[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI!* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book,special greetings to my siblings ,cousins and My lvly fans that have waited so long for Majidadi,and now am back da wani saban salon,I know u will luv it,cos I am in luv with it too.😘😍😀 Bismillah Page 1~5 Cikin sassarfa ta fito daga bedroom ɗin nata,hannuwanta riƙe da ƙaramin hijab tana ƙoƙarin sakawa ga scul bag goye a kafaɗanta ɗaya.tsayawa nayi tare da ƙare mata kallo sanye take cikin unifoam farare ƙal wando ne jikinta sai riga wacce bata ƙaraso gwaiwarta ba mai tsaga a duka side na rigan .farin socks ne a ƙafanta sai black tom's yayin da hannun hagunta ke sanye da agogon apple black itama hakan yasa na tabbatar da cewa tana karatun likitanci kenan. NIHLA UMAR kenan yarinya mai ƙananun shekaru dan ba zata haurawa shekaru goma sha bakwai a duniya ba.Nihla irin matan nan ne mararsa jiki sai dai tana da shape daidai misali mai kuma matsakaicin tsawo tana da kyau idan nace kyau ina nufin kyau sai dai bata cika haske ba.Nihla ƴa ɗaya tak ga Alhaji Umar. "NIHLA!,NIHLA!"shi ne abinda AUNTY ke faɗa tana ɗan ɗaga murya taci gaba da cewa"ba xaki fito ba sai kinyi latti?". Lumshe dara-daran idanuwanta tayi yayinda dogayen eyelashes ɗinta suka kwanto akan kyakyawar fuskarta cikin siririyar muryarta mai daɗin sauraro tace"Aunty ina xuwa".gyara hijab ɗin kanta tayi tana kuma janyota danta rufe mata gashin kanta dake kwance lub akan goshinta ta fito tana duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta.kai tsaye gaban Abbanta ta isa wanda yake zaune a chair hannunsa riƙe da jarida,ƙafafuwanta ta ajiye a ƙasa tare da ɗaura kanta akan cinyarsa tace"Abbana barka da safiya". Jaridar hannunsa ya ajiye gefe tare da zare eyeglasess din idonsa cike da so ƙauna ya dafa kan NIHLA fuska ɗauke da murmushi yace"barka dai Ammin Abbanta .kin tashi lafiya?". Itama fuskarta da murmushi tace"lafiya qlau Abbana". Kallonsu Aunty tayi tana kuma kissima wani abun a ranta kawar da tunanin hakan tayi ta matso dab dasu tana faɗin "tunda an manta da ni to yanxu na tuna da kaina". Waro ido NIHLA tayi tace"kiyi haƙuri AUNTY ganin Abbana yana mantar da ni komai a rayuwa." Dariya Abban yayi hakan yasa dukansu saka dariya kafin ya miƙe yana riƙe da hannun NIHLA har zuwa diniing area.zaunar da ita yayi tare da haɗa mata tea ya miƙa mata.karɓa tayi tare da soma sha sai da ta shanye tas sannan ya soma bata chips da kansa bataci da yawa ba ta miƙe da sauri tana faɗin"Abbana i'm full kuma xanyi latti". Hannu ya ɗaga mata tare da cewa"to Allah ya tsare sai kin dawo". Da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa AUNTY ta bisu dashi tare dayin ƙwafa tace"tau yanzu kazo kayi break tunda an samu ta tafi scul ɗin". Shafa ciki Abba yayi yace "bari na gama shiryawa ,yau baxan fita da wuri ba". Tankamemen filin da NIHLA ta fito na tsaya kallo lallai an tara dukiya dan gidan yafi ƙarfin ka kirasa da hause sai dai mantion.iya tsaru gidan ya tsaru tana fitowa Sale driver ya ƙaraso da sauri ya buɗe mata bayan motar ƙirar KLK ash colour ta shiga kafin ya zagaya mazaunin driver yaiwa motan key yabar gidan kai tsaye yahau titin dazai kaisa i zuwa makarantar tasu. Tunda Abba ya shiga Bedroom Aunty ta rumtse ido da ƙarfi tana jin zuciyarta kamar xata fasa ƙirjinta ta fito dan takaici,a duk duniya tana matuƙar kishin kulawar da ALHAJI UMAR ke nunawa akan NIHLA sam takan kasa jurar hakan duk da ta kasance ƙanwar Alhaji umar din kuma matarsa ta ko wanne fanni xata ansa sunan uwa ga Nihla saidai sam hankalin baya akan nan. Kamar ko yaushe Sale a bakin gate ya ajiye NIHLA inda ko ina ka duba ɗalibaine birjik yaran masu dashi ga duk ta in da ka duba danƙara dankaran motoci ne ke xagaye da wurin.kai tsaye cikin scul ɗin ta shiga ta isa cikin class ɗinsu.bag ɗin dake goye a kafaɗanta duka yakaiwa MIEMIE dake kwance akan desk,cike da masifa MIEMIE ta ɗago ganin NIHLA yasa ta saki murmushi tace"ae dama masan sai ke". "eh sai ni ,shine kika taho kika barni"NIHLA ta faɗa tana zama. Yatsina fuska miemie tayi tace"ta ina zan jiraki bayan dana shigo gidan babu alamun tashinki ma. Buɗe baki NIHLA tayi da niyar yin magana amma sai tayi shiru ganin har ana shirin fata lecture. Cikin takun ƙasaita da isa na zaratan maza yake safkowa daga stairs ɗin saboda sauri har haɗa bibbiyu yakeyi ga hannunsa dake akan rigarsa yana gyara bottons ɗin rigar black suit din dake jikinsa.Dogo ne sosai fari tas yana da faffaɗan kirji ga kansa dake ɗauke da tulin suma sai sheƙi takeyi tana ɗaukar hankali,yana da long face in da take ɗauke da ɗan ƙaramin pink lips sai sirirn hanci sai kuma eyes ɗinsa masu matuƙar ɗaukar hankali wanda idan ya kalleka dasu zaka ɗauka baccine be ishesu ba yarda suke a lumshe wannan ne ya taimaka wurin rage masa girman idanuwan nasa, DR ZAFAR MUHAMMAD KOFA kenan matashin saurayin da bazai gazawa 32 ba kuma shahararran ɗan kasuwa mai tudin tukiya daji da kansa...cikin sassarfa ya safko cikin babban parlon wanda tsayawa faɗan tsaruwansa ma ɓata lokacine,kai tsaye dining area ya nufa ya kuma kutsa kansa cikin kitchen bai tsaya wata wata ya rungume matar dake tsaye a gaban gas ta baya. Murmushi ta saki cike da so da ƙauna ta ɗago hannunta ta shafa gefan fuskarsa tace"masha Allah Muhammad ya fito ,barka da safiya farin cikin AMMINSA!" Nannauyan numfashi ya sauke tare da cewa"Ammin Muhammad barka da safiya,ina kwana". "lafiya Alhmdllh yaron kirki,muje kayi break nasan ka kusa yin latti"Ammi ta faɗa tana kashe gas ɗin dake gabanta. Tsadaddiyar agogon hannunsa ƙirar gucci ya lalla tare da ƙwaɓe fuska yana jan hannun AMMI suka fito wurin dining ɗin.xama yayi kafin ta fara haɗa masa tea ta miƙa masa.ƙarɓa yayi ya kumayi bismillah yakai mug ɗin baki,idanuwansa ya lumshe kafin ya waresu a fuskar Ammi yace"Ayyah Ammina sugar bai fito ba". Waro ido Ammi tayi kuma a lokacin na samu damar ganin fuskarta nan naga tsantsar kamar da sukeyi da Zafar kamar tayi kaki ta ajiye.baki buɗe tace"Muhammad bazaka daina san zaƙi ba kaikam".karɓar mug ɗin tayi ta ƙara sugar ta jujjuya kafin ta basa tas ya shanye sai dai duk yarda yaso yaci wani abun hakan ta faskara a dole ta haƙura ta barsa ya fita.yana fitowa Kabir PA ɗinsa ya tashi tare da ƙarɓar kayan dake hannunsa suka wuce mota,Masha Allah shine na faɗa lokacin da idona ya sauka akan tanƙameman haɗɗiyan gidan lallai dukiya tayi kuka a wajen. Zagaye tsakar parlon takeyi tare da bubbuga hannu tana huci yacce kasan tayi gasar tsere wani zazzafan huci ta sauke tace"never hakan bazai taɓa yiwuwa ba,Kamal bazan taɓa dauka ba,lallai dole kasan abunyi na gaji da ganin wannan baƙin cikin da nake kan kwasa a kullun".Aunty ta faɗa. Ɗago kyawawan idanuwansa yayi tare da ciza lips ɗinsa da suka ɗanyi duhu kaɗan murmushi ɗauke a fuskarsa yace"duk meye na zafin kan Hajiyata?,kinsan ko me kike buƙata a kuma ko ina yake xan aiwatar maki dashi fatana dai na daina ganin ɓacin rai a kyakyawar fuskar nam taki,karkiji komai Alhaji yana dab da fita daga hanyarki,ki kuma juya komai yarda kike so,wannan alƙawarin Kamal ne ga Auntynsa". Wani ajiyan zuciya Aunty ta sauke tana murmushi da kuma gamsuwa da kalaman Kamal tasan ko meye xai aekata ɗin tunda ya ambata. *ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN KARSHE* JORDERH CE✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 6~10 Jin muryar Abba yana ƙwala mata kira yasa ta juyo da sauri tana roƙon Allah yasa baiji abunda suke faɗa ba,da matuƙar fara'a Kamal ya tashi tare da sunkuyar da kai yace"barka da fitowa Abba". Sosai Abba yaji daɗin ganin Kamal dan sosai yake son yaron saboda yarce yake ganin natsuwarsa da kuma hankalinsa,hannu ya bashi sukayi musabaha kafin yace"Madallah Kamal ya aiki kuma?". Nanma ƙasa kamal yayi da kansa yace"lafiya qlau Abba zaka fita ,Allah ya tsare ya dawo mana da kai lafiya". Shafa kan Kamal Abba yayi fuskaraa ɗauke da murmushi yace"ameen ameen Kamal." Wani kallo Aunty kebinsu dashi ƙwafa tayi kafin tace"Abba kada kayi latti". Juyowa yayi tare da dubanta yace"to Aunty sai na dawo".karɓar jikkar hannunsa tayi tare da rufa masa baya suka fita. tunda lokacin tashin ɗaliban yayi kowa ke ƙoƙarin haramar fita dan ya samu yaje gida ya kawar da yunwa da kuma gajiyar dake tattare dashi wanda hakan yakan kasance ga duk wani ɗalibi hakan kuma ta faru ga Nihla wacce take kwance akan desk kamar mai bacci, kallo ɗaya zaka mata kagane tsantsar gajiyar dake tattare da ita.tsallake desk ɗin Miemie tayi tana saɓa bag ɗinta a kafaɗa tace"idan kin gama baccin kya taho ". Tsuka Nihla taja tana kuma saɓar bag dinta tana miƙewa tabi bayan Miemie.a hankali ta soma jin zuciyarta tana mata dukan ukku ukku kamar zata daka tsalle ta fito da ƙarfi ta matse hannun Miemie dake riƙe cikin nata da maganarta mai in'i'ina tace"Mi..e..mie ina..jin wannan faduwan..ga..gaban". Cike da tausayi Miemie ta kalleta tace"kiyi haƙuri kiyi addu'a kinji komai zai wuce soon zaki daina jin hakan". Gyaɗa kai Nihla tayi dan a lokacin batajin zata iya furta koda kalma ɗaya ne.a haka suka ƙaraso bakin gate ɗin.kamar daga sama Miemie taji anja bag ɗinta .tun kafin ta juyo ƙamshin turarensa ya sanar mata cewa shine saboda haka ta juyo fuska a sake cike da zumuɗi ta langwaɓar da kai gefe tace"Yaya Kamal sai yanzu?,ni gaskiya nayi fushi"ta ƙare maganar tana harɗe hannayenya a ƙirji tare da juya masa baya. Ta gabanta ya zagayo tare da kama kunnuwanaa ya ɗan duƙa ko kadan be damu da tarin ɗaliban dake kallonsu ba yace"affuwan farin cikin zuciyata wani abunne ya tsare maki mijinki da safiyar nan". hararan wasa Nihla tawa Kamal cikin sonyin magana tace"bah..ta..haku..ra ba". Dariya ya saka yace"in dai tiri zaki mun tab zanje na tiraki da naki gwanin IRFAN". Jin ambatar sunan IRFAN da kamal yayi yasa aji kab ta nemi damuwarta ta rasa wani sanyayyen ajiyar zuciya ta ajiye kafin ta kalli Kamal tace"ba za..ka taɓa iya...shi.shiga tsakanin anta da ji..jini ba kamal". Dukan wasa Miemie tayi mata tace"ƴar rainin ƙwalwa to nanma baki samu shiga ba dan tuni na daɗe da yafe masa". "Muje na ajiyeku gida,dan yau babu wacce driver ɗinta zai zo".haka suka tafi suna fira gwanin burgewa Nihla zai fara ajiyewa dan gidansu ne farko kafin ya shiga bayan gidan wato gidan su Miemie,tunda Nihla ta shiga motar tayi shiru abunta kamar bata cikin motar kwatakwata bata cika surutuba ko dan lalurar da Allah ya daura mata wato in'i'ina takan taƙaita magana shiyasa ba kowa ya fahimci tana da in'i'na ba. A ƙofar gate ya ajiyeta kafin sukayi banƙwana .wani iska mai tsananin ɗaɗi da daddaɗan kamshi taji yana ratsata kame jikinta tayi tana murmushi har jerarrun fararen haƙoranta suka bayyana kafin ta juya daidai inda tasan zatayi tozali da farin cikin nata,kuma cikar burinta wato Irfan. tsaye yake fuskarsa ɗauke da murmushi kamar kullun sanye yake cikin riga da wando na ƙananan kaya wandon black jeans sai blue t-shirt an mata rubutu da zanen baƙi,wasu haɗaɗɗun safarars ne a ƙafarsa wanda suka hau har akan wandon hirami ne rataye a kafaɗarsa ga yalwataccen gashin kansa da yasha gyara iska sai busashi takeyi ,IRFAN kyakyawan namiji ne wanda ko wacce mace xata yi burin samu a matsayin miji fari ne tas irin farin ibonnan mai daukar ido yana da tsayi sosai ga faffaɗan kirji duk da ya kasance ba mai kuɗi ba amma yana da rufin asiri ga tsabar iya gayu dole idan kayi masa kallo ɗaya sai ka sake.hannuwansa zube a cikin aljihu ya fara takun zaratan maza ya ƙaraso gaban Nihla hannusa ɗaya ya zaro daga aljihu ya shafa tulin sumar kansa yana kuma tsotsar baki ,ranƙwafowa yayi tare dayiwa Nihla rumfa ya kashe ido ɗaya yace"NIHFAN yada kallo haka?,sai kin gano munina?".ya ƙare maganar murya cike da shagwaɓa. Lumshe kyawawan idanuwanta tayi sai yanzu ta dawo daga duniyar tunanin data lula tana kuma karajin soyayyar IRFAN na ratsa duka wata kafa ta jikinta kallon soyayyah take masa kafin tace"NIHFAN ɗina..ba..bashi da muni...koda akwai shi ba..bazan...taɓa gani ba kuma". Girgiza kai yayi alamar gamsuwa da hakan yasa hannu ya karɓa bag din tata yace"muje na rakaki nasan yanzu gajiya,yunwa da kuma ƙishi sun tarunmun a kanki kuma bazan taɓa lamunta da hakan ba.kai tsaye ƙofan gate ɗin suka nufa a tare gateman ya buɗe masu suka shiga har wurin wata kyakyawar rumfa mai cike da iska da tarin furanni .ta haɗu sosai kafin su zauna ne kuma Aunty ta fito cikin shirin fita,da wani irin kallo tabi IRFAN mai wuyar fassaruwa da azabar ƙarfi zuciyarta kuma ta buga saboda yarda kyan yaron ya tafi da ita .ganin kallon da Aunty kebin Irfan dashi yasa NIHLA cewa "AUNTY fi...ta za..zakiyi ne?".firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lula cikin son kawar da tunanin da takeyi tace"eh Nihla amma bazan jima ba,waye wannan?". ƙasa NIHLA tayi da kai cikin jin kunya tace"AUNTY Ya..ya IRFAN ..ne". Ɗan duƙawa Irfan yayi tare da cewa"barka da fitowa Aunty,ina wuni". "lafiya qlau Irfan yaudai Allah yayi zan ganka,ku shiga daga ciki mana zakibar baƙo a waje haba NIHLA". murmushi tayiwa Auntyn suka mata sai ta dawo kafin suka wuce ciki.tafiya Aunty keyi tana kuma waigen IRFAN harda tuntuɓe.wani irin sanyin ɗaɗi ya kamata tana ganin matsowar cikar burinta tabbas IRFAN shine irin namijin data daɗe tana mafarki ta yaya tana xaune har Nihla ta samu irin wannan guy ɗin?tayiwa kanta tambayar da bata da ansa.dariya ta saki kafin tace"lallai dole na baxa komata na kuma raba ƙafa duk kuma wanda yake niyar hanani FARAUTAR FARIN CIKINA to tabbas ba tantama zan kawar dashi,ka saurareni muradina IRFAN!". *ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE* JORDERH CE✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 11~15 Hannu yasa tare da shafa kansa yanajin matsananciyar gajiya a tattare dashi shigowarsa asibiti kenan yau kam bayajin zai iya aikata komai zagen companies ɗinsu yaje jin wayarsa na ringing yasa ya mayar da kallonsa gareta AMMI shine sunan daya bayyana akan screen ɗin wayar fesar da iska yayi kafin ya ɗauki wayan bakinsa ɗauke da sallama. Daga ɗayan ɓangaren AMMI tace"Muh'd kana jina?". Lumshe kyawawan idanuwansa yayi tare da ciza laɓɓansa yace"na'am Ammi". "duk abunda kakeyi ka bari kazo gida,Hajiya Kaka tana nemanka kasan kuma idan ka daɗe meye zai iya faruwa"cewar Ammi. Damm damm haka zuciyarsa ta buga da ƙarfi yanajin kamar zuciyarsa zata fasa ƙirjinsa ta fito waje kasa furta komai yayi kashe wayan yayi tare da miƙewa tsaye ya tattara abubuwan buƙatarsa ya fito ganin Kabir ya taso ne yasa ya ɗaga masa hannu kawai tare da wucewa.a gurguje yaja motar kai tsaye ya nufi unguwar Nasarawa bai wani daɗe a hanya ba kasancewar babu nisa a tsakanin hospital ɗin nasa da kuma gidansu.horn yakeyi kamar zai huda kunnuwan mutane da gudu Idi mai gadi yazo ya buɗe masa gate ɗin yana kuma masa sannu da zuwa.ko kallonsa beyi ba hakan yasa Idi saurin ja da baya yana tunanin komai ya samu ZAFAR duk da yasan bashi da yawan fara'a amma yana da son mutane da kuma haba-haba dasu. Ko gama daidaita parking beyi ba ya fito da sauri tare da nufar tanƙamemiyar main entarance na gidan ,cikin takun ƙasaita ya ƙarasa cikin babban parlon gidan tsaye ya tsaya tare da riƙe ƙugu yana kuma juya brown eyesball's ɗinsa da suka soma tara ruwa sama sama suka ƙara haske.kanshi ya ɗaga yana kallon stairs ɗin ganin AMMI na safkowa yasa ya kawar da kansa dan bejin ayau zai iya sauraran hakurin da AMMI zata bashi.jin muryar Hajiya kaka a bayan Ammi yasa ya ɗago tare da ƙura mata ido. har gaban ZAFAR Hajiya kaka ta ƙaraso .Hajiya Kaka macace bamai haske ba sosai tana da kyau daka ganta zakasan irin gogaggun matan nanne da suka sha zaman duniya .Fuskarta dauke da murmushi kafin cikin iko da gadara tace"ZAFAR ga ƴar aminiyata nan a part ɗina sunanta Aysha bana son wata magana ko jin ƙorafi kaje ka ganta na gama maganar aurenku da iyayenta,sannan ina so ka sani wannan karon ba wasa nake ba. Wani irin kallo marar fassaruwa Zafar yabi Hajiya kaka dashi,numfashi yaja tare da shafa tattausan gashin kansa murmushi ya saki tare da cewa"ko a zamanin da tsohuwa anbar hakan,balle a wannan zamanin,ina maki gargaɗin daina yomun rakice-rakice wai na aura ni Zafar bana da lokacin mace ma bare kuma harna tsaya kallon xaɓinki". "Da uwarka Maryam kake gata nan tana jinka,to ko ibanka AL-AMEEN yayi kaɗan nasa doka ya karya balle kai karan kaɗa miya ba'a karyamun doka, ba kuma za'a fara a kanka ba Zafar dole kabi abunda nake so".Hajiya kaka ta ƙare magana tana huci. Lumshe idanuwansa yayi tare da waresu akan Hajiya kaka "idan kin tashi ki daina sakamun mahaifiya a ciki,ki sani a yanzu bazan iya ɗaukar wani cin zarafi a kanta ba,shi kuma ae Ɗanki ne dole yabi abunda kike....." "ZAFAR" da masifar ƙarfi Hajiya kaka ta kare kiran sunan tana huci,nuna shi tayi da yatsa tace"nasan uwarka ce ke gaya maka duk wannan to ina so ka sani ita kanta a ƙarƙashin ikona take bata da wani zaɓin daya wuce yimun biyayyah". Buɗe baki Zafar yayi da niyar ƙara yin magana AMMI tayi saurin shiga tsakiyarsu tace"Muhammad kada na sake jin bakinka a wurin nan". Juyowa tayi tana maida kallonta akan Hajiya Kaka tare da haɗa hannuwanta biyu tace"kiyi haƙuri Mama insha Allah zaiyi biyayyah akan zaɓinki". Da wani irin kallon mamaki Zafar yabi Ammi dashi kamar ƙwalwar kansa zata fashe haka yake ji bakinsa na rawa"not at this stage Ammi,bazan sadaukar da rayuwata akan wannan ba,bazata taɓa samun abunda take so ba never". Kallon Ammi Hajiya kaka tayi tace"kisan yarda zakiyi".bata jira cewarsu ba tayi hanyar part ɗinta kamar zata tashi sama. "Zafar meyasa kakeyin hakan?ko ba komai Kaka itace mahaifiyar Abbanka ya kamata ka mata biyayyah kodon darajar haifar Abbanka da tayi". Matsowa yayi tare da kama hannuwan Ammi yana kallonta yace"akan komai Ammina amma banda akan ƙuntata maki da kuma akan rayuwata,dan Allah kada kisa kanki a cikin lamarin dazan kasa maki biyayyah". Shiru Ammi tayi tama rasa abun cewa kafin tace"kaidai kayi addu'a,muhammad bana son rigimar nan dan Allah". Kai kawai ya iya gyaɗawa kafin ya zare hannuwansa daga na Ammi ya wuce sama.Ammi kam zamewa tayi akan chair ta zauna tare da dafe kanta dake barazanar tarwatsewa tana zancen xuci!shin sai yaushe farin ciki zai wanzu a rayuwarsu ada tasha wahala da ƙalubale kala-kala yanzu kuma akan yaranta?innalillahi wa'ina ilaihir raju'un shine abunda Ammi take maimaitawa harta samu taji saukin nauyin abunda ya danne mata zuciya. tunda Aunty ta fita wuri ta samu ta laɓe a mota tana jiran tsammani kamar daga sama ta hango IRFAN yana fitowa daga cikin gida,wani irin murmushin nasara ta saki take daɗi da kuma annashuwa suka lulluɓe duka jikinta a hankali ta taka mota tabi bayan IRFAN sai da taga yayi nisa da gidan babu mai hangosa sannan tayi saurin shan gabansa da mota.soma rage glass ɗin motar tayi,tsaye cak IRFAN ya tsaya yana so yaga waye wannan ya tsayar dashi,ganin Aunty ce yasa yayi ƙasa da kansa kafin yace komai ta fito daga mota fuskarta ɗauke da murmushi tace"sannu dai IRFAN ka fito?". Shima murmushin ya mayar mata yace"eh Aunty sannu da dawowa". Lumshe ido tayi cike dajin daɗi tace"eh IRFAN muje na saukeka naga akwai rana". "a'a Aunty na gode sosai zan ƙarasa"ya bata ansa. "bana son gardama Irfan kamar dai baka yarda dani bane,to kaga tunda ni ke baka son bi ga key ka tafi in yaso anjima da dare ka dawo da ita ,idan kuma kana da abubuwan yi ka iya barin motar a wajenka".bata jira cewarsa ba ta ajiye masa key ɗin tayi gaba abunta. Sake da baki haka Irfan yabi Aunty da kallo kasa cewa komai yayi a dole ya shiga motan ya wuce gida da ita,sam a ransa be kawo komai ba. Zaune a dining Aunty ta samu NIHLA chocolate's ne kala-kala gabanta tana sha.jin maganar Aunty saya Nihla juyowa da sauri tana ɓoye chocolate ɗin dake hannunta. Matsowa kusa da ita Aunty tayi tare dajan kunnenta ta tasheta tsaye tace"watau da kikaga ba kowa gidan shine zaki zauna ki soma shan zaƙi haka Nihla?kinsan matsalarki fa,kin dawo scul da kici abinci sai ki ƙare akan zaƙi ?idan bakya son kanki mu muna san lafiyarki". Kama kunnuwa Nihla tayi da alamun ɓata fuska kamar zata saki kuka tace"I'm sorry Aunty bazan sake ba.kiyi haƙuri dan Allah karki gayawa gawa Daddy".ta ƙare maganar tana faɗawa jikin Aunty. hannu biyu Aunty tasa tare da rungume Nihla a jikinta tana kuma sakin murmushii mai wuyar fasaruwa bare kuma gane in da ya dosa,a fiki kuma tace"that's mah gal,Allah yayi maki albarka". Da ameen Abba ya ansa yana kuma ƙarasa isowa in da suke cike da so da ƙauna yake kallonsu shafa kan Nihla yayi yana kuma kallon Aunty yace"haƙiƙa Fatima ke macace ta gari kuma ta kirki ina rokon Allah ya cike rayuwarki da dukkan haske ya kuma dubeki yarda kika dubi marainiyar ƴata kika riƙeta da kyau tare da bata tarbiya ta gari,irinki a cikin mata kaɗanne Fatima bazan gaji da gode maki ba dan kinyimun abunda har abada bazan taɓa mantawa da ke ba,na gode sosai". Gyara rungumar datayiwa Nihla tayi cike da nuna zallar soyayya tace"Abbanmu ai ɗa na kowa ne,ni baka ganin Allah bai bani ba?koda ma ya bani meye ribata idan na ƙuntatawa Nihla?ae bansan me riƙeni ba a duniya,fatana dai Allah ya bani cikar burina akan Nihla". *ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE* JORDERH CE✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 16~20 Kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki haka Zafar ya gitta Miemie da Ramadan dake tsaye a ƙofar ɗaki,da kallo suka bishi Miemie taja hannun Ramadan sukayi ciki,dafe kanta tayi cike da ɓacin rai tace"Yaya Ramadan kana gani?wacce irin sabuwar rigimar ce wannan tsohuwar ke niyan janyo mana?". Zama gefen bed Ramadan yayi yana sauke numfashi yace"bata so a xauna lafiya ne,and i'm very sure Yaya Zafar baxai taɓawa Hajiya biyayyah akan hakan ba" Hawayen baƙin ciki Miemie ta share tare da cewa "i wish ace Yaya Zafar zaiyi aure amma bana so a tursasa shi akan hakan kasan halinsa". Miƙewa Ramadan yayi tare da dafa kafaɗun Miemie yace"kada ki damu da yardar Allah komai zaizo cikin sauki,Allah zai kawo mana mafita,Allah maji roƙon bayinsa ne,a ko wanne yanayi nasan yana jin addu'armu kuma ina da yaƙinin ya ansa mana danshi a koda yaushe mai ƙarɓawa bayinsa roƙo ne". Murmushi ta saki tare da goge fuskarta tana kuma ƙara jin daɗin kasance tare da Ramadan. Zagaye ɗakin takeyi fuskarta fal damuwa ta rasa meke mata daɗi balle kuma tasan ta ina zata ɓullowa wannan al-amarin dake niyar doso ta,tabbas tasan ba ƙaramin rigima ce tafeba tunda Hajiya Kaka ta kawo wacce take so amma Zafar yaƙi amincewa,ita kanta tasan babu ta hanyar da Muhammad zai amince da wannan shigar danshi kab rayuwarsa bashi buƙatar wani ya masa kutse a cikin rayuwa.tana kuma gudun wahalar da kuma kuncin rayuwar data zauna hakan ya fuskanci yaranta musamman ma Zafar.hannu ta ɗaga sama tare da cewa"ya Allah ina roƙonka ka kare mun yarana ,ka kuma basu ikon jure duk wani abunda zai doso su,yh Allah na roƙeka ka dawwamar da farin ciki a cikin rayuwarsu Allah ka tsaremun Zafar".ta ƙare maganar muryarta a raunane kamar wacce take dab da zakin kuka. A hankali ya tura ƙofar ɗakinsa ya shiga kamar marar lakka haka yake taka tausassan capet ɗin daya mamaye tanƙameman parlon nasa,ɗakin gyare yake tsab sai fitar da masifar ƙamshi yake kamar ɗakin mace komai na ɗakin blue and white ne sosai ɗakin ya tsaru ga ɗaukar hankalo,kai tsaye kan sofa ya faɗa tare da shafa tulin sumar kansa yana kuma furta"hasbunallahu wani'imal wakeel ya Allah".shine abunda Zafar yake maimaitawa tare da runtse dara-daran idanuwansa da ƙarfi wanda harsun fara canza launi saboda tsananin ɓacin rai dake tattare dashi,zamewa yayi ya kwanta yana kuma sauraron bugun zuciyarsa wacce take matuƙar bugawa da ƙarfi,ji yakeyi kamar zata fasa ƙirjinsa ta fito ga wani irin zafin da take masa. Books ɗin dake gabanta take dubawa da alama tayi nisa cikin zurfin karatunta har Aunty tazo ta gitta bata ganta ba,murmushin nasara Aunty tayi tare da ficewa cikin filin gidan kai tsaye ta nufi parking lot,tafiya takeyi tana rawa da jiki ko ina na jikinta yana ansawa sanye take da red atamfa mai zanen yellow da black sosai riga da siket ɗin suka mata kyau gashi sun matuƙar kamata sai fitar da ƙamshi takeyi ko mayafi babu a jikinta.da fara'a ta ƙarasa wurin motonta tare dasa hannu ta buɗe marfin Driver seat.da kallo yabi Aunty shima fuskarsa ɗauke da murmushi ya ziro ƙafafunsa ya fito tare da cewa"barka da dare Aunty ga aro na maido". Murmushi tayi tare dayin far da ido tace"call me NAFISA "tasa hannu ta ƙarɓa key ɗin da yake miƙo mata. Cike da mamaki ya kalleta tana ta wani rawa da jiki basarwa yayi yace"Aunty ina Nihla". Lokaci ɗaya farin cikin dake fuskarta ya ɗauke juyawa tayi kamar zata tafi sai kuma ta tsaya tare da cewa"IRFAN meka gani a jikin wacce siririyar yarinyar daka maƙale mata?hasalima baka da kuɗin kula da gurguwar rayuwarta me zakayi da Sikila ga tarin in'i'na cike da baki,Nihla baxata iya ɗaukar buƙatunka na yau da kullun ba IRFAN ita kanta neman taimako takeyi a duk lokacin da cutarta ta rinca ɓe mata,IRFAN kayi tunani a shekarunka na yanxu shin ƙuɗi kake da burin nema ko Soyayyah?kayi tunani gobe ina jiran ansarka".ta ƙare maganar tana ajiye masa bandir na dubu ɗaiɗaya guda biyu ta wuce abunta. Da kallo Irfan ya bita kamar mai son koyon magana haka ya soma buɗe baki amma harshensa ya masa nauyi ya kasa furta komai face tsare bayan Aunty da ido kamar idanuwansa zasu faɗo ,sai da yaga shiganta ciki sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana bin kuɗin data ajiye ɓasa da kallo.yakai kusan 5mnt yana saƙawa da kwancewa kafin ya ɗauki kuɗin yabar gidan. Jin motsi a bayanta yasa ta juya da ido tabi Aunty da kallo harta ƙaraso gabanta murmushi Nihla ta saki ganin Aunty na binta da murmushi tace"Aunty da..da...daga ina?". Zama tayi tare da janyo Nihla a jikinta,tasa hannu ta soma naɗewa Nihla tattausan dogon gashin kanta dake baje har tsakiyar bayanta tace"na leƙa na karɓi key ne,Nihla ki daina xama ba hula bare kinga yanzu dare ya soma kinji ko?". kai Nihla ta ɗaga ba tare da tace komai ba,kallonta ta mayar ga agogon dake liƙe a bangon ɗakin 8:59pm ta gani kasa ɗauke idonta tayi tana nunanin shin ina Irfan?yau kuma meya hanasa zuwa kuma be kirata ba. Hannu Aunty ta tafa a daidai saitin fuskar Nihla tace"kina tunanin IRFAN ko?". Saurin yin ƙasa tayi da kanta sannan tace"tunda ɗa...