yana daga manyan mu wadanda su suke aikata laifin shi yasa ba a daukar wani mataki akai,to amma wannan karon sun shirya yaki da wannan matsala da ta riga ta zama kamar annoba a cikin garin nasu. Alhji Muhammad nuurr dake kallon su ta ƙatuwar laptop bai ce komai ba , saboda shi sam baya son yawan sako shi da gwamnan ke yi cikin lamarin siyasar su,saida Abba yahya ya nuna masa alama da ido akan ya ce wani abu, sannan ya danyi bayani a takaice daga nan aka rufe taro da addu'a kowa ya kama gabansa. _________ Aunty amarya na tsaye ta gama shirinta na bacci,idan da baya ne tare da zasu kwanta ,to amma saboda yanzu raihan ta fara zama budurwa yasa Aunty amarya ta fara barinta ita kaɗai amma fa duk farkawar da zata yi sai ta zo ta duba Raihan din da safaya key din da yake hannunta,duk da cewa Raihan a matsayin namiji duniya ke kallonta ,hakan bai sa aunty amarya ta yi sake da baki akan tilon yarta ta ba,sosai Raihan take karuwa da mahaifiyarta ta fannoni da dama,ta ɓangaren ilmi da kuma zaman takewar rayuwa,idan goggo Rahma ta shigo taga Raihan a kiching sai ta yi ta faɗa akan wai aunty zata maida yaro dan daudu,dama a hakan ma ya aka cika yana yin wani abu kamar mace bare kuma tana sa shi girki,antyy amarya takan ce kiyi hakuri goggo ai ko namiji ana so ya koyi aiyukan mata saboda baka san inda rayuwa zata kai ka ba"goggo kan tabe baki ta ce"ke dai fi'ili kawai da kuma takurawa yaro,to duk irin wannan tuni antyy amarya ta riga ta gina rayuwar RAIHAN da shi,sam Raihan bata da ƙyuya irin ta wasu sangartattun ya'yan masu kudin,da wannan tunanin antyy amarya ta gama lura da shirin Raihan din da duk wata tsafta ta kwanciya da ya kamata ta yi,ta kuma tabbatar babu wata matsala sannan ta yi mata addu'a bayan ta rufe ta cikin tattausan bargon dake malale a saman gadon,shafa kanta ta yi ta ce"kema kiyi addu'a kinji Allah Ubangiji ya tashe mu lafiya, murmushi RAIHAN ta yi sannan ta langabar da kanta ta ce"ina son ki mamina "Nima Ina sonki autata"auntyn ta faɗa tana sumbatar goshin Raihan din,marairaice fuska Raihan din ta yi tare da cewa dan Allah aunty zan dan bude data na,yau kwana biyu ke nan ban ga sakonni ba,nasan a na ta yi min ta aziya"dan jim aunty amarya ta yi kafin ta furzar da numfashi ta ce"to amma kar ki dade Kinga idan Allah ya kaimu za muje gidan sadaka dan haka ban so ki makara dan ma ba zaki yi tashin sallah ba"promise aunty bazan jimaba, Raihan ta faɗa a marairaice"shike nan Allah ya tashe mu lafiya"daga nan ta fita tare da rufewa Raihan kofar. Tana fita Raihan ta janyo wayarta ta kunna tare da kunna data,cikin kankanin lokaci sakonni suka fara rige_rigen shigowa,a shigowar sakonnin ne wani sako ya ja hankalinta saboda sakon daga Halima ne.....ɗiiiiiiiii Muje zuwa pg na gaba dan ganin sakon da Halima ta turowa Raihan me sakon ya kunsa kuma me sakon zai haifar? Kuyi min share tare da zazzafan comments din da zai kara min karfin gwiwa kar ku manta littafi na ɗaya kyauta ne,idan ba ku yi comment yadda ya kamata ba zan maida shi gaba dayan shi vip arewabooks 😌 Fatima y Adam ✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page10 ``` Kafin ta bude sakon wayar ta shiga fidda wani dan karamin sauti me dadi wanda yake nuni da cewa kiranta a ke yi,ganin wanda yake kiran yasa ta fasa abin da ta yi niya wato share kiran, ɗagawa ta yi tare da karawa a kunnenta,sallama ta yi cikin Muryar ta da tayi can ƙasa saboda alamun shirin bacci,amsawa Wazir ya yi tare da ɗora Mata da tambaya,ba kiyi bacci ba? Ji tayi gudun jininta ya ƙaru da ƙyar ta daidaita kanta ,ta ce" Banyi ba amma ina shirin yi"to ki kashe wayar ki kwanta"marairaice murya ta kuma yi wanda hakan ya bata wani amo me ratsa jijiyar jiki ,rintse idanun shi ya yi ba tare da yasan ya yi hakan ba,bai kuma san ma anar yin hakan ba,dan Allah ka barni wani sako zan duba kawai na kashe"kokawa ya fara yi da numfashin sa,ita kuma jin ya yi shiru yasa cikin wata irin shagwaba da ta riga ta ratsa jinin ta ,ta kuma cewa dan Allah fa dan Allah Hamma wazirrrrrr"wata yar ɓoyayyar ajiyar zuciya ya saki tare da sakin numfashinsa , sannan a hankali ya ce",wane irin sako zaki duba? Samun kanta ta yi da kasa fada masa gaskiyar cewa sakon kamar ya danganci halima ne,sai kawai ta ce"wani fans dina ne yake min ta aziya shine zan duba"ji ya yi kawai kirjin shi ya yi wani irin nauyi iskar shaka tana kokarin yi masa wuya,cikin son ƁOYE abin da yake ji ya ce"ok ki duba sai ki kashe kin san sammakon fita za mu yi,dan ya kamata ke da har yau ba kije ta aziya ba kije da wuri ,saboda kar hakan ya jawo hankalin mutane har su fassara hakan da wata manufa"shike nan insha Allah zan yi yadda ka ce" yana kokarin kashe wayar ta yi saurin dakatar da shi,da wani abu? ya fada a takaice, Hamma wazir jin ka nayi kamar ba a daidai ba,ji nayi ajikina akwai damuwa a tare da kai bayan wadda muka shiga ta rashin Halima da sauran abin da ya faru a tsukin nan?mamaki ne ya kama wazir chibado ya a ka yi Raihan ta fuskanci yaji damuwa akan ta? Duk da ya kasance me tsananin taka tsantsan da ƁOYE damuwar shi akan komai ,ta yadda mutane ba su taba fuskantar ta, Hamma wazir" ta faɗa cikin wata kasalalliyar Muryar da bata san ta yi ta ba,idan kowa zai kasa gane damuwarka ko walwalarka to kasa a ranka banda RAIHAN,ka kuma sa a ranka duk abin da kake yi da halin da kake ciki Raihan zata sani ta hanyar ji a jikinta da zuciyarta" daga haka ƙit ta kashe wayar tare da danne damuwar wazir. Shuru ya yi tare da zubawa wayar idanu tamkar zai ga Raihan din ta cikin wayar,sai kawai ya samu kanshi da fitar da wani tattausan murmushi wanda ya fito tun daga ƙasan zuciya. Bata saurari sakon kowa ba kai tsaye ta tafi ga sakon da yaja hankalin ta tun farko,wato sakon Halima. Wani irin bugu kirjin ta ya yi a yayin da ta ci karo da abinda Halima ta turo mata. Rahim duk yadda za ayi idan ƙurar mutuwata ta lafa kazo address ɗin nan ka duba wata alama a dai dai jikin bishiyar magarya ta baya a nan na ajiye camarar ,kuma duk abinda kuke so ku sani yana ciki,suna so su danganta abinda suke aikatawa da Gwamna wanda Ni kaji hakan da kunnena,dan haka ka kiyaye ko da zaka ji wata magana akan gwamna game da kisan da ake yi ,to ba haka ba ne sharri suke son yi masa,kai ka dai zan iya bawa wannan amanar, ina rokon Allah ya bar rayuwarka domin ceton al ummar da suke cikin tashin hankalin mugayen shugabanni,Rahim dan Allah kar ka dauki camarar nan yanzu sai bayan wani lokaci saboda kaima nasan zasu iya kashe ka idan suka gano camarar na hannun ka,amma zan gaya maka sunayensu koda baka samu damar dauko camarar ba domin ka sake yin sabon bincike akan su, Alhaji s......wayyo ga su nan sun biyo NI Rahim suna gab da cimma Ni,amma ka binciki D......a daidai nan sakon ya katse,,,, A rude RAIHAN take cewa su waye Halima karasa baki karasa min sunan S ba kika dauko min D me s take nufi me D take nufi? Innalillahiwa'inna ilaihi raji'un take fada kai ka ce waya suke da Haliman a lokacin ,duk tambayoyin da take kai kace Haliman zata amsa mata su ne a lokacin, Zubewa ta yi saman gadon kamar wadda babu laka a jikinta,kuka take son ta yi amma ji take kukan ma ya kasa fitowa ,wani irin zafi kirjin ta ke yi kamar ana gasa gurasa,cikin jan ajiyar zuciya ta fizgo kukan da wani irin ƙarfi,kuka ta yi sosai na ciwon mutuwar Halima da kuma rashin Makama akan takamaiman abin da Haliman take nufi da S da D,zabura ta yi tare da kara wawuro wayar ,sake duba address ɗin ta yi ,sai a lokacin ta dan samu nutsuwa tunda tana da tabbacin cewa ma anar S da D suna cikin camara. Har wajen karfe biyu Raihan bata yi bacci ba,tana nan ko kwanciyar ta kasa yi bare idan ta kwanta baccin ya saɗado ya dauke ta. kamar daga sama taji sassanyan ringing din wayarta,ba karamin mamaki ne ya rufe ta ba ,ganin me kiran, cikin sanyin da jikinta ya gama yi ta daga kiran tare da karawa wayar a kunnen ta,a hankali ya dan furzar da wani zazzafan huci daga bakinsa, tare da kara lumshe idanun da suke cike da gajiya da tarin damuwa,murya can kasa kamar me yin mura ya ce"RAIHANNN yadda yaja sunan cike da kasalar gajiyar dake tare da shi ya haifar mata da wani irin jin sanyi me ratsa kasusuwan jiki da bargo,bata san sanda ta fara rawar ɗari ba,dan kuwa tabbas Muryar WAZIR ta haifar mata da zazzabin farat daya,baki bacci ba? Ya tambaye ta cikin ƁOYE mamakin rashin jin batayi baccin ba"umm ta ce ba tare da ta bude baki ta yi magana ba,me yasa? Ya kuma tambayarta"kai me yasa ba kayi baccin ba Hamma wazirrrrrr? Ta maida masa da tambayar itama cikin dan mamakin kiranta da ya yi a daidai wannan lokacin,rufe idanun shi ya yi yana kokarin nemo dalilin domin ya bata amsa tun da shima yana so ta bashi amsar abin da ya hana ta baccin,to amma me zai ce mata? Gaskiyar maganar bata da wani ma'ana bare ya fadeta,to rashin ma'ana mana,idan ba rashin ma'ana ba ta yaya zai ce ya kasa bacci ne saboda yaji a jikinsa ba tayi bacci ba dalilin damuwarta da yake ji a can cikin ƙasan zuciyarsa, Hamma wazirrrrrr "ta kira sunan shi jin ya yi shiru"cikin dakiyarshi dake nunawa a zahirinshi ya ce"naji kamar wani abu yana faruwa bayan mun gama waya "shine ya hana ka bacci? Ta tambaya tana mai son boye mamakin ta da kuma damuwar da bata son ta fallasa har Wazir ya san da ita ya kuma tambayeta ba'asi,zazzafan huci ya fesar tare da ƙara gyara kwanciyar shi kana ya ce" ina ga haka ne"ke fa me ya hana ki bacci Raihan?cikin yanayin ta na shagwaba ta langabar da kai kamar yana gaban ta ta ce"Hamma wazirrrrrr babu komai kawai ina tunanin yadda zan ci gaba da tafiyar da rayuwata a haka ne bayan kuma ina jin cewa Ubangiji babbar baiwa da Ni ima ya yi min na kasancewata mace kuma musulma" duk da ya ji cewar kamar ta ɓoye masa wani abu bayan wannan,sai ya yi kokarin kwantar mata da hankali,rufe idanun ta tayi tana jin cewar kamar bata da matsala idan Hamma wazirrrrrr yana kusa da ita kuma yana tare da ita,haka nan ta ji ta samu nutsuwa akan yanayin ta na baya. RAIHAN ki nutsu ki yi bacci kinji"ya fada cikin lallashi da tausasa murya,to kaima za kayi? Ta faɗa a sangarce,lumshe idanun ya yi kafin ya bude, sannan ya ce" ba kince kina jin komai nawa a jikin ki da zuciyar ba? Ey mana ta faɗa da sauri kuma cikin tabbatarwa,yauwa to idan na yi bacci gobe za ki gaya min Nima idan kin yi zan gaya miki,duk wanda ya fada ba daidai ba to abin da ya fada na cewa muna tare da juna a cikin ko wane yanayi ba haka bane"cikin farinci ta ce"na yadda"ok to Allah ya tashe mu lafiya"ta amsa suna mai kashe wayar a tare,jin motsin antyy amarya yasa ta yi saurin kashe wayar ta rufe kanta tare da rufe idanunta ,saboda da gaske ta ji tana son ta yi baccin ko dan Hamma wazirrrrrr. Sai da aunty amarya ta zo ta bude ta ta tabbatar da lafiya sannan ta fita daga dakin,bayan ta kuma tofa mata addu'a (Ubangiji Allah ya sakawa iyayen mu da alkhairi Allah ya sa su gama da duniya lafiya,wadan da suka mutu Ubangiji ya yi musu rahama). Wazir ma dai ya samu ya yi baccin ,dan har sai da ya dan makara zuwa Sallah. Ita kuwa RAIHAN Saida aunty amarya ta shigo ta tayar da ita saboda yadda babu zato bacci me nauyi ya sureta,ko da ta tashi cikin sauri ta shirya ta fito falo su ka karya,itama antyy amarya a shirye take ,amma ba tare zasu tafi ba,ita za su tafi tare da goggo Rahma da jiddo, da kuma inna maimuna, Raihan ta dubi aunty amarya lokacin da take miƙewa daga saman dininng ta ce"wai aunty sun je kuwa? girgiza kai aunty amarya ta yi tare da dan haɗe fuska sannan ta ce" ba su je ba kuma bana tunanin zasu je" daga haka itama ta mike ta wuce bedroom dinta Dan dauko mayafi da jaka.taɓe baki Raihan ta yi tana mai gyara ƙatuwar jaket din da ke jikinta ,ta wuce daki ita zata dauko wayarta tana mai ɗan gyagygyara shigar ta wadda ta rufe kyakkyawar surarta ta me shirin zama cikakkiyar budurwa. Tsaf ya fito cikin shigar manyan kaya wanda su kayi masa matukar kyau ko dan bai cika saka su ba ne oho,hakan sai ya kara fiddo da kamalar sa dake nuna tsananin nutsuwar da yake da ita,tuni rabi a ta saki baki da hanci tana kallon tsayayyan namiji me cike da baiwa daban daban, innawuro dake saɓa mayafi ta dube shi tare da cewa ,kai irin wannan shiga kamar me shirin zuwa daurin aure ,anya kuwa mutanen nan ba za su ji haushin ka ba?tsalaf rabi'ta saka baki da cewa ke kuwa innawuro kin san cewa duk kayan da hamma wazir ya saka sai sun fidda kyawun shi da kwarjinin shi,dan haka ma ko ya canja sai ma dai kiga ya fi da yin kyau"innawuro ta ce"hakane maganar ki rabi,sai ka wuce muje"duban ta ya yi cikin haɗe fuska ya ce"ba tare zamu tafi ba"to saboda me"innawuro ta faɗa a harzuke,saboda zan biya wani wajen kafin na karasa can gidan addu'ar"to da wa za mu tafi? Da su Abbu zaku tafi na gaya masa"to shike nan amma ka tafi da rabi dan mota daya ba zata ishe mu ba"innawuro ta faɗa cike da kumbura fuska dan karma ya Musa mata,to ko bata yi hakan ba ma dama baiyi niyar magantuwa ba dan ya gaji da maganar,hakan yasa ya wuce cikin sassarfar takun shi me matukar birgewa,sosai Rabi'ah ta ji dadin abin da innawuro ta yi ,dan haka cikin sauri ta bi bayan shi dan ta san yana iya fecewa ya barta. A can wajen su Raihan kuwa tuni ta fito harabar gidan tana jiran wazir ,saboda antyy amarya ma da goggo Rahma sun fito,har zasu ta fi sai goggo ta dubi jiddo ta ce"ke ki tsaya Rahim kun taho tare dan kar a barshi ya yi jira shi kaɗai,da sauri Raihan ta dubi goggo ta ce"Ni zan iya jira abin da gidan da mutane ga yan aiki da masu gadi"goggo ta ce"a'a ta dai tsaya ku tafi tafiyar ta fi muku daɗi " jiddo ta ce" shike nan goggo sai mun taho ɗin"to sai kun taho"goggo ta fada tare da shigewa motar da har antyy amarya ta tayar da ita.har suka fita idanun Raihan akan motar yake ,ji ta yi ranta ya ɓaci da wannan shishshigi na goggo,ita kuwa jiddo murmushi ta yi tare da cewa Allah na gode maka yau zan zauna gani ga wazir abin da na dade ina son yi ban samu dama ba" ta karasa maganar tana kunshe bakin ta saboda dariyar hararar da Raihan ke ta zuba mata,ta sani sarai Rahim baya son hada ta da wazir tun da tasha nuna mata tana son raka ta aiki amma sai ta kufcewa hakan,ita dai jiddo bata kawo komai a ranta ba tun da ganin ta babu abin da zai sa namiji ya yi kishin namiji in dai ba akan wata harkar banza ba,wanda kuma ta yi yakinin cewa ko a mafarki ba zata saka Rahim a wannan jerin ba. A cikin hakane me gadi ya wangale katon gate din gidan nasu, kyakkyawar mota baka me tsananin kyau da sheƙi ta shigo farfajiyar gidan,duk da bata taba ganin shi da wannan motar ba amma ta ji a jikinta Wazir ne,ko da yake ita har yanzu bata gama tantance yawan motocin sa ba,har gaban su ya zo ya yi parking, cikin kamewarshi da gizagon dake ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarsa ya zuro kansa tare da zuba mata narkakkun idanun sa wanda kullum suke kamar na me jin bacci, Rabi'ah dake gefan sa sakin baki ta yi tana kallon sa,ban da kara birgeta da ya yi har da tsagwaran mamakin ganin yadda lokaci guda duk cin maganin da suka taho yana yi mata ya gushe ya maida gurbinsa da nutsutstsan murmushi mai matukar wahalar samuwa gare su da duk wani da ya yi masa farin sani. Ba sai ka fito ba bandirawo wazirrrrrr mu wuce kawai,ta faɗa tana zagawa bangaren daman sa wato kujerar me zaman banza,da sauri jiddo ta wuce ta bude gidan baya ta Wada dan kar ma tsautsayi yasa a fasa tafiyar da ita damar da take nema ta kufce mata. Wani irin jan burki RAIHAN ta yi ganin Rabi'ah zaune a gidan gaban bata da alamar motsawa,duk da cewa tun tahowar su wazir ya umarce ta da idan sun zo zata koma sit din baya,kafin kace me idanun RAIHAN sun ciko da kwallar da batayi mata wahala,cikin kosawa da lamarin Rabi'ah ya ce"fita "da sauri ta dube shi kafin ta ce"amma ina ga Ni ce ya da ce"na zauna kusa da kai tun da ina matsayin yar uwar ka kuma matar da zaka aura ko?"tamkar walkiya haka suka ga Raihan ta bar wajen da wani irin fasifar gudu,ya yin da take jin duniyar na wani irin juya mata tamkar fanka,cikin ɓacin ran da ya kasa ɓoyuwa a ran shi kamar yadda ya saba ya ce"me kika yi hakan? Cikin mamaki ita ma rabi a ta maida masa tambaya da cewa me nayi kuwa ai Ni ban ga abin jin haushi a kalamai na ba? Jiddo ta yi tsalam ta ce" ke ce baki ga abin bacin ran ba ,tun da baki san matsayin Rahim a wajen wazir ba kuma baki san matsayin wazir a wajen Rahim ba",ta karasa maganar cike da jin haushin rabi ar da take yiwa kanta ikirarin kanta a matsayin wadda wazir zai aura,cikin nutsuwa wazir ya fita daga motar ya bi bayan RAIHAN zuciyar shi fal damuwa da tsananin haushin rabi a da ta bata masa ran Raihan. Jiddo ta ce" ka ce zama ya ganmu tun da an tabo dan lele,ga shi rarrashin Rahim yana da wuya idan har a ka sake ranshi ya ɓaci Gara ma kai kana iya shawo kanshi da wuri" ta karasa maganar tana gallawa Rabi'ah harara tare da gwalo duk a lokaci ɗaya,ƙwafa kawai rabi a ta yi tare da fitowa daga gaban ta koma gefan jiddo,jiddo ta ce" a to mutum ya yi abin da Rahim ya ke so ko mu tafi mu bar shi"duk da haka dai rabi a bata tankawa jiddo ba saboda ba ita ce a gabanta ba yanzu tsananin kishin wazir ne kawai ke cin ranta da kuma son gano dalilin wannan kakkarfar alakar dake tsakanin wazir da Rahim. Kwance ya sameta tana faman kuka kukan da yake daukar shi na tsantsar shagwaba,dan ware manyan idanun shi da suke alumshe ya yi yana kallon yadda take ta kukanta babu abin da ya dameta,cikin sassarfar ya karasa bakin gadon tare da kiran sunan ta, RAIHANN, ya fada cikin jan sunan ta yadda yake shiga can cikin jini da bargon ta,shuru ta yi ba tare da ta amsa ba sai dai ta yi shiru da kukan,sai jan numfashi da take yi a hankali,zama ya yi tare da kamo hannun ta ya rike cikin tafin hannun shi, sannan a hankali cikin taushin murya ya ce" baki ji na ce ta fita ba? Me yasa kuma zaki damu kanki? Tura karamin bakin ta ta yi tana kokarin kwace hannun ta cike da yanayin shagwaba,mai makon ya sake mata hannun kawai sai ya jawo ta ya mikar da ita tsaye suna fuskantar juna,maida kanta ta yi kasa tana mai kin hada ido da shi,umm baki bani amsa ba"ya fada yana rintse hannun ta cikin nashi,cikin san fashewa da wani kukan ta ce"ba ita ce ba"ai nasan ita ce ki gaya min abin da ya bata miki rai saboda na ja kunnen ta kar ta sake"kai tsaye ta ce"ta daina cewa kai zata aura bana so"lumshe idanun ya kuma yi tare da fidda wani dan gajeren murmushi kana ya ce"Tom zan gaya mata kar ta kuma saboda Ni Raihan ce zata haifo matar da zan aura ko? Da sauri ta toshe bakin sa tana zaro manyan idanunta ta ce" yi shiru Hamma wazir kar ka fada a harshen Mala'iku" dariya su kayi gaba daya,janta ya yi zuwa bakin madubi yana cewa gyara fuskar kar su yi kiki dariya,shi ya dau abin shafa fauda ya gyara mata fuskar ta yi tass kamar ba ita ce ta yi kuka ba. Sai da ya tabbatar bata da sauran damuwar rabi a sannan ya ja hannun ta suka fita,bude mata gaban ya yi ta shiga sannan ya koma mazaunin sa ya shiga tare da tada motar,sai da suka fita daga gidan sannan jiddo tai magana cikin son turawa rabi a haushi ta ce" dama na gaya miki rarrashin Rahim sai Hamman sa wazir, sannan sanin matar wazir sai Allah wata kila ma Rahim ne zai zaba masa matar da ta da ce da shi dan haka ina ga ki shafawa kanki lafiya" a fusace rabi a ta ce" tunda Rahim din ne magabatan sa ai dole ya sama masa mata,kuma Ni da kike gani zabin iyaye ce dan haka babu yadda za ayi da Ni" zaro ido jiddo ta yi har da dafe kirji ta ce" au ashe ma matar cushe ce?tuni rabi a ta harzuko ganin haka yasa wazir taka musu burki ta hanyar daka musu tsawa dole suka ja baki suka tsuke,ita dai jiddo dariya ce kawai ke cinta ta yadda ta kunna rabi a kamar wutar karmami,ita kuwa RAIHAN batutuwan da suke tattaunawa sune su ke yi mata ciwo wanda har sai da fuskarta ta bayyana cewa ta kuma shiga damuwa,abin da wazir ya lura da shi ke nan ya yi saurin taka musu burki dan ya fahimci gaba daya RAIHAN bata cikin hankalinta. A haka suka karasa gidan makokin, suna tsayawa Raihan ta yi saurin fita dan karma ya ce zai tsaida ta dan shi kansa ji take kamar ta yi ta dukan sa ,dukan su haushin su take ji karma rabi a taji labari,babu yadda ya iya haka ya fito suka bi bayan ta. Wazir ya san cewa raihan bata isa ta zauna a cikin gidan ba a matsayin da take takawa na namiji, sannan kuma babu yadda za ai ya bari ta zo ta zauna cikin maza dan zama na wani dan lokaci,hakan yasa suna fitowa daga gaisuwar cikin gida ya yi sallama da baban halima akan cewa za su je wani dan aiki,jan hannun RAIHAN dake rakube a gefe ya yi suka nufi wajen motar sa,bude mata ya yi ta shiga har lokacin babu walwala a tare da ita,zuwan ta gidan ya dawo mata da sabuwar damuwar da ta binne cikin ranta,tunanin ta ya dawo sabo akan ta yadda zata fara gudanar da aikin cikin sirri kuma ita kaɗai...... Fatima y Adam ✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page11 ``` Jin sassanyan hannun shi ta yi saman nata hannun dake zube kan cinyoyinta,a ya yin da yake kokarin fita daga layin su marigayiya Halima,ajiyar zuciya ta saki a ɓoye ,tare da ɗan duban gefan fuskarsa inda hadaddiyar kasumbarsa take kwance lamban tana ta zuba sheƙi baƙa siɗik da ita,ina alkawarin mu na jiya? Ya tambaye ta dan son kawar mata da tunanin da take ta kokawa da shi,kawar da fuskarta ta yi daga barin kallon nasa tana mai jin wani irin nauyi a kirjinta wanda idan ya tasar mata numfashinta har wani sarkewa yake,bata san taka maiman abinda yasa take jin hakan ba,kawai dai tasan tun dazun da abin ya faru kirjin ta ya yi nauyin numfashinta ya nemi tokarewa,kuma har yanzu bata ji ya sassauta ba,sai ma haɗewa ya kuma yi da tunanin da take ta yi akan sakon camara,hakan yasa abin ya yi mata yawa matuƙa. Wane alkawari? Ta tambaye shi fuskarta babu alamun fara a sai tarin damuwa,huci me zafi ya dan fesar kana cikin nutsuwarsa ya ce"RAIHAN me yasa kike son takurawa zuciyarki? Me yasa kike son sawa kanki ciwo tun da kananun shekarun ki?me yasa kuma kike son fara boye min wani abu da ya shafi rayuwarki da zuciyarki? Kuka ta saka masa kawai saboda shi ka ɗaine hanyar da take jin zata samu sassaucin abin da take ji a ranta,dafe goshinsa ya yi tare da furta ya Allah "a hankali ya samu gefan titi ya tsaya,shuru ya yi yana sauraran kukanta da yake shiga ko wace kafa ta jiki da zuciyar shi,bai tsaida ita ba sai da ta yi me isar ta sannan ta share hawayen ta wanda take jin baza su taba daina zuba ba in dai zata ci gaba da rayuwa da wazir yana kula wasu matan ko kuma su suna kula shi,a yanzu tana jin bata da wata babbar damuwa me illata zuciya da gangar jikin ta sama da wannan, wannan damuwar ita ta hana ta samo mafita a kan batun camarar halima ,da ace babu damuwar wazir chibado tabbas da tuni ta samo mafita akan yadda zata yi ta dauko camarar da ma yadda zata gabatar da duk wani binciken ta cikin sirri,cikin wata irin murya me dauke da sautin da ke kashe gaɓɓan jiki ,ta ce "Ni ban sani ba Hamma wazir,ban san damuwa ta ba,abu daya na sani shine akan ka ne"cikin nutsuwa ya juyo ya fuskance ta tare da cewa me ya faru ki gaya min damuwar ki kawai nake son na sani hakan shine zai bani damar magance miki ita kamar yadda na yi miki alkawari"ya fada yana son shigar da kwayar idanunsa cikin nata,duk da ta ki bashi damar yin hakan, idanunta ta ɗago cike da kwallar da taƙi tsayawa kuma take tahowa da tsantsar damuwar dake dankare cikin ranta, HAMMA WAZIRRRRRR ta fadi sunan ba tare da tasan yadda ta tsinkawa wazir ɗin duk wata laka da jinin da ke gudana cikin jikin shi ba,bai san sanda ya kifa kanshi jikin sitiyari yana fidda wani irin numfashi me huci ba, cikin Muryar da ta kuma ci gaba da ratsa zuciyar shi da juya duniyar shi ta cigaba da cewa, wannan rabi din abin da ta faɗa da gaske ne? Me ta faɗa ya tambaye ta ba tare da ya ɗago kansa ba,ɗan matsowa ta yi daf da shi har ɗumin bakinta me fitar da ƙamshin minty da ya haɗe da ƙamshin kanumfari ya na bugun numfashinsa,cikin yin ƙasa da murya kamar me raɗa ta ce" wai ita zaka aura? Ɗagowa ya yi da sauri har sai da ya dan buge fuskarta dake daf da shi,zuba mata ido ya yi yana kallon yadda take ta kifkifta idanun kamar zata fashe da wani kukan, murmushin da yake da matukar wahala a gurin sa ya sakar mata tare da kama kumatunta yana cewa Kingan ki da rigima ko Raihan,idan ita ta faɗa miki haka to kin ji daga bakina ne?girgiza kanta ta yi dake cikin tafikan hannayen shi,to me yasa hakan zai dame ki bayan kin san me damuwarki ke nufi a wajen mutane uku da kike da muhimmanci a cikin rayuwar su?ƙifkifta idanun ta yi sai ga hawayen sun zabo ta ce"amma ai cewa ta yi iyayen ka sun amince" karya take' ya fada kai tsaye yana kuma share hawayen da suke tuttudowa daga cikin kyakkyawar idaniyar ta. Kallon shi take yi da dukkan zuciyarta tana jin abin da ya tokare mata kirji na sauka a hankali,kin yadda? Ya tambayeta bayan ya gama share hawayen,ga kuma mamakin sa a yanzun hawayen sun daina zuba ba kamar farko ba da suka ƙi tsayawa,rike hannun shi ta yi cikin marairaice fuska da shagwabar da ta zamar mata jiki ta ce", HAMMA WAZIRRRRRR"ya Allah ya kuma fada yana dan rintse idanun sa,bata kula da yanayin nasa ba ta cigaba da cewa kar ka kuma ɗaukar ta a mota ko Bama tare ka ji? Bazan kuma ba ya fada kamar wani karamin yaro, murmushi ta yi wanda ya bayyana lobawar kumatunta,hannu yasa a gurin yana cewa i like dis face"oya fada min"ta san abin da yake nufi saboda itama abin yana ranta,cikin shagwabar da ta riga ta saba yin ta a ko ina ta ce" jiya bayan mun gama waya ka kwanta ka kuma samu nutsuwa har kayi bacci wanda saura kiris yasa ka makara sallah" ta karasa fada da compidece"zaro ido ya yi kana ya ce" RAIHAN kin fada daidai hakan yana nufin abin da kika fada jiya haka ne" dariyar jin dadi ta yi ,kafin ya ɗora da cewa Nima naji a raina kin yi bacci me dadi kuma kema har kin makara sai da antyy ta zo ta tashe ki"waro manyan idanun ta tayi masu cike da wasu sirrin da suke matukar tasiri a gare shi,ta ce"HAMMA WAZIRRRRRR ka faɗa daidai fa"juyawa ya yi yana murmushi me sanyi wanda yake sanyayawa RAIHAN jiki da ruhi. Ina zamu je HAMMA WAZIRRRRRR? Gidan gwamnati ya bata amsa yana daukar titin da zai sa da shi da gidan gwamna, HAMMA WAZIRRRRRR me zamu yi a gidan gwamna?mai makon ya bata amsa sai kawai ya jefo mata tasa tambayar,me yasa kika iya fadar sunana kamar ke kadai kika iya fadar shi a duniya?zaro ido ta yi cike da mamaki ta ce"kai Hamma Ahmad da gaske kake?"numfashi ya furzar ba tare da ya ce da ita komai ba,itama shurun ta yi tunda ta fuskanci ya gaji da maganar,shi kuma a ranshi ba wai haka bane kawai dai ya fuskanci idan ya ci gaba da biye mata tana fadar sunayen shi da irin salon da ya tabbatar bata san tana yi ba,hakan zai iya sawa ya kasa nutsuwar yin tuki saboda halin da hakan ke jefa shi wanda ya kasa gane dalili,duk da cewa kuwa yana jin Gajiyar surutun da yake yi ,dan a tsawon rayuwar shi bai taba doguwar magana da mutum ba kamar yadda yake yi da Raihan. Da haka su ka karaso gidan gwamnati,duk da cewa gwamnan ya san da zuwan wazir din,hakan bai hana su fuskantar Matsala ba,amma tun da Hussaini p,a din sa ya karaso shike nan suka samu sa ida daga binciken da ake ta faman yi musu. Yauwa ku zauna nan da mintina goma insha Allah za ku shiga,inji p,a Hussaini,jin jina kai kawai wazir ya yi tare da duban Raihan da ta coge guri daya karamin bakinta a cune saboda haushin abin da aka yi musu wanda kuma ta riga ta san dole sai hakan ta faru,to su anyi musu da sauki ma tun da gwamna da kansa shi ya neme su,cikin yin ƙasa da murya sosai wazir ya ce" zauna mana" zama ta yi tana ci gaba da hararar hadadden falon tamkar shi yayi mata laifin ,cikin kunkuni ta ce" Ni ban san me yasa ka sa mu zuwa nan ba,idan magana zai yi damu ya same mu a inda muke mana"dan zaro idanu wazir ya yi kafin ya ce"Raihan gwamna ne fa"ƙwafa ta yi tare da cewa nifa ina jin banda a poster bam taba ganin mutumin nan ba,duk da cewa aminin Abbie ne kasan lokaci lokaci yana yi min aika shima fa bai taba ganina ba, ta faɗa a hankali idanunta akan katon hotamshi da na shugaban kasa,,bai ce mata komai ba kawai ya maida kanshi ya jinginar tare da lumshe lumsassun idanunsa,ji yake kansa har wani sarawa yake saboda yawan magana da hayaniyar da ya shiga kwanaki biyun nan. Itama RAIHANN shuru ta yi tana saka abubuwa masu yawa cikin karamar kwakwalwar ta me kaifin basira. Cikin mintuna goma kuwa sai ga p,a Hussaini ya fito tare da yi musu iso. Cikin kamilalliyar Muryar sa ya yi sallama Raihan na biye da shi a baya a matsayin RAHIM,cikin fara'a mayalwaciya gwamna ya amsa tare da nuna musu kujeru guda biyu dake gaban sa suna kallon juna,cikin nutsuwa suka zauna,ya yin da Raihan ta kuma kama kanta saboda ba a gaban wazir take ba,wanda shi ka dai ne a waje idan tana tare da shi take mantawa da cewa ita din namiji ce. Cikin girmamawa suka gaisa da gwamnan jihar Adamawa,kafin gwamna ya dan yi gyaran murya, sannan ya fara da cewa, Ahmad wazir hakika nayi matukar farinciki da amsa gayyatata da kayi ,duk da cewa baka san dalili ko kuma makasudin kiran ba,dan haka ina matukar godiya da hakan,sai dai kuma ban sani ba ko za mu iya tattaunawa kai tsaye, ya fada yana duban gefan da Raihan take idanun ta a kasa,shima wazir duban Raihan din ya yi kafin ya dan lumshe idanunsa yana cewa babu damuwa zamu iya tattaunawa in dai akan abinda ya shafi aiki ne ko kuma sirrin da ya kasance nawa ne,amma in dai kana ganin sirrin ka ne wannan bani da ta cewa" ya karasa fada yana mai bude dukan idaniyar shi da zuciyar shi akan Raihan da har yanzu bata ɗago kanta ba,duk da yadda take jin idanun wazir din akan ta,numfashi gwamna ya dan ja,tare da cewa shi ke nan,tun da ka yadda da shi babu damuwa. Kai tsaye ya ɗora da cewa,wazir ba komai ne yasa na kira ka ba,illa magana akan abubuwan da suke faruwa wanda kuma har yanzu mun kasa kawo karshen abun,ba komai ne ya kuma tayar min da hankali ba,illa kisan yar jarida halima,kuma kowa yasan cewa ina da kakkarfar dangantaka da gidan jaridar ku,hakan yasa na kara jin tsoron kar a dinga bin ku daya bayan daya ana kashewa saboda kawai kuna da kyakkyawar mu'amala da Ni,wanda sai a yanzu Nima na fara zargin daga inda wannan taadi yake fitowa,duk da cewa har yau ana kan bincike kuma akan wadan da muke tunanin,to amma Ni abin da na gani shine ina so bincike ya bi ta kan kowa ko Allah zai sa mu da ce,idan nace kowa kuwa to ina nufin har Ni" gaba daya su ka ɗago suka kalle shi duk da cewa ba wai sun iya duban shi ne kai tsaye ba,gane mamakin da suka shiga ne yasa shi jin jina kanshi fuskar shi dauke da wani irin yanayi na matukar jimami,ya ce"wazir hakan shine kadai mafita kuma shine zai fidda Ni daga idanun masu jingina Ni da laifin nan,dan haka daga yau na baku dama kai da staff din ka kuyi bincike me kyau a kaina da duk wanda yake tare da Ni defity ne shugaban jam'iya Alh Yahya duka ban dauke kowa ba,dan Allah Ahmad ka taimaka mana wannan shawarar ba yawa ba ce Ni ka dai shawara ce daga babban Aminina Alh Muhammad nuurr shi yasa na dauke ta da matukar muhimmanci ", Raihan bata yi mamakin ambatar sunan mahaifinta da gwamnan ya yi ba,dan mutane da yawa sun san shaƙuwa da alaƙa me girma dake tsakanin su,mutane basu kara tabbatar da haka ba sai da Abbie din ta ya kuma yin ruwa da tsayi ya tabbatar da hawansa kan kujerar Gwamna,so mutane da yawa sun san cewa gwamna da bazar Alh Muhammad nuurr yake taka rawa. (Alhji Garba shi kadai yasan muhimmancin Alh Muhammad nuurr, Alh Muhammad nuurr ya yadda da Alh garba wanda har ya kai ga bashi amanar dukiyar Raihan yake juyawa,babu wanda yasan wannan sirrin sai lauyan Alh Muhammad nuurr da kuma mahaifinsa da yakasance baya iya zartar da komai ba tare da ya sanar masa ba,kuma duk fadin duniya babu wanda yasan wani abu akan Raihan sai Alh Garba) Nasan zaka ce me yasa,ban sanar da wadan da alhakin binciken yake hannun sa ba,to ba komai ne yasa na yi hakan ba,sai dan cewa suma ba za a rasa munafukai a cikin su ba,koma na ce dukkan su munafukai me ƙaɗan daga cikin su ne masu amana,amma kai wazir na yadda da kai,nasan ba za a taba hada baki da kai a cuci al umma da jihar ka ba,kuma kai ne ka dai za kayi aiki cikin sirri ba tare da kowa ya sani ba, wannan shine amfanin kiran ka da na yi,kuma shine babban taimakon da yan jarida suke wa kasa da al'umma,saboda su din kai tsaye suke taimakawa hukuma wajen zakulo me laifi ba tare da an yi wata ciwa ciwa ko san zuciya ba,duk da cewa ko wane aiki a kwai me gaskiya da kuma makamancin hakan,dan haka ina mai kuma jaddada maka cewa na baka wuka da Nama kayi duk abin da ya kamata,babu wanda yasan za mu yi wannan zaman bare kuma sanin abin da zamu tattauna daga waje sai iya mu hudun nan ,dan ko p,a Hussaini bai san akan me na kira ku ba"ya kare maganar shi da zubawa wazir din Ido, don gane yadda maganar shi ta karbu wajensa,tun da yasan ba lallai ne wazir din ya tsaya ya yi masa bayanin da zai gamsu ba,ilai kuwa ,wazir sauke numfashi ya yi kana cikin nutsuwarsa ya ce"na gode ranka ya dade ,kuma zan yi duk abin da ya kamata insha Allah,fatan nasara ya fada yana miƙewa tsaye,mika masa hannu gwamna ya yi fuskar shi dauke da murmushi su kayi musabaha maida hannun shi kan Raihan ya yi yana cewa na gode ina fata ba za ku bani kunya ba"wani kallo wazirrrrrr ya bi hannun gwamna da shi kafin ya maida kan Raihan da yaga tana kokarin zaro hannun ta saboda rashin ta kamaiman mafitar kaucewa yin hannu da gwamnan,hannun yana gab da isa wazir ya saki wani wahalallan tari wanda shi kansa bai san ta yaya a kai ya fito ba,dan shi dai yasan ba ƙirƙirar sa ya yi ba,haka nan yaji tahowar kwarewar tamkar wanda ya ci wani abu,aiko da sauri Raihan ta janye hannun ta wanda dama kiris take jira,ruwan dake gaban su ta dauka ta mika masa tana faman yi masa sannu,shima gwamna sannu ya yi masa,ruwan ya karba ya kwankwada sosai,da sauri yaja hannun RAIHAN suka nufi kofa ba tare da ya kuma bi ta kan Alh Garba ba. ........ Suna shiga mota yaja wata doguwar ajiyar zuciya,Hamma Ahmad wai me ya faru? Kasa ce mata komai ya yi saboda ita kanta haushin ta yake ji wato da haka bata faru ba mikawa wannan katon hannu za ta yi da sunan sallama,dafe goshin sa ya yi saboda wani abu da ya tuna wato laushiin tafin hannun RAIHAN,ji ya yi jikin shi ya dauki rawa,saboda duk da cewa ba su yi hannun ba haka nan yake jin faduwar gaba da ta shin hankali,sai ya shiga tunanin yanzu haka ma duk mazan da suke tare a bokanan aikin ta ta hanyar masabaha suke gaisawa,Hamma wazir wai me ya faru ne? Ta kuma tambayar shi,banza ya yi mata tare da figar motar kamar zasu tashi sama,shuru ta yi zuciyar ta na wani irin nauyi,bata san meye dalilin bacin ran wazir ba,amma tana da tabbacin cewa ba ita ba ce ba,sai dai idan gwamna ne ta fada tare da kwarin gwiwa,da haka su ka isa gidan su,bai shiga ba bai kuma kalleta ba,murya a cushe fuskar nan babu kame kai ba ka ce sun taba maganar arziki da Raihan ba,ya ce"fita"wani irin tsoron shi ne ya kamata da sauri ta fita daga motar jikin ta har rawa yake,figar motar ya kuma yi kamar zai take mata kafafu, dafe kirjin ta tayi idanun ta na cikowa da hawaye,bata taɓa ganin sa a irin wannan yanayin ba,duk kuwa da cewa kullum fuskarsa a kame take babu wani sassauci amma ai ita yana rangwanta mata kai ita hasali ma ba ta taba sanin ainahin halin sa na miskilanci a kanta ba. Kai tsaye dakinta ta wuce duk da taga alamun dawowar su antyy amarya,tana shiga ta ciro madaukar murya da ta shiga da ita,ba tare da shi kansa wazir ya sani ba,kuma duk binciken da akayi musu ba a gano tana jikin ta ba,wani dan murmushi ta yi me ciwo tana duban madaukar ta ce" ganganci ne shiga irin wannan wajen a haka ga mu yan jarida,kasancewar mu ba ma raina abun magana ko mai kankantarsa,bare kuma Ni da nake Binciken wanda suka kashe halima ido rufe,ko kai Hamma wazir ba zaka taba sanin komai ba har sai nayi na gama idan nayi nasara shi ke nan,idan kuma aka samu sabani na mutu kamar halima to hakika nasan na dace tun da na mutu ne akan hanyar binciko gaskiya,karasawa ta yi ta yi masa kyakkyawan boyo duk kuwa da cewa ba wai tana zargin gwamna da cin dunduniyar su ba ne ga kuma abin da haluma ta kuma faɗa, to amma ya kamata ace binciken su yabi takan kowa kamar yadda gwamnan ya fada da bakin sa. Cikin sanyin jiki wadda damuwar halin da wazir yake ciki ya saka mata ,ta kammala shirin ta na bacci bayan ta gabatar da salla da cin abinci,wanda abincin ma dakyar antyy amarya ta takura mata ta ci kaɗan,antyy amarya bata takura mata da san jin damuwar ta ba ,dan a tunanin ta har yanzu batun mutuwar halima ne bai gama sakin ta ba. Wazir kuwa ,yadda ya bar Raihan a fusace cikin fushin da shi kansa yake jin ya kasa control din kansa,haka ya karasa gida da shi,bai kula su Ammi dake falon innawuro ba,ya wuce saman sa kai tsaye ,cikin yanayin takun shi na karfafan maza wanda yake kuma nuna halin fushi da motsawar halinsa na miskilanci,duk bin shi suka yi da kallo,kafin innawuro ta tabe baki ta ce"Ni wlh duk aikin nan na wazirin gida ya gundure Ni,sam bana son sa"ta karasa maganar tana mai ɓantarar farin goron ta,shukrah ta ce"wlh Nima innawuro fargaba aikin nan yake saka Ni,dan da shi da aikin soja ba su da wata maraba"ke dai bari 'yar nan cewar innawuro,Ammi dai bata ce komai ba,amma fa tabbas maganganun innawuro da auta shukrah sun yi matukar tasiri a gare ta,to amma ya su ka iya da kafiya irin ta Abbu da ɗansa,da anyi magana yanzu za su fara wa azin da ba sa gajiya da yin shi in dai akan aikin su na taimakon al'umma ne. Tun da ya shige bai ƙara lekowa falon ba sai da lokacin Sallah ya yi, sannan ya fito, a hakan ma babu wanda ya kula,to innawuro ma dai bata kula shi ba dan tasan idan wannan halin nashi ta motsa babu wanda baya nunawashi. A bangaren Raihan kuwa,haka ta kwanta da saƙe saƙen dalilin fushin Hamma wazir a kanta,gefe daya kuma tana kara tariyo hirar su da gwamna tana sauraro ko Allah zai sa ta tsinci wani abu da zai bata haske akan kyakkyawar niyar ta. Washe gari,tsaf ta fito cikin shirin ta na fara zuwa aiki tun bayan rasuwar halima ,wanda kusan dukan ma'aikatan sai yau din zasu koma sakamakon jimamin mutuwar ma aikaciyar su,driver ne ya dauke ta sam bata yi tunanin tsayawa jiran Hamma wazir ba,dan tasan abu nee me wuya yau din ya biyo,duk da cewa bata san takamaiman laifin da ta yi masa ba. Shima Wazir din kai tsaye office ya nufa ba tare da ya biya gidan su Raihan ba,kuma har yanzu yana nan tare da bakin ran nasa na tun jiya wanda abin da ya kusan faruwa tsakanin gwamna da Raihan ya haifar masa,har yanzu yana jin ɗacin abin a can kasan makoshin sa,duk lokacin da ya rufe ido hannun RAIHAN yake gani tana mikawa gwamna a domin su gaisa ,ko yanzun da yake tunanin abun a hanyarsa ta kusan isa office ji yake tamkar zai yi aaman zuciyarsa,dafe goshin sa ya yi tare da dan lumshe lumsassun idanunsa wanda suke cike da baccin da bai samu yin sa ba a daren jiyan,shi kansa so yake yasan dalilin zuciyarsa na shiga wannan halin akan abin da ya farun,sai dai kuma hakan ya gagara a gareshi,amma dai yana kokarin jingina hakan da dalilin son kare mutumcin Raihan a matsayinta Na kanwar sa.da wannan tunanin ya isa chibado fm. A daidai lokacin drivern raihan ya ajiye ta,tsayawa ta yi tana duban wazir din da yake rufe motar shi,yayi matukar kyau cikin shigar suet kwantacciyar sumar shi ta Fulani sai ƙyalli take tare da kayataccen sajen shi wanda ke kara mishi matukar kyau da kwarjini,ji tayi idanun ta sun kawo ruwa na rashin sanin cikakken dalilin da ya sa wazir din ya canja mata lokaci daya. Duk da bai waiga in da take ba ,amma jikin shi da zuciyar shi sun bashi tabbaci akan tana kusa da shi haka kuma yaji kaifin kyawawan idanun ta akansa,a hankali ya fara takun shi me cike da nutsuwa,dan kaiwa ga lifter da zata kai shi ga office din shi,duk yadda yaso kauda tunanin jiyan hakan ya gagara hakan yasa ya kara karfin takun shi dan barin wajen. Hannu tasa ta share hawayen da suka cika idanun ta ,tare da takawa cikin sanyin jiki dan wucewa bangaren office din su..........✍🏽 FATEEMAH Y ADAM *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page12 ``` Dukkan su haka suka fara aiki cikin sanyin jiki,sai abokan aikin suka dinga tunanin ko mutuwar Halima ne har yanzu take dukan su. ................... Inna maimuna ce zaune tana waya da Bashir faɗa take masa akan shashashancin da ya tsaya har ya samu matsala a jarrabawarsa yan uwansa duk zasu dawo amma ban dashi,Abba yahya yace", dole sai ya tsaya ya sake maimaita shekarunsa baya bukatar dawowarsa indai ba zaizo da abinda aka tura shi ya yi ba, inna maimuna duk hankalinta ya tashi bata san cewa shi hakan ya fiye masa ba domin zai samu karin lokaci da dama ta sheƙe a yarsa,sallamar Abba yahyan ce ta katse mata nasihun da take masa tare da kawo masa misalai akan kannensa,dan Allah ka maida hankali kaji ta faɗa tana kashe wayar tana maida hankalinta kan abban.duban sa ta yi cikin nutsuwa ta ce", Abban Bashir me kuma ya faru ne naganka haka ko har yanzu ɓacin ran Bashir dinne?zama ya yi yana dan sakin ajiyar zuciya sannan cikin damuwa ya ce",ba wannan ba ne, babu abinda zai sa na ci gaba da damun kaina akan Bashir yake kawai.ya yi rayuwarshi yadda yake so.to menene? ta tambaya duk da cewa bata ji dadin kalaminsa kan tilon ɗannata ba, haba maimuna kema kin san abin da yake damuna ba ya wuce maganar RAHIM tsakani da Allah bana son wannan aikinnasa kina dai kallo kullum da wanda za ace an kashe a cikin 'yanjarida,gashi shi kuma Nura ya ki dawowa bare mu sami mafita akan wannan lamarin gaba ɗaya ",numfashi inna maimuna taja kana cikin gasgata maganar Abba yahya ta ce",ko Ni dan ba yadda zanyi ne kullum maganata daya ce idan muka zauna da lamra, to amma yadda take bani kwarin gwiwa akan aikin yasa na hakura nake binsa da addu'a, Rahim yana son aikin nan dan haka mu yi hakuri mu barshi mucigaba da yi masa addu'a",Abba Yahya ya ce",haka ne amma dai nuran zai dawo dole a samu wani da zai dinga tsaronsa koda jami i ne ta haka ne kawai hankalinmu zai dan kwanta", wannan ma shawara ce me kyau Allah ya tsare mana su baki ɗaya,ta faɗa tana tashi dan samo masa ruwa me dan sanyi. _________ Misalin karfe biyu na rana ,gari ya hargitse da faɗa sakamakon taron siyasa da aka gabatar a cikin unguwar jabbama,abun har ya kai ga kashe rai,tuni 'yan jarida masu nema a kusa suka garzaya inda abun yake,a cikin su har da su Rahim da basu saurari cewar ogansu ba suka garzayo,tun da ita dama tun bayan haɗuwar da su kayi yayin shigowa bata kuma bari sun hadu ba. A can kuma gidan jarida na chibaɗo,sai bayan tafiyar su RAIHAN,wanda ba kowa ne ma ya Ankara da fitar ta su ba,ita da salim da Khalil da rufa'i da Ishaq ,sammani daya daga cikin ma aikatan su ne ya garzaya office din A wazirrrrrr dan kai masa rahoton abin da ke faruwa. Zubawa sammanin ido A wazir ya yi bayan ya gama sauraron jawabinsa,sai da ya dan numfasa kana ya ce"sammani kuje ku dauki rahoto da kai da su salim da khalil amma ina mai shaida muku cewa kamar yadda muka saba,bana son sauyi ina son rubutu da jawabi akan daidai abin da ya faru bana buƙatar ƙari ko ragi, iya ku kaɗai nake bukatar kuje kar ku bari Rahim ya bi ku wannan umarni na ne"in sha Allah oga za mu yi kamar yadda ka ce"sai dai fa ina ga su salim din tuni Rahim ya ja su sun wuce tun kafin na karaso nan"cikin nutsuwarsa ya ɗago ya kafe sammani da idanun sa masu tsoratar da mara gaskiya,sam ba za ka gane bacin ransa ko damuwarsa ba,amma shi ka dai yasan ɗacin da ya ji a makoshinsa da wannan batu na sammani,jin jina kai kawai ya yi tare da yi masa nuni da kofa. Sammani yana fita ya furzar da wani iska mai tsananin hucin zafi ,tare da maida kansa ya kwantar yana hango Raihan cikin dandazon maza ana kokawa da ita wajen son jin abin da ya faru wanda ba ayi a gaban su ba wanda kuma ya zama dole su sani dan fidda rahotansu yadda ya kamata.miƙewa ya yi tare da ɗaukar key din mota, fuskar nan ta shi kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwar uwar shi,takunshi ma ka dai ka kalla kasan yan maza sun motsa,duk inda ya gifta sai takunshi ya bada wani irin sauti na alamun takun mazantaka, buɗe motar ya yi ya shiga mazaunin driver kana ya tada ita ,ya kuma figeta a tsiyace,wanda hakan yasa sai da jama'ar dake harabar wajen suka bishi da kallo. Kamar yadda wazir ya lissafa to haka lissafin yake,dan kuwa RAIHAN na tsakiyar maza a na wawason daukar rahoto daga bakunan da suka ji suka gani,ga kuma gawarwakin wadan da aka kashe nan daga can gefe yan sanda na ta faman bincike da tutture mutanen da suke son ganewa idanun su ba wai a basu labari daga nesa ko gidan rediyo ba.RAIHAN dai sun sami cikakkun bayanai kamar yadda suke so,dan kuwa kamar ko yaushe labarin da suka samu babu wani gidan jarida da suka sami irinshi,saboda tsananin kwazon su da jajircewa akan aikin su,da kuma son tabbatar da gaskiya,akan idanun wazir wani dan sanda ya tura RAIHAN kan mazan da suke kokawar son ganin ƙwaf, saboda son aba su filin wajen,da kyar Raihan ta samu ta fito daga wajen da taimakon su salim da suma kusan rabin jikinta da hannun ta yana hannunsu saboda karancin karfin da take da shi ,ga kuma raunin ya mace a tare da ita,sai da suka fito fili sannan ta kwace hannun ta tare da daidaita abin maganarta ta fuskanci rufa i da ke haskata,cikin Muryar ta da mutane suke yawan cewa Muryar ɗan jarida Rahim irin ta mata ce,ta ce"to masu sauraren mu kamar yadda kuke gani kuma kuke sauraron mu,muna a tsakiyar wajen da yan bangar siyasa su kayi vannan babbar ɓarnar ta kashe rai,gashi nan yan uwan mamata suna kuka da fatan hukuma zata bi musu kadun hakkin ran yan uwan su,kai ba ma su ka ɗai ba har da sauran al umma saboda suna jin matukar ciwo akan abun da yake faruwa da al'umma,musamman kashe kashen da ake mana ba tare da mun ji mun gani ba,to masu sauraro ku ci gaba da bin mu cikin jaridar mu ta gobe me taken hakkin matattu yana kan yan siyasa" tana zuwa nan a labaran ta suka yi ido hudu da A.wazir wanda ya kafe ta da nasa idon da suke cike da bacin ran da ita kadai take iya gani da fuskanta,kafin ta yi wani motsi tuni ya tako cikin nutsuwa da kamalar sa da ta cike gurbin ɓacin ransa da ba kowa yake gani ba, hannunta ya kama ba tare da ya ce"ko mai ba,suka bar gurin, buɗe motar ya yi tun kafin ya ce"mata komai ta yi hanzarin shigewa motar kirjin ta na wani irin bugu saboda yadda ta ga tsantsar bacin rai da wutar bala'i a idon A. wazirrrrrr. Duban su salim ya yi ya ce"ku wuce a motar da kuka zo a kwai inda zamu"ok sir suka fada a tare a lokaci daya suna tafiya dan isa gurin motar su. .........…..……… Cikin tashin hankali inna maimuna ta nufi bangaren aunty amarya,sai ta tarar da aunty amarya ma kallon tashin hankalin da ake haskawa take,zama ta yi gefanta tana cewa yanzu lamra haka zamu zauna muna ji muna gani ana kashe 'ya'yanmu da 'yanuwanmu?nifa wannan lamarin ya fara fin karfin tunanina gaskiya",numfasawa aunty amarya ta yi tare da maida kallonta kan inna maimuna Macen da take da matukar kima a wajen ta,tasan cewa duk wannan rudewar da ta yi bai wuce akan Raihan,yasan cewa ita kadai ce a ranta ta saya ne kawai saboda yawan kwantar mata da hankali da take yi,sanin hakan yasa ta fuskanceta cikin nutsuwa da son kwantar mata hankali,ta ce",inna maimuna duk wannan abun da kike gani yana faruwa zai wuce ya zamo labari,babu abinda zai faru da Rahim ina ji ajikina Rahim zai iya zamowa silar daidaituwar al'amuran da suke faruwa,shi dan jariidane me kwazo gashi yana tare da A wazir,nasan cewa zasu tsaya tsayin daka dan ganin sun zakulo yantaaddan da suke wannan aika_aikar,duk da cewa su ba jami'an tsaro bane,amma mutanene da suke da muhimmanci wajen al'umma domin suna ƙoƙarin zakulo masu laifi wadanda ba asan da su ba, waɗanda suke boye suke aikata manyan zunubai,dan haka ki kwantar da hankalinki innar Bashir ". Ajiyar zuciya Inna maimuna ta saki alamun gamsuwa da maganganun aunty amarya,daga nan suka ci gaba da tattaunawa akanatsalar dake faruwa. ______________ Tunda suka fara tafiya bai kalli inda take ba,ya yin da Raihan gaba daya ta tsargi kanta akan wane irin laifi ne mai girma ta yiwa Hamma wazir da ya sa shi wannan bacin ran haka,da wannan tunanin taji ya yi fakin,ɗaga manyan idanunta da suka sauya ta yi saboda ganin inda ya kawo su,sai ta ga ashe gida ya dawo da ita,kafin ta yi magana ya rigata ta hanyar mika mata tattausan hannushi cikin cunkushewar murya ya ce"bani madaukar bayanan"miƙa masa ta yi jikin ta yana matukar yin sanyi,yana karba ya kuma cewa kije gida ki huta bana bukatar ganin ki wajen aiki har sai na bukaci hakan"waro manyan idanunta tayi gami da dafe kirjinta,cikin rawar murya ta ce"Hamma wazir me nayi maka zaka yi min wannan baƙin hukuncin?dan Allah kayi haƙuri Ni dai ko me ye bazan sake ba wlh"ta faɗa tana mai rushewa da kukan da yasa wazir rintse idanun sa saboda yadda ya bugi zuciyarsa,dan Allah kayi hakuri Hamma Ahmad wlh bazan sake ba duk da ban san laifin da nayi maka ba,gobe da akwai aiki me muhimmanci da zanyi kuma kasani cewa dole wannan hirar da za ayi da Dr sanate dole Ni ya kamata nayi ,dan Allah kar ka mun haka hamma wazir"ta faɗa tana mai ci gaba da raira kukan da yake jin sa tamkar wuta saboda yadda ya ke sukan zuciyarsa,is ok,ya fada can kasan makoshin sa, ɗago kanta ta yi tare da dan tura bakin ta ta ce"Hamma Ahmad me nayi maka? Shuru ya yi saboda shi kansa bai san ta kamaiman abin da zai ce ta yi masa ba. Dan haka sai kawai ya share tambayar da ɗan furzar da hucin bakinsa,tare da cewa shi ke nan jeki gida na yau dai ya wuce sai Allah ya kaimu goben ,sai kizo ki gabatar da hirar da kuma sauran rahotannin yau ɗin" ya fada yanayin fuskar shi na sauyawa da wani dan kara tsukewa saboda tuna abin da ya faru yau ɗin, Raihan dai ganin babu fuska yasa ta kaɗa mishi kai kawai tare da fita daga motar ,kai tsaye ta shige gida ba tare da ko waiwaye ba. Kaɗan ya bi ta da lumsassun idanunsa,bai tashi motar ba sai da yaga me gadi ya bude mata ta shige gidan ,sannan ya saki ajiyar zuciya tare da tada motar ya fice daga layin. Ko da Raihan ta shiga gida nan ta tarar da saukar su yaya Affan da yaya rufa'i sai kuma baba karami na wajen momy hanne,gidan duk ya cika.da murnar dawowar su ,wanda su sam basu san cewa yau din zasu dawo ba,duk da cewa sun san dawowar ta su a cikin satin,a nan dai Rahim ya shiga murnar dawowar yan uwan nashi,duban Hamma Affan ya yi ya ce" Hamma Affan su kuma su Hamma Hassan da Hamma jami'lu da Hamma Bashir da Hamma idi,yaushe zasu dawo? Affan da murmushi a fuskar sa ya dubi dan uwan nashi wanda yaga duk ya sauya masa ya girma sannan yayi kyau kamar ka taba shi jini ya fito,ya ce" Auta wani satin zasu dawo,shi kuma Idris gobe insha Allah yana hanya wani dan uzurine ya dakatar da shi shine ya tsaya su taho tare da Abbie" Allah ya kawo su lafiya cewar RAHIM (Raihan)Hamma rufa i ya ce" wai me aunty amarya take baka ne Rahim dan naga kafimu yin ja kamar kaine kaje kasar Wajen,dariya momy hanne ta yi kasancewar dukan su suna sashen Hajiya goggo, babu yadda za ayi su nuna bakin halin nasu harsu Affan din ma duk gimtsewa suke saboda Hajiya goggo,ta ce" dole kaga yafi ku samun jikin hutu tun da yafi ku komai da komai,kullum auntyynshi boye shi take kamar kayan tsafi ,innarshi maimuna ita kadai ke ganin shi duk sanda taso ba dole yayi ja kamar jan kosai ba"mama murja ta amshe da wata muguwar dariya har da tafa hannaye a hayye , dan ma bakuga da yadda ta bari yayi karatu har yake aiki ba,saboda kar a taba shi tun da kayan kudi ne shi ɗin,Hajiya goggo ce ta dakatar da su ta hanyar watsa musu harara ,ta ce "babu wadda ta isa ta zo gaba na tana aibata min jika,ku babu wanda ya aibata muku yara dan haka kar ku sake wannan banzayen surutan ehe"Raihan kuwa ta cika ta Batse kiris take jira ta fashe ,dan fa ita a rayuwar ta duk abin da zaka yi mata bata damuwa amma kar ka taba mata auntyn ta da innar ta,wannan a jinin duk wani dan halak yake me son gamawa da duniya lafiya,zata yi hakuri akan komai amma banda ciwa,auntynta mutumci,shi yasa sam basa ga maciji ita da kishiyoyin auntyn ,dan sun yi mata shedar mara kunya,akan tana tarewa auntynta cin mutumcin da suke mata,ko shashensu bata zuwa dama can bare kuma yanzu da ta san ciwon kanta,ko ada auntyn bata hana ta saboda wan can dalilin,to ita dama ta hana kanta saboda gujewa zagin da suke wa auntyn Tata. Taka musu burkin da Hajiya goggo ta yi shi ya hana Raihan tanka musu kamar yarda ta saba,a duk sanda a kayi irin haka,kuma dawowar ya'yan su ba zai sa idan sun ciwa mahaifiyar ta mutunci ta kasa ramawa ba,ta shi ta yi fuu cikin fushi ta bar falon tana kunkuni,momy hanne ta ce" kin ga Ni dai hajiya yadda yaron nan ya yi kamar zai buge Ni ga kuma zagin mu da bai fasa yi ba kamar yadda ya.saba,cikin mamaki Affan ya ce" zagi kuma? Ey mana kana mamaki ne cewar mama murja da take ji kamar ta janyo Rahim ta murɗe masa wuya ko sa huta da bakin cikin sa,ƙwafa rufa i ya yi yana cewa Allah ya bashi sa a akan zagin naku ya ga asalin yadda ake kwallo dan wlh sai na karya shi gida biyu na watsar". Salati Hajiya goggo ta sa tana mai tafa hannayen ta,ikon Allah yanzu ku dan Allah baku ji kunya ba,ga fa yadda kuke shirin batawa yara zumunci daga dawowar su,har kin fara saka musu mummunan akida na yan ubanci,( tab Hajiya goggo ai sai dai kar a kuma wannan abun ya dade da zama a zukatan su tun suna yara).ganin fadan Hajiya goggo yaki karewa yasa suka dinga barin sashen nata da ɗaddaya. Ko da Raihan ta isa sashensu haka ta dinga ƙunci har ta gama abin da take yi,ta dawo wajen aunty amarya da tun shigowarta taƙi tanka mata bare tambayar ta abin da ya faru,dan ta san dai tatsuniyar gizo bai wuce koki tun da taga fitowar ta daga ɓangaren kakar ta su,kuma tasan duk suna can,tun da itama basu jima da dawowa ba ita da inna maimuna,basu isa shigowa su gaidasuba sai sune sukaje musu sannu da zuwa,dan tabbas idan zasu shekara da dawowa baza su taba zuwa sashenta ita da inna maimuna ba,iyayen su sun koya musu raini dan ma Abba yahya yana ƙoƙarin taka musu birki da batun sai yafi haka. Zama ta yi gefan auntyn tana tura baki dan har yanzu fushin bai sake ta ba,saboda bata samu ta maida musu maganar ba, murmushi auntyn ta yi tana mai janyo ta jikin ta,da cewa haba autar aunty da Abbie 'yar lelen inna maimuna da Abba yahya ga kuma Hajiya goggo, duk wannan fushin fa,ke yanzu ai bake ba fushi gobe ne fa Abbie ɗinki zai dawo" ai kuwa da sauri ta washe baki kyawawan haƙoranta farare tas suka baiyana,ta ce" haka ne fa aunty natuna dan haka na yafe"yauwa autar aunty. Fatima y Adam ..............✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page13 ``` Da misalin karfe tara na dare bayan sun kammala cin abinci,dukan su suka had'e a sashen mama murja dan son tattauna babbar matsalar su,wanda suke ganin cewa yanzu ne lokacin fara babban yak'in ,saboda yaran su gaba daya sun girma sun mallaki hankalin kan su,kuma basu da matsala ta wajen fahimtar da su ,tun da sun jima da yin wannan yakin,kuma sun yi nasara,dukkan su a yanzu sun dawo ne da shirin ko ta kwana. Mama murja ce ta ɗan yi gyaran murya bayan dubawar da su kayi suka tabbatar da cewa babu me yi musu labe,ta ce"to alhamdulillah mun gode Allah da ya kawo mu wannan rana damuka daɗe muna jiran ta,duk da cewa ba ku haɗu dukan ku ba,to amma jinkirin tattaunawar zai iya kawo mana matsala a cikin yakin da muke son farawa da zafizafi,da farko dai kun san da cewa dukan ku munyi muku matan aure wadan da mukasan cewa ba za su cutar da ku ba,kuma ba za su saka mana ido akan yakin kwatar dukiyar mu wadda aka rike da sunan gaibu ba,kuma kun amince da hakan,saboda a yanzu dukan ku kun kai minzalin ajiye mata, ba ku ba har ma kannen ku,dan haka mun gama da wannan babin dama jiran dawowarku ake yi a kai kudin aure da sa rana,kamar yadda mahaifin ku da wancan dan ƙadafin(Abba yahya) suka tsara. Sai kuma abu na gaba shine shirin yadda zamu karbi dukiyar mu da aka dankarawa gaibu kai harma da wannan shegen Rahim ɗin me fuska kamar ta Aljani,dan haka kuje kuyi tunani akan yadda zamu mullowa lamarin dan wannan yaki ne wanda yake bukatar nazari,ta karasa fada tana sakin wani Marayan murmushi me cike da ma anoni,momy hanne ce ta dauka da cewa kuje kuyi tunani kafin dawowar yan uwan ku yadda idan sun dawo zamu ɗora da tasu shawarar" jin jina kai su kai fuskar su cike da shedar tabon tsanar dan uwan nasu Rahim da kuma babban matsalar ta su da suke kira da gaibu. Washe gari Raihan kin zuwa office ta yi saboda dawowar Abbie dinta,kasancewar wannan dawowar idan ya dawo ya dawo ke nan kamar yadda ya fada,duk wani dukiyar shi ya tattara guri daya,a cewar shi shima so yake ya samu nutsuwa da iyalan shi,kuma tun da yaran shi sun gama karatun su bashi da matsala ,duk zasu dawo ne su ci gaba daga in da ya tsaya ,duk da cewa shima din ba wai zama zai yi ba,kawai dai zai dawo da harkokin shi cikin ƙasar shi ne dan samun nutsuwa daga yawan zirga zirga. Tun da suka tashi suka fara shirye shiryen tarban sa,ita da auntyn nata ,harma da jiddo da ta shigo dan taya su,suna yi jiddo na wa Rahim dariya wai sun samu kuku,harararta Raihan kawai ke yi,cikin tsokana jiddo ta kuma cewa wlh aunty amarya ko acikin mata wadan da suka kware da girki ba za a samu wadda zata nunawa Rahim iya girki ba,gaskiya matar ka ta huta" aunty amarya murmushi ta yi ta ce" kin gan ki ko jiddo ai dai Rahim din yana jinki babu ruwa na idan ya kama ki" ɗan duban shi jiddo ta yi tana kunshe dariyar dake son kufce mata. Shigowar inna maimuna ce ta katse musu hirar su,inda ta jonasu suka cigaba da aikin tare. Tun da A Wazir ya zo office yaga Raihan bata zo ba duk sai yaji hankalin shi na neman ta shi,sai dai kuma miskilanci da kokarin ƁOYE abin da yake ji din ya hana shi ko da tambayar ta a wajen abokan aikin ta,bare kuma ya kai ga yi mata waya,haka nan yake jin wannan damuwar akan Raihan wanda ya rasa ta me cece bare kuma ainahin dalilin jin hakan,haka ya dinga gabatar da aiyukan shi cikin jarumta da son ya kice tunanin ta a ranshi,gizagon shi da tsananin kamewarshi ya da ɗa tasiri wajen boye yanayinshi, hirar da zata gabatar a ranar ma sai Allah yasa itama hajiyar tafiya ta taso mata wanda ya sa dole ta bada uzurin a bar hirar sai ta dawo,su kuwa a bokan aikin ta duk sun san dalilin rashin zuwan Rahim ɗin,ba su dai kawo cewar oga bai sani ba,to ko bai sani ba ma waye yake da zarran yi masa shishshigi wajen sanar da shi ba tare da ya tambaya ba,hakan ya sa babu wanda ya yi masa koda alamun maganar Rahim. Da misalin ƙarfe hudu,gwamna tare da Abba yahya suka wuce dan dauko amininshi da yake matukar ji da shi yawa tsoka daya amiya,cikin madaukakin farinciki suka rungume juna, Alh Garba gwamna ya rike hannun amininnasa bakinsa yawa gonar auduga ya ce", alhamdulillah naji dadin dawowarka kusa damu",shima Abba yahya cike da kaunar ɗan uwannasa ya rungumeshi yana nuna tsananin farin cikin dawowarsa gida,daga nan suka ɗunguma su da tarin motocin gwamna da suka yo musu rakiya suka raka shi har gida. ......... Lokacin da Raihan ta yi ido hudu da sanyin idaniyar ta Abbien ta me son ta tun kafin a san za a haifota,sai kawai ta rungume shi tare da saka kukan farincikin dawowar sa kusa da ita,cike da farinciki ya shafa kanta yana cewa to me haka da kuka kuma Rahim, bayan gani na dawo har ma da yan uwan ka da suka yi nesa da kai,ya. Fada yana janyo hannun jiddo kusa da shi,maza jeka tari dan uwan ka ga shi nan yana kallon ka kana kukan tabbara"da sauri Raihan ta juya inda Hamma Idris yake tsaye hannuwan shi soke jikin aljihun rigar shi babu abin da ke dauke a fuskanr shi sai murmushi wanda kana gani kasan na farincikin dawowar sa cikin ahlin sa ne,da gudu Raihan ta karasa gefan sa ta rike hannun shi tare da dan rungeme shi cikin farin ciki da shagwabar da ta saba yi masa tun kafin ya bar ƙasar ta ce"Hamma ido na na yi kewar ka sosai(kasance War a baya haka take fada masa Hamma ido maimakon Hamma idi saboda bata iya fada ba, a kwai shakuwa me girma tsakanin Idris da Rahim dan ko can baya shi kadai ya fita Zakka a cikin yan uwan sa,saboda shi kadai ne baya daukar hudu bar iyayen su akan aunty amarya da Rahim kai harma da gaibun Raihan,shi yasa ta su ta fi zuwa daya)ware idanun shi ya yi tare da dan bude baki irin na mamakin nan,ya ce"kai auta haka ka zama ƙato idan mun zauna sai kafada min abin da Hajiya goggo da aunty amarya da inna maimuna suke baka"juyawa yayi inda jiddo take kusa da Abbie suna kallon su cike da sha'awa,ya ce",jiddo babu magana bare sannu da zuwa? Abbie ya yi saurin tare mata da cewa ina ka bata dama kana can ka hadu da dan uwanka, murmusawa ya yi yana shafa sumar sa kana ya ce"sorry jiddo kin san dai halin abokin fadan ki idan ban gama da shi ba yanzu sai ya sa mana rigima anan gurin"babu komai Hamma ai nasan halin tabarar Rahim,gaisawa su kayi tayi masa Barka da zuwa,daga nan suka shige bangaren Baffa Ali dama tun da gwamna ya sauke su ,suka juya acewarsa ya samu ya gana da iyalansa kafin su zauna shima su gana, Sosai Baffa ya yi farin cikin dawowar dannasa tare da jikokinsa,yanzu saura Yamma Bashirne kawai baya tare da su, goggo kuwa kamar ta zuba ruwa akasa ta sha gida ya kammala yanzu za su fara kirankan su da cikakkun family. Tabbas inna maimuna da Abba yahya sunso ace Bashirma ya dawo gida,to amma ba yadda za su yi da shi kasancewar ya dage sai ya zauna a can Dubai ɗin matar da zai aura ma yar Cance,dole suka hakura ba dan sunso ba. Da ciwon kai ya dawo gida,gashi yana zuwa ya tarar da taron iyayen sa da innawuro ta haɗa duk akan sa,tun da ya gaida Abbu da Abban rabi a,ya wuce saman shi ko kallon inda innawuro take baiyi ba,idan ka kimtsa ka fito muna jiran ka cewar Abbu kenan,ok kawai wazir din ya fada tare da shigewa falon shi. Harara innawuro ta bishi da ita tare da mele baki ta bantari goron ta tana cewa, duk wani nunƙufurcinka kayi ka gama muna nan muna jiran ka aure ne dai sai kayi shi ehe,Abban rabi ya ce"innawuro a yi dai mana hakuri abi abun a sannu dan Allah, hmmm kawai ta ce"ta na ci gaba da hararar inda wazir ya bi kamar shi take gani a wajen. A bangaren su RAIHAN kuwa,kowa ya kammala shirin sa,kaf din su suna bangaren kakan su baffa Ali,idan ka cire Hassan da jami'lu da Bashir wanda sai wani satin zasu dawo gida banda Bashir da shi sai an ganshi kawai. Bayan bude taro da addu a ,baffa Ali yayi gyaran murya kafin ya ɗora da cewa,to alhamdulillah na gode Allah da ya kawo Ni har zuwa wannan lokacin dana hada zuri a masu albarka,ina fatan Allah ya yi muku albarka ya ci gaba da dafa muku,abu na farko da zamu tattauna shine maganar auren su Affan wanda idan Allah ya kaimu sati me zuwa za aje a gama komai tun da Allah yasa duk yaran na gida ne ,iyayen ku ne mata suka zaba muku su daga cikin dangin su,kuma yadda da tarbiyyar su ne yasa har suka yi muku sha'awar su ,dan haka binciken da za muyi ba zai bamu wahala ba,Ni dai iya abin da nake da shi a bakina ke nan"duban Hajiya goggo ya yi ya ce"idan kina da abin fada Bismillah"sosai Hajiya goggo ta hade fuskarta alamun dai abin da zata fada mai muhimmanci ne, cikin nuna bacin ranta akan abin da ya fara faruwa akan idanun ta ta ce"Ni ba wani dogon zance zanyi ba kawai dai maganar da zanyi tana da matukar muhimmanci,gyara zaman ta ta kuma yi tana mai sa idanun ta a cikin na Affan, ta ce"wallahi tun wuri ku kawar da abin da kuke kokarin sawa kanku wato yan ubanci da iyayen ku suke son koya muku,idan kuma ba haka ba tsaf zan sa mutum ya bar cikin ahlina dan bana son fitina ,hadin kai da zumunci nake bukata a cikin zuri'a ta,kashedi ne haɗe da umarni duk wanda ya ga kuma zai gwada bata mana zumunci to Bismillah ban hana shi ba"daga haka ta yi gum da bakin ta tana mai ci gaba da taunar goranta. Ajiyar numfashi Baffa Ali yayi sai kuma ya fara musu nasiha mai ratsa jiki akan zumunci,daga karshe shima ya kuma yi musu gargadi da akan duk wanda ya samu da tsiro da fitina acikin su tabbas shima zai dauki babban mataki a akan sa,dan haka su kiyaye, Abba yahya ma nasiha ya yi musu akan muhimmancin hadin kai,harma misali ya yi musu da kansu da suka hada kansu tamkar wasu yan biyu,hakuri suka basu tare da cewa insha Allah zasu kiyaye,su dai su mama murja ba su ce komai ba kuma basu nuna komai ba,sai dai kuma Allah kaɗai yasan irin ƙunar da zuciyar su ke yi, Baffa Ali ya bawa Abbie damar gabatarwa da iyalin shi abin da yake son sanar da su,cikin biyayya ya amsa umarnin baffa Ali,shima addu a yayi ,kafin cikin nutsuwa ya fara da cewa, da farko dai ina so nasanar da ku cewa,na dawo gida bani ba kara fita waje sai dai ziyara in sha Allah,abu na biyu kuma shine dukkan ku kowa yasan cewa acikin tarin arzikin da Allah ya bani akwai wanda ba nawa ba,wato na dukiyar RAIHAN,,,,,gaba dayan su suka zabura cikin dinbin mamaki,har hada baki suke mama murja da momy hanne wajen cewa ,wai har yanzu kana nan akan bakan ka na bawa gaibu dukiyar ya'yan ka to ko dai da akwai RAIHAN dinne mu bamu sani ba?wani mummunan duka kirjin aunty amarya yayi ,take itama ta zubawa Abbien idanu kamar yadda kowa na wajen yayi don son jin amsar da zai bayar. CHIBADO' s hause........... Fuskar nan tam haka ya zauna kai kace bai taba murmushi ba duk da cewa murmushin ma ba ga kowa ba ne,gyaran murya Abban rabi ya yi tare da cewa,to wazirin gida kaji dai karar ka da innawuro ta kawo akan kaki yadda kayi aure,yanzu kuma an kawo lokacin da ba za ta daga maka kafa ba,dan haka ka gaya mana wadda ka fitar a matsayin mata sai aje a nema maka auren ta mu huta da korafin innawuro "ya sauke maganar da murmushi akan fuskarsa,hararar sa innawuro ta yi kafin ta ce"ai dama bakin ku daya wai kai me d'a ko?to wlh anan zai fada mana wadda yake so idan ba haka ba kuwa sati me zuwa za ayi masa baiko da rabi"wani kallo wazirrrrrr ya ɗago rikitattun idanun sa da suke cike fal da gajiya da kuma damuwar da take son kara masa,ya wurga mata,ey ko wane irin kallon ka Ni ba zai firgita Ni ba,idan ma kayi ne saboda na ji tsoranka"shi dai Abbu har yanzu bai ce komai ba,Abban rabi ne ya kuma tambayar sa a karo na biyu, girgiza kai kawai wazir ya yi,Abbu da sai a lokacin ya yi magana ya ce"kayi mana magana yadda zamu gane dan bana gane wannan Yaren bebayen naka,a hankali cikin cunkushewar murya ya ce"Abbu Ni bani da wata duk yadda kuka yi shike nan,daga haka ya mike ya bar falon,ko kallon inda yake innawuro bata yi ba,sai Abban rabi da ta kalla ta ce" shike nan sati me zuwa za a kawo kudin na gani ina so,zai yi magana ta katse shi tana mai kara tsuke kyakkyawar fuskarta irin ta wazir din ta.dole yaja baki ya tsuke dan fa innawuro nan ba sauki ce, addu'ar alkhairi kawai su kayi daga nan suka ci gaba da tattauna yadda ko mai zai kasance. ________________ Gaba dayan su su uku ne a dakin sai dai kuma yau an samu karuwar wasu mutanen biyu,wanda ga dukkan alamu yaran su ne,daya daga cikin yaran ya ce" yallabai an gama komai kuma munyi nasarar gano lambar da aka turawa sako lokaci da rana duk gashi a rubuce,saurayin ya fada yana mikawa shugaban jam'iya takardun da bayanan ke ciki,wani irin washe baki yayi kai kace ba iya lamba aka samo ba har da mutumin,Dr ya ce" dakyau kyautar ka ta musamman ce,jagwal na gode me gida jagwal ya fada yana mai sakin murmushin jin dadin yabon sa da me gidan sa ya yi, Alh sale ya ce"to yanzu kuma me ye abu na gaba da ya kamata muyi? Jagwal ya yi saurin cewa idan kuna so a gano muku me lambar a daren nan zanyi trakin na samo muku shi"Dr ya ce"me yasa ba kayi hakan ba? Da sauri jagwal ya ce"sorry me gida bana son yin shishshigi akan aikin ka nafison ka bani umarni sai na aikata hakan sai ya fi daɗi"shike nan jagwal je kayi duk abin da ya kamata akan lambar nan Ni dai ina son cikakken bayani akan ko waye,to yallabai kar ka damu ka bani awa ashirin da hudu zan dawo maka da sakamako",Dr ne ya mika masa bondil din yan dubu dubu yana cewa jeka idan ka dawo da sakamako zaka ji alert"da rawar jiki jagwal ya karba yana faman zuba godiya tare da alkawarin cika aiki a kan lokaci,yana fita Dr ya kalli dayan saurayin ya ce"kai kuma shiga wancan dakin muna zuwa"ta shi yayi jikin sa a sanyaye kamar dai abin da ake shirin aikata masa dole a kayi masa,(to Ubangiji Allah ya shirya bayin sa masu shiryuwa). _______________ .....Muhammad nurr hause.. Murmushi Abbie ya yi ganin yadda duk suka maida hankalin su kansa,kuma dukan su zaka iya hango tsananin tashin hankalin da zuciyoyin su suka shiga,tsaida idanun shi ya yi akan aunty amarya kafin ya maida idanun sa kan autan sa Rahim (Raihan)tsira mishi ido ya yi yana jin wata irin soyayya da kauna kai kace shi ka dai ne dan da ya mallaka a duniya. Avangaren aunty amarya kuwa,da za a tsaga jikinta tabbas ba za a ga jini ko kadan ba,tsananin razanar da ta yi da kallon da Abbie yayi mata da wanda yake kan yiwa RAIHAN dinta,shi ya nemi sawa ta fallasa kanta tun kafin sanin ma anar kallon,bude baki yayi a nutse har yanzu idanunshi na akan Rahim ya ce"ina da R.........✍🏽 Fatima y Adam ✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page14 ``` ........tarin da ya sarke aunty amarya shi ya dakatar da shi daga abin da yake shirin fada,da sauri Raihan ta bude bottle din ruwa ta kafa mata a baki,sai da ta shanye ruwan tass, Raihan ta shiga goge mata zufar da ta shiga tsiyayo mata ta ko ina a cikin jikinta,sannu a ka shiga yi mata,idanun ta sun kada sunyi jajur,ji take kamar zata yi aman zuciyarta saboda tsananin tashin hankali,sai da Abbie ya ja wasu yan mintina kafin ya ci gaba da cewa,na bawa Affan asibitin bayan gari dama saboda shi na gina sa,tun da abin da ya karanta ke nan,ga takardun nan zan bashi a gaban shaidu kafin na kira lauyana,shi kuma Idris kamfanin takalma na gwarumfa,sai kuma kai rufa i tun da lauya ka karanta na baka gidan man City road,Amma zaka a jiye aikin ka ka kula min da babban kamfanin Raihan na shinkafa,shi kuma babana da shi da jami'lu da Hassan zasu rike kamfanin audiga wanda yake son na Kano sai yayi magana yaje can ya zauna da matar shi,tahowar biyun na nan sai ko wanne ya zaba wanda yake so. Baffa Ali ya ce"a'a kar kayi haka ka raba musu ko wanne ka bashi nasa kamar yadda kayiwa ragowar,saboda kar hakan ya zama rigima a tsakanin su"Hajiya goggo ta ce"wannan haka yake malam"jin jina kai Abbie yayi kana yace "to wannan sai mu bari sai sun dawo tun da basa nan,idan kuma dame wata magana yanzu ina sauraron ku, Affan ne ya jagorance su wajen mika godiyar su ga Abbien daga nan suma duk su kayi godiya,sai mama murja da ta ce"muma muna taya su godiya amma fa ba ka bamu amsar mu ta dazu ba, sannan kuma shi Rahim babu shi a yin kyautar cikin tawagar? sannan ina tunanin ba iya wannan ne dukiyar Raihan ba akwai wasu gidajen man a Kano da akwai gidajen haya sannan da akwai babban kamfanin auduga,duk su a hannun wa ka bari?ina ga ya'yan ka ne kawai ya kamata su kuka da wannan dukiyar tunda dai Yanzu kasan yadda amana ta yi ƙaranci?ba tare da Abbie ya nuna mata komai ba ya bata amsar ta ta biyu da cewa,har yanzu rahim yaro ne duk ranar da zan bashi tashi zan tara ku kamar haka"daga haka ya mike tare da yiwa baffan shi sallama,ya fita daga falon,hanne kuwa wata irin ƙwafa ta yi me cike da tsananin jin haushi da wani abu a cikin rai,wato ba zai sanar da su inda ragowar dukiyar take ba wanda ko rabin ta basa jin ya fada. Aunty dai ta dan samu nutsuwa duk da cewa ,tambayoyi ne cike a ranta da tsananin rudani,anya kuwa Abbie bai gano ɓoyayyiyar RAIHAN ba?idan ya sani ta ya a akai ya sani? Tabbas yau abbin ya saka ta cikin rudani wanda zai yi wuyar fita,jiki a sanyaye ta bar bangaren baffan,ita kuwa RAIHAN zaman ta tayi sai zuwa anjima,kowa ya tafi sai ita da Hamma idi da Baffa Yahaya a ka bari suna ci gaba da taya baffa hira,a nan baffa yake kuma yi masa nasiha akan rike amana,ya ce"kasan dalilin da yasa aka baka amanar wannan babbar dukiya me tarin yawa,mahaifin ka ya yarda da kai da nutsuwar ka shi ya sa baka wannan amanar dan haka sai ka rike karka bashi kunya"Hamma idi ya ce"in sha Allah baffa ba zan baku kunya ba"yauwa dan albarka,a daidai nan wayar sa ta yi kara alamun kira,dagawa ya yi bayan yayi sallama,ok mama gani nan zuwa"abin da ya fada ke nan ya mike yana maida wayar aljihun shi,to baffa zan wuce mama na kira na sai mun hadu da asuba in sha Allah"kai kuma Rahim a nan zaka kwana na ne?miƙewa ya yi yana cewa a'a tare zamu tafi Ni kam Hamma ido ka taba gani na kwana a gurin da ba dakina na gidan aunty amarya ba? Ey ban sani ba dai ko bayan tafiya ta ka fara "cewar Idris yana kokarin fita daga falon, Abba yahya ya ce"wannan matsoracin ai ko a bangaren kakar ku bai taba kwana ba"dariya su kayi suna kara yi musu sallama. Sai da Hamma idi ya raka ta har cikin falon su kana ya juya ya nufi bangaren maman nashi murja. Shima Abba yahya tashi ya fara kokarin yi,yana cewa Baffa Nima zan wuce dare ya fara yi,dakatar da shi Baffa ya yi yana cewa ,tsaya ai ban gama da kai ba, akwai maganar da ɗan uwanka ya ce nasanar da kai,saboda yana ganin lokaci ya yi da ya kamata kasanin.komawa ya yi ya zauna yana mai kara maida hankalinsa kan baffan,Baffa ya cigaba da cewa ka dai ji tambayar da murja ta yiwa ɗan uwanka akan manyan dukiyar da ya bawa Raihan ko? Jinjina kai Abba yahya ya yi,Baffa ya cigaba da cewa to ɗan uwanka dai ya riga da ya bawa Amininshi Alh Garba gwamna namu na Adamawa hakkin kula da ita,kuma ba tun yanzu ba ne an jima da yin hakan a tsakaninsu,babu wanda yasan da haka daga Ni sai shi sai kuma lauyansa da lauyan shi Garba,ko mahaifiyarku bata san da wannan maganar ba.jinjina kai Abba yahya ya yi kafin ya dan ja numfashi ya ce ",Baffa hakan da ya yi abune me kyau kasancewar muhimmancin Garba da halaccinsa gare shi,tunda za mu iya cewa duk abinda Muhammad nuurr ya zama da akwai sa hannun amininshi Garba,dan haka wannan ba wata matsala ba ce,sai dai muyi fatan Allah ya bashi ikon ci gaba da rike masa dukiyarsa cikin amana da Gaskiya", baffa ya ce",Amin ya Allah baki dadin yadda kafahimce Ni,dan haka ka ta shi kaje Allah ya bamu alkhairi,Amin ya fada yana mukewa da fita daga sashen. Kana ganin zaman da su kayi kasan na jiran sa ne,wani kallo maman ta wurga masa me cike da takaici,ta ce"yanzu kai dan rashin zuciya da sanin ciwon kai zama ka yi a can din kana surutu mara dalili bayan gashi mu nan muna jiran ka dan yin magana mai muhimmanci",zama ya yi yana cewa mama me kuma nayi daga dawowa ta? Kace me kayi mana kai yanzu baka ji haushin abin da ubanku ya yi ba?duba fa kowa zai zauna a kamfanin sa ya yiwa kansa kyakkyawan tanadi amma banda kai ,saboda kai an maida kai solobiyo ɗan solobiyo shine aka haɗa ka da aikin bautawa kamfanin gaibu, wannan kamfanin fa yana daya daga cikin manyan kadarorin Abbienku,akwai manyan kamfanonin da suke muhimmai wadanda ya boye su bayan ya mallakawa gaibu yarsa, sannan ya ƁOYE wanda ya bawa hakkin kula da su bare musan inda muka dosa,kai ba za kayi kishi da hakan ba bai hada ku da komai ba sai wasu ƙananun kadrori da basu taka kara sun karya ba?"momy hanne ta amshe da cewa yo kika san kyautar da za a yiwa wancan mata mazan ma kina ganin yadda aka ki bashi a gaban idanunmu kinga kuwa dole akwai muna furci cikin lamarin,dan haka tun wuri ku farka daga nannauyan baccin da ya kwashe ku,dan wannan kaɗai ya isa tabbatar muku da cewa mahaifin ku baya kaunar ku wancan gaibun da ba a haifa ba yake so da wannan mata mazan,dan haka yanzu ya rage naku ku kwatarwa kanku 'yanci ko ku tsaya kuna kallo ana wawashe dukiyar ku ana abinda aka so da ita" Affan cikin yanayin zuciya da alama dai an taso masa da abinda ya kwanta masa ya ce"wallahi mama ko da tsiya da tsiya tsiya sai mun karbi hakkin mu babu ruwan mu da wani kusanci ko ciki baya ku ka fito da mutum sai nayi duk yadda zanyi na kwaci hakkina"rufa i da yake ta huci kamar kububuwa ya zabura kamar zai kai duka ya ce" billahillazi ko me za ayi kai koda ya haɗa da shi mahaifin namu ne babu ruwan mu sai mun karba tun da shima ba kaunar mu yake ba,dan haka yanzu aiki ne babba a gaban mu dan dole sai mun san duk wasu dukiyoyi da ya tara wa Raihan tun daga lokacin da ya bata zuwa yau, dole ne mu binciko wanda yake riƙe da kadarorin,daga nan sai mu san hanyar da za muyi ƙwace su" Hamma idi ya dakatar da shi fuskar sa da wani irin yanayi na rashin jin daɗin abinda suke shirin yi ɗin , ya ce"amma ina ga abin da kuke shirin aikatawa ba daidai bane dan Allah ku yi hakuri da abinda kuka samu tun da shi din ma idan kuka jajirce watarana sai ya zama abin da baku taba zato ko tsammani ba, sannan ba hakkin ku ba ne kamar yadda kuke faɗa,idan da kuka duba duk abinda Abbie ya bawa Raihan ɗin da kuke magana akanta kuma ya baku sai dai kawai kuce ku baku juya naku ba har na waccan ɗin yake tsole muku idanu,da kunyi hakuri da naku watarana sai kufa kun samu abinda yafi wanda kuke son ƙwarya", dalla rufewa mutane baki wa yace maka abinda za mu yi ba daidai bane,?da kake kiran ba hakkinmu ba ne,to dukiyar ta uban waye aka dauka a ka bawa gaibu,ita fa wadda aka bawa dukiyar nan bata a duniya babu ita ko kadan,dan haka idan mun ci babu komai hakkin mu ne"cewar Affan ke nan da yake ta hura hanci zuciyar sa na kuma azalzala da kwadaituwa akan dinbin dukiyar da aka tarawa gaibun Raihan. Miƙewa tsaye idiris ya yi fuskar shi babu walwala ya ce,Ni dai babu hannu na a cikin wannan lamari dan haka idan ta kwaɓe muku kar kuce da Ni, kuma Allah ya ganar da ku"daga haka ya fice cikin sauri yana jin damuwa me tarin yawa akan abin da suke son aikatawa din. Bin shi su kayi da kallo,kafin momy hanne ta ce"ai dama har yanzu kana nan baka canja ba,na dauka girma yazo ka fara sanin ciwon kanka ashe dai har yanzu da saura"mama murja ta ce" rabu da shi mu za mu yi duk me yiwuwa dan samar da farinciki a cikin rayuwar mu,a haka suka ci gaba da tattauna matsalar da suke ganin ta Addabe su har zuwa tsawon wani lokaci kana kowa ya wuce makwancin sa. CHIBADO's hause....... Ko da rabi ta ji batun saka ranar auren su ita da wazir,farinciki tamkar zata yi hauka dan kowa sai da ya shaida hakan,maman ta ta fara kira ta sanarwa sannan kawayen ta da sauran duk wanda yasan kaunar da take yi wa wazir din,dan har sai da innawuro ta yi mata fada dan ita macece da sam bata son rawar kai da rashin aji ga koma waye. Shi kuwa wazir da kyar ciwon kan da ya addabe shi ya bar shi ya runtsa,saboda tsabar tunani da damuwa,wani sam baya barinsu su yi tasirin da zasu bayyana saman kyakkyawar fuskarsa bare har a gane abinda yake ta bunnewa. Muhammad nurr hause..... Sai yanzu da ta kebe dan kwanciya sannan damuwar wazir ta dawo mata sabuwa,dan tsuka ta yi tana mai shigewa cikin tattausan bargon ta,tare da rintse idanun ta,so take ta yi tunani akan camarar nan da videos din dake cikinta,duk da cewa lokacin da ta shirya dan fara bibiyar lamarin baiyi ba,a Haka bacci ya kwashe ta me cike da mafarkin wazir me dadi da mara daɗi. A bangaren aunty amarya kuwa ko da ta samu Abbie a daki cikin shirin bacci,kasa ce masa komai ta yi,amma tabbas zuciyar ta na cikin wasiwasi akan sa,da kuma dinbin tambayoyin da suke bakinta,sai dai tana tsoran fara tarar shi da maganar kar taje kuma abin da take tunanin ba haka bane,ta tunawa kanta asiri,shi yasa kawai taja bakin ta ta yi shiru ,harma ta yi kokarin daidaita nutsuwar ta duk dan kar ya fahimci a razane take,sai ma kulawa da ta yi kokarin bashi kamar yadda ta saba duk lokacin da yake wajen ta. _______________ Washe gari da wuri ta tashi ta yi shirin zuwa office saboda yau din akwai aiki sosai agabanta,tsaf ta fito cikin shirinta na kullum as a male,sai kamshi take zubawa wanda ya ke ta shi a hankali,a dinning table ta samu Abbie da aunty amarya suna karyawa,waje ta nema ta zauna bayan ta gaida su cikin kauna da soyayya, Abbie ya ce"manyan yan jarida yau za Afita aiki ke nan,an gama ɗokin dawowar abbie ne?dariya ta yi har fararen haƙoranta suka bayyana tare da lotsawar kumatun ta,zuba mata ido Abbi ya yi,yayin da shi kuma aunty amarya ta zuba masa nata idanun tana jin wata irin fargaba akan sa,ba komai ne yasa bata son Abbie ya san komai akan Raihan ba sai dan tasan idan ya sani din ba zai taba yadda ya ɓoye RAIHAN ɗin ba,dan soyayyar da yake mata ba zai bashi damar yin hakan ba, Abbie ya ce" Rahim me yasa wasu abubuwa naka suke yanayi da na mata ne shin kana sane kake yi ko kuma haka Allah ya yi k....kofin kunun tsamiya da ta kai bakinta tuni ya dawo tari ta fara sosai na alamun mummunan kwarewa,da sauri Abbie ya shiga shafa bayan ta yana mata sannu,aunty amarya kuwa mutuwar zaune ta yi saboda tsananin razanata da tambayar ta yi,ashe dama bai sani ba Gara da Allah yasa bata yi masa maganar ba jiya,tabbas da ta tonawa kanta asiri,to amma jiyan me yake so ya fada ya kuma fasa fada,daga karshe ma share tambayar ya yi,me ye manufar yin hakan,me yasa yayi wa Raihan tambayar da bai taba yi mata ba,ko dan yanzu ya samu nutsuwar zama da su ne yanzu ne hankalinsa ya dawo kansu?,idan kuwa haka ne aiki ne agaban ta ja,dan wlh baza ta taɓa yadda asirinta ya tonu ba,dan hakan yana nufin rasa tilon yarta ne. Dakyar tarin da Raihan take yi ya tsaya, amma idanun ta sunyi ja sun kuma kankance,sannu Abbie yake ta jera mata yana shafa bayanta,cikin tausayawa da nuna kulawa,kallon aunty amarya ya yi ya ce" ko dai asibiti zamu tafi a duba shi?kafin aunty amarya ta ba shi amsa, Raihan ta yi saurin tarar shi ta hanyar miƙewa tana tattara kayan ta,ta ce" haba Abbie daga kwarewa kuma sai asibiti kaga Ni na wuce office sai na dawo"to Allah yayi albarka ya dawo dakai lafiya ya kuma kare ka daga sharrin mahassada" Amin abbiena na kaina,ta faɗa da bashi sumba a hannun shi,haka tayiwa aunty amarya ta nufi kofar fita aunty amarya na raka ta da Tata addu'ar,a bakin kofa suka ci karo da Hamma idi,wai har ka fito broder? Me zan zauna yi, bari na gaida su Abbie na zo na sauke ki a office din,ya fada yana shigewa falon,yauwa Hamma ido na,bari na jira ka a waje amma kayi sauri dan yau din akwai aiyuka da yawa. CHIBADO's hause Fuskar nan babu walwala kamar ko yaushe, a haka ya sauko daga saman cikin takun shi na nutsatstsu kuma zaratan maza,bai ko kalli inda innawuro ta sa aka jere masa kayan karin kumallo ba ya nufi kofa kai tsaye,sai da ya kusa kaiwa kana ya dan dakata tare da juyowa inda innawuro ke hakimce tana bin sa da kallo,a hankali ya bude bakin sa kamar wanda a kayiwa dole ya ce" Barka da safiya Ni na wuce office" bai jira tankawarta ba ya fice cikin sassarfar tafiyar shi irin ta wanda yake son barin guri da gaggawa,amma ba kowa ne zai gane hakan ba saboda shidin komai nasa yana gabatar da shi ne ta cikin nutsuwa,ƙwafa innawuro ta yi tare da cewa duk tsiyar da zaka shuka ka yi ka gama aure ne dai babu fashi,kawun naka Mustapha ma yayi ya gama bare kai karamin jariri". Chibaɗo FM....... Kamar tare suke suna tsaida motar su ,shima tasa ta tsaya a wajen da aka tanadasa masa dan ajiye mota,sam Raihan bata kula da shi ba,tana can tana zuba murmushi me kama da dariya saboda labarin da Hamma idi yake bata na wata budurwar sa beyerabiya,,rufe motar ta yi tana daga mishi hannu,zan dawo na dauke ka, idan ka tashi ka sanar da Ni, Hamma idi ya fada yana tada motar,ok zan kiraye ka Rahim din ya fada yana juyawa dan shiga bangaren office din su. Ganin ta juyo yasa shi saurin dauke idanun daga kanta wanda ya zuba mata tun bayan fitowar ta,wuce wa ya yi ba tare da ya bari ta karaso in da yake ba,tura baki ta yi tana cewa zan biyo ka ne amma kayi ka gama fushin naka ,dan ba zanzo kana ci min magani kamar wani boss ba,da wannan kunkunin ta yi wucewar ta office din su.... ________________ Dr kana ganin yaron nan zai kawo mana sakamakon nan kuwa,tun fa dazu muke jiran sa amma gashi sama da'awa daya bai zo ba"cewar shugaban jam'iyya ke nan da duk yake a kage da son sanin wanda halima ta turawa sako,kafin Dr ya yi magana wayar shi ta yi kara,yauwa ga jagwal din nan, ya fada yana daga wayar,ka shigo kawai kai muke jira amma dai ka tabbatar babu wanda ya ga shigowar ka ko? Ok tom shike nan,daga haka ya katse wayar,cikin mintuna biyar jagwal ya shigo falon,mika masa hannu kawai shugaban jam'iya ya yi tare da cewa bani sai ka yi min bayanin yadda zan fahimta,mika masa takardun bayanan jagwal ya yi yana cewa,anyi nasara sir na gano har gidan da yaron yake me suna Rahim kuma shima ma aikaci ne a chibado fm,kuma na yi kokarin gano ai nahin sakon da aka tura masa" . Wata irin zabura shugaban jam'iya ya yi fuskar sa cike da wani irin annuri ya ce"Masha Allah yaro kayi abin da bazan manta da kai ba,dan haka za a ci gaba da tafiya me kyau da kai, Allah ya taimakeka yarinyar nan ta yi sanadin arzikin ka,dama ance mutuwar wani tashin wani,yi saurin sanar da Ni abin sakon ya kunsa",gashi nan a jikin wannan takardar kawo na karanta maka sir,ya fada jikin shi yana rawar farincikin tsintar dami a kala. Mika mishi ya yi,cikin ta rawar jiki jagwal ya fara karantto sakon kamar yadda halima ta rubutawa Rahim,babu kuskure ko guda har inda ta ajiye camarar,,,,,,tofa kaka tsara kaka Rahim baka dauko camara ba an gano inda camara take ya abin zai kasance ne,yaya gumurzun zai fara tsakanin Rahim da shugaban jam'iya harma da ragowar tsumammun da bamu san su ba.......✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page15 ``` Wata shegiyar dariya suka saki gaba dayan su irin ta manyan basawan nan,kafin su gimtse fuska duk alokaci guda,Dr ya ce"muyi gaggawar shiga gurin nan sai dai matsalar su tk basa kusa,kuma dole su ya kamata su je gurin tun da su ne suka sani,shugaban jam'iya ya shafa sankon kansa tare da cewa kuma bai kamata muyi jinkirin dauko camarar nan ba,tun da dai mun samu tabbacin bai dauke ta ba,saboda umarnin da yarinyar ta bashi na cewar kar aje dauko camarar a kusan nan"haka ne amma duk da haka sai munyi da jiki saboda samun matsala,waya ya dauko ya kira su tk,ya akai tk kun dawo daga wancan aikin ne? To maza yanzu ku jiyo ga abin da yafi wannan muhimmaci mu hadu a wancan gidan na bayan gari"daga haka ya kashe wayar,ya dubi shugaban jam'iya ya ce"ai sai muyi gaggawar isa kafin su karaso,sallamar jagwal su kayi sannan suka wuce a motar sirri wadda suke irin wannan fitar da Ita. RAIHAN.... Tana gama gabatar da shirinta na siyasarmu a yau,ta fito daga dakin daukar labarai, tana dan fitar da numfashin gajiya,duba lokaci ta yi wanda hakan ya yi daidai da wata irin mummunan faduwa da gabanta ya yi,dafe kanta da ya shiga sarawa ta yi kirjin ta na wani irin sama da kasa,kawai sai ta samu kanta da fasa shiga office ɗin,take wani tunani ya zo mata wanda sam babu shi a schedules din ta na yau,cikin sauri ta juya ta fita daga reseption din,daga nan tabi wata hanya ta bar cikin gidan rediyon. A.WAZIR..... Tun shigar sa office din yake jiran yaga ko zata shigo,amma shuru har lokacin break and prayer ya yi, cikin nutsuwarsa ya fito daga office ya hau lifter dan ragewa kan shi wahalar sauka, ta bangaren su RAIHAN yabi ,a daidai lokacin da su salim suka fito dan zuwa Sallah,gaisuwar Barka da rana suka mika,kafin su wuce,bin su ya yi da kallo miskilanci ya hana shi tambayar ina Rahim yake,fita ya yi kawai ba tare da ya samu ya fitar da abin da ke ranshi ba. RAIHAN..... Nafef ta samu ta hau, ta kuma yi kokarin samarwa kanta nutsuwa duk da yadda take ji kirjinta na duka da wani irin ƙarfi kamar zai hudo kirjinta ya fito,kasancewar wajen garine,wato hanyar barin gari yasa su ka yi tafiya ta kusan awa ɗaya,mika masa kudin sa ta yi tana mai duban hanyar da tunanin ta inda zata fara,sai da taga ƙulewar me nafef din sannan ta yi addu'a tare da bin hanyar da halima ta kwatanta mata,cikin bugun zuciyarta da ya zarta bugun da ake bukata ya yi, sosai take kurɗawa cikin ciyayi tana Daɗa nazarin hanyar dan kar taje ta kauce hanyar. ....... Shugaban jam'iya ne ya duba agogon da ke daure a tsintsiyar hannun shi,tare da sakin tsaki,ya ce"wlh ba daban karmu kuskure wajen ba da sai mu tafi haba tun tsawon awa daya muke jira amma sunki karasowa,da anyi magana sai su ce hodldop ya tare su,Dr ya ce" muyi hakuri dai mu jira da hakuri da rashin sa takin ƙalilan ne". Gaban ta ne ya kara faduwa saboda hango mota da tayi gaban wani kyakkyawan gida me matsakaicin girma,idan tunanin ta ya bata dai dai ke nan wannan ne gidan da mutanen suke kuma nan ne inda halima ta zo,da sauri ta kuma samun maboya ba tare da tsayawa wani tunani ba ta cigaba da bin kwatancen halima. A daidai wannan lokaci kuma su tk suka karaso, kuma ba tare da bata lokaci ba ,suka wuce gaba dayan su dan dauko camarar da suke da tabbacin cewa har yanzu tana nan a wajen. ______________ A wazir yana dawowa daga masallaci maimakon ya bi ta lifter ya wuce office din sa,sai kawai ya kuma biyawa ta wajen office din staff,a nan ya dan yi dube duben sa kamar irin yana duba aiyuka ne,nan kuwa so yake kawai yaga ta inda Raihan zata ɓullo,sai dai haka ta gama bin gurin da kallo baiga ko mai kama da ita ba,fita ya yi duk ranshi da zuciyar shi babu dadi,sai dai kuma babu mai gane hakan. Yana shiga office ya wuce toilet ya zubawa kanshi zuwa fuskar shi ruwa,haka nan yake ji kamar ba lafiya ba,duk inda Rahim yake baya cikin nutsuwar zuciya,saboda yadda yake jin tashi zuciyar na tsanani akan tashin hankalin rashin ganin nata,rufe idanun shi yayi yana jan hazbunallahu wani Imal wakil,fitowa ya yi tare da ɗaukar wayar shi ya shiga dealing nomber ta. RAIHAN,,,,,,,,,, Ta so ta samu matsala gurin gane ainahin gurin da halima ta binne camarar ,sai dai kuma cikin karfin addu'ar da ta rike a bakinta da kuma kyakkyawan niyar ta,tasa taga gurin ,cikin ƙanƙanin lokaci ta fito da dan karfen da ta zo da shi ta fara tone ramin,jin takun tafiya tayi harma da yan surutai daga dan nesa da inda take,gaban ta ne ya sake faduwa , addu'a da ta janyo ne ya bata karfin gwiwa wajen ci gaba da tone ramin. Su kuma tk da su shugaban jam'iya suna daf da karasowa wajen ne ƙaya ta soke Dr ta kasan takalmin shi wanda har ya faso cikin tafin kafar shi,suna kokarin dakatawa ya ce da su,maza ku wuce ku bari na biyo ku idan na cire" haka ne yasa suka ci gaba da tafiya. Jin karfin takun na ƙaruwa da kuma maganganun da take iya jiyo abin da suke fada yanzu yasa hankalin ta mummunan ta shi,ya akayi suka san camarar nan tana nan,me yasa sai yau suka zo dubawa? Ko dama sunyi mata tarko ne? Ji ta yi numfashinta na neman daukewa lokacin da ta hango wani garjejan basamude,ai kuwa da wani irin speed ta finciko camarar da dama ta zo gab da fitowa, saidai lokacin kuma su tk da shugaban jam'iyyar da sauran yaran sa suka bayyana a wajen,daji ne wanda yake da gonannaki tare da yalwar ciyayi hakan ne ya bawa Raihan damar ɓuya, wanda da har tayi tsammanin sun ganta saboda kusancin dake tsakanin su da kuma tazarar matsawarta daga gurin zuwa bayyanar su. A hankali suka fara bin gurin da kallo saboda son gano inda alamar da halima ta ajiye take,karaf kuwa tk ya gano gurin sai dai kuma abin da ya tsananta mamaki a gare su shine yadda suka.ga an tone gurin,da sauri suka karasa dukan su tare da yi wa wajen rumfa, cikin mamaki shugaban jam'iya ya ce" kuna nufin nan ne gurin?? Tabbas nan ne gurin cewar tk da sauran yaransa,to ai gashi alama ya nuna cewa an dauke camarar"shuru su kayi gaba dayan su suna mai zubawa gurin ido tare da nazarin wani abu,shugaba ne ya fara magana cikin tashin hankali ya ce" tabbas wajen nan yanzun nan aka gama tone shi dan alamu ya nuna hakan,ke nan duk wanda ya tone yana cikin jejin nan bai kai ga fita ba",tabbas oga maganar ka haka yake cewar duguja,da ya fara baza jajayen idanun shi kamar zai hango wanda ya tone ramin ya dauke camarar. Cikin daga sauyi na alamun tunzura da tashin hankali shugaban jam'iya ya ce"maza ku zagaye dajin nan ku nemo min yaron nan duk inda ya shiga ku kawo min shi da ransa",kafin kiftawar ido tuni sun raba kansu zuwa loko da sako na cikin jejin dan cika umarnin ubangidan su. Daidai inda Raihan ta buya a cikin ciyayi a nan shugaban jam'iya ya tsaya yana huci tare da baza ido ko Allah zai sa ya yi ido hudu da yaron nan. Kirjin Raihan babu abin da yake sai bugu saboda tsananin tsoratar da ta yi ,a inda take ko kwakkwan motsi ta yi zai iya jiyota,shi yasa ta kuma takure kanta da zuciyarta dake cikin wani irin razani,kara ƙanƙame yar karamar camarar ta yi tana ci gaba da karanto addu'a'in neman tsari,wayar ta dake makale a hannun ta ce ta fara bada sautin baburashin wanda hakan ya jawo hankalin shugaban jam'iya,zaro manyan idanun ta tayi tana mai toshe bakin ta da kukan tashin hankali ke son kufce mata, Allah Rahimi Maji rokon bayin sa wandanda suka dogara da shi akan shine kadai zai taimake su,juyowar da shugaban jam'iyya zaiyi maimakon yayi ido hudu da Raihan dake bayan shi,sai kawai yayi ido hudu da wani katon maciji ya kanannaɗe jikinsa tare da fasa kai,ihu shugaban jam'iya ya yi tare da yin baya,wanda hakan ya razana Raihan ta yi tunanin ganin ta yayi,sai kuma Allah ya bata kwarin gwiwar kasa motsawa daga gurin,dan tabbas da ta fidda razanar ta a fili da sai sun ganta,sai kawai mcijin nan ya fara silalowa wanda sai lokacin Raihan ta kula da shi,kara fiddo manyan idanunta tayi tare da dauke numfashi dan ta riga ta gama saddakarwa micijin nan gurin ta ya nufo ,shike nan ta kawo kanta inda ko ta mutu ba za a ga gawaarta ba, innalillahiwa'inna ilaihi raji'un ta shiga maimaitawa tare da ambaton kalmar shahada. A can bangaren A Wazir kuwa mamaki ne da tashin hankali ya kuma yi masa ruftu ganin yana ta kiran Raihan amma bata daga ba,to me ya ke faruwa? Ya tambayi kanshi da dan yin nazarin wasu sakanni,key din motar shi ya dauka ya fito cikin nutsuwa ,baza ka taba gane halin da yake ciki ba,saboda tsananin kamewar sa da nutsuwa,kai tsaye wajen motar ya nufa ya shiga tare da kunna ta ya nufi hanyar barin gidan ,ba tare da yasan inda zai nufa ba........ Rintse idanun ta tayi tana jiran taji daga inda zai bata sara,amma ga mamakin ta sai taji shuuu alamun wucewar sa ta gefan ta har sai da ya dan goge ta,bude idanun ta yi da sauri sai kawai taga ya nufi wajen su shugaban jam'iya kai tsaye yana wani irin huci me tsananin zafi,ganin haka yasa Raihan samun kwarin gwiwa dan haka ta yi saurin silalawa ba tare da sun ganta ba,tabi ta cikin ciyayi ta fita da gudu bayan ta danyi nesa da su. Tk ne ya saita bindiga zai harbi macijin sai kawai su ka ga ya yi wata girgiza yayo kansu,ai basu san lokacin da suka cika wandunan su da iska ba,hatta da Dr da ya gama cire kaya ya biyo bayan su yana dingishi bai san ya akayi ya mike kafar ya ranta a na kare ba. Raihan kuwa cikin nishin wahala ta fito bakin titi,cikin ikon Allah ta samu nafef ta shige,tana mai da numfashin wahala. Yana sauke ta a kofar gidan su,ta hango motar A wazir a wajen da alama ya dan ja wasu mintina da zuwa,kokarin saita kanta take yi ta hanyar kimtsa kanta daga hargitsewar da ta yi. Zuba mata ido ya yi lokacin da ya karasa inda yake tsaye hannuwan shi a harɗe a kirjin shi,kallo yake mata ciki da bai na san gano abin da take son boye Masan,sunkuyar da kanta ta yi cikin sanyin da gaɓobin ta suka fara yi na kallon da yake mata, Ina kika je?? Ya tambaye ta cikin cunkushewar murya wadda take nuni da bacin ransa da ba a cika ganewa ba,shuru ta yi saboda tasan ko ta yi masa karya sai ya gano ta,hasali ma bata iya yi masa karyar,kayi hakuri kawai ta iya fada cikin marairaice fuska kamar zata yi kuka,kawar da kanshi ya yi saboda baya san yanayin nata ya sauya shi,wayyo Hamma wazir cikina ya murda bari na shiga ciki",tana gama fadar haka ta juya da dan gudun ta ,buga kofar ta shiga yi da sauri har sai da basamuden me gadin su ya bar abin da yake ya zo ya bude mata kofa,bata saurari komai ba ta Wada gidan da gudu,duk securityn da ke tsaye kamar sojoji da wadan da suke zirga zirga a gidan sai da suka bita da kallo. Numfashi ya dan furzar yana mai kara lumshe lumsassun idanunsa,yana kuma jin zuciyar sa na daidatuwa da samun nutsuwa na tabbacin lafiyar Raihan,sai dai kuma yasan akwai abinda take ɓoye masa,wani dan murmushi ne ya kufce masa wanda rabon da yayi shi tun ranar da suka je gidan gwamnati,dama ita ka dai ce ke samun murmushin nasa lokaci zuwa lokaci, to ita ma din yanzu Murmushin ya gagareta,ba komai ne ya sa shi murmushi ba sai tunanin wayon da Raihan din ta yi masa,shafa tattausan sumar kan shi ya yi kafin kuma ya shige motar tare da barin layin. _________________ Amma wannan yaro kwai tantiri,tabbas wannan abin da ya faru ya nuna min cewa zamu yi gumurzu da yaron nan,domin kuwa shu'umi ne,cewar shugaban jam'iya da hankalin sa yake matukar ta she,Alh sale da zuwan shi ke nan, ya ce" Ni ba komai ne yake matukar bani mamaki da tsoratani ba akan yaron ba,sai tunanin yadda akayi yasan zamu nemi camarar nan a yau,ta yaya ya sani bayan gargadin da marigayiya ta yi masa akan kar ya tunkari wajen nan a yanzu??? Dr ya ce" Nima abin da yake sakani a ruɗani ke nan,da kuma tunanin anya ba shi ya turo mana macijin nan ba,saboda Ni macijin nan ya bani mamaki dan se nake ga kamar ma ba maciji ba", shuru su kayi gaba dayan su kowa yana tunanin mafita. Can Alh sale ya numfasa tare da cewa,duk wannan ba shi ne me muhimmanci ba,yanzu kawai tunanin yadda zamu karbi camarar nan a hannun sa kafin ya tona mana asiri,saboda ko mun kama shi idan har ya saki video nan babu amfani dan wlh nasan hukuma sai ta kama mu", Dr ya ce" bayan kama mu da zata yi bamu da mafita akan dukkan aiyukan da ake aikatawa na lefi a garin nan,kai tsaye mu za a ce ba tare da wani dogon bincike ba", shugaban jam'iya ya mike yana Safa da marwa a tankameman falon nasa na gidan tattaunawar su ta sirri, Lallai idan ba mu yi da gaske ba to tabbas akwai babbar matsala,na baku daga nan zuwa gobe kowa ya yi tunanin abin da ya dace.......✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page16 ``` A bangarensu ta tarar da Hamma Idris, ɗan hararar ta yayi tare da cewa ba nace idan zaka taho ka kirani naje na dauke ka ba?"dan dafe kanta ta yi cikin nuna alamun mantuwa ta ce"ayya Hamma wlh shaf na sha afa dake ma Hamma wazirrrrrr ne ya taho dani yanzun nan ya wuce"ta faɗa tana wucewa dakinta tare da yin istigfar akan karyar da tayiwa yayan nata,ok shike nan ba damuwa,dama so nayi na dinga kaika ina dawowa da kai kafin zuwa Monday na fara zuwa office kamar yadda Abbie ya ce"ok Hamma ba damuwa ta faɗa tana karasa shigewa dakin dan adana sirrinta. Chibaɗo's hause.... Bai shiga gidan ba sai da ya tsaya su kayi sallar magriba tare da kawunsa Abban rabi da Abbu,kasancewar kullum dama anan gidan yake sallahr magriba tun da wutowa yake daga office,kuma ka idar su ce sai sunzo gaida mahaifiyar su, Abban rabi yanzu ya dawo Abuja tun wata daya da suka wuce,saboda matsala da ya samu a wajen aikin sa,dan haka ɗan uwanshi ya ce"ya dawo Abujan ya cigaba da kula da kamfanin fulawar sa dake nan Abujan,tun farko dama yaso ɗan uwannashi ya rike ragamar wasu kamfanonin nasa tun da shi Abbu din yafi ga gidan rediyonsa,to amma sai Abban rabin ya nuna masa Gara dai shima yaje ya danyi aiki da takardunsa da kuma basirar sa,to gashi dai daga karshe yadda abin ya kasance dole dai ya dawo gidan da baya so kuma ya rike kamfanin abin da dai baya so ɗin,ko meye dalilin kun hakan oho sai a gaba za mu iya ji ,to ko kuma yanzu ya saduda ne tun da takardun nashi sunki bashi abin da yake so ɗin oho. Wazir a cikin masallacin ya bar su ya fito dan ya danyi bukatunshi kafin lokacin Isha i,tunda yau din bai samu dawowa da wuri ba, Sannu kawai ya ce"da innawuro ya haye samansa cikin kara tsuke tsukakkiyar fuskar shi da babu alamun fara a ko ta kwabo,gyatsine fuska innawuro ta yi tana bin shi da kallon banza ta ce,wlh aure ne kamar anyi angama fushinka babu abin da zai tsinana"yaji ta sarai amma sai bai nuna hakan ba ya yi shigewarshi koridon da zai kaishi asalin falon shi, Wanka ya yi tare da yin alwala ,cikin dan gaggawa ya goga turaren shi na gabbon ya taje lallausar suman shi ta asalin Fulani,blue din jallabiya ya saka mai tsantsi sai ƙyalli take zubawa ,ta kwanta luf a jikin shi ta fidda kirar shi ta karfaffan namiji me cikakken zati,silifas ya saka me taushi a kafarshi da kamar baya taka ta akan kasa,da sauri ya fice daga dakin jin ana ƙoƙarin tada sallar Isha'i. Muhammad nurr hause..... Zaune suke gaba dayansu a dining table,Dan sun kuma samun karin Hamma idi,duk kuwa irin fadan da mama ke mishi akan shishshigewar da yake yiwa aunty amarya da ahlin nata,amma shi ko ajikin sa,kansa tsaye yake yin komai nashi,dan wani sakewar da yake a ɓangare antyy amarya ko avangaren nasu ne iya haka zaiyi. Sai da suka gama cin lafiyayyan girkin Aunty amarya,kana suka dawo falo gaba dayan su, Raihan ce ta tsaya taya sahura kwashe kayan da su kayi amfani da shi dan kaiwa kiching. Kamar daga sama RAIHAN taji tambayar da Abbie yake yiwa aunty amarya,ya ce"Ramla wai me yasa kike son dawo min da yarona dan daudu"wata irin zabura Anty amarya ta yi tare da duban inda Raihan ta yi tsayuwar yan sanda,sai ta samu kanta da rikicewa da wadannan tambayoyin da abbie ya tsiri yi mata su daga jiya zuwa yau,bayan bai san halin da yake sa ta aciki ba duk lokacin da ya yi mata tambaya makamanciyar wannan,a hankali Raihan ta sulale tabar wajen,abin da kawai ta yankewa kanta shine daina zama tare da Abbie tun da hakan yana neman sawa Ummin ta hawan jini,dan ta tabbata cewa wadannan tambayoyin yana yin sune saboda kula da almuranta domin cike gurbin nesa ta kansa da su a baya haka kuma tasan tambayoyin suna taba zuciyar auntynta ta matuka da gaske,shigewa ta yi dakin ta tana cewa Hamma idi sai da safe a kwai wani dan aiki da za ta yi kafin gobe,jinjina kanshi ya yi a hankali.dan hankalinshi gaba daya yana kan kallon kwallon da ya sa a tashar aljazira. Juyawa ta yi gun abbie cikin basarwa ta ce" abbie good night idan kuma na fito shike nan,haka ta yiwa aunty tana karasa shigewa dakinta ,tare da sakin ajiyar zuciya. Zama ta yi a bakin gadon ta saitin madubi tana ƙara kallon kanta kamar kullum tun kafin tasan kanta a matsayin mace,idanuntane suka cika da kwalla, idan tace bata damuwa akan yanayin da rayuwarta ke ciki tabbas ta yi karya,sai dai tana matuƙar ƙoƙari gurin ganin ta yakice al'amuran da suke damun ranta,ba dan komai ba sai dan auntynta da tayiwa alkawari,share hawayen fuskarta ta yi tana jin wani abu na taso mata mai karfi da sanya gwiwa sacewa,shin yaya zata yi da abin da yake neman fin karfin ta,haka nan zata ci gaba da rayuwa a matsayin namiji ke nan Dan kawai kar aka sheta ?? Anya kuwa zata iya ci gaba da boye kanta?? Shin ƙaddararta ce zama a matsayin namiji ko kuma kaddarar mutuwar ce akan zaman ta a matsayin mace?? Anya kuwa babu sabon Allah akan wannan lamarin??? Hannu tasa ta goge fuskarta da ta yi ja saboda damuwa, Ita ka dai tasan yawan damuwar ta,ita kadai tasan yawan dafin dake cikin zuciyarta.. Raihan kiyi addu'a kawai akan duk abin da zai zama alkhairi a rayuwar ki Allah ya tabbatar miki da shi, wannan shine amma damuwa da tunani ba na ki bane ,kina yarinyar ki dake damuwa ta rugurguza rayuwar ki, dalla share komai ki manta ki ci gaba da walwalar ki ,ki kuma zubawa sarautar Allah idanu duk yadda ya yi dake shine alkhairi,wata ɓangare na ingantacciyar zuciyar ta ne ke bata wannan shawarar,miƙewa ta yi tana mai jin kwarin gwiwa akan komai na rayuwar ta. A bangaren abi da aunty amarya kuwa,zuba mata ido ya yi bayan shigewar Raihan daki,ganin bata ce mishi komai ba ya dan juya ya dubi , Idris wanda gaba daya hankalin shi da nutsuwar shi suke kan kallon boll,dawo da duban shi kan aunty amarya ya yi tare da dan yin gyaran murya,hakanne yasa ta juyowa ta kalle shi fuskarta babu alamun walwala,ɗage mata gira yayi tare da cewa ,to me kuma nayi ake wannan hade ran daga tambaya kawai,dan hararar shi ta yi tana cewa me kake nufi dan Rahim yana namiji bazan sashi aiki ba? A'a Ni ba haka nake nufi ba,amma a yi hakuri a maida wukar" ya fada cikin son maida abin wasa,itama Murmushin ta yi tana dan satar kallon Idris,daga nan suka ci gaba da yar hirar su,har zuwa lokacin da Hamma idi ya yi musu sallama ya wuce gidan su. A bangaren Abba yahya kuwa,tun bayan da Baffa ya sanar da shi wannan batu na dukiyar Raihan dake hannun aminin ƙaninnashi kuma gwamnansa shugabansa a wajen aiki,ya kasa zaune da tsaye, sam hankalinsa bai kwanta da wannan gurbin tunanin na ƙaninshi ba.wai Abban Bashir lafiyar ka kuwa?ka kasa cin abincin kirki sannan yanzu ka kasa zuwa ka kwanta dare sai yi yake anya kuwa lafiyar ka kalau? Cewar inna maimuna ke nan da fitowarta daga daki ta kusan hudu ke nan tana ganinshi a yanayin da ta shi,zama ya yi yana fidda wani numfashi ta hanyar fesar da iskar bakinshi,sai da ya yi ɗan jim,kana ya ce"maimuna wani abu ne yake damuna,a nan ya sanar mata da abinda ke faruwa,inna maimuna ta yi Murmushi tana cewa to kai meye naka na damuwa meye abun tashin hankali acikin wannan lamarin? maimuna ba zaki gane ba,me zai hana kuwa na gane idan ka fahimtar dani"juyowa Abba yahya ya yi yana duban inna maimuna cike da son ta fahimceshi,ya ce"Nura yayi wawtar dankawa Alh Garba dukiyarshi,har yanzu Nura bashi da wayo bai san masoyinsa ba,damuwata akan wannan al'amari bai wuce kar Alh Garba ya cutar min da dan uwa akan dukiya ba,ina matukar jin tsoran abinda zai biyo baya,saboda ɗan zaman da nayi da gwamna tsaf na karanci waye shi na karanci cewa shi ɗin akkuya ne da fatar kura mayaudari ne, cin amanar ƙasar bai zama komai share shi ba,bare kuma cin amanar amininsa cin amanar aminta da aka jima ana gina ta cin amanar wanda ya aminta da shi,tabbas ina tsoro ina tsoron wani al'amari ",cikin tashin hankalin kalamansa inna maimuna ta ce",me yasa ba zaka sanar da shi nuran ko Baffa ba?in dai har kana irin wannan tunanin kuma kasan wani abu akan Alhji Garba ka yi shiru daga baya wani abu yazo ya faru tabbas baka da fita kuma ɗan uwanka da mahaifinsa ba za su taba yafe maka ba,dan haka ina mai nusar da kai kayi wani abu kafin me faruwa ta faru". Mainuna ba za ki gane abinda nake hangowaba,yanzu idan nace zan sanar da su kai tsaye ba za su yadda ba karshe ma reshene zai juye da mujiya nine zan zama abin zargi za su ce ina bakin ciki ne dan ba abani riko ba an bawa bare,tabbas kaima kana da hujja ,to amma yanzu me kake tunanin yi akan taimakon nuran?inna maimuna ta tambayeshi idanunta akansa,dole zanyi wani abu zan taimaki dan uwana kamar yadda ya tallafi rayuwata,duk da nadan cewa ba zan iya biyansa dinbin alkhairin da ya yi min ba,amma dai zan kwatanta, Allah ya taimakeka akan niyarka Nima idan da taimakon da kake bukata daga gare ni zanyi koda shawarace. ____________________ Darene sosai ,wanda alokacin ko wane bawa ya sauke hakarkarin shi dan hutawa,masu dabara kuwa suna can suna bautawa Allah da neman biyan bukata ta hanyar salloli da karatun Alqur'ani, Da yawa kuwa daga cikin mabiya shedan,wadan da zuciyar su ta ƙone ƙurmus,kuma ta ƙeƙashe,suna can cikin wani dogon tsauni inda tsohuwa me jini ke zaune da mabiyanta wanɗanda suke nema a gare ta.. Jajayen idanunta ta ɗago ta ta kalli ɗaya daga cikin mutane goma dake durƙushe gabanta,kawunan su duk a kasa,ta buɗe bakinta me tsananin wari kato kamar kofar yin bahaya,ta ce"ina mai tabbatar maka da cewa shigowar ka wannan ƙungiya Tamkar samun nasarar ka ce ta rayuwa,juyar da fuskarta me dauke da ƙwalaƙwalan idanu ta yi kan na kusa da shi ta ce",kai kuma tun da ka kawo mana shi cikinmu nasarar ka yanzu ta fara,mu dai kawai mu na so ka ci gaba da aikata duk ta asar da muka sa ka aikatawa,duk inda ka sa kafar ka ya zamana cewa an zubar mana da jini domin jini shine muradin ya'yan tsohuwa mai jini,idan ka ci gaba da yin haka ina tabbatar maka da cewa siyasa da yin nasara ba ka fara ko mai ba,za ka ci gaba da nasara akan dukkan wani kudurinka,siyasa kuwa yanzu ta fara zama a hannunka sai kayi mulkin da babu wanda ya taba yin irinsa a cikin ƙasar nan,za ka samu ɗaukaka inndai har kana tare da mu,kuma idan ka ɗiba zaka dinga zubawa,to kuwa tabbas za kana kwashewa"...hahhhhhhhhh....ta saki wata shiɗaniyar dariya wadda ta sa gaba daya tsaunin ya shiga girgiza da kansa,bai tsaya ba har sai dai ta rufe bakin ta kai kace ba wajen ne yake girgiza ba,haka kuma kamar ba ita ce ta yi dariyar ba. Duban wanda aka kawo din ta yi tare da nuna shi da wata sandar tsafi,nan take kanshi yayi tas kamar Allah bai yi tsiron gashi akan ba,wanda ya kawo shi ta umarta da ya dauki kwaryar dake gabansa ya zuba masa akansa,babu musu ya dauki kwaryar ya zuba masa jinin dake ciki, ragowar kuma ta ce"ya bashi ya shanye. Sai da ya shanye jinin nan tas,yana faman runtse ido,kana tsohuwa ta kuma bushewa da wata mahaukaciyar dariya,wanda a wannan karon harsu kansu sai da jikin su ya dinga girgiza ba tare da sun girgiza da hakan ba, Daga yanzu ka zama namu,kuma zamu canja maka suna wanda a hankali zai bika sunanka na asali zai bace domin wannan shine muradinmu. Jin jina kansa ya yi ba tare da ya ɗago ba har yanzu ,dan wannan doka ce ta nuna ladabi ga tsohuwa. Duban wanda ya kawo shi ta yi ta ce" shuda daga yanzu sunan yaron ka,dunan duniya saboda yana tare da Aljani dunan duniya,dan haka za mu dinga kiran shi da dudu,gaba dayan su kawunan su na a sunkuye su ka hada hannayen su biyu tare da jinjina a gareta,.. Kai kuma duduu ka tabbata daga yau zaka fara cimma nasara a kan abin da ka dosa, sannan daga gobe muke son ka fara aikata manyan zunuban da muka umarce ka da yin su"......... ____________ Washe gari tsaf Raihan ta shirya ba tare da ta jira Hamma idi ba ta fito tana kiran driver,sai dai kuma fitowar Hamma din ya sa ta dakata da ga kiran drivern,karasowa ya yi yana cewa lil broth yadda mu kayi da kai ke nan? Wato na fahimci dai baka so na samu ladan kaika gurin aiki ko? Dan murmushi Raihan ta yi kafin cikin siririyar muryar ta ta ce" ba haka bane Hamma idi kawai bana son takura maka" girgiza kai ya yi yana mai kama hannun ta ya ce" ai Ni nace ka dinga kirana ina kaika da ɗaukoka kafin zuwa Monday Nima na fara zuwa nawa,idan kuma mun cigaba da tafiya tare shike nan duk hakan ba damuwa bane" bude gaban motar ya yi,tare da yi mata nuni da ta shiga,shiga ta yi tana cewa Hamma na gaskiya kana ji dani" to idan ban ji da kai ba dawa zanji? Ya fada bayan ya shiga wajen zamansa yana mai kokarin tada motar. Hira Hamma Idris yake yi da dan uwan nashi wadda ke cike da nuna kulawa tare da soyayya, Raihan din ma amsa shi take da kulawar dan har ji take kamar ya cancanta da ya san wacece ita a matsayin sa na ɗan uwanta me kaunar ta,to amma babu damar yin hakan saboda alkawari ne da ta ɗaukarwa auntyyn akan bayan wazir babu wanda zai kuma sanin asalin jinsin ta. Rahim motar nan kuwa ba mu take bi ba?Hamma idi ya tambayi Raihan bayan ya fara rage karfin gudun da yake dan son tabbatar da abin da yake hasashe,duban bayan su Raihan ta yi ta hanyar duba mirror din gefanta,tabbas kuwa mota ce baka me bakin gilashi a bayan nasu sai dai kuma kamar yadda ya fada basu da tabbacin su take bi. Ganin ya rage gudun da yake yi motar bata daina binsu ba,yasa shi ƙoƙarin sauka kan hanya dan yin parking cikin sauri da kokarin ƁOYE razanar da ta yi ta ce", a'a Hamma kar mu tsaya ba mu sani ba ko masu cutarwa ne,duban ta Hamma idi ya yi na ɗan wasu sakanni kamar yana son gano halin tsoran da Rahim din ya shiga, sai kuma ya ɗauke kansa tare da bawa motar wuta ya fice da mugun gudu,wanda hakan ya basu damar bacewa waccan motar. Tana kokarin fita Hamma idi ya dubeta kana ya dan furzar da numfashi ya ce"Rahim me kayi musu suke bin ka? Da sauri Raihan ta shiga girgiza kanta tare da cewa wlh ban sani ba kuma ai bani suke bi ba"ok shike nan,amma ina so ka dinga kula kasan irin binciken da zaka dingayi Rahim bana son wani abu ya same ka ta sanadin aikin nan,domin kuwa hakan ce take faruwa akan da yawan yan jarida masu gaskiya,dan haka ka kiyaye",jin jina kai Raihan ta yi kana ta fice jikin ta a sanyaye da al'amarin da ya faru yanzu kuma ta tabbatar da cewa ita din ake bi,gaban ta ne ya fadi lokacin da tayi wa kanta tambaya akan abin da suke shirin yi mata. Cike da mamaki Hamma idi yake kallon motar da suka baro tana bin bayan su,bai nuna ya ganta ba sai kawai ya juya ya koma cikin ma aikatar ya yi fakin tare da kwantar da motar kujerar ya kwanta,yana kallon masu shige da fice dan tabbatar da tsaron kanin nashi.... Hello sir aikin nan fa ya jike,cewar tk,da yake waya da Dr sanater,me ya faru ke nan baku samu damar dauko shi ba? Duk ya jera musu tambayoyin a ɗan rikice,tk ya ce"oga wani dan uwansa ne ya Ankara da bin su da muke a yanzu haka da ya ganmu ya koma cikin ma'aikatar yana gadin sa"ok to maza ku bar gurin kar ku bari kowa ya gane me kuka je yi" da wannan umarni suka bar bakin tafkeken buldin din chibaɗo FM din.. __________________ A hankali Dr ya sa hannu ya share zufar da ta karyo.mishi ,yana cewa na fi kowa shiga matsala ,saboda Ni komai nawa na sa ka gurin neman takarar senator, idan asirina ya tonu na shiga tara ya zamana bani da tsuntsu bani da tarko ma ana ba dukiya ba mutunci"ya karasa maganar da mikewa tsaye yana jin kamar ya je har inda rahim yake ya bindige shi kowa ya huta........ ✍🏽 Fyadams.........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page17 ``` Shugaban jam'iya ya ce"ai idan ma iya mutuncin ne zai zube to da sauki,karfa ku manta batu ake na kisa ta zahiri da ta boye,kuma duk akan mu,to dan me zai sa ku dinga yin tunanin zubewar mutunci ai ana kama mu Kuma kunsan meye makomar mu daurin rai ne kawai",numfashi Alh sale yaja ya fesar kana ya dauki kwalbar barasa ya dan zuka kana ya dubesu ɗaya bayan ɗaya mu,sai da yaja wasu yan sakanni kana ya ce"kai fa takarar senate ne nifa gwamnan kasa nake son karba idan baka manta ba,dan haka duk cikin mu shugaban jam'iya ne kawai Gara tun da shi bai kashe komai ba,duk a cikin kudin gwamnati yake facaka,shugaban jam'iya ya zabura yana cewa haba Alh sale duk kudin da nake facaka da su ɗin ba tare muke ci ba,kar fa ku manta a idon mutanene muke yan adawa amma a badini mudin aminan junane,kuma duk kudin da nake dannewa ba tare da sanin gwamna da yan kungiyar sa ba,ai tare muke ci,duk wata cuwa cuwa da za muyi da sauran masu muƙamin gidan gwamnati rabi ku nake kawowa ba tare da su na basu kasonsu ba,shine yanzu dan son kai zaku ce na fi ku kwanciyar hankali,a ganina ma ai sai nafi kowa tozarta",shike nan yanzu dai mafita ya kamata mu nema duk wannan batun mu ajiye shi,cewar Dr da kamar yafi su damuwa da lamarin, Alh sale ya ce" Ni ina da shawara,duk zuba masa ido sukayi cike da so da dokin jin abinda zaice" ƙasa ya yi da murya tare da ya fito su da hannun shi,aiko da sauri suka matsa kusa da shi suka sashi a tsakiya,raɗa ya yi musu wanda duk ƙwaƙwata na kasa jin abin da ya fada musu,dariya suka sheƙe da ita suna tafawa tare cike da farin ciki da alamu dai shawarar ba karamin dad'i da karɓuwa ta yi a gurinsu ba,nan suka ci gaba da tattaunawa kan yadda za su yi komai a tsare batare da asirin su ya tonu ta hanyar camarar nan ba. __________________ Jiki a sanyaye tasa kafar ta a cikin office din ya,zuciyarta ba karamin nisa ta yi akan lamarin wadannan mutane da har yanzu bata san ko su waye ba,kokarin ya kice abin ta yi dan sam Raihan bata barin damuwa ta yi tasiri a jiki da zuciyarta,ko mai takan kokarin ɓoyewa sai dai idan abin ya taso ba karamin kokawa take da shi ba kafin ya sake ta na wani lokacin,cikin himmar ta na son kawar da komai ta fuskanci abin da ke gabanta ta fara gudanar da aikin ta kamar yadda ta saba.. _______________ Duk yau din baya jin dadi shi yasa tun da ya shigo office din bai leka ko ina ba,hasali ma ya hana shiga office din sa daga bakin sakatariyar sa,kuma ya soke schedules din sa da kowa,haka nan yake jin damuwar rashin Raihan a kusa da shi kwana biyu,ga kuma sa ranar sa da a kayi shida rabi sati Uku,duk sai yake jin sa a wani iri,duk da cewa ba a cika gane damuwar sa ba,amma idan ka dube shi kana dan yin nazarin sa zaka san akwai abin da ya dan taba shi,ko da ya fita sallah bai biya ko ina ba ya dawo office ya kuma rufe kansa saboda baya son abin da zai kara mai damuwa. Sai da Hamma Idris ya tabbatar motar nan kome kama da ita ma babu a bakin buldin din chibaɗo FM, sannan ya tafi yana mai jin tsoron wannan aiki na Rahim. A hankali cikin sanyin jiki ta fito daga dakin madaukar murya,salim ne a gefan ta, yana sanar da ita wani labari da suka samo akan Hajiya Turai wadda a baya zata yi hira da ita aka samu matsala,kuma Yar takarar sanata a jam'iyyar gwamnati me ci a yanzu,wato abokiyar takarar Dr.dan tsaki ta saki tana duban salim din,ta ce"salim kabar min batun matar nan bana jin yadda akanta haka nan"salim ya ce"shi yasa nake so mu dan yi bincike akanta,hmm kana gani taki zuwa a yi hirar da ita ko me take tsoro oho mata,dariya salim ya yi ya ce"haba Rahim kai din ne fa ba kyau ko mutum yana da gaskiya idan kayi hira da shi sai ya koma mara gaskiya saboda tsauraran tambayoyinka masu kada yan hanjin mara gaskiya"yauwa Gara da kace mara gaskiya,cewar RAIHAN tana nufar office din ta. A bakin office dinta ta hadu da Khalid da wasu fayal a hannun sa da alama ya dan jima yana jiranta,ya akayi Khalid? cewar RAIHAN tana dubansa da kuma fayal din dake hannunsa,yauwa Rahim dan Allah wani taimako zaka yi min tun dazu nake zuwa office din oga sakateria na hanani shiga daga umarnin sa,wai baya jin dadi,to dole yau din ya kamata na yi submit din wadan nan fayals din dan Allah kaje ko kai zaka samu ya saurareka"ɗan jim Raihan ta yi kafin a hankali ta karbi fayal din ,shike nan bari na je na gani"yauwa Rahim na gode ya fada yana barin wajen shida Salim. Sai da ta ajiye takardun dake hannun ta , sannan ta fito dan zuwa office ɗin,kai tsaye lifter ta bi dan ragewa kanta aiki,tana isa ba tare da ta saurari sakateria ba ta nufi kofar kai tsaye,da sauri sakateria ta mike tare da saurin shan gaban Raihan,wani irin kallo Raihan ta watsa mata kafin ta raba ta gefan ta ta wuce,har tasa hannu kan handle din kofar sakateria ta ce",umarni ya bada kan cewa kowaye yazo kar ya shiga saboda yana bukatar nutsuwa"juyowa Raihan ta yi ta ce"to ai idan nutsuwa yake bukata ba a nan ya kamata ya same ta ba sai ya bari sai yaje gida"daga haka tasa kai ta shige office ɗin,tana mai kara jin haushin sakateria,itama sakateria bin sa ta yi da harara tana cewa wannan shu'umin yaron na kasa gane abin da ya taka da kuma matsayin sa gurin oga? (He sakateria daina wahalar da kanki ba zaki gane ba tukunna,kar ku manta sakataria a matsayin namiji take kallon Raihan dan haka dole ta shiga rudani akan lamarin nasu). A hankali ta yi sallama tana mai wara manyan idanunta a cikin ko wane loko da saƙo na office din,sai dai duk iya hangen ta bata hango shi ba,tsam ta yi da ranta tana kallon kofar toilet wanda budewar da akayi ne ya ja hankalinta,bin sa ta yi da kallo idanunta suna wani yin ƙasa ƙasa cike da rauni suna komawa kalar kuka da san zubda kwalla. Cikin wata irin kasalalliyar Murya wadda ke tafe da wani irin amo me karya garkuwar jiki,ta ce" Hamma wazirrrrrr"yadda taja karshen sunan haka yaji zirrrr din har cikin kwanƙwalwar kanshi,dan rintse idanun shi ya yi ba tare da ya juyo ko amsa mata ba,sai ma ci gaba da takawa da ya yi cikin kamewar shi me tafiya da yan matan Yola harma da na wasu jiha,tura dan karamin bakinta ta yi,tare da saurin tarar gaban shi ,langabar da kai ta yi tana kallon shi cike da wani irin yanayi da sauyawar tafiyar numfashi,zuba mata ido ya yi yana son kallon cikin idanun ta,ko Allah zai sa ta fahimci halin da yake ciki,tun da shi ya kasa ganowa,wala Allah tunda akanta ne kome ma yake faruwa watakila ita din ta gane tayi mishi bayani. Sai dai kuma taki bari su hada idanun kamar yadda ya so,saima lumshe idanun da tayi tana mai ɗora maganar ta da cewa me yake faruwa kwana biyu? Ka sauya duk da cewa ba a gane sauyinka bare ainahinka,amma Ni bakan kokarin gane ko wane irin sauyi naka ko yaya yake,akwai damuwa ne Hamma wazir,ta karasa fada idanunta na kara cikowa da kwalla har tana shirin zuba,sam bata jin daɗin yanayin saboda ba haka ya sabar mata ba,duk da cewa ita ma din ba tsira ta yi daga mugun miskilancinshi ba. Ba tare da ya amsa mata ko daya daga cikin tambayoyinta ba, ya raba ta gefan ta ya wuce saman kujerarsa, ya hakimce tamkar wani sarki,fuskar nan har yanzu tana nan a yadda kowa ya santa,ita sauna gani ta yi kamar ta kara tsukewa fiye da kullum,duk da cewa ta san wannan basarwa da gizagon halinshi amma sai taji duk ta takura dan ko ba komai ita din yana ɗan ƙoƙarin sakar mata wani lokaci,to meye yake yi hakane? Me yake tunani akan ta? Ko yana tunanin itama zata ce tana son shi ne kamar sauran yan mata?tabbas biri ya yi kama da mutum,tunda shi mutum ne da baya iya sakewa da mace, wannan tunanin da ta yi yasa ta yi saurin kama kanta tare da alkawarin kame kanta kamar yadda shima da yake namiji yake da tsananin kamewa,dole ne ta mutunta kanta a wajen sa ,a matsayin ta na mace. Wannan tunani da tayi a cikin mintin da bai wuce daya ba,yasa ta yi saurin mika masa fayal din hannun ta ,tana cewa sorry na shigo ba akan daidai ba kayi hakuri,dama wannan Khalid ya ce na baka saboda muhimmancin baka akan lokacin"karba ya yi,kafin ya yi tunanin cewa wani abun da wulakacin sa da sai yanzun ta ƙara fahimta,ta yi saurin juyawa ta bar office ɗin,bin bayanta ya yi da kallo zuciyarsa na shiga cikin wani irin yanayi akan sauyawar lokaci guda da ya ga tayi,to amma shi ya zaiyi duk yadda yaso daidaita kansa ya kasa,wanda har da wata iriyar Fargaba dake ƙassara duk wata gaba da lakar jikin shi. Lokacin tashinta na yi ,ta fito dan ko sake haduwa da shi bata yadda sunyi ba,daga ranar yau din ta dauki aniyar kaucewa duk wani abu da zai zubda darajarta ta mace a gurinsa, shima da yake namiji ya yi jan aji da kamewa bare kuma ita,ƙwafa ta yi abin yana dan cizon ranta,ganin Hamma Idris tayi a gaban ta ba tare da ta kira shi ba,yau ma tahowa kike shirin yi bayan kashedin da nayi miki harma da abin da yaso faruwa yau ɗin ko " girgiza kanta ta yi kana cikin kwantar da murya ta ce" kayi hakuri yanzu nake shirin kiranka sai kuma na ganka,ok sai ka wuce muje uban taurin kai" Hamma Idris ya faɗa yana hararar ta, murmushi ta yi wanda ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarta ya fito da jerarrun fararen haƙoranta har da lobawar kumatunta. Dai dai nan wazir ya fito shima cikin kamewar sa fuskar nan a kame kamar bai taba ko da murmushi ba, haɗa ido su kayi da Raihan amma sai tayi saurin kawar da nata idon,duk da cewa taga alamun son ya jefa kwayar idon sa cikin nata kamar yadda yaso ya yi dazun hakan ya gagara saboda kin bashi dama da ta yi,taku yake a nutse dan karasowa inda suke,sai kawai yaga Raihan din har ta shige motar ba tare da ta kara duban inda yake ba,shi ma din ba ita ya nufa ba,dan haka kawai sai ya mikawa Hamma Idris hannu suka gaisa,duk da cewa bai gama tabbatar da ko shi din waye a gurin Raihan ba,amma shi Hamma Idris din yasan wazir sosai ko ba a dalilin Raihan ba,tun da suna karanta jaridun su,da kuma kallon tashoshin su,ta hakan ne yasan shaharar da CHIBADO's din suke a fannin daukaka. Duk da cewa Hamma idi yaso jansa da 'yar hira kafin su wuce to amma hakan bai samu ba,dan baiga fuska daga A Wazir ɗin ba,shi abin ma mamaki ya bashi da yaga yazo takanas dan su gaisa, to amma da ya yi wani tunani sai yaga kamar dan dalilin Rahim ne hakan ta faru, dan haka kawai sai ya share su kayi sallama shima ya shige motar sa da Raihan ke jiransa. Bayan dawowar su affan abubuwa da dama sun faru,kamar tsaida ranar bikin su da akayi kamar yadda su baffa Ali da Abba yahya suka tsara tare da iyayen yaran, Allah yana nasa shirin mutane su na nasu. ___________ Gurfane yake a gaban tsohuwa tamkar zai kwanta mata saboda tsananin biyayya da ƙan da kai, gaba dayan ta hayaki ne ke zagaye da ita,daga ita har shi babu wanda yake magana,sai can tsawon wani lokaci tsohuwa ta yi wata irin ƙara tare da zabura wanda hakan yasa gaba daya kogon da yake saman tsakiyar kogin can wata ƙasa nesa da mu,ya shiga girgiza idan a wajen kogon kake zaka zaci jirgin ruwa ne yake neman lumewa cikin kasan tafkeken ruwan, Tana buɗe baki dan yin magana wani irin hayaki ya shiga fitowa tamkar wadda ke shan shisha,ta ce" shuda kada kayi sake ka samu matsala akan wannan karamin dan shilar,tabbas ina ganin wani duhu tattare da kusantar yaron nan da kake yi,sai dai nayi nayi na ga meye a cikin wannan duhu na gagara gani,amma tabbas ba abin daɗi ba ne a gare mu da kai,amma kuma jini ya tabbatar da cewa dole sai mun bibiyi rayuwar yaron saboda duhun da muke gani tare da shi hakan ya nuna muna da alaka da shi,a kwai boyayya lamarin da jini ya kasa nuna mana shi amma ba wai dan ya gare shi ko kuma bai sani ba ne,dan haka kuje ku fara aikin da zai kusanta mu da shi,,kuma ina tabbatar maka da cewa jini yana kokarin yin fushi saboda kwana biyu jini ya rage zuba"""dan haka sai kaje ku fara aikin da ya kamata hhhhhhhh,,,,,,ta shekar da wata irin dariya da lokaci daya ba zaka iya cewa dariya ba ce,dan tamkar karar injin markade me mugun kara haka take yin ta,lokaci daya kuma komai ya baje tamkar ba ayi ruwan ta a gurin ba,daga ita har shuda da tunda ta fara magana bai ɗago ba kuma bai ce kan zil ba,tun da bata nemi cewar tasa ba kamar yadda ƙa'idar su take................✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page18 ``` Haka kawai yau a ka tashi da wata iriyar hatsaniya wadda aka rasa daga inda ta bullo,yan sara suka ne kawai suke banna da zubda jini wani akashe wani a yi masa mummunan raunin da ba zai iya ta shiba,ba kajin komai sai ihu da karar rufe gidaje,a binda zai baka mamaki da tsoro shine baza ka samu wannan fitinar a manyan unguwannin masu kuɗi da mulki ba,duk abin da za su yi suna yin shi ne a unguwannin talakawa masu rangwamen karfi. Lokacin da ake wannan tashin hankali , Raihan suna can ana shan bikin yayye duk da cewa ba wai ta zage ta shiga mutane ba ne,dan bata da wannan damar amatsayin da take kai na amsa sunan rahim,hasali ma shigewa ɗaki tayi ta rufe ta janyo computer wadda a cikin sati biyu ta karbi shedar zama cikakkiyar kuma kwararriya a fagen sarrafa computer,ta online ta yi wannan cos din ba kuma tare da sanin kowa ba,dan hatta da auntyyn ta bata sanar da ita ba, itama bata san dalilin yin hakan ba,amma tasan ko meye ma nan gaba zai amfane ta. Tana cikin kurɗawa da shige shige dan kara fahimtar ilimin computer,wayarta dake kusa da ita ta fara kawo haske alamun kira,dubawa ta yi taga abu Huraira ne wato sabon ma aikacin da suka samu ya maye gurbin halima,bayan yasha interview masu zafi wanda Allah ya taimake shi ya tsallake su,ya samu damar zama a karkashin Rahim,tana ɗagawa ba tare da ya bari ta ce"komai ba ya ce"Rahim kasan abin da ke faruwa kuwa?ture computer da ke gabanta tayi cikin ɗan faduwar gaba ta ce" ban sani ba abu Huraira kasan dai yau din aka daura auren duka yayuna ko? Na sani Rahim amma fa abindake faruwa ya shafe mu, nan ya shiga bata labarin tashin hankalin da ake ta yi tun safiyar yau din ta Lahadi,cikin faduwar gaba da rawar jiki Raihan ta ce" abu Huraira kana ina ya zama dole mu ziyarci gurin nan, kafin wasu su riga mu yada karya da gaskiya barin ma gidan jaridar nasss"to amma Rahim gurin fa a rikice yake anya ba za mu ɗan bada ƙafa ba kar fa muje garin daukar rahoto ta rutsa da mu"tsaki Raihan ta yi kafin cikin yar fusata ta ce"haba Abu Huraira sai kace wanda aka canjaka dama mu ba mun ɗauki aikin jarida da yaki da duk abin da zai cutar da al'umma ba ne? Sorry Rahim mu haɗu a ja'e street bamu da lokaci" ok kawai ta faɗa ta tashi cikin hanzari ta yi shirin ta na kullum cikin bakar cot wadda ta fito da zahiran haskenta me sheki irin na yan itopia,kalar Raihan wata irin kala ce me matukar kyau ba fara ce irintas din nan ba sai dai kuma ta wuce ace mata coculate shi yasa ta bada wata kala me kyau da tsayawa mutum a rai,naɗe dogon gashinta ta yi ta cusa sa cikin irin hulunan da take sawar dan rufe gashin yadda ya kamata,tsaf dai ta kammala shirin ta duk cikin sauri wanda yake tafe da zallar nutsuwa da aji wanda tuni suka fara kamata a matsayinta Na mace me kamala,karamar wayar aiki ta dauka ,ta fice da sauri. Zagawa ta yi ta ɗauki mashin ɗin da tun bayan fara zuwan Hamma Idris office,tasa abbie ya sai mata,tun da ita sam bata son tukui gashi tun jimawa ta hana kanta bin driver,da farko suna tafiya da Hamma idi kamar yadda ya bukata ,to amma daga baya sai ta zame saboda matsalar datake jawowa tsakanin sa da mama,akan tafiya da itan. Ina kuma zaka je Rahim?? Muryar Hamma idi ta katsewa Raihan hanzarin da take na tada hadadden mashin din nata,sai dai kuma bata tsaya da abin da take kokarin yin ba ta bashi amsa da cewa sorry Hamma wani guri zanje yanzu zan dawo"haba Rahim ana wannan bikin auren na yayin ka amma zaka fita bayan ka kulle kanka kaki fitowa cikin mu"sorry Hamma idi idan na dawo ma yi magana" daga haka taja mashin din da gudu ta fita daga gidan ta baya wajen gate din gidan su Hamman nata. Tana fita wayar shi ta yi kara,ɗagawa ya yi ,sai dai kafin yayi sallama ,abokin shi sagir ya fara sanar da shi halin da ake ciki dan haka a dakata da dinner din da a za Afita anjima dan garin babu lafiya,wata irin zabura Hamma idi ya yi yana mai bin mashin din Rahim da yasan cewa a yadda ya fita yanzu ko ƙyallinshi ba zai gani ba,dafe kanshi ya yi cike da tashin hankali,dan kuwa ya tabbatar da cewa kaninnashi aikin da ya tafi yi ke nan,da karfi ya ce" wlh ba zai yiwu ba,Rahim dole sai ka dawo gida kuma sai ka hakura da aikin nan,domin masifun shi sunyi yawa"sai ka hana shi uban shi"yaji an fada daga bayan shi,juyowa ta yi cike da mamakin abin da ya kawo maman gurin,mama me kike anan ke da kike cikin jama'ah Hamma Affan ne ya ce"Ni ne na kira ta,saboda tun da naki abin da ke faruwa nasan cewa zaka iya bin bayan sa shi yasa na kira wadda ta isa da kai"wani kallon banza ya bi yayan nasa da shi,mama ta ce"eh ai Ni yayi min daidai kake masa wani kallo kamar zaka bigeshi,to wlh ina mai tabbatar maka idan kasa kafa ka fita daga gidan nan ban yafe maka ba" Affan ya yi dariya yana cewa Ni da ace da 'yan sara sukan za su yi masa wani abu da sun rage mana aiki wlh,maman ta wuce tana mai ci gaba da yi masa mummunan gargadi akan Rahim din. Sakaro ya yi kamar wani sakarai zuciyar shi na kuna akan halin 'yan uwanshi da maman shi,babu yadda ya iya dole ya hakura da bin bayan Rahim ya shiga yi masa addu'a'in fatan dawowa lafiya. A can bangaren inna maimuna ma taji labarin abinda ke faruwa,zuwa ta yi tana neman Rahim ɗin sai sahura me aikinsu take ce mata ai Rahim din yana daki bacci yake yace kuma dan Allah kar wanda ya tashe shi,da wannan inna maimuna ta samu nutsuwa har ta samu karfin komawa cikin jama ai su ita da aunty amarya ba tare da ta sanar da auntyn ko mai ba. _________________ Sassanyan ƙamshinsa kawai innawuro ta zuƙo ta yi saurin juyawa,shi dinne kuwa yake saukowa daga up stairs cikin wannan kamewar ta shi, ya yi kyau sosai cikin ash din suet da tayi matukar karbarshi,kamar wani Balarabe sumar nan sai ƙyalli take zabgawa,rabi dake kusa da innawuro zuba mishi ido tayi kamar zata cinye shi,zuciyarta na wani ƙara zurfi da maitar sonshi tare kishinsa me tsanani wanda take jinsa har wuyanta,sai ina kuma innawuro ta faɗa tana kallon yadda yake ta faman dauke kai da ƙara kame fuska,wanda yanzu kuma hakan da yake mata duk ya dameta,zan dan fita, aikine ya taso"amma kasan dai abin da ke faruwa a garin dan me zaka fita? Naga dai kai oga kwatakwata ne ba kai ka ke aikin nan ba,idan ma rahoto ne kana zaune za a dauka,to meye ne na sai ka fitan?dole ne dan haka Na da muhimmanci "daga haka ya wuce ta ba tare da ya dubi inda rabi take tana mai kwarkwasa da fadin Allah ya kiyaye ba,nan dai ya bar innawuro da mita kamar zata ari baki. Yana fita suka yi kicibus da Abban rabi,dakatar da shi yayi bayan ya gaida shi,ya ce" Ahmad ina zaka? Shuru ya yi yana tattara dan abin da zai faɗa,daidai nan Abbu shima ya ƙaraso dan duk labaran abin da ya faru ya baza ko ina tun da tuni yan jarida masu aikin Saida rai suka bazama dauko rahoto,yanzu ko wace gidan Radio da ta television da yanar gizo jaridu da sauran social network abin da zaka ji ke nan kuma ka gani yayin da yan jarida suke ƁOYE suna ɗaukar komai,Abbu ya ce kaima ai kasan inda za shi" to ai naga an riga an haska a gidan tv da radiyo na chibaɗo me kuma zaka je kayi?Abba fitar nawa ya na da muhimmanci" ok gaskiya yaya dole ne Ahmad ya yi hakuri a wannan karon ya karbi securityn nan duk da ya nuna baya so,to amma kasancewar sa tare da su yana da matukar muhimmanci,aikin ku aiki ne me hadari dan haka Ni zan kawo security ko guda biyar ne wadanda zasu na kula da kai"zaiyi magana Abban ya yi saurin katse shi da cewa, bana bukatar cewar ka umarni ne wannan "daga haka ya yi wucewar sa,Abbu ya yi murmushi tare da cewa SOYAYYA ce hakan dan haka sai kayi hakuri idan ya so ni zan lallaba shi ya bar batun biyar din ya kawo ko biyu ne ,tun da gidan ma muna da wadatar su", Jin jina kai kawai ya yi ya wuce abbun yana sa mishi albarka. Bai taba tunanin da Raihan a kayi aikin nan ba,sai bayan shigar sa office,da Khalid ya kawo masa bayanan da suka watsa na gidan tv da rediyo,tun da duk kusan ma aikatan daya ne,ƙalilan ne wadan da suke aiki a tv din chibaɗo ba sa aiki a rediyon ko jaridar su ta chibaɗo daily trues ,ma'aikata suka nutsu suka tara masu gaskiya da rikon amana,duk da dai sun san cewa ba ko ina ne ya zama dole sai ka samu yadda kake so ba,dan basu da tabbacin cewa dukan ma'aikatan su masu gaskiya ne,to amma Ahmad wazir da maihaifinsa suna da matukar kula da ma'aikatansu,dan haka ko da kana aikata rashin gaskiya cikin dan lokaci suke gano ka,shi yasa su ka haɗe ma aikatan duk suka zama ɗaya saboda gudun kawo Baragurbi. Lokacin da ya tabbatar Raihan ta ziyarci gurin nan, ba karamin bacin rai ya shiga ba,duk da bashi da dalilin hana ta tunda aikin ta ne,shi kan shi bai san me yasa yake jin bacin rai me tsanani ba a duk lokacin da Raihan ta fita irin wannan aikin da yasan cewa za agauraya da maza, abu na biyu kuma shine yadda al'amarin na yau ya kasance dole a kawai bukatar su yi taka tsantsan da rayukansu,amma Raihan ko tsoro bataji ba ta fita,wato dai mu'amala da cudanya da maza yasa ta koyi dakiya da rashin tsoro,sam baya ganin fargaba ko sarewa a cikin al'amarin Raihan,to amma idan ita bata jin tsoro ai su da ta zame musu tsokar jiki,suna jin tsoran faruwar wani abu da ita,abu na uku shine tsallake bikin gidan su da ta yi ta fita aikin lada domin Raihan ba dan wani abu take aiki ba face taimako da neman kusanci ga Ubangiji,numfashi ya dan ja kana ya fesar yana neman hanyar ganinta,duk da yasan cewa yanzu da baya ba daya ba ne,wata irin rayuwa suke yi yanzu kamar ta makiyan da suka shahara wajen kin juna,to wai duk me ya kawo hakan? Ya tambayi kanshi wanda shi kansa bai san amsar ba,kuma bai san adadin sau nawa yakewa kansa wannan tambaya a rana ba. Wayar office dinta ya nema kai tsaye,sai dai kuma yaji daga bakin abu Huraira cewar ai tana gama gabatar da rahotanni ta wuce gida saboda yanayin garin da kuma bata sanar da kowa da cewar ta fito ba,Nima wasu rubutu na zo dauka office din,ok"abin da wazir ya iya cewa da Abu Huraira dake ta ƙwaro bayanai ba,abinka da dan jarida. _________________ Oga komai ya kammala munyi duk yadda ka sa mu,yauwa dage,aikinku na kyau naji dadi da ba ku bari yan sanda sun kama ku ba,duk da cewa suma din sai da muka bi ta kansu sannan muka gabatar da al'amarin ,kuma hakan yayi daidai tunda sun cika alkawari da ba suzo gun ba har sai da mai afkuwa ta afku"mutumin da yake sanye da wata doguwar bakar riga me hula wadda ta rufe mishi fuskar shi gaba daya ,ya fada yana mai ci gaba da yin dariyar sa cikin shakewar murya..... Dr Senate ya yi wata irin zabura zufa na karyo mishi ya ce"garin yaya kuka bari aka kashe yaran mu,me yasa duk sanda irin haka zata faru kuke yin sakaci da rayuwar ku ne?shugaban jam'iya ya ce"to me ye na tashin hankalin tunda dai su sun tsira ba shike nan ba,karfa ka manta daukar su muke yi suna mana aiki kuma sun riga sun san cewa aikin na Saida raine amma suka karba suke yi,to kuma mu meye na mu ,aikin kawai idan an kashe wasu mu samo wasu shi ke nan kawai, Alh sale ya yi wata shegiyar dariya yana kallon su kafin ya ce" gaskiya shugaba ba Allah a ranka,amma fa maganar ka tana kan hanya dan haka ku kuje sai mun nemi ku"haka zugar yan daban suka.wuce su ka fita bayan suna ji da ganin cin mutuncin da akayi musu da maganganun da idan suna da hankali sun ishe su komawa ga Allah (wanda yayi nisa baya jin kira).... Lokacin da RAIHAN ta dawo gida tuni ,aunty amarya da innar agases(innar aunty amarya) da inna maimuna sun fahimci bata nan,innar agases din ce ta dinga bawa aunty amarya da inna maimuna baki ita da matar yaya giɗe ,wato yayan ta wanda tuni ya bar gadin da yake yi a Niger abbie ya sai musu gida babba kuma wadatacce, a garin yamai suka koma,bayan yayi yayi da su akan su dawo Yola sunki,innar agases ta ce",to ke kam banda abinki ramle,Rahim fa namiji ne kuma matashi to me yasa har kullum kike masa kallon yaro karami ko kuma mace ,tun da su ne kawai idan ba a gansu na tsawon awa ɗaya zuwa biyu ba za A damu, wannan kalma da ta ji daga bakin innar ta shi yasa ta daure ta kawar da tashin hankalin ta,itama inna maimuna sai ya zamana hakurin ake bata dan kowa yasan cewa itama bata da juriya akan al'amarin Rahim,baki suka ci gaba da basu har zuwa lokacin da Raihan din ta shigo falon cikin nutsuwa da sallama a bakin ta,wata boyayyar ajiyar zuciya aunty amarya ta yi tana kallon Raihan din da yar hararar da bata kai zuci ba,ta ce" Rahim wane irin abu ne haka ? Ya za ai ka fita a na wannan abun baka sanar da mu ba? Zuwa Raihan din ta yi ta rungume ta tana cewa sorry mamina,bazan kuma ba"innar agases ta ce" ja iri ka ce haka mana tun da ka daga mana hankali da wata zuciyar ka ta marasa tsoro"karasawa Raihan ta yi ta rungume inna maimuna tana cewa sorry sweetie na tayar muku da hankali bayan ƙara ba,shafa kansa inna mainuna ta yi tana cewa Rahim ka tayar mana da hankali dan Allah kar ka kuma yin irin wannan gangancin",jinjina kai ta yi daidai nan zubaida babbar yar giɗe take bawa innar agadex amsa da cewa " to ke inna idan namiji bai zama jan gwarzo ba me kike so ya zama? tsam Raihan ta mike ta nufi hanyar dakin ta,dan duk za ayi irin wannan maganar da ta shafa banbancin jinsi bata yadda ta zauna a gurin,da wani irin boyayyan kallo me cike da damuwa da tausayawa aunty tabi Raihan din da shi.. Dinner dai an fasa ta ,kawo amaren ma dan an tabbatar da tsaron jami ai ne kuma gari ya lafa tamkar babu abin da ya faru,dab da magriba a ka shiga da amare dakunan su bayan kowacce an mika ta gurin surikanta,da yawan baki sai gobe zasu koma yan Kano da yan niyame,harma da wasu garuruwan. Aunty amarya ce tsaye a gaban tafkekiyar wardrobe dinta tana dauko kayan bacci,kasancewar yau abbie ba a wajen ta yake ba,dan haka yana can bangaren sa,tana gama saka kayan ta feshe jikin ta da turare,so take ta je dakin RAIHAN su kwana tare dan kwana biyu ta yi kewar zama da ita,wayarta ta dauka zata fita sai kuma taga alamun shigowar sako,murmushi ta yi dan a zaton ta sakon abbie ne wanda ya saba turo mata duk dare kamar haka In dai ba girkin ta ba ne,ko da kuwa ya zo sunyi sallama,tunanin hakan yasa ta samu gefan gado ta zauna,dan bai kamata taje dakin RAIHAN ta karanta ba, Duk abin da kike boyewa na sani duk wani sirrin ki a tafin hannuna yake, ina muku fatan alkhairi ke da yarinyar ki RAIHAN..................✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page19 ``` Wani irin bugu kirjin ta ya yi sai wani mahaukacin jiri da ya kamata,wanda ba dan a zaune take ba, tabbas zata iya yin mummunar faduwa,gumine ya shiga yanko mata ta ko wace kafa dake jikinta,tashin hankali babu kalar wanda bata shiga ba ,sakon kuwa ta karanta shi har sau ba a dadi karshe ya zauna a harshen ta da ƙwaƙwalwar ta daram,waye wannan ko wacece wannan? Ya akayi ya san sirrin da take ta boyonsa tsayin shekaru? Shin ɗaga hankalinta zata yi ko Allah zata godewa da ya fara haska mata hanyar da take ta nema tsawan shekaru goma sha bakwai? A iya saninta bayan ita wazir da Raihan sai uwa uba Dr Sabo babu wanda yasan wannan sirrin,shi Dr Sabo ma baya ƙasar yau wajen wata biyar zuwa shida ke nan. To ko Raihan din ce ta fada wa wani bayan wazir? Kai Raihan ba zata yi haka ba,tabbas a kwai wani abu da yake a ƁOYE wanda bata sani ba,cikin ƙwarin gwiwar da ta fara samu dalilin tunanin da ta yi,ta janyo wayarta , ta yiwa Dr Sabo powordin saƙon tare da yi mishi bayanin da zai fahimta,dan ji ta yi ba zata iya yin maganar a cikin gidan nan ba ma, gani take kamar mugun yana tare da su kuma yana bibiyar su,shi yasa taki yi masa waya kai tsaye,ta danyi nisa a tunanin waye? Wacece ?ya a kayi? Sakon Dr Sabo ya shigo wanda shine ya kara sama mata yar nutsuwa,a sakon nashi ya nuna mata ne ta kwantar da hankalin ta wannan kamar wata hanya ce ta bude a gare su dan sanin abin da suka dade suna son sani din, sannan RAIHAN macece mai kamar maza wadda Allah ya bata baiwa mai tarin yawa,ita ma ta kawo karfin da ta ko ina ba zata bari a cuce ta ba sai dai idan Allah ya tsara hakan cikin littafin kaddarar ta da kuma raunin da aka san ko wace mace tana dashi, wannan abin da mu kayi na ƁOYE raihan mun sani ta wani bangaren mun yi daidai ta wani bangaren kuma munyi kuskure,amma abin da nake gani Allah ya riga ya tsara hakanne dan ya rubuto raihan sai tana matsayin namiji ne zata koyi abubuwa masu tarin yawa,kamar tarin ilmin ta na boko da na addini,da kuma aikin ta na taimakon al'umma, wan da nake ji a jiki na cewa al umma masu tarin yawa zasu samu taimako da tsira da ga sanadin ta na kadan daga cikin baiwar ilmi da Allah ya bata,zasu amfana da ita ta fannoni da dama wanda da ace tana a matsayin mace baza a bata damar yin hakan ba,ba kuma za a bata kwarin gwiwa akan kudirin ta ba,dan haka ki kwantar da hankalin ki,ki nutsu ki sa ido da zuciya gurin fuskantar al'amarin da yake da akwai kuma yake tunkaro mu domin kuwa yanzu na tabbata cewa kakwai babban yaƙi a gabanmu,Nima na kusa karasa cos din in sha Allah zan dawo very soon. Wadan nan kalamai ba karamin tasiri su kayi a gangar jiki da zuciyar Aunty amarya ba,dan haka kawai sai ta goge duka sakon da wanda aka turo mata da wanda ta yiwa Dr da reply din da ya dawo mata da shi. Kai tsaye ta sawa zuciyarta cewa yanzu haka ma bugar ciki ne makiyansu zasu mata saboda sun rasa yadda zasu yi,sai dai kuma basu san cewa da wannan dama zata yi amfani dan tona asirin su ba,da wannan tunanin ta bude dakin Raihan da key din hannun ta ,ta shiga,samun Raihan din ta yi tuni har ta yi bacci saboda yar gajiyar da take tare da ita,kwanciya ta yi tare da kara tofa musu addu'a, ta rufe idanun ta da san kawar da komai ta fuskanci abin da ya kamata ta fuskanta. Washe gari kowa ya watse aka bar gidan, amare na bangaren su da mazajen su,dan haka gidan ya koma ya yi shiru ,ga jiddo da ma kwana biyu bata gidan taje hutu kamar yadda ta saba zuwarma mamanta,to ko da aka gama bikin binsu ta kuma yi daniyar kara kwana biyu zuwa uku sannan ta dawo. Kamar yadda Abban rabi ya ce"hakan ya yi ,dan kuwa a cikin kwana biyu ya samo kosassun security guda uku,daya shi zai dinga tuka wazir duk inda zashi,ko da wadan can ba sa tare shi dai ya zama aikin sa ko da yaushe yana tare da Wazir,to haka dai wazir ya karba ba dan yaso ba. Sosai a kwana kin nan ake wata Irin rigima ta rashin imani,tuni gari ya kuma rikicewa,hankalin talakawa da abin ya shafa ya kuma tashi,cikin kankanin lokaci,gwamnatin da ake alfahari da ita me taimako da san talakawa,ta juye ta koma wata iri talakawa sai zaginta suke,meye amfanin baɗi babu rai abinda suke fada ke nan,kowa dai da abin da yake fada. Hankalin Gwamna ya matukar tashi,dan ya tabbata yan adawa ne suke wadan nan abubuwan duk dan sun san za a iya ra taya laifin akan gwamnatinsa,duk da cewa yana ƙoƙari gurin tabbatar da tsaro ,amma abin kamar ana kara iza wutar sa. Abu na biyu kullum talakawa su kasa kunne suna jira suga an kamo yan ta'addan ,amma kullum shuru kake ji sai ma wasu rigingimun da suke kuma ta shi,daga a tsinci gawar yaro an cire ido,sai atsinci gawar tsohuwa babu jini ko digo a jikinta,asibitocin ma idan anje babu ingantattun magunguna,ala cuta dai aka magani ta ko ina ba dad'i, Yan jaridu ne kullum suke kokarin yaɗa abubuwan da suke faruwa saboda jawo hankalin al'umma da jami ai ,dan duk a yi maganin matsalar amma ko an samu jajirtaccen jami'i me gaskiya da ya fara bincike ko ya ce"zaiyi sai a neme shi a rasa ko kuma a tsinci gawarsa. _________________ A hankali ya fito daga motar bayan dauko shi daga filin jirgi,sabon mataimakin Kwamishinan yan sanda HAIDAR YAHYA RINGIM,,, Nutsatstsan mutum me aiki da gaskiya matashi dan kimanin shekaru talatin da shida,me mata daya da yara uku,kwazon shi da himmar shi harma da gaskiyar shi su suka.kaishi kan wannan babban matsayi a cikin kananun shekarun da yake da su,baizo da kowa na shi ba,amma yace idan yaga yanayin aikin zai koma ya taho da iyalin shi,kai tsaye gidan da aka bashi driver ya kaishi domin ya samu ya huta,kafin gobe ya shiga office. Yallabai kana ganin babu abin da ya kamata muyi akan barnar da ake yi din?kamar me kake so kayi? Kwamishinan yan sanda ya gyara wayar dake kunnen sa ya cigaba da cewa, ina so ka bamu dama mu samu wasu daga cikin mutanen ku mu kama,saboda idanun talakawa yana kanmu harma da sauran al'ummar jihar nan,kasan duk abin da yan jarida suka sani bamu da halin boye shi,dan ko mu mun boye su ba za su yi shiru akan hakan ba,ko da sauran jaridun sun bi tsarin mu sun bar maganar,kasan wannan CHIBADO's din ba zasu bari ba,suna da matukar ƙarfi wanda yasa dole duk rahotonnin,da suka fara bullowa daga gare su musan abin yi akai,su ka dai suke rubuta bayanan gaskiya wanda kuma suke janyo hankalin al'umma da manyan kasa kanmu,shi yasa nake so mu yi wani abu akan hakan", Daga can bangaren cikin wata murya wadda ke nuni da isar da me Muryar ke da ita ,aka ce za ka iya yin hakan amma ba mutanen mu zaku kama ba,kuyi abin da ya dace kawai,amma dai karka sake matsalar ta shafe mu",ok sir za a kiyaye" yana sauke wayar aka bude kofar office din aka shigo ,da sauri HAIDAR ya yi solute din Kwamishina,daga nan su kayi gaisuwa ta mutunci da nuna sanin juna,Kwamishina ya ce" ina maka Barka da zuwa tare da taya ka murnar samun wannan babban matsayi, Allah ya bamu ikon tsayawa akan gaskiya,cikin jin dadi HAIDAR ya amsa,daga nan ya yi masa sallama ya wuce office din sa. Ko da RAIHAN ta je office ba ta nemi zuwa office din oga ba,duk da cewa akwai aikin da zata gabatar masa,ba ita ta nufi office din ba har sai da ta tashi daga aiki,sallama su kayi da abu Huraira ya wuce ita kuma ta nufi office ɗin oga. Gefe taja ta tsaya tana jiran sakataria ta yi mata iso,kamar yadda ake yiwa kowa,tun bayan da ta canja din ta shiga wannan tsarin wanda ya yi matukar bawa sakateria mamaki kai harma da sauran staff din dake saka idanun su akan lamarin da bai shafe su ba,shi kan sa oga kwatakwata wani iri ya ji lokacin da ta fara yin hakan,har yanzu kuma ya kasa sabawa ,duk lokacin da ta yi hakan sai ya ji wani irin abu can kasan zuciyarsa,yanzun ma ɗan jim ya yi kafin ya jinjina kai. Dubanta sactaria ta yi tare da cewa kana iya shiga,ok thanks" Raihan ta faɗa a nutse babu alamun wata damuwa akan fuskarta. A nutse ta yi sallama ta shiga,tsayawa ta yi bayan ta gaida shi,sai da ya nuna mata wajen zama sannan ta zauna ,tana mai kame fuskarta kamar yadda shima yake yi a koda yaushe,cikin nutsuwa ta gabatar masa da abinda ya kawota,tana kokarin tashi ya kira sunanta a hankali can cikin ƙasan makoshinsa,yana mai binta da kallon ƙasan ido ta yadda ba zaka taba fahimta ba,sai dai ita da take jin kaifi da tasirin idanun nasa a cikin gangar jiki da zuciya,ba ta amsa ba sai dai ta hakura daga kokarin tashin da take yi,kanta yana kasa,kafin ya ce"wani abu anyi knocked dor,izinin shigowa ya bada ba tare da ya.dainawa Raihan kallon ƙasa idon da yake mata ba,yauwa sir kana da bako a waje,na fada mishi kana tattaunawa amma ya nemi da a barshi ya shiga da alama dai wani babban jami'in ne",ok ce ya shigo", ya bata amsa yana mai tsaida idanun sa kan Raihan da ta tsuke fuska kamar zata yi kuka. Sallama ya yi cikin nutsuwarsa da kamala ya shigo,miƙewa wazirr ya yi su kayi hannu cikin mutunta wa,nuna mishi wajen zama ya yi kujerar da ke fuskantar Raihan, tashi RAIHAN ta yi tana mika gaisuwa a gare shi,kokarin fita ta fara yi ya kuma dakatar da ita da cewa ban sallame ka ba"juyowa ta yi tana duban shi cike da jin haushin tsaida tan da yake yi,sai dai kuma kamar ma bashi ne ya yi maganar ba,komawa ta yi ta zauna dan kar wannan bakon ya yi musu wata fassarar amma da wlh tafiyar ta za ta yi,mitar da take yi cike da kunkuni kenan,yana jin ta yana kallon ta dan duk wani motsinta a cikin jikin shi yake jin shi. Gyaran murya HAIDAR YAHYA RINGIM ya yi tare da fara gabatar da kansa a wajen su,ya ɗora da cewa ina so za muyi magana me muhimmanci da kai"ya fada yana ɗan duban Raihan da tayi kamar bata office ɗin,babu matsala zaka iya fadar ko me ye a nan din bani da damuwa da wannan ɗin,wazir ya fada saboda ya fahimci zaman Raihan ne ya saka shi fadin hakan. Kamar yadda na sanar da kai sunana da kuma aiki na,zan kara maka wani dan takaitaccen bayani dan kafahimci manufata me kyau,a yadda nake ji a bakunan mutane cewa gaskiya ta ce ta kawo Ni wannan matsayi,to na yadda da hakan,sai dai kuma naci na da son tabbatar da gaskiya yasa na dage sai an kawo Ni nan din,dan gaskiya ba Yola a ka so kaini ba,a kwai wani sako da na samu ta hanyar kutsowa da wani kwararren masanin computer ya yi kuma ina tunanin dan jarida ne,cikin shafina,in da na tarar da muhimmin sako wanda shine ya ingizoni zuwa nan din domin kawo taimako ga al ummar wannan jahar,a iya binciken da nayi na samu tabbaci akan duk abin da aka sanar da Ni ta hanyar wannan sako. To amma da zuwana tun jiya na fara binciken gidan jaridar da ya kamata na fara ziyarta dan kuma samun tabbaci da gaskiyar abin da yake faruwa,kuma alhamdulillah naji dadi saboda duk wanda zan tambaya cewa zaiyi indai gaskiyar batu nake so na tuntubi jaridar chibaɗo daily trues,ko kuma na bibiyi labaran su na chibaɗo fm, da duk sauran tashoshin ku,domin ku din masu nagartane wadanda suka tsaya akan Gaskiya. Da kamar Raihan ba za ta saurare shi ba,to amma jin bayanansa da kuma fara fuskantar inda suka dosa yasa ta fara bada hankalinta a sauraron bayanan nasa da yake yin su dalla dalla kuma daki daki cike da ilmi. Ina fata za ku bani dama da kuma lokacin ku domin nima din irin ku ne da nake son tabbatar da gaskiya da san kwanciyar hankalin yan uwana musulmi",shuru ya yi da alamun yana son a tanka mishi, Raihan ce ta yi magana ganin wazir ya kalleta, cikin nutsuwarta da kaifin tunani,ta ce" yallabai yanzu me kake so daga gare mu ko kuma wane taimako kake so mu yi wa wannan himma taka??? Jinjina kai ya yi cike da jin dadin tambayar da Raihan ta yi masa,ya ce" ku yan jarida ne wadan da suke da matukar muhimmanci a cikin rayuwar al'umma har da aikin da hukuma,sau da dama idan wani abu ya faru da ake bukatar dauki kune farkon mutanen da za a fara gani a gurin wanda ko da yan sanda ba su san da batun ba,zasu sani ta hanyar ku,haka.kuma duk batun da ya bullo ta bangaren yan jarida masu gaskiya hukuma tana bashi muhimmanci ko dan kar a yi musu mummunan zato akan aikin su,kuma ta hanyar ku ne kaɗai al umma suke kai kukansu akan wani tauyewa wanda ko da basu da karfin zuciyar tun karar hukuma ku din zaku zame musu jagora,dan wani lokacin da mutum ya tunkari hukuma kai tsaye Gara ya tunkareku , domin tunanin shi yana bashi ta hanyar ku ne kawai zai samu adalci,kamar yadda muke da Baragurmi a cikin hukuma haka kuke da Baragurbi a cikin yan jarida dan kuwa ƙalilan ne masu gaskiya,kamar yadda take akan ko wane aiki a cikin ko wace al'umma,dan haka ina so mu hada karfi da karfe domin bincike akan abin da yake a lullube game da abin da ke faruwa a wannan jihar,domin hakan shine zai kawo kwanciyar hankali a cikin al'umma", Duk da cewa kalaman Haidar sunyi matukar tasiri a gare su,domin kuwa dama irin su suka jima suna nema,duk da cewa ansha kawo irin sa din amma da an fara bincike ko yana shirin farawa,sai dai ka wayi gari babu mutum an nemeshi an rasa ko kuma a tsinci gawarsa a yashe anyi masa kisan wulakaci. Fuskantarsa Raihan ta kuma yi sosai tare da cewa shin me ka taka me nene kwarin gwiwarka akan hakan? Idan baka sani ba bari na gaya maka,mutane irin ku basa kaiwa labari a wannan jihar??? Murmushi Haidar ya yi yana fuskantar Raihan da yake kallo a matsayin namiji a idanun shi,kuma me matukar basira wanda ya yi matukar dacewa da aikin shi,ya ce" meye sunan ka saurayi?kwarin gwiwar ka yana burge ni domin wannan tambayoyin naka cike suke da ilmi wanda yake nuna tsayuwa da jajircewa akan gaskiya" , RAHIM MUHAMMAD NURR, Raihan ta bashi amsa tana kawar da kanta da satar kallon wazir da ya yi tamkar baya wajen,hasali ma kwanciya yayi jikin kujerar idanun shi a lumshe kamar me bacci,shi Haidar bai damu da wannan ba dan tun kafin ya karaso ya samu bayanin halin sa,duk da cewa ba a ce masa yana da girman kai ba,a halayyar da aka zaiyano masa kaf babu na Allah wadai, miskilancin dai shine,kuma shi bai ga abin damuwa da hakan ba,shi yasa da yaga haka kacokan ya maida hankalin sa kan Raihan ɗin, Kune kwarin gwiwa ta,da kuma me wannan sako da shi ne asalin komai,a yanzu haka wannan boyayyan dan jarida me suna tree full Y trues ,ya fara suna a can wasu jahohi kamar Kano Kaduna katsina da sauran su,nayi mamaki da baku san labarin sa ba,duk da cewa mu din bamu rufa wata daya da sanin shi ba,ko nace bai rufe wata da bullowar shi ba,kuma.ina kyautata zaton shafinsa zai ci gaba da zagayawa har ya zago cikin Yola da kewayanta,ya boye komai nasa duk irin shaharar ka a sanin computer ba zaka taba gano ainahin sunan sa da duk wasu bayanan sa ba.kalaman sa sune kwarin gwiwata da kuma gaskiyar da nake tafe da ita baban abin kuma dogaro da Allah domin idan har ya kawo karshen abinta sanadin mu to kuwa babu wanda zai mutu a cikin mu har sai mun ida kyakkyawar manufar mu". Sai a lokacin wazir ya bude lumsassun idanunsa da suka dan sauya kala,ya dubi Haidar kana cikin kamammiyar Muryarshi me cike da nutsuwa ya ce" Haidar baka da matsala in sha Allah muna tare da kai kuma duk abin da muka samu kaine farkon wanda zai ji kiranmu ko kuma ganin sakonmu"',na gode Chibado tun kafin nazo nasan bazaku taba sarayar da kwarin gwiwata ba",sai dai abu daya RAIHAN ta faɗa ba tare da ta dubi dayan su ba,ba ta saurari cewar dayan su ba, wanda dama wazir ba cewar zaiyi ba, ta ce" wannan ya zama sirri a tsakaninmu,kar karka sake ka fito da maitar ka da manufarka ta san gano gaskiya,za muyi komai a cikin sirri,kwantar da kai duk umarnin da na sama da kai su ka baka kabi,dan ina tabbatar maka da cewa ta wannan bangaren za mu yi babbar nasara,saboda kawo yanzu na gama tabbatar cewa da saninsu komai ke faruwa ma ana dai da hadin bakin su".gaba daya shuru su kayi hatta da wazir a yau sai da ya yi matukar mamaki da jinjinawa basirar Raihan,yar baiwa ya fada can kasan makoshin sa,shi kuwa Haidar kasa boye mamakinsa da fariincikinsa ya yi,sai da suka bayyana kan fuskarsa ta asalin bakano, kana ya kara da cewa,Rahim kai din na musamman ne gashi tun ba aje ko ina ba,ka fara aikin da muke son cimmawa, wannan tunanin yayi kyau kuma abin da ka fada gaskiya ne ,a gain dai zanyi yadda ka ce, wannan shine karamin su babban su,sosai zaka iya aikin jami in tsaro",miƙewa wazirr ya yi saboda gundurar sa da maganganun da Haidar yake wa Raihan ɗin su kayi,ranshi ya ji yana ɓaci,an ya ma kuwa zai yadda Raihan ta shiga wannan aikin ? Tun da gashi wannan Haidar din ya fara rawar kafa akanta"wata zuciyar ta ce masa,haba wazir relax mana,kar fa ka manta kai kadai ne kake kallon Raihan a mace... Haidar ya katse shi ta hanyar mika masa hannu ya ce" shike nan sai na ji ku na kuma gode da karamci,ga nomber ta nan ina fata zan samu ta daya daga cikin ku? Raihan ta san wazir ba bada tasa zai yi ba hakan yasa ta mika masa katin ta,tana cewa gashi nan za ka.iya neman daya daga cikin nombobin nan".....wani kallon kasa kasa wazir ya yi mata ita da katin da ta mikawa Haidar ɗin,ya na kasa hade yawun da ya daskare a bakin sa,godiya Haidar ya yi kana ya yi musu sallama ya fice zuciyarsa cike da fariincikin haduwa da Rahim. Tashi Ta yi zata fice,amma sai ji ta yi ya janyo hannun ta da dan karfi,wanda hakan yasa su kayi kusanci da juna har tana iya jiyo sautin bugun zuciyarsa....................✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page20 ``` "Zuba mata lumsassun idanunsa da suke karya lakar jikinta ya yi,yana son su haɗa ido amma sai ta rufe idanun ,hakan kuma sai ya bashi damar tsurawa kyakkyawar fuskarta ido,zuciyar shi na wani irin sanyi wanda yake shiga har cikin bargon shi,hannuwanta da ya haɗa ya rike take ta kokarin kwacewa saboda yadda jikin ta ya fara rawa zuciyarta na ƙoƙarin karyewa ,saboda a kallon da yake mata take fuskanta da kuma jin yadda abin yake damun shi,jan hannun ya yi hakan yasa suka kuma yin kusanci sosai, ɗauke numfashi ta yi tana kokawa da abin da ke tokare kirjinta da numfashinta,can kasan makoshinsa ta ji dakakkiyar Muryarsa wadda ke cike da wani irin amo me tsayawa a kwanya,ya ce"meye laifi na Ni? Da sauri ta bude idanun ta ta kalli fuskarshi wadda ke a kame kamar ba shi ya yi maganar cikin mutuwar jiki da Jigatuwar ruhi ba,kasa magana ta yi saboda fuskantar kamar ma ya raina mata wayo,wato ma ya manta shine ya fara kuma shi ya koya mata,amma yake tambayar meye laifin sa,bata da abin ce masa dan haka kawai ta kawar da kanta gefe dan bazata yadda da abinda yake son yi din ba,wato na son ta kalli cikin idanun sa,har yanzu kallon ta yake wanda hakan yasa take mamaki shi ko gajiya ba yayi ya yi ta kallo duk da cewa ta daɗe da sanin cewa ba dabi'ar shi ba ce,hasali ma ko namiji ɗan uwanshi bai tsayawa ya yi masa kallo fiye da biyu,duk sanda ake masa magana ko yake yi,zaka sameshine kansa a jingine idanun sa a lumshe idan a zaune yake,idan yana tsaye ne zaka ga yana duban wani gurin dan sai ka zaci ma baya tare da kaine,sai dai ba haka bane kawai ɗabi ar kallo ce bai da ita ,kuma shima bai so a cika kallon sa,shiyasa yake matukar jin haushin rabi a saboda kallonsa da take kamar zata cinyeshi ko kunya bata da shi a matsayinta na mace,baramma idan ya hada ta da Raihan wadda bata iya kallon cikin idanun sa,ita da take cudanya da maza kuma a matsayin da take da shi na namiji. Tura karamin bakinta tayi ,cikin ƙunƙuni take cewa yanzuma haka yake kallon yan iskan yanmatan da suke son shi mune yake nuna mana baya iya kallon mutum,sarai yaji me ta ce,amma sai ta fuske da cewa na baki iznin bashi nomber ki ne? Tambayar rainin hankali"ta faɗa ƙasa ƙasa,a fili kuma ta ce"ai naga kai ba bashi naka za kayi ba,kuma shi din yana da muhimmanci "yaushe kika san muhimmancin shi? Ya kuma jeho mata wata tambayar da take daukar su na tsantsar rainin wayo,idanuntane suka kawo ruwa, ta kasa ce masa komai sai hawaye, knocked dor din da akayi shi ya taimaketa daga tarkon da wazir yake danawa zuciya da gangar jikinta,sakin hannunta ya yi ,tayi saurin gyara fuskarta , Sannan ta nufi kofar,daidai nan ya bada izinin shigowa cikin kamammiyar Muryar shi da tsarewar gira,karo su ka ci da sakatarea ,ba tare da ta bari sun hada ido ba ta wuce ta gefanta, kai tsaye ta fice daga office din. Chibado's Hausa Kuka take wa innawuro kamar ranta zai fita, innawuro kuwa saka mata ido kawai ta yi,sai da ta yi me isarta,kana ta ja numfashi me dumi ta fesar,cikin shakurarriyar murya ta ce" yanzu innawuro kina kallon abun da hamma wazir yake min ya dace ?. Ki duba dai ki gani tun da aka yi maganar auren nan bai kalli inda nake ba bare nasa ran zai saurareni mu tsara rayuwar mu da yadda shirin bikin zai kasance,Ni gaskiya wannan abun yana damuna kawai kiyii mishi magana"',wani kallon banza innawuro ta wurgawa rabi kafin ta bude baki cikin gatsali ta ce"to uwa ta,ai idan ba uwar da ta haifeni ba,babu uban da ya isa ya sani a gaba da bani umarni,ke idan ba sakarya ba,kina fa kallon da yadda ya amince za ayi auren amma shine kike son mu daga masa hankali yadda zai yi kaura ya bar ƙasar da maganar auren gaba daya ko? To bari kiji na gaya miki Ni na gama nawa aikin sauran aikin ya rage naki ,ai ke macece idan kina da dabaru da salo na kwatar soyayya sai ki gwada,shawara daya zan baki shine ki fara karantar halin wazirin gida dan naga har yanzu baki san ko waye shi ba,idan baki fara sanin halinsa ba to tabbas zaki ci wuyar zama da shi",daga haka ta ci gaba da kallon ta hankali kwance ba tare da ta kara duban inda rabin ke zaune tana sharar hawaye ba. Ta shi ta yi ta nufi dakinta,tana mai lalubo wayar ta,kira daya a ka daga wayar da wata iriyar shewa a lokaci daya wadda ta kira tana cewa shegiyar duniya yau ke nan kin tuna daNi a duniya ko?ajiyar zuciya rabia ta ja ,kana cikin yar damuwar da take ciki ta ce" suryy dan Allah ina zan same ki ina bukatar shawarar ki a wannan gabar saboda kaina gaba daya ya kulle,matsalar wazir ta fara toshe min numfashi wata kila sonsa ne zai zama ajalinna",suryy ta kuma yin wata shewa irin ta yan duniya, Sannan ta ce" ruby ai na dauka yanzu bakya bukata ta a rayuwarki,saboda tun da kika koma wannan gidan fita ta gareki sannan kika daina hulda damu kawayen ki waike kinzo gidan mutunci kar a ganki da kawayen banza asirinki ya tonu to ai dai naga duk inda tuwo yake sunansa tuwo",ta karasa maganar cikin dan bacin rai. Dan Allah suryy ki yi hakuri mu bar maganar nan,yanzu ki gaya min inda kike",bazan fada ba sai dai Inzo gidan,dan jim rabi a ta yi kafin ta ce" to amma dan Allah suryy kiyi shigar mutumci bana so a gano boyayyan halina a gidan nan,kin san cewa badda kaman da nayi ne yasa har naja ra'ayin karkarmu ta amince da maganar auren nan",to shike nan in dai wannan ne kar ki damu dogon hijab zan saka har kasa,indai zaki barni na shigo gidan chibado's family"shi ke nan sai kinzo,daga haka suka yanke wayar rabi a ta fara kirga sakanni zuwa mintuna na zuwan kawarta suryy. RAIHAN na fitowa daga office din Ahmad wazir,su ka ci karo da abu Huraira a hanyar sauka, yauwa kai nake nema dama,tun dazu naji dadi da baka tafi gida ba,ɗan duban shi Raihan ta yi a wani yanayi wanda wazir ya jefa zuciyar ta a ciki,lafiya dai ko? Ta tambaye shi tana dan basarwa dan kar ya gano damuwarta,labari ne me zafi akan su Alh sale da Dr sanate",dan jim ta yi kamar me tunani,sai kuma ta ce"wlh abu Huraira na gaji gida zan tafi idan Allah ya kaimu ma tattauna idan kuma na hau online sai mu yi magana "ok to ka huta lafiya"sallama su kayi. Raihan ta gangara ta dauki mashin ɗinta ta yi gida. Chibado's hause Sai da rabi ta yi waya da security na gidan sannan su ka bar suryy ta shiga,a falo suka hadu tana gaida innawuro dake yi mata kallon tsaf kafin ta amsa babu yabo ba fallasa,duk kuwa da cewa suryy ta yi shigar mutunci dan sanye take da katon hijab dinta har jan kasa yake,cikin sauri rabi ta janye ta su ka haura sama dan gujewa baranbatamar da innawuro zata iya yi mata. Suna shiga dakin suryy ta yaye hijabin shedaniyar shigar ta ta bayyana,tana cewa gaskiya ruby dole kiji tsoran wannan tsohuwar kin ga wani kallon kurilla da take min kamar tana son ganin kayan dake jikina",rabi a ta ce"shi yasa nayi saurin janye ki dan wannan matar da kike gani bata da sauki. Sai da suka nutsu sannan rabi ta korawa suryy bayani akan wazir ,ta ɗora da cewa suryy ki bani shawara meye mafita? Ɗan jim ta yi kafin ta ce",yanzu matakin da ya kamata mu fara hawa shine samun tabbacin baya son kowa"kamar ya? rabi ta tambaya cikin rashin fahimtar zancan na suryy. suryy ta ce" ina nufin Mu fara bincike mu tabbatar da cewa babu wadda ta kama zuciyar shi da mahaukaciyar SOYAYYA,idan har babu to ina tabbatar miji da cewa duk irin taurin kan Ahmad wazir sai ya saurare ki akan tarkon da za mu dana masa,amma fa idan a ka samu akasin cewa yana da wata a zuciyarshi to shike nan ke da samun soyayyar sa har abada domin son waccen ba zai taba barin sa ya saurareki ba harma ya fahimci zuciyar ki, wannan shine hikmata". Shuru ne ya ratsa dakin na wasu yan dakiku,kafin ruby ta yi wani dan murmushi wanda kana ganinsa kasan na yake ne,ta ce" suryy maganar ki na kan hanya,sai dai kuma ina kokwanto akan zuciyar wazir,tabbas ina da shakku akan cewa zai iya son wata har haka,to amma mu jarraba mu gani". Murmushi suryy ta yi,kana ta ce" rubyy baki san irin su wazir ba,wuyar sha ani ne da su ,irin su baka gane takamaiman abinda ke cikin ransu,sun iya boyon SOYAYYA,ke karewa ma ko wadda suke so ba lallai ne ta fahimci hakan ba,dan haka.nace miki aiki ne a gaban mu babba,saboda kafin zuwan lokacin bikin ya kamata muyi wannan binciken,shi kuma auren Kinga lokaci kadan ya rage tunda baifi sati biyu ba". Haka ne maganar ki Surry , nifa yanzu wlh har kin sani cikin fargaba saboda bamu san wane irin sakamako zamu samu ba,wlh suryy duk na gano da akwai wadda wazir yake so wlh sai na kashe ta ko wacece. Sai daf da magriba rabi ta sauko daniyar yiwa suryy rakiya,a nan suka ci karo da kyakkyawar fuskarsa wadda ke gewaye da siririyar saje wanda ya kuma kawata fuskar tare da kamewar shi me saka mutum kama kai ko bai shirya ba,sanye yake cikin doguwar bakar jallabiya yar asalin Saudiya me matukar sheƙi,yana zaune a dinning yana cin tuwon farar shinkafa da miyar agushi wadda taji ganda da Nama,cikin nutsuwar sa da kamewar sa yake cin abincin kai ka ce wani sarki ne,ko yadda yake cin abincin wani abun burgewa ne da kallo wajen yanmata,tun daga nesa yake jin idanu akansa wadda hakan yana daya daga cikin dabiar da ya tsana,duk da cewa bai ɗago ya kalli ko da bangaren da suke ba,hakan bai hana shi gane cewa su biyu ba ne. Cikin mutuwar jiki suryy ta gaida shi,wanda ko motsi bai yi ba bare ta sa ran zai amsa,cike da jin haushi rabi a ta ce" hamma ƙawata na gaida ka fa",goge bakin shi ya yi da tisue ya mike cikin dan hanzari saboda kiran sallar magrib da aka kwala a Masallacin chibaɗo,ficewa yayi cikin nutsatstsan takunwanda yake gauraye da 'yar sassarfa me nuni da cewa sauri yake yi ya bar su da shaƙar mayataccen ƙamshin sa. Wani kallon kurilla suryy ta kuma binsa da shi ba tare da ta kula da wulakacin sa ba,ruby ce ta dube ta tana cewa kin gani dai da idon ki ba,?wannan yanzu a ce a haka Da kwai wata mace da zata zauna a zuciyarsa,wani irin murmushi suryy ta yi me cike da manufofi. Kana ta ce",za muyi yadda na sanar dake kar ki damu,da ga haka suka fita. A cikin wannan dare kuma shuda da dudu suka ziyarci tsaunin tsohuwa inda ta kuma basu sa a da tabbatar cikar burin kowannen su idan har suka kara dage damtse wajen habbaka fitinu da zubda jini kai dama duk wani aiki da za ayi Allah wadai da wanda ya aika,da kuma la.antar Ubangiji. A cikin kwanakin Raihan bata kuma bari sun hadu haduwa ta daga Ni sai kai ba,ita da wazir, sai kuma aiki da ya fara rincabe musu saboda yawaitar fituntinu da kashe kashe da ake ta yi. Abangaren Haidar ma tuni ya tasamma aiki da zuciyarsa da kuma ƙwanjinsa,(to sai dai muce Allah bada nasara malam Aliyu) Haka ta wajen Abba yahya sosai ya da 'yandabarunshi da kuma matsayinshi ya kuma samun shiga jikin gwamna da niyarshi ta rufe duk wata hanyar cutarwa da ake shirin yiwa ɗan uwanshi ko kuma a kayi masa. A bangare daya kuma wani shahararren masani akan iya aikin sirri kuma dan jarida me kwana aikin marasa gaskiya ya baiyana a cikin jahar ta su,a inda ya fara yiwa marasa gaskiyar yan kasuwa tone tone da ma yan siyasar da suke ta kokari gurin ganin cewa sun haye kujeru takarar su ta wannan shekarar. Hankalin manyan kasa marasa gaskiya ya fara tashi akan wannan dan jarida da yakewa shafinsa ko nace jaridar sa lakabi da tree full Y trues,wasu irin bayanai ne suke bayyana ta shafukan sa boyayyu wanda ko kafi kusa naci baka isa yi masa kutse ba bare har ka canko wane ne,babu wanda yasan shi, Macece? Namiji ne? Mutum ne? Aljan ne? Musulmi ne? kafiri ne? A ina yake? Duk babu wanda ya sani, ba su san komai ba sai tonen sililinsa.sirrikan yan siyasa da manyan shegun masu dukiya yake tonewa,su kuma jam'i ai kwashe su kawai suke yi ba tare da jan zance ba,domin su kansu akwai shafin da yake tsoratar da su akan muddin basu dauki mataki akan su ba,to suma yana gab da tona asirin su, wannan dalili ne yasa basa jinkiri wajen kame su,hatta lauyaoyin da zasu zauna a kotu da su sai anbisu da nasu kashedin. Lokaci kan Kani duniya ta san da zaman tree full Y trues talakawa sun sami abinyi kullum fatan su Allah ya bawa wannan bawa sa a akan masu sheke musu ya'ya da jikoki, Ita kanta Raihan yanzu burin ta tasan waye wannan,shi yasa ta dukufa bincike ita da abu Huraira. A bangaren Ahmad wazir chibado ba za ka san komai ba,dan sanin kansa sai Allah babu yadda za ayi ka gane halin da yake ciki akan wani abu,lamarinsa da halinsa daban suke da na sauran mutane,ko da a kallo ze yi wuya ka fahimci ainahinsa, Muje zuwa yanzu ne za a fara wasan ku gyara zama dan jin wannan cukurkudaddan al'amari me matukar tsayawa a rai,shin rabi zata cimma binciken ta na gano wadda ta mamaye zuciyar Ahmad? Aunty amarya fa?makomar Raihan fa? Yaya batun bidiyo dake hannun RAIHAN? Wanene shuda da dudu? Shin me su shugaban jam'iyyar suke shiryawa Raihan dake amatsayin Rahim? Abba yahya zaiyi nasarar kare dan uwansa daga cin amanar da yake tsakiyar tunanin gwamna nayi masa?Abun da yawa fa ku dai ci gaba da bina sannu dan warware kullin dake kulle.....✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page21 ``` Wannan al'amari ne yasa gaba ɗaya gari ya ɗauki ɗumi,ko wane gidan jarida burinsu su gano waye tree full Y trues,sai ya zamana gaba daya yanzu 'yan jarida da shi suke kishi,sai ya lamarin ya koma tamkar ya yi musu allura,sai ya kasance ko wanne gidan jarida bincike suke akan masu kuɗi yan kasuwa da uwa uba yan siyasa,saboda basa son tree full Y trues ya riga su fidda labari. Chibado's hause Kaiwa kawai take tana kawowa kamar wadda ke jin zawo,shigowar suryy ne ya dakatar da ita,nufota tayi da sauri tana saurin rufe kofar tare da sa key,suryy kin tayar min da hankali tun da muka yi wayar nan najiki ba daidai ba hankalina ya tashi", zama suryy tayi tana dan goge fuskarta da hannunta, sai da ta ja yan sakanni duk rubyy ta damu da jin sakamakon binciken da tayi akan A wazir,duban rubyy ta yi sannan ta ce" rubyy akwai matsala fa"zabura rubyy ta yi cike da tashin hankali tana cewa gaya min kawai wacece? a ina take? Yar uban waye?. Calm down mana rubyy ki saurareni nayi miki bayani", shiru ta yi tana saurarenta,suryy ta ce" babu abin da bincikena ya samo min sai sunan Rahim ,a yadda labari ya zo min wazir bashi da wani na kusa da zuciyar sa kamar Rahim ,babu dan adam din da yake kallo da idon kauna kamar RAHIM,to rubyy hakan yana nufin Rahim ne ya hana wazir ya saki a zuciyarsa kome? Idan ba haka ba meye dalilin? A yadda na samu labari Ma cewa a kayi Rahim shi yake fada da duk wata mace da ta kawo soyayyarta ga Wazir",wani miskilin murmushi ruby ta yi,kafin ta ce" duk nasan wannan suryy,me ye ya hada binciken mu da Rahim? Karfa ki manta Rahim namiji ne ba mace ba,dan haka ki cire shi daga cikin lissafinmu,duk wannan abun da Rahim yake kuruciya ce" kuma SOYAYYAR su da wazir Allah ne ya hadata,so muyi abin da yake gabanmu bani da damuwa da wannan Rahim ɗin ". Wani kallon baki da hankali suryy tayi mata,kafin ta yi Murmushin da ke nuni da cewa akwai fa ƙura,ta ce"rubyy ba zaki gane ba,amma insha Allah kafin zuwan satin bikinku sai na binciko gaskiyar abinda ke akwai,sai na gano abinda ke tsakanin wazir da wannan Rahim ɗin,saboda naga ke ƙwaƙwalwar ki baya aiki,idan har abin da nake tunani shine yake tsakanin su to ki tabbata Gara wazir ya yi soyayya da mace akan SOYAYYA da namiji,wadda ta fi ta mace Bala i",daga haka ta mike tare da ɗaukar jakarta ta bude dakin ta fice,kusan mutuwar zaune rubyy ta yi tana maimaita kalaman suryy cikin ƙwaƙwalwar ta tare da tace su dan son gano manufarsu. Alh Muhammad nurr hause.... Abbie Ni dai ka barni da mashin wlh nafi jin dadinsa,bana son mota, Abbie ya ce"haba Rahim kabar mashin din nan mana ka fara tuka mota amma ka dage kai sai mashin",hamma idi dake zaune yana aiki a laptop din sa ya ce"abbie ka rabu da shi mana tunda yafi jin dadin mashin din,ina tabbatar maka nan da wani dan lokaci zai nemi motar da kansa ko dan ya burge budurwarsa,cak aunty amarya ta tsaya daga kofar kiching din da ta sako kai dan fitowa hannunta rike da jog din da ta hadowa abbie lemon zobo, Raihan ma jikin ta ya so ya nuna alamun sanyi ,amma sai tayi hanzarin basarwa ta hanyar taya hamma idi din da cewa,kai Hamma Ni kam bazan yi budurwa ba ina kusa da auntyna da Hajiya goggo da abbie", hamma idi ya yi dariya tare da cewa to shike nan abbie kayi mana sheda duk ranar da yazo yana yar murya akan na ara masa mota zai je zance bazan bayar ba",na rike wannan cewar abbie yana yiwa aunty amarya sannu da hada zobon da ta yi, murmushi kawai ta yi ba tare da ta nuna musu taji kan hirar da suke yi din ba. Dariya da shewa kawai kake ji a sashen na mama murja, gaba dayansu ne a sashen banda surukansu,saboda suma idan zasu yi tattaunawar sirri ba sa bari su biyo su sashen iyayen nasu,Affan ne ya ce" wlh mama ina jin dadin yadda abi ya bamu wannan damar kamar yasan shirin mu akan su,Hassan ya yi ƙwafa tare da cewa" bibiyar yaron nan nake sosai kuma ina gaf da cimma nasara,wataran sai dai kawai a shigowa da amarya da yan koranta gawarsa,daga nan kuma ta ubansa ta biyo bayansa ba,cewar momy ke nan ta faɗa cike da karsashi,shigowar hamma idi ne ya sa gaba daya suka yi shiru sai harara da suka fara binsa da ita,girgiza kai kawai yayi tare da yi musu fatan shiriya,gaida iyayen nasa ya yi ya juya ya fita,dama abun da ya kawo shi ke nan,yana fita suka dora daga inda suka tsaya,babu komai a kalaman su da fatan su sai sharri da mugun nufi. ________________ Wai waye wannan tree full Y trues din? Shugaban jam'iya ya za ayi mu sani? honorable sani dan ƙusa ,ya ce"gaskiya ba mu ga ta zama ba,dole ne tun kafin mutumin nan ya biyo ta kanmu mu san yadda za ayi mu yi maganin sa",to ta yaya za mu yi maganin nasa bayan ba mu san ko mai akan sa ba,cewar shugaban jam'iyya da yake cikin taron yan jam'iyar su ta gwamnatin dake ci a yanzu,(idan baku manta ba Alh sale da Dr sanate ba jam'iyyar su daya ba a jam'iyyar adawa suke,kuma boyayyar alaka ce tsakanin shugaban jam'iya da su, kuma kamar yadda suke zaman sirri da su Alh sale da Dr haka suke yi shida yan jam'iyar ta su wadan da suke macuta masu ha intar gwamnati da kuma son cutar da gwamna a ta bayan fage). Alhaji Hamza ya ce" duk wannan surutun bashi da ma'ana,dan garin surutun ne bamu Ankara ba sai dai muji mu a fursuna,kawai yanzu abin da za ai shine mu gayyato manyan masana na'ura me ƙwaƙwalwa su yi mana kyakkyawan bincike ko za mu da ce" take kowa ya yi naam da shawarar sa,nan suka bar maganar akan gobe zasu tattaro yaran dan yi musu bicike a sirrance. CHIBADO FM......... Raihan na dakin daukar rahoto,bayan ta isar da sakon ta na yau,tattara komai ta yi ta fito,kai tsaye office dinta ta nufa,anan suka yi kicibus da abu Huraira shida Khalid,yauwa Rahim dama wajen ka muka nufa, Allah yasa lafiya Raihan ta faɗa idon ta akan abu Huraira dan ta fahimci ko ma meye daga wajen sa ne,dan yau kusan sati ke nan yana son su zauna su yi magana kamar yadda ya fada amma hakan bai samu ba,saboda aiki da ya dan cushe musu kwana biyu,lafiya kawai magana ne me muhimmanci zamu tattauna dan idan aka yi magana da kai kamar anyi da oga ne,idan ma kaje wajen sa cewa zaiyi muzo wajen RAHIM, Khalid yace mu shiga office din mana dan jarida uban zance", dariya su kayi gaba dayan su kana suka bi bayan RAIHAN. Sosai Raihan ta fuskanci maganar da yake so su tattauna din me muhimmanci ce,shi yasa ta bashi hankalin ta kacokan,ina sauraren ka abu Huraira,ta faɗa tana kallonshi,dan gyara zaman shi ya yi tare da yin gyaran murya kana cikin nutsuwa ya fara magana,Rahim magana ce akan wannan tree full Y trues din ,dan gaskiya ya tsaya min a raina sosai,gani nake kamar ya kamata mu danyi wani kokari dan mu gano shi,gano shi da za mu yi ba dan ko mai ba ne sai dan samun cigabanmu da kuma kwarin gwiwarmu,domin na fahimci manyan kasar nan sunyi matukar shiga firgici da tsoro a akan sa,shi yasa nayi tunanin mu zauna mu yi tunanin yadda za ayi mu samo shi",zuba mishi ido Raihan ta yi na wasu yan dakiku kafin taja dogon numfashi ta fesar,cikin kaifin basirar da Allah ya bata ta ce" abu Huraira me ye ribar mu na san lallai sai mun sami wannan mutumin? Khalid ya ce" Rahim maganar abu Huraira abin dubawa ce,sai dai Ni kuma ina ganin a me makon mu tsaya bata lokacin mu akan neman sa dan mu hada hannu da shi,ina ga Gara mu kara himma mu dage damtse domin ganin cewa muma munyi aiki kamar shi,saboda idan har muka ce sai mun neme shi to sai nake ga kamar bamu cika burinmu na kawar da miyagu ba, kuma ba muyi amfani da karsashinmu da kwarin gwiwarmu ba,tun da munyi amfani da basirar wani ne can da ban da kuma aikin sa",dan tafi Raihan ta yi tana duban Khalid ta ce" Khalid kamar ka shiga zuciyata ka debo abin da yake cikin ta,dubanta ta mayar kan abu Huraira tace" abu Huraira banƙi shawarar ka ba,shawararka me kyau ce domin na fahimci abinda kake nufi,saboda nima da farko hankalina ya tashi da bullowar wannan mutumin dan har na fara kokarin bincike akansa,sai dai kuma ban samu komai ba baya ga dinbin takaici na rashin samun nasarar hakan,daga baya kuma sai nayi tunani irin na Khalid da fatan ka fahimce mu?jinjina kai abu Huraira ya yi fuskar shi cike da gamsuwa. Sai magana ta biyu,ya faɗa idon shi akan Raihan da itama ta kuma bashi hankalinta, ya ci gaba da cewa akwai wani kokari da nayi akan wasu yan siyasa da suka yi badda kama a matsayin mutanen kirki,na samo kadan daga cikin bayanansu, wannan shine makasudin zaman namu",da sauri Raihan ta ce"su waye daga cikinsu?Dr sanate da Alh sale sai kuma shugaban jam'iyyar dake ci a yanzu,wanda abinciken da nayi na gano ɓoyayyar alakar dake tsakaninsa da yan jam'iyar adawa,hakan ya nuna cewa yaudarar gwamnan yanzu yake yana cin dunduniyarsa ta karkashin kasa",wani kayataccen murmushi Raihan tayi kafin ta ce"ashe ka fara aiki me kyau amma kake son mu bi ta kan wani? . Girgiza kai abu Huraira ya yi kana ya ce"Rahim wlh tsoran mutanen nan nake ji kai kan ka kasan cewa duk wani dan jarida ko jami i ko wani da yake son gaskiya,basa tsira da rayuwar su a wajen mutanen nan,idan ka duba abin da ya faru da a s p jatau da d p o Kasim,da sauran irin su harma da halima,duk abin da ya faru da su ke nan sun rasa rayukansu ne ta hanyar san tabbatar da gaskiya",tabe baki Raihan ta yi sannan ta ce"abu Huraira tsoro ba na mu ba ne tun da har muka ji muka gani muka ce za muyi dan haka tun wuri ka cire tsoro domin aikin mu ba na matsraci ba ne",na sani Rahim amma zaka ce haka saboda kai baka ji abinda naji ba,kuma wannan dalili ne yasa na fara kawo shawarar mu nemo tree full Y trues,saboda mu bashi bayanai ya fitar tunda shi boyayye ne,kuma shi kansa tree full din ya boye kansa ne saboda abin da yasan yana faruwa da irin mu irinsu". Khalid ya ce"maganar ka tana kan hanya,amma kuma kar ka manta da wani abu ,duk wanda ya mutu kwanan sa ne ya kare ,su kuma idan mun kasance mune karshen su Allah ba zai taba basu damar illata rayuwar mu ko wani abu makamancin haka ba,dan haka ka kwantar da hankalin ka ka sake mana record din muji ,dan musan ta ina za mu fara fidda bayanan mu",abin da ya kamata ke nan, Raihan ta faɗa ba tare da nuna karaya ko tsorata ba. Playing din voice din ya saka musu,shuru suka yi gaba daya suna saurara. Dr sanate yanzu kana ganin cewa yaron nan da ya dauki camarar nan ba zai samu dama ta tona mu ba,saboda bullowar wannan tree full Y trues din shine yake bawa yan jarida kwarin gwiwa akan ida nufin su akan mu,shi yasa nake tsoran ace yaron nan ya saki video nan,Gara tun wuri mu sauya tunani mu yi gaggawar kawar da shi",cewar shugaban jam'iyya ke nan da yake fitar da maganar cikin alamun tashin hankali da son karaya. Alh sale ya ce" duk ba wannan ba, nifa yanzu gani nake a ko da yaushe asirin mu zai iya tonuwa ko da ba ta hanyar videon nan ba,tun da shi wannan tree full Y trues din shu Umi ne babba,mun kasa gane ta hanyar da yake samun wadan nan bayanan da yake fitarwa",ai ba za mu sani ba sabo bai fito ba sai da ya shiryawa ko wannenmu,su kan su wadan da suke tare da mu din ba ku ga tsoran sa suke ji ba,jami ai da yan jaridun,su kansu bakandamiyya da muke harallar mu tare da su,yanzu a tsorace suke",kawai yanzu abin da ya fi dacewa mu kawar da wannan dan Marayan zakin in yaso sai mu tunkari babbar giwar ba tare da tunanin baya ba......... Dif maganar ta dauke alamun a nan ya tsaya da ɗaukar record ɗin,duk din su shuru su kayi kowa da abin da yake nazari a ransa,sai dai dukkan su sun zubawa Raihan ido suna sauraron abin da zata faɗa. RAIHAN jaruma ce akan abin da ya shafi aikinta,dan haka babu wani alama ta firgici ko nuna alamun tasan video da suke magana a kai,ta yi nisa ne wajen yin wani zuzzurfan nazari wanda ita ka dai ta barwa kanta sani,abu Huraira ne ya katse mata tunanin ta hanyar cewa,Ni yanzu damuwa ta shine musan wane dan jarida ne videon nan yake hannun sa, Sannan a wa ce gidan jaridar yake?taya akai kuma ya samu video? Me video ya kunsa?duk da cewa wannan ina da tabbacin cewa wani sirrinsu ne da basa son ya fita a cikin videon ", Khalid ya tari numfashinsa da cewa , wannan fa babban aiki ne a gare mu,kawai Ni ina ganin mu yi aikin da yake hannun mu ba wai neman wanda video yake hannun sa ba", Rahim ba ka ce komai ba? Cewar abu Huraira, Abun da Khalid ya fada shine abin yi",ta faɗa cikin rashin bawa maganar muhimmanci,abu Huraira ya ce" amma Rahim inaga kamar hakan baiyi daidai ba,saboda bamu sani ba ko acikin wannan gidan yake,nifa tunani na ya fara Bani cewa akan video nan aka kashe Halima kuma duk yadda akayi wanda yake dauke da record din videon a nan gidan yake,shi yasa hankalina ya tashi matuka",zuba mishi ido Raihan ta yi kafin ta maida kallon ta kan Khalid da shima yake wani dan nazari,ta ce" abu Huraira ko ma meye ba mu da hurumi da shi,maganar halima ta wuce Allah zai saka mata abin da aka yi mata,so batun mu barshi a nan idan kuma kana ganin kana da hanyar da za mu samu videon cikin sauki bamu da damuwa da hakan,sai muyi abin da ya da ce",yauwa Rahim ka fahimci abin da nake nufi, Khalid ya ce" amma fa Ni ina ga Gara mu fara wallafa wannan jaridar kafin binciken videon ya biyo baya kar muje tree full Y trues ya riga mu",ya fada da dariya a kan fuskarsa, su ma din murmushi su kayi daga nan suka yi sallama kowa ya wuce inda ya fi wayo. Yauma Raihan bata hau office din wazir ba,kai tsaye fitowa ta yi dan daukar mashin dinta... Barka dan uwa Rahim ", Raihan taji an fada daga bayan ta ,ya yin da take shirin hawa mashin dinta,juyowa ta yi cikin nutsuwa kafin ta ce" yauwa Barka amma da kin yi sallama ina ga sai yafi ko? Raihan ta faɗa tana kallon suryy dake ta faman murmushi jikin ta sanye da doguwar riga da dan madaidaicin mayafi kalar Les din dake jikinta, cikin lankwasa murya har da yin fari da ido ta ce" am sorry salamu alaikum",amsawa Raihan ta yi cike da gundura da tsayuwar,idan ba zaka damu ba ka bani nomber za mu yi magana saboda naga yanzu kamar ka tashi daga aiki",ey na tashi kamar yadda kika gani",ayya kayi hakuri amma dan Allah ka bani nomber ka,ganin macece yar uwarta yasa bata ja maganar ba kawai ta bata katinta,na gode,suryy ta faɗa tana bin RAIHAN da wani shegen kallo. Ba tare da ta kuma tanka mata ba,ta haye mashin dinta ta fita da dan gudun ta irin na kwarewa. Dariya suryy ta yi tana cewa yaro kazo hannun suryy,kuma nasha alwashin sai na gano ɓoyayyiyar dangantakar dake tsakaninka da Ahmad wazir chibado......................✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page22 ``` Abbie da aunty amarya ta samu a falon,babu hamma idi kamar yadda tafi samunsu, wasu lokuta,sannu da hutawa ta yi musu,ba tare da ta kuma cewa komai ba bayan haka,ta wuce dakin ta saboda yadda take hanzari wajen samun kebantuwa.duk da cewa antyy amarya na lure da ita,sai bata bawa hakan muhimmanci ba ganin abbie na wajen. Tana shiga ta rufe dakin tare da sa masa key.bincike ta fara har sai da ta lalubo inda ta yiwa camarar nan boyo.zuba mata ido ta yi na wasu yan dakiku,tunda ta dauko camarar bata taba tunanin bude ta ba har sai idanun masu bin ta ya kau daga kanta,duk da dai a wannan lokaci bata da tabbacin zasu daina bibiyar Tata,to amma yanzu lokaci yayi tun da har taji tabbaci akan neman da suke mata,kuma tasan cewa camarar suke son karba amma da tuni sun kasheta,rintse idanunta tayi tana jin cewa gwara ta fitar da video kawai tun da dai basu daina neman ta ba,tasan koda ta basu camarar nan dole sai sun kashe ta tun da ta riga ta san kadan daga cikin sirrin su,amma fa duk da haka tana matukar jin tsoran fitar da videon kai tsaye ta jaridar su,badan kanta kawai ba,sai dan ragowar mutanen da suke aiki a chibado fm wanda ta sani cewa babu wanda zasu kyale ,kai hatta shi kansa Wazir bata da tabbaci akan zai sha. Yaya zanyi na fidda wannan video ba tare da nayi sanadin rayuka da lafiyar wasu ba? Ta tambayi kanta cikin damuwar da ta gama baiyana a kan fuskarta. Duk da cewa ba ta yi wani mamakin sanin wadanda suka aikata kisan haluma ba,saboda ta riga tayi karatu me zurfi akan yanayin tafiyar siyasa. Shi yasa ko alokacin da tasan komai bata firgita ba,duk da cewa ta yi mamaki ganin fuskokinsu a matsayin masu aikata wannan mummunan laifi. TREE Full Y TRUES shine abin da ya fado ƙwaƙwalwar ta da tunaninta,shin ta yaya zan same shi? A ina zan ganshi?ya za ai na bashi wannan video? Zagaye dakin ta shiga yi cike da tsananta tunani,ya rufe komai nashi ,bai bar wata alama da za a iya tura masa ko dan guntun sako ba,shin ta yaya ne wai? DSP.Haidar ne ya wado mata,cikin sauri ta lalubo lambar wayar sa,bugu biyu ya daga,kana ina abin? da ta fara tambayar shi ke nan.ina hanyar zuwa gida,ok idan baza ka damu ba ina son magana da kai ka karaso gidanmu idan ba zan takura ka ba",No ba damuwa yanzu zan karaso.kashe wayar ta yi ,sai a lokacin ta dan samu nutsuwa har ta fita falo dan kar ta janyo hankalin iyayen ta su Ankara da abin da ke damunta. Magana su kayi me dan tsayi ita da Haidar wadda sam ban samu jin ko daya daga abin da suka tattauna ba.sai dai daga dukkan alamu shima ta samu wasu bayanai daga gare shi wadanda suka kara mata karfin gwiwa,ragowar kuwa sai nan gaba za mu sani. .......... Cike da farincikin fara samun kusanci da Rahim suryy ta kira kawarta rubyy ta sanar mata komai,daga nan ta ce" ta bata nan da kwana hudu duk abin da ya kamata su sani zasu sani akan Tsakanin Rahim din da Wazir. CHIBAƊO'S HAUSE...... Sosai shirye shiryen biki ya kankama ta bangaren iyaye da amarya,shi kan wazir da yake amsa sunan ango bai ma san anayi ba,hasalima bai san ranar aurenba, babu abin da ya dame shi da hakan ,sai dai kuma duk ya tuna auren idan ya ga wata alama sai ya tuna Raihan da abin da zai faru idan ta ji auren, gashi shi kuma miskilanci ya hana shi sanar da kowa,saboda yana jin sanarwarsa ga mutane yana nuna cewa ya na sane da auren ne ko kuma ya damu da maganar auren. Washe gari ma'aikatan yan jarida da jama'ar gari su ka wayi gari da sabon labari a shafin jarida ta tree full Y trues,labarin daya girgiza yan siyasa da su kansu 'yan jaridu, zuwa kan al'ummar gari wadanda kusan abin yafi shafar su. A shafin nasa ya bayyana wani babban al'amari me taba zuciya akan lamarin yansiyasar mu. A shafin nasa yake cewa akwai wani boyayyan sirri akan mutanen da bai gama gano su ba,wanda ya tabbatar da cewa idan ya tsaya bai bayyana wannan labarin ba har sai ya gano ai nahin masu ruwa da tsaki cikin al'amarin to tabbas abin zai ci gaba har ma ya fi na baya,saboda shirin da suke kuma yiwa lamarin. Ya ce" ya gano a cikin manyan mutanen mu akwai wadanda suke tada tarzoma a yi kashe kashe a zubda jini,bayan sunyi hakan kuma daga baya sai su bi kabarurruakan gawarwakin su tone su cire wasu sassa daga jikin gawarwakin. Ya ce" wannan abu ba karamin girgiza shi ya yi ba,shi yasa ba zai iya tsayawa har sai ya kammala binciken gaba daya ba,daga karshe ya ce"yana mai umartar jami an tsaro su yawaita su kuma saka idanu akan ko wane lungu da sako , su kuma saka idanu akan manyan kasa da yan siyasa,saboda yana da tabbacin wata babbar tarzoma da suke shirin kara tayarwa duk akan kudirin su. Daga nan ya ɗora da yi wa al'umma alkawari akan in sha Allah in dai yana raye da lafiya, sai ya binciko wadan nan mutane Sannan sai ya bincika a salin abin da suke yi da wannan sassan jikin gawar,amma yana mai yiwa jam'i ai kashedi da babbar murya kan su kula, su tsaya su yi aikin kare hakkin dan Adam kare al'umma shine aikin su ba kare dukiyoyi da rufawa marasa imani asiri ba. Wannan lamari ba karamin jijjiga zuciyoyin jama a ya yi ba,ya yin da bayanan tree full Y trues ga jam'i an tsaro ya yi matukar sa su cikin firgici da gudun tonan sililin da ya dauki hanyar yi musu,hakan yasa ta ko ina garin ya dau wuta da jiniyar yan sanda, wanda hakan yake nuni da sun tsorata za kuma su yi aiki ko dan Allah ko kuma dan gudun tsira da mutunci da rayuwarsu,wasun su kuma dama dole a ka yi musu,dan haka yanzu sai suke jin kansu a free su ka samu karfin ɗorawa daga abin da suka yi niya tun asali aka dakushe su ta hanyar barazana da rayuwarsu. Dsp,Haidar yana daga cikin masu karawa abin armashi ta hanyar kama wasu masu laifi da tun farkon zuwansa ya binciko su tare da taimakon su Raihan... RAIHAN na gama duba labarin ta ɗago kanta, ta dan zubawa su Khalid da abu Huraira da salim idanu na wasu yan dakiku,kafin cikin jan numfashi ta ce"gaskiya wannan ko ma waye ya cancanci girmamawa,ya kuma cika jarumi,ina tare da kwarin gwiwar shi da yake bamu ta hanyoyin da shi kansa bai zato ba,ina ga kawai mu yi rubutun mu akan su shugaban jam'iya kamar yadda mu ka tattauna a jiya", Abu Huraira ya ce" a'a bai kamata mu fidda labarin nan yanzu ba,a ganina za mu janyo hankalin su ya dawo kan mu har ma su yi tsammanin cewa da hadin bakinmu akan wannan Labarin,karshe ma su yi tunanin tree full Y trues yana cikinmu,kun ga tamkar mun janyowa kanmu masifa ne muna zaune kalau",wani banzan kallo Raihan ta yi masa kafin cikin jin haushin abinda ya fada din ta ce" wlh abu Huraira kana bani mamaki,wai shin ba aikin jarida ka karanta ba ne? Dan me yasa zaka dinga kawo mana tsoro a cikin aikin mu,idan ba za ka iya ba ka ajiye aikin a maimakon mu ka dinga sarayar mana da gwiwa,shi fa me aikin al umma kullum kwarin gwiwa yake so,amma kai kullum baka da batu sai na tsoro ",ganin yadda ran Rahim din ya ɓaci sai kuma duk ya ji kunya da nadamar abin da ya yi din,Salim ne",ya ce"gaskiya ne maganar ka Rahim ,abu Huraira duk ma'aikatan da ka gani a chibado fm chibaɗo tv chibaɗo daily trues to ina tabbatar maka da cewa ba gama garin mutane ba ne,shi yasa kullum muke aiki cikin nasara Allah yake daukaka mu,akwai amana a kwai gaskiya sannan akwai sadaukarwa,idan zaka iya shike nan idan kuma kana jin tsoron nan ma bamu da damuwa zaka iya bari",Salim yana ajiye wa Khalid ya dauka da cewa me yasa kaga duk lokacin da aka yi kisan dan jarida sai ka samu a wannan gidan nan,saboda kawai mana tsaye kan gaskiya ne,ko halima da sauran wadanda suka gabata yan sanda da 'yan jarida duk sunyi shahada ne saboda sun mutu ne akan hanyar Allah wato yaki da zalunci da aikata munanan aiyuka kamar dai irin wannan da aka baiyana yau, sannan mu da ka ganmu nan ,muna kara samun kwarin gwiwa ne daga uban gida Ahmad wazir chibado da matemakinsa RAHIM,kai ma ya kamata ace zuwa yanzu ka samu kwarin gwiwa da irin salonsu na aiki,duk da cewa kuwa Rahim shine yaro mafi kankanta da yake cikin wannan ma aikata,amma kwazon sa da himma ya sa ya zama babban kowa ,hatta da shi kansa oga wazir ya sakar masa da yawan ragamar aikin gidan nan,dan haka duk abin da Rahim ya ce ",mu yan bada shawara ne ba'yan dunkufar da shi ba". So sorry ku yi min gafara,amma in sha Allah bazan kara ba,kuma zanyi amfani da shawararku",ganin nadama sosai a tare da shi yasa Raihan tace "so babu damuwa mu ma ba a san ranmu mu kayi maka haka ba,kawai dai munga kamar kana son maida mu baya ne akan nasarar da muke samu ko nace ake samu a gidan nan tun kafin zuwan mu,Salim ya ce",ya kuke ganin za mu yi kenan? Shin za mu fitar a yau ko kuma mu bari zuwa gobe, idan yaso yau sai Rahim ya kaiwa oga,daga hannun oga koma sai mu bawa Xulaihah ta fara aikin,"Raihan ta ce",hakan ya yi Allah ya Kaimu goben",da Amin suka amsa. Salim ne ya dakatar da su da cewa kun san kuwa bikin oga baifi saura kwana bakwai ba,amma har yanzu ya ki sanar da kowa a cikin mu?Khalid ya dan zaro ido tare da cewa kai ma kasan ba zai gaya mana ba sai dai kawai muga katin gayya",dariya su kayi har da tafawa, Abu Huraira ya ce"ka ce su oga an kusa shiga daga ciki",suna maganar su ka fita ba tare da sun lura da mutuwar tsayen da Raihan ta yi ba,wanda su sam basu kawo cewar bata sani ba,dan shi Salim ma har da cewa ai laifin Rahim ne da bai sanar da su da wuri ba. Suna karasa fita ta koma jabar ta zauna,sam ta kasa gane wane irin yanayi ne take ciki,wani irin numfashi me azabar huci take fitarwa,kirjin ta har sama yake yana kasa,idanunta tuni suka koma wata kala,miƙewa ta yi tana ganin duhu a cikin idanunta ,ba tare da ta kula da yanayinda take ciki ba,ta fita daga office din,da lalube ta karasa inda mashin din ta yake,a hankali tasa hannu ta ciro key ɗin,duk da yadda take ganin bibbiyu hakan bai hana ta jan mashin din da wani irin speed ba..... Wani saurayi sanye da facemask ya fito daga bayan ƙatuwar bishiyar dake jikin buldin din da waya a kunnen shi ,oga ya fito kuma naga kamar yana a yanayin da za mu iya aikin mu cikin sauki,ok sir saurayin ya fada yana kashe wayar,da sauri ya shiga wata bakar mota suka ja da gudu suka bi bayan RAIHAN dake ganin titin na rabe mata huɗu. Wazir ya na ganin lokacin da Raihan ta fita,duk sai yaji hankalin shi ya tashi,cikin nutsuwa da boye abin shi a zuciya ya fito ba tare da ya saurari security n shi dake binshi kamar jela ba,ya fada mota kai tsaye bayan raihan ya biyo wadda cikin kankanin lokaci ta bace a titin kamar ma bata bi ta hanyar ba,ci gaba da tafiya ya yi cikin gudun da yake dan karawa da yakinin cewa zai same ta a gida.duk kuwa da cewa zuciyar shi na wani irin bugu da shiga yanayi me wuyar fassara akan fitowarta Raihan. Luf kake ji tun fitar labarin sun kasa yin wani motsi wanda zai sa a yi zargin su,duk wani me fada a ji ko dan takara yanzu yana cikin halin kaka nikayi ne,akan labarin da tree full Y trues ya fidda, zuciyoyin su cike suke da tsoran budewar ballin duk da cewa basu san komai akan lamarin ba ba kuma su san ta inda wannan shegen ya samo labarin nan ba,to amma duk da haka sun tsorata saboda ganin su da kuma tunanin su shine kan me uwa dawabi za ayi. Hatta gwamna sai da ya tara mittin din ujila, Cikin nutsuwar shi da kamala irin ta dattijon kwarai ,ya gama kallon fuskar kowa ya kuma karance su tsaf,duk da cewa ba wai ya karanci zuciyon su ba ne,kawai dai ya karanto tsoro sosai a cikin idanun su,sai da ya yi gyaran murya kana cikin nutsuwarsa ya fara magana da cewa,ya kamata ace zuwa yanzu ko mai yazo karshe ,ina so ku sani cewa mulki ba hauka ba ne,dan haka ya kamata a cikin mu nan idan da wanda yake da hannu a cikin wannan lamari to ya mika kansa ga jami ai,tun kafin wannan mutumin ya gano ko su waye,ina tabbatar muku da cewa idan haka ta faru wlh kashin kowa ya bushe daga masu ruwan har marasa ruwan,dan fa al'umma ba zata bar su ba",shugan jam'iya ya ɗora da cewa wannan haka.yake ranka ya dade domin kuwa kafin jam'i ai su yi wani abu jama ar gari sun babbakawa gidajen mu wuta,dan haka dan Allah idan muna da su a cikin mu to su yi kokarin fidda kansu tun kafin abin ya zama wani iri". Abba yahya dake zaune gefan da dufuty yake ,ya zubawa Alhji Garba ur exsellency ido,kallo ne da shi kadai yasan manufarsa,gyaran murya ya yi kana ya ce",tabbas ur exsellency maganar ka haka take,dan ko Ni nan na samu wanda yake aikata wannan abun wlh sai na sare masa kai ko waye shi. Nan da nan fa hayaniya ta barke har baka jin abinda wani ke cewa,kowa fada yake da rantsuwa akan bai san wannan lamari ba,da haka taron ya watse babu wani ci gaba. TSOHUWA....... Wani irin huci ne ke fitowa daga bakinta tare da wani irin hayaki wanda ke turnuke ilahirin dakin tsafin,cikin hucin bakin ciki ta ce",kai dudu zuwanka gare mu babu alheri me yasa haka bata faru a baya ba sai Yanzu? Me yasa na kasa ganin wannan hatsabibin yaron? Ta yaya akai ya gano wannan sirrin da muka riga muka binne da kuma tabbacin wanda ya tono shi sai jini ya sha jinin sa? Tabbas akwai ƙura ta faɗa tana wata irin girgiza me cike da tsananin bacin rai,su kansu yan kungiyar sun ga bacin ran tsohuwa wanda basu taba gani ba iya kafuwar kungiyar,bude idanunta da su kayi jajur kamar jini ta yi tare da nuna shuda, ta ce"lallai ya kamata ka yi wani abun a bangaren mutane lallai muna son sanin wannan dan jaridar,zan yi bincike iya bincike ba za ku kara jina ba har sai na gano waye wannan matsiyacin dan jaridar, dif suka watse daga gurin kamar yadda ta bace ,duk zuciyoyin su cike da damuwa,dan abin da ya fi karfin tsohuwa ba karamin babba bane.........✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page23 ``` Abba yahya yana kan hanyar shi ta komawa gida wayar ur exsellency ta shigo masa,dagawa ya yi tare da yin sallama cikin girmamawa kamar yadda suka saba yiwa junansu,daga daya bangaren ur exsellency ya ce da Abba yahya,idan ya samu lokaci zuwa anjima da dare ya dawo akwai maganar da zasu yi iya su uku kawai wato shi da dufuty yake son gani.ok Allah ya kaimu ya fada suna aje wayar lokaci ɗaya. Jinjina kai kawai Abba yahya yake zuciyarshi cike da kuma da mugun takaicin dan uwansa da ya kasa gane waye amininsa,to amma dai ko meye shine zai zama sanadin binne ur exsellency din da ransa domin har ya tabbatar da zargin da yake masa akan cin amanar dan uwansa da kuma cin amanar jiharsa, tabbas ba zai barshi ba.da wannan tunanin ya karasa gida. .............. Haka nan aunty amarya ta tsinci kanta cikin faduwar gaba,hakan yasa take ta gwada kiran wayar Raihan amma ba a daga ba,hankalin tane ya kuma tashi cikin rawar jiki ta kuma sake gwada kiran,ajiyar zuciya ta sauke jin an daga sai dai kuma a maimakon ta ji Muryar Raihan sai taji Muryar namiji, innalillahiwa'inna ilaihi raji'un ta shiga maimaitawa zuciyarta na wani bugu na tsananin tashin hankali cikin rawar baki ta ce",ina me wayar? A maimakon amsa sai kawai ta ji ansheke da wata muguwar dariya kafin daga bisani a tsagaita da dariyar,cikin Muryar dake nuna ko waye yana cikin nishadi ya ce"lamratu ina fatan kin shiryawa zuciyar ki akan rashin gudan jinin ki? Da karfi zuciyar Tata ta yi wani irin bugu har sai da ta dafe saitin zuciyarta,ya Allah ta ta fada tana mai runtse idanunta da take Ji tamkar za su fado saboda yaji,ya dai kin kasa magana ne? To babu damuwa yanzu dai gamu ga RAIHAN sai ki gaya mana abin da ya yi saura?wani mummunan jiri ne ya debeta badan tana zaune ba tabbas sai ya yi mata mummunan illah. Da kyar ta samu bakinta ya iya furta ,wacece RAIHAN? Cikin gatsali ya maida mata da cewa oh Rahim zan ce miki ba Raihan ba,tun da kema kin maida kanki kidahuma kamar yadda kika maida mutane,idan kuma har yanzu baki gane ba,to ina nufin kyakkyawar 'yarki da kika maida namiji Saboda son tsira da rayuwarta. wanda kuma hakan da kika yi Ni a gare Ni ya fi komai dadi a wajena,domin kin kawar min da hankalin sauran masu bibiyarta ,kin ga zanyi shagali na Ni kadai ke nan ba tare da sauran masu hari sun batan lissafi ba,kar ki dauka cewa zan tona wannan sirrin,a'a ba zan tona ba saboda nima yana min amfani,yanzu dai ga Raihan nan zan sake ta taho gida duk da cewa na fahimci ba Ni kadai nake bibiyar ta ba,amma dai ina da tabbacin cewa wani abu ne daban ba akan Ni wanda nake nema ba ne,na barki lafiya auntyn RAIHAN...daga haka kit ya kashe wayar yana mai kyalkyalewa da dariya,wayar ya mikawa wata budurwa yana cewa ku maida ita inda kuka dauko ta kar ku bude mata ido bare ku bari taga inda aka kawo ta",Yes oga ta fada tare da fita daga dakin. Tana zuwa ta kama Raihan da bata ma san inda hankalinta yake ba,dan tuni ta dade da sumewa. Wani irin kakkauran miyau aunty amarya ta hadiye tana mai jin wani irin tashin hankali da bata taba ji ba a rayuwarta,to ke nan ya kayi suka gano? Wane wannan ɗin? Shin wa zata zarga? Tana shirin sakin wani azababban kuka aka turo kofar aka shigo,kutt ta hadiye kukan lokaci daya ta nemo nutsuwarta da ta kasa zama akan fuskarta,zuba mata ido abbie ya yi kafin ya taka zuwa bakin madubi yana cewa ,duk lissafin me lissafi sai ya samu Wanda ya fi shi iyawa sannan shi buwayi gagara misali ba a yi masa wayo don duk dabarar ka akan kar ya jarrabe ka idan ya so sai ya yi ikon sa akan ka.dan haka damuwa ba ita ce mafita ba tuba da komawa turbar gaskiya shine daidai,wata kila hakan yasa Allah ya dubi bawansa da bai ji ba bai kuma gani ba ya taimake shi ya ƙare shi daga mummunan ƙaddara", yana zuwa anan amaganarsa ya dauki abinda zai dauka ya fice ya bar aunty amarya cikin wani sabon tashin hankalin da ruɗani me birkita ƙwaƙwalwa. Shin me maganganun abul Rahim suke nufi? Wane sako yake son isar min? Dan kuwa tabbas duk wanda ya ji maganganun nan zai tabbatar da cewa akwai gugar zana. Wata zuciyar ta ce",kawai ya fahimci kwana biyu kina cikin damuwa shi yasa yake miki nasiha ta wani sigar dan tayi saurin fahimta, ta gamsu da wannan tunanin dan haka sai ta shiga tunanin mafita da inda zata gano Raihan ba tare da kowa ya sani ba. Lokacin da Abbie ya koma falon baffa inda suke tare da wazir tun zuwansa tambayar da baffa ya yi masa na cewar ina Rahim shi ya sare masa gwiwa.duk da yasan cewa ba lallai ne baffan yasan Rahim ya dawo ba in dai ba shigowa sashen nasa ya yi ba, wannan dan nazarin da ya yi ne ya bashi kwarin gwiwar cewa ai Rahim ya riga shi zuwa gidan.abbie ya tashi ne dan ɗaukowa wazir katin daurin aurensa da Abbu ya kawo masa,a cewarsa ya bawa rahim ya rabawa ma aikata, tunda shi wazir din ba zai yi ba,shi kuma Abbie ya ce dole a bawa wazir din dan ba zai rasa wadan da zai bawa katin ba.shi yasa ya karba ya ce "shi zai bashi da hannun sa yasan ba zaiki karba ba. Wajen dauko masa katin ne ya tarar da yanayin da aunty amarya ke ciki,shine har ya tsaya ya danyi mata nasiha. Zama ya yi yana cewa wani abu ya dauke mun hankali ban duba Rahim din ba,amma bari na kira shi a waya ko zan same shi, shuru wazir ya yi ba tare da ya dakatar da Abbie din ba,tun da shi ya kira wayar wajen sau goma a kashe. Wayar bata shiga ba cewar abbie yana duban wazir da ya ke zaune a nutsen shi,fuskar nan a kame babu alamun wani abu na taba zuciyar shi. Baffa ya dan yi gyaran murya ya ce"ko ya kashe wayar? kasan haka yake da son kashe waya lokaci lokaci",shi dai wazir bai iya cewa komai ba ,amma tabbas ba zai bar gidan ba har sai yaga dawowar RAIHAN. A nan shima Abba yahya ya dawo ya same su zama ya yi yana amsa gaisuuwar A wazir cikin nutsuwa da mutumtawa. Tun suna jira a nutse har hankalinsu ya fara tashi, Abba yahya ya kira inna maimuna a waya ya tambayeta ko Rahim yana bangarensu,ta ce baya nan,daga nan itama tasan abinda ke faruwa, sai gata a falon Baffa hankali tashe kamar ance ba za a ga Rahim din ba. A nan suka ci gaba da zaman jiran tsammani har aunty amarya ma da ƙaraso yanzu,fuska jajir alamun taci kuka ta koshi. ................. Fitowar shugaban jam'iya daga wajen taro,kai tsaye gidan haɗuwar su na sirri ya nufa,a can ya tarar da su Dr sanate tare da alhaji sale,nan suka shiga tattauna abin da yake cizon ransu,tashin hankalin su bai wuce ace an dora wannan zargin akansu ba to amma idan suka tuna cewa dole sai anyi bincike sai hankalin su ya dan kwanta,duk da kuwa sun san cewa suma suna ruwa. Ya zamu yi da batun kashe wannan yaron?, Cewar Dr da rahim ya fi tsaya masa a rai, Alh sale ya ce"Ni ina ganin kawai mu kashe shi ko ma huta da ɗaya",shugaban jam'iya ya ce" babu yadda za ayi mu kashe shi ba tare da mun karbi video nan ba,fitar da video nan tamkar tashin alkiyamar mu ne,saboda duk alhakin abinda yake faruwa mu za mu dauka,Dr ya ce",yanzu goje ya tabbatar min da cewa suna gab da kama shi ,sai dai kuma wasu sun riga su dauke shi,sun yi niyar binsu gidan ,amma sai na hana su na ce su dakata idan suka ga basu sake shi nan da wasu mintoci ba,su shiga kawai su dauko shi ko tataya",wayar shi ce ta yi kara ya daga yana cewa goje kun taho da shi?yes hakan ya yi sai kun karaso",dariya ya yi bayan ya kashe wayar yana cewa,wadan da suka dauke shi sun fito da shi a sume ,sun kuma mayar da shi inda suka dauko shi,suna tafiya su kuma su goje suka dauko shi. Lokacin da su goje suka saka Rahim a mota akan idanun sury ne dan haka ta yi amfani da wannan damar wajen kara kusanta kanta da Rahim ɗin,dan alamu dai sun nuna cewa ba hannun mutanen kirki ya shiga ba.dabarar kiran 'yan sanda ne ya zo kanta,dan haka cikin sauri ta yi kiran bayan ta hau mashin ɗin a daidaita. Kasancewar yan sanda suna kewaye da ko ina na lungu da sakon garin,shi yasa Surry na fadar nomber motar suka gane cikin lokaci kankani suka kama su goje,da sauri suryy ta fito daga a daidaita tare dsp Haidar suka saka Rahim a cikin nafef su ka wuce har Haidar ɗin. A hankali wazir ya mike ya na duba agogon dake saƙale jikin tsintsiyar hannunsa,ɗan duban Abbie ya yi cikin nutsuwarsa ya ce"ya kamata mu fita tun da har yanzu babu wani labari",tun dazu dama kawai hakuri yake saboda abbie dake dakatar da shi,amma yanzu kam ba ya jin zai iya tsayawa jira,su ba sa ganewa ne amma sam hankalinsa ba a kwance yake ba. Aunty amarya ma da take jinta tamkar akan kaya tayi saurin miƙewa tare da cewa gaskiya zama bai ganmu ba,Rahim fa har yanzu yaro ne sannan ga irin aikin sa wanda yake cike da haɗari,dukan su miƙewa su kayi su ka fita har Hajiya goggo da ta fara daga musu hankali tun dazun.sai gashi gaba daya mutanen gidan sun fito ,abin da ya yi matukar bawa aunty amarya mamaki,mutanen da kome za ayi in dai akan batunta da na Rahim ne ba za ka ga kafar ko dayansu ba,daga su har surukan su idan ka ɗauke matar hamma idi,kallon su kawai ta dinga yi cike da nazarin su. Wazir yana kokarin shiga mota shida Abba yahya da hamma idi da dawowar sa ke nan,sai ga shigowar dan sahu nan har cikin gate ,hatta da securityn gidan gaba dayan su sun fita neman Rahim din da lokaci daya suka ji maganar batannashi. Kusan dukansu suka nufi a daidaita da suka fahimci Rahim ne a ciki,suryy bata da matsala ko da ace wazir ya ganta tunda tasan bai santa ba,dan ko lokutan da suke haduwa a gidansu tana gaida shi ba amsawa yake ba bare ya kalle ta,shi yasa kai tsaye ta fito a matsayin wadda ta taimakawa Rahim. Dsp Haidar ya bawa A wazir hannu tare da dukawa ya gaida Abba yahya da Baffa da Abbie,daga nan ya shiga basu bayanai akan komai kamar yadda Surry ta faɗa yadda abin ya faru,harma da machine din sa da aka taho da shi. Shi wazir ma bai saurari bayanan ba,tuni ya dauki Raihan cak ya yi sashen aunty amarya da ita. A hankali ya kwantar da ita saman lallausar katifarta,dan zuba mata ido ya yi har Saida yaji motsin antyy amarya da ta shigo da ruwa,Hajiya goggo da Inna maimuna na bayanta fuskokinsu cike da jimami akan abinda ya faru,Hajiya goggo kam faɗa take akan ita fa sai Rahim ya daina wannan aikin kar ake a kashe mata jika babu gaira ba sabar. Da kyar Abba yahya ya rarrashi Hajiya daga mitar da take yi,ya ce"da hamma idi ya rakata bangarenta,shi dama baffa bai cika fitowa ba saboda matsalar kafa. Ba dan Allah ba sai dan Abbie,su mama murja da surukansu ,suka zo duba Raihan ɗin,wadda ke sume har yanzu bata farfaɗo ba. Sai da kowa ya fice ,saura wazir da suryy da taƙi tafiya,sai kuma Abbie da aunty amarya,abbie ne ya ce" da suryy yarinya kema ki tafi gida kar a nemeki,mun gode Sosai da taimakonki", sunkuyar da kai ta yi kamar wata mutuniyar kirki,ta ce"shi ke nan Abba in sha Allah Gobe zan dawo na duba jikin nasa, Allah ya kiyaye gaba,"da Amin suka amsa amma bakin abbie da aunty amarya kawai ta ji,shi kuwa uban yan wulakacin har yanzu bata jin ya yi mata cikakken kallo daya kai tun shigowarta gidanma bata ji ko da tarinsa ba bare yayi magana.ƙwafa ta yi can kasan zuciyarta kafin ta mike tana mai yiwa Rahim fatan samun lafiya har waje aunty amarya ta rakata. Wlh sai na gano ko ma meye kuke boyewa,sai na cikawa Ruby alkawarinta,ta faɗa dai dai lokacin da security ya bude mata kofar sashen ta fita. A hankali Abbie ya dawo da dubansa kan wazir da ke tsaye saman kan Raihan idanun shi akanta,tamkar wanda a aka bawa gadinta. Abi ya ce" ya kamata ace ya farka yanzu, ko za a gwada zuba masa ruwa? Da sauri aunty amarya ta kawo ruwan robar da ke hannunta,karba wazir din ya yi,ya dan zuba a hannun sa kana ya sunkuya a hankali ya shafa mata a fuskar,bai sauke hannunshi ba,har sai da yaji ta kawo nannauyan numfashi ta ajiye,kafin kuma a hankali ta shiga bude idanunta da suka dan shige ciki. akansa idanunta suka fara sauka,saurin rufe idon ta yi tana tunanin ko mafarki ta ke,tunani ta shiga yi,sai dai ta gagara tuna komai bayan abinda ya faru a office da fitowar da ta yi sai haɗuwar ta da suryy,bayan haka ta kasa tuna komai. Maida kallonta ta yi kan Abi dinta,cikin raunin murya wanda ke nuni da halin da zuciyarta ke ciki, ta ce "Abi me ya faru da Ni ne?. Kama hannunta ya yi yana mai jin wani a bu har cikin ranshi,ya ce"babu komai Rahim ,amma dai yanzu ina so ka tabbatar min babu abin da yake damunka,"jin jina kai ta yi tana mai ɗan lumshe idanunta da take jin sunyi mata nauyi,aunty amarya za ta yi magana,abbie ya yi mata alamun ta yi shiru dan haka nan ya ji baya son duk wani abu da zata furta a wajen. Cikin kamewarshi ya dan dubi a gogon hannunshi ya ce"Abbie Ni zan wuce Allah ya bashi lafiya",Amin duka suka amsa, Abbie ya ce" ina so kayi saurin raba katin daurin auren nan,saboda ba mu da lokaci masu yawa kaji ko,in sha Allah Abbie zanyi yadda ka ce",daga haka ya fita daga dakin sai dai yana jin yadda idanun RAIHAN suke kanshi. Yana fita ta lumshe idanunta da suke kan bayanshi,tana binshi da kallon da ita kanta ba tace ga ma'anarsa ba. Samun kanta ta yi da Jefawa Abbie tambaya,ABBIE.daurin auren waye za ayi? Kai tsaye ya bata amsa da cewa daurin auren abokinka kuma ubangidanka,ko baka sani ba? Abbie ya kare ba shi amsar da tambaya,bata ce komai ba sai rufe idanunta da ta yi tana kokawa da zuciyarta da numfashinta kai da duk wani abu ma dake motsi a jikinta,aunty amarya ta ce" Rahim ka ta shi ka yi wanka ka yi salla zanje na kawo maka abinci kaji,sam Raihan bata gane abinda auntyyn ke fada,har suka fita daga dakin ma bata sani ba,kuma bata yi yunkurin yin wani abu daga cikin abinda auntyyn ta lissafa mata ba. Karshe dai har sai da auntyyn ta dawo ta taimaka mata da kanta ta kimtsa,ita kanta auntyyn bata da wata mutsuwa shi yasa ta kasa tantance halin da Raihan din ke ciki. Sai da Hajiya goggo ta kuma shigowa ta yi ta dubata,haka hamma idi da matar shi auntyy Zainab ,kusan a nan din suka raba dare kafin su wuce sashen su. Chibaɗo's hause........ A nutse ya kammala shirin sa na bacci,kafin ya janyo wayar shi ya danna kiranta. Zubawa wayar ido ta yi,sai kawai ta ji wasu irin kwalla masu zafi da rad'ad'isun wanke fuskarta,kafin a hankali ta saki shashshekar kukan da ya fara fitowa da wani irin sauti. Ya Allah ya furta a saman labbansa bayan jin ta daga wayar da biyowar kukannata da yake taba can wani guri ke bantacce daga cikin babbar zuciyarsa, RAIHAN ya furta cikin wani irin yanayi me kashe lakar jiki,jin ya kuma rikita ta yasa kawai ta kashe wayar gaba daya tare da kifa kanta tana ci gaba da fitar da hawayenta masu matukar radadi da taba zuciya. Shima rufe idanunsa ya yi, yana shuru da dogon tunani. _______________ Kwana biyu biki sai matsowa yake ,shirye shirye a gidan chibado kamar babu mutuwa,ji suke da bikin ko dan sun jima ba su yi auren ba ne,oho. A bangaren Raihan kuwa gaba daya ta ajiye zuwa aiki,ta rufe wayarta ,ta ki bari kowa ya ganta, Abbie bai tambaye ta komai ba,aunty amarya kuma tana cikin damuwar da ta fi ta Raihan a cewarta. Suryy kuwa tun da suka hadu da Raihan din zuwan ta washe garin abin da ya faru,bata kara bari ta ganta ba,saboda haka nan ta ji bata yadda da suryyn ba,ko ba haka ba dama can Raihan bata sakin jiki da ko wane mutum,idan har ba ita ta aminta da hakan ba. A bangaren Labarin da zasu saki a washe gari kamar yadda suka tsara , hakan bata samu ba,tunda mai gaiyya mai aiki bata zo ba. Tuni shelar auren AHMED WAZIR CHIBADO ta cika gari saboda masu abu da abin sune,kafafen yada labarai na su da na makotansu,tuni suka samu abin yi, sai dai fatan Allah ya Kaimu jibi juma a musha shagali......✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page24 ``` Haɗuwar tasu sai cikin dare ta kasance,haɗuwar takasance kebantacciya kuma ta sirri,daga ur exsellency sai Abba yahya sai kuma dufuty. Bayan shuru na wasu yan sakanni baka jin komai sai karar fanka da na urar sanyaya guri. Abba yahya ne ya fara magana bayan gyatta zamansa da ya yi tare da gyaran murya,ur exsellency ka kiramu kuma daga ji kiran yana da matukar muhimmanci dan haka muna saurareka",jinjina kai dufuty yayi cike da nuna gamsuwa akan maganar da Chip accounter Abba yahya ya yi.cikin nutsuwa ur exsellency ya dube su fuskarsa na nuna alamun damuwa,ya ce"abinda yasa na kira ku shine magana za muyi akan maganar takara da kuma waccan maganar da muka tattauna a dazu,gyara zamansa ya yi yana ci gaba da cewa,ina so muyi sulhu a tsakaninmu akan wanda zai ci gaba da rike kujerar gwamnati,abu na farko shine kunsan cewa ina da damar kara neman kujerar nan a karo na biyu,sai dai kuma ba zan yi hakan ba saboda gaba dayanku na karance ku akan son hawa kujerar nan,to gudun kar mu dannewa juna hakki ko kuma hakan ya kawo matsala a tsakaninmu yasa na ce mu zauna domin yin maslaha akan hakan,me kuke gani mu dai dukanmu a bu guda ne duk wanda ya hau bamu da matsala da haka a cikin mu ukunnan,Ni dai bani da matsala sai dai matsalar da nake hango mana wadda zata dakushe tafiyar mu bai wuce wannan babban al'amari dake faruwa a cikin jahar nan tamu ba,me kuke gani akan hakan?ya tambaye su idanunsa akansu yana mai nazarinsu. Dufuty ne ya fara magana da cewa,tabbas maganarka haka take,amma Ni dai a nawa tunanin da kuma hangen bai kamata ka sauka a kujerar nan ashekarar nan ba tare da kayi tazarce ba,kuma kaine muke da yakinin cewa talakawa zasu kuma zabenka sai dai wannan matsalar da take faruwa wadda ake son jinginata ga tafiyarmu",ko ya kace chip accounter?ya fada yana duban Abba yahya",numfasawa Abba yahya ya yi sannan ya dora da cewa,maganarka haka take dufuty yanzu muna akan cigaban zamanka akan gwamnati ,abinda ya kamata muyi yanzu shine zakulo inda matsalar nan take,muyi kokarin binciko wanda yake aikata wannan mummunan ta asar ko da kuwa acikinmu nan ne,kaga daga nan ne zamu san inda muka dosa",ya karasa maganar yana mai kafe ur exsellency da ido wanda shi kuma sam bai fahimci gugar zanar da Chip accounter yake masa ba,shi dai dufuty yaso ya gane wani abu saboda yanayin kallon da ya fahimci Abba yahya yanayi wa ur exsellency din,bai ɗaice komaiba ya hadiye tunaninsa da mamakin kalaman na Abba yahya a ransa. Maganarka haka take dan haka za muyi kokarin hakan in sha Allah kuma za muyi nasara", Allah yasa suka fada baki daya. ............ Suryy wai me a ke ciki ne ? Kin ga fa yau saura kwana biyu daurin auren nan,hankalina ba a kwance yake ba,kina ganin fa yau Even na uku fa ,amma babu wanda wazir ya halatta ,idan na yi wa innawuro magana sai ta ce na yi hakuri wai da yaya a kayi ya amince da auren ma, gaskiya fa suryy ba zan iya wannan rayuwar da wazir yake so na yi a gidansa ba,a yadda na tsara rayuwar SOYAYYA a gida na ban yi zaton auren zai zo min a haka ba, Kum....Surry ta yi saurin katse ta da cewa kar ki ce ko mai, rubyy kin san dama haka zata faru tunda kika ce kina son Wazir,kuma kar fa ki manta wazir irin mazajen da babu mai gane kan su ne idan ba Macen da suka mutu akan ta ba,ki ƙaddara cewa wazir ba zai taba sonki ba ko ya nuna miki soyayya in dai har da wata a zuciyarsa",suryy kullum haka kike fada amma har yanzu kin kasa gano min abun da ke lullube a zuciyar Wazir,wani kallo sury ta yi mata kana ta yi Murmushin takaici ta ce"wato duk kokarin da nake miki baki gani ba ko,ta yaya zan san wadda ke zuciyar wazir idan har ban bincika ba? Ganin ran sury ya fara ɓaci ya sa ta sauko,cikin kwantar da murya ta ce" sorry Ƙawata wlh hankalina ne a tashe, abin da ba za ki gane ba ne ina son Wazir karshen so,son da zan iya yin komai akansa, kuma duk abin da zai yi min zan jure,yanzu dai me ake ciki? Numfashi suryy ta fesar kana ta dubi rubyy ta ce" idan mun gano yana da wata kafin daurin auren me za ki yi a akan hakan? Sannan idan ba mu gano ba zaki fasa auren ne ko me kike nufi? Dan zubawa suryyn ido ta yi kafin ta yatsine fuska ta ce" ,amsar tambayar ki ta biyu shine bazan fasa ba za mu ci gaba da bincike ne har mu gano, kuma ko ina cikin gidan babu abin da za mu fasa kin ga daukar mata ki sai ya fi min sauki tun da ina a matsayin matarsane ba wadda yake shirin aura ba. Amsarki ta farko kuma,ke ma kanki kin san zan yi ko mai ne akan hakan ko da ya haɗa da kisa ne in dai akan wazir ne ", Na amsa miki tambayoyinki nima sai ki amsa min nawa,ta faɗa tana gyara zaman gashin da a ka kara mata. Dage kafadu suryyn ta yi alamun bata da damuwa da hakan,kafin ta gyara zaman ta , ta ce ",rubyy akwai wani boyayyan sirri da nake shirin bankadowa idan har na tabbatar wanda shine zai kawo karshen binciken mu,ina fata na samu kafin jibi,idan kuma ban samu ba to ina tabbatar miki da cewa ba zai dauki lokaci me tsayi ba,amma fa duk na tabbatar da hakan sai kin kwanta a gadon asibiti idan har bai zama sanadin bugawar zuciyar ki ba. Cikin tashin hankali rubyy ta bude baki zata yi magana,shukrah auta ta yi sallama tare da turo kofar ta shigo,lafiya? ta tambayi shukrah idanun ta na nuna tsananin tashin hankalin da ta shiga lokaci daya,ey innawuro ce ta ce kizo yanzu tana jiranki a kasa,to gani nan", shukrah ta ce",a'a fa aunty rabi ki ta shi muje kin dai san halin innawuro dan cewa ta yi mu taho tare,ina zuwa ta ce",da suryy tana tashi suka fice daga dakin. Fitar su bai fi da sakanni hamsin ba,wayar suryy ta fara kara alamun kirane ya shigo mata,ta dan jima tana kallon nomber ganin an yi hiding dinta,sai da aka kuma kira kana,ta daga ba tare da ta yi magana ba. Jin kuma anyi shuru yasa dole ta fara yin magana, hello wake magana? Ina fata ina magana da suryy kawar rubyy ne ko? Ey ita ce",ta faɗa cike da kaguwar jin wanda ke kiran. Na san duk wani bincike da kike a kan Rahim Muhammad nurr akan sanin alakar dake tsakaninsa da ubangidansa wazir,wanda za a daurawa aure ranar juma'a nan,dan haka ina so ki biyo wannan address ɗin kizo inda nake zan taimakeki da bayanan sa,amma akwai sharaɗin aiki tare da Ni,,,daga haka aka yanke wayar... Zubawa wayar ido ta yi bayan ta yanke,wani tunani ta yi da yasa ta yi saurin miƙewa. barin gidan ta yi ba tare da rubyy ta sani ba. Kai tsaye address ɗin ta bi,ko tsoran kar a cutata mata ba tayi ba,zuciyarta tuni ta tafi akan biyan buƙatarta,wanda ba wai tana yi dan kawar Tata ba ne,a'a kawai tana yi ne dan biyan buƙatar zuciyarta. A bangaren su shugaban jam'iya kuwa,tun da suka ji an kama mutanensu,hankulansu ya tashi,to amma kira daya suka yi a ka sake su ba tare da sunan ko daya daga cikin su ya fito ba,a cewar su wannan matsalar ba ta bangaren tree full Y trues ba ce,dan haka babu tunanin ma ya san da maganar bare ya yi musu kashedi da barazanar da ke matukar razana su,hakan da ya faru ya sa suka dan saurara da bibiyar Rahim din. Fuskar suryy cike da farin ciki ta fito daga mahadar ta su,duk da cewa ta yi matukar girgiza da samun bayanan kuma dama ta fara zargin hakan,sai dai tunaninta yadda hakan zai yiwu ne ya sa ta kasa gasgatawa take kuma son Dada zurfafa bincike dan samun tabbaci,sai dai kuma a lokaci daya ta samu yayewar bakin cikin saboda hanyar magance matsalar da ta samu a lokaci daya da abokin aikin nata da ko dan yatsan shi bata gani ba,hakan ya yi mata daidai idan ya so sai ta ji da matsalar rubyy,indai burin ta zai cika za ta iya yi masa ko wane irin aiki yake so,da wannan tunanin ta wuce gida ,daniyar sai anjima ta koma gidan bikin. AUNTY AMARYA....... Yanzun ko yaya ta ga wayar ta na haske sai zuciyarta ta buga,zubawa wayar ido ta yi tana tunanin ta dauka ko kar ta dauka,gashi kwana biyu sam bata samun wayar Dr Sabo shi yasa abin ya haɗe ya yi mata yawa,zuciyarta na bugu ta daure ta daga wayar. Cikin wata irin murya da kullum sai ta ji an sauya ta,a ka ce". Ki bawa yaro na auren 'yarki,in dai kuna son taci gaba da rayuwa,kuma cikin kwana uku tak nake bukatar hakan,shima saboda na bawa zuciya da kwakwalwarki dama ne,idan kuma ba haka ba to wlh sai na kashe RAIHAN.....ƙit aka kashe wayar. Wata irin zufa ce ta tsananin tashin hankali ta shiga keto mata,innalillahi bakin ta ke iya furtawa kawai,cikin kankanin lokaci idanunta suka kada kanta ya shiga wani irin sarawa kamar ana buga adda,jikinta kuwa babu inda baya yin rawa,tunaninta neman gushewa yake,yadda ta jike da gumi kaika ce shaya ta shiga,wani kiran ne ya sake shigo mata,wata irin zabura ta yi tana duban wayar da dukkan idanunta da zuciyarta da ke neman bugawa,dishi dishin da take gani yasa ta kasa fahimtar wanda ya kuma yin kiran,hannunta na rawa ta danna tare da rintse idanunta,tana shirin jin abin da zasu kuma bukata. Amma kuma sai ta ji sabanin Muryar da ta tsammaci ji ,Dr Sabo ta faɗa cikin rawar murya,kawai sai ta saka wani irin kuka me ban tausayi kamar zata hadiye zuciyarta,cikin kukan take cewa Dr Sabo ina cikin tashin hankali za su raba Ni da farinciki na,wlh ina son RAIHAN ba zan iya rabuwa da ita ba,idan har kaddarata ita ce ta rabuwa da Raihan,ina rokon Allah ya canja min ita ko Ni na mutu ita ta rayu,amma ba zan iya jurewa ba,ya isa haka ramla yanzu me ya faru? Da kyar ta nutsu ta yi masa bayanin abinda ke faruwa ba ta boye masa komai ba,tun da shine abokin cin mushenta. Ya jima yana shuru dan har ta yi zaton ya sauka daga kan layi sai kuma ta ji ya ce",amarya ki nutsu in sha Allah babu abin da zai faru akwai mafita ki kwantar da hankalinki,bana so ki tashi hankalinki har Raihan ta san abin da ke faruwa ta dalilin damuwarki,ki zuba idon ganina gobe in sha Allah,dan abinda yasa na kira ki kenan,sosai ya kwantar mata da hankali har sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan su kayi sallama,ta kuma kashe wayar ta gaba daya. ............. Abba yahya Sai da ya gama cin abinci ya nutsu tukunna , sannan ya fuskanci inna maimuna,gyara zamanta ta yi itama tana fuskantarsa saboda ta fahimci akwai magana a bakinsa. Kin san kuwa yau me ya faru?ya tambayeta da alamar shima abin yana taba shi tare da saka shi cikin mamaki,girgiza kai tayi ba tare da ta iya cewa komai ba,a nan ya zaiyane mata duk tattaunawar da su kayi da ur exsellency,kai me ka fahimta a nan? Inna maimuna ta tambayeshi, murmushi ya yi tare da cewa,da muka nuna cewa yaci gaba da jagorantar jahar mu,bai yi musu ba, sannan bai nuna min komai akan gugar zanar da nayi mashi ba,Ni dai na fassara hakan da tsananin kwarewa a makirci,zan ci gaba da bibiyarsa har sai na gano duk wani shirinsa da makircinsa akan dan uwana da kuma jahata",na baka goyan baya a kan hakan.. RAIHAN...... Sai wajen karfe goma na daren ta kunna wayarta,dai dai lokacin da take zama kusa da Abbie,jikin ta duk a sanyaye,fitowar ta ma daga dakin bai fi sau biyu ba tunda abin ya faru,yanzun ma daurewa ta yi saboda tasan auntyyn daurewa kawai take yi bata kula ta ba,sai dai bata san cewa itama auntyyn damuwa ce ke neman kwantar da ita ba. Duban ta Abbie ya yi cikin kulawa da wani yanayi na tausayi da ke shimfide saman fuskarsa,ya ce" Rahim ya dai ko har yanzu jikin ne? Murmushi ta yi wanda ya nuna sanyinta a fili,kana ta ce"Abbie jikina ne kawai a mace",ai kai naga baka gajiya da zaman daki kamar wata mace,kai dan irin abokan nan ma duk baka da su,dole ne ka dinga kadaici,numfashi ta dan fesar a ranta tana cewa anzo gun dama irin wannan maganganun da Abbie yake yawan yi ne yasa take kauracewa zama da su a falon,bata samu damar cewa ko mai ba wayarta ta shiga ringing wanda hakan ya yi mata dad'i,tsam ta mike ta nufi hanyar dakinta tare da kokarin duba fuskar wayar dan ganin me kiran. Zuba wa fuskar wayar ido ta yi,kafin a hankali kamar me ciwon hannu tasa hannu ta danna ok,shuru na kusan minti ɗaya ,kafin ya aje miskilancin nashi ya furzar da wani dan huci, sannan cikin kamammiyar Muryar sa me cike da tarin nutsuwa ya ce", lafiyar ki fa?runtse idanun ta ta yi cike da takaicin sa, wannan wace irin tambaya ce",me yasa kika koyi wannan abun?ya kuma jeho mata tambayar da sam bata fuskance ta ba. Da kyar ta bude baki ta ce"me ke nan? Shuru ana miki magana",ashe ba dadi ta faɗa kasa kasa,ƙit ta ji ya kashe wayar,tabe baki ta yi tana hararar wayar kamar ita ce tayi mata laifin. _______________ Wai Rahim ba zai fito mu tafi daurin auren ba ne?Abbie da ya fito a shirye sai kamshi yake ya yi kyau sosai ya fada yana duba a gogon da ke daure a hannun sa, RAHIM ba shi da lafiya auntyy amarya ta faɗa tana basarwa da mika mishi key din mota,dan jim ya yi kafin ya dubi Hamma idi dake shigowa ya ce" ,mu wuce kawai sai mun dawo,hamma idi ya ce",ina Rahim din? Baya jin dadi ba zai samu zuwa ba",zaiyi magana Abbie ya tare shi da cewa muje muna makara,yaya da Baffa na jiranmu,dole Hamma idi ya hadiye abinda zai faɗa ya juya suka fita aunty amarya na yi musu Allah ya kiyaye. Ajiyar zuciya ta sauke tana mai duban hanyar dakin RAIHAN ɗin,kafin ta nufi dakin. A kwance ta same ta, da alama dai ko tashi ba ta yi ba,tun sallaar asuba,karasawa ta yi ta shiga taba ta, Raihan lafiya dai har yanzu baki ta shi ba?ga shi sallar walha ba,,a hankali ta bude idanunta da su ka yi mata nauyi kamar an danne su da bulo,bata ce komai ba sai maida kanta da ta yi ta kuma rufewa,taba jikinta aunty amarya ta yi sai ta ji alamun zazzaɓi,ajiyar zuciyar damuwa ta dan sauke kafin ta juya ta fita daga dakin. Sai da aka gabatar da sallar juma a,kafin a fara daure dauren auren da ake da su ranar,sai da aka daura aure uku kafin a zo kansu,mamaki ne ya rufe wazir lokacin da yaga harda baffa a daurin auren,tunda yasan yana fama da ciwon kafa ba ko ina yake zuwa ba,bai gama da wannan mamakin ba yaga baba buzu duk da cewa bai sansu ba amma kallo daya zakayi musu kasan cewa jinin Raihan ne,daga shi har kawun Raihan ɗin,sai wani mutum da shima yake jerin su,wanda bai san fuskarsa ba,amma tunanin shi ya bashi a cikin abokan Abbu yake. kawar da tunaninshi ya yi da komawa kan tunanin abinda yake cin ransa,babu yadda za ayi ka gane wani abu akan fuskar sa farinciki ko sabanin haka. Daurin aurensa da rabi Mustafa chibaɗo aka fara gabatarwa,kafin ya ji wani abin da yasa ya kasa boye razanarsa da mamakin sa,duk da cewa tsananin jan ajinsa da kamewarsa ya biye kaso dari na razanar da mamakinnasa,da sauri ya dubi Abbie dake gefansa,sai dai kuma ya kasa cewa komai sai kawai ya maida kansa kasa yana kissima da tunano sunan da aka kuma daura auren da shi. RAIHAN fa,ya a kayi hakan ta faru? Waye yasan sirrin ƁOYAYYIYAR RAIHAN da har ya daura masa aure da ita?wai me ke shirin faruwa? Abban rabi ma zare ido ya koma yi saboda jin wani auren daga sama ba tare da zato ko tsammani ba. Na gode Dr Sabo yanzu za mu iya wucewa gida saboda mu tattauna,cewar Abbie kenan ya fada yana duban Dr Sabo dan jin me zai ce ",babu matsala Dr Sabo ya fada suna mai yin musabaha da Liman. Daga nan gaba daya suka rankaya suka fita daga masallacin,suna mai ci gaba da karbar gaisuwar masu fatan Alkhairi,wanda da yawa mutane basu san komai akan auren ba,bare su fara tunanin wace ce RAIHAN,ko yadda aka yi auren ya zama na mutum biyu.shi dai wazir bin su kawai yake da kallo ,sai dai baka taba gane yanayin da yake ciki,tunda da yawa mutane sun san yadda yanayin sa yake. Zamewa ya yi ya nufi mota inda securitynsa yake tsaye yana jiransa,sai dai kafin ya saka gangar jikinsa cikin motar,wayar shi na fara sanar da shi a na kiran sa,a hankali ya zaro wayar ya dan duba samanta,sai ya ga sunan abbie,karawa ya yi bayan ya daga,ba gida za ka wuce ba ka wuce can gidan saboda nan ne za mu yi magana a nutse babu hayaniya,",ok ya fada yana karasa shiga motar,gidan su Rahim za mu je",ya fada yana mai kwanciya tare da lumshe idanunsa yana ma rasa irin tunanin da zaiyi. Suma su Abbu nan suka nufa bayan sun gama sallamar bakin su,shi ma dai Abban rabi kallon su kawai yake bakin sa da jikinsa duk a mace saboda bai san komai akan abin da yayan nasa ya yi ba,wanda alamu duk ya nuna cewa yasan komai kuma dasa hannun sa komai din ya faru...........✍🏽 [12/21, 12:40]: *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page25 ``` A bangaren amarya rabi kuwa,tana can cikin farin ciki,duk da cewa tana jin wani faɗuwar gaba me tsanani tare da bacin rai,sai dai bata kawo komai ba tabarshi akan kawai basu samu yadda suke so akan bincikensu ba ne, sai dai kuma fariincikin aurenta da wazir ya danne wannan takaicin,hakan yasa ta Basar da wannan bacin ran ta cigaba da walwala a matsayin ta na amarya. Mummunan labarin da ya same ta daga gurin friend dinta maza da suka halarci daurin auren shi ya ruguza duk wani farinciki da walwalarta. Ko da taji labarin ba ita ka dai aka daura aurenta da wazir ba,zubewa ta yi a take a wajen ta sume. Cikin shakku innawuro take duban haffiz dan goggo ta Kano,wlh innawuro ba rabi kawai ya aura ba da wata, da kunnena naji amma idan baki yarda ba ki kira su Abbu a waya",dakatar da shi ta yi ranta a matukar bace ta ce" bari kawai duk inda su kayi ina zasu zo nan su same ni?,ta tambaye shi tana zuba masa idanun ta kusan irin na wazir,da sauri ya jinjina kai yana mai tashi daga gurin dan kar bacin ranta ya ɗora akansa,daga ita kuwa bai kara fadawa kowa ba ya shiga sabgar gabansa. A can sama kuma dakin amarya dakyar kawayenta suka samu ta farfaɗo da taimakon ruwan da suka dinga zuba mata. Kuka ta sa tana mai duban Surry cike da neman karin bayani tare da kallon tuhuma,fahimtar hakan da sury ta yi yasa ta yi saurin girgiza kanta,tana karawa da cewa wlh rubyy ban san komai ba,Ni kaina daga sama naji zancan da matukar mamaki ya nemi tafiyar da numfashina,duk wahalar da nake yi ban samu amsar ko mai ba sai lokacin da bashi da amfani,ta yaya aka yi wazir ya shammace mu? Wai shin ma wacece RAIHAN? Me yasa a duk bincike na ban taba cin karo da komai sunan ta acikin rayuwar wazir ba? Anya kuwa wannan al'amarin babu wani boyayyan abu a cikin sa? Tunawa da wani abu da ta yi wanda ya yi daidai da tuna sunan da ta ambata na Raihan yasa ta wata irin zabura ,idanun ta gaba daya a waje numfashin ta har wani sama yake yi. Kar dai mutumin nan yaudara ta ya yi? Ta faɗa tana mai figar jakarta,ko duban gaban ta bata yi ta fice daga dakin ba tare da ta saurari rabi dake tsimayin jin ta bakinta ba. Kai tsaye gidan abbie suka wuce,babu mai cewa komai har suka karaso,sai dai dukan su da akwai abin da yake damun su. A falon baffa suka yada zango inda suka sami wazir a can din yana jiran karasowar su,kamar ko da yaushe babu komai akan fuskarsa komai ya boye shi can kasan zuciyarsa, ba za ka taba gane cewa yana cike da dinbin mamaki ba,ba za ka gane cewa ya shiga rudani ba,yadda ya saba boye komai yau din ma ya boye abin shi,dan haka dukkan su babu wanda ya fuskanci halin da yake ciki. Zama su kayi tare da gabatar da addu'a,daga nan baffa ya dubi Dr Sabo ya ce ",Dr muna sauraron ka". Aunty amarya na kokarin shiga kiching wayar ta ta hau ruri kamar dama jira ake ta bude wayar,cikin dan kwarin gwiwar da take samu daga Dr Sabo ta daga ba tare da ta ce komai ba,dole zaki yi shiru saboda kin san munfincin da kika hada,to ki sani cewa ba tsira kika yi ba, sannan kuma ba ki tseratar da Raihan daga tarkona ba,auren da kika yi mata yana daga cikin makullin bude tashin hankali da wahala a gareku,dan haka ki jira yi sakamakon da zai biyo baya",ba tare da ya jira yi cewarta ba ya katse wayar. Sakaro aunty amarya ta yi tana mai zurfafa tunani,kallon wayar take kamar ita ce zata bata amsar tambayar ta. A falon baffa kuwa bayan su isu babu wanda suka kuma nema cikin zaman nasu,kaf Dr Sabo ya kwashe abin da ya faru tun daga haihuwar Raihan har zuwa yau ya sanar da su baffa,dukkan su labarin ya zo musu a ba zata , ya kuma dimautasu,sai dai daga abbie abun ba haka ba ne,dan ga dukkan alamu ya san komai. Abbie ne ya gyara zaman sa tare da yin gyaran murya ya ɗora da cewa,baffa abin da yasa ban sanar da kai ko yaya ba, shine nima nayi hakanne domin na bawa ramla mamaki na kuma nuna mata kuskuren abun da ta aikata ba tare da tunani ko shawarar mu ba,kai kuma nasan idan na sanar da kai zaka ce sai an zauna da ita an fada mata komai." Tun wane lokaci ne kai kasan da maganar?baffa ya tambayi Abbie fuskarshi cike da mamakin da ya kasa barinsa. Baffa na dan jima da sani dan zan iya cewa tun lokacin da Dr Sabo ya bar kasar nan,kuma bani na nema ba shi da kansa ya ga dacewar na sani din ba kuma tare da ya sanar da ramla din ba,dan duk lokacin da ya yi mata maganar ya kamata a sanar dani bata bari ,tsoro ne yake shiga ranta acewarta idan na sani hakan zai bawa makiyanmu kofar sanin RAHIM ba namiji ba ne.shi yasa ko da ya sanar da Ni ban yi wani yunkuri a gaban idanun ta ba,sai dai abin da ba ta sani ba ina biye da ita duk abin da yake faruwa na sani,ko da ban sani ba Dr Sabo yana sanar da Ni kamar dai abinda ya faru na shekaran jiya,ina zaune Dr Sabo ya turo min duk abin da ya faru tsakanin lamra da wannan me yi mata barazana ɗin,da farko mun so muyi bincike dan kama mutumin ,to sai kuma muka fahimci cewa abun ba karami bane dan kuwa ya toshe duk wata hanya da za abincike shi, Sannan bamu da wata hujja ta gano shi din waye. A lokacin da nake zaga babban office Dina na kamfanin audigar Raihan,a nan na hango katin daurin auren wazir a kuma take a wajen mafita ta zo min ,ban yi kasa a gwiwa ba na nemi a minina Alhaji chibaɗo babu mata lokaci ko noke noke na sanar da shi abin da ke faruwa ta yadda zai fahimta,sannan nazo da kaina nasanar maka a yadda muka tsara abun a gurguje kafin mu yi zama irin wannan,,shi ne dalilin da yasa muka hada aurensu duka biyun da rabi da Raihan,kuma shi wazir yasan komai hakan ba zai sashi ya razana ko daga hankali ba. Shi kuma Mustafha mun sa shi cikin lamarin ne saboda shine uban rabi ,dan haka muna so a ci gaba da rufa batun nan har zuwa wani lokaci tunda har yanzu bayan mu din babu wanda yasan wacece RAIHAN. Baffa ne ya tari mfashinsa da cewa, meye hujjar ka ta mu cigaba da rufe wannan al'amari?Dr Sabo ne ya amsa masa da cewa baffa muna so ne mu yi bincike a nutse mu fara gano wannan mutumin da yakewa amarya waya,mun tabbatar da cewa idan muka kama shi za mu iya samun ragowar wadan da suke tare da shi,dan abin da ya yi ya nuna mana cewa yana da hannu a wancan lamarin na farkon haihuwar Raihan da ake son kashe ta,kuma muna ci gaba da bincike akan nos din da lamra ta ji a na bawa wannan aikin.idan kuma har muka bari maganar nan ta fita zasu yi kokarin kufce mana ne ko da kuwa suna kusa da mu",jinjina kai baffa da abbu su kai cike da gamsuwa,Abban rabi ya ce",insha Allah wannan ba matsala ba ce,kuma babu wanda zai ji wannan maganar ,muna fata Allah ya bamu nasara akan makiyan mu,da Amin suka amsa baki daya. Abba yahya ya gabatar da addu'a tare da fatan samun nasara akan makiyansu na fili da na boye. Wazir dai yana zaune kamar wani status,har yanzu bai ce komai ba kuma babu wata alama da ta bayyana akan fuskar shi,baya ga sassaucin da take yi idan yana gaban iyayen shi,abbu ne ya dube shi cikin natsuwa da son karantar ko kadan ne daga abin da yake binne a zuciyar shi wanda yasan cewa da kamar wuya.ya ce"ya dai wazirin gida baka ce komai ba?cikin biyayyarshi da Ako da yaushe ke karawa iyayen nasa kaunarsa ya ce"babu damuwa Abbu Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi ",Amin ya rabbil alamin suka hada baki wajen amsawa,Abba yahya ne ya dan numfasa tare da cewa, sai dai kuma abu daya da nake tunanin yadda za ayi da shi ,shine ta yaya za a boyewa mahaifiyarsa da kuma kakarsa,tun da nasan cewa a yanzu haka tuni labari ya kai musu cewa da mutum biyu aka daura auren? Dan jim su kayi kafin, Abban rabi ya ce"wannan ai ba wani abu ba ne,karfa ka manta cewa mu ne ka dai muka san da Raihan ,dan haka ba sai mun sanar da su kan zancan ba,kawai dai wazir ya kawo matar da yake so an hada an aura masa duka biyun ",baffa ya ce" kuna ganin hakan ya yi dan bana so daga baya wata fitina ta bullo",Abbu ya ce"in sha Allah babu abin da zai faru in dai muna tare da addu'ar ku",addu a kam ai anayin ta sai dai kawai Allah ya cigaba da dafa mana ya kuma shiga tsakaninmu da makiyanmu,"Amin baffa suka amsa,daga nan su kayi sallama dan tafiya ,shi wazir ma kafin su mike shi ya riga su fita ba tare da ya bari sun fahimci abin da ya kumshe a zuciyar sa game da auren nasa da Raihan ba. CHIBADO's HAUSE........ Kallo kawai innawuro ke bin su da shi bayan sun gama bata labarin da take jin shi kamar tatsuniya,shi kuwa gogan naku ko binsu sashen abbu bai yi ba,dake a can suka kira innawuro saboda nan ne babu jama a.Abban rabi ne ya kuma duban rabin da suka kira ta itama dan fita hakkinta a matsayinta na uwargidan da a kayiwa amaryar bazata,kuka take kamar ranta zai fita ji take tamkar ta sokawa kowa na wajen wuka,kai ita fa ji take zata iya halaka kanta ta kuma halaka wadda ake kira mata a matsayin amaryar wazir,cikin fada me kama da tsawa Abbanta ya ce",Malama ki mana shuru kan ki faraune ko kuma ƙarau?Ni sai nake ga ma kamar wazir din shi ya cancanci ban hakuri saboda bake yake so ba amma ya hakura ya yi mana biyayya,to me yasa mu kuma ba za mu kyautata masa da bashi abin da yake so ba?wannan ma ai shirmen banza ne. Ya kare maganar da jan tsaki yana hararar ta. Abbu ne ya yi masa magana akan ya rabu da ita ai abinda aka yi mata akwai ciwo dan ta fitar da abin da ke ranta ba aibu ba ne. Innawuro baki ce komai ba?ya maida hankalinsa kan tsohuwarshi,wani banzan kallo ta yi masa kafin ta bude baki cikin takaicinsu da ya kasa barinta ,ta ce" to me kuke so na ce? Tun da ku iyayensa kun yanke hukunci da abinda kuke ganin ya fi ai Ni bani da ta cewa,amma ku sani cewa Ni sam ban yarda da wannan auren ba,saboda ban san wacece ba ,ban kuma san yar gidan wacece ba,dan haka ba zan yarda akawo min wadda ban san ya tarbiyyar ta yake ba ehe kunji da kyau.kallon juna su kayi kafin kamar hadin baki su ka fara bata hakuri,amma ko gezau innawuro ba ta yi ba,sai ma umartar su da ta yi su ta shi su bata guri kar ta faffalla musu mari agaban yarsu.babu yadda suka so haka suka tashi sumi sumi suka bar falon.ita kuma rabi abin da innawuro ta yi shi ne ya dan sama mata nutsuwa ita ma ta ta shi ta fita zuciyar ta na saka mata mugayen nufi akan ko ma wace aka aura ma wazir din,tunda dama nemanta suke ido rufe ,ita ce ta hana zuciyar wazir ta so kowa,kai ita fa gani take yi ma kamar karya ne ba wazir ne yake sonta ba,wata manakisar dai ake son shirya mata.(harda baban naki hhh). Suryy........... Cikin kankanin lokaci ta isa inda tasan zata iya ganin sa,tun da har yanzu bata san takamaiman matsugunin shi ba,zuciyarta da idaniyarta kukan zuci kawai suke yi,fatan ta kawai ta yi ido hudu da shi ta ji dalilin yaudararta da yayi,yanzu ne take ganin wautarta haka kawai bata san mutum ba ta dauki yarda da amana ta ba shi kaico da makauniyar zuciyarta,ashe ita ta yiwa kanta ramin da zata faɗa,ta jima a gurin tana jiransa kafin ta hango shi cikin shigarsa da ta fahimci kullum ita yake yi,har yau bata san fuskarsa ba,bata da hujjar da zata neme shi idan ya bace mata saboda bata taba sanin kamanninshi ba,hannun da yasa ya kifta idanun ta da shi ne ya sa ta dawo tunaninta wanda bata Ankara ba har ya samu mazauni yana fuskantarta da boyayyan fuskarshi sai idanun shi kawai da take gani su ma din ba ainahin su ba ne ta ke gani. Cikin bacin rai ta fara magana kamar zata yi masa duka saboda tsananin haushi da bakin ciki da takaici mai dimbin yawa da ya tokare kashin zuciyarta take ji har bata iya hadiyar miyau da sakin numfashi yarda ya kamata. Me yasa kayi min haka? Me ye shirinka akai na? Meye dalilinka na yin amfani da Ni wajen cikar burinka? Sannan kuma kai din waye kuma Me yasa ka haɗa auren wazir da Raihan a maimakon maganar da mu kayi da kai akan zaka sa a baka auren ta?. Shuru ta yi tare da zuba masa idanun ta ko Allah zaisa ta gano kamanninsa,sai dai ina hakan ya zama abu me wuya a gare ta,miƙewa ya yi tsaye hannayen shi goye,zagaya ta ya shiga yi sai ka ce wani me aikin sihiri,sai da ya yi hakan sau wajen uku kafin ya dakata ya kuma zuba mata jajayen idanun shi dake tsorata mutum me imani. Ke ba ki isa na yaudareki ba,ke baki isa na janyo hankalinki ta wata sigar ba,sannan kuma baki isa nayi miki dabara ba,idan ina bukatar ki kai tsaye zan janyo ki cikin aiki na ko kina so ko bakyaso kuma dole ki yi abin da nake so,dan haka ki sawa ranki cewa sai ki na tare da Ni zaki samu nasara akan abinda kike so,saboda nine tsanin nasarar baki daya", Surry samun kanta ta yi da kasa musanta mishi sai ma wani girma da kima da ya yi mata,haka kuma ta ji maganar sa ta yi mugun tasiri da samun mazauni a zuciyarta na cewa sai da shi din zata yi nasara. Muhammad nurr hause......... Aunty amarya kulle kanta ta yi a daki ita kadai,ko wayar Dr Sabo ta kasa kira dan a wannan karon kanta ya gama kullewa gaba daya,harma ta fara tunanin ko dai wannan mutumin ba mutum ba ne,idan kuwa mutum ne to ba karamin shu'umi ba ne,kanta ta dafe da yake wani irin sarawa saboda tsananin tashin hankali da shiga rudani,koda Abbie ya shigo ya taba kofar bedroom dinta ya ji a kulle bai kara kokarin san shiga ba,dan yasan tana cikin matsalar da yake ganin kamar ita ta jawa kanta. Abu daya ne yasa Abbie ke yi mata uzuri shine SOYAYYA,tabbas yasan cewa son da take yiwa RAIHAN shine tsanin da yaja ta har ta aikata abin da take ganin shi zai kubutar da Raihan ɗin. Ya mata uzuri akan haka saboda yana kwatanta hakan da kansa da irin son da yakewa Raihan tun kafin yasan zai dameta a rayuwarsa. Amma kuma abunda ya dan bashi mamaki shine ko lokacin da ta haifi Raihan a matsayin namiji,sai ya ji gaba daya soyayyar Raihan ta koma kan yaron,yana boyewa ne kawai saboda gudun haddasa fitina cikin iyalan sa,baya son ya kuma yin kuskuren da ya yi a baya,saboda ko mai da yake faruwa a yanzu shine sila duk da yasan cewa yana kan daidai kuma bai take hakkin kowa ba, sune dai suka kasa fahimtarsa saboda dukiyar Raihan ta samu kyakkyawan hannu kuma Allah ya yi mata albarkar da ta yi bunkasar da shi kansa yake mamaki wani lokacin,a ganinsa suma da tasu ta yi albarkar da ta Raihan tayi da za ta iya fin ta Raihan din ma.........✍🏽 [12/21, 12:40]: *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page26 ``` Dan numfasawa ya yi tare da kaucewa koridon da zai kai shi dakin aunty amarya, yana mai jin wani irin yanayi na tsananin tausayin lamra. Duk wannan budurin da ake yi ,su mama murja da ya'yan su babu wanda ya sani ,saboda su a yanzu duk gaba daya hankalin su ya karkata akan yadda za su wawushe dukiyar da suke kira da tasu kuma hakkinsu. CHIBADO's HAUSE........ Da kallo kawai Ammi ta bi Abbu ba tare da ta iya cewa komai akan bayanin da ya yi mata ba,tunani daya ne ya damu zuciyarta shine an hana yaron ta ya ji dadin rayuwa wanda kuma hakan yana da nasaba da auren zabinsa da aka hana shi yi.duk da cewa Abbu ya ce" zabin nashi aka ba shi yanzun amma hakan baisa ta ji gamsuwa ba,dan haka ta sha alwashin jin ta bakin wazir ɗin,kuma tasha alwashin indai dole aka kuma yi masa to kuwa ba zata yarda ba a karo na biyu a sake cusa masa Macen da ba ita ce zabin sa ba. TSOHUWA........ Cikin fidda haki daga manyan kofofin hanci da bakinta,ta nuna dudu wanda ke durkushe a gabanta tamkar me sujjada,ta ce",jinin tsohuwa ya ce,dole sai an hada da makirci saboda hadarin da ke tattare da lamarin,mun kasa gano jinsi bare yare babu abin da muke gani sai duhu,saboda haka jini ba zai iya ganin komai ba,ya ce" sai mun hada da bincike ta hanyar mutane,yanzu dole ne mu bawa kanmu hutun zaman kogo saboda wannan dalili,kuma hakan shi zai bawa jini damar yin kyakkyawan bincike akan komai dake tunkaro mu",daga haka ta nuna su da wata doguwar sanda me kan maciji,cikin wani karamin lokaci hayaki me ban tsoro ya turnuke wajen baka ganin komai sai hayakin da ya zama tamkar gajimare acikin sa suka bace kowa ya san inda dare ya yi masa. ...... Haka nan aka ci gaba da biki,dama can babu ango ake yi,shi yasa ko da hakan ta faru ma babu abin da ya sauya,sai dai daga zuciyar amarya da kakarta harma da wadan da ba muyi zato ko tsammani ba sam babu zaman lafiya ko alkhairi a acikinta. RAIHAN............. Sosai ta dauki fushi da ko mai da kowa,wazir kuwa hatta da nombobin sa sai da ta yi delete dinsu,sai dai kuma duk abanza dan duk tana da su akanta,haka kuma tunanin abin da ya faru ya ki barin ƙwaƙwalwarta, sannan ta kasa sanin dalilin da yasa duk take jin hakan,dan tsaki ta yi tare da janyo wayarta ta ci gaba da aikin ta da ta mayar da shi gida a kwana biyun,sai dai tana yi tana kumbura fuska da kyarɓe baki tamkar wanda wazir din ke gabanta,kamar yadda Abbie bai sanar da goggo da aunty amarya ba haka itama babu wanda yasanar mata da halin da ake ciki,bakin rai ne dai ta ke ta yinsa tun ranar da abin ya faru,kuma har yanzu bata san cewa sace ta aka yi ba. Bangaren Abba yahya ma bai sanar da inna maimuna komai ba,shiru ya yi da bakinsa tunda wannan sirrinsune na cikin gida,sai dai kuma a ransa ya kudurta taimakon ɗan uwannasa ta hanyar bincike a bangaren Alh Garba ur exsellency,dan ya lashi takobin cewa ba zai barshi ba duk ya bincika ya gano da sa hannunsa cikin wannan al'amari. Niamey.......... Ba tare da jin komai ba,baba buzu ya sanar da kakar Raihan komai bai boye mata komai ba,kallon shi kawai take ciki da tsantsar razani da mamaki wanda ya kasa boyuwa daga kan kyakkyawar fuskarta da har tsufa bai buya ba,shurunta da zurfin da ta yi a tunani ne yasa har sai da ya dan zungureta,yana cewa fatsima lafiya dai ko?cikin dan daburcewa ta ce",babu komai mamaki da tuajjibi shine ya hanani Magana,to yanzu ina ita Raihan ɗin? Amma dai ba yanzu za a ba shi ita ba ko? A'a ba yanzu ba sai komai ya lafa,duk da ba zamu tsaya muce har sai mun binciko komai ba,tun da ba mu san ranar da gaskiyar zata bayyana ba,wacce gaskiyar? Hajiyar agades ta kuma tambaya da alamun mamaki shima cikin mamakin nata ya ce" a'a to haka zamu zauna ba za mu nemi sanin makiyan da suke son kashe mana jika ba?da sauri ta girgiza kanta tana Murmushin da na kasa gane ko na meye,ta ce",ba haka nake nufi ba, wannan ma aikamar ya zama dole ne,sai dai kawai mu yi fatan Allah ya kare mu baki daya,Amin ya amsa yana kokarin barin dakin,amma dai ya kamata nima na leka su ko? Juyowa ya yi daga kokarin fita da yake yana duban ta cikin yanayin mamakinta,yau kuma ke kike cewa zaki gidan ramla bayan kuma ke ce me kin zuwa kamar wata Yar fari a gareki?shafa gashinta da ya kwanta ta yi tana cewa ,to yanzu na ce ina bukatar zuwa ,kuma idan na je ba yanzu zan dawo ba,dan sai na gano ɓoyayyiyar makiyan Raihan,daga haka ita ta bar shi a dakin tsaye yana jin jina lamarinnata da a yanzu yake daure mishi kai. CHIBADO's HAUSE........ Anyi biki an gama lafiya,zuciyoyin wasu babu dadi sai dai dannewa kawai da suke yi,haka nan basa bari a gane cewa suna cikin damuwar,a babban sashen sa dake cikin gidan ya ce",zai zauna dan haka nan aka kai amarya rubyy,duk da cewa ba ta so zaman gidan ba ,amma sai ta danne saboda ta hakanne kawai zata gane abin da ake kulla mata a cewarta. Katsaham aunty amarya taga hajiyar agades,bata kuma shan mamaki ba sai da ta ganta da uban kaya,tana kuma fada mata cewa tazo ne ta danyi musu kwana biyu ta debewa Rahim kadaici,ta faɗa alokacin da take duban RAIHAN da wani kallo da na kasa tantance manufarsa,ai ga guri nan sai ki ta zama", Raihan din ta faɗa tana barin dakin bakin da aka kai hajiyar,dariya hajiyar agades ta yi tare da cewa idan ma dai baka so zuwa na ba kai ka sani zama daram tunda gidan ɗiyata ne. Tunda Ruby ta tare bata sa wazir a idonta ba,abin da ya kuma daga mata hankali ke nan ya kuma tunzura zuciyarta akan yarinyar da aka aura masa,duk da cewa ta ji dadin ganin ba tare suka tare ba,to amma ba hakan yana nufin ta sakankance ba ne,dole ne ta tashi tsaye ta yi yaki da duk wata mace da ke son rabata da soyayyar wazir. Har kwana biyu babu wazir a bangarenta,kai ba ta ma da tabbacin ya dawo nan sashen ko bai dawo ba,haka ne ya sa ta kanas ta dauki waya ta kai kararsa gurin innawuro,tsaki innawuro ta yi tana balbaleta da masifa,yanzu ke rabi kullum ina nuna miki hanyar jan aji da kama kai amma ba zaki dinga ganewa ba,to wallahi indai wannan halin za ki ci gaba da yiwa wazirin gida to kuwa ba zaki taba samun SOYAYYAR sa ba,Gara tun wuri ki kama kanki kinemi hanyar da kika san zai so ki cikin sauki da saukakawa,ba kuma na ce ba zan mishi magana ba ne,zan yi mishi amma dole ki gyara dabi,arki ta san zama mace mara kamun kai",daga haka ta kashe wayarta ta bar rabi da sake baki tana bin wayar da kallo,zuciyarta kuma cike da sake sake,wai me tsohuwar nan take nufi da Ni ne?ta tambayi kanta tana kallon wayar kamar innawuro zata bata amsa ta ciki,numfashi ta sauke tare da ajiye wayar tana fadin idan ma da wata manufa azuciyar ki zan yi maganin kune, dan tuni na fahimci jikokin da kike so tsakani da Allah. A ranar innawuro sai da ta kasa ta tsare ta samu hanyar ganin wazir, duk da cewa ranta cike yake da takaicin rabi a din,amma haka ta daure ta yi wa wazir tass,daga bisani ta dawo nasiha da tuni akan hakkin da ya rataya akansa,wanda shine ya dan yi tasiri a zuciyarshi har yake jin zai iya hakura ya sauke duk hakkin rabi da ke kansa amma banda soyayyar sa. Misalin karfe goma sha daya na daren ranar ,ya nufi bangaren rabi ,cikin kamalar shi da kyakkyawar shigar shi ta pijamas na kamfanin eshar, sai kamshin mayataccen turaren sa hemo arara ud,a hankali yake takawa kafafunsa na nutsewa cikin tattausan Grass Capet din da yayiwa corridon kawanya,ba tare da yasan wane daki rabi a take ciki ba,daga cikin jerin dakunan dake wajen kamar na hotel zuciyar shi dai kawai ta canka mishi wanda zai shiga,sai kuma ya yi sa,a a nan din rubby take,zumbur ta mike daga wayar da take yi,jikinta har rawa yake saboda shigowar sa babu zato ko tsammani,duk da cewa kuwa ya yi sallama to amma sam bata ji ba saboda nisan da ta yi a wayarta,wanda ga dukkan alamu tana bata farinciki. Cikin rawar baki ta ce" da shi sannu da shigowa Hamma wazir,yauwa ya amsa a saman leban shi da yanayinshi na kamewa,kallon da take yi mishi ne yasa ta fahimci ya amsa,kiyi alwala kizo nan,ya kuma fada yana dan zama saman resttin chare guda daya dake dakin ba musu ta shige toilet din sai dai kuma zuciyarta bugu take a maimakon tayi farinciki,sam bata yi tsammanin zuwan sa a wannan lokaci ba,kai ba ta mayi tunanin cewa innawuro zata mishi magana ba,haka nan ta yi alwala ta fito jikin ta babu kwari. Bayan sun idar da sallah ya kama kanta ya yi mata addu'a Sannan ya yi mata yan tambayoyi akan addinin ta,wasu ta amsa wasu kuwa sai inda inda da zare ido,rabuwa ya yi da ita kawai ya shayar da ita madara,daga nan ya umarce ta da hawa saman gadon ta. Komai nashi a nutse yake yin sa kuma amutunce,wanda hakan yasa tuni rabi a ta manta da yar faragabar da ke zuciyarta,ta manta da wa take ta shiga maida masa martani da wani zazzafan salo da nuna zalama da doki a gare ta. Duk da cewa wazir yana injoyin abun amma Saida hakan ya haifar masa da mamaki,me ya kai budurwa yar Fulani yin irin wannan zumudin a darenta na farko?,bai bari tunanin ya yi tsawo ba ya kau da shi tare da yin addu'ar kusantuwa da iyali. Cak ya tsaya da yin komai,hatta tunanin shi tsayawa ya yi,runtse idanun sa ya yi da ya ji suna masa wani yaji yaji,haka makoshin sa lokaci daya ya bushe,wani irin takaici da bakin ciki ya gauraye dan ragowar fariincikinshi,a hankali ya ture ta da ga jikinshi ya tashi cikin nutsuwa kayan shi ya maida ya ɗaure ,kana ya tashi daga gadon kai tsaye ya nufi kofa,zuba mishi ido rabi a ta yi tana mai kasa cewa komai,domin jin kwarjinin shi ta yi ya hana ta yi mishi karya,tana kallo ya fita daga dakin ba tare da ta iya kwakkwaran motsi ba,sai da ya fita ta saka kuka tana jin nadamar abin da ta aikata ,wata kila da yanzu ta samu soyayyar wazir ta silar mutumcinta. Shaya ya sakarwa kansa ko zai samu salama daga radadin da zuciyarsa ke yi,duk irin yadda ya kama mutuncin sa amma Saida Allah ya jarabce shi da auren mazinaciya,shi din mutum ne me tsananin kyankyami shi yasa yake matukar kyamar zina harma da me yinta,shi ko tarin abokai irin makusantan nan baida saboda kar ya yi mu'amala da mazinaci,sai gashi yau ya kusanci mazinaciya,duk da cewa ba son rabi ya ke ba amma dole ne ya ji ta kaici da kishi akan ta,ko dan matsayin da ta taka na amsa sunan 'yar uwarsa,duk da yasan cewa matan yanzu basu da tabbas amma yana da yakinin cewa ba duka ne iri daya ba,akwai na banza akwai na gari shi yasa bai taba sako rabi a jerin wadan nan matan ba sai kuma gashi ta baka mamaki,sai kawai ya ji zuciyar shi na rawa akan ko wace irin mace. Tsaf ya fito cikin shirin sa na office,as usual cikin ash din cot wadda ta yi matukar amsar fatarsa me matukar sheƙi,sumar nan tasa kamar me saboda sheƙi da kwanciya. Da sauri rabi a da zuwa yanzu ta samu nutsuwar yi masa magana,ta tare shi da gaisuwa sai dai ta kasa haɗa ido da shi kamar yadda ta saba yi masa,sai dai shi da ya kafe ta da idanunsa masu matukar tasiri da hukunta me lefi cikin sauki.hakan ya sa ta shiga kame kame duk abin da ta haɗa dan fada masa take suka tarwatse ko mai ya kama hanyar sa,hakuri kawai ta samu kanta da iya furtawa,bai ce mata komai ba sai gewaye ta da ya yi ya fita cikin kamewarsa, Yana fitowa ya samu Samir securityn sa yana zaman jira,da sauri ya bude masa mota ya shiga, shi kuma ya shiga driver sit yaja motar da gudu suka fice daga tan kamemen gate din. Cikin nutsuwa ya lalubo lamban wayar Raihan,saida ta yi ringing wajen sau biyar sannan yaji sassanyan muryarta me cike da wani salon shagwabar da yake halittarta,lumshe idanunsa ya yi yana mai sakin wata sirrintaccenyar a jiyar zuciya,ina kwana ta faɗa tana tura baki ba dan ta so ba,sai dan kawai raina na gaba da ita ba tarbiyyar ta ba ce,lafiya ya amsa shima a takaice ,kafin ya ɗora da cewa ki fito office muna wajen gate",zaro ido ta yi tana kallon wayar da ya katse mata ,kan bala amma wannan mutumin ya raina min wayo",dole ta ta shi ta fito dama a shirye take tsaf. Hajiyar agades da ke tsaye tana sauraron ta,ta ce"mutum dai ya dinga kiyaye harshen sa dan kar ya je ya aikata zunubi ba tare da ya sani ba",wai me matar nan ke nufi ne?tunda ta dawo gidan nan take min wasu maganganu marasa kai",ta faɗa lokacin da ta samu aunty amarya a falo dan yi mata sallama,kafin aunty amarya ta bata amsa Abbie da yake shigowa ya riga ta amsa wa Raihan da cewa,wasa ne take miki tare da nasihar zaman Duniya irin nasu na manya da suka ga jiya suka ga yau". Tura baki ta yi ta fice daga falon tana daga musu hannu. Bude motar ta yi ta shiga tana faman ciccin magani, acewarta ta gaida shi dan haka ba za ta kara gaida shi ba. Har suka fara tafiya babu wanda ya tanka,ita ce ma take jin haushin shurun nashi ,ga kuma haushinsa akan auren da ya yi ba tare da saninta ba sai hakan ya kuma tunzura zuciyar ta,gani ta yi ya kuma yin wani kyau sai take ganin duk dan ya yi aure ne,ji ta yi kwalla ta cika idanunta har tana shirin zubowa,zuciyar ta kuwa ita kadai tasan halin da take ciki,idan baya kusa da ita tunaninta ya kan sassauta,yayin da tiririn zuciyarta da yadda abin ya ke toshe numfashinta duk yake bata mamaki a duk lokacin da ta tunashi da aurensa da kuma yawan matan dake sonshi,shi yasa ta dauki niyyar bashi iska na yanke haduwarsu ko ta samu ta manta da abinda yake damunta wanda satan hakan a bu ne mai matukar wuya,manta cewa wazir yana da aure. Duk wani motsinta da tunanunta ta yi ne tare da bugawar zuciyarshi,ko me nata akan idanunshi da zuciyarshi ne,yana da yakinin cewa ko motsi Raihan ta yi sai ya ga ne abin da take nufi bare kuma damuwarta,tsaf ya fahimci dalilin fushinta akansa,wanda dama can faruwar hakan yake tsoro shi yasa ya yi kokarin kaucewa hakan. Karasowarsu ma bata sani ba tana can tana fama da numfashinta da take ta kokawa da shi,jin sassanyan tafin hannunsa saman nata hannun shi yasa ta juyowa ta dube shi cikin yanayin karaya da sarewa..........jan hannun ta ya yi suka fita daga motar, Mai makon ya rabu da ita ta tafi office dinta kamar yadda ta saba sai kawai ya cigaba da tafiya da ita zuwa office dinsa binsa kawai take cikin bunjuma bunjuman kayanta na maza...................✍🏽 [12/21, 12:40]: *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page27 ``` Ganin inda suka nufa yasa ta ɗan dakilewa amma kallon da ya sakar mata shi yasa ta binshi ba tare da ta shiryawa hakan ba.hannu kawai yake dagawa ma'aikatansa da suke ta miko gaisuwa harma da masu yi masa Allah ya sanya alkhairi sakamakon rashin haduwa da shi ranar daurin auren. Suna zuwa kofar office din sakateria tazo ta bude masa tana faman zabga masa sannu da zuwa cikin rawar jiki,duk halin da Raihan ke ciki hakan bai hanata zabgawa sakataria harara ba,suna shiga sakataria ta rike baki cikin alhini da mamaki ta ce,"anya kuwa wannan Rahim ɗin ba dan daudu ba ne? Cikin sauri ta rufe bakinta tana mai leka hanya dan samun tabbacin babu wanda yaji ta. Suna shiga tacigaba da kokarin kwace hannunta,hakan bai samu ba saima janyo ta da ya yi gaba dayanta suna fuskantar juna,me ta yi miki kike harararta?taji tambayar kamar daga sama,tura baki ta yi tana mai kauda fuskar da ta fahimci so yake ya saka shu'uman idanunsa a ciki. dallin bakinta ya yi yana cewa zan yi maganin bakin nan",a hankali ya kuma matsawa daf da ita kamar wanda ake ja,wanda shi kansa bai san ya akayi ya samu kan shi da hade jikin shi da nata ba yana cewa me yasa kike haka? Me a kayi miki?ya fada yana kokarin cusa fuskarsa cikin wuyanta dake fidda wani Ni imtaccen kamshi,kokarin ture shi ta fara yi idanunta na cika da kwalla,dakyar ta iya buɗe baki ta ce",hamma me ye hakan bana so babu kyau",a hankali ya ɗago kanshi ya dan zuba mata ido kafin kuma ya saketa yana nufar wajen zamansa,kije ki yi aikin ki amma nan da awa biyu ki dawo za mu tafi",ya fada tamkar ba shi ya gama shin shine ta ba yanzu fuskar nan a kame kamar koda yaushe. cikin sanyin jiki ta fita daga office din wanda har ta fita tana jin yadda idanunsa suke kanta duk da cewa idan kallonsa kake ba za ka taba cewa kallon nata yake ba. Sai da ta fita ya samu nutsuwar yin abin da ya kamata. Itama din ji ta yi ta samu kwarin gwiwar yin aiyukan da suke gabanta,duk da cewa ba wasu aiyuka ba ne saboda tana ragewa daga gida. Su salim da abu Huraira sunji dadin dawowarta,dan haka kai tsaye suka fara gabatar da aiyukan dake gabansu. Karfe biyu na bugawa ta tattara komai ta wuce office dinsa kamar yadda ya umarce ta. Sai dai tana zuwa sakateria ta sanar mata cewa yana da bakuwa,turus ta yi tana duban sakateria wanda ita kuma sakateria ta yi hakan ne da biyu dan tasan cewa sanin yana da bako ko bakuwa ba zai hana Rahim shiga office din oga wazir ba,aikuwa ta samu abin da take so dan take a gurin yanayinta ya sauya zuwa wani sabon yanayin na bacin rai wanda kowa yasan ba ya boyuwa in dai akan wazir ne,sai dai kuma hakan bai hana ta shiga office din cikin nutsuwa ba. Idanunshi akanta ya amsa sallamar da tayi akan labban sa,ta gefan idanunta takalli hamshikiyar matar dake zaune a gaban wazir,bata kula ta ba ta wuce cikin dakin hutu tana jin takaici duk da dai taga matar babba ce. Sai da ta yi sallah sannan ta samu ta kashingida,tun tana jiransa har wani bacci me dadi ya dauketa ba tare da ta shirya ba. Yin Baccin ta da wajen mintuna goma ya shigo dakin bakinsa dauke da yar gajerar sallama, cikin takunsa na nutsuwa ya karaso gabanta tare da tsuguno a gaban ta yana sawa kananun jajayen lip din ta ido,a hankali ya kai hannu yana shafa su kamar me tafiyar tsutsa,kafin ya ji duk wata laka ta jikin shi ta mutu,cikin wani irin abu dake janshi gareta da wani irin ƙarfi ya kai tattausan leban shi saman nata ya bata wata irin sumba da sai da ta ji ta har kwakwalwar kanta,dalilin da yasa ke nan ta bude idanunta da suka sauya kala na alamun Baccin da take yi,waro idon ta yi tana kallon fuskarshi da leban shi da har yanzu yake saman nata,tuni idanunta su kayi raurau sosai take jin tashin hankali a duk yinin yau din akan canjawar halin wazir wanda take ganin kamar auren da yayi ne ya ke neman fitsarar da shi, wannan tunanin daya shiga ranta ne yasa ta yi yunkurin miƙewa sai dai kuma kafin ta zartar da hakan ta ji lallausar harshen sa me sanyi da zaki cikin bakinta,wanda yasa ta hadiye maganar da ta so yi tana faman kakkarwa kamar me rawa,yadda yake yi da harshensa a bakinta ne yasa ta kuma jin wani irin tsoro da fargaban abin da ke shirin faruwa da ita. Kukan da ta saki me karfi shi ya dakatar da shi daga nisan da ya yi wajen tsotse bakinta,a hankali ya janye fuskarshi yana mai kallon bakin da take ta gogewa tana kuma sakin kukan sakalci,bai kula taba sai miƙewa da ya yi tare da janyo hannunta ya mikar da ita tsaye,idan baki min shuru ba zan yi abin da ya fi haka",ɗuf ta yi kamar an dauke wuta sai dai zuciyarta batabar bugawa da razanin da ta shiga ba. Fita su kayi kai tsaye wajen mota suka nufa,Samir yayi saurin buɗe musu bayan suka shiga,ko kallon shi ta ki yi babu abin da take rayawa aranta sai cewa wazir ya zama ɗan iska kuma yanzu ba abin yarda ne a gareta ba,dan abin da ya faru ya gama tabbatar mata da cewa ko mai zai iya yi mata,wani irin haushi da tsanarsa ta ji na mamaye zuciyarta,har suka je gidan magana bata shiga tsakaninsu ba,saima tsananin takurewa da ta yi a gefe kamar ace ket ta zura a guje,suna tsayawa ta fita da sauri ko waiwaye bata tsaya yi ba bare ya yi zaton samun sallama daga gareta,a hakan kamar hankalinsa baya kanta sai dai kuma ta can gefen zuciyarshi yake jin motsinta da komai nata. Wuri wuri ta yi lokacin da ta shiga babban falonsu ta tarar da gaba dayan su aunty amarya har abbie,sannu da gida ta yi musu ta wuce kamar zata kifa,dan gani take kamar zasu gane abinfa ya faru da ita.aunty amarya na fakar idonsu ta mike kamar zata kiching amma sai ta yi kwana ta nufi corridon da dakin RAIHAN ɗin yake. Da sauri ta tari auntyyn tana cewa aunty wai me yake faruwa ne ina ji kamar da akwai abin da yake faruwa wanda mu ba mu sani ba",colm down Raihan me yake faruwa nutsu ki gaya min komai", Wani miyau ta hadiya kafin ta ce",aunty amarya wasu halayya ham......bata karasa ba aka turo kofar dakin kai tsaye, Abbie ne ya karaso yana cewa Rahim me ke damunka naga ka shigo cikin wani irin yanayi kamar da akwai damuwa ko?ey a'a dama kaina ne yake ciwo.......katse ta ya yi ta hanyar kama hannunta yana cewa muje Dr Sabo ya duba ka kawai",a'a abbie....shiii ya katse ta yana ci gaba da janta, da ido aunty amarya ta yi mata alamu akan ta yi shiru kawai su je. Abbie yana kokarin tada mota wayar baffa ta shigo masa,hakan yasa ya dakata ya daga,daga can baffa ya ce",kazo ina son ganinka kai da Raihan ",Tom shike nan baffa gamu nan dama muna tare,kashe motar ya yi yana cewa zo muje baffa nasan ganinmu idan mun fito sai muje Asibitin,jinjina kai ta yi ba tare da ta ce komai ba saboda har yanzu akwai damuwar abun da ya faru akanta. Shugaban jam'iya........... Dr ne ya dubi shugaban jam'iya ya ce",har yanzu ba a samu wani sakamako ba,kuma nasan hakan ba yana nufin kyale mu yaron nan ya yi ba,idan ba ayi gaggawar kwace video nan ba ina tabbatar muku zai je wajen TREE Full Y TRUES hakan kuma da zai faru tamkar zuwan karshen mu ne", Alh sale ya yi saurin tarar shi da cewa duk kokarin da muke yi baka gani,sai ka dinga nunawa kamar ka fi mu damuwa da wannan lamarin,karfa ka manta saura kiris asirinmu ya tonu fa,idan har ba ma bin abun nan a hankali to tabbas za muyi kwabar da zata kwabe da mu,tun da dai munsa ana mana aiki akansa ana bibiyar sa cikin sirri mu dakata mu ga abin da zai biyo baya,tun da dai har yanzu a binciken mu babu wanda yasan da labarin video nan bayan shi kawai ina ganin mu saurara muji daga ɓangaren dan leken asirinmu",yafi dai cewar shugaban jam'iyya, wannan matsayar suka tsaya ko waye dan leken asirin na su? Ko a wane bangare yake?macece?namiji ne?mu dai mu bi su mu samo kan zaren. BAFFA ALI............... Sai da suka dan taba wasan jika da kaka kamar yadda suka saba idan sun hadu,duk da cewa yau RAIHAN bata cikin wannan yanayin, Dan gyaran murya ya yi kafin ya maida dubansa kan Abbie ya ce ",yanzu AHMADU ya kira Ni ya kuma yi min bayani mai gamsarwa akan yana so a sanar da Raihan ko mai saboda hakki ne akan mu da ya zama dole mu sanar mata", Wata irin zabura Raihan ta yi jin yadda baffa ya kira ainahin sunanta kai tsaye ba kuma tare da yanayin tambaya ko bugar ciki ba,kafin ta fita daga wannan mamakin abbien ta ya kuma jefa ta cikin wani mamakin,saboda shima kai tsaye ya amsawa baffan da cewa,nima nayi tunanin hakan bana so dai kawai nayi abinda baya cikin umarninka tun da ga akan yadda muka tsaida magana". Gaba daya maida hankalinsu su kayi kan Raihan ɗin da ta yi mutuwar zaune kallon su kawai take kamar bata taba sanin su ba,,baffa ne ya ce",raihanatu kwantar da hankalinki,yanzun nan za mu fidda ke daga duhun da kika shiga",yadda numfashin ta yake sama da kasa ne yasa dole Abbie ya janyo ta kusa da shi ya shiga shafa gadon bayanta yana cewa nutsu Raihan ban san ki da saurin rudewa kamar mamanki ba,pls ki nutsu kinji,gyada kanta ta shiga yi tana jin numfashinta na dan daidaituwa,sai da suka tabbatar ta samu kanta, sannan baffa ya zaiyana mata komi cikin nutsuwa kamar yadda Abbie ya sanar da su a wancan ranar,kara rungume abbin ta ta yi tana jin kamar yau tasan shi saboda yanzu tana tare da shi ne kai tsaye ba tare da muku muku ko fargaba ba,yau kai tsayenta take tare da abin ta amatsayin RAIHAN ɗinsa ba boyayya ba,wasu hawayen farinciki ne suka gangaro mata,duk da cewa har yanzu tsugunne bata kare ba,tun da auntyyn ta bata san komai ba,ke nan baza tacigaba da sakewa da abbien nata ba in dai har auntyyn na kusa,ɗago kanta ta yi daga kafadarsa ta dubi baffa dake mata kallon tausayi ta ce",Baffa me yasa ba za ku sanar da aunty amarya ba?aunty amarya fa tana da matukar rauni a kaina kar ku ga lefin ta Ako mai ita din jaruma ce a kaina ne kawai take raunannasam bata da juriya akan duk abinda ya shafeni,ina son aunty amarya fiye da yadda take so na",shafa kanta abbie ya yi cikin nutsuwa ya ce",ki yi hakuri raihanatu ki ba mu hadin kai kamar yadda kika bawa mamanki, muna sane da komai kuma ba munyi haka ne dan ramako ko wata manufa ba,munyi ne dan kawai mun san hakan shi ne zai bamu damar kama makiyan mu a hannu,ina fata kin gane?jin jina kai ta yi, tana share hawayen ta. Baffa ya ce,"sai kuma abu na biyu da muka riga mu ka yanke shine aurar dake da mu kayi saboda wancan dalilin barazanar da aka yiwa mahaifiyarki akanki,ina fata zaki mana biyayya har zuwa lokacin da komai zai warware". Aure kuma? Ta tambaya cikin mamaki da tashin hankali. Ey aure mana shi muka daura muki', Abbie wane irin aure kuma? Ya za ayi ku yi min aure kuma kudinga tunanin ba za asan ko Ni wacece ba? Baffa ya ce ",ai ba wani bare muka bawa ba, AHMADU ne kuma ya san komai game da ke kin ga kuwa ba mu da wata matsala ke nan, Wane Ahmadun kuma? Yauwa gashi nan ma dan halak ya karaso dama tun dazu nace ya zo ayi komai agabansa shima,cewar baffa da ya karasa maganar tare da amsa sallamar wazir din. Guri ya samu a kasa ya zauna yana gaida Abbie kafin ya juya ya gaida baffa cikin tsananin biyayya,amsawa baffa ya yi cikin kaunar wazir din da yake ji har cikin ran shi. RAIHAN kuwa turbune fuska ta kuma yi tare da cusa fuskarta a bayan Abbie,baffa ne ya fara magana,yauwa to tun da gashi ya zo sai mu karasa magana danmu samu matsaya ko? Abbie ya ce", haka ne sannan ya juya kan Raihan yana cewa to yanzu kin gane wane Ahmad din ake nufi?to idan ma ba ki gane ba gashi nan wazirinki hammanki shi muka bawa auren ki", da sauri ta ɗago kanta dake bayan Abbie ta ce", amma shi ba ya yi aure ba? Dukanku ya aura", baffa ya yi saurin bata amsa,kuka kawai tasa har da gunji,Ni wlh baffa bana sonshi kuma Ni banzan yi aure yanzu ba har sai duniya ta sanni amatsayin mace", Abbie ya ce", raihanatu wannan fa duk ba matsala ba ne,shi kanshi wazir din ba tare da sanin shi ko neman shawararshi mu kayi hakan ba sai daga baya muka sanar da shi,dan haka tun da bakwa so gaba daya nayi muku alkawarin duk ranar da muka cimma manufarmu,komai ya warware zan sa ya sake ki shi yaje ya yi rayuwa da matarsa ke kuma ki samu wani ki aura,bashi ke nan ba ",ya fada yana kallon wazir da tun da Abbie ya fara magana ya samu kansa da zubawa bakin shi ido har ya kai aya,jin jina kai kawai wazirr ya yi ba tare da ya iya cewa komai ba,sai dai kuma yadda yaga baffa ya danyi murmushi shima abbien ya yi yana masa wani kallo yasa ya gane cewa wayo ake son yiwa RAIHAN ɗin ,shima samun kansa ya yi da ɗan sakin murmushi ba tare da Raihan ta lura ba. Shike nan na amince ta faɗa cike da wauta. To tashi kije an sallame ki,ta shi ta yi tana dan satar kallon wazir da ya yi tamkar bai san tana wurin ba,kwafa ta yi ta fice daga falon.sai yanzu ne ta gane dalilin da yasa yake mata abubuwan iskanci saboda yasan ya bada sadakinta ke nan?tabe baki ta yi tana jin farincikin da bata san na menene ba,nauyin zuciyarta kuma na raguwa. Ko da ta shiga Aunty amarya ta samu da hajiyar agades,zuba mata ido Aunty amarya ta yi tana dan mamakin yanayin nata na yanzu,to amma ganin cewa da Abbie suka fita sai ta danganta walwalarta ta da hakan,dan. Haka kawai sai ta share suka cigaba da hirarsu har Raihan din da take jin zuciyarta fresh,ko ba komai yanzu zata fuskanci aikinta ne kai tsaye ba tare da wani babban kalubale ba.(hmmm raihanatu ke nan kalubale kam da akwai shi saidai fatan sauki). ______________________ Ko mai akan idanun ta da kunnen ta ya faru, ba tun wannan lokacin ta kware a leke ba,shi yasa har ta gama naɗar komai babu wanda yasan tazo bayan window din,tun tana zama har ta zo ta kasa kaiwa kawai take tana kawowa, tashin hankalinta a bayyane yake damuwarta a bayyane take. Yanzu dama RAIHAN ɗin da suke tunanin gaubuce ba gaibu bace da akwaita? Dama tsinanniyar matar nan mace ta haifa? To wai ya akayi lamra ta shammacesu haka da yawa? Lallai yaki ne sabo me haɗe da guguwa ya tashi,domin kuwa ba zata taba barin burinta na tsawon shekaru ya mutu ba,kuma wannan abu zai zama sirrinta ne ita kadai, bazata taba bari ya'yanta da kishiyarta su san wannan al'amari me daure kai ba,ita kadai da zata ci gaba da yin yaƙinta har zuwa ranar da zata cimma nasara,idan haka ne kuwa tabbas aunty amarya ta yi ganganci a maimakon ta kashe labarin da yakin sai kawai ta yi masa rai ta hanyar yi masa kyakkyawan ginin da makiyan labarin zasu samu hanya me bullewa,shekewa ta yi da wata shakiyar dariya kafin ta yi saurin rufe bakin tana dan leke leke dan kar wani ya ji ta,inna ta ko ke ba zaki san ko mai akan wannan Labarin ba,a wannan karon yakin na murja ne ita kadai,a wannan lokacin boyayyan halin murja zai yi amfani,a wannan lokacin ko mai zai bayyana zan tayar da tsohuwar ajiya domin samun nasarar rayuwata....................✍🏽 [12/21, 12:40]: *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* Page28 Washe gari Raihan ta fito cikin shirinta na zuwa office,yau jin ta take kamar wata sabuwar mutum ,fuskarta cike da walwala ta nufi gurin abbien ta dake zaune saman dinning shida su aunty amarya harma da hamma idi da ya dawo daga tafiya yau da safen,Barka da safiya ta yi musu tare da ba su sumba kamar yadda ta saba,Hamma idi ya ce",Rahim anya kuwa bata samu ba?cikin sassanyan murmushinta ta dube shi kana ta ce"hamma idi ka dawo lfy gidan duk babu dadi kwana biyu da baka nan",ta faɗa tana dan spin ruwan Lipton da aunty amarya ta mika mata, murmushi ya yi yana miƙewa ya ce a'a kanina ban da dadin baki kai dai ko ka samu wani abun dadin ne kawai kake cikin nishadi",dariya ta kuma yi har kumatunta na lobawa,matsawa ta yi dinnin ta ajiye cop din sannan ta juyo tana cewa Hamma bari na wuce idan na dawo ma yi magana ta faɗa tana kallon a gogon diamond dake sakale a hannun ta,shima miƙewa ya yi ya ce",ok muje sai na sauke ka nima hanyar gidan na ku zanyi,sallama su kayi da su Abbie suka fita a tare. Sai da ya sauke Raihan ya ga shigar ta sannan ya juya ya tafi. RUBYY.............. Cikin fargaba ruby ta tura kofar dakinnasa ta shiga,dai dai lokacin da ya fito daga wanka jikinsa sanye cikin rigar wanka wanda ta tsaya iya gwiwarsa,tsayawa ta yi tana kallonsa ba tare da ta iya koda yi masa magana ba bare kuma magana akan batun da ya kawo ta,bai kalli inda take ba,a haka har ya gama shirinsa tsaf kai kace wani dawisu ne saboda kyawu da cikar kamala,sakaro ta yi da hanci da baki tana kallon tsagwaran kyau da kwarjini sai tsananin kamewa da take halittarsa,sai da ta ji ƙamshin sa da alamun takun sa me cike da nutsuwa sannan ta farga ,cikin in inar baki ta iya furta ina kwana Hamma AHMAD",lafiya ya fada yana mai cigaba da takawa cikin yanayinsa na gozago,bin bayanshi tashiga yi kamar wata escort dinshi,bata iya yi masa magana ba tana gani ya fice daga falon ba tare da ko kallo ta ishe shi ba bare ya tambaye ta dalilin bin nashi da take yi. Yana fita ta zube a gurin tare da sakin kuka me tafe da zallar nadama,sai da ta yi mai isar ta sannan ta rarrafa ta shige dakinta,ta janyo wayarta ta saka kiran suryy,bugu daya kuwa ta daga, kuka kawai ruby ta saka mata tana cewa suryy ki taimaka kizo aure na da birina na zama har abada a zuciyar wazir yana neman rushewa,da sauri suryy ta katse ta da cewa yi shiru gani nan zuwa baki da damuwa in dai ina numfashi. CHIBADO FM......... Kusan a tare suka isa gidan,duk da cewa shi ya tsaya ta gidan su Raihan din masu gadi suka tabbatar masa da cewa ko minti biyu ba su cika da fita ita da Hamma idi ba. Hannu su kayi shi da hamma idi kafin hamma idi ya mu su sallama ya fice daga building din.ko kallon shi ba tayi ba ta fara takawa dan tafiya office dinta,da Wani irin kallo ya bita kai kace zai cinye ta ne,cikin takunshin nan me cike da ginshira ya bi bayanta yana mai ci gaba da kalleta tamkar zai hadiye ta,duk da kuwa babu wanda zai ce ya ma san da ita a gabannasa bare a shaida kallon kurilla da yake mata.tana gab da shigewa bangaren su ta ji kamammiyar Muryarsa yana cewa nan da awa biyu kizo office,tana jinshi amma sai ta yi kamar bata san yana yi ba,dan har yanzu akwai haushinsa me girma a ranta,duk da cewa ta kasa gane dalilin fushin nata akan aurensa da yar uwarsa rabi,wata yar kwallar da ta saba zubo mata a duk sanda ta tuna hakan ta cika idanunta kokarin sharewa ta yi tana mai daidaita kanta dan gujewa tambayar abokan aikin ta. Yau din ma dai aiki su ka yi sosai, sun fitar da manyan labarai wanda kusan gaba daya sun danganci yan siyasa da kuma siyasar kanta, wannan shine ya dauke mata hankali har zuwa lokacin Sallah Sannan suka dakata da karbar sakonni tare da fitar da bayanan da a ka kawo mu su,a office dinta ta yi sallah, sannan ta fita suka wuce wajen da suka saba cin abinci ita da su salim. Ajiyar zuciya ya sauke tare da kara lumshe idanunsa,yana mai kokarin dauke idanunsa daga kansu,wani abu yake ji yana taso masa akan fitar da su kayi ita da su salim,duk kuwa da yasan cewa ya bata umarnin zuwa office dinsa a wannan lokacin,kai ba ma wannan ba ai yanzun ya ci ace ta daina wannan mu amalar da su salim tunda dai tasan matsayinta ya sauya zuwa matar aure,idan su ba su sani ba ai ita ta sani,huci me zafi ya fitar tare da komawa saman kujerarsa ya kwantar da kansa tare da lumshe idanun sa,zarazaran gashin idanunsa suka yiwa idanunsa rumfa,numfashi kawai ya fesar ransa duk babu dad'i . RAIHAN kuwa tana sane daga wajen cin abinci ta yi ficewarta,ba gida ta nufa kai tsaye ba,wani aiki ta fita ba tare da sanin kowa ba,saboda bata yadda da kowa ba dan a halin yanzu akwai wanda take tunanin yana musu zagon kasa a cikin group dinsu,shi yasa yanzu duk abinda zata yi takan yi da taka tsantsan tare da lura da dukkan su. __________________ Alh sale da shugaban jam'iyya sai Dr sanate,da sauran membobin da suke kungiya daya,kamar su Alh ja'e da barrister yunus,da sauran kannanun ministoci. Barrister yunus ne ya dan yunkura tare da yin gyaran murya ,ya ce",gaskiya Alh sale ya kamata mu daina wannan jiran gawon shanun,kunga har yanzu wanda muka sa ya yi mana aikin nan babu wasu manyan bayanai da ya samo mana, Sannan kuma gashi lokaci sai tafiya yake a kowane lokaci wannan shu'umin tree full Y trues zai iya bankado sirrikan da muka jima da rufe babinsu,zai iya binciko manyan sirrikan mu da muke fatan dauwamar su a rufe har kasa ta rufe idanunmu babu wanda zai san da su.to amma yanzu naga wankin hula nema yake ya Kaimu dare kuma duk laifinku ne,dan Bama gari bai kamata ku bari komai ya nemi lalacewa ba",tabbas maganar ka tana kan daidai, cewar Alh ja'e,ya cigaba da cewa dan ba ma nan ba shi yake nufin tunaninmu da hankalinmu baya nan ba,amma tun da ku kun gaza yin komai saboda kuna tsoran karamin yaro to mu za muyi duk abinda ya kamata duk da cewa ba mu shiga cikin video ba",wani irin kallo shugaban jam'iya ya watsa musu kana a dan fusace ya ce", haba Alh ja'e barrister me kuke nufi da irin wannan kalaman naku,shin ko kun manta mu din su waye a cikin wannan tafiyar? To idan kun manta ya kamata kuyi gaggawar tunawa,ku sani cewa mu duk abinda za mu yi sai munyi tunani mun gano makomarmu da abinda hakan zai haifar mana,babu irin tunanin da ba mu yi ba,karfa ku manta idan muka kashe yaron nan ba ku san in da ya kai camarar nan ko wanda ya bawa ba dan haka mun kashe maciji ne ba mu sare kansa ba,ko na ce mun bar baya da kura, sannan kuma idan ba mu yi takatsantsan gurin bibiyyarsa ba shima za mu kwantowa kanmu kura kasancewar shigowar wannan hatsabibin tree full Y trues,dan haka Ni ina ga ku yi hakuri da matakin da muka dauka sai dai idan da akwai wata shawarar makamanciyar matakin da kuke kai ku kawo saboda karawa aikin sauri",jin jina kai Dr sanate da Alh sale su kayi suna duban juna alamun dai kara tabbatarwa da yan uwansu abin da shugaban jam'iyyar ya fada haka ne babu kuskure,a nan dai yan cece kuce suka balle daga baya kuma duk suka nuna gamsuwar su akan matakin da aka dauka din tare da kawo wasu yan shawarwarin da zasu karawa dan leken asirin su kaimi da saurin samun nasara,daga nan kowa ya watse da yar faragabar abin da zai iya biyowa baya. RUBYY........ Da sauri ta rungume sury tana ci gaba da kukan da har yasa Muryar ta dashewa,kamata tayi suka zauna kafin ta dubeta cikin nuna tausayawa ta ce",rubyy me kuma ya faru ina tunanin komai ya wuce tunda kinriga da kin zama matarsa ko ba haka ba?da saura wlh suryy da sauran rina a kaba komai ya kuma dagulewa Ni da nake neman soyayya amma sai ga shi san zuciyata ya jawo min na rasa damata gaba ɗaya,a nan ta bawa suryy labarin abinda ya faru a daren jiya a ya yin da wazir ya sameta ba cikakkiyar mace ba. To sai me dan ya same ki ba a cikakkiyar mace ba?, da sauri rubyy ta kalleta idanunta shabeshabe ta ce", suryy ko dai baki ji abin da nace miki sosai ba?tabe baki Surry ta yi kafin ta ce", Ni ko naji abinda kika ce dama abinda hakan yake nufi sai dai kuma wannan ba shi ne zaisa mu karaya har mu fara tunanin faduwa ba, rubyy ki kwantar da hankalin ki tun da kika sako Ni cikin rayuwarki to kuwa tabbas Saina tabbatar da farincikinki ta hanyar samo miki mafita akan damuwarki,shi yasa kika ji na ce sai me,saboda Ni wannan ban dauke shi a komai ba,shi din kika san me yake yi a waje ai shi namiji me kyau da aji ba a shaidar sa,dan kuwa ko shi bai bi su ba su zasu bishi kuma komai ajinsa sai ya sauke kai agaban mace,bare kuma ke da kike matarsa ina tabbatar miki da cewa wazir sai ya zo hannunki kinyi yadda kike so dashi ba kuma da boka ko Malam ba,ke dai kawai ki bani lokaci ki kuma kwantar da hankalinki, sannan ina so ki sa shi ya baki aiki a gidan tv ku dan hakan shi zai bawa shirinmu damar tafiya daidai yadda muke so",ajiyar zuciya rubyy ta sauke tana jin damuwarta na raguwa,cikin nutsuwar data fara samu ta ce",to sury ta ya zan nemi aiki a wajensu bayan ba abin da na karanta ba ke nan, sannan kuma ba magana yake min ba duk ta yaya zanyi hakan? Murmushin samun nasara suryy ta yi kana ta ce",haba Ruby ta inda aka hau ai tanan ake sauka ki samu Abbanki ki sanar da shi idan bai yadda ba sai ki nemi Abbun nashi nasan shi ba zai ki yadda ba,ina tabbatar miki da cewa ba karamar nasara zamu samu ta wannan hanyar ba,dan haka sai ki yi kokari kuma dan ba abin da kika karanta ba ne wannan ai duk me sauki ne karfa ki manta a bu naku ne dan haka babu abinda zai gagara ke dai ki gwada kar ki tsaya sanya", ta faɗa tana saba jakarta tare da miƙewa tsaye, rubyy ta yi dariyar farinciki ta ce shike nan ƙawata zanyi duk yadda kika tsara kuma nasan ba zan sami matsala ba".daga nan Surry ta fita ruby na bin ta tana dan raka mata har sai da suka dangana da kofar falon sannan su ka rabu. Da sauri suryy ta shige dan sahun da ta barshi yana jiranta,fuskarta tarwai kana kallonta zaka san cewa tana cikin farin ciki,tana sane ta haɗawa ruby hanyar haduwa da ciwon zuciya,dan ta tabbatar da cewa idan rubyy ta fara aiki a inda zata dinga ganin Raihan da yanayin muamalarta da wazir to kuwa tabbas zata gane ko mai daga nan kuma wasan zai fara , Ruby ba zata taba iya jurewa Raihan ba shi kuma wazir ba zai taba iya jurar wulakanta Raihan ba,zata lalata komai idan ta lalata muamalar auren ruby da wazir sai kuma ta dawo kan Raihan wanda take ganin ba zai mata wuya ba,saboda Raihan ragowar maƙiya ce zagaye take da yan farauta dan haka bata da matsala da wannan. Sai misalin karfe biyar Raihan ta koma gida,sam ta ki bari tunanin laifin da ta yiwa wazir ya kashe mata jiki,hakan yasa tana shiryawa ta bi hajiyar agades bangaren Hajiya goggo dan debewa kanta kewa da kuma tunanin wazir din da ya hana zuciyar ta sakat. Shima sai wajen karfe biyar din ya koma gida,dan abinda ya hana shi tafiya Raihan din ce a tunanin shi zata dawo amma har ya taho baiji duriyarta ba,dan tsuka ya yi yana jin damuwar hakan aran shi,ji yake kamar ya hana ta aikin gaba daya sai dai kuma idan ya tuna burinta da aikin da tuna irin damuwar da zata shiga sai ya ji tsoron hanatan,to amma fa tabbas zata ci gaba da irin haka ko mai zai iya faruwa da aikin nata,da wannan tunanin securityn sa ya bude mishi kofa tare da sanar da shi karasowar su gida. ____________________ Kai wanene?kuma me yasa ka nemi zama da Ni?matar da take zaune fuskarta sanye da facemask da bakin glas ta faɗa tana mai tsatstsare mutumin dake gabanta da ido, murmushi ya yi tare da cewa me kike ci na baka na zuba tun da na neme ki ai kin san cewa Ni din abokin tafiya ne na hakika kuma Ni din me nasara ne wata kila ma nasarar dake tare da Ni tasa nasarar ki ta ta shi daga suman da ta yi",zuba mishi ido tayi kafin ta kyalkyale da wata muguwar dariya nuna shi ta yi da yatsa tana cewa amma wlh ka bani dariya to amma dai ba zan katse maka hanzari ba ina sauraron ka inji da abinda kazo", Jinjina kai ya yi yana mai ɗan kara duba wajen da suke, sai da ya tabbatar da tsaron gurin kafin ya yi gyaran murya ya ce",ina so ki bani dama mu hada hannu domin kawar da mutanen da suka zama shamaki ga burikanmu na son zamowa shahararrun masu arziki wadanda duniya zata dama da su",sosai take kallonshi tare da al'ajabin shi da tunani akan shi barkatai. Nasan tunanin da kike kuma bana so ki wahalal da kanki gurin tunanin yadda aka yi nasan cewa ke ce kika nemi kashe Raihan tun tana yarinya ,kuma.kece sanadin da yasa uwar Raihan ta boye halittarta ta mace ta bayyanawa duniya ita a matsayin namiji",yanzun ma duban shi take yi kamar idanunta za su fado ranta fal mamaki,sannan kuma tana jin cewa lokaci ya yi da dama tazo mata a karo na biyu wadda ba zata yi wasa da ita ba................✍🏽 [12/21, 12:40]: *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page29 ``` Kallonta yake shima cike da son fahimtar yadda zancan sa ya karbu a wajenta,sai dai bai gano komai ba sakamakon baya iya ganin fuskarta a bayyane. Murmushi ta yi wanda yake kunshe da ma anoni masu tarin yawa, sannan ta ce",na amince da bukatar ka sai dai har yanzu baka sanar da Ni manufarka da dalilinka ya yasa kake so mu hada kai da kai dan cimma burinka ba, sannan kuma ban san yaya aka yi muka hada tarayyar da har zamu cimma nasara a kan sa ba",ba tare da ya ce mata komai ba ya zaro hoton da yake rike da shi a hannun sa ya nuna mata,duk da cewa tana cikin facemask hakan bai hana shi ganin irin razanar da ta yi da ganin hotan ba,nuna hotan take da yatsanta har yana rawa ,cikin rawar baki ta ce", wannan din shine dai da na sani ko wani me kama da shi ne?,shi ne dai wanda kika sani,mayar da hotan ya yi sannan ya ɗago yana dubanta a lokaci daya kuma fuskarshi na sauyawa da wani irin fushi da ya fara tasowa tun daga kasan ransa, ya ce",kar ki tsaya tunani ko mamaki kamar yadda nima ban tsaya tunani da mamaki ba a lokaci da na gano ke ce makashiyar Raihan,dan haka ina so ki rufe bakin ki kawai mu dora daga inda kowannen mu ya tsaya,bai saurari cewarta ba ya ci gaba da cewa,zamu fara shirin mu kamar haka ya nuna mata wata doguwar takarda tare da dage girarsa guda daya irin dai na yan duniyar nan mara sa imani, jinjina kai ta yi tana bin shi da kallo,shi ke nan zaki iya tafiya ya fada yana shigewa cikin wajen kamar ba da shi ne suka gaba tattaunawa ba. Dan jim ta yi tana kallon takardar da ya bata da jerin sunaye da cikakken bayani akan ko wane tsarin sa,wanda kallon su kawai take yi ba tare da tana fahimta ba dan kuwa har yanzu bata fita daga shock din abin da ta ji kuma ta gani ba,da kyar ta samu ta yakice tambayoyin da ke ranta ta fita daga wajen cikin takun da take yin sa da rashin laka. Hhhhhhhh.katuwar dariyar da ta cika duhuwar dajin ke nan,wanda sautin ta yake fita da wani irin amo me karfi mara dadin saurara,bayan shudewar mintuna biyar sannan dariyar ta tsaya hayakin da ya turnuke wajen ya fara washewa a hankali har Saida ya gushe gaba daya,sai ya zamana wutar da ke ci ce kamar ana babbaka mutum ta fito tarwai a tsakiyar mutum biyar da suke gewaye da ita,cikin wata irin murya me tsananin girma da karaji tsohuwa ta bude wangamemen bakinta wanda hucinsa ke fita da wani irin hayaki kamar me shan shisha ta ce",ba komai ne yasa na kira ka ba dudu fa ce na sanar da kai cewa ka samu masu yi maka yakin sunkuru a bangaren duhuwar da idanun mu ke gani,duk da cewa har yanzu jini bai gano ko mai ba,to amma ina tabbatar muku da cewa an samu manyan shu'uman da suke da cikinsu tun tsawon shekaru,kuma su zasu yi muku yakin fili,mu kuma sai mu cigaba da yin duk abin da ya kamata akan siyasar ku da ta yadda abin zai ta fi ba tare da mun samu tangarda ba,dama wannan matsalar ita ce ta tsaida komai akan aikin mu na karbar kasar nan,to yanzu tunda muna da masu ɗauke mana hankalin su ba mu da matsala ta bangaren aikinmu ,mu dai kawai abin da za mu iya shine idan mun gano wata matsala mu yi saurin kauda ita. Cike da tsananin biyayya suka rissinar da kawunan su ,suna cewa mun gode ya shugaba,mun san cewa inda ke ba za mu fadi ba,kuma ba za mu tagayyara ba,mungode tsohuwa me share mana kuka,(a gidan banban ku ta zama me share muku kuka, Allah dai ya shirya wadan da suka bata Amin). ______________ Tsaf ruby ta shirya ta nufi bangaren Abbu, cikin ladabi ta gaida Ammi suka dan taba hira ita da shukrah ,kafin nan ta dubi Ammi cikin dan jin nauyi ta ce",Ammi Abbu fa?cikin sakin fuska Ammi ta ce",yana falonsa kuje shukrah ki rakata sai ki dawo yanzu na baro shi idansa biyu ",to Ammi shukrah ta faɗa tana yuunkurawa.... Da sallama suka shiga falon,yana zaune yana kallon tasharsu ta chibaɗo tv,amsa sallamar ya yi yana fadada fuskarshi da fara a,rabi a ce ku shigo mana",ya fada har yanzu fuskar shi da murmushi,juyawa shukrah ta yi ita kuma rabi a ta shiga ta samu gefan shi ta zauna,kanta a kasa ta gaida shi,amsawa ya yi ya kara da tambayar ta yadda zaman na su yake,har zata saki baki sai kuma ta tuna a gaban wanda take dole ta hakura ta maida maganarta in da ta fito,dole ta maye gurbin maganar da ba shi tabbacin suna lafiya babu wata matsala. Wajen mintuna biyu ta kasa cewa komai,fuskantar hakan da Abbu ya yi ne ya sa shi maida hankalinsa kanta yana cewa rabi'a da wata matsala ne naga kamar da magana a bakinki ko?jin jina kai ta yi kafin cikin taro karfin hali ta fara zaiyana masa dalilin zuwanta cikin tsari kamar yadda kawarta suryy ta tsara mata. Dariya Abbu ya yi irinta dattijon kirki kana ya ce",haba rabi akan wannan maganar ne kika tsaya kina dta nuku_nuku? To indai wannanne kar ki damu in sha Allah idan AHMAD din ya shigo zamu yi magana sai asan bangaren da ya kamata a baki tunda ba bangaren ki ba ne aikin jarida,kar ki damu ba zai gagara ba",wata ajiyar zuciya ta saki a boye kafin ta shiga godiya cikin nuna girmamawa,cike da farin ciki ta koma bangarenta , dan ko bangaren innawuro ba ta je ba,sauri kawai take ta sanar da suryy wannan kyakkyawan albishir. CHIBADO' FM...... Ganin har lokacin tafiyarsa Raihan bata dawo ba shi ya bashi tabbacin cewa tana sane ta yi hakan,tabe baki ya yi cikin rashin nuna damuwar hakan. Yana shiga gida bai ko kalli inda rabi take da wani kwalliyarta ba,ya shigewar sa daki.... Sai da ya Shirya cikin doguwar ash din jallabiya me bin jiki,ya fito yana takun nan na shi me cike da kasaita,waya ce a hannun shi yana yi, amma ba za ka taba cewa waya ya ke ba saboda yadda ya yi shiru yana sauraren wanda suke wayar da shi,yanzun ma da kallo rabi ta bishi tana hadiyar yawu,yadda ya yi kyan nan ji take kamar ta kwana tana juyi a kirjin shi,hadiyar yawu ta kuma yi tana kallon yadda jallabiyar ke wani kwanciya a jikin shi tana bin fatar jikin shi. Yana fita ,ta saka kuka tana jin duk wata tsiga dake jikin ta na tashi,babu abin da take so take muradi a yanzu irin ta ji ta a duniyar da wazir ya saka ta a daren jiya,shin yanzu lefinsa zata gani ko kuma laifinta?me yasa bata taɓa tsayawa ta yi tunanin wannan rana ba?me yasa bata taɓa bin maganar innawuro na karantar halayyar wazir ba?tabbas da ta yi hakan watakil ta gano cewa yana da matukar tsantsanin mazinaci da kaucewa hada guri da shi bare kuma shinfida ,ta sani cewa yanzu abu ne me matukar wuya wazir ya kuma dawowa gareta,kukan da nasani ta kuma rushewa da shi tana Dada jin haushin kanta. Tare suka fito da Abbun daga masallaci bayan idar da sallar Isha,kamar yadda ya saba bin Abbun ya yi zuwa sashen innawuro inda suke haduwa tun can baya dan yin dinner. Suna shiga innawuro ta fara washe baki tana dan tsokanar sa,bai nuna yadda da shirin da ta ke nema kai tsaye ba dan ya ɗora masa ayar tambaya,hakan yasa ya yi mata fuskar shi ta ko yaushe wato ya gaida ta cikin fuskar shi ta gizago babu yabo babu fallasa,bata damu da yanayinna shi ba,ta ci gaba da yi masa magana cikin yanayin kauna kamar yadda ta saba mishi a can baya kafin rabi a ta shigo ta fara hada su fada,wazirin gida yau nayi maka tuwon da kake so nasan za kayi murna", thanks ya fada saman labbansa yana neman guri kusa da Ammi yana zama, rike hannun Ammin ya yi yana gaidata cikin kaunar ta dake dulmiye cikin ran shi,itama cikin kulawa ta amsa tana tambayar shi lafiyar rabi a,bai kula da tambayar ba bare ya amsa sai ma maida hankali da ya yi kan labaran da ake yi a tashar su. Kamar yadda innawuro ta faɗa kuwa ,ya ci tuwon alkamar sosai,daga nan bayan duk sun gama suka koma falo,shukrah dakin innawuro ta wuce ta bar su dan wannan ce tarbiyyar da Ammi ta yi musu,duk lokacin da suka ga alamar za a yi wata magana da bata shafe su ba to sam basa zama a gurin sai dai In neman su aka yi. Gyaran murya Abbu ya yi yana d'an gyara zamansa ta hanyar barin bayan sa daga jikin makarin kujerar yana duban wazir da yake ta dan danna waya,ganin haka yasa wazir din dakatawa da danna wayar ya maida hankalinsa kan Abbun,cikin nutsuwa Abbun ya yi masa bayani kamar yadda ruby ta zo masa da shi , sannan ya dora da cewa sai ka duba wajen da ya kamata ka sata amma dai banda bangaren tv tun da kasan ba wai takaranci abin ba ne sai dan shi aikin jarida yana da bangarori da dama wanda yasa ake iya daukar mutum ko da baiyi karatun ba", innawuro ce ta fara magana ,to ya za ai ka yi masa haka bayan baka tambaye shi ko yana da ra ayin matarshi ta yi aikin ba?ta karasa maganar idanunta akan wazir da har yanzu bai ce komai ba,sai dai jin maganar da innawuro ta yi yasa ya ɗago ya dubi Abbun dan ganin yadda zai karbi zancen na innawuro,sai dai kuma kallon da Abbun ya yi masa take yasa ya karaya ya kuma gane karatun kurmancin nasa,dole ne ya hakura rabi a ta yi aiki tunda Raihan ma aikin take yasan da wannan Abbu ya yi amfani wajen kin ba shi damar jin ta bakinshi,to amma ai shi abbu bai san wacece rabi a ba, shi ka dai yasan wacece rabi a halin yanzu. Cikin kamammiyar Muryar shi ya ce",shike nan Abbu akwai wajen da zamu bata idan tana bukata sai ta zo ta maye gurbin",da ga haka ya mike yana musu sallama,Bin shi da kallo Ammi ta yi tana jin babu dadi akan yadda ake yawan tursasawa yaronta,ita kadai take gane karatun zucin wazir duk kuwa yadda ya kai ga boye abin da ke cikinta,yanzun ma kallo daya ta yi masa ta tabbatar da cewa bai gamsu da wannan bukata ta rabi a ba,zai yi biyayya ne kawai kamar yadda ya saba yi,bata da abin cewa tun da ba zata ce da wazir kar ya yi wa Abbun shi biyayya ba dan haka fatan Alkhairi ne kawai abin yinta. A hankali ya janye kofar gilas din da ta mamaye rabin bangon kofar,cikin nutsuwarsa ya saka zara zaran kafafunsa wanda take suka lume cikin tattausan Grass Capet din da ya mamaye dukan falon,bakin shi dauke da yar karamar sallama fuskar nan a kimtse babu alamun ya taba fara a ma bare kuma dariya. Zumbur ta mike daga zaman jiran shigowar ta sa kamar yadda ta yi alwashi ko da ba zai kula ta ba dole ne ta san matsayinta indai har ba so yake to koma ruwa ba. Da sauri tasha gaban sa duk da irin bugun da kirjinta yake saboda tsananin tsoro,Hamma wazir ta faɗa cikin rawar murya da aro jarumta,cak ya tsaya yana kallon yadda ta tare masa hanya,sosai ta boye yadda kwayar idanunshi da tsananin kwarjininsa ya daki fuskarta da zuciyarta har ya fara sata rawar kafa,Hamma wazir ta kuma fada cikin dakiya,yadda ya tsaya bai wuce ta ba shi ya nuna cewa yana sauraron ta, dan haka cikin dan kwarin gwiwar da ta samu ta fara magana cikin marairaita da son ya tausaya mata ta durkusa akan gwiwowin ta ce",dan Allah hamma wazir ka tausaya min wlh idan baka dawo gare Ni ba zan shiga cikin masifa wannan abun da ya faru tsautsayi ne,amma dan Allah kar ka juya min baya na yadda ka yi min duk hukuncin da zaka iya amma kar ka barni,kar fa ka manta Ni matarka ce kuma ina da hakki akanka wlh ina tabbatar maka idan baka sauke hakkina ba ko mai zai iya faruwa da Ni daga ciki kuwa har da komawa ta aikin da na riga na daina tun kafin muyi aure",wata irin tsawa ya daka mata wadda bata san sanda ta koma bayan kujera ta makure ba,tuni kanta ya hau juyawa saboda tsananin tasirin da tsawar ta yi a kanta,nuna ta ya yi da yatsa cikin wani irin ɓacin rai da bata taba gani akan fuskarsa ba,da wani irin sauti da ke fitowa da kauri da amo mai gigita wanda ake yiwa,ya ce",rabi a dan Allah ki koma idan kin ga dama ki dinga kwana da maza goma bai shafe Ni ba,yaushe kika rainani da har kika tsaya a gabana kina bani wasu shirmen zantukan ki?yaushe na zama sa anki?ya tambaye ta yana kuma zaro mata manyan idanunshi kamar dai yadda ake yiwa yaro idan ya yi abin rashin ji. Girgiza kai ta shiga yi jikinta na bari hawaye kuwa kamar an bude famfo. To ki sa a ranki cewa Ni dake har a bada in dai a shimfida ne domin ba zan ci gaba da kwana da kazama ba,yanzu ma dan baki san ko Ni waye a kan kyamar maxinaci ba shi yasa kika zo kina Min shirme,daga yau bana bukatar ko mai daga gare ki,in kin so ki ci gaba da aikin na ki da kika daina tun kafin auren, stupid girl ",ya fada tare da barin wajen cikin bacin ransa da ya gama bayyana saman kyakkyawar fuskarsa. Wani irin kuka ta sa har da birgima kamar karamar yarinya,tana yi tana dukan kanta kamar wata sabon kamu. Kai tsaye toilet ya fada tare dasakarwa kanshi shaya,idanun shi a lumshe yana kokarin saita kan shi da son mantawa da damuwar rabi a wadda yake ganin sam bata da wani amfani,ya jima kafin ya daura alwala ya fito. Zama ya yi kugun shi daure da karamin towel ruwa na sullbewa da ga lallausar fatar shi,hannun shi ya mika ya dauko wayar shi,haka nan zuciyar shi ta dinga jan shi tana rada mishi sunan Raihan ta na kuma zana mishi taswirar hotanta cikin idanunshi sannan kuma take nuna mishi kamar nan ne in da zai samu nutsuwarsa da rabi a ta yi fatali da ita. RAIHAN......... Fitowar ta ke nan daga bathroom wanka ta yi jikin ta daure da karamin towel din da ko cinyiyin ta bai rufe ba,haka kuma bai ritsa ta ba dan haka riko shi ta yi da hannu daya da niyar da ta shigo ta sa kayan bacci ta kwanta dan yau din ta gaji ba laifi. A kan wayar ta dake haske idanun ta suka sauka,hakan yasa ta karasa saman gadon da wayar ke yashe ta dauka,dan yatsina fuska ta yi tana jin haushinsa da na rabi a da ya kasa barin zuciyarta,dannawa ta yi ba tare da ta kula ba a bazata kuma ta ci karo da kyakkyawar fusk ar shi tare da kirar shi ta karfi da ke nuna alamun suna yawan samun giming,sakin wayar ta yi tana dan fiddo da fararen idanunta waje,da sauri kuma ta dauki wayar zata kashe,ganin me take son yi shi kuma ya bata kyakkyawan kashedi cikin kamammiyar Muryarsa,idan kika kashe wayar nan ko mintuna goma ba za ai ba zanzo har cikin gidan na dauko ki a gaban kowa da kowa na kawo ki nan ki kwana a cikin dakin nan a kuma kan kirjin nan",ya fada yana yi mata nuni da faffadan kirjinsa wanda ke cike da kwantaccen gashi baki sidik. Wani irin numfashi ta furzar tare da gyara wayar ta ajiye ta saitin ta, Sannan ta koma ta sunkuyar da kanta tana kananun hawaye tare da kumbura baki kamar fulawar da aka sawa yis,ita sam ta ma manta da yadda take ta idanuwanta kawai take da suke kara hasko mata kirar mazan takar AHMAD WAZIR CHIBADO. A hankali ya koma da kan sa ya kafe jikin gadon yana mata wani irin kallo na kurilla wanda take jin sa a cikin jikinta,wani kakkauran miyau ya hadiya saboda idanun shi da suka fara gano mishi tundun na Fulaninta wanda towel din da ta daura ya dan zame ya sauka, shine kuma ya bashi damar dan ganin nasu,jin yana neman kashe ta da kallon shi da yake tsira mata har can kasan zuciya yasa ta dan ɗago domin ganin me yake yi anya ma kuwa yana kan layi ba bacci yake ba?. Zuruf idanunta suka fada cikin nasa da ya ɗagosu daga kallon kirjinta ya dawo da su kan fuskarta da take wani irin glowing wanda ya yi sa a ita ma ta ɗago nata suka shige cikin nasa,bai yi kasa a gwiwa ba kuwa wajen sarkesu katamau cikin nasa ta yadda ta kasa fuzgewa daga kallon kwayar idanun sa. ..............✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page30 ``` Ƙif_ƙifta idanun ta shiga yi bayan kallon juna da suka yi na kusan mintuna biyu,da kyar ta samu ta kaucewa kallon kaifafan idanun nashi masu kama da mai jin bacci. Mulmula baki ta shiga yi cikin takaicinsa da ke kume a ranta. Kina magana ne? Ya tambaye ta cikin wani irin sauti da salon da yasa jikinta karasa macewa wanda har bata san lokacin da ta saki towel din dake jikinta ba,numfashin da ta ji ya saki kamar wani mai ciwon asma ne yasa ta bude idanunta da ta rufe su da tafukan hannayenta satar kallon shi ta yi take ta ci karo da idanun shi da ke tsaye kyam akan na shanunta da towel ya zame daga kansu ba tare da tasan da hakan ba,wata irin zabura ta yi tare da cukyikyiyewa cikin tattausan bargonta tana jin kamar kasa ta tsage ta shige ciki. Lumshe idanunsa da suka dan sauya ya yi tare da kashe wayar gaba daya, addu'a'in shi ya yi ya shige cikin bargo ba tare da ya sa ko kaya ba,dan ji ya yi ba shi da wannan zarrar zuciyarshi da jikin shi har ma da ruhin shi gaba daya sun mutu da wani irin dafi me zafi dafin da ya kasa tantance ko na meye har yanzu. Ita ma Raihan a haka ta yi bacci da towel da kuma tsananin kunyar da AHMAD WAZIR CHIBADO ya sanya ta. Rabi a kuwa haka ta kwana cikin kuka da takaicin wazir,tare da cin alwashi akan duk wata mace da ta yi sa ar sace zuciyarsa,ta yi alkawarin yadda bata samu wazir ba babu Macen da ta isa ta same shi,tabbas ta ci buri akan wazir kuma yanzun ma bata fidda rai ba,sai dai kuma ta hakura da samunsa a yanzu amma fa babu wadda zata same shi,dan ko zata yi yawo babu takalmi sai ta halaka ko ko nakasta duk wadda zuciyar wazir ke kanta, wannan alwashi ne da kuma alkawari me girma da ta daukarwa kanta. Dudu da shushu uban mashurikai dama sauran mabiya bayansu,yanzu hankalinsu ya kwanta dukkan su sun maida hankalinsu kan abin da ke gabansu wato siyasa dake gabatowa,kowa ya kwanta bacci da niyar wayar gari da ɗorawa daga inda ya tsaya da sababbin shirye shirye da suka samu daga uwar goyon su tsohuwa mai jini. Washe gari da mutuwar jikin da har yanzu bata sake ta ba Raihan ta tashi,tana gama shiryawa ta shiga dakin hajiyar agades,tsayawa ta yi tana kallon hajiyar da ta ga kamar bata ji dadin shigowar ta dakin ba,kai kamar ma wani abu take yi ganin Raihan din ya dakatar da ita,sharewa ta yi da yanayin nata ta shiga gaidata,sama sama ta amsa,ganin da Raihan ta yi kamar hajiyar agades din a kagare take da ta fita daga dakin sai kawai ta yi mata sallama ta juya dan fita daga dakin,Muryar hajiyar ta ji tana cewa Raihan ina so ki dinga kulawa sosai da duk wani na kusa da ke saboda kowa yanzu ba abin yarda ba ne",a mamakance Raihan din ta juyo tana duban hajiyar agades din da ta yi tamkar ba ita ce ta yi magana ba,dama ke ma kin sanni a matsayin Raihan?ta tambayi hajiyar cike da mamakin da ya kasa barinta,hajiyar bata ce mata komai ba,ita kuma Raihan ta kasa fita,wani dan tunani ta yi ashe fa kakan ta yasan ko mai to in haka ne kuwa ba abin mamaki ba ne dan hajiyar agades ta sani,to amma me yasa shi ita hajiyar su ta nan a ka ki sanar da ita me hakan yake nufi?me yasa kakanta ya sanar da hajiyar agades? Idan kika takurawa kanki da tunanin sanin abinda ke boye tabbas zaki saka kanki a rudani,kawai ki tafi da yadda kika fahimta wannan shine shawarata,cewar Hajiyar ta faɗa tana kokarin shiga bathroom,jin jina kai kawai Raihan din ta yi tare da ficewa daga dakin ƙwaƙwalwarta kuma na son fassara maganar Hajiyar agades. Yau bata tsaya jiran kowa ba,duk da dama can ba jiran take ba, da kanta ta tafi ba tare da mashin ko mota ba,dan sahu ta tare ta shiga. Kalle_kalle take yi kamar ance kalli can idanunta suka hango mata wata bakar mota me bakin galas,tare da wasu zaratan maza zabga zabga suna kokarin cusa wasu yanmata guda uku a cikin motar,dukkansu fuskarsu a rufe matan kuma da alama sun sumar da su dan cikin kwanciyar hankali suke saka su cikin motar kasancewar safiya ce babu yawan zirga zirga kuma area ɗin babu yawan jama'a. Cikin sauri Raihan ta ce",da me nafef,yi sauri kabi min motar nan amma dan Allah kar ka bari su fuskanci su muke bi,ok badamuwa me maching ya fada yana sawa adaidaitansa wuta. Daidai lokacin kuma Wazir dake kwance cikin lafiyayyar motar shi Ramadan drivan shi da kuma securityn shi suna gaba,ya bude idanunshi dake lumshe yana duban gefan hanyar da zata sada shi da gidan su Raihan wanda tafiya ƙalilan ta rage musu su karasa gidan,wani irin yanayi ne ya ziyarci gangar jikin shi, a hankali bugun zuciyarshi ya sauya,yanayin da yasan cewa sai Raihan na kusanto shi yake ji ya mamaye shi,bude manyan idanunshi ya yi sosai yana kallon hanyar wanda da sam hankalin shi ba akanta yake ba,giftawar adaidaitan kawai ya gani zuciyar shi ta tabbatar mishi da cewa Raihan ce a ciki,ku juya mu bi dan sahun ya fada cikin Muryar shi dake fita cikin dan kakkauran sauti. Ok oga,Ramadan ya fada yana gaggawar juya motar kamar yadda ya fahimci Muryar ogan nasa shima a gaggauce ya ba shi umarnin. Cikin kwarewa da sanin makaman aikinsa me nafef yadinga kurdawa yana bin motar nan ba tare da sun Ankara da hakan ba, Can cikin zuciyar wazir kuwa mamaki ne da jinjinawa dakiya irin ta Raihan,saboda lokaci kadan ya fuskanci me take shirin yi,tun bayan da yaga sun kaucewa hanyar office ɗin su. Can bangaren su Alhaji sale da su sanet tare da sauran memba da suke tare kuwa suna gidan gonar da yake mallakin Dr sanate suna jiran aikin da suka bada a yi musu,shugaban jam'iya bai san da wannan aikin ba,hasali ma bai san cewa suna munafuntarsa ta bayan fage ba,sai dai kuma abin da bai sani ba shine kamar yadda yake munafuntar uban gidansa gwamna Alhaji Garba to shima haka wadan da ya bawa yarda da amana suke munafuntarsa da son kokarin ganin sun mayar da wani gurbin sa. Zaman jiransu ne ya kare a daidai lokacin da bakar motar ta Kunno Kai cikin gidan gonar,gaba dayansu suka mike bakinsu a washe saboda ganin alamun samun nasarar aikin da suka tura ayi musu,Dr sanate ne ya fara takawa zuwa wajen motar wadda yake binta da kallon tsaf kamar yana son gano wani abu ajikinta,ganin haka yasa sauran ma suka bi bayansa sai dai su hankalin su ba akan motar yake ba ,yana kan yaransu dake fitowa daga cikin motar. Raihan dake daga bayan su ta inda ba kowa zai lura da ita ba,ta yi saurin saita camarar ta ta fara daukar su da fuskokin su daya bayan daya har zuwa kan yaran da motar wanda ta biyo baya,gani ta yi gaba daya sun yi cikin falon dake hagu da su,hakanne ya bata damar fitowa sosai tare da yin azamar zuwa ga motar dan tseratar da yaran da aka kwamushe. Tana sa hannu dan bude motar da bata da tabbacin a bude take taji wani sassanyan ƙamshin da hancinta ya jima da hadda ce shi,da sauri ta juya da mamakin da take ji taci karo da kyakkyawar fuskarsa nan me cike da kwarjini da wani irin haiba dake nuni da shi din cikakken namiji ne me tarin nutsuwa,waro ido ta yi tana buɗe baki dan fidda mamakinta na ganin nasa anan ɗin,kafin tace komai ya riga ta ta hanyar janyo ta daga jikin motar yana cewa kina kiyaye igiyar aure yarinya me karambani",daga hakan yasa hannu ya bude motar,take kuwa motar ta budu, kallon yanmatan dake kwance bayan motar su kayi kowa da irin tunanin dake ransa,mu bar gurin nan ya fada yana janyo hannunta,cijewa ta yi tana fidda camarar ta,kafin ya kuma yin wani abu tuni ta shiga recording yanmatan cikin sauri da nuna kwarewa,yana tabbatar da ta samu abin da take son samu ya kuma jan hannunta suka bar gurin ,barin su gurin ke nan su Dr sanate suka fito suna faman kyalkyala dariya alamun dai duniya ta yi musu da d'i,kafin su shiga motar ta yi saurin fuzgewa ta kuma saita camarar ta dauke su hoto dukan su a daidai lokacin da suke bude motar ana fidda yanmatan da suke kamar gawa. Trouble girl ya fada can kasan makoshinsa yana janyo ta jikin shi suka shiga motar a tare,tura baki ta yi tana kokarin janye wa daga jikinshi,bai hana ta ba ya bata damar hakan,cikin kankanin lokaci y'ansanda suka yiwa wajen zobe,wasu kuma kai tsaye su kayi kan su Dr senate wasu kuma suka shiga ciki dan fitowa da sauran,Saida wazir ya tabbatar sun kamu dukan su sannan ya bawa Ramadan damar barin wajen. Cike da rudani suke kallon junansu bayan duk an saka su cikin motar shiga ba biya fita Saida Allah ya isa,duk cikin su an kasa samun mai yin magana saboda yadda abun yazo musu a bazata,saidai kuma ba su wani tashi hankalin su ba saboda sun san duk cikin kankanin lokaci zasu fita daga tarkon da aka dana musu. Gidado road abin da ya fadawa Ramadan ke nan ya ci gaba da danna wayarsa,Ramadan da shi kadai ya fahimci abinda ogan nasa yake nufi take ya yanke hanya ya dau hanyar inda ka bashi umarnin zuwa. Ƙawataccen gida ne me hawa biyu wanda yake cike da kayan more rayuwa ,ba shi da wasu tarkace komai nasa a tsare yake kamar yadda me shi yake,babu wanda yasan da wannan gidan cikin jerin gidajen na wazir sai amintaccen drivan sa Ramadan,shi kansa securityn sa baisan da gidan ba dan haka sai ya yi tsammanin ko ziyara wazir din ya kawo,dan haka da ya ce", su ta fi bai kawo komai ba ya bi Ramadan suka tafi duk da cewa an bashi umarnin ya kasance tare da shi da duk wani motsinsa. Sai da ta tabbatar da barin su Ramadan gurin kafin ta fara neman ba asin kawo ta nan din da ya yi,banza ya yi mata ya bude yar kofar da bata da wani girma sai azabar kyau,nuni ya yi mata da ta shiga amma sai Raihan ta yi tsaye a gun tana kin motsawa,idan baki wuce ba kin san dai ba gagarata zaki ba ko?bata fahimci abin da yake nufi ba dan haka sai ta kuma yin fuska tana neman hanyar gudu,dan ita a yanzu babu abin da take muradi kamar ya barta ta tafi ta kuma kwaso rahoton police,dan tasan i zuwa yanzu yan jarida sun fara cika ofishin y'ansanda,shima yasan me take so ta yi din dan haka ya taho da ita nan din,bata Ankara ba sai jin ta tayi a sama,daukar amarya ya yi mata ya shige tare da rufe kofar, a hankali ya fara taka matakalar upstairs din da ita,rufe idanun ta ta yi tana kananan hawaye tare da dan kai mishi bugu a kirji, wazir dai nunawa ya yi bai san tana yi ba,ba shi ya sauke taba sai a saman wata lafiyayyar shimfida cikin wani lafiyayyar daki me tsananin kyau da sanyi tare da kamshi me sa mutuwar jiki da ta zuciya. Kamar daga sama shugaban jam'iyya ya samu wannan labarin,duk da cewa babu shi cikin wannan case din to amma fa yasan cewa tunda yaron nan ya iya dauko wannan hoton to kuwa tabbas yana gab da watsa videon nan,ba tare da bata lokaci ba ya fara shiri, abin ka da manya cikin awa daya ya samu ticket din barin kasar, wannan shine kawai abin da zai tseratar da shi da iyalansa,hatta da me gadin sa sallamar sa ya yi dan yasha alwashin ko ƙwaro ba zai bari a gidansa ba bare a samu hanyar kama shi. Tuni fa gari ya dau dumi,gidan jaridu television rediyo kowa da nasa irin labarin,saidai kuma kowa yana jiran safiya ne dan jin cikakken bayani na gaskiya daga gidan jaridar chibaɗo. Kafin lokacin tashinsa ya yi ya yi kokarin haduwa da dan leken asirinsu na gidan rediyon chibado,cikin tashin hankali shugaban jam'iyya ya bashi umarnin akan lallai kafin safiya yana so ya batar masa da wannan video,dan haka dole ne ya yi kokarin gano inda Rahim ya boye shi,ok sir zan yi kokarin hakan amma fa ina tunanin ba a office ya boye shi ba dan da anan ne da yanzu na gani ",cewar matashin saurayin da yake tsaye a gaban shugaban jam'iya cikin nuna girmamawa,shugaban jam'iya ya ce",to kuwa tunda kayi tunani cewa baya office to ina baka tabbacin cewa a office din zaka same shi dan haka ka yi gaggawar duba shi kafin wayewar gari ,idan ka ganshi ka sanar da ni kuma idan na samu isa zan kira ka,akan haka suka rabu kowa na tunanin abin da zai iya faruwa idan videon ya fallasa. GIDAN GWAMNATI......... Tun da labarin ya same shi yake kaiwa da kawowa cikin tangamemen falon da tsayawa bayyana tsaruwar shi da kyalekyalen shi ma bata lokaci ne,a hankali ya kuma kai hannu kan wayar shi dake kan d'an karamin senter table ya dauka tare da danna kiran shugaban jam'iya.bugu daya kuwa ya daga cikin girmamawa suka gaisa,Alhaji Garba ur exsellency ya dan numfasa tare da yin gyaran murya sannan cikin kamilalliyar Muryarshi ya ce", shugaban jam iya kana ina?ina son ganawa da kai a yammacin nan",da sauri shugaban jam'iya ya duba agogon da ke fuskantar shi sai ya ga yana da sauran awa ɗaya kafin jirgin su ya ta shi,dan haka cikin nuna girmamawa ya ce", shike nan ranka ya dade gani nan bisa hanya",daga haka suka katse wayar, Alhaji Garba ya ci gaba da dakon jiran shugaban jam'iya ba tare da ya koma ya zauna ba,saboda yadda abin da ke faruwa din yake tsinkulin zuciyar shi da saka shi cikin wasiwasin anya kuwa wannan tarzomar zata bar shi ya kuma hawa mulki,duk da cewa shi ba dan kansa yake kokarin komawa ba,sai dan al'ummar daya fuskanci cewa suna jin dadin mulkin nasa,to amma fa akwai ƙura indai wannan al'amari ya cigaba da faruwa a cikin jahar tasa. Cikin mintuna goma kuwa sai ga sanarwar zuwan shugaban jam'iya,babu bata lokaci ur exsellency ya bada izinin shigowa da shi,bayan sabuwar gaisuwa cikin mutunta juna kamar yadda yake a tsakanin su,cikin nutsuwa ur exsellency ya sanar da shi abin da yake damun ransa, ya ɗora da cewa yanzu shawarar ka nake nema akan abin da ya kamata mu yi dan asirin kowa ya tonu wanda ta wannan hanyar ne kawai za mu wanku daga zargin da al'umma suka fara yi akan mu",dan jim shugaban jam'iya ya yi kafin cikin nuna alhinin sa ya ce",ai ina ga ranka ya dade kawai ka gayyato HAIDAR YAHYA RINGIM tun da kaga shine wannan al'amari yake hannun sa,dan haka nake ganin kamar da shine ya kamata ku tattaunaa abun da ya kamata domin kawo karshen al'amarin",dan numfashi ya fesar kana ya bawa shugaban jam'iya hannu su ka yi musabaha yana cewa na gode zaka iya tafiya",dan rissinar da kan shi ya yi cikin girmamawa tare da yin sallama ya bar falon da gidan ma gaba daya yana mai duba sauran lokacin da ya rage masa su bar ƙasar,wanda bai wuce mintuna ashirin da biyar ba,a wannan lokacin cike yake da dokin barin kasar tun da yaga al'amarin ya kai ga ta shin hankalin Gwamna,to amma wani abu dake masa susa a rai shine me yasa ur exsellency ya neme shi shi daya ba tare da sauran ba kamar yadda suka saba,yasan cewa ba ne wanda ya cancanci da ur exsellency ya nema ba to amma me yasa ya neme shi? Ina Alh Yahya?ina dufuty?sannan me yasa ya kuma yi masa tambaya akan abinda suka riga suka shawarta tuntuni suka kuma sami mafita?kai gaskiya sam bai yadda da wannan zama nasu ba sai dai idan da akwai wata a kasa .....✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page32 ``` A daidai wannan lokacin da yake cikin zuzzurfan tunanin hanyar da zai kuɓutar da ahlin dan uwansa ,shi kuma ya danno masa kira,jikinsa babu kwari ya daga muryarsa a shake ya yi sallama,cikin girmama dan uwannasa Alh Muhammad nuurr ya ce ",yaya ku fito gaba daya idan muka yi sallar Isha sai muyi dinner ko?da sauri Abba yahya ya saita Muryarsa kana yace ok babu damuwa ganinan tawowa bari na sanar da maimunan, Rahim ɗin ya dawo ne yayi saurin tambayar nurr dan yaji yana kokarin aje wayar, Abbien ya ce",Rahim ya dawo gida tunkafin magrib,Tom gamu nan yanzu,a fito lafiya Abbie ya fada yana kashe wayar,ajiyar zuciya ya sauke ranshi duk a dagule,alwala ya daura ya fita dakin inna maimuna ya shiga samunta yayi itama ta ɗauro alwala ,cikin dan hanzari ya sanar da ita cewa idan ta kammala ta same shi a bangaren ƙaninnashi,amsashi ta yi tana kallon yanayin nashi wanda ko bata tambaya ba tasan tatsuniyar gizo bata wuce koki. Mama murja ce zaune a falonta tana faman isa da takama gata matar me kudi waya take yi da ƙawarta akan oder kayan kiching da tayi wadanda take saidawa,tun kafin ta gama wayar taga wani kiran na shigowa bata damu ba harsai da ta kammala kana ta duba dan bin kiran da akayi mata,amma sai taga anyi hiding nomber ,tsaki tayi tana shirin ajiyewa aka kuma kira,sai da tayi shakara kafin ta daga,ko kin daga ko baki ɗaga ba hakan ba zai dakatar damu daga daukar rayuwar daya daga cikin 'yayanki ba,dan haka ki shirya samun sakon gawar daya daga cikin yaranki",kit aka.kashe wayar,wata irin zufa ce ta shiga keto mata ta ko ina. Waye wannan yake min barazana da rayuwar yayana ? Waye wannan yake son kashe Ni da raina?'ya'ya na sune rayuwata sune kadarata,wai waye wannan din ta kuma tambayar kanta cikin tashin hankali,jummai jummai jummai ta shiga kwalawa me aikinta kiran mafarauta,da gudu jummai ta fito jikinta na rawa dan tasan halin uwar dakinnata,gani haj.......kafin ta karasa mama murja ta katseta cikin tsawa. uban me kike yi nake ta kiranki baki zo ba sai da kika ga dama?zata fara bata hakuri ta katseta a fusace tana cewa ki tashi yanzu kije sashen duka yarana ki duba min kowanne kitabbatar yana nan sai kizo ki fada min,Tom Hajiya ta faɗa tana mikewa cikin rawar jiki. Sintiri ta shiga yi tamkar me jin zawayi ,ita sam ta ma manta da wata waya shi yasa hankalinta bai kawo mata cewa ta kira su ba,zuciyarta cike take da tunanika iri iri na wanda yake shirin yi mata wasa da rayuwar ya'ya,anya kuwa ba Hanne bace? Tabbas hakan zata iya faruwa domin bazata taba mantawa da cewa kowa ta ciki na ciki bace rashin mafita ne kawai ya sa suka hada kansu,lallai idan haka ta faru kuwa Hanne kin shiga uku dan wallahi bazan taba barinki ba. Cikin nutsuwa suka kammala cin abinci,duk da cewa dai Abba yahya dakiya kawai yake,yana boye halin da yake ciki,koda suka kammala inna mainuna da aunty da Raihan da dakin hajiyar agadex suka nufa dan tayata hira. Gyara zama Abbie yayi bayan sun dawo falonsa,sannan ya dubi Abba yahya ya ce", yaya wai me yake damunka? Saboda na lura tun shigowarka kamar baka cikin nutsuwarka. Wani Murmushi Abba yahya yayi me ciwo kana ya ce", Muhammad duk abinda zan fada maka baza ka yadda ba amma duk da haka bazan kasa tofawa ba,domin duk wanda ya yi sanadinka ba kowa yayiwa asararka ba sai mu,nuna mishi test din da akayi masa ta email dinsa ya fara yi,Abbie yana gama karantawa ya saki Murmushi wanda kai tsaye ba zaka bashi fassara ba,mika masa wayar yayi kana ya ce", yaya karka damu kanka babu wanda ya isa daukar rayuwarmu face Allah ya bai kawo lokacinmu ba ,duk wanda kaga ya mutu lokacinsa ne yayi",zuba masa ido Abba yahya yayi kafin ya girgiza kanshi ya ce",wato nuurr har yanzu baka girma ba, na yadda da maganarka amma abinda nake so ka duba shine wahala ake gudu sannan da wadanda a kaiwa asarar wato iyalanka,dan haka Inaso nayi maka wani jankunne,dan shuru yayi sannan ya cigaba da cewa Nura mutane da kake gani basu da imani ba kowa ne yake da irin zuciyarka ba dan haka Inaso ka kula da mutanen da suke kewaye da kai,ba kowa ne yake da amana ba kai hatta da ɗan cikinka zai iya ci maka amana akan dukiya,dukiya da kake gani shu'umar abace kana cikin talauci baka huta ba arzikinma ba kasami kwanciyar hankali ba,dan haka ka kiyaye",bai saurari cewarsa ba ya tashi yana danna kiran inna maimuna dan ta fito su tafi saboda dare ya fara yi. Abbie shuru yayi cike da tunani tun bayan fitar Abba yahya,nazari yake akan maganar Abba yahya,sai ya zamana kamar ya haska mishi wata hanya ne game da binciken da suke yi akan me neman rayuwar Raihan,sosai ya shiga tattara maganganunshi yana tarasu da ɗebewa,lallai ya kamata ya zauna da Dr Sabo da ur exsellency. Cikin wannan tunanin aunty amarya ta sameshi,Abban Rahim me ya faru naga kamar kana cikin bad mood? Murmushi ya kirkiro yana mai janyota jikinshi,bai bata amsa ba harsai da ya bata kyakkyawar sumba a gishi tukunna ya ce",wani labarin tausayi Yaya ya bani yanzu shi yasa duk kika ganni haka",oh to Allah ya taimaki bayinsa na gari Amin ya amsa yana mai lalubo tashar CHIBADO tv da remote din da ya dauka. A bangaren mama murja kuwa bata samu nutsuwa ba harsai da ta samu tabbacin duka yaranta suna lafiya,daga nan ne ta fara saka yadda zata yi maganin Hanne da zuriarta dan tasha alwashin ko ciwon kai yaranta su kayi sai ta dau babban mataki me girma akan duk ahlin Hanne. Wajen misalin biyu na dare mama Hanne na tsaka da bacci ta ji sautin karar wayarta da bata cika kashewa idan zata kwanta ba,cikin magagi ta daga wayar dan jin wane dan iskannee yake sharara mata kira cikin dare haka. Ki tashi daga baccin da kike domin bashi ya kamace ki ba a yanzu,abinda aka fara fada kenan,babu shiri momi Hanne ta murtsike idanunta tana cewa to ubanme ya kamaceni gadin mutanen duniya a ka bani da bazan yi bacci ba? Ba gadin mutanen duniya aka baki ba,gadin 'ya'yanki zaki gwadayi ko hakan zai sa su tsallake mutuwar dake binsu,wata irin wuntsilowa Hanne tayi daga saman gadon da take sharara baccinta cikin jin dadi tayi tana cewa bana son irin wannan wasan kai waye?madaukin ran ya'yan ki ne", ya na fadar haka ya kashe wayar,kan bala'i Ni murja zata yiwa haka ,ai dama nasan wasan bai kare ba shi yasa Nima na daura damarata tun wuri,dan haka muje zuwa yanzu ne asalin wasan zai fara dan wallahi babu wanda ya isa ya taba 'ya'yana na barshi yasha ruwa adoran kasa. *TSOHUWA ME JINI* Hhhahhhhhahh .........shuda aikinka yana kyau,cewar tsohuwa tana maganar bakinta na fitar da wani irin hayaki me tsananin zafi kai kace wuta ce ke ci a cikin bakin,shuda dake durƙushe agabanta kansa a sunkuye ,cikin tsananin biyayya ya ce",jini ya temaki TSOHUWA muna tare dake duk runtsi umarninki nake jira naki fada nawa cikawa,hahhhhh ta kuma ɓarkewa da wata mahaukaciyar dariya har kogon na girgiza kamar zai rabe biyu,sai da tayi me isarta sannan kuma ta haɗe yamutsatstsiyar fuskarta me kama da an dama fura,ta ce", lallai jini na bukatar karin jini daga jikin ahlin wancan mutumin ka tafi kayi hanzari kar jini yayi fushi,jinjina kai ya yi kafin ko mai ya shafe kamar babuu wata halitta da ta ke zaune a gurin. *WASHE GARI* Cikin farin ciki yau rabi'a ta tashi saboda fara shigarta office,cikin gaggawa ta kammala shirinta dan duk a tsammaninta tare zasu tafi, Har abun kari tayi kokarin yi masa duk da cewa tasan ba ci zaiyi ba,zaman jiran fitowarsa ta yi na tsawon mintina goma sha biyar,kafin ta fara shako sihirtaccen ƙamshinsa wanda duk ƙwaƙwar mutum bai isa gane turaren da ya ke amfani da shi ba sai dai hasashe,zuba mishi ido ta yi tamkar zata cinye shi danye,tafiya yake tamkar wani saraki cikin hanzari irin wanda ke nuna cikakkiyar lafiyarsa. Ina kwana hamma WAZEER,tayi saurin gaidashi ganin yana neman ficewa ba tare da ya kalli inda take ba,lafiya,ya amsa cikin ƙasaitacciyar muryarsa ,idan kun shirya habu driver ya kawo ki",bai saurari abinda zata ce ba ya yi ficewarsa. Kwafa tayi kafin ta figi jakarta tabi bayansa,bata taɓa tunanin zaice ta tafi ita kadai ba,dole ta bi umarninsa badan ranta yaso ba sai dan tasan ko shiɗin waye. *RAIHAN* Ke Raihan ki tashi daga wannan baccin ko baki san lokaci yaja ba?juyi tayi asaman gadon tana kuma kanannaɗewa cikin tattausan dovet ɗinta. Hajiyar agadex zata kuma yi mata magana aunty amarya ta shigo bakinta ɗauke da sallama,dole hajiyar agadex ta sauya salon tashin Raihan ɗin da cewa, kai kuwa Rahim wannan wane irin bacci ne kake ko baza ka je office ɗinba yau?jiki a sanyaye aunty amarya ta karasa bakin gadon,tana cewa Hajiya kije zan tasheshi ina ga yau baza shi office din ba",mele baki hajiyar agadex ta yi kana ta juya tabar ɗakin ,cikin zuciyar ta kuwa fadi take , yau naga wani abin al'ajabi ,idan banda abin ramla ai zuwa yanzu yaci a ce ta daina boye min Raihan tunda dai tasan muna tare waje daya kuma dole duk ɓoyonta wata rana idanuna su gane min wacece Raihan,tunda bata da dabarar sauyawa Raihan ɗin halitta a karo na biyu,jinjina kai ta yi tare da cewa zan biki naga inda rainin hankalinnaki zai tsaya. Sai da ta tabbatar hajiyar agadex ta yi nisa da barin ɗakin, sannan ta shiga jijjiga Raihan tana cewa,ke Raihan tashi bana son sakarci da irin wannan sokoncin naki ne zaki janyo hankalin Hajiyar agadex har ta fuskanci me muke ciki,dan Allah Raihan ki rufa min asiri kar na rasaki wallahi ina matukar jin tsoran wannan rana,ki taimaka ki cigaba da bani haɗin kai har zuwa lokacin da zan gano waɗanda suke son kashe minke",ta ƙarasa maganar cikin karyewar zuciya da sanyin jiki,a hankali Raihan ta shige jikinta tana mai jin tsananin tausayin mahaifiyarta,anya kuwa ba za ta gaya mata abinda su Abbie ke ɓoye mata ba?ya za ai ta cigaba da rayuwa a matsayin matar WAZEER ba da sanin mahaifiyarta jigon rayuwarta ba?anya ko zata iya boyewa kamar yadda su Abbie su ka ɓoye?wasu siraran hawayene suka ɓalle mata na tsananin damuwar halin da auntynta take ciki,gaskiya dole tayi magana da Abbie akan wannan al'amari tana bukatar Umminta tasan halin da ake ciki hakan sai yafi kawo kata kwanciyar hankali. Ɗago kanta ta yi tana kallon fuskar mahaifiyarta cike da ƙauna da wani shauƙi ta ce",karki damu ummina zanyi duk abinda kike so Ni dai buri na kiyi farinciki dan Allah ki daina damuwa kinji auntyna", ta kare maganar da goge mata yan guntun hawayen da suka fara ɓata kyakkyawar fuskarta,"jinjina kai aunty amarya tayi tare da cewa ba zaki je wurin aikin ba?. Tura baki tayi cikin ƙunƙuni ta ce",Hamma wazir ya ce ",kar na fito sai ya nemeni", murmushi aunty amarya ta yi kana ta ce",ina jin dadin yadda wazir yake kokari a kanki shi yasa na bashi amana kuma na yadda dashi akanki dari bisa dari,tashi kije kiyi wanka ki ƁOYE jikinki ki dauko kayan da Dr Sabo ya kawo miki dan naga kara cika kike gwara ki fara saka su tun yanzu, sannan ki saka wular kannan dan itama naga kwana biyu bakya son sawa,bayan kin san wannan gashin naki ba ɓoyuwa yake sosai yadda ya kamata ba", Kai aunty amarya duk wannan bayanin kamar kin same Ni da yin ba daidai ba cikin irin shigar da kike so nayi? Ba haka bane Raihan naga yanzu kullum kara girma kike halittunki har sun fara kai munzalin da baza su ɓoyu ba shi yasa nake ƙara shiri akan hakan",Tom shike nan in sha Allah zanyi fiye da baya. komai nawa zai kasance a kimtse kuma a ƁOYE kamar yadda kike so my aunty,ta karasa maganar da shigewa bathroom dan tsaftace jikinta. Tashi itama ta yi ta fita zuwa dakin hajiyar agadex,ji take duk a takure take saboda sun saba rayuwarsu free,amma yanzu tun dawowar Abbie da kuma zuwan Hajiyar agadex ta shiga cikin wata irin takura ,saboda kullum kaf_kaf take da Raihan gani take kamar duk wani motsinsu akan idanun Hajiyar agadex da Abbie yake,uwa uba kuma ga wani dan takurar da ƙarfi da yaji ya shiga jikinsu da kyawawan halayensa,(hamma idi) ga su inna maimuna duk da cewa su bata damuwa da kusancinsu dasu,dan tana da tabbaci akan Inna maimuna da Abba yahya hankalinsu kwatakwata baya kansu bare har su saka musu ido,shima Hamma idi bata masa wani zato to amma dai ya kamata ace kullum tana cikin takatsantsan,ita fa sam ta kasa ganin dalilin zaman Hajiyar agadex a gidan nan dan dai kawai bata da halin cewa bata bukatar zamanta ne.da wannan tunanin ta kai har dakin hajiyar agadex ɗin. Turus aunty amarya ta yi lokacin da ta fito falo ita da Abbie taci karo da Hamma idi da matarshi rukayya a saman dining wai sun zo yin break a nan.kokarin saita kanta ta yi ,sai ɗan duban gefan da Raihan take da tayi, ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta saki ganin Raihan ɗin cikin shigar da tafi bukata tayi editing ɗin kanta sosai dan yanzu ta kware a wannan fannin, ayanzu ko wata aka kawo mata akace ta yi editing ɗinta zuwa namiji tsaf zata iya..............✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page31 ``` A bangaren su Alh ja'e da su sanater kuwa ,wani abun mamaki ne ya faru ,tun kafin su shiga cikin station din dpo ya samu waya daga can sama na umarnin cewa ya saki mutanen da ya kama kuma cikin mutunci da mutuntawa. Wannan lamari bakaramin tsoratar da shi ya yi ba,shi din bawai baya son sakin su ba ne, a'a kawai yana tsoran shiga list din treefull Y trues,babu yadda yaso haka ya sake su ba tare da ya bari cincirindon mutane da yan jarida sun Ankara ba,dakyar suka samu suka kori jama a da yan jaridar da suke son ganin ƙwaf. Tunda ya shiga office dinsa yake sintiri cikinsa cike yake da zawo saboda tsabar tashin hankali,tunaninshi ta ina zai fara warware wannan matsalar mezaicewa mutane da suke ta murnar kama su sanater?idan tree full y ya gane hakan wane hukunci zai dauka akansu?to kai ba umarni aka baka ba,cewar wani bangare na zuciyarshi, wannan tunani da yayi shi ya dan bashi kwarin gwiwar ci gaba da ayyukanshi. *SHUGABAN JAM'IYA* YAna gab da shiga jirgi ya zaro wayarshi dan kashewa gaba daya saboda baya son wani abu da zai iya dakatar dashi daga barin kasar.tesx yaci karo dashi har zai share sai kuma ya shiga dubawa,(kar ka je ko ina ka dawo mun kashe maganar babu wata matsala)ita abinda aka rubuta ke nan, sannan ta email aka turo sakon bai san daga inda sakon yake ba,shigewa jirgi yayi yana tunanin cewa gasar zare ake son hada masa don ya dawo a kamashi,dan haka ba tare da bata lokaci ba ya hada kan iyalanshi suka shige jirgi suka daga. ___________ Su Alh DR sale ma dai mamakin wanda yasa aka sake su suke,tunda sun san cewa babu wanda su kayi wa waya dan sanar da abinda ke faruwa,duk wadanda suke tunanin sune suka sa aka sake su sunyi magana dasu amma abin mamakin sai suce basu bane hasalima basu san ankamasu ba, wannan lamari ba karamin sakasu a caji yayi ba. *SHUDAA..........* Wata irin dariya ce ke fitowa daga matsakaicin falon me kama da gurnanin zaki,sai kuma daga can wata murya me babban sauti da karfin amo ta fara magana,an gaya mu ku mu shashashai ne da za mu bari ku shiga prixin,idan muka bari kuka tafi a bayan wa zamu ci gaba da laɓewa muna aikata laifinmu ,Ni shuda bazan taba bari ku tafi ba saboda kuna mun amfani, kudin babban bango ne agareni bayan tsohuwa me jini",hhhahhhhhahh ya kuma ɓarkewa da wannan shegiyar dariyar da sam bata da daɗin sauraro,duban yaransa ya yi tare da cewa kuje idan ƙura ta ɗan lafa ku samo min idon zawarawa guda goma kuma da ransu zaku cire ba sai kun kashe su ba",mun bika ogah shuda zamu yi biyayya akan abinda ka ke so ,tsohuwa ta kara maka karfin iko",batare da yace musu komai ba yayi musu alamar jinjina da hannu kana ya basu umarnin tafiya . Abba yahya,kuwa tunda ya samu labarin nan ya shiga cikin zuzzurfan tunani, hankalinshi ba karamin tashi ya yi ba,duk sanda aka ce wani abu ya faru a cikin jahar nan ba kowa yake tunawa kuma yake hangeba sai dan uwansa,a cikin wannan yanayi inna maimuna tazo ta sameshi,zama tayi gefansa tana mai cire masa tagumin da yayi,cikin taushin murya irin na matar dake son kwantarwa da mijinta hankali ta ce",abban Bashir,dan Allah ka daina wannan zurfin tunanin kar fa kaje ka hadu da wata cutar ,me yasa baka son bin abu a sannu?janye tagumin ya yi tare da sakin wani kakkarfar huci kana ya dubeta ranshi duk a jagule ya ce", maimuna wallahi ina tsoran shu'umancin ur exsellency ina tsoran irin abinda yake shiryawa ɗan uwana", Inna maimuna ta ce",to ai dama dole a ji tsoran irin waɗannan mutanen da suke rufe ainahinsu ,wato a zahiri su din mutanen kirki ne amma a baɗini halinsu ko kare ba zai ci ba",jinjina kai ya yi yana ɗan rufe idanunshi da buɗewa a lokaci ɗaya, mainuna tunanina kullum bai wuce ta yadda zanyi na kuɓutar da ɗan uwana daga kaidin mugun aboki ba,yanzu bani da aiki sai na gadin rayuwar Nura,kai harma da ta iyalansa dan ina da tabbacin cewa rayuwar Rahim tana cikin hatsari,amma nasan abinda ya kamata nayi wallahi ba zan bari ya halaka dan uwana da iyalansa ina ji ina gani ba, Inna maimuna ta ce",nifa shi yasa sam bana son wannan aikin da Rahim yake saboda za a iya samun dama da mafaka a cutar da shi ta dalilin aikin",kar ki damu maimuna zan yi duk abinda ya dace indai akan ɗan uwana ne",ya fada yana tashi daga gurin,binshi ta yi da kallo cike da tausayinsa shida dan uwannasa. ____ Duban sa Raihan take kamar zata fashe idanunta sunyi ciki saboda tsabar tunzura,ƙunkuni ta shiga yi tana rufe idanuwanta da tafukan hannayenta saboda yadda yayi wata tsayuwar sarakai yana binta da wani shu'umin kallo wanda yake shiga loko da sakon jiki da jini yana bin ƙwaƙwalwa tare da direwa cikin zuciyarta,wani sanyi sanyi ta fara ji a jikinta saboda yadda kallon yake tasiri a gareta,ganin yadda tayin sai kawai yanayin ya tafi dashi,a hankali ya shiga takawa cikin wannan takunnashi na nutsuwa da nuna cewa shi ɗin me aji ne,yana karasowa ya yi wani irin sunkuyowa samanta yayi mata rumfa da faffadan ƙirjinshi yana ci gaba da yi mata kallon da take neman haukatata. Cikin tura baki da kifkifta idanuwa ta ce",nikam ka rabu dani gida zanje,idan Abbie ya neme Ni me zance masa? Kice masa kina tare da mijinki?yayi maganar yana mai kawar da fuskarshi gefe tare da zama daf da ita tamkar bashi yayi maganar ba,zaro manyan idanunta tayi baki bude cikin yanayin mamaki cike da yarinta ta ce",kanbu Abbie zancewa haka?to ai ko Baffa da hajiyar agadex da Hajiya goggo bazan iya fada musu haka ba",bai tanka mata ba sai tashi da yayi ya fita daga dakin,binshi ta yi da kallo tana kebe baki. A hankali ya fesar da wani zazzafan huci yana mai dan murza goshinsa cikin yanayinsa na kullum da ba a gane ainahin zuciyarsa,zubawa wayar ido yayi yana mai jin ɗacin sakon da aka sanar dashi yanzun,wai an sake mutanen da Raihan tayi sanadin kamasu,numfashi ya kuma fesarwa ,kafin kuma cikin saurin da kazarkazar dinsa ya koma dakin da yabar Raihan. Da sauri ta mike tsaye tana kallonsa ,duk da cewa babbar wata alama da zai nuna yana cikin damuwa ba,amma hakan bai sa Raihan ta kasa gane cewa da akwai wani abu ba,mu tafi yace mata yana juyawa,dan jim tayi sai kuma tayi saurin bin bayansa dan ttasan kadan daga aikinsa ya tafi ya barta a wannan gidan. A kofar katon gate dinsu ya ajiyeta ba tare da yace mata komai ba,ganin haka yasa itama ta kuma kama kanta yadda bai tanka mata ba haka itama bata tanka mishi ba, tasa hannu ta bude kofar hatta zura kafarta daya a waje taji kamilalliyar Muryarshi yana cewa kar ki sake fitowa sai na nemi hakan zaki iya tafiya,wai me mutumin nan take nufi da ita ne?tambayar da tayiwa kanta ke nan tana mai ficewa daga motar tare da rufowa cikin dan yanayin tunzura,bai bar wajen ba sai da yaga me gadi ya bude mata karamar kofa ta shiga sannan ya ja ya tafi. Fada yake wa securitys din tamkar zai ari baki,dan me zaku barshi shi kadai babu drever babu ku? Me ye amfaninku indai zaku dinga barinsa yana yawo shi kadai,to wallahi duk abinda ya sameshi Hasan rabu daky ba",abban rabi a ke nan idanunshi har wani ja suke saboda masifa,Abbu ne ya dakatar dashi ta hanyar dafa kafadarsa yana masa magana cikin lallami. Haba Mustafha WAZEER fa ba ƙaramin yaro ba ne dan Allah ka rabu dasu zai dawo gida lafiya, innawuro da hayaniyar ta fito dasu gaba daya ta ce",wai Mustapha kana nufin kafini son wazeerin gida da kake wannan haƙilon? Wannan wane irin makahon so kake yi masa haka? Shuru ya yi yana muzurai kamar wanda aka ce masa wazir din ya yi hatsari,Abbu ne ya kamo hannunshi yana cewa rabu dashi innawuro don da yake masa ba matsala ba ne kawai dai ya dinga control dinsa ta hanyar da ya dace. Juyawa rabi a ta yi tana zuba tsaki,duk komai akan idanunta ya faru,wani abu me kama da kishi taji yana yawo a zuciyarta,tun ba yanzu ba ta fahimci cewa abbanta yana Bala in son WAZEER don ko aurenta da shi da andaka ta abban nata da ba ayi shi ba,wai me yasa kowa yafi son WAZEER ne ? Dame yafi sauran ya'ya? Da abinda kika gani a tare da shi kema kike sonshi ,wata zuciya ta bata amsar tambayarta,tsaki tayi tana kuma jin kishin na karuwa aranta. Innawuro ta dubi abban rabi a ta ce",bana son sakarci Mustafha daga yau kar na kuma ganin kasa yaran mutane a gaba kana musu fadan ba gaira babu dalili,su ba uwaye ne suka haifesu ba? Idan yace su taho ya zasu yi dashi? Kai baka san halin dannaka ba,sam wannan ba tarbiya bace su sauran yan uwanka haka kaga suna yi? . Kiyi hakuri innawuro baza a sake ba in sha Allah,yana rufe baki suka fara shako ƙamahinsa da sautin nutsatstsan takunsa,a hankali ya yi sallama,bai shigo ba har sai da innawuro ta amsa masa kana ya ƙaraso tsakiyar falon inda iyayensa ke zaune. Sannunku da gida,yauwa cewar su baki daya, innawuro ta ce",ina kaje ka tayarwa da abbanka hankali tamkar wani karamin yaro ya fita?ɗaga lumsassun idanunsa yayi waɗanda bakin gashi yayi kwance luf asamansu ya dubi gefan da Abban rabi a yake sannan a hankali ya ɗaga fatar leɓbansa ya ce",ina bukatar pravency ne,daga haka ya mike yaɗan rissinar da kanshi alamar biyayya sannan ya wuce saman shi.innawuro dawo da kallonta kan abban rabi tayi ta ce",to yanzu ka gamsu ko kuwa da sauran magana? Girgiza kanshi ya yi yana dan guntun Murmushi na jin kunya. Yana ɗaukar abinda zai dauka ya kuma saukowa yayi musu sallama,bangaren Amminshi ya nufa,can yaci abinci suka ɗan tattauna kafin ya tashi ya yi mata sallama ya wuce bangarensu. Lokacin da Raihan ta shiga falonsu , babu kowa,har zata wuce dakin aunty amarya sai taji alamun su a kiching,hakan yasa ta fasa shiga koridon da zai Kaita dakin aunty amarya.kichin din ta shiga da sallama,inna maimuna ce ta amsa tana cewa Barka da dawowa Rahim yau dai da alama kayi nisan zangon",karasowa Raihan tayi da murmushi kan fuskarta tana cewa inna maimuna yau kam nashiga rububi,sannunku da aiki ta faɗa tana dan bawa auntynta sumba a gefan fuskarta, yauwa kawai aunty amarya ta ce ta cigaba da tuƙa tuwon semon da take yi,ina hajiyar agadex ta faɗa tana duban inna maimuna?kaima ka san inda zaka sameta ai,cewar aunty amarya,inna maimuna ta ce",tana bangaren Hajiya goggo,ok bari naje na dan watsa ruwa na fito",a fito lafiya. Nan ta barsu suna ci gaba da aikinsu saboda yau anan bangarennasu zasu yi dinner gaba daya har Abba yahya. _________ Yana shiga ya ci karo da rabi a zaune a kujerar farko,ga dukkan alamu jiran shigowar sa take yi,tana ganinsa kuwa tayi saurin mukewa bakinta na rawa tace sannu da zuwa Hamma WAZEER ",yauwa ya amsa a hankali wanda ba daban tana kallon fuskarshi ba bazatasan cewa ya amsa ba ,dan Allah Hamma ka saurareni mintinan da zaka bani basu da yawa",ki fadi abinda zaki faɗa ina abunyi masu muhimmanci",ya fada ba tare da ya daina takun da yake yi ba,wani kakkauran miyau ta hadiya kafin cikin in inar da tazo mata alokacin ta ce",dama maganar aikine ko abbu ya yi maka maganar?gobe ki same bi a office", daga haka ya wuce tabbarta tsaye kamar wata kunki. Har zata sa kuka sai kuma tayi saurin hadiye abinta ,tare da cewa WAZEER Hasan ƙara yi maka kuka ba sai dai kai kayi bazan ƙara bari zuciyata ta yi wahala akanka ba sai dai taka zuciyar ta yi ,nasha alwashin ko da baka soni ba to tabbas kaima bazaka samu abinda kake so ba, wannan alkawarinane. *ABBA YAHYA* Wata irin zabura ya yi bayan gama karanta sakon da aka turo masa ta email address,wata irin zufa ce ta shiga karyo masa duk kuwa da cewa bayan fankar dake kaɗawa a dakin har da na urar sanyaya guri wadda ke fitar da sassanyar iska me dadi ,dafe goshinsa ya yi yana mai zubawa fuskar wayartasa ido tamkar zai gano wanda yaturo sakon ta ciki. Ka fara tanadar likkafanin da zaka rufe gawar dan uwanka da kuma ta iyalansa abu mafi soyuwa agareka,zaka fara dan dana ɗacin rashin ɗan uwa me zumunci kafin ka dan ɗani taka,dan wallahi nayi rantsuwa da Allah babu wani majibincinsa da zan bari a doron duniya balle ya kawo min cikas gurin kwatar hakkina. Da ɗaddaya saina ƙarar da duka ahlinsa domin nadan kowa idanunsa nakan abinda ya tara, dan haka ka shirya lokacinku ya fara mutuwa ta biyo ta kanku...... Waye wannan?anya kuwa ba wani ne daban ba bayan ur exsellency? Asanisa yasan cewa ur exsellency ne kawai yake da wannan burin a ransa shi ma kuma bai gama tabbatarwa ba yana yin bincike ne kawai dan san tabbatarwa ,dan yasan inhar bai tara hujjoji ba kaninsa bazai taba yadda ur exsellency zaici amanarsaba,lallai ashe yaki ne babba a gabansa dole ya farka daga baccin da ya tafi dan lalubo ta inda zai fara kare iyalan dan uwannasa,domin yasan duka yayansa babu wanda zasu kyale tunda sune masu dukiyar da koma waye yake tunƙahon zai ƙwace. .to wai ma ta ina dukiyar Nura ko yace ta Raihan ta zama hakkinsa? Kai shi da kansa ya kulle dole yana bukatar nazari me kyau......✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page34 ``` A hankali ya shiga bubbuga bayanta batare da ya iya cewa da ita komai ba,memakon shiru sai wani kukan da ya kuma gocewa kamar dai dama jiran inda zata sauke shi take yi. Bai ce komai ba har sai da ta yi ta gama dan kanta tayi shiru,cikin tura kanta ƙirjinshi ta fara magana,hamma akwai wanda nake zargi cewa Turo shi cikinmu akai dan kawai ya dauke videon nan",dago kanta ta yi tana kallon kyakkyawar fuskarshi, sannan cikin tunawa da wani abu wanda fuskarta ta nuna alamun hakan,ta ce",hamma wazeer to waye ya sace Haidar kuma saboda me aka sace shi? Idan har masu video ne me yasa zasu Turo wani dan ya sace musu videon? Da sauri ta zare jikinta daga nasa computer sa ta nufa ta shiga saita wannan abun da ta zaro daga jikin labulen office ɗinta,zama ya yi saitin computer hakan yasa ta koma ta bayanshi suka zubawa fuskar computer ido,dukkan su suna cike da mamakin wanda suka gani matsayin dan leken asirin su Dr sanate. Wayyo hamma wannan fa khalid ne bashi nake zato ba,wlh abu Huraira nake zargi,to amma ya akai haka? Kanta ta shiga duka.cike da ruɗani da ake son jefa mata. Da dan karfi ya janyota sai gata akan cinyarsa dabas,dubanta ya shiga yi yana son ta bari su haɗa ido,sai dai ina Raihan ta shiga ruɗani yadda take yi din tamkar wata zararra. ___________ Acikin safiyar dai momy Hanne ta yi kokarin ganin dukkan yaranta,Saida ta tabbatar da cewa lafiya suke sannan taja musu kunne akan cewa lallai suyi takatsantsan da kowa na gidan nan kar su yadda da kowa saboda koda yaushe za a iya cutar dasu,ta nuna musu cewa su ma suyi ɗamarar yin yaki da dukkan makiyansu da suka fara bayyana,duk dai da cewa bata sanar dasu sakon da aka turo mata dashi ba. Abangaren ur exsellency da Abbie da kuma Abba yahya,sun hadu ne su uku dan tattauna matsalar da ki karewa saima karuwa da take da ɗa yi. Cikin nutsuwa ur exsellency ya ce",ku yi hakuri babu wanda zan iya yin wannan maganar idan ba ku ba,saboda kune kadai mutanen da na yadda dasu a wannan kadamin", Abba yahya ya danyi murmushi kafin ya ce,ai ur exsellency babu wani abin yadda yanzu koda mu ɗin ne kuwa ina mai baka shawara cewa kar ka zurfafa yadda domin wanda kabawa amana da yadda shi yafi ci maka amanar,muskutawa ya yi kana cikin dan nuna girmamawa ya cigaba da cewa,bayan wannan ur exsellency ina da korafi akan ɗan uwana",duk zuba mishi ido su kayi kana ur exsellency ya ba shi damar magana,na gode Abba yahya ya fada sannan ya cigaba da cewa ur exsellency a ganina bai kamata idan za muyi tattaunawa ka dinga kiranmu gidan gwamnaty ba,sai nake ga kamar ka ture maganar dan uwana da tun kafin yau ya sanar da kai cewa baya bukatar shiga siyasa wanda hakan ne ya kaika kan kujerar da kake zaune akai,bayan wannan kuma hakan yana iya kawo mana matsala domin kuwa kowa yasan cewa duk wanda yayi motsi a cikin gidan gwamnati to tamkar yayi akan idanun mutanene,za a iya fassara zaman mu da wata manufa,kuma abin akan Nura zai kare saboda kowa yasan cewa bashi da sha'awar mulki mutane zasu ce to yanzu me ya sanya shi shiga,abu na biyu babu yadda za ai zaman da mu kayi ya buya sai dai maganar da muka tattauna itama kuma babu tabbas,dan haka ina rokon alfarma dan Allah duk sanda kake bukatar magana damu ko shi kaje inda yake kamar yadda kuka saba a can baya,za ka iya badda kama kaje gidansa amma shi ba zai iya ba domin gidan gwamnaty ba wasa ba. Tunda Abba yahya ya fara magana ur exsellency yake jinjina kai wanda ke nuna cewa yana karbar maganar da Abba yahya ke yi,duk da cewa ya dan ji kalamansa akwai kausasawa a ciki ,to amma bai damu da hakan ba tunda yasan tun baya ABBA YAHYA shike yi musu fada akan duk abinda su kayi ba daidai ba,to yanzun ma haka ya dauka. Shima abbien yaji dadin maganar da Abba yahya yayi duk da cewa ya dan ji nauyin wasu kalaman,amma dai duk inda aka je aka dawo maganarsa akan daidai take. Cikin nuna girmamawar da ya saba yi masa ur exsellency ya ce",tabbas wannan maganar haka take kuma in sha Allah za a gyara kamar yadda muke son gyara al'amarin jihar nan",yauwaa cewar Abba yahya, Abbie ne ya dan kawo numfashi kana ya ce",to yanzu ta ina kuke ganin zamu fara? Ur exsellency ya ce",Ni ina ga kawai mu baza jami'an tsaro ta ko ina duk wanda suka kama da wani laifi makamancin wannan su kama shi,idan aka kama yaran zasu fadi manyan daga nan har a samu a cimma gaci. Abba yahya ya ce", ban tari numfashinka ba amma kai kasan hakan baza ta yiwu ba,saboda anyi hakan sau ba adadi amma daga karshe sai kaji an sake su kuma a rasa daga ina hakan ke faruwa ,an canja Kwamishina ya kai sau goma amma duk bata canja zani ba,ina ga kawai mu ci gaba da addu'a musa malamai suyi ta sauka a ana sadaka domin sadaka maganin masifa ce, sannan mu je kowa ya zurfafa tunaninsa bincike koda ta sirrine mu samo masu yin taasarnan dan ina da tabbacin cewa acikin mu ne,kaga kuwa babu wadanda zasu iya gano komai sai dai a tsakanin namu mudinga kula da motsin kowa idanun mu ya zamana kullum a bude suke kan mutanan mu",tabbas wannan shawara tayi cewar ur exsellency har fuskarshi na fidda annuri na irin jin dadin shawarar da Abba yahya ya kawo,shima abbie ya ji dadi sosai.. Daga nan suka dan tattauna wasu al'amuran ,sai misalin ƙarfe hudu suka fito daga gidan gwamnaty, Abba yahya ya dubi abbie bayan sun hau titi ya ce",to gida ko Company wanne zaka? Duba agogo Abbie ya yi kana yace muje gida kawai lokaci ya tafi sai Allah ya kaimu gobe",daga haka suka dau hanyar komawa gida. Abba yahya ne ya kula da wata ƙatuwar motar daf cike da simintyy tana bin bayansu da gudu kamar zata bi ta kansu, Abba yahya yace",Nura wannan motar kamar mu take so ta taka ga yadda yake tukyi kamar da hujja",kamar Abba yahya ya sani kafin ya rufe baki motar tayi kansu da gaske so take ta murkushesu,wani irin juya kan motar yayi suka gangara can gefan titi wanda hakan Saida ya jawo musu buguwa,wucewar su taki kadan babbar motar ta gifta su da wani irin gudu har na kusa da driver yana lekowa yana kallon su Abbie da suma kallonsu suke cike da mamaki,yatsa ya nuna musu alamar kashedi. Baki sake Abbie ya ce", to me mu kayi musu waɗannan mutanen haka? Abba yahya yana gyara motar dan cire ta daga inda ta maƙale yace", turosu akayi wannan ba abin mamaki bane Allah ya shiga tsakaninmu dasu, Amin Abbie ya fada yana shiga motar bayan Abba yahya ya cirota ya gyara fakin,dan gurjewa su kayi ba mai yawa ba,har suka je gida ta ajjubin abin suke,ba su bari kowa ya ji ba gudun kawo tashin hankali da damuwa a wajen iyalannasu. Bayan fitar su Abbie ur exsellency ya kira waya shi kadai yasan me suka tattauna da wanda yayiwa wayar amma dai alamu sun nuna cewa abune me muhimmanci a gareshi. CHIBAƊO FM........ Sai da ya tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya dago fuskarta da tayi jajur,dage mata gira ya yi tare da nuna mata fuskarta da girarsa,juyawa ta yi ta kalli fuskarta cikin mudubin dake gefanta ,anan taci karo da kanta saman cinyar wazeer CHIBADO dare dare,da wani irin hanzari ta mike tana lallubar hanyar guduwa,takaici kunya haushi duk sun dabaibaye ta. A tare suka bude kofar da rabi'a ita zata shiga ita kuma Raihan zata fita,turus su kayi gaba dayansu suna kallon juna,kowacce ta gane yar uwarta, Raihan bata iya cewa komai ba saboda yadda zuciyarta ke wani irin halbawa da karfi ,ratsawa tayi gefan Rabi'ah ta shige,sake da baki rabi'a ta bi bayan Raihan da kallo,kallo tayi mata sosai wanda har sai da ta fara jin wani irin tsoro wanda ta kasa gane ko tsoran meye,da kyar ta daidaita kanta ta karasa shiga office ɗin,wai me wannan yaron yake nufi ne? kai ta bakin suryy fa wlh bata yadda da wannan yaron ba akwai wani ɓoyayyan abu dan haka dole tasa ido akansa. A cikin nutsuwarsa ya juyo a tunaninsa Raihan ce ta dawo amma sai yaga saɓanin haka,tsaf fuskar ta kuma hadewa ta dinke kai kace wani mugun sakon aka aiko masa dashi. Duk da cewa jikinta yayi sanyi amma hakan bai sa ta kasa karasawa ba. Me ya kawo ki? Turus ta yi jin tambayar da ya watsa mata amma kai ka ce bashi yayi maganar ba. Yanzu Hamma WAZEER dan nazo wajenka sai ka tuhumeni? Tunda baki da amsa jeki", Wani abu ne ya tsaya mata,har ta kasa hadiyewa cikin fushi ta ce",amma shi wancan dan iskan yaron yana zuwa duk lokacin da yaga dama amma Ni da nake matarka kana kokarin samun get da shigowa inda kake", Idan ba maganar aiki ce ta kawo ki ba kar na kuma ganin ki a nan',ya fada yana kuma kame fuskarshi wadda take kamar zata yi aman wuta. Ganin babu sauki yasa dole ta juya ta fita cikin wani irin fushi da alwashi iri iri aranta. BAYAN SATI ƊAYA......... Shugaban jam'iya dai sai da ya tabbatar da cewa babu wata damuwa sannan yabar iyalansa a can ya dawo,yayi hakan ne koda zata kwaɓe sai yaji da kansa iya shi kadai. Bai damu da tuhumar su Dr sanate ba saboda yasan shima ba haka ya zaunaba,dan haka ya bisu aka dora daga inda aka tsaya,dan kuwa babu abinda suka rage daga irin sharrinsu da kuma kulle kullensu duk akan kujerun da suke son hawa. A bangaren su RAIHAN kuwa tun ranar da suka.gane Khalid har yanzu basu kuma sashi a idanunsu ba,bare kuma ya shigo da sunan aiki,duk da cewa Raihan har yanzu bata yadda cewa Khalid ne da Wannan aika aika ba,saidai ta dauki matakin tsayawa tsayin daka dan yin kyakkyawan bincike akan sarkakiyar da suke ciki ta kuma sha alwashin sai ta nemo inda Haidar yake a mace ko a raye. Batun rabi'a kuwa tun ranar ta fara kafawa Raihan duk wani abu da yasan zata yi ya kuntata Rahim to shi zata yi ,ta dauki wata irin tsana ta ɗorawa Rahim ,yayinda ita kuma Raihan kallonta take a matsayin mahaukaciya duk da cewa tana jin wani irin abu me tsananin zafi duk ta tuna cewa rabi'a matar WAZEER ce. A hankali ta gyara likaf ɗin dake sanye a saman fuskarta kafin cikin takatsantsan ta gyara zamanta tana mai fuskantar mutuminnata. Ta ce", na karanta duk bayananka da kuma kudurinka akan ahlin CHIBAƊO,tun lokacin nake jiran sakonka sai dai amma shiru kamar maye yaci shurwa,shin kana tunanin a wannan tafiyar wahainiyar zamu cimma burikanmu? Shima gyara zamansa ya yi tare da zaman fecemack dinsa kana ya ce", me lullubi duk abinda kike tunani ba haka bane,ina can ina shirya mana makaman yaki wadanda za muyi fita daya zuwa biyu dasu mu cimma kudurinmu,ke Raihan kike son ganin baya Ni kuma surukin Raihan da mijin Raihan Kinga kuwa dole mu cure waje daya tunda minti tarayya akan manufa daya,ba iya Raihan nake son ganin baya ba harda yan uwanta da mahaifinta kai da duk wani me ruwa da tsaki a cikin dukiyar Nura,ina son daukaka shahara shura sai dai kuma kash wadannan abubuwa basa yiwuwa sai da kudi Ni kuma bani da kudi,ina son shiga cikin manya a dama dani bazan iya kirga maka adadin burikana ba,wadanda kuma basa taba samuwa gareni sai da kudi.dan haka dole na kashe Nura da da Raihan dan na samu abinda nake so,yaransa su zasu zame min katanga domin kowa burinsa ya samu dukiyar da take a matsayin ta Raihan ",... In tambayeki mana? Abokin cin mushenta ya tambayeta,ina jinka? Wai me yasa kowa keson dukiyar Raihan? Shin da ya bata dukiyar nan bai bawa Kowa daga cikin iyalansa ba? Kuma me yasa dukiyar Raihan tafi ta kowa yawa da haɓaka? Wani dan Murmushi tayi kana ta ce", wallahi Allah daya kenan nur ya fita hakkin iyalansa domin duk abinda ya bawa ƁOYAYYAR RAIHAN sai ya fitar da na sauran iyalansa, sannan abinda yasa dukiyar Raihan tayi yawan da me zato bai taba zata ba tayi yawan da har tazo ta ninka ta ubanta sau dubu shine duk lokacin da ya cire wa Raihan wani abu adukiyarsa juya mata ake yi su kuma ragowar yaransa tunda sun kasance maza kuma suna nan sai yake warewa yana aje musu,duk wani Company da kaga Ni ko gidan mai ribar Raihan ce ta samar dasu,a lokacin da Nura ya dankawa yaransa dukiyoyinsu a lokacin tuni dukiyar Raihan ta kai inda me zato bai zata ba. Sai dai cash ba kowa ne yasan wannan labarin da nake baka ba,domin duka yayansa kallon mahaifinsu suke a wanda baida adalci ya dauki hakkinsu ya baiwa gaibu dan haka dole kowa yanzu yake haƙilon yadda zaiyi ya kwaci dukiyarsa,ina mai kuma jaddada maka cewa babu wanda yasan wannan sirrin wato asalin sirrin dukiyar Raihan. Ke ya akai kika sani? Dariya tayi me dan sauti kafin ta ce ", haba abokina ba sai kaji wannan ba,iya wannan ma da na gaya maka ya ishe ka,yanzu dai wa kake ganin za mu fara aikawa uban ko yar? Ta bangarenka kuma wa za a fara kawarwa uban ko ɗan? Girgiza kai ya yi kafin ya ce", ta kananun za mu fara wato yaran Alh nur maza saboda sune suke kawo hari akan dukiyar Raihan idan an gama dasu sai uban",a bangarena kuma yanzu ya kan yaron zan fara saboda yafi uban wahalar sha ani nasan wanda zan tura ya yi min wannan aikin", dan jim ta yi kafin ta ce", ta wacce hanya zamu aika yaran sannan da wa za mu fara? Hoto ya nuna mata ba tare da ya bar hanyar da wani zai iya gani ba,dariya tayi kana suka mike gaba daya kowa yabi hanyar da ya bullo. RAIHAN Kinga takanki........✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page33 ``` Aunty Rahim sannu da fitowa rukayya ta faɗa cikin yanayin girmamawa,yauwa rukayya ,Aunty amarya ta faɗa tana zama a kujerarta dake gefan Abbie, Hamma Idris ma gaidasu ya yi cikin girmamawa da wayewar da ke nuna cewa akwai fahimtar juna a tsakaninsu. Cikin kwanciyar hankali suka fara karyawa,wayar Raihan ce ta dan kawo haske alamun shigowar sako,ɗan dakatawa ta yi da kai ruwan Lipton bakinta tana mai duban wayar,bata cika daukar waya idan tana cin abinci ba,kamar yadda iyayenta suka dorata kai. Sai dai kuma haka nan taji bazata iya jurewa har ta kammala kafin ta ɗaga wannan sakon ba,sai da ta fakaici idanun Abbie Sannan ta yi saurin daukar wayar ta bude inbox. Zaro manyan idanunta ta yi,kana cikin mamaki har bakinta na rawa ta ce", what? Duk kuma sai hankalinsu ya dawo kanta,cikin fargaba da tsoran da ya riga ya zauna mata aunty amarya ta ce",lafiya me ya faru?cikin wani irin takaici da tasowar tsohon miki Raihan ta ce", Abbie wai kaji an sake mutanen da aka makama jiya,a yadda labarin yazo min ance ko shiga station din ba su yi ba aka bada umarnin sake su. Jinjina kai Abbie yayi yana mai jin ɗacin hakan a ransa,Hamma idi kuwa zabura ya yi cikin nasa takaicin ya ce",gaskiya Abbie ya kamata a dakatar da wannan abun haka,ya za ai ana tufka wasu shegu na warwarewa gaskiya da sake,Ni wallahi na fara zargin gwamnatin nan kamar yadda da yawa mutane suke zargin da sa hannunta a kan duk abinda ke faruwa", Abbie ne ya dakatar da shi cikin rashin jin dadi ya ce",Idris ka nutsu bana son rashin ɗa a", kayi hakuri Abbie Hamma Idris ya fada yana kallon yanayin fuskar abbien da ta nuna rashin jin dadin kalamin da ya yi akan gwamnati. Cikin damuwa Raihan ta dubi abbien ta ce",Abbie kayi hakuri da abinda zance,ta cigaba da cewa Abbie ko Ni ina zargin gwamnatin nan da rashin gaskiya idan ba haka ba Abbie ya za ai ace an kama mutane kuma ansa an sake su ba tare da ko cikin station din sun shiga ba?kuma babu me karfin hakan sai gwamnatin da ke kan mulki,Abbie mutanen nan fa duka bakinsu daya. a idanun duniya ne suke makiyan juna amma a bayan fage kansu a hade yake ,yarjejeniya ce a tsakaninsu,wallahi Abbie yau sai nayi rubutu akan haka sai na fidda abinda suke boyewa duniya dan naga idan ba muyi da gaske ba mutanen nan so suke su halaka mu baki daya",wani irin kallo aunty amarya ta yi mata kafin ta ce", Rahim kar naji kuma kar na gani babu ruwanka da abinda suke yi,bana son ka jawowa kanka wani bakin jinin bayan wanda kake ciki dan Allah kabarmu muji da wanda yake damunmu",duk zubawa aunty amarya idanu su kai suna kallon fuskarta da idanunta da suke cike da fargaba da tashin hankali,Abbie ne yayi gyaran murya sannan cikin nutsuwa ya ce", duk me ya kawo wannan batun? Dan Allah ku kwantar da hankalinku yanzu fitar da zanyi ur exsellency ne ya kirani nasan kuma ba zai wuce wannan maganar ba,idan ma da sa hannun wani a gwamnatin duk za mu bincika kuma za a kamasu a yi musu hukunci daidai da laifinsu",daga haka ya mike yana shirin fita, Raihan ma mikewa ta yi dan ji ta yi sam ba za ta iya bin umarnin Hamma wazir ba,dole ne taje office ta gabatar da abinda ke ranta, ranar bude video ce yau Allah ya kawo,tunda su basu san zuru ba,to duk yau zatai maganinsu,tana ganin fitar da videon nan ne kawai zai iya kawo karshen mutanennan. Abbie tsayani mu tafi tare",tafada tana yin hanyar dakinta dan dauko wasu muhimman abubuwa. A'a kuje idiris ya kaika,saboda tare za mu fita da yaya Yahya", Allah ya kiyaye su kayi masa, ya fita yana amsawa, tare da kokarin lalubo wayar Abba yahya. Anty amarya dai ranta baiso ba ta bari Raihan ta fita, a hakan ma ji take kamar ta bi sawunsu ,gani take kamar wani abun zai iya samun Raihan ɗin,sai dai da ta tuna Allah sai tayi istigfari ta yi mata addu'ar kariya. Ruby......... Tana ganinta a cikin kyakkyawan office din da ya zama mallakinta tayi juyi tare da yin shewa sannan ta fara neman lambar Surry dan ta fesa mata labari. WAZEER yana tsaye a jikin window office dinsa,idanuwansa ba ko ina suke kallo ba sai kyakkyawan titin da zai kawoka har babban building ɗin nasu na CHIBADO FM,motocine kawai ke kaikawo cikin tsari da bin dokar gwamnaty, sam ba zaka iya tantance halin da zuciyarshi ke ciki ba,dan babu wata alama da ya bari da zai nuna maka ainahinsa. A hankali yake kokarin janye idanunshi da gangar jikinshi daga jikin dogon ginin office ɗinnashi,kamar ance ya kuma duban wajen sai kuwa yaci karo da Raihan dake fitowa daga motar Hamma Idris,cikin yanayin dake nuna ɓacin rai da damuwa,yana kallo ko sallama bata yiwa Hamma Idris ɗin ba tayi gaba cikin ɗan hanzarin dake nuna akwai abu me muhimmanci dake gabanta. Furzar da wani zazzafan huci ya yi tare da barin gurin,ayyanawa yake a ransa yasan za ayi haka,wuyarta ace bata ji abinda ya faru ba,amma yasan halin kayansa muddin ta samu labari to tabbas sai ta shigo building ɗin kamar dai yadda ya zata. RAIHAN dai babu wanda ta kula kai tsaye office ɗinta ta nufa. Turus ta tsaya tana kallon yadda a kayi kaca_kaca da wurin,an janyo durowowi an wargaza mata duk wasu takardu da suke shirye. Waye da wannan aikin? Ta tambayi kanta cike da mamaki, Dan Murmushi ta saki tana cewa dama nasan za a zo wannan gurin", A hankali ta karasa jikin window dake saitin kofa ta cusa hannunta jikin labulen ta can sama yadda ba kowa zai kawo da wani abu a gurinba,wani dan karamin abu me kamar kwallo ta dauko,juyashi ta shiga yi tana kallonsa fuskarta ɗauke da Murmushi,bata yi wata wata ba ta juyya ta fita daga office ɗin. Lifter tabi ta ta karasa office ɗin AHMED WAZEER CHIBAƊO. ______ Suryy na tare da boyayyyan mutuminta kiran ruby ya shigo wayarta,duban ɓoyayyiyar fuskarsa ta yi tana masa nuni da fuskar wayarta.nuni yayi mata da ta daga ta saka a amsa kuwa. Yadda ya umarceta da yi haka tayi,saiga Muryar ruby ta fito raɗam cikin yanayin dake nuna komai yana tafiya daidai,tace",Surry aikinki na kyau yau dai gani cikin office ɗin CHIBAƊO FM a matsayina na me karbar korafin sirri akan jami'an tsaro ya kika ga wannan lamari?dariya suryy ta yi cike da nata jindadin na ganin cewa duk yadda suka shirya ko mai na tafiya dai-dai,gyara zamanta tayi saman kujerar da take kai sannan ta ce", ruby ki nutsu kiyi abinda ya kai ki karki yi shirmen da zaisa a ganoki dan naga alamun wannan rawar jikin da kike ya soma yin yawa ehem kinutsu ina kuma jaddada miki,yanzu dai ki bani lokaci na tsara abu na gaba zuwa anjima zan kira ki",ruby ta Dan ja numfashi kana tace haba suryy ya kike min kamar ba danni kike komaiba ya za ai nayi abinda WAZEER zai dago jirgina karfa ki manta idan hakan ta faru ba kece a ruwa ba nice a ruwa tsundum kusa da kada,dan haka ki daina min wannan kashedin ina jiran kiranki anjiman",tana gama fadar hakan ta kashe wayarta tana jan tsakin rainin da suryy ta yi mata. Dariya suryy ta fashe da ita tana cewa yarinya fadi ki kara fada tabbas kece a ruwa,dan ma baki san irin aiyukan da zaki mana ba ke nan. Menene netx plan ɗinmu oga?gashi dai nasa rubyy ta shiga CHIBAƊO FM da sunan aiki ko meye shirinka akan haka? Wani shegen Murmushin da ba a gani ya yi , sannan cikin Muryarshi da kullum take sauyawa baka taba cewa ga Muryarshi guda ba duk yadda ka jima da shi kuma kake da shi,ya ce suryy aikinki ya yi kyau,ke dai ba burinki wazer ya rasa su duka biyun ba kema kuma daga nan sai ki kutsa cikin rayuwarsa ba? Jin jina kai tayi cike da bashi tabbaci akan tambayar da yayi mata,woldon ya fada yana duba fuskar wayarshi sannan ya dago ya dubi suryy ya ci gaba da cewa,asirin Raihan zai tonu ne ta wajen Ruby", zuba mishi ido suryy ta yi cike da son ƙarin bayani, fahimtar hakan da ya yi ne yasa shi jinjina kanshi yana mai ci gaba da cewa duniya zata san cewa RAHIM ba namiji ba ne macece,kuma ba kowa ne zai fidda wannan labarin ba sai rubyy matar WAZEER,za musata ta fidda labarin ta wata sigar daban yadda za mu jawo hankalin mutane kan Raihan wata ƙil ma hakan ya jawo mata bakin jini domin idan aka hau teburin malamai lallai sun tafka kuskure kuma malamai zasu kalubalance su akan wannan abu da su kayi". Cikin zakuwa suryy ta ce", to meye amfanin hakan agaremu? Dariya yayi yana mai jingina bayanshi da kujerar da yake kai zaune, sannan ya ce", sury me yasa kanki baya ja ne a wasu lokutan? Kaima kace a wasu lokutan dan haka bani haske", Suryy duk duniya waye bare da yasan sirrin Raihan da mahaifiyarta? WAZEER ne", ta bashi amsa kai tsaye kuma cike da zakuwa,yauwa idan har wannan labarin ya fita kuma daga jaridar CHIBADO daily trues me kike ganin zai faru? Wa Raihan da mahaifiyarta zasu zarga? Idan mahaifiyar Raihan ta tsani WAZEER me kike gani zai faru?bare kuma idan Raihan da kanta tayiwa WAZEER tsana mafi muni ita da mahaifiyarta to ya kike ganin wasan zai kasance? Bari na tuna miki daya daga cikin halayyar da Raihan tafi tsana tsana mafi muni,cin amana da yaudara, sannan abinda tafi ƙauna ƙauna mafi ƙololuwar daraja itace mahaifiyarta duk abinda take yi tana yi ne don farin cikin mahaifiyarta bawai dan tana tsoron mutuwa ba,to tayaya kike ganin tsanar zata kasance saboda ta kasance ninki biyu",? Baki sake suryy take kallon fuskar da bata ganin ainahinta,wani mutum guda da take ganin cewa makircinsa da sharrinsa ya fi na mata dari,da ta rasa abin cewa kawai sai ta kama hannunsa ta ƙanƙamr cike da wani irin farin ciki kai kace ta samu wazer dinne ta gama. Sai da ya bata dama ta gama fariincikin sannan ya magani da cewa,yanzu kin fahimci ribar tamu?na fahimta oga to amma idan mun kawar da Raihan daga rayuwar WAZEER to ita kuma Ruby fa?tafa hannayensa ya yi cike da jin dadin tambayar da tayi masa yace", wannan tambayar nake jira domin nafison duk abinda zan fada ya zamana cewa an tambayeni hakan na kara kawo min dabaru cikin ko wane shiri da zan gabatar. Cike da burgewa Surry take kallonshi saboda yanzu ji take haɗuwa dashi ya zame mata babbar riba,yayi mata amfani yayi mata rana ranar da baza ta taba mantawa da ita ba,fahimtar abinda take saƙawa ya sa shi ci gaba da cewa,"WAZEER ya iya ɓoye abinda ke zuciyarshi,dan haka har yanzu bamu da tabbacin cewa yana son Raihan ko baya sonta,abinda dai muka sani shine ya ɗauketa da matuƙar muhimmanci ta wani ɓangaren kallon ahlinsa yake mata, sannan bincike na ya tabbatar min da cewa WAZEER yayiwa amarya mahaifiyar Raihan alƙawari akan cewa ba zai taba sanar da kowa wannan sirrin ba,ya ɗau amanar Raihan da hannu biyu,shin ya kika ga abun zai kasance idan yasan cewa matarsa rabi itace ta fitar da wannan sirrin ? Dama bata cikin ransa fit zata kuma fita zaiyi mata tsana me muni akan yanzu, wazer yana da taurin kai sannan mutum ne me tsayawa akan magana guda idan yace ya rabu da rabi har abada to har abadan yake nufi. Tafi sury ta kuma yi masa cike da gamsuwa da duk abinda ya zana,oga baka ganin cewa idan ya gano gaskiya zai iya zuwa ya warwarewa Raihan da mahaifiyarta ? Idan suka yadda fa kaga dai Raihan ta dawo ke nan", tabe baki ya yi kana yace", ba zamu bari hakan ta faru ba,zamu bi duk wasu hanyoyi na ganin cewa shiima ya samu Raihan da wani laifi wanda zai hana shi zuwa garesu dan warware musu gaskiya, sannan ba alokaci daya za muyi wannan ba,idan labarin ya fita sai mun tabbatar da cewa komai ya cakuɗe kamar yadda muke so sannan mu tonawa rabi asiri ta yadda wazer zai kamata da laifin redhand",. Ok na gane oga zanyi komai cikin takatsantsan har mu cimma gaci,amma inaga wannan aikin kamar nawane Ni kadai shin meye kudurinka akan Raihan? Wani duba ya yi mata kafin ya nuna mata yatsa ya ce",ki tsaya matsayinki kar ki ƙara min wannan tambayar wannan sirrina ne ", ganin yadda yayi lokaci daya sai hakan ya ɗan bawa suryy tsoro babu shiri ta mika wuya tare da bada hakuri....... RAIHAN tana kokarin shiga office ɗin tana ci gaba da gwada wayar asp Haidar,ta rasa me yasa yau kusan kwana shida ke nan tana gwada kiranshi amma ta kasa samunsa,sai yanzu hankalinta ya fara tashi saboda tun ranar da ta kira shi suka tattauna ya tabbatar mata da cewa yana da wasu manyan bayanai akan mutanen da bata taba zato ko tsammata ba,shi yasa ta dauki video ta bashi akan ya haɗa da bayanan wajensa idan lokaci yayi sai su fitar baki ɗaya,ta tuna tun ranar basu kara yin waya ba kuma ko a chat bata ganinsa. Cikin wannan tunanin ta shiga office din,zuba mata ido wazer ya yi ganin kamar bata cikin hankalinta,sauke wayar tayi tare da aje numfashin damuwa idanunwanta cike da kwallar tunanin da yake zuwa mata akan Haidar ta ce",Hamma wazeer dan Allah kira wayar Haidar ko kai zaka.iya samunsa",bai ce mata komai ba ya dauki waya ya shiga neman Haidar ɗin sai dai shima bai samu ba yadda ake ce mata akashe take shima haka aka gaya masa. Wayyo Allah Hamma shima sun kashe shi kuma sun boye shi,kamar yadda suka yiwa halima", ganin yadda duk ta birkice yasa shi tashi cikin natsuwa ya ƙaraso inda take tsaye tana yarfa hannu idanu cike da ƙwallah,gaya min me yake faruwa? Me kike boye min?. Cikin kamekame ta sanar dashi maganar videon da yadda akayi ta bawa Haidar ɗin.zuba mata ido ya yi fuskarnan kamar hadarin gabas,cikin fitar maganar shi daidai ya kira sunanta", Raihan",cike da tsoro take kallon fuskarshi dan kuwa tasan tayi babban laifi,kin iya boye min irin wannan abun dama? Yarfa hannu ta ci gaba da yi kana cikin tsoro ta ce", Ni tsoro nake ji kar suyi maka wani abu",gashi sunyiwa Haidar ya fada yana watsa mata kallonnan nasa me firgita me laifi,kuka tafashe dashi me ciwo wanda dan dole yasa shi sassauta kallon tuhumar da yake mata,ganin taƙi yin shiru yasa shi takawa daf da ita ya kamo hannunta,baiyi kasa a gwiwa ba a hankali ya janyota cikin faffaɗan kirjinsa domin baki ba zai wadatar dashi wajen rashin ta ba............✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page35 ``` Abba yahya bai sanar da inna maimuna abinda ke faruwa ba,wanka ya shiga yayi ya saka doguwar jallabiya sannan ya fito falon. Samun inna maimuna yayi zaune hannunta rike da waya fuskarta cike da damuwa kamarma dai kuka taci saboda yadda idanunta suka yi jawur dasu kamar an bada musu barkonon tsohuwa,zama yayi gefanta yana yi mata duban tambaya,ganin yadda ta bawa banza ajiyarshi yasa shi magantuwa da cewa maimuna meke damunki ne haka?cikin fusatar da bai taba ganinta da shi ba ta ce", haba Abban Bashir wane irin uba kake so ka zama wanda bai damu da rayuwar iyalanshi ba,yau kwana na uku ina neman wayar Bashir amma bana samu kuma kai banga alamun damuwar haka a tare da kai ba,karfa ka manta kaine kasa yaron nan yaki dawowa mahaifarsa akan kana son hukunta shi akan kuskuren da yayi wanda bai wuce kan kowa ba,"au kuskure ma kike kiran wannan bakar halaiyyar tasa dashi,har kin manta halayyar dannaki ko? Zata yi magana ya dakatar da ita. Dakata maimuna wannan fadan naki na rashin daliline,me yasa lokacin da na dauki matakin kika bada goyan baya,ke yanzu ba abun kunyarmu ba ne ace yaron nan ya tafi tare da yan uwansa kowa ya dawo da abinda aka tura shi nema banda shi,me yasa ya biyewa shashashan abokai har ya fadi jarrabawa idan bance ya zauna ya maimaita ba ya kike so nayi? Sassauta murya ta yi kana ta ce", nasan Bashir yayi laifi amma da mun sani ba mu boyewa Nura ba,kaga fa daga karshe ce mana ya yi yayi aure kuma nasan cewa wannan yarinyar da ya Turo mana baza ta kasance me tarbiya ba,kuma be kamata kayi fushin zuciya dashi irin haka ba,duk lalacewar naka ai naka ne."yanzu me kike so nayi? Idan banyi masa haka ba ya kike so nayi ?wai ko anya maimuna kinsan irin manyan taasar da danƙi yake yi a can? Shiru tayi ranta sam babu dad'i,dan nisawa tayi tare da cewa abban Bashir kayi hakuri dani amma duk laifin Bashir Ni uwa ce babu ta yadda zanyi na cireshi a raina kamar yadda kai kayi, sannan ina neman alfarma dan Allah ka barni naje na dubo lafiyarsa a karo na farko dai kayi min wannan alfarma",shi kadai gareni Banason wani abu ya sameshi", Tashi Abba yahya yayi ba tare da yace mata komai ba,binsa ta yi da kallo ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a maleshiya. _____________ Dawowarsa ke nan daga campanin auduga na Raihan wanda karkashin kulawarsa yake hannun babban dan ur exsellency wato Yusuf,sosai yaji dadin halartar Company saboda lissafin da aka fitar wanda aka ware ribar da aka samu a ka ware kudin albashin ma aikata da na zakka da dai sauran duk abinda ya kamata comfani ta yi a shekara,dadin da Abbie ya ji shine irin ribar da aka samu a wannan shekarar kamar wanda ake zubin dashinta kullum. Kai tsaye sashen Baffansa ya nufa a nan ya samu Abba yahya,bayan sun gaisa Baffa ya dubi Abbie ya ce", Muhammad da alama yau kana cikin farin ciki bani nasha",dariya Abba ya yi yana cewa haba Baffa kaima kasan babu wani abu da zai samu Nura wala na alkhairi ko akasinsa da zai sameshi bai sanar da mu ba ko ba haka ba Nura? Ya fada fuskarshi cike da annurin da tasamu bayan ganin farincikin dan uwannashi. Dariya Abbie ya yi ya ce, wannan haka yake yaya daga nan ya gyara zamansa ya sanar dasu komai harma da na sauran companies din dan wannan shine na karshe a fidda lissafin,masha Allah alhamdulillah suke ta maimaitawa bayan jin wannan daddaɗan labarin,fuska cike da walwala zuciya fari kal suka gabatar da addu'a daga nan suka fita sallar la'asar. Sosai Raihan ta sawa ranta lallai sai ta gano abunda ke boye dan kuwa ɓatan Haidar ba karamin girgizata yayi ba,tuni suka saka sanarwar ɓatansa a kafafen sadarwarsu,kanka ce wannan gari ya dau dumi,tuni jam'i an tsaro suka fara aikinsu wasu dan Allah suke yi wasu na musu barazana wasu kuma an siye su da kudi,kai wasu ma aje aikin sukeyi dan ganinsu da su aikata ba daidai ba Gara su hakura da aikin. Ur exsellency da kansa ya nemi yin hira a gidan tv CHIBADO kuma yace yana so a nuna live kai tsaye ga masu kallo,cikin kankanin lokaci a ka shirya zaman su abu Huraira tuni suka bada sanarwa.raihan tare da wazeer su zasu jagoranci shirin. Da misalin ƙarfe biyar aka fara haska tattaunawar. RAIHAN cikin shigarta ta basaja wadda duk kokkofinka baza ka iya gano sirrin matantakanta ba,cikin gyara zama da yin gyaran murya irin dai yadda aka san yawancin maza nayi,ta ce", ur exsellency muna yi maka Barka da zuwa a madadin ɗaukacin al'ummar dake cikin wannan gida da kuma masu kallonmu a daidai wannan lokaci,amsawa ya yi cikin daddakonsa,kana Raihan ta ɗora da cewa ur exsellency za mu so jin abinda ke bakinka damu da masu kallo akan abubuwan da suke faruwa a cikin jahar nan", Dan gyara zama ya yi fuskarshi na nuna alhinin abinda yake faruwa ya ce", Assalamu alaikum jama'ata ,hakika na nemi magana ne domin kawai na baku hakuri akan dukkan abinda ke faruwa daku da mu baki daya,duk da cewa nasan hakan ba zai rage muku ko kadan daga cikin zaluncin da ake yi muku ba,amma duk da haka dole na baku hakuri da kuma sanar da ku cewa lallai za izinin Allah za mu kawo karshen rikicin da ke faruwa zamu yi kokari da jikinmu da aljiihunmu muga cewa mun samar da zaman lafiya a jiharmu ,hakika muna jin raɗadi akan abinda ke samun jama armu,to amma kuyi hakuri domin duk abinda kuka ga ya yanke sai da izinin Allah,dan haka ina rokon ku da ku ci gaba da addu'a kamar yadda muma muka sa ake yi babu dare babu rana akan Allah ya tona mana asirin duk wanda suke kawo fitina da kashe rayukanmu a banza asiri,in sha Allah Allah zai tona musu asiri, na gode", muma muna godiya ur exsellency. A hankali wazer ya maida dubansa kan ur exsellency,kana cikin mafamarshin nan me janyo hankalin yan mata kanshi,ya ce",ur exsellency muna godiya wannan karramawa,juya kyakkyawar fuskarshi kan abun haskawa ya yi yana ci gaba da cewa to masu sauraron mu, kun dai ji ta bakin ur exsellency saura kuma zamu saurari ra ayoyinku wanda aka baku lokacin yin tambaya ga ur exsellency za ku iya Turo sakonninku ta wannan lambar 0805443.....sai kuma kira ta wannan lambar kamar haka 0912626.......muna sauraronku...... RAIHAN dai ganin wannan yanga ta wazeer abun ya bata bata rai dan ita kadai take harare harare tare da dan ƙunkuni ta yadda babu wanda zai fahimta.sai dai shi ogannata tsaf yake ganinta ta cikin glasses din da ya kara kawata kyakkyawar fuskarshi. Cikin sauri Raihan ta dauki kiran da ya fara shigowa ,hello salamu alaikum,amsawa ta yi ta ɗora da tambayar wanda ke magana, sunana .....ya bata amsa daga nan ya yiwa ur exsellency Barka da zuwa da fatan komawa gida lafiya. Ajiyewa yayi daga nan ta amsa sakon message,wanda yake cewa Salam sunana Hashim Yusuf,tambaya ta anan shin ur exsellency ya tabbatar da cewa babu sa hannun gwamnaty cikin wannan al'amari dake faruwa da talakawa?. Murmushi ur exsellency ya yi kana ya ce ", bani da sani akan gaibu Allah shine yasan gaibu dan haka ba zan baka tabbaci akan abinda Nima nake son sani ba. Wani kiran ya shigo,tambayar da wannan bawan Allah ya yi tayi matukar girgizasu,ya kashe kuma ba tare da ya fadi ko da sunansa ba. Abinda yake tambaya shine ,ur exsellency munji a majiya me karfi cewa,dukiyarka da mulkin da kake kai duk ba naka bane,kana yin komai ne da bazar dukiyar amininka Alh Muhammad nuur shin gaskiya ne ko ba gaskiya ba? Da sauri Raihan ta tari numfashin ur exsellency dake kokarin yin magana cikin wani irin sagewar gwiwa da zuciya,ta ce",malam ka sauka daga kan layi ba maganar dukiya ko pravency din ur exsellency aka ce ka tambaya ba, wannan abinda ya shafe shi shida ahlinsa ne dan haka bamu karbi wannan tambayar ba,daga haka ta ɗora da cewa duka duka a nan ne muka kawo karshen wannan tattaunawa tare da gwamnan yanzu wato Alhji Garba me fata,a cikin dandalinmu na siyasarmu a yau,Ni da nake gabatarwa Rahim Muhammad nuur Aliy .tare da abokin aikina,se ta bawa wazer damar magana ya dora da cewa AHMED WAZEER CHIBAƊO. Tunda ya baro gidan tv ya fara nemo lambar amininshi sai dai bai samu ba,hakan yasa ya hakura da kudirin dole anjima yayi fitar sirri dan ganawa da amininnashi. Ki biyo NI office wazer ya fadawa Raihan lokacin da yake wuceta dan hayewa lipter. Ƙasa_ƙasa take ƙunƙuninta,haka ta bishi ta na faman cuna baki,akan idanun rabi komai ya faru duk da cewa bata ji abinda yace da Raihan ɗin ba,ji ta yi bazata iya jura ba hakan yasa ta bi bayansu ba tare da su sun lura da ita ba. Har zata shiga sai kuma ta dakata,tasan halinsa sarai zai iya dizgata agaban yaronnan kuma tajawa secteriya wadda bata san ma ta shigo main office din wazer din ba,hakan yasa ta ɗan saka kanta ta kafar key ko zata iya ganin wani abu sai dai ina kofar ba irin ko wace kofa ce da ta sani ba,dan kofa ce me security babu ta yadda za ai na waje ya jiyo Muryar na ciki sai dai na ciki zai iya jiyo Muryar na waje,saboda tsoran kar ya fito ya same ta yasa ta hakura ta juya ranta a matukar ɓace. Tana shiga office ɗinta ta samu suryy wanda hakan ba karamin dad'i ya yi mata ba,janta Surry ta yi acewarta Gara su tafi can gida saboda maganar da zasu yi bata nan ba ce. Suna shiga office ɗin ya juyo yana hasketa da wannan idanun nashi masu kama da me jin bacci,kif_kifta nata idanun ta shiga yi saboda yadda nasa ya yi mata ƙarfi,bata san yaushe har ya ƙaraso gabanta ba ,sai din hucin numfashinsa ta yi a fuskarta ,dan firgita ta yi zata ja baya ,cikin wani zafin nama wanda yake tafe da wani irin salo yasa dogayen hannayensa ya tarota,sai ga fiskarta daf da tashi jikinsu na neman hadewa da na juna,waro manyan idanunta tayi zata yi magana sai me wani irin ɗumi da zaki zaki taji ya sauka saman harshenta,mukut ta haɗiye wani kakkauran miyau ba tare da ta shirya ba,bata iya tantance komai ba ta ji wazer ya ci gaba da juya harshensa cikin bakinta cikin wani irin salo da gwanancewa,komai na wazer da ban yake kamar yadda yake,shi kansa sumbar tasa ta dabance a kuma gurin mace ta daban a rayuwarshi. RUBY..... Har sun shiga mota,sai kuma ta fara kokarin fita,da sauri suryy ta riketa tana cewa ina kuma zaki Hajiya? Cikin bakin cikin da ya kasa barinta idanunta har wani ƙankancewa suke saboda bala'i ta ce",suryy bazan iya tafiya ba, wallahi bazan iya ba ya za ai na tafi banga fitowar wannan tsinannan yaron ba,anya kuwa suryy ba neman juna wazer yake da yaronnan ba? Da sauri sury ta toshe mata baki tana cewa ke wace irin macece ruby so kike aikin mu ya lalace? To tun wuri ki kama bakinki kuma komawarki bata da wani amfani maganar da za muyi nida ke yafi abinda kike shirin yi tunda duk maganar kusan daya ce.dakyar ta samu ta lallasheta suka ja motar suka tafi. RAIHAN kuwa rasa inda zata yi da numfashinta ta yi saboda yadda yake sama da kasa yana gauraya da numfashin wazer da suke fitarwa a tare,dogayen hannayensa yasa ya tallafo kugunta a hankali ya ƙarasa hadeta da jikinsa ba tare da ya bar abinda yake yin ba. Shi kansa mamakin kansa ya shiga yi, baisan wane irin maganaɗisu Raihan ke tare da shi ba,sam ji yake yana kasa sarrafa kansa da tunaninsa akanta,to meye hakan wai? Wace irin macece ita din da yake jin ta daban da sauran mata? Me yasa ko mai nata yake ganinsa na musamman,bai taba yin kiss da wata mace ba amma ji yake kamar ba za a taba samun ɗadin harshe da baki kamar na Raihan ba,ita din fa tabbas ta musamman ce... Ƙarar wayarshi da baya fita sosai shine ya ƙwaci Raihan,duk da cewa shi a gareshi ba wani dalili ba ne hasalima ba zai dau wayar ba,a hankali ya ƙarasa kujerar shi cikin takunshi dake kara bada tabbacin cewa shi ɗin fa namijin gaske ne.zama ya yi fuskar nan ɗif kamar ba shi ya gama tsottse bakin yar mutane ba. RAIHAN kuwa na samu ta kubuta sai ta fara lalubar hanyar gudu,gam taji kofar a rufe wanda yasa ta tsayawa tana kallon kofar ba tare da ta juyo ta kalli inda yake ba bare kuma ta tanka. Yi ya yi kamar baisan dalilin tsayuwartata ba,Saida ya gama hada tarkacenshi sannan ya nufota,da sauri ta rintse idanunta a tunanin ta irin na dazun zai kuma maimaitawa,ji ta yi yasa key ya bude kofar kana a hankali ta ji muryarsa yana cewa idan kin gama tsayuwar ki same Ni a mota",da sauri ta bude idanunta alokaci daya kuma tana bin bayanshi da dan gudunta,babu abinda take a ranta sai mita,shi wai wannan mutumin baya jin damuwa akan wannan halaiyan nashi? tab gaskiya wannan matarshi zata gane kurenta,au ashe fa Nima matarsa ce, ta faɗa tana da dafe bakinta, dan tabe fuska ta yi kamar da wani take zancan ta kuma cewa ai Ni matar wucin gadi ce haka Abbie ya fada daga haka ta karawa sawunta mai dan kokarin taddashi........✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page36 ``` Wannan tambaya da mutumin nan ya yiwa ur exsellency ta yi matukar jawo hankalin mutane da sanya cece kuce a cikin jama'a . A ranar dai ur exsellency bai samu ganawa da amininnashi ba kamar yadda yaso.sai dai ya kwana da wata irin damuwa da jin kunya wanda bai taba shiga irinsa ba,hatta da iyalansa kasa fita ko ina su kai.kowa ya yi jugum jugum cike da tunanin ta inda maganar ta fito.su iyalansa ma gani suke sharri ne tunda su kansu basu taba sanin ko mai akan hakan ba,babban dansa Yusuf ne kawai ya sani wanda yake rike da daya daga cikin comfanonin Raihan ɗin,sai kuma lauyansa. _________ A bangaren rabi a kuwa suna zuwa gida,ko zama ba su yi ba rabi a ta ce", Surry gaya min abinda za ki gaya min saboda hankalina ya kwanta", Ganin yadda rabi a ta birkice yasa sury jin shakkar sanar da ita wata magana yanzu hakan ya sa ta yi tunanin dabarar da za ta yi mata yanzu. Kamo hannunta ta yi suka zauna, sannan ta ce", haba ruby me yasa kike son kidinga acting like wata mahaukaciya? Dole fa sai kina sarrafa tunanin ki akan wannan bukata taki,idan baki sawa kanki nutsuwa ba kina tunanin za mu samu mu nemi mafita akan matsalarki,"ganin kamar ta dan fara samun kan rubyn yasa ta yi saurin bude jakarta ta fiddo wasu kwalabe guda uku,mika mata ta yi tana cewa karbi wannan ki sha zaki samu nutsuwa ", zubawa kwalaben ido ruby ta yi ba tare da ta karba ba,karbi mana ruby ba sai na gaya miki ko menene ba ai",dubanta ta dauke daga kan kwalaben ta maida kan sury kana ta ce",sury kin san dai duk iskancina bana shan wadannan kayan ko?da sauri suryy ta amsa da cewa na sani amma ki sani cewa yanzu lokacin amfaninsu yazo a wajenki, wannan da kike gani su kadai ne zasu baki damar aiwatar da duk abinda kike son aiwatarwa akan wadda ta ke kokarin raba ki da farincikinki wadda ta raba tsakanin zuciyarki data wazeer,rabi'a dole ne ki koyi mu amala da waɗannan kayan domin sune zasu dinga doraki akan saiti koda bana kusa,kuma wannan da kike gani su zasu kawo miki nutsuwa yayin da kika fuskanci gaskiyar abinda nake son sanar dake,domin kuwa jinta ba tare da kin shirya ba babban hadari ne,dan haka Ni ba zan sanar da ke komai ba idan har baki sha Wadannan maganinba. Tana gama fadar haka ta ajiye mata kwalaben kan cinyarta ta dauki jakarta ta rataya,idan kin canja shawara sai ki kirani ", binta da kallo ruby ta yi bata iya cewa komai ba har Surry ta fice,dawo da dubanta kan kwalaben ta yi tana jin zuciyarta na wani irin luguden fargaba akan labarin da sury take shirin bata, tabbas ya kamata tasan abinda tazo da shi. Sai kuma tunaninta ya koma kan maganganun sury akan magungunan,kamar fa gaskiya take fada ,ta faɗa tana juya kwalba daya a hannunta,zan gwada amma fa idan har naji abinda ta faɗa ba haka bane to zan bari da zarar ta sanar da Ni abinda take son sanar dani din,har za ta fara sha sai kuma ta tuna ba lallai sury ta yadda cewa ta sha ba,dan haka zata bari zuwa safiya sai ta kirata ta zo tasha agabanta sannan ta sanar da ita labarin. _________________ Lokacin da Raihan ta shiga falon Abbie samunsa ta yi shida Abba yahya da aunty amarya suna tattaunawa akan abinda ya farun,waya ce a hannunshi yana ta neman wayar ur exsellency ya kasa samunsa da alama dai kashewa ya yi ko kuma matsalar network,itama take sai jikinta ya yi sanyi abun ya kuma dawo mata,zama ta yi gefan Abbie tana musu sannu da gida, Abbie dan Allah kayi hakuri nasan damuwar ur exsellency damuwarka ce amma dan Allah kayi haƙuri,kaga bamu amsa tambayar ba duk da cewa mun san bata da wani tushe bare makama,ta yaya za a ce dukiyar ur exsellency ta ka ce ko ma taka ce su me ye ruwansu ba tsakaninku ne ba", Abba yahya ne ya dakatar da ita da cewa shike nan Rahim ta shi kaje ka huta Allah ya kiyaye gaba", Tom ta faɗa tana tashi jikinta a sanyaye idanunta akan Abbie da take ganin kamar fushi yake yi da ita,aunty amarya ce ta tashi taja hannunta suka fita,ita kanta aunty amarya mamaki da ne cike fal akanta da kuma tunanin hakan zata iya kasancewa,to amma me yasa bata sani ba ? Bata da wannan amsa hakan yasa ta ture tunanin taka Raihan dan bata abinci da rarrashinta saboda yadda taga dukiya damu da yanayin Abbien nata. _____________ Shi kuwa wazir dama babu wanda ya yi masa maganar tunda babu wannan fuskar,ko abban rabi a baiyi masa hirar ba,amma dai kowa ya ga tattaunawar tunda live aka nuna haka sun tattauna maganar a tsakaninsu. _________ Take sauran gidajen jaridu suka fara yada karya da gaskiya, wasu har cewa suke ur exsellency ya amsa tambayar nan. Hankalin Abbie ba karamin tashi yayi ba da ganin wannan abu,take zuciyarshi ta tafi tunani da nemo ta inda maganar nan ta fita,so yake ya fita ya hadu da ur exsellency amma hakan ya gagara domin tun jiya da abin ya faru kofar gidansa cike yake da manema labarai yan jarida da sauran yan bani na iya,kowa so yake ya ji ta bakinsa. RAIHAN kuwa da kyar ta samu hanyar fita saboda yadda kofar gidannasu ya koma. Mama murja da momi Hanne basu san lokacin da wannan masifar ta sa suka kuma hadewa ba,tuni suka manta da komai,ko wacce ta manta da zargin da takewa yar uwarta sun koma jajen ashe abinda suke yi wa ma baya kusa da su,tunaninsu ya fara juyawa ta yadda zasu karbi komai daga hannun ur exsellency,burinsu da damuwarsu ta kuma yawa saboda yawan dukiyar da suke hangowa ta wuce misali. ____________ *Ogan suryy* Wani irin duka ya kaiwa teburin gabansa idanunsa har shudi suke saboda tsananin ɓacin rai da damuwa,yaransa gaba daya sunkuyar da kawunansu su kayi umarninsa kawai suke jira. Hannu yasa ya kuma gyara fuskar da yasa kafin ya fara magana cikin wata irin murya wadda kana ji kasan cewa mamallakinta yana cikin damuwa me tsanani ya ce", duk wannan bulayin da nake yi ashe na banza ne,idan haka ne kuwa tabbas ya jawa amininshi dan ko da zan yawo tsirara saina gabayan duk wani wanda yasan da dukiyar nan ko kuma take hannunsa wallahi babu wanda zan kyale dole na samu abinda zuciyata ke muradi kudi nake so ko ta wace hanya dan haka zan kwato dukiya ko ta wace hanyaaaa.ya fada da wani irin ƙaraji wanda ke bayyana kwadayinsa da burinsa akan bukatar tasa. Sintiri take tana kaiwa tana kawowa idan ta yi kamar zata zauna sai ta kasa ji take kamar ta aikata komai ya wuce burinta ya tabbata,me yasa sai a lokacin da take ganin komai nata ya kusa kammala sannan wannan mummunan labarin ya baiyana? zuciyarta da idaniyarta babu abinda ta jima tana son gani sai mushen Raihan da ubanta,to sai kuma ga wani mummunan labarin da yake ta yawo yake zagaye jahar tasu,hakan fa yana nufin sai ta karo makaman yaki,hakan yana nufin ta samu kishiya akan burinta domin ta tabbatar da cewa shi kansa ur exsellency ɗin da nasa target din,babu wanda zai yadda yaga samu da rashi,yasan cewa ur exsellency likimo yayiwa amininsa ta yadda sai ya gama yadda dashi zai yi masa me gaba daya,to amma ita ta yaya za ta yi ta karbi dukiyar daga hannun ur exsellency? Karbar dukiyar nan a hannunsa fa tamkar yankan tiikintin mutuwa ne saboda wahalarsa. Duk wanda zai karbi wannan dukiya to sai ya taka matakai masu tarin yawa kafin ya cimma gaci. Wani irin numfashi ta aje me tsananin zafi da huci,tana mai birkita gashinta kanta idanunta kuwa tamkar garwashi saboda ja. Lissafo dan abinda ƙwaƙwalwarta ta hasasho mata ta fara yi. Dole fa sai nasan wasu sirrika akan dukiyar,ta wace hanya ke nan? Dole sai ta samu kusanci da ur exsellency,ta wace hanya ke nan? Dole sai na san adadin campanin nasan ma'aikatan da suke aiki a karkashin Company's,to ta yaya? Wata irin zabura ta yi zuciyarta na cewa ki nemi wanda yayi test din tambayar nan,dan shine zai share miki duk wata tantance,to ta yaya? Sam bata yi tunanin neman abokin cin mushenta ba saboda ganinta babu wani abu da zai iya tunda har ita yake neman gagararta. Ji ta yi kanta ya fara juyawa kawai sai ta lalubo kwalbarta ta tuttula a bakinta domin hakan shi ne mafita akan zarewar da take son yi. Kokarin fita take yi hamma idi da ya kawota yayi saurin rike hannunta ,fuskarshi cike da damuwa ya ce", RAHIM ka kwantar da hankalinka Abbie da ba fushi yake da kai ba kamar yadda kake zato,kawai dai abunne yake damunshi kuma har yanzu bai samu hanyar ganawa da ur exsellency ba kin ga dale ya damu,nasan tunanin shi bai wuce yadda ur exsellency zai dau maganar ba wata ƙil ma yayi zaton Abbie ne ya fitar da maganar tunda yasan shi kadai yasan abinda suka binne a tsakaninsu", zame hannunta ta yi tana share kwallar damuwar da suka fara sakko mata,bata iya cewa komai ba ta sa hannu ta bude kofar ta fita.binta yayi da kallo zuciyarsa cike da tausayin kanin nashi. Tun daga saman office dinsa yake hangota,tun daga yanayin tafiyarta ya ganewa cewa tana cikin damuwa,sai kuma yaga tana share fuska. Neman layinta ya fara yi bayan ya dawo cikin office din, ringing daya ta dauka miryarta a sanyaye ta yi masa sallama,cikin dakiyarshi ya amsa mata kana ya dora da bata umarnin zuwa office dinsa.dan bin wayar da kallo ta yi kafin ta canja akalar ta zuwa inda Lipter take. A can bangaren ur exsellency kuwa,shiga yayi ta badda kama ya nufi gidan amininshi,dakyar ya samu hanyar shiga saboda har yau din yan jarida ba su bar zuwa kofar gidan Alh Muhammad nuur ba. Abbie yana ganinshi ya gane shi,kai tsaye suka nufi can karamin falonsa da yafi ganawar sirri a cikinsa,dukkansu duban juna su kayi na tsawon wasu sakanni kafin suja numfashi a tare, Abbie ne ya fara magana da cewa bansan abinda zance da kai ba wallahi kunyar haɗa ido nake da kai, sannan bansan ta ina zan kare kaina daga irin zargin da nasan cewa zaka yi min ba",amma da fari ina mai baka hakuri tare da kara jaddada maka amanar dake tsakaninmu wall........da sauri ur exsellency ya katseshi ta hanyar dakatar da shi da cewa yi shiru dan Allah Nura,ranshi a ɓace ya ci gaba da cewa ban taba tunanin za yi irin wannan tunanin akaina ba,karfa ka manta cewa bani ne na nemi ka dinga tara dukiyar Raihan a hannuna ba, sannan bani ne na baka shawarar na riketa na dinga juyawa ba,sai dai nasan na baka shawara akan cewa ka dinga juya mata a maimakon ajiyar da kake yi kamar yadda kake ajewa sauran yaranka,domin ba a san me gobe za ta yi ba kuma ba mu san irin albarkar da zasu yi ba,daga Ni har kai bamu san gaibu ba dan haka ba musan zaka samu Raihan ba,har daga karshe Allah ya baka ita ba tare da kasancewa itan ba ce,to yanzu duk a nan me ye laifinka ko laifina da har zaka yi tunanin zan zargeka akan wannan abu? Wallahi Nura ban taba tunanin cewa zaka yi min ko abinda bai kai wannan ba bare kuma wannan,dan haka ka kwantar da hankalinka,Ni yanzu tashin hankalina daya ne", zuba masa ido abbie yayi yana jiran abinda zaice gefe daya kuma na zuciyarshi suna kara kauna da ganin kimar amininnashi. Ur exsellency ya ce", Raihan ita ce tashin hankali na,nasan cewa tunda har aka san cewa dukiyarta na hannuna to kuwa tabbas a na gab da fasa kwan cewa Rahim ba namiji ba ne,domin tunda har kowa ye yasan da wannan tsohon sirrin to ba zai kasa sanin wannan ba,damuwata kar wani abu ya samu Raihan. Da sauri tayi ƙasa da kanta tana kuma shigewa cikin fulawas din da suke bayan falon ta inda karamin window dake falon yake,babu abinda kake gani a fuskarta saboda yadda ta nannade fuskar da farin rawani tamkar wani buzu,abinda kawai zaisa ka fahimci cewa macece shine shigar jikinta ta doguwar a baya. Ur exsellency ya ce", kamar motsi nake ji a ta wajen can ko? Ya fada yana duban Abbie,dan zubawa window wajen ido su kayi gaba daya kafin su tashi ba tare da sun kara cewa komai ba. Shirun da ta ji ne yasa ta bar wajen cikin takatsantsan. Abbie suna fitowa falon babu kowa sai Hajiya goggo,cike da mamaki Abbie yake kallonta saboda yasan bata cika shigowa bangaren surukanta ba sai dai su suje can din,Hajiya tun yaushe kikazo kuma ke kadai ba na ramlar?a'a Ni ba wajen ramla nazo ba wajen hajiyar agadex nazo hira tunda jiddo dai iyayenta sun rike abarsu",durkusawa ur exsellency yayi yana gaidata,amsawa ta yi tana kallonshi cikin mamaki au wai dama kaine? Ikon Allah wannan irin badda kama haka", Abbie ya ce", to Hajiya aikin san su manya dole sai da irin haka", to wannan wane irin zuwa ne da sai am boye kama? Da sauri Abbie ya kuma tare ta da cewa Hajiya saboda abinda ya faru ne to kinsan yan jaridar nan yadda suke ta son su yi magana da mu", tabe baki ta yi tana binsu da wani kallo kana ta kuma cewa to idan kun san kuna da gaskiya meye na tsoran maganar ? Bari na raka shi saboda ba a san ya fito ba, Abbie ya fada yana takaicin baranbaramar hajiyar tasa. Ur exsellency ya ce",Nura za mu samu lokaci muyi tunanin abinda ya kamata da kuma wajen da ya kamata mu hadu ban yadda da gidannan naka ba sam............✍🏽 [12/21, 12:40] : *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page37 ``` Tunda ta baro bakin window take faman zirga zirga ji take kamar zuciyarta zata fashe tunani ya cunkushe kanta,mafita kawai take nema,shin yaya za ta yi ta samu hanyar shiga jikin ur exsellency? Me ya kamata ta yi a wannan bigiren? Waye ya ke da karfin zarrar da zai iya shiga ahlin ur exsellency ya kwaso mata wannan Dukiyar?gaskiya amma Nura ya shammace su,dama ashe wannan campanin da ya bawa yaaran gidannan na auduga su kula da shi ashe ba su ka dai ba ne? Wato yayi hakanne domin ya kawar da kan kowa daga dukiyar Raihan da tunanin yawanta.turkashi lallai jan aiki ne a gabanta domin kuwa tasha alwashin karar da kowa akan wannan burinnata,domin shine asalin abinda ya kawota gidan, wannan burinne yake zaune da ita a gidan,dan haka dole ta samu mafita tun kafin wani yayi mata kutse cikin lamarinta. CHIBAƊO FM..... Cikin yanayin damuwar da take ciki ta shiga office ɗin,idanuta sun iankance kana ganinta kasan cewa tana cikin yanayi mara dad'i. Zuba mata tsumammun idanunsa ya yi ,tuni jikinta ya kuma yin sanyi,sai kawai ta kuma rushewa da wani irin sassanyan kuka wanda shi kansa kukan wani irin salo yake bayarwa tamkar ana busa sarewa,a hankali ya maida idanunsa ya lumshe tare da komawa saman kujerar ya kuma kwantar da kansa yana jin wani iri a cikin jinin jikinsa,jin kukannata yake kamar har cikin bargonsa,tsikar jikinsa ce take wani mimmiƙewa kamar wanda ake sosa masa,tashi yayi cikin wannan kamewartasa da wani taku tamkar a saman gajimare,fuskarshi babu murmushi ko daya sai wannan yanayinnasa na ko da yaushe. Kanta yana sunkuye bata san lokacin da ya ƙaraso ba sai dai jin tattusan hannunsa ta yi saman wuyanta yana ƙoƙarin dago kanta,saurin dago kannata ta yi tana kallonshi ƙasa ƙasa ba tare da ta bari idanunsu sun haɗu ba,cikin kimtsatstsiyar Muryarshi me dan kauri da sanyin sauti ya ce"me ke damunki?rumtse idanuta tayi sai ga wasu ƙwallan suna rige_rigen sauka saman kuncinta, kwaɓe fuska ta yi tana shirin fasa kukan,kafin ta kai ga yin haka sai jin wani irin sanyi da ƙamshi tare da zaƙi tayi cikin bakinta wanda hakan yasa babu shiri tayiwa kukannata wata irin haɗiya ya koma cikinta tare da hadewa da harshen WAZER,a hankali ya sake tallafo kanta camly kamar wanda ke taba ƙwan da baya son fashewarsa,cikin kwarewarsa da a jinsa wanda yake a jininsa ya shiga bin labbanta da harshenta yana tsotsewa ba tare da shi kansa yasan yadda hakan yake faruwa ba,shi dai abu daya ya sani indai RAIHAN na kusa bai cika gane kansa ba,ta fuskane kawai zaka iya cewa kalau yake amma can kasan zuciyarshi da gangar jikinshi basa iya gane komai indai RAIHAN na kusa,tamkar mayen karfe haka yake jinta a duk lokacin da ta fara kusanto shi,shi yasa baya iya sarrafa kansa da duk wani ajinsa. RAIHAN kuwa jin kanta take tamkar a sararin samaniya,dama can ita bata da zarrar sarrafa kanta a gaban WAZER, ƙwaƙwalwarta bata gane komai sai ƙamshinsa bata fahimtar komai sai kalamansa bata ganin komai sai kyakkyawar fuskarsa me dauke da 'yar ƙasumbar da ke ƙara masa kyau da kwarjini. Numfashinta ne taji yana sama_sama saboda yadda ta ji wazer yana ƙoƙarin sauya salon wasan nasa,cikin fitar hayyaci ta rike hannunsa da yake kokarin fara zagawa dashi cikin jikita,da kyar ta yi kokarin zare bakinta dake cikinnasa yana masa wata irin sarrafawa,cikin karkarwar baki ta ce", Hamma WAZEER", Wani irin shock ne ya kama shi saboda yadda taja sunan a saman harshenta,a maimakon ya sake ta kamar yadda yaso,sai kawai taji sabanin haka dan cusa kansa ya shiga yi cikin wuyanta yana sunsuno daddan kamshin humrarta wanda ta kama jikinta,camly yake sumbatar wuyan yana dada cusa fuskarsa kamar zai hadeta a cikinsa. Ganin yadda yake dinne kamar wanda ya fita a gayyacinsa yasa ta fashewa da wani irin kuka tana yi tana kame jikinta tare da dan tuttureshi da fuskarta dake saman kanshi,a hankali ya dago kanshi ya kuma mike sosai sabanin da da ya sunkuya saboda tsayin da ya dara mata da shi sosai.rungumeta yayi yana furzar da wani irin huci me sanyi,kana cikin nutsuwarshi da kamewarshi ya ce",umm zaki iya fadin damuwarki ko sai na maimaita? Tura karamin bakinta ta yi sannan cikin tsoran abinda zai kuma yi din ta ce", ba Abbie ne yake fushi da Ni ba saboda abinda ya faru jiya", dan waro ma daidaitan idanunsa masu haske ya yi kana ya ce", shine ya fada miki haka?girgiza kanta dake ƙirjinshi tayi tana matso kwallar shagwaɓa,dan lakuce mata goshi yayi fuskarshi kadaran kadaran kana ya ce", sorry Abbie baya fushi dake damuwarsa akan yadda aka tozarta amininshi ne a idanun duya so kar ki damu uhmm", ya karasa fada yana wani dage mata gira in a emotional way,rufe idanunta ta kuma ta ɗan sakin ajiyar zuciya alamun dai ta samu nutsuwa. Janyeta yayi daga jikinshi tare da komawa wajen zamanshi yana cewa ki gyara fuskarki ki wuce ki fara aiki", daga haka ya dora dogayen hannayen shi masu cike da kwantacciyar gargasa saman computer shi yana ci gaba da aikinsa.ba tare da tace komai ba ta wuce bathroom dinshi ta wanko fuskarta,fita ta yi ba tare da ta sake masa wata maganaba,dan kuwa sosai itama take koyarshi wajen kamewa da basar da abu ko da ya kula da abun,kasa_kasa ya bita da wannan shu'umin kallonnasa da take jinsa har bargonta. RUBY....... Tunda ta gama shirin fita office ta zauna zaman jiran sury,kasancewar tana farkawar ita ce mutum ta farko da ta fara kira tana nema,sai dai kuma gashi sai ja mata rai take tunda gashi tsawon awa daya da rabi da kiran amma har yanzu bata karasoba. Ita kuwa sury tana can wajen oganta yana shirya mata kalaman da zata yi amfani da su wajen kara cusawa ruby hauka a kan Raihan ta yadda zata yi saurin amsar aikinsu a matsayin shawara a gareta,saida suka gama kulle kullensu sannan suka rabu. Kai tsaye CHIBAƊO family ta nufa.yayin da shi kuma ogan ta barshi cikin jinyar zuciya da neman mafita akan yadda za ai ya kutsa rayuwar ur exsellency dan cikake babban burinsa. Da sauri ruby ta rungume sury bayan ta zuge mata kofar glass din da tayiwa rabin bangan kawanya. Haba sury me yasa zaki min haka? Tun yaushe na kira ki amma dake kinso jamin rai baki ƙaraso ba sai yanzu bayan kuma kinsan zan fita office ",tabe baki sury ta yi tana yin gaba zuwa cikin falon ta ce", to me kike so dani? Duk ma ba wannan ba yanzu ba gani nazo ba dan haka sai ki saurara min da wannan shegen mitartaki,ta karasa fada tana zama daya daga cikin manyan kujerun da suka kara ƙawata falon kamar wani fadar shugaban kasa. A can cikin gidan CHIBADO family kuwa,Abbu ne zaune gefan innawuro fuskarshi a cunkushe da alama dai akwai wani babban lamari da ya Kunno masa, cikin damuwa innawuro ta ce", yanzu dan nan ma aikatan nan abinda suka shirya ke nan? Me yasa mutane basu da amana ne, wanda kayarda dashi ka bashi amana shine yake cutarwa ? Girgiza kai Abbu ya yi yana cewa a'a innawuro ba kowa ne ba akwai masu gaskiya da amana kawai dai sunyi karanci ne mahainta sunfi yawa,wallahi innawuro ban taba tsammanin za a hada baki da ma'aikatana a cuce Ni ba amma sai gashi lokaci daya hakan ta faru,ban san da me ragesu ba duk wani hakki nasu ina cikawa to amma me zaisa su yi mana haka eye? Ya fada duban innawuro da ta yi zukudi cike da tunanin ta inda matsalar ta ɓullo. Yaci gaba da cewa ki duba ki gani wannan kwangilar da zamu karba yadda akayi kutu_kutu aka toshe aka hana abani ga kuma yawan asarar da nake tararwa a Company's,idan kuma na tara su sai kowa yaci laya kwanaki har bincike nasa aka fara min amma babu wani abu da zai sa na zargi wani da aka samo to yanzu kuma gashi an samu wani mugun da ga cikin makiyanmu ya siye rabin shares din da muke dasu , saboda duk kudin da muka saka sai an samu wani daga sama ya kara ba tare da nasan waye ba", shigowar abban rabi yasa ya dan dakata daga maganganunshi da yake wanda suke nuna zallar ɓacin ransa.zama abban rabi ya yi yana duban dan uwannashi cikin tausayawa yace", yaya dan Allah kayi hakuri karfa ka manta cewa shares din mu na kafanin da nake riko yana nan bai kuma babu wanda ya janye nasa to dan wancan sun janye nasu wani kuma ya siya ai ina ga ba sai ka daga hankalinka ba,kuma fa duk wannan din ba zai taba komai daga cikin irin arzikin da Allah ya baka ba,kayi hakuri na tura mutanena cikin ma'aikatar domin su sa mana ido sosai ", Dan numfasawa innawuro ta yi sannan cikin lallashin ɗannata ta ce", Ni gani nake kawai ka dawo da Nasiru da Khalil su cigaba da rike Company's din tunda sati mai zuwa zasu dawo, idan da hali ma rumana ma ta fito ta fara aiki duk ka raba su tunda abin ya zama haka dole idan suna nan wata rana asirin masu yi zai tonu", Masha Allah Abbu ya fada cikin farin cikin shawarar da mahaifiyarsa ta kawo,ya ci gaba da cewa tabbas innawuro kin kawo shawara kuma mafita me kyau kai wallahi dole wanda bai da uwa yayi kuka, ina ganin ma ai har mijin rumanan ya dawo tunda dama a karkashin wancan Company na Alh sale yake hakan sai yafi samun kwanciyar hankali suna tare da matarshi", Abban rabi ya ce", tabbas wannan shawara ta yi Nima ina goyan baya,kaga an raba ke nan rabi da wazeer suna rike da gidajen media su kuma sauran suna rike da Company's hakan yayi Allah ya kara dora mu akan maƙiya,Amin ya Allah innawuro da Abbu suka fada a tare, innawuro ta ce", kaga sai su dawo a daidai ke nan,wallahi Ni duk na manta banyi wannan tunanin ba ko dan basa kusa da mu ne oho? Abban rabi ya ce", ai gashi yanzu innarmu ta tuna mana hakan ko? Ya fada yana dariya sosai suka ci gaba da taba hira cikin kwanciyar hankali da kaunar junansu. A can wajen rabi a da sury kuwa,rabi a ce ta dubi sury ta ce,to shike nan naji amma dan Allah kiyi hakuri wallahi na kagu naji me ke bakinki jiya ko baccin kirki ban samu ba saboda tunanin abinda zaki fadan", to zauna mana ko daga tsaye za kiji ko ma meye? Zama rabi tayi jikinta har rawa yake a kage take matuka da son jin abinda ke bakin sury. Zuba mata ido suryy ta yi kafin ta ce", ina kwalaben maganin da na baki jiya? Da sauri rabi ta bude jakarta ta dauko su tare da mika mata. A'a Ni ba karba zanyi ba ki rikesu a hannunki ina gama baki labarin zaki sha idan ba haka ba kuwa zaki iya haukacewa", tuni rabi a ta kuma rikicewa cikin rawar baki ta ce", sury ina hadaki da girman Allah ki fada min domin kuwa wannan surutannaki ma kadai sun isa haukatani dan haka ki gaggawa ki sanar dani",kadan sury ta tabe baki kana kuma ta fara magana da cewa", rabi ki nutsu kar ki yi min hauka bana bukatar bakinki anan har sai na kai aya ", ita dai rabi a ba ta ce komai ba saboda idan ta bude baki ashar kawai zata dannawa sury tana yin hakan kuma tasan ta yiwa kanta sury bazata saurareta bare ta sanar da ita labarin",, ganin yadda ruby ta yi yasa suryy ta tabbatar da cewa tarkonta ya gama ɗanuwa dan haka sai ta gyara zamanta tare da yin gyaran murya. Rabi koyi hakuri na gama duk wani bincike da sanyi akan zuciyar wazer akan wadda ta hanaki shiga zuciyarsa,tabbas da ace bata shiga ransa ba to kuwa ina mai tabbatar miki da cewa WAZEER sai ya soki tunda ke yar uwarsa ce kuma mace,ba dan ta tsare wajen ba to dabararki zata iya kwato miki zuciyar wazer. Cikin tashin hankali ruby ta bude baki zata yi magana, da sauri suryy ta dakatar da ita tana cewa ba haka mu kayi dake ba dole ki dakata na gama kafin ki yi magana", mukut ruby ta haɗiye wani kakkauran miyau me daci ta yi shiru tare da ci gaba da kallon sury idanunta kamar zasu fito waje. Suryy ta ci gaba da cewa, nadan tambayar da kike son yi min wacece shine abinda kike son tambayata, dan haka na hutashshe dake zan baki amsa,nasan kinsan waye RAHIM,to RAHIM shine ya shiga zuciyar wazer yayi kane kane saboda shi din ba namiji ba ne macece, RAHIM dai ƁOYAYYIYAR RAIHAN ce ,ai Nahin sunanta RAIHAN,kai tsaye tashiga bata labarin dalilin maida Raihan namiji duk da cewa ba komai ta sani ba kamar yadda ogan nata bai san ainahin dalilin da yasa aka boye Raihan dinba,kawai dai yai hasashe ne bai san cewa kasheta aka so yi tun tana jaririya ba. Iya labarin kawai ya umarceta ta sanar da ruby banda aikin da zata yi musu akan fallasa Raihan ɗin. Wata irin ƙara ruby ta saka sai kawai sury ta ganta kasa yashe babu alamun numfashi........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page38 ``` Da gudu sury ta yi kanta tana jijjigata cikin tashin hankali, wayyo Allah nayi kisa shike nan tawa ta kare ba tare da na cika burina na zama matar WAZEER ba", abinda take fada ke nan wanda kuma haka yake har zuciiyarta, sai da ta dauki kusan mintina goma tana neman mafita kafin tunanin zubawa ruby ruwa ya zo mata,da gudu ta tashi ta nufi kiching gorar ruwa me sanyi ta zundumo a prige,tana zuwa bata yi wata_wata ba ta sheka mata a fuskarta,a matukar firgice ruby ta farka bakinta ɗauke da sambatun mafarkin da take tunanin ta yi. Allah na gode maka da ka tasheni daga wannan mummunan mafarki, ya Allah ina rokonka kar kasa na kuma maimaita ko makamancinsa ne", girgizata sury tayi tana cewa dalla Malama tashi ba mafarki kike ba duk abinda kika ji gaskiya kika ji,kawai ki tashi kiwartsake mu nemo mafita dan wannan haukar ba zata fishsheki ba, ware idanunta tayi sosai kan fuskar sury ba komai take kallo ba sai bakin sury domin ta tabbatar daga bakinta maganar ke fitowa, sai kuma ta yi wata irin zabura ta cukeme sury cikin kumar baki da masifar dake azalzalar zuciiyarta ta ce", karya kike haka bazata taba faruwa ba,ko da ace dau hakurin kallon wata da wazeer to wallahi ba zan taba iyawa da wancan dan iskan yaron da kike cewa mace ne ba,raiha yake ko Raihan ko ma meye bazan taba dauka ba wallahi sai naga bayanta sai na halakata,inaaaaa bazai taba yiwuwaba,tuni ta fara birkita falon duk abinda yazo hannunta wurgi kawai take da shi,ta haɗa uwar zufa kamar wadda tayi tafiyar shekara cikin sahara,dakyar sury ta samu ta riketa,bata yi wata wata ba ta antaya mata magungunan da ta kawo mata jiya ta haɗa mata har da kwaya,cikin kankanin lokaci ruby ta lafke jikinta ya sake abinka da farin shiga,duk da haka dai bakinta bai yi shiru ba,a haka Surry ta samu ta kimtsa ɓannar da tayi ta gyara komai kamar wani abu bai faru ba,bayan ta gama ta dawo inda ruby take tana ta sambatun hauka dan kuwa tuni ta hau kan layi jinta take a can wata duniya,kai hatta da kanta Ruby ta manta,da kyar ta samu ta dagata kamata ta yi ta nufi dakinta da ita,watsar da ita tayi saman gadonta tana sakin wata shu'umar dariya,harde hannunta tayi tana kallon Ruby da ta fara kumshe idanu tare da ci gaba da sambatun haukanta, ta ce ruby daga yau taki ta kare daga ke har RAIHAN ɗin yanzu zan fara samun salama a cikin rayuwata,Yes koda ban auri wazer ba dole sai na tabbatar da cewa babu wata mace da tayi saura a cikin rayuwarsa,idan ban aureshi ba to babu wacce ta isa ta aure shi indai ina numfashi,daga haka ta fice daga dakin, a falo ta dauki jakarta da mayafinta wanda dashi Gara babu ta fice daga gidan ranta fes. CHIBAƊO FM Duk sanda Raihan ta gama gabatar da shirinta na siyasarmu a yau sai ta shigar da cikiyar cp haidar ringim,abun yana matukar damunta kuma tana nan kan bakanta na nemo shi a duk inda yake a raye ko a mace ko kuma labarin mutuwarsa ko inda ya mutu insha Allah. ALHAJi MUHAMMAD NUR HOUSE....... Shirun da Hanne taji yasa ta dan fara sakankancewa da cewa dama duk burga ce murja ba abinda zata iya,ko kuma wannan labarin na cewa Company da aka bawa rufa i ba shi kadai bane kadarar Raihan kamar yadda suka zata shi yasa ta aje makamanta tana neman mafita kamar yadda itama a yanzu mafitar suke nema na ganin sun kwace komai daga hannun ur exsellency,kawai sai ta aje tunanin murja ta koma neman mafita,tabbas ba za su samu cika burinsu ba har sai dai idan mutuwa waɗan mutane biyu su kayi ,ur exsellency da kuma nur, ita dama RAIHAN gaibu ce tunda ba yar kowa ba ce sun san dole a raba dukiyarta a bawa yaransu maza,to tayaya zasu mutu? Zuciiyarta ce tayi mata wannan tambaya,dole ne su mutu kuwa ko ta halin yaya ne,ta faɗa cike da confidence,kai hatta da su Rahim din ma da sauran yaran murja duk ya kamata su wuce dan haka ne kadai zai basu damar cin karensu ba babbaka,dan ta wadannan tsofaffin mai sauki ne,wata dariya ta sheƙe da ita kai kace ta samu abinda take so ta gama.. Affan ne tafe kan hanyarshi ta dawowa gida bayan ya tashi daga office,yana gab da karasawa gida wayarshi ta yi haske alamar shigowar sako,ganin cewa sako ne yasa shi dauka ya buɗe sakon. Kashiryawa mutuwarka nan kusa, ina gaya maka haka ne domin kar ka shagala ka dinga sa rai za kayi tsawon rayuwa wannan damace muka baka. Cikin gaggawa ya shiga duba daga inda sakon yake sai dai ina babu wata alama da mai sakon ya bari da za a iya gano shi,sosai fa hankalin affan ya fara tashi,saura kiris ya bugawa wata anaconda ya samu ya kauce batare da ya buga din ba, cikin wannan tashin hankalin ya karasa gida, cikin wani irin fushi yake danna hon,ta yadda su kansu securitys din sun gane cewa akwai wani abu,ko rufe motar baiyi ba bare ya kwashi tarkacensa, wayoyinsu kawai ya dauka ya shige bangaren mamansa kamar zai kifa. Mama mama mama", ya shiga kwala mata kira da shigar shi main falon maman. fitowa ta yi da sauri har tana cin tuntube da dan damalin da zaka haura daga koridon da zai kaika dakinnata zuwa falo,lafiya Affan kake min irin wannan kira kamar wani mafarauci? Ba tare da ya bata amsar tambayar da tayi mishi ba ya karasa inda take tsaye yana nuna mata wayarshi ya ce", mama Kinga yanzu ina kan hanyata ta dawowa gida sai naji karar shigowar sako to da na duba Kinga abinda na gani",ya karasa fada yana mika mata wayar.zaro ido tayi baki bude ganin makamancin sakon da aka Turo mata kwanaki biyu da suka wuce,daɓar ta zauna kan kujerar da tafi kusanci da ita,duba sakon ta kuma yi yanzu dai kam ta tabbatar da cewa Hanne ce keson ganin bayansu,wato saboda taji wannan labarin na dukiyar Raihan yasa ta kara kaimi akan shirinta, yanzu dai ta fahimta Hanne so take ta kashe kowa ta gaje dukiyar ita da ƴaƴanta to wallahi bata isa ba kuma tayi kadan,mu zuba Ni dake", wai mama lafiya? Kin barni tsaye kina tunani,zauna Affan ta faɗa fuskarta babu alamun wasa,zama ya yi yana kallonta cike da mamaki,dubanshi ta yi sannan ta ce", Affan kasan me nake so da kai? Girgiza kai ya yi yana kallonta da dukkan nutsuwarsa,gyara zama ta yi ta ci gaba da cewa ina so ka nutsu kasa mana ido akan waccan matar da ƴaƴanta saboda zargina ya tabbata cewa ita ce take son ganin bayana nida ahlina baki daya", cikin mamaki Affan ya ce", me yasa kika ce haka mama naga fa duk tare muke kulle_kullen kwace dukiyarnan? Wayarta ta dauko ta kunna kai tsaye ta shiga inbox message din ta shiga nema Sa dai kuma wani abin mamaki babu shi babu labarinsa ,to ita dai da hannunta tasan bata goge ba kuma ba wani ne yake daukar wayarta ba sannan babu kowa a cikin gidan daga ita sai mai aikinta duka yaranta suna bangarensu da iyalansu to me hakan yake nufi? Wa ye ya goge sakon? Wannan amsar take bukata sai dai bata san ta inda zata sameta ba", mama mama mama Affan ya fada da karfi ganin yadda maman tayi zurfi cikin tunani,me Zakaria nuna min ? Anya ko mama lafiyarki lau? Cikin tashin hankalin da ta fara shiga ta ce ", Affan na shiga ruɗani kaina ya kulle anya ko hannece take mana wannan barazanar? Yanzu gaskiya na shiga kokonto,me yasa sakon ya goge? Waye ya goge shi? Sako zai goge kansa ne? Me yasa babu abinda ya goge akan wayar sai iya shi kaɗai?mama ki yi min bayani saboda Ni kaina na shiga ruɗani bana gane komai", Affan ya fada cikin damuwa. Da kyar ta iya saita kanta ta bawa Affan labarin sakon da aka tura mata da abinda ya kunsa,ta ɗora da cewa amma Affan abin mamakin shine yanzu na duba wayar zan nuna maka dan ka ganewa idonka sai dai kuma babu sakon babu dalilinsa abin ya razanani Affan ina cikin ruɗani karfa abinda aka fada nake daukarshi a barazana ya tabbata", ta karasa maganar cikin zubar hawaye zuciyarta kuwa tuni ta karaya tana jin damuwar rasa ƴaƴanta da take kallo a matsayin ƙadara ya'yan da ta kwallafa rai da su,shi kansa Affan da yake namiji ya shiga tashin hankali da kyar dai ya boye nasa damuwar ya rarrashi maman,duk da haka bata samu nutsuwa ba sai da ya kira mata rufa'i da yake Kano taji lafiyarsa tukunna ta danji sanyi Idris ma da yake kusa da ita sai da ta tabbatar yana lafiya kafin nan Affan ya nufi bangarensa. Dukkan su sun kasa samun nutsuwar zuciya,momy Hanne mama rabi da kuma Affan da yake cikin tsoran test din da a kayi masa,ko wa da abinda yale sakawa kuma yale zato a ransa,shi dai affyya kasa yin tunanin komai domin bai zargi kowa ba tunda su har yanzu kananun kwari ne akan neman duniya har yanzu ba su taka wani matsayi ko buri aiam dukiyar da suke ikirarin ta su ba ce,hasalima wani abin duk kurine iyayensu ma sun fi su kwarin gwiwa da nuna cewa zasu iya komai akan Dukiyar,shi yasa duk yabi ya razana dan ragowar burin da yake dashi na neman sarayewa. *RAIHAN* Tsaf ta gama shirin baccinta, tayi kyau tamkar ka saceta ka gudu,rufke gashinta ta yi ta saki jekarsa kan kafadarta,fuskarta sheki take da akwai yanayinta na shagwaɓa da ya kama jikinta,wanda da yawa mutane suke mata kallon sakaran namiji me yanayi da mata. Zama ta yi gefan gadonta tana murza turarenta na gabon tare da kwalaccarta me sanyi kanshi wanda ya riga ya kama ko ina nata, laptop ɗinta ta jawo ta buɗe. Cikin nutsuwa ta fara binciken shafin tree full y trues,haka nan take jin yanzu kamar ya zama mata dole akan ta nemi taimakon ko su waye waɗannan tree full y trues din dan ajikinta take jin cewa ba mutum daya ba ne sai dai idan kungiya ce me zamanta kanta. Wayarta ce ta yi alamun haske ɗan dakatawa ta yi da abinda ta fara tana duban wayar,kamar ba zata daga ba sai kuma ta dauka tare da karanta abinda aka turo mata,me kike yi har yanzu baki bacci ba? Abinda Wazer ya rubuta a sakon ke nan.zubawa rubutun ido ta yi fuskarta na kokarin tona abinda ke cikin zuciyarta duk kuwa da cewa tana kokarin kaucewa hakan,a ta wani bangaren kuma ta so yin mamakin yadda akayi yasan cewa batayi bacci ba,me gani har hanji ta faɗa saman lebanta,tana kokarin maida masa kiranshi ya shigo,sai da ta yi ringing ta ta mutu ya kuma kira sannan ta dauka tare da yin sallama cikin nutsuwa da dan fidda sautin da zai nuna cewa daga bacci ta tashi,tura karamin bakinta tayi jin yaki cewa komai cikin yanayin ƙunkuni me haɗe da shagwaɓa tace", nikam ina jin bacci", da me ya hana ki yi? Ya tambayeta cikin Muryarshi me cike da wani irin sautin da ke nuna cewa shi ɗin fa miskiline na bugawa a jarida,umm Ni ", shiiiiii ya katseta yana kuma cewa na sani baki bacci ba me kike da computer?da sauri Raihan ta fara juye_ juye dan yanzu ta fara tunanin ko dai tana cikin dakinne? Idan ba haka ba me yasa yasan duk abinda take yi yanzu", kafin ta Ankara ya maida kiran video, saurin kallon jikinta tayi dan ganin wace irin shiga ce a jikinta dan zuwa yanzu wazer ya shafe komai na tunaninta ko mai sai ta tuna shi a wannan gabar, wazer ya wuce duk yadda take tunaninsa wani irin mutum ne dan baiwa wanda yake tare da wasu ilhamomi shi yasa yake da kwarjinin da kowa ke kasa tunkararsa kai tsaye. Ganin yadda take yi din sai abun ya dan bashi dariya ,amma ba zaka raba fuskanta ba domin babu komai saman kyakkyawar fuskarshi sai gizagonshi da kuma wani sirri da yake boye can cikin kasan zuciyarshi. A hankali ya maida idanunshi ya lumshe su yana mai dan fesar da iskar bakinshi,zuciyarshi na bugawa a hankali,jikinshi na wani irin sakewa da irin sakewar da yake yi duk lokacin da idaniyarshi suka yi arba da Raihan,kasa_ kasa yake ci gaba da karewa halittarta jikinta da ta bayyana cikin ƙananan kayan baccin da tasa,wanda ita a yanzu take da ta sanin sawa da tasan cewa zai yi mata irin wannan kiran,yana kallon yadda take ta muku_ muku tana kakkare ƙirjinta da ya fi komai bayyana cikin kayan baccin. A hankali cikin son basar da abinda ke tsunkulin zuciya da gangar jikinsa ya ce",baki bani amsa ba", a hankali ta kalli fuskar wayar fuskarta da zuciiyarta na son kasa daukar abinda take ji,ta ce", yanzu zanyi", ko dai kina son nazo ne? Diri diri ta fara yi jin tambayar da yayi mata,kafin ta fita daga kunyar da ya jefa ya kuma sakin mata wani zancen da cewa,kina son nazo na sumbace ki fiye da na ɗazu kina son ki kwanta jikinsa fiye da yadda ki kayi dazun uhm bani amsa mana Raihan ", tuni jikin Raihan ya shiga wata irin rawa da wani irin sanyi kai har da wani irin tashi da duk wata tsigar jikinta ta shiga yi,da kyar ta budi baki cikin rawar bakin ta ce", plz dan Allah Hamma wazer kayi HAKURI ", nayi hakurin shike nan kwanta ba zan sake ba sai idan muna tare", da sauri ta kuma duban shi sosai ta kalli bakinshi da fuskarshi sai take ganin kamar bashi ne ya yi duk wannan din ba,dage mata gira ya yi ya nuna mata bed dinta da ido, cikin mutuwar jiki ta kwanta kamar yadda ya umarceta nuna mata yya kuuma yi ta ja bargo ta rufe jikinta dan da alama dai maganar da yayi yanzun har ta gaji da shi,nan ma bata Musa ba ta rufe jikinta sai kuma addu'a da yasa ta yi,karshe dai bai kashe wayar ba har sai da ya tabbatar ta yi bacci. Kashe wayar ya yi yana ɗan sakin murmushin da ace da mutane a kusa dashi tsaf za suyi suman wucin gadi saboda tsananin kyawun da ya yi wa fuskarsa,ta shi ya yi ya shiga bathroom zuciyarshi cike da tunanin Raihan da komai nata, wannan hirar da yayi da Raihan ita ta mantar da shi duk wani ɓacin ransa akan rabi. *Washe gari* *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page39 ``` *RUBY* A hankali take bude idanunta,dishi dishi ta fara gani, sai da ta yi kusan sakonni goma kafin ganinta ya dawo dai-dai,take mafarkin da ta yi ya shiga dawo mata, da sauri ta tashi zaune tana dube dube kayan dai dake jikinta a mafarkin sune har yanzu a jikinta, wannan wane irin mafarki ne haka? Bata taba yin mafarki ta yi addu'a ba sai yau, hannu ta daga sama ta ce", ya Allah ina rokonka kar na sake maimaita irin wannan mafarkin bare har ya kasance haka ta faru a gaske ,tashi ta yi tana kallon agogon dakin da ya nuna karfe takwas daidai na safiya a ranta ta kissima cewa bata makara ba dan haka cikin sauri ta shirya ta dauki jakarta ta fito,ba ko kalli bangaren wazir ba dan tasan yanzu ya tsufa a office. Da kanta ta tuƙa kanta zuwa office. *RAIHAN* Tunda tazo ta kashe wayarta a cewarta wazer da kiranshi suna son hanata aiki,to amaimakon ta samu sukunin aikin tunda ta kashe wayar sai hakan bata samu ba,tunaninshi da duk wasu alamuransa sunyi cunkus a zuciiyarta, idan ta tuna moment dinsu na jiya zuwa hirarsa ta daren jiyan se ta ji duk jikinta ya mutu,, ko me take yi kuwa sai ta dakata sosai take kokarin ganin takawar da duk wasu tunanin wazer ɗin amma hakan ya gagara. Wazir shi kansa bai neme ta ba don a ranshi yaji kamar idan ya ci gaba da irin hakan tabbas wataran zai zubda girmanshi a idanun yarinyar,kwarin gwiwa ya shiga son bawa kanshi tare da kokarin danne abinda yake kokarin gagararshi rikewa. Ruby tana zuwa kai tsaye dakin daukar rahoto ta nufa,ji tayi zuciiyarta na ta buga da karfi lokacin da ta yi arangama da Raihan,tsayawa ta yi ta zuba mata ido tana tuni mafarkinta na jiya,jin kamar numafashinta na san daukewa yasa ta yi saurin kawar da abin a ranta,dan bata son ta zurfafa bincike har abinda take gudu din ya zama gaskiya,karasowa ta yi ta zauna tana dan sake fuskarta,su abu Huraira ne suka gaisa da ita, ita ko Raihan ko nuna alama na cewa tasan wani ya shigo ba tayi ba,ruby dince ta hadiye wani irin yawu me daci da kauri ta ce", Rahim kai baka iya gaisuwa ba ne? Ko manya ba su koya maka ba? Ba tare da Raihan ta dubi inda take ba tana kuma ci gaba da aikinta ta ce", ey mana basu koya min gaida wanda bai iya sallama ba", cikin harzukar da ma aikatan basu san dalilinta ba,ruby ta ce", kai dan daudu bana son fitsara da rashin kunya maza ka saita kanka ba agaban kawayenka yan daudu kake ba bare kayi min karairaya da salon iskanci", ɗif dakin ya kuma ɗaukar shiru har da wadanda suka tsaida aiyukansu duk a sanadin furucin da ruby ta yi. Ita kanta Raihan maganar ba karamin shigarta ta yi ba bare kuma wazer da yake kawo kansa cikin gurin a kuma daidai lokacin da ruby ke yabawa Raihan mummunan kalaman,ba tare da Raihan ta tanka mata ba ta mike dama ta gama gabatar da shirinta, sai da ta zo fita ne ragowar suka san da zuwan wazer,ita kam Raihan dama tuni yasan da zuwansa saboda yadda taji yanayin bugun zuciiyarta ya sauya hancinta kuma ya shako mata ƙamshinsa da ya zama hadda a gareta,tuni kowa ya cigaba da aikin gabansa suna nuna alamun tsoro na tasirin kwarjininsa,ita kanta Ruby ba karamin shiga shock ta yi da ganin nasa ba,amma dake yar duniya ce tuni ta fiske ta dubi wazer ɗin tana murmushi ta ce ", my Suger ƙaraso mana idan kana son ganina ai sai ka kirani ba sai ka zo dakanka ka wahalar min da kanka ba", wani irin kallo ya wullah mata wanda babu shiri ta shiga taitayinta,juyawa yayi ya fita, ba tare da ya tankawa kowa ba. Kasa_ƙasa staf din suka fara dariyar dizgin da wazer yayiwa wadda take ta jin kai tana tutiyar ita din matarsa ce,wasu kuma wadanda da yawa suke jin haushin Rahim na yadda yazo a bayansu lokaci daya yayi musu kaka gida ya tare gaba da baya na cigabansu acewarsu,suka shiga tunani akan maganar ruby harma maganar daudun ta zauna daram a kansu da kwakwalwarsu. Tuni ruby ta kuma shaka ta kuma ci alwashin cewa sai ta rama akan Raihan, wannan wulakancin da akayi mata sai tasa anyiwa Raihan gomanshi. Raihan tana fita kai tsaye waje ta nufa ba tare da tasan inda ta nufa ba, wannan kalmar ba ba bakuwar kalma bace a cikin kunnuwanta sai dai ba ita ake kira da ita ba,tana dai ganin masu halaiyyar ta kuma san me kalmar ke nufi tunda har da case din a cikin case din da take shirin tonawa na su shugaban jam'iya,shi yasa tayi matukar yi mata ɗaci,sai take ganin wata ƙil ma da yawan mutane da abinda suke kallonta ke nan tunda da yawa suna cewa muryarta na kama da ta mata ko tafiyarta ko salonta da dai makamancin wannan,bata taɓa tsayawa tayi nazari akan hakan ba sai yanzu da rubby ta kasa sakayawa kamar yadda mutane suke sakayawar ta jefe ta da kalmar kai tsaye,ji tayi wani tattusan hannu ya riko nata hannun bata yi wani dogon nazari ba tasan cewa wazer ne,dago idanuta da suka cika da ƙwallah ta yi tana kallon ta shi dake hade kamar hadarin gabas,bai ce mata komai ba ya yi mata nuni da motar da ya fito da ita,bata Musa masa ba ta shiga,shima zagawa yayi ya shiga ya fizgeta da gudu,wanda ta hakanne Raihan ta gane ransa a matukar ɓace yake. Shiru ne ya ratsa tsakaninsu,a hankali ya koma tafiya bayan ya shigo hadaddiyar unguwar da gidannasa yake. Bata Ankara da inda suka dinba sai data ji tsayawansu,cikin nutsuwarsa da kamewa irin wadda ba za ka taba fahimtar tafarfasan da zuciyarsa ke yi ba ya sa hannu ya bude bangarenta ya janyo hannunta kai tsaye kuma ya nufi cikin gidan da ita,kasa yi masa musu ta yi saboda bata da zarrar yin hakan,kaf tunaninta yana irin kalar dizgin da rabi ta yi mata,tana jin zuciiyarta babu dad'i sosai akan abinda ya farun. Jin sanyi da ƙamshinsa da ya kama dakin tamkar kullum din yana rayuwa cikinsa ne,yasa ta Ankara da cewa har sun shigo dakin,dan dawowa hankalinta ta yi tana bin dakin da kallo,ko mai nasa a nutsu a tsaftace kuma abirgance,haka kuma na musamman wani abinda take gani tare da shi din duk kudinsu sam bata sani se ya zamana tamkar ko mai nasa yi masa ake yi. Zaunar da ita gefan hadaddiyar gadonsa da taji shimfida ta alfarma ya yi,ji ta yi tamkar yau ne ta fara shigowa dakin saboda yau din ne ta dan yi masa kallon nutsuwa.sanyin tafin tattusan hannunsa da ya sauka kan fuskarta shi ya dawo da ita gayyacinta,se kuma alokacin wasu hawayen masu zafi suka ci gaba da sauka tana kara tunawa da duk zantukan na rabi,zuba mata idanunsa da suke matukar rikitata ta jefa ta cikin halin da take kasa tantance waye ita yayi yana yi mata kallonnnan nashi na kai tsaye me shigewa kanta ba tare da wani shamaki ba.rikicewa ta fara kokarin yi ,cikin sanyi ta yi kasa da kanta tana ci gaba da jin dukkan idanunshi da zuciiyarsa a cikin jikinta dan kame jikinta ta yi saboda rawar da ya soma saboda kusancinsu yar ta zarar dake tsakaninsu kuwa tuni ya haɗeta,a hankali yasa hannu shi ya dago fiskartta wadda har yanzu ba ta daina danshin hawayen da suka yi tsayawa ba,cikin wani irin sanyin jiki ya haɗeta da jikinshi yana sakin siririyar ɓoyayyiyar ajiyar zuciya,da sauri yake jin zuciyarshi na bugawa da wani irin tururin zafinso wanda ya dade da yi masa illa ba tare da yasan shi din ba ne,se kuma a yanzunne yake gane komai ta yadda yake kasa control din kanshi da zuciyarshi akan duk abinda ya rabi Raihan ɗin bare kuma ya shafi ita da kanta,sosai yake jin takaicin rabi da tsanarta dake son mamaye zuciyarshi. Itama ce kin tsanantar bugun zuciya tare da sanyin jiki da kasala ta shige jikinshi tana shaƙar ƙamahinsa da bayanshi bata taɓa jinsa a tare da wani ba duk tsawon rayuwar da ta yi cikin maza ya'yan manya yan gata masu ji da Naira ko a wannan bangaren tasan shi din na dabanne,ji take tana mantawa da wata rabi bare kuma kalamanta,bata jin ko mi bata ganin komi sai dan Ammi da Abbu jikan innawuro da CHIBADO,wani kasala take ji da sanyin kaunarshi dake bin duk wani loko da sako na jikinta da zuciyarta kai dama duniyarta gaba ɗaya,dago fuskarta ya yi yana mai zuba mata lulu eyes dinshi masu kashe jiki da sakata taji kamar ba a duniyar mutane take ba,maganar shi ta ido da gira yayi mata sarai ta fahimci me yake nufi ita bata iya shurunnan ba shi yasa ta bude bakinta da niyar bashi amsa,amma se me? Sanyin harshenshi da kamshin mauth fesh na kamfanin mint bon ya shige mata kai har can can ga taushin harshensa da ya nemi zautata kamar yau dinne ya fara kissin ɗinta,samun kanta ta yi da maida masa martani ta hanyar bashi wani irin fationality kisses da ya nemi tsatse ruwan kan Chibado,se yake ji tamkar ba a duniyar yake ba,bai taba kisin wata mace a rayuwanshi ba saboda haka bai san ya ake ji idan mace na maida martani kisses din ba,shi dai ya ji a duniyar shi babu baki irin na Raihan babu harshe irin na Raihan kai harda haƙoran ma babu ya nata,a hankali ya fara shafe jikinta da wani irin sanyi kamar wanda ke taba kwai ,jin inda hannunshi ya sauka ya sashi manta kanshi da tuna shi din waye a ego,ya manta waye shi bare jin kanshi da wani kiskilancin shi,duk da cewa da bra a jikinta irin wadda take sawa dan tieting din jikinta ta saje as a male,cikin nutsuwarshi da sam baka gane yana kokarin ficewa hayyaci ne ya dago ta jikinshi kan kafafunshi suka kuma hadewa sosai,sosai ya fara dan cakudata yan son kai hannunsa inda ya ke muradi ta hanyar son jinsu a asalinsu ba cikin kaya ba, kokarin zame rigar cot din da take masa shamaki da naked asalin fatar Raihan ɗin yake,wayarshi ce fara haske wanda ba na farko ba ne,a hankali cikin kasala da jin dan ciwon kai na son mamayarsa ya bude gajiyayyun idanunsa da suka shige ciki ya dan kallo fuskar wayar sai kawai yayi katari da sunan Amminsa baro baro saman screen da din wayar. Dan furzar da iska ya yi yana dauke idanunshi daga kan wayar,dago fuskar Raihan ya ya yi sai yaga har ta yi bacci, wani irin bacci me cike da nutsuwar zuciya take yi dan haka cikin tattashi da kallaɓawa kamar wata jaririya ya zame cot din jikinta da head scap din da yake rufe asalin kyakkyawar sumarta me tsayi da yawa ga baki kamar rinin dayin yana cire hular gashin ya baje saboda irin me santsin nanne da gazar gazar kamar gashin gira,shafa kan yayi cikin wata lallaɓawan ya cire duka nannauyan kayan jikinnata bai bar mata komai ba sai fara sol din singlet da tiet bra din jikinta gyara mata kwanciya yayi tare da ja mata tattusan doved dinsa da yake ta zuba ƙamahinsa, Cikin nutsuwarsa ya dawo ya dauki wayar ya fita danyin waya da Ammintasa. *Ruby* Ruby kasa zama ta yi a buldin din, ji take kanta yana wani hayaki kamar tana bukatar wani abu,fita ta yi ta nufi Motanta dan komawa gida,karon da suka ci da Surry shine yasa ta ja da baya, take mummunan mafarkinta na jiyan ya shiga dawo mata, ji tayi kamar zata fita a hayyacinta hakan yasa ta yi saurin yin gaba Surry ta biyota a baya a tare suka bar buldin din zuwa can chibado's,haka suka taho kamar kurame, Surry ba ko mai yasa tayi shiru ba sai mamakin yadda rabi bata nemeta ba sannan kuma yanzun bata ga wani alamun tashin hankali a tare da ita ba. A haka suka isa chibado's ko wacce ta dauki jakarta sannan suka rankaya zuwa bangaren rabin. Koda suka shiga zama Surry ta yi tana ci gaba da yiwa rabi kallon mamaki ganin yadda take komanta kai tsaye kamar babu wani damuwa cikin rayuwarta,kasa shiru ta yi ta dubi rabin lokacin da take zama kujerar dake fuskantar Surry tana buɗe bottle din ruwan da ta dauko a Fringe,da kyar Surry ta ce", wai ruby lafiyanki kuwa naga babu wani abu da ya nuna kina cikin damuwar abinda ya faru jiya akan labarin Raihan da na kawo miki?karfa ki manta mijinki take aur.........wani irin mugun tari ne ya sarke ruby ruwan da ta sha suna dawowa ta hanci ta baki.......✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page40 ``` Sosai take tari saboda kwarewar da maganar Surry tasa ta yi,da sauri Surry ta taimaka mata har ta samu tarin ya lafa.dago idanunta da suka yi jajur ta yi ta kalli Surry kafin cikin dashewar murya ta ce", Surry ya akayi kikasan mummunan mafarkin da nayi jiya ba tare da na sanar dake ba? Wani mugun kallo Surry ta bi ruby da shi kafin cikin takaici ta ce", No wonder naga kina harkanki kamar me nutsuwa,to bari na kuma tabbatar miki abinda ya faru jiya ba mafarki ba ne zahiri ne kuma da gaske idan zaki nutsu mu sami mafita ki nutsu, dan wallahi idan baki maida hankalinki jikinki ba to kina ruwa tsundum cikin bakin kada idan baki tashi tsaye kan Raihan ba tas zata tsigeki daga dan matsayin da kika samu na aurensa. Wani irin ja idanunta su kayi tamkar wadda aka zubawa barkono,jin zuciyarta take na wuta dan abinda take ji yafi karfin zafi sai dai wuta,wani irin tsanar Raihan na ninninkuwa a zuciyarta,ko sunan Raihan bata son ji ko me sunan bata so, lallai Raihan ta shammaceta,to me yasa ta boye kanta take amsa sunan namiji? Shin da sanin iyayenta?to ya akayi wazer yasan cewa ita din macece? Ji ta yi kanta na neman bugawa hauka take neman yi dan kanta ba zai iya dauka ba,cikin sauri Surry ta fito da guzurin da ta yo na kwalaben magani har ma da wasu kwayoyin,mikawa ruby ta yi tana cewa karbi wannan kisha zaki samu salama idan baki sha ba zaki iya haukacewa da wannan kalar tashin hankali....kafin Surry ta gama fada ta finciki bottle din maganin ta afa zuwa bakinta ba tare da wani tunani ba, haka kwayoyin ma ta bata su ta shanye tana faman sakin ajiyar zuciya. A hankali ta fara lumshe idanunta tana ganin Surry bibbiyu,ganin haka yasa Surry ta taimaka mata ta kai ta dakinta,dawowa ta yi ta kwashe ko mai domin ba yanzu ne take son wazer yasan rabi na shaye shaye ba ,da sauran lokaci lokacin da ya zo daidai da cika nata burin bayan ta gama dasu duka. _________ Tunda ya dawo gida yake faman kaiwa da kawowa, hankalinsa tashe yake akan dawowar yaran abbu don karbar ragamar comfanis,to amma yanzu me ya kamata ya yi ? Tabbas idan ya yi shiru ya zuba ido zai yi asarar tsawon shekarun da ya jima yana son cika burinsa ,wallahi ba zai yuwu ba,wayarshi ya janyo ya daddanna wasu nombobi jim kadan aka daga,ba tare da ya saurari gaisuwar da ake masa ba ya ce", lallai ina son a saka min ido akan iyalan Alh Chibado ina so ranar da zasu dawo kafin su ƙaraso gida gaba dayansu a gama min dasu duk wanda ya rabe su shima a hada da shi", ok sir aka fada ta can ɓangaren,kashe wayar ya yi yana huci kamar wani mayunwancin zaki,shi sam bai ga amfanin sako matar nan cikin tafiyarsa ba,se yanzu ne yayi tunanin hakan,to amma yasan tabbas watarana zata yi masa rana,ko dan kusancin da suke dashi da matar WAZEER. _______ Cikin fushi tsohuwa ta nuna shuda da sandar tsafin dake hannunta bakinta na wani irin fitar da huci me tsananin zafi ta ce", shuda tabbas badan karin da ka kawo mana ba da yanzu hukuncin jini ya hau kanka saboda bamu taba aiki me tsauri wanda yaja mana lokaci irin naka ba,da ace a iya mulki abin naka ya tsaya da yanzu an wuce gurin to amma wannan tsinannan ahlin da ka sako a ciki shine abinda yake tokare duk wata sa'armu,dan haka dole yanzu mu fara shan jinin daya daga cikin alhlin Alhaji Muhammad nuur saboda shine matakin nasararka akan komai kuma shine zai yaye duhun da ya lullube idanunmu muka kasa ganin ko mai akan al'amarin gidan, dan haka kaje mune za muyi zaɓin wanda zamu dauka cikin yaran matansa guda biyu ", daga haka komai ya shafe tamkar ba ayi ruwansu a gurin ba. *Shugaban jam'iya* Duk da ya samu tabbacin babu wata damuwa a bayan sakin abokansa hakan baisa ya kwantar da hankalinsa dari bisa dari ba,shi dai yana ji ajikinsa ba shike nan ba dole akwai wata ɓoyayyiyar manufa a bayan sakin su da akayi,dan haka a ƁOYE ya shiga nazari da binciken ta inda aka haihu a ragaya. Abangaren su Alh ja'e da su sanater kuwa kwantar da hankalin su su kayi sukanci gaba da sharholiyarsu.ba komai ne yasa su hakan ba sai kawai tabbacin da suka samu ta ɓoyayyiyar wasikar email akan cewa su kwantar da hankalinsu akan wannan video domin tuni an riga da anbatar da videon babu shi,duk da cewa sun so rudewa da wannan lamari to amma da su kayi wani nazari akan yadda Rahim ya kasa fitar da videon tuni suka watsar da tunanin komai,saboda acewarsu da ace Rahim yana da video nan to tabbas da yanzu ya tona musu asari ko dan ganin yadda aka kamasu kuma aka sake su ba tare da anyi musu ko wace irin tuhuma ba,sun tabbatar da cewa lallai akwai wani a cikinsu da yake da babbar alfarma,shi kuma wanda ke yi musu duk wannan gatan sun ƙaddara cewa yana daga cikin manyan mutanen da ba zaiso a sanshi da daurewa irinsu kugu ba, wannan ke nan. __________ Mama murja ce zaune a falo kana ganinta zaka tabbatar da cewa hankalinta ba a wani kwance yake ba,tunda ta san cewa akwai me bibiyar rayuwar yaranta shike nan bacci ya gagara idanunta,gashi ta kasa gayawa Abbie tana tsoran kar allura ta tono garma tunda suma ba gaskiyar suke kullawa ba,sai yanzu ta gane a she karyar son kudi take tunda gashi wata yar barazana ta na neman hanata bacci da kwanciyar hankali,ita yanzu ji take ta hakura da komai in dai za a bar mata yaranta sanyin idaniyarta,karar wayarta ce ta katse mata tunaninta, a dan zabure ta kalli wayartata dake gefanta zubawa wayar ido ta yi tana mai jin wani irin bugun zuciya ga wani irin rawa da jikinta ya fara kamar wadda ake bugawa ganga. Saida wayar ta yi ringing sau uku kafin ta kai hannunta dake rawa ta daga tana karawa a kunnenta Affan yana shigowa,ganin yanayinsa yasa jikinta ya kara tsananta rawa kafin affan yayi magana taji wani irin kuka na tashin hankali daga cikin wayar,bakinta na rawa ta ce", waye? Zainab matar rufa'i dake kan wayar ta kuma saka wani mahaukacin kuka tana cewa mama shike nan ya mutu rufa'i Faisal ya zama Maraya na zama me takaba", wayar ce ta zame daga hannun mama idanunta na kallon affan bibbiyu Muryar Zainab nayi mata amsa kuwa cikin kunnuwanta,kafin affan ya Ankara ta zube kamar matacciya. *Wazir* A hankali take bude idanunta,har ta bude su gaba daya,bin dakin ta shiga yi da kallo sai kuma abinda ya faru ya shiga dawo mata,da sauri ta yaye duvet din da ya rufe ta dashi tana duba jikinta da babu kaya,dafe kirjinta ta yi tana fidda manyan idanunta waje sai kuma ta shiga duba dakin tana neman inda zata Ganshi,ganin baya dakin yasa ta ɗan saki ajiyar zuciya amma ba wai ta gamsu cewa bai ganta ba,tunda alamu sun nuna shine ya cire mata kaya. A hankali ta sauko daga gadon tana kara kallon jikinta tana ƙunkuni da jin takaici har cikin ranta,sai da tazo tsakiyar dakin dan shigewa toilet kawai taji bude kofa da shigowarsa duk alokaci daya yana fidda sallama can ƙasar makoshinsa,da sauri ta juyo tana mai saka hannayenta duka tana kalmashe kirjinta,ƙunkuni ta shiga yi tana hade fararen ƙafafunta guri daya,haka kawai an samu ancirewa mutum kaya dan anga yana bacci," wani tunanine yazo ranta wanda take ta kuma zaro ido tare da karasawa inda yake tun shigowarsa a tsaye yana kallon yadda take yi din,plz Hamma wazir me kayi min? Ka kalleni ko? Ka taba Ni ko? Ina ka taba dan Allah? Ta faɗa tana fashewa da kukan tsoro, wani munafikin Murmushi ya sake yana mai riko hannuwanta duka biyun kafin cikin deep voice dinsa ya ce", haba ke kam wannan fa kawai na gani da wannan ya fada yana kai hannunsa saman kirjinta kamar zai taba,ai cikin zafin nama ta manne da kirjinsa dan hana shi wannan damar,sai kuma cikin rishin kukan sakalci ta ce", Ni kam me yasa kayi hakan? Ta faɗa tana dan bugun kirjinsa", rike hannun da take bugunsa dashi yayi sannan a hankali ya kai bakinsa kunnenta sai da ya fara sakin mata hucin numfashinsa sannan cikin deep voice dinshi me tsinka jinin jikinta ya ce", saboda halalne a gare Ni,oh wai sai yanzu kike tunawa da baki so bayan tun ɗazu kin gama tsotsewa Ammi danta baki bar masa ko miyan haɗiya ba", ai da wani irin sauri ta fizge daga jikinshi ta faɗa bath da gudu tana sharbar hawayen kunyar da wazir ya gama bata. Murmushin dake kara masa kyau da kwarjini ya sake yana tsirawa bayanta ido har ta shige bath din,shafa sumar kanshi me kyalli da taushi yayi kafin ya dawo da hannun saitin zuciyarshi yana saurarar bugun da take yi da dan sauri,cije lips din shi yayi yana mai ambatan sunanta a hankali can kasan makoshinsa cikin wani salo na jan hankali kai ka ce RAIHAN ɗin na gefansa. Fuskanta yayi idan ba fita yayi ba to baza ta shirya ba,har zai fita sai kuma ya koma jikin kofar bath din ya dan yi knock kafin ya ce", fitowarki da wuri shine komawarki gida idan baki fito nan da minti ɗaya ba wlh sai dai ki kwana",daga haka ya bar kofar ya fita daga dakin gaba ɗaya. Aiko ko rufe kofa bai gama yi ba sai gata ta fito tana ɗigar ruwa dan ko rigar bath bata saka ba sai guntun showel din da ta fizgo ta dan daura shi iya saman kirjinta dan da alama ma dai na tsane kai ne. Yana jinta dan haka ya dan saki Murmushi kawai yana mai karasa ficewa dan bata damar shiryawa a nutse. Cikin mitunan da basu wuce goma ba ta fito bayan ta maida kayanta da tazo da su ba dan ranta ya so ba,kallo daya ya yi mata ya mike fuskar nan babu yabo babu fallasa yayi gaba,dan tura karamin bakinta ta yi tana harararshi kasa_kasa,binsa ta yi a lokacin har ya shige mota hakan yasa itama tayi saurin shiga ya tayar suka bar unguwar gaba daya. Muhammad nur..Hause... Da gudu Affan ya tarairayota yana kiran sunanta kamar makoshinsa zai tsage,sai dai babu alamun tasan yanayi,da karfi ya shiga kwalawa me aikinta kira,wanda kiran ya jawo hankalin momy Hanne da ta kasa samun nutsuwar zuciya kullum a firgice take tana jiran jin ta inda masifar da ake son jefa su bullowa,a zabure ta tashi daga kujerar falonta dake bangarenta kasancewar sunfi kusa da mama murjar shi yasa iska ta debo Muryar Affan ta kawo mata kuma dama hankalinta yana kan murjar da ahlinta saboda tana tunanin komai zai iya faruwa ta bangaren mama murjar. Da gudun kafafu dana zuciya ta fita daga sashenta ta nufi na mama murjar inda har alokacin tana jin Muryar Affan dake ta kiran maman tana dan marin fuskarta,dai dai lokacin da ta shiga suma su Hajiya goggo da su hajiyar agadex har su Anty amarya da kafutanen gidan suka ƙaraso saboda kiran da salame me aiki tayi musu,cikin tashin hankali suke tambayar abinda ya faru,cikin kuka Affan ya shiga basu labarin mutuwar rufa'i,salati suka tafka aunty amarya kuwa kuka ta saka harma da momy Hanne dasu inna maimuna da sauran surukan gidan,inna maimuna ce ta yi karfin kiran Dr Sabo ( karki manta Dr Sabo shine likitan family din Alhji Muhammad nuur) cikin lokaci kankani gida ya rikice da koke koke har zuwan Dr Sabo da su Abba yahya, mutuwar rufa'i ta daki Abbie da duk wani namiji dake gidan dan Baffa ma duk dauriyarsa sai da ya share hawaye,Hamma idi da sauran kannensa kuka suka dinga yi kashirban. Da kyar aka samu mama murja ta farfaɗo da taimakon Allah dana Dr Sabo,sai dai kukan da take yi shi ya kuma karyawa duk wanda ke gurin zuciya. Daidai lokacin masu gadi suka budewa wazer tangamemen gate din gidan, sai da ya samu guri yayi fakin sannan ya juyo yana kallon RAIHAN da taki yadda su haɗa ido,hannu ya kai ya dan tsunkuleta wanda hakan yasata zabura har ta juyo gare shi idanu cike da ruwan hawaye,bude baki tayi zata yi magana sai dai bata samu damar hakanba wannan maganaɗisun dake jan zuciyarsa gareta yaja shi ya haɗe bakinsa da nata tare da tarairayota jikinsa gaba daya,wani irin tsinkewa zuciyar Raihan ta yi wani tsoro ne ya kamata na kar wani ya gansu duk da cewa glas din motar tintank ne...... More comments and share 🙏..........✍🏽 Pg 41 Baisan ya akai ba shi dai kawai ya samu kanshi da kasa rike kanshi akan RAIHAN wani salon kisses yake mata me matukar tsayawa a rai da zuciya,tun zuciyarta na bugawa da tunanin kar wani ya gansu har taji tunaninta ya tsaya akansa bata jin komai sai ruwan sanyin harshensa a duk wata gaba me amsa sunan gaba dake jikinta,duk da cewa rigar dake jikinta tana takurashi amma hakan bai hana shi cakudata da salonshi da shi kansa baisan ya iya ba sai akan RAIHAN din. Tunda ta fito daga ɓangaren mama murja taga shigowar motar family din wazer tasan cewa shine,zubawa motar ido ta yi tun tana irga sakonni ta koma mintina sosai abin ya tsaya mata a rai ganin babu wanda yayi kokarin fitowa daga motar,wani tunani da ya shiga ranta yasa zuciyarta fara bugu da sauri sauri, me RAIHAN take yi tare da wazeer a mota? Dan tasan tabbas ita ya kawo gida,numfashi aunty amarya ta saki tana kokarin daidaita kanta daga tashin hankalin da take son shiga da wasi_wasi akan yartata da kuma amintaccen maigidan RAIHAN ɗin wazer. Da kyar RAIHAN ta samu ta zame daga rikon gudun kar ki barni da wazer ya yi mata,sosai ta haɗa fuska saboda tunawa da abinda yace mata ɗazu," wai ta tsotseshi,cikin kasalalliyar murya ta ce da shi yanzu waye yake tsotse wani? Bata jira abinda zaice ba tayi saurin bude motar ta fice tana jin sanyi a ranta akan ramuwar da ta yi", maida kansa ya yi ya kwantar yana mai tsirawa hanyar da tabi ido, shi ka dai yasan azabar da yake ji da radadin da zuciyar shi ke yi akan RAIHAN,da kyar ya saita kansa yaja motar ya fita bayan masu gadi sun bude masa kofar. Yana fita aunty amarya ta yi saurin bin bayan Raihan wadda tuni ta kai falonsu da yayi tsit babu motsin kowa saboda duk suna can bangaren mama murja,tana shirin shigewa dakinta dan kimtsa kanta saboda bata so aunty amarya ta ganta a birkice haka,bata kai ga shiga ba aunty amarya da ta shigo cikin wani irin fushi da sassarfa ta cafko hannunta, a tsorace RAIHAN ta juyo ganin aunty amarya yasa ta Dan ja ajiyar zuciya sai dai yanayin da taga auntyn ya tayar mata da hankali,dan haka cikin rawar baki ta ce", Mami me yake faruwa ne? Wani kallo ta jefa mata kafin taja ta su yi dakin RAIHAN ɗin, Abbie da komai ya faru akan idonsa har zai rabu da su sai kuma ya bisu dakin,ganinsa yasa aunty amarya duk ta daburce ta rasa ta ya za tayiwa Raihan tambayar dake cin ranta,ganin haka yasa Abbie ya dan saki Murmushi me ciwo dan har ga Allah mutuwar dansa ta dake shi,ya ce", me kike son sani ramla? A dan rikice ta dube shi sai dai kafin ta yi wata magana ya tari numfashinta da cewa dan Allah ramla ki bar yarinyar nan ta samu salama ko yaya ne ɓoyan ya isa haka, idan kina zargi akan ita da wazer ne to ki daina saboda tuni aka ratayawa Raihan igiyoyin auren WAZER", daga haka ya fice daga dakin ya bar aunty tsaye da alama ko mai nata ya daina aiki na wucin gadi,tsoro razani firgici mamaki duk su ne suka hadu su kayi dabaibayi a kwakwalwarta. sai kuma tarin tambayoyin da babu wanda zai iya amsa mata su sai Abbie din da kansa sai kuma RAIHAN da wata ƙil ta san wani abu akan hakan saboda ganin yadda bata firgita ko shiga shock akan maganar Abbie ba. Shigowar hajiyar agadex yasa Dukansu suka zuba mata ido,me ye hakan kuka tsaya ciki cirko kamar wasu sassake?ke Raihan baki san me yake faruwa a gidan ba ne? Da sauri RAIHAN ɗin da aunty amarya da ta kuma shiga ruɗani da tsananin mamakin yadda hajiyar agadex ta kira sunan RAIHAN kai tsaye ,ita kuma Raihan abinda ke faruwa din da Hajiyar agadex ta ambata shine yaja hankalinta. Da sauri aunty amarya ta matsa gaban hajiyar tare da kama hannunta cikin rawar jiki da ta baki ta ce", Hajiya ke ka kin sani? Tayaya kuma yaushe? Ashe Ni kallon mahaukaciya kuke min kowa ya san sirrin da na binne nake ta kunbiya_kunbiya akansa amma kuka barni ina takurawa zuciyata data da hana rayuwata sakat duk gurin ɓoye RAIHAN?wani kallo hajiyar agadex ta yiwa aunty amarya kafin ta ce", kece kika maida kanki mahaukaciyar tunda a kullum ta Allah sai wani daga cikinmu ya nuna miki alama amma saboda zuciyarki da idanunki a rufe suke sun kasa gano miki ko mai,amma tunda yanzu kin warke daga makanta zauna na gaya miki abinda kike son sani", cikin sanyin jiki ta zauna gefan gadon RAIHAN ita kuwa hajiyar agadex kan sofar dake dakin ta zauna, Raihan ɗin kuma toilet ta shige jikinta sanyi kalau duk da cewa tana jin wani sakayau nakasanxewar maminta zata san ko mai kamar yadda Abbie ya sani akanta. Bathroom ta shige ba tare da ta tsaya sauraren labarin da Hajiyar agadex zata bawa maminta ba. Dan numfashi Hajiyar agadex ta sauke kafin cikin nutsuwa ta fara da cewa ramla kafin nace da ke komai ya kamata na fara nusar dake abinda kika manta tunda dai_dai gwargwado kina da ilimin addini me zurfi,to amma idan mu kayi la'akari da kaddarar da ta rigayi fata sai muce ita ce ta zama sanadi. Dan muskutawa ta kuma yi sannan ta cigaba da cewa", ramla abinda kika yi ya sabawa Shari'a dan me ya sa zaki lullube abinda Allah ya bude sam baki da wannan damar dan haka ki yi istigfari dan kuwa kin shiga hurumin Ubangiji ,shi yasa ya jarrabeki da rashin kwanciyar hankali da tashin hankali rashin nutsuwa, daga karshe kuma duk abinda kike boyan ya ki boyuwa a gurin wanda kike boyan dansu,tunda makiyan dai suna nan kuma baki sansu ba har yau da ko mai yake son fallasa ga kowa,cikin nutsuwa Hajiyar agadex ta sanar da ita dukan abinda ya faru da yadda akayi Abbie ya sani har zuwa kan auren RAIHAN da WAZER....... Kuka aunty amarya ta saka tana jin wani irin tsoro na kuma shigarta har yanzu bata jin cewa tayi kuskure akan abinda tayi,kallonsu kawai take a dan basu suka haifi Raihan ba basu san irin son da take mata ba,kuma har yanzu bata jin zata amince a tonawa duniya wacece RAIHAN. Cikin kukan aunty amarya ta ce", bayanku waye na waje ya san da wannan sirrin? Girgiza kai hajiyar agadex ta yi tana bantarar goranta kana ta ce", ai bayan shi Ahmad Chibado wato baban wazeer da kuma dan uwansa babu wani da ya sani a waje kuma ina da tabbacin yadda muka rufe maganar a cikin gidannan ta rufu babu wanda zai kuma sani idan har hakan kike so,(Hajiyar agadex ta boyewa aunty amarya ur exsellency yasan da maganar saboda bata san batun dukiyar Raihan tana gurinsa ba,shi yasa taki sanar da ita saboda wannan ba hurumin ta ba ne) RAIHAN tana jinsu bata ce komai ba karewa ma tuni tayi shirin bacci,dan kallon RAIHAN ɗin aunty amarya ta yi kafin ta dubi Hajiyar agadex ta ce", zanje na roki Abbie kar ya bari kowa ya sani saboda yanzu mun hau matakin nasara akan gano makiyanmu bana so sai da muke gaf da cimma burinmu komai ya lalace zanso sirrinnan ya cigaba da ɓoyuwa zuwa nan da ɗan wani lokaci,wallahi Hajiya duk wanda ya ce ", zai bankaɗa sirrinnan wa duniya zan iya raba rayuwa da shi zan kuma yi mishi tsana mafi muni dan haka mu ci gaba da killace RAIHAN dani da ku gaba daya har mu cimma nasara", jinjina kai kawai Hajiyar agadex ta yi tana ci gaba da tauna goronta kafin ta ce", shike nan nima dai a yanzu ina bayan hakan tunda an riga an fara dole a daure a karasa fata dai shine Allah ya bamu nasara,ajiyar zuciya aunty amarya ta sauke jin kalaman Hajiya sai taji ta ɗan samu sauƙi, tashi ta yi tana kallon RAIHAN da ta dunƙule kanta tana jinsu, RAIHAN ki yi hakuri ki ci gaba da yi min Alfarma akan ɓoye kanki,kuma ki toshe duk wata hanya da kika san asirinmu zai iya tonuwa dan Allah RAIHAN ",ta karasa fada tana haɗe hannayenta alamar roƙo", da sauri RAIHAN ta girgiza kanta hawaye na tsatstsafowa daga idanunta,ta ce", mamina ki daina roƙona a kan abinda ya zamar min dole duk abinda kike so shi nake so kuma na miki alƙawarin kiyayewa da toshe duk wata hanyar da nasan asirinmu zai iya tonuwa", murmushi aunty amarya ta yi tana cewa karki manta daga ciki har da kiyaye mu'amalarki da WAZER", dummm RAIHAN ta ji kamar jinta ya dauke tana kallo mamin ta fita daga dakin Hajiyar agadex ma tashi ta yi tana mata bankwana,sai dai ita Raihan ta kasa motsa koda yatsunta,haka nan maganar aunty ta shigeta ta kuma tsaya mata a rai,shin me take nufi da maganarta ta karshe? Saurin kawar da tunanin ta yi tare da kwanciya tana kokarin yakice komai saboda bata son zuciyarta ta tabbatar mata da manufar maganar aunty amarya akan hasashen da take yi. A wannan dare da yawan rayuka da zuciyoyi basu kwana cikin jin dadi ba ta bangaren ahlin Alh Muhammad nuurr,mama murja ta yi kuka tayi sambatun har an kasa gane inda ta nufa sai tofi da mahaifiyarta da ta ƙaraso a daran take mata, tuni yan uwanta sun cika gidan kafin washe gari a ƙaraso da gawar a shiryata anan. Tabangaren momy Hanne ma hankalinta bakaramin tashi ya yi ba,tunani biyu ne yake kuma daga mata hankali shine murja zata iya zarginta sannan kuma duk wanda ya kashe rufa'i tabbas zai juyo ne kan nata ya'yan tunda itama anyi mata wannan barazanar, koda yake wannan yafi karfin barazana tunda gashi kowane ya tabbatar da abinda ya fada ya aikata,a ranar dai a tafe ta kusan kwana saboda sunturin zuwa sashen surukanta dan duba lafiyar yaranta. A bangaren Affan ma dai kusan haka ne, saboda shi yasan komai akan mutuwar dan uwansa, ga tashin hankalin rasa dan uwansa ga kuma tunanin shima da harinsa ake wanda a iya tunaninsa yasan cewa shine za aka she sai kuma mutuwar ta faɗa kan dan uwansa,to fa shi dinma yasan ba sha ya yi ba,dan haka shima idanunsa bai ga bacci ba duk da yake barawo. _____________________ Lokacin da dare ya tsala, alokacinne su kuma ranarsu take haskawa saboda a wannan lokacinne suke nasu kasuwancin. Yadda garin yayi shiru su kuma a wajensu ba haka bane,saboda wata iriyar dariya da tsohuwa me jini ke yi tamkar zata tsaga dajin da abinda ke cikinsa,komai girgiza yake wani abinma saboda tururin bakinta wuta yake kamawa da shi,su kuwa su shuda suna tsugunne akan gwiwoyinsu kawunansu duka a kasa,ko wanne sanye yake da jar riga iya gwaiya sai jan kyalle ɗaure a goshinansu,hannayensu kuwa dauke da ƙokuna wanda ke dauke da jinin rufa'i. Sai da kowanne ya shanye sannan suma suka fara sheka wata muguwar dariya tamkar da yawansu ba musulmi ba ne,bayan mintina uku gurin yayi tsitt tamkar babu wata halitta a gurin. Maganar tsohuwa ce ta karaɗe dajin cikin wani irin amo da sauti mara dadin sauraro, ta ce", shuda a wannan karonma kayi nasara dan haka zaka yi ta ganin nasara babu wanda ya isa hanaka kujerar mulki sannan babu wanda ya isa yi maka shamaki da dukiyar da kake nema, sunan ka zai ta fita yana linkaya cikin duniya baki daya, sirrin nasarar arzikinka yana jikin ahlin Alh Muhammad nuur,yanzu nasara ta fara zuwa zamu yi ta daukar ahlinsa har zuwa kan wadda muka fi buƙata,duhun da ya lullube idanunmu ya yaye jini yaga abinda ke boye," hahhhhhhh Ta kuma babbakewa da wata muguwar dariya,kaje kaje kaje shuda nasararka na tare da kai da duk wanda ka kawo ko ya rabeka. Washe gari tuni gida ya cika makil da manyan mutane, tuni gawar rufa'i ta iso tare da ahlinsa. Lokacin da RAIHAN ta tashi ta ci karo da wannan tashin hankali ba karamin kuka tasha ba,duk da cewa ba kaunarta su rufa'i keyi ba, amma hakan baisa ta kasa jin radadin mutuwarsa ba. Wazer ma sammako su kayi shida su Abbu da Abba rabi, Cikin lokaci aka gabatar da salla aka mikashi makwancinsa sai dai halinsa na gari ya bishi, daga nan aka ci gaba da karbar gaisuwa,har zuwa kwana uku...........✍🏽 Comments and share 🙏 Pg42 Sosai yake son ganinta dan tabbas yasan tana cikin damuwa,tun ranar da abin ya faru bai karasata a idanunsa ba,wani irin damuwa yake ji akan rashin ganinnata,dan haka yasawa ranshi ganin nata a yau da akayi sadakar uku. Rabi'a kuwa rabuwa ta yi dashi bata kuma gigin shiga sabgarsa ba,domin ta riga ta shirya makamanta na tarwatsasu daga shi har yar sonnashi,tuni suryy ta dorata akan shirinsu na gaba wanda take saran shine bom na karshe da zai tarwatsa dukkan wata muamala dake tsakanin RAIHAN da shi da kuma yar karerentasu wato Ruby. Tunda yayi gaisuwa yake zaune guri daya a kamenshi ,fuskarnan babu yabo babu fallasa,Hamma ido dake kusanshi ne ya dann matso saitin kunnenshi ya ce ", wazer shiru baya takuraka kuwa naga tunda ka fara zuwa zaman makokinnan a takure kake baka iya hira da kowa,shi kuma wanda ka saba dashi matsoracine,ya cigaba da cewa na rasa me yasa duk wata sabga ta mutane Rahim baya son shigarta,kamar daurin auren gidannan duk yadda muke dashi fa ko leke bai leka ba,sannan baya son zuwa Masallaci duk da dai yace min kuna zuwa tare,sannan ga mutuwar dan uwanshi ko sau daya ya kasa zuwa ya zauna dan a karbi gaisuwa dashi,gaskiya wazer kayiwa kaninka fada ,duk da cewa ina yi mishi uzuri saboda tun farko an sanar mishi da irin wannan rayuwarne wato rayuwar killace kai da kadaici,shi yasa nake mamakin yadda ya iya yin aikin media SANA'AR hulda da mutane maza da mata. Tunda Hamma Idris ya fara surutunsa wazer bai dago ya yi masa cikakken kallo ba bare yasa ran zai bashi wata gamsashshiyar amsa,shiru na kusan minti ɗaya har Idris ya cire ran tankawartasa sai kuma daga can kamar tsinkayi deep voice dinsa yana cewa,ina son ganin Rahim din ", ba wai dan yasan me dame ye ne Idris ya fada ba kuma bawai dan zaiyi wani abu akan abinda ya fada din ba ne yasa ya nemi yin magana da Rahim din ba,a'a sai dai kawai dabarar da ya samu zai fake da ita yaga RAIHAN ɗin. Idiris da yayi tunanin karar da ya kawo ta Rahim ce yasa wazer ɗin ya bukaci ganin Rahim ya sa shi saurin tashi yana cewa taso muje na rakaka har dakin sa", wazer bai tanka ba ya mike ya zura saucikinsa da yake ta daukar ido tamkar alokacin ya fito daga kamfani,bin bayan idiris din yayi yana jin zuciyarshi na dan yi mishi nauyi akan damuwar rayuwar da Raihan ke ciki,wanda take fuskantar kalubalen rayuwa iri_iri. Ur exsellency dake can gefe inda suke tare da su Abbie ya ɗan zubawa su wazer da Idris da suka tashi ido,Abba Yahya da shi kuma hankalinsa yana kan ur exsellency ɗin da duk wani motsinsa ya yi tsai da tunaninsa yana kallonsa tare da son gano manufar kallon da ur exsellency yakewa su wazer ɗin. wanda acikinsu bazaka tantance wanda yake kallan ba,sosai ur exsellency yayi zurfi cikin tunani tabashin da Abbie yayi ne yasa shi dawowa hayyacinsa a dan firgice, Abbie ya ce",dan Allah ur exsellency ka daina wannan dogon tunanin komai fa da kake ganinsa yana da karshe,idan cuta ta kwantar da kai fa su babu ruwansu mu da iyalanka da kuma talakawa abun zai shafa dan Allah ka daina kaji", Abbie ya karasa maganar cikin yanayin tsantsar tausayawa. Jinjina kai ur exsellency yayi yana ɗan sakin murmushin da na kasa bashi ma'ana. Abba yahya kuwa da ya gama sauraren nasihar da dan uwanshi kewa amininsa,kwafa ya yi yana jin taisayin dan uwannashi da ninkaya cikin tunanin hanyar da zai samu ya tseratar da ahlinsu daga hannun mugun aboki. Suna saka kai falon da karadin Hajiya goggo suka fara cin karo ita dinma dai fada take akan halin RAHIM,na son kadaice kansa.haka kawai yaro ka maida kanka mace" babu yadda za ayi a ganka cikin taron maza kowa yana waje yana amsar gaisuwa kai kuwa kana daka,duk wanda ya zo maka gaosuwa sai dai ya shigo gida a kira masa kai,yo wannan wace irin rayuwace,ko da yake ba kowa ya jawo hakan ba sai uwarka dake boyeka tamkar wani sisin gwal", take ƙananan maganganu suka fara tashi da yawa suna ganin maganar goggo akan hanya take dan haka cikin lokaci kankani aka fara gulma,wasu da yawa abin yana cin ran su sai yanzu suka samu damar yada magana. Aunty amarya dai tunda taga haka ta samu ta silale ta bar falon,Hajiyar agadex ma shiru ta yi bata ce komai ba,sai dai ragowar yan uwan aunty amarya sun bi bayan Hajiya goggo akan zancanta fa gaskiya ne. RAIHAN kuwa tana can daki bata san wainar da ake toyawa ba,dan tun sa ilin da aka yi mata gaisuwa ta dau hanyar komawa daki Hajiya goggo ta fara sababinnata shi yasa bata tsaya sauraren abinda zai bata mata rai ba tayi shigewarta daki ta maida kofa ta rufe. Duk hakurin da inna maimuna ke bawa Hajiyar agadex a banza , bata samu yin shiru ba sai da sallamar wazer da Idris ya katseta. Cikin nutsuwa da Dattaku wazer ya kuma gaidasu da yi musu ta aziya,duk da yadda yaji na kasancewar samun mata a wajen to amma ya ya iya da zuciyarshi da take tamkar mayen karfe akan RAIHAN, Idris ne yaja shi yana masa iso zuwa dakin Raihan ɗin,a nan Hajiya goggo ta kuma sakin tsaki tana binsu da wata ƙatuwar harara tamkar idanunta zasu fado, kwafa tayi ba dai kuma cewa komai ba amma kana ganin fuskarta kasan cewa da kwai mugun haushi dake cin ranta. Hajiyar agadex kuwa Murmushi ta yi bayan ta dauke idanuta daga kallon da take yiwa Hajiya goggo,ci gaba ta yi da ballar goranta ba tare da murmushin kan fuskarta ya gushe ba,wanda hakan yasa hajiya goggo tsarguwa. A hankali Abban rabi ya dubi abbu ya ce",wai yaya da yaushe jirginsu Khalil zai sauka ne? Karfa mu sakankance suke su yi ta jira",Abbu ya dan numfasa tare da cewa har yanzu sunki fada min lokacin da za su sauka nara dalilinsu nayin hakan,kuma ina tunanin wannan tsarin yayansu ne WAZER ",wani dan dumm abban rabi yayi kamar irin ya shiga shock din nan,sai da abbu ya taba shi sannan yayi zunbur ya wayance da sakin Murmushi yana cewa kasan tun can baya ba ajin kansu shi yasa zasu dora daga inda suka tsaya,to Allah ya dai ya kara mana zumunci da kaunar juna", Amin ya rabbil alamin suka amsa har da su Abba yahya da suke tare a mazauni ɗaya. Hamma idi yana yi masa nock din dakin Raihan ya juya ya bar gurin.a nutse wazer ya dan bishi da kallo kafin ya dawo da kallonshi kan kofar dakin da har yanzu bata motsa ba bare yasa ran wadda ke ciki zata buɗe,a maimakon ya kuma bugawa sai kawai ya zaro yar karamar wayarshi wadda Bama nom kowa ne a ciki ba sai wadanda suke da matukar muhimmanci a cikin rayuwarsa.dannawa ya yi sannan ya kara a kunnenshi ko sakanni biyar ba ayi ba ta daga,ba tare da ya saurari abinda zata ce ba ya bata umarnin bude kofar. Da sauri RAIHAN ta kalli fuskar wayarta sai kuma ta kalli bakin kofar,tasan shi ba ma abocin wasa ba ne bare tayi tunanin wasa yake mata,a hankali ta zuro ƙafafunta kasa tare da zura silifas din dakin me tsananin taushi kai tsaye ta bude kofar tana mai sauke kyawawan idanunta akan ƙayatacciyar fuskarsa wadda ke ta fitar da wani irin haske kamar wata dan daren goma sha biyu,yadda ya kafa mata idanunsa masu kaifi da tasiri ga duk wanda ya ci karo dasu yasa ta matsa ta bashi hanya cikin sanyin jiki,shigowa ya yi ba tare da ya dauke idanunsa daga kanta ba,maida kofar yayi ya rufe sannan ya Murda key ɗin,sosai ya shigo tsakiyar dakin yana mai ci gaba da yi mata kallon kurulla wanda ya sa ta fara tura bakinta tana dan kakkawar da fuskarta gefe,to nikam wannan kallonfa? Ta tambayeshi cikin dan murguda bakinta gefe,bata Ankara ba taji ya yi mata zobe da dogayen hannayensa kana a hankali ya sunkuyo da kansa ta gefen wuyanta ya daidaita fuskarsa da Tata cikin wani salo me tafiya da hankali ya shaki daddaɗan kamshinta yana mai lumshe idanunsa a lokaci daya. Tunda wazer ya wuce Hajiya goggo ta tsurawa kofar dakin Raihan idanu tamkar wadda take son ganin abinda ke wakana a dakin ata cikin kofar. Inna maimuna da ke daga can dan gefe da Hajiya goggo akan kujerar dake fuskantar Hajiya goggon ta zuba mata ido tana son karantar ko ta ce gano ma'anar kallon da takewa kofar RAIHAN,da dai taga abin ba na kare ba ne,sai kawai ta yi gyaran murya tare da cewa Hajiya goggo ya dai naga kamar kinyi zurfi a tunani?firgita Hajiya goggo ta yi tamkar wadda aka tasa daga barci cikin yan kame_kame har da cire dankwali ta gyara ta ce", ey ah ahhhh ina tunanin halin yaronnanne wlh sam bana jin dadin kuntata kansa da yake", Murmushi inna maimuna ta yi kamar dai bata gamsu da abinda Hajiya goggo ta ce ba,to amma ya ta iya dole ta ja bakinta tayi shiru tunda bata da halin cewa bata yadda ba suruka sukutum guda. Abban rabi kasa daurewa ya yi wazer ya fito saboda abinda ke cin ransa,tashi yayi daga cikin mutane yayi can baya ta wajen bangaren surukan gidan,wayarshi ya dauko daga aljihu jikinshi har rawa yake wajen neman sunan wazer,danna masa kira yayi ya tsaya yana sauraren ringing din da ta fara. *RUBY* Duk da yadda zuciyarta ke kuna akan lamarin haka ta daure ta shirya dan zuwa yiwa Raihan gaisuwa wadda ba wai dan Allah zata ba sai dai abinda take kullawa a ranta domin kuntatawa RAIHAN. Lokacin da taje bangaren innawuro, innawuro kallonta tayi kafin ta dan tabe baki ta ce", saboda gulma da za muje baki bimu ba sai yanzu zaki wani shirya wai zaki gaisuwa,hmm Tom sai kin dawo Allah bada sa a", dan tura baki rabi ta yi tare da ficewa tana maganganu kasa_kasa,kai tsaye mota ta dauka ta fice daga gidan. *WAZEERRAIHAN* A hankali ya kai bakinshi cikin kunnenta tare da hura iska kadan wanda hakan yasata kankame jikinta, tana dan mutsu_mutsu ganin kamar tana son ƙwacewa yasa shi ƙara ƙarfin rikonsa gareta sosai ta hadu da jikinsa ƙamshin turarensa da nata ƙamshin ya haɗe ya sakar mata wata irin kasala me tsananin sanyi tamkar ana hura mata iska cikin bargonta. Juyo da ita ya yi tana fuskantarsa, ƙasa ta yi da kanta dan kaucewa kaifafan idanunsa masu sata taji wani irin kunyarsa,cikin wani irin deep sound ya ce", kina jin me wancan kakarnaki ke fada? Jinjina kai ta yi idanunta na kawo ruwa kafin yace", wani abu tuni ta fara ruwan hawaye, ɗan ware idanunshi ya yi akanta sai kuma yasa hannunshi me taushi saman kuncinta ya dauke hawayen ya daga yatsan yana kallo kamar wanda ke kirga yawan hawayen,sai kuma ya kalleta tare da daidaita fuskarshi da Tata yana kallon hawayen da suke ƙara saukowa da gudunsu, a hankali ya matsar da bakinshi daf da fuskarta bata yi aune ba saijin ɗumin bakinsa tayi saman idanunta wani irin ajiyar zuciya ta saki sai kuma samun kanta ta yi da ƙamkame shi saboda tsananin zummm din da taji har cikin kwakwalkwarta,a hankali cikin ajinshi da iyawarshi ya ci gaba da lashe hawayen da duk wani abu dake gangarowa daga idanunta,gangarowa ya cigaba da yi zuwa kan dan ƙaramin bakinnata........✍🏽 Comments Comments Comments Yawan comments yawan post.. Pg43 Haɗe bakinshi da nata ya yi kafin a hankali cikin salon kwarewar da baya sanin yana dashi sai kanta, ya shiga tsotse harshenta tamkar wanda ya samu alewar da yake matukar so,yadda yake yi din dolene ya tsaya a yar karamar ƙwaƙwalwarta da zuciyarta harma da gangar jikinta.salon na dan gidan Ammi jikan innawuro dabanne da na kowa harma dana 'yan Indiya inji Raihan,cikin nutsuwarsa da kamewa ya cigaba da bata wani zazzafan kissess,a hankali ƙafafunta suka fara rawa saboda yadda take jin abin har can maƙurarta,wani irin sha yakewa miyanta wanda yake jinsa tamkar wani zuma. Ganin yadda ƙafafunta ke neman lanƙwayewa saboda yanayin da yanayin da dan Ammi ya jefata ciki ,yasa shi tarairayota gana dayanta tamkar jaririya ya wuce da ita zuwa saman tattausar shimfidar gadonta,zama ya yi da ita yana kallon fuskarta da yake jin tana matukar ɗebe kishi kewar kadaicinsa na nunkufurci da yake dabiarsa,ajikinta take jin kallon dake mata wanda yake wucewa kai tsaye yana shiga ko wace kafar sadarwa dake da rai ajikinta, sosai ta rintse idon rana kasa budewa,shi kuwa kallon fatar idon yake da wani irin burgewa saboda yadda take dan motsi tana dagawa gashin idon na wani irin kwanciya hakan ya bashi sha'awa matuka har baisan lokacin da ya kai hannunshi saman idanunta ba,ita kuma hakanne yasa ta bude idon da sauri zuruf kuwa sai acikinnasa idon. Wayarshi da ta yi kara a karo na uku ya dan kalla bayan ya zarota daga gaban suet dinshi kashe wayar ya yi duk da yaga sunan me kira domin baya son damuwa ko wace iri ce ta gitta masa a daidai wannan tsukin. Wani irin kwafa tare da cije yatsa Abban rabi yayi, Ni wannan yaron zai kashewa waya", lallai Wazer kullum idanunka kara tsauri suke lallai ya kamata nasan abin yi tun kafin guri ya ƙure min", juyawa ya yi dan barin gurin sai dai kuma cak ya maida numfashinsa ya tsayar saboda ganin mutum bayanshi ba tare da ya yi zato ba. Dai-dai lokacinne kuma Hajjaju rabi ta danno da motarta cikin gidan,duk da cewa da yawan jama a a gidan amma bazaka taba gane hakaba saboda girman gidan da yawan dakuna da bangarori,shi yasa ko bangaren aunty amarya babu wasu mutane sai iya danginta wanda basu wuce mutum biyar ba,sai kuma Hajiya goggo da tayi kaura ta bar sashenta tazo nan ta kasa ta tsare bayan kuma yan uwanta da suma suna can bangaren nata ta barsu,shi yasa inna maimuna ta sa mata ido saboda haka nan taji bata yadda da motsin surukartasu ba. Ganin maza hakan bai sa rabi taji nauyin isa gurin ba,haka ta karasa ta zube ta yiwa su Abbie gaisuwa da su Abba yahya sannan ta kuma karasawa wajensu Baffa suma tayi musu gaisuwa daga nan ta tashi ta nufi cikin gidan tana tunanin inda WAZER yayi dan duk iya hangenta ta hanga bata ga ko kyallinshi ba,da wannan tunanin ta shiga falon da yar gajeriyar sallama,kasancewar falon yana girma dan kujerun cikinsa set uku ne sai ya yi kamar ba falo daya ba,shi yasa idan ba da karfi kayi sallama ba bakowane zaisan ka shigo ba,Hajiya goggo da inna maimuna sune suka amsa mata saboda sune a set din farko,zama ta yi cikin nuna ladabi tana gaidasu tare da yi musu gaisuwa,inna maimuna na cewa sai dai bamu shaidaki ba", sai ga aunty amarya ta ƙaraso zama ta yi itama tanawa ruby kallon rashin sani. Da sauri cikin tsananin ladabi rabi'a ta zame daga kujerar da take kai ta gaida aunty amarya saboda ta shaidata dan sun taba haduwa gidan gaisuwar Halima marigayiya,amsawa aunty amarya tayi tana dan tuna rabi ar kaɗan,cikin sunkuyar da kai rabi a ta ce", baku game Ni ba ko? Bata bari sun amsa mata ba ta ci gaba da cewa", rabi a ce matar WAZEER ",yadda ta faɗa matar WAZEER din cikin kunya sai ka dauka ko haɗa ido da surukatar bata yi,Hajiya goggo ce ta ce", ayyo sannunki da zuwa bari a kira Rahim ɗin shima Wazer ɗin ai yana ciki tare da Rahim din""" wani irin duka kirjin rabi a ya yi har wani jiri_ jiri ta fara gani,sai dai kuma ba zata iya bayyana komai ba yanzu saboda abinda take shiryawa ya tafi dai_dai,ayya to Allah ya kara hakurin rashi ta faɗa tana ƙaro murmushi kan fuskarta,Hajiya goggo na shirin tashi aunty amarya ta riga yunkurawa saboda karfin jikin ba daya ba", dole ta koma ta zauna ba dan taso ba. Inna maimuna kuwa Murmushi tayi dan kuwa taji dadin hakan da mamin RAIHAN ta yi. Ƙur rabi'a ta zubawa aunty amarya ido tana jin kamar ta yi musu duka gaba dayansu,to amma me abun duka kissafine dole sai ta nuna musu ita din ta Allah ce kafin ta aiwatar da shirinsu saboda ko da maganar ta fallasa ta kuma batar da tunaninsu akan ta koda kuwa daga baya sun gano ta san sirrin da suke boyewa. Duk da cewa sai anbi corridor dogo za a isa dakin Raihan ɗin to amma tunda kofar dakin na kallo falon na farko dole zaka iya ganin me shiga da fita, a hankali aunty amarya ta kai hannunta dan yin nocking din dakin zuciyarta kuwa kamar zata wantsalo saboda tunanin abinda yake wakana a dakin,kwankwasawa ta yi cikin taraddadi. Acan cikin dakin kuwa tunda Wazer ya kashe wayar da Abban rabi yayi masa,sai kawai ya kwantar da jikinsa kan gadon tare da RAIHAN dake jikinsa kamar jaririya,tunda suka kwanta ta samu ta cukyikyiyeshi tana shaƙar ƙamahinsa me dadi yana shigewa kofofin hancinta,a hankali ta fara lumshe ido cikin kankanin lokaci Wazer ya fara jiyo tashin numfashinta cikin nutsuwa tamkar ba me bacci ba,dan dago kanta ya yi yaga tabbas dai baccin take yi, kawai sai ya tashi ya kwantar da ita sosai yasa bargo ya rufeta ya koma kan kujerar dakin ya zauna,zamansa baifi da minti ɗaya ba aka kwankwasa dakin. Ganin aunty amarya baisa shi diriricewa ko shiga halin kunya ba ,dama Abbie ya fada masa aunty amarya yasan komai shi yasa baiji wani damuwa dan yagantaba,ita aunty amaryar ce ta kasa kallonsa kai tsaye kamar yadda take yi a baya,cikin nutsuwa ya gaidata yana kaucewa daga hanya, a'a ina Rahim din", ta faɗa tana dan leka dakin ba tare da ta shiga ba, cikin kamewarsa dake nuna biyayyarsa cikin lafazinsa ga manya ya ce", ta yi bacci", aunty amarya ta ce", to aiko a tasheta matarka ce tazo mata gaisuwa", luuu yayi da idanunsa kamar zai lumshesu sai kuma ya budesu fes akan hanyar falon,kafin cikin dakewarsa ya kuma cewa sorry Mami ki barta ta samu bacci zata iya tashi da headeach yanzu aka tasheta,aunty amarya da abin da wazir din ya yi yaso burgeta da kuma dan sata jin kunya ta fita daga dakin tana cewa shike nan kai sai ka fito kasan abinda zaka ce mata nikam ina jin kunya", wani sassanyan Murmushi ne ya subce masa wanda ba kowa ne zai lura da hakan ba,komawa ya yi dakin ya kuma gyara Raihan ɗin yana jin kamar ya zauna yayi ta gadinta har ta yi baccinta ta tashi ,zubawa ɗan ƙaramin bakinta idonu ya yi sai kuma yaji ya kasa jurewa tamkar wanda ake ja haka yaji ya kai bakinshi samannata da niyar sumba ɗaya ya fice,sai kuma ya bige da lasar lips din kamar alewar da baya son karewarta,ɗumin harshensa da ya sanar da ita bakuncin bakinshi yasa ta bude ido a hankali idanunsu ne suka sarke,da sauri ya zaro idonsa na mamakin ya akayi ya tasheta,dan langabar da kai yayi alamun hakuri,amma abin mamakin yaki dagata dan yanzun gaba daya nauyi shi ya sauke akanta,marairaice fuska ta yi idanunta sukayi narai narai kamar zata yi kuka se alokacin ya Ankara, maimakon ya tashi sai kawai ya mirgina da ita ya koma kasa ita kuma tana samanshi,ƙaramin bakinta ta tura kafin cikin alamun baccin da bai gama sakinta ba ta ce", Hamma WAZEER bacci nake ji", wani irin yamma yaji har tsigar jikinsa na tashi lumshe idanunsa ya yi tare da kuma sarketa cikin jikinshi tamkar zai hadiyeta,bai ce komai ba saboda baya jin zai iya cewar dakyar yake iya control din kanshi in dai yana tare da RAIHAN tun can baya ma bare yanzu da ya gane me yake ji ya kuma fahimci nisan da yayi cikin azabar so,so da yawa yakan yiwa kansa tambaya wai dama haka so yake idan ka samu abinda zuciyarka ke so? RAIHAN ko sunanta na musamman ne a gareshi wani irin zuzzurfanso ne wanda bai taba jin irinsa ba a wannan zamanin namu. Hamma WAZEER ta kuma fada ganin yadda ya zuba mata ido ko kiftawa ba yayi,tashi ta fara kokarin yi saboda tasan idan ya fara wannan kallonnasa zai iya daukan awowi a haka ba tare da ya gajiya ba,bai bata damar hakan ba sai janyota da ya yi ya maida ta gefe ya ja duvet ya kuma rufeta sannan ya tashi ya subaci idanunta wanda take ta ji baccin da take ya kuma dawowa hakan yasa tunda ta lumshe ido bata kuma budewa ba har ya fita daga dakin ya rufo mata. Tun bayan fitowar aunty amarya suke dakon bullowarsa sai dai shiru,sai da aka cinye mintina ashirin kafin su Ganshi ya fito cikin takunshinanna, idon rabi a kanshi tana jin zuciyarta na babbaka da wuta tana ci ,ji take kamar ta kashe su shida Raihan ɗin ,shin me suke yi a daki shida RAIHAN ɗin? Yadda tale kallon idanunshi kai tsaye yasa ta fahimci wani irin so me zafi wanda shi kansa Wazer ɗin ba zai iya ƙididdigeshi ba,wani irin tashin hankali ta kuma shiga ji take kamar ta yi hauka anya kuwa zata iya raba WAZER da RAIHAN? Ai ko ba zan iya ba sai na gwada idan hakan ya gagara na kashe kowa kowa ya huta,ta faɗa hakan cikin ranta tamkar tayi aman zuciyarta. Aunty amarya kuwa da tun fotowarta tace gasu nan bata kuma cewa komai ba,mikewa ta yi ta bar gurin saboda kumyar Wazer ɗin da taji ta lullubeta,dan kallon rabi a ya yi Sannan ya dauke kansa yana ci gaba tafiya dan fita daga falon ya ce ", Rahim tun ɗazu ya yi bacci baya bukatar hayaniya yanzu", daga haka ya zura dogayen kafafunshi waje bayan ya bude kofar ta zallar zaiba ya ciewarsa ba tare da ya damu da abinda yace din ba. Dakyar rabi a ta hadiye abinda yake taso mata sannan ta dubi inna maimuna da goggo ta ce", shike nan Ni zan wuce idan ya tashi a yi masa gaisuwa", inna maimuna ta yi saurin cewa bari a rakaki can wajen mahaifiyar me rasuwar ki mata gaisuwa", itama rabi'a cikin dakiya ta ce", ai can na fara zuwa Allah kara hakuri", daga haka ta fice daga falon kamar zata kifa dan ji take idan ta kara minti ɗaya komai zai iya faruwa,yadda ta ja motar ma a sukwane da ace da yawan jama a a gurin sai ta jawo hankalinsu. Suryy da taga fitowarta ita da oganta tuni ya yi mata alama da tabi bayanta ,aiko cikin sauri ta ja motar da ya sai mata ta bi bayan rabi a,binsu da kallo ya yi yana wata banzar dariya kafin ya dawo da kallonsa kan gidan ji yake tamkar ya shiga cikin gidan ya shake Raihan,sai dai kuma bashi da wannan ikon saboda a komai na dukiyar Raihan ana bukatar saka hannunta shi yasa yake bin komai a hankali mataki kan mataki duk dan ya samu burinshi ya cika ya je can ya bude rayuwa sabuwa. Acan falo kuma Hajiya goggo ta dubi inna maimuna ta ce", amma naga yarinyar nan kamar bata ji dadin abinda akayi mata ba,hmm inna maimuna ta ce", to ai mijinta ne ya yi mata dan haka ita su,daga haka itama ta koma wajen su hajiyar agadex dan ta tabbatar dai yanzu Rahim ya samu tsaro. A can bangaren Abban rabi kuwa zubawa juna ido su kayi shida Abba yahya da ya zago wajen dan amsa waya,zuciyarshi kuwa har wani dinlin_dinlin take fatanshi dai ace Yahya bai ji abinda yake fada ba,to fatan nashi ya karbu dan kuwa Abba yahya nuna masa ta yi baiji ko mai ba,se ma ce masa da ya yi kai ma wayar ka zago ka yi? Ey ey cikin dan in ina ya fada alamun rashin gaskiya duk sun bayyana a tare da shi, murmushi Abba yahya ya yi sannan ya ce", ai kasan idan ana hayaniya ko yaya take waya bata yiwuwa dan ma Allah yasa daga yau an gama zama sai kuma bakwai shima addu'a za ayi a masallaci Allah dai ya jikansa da Rahma mu kuma ya kyauta namu karshen", da sauri ABBAn rabi ya kama da Amin ya Allah Amin ya Allah,cikin sauri ya bar gurin jikinshi har rawa yake yi,da kallon mamaki Abba yahya ya bishi yana jinjina halin dan Adam wato dai shi mutum duk inda ka ganshi kalleshi kawai sanin zuciyar mutum sai Allah, Allah dai ya raba mu da sharrin zuciya ka tsare imaninmu da hangenmu,daga haka bar wajen dan ya ma manta amsa waya yazo yi wajen.......... ______________ *HAIDAR* A hankali yake bude idanunsa da suka kumbura su kayi wani irin taruwar jini bakin shi kuwa ko buɗuwa ba yayi saboda tsananin kumburin da yayi jikinshi kuwa gaba daya shatin bulalane da kwantaccen jini,kai duk wanda yasan haidar ringim idan ya Ganshi a yanzu da wuya ya ganeshi,duk da ya bude idon ma dai duhun yake gani don yasa ba da duhun saboda tun ranar da aka kawoshi gurin bai ga kowa ba sai dai duka da yake ji ta ko ina da naunshi baya jin Muryar kowa abinci kuwa a duhu ake tsayawa a bashi shima dan kar ya mutu ne saboda ba mutuwar tasa ake bukata a yanzu ba........✍🏽✍🏽 More comments and share 🙏 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page44 ```Pg44 Allah ne yasan manufarsa da baisa rabi a tayi hatsari ta samu mummunan ranuni ko rasa ranta ba,saboda irin tukuin da tayi ya kawota gida,ko Surry dake bin bayanta cike take da fargaba gani take kafin su karasa me afkuwa ta afku,sai dai cikin hukuncin Allah tazo gidan ba tare da ko bugawa wani mota ta yi ba.shigowa gidan ma baisata ta nutsu ba haka nan ta ake motar a waskace ta fice ba tare da ta dau ko wayarta ba,shukra dake kokarin shiga bangaren kakarsu ta tsaya tana dubanta cike da mamaki,sai dai ganin yadda rabin tayi kamar bata ganta ba yasa ta tabe baki ta yi shigewarta. Surry kuwa tana can tun gate din farko securitys sun hanata shigowa da mota,barinnata ma da su kayi dan sun santa tare da rabinne,aiko kafin ta shigo ko ƙurar rabi bata gani ba,hakan yasa tayi azamar Binta can sashenta. Shukra tana kaiwa innawuro sakonta, to koma bangarensu ,tana shiga ta samu Ammi a kiching kamar yadda ta barta,dubanta Ammin ta yi tana ci gaba da kwaba fulawar da zata yi fankaso,ta ce",yana ga har kin dawo nasan dai ba dawowa kikayi dan tayani ba?dan tura baki shukra da bata wuce sa ar RAIHAN ba ta yi, Sannan ta ce",wlh Amma gaba daya banji dadin wannan auren na yaya da aunty rabi a ba,saboda bata da hali kinsan boye halayyarta take yi a nan amma wlh sam bata da kamun kai",ba shiri Ammi ta bar abinda take yi ta juya tana kallon shukra cike da tuhuma kafin ta ce",shurka ina kika samo wannan halin? Meye ruwanki da abinda me shafeki ba,bana son irin wannan wannan abinda kika yi babu kyau tunda ba taba gani kika yi ba",wlh Amm......kallon da Ammin ta yi mata ne yasa ta maida bakinta ta rufe tare da hadiye yawunta sum_sum ta fice daga kiching din amma dai bata ji dadin yadda ammin ta ki fahimtarta ba. *HAIDAR* Ci gaba ya yi da kallon gurin ko da dai baya ganin komai sai tsananin duhu,wajen sakon ashirin da farkawarsa yaji alamun shigowa shifa ko inda kofar take ba a bashi damar sani ba,bai san ta inda aka shigo dashi ba bare ta inda zai fita,alamun aje kujera da zama duk alokaci daya yaji daf dashi har hakan yasa shi shaƙar ƙamshin dake tare da mutumin. Saukar murya kawai yaji cikin isa da takama yana cewa,mu zo lokacin da zaka iya magana a tunanina wahalar da kasha ba zata bari kayi min haddama ba,ina ainahin Flash din da kake da shi akan duk binciken da kuka yi kaida tree full y trues, sannan kuma ina so ka gaya min waye tree full y trues wannan kawai zaka yi min na Barka ka fita da ranka", Wani irin Murmushi dake fita dakyar HAIDAR ya yi kafin ya tofar da miyan bakinsa da yasan jinine,a hankali ya bude bakinsa bai kula da zugin da fuskarsa da duk wani abu dake fuskar ke masa ba ya ce",au dama kaine kasa a ka kwamusoni?to bari kaji na gaya maka duk abinda zaka yi min bazan taba baka Flash din nan ko gaya maka inda yake ba,sannan a bakina bazaka ji ko wanene tree full y trues ba,da kake maganar kasheni to ai na san cewa ko da na fada maka ba zaka kyale Ni ba domin ba dabiar ka ce wannan ba,nama bai taba shiga hannunka ba tare da ka cinye shi ba...bai gama kai aya ba yaji wani irin barin makauniya wanda har sai da jini yayi tsartuwa daga hanci da bakinsa,duk da haka bai yi shiru ba cikin jan numfashin wahala ya ce",idan kana da iko kaje tsafinka da tsohuwar mashrikarku ta bayyana maka abinda baka sani ba,"wani irin naushi aka kuma kai masa ta gefen cikinsa wanda har sai da ya saki ƙarar azaba, mutumin bai ce ko mai ba har sai da ya kai hanyar fita daga akurkin dakin sannan ya ce",tabbas ka fadi gaskiya babu wanda ya taba shigowa gonata ya fita da ransa dan haka kaima ba zaka fita ba sai dai gawarka amma ina tabbatar maka da cewa sai ka fadi duk abinda nake son ji daga gare ka Sannan kayi wulakantacciyar mutuwa,ƙarya kake kaine za ka yi wulakantacciyar mutuwa mugu tsohon mushriki mayaudari azzalumi ko ban fada ba karshenka ba zaiyi kyau ba,haidar ya fada yana fitar da maganganun dakyar cikin azaba, well-done jarumi shima daya jaruminnaka yana nan tafe dan nasan mace bazata zama ita ce tree full y trues ba",kafin ka bankadosu su zasu fara bankadoka", cak mutumin ya tsaya daga shirin fita da yake yi,dariya ya yi tare da cewa kaga tun kafin ake ko ina ka fara bani satar amsa ashe ma ba mutum daya ba ne? Ba mutum daya ba ne amma ka sani cewa duk cikinsu babu wanda zaka iya kamawa su din kamasu ba abune me sauki ba", da alamu dai maganganun haidar sun soki mutumin dan bai kuma cewa komai ba ya fice daga duhuwar dakin. ______________ Surry na shiga ta yi saurin fitowa da guzurin kayan mayen da ta tahowa ruby su,mika mata kawai ta yi, da sauri ruby ta karba ta bude ta afa , dan yanzu abun ya fara shiga kanta ta fara jin dadin sabuwar halayyarta,lumshe idanunta ta fara yi dan har yanzu ba su yi mata shigar da zasu kasa sara maye ba,da sauri ruby ta taimaka mata ta shigar da ita daki Sannan ta juyo ta fita ta rufi mata gidan,fuskarta dauke da murmushin nasarar da take tunkarota. ABBAN rabi dai bai samu yadda yake so na sanin lokacin dawowar su Khalil ba dole ya hakura dan kar ya sawa zuciyar dan uwanshi zargin wani abu,sai dai ya koma ta bangaren securitys din da ya kawowa Wazer dan ya bincika masa ya kuma sa masa ido akan duk wata waya da WAZER ɗin zai yi daga yau din nan. Har yanzu mama murja ta kasa sakewa gani take kamar za a kuma cewa wani daga cikin yaranta ya mutu shi yasa take a firgice goggonta ce da yayarta lantana suke tare da ita. Itama dai momy Hanne ba ta cikin nutsuwa kullum cikin taraddadi take da tsananin fargaba da tsoron halin da zata tsinci kanta a ciki take. Sosai inna maimuna ta ji zuciyarta ta kasa yardar mata da Hajiya goggo,to amma idan bata yarda da ita ba me take nufi da hakan tabbas akwai sittin da ake boyewa a cikin gidan dan ta ga gaba daya jama'ar gidan basu da nutsuwa. Wazer tunda ya fita office ya wuce Ya gabatar da wasu muhimman aiyuka cikin awa daya ya fice ya nufi gidansa da yake kai Raihan,yana zuwa kofar gidan ya samu securitynsa a wajen,cikin boye mamakinsa ya dube shi kafin a hankali ya bude baki ya ce", lafiya dai? Sosa kansa ya shiga yi cikin dan daburcewa ya ce", oga ya ce", mu daina bari kana yawo kai ɗaya saboda akwai risk a cikin hakan", ɗan zuba mishi ido Wazer ya yi sannan ya gyada kanshi cikin yanayinshi na basarwa ya ce", ok zaku hana min mutuwa ko kuma faruwar abinda yaso zai faru dani ko? Wani iri secuerityn ya yi duk sai ya daburce kana kallonsa zaka sancewa akwai rashin gaskiya tare da shi,murmushin gefan baki Wazer ya yi kafin ya dan motsa motar kamar zai wuce sai kuma ya tsaya ba tare da ya dubeshi ba ya ce", na baka hutun sati guda saboda ina son privency bana son damuwa", daga haka ya wuce cikin gidan,sakalo secuerityn ya yi duk sai ya ji tsoran Wazer ɗin ya karu a ransa, shi kan dama sai da ya ce, ba zai iya wannan aikin ba dan babu wanda baisan halin Wazer ba yasan duk ranar da ya sameshi da rashin gaskiya sai ya gayawa yan garinsu. Yana shiga dakinsa ya wuce, kai tsaye ya fada toilet ya sakarwa kansa shaya sai da ruwa ya zuba ajikinsa na kusan mintina goma kafin ya yi wanka ya tsaftace ko mai nashi ya fito yana jin jikinshi na sakewa,zama ya yi yana dan furzar da iskar bakinshi yana ɗan taune lips dinsa duk a lokaci guda saboda yadda yake ji RAIHAN na yawo a cikin jininshi,tamkar wani mace haka ya shirya kansa kafin ya dan hada copy yasha,bai nemi cin komai ba ya kwanta ya shige bargonsa da yake ta ƙamshin RAIHAN,janyo wayarshi ya yi ya buga video call saboda yadda yake jin bukatar ganinta na hawansa kamar wani karamin yaro dake neman uwarshi dan ta ciyar dashi. A dai dai lokacin RAIHAN ɗin ta kwanta bayan gama shirinta na bacci ta kashe fitila ke nan wayarta ta hau karkarwar. A dai-dai lokacinnan da kowa ke kokarin kwantar da hakarkarinsa dan ya huta su kuma lokacinne kasuwancinsu ya bude,lissafi suke akan haidar da kuma babban kamunsu na gaba wanda suke fata daga kanshi ko mai ya kawo karshe zasu bude sabuwar rayuwar jindadi. A hankali ta daga wayar tare da kaiwa kunne, kafin cikin kasalar dake tare da ita ta yi sallama cikin sanyin muryarta da ta kuma kashe masa jiki,lumshe idanunsa ya yi kafin ya ce", reihann baki bacci ba? Wani irin abu taji har zuwa tafin ƙafafunta har wani runtse ido ta yi tare da ƙamkame jikinta,tabbas sunan da ya kirata da shi da yadda ya fadi din ba karamin tasiri ya yi a tare da ita ba,ki kwanta ki bacci kiyi addu'a kinji", ya fada cikin wani murya kamar me rada ,jinjina kai kawai ta yi tare da zame wayar daga kunnenta tana jin wani sanyi na ratsata wanda bata ji shi ba sai yanzu,yadda jikinta ya yi yasa ta kamar ciwo gabobinta suke ,sauka ta yi daga gadon tare da ficewa daga dakin ,yanzu sam bata da matsalar yawo a bangarensu baranma a wannan lokacin da tasan cewa iya su kadaine a cikin gidan,dakin hajiyar agadex ta nufa dan ta karbo man zafi tunda tasan itama tana amfani da shi. Har ta zata Murda kofar dakin ta ji kamar motsi a kiching har zata share sai kuma taji kamar magana ake ƙasa_ƙasa hakan yasa ta fasa shiga dakin hajiyar agadex ɗin ta dumfari hanyar shiga kiching ɗin. Ruby kuwa yau bata yi dogon bacci ba, cikin dare ta farka ta haɗa sallolin da ake binta ta yi su cikin hanzarin da rashin nutsuwa, tana idarwa ta janyo wayarta ta danna kiran Surry,kamar jira take kira daya ta daga tare da cewa ya dai kawata kin wartsake? Na wartsake daga bacci amma zuciyata bata da ranar wartsakewa sai ranar da na tabbatar da cewa na gama da Raihan na kassara rayuwarta shike nan sai na samu nutsuwa ", Surry ta yi dariya kafin ta ce", hakan zata faru kawata ke dai ki ci gaba da yin abinda ya kamata kuma ki tabbatar kinyi komai cikin nutsuwa yadda ba za mu samu wata matsala ba",suryy ba zan iya bari na kai sati Daya ban watsa rayuwar Rahim ba wallahi bazan iya ba goben nan zan watsa labarai da jaridu na fallasa rayuwarta tare da ƙagen da har abada ba zata taba mantawa ba duniya ma ba zata manta ba,shi yasa ma na kira ki saboda kar kice ban sanar dake ba", ajiyar zuciya Surry ta yi tana jin zuciyarta na yadda da hakan itama Gara ayi komai a wuce gurin,dan haka kawai ta ce", shike nan ruby amma ina kara jaddada miki akan kiyi taka tsantsan kar ki bari a gano ki idan ki bar hanyar da Wazer zaisan cewa ke kika yi abinnan to fa biyu babu zaki dan wallahi sai ya rabu dake tare da horan da baki taba zato ko tsammani ba", na sani suryy jiya na ga hakan na tabbatar da cewa Wazer zai iya yin komai akan Raihan na ga wani irin so me zafi wanda ban taba gani ba ban kuma taba ji ba,dan nasan shi kansa baisan irin son da yake mata ba,shi yasa naji ba zan iya hakuri ba suryy",shike nan ruby kinyi dai-dai ina miki fatan nasara,daga haka suka yanke wayar. _____________ A hankali ta kai kunnen ta jikin kofar dai-dai kafar key wanda shine zai bata damar jin abinda ake yi a kiching din. Wani irin duka ƙirjinta ya yi lokacin da ta ji Muryar Hajiyar agadex tana cewa,ba zan bari haka ta faru ba dole nayi wani abu,to me zaki yi ta ji muryar kakanta baban agadex wanda a tunaninta ya tafi yau din bayan share sadakar uku duk da cewa a ranar yazo ba kwana ya yi ba,cikin kuka hajiyar agadex ta ce", wallahi bazan bari a cutar min da yarinya ba zan fasa kwai na gaji da boyewa ,tabbas idan aka taba Raihan ramla zuciyarta bugawa zata yi, nasan kuma tunda aka fara daukar yaran nan to tabbas Raihan ita ce ta gaba",haba me kike yi haka meye tabbacinki kar da ki manta ba komai aljanunnaki suke fada miki dai-dai ba dan suma ba komai suka sani ba", wani kallo ta watsa masa tamkar ba ita ba sannan ta ce",tun da haka ka ce shike nan amma ina tabbatar maka da cewa idan wani abu ya samu RAIHAN ko lamra bazan taba yarda ba dan wallahi har kai ba zan bari ba,bata saurari cewar shi ba yana kiranta ta yi hanyar barin kiching din,dan haka RAIHAN ta yi saurin labewa kasan dininng, bata dago ba sai da ta ji shigar Hajiyar agadex daki sai kuma baba buzu da ya fita ta can hanyar kofar kiching wadda zata bulla da shi manyan dakunan bakin da suke sauka a ciki idan sun zo. A hankali ta fito tana goge zufar da ta jiƙa mata jiki numfashi take maidawa tamkar wadda ta yi gudun awa Biyar,to wai me ke faruwa a gidan haka,dama hamma rufa'i kashe shi akai? To waye ya kashe shi? Me yasa kuma ya kashe shi? Kai ko dai saboda ita ne tunda taji hajiyar agadex na cewa bata son akashe ta,shin wa ye zai bata amsoshin tambayarta? Anya kuwa ba zata tun kari Hajiyar agadex ta nuna mata cewa taji tattaunawar da su kayi ba? Dafe kanta ta yi saboda juyawar da ta ji yana yi kamar zai cire innalillahi kawai ta shiga ambata akan harshenta domin shine kawai zaisa taji sauƙin abinda take ji........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page45 ``` Da bin bango ta lalubi hanyar dakinta ta faɗa,tunda ta kwantar da jikinta saman gadon take fidda wani wahalallan numfashi,rufe idanunta ta yi tana son bacci yazo ta karfi amma hakan ya gagara,jin komai ya tsaya mata yasa ta kuma tashi tana layi ta shige toilet, kyakkyawar alwala ta daura sannan ta dawo dakin ta saka dogon hijab ta shimfida sallaya daga nan ta tada kabbara domin mikawa sarki zuljalalu kukanta,sam shi yasa RAIHAN damuwa bata cika zauna mata ba saboda da taji irin wannan mummunan tashin hankalin take saurin ƙara kusanta kanta ga Allah da izininsa kuma cikin ikonsa sai kaga ta koma kamar ba ita ba,yarinya ce da ta yadda Allah daya ne kuma shi zai magance mata dukkan wata matsala da take ciki. Ba ita ta dakata daga kai kukanta ga Allah ba har sai da ta ji am fara kiran sallah,dan haka ta dakata ta yi addu'a da lazumi,tana zaune a ka tada sallah ,tashi ta yi tayi raka atanal fijr Sannan ta kawo farilla cikin nutsuwa da kushu'i. Sai alokacin ta ji wani irin bacci me dadi yana dibarta,dan haka kawai tashi tayi ta cire hijab ta haye gadonta ta kwanta cikin salamar zuciya da ta gangar jiki. Wayewar garin yazowa mutane da yawa ta hanyoyi dabandaban ,wasu farin ciki suke zasu gudanar da ayyukan alkhairi wasu mutuwa akayi musu wasu aure zasu yi wasu wani burinne zasu cika shi ,kamar dai yadda ta kasance a wannan familys kowa da yake da buri kyakkyawa ko akasin haka ya tashi da burin cika shi. Tun daren jiya kallonsa kawai take tana saka abubuwa da yawa ,yadda taga ya tashi yana ta saurin shiryawa ya fice yasa ta kasa rike abinda ke ranta,cikin damuwa inna maimuna tace",wai Ni ko ABBAN Bashir meke dakuna ne? Na kula da kai tun jiya baka cikin nutsuwa da alama akwai damuwa a tare da kai",ba tare da ya karbi shayin da ta haɗa masa ba ya ƙarasa daura agogonsa sannan ya dubeta fuskarshi cakude duk sai ya wani sauya kamar ba shi ba,ya ce",maimuna ina cikin damuwa sosai kuma akan his excellency ne da yadda yake son kashe nurr a yau ko ta halin kaka, innalillahi wainna'ilaihi raji'un inna maimuna ta faɗa cikin tashin hankali tana faman zare ido,to yanzu me ye abinyi ? Ta faɗa muryarta kamar zata yi kuka,shine yasa nake ta sauri kada wani abu ya faru saboda na tabbata zai kira Muhammad nuur ɗin", kafin inna maimuna ta yi magana tuni har ya fice daga falon. Tun adaren jiya Abbie ya samu kira daga his excellency shi yasa da sasafen ya shirya ya fice. Sai bayan fitarsa hajiyar agadex ta tashi saboda bacci da ya dauke ta bayan sallar asuba,tana fitowa abinda ta fara tambayar mami shine ina Muhammad yake", cike da mamaki aunty amarya ta kalleta harma ta kasa boye mamakinta,ta ce", Hajiya lafiya? Baki bani amsa ba kina maida min da tambaya", hajiyar agadex ta faɗa ranta a hade,jinjina kai aunty amarya ta yi tana tunanin abinda ke damun hajiyarsu a kwanakinnan saboda dai ita a iya saninta akwai kunya tsakanin hajiyar agadex da Abbie din to amma yanzu abinda take yi ya fara damun aunty amarya dan tasan tunda ta ga haka to da kwai wani abu a ƁOYE. Ba zaki fada min inda ya je ba? Ta tambayi aunty amarya wadda tayi nisa a tunaninta,firgit aunty amarya ta yi sannan ta ce",tun ɗazu ya fita dan ko bakwai ba tayi ba lokacin da ya fita his excellency ne ya kira shi ina ga dai akwai abu me muhimmanci da ya taso", shiru hajiyar agadex tayi kafin ta jinjina kai ba tare da ta ce komai ba ta juya ta bar aunty amarya tsaye, Raihan ma dake tsaye jikin kofarta tana hango su kuma tana jin abinda suke fada,ta juya ta shiga dakinta,bata jin zaman gidan aiki zata fita kawai tunda anyi uku idan ba haka ba zaman zai iya haifar mata da damuwa,shiryawa ta yi tsaf cikin shigarta ta basaja kai idan ka kalleta sai ka dauka namiji ne ,amma tabbas yanayinta na mace da salo na mace da yake jikinta sai wasu su dinga kallonta kamar dan daudu ,saboda da yawa a hakan ake kallonta a bayan idonta ana yin zundenta da hakan,ba ta yiwa hajiyar agadex sallama ba ta yi ficewarta aunty amarya ma a tsaitsaye ta yi mata sallama ta fice ,yau dai sabuwar motarta ta shiga ta tafi office,jikinta da zuciyarta duk babu dad'i hakanan take jin faduwar gaba da fargaba lokaci_ lokaci sai dai bakinta dake dauke da ambatan Allah yasa abin yayi mata sauki sosai cikin wannan yanayin ta isa office. Shi kam Wazer bai yi tunanin Raihan zata iya fita ba yau,shi yasa bai tashi da niyar zuwa office ba,zama yayi a gidan zuwa lokacin da jirginsu Khalil zai sauka sai yaje ya dauko su da kansa. Ruby kuwa bata san bai kwana gidan ba,ita ma din da wuri ta shirya ta fice zuciyarta fal farin ciki gani take kamar komai ya faru ya kare,har hango RAIHAN cikin tashin hankali take yi,idan ta tuna hakan har wani makirin murmushi ne ke subce mata,da wannan dokin ta isa office. Gidan gwamnati......... Duk sammakon da ya tafka haka yazo ya sami his excellency a falonsa na ganin baƙinsa masu muhimmanci,cikin mamakin kiran Abbie ya ce", ka tayar min da hankali meke faruwa ne haka? Murmushi his excellency ya yi sannan ya ce", to ka zauna mana idan yaso sai kaji ko ma meye", zama Abbie ya yi yana kallonsa zuciyarsa cike da tunani da damuwa, Shiru falon ya dauka na tsawon mintina biyu kafin his excellency ya yunkura da kansa ya isa prige dake can kusurwar falon ta hannun hagu budewa ya yi , maimakon ya dauko lemon da yayi niyar dauka sai kawai ya tsaya yana kallon prige din tamkar wanda ke ƙirga yawan lemon dake ciki, Abbie dake kallonshi daga inda yake zaune ya kuma cika da mamakin al'amarin his excellency ɗin,kafin ya ce", wani abu his excellency ya dauko lemon kwali daya da ruwan kwalba ya nufoshi fuskarsa a sake,sai hakan ya kara saka Abbie cikin zargi da damuwa,yana zuwa ya mikawa Abbie lemon tare da cup din da ya dauko, Abbie bai ce komai ba ya karba ya aje ba tare da ya zuba ba,ɗan numfasawa his excellency ya yi sannan cikin raunin murya ya ce", abokina ka yafe min abinda zan iya cewa da kai ke nan saboda a halin yanzu baka da wani lokacin sauraren wani abu ko jin wani bayani dole ne na aikata abinda nake ganin shine zai fiddani daga ruɗani da kokonto,ka dauka cewa duk mutumin da ya mutu to wa'adinsane ya cika,,,,,karaf wannan kalma ta shige kunnen Abba yahya dake ta baya jikin window din falon,ɗan rintse idonsa ya yi cike da tashin hankali da fargaba,gashi ba damar shiga falon saboda an rufeta ta ciki,zufa ce ke kwararo masa ta ko ina. Abbie kuwa samun kansa ya yi da kasa cewa komai sai bin his excellency da kallo yake cike da son jin karin bayani dan shi sam baya gane Yaren da yake masa magana dashi,muje mu yi karin kumallo his excellency ya fada yana mikewa tsaye.girgiza kai Abbie ya yi kafin ya samu ya iya daga harshensa dakyar ya ce",bana jin zan iya kai komai bakina idan banji dalilin wadannan maganganun da manufarsu ba", nan da nan his excellency ya haɗe ransa tamkar hadarin gabas ya ce", Nura dole ne kayi karin kumallon nan idan ba haka ba duk abinda ya biyo baya kar kayi kuka dani," cike da mamaki Abbie ya ke kallonsa harma baisan lokacin da ya tashi ya bishi zuwa dininng dinba, gaba daya sai yake ganin kamar mafarki yake saboda yadda abubuwa suke neman cakude masa a lokaci guda,da kansa his excellency ya zuba masa duk abinda yasan zai bukaci cinsa kafin ya ce",Bismillah ", a hankali Abbie ya dauki cup din shayin da his excellency ya haɗa masa ya kai bakinsa yana jin wani irin bugun zuciya tamkar zuciyar zata fito waje. Runtse ido Abba Yahya ya yi yana jin tamkar numfashinsa zaibar jikinsa ,cikin rawar baki ya fara kiran sunan nuran a jere har sau uku tamkar dai nuran zai ji shi,sai dai ina tuni Nura ya kai shayin bakinsa. Ruby na zuwa kai tsaye ta wuce sashen buga jaridu,babu wanda ya hanata shiga saboda ansan wacece ita duk da sun san ba bangarenta ba ne,tana yi tana share gumi ganin kamar zata samu matsala saboda rashin kwarewa yasa ta yi amfani da Google nan da nan kuwa ta samu abinda take so cikin kankanin lokaci ta yi rubutu akan wacece RAIHAN ta sigar jan hankali,ta yi rubutun ne a matsayin labari kamar yadda aunty amarya ta sanar da wazer daga karshe ta ce ", na nemi na fallasa sirrinnanne saboda makala min ita da aka yi matsayin mata alhalin bana sonta ina da wadda nake so harma anyi mana baiko. Tana gamawa ta fita bayan ta yi copy kusan dubu,sai da ta tabbatar babu kowa ta bangarenta sannan ta kira Surry ta ce",tazo ta kammala. Cikin mintinan da basu wuce ashirin ba Surry ta ƙaraso da ƙatuwar bakko suka ɗure jaridar suka fita da ita ba tare da tsoro ko tunanin komai ba. Karfe biyu WAZER ya gama shirinsa tsaf ya fito cikin kamalarshi, ya shiga sabuwar motar da yasa aka kawo masa ita a jiyan,kaitsaye filin saukar jiragen sama na Yola ya nufa dan dauko kannensa da babu wanda yasan ranar zasu dawo bayanshi,wanda shi ya san dalilinsa na yin hakan. RAIHAN kuwa ji ta yi gaba daya bata jin dadin zuciyarta,haka kawai take jin faduwar gaba,hakan yasa ta nufi office din WAZER, tana kokarin shiga kamar yadda ta saba sactariya ta dakatar da ita tana mata wani kallon kin shiga uku,sannan ta ce", oga yana ciki ya ce", kuma baya bukatar ganin kowa expicialy ma kai Rahim ya ce", kar na Barka ka shiga , a wannan lokacin matarsa ruby kadai yake da bukatar gani dan halin yanzu ma tana ciki", wani irin miyau Raihan ta haɗiya me matukar daci kafin ta samu damar yin magana am fara kokarin bude kofar, ruby ce ta leƙo kanta babu ɗan kwali gashin kanta kuma duk a jiƙe,cikin yauƙi ta dubi sactariya ta ce", me yake faruwa ne anan? Cikin biyayya sactariya ta ce", kiyi hakuri ranki shi dade dama Rahim ne yake son shiga shine na ke fada masa sakon oga", a yatsine ta dubi Raihan sannan ta ce", Rahim sorry ka je sai zuwa anjima yanzu miji yana ganawa da matarsa ne so dan haka yana bukatar privency", daga haka ta juya ta rufo kofar da karfi. Yadda kofar ta yi ƙara haka zuciyar RAIHAN ta yi ƙara har da ƙoƙarin tarwatsewa, idanunta har wani dishi dishi suke saboda tsananin tashin hankali da ɓacin rai,a duniya babu wanda zai wulakantata taji tashin hankali me tsanani kamar wazer,a hankali ta juya ta fara tafiya tamkar zata kifa saboda yadda jiri ke dibarta,a haka ta samu ta sauka motarta kawai ta nufa ta shiga,sai da taja sama da mintina goma kafin ta ja motar a hankali ta fice daga buldin ɗin. Surry da ruby da komai ya faru akan idonsu suka juya suka tafa da hannu biyu,kafin Surry ta ce", ruby komai fa yana tafiya dai-dai da yadda muka tsara,to amma abinda ya bani mamaki ya akai kika san wazer baya nan har kika hada baki da sactariya? Dariya ruby ta yi sannan ta ce", ai na shigo office din lokacin da naga banga motarsa ba,da har nayi tunanin ko suna tare da RAIHAN ɗin to sai kuma naga shigowarta,hakan yasa nayi saurin samun sactariya na shaka mata kudi na kuma shirya mata duk abinda nake son ta yi min", tafawa suka kuma yi tare da shekewa da dariya,cikin sauri suka bar office din dan kar oga wazer ya dawo ya samesu. Dakyar take tuƙin har Allah ya dawo da ita gida,ko key ɗin motar bata tsaya cire ba ta faɗa bangarensu, bata samu kowa a falon ba hakan yasa ta shige daki ta saka key, dan bata son cin karo da kowa a wannan yanayin da take ciki,so take ta yi kuka ko yaya amma hakan ya gagara hadiyar zuciya kawai take tana dafe kirjinta dake yi mata wani irin suya kamar ana soya fanke,wani irin zafi take ji a dukan jikinta hakan ya sa ta kuma ficewa zuwa gading dinsu. Cak ta tsaya daga inda take tana kallon bayan matar da ta juya sanye da a baya ta lullube kanta sosai bata ga fuskar matarba,abinda matar ke cewa ne yaja hankalinta. Lallai ina so kafin yau ɗin nan ta kare ku batar min da Yahya ku kaishi inda mutum bai taba zato ba ku boye shi har sai sanda na neme shi",domin tabbas idan na bari yayi nasarar kubutar da Muhammad nuur to fa babu shakka zai samu nasarar rayuwarsa dan haka Inaso ku bishi har cikin gidan gwamnatin ku batar da shi....tamkar iska haka maganganun matar suka dinga shiga kunnen RAIHAN,da sauri taga matar ta kashe wayarta ta cusa cikin jikinta kafin ta fara waige dan tabbatar da cewa babu wanda ya ganta.... A yadda take waigen yasa RAIHAN taso gane wacece", wani irin duka kirjinta ya yi saboda gane matar da ta yi waro ido ta kuma yi ta kasa ko da motsi har matar ta bace daga idanunta.........✍🏽 Tofa wa kuke tunani a cikin matan gidan? Burin rabi zai cika? Me his excellency yake kullawa? Ya zata kaya tsakanin ABBAN rabi da wazer? Kai rikita rikitar fa da yawa ku dai ku tabbata kunyi comments masu yawa domin hakan shi zai bani damar fede muku biri har wutsiya... *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page46 ``` Cikin daukewar numfashi ta janye ƙafafuwanta da su kayi mata matukar nauyi ta koma dakinta,shigewa ta yi cikin bargo jikinta na wani irin karkarwar sanyi wanda da alama dai zazzaɓi me karfi ya kamata. A hankali yake tafiya bayan ya dauko su Khalil daga filin jirgi,tun bayan gaisuwar farin cikin ganin juna da su kayi bai kara shiga cikin surutunsu ba,to dake dama sun san hali shi yasa ba su wani damu ba. Kai tsaye family house dinsu ya nufa,hon daya ya yi masu gadi suka wangale babban gate din da ya cinye rabin unguwar,shiru gidan kasancewar tsakiyar rana ce, kowa yana can ya kule a daka daga me bacci sai me kallo,hakan yasa babu wanda yaji alamun shigowarsu. Shine a gaba suna baya hakan ya hanasu yin kwarafniyar dawowa gida cikin ahlinsu,sallama su kayi suna saka kai cikin tafkeken falon kakartasu,ita kadai ce a zaune akan kujerarta tamkar ta gado,zuba musu ido ta yi bayan ta amsa sallamarsu, tabbatar dasu dinne yasa ta mikewa cikin tsananin farin ciki tana cewa Masha Allah marhabin da dawowar jikokina jabbama jabbama ta koma fada da filanci,da sauri duka su biyun suka rungume ta cike da farin cikin samunta lafiya. Kankace me gida ya rude da dawowarsu Nasir falon innawuro take ya dau haramar yan uwan junan,hatta da umma rumana ba a barta baya ba sai da ta halarto gidan duk da tsohon cikin dake jikinta,kowa yana gidan idan ka cire rabi a da Abbanta,dan hatta da wazer bai kuma fita ba yana can sashensa na bangaren innawuro,tunda ya shiga yake faman kiran wayar RAIHAN amma bata dauka ba,tun yana jinta a kunne har yaji an kasheta,cike da mamaki yake duban wayar,sai kuma yaji hankalinsa yana neman tashi, bai tsaya wani tunani ba bayan wanda yayi na zuwa gidan ya gano ko lafiya,hakanne yasa ya yi saurin yin wanka ya sanya ash din jallabiya ya feshe jikinsa da turarukan da na kasa tantancesu,no wonder mana idan ya fito ake kasa gane kalar ƙamshinsa,manyan turarukane na alfarma kusan kala goma kuma ko wanne sai ya fesa shi yasa ba ka isa tantance kamshinsa ba. Dai-dai lokacin aka fara kiran sallar la'asar,a kuma lokacinne Abban rabi ya dawo sai kawai suka rankaya gaba daya zuwa Masallaci. Gidan gwamnati.......... Tun bayan gama karin kumallonsu suka koma falon,zaune shiru su kayi his excellency bai bawa Abbie damar tafiya ba shi kuma bai nemi tafiyar ba saboda son jin abinda abokinnashi ke shiryawa,suna nan har aka kira zuhur a nan suka yi sallah, daga cikin gida kuku ya shigo ya shirya musu abinci,a nan ma Abbie yaso yin gaddamar cin abincin amma sai his excellency ya nuna masa idan fa baici ba to babu abinda zai ji daga gareshi,haka nan ya hakura ya tsakuri abincin.. Shi kuwa Abba yahya ganin zaman bana kare ba ne kawai sai ya tafi da niyar aiwatar da shirinsa na tonawa his excellency asiri tun kafin ya kashe masa ɗan uwa. Cikin tashin hankali Abbie yake kallon his excellency fuskarshi dauke da wani irin mugun mamaki,tunda yake a rayuwarsa bai taba ji ko ganin makirci da cin amana irin wanda aka yi masa ba,kafin ya samu abincewa tari ya sarƙeshi ya fara shi kuwa babu kakkautawa tun yana yi daga zaune har takai shi da faduwa kasan cafet hannunshi dafe a kan ƙirjinshi dake yi masa wata irin suya,jinin da ya fito daga bakinshi da wani farin abu yasa ya yi saurin kallon his excellency, wannan shike nuna alamun cewa gubar ta fara aiki a jikinshi,kai tsawon lokacin ma ya isa ace ta gama dagargaje kayan cikinshi tunda sau biyu yana cinta,magana yake son yi amma ina tuni ya fara kokuwa da numfashinsa dake son kufcewa daga makogaransa. Dai-dai lokacinne kuma motar yan sanda ta shigo gidan gwamnatin sakamakon kiran gaggawar da Abba yahya ya yi musu akan cewa su zo gidan gwamnatin domin an samu mutumin da ake nema ruwa a jallo. HAMMA IDRES....... Traffic ne ya tsaida shi akan hanyarsa ta dawowa gida kasancewar yau ya tashi da wuri saboda har yanzu ana zuwa musu gaisuwa shi yasa ko da suka koma bakin aiki basa kaiwa dare suke dawowa gida,me saida jarida ne yazo jikin glas din window motar yana tura masa yallabai ga sabuwar jarida me dauke da abin mamaki ka siya kaji kanun labarin na tabbata zaka ƙaru", dan tsaki Hamma Idris ya yi shi sam ba ma' bocin karanta jarida ba ne,to amma jin abinda me sayar da jaridar ya fada ya dauki hankalinshi har ya karbi jaridar tare da bashi kudinsa,a lokacinne kuma aka basu hannu, Bai kalli jaridar ba har sai da ya ƙaraso gida,fita yayi daga motar har ya manta da jaridar sai kuma ya tuna ya dawo ya dauketa. Wani irin bugu ƙirjinshi ya yi ganin hoton Rahim kaninshi a jikin shafin Farko na jaridar,cikin sauri ya shiga karanta rubutun take wani irin duhu ya mamaye ganinshi,da gudu ya ya taka zuwa sashen aunty amarya jikinshi har bari yake cikinshi kuwa juyawa yake kamar zaiyi zawo,da aunty amarya ya ci karo ta fito daga kiching. Kai Idris lafiya kuwa irin wannan gudun haka? Bai iya bata amsa ba sai mika mata jaridar da yayi yana mata nuni da ta karanta. Bin rubutun kawai take da kallo tana karantashi da wani irin zafin zuciya idanunta har wani yalo yake yi saboda tsananin tashin hankali,shin ita kuwa me ta yiwa wazer da ta cancanci wannan tozarcin a wajenshi? Babu abinda ya fi bata mamaki ma sai rubutun da ya yi da cewa ta yi haka ne saboda ta samu gado me yawa shi yasa ta boye halittar RAIHAN ta mace ta maidata namiji saboda kishiyoyinta duka maza garesu. Jagwab haka ta zube a kan kujerar da ta fi kusanci da ita ,wani irin numfashi kawai take fitarwa tamkar wadda ake shirin zare ranta,ita wazer zaiciwa amana,to meye ribarsa na yin hakan",ko dai shima yana da wata boyayyar manufa akansu ne? Mamin Rahim dan Allah ki yi min bayani ki fitar dani daga cikin duhu wallahi duk na rude da wannan labarin ,shin ma wai taya hakan zata faru ? Kuma da gaske ne Rahim Macece kika boyeta ? Idan haka ne taya kika iya yin hakan? Kuma saboda me? Ni dai iya sanina Abbie yana matukar son samun ɗiya mace shi yasa nake ganin kamar da wuya ace Ansamar masa mace amma an ɓoye hakan? Idris ka rabu dani da wannan tambayar abu daya zan iya amsa maka shine ey RAHIM ba namiji ba ne macece kuma ita ce", RAIHAN dan Allah ka rabu dani daga haka",tana gama fadar hakan ta mike ta bar falon wasu hawaye Masu radadi suna gangarowa daga cikin idaniyarta. Sakalo hamma Idris ya yi yana bin hanyar da ta yi da kallo ji yake tamkar mafarki ne yake yi.sallamar wazer ita ta katse masa dogon nazarin da ya tafi,a hankali ya juya yana kallon Wazer ɗin da kwarjininsa sai ya samu kansa da kasa cewa wazer ɗin komai,bin gefansa kawai ya yi ya fice daga falon zuciyarshi cike da tunani da son jin yadda a kayi hakan ta faru,sai yanzu abubuwa da dama suke dawo masa akan ɗabiun RAIHAN da yadda take acting like male,da wannan tunanin ya nufi bangaren mahaifiyarsa mama murja. ,,,Ɗan bin bayan idiris din da kallo ya yi kafin ya ɗan sauke numfashi,ganin babu kowa a falon yasa ya nufi corridorn dakin RAIHAN,sai dai yana sa hannunsa dan bude kofar yaji Muryar aunty amarya cikin kaushi wadda ke fidda tsananin ɓacin ranta da kuma tashin hankalin abinda fallasar sirrin zai jawo musu,ta ce",,kar ka sake ka shiga inda ɗiya take ka fice ka bamu guri Bama bukatar kara ganin wannan fuskar taka a cikin rayuwarmu,dan haka ina jiran takardar sakin RAIHAN zuwa nan da gobe idan kuma ka shirya ka bani ita yanzu",fuskarshi sam bata sauya ba dan ba kowa ne yake gane manufarsa akan fuskarsa ba,cikin nuna halin ko in kula da maganganun surukartasa ya dago shu'uman idanunsa masu tasiri akan me laifi,cikin kamilalliyyar muryarsa dake nuna ladabinsa ga surukuwarsa ya ce",Mami lafiya dai ko? Wani mugun kallo aunty amarya ta wurga masa Sannan cikin kara jin zafinsa ta ce",Ni za ka tambaya Me ya faru saboda kana son yaudarata kamar yadda ka shammace Ni kayi min yanzu", bata saurari cewar sa ba ta koma falon ta dauko jaridar da hamma Idris ya kawo mata ta wurga masa ita tana cewa duba kaga duk da cewa kafi Ni sanin abinda ka rubuta, wallahi wazer ban taba tunanin za ka iya cin amanar RAIHAN ba dani kaina,"ta faɗa muryarta na fidda sautin kukan da yake cuunkushe a makoshinta ta kasa fitar dashi. A hankali ya sunkuya ya dauki jaridar yana dubawa cikin nutsuwa,sam babu wani alamun tashin hankali a kan fuskarsa amma da zaka tona zuciyarsa ka gani da mutum yasha mamakin yadda tayi wani irin baƙi saboda tsananin wutar da ta kama a cikinta,taya hakan ta faru idan bai manta ba yau sam bai je office ba,to ya akayi aka fitar da jaridar nan ba tare da saninsa ba? Ya akai aka rubuta ba tare da sa hannunsa ko na RAIHAN ba? Wai meke shirin faruwa ne? Hannu yasa ya shiga murza goshinsa da karfi wannan ita ce ka dai alamar da wanda yasan shi zai san cewa yana cikin tashin hankali da ruɗani. Murmushin takaici aunty amarya ta yi sannan ta fizge jaridar tana cewa ba ka yi zaton zan iya gani ba ko shi yasa ka aikata hakan? Ko kuma so kake ka nunawa duniya cewa cusa maka RAIHAN aka yi baka sonta? Wannan kalaman su suka yi tashin fiffike suka shiga kunnuwan RAIHAN da ta tashi dakyar ta yo hanyar fitowa,wani irin dum kirjinta ya yi,bude kofar ta yi a hankali saboda tana son sanin dawa mamin take wannan maganganun. Gidan gwamnati...... Kifawar Abbie cikin tsananin ciwo ya yi dai-dai da shigowar jami'an tsaro ko wanne da zabgegiyar bindiga fuskar nan babu alamun fara a bare a sa ran tausayawarsu,Ur under arest cewar daya daga cikin jami in wanda da alama shine babba ya fada yana dora tsinin bindigarsa saitin goshin his excellency,cikin tashin hankali Abba yahya ya nufi dan uwansa yana jinjigashi da ambatan sunansa,sai dai kuma da alama Abbie baisan yana yi ba dan a halin yanzu kokuwa yake da numfashinsa da mala' ika a Zara'ilu yake shirin zarewa,dagowa ya yi cikin wani irin fushi ya yi kan his excellency da tuni ya yi sarander shako wuyansa Abba yahya ya yi cikin wata irin shaka yana cewa mugu azzalumi babu abinda abotarka ta amfane mu dashi sai Bala i, wallahi yadda ka kashe dan uwana da sauran al ummar dake a karkashin ka kaima sai ankashe ka kisa irin ta wulakanci,ka she dansa ko bakwai ba ka bari ya yi ba ka kashe uba kai wane irin azzalumi ne mara imani tur da mugun halinka",ya karasa fada yana rushewa da wani irin kukan bakinciki, dakyar jami'an tsaro suka banbare shi daga jikin his excellency da ya ƙi cewa ko mai ,kai hatta da idanunsa a bushe suke zuciyarsa ma dai abushen take,suna kada keyarsa motar anbulas ta shigo har bakin falon,cikin gaggawa suka yayi mi Abbie suka sakashi dan bashi taimakon gaggawa. His excellency kuwa har aka saka shi a mota idanunsa suna kan Abba yahya,wanda hakan yake dauke da manufofin da shi ka dai ya barwa kansa sani,ai kuwa wannan kallo ya yi tasiri a jiki da zuciyar Abba yahya dan kuwa take ya fara hirji da neman tsari da duk abinda zai shiga gabansa. Sai da motar yansandan ta wuce shima ya yi saurin shiga tashi ya bi bayan motar asibiti. Abba yahya ba karamin mamaki ya yi ba ganin lokaci kadan yan jarida sun fara yayata wannan labarin saboda da ya fito yaga garin duk a harmutse,shi kansa da kyar ya samu ya kufcewa tambayoyin yan jarida,sai da ya samu kanshi ne ya kula da wani me dan sahu yana binshi, da da farko baiyi zaton shi suke bi ba sai da ya ga yazo har gab da asibitin basu daina binshi ba sannan ya tabbatar shi din suke bi,ganin haka kawai sai ya shammacesu ya juya kan motar kan kace me tuni ya bace ko kyallinshi basa gani. Wani irin bugu ya kaiwa sitiyarin dan sahun yana cewa shet ya gano mu,na kusa da shi ya ce", oga ina ga dole sai mun bi a hankali dan na ga alama shima yana da wayo", na bayan yace ai Ni ban ga amfanin kamashi ba,tunda hajjaju cewa ta yi kar mu bari yayi nasarar kubutar da Muhammad nuur domin hakan yana daga cikin babban kuskuren da za muyi",dayan yace",yanzu dai mu bari mu yi magana da hajjaju sai musan abinda ya dace muyi", gamsuwar da su kayi da hakan yasa suka ja mashin ɗinsu suka wuce inda su kafi wayo. Sai da ya tabbatar sun tafi Sannan ya fito daga maboyarsa ya nufi asibitin zuciyarshi cike da sakesaken wanda yasa a biyo shi. Can babban headquarters suka kai his excellency kafin kace meye kobo manya sun san da maganar ,cikin kankanin lokaci aka fara tafka muhawara tsakanin talakawa da masu kuɗi harma da masu mulkin. RAIHAN WAZER...... Aunty amarya ta ci gaba da cewa Wazer baka kyauta min ba sam baka kyauta min ba,ka zubda mutuncinka da kimarka da nake gani a idona", a hankali cikin wata irin murya ya bude baki ya ce", Please Mami ki saurareni wallahi ban san waye yayi wannan aikin ba,hasalima yau banje office ba ki tsaya mu fahimci juna kar muyi abinda za muzo muna da nasani", wani banzan kallo ta yi masa sannan cikin takaicin kalamansa ta ce", haba wazer da na sani kuma na nawa ai nice a cikin nadama da danasani dumu_dumu,dan haka ka zo ka fice bana bukatar ganinka kuma kamar yadda na gaya maka ina sauraren takardar sakin RAIHAN,wani irin runtse ido ya yi a karo na farko da damuwarshi ta bayyana saman fuskarshi,tunda suka fara magana maganar sakin RAIHAN shine abu mafi tsananin ɗaci da ya fuskanta. Tuni ƙafafun RAIHAN suka fara rawa wani irin juwa na ɗibarta, wai wane irin mafarki ne take tayi yau marasa dadi, har yanzu abinda ta gani ta kuma ji da kunnenta ya kasa guguwa ya kasa barinta sukuni ko runtse ido ta yi sai taga fuskar matar da ta gani dazun me shirin ganin bayan Abbanta Yahya,kai Bama iya Abbanta ba har ita, dan kuwa tabbas ta gane ita ce me son kasheta tun tana cikin mahaifiyarta,to bata gama da wancan ba ta kuma riskar wani. Dakyar ta iya bude baki cikin dan karamin sauti ta ce", Mami meke faruwa? Gaba daya juyawa su kayi suna kallonta,da sauri wazer ya sunkuya zai dauki jaridar gudun kar RAIHAN ta gani tunda a yanzu ya fahimci bata san komai akan jaridar ba,sai dai kafin ya kai nashi hannun Mami ta riga shi,bata yi wata wata ba ta mikawa RAIHAN tana cewa duba kiga cin amanar da wazer ya yi mana........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page47 ``` .......karbar jaridar ta yi jikinta da zuciyarta na wani irin harbawa,a hankali ta dubi wazer da ya zuba mata ido fuskarshi a cunkushe, shi kadai yasan irin tashin hankalin da yake ciki,shi bai ma taba sanin akwai abinda zai dugunzuma rayuwarsa da farin cikinshi ba sai yau da mami ke bashi umarnin sakin RAIHAN,da sauri ta kawar da kanta tana maidawa kan jaridar,da fuskarta ta fara cin karo kafin ta fara bin rubutun daki_daki tana karantawa,gaba dayansu sun zuba mata ido har da hajiyar agadex da ta fito daga daki saboda jin yar hayaniya,itama raihan din dago kanta tayi daga karanta jaridar bayan rubutu na karshe da ta karanta,a kan wazer ta sauke idanunta da suke neman rufewa babu abinda take gani sai jiri,aunty Amarya ce ta karɓe jaridar tana cewa Kinga Ni da idanunki dai ba kage a kayi masa ba,domin babu yadda za ayi a fitar da labari ko jarida ba tare da saninsaba,kin ga kuwa ko da ace ba shi ya wallafar da jaridar ba to tabbas da saninsa bare ma kuma babu wani ja shine ya shammace mu ya ya yaudaremu", hajiyar agadex ce ta kula gaba daya RAIHAN bata cikin hankalinta saboda yadda ta kafe a gurin kamar status,sai kuma ta tafi luuu zata fadi cikin zafin nama wazer da ya fi kusanci da ita ya tarota ta fado saman kirjinsa,da sauri su kayi kanta suna kiran sunanta,wazer bai sauraresu ba ya nufi dakinta tana dauke a hannun shi,kafin su aunty amarya su shiga tuni ya rufo dakin kuma babu wanda ya isa budeshi ta waje,cikin wani irin takaici aunty Amarya taja birki tana yaba tsarin ido irin na WAZER ɗin,kafin cikin kwafa ta ce", ko me za kayi sai ka sakar min yarinya butulu kawai a baka amana saboda an yarda da kai shine daga karshe zaka watsa mana kasa a ido", Hajiyar agadex ce ta kama hannunta suka nufi falon tana cewa zo ki gaya min meke faruwa danni har yanzu Ban gane kan zancen naku ba", a tare su ka zauna mai makon ta yi mata bayani sai kawai ta fashe da wani mahaukacin kuka me tsanani wanda duk wanda ya jishi zai tabbatar tun daga can kasan zuciya yake fitowa,sam hajiyar agadex bata hanata ba, barinta ta yi tayi me isarta dan kanta ta yi shiru , Sannan ta karantawa hajiyar abinda jaridar ta kunsa,shiru hajiyar agadex ta yi na yan sakanni kafin ta dan nisa ta ce", lamra abinda nake so dake ki nutsu mu yi bincike akan wannan lamarin kar idanuwanmu su rufe mu kasa ganin gaskiya,abinda nake nufi shine kar ki saurin yankewa wannan yaron hukunci mu tsaya muyi tunani da kyakkyawar zuciya kuma mu saka lura cikin lamarin , Sannan ki daina zafafawa kanki, wannan abin da duk aka bi shi a sannu ba wani abin tada hankali ba ne,kasancewar ita kanta RAIHAN tashin hankalinki ne yasa ta cikin wannan ɗimuwar amma sam wannan bai kai tashin hankalin da yake kokarin tunkaromu ba", yadda aunty Amarya ta zuba mata ido cike da mamaki a kalmar ta ta karshe ne yasa ta anka da cewa ta yi subul da baka.kafin ta nemi abin kare kanta aunty Amarya ta jeho mata tambaya da cewa", Hajiya akwai wani abu ne? Me yake faruwa? Meye zai samemu da har zaifi wannan tashin hankali a gurina? Cikin son kawar da maganar hajiyar agadex ta ce", a'a ramla ba haka nake nufi ba dan Allah ki kwantar da hankalinki kar ki jefa kanki cikin wata matsalar daban. Girgiza kai aunty Amarya ta shigayi tana cewa a'a Hajiya dan Allah ki fada min ina ji ajikina akwai wani abu daban bayan wannan,saboda tun jiya nake jin zuciyata da gangar jikina ba daidaiba", haba ramla ki nutsu mana nace miki babu wani abu dagata hajiyar ta yi tana ci gaba da cewa muje ki samu ki dan kwanta nutsuwarki ta dawo", kuka Aunty Amarya ta kuma fashewa da shi tana cewa haba Hajiya ina naga ta bacci muna cikin wannan tashin hankalin na tabbata yanzu zaki yan jarida sun cika kofar gidannan shin me zance musu ta ya zan gyara abinda aka riga aka batashi? Cewa da su kayi na sauya RAIHAN a matsayin Rahim saboda gadon namiji ya fi na mace,taya kike ganin zan goge wannan? Ɗan jim hajiyar agadex ta yi kafin ta ce", ai sai kin fita duk zasu yi miki wannan tambayar ko? To babu inda zaki muje ki kwanta ko mutanen gidannan babu wanda zai ganki", ta gamsu da maganar Hajiya hakan yasa ta bita jikinta a sanyaya ga wani irin zazzaɓi da ya kamata farat daya. Ko da hamma Idris ya shiga bangarensu kasa yin komai ya yi,hatta matarsa kasa yin magana ya yi da ita, damuwa tasa ya kasa rike wannan babban almaraiin hakan yasa ya fita zuwa bangaren mamansa murja. RAIHAN WAZER......... A hankali ya kwantar da ita saman lafiyayyan gadonta da yasha wani hadadden bedsheet, dan karamin Fringe ɗin ta dake dakin ya nufa ya ciro bottle water,cikin nutsuwa ya dawo ya zauna saitin kanta ya bude kwalbar ruwan ya ɗan zuba a tafin hannunta sannan ya shafa mata a fuskarta sai da ya yi haka sai biyu,kana taja wani dogon numfashi tare da bude idanunta da suke kallon dishi_dishi,sai da ta samu minti ɗaya kafin ganinta ya dawo dai-dai,zuba mishi ido ta yi tana son tuna abinda ya faru saboda gani take kamar mafarki ta yi,bude bakinta ta yi a hankali saboda ta gasgata ba mafarki take ba,ta ce", da gaske ne komai da na ji na gani ya faru? Ta tambayeshi zuciyarta na tafiya da sauri saboda fargabar amsar da zai bata ,jinjina mata kai ya yi kafin ya ce", haka ne amma ban san komai ba ban san ya akai hakan ta faru ba", wata irin zabura ta yi ta tashi zaune idanuta cike fal da ruwan masifa ta ce", Hamma wazer karkace komai domin ba yadda zanyi ba,idan har ba kai ba ne me yasa zanje har office dinka amma kace baka bukatar ganina baka bukatar ganin kowa saboda kana ganawa da matarka rabi,akan idona rabi ta fito daga office din tana ce min wai mun dame ku", ta karasa faɗa hawaye na zuraro mata dan ita kadai tasan irin zafin da take ji akan hakan,lumshe idanunsa ya yi sannan ya kuma bude su akanta kafin cikin taushin murya da ke nuna lallashi ya ce", da ita plss RAIHAN yau banje office ba ban san me ya faru a wajenba,ko mai da ya faru shirine so plz kar ki bari yardar dake tsakaninmu ta rushe domin abinda wanda ya yi hakan yake bukata ke nan", harara ta watsa masa kafin cikin turo karamin bakinta ta ce", to idan wancan shirine shifa wannan na jaridar ai dai mu munsan cewa kaine kawai kasan wani abu da ya shafi wannan sirrin namu dan haka kaine ka fitar", bani ba ne RAIHAN", ya fada cikin sallamawa da wata irin karaya,wani iri ta ji ajikinta da yadda ya yi ɗin, hakan yasa ta kawar da kanta dan kaucewa kallonshi me kashe dukkan wata laka dake aiki a jikinta,kara matsawa ya yi jikinta yana kama hannunta dake ta faman murzawa ya cigaba da murza yatsun a hankali yana mai ci gaba da yi mata kallon har hanji, sannan cikin kamewa ya ce", kin yarda ba zan ci amana ba? Shiru ta yi tana tunanin to idan ba shi ba ne waye? Kafin ta dawo daga dan tunanin da ta tafi sai jinta ta yi cikin jikinshi ya tarairayo fuskarta cikin tafukan hannayenshi,kana a hankali ya ce", kalli nan ki gani",yana nufin idanunshi,dago idan yin ta yi dan ganin abinda yake nuna matan,a maimakon taga wani abu daban sai kawai tsintar idanunta cikin nashi ta yi ,take tafa marmar da kwayar idanunta tana son kufcewa rikon da yayi wa kwayar idonnata,ɗan murmushin gefan baki ne ya kufce masa kana ya kuma cewa", trues me my angel", tsintar kanta kawai ta yi da jinjina mishi kai domin zuciyarta ta ki bata damar kin yadda da wazer sosai take ji a ranta ba zai taba yin abinda aka ce ya yin ba,a hankali ta sauke kanta tare da cusa fuskarta cikin faffadan ƙirjinshi tana sauke ajiyar zuciya,shima ɗin numfashi ya furzar tare da kara kalmasheta suna shaƙar numfashin juna. __________ Cikin kankanin lokaci labaran nan guda biyu suka fara baza gari labarin Rahim Raihan da kuma kamun da aka yiwa his excellency dumu_dumu yana son kashe amininshi dan kawai ya gaje dukiyar da ya bashi amana. Sosai labarin ɓoyayyiyar Raihan ya bigi zuciyar mutane,a maimakon wannan ya zama abin tozarci gareta da ahlinta sai ya zama labarin da ya kara haskaka tauraronta,abin mamaki sam babu wanda ya dauki manufar da aka rubuta da wani abu daban kamar yadda ruby ta so,hasalima labarin his excellency shine ya danne na RAIHAN saboda yadda mutane suka jima suna fatan Allah ya bayyana musu wanda yake kashe musu yaya da mata. Abbie kuwa za mu iya cewa an samu nasarar kashe gubar da ya ci saboda bata riga ta yi aikin da zata iya kasheshi ba,sai dai fa yana cikin mummunan yanayi,an sa masa abin shaƙar numfashi yana kwance tamkar gawa,sai dai ayi fatan farfadowarsa cikin lokaci. A yanzu duka ahlinshi sun san komai saboda abune da ya haɗa da social media,dan aunty Amarya da hajiyar agadex ma tuni suka baro gidan RAIHAN ce kawai basu bari ta sani ba,saboda halin da take ciki,dakyar aunty Amarya suka ya kicewa tambayoyin yan jarida. Mama murja duk da halin damuwar rashin danta da take ciki ba karamin shock ta shiga ba lokacin da wannan labarin na RAIHAN ya risketa ,haka momy Hanne ma, sai dai a wannan gabar basu da abincewa. Tunda suka isa asibitin suka zauna a reseption mama murja take kallon Aunty Amarya,mamakin yadda yarinya kamarta ta iya juya tunaninsu take yi,kuma ita akarankanta tasan ramla ta yi haka ne saboda tsoran kar su cutatawa yarta,lallai Allah mai kudurane,gashi dai duk fadi tashin da suke na kar a samu RAIHAN a zuriyar Muhammad nur sai da Allah ya yi ikonsa,kuma dan yana son tarayu domin izna a garesu ne ya bawa Aunty Amarya basirar badda ita cikin jinsin mata,dake kuma shidin shine me yadda yaso sai yaso zamanta a hakan ba tare da asirinta ya tonuba har sai da yaso hakan lokacin da RAIHAN takai munzalin girma zata kuma iya kare kanta a duk inda ta shiga,kuma yasa igiyar aure tsakaninta da jajurtacce kuma kamilallan mijin da zai iya tsayawa ya kareta a ko ina,take mama murja taji wani tsoran Allah nashirgarta baranma da ta kuma yin nazari kan yadda ta rasa danta,wanda ta yi tsai da ranta ta tabbatar da cewa isharace Allah ya yi mata,lallai ta tabbata cewa akwai wata hikima ta Ubangiji a yin hakan,sai kuma tunaninta ta juya kan his excellency da abinda ya yiwa mujinnasu,sai kuma taga da ace yasan da RAIHAN fa da ita zai fara kashewa,( bata san cewa yasan da zaman RAIHAN ba)jinjina kai kawai take tana kuma jinjina irin wannan cakwakiyar da ita kanta har yanzu bata gama ganeta ba", dole ta ce", haka mana tunda bata san me ya shigo da ƴaƴanta cikin wannan rigimarba da har zai fara yi mata dauki daidai dasu.wata zuciyar ta ce", mata idan babu Muhammad nur ai sune maganadansa dan haka dole ya yi kokarin kawar da duka ahlinsa tare da shi uban gayyar,tabbas haka ne ta faɗa a fili,amma dake hankalinsu ba kwance yake ba babu wanda yasan me take ciki. Dr Sabo ne ya fito ya basu umarnin ganinshi na yan mintina amma da sharadin ba a bukatar hayaniya ko dogon motsi a dakin dan haka dole su kiyaye", jiki a sanyaye suka shiga dakin don duba shi, tsaf kuwa dakin ya cinye su kasancewarsa babban daki na masu iko. Addu'ar samun lafiya Baffa da su Hajiya goggo su kayi masa,su kuwa matansa kuka suka saka,dan haka Baffa ya ce su fita duka a rabu da shi dan gudun wata matsalar,ba dan sunso ba suka fita,a wajen ma babu wanda aka bari gaba daya suka wuce gida saboda akwai masu kula dashi. Kasancewar dare ya yi shi yasa basu samu cincirindon yan jarida masu jiran fitowarsu ba, Abba yahya dai yasha albarka wajen Baffa da Hajiya goggo, Abba Yahya ya kuma shiga ran Baffa saboda yakasance wanda bai manta alkhairi da halaccin da aka yi masa ba. *RUBY* Tunda ta baza jaridarta ita da sury suka dawo gida suna jiran sakamako, sai dai har magriba basu komai ba,Surry ce ta ankarar da su cewa babu yadda za ayi su san halin da ake ciki tunda basu kunna tv ba,hakan yasa suka kunna labarai dan kawai su ji sakamakon abinda suka kulla. Anan ne suka ci karo da abinda yake faruwa,ey labari ya yadu kamar yadda suke so sai dai kuma ta wata fuskar ya juya saboda dai tozarcin da suke so a yiwa Raihan bai samu ba, hankalin ruby har ya fara tashi , Surry ta yi saurin calming dinta,da cewa haba ruby yau fa abinnan ya faru bai kamata mu yanke hukunci tun yanzu ba,muna gobe muna da jibi ina tabbatar miki da cewa gobe za mu iya samun abinda muke so,a yanzu ma wannan labarin na his excellency ne ya doke nata", cikin fargabar da sai yanzu ta fara jinta ruby tace", sury da mun san wannan abun zai faru da mun bar fitar da labarin a yau sai kura ta lafa", harara Surry ta watsa mata sannan cikin takaicinta ta ce", ke kika so hakan ta faru dan nasan a lokacin koda na dakatar dake ba zaki dakatu ba,dan haka Ni babu ruwana da wannan banzar nadamar taki", daga haka ta figi jakarta tana cewa Ni Kinga tafiyata kar wannan dodon mijinnaki ya zo ya sameni",Binta da kallo rubuta yi tana fatan hakanta ya cimma gaci dan idan har ta faɗi a wannan wasan kashe kowa za ta yi duk su yi biyu babu.... *RAIHAN WAZER......* Yadda yake kulawa da duk wani motsinta sai ka dauka cewa ƙwan tsafin da ba ason fashewarsa ne,a bathroom dimta ya yi alwala,idanunshi akanta har ya fita ya kullota yaje sallah magrib, lokacin da ya dawo ne ya samu hajiyar agadex a falo tana jiran fitowar aunty Amarya su tafi asibiti,sannu da kokari yaron kirki ka yi hakuri da abinda ya faru Ni nasan cewa da wani abu a kasa kuma in sha Allah ko mai zai warware,a nan take sanar da shi kadan daga abinda yake faruwa dan haka ta bashi amanar RAIHAN har suke su dawo...... Wannan shine dalilin yin sallar isharsa a dakin RAIHAN ɗin yana kula da duk wani motsinta,tamkar wadda aka ce za asaceta.......