Compiled by Umar Dalha. 💝 *A SANADIN SON KI* 💝 *Written by* Aishat A Muh'd ✍🏻 ♻£xclusive Writers Forum *Dedicated to my Sadeey (saNaz)* *PAGE 1-2* Wata mata ce durk'ushe a filin tsakar gidan tana faman risgar kuka, har da shashshak'a kamar zata sume saboda tsabar kukan da take yi, sakamakon fad'an da mijin ta yake mata, gefe d'aya kuma yaran ta ne su biyu namiji da mace suna rungume da junan su, suna taya kan su da mahaifiyar su kukan tausayin kansu. Tsinkar muryar mahaifin nasu naji cikin tsantsar 6acin rai da rashin mutunci yake cewa " tun da abin haka ne zan tafi na bar muku garin gaba d'aya, na sha fad'a miki ni bana son haihuwa kwata kwata, ban shirya yin ta yanzu ba saboda bana son ta, ga kuma shegen bak'in talaucin da muke ciki, amman ke kamar kaza kina haihuwa babu dad'e wa ki dad'a samun wani cikin ni na gaji " Ya k'arasa fad'i yana wani sauke numfashi, sakamakon hayagagar fad'an da ya gama yi cikin d'aga murya da tsawa, hararar matar tashi yake da 'ya'yan nashi, zuciyar shi cike da mugun tsanar su, ji yake kamar ya shak'e su, su mutu ko ya huta da ganin su. Cikin shashshak'ar kuka matar tace "Kayi hak'uri maigida, ni kaina ba ni na bawa kaina haihuwar ba, Allah ne ya bani su taya zan butulce mishi wajen zubar da cikin da ba shege ba ne, ka tuna haihuwa rahma ce wasu da kud'in su nema suke basu samu ba, amman kai da Allah ya bawa kyauta kana neman butulce mishi" Ko gama rufe bakin ta bata yi ba ya d'auke ta da wani azababban mari har guda biyu bisa kyakkyawar fuskar ta, sake durk'ushe wa tayi tana rik'e da fuskar ta inda ya mare ta, hawaye ne kawai yake zuba a idanun ta. Nuna ta yayi da d'an yatsan shi, cikin masifa yace "bana buk'atar jin shawarar ki ko wa'azin ki, idan baki bi maganar da na fad'a miki na ki zubar da wannan cikin ba, to wallahi zan bar garin don ban shirya rainon 'ya'ya ba, naji ma da uban talaucin da ya dame ni" Yana gama fad'in haka ya juyo kan yaran, tsawa ya kwantsama musu ba shiri suka shige d'akin uwar ta su da gudu, jikin su na 6ari na tsoron mahaifin nasu. Tsaki yaja tare da cewa "shegun 'ya'ya da munafurcin tsiya da sun ga uwar su na kuka, su ma zasu fara kukan 'yan iska kawai " Yana k'arasa fad'in haka ya sake makawa matar tashi harara tare da jan tsaki ya kad'a rigar shi ya fice fuuuu a fusace kamar ya hantsila saboda sauri. A hankali yaran suka d'aga labulen d'akin suna lek'en ko mahaifin nasu ya tafi, saboda jin shirun da suka ji, ganin ya fita ne yasa su fito wa da sauri suka nufi inda mahaifiyar su take tsugunne tana kukan nata. Rungume ta suka yi suna rarrashin ta da tayi hak'uri ta daina kuka, daman sune masu rarrashin nata idan uban nasu ya gama yi mata rashin mutunci. Dak'yar ta iya mik'e wa tsaye suka shiga cikin d'aki, zama suka yi akan tsohuwar tabarmar su wadda ke shimfid'e a k'asa, kallon yaran nata tayi cikin matuk'ar tsantsar kaunar su tare da mugun tausayin su, ta kamo hannun su ta had'a waje d'aya tare da bud'e bakin ta tace "Aliyu ga amanar Suhaima nan ko da bayan rai na ina son ka kular min da ita, bana son tayi kukan maraicin na, ina son ku tsaya tsayin daka ku nemi ilimi saboda inganta rayuwar ku ko da bana raye, ina son mahaifin ku yayi alfahari da ku a gaba, ku kasance cikin yi wa mahaifin ku biyayya a duk abin da yace muku, ku cigaba da addu'a watarana sai labari komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba." Cikin kuka Aliyu yace " Umma ki daina furta cewa zaki mutu ki bar mu, zamu rayu da ke Umma insha Allah, kuma zan rik'e k'anwa ta da kyau zan kula ta da ita Umma duk wani kyautata wa da bata farin ciki zan bawa Suhaima a cikin rayuwar ta." Ya k'arasa fad'i hawaye na zuba a idanun shi, cikin zuciyar shi tsanar mahaifin shi taf a ciki, Suhaima da bani wayo ne da ita ba sosai, kallon su kawai take tana kuka. Nan Umma ta janyo Suhaima jikin ta, rarrashin ta take har ta yi shiru sai sauke ajiyar zuciya da take, kafin kuma ta bud'e baki tace "Umma ni yunwa na ke ji." Umma kallon Aliyu take shima kallon Umman yake, cikin zuciyar su suna tunanin me zasu bawa Suhaima a yanzu taci, don basu da komai a gidan daman wani lokacin Aliyu ne yake fita yin 'yar sana'a ta k'arfi ya nemo musu abin da zasu ci, idan kuwa ta uban nasu ne kuwa gwara su mutu da yunwa akan ya basu abin da zasu ci. Gaba d'aya ba wanda yayi k'arfin halin bawa Suhaima amsa, jin haka ya sanya ta fashe da kuka don ko karya wa basu yi ba gashi yanzu azahar tana kok'arin yi, cikin rarrashi Aliyu ya janyo hannun ta yana goge mata hawayen fuskar ta yace "yi hak'uri 'yar k'anwa ta yanzu zan fita na samo miki abin da zaki ci, amman kada kiyi wa Umma kuka kin ji " Gid'a kanta tayi tana mai had'iye kukan nata, da sauri Aliyu ya fita daga d'akin, yayin da Umman ta bishi da kallon tausayi, yaron da bai fi ace yana k'ark'arshin kulawar iyayen shi ba amman shine yake kula da kanshi, mahaifiyar da k'anwar shi, saboda rashin dace da samun managarcin uba a gare su. Tun Suhaima na jiran Aliyu har bacci yayi awon gaba da ita a jikin Umma tana mai tsotsan 'yan yatsun ta a bakin ta, sai da bacci yayi k'arfi sannan Umma tayi mata shimfid'a ta kwantar da ita. Tashi tayi ta fito zuwa tsakar gidan tsintsinya ta d'auka ta laushi ta fara share filin tsakar gidan, tana yin sharar idanun ta na zubar hawayen tausayin kansu, wani 6angare na cikin zuciyar ta addu'a take yi tare da godewa Allah a halin da ta tsinci kanta a ciki, k'addarar tace ta auren wannan mugun mijin nata mara tausayi, mai butulce wa Allah da baiwar 'ya'ya biyu da ya bashi ga cikin na uku a jikin ta. Tun da Aliyu ya fita bai dawo gidan ba sai daf da mangarib, hannun shi rik'e da 'yar k'aramar leda bak'a, Suhaima na ganin shi ta mik'e da gudu ta k'arasa inda yake tare da kar6ar ledar hannun shi tana duba wa. Garin kwaki ne a ciki sai k'ullin sugar, kallon shi tayi fuskar ta d'auke da murmishi tace "Yaya mun gode Allah yasa ka samu sana'a kana samun kud'i kamar yanda Yayan k'awata yake aiki yana samun kud'i yana siyo musu abin dad'i " Cikin murmishi ya shafa kanta tare da cewa "Amin 'yar k'anwa ta ki cigaba da yiwa Yayan ki addu'a da Umman ki ." "Toh Yaya ina yi kullum idan nayi sallah, amman bazan yiwa baba ba tun da shi mugu ne yana dukan Umman mu, kuma yana zagin mu da dukan mu kullum, nima na tsane shi kamar yanda yace baya son mu ya tsane m........ " Kafin ta k'arasa fad'in maganar taji an zabga mata wani wawan mari wanda yasa ta hantsila k'asa, ledar garin kwakin ta baje a k'asa ta tarwatse cikin dandaryar k'asar tsakar gidan. Ashe basu ankara da shigowar baban nasu ba gidan, yaji abin da Suhaima ta fad'a shine yayi mata wannan marin da ko babba aka yiwa sai haka, cikin rashin imani ya kama Suhaima ya hau dukan ta kamar Allah ya aiko shi, Umma tana d'aki idar da sallahr mangarib d'in da tayi kenan tana sauri ta fito don ta jawa Suhaima kunne ta daina wad'annan maganganun, don lokacin da dawowar uban su gida yayi, sai kawai taji saukar dukan da yake yiwa Suhaima runtse idon ta tayi da k'arfi hawaye na fita a cikin su tana mai addu'ar Allah yasa kada yayi mata bugun da zai illata ta. Yana dukan ta cikin fushi yana cewa "shegiya tsinanniya daman ni ai ba son ku nake ba, da zaki ce baza ki min addu'a ba sai uwar ki da Yayan ki, na tsane ku bazan ta6a kaunar ku 'yan iska matsiyata " Cikin kuka Aliyu yace "Don Allah Baba kayi hak'uri ka dai na dukan ta, ka ga Suhaima yarinya ce k'arama ba zata jure dukan nan ba " Sakin Suhaima yayi yana haki kamar wanda yake jibgar k'atu, harara ya dalla wa Aliyu tare da cewa "Don uwar ka ni zaka fad'a wa gaskiya koh ?" Kafin Aliyu ya ankara tuni Baban ya kawo mishi duka nan ya had'a su ya dunga duka kamar Allah ya aiko shi, sai da yayi musu lilis tukunna ya ce " yanzu na fara dukan ku 'yan iska, Allah yasa ku mutu na huta da ganin ku" Da sauri Umma ta runtse idon ta tana rushe wa da kuka jin mummunan kalaman da uban su yake yiwa 'ya'yan ta wanda ba yau ta saba jin su a bakin shi ba. Yana gama fad'in haka ya fice daga gidan yana fad'a kamar wani ta6a66e, Umma tana jin yana fita ta fito waje da sauri zuwa wurin 'ya'yan nata da suke kwance magashiyan a k'asa suna kukan azabar dukan da aka yi musu. Nan Umma ta rasa me zata yi musu kawai sai ta had'a ruwa mai d'umi ta fara yiwa Suhaima wanka, daman ta d'ora ruwan tun kafin mangarib, sai da ta gama yi mata wanka ta gasa mata jikin ta, tukunna ta kai ta d'aki ta kwantar da ita, sannan ta dawo wajen Aliyu ta kai shi band'aki tare da ruwan wanka tace "kayi hak'uri Aliyu na, maza kayi wanka ka gasa jikin ka " Gid'a mata kai kawai ya iya yi, sannan ta fito ta tattara garin kwakin da ya zube ta tsince shi tukunna ta jik'a musu. Dawo wa d'akin tayi ta tashi Suhaima sanya mata kaya tayi sannan ta zuba mata garin a kofi ta mik'a mata, ai kuwa da sauri ta kar6a ta hau shan shi babu k'akk'auta wa. Ido Umma ta tsura mata tana kallon kumbararriyar fuskar ta ta zuciyar ta fal tausayin su, tana nan zaune Aliyu ya shigo d'akin dakyar ya iya yin sallah sannan ya zauna, mik'a mishi nashi garin Umma tayi girgiza kanshi yayi yana cewa "Umma ki sha kawai na k'oshi " Girgiza kanta ita ma tayi idanun ta fal hawaye tace "A'a Aliyu ka kar6a kasha idan kana son ganin kwanciyar hankali na " Bashi da yanda zai yi ya kar6a ya fara sha a nutse, ita ma Umma ta d'auki ragowar tana sha, bankad'a labulen d'akin aka yi tare da shigowa ba sallama, babu wanda ya d'ago kan shi ya kalli kofar saboda sun san wane mai shigo wa d'akin a haka. Ko kallon su bai yi ba ya shige k'uryar d'akin ya zauna saman gadon tare da bud'e kunshin tsire da gurasar da ya siyo ya hau cin abin shi hankali kwance, tuni d'akin ya d'umame da k'amshin naman da gurasar suka hau had'iyar yawu dukanin su har da Umma. Abin ka da mai ciki akwai kwad'ayi gashi ba ci ake ba nan ta shiga had'iyar yawu akai akai haka ma Suhaima, kallon Aliyu yake yi zuciyar shi tana zafi na tsanar halayyan mahaifin nashi, tashi tsaye yayi tare da cewa "Umma zan kwanta sai da safe " Don idan bai fita daga d'akin nan ba zai iya had'iyar zuciya ya mutu saboda tsabar bak'in ciki, kallon shi Umma tayi tare da cewa "Allah ya tashe mu lafia " "Amin " Yace tare da fice wa a fusace. "shege mai zuciyar tsiya da bak'in hali " Babu wanda ya tanka mishi har Suhaima bacci ya d'auke ta tana had'iyar yawu na son cin naman, kwantar da ita tayi tare da lullu6e ta da zani saboda lokacin hunturu ne. Tashi tayi tare da nufar gefen gadon k'arfen nata ta kwanta a can k'arshe tana mai tunanin makomar rayuwar su a gaba, ga cikin ta da yake k'ugin yunwa da haka bacci ya fara d'aukan ta, can cikin baccin nata taji mijin nata na lalubar ta alamar akwai abin da yake nema a wajen ta, wasu hawaye ne masu zafi suka dunga fita a idanun ta, duk dare ta saba da wannan halin mijin nata gashi ba abinci kirki yake basu ba, shi yasa kullum take tashi jiki ba kwari a gala6aice, tana kuka shi kuma yana sha'anin gaban shi har zuwa lokacin da ya rabu da ita ya juya mata baya, ba dad'e wa ta fara jin saukar minsharin shi, dakyar ta iya mik'e wa ta fito zuwa band'aki tayi wanka don bata iya bacci a haka, tana fito wa ta ga Aliyu zaune a tsakiyar gidan ga tsananin sanyin da ake zabga wa cikin mamaki tace "Aliyu lafiya? " D'ago kanshi yayi tare da cewa "Umma na kasa bacci ne, zuciya ta rad'ad'i take min " Ya k'arasa fad'a hawaye na fita a idon shi, cikin tausayin shi tace "kayi hak'uri Aliyu komai tsanani yana tare da sauk'i, bana son kana sa damuwa a ran ka wani ciwon ya kama min kai, kasan kai ne mai taimakon mu, yanzu tashi kayi alwala kayi sallah tare da addu'a, ka mik'a wa Allah buk'atun ka " Tana nan tsaye yayi alwala sannan ya shige d'akin shi, tukunna ta juya ta shige d'akin ta kwanta, jikin ta babu k'arfi da ita ma nafilar zata yi ta fad'a wa Allah matsalar ta, amman duk da haka sai da ta janyo carbi ta fara istigifari tare da salatin Annabi (SAW), da haka bacci mai k'arfi ya d'auke ta........... *** **** *** *ASALIN LABARIN SU* Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 *A SANADIN SON KI*💝 *written by* Aishat A Muh'd ♻ £xclusive Writers Forum *Dedicated to My Sadeey (SaNaz)* *PAGE 3-4* Umaru direba miji ne a wurin Fatima, auren so da kauna suka yi don sai da suka d'an jima suna soyayya kafin su yi aure. Bayan sun yi aure ne suna zaman su lafia cike da so da kulawar junan su, don ma bai fiye zama a gida ba tun da direba ne shi suna tafiye tafiye zuwa garuruwa daban daban, amman hakan bai hana shi kula da ita ba sosai kwatsam ana haka sai Fatima ta samu ciki tun daga lokacin ta rasa gane kan Umaru don gaba d'aya ya canja mata, duk wata kulawa da yake bata ya bari. Saboda sam shi baya son yara gaba d'aya wahala ne rainon su kawai, yayi rarrashin da ban bakin don kawai Fatima ta yarda a zubar, amman sam tak'i yarda saboda tana matuk'ar kaunar yara sosai, ganin tak'i yarda da buk'atar shi na zubar da cikin yasa shi fara gallaza mata tare da yi mata wulak'anci da rashin mutunci kala kala. Amman duk Fatima ta shanye wannan wahalar da yake bata har zuwa lokacin da Allah ya sauke ta lafiya ta samu d'a namiji inda ya ci sunan shi Aliyu, saboda rashin babu ko suna ba'a yi ba balle yiwa yaro yanka kamar yanda ake yi a al'adance, saboda iyayen Fatima basu da k'arfi su ma kuma waje ba d'aya ba don suna da d'an nisa a tsakanin su, tun kafin ta haihu da Umaru ya sanya k'afa ya bar garin bai dawo ba har sai da tayi wajen wata biyu da haihuwa sannan ya dawo duk da kuwa yaji labarin haihuwar. Nan ya bi ya tsani Aliyu ko kad'an baya kaunar yaron, ga zafin talauci da ya kunno mishi kai saboda motar da yake aiki da ita mai shi ya kwace abar shi, sai buga buga da yake faman yi. Aliyu na da watanni 10 cif, Fatima ta sake samun wani cikin nan Umaru bak'in ciki ya isheshi, a lokacin babu irin cin mutuncin da bai yiwa Fatima daga k'arshe sai da yasan yanda yayi ya zuba mata maganin zubar da ciki a lemo, ya bata tasha babu dad'e wa ciki ya zube nan farinciki fal cikin zuciyar shi, yayin da Fatima bata zarge shi ba ta d'auka kawai 6ari ne tayi nan ta cigaba da rainon Aliyu wanda uban bai ta6a d'aukan shi ba, ko kallon mutunci baya yi mishi saboda tsabar tsanar da yayi mishi kamar ba shine uban shi ba. Bayan zubewar ciki ne ya dawo da d'an bata kulawa kafin daga k'arshe kuma wani cikin ya sake bayyana a jikin Fatima, wannan karon ma zubar mata da cikin yayi wanda sai a lokacin Fatima ta ankara da hakan, nan tayi kukan bak'in ciki da takaici na abin da mijin nata yake yi mata na mugunta. Sai da Umaru ya zubar wa mata da ciki sau uku bayan haihuwar Aliyu, ana hud'un ne kuma bai samu nasarar zubar wa ba har aka haifo Suhaima, sai da Suhaima tayi shekara 5 sannan ta sake samun wani cikin wanda har Fatima ta fitar da ran sake haihuwa ganin shekarun Suhaima sun d'an ja, kwatsam ta samu wannan cikin wanda ya sanya Umaru dana sanin auren Fatima a rayuwar shi ga talaucin da yake fama dashi mai tsanani. Har zuwa yanzu babu abin da ya canja daga tsanar da yake yiwa Aliyu, Suhaima da kuma cikin da yake jikin Fatima, daman abinci ba basu yake ba komai na abin da ya rataya a wuyan shi na hakk'in matar shi da yaran shi baya yi, kanshi kad'ai ya sani idan ya samu kud'i zai ci mai dad'i a cikin shi, wani lokacin agaban su zai ci abin shi sai dai su yi ta had'iyar yawu, amman ko kad'an ne bazai ba su ba, sai dai da dare ya bi ya tak'ura wa Fatima da buk'atar shi, bayan kuma ko abincin kirki baya bata wani lokacin ma tun karyawar safe har zuwa daren ba zata samu cin wani abincin kirkin ba, haka zai bi ya gala6aitar da ita shi yasa kullum sake rame wa take ga jiki babu k'arfi. Ban da uban dukan da su Aliyu da Suhaima suke sha a hannun shi, don kusan akan su yake huce haushin shi, har zuwa lokacin da Aliyu ya fara fita d'an aikin k'arfi yana d'an samun wani abin wani lokaci ya siyo musu abin da zasu d'an sa a cikin su, ko kuma idan makobcin su idan anyi girki da d'an yawa suna taimaka musu saboda sun san halin da suke ciki, bama iya su kad'ai ba kusan k'auyen gaba d'aya ma sun gane halin da suke ciki. *** *** *** *CIGABAN LABARI* Haka su Fatima suka cigaba da rayuwar wahala a hannun mugun mijin ta uban yaran ta, da ita da yaran nata don gaba d'aya had'a wa yake ya ci musu mutunci son ran shi. Kamar yau da sassafe suna zaune cikin d'aki, a gaban su garwashin wuta ne a cikin kasko suna jin d'umi, duk sun yi jigum jigum Fatima da Aliyu suna tunanin hanyar da zasu bi don su samu abin da za'a karya dashi, yayin da Suhaima kuma ta fara hawaye saboda yunwar da take nuk'urk'usar ta. Bankad'o labulen d'akin aka yi aka shigo, kamar kullum ba wanda ya kalle shi, cikin sauri ya wuce uwar d'aki ko kallon inda suke bai yi ba, babu jimawa ya fito hannun shi rik'e da jakar kayan shi kaf. Kallon matar ta shi yayi tare da cewa "to ni Fatima tafiya zan yi, kuma bansan ranar dawowa ta ba, watak'il na dawo ko kuma na tafi kenan, tun da kin k'i yin abin da nake so, zan tafi zan yi nesa da rayuwar ku, zan bar ki ke da yaran ki." Tun da ya fara magana Fatima take kallon shi tana kuka, yana k'arasa maganar shi ya sanya kai zai fice zuwa waje babu alamar damuwa a fuskar shi, da sauri Fatima ta rik'o rigar shi cikin kuka ta fara cewa "yanzu tafiya zaka yi ka barmu? " Babu wata damuwa yace "tabbas tafiya zan yi, bazan zauna bak'in cikin 'ya'yan ki ya kashe ni ba, tun kafin lokaci na yayi " Cikin tsananin kuka Fatima tace "Don Allah kayi hak'uri ka dawo mu zauna, kada ka mance ina da auren ka akai na, sannan kuma ga yaran k........." Kafin ta k'arasa fad'in maganar ta, Umaru ya sanya hannu ya ture ta da k'arfi, ta fad'i da6ar a k'asa, tuni marar ta tayi wani mugun d'aure wa, da sauri Aliyu ya nufi wajen Fatima shi da Suhaima suna mata sannu, cikin hassala da rashin mutunci yace "kada ki k'ara danganta ne da wad'annan shegun yaran, kuma zan tafi babu uban da ya isa ya hana ni tafiya " Yana gama fad'in haka ya kad'a kanshi ya fita, cikin zuciyar shi wasai babu damuwa ko kad'an. Dakyar Fatima ta iya gyara zaman ta, saboda mugun ciwon da marar ta yake, sakamakon ture ta da mijin nata yayi ta fad'i, wani irin zugi zuciyar ta take lokaci d'aya ta nemi hawaye ta rasa, ta kafe idon ta waje d'aya tamkar wata mara rai don ko motsin kirki bata yi. Tun motsawar da tayi bayan ta fad'i, a hankali wani abu mai d'umi ya fara zubowa ta jikin ta, sai a lokacin ta motsa idon ta, zuwa kallon jikin nata, sai ta ga jini ne yake zuba sosai, alamar cikin nata yana cikin hatsari, koma yana daf da fita, sai a lokacin taji wani kuka ya zo mata mai k'arfi. Cikin kid'ima Aliyu yace "Umma jini a jikin ki, na kirawo miki Babaa lantana? " D'aga kai kawai ta iya yiwa Aliyu saboda yanda take jin jikin nata, yayin da Suhaima take kuka sosai, saboda ganin halin da mahaifiyar tasu take ciki, da gudu Aliyu ya fice daga gidan har yana cin tuntu6e da dutse, yana saurin k'arasa wa gidan Babaa lantana mak'ociyar su, domin neman taimakon ta......... Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 *A SANADIN SON KI* 💝 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ £xclusive Writer's Forum Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 5-6 Da gudu Aliyu ya shiga cikin gidan Babaa Lantana yana kuka sosai, Babaa Lantana mak'obciyar su fatima ce, mutunci sosai suke yi, tana tsananin tausayin Fatima da yaran ta, ita da mijin ta shi yasa wani lokacin suke taimka musu da abin da Allah ya hore musu, don su ma ba wani kud'i suke dashi ba sai rufin asirin Allah, suna da yarinya d'aya mai suna Aliyah ta d'an girmi Suhaima da kusan shekara hud'u, ita kad'ai Allah ya basu rayayyiya cikin duk yaran da take haihuwa suke mutu. A madafa Aliyu ya tarar da Babaa Lantana tana sauke abinci daga kan murhu, d'ago kanta tayi da sauri ganin yanda aka shigo mata gida kai tsaye babu sallama, mamaki ne ya kamata ganin Aliyu ne ya shigo yana kuka, cikin mamaki tace "Aliyu lafiya, mai ya faru kake kuka? " Cikin rawar murya da hakin gudun da yayi yace "Babaa Lantana ki taimaka mana, Inna ce bata da lafiya gashi ji...... ' Kafin ya k'arasa maganar da yake yi ne, tuni Babaa Lantana ta d'auko fallen zanin ta na atampa a saman igiyar shanya ta lullu6a shi a kanta, ta fita da sauri shima Aliyu ya bi bayan ta, har suna rige rigen shiga gidan. Cikin d'akin suka shige da sauri inda Fatima da Suhaima suke, Fatima sai murk'uk'usun azabar ciwo take tana hawaye, yayin da Suhaima take zabga kuka da k'arfi don ganin halin da Innar su take, da sauri Babaa Lantana da Aliyu suka k'arasa inda take, ganin halin da take ciki ne ya sanya Babaa Lantana cewa "Subhanallah Fatima 6ari ne sannu Allah ya baki lafiya " Kallon Aliyu tayi tace "Aliyu kama hannun Suhaima ku fita tsakar gida " Girgiza kai Aliyu da Suhaima suka yi lokaci d'aya, kafin Aliyu ya iya cewa "Babaa Lantana kiyi hak'uri ki bar mu a wurin Innar mu " Itama girgiza kai tayi tare da cewa "A'a Aliyu kayi hak'uri ku je waje " Dakyar Babaa Lantana ta shawo kan Aliyu ya kama hannun Suhaima suka fita waje, suna waiwaiyar Innar su, da batasan halin da take ciki don ta fara fita a hayyacin ta. Bayan fitar su ne Babaa Lantana ta fara yiwa Fatima dabarin su irin na zamanin da, ganin abin yana kok'arin gagarar ta ne ya sanya ta fito waje inda Aliyu suke raku6e waje d'aya, kallon su tayi wani tausayin su ne ya kamata dakyar ta iya cewa "Aliyu kayi sauri kaje ka kirawo Ladi ungozoma " Gid'a kanshi yayi sannan ya fita da gudu, ita kuma Babaa Lantana ta koma cikin d'akin wajen Fatima, ta bar Suhaima anan zaune tana kuka. Babu dad'e wa Aliyu ya dawo Ladi ungozoma tana bin shi a baya, d'akin da Fatima take ciki ya iya nuna mata da d'an yatsan shi, Ladi ungozoma kuwa wadda ke d'auke da k'aramin buhu a hannun ta na kayan aikin ungomanci irin na zamanin da, ta shige cikin d'akin. Duk yanda suka yi kok'ari wajen kada cikin Fatima ya zube, sai da cikin ya zube sai dai jini yak'i tsayawa sai zuba yake, nan dai ungozoma ta bayar da maganin da za'a jik'a mata ta sha, sannan Babaa Lantana ta biya ta kud'in ta, ta had'a kayan nata ta tafi. Babaa Lantana sai da ta gyara jikin Fatima tsaf da d'akin, sannan ta kirawo Aliyu da Suhaima don su zo wajen ta, sannan ta tafi gida don d'ebowa Fatima abinci don ba k'aramin gala6aita tayi ba sosai, tun da ba wani abincin kirki take samu ta ci ba, da sannu Allah zai saka ita da yaran ta a wajen Umaru, tabbas yaci amana bai rik'e amanar da Allah ya bashi ba ya azabtar da su, duk don son rai irin shi nashi. Suna shiga d'akin wajen Fatima suka nufa, zama suka yi a gefen ta gaba d'aya sun zuba mata suna kallon ta tamkar yau suka fara ganin ta. Kallo d'aya mutum zai mata yasan bata da ishashshan jini a cikin jikin ta, saboda yanda tayi wani fari sosai, gashi ta rame sosai dakyar take iya motsi ma, kallon yaran nata tayu tana daga kwance, wani tausayin sune ya kamata, a hankali wasu hawaye suka shiga zubowa daga idanun ta, bud'e bakin ta tayi wanda ya bushe saman le6en yayi fari tace "Aliyu ga Suhaima nan koda na mutu ka rik'e ta cikin amana, ina horan ka da ka tsaya tsayin daka ku nemi ilimi, don zama da jahilci bashi da amfani, sannan kada ku ce zaku ji haushin mahaifin ku, ku cigaba da yi mishi biyayya koda ya dawo wajen ku, ku kasance cikin yi mishi addu'a Allah yasa ya gane gaskiya, yasan 'ya'ya rahma ne, komai runtsi ina son ka kasance da Suhaima kada ka guje ta, duk laifin da tayi maka kayi hak'uri kai babba ne " D'an dakatawa tayi ta had'iyi