ɗazu be ki..ki..kira ba kuma bexo ba". Matsowa Aunty tayi sosai kusa da NIHLA tace"kada ki damu ,may be wani abunne ya tsareshi,kinsan yarda Irfan ke sanki ya kuma damu dake nasan ba ƙaramin abu bane zai tare maki shi harya hanasa zuwa gareki". Murmushi Nihla ta saki kafin ta miƙe ta kwashi books ɗinta ta wuce sama zuwa ɗakinta.harta soma tafiya Aunty tace"ina wayanki?". Juyowa Nihla tayi kamar mai tunanin wani abu sai kuma ta wuce dining area tare da dakko wayan akan table ta miƙawa Aunty. Karɓa tayi ta fake kamar zata tura wani ta shiga contact JININI JIKINA shine sunan da Nihla tayi saving a number IRFAN ,cikin hikima ta kwashe number kafin ta bawa Nihla wayan ta mata sai da safe. Nihla kama ƙarban wayan tayi ta wuce abunta. Dariya sosai Aunty ta saki tana kallon number IRFAN tace"kaine duk wata hanyar kuma bango abun jinginata Irfan,ma damar ka shigo hannuna to ko wanne aiki zai wakana da nasara,kiyi haƙuri Nihla baxan iya bar maki Irfan ba gani ɗaya zuciyata ta kamu da matsanancin son shi na fiki buƙatarshi shiyasa bazanyi jinkiri ko jin kunya wajen FARAUTAR FARIN CIKINA ba Nihla". IRFAN kam tunda ya fita daga gidansu Nihla sam ya kasa gane in da ya dosa tafiya kawai yakeyi yana kuma haɗa step kamar iska zata ɗaukesa ta jefar haka yakeyi babu abunda ke masa yaso sai maganganun Aunty sam ya kasa gane ta yaya zai iya ɗaukar wannan al-amarin,lokacin daya shiga gida yayi sa'a mahaifiyarsa harta kwanta dan haka ya wuce ɗakinshi shirin bacci yayi kafin yazo ya kwanta yana kallon silin saurin miƙewa yayi yana faɗin"zanyi tsaɓi tsakanin soyayyah da kuɗi?,tabbas ina buƙatar kuɗi domin nima rayuwata tayi kyau na kuma taimaki kaina,sai dai kuma itama NIHLA wata ɓangarene ta labarin rayuwata soyayyah ta tsawan shekara 6 ko kuma tulin dukiya?".wani murmushi ya saki har jerarrun fararen haƙoransa suka bayyah lafin ya juya ya kwanta zuciyarsa fal farin ciki.dandanan bacci mai daɗin gaske yayi awan gaba dashi. *ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE* JORDERH CE [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 21~25 Wani irin sukuku haka Nihla ta shiga Ɗaki a bedside drower ta daura book's ɗin data shigo dasu,ji takeyi gaba ɗaya jikinta babu ɗaɗi ko ina ciwo yake mata a hankali ta ɓalla drugs ɗinta ta sha sannan ta ɗauro alwala tayi shirin bacci ta kwanta idanuwanta na kallon sama ta lula duniyar tunani,a hankali wasu zafafan hawaye suka soma gangara ta gefan fuskarta,waya ta ɗakko ta dannawa number Irfan kira amma a kashe taji.wani irin mumunan faɗuwa gabanta yayi hakan yayi daidai da wani irin sarawa da kanta yayi take taji wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufeta ta soma kyarma da rawan sanyi... Next day Da ƙyar Nihla ta soma buɗe lumsassun idanuwanta wanda suka sauya kala saboda tsananin azabar ciwon da tasha da dare,da ƙyar ta iya taka ƙafanta ta shiga toilet wanka tayi tare da ɗauro alwala kafin tayi sallan asuba ,tun lokacin ta soma kiran numbern Irfan amma still har time ɗin a kashe ji tayi wani abu mai nauyi ya tokare mata ƙirjinta take ta fashe da wani matsanancin kuka mai cin rai,ji takeyi a ranta kamar tayi shekara bataji muryar Irfan ba,fatan ta dai ya kasance yana lafiya da ƙyar ta rarrafa ta koma akan bed ta faɗa rubda ciki tana jin ƙasusuwanta kamar zasu karye ko ana buga mata gatari a duka sassan jikinta. Sai 7:30am Aunty ta fito daga bedroom ɗinta sanye da tattausan jan dogon riga na less rigan tayi matuƙar ƙarban jikinta ga ɗaurin zara buhari ta murza a kanta sai wani sanyayyan ƙamshi ke tashi a jikinta,riƙe take da bag ɗin Abba a hannunta shi kuma yana bayanta cikin shiga ta kamala da alama shirin fita aeki yayi,kai tsaye dining area suka wuce fuska ɗauke da murmuahi taja masa kujera ya zauna tare da cewa"sannu da ƙoƙari Nafisa Allah yayi maki albarka"." Ameen ameen Abbanmu,bara na duba naga ko Nihla ta shirya".gyaɗa kai Abba yayi yana kuma ƙarajin ƙaunar Aunty a ranshi yace"ba damuwa".juyawa tayi kai tsaye ta wuce part ɗin Nihla,tura ƙofan ɗakin tayi ta shiga wani sanyayyan ƙamshi ya bigi hancinta ɗakin na gyare kamar ko yaushe kallonta takai ga ɗan ƙaramin pic ɗin Irfan dake ajiye akan ƙaramin fridge ɗin dake ɗakin da kuma tabkeken pic ɗin mahaifiyar Nihla da Abbanta,wani ƙululun takaici yayiwa Aunty tsaye a rai,ji tayi kamar ta kurma ihu dan ganin pic ɗin Umman Nihla,kallonta ta mayar ga bed ɗin da Nihla ke naɗe cikin bed tana faman juyi da murƙusoso.murmushi ta saki cikin ranta tana cewa indai damuwa kika saka a ranki lallai yanzu wannan shegen ciwan sikilan nayi ya fara tashi.da takun sassarfa ta ƙarasa akan bed ɗin tana kiran "Nihla ,Nihla subhanallah meke damunki?baki da lafiya ne?"ta ƙare maganan tana yaye duvet ɗin dake lulluɓe a jikinta tare da kai hannunta akan wuyanta saurin janyewa tayi saboda jin wani irin zafi kamar garwashi ga hawaye nabin kefan fuskarta da ƙyar ta iya buɗe rinannun idanuwanta tana nishi a hankali tace"Aunty ,Aunty Ƙafana zai cire,dan Allah ki ciremun wannan ciwon Aunty bayana kaina hannuna duka ko ina ciwo yake mun Auntyna".saurin janyo Nihla Aunty tayi a jikinta tana mata sannu a rikice tace"kinsha magungunanki kuwa Nihla?" Cikin ciwan azaba ta gyaɗa kanta tana kuma yin goho dajin kamar bayanta zai cire gaba ɗaya. "Abba,Abba,Abba Umar"shine sunan da Aunty ke ƙwallah kira iya ƙarfinta kamar a gaske,rungume Nihla tayi a jikinta sosai wanda a lokacin idanuwanta ke kakkafewa. Kamar daga sama haka Abba yaji muryar Aunty na ƙwala masa kira a rikice,da sauri ya miƙe yayin da duk takun da zaiyi kuma zuciyarsa ke bugawa dib dib dib da sassarfa ya shiga ɗakin Nihla,ganin Aunty rungume da Nihla kuma tana kuka yasa yayi saurin isa a gadon jikinsa har kyarma yake yasa Hannu ya janyo Nihla jikinsa wanda a lokacin jikinta komai ya gama sakewa alaman ta suma,da sauri ya rungumota kamar ya ɗauki baby ya fito da sauri a rikice yake jiran Bala Driver ,da gudu Bala Driver ya iso gaban Abba ganin Abba rungume da Nihla yasa ya nufi mota da gudu ya buɗe masa baya ya shigar da ita,key ɗin ya fizga a hannusa ya tashi motan da kansa tun kafin ya ƙarasa gate ya soma sakin horn a rule mai gadin ya buɗe masa gate ya fice da wani irin masifaffan gudu yanayi yana juyawa baya yana kuma suban Nihla dake kwance tamkar gawa. Tsaye Aunty tayi tsakiyan parlo tare da goge hawayen dake zubo mata tace"Allah dai ya baki ikon cire tunanin yaron nan a ranki dan bazan iya haƙurin bar maki farin cikina ba,ina da yaƙinin na fiki san IRFAN,idan kam baki sakawa ranki haƙuri ba tabbas kin riƙa tashin ciwanki kenan"ɗakinta ta nufa ta ɗauko key da mayafinta ta fice tare da bin bayan Abba itama ta ɗauki hanyar *ZAFAR SPECIAL HOSPITAL KANO*. Bangaren Abba kuwa ikon Allah ne kawai ya kaishi asibitin yana isa ko daidaita parking beyi ba ya fito tare da buɗe bayan ya rungumo Nihla tare da nifo cikin asibitin da ita.Nurses ne biyu suka zo da gudu tare da ɗaura Nihla a bed ɗin mararsa lafiya suka turata zuwa cikin emergency Abba na biye dasu sai da sukaje daidai kofan shiga sannan daya daga cikin nurses ɗin ta tareshi tare da cewa"ƴallaɓai kayi hakuri insha Allah zata samu lafiya ka jiramu".tsaye Abba ya tsaya yana furta kalmar"hasbunallahu wani'imal wakeel,yh Allah ka bawa Maryamata lafiya,Yh Allah yarda ka jarabceni da rashin mahaifiyar Nihla Maryam na roƙeƙa a yanzu ka rayamun ƴata maryam kada ka jarabceni da rashinta a yanzu"ya ƙare maganarsa cike da rauni. Da ɗan sassarfa yake taku cikin ƙasaita da zallar izza sanye yake cikin ash suit sai inner lite blue,yayinda rufaffun tsadaddun takalmansa suka kasance blue hannunsa na hagu sanye yake da tsadaddiyar agogo ta kamfanin gucci,idanuwansa kam suna sanye da siririn farin glasses sai fitar da sihirtaccen ƙamshi yakeyi yau ta kasance ranar Talata kuma rana ɗaya ɗaga cikin ranakun da yake zuwa duba mararsa lafiya a asibitin nashi ,DR ZAFAR shine kuma likitan dake duba Nihla duk lokacin da ciwanta ya tashi idan kaga wani ya dubata to sai wanda ya aminta da aikinsa idan bashi garin kenan sannan hakan take kasancewa.kai tsaye ƙofar emergency ɗin ya nufa ganin Abba yasa ya isa wurin da sauri tare da cewa"Abba kada ka damu kanka insha Allah zata dawo daidai". Gyaɗa kai kawai Abba ya iyayi tare da ɗaura hannunsa akan tulin sumar gashin Zafar murya bata fita sosai yace"Allah yayi maka albarka Muh'd". Da ameen Zafar ya ansa kafin ya shiga ciki dan duba Nihla.yakai tsawon minti 20 kafin ya samu damar Nihla ta dawo cikin hayyacinta allurai yayi mata tare da ɗaura mata drip ya kuma saka mata allurar bacci,nannauyar ajiyar xuciya ya sauke yana kuma jin tausayin Nihla na kamasa yana kuma ƙara mamaye dukkan wani jini,jijiya da ɓargonsa umarni ya bada a mayar da ita ɗakin hutu sannan ya fito shima,hakan yayi daidai da isowar Aunty tana tambayan Abba ya jikin Nihlan,kafe Zafar tayi da mayun idanuwanta wani irin mumunan kallo ya jefa mata wanda yasa hantar cikinta juyawa ta kuma ɗauke fuska da sauri, Zafar kam gaban Abba ya tako tare da duƙawa gabansa yace"Alhmdllh Abbana yanzu tana cikin koshin lafiya tana ɗakin hutu". Hannu Abba ya ɗaga yana godewa Allah daya bashi lafiyar ƴarsa kafin ya ɗaura da godewa Zafar.murmushi yaɗan saki tare da cewa"Abbana ka daina godemun yiwa kaine itama ae kamar ɗaya take da Miemie a wurina". "DR mun gode ƙwarai,Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci ya kuma ƙara ɗaukaka". Wata irin juyowa Zafar yayi yana taune lips ɗinsa kamar zai huda iska mai zafi ya fesar kafin ya tashi yabar wajen.da wani irin mayataccen kallo Aunty tabi Zafar tare da haɗiye yawu muƙuttt kamar a yau ta fara ganinsa kullun idan zata gansa da irin kallon da take binsa dashi kenan. Miƙewa Abba yayi tare da cewa"Hajiya Nafisa muje mu ganta". Firgigit Aunty ta dawo daga duniyar tunanin data lula tana kallon Abba tare da sakin murmushi kafin tabi bayanshi suka shiga ɗakin da Nihla take,drugs Abba ya gani duka an siya kallon nurse ɗin dake ɗakin yayi yace"Muhammad bai gajiya shine ya siya maganin ko?" Fuskarta ɗauke da fara'a tace "eh ƴallabai". Sosai Abba ke jinjina karamci da tausayi irin na Zafar wanda daya biye mahaifinsa da yanzu baya tare dasu balle har ya zama Garguwa ga cutar da Allah ya ɗaurawa Nihla. Ganin Nihla nata baccinta hankali kwance yasa Abba cewa zaije ya dawo amma nazai jima ba,sai da Aunty tayi masa rakiya har ƙofar ɗakin kafin ta dawo ta zauna tana saƙawa da kwancewa a rai. Wayanta ta ɗauko tare da dannawa number Irfan kira,zaune yake a gefan katifarsa yana ɗaure igiyoyin takalminsa da yake sakawa yaji wayarsa na ruri,hannu yasa tare da ɗaukowa,tsurawa number ido yayi ganin besanta ba tana kuma niyar tsinkewa yasa ya ɗauka tare da faɗin "hello" Wani irin lumshe idanuwa Aunty tayi tana jin muryar Irfan na ratsa duka wani lungu da saƙo na sassan jikinta cikin salo da jan hankali ta langwaɓar da murya tace"barka dai farin cikina! haba ya kake son wahalar da zuciyar da tunaninka ya riga ya gama hudata Irfan? haƙiƙa bana da wani sukuni ko farin ciki idan har ka kasance da yiman rowar kanka ko muryarka,ina fatan ka gama tunani dayin zaɓi mai amfami akan tayin dana maka Irfan ina matuƙar sonka kuma na maka alƙawarin yi maka komai sa sadaukar da komai akan soyayyarka,kaine namiji na farko dana fara so ,ina fatan bazaka taɓa bani kunya ba". Tunda Aunty ta fara magana Irfan ya rasa wacce duniya yake shin sama yake ko ƙasa?,duk yanda yake ji sai dai hakan bazaisa ya cutar da kansa ba ko ya kori alkhairin daya doso shi cikin ƙaramin lakaci. Murmushi ya saki yana jin wani sanyi har cikin ransa cike da ɗauki da daɗɗan murya yace"ki ɗauka a ranki cewa IRFAN nakine Auntyna kece mai sarrafa farin cikinsa da duk wani akalar rayuwarsa,Irfan bazai taɓa kaiwa ko ina ba in har babu ke Masoyiyata ,waye zai zaɓi wahala da soyayyah akan kuɗi da tsaleliyar Hajiya irinki,ke kyajyawace danni idan ina kallonki ina maki kallon ƴar shekara 18 ne dan zan iya cewa kin fisu komai ma Hajiyata". Wani irin daɗi farin ciki,natsuwa suka dirarwa Aunty lokaci ɗaya baki na rawa tace"na gode farin cikina,nayi maka alƙawarin sauyawar rayuwanka tun daga yau" *ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE* JORDERH CE✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *wannan page din sadaukarwa ne ga farautar farin ciki fans,ina jin dadin comments dinku dan haka ga kyautar page kuyu yacce kuke so dashi* Page 26~30 Sauke wayan AUNTY tayi tana jin farin ciki na ratsa duka sassan jikinta,ji takeyi kamar duk duniya tafi kowa gata da samun dace,wani irin murmushi ta saki tana cewa"yesss sora kuma plan b yanzu ne lokacina yayi".Jin tarin NIHLA yasa tayi saurin juyowa tana fadin"Alhmdllh sannu Nihla ya kikejin jikin naki?". A hankali ta soma bude lumsassun idanuwanta wanda suka mata nauyi,kallonta takai ga Aunty kafin tayi kokarin sakin murmushi mai kama da kuka cikin nishewan murya tace"ruwa". Karasowa tayi tare da taimaka mata ta tashi,sannan ta zuba mata ruwa a glass cup ta dauka tare da kaiwa bakinta,biamillah tayi ta daura hannunta akan na Aunty ta soma shan ruwan tasha da yawa kafin ta janye bakinta daga cup din tana mayar da numfashi.sannu cewar Aunty.kai kawai ta gyaɗa mata kafin tace"AUNTY Irfan". Wani kallo mai wuyar fassaruwa Aunty ta jefa mata kafin tace "meye ya faru da IRFAN din kuma?". ƙasa NIHLA tayi da kai ta kasa cewa komai ta fara wasa da ring ɗin dake sanye a zara~daran fararen yatsunta.dafata AUNTY tayi kafin tace"Maryam kin ɗaukeni kamar mahaifiyarki,munyi zaman lafiya da Amminki hakan yasa tana haiguwarki ta bani ke a matsayin amana,baki buɗe ido kika ga wata ba matsayin uwa sama dani kuma Allah yasan nayi kokarin riƙeƙi amana Maryam,ki ɗaga ido ki gaya mun damuwanki tun jiya nake lura dake baki da sukuni". Hawayen da suka soma zubo mata a fuska tasa hannu ta share cikin dishewan murya tace"A..a...Aunty sh..shi..shine inata kiransa wayan bata..ta..ta shiga". Murmushi Aunty ta saki tace"na farko dai da zan bawa ƴata shawara ta ɗauka yau dana gaya mata ta kwantar da hankalinta ta daina tashin ciwanta akan IRFAN,duk abunda yake naka ne zaizo gareka duk daɗewa,Maryam bana so ki riƙa raunata kanki akan soyayyar da bata kamace ki ba,kisa ranki a inuwa ki kwantar da hankalin ki in Allah yaso komai zaiyi daidai ,ki daima tashin hankalinki". Gyaɗa kai kawai NIHLA tayi dan ita kadai tasan me takeji a ƙahon zuciyarta,kamata Aunty tayi ta kaita toilet ta hada mata ruwan wanka bayan ta gama ta taimaka mata ta shirya kafin ta tsareta tayi breakfast ta kuma bata drugs,tuni taji daɗin jikinta sai dai rashin ƙarfin jiki. Jib dib dib haka zuciyoyinsu ke bugawa a duk lokacin da suka zo kusa da juna,tsayawa yayi jikin ƙofar tare da runtse ido da ƙarfi kafin yayi ƙarfin halin tura ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.Aunty ce ta ansa sallaman da ido ya bita yana kuma yin kicin-kicin da fuska ya rasa me yasa yakejin tsanar matar nan duk lokacin dazai ganta sai yaji kamar ya haɗiye zuciya saboda tsabar takaici da ƙunci.ɗaure fuska yayi kamar an masa sanarwar mutuwa ya ƙarasa shigowa kai tsaye gaban gadon Nihla ya isa cikin murya da sai ka saurara sosai zakaji me yake fada yace"akwai in da yake maki ciwo ne?". Ɗago dara-daran idanuwanta tayi ta kalleshi suna haɗa ido tayi saurin yin ƙasa da kanta tayi narai narai da fuska kamar zata fasa ihu.wani irin haushi da takaici suka saka ZAFAR a gaba hannu yasa ya bige mata ɗan ƙaramin bakinta da take turowa ya kuma ɗaga hannun da niyar kama kunnenta. Kuka ta saki tayi saurin kaucewa tana faɗin"ni ba abunda yake mani ciwo". Harara ya watsa mata tare da sakin siritin tsaki yayi waje abunsa .bayanshi tabi da harara tana guni ƙasa ƙasa.sarai yana jinta amma beko juyo ba ya fice abunsa. Kai tsaye gida [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *wannan page din sadaukarwa ne ga farautar farin ciki fans,ina jin dadin comments dinku dan haka ga kyautar page kuyu yacce kuke so dashi* Page 26~30 Sauke wayan AUNTY tayi tana jin farin ciki na ratsa duka sassan jikinta,ji takeyi kamar duk duniya tafi kowa gata da samun dace,wani irin murmushi ta saki tana cewa"yesss sora kuma plan b yanzu ne lokacina yayi".Jin tarin NIHLA yasa tayi saurin juyowa tana fadin"Alhmdllh sannu Nihla ya kikejin jikin naki?". A hankali ta soma bude lumsassun idanuwanta wanda suka mata nauyi,kallonta takai ga Aunty kafin tayi kokarin sakin murmushi mai kama da kuka cikin nishewan murya tace"ruwa". Karasowa tayi tare da taimaka mata ta tashi,sannan ta zuba mata ruwa a glass cup ta dauka tare da kaiwa bakinta,biamillah tayi ta daura hannunta akan na Aunty ta soma shan ruwan tasha da yawa kafin ta janye bakinta daga cup din tana mayar da numfashi.sannu cewar Aunty.kai kawai ta gyaɗa mata kafin tace"AUNTY Irfan". Wani kallo mai wuyar fassaruwa Aunty ta jefa mata kafin tace "meye ya faru da IRFAN din kuma?". ƙasa NIHLA tayi da kai ta kasa cewa komai ta fara wasa da ring ɗin dake sanye a zara~daran fararen yatsunta.dafata AUNTY tayi kafin tace"Maryam kin ɗaukeni kamar mahaifiyarki,munyi zaman lafiya da Amminki hakan yasa tana haiguwarki ta bani ke a matsayin amana,baki buɗe ido kika ga wata ba matsayin uwa sama dani kuma Allah yasan nayi kokarin riƙeƙi amana Maryam,ki ɗaga ido ki gaya mun damuwanki tun jiya nake lura dake baki da sukuni". Hawayen da suka soma zubo mata a fuska tasa hannu ta share cikin dishewan murya tace"A..a...Aunty sh..shi..shine inata kiransa wayan bata..ta..ta shiga". Murmushi Aunty ta saki tace"na farko dai da zan bawa ƴata shawara ta ɗauka yau dana gaya mata ta kwantar da hankalinta ta daina tashin ciwanta akan IRFAN,duk abunda yake naka ne zaizo gareka duk daɗewa,Maryam bana so ki riƙa raunata kanki akan soyayyar da bata kamace ki ba,kisa ranki a inuwa ki kwantar da hankalin ki in Allah yaso komai zaiyi daidai ,ki daima tashin hankalinki". Gyaɗa kai kawai NIHLA tayi dan ita kadai tasan me takeji a ƙahon zuciyarta,kamata Aunty tayi ta kaita toilet ta hada mata ruwan wanka bayan ta gama ta taimaka mata ta shirya kafin ta tsareta tayi breakfast ta kuma bata drugs,tuni taji daɗin jikinta sai dai rashin ƙarfin jiki. Jib dib dib haka zuciyoyinsu ke bugawa a duk lokacin da suka zo kusa da juna,tsayawa yayi jikin ƙofar tare da runtse ido da ƙarfi kafin yayi ƙarfin halin tura ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.Aunty ce ta ansa sallaman da ido ya bita yana kuma yin kicin-kicin da fuska ya rasa me yasa yakejin tsanar matar nan duk lokacin dazai ganta sai yaji kamar ya haɗiye zuciya saboda tsabar takaici da ƙunci.