[1/10, 11:05 AM] Nordin: *JIRWAYE....* *DAGA ALK'ALIMIN NABEELA DIKKO* *AUREN DOLE!* _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM..._ *Shimfid'a:Da farko dai Aure shi ne Alak'ar zaman tare tsakanin namiji da mace,A bisa yardar juna da Amincewar Dangi,Ta hanyar cika wasu ka'idoji,Na Al'ada da Addini.* *Shi kuma Auren Dole:Shi ne tilasta yaro ko yarinya auren Wanda kowa acikinsu baya so,ko kuma baya kauna mafi yawa iyaye da kakanni ne ke tilasta shi."* *SHAFI NA D'AYA* "Zaune take a gaban kakanta, mallam Buba mak'eri,Banda k'arajin kuka ba abinda takeyi!" "A fusace mallam Buba,Ya ce "Kinji dai na gaya maki...Wato ke gaki gagarau Ma'u!"Ni zan gindiya sharad'i kice ki shure ki wuce!"Saboda kin raina ni,Ke da muguwar uwarki!"To daga ubanki!Har uwar taki nafi karfinsu!"Aure ba fashi!Ko da ki amsa ki yarda kiyi Auren soyayya ko kuma ki karbe shi a matsayin *AUREN DOLE*" "Cike da firgici!Ta dago kanta!Tana kallon Baba mallam(Kakanta)Hawaye ke zuba a idonta kamar an bud'a famfo!" "Rik'e kafarsa tayi tace "Dan Allah kaka kayi min rai!Wallahi na tsani tsohon nan yafa tsofewa Babana!"Ka taimake ni!Ka had'ani da wani Kaka....!" "Marin da Kaka ya watsawa Ma'u ne ya katse maganarta..."Tasbahar da ke hannunsa ya dinga zuba mata ta ko'ina!"Kururuwa!tah ta fito da ilahirin jama'ar gidan mai d'auke da lungage..."Suna kallon Ma'u da ke kuka!Babu halin cetontah!"Saboda gudun b'acin ran Kaka." "Ta da muryarsa yayi sosai!"Ya ce, Yoo....Duk gidan nan akwai mai yimin musu sai ke!Ma'u to kinci gidanku kin qara tunzura ni nadawo da ranar aurenki kusa,idan yaso ki mutu agidan Alh.Kalle nafi farin cikin hakan da in barki ki auri shashashan yaron nan da kike so Kamalu!"Me yake da shi!me ya ajiye ke in kinsan asalin talaucin su baki kaunar ki aure shi!Saboda talauci n su na gadi ne!A jinin su yake..!" "Ma'u tashi tayi cikin kunar rai!Ta nufi sashen su jikin Innarta ta fad'a tana rusa kuka!"Kamar ranta zai fitaa!" "Kaka ahasale ya bar kofar dakinsa da ke gabas din gidan...butar da yasamu ajiye a hanyar fita waje,yayi shuri da ita,yace munafukan banza!To ku koma tsayin me kukeyi anan!?"Yana hararar sarakunan nasa da suka fito gulma.."Sum-sum kowacce ta fice sashenta domin sun San kaka sarai da masifa!!!" "Lami ta kalli 'yartah rai!Babu dad'i!"Ta ce Kiyi hak'uri Asma'u ki yarda da zab'in Baba mallam shi ne mafita agare mu,kinsani sarai ni ko Babanki bamu isa muja da shi baah!" "Duk gidan nan ba mai karya dokarsa!Kar ki bari zuciyarki ta rud'eki akan ki karyata,Ki barwa Allah komai!Kin sani sarai, " *AUREN DOLE* A gidan nan Ba akanki aka fara ba!Bare ak'are kanki!" "Asma'u ta tashi zaune,Ta kalli Inna tare da kama hannayenta,Ta ce"Yanzu Inna kuna kallo Baba mallam zaiyi min *AUREN DOLE!?"* Saboda yana son cimma wata manufa tasa!"Tare da kwad'ayin Abin Duniya!" "Wallahi na tsani!Alh.kalle,Inna bana sonsa,ba zan iya rayuwa da shi ba!Yafa tsufa!Yaransa duk sun girmeni!"Aure na zaiyi kawai, saboda budurwar zuciya!Da son zuciya!"Shi ne ya zubawa kaka kud'i domin yabashi Ni,A dole!"Shin meye haka!Addini ko Al'ada!!?"Na rasa amfanin wannan baqin aure da ake mana agidan nan......Wani Sabon kuka!Asma'u ta ke rerawa...."Inna Lami ma hawayen tausayi 'Yarta ke zuba a kyakkyawar fuskarta,Tare da cigaba da rarrashin Asma'u,da ido yayima luhu-luhu saboda kukaah!!!!" [1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA BIYU* *ALK'ALAMIN NABEELA DIKKO* "A cikin jihar kebbi akwai wata qaramar hukumar mulki da a ke kira Argungu,"Babban gari ne,Mai cike Al'umma,Ga su da manyan yan boko maza da mata,kuma ma'aikatan gwamnati ne a kowanne fanni,Bugu da qari Albarkokin Allah sun yawaita A garin,Domin Allah ya albarkace su da manyan rafi masu dauke da Kifaye naji, na gani na fad'a,kuma mafi yawa daga cikin su asalin su D'aya ne akwai Kabawa,Lekayawa,Fulani,Zabarmawa da kuma gobirawa, noman shinkafa,da kayan lambu ne,da na masarufi sune Ayyukan su,Mutane ne masu rik'e da Al'ada ko kuma sana'ar gidan su ta gado!"Argungu gari ne na kabawan Asali wad'anda sukayi fice ciki da wajen Nigeria."Akwai cigaba mai yawa da suka samu,sunyi suna dalilin bikin kafun kifi(Fishing Festival) da akeyi aduk k'arshen shekara."Acikin wannan gari akwai wata unguwa da ake kira Gobirawa,yawancin mazauna unguwar ada caan baya zabarmawa ne,Daga baya hausawa suka yawaita acikinta."Gidan Mallam Aminu yana daga cikin unguwar layi na uku,Gabas da masallaci Sheik Bashir."Da ke Unguwar." "Mallam Aminu,mutumen kirki ne,Wankan tarwada mai tsayi da jiki,yana cikar zati da haiba daka ganshi kaga irin malamman nan masu Da'awa,Sannan kuma ya fito daga gidan sarkin mallaman garin,Duk gidan su malammai ne kuma shi ne magajin gidan, ya kasance babban malamin da akeji da shi a jihar kebbi da kewayenta."Allah ya albarkace shi da samun ilimi mai yawa,ya na ba mutane da yawa karatun addini."Yana da mata d'aya malama juwairiyya itama tana da islamiyya ta kanta,mace ce mai kyau,ga kirki abin burgewa tana da ilimin addini,mutunci da sanin girman Dan Adam,Sai yaran su akwai Muhammad Yaseer da yaseera sai qaramin Abdul raheem."Yaran su sun taso acikin rayuwa mai kyau wato ilimin addini da na zamani."Tare da tarbiyya."Muhammad Yaseer yana karatun aikin likita,A jami'ar Danfodio Sokoto."Sai Yaseera da ta kammala karatun sakandaren mata a wannan shekarar,Abdul kuwa zai tafi aji d'aya a sakandare."Dukkan yaran kan su a had'e yake suna da zurfin ilimi mai yawa,kowannen su ya haddace Alqur'ani mai girma tare da wad'an su littafan sa ni,"Suna da kyau matuka,ga biyayyah da kamun kai da nutsuwa." "Kamar kullum matukar mai gidan yana gari ko baya nan hakan ke faruwa agidan,wato karatu tun kafin sallah Asuba har zuwa wayewar gari, Mallam ne acikin iyalansa,Suna ta karatu ya fadiwa matarsa da yayansa,daga bisani Addu'a sukayi kowa ya shafa,Daga nan suka cigaba da fira kowa na fadin ra'ayinsa ko buqatun su da abinda suke so."Kasancewar Yaseera da Abdul ne kawai agida domin yaseer yana makaranta." "Mallam ya tambaya Abdul na tambayeka ba ka bani amsa ba!?" "Abdul ya ce"Abbu daman ni inason idan nagama karatuna na sakandare ka kaini jami'ar nan ta madina ina so nayi karatun likitan musulunci." "Dariya mallam yayi tare da miqawa Abdul hannu sukayi musabaha yace masha Allah, "Allah ya cika maka burin ka Abdul raheem,Amma kasan tufin Asirin Allah ne,muke da shi idan Allah ya kaddari hakan zanji dadi Allah yaqara tufa mana Asiri." "Ameen ya rabbi,Umma ta itada Yaseeara suna dariyar Abdul." "Naga bakin ki na motsi ke kuwa me kike buqata?.Umma ta tambayi yaseera tana murmushi." "Abbu ni yaushe zan tafi makanta!?"Yaseera ta tambaya." "Amsa ya bata na gaya maki makaranta ba yanzu ba!Ki k'ara hakuri akwai tunanin da nikeyi akai!"Inji Abbu. "Yanayin yaseera ya sauya!Domin tana son cigaba da karatun ta wataqila Abby bazai barta ba!Tace acikin zuciyarta!"A cewa fili cewa tayi to Abbu,Nagode." tashi tayi ta nufi madafar Abinci domin hada abin Karin safe." "Abdul ma yasan aikin falon Abbu yaje ya share tare da harabar gidan,sannan ya fara wanke motar Abbu da yake yau Assabar ba makaranta sai goma suje islamiyya su dawo sha biyu,su koma karfe biyu,su komo shidda na yamma." "Abbu ya kalli Umma yace"Juwairiyya ina ganin kamar lokaci yayi da zan fadawa yaseera mijin da na zaba mata,saboda naga tana son karatu ni kuma sai anyi auren su nikeson ta tafi makaranta tana gidan mijinta,ba wai saboda na raina kamun kanta ba!"Wannan shi ne ra'ayi na amma me kike ganin ya race!?" "Umma Ta numfasa tace Mallam nima,In bayanka gwara kawai tayi karatunta bayan auren,sai dai wani hanzari ba gudu ba!"Ya kamata tasan da maganar Aurenta da Najibullah shi yafi cancanta." "Hakane In sha Allah an juma da dare zan sanarda ita!"Inji Abbu." "To Allah ya yarda yasa mudace saboda kowacce uwa tana alfahari da samun suruki kamar n Najibullah...Umma tace tana kokarin tashi,Bari naje na duba me ake hada mana na kari,Abbu yace to kuyi himma Ku gama Ina son nafita yanzun nan." "In sha Allah,mallam yanzu za'a gama.."Umma tace ta nufi hanyar madafa." *GIDAN MAK'ERA* "Babban gida ne,Mai dauke da lungage da dama,Mallam Abubakar wanda akafi sani da (Malam Buba)shi ne shugaba agidan,Yana da mata biyu Inna Karime wato uwar gidansa wacce ta rasu shekarun baya!tanada 'ya'ya tara maza biyar,Umar,Nasiru,Aliyu,Badaru da sani sai mata,lubabatu,sahura,sai