yawu sannan ta d'an yamutsa fuska saboda jin yanda marar ta take wani murd'awa wa, cikin kuka Aliyu ya kamo hannun ta yace "A'a Inna baza ki mutu ba, zamu rayu tare da junan mu, don Allah ki daina wannan maganar Inna, hankali na yana tashi wani tunani yana d'arsuwa a zuciya ta sannan gaba na yana fad'uwa " Wani d'an murmishi Fatima tayi tare da cewa "Kayi hak'uri d'ana ni kaina bansan dalilin yi maka wad'annan maganganun ba, ina son duk lokacin da mahaifin ku ya dawo ku sanar dashi na yafe mishi duk abin da yayi min, nima kuma ya yafe ni idan nayi mishi wani laifin a zaman mu, Allah ya albarkaci rayuwar ku, Allah ya raya min ku ya baku ilimi mai amfani ya kuma kare min ku a duk inda kuke 'ya'yana, ku rik'e Babaa Lantana da Baba Adamu a mataayin iyayen ku, don mutanen kirki ne kuma zasu rik'e ku tamkar Aliya 'yar su, duk abin da suka baku shawara kuyi amfani da ita don nasan baza su baku mummunan shawara ba Allah yayi muku albarka " Fatima ta k'arasa fad'in haka tana hawaye sosai, nana Aliyu da Suhaima suka sake fashe wa da kuka sosai, ana cikin Babaa Lantana ta shigo d'akin turus taja ta tsaya ganin su da tayi suna kuka, jikin ta ne yayi sanyi sannn wasu hawaye na tausayin su ya zubo mata, wayance wa tayi tare da fakar idon su don kada su ganta ta goge nata hawayen sannan ta k'arasa inda suke tace "Haba Fatima taya zaki na saka su a gaba kina kuka suna yi, ke da zaki rarrashe su ki kwantar musu da hankali " Murmishin yak'e kawai Fatima tayi, nan Babaa Lantana ta rarrashe su dakyar suka yi shiru, sannan ta basu abincin suka fara ci hannu baka hannu kwarya. Sannan ta d'ago Fatima a hankali ta kara mata kofin madarar shanu mai d'umi a bakin ta, a hankali Fatima take kur6a har ta gama shan kusan rabin kofin, sannan ta zame bakin ta a bakin kofin tana girgiza wa Babaa Lantana kai alamar ya ishe ta. Sauke kofin tayi a k'asa ta ajiye, tukunna ta d'auko kofin maganin da aka jik'a ta bawa Fatima tasha, bayan ta gama ta kwanta tana mai mayar da ajiyar zuciya, ita kad'ai tasan abin da take ji cikin jikin ta. Babu dad'e wa bacci ya d'auke ta, fito wa suka yi zuwa tsakar gidan gaba d'ayan su don kada ayi hayaniya ta tashi, Babaa Lantana da Suhaima suka fara kimtsa gidan da yake Fatima bata sangartar da ita ba, tana d'an sata aikace aikacen da zata iya wanda baifi k'arfin ta. Aliyu kuwa fita yayi a gidan don zuwa neman wani aikin da zai siyo wa Inna lemo da kankana don tasha, tun da yasan mara lafiya yafi son cin kayan itatuwa fiye da komai. Babaa Lantana tana wanke wanke ne Aliya d'iyar ta ta shigo gidan, nan ta kar6i aikin da Babaa Lantana take yi ta cigaba da yi, gefe d'aya Suhaima nayi mata dauraya. Lokacin da Farima ta farka daga baccin jikin ta da d'an dama don ta iya tashi taje band'aki da kanta, sai dai har zuwa lokacin jini yana zuba a jikin ta, amman ba mai yawa sosai ba, sai bayan ishsha Babaa Lantana ta tafi gida, ta bar Aliya anan wurin Fatima ko zata na taimaka mata da wani abin a yafi k'arfin Suhaima. Bayan tafiyar kenan Aliyu ya dawo gidan da yankan kankana a hannun shi k'arami sai lemo mai 6ayo guda biyu, dakyar ya same su bayan yasha wahalar ferar lemo mai tarin uban yawa da mai siyar da lemon ya bashi, sannan ya bashi wannan kankanar da lemon tare da nera ashirin, cikin farinciki ya taho gida. Bayan ya shigo gidan duk suna d'aki don haka ya shiga kitchen ya d'auko silver da wuk'a ya yanka su k'anana sannan ya shiga d'akin da sallama, Fatima, Aliya da Suhaima suka yi amsa mishi, da sauri Suhaima ta mik'e tana rik'e shi cikin shagwa6a tace "Yaya shine kayi zaman ka ina ta jiran ka, kasan bana son ka fita ka dad'e " D'an murmishin yak'e yayi tare da shafa kanta yace "Yi hak'uri 'yar k'anwa ta aiki ne ya tsare ni " "Toh Yaya na " Fatima kallon su take kawai, kafin wasu hawaye su zubo mata, da sauri ta sanya hannun ta, ta goge su don kada su Aliyu su gani, don ma babu wadataccen haske a d'akin. K'arasa wa yayi inda take ya zauna tare da mik'a mata silver d'in yace "Inna gashi kisha, ya sauk'in jikin naki? " "Da sauk'i Aliyu nah, nagode Allah yayi muku ya albarka " "Amin Inna" Aliyu ya amsa, nan ya fara bata a baki a hankali, bayan ya d'an sanwa Suhaima don Aliya k'in kar6a tayi. A hankali yake bata har ta shanye tas, sannan ya d'auke silver d'in ya bawa Aliya takai kitchen, shi kuma ya fara jera wa Fatima tambaya akan yanda take jin jikin nata, Fatima kuwa amsa mishi kawai take da sauk'i, har zuwa lokacin kwanciya bacci, har ya tafi Fatima ta kirawo shi tana dad'a yi mishi nasiha tare da k'ara bashi amanar ya kula da kanshi da Suhaima, jiki a sanyaye Aliyu ya fito ya shige d'akin shi. Can cikin dare wajen asuba ne jini ya tsinke wa Fatima kafin kace me tuni ta fara fita daga hayyacin ta, aikuwa Suhaima da gudu ta shiga d'akin Aliyu ta taso shiga, daman ba baccin yake ba, don gaba d'aya ji yayi baya jin bacci a idanun shi, ganin Suhaima tana kuka ba k'aramin d'aga mishi hankali yayi ba, ko tambayar ta bai tsaya yi ba ya fito daga d'akin nashi ya fad'a d'akin Fatima. Yana shiga yaga abin da ya gigita shi, ya rud'u iya rud'ewa kamar wani babban mutum, da sauri ya k'arasa wajen Inna Fatima ya rik'e ta yana fashe wa da kuka yace "Inna don Allah kada ki tafi ki bar mu, ki bud'e idanun ki " Ya fad'i hakan ganin yanda take lumshe ido tana jan numfashi da dakyar, gashi ta kasa magana sai kok'arin bud'e baki take tayi magana ta kasa bud'e shi, kallon Aliyu kawai take da Suhaima. "Yaya Aliyu ka kirawo Babaa mana " Yaji saukar muryar Aliya a kanshi, sai lokacin ya tuna hakan, aikuwa ya ajiye Inna a hankali ya fita da wani irin gudu. Fatima bin shi da kallo tayi Sannan ta mayar da kallon ta kan Suhaima, sai kuma a hankali ta bud'e bakin ta zata yiwa Suhaima magana, amman sai kawai taji ta tsinci bakin ta da furta kalmar shahada, a hankali ta k'arasa fad'a sannan Lokacin d'aya kuma numfashin ta ya tsaya da aiki, idanun ta kuma a lumshe suke har zuwa lokacin da zuciyar ta tabar bugawa komai na jikin ta ya tsaya cak da aiki ya daina motsi, ta koma tamkar wadda ta mutu ko irin ta suman nan. Da iyakacin k'arfin shi yake bugun gidan Babaa Lantana yana d'aga murya da k'arfi yana kiran Babaa Lantana da Baba Adamu, sam kamar Aliyu baya cikin hayyacin shi yama mance da wani dare ne Saboda tsabar rud'ewa. Da sauri Babaa Lantana da Baba Adamu suka fara rige rigen bud'e kofa, jin muryar Aliyu, Baba Adamu ne yayi nasarar bud'e kofar saboda Babaa Lantana zaninin jikin ta da kunce yana kok'arin sullu6e wa k'asa. And rikice Aliyu ya rik'e hannun Baba Adamu yana cewa "Ku taimaka min Inna ta " Abin da ya iya furta kenan, aikuwa tsakanin Babaa Lantana da Baba Adamu tare da Aliyu suka kasa tsere don shiga gidan. D'akin Fatima suka fad'a dukanin su, kallo d'aya Baba Adamu yayi wa Fatima yasan bata numfashi, ganin haka ya sanya korar Aliyu, Aliya da Suhaima daga d'akin. Suna fita Baba Adamu ya kalli Babaa Lantana ido jawur yace "Sai dai mu yi hak'uri Lantana Fatima ta rigamu gidan gaskiya " Hannu Babaa Lantana ta sanya a kanta dukka hannun tare da zaro ido tace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Malam da gaske Fatima ta mutu ko suma tayi ne " Cikin dauriya Baba Adamu yace "Haba Lantana ki kalle ta da kyau, ai kina kallon Fatima kinsan gawa ce " Lokaci d'aya Babaa Lantana ta rushe da kuka sosai, yayin da Baba Adamu ya sanya zani ya lullu6e ta tun daga saman kanta har k'afar ta, Sannan ya kamo hannun Babaa Lantana suka fito waje tsakar gida, ina Suhaima da Aliyah suka yi tsuru tsuru suna kuka, yayin da Aliyu ya kasa zama waje d'aya sai safa da marwa yake yi. Ganin fitowar Babaa Lantana da Baba Adamu jikin su a sanyaye ga Babaa Lantana tana kuka, yasa Aliyu tahowa wajen su da sauri yana cewa "Ku fad'a min meke faruwa, ina Inna ta, kada ku ce min ta mutu don Allah " Babu wanda yayi karfin halin yi mishi magana, ganin haka ya sanya shi kutsa kai d'akin Lokaci d'aya kuma gaban shi na bugawa da k'arfi sosai...... Sai kun yi hak'uri da wannan page d'in banyi editing ba. Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻£xclusive Writer's Forum Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 7-8 Babu wanda yayi k'arfin halin yi mishi magana a tsakanin Baba Adamu tare da Babaa Lantana, ganin haka ya sanya shi kutsa kai cikin d'akin, lokaci d'aya kuma gaban shi na bugawa da k'arfi sosai. Aliyu yana sanya k'afar shi cikin d'akin idanun shi suka hango mishi Umman shi kwance an lullu6e da zani, da sauri ya k'arasa wajen gaban shi na tsananta fad'uwa, hannun shi na rawa ya sanya akan zanin ya fara janye shi a hankali, fuskar Fatima ce ta bayyana kamar an kirata ta amsa, sai kace ba matacciya ba, tuni Aliyu ya durkushe tare da sakin wani irin kuka yana cewa "Umma ki tashi don Allah kada ki tafi ki barmu a wannan duniyar mu kad'ai" Kuka sosai Aliyu yake yana sumbatu, ganin haka ya sanya Baba Adamu ya janye shi daga gaban gawar Fatima dakyar don shima hawayen yake yi, Babaa Lantana kuwa da Aliyah Suhaima kuka suke yi sosai. Daga k'arshe Baba Adamu ya fita don sanar wa da jama'ar gari, cikin k'ank'anin lokaci mutuwar Fatima baiwar Allah ta zagaye cikin k'auyen nasu, sosai mutane sun jimanta rasuwar ta tare da yaba kyawawan halayen ta, da irin yanda take hak'uri da jure irin rashin mutunci irin na mijin ta wanda sam kanshi ya sani. Babu jimawa mutane suka taru akayi wa Fatima wanka aka had'a ta cikin likkafani, sannan daga k'arshe aka sadata da gidan ta na gaskiya, gidan da shi muke jira Allah ya jik'an wad'anda suka mutu mu kuma Allah yasa mu cika da imani Amin. Aliyu da Suhaima sun sha kuka kuwa, musamman Aliyu don yafi Suhaima hankali sai yafi jin rad'ad'in mutuwar fiye da ita, su Baba Adamu da Babaa Lantana ne suke tausar su tare da yi musu nasihar yarda da k'addara, lokacin Fatima ne yayi don haka Allah ya d'auki abarshi, kowanne mutum da iyakacin lokacin da Allah ya d'ibar mishi yanzu Fatima addu'a tafi buk'ata fiye da komai, Allah yasa mu dace duniya da lahira Amin. Haka Aliyu da Suhaima suka rungume maraicin su, sun koma abin tausayi, bayan sadakar bakwai ne 'yan uwan Fatima suka nemi tafiya da Suhaima shi kuma Aliyu ya zauna a wajen 'yan uwan uban shi, amman k'ememe Aliyu ya yak'i yarda da tafiya da Suhaima, anyi rarrashin sunyi fad'an amman ina yak'i aminta dole suka damk'a amanar su hannun Babaa Lantana da Baba Adamu, tukunna suka tafi bayan su bawa Aliyu wani d'an taimakon da zai nemi wata sana'ar ta domin kula da kansu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, inda Aliyu da Suhaima suka sake shak'uwa da junan su, komai Aliyu ya samu zaka ji bakin shi na ambatar Suhaima, kulawa sosai yake bata don shi yafi tausayin ta fiye da kanshi, sai dai ita Suhaima ta koma gidan Babaa Lantana da zama sai dai tana shigowa wajen Yayan nata tana tayashi 'yar hira. Aliyu ya dage da yin sana'a kowacce iri ce indai zai samu halal d'in shi, aiki yake yi sosai na k'arfi kuma, haka ya dunga tara kud'i har ya sanya Suhaima a makarantar primary tana nan cikin k'auyen nasu tare da islamiya, babu dad'e wa Suhaima ta fara zuwa makaranta hankali kwance, kullum shi zai kai ta a tsohon keken da Baba Adamu ya cika mishi kud'i ya siya, haka idan aka taso su zai zo ya d'auke ta. Ganin Aliyu ya fi karkata akan son yin noma da kiwo yasa Baba Adamu bashi aron gonar shi guda d'aya don yana yin amfani da ita, shi kuma ya rik'e guda d'aya, da yake gonakin nashi guda biyu ne manya, gashi gonar da ya bawa Aliyu aro a kusa da gidan su Aliyun take, idan ma mutum bai kula ba ya d'auka kamar gidan a tsakiyar gonar yake, sosai Aliyu yayi murna da wannan karamcin da Baba Adamu yayi mishi. **** **** **** Haka lokaci ya cigaba da tafiya watanni da shekaru na wuce wa kamar kiftawar ido, Suhaima an fara zama 'yammata an don har ta kammala makarantar primary sun zana commen interest tana gida ana jiran fitowar result sai makarantar islamiyya da take cigaba da zuwa. Yayin da Aliyu an zama matashin saurayi, ya zama cikakken manomi a yanzu, don ya rik'e sana'ar noma da kiwo, da wannan gonar da Baba Adamu ya bashi aro yake noman shi and cikin ta har zuwa yanzu da ta zama mallakin shi, don tuni Baba Adamu ya siyar mishi da ita, bayan aikin noma kuma yana yin kiwo irin su kaji, awakai da shanu sai kuma yana siyar da kwan kaji sosai yake samu bud'i a harkar shi, ga taimakawar wani amintaccen yaron shi da Baba Adamu ya sama mishi yana taimaka mishi. Ya gyara gidan su sosai yayi kyau, inda a lokacin kuma Baba Adamu ya nemi da yayi aure, babu 6ata lokaci ya sanar musu da Aliyah d'iyar shi yake sosai, babu wanda bai yi farinciki da hakan ba don haka babu 6ata Lokaci akayi aure amarya ta tare a gidan ta, nan kusa da gidan su tun da Aliyu a asalin gidan su ya zauna, a lokacin kuma Suhaima ta dawo hannun Yayan ta da zama, zaman su suke cikin kwanciyar hankali da farinciki, Aliyu ya mayar da hankalin shi sosai kan sana'ar tashi, ya dad'a zama wani babban mutum musamm da yanzu yayi aure. Kamar yau ne ranar laraba ranar da kasuwar garin nasu take ci, tun safe Aliyu ya bar k'auyen nasu ya tafi cikin birni kai wasu kwai masu yawa, wajen mutumin da yake kaiwa ya siya a kan machine d'in shi, don haka gidan ya rage daga Aliyah sai Suhaima a ciki. Ranar Suhaima cikin farinciki take saboda Yayan ta baya nan, zata je cin kasuwa don haka da wuri tayi wanka ta ci gayun ta cikin wata atampa mai kalar milk da brown a jiki, ta sanya hijab d'in ta k'arami kalar brown, sannan ta fito daga d'akin ta zuwa wajen da Aliyah take. Aliyah tana zaune tana gyaran kayan miya don tana son gama girki da wuri kafin Aliyu ya dawo, ta hango Suhaima tana tahowa zuwa wajen ta, fuskar ta d'auke da murmishi tace " Suhaima wannan gayun fa ina zuwa? " Cikin dariya Suhaima tace "Yaya Aliyah nayi kyau ne?" Itama Aliyah tana dariya tace "Sosai ma 'yar k'anwata kinyi kyau, ina zuwa? " "Cin kasuwa zan je " Zaro ido Aliyah tayi tare da cewa "Haba Suhaima kin mance Yayan ki baya son kina zuwa koh, yanzu idan ya dawo bakyanan nasan fad'a zai mana ni da ke " Shagwa6e fuska Suhaima tayi tare da cewa "Haba Yayah Aliyah kafin ya dawo fah na dawo, ba dad'e wa zanyi ba " "Toh shikenan amman don Allah kada ki dad'e " "Yawwa Yayah Aliyah nagode, kuma bazan dad'e ba " Murmishi suka yiwa junan su, sannan Aliyah ta d'auko kud'i ta bata, godiya tayi tukunna ta tafi cikin zuciyar ta fal farinciki. Tana fita waje ta tarar da k'awayen ta suna jiran ta, nan suka tafi kasuwar suna tarar ana tacin kasuwa ga mutane daban daban har da na maraya ma suna zuwa cin kasuwar. Suhaima bata dad'e ba tace wa k'awayen ta zata tafi gida, don kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata dawo ba yayi mata fad'a, aikuwa suka ce sai dai tayi gaba su ba yanzu ba, haka Suhaima ta kamo hanya tana tafiya ita kad'ai cikin sauri. Sauri sauri take gaba d'aya hankalin ta yayi gida, tana tsoron kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata nan. D'ago kan da zatayi ta hango wata kyakkyawar yarinya a tsaye kusan sa'ar ta, sai dai zata ba Suhaima wajen shekara biyu, sai wani dattijo a tsaye shima a gefen ta a tsaye da alama sun k'agu da tsayuwar da suka yi. A hankali Suhaima ta k'arasa inda suke tsaye har zata wuce su, da sauri yarinyar nan ta k'arasa wurin Suhaima tace " 'yar uwa idan baza ki damu ba don Allah muna son ki taimaka mana da ruwa zamu sanya a mota " D'ago kanta Suhaima tayi ta kalle ta sannan tace "Toh ba matsala bari na k'arasa gida na d'ebo muku" Murmishi yarinyar tayi tare da cewa "Idan baza ki damu ba zan bi ki don na gaji da tsayuwar " "Ba komai mu je " "Ngde 'yar uwa " Kallon dattijon nan tayi tare da cewa "Malam Habu bari mu je gidan su mu kawo ruwan " Sai da dattijon nan da yarinyar ta kirawo da Malam Habu yayi d'an jim kad'an kafin yace "Toh amman kada ki dad'e kinga kada yamma tayi mana a hanya " Gid'a kanta tayi sannan ta juya wajen Suhaima tace "Mu tafi koh? " A nutse suka fara tafiya yarinyar tana yiwa Suhaima hira sai dai bata fiye bata amsa ba daga ehh sai a'a, can sai kuma tace "Ni sunana Hauwaa amman 'yan gidan mu na kirana da Jiddah saboda sunan kakar mu ne " Murmishi Suhaima tayi tare da cewa "Sunan ki mai dad'i " "thank you, ke fah what's your name? " "My name is Suhaima Umar" "Wow nice name, daman kina jin turaci? " "Yeah but kad'an kad'an." "Good, kin gama primary ne " "Ehh na gama ina jiran result ya fito na cigaba " "Amman kin birge ni Suhaima, zamu iya zama friends? " "Why not " Cewar Suhaima, nan kowacce ta bada d'an yatsan ta suka k'ulla friendship, tukunna suka k'arasa shiga gidan da sallama. Gaban Suhaima ne ya fad'i ganin Yaya Aliyu a tsaye yana safa da marwa, ga Yaya Aliyah ma a tsaye fuskar ta d'auke da damuwa da alama dai ita ake nema. Suna ganin ta gaba d'aya sukayo inda take Aliyu ya sanya hannun shi saman kafad'ar ta ya rik'e da d'an k'arfi yace "Ina kika zauna Suhaima, ba na hana ki fita kasuwa ba " Idanun tane yayi raurau kamar zata yi kuka, batason ganin damuwar Yayan nata ko kad'an, don haka sai tace "Kayi hak'uri Yaya bazan sake ba " Kallon ta kawai yake bayason wani abu ya samu tilon k'anwar tashi. "I'm so sorry Yayah bazata sake ba " Aliyu da Aliyah suka ji saukar muryar Jiddah, da sauri suka kallo inda take don sam basu kula da ita ba hankalin su gaba d'aya yana kan Suhaima. Kallon Suhaima Aliyu yayi irin na neman k'arin bayanin ina ta samu wannan yarinyar, fahimtar hakan da Suhaima tayi ne ya sanya ta bud'e baki tayi mishi bayanin had'uwar su. Ba wanda yayi magana sai da Jiddah ta gaida su sannan suka amsa, kallo d'aya zaka yiwa Jiddah kasan ta samu tarbiyya mai kyau a wajen manyanta. Babu 6ata lokaci Aliyu ya samu jarka ya zuba ruwa taf a ciki, sannan ya d'auko ta Suhaima da Jiddah na bin shi a baya har zuwa wajen da motar su tayi parking. Bayan sun k'arasa ne Aiyu suka gaisa da Malam Habu sannan ya kar6i ruwan ya zuba a mota yana godiya, mik'a wa Aliyu jarkar ruwan yayi yana sake godiya, girgiza kai Aliyu yayi tare da cewa "A'a ka barshi a wurin ka idan buk'atar hakan ya taso muku a gaba kwayi amfani dashi " Malam Habu cikin girmama karamcin Aliyu yace "Mun gode d'an samari Allah ya saka da alkhairi " Daga haka Malam Habu ya shiga cikin mota yayi mata key ya tasar da ita, sannan ya d'ago kanshi ya kalli Jiddah da bata da alamun shigo wa motar yace "Jiddah taho mu tafi yamma nayi " Maimakon ta bawa Malam Habu amsa, sai ta juya wajen Aiyu ta rik'e hannayen shi duk biyun tace "Don Allah Yaya Aliyu zan na zuwa nan ganin Suhaima, Allah tun da na ganta naji ina sonta sosai, gashi mun k'ulla k'awance da ita, kuma ina son ka zama Yaya nah " D'an murmishi Aliyu yayi shi duk wanda yake k'aunar 'yar k'anwar shi, to shima yana son shi, dafa kan Jiddah yayi tare da cewa "Kada ki damu Jiddah na d'auke matsayin k'anwa, kuma duk lokacin da kike son zuwa wajen Suhaima ki zo ki ganta " Dariya Jiddah ta sanya ita da Suhaima kafin tace "Nagode sosai Yaya Aliyu " Sannan ta jiyo wajen Suhaima suka rungume junan su, dakyar ta iya sakin Suhaima ta shiga mota har da d'an hawayen ta, don ji tayi kamar ta zauna a wurin su, suna tsaye Aliyu da Suhaima suna d'aga musu hannu har suka daina hango motar su. Sannan Aliyu da Suhaima suka juya zuwa gida, sosai Suhaima ta fara jin kewar Jiddah kamar wad'anda suka shekara da sanin junan su, ita haka kawai taji Allah ya sanya mata son Jiddah kamar irin 'yar uwar nan ta jini... Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM DEDICATED TO MY SADEEY SANAZ PAGE 9-10 Haka lokaci ya cigaba tafiya, zumunci tsakanin Suhaima da Jiddah ya k'aru sosai wanda takai duk weekend sai ta zo ganin Suhaima, sai dai Aliyu sam yak'i bata fuskar ta tambaye shi taje gidan su Jiddah, sai dai ita duk weekend k'afar ta yana hanyar zuwa gidan su Suhaima ko kad'an bata damu da rashin zuwan Suhaima gidan su ba, tasan komai lokaci ne akwai lokacin da zata zo mata gidan su, aminci sosai suke yi. Haka Aliyu, Aliyah dasu Babaa Lantana da Baba Adamu duk sun saki jiki sosai da Jiddah, saboda kirkin yarinya ga kuma yanda take girmamasu, duk da sun san daga gidan kud'i ta fito, don da ganin irin sutturar da take sanya wa da irin motar da ake kawo ta a ciki kasan iyayen ta ba k'aramin masu kud'i ba ne, gashi indai zata zo kowa a cikin su da irin tsarabar da take kawo mishi, musamman Suhaima k'awar ta, yini guda cur zata yi musu suyi ta zagaya gonar Yaya Aliyu da wurin da ya ke6en ce don yi kiwo a ciki, sam Jiddah ko a fuska bata nuna tana kyamar su. Ana cikin haka exam d'in su Suhaima ta fito taci wata makarantar secondary da take a birni, nan Yayan ta yayi mata ciko ciko ta samu gurbin karatu na jss 1. Cikin k'ank'anin lokaci Suhaima ta fara zuwa makaranta, Jiddah tayi murna sosai da cigaban makarantar Suhaima, gashi kuma Jiddah idan tazo wani lokacin tana k'ara fahimtar da ita wasu abubuwan na fannin boko, ga kuma kwalliya da gayu da take koya mata, saboda Jiddah tana son duk ranar da Suhaima zata gidan su ya kasance ta iya komai na wayewa yanda 'yan uwan ta basu su kyamace mata ko su raina saboda sanin halin su da tayi, sosai Suhaima ta mayar da hankalin ta tana karatu babu wasa, Aliyu ne mai kaita ya kuma d'auko ta daga makaranta yana alfahari da 'yar k'anwar tashi. *** *** *** AFTER SIX YEARS "Suhaima! Suhaima!! Suhaima!!! " Naga wata matashiyar kyakkyawar yarinya chocolate colour tana tsaye a tsakar gida tana kwallawa Suhaima kira, nima gaba d'aya na baza ido na hango fitowar Suhaima don na kwana biyu ban lek'o gidan ba daukan rahoto lol. Wata kyakkyawar yarinya na hango tana fitowa daga d'aki da gudu jikin ta sanye da wata gown ash colour mai touch d'in red a jiki, gashin ta a sake ya kwanta a gadon bayan ta hannun ta na rik'e da veil na gown d'in shima red colour. Da gudu ta k'araso wajen matashiyar yarinyar nan mai kiran ta, tana zuwa ta rungume ta tana dariya ita ma d'ayar dariya take, kafin kuma ta d'an ture ta tana 6ata fuska tace "Ni ai nayi fushi Jiddah da ke ace ranar graduation d'ina ki k'i zuwa koh" Wadda aka kirawo da Jiddah ta langa6e kai tare da cewa "I'm so sorry friend kinsan a time d'in na tafi raka Ammi na london yin check off, nima kaina ban ji dad'in hakan ba please forgive me " Wani kyakkyawan mirmishi Suhaima ta saki wanda ya fallasa dimple d'in ta sannan ta rik'o hannun Jiddah tace "Tsokanar ki nake besty kinsan Yayah Aliyu ya fad'a min " "Yawwa tawan har naji dad'i " Sake rungume juna suka yi suna dariya, Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suna tsaye suna kallon su sai murmishi suke su ma. A dai dai lokacin kuma driver d'in da ya kawo Jiddah ya fara shigo da kaya yana ajiye wa, sakin juna suka yi sannan a lokacin idanun Jiddah suka sauka akan Yaya Aliyu da Aunty Aliyah sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya tace "Auuu Yaya Aliyu da Aunty Aliyah daman kuna nan, ai ni ban kula da ku ba " "Daman ina zaki kula damu hankalin ki yana wajen Suhaima " Cewar Aunty Aliyah tana rik'e ha6a, Yaya Aliyu kuwa ban da murmishi babu abin da yake. Langa6e kai tayi cikin shagwa6a ta had'e hannayen ta biyu waje d'aya tare da cewa "Afuwan Babban Yaya da Aunty na bazan k'ara ba " Dariya suka sake yi kafin Suhaima ta rik'e hannun Jiddah taja ta zuwa cikin wata rumfa wanda aka ajiye wasu kujeru na sak'i, zama ake akan su don hutawa, gaba d'ayan su suka zauna ana hira cikin farinciki da annushuwa, kafin daga bisani Jiddah ta d'auko wani kwali ta bud'e