ɗaure fuska yayi kamar an masa sanarwar mutuwa ya ƙarasa shigowa kai tsaye gaban gadon Nihla ya isa cikin murya da sai ka saurara sosai zakaji me yake fada yace"akwai in da yake maki ciwo ne?". Ɗago dara-daran idanuwanta tayi ta kalleshi suna haɗa ido tayi saurin yin ƙasa da kanta tayi narai narai da fuska kamar zata fasa ihu.wani irin haushi da takaici suka saka ZAFAR a gaba hannu yasa ya bige mata ɗan ƙaramin bakinta da take turowa ya kuma ɗaga hannun da niyar kama kunnenta. Kuka ta saki tayi saurin kaucewa tana faɗin"ni ba abunda yake mani ciwo". Harara ya watsa mata tare da sakin siritin tsaki yayi waje abunsa .bayanshi tabi da harara tana guni ƙasa ƙasa.sarai yana jinta amma beko juyo ba ya fice abunsa. Kai tsaye gida ya wuce,Kabir ne yake jan motar har suka karasa gida bece komai ba a motan yanata dannar labtop din shi,a parking lot ya ajiye motar sannan suka fita a tsaye ya samu Idi mai gadi yana masa sannu da xuwa,fuskar shi kadaran kadahan ya basa hannu cike da girmamawa yana fadin "BABA IDI barka da ƙoƙari". "barka dai magajin Alhaji,,,,sannu da wowa". Ansawa yayi tare da juyawa yana kallon jerin motocin da aka ajiye ,kafin ma yayi magama Idi yace"yanzu ba dadewa Dan uwanka yaje ya dauko ALHAJI basu daɗe da shigowa ba". Jinjina kai yayi tare da cewa"bara na shiga ciki"a fito lafiya suka masa kafin ya wuce cikin gidan. murmushinsa mai kyan gani ya saki lokacin da idanuwansa suka sauka a kan wani farin kyakyawan Dattijo dake zaune cikin shiga ta alfarma gefansa Ammi ce sai a ƙasa Ramadan da Miemie kowa fuskaraa cike da fara'a.cikin takunsa mai ɗaukar hankali ya ƙarasa gaban Daddy tare da ajiye gwaiwowinsa a ƙasa tafukan hannayenaa ya ɗaura akan cinyar Daddy murya a disashe yace"ko dai nayiwa Daddyna laifi ne,da zai shigo gari ba tare da sani na ba?kuma be nema naje ɗaukosa ba" Janyo hannunsa Daddy yayi ya miƙar dashi ya kuma zaunar dashi a kusa dashi,,hamnunsa ya ɗaura akan kafaɗar Zafar fuska cike da fara'a yace"bana tunanin Zafar zaimun laifin dahar zan kasa saka shi ɗakko ni,naga kana da ayyuka da yawa ne shiyasa nasa Ɗan uwanka ya ɗauko ni". Gaɗa kai Zafar yayi alamar gamsuwa kafin yace"ina fatan ka dawo cikin aminci kuma lafiya qlau?" "lafiya Alhmdllh,ku tashi muje mu gaishe da Hajiya dama jiranka nakeyi ka dawo". Kicin kicin da fuska Zafar yayi tare da danne jajayen lips ɗinsa kamar zai huda amma ya kasa faɗin komai. Miƙewa Ammi tayi tace"to sai kun dawo bara na shirya dining kafin ku dawo". Miƙewa Miemie tayi tana sharara dariya ganin Ramadan yana ta cin magani shima. Wani banzan kallo ya mata yace"hala na zama taaran wasan ki?". Buɗe baki tayi da niyar fara surutun nata,"kada ku dame mu a nan"sukaji Zafar ya faɗa kafin kace me duka kowa ya adana maganar da yake niyar yi suka yi gaba. Tsaki yaja kafin ya miƙe sukabi bayan su Miemie zuwa parr ɗin Hajiya kaka. Sallama ɗauke a bakinsu suka shiga ,zaune yake akan capet tayi ɗaiɗaya ga apple a hannunta tana ci yayin da ƙafarta ke miƙe akan tum tum sai cika take tana batsewa.kallon su ta soma yi ɗaya bayan ɗaya sai da kowa ya gama zama sannan ta saki fuska tace"a'a Aminu sannu da shigowa,ya hanya?yanxu nake cewa na shigo sai ka rigani kuma sannu da zuwa". Kan Daddy a ƙasa yace"yauwa Hajiya,barka da gida ". Ramadan da Miemie ne suka haɗa baki wajen gaiaheta fuska a sake ta ansa tace"ke uwar kilbibi me kila dawo yimun a gida?". Dariya miemie ta saka tace"da kika samu nazo ko?ina nan zaki zo nemana" Sai a lokacin Zafar yace"barka da hutawa". Kamar jira take ta ɗago tana zabga masa harara cike da masifa tace"da ban wuni ba da zaka ganni sarkin mararsa kunya?tun ranar daka gama ɗebemun albarka ka kara shigowa ka gaishe ni ne?to bari kaji dama na tsaya ubanka ya dawo ne sai in ji ta ina ya samoka da har zanaa doka kabi ka take,shege labcecen banza". Wani irin takaici ya turniƙe Zafar yace"dama gudun wannan faɗan naki yasa bana shigowa ɗin,zancen gaskiya kuma a zamanin nan ba'ayin haka ,ido kika fini ne da zaki min zaɓin mata?". Hararan da Daddy ya zabga masa ne yasa ya miƙe da sauri yana ficewa daga part ɗin,KAKA na ƙwala masa kira amma ko juyowa beyi ba bare tasa ran zai ansa mata. "Aminu kana gani,akan idonka Ɗanka ke wulakantani amma ka saka ido kana kallo to ina so kaje ka gaya masa har gidan nan sai nasa ka koreshi dan be isa ya gaya mun maganar banza ba". ƙasa Daddy yayi da kai yace"Hajiya dan ALLAH kiyu haƙuri insha Allah zan masa magana hakan bazai kuma faruwa ba abunda kike so kuma shi za'ayi". Tsaki taja tana faɗin "yadai fi maku wallahi"ta ƙare maganar tana cin apple ɗin dake hannunta.sallama suka mata kafin suka taho. Zafar kam yana shigowa parlo yaci karo da glass jug na ruwa ƙafa yasa ya halbasa ya tarwatse akan tayil lafin yabi ta ciki ya wuce yana huci. Ammi dake tsaye hammunta riƙe da kula ta bisa da kallo ita kam ta rasa wacce irin zuciya Zafar ke gareshi kuma ina ya gadota ita lamarinsa ma har tsoro yake bata,girgiza kai tayi tace"Allah ya shirya,Lantana kizo ki gyara parlon nan"ta ƙare maganar tana ci gaba da harkokinta. Tsaye take da waya a kunne shiru tayi alamar tana jin abunda ake faɗa kafin tace"komai ya daidaita Kamal yanzu shiri na gaba kawai ya kamata,banga dalilin sake ɗagawa ba kuma ina so nan da kwana huɗu komai ya tafi mun yacce nake so". Dariya sosai Kamal yayi kafin yace"da kyau giwar mata cika burinki yana burgeni zuwa gobe zan shigo sai ayi komai yarda ya kamata amma ina so ki kula da kyau". "baka da matsala da wannan"abunda Aunty ta fada kenan tare da kashe waya. a ranar aka sallami Nihla daga asibiti danta warke dama haka ciwan mai sikila yake kamar bugun aljannu. *ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE* *Gobe bazanyi typing ba dan zanyi tafi* JORDERH✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 31~35 Da matukar karfi Zafar ya fizgi kofar dakinsa ya shiga ,jujuya kai ya soma yana jin kamar zuciyarsa zata fasa kirjinsa ta fito dan takaici,hannuwansa duka biyu yasa yana cukuikuya sumarsa,fadawa yayi akan chair yana fesar da numfashi,jiki a sanyaye Ammi ta gama jera abincin ta fito ta haura sama dan duba Zafar. Bakinta dauke da sallama ta shiga dakin,tsaye tayi tana kare masa kallo yacce ya hada kansa da gwaiwa daga gani kasan kwata-kwata bashi cikin hayyacinsa karasowa tayi tare da zama gefansa cikin sanyayyar murya tace"Muh'd? A hankali ya dago rinannun idanuwansa wanda suka soma sauya kala ya zubawa Ammi su ,hannuwansa duka biyu ta runtse cikin nasa tana furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Allahumma ajirni fi musibati wa'akilibni khairan min ha". Kamar mai koyon magana ya soma maimaita duk wata addu'a da Ammi ke karantawa cikin kankanin lokaci yaji zuciyarsa ta masa sanyi kwantar da kansa yayi akan kafadar Ammi yana sauke ajiyar zuciya. Murmushi tayi cikin san jan hankalinsa tace"kada ka sake fushinka ya rinjayi tunaninka muh'd,ko wanne irin hali ka kasance a ciki karka manta da neman dauki daga mahaliccinmu nasan ka sani kuma ka iya amma wannan zafin zuciyar naka ya daina rudarka kaji". Ido ya zubawa Ammi kafin ya dauke tare da furta"insha Allah Ammi zanyi kokarin yin haka". Hannu ta daura a tulin sumar kansa tace"Allah yayi maka albarka muh'd,Allah ya zama gatanka ya kyautata mun rayuwarku kai da y'an uwanka". Wani kyakywan murmushi ya subuce masa tare da furta"ameen ameen Mamana". Janyeshi tayi daga jikinta ta mike tare da kama hannunsa tace"muje kaci abinci". Bai iya mata musu ba haka yabi bayanta har suka safko,a dining suka iske su Abba suna zaune Miemie harta zuba masu abinci suna niyar fara ci. Karasowa sukayi Ammi tace"Affuwan Daddy bansan kun shigo ba". Murmushi yayi yana kai spoon cike da shinkafa a bakinsa yace"don't u worry,ae kara a lallaso sarkin zuciya ,kafin ya gama fushin yazo kuma yayi biyayya akan zabin kakar tasa". Wani irin kwalalo dara-daran idanuwa Zafar yayi baisan lokacin da yace"Daddy badai ka aminta da abunda Kaka ta fada'a ba?". "sam ko daya bana nufin hakan,amma dai ina so ka sani mahaifiyata ce ita dole zan bata duk abunda take bukata daga gareni,aiki ya rage naka sai kai kokarin nusar da ita zabinka final".Daddy ya fada. Shiru wurin yayi babu mai cewa komai kafin Ammi ta zaunar da Zafar ta saka masa abinci,wasa kawai yayi da spoon ya tashi ya kama gabansa ba tare da ya wani ci abin kirki ba. Zaune take yayinda kanta ke jikin kafadar Abbanta mug ne a hannunta na kunu tana sha a hankali,murmushi ya mata tare da shafa gefan fuskarta yace"sarkin rigima ki mayar da hankali ki shanye kunun nan tas kinji,ko kya kara karfi karfi". Zunburar baki tayi gaba kamar tuguhwar tsire tace"Abba nasha da yawa fa ka tambayi Aunty". "sosai kuwa y'ata kinsha da yawa kuma kin kara karfi,ni murnata daya da kika samu lafiya kinga gobe sai school ko?"cewar Aunty Jijjiga kai Nihla tayi tana ansawa da alamar eh. Sallamar Kamal ya katse masu firansu,fuskarsa cike da fara'a ya shigo tare da zama a daya daga chairs na parlon yace"Abbana sannu da gida". Fuska fal fara'a Abba ya mike tare da gyara zamanshi yace"lafiya qlau kamaladdin ya kokari da hididdimu?" Kansa sunkuye yace"lafiya alhmdllh Abba,ashe Nihla bataji dadi ba?dazun nan Aunty take fada mun". Kallon Nihla Abba yayi yace"alhmdllh ai taji sauki sosai ma,a jiya ne jikin nata yadan motsa". Jinjina kai Kamal yayi yace"to Allah ya kara lafiya ya kara tsarewa". Da ameen suka ansa ,sai lokacin Kamal ya gaishe da Aunty sannan Nihla ta gaishe shi tana mikewa tare da barin parlon. mai aekin Aunty ce ta karaso wurin tare da dukawa tace"Hajiya an gama jera abincin". Da to ta ansa ta bata izinin tafiya,sannan ta mike ,kallonta Abba yayi yace"Aunty badan karna baki wahala ba aeda nace kin zubo abincin kin kawo mana a nan,ki hadamun tare da Yarona muci tare". Murmushi dukkansu suka saka kafin Aunty tace"As u wish ranka ya dade". Mikewa kamal yayi tare da fadin bari na tayaki da tattaro wani kayan,be jira ansar kowa ba ya karasa dining din,bin bayansa tayi ta soma harhada abubuwan da zasu bukata,jujjutawa Kamal yayi ya tabbatar babu mai kallonsa kafin ya ciro wani karamin kulli a aljihu cikin bakar leda ya bawa Aunty.Wani irin murmushi ne ya subuce mata kafin ta soma hada abincin ,ta kuma shiga kitchen ta barbada abun a daidai in da tasan zata ajiye a gaban Abba.Kafin ta fito ta kawo masu abincin a lokacin Kamal harya dawo parlon yana jiranta. Cike da fara'a tace"sorry Abbanmu na barka a zaune kai kadai amun afuwa dan Allah mai gidana". "karki damu,ai baki laifi,idan ban jinjina maki ba to bazanga laifinki ko gazawarki ba a wurin kula dani da y'ata sai dai nace Allah yayi maki albarka ya kuma saka maki da gidan Aljanna".cewar Abba. da ameen ameen suka ansa kafin ta kalli kamal tace"bismillah"tare da kashe masa ido daya. Spoon Abba ya dauka ya soma juya lafiyayyar julluf din shinkafa da wake dake gabansa wacce taji zallar naman kaji,ya iba tare da bismillah yakai bakinsa,tuni dadinta da dandanonta ya gauraye bakinsa ya soma taunawa a hankali. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya Aunty ta sauke yayinda zuciyarta ta cika da tsantsar farin ciki wanda take hangosa bazai taba yankewa b,a lokacin ne natsuwa kwanciyar hankali da hango ta farautaro farin cikinta da cikar burinta wanda ta dade tana saka da kwancewa a ranta tun lokacin y'an mataka.Ko kadan fara'a ta kasa daukewa akan farar kyakyawar fuskarta.a haka tana kallo sukaci Abincin Kamal bai wani ci da yawa ba ya tashi,kasancewar anwa Abba abincin da yafi so yasa ya saki jiki yaci sosai.Bayan kammala cin abincin nasu Kamal yadan jima kafin ya tashi zai tafi,Aunty na ganin fitar kamal ta mike da sauri tana cewa"Abbanmu na manta ban basa sakon nan ba,bara nayi sauri kada ya fice kuma". Da to ya ansa mata ya kuma mayar da hankalinsa akan kallon news,itakam ta fite a balcony ta samu Kamal tsaye yana jiranta ,a baranda suka karasa kafin ta kallesa fuska kunshe da doki da fara'a tace"aikinka yana kyau kamaladdin ka sani tukuicinka sai yafi karfin tunaninka". murmushi yayi yace"sai ki fara kirgar awanni da mintina dan yaci,kwanaki sun gajarce ki kumayi sallama da fatan bude sabuwar rayuwarki cikib salama da farin ciki,hakika ina matukar son mata irinki wanda zasu iya sadaukar da komai nasu dan farautar farin cikin su ta ko wacce hanya,badan ina da Miemie na ba da tuni na kutso kaina a sahun manemanki hajiyata". Far da idanuwa Aunty yayi tace"nikan ae ka zama matattakalata zuwa ga farin cikin nawa,kaine Garkuwata kuma sirrina bana yi sai da kai kuma kaima baka yi sai da ni,ko a hakan ae akwai alakar da bazata taba rabamu ba,kaje sai munyi magana". Be kuma cewa komai ba ya juya ya wuce ita kuma ta dawo parlo suka ci gaba da kallo. A daidai wannan lokaci Nihla ta gama yarda da shawarar da zuciyarta ta bata,mayafin dogon rigar jikinta ta janyo ta yane kanta dashi ta kuma janyo bag dinta da phone tayo waje a lokacin tayi sa'a babu kowa a parlon hakan ya kara bata dama da karfin gwaiwar ficewa da sauri daga parlon Idi driver na ganinta ya taso da gudu ,hannu ta mika masa tace"bani key bazan dade ba Zan dawo"sai kin dawo yayi mata tare da bata key din,taja motar tabar gidan. *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* JORDERH CE✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 36~40 A hankali take tukin motar kamar babu in da take san zuwa har ta iso kofar gidan su Irfan,ta dan jima tana sakawa da kwancewa kafin ta bude motar tare da zuro kyakyawan fararen dogayne kafafuwanta kafin kuma ta fito gaba daya,lumshe idanuwanta tayi tana mayar da lumfashi a lokacin da iskar wurin ta buso iska mai sanyi,cike da natsuwa kamala ta soma daya zara-daran eye lashes dinta da suka kwanta akan kyakyawar farar fuskarta .Tun daga kafa ta soma kallon butt shoe din dake sanye a kafarsa ta dago zuwa ga black jeans dake jikinsa ,ga red shirt mai karamin hannu daya saka a gaba anyi rubutu da bakin kala an rubuta handsome a kafadansa kuma hirami ne rataye kamar ko yaushe haka har ta sauke idanuwanta akan fuskarsa ,wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin sanyayyan murmushi ta kuma hada haruffan bakinta wajen furta"Yayana!" Kallonta kawai Irfan yakeyi kafin ya kawar da kansa gefe tare da fadin"yan mata Nihla sai ina❓" Dam dam haka kirjinta ya bada sautin bugawa da matukar karfi,zata iya rantsuwa da Allah wannan karon shine karo na biyu da Irfan ya kirata da sunanta.Wani irin faduwar gaba ne ya dirsan mata a matukar tsorace tace"Yayana ka daina kirana,ka kuma daina zuwa in da nake,ka kuwa san hakan irin cutarwar daya haifar mani❓,ko nayi maka wani laifi ne❓". Daga gira daya sama Irfan yayi yana kuma sakin kyakyawan murmushinsa yace"Maryam matsawa nayi na baki wuri kidan sha iska,kinsan idan ka tsaya wuri daya baka hangen abunda zai zo a gaba hakan yakan zama cutarwa ga rayuwar mutun! ke babu abunda kika nema kika rasa,shiyasa nima na fita neman abunda zan rufawa kaina asiri". Kallonsa kawai take kamar idanuwanta zasu fado,a iya dan karamin tunaninta na shekarunta da fahimtarta ta tsaya ta auna kalamansa amma sam ta kasa fahimtar in da ya dosa,kawar da tunanin tayi a ranta tare da cewa"ban fahimceka ba". Fuskarsa ya shafa kafin yace"is a matter of time,soon zaki fahimta yarayen gwari-gwari,excuse me"Irfan be jira cewar Nihla ba ya juya yayi cikin gida tare da zuba hannuwansa duka biyu a cikin aljihu yana wata tafiyar kasaita.Wasu irin hawaye ne masu matukar zafi suka samu nasarar gangarowa daga idanuwanta zuwa kan fuskarta,dan bubbga kanta tayi taga ko mafarki takeyi,lallai ilaihi kam idonta biyu haka ta raka Irfan da idanuwa harya karasa shigewa cikin gida,dafe kanta tayi tare da fadin"me yake shirin faruwa ne da ni❓"tayiwa kanta tambayar da babu wanda zai iya ansa mata ita.Fizgo marfin mota tayi da sauri ta shige ta kama hanyar gida zuciyarta cike da tunani fal.Wani irin fargaba mai cakude da tsantsar gangariyar tsabtatacciyar soyayyar Irfan ke kuma taso mata ,lokaci zuwa lokaci takan share hawayen dake zubo mata a haka harta isa gida,damuwa ta dabaibayeta ko abincin dare kasa fitowa taci tayi a haka ta kwana tana kallon babu dare mai cike da kunci da tsawo irin na wannan rana data riska,sai wurin asuba kafin wani wahalallan bacci mai cike da mafarkai mararsa dadi iriri data yi.Juye-juye takeyi da kanta kallo daya zaka mata kasan cewa tana cike da tsananin tsoro ga wata irin zufa dake keto mata a duk ilahirin jikinta,duk ACn dake dakin hakan bai hanata hada uban gumi ba,hannuwanta duka biyun rirrike suke da tattausan farin blanket din dake shimfide a gadon,idanuwanta dake rufe sai kyarma sukeyi yayinda hawaye suka yowa gefan kunnuwanta saukar aradu suna zuba babu kakkauta,da matukar karfi ta furta Abba,tare kuma dayin zumbur ta farka daga baccin wahalan daya dauketa,da matukar karfi kirjinta ke bugawa ,da rairafe ta safko daga bed dinta tayi waje da gudu. Zaune yake a chair yana karatun jarida kamar yacce ya saba duk safiya,duk da yau ya tashi bai jin dadi sam balle kuma karfin jiki ,a guje ta fada a kansa tare da rungumesa da matukar karfi tana rawar sanyi tana fadin"Abb...Abba,Abbana".Abba kam sakin jaridar hannunsa yayi tare da rungume Nihla da karfi a jikinsa a tsorace yake duba bayanta ko wani abu ya biyota ne,babu komai hakan yasa ya soma bubbuga bayanta ganin sam bata cikin natsuwa bata ma san me takeyi ba,addu'a ya soma tofa mata kafin a hankali ta fara dawowa daidai ,yanajin yarda zuciyarta ke bugawa da karfi,dagota yayi tare da zuba mata idanuwa hannu yasa ya tattara mata tulin sumar kanta data baje duk a fuskarta yace"menene❓meke damunki haka❓". Numfashi ta mayar tare da zaro kwala-kwalan idanuwanta ta daga hannu tana shafa fuskar Abba,wani sanyayyan ajiyar zuciya ta sauke murya na rawa tace"Abbana kai....Kaine❓" Murmushi ya sakar mata tare da cewa"kwarai kuwa y'an matan Abbanta ni ne da kaina Abbanki farin cikinki maganin matsalarki,meye ya rudani haka❓". Kasa tayi da kai tare da share hawaye tace"Abbana nayi ma..mafarki ka...Katafi ka barni".Cewar Nihla Jan kumatunta yayi yace"kice yau da rigima kika tashi dai,gani a zaune babu in da zan tafi na barki,idan ma zan barki sai na tabbatar na baki Garkuwa wanda da taimakon Allah zai kula mun da ke,bana son maganan maza tashi kije kiyi shirin scul you're running out of time Dear,and look at your body". Sai lokacin hankalinta yakai akan shigarta,sanye take da trouser ash colour iyakarsa rabin cinyarta sai vest,sam ta manta yarda ta fito sai a lokacin taga jikinta,mikewa tayi ta soma tafiya tanayi tana waiwayen Daddy wanda fuskarsa ke dauke da murmushi,tana shiga bedroom ya kuma yin murmushi tare da dafa saitin zuciyarsa wanda yake jinta kamar an daura masa dutse kuma take shirin daina aeki yanzu. Aunty dake tsaye a baya tana kallonsu ta saki dariya ciki-ciki tare da cewa"naga in da karshen soyayya zata kai,duk wannan iskancin zaki daina shi ne nan da lokaci kadan kizo ki fuskanci duniya,katuwar banza da ke amma kina rungumar ubanki har yanzu".Ganin Abba zai juyo yasa Aunty saurin karasa cikin parlon tana fadin"ranka ya dade an shirya komai kazo kayi wanka bana so ka makara a office". Gyadawa Aunty kai kawai yayi ya mike ya wuce daki yayin da ita kuma ta raka bayansa da harara tare da jan siririn tsaki. 30mnt later. Parlon ta fito tana saka agogo a hannunta kamar kullun sanye take cikin white unifoam dinta tayi masifar kyau ga scul bag dinta goye a baya,zaune ta samu Daddy yana zaman jiranta shima sanye cikin farar shadda malum-malum murmushi ne ya yalwata akan fuskarta ta matso kusa dashi da sauri tace"Abba ka...Kayi kyau...So..Sosai". Dariyace ta kwace masa yace" A dan tsoho dani mai sunan Matana❓" Hannu tasa a baki tace"shiiiiii Aunty zata jika"ta fada bayan tayi kasa da muryarta. Dariya yayi kafin ya mike yace "mujr kiyi break,girgiza kai tayi tare da fadin"a'm not hungry yet Abba". Ba yarda ya iya haka sukawa Aunty sallama suka fita ba wanda ya karya a cikinsu,yau Abba da kansa yakai Nihla scul,farin cikinta kam yaki misaltuwa dan zama da Abba ya kawar mata da duk wani kunci da tunanin Irfan. Cup din tes yakai bakinsa tare da surfa kadan ya ajiye cup din ya mike ya tattara keys dinsa yana shigowa parlon "Ammi i'm going" ,shine abunda ya fada. Wani banzan kallo Hajiya Kaka ta masa tace"kai karka damemu da wata shakakkiyar muryarka a wurin nan,ina uwarka❓". Abu ya hadiye da kyar kafin ya raba ta gefen kaka zai wuce,cukuikuyishi tayi tare da janyo shi tace"kutumar uba! dan kaza -kazanka ko Aminu zai mun haka ne❓bare kai lafcecen banza marar mutunci". Runtse ido da matukar karfi Zafar tayi yasa hannu tare da cire hannun Kaka daga jikinsa a kausashe yace"wannan ya zama na karshe da zaki kara rikeni! nasha fada maki Daddy haifarsa kika yi while Zafar a santa kuka hadu,wallahi ina dab da yi maki rashin mutunci a gidan nan" Zaro ido da karfi Hajiya Kaka tayi ko kadan babu alamun mamaki a tattare da ita tace"yau ka fara ne❓ae bazanji komai ba danka wulakanta ni tunda haka uwarka Maryam ta koya maka,ina so ka sani yau zan gwada maka isa da iyawata zanga me zaka iyayi" Murmushi kawai yayi yace"gulmarki da mulkinki su tsaya kan abunda kika haifa da wanda yaji zai iya dauka,ina binki ina maki biyayyah amma tunda kin zaba mu barar da darajar tamu to bismillah,ina kara tunatar da ke ba'awa Muhammad Zafar dole".Be jira cewarta yayi gaba abunsa.Da kallo Kaka ta bisa kafin da karfi ta soma jiran "Aminu,Al-ameen". Da sassarfa Ammi ta fito daga kitchen tana dukawa gaban Hajiya kaka tace"Hajiya ya fita tun safe". "eh dole zaki gaya mun ya fita,shiyasa ashe kika zugo danki yazo ya karemun rashin daraja da tarbiya a kaina❓to bari Aminun yazo gidan ,sai kin gaya mana in da kika samo wancan marar tarbiyar yaron dan ni kam ba jinina bane sam"ta juya ta fice da sauri. Mikewa Ammi tayi tana jin kuna da zafi a ranta,ita kam ta rasa yaya zatayi da matsaltsalun dake dosota,yanzu kam bata san meye Kaka zata kuma zuwa dashi ba. *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 41~45 Kallon time Miemie tayi a agogon dake daure a tsintsiyar hannunta,kallonta ta mayar ga Nihla data zabga uban tagumi ta lula duniyar tunani,buga desk din da suke zaune tayi da karfi,firgigit Nihla ta dawo daga duniyar tunanin data lula a tsorace,kallonta Miemie tayi tare da cewa"malama ki kalla agogo 5mnt da tashi amma ina tsaye a kanki kina tunani". Murmushi Nihla tayi jiki a sanyaye ta mike tare da saba bag dinta a baya tace"muje". Juya ido Miemie tayi tare da fadin"Allah ya sawake,amma kima cirewa kanki tunani akan wannan gantallan yaron". Saurin juyows Nihla tayi fuska daure tace"yanzu Miemie Yayan nawa ne gantalalle❓" Tsaki kawai miemie tayi tace"ko nayi rantsuwa baxanyi kaffara ba,tabbas wannan iskancin daya tsiro akwai dalilinsa gara maki ma ki farka daga mafarkin da kikeyi ki gane a gaske kike". Shiru Nihla tayi batace komai ba taci gaba da tafiya abunta zuciyarta cike da tunani,bin bayanta Miemie tayi suka karasa gate,yau kam Drivern Nihla ya fara zuwa."muje "cewar Nihla. "a'a zan jira Driver nasan yana hanya"Miemie ta bata ansa.Daga kafada tayi alamar ba komai ta shiga mota idi yaja suka tafi.ji tayi wata irin masifaffan yunwa na kartar mata ciki dan duk yau babu abunda ta saka a cikinta ko a lokacin da bata lectures ta gagara cin komai,runtse ido tayi tare da daura hannu akan cikinta ji takeyi kamar ta bude ido ta gansu a gida ,shiru tayi ta soma sauke ajiyan zuciya har suka iso gida,Alhmdllh shine abunda ta fada kafin ta bude motar ta zuro kafarta sannan ta fito gaba daya,tun a bancony ta cire hijab da bag dinta tana shigowa ta jefar dasu akan chair zare shoe da sock tayi ta wuce kitchen ,Murmushi tayi tare da gaishe da Aunty Lami.Dafa kanta Aunty Lami tayi tace"yau an dawo da yunwa ,kin koyi sa'a yau na maki abunda kika fi so". Rungume Aunty Lami tayi tare da cewa "na gode ,yau zanci Danwake". "keee meye kikeyi haka Nihla ❓watau bazance ki daina abuba ki daina,meye na wani rungumarta❓,your'e the princess and u will always be ki kama kanki fice mun a nan". Rau-rau da ido Nihla tayi alamun zatayi kuka murya na rawa tace"Aun...Aunty zan....Zu..Zuba Danwake ne". Shiru Aunty tayi mata ta dauki knife ta wuce waje abunta....Kasa cewa komai Nihla tayi ta wuce kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta dauki plate ta saka Danwaken ta raba ta gefen Aunty lami ta wuce. Da k'yar ya iya karasowa gida,yana tangadi ya samu ya shiga parlon,dafe kansa yayi da karfi wanda ke barazanar tarwatsewa ji yayi lokaci daya komai nasa yana niyar dainawa,a hankali ganinsa ya soma daukewa hakan yayi daidai da tsayawar bugawar zuciyarsa ya kuma zube akan gwaiwowinsa yana jujjuya kai lokacin da wani tari ya turnukeshi,Fitowarta daga kitchen kenan idanuwanta suka sauka akan Abba wanda ke niyar karasa faduwa.Plate din hannunta ta saki ya tarwatse abincin ciki duk ya bata mata fararen kayan dake jikinta da matukar karfi ta furta"Abba" a guje ta kuma karaso garesa ya fado akan cinyarta.Rirrikesa tayi tana bubbuga gefan fuskarsa tare da kiran sunansa.Ganin komai nasa ya tsaya idanuwansa a rufe yasa ta fashe da kuka tana girgiza shi,beko motsa ba hakan ya kuma tayar da hankalinta janye kansa tayi daga kan cinyarta ta mike tare dayin waje da gudu har tana neman kifewa kai tsaye gate da taga an bude tayi a guje,gashin kanta data nannade duka ya tarwatse a bayanta da fuskarta har bata ganin gabanta.Da matukar karfi ya taka burki ganin ta dososa a guje,duka ya kaiwa sitiyari tare da rikesa da karfi yana kallon yarda jikinta ke jijigawa juyawa yayi yana kallon su Idi driver da sauran masu aekin gidan da kowa ya tsaya kamar an dasa shi yana so yaji meke faruwa a cikin gidan,wani irin zafi da kunci ya ziyarci zuciyarsa lokaci daya,da karfi ya runtse idanuwansa da suka soma sauya kala ganin tayi taga-taga zata kife duk rabin breast