Mariya da sakina dukkan sunyi aure har da yaran su wasu kuma sunada jikoki,Sai matarsa ta biyu Amina wacce suke kira da (Anna)Da dadewa suka rabu da ita akan masifar sa,yanzu hakan shi kadai yake rayuwa sai halinsa,Anna tana da 'ya'ya shidda,Tare da Malam Buba,Mata biyar,Zainab,Ruqayya,Hassana da usaina,Aysha,sai namiji d'aya kuma shine babba acikin su wato Yusuf Mahaifin Asma'u."Tunda Anna tabar gidan malam tayi aure a kauyen felande yanzu hakan scan take rayuwa da yaranta biyu maza da ta samu Idirisu da mustafa." "Dukkan gidan kowa na tsoron Baba mallam,Saboda mutum ne,mai akida da dokoki,Shi ke hada aure shi ke saki harkar gargajia ta yalwatu arayuwarsa Duk yaransa maza agidan suke zaune da iyalan su kowa da nashi lungu." "Gidan mallam Buba,Babban gida ne,Wanda 'ya'yansa da jikoki har tantab'a kunne ke rayuwa acikin gidan,Sana'ar gidan tun kaka da kakanni ita ce Kira, kamar irinsu(Wuk'a,Adda,b'ota,gatari,da kwasa,tsinke da sauran su,)Shiyasa akafi sanin gidan da gidan mak'era."Suna bayarda taimakon wuta hakan da sauransu." "Duk 'yammatan gidan da sun tasa mallam Buba ke zab'a masu miji,suyi aure,tun kan diyansa mata da maza har izuwa kan jikoki,"Gulma da hassada ta yawaita acikin gidan saboda kowa naji da kansa."Ba komai bane yakawo haka saboda bawani ilimi ne da su ba bare matansu da Baba mallam ke nemo musu." "Lungun yusuf,shi ne daban agidan saboda yasa mu mata mai kirki,Wato sadiya (Lami)yar gidan limin,Haka yaranta uku Asma'u,Sauda,da Baraka,sunada tarbiya sosai." "Duk gidan suna jin haushin lami wacce suke kira da uwar mata!Wai batada d'a namiji!Sun tsaneta bata jin sanyi kowa agidan sai Baba mallam domin shi ba ruwan shi da bambanci,Duk Wanda ya taka dokarsa takashi yake! ,Kaf mazan gidan,kyashi da shin yusuf Saboda shi kadai ne namiji dakin su,sai qannansa mata da yake taimakawa kuma suna masa biyayya, Akai kai suna zuwa garin da Anna ke aure su dubata tare da mata sha tara na arziki,Su Asma'u suna son kannen babansu domin sune masu kaunar maman su,komaina yusuf shi kadai yake yinsa sai qannan sa mata,shiyasa aka fitarda shi daban agidan haka matarsa lami batada shaqat acikin matan saurinta(facaloli)shiyasa suke hade mata kai,Kullum cikin tuggu gulma da shirya mata munafunci sukeyi agidan,Mijinta Yusuf ko duk acikin yayan malam babu yafisu tufin asiri,Shiyasa yake sakewa Baba mallam kudi,shi kuma yana sonsa da diyansa sosai."Kuma wataran yana auda kai!A al'amuran su saboda akwai kwadayi da son abin duniya,Abu daya ya hadasu nacewar Yusuf yayi akan sai yaransa sunyi karatun boko,Wanda al'adar gidan Arabic kawai ake,Asma'u kawai ce tauraruwar da tayi nasarar gama sakandare,daga kanta mallam yayi rantsuwa ba Wanda zaiyi boko sai bayan ransa! shiyasa mallam ya tilasta mata aure yanzu,domin ya zaba mata miji mai arziki."Duk gidan sunji bakin cikin auren da Ma'u zatayi."Amma agefenta ita da Iyayenta baso sukeyi ba!Hakuri kawai zasuyi saboda gudun zuciya da masifar Baba mallam,A ganin Yusuf ya karya dokar Mahaifinsa Asma'u tayi karatun boko,yanzu kuma taya zai karya auren hadin da za'ayi mata,Saboda koshi din dan yayi dace da tagari ne,Amma yana bakin cikin Asma'un sa yarinya mai ladabi da biyayya mai kyau da ilimi ta auri jahili kamar Alh.kalle,Wanda aqallah zai girme masa,Gashi da mata har uku da yaran da shi kanshi bazai san adadin su." "Cikin sati d'aya Asma'u duk ta rame!tayi baqi damuwa ce,A zuciyarta abubuwa da dama take ayyanawa aranta!Ko ta gudu tabar gidan...kuma tana tausayin rayuwarta da ta iyayenta!"Domin kuwa barin gida babbar illa ce ga rayuwar 'ya macce." "Ta rasa ya zatayi an rabata da Wanda takeso matashi dai-dai aurenta!"Za'a yi mata *AUREN DOLE* da sa'an mahaifinta!"Kuma babu Wanda taga alamar zai takawa Baba mallam burki!" "Duk mutunci da tarbiyar Asma'u ta dauki aniyar ajiye su gefe domin idan Alh.kalle yazo gidan tatas take masa,Amma dariya yake mata ko tausayinta bayaji aganin kurciya ce,ke damun ma'u." "Ana hakan har akasa ma'u ruwa saura sati d'aya ayi aurenta Alh.kalle an kawo kayan lefe akwati biyu,Wanda shi aganin sa ya nuna bajinta...haka agidan sai nuna baqin ciki sukeyi tare da kyamar su Asma'u." "Gidan Gwaggo Hassana kanwar Yusuf,Asma'u ta tafi abinta,Rarrashinta gwaggo,keyi...Domin ta hakura da zabin mahaifinsu,Suma haka akayi musu auren gashi har yanzu sun zauna lafiya harda yara." "Shirye shiryen aure akeyi ta kowanne fanni Alh.Kalle ya gyare gida an fente ko ina,Matansa sai dariyarsa sukeyi suna kiransa da mijin yarinya." [1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA UKU* *ALK'ALAMIN NABEELA DIKKO* *BABI NA BIYU* *GIDAN MALLAM AMINU* "Bayan sallar isha,Mallam ne zaune acikin qayataccen falon sa mai kyau da tsari,da yake yana da tufin asiri,yana da shaguna magungunan musulunci,ga makarantu sannan yana aikin gwamna gidan marayu."Shiyasa yake da tufin asiri dai-dai gwargwadou."Fira yakeyi shi da matarsa,Suna kallon wa'azin sheik Daurawa,A sunnah t.v, daga bisani umurni ya bata da takira masa yaseera." "A dakinta ta sameta tana karatun Alqur'ani mai girma." "Bayan ta kai aya,juyowa tayi ta kalli ummanta tare da gaita." "Umma ta ansa sannan tace"Idan kin gama Abbunku yana kiranki." "Yaseera tace"yawwa Umma daman nagama kuma yunwa nikeji abinci zanci muje!" "Tare suka jira ita da ummata sai da suka kai kofar falon yaseera ta dawo baya Umma ta fara Shiga sannan yaseera ta biyo bayanta,aqasan lallausan kafet din,ta zauna dai dai kafafuwan Abbu tare da gaida shi." "Umma ko agefensa tayi mazauni saman kujerar nan ta zaman mutim uku," "Amsa gaisuwar yayi,fuskarsa asake." "Sai dai yaseera jikinta yayi sanyi!"Duk gabban jikinta rawa ya ke saboda wata fargaba da taji ta ziyarci gangar jikinta." "Gyaran muryar Abbu,ya dawo da ita hankalinta.." "Ya ce, ''Yaseera dazu naji kinyi magana akan kina son ki koma makaranta ko?" "Eh,Abbu tace da sauri!tare da ajiyar zuciya." "Ya ce,Masha Allah."Zaki tafi makaranta amma da sharad'i d'aya...sai nayi miki aure,Idan mijinki ya amince sai kitafi kina a matsayin kamilar macce,Hankali yafi kwanciya kina gidanki kina karatu saboda ina tsoron wannan zamani mai cike da abubuwan tashin hankali da al ajabi."Na sanki da hankali da nutsuwa kuma ina da kamun kai,Amma ita rayuwar nan da kike gani komai yana iya canjawa ko dole,ko ta wuya ko kuma ta dadi!" "Dan haka nayi tunanin zab'a maki miji nagari!Wanda zai iya riqeki da gaskiya da Amana wato Najibullah Dan gidan Alaramma Usman..." "Tunda Abbu ya ambaci kalmar aure yaseera ta sadda kanta aqasa zuciyarta nayi mata tafarfasa!Domin sam batasa aure agabanta yanzu ba!Karatu takeso shiyasa ba ta kula duk wanda zaice yana sonta,kwallah!ke kokarin gangaro akan lafiyayyar fuskarta mai kyau kallo,kokarin hadiye kukan take!"Sai taji Abbu na cewa..." "Nasan zakiji maganar kamar a mafarki!To gaske ne,Tun kina makaranta mukayi zancen auranku da najibullah,ni da mahaifinsa,kin sani sarai mu abokan juna ne duk wa'Azi tare muke zuwa,Alfarma ya nema gareni ni kuma na amince saboda nasan irin tarbiyar da na baki Yaseera." "Sannan Najib yaro ne mai zirfin ilimin addini da na zamani,shi kan shi Alaramma ne,yana da hakuri,ga shi ya san girman manya,yana da mutunci,Hakika na tabbata rayuwarki zata inganta agidansa,yana da abinda zai ciyarda ke yayi miki sutura sannan ya kula da lafiyarki dan kuwa yana aikinsa da 'yan Sana'oi,sannan zai cigaba da baki ilimi har karsheb rayuwarki." "Yanzu hakan ya tafi madina yayi wani kwas,na wata shidda,tun kina makaranta,in sha Allah munasan ran zai dawowarsa akarshen watan nan na muharram sai kuka juna sannan ayi buki,bayan nan idan yabarki kiyi karatun idan kuwa bai barki ba sai ki hakura!" "A karshe ina rokon ki alfarma yaseera idan har zabin da nayi maki baki gamsu da shi ba!Kina da damar zabin wnda kike so kike ra'ayi domin *AUREN DOLE* ba aure bane matukar matsaloli zasu dinga kunno kai!"Ni dai amatsayina na mshaifinki kinga ya dace in san waye zanba aurenki,"Kuma hakkina ne nazaba maki miji nagari mai nagarta,Wanda Addini sa da dukkan halayensa sunyi dai-dai da fadar Allah (SWT) da manzon rahma Annabi (SAW)" "Amma kuma Allah yace"Muji tsoronsa muyi muku adalci shiyasa nace idan baki ra ayinsa ba komai nasan yadda zanyi na sanarda su!Farin cikinki shi namu." "Ya kalli umma ya ce,"juwairiyya ko ba haka ba!" "Umma ta ce"Hakane Abbu,Hakika