sai ga chocolate cake ya bayyana, nan ta ajiye shi saman table d'in da yake ajiye inda suke zaune, sannan ta tashi da sauri ta nufi kitchen. Bata jima ba ta fito hannun ta rik'e da ashana, su dai bin ta da ido kawai suke, tana zuwa ta kunna ashanar ta sanya wutar jikin d'an candle d'in da yake tsakiyar cake d'in wanda ake sanyawa a jikin cake, kamo hannun Suhaima tayi sannan tace "Are you ready? " Gid'a kanta Suhaima tayi fuskar d'auke da murmishi, babu 6ata lokaci suka hure wutar a tare sannan suka yanka cake d'in kowacce ta bawa 'yar uwar ta a baki, sannan Suhaima ta bawa Aliyu ita kuma Jiddah ta bawa Aunty Aliyah. "Happy graduation sister " Rungume Jiddah tayi tare da cewa "thank you so much dear" "Haba never mind 'yar uwa" Daga nan Yaya Aliyu ya fita Aunty Aliyah kuma ta wuce kitchen, sannan Suhaima da Jiddah suka kwashe kayan da ta kawo wa Suhaima suka wuce cikin d'akin Suhaima, kan bed suka zube suna hira don sun jima basu had'u ba. Yinin ranar hira sosai suke har Jiddah na bawa Suhaima labarin an kawo kud'in ta an sanya rana nan da two month's biki su Abban ta suka sanya, da yake kuma Jiddah har ta shiga University tana level 2, mass com take karanta bata da ra'ayin sai ta gama schl zata yi aure, ta fison tana cikin karatun tayi idan yaso zata k'arasa a gidan ta da yake iyayen ta irin basu da shiga hak'ik'in yaran su a kan abin da suke so suna yi musu, sai dai idan abu bai yi musu wannan ne kuma akwai tashin hankali. Suhaima ta taya murna sosai tare da yi mata fatan alkhairi tare da alk'awarin zuwa gidan su biki, d'an hararar ta tayi tare da cewa "Ba daga baki ba fad'ar Allah yasa ki zo " Dariya ce ta tahowa Suhaima da sauri ta sanya hannu ta rufe bakin tana cewa "Ni na isa ace bikin besty guda ban je ba, da ban yiwa kaina adalci ba " "Kada ki zo d'in yarinya kiga yanda ake rashin mutunci " "Ah Ah ma basai kinyi rashin m ba zan zo ba " Daga nan kuma ta fara kok'arin tafiya gida ganin yamma tayi, Yaya Aliyu da Aunty Aliyah sun taya Jiddah murna sosai na auren da zata yi sannan sun yi mata alk'awarin zuwa idan lokacin yayi, sannan tayi musu sallama ta tafi, har wajen mota Suhaima ta rako ta suka sake yin sallama sannan ta shiga motar ta rufe driver yaja motar suka tafi suna d'aga wa junan su hannu, sai da motar ta k'ule Suhaima ta daina hango ta tukunna ta sauke hannun ta tare da sauke numfashi ta wuce cikin gidan su zuciyar ta fal farinciki yau Jiddah tazo don rabon da tazo anyi wajen one month's. *** *** **** Wata hamshak'iyar mata na hango tana rik'e handle d'in kofar wani d'aki tana bud'e wa tare da shiga ciki, kallo d'aya zaka yiwa matar kasan ta jik'u da naira, d'akin duhu dulum da ta shiga ciki. Da yake ta lak'anci wajen makunnar bulbs na bedroom d'in sai ta k'arasa ta kunna nan take haske ya gauraye cikin d'akin, wow nice room na furta lokacin da naga had'uwar d'akin, komai na d'akin blue and white ne hatta fentin bangon d'akin gashi k'ato ne room d'in sosai. Kai tsaye matar wajen tafkeken Italian bed d'in ta nufa, inda one and only lovely son nata yake sleeping hankalin shi kwance, ya lullu6e hatta kanshi da lallausan blanket wanda ya kasance shima blue ne and kwalliyar flower's white ajikin shi. Zama tayi gefen bed d'in tare da sanya hannun ta tana bud'e blanket d'in, har tayi nasarar bud'e face d'in, tubarkallah masha Allah nace a time d'in da na hango beautiful face d'in shi, bacci yake amman fuskar shi a sake tamkar wanda yake murmishi. A hankali ta sanya hannun ta tana bubbuga shi a nutse tana cewa "Hey son wake up " Sai da ta fad'i hakan sau biyu ana ukun ne ya fara bud'e lumshashshun eye's nashi wanda dogayen eyelashes ya rufe su, ya kallo Mummyn tashi cikin muryar shagwa6a yace "Why Mummy da zaki tashe ni a bacci, shiyasa sam ban so na dawo nigeria ba coz yanzu za'a fara sawa mutum headache " Ya k'arasa fad'i yana yatsine fuska, da kan ganshi kasan d'an shagwa6a ne na ajin k'arshe ma. Murmishi Mummy ta saki tare da cewa "Haba my son kasan yau ne na had'a partyn murnar dawowar ka gida lafia da kammala karatun ka koh" D'an yatsina fuska yayi tare da sake 6ata fuska yace "No need Mummy kinsan ban son hayaniya right? " Hannun ta ne saman gashin kanshi tana shafawa tace "Nasan da haka son but kamar kai ka dawo daga wata k'asar ka kammala karatu cikin sa'a kace bazan had'a party ba I'm sorry to say son sai nayi " Bai kulata ba ya yaye blanket d'in jikin shi ya zuro k'afafun shi a k'asa tare da tashi tsaye daga shi sai short niker white colour irin skin tight d'in nan ya wuce toilet a fusace, don sam bai jin dad'in dage wa da Mummy tayi ba aka wannan party da ta had'a mishi. Da murmishi Mummy ta bishi da kallo cikin so da kaunar shi tace "Son d'an rigima kenan, bazan biye maka balle ka hanani nuna wa duniya cewar kai d'an gatan family d'in Alhaji D'an fillo ba ne gaba da baya " Tana gama fad'in haka ta bar bedroom d'in don ba k'aramin aikin son ba ne yasa ta a gaba ba sai ta shirya shi saboda tsabar gata da sangarta irin ta d'an nata SABEER... AISHAT A MUH'D ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💖 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM DEDICATED TO MY SADEEY SANAZ PAGE 11-12 Yana fito wa daga bathroom yaga Mummy bata cikin bedroom d'in, ta6e fuska yayi kamar zai saki kuka ya dafe gishin shi yana cewa "Oh my God shine Mummy kika gudu koh? " Yana gama fad'in ya k'arasa wajen tafkekiyar wardrobe d'in shi ya bud'e ta a kasalance, don Sabeer ba k'aramin sangartacce ba ne komai idan zaiyi a sangarce yake yi. Dakyar ya iya d'auko wani white 3quater da T-shirt yellow mara hannu ya sanya su, tukunna ya k'arasa wajen dressing mirror ya gyara gashin kanshi sannan ya sanya perfumes different colour designer, masu matuk'ar k'amshi yana gama wa ya sanya hannun shi ya d'auko d'aya daga cikin favorite phone nashi. Sannan ya nufi hanyar fita daga d'akin nashi, idan mutum ya kalle shi sai ya zaci irin jarumin namijin nan saboda k'irar k'arfi da yake da ita, amman idan mutum yasan irin yanda yake matsoraci gashi sangartaacce ne na ajin k'arshe, don iyayen shi ba k'aramin sangartashi suka yi ba gashi Shagwa66e6e ne. Cikin takun tafiyar shi ta kalar Shagwa6a ya k'arasa sauka zuwa k'asan stairs, kai tsaye inda parents d'in shi suke ya nufa a dinning table inda suke breakfast, wajen dinning table d'in kanshi abin kallo ne ya had'u sosai gashi babba wanda a k'alla zai d'auki mutum goma. Suna hango shi suka fad'ad'a fara'ar su kallon shi suke cikin so da k'auna tamkar yau suka fara ganin shi, a tsakanin Mummy da Daddy baza ka iya tantance wanda wani yafi k'aunar tilon d'an su ba, tashi Daddy tsaye yayi tare da yin hugging d'in shi har da wani bubbuga bayan shi kad'an yana cewa "My lvly son good morning" Cikin shagwa66iyar murya Sabeer yace "Morning Dad " Bayan sun gama gaisawa Daddy yaja mishi kujera ya zauna, sannan yace "Son me zaka ci Mummyn ka tayi serving naka " "Nothing" D'an zaro ido yayi kad'an yana kallon Sabeer kafin yace "What! Son kasan bazan barka da yunwa ba don haka oya tell me " Duk wannan maganar da suke Sabeer ko kallon inda Mummy take bai yi ba sai wani 6ata fuska yake tamkar irin wanda ake mintsina sannan aka hana mutum kuka haka Sabeer yake. Ganin hankalin Daddy ya tashi ne yasa shi cewa "Okay Daddy na don't worry, a bani one cup of coffee ma" "Yawwa Son ko kai fa " Sai lokacin hankin Daddyh ya kwanta but yasan an 6atawa Son nashi rai cox haka yake fushi da abinci idan an 6ata mishi rai. Cikin murmishi Mummy tace "I'm so sorry my son nasan dalilin fushin ka" Ta k'arasa fad'a tana rik'o hannun shi cikin sigar rarrashi take mishi magana, kallon ta Daddy yayi tare da cewa "Oh I know ke kika 6ata mishi rai, tun da naga yak'i kallon inda kike " "Bafa wani abun babba ne ba fah Daddy" Cewar Mummy. "Fad'a min abin da ya had'a ku " Murmishin dai har yanzu Mummy take tana had'a wa Sabeer coffee sai da ta gama had'a shi tukunna ta bawa Sabeer cup d'in a hannun shi, sannan ta kalli Daddy da har yanzu kallon ta yake yana jiran ta fad'a mishi abin da ya had'a ta lvly Son d'in shi. Cikin yanayin k'sisina da karya murya tana wani fari da eye's nata tace "Daddy ka tuna lokacin da na sanar da kai idan Son ya gama karatun shi zan had'a mishi party na gayyato k'awaye na da abokanan arzik'i mu taya shi murnar kammala karatun shi lafiya, akan na sanar da shi fah ya fad'a min baya so shine ni kuma nace yayi hak'uri zan yi, shine fah yake fushi da Mummyn shi " D'an murmishi Daddy yayi don yasan halin Mummy wajen son nuna wa duniya d'an nata d'an gata ne duk abin da Sabeer yake so a wajen ta zata siya mishi indai akwai shi a duniyar nan, bata wasa da al'amarin Sabeer indai kuwa abin yayi mata tana rawar jiki zata yi mishi. Kallon Sabeer yayi yaga ko kallon inda suk bai yi ba hankalin shi yana kan wayar time to time yana kur6ar coffee nashi tamkar baisan abin da suke magana akai ba. Daddy ya rasa yanda zai yi baya son 6atawa d'an nashi rai haka kuma baya son ran Mummy ya 6aci, gashi ta zuba mishi eye's d'in ta da suke matuk'ar rud'a shi sai wani salo na daban take mishi. Da ido yayi wa Mummy alamar bari ya gwada rarraso shi, hannun Sabeer ya rik'o tare da cewa "My son kayi hak'uri da abin da Mummyn ka zata yi, kasan saboda son da take maka shi yasa take yin komai don taga ta faranta maka rai, gashi ta gama kashe kud'i masu yawa domin tayi maka abun da zai sanya ka farinciki, please Son kayi hak'uri ka bata wannan damar kada kace a'a son " Shiru suka yi dukannin su suna jiran abin da d'an lele zai ce, cikin zuciyar Mummy tana addu'ar Allah ya sanya Sabeer ya amince, sai da ya k'arasa shanye coffee d'in shi tukunna ya mik'e tsaye har ya juya bayan shi zai tafi. Gaba d'aya Mummy ta gama hak'ura da zai amince da party, sai kuma suka ji amon sautin muryar shi yana cewa "Alright naji Mummy but 30 minutes only zanyi a wurin " Yana gama fad'in haka ya juya ya tafi, cikin Farinciki Mummy tace "Yes! Daddy i can't believe ya amince min" Murmishi Daddy tare da cewa "Daman kece baki bishi ta rarrashi ba kinsan d'an naki sometimes sai da rarrashi " Mik'e wa tsaye suka yi Mummy saboda jin dad'i tayi hugging d'in Daddy tare da bashi peck a cheek d'in shi. Murmishi suka sakarwa junan su a lokaci d'aya, tukunna Daddy yace "Hey Mrs Hussein d'an fillo thanks for ur fantastic kiss" Fari da eye's nata Mummy tayi tare da kama hannun shi suka nufi upstairs don ta shirya shi zuwa fita office. WANE NE SABEER HUSSEIN D'AN FILLO? SORRY FANS BAN DA CHARGE NE, MU HAD'U A NEXT PAGE DON SANIN WANE SABEER. AISHAT A MUH'D ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 13-14 Family d'in Alhj d'an fillo asalin su irin fulanin nan ne wanda suke da arzik'i sosai na dukiya da ababan kiwo, Alhj Ahmad d'an fillo shine d'a d'aya a wajen mahaifin shi da mahaifiyar shi sai 'yan uba k'annen shi su uku dukka mata shi d'aya ne namiji mazauna garin adamawa state, shi yasa mahaifin shi ya tsaya akan bashi ilimin boko, duk da su ma matan ya sanya su a makarantar iyakar su secondary ya aurar dasu. Bayan Ahmad ya kammala karatun shi na fannin Lafiya ya samu aiki sai iyayen shi suka aura mishi wata Hauwaa wadda ta kasance 'yar uwar shi ce, watannin su uku da aure iyayen shi suka yi accident a hanyar su ta zuwa airport don zuwa k'asa mai tsarki domin gabatar da hajji, dukannin su suka rasu, mutuwar ba k'aramin girgiza Ahmad da matar shi Hauwaa tare da sauran 'yan uwan su tayi ba, sosai mutuwar ta shige su amman haka suka rungume hak'uri don sunsan haka Allah ya tsara zata faru. Bayan shekara d'aya da rasuwar iyayen shi matar shi Hauwaa ta haihu 'yan biyu suka samu, sunyi matuk'ar murna da farinciki, inda suka bar musu sunan su na Hassan da Hussein, sun cigaba da rainon yaran su cikin kulawa, watan su uku da haihuwa Hassan ya rasu sakamakon zazza6i mai zafi da ciwon ciki da yayi wanda kwanaki biyu yayi yana jinya a hospital ya rasu, sosai mutuwar Hassan ta bige su don sai zafin mutuwar iyayen shi ta dawo mishi sabuwa a lokacin, haka suka dangana suna masu bawa Hussein kulawa. Hussein yana da shekara hud'u Dr Ahmad d'an fillo ya samu transfer zuwa Malam Aminu kano teaching hospital, ba 6ata lokaci ya tattara komai nasu suka dawo garin Kano, sai da ya fara zama a gidajen hospital d'in kafin ya gina nashi gidan, don zaman garin Kano yayi mishi dad'i. Bayan an gama mishi ginin suka dawo cikin sabon gidan su a lokacin Hauwaa ta haifi d'an ta na biyu Omar, bayan shekara biyu ta sake haihuwar Usman, daga Usman sai Aminu sannan autar su Fadilah, sun cigaba da rainon yaran su cikin kulawa da k'auna makarantu masu kyau da tsada Dr Ahmad d'an fillo ya sanya yaran shi, sai dai sun fi bawa boko mahimmanci fiye da ilimin Islam, a lokacin Dr Ahmad d'an fillo ya tsunduma harkar business sosai wanda nan da nan kud'i sosai suka fara samuwa ba kad'an ba. Haka lokaci ya cigaba da tafiya yaran shi dukka sun girma kowannen su ya gama karatun shi yana aiki, Hussein business d'in da mahaifin shi yake ya tsunduma a ciki, Omar kuma yana aikin Bank, Usman kuma a wani babban company na abokin Dr Ahmad d'an fillo yake aiki a matsayin GM na company d'in, sai Aminu da yake lecturing a BUK, sai k'aramar su Fadilah da take karatun degree a wannan lokacin, wanda gab take da ta kammala har an sanya lokacin auren ta da wanda zata aura, iyayen shi masu kud'i ne shima haka yana da kud'i abokin yayan ta Omar ne, lokacin da ya nuna yana son ta sosai iyayen ta suka yi farinciki da hakan, saboda suna da kud'i don Dr Ahmad d'an fillo da 'ya'yan shi basa harka da talakan mutum sai ta kama, don akwai su da kyamar talaka harkokin shi sai da masu kud'i 'yan uwan shi. Shiyasa ba 6ata lokaci aka sanya lokacin auren Fadilah da Mustapha, bayan ta kammala degree d'in ta aka yi biki sosai sun kashe kud'i a bikin, bayan auren Fadilah suma Yayannin ta kowanne ya fito da matar aure duk yaran masu kud'i ne daman gashi akwai su da kyau irin na fulani ga kud'i kuma da wayewa, sai da ban da Babban Yaya Hussein don shi harkar neman kud'in shi ya sanya a gaba bai fiye, kuma iyayen nashi sam basu tak'ura mishi ba da yayi aure, kafin bikin ne Dr Ahmad d'an fillo ya gina k'aton gida mai d'auke da part's biyar kuma kowanne part babba ne sosai kuma upstairs ne, an kashe kud'i sosai a wannan gidan kafin bikin suka koma can da zama abin su. Sai da Omar, Usman da Aminu suka haifi yara kowanne biyu biyu kuma kowanne yaro da tazarar shekara wajen uku a tsakani,tukunna Hussein ya kawo matar da zai aura Dr Faridah cikakkiyar likitar mata ce wato gynecology a k'asar India tayi karatun ta, iyayen ta masu kud'i ne sosai ne kuma abokin Dr Alhj Ahmad d'an fillo ne sosai da sosai, lokacin da Dr Ahmad d'an fillo yaji d'an shi Hussein Dr Faridah zai aura ba k'aramin farinciki suka yi ba shi da Hajja Hauwaa, nan aka sanya lokacin biki two weeks kawai, an kashe kud'i bana wasa ba a wannan auren, don su kansu matan Omar, Usman da Aminu sun san an auro matar so kuma ta gaban goshin surukan nasu don yanda suka ga ana ji da ita tun kafin ta shigo gidan. Dr Faridah Bashir kyakkyawa ce kuma wayayyiya ce sai dai akwai ta da wulak'anci ba kad'an ba, gata kuma ta tsani wani talaka ya ra6e ta, kanta kawai ta sani, ga nuna tak'ama da tsantsar ak'idar Boko, kuma mahaifin ta hospital babba ya bud'e mata nata na kanta don su biyu kad'ai Allah ya bashi daga Faridah sai k'anwar ta Zahra, ga zata auri mai kud'i don Hussein duk yafi 'yan uwan shi kud'i, wad'annan halayen nata su suka k'ara mata matsayi cikin zuciyar surukin ta Dr Ahmad d'an fillo fiye da sauran surukan nashi, yana ji da ita matuk'ar gaske. Bayan auren Hussein da Dr Faridah sai da suka yi wajen shekara uku ko 6atan wata bata ta6ayi ba, sosai hankalin su ya tashi nan aka shiga ziyartar asibitocin k'asashen waje domin bincikar lafiyar su, amman k'alau suke lokaci ne bai yi don komai kud'in ka sai lokacin da Allah ya nufa zaka samu abu zaka same shi, balle haihuwa da lafiya wanda kud'i baya ta6a siyan su sai lokacin da Allah yaso zai baka, gajiya sukayi da zuwa hospitals suka zubawa sarautar Allah ido tare da tsananta addu'a sosai a wajen Ubangiji, Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suma duk'ufa da addu'a suka yi sosai don suna k'aunar son ganin jikan su na wurin Hussein da Dr Faridah. Sai da suka kwashe shekara hud'u da aure kafin Allah ya bawa Faridah ciki, murna da farinciki bazai fad'u ba irin wanda suka yi, nan suka dunga rainon cikin cikin so da k'auna. Bayan wata tara Faridah ta haihu an samu baby boy kyakkyawan yaro dashi, anyi murna da farinciki sosai, ranar suna ansha taro an kashe kud'i duk wanda yaje sunan yasan an haifi d'an lele kuma d'an gata, anyi suna Lafiya an tashi Lafiya inda yaro yaci sunan shi Muhammad Sabeer wanda Dr Ahmad d'an fillo ya rad'a mishi sunan da kanshi, inda kuma ya bawa Dr Faridah kyautar wani gida babba mai kyau da wata had'add'iyar mota jeep duk gift ne na jin dad'in haihuwar Sabeer, Hajjah Hauwaa kuwa gift d'in sark'ar gold ta bata tsadaddu dasu tun daga sark'a, d'an kunne abin hannu (warwaro), sark'ar k'afa da kuma rings guda biyu kud'i sosai ta fitar ta siya mata su. Haka Sabeer ya cigaba da girma ana ji dashi sosai, makarantar shi dukka a k'asar waje yayi su, Sabeer kyakkyawan matashin saurayi ne d'an shekara 27-28 ya had'u ta ko'ina ga kyau ga kud'i, sai dai sangartacce ne na ajin k'arshe gashi d'an shagwa6a don iyayen shi da kakannin shi sunyi matuk'ar sangartashi, so suke nuna mishi sosai gashi daman shi kad'ai Allah ya basu ba kwa6a ba harara duk abin da yake so suna yi mishi sosai, Sabeer bai ta6a neman wani abu ya rasa ba, duk abin da yace yana so jiki na 6ari ake yi mishi don kada ranshi ya 6aci, gata sosai yake samu gashi yanzu ya kammala karatun shi ya dawo gida. **** **** **** CIGABAN LABARI... Yana fita daga side d'in nasu part's d'in kakannin nashi ya nufa yana wani yatsina fuska tamkar wani mai jin amai, ya sanyo kanshi cikin babban parlour d'in sai ga wata house girl ta taho fita hannun ta d'auke da tire wanda saman shi jug ne mai d'auke da so6o sanyaye sai k'ananun cups akai guda biyu da d'an wani bowl guda uku 'yan manya d'aya na d'auke da cup cakes, d'aya kuma egg rolls sai na k'arshen samosa, irin tazo zata wuce ta kusa da Sabeer sai tsautsayi ya sanya tsantsin tiles ya kwashe ta gaba d'aya tayi baya kayan hannun ta kuma suka yi kan Sabeer. Unexpected yaji saukar abu mai sanyi da d'umi a jikin shi sai wani cup d'aya da ya fad'o kan k'afar shi ya had'u da tiles ya tarwatse har ya yanki Sabeer a k'afa kad'an jini ya fito, baisan lokacin da ya bud'e baki ya kwalla wata k'ara mai k'arfi tare da yin wani tsalle don ba k'aramin firgita yayi ba don ko kula da tahowar ta bai yi ba, ga zafin yankewar da yayi. Hajjah Hauwaa tana bedroom d'in ta taji k'arar d'an lele da sauri ta tashi ko takan d'an kwalin ta bata bi ba tayo downstairs da d'an gudu irin na tsofaffi a rud'e. House girl d'in nan kuwa tuni ta tashi daga fad'uwar da tayi a k'asa duk da kuwa zafin da taji na fad'uwar haka ta daure ta tashi ta tsugunna tana kuka tare da bawa Sabeer hak'uri, don tun kafin ya dawo ake jan kunnen su da 6ata mishi rai su kiyayi 6acin ran shi, sai gashi yau tsautsayi ya ritsa da ita daga dawowar shi jiya. Sabeer tsalle da ihu kawai yake yi, a dai dai lokacin Alhj Ahmad d'an fillo ya sanyo kanshi cikin parlour ranshi a 6ace, saboda bak'on da yayi yana jiran a kawo musu abin ta6awa a baki ba'a kawo ba shine ya taso da kanshi, abin kamar a mafarki yaji ihun Sabeer aikuwa da sauri ya k'arasa parlourn jiki na 6ari. Lokaci d'aya Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suka shigo parlourn, wajen Sabeer gaba d'aya suka yi cikin matuk'ar tashin hankali don sam basu kula da house girl d'in da take durk'ushe tana zunduma kuka. Alhj Ahmad d'an fillo janyo Sabeer jikin shi yayi ya rungume shi cikin rawar murya ya fara cewa "Sabeer what happened to U? "waya ta6a min kai? " Duk wannan tambayar Alhj Ahmad d'an fillo yayi ta a rud'e. Cikin sangarta da salon shagwa6a Sabeer ya nuna jikin shi da k'afar shi da take fitar da jini, a kid'ime suka kalli jikin nashi da k'afar shi saboda tsabar rud'ewa sai yanzu suka kula, cikin tashin hankali Hajjah Hauwaa tace "wa yayi maka wannan rashin mutuncin Sabeer? " Ta fad'a tana mai dafe kirjin ta tare da zaro idon ta waje, Alhj Ahmad d'an fillo kuwa saboda tsabar tashin hankali kasa magana yayi sai zuciyar shi da take bugawa da k'arfi. Hajjah Hauwaa ta kama hannun Sabeer tare da cewa "Sabeer open your mouth and explain me please " Bai yi magana ba sai hannun shi da ya d'aga dakyar ya nuna saitin da 'yar aikin take tsugunne tana kuka jikin ta na rawa, zaro idanun su suka yi lokaci d'aya sannan Alhj Ahmad d'an fillo ya bud'e baki cikin tsawa mai matuk'ar firgita wa yace "keeee zo nan " 'yar aikin a kid'ime ta tashi ta nufi inda suke tsaye, jikin ta na matuk'ar rawa ga hawaye na zuba a idanun ta, hannun ta gaba d'aya a saman kanta don tasan ita yau ta ta, ta k'are.... Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz _This page is for you my Namecy Ayusher Ilias writer d'in YA SAYYADI, ina tayaki murnar kammala littafin ki YA SAYYADI Allah ya k'ara basirah da k'arfin ido ina yin ki sosai Namecy Allah ya bar zumunci😍 PAGE 15-16 Tana k'arasowa inda suke Alhj Ahmad d'an fillo ya sanya hannun shi ya wanka mata mari a kumatu, kafin ta dawo hayyacin ta Hajjah Hauwaa ita ma ta wanka mata marin a d'ayan kumatun, ihun kuka kawai 'yar aikin take yi saboda ba k'aramin shigar ta marukan suka yi ba, kallon ta suke sai huci sukeyi cikin harara Hajjah Hauwaa tace "me kike kallo da zakiyi wa Sabeer haka, baki da hankali ne, ina so kafin cikar mintuna 5 Ki barmin gida " Duk da tsananin zafin marin da 'yar aikin tasha hakan bai hanata durk'usawa a k'asa ba cikin kuka take cewa "don Allah kuyi hak'uri tsautsayi ne amman kada ku kore ni bazan sake kwatanta hakan ba " Cikin 6acin rai Dr Ahmad d'an fillo yace "baki ji abin da aka ce miki ba sai na kira police sunyi gaba da ke, wlh kika bari na kirawo police gidan nan sai kin yabawa aya zak'in ta " A kid'ime 'yar aikin ta mik'e jikin ta na rawa ta fara kok'arin barin parlourn, Sabeer wanda yake jikin Dr Ahmad d'an fillo ya lafe yana sauke ajiyar numfashin ihun da ya gama ya bud'e baki dakyar yace "keee ki zauna kada ki tafi but ki kiyaye gaba, kika sake min haka bazan Kyale ki ba " Cikin mamaki Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suke kallon shi sun ma kasa furta komai, da sauri 'yar aikin ta tsugunna tana murmishin farinciki cikin rawar murya tace "Ngde yalla6ai Allah ya kare ka yanda ka taimake ni kai ma Allah ya taimake ka a duk inda kake, kuma zan kiyaye gaba insha Allah ngde ngde sosai " D'aga mata hannun shi yayi d'aya tare da cewa "is okay zaki iya tafiya " Jiki na 6ari ta bar wajen Sabeer ya bita da kallon tausayi don tabbas tausayin ta ne ya sanya shi barin ta don ta cigaba da aiki. Kallon Hajjah Hauwaa yayi wadda take mishi kallon mamaki ya yamutsa fuska yana cewa "a had'a min ruwa a toilet zan yi wanka " Sai lokacin bakin ta ya bud'e ta iya cewa "yanzu shikenan Sabeer an barta baza'a d'auki mataki a kanta ba " "ni tayiwa laifi koh, kuma nace ta zauna kada ta tafi ko'ina don haka ku Kyale ta idan kuma naji anyi mata wani abun raina zai iya 6aci kum......" Kafin ya k'arasa fad'i abin da zai fad'a Dr Ahmad d'an fillo yace "kayi hak'uri kada ranka ya 6aci Sabeer baza'a yi mata komai ba komai ya wuce " ya k'arasa fad'i yana shafa kanshi tamkar wani k'aramin yaro. Kan shi ya gid'a idon shi na kan ciwon da ya d'an ji akan k'afar shi, Dr Ahmad d'an fillo ya kalli Hajjah Hauwaa yace "ba'a haka yace a had'a mishi ruwa zai yi wanka ba? " Dafa kafad'ar Sabeer tayi tare da cewa "zo muje da kaina zan had'a maka " Kamo hannun shi tayi ta jashi zuwa upstairs inda bedroom d'in shi yake (da yake yana da bedroom a side d'in kakannin nashi), da kallo Dr Ahmad d'an fillo ya bi Sabeer har ya daina hango shi tukunna ya juya ya fita. Bayan Sabeer yayi wanka ya fito ya shirya cikin Kayan da Hajjah Hauwaa ta ajiye mishi saman bed, ya sanya su sannan ya kwanta kan sofa hannun shi d'auke da I pad d'in shi yana research a ciki. "Assshhh " Ya furta a hankali sakamakon maganin da Hajjah Hauwaa ta sanya mishi a d'an ciwon da glass cup ya ji mishi, bakin ta ta sanya tana hura mishi k'afar tare da cewa "sannu " Ta furta hakan tana rufe robar cream d'in da ta shafa mishi, d'an 6ata fuska yayi yana cewa "shine baki fad'a min zaki sa min ba koh? " Da shagwa6a ya fad'i hakan, nan ta fara rarrashin shi sai da ta ga ya hak'ura tukunna ta fita daga bedroom d'in don ta barshi ya huta. 8pm Sabeer ne tsaye gaban dressing mirror yana sake gyara necktie d'in suit d'in shi, yayi kyau sosai cikin blue d'in suit ba kad'an ba shoes d'in shi black ne haka watch d'in hannun shi samfur d'in Gucci yayi kyau gashin kanshi yasha gyara sai shek'i yake. Turo kofar bedroom d'in akayi Mummy ce ta shigo tasha gayun ta cikin wani tsadaddan black less mai adon flowers ash Sai ta nad'a laffaya ash colour mai kyallen duwatsun silver sai manya flowers black a jikin laffayar tayi kyau sosai baka d'auka ta haifi Sabeer ba gefen ta kuma wata matashiyar kyakkyawar yarinya ce tana sanye cikin wata gown na English wears sun kamata sosai daganin ta kasan idon ta a bud'e yake tasha wani uban hill shoes ga attachment da tasha sai farce daga ni sanya su tayi, fuskar nan tasha heavy make up sai wani iyayi take, kallo d'aya zaka yi mata kasan kusan sa'anni ce da Sabeer a shekaru. Kallo d'aya Sabeer yayi mata ya d'auke kai don bai ga alamun tana da hankali ba irin wannan haukan kwalliyar da tayi, matsalar shi da Mummy kenan jajibo irin wad'annan yaran marasa kamun kai. Cikin murmishi d'auke a fuskar Mummy ta k'arasa inda Sabeer yake tayi hugging d'in shi tare da cewa "Wow son ka ganka kuwa U look so cute " "Thanks Mumy" Ya furta tamkar baya son magana, cikin murmishi Mumy tace "Son ga Fadilah ko baka gane ta ba ne? " D'auke kanshi yayi tare da cewa "bansan ta ba" Yana gama fad'in yayi gaba, kunya ce ta d'an kama Mumy don bata zaci Son zai mata haka ba ya kunyatar da ita a gaban d'iyar k'awar ta, wayance wa tayi da cewa "Kyale shi Fadilah ranshi ne a 6ace don baya son wannan party da na had'a mishi " Sai lokacin matashiyar yarinyar da Mumy ta kirawo da Fadilah ta saki murmishi don ta shiga damuwa a time d'in da Sabeer ya nuna baisanta ba. Kamo hannun ta Mumy tayi suka fito zuwa compound d'in gidan friends d'in Mumy da yaran su zuwa 'yan uwan Sabeer ne sai shiga mota ake suna tafiya zuwa hall d'in da za'a yi party. Wata black Range Rover na hango a tsakiyar compound na gidan sai shek'i da d'aukar ido take daganin ta kasan sabuwa ce, nan na hango Sabeer ya nufi wajen cikin takun tafiyar shi kamar bayason taka k'asa, kafin ya k'arasa wajen tuni driver ya bud'e mishi bayan motar yana k'araso wa shiga yayi ya zauna sannan driver ya rufe murfin motar, cikin sauri ya shiga mazaunin driver ya yiwa motar key ya fara tafiya a hankali don Sabeer bai fiye son ayi gudu dashi a mota ba idan bashi yake driving ba. Suna k'arasa wa katafaren hall d'in da aka kama don yin partyn ko'ina yasha decorations na blue white, wajen yayi kyau sosai ta had'u ga wani cake mai hawa uku shima kalar shi blue and white ne yayi kyau sosai ya tsaru. Ga manyan hamshak'an masu kud'i friends na Mumy da yaran su, ga 'yan uwan Sabeer nan mazan su da matan su kowa yasha gayun shi na kece raini don kowa yana ji da kanshi ta fannin kud'i da gogewar ilimi da wayewa. Driver yana yin parking motar da Mumy take ciki tayi parking kusa da motar da Sabeer yake ciki, nan Mumy ta fito ita da wannan Fadilah suka k'araso inda Sabeer yake, Mumy ta bud'e kofar motar tare da cewa "Son fito mu tafi mutane na jiran mu " Cikin wani tak'ama da had'e fuska ya ziro k'afar shi d'aya waje sai da ya d'auki wasu seconds tukunna ya fito da d'ayar kafin kuma ya fito da dukka jikin shi zuwa waje. Kallon shi Fadilah take tamkar ta lashe shi saboda tsabar maitar son shi da take, ita fah da zai aminta da ko bazai aure ta ya yarda suna biyawa kansu buk'ata don tasan Sabeer irin shine wanda zai yi mata yanda take so, amman zata fara gwada sa'ar ta ko zatayi nasara... Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz This page is for U my Momma na (Aunty Maijiddah Musa) thanks for luv nd support, Allah ya raya zuri'a Allah ya bar zumunci ❣ PAGE 17-18 Yana gama fitowa a mota ne Mumy ta kama hannun shi suka fara tafiya zuwa cikin hall d'in, sai da suka kusan shigewa hall d'in tukunna Fadilah ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad'a da sauri ta bi bayan su don tana Buk'atar jerawa da Sabeer. Bayan sun shiga ciki ne Mumy da Sabeer suka zauna waje d'aya sai wani 6a66ata rai yake, gaba d'aya hayaniyar duk ta isheshi ya gaji ga 'yammatan da suka dame shi da hayaniyar su kowacce tana kok'arin cusa kanta a wajen shi, amman yanda kasan da dutse suke magana haka yake share su, Gashi kowacce da nata gift's da takawo mishi, Mumy sai wani murmishin jin dad'i take ganin yanda ake son d'anta. Gaba d'aya Mumy ta mance da 30 minutes kawai Sabeer yace zai yi, bata ankara ba taga sun d'auki wajen 25 minutes a wurin ai kuwa da sauri ta kallo inda Sabeer yake zaune yana danna wayar shi gefen shi kuma Fadilah ce ke faman yi mishi surutu tana wani karairaya da iyayi ita a dole so take ta birge Sabeer, k'arasa wa Mumy tayi wajen ta dafa kafad'ar shi cikin k'aramin sautin magana tace "Son kazo ka yanka cake " Daman gaba d'aya a takure yake da yabar wajen don haka ya mik'e tsaye Mumy taja hannun shi har zuwa inda aka ajiye cake, knife Mumy ta bashi suka rik'e tare tukunna suka yanka nan Mumy ta bashi a baki shima ya bata, nan kuma kowa ya fara bashi kyautar gift nashi da zai bashi Sabeer sai faman jan tsaki da 6ata rai yake ganin har ya k'ara 5 minute akan 30 minutes d'in da zai yi, sai kallon Mumy yake yana son sun had'a ido dashi yayi mata magana, amman tak'i yarda su had'a ido kwata kwata saboda tasan halin d'an nata gashi duk wanda zai bashi gift idan baisan shi ba sai ya tsaya gabatar da kanshi. D'ago kan da zaiyi ya kalli Mumy akayi sa'a ita ma ta kallo inda yake da ido yayi mata alamar ya gaji gashi time d'in da ya d'auka ya wuce yana nuna mata agogon hannun shi gashi kuma 'yammatan da suka bi suka dame shi Sabeer dai yaga ta kanshi tamkar zai fashe da kuka haka yake ji duk Mummy ce ta ja mishi, Mumy tamkar ta fashe da dariya haka taji lokacin da ta ga Sabeer yanda ya koma amman sai ta danne dariyar ta tare da marairaice mishi fuska da ya d'an yi hak'uri na d'an wasu minutes, daga nan kuma aka fara ciye ciyen abubuwan ci dana sha, a wannan lokacin Sabeer ya zame ya tafi abin shi gaba d'aya a wani gala6aice yake kanshi har ya fara ciwo. Shiga mota yayi driver yaja shi sai gida, yana parking ya fito daga motar ya nufi side d'in su, kai tsaye bedroom d'in shi ya nufa yana shiga ya fara cire kayan jikin shi yana wurgi dashi sai da ya cire komai sai iya dogon wandon shi ya bari tukunna ya shige toilet, shower ya sakarwa kanshi na tsayin 2 minute kafin ya fad'a cikin bath tub ya fara wanka bayan ya gama ne ya d'aura alwalar sallahr ishha tukunna ya fito daga toilet. Wata white jallabiya ya sanya cikin nutsuwa ya gabatar da sallahr ishha bayan ya idar ne bai wani tsaya yin wata addu'a ba ya mik'e tsaye tare da cire jallabiyar ya kwanta daga shi sai three-quarter a jikin shi kwanciya yayi saman bed yana mai runtse idanun shi hannun shi d'aya saman goshin shi ya dafe, a hankali ya wani bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi daman ya gaji sosai. Mumy koda ta duba bata ga Sabeer ba tasan ya tafi, don haka nan ta sallami friends nata da wad'anda suka zo, kowa ya tafi gida tukunna ta shiga mota zata rufe murfin motar taji an rik'e, cikin d'an mamaki ta jiyo don ganin wane, had'a ido tayi da Fadilah fuskar Mumy cike da mamaki tace "Fadilah daman baki tafi gida ba " Cikin marairaice fuska Fadilah tace "ni Mumy bin ki zanyi fah acan zan kwana " Murmishi kawai Mumy ta saki don tasan dalilin kwanan Fadilah a gidan nata, cikin kulawa Mumy tace "alright dgter shigo mu tafi " Fadilah jiki na rawa ta shige cikin motar ta zauna burin ta kawai a yanzu da tunanin ta shine yanda zata shawo kan Sabeer ya amince da ita ya aure ta ko suna hutawa da junan su, don ita Fadilah bata da ra'ayin aure a zuciyar ta sai da taga Sabeer, ita kawai 'yar aji dad'in rayuwa ce bata tunanin makomarta anan gaba matsayin ta na d'iya mace. Hira suke tsakanin Mumy da Fadilah har suka k'arasa gida driver yana yin parking suka fito a motar direct part d'in Mumy suka nufa, suna shiga cikin parlourn babu kowa amman a gyare yake tsaf dashi sai tashin k'amshin turaren wuta yake da air freshener, upstairs suka nufa nan Mumy ta nunawa Fadilah room d'in da zatayi amfani dashi, amman sai Fadilah tace "Mumy ina ne bedroom na Sabeer naje mu yi hira kinsan har yanzu yak'i sake min sosai " Murmishi Mumy ta saki tare da nuna mata wani d'an corridor da hannunta tace "kin ga bedroom d'in shi can nasan yanzu yana ciki " tana gama fad'in haka Mumy ta nufi hanyar da zai kai ta bedroom nata ta bar Fadilah anan. Wani dad'i ne ya kama Fadilah cikin rawar jiki ta juya zata nufi room d'in Sabeer sai ta kalli kayan jikin ta wani d'an Tunani tayi kad'an kafin ta juya kuma da sauri ta koma bedroom d'in da Mumy ta nuna mata. Da sauri ta shige bathroom ta fara yin wanka bata dad'e ba ta fito babu batun yin alwala balle sallah, cikin sauri ta gyara jikin ta sannan ta shirya cikin wata white d'in sleeping dress tsayin ta iyakar shi cinya mai siririn hannu sannan ta d'ora 'yar saman ta wadda take har k'asa sai dai gaban ta a bud'e yake sai 'yan igiyoyin rigar da ake d'aure wa, perfumes ta sanya masu matuk'ar k'amshi da tada hankali sannan ta fito zuwa room d'in Sabeer. Tura kofar room d'in tayi ta shiga tare da rufe kofar ta jingina bayan ta a jikin ta, shak'ar k'amshin turaren Sabeer tayi tare da lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya, kafin ta bud'e idanun ta a hankali ta zube su akan Sabeer da yake baccin shi hankali kwance, wani shu'umin murmishi ta saki tana mai k'arasa wa wajen bed d'in, hankalin ta kwance ta cire 'yar saman rigar ta tukunna ta haye kan bed d'in. Kallon Sabeer take tamkar wata kura taga nama, sai wani had'iyar yawu take musamman da takai eyes nata kan kirjin Sabeer a hankali ta d'ora hannun ta inda take Buk'atar ajiye shi a cikin jikin Sabeer ta fara shafawa cikin kwarewa da gwanin ta.... Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey (saNaz) Where are U Bilkisu Bk this page is for U autan Exclusive thanks for luv and care, Allah ya bar zumunci thanks once again dear 👄 PAGE 19-20 Sabeer yana tsaka da yin sleeping nashi mai dad'i yaji tsikar jikin shi yana tashi, wani yanayi yana shigar shi a hankali mara fasaltuwa ya rasa tantanci shin mafarki ne ko ido biyu yake jin haka. Fitinannen k'amshin Fadilah ne ya cika kofofin hancin shi har takai da ya fara kok'arin bud'e idon shi, gaba d'aya Sabeer ya gama tsorota don yana tunanin ko aljanna ce ta zo mishi tun da a lokacin ya tabbatar da ba mafarki ba ne kuma yasan wace mace ce zata zo mishi a wannan daren idan ba aljanna ba, har jiki shi ya fara d'an rawa don Sabeer akwai tsoro dakyar ya iya yunk'urin bud'e idon shi ya zuba su akan Fadilah da take kok'arin kissing lips nashi, don ta had'a fuskar ta da tashi daf take da ta had'e lips nasu waje d'aya. Zaro ido Sabeer yayi cike da tsantsar mamaki yana kallon ta, ranshi a 6aci sosai so yake ya tuna inda ya santa, amman kafin ya tuna d'in tuni Fadilah ta had'e bakin ta da nashi, wasu abubuwa take yiwa Sabeer wanda duk d'a namiji cikakke mai lafiya bazai iya jurewa ba, tuni Sabeer ya fara sakin layi yana mayar mata martanin abin da take mishi. Tuni Fadilah an saki jiki sosai tayi luf a jikin Sabeer tana mai kar6ar sak'onnin da yake aika mata dashi cikin rawar jiki, sun yi nisa cikin wannan yanayin sosai kamar wanda wutar nepa taja haka Sabeer yaji a jikin shi wanda ya haddasa mishi barin jikin Fadilah da sauri ya mirgina can k'arshen bed d'in, yana mayar da wani irin numfashi tare da sauke ajiyar zuciya. Kafin kuma ya fara tunanin abin da ya kusan faruwa a yanzu tsakanin shi da Fadilah, zumbur ya mik'e tsaye yana furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yana dafe da kanshi cikin zuciyar shi yana mai godewa Allah da ya tseratar dashi daga hannun wannan shaid'aniyar 'yar iskar yarinya. A zuciye yayi kan Fadilah wanda idanun ta a lumshe tana jiran Sabeer ya fara aiki gaba d'aya cikin wani buk'atuwa take dashi, don ta d'auka ya tsaya cire 3quater d'in jikin shi yake, don haka ita ma sai ta fara kok'arin k'arasa cire sleeping dress d'in jikin ta daman gashi room d'in babu haske sosai, don haka bata ga tahowar Sabeer wurin ta ba bata kai da gama cire rigar ba a fusace yakai hannun shi saman fuskar ta ya wanka mata mari har guda biyu wanda sai da Fadilah taga wasu star's a idanun ta jinta ya d'auke na wucan gadi, don tun da Maman ta ta haifeta ba'a ta6a yi mata irin wannan marin ba, kafin ta dawo hayyacin ta daga marin Sabeer ya zage iyakar k'arfin shi ya hau dukan ta da belt, tuni Fadilah ta fara ihun kuka da neman agaji da k'arfi sosai take ihun wanda ya sanya k'arar ihun ta ya tashi Mumy da Daddy daga baccin su, a kid'ime suka fito daga bedroom d'in Daddy suka yo d'akin Sabeer don tanan haka suke jin k'arar ihun. Da k'arfi suka tura kofar suka shiga hankalin su a tashe sosai, ganin duhu ne ya sanya Daddy kunna bulbs d'in room d'in tuni haske ya gauraye d'akin, hango tilon d'an su suka yi yana dukan Fadilah cike da fusatar da basu ta6a tsammanin yana da ita ba. Da sauri Daddy ya nufi wajen shi yana cewa "Son What wrong with U? " Amman Sabeer bai kula shi cigaba yake da dukan ta kawai wanda yanzu babu bakin kuka sai hawayen da suke zuba cikin idanun ta, ganin bazai tsaya da dukan ya sanya Daddy rik'e shi gam a cikin jikin shi tare da kallon Mumy yace "Janye Fadilah ki fitar da ita " Jiki ba kwari Mumy take kok'arin d'aga tana kallon fuskar d'an nata wanda take hango kwantaccen 6acin rai akan fuskar tare da wasu hawaye da suke zuba a kan fuskar tashi gaba d'aya sai taga ya rikid'e mata ya zama wani mutum na daban kamar ba Sabeer ba, gashi idanun shi sunyi ja da fuskar shi, jikin Mumy gaba d'aya yayi sanyi haka ta ja Fadilah suka fita daga bedroom d'in ta tana tunanin me ya had'a Fadilah da Sabeer har yayi mata wannan mugun dukan. Bayan sun fita daga bedroom d'in Daddy ya zaunar da Sabeer kan bed amman sai Sabeer ya zame ya zauna akan lallausan carpert d'in d'akin ya dafe kanshi da dukka hannu biyun yana hawaye wai yau shine yake kok'arin aikata zina wannan wacce irin bak'ar rana ce a wajen shi. Bottle d'in faro Daddy ya d'auko a frige tare da glass cup ya tsiyaya a ciki tukunna ya rufe bottle d'in ya d'ora saman frige sannan ya k'arasa wajen Sabeer ya dafa mishi kafad'a tare da d'ora mishi bakin cup d'in a tsakanin lips nashi bai yi musu ba ya bud'e bakin ya sha ruwan sosai tukunna ya zame bakin shi ya kwanta a k'asan yana d'ora kanshi saman k'afafun Daddy. Hannun shi Daddy ya sanya yana shafa lallausar suman kan Sabeer sun d'auki wajen 5 minute a haka, tukunna Daddy yace "Sabeer sanar da ni abin da ya faru tsakanin ka da Fadilah har kayi mata wannan mugun dukan? " dakyar Sabeer ya iya bud'e bakin shi yace "Ba komai " Hangame baki Daddy yayi yana kallon shi cikin mamaki har zai sake magana sai ga Mumy ta shigo room d'in cikin tashin hankali zata fara magana Sabeer ya dakatar da ita yana cewa "Mumy leave me alone please" Zata matso kusa dashi da sauri ya tashi ya koma saman bed ya kudundune cikin blanket zuciyar sai wani tafasa take sosai yake jin haushin Mumy don yasan duk ita ce ta nuna mata room d'in shi, kallon Daddy Mumy tayi ta marairaice fuska hannun ta ya rik'o tare da cewa "Yana buk'atar hutu ne na fuskanci ranshi a 6ace yake sosai " Cikin damuwa Mumy tace "Yanzu bai fad'a maka abin da ya faru nima Fadilah tak'i fad'a min sai kuka kawai take" Ta k'arasa maganar tamkar zata fashe da kuka, cikin kwantar da hankali Daddy yace "Ki bari zuwa gobe nasan ya huce zai yi bayani amman nasan Fadilah tayi mishi laifi babba " Haka suka fito duk jikin su a sanyaye sosai baccin ranar basu iya bacci ba tsakanin Sabeer, Mumy, Daddy da kuma Fadilah kowa sai juyi yake akan bed da tunani kala kala cikin zuciyoyin su. Bayan sallahr asubah ne Sabeer ya fito daga side d'in su cikin shigar white T-shirt da 3quater yellow ya shiga motar shi k'irar Benz driver yaja shi, sai da suka yi tafiya mai d'an nisa tukunna driver yace "Yalla6ai ina zamu je? " D'an shiru Sabeer yayi yana tunani kad'an kafin yace "Ina son ka kaini d'aya daga cikin wani k'auye mai kyau da ke makwabtaka da mu " D'an murmishi driver d'in yayi tare da cewa "Angama yalla6ai " Yana gama fad'in haka ya nufi wata hanya, yayin da Sabeer ya kishingid'a a bayan motar a hankali yake jin zuciyar shi na yin sanyi... Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz Wannan shafin naki ne kyauta Zahra Maman Kausar da Ahmad thanks for luv and support, ina jin dad'in yanda kike k'aunar nvls d'ina, Allah ya bar zumunci ya raya mana Kausar da Ahmad, Amin ❣ PAGE 21-22 Cikin nutsuwa Suhaima ta fito daga d'akin ta cikin shirin uniform na tahfiz da yake ranar asabar ce, cikin kitchen ta k'arasa inda Aunty Aliyah take had'a abin karin kumallo ganin sinasir take yi ne ya sanya Suhaima sakin murmishi da yake tana son sinasir sosai, cikin jin dad'i tace "Wow Aunty sinasir kike mana yau amman naji dad'i sosai bari nayi sauri na tafi kada nayi latti " Murmishi itama Aunty Aliyah tayi tare da cewa "Ai shikenan sai kin dawo, zaki sha 'yar tafiya kuwa yau don Yayan ki ya fita tun asuba zuwa kai kaji da kwayaye kasuwar birni " D'an murmishin ta mai kyau Suhaima tayi tare da cewa "Yeeeeee ai ni yau naji dad'in haka zan tafi a k'afa saboda kullum shi Yaya shi yake kaini kuma yaje ya d'auko ni ko'ina mutum zai je sai dai a kai shi ni fah yanzu na girma " ta k'arasa fad'i tana rawa har da juyi duk dad'i ya ishe ta. Rik'e baki Aunty Aliyah tayi tana cewa "Tabbb kenan dad'i kike ji ai kyasha tafiya kuwa yau " "Eh naji Allah ya dawo da Yaya lafiya ni na tafi kada ki ja min latti " Suhaima ta k'arasa fad'a tana dariya ta fice daga gidan da sauri, tabar Aunty Aliyah itama tana dariya kafin ta mayar da hankalin ta kan abin da take yi. Cikin d'an sauri Suhaima take tafiya saboda ganin ta kusa latti aikuwa tana shiga cikin makarantar aka rufe kofa lokacin kaman 'yan latti yayi, wata ajiyar zuciya Suhaima ta saki ganin Allah ya taimake ta bata sha dukan latti ba da sauri ta wuce cikin ajin su, da yake k'auyen nasu babu laifi akwai masana ilimin addini dana zamani dai dai gwargwado, musamman ma ilimin addini sun fi bashi muhimmanci fiye dana boko, shi yasa suke da makarantar islamiyya da tahfiz. K'arfe 11 na safe aka tashi su Suhaima nan tayi sallama da k'awayen ta ta wuce zuwa gida, don ba 'yan kusa da su a makarantar, saboda sune kusan gidan su na k'arshe k'arshen k'auyen, a nutse take tafiyar ta kanta a sunkuye yake tana tilawar karatun alqur'an a hankali koda kana kusa da ita ba lallai kaji abin da take fad'a ba sai dai kaga le6en ta na motsawa a hankali alamar dai akwai abin da take karantawa. Tayi nisa da tafiyar ta don tayi wajen rabin tafiyar da zata kaita gida, horn taji ana yi mata amman sam batasan da ita ake ba tafiyar ta take kawai abin ta hankalin ta kwance. Bata ankara ba taji mota ta goge ta kad'an a jikin ta har sai da madubin motar na waje ya bige ta a gefen hannun ta, wani irin zafi Suhaima taji a hannun ta da sauri ta d'ago kanta tana kallon motar da ta bige ta zata wuce saboda hanyar bata da kyau sosai akwai 'yan kwazazzabai shi yasa bata sauri, ganin mai motar bashi da alamin tsayawa ya bata hak'uri ko yayi mata sannu ne yasa Suhaima cikin fusata tace "Kan ubancan! lallai mutumin nan baka da mutunci a bige ka ko sannu babu ka wani wuci kamar ka bige dabba ba mutum ba " Ta fad'a da k'arfin ta ranta a 6ace, ganin ba alamar tsayawa yasa ta d'auki wani dutsen wuta a k'asa ta saita glass d'in motar ta jefa da iya k'arfin ta sai dai bai samu glass d'in ba sai fitilar motar ta baya ta samu, aikuwa babu 6ata lokaci ya ba da sautin k'arar fashewa, babu shiri mai driving d'in motar yaja motar ya tsaya. Suhaima kuwa dad'i ne ya kamata da taga hakan taso ma glass d'in ta samu ta fasa tun da bashi da mutunci har da sakin wani murmishin mugunta. Cigaba tayi da tafiyar ta abin ta har ta k'araso inda motar tayi parking amman babu wanda ya fito daga motar gashi glass d'in motar mai duhu ne ba'a ganin na ciki, sai dai na cikin ya gan ka, ita Suhaima ko alamar tsoro babu a tattare da ita ta wuce motar, baifi taku hud'u tayi ba tsakanin ta da motar taji alamar an bud'e kofar motar amman bata jiyo ba saboda bata da ra'ayin ganin wanda ke cikin motar. Cikin fusata na cikin motar ya nufi inda Suhaima take tafiyar ta cikin zafin nama ya sanya hannun shi ya janyo hijab d'in ta na baya, tare da jiyo da Suhaima saitin inda yake ya d'aga hannu zai mare ta cak ya tsayar da hannun shi ya kasa karasar dashi kan fuskar Suhaima kamar yanda yayi niyya, sakamakon had'a ido da yayi da ita duk wani 6acin rai da ya kwaso shi yaji ya tafi a lokaci d'aya. Kallon kyakkyawar face nata yake da eye's nata masu matuk'ar d'aukan hankali, runtse idon ta Suhaima tayi cikin tsoro jikin ta har ya fara 6ari na tsoro don ta zaci mari zata sha, eyelashes d'in ta yabi da kallo yanda suka bi idon suka kwanta kan beautiful face nata. Jin bataji saukar mari ba ya sanya ta bud'e idanun ta a hankali ta sauke su kan fuskar kyakkyawan saurayin da yake gaban ta, ganin yanda ya zuba mata ido yana kallon ta ya sanya ta fincike hijab d'in ta da ya rik'e mata tare da gyara taayuwar ta aka wani rik'e kugu cike da tsiwa tace "Malam lafiya da zaka wani rik'e min hijab? " Sai da ya guy din ya lumshe idanun shi don jin saukar dadad'ar voice d'in Suhaima kafin ya sake bud'e idon nashi yana cigaba da kallon ta tamkar wadda ya samu wata tv yana kallo ko motsin kirki baya yi, sosai abin ya bawa Suhaima mamaki cikin zuciyar ta take cewa shi wannan baya jin tana magana ne ko kurma ne shi? da alamar ma daga birni yake. Cikin tsiwa ta sake cewa "wai malam baka ji ina maka magana ko kai kurma ne? " Ganin again ya kuma share ta sai kallon ta kawai da yake yi ne har da wani hard'e hannaye saman kirjin shi yasa Suhaima juya bayan ta cikin sa'a ta hango wani yaro na kusa da su hannun shi rik'e da robar ruwa a kanshi ya d'auko zai tafi gida. Dad'i ne ya ishi Suhaima har da d'an murmusawa na mugunta don tasan abin da zata yiwa wannan mayen d'an birnin, yaron yana k'arasowa inda suke zai wuce da sauri Suhaima ta sanya hannunta saman kanshi ta d'auke robar ruwan. Kafin yaron ya juyo tuni ta watsawa wannan guy d'in ruwan a jikin shi dukka tare da jefar da robar gefe d'aya, lokaci d'aya drivern da yake tsaye jikin motar da wannan yaron da Suhaima ta d'auki ruwan shi suka d'ora hannu a kansu cikin tashin hankalin da abin da Suhaima ta aikata, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke lokaci d'aya jin wannan ruwan mai shegen sanyi a jikin shi tsikar jikin shine ya tashi kafin ya sanya hannun shi a fuskar shi yana goge ruwan da yake di'gowa daga saman gashin kanshi yana kok'arin bud'e idon shi. Ganin haka ya sanya Suhaima kwasa da gudu ita da yaron har ma yafi Suhaima gudu tamkar shi yayi laifin daman tuni ya mance da wata robar shi don anashi tunanin aka tashi kama da Suhaima har dashi za'a had'a, sai abin ma ya bawa guy d'in dariya sosai ganin yanda suke gudu kallon su yake fuskar shi d'auke da murmishi har sai da ya daina ganin su.... Ku hak'uri da wannan ban da charge wollah, ku biyo ni next chapter don jin abin da zai faru. Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz Ina kike Basmah Er lele wannan shafin naki ne kyauta ina tayaki murnar kammala littafin ki TAURA BIYU Allah ya Kara basirah da k'arfin ido, Allah ya bar zumunci. 👄 PAGE 22-23 Sai da ya daina ganin su tukunna ya dawo da idanun shi jikin shi inda yaga yanda ya jik'e sharkaf da ruwa, wani irin sanyi ne yake ji yana ratsa cikin jikin shi sosai. "Yalla6ai kayi hak'uri don Allah kada ka fad'awa su Alhj da Hajia nasan korata zasu yi, ka rufa min asiri amman sam wannan yarinyar bata kyauta ba " D'an murmishi Sabeer yayi ya bud'e baki zai yi magana atishawa ta taho nan ya fara yin ta sai da ya jira ta sau 4 tukunna ta tsaya, driver sai sannu yake yi mishi gaba d'aya hankali shi a tashe. "Don't worry driver kwantar da hankalin ka mu tafi gida sanyi nake ji " Sai lokacin driver ya d'an ji hankalin shi ya kwanta, da sauri driver ya bud'e mishi kofar mota ya shiga sannan ya rufe tare da komawa driver sit ya zauna tukunna yayi wa motar key suka bar wajen. Sanyi sosai Sabeer yake ji ga atishawar da yake faman yi but still idanun shi nakan hanyar da Suhaima tayi, sosai yake jin wani abu game da yarinyar da ya gani tsiwar ta ta birgeshi yana fatan ya sake sanya ta a cikin idanun shi anan gaba. Har suka kusan k'arasa wa gida Sabeer na tuna abin da ya faru tsakanin shi da Suhaima yana wani murmishi shi kad'ai, abin ba k'aramin mamaki yake bashi ba ganin ta tsaye mishi a rai, gate man yana bud'e gate Sabeer ya hango ilahirin Iyalan Alhj Ahmad d'an fillo sun firfito suna tsaye kallo d'aya mutum zai yiwa Alhj Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa da Alhj Hussien Daddy da Hajia Faridah Mumy a karanto tsantsar tashin hankali saboda sun nemi d'an lele an rasa inda yake kuma ba'a san inda ya tafi ba ga wayar shi a gida ya barta, tuni jikin driver ya fara 6ari na tsoro. A hankali Sabeer ya bud'e motar ya fito ko driven bai tsaya jira ba, suna ganin fitowar shi suka saki ajiyar zuciyar kwanciyar hankali tare da tahowa inda yake hankalin su a tashe ganin jikin shi jagwab da ruwa, cikin rud'ewa Alhj Ahmad d'an fillo ya rik'o kafad'un Sabeer yace "Sabeer wane shege ne ya jik'a ka haka? " D'an murmishi Sabeer yayi kafin yace "Ba damuwar ku bace kada wanda ya sake min wani tambaya ku rabu da ni and then kada wanda yace zai tak'urawa driver ya fad'a mishi " Yana gama fad'in haka ya jiyo zai tafi da sauri Mumy ta rik'o hannun shi tare da cewa "Amman son........ " Bata k'arasa fad'in abin da zata ce ba ya dakatar da ita da hannun shi tare da cewa "Please Mumy " Ya zame hannun shi yayi gaba zuwa part d'in su, gaba d'aya jikin su yayi sanyi sosai kuma hankali ya tashi sosai musamman ganin shi a jik'e kuma yana ta atishawa, suna ganin driver ya wuce ta gaban su bayan ya gama parking motar basu da ikon yi mishi magana saboda kada su 6atawa Sabeer rai. Sabeer yana shiga bedroom d'in shi toilet ya shige wanka yayi da ruwan d'umi tukunna ya fito ya gyara jikin shi tsaf cikin wani 3quater ash colour da T-shirt white mara hannu, fesa different perfumes yayi bayan ya gama ya kwanta tare da lullu6e jikin shi da lallausan blanket, lumshe idanun shi yayi tamkar mai jin bacci amman ba baccin yake tunanin kawai Suhaima yake ya dad'a tuno d'an k'aramin bakin ta tana mishi tsiwa, shi kad'ai yake juyi kan bed yana murmishi, yana tuna yanda ta watsa mishi ruwa ta gudu dakyar bacci ya d'auke shi mai nauyi zuciyar shi fal tunanin yarinyar da suka had'u da ita. Duk wannan abin da yake Mumy na tsaye ta jikin window duk abin da yake tana kallon shi cike da mamakin murmishin da yake, tana tunanin me yake tunani haka yake irin wannan murmishin, ganin ya samu bacci ne yasa ta bar jikin windown zuciyar cike da tunani. ***** ******** ***** Suhaima sai da ta k'arasa kofar gida tukunna ta tsaya da gudun da take, sai da ta daidaita kanta sannan ta shiga gidan da sallama a nutsen ta, kamar ba itace mai gudu yanzu ba, Aunty Aliyah da ke zaune kan kujera tana wankin kaya ta amsawa Suhaima sallamar tana d'ago kanta ta kalle ta tare da cewa "Suhaima sai yanzu kin dad'e yau hala surutun kuka yi aka tsayar da ku " Wata dariya ce ta kubce wa Suhaima ta fara yi har da rik'e ciki da hawaye, cikin mamaki Aunty Aliyah take kallon ta kafin ta kuma cewa "Lafiya Suhaima dariyar me kike haka? " Amman Suhaima ba bakin magana sai da dariyar ta take, sosai Aunty Aliyah ta saki baki da hanci tana kallon Suhaima da ke dariya tamkar wata mahaukaciya har abin ya fara bata tsoro har ta fara tunani ko gamo tayi a hanyar makaranta, dakyar Suhaima ta tsayar dariyar saboda ganin yanda Aunty Aliyah ta fara rawar jiki na tsoro, zama tayi kan saman kayan wankin da Aunty Aliyah ke wankewa tace "Aunty wani abu ne ya faru lokacin da nake tahowa gida shi yasa kika ga ina dariya " Ajiyar zuciya Aunty Aliyah ta sauke ta kwanciyar hankali don sai yanzu taji hankalin ta ya kwanta, kafin ta bud'e baki tace "Me yafaru? " Nan Suhaima ta bata labarin abin da ya faru tsakanin ta guy d'in nan, don Suhaima bata iya 6oyewa Aunty Aliyah abu saboda shak'uwar da suka yi da juna sosai sun zama tamkar wasu k'awaye ko irin Yaya da k'anwar ta, sosai abin ya bawa Aunty Aliyah dariya don har yanda Sabeer yayi Suhaima take kwatanta mata, cikin dariya tace "Allah ya shirya ki Suhaima, yanzu da ace ya kama ki fah ko ya mare ki " "Tabbb da sai na rama Aunty duk da yafi ni tsayi sai nayi tsalle na rama, amman fah Aunty kyakkyawa ne kingan shi tamkar wani balarabe mybe ma baya jin hausa shi yasa yake kallo na " "Uhm Allah dai ya kyauta, amman Suhaima ki daina irin wannan gangancin don kada ki tsokani wani wataran mara hak'uri ya cutar mana da ke " "Toh Aunty na daina insha Allah, har yanzu Yaya bai dawo ba? " "Eh bai dawo ba mybe akwai abin da ya tsayar dashi " "Allah ya dawo dashi lafiya " "Amin " D'an shiru suka yi na 'yan minutes Aunty Aliyah na cigaba da wanki, can tace "Ni kuwa Suhaima ina Jiddah ne kwana biyu shiru? " D'an murmishi tayi tare da cewa "Aunty Jiddah tana nan lafiya, hidimar biki ce ta sanya ta a gaba amman mun yi waya da ita jiya da yamma a wayar Yaya " "Oh haka ne fah sauran kwanaki nawa auren " "Sauran 2 week's fah Aunty gashi na rasa me zan siya mata matsayin gift's " Suhaima ta karasa fad'a cikin yanayin damuwa. "Kada ki damu anjima zamu yi magana yanzu kije ki cire uniform kizo ki karya tukunna" "Toh Aunty " Tashi tayi ta nufi bedroom nata don canja kayan jikin ta, bayan ta canja kaya ne sai kawai ta k'urawa mirror ido tana kallon shi, ta fad'a tunani beautiful guy d'in da ta yi mishi tsiwa d'azu ta d'an jima tana tunanin shi a haka har sai da Aunty Aliyah taji ta shiru ta fara kwalla mata kira tukunna ta sauke ajiyar zuciya ta fito waje tana amsa kiran da take mata... Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz Where are U guys dis page is dedicated to oll My sisters of (Exclusive Writers Forum), i luv U all my sisters i really luv U guys like totally 👄 PAGE 24-25 Bayan kwanaki 2 kamar yau ranar laraba da yammaci wajen 4:30,Suhaima tana zaune a bedroom nata gyaran wardrobe d'in ta take gefe d'aya kuma Aunty Aliyah zaune gefen gadon tana mik'o wa Suhaima kayan da ta linke ita kuma tana jera su a wardrobe sai hirar su suke cikin kwanciyar hankali. "Assalamu Alaikum " Kamar a mafarki Suhaima ta jiyo sallamar Jiddah, aikuwa da sauri ta wullar da kayan hannun ta da Aunty Aliyah ta mik'o mata, da gudu ta fita waje zuwa tsakar gidan cikin farinciki. Jiddah tana tsaye a tsakar gidan sai murmishi take tana rarraba ido don hango ta inda Suhaima zata fito, tana hango fitowar ta a d'aki aikuwa da gudu ta k'arasa inda take suka rungume junan su suna dariya cikin tsantsar farinciki na jin dad'in ganin juna don anjima ba'a had'u ba. Cika junan su suka yi cikin murmishi Suhaima tace "My besty sannun ki da zuwa" Kunshe da marmishi kan face d'in Jiddah tace "Yawwa tawan kwana da yawa " Ta fad'i hakan suna kok'arin k'arasa shiga d'akin Suhaima, cikin fara'a Aunty Aliyah tace "Lale maraba da mutanen birni Jiddah kece tafe yanzu da yamma? " Zama Jiddah tayi akan sallayar da Suhaima ta shimfid'a mata a k'asa ganin kan gadon kaya ne akai, sannan Suhaima ta fita zuwa kitchen don samo wa Jiddah abin motsa baki. "Aunty kam nice tafe yanzu, ina yini? " "Lafiya qlau Jiddah, ya gida da iyayen ki? " "Duk suna nan lafiya Aunty suna gaida ku " (Hmmm Jiddah ta fad'i hakan ne kawai, amman gaskiyar zance iyayen ta basu san wasu su Aunty Aliyah ba, kawai suna jin tana basu labarin Suhaima duk a zaton su friend nata ne na schl, ko zuwa nan gidan nasu da take basu san da zuwan ba). "Muna amsa wa, ya fama da hidimar biki don nasan satin da zamu shiga shine na bikin koh? " Aunty Aliyah ta tambaye ta tana mik'ewa tsaye, cikin d'an jin kunya Jiddah tace "Ehh Aunty haka ne, ina Yaya Aliyu? " "Ya zagaya cikin gona ne amman yanzu zaki ga ya shigo " Har Aunty Aliyah zata fita daga d'akin da sauri Jiddah ta tsayar da ita tare da sanya hannu cikin hang bag nata ta d'auko wani kyakkyawan invitation card guda biyar ta mik'awa Aunty Aliyah tare da cewa "Aunty wannan card d'in d'aurin aure ne na Yaya Aliyu da na Baba Adamu ne " "To shikenan zan bashi idan ya shigo " D'an marairaice fuska Jiddah tayi tare da cewa "Amman Aunty zaku je ai? " D'an murmishi tayi tare da cewa "Me zai hana Jiddah insha Allah zamu je, Allah ya kaimu dai lokacin da rai da lafiya " "Amin Aunty, sannan don Allah ki dad'a tunawa Yaya Aliyu sauran kwanaki 2 d'aurin aure zan zo na tafi da Suhaima " "Zan fad'a mishi Jiddah kuma zai barta insha Allah " 'Yar dariyar farinciki Jiddah tayi tare da cewa "Yawwa Auntyn mu ngde " Daidai lokacin Suhaima ta shigo d'akin hannun ta d'auke da k'aramin tire wanda ta sanya abinci aciki da kuma lemon so6o acikin k'aramin jug na roba sai cup d'in shi k'arami, ajiye wa tayi gaba Jiddah Aunty Aliyah kuma ta fita don ta barsu su yi hirar su. Bud'e plate d'in Jiddah tayi aikuwa ta had'a ido da wani lafiyayyen dambu wanda yasha zogale da gyad'a ga ainahin man k'uli da kuma yajin da aka daka da kayan k'amshi da tafarnuwa, muk'ut Jiddah ta had'iyi yawu saboda tana son dambu sosai, dariya ce ta kubce wa Suhaima ganin yanda Jiddah take had'iyar yawu don kawai taga dambu. Hararar wasa Jiddah tayi mata tare da cewa "Tun da dariya kike min na fasa baki cup cakes d'in da nayi miki Aunty Aliyah da Yaya Aliyu zan bawa " Danne dariyar ta Suhaima tayi tare da rik'o hannun Jiddah tana cewa "Haba tawan just kin ban dariya ne ganin yanda kike had'iyar yawu but na daina" Gid'a kai Jiddah tayi kawai saboda ta cika bakin ta da dambu ba damar tayi magana har wani lumshe ido take saboda dad'in da yayi mata, hannu Suhaima takai kan jug ta zuba mata so6on a cikin cup ta ajiye mata kusa da ita, sannan ta koma wajen wardrobe tana cigaba da gyaran kayan suna d'an hira da Jiddah jefe jefe har ta kammala cin abincin ta taya Suhaima k'arasa gyaran kayan, bayan sun gama suka fita zuwa tsakar gidan inda Aunty Aliyah da Yaya Aliyu suke zaune a saman tabarma shigowar shi kenan babu dad'e wa, nan suka gaisa da Jiddah tare da yi mata fatan alkhairin auren da zatayi tare da 'yar nasiha, sosai Jiddah taji dad'in haka tare da yi mishi godiya duk jikin ta yayi sanyi. Suna nan zaune akayi kiran sallahr mangarib nan Yaya Aliyu yayi alwala ya wuce masjid, yayin da Suhaima, Jiddah da Aunty Aliyah suka yi nasu alwalan tare da gabatar da tasu sallahn. Bayan sun idar ne da sallahr Jiddah tayi wa driver d'in ta waya, babu dad'e wa yayi sallama a kofar gidan Jiddah ta tashi taje inda yake tsaye kofar gida ta kar6i abin da ta buk'aci ya kawo mata wata 'yar bag ce black mai kyau madaidaiciya wadda zata cinye kayan mutum set 5 a ciki. Shigowa gidan tayi tare da ajiye bag d'in gaban Suhaima tace "Besty ga ankon ki fah ki duba ki ga yayi miki " Sakin baki Aunty Aliyah da Suhaima suka yi suna kallon ta cike da mamaki, bayan d'azu da safe Yaya Aliyu yace gobe zai bata kud'in ankon da na gifts d'in da zata siya mata sai gashi kuma Jiddah ta zo mata dasu. Murmishi Jiddah tayi ganin yanda suke kallon ta kafin tace "Aunty wannan kallon fah, ni ku duba kuga yayi? " Ta k'arasa magana cikin shagwa6a ganin sun k'i bud'e bag d'in tamkar masu jin tsoron akwai wani mugun abun aciki, ya sanya Jiddah ta janyo bag d'in kusa da ita ta bud'e, sai ga wasu tsadaddun kaya kala hud'u ta fito dasu masu matuk'ar kyau da tsada, swiss atampha, lace guda biyu da kuma wa wani material Light pink mai haske da abin nad'in kai pink shima amman mai duhu, anyi d'inkin gown ajiki yayi masifar yin kyau, sai shoes and hang bag set d'aya da su watch k'irar gucci na mata da kuma abin hannu, sark'a d'an kunne kai abubuwan kyalakyale sosai Jiddah ta zuba wa Suhaima. Rasa bakin godiya Suhaima da Aunty Aliyah suka yi har sun bud'e baki zasu fara godiya Jiddah ta hana su dole suka hak'ura amman gaskiya Jiddah mutum ce tayi musu hallaci tayi musu abin da baza su ta6a mance wa da ita ba har abada, abun kyautata wa take musu tamkar wasu shak'ik'an 'yan uwanta na jini, babu tsangwama ko kyankyamin su da take duba daga inda ta fito, su kansu sun san Jiddah iyayen ta masu kud'i ne sosai bana wasa ba. A haka Yaya Aliyu ya shigo ya same su sam ya nuna wa Jiddah bai ji dad'in abin da tayi ba da ta bari shi zai bata kud'i taje ta siyowa Suhaima kayayyakin ko nawa ne, nan Jiddah ta nuna mishi ita fah yanda ta d'auki Suhaima tamkar 'yar uwarta ta jini zata iya yi mata komai har idan tana dashi dole yasa Yaya Aliyu hak'ura yayi mata godiya daga k'arshe kuma ta tashi zata tafi har bakin motar su Suhaima da Yaya Aliyu suka rakata suna godiya tana nuna musu batasan godiyar nan, anan Aliyu yayi mata alk'awarin zuwa ta tafi da Suhaima idan ta dawo sosai Jiddah da Suhaima suka ji dad'in hakan, Kafin suyi sallama kuma ta shiga motar driver yaja suka tafi suna masu d'agawa junan su hannu har sai da motar ta k'ule tukunna Yaya Aliyu ya rik'o hannun Suhaima suka wuce gida. ****** ********** ******** Kwance yake saman kujera cikin garden ya zurfafa a cikin tunanin yarinyar da suka had'u, tsawon wajen kwanaki 5 da had'uwar su amman ya kasa manta ta koyaushe cikin tuna beautiful Face nata yake, cikin mafarkin shi da farke yake tunanin yarinyar da baisan sunan ta had'uwar su ta farko da junan su. Shi yasan ba sonta yake ba duk da bai ta6a son wata mace ba, but why ya damu da ita har haka, duk san da ya tuna ta yana jin bugun heart nashi na k'ara k'arfi yana son tunano muryar ta da kyakkyawar surar ta yana son Allah ya k'ara had'a su koda sau d'aya ne ya ganta ya sake jin daddad'ar muryar ta. Sake gyara kwanciyar yayi yana mai lumshe ido hango kyakkyawar face nata yayi lokacin da take mishi tsiwa tare da yanda cute lips nata suke motsawa kamar a lokacin take mishi tsiwar haka yake ji. Ji yake bazai iya jure ba zumbur ya mik'e tsaye tare da nufar side d'in su da saurin shi kamar ba Sabeer ba, yana tashi a wajen Fadilah ta fito daga ma6oyarta ta zauna kan kujerar da ya tashi tana mai shinshina kan kujarer tamkar Sabeer ne zaune a wajen tsabar fitinar ta, d'ago eye's nata tayi wanda suka yi ja cikin wata irin murya tace "I luv U Sabeer, ina maka son da bazan iya zuba ido ka so wata mace a rayuwar ka ba dole nasan ta yanda zanyi na karkato hankalin ka gare ni " Tana gama fad'in haka ta tashi tare da wuce wa side d'in su Sabeer... Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 26-27 Yana k'arasa wa part d'in su bedroom nashi ya shiga yayi wanka tare da shirya cikin wani blue jeans da T-shirt red yayi kyau cikin sauri sauri ya fesa perfumes tare da d'aukan phone's nashi ya fito zuwa parlour. Akan dinning table ya hango Mumy, Daddy da Fadilah suna yin lunch abin su, ganin shi da Mumy tayi yasa ta cewa "Son k'araso kaci abinci " Yana nufar hanyar fita a parlourn yake cewa "Mumy sauri nake zan fita sai na dawo " Kafin wani ya k'ara magana ya fice da sauri, da ido suka raka shi cikin zuciyar Mumy tana mai mamakin abin da ya canja mata yaro lokaci d'aya don da ba haka Sabeer yake mata ba. Yana fitowa harabar gidan ya hango driver da hannu yayi mishi alamar yazo da sauri driver ya k'araso inda Sabeer yake tsaye, key d'in motar dake hannun shi ya mik'a mishi hannu ya sanya ya kar6a tare da nufar inda motar take ya shiga key yayi mata tare da jan ta zuwa gaban Sabeer, kafin driver ya fito ya bud'e mishi k'ofa tuni Sabeer ya shiga cikin motar, don haka kawai driver tuk'i ya fara gate man ya bud'e musu gate suka fita. "Yalla6ai ina zamu je? " Driver ya tambaya, ba tare da Sabeer ya kalli inda yake ba yace "D'an k'auyen nan da muka je zaka mayar da ni " "Toh Yalla6ai " Driver ya fad'a cikin mamakin mai Sabeer zai je yayi a wannan k'auyen kuma, gashi babu fuskar tambaya sai kawai yaja bakin shi yayi shiru ya mayar da hankalin shi kan tuk'in da yake. Bayan sun isa k'auyen ne inda Sabeer ya had'u da Suhaima nan driver yayi parking a wurin, fitowa Sabeer yayi daga motar yana faman kalle kallen wajen da kuma hanyar da Suhaima tabi ranar ko zai ganta, amman har ya gama wurwurga idanun shi baiga ko mai kama da Suahima ko wannan yaron, gajiya yayi da tsayuwa ya shige mota ya zauna but still eyes nashi na jikin window yana kallon waje, driver dai kawai ido ne nashi. Tun rana wajen k'arfe 2 suke wajen har yammaci wajen 5 na yammaci Sabeer bai ga mai kama da Suhaima ba, sosai abun ya dame shi ya rasa yanda zai yi yana son sake ganin yarinyar ne, sallahr la'asar anan suka yi ta cin abinci ne babu batun yin shi, Sabeer ko yunwar baya ji ma rabon shi da abinci tun breakfast na safe driver kuwa daurewa kawai yake don kuwa yunwa ce take kwakwalar 'ya'yan cikin shi, yana tunanin abin da ya tsayar dasu anan waje tsaya wajen awa 4, addu'a yake cikin zuciyar shi Allaj yasa Sabeer yace su tafi gida. "Driver mu tafi gida " Abin da Ado driver ya ji kenan wani sanyi dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar shi ko ba komai yasan nan ba da dad'e wa ba zai samu abinci ya ci, key yayi motar suka bar wajen amman idanun Sabeer akan hanyar da Suhaima ta wuce da gudu gaba d'aya wata damuwa ce cikin zuciyar shi, jinshi yake wani iri daban yaso sake ganin beautiful face nata a yau, haka suka k'arasa gida jiki ba k'arfi Sabeer ya shige bedroom nashi ya kwanta kan bed zuciyar shi cike da tunani kala kala duk akan Suhaima. **** ****** ******* Aunty Aliyah ce durk'urshe a bakin makwarara tana faman kelaya amai sosai hannun ta dafe da da cikin ta d'ayan kuma dafe da k'asa, Suhaima da Yaya Aliyu sai sannu suke mata tamkar zasu yi kuka yanda fuskokin su ya nuna musamman ma Suhaima ganin yanda take shan wahala, sai da ta gama aman tsaf Yaya Aliyu ya wanke mata bakin ta tare da kamata suka wuce rumfar ya zaunar da ita kan tabarma, yayin da Suhaima kuma take gyara wajen da aka 6ata. "Sannu Aliyah bari na fito da machine mu tafi asibiti tun jiya da yamma kike aman nan gashi har gari ya waye kina yi duk abin da kika ci sai ya fito koda ruwa ne ya kamata mu je kiga likita " Yaya Aliyu ya fad'i hakan yana mik'a mata hijab d'in ta, bata yi musu ba ta sanya hannu ta kar6a tare da sanya wa, daidai lokacin Suhaima ta gama gyaran wajen ta k'araso rumfar, kallon ta Aliyu yayi tare da cewa "Ki tafi gidan Babaa Lantana ki zauna zamu je asibiti ne " Fuskar Suhaima d'auke da tsantsar damuwa tace "Toh Yaya Allah ya dawo daku lafiya, Aunty Aliyah sannu Allah ya baki lafiya " "Amin ya rabbi " Cewar Aliyu don Aliyah bata iya magana saboda jin jikin da take yi, d'aki Suhaima ta shiga ta d'auko hijab d'in ta sannan ta fito hannu Aliyah ta rik'e suka fito zuwa kofar gida, inda Yaya Aliyu ya fito da machine d'in, sai da ya kulle gidan tukunna ya hau machine d'in dakyar Aliyah ta iya hawa saboda rashin jin dad'in jikin ta, sai da Suhaima ta ga tafiyar su sannna ta k'arasa gidan Babaa Lantana. Da sallama ta shiga gidan Babaa Lantana da take wajen marhu tana soya gyad'a ta siyar wa ta amsawa Suhaima sallamar tana cewa "Tabbb yau wa nake gani a gidan nan ba dai Suhaima ba?" Ta fad'a cikin sigar wasa, d'an murmusawa Suhaima tayi tare da cewa "Ni ce nan Babaa Lantana ina d'an tsohon ki? " Suhaima ta k'arasa fad'i tana zama kusa da Babaa Lantana. "D'an tsoho ya fita can gidan mai unguwa zasu tattauna matsalalon mu na garin nan musamman akan al'amarin matasa" "Yayi kyau hakan " Cewar Suhaima kenan "Lafiya dai kike koh? " Cewar Babaa Lantana tana sauke kaskon suyar gyadar, kallon ta Suhaima tayi tare da cewa "Me kika gani? " "Ganin ki nayi kamar fuskar ki da damuwa ne " "Uhm Babaa Aunty Aliyah ce bata da lafiya yanzu haka sun tafi asibiti da Yaya " Da sauri Babaa Lantana tace "Me yasame ta? " "Tun jiya take kwara amai har yau bai tsaya ba ko ruwa tasha sai ya dawo duk ta rame " D'an shiru Babaa Lantana tayi kafin kuma ta saki murmishi akan fuskar ta daman tayi hasashen haka don taga alamomi sosai a jikin d'iyar ta ta magana ce bata yi ba. Kallon mamaki Suhaima take yiwa Babaa Lantana ganin tana murmishi kamar wadda tayi mata wani babban albishir ba lalura ta fad'a mata ba kasa hak'ura tayi Babaa Lantana tayi magana tace "Wai Babaa lafiyar ki kalau ina fad'a miki rashin lafiyar Aunty kina murmishi? " "Uhm Suhaima ai abin farinciki ne ya samu shi yasa kika ga ina murmishi " Cikin rashin fahimta Suhaima tace "Rashin lafiyar Auntyn ne abin farinciki? " 'Yar dariya Babaa Lantana tayi tare da cewa "Matsala ta da ke Suhaima rashin gane wa ina nufin Auntyn ki ciki ne da ita wannan lalurar da take yi ta laulayin ciki ne kin fahimta? " Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Suhaima daman burin Aunty Aliyah ta samu ciki ta haihu kusan kullum sai ta fad'a wa Suhaima ta taya ta da addu'a Allah ya bata 'ya'ya, sai gashi Allah maji rik'on bawan shi ya bata, lallai yau Aunty Aliyah da Yaya Aliyu akwai murna an samu abin da ake so, amman duk da haka sai da Suhaima tace "Da gaske kike Babaa? " "Insha Allahu kuwa Suhaima " Washe baki Suhaima tayi tana mai jin dad'i farinciki fal cikin zuciyar ta tana jiran dawowar su Yaya Aliyu. Suna nan zaune Suhaima na taya Babaa Lantana d'aurin gyad'ar a leda suka ji tsayuwar machine d'in Aliyu a kofar gida, da gudu Suhaima ta fita har tana wancakali da faratin gyad'ar ya watsowa Babaa Lantana a fuska amman Suhaima bata tsaya ba