dinta a waje baisan lokacin daya fizge murfin motar ba ya bude ya fito da sauri,a lokacinne Nihla take neman gittashi ,hannu yasa tare da fizgota da karfi beyi wata-wata ba ya wanke fuskarta da mari cikin kausasshiyar murya yake fadin"ke mahaukaciyar ina ce❓ki kalli jikinki a haka kike fitowa kina gudu maza na kallonki❓"ya kare maganar tare da girgiza kafadunta da karfi. Wasu taurarin wahalane suka gitta mata,ta hadiye busasshen yawu da kyar ,sai lokacin hawaye ya samu damar gangarowa daga cikin idanuwanta ta soma fadin"Abba...Ab...Abbana ka taimaka ..M..Mun" Sai lokacin Zafar ya kuma binta da kallo farar rigar jikinta shara-shara har bra dinta kana kallo,wani takaicin ya kuma rufesa ji yayi kamar ya shakareta uban kowa ya huta a tsawace yace"tsayuwan me kuke a nan kuje kuci gaba da aikin ku mana"sai a lokacin ma'aekatan gidan suka watse jin maganar Zafar cike da fushi. Tsaki yaja yana kallon yarda jikinta ke rawa sam bata cikin hankalinta yasan kome zaiyi ba fahimtarsa zatayi ba,button din black suit din jikinsa ya balle ya zare rigar daga jikinsa ya kama hannunta tare da saka mata,gashin daya bazo mata ya tattare baya tare da daurewa yaja hannunta da karfi har tana had'a steps yayi cikin gidan da ita,sai da suka shigo parlo kafin ya saketa aeko har rige-rigen isa wurin Abba dake kwance suke,sai lokacin Aunty ta fito "innalillahi"ta fada tare da fashewa da kuka tayo kansu da gudu tana fadin"Maryam meya samu Abban❓yaushe ya shigo❓" Tsaki Zafar yaja tare da kuma tamke fuska kamar an aeko masa da mutu yace"ke saka hijab dinki ki taimaka mu saka shi mota" Mikewa Nihla tayi tare da share hawayen dake ambaliya akan face dinta ta soma juye-juye ta rasa ma ina zatayi.Haushine ya kashe Zafar a tsawace yace"wai hauka ne ya shiga kanki ko uban meye❓ga hijab dinki a chair malama" Sai lokacin ta kallah inda ya nuna mata da sauri ta fizgi Hijab ta saka a juye tazo da sauri ta kama Abba,bata da karfi bana da abunda zata iya taimakawa amma a haka ta rike Abba dan daukar gaba daya Zafar ne yayita a haka suka isa mota,shiga tayi ya daura mata kanshi a cinyarta ya rufesu ,be jira cewar kowa ba ya figi motar ya nufi asibiti. Tun kafin ya isa yasa an hada masa komai,mintoci kadan suka kaisu asibitin saboda irin gudun da yayi,a gadon daukar mararsa lafiya aka dauki Abba,a guje Nihla tabi bayansu har suka isa kofar emergency a nan ne Nurse ta tsayar da ita suka wuce da Abba ciki,akan gwaiwowinta ta fadi she's hopeless and spechless ji takeyi kamar ba'a duniyar take ba,gaba daya hankalinta bai kanta da kyar take fitar da numfashi sai haki takeyi,sai lokacin Zafar ya karaso wurin yana gyara xaman handgulofs a hannunsa da gefen ido ya kalleta ya wuce ciko abunsa. Da sassarfa Aunty ya karaso wurin fuskarta tab da hawaye,Nihla na ganinta tayi jikinta ta fada tana fadin"Aunty...Ab...Abba Aunty kice ya ta..tashi kada ya barni". Bubbuga bayan Nihla ta soma yayin da ta saki wani kayataccen murmushi sai kuma ta daure fuska cike da damuwa take fadin"kiyi hakuri insha Allah zai samu lafiya,bazai tafi ya barmu ba a lokacin da muke tsakanin bukatarsa,zai dawo garemu shine Garkuwarmu kuma nasan Allah bazai dauke mana shi ba,ki daina damun kanki kinsan baki da lafiya,bansan ya zanyi da rayuwata ba idan kema wani abu ya sameki ba,bana so ku barni bana da kowa sai ku dan Allah ki kwantar da hankalinki kiwa Abbanki Addu'a". Karar bude kofar emergency yasa Nihla saurin sakin Aunty ta juyo,tsaye tayi tana kallon Zafar da yake tsaye fuskarsa cike da tsananin damuwa ,da matukar karfi kirjinta ya buya ta fara raba ido,cikin sanyayyar murya yace"well Allah yayi ma...."Da karfi ta ingije Zafar tayi cikin dakin a guje..... *Allah ka gafartaws iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 46~60 Runtse idananuwanta tayi da karfi tana karanto duk wata addu'a da tazo q bakinta,gyaran murya yayi tare da cewa"ki shiga Abba naso ya ganki"be jira cewarta ba ya raba ta gefanta ya wuce da sarsarfa da kuma rokon Allah ya bashi nasara akan abunda zai tafi nema.da gudu Nihla tayi cikin emergency din kai tsaye gadon da Abba ke kwanta ta isa gabansa ta duka fuskarta na zubar da hawaye hannun Abba ta riko, Idanuwansa dake lumshe ya soma budewa a hankali kallo daya zaki masa kisan ya jigata ciwo yaci karfinsa,sanyayyan murmushi ya sauke tare da daura hannunsa akan Nihla ya shafa muryarsa bata fita sosai yace"kina matukar kyau idan kina fushi musamman idan kika tura gakin nan a gaba kina hawaye"ya kare maganar tare da dan tura bakinsa a gaba.Murmushi sosai Nihla ta saki tare da share fuskarta ta daura kanta akan kirjin Abba tare da cewa"Ab...Abba ka...ka tsorata ni sosai,..Bana so ka...ka tafi ka barni". Dogon hancinta yaja yace"ita dai Maryam dita da kika gaji sunanta ko kadan ba ragguwa bace,takan tunkari komai ya taso mata takanyi addu'a kuma bata yawan kuka har Allah ya bata nasara akan abunda take nema".Yunkurawa Abba yayi da niyar tashi,tashi Nihla tayi ta taimaka masa ya zauna tare da jingina a bango,gefansa ta zauna hannuwanta cikin nashi tare da tsura masa dara-daran idanuwanta wanda suka sauya launi saboda tsabar kuka. Kallonta Abba yaci gaba dayi tare da cewa"Maryam! bana so ki zama ko yaushe a cikin kuka da kunci,ki sani Allah baya jarabtar bawansa da abunda yasan bazai iya dauka ba,kuma duk abunda Allah ya tsara bashi da mahani Maryama,kiyi kokari wurin bin dokokin Allah ,ki kula da kanki ,Faduwa bashi ke nuna rashin nasara ba a rayuwa,hasalima shine matakin da zaki kara dage damtse ki kuma fuskanci kurakuren ki har ki samu daman gyarawa,ki zama mai gaskiya a rayuwa duk halin da kike ki zama mai gaskiya da rikon amana,babban shawarata a gareki shine a duk in da kike,yanzu ne ,anjima ne,gobe ne jibi ne ko a wanne lokaci ki kasance mai hakuri". Matse hannun Abba tayi da karfi tuni hawaye sun wanke mata fuska kyarma ta kwace mata cikin muryar kuka tace"Abba ..Kana mun ..Ma..Magana kamar Ka..Kana mun wasiyyah...Idan ka ta..tafi waye zai kula dani❓waye zai za..zauna dani❓" Dayan hannunsa ya daura akan nasa yace"ba wasiyyah nake maki ba ,ina baki shawara ne a matsayina na mahaifinki kuma masoyinki mutuwa kam zata iya zuwa ko wanne lokaci ba babba babu yaro,gare ni ko gareki,kina da wanda ya fini Maryam,Allah shine gatanki kuma shine zai yi yanda yaso da rayuwarmu ,Allah baya daukewa bawa wani abun ba tare daya basa wani abun ba". Aunty ce ta shigi dakin hakan yasa Abba kura mata idanuwa da wani irin murmushi a fuskarsa mai wuyar fassaruwa,maido da kallonsa yayi ga Nihla yace "kije gida ki canza kayanki ki taho mana da abubuwan bukata".Shiru tayi girgiza hannunta yayi tare da cewa "ba abunda zai faru kije kinji".Gyada kai tayi tare da mikewa ta fita daga dakin. Hannuwansa zube a cikin aljihun wandon suit dinsa ya shigo parlon nasu,tafiya yakeyi cikin kasaita,izza da isa tafiyar yakeyi kamar marar lakka a jiki sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke ganin Ammi da Daddy zaune a parlon sosai yaji dadin ganinso rufaffun takalman kafansa ya zare tare da karasawa cikin parlon a kasa ya zauna gaban Ammi da Daddy kansa na kallon kasa. Dafa kafadunsa Daddy yayi tare da cewa"meke faruwa Zafar❓ yanayinka ya nuna kana son wani abu" Dago jajayen idanuwansa yayi tare da hada hannuwansa biyu kamar zai fashe da ihu yace"Daddy ,ina matukar sonka! ina kuma alfahari da kai,kaine daya wanda nake da zan nuna a duniya nayi kuma alfahari da duk abunda na nema kana kokarin bani,Shin Daddy kana sona kuwa❓ kuma a shirye kake da sadaukar da komai a kaina❓" Matsowa Daddy yayi daga jingine a jikin kujera da yake cike da matukar mamaki da tarin tambayoyi yake kallon Zafar sannan yace"me yake faruwa da kaine Zafar❓ wannan wacce irin tambaya ce❓" Kasa yayi da kansa yaci gaba da cewa"Daddy ka ilmantar dani ,kuma ka koya mun tarbiyyah babu ta in da ka rageni ,kai ka biyamun islamiyyan da nayi karatu nasan abunda Allah da manzon sa suka ce,ina neman alfarma a gareka da rokonka akan ka taimaka ka tashi muje asibiti kaga Babban Amininka Abba Umar,tabbas yana cikin matsanancin hali da babu wanda ya kamata ya zauna tare dashi sama da kai,ina rokonka ka manta baya ka manta komai kaje ka rungumi amininka ko da sau daya ne komai zai faru dashi ya faru a gabanka,Daddy ina mai takaicin gaya maka Abba Umar an ciyar dashi guba mai tsananin karfin data kwana biyu a jikinsa tana yawo,ina mai gaya maka yanzu haka yana matakin karshe da bazai iya haura y'an awanni ba a duniya,munyi iya yinmu sauran kuma yin Allah ne Daddy". Tunda Zafar ya fara magana komai na jikin Daddy ya tsaya cak,kallon Zafar yakeyi kamar yau ya fara ganinsa da matukar sauri ya mike tsaye tare da furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,hasbunallahu wani'imal wakeel".Ammi kam tuni fuskarta ta jike jagab da hawaye gaba daya ta rasa natsuwarta ganin Daddy yayi hanyar fita yasa ta figi mayafin dake kusa da ita ta bisa baya harda dan gudu-gudunta.Da sauri Zafar ya mike shima yabi bayansu kafin ya fito har su Daddy sunbar gidan,motarsa ya shiga shima ya rufa masu baya,sosai ya tsorata da yarda Daddy ke driving din ikon Allah kawai ya kaisu asibitin,ko daidaita parking beyi ba ya fito da sauri Ammi tabi bayansa,wata Nurse ya tambaya ta fada masa in da yake be jira komai ba ya wuce emergency din.Yana shiga idanuwansa suka sauka akan Abba dake kwance tamkar gawa idanuwansa a lumshe ga Aunty zaune a kusa dashi sai magana take masa amma ya ki kulata,gaban bed din Daddy ya karasa tare da daura hannunsa a hannun Abba,wani sanyi ne ya ratsa shi tun daga kasan kafarsa har izuwa tsakiyar kwakwalwar kansa wasu sanyayyun hawaye ne suka soma zuba ta gefan idanuwansa ko be bude ido ba yasan Al-ameen ne,haka kuwa akayi Daddy yace"Umar ka gaya mun wanda yayi maka haka,na maka alkwari ko da komai nawa dana tara zai kare zan kare rayuwata wurin nema maka hakkinka". Sai lokacin Abba ya bude idanuwansa tare da kallon Aminin nasa ya saki murmushi,idanuwansa ya sauke akan Aunty sai lokacin ya kulata yace"ki bamu wuri".Jiki a sanyaye ta mike tare da bin gefan Ammi ta wuce waje tana sharar kwalla.Murmushi Abba ya saki tare da cewa"wannan farin ciki kawai ya sakani Al-ameen ta dalilin hakan yau gashi tsawon shekaru ka dawo gare ni,ni hakan ma ya isheni ina kuma so kamun alkwari ko bayan raina kaji wanda yamun hakan ka barsa kada kayi kokarin daukar mataki balle tona asirinmu". Zama Daddy yayi tare da cewa"bana da wanda yafi mun kai,kuma kake kokarin sakani yafewa wanda ya cutar mun da kai❓" "ka yafe mani"shine abunda Abba ya fada.Saurin rikesa Daddy yayi yace"a kullun rana bana da burin daya wuce kasancewa tare da kai,bansan da wacce fuska bane zan iya kallonka ni ya kamata na baka hakuri,nikan na manta komai na kuma yafe maka". Hawaye ne ya zubo masu su dukkansu,dariya sosai Abba yayi tare da cewa"ta yaya ni da kaina kuma zan iya fushi da farin cikin rayuwata! kullun cikin Farautar sa nake da neman ya dawo a rayuwata".Tashi yayi zaune suka rungume juna,sosai farin ciki ya ziyarci zuciyar Zafar dake tsaye yana kallonsu,hannu ya tafa tare da sakin dariya ,sosai dariyan tayi masa kyau,kasancewar yaune rana ta farko da fuskarsa ta kasance da yalwatacciyar dariya haka..... Da saurinta ta dawo tsaye tayi a bakin kofar emergency din ,jikkar hannunta ta saki tuni jikinta ya kama kakkarwa ta tsurawa Daddy da Ammi ido da suka fito fuskar Ammi duk hawaye yayin da Daddy ke goge idanuwansa da gefan babbar rigarsa. A guje tayi cikin dakin,tur kashi nan ake yinta tsaye tayi kamar statue ganin Zafar yaja zanin gado tare da rufe Abba dashi cikin sanyin murya yana fadin"Allah yaji kanka Abba,Allah ya kama rahma". Wata irin gigitacciyar kara Nihla ta saki tare da fadin"Abba"da matukar karfi,kafafuwanta kasa daukarta sukayi kyarma suke mata da rairafe ta karasa jikin bed din ta jaje zanin gadon ,fadawa tayi a cikinsa tare da sakin wani irin kuka mai ciwo,cin rai da kuna zuciyar mai sauraro,gaba daya ta firgice ta gama fita a hayyacinta. *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 61~65 Runtse ido da karfi Zafar yayi,dan ko kadan baya son hayaniya yanzu zata sauya tunaninsa gaba daya,hannu yasa tare da dago Nihla daga jikin Abba ido cikij ido ya kalle tare da cewa"pray for him,banga amfanin kukan ba"yana gama fadin hakan yayi waje da ita yayin da aka hada gawar Abba zuwa gida,tun daga wannan lokacin wani ciwan kai mai tsananin zafi ya dirarwa Nihla ko kadan ta nemi hawaye ta rasa wata irin kuna zuciyar keyi shiru tayi sai raba idanuwa takeyi kamar wacce tayiwa sarki karya a haka take zaune kamar wacce aka dasa har suka isa gida,da kyar ta samu damar taka kafafuwanfa saboda wani irin kyarma da suke mata ta samu ta shiga parlo tare da fadawa akan kujera ,sam bata gane komai bare kuma hakurin da Ammi ke bata,da ido tabi gawar Abba da kallo wanda Alhaji Al-ameen wato Daddy da Zafar da wasu ma'aekatan asibiti da suka dauko har suka bacewa ganinta.Aunty dake jikin window dakinta tana leke tabe baki tayi tare da fadin"saboda wulakanci da neman sababi wai sai an kawo man gawarsa a gida ,uban meye zai mun in ba salan a bata ma mutane tayil da carpet din gida ba,ko kadan basu kyautata mani ba wallahi". Murmushi kamal dake jinta a waya yayi tare da cewa"duka minti nawa zaiyi a gidan da har zaki damu kanki Hajiyata❓yanzu ae farin ciki ne naki kin rabu da Allah kakai sai kuma ayi shirin fara sabuwan rayuwa"dariya suka saka Aunty na fadin"wallahi Kamal baka da dama". "kice bama da dama dai ,gani nan shigowa gidan yanzu kin sanmu akwai saurin rakiya kabari"Kamal ya kare maganar yana kashe wayar hannunsa. Sai lokacin ta zira Hijab ta fito parlon ita ma,a hankali gidan harya fara daukar mutane dan parlon babu masaka tsinke,tana fitowa kowa hankalinsa ya koma kanta bata san lokacin da ta kakaro hawayen dole ba,anan masu kuka suka fara masu bada hakuri suka fara zama tayi kusa da Ammi tana sharar kwallah,Nihla kam da ido kawai take binsu ko kwakwaran motsi ta kasa yi. Cike da natsuwa ya shigo cikin parlon tare da cewa"Nihla kizo kiwa Abba addu'a,sai kuma iyalin shi"Zafar ya kare maganar yana komawa ciki,zumbur Aunty ta mike tayi gaba har hada steps takeyi.Girgiza Nihla Ammi tayi tare da mata alama da ido akan tabar damuwa.Jijjiga kai tayi tare da mikewa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tayi hanyar dakin Abba har ta iso bakin kofar,tsaye tayi tana jin yarda bugun zuciyarta ke tsananta,kokarin tattaro sauran kuzarinta tayi tare da daga kafarta ta shiga dakin tare dayin sallama ciki ciki,karasa tayi a in da gawar take ajiye tare da durkusawa akan gwaiwowinta. Kuka rurus Aunty keyi tare da fadin"Allah kajikan mijina,hakika nayi rashi wanda bazai musaltu ba ,bani da wanda ya fika ba kuma zan taba samu ba,tunda nake da kai baka taba cuta mani ba,halinka na gari ya bika Abbanmu,ka tafi kabar mani y'ata marainiya,insha Allah zan rike Nihla kamar nice na haifeta Allah ya maka rah..."maganarta ta sarke sakamakon wani sabon kukan daya kubce mata mikewa tayi da sauri tare da barin dakin tare da toshe bakinta.da kallo kowa ya bita.Hannun Nihla na kyarma ta dauka tare da daurasa a jikin Abba,trying had not to cry,da kyar ta iya bude baki tare da fadin"Allah yayi maka rahma,Allah yakai haske kabarinka,zanta yi maka addu'a kai da Momyna"hannunta ta janye tare da dukar da kanta kasa.Saurin dagowa tayi tana kallon su Zafar da suke kokarin daga Abba daga dakin,Tashin hankalin da ba'a saka masa rana tuni ganinta ya fara komawa dishi-dishi yarda numfashinna ke fizga,shakar iska na kokarin kubucewa hunhuna,ashe ko bayan dara akwai wata caca,tirkashi,bugun zuciyata sai kara jaddada mani rashin kwarin daukar nauyin dake shirin hawanshi,hawaye ne dana dade ina farautar su ruwa a jallo,a mamakina sai ga su suna tsiyaya tamkar idaniyar ruwa mai wuyar toshewa,sai lokacin ta fara hasko tsantsar tashin hankalin rasa Abbanta da tayi,sanadin idasa fitar da akayi dashi yasa ni saurin mikewa tare da fara tafiya da sassarfa,yayin da gabobin jikinta ke nuna tsantsar gajiyawa wurin tafiya.Tafiyata baya rasa nasaba da jarumtar dana dauko na saka wa kaina.Dole kanwar naki.Wani irin zullumi tare da karyewar zuci suka dirsan mun nayi faduwar kasko akan kafata ragab haka na fada,lokacin da aka ida fitar da gawar Abbana daga cikin gidanmu,sunkuyar da kai nayi tare da bude busasshen bakina na furta"ya Allah".Tari ne ya turnike Nihla kan kace me? cikin kuka ta furta"yauce rana mafi muni a gare ni,tunda na ga fitar Abbana ta karshe daga gidan mu".Ban kuma sanin in da kaina yake ba saboda tsantsar ciwo da kuncin da zuciyata take ciki,tuni Sikila tace mun salamu alaikum da sauran ciwa ce ciwacen da ba'a rasa ba,sai ranar sakadakar ukku na dawo hayyacina na fara rarrabe tsakanin mutuwa da rayuwa.Na fahimci Mahaifina yamin gatan da ba ko wacce y'a ke samu a wurin mahaifinta ba.Nayi kuka nayi kuka in da Yaya Zafar ne kawai ya kasance mai lalashina,ban kuma sanin gidanmu ya tashi daga gidan farin ciki ba ya koma mana kamar makabarta sai bayan sati daya da kowa ya gana watsewa duk da a lokacin na dawo hayyacina bana jin ciwo sai dai tsananin fargaba da damuwan da suka yiwa ruhina kawanye tare da lullube ni,kewar Abbana da fargabar sabuwar rayuwa wanda take cike da duhu da kuncin rasa mahimman mutanan da nafi so fiye da kaina a rayuwata dan a yanzu kam na ida tabatarwa Irfan ya gama sallama rayuwata gefe. Parlo na fito duk da tsananin raman da nayi hakan be boye tsakanin kyawuna ba,saurin nemawa kaina burki nayi tare da kwalalo dara-daran idanuwana kamar zasu fado kwakwalwata na niyar juye mani sakamakon ganin Irfan da Aunty da nayi zaune akan kujerar parlon mu tana mika masa lemu a kofin tangaram. Murnushi Aunty ta saki tare da cewa"yauwa Nihla sannu da fitowa ,karaso ki gaishe da sabon Abban naki". Dam dam haka zuciyata ta buga kamar fashewar bomb na tattaro kalaman Aunty cikin rashin fahimta nace"wa..Waye Ab..abbana kuma❓"na jefa mata tambaya. Cikin takun kasaita da isa ta iso gareni tare da dafa kafaduna tace"Nihla Irfan shine wanda nike so a yanzu ko nace muke son juna,kuma shine dana gama takaba zamuyi aure insha Allah,kinga kuwa shine sabon Abbanki wanda zai kula dake". Saurin ture hannun Aunty nayi daga jikina,ina mata kallon da ni kaina bansan ma'anarsa ba cikin kyarmar baki nace"Aunty...Ir..Irfan fane...Masoyina...Ko kin ma...manta shine ke zuwa wurin y'arki❓" Shafa gefan fuskata tayi tare da cewa"na sani mana,tunda ba aurensa kike ba ae hakan bai haramta ba". Dafe kaina nayi da karfi tare da nufar hanyar dakina a guje ina dafe da saitin zuciyata dake barazanar tarwatsewa. Aunty kam wurin Irfan ta koma tana fadin"kasan sha'anin yara sai a hankali,amma cikin lokaci komai zaiyi daidai" Dariya yayi tare da fadin "hakane matata" *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 66~70 Nihla kam tana shiga dakinta ta banko kofan da karfi,saman bed ta fada tare da sakin wani irin kuka,,,gaba daya jijiyoyin kanta sun fito rudu-rudu,tashin hankali! tsantsar tsoro da fargaba sune sukayi nasarar tasiri a cikin zuciyarta gaba daya,ji tayi kamar a yanzu ne ta fara son Irfan jin soyayyarsa na kuma bijiro mata,tashi zaune tayi da sauri tana bubbuga kanta da jujuyawa tana karewa dakin kallo,gani takeyi kamar mafarki take yi,ina! komai yake faruwa da ita a zahiri ne,dafe zuciyarta tayi da karfi naji kuma jin gazawan zuciyar nata wurin daukar gaggarumin nauyin dake shirin hawanta,soma karanta duk wata addu'a da tazo bakinta take yi,a hankali hawaye masu dumi suka soma zarya akan kyakyawar fuskarta. Shigowarta gate din gidan kenan,fuskarta fal fara'a ta kalli Irfan dake shirin fita,cike da zolaya tace kaga Nihfan ,halan an zo ganin masoyiyar ne ❓ku da bakwa iya rabuwa da juna ko yaushe ana mak'ale. Yaken dole Irfan ya saki tare da cewa"Miemie baki da dama,hali dai na nan". Dariya tayi tare da cewa"in dai halinku na nan ae muma na mu da soyayyar ke burge mu ba zai tafi ko ina ba".ta kare maganar tana wucewa ciki.Da Sallama ta shiga parlon babu kowa sai Aunty dake zaune tayi daya kan daya tana kurbar lemu a hankali ,ajiye cup din tayi fuska fal fara'a tace"a'a yau Miemie ne a gidan namu❓tun bayan rasuwa rabon ki da gidan nan kenan" Kasa Miemie tayi da kai alamun jin kunya,sosai take jin kunyarta dan tana ganinta kamar mahaifiyar Kamal ce cikin sanyin murya tace"Aunty makaranta ne bata bari,yau ma na dawo da wuri ne shiyasa na samu damar zuwa"sosai suka gaisa kafin ta tashi ta wuce dakin Nihla,tura dakin tayi tare da shiga,kwance ta hangota a bed tayi rub da ciki,tausayinta ne ya kamata dan tasan lallai anwa Nihla rashi,tasan irin tsantsar soyayyar dake tsakaninta da Abba,karsawa tayi tare da zama akan gadon tasa hannu tare da dafa bayan Nihla,lumshe ido Nihla tayi hawaye na safkowa daga cikinsu jin Miemie ta anbaci sunanta yasa ta dagowa tare da share fuskarta,kwabe fuska Miemie tayi kamar zata yi kuka tace"haba Nihla?shiyasa nace ki dawo scul,babu amfanin ki rika zama kina kuka haka kinsan kuma ba lafiya gareki". Dago blue eye's ball dinta tayi tare da daurasu akan Miemie,wani kukan ke niyar kwace mata tayi saurin rufe bakinta cikin sanyin murya tace"Miemie Irfan ne". "Irfan kuma?,ina yanzu nafa yabar gidan?kuma na tabbata in dai Irfan yana kusa da ke ba zai bari kiyi kuka ba". Rike hannuwan Miemie Nihla tayi tare da cewa"Irfan shi ne silar kukana Miemie,ina son Irfan fiye da kaina,zan iya sadaukar da komai dominsa,amma yau shi da kansa ya guje ni Nihla,Irfan ba ya so na ,Miemie Irfan Aunty yake so,ko fitarsa da kika gani daga wurinta yake ba wurina ba". Saurin janye hannuwanta Miemie tayi daga rikon da Nihla tayi mata da karfi ta mike tsaye tare daja baya tace"anya kina cikin hankalinki kuwa? kin kuwa san me kike fada? wannan ae abunda bazai taba yiwuwa bane". Murmushin da yafi kuka ciwo Nihla tayi tare da cewa "sai gashi yau ya yiwu Miemie,farin cikina daya tak daya rage yau ya janye mani,abun takaici kuma ya dawo wurin matar babana". Razana,al-ajabi,tsoro tsantsar tashin hankali da fargaba shine abinda ya dirarwa Miemie lokaci daya.Bugawan da zuciyarta tayi yayi daidai da zubo war hawaye mai zafi akan fuskarta,saurin gogewa tayi tare da fadin"Never,hakan bazai taba yiwuwa ba,ko da shi ne abunda zan aikata na karshe a rayuwata tabbas yarda kika rasa Irfan haka zalika Aunty Nafisa sai ta rasa Irfan". Kuka sosai Nihla ta kuma sakawa tare da cewa"Miemie ina san sa,bana so na rasa shi,ina so ya dawo gare ni" Dafe kai Miemie tayi tare da cewa"tunda kina so ya dawo,sai ki tashi kiyi fada akan soyayyarki,kije ki roketa idan hakan be biwu ba sai kisan abunda zakiyi bawai ki zauna kina koke-koke ba".jan hannun Nihla Miemie tayi da sauri tare da fitowa da ita daga dakin,kai tsaye gaban Aunty ta kaita tare da sakin hannunta. Dukawa Miemie tayi akan kafarta tare da hade hannayenta duk biyun tare da cewa"Aunty ke uwa ce,kada ki watsar da kimarki akan biyan wata bukata naki,Nihla kamar yar da kika haifa ce,Aunty ana barin halas ko dan kunya,a tunanina ko da ke ke son abu Nihla ta nuna tana so zaki iya hakura ki bar mata,dan Allah Aunty na rokeki kibarwa Nihla masoyinta". Murmshi Aunty tayi tare da mikewa,dafa kafadan Miemie tayi tare da cewa"sirikata kada ki damu,bawai na dauke Irfan daga wurin Nihla bane a'a,shi da kansa yaga ya dace ya canza akalar soyayyarsa,kuma ni bance ta daina son sa ba,tana da damar da zamuyi tarayyah a soyayyah nayi mata alkawari in har ya nuna ita yake so to zan bar mata shi"tana gama fadan hakan ta wuce part dinta abunta. Zage dakin yake yi hannunsa zube cikin aljihun