yadda kayi shi yafi cancanta ga kowane uba nagari yasan wa yarsa zata aura meye addininsa,muhallinsa da kuma aikin yinsa,yadda yarinya bazata shiga acikin wani hali ba!"Yaseera nasanki da nutsuwa to ki nutsu kiyi tunani mai kyau akan ra'ayin Mahaifinki ba wai ya tilasta ki bane ko zai maki *AUREN DOLE* A'ah idan baki sonsa ki fada mana!Mu hakki da Allah ya daura mana akanki mukeson saukewa saboda Yadda muke da hakki!Akanki hakan kema kinada hakki akanmu yaseera!" "Saboda haka wajibi ne,agaremu sauke Hakkin ki da ya rataya awuyan mu,saboda Annabi (SAW) ya ce,Hakkin D'a akan iyayensa,sune :"Na farko,Ya sanarda shi karatu,da rubutu." "Abu na biyu,Ya kyautata sunan sa, Sai Abu,na uku Ya aurar da shi idan ya balaga." "Yaseera mu baki ilimin addini da na zamani,kinsan yadda zaki iya bautar Allah kuma kinsan yadda zaki kare kanki daga wuta.. "Domin Allah (SWT) ya ce "Acikin Alqur ani mai girma,"Yaku wad'anda kukayi imani,ku kame kanku da iyalanku daga wuta,wadda take makamashinta mutane da duwatsu ne!"Allah ya karemu." "Ameen Abbu yace"cikin jin dadin kalaman matarsa,azuciyarsa yana alfahari da samun mace mai ilimi amatsayin uwar yayansa..."Muryarta ta katse masa tunani.." "Inda ta ce"sannan kinga Abbunki ya sanyawa maki suna mai ma'ana irin na addinin musulunci,"Kina ganin sunaye,da yawa agari maras ma'ana wasu iyayen ko da za'a kashe su baza su iya fad'in ma'anar sunan da suke kiran yaransu da shi ba,To ki godewa Allah yaseera saboda ke da kanki kinsan meye ma'anar sunanki!kuma kinsha karanta alqur'ani,Kina ganin yaseerah aciki." "Kinga anan kowanne daga ciki munyi iya kokarin mu wurin yi maki biyun na ukun ne mukeson mu cika da yardar Allah." "Ni da Abbu saida mukayi shawara da juna kafin mu sanarda ke, Saboda haka ba wata shawara da zakiyi daman dai nice babbar qawarki kuma abokiyar shawararki,Sai ki fad'a mana ra'ayinki muna saurare..."Umma ta qarashe zancenta tana kallon 'yartah da sadda kai tana sauraren jawabinsu." "Duk da ba hakan taso aranta ba,Amma ahankali tunani ya fad'ou mata arai!"Cikin sanyin murya ta motsa labban bakinta da sukayi mata nauyi,domin wata kunya da nauyin iyayenta taji ya kama jikinta.." "Numfashi tayi sannan tace ahankali"Abbu!"Umma"Ba abinda zance da Ku sai dai godiya!"Ina rok'on Ku da kada kusake tambaya ta abu,idan zakuyi min,Ku iyaye na ne bai kamata Ku nemi wata alfarma awurina ba,domin yi maku biyayya wajibi,Nasan Baku kaini inda zan nakasa ba!kuna sona!Hakika kunyi min komai rayuwa,fatana Allah yaqara maku rai da lafiya,yasa ayi karshe mai kyau." "D'ago fuskarta tayi ta kalli,iyayenta Wanda hasken annuri da farinciki ya bayyana afuskokin su,itama murmushi tayi tace,Ina alfahari da Ku,A kullum ina rokon Allah yasa inyi rayuwa irin taku,Wadda dole sai nasamu miji,nagari hakan zata kasance Alhamdulilah Abbu ya zaba min Alaramma najibullah,mai addi,mai ilimi,mahaddacin Alqur ani,Nagode Abbu,na yadda na amince koda za'a iya kiran aurena da *AUREN DOLE* na tabbata agurina aure ne Wanda iyayena sukaga yadace da ni dan haka agefena babu *AUREN DOLE!*." "Umma,Tabbas ina da hakki akanku,Amma naku yafi yawa akaina,saboda duk abinda yakamata kuyi mana kunyi mana shi.."Bazan manta Acikin suratul Isra'i,Allah (SWT)Ya ce"Kuma ubangiji ya zartar da hukunci kar abautawa kowa sai shi,kuma dangane da iyaye biyu Ku kyautata musu,ko da dayansa yakai ga tsufa to karkace dasu tir!"Kuma karka tsawace su,sannan kuma ka gaya musu magana mai karamci." Sannan Manzon Allah (SAW) yana cewa yardar Allah tana tare da yardar iyaye,kuma fushin Allah yana tare da Fushin iyaye," "Dan haka umma ...Abbu nabi Allah da manzonsa,kuma na biku,kuma in shaa Allah zan cigaba da bin umurninku tare da yimuku biyayyah har karshen rayuwata..."Yaseera tace cikin ladabi.." "Ajiyar zuciya Abbu ya sauke yace Alhamdulillahi Alaa kulli haliin..Tabbas nasamu mata,kuma uwa tagari wacce tayima yarana tarbiya tagari,Juwariyya nagode abisa namijin kokarinki akan yaran nan,Domin kece mai kula da su tare da sanya ido akansu da duk wasu lafuzza dazAsu fito daga bakinsu..." "Umma tayi murmushi tace"Mallam kenan, ai Kaine ka karantar da ni har nike sanarda su,karfa ka manta Kaine jigon gidannan...daga ni har su muna bisa turbar inda ka ajiye mu,wannan tsarinka ne,kuma kokarinka ne,Domin ko kana gida ko baka gida,ka tsara yadda za a tafiyarda rayuwa da kuma mu'amulat agidanka."Sai dai mu godewa Allah nida yarana da yabamu garkuwa mai kyau,mai kuma inganchi amatsayin jagoran mu." "Dariya Abbu, yayi yace Masha Allah, Ya kalli yaseera da ke wasa da zoben azurfa dake yatsanta,Ya ce Yaseera....." "TaceNa'am,Abbu tare da dagou kanta.." "Ya ce,Allah yayi miki,Albarka kinji,Kuma yadda kikayi mAna biyayya Allah ya ba ki wadanda zasuyi miki,Hakika akullum ina alfahari da Samun 'ya macce irinki!"Allah ya sanya alkhairansa da albarka a lamarin nan." "Ameen,Ameen."umma tace tana murmushi.." "Yaseera murmushi tayi cike da kunya,sai Abbu yace zaki iya tafiya abinki.."Aykuwa da gudu yaseera tabar falon." "D'akinta ta fad'a,da yake cikin dakin falon umma yake,A falon,akwai dakuna uku, biyu da falo na umma,dayan nata,Shi kuma Yaya yaseer nashi na daga waje,Abdul kuma nashi na daga cikin falon Abbu,na shi daga gabas na Abbu daga yamma."Haka suke rayuwarsu kowa da dakinsa daban agidan,mazan ba ruwansu da harkokinta itama bata shiga lamarin su,wannan tsarin yasamo asaline daga iyayen su,Kuma wannan bai hanasu so da kaunar junansu ba,tare da sanin girma da kimar kansu Sam babu raini atsakaninsu." "Yaseera saman gadonta da ke dakin tafada wasu hawaye masu zafi da ta kasa bambance ko na meye, ke zuba afuskarta!"Abincin da bataci ba!kenan adaren, duk da kasancewar tanajin yunwa,Tashi tayi,bayi ta fada domin dauro alwala,sallah ta tada bayan ta fito,sai da tayi Nafilfili,tare da azkharul naumy,sannan tayi shafa'i da wutiri,Akarshe addur ar istihara, ta karanto tare da fatan wannan zabi yazamo mata nagari,sannan ta tashi, kwantawa"Har kasan zuciyarta taji sanyi da nutsuwa yana yatsa dukkanin jikinta..." *WANENE ALH.KALLE* "Alh.Kalle babban dan kasuwa ne,da yayi suna agarin Argungu,Yana kantina da dama na kayan masarufi."Yana da arziki kwarai da gaske amma kuma kowa yasan jahili ne,ba boko babu mahammadiya,yana da mata uku a halin yanzu,wad'anda yake aure yana saki basu kirguwa, saboda haihuwa yake rabuwa da su,Da zarar macce tayi ciki yagama da ita matsawar bazata zubar da shi ba!"kuma da ya gama yayin macce shikenan,Duk da hakan yana da tsabar yara goma sha bakwai,cikin daga wasu na hannunsa wasun kuma suna ga iyayensu mata." "Alh.kalle Sam baida addini ko sallah da kyar yake cika biyar ayuni,Katon gaske ne ga girma ga tsayi bakine wulik Wanda akalla zai kai shekara sittin adunia."Yanada yara yammata biyar da sukayi aure har sun hayayyafa,harda ,maza uku,yayiwa aure,ko yanzu tare da diyan sa uku mata za'ayi auransa,rana daya.zasuyi sa'annin Asmau"Bai da mutunci ko kadan,duk matansa suna tsoronsa da shakkun masifarsa,Sakin mace da aurenta awurinsa yafi sanya hula da sauketa akai sauki."Gashi da sakewa mata kudi awaje,amma da zarar sun shigo wayam,sai wuya da wahala,yaransa kullum kamar almajirai saboda baya kula da suturunsu acewarsa sunyi yawa,cishesu kawai aikine,Idan Alh.kalle yaga macce ya hadiye mata miyau to saidai wani ikon Allah,Domin kudi zaisa ko da so ko da *AUREN DOLE* sai ta shigo gidansa."Hakan ce tafaru domin tunda yaga Asma'u fara kyakkyawa yar kimanin shekaru sha takwas,ya liqe mata tayi masa wankin babban bargo!"Tana tare da kamalu,shima ya ci mutuncin Alh.kalle,suka wuce abinsu,shine yaji zafy!"Yayi alwashin rabata da kamilu,sai kawai ya mannewa kakanta malam Buba akan sai ya aura masa ita,kudade masu yawa yake damkawa mallam Buba,Dan kawai ya samu Asma'u wacce suke kira da (Ma'u)" "Daman Hausawa sunce rana bata qarya, sai dai uwarda bata shirya ba,taji kunya."Domin yau takama Assabar tun safe ake kid'e kid'e da wasannin Al'ada da kuma gadon gida wato na mak'era,Kofar gidan mallam Buba mak'eri cike take timjin da yara matasa,da mutan gari,Mallam Buba ansha babbar riga sai washe baki yake yana d'aga robar fanta sama,yana sha,shi da abokinsa mallam iro ."Zaune suke akan kujerun roba da aka dazAwa mutanen da ke zaune,kofar gidan suna kallon jikokin gidan dake wasa da wuta.." "Hatta yara qanana yan kimanin shekaru