tayi waje da gudu. "Oh ni 'yasu Allah ya shiryi Suhaima ji yanda ta zubar min da gyadar nan " Cewar Babaa Lantana tana tsince gyadar da ta zube a k'asa. Suhaima tana fitowa kofar gida ta hango su har ma Yaya Aliyu ya bud'e gidan sun shiga, da sauri Suhaima ta k'arasa gidan ta shiga kallon fuskar Yaya Aliyu tayi taga sai washe baki yake haka ma Aunty Aliyah duk da kuwa jin jikin da take hakan bazai sa mutum ya kasa fahimtar farincikin dake shimfid'e a fuskar ta ba, nan Suhaima ta tabbatar da ciki ne dai da ita zancen Babaa Lantana ya zama gaskiya. "Albishirin ki " Cewar Yaya Aliyu yana kamo hannun Suhaima, cikin murmishi tace "Goro fari tas Yaya " 'Yar dariya yayi kafin yace "Auntyn ki ciki ne da ita zata haifar miki d'a " Wani tsalle Suhaima ta daka ta rungume Yaya Aliyu tana dariya kafin ta cika shi ta rungume Aunty Aliyah tana cewa "Wayyo dad'i Allah mun gode maka " Hannun Yaya Aliyu ta rik'o dana Aunty Aliyah tace "Yaya Aunty na taya ku murna sosai Allah ya fito mana dashi lafiya " "Amin Thumma Amin " Suka fad'i fuskar su k'unshe da murmishin farinciki, ana haka Babaa Lantana ma ta shigo ita da Baba Adamu don dawowar shi kenan Babaa Lantana take sanar mishi shine suka taho duba jikin Aliyah. Anan Baba Adamu yaji abin farinciki daman Babaa Lantana ta hasaso hakan, nan suka taya juna murnar samun k'aruwar da zasu samu kafin daga baya su yi musu sallama su tafi...... Aishat A Muh'd 🏌🏻‍♀ 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 28-29 Tun daga lokacin ya kasance Aunty Aliyah bata da ishashshiyar lafiya a jikin ta yau lafiya gobe ciwo, duk ta rame sosai saboda laulayin da ya sanya ta a gaba, aiyukan gidan kuwa Suhaima ce mai yin su don Aliyah bata iya komai sai kwanciya saboda rashin k'arfin jikin ta dakyar take iya tashi zaune, ga baccin da take sosai abinci ma ba kowanne take iya ci ba ba k'aramin walaha take sha ba. Da haka aka cinye kwanaki biyar Aunty Aliyah tana fama da azababben laulayi, ya rage sauran kwanaki biyu a fara bikin Jiddah kuma ayau ne ranar da Jiddah ta fad'a zata zo ta dauk'i Suhaima su tafi gidan su don fara hidimar biki, gashi Aunty Aliyah ba lafiya Suhaima ma ta fitar da ran zuwa bikin Jiddah saboda ganin yanda jikin Aunty Aliyah yak'i sauk'i duk hidiman gidan ita kad'ai ce mai yi don ma wani lokacin Babaa Lantana na zuwa taya ta 'yan ayyuka. Wajen k'arfe biyun ranar laraba Jiddah ta zo lokacin Suhaima ta kammala girkin rana tana share gidan taji da sallamar ta aikuwa yar da tsintsiyar hannun tayi da gudu ta k'arasa inda take suka rungume junan su cikim tsananin jin dad'i. "Amarya kinsha k'amshi sai wani kyalli kike tun kafin a fara jin amarcin " Cewar Suhaima cikin murya k'asa k'asa tana dariya, dukan wasa Jiddah ta kawo hannu zata yi mata da sauri Suhaima ta goce suna dariya. "Allah Suhaima kin fara zama mara kunya, zan fad'a wa Yaya Aliyu yayi miki aure ke ma " Rik'e bakin ta Suhaima tayi da hannun ta d'aya kafin tace "Wooh rufa min asiri ni har yanzu yarinya ce da saura " Hararar wasa Jiddah tayi mata tare da cewa "Uhm a hakan kike yarinya ai kuwa ki zuba ido ina aure zan ziga Yaya Aliyu yayi miki ke ma nace ke kika fad'a min na fad'a mishi aure kike so kina jin kunyar sanar dashi shi yasa kika aiko ni " Jiddah ta k'arasa magana tana dariyar mugunta, kwa6e fuska Suhaima tayi tare da cewa "Wayyo Allah nah Jiddah ki rufa min asiri, waiii idan Yaya yaji hakan ina tunanin 6a66ala ni zai yi " "6a66alawar lafiya, ai ba wani mugun abu kika yi " "Besty albishirin? " "Goro fari tas mai ya faru k'awata? " "Aunty Aliyah tana da ciki taawon 3 month's " Wani uban tsallen murna Jiddah ta doka tare da rungume Suhaima tana cewa "Da gaske kike Suhaima don Allah? " Cikin tabbatar wa Suhaima tace "Da gaske ne wlh Jiddah, sai dai yana bata wahala baki ga yanda ta koma ba duk ta rame ko abincin kirki bata iya ci " Suhaima ta k'arasa maganar cikin yanayim damuwa, nan take Jiddah ita ma fuskarta ta koma kalar damuwa, hannun Suhaima ta rik'o suka nufi d'akin Aunty Aliyah tana cewa "Kada ki damu Suhaima Aunty Aliyah zata samu lafiya, kinsan wani cikin yana bawa mace wahala sosai kafin ya girma, da zarar ya girma insha Allah zata samu sauk'i addu'a zamu cigaba da yi mata " Gid'a kai Suhaima tayi kawai a lokacin suka k'araso kofar d'akin Aunty Aliyah sallama suka yi mata, dakyar ta iya amsa musu sallamr k'asa k'asa cikin irin sanyin muryar mara lafiyar nan wanda yake jin jiki sosai, d'aga labulen d'akin suka yi tare da shiga ciki tana kwance a falo saman sallaya da hijab a jikin ta alamar yanzu ta idar da sallahr azahar. Zama suka yi kusa da ita sosai Jiddah hankalin ta ya tashi ganin yanda Aunty Aliyah ta koma wata iri duk ta rame sosai ta fita a hayyacin ta tamkar ba ita ba. "Sannu Aunty Aliyah Allah ya baki lafiya " Cewar Jiddah kenan, murmishin yak'e Aunty Aliyah tayi tare da cewa "Yawwa Jiddah, Amin " Dakyar take maganar tana jan numfashi irin wanda yake idan mutum yana jin ciwo sosai idan yayi magana yake yi. "An kaita hospital kuwa Suhaima? " Jiddah ta tambayi Suhaima tana kallon ta. "Eh Yaya ya kaita amman magani suka bata " "Wanne hospital ne wannan da ko drip baza su sanya mata, jiki babu kwari ga ba cin abinci, yanzu da sun sanya mata drip zata ji k'arfin jikin ta " Tana gama fad'in haka ta ciro wayar ta dialing d'in digit na Yaya Aliyu tayi bayan sun gaisa ta fad'a mishi tazo tana son ganin shi, babu dad'e wa sai ga Yaya Aliyu ya shigo bayan sun dad'a gaisawa ne tace "Yaya Aliyu don Allah ina son kayi min alfarma mu kai Aunty Aliyah hospital d'in da muke zuwa, ba don na raina kulawar da kake bata ina son zan kaita inda zasu duba ta sosai " Girgiza kai Yaya Aliyu yayi tare da cewa "Baza'a yi haka ba Jiddah wahalar zata yi yawa, ki fad'a min sunan hospital d'in gobe zan kaita da kaina a duba ta " "Don Allah Yaya ka daure mu je na roke ka " Nan Jiddah tayi ta rok'an shi dakyar daga k'arshe ya amince don har Jiddah ta fitar da ran zai barsu, nan da nan suka shirya tafiya hospital a motar da Jiddah tazo, Yaya Aliyu da driver a gaba Jiddah, Suhaima da Aunty Aliyah a baya su bayan sun yiwa Babaa Lantana sallama, sai addu'ar fatan alkhairi Babaa Lantana take yiwa Jiddah. Wani had'add'en private hospital wanda Jiddah da families d'in ta suke zuwa nan ta sanya driver ya kaisu, babu 6ata lokaci aka kar6i Aunty Aliyah saboda sunsan wace Jiddah, nan aka shigar da Aunty Aliyah special room ita d'aya sai doctor da kuma nurse guda biyu. Sun d'auki tsawon lokacin suna checking nata kafin daga k'arshe su sanya mata drip tare da yi mata injection na bacci kafin su fito a room bacci mai nauyi ya d'auke ta. Bayan sun fito ne likita ya buk'aci ganin su cikin office d'in sa bayan sun shiga sun zauna ne, sai da yayi rubutu cikin file sannan ya fara cewa "Ciki ne da ita na tsayin 3 months so kunsan kowacce mace da irin halittar ta na laulayi ciki kafin yayi kwari, shine yake bata wahala baya ga wannan babu wani abu babba sai malaria, zamu yi iya kok'arin mu na ganin koda cikin kashi biyar ne ta samu saukin kashi uku sauran kuwa sai a hankali don haka mun bata gado zamu rik'e ta har zuwa gobe insh Allah " "Okaya doctor thank U very much, yanzu zamu iya ganin ta? "Why not sai dai ban da hayaniya please and kuma ga maganin da za'a yi amfani dashi na rubuta ana buk'atar shi da wuri don tana tashi zata sha " "Okay doctor ba damuwa" Nan doctor ya bawa Aliyu suka yi musabiha tare da cewa "Allah ya bata lafiya ya kuma raba su lafiya congrats Yalla6ai " "Amin nagode likita " Sam doctor yayi tuanin cousins d'in Jiddah ne ganin su suma kyawawa dasu tamkar family d'in su Jiddah shi yasa bai kawo komai a ranshi ba, sai dai yanayin su da ya nuna basu da kud'i kamar su Jiddah. Bayan sun shiga room d'in da aka kwantar da Aunty Aliyah ne suka zauna shiru kowa da nashi tunani ta 6angaren Aliyu yana tunanin da kunya ya iya kallon idon Jiddah yace bazai bar Suhaima ta tafi bikin ta ba ganin irin d'umbin hallacin da tayi musu bai kamata ya hana Suhaima zuwa ba, gashi kuma Aliyah na buk'atar kulawa sosai gashi idan suka koma gida gobe Suhaima ce k'arfin ayyukan gidan idan ya barta ta tafi ya zasu yi?... Kuyi hak'uri da wannan fan's sai gobe kuma insha Allah. Aishat A Muh'd 🏌🏻‍♀ 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz This page is for U my Ramlat ar manga (Real mai dambu 🥗) thanks for luv nd everything Allah ya bar zumunci ya raya zuri'a, ina matukar alfahari dake wannan shafin naki ne kyauta 👄 PAGE 30-31 Tashi Jiddah tayi tsaye tare da d'aukan bag d'in ta gida take son tafiya saboda yau ne ranar kamu sai faman kiran ta ake a waya ana tambayar ta inda take, kallon ta Aliyu da Suhaima suka yi, ita ma kallon su tayi tare da cewa "Yaya Aliyu zan tafi gida ana nema na, zan dawo gobe da safe na mayar da ku gida Allah ya bawa Aunty Aliyah lafiya " Kallon ta Aliyu yake gaba d'aya ya rasa ma mai zai ce mata dakyar ya iya bud'e bakin shi yace "Amin Jiddah nagode sosai da karamcin ki gare mu, nasan kina son tafiya da Suhaima koh? " D'an murmishi tayi tare da cewa "Haba Yaya Aliyu taya zan tafi da ita bayan itace ke kula da Aunty babu komai wlh nasan lalura ce taja hakan " Girgiza Aliyu yayi kafin yace "Idan lokaci bai k'ure ba ki d'auki Suhaima kuje gida ta d'ebi kayan da zata yi amfani dasu, sai ku taho da Babaa Lantana ta zauna da mu anan zuwa gobe " Duk da Jiddah taji dad'in abin da Aliyu yace mata amman sai da ta sake cewa "Ka barshi Yaya yanzu babu lokaci sauri nake sai kirana ake lokacin kamu yayi amman insha Allah gobe zan dawo sai mu tafi tare " "Shikenan Jiddah Allah ya biya ki, Allah ya sanya alkhairi " "Amin Yaya, amman godiyar ta isa haka " Murmishi suka yiwa junan su kafin Suhaima da Aliyu su tashi rakiyar Jiddah har zuwa compound d'in hospital d'in suka sake yin sallama kafin ta shiga mota driver yaja motar su tafi, Aliyu da Suhaima suka dawo cikin room d'in da aka kwantar da Aunty Aliyah har yanzu dai bacci take bata farka ba zama suka yi jigum jigum, sai jefi jefi suke d'an ta6a hira sannan nurses suna shigowa duba Aliyah, da dare sai da Jiddah ta aiko driven da suka zo tare da takeaway na abinci sai kayan tea acikin leda bak'a 'yar babba, sosai Aliyu da Suhaima suka ji dad'in haka daman a lokacin yake tunanin fita neman masu abin da zasu ci sai gashi, nan Aliyu ya sake jinjina k'aunar da Jiddah take yiwa Suhaima dasu kansu basu da abin da zasu biyata abin da tayi musu sai dai addu'ar fatan alkhairi. Washe gari da safe Aliyah ta tashi jikin ta da sauk'i sosai ta samu k'arfin jikin ta, tana cin abinci sai dai wani ya zauna wani ya fito amman sosai sun ga sauk'i fiye da lokacin da suka zo jiya tun da tana tashi da kanta ba tare da an taimaka mata ba. Ganin haka ya sanya likita basu sallama tare da rubuta mata maganin da zata nayin amfani dashi, sannan ya fad'a musu idan taji wani canjin yanayi a jikinta ta dawo hospital d'in tun da file Jiddah ta sanya aka bud'e mata. K'arfe 11:25 na safe sai ga Jiddah ta shigo room d'in sosai taji dad'in ganin Aunty Aliyah jikin da sauk'i, bayan an gaisa kuma suka fito daga cikin asibitin zuwa inda motar da Jiddah tazo da ita, yau babu driver ita d'aya tazo da kanta tayi driving, bayan sun shiga motar ne suka d'auki hanyar zuwa k'auyen nasu. Bayan sun isa gida ne a gurguje Suhaima ta gyara gidan tsaf tana kok'arin d'ora girki Babaa Lantana ta shigo gidan ta kar6in aikin tare da ce mata ta shirya su tafi, aikuwa nan ta shiga wanka bayan ta fito ne ta shirya jikin ta a lokacin Jiddah har ta gama had'a mata kaya a cikin bag d'in da ta bata suka fito zuwa tsakar gidan. Inda Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suke zaune zama suka yi suma a k'asan tabarmar da suke kai, nasiha sosai mai ratsa jiki Yaya Aliyu yayi wa Jiddah na irin rayuwar da zata shiga nan da kwana d'aya, haka Babaa Lantana ma tayi mata nasiha sosai Aunty Aliyah ce babu k'arfin yin magana sai murmishi da take mata cikin zuciyar ta tana mata addu'a. Daga k'arshe Jiddah ta fito daga gidan da bag d'in Suhaima a hannun ta, saboda taga alamar kamar akwai abin da suke son fad'a wa Suhaima, aikuwa tana fita Yaya Aliyu da Babaa Lantana suka yi mata nasiha na ta tsare mutunci kanta ban da kula samari da rawar kai komai ta gani ta kawar da kai tana yin alkunya kodan saboda Jiddah sannan Yaya Aliyu daga k'arshe ya gargad'i ta da babbar murya kada tayi shiga matsatstsiya na sutura, ta suturce jikin ta matsayin ta na 'ya mace. Bayan sun gama mata nasihar ne Yaya Aliyu ya bawa Suhaima kud'i masu dama sannan yace "Wannan kud'in ki nemi abin da zaki siyawa Jiddah gift's dashi ki rage wasu kuma don ki rik'e a hannun ki " Aunty Aliyah cikin muryar marasa lafiya tayi wa Suhaima magana da ta shiga d'akin ta ta d'auko mata wani box cikin drower d'in gadon ta, nan Suhaima taje ta d'auko ta mik'a mata kar6a tayi ta bud'e sai ga wata sark'a, d'an kunne, zobe da warwaro guda uku sai sark'ar k'afa masu kyau sai kyalli suke da d'aukan ido farare ne. "Ki bawa Jiddah kice mata ba yawa tayi hak'uri " Cewar Aunty Aliyah kenan cikin sanyin murya, rik'e hannun ta Suhaima tayi tana murmishi tace "Toh Aunty zan bata insha Allah " Daga haka Suhaima ta tashi haka ma Yaya Aliyu suka fito zuwa nan kofar gida inda Jiddah take zaune cikin mota, shiga seat d'in gaba Suhaima tayi tare da rufe k'ofa, nan Jiddah tayi wa motar key suka fara tafiya sannan Yaya Aliyu ya buga machine d'in shi yana binsu a baya don ganin gidan su Jiddah saboda zuwa d'auko Suhaima. "Malama da haka zamu tafi kina min hawaye salon ace na sato ki " Fad'in Jiddah cikin sigar tsokana, "Kewar gida na fara yi Jiddah tun da nake ban ta6a zuwa wani wajen kwana ba sai yau" Cewar Suhaima tana kwantar da kanta a jikin kujera. "Lallai da drama duk lokacin da kika yi aure za'a kai ki gidan miji kenan, tun da shi fatan zama na har abada ake " D'an zaro ido Suhaima tayi tare da cewa "Tabbb ni fah auren ma baya gaba na Jiddah, har yanzu ban ta6a tsayawa da wani ba da sunan zance ba " "Lallai yarinya da sauran ki kina tunanin Yaya Aliyu zasu zuba miki ido babu aure? " D'an marairaice fuska Suhaima tayi tana cewa "Ni fah da za'a bi tason ra'ayi na karatu zan cigaba da yi wlh tun da gaba d'aya ni yarinya ce nawa na ke " Hararar wasa Jiddah tayi wa Suhaima kafin tace "Ai yanzu tsab za'a yi miki aure ki zauna akwai wad'anda basu kai ki ba ake musu su zauna lafiya ma " D'an shiru suka yi na 'yan minute's kafin Jiddah tace "Ni kuwa Suhaima wane irin Namiji kike son aura i mean halayyar shi, yanayin shi and everything da kike son mijin ki ya kasance? " Shiru Suhaima tayi na tunani kafin ta sauke ajiyar numfashi tace "Ni a tsarin rayuwa ta bana son auren miji mai kudi da yawa nafi son auren talaka dai dai ni wanda bazai wulak'anta ni ba da 'yan uwana ba ko dangin shi su na wulakanta mu ba, kuma bana son auren miji mai irin kyan nan da yawa ina da kishi wallahi bazan iya jure ganin 'yammata suna kai mishi farmaki ba, sannan bana son mai saurin fushi,ina son kuma mijina ya kasance mai ilimi both side addini da boko kuma...... " "Kaiii Suhaima idan kuma Allah ya baki handsome mai kyau da kudi fah, kamar yanda kike da kyau ke ma? " "Hmmm bana fatan haka Jiddah na fison talaka d'an uwana, ni koda misali wani mai kud'in zaice yana sona bazan amince mishi ba wulak'anci zan tayi mishi har ya hak'ura ya bar ni, nasan ma bazai jure wulakanci ba zai rabu da ni " Dariya sosai Jiddah tayi kafin tace "Koda wanda kika watsa mishi ruwa ne idan ya dawo yace yana son ki fah ya zaki yi? " "Tabbb ai korar shi zanyi balle nasan bazan sake ganin shi ba har abada ma" Cikin zolaya Jiddah tace "Kika sani ko shine mijin naki Allah ya kawo miki " Dukan wasa Suhaima ta kaiwa Jiddah da sauri ta goce tana dariya tare da cewa "Haba Besty daga wasa sai duka kin mance ni amarya ce zan had'a ki da my sweet darling fah" D'an murmishi Suhaima tayi kawai ta d'auki phone d'in Jiddah tana kallon pic's d'in ciki, da haka har suka k'arasa gidan su Jiddah amman daga waje tayi parking bata shiga cikin gidan ba, Wow! abin da Suhaima tace kenan ganin irin unguwar su Jiddah ta manyan masu kud'i ce ganin gidan su Jiddah kuwa sai da gaban Suhaima da na Yaya Aliyu ya fad'i. Anya basu yi gangancin sake wa da Jiddah ba irin wannan k'aton gidan daga ni Iyayen ta ba k'aramin masu kud'i bane, lokaci d'aya jikin su yayi sanyi sosai, nan Jiddah ta k'arasa wajen Yaya Aliyu suka yi sallama bayan ta tabbatar mishi da jibi da yamma yazo d'aukan Suhaima idan yazo ya kirawo ta a waya daga haka suka yi sallama ya buga machine d'in shi ya tafi jiki a sanyaye yana dana sanin sakewa da Jiddah da suka yi har haka, kada a wulak'anta mishi k'anwa ko kuma su bud'e mata ido da rayuwa amman da ya tuna irin tarbiyyar Jiddah sai ya d'an ji sanyi cikin zuciyar shi but still jikin shi a sanyay dakyar yake tuk'a machine d'in yana addu'a cikin zuciyar shi Allah ya tsare mishi Suhaima har taje ta dawo lafiya... Aishat A Muh'd ✍🏻 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz Dis page is dedicated to Ayusher Ilias my Namecy Biebie dee tawa My Zeee yabour Asy khaleel, kirkin ku daban ne ina yin ku sosai sister's Allah ya bar zumunci a tsakanin mu ❣ PAGE 32-33 Bayan tafiyar Yaya Aliyu ne Jiddah ta shigo motar tayi mata key maimakon su shiga gidan sai Suhaima taga ta juya sun bar unguwar gaba d'aya, cikin tsokana Jiddah tace "Baki ji tsoro ba kada na siyar da ke naga baki tambaye mu ina zamu je ba " D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa "Na yarda da ke ne sosai Jiddah nasan son da kike min bazai sa ki cutar da ni ba " "Haka ne tawan Allah ya bar mu tare har 'ya'ya da jikoki, waiii ya kaga Suhaima da jikoki suna cewa goggo Suhaima " Dariya kawai suka yi adaidai lokacin Jiddah ta k'araso inda zasu je wani katafaren shagon yin gyaran jiki, saloon, manicure and pedicure da kuma make-up sai lalle, parking Jiddah ta samu tayi suka fito zuwa cikin shagon sosai wajen ya burge Suhaima, matar wajen tana ganin Jiddah ta fara washe baki da alama ta saba zuwa wajen. Babu 6ata lokaci Jiddah ta fad'a wa matar abin da za'a yi wa Suhaima, aikuwa nan suka shigar da Suhaima wani room suka farayi mata gyaran jiki na dilka sosai suka tsaya suka gyara Suhaima sun san zasu samu kudi masu tsoka, bayan an gama gyaran jikin aka yi mata gyaran su farce sannan aka dawo kan lalle daga k'arshe kuma aka gyara mata gashi wanda basu sanya mata relaxer ba cos gashin Suhaima yana da tsantsi irin na asalin fulani sai suka wanke mata kan da kalolin shampoos and conditioner different color's, sannan suka busar mata da dogon gashin ta da hand dryer tukunna suka gyara mata in style. Kyan da Suhaima tayi 6ata lokaci ne wajen fad'ar shi tayi kyau sosai tamkar ba ita ba, har wasu kayan Jiddah ta bata ta sanya wata milk d'in gown mai adon light green sai veil light green shima nan ta sanya kayan aka yi mata light make up sosai tayi kyau, rolling d'in veil d'in suka yi mata akanta ba k'aramin had'uwa tayi ba idan kaga Suhaima ka d'auka irin mai kud'in nan ce ba daga k'auye ta fito ba. Ita kanta Jiddah bata zata haka Suhaima take ba sai yanzu hankalin ta ya kwanta tasan dai ba lalle iyayen ta su gane daga inda Suhaima ta fito ba, kuma ba laifi kan Suhaima a waye yake bata da dahun kai, nan Jiddah ta biya kud'in suka fito daga shagon kai tsaye gida suka nufa. Horn Jiddah tayi gateman ya bud'e mata kofa ta shigo ciki a parking lot tayi parking tukunna suka fito daga motar, sakin baki da hanci Suhaima tayi ganin irin girman gidan su Jiddah gashi part part ne sosai gidan ya birge Suhaima amman bata kuma aha'awar zaman irin cikin gidan nan don tasan dole a samu masu wulak'anta mutane, ta6o ta Jiddah tayi tana murmishi tace "Alhamdulillah yau Allah ya nufa Suhaima zata zo gidan mu, ina cikin farinciki yau sosai, Suhaima ga gidan mu nan kina ciki yau anan aka haife ni na girma, daman na fad'a miki gidan mu muna da yawa don kakan mu da iyayen mu duk a ciki muke zaune " Gid'a kai Suhaima tayi tana k'ak'alo murmishin yak'e kafin tace "Masha Allah wannan gidan naku yayi kyau sosai Jiddah " Kamo hannun Suhaima tayi tare da cewa "Thank U my dear " D'auko bag d'in Suhaima tayi suka nufi wani part, duk taku d'aya da Suhaima take sai gabanta ya fad'i sosai gaba d'aya a tsorace take kamar wadda za'a sace haka take jin ta. Suna shiga cikin k'aton parlourn wani sanyin Ac da k'amshin turare ya bugi hancin Suhaima ko'ina tsab dashi duk da mutanen da suke zazzaune cikin parlourn kuwa, kusan gaba d'aya mutanen kallon Jiddah da Suhaima suke. Tuni Suhaima ta fara tsarguwa da kallon, wata matashiyar budurwa ce kamar sa'ar Jiddah ta taso da gudu ta rungume Jiddah tana cewa "Ga amarya ga amarya nan ta dawo, ina kika shige muna ta neman ki? " D'an murmishi Jiddah tayi tare da cewa "Na d'an fita ne wani wajen " Kallon budurwar tayi tare da cewa "Zahra meet my friend Suhaima Omar, Suhaima meet my sister Zahra 'yar gidan K'anin Abban mu ce " Cikin murmishi Suhaima tace "Ina yini? " Wani banzan kallo da Zahra tayi wa Suhaima sai da ta kusan zubewa a k'asa saboda rawar da jikin ta ya fara, wani banzan tsaki Zahra ta saki tare da hararar Jiddah tace "Kefa tsiyata kwashe kwashe ne dake ina kuma kika samo wannan villagers girl d'in? " Dumm gaban Suhaima da Jiddah ya fad'i, duk gyaran da ta kashe kudi tayiwa Suhaima don kada su gane daga inda ta fito sai da Zahra ta gane, wannan maganar a cikin zuciyar ta Jiddah tayi bayan ta gama k'arewa Suhaima kallo inda taga ita bata hango makusa ba sai ma kyan da Suhaima tayi, amman sai ta dake ta harari Zahra tare da cewa "Ni fah bana son iskanci Zahra wannan fa friend d'ina ce tare muka yi schl itace fa Suhaiman da nake baku labari" Wata shegiyar dariya Zahra ta saki tare da nuna Suhaima da d'an yatsa tace "Dis villagers girl ce kuka yi schl tare kin ma raina min hankali nafa sanki da kwashe kwashe " Haushi ne ya turnik'e Jiddah a fusace taja hannun Suhaima wanda idanun ta sun ciko da kwalla taf suka nufi hanyar da zata kai Jiddah part d'in Umman ta yayin da Zahra da sauran mutane wanda suka karkata hankalin su da jin hirar tasu tuntsire wa da wata irin dariyar ta rainin hankali. Wani parlour suka dad'a shiga tsayawa Jiddah tayi tare da jiyowa ta kalli Suhaima tace "Don Allah Suhaima kiyi hak'uri da abin da Zahra tayi miki bata kirki ne " Mayar da kwallar Suhaima tayi tare da kwakwalo murmishi yak'e tace "Kada ki damu Jiddah duk abin da akayi min zan d'auke kai saboda ke " Rungume ta Jiddah tayi cikin farinciki da jin abin da Suhaima tace mata "Thank U so much dear " "Jiddah ke da wane? " Da sauri Jidd ta saki Suhaima jin maganar Umman ta wani kallo Umman take yiwa Suhaima kamar irin kallon da Zahra tayi mata. Da murmishi akan fuskar Jiddah taja hannun Suhaima zuwa kusa da Umma tace "Umma ni da Suhaima ne, itace wadda nake baki labari, Suhaima wannan ce Ummana" Da sauri Suhaima ta durk'usa k'asa cikin girmama wa tace "Umma ina yini? " "Lafiya " Cewar Umma cikin halin ko inkula daga k'arshe ma cewa tayi "Jiddah kiyi sauri ki wanka yanzu mai makeup zata zo kinsan yau ne dinner wadda Hajia Faridah ta shirya na family koh" Tana gama fad'in haka ta wuce ko kallon inda Suhaima take bata sake yi ba ta wuc abinta cikin tak'aici Jiddah tabi bayan Umma da kallo kafin ta dawo hankalin ta kan Suhaima da har yanzu take durk'ushe ta kasa tashi saboda mugun sanyin da jikinta yayi na abin da