wandon dake jikinsa,sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da zama akan daya daga cikin fararen kujerun dake cikin wurin shakatawar,langwabar da kai yayi tare da lumshe kyawawan idanuwansa babu abunda yake masa yawo a kai sai kalaman Abba dana Momy kafin rasuwarta furzar da iska yayi tare da sake lulawa cikin duniyar tunanin data zamar masa abun fira...... *Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation Page 71~75 17 year's back Rike hannun Zafar Mummy tayi tana cikin radadin ciwo,sam ta gama fita daga hayyacinta ,gyara zamanta tayi tare da jingina jikin gadon asibitin da take zaune tayi,kallon jaririyar dake kan k'afarta tayi fas kyakyawa da ita,wanda haihuwarta kenan yanzu,hawaye ne suka zubo a kan kyakyawar fuskarta ta dauki y'ar hannunta na rawa ta daurata akan hannun Zafar dake zaune kusa da ita,da ido kowa na dakin yabi Mummy da kallo harta Zafar kasa dauke idonsa yayi daga kallon da yakewa Mummy na alamar tambaya,hannunta ta mike daidai gaban Zafar kafin ta fara cewa"Zafar ga K'anwarka nan na baka iko da ragamar kula da rayuwarta,ka zama Garkuwanta kuma gatanta kada ka bari wani ya wulakantata ,kada tayi kukan rashin mahaifiya,ko Yaya ko kane,,idan harka aminta da amanar dana baka ka mun alkawari ka daura hannunka akan nawa Zafar"ta kare maganar tare da share hawayen dake zubo mata. Kallon babyn Zafar yake yi,tuni idanuwansa sun gama canza launi ,tsantsar tashin hanlali ne kawai zaka hango a tattare dashi,taya zai iya rike wannan amanar mai girma haka? yawa kansa tambayar da bashi da ansa,ashe maganar tasa ta fito fili. Murmushi Mummy tayi tare da cewa"zaka iya Zafar kai din adaline kuma mai kula da duk wani nauyin dake kanka,,duk da kana d'an shekara 16 Zafar amma kana da hankalin yan 30 kuma kana yin abunda suka gagara yi". Jinjina kai Zafar yayi tare da daura hannunsa akan na Mummy yace"nayi maki alkawari Mummy bazaki taba dana sanin Amanar da kika bani ba,zanyi iya yina,zanyi da karfina,da dukiyata da duk wani abun dazan mallaka bazan taba barin Amanata ta shiga kunci ba". Hadasu duka biyun Mummy tayi tare da rungumewa,tana jin sanyi a ranta,a kan idonta Zafar ya daga babyn tare da mata huduba da Maryama ,murmushi yayi tare da mikewa yabawa Abba babyn yace"Allah ya raya mana mamana taci sunanta Maryama zamuna kiranta Nihla.Sosai farin ciki ya cika zuciyar ,Abba ,Daddy Ammi da kuma Aunty dake tsaye kusa da Abba. Allahu akbar,Allah akbar Allah mai girma da daukaka maiyin yarda yaso a duk lokacin da yaso,idan da ranka baka gama ganin ikon Allah da girmansa da daukakarsa ba ,lallai mutuwa dole ce,dole duk wani mai rai ya dandana dacin mutuwa, A lokacin da kowa ke murnar zuwan Nihla duniya a daidai wannan lokacin kuma Allah ya karba mahaifiyarta ba tare da tasan dadin uwa ba bare ko da sau daya ta kurbi nonon mahaifiyarta a matsayin abincinta na farko a duni,,,wani tsalelan kuka Nihla ta tsala da matukar karfi a lokacin da ran Mummy maryam ya gama fita,fitan rai mai sauki da dadi babu shure shure babu raki ,mutuwa ba tare da wanda suke daki daya sun fahimci hakan ba,(Allah ka azurtamu da saukakakiyar mutuwa).Sai a lokacin kowa hanlalinsa ya dawo akan mummy wacce ta ansa kiran mahaliccinta. Saurin mikewa tsaye Zafar yayi tare da shafa gashin kansa tare da fezar da iska mai tsananin zafi yana kuma kara jinjina karfin girman alkawarin daya daukarwa Mummy.runtse idonsa ya kuma yi da karfi maganganun Abba na kuma masa yawo kafin rasuwarsa. Sati daya daya wuce Rike Zafar sosai Abba yayi cikin wahalan ciwo yake masa magana"Zafar hakika kai da na gari ne,ka gyara amintakata da mahaifinka ko yanzu na mutu burina ya gama cika Zafar,tunda raina kana kula da Nihla baka taba gazawa ga Amanrka ba,yauma ga wata Amanar daga bakin mahaifi zuwa D'ansa,,ka rike mun Nihla ka kula mun da ita,ko kadan kada ka barta tayi zaman maraici,tabbas bayan mutuwata a lokacinne Nihla zata gane mabanbantan rayuwa,a lokacinne duniya zata mata baki ta kasa gane komai,tana da kananun shekaru Zafar ka kula da kanwarka kaci gaba da zama Garkuwarta a kp yaushe,karka sakarwa Nafisa kula da Nihla domin Nafisa mata ce mai fuska biyu,Nafisa ba zata iya rike mun y'ata ba,hasalima ita ce zata zama bangon bakin ciki da zai ruguzawa Nihla farin cikinta,ka saka ido sosai a kanta daga karshe zaka gano abunda nake fada maka Zafar".I zuwa wannan lokacin kan Zafar wani irin sarawa yakeyi da matukar karfi,duka jijiyoyin jikinsa sun fito radau-radau,saurin dago rinanun idanuwansa yayi yana zubawa Miemie data shigo dakin tana cizgar kuka,akan Zafar ta tsaya cikin tsantsar kuka tace"Yaya anya zaka iya ci gaba da rike amanar daka dauka kuwa❓,a yau Nihla tana cikin tsananin bakim ciki,tayi kuka tayi kewa a yau ta tabbata marainiya wacce ta rasa gata ta kuma rasa wanda zai lalasheta ya tallafeta". Murmushin takaici Zafar yayi cikin sanyin murya yace"bawai na daina zuwa duba Mamana bane sai bazan iya jurar ganinta tana kuka akan mutuwar Abba ba,wannan kuma nasan bana da ikon hanata yin kuka akan rashin bango abun jingina gareta"bai tsaya takan Miemie ba data fadi akan kafarta tana kuka kamar zata mutu ba ya fice yaja dakin,cikin sanyi ya soma safkowa daga stairs sai da yazo tsakiyar parlon sannan ya tsinci maganar Hajiya Kaka tana fadin"Zafar kai nake zaman jira fa,gashi kana kallona kuma zaka wuce". Ba tare daya tsaya ba,yace"zan dawo ba jimawa,zan iskeki wurinki".Ba tare da ya jira yaji ansarta ba ya fice da sauri.Beko tsaya ansa gaisuwar da Baba mai gadi ke masa ba ya bude gida ya fice,cikin sassafar yake tafiya tare da zagayawa layin dake kusa da nasu,unguwar shiru kasancewar irin wannan unguwannin baka samun mutane a waje sai yan tsirarin motoci dake gittawa,yana isa yayi sa'a kuwa gidan a bude yake yasa kai tare da wucewa ciki. Tsakiyar main parlon gidan ya tsaya tare da zuwa hannuwa cikin wandon aljihun jeans dake jikinsa,dara-daran idanuwansa da suka koma red red ya daga tare da watsawa Aunty Nafisa su ,da sauri ta janye idanuwanta data zuba masa kamar tsohuwar mayya.Ta gefan Aunty ya raba zai wuce tare da sakin siririn tsaki,da sauri zuciyarta na matukar bugawa tayi gefe ranta cike da tsantsar tsoro.Tsaye yayi cak,jin an rungumesa ta baya ga sautin kuka mai cunkushe da tsantsar fargaba da tsahin hankali duk mai yinsa kasan ba karamin kuna yake ji a zuciyarsa ba,ya zama kamar wanda ruwa ya kama neman agaji yake kota wacce hanya,runtse idanuwansa yayi tare da kawar da kansa gefe yayin da zuciyarsa ke dukan ukku ukku kansa da tunaninsa na niyar tarwatsewa lokaci daya,ita kam iya karfinta take rungume dashi kamar wacce za'a kwacewa shi kyarma kawai take hannuwansa yasa tare da rabata daga jikinsa ya juyo tare da fuskantarta,batayi wata wata ba ko jinkirtawa wajan kara fadawa a faffandan kirjinsa ta kuma rungumesa,still hannuwansa yasa tare da dagota daga jikinsa cikin sanyin murya yace"Mamana kin girma yanzu,ki daina kokarin rungumata haka".Ganin bata fahimtar komai in ba yarayen kuka ba,be da wani zabin daya wuce karbarta a wannan lokacin riketa yayi sosai a jikinsa yana bubbuga bayanta tare da hura mata iskar bakinsa alamar lallashi. Wani kululun bakin ciki ya turnike zuciyar Aunty wani mugun kishi ya soma dawainiya da ita,ji take kamar ta shakare Nihla ta cireta daga jikin Zafar ko taji saukin abunda take ji a ranta,hawaye ne suka soma zarya akan fuskarta da sauri tayi part dinta kafin zuciyarta tayi boosting. A hankali ta soma yin shiru sai ajiyar zuciya da take saki a kai a kai,a sannu komai nata ya fara sakewa a jikin Zafar alamun bacci ya dauke ta a tsayen da take,hannu yasa tare da janye dogon gashin dayawa fuskarta rumfa,sosai yake jin nunfashinta na sauka a kan kirjinsa,rasa abunda zaiyi yayi a dole ya dauketa kamar ya dauki baby ya wuce part dinta da ita,da kafa ya bude door din kafin ya shiga a bed ya daurata yana niyar tashi daga sunkuyan da yake riganta ta shige cikin aninayen rigarsa har kusan fada mata yayi,da sauri ya dafa gadon yana mayar da numfashi,zare rigan nata yayi daga jikinsa ya samu ya mike,lullubeta yayi ya kashe ACn dake kunne a dakin kafin ya koma akan karamar chair ta dakin ya zauna yana kallon pic din Mummy da Abba sai nashi dana Nihla lokacin tana karama da suke ajiye akan drawan ya lula tunanin rayuwarsu ta baya...... *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawsn karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation 76 ASALIN LABARIN ALHAJI UMAR shi ne asalin sunan Abba ,ALHAJI AL-AMIN shi ne sunan Daddy.Asalin amincin su ya samo asaline tun daga iyayensu haka suka tashi suka ga kansu a wuri daya amincinsu ya zama kamar yan uwa,daya baya zama sai da daya harda kalar kayan jikinsu basa banbantawa,ko a makaranta wajen zaman su daya,iyayen su maza da kuma Hajiya Aysha wato mahaifiyar Umar sun rasu ne ta hanyar hadarin jirgin sama daya ritsa da su.Ba karamin tashin hankali Hajiya Jamila(Hajiya Kaka) ta shiga ba duk da ta kasance jarababbiya kuma mafadaciya amma bata da mugunta haka ta kama Umar da Al-amin ta rike a hannunta har zuwa lokacin auren su in da Al-amin yake auran Maryam yar asalin garin Adamawa ce,mata mai tsanin tsoron Allah da son mutane,a yawon kasuwancin sa ya hadu da ita.Shi kuma Umar a nan cikin garin katsina ya hadu da matarsa mai suna Maryam mace mai tsanin kunya,hankali da rashin son hayaniya.Ko kadan Hajiya kaka bata masu sauki akan yin wani abunda bai dace ba ko kuma wani ya kauce fadanta ma kadai ya ishe ka.Tun bayan auren su Allah ya kara sakawa kasuwancin su albarka dukiya ta habbaka tayi yawan dasu kansu mamalakanta basu san iyakarta ba,a daidai wannan lokacin ne kuma Hajiya kaka ta bijiro da masifar an auro mata ba mai niyar Haihuwa ba kamar matar Al-ameen wato Ammi ba wani jinta take a ranta ba saboda kasan cewarta ba yar masu kudi ba.Wannan dalilin yasa Hajiya kaka cewa dama dan ta kwashe masa dukiya ta aure sa wannan shine asalin rashin shirin Ammi da Hajiya kaka.Ana tsaka da wannan fitanan Maryam(Ammi) ciki ya bayyana,duk da tsananin farin cikin da suka yi hakan besa Hajiya kaka ta sake da Ammi ba.Wata tara ta sanbalo yaronta kyakyawa ajin farko ,saboda tsananin murna maryam(Mummy) tayi kukan murna tayi sadaka ta bayar da abubuwa da dama dan ji take kamar ita ce ta haifi yaron,ganin hakan da take yi a ko yaushe it Ke dawainiya da jaririn yasa Ammi mallakawa mummy jaririn da ko sunansa ba'ayi ba,har ranar suna tazo akayi fatali da dukiya akayi suna na azo a gani ,yaro yaci suna MUHAMMAD ZAFAR wanda Mummy ce ta zaba masa wannan sunan.Sosai Hajiya Kaka ke matukar nuna soyayyah da kulawa ga Zafar sai dai shi sam tun yana jariri baya zama inuwa daya da ita,tana taba shi yake fara tsallara ihu .Ta kasance da yin tsawa da masifa hakan yasa ko kallonta Zafar yayi zai fashe da kuka ko kadan baya son hayaniya da fada.Tunda akayi yayen sa Ammi ta hada kayansa ta bawa Mummy ya koma part dinsa,shakuwar Mummy da Zafar ta wuce tunanin duk mai tunani komai ita ke masa baya cin abinci idan ba ita ta basa ba,bashi bacci idan ba jinta yayi a kusa da shi ba.Haka rayuwa taci gaba da tafiya in da hankalin Hajiya kaka kab ya dawo akan mummy sbd rashin haihuwarta. 5year's later Zaune suke a babban parlon gidan fira suke yi tare da fara'a fal fuskar su,daukar yankan apple Mummy tayi wanda Zafar ne ya saka mata Mummy ,yake kiran Mamansa Ammi ,Umar kuma Abba ,Al-ameen kuma Daddy,ta kai bakinsa ,bude baki yayi tare da ansa ya kuma mayar da kansa akan kirjinta ya kwanta,a lokacin yana dan kimanin shekara biyar.Gyara zama Ammi tayi tare da sakin nishi tana tallabar katon cikin dake gabanta haihuwa yau ko gobe.Fuska daure Hajiya Kaka ta shigo dakin ta zauna a chair tare da yin daya kan daya.Saurin safkowa kasa Mummy tayi tana kara rungume Zafar a jikinta bakinta na rawa fuska cike da tsoro tace"Hajiya ina wuni".Banza Hajiya Kaka tayi mata ta juya tana ansa gaisuwar sauran yaran dake gaisheta a parlon.Mikewa Zafar yayi tsaye tare da jan hannun Mummy yace"tashi,tashi muje daki,kar Allah yasa ta ansa gaisuwan dama ke kike gaisheta".Kafin ,Zafar ya rufe baki Hajiya Kaka ta tangare masa keya,a fusace ya juyo fuska murtuke yace"kar dai kimun ihu a kai".Saurin janyosa Mummy tayi tare da cewa"Muhammad zamu bata kanawa manya rashin kunya". "har kina da bakin fadin hakan?ae duk abunda Zafar zaiyi laifinki ne ke kika bashi tarbiya kuma sunan da yake ansawa naki ne,dole zaiyi abunda yake so". "ki daina wa Mummyna fada,babu ruwanta ni ne nake so na gaya maki haka saboda kina takura mata"Zafar ya bada ansa. A fusace Hajiya kaka tace"zanyi maganin ku kai da uwar rikon tana,Umar ina so kayi aure,Umarni ne na baka ba shawara ba,ina so naga jikanka kafin na rasu,idan kuma bani da iko da kai zaka tabbatar mun ba nono kasha ba sai ka bijirewa Umarni na". Kasa Abba yayi da kai tare da cewa"Hajiya duk yarda kike so haka za'ayi,insha Allah zaki sameni da bin umarninki a ko wanne lokaci". "Allah yayi maku albarka "ta fada tare da ficewa yabar parlon. Wasu zafafan Hawaye masu dumi suka zubo a fuskar Mummy,da sauri Zafar ya tallabi fuskarta tare da cewa"kibar kuka Mummyna ,ki daina biye mata,ita fada kawai tasa gaba,idan na girma zan zana soja in halbe maki ita,Insha Allah kuma zaki haifo mana baby mai kyau kamar ki".Murmushi ne ya subucewa Mummy ta rungume Zafar.Ana cikin wannan yanayin ne Ammi kuma ta sake sanbalo yaronta kyakyawa ranar suna yaro yaci suna Ramadan,duk da tsananin kulawar da Zafar ke nuna masa da tsananin so amma sam bai yarda ya dau lokaci a bangaren Ammi.Watan Ramadan ukku Hajiya kaka ta samowa Abba matar aure,yarinya mai tashe da kyau da halayyah mabanbanta mai suna Nafisa,tayin farko Nafisa ta amince da auren Abba duk da ba wani son sa take ba dukiyarsa kwai take kwadayi,a lokacin Nafisa tana yar shekara 23.Auren Nafisa shi ne dalilin rushewer wannan Familyn ta kasance itace wacce take rike da kaddarar gidan,ita ce asalin kawo bakin ciki da rarrabuwar kan ko wanne a gidan su,tayi amfani da damar zama mata a gidan ta hanyar cika burukanta da dama,sati biyu da haihuwar Ramadan Aunty ta shigo gidan a matsayin matar Abba. A fuska Nafisa mata ce mai tsakanin kirki,son kowa da kuma kyautatawa duk wani dake gidan.Zafar ne ya taso da tsananin kiyayyarsa duk soyayyarsa da abu data taba shi to ya gama amfanarsa ko menene,ko parlo yake zaune tana fitowa zai tatara kayansa yabar mata parlon.Duk wata y'ar tsamarsa da Kaka ya janyeta ya dawo da ita akan Nafisa wanda su Mummy ke kira da Aunty.Nafisa ta kasance tauratuwa kuma masoyiya ga Hajiya Kaka ta kwacewa kowa fada,komai lamuran Hajiya kaka a wurinta suke,da komai daya shafi gidan. Wannan kenan. Zagaye daki take yi,maganganu da yawa suna mata yawo a kai.Kwatakwata ta rasa sukuni babu abunda take buri da so daya wuce mallakar dukiyar Familyn gaba daya da kuma babban burinta na raba Mummy da Abba.Kamar wani gunki haka ya iso ta gefanta tare da rabawa zai wuce.Saurin juyowa tayi tare da daga hannu tana kokarin janyo hanun Zafar.Da matukar karfi ya bige hannunta kafin ya karasa a hannunsa,dara-daran idanuwansa ya kuma zazzarosu waje tuni sun sauya kala da kawo k'yalli k'yalli alamun ruwa ya fara taruwa a cikin su,hannu ya daga tare da nuna ta da yatsa tare da cewa"karki kuskura,har abada duk ranar da kika yi gigin taba ni nayi maki alkawari da wanda raina yake a hannunsa a ranar sai na cire maki wannan kazamin hannun naki".Hannu yasa tare da damkar sumar kansa ,da sauri ya karasa ya dauki qur'an din da yazo dauka ya dauka ya wuce Mummy da Ammi dake tsaye cike da tsananin al-ajabi sun daskare da ganin yaro karami yana irin wannan halayyar.Zafar kam ko kallonsu beyi ba yabar parlon yayin da zuciyarsa ke cike da tsananin kiyayyar Aunty tana kuma bugawa da matukar karfi.. *Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation 77 Mummy ce ta katse shirun da duban Aunty tare da cewa "dan Allah kiyi hakuri,kinsan lamarin yara ba kamar Zafar mai wuyar sha'ani zan masa fada insha Allah bazai kuma ba". "wallahi Mummy babu komai,kada ki damu kanki waye besan yara ba?komai ya riga ya wuce".Aunty ta bata ansa tana wuce wa ciki. Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tare da cewa"lallai yaron nan so yake nayi maganinsa ,kiji daukar magana yanzu idan Kaka taji wannan maganar fa?". Dafa kafadunta Mummy tayi tare da cewa"insha Allah ba zata ji ba,bari naje na same sa"batajira cewar Ammi ba ta bi bayan Zafar kai tsaye dakinsa ta nufa,zaune yake akan prayer mat ga al-qur'ani a gabansa yana muraji'a,shigowa ta yi ciki ta zauna a gabansa,sai da yakai ayar da yake yi karshe kafin ya dago ya kalli Mummy .Ba laifi fuska a sake yace "Mummy wani abun na damun ki ne? ." Kuma daure fuska tayi kafin tace"ai dole abu ya dame ni Son,yanzu kai ya dace ace matar Abbanka ka ke wa magana haka?". Saurin ja da baya Zafar yayi dan da nan annurin fuskarsa ya guje, taune lips dinsa ya yi kamar zai huda ya kasa cewa komai."Zafar magana na ke maka fa". Kallon Mummy yayi tare da cewa"to Mummy ban san me zance ba ae,dan Allah ki daina shiga tsaka ni na da waccan matar na roke ki". Sake da baki haka ta bisa da kallo,rasa me zata cw ma tayi hakan yasa ta mike tabar dakin.Shikam nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana kuma jin tsantsar tsanar Aunty a ransa. 2yrs later Abubuwa da dama sun faru masu dadi da mararsa dadi,dama rayuwa haka ta gada. Ammi ce zaune a gado ,kowa na gidan yana parlon a lokacin Zafar yana shekara 16 Ramadan na dan shekara 11 ,ko wanne ka gani cikinsu fuskarsa dauke take da yalwataccen murmushi marar yankewa,cike da fara' Daddy ya mikawa Mummu babyn dake hannunsa tare da cewa"Allah ya raya mana Nana Aisha." Wani irin murmushi ne ya subucewa Abba yana kallon Daddy cikin hanzari ya karba babyn daga hannun Mummy yana cewa "masha Allah yau Hajiya ta dawo,ina godiya da wannan karamcin insha Allah daga yau zamuna kiranta Miemie ,kuma na mallaka mata kamfanina na gidan Ashana dake nan garin kano". Wani irin yunkurowa Aunty tayi da karfi har tana niyar fadowa daga kujera tace"haba Alhaji daga haihuwar yarinyar?". Wata uwar harara Zafar ya afka mata cike da masifa yace"an kasa da ke ne? kiyi kokari ki haiho Aminiyarki Jamila sai ita a bata ta hassada sai ta kare". Dakuwa Ammi ta masa tare da cewa"ungo nan Muhammad,sai dai ta haifo Maryam badai Uwar mu ba". Dariya Ramadan ya saka tare da cewa"wallahi Yaya duk ranar da Hajiya kaka ta ji kana cewa a haifota wallahi ka shiga rububi". Harara Abba ya masu yana cewa"ku kama kanku a wurin nan,bama son shakiyan ci". Gyara zama Mummy tayi tare da tallabar k'aton tsohon cikin dake gabanta haihuwa yau ko gobe tace"mu dai a bamu babyn mu yunwa take ji". Da sauri Ramadan yace"Mummy wannan babyta ce Ammina ta siyo mun". Mugun kallon da Zafar ya jefa masa yasa yayi shiru da sauri,tsaki yaja tare da dafa cikin Mummy yace"na raye gori,insha Allah nima Mummyna mace zata haifa mun mai kama da ita,in kuma saka mata sunan Mummy". Kowa fuskarsa fal fara'a ,kama Mummy Zafar yayi ya tusata gaba da rigima dole sai da suka tafi part din su. Bayan sunan Miemie da kwana biyu Mummy ta tashi da nakuda,cikin sauri aka tafi da ita asibiti,tafiyar ta karshe,barin gidan nata da ahalinta da rai na karshe,hakika mutuwa dole ce kuma ance sabo ake wa kuka ba mutuwa ba...Tun daga mutuwar Mummy komai na rayuwar Zafar ya gama canzawa dandanan yake kasancewa cikin tsakananin fushi da kunci,ko kadan be son hayaniya magana ma gaggararsa take yi,a ko yaushe yana rike ne da Nihal,saukin sa daya gama zana jarabarwar gaba da secondry ne kullun yana gida,ko daidai da second baya barin Nihal wani irin tsantsar so da kulawa mai cakude da tsantsar tausayi.A bangaren Nihal ma hake ne,tunda ta fara wayau bata yarda kowa ya bata ta daga Abba sai Zafar.Lokacin da Zafar zai tafi makaranta ba karamin daga aka sha ba dan da kyar aka samu ya tafi dan kafewa yayi ya jingine makarantar wai shi ba zeje ba,sai da Abba ya dage kafin aka samu ya koma makaranta...A lokacin ne kuma fir Aunty ta dauke Nihla daga hannun Ammi ta lullubeta da soyayyar karya ,tun Nihla na kukan Zafar harta hakura ta saba da zama da Aunty.A wannan lokacin ne kuma Aunty ta shammaci kowa da soyayyarta ta karya,ta kwashi dukiya mai tsananin kauri da yawa wanda ita kanta bata san iyakarta ba ta hanyar Abokin ta'addancinta data hadu dashi wato Kamal shine yabi mata duk wata hanya ya bata kwarin gwaiwar da nema mata wanda suka iba kudin ta hanyar office din Abba,wanda sosai companyn nasu ya raunana har masu hannun jari a ciki duka suka janye.Wannan dalilin ya kawo babban sabani ga ahalin guda biyu da rikici yaki cinyewa Hajiya kaka ta kira Abba a matsayin mayaudati maciyi amana ta kuma yanke duk wata alaka dake tsakanin su dashi,sai a lokacin Aunty ta samu sukuni ganin ta samu galabar rarraba ahalin.Ba karamin wuya Abba yasha ba kafin Allah ya tado masa da dukiyarsa ta hanyar wasu da yake bi kudade sukaita maido masa nan Allah yasawa kudin albarka suka bunkasa ya tsaya da kansa tsayuwar da ko shi kansa besan iya abunda ya tara ba. Lokacin da Zafar ya dawo,yayi bakin ciki itace rana ta farko daya fadi akan kafafunsa hawaye masu tsananin zafi suka zubo masa,jujuya kai yakeyi cikin tsananin bacin rai ya dago idanuwan sa da suka gama sauya kala ya kalli Hajiya kaka tare da cewa"Dan da kika raina a hannun ki,shin ke kin yarda zai iya aikata haka? a duk gidan nan akwai mai riko da gaskiyarsa da kuma amanarsa?,Ammi kema kin yarda? Daddy kaima?" a rikice yake gaba daya.Cikin tsananin tashin hankali yace"to idan kin raba shi da saura ni bazaki taba yanke alakata dashi ba kada ki manta Amanata tana hannunsa,kuma duk kiransa da nake muna waya da ita bai taba shaida mun cewar bakwa tare ba". "kayi mun shiru Zafar,babu abunda ke damunka daya wuce yarinta,duka shekaranka nawa,to ina so ka sani baka ba wannan amanar".Hajiya Kaka ta fada. Buga kansa yayi da karfi tare da cewa"a hannun dana karba bata raye bare na mayar mata da nauyin dana dauka,ina so na gaya maki babu kuma yarda za'ayi na janye jikina daga cika alkawarin dana dauka duk runtsi kuwa".Yana fadin haka ya fice daga gidan da sauri.Kiran Abba yayi kafin ya samu ya gane bayan gidan su suka koma,a lokacin Nihla na da shekara hudu ,ko da ya shiga gidan ba karamin tashin hankali ya shiga ba ganin Nihla ba lafiya anata fama a kuma lokacin ne Abba ke sanar masa Nihla sikila ce,Zafar yayi tashin hankali kunci damuwa akan ciwan Nihla,hakan ne yasa ya sauya ra'ayinsa daga zama Soja ya juya mafarkin sa zuwa karantar Likitanci dan ya kula da amanar. Ci gaban labari. *Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation 78 A hankali ta soma bude idanuwanta da suka mata nauyi alamun baccin bai gama isarta ba,sam baya mata dadi yasa ta farka,akan tuskar Zafar idanuwanta suka sauka wanda ya kureta da ido fuskarsa a sake,kokarin tashi yake yasa ya karaso gabanta tare da taimaka mata ta tashi zaune,ji yayi jikinta zafi sosai alamun zazzabi na neman rufeta yasa yace"ki daina wannan koke koken,kinga zaki janyowa kanki ciwo". Rau rau tayi da ido tare da fadin"Yaya Irfan ne". Hannu yasa tare da dalle mata baki yace"kada na sake ji kin ambata mun sunan nan,in ba haka ba ranki zai baci" Kasa tayi da kanta ta soma wasa da yatsun hannunta ganin duk ta takura kiris take jira ta saka kuka yasa yace"kiyi hakuri kinji Mamana,bana son damuwar nan taki ne,ko dan lafiyarki ya kamata a ce kiyi hakuri,Mamana kika rasa Mahaifiya kika rasa Mahaifi sai saurayi ne zaki kasa hakura da shi? saurayin ma irin Irfan ?" "Yaya ba barina da yayi yake mun ciwo ba,amma sai ace