bakwai,Da mazan gidan an zuba musu kalanzir ajiki, an kunna wuta ajikkin kayan nasu,wasu a zaune cikin wutar,wasu ko suna tura makamashin wuta abakinsu,Amma sam wutar bata cin jikinsu,kuwwa sukeyi da shewa suna fad'in gado sai dan gad0,saimu diyan mak'era ba dai wuta ta ci mu ba,sai wani ikon jallah,Mune jikokin mallam Buba mak'eri ikon Allah,Ina Wanda wuta taci taki warkewa,ina Wanda wuta kema gaddama!"Kuzo ga yayan guduma,....."Masu kida ko sai kara kaimi sukeyi...can farinciki ya kama Baba Malaam." "Baisan lokacin da yafada filin wasan baa,domin tuni yace yabarwa diya da jikoki,Cikin kwarewa Jikinsa sai mazari yakeyi galan din fetur yatada yana zubawa ajikinsa, wutar kara ya dauko tana ci ya goga ajikin kayan sa,amma Sam wuta taki kamasu....shewa aka dinga yi, mallam buba kudinsaya kwakulo duka ya zube aqasa yasa wuta ajikinsu, taki cinsu...sake kuwa akayi"daga yan kallo har jikokinsa kowa tsaye suna kallon Baba malam sunajin dadi,tofi yayi awuta sai kawai takama ajikinsa da kudin harda tururin hayaki amma ko alamun cinsu batayi ba....Yace,ina mai ja da Buba dan gambo jikan ila makerin manya!kowa yabar gida,"gida ya barshi,Cigaba yayi aikin gadou mai kidi naqara kashe kid'a...."Mallam iro ne dai yazo da Sauri ya janye malam Buba hakan nan."Nan wasa ta cigaba da kyau kowa na nuna tashi gwaninta." "A cikin gida kowa sai hidima akeyi anci an sha masu farinciki da murna nayi masu bakinciki kuma sunayi." "Asma'u kuka takeyi kwarai tun alokacin da taji labarin an dawo daurin aurenta da Alh.kalle."Ko wanka da kyar su Gwaggo husai suka tilasta ta,babu abinda takeji sai haushin kanta da batayi tunanin guduwa tun wuri ba,Kamalunta ya dade da cewa su gudu wani,wurin daban har ayi aurensu,sai su dawo!Amma tsoronta ya hanata binsa gashi yanzu ya Shiga dunia sanadin soyayyarta!,Kuma Batasan a ina yatafi ba, domin ahalin yanzu tafi son ta fada uwa duniya,da akaita gidan Alh.Kalle,kazami mai Faso da warin baki,kuma tsoho..."Kukanta ta cigaba da yi har lokacin da aka zo daukarta bayan tasamu horo awurin iyayenta,Baba mallam ko kashedi mai kyau yayi mata akan ta zauna da mijinta,kishiyoyinta,da tawagar yaransa lafiya."A lokacin hankalin Asma'u ba ya tare da su, ko A bata kama ba, acikin horonsu zuciyarta na ta shirya mata yadda zatayi,jin takeyi arantà!zata iya yin komai harta kisa! matukar kalle bai saketa ba!!!" [1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA HUD'U* *ALKALAMIN NABEELA DIKKI* "Yaseera da qawarta Raudhat a hanyarsu two dawowa Islamiyya,Fira sukeyi sosai,Nan ne Yaseera ta labartawa Raudhat Mas'ud duk abinda ke faruwa." "Dan tsakaita tafiyar sukayi,Raudhat ta dafa qawarta cikin nutsuwa,Ta ce,Yaseera nasanki kuma nasan dukkanin halaye,Ba sai na baki shawara ba,A kan cewa ki amshi zabin su Abbu." "Na tabbata wannan aure naki da Najibullah alheri agareki!Ina miki fatan Alheri,Allah ya nuna mana lokaci,wallahi nayi farin ciki matuka domin kin samu miji na idon duniya,Ga ilimi,mutunci tarbiya da asali mai kyau,"Kinsani sarai wadannan su ne halayen miji nagari,Ina son ki kwantarda hankalin ki,Kada ki sanya musu acikin lamarinki sai karshen sa yayi kyau."Raudhat ta qarashen zancen tana murmushi tare da zubawa aminiyarta ido." "Hannayenta yaseera ta hade da nata,Ta ce tabbas kice kawa tagari mai sona,nagode Raudhat hakika shawararki mai kyau ce,Daga yanzun nan zan dauki najibullah da zuciya daya, amatsayin mijin da nake fatan yazamo uban yaranah.." "Haba tawan ba godia haka atsakanin mu, Raudhat..Ta ce tana dariya." "Saleem da Abdul suka zo,Inda suke tsaye." "Abdul ya ce kagan su ko sale,daman nagaya maka sai mun cimma su,suna nan suna surutu..." ''saleem qanen Raudhat yake,yayi yace tabbas abokina naga zahiri kamar kullum wato su yayah basa gajia da fira,Dariya suka sa dukkan su." "Sallama da juna sukayi da zummar gobe zasu hadou Islamiyya,Tunda qannan su sun saka masu ido,Kowacce hanyar gidan su tabi itada qananta da yake layin gidajen su ya bambanta sai dai duk a unguwa d'aya ne." "Ko da su yaseera suka dawo gida sun sami yayansu yaseer ya dawo daga makaranta,Ai kuwa murna aka shiga yi,Musamman Abdul da akayiwa tsaraba da yawa,Yaseera kayan kwalliya da hijab aka saya mata." "Nan take ta fada kichen umma ta samu tana sanwar rana,zage hannu tayi ta tayata,bayan sun gama dan wake da zobou tayiwa yayanta domin shi yaya yaseer yafiso,dan kawai ta faranta masa yadda yayi musu abin alheri." ******************** "Tunda aka kai amarya Asma'u agidan mallam kalle kullum cikin masifa da rashin mutunci take,Allah ya jarabci Alh.kalle da ciwon son Asma'u Wanda ya haifar masa da jin tsoronta." "Kusan kwanaki hud'u da auren su amma har yau Asma'u bata bashi dama ya dama ba kamar kowane Ango." "Gidan Babban gidane mai dauke da ciki da falo hud'u na matan gidan,Uwargidan sa uwani,sai mai binta sahura,saina Asma'u,dayan arufe yake ba kowa,sannan dakin yammata biyu da filin gida, sai turakar mai gidan,,shimaa babban falone,da daki da bayi."A harabar gidan akwai dakunan yara maza uku,da wurin ajiye motoci,duk gidan tayal ne,an fenti shi da farin fenti,har qatoun get din gidan." "Dakin Asma'u an gyare shi tsaf,ansa mata gadon jan katako,kalar jinin kare,da madubi,da wadirof,afalo ko kananan kujeru ne saiti daya,suma kalar kayan dakinta da labule."Alh.kalle shi yayi gadara ya sanya mata talabijin da bidiyo duk gidan dakinta ake kallo,saboda ba mai kayan sai ita,da sashen Alhajin kuma shi idan yasa ba mai shiga yayi kallon." "Yadda Asma'u tayi tsammani agidan ba haka bane,domin kowa tsoronta yake ita kuma sai rashin mutunci takeyi." "Batasan cewa Alhaji yayiwa matansa da yaransa kashedin kwarai akanta ba!."Shiyasa kowa ya zuba mata ido sai yadda taga dama." "Tun a kasuwa Alh.Kalle ya kudurta aiwatar da kudirin sa ayau,shiyasa ana tashi kasuwa yadawo gida tun wuri."Asma'u ko tun safe suke Abu daya wato kallo ita da larai da Jummai yayan Alhaji da bazasu wuce sa arta ba,A yanzu sune manyan abokanta agidan,shiyasa ta daina yiwa uwani da sahura rainin wayo daman can da mama take kiransu."Tana zaune lafiya da su sai kurciya take zubawa agidan da hauka duk da Alhajin ya saketa dan har girki batayi sai dai taci ta kwanta acewarta bata iya ba,kuma ko ta iya bazata yiwa katti da yawa abinci ba!'' "Da misalin 12 na dare Alh.Kalle ya fad'a dakin Asmau da yake yanada mukulayen dakinta,shiyasa bai samu matsala awurin budesu ba!"Kwance ya sameta rashe-rashe akan gado,Baccinta takeyi cikin nutsuwa,Tasbaha ce rike a hannunta ga alamu tana janta ne bacci barawo ya saceta,Sam Asma'u bata bar addininta ba!Bata wasa da lokacin ibada,tarbiyarta ce,kawai tayi watsi da ita,saboda *AUREN DOLE* shiyasa take rashin mutunci kamar ba ita ba!" "Ba kunya bare tsoron Allah Alh.kalle ya farma Asma'u,Warin 'ya'yansa mai karamcin shekaru." "Tashin hankali marar misaltuwa tasamu kanta aciki,kusan sati d'aya ana jinyarta!"Tayi kuka harta godewa Allah,kishiyoyinta ke kula da ita tare da bata baki,akan tumasancin da mijinsu yayi mata,Batayi mamaki ba!Saboda daman can jahili ne!shiyasa ya nuna mata karfi!" "Lami mahaifiyar Asma'u da gwaggo usaina sun zo da kansu har gidan,sun duba yarsu,ran su yabaci matuka!"sai dai hakuri suka ba Asmaun!!"Wacce banda kuka da cewa ita bazata zauna ba!zata bisu ba abinda take fadi!" "Amma kashedin Baba mallam, Gwaggo ta tuna mata!"Wanda yayi sanadiyar katse mata hanzari!"Kuka ta cigaba da yi tamkar ranta zai fita!"A haka suka lallabata suka koma gida rai ba dadi musamman mahaifiyarta lami!!" "Zama ta cigaba da yi agidan Alh.kalle zaman bakin ciki da ganin azaba domin da girkinta da na kishiyoyinta duk Alhaji farmata yakeyi ya mayarda ita kamar wata baiwarsa akullum cikin kuka take!tare da dinbim da nasani akan zaman da tayi ta zuba ido har igiyoyin *AUREN DOLE* suka rataya awuyanta!" ***************Najibullah,Ya dawo gida lafiya,kuma kwas din da yaje madina yayi nasara domin yadawo gida Nigeria da sakamako mai kyau." "Mahaifinsa malam Usman,Babban Alaramma ne,yanada ilimi sosai yanada mata biyu,Hajiya Rabi'a da Hawwa suna zaune lafiya,sai yaran sa biyar Najibullah ne babba,sai Rahma,da Sudais dukkansu yayan Hajiya Rabi ne,Sai Nabeela da Khadija yayan Hjia Hawwa."Suna zaune lafiya cikin karamci da son junansu,haka kan yaran ahade yake suna da ilimi da tarbiya mai kyau." "Najibullah matashi ne kyakkyawa