✍🏽 48 *ƁOYAYYIYAR RAIHAN* A nutse ya mike daga kan abin sallar bayan yayi shafa' i da wuturi,matsawa ya yi dai-dai kanta saboda motsawar da ya ga tana yi alamun dai zata farka. A hankali take bude idanunta tun suna ganin dishi_dishi har suka bude tarwai akan kyakkyawar fuskarsa dake cike da kamala da wani irin haiba tamkar wani sufi,kura masa ido ta yi cikin mamakin har yanzu yana nan bai tafi ba,maida idanunta kan agogon dakin ta yi sai taga lokaci yaja sosai dan lokacin tara saura kwata,idan kuma bazata manta ba tun wajen biyar yake cikin gidan,kara maida kallonta kansa ta yi fuskarta na ci gaba da nuna mamakinta,kafin cikin sanyin murya ta bude baki ta ce", har yanzu kana nan? Ɗage mata gira ya yi ba tare da ya bata amsa ba,saima dagata da ya fara kokarinyi,ganin hakan yasa ta ɗan ture hannunshi tana cewa barni zan iya tashi da kaina, bai barta din ba kamar yadda ta bukata sai ma ɗaukarta da yayi cak ya nufi bathroom da ita, ɗan bugunshi ta fara yi a kirji cikin sakalci tana cilla kafa duk dan ya sauke ta,bai nuna yasan yanayi ba,dan haka bai direta a ko ina ba sai cikin bath din, sai alokacin ya yi mata magana cikin deep voice dinshi ya ce",ko na yi miki wankan? Ware idanunta ta yi har da baki cikin tsoron kar ya aikata abinda ya fada din,bai nuna ya damu Da mamakin da ta shiga ba ya kuma tambayarta kina bukata ke nan? Baki ta bude zata bashi amsa,sai dai kafin ta bashi amsar shi kuma tuni ya isar mata sakon zuciyarshi ta hanyar rufe bakinta da nashi.mukut ta hadiye maganarta har da ragowar yawunshi saboda jin tattausan harshensa cikin bakinnata,,ji ta yi numfashinta na wani daddaukewa saboda yadda ya fara juya harshennasa cikin bakinta tamkar wani mayunwaci,cikin salonshi wanda ya fahimci yana dauke mata hankali ya fara cire rigar jikinta, RAIHAN bata Ankara ba sai jinta tayi daga ita sai tiet bra dinta da fant,kokarin kwace kanta ta shiga yi saboda jin yana ƙoƙarin cire bra din,gashi babu damar magana dan har yanzu bakinta na cikin nashi yana yadda yake so dashi. Hannunta ta saka a bayanshi tana ɗan bugunshi tana dan rigarshi,sai dai fa ina wanda yayi nisa baya jin kira, amaimakon ta samu nasara ƙwacewa ma sai motsawar da take yi ya kuma bashi wata dama ta motsawar duk wata gaba dake jikinshi,bai saurara ba har sai da yayi nasarar cire bra dinta zuwa fant din dake jikinta, Kuka ta saka tare da shigewa jikinsa tana boye jikinta dan kar ya yi nasarar kallonta,babu wani bata lokaci yasa hannu biyu ya karbeta tsaf ta shige cikin ƙirjinshi kai kace babu wata halitta a wajen saboda yadda tayi tsirit a ƙirjinshi,hannu yasa ya banbareta daga jikinshi yaso suyi wankan nan tare to amma idan ya yi wanka ko ya jika kayanshi bashi da wani da zaisa , sai dai kuma idan na RAIHAN ɗin zaisa, takwa anyi abin kunya a gidan surukai ya ayyana hakan a ranshi fuskarshi fidda wani annurin Murmushi. Cikin kasa da murya ya rada mata da cewa kiyi wankanki babu ruwana ba zan tsaya na kalleki ba, amma fa idan kika jima zan dawo kuma idan na dawo Ni zan sake miki wani wankan," da sauri ta jinjina kanta dake kasa ta kasa haɗa ido da shi, hannu yasa ya dago habarta amma sai ta yi saurin runtse idon hakan ya bawa kwallar da ta cika su damar kwaranyowa kuma ba ta komai ba ce sai ta tsananin kunya,lakace dogon hancinta ya yi Sannan ya juya ya fita cikin nutsuwar zuciya. Bude idanta ta yi bayan taji alamar fitarsa, kofar ta zubawa ido kamar zata Ganshi ta ciki,sai kuma a hankali cikin sanyin jiki ta bude tap ta fara tsaftace jikinta dama ba sallah za ta yi ba dan haka wankan kawai ta yi da goge baki Sannan ta fito bayan ta rufe jikinta da manyan towel dake bathroom ɗin. Dai_dai lokacin mutanen gidan suka dawo,Baffa Ali ne ya umarci kowa da yaje ya kwanta zuwa gobe aga abinda Allah zaiyi,amma kafin hakan ya umarce su da su yi sallar dare su riki Allah sauƙin alamura,duk sun gamsu da bayaninsa,har zasu wuce sai ya kuma dakatar da su ya dubi Aunty Amarya cikin nutsuwa kana yace", kafin mu tafi asibiti ina son ganin kowa a falona har da RAIHAN", cak numfashin aunty Amarya ya tsaya tunawa da wannan babban kalubalen da zasu shiga ita da RAIHAN muddin me son ganin bayan RAIHAN ɗin bai saduda ba,dakyar ta amsa masa da in sha Allah", daga nan ya dubi su mama murja ya ce", ina fara za ku amsa kirana akan lokaci saboda muhimmancin maganar da za mu tattauna", amsawa su kayi cikin ladabi daga nan kowa yayi inda ya fi wayo zuciyoyinsu na saka da warwara. Yana ganin fitowarta ya mike a nutse ya nufeta,fuskar nan babu yabo ba fallasa,dan kallonshi ta yi tana jinjina halin kiskilancinsa,dubeshi kamar ba yanzu ya gama tsotse mata ruwan jiki ba,kamo hannunta da yayi ne ya sa ta dawo hayyacinta daga ɗan gajeren tunanin da ta tafi,zaunar da ita yayi kan stole din madubi yayin da shi kuma ya tsaya ata bayanta yana kallon fuskarta tarwai a cikin madubin,ba tare da ya yi mata magana ba ya janyo man da ya tabbata shine take shafawa lakatowa ya yi ya murza cikin tafin hannunsa,a hankali ya shiga murtsika mata a saman kafadunta in da ya zame towel din da ta rufa, Raihan dai kawai kallonshi take tana mai kara jin mamakinsa a ranta,jin ya zame towel din dake daure a jikinta yasa ta wata irin zabura wanda hakan ya bawa towel din damar sauka gaba ɗaya,kara ta saka me karamin sauti tana mai fadawa jikinsa ta cukwikwiye shi tana sakin kwallar takaici da kunya.lumshe idanunsa ya yi yana jin sanyin jikinta na taba shi kasancewar jallabiya ce me kwanciya a jikinshi,a hankali ya dauki hannayenshi duka biyun ya dora bisa bayanta dake bude yana sheki da dan sanyin ruwan da bai gama bushewa ba,a nutse ya shiga shafa man dake hannunshi a bayanta yana yin sama da kasa da hannunshi. Cikin kukan sakalci tasa hannunta a bayanshi tana bugunshi,Ni kam ka rabu dani ka tafi ban son wannan abun,haka nan sai Mami ta shigo tace muna iskanci....wata yar makalalliyar dariya ce ta kufce masa sai dai baiyi dariyar ba baya ga ƙayataccen Murmushin da ya saki wanda ya kara ƙawata kyakkyawar fuskarshi me cike da gwarjini yana ci gaba da shafa jikinta har yana zuro hannun ta cikinta dan kawai ya kuma tsokanarta,ai kuwa zabura ta yi idanunta na kuma cika da ƙwallah ta ce",meye ne hakan kake yi? Cikin son ta kalleshi ya dan hade labbanshi sannan ya ce", iskanci.....zaro ido ta yi kana cikin sauri ta kwaci kanta daga jikinshi ta sunkuya ta dauki towel dinta ta maida tana faman tura baki da kananun maganganun da bata san yana jinta ba,Ni kam ka tafi kar Mami tazo",da sharadi", ya fada yana leka fuskarta,meye sharadin? Ta tambaye shi tana tafiya zuwa bakin sip din kayanta ", zaki sha wani abu kafin ki kwanta", na yarda ta faɗa tana dauko rigar baccinta daga sip. To zo muyi sallama", ya fada idon shi akanta yana mata wannan kallon dake kashe duk wata laka dake jikinta banza ta yi da shi kamar bata ji ba", hucin numfashinsa kawai taji a bayanta kafin ta yi wani yunkuri tuni ya haɗe tazarar dake tsakaninsu sannan a hankali ya juyo da ita ya karbi rigar daga hannunta, saka mata rigar ya yi ta yadda ba za su yi fada ko ta hanashi ba,tsayawa ya yi yana ganin yadda rigar ta yi matukar yi mata kyau da amsar dirarran jikinta,sai yake ganin kamar tafi ko wace mace kyau da tsari,wata ƙilma Allah ne ya dubeshi shi yasa kaddararta tazo a matsayin namiji domin killace masa ita ba tare da ko wane kato ya gane masa sirrin da Allah ya boye a jikinta ba, ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya saki kafin ya kai fuskarshi dai-dai da Tata ya haɗe goshinsa da nata sannan tsinin hancinsu na gugar juna,haka labbanshi da nata suna hade,a hankali ya bude bakinshi ya sumbaci labbanta daga nan ya sumbaci goshinta ido zuwa kuncinta,kafin cikin wata nutsatstsiyar murya ya ce", good night my angel", daga haka ya sake ta ya fita ba tare da ko waige ba,dan ya tabbata idan ya biye ta zuciyarshi da gangar jikinshi to tabbas zai iya kwana a dakin tare da tafka abin kunya a gidan surukai. Sassanyan ajiyar zuciya ta sauke, tana mai takawa a hankali zuwa bakin window dan kawai taga fitar shi daga gidan. Yaci sa a bai hadu da kowa a falon ba dan haka cikin kwanciyar hankali ya fice,har ya bude motar zai shiga sai kuma ya fasa ya dan tsaya jim yana kallon window raihidake ta can nesa sosai da shi ta cikin gadin din gidan,tabbas yaji a jikinshi tana kallonshi. Da sauri tabar window tana dafe saitin zuciyarta,kafin ta yi sufa saman gadonta tana fidda numfashi a hankali,, Murmushinnan nasa me tsada ya yi sannan ya shige motarsa ya fice daga karamin gate din. Tunawa ta yi da alkawarin da ta yi masa akan cewa zata ci wani abun, hakan yasa ta mike da sauri ta fita zuwa kiching,shiru gidan da alama kowa ya nufi makwancinsa saboda rashin dadin zuciya da suke ciki,ita ma sai alokacin ta tuna da matar da ta gani a jiya,take komai ya shiga dawo mata ya kice abun ta fara kokarin yi duk dan saboda bata son zuciyarta ta yardar mata da wadda ta gani a matsayin makashiyarsu,da wannan shawara ta zuciyarta ta yi amfani har ta samu ta dan hada shayi me kauri ta dauko cake ta koma daki, sama sama ta ci ta mayar,sai kuma take jin wani irin kewar Abbie dinta saboda wunin ranar kaf bata sashi cikin idonta ba. ______ Kowa yana bacci wani kuma yana kusanta kanshi da Allah buwayi gagara misali,amma ita tana tsaye a cikin dakinta tana sunturi kamar me yin fareti,zuciyarta a dungunzume take ,gaba daya lissafinta so yake ya kwance kai zata iya cewa ma ya kwance din,wai me yasa duk fadi tashin da take yi dan ganin ta samu abinda take so hakan ya gagara,suna daukaka da alama dai bazata samu ba,ey ba zata samu ba mana tunda gashi wanda komai yake hannunsa ma abin yagagareshi daga karshe ma asirinsa ya tonu,anya itama Yahya ba zai gano ta ba kuwa? Kai ba zai yuwu ba Yahya dole na kawar da kai domin na fahimci kaima wani babbar katangane da zai hanani cikar burina,shi dai wancan an gama dashi tunda yaci guba babu tabbacin zai rayu,ko acan gadon asibitin zan iya karasa shi,shi kuma his excellency yana garkame,ɗan jim ta yi sai kuma can ta kyalkyale da dariya tana cewa idan haka ne kuwa ai an rage min aiki,yanzu babu abinda ya kamata nayi sai kokarin kawar da Yahya ina kawar dashi zan karasa Muhammad nur daga nan sai RAIHAN daga nan sai ramla,kafin cikin basira da hikimata dukiyar ta dawo hannuna. *WASHE GARI* Da sassafiyar yau mutane suka tashi da al'amarin da suka kwana dashi suka kuma tashi dashi. Kamar yadda baffa Ali ya umarci surukansa da yayansa da jikokinsa taron tattaunawar cikin falonsa, to haka ce takasance,karfe takwas duk sun hallara a babban falonnasa wanda yakasance kamar nanne waje duk wata mitin da za su yi a gidan. Ba tare da wani bata lokaci ba yayi musu addu'a tare da fatan samun lafiyar bangonsu wato Alh Muhammad nur,kafin cikin tsanaki ta kuma sigar da zasu fahimta ya yi musu bayani akan rayuwar RAIHAN da mafarin dalilin da yasa mahaifiyarta ta boyeta a matsayin mace ta bayyanata a matsayin namiji,cikin ikon Allah kuma Allah ya rufe sirrin har zuwa yanzu da yaga shine lokacin bayyanuwarta. Ba karamin firgici suka shiga da jin wannan hikima ta Ubangiji ba,gaba daya. Sai aka shiga kallon kallo a tsakanin matan,ko wacce nason ta gani ko zata gano me wannan aika aikar,shi kansa baffa da Abba yahya zuba musu ido ya yi yana son ganin motsin kowa,haka Aunty Amarya da RAIHAN da kuma hajiyar agadex. Shiru falon ya dauka na tsawon mintuna goma kowa yana tunani a ransa,sai dai duk yadda kowa yaso gane wata alama da zai nuna matar tana cikinsu hakan ya faskara", anan Aunty Amarya ta kuma tabbatar da cewa ko wacece wannan bakaramar shuuma ce da iya taku ba", Baffa Ali tsoho me ran karfe shi ya kore shirun da cewa, ba zance ko wacece kar ta fasa yin abinda ta yi niya tun haihuwar RAIHAN ba,amma ina so ta sani cewa Allah da ya halicci RAIHAN shine ka dai yake da ikon daukar ranta,dan da ace ita din tana da iko to tabbas da alokacin da taso kasheta ta samu dama,daga karshe muna rokon ALLAH da ya bayyana mana makiyan mu na boye, Allah kuma ya tashi kafadar Muhammad nur ", gaba daya da Amin suka amsa, ita kuwa Raihan babu abinda ya dame ta sai halin da Abbie yike ciki, dan tun da baffa yasanar da ita komai da ya faru take kuka, tana son Abbie matuka son da ba zai musaltuba domin kuwa shima yana sonta,dan kuwa son da yake mata ne ma yajawo duk wannan halin da suke cikin daga shi har ita.baffan ne da kansa ya dinga rarrashinta,dakyar ya samu ta yi shiru saboda ya ce", idan bata yi. Shiru ba zai hana ta zuwa ganinsa. ____________ Za mu iya cewa mutane da yawa sun samu salama da nutsuwar zuciya akan kama shugabansu da ya zama maci amana kuma baragurbi acikin al'umma, Abba yahya dai yasha addu'a da fatan gamawa da duniya lafiya,sai kuma babban al'amarin da talakawa su ka fara zuwa da shi a safiyar ta yau,akan su kam sunyi mubaya'a lallai suna so a maida Abba Yahya kan kujerar Gwamna a matsayin me rikon kwarya,har zuwa lokacin da za ayi zaben gwamnoni, kuma suna rokon jam'iyar su da su tsayar musu dashi a matsayin dan takarar da zai maye musu gurbin gwamna,zasu zabe shi a matsayin gwamnansu na gobe in sha Allah. Kafin kace wani abu an fara hawa teburin shawara da tafka muhawara tsakanin jam iyu da kuma manyan yan takarar da suke cikin jam'iyar dake ci a yanzu,kai ya dau zafi an kasa samun matsaya, talakawa kuma sun hura musu wuta akan su fa lallai ga wanda suke so a matsayin gwamna idan ba haka ba ba za su bawa Kowa kuriar su ba. RUBY Itama da nata burin ta tashi a yau, shi yasa ta shirya da wuri ta fice dan kawai tasan halin da ake ciki, a kuma ina makircinta ya kwana......✍🏽 Pls ayi comments kaina ya dau zafi ina bukatar kwarin gwiwar ku😀 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page49 ``` *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page49 ``` 49 Abba yahya da su baffa kai kaf dinsu ma basu san abinda yake faruwa ba sai da suka fito daga gidan dan zuwa asibiti suka ga yadda yan jarida da al'umma suka yanyamesu,duk kokarinsu na son kaucewa tambayoyin yan jaridar amma hakan yaci tura ,sune rakiya a kafa har zuwa asibitin da Alh Muhammad nur yake kwance. Yadda mutane su kayi cincirindo a jikin motocinsu babu ma hanyar da zasu wuce yasa,baffa Ali ya ce su tsaya su saurari yan jaridar ko dan Aunty amarya ta samu damar wanke kanta daga zargin da ake yi mata. Ita dai Raihan gaba daya ta kasa sakewa saboda yau jinta take wata daban,bata taba shiga cikin mutane da shigarta ta ainahin mace ba,bata taɓa tsayawa gaban mutane a matsayinta Na mace ba,abu daya ne ya rage mata armashi shine halin da suka tsinci kansu,ga Abbie babu lafiya ga tarkon makiya dake zagaye da su. Sanye take cikin wata hadaddiyar doguwar rigar Kuwait wadda ta zauna ajikinta ta fidda ainahin dirarriyar surarta ta cikakkiyar matashiya me dauke da sirrin kyau me tsayawa a zuciyar mutum,yadda ta yafa mayafin a rashin iyawa sai ya bada wani sitayal na daban, babu komai a fuskarta sai kwallin da Hajiya goggo ta zizara mata, a cewarta kwalli shi zai kara banbantata da namiji,duk da cewa Hajiya goggo na fushi da RAIHAN da kowa ma da ya boye mata wannan babban al'amari amma hakan bai hanata nunawa RAIHAN ɗin wata irin soyayya ba,a cewarta ita ce kadai jikanyarta mace,sai dai duk motsi sai ta zabgawa Aunty Amarya harara tana cewa cutata kawai a kayi Allah ya bani jika mace kamar wannan zankadediyar balarabiyar amma a kasa gayan duk da cewa nayi miki uzuri to amma me yasa lokacin Da kowa ya sani a ka ki sanar dani? Ita dai Aunty Amarya hakuri ne nata domin yanzu bata da wani power komai yinsa take a sanyaye gani take kamar lokacin rabuwar ta da RAIHAN ɗin ta ne ya zo. Da yawan yan jaridan ba komai ne ya sa suke son hira da RAIHAN ba sai dan kawai suna son ganinta a ainahinta na RAIHAN. Abba yahya ne ya fara fitowa daga mota ai take guri ya dau sowar talakawa ana sai kayi da yardar Allah,hannu ya daga musu fuskarshi cike da murmushi,dan jaridar dake kusa da shi ya yi saurin yi masa tambaya da cewa, yallabai ka dai ji abinda mutane suke fada akan ko nace talakawanku shin me zaka iya cewa a game da ra ayin su na son tsayawa dan takararsu dan ci gaba da jagorantar su? Dan gyaran murya ya yi kafin cikin kyakkyawan kalami ya ce", alhamdulillah babu abinda zance da jama a sai godiya,game da abinda suke fada Ni a yanzu bani da ta cewa har sai mun kai da tattaunawa a zauran majalisa", wani dan jaridar ya kuma wulloasa tambaya da cewa", yallabai shin dama kana da ra ayin tsayawa takarar gwamnan jahar nanne ko kuma dai za ka bi ra ayin yan jahar? A'a bani da wannan ra ayin a yanzu dan mu ra ayin mu shine gwamna ya cigaba da rike kujerarsa ya karasa shekara hudu idan Allah yasa muna da rai", wanda ya fara yi masa tambaya da farko ya kuma watsa masa wata tambayar, yallabai wannan abun da kayi na ceton dan uwanka da sauran talaka shin kayi ne dan Allah ko kuma kayi ne dama dan kasan talakawa zasu ce suna muradin ka?. Ɗuf wuta ta daukewa mutane har masu kallo kai har su RAIHAN dake cikin mota", Murmushi Abba yahya ya yi yana kuma fuskantar dan jaridar tare da kare masa kallo kafin cikin nustuwa ya ce", banyi wannan jihadin dan kowa yasoni ko yace a tsaudani takara ba, nayi ne domin Allah da dan uwana da kuma talakawan da suke cikin halin kakanikayi da cutar da su da akayi ta hanyar kashe ƴaƴansu da matansu", Baffa Ali dake cikin mota daya da su Hamma Idris ya dubi Hamma Idris din ya ce", maza ka ce ", da su RAIHAN su fito daga mota nasan ganinsu zaisa yan jaridar nan su rabu da Yahya ", wannan tambaya haka ai duk gaskiyar mutum sai su sa ya mozanta", da sauri IDRES ya fita dan cika umarnin kakannasu,dakyar shima ya samu ya kai ga motar su Aunty Amarya.lokacin da ya fada mata sakon sakalo ta yi tana kallon dubban jama'ar dake wajen tana tunanin ta yadda za ayi ta fara magana da su," Raihan ce ta riko hannunta sannan cikin taushin murya ta ce", Mami karki damu ki zauna ba zaki iya magana da su ba saboda baki taba yi ba,dan haka zan fanshe ki zan basu duk wata amsa da suke bukata in sha Allah ", ajiyar zuciya Mamin ta sauke tana kallon RAIHAN ɗin da ta saki hannunta tana kokarin fita daga motar,inna maimuna ce ta dafa ta tana cewa kar ki damu Raihan zata yi komai tun da ita aikinta ne babu abinda zai gagareta. *KALLO YA KOMA SAMA* Bude murfin kofar motar da a kayi yasa mutane da yan jarida maida hankalinsu kan motar,kafarta ta fara zurowa wadda ke sanye cikin wani haddadan takalmi flat me madauri baƙi wanda ya matukar haska farar kafarta da tamkar bata taka kasa da da ita,kafin a hankali ta zuro gangar jikinta zuwa ƙayatacciyar fuskarta da take ta sheki da walwali duk kuwa da cewa tana cikin alhinin abinda ke faruwa,tsayuwar ta a gurin yasa gaba daya muntane suka jiyo kanta, yayin da maganganu suka fara tashi a gurin kowa da abinda yake fada wasu Masha Allah tubarakalla,wasu wowww wannan halittarfa, Allah kadai yasan manufarsa ta boye RAIHAN domin wannan ba dabarar mahaifiyarta ba ce,cewar wasu dattijai. Take yan jaridar suka fara wawason son hira da ita harma ta fara rasa tambayar da zata amsa, idanunta ne suka sauka kan salim abokin aikinta a Chibado FM hakan yasa ta yafitoshi,da sauri ya matsa yana saita abin maganarsa,sannan ya fara da cewa ", Hajiya RAIHAN ko za ki bamu hadin kai mu gayyatoki gidan. Rediyon mu dan tattaunawa akan abinda ya shafi rayuwarki?wani aikin sai gidan rediyon Chibado tabbas wannan dabara ta salim ta yi mata hakanne zai bata damar fedewa al umma buri har wutsiya,dan haka cikin taushin muryarta da a da ake kiranta da Muryar mata ta ce", in sha Allah zan baku wannan damar duk sanda kuka nemeni zan amsa kiranku", wani dan jaridar ne ya yi mata tambaya da cewa ", shin me zaki iya cewa a game da sabon yanayin da kika tsinci kanki a ciki ma ana da kina fitowa cikin mutane a matsayin namiji yau kuma gashi kin fito a matsayin mace? Duban dan jaridar ta yi sannan cikin kamewarta ta nutsatstsiyar budurwa me cike da aji wanda a da sam basu bayyana ba Bama tasan tana da su ba,ta ce", ey naji wani iri naji kamar ba Ni ba,ummm a takaice dai ji nake kamar an sauyani", zai kuma yin wata tambayar ta dakatar da shi da cewa pls duk abinda kuke so kuji daga gare Ni zaku ji shi amma yanzu ku danyi excuse Dina ina son duba mahaifina bana cin mood din da zan iya fada muku abinda kuke sonji", Tana gama fadar haka sai ga yan sanda wanda aka turosu musamman dan tsaron lafiyar Abba yahya sune suka kore mutanen da suka hana su wucewa,tare da yan jarida, duk da haka dakyar suka samu suka shige cikin asibitin. Wasu irin ƙwallah ne suka cika idanun ruby da komai ya faru akan idonta ,me ta yi haka ne ? Ita da ta yi wannan abu dan tozarta RAIHAN da ahlinta amma shine yake nema zama silar ɗaukakarta,wata zuciyar ta ce", da ita ke banza ce ai ba dan wannan ka dai kika yi ba ,babban abinda kika yi danshi ai ya yiwu tunda gashi babu wazer a gurin yanzu haka ma sunyi tsiya_tsiya tun jiya ke baki sani ba",to amma tozarcin da RAIHAN zata yi shine zaisa su ji zafin wazer ɗin matuka anya kuwa bata haka rami ta zuma kanta ba?to dai ga wazer baizo wajen ba to dukkan alamu ta yi nasara", wannan tunanin da ta yi yasa ta ɗan sauke ajiyar zuciya.sai dai me juyawar da zata yi sai ganin sabuwar motar da wazer ya yi oder su a cikin satinnan ta yi, kafin ta gama tabbatarwa shidinne ko ba shi bane,tuni ya yi fakin kusa da motarta kafin ya fito kuwa tuni kamshinsa ya gama baibayye wajen,wani irin kakkauran yauwu ta hadiye kirjinta kuwa babu abinda yake sai sama da ƙasa, a hankali aka bude motar dake bayanshi wani kakkarfan body gard ya fito ya zo ya bude mishi kofa. A hankali ya zuro kafarshi dake sanye cikin wani arnan coversue yana ta zuba kyalli,kafin a sannu gangar jikinshi ta biyo baya,kamshinsa kuwa tuni har kewaye rabin faffadan filin harabar aje motocin dake a sibitin,sanye yake cikin kayanshi na kullum ash din cot sai sunglasses da ya kara bawa gewayayyen sajenshi damar fitowa kasancewar glas din fari sai yasa kake hango kwayar idonshi tar a cikinsa.bai san meye kalle _ kalle ba dan haka bai lura da motar rabi a ba,kai tsaye ya wuce cikin hospital din gard din da Abbu ya kawo mashi sabbi wadanda suka san aikinsu na take mishi baya wasu kuma sun kame wajen motarshi saboda tsaron lafiyar shi,a hankali yake takunshi me cike da nutsuwa, kallo daya za kayi masa ka kasa yin na biyu saboda kwarjini da haiba tare da ilhamar da rabbi ya hore masa namiji ne iya namiji da duk wata mace mai suna mace zata yi burin mallakar sa matsayin miji uba zaiso ya same shi matsayin ɗa haka uwa zata so a ce danta ne", Masha Allah abinda mutanen da yake giftawa suke faɗa ke nan. Wani irin ihu me tafe da kuka rabi a ta saka tana mai dukan sityarin motar,ji take tamkar zata yi hauka,wai me yake shirin faruwa ne ? Anya abinda Surry ta sa nayi hanya ce me bullewa? Ina ba zai yiwu ba wallahi,in dai a wannan lokacin banci nasara akan RAIHAN ba to wallahi sai dai kowa ya rasa zan kashe wazer ɗin kowa ya huta wallahi ba zan yadda ina ji ina gani ya zama nata ba bazai yiwu ba", ita kadai ke ta mannawa kanta hauka a cikin mota tamkar dai ta zare din da gaske.da sauri ta goge fuskarta ta fito daga motar to nufi cikin asibitin, dan bata jin zata iya tafiya ba tare da ta ga sakamakon da zai kwantar mata da hankali ba,dole ta bishi taga yadda zata kaya idan hakanta bai cimma ruwa ba sai ta san irin shirin da zata yi a gaba. _____________ Hankalin yan takarkaru fa ya tashi da wannan hukunci da to lakawa suka yanke,dan haka babu shiri shugaban jam iya ya haɗa mittin din gaggawa,yan majalisu da sauran masu mukamai tuni a aka halla dan yanke hukunci,akan wannan zaɓin da talakawa su kayi. Anyi muhawa an tafka gumurzu anyi kace nace daga karshe a ka tsaya a matsaya daya a shawarar shugaban jam'iyya", acewarsa idan har suka ki yadda da abinda suke so na tsayar musu da Abba yahya to tabbas zasu shiga cikin zargin mutane akan cewa da hadin makinsu tsohon gwamna yake aikata duk ta asar da yake yi,amma idan suka tsayar dashi dantakara to tabbas talakawa zasu yadda dasu za kuma aciresu daga zargi a matsayinsu na yan jam iya daya da gwamnan kuma wadanda suke karkashinsa,sai dai fa sunce ba su yadda da rikon kwarya a ba saboda a yanzu dufuty ne kawai ya cancanta da yayi rikon kwarya har zuwa lokacin zabe,shima kuma wannan dama ce a gare shi ta tsayawa yayi jinyar dan uwanshi a nutse,kowa ya yi na an da hakan ƙalilan ne basu amince ba sai dan basu da yadda za su yi, wannan muhawa da aka tafka babu Abba yahya a ciki kasancewar sunyi masa uzuri akan rashin lafiyar dan uwansa. Bayan fitowa daga wannan tattauwarne suka zanta da yan jarida in da shugaban jam'iya ya basu tabbacin cewa sun tsaida Alhji Yahya matsayin dan takarar gwamnan gobe,amma fa ba zai yi rikon kwarya Ba saboda bashi ya cancanta ba matemakin gwanane kawai yake da wannan damar, ya dora da cewa a ganina shima zai samu nutsuwar fuskartar abinda yake gaban shi wato jinyar Muhammad nur,idan yaso sai ya tsaya a matsayin dufuty. Talakawa sun gamsu da jawabin shugaban jam'iyya dan haka kowa ya shiga yiwa Abbie fatan samun lafiya da fatan zuwan zabe lafiya domin su cika burinsu na bawa Abba Yahya kuri'arsu wanda suke ganin ita kadaice hanyar saka mishi akan jihadin tsamosu daga hannun baragurbi da ya yi. _________ Cikin tashin hankali Dr sanater ya dubi shugaban jam'iya bayan dawowarsa daga mitin din da suka yi da tattaunawarsa da yan jarida,ya ce", haba shugaban me kake nufi da yin hakan,kasan cewa idan har kuka tsaida mutumin nan takara tabbas babu makawa sai ya ci", idan kuma ya ci tabbas mune a ruwa saboda duk wata hanyar samun arzikinmu sai ya tosheta", Alh ja'e ya dora da cewa wannan maganar haka taka haka take Dr dan haka kai shugaban jam'iya sai ka yi mana bayanin da zamu gamsu",dan jan numfashi ya yi kafin ya ce,tabbas abinda kuka fada haka ne to amma Ni nayi hangen da ku kuka kasa yinsa,kun san dai kuma da tabo gurin yansandar jahar nan, a wancan karon ba dabarar ku ce ta fidda ku ba,dan haka dole muyi takatdantsan gudun tonon asirinmu,mu dai kunga iya kar Musa akashe mana,mu wawashi kudin talakawa mu zuba a susunmu,kunga kenan harsabibancinmu bai kai na wancan shahararren gwamnan ba,to asirinsa ya tonu mu kuma su waye da asirinmu ba zai tonu ba,dan haka dole komai mu bishi a sannu in dai ba so muke rayuwarmu ta kare a gidan bursuna ba", kallon kallo suka shiga yi kafin duk su jinjina kai alamun dai sun gamsu da hujjojin shugaban jam'iyyar yan adawartasu... ___________ Tunda suka samu suka Ganshi aka umarce su da su barshi saboda ba ason yawan hayaniya akansa, Raihan dai dakyar baffa ya rarrasheta suka fita amma cewa ta yi babu inda zata tana kusa da Abbie dinta, Abun bakaramin mamaki ya bawa Aunty amarya da Hajiya goggo ba ganin mama murja har da ita a lallashin Raihan, wannan abu ya mugun dasa ayar tambaya a zukatan wadannan mutane ukun,Aunty amarya momy Hanne HAMMA IDRES,da kuma hajiyar agadex......✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page50 ``` 50 .....Sam mama murja bata kula da irin kallon da suke mata ba zuciyarta daya take rarrashin RAIHAN. Tana tsaka da kukanne hancinta ya fara shako mata ƙamshin da a duk inda take ba za ta kasa gane shi ba,kanshin da bata taɓa jinsa a tare da kowa ba sai wani mutum daya da ya zama wani babban jigo a rayuwarta,ɗif kukanta ya tsaya kamar daukewar wuta", kafin a hankali ta dago kanta dake jikin inna maimuna,idanunta da su kayi ja basu sauka a ko ina ba sai kan WAZEER da yake takowa zuwa garesu cikin wani nutsatstsen taku tamkar wani Basarake me iko da birane goma", samun kanta ta yi da kasa dauke idanunta akansa saboda wani irin kyau da taga ya mata,sai take ganin yadda take jinta daban shi dinma haka take kallonsa a daban saboda yau ne rana ta farko da ta Ganshi a Raihan dinta ba wai ƁOYAYYIYAR RAIHAN ba. Yana karasowa daf dasu ya rissina gaban baffa da Abba yahya ya mika gaisuwa cikin nutsuwarshi dake hade da wani irin girmamawa. Hamma Idris da Hamma Affan dukkansu hannu ya basu su kayi masabaha,kafin ya gaidasu hajiyar agadex yana musu jaje da fatan samuwar lafiyar Abbie,duk abinda yake idanunshi da zuciyarshi na kan Raihan,wani irin kyawu ta yi masa me tsayawa a rai gani yake kamar yau ya fara ganinta ,eh zai iya cewa yau din ya fara ganinta amma a cikin shigarsu ta mata yaune ta fito masa sak kyakkyawar mace matashiyar da ta fi ko wacce mace a idanunsa da kuma zuciyarsa.juyowa yayi da nufin gaida aunty Amarya amma sai wayam babu ita a gurin, ɗan lumshe idanunsa ya yi yana maida kallonsa kan RAIHAN da idaunshi suka kasa daina zagawa a kan jikinta da duk wani motsinta,yayin da ita kuma ta yi zukudi tana kallon inda mamin ta yi,sarai yasan saboda shi tabar gurin RAIHAN ma tasan haka,ragowarne dai basu fahimta ba,saboda ba kowa ne ma ya kula da tashin nata ba. Shigowar Dr Sabo reseption dinne yasa suka maida hankalinsu kansa, hannu ya bawa Wazer yana cewa surukinmu Barka da zuwa",yauwa Dr ya jikin Abbie fatan babu wata matsalar? Babu in sha Allah zai tashi normal kamar komai bai faru ba", Allah yasa zan iya ganinsa? Wazer ya bukaci hakan daga wajen Dr Sabo ", ey me zai hana yawan hayaniya ne kawai ba a so anayi akansa shi yasa muke hanawa",, ok thanks wazer ya fada yana nufar dakin", da sauri RAIHAN ta mike bata saurari komai ba ta bi bayanshi dan har ga Allah so take ta kuma ganin Abbie din...da kallo suka bi ta cike da tausayi. Rabi'a dake makale tana kallon duk abinda ke faruwa ji tayi zuciyarta kamar zata fito waje,kallon da taga wazer yana yiwa Raihan ba karamin tayar mata da hankali ya yi ba ita kadai ta san me ta hango cikin wannan kallon duk kuwa da cewa tana dan nesa da su,to amma dake hankalinta yana kansu babu abinda bata gani, da da yadda za ta yi ta bi su dakin da sai ta bisu ko dan ta Korewa kanta shakkun result dinta,tunawa ta yi a kwai window ta can baya yasa ta yi a zamar juyawa ta fita daga reseption din,motar gidansu ta hango ta shigo da alama su Abbu ne suka zo dubiya ta aiyana hakan a ranta.tsayawa ta yi dan ganin dawa dawa suka zo,sai dai bata bari sun ganta ba. Abbu Ammi da su salim shukra har da umma rumana,gaba daya dai family din wazer innawuro ce bata gani ba da alama har yanzu bata yi amanna da auren ba,ji ta yi idanunta suna wani tsaki tsaki saboda azabar bakinciki,ganinsu da ta yi gaba daya ya bata tabbacin cewa suna tare da RAIHAN ke nan, ganin suna kosanto in da take yasa ta yi saurin barin gurin ta nufi inda zuciyarta ke tunzurata zuwa. Hasashen rabi a ya yi daidai dan kuwa lokacin da wannan sirrin ya fasu,Abbu bai yi wani nuku nuku ba gurin fayyace musu komai ba,sai dai fa innawuro ta yi tsalle ta dire akan ita fa sam bata yarda da wannan cakudaddan al'amari ba,jikanta ba zai zauna da mata maza ba", a haka gayyar taron ta watse ba tare da Abbu ya samo kan innawuro ba, Ammi kuwa bata ji komai ba sai son RAIHAN da tsananin tausayinta ta ji kuma zuciyarta ta karbeta da hannu bibbiyu kai ji take ma fa kamar sai yanzu ne ta yi suruka ta hakika.haka shukra da taji tana wani irin dokin zama da RAIHAN a matsayin matar Hmmansu WAZEER, wannan dalilin ne yasa innawuro bata zo dubiyar Abbie da jajanta musu ba,shi kuwa Abbu hatta su salim da Khalid bai bari ba ya sako su gaba dan duba abokinsa kuma surukinsa. Abban rabi ne zaune a falonshi yau yini guda ya kasa fita, duk abinda yake faruwa a tv yake kalla,zuciyarshi ce kawai ke kaiwa da kawowa da tunanin yadda za ayi yafi dan uwansa,abu na farko da ya fara tsole masa ido shine bataliyar arzikin da Allah ya bashi da daukaka ta hanyar gaskiyar shi dake amfani ta kafafen yada labaranshi,na biyu soyayyar da yake ganin mahaifiyarsu tana nuna masa,na uku ya samu irin matar da yake da burin samu a rayuwarshi, uwa uba yazo ya samu ya'yan da duniya take alfahari da guda daya gashi biyun ma sun dawo za a fara amfana da su wanda idan ya yi sake bai san su kuma irin gudummawar da zasu kawo har a fara jerasu a manyan attijirai ba,duk inda ya kalla sai yaga shine koma baya a cikinsu,Gara ma yaya ita Macece kuma ta yi aurenta, shi fa babu dukiya babu suna sannan babu ya'ya. Ina ba zai yuwu ba tabbas ba zai yuwu zuciyata da idaniyata ba za su taba lamuntar ganin yaya Chibado cikin dukiya walwala daukaka ba,dan haka duk yadda zanyi sai nayi ko da ace ban samu dukiyarsa ba to na dau alkawarin babu wani cigaba da zai kara samu dole mu dawo daya da shi, dole ya rasa dukiyarsa ko yayansa ko ɗaukakarsa,ba zan iya jurar ganinshi cikin duka wadannan abubuwan ba, WAZER ya ambaci sunan cikin kaunshin murya wazer ɗin na gurin, kana ya cigaba da cewa kaine ka dai yafi cancanta da kabar duniya na san idan har na taba ka tamkar na taba rayuwar zuriyar Chibado ne,da wannan kadai ya isa na tarwatsa farin cikin Chibado tunda na fahimci shine kashin bayansa,karasawa ya yi gaban katon hoton su da suka dauka fuskokinsu cike da fara a,shafa hoton yayi dai dai fuskar Abbu kana ya ci gaba da magana tamkar wani zararre,yaya kayi hakuri ba zan iya juraba ,yadda ka raba Ni da soyayyar mahaifiyata kaima sai na raba ka da soyayyar da guda da yafi soyuwa a zukatan ku daga kai har innawuro,da zan samu yadda nake so to tabbas sai mun dawo dai-dai da kai,ma ana 'ya ɗaya babu dukiya babu daukaka babu 'ya'ya," ya karasa fada yana hadiye wani kullin abu da ko ya hadiye shi ba ya sauka, ya kuma tabbatar da cewa ba zai taba wadawa ba har sai ranar da ya cimma burinsa akan kudurinsa na tarwatsa rayuwar dan uwansa. ___________ Duban Surry yake cike da jin haushi,kafin ya ce", yanzu dai wannan shirin namu ya wargaje akan tarkon da mu kayiwa Raihan ke nan? Shiru Surry ta yi na yan wasu sakanni kafin ta bude baki ta ce", yallabai Ni ina ganin mu saurara tukunna muga abinda zai faru tsakaninsu,kar muyi saurin yanke hukunci tunda kaga yanzu ita rabin ta bisu can asibiti dan ta samo mana rahoton abinda ke faruwa", zuba mata ido ya yi ta cikin facemask dinshi da jajayen idanunshi da suke boye cikin bakin sunglasses,Surry har ta fidda ran maganarshi sai kuma cikin wata irin murya wadda bata isa tantance Muryarsa guda ba,ya ce", shike nan na baku sati guda idan banji abinda nake son ji ba to tabbas zan dau hukunci na gaba", daga haka ya mike daga kujerar da yake zaune ya fice daga gurin cin abincin ba tare da ko waige ya yi ba. RAIHAN WAZER.... Yana shiga kafin ya rufe kofar itama ta sa kai , a tare suka karasa gadon da Abbie yake kwance tamkar gawa. Tsayawa ta yi a gefenshi ta inda ta ke iya kallon fuskar Abbie dake rufe hancin shi sakaye cikin abin jan numfashi,a hankali zuciyarta ta fara rauni har idanunta da gangar jikinta suka shaida hakan,saboda yadda idanunta suka fara zubar da ruwan hawaye gangar jikinta kuwa ta fara rawa saboda rausayin halin da Abbie din yake ciki da su kansu ma ahlinsa. Kukanta ne ya fara karfi kafafunta na son kasa daukarta,tana gab da zubewa kasa ya saka dogayen hannayensa ya tarota ba tare da ya bari gwiwowinta sun sauka kasa ba,gaba dayanta ya yi mata masauki me kyau cikin lafiyayyan ƙirjinsa me fadin dake nuna alamun cikar namiji,samun kanta ta yi da kara narkewa ajikinshi idanunta na ci gaba da tsiyayar ruwan hawaye.dago fuskarta ya yi ya saita da tashi fuskar sannan a hankali ya shiga hura mata iskar bakinshi da ke fitowa da wani irin lafiyayyan ƙamshin banana strawberry,kif_kifta idanun ta shiga yi hawayen na bushewa suna daskarewa a kan kuncinta,ganin yadda take farfari da idanun ya sa shi fidda wani dan asirtaccen murmushi da babu me zarrar ganinshi sai wadda yake rike da mukullin zuciya irin rikewar nan ta har abada wadda bata da karshe.dan kawar da fuskar ta yi tana son basar da abinda yake mata yawo a can kololuwarta ,sai dai kuma hakan ya ki samuwa,dan kuwa dan gidan Ammi jikan innawuro ya yi zarra ya kai can_can kololuwar da bata jin zata iya sarayar da abinda take ji akansa, wannan dalilinne yasa ta kalleshi kallo me cike da sirrinkan da ita kanta bata iya kidayesu da yi musu fassara me sauki,cikin hikimarsa ya sarke idanunnasu yayin da bugun zuciyoyinsu ke tafiya a tare cikin wani irin yanayi me taba ruhi da gangar jiki,hannu ta sa ta taɓa sajenshi da yake matukar kayatar da ita sannan cikin tura karamin bakinta ta ce", Hamma wazer ina son Abbie bana so wani abu ya sameshi", a hankali ya kai tattausar labbanshi jajayen saman nata ya bata wata kyakkyawar sumba kana cikin deep voice dinshi me cike da kamewa ya ce", Nima haka ina son Abbie saboda ya bani wani abu guda me muhimmanci da tsadar da yafi tsada tsada dan haka ina mishi addu'ar samun lafiya ko dan yaga irin da kyakkyawar tsadar da ya bani zata ajiye masa a matsayin sanyin idaniyarsa", sam RAIHAN bata fahimci ko guda daga saurancan da wazer ya yi mata ba,hakan yasa ta kalle shi cike da yarinta ta ce", HAMMA WAZEER me Abbie na ya baka ban sani ba? Za ki sani nan gaba kadan ranar da na fidda irin daga cikin tsadar? Tsaf ya kuma kulle kanta dan haka cikin sakalcinta ta kuma bude baki za ta yi magana amma sai caraf dan gidan Chibado ya cafe harshen da bakin gaba daya idanunshi cikin nata da ta zarosu tana duban inda Abbie ke kwance gadon asibiti. Wani irin numfashi me tsananin zafi da kuna rabi a ta fesar yayi da ta bude baki kamar zata yi ihu sai kuma ta yi gaggawar dinke bakin da tafukan hannayenta,amma fa ta kasa hana zafafan hawayen da suka fara tsere saman kuncinta zuba, wannan wace irin masifa ce haka? Ji ta yi tana neman zarewa gashi ta kasa matsawa daga jikin window din da take leken su kasancewarsa glass me garaigarai yasa take ganin komai kamar a gabanta. Wazer da baisan me ke faruwa ba ya sa hannunshi ya tallafi keyar Raihan yana kuma yi mata brosh da harshensa tawunsa yana zagaye ko ina na cikin bakinta,taba kofar dakin da akayi ne ya bawa RAIHAN damar son kwace kanta,amma sai wazer bai bata damar hakan ba hasalima shi kunnuwansa ba ji masa alamun shigowar da ake yi ba,da kyar RAIHAN ta samu ta kwace bakinta daga nashi amma ta kasa kwace jikinta da yake rike da shi kamar ance za a raba shi da ita,ɗan kallon idanunshi da suke a lumshe ta yi sannan cikin rada ta ce da shi HAMMA WAZEER za a shigo fa ina ga su baffa ne", ko gezau baiyi ba saima hannunsa da ya shiga yawo da shi a sassan jikinta,doke hannunshi ta yi za ta kuma yin magana amma sai maganar ta tsaya cak dalilin shigowar su Abbu da Ammi da kannanshi su salim sai kuma Abba yahya da yayi musu jagorar shigowa duba Abbie ɗin,wani irin kakkauran miyau Raihan ta haɗiya na tsananin kunya da tsoro,rasa yadda za ta yi da abin kunya yasa ta fashewa da kukan da ya fahimci sam baya yi mata wahala, a hankali ya bude idanunsa da suke a lumshe dan dubanta ya yi sannan ya maida kallonsa kan su Abbie da su kayi kamar basu gansu ba,fahimtar abinda yasa ta kukanne yasa shi ɗan zame ta daga jikinshi ya rike Duka hannayenta kanta a kasa tana faman murza idanun da suka ki tsayawa da ruwan hawaye,ji ta yi kawai yaja ta ba tare da tasan inda ya nufa da ita ba ta bishi,hannunta ya cire daga nashi ya saka a na Ammi odanunshi akan Ammi din da ta ki kallonshi,yasan wacece mahaifiyarshi sarai yasan abinda ya hanata kallonshi,ɗan murmushin da ba ko da yaushe aka cika ganinshi a kan fuskarsa ba ya yi kafin a hankali cikin sautin Muryarshi me tafiya da wata irin Hausa irin ta Fulanin da suka ji boko turanci ya zauna a bakinsu ya ce", Ammi ga RAIHAN", jin haka yasa RAIHAN saurin dago da kanta aiko ta ci karo da fuskar kyakkyawar mace me cike da kwarjini irin na danta tana yi mata kallon da zamu iya kiranshi kallon kauna ta fisabillihi da yadda da jin cewar ey lallai nayi suruka. Sosai Ammi ta damƙe hannun Raihan tana mata murmushi,ganin raihidin ta rasa sukunin sakewa da kunyar da wazer ɗin ya bata yasa Ammin janta jikinta tana cewa ya dai Raihan duk kukan rashin Abbie ne? Girgiza kai Raihan ta yi kafin cikin dan son sakewa ta ce", ina wuni Ammi? Lafiya kalau Raihan ya me jikin kuma? Alhamdulillah ta faɗa tana satar kallon Wazer da take jin idanunshi na yawo a jikinta, Ammi ta ce", ki yi hakuri kinji Raihan ko mai yana wucewa kamar ba a yi ba, kuma duk abinda kikaga ya faru da bawa to haka Allah ya tsara masa babu tsimi babu dabara abinda Allah ya zanawa mutum sai ya faru in sha Allah zai samu sauki kinji", a wannan karon sosai ta kalli Ammin kafin cikin jin wani kwarin gwiwa ta rungumeta tana ji kamar maminta ta rungume. Haka Abbu ta yiwa Raihan nasiha da rarrashi cike da nuna kulawa da kauna,shukra da kananan wazer duka babu wanda aka bari a baya wajen nuna tattalinshi da kauna akan Raihan ɗin,sosai Raihan taji kaunar wannan ahli masu tsananin mutunci karamci sanin ya kamata da uwa uba ilmin addini wanda komai za su yi sai sun saka Allah da manzo a ciki", wani irin sanyi zuciyarta da gangar jikinta su kayi, saboda yadda a cikin mintuna ta ga tsagwaran ƙauna daga ɓangaren wazer ɗinta, dole ne wazer ya kasance na musamman domin alhlinsa ma na musamman dinne. Duk suka fita daga dakin Raihan na tsakiyar umma rumana da shukra da suke ji kamar su tafi da ita gidansu tun yanzu. Rabi da a na mutuwa a dawo to zamu iya cewa ta mutu sau kusan dari ta dawo,a wannan karon ta kasa yin sambatun sai zare ido da take yi tana jin zuciyarta kamar zata faso kirjinta ta fito,tunda take gaisuwar mutunci ma bata taba samu daga shukra da rumana ba amma wai sune suke neman maida Raihan cikinsu saboda kauna,Ammi da bata taba kama hannunta ko da sunan fada ba bare har ta samu runguma ,amma yau Raihan makiyiyarta wadda ake kira da kishiyarta ita ce rungume jikin Ammi tana bata kulawa kamar ƙwan da ba ason fashewarsa,tafiya kawai take bata san in da take jefa kafafunta ba,duniyar ce kawai ke juya mata kamar katantanwa. Surry da tun ɗazu take zagayen neman inda zata ga ruby ta hangota kamar zata kifa bata san inda take cilla kafarta ba,da ace motoci na yawo a harabar gurin tabbas babu abinda zai hana wata motar yin awan gaba da ita,da sauri ta janyo ta tare da jefata cikin motarta da sauri suryn ta shiga mazaunin direba ta figi motar da gudu suka bar harabar asibitin. Haba ruby wai so kike ki tona mana asiri ne? Ke me yasa baki daukar abu ta yadda zai yi miki sauki? Wannan zafafawar da babu abinda zata yi mana saima aikin danasani da za ta yi mana", ihun da Ruby ta saka ne ya firgita sury har ta nemi sakin sityarin motar,amma dake Allah bai tsara musu mutuwa a lokacin ba sai ta yi saurin taka burki a gefan Titin tana maida numfashin firgici da tashin hankalin da ta shiga,idanunta akan ruby da ko gezau bata yi ba........✍🏽 Pg51 ƁOYAYYIYAR RAIHAN A tsorace Surry ta iya karasawa da ruby gida saboda yadda duk ta firgice kamar me haukan gaske,yau kayan mayen ma hauka ta yi musu dan sha kawai take yi babu lissafi bare tunani,ita dai Surry ta samu ta bar gidan dakyar zuciyarta cike da rashin jin dadin yadda plan dinsu ya rushe,gida ta wuce saboda ta samu nutsuwar yin tunanin abu na gaba duk da tasan cewa oganta zai yi wani abu akai. Ranar dai gaba daya a cikin asibitin suka yini sai dare suka koma gida,lokacin da su Ammi zasu ta fi ji ta yi kamar ta tafi da Raihan ɗin,to bare kuma oga wazer dan kuwa ba dan idanun baffa Ali da yake jin nauyi ba to da sai ya tafi da Raihan gidansa ko dan ta samu nutsuwar zuciya. Da yawa zuciyoyi sun dan fara samun salama,wasu sun dauki wani sabon burin wasu kuma suna ci gaba da yakin neman na baya,yayi da wasu suka yada makamansu kamar su mama murja da Mom Hanne ke nan,yadda suka yada makamansu haka suka jawa ƴaƴansu kunne suka fara gyara abinda dama sune suka bata. Washe gari dakyar RAIHAN ta hakura ta yi shirin fita office saboda rarrashinta da baffa Ali ya yi da kuma IDRES,wazer ne yazo har gida ya dauketa tare da sabbin gerd dinsa. ABBAN rabi ba karamin haushin wannan abu ya ji ba,da saka innawuro ya yi a gaba yana fada kamar zai a ri baki,a kan me wazer zai kori securitys din da ya kawo masa ya nemi nasa da kansa,dan shi bai san Abbu ne ya kawo su ba,sai da innawuro ta faɗa masa sai kuma duk yasha jinin jikinsa,bai dai kara cewa komai ba amma tabbas ya tsargu. Rabi dai bata iya komawa aiki ba saboda jinyar zuciyarta da bata gama ba,sannan har lokacin bata samarwa kanta mafita ba,gashi ganin wazer ɗin ma ya yi mata wuya.abin duniya duk ya dame ta,fargabarta bai wuce ace asirinta ya tonu ba,fatanta a yanzu Allah yasa kar wazer ya gano ita ce ta fidda jarida. Dufuty ya haye kujerar Gwamna a matsayin me rikon kwarya, Abba yahya kuma ya zama mataimakin sa ,ta wani bangaren kuma ɗan takarar gwamnan gobe,yanzu jiran lokaci kawai ake yi. Yau kwana goma sha biyu da abinda ya faru, Abbie har yanzu yana cikin commer,babban abinda yake damun ahlinsa ke nan shi yasa yanzu gidan ya koma tamkar gidan makoki,babu wanda ya fi RAIHAN shiga halin damuwa saboda ita abin biyu ya haɗe mata,har yanzu idan ta kalli hajiyar agadex sai taji faduwar gaba da tashin hankali saboda abinda taji tana fada ranar da ta fita gadin,gashi ta kasa yi mata maganar,hatta da wazer ta kasa gaya masa,kuma ba komai take tsoro ba sai amsar da zata ji daga hajiyar agadex ɗin bata san manufarta nayin abinda ta yi ba,ita yanzu zata iya cewa ma sam bata yadda da kowa ba a cikin gidannan tunda har zata iya kama kakarta da wannan mummunan laifin. Yau Sunday hakan yasa Raihan bata fita ko ina ba,tunda ta gama abinda take yi ta gudu bangaren inna maimuna,can ne kawai take zuwa ta samu yar mutawa saboda yadda inna maimuna ke matukar ɗebe mata kewa, Suna zaune a falon kanta na kan cinyar inna maimuna tana mata susar gashi da hakan ke matukar yi mata dadi, Abba yahya ne ya shigo ganin Raihan ɗin yasa shi sakin Murmushi yana cewa Raihan yar gatan mutane da yawa", dariya ta yi tana tashi daga kwancen da take ,gaida shi ta yi ta ɗora da cewa a'a fa Abba karfa ka manta wannan Raihan ɗin har yanzu zagaye take da makiya tunda har yanzu ba a gama gano su ba", inna maimuna ta yi saurin cewa hakane amma in sha Allah suma asirinsu na gab da tonuwa", Abba yahya ya ce in sha Allah kuwa, mikewa ya yi yana cewa bari na shiga ciki", yana wucewa Raihan ta dubi inna maimuna kana ta ce", innata ki tashi kije ki aikin lada kinsan dai Abba daga gidan gwamnati yake dole yana bukatar ki a kusa", rike baki inna maimuna ta yi cike da mamakin Raihan ɗin har zata yi magana sai kuma ta fasa amma fuskarta yalwace take da murmushi, itama raihan din murmushinne akan fuskarta har inna maimuna ta bace mata idanunta na kanta,sai dai kuma a yanzu wani irin kallo take Binta da shi idanunta har sauyawa su kayi,wata ƙil tausayin inna maimuna ne yake dagula mata lissafi kasancewar basu da yawan 'ya'ya shi kuma dayan da Allah ya basu ya zabi duniya a akansu. Numfashi ta ajiye tana mai daukar wayarta dake nuna haske alamun kira ne ke shigowa. A hankali ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya bayan jin sassanyan Muryarta da ya yi tana mishi sallama. Amsawa ya yi yana ƙoƙarin boye sirrin zuciyarshi da a kullum kara bayyana kansa yake,reihann ya fada cikin Muryarshi me zurfi da dadin amo", har tsakar kanta saida ya motsa saboda yadda Muryar tashi ta karbu a duk wata kofa dake jikinta. A hankali ta amsa tana kallon saitin corridorn da falon Abba yahya yake,me kike yi yanzu?babu ta bashi amsa har yanzu idanunta akan hanyar kamar me son gano wani abu", ok ga nan direba a waje ki fito ki same shi zai kawo ki inda nake", turo karamin bakinta ta yi kana ta ce", Ni kam me za kayi min? Cinye ki zan yi", ya fada yana wani lumshe shanyayyun idanunsa,uhmm ai dama ka saba cinye nin", ta faɗa kasa_kasa dan kar yaji,sai dai kuma ta makaro dan yaji abinda ta ce,amma sai ya basar cikin halin nashi na fuskewa,ki yi sauri yana jiranki" daga haka ya datse kiran, bin wayar da kallo ta yi,kafin ta mike a hankali can kasan ranta tana jin ba zata iya sarayar da bukatar wazer ɗin ba,duk da ta wani gefen tana tunanin amincewar maminta. Wayar da Abba yahya yake yi ya datse yana kallon inna maimuna dake tsaye tana kallonshi,lafiya naga kin tsaya haka kamar sojiya? Dawa kake waya? Abinda ya fito daga bakinta kenan a maimakon amsa masa tambayarsa,shima kai tsaye ya ce", da ita da danki bashir nake waya ko da wani abu? Babu ta faɗa tana kawar da fuskarta daga kansa zuwa bangaren wata sip dinsa dake dakin ta can kusarwar dake gabas maso yamma,kallon wajen da ta yi yasa shima ya kalla yana cewa maimuna lafiya dai ko? Dan ajiyar numfashi ta yi tana dawo da dubanta kansa sannan ta ce", babu kawai dai jiya ne misalin uku na dare na farka shiga toilet sai na ji kamar magana kasa kasa daga cikin kwabar nan", magana kuma maimuna a'a sai dai idan tsorata kika yi amma ya za ayi kwabar da ake aje kaya ta yi magana,da Allah ki kwantar da hankalin ki naga kwana biyu duk a firgice kike idan kuma da abinda ke damunki ki fada min,ya karasa maganar cikin kwantar da murya", babu wani abu na gaya maka ABBAN Bashir bari na hada maka ruwan wankan", binta da kallo ya yi kawai har ta shige bathroom ɗin. Lokacin da Raihan ta koma bangarensu bata sami aunty amarya ba,hajiyar agadex ke sanar da ita ta koma asibiti,dan haka sai kawai ta sanar da Hajiyar agadex cewa itama zata bisu yanzu wazer yana jiranta a waje, hajiyar agadex bata hanata ba tunda tasan waye wazer a wajensu baki daya. Daki ta Wada ta danyi represh din kanta tare da zura doguwar a bayar da a yanzu tunda ta fara shigar mata shigarta ke nan saboda tun a baya shigar doguwar riga ko wace iri ce tana burgeta. Tunda ta fito daga gate din farko take yan kalle kalle,har yanzu jin kanta take wata da ban,duk lokacin da ta yi shigar mata ta kanji alfahari da hakan kuma duk ta fito sai ta rude saboda yadda mutane ke kallonta kamar wata sabuwar halitta ta daban.yanzun ma tunda ta fito daga gate din security ke satar kallonta haka bayan fitowarta yan tsirarun mutanen da suke kaikawo a anguwar suke kallonta ba ko kunyar kallon dan ko ta kama mutum yana kallonnata baya dainawa,Tom inda sabo ta saba da hakan yanzu, tun daga ranar da ta fara fitowa a zahirin siffar ta ta cikakkiyar budurwa me tsananin kyawu. Ko a wajen aiki bata tsira ba da yawa mutane son mu amala suke da ita, dan kuwa kallonta suke a wata diya da Allah ya bawa baiwa ta musamman,hatta yan koren rabi a yanzu basa iya kallon RAIHAN su dauke ido, sactariya kuwa bata iya haɗa ido da Raihan saboda kunya da nadamar abinda ta rinka yi mata,ita kuwa Raihan bata cewa karkarinta gaisuwa dan kuwa ita kadai wazer ya bata damar yi da abokan aikinta sai kuma abinda ya shafi aiki",tsaf a cikin kwanakinnan take kiyayewa saboda ta lura da take takensa so yake ya hanata aikin gaba ɗaya. Da wannan tunanin suka ƙaraso gidannasa da a yanzu ta gama haddaceshi saboda zuwan da ta dan yiyyi. ___________ Zaune take bakin gadon da yake kallon Abbie,kallonsa take cike da tausayawa da karayar zuciya gani take kamar ba zai farka ba,idan ta tuna hakan ji take kamar zata yi hauka saboda tashin hankali,a hankali ta sa hannu ta share hawayen da suka gangaro mata kan kunci,wayarta ce ta yi ƙarar kira,duban wayar ta yi kamar ba zata daga ba sai kuma ta sa hannu ta danna ok tare da kara wayar a kunnenta,kafin cikin nustuwa ta yi sallama........ Cikin gaggawa Abba yahya ya gama shiryawa ya fito ,inna maimuna ya samu ta gama jera masa abinci,dubansa ta yi tare da cewa ina kuma zaka baka ci abincin ba? Bar abincin nan maimuna kira na samu daga gwamna me rikon kwarya,jin jina kai ta yi tana cewa shike nan Allah ya dawo da kai lafiya", Amin ya Allah ya fada yana karasa daura agogonsa. Aunty Amarya Tsugunne bata kare miki ba hajiya ramla akwai wani abu a ƁOYE Sannan akwai lauje cikin naɗi game da abinda ya faru a kwanakin nan,na baki satar amsa kyauta dan haka ki zuba ido kiga abinda zai faru,Ni masoyin ku ne dan haka kar ki shakku a kan dukkan abinda na fada mik....ji ta yi kamar an kwace wayar tare da kai duka me karfin da yasa ta runtse idanunta,ƙirjinta kuwa babu abinda yake sai duka,me wannan mutumin yake fada haka? Kuma waye shi? Meye a lakarsu da shi? Sannan me ye lauje cikin danin da yake fada? Akan wa laujen yake? maganar gwamna da mijinta ko maganar bayyana sirrin RAIHAN? Dafe kanta ta yi da yake matukar sara mata hakan ya sa ta mike da sauri ta fita daga dakin, kai tsaye office din Dr Sabo ta nufa dan warware masa wannan sabon tashin hankalin da ya kuma Kunno musu. WAZER....... A hankali yake juya dan karamin Flash din dake hannunsa,tunanin ta yadda a kayi ya shigo cikin kayansa yake yi danshi dai bai san na meye ba,gyara zamansa ya yi tare da janyo laptop dinshi dan saka plash din yaga me yake ciki yasan dole ta wannan hanyar zai gane na waye,sallamar da Raihan ta yi cikin sassanyar Muryarta ne ya dakatar da shi daga abinda yake shirin yi,aje plash din ya yi a gefansa yana Binta da kallon da take jinsa yana matukar tasiri a dukkan gabobin dake jikinta. Mika mata hannu ya yi alamun ta ƙaraso amma sai ta noke ta samu waje daga can gefe ta zauna tana sunkuyar da kanta, ganin haka ya sa ya dubi jikinsa,sai a lokacin ya tuna shigar dake jikinsa,babu riga a jikinsa daga shi sai dan shot boxer iya cinyarsa,maida kansa ya yi ya kwantar saman kujerar yana ci gaba da bata wasu irin kallo da take rasa inda zata saka ranta dan takura.a sace ta dago dan kallon shi sai a kayi katari idanunsu suka sarke,kokarin kwace kwayar idonta take yi amma hakan ya gagara sosai ya sarke nata cikin nasa,bata Ankara ba sai jin numfashinsa ta yi a gefanta har jikinta na gugar nashi, dan muskutawa ta yi cike da rashin sabon hakan,hannunta ya kama a hankali ya shiga murza yan yatsunta,kafin cikin gizagon shi fuskarshi kadaran kadaran ya ce ", ina aikin da na sa ki? Du ban shi ta yi kafin kawar da kai tana cewa Ni sam ban ganewa wannan aikin da ka sani yi ba, ai ba so nake ki gane ba", ya fada yana juyo da ita suna fuskantar juna", musayar numfashi suka fara yi,cikin sauri ta rufe idanunta tana cewa dan Allah hamma wazir ka sa kayanka ban iya zama kana a haka", mutum ma ko kunya baya ji ta karasa fada kasa kasa.mikewa ya yi kamar zai bar wajen sai kuma ya dawo a hankali ya sunkuya ya dauketa gaba dayanta yana cewa muje ki fada min me kika fara ganowa akan aikin da na baki idan kuma ba ki yi ba ton sai na cinye wannan dan bakin tsiwar drama queen kawai", harba kafafunta ta fara cike da yarinta tana cewa dan Allah kar ka cinye min baki dame zanci abinci idan ka cinye,ba Gara ga kaci kayan dadi ba kuma ma ai Mayu ne suke cin naman mutum", dan ware idanunshi ya yi a kanta daidai lokacin suna kawowa cikin hadaddiyar bedroom dinsa da take tashin wani irin kamshin sa da ya gama kame komai nasa,a jiyeta ya yi yana lalubo idanunta dan mayar mata da martanin maganarta,bai samu kallon tsakiyar idanunnata ba hakan yasa ya janyota zuwa naked jikin nashi da take gudu yana cewa babu wani kayan dadi da ya wuce wanda ke tare dake sannan maita ai kowa ma maye ne akan kayanshi dan haka ki fadi abinda kike so ko me za ki yi yau sai na cinye ki gaba dayan ki", wayyo Allah Mami Abbie ta faɗa idanunta na cika da ruwan hawaye saboda bata san wani irin cinyewa zai yi mata ba dan haka ta ji tsoro sosai ɓaram ma da ta ji yana wani irin shafa jikinta da take tafiya da sulbin doguwar abayar dake jikinta .........✍🏽 52 ƁOYAYYIYAR RAIHAN Girgiza kanta ta fara yi saboda yadda take jin tsigar jikinta na wani tashi da abinda yake matan,mutsu_mutsun kwace kanta ta fara yi dan kaucewa abinda ke shirin faruwa wanda sam bata shirya masa ba,rike ta wazer ya yi sosai yana wani shigar da idaunsa ciki tamkar wanda yake jin bacci,cikin rawar murya ta ce", umm um zanje hospital Mami na can tana jira na", wannan aikin da za ki yi yafi na Mami lada", ya fada yana sauke zip din rigarta kasa ba tare data sani ba,bata san sanda tasa hannunta ta zagaye shi ba tana cewa dan Allah dan Allah ka bari", waro idanunta waje ta yi jin rigarta na yin kasa,wata irin kara ta ƙwallah tare da hade jikinta da nashi da yake naked ta wani irin kamkameshi,kasancewar ya sake jikinshi kawai sai suka faɗa saman tattausar shimfidar gadonshi tana samanshi yana ƙasa,sosai Raihan ta fashe da kukan tsoratar da ta yi,shi ko wazer wani miskilin murmushine ya kwace masa yayin da tuni kwakwalwarshi ta fara aikin manta a duniyar da yake ciki sakamakon jin tudun breath din ta a ƙirjinshi, Raihan kuwa tashin hankalin da ta shiga ba kadan bane saboda tasan ba bra a jikinta doguwar rigar kawai ta zura ta fito bata taba tunanin za a kai matakin da wazer zai cire mata riga ba. Dago ta ya shiga kokarin yi amma kam ta manne shi tana faman zubar hawayen sangarta,ash ya fada yana ɗan rintse idanunsa, da sauri ta dago kanta dan ganin abinda ya sashi yin wannan dan ihun,tana dagowa ya nuna mata ƙirjinta da girar shi,duka ta shiga kai masa tana kananun kukanta,hakan ya bashi damar kara kusanta ta da shi tare da dago kanta ya shiga lashe hawayen da yayi dama_dama a saman fuskarta a hankali har ya gangaro bakinta wanda baiyi wata_wata ba ya shiga bata zazzafan kissess din da yasa ta hadiye kukanta ba da shiri ba,ta kuma manta da cewar babu kaya jikinta. Cikin wata irin kwarewar da baisan yana da ita ba ya shiga juyata da bata wani irin zazzafan romance da ya kusa zauta karamar ƙwaƙwalwarta,shinshina take yi yana shakar kamshinta ji yake tamkar ya maida kansa jikinta saboda yadda kamshinta yake gigitashi lasar wuyanta yake zuwa ƙirjinta yana sakar mata wani dan Marayan nishi wanda yake sata jin sanyi har ciki bargonta..... Aunty Amarya..... Kuka sosai take yi tana bawa Dr Sabo labarin abinda mutumin ya ce mata babu ko batan wasali saboda yadda abin ya zauna mata tamkar karatu,bai hana ta kukan ba sai da ya bata lokaci ta Gama dan kanta ta share hawayenta sannan cikin nutsuwa ya ce", ramla ki yi hakuri in sha Allah komai zai zo karshe kuma ina so ki rike wannan kar ki sanar Da kowa dan yanzu ba kowa za mu saki jiki da shi ba,shi kansa gidannan naku yana bukatar saka idanu,shi yasa nake so ki kwantar da hankalinki dan mu samu damar bincike a nutse,shi mutumin da nomber ya kira ki ko ya boyeta? Mika masa wayar ta yi dan ita bata da lakar iya dubawa.karba ya yi ya duba jim kadan ya dago ya kalleta kana ya ce", nomber ce dan haka zansa a yi tracking nomber in sha Allah za mu gano duk wani mugu da ke tare da mu,jin jina kai ta yi ba tare da ta iya cewa komai ba....ta shi ta yi ta fito daga office din tana jin kwarin gwiwa duk da cewa har yanzu tsoran bai sake ta ba,tsoran rasa Raihan da mijinta, Tana bude kofar ta yi mummunan gani,ganin da yasa jinta da ganinta suka fara gushewa,matar da ba ta gane ko wacece ba ta gani kan Abbie tana danna masa filo da iya karfinta burinta kawai Abbie ya karasa inda ba a dawowa,karar da aunty Amarya ta saki ne ya sa matar sakin filon da sauri ta juyo kasancewar facemask dake fuskarta shi yasa Aunty Amarya bata shaida ko wace ce ba, duk da yadda jikin Aunty Amarya ke bari hakan bai hanata kokarin kama matar ba, sai dai ina tuni matar ta angije Aunty Amarya ta fice a sukwane,duk da yadda Aunty Amarya ta yi matukar buguwa hakan bai hanata ci gaba da kokarin tashi dan kama matar ba.da gudu securitys suka shigo saboda jin karar da Aunty Amarya ta yi,suna shigowa suka tarar da ita kwance tana taga tagan tashi hannunta na nuna kofar shigowa, da sauri nos suka dagata suka dora akan gado cikin kankanin lokaci suka fara bata taimakon gaggawa,Dr Sabo ne ya shiga musu fada akan abinda ya faru duk da basu san komai ba,dakin cc camara ya nufa bayan ya tabbatar da tsaron dakin tare da gargadi me girma ga Saken da securitys din sukayi,lokacin da cc camara ta shiga nuna abinda ya faru kasake ya yi yana kallo cike da mamakin wayo irin na matar,baya yasa aka dawo maana tun shigowar matar,a nan yaga yadda ta yi ta shiga wato wasu ta fara turowa bakuwar fuskar da ba a sansu ba suka nemi shigowa nan securitys din suka hana shigar ta su wanda hakan ya janyo cece kuce tsakanin mutane biyun da securitys din,wanda ita kuma da wannan damar ta yi amfani ta shige reseption din har ta shiga dakin ba tare da hankalinsu ya kai kanta ba. Hankalin Dr Sabo ba karamin tashi ya yi ba,da sauri ya koma ya kira sauran likitocin da alhakin kula da Abbie yake hannunsu suka rufu akansa dan duba lafiyarsa,cikin ikon Allah suka ga bata yi nasarar karasashi ba amma fa tabbas Abbie yana cikin critical condition sai dai kawai mu bi shi da addu'ar samun sauki,tunda rayuwar ba a hannunmu take ba. Sosai take aje numfashi bayan fitowarta daga asibitin Allah ne ya taimaketa duka securitys din duk yawansu basu kula da ita ba amma tabbas da sai sun biyota kuma sai sun kamata,har yanzu ƙirjinta bai daina bugu ba dan kuwa hakika ta tsorata,kallon mai nafef din nata ta yi tana cewa maza maidani inda ka dauko Ni", ok Hajiy... Bai karasa fada ba yaga mutum ya zauna gefan nafef din yana cewa muje fuskarshi sanye da facemask shima", cikin razana ta ce", kamar ya muje babu inda zaije sai ka sauka inda zaka ba nan muka nufa ba", ke da ba mashin ɗinki ba Hajiya ina ruwanki", ya fada yana juyawa tare da yin kasa da facemask dinsa,wani irin dafe kirji ta yi kafin cikin rawar baki ta ambaci sunansa Yusuf meya kawoka nan? Abinda ya kawo ki shi ya kawoni", ya bata amsa yana maida facemask dinsa,kar ki tsoarata ba tona miki asiri ne ya kawoni gareki ba,kawai ina so mu hada hannu ne,dan da ace tun farko nasan me yasa aka boye RAIHAN da tuni na nemo makashiyar RAIHAN ɗin dan hada hannu da ita kuma da baki riski kanki a tashin hankali irin na yau ba,dan haka kai me dan sahu muje waje mafi sirri inda za muyi ɓoyayyiyar ganawar sirri tsakanin masu son kama abu guda,ba dan ta gamsu da abinda ya fada ba ta amince sai dan kawai tana tunanin ko da da wata manufar yazo ita tafi shi wayo da sanin duniya dan haka tasan yadda zata fidda kanta ta barshi. Tun fitowar su Khalid ABBAN rabi yake tsaye yana kallonsu jin zuciyarsa yake tamkar zata buga saboda tsananin tsana da kyashi da hassada,tunda suka dawo wazer ya dora su akan harkar Companys ya tsara musu komai dan haka suka bi suka dabaibaye komai,ya zamana bashi da wani babban matsayi duk abinda zai shiga ko ya fita sai da saninsu,gashi kuma bayan su din har wasu ma'aikatan wazer ya kuma diba masu tsananin kaf_kaf ko mai a tsare yake tafiya yanzu sabanin da,gashi yanzu cikin kwanakin da basu fi goma ba abubuwa sun fara daidaita a Companys din,shi yasa ABBAN rabi yake cikin wata irin takura gashi duk wata hanya da zaibi dan ganin ya kawar da wazer hakan ya ci tura,wata irin kwafa ya yi yana jin ba zai iya ci gaba da kallon kayan takaici ba a gurin shi,dan haka a maimakon ya shiga gidan kawai sai ya koma cikin motarsa ya bata wuta ya kwashe ta a tsiyace", duban juna salim da Khalid su kayi kafin suka kwashe da dariya dan su din shakiyai ne na kin karawa ba kamar yayansu suke ba,duk tsayuwar da abban rabin yake suna kallonsa kawai sun dauke kansu ne a zuwan basu Ganshi ba dan duk hakan yana daga cikin tarkon da suke son yi masa. Cikin bakin ciki ya shiga falon gidansa a nan kuma ya yi katari da rabi a gaban mahaifiyarta tana rusa mata kuka", turus ya yi yana kallonta kafin cikin tsawa da son huce haushin kaza kan dami ya ce", ke kuma sakarya me aka yi miki kike mana kukan jan mutuwa? Rarrafawa ta yi gaban shi ta rike kafafunshi tana cewa Abba wazer ne baya sona yau kusan kwana goma ban sashi a idona ba wai kuma a matsayin muna gida daya,idan na kai karar sa gurin innawuro sai ta hauni da fada wai bani da aji su kuma iyayensa ba ganin laifinsa suke ba,Abba tunda aka yi auren mu sau daya ya yi kwanciyar aure da Ni," zama ABBAN rabi ya yi ba tare da fuskarshi ta nuna alamun rashin dacewar maganarta ta karshe ba,saima cewa da ya yi rabi har yanzu kina son Wazer? Abba a da ina son wazer amma tunda ya ci amanata ya auri waccan yar daudun shike nan na ji ya ficen a rai wallahi Abba yanzu ko kasheshi zan iya yi,amma fa da zai dawo gareni ina son shi ba zan iya rayuwa babu shi ba", kai kaji sakarya da wani zance inji mamanta da duk zancan bai wani shigeta ba,shike nan yi shiru kisha kuruminki ba dai waccan aljanar yarinyarce ta hanashi kallonki matsayin mace ba? Jinjina kanta ta yi kamar wata yarinya,yauwa to kisha kuruminki dan waccan aljanar bana ji zata kai labari saboda gaba daya kewaye take da makiya na gida dana waje kinga kuwa wannan ba abinda zai dame ki ba ne kina zaune cikin inuwa zaki ji mummunan labari akanta,Ni dai fatana ki samu ki jawo hankalinsa ki samu ciki dashi a yanzu wannan shine babban burina ", ya fada yana sake wani lissafin da tun abaya bai yi shi ba sai yanzu lallai lokaci yayi da zai amfani da rabi a domin samun cikar burinsa,da zarar rabi'a ta samu ciki da wazer zai kashe shi idan ya kashe wazer kuwa dukiyarsa dole ta rabi a da dan dake cikinta ne,wani bushashshan murmushi ya yi yana dan jin salama a ransa. Kebabban gurine da ba kowa ne yasan da gurin a cikin yalwataccen birnin na Yola ba,sai daidaikun mutane basu cika son shiga jama a ba,zaune suke a kan kujerun gurin sai tebur dake tsakaninsu,har yanzu bata bayyana masa fuskarta ba domin bata gama yadda da shi ba,numfashi ya aje kafin ya ce", duk da cewa na bibiyi labarin abinda ke faruwa da Raihan kuma ta haka ne na nemo ki amma ba shine yake nufin cewa nasan ko ke wacece ba,nasan dai kina cikin gidan nan amma ban san wacece daga cikin gidan ke son daukar ran Raihan da mahaifinta ba,tunanin da nayi kuma yasa na biyo ki shine na son abu guda da mu kayi tarayya a ciki,duk kuwa da cewa mahaifina ya so yin hakan sai dai bai kai ga ci ba asirinsa ya tonu,yanzu ina so na dora daga inda mahaifina gwamna ya tsaya dan haka zanso sanin ko ke wacece saboda amanata da zan baki",kuma ki sani cewa wannan abun da za mu yi kusan kece da ribar fiye dani", wani makirin murmushi ta yi kafin ta numfasa ta ce", Yusuf karka sake ka yaudare Ni domin fada dani babu abinda zai jawo maka sai karewa a fanko", shima murmushin ya yi Sannan ya dauko jakar da take makale a wuyanshi ya budeta,takardu ya shiga zarowa har sai da ya zarosu duka sannan ya dubeta kana ya dubi takardun,mika mata su ya yi gaba daya yana cewa ki duba wannan kadan daga cikin kadarorin RAIHAN ne dake wajen mahaifina", tirkashi cikin rawar jiki ta karba hannunta na rawa ta shiga dubawa,iya dubawarta bata ga alamar fake ba, tabbas wadannan takardun na gaske ne,dagowa ta yi tana kallonshi da idanunta da suka nuna tsananin mamaki ta ce", ya akayi ka samesu? Dage kafada ya yi kafin ya ce", wannan ba abin mamaki ba ne a wajena tunda kinsan dai waye mahaifina a wajen Abbie kuma kinsan cewa komai na RAIHAN yana gunsa idan kika cire biyun da Abbie ya bawa yan uwanta dan sukula mata dashi", tabbas a yanzu na yadda da kai to amma me yasa tunda ka samesu ka biyo ta gurina ? Gyara zamanshi ya yi tare da cewa kinyi tambaya mai kyau,na farko dai dole ne na samu mataimakin da zai dinga share min hanyar bi", na biyu kuma dole ana bukatar sa hannun mallakar wannan dukiyar Kinga ke nan dole muna bukatar sa hannun RAIHAN,kuma ba kowa ne zai yi wannan aikin ba sai ke,tunda a gidansu kike tunda kike cikin gidan kuwa dole kina da kusanci da RAIHAN dan haka ke zaki yi duk dabarar da zaki yi Raihan ta sa mana hannu da zarar tasa hannu shike nan komai ya zama namu", ya fada yana kallon fuskarta", wata irin dariya ta sheke da ita babu kakkautawa,har zuciyar Yusuf ta fara rawa da shiga fargaba sai kuma ya ji ta tsagaita da dariyar tana cewa ban taba shiga yanayi na farinciki irin yau ba tabbas Yusuf ban san abinda zan saka maka dashi ba,sai yanzu na kuma yarda da kai da nayi wani tunani barewa ba za ta yi rarrafe danta ya kasa ba dan haka na amince za muyi tafiyarnan tare,amma duk da haka ba zaka ga fuskata ba sai ranar da komai ya daidaita na karbi sa hannun RAIHAN ", wannan ba damuwa ba ne danni ban damu da nasan koke wacece ba kawai fatana shine ki rike amana kalas", daga haka ya tashi ya barta zaune bayan ya karbe takardun a zuwan idan ya gama tattara su gaba daya zai dawo mata dasu. WAZEER RAIHAN.... Sosai wazer ya yi nisa gun bawa kansa nutsuwa ta hanyar romance din Raihan,yadda yake fada zai cinye ta din ko tabbas ya kusa cinye tan,saboda yadda yake lashe komai nata bakinta kuwa tamkar zai tsinkeshi saboda tsotsa har yana jin ba zai iya barin Raihan ɗin ba duk da zuciyarshi na mashi rawa da tuna yadda ya samu rabi a,to amma yasan zuciya ce kawai Raihan dinsa da ta yi rayuwa a matsayin namiji killatacciyar matar da Ubangiji ya yi masa,shi kansa yasan idan zuciyarsa tayi shakku akan Raihan to lallai shedan ke son hanashi samun nutsuwar da bai sameta akan rabi a ba,yaso samun nutsuwarsa da Raihan amma tausayinta da sonta sun hanashi karasa kaiwa inda yake son zuwa," cikin maida numfashi ya jawota jikinshi sosai ya rungume yana jin ɗimin jikinta na ratsashi ga wani kamshi da bai taba jinsa a ko ina ba yana shigewa hancinsa yana kuma bashi nutsuwa. Ita kuwa Raihan tsananin kunyar cinyetan da wazer ya yi yasa ta kasa ko kwakwkwaran motsi dan har ga Allah kunyar haɗa ido take yi dashi,a hankali yasa hannunshi saman lallasar fatar bayanta yana shafawa kamar me shafa kwai,cikinta da ya shafa yasa ta ɗan motsawa,a hankali cikin kamammiyar Muryarshi ya ce", kina son zuwa gida"? tura baki ta yi idanunta har sun kawo ruwa saboda tunanin abinda zata cewa maminta,zata yi magana kenan wayar shi ta fara fidda wani sauti me sanyi,kamar ba zai dauka ba sai dai tuni Raihan da tafi kusa da bedside drower da wayar ke aje ta janyota, a hannunta yaga me kiran hakan ya sa ya karba wayar yana mai komawa asalin wazer Chibado ba wazer ɗin dake gaban Raihan ba.assalamu alaikum ya fada cikin dakakkiyar Muryarshi ta mazan da suka san kansu,Yusuf ya akayi ina fatan ansamu cigaba?.........😨wane yusuf din kuma jama a ku taya Ni ji....✍🏽 53 ƁOYAYYIYAR RAIHAN Ina fatan dai kai kadaine? Yusuf ya fada daga can bangaren", umm um wazer ya fada yana kallon RAIHAN da ta zura masa ido", to ka dan matsa maganar tana da dan tsawo", A hankali wazer ya zare Raihan dake kanannade a jikin shi,kana ya sauka daga gadon ya fida daga dakin gaba daya wayar na a kange a kunnenshi. Wani irin kallo Raihan ta bishi da shi haka nan zuciyarta take saka mata cewa da budurwa zaiyi waya shi yasa ya kebe kansa dan kar taji,ji ta yi ƙwallah sun cika idanunta,ta shi ta yi ta faɗa toilet ta wanke jikinta sannan ta fito ta zura doguwar rigarta,gaban mirror da yake cike da manyan turaruka ta tsaya tana kallon turaren duk saninta da turare sai taga wasu da yawa bata sansu ba,dan tabe baki ta yi tare da daukar daya daga ciki nanfa ta samu abinyi dan duk yawan turarukan da suke gurin sai da ta yi wanka da su,dan ma suna da sanyin kanshi da ita kanta sai sun dameta. A hankali ya samu daya daga cikin kujerun da suka kuma ƙawata dan kyakkyawan lambu ln wanda yake cike da shukar kayan marmari ga wani dan sweeming pool wanda baifi ya ci mutum uku ba a wadace shima ya kuma kawata lambun,zama ya yi tare da harde kafafuwanshi waje guda sannan cikin deep voice dinshi ya ce", Yusuf ina jinka, dariya Yusuf ya yi kafin cikin shaƙiyanci ya ce", ai na dauka ka koma ruwa ne ka cigaba da gurzar yar mutanen,mutum a haka kamar ba zai aikata ba,nan kuwa SOYAYYA ce fal cikinsa", ban san iskanci ka sanar dani abinda ya faru ko na kashe wayata", cikin komawa serious Yusuf ya ce", ok gaskiya wazer tunaninka me kyau ne duk da cewa kafin na kama matar nan nasha hawala amma gashi daga karshe munyi nasara", ka gano fuskarta? Wazer ya tambaya Yusuf cikin kara maida hankali kan batun,a'a gaskiya ban samu ganin fuskarta ba saboda tana da matukar wayo,duk bibiyar da nake mata dan mu samu haduwa banci nasara ba sai a yau da ta shiga asibiti dan karasa Abbie",runtse ido Wazer ya yi yana hadiye jin zafinsa,bai yi magana ba shima yusuf din yasan ba maganar zaiyi ba dan haka ya cigaba da cewa, wallahi wazer na so matar nan ta nuna fuskarta saboda mukawo karshen makircinta ita da irirenta,sai dai ban samu hakan ba,amma duk da hakan munyi nasara tunda har ta yarda dani daga karshe ma nuna mata nayi bana bukatar ganinta aiki ne ya hada mu dan haka mu yi abinda yake gabanmu kawai,da wannan na kawar da tunaninta har ta yi min alkawarin duk ranar da Raihan ta sa hannu a takardun nan zata bayyana min kanta,kaga ke nan ya zama dole mu sanar da Raihan iya abinda ya sauwaka dan ta bamu hadin kai gurin gano matar ta hanyar sa hannunta", na gode Yusuf ina fata dai bata samu nasara akan Abbie ba ? Yusuf ya bashi amsa da cewa ey bata samu ba amma gaskiya a yadda na saurari bayanin Dr Sabo tabbas yana cikin condition din da sai dai mu taya shi da addu'a ,sai ita kuma mami matar ta Yar da ita dan haka ita ma an bata gado amma itama lafiya in sha Allah rauni ne kawai a goshinta saboda buguwar da ta yi", ajiyar zuciya wazer ya dan saki kafin ya ce", da Yusuf na gode Yusuf", wazer ba kaine zaka min godiya ba nine zanyi godiya hakika ba dan kai ba ba za mu taba Ankara da abinda ke faruwa ba daga Ni har Abbana,jin jina kai wazer ya yi kana ya ce", shima haidar muna kan bibiyar lamarin za mu samu abinda muke so very soon his excellency zai fita daga kullin da a kayi masa", daga nan sallama su kayi. Yusuf yana aje wayar ya dawo da kallonshi kan mahaifiyarsa da baya boye mata komai,sannan a ganinshi dole itama tana da hakkin sanin saboda mijinta a garkame a matsayin me laifi,Hajiyata wallahi wazer aminin kwarai ne shi yasa bana fatan abinda zaisa na juya masa baya ko na ha ince shi", jinjina kai Hajiya Turai ta yi kafin cikin sanyin jikin da ya sarketa tun bayan kama mijinta da hukuma ta yi ta ce", yanzu yusiwa kuke tunani da wannan kullin? Hajiyata har yanzu akan bincike muke,amma yanzu da ace za mu samu haidar to tabbas kamar mun gano mai laifi ne,kaf gidan suna cikin zargi shi yasa ba mu tsaya akan mutum biyu da muka fi zargi ba,hatta da matansa bincike muke akansu dan acikin wannan kullin babu wanda zamu bari kowa abin zargi ne in kika cire baffa Ali da mahaifiyarsu,ita kuma Hajiyar agadex wazer yasanar dani cewa yana zargin kamar ta san wani abu da ya shafi abinda ya faru da Abbana,dan haka itama Binta muke sannu a hankali,in sha Allah gaskiya zata bayyana.allah yasa ta faɗa tare da cewa to batun jaridar bayyana RAIHAN fa? Dariya Yusuf ya yi sannan ya ce", Hajiya baki san waye wazer ba,jinsa kawai kike, wannan batun tun a ranar ya gama da shi cikin awa daya ya gano matarsa ce rabi a", dalilin da yasa bai dauki wani mataki ba shine ita kanta rabi'ar bai yadda da wannan kawar Tata ba ya ce itama yana zargin wani takewa aiki akan Raihan ɗin shi yasa ya kyale su ai talala ya yi musu kawai", to alhamdulillah Allah Ubangiji ya da da kare mu, Ni wallahi tausayin ramla duk yafi damuna gashi nan duk abinda ta yi na boye RAIHAN ɗin babu abinda ya kara mata,umm um Hajiyata ya kara mata mana akwai hikima da kaddarar Allah a cikin abinda Aunty amarya ta yi,dan haka mu jira muga abinda Allah zai yi gaba. WAZEER RAIHAN........ Tashi ya yi cikin nutsuwa,ya fita daga lambun ya koma cikin falonshi ta wata kofar da ban ba wadda ya shigo ba, Da RAIHAN ɗin ya ci karo a tsaye a falo ta cika ta yi fam idanunta har sun gaji da zubar ruwan hawaye,cikin takunshi na cikakkun maza masu ji da kansu ya ƙaraso inda ta kafe tana son fashewa,Mrs WAZER CHIBADO me kuma ya faru? Kwabe fuskar ta yi hawayen na sake gangarowa,cikin wani salo ya fidda idanunshi waje ganin hawayennata kana ya kuma cewa haba Queen of tears ya haka da kuka? Janyo hannunta yayi ya haɗe da nashi kafin ya fara leken idanunta da ta ki bari ya kalla,umm waye ya taba ki yanzu na bulale shi? Jin batun bulala yasa ta yi saurin Dagowa tare da nuna shi da yatsanta manuniya,kawar da fuskarshi ya yi yana ɗan sakin murmushinsa me sanyi,kafin cikin nutsuwarsa ya kuma cewa me nayi to Kinga ba a yin hukunci saida dalili ", cikin san fashewa da kukan da take ta makaleshi ta ce",kaine saboda zaka yi waya da budurwarka ka tashi kabarni a daki Ni daya ba,ta kare maganar cikin kukanta me karamin sauti,sosai murmushi ya kwace masa amma dan kar ya kuma yin laifi yasa ya haɗe jikinsu ya cusa fuskarsa cikin wuyanta yana cewa sorry ba da budurwa nayi waya ba,ai kin san wazer bashi da budurwa bashi da kawa,ko na baki wayar ki duba? Shiru ta yi bata bashi amsa ba,numfashi ya sakar mata me dumi yana cewa Raihan kina nufin da wannan turaren zaki fita ?wa ya ce ma ki saka ? Baki san ke matar aure ba ce? Yadda yake maganar kasa_kasa yana feso mata hucin bakinshi da yake hade da kamshin strawberry shi yasa ta ji tsigar jikinta na wani irin tashi,dago fuskarta ya yi suna fuskantar juna fuskarta cikin tafukan hannayenshi,bakinshi ya kai a hankali ya tsotsi tsinin hancinta sannan ya lashe hawayen kafin cikin Muryarshi dake fita kasa kasa ya ce", kina min asarar hawaye da yawa idan na shanye wasu nasan dole wasu zasu zuba yadda kike Sarkin hawayen nan", sauke kanta ta yi murmushi na fita daga kyakkyawar fuskarta, zuba mata ido ya yi yana jin kamar su yi ta zama ahaka,kaf rayuwarshi bai san da akwai abinda zai kaunata bayan mahaifiyarshi ba,bai taba sanin zai so wata mace kwatankwacin son da yake yiwa Raihan ba, Raihan wata tsokace me haɗe da jini a cikin jikinshi,ba zai misalta ba ,ko da a aikace ne sai dai ya kwatanta, gangar jikinshi da zuciyarshi sunyi kadan su iyakance kaunar da yake wa yarinyar nan, Jin shiru ya sa ta dago kanta aiko idanunta da nashi suka yi arangama, da sauri ta yi kokarin kawar da fuskarta shi kuma yayi zafin naman rike fuskar, kafin a hankali ya kaiwa idanunta sumba yana cewa i lake dis eyes and dis ya fada yana dawo da bakinshi kan hancinta shima ya bashi sumba ɗaya, sannan ya dawo kan bakinta yana cewa i lake dis cute mauth so much", ya karasa fada yana hade bakin su waje guda, sumbatar bakin yake idanunshi akanta,sam baya jin zai gundura da yarinyar na. Sosai fa ta yi masa mamaya,yana so ya hakura ya Kaita gida amma mayen sonta ya na hanashi yin nesa da ita,shi bai da tabbas Raihan na sonshi amma ya na da tabbacin zai iya zama da ita ko bata sonshi ya kare rayuwarshi cikin bautawa SOYAYYArta. Sassanyan Muryarta ce ta dawo dashi daga duniyar soyayyar da yake ji babu kamar tasa,Hamma gida ina tsoran mami ta rigani dawowa kasan ita fa har yanzu haushinka take ji", kina so ta daina jin haushina? Ya tambayeta alokaci daya yana zama da ita akan kushun din dake daf dasu,bata bashi amsa ba sai kokarin tashi dake yi,maida ta ya yi bisa cinyarshi a maimakon da take kusa dashi,yar harara ta bashi shi kuma yaja dogon hancinta yana cewa yarinya naso tana kaiwa kasuwa", turbine fuska ta yi tana kai mishi karamin duka a kirji,rungumeta ya yi sosai yana shakar kamshinta da ta bulbula kusan mintuna goma suna a haka kafin ya sake ta dan kanshi yana cewa ki zauna na shirya na kaiki muga mami sai mu dauketa mu wuce gida", ta ce tana asibiti ne har yanzu? Ta tambaye shi tana duban hadaddiyar agogon dake rataye a bangon falon", shafa fuskarta dake da matukar kaushi ya yi yana cewa in sha Allah tana nan", daga haka ya shige bedroom. Maida idanunta ta yi ta lumshe su tana jin wani abu me girman dala da gauran dutse a cikin ranta,tunawa ta yi ta ce", da baffa Ali bata son wazer idan komai ya daidaita za a raba auren", wani irin tashi ta yi zaune daga kashingiden da take,hannunta dafe saman ƙirjinta,to ke Raihan me ye hakan ai kin san dama dole zaku rabu tunda shi dama yana na da matarsa azabbiyar mata kuwa,mele bakinta ta yi tare da kaiwa kofar bedroom dinshi kallon harara tana cewa Ni kam ba zan zauna da wannan mahaukaciyar ba,Gara a rabu,a rabu fa,duk sanda ta ambaci kalmar sai ta ji faduwar gaba,girgiza kai ta yi tana kuma cewa a'a ba wannyne me muhimmanci ba sanin inda haidar yake shine me muhimmanci duk inda muka samu haidar na tabbata za mu samu videon nan daga nan dole a kama su shugaban jam'iyya da Dr sanater,dama hujja kawai muke nema",ta gumi ta yi da hannayenta biyu tana tunanin ta yadda za su samo HAIDAR, Tree full y trues in sha Allah sai na samoka ko namiji kake ko mace nasan kai kadai zaka yi min wannan taimakon", waye kuma tree full y trues? Wazer ya tambayeta yana fitowa daga dakin cikin shigar kananan kaya da suka yi matukar amsar jikinsa da yake shan geming ,tashi ta yi tsaye dan bata bukatar su kara bata lokaci ba tare da sunje asibitin ba, Sannan ta dubeshi cikin irin basarwar da ta koya a gurinshi ta ce", ai kasan ko waye, ina son samo shi saboda ya taya Ni neman haidar da inda videon su shugaban jam'iyya yake dan shine kadai abinda zan tabbatar a samu a kamasu ba tare da anyi wata makarƙashiya an sakesu ba,da ace iya shaidata ta baki zata gamsar da kotu tabbas da tuni an shafe babinsu an wuce gun", ana ta gagga wa yake ta wasu kananan kwari", ya fada yana jan hannunta,su waye manyan kwarin to? Bai bata amsa ba har suka fita ya bude mata gaban motar ta shiga,kallonshi kawai take tana jiran amsarshi sai dai shi din uban yan miskilanci ya fiske tamkar bashi ya yi maganar ba,ganin haka yasa itama ta yi shiru har suka fita daga gidan babu wanda ya kuma tankawa dan uwansa. Wazer na yin fakin a harabar asibitin hamma Idris ma ya yi fakin, a tare suka fito suna nufar juna", hamma Idris ne ya fara bashi hannu suka yi masabaha yana cewa ashe kana tare da mutuniyar", ya tambaya idanunshi akan RAIHAN da ta yi kicin kicin saboda amsar da wazer ya ki bata,wazer bai bawa Idris amsar tambayarsa ba saima wucewa da ya yi cikin reseption din kai tsaye, sosai securitys din suka bincika su kafin su barsu su shiga duk kuwa da cewa sun san dangantakar dake tsakaninsu da me jinyar,amma wannan umarni ne me zafi daga ogansu me asibitin wato Dr Sabo akan cewa ko waye ya zo su tabbatar da sunyi bincike me kyau kafin barin sa ya shiga, Idris ne ma yaso yin gaddama acewarsa yana ɗan Abbie amma ace sai an bincike shi bincike me zafi kafin ya shiga wajensa, Raihan ce ta rarrasheshi sannan ya hakura yabarsu su kayi aikinsu. Turus Raihan ta yi ganin bandeji a kan maminta,sai kuma ta karasa da gudu ta rungumeta cikin rudewa ta fara tabata tana cewa me ya sameki Mami ? Waye ya miki haka? Rike RAIHAN ɗin Aunty Amarya ta yi ganin yadda duk ta rude har ta fara halinnata wato kuka", calm down Raihan ki nutsu babu abinda ya same Ni faduwa na yi a bathroom shine a ka yi min dressing", kwanciya ta yi ajikinta cikin damuwa tana cewa to Mami amma babu zafi ko? Babu zafi Raihan gida ma nake shirin tafiya na kira Idris ya kaini,ey na Ganshi tare muka shigo ya tsaya duba wani abokinsa ne, Raihan ta faɗa tana dago fuskarta daga jikin mamin tare da kallon inda wazer yake ", karasowa ya yi cikin nutsuwa yana gaida Aunty Amarya da yi mata sannu da fatan Allah ya kiyaye,ganin yadda Raihan ta zuba mata ido idanunta cike da kwallar da take jiran kiris ta zubo yasa ta amsawa babu yabo babu fallasa,daga haka ta mike ta shiga hada kulolin abincin da suka kare tana cewa Raihan ki sallame shi ya wuce mu zamu tafi da Idris", kallon Wazer ɗin Raihan ta yi fuskarta a marairaice kafin ta yi magana ya sa hannu ya yafitota,kana ya juya ya fita,duban mamin ta yi sannan ta ce", to Mami bari na gaya masa na dawo", ina jiran ki ta faɗa tana ci gaba da gyarawa Abbie mayafinsa, zuciyarta kuwa babu dad'i dan ba a san ranta zata tafi ta barshi ba,dan kawai Dr Sabo ya bata baki ne kuma ya tabbatar mata da cewa Abbie yana cikin tsaro me kyau in sha Allah babu abinda zai kuma faruwa. Tana fitowa ta sameshi a mota ya kwantar da kansa jikin sitiyarin idanunsa a lumshe kamar me bacci,shiga ta yi motar tare da dan taba kafadarshi tana cewa yaya wazer kayi hakuri ka ta fi za mu tafi da mam.....kafin ta larasa fadar abinda ke bakinta ya tashi motar tare da rigarta duk alokaci guda cikin zafin namanshi, wayyo dan Allah ka bari za mu tafi da mami", ba za ta same ki a gidan ba inda kika fito zaki koma,yanzu sai ki fada min wanda ya fi iko tsakanin Mami da mijinki? Ya karasa fada yana dage mata girarshi guda so very gentle.zata fara halin ya dora yatsanshi kan bakinta tare da cewa kar ki sake ki fara bana bukatar zubarsu a kasa ko bari idan munje gidan sai kiyi Nima a nan ne zanfi shanye sh dakyau", aiko mukut ta hadiye su ta kuma kame bakinta ta yi tsit kamar wata yar babyn dake tsoran bulala.........✍🏽 TOFA WAI YA HAKA NE INJI GWANJA, KALLO DAI DA ALAMA ZAI KOMA SAMA TABBAS DAI BAYA CE ZATA HAIHU MAKIRA KIN KUSA ZUWA HANNUN MAZA. HIS EXCELLENCY WAI ME YE A KASA NE....IDAN BA KAI BA NE WAYE? ABBAN RABI KIFI FA NA GANINKA ME JAR KOMA HAJIYAR AGADEX WAI YA TAKE NE MUNA SON SANI NI DA MASOYAN RAIHAN...... KU BULBULO MIN COMMENTS NI KUMA NA BULBULO MUKU AMSOSAHINKU IDAN BA KUYI COMMENTS BA ZAN TAFI YAJIN AIKIN KWANA GOMA KO NA MAIDA SHI FAIN NA TAFI AREWABOOKS NA SAMU YAN CANJI NA😂 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivat the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page54 ``` 54 ƁOYAYYIYAR RAIHAN Aunty Amarya tana gama hada kayan ta fito dan tarar Raihan a waje sai su wuce, Duban HAMMA IDRES ta yi tana cewa wai ina Raihan dinne? Dariya Idris ya yi yana cewa aunty Amarya kawai kizo mu wuce dan ita Raihan akan idona tabi mijinta suka tafi", ɗan jim ta yi kafin ta yi kwafa ta shige motar, shima Idris din shiga ya yi yana kunshe dariyarsa, dan kuwa abin ya bashi dariya lallai Aunty Amarya ta hadu da sirikin zamani. Suna zuwa gidan HAMMA IDRES ya yi mata sallama ya wuce bangaren mahaifiyarshi,lokacin da ta shiga falon babu kowa dan haka kai tsaye dakin Raihan ta nufa,wayam babu ita har bathroom saida ta leka amma babu Raihan babu dalilinta,fita ta yi ta shiga dakin hajiyar agadex in da ta samu HAJIYAR AGADEX na lazumi,katsewa ta yi tana duban Aunty Amarya ta ce", ke kuma lafiya ruɗadɗa gaba daya kin kasa kwantar da hankalinki sai ka ce akanki a kafara jarabta,ganin HAJIYAR ta fara fada yasa ta ɗan nutsu sanan ta tambayeta ko Raihan ta dawo? Bata dawo ba wani abu ya kuma faruwa ne? Girgiza kai Aunty Amarya ta yi kana ta ce" wazer ne ya ce ze kawota gida ni kuma mun taho tare da Idris shi yasa nake tambaya ko sun ƙaraso" to basu ƙaraso ba wata kila suna hanya,to wai ke meye damuwarki da haka wazer fa mijin Raihan ne duniya ta shaida hakan dan haka ki bar wani rawar jiki nan kusa kusa zata tare a gidanta dan munyi magana da shi Baffan harda iyayen wazer ɗin dan haka sai ki fara shiri ", Hajiya tarewa fa kika ce? A haf zancan kike so ,Ni a ganina hakan shine maslaha kuma Raihan sai tafi samun tsaro idan tana gidanta tare da mijinta,yau muka yi maganar shi yasa ban samu gaya miki ba,itama raihan din daina fita ko ina za ta yi saboda gyara za a fara yi mata", ko mai Aunty Amarya bata ce ba,dan tasan cewa ko da son ranta ko babu tunda suka yi niya sai sun Kaita,yo a kayi auren ma ba da saninta ba bare kuma tariya,fita ta yi daga dakin zuciyarta cike da wasiwasi akan wazer ɗin, to amma fa maganar hajiyar su tana kan hanya tabbas Raihan sai tafi samun nutsuwa a gidan aurenta gidan aurenma gidan WAZER. Cikin nutsuwa baffa Ali ya dubi Abba yahya kafin ya dan yi gyaran murya ya ce", yahya abinda yasa nace duk dare idan ka shigo ka biyo nan ina son magana shine a ɗazu da yamma munyi wata shawara nida iyayenka mata hajiyarku ta nan da ta can agadex akan cewa mu sanar da iyayen wazer da shi kansa Raihan ta tare nan da sati daya hakan sai yafi kwantar mana da hankali akan duk wani tashin hankali da muke ciki, Allah ne me kiyaye bayinsa amma duk da haka idan tare sai ta fi killatuwa da samun tsaro a gidanta",a hankali Abba yahya yasa hannu ya dan share zufar da ta fara tsatstsafowa akan goshinsa sannan ya dubi baffa Ali cikin fitar da murmushin yake ya ce", haka ne Baffa amma Ni a ganina a dan dakata zuwa sati biyu domin muga yadda jikin Nura zai kasance idan so samune Raihan ta tare bayan warkewar mahaifinta saboda ita kanta sai ta fi samun nutsuwar da muke yi mata fata,nifa a tawa shawarar",ya karasa fada idanunsa akan baffa Ali domin ganin yadda zai karbi zancannasa, jinjina kai baffa Ali ya yi sannan ya ce", kazo da magana kaima,amma ai kaima uba ne ba shawara ya kamata ka bayar ba umarni za ka bayar tunda da kai da kaya duka mallakar wuya ne dan haka zamu bari zuwa nan da sati biyun idan har Allah bai sa Nura ya farka ba to TABBAS RAIHAN zata tare a dakinta,sai dai cikin ikon Allah muna fatan farkawar nur in sha Allah", na gode baffa hakika babu abinda zance da kai sai dai na ci gaba da yi maka addu'a har kashen rayuwarka abinda ka yi min ko mahaifina ne sai haka,ina alfahari da kai ta yadda ka samar min da dan uwa na gari wanda duniya ke alfahari da shi,tunda gashi har zuwa yau babu wanda yasan cewa ba kaine ka haifeni ba hatta da matata bata san cewa ba kaine mahaifina ba", ya karasa maganar yana zubar da hawayen nuna tsananin kaunararsa ga wannan bawan Allah", murmushi baffa Ali ya yi kafin ya dafa kan Abba yahya ya ce", bana son kana damun ka ko ka dinga taso maganar da muka binne ta iya mu imu Allah shine shaida ban daukeka a dan mata ba sai dana na cikina", na gode baffa", daga haka ya mike tare da yiasa sallama ya fita daga falon. Kamar walkiya haka ya ganta a gabansa ta na binshi da kallon mamaki ta cikin hasken da ya dallare farfajiyar katafaren gidan", cikin mamaki shima yake kallonta kafin ya bude baki ya yi magana ta rigashi ta hanyar daga masa hannu fuskarta na fidda wani irin haske me kyalli ta ce", Yahya dama kai ba dan cikin Ali ba ne? Bata saurari amsarsa ba ta cigaba da cewa tabbas buri yayi kama da mutum", HAJIYAR AGADEX me kike nufi da biri ya yi kama da mutum? Dariya ta yi matsakaiciya sannan ta ce", Yahya saboda kai na cire kunya na dawo gidan suruki da zama shin kai hakan bai baka mamaki ba asa ilin da ka tsinci mace mai alkunya da kawaici cikin gidan surukinta a matsayin mazauniya ba,? Tabbas Yahya jinnu ba karya ba ne sai dai ba komai suke sani kamar yadda mutane suke zato ba ,suma basu san gaibuba duk abinda kafa sun sani to tabbas ya wanzu ne a lokacin da suke kusa da gurin saboda su su kasance iska shi yasa suke finmu sanin abinda yake ɓoye,amma ba ko mai ne Allah yake basu damar sani ba Allah shi kadai yake da sani a kan komai kuma shine yasan gaibu, shi yasa Nima ban gama sanin komai akan ka ba sai a hankali ta hanyar bincike na da bin kokofina Allah ya ke nuna min daya bayan daya,dan haka ka daina bacci da sanin cewa babu wanda yasan abinda kake shukawa kuma ka daina bacci da tunanin cewa asirin boye ba zai bankaɗa ba,dan haka ka zauna cikin shirin ka domin maza suna nan bisa kanka saura kadan dan hakin da ka raina ya tsole maka duka idanunka", ba tare da ta bashi damar yin magana ba ta yi gaba ta barshi a wajen tamkar wani status. ________raihanwazer....... Bata san me yasa ya sauya tunani ba dan har sun kusa karasawa gidannasa sai kuma.ya juyo ba tare da ya tanka mata ba,ajiyar zuciya ta sauke ganin ya dawo da ita gida,yana yin fakin ba tare da ya dubeta ba ya ce", ina so ki min wani aiki amma bana bukatar tambayar ki ko guda kawai kiyi abinda zan umarce ki", bata ce komai ba amma dai tana saurarenshi, dan cije labbanshi ya yi yana kewaye gidan da idanunshi sannan ya ce", ina so ki samun ido akan fuskar duk wadda ta baki wasu takardu dan saka hannu ko ta wace irin siga ce,ki rike min fuskarta ko ita wacece a gidannan da kuma matsayinta ", daga haka ya ce", muje na raka ki", duk da cewa zuciyarta cike take da wasiwasi da dinbin tambayoyi akan abinda yake kira da suna aiki,haka nan ta fito ba tare da ta furta su ba,kuma dole zata yi masa abinda yake so domin ta hakikance ba zai taba cutatawa rayuwarta ba. Saida yaga shigarta sannan ya juyo, dai-dai lokacin Abba yahya ya baro gurin da HAJIYAR AGADEX ta tsaida shi da maganganunta da suke neman saka shi hauka,baima san cewa ba hanyar bangarensa ya ya nufa ba saboda tsabar yadda yake jin kwakwalwarshi na tsalle tana hargitsa duk wani tunaninshi,kicibus suka yi da wazer ɗin da yake takawa dan zuwa gurin da ya aje motarshi, kallonshi wazer ya tsaya yana yi saboda ganin gana daya baya hayyacinsa baima ga wazer ɗin ba,gyaran murya wazer ya yi Sannan cikin nutsuwarshi ya ce", Abba yahya Barka da War haka", a dan zabure Abba yahya ya dawo da hankalinshi bakinshi na rawa yana cewa lafiya lafiya me kike nufi da wanɗannan maganganun naki? Zuba masa ido Wazer ya yi kafin ya jefa masa tambaya ", Abba yahya lafiya kake kuwa", sai alokacin ya dan dawo hanya cikin rawar baki ya ce", lafiya umm umm sai kuma alokacin yaga inda yake nufa dan haka cikin hanzari ya juya ya nufi bangarensa jikinsa da komai nasa dake motsi rawa yake", binsa da kallo wazer ya yi kafin ya dan dage kafadunsa sannan ya shiga mota ya bar gidan. Kamar anjefoshi haka ya fada falonsa,inna maimuna dake zaune tana jiran shigowarsa ta yi saurin mikewa tana cewa lafiya dai ABBAN Bashir? Bai kulata ba bare ta san ran zai bata amsa,wucewa ya yi kamar wata kububuwa yana shiga dakin ya rufo da key dan karma ta ce", zata biyo shi,cikin rawar jiki ya fara danna kiran BASHIR", kira daya ya daga daga dake su a lokacin dare baiyi sosai ba,Bashir duk yadda za ayi ka bar kasar nan ka dawo gida gobe a yanzu babu bukatar zamanka anan," to Abba me ya faru ne? Na ce maka ka dawo ko Bashir ya fada cikin tsawar da bai taba yi masa ita ba", to Abba An dawo amma ya zanyi da jeniper? Iska Abba yahya ya fesar sannan ya ce", ka ka taho da ita kasan dole muna bukatar ta dan ita ce last hope din mu gurin tsohuwa me jini barinta a nan hatsari ne," shike nan Abba yanzu zan fita na yi buking pilot ", daga haka ya sauke wayar ya shiga kewaye dakin kafin daga karshe ya dangana da toilet dan zubda ruwan da ya cika masa ciki. Raihan dakin hajiyar agadex ta nufa kai tsaye,tana shiga HAJIYAR ta ce", dama nace mata kina hanya", zubawa HAJIYAR ido ta yi tana jin zuciyarta na kasa yadda da abinda ta ji kuma ta gani tun a wancan ranar, wannan abun yan daya daga cikin dalilan da suke hanata sukuni duk lokacin da ta tuna,hakan yasa ta juya ta bar dakin ba tare da ta tankawa HAJIYAR ba, murmushi HAJIYAR AGADEX ta yi tana cewa zaki fahimci ko mai in sha Allah,komai ya kusa zuwa karshe an kusa yin walkiya kowa ya ga fuskar munafukai ", daga haka ta kashingida a katifarta tana ci gaba da laziminta cikin tsarkake Ubangijin talikai wanda ya halicci zuciyoyi. Kai tsaye wazer main Hause dinsu ya wuce kasancewar dare yayi shi yasa bai shiga ko ina ba ya wuce bangarensu,har zai wuce dakinsa sai kuma ya dawo da baya ya bi ta kofar falonsa ya nufi dakin rabi a", kokarin murɗa hadle din kofar yake amma sai ya dakata saboda surutu da ya jiyo sama sama kamar ma hayaniya ce ta barke tsakanin masu tattaunawar,cikin fusata rabi a dake magana a yanzu ta ce", Surry ban fa kira ki kwana a gidana dan kici mun mutunci ba wai ya kike so na yi duk abinda muka shirya akan Raihan sai ya wargaje idan ban dauki matakin kasheta ba me zanyi? Surry ta ce", ba za ki fahimceni ba rabi a ba ina nufin ki rabu da Raihan ta ci bulus ba ne kawai so nake ki dinga bin abun a hankali idan ba haka ba kuwa kwabarmu zata yi ruwa ba tare da mun cimma abinda muke son cimmawa ba,dan haka nake so ki bar maganar kashe Raihan yanzu mu bi tsarin oga a karo na biyu", tsaki rabi a ta kuma yi a karo mara adadi sannan ta ce", wai rabi a waye wannan ogan dakike ta faɗa nifa bana son shigo da bare cikin aikina kar a samu sabani", dariya Surry ta yi sannan ta ce", Nima kaina so nake na san ko waye abinda kawai na sani a kansa shine yana da kusanci da RAIHAN harma na fara tunanin anya ba a cikin yayyayenta yake ba,abinda isa ban maida hankali kan sanin ko waye ba bashi ne a gabana ba cikar burina shine kawai abinda nake kallo", wani kallo rabi'a ta watsa mata kafin ta watsa mata tambaya,cikar burinki ko cikar burina,? Dubanta auri ta yi sannan cikin mamaki ta maida mata da tambaya", burinki ba nawa ba ne kawa? Ajiyar zuciya rabi'a ta sauke tare da cewa haka ne, Ni yanzu bani waɗan nan abubuwan na dan kora so nake nayi bacci sosai ko na dan samu nutsuwa," Barin bakin kofar ya yi yana dan dade kanshi,bai yi mamaki ba saboda dama yana zargin rabi a da kawarta,tunanin yadda zai bi takansu dan ya san komai cikin nutsuwa ya fara yi,tabbas ta hanyar Surry ne kawai zai gano dayan makiyan boyen da ya shige cikinsu yana basaja da fuskar muminai,talala zanyi muku gaba dayanku sai kuma shigo hannu ba tare da kunyi zato ko tsammani ba,ya fada yana shigewa cikin shaya bayan shigar shi bathroom dan samarwa kansa nutsuwa ta hanyar zubawa kanshi ruwa. WASHE GARI __________ Cikin nutsuwarsa da kamala ya fito fuskar nan a gimtse kamar me", kamshinsa tare da takunsa shi ne ya karade gidan gaba ɗaya. A bazata suka Ganshi sam basu san ya dawo gidan ba balle su yi tunanin yana cikinsa,zaune suke a falo sunyi baja_baja da kayan kari Surry a na ta zubi saboda babu a Hause,tuni lomar farfesun da take shirin kaiwa bakinta ta tsaya ita bata sauke ba ita bata kai bakinta ba, ruby kuwa kallonshi ta tsaya tana yi tana hadiyar miyan da ta babu ranar da zata daina hadiyarsa,bai kalli ko wacce daga cikin su ba,ya nufi hanyar kiching,basu san me ya shiga yi ba sun dai ga ya fito ya nufi hanyar fita falon gaba daya,sai da yazo gab da fita sannan cikin dakakkiyar Muryarshi me tafiya da wani irin amo ya ce", kar na dawo a same ki a gidannan tare da dan juyowa yana watsawa sury kallon da ya kusa sata datse harshenta,daga haka ya fice cikin sassarfar takunsa me cike da izza. Yana ficewa Surry ta shiga hada kayanta tana cewa bari ki ga na bar masa gida tun kafin yasa a yi yaga yaga da namana,ko sauraren ruby ba ta yi ba ta bar gidan tana ayyana ranar dawowarta a matsayin matarsa dan tasha alwashi ko da tsafi sai ta aure WAZER. *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivat the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page54 ``` *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page55 ``` Tana fita ta samu wani me a daidaita yana ɗan kakkabe nafef dinshi da alama dai wani ya aje ya tsaya yana ɗan tsaftace nafef din da alama kuma irin gayun nan ne masu tsafta, tafiya za kayi? Ta tambayi me nafef din da sai alokacin ya juyo yana kallonta hannunshi rike da duster ya ce", haba Hajiya tafiya zanyi mana Ni da na fito neman kudi har a tambaye Ni tafiya zanyi",ina zaki je? Ya dora Mata tambaya bayan ya gama bata amsa,shiga nafef din ta yi tana cewa muje zan nuna maka inda zani,haba Hajiya ya za ai na dauke ki bamu yi tsada ba," ko nawa ne zan baka muje kawai", ok Hajiya dama irinku muke son dauka wannan shi ake kira dauka daya yafi yawon awa Biyar ", ya fada cikin irin muryarsa ta gayun samarin erea,shiga ya yi yana shirin tada Babur din wani saurayi ya ƙaraso gurin da sauri yana cewa kai haba dady da wucewa za kayi ka barni dan rashin amana? Dariya wanda aka kira da dady ya yi yana cewa kudi na gani ya za ai na tuna na daukoka dalla shiga mu wuce kana batawa Hajiya lokaci",ita dai Surry har yanzu bata ce komai ba sai wayarta da ta dauko ta danna tare da karawa a kunnenta ta ce", oga a ina zan sameka? Ban san me aka ce mata daga can bangaren ba ta dai kuma bada amsa da cewa ey ban fito da mota ba yanzu haka ina cikin a dai-daita, ko me ya ce mata da yasa ta ɗan kalli me a daidaitan da wanda ya dauka daga baya dake gefanta sai kuma ta maida hankalinta kan wayar ta cigaba da cewa banga alamun matsala a tare da su ba amma tunda baka amince da zuwana a nafef din ba bari na sauka sai ka turo a dauke nin kamar yadda ka ce ", tana kashe wayar ta dubi me adaidaita da aka kira da suna dady ta ce", yauwa bari na sauka a nan kawai", ok Hajiya ba damuwa ya fada yana gangarawa bakin hanya,daidai lokacin da wanda ya dauka daga baya ya dan sunkuya kamar zai dauki wani abu bai fi sakan goma ba kuma sai ya dago ya cigaba da sha'anin gabansa,kokarin bude jakarta take yi ta bashi hakkinsa amma sai ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa jeki kawai Hajiya ai ba mu yi tafiyar da zaki bada kudi ba", fasa bude jakar ta yi tana cewa shike nan na gode amma da ka bari saboda na yi niyar yi maka kyauta",,no maind Hajiya ya fada yana jan Babur din da dan gudu. Tabe baki Surry ta yi kafin cikin bayyana murya ta ce", ka huta. Sai da suka tabbatar sunyi mata nisa sannan dady ya dubi abokinsa yana cewa ka tabbata ka ɗauke wayar kuma ka makala mata wannan madaukar? Dariya Salim ya yi yana cewa kasan bana wasa da aikin oga baya goya marayuya fada yana nuna masa wayar sury", haka ne cewar dady yana ɗorawa da cewa Wallahi salim har yanzu Ban yadda cewa Khalid ya ci amanar oga ba gani nake kamar akwai wani abu a kasa ",tabbas tunanin mu ya zo daya kuma Ni ba kowa nake tunani ba sai abu Huraira", exactly tunaninmu iri daya ne", to idan haka ne kuwa salim lallai ya kamata bayan wannan aikin muma ya kamata mu bada tamu gudummawar domin sakawa wazer da RAIHAN hidimar su a garemu duk da cewa ba za mu iya sakawa Wazer abinda ya yi mana a rayuwa ba",sanan shi kansa Khalid ya kamata musan wani abu akan shurunsa dan ko da ace ya aikata wannan laifin ba za mu kasa haduwa a wani waje ba in dai yana garinnan",ɗan jim Salim ya yi sannan ya ce", gaskiya dady dole mu binciki abu Huraira dan gaskiya ina matukar zarginsa kuma ta wajensa ne ka dai za mu san inda Khalid ya ke", dady ya ce in sha Allah za mu yi abinda ya kamata,yanzu dai yi sauri ka karasa copy din wayar nan mu mayar mata kar ta gano mun dauka bare tunaninta ya kai kan mun canja mata", ai har na gama ya fada yana maida wayar aljihunshi. Juya a daidaita sahun Dady ya yi suka koma wajen da suka aje Surry ,daidai lokacin ne wata bakar mota ta yi fakin a gabanta,da sauri Salim ya fita yana cewa Hajiya dan tsaya", tsayawa ta yi tana kallonsa cike da mamaki,kafin ta yi magana ya mika mata wayarta yana cewa ina ga garin sauka ki ka yar da wayarki", da sauri ta karba tana cewa kuma wlh ban Ankara ba amma gaskiya na gode sosai", abubuwan da suke dauke a wayar nan suna da matukar muhimmanci na gode sosai ta kuma fada cike da jin dadi", kar ki damu Hajiya", ya fada yana shirin komawa cikin nafef din,da sauri ta dakatar da shi tana cewa ko zaku bani nomber ku duk sanda nake bukatar zuwa wani wane na kira ku,kasan karfen nasara ba tabbas gare shi ba", haka ne hajiya kawo na saka miki", mika masa wayar ta yi ya saka mata nomber sannan ta kuma yi masa godiya ya koma cikin adaidaita suka wuce,ita kuma ta shige motar da oga ya turo mata suka tafi. Tafawa su kayi salim ya ce ", aiki ya tafi dai-dai yanzu mu wuce office kawai mu fara takan abu Huraira muga shi kuma dame za mu same shi", haka za ai Dady ya fada yana kuma bawa nafef din wuta. __________ Sury na fita daga gidan rabi a ta nufi kiching jikinta har rawa yake", saliha me aikinta ta gani tana wanke_wanke,ke salaha me wazeer ya shigo ya yi a kiching dinnan? Cikin dan mamaki salihar take duban ruby kafin cikin rashin sanin abinda uwar dakinnata ke nufi ta ce", yaushe ya shigo ai Ni tunda na shigo babu wanda ya shigo kiching dinnan", ke dalla rufewa mutane baki,ruby ta faɗa cike da hasala,bata kuma cewa komai ba ta bar kiching din. Binta da kallo saliha ta yi kafin cikin sanda ta fidda kananun madaukan da wazer ya bata har guda uku,ya ce", daya ta tabbata ta saka a dakin ruby daya kuma a falo dayan kuma tasa a kiching ɗin,dan haka cikin sauri ta nemi guri mafi sirri ta makala ɗaya,sannan ta cigaba da wanke_wankenta kafin kuma ta samu damar makala na falon da dakin tunda tasan ruby zata fita aiki". Cike da matsanancin mamaki inna maimuna take kallon dannata tare da matarshi,murza idanunta ta kuma yi dan tabbatar da abinda idanunta ke gani ba mafarki ba ne", fitowar Abba yahya da jin Muryarshi yasa ta kuma tabbatarwa ba mafarki take ba,me ya kawoka gidana? Tambayar da Abba yahya ya jefawa Bashir ke nan bayan shigowarsa tsakiyar falon,diri_diri Bashir ya shiga yi irin na marasa gaskiyar nan sannan cikin nuna nadamarsa ya shiga bawa ABBANnasa hakuri ,dan Allah Abba kayi hakuri ba zan iya jurar rayuwa babu ku ba shi yasa na tattaro iyalaina na dawo gida", da sauri inna maimuna ta ce", dan Allah abban Bashir kayi hakuri hannunka fa baya rubewa ka yanke kayar yaron nan shi kadai Allah ya bamu to me zai sa mu sarayar da abinda Allah ya bamu", kamo hannunsa da na matarsa ta yi tana cewa muje ku huta kuci abinci daga baya ma yi maganar", wani irin duba dan da uban suka yiwa juna tare da murmushin da yake dauke da manufofi masu tarin yawa. Suna shigewa Abba yahya ya mike yana cewa Finally Bashir ya dawo dan haka ba zan taba bari abinda yake shirin faruwa ya faru ba indai na cika Ni din jinin babana ne", daga haka yasa kai ya bar gidan gaba ɗaya. ____________ RAIHAN tana gama shirinta ta fito tsaf kai baka ce ita ce wannan Raihan ɗin dake shigar maza ba,sanye take cikin doguwar rigar a tamfa me zaiba kalar Koriya wadda ta yi matukar amsar dirarran jikinta fuskar nan tayi fes da ita danma akwai alamun damuwar yanayin da suke ciki a tare da ita ", sama_sama ta sha tea da dan chips da maminta ta tsareta taci duk da cewa cike take da Raihan ɗin akan Wazer", Raihan dinma na sane da hakan amma sai ta basar taki bari ma su haɗa ido da mamin bare tasha tuhuma ta ido tunda babu damar magana HAJIYAR AGADEX na kusa ta tsare gaba ta tsare baya. Tana fitowa suka hadu da hamma Affan da Idris zasu fita tare", cikin mayalwaciyar fara'a wadda a yanzu take bawa Raihan mamaki hamma Affan ya ce", kanwa har kin fito? Aje mamakinta a gefe ta yi itama tana marabtarsa da ƙayataccen Murmushin dake karawa fuskarta kyau", ta ce", ey wlh hamma Affan na fito ai yau ban fito da wuri ba ma",Barka da safiya", ta faɗa idanunta na komawa kan yamma idiris da yake kallonsu cike da jin dadin yadda yan uwannashi suka fara gane Gaskiya ", HAMMA IDRES Barka da safiya ? Barka dai my sis", za ki biya ta asibiti ne ko sai kin dawo? Hamma Idris ya tambayeta", a'a sai dai idan na dawo yau da akwai aiki da dan yawa a office", ok mu can zamu fara zuwa mama Hanne tun da sassafe ta wuce( kasancewar yau girkinta) ok RAIHAN ta faɗa tana shiga motarta. A tare suka bar gidan kowa ya nufi inda zashi. A tare suka shigo buldin din da rabi a ,ita Raihan bata kula da ita ba ,amma ita rabi'a kaf hankalinta na akan Raihan ɗin,cikin nutsuwa ta kashe motar ta fito cikin kamshinta dake dauke hankalin mutum duk da cewa kuwa kadan ta saka saboda dokar wazer amma saboda yadda ya kama jikinta yasa baya buya,tana bayyana a guri shine zai fara isar da sakon zuwanta,ga karin cabbasa da tun fil azal take matukar sonshi idan maminta na yi amma sai ta hanata ta ce", na mata ne,shi yasa yanzu da ta yi free kullum cikin turara jikinta da kayanta take yi. Wani kallon uku saura rabi a ta yi mata tana wani yatsina fuska da hanci saboda yadda kamshin RAIHAN ɗin ya bugeta, Allah wadaran naka ya lalace matar shige dai ba daraja take yi ba", sai a lokacin Raihan ta kula da ita dan haka ba tare da ta kalli inda rabin take ba ta wuce zuwa office dinta dan ita kallon mahaukaciya takewa rabin yanzu dan haka bata da lokacin sauraren ta. Wannan abu da Raihan ta yi ba karamin cin zuciyar rabi'a ya yi ba dan haka tasha alwashin kafin a tashi saita saka Raihan kuka, ba dai ta bari tasan lagonta ba(kishi) murmushi ta saki tare da kwafa tana wucewa office din ta. A office dinta ta samu Salim da Dady,cikin mamaki take dubansu kafin ta ce", ya da sammakon jira? Dady ne ya amsa mata da cewa matar oga da wuri ake kama fara shi yasa muka garzayo gurinki dan ki fara bamu taimakon farko na dabarun kama fara", zama ta yi tana aje karamar jakarta da laptop dinta akan teburin dake mamaye a gurin, sai da ta aje kana ta dube su cikin son su fahimtar da ita abinda suke nufi. Fahimtar hakan yasa cikin nutsuwa salim ya warware mata abinda suke bukata da kuma nazarin da suka yi akan al'amarin", murmushi ta yi sannan cikin gamsuwa da bayaninsu ta ce", na gode Salim kuma Naji dadin wannan batu na ku in sha Allah zan baku hadin kai mu yi bincike me kyau,duk da cewa akwai aiyuka masu tarin yawa akanmu to amma shima wannan din babban al'amari ne da Yakamata a duba,so amma ba za mu dinga haduwa a nan ba a duk lokacin da wani abu ya taso saboda Bama son wani ya Ankara da dukkan binciken da muke yi gudun samun mishkila", haka ma ya yi cewar salim daga nan suka yi mata sallama suka koma bakin aikinsu". Misalin karfe biyu ta nufi office din wazer dan gabatar masa da fayals din sabbin rahotonnin da zasu shigar a wannan satin. Rabi a da duk wani motsin Raihan yake kan idanunta ta yi saurin bin bayanta,bata bari sun hadu ba ita sai tabi ta lipter dan ta rigata zuwa,ita ko Raihan ta upstairs ta bi,hakan yasa rabi'a ta rigata isa office din OGA. Rabi'a da ta fara zuwa ita ta fara shiga kafin Raihan ta iso,ɗan jim sactariya ta yi gashi babu halin ta hana Raihan ɗin shiga dan tasan cewa Rabi'ah na ciki kuma tabbas akwai abinda ta shirya tunda ta ganta cikin gaggawa dan ko iso bata bari ta yi mata ba ta shige. Haka nan tana ji tana gani Raihan ta bude office din ta shige. Dan turus ta yi ganin rabi'a a tsaye tana dan waige_waige da alama inda zata ga wazer ɗin take nema", Raihan bata kulata ba aje takardun dake hannunta ta yi sannan ta nufi dakin dake cikin office din,zaro ido rabi'a ta yi tana cewa kan uba lallai yarinyar nan har yanzu baki san waye wazer ba,to wallahi in kina son kanki da arziki kar ki shiga masa dakin office danshi dakinsa sirrinsa ne babu wanda yake ganin makwancinsa sai ishashshiyar mata", ta karasa fada tana sakin dariyar mugunta saboda tasan tabbas Raihan bazata bar shiga ba shi kuma wazer ba zai bar dizgata ba. Ko kallo bata ishi Raihan ba kuma bata daina tafiya ba,shiru rabi'a ta yi tana jiran ta jiyo tsawar da wazer zai yiwa Raihan me by ma har hankadota zaiyi dan ba mutunci ya cika ba a fadarta. Bai jima da dawowa daga sallah ba ya shigo room din offece din dan ya samu ya dan huta, dan sosai yau din ya gaji saboda kai kawon da ya danyi akan binciken da yake.a hankali ya shiga bude idanunsa da suke a lumshe ga kuma alamar gajiya da ta kuma maida su wani iri,kamshinta ya shaka kafin cikin kasalar da ta kara lullubeshi ya mika hannunsa gareta,a hankali take takawa zuwa inda yake yayin da ya kafe ta da ido yana kallon yadda jikinta ke kadawa kamar reshen bishiya gashi dai ba wasu kayan fidda halitta ta saka ba amma gani yake komai nata ya fito kirjinnan das da shi kamar an dorasu Masha Allah. Ganin taki karasowa ya kasa hakuri ya mike Gaba dayansa ,taku daya ya yi ya cimmata baiyi wata wata ba yayi mata wata kyakkyawar runguma tare da bata sumba a forehead dinta yana cewa Miss U MSR AHMAD bakaramin ba zata kalmar da rungumar su kayiwa rabi'a da ko mai ya kasance akan idonta saboda yadda ta kasa hakurin ganin Raihan cikin fushi da damuwa. Kafin ta fita daga tashin hankalin da ta shiga ta kuma fadawa wani,saboda yadda wazer ya kama lips din Raihan yana tsotsesu kamar dama jira yake yi........