ya rasa wacce zai so sai Auntyna,wacce nake dauka a matsayin mahaifiyat..."bata karasa magana ba Zafar ya daura yatsan shi akan bakinta tare da cewa"ba ta haife ki ba,ba kuma zata taba zama mahaifiyarki ba"tashi yayi ya hado mata drugs dinta ya bata ta sha,Hijab ya bata ta saka yace"tashi muje". Bata musa ba ta mike tare da saka platshoe dake gabanta ta bi bayansa,babu kowa a parlon haka suka fice,yana gaba tana binsa har suka zagaya bayan gidan su.Saurin cin burki tayi ko kwakwaran motsi ta kasa.Dama yasan za'ayi haka kallonta yayi fuska a daure tare da cewa"wuce muje mana". Girgixa masa kai tayi,tana kokarin yin baya,hannunsa yasa tare da riko nata ya soma tafiya cikin muryar tsoro take fadin"dan Allah ka barni bazan shiga ba,ni gida zan koma".Wata uwar harara daya aika mata da ita yasa ta yi saurin hadiye sauran maganar cikin hade fuska yace"Billah na kuma jin bakinki sai na mammare ki". Gate din gidan ya tura tare da shiga,lumshe idanuwanta tayi,hawayen dake makale suka sauko akan fuskarta,abubuwa da yawa suke dawo mata a kai,ta zo gidan yafi a kirga lokacin yarintar ta amma Hajiya kaka na korata,hakan yasa tun tana naci harta hakura ta saba da rashin zama a gidan,ganin ya nufi main entarance na gidan yasa ta danji sanyi sanyi,kanta a kasa take binsa.Dam dam dam haka kirjinta ya bada sauti lokacin data dago idanuwanta ta ganta a tsakiyar parlon gidan ga Hajiya Kaka hakince a kan kujera tana aika mata da sakon nin harara.a take kyarma ta kwace mata tana niyar rantamawa da gudu.Murza hannunta Zafar yayi tare da kuma rikesa a nasa hannun.A hankali ya soma taku zuwa benen da zai sada shi da part din sa. "Zafar!" shi ne abunda Hajiya kaka ta fada cikin tsananin bacin rai,kai tsaye gabansa ta dawo ta tsaya tare da nuna Nihal da hannu tace"menene jinin Umar yake yi a gidan nan?". "tazo gaishe da yan uwanta ne ta kuma ga Amminta wacce take matsayin uwa a gareta"Zafar ya bata ansa. "karya kake ! wacce alaka ce a tsakaninta da yan gidan nan❓,balle harda raina ina cikin gidan nan ka shigo mun da ita a gida"Kaka ta fada a hassale. Murmushi yayi tare da cewa"Hajiya kaka,alaka da yawa mana,to tazo gaishe da Kakarta ne"ya fada tare da turo nata Nihal a gabanta. Da matukar karfi Nihal ta juyo tare da afkawa a kirjin Zafar ta rungumesa da karfi ko ina a jikinta kyarma yake ,tuni hawaye sun fara zarya a kan kuma tunta,wani irin tsoron Hajiya Kaka ya taso mata lokaci daya. Saurin kawar da kai Hajiya kaka tayi tare da cewa"ka ce mun kuma rashin tarbiyar har ya kai a gabana kake rungume mace?,kaji kunya yarinyar da aka haifa akan idonka? ka fitar da ita daga gidan nan yanzu kafin nayi abunda raina yake raya mun". kallonta Zafar yayi tare da cewa"shiyasa zan kaita part dina ba naki ba nace,tsabar gulma ce ta kawo ki nan din ai". Wani uban rankwashi ta kai masa a kai,ashh ya fada tare da rike mata hannu yace"wallahi kika kara dukana nasan mi zan maki,naga in da aka taba hana Mata shiga dakin Mijinta"yana fadin haka ya suri Nihal da gudu ya wuce ta gefan kaka. Tamkar saukar aradu haka Kaka taji maganar Zafar na ansa kuwwa a cikin kunnuwanta,tuni kyarma na niyar kwace mata ,bata tsaya sauya shawara ba ta rufawa Zafar baya,sai da yaga tazo dab da kofar tasa ya mata gwalo tare da dannawa kofar key yana murmushi da tunanin fitinar daya taro a gidan nan yau. A kan chair ya ajiye Nihal tare da cewa"matsoraciya ni sake ni,sai kace wacce na sato". A hankali ta soma dago kanta daga jikin shi zubawa fuskarsa ido tayi ,uwar harara ya watsa mata da sauri tayi kasa da kai tana turo baki,tureta yayi daga jikin sa ya gyara zama tare da jawo table din gabansa ya fara dube-dube a laptop.Hannuwansa biyu yasa tare da toshe kunnuwansa yace"wallahi Hajiya Jamila idan zaki kwana nan bazan bude maki kofar nan ba,in yaso ki karya ki shigo". Kuka Hajiya kaka ta fashe da shi tare da cewa"walllahi haihuwarka annoba ce Zafar,shege debabban albarka,wallahi ba zaka samun hawan jini ba sai dai ka kashe uwarka Maryam,labcecen banza,dana sani tun a ciki nasa an zubar da cikinka,kuma wallahi baka isa ba ka fiddo wannan yarinyar ka mayar da ita gidan ubanta,jinina yafi karfin jinin barayi". "kibar cika mun kunne,ke kika koya masa satar tunda ke kika raine sa ae,kuma ke kika gayyato barauniyar a gidan,wallahi ki fita harkata a gidan nan kafin na maki rashin mutunci". Hannu kaka ta daura a kai tayi dakin Ammi da gudu tana rurin ihu,a tsakiyar parlon Ammi ta fadi tana kuka wiwi kamar wacce ake fitarwa rai. Dariya sosai Ramadan ya saki suka tafa tare da Miemie kafin yace"maganin ki kenan,tsab zai mana maganinki tunda shi kadai ke iya maki" Dariya kamar zai kashe Miemie kafin tace"amma dai kasan duk yau bamu ba kwanciyar hankali ". Da gudu Ammi ta fito daga bedroom har tana tuntube gaban kaka ta fadi tana salati "Mama lafiya ❓"shi ne abunda ta ke fada. Gefan zani kaka tasha tare da share kwalla tace"Maryam kin haifo mani bala'i,amma ina so ki sani ajalinki kika haifa ba dai ni ba,wallahi ba'ayi dan da zai kashe ni ba,ni Zafar ke kika barauniya,kuma zai wulakanta ni"wani kukan ta kuma saki taci gaba da cewa"ki kira mani Aminu yau sai ya zaba ni ko Zafar a gidan nan,kuma yazo ya fitar mun da karuwar daya kawo a gaban idona ya dauketa ya haura sama". "Hajiya dan Allah kiyi hakuri,wallahi bansan yayi haka ba,dan Allah kibar kuka,yanzun nan zan maki maganinsa,dan Allah kaka ki share hawayenki"Ammi ta fada. A hassale kaka tace"to uban waye yace kuka nake❓,bakin ciki ne yamun yawa da bansan ruwa ya fara fita a idona ba,wallahi wallahi nan da sati mai zuwa sai an daurawa yaron can aure,zamu gani ni da shi waye a gaba,idan bazaiyi aure ba sai dai yabar gidan nan,dan bazai janyo mana abun kunya ba,Duk laifi ai naki ne,ko tarbiya ta gagare ki❓wallahi kin ban kunya Maryam"bata jira cewar Ammi ba ta fice daga dakin tana kwalawa Ramadan kira. Da sauri Ammi ta mike ta nufi hanyar dakin Zafar ,tana zuwa ta soma buga kofar tana fadin"Muhammad ka bude kofar nan yanzu". Jin muryar Ammi yasa ya yunkura,saurin rikosa Nihal tayi tana gada masa kai cikin muryar kuka take fadin"Kaka zata kashe ni idan ka bude,ni sai ka mayar da ni gida". Shafa kanta yayi tare da cewa"babu abunda zai sameki".Cire hannunsa tayi daga rikon data masa yazo ya bude kofar. Carab Ammi tayi da kunnansa tare da murdawa tace"kai kullun burinka ka janyo mun fitina kaji dadi ko Muhammad" "ahhhh,ashhh Ammi kunnena zai cire,ki daina biyewa rikitacciyar tsohuwar can wallahi". *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* *Dan Allah duk wanda ya karanta ya taya ni da addu'a ina da bukata a wurin Allah,fatana Allah ya cika mana burukan mu gaba daya* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation 79 "Kakance kake kira da haka❓neman maganarka yayi yawa ko Muhammad"cewar Ammi ta kare maganar tana duban in da Nihla take duk ta takure alamar a tsorace take.Sakin kunnan nasa tayi tare da sakin kayataccen murmushi lokaci daya ta furta" 'yata". Jujuyawa Nihla tayi ta hango ko ba kowa a tare da Ammi,ganin ba kowanne yasa ta kara so da sauri tare da tafiya zata duka a gabanta.Saurin riko kafadunta tayi tare da rungumeta a jikinta tana sakin ajiyar zuciya kafin ta zaunar da ita a chair suka koma suna fuskantar juna.Sunkuyar da kai Nihla tayi tare da cewa"Ammi ina ina wuni" "lafiya qlau alhmdllh,ya hakuri da rayuwa❓"Ammi ta bata ansa. "Alhmdllh"shi ne abunda ta samu damar furtawa kawai. "ki saki jikinki Nihal ,ko kin manta a nan din gida kika dawo❓,ki daina tsoron Hajiya nasan duk abun nan da take yi ba zata iya cutar da ke ba.Hajiya tana da kirki sosai misalinta kamar kwakwa ne,a waje tana da matukar tauri da wuyar fahimta amma a ciki tana da tsananin taushi da tausayi sosai".Ammi ta fad'a. Kwanto da Kai Zafar yayi akan kafadun Ammi tare da cewa"ke dai dan tana sirikarki shi yasa ko yaushe kike a bayanta". Wani irin dundu da aka saukewa Zafar a baya yasa shi saurin dagowa yana so yaga wanne isashen ne,wa idon sa zai gane masa in ba Hajiya kaka ba❓.Fuskarta a matukar daure babu alamun annuri a tattare da ita. "nayi maki wani abunne da zaki mun dukan nan❓"Zafar ya tambaya. Ko kadan Kaka batayi ta kansa ba illa kallonta data mayar ga Nihla tare da cewa"ke maza ki bace mun da gani,ki kama gabanki wannan ya zama takunki na karshe a cikin gidan nan". Da sauri Nihla ta mike tana niyar antayawa da gudu,ko ina a jikinta banda tsananin kyarma babu abunda yake yi,rike hannunta Zafar ya yi ya juyo yana kallon Hajiya kaka tare da cewa"shiyasa na kawota dakina,kuma bangarena ba naki ba,ban kuma san lokacin da kika fara kirgawa yan gida mutanan da kike so su shigo ba". Nu na shi tayi da yatsa tana cewa"ba da kai nake ba,ka bari nayi magana da wacce zatayi ta kanta a gidan nan". Saurin mikewa Ammi tayi tana fadin"Hajiya dan Allah kiyi hakuri,kai kuma Muhammad kada na sake jin bakinka a wurin nan". Sallamar Daddy ce ta katse masu maganar su,da sauri Nihla ta janye hannunta daga rikon da Zafar ya yi mata ta karasa gaban Daddy da sauri,wani irin kauna bege da kuma tsananin tausayin kanta ya taso mata ganin Daddy ya kuma tunzura ta tana ganin kamar zata ga Abba a bayansa,wasu zafafan hawaye ne suka kawo a idanuwanta.Tsaye ta tsaya cak ta kasa motsa tare da zuba idanuwanta akan fuskar Daddy. Murmushi ya sakar mata tare da bude hannuwansa yace"shikenan tunda ba Abba Umar bane kin rasa damar zuwa ga mahaifinki❓ ba za ki sake jin dumin Mahaifi ba❓ " Wani irin kuka ne ya kubce mata da matukar sauri ta fada jikin Daddy tana shashekar kuka.bubbuga bayanta Daddy ya shiga yi tare da fara lallashinta. Kamar wata statue haka Hajiya kaka ta daskare,ido suka hada da Zafar ya yi mata kwalo,saurin kawar da kai tayi tare da fadin"Al-ameen". Ansa kiran Daddy ya yi tare da karasowa gabanta.Cike da isa da gadara tace"ina so yarinyar nan ta bar gidan nan.Bana kuma fatan sake ganin kafarta a gidan nan,ina kuma umurtarka da cewa nan da sati daya ka daura auren Zafar da Aisha". "to" shi ne abunda Daddy ya fada sannan yaci gaba da cewa"bawai naki ta taki bane Hajiya,sai dai yau gani a gabanki a matsin Umar ina rokonki da kuma baki hakuri,Umar yana gabar mutuwarsa amma ke yake ambata da kuma tabbatar mun da cewa shi bai aikata abunda kike zarginsa da shi ba,yana kuma umurtata da in nema masa yafiyarki,in kuma rike masa Maryama amana,Maryama marainiya ce Hajiya bata da kowa kuma kinsan ita din dawainiyar Zafar ce tun daga ranar data diro duniya,haka zalika Mahaifinta ya kuma damka masa amanarta ,kuma Zafar bai gajiya ba ya ansa ya kuma yi alkawarin riketa kamar yarda yawa mahaifiyarta,shin Hajiya zaki so jininki jikanki mafi soyuwa a kama shi da laifin cin amana❓da kuma kasa rike alkawarin daya dauka❓ wannan karan amanar daya kuma dauka tana da matukar girma fiye da wacce kika sani" Hannu ta daga masa alamar ya isa kafin tace"idan bashi ya yi ba wa ya yi❓ shi kuma jikan nawa a haka zai kare da rikon amanar mai lalura❓duk wani abunda ya tara sai ya kare a kanta❓" Murmushi kawai Daddy ya yi kafin yace"Ummana idan lokaci ya yi zaki sani,dan Allah ki yafewa Umar ki kuma bari Zafar ya sauke nauyin daya dauka akan Maryama,ka da ki hukuntata da laifin da aka aikata tun tana zanin goyo". Kasa furta komai Hajiya kaka tayi ta raba ta gefan Daddy ta wuce da sauri shi da Ammi suka bi bayanta. Saurin mikewa Nihla tayi bakinta na rawa take fadin"Yaya zan tafi gida,dan Allah kada ka hanani".Kafin Zafar ya yi wata magana tuni ta runtuma a guje .Murmushi kawai yabi bayanta da shi,sosai murmushin ya haskaka fuskarsa ya yi matukar yi masa kyau ya kuma fito da ainahin zallar kyawu na fuskarsa. Ko kadan Nihla bata tsaya ba sai da ta shigo cikin tsakiyar parlon su,a nan ta tsaya tana mayar da numfashi.A hankali ta soma bude idanuwanta ta kuma bude su tar akan fuskaf Irfan dake fuskantar ta amma idanuwansa a kasa ya kasa kallonta. "lafiya kuwa❓waya biyo ki Nihla❓Aunty ta fada. Kafin Nihla ta bada ansa Miemie dake shigowa tace"babu wanda ya biyota tsabar farin ciki ne kawai" Sosai Aunty ta sake fuska tare da fadin"to Alhmdllh,Nihla ki kawo wa bakona ruwa,su lami basa nan". Gyada kai Nihla tayi alamar to ta juya tare da nufar hanyar kitchen tana kokarin mayar da hawayen da suke kokarin zubo mata,ruwa da kuma lemu da cup ta daura a plate ta dauko ta dawo parlon a saman table na tsakiyar dakin ta ajiye tare da juyawa zata wuce dakinta,yayin da zuciyarta ke dukan ukku ukku a yanzu kam bata da iko ko karfin zuciyar tsayar da ruwan dake kwaranyowa daga cikin idanuwanta zuwa akan fuskarta.Tsaki Miemie taja tare da fadin "amma dai Irfan kaji kunya wallahi". Murmushi kayace a fuskarsa yace"anya dai Miemie yau kinyi gaskiya kuwa❓miye abun jin kunya a tattare da soyayya❓lamarine na zuciya ka kuma mikata a in da ya dace in da kuma kasan zaka samu kwanciyar hankali da tsantsar kulawa". Saurin juyowa Nihla tayi tana kare masa kallo,tana kuma jin maganganunsa kamar saukar aradu a kanta,cike da karfin hali ta tako zuwa gabansa,da sauri ya dauke kansa tare da juyawa idonsa daga kallonta."sau daya dai Irfan ka kalle ni ka kuma fuskance ni,wanne irin mutun ne kai❓ haka shi ne tukuicin soyayya❓ kana tunanin yin hakan da kayi zai haifar maka da nasara ne a rayuwarka❓ barina da kayi bai taba mun ciwo ba Irfan,amma ka rasa wacce xaka so sai Matar mahaifina❓" "Nihla wannan ba tarbiyar dana baki ba ne,ki tsare manya kina masu tambayoyin da kika ga dama,kamar yarda ya fada lamarine na zuciya kuma ita take da hukunci akan wanda zata so ko kuma wanda zata ki,shin laifi ne dan Irfan ya nuna ni yake so❓ ta ina hakan ya zama kuntatawa❓ Irfan ina so yau ka bayyana zabinka a cikin mu biyun,Shin ni ce ko kuwa Nihla❓ina ga hakan shi xai kawo karshen duk wannan". "ka daga kanka Irfan ka kalli cikin idanuwan Nihla ka gaya mata baka santa "Miemie ta fada. Kallonsa ya mayar ga Miemie tare da cewa"Haba Miemie nasan kinsan furta kalmar kiyayya bata da dadi ko a wurin makiyinka balle kuma ni da Nihla take so,bazan iya kallon idonta ba dan hakan ya haramta a gare ni"kallonsa ya mayar ga Aunty fuska cike da fara'a yace"Auntyna a soyayyah bana ganin kowa sama da ke,kece cikon rayuwa da farin cikin Irfan,rasa shi tamkar wata illace ce ko tawaya a rayuwata,ke ce zabina kuma mafarkina a ko yaushe". Wani irin kuka ne ya kubcewa Nihla tayi part dinta da gudu cike da tsananin tashin hankali da rashin sanin madafa. Fuska cike da hawaye Miemie ta kallesu tare da cewa"shi fa sharri kare ne duk in da ka aikasa zai dawo maka,da yardar ubangiji yarda Nihla tayi kuka dukanku sai kun koka,yarda kuka tozarta rayuwarta sai taku ta tozarta,yarda kuka ci amana sai amanar Allah ta ci ku,ko Nihla ta fada ko karta fada Allah yana kallonku kuma zai mata sakayya".Kuka ne yaci karfinta ta masa ci gaba da magana ta juya zata wuce taci karo da Kamal dake tsaye ya daure hannuwansa a kirji yana kallonta.Karasowa yayi tare da jan hannun yana nuna mata alamar tabar kuka..... *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation 80 Rike hannun Kamal tayi da karfi cikin nata,hawaye kuma na zarya akan fuskarta.Janta yayi zuwa dakin Nihla yana kuma lallashinta,tsaye tayi gaban bed din da Nihla ta fada tana kuka kamar ranta zai fita.Rungume juna sukayi da kyar Kamal ya samu ya shawo kansu tare da basu baki,rike kafadun Nihla Miemie tayi suna fuskantar juna cikin sanyin murya ta fara magana"Nihla meye a tattare da Aunty da har baki iya daukar fansa a kanta❓kina zaune kina kallo garin ta Farauto farin cikinta ke tana salwantar da naki Farin cikin❓ me ake da mata irin wannan". Murmushi mai tsananin kyau Nihla ta saki har jerin fararen hakoranta suka bayyana,hannu tasa tare da share sauran hawayen daya rage akan fuskarta "Auntyna duniyata ce,Auntyna matsayin uwa take a gare ni,Auntyna taci kashina taci fitsarina duk da hakan ya kasance a fuska biyu ne,Auntyna tana da daraja a idona,tafi gaban wulakanci a gabana,ko ba komai zan kirata uwa wacce ta tsaya mun a lokacin farin ciki da akasinsa,ta jajirce a kaina kuma duk yarda take da fuska biyu hakan besa ta bani gurbatacciyar tarbiya ba,ta kula da ni tamkar yar data haifa a cikinta.Lokacin da Yayana Zafar ya yi tafiya itace mace data tsayawa maraicina ta kula dani ,haka zalika lokacin dana rasa mahaifi na kalleta a matsayin family tawa daya tak data rage mun a duniya wanda take da alaka da mahaifina,shin ki gaya mun duk wannan alkhairan data mun be isa na kauda kai akan abunda ta nuna tana so ba❓ba amfanin idan an cuce ka ka rama da cuta ilimun mu bazai mana amfani ba kenan,ina kuka ne badan abunda Aunty tamun ba ,a'a ina kuka ne ta dalilin wai Irfan ne zai maye gurbin da Mahaifina ya bari,ina kuma kuka ne akan na zama sakara dana mika yardata ga wanda besan darajata ba"Shiru Nihla tayi tana mayar da numfashi. Girgiza kai Miemie tayi tare da janye jikinta daga rikon da Nihla tayi mata tare da cewa"ya ishe ni haka,na gaji dajin wannan maganganun naki da basa da hanyar kamawa balle dadin rikewa,yardarki da yawa shiya bawa waccan matar lasisin cutar da ke,ki gane mana Maryam karki kuma zama wata sakara akan wasu hujjojinki da bazan taba ansa ba,Nafisa ba zata taba zama uwa a gareki ba,garama kisan abunda kikeyi"jan mayafinta tayi tana niyar barin dakin,saurin rike gefen mayafin Nihla ,a fusace Miemie ta juyo tana zabgawa Nihla harara.Murmushi Nihla tayi tare da cewa"yau kuma zakiyi fushi da Aminiyar taki ne❓idan kika yi fushi da ni baki yi tunanin zafin dazai kuma shigata ba❓". Can't control her tear's of happiness da matukar farin ciki tayo baya tare da rungumar Nihla a jikinta tare da cewa"Allah ya barmun ke,ya kuma kawo maki karshen duk matsalolinki" .Da ameen Kamal ya ansa tare da fadin"tunda an manta da ni a nan tsaye sai azo mu tafi ni na tuna da kaina".Bye bye Miemie tayiwa Nihla tabi bayan kamal suka tafi. Sai lokacin wani radadi da rashin kwarin gwaiwa ya dirsar mata,kamar wata gunki haka ta daskare a wurin kwakwalwarta na tunasar da ita kalaman Irfan da suka kasance kara a zuba mata garwashi a kunnuwanta "shi ne wanda na fara so!a rayuwata irin son da bana hadasa da komai,irin son da zuciyata zata iya fashewa idan naga wani na rabarsa,son da wani irin zazzabi ke rufe ni idan har ban gansa ba! irin son da yake rufe ido wanda bana ganin kowa sai shi,irin son da a kansa na daina bacci sai dai naita juye-juye,akan sonsa na daina koshi wanda hakan ya haifar mun duk dadin abinci bana iya kaisa bakina balle harna iya gane dandanonsa! ,yanzu duk wannan son besa Irfan ya ji tausayina ba ya kuma tallabi maraicina😭❓ ta kare maganar wasu siraran hawaye na gangarowa akan fuskarta.A hankali ta zame hular dake rufe da yalwataccen gashin kanta,ta yi kokarin yiwa kanta masauki akan pillown dake bayanta ta kuma lulawa duniyar tunani. Hannusa zube cikin aljihunsa yake taku tamkar kasa zata tsage saboda yacce take ansa takun nasa cike da izza,mulki da isa! hannunsa daya ya zaro daga aljihu tare da b'alle bottum din wuyansa na rigar suit din dake jikinsa.Bakinsa dauke da siririyar sallama ya saka kansa cikin parlon Hajiya kaka.Tsaye ya yi tare da dago kyawawan golding eye's ball's dinsa ya sauke su akan Hajiya kaka dake zaune tare da wata matashiyar budurwa. Baki Hajiya kaka ta washe fuska dauke da yalwatacciyar fara'a ta mike tare da cewa"Aysha yau ga Zafar a gabanki,kuma mijinki nan da kwana shidda insha Allah".Budurwar da aka kira da Aysha ta dago kanta a hankali tana sauke idanuwanta akan Zafar Ma sha Allah shi ne abunda ta fada tana kuma kara fadada fara'arta dan wannan shi ne ganin Zafar na biyu da tayi kuma tun ganin farko ya tafi da dukkan tunaninta da wata farin cikin rayuwarta,tun daga ranar take jin babu wanda ya cancanta da ita sai shi"kura masa ido tayi ta kuma kasa janyewa,lokacin daya tayi saurin runtse idonta da matukar karfi sakama kon idanuwan Zafar da suka shiga cikin nata,wani irin suck taji wanda yasa ta kasa ci gaba da kallonsa tayi sakama kon kwarjin daya yi mata. Karasa shigowa yayi tare da zama akan chair dake fuskantar Kaka cikin natsuwa ya furta"Ga ni!". Lumshe idanuwa Aisha tayi yayin da so da tsantsar kauna suka soma daukar mata daddadar muryarsa tana mata yawo a kai. "wannan itace Aysha matar dana zaba maka Zafar,ka ganta dan ita ta riga ta ganka kuma ka fara shirin biki "Kaka ta fada. Shiru Zafar yayi tare da dago kai ya kalli Kaka yace"ki bamu waje to". Alhmdllh shine abunda Hajiya kaka ta fada tana kuma cewa"nasan ai dole kaso zabina ,kaine jika mafi soyuwa a gare ni kasan bazan maka zabi marar kyau ba,ku zanta da kyau,Allah yayi maka albarka".Ta kare maganar tana wucewa bedroom dinta. Murmushi kawai Zafar ya saki,wanda hakan ne yasa Aysha shagala da kallonsa dan ba karamin kyau yayi mata ba.Yana juyowa da kallonsa tayi saurin yin kasa da kai zuciyarta na bugawa. "a wannan zamanin ban tunanin akwai wadda za'awa zabin miji ko mata haka kawai ya amince,shin ke sanina kika yi ne da kika amince da zabin kaka ta❓ Aysha ba abunda kika rasa bare nace bana sonki,ko a ina babu wanda zai kushe halittarki,sai dai ina mai matukar baki hakuri ,bana da ra'ayin yin wani aure a yanzu". Saurin dagowa tayi tare da dubansa cikin sarkewar murya tace"ni naga kayi mun,kuma zan iya jiranka ko yaushe ne"Cewar Aysha. Hannu yasa tare da shafa tulin sumar kansa kafin ya bata ansa da cewa"ki gane bana da ra'ayin son mace biyu danni ina da wacce nake so kuma na riga na zama mallakinta i'm sorry"ya kare maganar tare da mikewa ya yi hanyar fita. Da kallo tabi bayansa dashi ,sai da ya kurewa ganinta sannan wasu hawaye masu dumi suka samu basarar gangarowa akan fuskarta.... *Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation 81 Da kallo Aysha tabi bayan Zafar harya bacewa ganinta,dukar da kai tayi tare dasa hannu ta soma share zafafan hawayen da suka gama wanke mata fuska,sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da dagowa tana kallon Hajiya kaka dake tsaye gabanta ta kureta da ido. "me yake faruwa❓,ina Zafar din❓,Aysha kina jina fa"cewar Kaka,"Kaka ya tafi"Aysha ta bata ansa tare da mikewa tana kokarin barin wurin.Rike mata hannu kaka tayi tace"ki gaya mun me lalaceccen ya yi maki❓". Dayan hannunta ta daura akan na Kaka fuska cike da murmushi tace"kaka beyi wani abunda ba daidai ba,ya fada mun yana da wacce yake so,kuma kinga ni bazanyi kokarin raba masoya ba ko Kaka❓". Saurin janye hannunta Kaka tayi daga rikon da Aysha ta mata"ke dai Allah wadanki,nafa gaya maki halin yaron nan kab,to karya yake yayi haka ne dan ki rabu dashi,ke baki san ciwan shi na gudun mata ba❓wallahi karya yake,bakin hali ne irin nasa,amma kab kinfi ban haushi da bata mun rai wallahi"kaka ta fada. Murmushi kawai Aysha tayi tare da daukar jakarta ta bar bangaren kaka.Da matukar sauri kaka tabi hanyar harda tuntube ta shiga main part na gidan,da Miemie taci karo janyota tayi tare da cewa"ke ina wannan labcecen banzan ❓". Dariya Miemie ta kunshe tana kallon Zafar dake niyar ficewa ta bayan Kaka wanda fitowansa daga dakin Ammi kenan. Carab kaka tayi da belt din Zafar ta rike da karfi "au guduwa zakayi Zafar❓kai duk duniya lamarinka babu albarka a cikinsa❓ko kadan baka da gaskiya "cewar kaka Kamar safkar mutuwa haka Zafar ya daure fuskarsa babu alamun annuri a tattare dashi hannu biyu ya hada tare da cewa"Kaka ki daina damun kanki dan Allah,badai aure ki ke so nayi ba❓insha Allah ranar satin zan kawo maki wacce nake so,amma dan Allah ki tsayar da wannan rigiman bana so ya koma wani abu na daban". Shiru kaka tayi kamar mai tunani sai kuma ta saki murmushi tare da dafa kan Zafar tace"kayi alkawari zaka kawo mun❓". Ajiyar zuciya Zafar yayi tare da sakin yalwataccen kyakyawan murmushin shi mai wuyar ga ni ya janyo kaka jikinshi sosai ya riketa tare da cewa"eh nayi alkawari Nanima!". Dariya kaka tayi tare da rungumar Zafar tana saka masa albarka kafin ya fita daga gidan,wani irin dadi ne ya kwaranya a zuciyar Ammi tabbas tasan Kaka na matukar son Zafar da duk rigimarta shi kadai ke iya mata a gidan,sai dai ta wani bangaren cike take da matukar tsoro da firgicin ranar da Kaka zata gane gaskiya akan abunda suke boye mata,hannu ta daga tare da cewa"ya Allah ka bamu mafita akan wannan al-amarin". karab idonuwan Ammi suka sarke cikin na Hajiya kaka,tsaki taja tare da cewa"maryam bansan gulma tsayuwar me kike a nan❓ ko baki so aurem Zafar din bane,to ahirdinki wallahi" Kaka ta kare maganar tana fita daga part din,dariya Miemie ta kwashe da shi tare da yin sama da gudu gudun kada Hajiya kaka ta jiyota ta tayar mata da balli. 