wanda mata keta kai kawo akansa,Allah yayi masa baiwar kira'ah kamar sheik sudaisi idan yana karatu.Gashi da dimbin Ilimi bayada makosa ko daya iyayensa na alfahari da shi kwarai da gaske." "Da dadewa mahsifinsa ya sanarda shi zancen aurensa da yaseera,sai dai shi ya amsa masu domin kawai bin umurnin iyaye,Amna aganinsa yafi son zabin sa, ba hadin iyaye ba!"Kasancewar bai taba haduwa ita ba,akan tana makaranta har yayi tafiya,shiyasa Mallam usman ya kirashi tare da bashi umurnin,ya tafi gidam malam Aminu ya ga yaseera wato matar da zai aura nan da wata d'aya." "A zuciyar Najibullah mamaki da tunanin wannan aure nasu yakeyi shin *AUREN SO NE!KO KUWA AUREN DOLE* ne za'ayi musu."Amma afili da ladabi ya amsawa mahaifinsa da in shaa Allah zai tafi bayan magrib,godiya yayi masa tare da sanya masa albarka." "Murmushin jin dadi najib yayi kana yabar falon mahaifin nasa cike da zancen zuci,"Da tunani wannan wace irin mata ce!?Shin tayi dai-dai da ra'ayinsa,irin kalar macen da yakeso ce!?"Oho dai ido kannan kai..."Inji Nabeela Dikko "Kofar gidan,Ya tsaya yana nazarin ta ina zai fara,Sai kawai ga Abdul Raheem riqe da leda a hannu ga alama daga ake yafito,Fuskarsa a sake yace,Abdul ne ko?" "Abdul da ya kada fadarsa daya a bakin get din gidan,ya waigo kasancewar bai lura da Nabullah ba.." "Da sauri ya karaso wurinsa ya gaida shi aladabce..." "Amsa masa Najib yayi saboda daman sun san juna,Domin yaseer mutumensa ne." "Abdul,"Ya ce "Yaya Najibullah ne!"Hannu ya bashi sukayi musabaha..."Ya ce Yaya,kayi hakuri ban ganka bane,Saukar yaushe!"Andawo lafiya!?Ya hanya!?" "Murmushi yayi sosai,Sannan yace"Duk lafiya qlaw,Shekaranjiya na dawo."Inji Najibullah." "Masha Allah,Abdul yace Allah ya taimaka." "Ameen,Abdul,Am nace yaseera fa tana ciki,"Najibullah ya ce"da Abdul." "Eh,Yaya Yaseera tana nan.''Abdul ya ba shi amsa." "Yawwa Dan Allah kayi min magana da ita," "To Yaya bismillah mu shiga daga ciki,Bayan Abdul din Najibullah ya bi,har babban falon Abbu,Ruwan faro,da lemu Abdul ya ajiye wa Najibullah,tare da Kofi sannan yace Yaya ga ruwa bara na kirata,Ledojin sa ya dauka ya fice daga falon." "Dakin umma,ya nufa ya bata saqon aikenta,Ya ce "Umma Yaya Najibullah dan gidan Baba Alaramma ne yazo wai in kira masa Yaya Yaseerah," "Umma ta ce"To Ashe dan nawa yadawo Hajia Rabi bata sanar min baah."Yanzu kace ya shigo daga ciki kaje ka sanarda ita." "Abdul ya ce"Umma ya na falon Abbu,Bara na kira yayar,Umma halan sonta yake naga kamar yana jin kunyata..." "Katse shi umma,tayi tace,bana son gulma Abdul jeka ka tambaye shi!" "Dariya yayi,yace kai Umma,Sannan yayi hanyar dakin yaseera,Buga kofar yayi har sau biyu,Fitowa tayi sanye da hijab,Ta bude ganin Abdul yasa ta ce"Daman nasan Kaine meye haka kamar zaka balla min kofa!!"Yaseera tace ahasale!" "Allah ya baki hakuri!"Aikoni akayi kinyi bako yana falon Abbu!"Yana jiranki!"Abdul yace ya juya abinsa saboda da kyar ba'a saida halin ba!Shi da yayarsa." "Ras!taji gabanta ya fadi to waye!?Ga shi tayi fada da Abdul din ta bare ta tambaye shi." "Dakinta ta koma,Gyara fuskarta tayi,Hijab ta sanya!Ta fito afalo ta samu Umma ga alama da Abbu take waya domin yayi tafiya,Durkusawa tayi agaban Umma,Domin neman izinin tafiya,Alama umma tayi mata da hannu ta tafi,Duk da taso ta tambayi Umma ko waye!Dan tasan cewa Abdul bazai rasa gayamata ba."Tashi tayi jiki ba sanyi ta nufi falon da sallama kanta sunne."Tafiya take ahankali cike da nutsuwa." "Amsa mata yayi,tare da dago idonsa gareta,Tozali yayi da kyakkyawar budurwa wankan tarwada,mai zubi da tsarin halitta mai kyau,Duk da hijab ne ajikinta bai hanashi hango cikar sura da halitta mai Jan hankalin mai dubanta ba," "Da sanyin murya ta gaida shi,"Saboda irin kallon da yake mata taji wani iri." "Amsa gaisuwar yayi,Wuri ta samu a kujerar zaman mutim daya shi kuma yana kujerar zaman mutum uku,Nan dai musayar gaisuwa sukayi." "Ya ce,Nasan baki sanni ba,sunana Najibullah usman." "Kallon shi tayi taqasan ido,kyakkyawqn matashi ne nan take yayi mata wani kwarjininsa." "Murmushi tayi tace gaskiya ban gane ba...,Inji yaseeea" "Ya ce,Kin san kina makaranta, "Hakane gaskiya" "Nan ya fada mata duk abinda ke tafe da shi,cikin hikima da iya zance."A zuciyar yaseera wani farinciki taji yadda Iyayenta suka hadata da miji nagari." "Sun fahimci junansu da yake kowannen su yanada ilimi,sai kakkyawar alaqa ta shiga atsakanin su,Najibullah bai bar gidan ba!Har sai da suka aminta da junansu." "Asma'u sau uku tana samun ciki yana barewa!Bayan wuya da azabar Alhaji kalle da ta addabi rayuwarta,Ana hakan tasamu wani ciki!"Babu yadda Alhajin baiso azubar da shi ba!"Amma Asmau ta hana saboda tasan irin ciwon da takeji alokacin da take barin da Allah ya kawo da kansa,Bare na likitoci...Dalilin kafiyarsa yasa Alhaji dukanta!"Tare da juya mata baya!Gashi batada halin zuwa gida yaji!domin Baba malam dukan kawo yuka yake mata!"Kwanaki da taje yaji yayi rantsuwa duk tadawo bakin auren lami da yusuf(Iyayenta)Shiyasa take hakuri kullum cikin kuka!"Ga rainon ciki ga hawan jini da ciwon zuciya!"Da ke damunta,babu wata kulawa tsakaninta da Alh.kalle su sahura da uwani ne ke taimakonta."Tuni Alh.kalle yafara kokarin neman aure na hudu banda tasko da wulaqanchi babu abinda matansa ke fuskanta." "Najibullah da Yaseera sun gina rayuwarsu abisa gaskiya da amana,duk a dalilin yiwa iyayen su biyayya."Shirye shiryen auren su akeyi,Hakan gefen Yaya yaseer da Raudhat,Qawarta soyayya ta dunke,A dalilin zuwanda takeyi inda yaseera,An sa ranar auren su dukkan su alokaci daya." [1/10, 11:05 AM] Nordin: *NABEELA DIKKO* SHAFI NA BIYAR "A yau jumma'a Dubban jama'a suka shaida da daurin auren Alaramma Najibullah Usman,Da Yaseera Aminu sai Muh'd yaseer Aminu da Raudhat mas'ud ,Wanda aka daura a masallacin Makka da ke sabon garin kanta Argungu,Daurin auren yasa mu halarta manyan malamman Addini da jami'an gwamnati,Da sarakunan gargajiya da ke ciki da wajen jihar kebbi." "Gefen Amare ba laifi domin gagarumar walima,Aka shirya ta mata Zalla,Domin taya su murnar aure,Haka da dare an sake baje kolin wa'azi a masallacin,Sannan aka kai amare dakin su."Bayan sun sha nasihohi da dama awurin magabata,Yaseera na unguwar lowcost,yayinda yaseer ke zaune a shagari quarters Argungu."Dukkansu sunyi gini na zamani yayinda iyayen suka baje basirar su da iyawar su wurin sanya albarkatun daki,Raudhat da yaseera kowaccen su gida saidai masha Allah." "Fadin irin farin cikin da iyayen Yaseera da najibullah suka samu Kansu aciki baima taso ba."Saboda suna alfahari da yaran su yadda sukayi biyayya akan hadin su,fatan su Allah ya basu zaman lafiya da zuriya dayyaba." **********Lamarin Asma'u sai dai Addu'ah domin ta koma yau ciwo gobe lafiya,ga bakin cikin rayuwar da take agidan Alh.kalle."Gashi yanzu tayi nauyi domin cikinta ya tsofa sosai." "Alh.kalle zaman hakuri yake da Asma'u,Yaki sakinta ne saboda kakanta(Baba mallam)Yasan shi sarai da masifa,kuma irin su mutanen daaa,ba'ayi masu garaje mayarda mutim kunkuru ko wani abu mai muni,ba komai ne ba,Agun su."saboda haka yake shakkun sakinta, amma ya dauki aniyar walakanta ta, har sai tagaji ta bar gidan da kanta!"sai shirye shiryen sa aure yakeyi,Ba ruwansa da matansa!" "Watarana Asma'u tasamu ta fita da kyar,taje gidan su a hanyarta ta dawowa ta hadu da kamilu!" "Cikin firgici ta ce kamilu!!!!!ne...." "Da mamaki ya waigo!Domin sam bai ganeta ba!tayi baqi ta rame!ga qaton ciki!!!!"Ko a mafarki ba zai taba manta fuskar da yafi kauna ba,Arayuwar sa!!!" "Asma'u!!!!?Kece nike gani kodai idona ne!Kemin gizo!?"Kamilu ya ce a razane." "Hawayen da take kokarin hadiyewa ne ya zubo mata a fuska!!!Ta ce nice kamilu daga ina!?"Na ganka da jakar kaya!?Kamilu shi ne ka tafi ka barni akai min *AUREN DOLE!*" "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yace tare da sakin jakar kayansa ya durkushe agabanta yana kuka!!!!" "Itama kuka take har cikin ranta!Abinda ke cikinta sai da ya motsa!"Tashin hankali ne ya bayyana afuskarta!"Cikin kuka tace kamilu kai min magana ko zanji sanyi araina,wallahi ina sonka!!....." "Dakata!!!!Asma'u kina so na kika zauna gidan wani da sunan *AUREN DOLE!