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page56 ``` Runtse idonta ta yi tana jin numfashinta na kaiwa sama kamar za a fincike shi,wai me yasa duk sanda ta yi shirin mugunta wa Raihan sai abin ya koma kanta, bata taɓa tabbatar da cewa Wazer yana yiwa Raihan son so so irin na mutuwa wanda zaka iya sadaukarwa ba sai yau,tasan halin Wazer sarai ko lokacin da take zuwa gidansu kwanaki kafin yasan tana son sa sam baya bari su shigar masa daki daga ita har Ummu rumana bare kuma shukra,kai ko innawuro duk yadda suke bata jin ta taɓa shiga dakin wazer haka kawai,kuma ita ma ko da ya aureta sai da ya yi mata kashedi in dai har bashi ya kirata ba kar ta sake tana shigar masa daki kai tsaye,shi yasa ko yanzun tayi tunanin zai koro Raihan,duk da tasan cewa Raihan tana da matsayi a gurinsa amma bata yi tunanin abin ya kai haka ba,a hankali ta fara ja da baya hannunta saitin zuciyarta da take jin kamar zata fashe. Wata irin tsanar wazer take ji tare da sonshi me zafi suna kuma babbaka zuciyarta. RAIHAN sarai ta hango rabia ta jikin glass din window,shi ko oga kwata_kwata baisan ma tazo aikin ba bare yasan ta shigo office dinsa. _________ Sury baki da wani amfani tunda har yanzu kin kasa yi min komai akan Raihan ", me kake nufi OGA ? Karfa ka manta Ni nafika kin Raihan saboda rabia ba komai ce a gurina ba dan da ace ita kadaice da wazer da yanzu na gama da ita", numfashi ya furzar kana cikin cunkushewar muryarsa ya ce", Surry dole zan sace Raihan sace Raihan shi kadai zaisa na samu rabona,zanyi kidnaping dinta Kinga dole a bani comfanis din da nake so dan kawai na bada ita,uwarta babu abinda bazata iya sadaukarwa akan Raihan ba dan haka wannan shine plan e wato plan Dina na karshe kuma na tabbata a shine zanyi nasara", Idan suka baka abinda kake bukata kawai ka kasheta Ni kuma nayi maka alkawarin sato maka RAIHAN", Surry ta faɗa cike da gamsuwa akan tsarin ogannata,jinjina mata ya yi tare da cewa zan cika miki alƙawarinki dan haka daga yau aikinki ya fara. BASHIR kana inane? cewar Abba yahya da yake dauke da waya a kunnenshi", ganinan Abba na kusa karasowa kasan dole sai na yiwa inna yan dabaru kafin na fito tunda tasan babu wani aiki da nake yi a nan ko kuma wasu abokai", Tom shike nan ina jiranka", daga haka Abba Yahya ya aje wayar yana ci gaba da tsayuwa a gaban tafkeken ruwan da yake can karshen gari,dole a nan ne ka dai yake da nutsuwar ganawa da dannasa tunda ya fahimci akwai masu bacci da rabin ido. Baffa Ali ya dubi Aunty Amarya sannan ya dan nisa tare da gyaran murya irin nasu na manya,kana ya ce", ramla na nemi ganinku ne saboda nasanar daku shawarar da muka yanke akan cewa Raihan zata tare a gidanta saboda yanzu zaman nata bashi da wani amfani tunda abinda ake gudu ya riga ya faru", to amma sai babanta Yahya ya nemi da a bari zuwa nan da sati biyu ko Allah zaisa Nura ya farka hakan zaifi bawa yarinyar nutsuwa da kwanciyar hankali ga duka mu din nan ", ya yi shiru bayan ya kare maganarshi, Hajiya goggo ce ta dan numfasa sannan ta ce", ey shima Yahya yazo da magana dan haka a nawa bangaren ba abinda zance sai dai Allah ya nuna mana kuma Allah ya bawa Muhammad nur lafiya", amsawa su kayi da Amin ,sannan HAJIYAR AGADEX ma ta tofa da cewa itama ta gamsu Allah ya nuna mana lokacin,aunty Amarya ma babu abinda ta ce sai fatan samun lafiya ga mijinsu,haka su mama murja da Hanne harda inna maimuna duka kowa ya tofa da yin kyakkyawar addu'a ga Muhammad nur,daga nan kowacce ta koma bangarenta.ita momy Hanne dama asibiti zata koma sai zuwa dare zata dawo Hajiyar agadex kuwa ciki ta bi Hajiya goggo tana bata labarin baturiya da ko Hausa bata ji wato matar Bashir. __________ *SHUDA DA DUDU......* Tunda Bashir ya karaso gurin da Abba yahya yake jiranshi,ba tare da ya ce mishi komai ba shima ya tsaya yana fuskantar wannan tafkeken ruwan Dukansu idanunsu a rufe hannayensu kuma bisa kawunansu,wasu irin surutai suke yi wanda kana jinsa kasan cewa ba abin arziki ake fada ba, can bayan shudewar wasu mintoci gurin ya fara hadewa yana turnukewa da wani irin bakin hayaki yayin da garin ya koma kamar tsakiyar dare a lokaci daya wannan ruwa ya shiga rikidewa zuwa jini,cikin dakika biyar tsohuwa ta bayyana akan tsakiyar ruwan da a yanzu ya koma jini.fuskarta gwanin ban tsoro saboda yadda take a wani yamushe idanunta a waje kwala kwala dan duk daya zaiyi girman yar karamar boll ta jikin roll on,fuskarta cike take da fushi irin na fusatar nan,bude baki ta yi zata yi magana gaba daya gurin ya dauki wani irin girgiza dan hatta da jinin ambaliya ya shiga yi tamkar wanda ake girgiza shi,bakin hayaki kuwa tuni ya kuma turnuke gurin har ya zamana ko tafin hannunka baza ka iya gani ba,zafi da hucin da yake fitowa daga bakinta tamkar wani oven din gasa tsire. Lallai shuda kayi sake dan zaki ya girma,wai shin me kake jira da wadannan yan tsakinne da ba za a yi romansu ba? Lallai ina so ka sani idan wadannan yan tsakin tare da kakarsu suka bamkado boyayyar sirrinnan to tabbas ba ku kadai ba mu kanmu kashinmu ya bushe dan kuwa tsaf zasu ƙona tsibirinmu wannan dalilin yasaba za mu kyale su ba", da uban da yar duka za mu shanye jininsu, za mu kashe nur amma dole sai ya farfaɗo daga suman da ya tafi ita kuwa yar karamar shilar tun yanzu zan fara mata aike", hahaha ta sheke da wata muguwar dariya, sannan ta nuna Bashir da wanann sandar tsafin kana ta ce", kai kuma anyi Sa'a lokacin tahowarka ya yi lokacin da muka diba maka ya yi amma da be yi ba tabbas sai ka mutu kamar yadda ka sani dan haka zaka zauna nan mu cigaba da aiki har zuwa ranar da zaka bawa jini jinin matarka yasha daga nan ne kuma zaka auri matar da muka nuna maka ita a mafarki", jini ya taimaki tsohuwa Ni har yanzu ban samu ganin fuskar matar ba fa,"cewar Bashir ke nan ya fada cike da rashin jin dadin abinda tsohuwa ta ke shirin yi masa, zaka ganta yanzu ta faɗa tana nuna cikin ruwan da ya zama jini da sandar tsafinta,sai ga Surry kwance akan katifarta ta gidansu yana sharar bacci abinta hankali kwance, wannan ita ce matar da muke so ka aura dan haka kar ka kara yi mana tambaya duk abinda kake so ka sani zamu nuna maka za mu haɗaka da ita da zarar lokaci ya karasa,bana bukatar cewarku", daga haka ko mai ya baje ya koma yadda yake hatta Abba Yahya da Bashir da suka sauya cikin shigar tsafi a lokacin da tsohuwa ta bayyana sai gashi yanzu sun koma normal da asalin shigarsu da suka zo da ita. ___________ Tunda Aunty Amarya ta koma sashenta ta shiga sunturi tare da saka da warwarar abinda ya kamata ta yi", wani irin nutsuwa ta yi tana nazari da dawo da komai dake faruwa cikin gidan tana bazashi a fefe,fuskar kowa take hangowa domin tantance abinda ya kamata ta yi,wani irin kwarin gwiwa take ji a yanzu dan haka take son karfafa zuciyarta domin yin yaki da dukkan makiyansu,lallai tana ji a jikin ta lokaci yayi da zata aje duk wani tsoro da fargaba a gefe ta fito fili ta yi yakin sunkuru", ta ina zan fara abinda ta faɗa ke nan tana kafe hoton RAIHAN da ido", a hankali ta fara tunani akan Hajiya goggo kafin ta fara akan mama murja daga nan ta gangaro kan Hanne, sai kuma inna maimuna,tsam ta yi da ranta tana son tantance takan wadda bincike zai fara hawa kanta,mace daya zuciyarta ta hasaso duk da cewa ta wani bangaren bata tunanin zata iya aikata wannan mummunan al'amarin ,to amma kuma haka nan zuciyarta ta fi dagewa akanta zarginta ya fi tsayawa akanta wanda ita kanta bata san dalilin hakan ba,sai kuma namijin nan da yake mata waya shima cikin nutsuwa ta rufe idanunta,wanda zuciyarta ya hasaso mata ne yasa taji faduwar gaba anya kuwa zai aikata? Ta tambayi kanta,sai kuma ta bawa kanta amsa da cewa mutum mugun icce ne lallai biri ya yi kama da mutum. Take wasu alamura da suka dinga faruwa suka shiga dawo mata,lallai duk wanda yake aikata hakan yana da kusanci da su", take ta kudurce cewa lallai sai ta gano wadannan mutane biyun da suke yiwa rayuwarsu barazana. _________ Cikin layi ta faɗa office dinta, idanunta kamar zasu fadi kasa saboda azabar da suke yi mata,waya ta daga ta shiga kiran Abbanta,ba tare da ta saurari abinda zaice ba ta fashe masa da kuka saboda tasan shi kadai ne yake daure mata kugu shi yasa duk haukar da ta kwaso shi take tunkara", lafiya me kuma ya faru Abbanta ya shiga tambayarta duk da cewa yasan tatsuniyar gizo bata wuce koki", cikin rishin kuka ta fara mishi zance tamkar wata mara kan gado", wallahi Abba sai na kashe yarinyar nan Raihan idan yaso Nima a kashe Ni", shi kansa Wazer ɗin bana jin idan naga za a luma masa wuka zan dakatar wallahi Abba na tsane su kayi wani abu akai ", kwantar da hankalinki rabi cikin ma amfasa yi da wuri zan dau matakin da ya dace akansu,ai ba ke kadai suka shigewa hanci ba,ki kwantar da hankalinki kisaurari abinda zai biyo baya kawai", Tom shike nan Abba na gode", kashe wayar ta yi tana share hawayenta saboda dan sanyi da ta ji a ranta dan tasan tunda ABBAN ta ya shiga maganar bata da wata matsala kuma tunda ya ce zaiyi to fa zaiyin . Fujin fujin ya shigo falon innawuro dan dama lokacin da rabi a ta kira shi ya shigo gidanne bai karasaba, Kai kuma lafiya ka shigo min haka ko sallama babu"? Cikin fidda hucin Bala in da yake cinsa ya ce", innawuro wallahi na gaji da kawaici na gaji da cin rafin da wazer yake.yiwa rabia dan dai kawai yaga bata da gata bata da wanda zai goya mata baya", shikenan duk cin kashin da ya dauko sai ya jifga mata ga nasa ga na matarsa da wanne zata ji,to gaskiya na gaji da kawaici tunda kowa nasa yake so to nima gara na nuna lwa kowa ina son yata", ya aje maganar ya sauke numfashin Da yaki ajewa tunda ya fara maganar,kallon sama da kasa innawuro ta yi masa sanann ta ce", to yanzu kana nufin a wannan haukar taka zan fahimci abinda kake nufi? Zama ya yi yana faman ƙunkuni kamar wani karamin yaro,to iina jinka idan zaka iya min bayanin da zan fahimta innawuro ta faɗa fuskarta itama babu wasa, gyara zama ya yi ya shiga rattafo mata laifin wazer wanda yasan anyi da wanda bai sani ba,ko kunya babu shima ya maimaita mata abinda rabia ta faɗa masa na cewar wazer baya kwanciyar aure da ita ", ga kuma wulakanci da suke mata shida matarsa a can wajen aikin kala kala,kai zance dai mai ma'ana da mara kan gado haka ABBAN rabi ya yi ta suburbudoshi. Sai da innawuro ta gama saurarenshi tsaf sannan ta ce ya je anjima da dare tana son ganinsu gaba daya,bai ce mata komai ba ya tashi ya kada babbar rigarsa fujin fujin,dama yau haushi ne ya haɗar masa,saboda a Companyn shinkafa yasa a fitar da buhun shinkafa hamsin amma Khalid kememe yaki sa hannu wai sai yaji dalili da inda za akai tare da shaidu to wannan abun shine ya kuma fusata shi,dan a gaskiya yaran suna Gara shi ko abun kwandala basa bari ya fita ba tare da sun san ina zashi da wanda za akai wa ba,gashi shi kansa cashiya da accounter sun samu irinsu shakiyay wadanda suka san kan duniya shi yasa dukan ya yiwa ABBAN rabi yawa ta ko ina,yanzu bashi da abinda yake buri irin yaga bayan wazer saboda yasan cewa komai daga gurinshi yake fitowa duk wani abu da zasu yi ko wani sabon tsari shi yake kawowa sunan dai baya aiki a maaikatunne kawai. _______&& Laluben jikinta da ya fara yi shi ya ankarar da ita,da sauri ta rike hannunshi da ya fara kokarin cusawa cikin rigarta,fuska ta marairaice tana kallon tashi fuskar da idanunshi suke a lumshe yana kokarin kwace hannunshi da ta rike. Cikin wata irin murya da ke fita can kasan makoshinsa ya ce", zaki taya Ni bacci", ya fada yana kai hancinshi wuyanta zuwa ƙirjinta yana sinsino kamshinta dake rikita kwakwalwarshi,umm hamma aiki muke dama na kawo maka rahotannin da za a fitar a wannan satinne", ta karasa fada cikin wani irin rawar muryar da abinda yake mata ya haifar mata,wani irin waiwayi yake mata da fuskarsa a wuyanta zuwa ƙirjinta yana bi yana fesa mata hucin bakinsa wanda yake tafe da wani irin kamshin strawberry da a kullum baya rabo dashi,hannunsa ya kai kan zip din rigar ta ta baya a hankali ya shiga yin kasa da shi yana cewa cikin kasalalliyar muryarsa,' ya yi kyau kinzo a lokacin da ya dace matar kirki ", wayyo wazer fa nema yake ya kasheta bata ga farfadowar Abbie dinta ba,kafin ta yi wani yunkuri tuni ya yi kasa da rigar. Wayyo hamma wazer," ta faɗa tana fadawa jikinshi tare da kamkameshi,wani dan munafikin murmine ya subce masa sai kawai ya ruketa suka Wada saman faffadar kujerar da ya tashi daga kai,aoch ya fada yana dafe saitin zuciyarshi,tana jinshi ta ki Dagowa saima kuma manne masa da ta yi,aoch ya kuma fada sai yanzu ta dago a saɗaɗe kamare tsoran wani abu", haɗa ido su kayi sai ya dan turbine fuska tare da kashe mata ido ɗaya sannan ya nuna mata saitin zuciyarshi da kanshi kafin ya bude baki a hankali ya ce", zaki kashewa Ammi yaro bayan lalata mata shi da kika yi kin samu zuciyarsa kin cinye kin lalataasa tunani baya jin komai sai ke baya ganin komai saike anya ko Raihan ba za ku yi Shari'a da Ammi ba? Idanunta me suka yi raurau dan har ga Allah bata fahimci me ya ke nufi ba,HAMMA yaushe na lalataka?dame na lalataka kuma? Yaushe kuma na cinye zuciyarka? yaushe na lalata tunaninka? Ta karasa fada hawayen da basa yi mata wuyar fita suna gangarowa. A hankali ya fidda harshensa yasa ya lashe hawayen yana cewa ki yi ta hawayenki Ni kuma bazan fasa shanye kayana ba,bana kusa ne kawai banyarda ki zubda wadannan hawayen ba,dan nasan muddin bana kusa hawayenki bana sangarta ba ne na damuwa ne", rufe idanunta ta yi tana jin ɗumin harshensa da ya dora a kumatunta yana tsotsa kamar wanda ya samu sweet..........✍🏽 Haba wazer ya da haka kayi hakuri mu kai maka ita mana😂 Gaskiya a kyalemu haka kar a haukata mu mu kasa rike kanmu😂 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page57 ``` A hankali take sauke numfashin wahalar da gangar jikinta da zuciyarta da wazer yake yi", bata da yadda ta iya dole ta biyeshi dan taya shi Baccin kamar yadda ya bukata. ______________ A wannan yinin abubuwa da yawa sun faru wanda suka danganci nasarar masu gaskiya da kuma faduwar marasa gaskiya. A bangaren Dr Sabo ma baiyi da wasa ba wajen binciken wanda ya yi waya da Aunty Amarya,dan haka shima tabangarenshi yana samun cigaba,haka nan Allah ya haɗa kauna tsaftatacciya tsakaninsa da nur da Aunty Amarya shi yasa yake jin zaiyi komai akansu domin yin hakan jihadi ne gareshi. __________ Tunda aka kaishi magarkama aka aje har yanzu ba a sake waiwayensa ba,kullum jira yake a fito dashi dan yanke masa hukunci akan abinda al'umma take zaton ya aikata amma sai shiru yake ji,gashi an hana kowa ganinsa duk wata kofar da zaiga wani nasa an hanashi wanda shi yasan ko daga ina hakan ta faru,lallai da duniya zata bashi damar fito da ainahin waye Abba yahya to da tabbas tasha mamaki kuma ta koka akan lamarin mutanen duniya,to amma ya ya iya tunda bashi da karfin da zaija da Yahya ya riga yayi amfani dashi wajen gyara sunansa ya rufe ainahin fuskarsa,dan haka ko ya bayyanawa duniya ba lallaine ta yadda ba, sai dai idan yana da hujjojin gani da ido shi kuma a yanzu bashi dasu,Flash din da suke takama dashi yana hannun haidar HAIDAR kuma ya bace,kuma shima baya da wata tantama akan cewa Abba yahya ne ya daukeshi,dan gyara zamansa ya yi a saman dan gadonshi yana jin zuciyarshi na kuna da tafasa akan halinda amininsa yake ciki,a yanzu bashi da wani buri illa ya taimaki nur da Raihan daga hannun azzalumi dan yana da tabbacin wannan lokacin shine daidai lokacin da Abba Yahya yake son cimma burinsa akan RAIHAN da abinda ta mallaka. __________ Akan idanun rabi a suka fito daga office dinsa suka hayo lipter,fuskar nan tashi babu alamun Rahma a gimtse take,sai dai binda ya fara janyo hankalin staff din kansu shine yadda ya ke rike da hannun Raihan ɗin kam tamkar ana damben kwatarta a hannunsa,duk inda suka gifta sai dai kaga ana sadda kai kasa dan babu halin yin kallon kurulla sai dai daga nesa nesan,a haka suka karasa har motarta, securitys ne suka shigo nasa suka biyo bayansu dan kasa barin Raihan ya yi ta tafi ita kadai,haka nan yake jin ba daidai ba tamkar dai wani abu na shirin faruwa. Wani mugun tsaki rabia ta saki sannan itama ta fito dan tafiya,babu abinda ya kuma bakanta ranta irin yadda aka dinga nunata Allah kadai yasan me mutane suke fada akanta abinda taso ace Raihan akewa sai gashi ita ake yiwa,a fusace taja motar ta fita tana ayyana cewa idan Abbanta bai dauki mataki ba to lallai ita zata dauka, dan dama tuni ta cire Surry daga almarinta duk da dai bawai ta rabu da ita ba ne,dole watarana zata yi mata amfani. Karfe biyar shine akafi sani da lokacin tashin ma'aikata hakan yasa a daidai wannan lokacin tituna suka cika da ababan hawa kowa kokari yake yaga yakai zuwa muhallinsa dan haka suma wadannan ahli gida biyu suna daga cikin masu hanzari dan komawa ga muhallinsu, A tare motar Raihan data su Affan suka shigo gidan,wazer ne ke driving dan haka cikin nutsuwa ya samu guri yayi fakin sannan suka fito Dukansu a tare", hannu HAMMA Idris ya mika masa suka yi masabaha haka Affan ma, Raihan ta ce", mun dawo a tare duk da dai mu mun biya wajen Abbie ", ta faɗa tana kallon hamma Idris, Affan ne ya ce", gaskiya ne mu dinma mun dan tsaya ta wani guri Idris ya dan yi uzuri", mika mata key wazer ya yi yana cewa zan shigo anjima ina son magana da mami", jinjina kai ta yi tana karbar key ɗin ,maimakon ya bata sai ya haɗa da hannunta ya riƙe dan duban gefansa ya yi yaga su Affan sunyi gaba hakan yasa ya karasa janyota jikinsa alokaci daya yana bata kyakkyawar sumba a tausasan labbanta da suka yi ja saboda tsotsan da suka sha a gurinsa ", good night ya fada yana sakinta tare da ja baya har ya juya dan fita cikin nutsatstsen takunsa,kasancewar motocinsa suna waje basu shigo ba yasa dole sai ya yi tafiya me dan tsayi.kasa tafiya tayi tana kallonsa har sai da yazo bakin kofa sannan ya dakata tare da juyowa alama ya yi mata da ta shiga gida,cikin sanyin jiki ta juya tana jin idanunsa a jikinta har ta shige ƙatuwar kofar glass din sashensu. A hankali ya ɗan sauke numfashi kafin ya fita daga gidan yana dagawa securitys din gidan hannu. Da misalin karfe tara na daren ranar, innawuro ce zaune kan kujerarta ta mulki sai Abbu da abban rabi da yake ta cika yana batsewa,dan a kwanakinnan sosai yake kasa boye mummunan halinsa da hassadarsa akan dan uwannashi,sai kuma Ammi da OGA kwata kwata Ahmad wazer,da matarshi rabia Mustapha Chibado,bayansu ba a bawa Kowa umarnin zama ba hatta su Khalid hayewarsu su kayi sama inda dakunansu yake. Cikin nuna girma na amsa sunan uwa me faɗa aji da kuma fada gurin diyoyinta, innawuro ta fara magana, Mustapha Inaso ka maimaita abinda ka fada min dazun saboda inason duka nan suji laifin dansu akan yarka kamar yadda ka fada", ta faɗa idanunta akan ABBAN rabi da lokaci daya duk ya dabarbarce kai kace bashi ne yake wannan kumfar bakin dazu ba,dan muskutawa ya kuma yi a karo na wajen hudu tare da dan goge goshinsa da gumin rashin gaskiya ke tsatstsafo masa,shiru na kusan mintuna uku kafin innawuro cikin kufula ta kuma cewa kaifa muke sauraro Mustapha ", um ey dama rabi ce dazun ta kirani take kuka akan rashin adalcin da wazer yake mata sannan suna mata rashin dacewa shida matarsa a can gidan jarida,kullum sai sun sata kuka bakincikin hakan yasa ta kirani ta faɗa min,gashi kuma ta ce", gidan ma ba ya dawowa wataran ma ba ya kwana,GASHI KUMA BAYA BIYAN HAKKIN AURENTA DA YA RATAYA AIANSA.....ɗuf falon ya yi baka jin karar komai sai ta fanka da a,c,Ammi kam kasa kallon kowa ta yi a wajen shi kansa abbu bakaramin kunyar maganar nan yaji ba. Innawuro ce ta kore shirun da ɗan sauke numfashi sannan ta dubi wazer tana cewa, kaji abinda matarka ta fadawa ubanta akanka me zaka ce game da hakan shin gaskiya ta faɗa? . A hankali ya dago kansa dake kashingide tun dazun, kai idan ba lura ka yi Bama sai kayi zaton baya falon,bude idanunsa ya yi sosai akan rabi a dake rakube a gefe idanunta tarwai akansa babu alamun karaya ko jin nauyi a tare da ita,ji ya yi yana rasa abin cewa yo haka kawai ma ya rasa abin fada bare kuma irin wannan lamari me zafi haka,maida dubanshi kan innawuro ya yi kana a hankali ya bude bakinshi da yayi masa nauyi ya ce", innawuro bansan daga ina wannan maganar ta fito ba dan haka bani da abin cewa", idan kuma.kuka ce lallai sai na ce ɗin to tabbas abinda zan fada akanta ba zaiwa kowa dadi ba har ita ɗin ", daga haka ya mike yana wa Amminshi sai da safe,ko kallon inda ABBAN rabi yake sake da baki baiyi ba. To ke rabi kinji abinda ya fada kuma kinsan halinsa baya zama dan ya yi maganar shirme,cewar innawuro tana duban ABBAN rabin", aiko cikin fushi ya mike yana cewa tashi mu tafi rabi wallahi wazer zaisan Ni yayiwa wannan cin fuskar ko da yake ba laifinsa ba ne daurin kugu ya samu shi yasa yake abinda yaga dama a gida da wajen aiki hatta inda ba zuwa yake ba zuba iko yake a gurin, wallahi wannan laifin na yaya ne innawuro haka kawai ya zauna yaro karami yana juyashi tamkar shine ɗan ba uba ba,to Ni 'yata ba zata zauna ta yi zaman boranci ba dan haka duk ranar da aka isa dashi yazo ya tafi da ita", daga haka fuu yaja hannun rabi suka fita daga falon. Abbu zaiyi magana innawuro ta dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu,sannan ta ce", tashi kaja matarka ku koma bangarenku Allah ya yi muku albarka shi kuma Allah ya ganar dashi", Amin ya Allah abbu ya fada yana tashi ɗan bin umarnin mahaifiyar tasu. Innawuro ta jima tana saka da warwara akan ABBAN rabi,tabbas ta fahimci akwai wani abu tsakanin Abbu da Mustapha sai dai amma tafi danganta matsalar daga ɓangaren ABBAN rabi,shi yasa bata dakatar da wazer ba ta barshi saboda tunda taga ya yi haka to lallai akwai wani abu akasa,amma in sha Allah ba zata zama sakaryar uwa ba koma meye zata gano tunda dukansu babu wanda bata san halinsa ba ciki da bai. ______&& DUDU Sosai dare ya tsala tunda wannan lokacin zamu iya kiransa da tsakiyar dare,kwance suke shida baturiyar matarsa,bacci take sosai yayin da shi kuma yake ta duban agogo daga gani dai a kage yake,saura mintuna biyu lokacin da tsohuwa me jini zata zuke jininta ya yi, amatukar kage yake saboda wannan aikin shine mataki na karshe da zai kai dan cimma mafarkansa.saura minti ɗaya. A hankali jeniper ta bude idamunta wanda ita kawai ji tayi kamar an ce ta farka,a can kasan makoshinta ta fara ambatan sunan alhakimu, wanda ji ta yi kawai ta ambata duk da bata kasance musulma ba,kafin a hankali ta bude idanunta gaba daya akan bayan mijinta da ta Ganshi tsirara haihuwar uwarsa yana tsugunne yana karanta wasu ɗalasumai da ko a Yaren Chaina bata taɓa cin karo da makamantansu ba,sai kawai ta koma ta yi luf ,duk da yadda kirjinta ke bugawa kamar zuciyarta zata fito,amma hakanan ta daure tana so taga abinda Bashir din ke son yi. Wani irin bakin hayaki me tsananin kauni ne ya turnuke dakin kafin cikin kankanin lokaci tsohuwa ta bayyana,fuskarnan Tata kamar kayi amai saboda kyama,wangamemen bakinta ta bude wanda ke fitar da wani irin wari wanda ke gairaye da bakin hayaki ta ce", DUDU wannan matakin shine matakinka na ƙarshe daga wannymatar taka ka gama bamu jinin nasara sai kuma jinin musulmi,kamar yadda ka sani mu muke hasko maka matar da zaka aura wadda jininta zai mana amfani,to a wannan karonma haka za muyi kuma ba tun yau ba mun nuna maka matar da muke so ka aura a musulmai kuma ka ganta,dan haka muna karbar wannan jinin gobe zaka fita domin farauto waccen yarinyar, saboda ita dama wannan ba wani abu za ayi wa gawarta ba tunda ba musulma ba ce", jinjina kai kawai Bashir yake yana sauraron bayanan tsohuwa. Jeniper kuwa tuni zuciyarta ta buga da yin wannan mummunan ganin tun kafin su shanye jininta ta ce ga garinku nan. Kai tsaye tsohuwa ta yi kan jeniper dan tsotse jininta amma sai cak ta dakata tana kallon jeniper da jajayen kwalakwalan idanunta,kafin cikin muryarta mara daɗi ta ce", DUDU wannan aikin ya lalace dan wannan ta riga ta mutu jininta babu abinda zaiyi mana dan haka sauranka jinin mace biyu aikinka ya dawo baya",runtse ido ya yi yana jin wani irin mugun takaici kafin cikin neman rangwame ya ce", me jini shin bazan samu wata hanyar kawo kowa ba dole sai ta wannan hanyar? Babu hali DUDU dole duk macen da zaka bamu sai ka sadu da ita,alfarma daya kawai jini zaiyi ma shine zaka iya kawo jinin matar da ka sadu da ita ko ba ta hanyar aure ba,ma'ana dai ba sai ka aureta ba,amma wannan sai daga karshe sai bayan ka auri waccan yarinyar da muka zaba maka idan yaso wancan aikin sai ya zama shine na karshe", daga haka ta bace daga dakin,shi kuma Bashir ya fasa kukan mutuwar matarsa. Washe gari rasa yadda za ayi da gawar jeniper a kayi daga karshe dai Bashir ya ce", ya tuna tana da yar uwa a nan ,dan haka ya kirasu suka zo suka dauki gawar.daga nan Bashir ya fara laluben neman suryy. A yau dinne da takansance weak end ranar Hutu ga daukacin ma aikata,dan haka Raihan tana gida babu inda ta fita,asibiti ne wazer kuma ya ce ta bari sai yazo za su je,saboda yana son zama da Aunty Amarya jiya bai samu dawowa ba sakamakon kiran innawuro. ___________ Mikawa Yusuf takardun ya yi yana cewa ka tabbaida cewa ka bata su a yau", Ni kuma nasan cewa dole a cikin kwana biyu nan na Hutu zata yi kokarin bawa Raihan yusuf kafin kwana biyu nake so nasan wacece wannan matar," wazer ya fada fuskarshi tana a yadda take kullum cikin gizago da nuna rashin son wasa", in sha Allah yau zan bata su dan yanzu haka ma Ni take jira dan na gaya mata mu hadu zan bata takardun",hannu suka yi da juna kafin Yusuf ya fice daga motar wadda ke cikin gidansa na ,g,r,a hore fillo. Haduwarta su bata wuce yan mintuna ba,dan Yusuf bata takardun kawai ya bata tare da cewa yana so duk yadda za ta yi ta yi Raihan tasa hannu a takardun nan tunda kwana biyu tana Hutu, cike da kwarin gwiwa ta bashi amsa daga nan su kayi sallama. _____________ Cikin sauri Aunty Amarya ta fito daga dakinta tana zura hijab alamun dai sun nuna fita zata yi, Raihan da taga tana neman fita bata ce mata komai ba,yasa ta yi saurin cewa Mami ina zaki ne haka kamar ba babu shirin fita akanki yau? Ba tare da ta kalli Raihan ɗin ba ta bata amsa da cewa asibiti zani yanzu zan dawo",a daidai lokacin ta karasa saka hijab din har da karin facemask ta fice da sauri", ɗan jim Raihan ta yi sai kuma ta mike ɗan bin bayan aunty Amarya wadda suka hadu da hajiya goggo a waje ta ce mata asibiti zata je ta dawo", dan haka haniya goggo ta nufi falon kai tsaye anan suka yi kicibus da Raihan zata bi maminta, Kamo hannunta hajiya goggo ta yi tana cewa dawo ina zaki bita yarinya kin girma amma baki san kin girma ba,dawo nan wani dan aiki nake so kiyi min", Hajiya goggo ta faɗa tana jan hannun RAIHAN.. A daidaita Aunty Amarya ta tara ta nuna masa motar mutumin da ta ji yana waya a bayan gadin ,a lokacin tana gadin din,bata bari ya ganta ba shi yasa har ya gama wayar akan tsarin da ya yiwa yaransa na sace Raihan bai ganta ba,itama bata ga fuskarsa ba kawai dai ta gane muryarsa wadda ya fara yi mata waya da ita ya shaida mata cewa yasan sirrinta na boye RAIHAN. Shi yasa ta dawo cikin gida ta kofar kiching ta dauko hijab ɗan bin bayansa,so take ta ga waye ,haka nan take jin wani irin kwarin gwiwa,dan haka take fatan kawo karshen zaluncin daya daga cikin makiyansu.......✍🏽 Tofa wai ya take nake ne? Me Hajiya goggo ke nufi da dakatar da Raihan? Shin Bashir zai samu nasarar auren sury? To ya batun Abba yahya ne? In sha Allah a pg na gaba za ayi walkiya muga fuskokin wasu... Da kuna yin comments da yanzu mun gama Da yanzu babu wannan gantalewar😂 Walle Nima na gaji🙄 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page58 ``` A bangaren Bashir kuwa suna mika gawar jeniper ya shiga gari bulayin inda zai hadu da sury ba dan yasan zai gantan ba,sai dan kawai yasan duk wannan yana daga cikin aikin tsohuwa shigo da suryn cikin rayuwarsa. ___________ OGA yana fitowa ya daga waya ya kira Surry ta same shi inda suke haduwa", cikin sauri ta karasa fita dan dama tana shirin fitowa ne ya kira ta,duk a kwanakinnan bata da mutsuwa saboda tunanin ta yadda zasu sace Raihan,wayar da su kayi dashi ne a safiyar yau akan su hadu dan tsara hanyar da zasu saceta yasa ta ɗan samu nutsuwa tasan zai taimaka mata duk da cewa ita ta dauki wannan alhakin. Motarta babu mai dan haka ta saka kiran masu nafef dinta akaro na farko tun bayan haduwarsu da karbar lambar. Da sauri Dady ya daga wayar yana cewa ranki shi dade hajjaju", tare da naka ta faɗa tana ɗorawa da cewa dan Allah ina son zanje wani guri idan kana kusa kazo ka ɗaukeni", babu damuwa turo min address din gun", ok ta faɗa tana kashe wayar,da sauri Dady ya tashi ya fito daga office dan kiran Salim", dan dama su ba kasafai suka fiya yin Hutu ba,kicibus sukayi da Salim din hakan yasa bai tsaya bata lokaci ba ya yi mishi bayani,take shi kuma salim ya kira wazer ya sanar dashi,shi kam dama wazer kullum a shirye yake dan haka cikin nutsuwa ya ce", dasu su tafi amma suyi komai da takatsantsan,idan suka ga zata ganosu su rabu da ita tunda duk wasu bayanai da kiran da suke shiga wayarta da wayar da take yi duk yana dasu ta hanyar wannan madaukar da kuma canjin wayar da su kayi mata wanda har yanzu bata Ankara ba. Cikin mintuna goma suka isa gidansu Surry,tana shiga suka figi nafef din da su kara tabbatar mata da cewa su din yanjagaliya ne. Take wani tunani ya darsu a zuciyar Surry,tunanin da ta yi ne yasa ta yi saurin daukar wayarta ta har zata ogan sai kuma ta fasa,tana gani tunda haduwa zasu yi sa yi maganar ta yadda zai fahimceta,tabbas wadannan matasan zasu taimaka mata gurin sace Raihan", murya saki tana jin wani sanyi a ranta na samun mafita. Aunty Amarya........ Karka bari ya bace mana pls kaji", in sha Allah bazai nace mana ba,cewar me nafef da yake bin bayan ogan Surry cikin takatsantsan. Hajiya goggo......... Suna shiga falon Hajiya goggo ta dubi Raihan tana cewa ina hajiyarki ta agadex", dan hararar kofar HAJIYAR AGADEX din ta yi sannan ta ce", tana bacci har da wani cewa kar a tasheta",zama Hajiya goggo ta yi sannan ta zaunar da Raihan ɗin,cikin nustuwa ta ce", Raihan wani taimako zaki min", taimako kuma? Raihan ta faɗa gabanta na faduwa", ey taimako Hajiya ta faɗa tana zaro takardun da suke nade a kugunta tana warware su a lokaci ɗaya", biro ta ciro a tsakiyar takardun sannan ta mikawa RAIHAN tana cewa wajen da aka bukaci sign kawai zaki dinga bi kina yi min,kin sanni ba wani abu na sani a harkar boko nan ba", take tunanin Raihan ya tsaya duk da cewa bata san nufin wazer akan tasawa duk wadda zata bata takardu ido ba amma tabbas tana hasashen akwai wani abu akasa", karba ta yi tana tuna kashedin wazer akan kar tayi gaddama kuma kar tabi kokkofi akan takardun bare takai ga karanta abinda yake ciki", jinjina kai ta yi kawai ta shiga sa mata hannun,bata dago ba har sai da ta gama tare da mikawa Hajiya goggo takardun", murmushi Hajiya goggo ta yi tana cewa na gode jikallena Allah ya yiwa rayuwar aurenku albarka, Amin Raihan ta faɗa tana bin Hajiya goggo da kallo har ta fita daga cikin falon. Da sauri ta dauki wayar da wazer ya kira tana karawa a kunne", wacece ita? Abinda ya fara tambaya ke nan" jin a kagauce yake yasa itama ta yi saurin bashi amsa da cewa hajiya goggo ce", runtse idanunshi ya yi kafin ya taune labbanshi da suka bushe sannan dakyar ya ce", da ita maza tashi ki bita sashenta kiga dawa zasu hadu amma kar ki bari ta ganki,amma ina so ki tabbatar min daga ainahin wadda takardun nan suka fito", shike nan ta faɗa tana tashi a lokaci daya jikinta a matukar sanyaye. Kai tsaye sashen hajiya goggo ta nufa tana gab da karasawa ta hango inna maimuna ta fito daga bayan window falon Aunty Amarya cikin sauri tana yi tana waige da alama bata so wani ya ganta,ganin haka yasa RAIHAN tayi saurin boyewa a bayan bishiyar dabinon dake girke a wajen,bata fito ba har sai da taga inna maimuna ta shiga falon Hajiya goggo,sannan ta fito cikin sanda da yan waige_waige a hankali ta bude falon ta shiga cikin tsananin takatsantsan,babu kowa a falon hakan ya bata damar saurin karasawa corridorn da zai sadaka da dakin Hajiya goggon,rabewa ta yi a jikin kofar tare da kafa kunnenta,bata jin komai bata ganin komai hakan yasa ta canja shawara dan haka cikin sauri ta fita daga falon ta koma ta can bayan dakin daidai jikin window ta tsaya tare da dan zuge glass din,zuciyarta na gudu ta daure ta dan yaye contain din yadda zata iya daukar fuskokinsu dakyau kamar yadda wazer ya umarceta. A bangaren inna maimuna kuwa tana shiga falon bata ga Hajiya goggo ba sai kawai ta wuce bedroom dinta,anan ta sameta ta fito daga bathroom,kallonta hajiya goggo ta yi a dan mamakance tana share ruwan fuskarta da alama alwala ta ɗauro,maimuna kece a tsakiyar ranarnan haka? Goggo ta faɗa tana zama a kan kujerar dakin,dan muskutawa inna maimuna ta yi sannan cikin fara a ta ce", ey wlh zuwa nayi na karbi takardun saboda da sassafe zan fita dasu na kaiwa yayana na can kusurwa,haka ne", Hajiya goggo ta faɗa tana janyo takardun sannan ta ɗora da cewa amma maimuna ban yadda da hujjarki ta ƙin bawa Raihan takardunnan ta sa hannu ba zanso kiyi min bayanin da zan gamsu,sannan ki fada min su din takardun na meye? Kuma daga ina suka fito? Da sauri inna maimuna ta karɓe takardun tana cewa Hajiya zanyi miki bayanin komai idan na kai takardun na dawo amma fa karki tada hankalinki dan ba wani abu ba ne",daga haka ta mike da takardun a hannunta ta fito daga dakin ta bar Hajiya goggo sake da baki. Sai kuma ta dan tabe baki tana cewa haka kawai dan wani sanabe ki kawo min shirgin takardu waike kunya kike ji kicewa Raihan baki iya sign ba,dan Allah na bata tunda tasan Ni banyi boko ba kuma Ni kakarta ce akwai wasa tsakaninmu",ta karasa fada da kuma mele baki tana jin abun wani banbarakwai kai sai yanzu take ji kamar tayi sakarci wai surukarta ta aike ta duk yadda take da jajircewa akan surukanta kai duk yadda akai da akwai abinda maimuna take boyewa dan yaran yanzu ba abin yarda ba ne. *RAIHAN* ...... Tana gama daukar komai ta janye jikinta saboda ganin inna maimuna ta fito,ba ta fito ba saida ta tabbatar da cewa inna maimuna ta kai ga sashenta,sannan ta yi saurin komawa bangarensu,tana shiga daki ta turawa wazer video dan ita kanta ta kagu tasan abinda yake faruwa. Yana kashingide amma baisan sanda ya tashi zaune ba,a nutse ya gama kallon video kafin ya saki wani kasaitaccen murmushin gefen baki, send ya yiwa Yusuf,shima yusuf din yana gani ya kira shi ,wazer yana dagawa Yusuf ya ce", wazer na sarawa zurfin tunaninka anya kuwa kai din ba aljan bane? Murmushin ya kuma saki yana sauraren Yusuf da ya cigaba da cewa,kaga shegiyar mata wato tayi hasashen wani zai iya bibiyarta ta hanyar Raihan ɗin shi yasa ta canja tunani ta kaiwa Hajiya goggo takardun kaga koda zata kasance akwai me bibiyarta ke nan Hajiya goggo ce zata zama suspect dinsa", wannan shine abinda nayi tunani na kasa yadda cewa Hajiya goggo ce", cewar wazer kenan ", ajiyar zuciya Yusuf yayi sanan ya ce", amma kaga nifa harna yadda wallahi", cikin dan gajiyawa da maganar wazer ya ce",ba zai yuwuba Yusuf sam ba zai yiwu ba,da zai iya cutar uwarsa dan uwa zai iya cutar dan uwansa komai shakuwar dake tsakaninsu,amma banda uwan Yusuf soyayyar da uwa takewa danta dabance son da uwa takewa danta dan bayayi mata kwatankwacinsa,dan haka ka cire wannan aranka Hajiya goggo ba zata taba cutarwa Abbie ba har fa da kokarin kisa tun anan lissafin zai canja indai har ita ce ta haifeshi ko da kuwa shidin yakasance ba mutumin kirki ba ne. Tabbas maganarka dutse wazer wallahi har ka sa na kuma jin tsananin son Hajiyata lallai iyayenmu abin alfaharinmu ne Allah Ubangiji ya kara musu lafiya ya kuma saka musu da gidan aljanna Amin ya rabbil alamin 🙏", wazer ya fada yana ɗorawa da cewa Yusuf zamu hadu mu tattauna yanzu ina jiran sauran bayanan da su Salim zasu kawo game da dayan dan ta addan shi kuma kowa za mu gani? Allahu a'alamu cewar Yusuf daga nan suka yi sallama kowa ransa cike da mamakin halin dan Adam ,ko acikin mutanen da suke hasashe babu inna maimuna a ciki lallai matar nan ta san takan munafurci da iya taku,cewar yusuf da yake magana shi kadai bayan kammala wayarsu. BASHIR Share zufar da ta gangaro masa ya yi bayan ya gama zagaye garin bai samu Surry ba,samun gefen hanya ya yi ya faka,sannan ya fito ya jingina jikin motar yana kallon cikin hotel din da yake fuskantarsa. Daidai lokacin motar ogan Surry ta ƙaraso cikin sauri securitys suka bude masa gate,saurin shigewa ya yi saboda ganin Bashir a gurin,sosai yake cikin mamakin ganin Bashir din, Allah yasa dai tsayuwarshi a gurin bai danganci zuwansa ba. abinda ya ayyana a ransa kenan,yana samun guri danyin fakin. Gaban aunty Amarya ne ya fadi ganin Bashir dake tsaye jikin motarsa yana ɗan kalle kalle,gaba daya sai tunaninta ya nemi tsayawa cak,gabanta ya shiga faduwa,me ya kawo Bashir nan?ko dai shine na cikin motar? Kai bashi ba ne? Ai tana ganin sanda motar ta shiga hotel din dan haka bashi ba ne,sai dai idan shima da abinda ya kawoshi ko kuma tare suke da na cikin motar, wannan tunanin da ta yi ne yasa ta umarci me nafef din da ya sauketa ya tafi,dan ita dole ta yi dabara wajen shiga hotel ɗin saboda kar Bashir ya ganta. _________ Hajiyar agadex ce ta shigo dakin Raihan tana cewa ke taso maza me gyaran jikin da na dauko tazo yau din nan za a fara gyara min ke dan ba zan yi sake rana tsaka a zo ace in fito dake za a kaiki ba," tura baki Raihan ta yi sannan ta ce", Hajiya wane irin gyaran jiki? Gyaran jiki irin na amaren da za akai gidan miji", au na manta ma ashe ke rabuwa za ku yi da zarar nur ya farka amma dai duk da haka za ayi miki saboda sabon mijin da zaki aura", ta karasa fada tana kamo hannun Raihan ɗin,da sauri RAIHAN ta fincike hannunta kafin cikin zubo da hawaye ta ce", Hajiya dama ana aure biyu? Tsayawa hajiyar ta yi daga kokarin kamata da take yi sannan cikin hade fuska ta ce", ai shi wannan din raba shi za ayi tunda dama haka mukayi dak.....kafin hajiyar agadex ta karasa RAIHAN ta saki kukanta me karfi harda shura kafa, sakin baki hajiyar agadex tayi tana kallon abinda ya isheta,tafa hannuwa ta shiga yi tare da cewa yo kaji iskancin banza ina ji ke kika ce bakya sonshi,mu kuma muka bi abinda kike so muka ce idan komai ya daidaita sai a raba auren kowa ya auri wanda yake so,sallamar wazer cikin deep voice dinshi ce ta dakatar da hajiyar agadex daga magana", yauwa tunda kazo sai ayi a gabanka wata ƙilma yanzu zaka rubuta mata takardar kowa ya huta", dan zaro manyan idonshi da ako da yaushe suke a lumshe ya yi yana furta ya Salam akan labbanshi idanunshi akan Raihan da yake jin kukanta a tsakiyar kansa", me ya farune? Ya tambayi Hajiya ba tare da ya dauke kallonshi daga kan Raihan ba,kora mishi bayani Hajiyar agadex ta yi daga karshe ta ce", shine kuma zata zo tana kukan sakarci saboda na fadi gaskiya ", kawar da kanshi ya yi yana dan fidda karamin murmushin dake kan labbanshi,au baza ka ce komai ba ko kana so kace min ba haka a kayi ba? Haka akayi Hajiya amma yanzu ki yi hakuri idan ta ce tana sona ba sai an raba auren ba tunda dama dan ta ce bataso ne", Tom shike nan hakan ya yi bari na fita na barku abinda ake ciki sai kasanar dani dan da zancen tarewa nake yi to amma tuna wannan sharadi yasa na daina maganar", ta karasa maganar tana fita tare da sakin dariyarta da take ta kannewa tun dazun. Tana fita ya taka a hankali ya isa inda Raihan ɗin ke kwance a ruf da ciki tana fama da hawayenta na shawagaba,a hankali ya bi bayanta cikin wani irin shauki dake tasowa tun daga can kololuwarsa,bai sakar mata nauyinsa ba amma gaba dayan jikinsa ya haɗe da bayanta har tana jin tudun jikinsa a nata,runtse idanunta ta yi tana sauke wani irin numfashi dake gauraye da wata irin kauna mara algus,cikin Muryarshi dake kara narkar da ita cikin duniyarsa ya ce", meye na kuka keda kika ce bakya so yanzu kuma ana ƙoƙarin yi miki gata na rabaki da abinda bakyaso ai ina ga sai tsallen murna tunda an rabaki da abinda bakyaso ko? Bata san lokacin da ta yi wata irin juyowa ba saiga dan Ammi akasa yar Mami a samansa dukan ƙirjinshi ta fara yi tana ci gaba da kukanta cikin kukan ba tare da ta saurara da dukan da take mai ba ta ce",Ni bansan meye ƙi ba in dai akanka ne,ko kai dinma ai basona kake ba", rike hannunta ya yi yana son ganin fuskarta da taki bari ya kalla sannan cikin yanayin da take sake jefa shi na shaukin ƙaunarta mara ƙarshe ya ce", Raihan na fi kowa sonki in kika cire Mami da Abbie su dinma fa ba su fini sonki ba", Raihan ina miki kaunar ƙauna wadda harshe ba zai iya fadinta ba,ban san me zance akan sonki ba Raihan i love You ya karasa fada yana hure idanunta da tunda ya fara tsakura mata son da yake mata ta kafeshi da su,kasa cewa komai ta yi sai kawai ta kankame shi tana bin fuskarsa da sumba a ko wane loko da kusurwa na fuskarsa. Aunty Amarya...... Tana cikin tunanin ta yadda za ai ta shiga hotel din,sai ga adaidaitar su Surry ta tsaya a gaban motar Bashir,Bashir dake dan kalle kalle ya yi kyakkyawan gani saboda Surry da ya gani tana fitowa daga adaidaitan hakan yasa gaba daya hankalinsa ya koma kanta wannan shine ya bawa Aunty Amarya damar shigewa hotel din ba tare da Bashir ya ganta ba.....✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page59 `` Uch innawuro Raihan zata cinye miki jika wazer ya fada yana lumshe idanunsa saboda yadda yake jin ɗumin bakin Raihan a duk sassan fuskarshi,hakan ba karamin tasiri yake yi a jiki zuciya da ruhinshi ba,duka ta shiga kai masa tana hawayen sakalci daga karshe ya rike hannayenta ya haɗe ta da jikinshi ya shiga aika mata da sabbin darussan da yake son ta fara dauka kafin a kai masa ita inda zai karbi ladar Koyarwarsa. Aunty Amarya...... Ƙirjinta na dukan tara tara ta shiga laluben inda zata Ganshi sai dai bat yayi mata batan dabo,ke Hajiya me kike nema ne?cikin razana aunty Amarya ta juya tana kallon me maganar,ganinshi da uniform yasa ta gane cewa security ne dan haka ta yi saurin saita kanta tare da hadiyar kakkauran miyan da yake kin tafiya zuwa makoshinta,budar baki ta yi ta ce", ban taba shigowa ba Ni bakuwa ce shi yasa nake neman hanyar da zata kaini reseption", ok biyo Ni ya fada yana yin gaba,takun da aunty Amarya zata yi sai ji ta yi an toshe bakinta da handkichip ba a yi wata wata ba aka janyeta daga gurin, security dai sai juyowa ya yi yaga wayam cikin sauri yabar gurin yana kiran gexos domin shi a tsammaninsa gamo ya yi. Cikin yabawa da aikin yaronnasa yasa suka saka Aunty Amarya a mota ba tare da kowa ya Ganshi ba,kasancewar hotel din manya ne ba kowa ke kama shi ba shi yasa ko da yaushe zaka same shi tsit,kuma bai yi hakan ba sai da ya shirya dan sai da ya fara hada baki da staff din da alhakin cc camara ke hannunshi shi yasa ya yi aikin cikin kankanin lokaci. Surry dake kokarin fita daga nafef ta dakata saboda tareata hanyar da Bashir ya yi,bude baki ta yi zata fara zazzaga masa rashin mutumci amma sai ta ji tamkar an shake mata wuya ga wani irin tsoran Bashir da ya shigeta farad daya dan haka sai kawai ta hadiye kalaman da take shirin yi tare da komawa kalar tausayi sannan cikin tausasa harshe ta ce", plz bawan Allah dan bani hanya wallahi sauri nake yi", wani kallon raini ya yi mata kafin ya ce", fito ki biyo Ni saboda bukatar dake tare dani akanki tafi uzurin da kike dashi", yana gama fadar haka ya saki karfen nafef din ya yi gaba zuwa gurin motarsa, cikin mutuwar da jikinta yake kuma yi ta fita daga nafef din ta bi bayanshi, su kuwa su Dady tsayawa su kayi suna kallon abun mamaki saboda su dai a iya fahimtarsu basu ga wata alama dake nuna cewar Surry tasan wannan mutumin ba,cikin dabara Salim ya dauki hoton fuskar Bashir saboda su nunawa Wazer wata ƙil yasan ko shi din waye. Daidai lokacin da Surry ke bude gaban motar Bashir zata shiga,a daidai lokacin ne kuma oganta ya sako hancin motarsa dan fitowa daga cikin hotel ɗin,karaf idanunsa suka sauka akan Surry da Bashir,wani irin kallo ya bisu dashi zuciyarshi na masa mugun tunani akan Surry,wata irin kwafa ya yi tare da kallon gefan da yaronsa yake yana cewa ina so ka fita ka bi su kaga duk inda zasu daga karshe ka kawo min bayanai akan alaƙar dake tsakaninsu", ok OGA yaron ya fada yana saurin fita daga motar da gudu ya figi motar baka ganin komai sai ƙurar gurin da ya bari. Inna maimuna Yusuf.... Cikin kebabban gurin da suka saba haduwa suke zaune suna fuskantar juna,kowanne fuskarsa cikin walwala wanda hakan yake nuna cewa suna cikin farin ciki,mika mata hannu Yusuf ya yi dan ta bashi takardun amma sai ta yi biris dashi shi kuma bai janye hannunsa ba ya tsaya yana son ganin gudun ruwanta wanda dama hakan suke fata domin ta shiga tarkon da suka dana mata,fuskarta ce ta sauya daga murmushi zuwa fusata kana ta ce", banzo dasu ba, shima hade fuskar ya yi sannan ya ce", saboda me? Saboda hakan shine tsarina", ta bashi amsa babu alamun wasa a tare da ita", murmushin gefen baki ya yi kafin ya ce", to me kike nufi da hakan? Cin amana ko me? Ka bawa kanka amsa ta faɗa tana mikewa sannan cikin tsare shi da idanu ta ce", Yusuf kana tunanin da zan saida raina a banza ne? To idan kana tunanin hakan ka daina domin wannan aikin da nayi daidai yake da saida rai domin za a iya kamani amma saboda yadda nake son kudi da yadda na yi tsawon shekaru ina farautarsu na amince da hanyar da ka kawo min domin samun mafita,yanzu dai babu abinda zanyi maka sai godiya", kar kiyi min haka bakya tunanin zan iya tona miki asiri? Bana tunanin haka Yusuf saboda na Fika wayo nasan takan iya shege kala kala shi yasa ban yadda na baka kofar da zaka san ko Ni wace ba", dan Allah karki min haka", ya fada cikin marairaice murya irin ta tausaya masa dinnan,dariya tasa tana cewa taimako daya zan iya yi maka shine zan iya sammaka wani abu daga cikin abinda na samu ma'ana dai kudin aikin da kayi min na samo min wadannan dukiya da nake ganin zasu yi matukar bani wahala gurin samuns.......muryarta ce ta katse saboda jin wani abu kamar bakin bindiga a saitin kunnenta,wani irin miyau ta haɗiya kafin a hankali ta juyo da kanta zuwa saitin da aka ritsata da bindiga,ido hudu ta yi da wasu manyan kattin jami'an tsaro kusan su shida zagaye da ita hannayensu dauke da manyan bindigu Dukansu sunyi mata saiti alamu dai ya nuna jiran kiris suke su sakar mata harsashi. Dariyar da yusuf yake yi ce yasa hankalinta ya dawo kansa kallonsa take yi bakinta yana kasa motsi ta rasa wane irin kalar tunani zata yi bare akai ga batun furta wani abu,katse mata tunani ya yi da cewa inna maimuna kina tunanin kinci bulus ne? Zaro ido ta yi tana mai kuma cika da mamakin yadda akayi yasan ita ce", take wasu hawayen bakin ciki suka shiga zuraro mata, adaidai lokacin da take ji duniya ta dawo mata sabuwa a daidai lokacin ne kuma ƙaddara ta yi mata shammata tabbas Yusuf ya shammace ta, wai duk ma ta yaya akai hakan? Kamar yasan tambayar da take yiwa kanta ya bata amsa da cewa Kinga haziki fasihin da ya shirya wasan Ni kuma na aikataahi dai dai da yadda ya tsarashi ya fada yana nuna mata hoton wazer dake kan wayarsa ya cigaba da cewa Hajiya inna maimuna me wayo wato da ace wazer ba kwararre ba ne da tabbas kece zaki ci wasan domin kuwa kinyi kokari ta yadda kika dora surukarki a poster film din da yanzu ita ce a hannu bake ba,to da ke Allah yasan zuciyarta yasan alkhairinta akan danta shi yasa ya bawa Wazer fasahar tunani har ya gano shirinki ya kuma wargazashi,", kuje da ita kafin mu tunkudo keyar ragowar shedanun ya fada yana juyawa da barin gurin duk alokaci ɗaya. _____________&&&& A hankali yake kwantar da ita tamkar wata jaririya,dan motsawa tayi kamar zata tashi hakan yasa ya fasa kwantar da ita ya cigaba da rikonta a jikinsa a hankali yake shafa bayanta yana ɗan jijjigata,ita ko Raihan hannuwa biyu tasa ta kuma zagayeshi tana kuma lafkewa a jikinshi,numfashi take fitarwa a hankali cikin nutsuwa kallo daya za kayi mata kasan cewa ba karamin jin dadin Baccin take yi ba,wayarshi ce ta fara dan zumm zumm na baburashin kallon fuskar wayar dake saitin fuskarsa ya yi,sai da ya dauki sakanni kafin ya dan furzar da iskar bakinshi yana tunanin ta yadda zai kwantar da Raihan ya dauki kiran da Yusuf ke yi masa dan ya tabbata kiran me muhimmanci ne,cikin ainahin nutsuwarshi ya shiga kokarin kwantar da ita a wannan karon bata motsaba har sai da ya kwantar da ita ya daga dan mikewa kawai sai ji ya yi tasa hannu ta kuma janyoshi tare da tura karamin bakinta fuskarta akwabe alamun sakalci sai da ta janyo shi ya dawo jikinta sannan ta ci gaba da baccinta cikin kwanciyar hankali,wani irin kasaitaccen murmushin da ba a cika gani akan kyakkyawar fuskarsa ba ya yi tare da sa hannu ya shafa lallausar kumatunta,sai da ya dauki kusan mintuna biyu a haka sannan ya kara gwada tashi cikin takatsantsan din kar ta farka. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dan gyara jikinshi Allah yaso shi ba manyan kayane a jikinshi ba da ya sha tsiyar hajiyar agadex,rufeta ya yi da tattausan bargonta sannan ya bar dakin cikin dan hanzari yana danna kiran Yusuf da har ya gaji da kiransa ya kyaleshi. Sai yanzu ka ga damar dauka baban SOYAYYA? Yusuf ya fada cikin dan kufula, lumshe ido Wazer ya yi kafin cikin deep voice dinsa ya ce", sorry man ina fata komai ya tafi yadda muke so?ajiyar zuciya Yusuf ya sauke sannan ya bashi amsa da cewa komai ya tafi daidai da ikon Allah", thanks ya fada yana fita daga tafkeken gate din gidansu Raihan. Haka kawai zuciyarshi ta shiga raya mishi ya sake komawa asibiti wajen Abbie duk da cewa dazu ya je", wannan tunanin da ya yi yasa ya karya kan motarshi zuwa hanyar da zata maidashi asibiti. Dady da Salim wajen aiki suka koma amma zuciyonsu cike suke da tambayoyi akan mutumin da ya dauki suryy,duk da cewa basu da damuwa akan ko wane motsi na Surry tunda sun riga sun gama dana tarkonsu akanta,Dady ne ya dubi Salim ya ce", bari na dan zaga dan wallahi cikina ya Murda ", dariya Salim ya yi tare da cewa kai fa zabone wallahi wasa_wasa abu kadan ke razanaka", naji din Dady ya fada yana nufar hanyar toilet dinsu na maza. Shiga ya yi sai kuma ya fahimci kamar da mutum a toilet din kusa dashi,kasancewar toilet din irin me kashi_kashinnanne,tsugunne ya yi , sai dai kuma abinda yaji yasa shi kasa yin tsugunnen sai dai yana kai bai motsaba,waya ake yi daga katangar toilet din ta gefanshi, wannan ba Muryar abu Huraira ba ce? Ya tambayi kansa,kafin ya samo amsar tambayarsa ya kuma tsinkayar Muryar cikin rada rada yana cewa gaskiya OGA na kammala aikina dan haka kawai ka sallameni dama tun farko ba kai nazo yiwa aiki a gurinnan ba su shugaban jam'iyya nake yiwa aiki kai kuma ka siye Ni dan kawai na kashe maka OGA wazer", zaro ido Dady ya yi zuciyarshi na cika da mamaki da matsanancin tsoro,ɗan jim abu Huraira ya yi alamun ana magana ta wancan bangaren,ɗan numfasawa ya yi bayan ya gama sauraron me maganar sannan ya ce", duk nasan haka Nima ba dan ka kawar da Khalil din ba ai da yanzu ina garkame tunda shi ya ganni red hand na zubawa OGA wazer guba a lemunsa kuma ba tare da tsoro ba ya zubar da ita ya kuma ci alwashin tona min asiri, awannan lukacin da ban yi saurin turo maka test na gaya maka ba da tuni ya sanar da wazer,sai gashi kuma mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya saboda ina tsoran zai tona Ni ban tsira da aikin kowa daga cikinku ba,shi yasa nayi tunanin naje offece din Raihan neman videon su Dr sanater,to banga video ba kai kuma ka ɗauke khalil yayin da nake shirin guduwa, dauke shin da ka yi ne ya bani kwarin gwiwar zama saboda shirin da na yi na dora alhakin hargitsewar office din Raihan akansa to ashe ma shegiyar itama tana ankare da komai shi yasa ta ki aje videon a offece din a inda Allah yaso Ni shine bata gama gano waye acikinmu maci amanar ba," ya kare maganar da dan waigawa bayanshi saboda shi kanshi bai san dalilin da yasa ya shiga maimaitawa ogannasa abinda ya faru a baya ba,bayan kuma shima yasan komai. Dady kuwa wata irin zufa ce ta shiga kwaranyo masa,ji ya yi ba zai iya ci gaba da zama a kan toilet din ba, cikin sauri ya dannawa recording din da tayi save, kasa jurewa ya yi kawai ya fita a zuciye ya yi gaba da gaba da abu Huraira wanda ya yi matukar razana da ganin dadyn,kafin ya yi wani tunani yaji wani irin kakkarfan naushi a fuskarsa wanda take yasa shi suma, bayan jini da majinar da yake fitarwa ta hanci da baki.jansa Dady yayi tamkar kayan wanki ya fita dashi har faffadan filin gidan jaridar. Surry dai tunda suka fara tafiya tayi tsuru_tsuru ga baki dai amma ba halin magana,duk lokacin da ta kalli Bashir dan ta ce ya sauketa sai taji ta kasa,sai da suka yi tafiya me nisan gaske kafin su isa inda yake son su isa ɗin,fita ya yi ya kulleta a mota kai tsaye ya nufi bakin ruwan da suke kiran tsohuwa me jini shida abbansa,yana zuwa ya shiga karanta ɗalasumansu na tsafi bai saurara ba har sai da tsohuwa me jini ta baiyana cikin mummunan suffarta.nunashi ta yi da sandar tsafinta sannan ta ce", ka gama aikinka kaje gobe a daura maka aure da ita da kaje gidansu za a baka babu jinkiri,hahhhhh ta shiga babbaka dariyarta mara dadin sauraro kafin ta bace cikin hayakinta na tsafi. Har gida ya maidata sannan ya yi magana da babanta akan cewa zai turo magabatansa gobe a daura musu aure,baban Surry kuwa yana jin wanda zai aure masa marajin yarsa ya amince ba tare da wani dogon nazari ko bincike ba. __________ Kamar yadda yake ka ida duk wanda yazo sai securitys sun bincike shi,to haka ta kasance ga wazer. Kai tsaye dakin da Abbie yake ya nufa,duk da yana dan jin nauyin haduwa da Aunty Amarya saboda yau girkinta ne kuma Raihan ta ce masa ta taho nan din tun dazu,ga mamakinsa bai samu securitys a bakin kofarba,bai kawo komai a ransa ba yasa hannu ya Murda handle din kofar tare da yin sallama can kasan makoshinsa,cak ya tsaya yana kallon mutumin da ke tsaye kan Abbie da wani jan kyalle a hannunsa sai kwarya ga kuma wasu yan tarkace nan a gefe ko wanne da amfaninsa. Innalillahi wainna'ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fil musibati wakalufni Khairan Minha", addu'ar da wazer ya shiga maimaitawa ke nan akan harshensa,yayin da Abba yahya ya ke can yana ci gaba da aikinsa ba tare da ya san me ke faruwa ta bayansa ba. Abba yahya aji tsoran Allah, Allah Ubangiji ka tsare mu daga bin sharrin zuciya ka yaye mana son kai irin na hassada,kasa mufi karfin zuciyarmu,ka bamu ikon zama lafiya da makiyanmu Allah kar ka bamu ikon cutar da ko makoyinmu bare masoyi ya rabbil alamin 🙏 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page60 ``` HAIDAR........ A hankali yake buɗe idanunsa da suka yi masa nauyi saboda yadda suka yi matukar kumbura,laluben inda zai ga kwanon abincinsa ya fara yi,dan dama kullum haka yake sai yaga yunwa tana neman kasheshi yake daukar abincin da suka kawo masa yaci,a maimakon ya taba kwanon abinci sai kawai yaji hannunsa yana shafa karamar wayar Tecno me madannai,cikin wani irin rawar jiki ya danko wayar a hannunsa yana fata ace ta gaske ce ba fanko ba,abin kamar almara ko mafarki yana kunnawa sai ga haske ya kawo sa hannu ya yi ya rufe bakinsa saboda ji yayi kamar zaiyi ihu saboda dadi amma sai ya yi saurin nutsar da kansa tare da yin hamdala ga Ubangiji da ya kawo masa mafita cikin sauki ba da wayo ko dabararsa ba,cikin sauri ya shiga tafa nomber WAZER hannunsa na rawa kamar wayar zata subce. Aunty Amarya........ Tunda ya kawota gidansa da yake aikata Masha arsa yasa yaransa suka daureta ajikin kujera ta yadda ko motsi bazata samu sukunin yi ba,kujera suka aje masa a gabansa ya zauna yana kare mata kallo kafin ya basu umarni su bashi ruwa,da sauri suka bashi robar faro bayan sun bude masa murfin,babu imani ya shiga tuttulawa aunty Amarya ruwan masu sanyi a fuskarta,wata irin sheshsheka ta yi tamkar zata shide tare da bude idanunta a gigice a lokaci daya tana yunkurawa dan tashi amma sai taji ko ina a daure,ɗaga kanta ta yi dan ganin a inda take dan sai yanzu abinda ya faru ya dawo mata,zare idanuwa ta shiga yi,kafin ta tsaida idanunta akansa idanunsa take kallo tana son gane inda tasan wannan kalar idon,katse ta ya yi cikin shakakkiyar muryarsa da cewa waike jaruma ko? To yanzu ina jarumtartaki da wayonki suke?kin boye RAIHAN na nemo ta yanzu kuma kin biyoni saboda kisan ko ni waye sai kuma gashi reshe ya juya da mujiya ke kika zo hannuna ba tare da na shirya hakan ba,enyway dama Raihan na shirya kwamushewa amma tunda ke kin rigata samuwa zanyi amfani da hakan wajen cimma burina,nasan zan cimma nasara tunda ke dinma Raihan na sonki dan haka duk abinda nace ta bani zata bani koda bata san inda dukiyarta suke ba nasan zata nemo su ta kawo min dan ta fansheki", ya kare maganar yana zukar sigarin da yaronsa ya mika masa bayan ya kunna masa. Tuf yaji kakkauran miyan da ta kasa hadiyeshi akan fuskarsa cikin idanunsa dan saida ta daidaici inda babu facemask sannan ta tofeshi,shafo gurin ya yi yana kallonta yana kallon miyan,kafin ya samu abin cewa ta riga shi cikin kakkausar murya da bushewar zuciya ta ce", tur tur wallahi da masu mugun hali irin naka kuma in sha Allah wannan shine sanadin karshen zaluncinka, Allah na tuba fir auna ma fa ya yi ya gama bare kuma kai karamin alhaki dan haka ina shaida maka da babbar murya wallahi wannan abun da ka yi shine sanadi, fitowar da nayi banyita a banza ba,Kum......kafin ta karasa ya wanke farar fuskarta da wani mahaukacin mari tuni jini yayi tsartuwa ta hanci ta baki,duk da haka bakinta bai mutuba ta ce", kasa a ranka Raihan sai ta yi maka mafiyin wannan dan wallahi sai ta rama min", dariya ya saka cikin izgili ya ce", har yanzu lokacina baiyi ba dan babu wanda ya isa ya hana min cikar burina ke din nan baki isa ba kuma kinyi kaɗan", idan Ni ban isa ba ai wanda ya halicceka ya isa dan haka shi zai isar mana", shiru ya yi yana mamakin karfin halinta,bai sake cewa komai ba ya mike tare da bawa yaransa umarnin su kula da ita kafin zuwa gobe su shigar da bukatarsu gurin Raihan. Wani irin ihu inna maimuna ta saka lokacin da ta ganta cikin wani tsukakken daki baki kirin wanda koda tafin hannunka baka isa gani ba,ko zama ta kasa yi saboda kankantar gurin hatta da taga yar karama a kayi itama saboda kar a mutune,kuka take yi amma ba kukan nadama ba,kuka ne irin na wanda bai samu abinda yake so ba,babu abinda take shiryawa a kwakwalwarta sai hanyar da zata tsere domin daukar fansa akan wazer da Yusuf,sai ina duk wani tunani da zata yi tayi karshe ma kasa tunanin ta yi saboda yadda kuncin zaman gurin ya fara damunta. CHIBADO FM...... Dukansa suke kamar Allah ne ya aikosu,duk wanda yazo jin ba asi da zarar Dady da Salim sunyi masa bayani,zakaga shima ya fara tattare hannun riga an shiga fafatawa dashi,dakyar wasu daga cikin manyan dattijan staff suka kwace shi tare da bada shawarar su kulleshi har sai wazer ya zo,da wannan shawarar su kayi amfani suka kulle shi a daya daga cikin dakunan da ake aje tsofaffin jaridu babu ruwansu da abinda zai cije shi suka kulle suka kama gabansu, kowa da abinda yake fada akansa dan kuwa sosai suka ji ciwon yadda yake son kashe me gidansu da suke samun na rufawa kai asiri a karkashinsa. ___________ Dr Sabo dake kokarin shigowa shima tsayawa ya yi cak yana leken abinda ke faruwa wanda ya hana wazer ci gaba da takawa zuwa cikin dakin,zaro ido ya yi shima cikin wani irin al'ajabi da tsananin tsoro,kallon Wazer ya yi sai yaga bakinshi na motsi daga dukkan alamu dai addu'a yake yi,a tsaye yake kyam fuskarshi babu alamun tsoro ko razana tun shigowar da yayi yaga abinda Abba yahya yake yi ya fara innalillahi tare da jero addu,o'in karya sihiri, hakan da Dr Sabo ya gani shima kawai sai ya bi wazer ya shiga karanto nashi addu'ar. A bangaren Abba yahya kuwa har yanzu bai san abinda ke faruwa ba,hankalinshi kwance yake tsafinshi akan Abbie saboda tsohuwa me jini ta bashi tabbacin cewa babu wanda ya isa ya shigo ko da an shigo ma babu wanda zai Ganshi idanunsu makamcewa za suyi daga kansa,shi yasa ko a mafarki baiyi zaton wani zai shigo har ya Ganshi ba,ya yadda da tsohuwa fiye da yadda ya yadda da Ubangiji (subhanallah Allah kasa mu fi karfin zuciyarmu Allah ka karemu daga aikata shirka komai kankantarta ka karemu daga yadda da waninka, Allah mun yadda kaine Allah mahaliccin sammai da kassai mahaliccin duniya da lahira wuta da aljanna muna rokonka ka rufe idanunmu daga kallon wani a matsayinka ka toshe kunnuwanmu daga yadda da kalmar waninka,ka kuma rufe zuciyoyinmu daga jin Dar akan ikonka da kudurarka tare da buwayarka ya arhaman Rahimin). Cikin mamaki yake taba kayan tsafinshi yana kuma maimaita ɗalasuman tsafin sai dai kuma har bayan wasu sakanni babu motsin komai,hannu yasa ya kuma taba saitin zuciyar Abbie yaji ko dai aikin ya kammala ne ba tare da ya nuna masa wata alama ba,sai dai kuma kudura ta Ubangiji da buwayarsa wanda ke dayawa da kashewa a maimakon yaji zuciyar Abbie ta daina aiki sai kawai ya ji tana bugawa a hankali kallon fuskar Abbie da zaiyi sai kawai suka haɗa ido,kallonsa yake ido cikin ido,da sauri Abba yahya yasa hannunshi ya taba kwayar idon Abbie wai ko mutuwa yayi sai kawai yaga Abbie ya juya kwayar idonsa har ma da guzurin hawaye, a matukar razane Abba yahya yaja baya yana nuna Abbie kafin cikin rawar murya ya ce", a'a sam hakan ba zai yiwu ba saboda tsohuwa ta ce", ba zaka taba tashi ba har abada saboda ita ta kwantar da kai ba wai coma kashiga ba dan haka ba zaka tashi ba har sai mun gama aikinmu akanka wanda cikin dayan biyu zaka yi daya ko mutuwa ko tashi ga hauka", To Allah da rayuwa da mutuwa ke hannunshi bai nufa ba", ya ji an fada daga bayanshi,a razane ya kuma juyawa sai kuwa karaf suka haɗa ido da wazer sai Dr Sabo dake gefanshi yana kallon abinda tunda yake a duniya bai taba gani ba sai dai yaji labari tsafi ba,to yau dai gashi ana aikata tsafi agaban idanunshi. Wata irin zufa ce ta shiga kwararowa Abba yahya tamkar wanda ake jikashi da ruwa,cikin tashin hankali ya shiga neman tsohuwa saboda tazo ta taimakeshi,amma kiran duniya ya yi babu ita babu labarinta,a hankali cikin nutsuwa wazer ya taka zuwa gaban Abbie da yake ta kokarin tashi saboda jikinsa da yake son motsawa,cikin dan gaggawa wazer ya karasa ya dagoshi yana jera masa sannu,ina RAIHAN? Abinda Abbie ya fara tambaya ke nan farkon bude bakinshi,tana gida cikin koshin lafiya", wazer ya yi saurin bashi amsa saboda samun nutsuwarsa,jinjina kai ya yi sannan ya kuma cewa ina his excellency? Abbie ka nutsu in sha Allah za kaji komai shima his excellency ɗin yana nan lafiya", murmushi me ciwo Abbie ya yi yana kallon Dr Sabo da ya bashi amsa sannan ya ce", bana jin his excellency zai zama cikin koshin lafiya saboda hatsarin da Yahya ya jefashi a ciki,nasan ba wanda zai fahimce shi saboda sarkakiyar lamarin", haka ne cewar wazer,Dr Sabo gida kawai zan tafi babu bukatar zamana a nan", Abbie ya kuma fada yana ƙoƙarin tashi,da sauri wazer ya rike shi ya taimaka masa ya mike,Dr Sabo bai hanasu tafiya ba saboda shiima ya fahimci Abbie yana bukatar shiga cikin iyalansa ko dan rage radadin da yake ji a yanzu,ai shi yaga kokarin Abbie dan da wani ne ba zai iya juraba,wata wajen biyar yana kwance ranar farko da ya farka ya tsinci dan uwanshi jini daya a kanshi yana kokarin kasheshi ta hanyar tsafi,dan uwan ma da ya bashi yarda dari bisa dari kai wallahi yayi kokarin yin takwakkaloli,hirar Dr Sabo ke nan a cikin ranshi. Dr Sabo juyowa ya yi dan su kama Abba yahya amma sai wayam babu shi babu alamunsa ya gudu,Dr Sabo ya fada yana kuma ware idanunsa a Loko da sako na dakin,babu damuwa duk inda yake zamu kamashi cewar wazer da yake sakale da hannun Abbie suna takawa a hankali. Sai da Dr Sabo yaga fitarsu daga asibitin sannan ya dawo yana kuma tuajjibi da tsarkake Ubangijin talikai. HAIDAR........ Karaf ya ji an rike hannunsa cikin duhun gurin da baya iya kallon ko abinda ke gabansa,kafin yaji kakkausar Muryar da ta saba yi masa magana duk lokacin da ake son yi masa magana tana,kana kiran wayar nan tamkar ka kira ajalinka ne dan OGA DUDU ba zai Barka ba,daga haka aka fizge wayar tare da fita daga dakin, sai alokacin yasan cewa ashe shigowa akayi tsabar baya cikin hayyacinsa ne yasa baiji motsi ba,in sha Allah na kusa barin gurinnan da numfashina,ya fada yana maida tsatstsaman jikinsa zuwa jikin bangon dakin dan jingina. Kamar daga sama securitys din gidan suka ga Abbie ya fito daga mota,kafin wazer ya fito tuni sun ƙaraso cikin madaukakin farinciki suna jera masa sannu tare da taya murnar samun lafiyarsa,kafin wani lokaci tuni su mama murja da ahlinsu wadanda suke nan sun hallara a wajen,Hajiya goggo rungume shi ta yi tana kukan farinciki haka masu aikin gidan suka fito suna murna bangonsu ya samu lafiya,baffa Ali kuwa kama hannunshi ya yi suka nufi bangarensa da shi saboda ya fahimci Abbie yana cikin wani mummunan yanayi dan babu farinciki ko daya akan fuskarshi idan ka kula ma zaka ga lokaci lokaci yana share hawaye cikin dabara,baffa Ali ya ce", kowa ya tafi zuwa anjima kan sannan Abbie ya ɗan samu nutsuwa ya huta. Wazer da yake shirin shiga dan duba Raihan ya dakata saboda sakonsu Dady da ya tarar rututu a wayarsa hakan yasa ya dakata da shiga falon ya koma ya fada motarsa yana jin wani irin rashin dadi ga wata irin gajiya da yunwa da suke ta cinshi saboda rashin samun Hutu ko nutsuwa a cikin kwanakinnan idan ka kula ma har wata yar rama ya yi. Da sauri yaron dake biye da wazer ya kira wayar ABBAN rabi,yana dagawa ya ce", OGA ya fito daga gidan yanzu", ABBAN rabi ya ce", yauwa bari na kira ciska,kashe wayar ya yi ya kira su ciska.ciska yana dagawa ABBAN rabi ya ce", ku bishi da kun samu dama ku harbeshi a ko ina", ok OGA baka da matsala cewar ciska,kashe wayar su kayi tare da jan motar da suke ciki suka bi bayan wazer da yake tafiya kamar mara laka,ta window ya kula da masu binshi hakan yasa ya canja hanya cikin kwarewa da sanin makamar tuƙi. Dakarfi ciska ya daki abinda ke gabanshi yana cewa shet wannan babban kaine ban taba aikin da aka wahalar dani irin haka ba,gaskiya idan na samu gayennan sai nayi masa kisan wulakanci saboda ya karya min record ", ciska ya fada cike da jin haushi. Wazer yana ganin ya tsere musu ya dan dafe kanshi cike da gajiya,gidansa ya karasa, komi baiyi ba ya shiga kunna computer tare da yin cineccting din wayar Surry,take abinda ya faru ya shiga maimaita kansa ta hanyar murya,sai kuma ga hotan Bashir da su dady suka ɗauka ya fito baro baro,dan jim ya yi kafin ya furzar da iskar bakinshi, rufe computer ya yi tare da mikewa ,tashin da zaiyi sai ga wannan Flash din ya fado daga jikin kujerar da ya aje shi wancan karon,yanzu ma har zai basar saboda abubuwan dake gabanshi sai kuma ya koma ya zauna tare da daukar Flash din ya jona. Runtse idanunshi ya yi saboda abinda suka gane mishi,duk da cewa yaga makamancinsa a asibiti ,ba komai ne a ciki ba sai irin barnar da Abba yahya yake ta kashe kananun yara da yanmata da yadda yake sawa ana kamo su ana cire musu wani sassa na bangaren jikinsu da yadda yake sawa yan dabanshi suna tada tarzoma dan kawai a zubda jini,gungun yan sara suka ne dashi sun kai su dari babu abinda yake sasu su yi sai barna da kashe rayuka,ashe ba iya nan ba ne rarraba su yake yi jiha jiha suna sato masa kananan yara yana bawa tsohuwa me jini jininsu dan kawai yana son mulki da kuma uban kudin da Abbie ya tarawa Raihan da shi kansa wanda Abbie yake dasu,karshe wazer kasa ci gaba da gani ya yi saboda muguwar barnar da ake yi,kashewa ya yi yana tunanin ta yadda aka yi aka tara wadannan shaidu duk a guri daya,duk da cewa hadasu a kayi to amma wane dan tsautsayinne ya ke shiga wadannan guraren yana dauka ba tare da an Ganshi ba? Duk da cewa video bai nuna fuskar Abba yahya ba ma ana dai wanda ya haɗa videon baisan waye me wannan barna ba,to amma ya akai yazo wajen shi? RAIHAN ya furta akan labbanshi cikin daukaka mamakinshi tabbas ita ce,da sauri ya mike tare da daukar Flash ,yana kokarin fita ya tuna da karamar wayarshi da yau kaf bai dubata ba,bayan tana daga cikin manyan wayoyin da yake yi na sirri akan aikinshi,duba fuskar wayar ya yi bayan ya kunna haskenta,miss call ya gani da bakuwar nomber,a yanzu baya kin bin nomber ko yaya take dan haka ya shiga kiran nomber amma sai aka ki dagawa,kallon fuskar wayar ya kuma yi sai yaga alamun sako hakan yasa ya yi saurin shiga inbox ya bude sakon. Wazer kayi tracking number nan ko kuma kasawa Alh Yahya ido domin duk abinda ke faruwa shine a yanzu haka ina hannunsa dalilin sirrinsa da yake tunanin cewa Ni na bankadosu bayan bai san cewa Raihan ce ta haɗa video nan ba,Ni nawa shine gano shine a cikin video da nayi,ganin bai gano Raihan a cikin case dinba shi yasa naki sanar dashi inda Flash din yake ko kuma wanda na bawa,sanin cewa za a iya kamani shi yasa na yi dabarar yi maka text ina fata zaka taimakamin ka kuma taimaki his excellency ta hanyar watsa wannan abin ta boyayyar jaridarka me suna tree full y trues.........✍🏽 Mu hadu a netx pg dan sanin waye ogan Surry *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page61 ``` ......Yana gama karanta sakon ya damƙe wayar a hannunsa tamkar zai rabata biyu,sai da ya dauki kusan sakon goma a haka kafin cikin sauri ya dauki nomber da haidar ya Turo masa sako ya turawa Yusuf tare da yi masa short din sako da cewa yana so a yi tracking nomber nan a ranar nan, yana gamawa aka kwala kiran sallar magriba, dan haka ya koma ya dauro alwala ya fita sallah. Baiyi gaggawar tashi daga Masallaci ba har sai da aka kira isha ya gabatar da ita cikin jam'i sannan ya baro unguwar gaba daya, zuciyarsa cike da tsoran Allah tare da mamakin abinda mutanen duniya suka zama akan son zuciya. Duk abinda ke faruwa Raihan bata sani ba,saboda Baccin da take yi,sai dab da magrib hajiyar agadex tazo ta tasheta tana cewa haba Raihan wannan wane irin bacci ne haka? Ku dai yarannan na zamani gaba daya baku da kunya duba dai daga Zuwan mijinki har kin ware kina bacci kamar bake ce me yiwa mutane bore akan bakya sonsa ba fi'ilin banza fi'ilin wofi,shima da nake jira yazo ya sanar dani abinda ake ciki banga idanunsa ba tun ina jiransa har na hakura Ni ma na kama Baccin rashin abinyi,da wannan mitar abakinta ta fita,ita dai Raihan bata tanka mata ba, tashi ta yi ta Wada toilet ta ɗauro alwala ta yi sallah sannan ta fito falon tana raba idanu dan ganin ta inda Mami zata bullo,tunda ta shiga dakinta bata ganta ba ta fito ta shiga dakin hajiyar agadex tana tambayarta Mami bata dawo ba? Kafin hajiyar agadex ta bata amsa sunji sallamar Abbie da ya kasa jure rashin ganin Raihan da maminta ya gudo bayan ya yi wanka ya yi tsaf dashi kai baka ce shine yake kwance tsawon watanni babu motsi ba. Ko a mafarki Raihan taji Muryar Abbie dinta sai ta gane shi,dan haka cikin wani irin gudu kamar zata kifa ta fito daga dakin Hajiya tana baza ido dan tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiyo mata,aiko da fuskar Abbie ta ci karo yana tsaye a tsakiyar falon fuskarsa akwai walwalar da babu a dazu farkon zuwansa, alhamdulillah abinda Raihan ta faɗa ke nan tare da kankame Abbie tana zubda hawayen farinciki,cikin wata irin kauna mara misaltuwa Abbie ya yi mata masauki a jikinshi yana shafa kanta cikin kaunar da baki ba zai iya fadinta ba,dukkansu babu wanda yake iya magana sai ajiyar zuciya da suke saukewa a tare,tabbas wani farincikin ya wuce gaban a kwantantashi ko a tsaya fadarsa da baki. Hajiyar agadex kanta da ta fito ruwan hawaye take matsewa daga idanunta dan su abin yazo musu a bazata daga ita har Raihan ɗin. A hankali ya janyeta daga jikinshi tare da kama hannunta suka zauna akan kujera,itama hajiyar sai ta zauna tana kallon Abbie cike da son karin bayani,fuskantar hakan da ya yi ne yasa shi murmushi sannan ya ce", Hajiya mun sameku lafiya? ya a kaji da wannan tashin hankali? Alhamdulillah Nura ko mai ya wuce tunda Allah ya baka lafiya ya tasheka ba tare da iyawar masu iyawa ba,ya nufe ka da bude ido dan ya nuna shi din ishashshene me yi a sanda yaso,lallai Allah alhakimune babu abinda zamu ce sai godiya gareshi", ta karasa maganar tana goge ragowar hawayenta, jinjina kai Abbie ya yi sannan ya dan kalli Raihan yana cewa ina maminki take banji motsintaba? Da sauri RAIHAN ta kalleshi tana mai fiddo manyan idanunta da suka nuna tashin hankali a lokaci ɗaya,sannan ta ce", Abbie tun wajen la asar Mani ta fita cikin damuwa ta ce min wajenka zata zo kuma har yanzun bata dawo ba," shiru ya yi yana son tuna lokacin da ya farka,lallai lokacin da ya farka babu ramla a asibiti dan da tana nan Abba yanzu ba zai samu damar shiga ba duk da cewa yana takama da tsafinsa ne a lokacin", idan haka ne ramla ba taje asibiti ba ke nan", wannan tunanin da ya yi yasa kirjinshi dukan tara tara, Allah yasa ramla bata shiga komar Yahaya ba dan lokacin da suka fito ya gudu idan haka ne ke nan har yanzu wasan baizo karshe ba, innalillahi wainna'ilaihi raji'un ya furta can kasan ransa saboda baya so Raihan ta fahimci wani abu dake faruwa bare har ta tayar da hankalinta. Cikin dabara ya dubi Hajiyar AGADEX yayi mata alamar cewa dakwai matsala,take ta gane abinda yake nufi dan haka cikin saurin danne Tata damuwar ta ce da Raihan ", Kinga Raihan na manta ban gaya miki ba maminki can AGADEX ta tafi zata karbowa Abbie dinki wani magani to gashi cikin ikon Allah ma kafin yasha maganin sauki yazo daga rabbil alamina,dan haka ina tunanin bata samu jirgi bane shi yasa ta bari sai gobe", cikin gamsuwa da maganar hajiyar Raihan ta gyada kanta tana cewa amma me ye na boye min din? Kar ki damu da wannan kinji auta cewar Abbie yana kallonta cikin tausayawa,shike nan Abbie ta faɗa tana barin falon. Shiru su kayi bayan barinta falon kafin Abbie ya ɗan numfasa cikin damuwa ya ce Hajiya yanzu ta ina zamu fara neman ramla dan na tabbata cewa Yahya ne ya dauketa,Nima haka nake tunani cewar Hajiya,mikewa ta yi tana cewa Nura ka kwantar da hankalinka ramla zata dawo tashi ka koma wajen iyalanka in sha Allah zan yi wani abu", bai Musa bata ba ya tashi ya bar dakine,sai da ta tabbatar ya tafi Sannan ta tashi ta koma dakinta,tsaf ta gama shiri cikin dogon hijab sannan ta kuma fitowa kai tsaye ta dau hanyar barin gidan,aljanarta ce a tare da ita dan haka ita tale haska mata kogon tsafin su tsohuwa me jini,bakinta dauke da karatun bakara sura me tarwatsa rundunar aljannu,zuciyarta cike da son tarwatsa wadannan mutanen mushrikai makiya Allah in sha Allah yau sai na kawo karshen ku da izinin Allah ta faɗa a fili tana ci gaba da tafiya me nisa ba tare da gajiya ko gazawa ba. Wazer kai tsaye gidan Alh Muhammad nur ya taho,duk da cewa dare ya dan fara yi to amma be ji zai iya zama a gida ba tare da yasan yadda Raihan ta yi ta haɗa wadannan videos din ba dan shi har yanzu mamakin hakan yake,bai taba tunanin cewa kwazo da jarumtar matartashi ya kai haka ba. Yana yin fakin ya fito ya nufi inda yaga Abbie tsaye shida Bashir da shima bai jima da dawowa ba,a maze yake duk da cewa ya shiga tsananin shock da ganin Abbie sai bai nuna ba ya shiga nuna farin cikinsa anan Abbie yake tambayarsa yaushe ya dawo yake sanar dashi bai jima ba dan ko sati baiyi da dawowa ba matarshi ma shekaran jiya ta rasu,,sosai Abbie ya jajanta masa daga nan ya umarce shi da su wuce sashen baffa Ali saboda yana son ganinsu gaba daya gidan,bai Musa ba ya bishi a nan ne su ka ci karo da wazer,janyo hannunsa Abbie yayi yana cewa zo muje kai dinma ka zama ɗan gida kome za ai ya kamata ayi da kai itama Raihan ɗin yanzu zata fito", hakan yasa wazer ya bisu suka rankaya gaba daya zuwa part din baffa Ali. RAIHAN dai bata fito ba dan gaba daya hankalinta ya koma kan maminta,waya ta dauka ta kirata akaro na kusan biyar yanzuma tana ringing ba a daga ba wanda hakan shi ya tayarwa da Raihan hankali. A daidai wannan lokacin Aunty Amarya na kulle jikin kujerar da suka daureta masu gadinta suna can daga waje,sam babu wanda ya lura da wayar Aunty Amarya dake yashe daga can gefe inda ta fadi lokacin da suke kokarin kulleta,tana kallon wayar sai dai babu halin dauka dabara ce ta fado mata,hakan yasa cikin sauri ta tura kafarta dake daf da wayar cikin dabara ta dinga janyo wayar tana yi tana kallon kofa,cikin ikon Allah wayar tazo daf da ita sai dai kuma yadda zata yi ta dauki wayar ne tashin hankali,tana kallo wayar ta mutu Raihan ta kuma kira,da sauri ta hade hannunta ta fara kici kicin kunce daurin,idan Allah zai kawo maka mafita tofa zai kawo maka ne ta inda baka taba zata ba dan daga baya dakanka idan kayi tunanin hanyar sai ka shiga al'ajabi da mamakin yadda akai hakan ta faru,itama Aunty Amarya haka ne ya faru da ita dan kuwa cikin ikon Allah sai gashi ta kunce daurinnan tas,take ta yi hamdala ta godewa Allah sannan ta yi azamar daukar wayar wadda ta sake katsewa a karo mara kirguwa,kiran RAIHAN ta fara yi. Raihan da ta gaji da kiran mamin ta aje wayar cikin sarewa da tsananin damuwa, har zata fita daga dakin ta ji wayar na ringing,da gudu ta koma ta dauki wayar hannunta da muryarta duka rawa suke gurin daga wayar da kiran sunan maminta,Mami kina ina? me ya same ki ? Me ya faru kika ki daga wayar? Cikin yin kasa da murya aunty Amarya ta ce", Raihan ina cikin hadari amma ina so ki kwantar da hankalinki kar ki sanar da kowa sai wazer, Raihan daya daga cikin butulayen gidannan yayi garkuwa da Ni ,take ta sanar da Raihan manufarsa ta saceta,ta ɗora da cewa nasan dole zai kira dan haka ki shiru ki kwantar da hankalinki nasan wazer ba zai taba barin ko waye ba.cikin kuka Raihan ta ce", Mami ina cikin farin cikin tashin kafadun Abbie ke kuma kika fada wannan hadarin ke nan har yanzu ba zan samu cikakken farinciki ba? Wane Abbie din kike fada? Mami Abbie mijinki Allah ya tasheshi cikin ikonsa da buwayarsa a yanzu haka yana falon baffa Ali ya ce", yana son ganin kowa da kowa," alhamdulillah ala kulli halin RAIHAN bani da wata damuwa in sha Allah za muyi galaba akan makiyanmu,yanzu ki tashi ki je ,ina so ki kula da wanda baya gurin ko wanda zai shigo yanzu saboda shi wanda ya sace nin yanzu ya taho gidan dan haka nasan zuwa yanzu bai ƙaraso ba saboda gurin yana da nisa,Ki kula da motsin kowa shine abinda ya kamata ki fara yi domin gano mana wannan mugun", Tom shike nan zanyi yadda kika ce", Raihan ta faɗa tana share hawayenta. Da sauri aunty Amarya ta share hawayenta tare da maida wayar cikin jikinta. Itama Raihan fita tayi cikin sauri ta nufi bangaren baffa Ali,tunda ta shiga take rarraba ido dan ganin waye baya nan ,kowa yana nan idan ka ɗauke Hamma Idris da Hamma Affan,take tunaninta ya rabu gida biyu,da sassarfa ta nufi kusa da aunty Khadija matar hamma Affan ta zauna. Tunda ta shigo take jin idanunsa dake yawo akanta,bata san cewa yana falonba amma jin yadda bugun zuciyarta ya sauya da yadda take jin idanunsa ajikinta yasa ta gane cewa yana zaune a falon,sai ta samu kanta da jin nauyin su Abbie da baffa Ali,dan ta tabbata dole su fahimci rashin hakurin wazer akanta,to amma ta wani gefen taji dadin kasancewarshi atare da ita ko dan ta yi sharing din damuwarta da shi,tunda mamin ma shi kadai ta ce", ta sanarwa da damuwarsu duk da cewa tana fushi dashi,satar kallonshi ta yi saiko karaf idanunta cikin nashi,girgiza kai ta shiga yi idanun na cika da ruwan hawayen da bata san ko na meye ba,saboda yadda ya rike kwayar idanunta ya ki bata damar janye nata idon,kallon da yake aika mata wani kallo ne na musamman da yake tahowa da wasu irin sinadarai masu saka gangar jiki da zuciya yin sanyi,yadda jikinta yake mutuwa da wani irin so kauna tausayi da kewa yasa ta fashewa da kukan da kowa saida ya kalleta,hakika ba zata iya jure abinda take ji akan wazer ɗin ba da wannan sakon da yake aika mata shi a yanzu,rasa mafitar ne yasa ta fashewa da kukan,duk da cewa a cikin kukan akwai dalili bayan dalili na kewa da wutar son wazer harda na soyayyar uwar da take jin bata da kamarta a duniya. Rufe idanunshi ya yi yana jin tamkar ya je ya rungume abarsa yasata acikin jikinshi ya yi mata rarrashin da zaisa ta manta da komai na damuwa,rasa yadda zaiyi yasa shi dauke kansa daga kanta tare da jingina bayanshi a jikin makarin kujerar da yake kai tare da maida narkakkun idanunshi ya lumshesu tamkar me yin Bacci. Baffa Ali ne yayi gyaran murya sannan ya shiga lallashin Raihan,a zatonshi kukan murnar samun Abbie ne,shi kuma Abbie tausayinta ne ya kamashi da nashi zaton da baiyi kuskure ba na cewa kukan rashin mahaifiyarta take a kusa duk da cewa baisan sunyi waya da mamin ba. Bayan sunyi addu'a ne baffa Ali ya kuma yin gyaran murya tare da dan muskutawa ya fara da cewa alhamdulillah aka kulli halin dukkan godiya ta tabbata ga Allah me Rahma da jin kai,abinda yasa na ce kowa ya hallara a nan shin..........maganarshi ta katse saboda shigowar HAMMA... _______________ Cikin hikima ta Ubangiji da taimakon aljanarta Hajiyar agadex tazo har babban kogon da tsohuwa me jini take aikata shirkarta ita da mabiyanta.daji ne me suna daji wanda idan ba wadanda suka ɗebe kayansu daga gaban ma'iki suka fito neman duniya ta wannan hanyar ba babu wanda zaka gani a gurin,to amma saboda suma din ababen tsoro ne shi yasa suke rayuwa a gurin batare da tsoron muggan halittun da suke rayuwa a dajin ba. Kurdawa ta yi har cikin kogon da idan ba kaima irinsu ba ne to baka isa ganin gurin ba,to dake Allah ya kawo karshensu shi yasa ya bawa aljanar hajiyar agadex ikon zuwa gurin take kuma ganin komai ba tare da wani shamaki ba,duk da kasancewarta aljana sai da firgita da ganin irin barnar da ake yi wajen da irin mutanen da suke rayuwa a wajen,manyan mutanene wadanda baka taba tsammata za su aikata wannan mummunar aikin ba take gani a gurin kowanne da nashi kalar aikin tsafin,ita dai bata bar karanta Alkur'ani ba wanda take karanta shi da wani irin kushu'i ta yadda tsikar jikin me sauraro zata na tashi me imani,mara imani kuwa sai dai ya dagargaje. A wannan lokacin Abba yahya yana gurfane gaban tsohuwa wadda ya maidata Ubangijinsa roko yake yi da banbadanci akan a sake masa aiki me karfi wanda zai rufe bakin duk wanda yasan yana aikata wannan barna,ko kuma duka su mutu cikin biyu yana so ayi daya babu wanda yake so a kyale harda hajiyar agadex da yake kiranta shuumar tsohuwa me gani har hanji.cikin muryarta mara daɗi da fitar da bakin hayaki ta ce", SHUDA tabbas a yanzu tsoran ci gaba da mu'amala muke da kai saboda abinda zaka iya jawo mana dan tabbas muka ci gaba da shiga cikin lamuranka to muma sai mun zama tarihi dan haka kayi gaggawar barin gurin nan, idan kana son taimako yanzu sai dai danka DUDU ya taimaka maka tunda shi har yanzu da sauran shan ruwansa a tare da m....kafin ta rufe bakinta sai ga hajiyar agadex tsakiyarsu tamkar an jefota,bakinta dauke da adduoi masu zafi.........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page62 ``` ....Idris,da kallo ya fara bin mutanen falon kafin ya ƙaraso kusa da Abbie cikin shauki irin na kaunar dake tsakanin *ɗa* da mahaifi, cikin farinci Abbie ya tarbeshi cikin nasa farincikin yana cewa dan albarka ina ka shiga ne? Tun da na dawo nake tambayarka domin ina son saka duka yarana cikin idaniyata", zama hamma Idris yayi a kasan kafafun Abbie sannan ya ce", Abbie na danyi nisa da gari ne,ashe ban sani ba ana nan ana farinciki babu Ni gida ya haɗu ", ai kam dai to ina shi Affan din yake na dauka ma kuna tare cewar Hajiya goggo ke nan,girgiza kai hamma Idris ya yi tare da cewa Bama tare da Affan sai dai idan shima wani uzurinne ya rikeshi", to Masha Allah baffa Ali ya fada yana ɗan zagaye falon da idanunsa sai kuma ya tsaida idanunsa a kan Raihan kafin cikin mamaki ya ce", raihana ina maminki take ne tun dazun nake zuba idanun ganin shigowarta amma hallau shiru? Tsit falon ya yi kowa na sauraron amsar da Raihan zata bada,hatta da wazer sai da ya bude idanunsa da suke a rufe ya zuba su kan Raihan ɗin da tambayar ta zo mata a bazata, yanzu me zata ce da su? Ta tabbata shi kansa Abbie yana bukatar wannan amsa tunda ita tasan cewa abinda ya fada mata akan rashin dawowar mamin ya fada ne kawai dan ya kwantar mata da hankali,Dagowa ta yi zata yi magana sai sautin babureshin din wayarta ya katseta,maida idanunta ta yi kan wayar kafin cikin sauri da rawar jiki ta daga kiran tare da sawa a amsa kuwa domin ba zata iya jura ita ka dai ba dole ta take maganar Mami na cewar kar ta bari kowa ya sani dan tana da tabbacin sune suka kira dan neman kudin fansa. Aiko ba ta ida tunanin da take yi ba,wata murya me karfi ta fara magana da cewa muna magana da Raihan Muhammad nur ne? Ey nice ta faɗa cike da gwarin gwiwar da wazer yake bata daga cikin idanunsa,dariya mutumin ya yi kafin ya dora da cewa maminki tana hannunmu idan kin yadda da sharadinmu zamu baki ita lafiya ba tare da ko sauro ya cije ta ba,idan kuma kika sabawa sharadinmu da abinda muke so to tabbas zaki tsinci gawar maminki a kwalbati", me kuke so ta faɗa cikin rashin tsoro? Yauwa yar gari nasan kina son maminki ba za ki so ta mutu a banza ba dan haka bukatarmu a gareki shine ki tattaro kudi kimanin biliyan hamsin ki kawo mana mu kuma za mu sake mahaifiyarki,sharadinmu kuma shine....karasa masa ta yi da cewa babu 'yan sanda cikin lamarin idan kuma na samar da jami'an tsaro zaku kashe mamina kalas ba shi ne abinda zaka fada ba? Dariya yayi sosai sannan ya ce yauwa yarinya me wayo da basira na sara miki wannan shine abinda zan sanar dake dan haka ina jiranki gobe da misalin ƙarfe shida na asuba,zan turo miki address din inda zaki aje mana kudin," idan na baku kudin mahaifiyata fa? Idan kika aje ki tafi zaki samu mahaifiyarki a kofar gidanku ko a cikin motar da kikazo da ita ko a wani guri da zaki iya ganinta", shike nan zamu yi kokarin hada kudin a darennan in sha Allah ", da haka suka kashe wayar. Falon ya jima shiru kowa da irin kalar nashi tashin hankalin,yanzu me ye abinyi kudin za mu basu ke nan? Cewar baffa Ali fuskarshi na nuna alhinin jarabtar da suke ciki,girgiza kai hamma Idris ya yi Sannan cikin zuciyarshi da ba ko yaushe take tasiri ba ya ce", baffa ba za a basu kudin nan ba duk da cewa akwaisu amma ba za a basu ba," a nutse wazer ya dago daga jinginen da yake tun dazun sannan ya dubi Abbie da ya kasa cewa komai baya ga da hadiyar yawun bakinciki da yake yi,dan rissinar da kanshi ya yi cikin girmamawa ya ce",baffa maganarka akan hanya take kudin za a basu kuma ayi yadda suke so kar a sanarwa da jam'i an tsaro saboda gujuwa abinda zai faru da mami", Hajiya goggo ta ce", kwarai kuwa nima dai abinda na gani ke nan tunda dai akwai kudinnan," a nan dai kowa ya shiga tofa albarkacin bakinsa kafin daga bisani baffa Ali ya nemi da su yi shiru dan a tsaida magana. Shiru duk su kayi bayan tsawon yan mintuna da basu wuce biyar ba,baffa Ali ya ja numfashi sanann ya ce da Abbie kaje ka shirya kudin za ayi yadda suke so", shi dai Hamma Idris fuskarshi ta nuna rashin gamsuwa da wannan shawarar kawai dai dan an rinjayeshine. Cikin mutuwar jiki Abbie ya amsawa baffa tare da mikewa dan barin falon,sallamar hamma Affan ce ta sasu kallon kofar baki dayansu,ganin Abbie yasa shi rungumeshi cikin tsananin farin ciki har da yan hawayensa shidinma Abbie sai da ya yi hawayen da dama suna hanyar fita daga haka ya saki Affan ya fita daga falon yana ci gaba da share guntayen hawayen da baya so su gani,da sauri Affan ya karasa gurin baffa Ali yana cewa meke faruwa ne baffa? Kama hannunshi baffa Ali ya yi ya zaunar dashi a gefansa sannan cikin hikima ta yadda zai fahimta ya sanar dashi abinda ke faruwa da kuma irin shawarar da kowanne ya kawo", gaskiya ne baffa shawarar da kuka yanke ita ce shawara Gara a basu sannan abi sharadan da suka bayar saboda gujuwa abinda zai faru", Wani irin kallo Raihan take masa tun shigowarsa zuciyarta bata gama gasgata mata abinda take tunani ba sai da taji lafazin bakinsa,lallai kuwa indai har Affan shine ya yi garkuwa da mami to wallahi ba zata yafe ba,a hankali ta saki siririn kukan da yake ta cin ranta kamar ana yakushin zuciyarta,dan gaba daya ji take kamar ba ita ba damuwa ta yi mata rufdugu ta ko ina ji take bata jin dadin rayuwar saboda halinda Mami ke ciki da kuma tarin kaddarorinsu. Sai da kowa ya fita sannan ya mike cikin nutsuwarsa da kamewar dake sa ba a iya gane ainahinsa,kama hannunta ya yi ya mikar da ita sannan ya yiwa baffa da Hajiya goggo sallama suka fita yana rike da hannunta. Suna fitowa ya shigar da ita jikinshi yana ɗan shafa fuskarta saboda ya tare hawayen da suke zuba a kasa,hamma wazer me yasa haka take faruwa dani? Me yasa saini duk me ya jawo hakan ne? Kudine sanadi ko to zan hakura da komai da nake dashi ko zan samu na zauna lafiya nida iyayena da ahlina gaba ɗaya", ta karasa maganar cikin kara fashewa da kuka. Kar kiyi saɓo RAIHAN Allah yana jarabtar bayinsa talaka ko me kudi me lafiya ko nakashashshe,ba sai masu kuɗi Ubangiji ke jarabta ba kuma ba sai talaka Ubangiji ke jarabta ba, jarabta tana daga cikin wani yanke na imani dan haka kar ki fushi komai zai wuce,yanzu muntafi can gida inason ki samu nutsuwa ko yaya ne umm", rungumeshi ta kuma yi tana cewa na gode da tunatarwa", Da kansa ya sakata a mota sannan ya koma mazaunin direba ya shiga yaja suka bar gidan. A hanya ya kira Salim ,yana dagawa ya ce ", ina Dady? Gashi muna tare", Salim ya fada yana sauraron abinda wazer zaice", ok har yanzu ba ku fitar da ainahin Muryar ba", Dady ne ya amsa a wannan gabar yana cewa sir kashim ya fitar da ainahin Muryar wanda Surry ke waya dashi a halin yanzu ma Turo maka muke kokarinyi sai dai muna kokonto dan ganin kamar dare ya yi", no Dady ka Turan kawai", ok sir dady ya fada yana ɗorawa da cewa sir ya batun abu Huraira ? Dan dafe kai wazer ya yi tare da cewa yana ina? Salim ya ce", yana can dakin ajiya", to ku barshi a wajen zuwa gobe in sha Allah zanzo idan banzo ba kuma kuje ku fara matsashi ya fada mana wanda ya turoshi da kuma inda suka kai khalil", ok sir suka faɗa a tare", na gode ya fada yana kashe wayar", kallon RAIHAN da duka hankalinta yake kansa ya yi sananan ya maida hankali kan tukuinsa yana cewa ya dai da wani abu ne? Hamma kana boyen abubuwa da yawa da suke faruwa akaina dan Allah ka fada min wani abu ko naji sanyi kuna barina a duhu sosai",in sha Allah zan sanar dake abinda ya kamata ki sani kar ki damu ya fada yana shafa fuskarta,jinina kai ta yi tare da lumshe idanunta. __________ Shet ya fada bayan gama wayarsa da ciska,lallai wannan yaron dan baiwane ba kowa ne yake tsalleke tarkona ba amma shi duk sanda na nada masa tarko sai ya tsallake,cizon yatsa ya yi idanunshi sunyi jajur saboda tsananin bakinciki, wallahi ba zan Barka ba wazer dole sai nayi nasara akanka,ya fada zuciyarshi cike da bakincikin da yake ji zai kasheshi. ___________ Cikin bakinciki hajiyar agadex ta nuna shuda Abba Yahya da yatsanta tana cewa kai dai ka cika tabbatacce la anannan Allah, Allah Ubangiji ya yi mana tsari da irinku masu bakar zuciya zuciyar kafurci zuciyar shaidan wallahi Yahya kayi asarar rayuwa duniya da lahira kuma in sha Allah sai ka girbi abinda ka shuka dan Allah baya barin azzalumi da zalunci butulu kawai",juyowa ta yi kan tsohuwa tana cewa ke kuma tsohuwar najadu tsinanniya wadda Allah ya tsinewa in sha Allah yau karshen barnarki yazo", ke dakata tsohuwa ta faɗa tana nuna hajiyar agadex da sandar tsafinta,sai dai kuma ga dimbin mamakin tsohuwa taga babu abinda sandar ta yi hasalima sai gani su kayi sandar na narkewa tamkar ana narka roba da wuta,cikin tsananin razana tsohuwa ta yi kan gunkinsu da suke bawa jini a karo na biyu danyin Abinda ya dace tun kafin hajiyar agadex tayi nasara akansu,tsayawa ta yi can saboda ganin shima gunkin yana rushewa yana zubewa a wajen tamkar ba ayi shi ba,da wani irin tsoron da ya kama dukan mabiyanta da suka hallara lokaci daya a gurin suke kallon hajiyar agadex dake tsaye kyam bakinta dauke da addu o'in kariya daga sihiri wanda Annabi ya umarcemu da mudinga yi a sa'ilin da muka ga wata masifa ta tunkaromu. Kamar abun almara sai ga ginin kogonnan ya fara rushewa yana zubowa a hankali tamkar wanda ake sa hannu ana baroshi,cikin tsananin tashin hankali da firgici wanda basu taba shigarsa ba tun bayan kafa kungiyar suka fara darewa kowa yana neman gurin tsira daga cikinsu har da Abba yahya da ya fara kokarin yin takansa,cikin wani irin zafin nama hajiyar agadex ta cafko shi take ta samu igiyar da suke amfani da ita wajen tsafinsu ta daureshi katamau sannan ta jashi suka fice daga kogon,tamkar jira kogon yake ta fita wuta ta fara kama duk wani abu dake wajen hadda mutanen da basu riga sun fita ba. Ita kanta tsohuwa neman hanyar tsira ta fara yi sai dai ina duk da haka sai da wuta ta fara kama wasu bangare na jikinta,dakyar ta samu ta fita tsakiyar dajin, tunaninta tunda wuta bata cinyeta gaba daya ba ta tsira ,to amma ina ashe tsugune bata kare mata ba,dan kuwa bayan ta samu wutar jikinta ta mutu dakyar ta fara tafiya dan canja sheka,katsaham ta ji wani abu me nauyi ya nannadeta dubawarnan da zata yi ta ci karo da wata narkekiyar mesa,ta fasa kai tana razanata da mugun dafinta,tsohuwa bata taɓa tunanin akwai abinda zai bata tsoro ba sai yau da ta gamu da gamonta abinda take takama dashi kuma babu,bude baki tayi zata fasa ihu sai caraf mesarnan ta cijeta akan harshe ,tsohuwa tana jin haka tasan cewa mesar ta shirya azabtar da ita ne kawai. _____________ Hajiyar agadex tana zuwa bakin gate din gidan ta kwankwasa, securitys suna ganinta suka bude mata kofa,bakinsu ne ya mutu lokacin da suka yi arba da Abba yahya dake rike a hannunta tana jansa kamar kayan wanki,alamu ta yi musu da suyi shiru hakan yasa suka maida bakinsu suka kulle,wani tsohon daki dake can boyquaters ta ce su bude mata, aiko cikin hanzari suka bude mata,suna kallo ta jefa Abba yahya a ciki ta kulle ta bar gurin da key din a hannunta. ____________ Tunda aka gama taron ya dawo bangarensu yake sunturi da da leken ta inda zaiga inna maimuna ko abbansa,duk sakan sai ya duba a gogo,to me yake faruwa ne? Ya tambayi kanshi a karo mara adadi,wayarshi ya kuma dagawa ya kira inna maimuna shiru dai har yanzu,sai ya koma kan abbansa shima kuma layin yana shiga a wannan karon sai dai ba a dauka ba,tsaki ya yi yana zama saman kujera dabar,shi rashin ABBAN bai esameshi kamar innarsa ba,take wata dabara tazo mai,hakan yasa ya tashi da sauri ya nufi dakin abbansa. Wannan kofar da babu wanda yasan da ita sai shi da Abba yahya ya bude,shiga yi ya duba ko abban yana ciki saboda lokuta da dama tsohuwa na sasu yin aikin tsafi na kwanaki a dakin wani lokaci har kwana biyu yana yi a dakin ba tare da kowa ya sani ba,Turus Bashir ya yi ganin dakin a kone kurmus da alama ma bai jima da konewa ba,kauri da yahakin da dakin yake yi yasa Bashir saurin fitowa daga dakin yana maida nunfashin da ya rike tun shigarsa dakin. __________ Daidai lokacin da wazer yake yin fakin a harabar gidansa sakon su Dady da na Yusuf suka shigo a lokaci daya,bai duba ba ya bari har sai ya shiga gidan sai ya duba a nutse,daukar Raihan da bacci ya dauketa ya yi tare da rufe motar da gidan gaba ɗaya,sannan ya shiga falon dauke da Raihan a kafadarsa. Kwantar da ita ya yi a nutse,sanan ya zauna a gefenta yana duba wayar da sakonnin suka shigo. Na Yusuf location din inda haidar yake ne,sai na su Dady da yake dauke da ainahin Muryar ogan Surry. Tashi ya yi zai bar dakin sai yaji hannun Raihan ta riko shi,juyawa ya yi yana kallon kyakkyawar fuskarta a tunaninshi ko cikin bacci ne amma sai yaga idanunta a bude tana kallonshi, akwai alamun bacci a idanunta hakan yana nuna cewa yanzu ta farka ke nan,dawowa ya yi kusa da ita ya zauna tare da daukar kanta ya dora kan cinyarsa,a hankali ya shiga shafa fuskarta zuwa wuyanta yana mata susar da tasa ta lumshe idanunta, kafin a hankali cikin sanyin muryarta ta ce", me kake boyen?.........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page63 ``` ,,,,,,,Babu abinda na boye miki don son raina,zan gaya miki komai amma da fari ki min alkwarin ba zaki tayar da hankalinki ba",in sha Allah ta faɗa cikin mutuwar jiki,gyara mata kwanciya yayi a jikinsa ,sannan cikin nutsuwarsa dake tare da shi ko da yaushe ya bude baki ya fara bata labarin komai da komai,salon da ya yi amfani dashi gurin bata labarinne ya hanata shiga wani hali akan lamarin yangidansu,babu labarin da yafi jijjigata kamar na inna maimuna domin kuwa har ga Allah tana son inna maimuna dan itama ta nuna mata so duk da cewa na karya ne,tasha mamaki da yakasance itace sanadin da yasa tayi rayuwa a matsayin namiji,me yasa duka suka kasance masu son zuciya? Me yasa ba a samu wani daga cikinsu ya zama na kirki ba? Tambayoyin da ta yiwa wazer ke nan idanunta na zubar da hawayen bakinciki,hannu yasa yana share hawayennata sannan yace", kaddararsu da rayuwarsu ce tazo a haka,son zuciyarsu yazo daya miji da mata,shi kuma da ya tsotsa wannan shine kawai, Raihan shi butulci wani abu ne da yake hade da son zuciya da kuma hassada,ma ana ,sai kana da son zuciya kake yin butulci shi kuma butulci ya samo asali ne daga hassada, Allah Ubangiji ya kare mu da wadannan abubuwa", Amin ta faɗa,yanzu saura mutumin da ya sace Mami jikina yana bani cewa hamma Affanne", karki saurin yanke hukunci wannan bincikene zai bamu tabbaci bamu da matsala tunda gashi an turo Muryarsa ta asali ya fada yana daukar wayar da su Salim suka turo Muryar,kunnawa ya yi tare da jingina bayanshi da makarin gadon dan kara samun nutsuwar fahimtar me Muryar. BASHIR dai ya rasa inda zai saka ransa saboda ya gwada kiran tsohuwa yafi sau shurin masaki amma shiru babu ita babu hayakinta,tamkar zaiyi hauka haka yake ji,dole akwai abinda ke faruwa,ya faɗa yana gwada nomber ɗaya daga cikin abokannansu na ƙungiyar,sai dai abin takaicin ya kira wajen mutum biyar amma duka babu wanda yasamu, wannan dalilinne ya kuma tayar masa da hankali,zufa yake yi kawai tamkar yana cikin tukunyar gashi,bacci kam ranar babu shi a idon Bashir. Inna maimuna....... Tun tana daurewa zafi da sauro har abin ya fara cinta, ta shiga soshe soshe da fifita da hannu,zuciyarta da rayuwarta duka a ƙuntace,bata iya daurewa ba sai da ta fara zubar da hawayen bakinciki da kuncin da take ciki,duk da haka fa zuciyarta bata karaya akan daukar fansa ba,ji take ko yanzu ta samu dama sai ta ida karasa abinda ta fara,saboda wannan shine mafarkinta tun tana yarinya karama. A cikin wannan daren Yusuf ya dauki jami'an tsaro suka tafi karshen gari inda gidan sirrin Abba yahya yake, take a ka kame Duka yaransa, suka dauko haidar da numfashinsa yake tsakanin rayuwa da mutuwa,kai tsaye asibiti ya nufa dashi Dr sabo da yake jiran karasowarsu ya karbe shi da taimakon sauran likitoci,cikin kankanin lokaci aka fara yunkurin ceto rayuwarsa. ___________ A bangaren rabi a kuwa kwana tayi da shirin zuwa gidan su Surry saboda a yanzu babu abinda take bukata sai wazer wata irin soyayyarsa ce ke dawainiya da ita,tamkar zata wuce da numfashinta,shi yasa ta bar batun kasheshi yanzu hanyar shiri take nema,zaman da tayi bata ganin ko gilmawarsa ba karamin azabtar da ita ya yi ba,ita bata taba sanin tana son wazer irin haka ba sai yanzu da basa tare ji take yi bazata iya rayuwa idan babu shi ba. *Abba yahya.....* Tunda hajiyar agadex ta rufe shi a dakin yake gwada siddabarunsa ko zai samu ragowar wani abu,amma ina tun yana sa ran zai iya fita daga gurin ta hanyar tsafinsa har ya fara sarewa,gaba daya ya rasa wane irin tunani zaiyi shin nadama ya kamata ya yi ko ci gaba zaiyi da gwada dabarunsa? Tsinuwa dai hajiyar agadex tasha ta babu adadi,mafita kawai yake nema ya bar gurin saboda yasan indai ya fita Bashir zai iya taimaka masa tunda shi har yanzu da sauran rufin asirinsa,gyangyadi ne ya fara dibarsa saboda rashin bacci da yake fama dashi a kwanakinnan,sai dai zunbur ya tashi saboda kukan yara da ya kaure dakin kowa da kalar nasa,kafin ya dawo daga gigitar da ya shiga sai ga inuwar mutane ta fara gilmawa bai gama tsorata ba sai da ya tabbatar da cewa fatalwar mutanen da ya kashece take tsorata shi,tun yana dakewa a matsayinsa na gogagge a cikin harkar tsafi da babu abinda ya isa tsoratashi,sai ga Abba yahya da mikewa tsaye yana rasa inda zai samu matsuguni saboda tsabar tsoro da yadda suke firgita shi,cikin kankanin lokaci ya firgice kunnuwanshi suka daina sauraron ko wane irin sauti idan ba kukan yara da jarirai ba,idan kuma ya bude idanunshi haka zaiyi gamo da mummunan fatalwar da suke mishi gizo suna razanashi. WAZEER RAIHAN....... Sosai Raihan ta tsorata da lamarin duniya jin muryar wanda bata taɓa tsammanin zai iya cutar da wani ma ba ita ba,kukan ta ne ya kasa rikuwa dole ta sakeshi ya taho da karfinsa,wani irin nauyi take ji a kirjinta na tsananin damuwa da tsoran lamarin mutanen duniya ,wani irin imani da tsoran Allah ne ya ke kuma shigarsu saboda yadda Allah yake ta karesu akan makiyansu da suke tare da su suke kwana dasu bangare da su sun sansu ba,wazer bai hanata kukan ba sai dai bai yadda hawayenta sun zuba a kasa ba hakan yasa shi tara hannunshi suna zuba cikin tafukanshi,sai da ya tabbata ta samu salama saboda yin kukan sannan ya dagota gaba dayanta ya zaunar akan cinyarsa tare da juyo da fuskarta tana fuskantarsa,idanunshi ya lumshe sanann a hankali ya kai harshensa saman idanunta ya shiga lashe ragowar hawayen bayan ya shanye wanda suka zuba a hannunshi,sai da ya lashe fuskarta Tas ya tabbata babu ragowar digon hawaye sannan ya maidata cikin jikinshi yana cewa shike nan wannan shine na karshe bana son ki sake wani ko nan gaba in dai ba na farincikin ganin maminki ba",samun kanta ta yi da murmushin maganarsa sannan a hankali ta ɗora hannunta kan fuskarshi tana shafawa kafin cikin muryarta da ta dan dashe ta ce", ina sonka hamma wazer ina fata na ci gaba da sonka har karshen numfashina", lumshe idanunsa ya yi saboda jin dadin kalmar kafin ya budesu a kanta bai jira wani abu ba ya shiga sumbatarta ta ko ina,wata irin soyayyace me zurfi da wahalar misali yake mata shi yasa bashi da bakin fadin ina sonki sai dai ya fada dan rage radadi, wannan hanyar ita kadaice hanyar da zai iya nuna mata tsagwaran son da yake mata wanda ke tafiya da numfashinsa,zip din rigarta ya zuge tare da saka hannunshi cikin jikinta yana aika mata da wasu zafafan sakonni wadanda suka fi karfin karamar ƙwaƙwalwarta, Raihan dai tun tana alkunya har abin ya fi karfin iyawarta ta fara maidawa malaminnata amsa amsa cikakkiya da ta wargaza duk wani lissafinsa,sosai take maida masa martanin Koyarwarsa koyarwar da ita kanta bata taba sanin cewa tana daukar darussan ba sai a yau,ey dole ta ce", haka domin kuwa malaminnata kwararre ne in dai amfanin soyayyarta ne. Kuka ta saka me karfi saboda jin ya karanta addu'ar haduwa yana daidaita abinshi a cikin jikinta,jin kukanta yasashi dakatawa daga kokarin zamar da ita mallakinshi ta har abada,shiru yayi yana ɗan maida numfashi kafin ya mirgina gefe idanunshi a rufe yana ƙoƙarin maida kwadayinsa,ey shima ya ga hakan bai dace ba saboda har yanzu Raihan bata gama samun nutsuwa ba saboda rashin maminta a kusa,zuciyarshi ta ainayana mishi da yayi hakuri zuwa akawo masa Raihan har gida ko shi din sai yafi samun nutsuwar maidata matarshi,jin shirun da ya yi ,duk sai ta ji babu dad'i a tunaninta fushi ya yi,hakan yasa ta matsa jikinsa tare da dora kanta a kan kirjinsa hannunta zagaye da cikinsa,sannan cikin karamar murya ta ce ", sorry ba zan kuma ba," shiru bai tanka ba,sai ta kuma shiga damuwa tana cewa hayatty ba zan kuma ba kayi hakuri", tausayinta ne ya kamashi hakan yasa ya kuma manneta ajikinshi yana cewa wa yace miki fushi nayi? Raihan ko zan yi ta zama dake ba tare da wani biyan bukata ba wallahi bazanji haushinki ba kuma ba zan damu ba,ke din nake so ba wani abu naki ba,nifa hasalima ban san ina da wani peeling ba sai akanki so kar ki damu banyi fushi ba", dago kanta ta yi tana cewa ka tabbata ba za ka kwana da fushina ba? In baki tabbaci? Ya tambayeta lumsassun idanunsa akanta,gyada kai tayi tana karamin murmushi,ok ya fada yana maida hannunshi cikin jikinta yana shafawa, dan zaro ido ta yi jin a inda ya tsaida hannunshi,shima zaro idon ya yi yana cewa ashe yarinyar tana daukar darasi yadda ya kamata anya ko RAIHAN nan gaba ba zaki karasa cinyewa Ammi Ni ba? Ihun kukan shagwaba tasa tare da hayewa ruwan cikinshi tana kai mishi kananun duka har da yan guntayen hawayenta,sai da ya barta ta yi san ranta ta gaji sannan ya rungumeta yana ci gaba da bawa junansu farinciki ta hanyar yan lalube_lalube.asuba ta gari raihanwazer. Ƙarfe shida daidai.... Karfe shida daidai ita ce tayiwa Raihan da wazer a gurin da me garkuwa da aunty Amarya ya yi dasu zasu aje kuɗi,aje kudin Raihan ta yi tare da komawa cikin motar,tare da barin wajen kamar yadda suka umarceta. Cikin sanda da yan dube dube wanda zai dauki kudin ya fito,sai da ya tabbatar babu kowa a gurin sannan ya duka ya dauki kudin yana dauka ya juya dan barin wajen amma sai yaji numfashin mutum da bakin bindiga akansa,cak ya tsaya yana ɗan juyowa a hankali. ido biyu yayi da jami' in tsaro na farar kaya fuskar nan yawa an aiko masa da mala ikan mutuwa,ina take? abinda jami' in ya fara tambaya ke nan yana kuma saita shi da bindigarsa,cikin tashin hankali mutumin ya ce", tana can gidan da muka ajiye t.....kafin ya karasa fada wayarsa ta kama ringing,cikin tsawa jami in ya ce", dauka wayar kace ka karbi kudin yanzu zaka taho", haka ce ta faru yana dagawa ya basu tabbacin cewa kudi suna hannunsa harma ya kusa.karasowa maboyarsu,dariya na cikin wayar ya sheke da ita sannan ya ce maza ka kawo kudin sannan na aikata sun dauka zan basu ita sai kace mahaukaci bayan nasan zata iya tona min asiri duk da cewa bata ga fuskata ba,maza ka kawo ina jiranka", A gaba jam'i an tare da motar Raihan da wazer suka saka shi har zuwa gidan. Bai taba zato ba kawai sai ganinsa ya yi zagaye da jami'an tsaro. Bai gama fita daga razanar da ya shiga ba sai jin saukar hannun Raihan yayi a fuskarsa ta zuba masa wani lafiyayyan mari kafin cikin kumar zuciya ta nuna shi da Yatsa. Wallahi HAMMA IDRIS ban taba tunaninka cikin masu ha inci da yau dara ba, ban taba kawo ka cikin muguyen mutanen da basa sonmu ba,ka bani kunya Allah ya isa tsakaninmu da kai wallahi Abbie ma ba zai yafe maka ba saboda kaci amanar haihuwarka da ya yi anya kuwa ba Abba yahya ne ya haifeka ba? Gaskiya ina tantama,ta faɗa tana goge hawayen da suka kasa daina zuba,wazer kuwa shi yaje ya kunce Aunty Amarya daga daurin da su kayi mata ya taimaka mata ta tashi. Da sauri RAIHAN ta rungumeta tana jin damuwarta na raguwa cikin kaso dari babu tamanin saboda samunta lafiya, murmushi Aunty Amarya ta yi sannan ta ce ", kaga abinda nake fada maka ko Idris kai zatonka ban gane ka ba ko? Girgiza kai ta yi tana cewa Wallahi nasan dole sai karshenka yazo bakin azzalumi ta bakin Raihan ɗin wata ƙilma Yahya ne ya haifoka bakin iri kawai", kada keyarsa jam'i an tsaro su kayi ba tare da ya iya cewa komai ba saboda ji yake bashi da abin cewar,tun daga cikin motar ya fara zubda hawayen takaici da nadama tun kafin ake ko ina. Raihan wazer Aunty Amarya kuwa gida suka wuce suka kai aunty Amarya,basu shiga ba amma basu tafi ba sai da suka tabbatar ta shiga falonta,sanann suka bar gidan saboda akwai aikin da zasu gabatar dashi a cikin wannan safiyar WASHEGARI....... Wannan safiyar an wayeta ne da tarin abubuwa na ban mamaki,tree full y trues ya bankado abubuwa masu tarin yawa daga ciki har da videon su shugaban jam'iyya wanda shi ya fara bayyana, jami'an tsaro basu yi wata wata ba suka dangana da gidan shakatawarsu suka kamesu suna kan aikata Masha arsu,su Dr sanater basu taba zato ko tsammani ba saboda yadda labarinsu ya shude acikin masu aikata laifi shi yasa suka ci gaba da cin karensu babu babbaka hankali kwance ba tare da sun tuna ranar nadama na zuwa ba. Yadda mutane suke tururuwar jifansu kai kace jifan shaidan suke yi,fadi suke Allah ya tona muku asiri kamar yadda ya tonawa his excellency..... A daidai lokacin da ake wannan zanga zanga ta kama su shugaban jam'iyya,a lokacin karfe tara na safe daidai,Abbu Chibado ne da RAIHAN da WAZER zaune a gidan wazer da suka kwana. Gaba dayansu ko wanne da computer a gabansa ga kuma tv da suke kallon abinda ke faruwa a cikin tashar Chibado tv. Finally Abbu mun fitar da videon su shugaban jam'iyya saura uwa uba Yahya ", jinjina kai Abbu ya yi idanunshi akan fuskar computer ya ce", mu dan jira wannan ƙurar ta lafa dan idan muka saki wannan videon garin zai kuma hargitsewa dan haka mu bari zuwa anjima idan HIS EXCELLENCY ya ƙaraso kamar yadda muka shirya muna bukatar hirarsa da jama a ko dan ya kuma wanke kansa ", Abbu ai wannan videon ya isa wanke Abba Garba dan haka ina ga ba sai yayi magana ba yau mu bari ya dan samu nutsuwa da ahlinsa shima in yaso daga baya sai mu bukaci hira dashi ko? Raihan Ta faɗa cikin tsananin nuna biyayya ga surukinnata,shike nan wannan ma shawarace me kyau, dan haka Ni bari na saita komai anjima karfe sha biyu zan sake shi ta shafin tree full y trues,ya fada cikin dariya yana kallon fuskar wazer da shima yake wani ƙayataccen Murmushi bai ce komai ba dai, Raihan ce ta ce", Abbu gaskiya mun ɓatar da hankalin mutane akan wannan tree full y trues din dole kayi dariya", wazer ya ce", ke baki ga rainin hankalin da kika dinga yiwa ma'aikatanki akan son sanin waye tree full y trues ba? Rufe fuskarta ta yi tana dariyar da har sai da kumatunta suka loba", kafin ta bude tana kallon Wazer cikin son ya bata amsar tambayar da zata yi masa ta ce", dan Allah hamma wazer me yasa ka cire ai nahin karshen sunayenmu ka maida shi y bayan naga babu y a sunanmu? Abbu ya ce", Nima dai ina bukatar wannan amsar dan da farko Nima sai da kayi wasa da hankalina na", a hankali wazer ya kawar da kansa daga kallon da yake jifan Raihan dashi, shiru ne ya ratsa falon kamar ba zai tanka ba sai da ya mula dan kansa sannan cikin deep voice dinsa da ke fitowa a nutse ya ce", Nayi tunanin mutane irin su shugaban jam'iyya da Abba yahya zasu yi saurin gano ko su waye masu wannan sirrintacciyar kungiyar jaridar, shi yasa na dauke wancan sunan na maida shi tree full y trues saboda batar da hankalin masu bin kwakkwafi dan da ace ban yi hakan ba da tuni wadanda muka yi nasara akansu a baya sun ganomu hatta su shugaban jam'iyya da tuni sun gano mu saboda binciken da suke yawan yi akan son gano tree full y trues,kuma nayi la akari da yadda Abba yahya yake da matukar wayo yake shiga jikin mutane yana amfani dasu dan ko su shugaban jam'iyya shine ya dinga fito dasu daga sel da zarar an kama su saboda yana buya a bayansu yana aikata bannarsa son ransa,duk da cewa lokacin bamu san waye me laifin ba. Salut dinshi suka yi a tare kamar sun shirya yin hakan sai hakan ya bada wani irin salo me burgewa, Raihan ta ce", batun inna maimuna fa za mu fitar ko zamu rabu da ita? Abbu ya ce", rabu da wannan kawai yanzu ta wadannan muke kafin kuma mu gano wanda yasa abu Huraira ya baka guba,tsugune fa bata kare ba", ya fada yana rufe computer shi", murmushi kawai wazer ya yi ba tare da ya ce komai ba,saboda Abbu bai san komai akan gwagwarmaya da yakin da yake akan dan uwanshi Abba Mustapha ba,shi yasa kawai ya yi masa shiru idan ya gama tabbatarwa shima asirinsa zai tonu kamar yadda na sauran ya tonu. Abbu Allah huta gajiya RAIHAN ta faɗa tana rufe Tata computer, Allah yayi muku albarka amma dan Allah kar ku tsaya shiririta ku fito da wuri,in sha Allah Abbu wazer ya fada yana rufe kofar falon bayan fitar Abbu. Yana zuwa ya dauke ta cak yana cewa kema ina da tarin tambayoyin da nake so ki amsa min na daga mikii kafa amma shine ɗan Kinga Abbu har zakulo min tambaya kike ko? Ya karasa fada tare da kwantar da ita saman kyakkyawan gadon da ya sha shimfidar alfarma.......✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page64 ``` .....Shima bin gefanta ya yi ya kwanta tare da janyota jikinshi,kafin cikin yanayinsa wanda ke cike da nutsuwa wanda har a kalaminsa take bayyana ya ce ", fada min ya akayi kika yi duk wannan ban sani ba? Kara mannewa ta yi a jikinshi tana shaƙar kamshinsa da bata gajiya dashi,sannan cikin kwantar da murya wanda ke fitowa da wani sanyin jiki da hakan ya kashewa wazer nasa jikin ta ce", lokacin da wannan kashe kashen ya fara faruwa ya faru ne tun bayan karbar kujerar da HIS EXCELLENCY yayi ne,hakan yasa nafi dora zargina akansa kamar yadda sauran jama'ar gari suke,ko lokacin da muka je wajensa tare sai da nayi wasu yan bincike ba tare da kai ka kula ba dan har muryarsa saida na dauka,tun daga wannan lokacin Ni kuma na dage akan lallai sai na samo wanda yake da hannu akan wannan matsalar da jahar mu take ciki,hakan yasa na shiga bincike ka in da na in har na samu na fara bibiyar mutumin da ban san ko shi waye ba,a hankali a hankali ina biye dashi har na fara samun bayanai masu muhimmanci akansa,kamar yaransa da yake sawa suna hada tarzoma a gari dan kawai a zubda jini da kuma mu amalarsa da matsafa a haka har na samu na tara vidoos da muryoyi masu dama, saida na tabbatar da cewa na hada hujjoji masu ma ana, sanan na tunkari haidar wanda nake da yakinin zai taimaka min a matsayinsa na jami'i me kishin kasarsa,abinda yasa ban sanarda kai ba a lokacin shine ganin yadda kake hanani irin wannan shige_shigen masu hadari,karshe dai ranar da haidar yazo na bashi Flash din da kuma na su shugaban jam'iyya washe gari aka saceshi,shi yasa kaga hankalina ya tashi ga kuma matsalar Khalil duk a cikin ranar,na tsorata da sace haidar matuka duk da cewa hasashena ya bani cewa sun jima suna bibiyarsa." A hankali ta ɗan sauke numfashi tana jin wani irin daci a makoshinta. Hannunsa ya dora akan lallausar sumar kanta yana mata tafiyar tsutsa, sannan a hankali ya bude baki ya ce", ya a kayi Flash din yazo cikin kayana? Itama ɗan jim ta yi kafin ta dago kanta ta kalli fuskarshi dake wani irin sheki na tsabar Hutu da jin dadi dan jan gemunshi ta yi tana cewa wannan amsar a wajen haidar za mu sameta dan Nima ban sani ba", kuma ka tashi mu tafi ka maida Ni gida kasan Abbu ya ce", kar mu tsaya shiririta mu tafi gida kafin sha biyu", Yadda yake kallon bakinta ne yasa ta yi saurin rufe bakinta tana dan ƙunkuni akan mayen kallon da yake mata ko a gaban waye kuwa. Uhm ina jinki", ya fada yana juyo da fuskarta da takawar gefe,cike da kuruciya ta bude bakin zata yi magana aiko caraf wazer dan Ammi ya cafe harshenta cikin bakinshi ya shiga juya shi yana binta da kallon har hanji,rufe idanunta ta yi tana jin wani irin yam tsigar jikinta na mikewa,samun kanta tayi da rike shi kam saboda ji ta yi kamar zata yi luxing temper nata,kai wazer karshe ne a fagen so da nuna so wadda bata samu soyayyar wazer ba tabbas bata samu soyayya ba,ita kadai take wannan surutun a ranta,sai da ya yi me isarsa ya gama cakudata sannan ya dauke ta cak ya yi toilet da ita. Saurin rike rigarta da ya yi zipin dinta zata yi kasa ta yi,tana marairaice fuska tare da kankame jikinta, Kallon ido cikin ido ya yi mata kafin cikin deep voice dinsa ya ce", me ne hakan? Ko bai da ce ba? Tura bakinta ta yi tana kara kankance idanunta tare da kif_kifta su kamar wata mara gaskiya,shi dariya ma ta bashi hakan ya sa shi ɗan murmusawa,zaro manyan idanunta ta yi tana cewa kai hamma wazer kaga yadda ka koma kuwa? Me na koma ya fada cikin sauraron jin serious zance amma sai ya ji ta ce", kyau mana murmushi yana maka kyau sosai ko dan baka fiye yinsa ba ne,dan Allah Ni dai hamma wazer kana yi min wannan murmushin ko da yaushe kaji", wani murmushinne wanda yafi wancan fadi ya kuma subce masa aiko Raihan bata san sanda ta saki rigar da ta ke rike da ita Katamau ba, tare da yin wani dan tsalle irin wanda yara suke idan a kayi musu abinda suka ji dadinshi, wannan ne ya bawa Wazer damar sakar musu shaya akansu a lokaci daya yana daukar shawa jel me azabar kamshi da tsada ya zuba a hannunsa ya soma gogawa ajikinta,take bakinta ya mutu mut, yanzu kam babu halin magana dan aikin gama ya gama. Sosai wazer ya wanke Raihan dinshi tas,kafin ya zaunar da ita a kan kujerar bath ya shiga kokarin cire boxer din dake jikinshi,bata dakatar dashi ba tsayawa ta yi kallon gudun ruwanshi dan a tsammaninta ba cirewa zaiyi ba tsokanarta zaiyi,wani dan ihu ta saka tare da rufe fuskarta da tafukan hannayenta guda biyu jikiinta na wani irin bari dan kuwa sosai ta razana da ganin bazata da ta yiwa hamma dinnata, tsayawa ya yi da abinda yake yi yana kallon zallar haukan kuruciya gurin matartasa a ransa yake ji dama ya yi abinda ya yi niya a jiya da tuni ya yi maganin wannan sakarcin nata,bai ko kalli inda take ba ya shige cikin bathwash yana tunanin abinda ya kamata ya yi dan yin maganinta. Shirun da taji ne yasa ta ɗan zame hannunta tare da kyalla ido guda dan ganin ko ya maida boxer dinsa,ai ko gwammacewa ta yi bata bude idon ba dan ko ta yi mugun gani a fadarta amma,kuka ta saka masa akan ya bude mata kofa ta fita ita ba zata iya wannan rashin ta idonba,kai ko kunya baka ji zaka cire kaya a gabana kai hamma wazer dama haka kake ana kallonka sumi_sumi", bude idanunshi da suke a lumshe ya yi kafin cikin wani irin zafin nama ya fizgota ta fado cikin ruwan da yake a lokaci daya yana hadeta da jikinshi,bude baki ta yi zata yi masa kwakwazo take kuwa ya hade bakin da nashi ta yadda babu wani harafi da zai samu damar fitowa daga matsiwacin bakinnata, Raihan bata san cewa muguntar wazer ta shahara ba sai da ta ji ya damƙi hannunta ya dora akan mararshi da ke wani irin harbawa da sauri da sauri, Raihan kam shidewa ne kawai bata yi ba amma Allah ya saka mata ta yi yafi sau shurin masaki,rantsuwa kuwa akan bazata kuma biyoshi gidannan ba ta yi babu adadi idanunta sunyi ja saboda kukan tsoro da tashin hankalin ganin abinda bata taba gani ba a rayuwarta,sai da ya mula dan kansa ya kuma tabbatar ta yi laushi sannan ya daurayesu ya daura towel itama ya daura mata suka fito yana kunshe dariyar dake ta cinshi a ranshi. Aje ta yayi ya gama shiryawa sannan itama ya shiryata ya sa mata kaya,duk tana jinshi ta kasa haɗa ido dashi bare ta tanka masa,dubanta ya yi lokacin da ya ganta tsaf cikin doguwar rigar leshin da yake ta ajiyarsu a gidan duk saboda ita,dan kanne idonsa ya yi tare da rissinawa a gabanta ya ce", tuba nake matar wazer,banza ta yi da shi saima ƙwallah da suka kuma cika idanun, da sauri ya mike yana cewa haba tawan ki yi hakuri da duk wannan alwashin da kike dauka da rigimar nan sai ranar, dan idan suka kare baki da nayi wannan ranar me zuwa,saboda haushi da kunya ko tambayarshi wace rana yake magana bata yi ba ta fita fuuu daga dakin tana cewa nayi gaba sai ka taho", dariya yayi wadda bai taba yin irintaba kafin ya bi bayanta yana aiyanawa a ransa idan suka tare RAIHAN wace irin dariya zata dinga saka shi,tabbas ke ce farincikina ya fada yana zama a kujerar dereba,a kunnenta wannan tsadaddiyar kalma ta sauka hakan yasa ta ji duk wata fushi da damuwarta sun kwaranye sai wani irin so me sanyi da kauna me sanyi saboda samun abinda kake so a kusa da kai,da wannan shaukin suka bar gidan. RABY.. SURRY...... A safiyar yau da Surry ke tsammanin daurin aurenta da mutumin da ko sunanshi bata sani ba ne, aka tashi da wannan hatsaniya, yayin da a bangarenta take jin kamar an sauke mata wani kaya, ji take yi a jiya kamar ba ita ba,sai kuma gashi yau din abinda ke jikiinta ya sake ta,ey tabbas ta san cewa jiya ba kalau take ba,take duk bojet dinta suka dawo ta dawo cikin walwalarta da lissafin mallakar wazer mijin aminiyarta, waya ta kuma dauka dan kiran oganta wanda a safiyar zuwa yanzu ta kira yafi sau ashirin amma wayar akashe,ke Surry anya ko wannan mutumin ba yaudararki ya yi ba kamar yadda kike yaudarar kawarki? Zuciyarta ce ta yi mata wannan tambayar aiko take ta dura wani uban Ashar da yayi sanadiyar dakatar da rabi a dake shirin shiga dakin,abinda ya biyo saura daga bakin suryy ne ya tsaida duka ruwan jikin rabia . Wallahi ko da yayi nadama mara amfani,ai Ni babu wanda ya isa ya yaudareni saboda Ni ba sakarya ce kamar rabia ba,ko rabi a idan tayi wani abun haushinta nake ji,to wai me yasa wasu suke kamar galahanga ne gurin sakarci?kai gaskiya na sha da rabi a wato ita nan saboda sakarci sakin baki ta yi na kawo mata mafita ko? To zata ga mafita kuwa , wallahi sai ta yi da ta sanin wannan sakarci da ta yi,dadinta ma babu abinda nayi masa bayan tozarcin da aka yiwa Raihan,Ni kuma yanzu da kaina zanyiwa kaina maganin rabi a da RAIHAN,saboda sune matsalata kai ko da su in dai har wazer zai aureni bani da wata damuwa,dariya ta sheke da ita tare da buga cinya tana cewa da nice rabi a bin Raihan zanyi sau da kafa dan na kama kafa da ita na zauna da mijina lafiya amma dake sakarya ce tayi watsi da a binda ya kamata tabi shawarata,gaskiya rabi a mahaukaciya ce"...... Gaki nan babbar mahaukaciya maha'inciya maci amana", rabi a ta faɗa tana shigowa cikin dakin idanunta na zubar da hawayen bakinciki da nadama,gaskiya ne da ake cewa kayi abota da mutumin kirki aiyukanka zasu gyaru,da ace nayi dace da kawa ta gari tabbas ba zan aikata kuskuren da na aikata ba,Surry kije na barki da Allah idan har zaluntata kika yi zaki gani",, daga haka ta fita daga gidan tana sharbar kuka kamar ance da ita iyayenta sun mutu. Ita ko sury wani uban tsaki taja tana cewa baki ga komai ba rabi a sai ranar da kika ganni matsayin matar tsohon mijinki dan nasan lokacin tuni ya jima da baki red card,hada kayanta ta yi ta dauki jakarta tana kuma duba adireshin wajen bokan da aka bata,fita ta yi ba tare da ko sallama ta yiwa mahaifiyarta ba,ita dama mahaifiyarta ta saba shi yasa ko ajikinta ta cigaba da sabgoginta a ranta tana cewa surayya da ke kadai na haifa da tuni kin kasheni. Muhammad nur House.... Lokacin da Aunty Amarya ta shiga falon bakinta dauke da sallama babu kowa,hakan ya bata damar wucewa dakinta kai tsaye,turus ta yi ganin Abbie kwance ya rungume wata rigar baccinta idanunsa a rufe,hawaye ta ji sun fara zubo mata saboda tsananin tausayin kansu,wai shin wace irin rayuwa muke yi a yau? Me yasa san zuciya da rashin adalci su kayi mana yawa? Shin ina zamu kai kudi ko zamu tafi dasu lahira ne? Anya ko mutane suna tunawa da mutuwa bare kuma hisabi? Jin wata irin runguma da kayi mata ne ya tsinke mata tunaninta,ba tayi wata_wata ba itama ta rungumeshi suka hadu suna kukan farinciki da bakincikin abinda ya samu zuriarsu dan ko ba komai Abba Yahya jininsu ne. Wazer bai tsaya a ko ina ba sai cikin gidansu Raihan inda suka samu duka jama'ar gidan suna jajantawa junansu,sai alokacinne wazer ya bayyana musu wanda ya yi garkuwa da mami da ma duk abinda ya aikata a baya,akan son samun dukiyar Raihan,sosai suka shiga shock da wannan labari,mama murja kuwa sumewa ta yi saboda tsananin razana dan ko a mafarki bata taɓa kawo Idris dinta cikin masu son dukiyar Raihan ba saboda yadda ya nuna musu rashin goyan baya lokacin da suke kan ganiyar son zuciyarsu,ga kuma yadda ya dinga nunawa RAIHAN da Aunty Amarya soyayya kai gaskiya mutum mugun icce ne,cewar hajiyar agadex tana kuma jinjina lamarin dan ko ita ta girgiza. Baffa Ali kuwa sai da zazzaɓi me zafi ya kamashi jin abinda Abba yahya ya aikata,ba karamar girgiza ya yi ba,dan har ya fi Hajiya goggo shiga damuwa,dan ita cewa ta yi wallahi ta yafe shi kuma ita bata da wata damuwa tunda tana da kamar Muhammad nur,uwa ke nan tsabar ɓacin raine yasa ta fadin wannan kalaman amma tabbas can kasan zuciyarta Allah ka dai yasan irin damuwar da take ciki. Momy Hanne kuwa hamdala ta dinga yi da bata samu damar cutarwa ga kowa daga cikinsu ba,tabbas sunyi nadama tuba irin wanda ake so,babu komai a zuciyarsu sai tsananin tsoran Allah da gujewa duniya yanzu kowa fatanshi ya samu ya cika da imani. ________ Sha biyu daidai videon bannar da Abba yahya ya dinga shukawa ya fara trending a ƙafafan labarai da social media,kafin kace me gari ya dauka kowa da irin abinda yake tofawa, HIS EXCELLENCY kuwa tuni ya tsufa a gida cikin iyalanshi,yan jarida babu abinda suke son ji daga bakin HIS EXCELLENCY sai yadda a kayi Abbie yaso mutuwa a hannunsa da yadda gubar tazo gidan har cikin abincin his excellency wanda Abbie yaci kuma shi baici ba", wannan tambayoyi ne da mutane suke buƙatar jin amsarsu daga ciki har da ahlin nan guda biyu. Alhamdulillah haidar ya farfaɗo da taimakon Allah da na Dr Sabo,takanas Abbie yasa aka je aka ɗauko masa yan uwansa da matarsa da dansa harda mahaifiyarsa,kai kana ganin murnar da suke kasan cewa suna matukar son haidar ɗin. Jama ar gari fa sun gama shan alwashin Abba yahya a hannundu zai mutu dan wallahi sai sun dauki fansar jinin yan uwansu dan haka su kayi mummunan shiri akan kisansa,dan baza su taba bari akaishi kotu ba dan basu da tabbacin za a iya zartar da hukunci bisa adalci,karshe dai ayanke masa hukuncin son zuciya wanda ba zai musu dadi ba.........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page65 ``` Duk abinda ke faruwa BASHIR yana cikin gidan kuma ya ga komai sarai,amma tsananin tashin hankali da kunya ya hanashi fitowa,tuni wannan tashin hankalin yasa shi mantawa da wata suryy da aurenta,yadda zaiyi ya fidda mahaifansa su gudu kawai yake tunani,to ta yaya inna maimuna tana hannun yan sanda ABBAN kuwa babu wanda zaice ga inda yake dan har yanzu hajiyar agadex bata ce musu ga inda yake ba. A bangaren rabi a kuwa gidan innawuro ta nufa kai tsaye tana ruwan hawaye,ko kallo bata ishi innawuro ba,bare ta tanka mata,hakan yasa dole da taga uwar naki ta magantu ta hanyar tsuguno a gaban innawuro tana faman bata hakuri akan abinda ya faru", wani kallo innawuro ta watsa mata kafin ta ce", duniya ta koya miki hankaline ke da ubanki shine kika zo bada hakuri? To maza ki tashi ki bani guri ba zan karbeki ba har sai ubanki da ya tafi dake ya tako gidannan rike da hannun ki ya ce min ya dawo dake tare da bada hakuri ga wadanda ya batawa,dan haka fita ki bani guri", innawuro ta faɗa cikin tsawar da ta razana rabia ta mike ba tare da ta shirya ba,da harara innawuro ta raka ta tana jin takaicinsu ita da mahaifinta,ai ko dan ta kona musu rai kamar yadda su kayi mata dole ta yadda da wannan yarinyar Raihan a matsayin matar wazer,ana gama wannan hatsaniyar wani satin zata basu dama su kawo ta kowa ya huta. Suryy tun tana ganin tafiyar me karewa ce har ta sare ta fara gajiya,duk tayi wani figai figai da ita abinka da ba a saba ba,tana shirin cewa a sauketa ta shiga motar komawa gida sai taji ana kiran sunan garin wanda hakan ke nuna cewa sun iso,hamdala ta yi ta sauka ta kuma hawa dan acaba dan shiga da ita cikin ainahin kauyen da bokan yake", nan ma wata tafiya ce mikakka wadda Surry ta fara danasanin zuwa. Bayan share doguwar tafiya suka karaso gurin sa arta daya babu layi hakan yasa ta shiga kai tsaye bayan an yi mata iso,kafin ta yi magana bokan ya katse numfashinta ta hanyar sanar da ita abinda ke tafe da ita, wannan abu ba karamin burgeta ya yi ba,take ta ji duk gajiyar da ta kwaso ta gushe,ya tabbata zai yi mata aiki amma shi ladan aikinsa ba kudi ba ne,to me Nene? Ta tambaya cikin jin kwarin gwiwa akan kome nene zata yi in dai bukatarta zata biya,gyara zamanshi ya yi tare da cewa ladan aikinmu shine za mu mu'amalantu da baiwarki ta 'yaa mace kuma muddin mace ta shigo gurinnan dole sai ta amince damu idan ba haka ba zata fita cikin hauka tuburan babu ita babu gida sai bin bola,"dafe kirjinta ta yi tana kwalalo ido waje bakinta har rawa yake wajen furta na shiga uku Ni surayya", daga karshe dai dole sury ta amince da bukatar boka saboda bata da wata mafita tunda ta riga tazo,tana ji tana gani wani katon tsohon kauye me wari da warin baki ya haye mata,da kuka ta bar wajen saboda tsabar ta kaici ko fahimtar yadda zata yi da maganin bata tsaya tayi ba,barin garin ta yi tana jin kamar zata yi nadama.... ABBAN RABI........ Cikin tsawa ya ce", da ciska maza ina so kafin sha biyu na rana a batar min da abu Huraira,shi kuma Wazer ku tabbatar min cewa ku din killers ne na karshe gurin kawo karshen rayuwarsa,dan tabbas idan na bari a ka gama da wannan hargitsin ban kawo karshensa ba to Ni ne target dinsa na gaba dan haka maza ku bace min ba zan fita daga gida ba har sai Naji an fasa kukan mutuwarsa, Karaf sai a kunnen Rabia da ta sawo kai dan sanar dashi sakon innawuro kuma ta jaddada masa ya maida ta gidan mijinta zata zauna da ko wace a matsayin kishiya,cak ta tsaya tana karewa samudawan samarin majiya karfi da suke fitowa daga falon Abbanta kallo, Shiga ta yi falon idanunta akan Abbanta da yake kaiwa yana kawowa hannayenshi biyu goye a bayanshi,me kuma ya faru ya tambayi Rabia yana tsareta da idanunsa da suka canja kala", durkushewa ta yi a gabansa tare da rike kafafunsa idanunta cike da hawayen nadama ta ce", Abba dan Allah ka dakatar da duk wata mugunta da ka shiryawa hamma wazer in dai saboda nine wallahi na hakura yanzu ma zuwa nayi na gaya maka ka maidani gidan mijina kamar yadda ka daukoni,saboda naje gurin innawuro ta ce", ba za ta karbeni ba sai tare da kai",wata muguwar bankaɗa ya yi mata kafin cikin masifa da kumfar baki ya ce ", kin gani ko wato ma koroki ta yi to wallahi in dai ina raye kin gama zama a wannan gidan saboda an riga an gama nuna mana matsayinmu,Ni kam yanzu tantama nake akan anya innawuro ita ce ta haifeni kai da walakin tabbas akwai lauje cikin naɗi, dan Allah Abba kayi hakuri wallahi ina son wazer kamar raina ba zan iya rayuwa babu shi ba", ki mutu nace ki mutu in dai akan wazer ne wallahi sai dai ki mutu," daga wannan magana ya bangajeta ya bar mata gurin tana faman rusa kuka,kamar ranta zai fito. 12:00AM..... Duk wanda ka kalla zaka Ganshi da waya a hannu baki sake idanu a waje,kasancewar waya ta zama abincinmu ko da yaushe tana tare da mu,shi yasa mujallun tree full y trues suke saurin zaga duniya,cikin kankanin lokaci videon ta addancin Abba yahya ya kewaya kasa,saboda tsananin al'ajabi garin shiru ya yi saboda masu magana sun rasa abin cewa. Tuni jiniyar yan sanda ta cika anguwannin da suke kusa da gidan Alhaji Muhammad nur,kan kace kobo jami'an tsaro sun kewaye gidan ko wanne dauke da bindiga me cin alburusai,idanunsu da fuskarsu babu alamun Rahma ko tausai ga munafiki. A daidai lokacin mutanen ABBAN rabi suka karaso suka shige cikin mutane, saboda suna da yakinin cewa zasu iya farmakar wazer ta wannan hanyar. A can cikin gida kuwa hajiyar agadex ce kan gaba dan zuwa fito da Abba yahya wanda har yau babu wanda yasan inda yake sai ita,sosai mamaki ya cika mutan gidan lokacin da suka tabbatar da cewa duk budurin da ake yana cikin gidan dakin da hajiyar agadex ta boyeshi,zuba ido suka yi suna kallon kofar da securitys suke kokarin budewa. Kwance yake a wajen kai baka ce shine ba,babu abinda dakin yake sai wari saboda yadda yayi faca_faca da kashi duk saboda tsananin tsoro da razanar dashi da ake yi,yayi wani zuru zuru ya yankwane alokaci daya fatarshi ta kwakkwaile kamar tsohon da ya shekara dari,idanunshi kuwa dakyar yake iya budesu saboda yaji da ciwon da suke masa saboda kukan da yasha. Kukan Bashir suka tsinkaya wanda basu san lokacin da ya zo gurin ba,zubewa ya yi gaban Abbie tare da rike kafafunshi yana cewa dan Allah Abbie kayi hakuri kar ka bari yan sanda su tafi da Abbana ,duba ka ga wannan wahalar da yasha ma kadai ta isheshi ishara dan Allah Abbie ka taimakawa rayuwata kar na shiga cikin maraici,baffa ne ya katse shi da cewa Bashir ka tashi kuma kabar wannan batun dan kasan babu yadda za ayi mu kubutar da Yahya saboda bamu yayiwa laifi ba dan haka dole ne a hukuntashi bisa laifin da ya aikata,idan da ace laifinsa iya wanda ya yiwa nur ne tabbas zamu yafe masa tunda a halin yanzu ma yana tare da yafiyar mune,kayi hakuri kawai ita dai mahaifiyarka in sha Allah za a fito da ita", kuka ya kuma rushewa da shi yana fadin kaiconmu wallahi kaiconmu da irin wannan mummunan sonzuciya wanda bai diremu a ko ina ba sai tashar nadamar da bata da amfani ba zan iya jurar ganin masifar da nake ciki ba Gara Nima a tafi dani a yanke min hukuncin laifin da na aikata,tabbas mun tafka kuskure wanda ba zai taba gyaruwa ba,baffa Nima ina cikin kungiyar Abbana ko mai tare muke aikatawa banbancin kawai shi a nan yake Ni kuma a can nake yin nawa saboda dodon tsafinmu ya ce", nasararmu ba zata tafi yadda ake so ba dole sai mun hada da shan jinin jar fata, wannan shine dalilin da yasa Abbana ya hanani dawowa ku kuma ya yi muku karyar cewa ina can ina kasuwanci da auren da nayi wanda nayi shine ba dan radin kaina ba sai dan umarni ne daga tsohuwa me jini,munyi abubuwa masu tarin yawa wanda a baki ba zasu lissafu ba,dan haka Nima dole a yi min hukunci tare da Abbana. Ya kare maganar yana kuma sakin kukan da bashi da wani amfani a yanzu,tuni Salim da Raihan ta kirashi Ya shigo ta can kofar baya ya kuma gyara zaman abin daukar maganarshi tare da maidashi kan Abba yahya da yake fidda numfashi a hankali saboda shaƙar Ni imtacciyar iska da yayi,gyaran murya Salim ya yi sannan ya ce", Alh Yahya shin abinda danka ya fada gaskiya ne ko kuma kana da ja? Girgiza kai Abba yahya ya yi yana fitar da ruwan hawayen nadama da tsananin wahala dan shi kadai yasan irin azabar da yake sha, Alh Yahya muna bukatar jin muryarka domin bamu tabbaci idan hakan zai samu", cikin wata irin murya me zurfi da rashin dadin sauraro Abba yahya ya ce", wannan abinda Bashir ya fada babu dad'i a ciki sai ma ragi da yayi akan wasu munanan aiyukan da muka aikata daga ciki har da sallamawa tsohuwa jinin dan dan uwana da ya rasu wato marigayi rufa'i." Wani irin kuka ne ya ƙwacewa mama murja,yayin da gaba daya gurin aka kaure da salati cikin wani sabon tu ajjibin,baba karami dan gidan momy Hanne shi ne yayi wani irin kukan kura yayi kan Abba yahya saboda duk yafi su zuciya, Abbie ne ya tare shi yana girgiza masa kai,hamma Hassan ne ya rike shi yana cewa barshi me sunan baffa baka gani ba tun kan aje ko ina duniya ta fara koya musu hankali ba, Affan kam bai ce komai ba sai share hawaye da yake haka Hamma Jamil ma dan wani tashin hankalin yafi karfin magana. Raihan kuwa kara lafewa ta yi a jikin Hajiya goggo tana jin wani irin tsoran duniya na kuma shigarta gani take kamar wannan abun duk ba zai wuce ba. Wazer ma kallonsu kawai yake hannunwanshi cikin aljihun cot dinsa,nazari yake akan mutanen duniya tare da hararo nasu maci amanan da yake gab da zuwa hannu ba tare da ya cimma burinsa akansu ba. Dady da shima ya samu damar shigowa ya saita abin maganarsa ya kuma watsawa Abba yahya tambaya akan abinda kowa yake son sanin ya akayi kuma ta yaya? Yahya shin ko zaka gayawa masu sauraro yadda akayi HIS EXCELLENCY ya shiga cikin wannan al'amarin har aka kamashi dumu_dumu da zubawa amininsa guba a abinci? Garin ne ya yi tsit kowa ya zubawa waya da tv idanu,hatta da HIS EXCELLENCY da yake cikin gidansa tare da iyalansa bayan ya samu nutsuwa zubawa tv ido su kayi gaba dayansu suna jiran wannan amsa da za ta iya bawa Kowa mamaki saboda shi kansa his excellency ɗin bai san ya akai hakan ta faru ba. Hatta da jam'i an tsaro da suka yiwa gidan dafifi sun yi tsit ne tare da wayoyinsu a hannu suna jiran wannan amsa daga bakin Abba yahya. Surrya dake kwance kan katifarta tana fama da kaikayin da ya fara mata yawa tun bayan dawowarta daga gurin boka,zubawa tv ido ta yi idanunta,na zubda hawaye ashe dama mutumin nan da yake shirin aurenta matsafi ne? Ey lallai biri yayi kama da mutum,ashe da yanzu tana can ana watanda da jininta,runtse ido ta yi tana jin tsigar jikiinta na tashi kamar dai ana yanka tan,hamdala take ga Allah da bai bashi dama akanta ba,to idan shi bai samu dama akanki ba ai kin kai kanki da kanki inda aka samu damar a kanki,wata zuciyar ke yi mata wannan jawabin da take ya kuma karyar mata da zuciya. A gidansu wazer kuwa innawuro kuka ta saka da ganin wannan ta addancin baranma da ta ji labarin Raihan da dalilin da yasa mahaifiyarta ta boyeta,wanda Abbu ya sanar da ita,wata irin kaunar Raihan taji tana shigarta tana mai nadamar abinda taso yi na raba aurensu da wazer,yau din dama gaba daya suna gida hatta Ummu rumana tana gidan ita da mijinta,hajiyar Kano ma kanwarsu wadda ABBAN rabi ke bi tazo,gidan dai ya gama zama completely,wazer ne kawai ba ya nan sai ABBAN rabi da ahlinsa. Inna maimuna dake sel itama fito da ita aka yi dan ta gani,saboda wannan al'amari ne da ya kamata kowa ya gani saboda ya zama darasi ga masu son aikata makamancinsa ko wadanda suke aikatawar dan su san cewa ba fa zasuyi ta yi ne ba tare da karshensu ya zo ba, wannan izna ce. Lokacin da taji abinda danta yake fada ba karamin kuka ta yi ba,nadamar da ba tayi ba sai yanzu ta fara yinta da ta tabbatar da cewa wadanda su kafita ma Allah ya Kawo karshensu bare ita,wai kuma duka ahlinta wannan abu shi yake saka ta kuka har ta yi shi ta ba uku lada,saurarawa ta yi da kukan daidai lokacin da ta ji Muryar mijinta ABBAN Bashir ya fara magana da cewa. Sunana Yahya kamar yadda kowa ya sani,sannan Ni yaya ne ga Muhammad nur uwa Daya amma ba uba daya ba", Take kallo ya koma sama mutane suka fara surutu,saboda babu wanda yasan ba uwa daya uba daya suke ba,hatta su Raihan zaro ido su kayi suna kallon baffa da alama shima suna son jin tabbaci daga bakinsa,hakan yasa shi jinjina musu kai,ba tare da ya iya furta komai ba. Ci gaba da magana da Abba yahya ya yi ne yasa kowa ya gimtse mamakinsa yaci gaba da sauraronsa. A agola mahaifiyata tazo dani,amma tun da ta shigo dani gidan baffa Ali yace bai san wannan Magana ba sunana ya tashi daga agola ya koma dan me gida,dan kuwa baffa Ali ya karbeni ya rikeni tamkar shi ya haifeni har sai da aka haifi dan uwana Muhammad nur,duk da haka bai banbantamu dan ya samu nasa ba wani abun da yake min baya yiwa nur shi,kai hatta kai da cewa jikokinsa ma basu san cewa Ni ba dansa ba ne haka yarona da matata har zuwa kan duniya , kowa da dan cikinsa yake kallona", na fara zama butulu me son zuciya da hassada ne lokacin da Muhammad nur ya fara mallakar dukiya da ilimin da Allah ya bashi ya samu kudi ba na wasa ba,wanda take zuciyata ta fara kitsa min hanyar da zan kwace komai daga gareshi, Muhammad nur ya yi suna duniya ta sanshi dan haka Nima nake so duniya ta Sanni ta ko wane hali,karfa ku yi zaton Muhammad nur da mahaifinsa ba sa jikani da irin arzikin da Allah ya basu ,a'a sam duk wani abu da kuka san me kudi zaiyi shi nake yi saboda ya mallaka min kadarorin da Ni ma zan tsaya da kafafuna amma hakan baisa Naji a raina zan hakura da iya kyautatawarsu gareni ba. Alhji Garba me fata Asalin mahaifiyarsa yar Gombe ce Mahaifinsa shine bafulatani,ban taba sanin Nura da wani amini da ya aminta dashi ba sama da Garba,kuma ban taba sanin cewa akwai sirri me girma tsakaninsu ba sai a wani lokaci da na tsinkayi hirarsu bayan haihuwar RAIHAN da ake kira Rahim a lokacin ba,ba komai na ji ba sai maganar dukiyar da yake bawa Raihan wanda kowa yasan wacece RAIHAN ,ashe duk abinda ya bawa Raihan suma yan uwanta sai ya kwashi na su ya bawa baffa Ali a jiya saboda gudun hakki,yayin da ita kuma Raihan yake mikawa amininshi nata yana juyawa a maimakon ajiya wanda wannan juyawar da akeyi shine dalilin habbaka dukiyar ta shahara ta zama wani abu da har ake son mallakarta,sosai nayi bakin ciki da jin takaicin wai aboki ya fini a wajen Nura,to amma sai ban nuna komai ba na cigaba da binsa a yadda muka saba,katsaham kuma sai mutane suka nemi da Muhammad nur ya tsaya takarar gwamna wanda shi kuma baya da sha'awar siyasa hakan yasa ya maida Garba a matsayinsa ya tsaya masa har ya ci gwamna dan acewarsa shi kadai ne mutumin da ya yadda zaiwa talakawa fiye da abin da shi zaiyi musu, wannan ma ya kuma tunzura zuciyata akan kiyayyar Garba hakan yasa naci alwashi akansu su duka biyun. A lokacinne farkon shugata kungiyar matsafa,dan duk na samu sanara akan burina da nasa a gaba,ko matata bata san na shiga ba sai dana wan da shi sai daga baya na kaishi a matsayin tagomashin da zan bawa kungiya.dake kusan burinmu daya da Bashir sai kawai ya amince ba tare da na yi masa wani dogon turanci ba.....✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page66 ``` Numfashi ya ajiye yana goge hawayen da suka ki dakatawa daga zubar da suke daga cikin idanunsa. Sanan ya dora da cewa. A lokacin da Garba ya samu kujerar Gwamna yaso a ce Muhammad nur ya karbi mukami amma sai ya yi fur ya ce", baya so,abu na farko da ya faranta min shine yadda Muhammad nur ya bukaci da a bani wannan kujerar a madadinsa hakan kuwa a kayi ba tare da wani jan magana akan cewa bani da ilimi ba,mataki na farko ke nan da na fara takawa sai nake jin a cewa lallai fa wannan ƙungiya ta tsafi ita ce ta sa na fara samun wannan nasarar kamar yadda suma suke fada,hakan yasa na kuma jajircewa da yin dukkan abinda kungiya ta bukaci nayi. Dama ta farko da na fara samu akan his excellency shine yadda talakawa suka fara zarginsa da kashe kashen da ya fara yawaita bayan hawa kujerarsa ta gwamna bayan kowa yasan cewa a baya ba haka ce take faruwa ba duk da cewa basu ji dadin mulkin gwamnatin da ta sauka ba, wannan abu ne ya sa muka kara kaimi wajen kwamushe ya'yan mutane muna amfani da wasu sassa na jikinsu dan cimma manufofinmu,haka kuma wani lokacin tsohuwa me jini zata bukaci a tada tarzoma a gari dan Musa yaranmu su yi kashe kashe mu kuma mu yi amfani da ga warwakin shi yasa wani lokacin ko gawar yan uwanku bakwa samu. Haka dai mu ke aikata duk abinda muka ga dama muna shigewa rigar gwamnati hakan yasa ko lissafi ake yi babu wanda yake kawo mu ciki, A bangaren su shugaban jam'iyya kuwa tabbas suna da nasu laifin amma basu da laifi akan kashe kashen da ake yi,ko da suna yi na su kadanne akan nawa kuma sai an shiga gonarsu,a garin hakane halima ma aikaciya a gidan jaridar Chibado ta bibiyesu har ta gano sirrinsu na kamo maza yara ƙanana da samari suna amfani dasu kamar dai yadda kuka gani a wannan videon nasu da nasan dole yanzu an sake shi,kuma ta gansu lokacin da suke kashe wani yaro da shima sirrinsu ya gano wannan dalilin ne yasa suka kasheta ba tare da sun san ta riga ta yi musu videon ba har sai bayan da suka kasheta. A nan labari ya tafi kan yadda su shugaban jam'iyya suka daga hankalinsu kan neman videon da wanda ta turawa..... Ya ci gaba da cewa duk lokacin da aka kamasu nine nake sawa a fitar da su saboda suma ina jin dadin yadda nake aikata barna ana canki waye tsakanin su da HIS EXCELLENCY.wannan shine dalilin da yasa nake bin wasu hanyoyi dan a sake su. Lokaci na farko da na fara muzanta HIS EXCELLENCY shine lokacin da aka yi hira da shi a Chibado FM,idan mutane zasu tuna a lokacin an yi kira dan yiwa his excellency tambayoyi,to Nima da wannan damar na yi amfani wajen sa daya daga cikin yarana su yi min wannan aikin,wanda hakan ya yi matukar tasiri saboda na bankaɗa abinda mutane basu sani ba kuma na kara saka zarginsa a zuciyar mutane wanda ko da a gaba nasan duk abinda aka ce yayiwa Muhammad nur ba za a Musa ba kamar dai yadda ta farun. Mataki na karshe shine dabarun da na yi amfani dasu wajen sakawa Muhammad nur guba,dama na gama tsara yadda komai zai tafi,daga cikin wadanda na samu hadin kansu a kwai kukun HIS EXCELLENCY,ta kansa na fara bi amma kafin na je masa da maganar sai da tsohuwa ta rufe masa baki ta yadda ba zai iya musu akan bukatar da naje masa da ita,dan haka kai tsaye bashi gubar nayi nace duk runtsi ya zuba a cikin abincin da Muhammad nur zaici,daga haka na shiga tunanin dabarar da zanyi dan Muhammad nur yaje gidan his excellency,har kusan karfe biyar na yamma ban samu mafita ba,sai daga can dabara ta fado min,wajen tsohuwa na nufa na kai mata kukana,a nanne ta bani wata laya ta ce", na makalata a bakina naje gurin his excellency na fada mai bukatata zai amsa min. To amma da naje gurinsa sai na samu kaina da jin tsoran fada masa,ban taba kokonto akan aikin tsohuwa ba sai a ranar, hakan yasa na yi yan kame kame na na tashi zan tafi,maganar da his excellency ya yi min ita ta dakatar dani daga fita daga falon da nake kokarin yi,kun san me ya ce min? Yahya kaji tsoran Allah ka sani cewa akwai ranar da Allah zai tsaidamu a gabansa,dan Allah Yahya ka daina kokarin cutar da dan uwanka,Ni ba zance kar ka cutar da Ni ba amma shi dai ina rokon alfarma kar ka cutar dashi domin zuciyarsa me kyau ce", ban taba sanin cewa Garba ya san abinda nake aikatawa ba sai ranar wato zuru ya yi min kuma bai tona min asiri ba,a maimakon naji shawararsa ko nace nasiha sai kawai hakan ya kara harzuka Ni na fice daga gidan fuuu ina kumfar baki da borin kunya,ranar banyi bacci ba ina ta saka abinda ya kamata nayi daga karshe na tsaya akan shawarar da zuciyata ta bani na samu karfin gwiwa sosai akan tunanin da nayi,ko da his excellency ya fadawa nur ba zai taba yadda ba idan har ba shaida ya bashi ta gani da ido ba,to suma shaidun a daren nasa aka kama minsu wato haidar wanda nake da tabbacin cewa Flash din da shaidar ke ciki tana hannunsa idan kuma na kama shi ai his excellency bashi da wuri aya shaida, wannan dalilin ne yasa na kama haidar wanda dama cikin shirin kama shi nake saboda bincikena da ya nuna min akwai shaidar da yake shirin gabatarwa a hannunsa. Ban san ya akai ba washe gari na shiga bangaren nur dan ribatarshi zuwa gidan gwamnati sai kawai mamin Raihan take sanar dani ai tun sassafe ya fita his excellency ya kira shi yana nemansa da gaggawa,duk da cewa ban karaya ba amma tabbas na tsorata dan nariga na kwana da sanin cewa batuna zai sanar da nur. Hakan yasa nayi azamar bin bayansa,ganin har lokacin his excellency bai sanar da nur ba sai hankalina ya dan fara kwanciya na samu window falonsa na musamman ta can baya na labe ina leke da kasa kunne,to amma abinda ya bani mamaki his excellency ya kasa sanar da Nura komai akaina har wani tsawon lokaci suna zaune babu wata hirar nishadi bare ta ɓacin rai tamkar dai masu zaman makoki, shi kuma Nura bai tambayi his excellency komai ba yana dai binsa da yadda yake so akan zaman shirun da ya ƙirƙirar musu. Har lokacin Sallah ya yi suka tashi sukayi sallah wanda Ni kuma da wannan damar nayi amfani wajen zagawa kiching wajen kukun da na bawa wannan aikin na saka shi a gaba sai da na tabbatar da ya saka wannan gubar a karo biyu duk da cewa ya tabbatar min da ya saka a karin kumallonsu na safe,dake ba akan idona suka ci ba sai nake kokonto akan cin nasu shine dalilin da yasa na kuma zuba musu. Cikin sauri na koma inda nake a tsaye ko gajiya banyi saboda na sakawa raina cewa yau sai Muhammad nur ya mutu his excellency kuma sai ya kwana a gidan yari kafin shima a yanke masa hukuncin kisa kunga na jefi tsuntsu biyu da dutse daya ke nan. Dan shiru ya yi kafin ya cigaba da cewa ba saina baku labarin abinda ya biyo baya ba nine na kira yan sanda suka tafi da his excellency. Burina na hawa wani mataki a siyasa ya cika sannan burina na duniya ta Sanni ya cika duk a wannan lokacin,abu daya ne yazo min a tamgarda shine Muhammad nur bai mutu ba,kuma dole sai ya mutu ne za a yankewa his excellency hukunci tunda wadancan laifukan babu shaidar da ta tabbatar da cewa shine ya ke aikatasu hakan ya nuna min cewa tsugunne na bata kare ba. Yana zuwa nan alabarinsa ya fashe da wani mahaukacin kuka wanda yake yinsa bil hakki da gaskiya,yana jin takaicin rayuwarsa da ta ahlinsa. Take garin ya hargitse kowa da irin kalar tsinuwar da yake yiwa Abba yahya,wasu kuwa kuka suke na tunawa da yan uwansu da ya yi sanadinsu. His excellency da iyalansa kuwa hamdala suka dinga yi ga Ubangiji, fuskokin su cike da farin ciki na wankesu da Allah ya ya yi ba tare da tsuminsu ko dabararsu ba. Jami'an tsaron da suke kewaye da gidan dana cikin gidan kuwa basu yi wata_wata ba gurin kama Bashir da Abba yahya,su Hajiya goggo na gani a ka saka danta a motar da take da tabbacin baza ta taɓa dawo dashi ba,tana kallon lokacin da yake hade hannayensa biyu yana rokon gafararsu ita da baffa da Abbie,a hankali take jin zuciyarta na sosuwa,lallai na yadda cewa ɗa duk lalacewarsa ɗa ne kuma uwa sonshi take yi kamar yadda a wajen da uwa duk lalacewarta take uwa a wajensa,tabbas Hajiya goggo taji daci da bakincikin fitowar Yahya daga tsatsonta amma ya ta iya da wannan kauna da jin kan dake tsakanin ɗa da mahaifi,hannu tasa ta share hawayenta tana mai binsa da addu'a ba wai dan tana da tabbacin zai zama wankakke kuma me tsarki ba, Hatta da Abbie sai da yayi kuka dan wallahi yana son dan uwanshi so na hakika shima dai daga karshe addu'ar ya raka Abba yahya da ita. Jiki babu kwari suka rankaya suka koma cikin gida kowa da nasa ciwon zuciyar wanda basu san ranar warkewarsa ba,wazer yana kallo hajiyar agadex ta janye raihan su kayi ciki tana cewa muje kema ki ɗan samu nutsuwa", numfashi ya sauke tare da bude idanunsa sosai akanta cikin zuciyarshi yake cewa duk ki gama wayon naki daga karshe dai dole ki bani matata dan babu wata nutsuwa da zata samu a wajenki", motarsa ya shige securitys din da ya riga ya fara sabawa da bibiyarsa da suke suka take mishi baya. A halin yanzu babu cikowar mutane a kofar gidan saboda an tafi da wanda suke son gani yan jarida kuma suke son tambaya, tunda a halin yanzu kowa ya samu amsar tambayar dake cizon zuciyarsa,hakanne yasa babu mutane sai yan tsirari suma yan cikin unguwar ne da suka tsaya maida magana. Da wannan damar mutanen ABBAN rabi su kayi amfani wajen saita makamansu don cika umarnin ogansu,ko wanne yana labe a maboyarsa yana saita kibiyarsa ga abin harinnasu. Tamkar wani waliyi haka wazer yaji a jikinsa akwai wani abu da aka shirya masa a wajenann,hakanne yasa yasa drivansa ya tsaida motar,sir lafiya dai ko? Drivannasa ya tambaya cikin ladabin da akasan ko wane mutum yana wa uban gidansa,ina ga fa akwai matsala maza kira min wayar motar su daniyal ok sir ya fada cikin sauri tare da cika umarnin ogannasa,bayan yaji alamar dagawa yayi saurin saka wayar a amsa kuwa,cikin nutsuwarshi dake bayyana a dukan aiyukansa ya ce", daniyal ina so ku fito cikin dabara ku duba wasu wurare a wajenann duk wanda kuka ga alamunsa da rashin gaskiya ko da makami a hannunsa ku kamashi is don daniyal ya fada cike da fatan cika umarni. Ciska da suke can labe suna zura idon ganin wazer ya fito daga cikin mota,saboda a tunaninsu wannan tsayawar da yayi akwai wanda yake jira Wata kila ma matarsa yake jira sun san kuwa idan ita ce dole zai iya fitowa shi yasa basu harba kibiyar a jikin tayar motar Ba kamar yadda da farko suka tsara,sam dukkansu babu wanda yayi zato ko tsammani kamar daga sama haka suka ga garadan samudawan securitys din wazer akansu ko wannensu hannunsa rike da bindiga me rai wadda suke da lasisin riketa da yin harbi,zube makamansu su kayi tare da yin saranda domin duk rashin tsoranka ka haɗa hanya da wadannan mutanen dole zuciyarka ta girgiza,kaɗa ƙeyarsu su kayi gaba ɗayansu su biyar ɗin,.waya daniyal ya kira daga can headquarters dinsu akan a basu jami ai,cikin kankanin lokaci sai ga jami'ai na fararen kaya sun bayyana,ba tare da wani bata lokaci ba suka kaɗa keyarsu ciska zuwa gun wanda ya turosu,ba su yi gardama ba kuwa suka jagorancesu har zuwa gidan ABBAN rabi da ya basu tabbacin cewa babu inda zashi har sai sun kawo masa kyakkyawan sakamako akan wazer ɗin. Tun bayan gama sauraron labarin da Abba yahya ya bayar sai kawai ya tashi ya shige dakinsa,yana ji kamar jikinsa zaiyi sanyi,zama ya yi bakin gadonsa ya zuba tagumi,tunani yake yi idan har irinsu Abba yahya zasu shuka irin wannan ta asar kuma asirinsu ya tonu to shi din karamin alhaki tayaya ne nasa ba zai tonu ba?tayaya Allah zai kawo karshen irinsu tsohuwa shi ba zai kawo nasa karshenba? Anya kuwa idan ya cigaba da haka ba zai iya samun kansa cikin katuwar nadama irintasu Abba yahya da inna maimuna ba? Kafin ya bawa kansa amsa ne wayarshi ta fara kara alamun kira na shigowa,dubawa ya yi yaga ciska ne,da sauri ya dauka yana fatan basu aikata aikin da ya sasu ba,ka fito muna waje", abinda ciska ya ce dashi ke nan wanda hakan umarni ne daga jami'in da ya bashi damar yin wayar. Jiki na rawa abban rabi ya fito a tunaninshi ko basu samu nasara ba,wanda a Yanzu shine babban fatanshi,sai dai abinda ya gani shi yayi matukar razana shi da saka shi cikin tashin hankali wato dai abinda yake gudu din ya riga da ya faru,asirinsa ya tonu,ji yayi baya tsoran hukuncin da za ayi masa amma yana tsoran idanun mahaifiyarsa da dan uwansa shin ya Abbu zaiji idan yaji cewar dan uwanshi ciki daya yana son ganin bayan ahlinshi? Kafin ya ci gaba da tunanin da yake yaji an sakale hannunwanshi da sarka,ku bashi dama ya sanar da iyalansa", wani daga cikin mota ya fada da alama shine babbansu,tasa keyarshi mutum biyu su kayi har cikin falon gidan,inda suka sami rabi a da mamanta tana faman rarrashinta akan ta ci abinci kar yunwa ta kamata. Da sauri suka mike tsaye jikinsu na rawar tashin hankali,abban rabin bai iya ce da su komai ba,sai daya daga cikin jami an ne ya basu shedar ko su su waye ta hanyar nuna mu ID dinsa,sanan ya juya suka fice da abban rabi,kuka rabi a da mama suka saka suna binsu akan su yi hakuri amma tamkar da dutse suke magana ,haka suna ji suna gani aka tafi dashi suka barsu a bakin gate suna kuka kamar ransu zai fito. Biyu daga ciki ne suka wuce suka fito da abu Huraira wanda babu wani ja ya sanar dasu wanda ya sa shi ya zubawa wazer guba,basu da duwa da haka tunda shima a halin yanzu yana hannu,dan haka suka wuce da abu Huraira akan idon sauran staff da hakan ya matukar tsorata su shi yasa kowa ya shiga karkace zuciyarsa idan ma da wani abu makamancin Wannan a cikinta to sun kade shi, Allah Ubangiji ya raba mu da son zuciya. Sai yanzu wazer yaji ya dan samu nutsuwa,ko da ya je gidan bai shiga bangarensa ba sai da ya tabbatar ya sanar dasu innawuro abinda ke faruwa iya wanda ya sani,daga haka ya kabe jikinsa ya wuce samasansa ya barsu cikin wani sabon tashin hankalin, innawuro kam tasha kuka baranma da su Khalid suka kara sanar da ita abubuwa da yawa da suka faru da irin tsallake tarkon abban rabin da yayansu yake yi,Abbu da hajiyar Kano ma sunyi kukan takaici da bakincikin rayuwar da dan uwansu ya saka kansa a ciki,daga karshe dai dole kowa ya hakura, innawuro da kanta ta ce", gobe Khalid zai Kaita gidansu Raihan dan tayi jaje sannan ta faɗa musu sati na gaba za ayi biki Raihan ta tare a gidanta, wannan maganar ita ce ta sanyaya musu rai daga kunar da suke ji,hadiyar Kano kuma ta kara da cewa zata karbi kudi wajen wazer su tafi Dubai ita da Ruma da shukra su hadowa RAIHAN lefe na kece raini,ba su tashi da ga wajen ba dai sai da suka tabbatar sun maye gurbin bakincikinsu da farinciki,duk da cewa ba wai abin ya bar ransu ba ne......✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page67 ``` """""Komai yayi farko yana da karshe,duk a baya gani suke kamar zuciyarsu ba zata yi sanyi ba,gani suke kamar abin ba zai wuce ba,sai gashi yau da ake cinye sati daya da faruwar komai suna cikin walwala da farinciki,gashi duk inda ka duba gidan mutanene cike yan uwa na nesa da na kusa kowa yazo dan tayasu farincikin shagalin bikin yar gata yar so wato RAIHAN MUHAMMAD NUR,bikine aka shirya na manya da sarakuna wanda aka tsarashi cikin tsari me kyau da burgewa,ta bakin mutane da suke cewa saima ranar,jiddo ita ce aminiyar amarya tun da can wanda Raihan take shan shaƙiyanci a gurinta,wai ashe dama duk wannan abun da take yi akan wazer so ne wanda ya haifar da kishi, Raihan bata ce mata komai sai dai harara dan ita kadai tasan azabar da take sha na hanata ji da ganin wazer da aka yi sai wani uban gyaran jiki da ake ta yinsa wajen sati biyu,yanzu hatta kai da cewa ita kanta kamshin da take yi ya fara damunta dan duk inda ta motsa ko ta gifta sai kaji wannan sihirtaccen kamshin hadin turarukan da yar me duguri ta ke yi mata. A Bangaren gidan su wazer ma yau hajiyar Kano ta dawo ita da shukra da Ruma,lefe suka hado na gani da bada labari,tabbas idan na tsaya gaya muku abinda lefennan ya kunsa za mu cinye lokaci ne ba tare da mun gama ba, komai classqui aka saka saboda wazer ya ce Raihan ta musamman ce dan haka komai nata dole ya kasance na musamman,to suma dai a bangarensu sai dai muce alhamdulillah dan kuwa kowa ya saki ransa yana walwala yadda ya kamata,sanann sun rufe komai iya su ba tare da sun bari dangi na waje sun san abinda abban rabin ya aikata ba, wannan ne yasa wasu yan uwan da yawa suke tambayarsa. A bangaren Rabia kuwa za mu iya cewa abin ba sauki, dan sosai ta kwanta ciwo babu kowa tare da ita sai mahaifiyarta wadda take ci gaba da yi mata fadan bin rayuwa a sannu,ita dai bata da abincewa sai ruwan hawaye dan yanzu bata da wani buri illa ta bude idanunta ta ganta a dakin mijinta kai ita fa ko da wazer ba zai dinga kallonta ba zata iya zama dashi dan soyayyarsa ta zame mata ciwo me mugun muni. Surry kuwa ta debowa kanta jaraba dan abin ya ci gaba tun tana tunanin warkewa daga karamar cutar da ta fara har abin ya fara bata tsoro,daga karshe dole iyayenta suka sani a ka shiga nema mata magani amma abin kamar kara mata shi ake yi,dan yanzu ta kai ga cewa ko fitsari bata iya yi saboda yadda gabanta ya koma,wasu irin kuraje ne masu wari suke fitowa a duk inda ta sosa daga nan kuma sai su kumbura wannan ne yasa gabanta gaba daya ya zama baya moruwa,a hankali dakin ya fara daina shiguwa saboda azabar wari,mahaifiyarta kanta bata iya shiga dakin. Tsohuwa me jini ...... Tun lokacin da wannan mesar ta kanannadeta bata kuma barinta ta motsa ba,ga dai ta da ranta amma wannan mesar tana tare da ita babu abinda take sai azabtar da ita,a maimakon ta sareta a'a sai ya zamana cizonta kawai take duk sanda taso,daga baya kuma ta fara cinye wasu sassa na jikinta wanda tsohuwa tana ji tana gani sai dai ta yi kuka da iya idanunta da kuma zuciya,a hankali mesar nan take cinye tsohuwa tana kuma janyota daga cikin dajin zuwa cikin gari saboda al umma suga irin mutuwar wulakancin da zata yi ko hakan ya kuma zama izna ga al'ummarmu. Su Abba yahya kuwa suna can a garkame babu wanda ya kuma waiwayarsu,hatta da lauyansu ya gujesu,shi yasa Bama su san ranar shiga kotun ba,yo wane lauya dama ya rage musu ai su yanzu sun san tasu ta kare. Shima Idris Shari'arsu rana daya duka a kasa har da inna maimuna me yunkurin yin kisa har sau biyu,Dukansu cike suke da nadamar da bata da wani amfani garesu tunda sun riga sun aikata laifukansu. A bangaren his excellency kuwa dakyar mutane suka bari yayi hutun kwana biyu sannan ya koma gidan gwamnati shida iyalansa tare da rakiyar dubban al'ummarsa da suke a karkashinsa,cikin kwanakin da ya dawo bakin aiki yayi abubuwa masu dama wa'danda sai dai muce sambarka. Haidar ma ya samu sauki ya koma gida tare da ƙarin girma zuwa Kwamishinan yan sanda. Abban rabi da su abu Huraira da yaransa duka tare aka kullesu aka saka ranar Shari'ar su bayan kwana ɗaya da yin shari'ar su Abba yahya,daga karshe dai yan sanda sun matsashi ya sanar dasu sawa ya yi a kashe Khalil,ciska da shi aka saka ya yi aikin ya bada tabbacin cewa bai kashe kalil din ba,fansar kansa ya yi ta hanyar bashi kudi masu yawa ,dan haka ya sake shi amma ya bashi damar barin kasar saboda kar abban rabin yasan bai kasheshi ba,jin haka yasa take kwamishina ya baza cikiyarsa tunda har iyayensa basa nan bare a nemi sanin inda yake ta hanyarsu. _________ Biki buduri.....ranar Alhamis aka saka Raihan a lalle. Ranar juma'a kuma akayi kamu,wani irin kamu na burgewa wanda aka yi shi da al'adun kamu biyu,kamun buzaye bangaren uwa ke nan,sai kamun Fulani wanda bangaren uba suka kamata daga nan a ka raba kayan al'adu na ko wane yare fillo da buzanci,idan nace muku kayatuwa da haduwa to na rage muku armashi,sai mu ce Masha Allah,a bangaren amarya kuwa duka shigar da ta yi babu batun tsayawa bada labari kunsan wacece RAIHAN dan haka kawai kuce Masha Allah domin kyaune ya taka rawarsa ranar. A ranar kuma aka karbi lefen da ya gigita jama a da dama ya shiga bakunan mutane da dama,wasu alkhairi suke fada wasu kuwa sai hakuri dan mutum ba a iya masa. Lokacin da wazer yayi arba da hotonta da yasa jiddo ta tura masa, sai da yaji kamar numfashinsa zai tsaya,ji yayi kamar ya ce", a hakura da bikin haka saboda yasan ko yau babu maza hotunanta zasu yi yawo a social media a matsayinsu na sanannu,ji yayi duk ranshi ya ɓaci bashi da damar dakatar da matan da suka ziyarci bikin ɗorawa a social media,rufe idanunsa ya yi yana hasaso yawan mutanen da zasu ganta maza da mata,anya ko zai iya bari a karasa bikinnan wannan kwalliyar fa shi kadai ya dace da ya gani", me makon ganin hoto ya faranta masa sai ya zamana ya wuni da ɓacin rai,duk tsokanarsa da Yusuf ke yi bai tanka ba,shi ko Yusuf bai damu ba dan yasan halinsa,damuwarshi yanzu bai wuce ya bashi fuskar yiwa ƙaramar kanwarsu shukra magana ba,dan Allah ya gani yarinyar ta tafi dashi matuka. A haka daga ango har amarya suka dinga ɓacin rai har zuwa yau asabar da za ayi dinner daga nan ango ya wuce da matarsa washe gari kuma sai yan uwa na nesa suje ganin gida. Ƙin tsayawa ta yi a yi mata kwalliya sai da Auntyy Khadija ta je ta gayawa hajiyar agadex,,hajiyar agadex tana shigowa dakin da ake shiryatan ta yi mata dakuwa tana cewa yau dai naga baƙin rannan da kike zai kare tunda yau zamu mikaki gun wanda kikewa,ko kinyi zaton ban san abinda kikewa ba?,fadin haka da hajiyar agadex ta yi kuma duk sai ta ji kunya babu shiri ta tsaya aka tsantsara mata kwalliyar da ita kanta saida taji tsoran kanta,Masha Allah tabarakalla haka me kwalliyar take ta faɗa tun kafin ta kammala shirya RAIHAN ɗin.. Babban hol din dake cikin gidan gwamnati yayi tsit kai ba ka ce mutanene wadanda suka haura dubu ba aciki,tun bayan sanar da shigowar ango da amarya gurin yayi tsit saboda karramawa ta musamman ga ango da amarya. Motar da aka dauko RAIHAN daban motar da aka dauko wazer daban,dan haka har yanzu basu ga juna ba. Bude motar escort din ango su kayi ango ya fito,waww abinda zan iya cewa kenan,hakika ba zan iya kwatanta muku irin kyau da wazer ya yi ba,to kyaune ya hadu da kwalliya da aji da kuma kasaita dan haka kuwa sai abinda aka gani. Har bakin motar da Raihan ke ciki a hakimce suka rakashi daga nan suka ja baya su da EXCO din amarya suka yi nasu comber din suna tsimayin fitowar amarya, A hankali ya duka bayan ya bude murfin bangaren da take Sannan ya dan zura kansa,take yaji numfashinsa na sarkewa saboda wani azababban kamshi me sanyi da sanyaya zuciya kafin idanunshi su yi arba da abincin da aka hanashi gani bare tabawa tsawon kwanaki goma,jan numfashinsa ya yi a nutse sanann ya furzar dashi,a hankali ya mika dogayen hannayensa da suka ji adon agogo samfurin alben me tsananin walwalin gold da sheki ya kamo nata da suke kawace da adon jan lalle da baki da bangle din gold da zobuna,dukkansu ji su kayi numfashinsu na kokuwa saboda yadda zuciyoyinsu suka amsa da wani irin kewa bege shauki me ban mamaki,duk da cewa ita Raihan har yanzu ta kasa dago kanta ta kalli kyakkyawar fuskarshi dake sheki da haske tamkar wata,duk yadda take jin kewarsa da begensa sai taji sam yanzu bata iya kallonsa saboda wata irin kunya wadda ke hade da wani irin shauki ta baibayeta,(tabbas kai budurci gidan miji koda irin na su Raihan ne da aka daura aure yana da muhimmanci, yanzu da wazer ya amshi budurcin Raihan da wannan shaukin ko da zai jishi ba wani cancan ba,kuma ita ma ba zata kai masa wannan nagartacciyar kunyar da aka san ɗiyan Hausa Fulani da ita ba.shi kuma Wazer ba zai ji irin kewar da yake ji a yanzu ba,saboda ya riga ya samu wani bangare na farincikin aure ko na ce abinda ake yin aure dominsa daga gare ki,ki sani cewa duk SOYAYYA da mijinki yake miki ko zai miki muddin babu wannan budurcin wallahi kin zama sorry ,ey akwai son ba babu ba,amma akwai jin haushi me tsanani wanda zai iya rinjayar wannan son,kuma tsautsayi kadan zai iya giftawa ya yi miki gori duk daren dadewa ko akanki ko akan yayanki,dan haka ina kira garemu ke da baki auren fari ba,ki rike darajarki da mutuncinki har zuwa gidan mijinki,idan ba haka ba akwai nadama,ba iya budurwa ba har zawaran duka ina kira gareku Allah yasa mu dace). Wazer ji ya yi tamkar yaja matarshi su koma gida saboda baya jin zai iya jurar kallon daruruwan mutanen da zasu samu kallon fuskarta da gangar jikinta,wata kila ma wani zai iya raya cewa inama wannan matarshi ce", runtse idanunshi ya yi tare da hannunta dake cikin nashi,kasa barin wajen ya yi har sai da Yusuf ya matso ya sanar dashi su fa ake jira,dole ba dan yaso ba sai dan kar ya bar iyayensu da jin kunyar manyan mutanen da suka samu halartar wajen. Daga kafarshi yayi sannan itama ta daga,yadda zuciyarshi ke bugawar azabar kishi haka Raihan da har yanzu bata ga kwalliyarsa kanta yana kasa Tata ke bugawar yawan yanmatan da zasu gane mata shi,tasan cewa Wazer ko bai kwalliya ba shi din me kyaune kuma me aji ne dan haka bata da bukatar yin la'akari da kwalliyarsa. Wani irin taku ne suke yin shi me cike da aji da kasaita wanda yakasance tamkar umarnin yinsa a ke basu,kamshinsa da nata kuwa tuni ya buge ko wane kamshi dake wajen. Cikin girmamawa duka mutanen dake gurin suka mike ba tare da ambasu umarni ba, yayin da wani irin sassanyan sautin kida ke tashi a wajen cikin slow. Cikin takunnan da suke yinsa ɗai-ɗai tamkar suna saman gajimare suka isa mazauninsu,basu zauna ba sai da wazer ya daga hannunsa dake sarke da na RAIHAN yayi wavin din yan uwa da abokan arziki alamun Barka da zuwa,suma daga musu suka yi sanann wazer da Raihan suka fara zama kafin sauran mutanen suka zauna a lokaci daya suna sakin tafi taf raf raf,,,,,idan na ce muku katarwa to karshen kayatuwa nake nufi,ba kida a kayi a wajen ba,manyan mutanene suka dinga yiwa amarya da ango kyauta dangin ango na yiwa amarya dangin amarya na yiwa ango abun burgewa daga karshe a kayi wa azi me ratsa zuciya aka rufe da karatun Alqur'ani da a marya ta rera wanda ya sa mutane da yawa zubar da hawaye saboda kushu'i da aka samu a cikin karatun alhamdulillah Masha Allah abinda mutane suke fada ke nan,da haka taro ya watse ango da Amarya basu bar gurin ba suna mazauninsu duk wanda zai tafi zai karaso su gaisa su yi hoto har kowa ya watse ya rage saura abokan ango dana amarya da sune karshen tafiya tare da ango da amarya saboda jagoranci da za suyi musu zuwa gidansu rakiya. Kai tsaye main Hause suka wuce saboda sai ya fara Kaita wajensu Ammi da innawuro kafin su wuce can gidansa da ya tanadeshi domin farincikinsa Raihan. Duk wannan budurin da akayi akan idanun Rabia da take gani a acikin tashar Chibado da ake haskawa live,ganin yadda numfashinta yake neman barin kirjinta yasa mamanta ta kashe tv sannan ta karaso tana rarrashinta da kwantar mata da hankali. ________ Innawuro dakanta ta fito tarbar RAIHAN iyalanta zagaye da ita suna take mata baya,da kanta tayi Bismillah sannan ta riko hannun Raihan ɗin ta fito da ita,wata yar uwar innawuro ta sanya budu kafin nan suka rankaya su kayi cikin katon falon innawuro,ta ciki suka bi suka wuce zuwa babban falon Abbu inda suke tare da Ammi. Zaunar da ita innawuro ta yi a gaban Abbu da Ammi sannan itama ta samu guri ta zauna. RAIHAN kanta yana sunkuye ta fara gaida surukannata,amsawa su kayi suna mai sa mata albarka,daga nan kowa ya bar falon sai su isu,Yusuf ne ya shigo da wazer kamar yadda Abbu ya umarceshi da ya rakoshi. Bayan nasiha me ratsa zuciya da suka gabatar wa yaran nasu,daga karshe innawuro ta kuma fito da Raihan har cikin sabuwar motar da Abbie ya bata wadda suka zo a ciki, Allah ya yi muku albarka ta fada sannan ta ɗora mata kyaututtukan da bata san ko meye ba a cinyarta,na gode innawuro Allah ya saka da alheri ya bamu ikon binku sau da kafa..........✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page68 ``` Ameen innawuro ta amsa tana rufo kofar bangaren da RAIHAN ɗin take,komawa ta yi wajen wazer kasancewar driver ne yanzu zai tukasu,dan haka ta dawo bangaren da yake shima ta yi masa sai da safe,tana shirin tafiya taji ya riko hannunta tare da saka mata wata yar karamar takarda,duban takardar ta yi sannan ta dubeshi dan son jin karin bayani,basarwa yayi sannan ya daga fatar bakinshi a hankali ya ce", ta jikarki ce ki bata tunda dama ke kika hada", zuba mishi ido ta yi tana masa kallon anya abinda kayi ka kyauta kuwa? Kamar ya san abinda take tunani dan haka ya kuma yin kasa da murya sannan ya ce", bazan iya ba innawuro akwai wahala rike mata biyu,sannan Allah dakanshi cewa yayi ku yi daya idan har ba za kuyi adalci ba,to Ni kam ba zan yi ba Allah ya gani kuma ya sani", daga haka ya koma cikin motar tare da rufewa wanda hakan shi ya bawa driver damar jan motar a hankali cikin nutsuwa ya fita daga tafkeken gate din da securitys suka wangale shi. Ajiyar zuciya innawuro ta saki tare da kara kallon takardar tana jin jikiinta na yin sanyi,tabbas abinda wazer ya fada gaskiya ne,to amma ya za ta yi da rabi a? Bata so taga kamar dan ubanta yayi wannan halin an wareta ko kuma taga kamar ba a sonta kamar yadda take gani a baya,to amma babu yadda ta iya rabi a da ubanta su suka jawowa kansu,tana shiga falon ta bawa Abbie takardar bai tambayeta ba ya shiga budewa,(Ni Ahmad wazer Chibado na saki Rabia Mustapha saki daya bisa dalilan da ba zan iya fadarsu ba amma daya daga ciki shine ba zan iya adalci ba) Wani irin sanyi Ammi ta ji dan kuwa yanzu gaba daya ta tsinke da almarinta itama zata iya kashe wazer ɗin tunda halin ubanta ta yi ", Abbu kuwa komai bai iya cewa ba sai innawuro da ya mikawa takardar sannan ya iya cewa Allah yasa haka shi yafi alkhairi dashi da ita", Amin suka amsa gaba daya. ___________ A hankali motar take tafiya saboda umarnin da aka bawa matukinta da yaja a hankali saboda zinariyar dake cikinta,ba kajin komai amotar sai sassanyan ƙamshinsu da ya haɗe guri daya ya kuma bada wani kamshin na musamman,sai kuma na urar dumama guri da ta cika motar da dumi me dadi wanda ba zai cutar da mutum ba,kasancewar mun fara shiga cikin yanayin sanyi wanda ya taho da karfinsa a lokaci ɗaya. Can gefe RAIHAN ta matse jikinta kanta kasa tana jin wani irin kewar gida wanda yasa ta zubar da hawaye,daga nan ta fara kuka kasa kasa kamar me tsoran ajita,bata san lokacin da ya matso kusa da ita ba ita dai kawai ta tsinci tattausan hannunsa saman kafadarta kafin a hankali ya janyota gaba dayanta ya manneta da jikinshi,alokaci daya suka saki ajiyar zuciya,lumshe idanunsa ya yi ya bude su fes akanta yana kallon daurin kanta da yake ganin zai iya damunta, wannan tunanin da ya yi ne yasashi zame dankwalin daga kanta take sassalkan gashinta baki me sheki ya bayyana yana zuba wani ubansu ƙamshin da yasa wazer dora fuskarshi akannata yana shakar kamshin da yake ji bai taba jin irinsu ba,tamkar wani maye haka ya shiga bin kanta zuwa wuyanta yana shinshinawa har ma yana neman manta inda suke. Itama Raihan ɗin tun bayan jinta da tayi manne da faffadan ƙirjinsa kukanta ya tsaya ba tare da ya yi mata rarrashin baka ba,wanda dama shi bai iya shi ba sai dai yayi shi a aikace. Tsayawar da motar ta yi shi ya ankarar da wazer inda suke,dakyar ya iya dago kansa dake wuyan Raihan tun dazun sannan a hankali ya bude baki ya ce," da driver isah ina sakon da Yusuf ya baka?cikin sauri isah dake karasa kashe motar ya ce", suna nan gaba yallabai", "Ok ka shiga dasu ciki", An gama yallabai", Daga haka ya fita daga motar bayan ya dauki manyan ledojin da suke gaban me zaman banza. Shiru wazer yaki fita har sai da Raihan ta dago da kanta ta kalli fuskarsa ta cikin dan hasken da ya haska cikin motar ,sarai ya gane me take so tace amma sai ya basar,bai ce komai ba har sai da isah ya dawo ya bashi key ɗin motar yayi masa ihsani ya kuma tabbatar securitys sun bude masa gate ya tafi Sannan ya daga Raihan ɗin cak suka fito tana hannunshi tamkar wata jaririya,a haka ya nufi cikin gidan da ita. Idan na ce zan tsaya fasalta muku haduwar wannan gida lallai kuwa zan gundureku dan haka ku ƙiyastashi a ranku da karshen haduwa,sai dai muce Masha Allah Allah ya bamu wanda ya fishi a nan da kuma aljanna", Bai tsaya da ita a falon ba kai tsaye ya haye up stairs da ita ,ya shige da ita hadadden dakinta da yake ta zuba kamshinta da yake manne da komai nata,a hankali cikin nutsuwa ya kwantar da ita,a yanayin yadda ta tafi luuu yasashi dan kallon fuskarta da take ta sheki,dan murmushi ne ya subce masa ganin wai har ta yi bacci,kyaleta ya yi bai tasheta ba har sai da ya kammala shirinsa tsaf sannan yazo ya zauna a gefanta ya shiga dan tafin fuskarta cikin wata irin lallabawa da tarairaya kamar kwai,aiko a hankali ta shiga bude idanunta da suka dan fara canja launi saboda bacci,mirgiinawa ta yi zata ci gaba da baccinta yayi saurin rikota tare da tayar da ita zaune. Fuska ta kwabe tana shirin sakin kuka alamun ya takura mata, langabar da kanshi gefe ya yi sannan a hankali ya ce", sorry freety yanzu ba lokacin bacci ba ne", to lokacin me ye? Ta faɗa tana kokarin zamewa dan kara kwanciya,shima yayi saurin kuma tarota yana cewa lokacin yin ibada ne sallah za mu yi kici abinci", na koshi kuma nayi sallah", a'a hibban wannan sallar ta godiya ga Allah ce da ya kawo mana duka karshen makiyanmu ba tare da tsuminmu ko dabararmu ba", dan shiru ta yi bata ce komai ba sai murza idanunta da take yi tana so ta dan wartsake. Sorry ya fada cikin wata irin lallabawa da son yin calming dinta duk dan kar ta damu. Bude idonta ta yi sosai akan shi kafin cikin sakalcinta ta ce", to amma muna yin Sallah zanyi bacci ko? Jinjina mata kai ya yi ba tare da ya iya furta komai ba,tura karamin bakinta ta yi tare da kwabe fuskar kafin ta ce", ai baka amsa ba Ni kam sai ka amsa min da baki sanann zan Yadda", na amince zaki bacci", ya fada a hankali yana ci gaba da kallon fuskarta da baya gajiya da kallah,bai bari ta kuma yin wata maganar ba ya dauketa cak yana farawa da zame mata hadaddiyar rigar dinner dinta,har ta fara wurga kafafu akan ya barta zata yi da kanta amma yadda ya haɗe fuskarnan ya dawo asalin wazer dinsa yasa ta yi gum. Tana ji tana gani yau dinma ya sabeta tas ya kuma danota cikin katon showel yazo ya shiryata cikin wata hadaddiyar rigar bacci wadda tasa ta jin kunyar da bata shirya mata ba,hijab ya saka mata sannan ya nuna mata wajen sallar da aka kebance shi kamar fadar Sarkin Makka. salloli su kayi wadanda Raihan bata san adadinsu ba,sai da yaga Raihan na neman kwanciya kana ya hakura su kayi zaman addu'a,sosai ya yi mata addu'a tare da yi mata tambayoyi akan addininta daga karshe yasa ta rera masa karatun Alkur'ani ayoyi goma daga cikin suratul kahfhi cikin zazzakar muryarta wanda yaji tamkar kar ta daina,amma ba yadda ya iya haka suka shafa,a hankali ya kamata yazame mata hijab din ya maidashi muhallinsa,kunya ce ta kuma kamata ta shiga rufe jikiinta da yake duk a waje,shi kam Wazer ko ajikinsa sai ma fita da ya yi ya dauko kazar da ya tsaya ya yayyankata kananu ya kuma zubo madara a Glass cup guda biyu ya kawo ya dire yana ɗan yatsina fuska saboda yayi aikin da bai saba yi ba. Zuwa yayi ya janye bargon da ta shige yana cewa baki yi dayan aikin ba zaki kwanta,bude idanunta da suke cike da bacci ta yi ta dan kalleshi sannan ta juya ta kalli abinda ya shigo dashi din,kamata ya yi ya dagata ta tashi zaune,janyo dan teburin da ya aje madarar ya yi gabansu ita kuma ya janyota jikinsa yayi mata makari da kirjinsa,a hankali ya shiga bata tsokar naman kazar tana ci cikin nutsuwa shi kuma yana karewa dan karamin bakinta da yake taunar cikin salon da bata san tana yinsa ba kallo,ganin yana kallonta yasa ta bata fuska sanann ta dauki kazar da hannunta tayi hanyar bakinshi da ita,bai Musa mata baya bude bakin amma memakon ta sa masa sai kawai tayi kwana da ita ta jefa a bakinta tana masa gwalo da cewa punishment din kallon da kake min kana neman sani kwarewa. Au haka ne? Ya tambayeta yana ƙoƙarin saka mata wani naman abakinta", dage mai gira ta yi, murmushi kawai yayi yana cewa azuciyarshi ki yi komai kike so yanzu lokacinkine,kafin nan da wasu mintuna nawa lokacin ya fara. Madarar ya bata tasha sannan ya danci kadan shima yasha madarar kana yajata suka je su ka kuma yin brush. Yana kallon hammar da take tayi akai akai sai da ya ce hmm azuciyarshi. Kwanciya ta kuma yi tana jan tattausar duvet dinta daya ke ta zuba kamshi me sanyin dad'i,gefanta ya kwanta yana shigewa cikin jikinta tare da sakala hannunshi ya zagaye cikinta a hankali kuma ya burkitota ta dawo suna fuskantar juna,kifkifta idanunta ta shiga yi dan tsoro ya fara shigarta,yatsanshi ya saka saman idanunta yana zagaye idanunta in a emotional way sannan a hankali ya bude bakinshi ya ce ", daga yau bake ba juya min baya ko da kina a halin fushi dani plzz ina miki wannan rokon hibban", ya karasa furta kalmar cikin wani irin shauki da raunin da ya gama bayyana akan fuskarshi,kada kanta kawai ta shiga yi tana jin anya ko a kwai ranar da zata ji haushinsa har ma takai ga yin fushi dashi? Kai da wuya amma zata barwa lokaci danshine alkali. Kafin ta ida tunaninta taji saukar harshensa me dumi saman fuskarta,se alokacin ta Ankara ashe hawaye take na tsananin kauna,shi kuma ya shiga lasheshi tamkar wani zuma,daga wannan labarin ya soma canja salo. Wata irin kalar so ya shiga fesawa RAIHAN wadda taji ta tamkar ba a duniyar take ba,babu inda bai tsotsewa yana lashewa ajikinta,ji tayi tana neman shidewa saboda yadda taji ya sanya harshensa saman na shanunta abinda bai taba ko tabawa ba duk budurin da suke iya baki yake tsayawa da wasu guraren amma dukiyar fulaninta sai dai ya gani ya hadiye yawu shi yasa yau din yake wani irin hucewa akansu,sam bai musu ta sauki,tun Raihan na dar-dar har dai itama ta shiga maidawa malaminnata martanin Koyarwarsa wadda take ta gama ruda masa kwanya,tabbas idan na ce muku Wazer ya susuce kar ku yi musu domin mutuniyar taku kaf ta kulle mishi kai akan dan darasin da ya koyar da ita,salon na dabanne na iya daren farko kuma a matsayinta Na wadda bata san komai ba sai iya dan abinda ya koyar da ita. Sai da ya karanto addu'ar haduwa da iyali sannan ya haɗe bakinshi da nata ya shiga bata wata kyakkyawar sumba me sufuri,kafin cikin hikima ta mazajen da suka san kansu da muhimmancin matansu da sanin daraja da tausayi ya fara kokawar bin hanyar garin da bai taba tunanin zaije shi tare da mace me daraja da kima kamar Raihan ba. Duk yadda ake zabga sanyi hakan bai hana wazer wata irin zufa ba,saboda yadda yake ta kokarin shiga ta hanyar da yasan ba zai cutar da ita ba,to amma da alama hakan ba zai yuwu ba dan kuwa Raihan tana daga cikin jinsin matan da mazajensu suke kiransu da yan baiwa,tausayinta ne ya kamashi ganin yadda kafin aje ko ina ta fara hada zufa sai faman girgiza kai take alamun dai tana shan azaba,har zai hakura sai kuma ya yi wani tunani to idan ma baiyi yanzu ba dole dai zaiyin kuma wannan wahalar ita za a kuma sha Gara kawai yayi gaba daya ya wuce gun ko itama raihan ta samu rangwame a gaba,dan haka kawai ya runtse idanunshi yasa karfi yayi me gaba daya duk da cewa hakan ma ba karamin wahala yasha ba ita tana kuka da yakushinsa shima yana kukan kauna kukan dadi kukan dace,saiga mutumin da yake lallabawa ya na neman manta komai dake cikin duniya harma da dan tausayinta da yake ji,yakushi kam da duka da cizo ya shasu babu adadi,maganganu kuwa babu abinda bata ce dashi ba,yan gidansu ma babu wanda bata kira ba, wallahi ba zan kara ba bazan kara yarda ba kuma sai na gayawa innawuro abinda kayi min ai dama ta ce komi kayi min da banji dadi ba na gaya mata", hamma wazer dama karya ne baka sona", kai maganganu dai kala kala haka raihananku ta dinga sakinsu. Janyota jikinsa yayi yana maida numfashi ga wani irin zazzafan zazzaɓi da ya rufe su gaba da yansu. Sai da suka dauki mintuna kusan sha biyar a haka sanann ya lallaba ya tashi yana haɗa hanya har ya shige bathroom,ruwa me zafi ya tara ba tare da ya zuba komai a cikinshi ba,sannan ya fita, ji tayi kawai anyi sama da ita a firgice ta bude idanunta da suka kumbura suntum,harara ta zabga mishi tana cewa Ni ka rabu dani ", bai kula ta ba ya shige da ita bathroom tare da sakata cikin ruwan,wani irin azaba taji wanda yasa ta tsala ihun da ba dan muryarta ta dasheba tabbas idan da makota a kusa zasu iya jita. Bai saurara mata ba sai da yayi mata ruwa uku zafafa sanann ya yi mata wanka ya tsaya akanta tayi na tsarki tana yi tana hawayen shagwaba dan zuwa yanzu kam ta samu relief. Tana gamawa ya bata brush ta yi sannan ta daura alwala duk da lokacin Sallah baiyi ba amma hakan yana da kyau kasancewa da alwala ko da yaushe,nadeta yayi a showel ya rungumeta ya fita daga bathroom ɗin,a hankali ya kwantar da ita saboda fahimtar da yayi har Baccin wahala da yar nutsuwar da ta samu ya fara daukarta,cikin hanzari ya saka mata doguwar rigar bacci me taushi da nauyi kamar rigar sanyi ya shafa mata turarukanta masu sanyi na humra sanann ya rufeta ruf ta ci gaba da baccinta cikin nutsuwa dan da alama dai Raihan jarumace ba za ta kasance raguwar mace a turakar mijinta ba,saboda ko dan zazzabin da ya rufeta tuni ya fara sauka. Sai alokacinne shima ya samu nutsuwar kimtsa kansa,a hankali ya shige bargon ya manne a jikinta tare da lumshe idanunsa yana jin wata irin nutsuwa da farincikin da bai taba samun kansa a cikinsu ba,lallai mace ta gari Rahma ce kuma cikon addini,shi kam ji yake ya kammala bashi da sauran damuwa ko matsala,hamdala ya shiga yi ga Ubangiji yana ambatan sunayensa tsarkaka cike da jin tsoransa da kuma sallamawa kudurarsa.. Yadda wasu suka yi Baccin farinciki wasu kuwa na bakinciki su kayi,kamar dai rabi a da idanunta suka kasa runtsawa kwana ta yi kuka,gashi bata da dabarar idan abu yameta ta tashi ta kaiwa Allah kukanta dan yaye mata ba,shi yasa sam bata samun sauki daga azabar son wazer da ya ke neman zamar mata cuta wanda zamu iya kiranshi da hakkin RAIHAN. Maganganun mahaifiyarta ne suka shiga dawo mata bayan ta bata labarin yadda ta dinga kokarin cutatawa Raihan ta ko wace hanya,(Kinga irin abinda nake gaya miki ke da mahaifinki ko? Gashi nan tun ba aje ko ina ba Allah ya yi wadanda kuka cuta sakayya,rabi a ki sani cewa gaskiya bata taɓa karewa sai dai karya ta kare tunda gashi taku ta kare ba tare kuma da Allah ya baku damar cimma burinmu na cutatawa bayin Allah ba,ga kuma abinda kawa ta yi miki duk wannan yana daga cikin ishara da kuma izna,dan haka ki farka daga bacci ki yi sauri tunda sauran damarki ki tsarkake zuciyarki ki zauna da kowa lafiya da kuma zuciya daya,domin dai Kinga yadda sharrinki yayi miki butulci tunda dama shi ɗan aikene, Allah ya rabamu da mugun hali da aikata aikin danasani) tana zuwa nan a tunani ta ta kuma rushewa da kuka tana jin dama baya ta dawo dan ta gyara abinda ta bata,( rabia shi Allah gafururrahim ne me jin kan bayinsane kuma me yin Rahma a garesu ne yanzu ma lokaci bai kure miki ba,zaki iya neman gafararsa tare da wadanda kika cutar,in dai har kinyi tuba irin wanda Ubangiji yake so to tabbas zaki samu salama).......✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page69 ``` Dakyar da lallama Raihan ta tashi daga nannauyan Baccin da ya kwasheta me dadi tare da mafarkai masu dad'i,da kansa ya kuma Kaita tayi alwala sannan ya Kaita wajen sallah ya ce", tayi nafila kafin a gama kiran sallah daga nan ya fita tashi sallar. Hajiya RAIHAN manyan mata ,tana idar da sallar ta yi addu'a ta kuma nadewa cikin duvet tana cewa Wallahi bazan iya zaman karatu ba,ta fada tana hawayen da basa yi mata wuya,bata jima da kwanciya ba ya shigo idanunsa akanta,akarosawa yayi ya dan ja duvet din da ta rufe har kanta yana cewa my angel tashi muje na kuma gasa miki jikinki saboda banaso kowa yazo ya sameki kina tale kafa kamar yar kaciya ", mikewa ta yi da sauri har bargon yana yin kasa saboda yadda ta bankadashi a fusace,cikin kukan da ya taso mata kukan shagwaba ta ce", hamma wazer kaciya kuma ta nawa ai Nima ita ka yi min", zama yayi a hankali gefanta fuskarshi na murmusawa da wani tattausan murmushin da idan ba Raihan ɗin ba babu macen da ta isa ganinshi,kama hannuwanta ya yi yana cewa sorry my hibban bazan kuma ba muga Ni wajen ko naji miki ciwo ", ya fada yana ɗorata jikinshi yayin da yake kokarin buda kafafunta,da sauri ta hade kafafunta ta matsesu tana cewa ba sai ka gani ba amma da ciwo a wajen, really ya fada cikin nuna mata serious din maganartata,hakan yasa ta kuma narkewa hawayenta na kuma gudu tana cewa yanzu baka so na tunda kamin mugunta ko? Girgiza kanshi yayi yana jin wani yanayi na saukar masa saboda yadda take masa magana a tabare wanda ita kuma bata san yanayi ba dan ita haka yanayinta yake a koda yaushe, sorry ya fada yana kai harshensa kan fuskarta a lokaci daya yana shanye hawayen da yake ta zuba,juyawa yayi da ita ajikinshi ya janyo duvet din da ta yar ya rufesu yana cewa tom shike nan tunda baki son ruwan zafin bari na fama ciwon in yaso sai ayi gaba ɗaya", kar ka fama min ciwo ta fada ba tare da ta fuskanci inda maganarsa ta dosa ba", Ey ba sosai zan fama ba, Duba Miki zanyi a hankali kinji yar albarka", Gyada kanta ta yi bakinta nayin shiru badan ta fahimceshi ba sai dan abunda ya fara yi mata a can kasanta,lumshe idanunta ta yi tana jin susar ko nace waiwayin da yake mata a gurin wanda jin dadi yasata lumshe idanunta tana jin abin har tsakar kanta. A hankali ya janyota jikinsa tare da dago fuskarta yana kallon zarazaran eye lashes dinta da su kayiwa idanunta rumfa ta sanadin rufesun da ta yi,saukar numin bakinshi kan idanun yajawo wata nutsatstsiyar ajiyar zuciya a gareta kafin ta dawo hayyacinta ta kuma jin saukar harshensa kan dan ƙaramin bakinta da yake dan rawa kamar wadda take son cewa wani abu,lasar labban yake a hankali cikin wani irin salo da zai tsaya a kwanyar yar gidan mami daga nan ya dinga gangarawa yana yin kasa har zuwa wuyanta da ya shiga yi masa wani irin lasa da kissess masu zafi tamkar zai cinyeta,yanayin yadda yake sumbatarta ta wata irin hanya ta tattali da tsananin kula yasa ta kasa dakatar dashi daga abinda taji yana shirinyi,runtse idanunta kawai ta yi tare da kamkameshi tamkar zata huda yatsunta ta cikin fatarsa,yanzunma dai babu wani banbanci da daren jiyan daga shi har ita sunci wuya,sai dai shi dadi yafi mishi yawa domin ji yayi tamkar zai cinye RAIHAN ɗin kowa ya huta. Ajiyar numfashi suke gaba dayansu,yayin da ita take yin kuka kasa kasa shi kuma tare hawayenta yayi da harshensa hawayen suna zuba akai hannunwanshi duka a jikinta yana shafata cikin tarairaya da so wanda bai da iyaka. Sai da suka dau sama da mintina goma sannan ya tashi yaje ya kuma hada ruwa kamar na jiya ya dawo ya dauketa cak,sai kawai jinta ta yi cikin ruwan zafi,kuka tasa wanda baya fita sosai saboda yadda muryarta ta dashe sai dai bata yi kokarin hanashi gasata ba,shi kuma haka ne ya bashi damar gasata sosai da kyau har sai da ta samu nutsuwa ta hanyar saukar da ajiyar zuciya da take ta yi akai akai. Sai da ya gama gasata sannan ya bata umarni da tayi na tsarki,tana cikin yi bata Ankara ba ta jishi cikin bap din,zaro manyan idanunta da suka kankance saboda kuka da bacci ta yi sai dai ta kasa cewa dashi komai,can gefe ta matsa har ya gama wankanshi na tsarki ya janyota jikinshi yana ƙoƙarin sabeta da soso da sabulu,nanma bata hanashi ba sai dai kunya me tsanani tasa ta kasa haɗa ido dashi,bata kalleshi ba har ya gama yi musu wankan ya daurayesu. Shiryata ya yi tsaf tamkar wata jaririya,cikin wani dakakken Les wanda a kiyasina zai kai dubu ɗari biyu blue ne da adon pich kadan wanda yayi matukar haska farar fatarta me kyau da sheki,a wajen daurine a ke yinta dan ya daura yafi sau biyar yana kuncewa,dariyar da take kunshewa ta saka sosai har da kyalkyalawa ganin yadda ya dage yayi kicin_kicin waishi dauri yake son yi,lumshe idanunsa ya yi saboda yadda sautin dariyartata ke shigarsa tana wani tsunkulinsa,ey dole yaji haka mana saboda dariyar ba dariya ce gama garin dariya ba,(duk abinda zaki yi a gaban mijinki ya kasance na musamman idan kika saba ba sai kin kirkira ba zai zama kamar halittarki ce ko acikin mutane sai kin zama ta daban saboda komai naki ya zama na daban kuma cikin nutuswa da aji me burgewa sam kar ki kasance me rawar kai a gurin mijinki kamewa da nutsuwa mace aka sani dasu ba wai maza ba,so be careful baby). Zama yayi gefanta yana ɗan kwabe fuska kafin ya ce", nury dariya kike min saboda bazan iya cike ladana na shiryaki ba? Girgiza kai ta yi a hankali ba tare da ta amsashi da fatar baki ba,haka ne mana", ya fada yana kallon cikin idanunta,sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta,kama yatsun yayi yana murzawa sannan cikin deep voice dinshi ya ce", mar atissaliha Allah ya miki albarka Allah yasa na baki yan biyu a daren jiya da safenann na kuma baki biyu Kinga yan hudu kenan zaki haifomin", zaro ido ta yi sai dai har yanzu bata ce komai ba baya ga amsa addu'arsa da take yi a hankali. Ey mana RAIHAN ranar da bansan ya zanyi saboda farinciki ba", Raihan me zan baki na faranta miki koda kadanne daga cikin farincikin da kika bani? Dago habarta yayi ya saka idanunshi cikinnata,a hankali ta shiga motsa labbanta tana cewa hamma wazer ka riga ka bani farinciki saboda kaine faruncikina kuma rayuwata idan har zaka ci gaba da kasancewa tare dani cikin ko wane irin hali shike nan Ni kam ka biya Ni ", shigar da ita yayi cikin faffadan ƙirjinshi yana cewa ba wannan ba saboda wannan batun ya wuce Raihan tun can Ni bako ne saboda ke Allah ya halicce Ni Ni mijinkine har aljanna dan haka nemi wani abu ba wannan ba", zagayeshi ta yi da hannuwanta da basu ritsashi ba tana cewa bani da wani buri ko farinciki sai wannan zauji ina sonka", sumbatarta yayi a saman goshinta sannan yace ",, duk da haka kina da tukuici tashi muje tun dazun innawuro ta aiko da breakfast", tashi tayi yana rike da hannunta har suka isa falo ya karasa da ita daning ya zaunar da ita ya zuba musu komai a plet daya hatta da ruwan tea a cup daya ya haɗa musu,kana ya dawo ya zauna ya shiga ciyar da ita. ____________ A gaban Rabia innawuro tasa aka tafi kaiwa su RAIHAN breakfast,wadda ta yi sammakon zuwa don bada hakuri,sai kuma ta samu ashe ba a gidan suka zauna ba kamar yadda take tunani. Hakuri da nasiha shine abinda innawuro ta fara yi mata kafin ta dauki takardar sakinta da wazer ya bayar a bata,ta bata,kuka rabi a tasa yayin da ta gama duba takardar tare da zubewa kasa tana rokon innawuro akan ta yi hakuri tasa baki Wazer ya maida ita tayi alkawarin cewa zata gyara halinta za kuma ta zauna da Raihan lafiya da zuciya ɗaya,girgiza kai innawuro ta yi sannan ta ce", Ni kam nayi na farko dan haka ba zan kuma ba,sai dai ke kije da kanki ki rokeshi idan har yaga zai iya to sai mu yi muku addu'a da fatan zaman lafiya amma Ni kam babu Ni cikin wannan", daga haka ta mike ta bar mata falon tana ci gaba da kukan nadama da ya ki karewa. A bangaren Surry kuwa dakyar yayanta ya hakura suka tallafa suka Kaita asibiti inda aka fara yi mata treatment din gaggawa saboda yadda gabanta ya rube,karshe dai dole sai da aka kai ga yin aiki wanda ya ci kudade,inda Allah ya taimaketa yan uwanta suna da rufin asiri sannan itama tana da kudaden da ta tara na wajen oganta,to Allah ya taimaketa anyi aikin lafiya daga yau din kuma zata ci gaba da karbar magani. Kaf yan biki na nesa dana kusa haka aka saka su a mota dan gano dakin amarya daga nan kuma su wuce AGADEX,duka wazer ne ya dauki nauyin komawarsu ta hanyar siya musu tiket. Tarba me kyau suka samu daga wajen wazer da RAIHAN saboda duk da cewa Wazer miskiline amma bashi da wulakanci yana da son mutane idan ka fahimceshi, bare kuma Raihan da dama ita din ta mutanece yan uwan mahaifiyarta sosai suke ƙaunarta,tana da kyauta kuma tana da son yan uwanta,haka suka samu kyaututtuka daga wajen Raihan da mijinta kai hatta da Ammi da innawuro da Abbu sai da suka samu kyautar su,haka suka tafi suna san Barka tare da yi musu fatan alkhairi dan kuwa Dukansu sunyi dace da samun surukai na gari daga Raihan ɗin har wazer ɗin abinda suka tafi suna fada kenan. A ranar rabi a bata je gidansu wazer ba gida ta koma da niyar gobe ta je,amma da ta koma sai mamanta ta hanata acewarta ko wazer ya maida ita ba za ta taba yin daraja a idanunsa ba dan haka kawai ta hakura,Rabia dai ba dan ta hakuran ba ta yi shiru sai dai tabar niyarta na zuwa a kusa sai zuciyarsa ta yi sanyi. Hankula sun kwanta ko wane vangare ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali. A bangaren wazer da Raihan kuwa babu abinda zan iya ce muku sai alhamdulillah Masha Allah,a yau da suke samun kwana biyar da tarewa tuni Raihan ta ware ta samu cikakkiyar koyarwa daga malaminta mijinta abin alfaharinta,duk abinda tasan zai faranta masa shi take yi,duk da cewa Raihan tana daga jinsin mata yan baiwa sam hakan baisa ta nuna gazawarta ko nuna gajiya da mijinta ba,duk sanda yake bukatarta zata karbeshi da farinciki ba tare da bata fuska ba,takasance me juriya a shimfidar mijinta wannan abu yana daya daga cikin manyan dalilan da suka kuma ɗaga darajarta a idanun wazer,ji yake babu ya ita a duniyarsa ta riga ta mallakeshi ba tare da boka ko malam ba. Soyayya suke zubawa kamar babu gobe ,babu abinda suke kallo sai junansu,komai tare suke yi har girki tayata yake idan tace ya bari sai yace Raihan wannan koyarwa ce ta Ma'aiki ya kasance yana taya matansa aikace aikacen gida dan haka ki bari Nima na samu ladan", da haka yake kashe mata baki,tana wankewa yana mata dauraya ko yana yanka mata wani abu. Raihan Sarkin tsafta kullum sai ta yiwa gidanta tsafta ta musamman wadda ko da zata yi kwana biyu bata taɓa shi ba ba zai canja ba, wannan horone ta samu daga maminta sam bata hori Raihan da san jiki da nuna gata da so mara amfani ba,kar dai ku manta tun tana namijinta a haka maminta take sa ta aiyuka da girke girke har Hajiya goggo ta yi ta fada akan ta maida Rahim namiji,shi yasa a yanzu mami take bacci har da minshari saboda tasan ta nunawa yarta karshen gata ta bata horon da sam ba zata bata kunya ba, wannan kenan. Yau Litinin ranar da tai daidai da cikar Raihan da wazer sati daya da tarewa,kuma ita ce ranar da za a saurari shari'ar su Abba yahya da hamma Idris. Tun sassafe mutane su kayi dandazon cika kotun sabida ma kar wani ya rasa wajen ganin idanun alkali da irin hukuncin da za a zartar musu. A bangaren RAIHAN tunda ta tashi take shiri cikin sauri ta yi ta gama komai saboda zuwa cotu,duba agogo ta yi bayan ta gama shiryawa cikin wata exclusive atamfa me shegen kyau tayi daurin zara Buhari ,kamshinta kuwa tuni ya isarwa wazer dake baccinsa hankali kwance. Fita ta yi daga dakin da ta shirya zuwa dakin da suka kwana,taku take tamkar wata dawisu kamshin kabbasa da na turarukan da take amfani da su kuwa babu magana fuskarnan sai sheki take tana glowing kamar ka kalli kanka a cikinta,turus ta yi ganinsa da tayi kwance dan a tunaninta tuni ya tashi saboda yau guduwa ta yi ta shirya ita kadai idan ba haka ba shiririta zasu yi ta yi wajen shirin har a tashi a Shari'ar,kugu ta rike tana cika baki da iska kafin ta tako cikin nutsuwa tazo daidai kansa ta zauna,hannunsa ta fara kamawa kafin ta shiga yi masa massege a hannun,ganin yaki motsawa sai kawai ta sauko kasan gadon tare da rankwafawa ta hade bakinta da nashi tana tsotsa,caraf ya cafke jin ya farka yasa ta fara kokarin zare bakinta amma ina hakan ya gagara dan ɗan gidan Ammi ya ce", bai san zancen ba", tarairayota yayi jikinshi ya ja duvet yana cewa yauwa yar albarka kamar kinsan bannkoshi ba", zaro ido ta yi kafin ta kwace bakinta cikin marairaice fuska ta hade hannayenta biyu alamun roko ta ce", pls hayatnur kaga fa na shirya kaima ka tashi ka shirya kar a gama Shari'a ",waya ce miki zan bari ki shiga cikin maza eye? Ya fada yana ci gaba da bata sumba da kisses ta ko ina ba tasamu damar amsa masa ba,ko nace bai bata dama ba ya shiga bata zazzafan kissess masu rikita kwanya dole yar gidan Abbie ta yi gum saima taimaka masa da ta shiga yi dan ya samu nutsuwa,yadda Raihan ke tafi da mijinta a shimfida abin ba acewa komai duk wani salo da ya koya mata sai ta fishi kwarewa duk abinda ta fuskanci yafi so shi take yi masa, daga nan labarin ya sauya wannan sirrinsune Raihan ta rufe min kofa dole na hakura na fito. Sai da suka gama shiryawa Raihan ta daga kai ta dubi agogo take ta kwabe fuska tare da neman guri ta zauna dan tasan zancen zuwa kotu ta tashi daga aiki kamar yadda ya fada. Zama yayi kusa da ita yana cire mata tagumi tare da cewa bari na kunna miki kigani ", daukar remote control yayi ya kunna ƙatuwar plazima da ta kusan cinye rabin bangon. A can bangaren kotu kuwa, anyankewa abba Yahya daurin rai da rai shida dansa,shi kuma Idris anyanke masa shekaru biyar tare da tara ta miliyan biyu ba tare da beli ba,inna maimuna kuma anyanke mata zaman kaso na shekara ashirin da biyar tare da tarar miliyan uku ba tare da beli ba. Take kotu ta tashi jama a kowa ya yi shiri kamar yadda suka shirya,ana fitowa da su Abba yahya dan shiga mota ai sai jin saukar ruwan duwatsu su kayi akansu,duk yadda jam'i an tsaro suka so hanawa abin ya faskara barkonon tsohuwa da harbi kuwa babu abinda ya yi musu,inna maimuna ma da Idris sai da suka samu rabonsu,da dai jami'an tsaro suka ga suma abin yana shafarsu sai kawai suka bawa mutane waje suka ci gaba da jifan Abba yahya da Bashir,inna maimuna da Idris dai sun bari an shiga dasu mota,yadda su kayiwa Abba yahya da Bashir abin babu kyan gani tuni ido ɗaya ya cire na Abba yahya Bashir kuwa karaya fuskarsu ko ganuwa ba tayi saboda yadda ta ɓaci da jini faca faca ( dama ai abinda ka shuka shi zaka girba) Rabi a kuwa tuni ta faki idon mama ta fita daga gidan dan zuwa gidan wazer isar da sakon zuciyarta? To ko wazer zai karbeta ?😂 Fatima y adam..... ✍🏽 *Typing* 💕 *BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ```Page70 ``` Kawar da kanta daga kallon ta yi lokacin da ya kunna saboda daidai lokacin da ake jifansu Abba yahya ne,shi dinma runtse idanunshi yayi cike da alhini da tausayin yadda karshensu yazo,kashewa yayi yana matsawa jikiinta Kamota ya yi tare da tara hannunshi akasan habarta saboda yadda hawayenta suka fara gudu, sorry my friend addu'a zaki musu Allah ya sassauta musu amma banda kuka", jinjina kai ta yi tana shigewa jikinshi,ehem Madam garama da baki je ba Kinga anjima sai muje gida muyiwa su Hajiya goggo jaje ko? Da sauri ta daga kanta cike da murna ta bashi kyakkyawar sumba a kuncinshi sannan ta sakeshi ta mike da sauri ta bar falon,Binta da kallo yayi kafin a hankali ya lumshe idanunsa da basa gajiya da kallonta. Dakyar aka samu aka dakatar da jama'a sannan aka kwashe su ba tare da tunanin zuwa asibiti ba,kai tsaye gidan yarin aka nufa dasu wanda sai acanne aka basu gado a sashen asibitin gidan,ba dan a na zaton musu rayuwa ba. Jama a suna kokarin fashewa sai ga tsohuwa me jini ƙatuwar mesarnan ta kawota cikin tsakiyar mutane dan su kara rage haushinsu,kai abun babu kyan gani gaba daya ta dagargaje amma dake Allah yana son nuna izna sai yabarta da ranta duk da yadda ta koma din yaci ace ta mutu inda ana dawowa ma to yaci ta mutu sau goma ta dawo,numfashin da take fitarwa shi kansa wani irin hucin zafi yake yi,gaba daya fatar jikinta ta kwaile gashi babu kafa babu hannuwa gaba daya mesar nan ta cinyesu,idanunta kuwa ras sai fuskar da ta yagalgale tayi wani irin rashin kyan kallo. Har mutane zasu fara guduwa sai suka ji wata mata tana cewa wannan fa ita ce annamimiyar tsohuwa me jini da ake kaimata sassan jikin yayanku dan haka itama ku karasata ko kwa kara rage radadi ", aiko take mutane suka fara yi mata ruwan dutsuna wani dutsen ma yafi karfin hannuwansu amma haka suke dauka su jefa mata,tuni su Dady da Salim wakilan tashar Chibado FM suka fara kwasar labarai harma da sauran yan jaridu masu jiran kiris. Kafin kace me tuni an dagargaje kan tsohuwa yayi kwatsa_kwatsa a gurin tamkar an saka shi a turmi an daka,(kai Allah Ubangiji kasa mu dace ka shirya mu kasa muyi kyakkyawan karshe Amin ya rabbil alamin 🙏)a hankali mesar nan ta juya ta silale tabar cikin mutanen bayan ta tabbata tsohuwa tayi irin mutuwar da take ganin ita ce ta dace da ita(wannan mesar daya daga cikin jinnun da tsohuwa ta cutar ne ta hanyar korarsu daga tsibirinsu ta gaje shi ita da mukarrabanta ne,ba iya mutane kadai mutanen nan suka dau hakki ba harda jinsin da ba namu ba bayin Allah da ba ruwansu da kowa rauhanai). Wannan abu da ya faru tuni ya kuma baza garin baki daya har da wasu garuruwan ma abinka da social media,sosai mutane suka ji tsoron Allah akan abinda ya farun dan kuwa abu ne da bai taba faruwa ba ko a labari shi yasa ya zama izna da tsoratarwa ga masu son zuciya masu ragowar imani wadanda basu riga sunyi zurfi ba kuma wadanda suke da rabon shiryuwa,to Allah ya kara shirya mu damu da zuriarmu baki ɗaya. ___________ Yana nan zaune tunda RAIHAN ta gudu, laptop ce kawai a gabanshi yana posting din wani labari akan shafinsu na tree full y truest,danjar dake nuna cewa da bako a waje ce ta kama haskawa, ɗan dafe goshinsa yayi tare da juyawa yana kallon kofar kafin ya janyo remote din security cord din kofar ya latsa saiga shi wanda ke wajen ya samu damar shigowa ,bai damu da sanin ko waye ba dan ya riga da yasan cewa dole yanzu zasu dinga baki a kai akai. Rabi a da take ta kallonsa tare da gidan gaba ɗaya ta fara takowa tana ji kamar ta rungumeshi tayi ta kuka a jikinshi,wani irin kyau taga yayi na musamman kalarnan tashi me kyau ta kuma haskawa yayi yar kiba wadda tasashi yin dan tumbin da ya yi matukar yi masa kyau, lafiyayyan gemunannashi sai kyalli yake tare da dan siririn sajenshi da Raihan bata gajiya da gyara masashi,ji yayi gaba daya ya takura saboda alamun ido da yaji a jikinshi,hakan yasashi dan Dagowa fuskarnan a kame wato dai asalin kamammen wazer miskilin nan dan gidan Ammi jikan innawuro ba wai wazer mijin Raihan bawan Raihan ba. Ai tuni rabi a ta zame kasa kafafunta har rawa suke yi bakinta kuwa tuni ya shiga karkarwa. Meye ya kawoki ? Haɗe hannunta ta yi bakinta na rawa idanunta na zubar hawaye ta ce", dan Allah dan kaunarka da Ma'aiki dan girman zatin Allah hamma wazer ka dubeni ka maida Ni dakina wallahi na yi karatun ta nutsu na sauya halina zan gyara duka kuskurena dan Allah ka maidani kaji", Dama kina da daki a nanne? A'a amma ko canne gida zan cigaba da zama", To bani da wannan ikon", Kuka ta saka tana ci gaba da yi masa magiya. Rabi'a", Ya kira sunanta wanda yayi daidai da fara takun RAIHAN daga saukowa downstairs, Duk da yadda sunan ya daki zuciya da ƙwaƙwalwarta hakan bai hanata ci gaba da takunta cikin nutsuwa da burgewa ba, Wata halitta ce ta musamman a gareshi me tsananin ado da kawatarwa, ɓoyayyiyar Raihan ce hakan yasa duk sanda ta yi ado da wani abu sabo na mata sai ta kusa zaunta bawan Allah dan Ammi da Abbu,shi kam zai iya cewa bai taba sanin da akwai halittar da kananun kaya suke yiwa kyau fiye da kowace mace a duniya ba sai yanzu da RAIHAN dinshi ta sako,me yasa kome ta saka sai yaji kamar ba a taba saka irinshi a duniya ba? Kasa ci gaba da jurar zama yayi dan haka ya mike tsaye idanunshi na cigaba da karade lungu da sako na jikiinta da kallo,sanye take cikin wata karamar riga me haɗe da bra hannunta dogone amma kalarshi kalar fatar jikiinta ne hakan yasa baza ka tantance ba har sai ka taba,jikin rigar kuwa dack brown ne wato copy,sai wandon da ya kasance kalar jikiinta shima amma Dan gajere ne kuma ya kamata dan haka sai tayi kamar bata saka komai ba,gashinta kuwa wani irin ado tayi masa daga gaban goshin sai yayi wani irin kwanciya tsagar ta fito rada rada,sai ta raba shi biyu tayi masa two baby's ta kuma kitseshi daga karshen jelar ta saka masa karamin rebom baby pink,sai ta zama kamar irin yaran Larabawannan masu waka,lip balm ta saka shima baby Pink,Masha Allah tubarakallah karshen kyau matar Ahmad wazer tayi shi. Jiran karasowarta yake amma sai yaga kamar ma komawa baya take yi,sai kawai ya shiga takawa dan tarota,falon kuwa tuni kamshinta da nasa ya zauna a ciki daram ga kuma wanda ake yi na turaren wuta wanda shima ya zauna Kamar a lokacin ake yinsa,fuskarta babu yabo babu fallasa suka hade da wazer da yaje tarota,basarwa ta yi cikin wani aji da bata taba sanin tana da shi ba ta bude baki tare da cewa hayatnur wac....bai bata damar karasawa ba ya haɗe bakinsu guri daya ya shiga maida mugun yawuun da ta tsinka masashi yake tafiya babu doka bare oda, Zaro ido ta yi tana son nuna mishi akwai baki fa a falon,amma ina shi tuni yayi nisa dan har ga Allah ya manta da wata Rabia a gurin,sosai raihan din ta tafi da imaninshi ta riga ta gama tashin kansa tuni komai ya kwance masa", Rabi a kuwa sunkuyar da kanta ta yi tana share hawayenta,bata taɓa tunanin wazer zai iya yiwa mace irin wannan soyayyar ba sai gashi ta ji ta kuma gani da idanunta,duk da cewa zuciyarta ta karaya amma sai taji ta kasa tafiya wata zuciyar ta ce ki kama kafa da Raihan ɗin wata kila ya amince,take ta ɗan samu kwarin gwiwa da wannan shawarar da zuciyarta ta bata. Dakyar RAIHAN ta dakatar da babynnata daga kokarin zarcewa da yake dan har ya fara cusa hannunsa cikin rigarta yana ƙoƙarin yi mata aika aika gaban idon baƙi. Tsaf ya haɗe fuskarnan ya kuma dinketa tamkar bashi ya gama tsotse Raihan ɗin gabanta ba,sai da suka dawo cikin falon sosai sannan ta tabbatar da rabi an ce ba wai jin kunne ta yi ba,fuskarta ta saki cikin murmushin karfin hali ta ce", aunty rabi a ce sannu da zuwa", Sai a lokacin rabi a ta kuma samun kwarin gwiwa,dan haka ta dan muskuta tana cewa nice Raihan ya gida da amarci?wazer ta kalla tana dan kashe masa ido ɗaya tare da langabar da kai wai ya bawa Rabia amsa ita kunya take ji", bai kalli rabi ar ba sai dai hankalinshi gaba daya yana kan Raihan fuskarnan tashi babu fara a ko digo dan baiyarda wata mace taga fara arshi ba bayan RAIHAN. Bari a akawo miki abin tabawa", A'a ki barshi a koshe nake", Kawai dai kice bazakici girkin yara ba", Raihan ta fada har yanzu da murmushi akan fuskarta,girgiza kai rabi a ta yi sananan ta yi gyaran murya tare da marairaice ta ta ce", Raihan ko zaki tayani bawa hamma wazer hakuri akan ya maida Ni dakina dan tuni na riga na tuba bazan kuma bari shedan ya yi min kida ba", Ɗan jim Raihan tayi(kar ku manta Raihan bata san wazer ya saki rabi a ba)duk da cewa ita kadai tasan yadda zuciyarta ke kida to amma ba ta bari rabi a ta gane ba (ta koyi darasi tun lokacin da Rabia ta dinga yi mata wulakanci da karya akan wazer saboda nuna mata kishinta a fili da ta yi) Rabia wannan maganar tsakaninku ce ba tawa ba ce, saboda aurenki ba a hannuna yake ba a hannunsa yake", ta karasa fada tana kokarin mikewa dan basu waje,kamar ya fahimci abinda take shirinyi dan haka ya yi saurin rike hannunta tare da girgiza mata kai alamar kar ta tafi", duban rabi a r ta yi sannan ta dubeshi ta bude baki zata yi magana ya janyota ta wado jikinshi yasa hannunshi yayi mata rumfa yadda ko hangota baka iya yi a cikin faffadan ƙirjinshi. Zaki iya tafiya saboda ina da bukatar privency ", Ya fada fuskarnan kai kace bai taba yin murmushi ba,nan ko idan ya samu guri da yar raihananshi harda su dariya. Dan Allah hamma wazer kayi hakuri", ta kuma fada cike da nuna naci irin na mata marasa aji. Kije zanzo gidan", Ai tuni RAIHAN ta yi wata irin zabura zata tashi, take kuma ta tuna cewa har yanzu fa rabi'a matarshice,komawa ta yi ta kwantar da kanta yayin da ya shiga sara mata ƙirjinta kuwa tuni ya kasa jura ya fara yin sama da kasa tamkar numfashinta zai fizge,sosai take kokarin danne azababban kishin da Allah yayi mata mai tsananin zafi,to amma kamar hakan gagararta yake son yi. Ita ko rabi'a cikin jin dadin maganarshi da bata yi zato ba ta mike tana cewa shike nan ina jiranka Allah ya kawoka," bai kulata ba bare ta sa ran samun amsa daga bakinshi. Tana fita ya dago fuskar RAIHAN wadda yaji ta shiru ta daina mutsu_mutsun da take yi. RAIHAN ", RAIHAN", Ya shiga kiran sunanta a dan ruden da ba a cika ganewa akan fuskarshi ba,a haka baza ka taba tunanin cewa a tsananin tashin hankali yake ba,amma shi kadai yasan irin gudun fanfalakin da zuciyar take yi saboda ganin idanun Raihan a kafe numfashinta kamar ya tsaya. Kwantar da ita yayi ya nufi karamin Fringe dake falon ya dauki ruwa ya dawo,shafa mata yayi a fuskarta cikin kankanin lokaci taja wani irin dogon numfashi idanunta suna dai-daituwa akan fuskarshi. Me ya faru? Me ya same ki lokaci guda haka? Babu ta fada tana tashi zaune tare da kawar da fuskarta,dan dube dube ta shiga yi wanda hakan yasa ya harbo jirginta,ey yasan Raihan tun can tana da kishi amma bai yi zaton abun ya kai ga haka ba,juyo da fuskarta saitinsa ya yi sannan ya haɗesu har karan hancinsu na gugar juna,a hankali kuma cikin nutsuwarnan tasa ya ce", me ne kike haka Raihan? Suma fa kikayi saboda kishi? To yanzu da ace ban saki rabi a ba ya za ayi ke nan? Da ace ƙaddara ta ratsa miki zama da kishiya yake nan? Pls Raihan ki sassauta saboda bamu san inda kaddararmu zata tsaya ba, bamu san abinda gobe zata yi ba,dan haka Kinga bamu da tabbacin zamu yi rayuwa iya mu biyu har abada,Ni a lissafina babu batun zama da mace biyu amma ban san ya gobe zata kasance ba,shi yasa ba zan miki alƙawarin zama dake ke daya ba duk son da nake miki kuwa,domin idan nayi haka tabbas na cutar dake." Kuka take yi kasa kasa,tabbas maganganunsa haka suke kuma shine daidai akan duk namijin da yasan kansa ya kuma san ƙaddara yasan cewa tsarin rayuwarmu ba a hannunmu take ba. Raihan na bata miki rai ko? Bakya son kishiya ko? Kin fi so nayi Miki alƙawarin zama dake ke daya ko? Girgiza kai ta yi sananan cikin sanyin murya ta ce," a'a idan son zuciya zamu bi haka nake so ,amma idan muka ture batun son zuciya ba haka nake so ba,Nima banson wannan kishin nawa yana takura min hayatty bani na sawa kaina ba ina kokarin dannewa amma hakan ya gagara kayi hakuri bazan kuma ba", Rungumeta ya yi cikin so kauna da wani irin tausayi sannan ya ce", no habebty ba laifinki na gani ba,kawai nayi abin da ya kamata ace ko wane namiji ya yi ke nan,akwai manyan dalilan da suka saka na rabu da rabi a daya daga ciki shine wallahi Raihan duk na sake na hadaki da wata mace to tabbas zan iya tashi ran alkiyama da shanyayyen barin jiki domin bazan iya adalci ba, wannan bayanan ina yi miki su ne saboda ba a hannayenmu kaddarorinmu suke ba,Kinga bamu san abinda gobe zata yi ba,tunda komai yana wajen Allah assamadu lamyalid walam yulad," hayatty na fahimce ka maganarka gaskiya ce ko Nima zan iya samun sauki ta hanyar wannan kalaman naka da kuma addu'a daga bakinka", in sha Allah habebty,ya fada yana daukarta da cewa muje na bada tukuicin wannan kwalliyar,dariya tayi me sanyi zuciyarta na yin sanyi da samun miji irin wazer alhamdulillah ta fada a fili, ya amsa da Masha Allah daidai lokacin suka rufo kofa. Washe gari aka yankewa abban rabi hukunci shida makarrabansa,sa arsa daya angano Khalid da ya gudu saboda shi,shi yasa ya samu sassauci ta hanyar yin shekaru ashirin a gidan yari suma yaran nasa haka duka aka yanke musu hukunci, suka tafi suna kukan nadama da rokon yan uwa gafara. Su Abba yahya kuwa sai dai muce Allah kyauta makwanci domin kwanansu biyu suka ce ga garinku nan, Surry ma ta samu sauki ba laifi, sun dawo gida a nan ne mahaifinta ya bada ita ga wani almajirinsa wanda shi da kansa ya ce yana so, dan haka ya bashi ba tare da wani ja ba,ita ma haka ta hakura saima godiya da suke masa saboda taimakonta yayi,rayuwa ke nan Allah yasa mu dace", Rabi a kuwa haka ta gaji da naci ta hakura dan daga karshe hanata shiga gidan yasa a yi har office dinsa saida ya hana a hanata shiga,dole taga uwar naki ta samu ta daidaita da wani dattijo me mata uku ita ce ta hudu aka lallaba aka kaita ta fara zaman hakuri,(kin kasa yin hakuri da daya gashi yanzu kin kare da uku) dama haka rayuwar take. Yusuf ma tuni ya kai kudinsa aka sa masa rana da shukra duka za a hada auren da yayyayenta, jiddo khalil zai aura abu ya koma auren gida Masha Allah,zumunci dai ya kuma kulluwa tsakanin gidajen biyu,sai fatan Allah ya dorar da zumunci Tare Da farin ciki. Su Raihan sarakan soyayya tunda ta samu ciki take shan tarairaya Baga wazer ba Baga innawuro ba Baga Ammin da maminta ba,kai hatta hajiyar agadex sai da tazo ta zauna wai renon ciki,amma ko kwana uku bata yi ba ta tsere saboda taɓarar Raihan da yadda yake biye mata ko kunyarta basa ji dole ta bar musu gida. Komai yayi farko yana da karshe,daidai lokacin da aka yi bikin su shukra a lokacin ne kuma Raihan ta sunkuto kyawawan tagwayenta masu kama da wazer kamar an tsaga kara,ba sai nace muku komai akan shagali da murnar da akayi ba,yara sunci sunan Abbu da Abbie saura Ammi da mami cewar wazer, Anyi zabe kuma his excellency ya lashe sai dai fatan nasara a rayuwa,dama duk wanda ya rike gaskiya zai ta ganin daidai a rayuwarsa Allah ya bamu ikon kwatanta gaskiya. Gidajen uku sun hade sun zama tsintsiya madaurinki daya babu mai jin kanmu,tamkar wani mummunan abu bai taba faruwa ba. Raihan kam ta kama wazer yadda ya kamata,ta hanyoyi masu dama wa'danda na lissafa kadan daga cikinsu,tare suke tarairayar junansu suke tattalin junansu ,ko fada su kayi basa nisan zango suke shiryawa saboda sun san kansu kuma sun fahimci junansu sun san halin junansu,ga yaransu abin sha'awa suna tattalinsu ta hanyar da ta dace duk da cewa basu cika zama gidan ba. Tsaye take bakin madubi tana gyara dogon gashinta,shigowa yayi cikin kamalarshinnan da sallama bakinshi,amsawa ta yi tare da mika mishi brush din da take gyara kan", karba yayi fuskarshi cike da wani irin Murmushi dake nuna cewa yana cikin farinciki,ya ce", yarinya tasa komai na iya kamar wata mace harda su girki,kasancewar daga kiching yake", tura karamin bakinta ta yi tana cewa ai kaine kace babu abinda zanyi saboda kar yayanso su jigata Bama Ni ba", zagayeta yayi da hannayensa yana shafa dan cikinta da ya fara tasawa insha Allah yan biyu zaki kuma haifa Ammi da mami ke nan", Amin ta amsa tare da juyowa ta kama fuskarshi ta sumbaci labbanshi sannan ta ce", tunda Ammi ta kwace wadancan dole muyi addu'a mu samu wasu", su dinma na Mami ne", ya fada yana kissing bakinta, ok haifa musu za mu tayi muna basu? Arzikin ke nan my angel nets kuma sai mu rike ko? Bai bari ta amsa ba ya dauke ta cak ya dora bisa gadon yana cewa zo kiji wata magana sirrice bana so Fatima y Adam ta ji bare ta je ta cigaba da bazamu a duniya mu rufe kofa lada ya isa haka ,a barmu mu huta,daga haka ya rungume matarshi yana cewa Allah ya yi miki albarka RAIHAN alhamdulillah da samun mace ta gari,Masha Allah da samun miji na gari ta fada tana rufe su da bargo, Nima fitowa nayi cikin jin kunyar kamani da su kayi ina satar labarinsu,to nima dama na gaji alkur,an Masoyan ɓoyayyiyar Raihan ko nace masoyana ina yinku ina muku sonso alherin Allah ya kai muku a duk inda kuke. Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Allah ya yafe mana kurakuren da mu kayi ya bamu lada akan daidai sai mun hadu netx book WASU ALƘALAN...✍🏽