4 days later Sanye take cikin riga da siket na material red colour,daurin zara buhari ne a kanta sosai dinkin yayi matukar yi mata kyau duk da kasancewarta marar kiba amma ko ina das ,simple make-up ne a fuskarta sai baza kamshi take ta tako a hankali zuwa cikin tabkeken parlon nasu,kawar da kai tayi saka makon ganin Irfan da Aunty zaune suna sheka dariya kasa-kasa Aunty ke fadin"ai duk wasu takardu na yawancin dukiyar na dauke in gaya maka,sora wanda ba'a rasa ba shima tare za'a raba mana gado,bakin cikina daya takardun dukiyar da uwarta ta mallaka mata duka suna hannun Dr Zafar kuma kasan ansarsu bazai taba yiwuwa ba". Dariya Irfan ya yi tare da mikawa Aunty ledar hannunsa yace"kinga ga IV na auren mu nan nan da sati ukku masu zuwa,maza tattaro mun takardun na fita dasu daga gidan nan". Wani irin sanyi,farin ciki,natsuwa gami da annashuwa na jin dadin cikar buri yasa hawayen farin ciki safkowa a fuskar Aunty bakinta ta bude tare da furta"Alhmdllh,ga kuma takardun duka a jakkar nan Baby".Hannu Irfan yasa tare da karbar jikkar a hannunsa.Ganin Nihal na niyar wucewa tasa Aunty cike da dauki tace"Nihal kizo kiga abun farin cikin daya doso Auntynki dan Allah". Cak Nihal ta tsaya tare da dago kanta dake duke,saurin kawar da hawayen dake kokarin zubo mata tayi ta maye fuskarta da Murmushin data kakalo ta dawo kusa da Aunty tare da cewa"menene wannan ya samu Auntyna❓". Janyo hannun Nihal Aunty tayi tare da zaunar da ita suna fuskantar juna ta dafa kafadunta "Nihlal yaune ranar farin ciki a gare ni tun bayan rasuwar Mahaifinki,Nihal yaune na fara ganin cikar burina na tun yarinta,Nihal ki kallah katin aurena da Irfan!" Dam dam haka kirjin Nihal ya bada sauti cak numfashinta ya tsaya na wasu seconds,kamar statue haka Nihal tayi hucking,wani irin ajiyar zuciya ta saki wanda hakan ne yasa ta soma rarrabe yanayin da take ciki,saurin kawar da damuwarta tayi tare da sakin murmushin da yafi kuka ciwo ta kuma soma bude bakinta dake kyarma ,sai da tayi da gaske wurin harhado kalamanta cikim tsananin tsoro da firgici tace"Au..A...Aun...Aunty na ta..ta..taya ki farin...Ciki"shine kawai abunda ta iya furtawa ,bude hannuwa Aunty tayi da niyar Rungumar Nihal itama jikinta ta shiga suka rungume juna,idanuwa Nihal ta lumshe tuni hawayen da take boyewa sun samu damar bayyana a sarari a yanzu sun kai lokacin da bazata iya controlling nasu ba,rokon Allah ta keyi yasa ta farka daga mumunan mafarkin da take yi,sai dai kash ko da ta bude ido hakan ya kuma kara tabbatar mata da cewa a gaske ne ,samu tayi ta janye cikinta daga na Aunty ta mike zata wuce. "ba zakiyiwa Abban naki murna ba Nihal❓".Kalaman Aunty suka darsu a kunnuwan Nihal,saurin dafe zuciyarta ta yi dake dab da tarwatsewa saboda tsananin tashin hankali cikin sarkewar Murya tace"i..I..Ina taya ka murna,Allah ya..yasa alkhairi,A ko da ya..ysushe zan kasance mai maka fatan al...alkhairi da addu'a"ta kare maganar tana tafiya i zuwa dakinta,key tasawa kofan tare da silalewa kasa ta fadi akan gwaiwowinta tare da sakin wani irin kuka mai kuna da cin rai,Dan kwalin kanta ta cire tare da jefarwa tasa hannu tare da barbaza yalwataccen dogon gashin kanta,kanta ta dafe da karfi tana kuma fashewa da kukan ,da gudu ta mike ta isa gaban hoton Abba da Mummy dake ajiye a dakin,rungumesa tayi a kirji cikin muryar kuka ta furta"yau na cika kuma na tabbata cikakkiyar Marainiya ni Marya,da ace zai yiwu zan iya bada komai nawa ko da na sati daya ne a dawo mun daku duniya,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,yau na tabbata cikin tashin hankali Abbana lallai kamun gata Abbana nayi kewarka,Abba bazan iya daukar wannan ba ko kadan,Abba nima yau na roki mutuwa fiye da rayuwata,idan na zauna nan zuciya zata fashe bazanyi mutuwa mai sauki ba Abba,Abba ka g..ga...gafarce ni...Yau zan bar ..Gidan nan".Da gudu ta nufi wadrope ta janyo hijab da akwati ta dinga jefa kayanta tamkar sabuwar zautacciya,kudi ta zuba a ciki ta rufe ta janyo shi zuwa kofan daki ta bude wani irin jiri da tari ne ya turniketa dafe kirji tayi tare da sulalewa a kofar dakin a sume...... *Allah ka gafartawa iyayenmu,kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation 82 Da matukar sauri Irfan yakai hannunsa da niyar taba Nihla wanda isowarsa wurin kenan,wani irin riko yaji anwa hannunsa tun daga kasa ya fara kallon wanda ya rike masa hannu har i zuwa akan fuskarsa ,fuska daure babu alamun murmushi Zafar ya gyada wa Irfan kai kafin ya jefar da hannun nasa,dukawa ya yi akan gwaiwowin sa ya tallafo Nihla yana girgizata ganin ko kadan bata motsiya yasa ya dauketa zuwa mota,da matukar gudu ya figi motar zuwa asibitin shi,kai tsaye emergency ya tafi da ita,ja da baya yayi tare da dafe kansa da karfi wanda yake jin kamar zai tarwatse masa,Dr Aminu ne ya karasa gareta ya fara kokarin ceto ranta.Zafar kam da tsananin firgici ya gama kama shi ga zufa da taketa keto masa ta ko ina,saurin fitowa ya yi daga dakin,kamar an saukar masa da mutuwa haka ya zaro dara-daran idanuwansa yana jefawa Aunty da Irfan mugun kallo kamar idonsa zai fado.Saurin ja da baya Aunty tayi tana mayar da nunfashi saboda tsoron daya gama bayyana a tattare da ita,hannu ya daga tare da nu na su cikin tsananin hassala yace"we don't need u here,get lost,billah Irfan idan na bude idona na ganka a nan tabbas za'a baka gado". Kafin Irfan ya yi wani yunkuri tuni Aunty yaja hannunsa da karfi sunyi baya,cijewa yake yi a tsawace Aunty tace"kayi hauka ne Irfan❓,kai baka san waye Zafar ba❓na tabbata tun da akan Nihla ne bazaiyi tunani so biyu ba wajen illataka".Dafe kansa yayi yana jin wani iri saurin kawar da damuwar ya yi tare da kallon Aunty tare da sakin murmushi yace"muje Baby,tunda kina tare da ni meyasa zan damu da abunda ya damu da Nihla".Tafiya suka yi suka bar asibitin. Zama akan chair dake bakin emergency din Zafar ya yi yana jin zuciyarsa kamar zata fasa kirjinsa ya fito,dukar da kai ya yi tare da daura hannuwansa akai yana cakuda yalwataccen gashin kansa.Fitowar Dr Aminu yasa ya yi saurin dago ido yana kallonsa yana so ya yi magana amma sam ya kasa furta komai,gane abunda yake nu fi yasa Dr Aminu dafa kafadarsa tare da cewa"Relax Dr,Alhmdllh ta dawo a hayyacinta,amma kasancewar firgicin da take ciki yasa kwalwarta na bukatar hutu yasa na mata alluran bacci,later on sai ka dubata akan ciwonta daya tashi". Rinannun idanuwansa da suka gama rinewa ya dago tare da kallon Dr Aminu Murmushi kawai ya masa a matsayin godiya tare da gyada kai sannan ya mike tare da shiga dakin da Nihla take ciki. Kamar wanda be son taka kasa haka yake tafiya harya karasa a kusa da gadon da take,hannunsa ya daura a kanta dake baje babu dankwali janye mata gashin kanta daya rufe mata fuska ya yi,kallonta ya soma yi kamar wacce xata bace masa,a hankali ya soma magana "Mamana bazan taba bari wani kuncin ya sake shigarki ba,kin sha wahala a rayuwa,kinga jarabawa kala-kala ko ince kina cikin gani Nihla,tabbas zaki samu y'ancin da ko wanne Dan adam ya kamata ya samu,zaki samu y'ancin karbar abunda yake naki ne amma ake ta faman boye maki an kasa fito da hakan saboda tsoro,insha Allah wannan alkawarina ne gareki,kisa a ranki wahalarki tazo karshe yanzu babu abunda ya rage gareki face ki karbi kaddararki da hannu bibbiyu ki karbi ki kuma yarda da canjin da Allah ya yi maki Nihla".Kallonta yake ci gaba da yi kallo daya zaka mata kasan baccin wahala take kuma ko kadan bata cikin natsuwa,hannu yasa ya goge mata hawayen dake bin gefan idanuwanta suna zubowa kafin yabar dakin.Nurses ya saka su kula da Nihla zaije gida ya dawo. Tunda ya shigo gida bai ansa ko gaisuwar da masu aikin gidan suke masa ba ,ya wuce ciki da ido Ramadan ya bisa da kallo kafin yace"Yaya lafiya kuwa❓".Dafa kafadar Ramadan ya yi tare da gyada kai ya karasa shiga tsakiyar parlon be wani yi tunani sau biyu ba yace"Ammi ki shirya Nihla ba lafiya taba asibiti".Zumbur Miemie ta mike har idanuwanta sun kawo ruwa tace"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Yaya meya sameta❓dan Allah ka kaini in ganta". "babu wanda zai fita a gidan nan bare yaje ganin wannan yarinyar da na ciga na cireta daga cikin wani da zai iya rabarmu".Cewar Kaka dake shigowa Parlon fuska a matukar daure. Ras ras haka plate din dake hannun Ammi ya fadi ya tarwatse hawaye ne suka kawo idonta da sauri ta iso gaban Kaka tare da hada hannuwanta biyu tare da cewa"Kaka dan Allah kada kice haka,Kaka in kinso zaki iya mana komai amma kada ki hana mu zuwa duba abunda yake dawainiya a kanmu,na rokeki ko sau daya ki sassauta zuciyarki akan Nihka kaka ,Nihla bata da laifi in ma Mahaifinta yayi laifi kaka ba itace mai laifi ba". "ya ishe ki haka Maryam"kaka ta fada a tsawace,wanda ya haifarwa wanda ke wurin kullewar ciki. Da sauri Daddy ya iso gabata tare da cewa"Hajiya dan Allah". "ni yau har ta kai kuna fada mun abunda ya kamata nayi❓Maryam ke da kanki❓a yaushi kika dauki alhakin kula da waccan yarinyar ba ni da labari❓yarinyar da cuta duk ta gama kanainayeta❓"Kaka ta kare maganar tana kallon Ammi. Runtse ido da karfi Zafar ya yi yana kuma jin zafin kalaman Kaka akan Nihla,juyowa ya yi tare da cewa"har ke xakije ganin Nihla ba iya y'an gida kadai ba". Cakumar kwalar Zafar tayi tare da girgiza sa da karfi tace"kayi hauka ne❓ko kuma ka fara shan wani abu ban sani ba❓to ka bude idonka da kyau bazan taba taka kafata ba da sunan naje ganin jinin Umar har abada" "shin da sauran kakannin mu ne zasu goyi bayan hakan daga gare ki❓,idan da Kaka Aysha kika barwa Abba shin zaki tsammaci hakan daga gareta❓haka ne rikon amana kaka❓Abba Umar amanarki ce ya tashi beda uwa bare uba baida wasu dangi da suka wuc naki sai lokaci daya ki fitad dashi❓kuma harki mayar da hakan akan y'ar daya haifa ❓yau dai ko sau daya Kaka ki bude idonki ki kalli gaskiya,ina so ki biyoni na nuna maki wani abu idan yaso daga baya zaki iya yanke hukunci da kanki komai kike so shi zaki yi". Hannu yasa tare da cire hannun Kaka daga rikon data masa,kallonta yayi ganin akwai mayafi a jikinta dama kuma bata taba zama ko a cikin parlo ne yasa yaja hannunta ya fara tafiya da ita,bata musa ba ta soma binsa,ganin hakan yasa duka yan gida rufa masu baya mota biyu sukayi,Zafar kam bai tsaya ko ina ba sai cikin harabar asibiti.Kashe motan ya yi ya zagayo ya budewa kaka mota ya taimaka mata ta fito nan ma still hannunta ya kama har zuwa cikin emergency tsakiyar dakin ya tsaya cak hakan ce ta faru da duka yan gidan da suka biyo su,hannu ya daga tare da nuna Nihla,tare da cewa"Kaka ki kallah".Kamar bata son juyawa hakan ta juya tare da kallon in da Nihla ke kwance duk na'u'rori a jikinta,cikin tsanannin raunin murya ya fara magana"shin kaka akan waccan kike fada❓jikarki da take gwagwarmaya da rayuwarta❓yarinyar da ko sau daya take fatan ta rayu,kaka Nihla bata taba karaya ba duk da yarda ta taso cikin maraici wanda kuma yake bango abun jingina a gareta shima Kaka ya kauce,Nihla bata da kowa sai mu,wanda take so kuma take burin kasancewa da shi ya cuceta a yau nake fada maki ya fiddo katin aurensa tare da Aunty wacce ta taka matsayin uwa a gareta".Ba kaka kadai ba kowa na dakin ya firgita da shiga tsananin tashin hankali sabanin Miemie dako a jikinta dan tasa a ranta Aunty zata iya aikata fiye da haka ma. "shin yanzu wannan bata cancanci tausayawarki da yafiyarki ba❓,kinsan Nihla dawainiyata ce a yau nake shirin kara gaya maki wani dawainiyar data rataya a kaina,ba kina so kiga matar da zan aura ba❓". Gyada kai kaka tayi dan bata jin zata iya magana a wannan lokacin ita kanta ta rasa gane meke damunta❓ko wanne irin yanayi take ciki,abunda ta sa ni kawai shine dai kunnuwanta na sauraran kalaman Zafar. Rike hannuwanta biyu ya yi sosai a cikin nashi,kafin yace"ina mai fada maki cewa Nihla Umar Matata ce ta sunnah da aka aura mun yarda musulunci ya tana da na biya sadakinta da kuma shaidu sun tabbatar Nihla ta zama Matata ta sunnah" *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *MARUBUCIYAR* *SANADIN GATA* *YAUDARA KO BUTULCI* *DALILIN SO* *SO DAYA* *ASALINA* *ADDININA* *SHI NE AJALINA* *RUHIN FANSA 1&3* *HANAN* paid book *ABU BILAL* Paid book *FARAUTAR FARIN CIKI* ✍🏻🤸🏻‍♀️ 83 Tsurawa Zafar idanuwa Kaka ta yi ko kibtawa bata yi jin jiri na neman daukanta ta tafi tagal-tagal zata fadi yasa Ammi saurin riketa,hannu Kaka tasa tare da rike Ammi ta kuma sauke wata nannauyar ajiyar zuciya,kwatakwata ta kasa yarda ace yau jinin Umar shi ne matar jikanta,jika mafi soyuwa aduk jikokinta,ko a mafarki bata taba tunanin hakan zai iya faruwa ba,shin ashe duk yarda ta yi hakan bazai iya nesanta yaran ba,dafa kai tayi tana kuma kawai da kai jin Zafar ya kuma rike hannuwanta tare da cewa"shin Kaka zaki iya gudun Nihla❓ Zaki iya rabani da abunda na rayu da soyayyarsa❓Kaka na rayune saboda Nihla,na canza duk tsarin rayuwata saboda Rayuwarta,ina mata son da bana yiwa kaina". Ja da baya Kaka tayi tare da zama akan kujeran roban dake kusa da ita cikin dushewan murya tace"ka gaya mun lokacin da ka auri Maryam". Akan gwaiwowinsa ya tsuguna ya daura kansa akan cinyar Kaka yana jin zuciyarsa na suya yace"na Auri Nihla ne a ranar da Abba ya rasu,kuma akan yarda addinin mu ya tanada,Daddy ,Ramadan da Dr Aminu su shaida ne,na biya sadakin Nihla an kuma daura mun aurenta,hakan ya faru ne ta dalilin Amanar da Abba ya kuma daura mun mai girma ta zamowa Garkuwan Nihla ,shi ne suka yanke hukunci akan cewa Aura mun ita shi ne kadai zai ba ni tabbacin kula da ita ta ko wanne fanni,Sannan kaka ko kadan Abba bashi da hannu akan zargin da kike masa,idan lokaci ya yi zan sanar da ke hakan da duk wasu sheduna idan kina bukata". Hawaye suka zubo akan fuskar Kaka kasa furta komai ta yi. "Hajiya Dan Allah ki bar zubar da hawayen ki ,nayi maki alkawari idan kika nuna bakya so zan saka Zafar ya sawwakewa Nihla tunda bata san da auren a kanta ba,amma ina rokonki da kada ki hana mun rikonta a matsayina na wanda take kallo uba gareta"Daddy ya fada. Dafa kan Zafar Kaka ta yi tare da cewa"wacece ni da zanja da hukuncin Allah Zafar❓duk iya kokarina na nisanta ku amma sam ba haka Allah ya so ba,gashi ya yi ikonsa a kanku wanda ba ni da yarda zanyi,ni bazan dauki alhakin kowa ba,ba kuma zan kashe aure ba rabo ya kashe ni,itama wani sauyi ne Allah ya yi mata na wancan algunguman da ke son cutar da ita,duk da ba ita na so ka aura ba amma kuma ita Allah yaso maka,Allah ya bata lafiya,ku mayar da ni gida ina so in huta". Sanyi,dadi,farin ciki mai cakude da sanyayyar annashuwa ce fa dirarawa duk wani Dan Adam dake cikin dakin asibitin musamman ma Zafar sai dai sam beji mamakin abunba tabbas yasan Kaka kamar kwakwa take wajenta akwai matukar tauri sai dai cikinta ta fi komai laushi da kuma tausayi,hamdala ya yi ga sarki Allah kafin ya furta"Alhmdllh,ni da Kaka fada ya kare kuma". Dungure masa kai tayi tace"da'allah labcecen banza ni ba ni wuri na wuc....."kasa karasa maganan tayi jin Muryar Nihla na kiran "Yaya...ya...ya"idanuwanta a rufe gq hawaye na gangarowa da ga cikinsu,saurin mikewa Zafar ya yi ya karasa kusa da bed din ya rike hannuwanta yana cewa"Nihla,ga Yayanki a kusa da ke,me kike so❓"kamar wacce ta yi mumunan mafarki firgigit haka ta mike ta rungume Zafar da iya karfinta kamar za'a kwace mata shi a hankali sautin kukanta ke tashi yana zagaye ko wacce kusurwa da lungu na dakin,ta yananayin kukan nata kadai ya isa ka gane kuka ne mai cike da tarin kunci,takaici da kuma tsananin kewa. Runtse ido kaka ta yi tana kuma jin wani irin yanayi yana shigarta,lokaci daya jikinta ya dauka tsam kamar wacce aka soka da allura,hanyar waje ta yi hakan yasa Ramadan da Ammi suka bi bayanta don mayar da ita gida. Miemie kam a guje ta iso wurin gadon ta hada Zafar da Nihla ta rungume tare da fashewa da kuka. Jin muryar Miemie na yawo a kanta yasa ta dago idanuwanta da suka gama rinewa tare da yi mata nauyi ta zuba su a cikin na Miemie"ki..ki daina..Ku..kuka"ta fada. Murmushi ne ya subucewa Miemie taja Dogon hancin Nihla tana cewa"kukan farin ciki nake in law". Zumburar baki Nihla ta yi tare da murgudawa Miemie baki ta juyar da kai,ba Miemie ba hatta Zafar sai da ya murmusa sosai hakan ya yi mata kyau duk da tana cikim jinya. Karasowa jikin bed din Daddy ya yi yace"y'ata❓sannu kinji,ina yake maki ciwo❓". Jin muryar Daddy yasa ta tashi da sauri tace"Daddy". Da na'am ya ansa mata yana kara matsowa kusa da ita. Ganin Daddy a kusa da ita yasa take ganin kamar Abbanta ne a kusa da ita tace"Abba,kaina kafana ,hannu Abba da ko ina ciwo yake mun". "Allah ya baki lafiya,sannu insha Allah zai daina kinji,kiyi hakuri haka Allah ya kaddara maki,sannu"Daddy ya fada. Dr Aminu ne ya shigo bayan sun gaisa da Daddy ne yace"Dr muje a iba jinin". Kai Zafar ya gyada tare da gyarawa Nihla kwanciyarta kamar jira take ta lumshe ido sai bacci. Daddy ne yace"jinin za'a kuma saka mata❓" Da eh Zafar ya ansa "kamar ko yaushe jinin nata ya kone ne ,tana bukatar kari". "Allah ya baka lada Zafar,Allah shine kawai xai biyaka akan kokarin rike amanar da ka ke yi,Allah ya dafa maku ya kuma biya maku bukatunku na alkhairi". Da ameen ameen suka ansa sannan Daddy ya tasa keyar Miemie gaba suka wuce gida,dan yasan idan tana nan ba zata taba bari Nihla ta huta ba. A harabar gidan su Daddy suka iske Kamal yana jiran Miemie a mutunce Kamal ya gaishe da Daddy sannan suka zauna shi da Miemie kallonta ya yi tare da cewa"yan matana wannan fara'a haka❓duk ta mecece❓ke da kika dawo daga asibiti nasa xan ganki fal fa damuwa shiyasa nazo rarrashi tunda tabin ranmu ba lafiya". Kallonta ta maido gareshi tace"ya akai kasan muna asibiti❓". "Aunty ce ta gayamun Nihla ba lafiya"ya bata ansa. Wani irin hade fuska Miemie tayi tare da jan dogon tsaki tace"matsiyaciya kenan,wallahi hakki baxai taba barin Nafisa ta zauna lafiya ba da ita da duk wani mai goyon bayanta cikin tarwatsewar rayuwar yar uwata,sai dai kuma wani hanin ga Allah baiwa ne,cin amanar da zaluncin da tayi hakan be hana Allah zabawa Nihla zabi na gari ba". "My luv yau kuma Auntyn tawa ake xagi a gabana"Kamal ya fada. "fin zagima My luv,komai zan iya yi a kanta,tunda bata da tausayi bata da kuma mai fada mata ta ji,a kullun ina takaici da bakin cikin kasancewarta wani bangare a cikin rayuwarka,da ina da yarda zanyi to tabbas zan kankare hakan na raba duk wani alaka a tsakaninku tunda kaima bana da tabbas din ba taudararka zata yi ba,kai nifa ko menene nawa na gane yana da alaka da wannan butulalliyar matar da tayi silar tarwatsewar ahalina wallahi wallahi bazanyi jinkiri wurin rabuwa da shi ba,any way na manta ban fada maka cewar a yanzu Nihla matar Yaya Zafar bace". Dam dam haka zuciyar kamal ta bada sauti,tuni gumi ya gama rifeshi ga wani irin sanyi dake ratsa jikinsa yace"My luv me nake ji hakan yana fitowa daga bakinki❓wanne irin aure kuma tsakanin Zafar da Nihla❓a yaushe aka yi shi❓kina nufin ko nine nake da alaka da Aunty zaki iya rabuwa da ni❓"kamal ya jerowa Miemie da wadan nan tambayoyin a lokaci daya ya kuma tsareta da idanuwansa da tuni suka gama fita a hayyacinsu,kunnuwansa suka kara tsayi da budewa suna neman ansa kota halin yaya. Murmushi Miemie tayi tare da cewa"aure da kasan anayi mana,to shine a tsakanin su,da Allah ya rabata da Irfan sai ya bata Namiji adali wanda yasan ciwanta wato Yaya Zafar.Kuma da kake hada kanka da ita dan Allah kama daina,kai ba maciyi amana bane,ba kuma zaka taba kasancewa irinta ba karma ka batamun rai". Jiki kam na Kamal tuni ya gama sanyi da daskarewa kwakwaran motsima da kyar yake iya aikata shi lallai allura zata tono garma kenan! akwai daukar dala ba gammo kenan sai dai ko da a wasa bazai iya daukar rashin Miemie a tare da shi ba,dan itace rayuwarsa kuma bugun numfashinsa rayuwarsa ma fansa ce ga tata. Tafa hannu Miemie tayi akan fuskar Kamal tace "ya ya dai❓". "babu komai,kije gida zan kiraki"be jira ansarta ba ya tashi yabar gidan,a guje yaja motarsa kamar wanda zai tashi sama .Da kallo Miemie ta bishi kafin ta wuce cikin gida tana jin yau jin kanta take kamar wata sarauniya. Ko daidaita parking Kamal beyi ba ya fito yabar motar a kofar gida da key a jiki ya shiga gidan su Nihla garin sauri har hadawa yake da gudu gudu.Tsakiyar parlon ya yi wa kansa masauki. A tsorace Aunty da Irfan suka tashi tare da hada baki wurin tambayar ko lafiya.Ruwan sanyi Kamal ya dauka tare da shararawa kansa daga tsaye kafin yace"lallai akwai tashin hankali da matukar damuwa,ina mai bakin cikin sanar da ke cewa Zafar ya Auri Nihla". Dib haka jin Irfan ya dauke kamar wani gaula haka ya soma bin Kamal da kallo a matukar tsawace yace"karya kake,hakan bazai taba yiwuwa ba,wannan wacce irin zance ne marar kan gado,yarinyar dake asibiti kwance❓". Ragab haka Aunty ta fada akan kujera tana cewa"Kamal anya ba wani abu kasha ba❓". "tunda kike da ni kin taba ganin nasha wani abun maye❓maganar gaskiya nake gaya maki Zafar ya auri Nihla". Wata irin dariya Aunty ya saki tare da mikewa a hassale tace"lallai dole Zafar zai mutu ko da lokacin mutuwarsa beyiba,tabbas idan hakan ta kasance aikin da nayi tsawon shekaru zai iya ruguza shi a yan kwanaki,tabbas shi zai mutu kai idan ya kama har Nihlan ma ta mutu,dole ka kashe su Kamal". Wani irin zabura Irfan ya yi kamar wanda ciwan hauka ya taba yace"nevee babu jaddawalin kisa a tsarin nan,kina nufin zaki iya kashe Nihla❓". "Ko kadan banso hakan ba,amma ya zanyi tunda kaddara ta tunzura ni❓"Aunty ta fada. Kamar wani sakarai haka Kamal kebin Aunty da kallo,tsab kalaman Miemie ke masa yawo da ansa kuwwa a kai,glass cup din hannunsa ya yi wurgi dashi tare da sakin wata kara yace".... *Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *MARUBUCIYAR* *SANADIN GATA* *YAUDARA KO BUTULCI* *DALILIN SO* *SO DAYA* *ASALINA* *ADDININA* *SHI NE AJALINA* *RUHIN FANSA 1&3* *HANAN* paid book *ABU BILAL* Paid book *FARAUTAR FARIN CIKI* ✍🏻🤸🏻‍♀️ 84 "kina tunanin zan iya sadaukar da soyayyata dan biyan bukatanki ne❓,meyasa zan kashe Yayan wacce nake so❓ni da ke da kowa kuma munsan yarda take son shi❓sam hakan bazai taba yiwuwa ba Nafisa kidai canza abunyi".Kamal ya fada. "kamal me yake damunka ne❓har yaushe zaka zabi soyayya akan rayuwarka❓tunda ka riga ka shiga lamarin ya zamar maka dole kamun biyayya kamun kuma abunda nake so ,idan kuma har kayi wasa a kan hakan har ita Miemien da kake takama da ita ina mai tabbatar maka ba zata tsira ba". Tas tas haka kike jin Kamal ya dauke Aunty da tagwayen maruka har biyu,da sauri Irfan ya shiga tsakiyarsu tare da cewa"dan Allah ku daina wannan fadan,ta hakan ku gaya mun ta ina zaku samu mafita❓rabuwar kai bazai taba kawo masalaha ba". "ka mare ni❓wallahi ina mai tabbatar maka sai kayi