* Ina can ina haramar dawowa in aureki ashe ke har cikine da ke!"Asma'u ki cuceni!!!"Nayi dana sanin dawowata garin nan yau,domin nayi tozali da abinda zai zama silar mutuwata!"kamilu ya qarashe zancen yana kokarin tashi domin barin wurin da kayansa..." "Tafiya ya fara...A hankali ta rike jakarsa tace kamilu...ina son kasan cewa har gobe kana raina!"Kuma wallahi ban auri kalle ba!Sai domin in fito injira dawowarka na aureka,bayan shekara daya kamar yadda mukayi alkawari!Sai dai kaddara ta riga fata!domin yaki ya sakeni har Allah ya hadani da cikinsa!!!"Amma wallahi ban sonsa,ban taba kaunarsa ba!Kamilu ka yarda ni ka aminche da soyayyata na dauki alqawarin zan rabu da shi nan ba da jimawa ba!!!!!!"Asma u tace cikin kuka!Tana kallon kamilu da yayi mur kamar bashi baah." "Lura da yaran unguwar sun fara taruwa suna kallonsu yasa,Asma'u sakin jakar kamilu tana share hawaye!"Wani kallon tsana yayi mata yace ba komai Asma'u nagode,Amma kisani sonki da kaunarki tare da kishinki zai zamo ajalina!!!"Ficewa yayi abinsa yana hawaye!"Asma'u ma kuka tayi har tagaji kana ta lallaba da kafafunwanta da sukayi sanyi,rai babu dadi,Tare da daukar alqawarin sai tabar gidan Alh.kalle ko da dadi ko da ciwo..." "Rayuwar Najibullah da yaseera rayuwa ce,mai dadi cike da fahimtar juna,suna mutunta junan su sosai!"Auren su kamar auren soyayya,suna zaune lafiya cikin tufin Asirin Allah.'' "Hankalin Muh'd yaseer da Raudhat ya kwanta domin kowa ya samu abinda yakeso."Raudhat yarinya ce mai kirki,ta fito daga gidan mutunci,iyayenta basada makosa."Shiyasa tasu tazo daya da yaseera,har yanzu suna kawancen su tare da girmama juna." "Kamilu da kyar ya isa kofar gidan su saboda jiri! Da ke dibansa,A daddafe yaqaraso kofar dakin Mahaifiyarsa malkah!"Jin abu tiiiim...A kofar dakinta,yasa ta fitou da sauri!"Ganin kamilu akwance dafe da zuciya yasa ta razana!"Tasalima tayi kana tace"me zan gani!Kamilu!?"Yaushe ka dawo!?"Meke faruwa na shiga uku!"Kuka takeyi tare da tallafo shi!"Ruwan randa ta doubo tana bashi yana shaaa,Ajiyar zuciya yayi!yana kallon innarsa dake kuka!!!!" "Shima kuka yakeyi!yace inna kuyi hakuri mutuwa!zanyi ciwon so zai kasheni!!!"Inna Asma'u nagani yanzu da ciki!" *AUREN DOLE!* da akayi mata yayi albarka!"Ina caan na gudu kuma na dawo akanta!"Amma ashe ita tama manta dani...."Kamilu yace yana nishi...cike da wuya!" "Malkah tace kamilu ko ita naji labarin baso take ba!"Zaune kawai take domin ba yadda zatayi,na tabbata har gobe Asma'u kai takeso!"Amma aure ya rabaku,kayi hakuri kabarwa Allah kamilu,Allah yabaka wacce ta fita,cikin sigar rarrashi inna malka ta ida maganar." "Kokarin tashi yayi,tare da taimakonta,ya isa dakin sa,kurar da dattin da yayine yasa Inna tace suje dakinta,kwantawa yayi,ita kuma abincin zaici tayi kokarin sama,masa." "Asma'u tana zuwa jugum tayi adaki tana Neman mafita,tashi tayi tare da shirya kayanta tsaf a akwatina,Daman ka'idarsa ne duk dare sai ya yada zango adakinta,shiyasa ta shirya komai nata,yadda ta tsara!" "Misalin karfe 11:30 dare ya diro dakin,yana kada kafarsa ya subule suuuuuu sai qasa titif!!!!!!"kokarin tashi yayi da kyar!domin har jiri saida yagani,tare da rike kugunsa da ya bugu!!!"Sai dai yana mikewa ya dauki kafarsa daya yasake subulewa ya fadi kaaakaaas!!!!!"ya bugu da gefen gadonta nan take,goshinsa ya fashe,Da karfi yace wayyo!!!!!Wayyo!!!!Wash!!!!!Ina kike Asma'u!!!?"tare da dafe kai!!!!" "Asma'u da ke kwance kan gado ta lafe!,tana kyalkyala dariya,ta motsa tare da hamma kamar agigin bacci ta tashi!!!"Ta ce lafiya!?" "Cikin yanayin ciwo yace subulewa nayi na fadi taimaka min in tashi!!" "Mtwssss!!!wallahi bazan iya baah Allah ma yasa ka mutu in huta!!!"Asma'u tace "Alhaji yace "Dan Allah." "Tashi tayi tadauko tsumma ta goge duk ruwan omo da karkashin da ta lema a qasan tayils din, sannan ta koma gado tayi kwanciyarta cike da murna."Tace wallahi banajin tausayin,mugu!Azzalumi!Yadda baka jin tsoron Allah ba,kasa aka tilasta ni aurenka adole,Bazan ji kunyar ramawa ba!Ina son ka sakeni Dan Wanda nike kauna,matashin yaro kamilu ya dawo!" "Kuka da nishi yake,"Ya ce ashe bakida kirki Asma'u!To anqi asake kin!"Marar mutunci!"Meye amfanin zamanki agidana!!!!"Sai nafadawa iyayenki rashin mutuncin da kikayi min."Alhaji yace yana murza goshinsa da ya taso ya kabe!" "Kanka akeji yanzu saki kuma ba fashi!Ko kuma ka hadu da danasani,Saboda banson ganinka arayuwata!"Asma'u tace tare da juya masa baya!" "Cikin bacin rai!"Da zafyn nama ya tashi yana jan kafarsa ransa abace har wurin gadon ya sharara mata mari,ya ce!Asma'u daman ina ragamiki ne saboda Mallam Buba amma na gane bakida tarbiya,ni sa'anki ne da zaki min rashin mutunci,To ubanki zanci sannan in koraki gidan Ku,Na sakeki saki uku!Daman dalili nike nema!!!"Dukanta ya dinga yi,cikin zafyn Nama ta tureshi,tace tafi nono fari,Allah na gode ma yanxu basai gobe ba!"Zan tafi gidanmu...."Sake dukanta yayi abaki!saida ya fashe!Aykuwa cikin bacin rai ta ture shi,saboda taga zai illata ta,da ciki!"Abinka da jiki yafara mayyanta suluuuuu!Sai qasa ya fadi,Nan take kafafunsa da hannu suka kwange!" "Mayafinta ta dauka!Tsalke shi tayi ta fita da akwatinta!harabar ba motsin kowa,bacci suke,Kofar fita tayi,cikin sa'a ta bude kofar ta fita abinta,Misalin sha biyu na dare,kafafun mutane sun dauke,sai yan kadan haka,ababen hawa sun rage,"A hakan Asma'u tajanyo akwatinta cikin duhun dare!"Karnuka na mata haushi!!!"A daddafe ta kawo kofar gidan makera."Tana tafiya tana kuka! Amma faah na farinciki takeyi."Kauren gidan ta tura daga ciki Wanda aka rufe da qaton turmi,tayi sa'a turmin ya fad'i tuiiii..." "Shigowa tayi da akwatinta da kyar!Saboda ta gaji!"Hasken fitilar Baba mallam ce,ta haskake mata ido, "Cikin daga murya yace"Ashe!Waye nan..."Yana kokarin fitowa daga cikin gidan sauron da yake kwance atsakar gidan." "Gabanta ya fadi raaas!!!"Ta ce ni ce!" ''Ke wa!!!" "Ma'u ce Baba mallam." "Da hanzari ya qaraso wurinta yana zare ido,wasu abu ya karanto ya tofa mata,sannan ya taba ta,yace eh,lalle tabbas mutim ce,ba aljana,ba daga gidan uban wa kike!!!? "Hawayenta ta goge,tace Kaka,Alhajine ya dakeni kuma ya sakeni saki uku...Wai domin zai kara aure, kuma yace ko na haihu bayason D'an ya bar mana...."Ta qarashe zancen tana kuka!"Hijab dinta duk jini bakinta yayi suntum.." "Baba malam,Ya hasala!"Sai huci yakeyi!"Ya ce'kwal uba!ni kalle zaiyiwa rashin mutunci!yayi inda akeyi!Allah ya kaimu gobe lafiya!"Muje ki shige lunguku!"Da karfi ya fara buga kofar gidan yana cewa kai Isuhu!!!"Duk mazan gidan sai da suka fito waje,Ganin Kaka da Ma'u yasa su,tsayawa domin sun san tatsuniyar gizo bata wuce koki!"Yusuf ne ya bude kofar yace Baba lafiya!" "Ina lafiya mutumen banzan caan ne ya turo ma'u cikin dare nan harda tsarabar saki,abin bakin ciki babu gyara!" "Duk ranshi ya sosu amma yaki nunawa yace Allah ya sauwaqa shige daga ciki Asma'u kiyi hakuri da kaddara!" "Tana shiga mamanta lami ta rungumeta suna kuka!" "Kaka juyawa yayi ya koma yana masifa!"Tare da tsinewa Alhaji kalle." "Matan gidan sai murna sukeyi,tare da cewa kwadayi mabudin wahala,A haka dai kowa ya koma bacci wasu na murna wasu kuma na bakin ciki." ********Wayewar garin Assabar ya zamewa Asma'u mafi munin rana arayuwarta!"Saboda tunda safe labarin mutuwar kamilu saurayinta ya bazu agarin,Wanda ya mutu sanadin shan maganin bera dalilin soyayyar sahibar Asma'u." "Tashin hankalin da Asma'u ta shiga aciki baya,misaltuwa domin wayewar gari take jira taje gidansu,ta shaida masa mutuwar aurenta,Babban burinta da zarar ta haihu ta auri kamilu!Amma wai ya kashe kansa sanadinta!!!"Kuka Asma'u tayi Wanda akarshe ya haifar da daukewar shedarta ta fadi sumammiya!!!"Lami sai kuka!takeyi yayinda Yusuf ke kokarin yayyafa mata ruwa!"Baba malam ya rude hawaye yakeyi!"Tare da danasani domin tun safe mutane ke zaginsa,Wai ya raba masoya yayiwa yarinya *AUREN DOLE!* har gashi kamilu ya mutu!"Yanzu ga Asma'u ta fadi ba rai!"Duk da baya bari akai yaran gidan sa asibiti, dole yabari aka wuce da Asma'u asibiti babba."Saboda ciwonta ya tsananta!" "Cikin adaidaita sahu suka wuce da ita, Asibitin tare da Baba mallam,Lami da yusuf ,Hankalin su atashe!Suna zuwa aka yanka mata kati,sannan aka bata gado,Likita ya dubata daga karshe dakin haihuwa aka wuce da ita,domin lokacin haihuwarta yayi kusa bacin rai!ya tadota ga jininta ya hau!"A hakan likitoci da ungozuma suka dinga kulawa da Asma'u."Babanta Yusuf sai kai,kawo,yake!Lami tayi zaune tare da tagumi tana jiran hukuncin ubangiji!"Baba mallam ko zaune yake yana tunani aransa ko yaje gidan Alh.kalle domin jin ba'asi saboda sai ya ci mutimcinsa,sai ya nuna masa ba irin jikokinsa ake cin amana ba!!!" "Tafiya sukeyi da sauri domin isa dakin sayarda magani da ke cikin asibiti!!!"Ido sunyi musu jajur,sai suka hango lami....Da sauri Sahura takaraso wurints,uwani da yaransu maza biyu da mata uku na biye!" "Sahura ta ce "Lami Ina Asma'u muna nemanta!" "Hawayen da ke mata zuba ta goge,tare da nuna musu kofar dakin haihuwa!Tace tana ciki!" "Uwani tace"tirkashi Allah ya sauwaqe,Ashe bakusan meke faruwa ba!Mu fa bamu ma san bata gidan ba wallahi!!!" "Baba mallam,da Yusuf ne suka qaraso wurin bayan sun dawo daga masallaci,ganin su sukayi cirko-cirko." "Lami tace"meyafaru sahura,uwani kusanar da ni,kuna nufin bakusan dukan da Kalle yayiwa Asma'u ba!!?" "Duka!Sahura tace tare da Buga kirjinta da zaro ido,Wallahi bamu San ya daketa!Mu dai mun tashi!bamuji motsin su ba har lokacin fitar shi kasuwa,yayi bai fito ba,har sha daya,shiyasa muka leqa dakin bamuga Asma'u ba!kwance mukasame shi harshe ya kare!yana magana bamu fahimta,Shiyasa muka kira yaran gidan da abokinsa aka kawo shi nan,yanzu hakan likita yace mana!!!!Kuka!ne ya kwace sahura saboda bacin rai,majina ta sharce!"Tace wai Alhaji ya hadu da bugun zuciya mai karfi,kuma ya fadi dalilin hakan yasamu mutuwar barin jiki!"Jininsa ya buga sosai,."Yanzu hakan magani ne zamu sayo ashago na ganki,Amma wallahi lami mu Neman Asma'u mukeyi ta fada mana yadda sukayi da Alhaji domin shi harshensa ya kare ba ajin maganarsa!!!"Sahura ta ida zancen tana hawaye!" "Baba malam,da ke tsaye yana sauraron sahura yace "Ai kalle bai gama gani ba!"In banda yana azzalumi yarinya da ciki ka daketa!Kai mata sakin uku!Ta Yaya Allah zai barshi ya kwana lafiya da wannan hakki!!" "Uwani tace Mallam saki fa,innalillahi wa innailaihir raju'un!!!"Mukam bamu da labari!"Har muna zargin Asma'u!!!" "Asma'u batada laifi inaga bayan sun samu hatsaniyar ya korata gida acikin Daren zuciyarsa ta buga akan bacin rai!"Gashi itama sanadin Bacin rai!Ya haifar mata nakuda,kuma jinintaa,hau,sai dai Addu'ah Allah yabasu lafiya!!"Lami tace." "Ameen sukace dukkan su banda Baba malam,da yayi tsaki ya zauna yana jan tasbahar shi,Jikansa madou yazo da hanzari hannunsa,dauke da langa,ya mikawa kakan Nsu,Ya ce Gashi nan inji malam tankari,"ya ce,abata tasha awanke mata fuska," "Madallah Baba mallsm,yace tare da ba lami,taje takai rubutun taimakon haihuwa aba Asma'u tasha." "Amsa tayi ta shige dakin tare da sallama da su sahura da ke kokarin wucewa,Yusuf ko abinda duniya ya dameshi fatan shi Asmau ta sauka lafiya." [1/10, 11:05 AM] Nordin: SHAFI NA SHIDDA **************** "Alh.kalle agadon Asibiti,sai dai Addu'a!Saboda ciwonsa ya tsananta,Komai baya iya yi sai an masa!duk gefen jikinsa na dama ya mutu!!!"Iyalansa sun sha kuka har sun godewa Allah,Gashi baya kula yan uwansa shiyasa suka juya masa baya!"Ba mai zuwa gidansa ko yanzu asibitin ba Wanda ya zo!" "Cikin hutuncin ubangiji bayan tsawon awowin da Asma u ta dauka tana nakuda,Tasha wuya da azaba!A karshe ta haiho 'yartah qatuwa,wacce nauyinta da ya wuce misali,Bayan likitoci sun gama gyara Asma'u da yartah,Dakin hutawa aka wuce da su."Su uwani sun zo sun duba yarinyar cikin murna da godiyar Allah Asma u ta sauka lafiya." "Bayan mintici gab da magariba qannan lami suka bayyana a asibitin da su Gwaggo husai da Mariya suna farin ciki agefe suna tausayin Asma'u tare da zagin Alh.kalle,anan sukaji labarin shima bayada lafiya." "Mutuwar Kamilu,ta kasance abin cecekuce a cikin gari!Kowa da abinda yake fad'a,Wanda a haqiqanin gaskiya,Maganin bera ya sayo a kanti,ya sha saboda ciwon so da kaunar Asma'u wacce aka raba shi da ita akai mata *AUREN DOLE* da Alh.Kalle," "Innar Kamilu tayi kuka kamar ranta zai fita,yaro mai hankali kamar kamilu ace ya kashe kanshi saboda macce,Abin ya kona mata rai!"Saboda ba halinsa bane!"Kowa ya sanyi da nutsuwa!"Wannan kaddarar ta afka masa."Rarrashinta yayyensa da 'yan uwanta keyi!yan gulma ko sunzo daukar rahoto!"Nan ne wata makociyar su Balki ta ce"Allah dai ya sauwaqa ya Baku hakuri malkah,Abin nan shi kadai ake yi kuma duk fa wannan masifa akan *AUREN DOLE* Ku duba nan shekaranjiya wata yarinya ta sanya hetur ajiki tasa ashana ta kone kanta akan *AUREN DOLE* da iyayenta zasuyi mata shi kuma saurayin yana jin labari ya kashe Kansa!!! "Ke balki yaushe wannan labarin ya faru wata mata ta tambaya cike da mamaki." "Wacce ke kusa ga balki tace wallahi ko nan garin ga anyi shi kun mance yarinyar nan Asabe yar gidan dillaliya...da tasha guba akan za'ayi mata *AUREN DOLE* tanada Wanda take so,shima faah ance yanada sana'arsa da yasamu labari,duk kudaden dinkinsa gina yayi ya turbudesu aqasa sannan shima ya sha guba ya mutu!sai lahira." Kuka inna malka ta fasa tace kaicoh!yanxu shima kamilu za a fara jera shi acikin masu kisa Kansu akan soyayyah Allah ka yafe mai ya Allah!!!!" "Kiyi hakuri malkah,wannan kaddara ce!kowa da tashi!haka Allah ya nufa da shi!Domin kowa na yabonsa, Allah dai ya yafe masa!"Inji qanwar ta." "Ameen sauran jama"ar wurin sukace."Nan dai suka cigaba da hirar su da yan gulmace gulmace da yake yanzu an mayarda gidan ta'aziyya kamar gidan buki,Yanzu zaman ba yada wani amfani,ba asamu lada ba akwashe zunubi,Hattara mata!!!!" "Baba mallam ne,Ahanyarsa ta dawowa daga asibiti Wanda da kyar dansa Yusuf ya rarrashe shi,akan yadawo gida ya huta,tunda ma'u tana bacci,kuma tasamu sauki har zuwa gobe, ganin dare yayi."yana shigowa unguwarsu wato Allugu,majalisin su ya biya cikin sa'a yasamu su mallsm Iro,da dauda suna fira!"Da Sallama Malam Buba,Ya isa tare da musayar gaisuwa da su malam Iro." Mallam Iro,Ya ce lafiya yau duk bamu ganka ba!?" "Ina lafiya!Ma'u ce kwance a asibiti!" "Ma'u ko mijinta Alh.Kalle!?Shi mukaji labarin ya fadi rai a hannun Allah!"inji malam iro. "Mallam Buba,Ya ce"Haihuwa ce ma'u tayi shi kuma ance ya hado da mutuwar barin jiki!" "Malam Dauda dake gefe zaune ya ce "Allah ya sauwaqa." ''Ameen,Dauda inji Baba mallam." "Mallam iro ya kalli amininsa cike da damuwa yace "Ashe yaron nan kamilu ya rasu,kanada labarin maganin bera yasha akan jikar ka ma'u da kace har abada shi da ita!" "Haka naji ana fadi agari shi ya mutu kafiri ba wani ba!Allah ya qaddaro Ma'u ba matarsa bace haukar banza ce sukeyi,kuma duk Wanda yace ni ko jikata ne sanadi Allah ya isa!"Mallam Buba yace ahasale!!!" "Allah ya bamu hakuri Buba kasan ita duniya daman budurwar wawace!"Inji Dauda. "Kaga ni daman tahowa niyyi na ganku mu gaisa daga asibiti nake,zan wuce gida na kwanta duk jikina ciwo yake!!"sai gobe idan Allah ya kaimu "To Buba agaida gida Allah ya huce gajiya ya basu lafiya!"Inji Iro "Ameen,Buba yace kana ya nufi gidansa." ************** "Najibullah da amaryarsa Yaseera ne,suka kawowa iyayen su ziyara,Amarya an sha kyau cikin shiga ta alfarma,fuskarta sai haske da sheki take cike da annuri,kyaunta ya qara fita tayi jiki gwanin Sha'Awa,Da zarar kayi tozali da yaseera da najibullah zaka fahimci akwai zaman lafiya fahimtar juna da kwanciyar hankali arayuwarsu,Shi kanshi Najibullah,ya qara cika,kwarjini ya wadace shi,Hankalinsu akwance." "Bayan sun gaisa da iyayen su sun sanya masu albarka cike da farin ciki,cike da murna suka nufi gidansu yaseera nan ma sukayi sa'a kowa na gidan,A babban falon suka same su har yaseer da matarsa Raudhat tana cin Dan wake batada lafiya ta kamu sai kwadayi da sangarta take ma su Umma,suka ma sai rarrashinta ake komai takeso shi ake mata." "Bayan sun gaisa umma ta kira Abbu shima ya fito,Gaisawa sukayi sunyi farin cikin ganin yaseera a kamile,batada wata damuwa,nan fa najibullah da yaseer suka samu wurin fira,Umma madafa ta nufa domin shirya musu abinci,Abbu ma kanti ya wuce domin sayo masu kayan masarufi azuciyarsa yana godewa Allah akan zabin da yayiwa yarsa,Yaseera tuni yawunta ya tsinke ganin qawarta bata sammata Dan waken ba,yasa ta dauke kwanon duka tayi hanyar madafa tana ci tana dariya." "Bayanta Raudhat tabi tana mitar ta bata kayanta ba dandane." "Yaseera tace "nasan ke kade ce mai cikin,to nima ina da lalurar kwadayi." "Umma suka samu tana daura sanwa,Kallon su tayi tana murmushi tace"toupha kun fara ko!?"Shin ke yaseera bakisan batada lafiya ba!?"Dan Allah ki daina wahaladda ita, ki bata Dan wakenta duk kin