dana sanin marin nan da kayi,tabbas marin nan shine silar rabuwarka d wannan yarinyar da aka haifa a tafin hannuna amma ka wulakanta ni saboda ita"Aunty ta fada. Hade fuska Kamal ya yi tare da cewa"muddun sunan Miemie bai fita a bakinki ba to ina mai tabbatar maki ke zaki fara yin dana sa ni a rayuwarki,wanda nasan sai kinyi din ma,ki sa ni duk wani iya shege da iskanci da kike nema gidan shi ki ka zo,bazanyi jinkiri ko daukar lokaci ba wurin yin maganinki ki tuna wannan"be jira cewarsu ba ya yi gaba abunsa. Daura hannu a ka Aunty ta yi tare da koma sharab akan chair ta fada tana fadin"innalillahi tabbas rabuwa da Kamal kamar wani tonan asiri ne na rayuwata". "kin aikata wa ni abun ne da baki so kowa ya sa ni❓"Irfan ya tambaya tare da zuba mata idanuwansa wanda tuni sun gama canza kala dauriya ce kawai yake yi. "a'um dama ba ga dukiyar dana kwasa ba nan na baka,shi ne nake gudun tonuwar hakan".Aunty ta fada a daburburce. Gyada kai kawai Irfan ya yi kafin ya fita daga parlon.Tafiya yake amma kamar wanda bashi da lakka ,kwata-kwata be ga ne gabas bare yamma ko kadan be san wacce duniya yake ba,kamar wani zautacce haka yake tafiya,hannunsa ya daura a kan kumatunsa tuni yaji damshin hawaye ,gyada kai kawi ya yi yana tunanin iya tsawon shekarun daya dauka beyi kuka ba,lallai dara taci gida,yau wani aikin ya juye da farin cikin rayuwarsa,tabbas ya dauki tsawon lokaci ya na farautar farin cikinsa amma yau rana daya kab komai ya rushe duk danadin da ya yi akan hakan amma ya tashi a tutar ba bu,lallai Al-amarin Allah sai kallo,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un sune kalaman dake fitowa daga bakinsa,hakan ya yi daidai da faduwa akan gwaiwowinsa da ya yi ya fashe da wa ni irin matsanan cin kuka mai matukar cin rai da kunci. A hankali take taka kafarta tana bin bayan Zafar tsab ta warke ras sai dai rashin kwarin jiki a haka har suka shiga mota suka bar harabar asibitin dan kishin gidawa ta yi tare da lumshe idonta,tsayawar da motar ta yi yasa ta dago lumsassun dara-daran idanuwanta ta zuba su a cikin in da suke,wani irin zabura ta yi ta mike sosai a motar tana rau rau da ido kamar zata fasa ihu cikin rawan murya tace"Ya..ya..yaya meyasa ka..ka..kawo ni nan❓ka mayar da..da ni gida". Ko kallonta be yi ba yace"nan ne gidanku da ga yanzu dan haka ki fito bana son shirme". Kara rudewa ta yi jin ya ambaci nan ne gidan su,a tsorace ta saka kafarta da sauri ta fito ta kama rigarshi daga baya ta rike kamar wanda ya yi mata sata,kyafta ido kawai take daka ganta kamar an tsoma kaza a ruwan zafi. "ki sa ke ni mana".Saurin girgiza kai ta yi ta kara boyewa a bayansa tace"Dan Allah ka mayar da ni gida,wurin Aunty zan je". Kamar wanda aka safkarwa da mutuwa haka ya hade fuska yace"idan kika karw kira mun wannan sunan a gidan nan sai na sassaba maki,oya wuce muje". Make kafada ta yi a dole ya yi gaba ta bisa baya tana rike da shi har cikin parlon.Kuuuuu haka cikinta ya bada sauti kamar zata saki zawo a wurin jin muryar Hajiya Kaka a parlon afkawa ta yi bayan Zafar ta rungumesa da karfi tuni kyarma ta kace mata ko kadan ta kasa lekowa ta kalli parlon,cak Zafar ya tsaya jin an cukuikuye shi,dariya Ammi ta yi tace"a'a Malan Muhammad a karaso mana". Shafa kai ya yi kafin yace"taya zan karaso bayan ta mun daurin goro?" Nokews suka yi kowa a dariya,kamar daga sama haka Muryar kaka ta karade parlon tana fadin"Maryama zo nan kinji". Raba ido Nihla ta fara yi,janye jikinsa Zafar ya yi kafin ya juyo yaja hannunta,suna tafiya a hankali tana tsaitsayawa a baya,gaban Kaka Zafar ya tura Nihla,kamar wacce tawa sarki karya haka ta dukar da kai tare da kama jikinta jira take a ce ar ta saka gudu. Kallon yarda take yi ne yasa Miemie da Ramadan sakin dariya ,hararar da Zafar ya jefa masu ne yasa sukayi shiru ba shiri. Kamar da ga sama ba zato ba tsammata sai dai aka ga Nihla a jikin Kaka ta rungumeta,fuskarta fal farin ciki ga hawaye na bin gefan idonta. Sosai kowa ya cika da mamakin hakan,dan ko da wasa babu wanda ya taba kawo wa ransa hakan zata faru ko Kaka zata karbi Nihla ta sauki haka . Basu gama karewa da Mamaki ba sai da kaka ta dago Nihla ta tarbi fuskarta da hannu bibbiyu ta fara magana"ban taba tunanin kara sake dawowarki a gidan nan ba,sai gashi da kika tashi dawo wa ba kin dawo a matsayin jika ba kawai kin dawo harda matsayin da nake da buri a kanshi,lallai kina da sa'a daya kasance kin kama zuciyar jika mafi soyuwa a gare ni,duk wani farin cikin mu yana tattare da nashi,barka da zuwa Maryama Zafar Al-ameen sirikar gidan nan ta farko". Dib haka jin Nihla ya dauke ko kadan tama kasa fahimtar menene kalmar sirika ke nufi❓kamar wata doluwa haka take bin Hajiya Kaka da kallo,ganin yananyin da take yasa Ammi zuwa ta kamata tare da cewa"muje kiyi wanka ki huta kinsan yanzu kika dawo da ga asibiti".Bin Ammi kawai take duk abunda take tana daga mata kai ne kawai amma sam bata ko fahimta kwatakwata ta kasa gane tareyen da Hajiya kaka tayi mata,a haka ta samu tayi wanka tea kawai tasha kasa kara saka wani abun a bakinta ta yi gaba daya zuciyarta a cushe take bata gane ma duniyar da take,kamar daga sama a jikin window din da take ta hango Irfan na shigowa cikin gidan taku yake yi irin na cikkakun maza,ganin yana doso kasan window d take yasa ta dukar da kanta dan taga shin wai da gaske nan yake tahowa❓lallai kam Zafar ta ga ni tsaye ya zuba hannuwansa cikin aljihun wandonsa a hankali yake taunar lips dinsa tare da tsotsa kamar zai huda.Baya tayi zata fadi sai tayi saurin dafa bangon da take ji,ganin sunyi musaba yasa ta saurara dan jin abunda suke fada. "kamar ko yaushe Zafar da nake gaya maka bana da niyar futar da Nihla,Nihla ita ce rayuwata,itace farin cikina,zan iya sadaukar da rayuwata dominta,amma yau naji wani batu wai Nihla ta kasance mata a gareka,tabbas bazance nayi bakin ciki ba sai dai zance nayi farin ciki da hakan dan tabbas nasan Nihla zata samu kula,zata samu kuma wanda zai iya sadaukar da komai nasa a kanta wanan shine burina tun asali ko ni idan zan gagara kula da nihla zanyi fata allah ya turo mata da jagora wanda zan jibanci maraicinta alhmdllh addu'ata kuma ta ansu". Hannu Zafar ya daga tare da tsayar da Irfan yace"duk menene na wannan maganganun❓kana son farin cikinta kuma ka zabi cutar da ita❓kaine jigon bakin ciki da kuncin rayuwar Nihla a yanzu bata da matsalan daya wuce kai Irfan ya kamata ka gane haka,dama dan ka gaya mun wannan maganganun akan Matata yasa kazo nan❓,to thank u find a way just leave". Wasu hawayen bakin ciki ne suka zubowa Irfan yace"komai zaka gaya mun bazan taba jin haushi ko kunci a kai ba,nasan duk kallon da kowa kemun kenan,amma ina so na fada maka har gobe har jibi ba za'a tabayin namijin da zaiwa Nihla soyayyar da nake mata ba,sai dai na yarda Allah bai halicce mu dan mu kasance tare ba,ni ban zabi na kuntatawa Nihla ba sai dai rayuwa ce ta zo da haka,nayi hakan ne na sadaukar da soyayyata dan na ceto Nihla daga tarkon da take niyar fadawa na kishiyar uwa,na sadaukar da farin cikinmu ne dan na samawa Nihla rayuwa mai kyau a gaba,nayi duk wannan ne dan gujewa rudin zuciyar Nafisa da take kokarin mallakar dukiyar Nihla kota halin yaya,na anshi soyayyar Nafisa ne badan ina sonta ba sai dai amfanin masoyiyata wanda nasan da naki hakan tabbas wani labari ake yi ba wannan ba"jikka ce Irfan ya mikawa Zafar yaci gaba da cewa"ka ansa wannan duk wani dukiyar Nihla ne da Nafisa ta bani akan na adana mu yudu da shi,ni kuma bazan iya cin hakkin wani bawa a duniyar nan ba,tabbas hakan ya yi mun amfani ko da zan kasance cikin bakin ciki amma nasan Nihla zata rayu cikin farin ciki,and shawara daya ka yi kokari ko ta halin Ya ya ka kubutar da Miemie daga soyayya da Kamal"yana gama fadan haka ya juya zai tafi,hannunsa Zafar ya rike tare da cewa"kana nufin kayi duk wannan ne dan kubutar da nihla❓" Murmushi kawai Irfan ya yi tare da gyada kai yace"ni zan wuce". "hakika baki da duk wani abu da zan malllaka maka yayi kankanta wajen gode maka ,kai namijin kirki ne,wanda irinku ko wacce mace zata bukata ta samu,tabbas kowa ya kalleka da mumunar fuska sai dai hakan bai gushe ba face sai da alkhairanka suka bayyana gare mu,kayi hakuri da nesanta ka da farin cikinka da na yi,Abba ya daura aurena da Nihla ne a ranar da zai bar duniya badan haka ba babu abunda zai hanani sadaukar maka da soyayyata dana raina na jima ina jinta tun kallon farko dana dauki Nihla a ranar da aka haifeta,na rayu ne akan soyayyarta kuma soyayyarta ita ke bani kwarin gwaiwa da jarumta da kara son kasancewa tare da ita". "Wannan bazai taba zama da matsala ba Dr,tabbas na cika da farin ciki da kai ka auri Nihla nasan ko bayan raina kai Garkuwanta ne"Irfan ya fada fuskarsa cike da fara'a Juyawar da zaiyi idanuwansa suka sarke a cikin na Aunty wacce take tsaye bayan Irfan ta kuma gama jin duk wani batu da suka tattauna,wani irin kuka ne ya kubce mata ta yi waje a guje .Share guntun hawayen da suka zubo masa ya yi kafin ya yiwa Zafar sallama ya fice faga gidan shima. Kamar watq statue haka take sulalewa zuwa kasa,ko kadan bata iya banbance tanayin da take ciki,wani irin kuka mai cin rai ta saki tare da kwala kiran sunan Irfan da iya karfinta,a guje ta mike zata yi waje ,Daddy ne ya yi saurin tare kofar da take niyar fita,ko ina a jikinta kyarma ya ke bakinta rawa take ta kasa furta komai face nuna hanya da take yi.A haka Zafar ya shigo dakin yana karewa Daddy da Nihla kallo. *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻 [3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FARAUTAR FARIN CIKI* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi``` *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *MARUBUCIYAR* *SANADIN GATA* *YAUDARA KO BUTULCI* *DALILIN SO* *SO DAYA* *ASALINA* *ADDININA* *SHI NE AJALINA* *RUHIN FANSA 1&3* *HANAN* paid book *ABU BILAL* Paid book *TABON 'DA NAMIJI* *FARAUTAR FARIN CIKI* ✍🏻🤸🏻‍♀️ END END END Ido cike da hawaye Nihla ke kallon Zafar kamar idanuwanta zasu fado,kai ya gyada mata da karfi ta fada kirjinsa tana fashewa da kuka tare da cewa"Yaya dan Allah ina so na gan shi,ina so nayi magana da Yaya Irfan".Kuka ne yaci karfinta bubbuga bayanta yake yi tare da alamar lallashi.Kamota Daddy ya yi tare da zaunar da ita,kallonta ya yi "Nihla kiyi hakuri babu wanda yasan da hakan,shiyasa Abbanki ya bawa Zafar aurenki yana kuma ganin babu wanda zai iya kula da ke sama yarda Zafar zai iya kula da ke,kiyi hakuri ki yi biyayya akan kaddarar data sameki."Daddy ya kare maganar yana kallonta. Kasa tayi da kanta shiru tayi hawaye na zuba a fuskarta cikin karfin hali tace"Daddy i'm not complaining,Allah yasa haka shine alkhairi a rayuwata,ni hakw tawa kaddarar tazo amma Daddy dan Allah ka ce masa ya barni nayi magana da Yaya Irfan ko sau daya ne". Cike da tausayinta Daddy yace"Maryama ki daina wannan kukan zakiyi magana da Irfan insha Allah,bana so ciwanki ya kuma tashi saboda wannan wahalan da ki ke yi,har gida Irfan zai zo ya sameki nayi maki alkawari". Kasa da kai Zafar ya yi kafin ya kalli Ramadan da shigowarsa kenan yace"ka dauki kuje da Nihla dakin Ammi,zamuyi magana ne". Da kallo kawai Nihla ke binsa rashin gane wacce magana za'ayi yasa ta mike tana yin gaba Ramadan na bin bayanta. Daddy,Ammi,Kaka kowa hankalinsa ya mayar ga maganar da Zafar keyi. Sake da baki haka Daddy ke bin Zafar da kallo gaba daya he's spechless wani irin rudu da tashin hankali ne suka tarar masa gaba daya,cikin son tabbatarawa da kansa abunda yaji yace"kana nufin Kamal ya bawa Nafisa gubar da Alhaji Umar yaci❓". "kwarai kuwa Daddy,mutuwar Abba ba hakanan tazo kai tsaye ba,hakan ya faru ne ta dalilin kashe sa da akayi,ina da rahoto na asibiti,sannan kuma Abba da kansa ya fada mun muguntar da Aunty ta ke shirin yi akan dukiyar Nihla,ya gane hakan ne bayan wata rana daya dawo daukar wasu files a nan ya sameta tana waya da Kamal sai ya wayance kamar beji komai ba wannan dalilin ne yasa ya daura aurena da Nihla"kallonsa ya mayar ga Hajiya kaka yace"kinata zargin Abba akan satar hakudan kudade ga takardu ki duba Kamal da Nafisa sune wanda suka saci kudin a office din Abba,wanda dukanku kusan yarda Kamal yake amintacce a wurin Abba". innalillahi wa'inna ilaihir raju'un shi ne abunda Kaka ke maimaita ta kuma fashe da kuka hannu ta daura a kai cikin muryar kuka tace"yau naga abunda ya ishe ni,ni da kaina na auro wa 'Dana bala'in daya tarwatsa mun kan zuri'a Allah bazai bar Nafisa ba,ga Umar harya mutu banje na ganshi na roki gafarar shi ba,innalillahi wa'ina ilaihir raju'un."kuka rurus haka Kaka ta saka kamar zata shide. Riketa Ammi ta yi duk da ita ma bata da bakin magana kuka kawai take yi,Daddy kam hularsa ya cire yana yin fita da ita,tuni zufa ta gama rufe shi ta ko ina,bai taba tunanin rashin Imanin Nafisa ya kai haka ba duk da dama yasan rashin kirkinta da kuma irin satar da takeyiwa Abba. Kamar wacce aka ingizo haka Miemie ta shigo dakin,fuskarta caba caba da hawaye kamar wata zautacciya haka yake binsu da kallo ya yin da hawaye ya kasa tsayawa a idanuwanta.Wani irin zaro ido Zafar ya yi cikin dakewa yace"ke me ki ke yi a nan❓." Cikin muryar kuka take magana"shin Yaya bai kamata na san halin da Kamal ke ciki ba ne❓,Kamal shine rayuwata shine farin cikina kowa cikin ku yasan haka,na rayi da son shi na bude idona da son shi dan mi yasa zaku zabi boyemun hakan❓." Kasa karasa magana ta yi tuni kyarma ta kwace mata juyawa tayi tabar dakin tana gudu ,kamar wacce aka jefa haka ta harde steps tayi kasa kafin ta karasa kasa taji ta fada jikin mutun ,duk da idanuwanta na rufe hancinta da bugawar zuciyarta basu yi kasa a gwaiwa ba wajen sanar mata da zabin zuciyarta ne wa to kamal,a hankali ta soma bude idanuwanta da suka soma sauya launi,da duk iya karfinta daya rage mata tasa wurin ture Kamal ta mike da sauri,a tsawace take fadin" meya kawo ka wurina❓ko akwai wani daya rage zaka cutar a nan❓ni ko iyayena❓yayyena ko kuwa Nihla❓,nayi dana sanin saninka a rayuwata kamal,na kasa yarda ni ce naso makashi ,mayaudari,maciyi amana,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"karar kukan Miemie yasa kowa fitowa,dib haka jin Nihla ya dauke na wani lokaci janye dogon riganta dake jan kasa tayi tare da soma safkowa daga stairs a guje ko ganin kirki bata yi,sai da ta iso tsakiyar parlon ta tsaya tana haki kamar wata zautacciya haka take bin Miemie da kallo tana bakinta na rawa take fadin"Mie..Mie Kamal da A...aunty suka kashe ...Ab...Abba❓". "Kwarai da gaske,Kamal shi ne wanda ya bada gubar da aka ciyar da Abba naji hakan da kunnena,nayi danasanin rayuwata Nihla,a kullun rayuwarki nake tausayi ban sa ni ba ashe tawa ma abun tausayi ce,wanda na bawa yarda da duk soyayyata shi ne wanda ya zama sanadiyar tarwatsewar ahalina"Miemie ke fada cikin kuka. "ya isa,ya isa haka"Kamal ya fada da karfi,cikin daga murya da tsananin fushi yaci gaba da cewa"nayi hakan ne duk dan saboda ke ne,nayi hakan ne dan na baki rayuwa mai kyau,bani da kowa sai ke soyayyarki itace ta mayar da ni mutun,idan da ban biyewa Nafisa ba taya zan sameki ❓bayan tana ikirarin idan na juya mata baya zata saka a koreni aiki,Aysha ta ina zan ganki har ki soni❓,na rokeki duk abunda zaki mun kimun amma karka gujeni dan Allah"ya kare maganar nasa tare da hada hannuwa wuri daya,for the first time da hawaye ya fara gangarowa akan fuskar Kamal. Ragab haka suka ji karar faduwa Nihla ta fadi akan gwaiwowinta tana jujuya kai da sakin wani irin kuka mai kara,da sasasarfa Zafar ya yo kasa shima ya tsugunna akan kafarsa,janyo Nihla ya yi yana lallashinta,a jikinsa ta fada tana wani irin kuka mai cin rai da tsananin kuna,ji takeyi zuciyarta ta yi mata nauyi kamar zata fasa kirjinta ta fito,lallai wani kukan da hawaye salama ne,a wannan lokacin ne ta nemi ruwan hawaye ta rasa lallai ashe bayan duk kuncin da tayi a baya salama ne akan na yau da take jin kanta dama mutuwa tayi ta huta,lallai Aunty da kamal sun kasance wani jigo na turata ga kusantar bakin cikinta da kewarta.'Dago idonta tayi tana kallon Aunty dake shigowa parlon da iya karfin tana fadin"ina Nihlan da Irfan suke❓lallai tunda yaci amanata yau tashi tazo karshe". Janye jiki Nihla tayi daga jikin Zafar ta mike,saurin riketa ya yi yana girgixa mata kai,alama ta yi masa daya saketa,cikin takun karfin hali ta isa gaban Aunty,kallan kallo sukeyi kafin Aunty tace"saboda ke,saboda ke yau na gagara cika burin da nake dauke da shi na tsawan shekaru,kinsa Irfan ya guje ni ya kuma yaudare ni,abunda wani bai taba yimun ba,naso har na gama abunda nake na tafi na barki ba tare dana taba lafiyar jikinki ba amma kinki bani damar hakan,kada ki zarge ni a duk abunda xai faru da ke Nihla,komai laifinki ne". Cikin muryar kuka Nihla tace"yanzu duk abunda kika aikatamun yafi ace raina kika dauka da ki rabani d mahaifina,shin kinsan menene shi a gareni? shine duniyata,alfaharina da duk wani abu da zanyi takama dashi,na miki kallon Uwa ban taba jin daidai da rana tsaya zan iya saba maki ba duk da Irfan da kika dauke a wajena ,ashe kedin me fuska biyu ce,kedin rayuwata kike nema kin kuma ci nasarar rabani da duk wani farin cikina,sai dai ina mai farin cikin sanar da ke cewa babu wani da zai kaiki kotu ko wani wuri kara,hakkin ran salihin bawa kadai ya isa ya hanaki jin dadin duniya,Allah kadai xai iya maki sakayya akan abunda kika aikata,duk wata kotun duniya tayi kadan wajen daukar fansan ran mahaifina,dukiya kike so❓dukiya ta saka ki yin duk wannan❓ki dauki komai kije dashi ,da nasan wannan ne burinki wlh raina da duk wata dukiyar dake garemu fansa ce ga ran mahaifina"kuka ne mai tsananin karfi ya kwacewa Nihla,bata ankara ba taji an fizgeta da karfi gefe,feee haka garin maganin ya soma bin iska wanda ke hannun Aunty da taso zubawa Nihla.Kamar statue haka Aunty ta tsaya tana kallon Irfan daya zanje Nihla,kwararo ido tayi kamar mayya sabon kamu kafin ta fasa kara da karfi tace"ka kuwa san abunda kayi mun Irfan❓Malan ya gaya mani ma damar wannan maganin behau jikin Nihla ba to tabbas ni zan haukace ba ita ba" Kowa kallon Aunty yake yana jinjina rashin imani irin nata,"bakin halinki da mugun abunki kab kanki zai kare badai kan jikata ba,baka mai bakar aniya wacce bata san abun arziki ba,tsintacciyar mage Allah wadaran halinki Nafisa ,Allah shi zai mana sakayya akan abunda kika aikata mana".Kuka kaka ta fashe da shi,jin shewar Aunty yasa tayi wuki-wuki da idi tana kallon Aunty dake kururuwa tuni ta cire Dan kwalinta ta baje guntun gashinta ya gama mikewa tsai-tsaye kartar jikinta takeyi da akaifan dake hannunta,ihu take tana fadin duk wani abu data aikata.Da sauri Zafar yaso ya janye Irfan da Nihla wanda aunty ke niyar kaiwa hari.Saurin ja da baya tayi tana rufe ido dan wani irin tsoro da kwarjinin Zafar ya kuma dirar mata a guje tayi hanyar waje tana sambatu da jiwa kanta ciwo. A tsawace Miemie tace"kaima kabar gidan nan bana bukatar ko a lahira na kuma ganin wannan mumunar fuskar taka Kamal,na tsaneka na tsaneka". "baxan iya rayuwa babu ke ba Miemie,idan kika rabu da ni hakan shine karshen rayuwata,amma ina so ki sani ina matukar sonki"kamal ya kare maganar yana yin hanyar waje da sauri.Fadaww jikin Ammi Miemie tayi tana kuka kamar ranta zai fita. Daddy ne ya dauko tsadaddiyar zoben azurfa da kuma zoben zinari ya saka su a yatsun hannun Nihla tare da cewa"wannan shi ne sadakinki da ni a matsayina na wakilinki na karba a hannun Abban Zafar da kuma shi,ina fatan ba zaki bamu kunya ba ,duk da labarin ya sauya kala Nihla kiyi hakuri ki karbi Zafar a matsayin zabin da Allah ya yi maki". Hawaye kasa tsayawa sukayi a fuskar Nihla,kai kawai take gyadawa Abba amma ta kasa furta komai. A rude Ramadan ya shigo gidan yana fadin "innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Mota ta kade Kamal ko kamanninsa ma baka ganewa wani mumunnn hadari ya faru da shi,kuma a take a wurin ko shurawa beyi ba".Saurin Jan Miemie Ammi tayi ta wuce sama da ita. 5years later. Fitowarta daga mota kenan sanye take da fararen kaya na nurses sosai kayan suka mata kyau,tayi kiba a bunta murmushi shinfide akan kyakyawar fuskarta.A hankali take taku harta iso kofar da zata sadata da cikin gidan.Da gudu Karami yaro Dan kimanin shekara ukku ya rugo ya rungumeta yana fadin "oyoyo Mummy".Tuni fara'a ta kuma yalwata akan fuskarta ta duka tare da daga yaron sama tace"Faruk sarkim rigima,oyoyo Abbana"Nihla ta fada.Rungumeta yaron ya yi wanda kallo daya zaka masa ka gane tsantsar kamarsa da Zafar kamar ya yi kaki ya ajiye.Da shi a kafadunta ta karasa ciki parlon yana ta zuba mata surutu.Da gudu Famal da Faman yaran Mieme da Irfan suka rugo tare da rungumarta suka rike mata kafafu suna ihun murna.Jin ihun murnar yara yasa Zafar dake zaune yana aiki a laptop ya tureta ya fito da sauri yana fadin"Miemie kina aikin me❓idan kuma suka sakamun mata ciwo fa❓"da sauri ya karaso ya karfi Faruk tare da janye Faman da Famal yana cewa"ku bar Mummy ta huta yanzu ta dawo aiki fa". Miemie dake zaune tana wa Little Nihla wasa tace"haba Yaya oyoyon ma,to idan ka hana kowa riketa ai baka hana ta dauko takwararta ba,maza karbeta kafin Abban su Famal ya shigo mu wuce". Dariya Nihla ta sanya tace"kwarai kuwa Abba Irfan ai yamun takwara dole na dauke kayata,ana yayeta ma ko mutun be so dole ya bani takwarata". Juyar da kai Miemie tayi tare da cewa"kanki ake ji,ni da tun yanzu zaki dauketa ma aida kin faranta mun". Dariya Aunty Aisha ta saka dake xaune(Aysha yanzu ita ta auri Ramadan dam sam Kaka taki bari ta kubucewa Family dinta),tace"ku kullun dakun zauna musun ku kenan,ni a hada mun duka yara na fiku bukata,kunga Affan(Al-ameen shine yaci sunan Daddy) sai yama yini ban gansa ba daga wannan ya figa sai wannan ya figa". Tsuke fuska Hajiya Kaka tayi wacce shigowarta kenan parlon ga alamun kara tsufa duk ya bayyana a jikinta tana cewa"Allah kadai zai saka mun Aisha anshi yaron ki tunda baki bani da zuciya daya,daga yauma na gama tabq yaron uban kowa".Ta kare maganar tana ajiye mata Affan akan cinyarta Dan kimanin shekara 1. Murmushi Nihla ta yi ta daura hannuwanta akan kafadar Kaka tace"rabu da su Hajiya kakata,ga Faruk nan ba baki baki daya ". "Yimun shiru ko zan dauki kowa banda gadon rashin kunya,wancan yaro tsab ba abunda ya baro na labcecen ubansa,in daukesa Zafar yazo ya kare mani rashin daraja da rashin arziki ba ruwana ni kinga tafiyata".kaka ta fada. Murmushi Zafar yayi yace"eh ban badawa dai".Harara Daddy ya jefa masa yace"ya isheka haka Zafar,duk yaron da Kaka take so dole ta dauka".Cikin tabbatarwa Ammi tace"kwarai kuwa". Irfan da Ramadan da shigowarsu kenan Irfan yace"ta dauki kowa banda little Nihla".Sake da baki Ramadan yace"kaima ta baka ansa daidai da kai yanzu ai"duk parlon suka saka dariya cike da tsananin farin ciki da jin dadi.Kallo daya zaka masu kasan cewa lallai farin ciki ,natsuwa da kwanciyar hankali sun gama ratsa ahalin duk da kalubalen rayuwa iri-iri da suka fuskanta amma yanxu ya zama tarihi babu abunda suke fama dashi sama da tarin farin ciki da kaunar juna,bakin ciki ya kau...... Alhmdllh *kyakyawar gaisuwata ga Maman noor,Hassan Atk,Muhammad kareeem Mk,Sdeen,ina maku fatan alkhairi aduk in da kuke,hakika nayi farin ciki ta yarda kuka bada gudumawa akan yadamub littafin nan har inda banyi tunani ba,na gode sosai Allah yabar zaman tare* *ina rokon Allah ya albarkaci abunda na rubuta na daidai a littafin nan,wanda yake akasin haka ina rokonsa ya yafe mana,ya kuma bamu ikon yin amfani da darasin dake cikin littafin* *Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe* Jorderh✍🏻