kusa cinye mata abu,naga dai yanxu yayarki ce ba qawa ba,to raini na meye!?" "Raudat tayi dariya tace yawwa ummana gaya mata" "Dariya yaseera tayi tace''Yanzu Umma,akan dan waken yaya babba ake min hakan!"Nima fa ina son sa,kuma ta ci fa,Amma ba komai nima zance surukar tawa tayi min,sai ma yafi naku dadi!" "Munji Raudat,tace tana yiwa yaseera gwalou, "Nan suka hada hannu suna taya Umma girkin faten tsakin masara da kayan lambu."A lokacin ne ma umma ta fahimci ko yaseerarta ta kamu saboda yawan rufe hanci ba qamshin komai takeso ba da zubarda yawo,Ta ce yaseera kenan kema sai ahankali!?"Sunkuyar da kanta tayi cike da jin kunya." "Umma tace lalle zan qara yiwa Abbu albishir na biyu kenan,Allah ya saukeku lafiya yabaku zuriya dayyaba ya qarou arziki da farin ciki arayuwar ku,Tabbas muna alfahari da samun Ku amatsayin yaranmu,Allah yayi muku Albarka." "Ameen,Umma sukace dukkan cike da jin dadin kalamanta,sannan suka cigaba da ayyukan su." _Allah Sarki,Hakan rayuwar Duniya,take yadda duk ka dauketa da sauki,ko wuya,sai tazo maka ahakan,Zabin iyaye ba aibu ba ne,idan har kayi dace da zabi nagari,Hadisi ne ingantacce,Annabi Muh'd (S.A.W) yana cewa "yardar Allah tana tare da yardar iyaye,haka fushin Allah yana tare da na iyaye"Shiyasa aduk lokacin da iyaye suka baka umurni,to ka umurnin matsawar ba sabon ubangiji ba ne,Domin babu d'a 'a ga abokin halitta wurin sabawa Allah."Saboda hakan mummunan umurni kawai iyayenka zasu saka aikatawa,ka girgiza,musu koshi acikin sigar rarrashi da nasiha,Babu auren Dole,Domin Hakkin iyaye ne su zabawa yaran su maza nagari masu ilimi,mazan da suka yadda da addinin su,da kuma nasabar su tsakani da Allah.Ba domin kwadayi ko buri ba,Saboda wajibi ne suyiwa yaransu Adalci."_ _Abin lura anan duk lokacin da D'a ya bi umurnin iyayensa sai yaga haske arayuwarsa sannan aduk lokacin D'a yake baqantawa iyayensa sai duk al'amuransa su jagule!"Ita Tarbiyya abu ne mai Kyau,arayuwa muyi kokari mu kasance yara nagari wadan da duniya zata yaba!"Kuma iyaye suyi alfahari su,Duk abinda kayi khairan ko sharran kada ka manta yana bibiyar rayuwarka da zuriyarka,Auren zumunchi,Auren Abota,Auren Hadi da sauran su duk sune aka rikede aka mayar *AUREN DOLE!* Saboda da wuya asamu dukkan yaran nason junan su,Daman karshen wuya sai dadi,kuma dogaro ga Allah jari ne,Kunga yadda Yaseera da mijinta najibullah suka kasance abin alfahari ga iyayen su,suka samu jarin rayuwa da haske mai daurewa arayuwarsu dalilin biyayya,Allah yasa mudace Ameen._ *********Tunda Asma'u ta dawo hayyacin ta,take kuka har yanxu takasa hakura da mutuwar kamilu!"'yan uwa da dangi sai hakuri suke bata." "Bayan kwana biyu aka sallameta suka dawo gida!"Sai dai sabon ciwon da ya bayyana agareta bata iya riqe fitsari ko da aka koma asibitin ciwon yoyon fitsari ya kamata aiki akai mata tare da bata magani!"A hakan ta cigaba da fama da lalurar,Bacin rai da suke ciki itada iyayenta baya misaltuwa, "Kishiyoyinta sunzo duba yarinya,Da diyan Alhaji da ke jin haushinta domin aganinsu itace sanadin ciwon mahaifin su,Da kyar da rarrashi suka zo gidan su Asma'u," "Abokin Alh.kalle ya kawo ma yarinya kaya Asma'u zanen atamfa uku,da rago ayanka ma yarinya."Duk acikin kudaden Alh.kalle da ke kwance asibiti babu bakin magana."Gashi yaran sa uku maza suka sako yana kwancen ba lafiya yanzu hakan suna nan zaman gida,mutim dayan ma nata na garaje!"Ga yammata biyu ba mazan aure!"Banda nadama tare da danasani ba abinda ake hangowa acikin idanuwansa da ke zubar da hawaye ba dare ba rana." _"Daman ance idan zaka gina ramin mugunta....."Duk abinda kayiwa Dan wani sai anyiwa naka!"Kayi kokari ka Gina rayuwarka da ta iyalanka akan turbar gaskiya sai kaga sakamako mai kyau,Idan zakayi kayi Dan Allah haka idan zaka aikata kayi Dan Allah,Kasance mai Sara kana duban bakin gatari!"_ "Ranar suna yarinya ta ci sunan (Anna) wato Amina sunan kakar Asma'u Wanda mahaifinta Yusuf yayiwa innarsa takwara!"Duk jama'ar gidan sunji labarin Alh.kalle ya saki Asma'u yanzu kuma ta haihu ta gama iddah." "Mallam Buba ya tausayawa rayuwar da ma'u ke ciki ga raino ga fama da cutar da ke damunta,Yayi kuka da nadama aganinsa kamar shine sanadi!"Saidai ana cigaba da nema mata maganin asibiti Dana gargajiya." "Bayan wata daya abubuwa da dama sun faru,Wanda akarshe mallam buba yayi kokarin kashe duk wata fitina da ta kunno kai agidan makera,da gulma tayi yawa acikinsa,ya hada kan iyalansa duka komai ya zama tarihi,Kuma yace''Daga Asma'u ba zaya qara tilasta Iowa *AUREN DOLE!* ba sai dai da kashedin duk Wanda za a kawowa to akawo mai kirki da ilimi."Idan akasamu sabanin hakan bazai aminta ba!" "watarana da safe mallam Buba ya fita majalisar su, malam Dauda ya samu shi kadai zaune a teburi yana shan kunu,da kosai,da yake yanayin sanyi ne,hantsi na rasa jikinsa,Bayan sun gaisa ne,Malam Buba,ya rokeshi akan ya yafe masa duk abinda yake masa,Dan Allah yayi hskuri!saboda ada can baya ya kullace shi,kamar yana bakin cikinsa,sai yanzu ya gane!kuransa na tilastawa Asma'u auren da bataso domin gashi akarshe abin baiyiwa kowa dadi ba!"na tabbata kai mai sona ne,domin masoyinka kadai ke gayamaka gaskiya!" "Murmushi malam Dauda yayi yace komai ya wuce malam Buba daman naso ace ka fahimce ni amma giyar kudaden da Alh. Kalle ke baka,ta bugeka bakaji baka gani sai yanzu ta sakeka,bayan wasa takarewa Dan kada!!" "Shi *AUREN DOLE* Da kake gani mallam Buba akan gina shi ne abisa tilasta yaro auren Wanda bayaso kamar yadda kayiwa Ma'u!"Sannan mafi yawan lokuta akan samu banbamcin ra'ayi ko shekaru masu yawa tsakanin ita yarinyar da Wanda aka tilasta mata aure."kamar Alh.kalle mai shekaru sittin da ma'u mai shekaru sha bakwai warin yarsa ta kusan biyar,Sannan son abin duniya shine son dukiya gaba da soyayya,irin wannan aure ana yinsa domin tsammanin asamu dukiya,ko hanyar samunta,Yanzu mallam Buba kaga duk abinda kasamu ka Tara adalilin auren ma'u yanzu yaqare gurin nema mata magani!"Meye amfanin badi ba rai!!" "A ganina *DALILIN da ke sa AUREN DOLE!* *sune idan akayi la'akari da iyayen yaro ko mijin suna da nasaba.* *Anayinsa domin kasancewar yaro jarumi.* *Anayinsa Dan kara dankon zumunci ko abota.* *Anayinsa domin kwadayi da son abin duniya!* *Anayinsa domin rashin Sabin hakkin 'ya'ya.* *A karshe anayinsa idan anga yarinya tafara lalacewa.* "Mallam Buba anan ni nasan cewa kaima kasani Alh.kalle kowa yasan cewa ba'san asalin su ba!Taho nataho ne!"Sannan baida mutunci,auri saki yake!Kuma kasan ya tsofewa ma'u sosai,Ance hadda sallah bata dame shi ba!"Amma ka hadashi da yarinya kamila mai kirki wacce dubban mutane sun yaba da hankalinta,ka rabata da Wanda takeso yake sonta!" "Wallahi Dauda na tuba!"Yanzu meye mafita!?"Malam Buba ya tambaya cikin damuwa!" "Malam Dauda yace *"MAFITA* daya ce shi ne Mallam Buba *Adinga yin Aure domin Allah.* *Asan Hukunce-Hukuncen Aure.* *Ladabtar da mata kafin aure* *Sannan Adaina tilastawa 'ya'ya Auren Dole!* "Kaga yin hakan shine mafita!"Buba "Tabbas haka ne nagode Dauda kuma daga yanzu nayi karatun ta nutsu!"Domin ga ma'u nan da ciwon da bamusan raner warakarsa ba!"inji malam Buba yana share kwallah!!" "Allah ya sauwaqa!zanje na karbo kekana wurin tanko mai faci!Iska nakai asaka min tun jiya da dare,malam Dauda yace yana kokarin tafiya!" "To nagode!Dauda sai ka dawo,malam Buba yace,nan ya cigaba da zama shi kadai yana nazarin zantukan Dauda." "Bayan wani lokaci Asma'u ta warke harda Ameena ta yaye tayi wayonta,wacce tuni mahaifinta Alh.kalle ya amsa kiran Allah."Asma'u har tayi aurenta da wani Jamilu duk da auren soyayya ne tayi da shi amma zaman hakuri takeyi agidansa!"Nan taga izina domin auren Marigayi kalle,tace auren dole ne!"Gashi yanzu tayi na soyayya da Jamilu bawani dadi takeji ba!"Sai dai hakuri,Tabbas kowane aure,"Aure ne addu'ar nagari shiyafi dacewa ga kowacce mace!" _Hattara mata da maza masu kokarin hallaka kan su,kashe Kansu,shiga duniya duk akan *AUREN DOLE!* ya kamata kuyi karatun ta nutsu kuji tsoron Allah Ku gujewa sabawa Allah,Ku daina bijirewa umurnin iyaye,matukar kuna son ganin haske da cigaba arayuwar Ku."Wannan shi ake kira da "JIRWAYE NE!MAI KAMAR WANKA,SAi naga Kuma ai gyara kayanka ba sauke mu raba ba!"Amma fa tun rana gini ran zane! Haka komai Nisan jifa qasa zai dawo!ALLAH YAYI MANA JAGORA AMIN._ *_TAMAT BII HAMDILLAH._*