ta fara cin karo dashi tun shigowar ta gidan su k'awarta Jiddah. A lokacin hankalin Suhaima ya tashi sosai ta d'auka Umman Jiddah zata kar6e ta da fara'a ba kamar Zahra ba, shi yasa tayi wa Jiddah alk'awarin kauda kai daga abin da akayi mata, amman fah Jiddah tayi mata abubuwan da zata iya jure duk wani cin kashin su akanta na tsayin kwana biyu daga lokacin da tafi gidan su babu wanda zai sake ganin ta balle har yayi mata kallon banza. "Kiyi hakur..... " Jiddah ta fad'i hakan tana d'ago Suhaima fuskar ta da tarin damuwa sosai, da sauri Suhaima ta toshe mata baki da tafin hannun ta tare da k'ak'alo murmishin dole tace "Kada ki bani hak'uri Jiddah me akayi min babu komai kada ki damu please " Girgiza kai Jiddah kawai tayi tare da rik'o hannun ta tana cewa "Mu tafi bedroom d'ina ki huta kiyi hak'uri da halin 'yan gidan mu kusan haka suke " Gaban Suhaima ya sake fad'uwa da jin abin da Jiddah ta fad'a anya zata iya zaman gidan nan kuwa... Aishat A Muh'd 🏌🏻‍♀ 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 34-35 Hannun ta d'auke da cup wanda coffee ne aciki ta shigo cikin bedroom d'in turus ta tsaya ganin shi a zaune ya zabga tagumi, ta rasa abin da yake damun d'an nata gaba d'aya ya canja tun ranar da ya doki Fadilah, ajiye cup d'in tayi saman center table d'in k'arasa wa inda yake tayi har zuwa lokacin Sabeer baisan da zuwan Mumyn nashi kusa dashi ba, girgiza kawai tayi tana kallon shi kafin ta sanya hannun ta d'ora shi tayi saman kafad'ar shi tace "Son tunanin me kake? Me yake damun ka ne kwananan " Girgiza kai yayi tare da cewa "Nothing Mumy " Zama tayi kusa dashi tana mai kamo hannun shi cikin nata kallon shi take cikin kulawa tace "Son baka da wanda zaka fad'a wa damuwar ka duk duniyar nan sama da ni, ka sanar dani ko zan iya baka shawara please " Cikin gajiya da maganar Mumy yace "Nace miki babu komai ki rabu da ni please " Ya k'arasa maganar da d'an tsawa kad'an. "Shikenan Son koma mene Allah ya yaye maka " Cikin zuciyar shi ya amsa da Amin. "Ga coffee kasa na lura tun breakfast baka k'ara cin wani abin ba, idan ka gama ka shirya ka kayan ka saman bed kasan yau ne dinner na sister d'in ka Jiddah kuma kowa na family zai je don haka ina buk'atar ganin ka please Son " Shiru yayi mata bai kulata ba itama bata sake bi ta kanshi ba ta wuce ta fita don idan da sabo ta saba da shariyar Sabeer wani lokacin musamman idan yana cikin damuwa bai fiye son magana ba. Mumy tana fita ya zame ya kwanta kan sofa yayi matashin kai da hannayen shi, idanun shi lumshe su yana tunanin Suhaima sosai yake mamakin yanda yarinyar ta tsaya mishi cikin zuciyar shi, shi baisan so ba amman da alama ya fad'a son wannan yarinyar, dummm gaban shi ya fad'i da ya tuna yanda 'yan uwanshi da iyayen shi suka tsani talaka balle ita a k'auye ma take, yanzu shi ya zai yi zuwan shi wajen uku k'auyen ko mai kama da ita bai gani ba ya rasa yanda zai yi. Son da yake mata bazai iya hak'ura da ita dole ne yasan yanda zai 6ullowa al'amarin, bayan bikin Jiddah dole ya koma k'auyen ya neme ta, zai nuna mata so sannan zai bawa iyayen ta kud'i sosai ya basu gida da mota da jari sosai yanda bazai samu matsala ba ta 6angaren iyayen shi idan suka ga iyayen ta masu kud'i ne, wani murmishi ya saki na kamar wanda ya samu nasara ma sai lokacin hankalin shi ya kwanta, kiran sallahr mangarib ne ya katse mishi tunani, toilet ya shiga yayi alwala ya fito kai tsaye masallaci ya wuce. Babban hall ne wanda ya k'ayatu da decorations masu kyau da k'ayatuwa wajen ya tsaru yayi kyau sosai, ga haske tamkar ba dare ba sanyi Ac ta ko'ina ban da k'amshin tsadaddun turaren jikin manyan masu kud'in da suke zaune a wajen kamar anyi 6arin turare a wajen. Manyan hamshak'an mutane ne masu kud'i sosai a wajen ansha kwalliya ta kece raini ga tsadaddun sutturu da aka sanya mutane suna zazzaune a wajen da aka tanadar musu, slow music ne ke tashi kawai a wajen duk mutane an hallara, family d'in Jiddah gasu nan ga friends na iyaye dana amarya sai na yayyanin amarya dana k'anen ta abin dai ya tsaru gwanin sha'awa kowanne da kalar ankwan su, haka 6angaren dangin ango gasu nan da nasu ankon daban suma sunyi kyau sosai. Amarya da ango ake jiran shigowar su babu dad'e wa mc ya fara sanar wa shigowar ango da amarya kowa ya nutsu ya zubawa kofar shigowa kallo don ganin shigowar amarya da ango. Cikin takun k'asaita da nutsuwa Jiddah da angon ta khaleel suka shigo hannun su sark'e da junan su, Jiddah tana sanye da wata farar gown har tana jan k'asa sai ash head da ta sanya yana da kwalliyar flowers silver ajiki pose da hill nata dukka ash ne masu kwalliyar silver ajiki tayi kyau sosai abin ta, haka angon ma Khaleel yasha shadda ash colour sun yi matukar kyau da dacewa da junan su, sai watsa musu wasu fararen furanni da red ake yi. Bayan su kuma Suhaima ce tasha light pink na gown sai head nata pink mai d'an duhu tasha makeup tayi matukar kyau tamkar ba Suhaima ba, ba wanda zai ganta ya zaci daga k'auye ta fito tama fi 'yan birnin kyau a wajen don ba k'aramin haskawa tayi ba tamkar itace ma amaryar ba Jiddah, don kallo dawowa yayi kanta abin da yasa duk ta dibirbice ta rasa inda zata yi saboda idanun mutanen da suke kanta sai murmishin yak'e take. Da haka ta samu waje ta zauna bayan ango da amarya sun wuce wajen zaman su, nan aka fara gabatar da dinner cikin nutsuwa da wayewa, gaba d'aya Suhaima a tak'ure take saboda bata saba zuwa irin wad'annan wuraren ba, har zuwa lokacin da amarya da ango suka fito domin taka rawa nan 'yan uwa da abokanan arzik'i suka fito domin yi musu lik'i. Dr Faridah ce ta fito filin wajen nan mutane suka bata hanya ta wuce zuwa inda su Jiddah suke tsaye ita da angonta suna taka rawa a nutse, bag d'in hannun ta ta bud'e ta fito da bandir d'in 1k ta fara watsa musu tamkar bata san zafin kud'i ba sai da ta gaji tukunna ta bar wajen. D'ago kan Suhaima yayi dai dai da barin Dr Faridah wajen aikuwa suka had'a ido wani irin bugawa zuciyar Suhaima tayi da k'arfin gaske haka ma a 6angaren Dr Faridah d same abin da Suhaima taji haka taji itama, amman sai ta kawar da kanta daga barin kallon ta cikin zuciyar tana tunanin irin wannan kyan na yarinyar da bata ta6a ganin ta ba sai yau, gashi ta d'an birgeta kad'an da taga duk da kyan da take dashi but bata da rawar kai irin na 'yammatan da suka waye sosai kafin kuma watsar da tunanin ganin Suhaima ta cigaba da sha'anin gaban ta. Har zuwa lokacin da aka buk'aci amarya da ango su yanka wedding cake nasu, nan 'yan uwan amarya da ango 'yan kad'an suka rakasu wurin cake d'in babu 6ata lokaci suka yanka Khaleel ya bawa Jiddah a baki itama ta yanko tare da d'an tsugunna wa kad'an ta bashi nan aka hau tafi. Suhaima ba k'aramin birgeta suka yi ba sai sakin murmishi take ita kad'ai, zuwa yanzu ta d'an saki jikin ta da zaman wajen, amman sam duk da haka har yanzu bata ji sha'awar ta auri irin d'aya daga cikin wad'annan masu kud'in ba, tana kallon yanda su Zahra da sauran sisters d'in Jiddah suke wurgo mata harara tsanarta k'arara akan fuskar su, d'aga kafad'ar ta tayi alamar ko a jikin ta, tana fatan jibi iyanzu tana k'auyen su cikin gidan su, sai su harari wata ba ita ba. Ana gaf da tashi a wurin Sabeer ya shigo cikin hall yana sanye cikin wata light blue sky na shadda tsadaddiya har da hula akanshi, d'inkin shi irin wanda matasan yanzu suke yin shi ba k'aramin kyau yayi ba, a daidai lokacin kuma Suhaima ta taso zata fita daga hall d'in don amsa kiran wayar da Yaya Aliyu yake yiwa Jiddah. Karo suka yi da junan su inda Suhaima ta bige kanta da kafad'ar shi, dafe goshin tayi tare da yamutsa fuska tace "Washh Allah na " D'ago kan da zata yi ta bashi hak'uri suka had'a ido da junan su, kallon second 3 Suhaima tayi mishi ta gane ko wane tuni jikin ta ya fara rawa tsoro ya kamata kada ya d'auki fansar abin da tayi mishi a wajen da batasa kowa ba sai Jiddah, shima Sabeer kallon ta yake cikin mamakin me ya kawo ta nan kuma don ko acikin mafarki ya ganta sai ya gane ta wane ya kawo ta wajen bikin k'anwar shi? Ta dalilin wata zo nan? wad'annan tambayoyin ya yiwa kanshi a lokacin d'aya. Ganin ya zuba ido yana kallon ta yasa ta saurin fita daga hall d'in, cikin zafin nama ya bita yana cewa "Hey tsaya mana kece wan...." Kafin ya k'arasa maganar tashi yaga wayam babu kowa a wajen, ta gudu kenan abin da zuciyar shi ta fad'a ba guduwa tayi ba 6oya tayi, ina ta 6uya kuma?. Daga d'an nesa kad'an na hango Suhaima tana lek'en shi jikin ta na 6ari zuciyar ta na bugawa da k'arfi, ganin yana dube dube a wurin ya sake fad'ar mata da gaba, bata k'ara rud'ewa ba sai da taga ya nufo inda take. Yana daf da k'arasa wa inda take ne yaji an rik'o hannun shi da sauri ya juya ga ashe Mumy ce da tarin kannen shi, wayyo Allah ya furta cikin zuciyar shi don yasan yanzu yaran nan zasu sa mishi ciwon kai da hayaniyar su "Yah Sabeer kazo mu d'auki pic's please " Cewar wata sistern shi zai yi magana kenan Mumy tayi musu magana da ido, dariya suka yi don su fahimci me take nufi, aikuwa hannun shi suka kama zuwa cikin hall d'in bashi da yanda zaiyi ya bisu yana tafiya yana dube dube har sai da suka wuce ciki sam ranshi babu dad'i ba haka yaso ba yaso ta tsaya su yi magana ta fahimta amman dole ya binciko wanda yayi inviting d'in ta zuwa wajen nan. Fitowa Suhaima tayi daga inda ta 6uya tana sauke ajiyar zuciya har da gumi ta had'a duk tayi wani iri kallo d'aya mutum zai mata yasan a firgice take, zama tayi a gefen wasu flower's tana sauke numfashi.... Aishat A Muh'd 🤸🏻‍♀ A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 36-37 Suhaima ta d'auki wajen 5 minutes kafin ta d'an nutsu ajiyar zuciya ta sake saukewa a karo na ba adadi tace "Alhmdllh Allah nagode ma da wannan mutumin bai kamani ba da yau nasan zai ya rama abin da nayi mishi" Suhaima ta furta hakan a sarari, wayar hannun ta ne ya cigaba da ringing dole ta dai daita nutsuwar ta tayi picking ganin sunan Yaya Aliyu ne akai. Bayan sun gaisa ta tambaye shi jikin Aunty Aliyah daga nan shima ya tambaye ta yanayin zaman nata don tun da ya tafi hankalin shi yak'i kwanciya sam ga jikin Aliyah sai a hankali, boye mishi gaskiya Suhaima tayi tace tana nan lafiya yanzu ma suna wajen party dinner d'in Jiddah, daga k'arshe yayi mata nasiha sosai tukunna suka yi sallama ta ajiye phone d'in saman k'afarta tare da rafka tagumi tana tunanin yanda za'a yi ta koma cikin hall d'in bayan taga Sabeer ya shiga ciki, nan take zuciyarta ta bata shawarar zaman ta anan waje har a tashi nan take ta aminta da shawarar zuciyar ta sake gyara zama tayi tana jiyo sautin kid'an da yake tashi a wajen partyn. Sai wurin 11 na dare aka tashi lokacin Suhaima har ta fara gajiya da zaman jiran Jiddah ta fara gyangyad'i a wurin, sam Suhaima batasan har an tashi ba gyangyad'in ta kawai take sabida ta gaji gashi bata saba kaiwa wannan lokacin ba batayi bacci ba gashi ba'a saitin k'ofar shiga hall d'in take ba balle a taji fitowar mutane. Sai da aka watse a wurin bai fi mutane d'ai d'aiku ba Suhaima ta farka daga gyangyad'in da take tamkar wadda aka tasa haka ta bud'e ido firgigit, ganin yanda duhu yayi sosai yasa Suhaima rarumo wayar Jiddah dake saman k'afarta ta duba time, wani zabura tayi ta mik'e tsaye cikin tashin hankali ganin har k'arfe 11:30 tayi na dare, ai d'ora hannun ta tayi dukka biyun a saman kanta tace "Wayyo Allahna na shiga uku ni Suhaima yau nice a waje har k'arfe goma sha d'aya da rabi innalillahi " Lokaci d'aya hawaye suka fara zubo mata ga wani mugun tsoro da sanyi da take ji, tafiya ta fara yi ta nufi k'ofar hall d'in taga duk yawan mutanen nan wayam sai wasu d'ai d'aiku wanda batasan fuskar su ba, tuni Suhaima ta samu waje d'aya ta raku6e ta fara rasgar kuka kamar wadda akai mata dukan tsiya. Kuka sosai take har da majina ta rasa mafita don duk a rud'e take ta kasa dai daita nutsuwar ta balle ta sami mafita gashi phone d'in Jiddah a hannun ta wa zata kirawo acikin familyn ta mutanen da basu yi maraba da zuwan ta cikin su ba matsayin bak'unta na kwanaki biyu, balle ta samu damar kiran wani daga ciki ya taimaka mata, gashi idan ma ta kirawo Yaya Aliyu d'aga musu hankali kafin ma yazo ma koma mai ne ya cinye ta kuma bata yi wa Jiddah adalci ba idan ta fad'a mishi yanzu ya zata yi wayyo Allah na, sake rushe wa da kuka Suhaima tayi sosai tana nan a raku6e taji an dafa mata kafad'a tare da cewa "Hey what are you doing here? " Wata irin firgita Suhaima tayi tare da jiyowa a tsorace had'a ido tayi da wannan guy d'in na d'azu yana tsaye daf da ita ya hard'e hannun shi a kirji, wani k'ugi cikin ta yayi wanda tana tunanin ma Sabeer yaji k'arar da cikin nata yayi matse k'afafun ta ta fara yi saboda daf take da sakin fitsari a tsaye jikin ta kuwa sai rawa yake wanda ya sanya wayar Jiddah ta fad'i a k'asa da bag d'in ta. Kallon ta Sabeer yake up and down yana sakin wani murmishi wani sanyin dad'i ne yake ratsa cikin zuciyar shi da gangar jikin shi, sauran kad'an dariya ta kubce mishi ganin yanda take matse k'afa tamkar wanda yake jin fitsari ya matse shi irin sosai d'in nan har k'arar da jikin ta yayi sai da yaji sautin. Ganin murmishin da yake ba k'aramin sake rud'ar da Suhaima yayi ba aikuwa fakar idon shi tayi ta tattara gown d'in ta da hannun ta kafin Sabeer ya ankara yaga Suhaima ta zura da gudu tayi hanyar fita daga gate, ba shiri shima ya d'auki phone d'in da bag nata da suka fad'i ya bita da gudu shima. Suhaima da ta bud'e kofar gate d'in zata fita da sauri ta dawo baya jin wani irin sanyi da ya busa ta gashi wajen duhu babu wadaccen haske sosai a wurin nan ta tsaya waje d'aya tana rawar jiki, da haka Sabeer ya cimmata tana tsaye sai ruwan hawaye da yake tsere saman kyakkyawar face d'in ta, ganin Sabeer a kusa da ita da sauri Suhaima ta bud'e baki tace "Don girman Allah kayi hak'uri da abin da nayi maka tsautsayi ni bazan sake ba har abada kayi hak'uri kada kayi min komai bansan kowa anan ba " Sosai ta bashi tausayi ganin irin rud'ewar da tayi cikin sanyin murya yace "Hey calm down babe babu abin da zan miki just I'll help you" Kamo hannun ta yayi ganin har yanzu bata daina rawar jiki ba kuma a rud'e take, jan hannun ta yake har cikin mota ya zaunar da ita tukunna ya zagayo seat d'in driver ya zauna kallon ta ya tsayayi na tsayin wasu minutes, kallon yake cikin wani irin yanayi ita kuwa kanta a sunkuye batasan abin da yake ba tsoro ne fal a tattare da ita addu'a take cikin zuciyar ta Allah yasa kada ya cutar da ni, kafin yayi wa motar key suka bar wajen sun d'an yi nisa suna tafiya tukunna ya jiyo ya kalle ta still har yanzu kanta a sunkuye. D'an girgiza kai yayi tare da sakin dan murmishi yace "Ina zamu je, i mean ina ne gidan da zan kai ki? " D'an satar kallon shi tayi ta fad'a duniyar tunani ita da take bak'uwa a garin yau ne zuwan ta na farko ina zata gane gidan, don haka sai tayi shiru kawai. Ganin haka yasa Sabeer yace "Ina jiran ki fah kinsan dare yayi fah idan baki da wajen zuwa kuma sai mu wuce guest house d'ina mu d'an huta zuwa gobe " Wani zaro ido Suhaima tayi tamkar idanun ta zasu firfirto wani tsoro da nadamar shiga motar shi ya dirar mata lokaci d'aya ashe d'an iska ma ta shiga motar shi yau na shiga tara ba uku ba, dariya sauran kad'an ta kubce wa Sabeer ganin yanda Suhaima ta koma. "Don Allah kasan gidan su amaryar Jiddah? " Suhaima ta fad'a cikin rawar murya, da mamaki ya kalle ta kafin yace "Oh nan zaki je kenan? " Da sauri Suhaima ta d'aga kanta alamar eh, mamaki ne sosai ya kama shi ta yanda akayi Suhaima tazo gidan tun da yasan halin 'yan gidan su da basa huld'a da talaka sai mai kud'i d'an uwan su. Kuyi hak'uri da wannan fan's mu had'u a next page muji ya zata kasance. Ga Sabeer da Suhaima sun had'u shin komai zai faru kuma?... Aishat A Muh'd ✍🏻 A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 38-39 Babu wanda ya sake magana a cikin su kowannen su da tunanin da yake cikin zuciyar shi, amman Suhaima har yanzu hankalin tashe yake ganin har yanzu basu zo gidan ba ta sadaukar sace ta ma yayi tuni wasu sababbin waye sun cigaba da zuba saman fuskar ta, d'an kallon ta Sabeer yayi kad'an yana girgiza kai cike da mamakin ta ko wahalar kuka bata yi. Da haka suka k'arasa gidan Suhaima tana ganin an shiga cikin gidan ta tabbatar shine sai da ta saki ajiyar zuciya na kwanciyar hankali kafin ta sanya hannun ta saman face nata da niyyar goge hawaye sai taga an mik'a mata tissue kar6a tayi ta goge tukunna ta fara kok'arin bud'e kofar motar, kamar ance ta jiyo ta kalli side d'in su Jiddah aikuwa ta hango Jiddah tana tafiya cikin sauri tana goge fuska, da sauri Suhaima ta k'arasa fita kamar abin arzik'i ta rufe kofar motar sai ta zuro kanta ta jikin window da yake ya sauke glass d'in. Sabeer har zai yi wuce zuwa parking lot sai yaga ta zuro kanta sai ya tsaya ya d'auka godiya zata yi mishi sai hasashen shi yasha banban da na Suhaima don cikin tsiwa ta fara cewa "Uhm Malam ka d'auka godiya zan maka da ka zuba ido kana kallona har da bud'e kunnuwa don jin abin da zance, to ban gode ba kuma hak'urin da na baka d'azu in mistake ne, me yasa ma ka tausaya min ka d'auko ni da ka barni acan ma da nafi jin dad'i... " Da sauri Suhaima ta fitar da kanta tare da zurawa da gudu zuwa inda ta hango Jiddah a tsaye sai safa da marwa take, sakamakon wata cafka da Sabeer ya kawo mata ganin ta gudu ne yasa shi dunk'ule hannun shi ya naushi d'aya hannun kafin ya jingina kanshi jikin kujera yace "Hmmm lallai babe d'in nan da na kama ki yau a hannuna da sai gane kuren ki sai tsiwa da shegen tsoro fal ciki" Shi mamakin ta ma yake tun da suka taho take kuka jiki yana rawar tsoro, amman wai har ta samu bakin tsiwa da taga ya kawo ta inda take buk'ata, kwafa yayi tare da k'arasa wa parking lot yayi parking tukunna ya nufi part d'in su yana cilla key yana cafewa zuciyar shi yau cike take da farinciki da nishad'i ya ganta a inda bai ta6a zaton zai ganta ba kuma yana kyautata zaton dalilin Jiddah tazo tun da yasan itace mai shige shigen talakawa sosai a cikin families d'in su yayi mamakin yanda Jiddah har tasan k'auyen su Suhaima ta ganta suka fara k'awance. Da wannan tunanin ya k'arasa cikin part d'in su kai tsaye bedroom nashi ya wuce yayi wanka sannan ya sanya wasu fararen sleeping dress ya kwanta amman ya kasa bacci sai tunanin abin da ya faru tsakanin shi da Suhaima yake yana zuba murmishi shi kad'ai. Da gudu Jiddah ta k'araso wajen Suhaima a lokacin da ta hango ta rungume ta tayi tana kuka tace "Suhaima don Allah kiyi hak'uri wallahi na d'auka kin biyo wasu ne sai da na neme ki na rasa na d'auka kina gida sai da na dawo na neme ki na rasa, hankali na ya tashi sosai yanzu haka da kika ga na fito komawa zanyi na duba ki sai na hango ki... Waya kawo ki? Naga kamar motar Yah Sabeer kika fito ko shine ya dawo da ke? " Duk wannan maganar da Jiddah take da tambaya babu saurarawa tana yi tana kallon Suhaima, abin ma sai ya bawa Suhaima dariya kafin ta bud'e baki tace "Kaiii Jiddah irin wannan tambayar gashi na dawo sai hankali ya kwanta amman ni bansan sunan wanda ya taimaka min ba naga dai kuna yanayi dashi " Ajiyar zuciya Jiddah ta sauke ta kwanciyar hankali kafin ta tace "Mybe shine tun da naga motar shi ce amman naji dad'in abin da Yah Sabeer yayi dole nayi mishi godiya, gaskiya Suhaima kinci sa'a sosai don Yah Sabeer sai a slow wallahi" "Koh? " "Eh mana don baki san halin shi ba ne, gashi da miskilanci da shagwa6a don ko k'aramin yaro bazai nuna mishi shagwa6a ba " "Hmmm ni bacci nake ji na gaji wallahi " "Ai dole zo muje kiyi wanka ki kwanta " Hannun ta Jiddah ta kama suka nufi side d'in shi shiru kake ji ko'ina kowa yayi bacci, don haka d'akin Jiddah suka nufa kai tsaye, bathroom Suhaima ta shiga wanka tayi tare da yin alwala ta fito wata catton sleeping dress dogowa Jiddah ta bata ta sanya da hula sannan ta sanya hijab sallahr isha'i tayi tare da yin shafa'i da wuturi tayi 'yan addu'o'in ta kafin ta tashi ta koma inda ta ajiye bag d'in da ta zo dashi. D'auko wa tayi ta bud'e gift's d'in da Aunty Aliyah ta bata ta d'auko taso wa tayi ta zo inda Jiddah ta kwanta saman bed tace "Jiddah ga gift's d'in da Aunty Aliyah ta bani na baki " Cikin mamaki Jiddah ta tashi zaune tare da kar6ar sarkar tana dubawa, nan take ta fad'ad'a fara'ar ta sannan ta rungume Suhaima tana cewa "Wayyo dad'i nagode sosai tana da kyau, me yasa baki fad'a min da wuri nayi mata godiya ba " Suhaima fuskar ta d'auke da murmishi tace "Itace ta hana na fad'a miki don babu waya tace sai mun tafi na baki " "Naji dad'i sosai kiyi mata godiya Allah ya bata lafiya ya raba ta da abin da take d'auke dashi lafiya" "Amin " Cewar Suhaima kafin ta d'ora da cewa "sai wani godiya kike tamkar wadda aka bata wani babban abu " D'an hararar ta Jiddah tayi tare da cewa "Hmm ke kika ga haka Suhaima amman tabbas wannan kyautat a wuri na babba ce " 'Yar dariya Suhaima kawai tayi ta kwanta ita ma bayan Jiddah tayi light off ne Suhaima tace "Jiddah ina son gobe ki had'a ni da driver ya kaini wani mall zan yi siyayya " "Me zaki siyo? " "Ina ruwan ki idan na siyo kya gani " "Alright Allah ya kaimu goben" "Amin " Da haka kowannen su yaja blanket ya lullu6a tare da addu'ar bacci babu dad'e wa bacci ya d'auke su mai nauyi da yake an gaji saboda hidima ta biki. Washe gari da safe wajen k'arfe 11 aka d'aura auren Jiddah da Khaleel wanda d'umbin mutane masu kud'i goggagun 'yan boko tare da 'yan siyasa manyan likitoci da 'yan kasuwa suka halatta bayan d'aurin aure ne suka wuce reception ta maza, cikin gida kuwa matane a ciki taf ana hidimomi irin na biki. Jiddah ce gaban dressing mirror tana sanya sark'ar da Aunty Aliyah ta bata sai da ta gama sanyawa tsaf ta jiyo ta kalli Suhaima wanda taci gayun ta cikin wani lace ash mai touch d'in flowers pink tayi kyau tamkar itace amaryar sai kashe selfie take abin ta. "Yah babe kin gani koh na had'u? " Cewar Jiddah kenan tana kallon Suhaima, kallon ta Suhaima tayi a haka sark'ar tayi mata kyau amman bai kamata ta sanya ta yanzu a lokacin bikin ta don tayi arha da yawa tana kallo ta ajiye gold d'in ta a gefe ta d'auki wannan ta sanya. D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa "Wow amarya a gidan Khaleel kinyi kyau sosai sai dai ki cire sark'ar nan please " "Because of what? " "Bata cancanta ki sanya ta ba yanzu " Har Jiddah ta bud'e baki zata yi magana aka turo k'ofar bedroom d'in aka shigo, Umman Jiddah ce ta shigo tasha kwalliya cikin wata tsadaddiyar shadda an zuba gold's a jiki sai fitar da k'amshin turare take, da sauri Suhaima ta gaida ita ba yabo ba fallasa ta amsa tana nufar Jiddah wadda take tsaye, cikin mamaki tace "Me zan gani Jiddah, mene haka a wuyan ki? " "Uhm Umma sark'a ce tayi kyau? " Wata harara Ummna ta zabga mata tare da cewa "You're very stupid Jiddah na rasa mene akan ki wallahi ranar bikin ki zaki sanya wannan banzan sark'ar mai araha haka ko 'yan aikin gidan nan zasu sanya sark'ar da suka fi wannan tsada balle ki, wanne stupid ne ya baki ita?" A hankali cikin sanyi jiki Suhaima ta tashi ta nufi bathroom ta shige idanun ta suna fitar da hawaye yau a gabanta ake kiran Aunty Aliyah stupid wadda ta d'auke ta tamkar mahaifiya a wajenta yau da ace wata ce ba Umman Jiddah ba da sai inda k'arfin ta ya k'are wallahi. Gaba d'aya ran Jiddah ya 6aci sosai cikin jin haushin abin da Umman ta fad'a, Jiddah ta bud'e baki tace "Haba Umma me yasa kike haka ne " "Dalla can rufe min baki kafin ranki ya 6aci kiyi maza ki cire ta sannan ki fito parlour za'a d'auki pic's sauran ki taho mana da yarinyar nan " Tana gama fad'in haka ta fice daga d'akin, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata me yasa me yasa iyayen ta suke wannan halin na kyamar talaka me yasa suke abu tamkar basu da ilimi sun san Allah ne mai azurta bawan shi a lokacin da yaso, ba wayon su ko dabarar su ne yasa suke da kud'i ba a yanzu idan Allah yayi sai ya kwace kud'in. Da sauri ta sanya hannu ta goge hawayen fuskar ta tare da jiyowa jin an dafa kafad'ar ta, Suhaima ta gani tana murmishi itama murmishin yak'e tayi kafin tace "I'm so sorry Suhaima akan abin da Umma tayi miki" "Haba Jiddah ni fah babu abin da akayi min " Ta k'arasa fad'i tana cire sark'ar jikin Jiddah bayan ta gama cirewa ne ta d'auko mata wanda su zata sanya ta d'auko wannan ta sanya. "Wow kin had'u tawan ni yanzu ki had'a ni da driver na tafi " "Okay dear " D'auko phones nata tayi ta kirawo driver magana tayi na tsayin 2 minute's sannan ta mik'a wa Suhaima wayar tace "Yana waje yana jiran ki driven " "Okay thank U " Daga haka ta d'auki bag nata suka fito tare ta kofar baya Jiddah ta nuna wa Suhaima ta fita don batason wani ya sake 6atawa Suhaima rai, bayan Suhaima ta fita driven shi ya hango ta yayi mata magana aikuwa nan ta shiga mota yaja suka bar gidan. Tun da Suhaima ta fito daga part d'in su Jiddah tazo ta wuce ta shiga mota yana kallon ta, wani mirmishin mugunta ya saki duk gajiyar da yayi dakyar yake d'aga k'afa gudowar shi daga wajen reception ko gamawa ba'a yi ba ya taho don duk ya gaji da hayaniya ganin Suhaima ne yasa duk yaji gajiyar ta wartsake cikin sauri ya shiga mota ya bisu a baya... Aishat A Muh'd ✍🏻 A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 40-41 Tafiya suke Suhaima sai wara ido tana kalle kalle sosai taji garin na Kano ya birgeta daman Yaya Aliyu yana bata labarin yanda yanayin garin yake kodayaushe cikin sha'awar zuwa take sai gashi a dalilin Jiddah tazo ta, karatun Qur'an ne yake tashi a motar k'ira'ar Shureim cikin suratul Ma'idah sosai karatun yake ratsa cikin zuciyar Suhaima har wani lumshe ido take tana bin karatun a hankali cikin k'asa k'asa da muryar ta. Agaban wani k'ayataccen mall driver yayi parking tare da cewa "mun iso ranki ya dad'e" D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa "Okay bari na shiga na fito " "A fito lafiya " Bud'e k'ofar motar tayi ta fito cikin takun nutsuwa take tafiyar duk da kuwa yanda gaban ta yake fad'uwa don bata ta6a zuwa irin wannan wajen ba, kawai d'auriya tayi kada ta ba da kanta amman zuciyar ta fal tsoro kamar ace kyat ta zura da gudu, har ta k'arasa wajen k'ofar shiga ta shiga ciki. A hankali Sabeer yayi parking kusa da motar da ta kawo Suhaima, fitowa Sabeer yayi sannan ya k'arasa wajen motar tun kafin ya k'araso drive ya ganshi don haka da sauri ya fito daga motar yana cewa "Yalla6ai barka da rana" Sabeer bai tsaya bawa driven amsa ba yace "Salisu me kake anan? " "Yalla6ai na kawo k'awar Jiddah nan zata yi shopping " "Okay zaka iya tafiya gida " D'an shiru Salisu yayi kafin yace "Yalla6ai Jiddah tace na jirata ta gama na mayar da ita gida don bak'uwace anan " D'an shan mur Sabeer yayi kafin yace "Oh baza kayi abin da na saka ba? " Cikin d'an tsoro da biyayya Salisu yace "Ayi min afuwa Yalla6ai yanzu zan tafi " Yana gama fad'in haka ya shiga mota yaja ya bar wajen zuciyar shi cike da d'an tsoro yanzu idan ya koma gida me zai cewa Jiddah idan ta tambaye shi ina k'awar ta, gashi bazai iya musu da Sabeer ba don kada ya rasa aikin shi don dashi ya dogara. Salisu driver na tafiya Sabeer ya saki wani murmishi dani kaina bansan ma'anar shi ba kafin ya shiga cikin mall d'in cikin takun shi na k'asaita, zuciyar shi cike da tunanin yanda yarinyar da ko sunan ta baisani ba zai tunkare ta da magana mafi daraja a wajen shi wanda babu 'ya macen da ta6a furtawa. Bayan Suhaima ta gama duk siyayyan gift's d'in da zata bawa Jiddah ne ta nufi wajen biyan kud'i, ga mamakin ta akace an biya mata cikin mamaki take kallon matar da ta fad'a mata da gani yare ce don hausan ta baya fitowa sosai. "Wane ya biya min anya nice?" Suhaima ta tambayi matar, d'an murmishi tayi tare da cewa "Yes kene aka biyawa ba ke da mijin ka bane? " Ad'an tsorace Suhaima tace " A'a ba mijina ba ne ko zanyi iya sanin wanda ya biya min?" Da mamakin abin da Suhaima ta fad'i tace mata "Yawwa ga Yalla6an can wanda ya biya miki " Matar ta nuna wajen da d'an yatsanta, bin d'an yatsan matar Suhaima tayi kallo zuwa inda take nuna mata wani irin buguwa zuciyar Suhaima tayi sakamakon had'a ido da Sabeer da tayi yana wani kasheta da murmishi zaune yake kan kujera yana kallon ta suna had'a ido ya d'aga mata gira tare da yi mata wink, wayyo Allah nah yanzu wannan mutumin duk inda nayi sai ya biyo ni yanzu ya zanyi na guje mishi?, fad'in haka cikin zuciyar ta. A sace ta k'ara kallon matar inda Sabeer yake sai taga ya tashi tsaye yana gyara rigar dake jikin shi, da sauri ta fara tafiya zuwa hanyar da zai kaita ta fita sauri kawai take tana fatan ta ganta a cikin mota ta shiga ciki ta zauna sun bar wajen. Tana fitowa ta k'arasa inda suka yi parking amman wayam bata ga motar ba nan ta sake dudduba wa ko ba wurin ba ne taga dai still anan suka yi parking, toh ina motar da driven? Zuciyar Suhaima ta ambata. "Ni nace ya tafi " Fad'in Sabeer kenan wanda ke tsaye a bayan ta tamkar yasan abin da zuciyar ta take sak'amata, bata kula shi ba ta fara tafiya a wajen don bata da abin cewa tun da driven su ne d'auko shi suka yi yana musu aiki su biyashi dole yaji maganar shi tun da ita ba komai bace. Ganin tana tafiya yasa Sabeer bin bayan ta yasha gabanta yana cewa "Hey beauty kizo nayi dropping naki zuwa gida " Ja Suhaima tayi ta tsaya tare da d'an kallon shi gaban ta na fad'uwa ta daure tace "Bana so zan kai kaina inda nake buk'ata " Tana gama fad'i haka ta kauce tare da zagaye shi zata wuce da sauri ya rik'o hannun ta, tsayawa Suhaima tayi tare da jiyowa ta kalli tsintsiyar hannun ta inda ya rik'e mata wani bak'inciki ne ya kamata ganin namijin da ba mijin ta ba muharraminta ba ya rik'e mata hannu a cikin bayyanar jama'a, ko jiya ma da ya rik'e mata hannu ba cikin nutsuwar ta take ba. Wasu hawaye ne suka hau zubo mata a idanun ta kallon shi tayi tare da cewa "Ka cika ni " Muryar ta can k'asan mak'oshi ta furta hakan, ganin babu wasa a fuskar ta ya sanya shi cikata tana ganin haka yasa Suhaima juyawa zata cigaba da tafiya, cikin wata irin murya Sabeer yace "Banason ki k'ara tafiya ba tare da na fad'a miki wani abu ba ina son kizo ki shiga mota akwai maganar da zan fad'a miki please " D'an jim Suhaima tayi daman ko da zai barta ta tafi batasan inda zata nufa ba gashi ta bar wayar Jiddah a cikin mota. "Na rok'e ki please " Sabeer ya furta hakan yana kallon ta, juyawa tayi ta fara tafiya kawai shima bin ta yake a baya har suka k'arasa inda yayi parking motar shi ya bud'e mata seat na gaba ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya koma ya shiga mazaunin driver ya zauna yana nai mamakin kanshi yau wai shine yake bud'e wa wata mace k'ofar mota ta zauna lallai so ya canja shi daga d'abi'un halayyar shi na da zuwa wasu daban. "Suna na Sabeer Hussein d'an fillo, ke mene sunan ki? " Shiru Suhaima tayi bata yi mishi magana ba shima bai k'ara cewa komai sai da suka yi nisa da tafiya ta bud'e baki tamkar batason magana tace "Suhaima " A hankali ta furta hakan bata d'auka yaji ba sai da taji yace "Nice name " Jingina kanta tayi jikin kujerar da take zaune ta lumshe idanun ta, dan kallon ta Sabeer yayi ganin ta rufe idon ta ne yasa shi jan wani birki, a rikice Suhaima ta bud'e idon ta har ta buge kanta ta kalli gaban su ta d'auka wani abin ya faru sai taga ya cigaba da tuk'in shi ko kallo inda take bai yi ba, hararar shi tayi ta gefen ido tare da murgud'a bakin ta kad'an kafin ta koma ta sake lumshe idon ta. Dariya ce taso kubce mishi amman ya danne cikin zuciyar shi yana cewa wanna yarinyar akwai tsiwa huh, gaban wani gida yayi parking mai kyau da gani gidan kasan sabo ne tun daga wajen kasan an kashe kud'i sosai idan ka kalla. Jin an tsaya da motar yasa Suhaima bud'e idon ta ganin ba irin yanayin unguwar gidan su Jiddah ba ne yasa jiyowa ta kalle shi na alamr tambaya nan ina ne. Bai ce mata komai ba ya fito daga cikin motar ya bud'e mata ita ma sai tak'i fitowa tace "Nan ba gidan su Jiddah ba ne don Allah ni ka kai ni gidan su... " "Zan mayar da ke gida Suhaima but ina son ki bani wasu minute's akwai maganar da zamu yi " D'an kallon shi tayi sai taga babu wasa saman fuskar shi duk da a tsorace take dashi haka ta fito daga motar ya rufe sannan suka nufi cikin gidan duk takun d'aya da Suhaima zata yi gaban ta fad'uwa yake. Tura k'ofar gate d'in yayi ya shiga tana biye dashi, gate man na ganin shi ya zube yana gaida su Sabeer ne ya iya amsawa dakyar Suhaima kuwa bakin ta ne yayi mata nauyi ta kasa bud'e shi, gidan babba ne ya had'u sosai cikin parlourn gidan suka shiga. Zama yayi akan kujera ya d'ago kanshi yana kallon Suhaima wadda take tsaye k'ik'am tamkar wata soja yace "Suhaima ki zauna ina son ki ban hankalin shi da nutsuwar ki " Ba tare da ta kalle shi ba ta zauna don ta k'osa ta ganta a kusa da Jiddah. Shiru suka yi tamkar babu mutane a cikin parlourn har sai da Suhaima ta k'osa da shirun nashi tace "Kai nake jira fah " Tashi tsaye yayi ya dawo gaban ta ya zauna akan carpet d'in dake shimfid'e a k'asa, tsugunna wa yayi tamkar mai neman afuwa yace "Suhaima kin tuna ranar da muka fara had'u wa da ke tun daga lokacin na kasa manta ki zuciya kullum cikin tunanin ki take haka idanuna kullum cikin son sake ganin ki suke, na je wajen sau uku k'auyen ku neman ki but ko mai kama da ke ban sake gani ba sai ajiya Allah ya nufa zan sake ganin ki " Dan shiru yayi yana kallon Suhaima wadda take kallon shi take kuma sauraren abin da yake cewa cikin mamakin shi, ajiyar numfashi yayi kafin ya cigaba da cewa "Naji dad'i Sosai a lokacin da na ganki a takaice Suhaima zan sanar miki zuciya ta ta kamu da son ki! I luv U Suhaima i really luv U, ban ta6a son wata mace a duniyar nan ba sai ke ina son ki bani had'in kai na nemi soyayyar ki auren ki nake son yi da gaske Suhaim..... " Kasa k'arasa abin da zai fad'a yayi sakamakon ganin Suhaima da yayi a tsaye tana girgiza kanta cikin wani irin yanayi wanda na kasa banbance na tsoro ne ko na firgita da tayi daga jin abin da Sabeer ya fad'a mata. Mik'e wa tsaye shima yayi tare da cewa " ina son ki! Ina son ki Suhaima zaki aure ni? " Toshe kunnen ta Suhaima tayi da dukka hannun ta biyu don batason jin abin da Sabeer yake ce mata tana cewa "Bana son ka Sabeer bazan iya auren ka zaka iya neman wata " Tana gama fad'i haka ta juya zata fita daga parlourn da tasan wannan shirmen maganar zai fad'a mata da bata biyo shi ba balle ta tsaya sauraren shi don ko a mafarki bazata ta6a aminta da abin da Sabeer ya fad'a mata balle ido biyu. Fisgo hannun ta yayi da k'arfi wanda ya sanya ta fad'a wa cikin jikin shi ta buge kanta da faffad'an k'irjin shi, d'ago kanta yayi da dukka hannun shi biyun ya matse kan nata da k'arfi wanda ya sanya d'an kwalinta ya fad'i lallausan dogon gashin kanta ya bayyana a sarari, kallon shi Suhaima take wanda taga idanun shi sun yi ja sosai idan ba gizo idanun ta suke tamkar ruwan hawaye take hangowa cikin eye's nashi, ko kwakkwaran motsi ta kasa saboda rik'e mata kan da yayi cikin kakkausar murya yace "K'arya kike Suhaima dole ki soni tun da har na soki, ina son ki fad'a min kina sona? " Duk da tsoro da fad'uwar gaban da Suhaima take ga kuma zafin matse mata kan da yayi sai da ta bud'e baki tace "Sabeer na fad'a maka bana son ka ba'a so dole ka rabu da ni please you're hurting me" Idanun shi na zubar hawaye yace "Are you sure baki sona? " "Yes I'm very sure " Cikin tabbatar wa Suhaima ta fad'a ba tare da shakka ba, a hankali taji ya cika ta ya koma ya zauna jagwab saman kujera kafin ya had'e kan shi da gwiwa hawaye ne masu zafin gaske suna zuba a idon shi yau wai Shi Sabeer Hussein d'an fillo mace yarinya k'arama take cewa bata son shi why? " Suhaima kuwa ranta a 6ace ta d'auki d'an kwalinta ta daura tana me shafa wuyanta da d'an k'age, ko kallon inda Sabeer yake bata yi ba ta fita daga gidan ta barshi. Ta d'auki wajen 10 minutes a tsaye ta rasa inda zata nufa sai ta ga motar Sabeer wanda yayi amfani da ita yanzu kauda kanta tayi gefe guda ganin an tsaya. "Yalla6ai yace ki shigo na mayar da ke gida " Wata murya ta daban ta furta mata hakan, kallon wajen tayi ta ga wani bak'on fuska ne ba Sabeer ba ne, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta shiga motar bayan ya bud'e mata k'ofar motar. Babu dad'e suna tafiya ba aka suka k'araso gidan su Jiddah bayan yayi parking ta kwashe kayan ta da tayi shopping ta fito daman a motar ta bar su, tana shigowa d'akin Jiddah sak'on harara ne ya fara ziyartar Suhaima a wajen su Zahra da sauran cousin's d'in Jiddah sa'annin ta, bata kula su ba ta k'arasa wajen Jiddah taya zata iya aminta da soyayyar Sabeer alhalin 'yan uwan shi suna kyamatar ta bazata kai kanta cikin matsala ba. Daga baya ma sai suka zame suka bar musu d'akin daga Jiddah sai Suhaima, nan Suhaima ta bawa Jiddah gift's din da ta siyo mata hannu biyu Jiddah tasa hannu ta kar6a tana yiwa Suhaima godiya, tuni Suhaima ta watsar da abin da ya faru da ita da Sabeer ta fara harhad'a kayanta don gobe ana gama bud'an kai Yaya Aliyu zai zo ya d'auke ta zata koma k'auyen su inda hankalin ta zai fi kwanciya. Da dare kuma dinner d'in da friends na ango suka had'a aka gabatar wanda iya k'awayen amarya da na ango ne kawai, daga nan kuma aka wuce da amarya gidan ta wanda yake nasarawa GRA gidan ya had'u sosai, nan Suhaima da 'yan uwan amaryar suka kwana. Washe gari kuma da safe akayi walima anan farfajiyar gidan nata wanda ya had'a manyan malaman addinin musulunci mata suka gabatar da lectures akan rayuwar aure da tarbiyyar yara zuwa 1 aka tashi daga walimar bayan anci an sha. Sallahr azahar Suhaima tayi bayan ta idar ta ne babu dad'e wa Yaya Aliyu yayi wa Jiddah waya yana k'ofar gidan, nan Jiddah da Suhaima suka rungume junan su suna kuka sosai dakyar dai Suhaima ta zame jikin ta ta d'auki bag nata suka fito babu wanda Suhaima tayi wa sallama cikin families d'in Jiddah don basu yi maraba da bak'unta suka yi ba. Har compound d'in gidan Yaya Aliyu ya shigo suka gaisa da Jiddah tare da bata hak'urin rashin zuwan su da basu yi ba saboda jikin Aliyah sai a hankali, nan ta nuna ba komai yayi mata fatan alkhairi na zama lafiya, sannan suka yi Jiddah sallama suka tafi bayan kayan da Jiddah ta had'a wa Suhaima sosai, tana tsaye a wurin har suka fita daga gidan kafin ta koma ciki tana zubar hawaye na kewar Suhaima don tasan zasu kwana biyu basu had'u ba sai a waya. Bayan Yaya Aliyu ya tada machine d'in shi suka fara tafiya Suhaima na bashi labarin yanda bikin ya kasance amman ba komai ta sanar mishi ba don bata sanar shi had'uwar ta da Sabeer ba da kuma yanda 'yan uwan Jiddah suka kar6e ta, murmishi kawai Yaya Aliyu yake na jin dad'in ganin tilon k'anwar tashi cikin koshin lafiya..... Sai dai kuyi manage da page d'in nan ban samu time d'in da zan yi editing ba, mu had'u a next page don jin ko Sabeer zai hak'ura da Suhaima? Ko mai zai kasance a gaba?... Aishat A Muh'd ✍🏻 A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 42-43 Bayan sun k'arasa gida ne Yaya Aliyu nayin parking d'in machine Suhaima ta sauka da d'an gudunta ta nufi k'ofar shiga gida, a zauren gidan suka yi ki6is da Aunty Aliyah fuskar ta d'auke da murmishin farinciki, rungume Aunty Aliyah tayi cikin farinciki tace "Aunty nayi kewar ki " Cikin murmishi Aunty Aliyah tace "Nima haka Suhaima ba k'aramin kewar ki nayi ba, tun da kin dawo lafiya Alhmdullilah naji dad'i " "Aunty ya jikin ki da babyn mu? " "Jiki Alhmdullilah Suhaima, ya kika baro Jiddah amarya? " "Jiddah mun kaita gidan ta Aunty yayi kyau gidan tace tana gaida ke nayi miki sannu da jiki kuma ta gode sosai, bari dai anjima zan baki labarin yanda bikin ya kasance" 'Yar dariya Aunty Aliyah tayi tare da kamo hannun Suhaima suka wuce cikin gida, suna shiga Yaya Aliyu ya shigo hannun shi d'auke da bag d'in Suhaima da sauran kayan da Jiddah ta had'a wa Suhaima su. A tsakar gida ya tarar dasu a zaune saman tabarma Suhaima na yiwa Aunty Aliyah hira, d'an murmishi yayi kafin yace "Oh Suhaima surutu ko hutawa baki yi ba zaki dame mu da surutu " Dariya Aunty Aliyah tayi yayin da Suhaima ta turo baki na shagwa6a tace "Kai Yaya daga dawowa ta zaka ce na dame ka da surutu bayan yanzu Aunty tace lokacin da na tafi har d'akina kake shiga ka zauna ciki saboda kewa ta da kayi " Dafe goshin shi yayi yana girgiza kai kafin yace "Oh Aliyah har kin sanar mata me yasa kika fad'a wa wannan sarkin surutun? " Aunty Aliyah na dariya tace "ai gaskiya ne gwara na fad'a mata tasan ni da Yayan ta mun damu da ita sannan munyi kewar ta na tsayin kwanaki biyu " "Yawwa Aunty naji dad'i da kika fad'a min, kai kuma Yaya nayi maka yajin aikin magana na minti d'aya " Dariya suka kwashe da ita kafin Yaya Aliyu ya janyo hannun ta zuwa kusa dashi ya zaunar da ita, cikin k'asa da murya yace "Haba 'yar k'anwata ayi wa wannan Yayan naki afuwa bazan iya jurewa ba " Rungume shi Suhaima tayi kafin tace "Yaya ina son ka ina alfahari da kai Allah ya bar ka da Aunty Aliyah, Allah ya jik'an Umma " Jikin su ne yayi sanyi sosai nan yasa hannun shi ya bubbuga bayan ta tare da cewa "Amin Suhaima, maza kije kiyi wanka kizo Babaa Lantana tayi miki gashin kaza mai dad'i irin wanda kike so" K'ara yin kasa da murya yayi kafin ya cigaba da cewa "amman fah mun ci miki ni da Auntyn ki " D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa "bakomai Yaya nah Aunty babyn mu yake so ci ai, kai kuma Yaya kwad'ayi ne koh? " Dariya suka sanya dukkan su kafin Suhaima ta tashi d'aukan kayan nata tayi zuwa cikin d'akin ta, lumshe idon ta tayi saboda shak'ar k'amshin turaren wuta da taji ya daki hancina kafin ta bud'e idon, d'akin fes yake ko'ina a gyare tsab kamar tana nan, cire kayan jikin ta tayi ta d'aura wani zani wanda take wanka dashi sannan ta fito daga cikin d'akin zuwa tsakar gida inda toilet yake. Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suna nan zaune suna hira, ruwan d'umi ta gani akan murhu nan ta d'iba bokitin wanka ta had'a da ruwan sanyi dai dai yanda take buk'atar ruwan ya kasance ta d'auka ta nufi toilet. Tana shiga ta ajiye bokitin har zata cire zanin ta sai ta had'a ido da abin da tafi tsana wato cockroach aikuwa ta runtse ido tare da sakin ihu da k'arfi ta fito, wanda ya sanya Yaya Aliyu da Aunty Aliyah taso wa da sauri, da gudu Aliyu ya nufi inda Suhaima take ya rik'e ta k'am yana cewa "Suhaima meyafaru lafiya? " Kusan lokaci d'aya suka yi mata maganar, cikin rawar murya tace "Yaya kyenkyaso ce a cikin band'akin " Shafa kanta yayi da hannun shi d'aya d'ayan hannun kuma yana goge mata hawayen fuskarta, tun Suhaima na k'arama yasan ta tsani wannan kwaron duk lokacin da ta ganshi ba k'aramin tsorota take ba shi yasa yake yawan yi feshin maganin kwari saboda ita. "Kiyi k'anwata bari na fitar miki da ita kin ji? " D'aga kanta tayi kafin ta cikata ta rik'e Aunty Aliyah, toilet d'in ya shiga da tsintsiya ya maketa tukunna ya fito da ita ya yar cikin shara, sai lokacin hankalin Suhaima ya d'an kwanta amman duk da haka sai da tace "Yaya ka duba babu wata " "Na duba Suhaima babu komai kije kiyi wankan ki " A tsorace ta shiga band'akin don ji take kamar zata sake ganin wata ko ma ta hak'ura da wankan gaba d'aya, yayin da suka juya suka koma inda suke zaune suna hirar su daga k'arshe Aliyu ya fita daga gidan gaba d'aya. Sai fitowa daga wanka tayi taga baya nan sai Aunty Aliyah a zaune, tsokanar ta ta fara yi na ihun da take musu murmishi kawai tayi ta shige d'aki, shiryawa tayi cikin wata gown mara nauyi mai k'aramin hannu ta gyara gashin kanta sannan ta sanya hula ta fito nan inda Aunty Aliyah take zaune hira suke tana cin gashin naman da akayi mata cikin jin dad'i saboda dad'in da yayi mata bayan ta gama ci ta d'ora da madarar shanu mai d'umi, suna nan zaune akayi kiran sallahr mangarib suka yi alwala kowa ya wuce dakin shi don gabatar da faralli. ****************** Tun lokacin da Sabeer ya zube kan kujera ya had'e kanshi cikin jikin shi, yana jin fitar Suhaima ya kirawo driven shi a waya yazo ya kai Suhaima gida yana gama wayar ya koma ya kwanta saman kujera ya tuk'unk'une jikin shi waje d'aya hawaye ne masu zafi suke zuba cikin idon shi. Wai shi yau yarinya k'arama take duban tsabar idon shi tace bata son shi, wad'anda suka fita girma da komai ma na wayewa suna nuna mishi so tamkar su cinye shi amman ita ta samu ma yace yana son ta zata wulak'anta shi, wayyo Allah nah yanzu ya zanyi gashi son yarinya ya shiga zuciya ta dole nasan yanda zan shawo kanta ta amince ta kar6i soyayya ta, duk wannan maganar cikin zuciyar shi yake tashi zaune yayi idon shi sunyi ja sun kumbura kallo d'aya mutum zai mishi yasan cewa yayi kuka daman abin ka da shagwa6a66e bashi d wahalar yin kuka, kanshi ciwo yake tamkar ya cire haka yake ji. "Dole ki soni Suhaima sai nasan yanda nayi na cusa miki son na cikin zuciyar ki, A SANADIN SON KI zan iya shiga kowacce matsala na sani amman har idan zan samu nasarar ki soni komai mai wuce wa " Yana gama fad'in haka ya tashi tsaye kafin kuma ya fita daga parlourn a compound na gidan ya had'u da driven da ya mayar da Suhaima gida mota kawai Sabeer ya shiga ya zauna nan driven ya gane me yake nufi da sauri shima ya tashi ya shiga motar yayi mata ya tada ita suka fita daga gidan. "Yalla6ai ina zamu je? " Driver ya buk'aci son inda zasu je, dakyar Sabeer ya iya cewa "gida zaka kai ni" Yana gama fad'in haka yayi shiru nan driver ya cigaba da tuk'i har suka k'arasa gida ko gama dai daita parking bai yi ba Sabeer ya fito daga motar. Daf da zai shiga part d'in su ya kusan cin karo da Alhj Alhmad d'an fillo wato kakan shi, ganin Sabeer d'an lele a yanayin da bai ta6a ganin shi a haka ba yasa gaban shi ya fad'i tare da kamo hannun shi yace "Sabeer what wrong with U?" Fincike hannun shi Sabeer yayi tare da yin gaba don gaba d'aya ba'a cikin nutsuwar shi yake ba yana tafiya hawaye na zuba cikin idon shi " Cikin tashin hankali Alhj Ahmad ya bishi a baya yana kiran shi amman ko waiwayen shi bai yi ba, yana shiga parlourn a dai dai lokacin mai aiki ta fito daga kitchen hannun ta d'auke da babban farantin saman shi foodflaks ne da plates zata jera a dinning table. Sabeer yana k'arasa wajen zai haura stairs ya sanya hannun shi ya ture abin da ke hannun ta, ai kuwa gaba d'aya tayi baya ta zube haka foodflaks da plates din suka zube a k'asa na fashewa suka fashe, ko takan ta Sabeer bai bi ya haye stairs still kuma hawayen na zuba don ya kasa rik'e su zuciyar sai bugawa take da k'arfi kanshi yana mishi ciwo sosai. Duk wannan abin akan idon Alhj Ahmad aikuwa ya dad'a rud'ewa sosai ya bi bayan Sabeer da sauri, haka ma Mumy wadda take kitchen k'arar fad'uwar abu ya fito da ita da sauri hango tilon d'an nata tayi yayi upstairs kamar a fusace ga surukin ta yabi bayan shi ya sanya itama ta bisu cikin tashin hankali. Babu wanda ya kula 'yar aikin haka ta tashi cikin sanyin jiki da zafin fad'uwa ta fara tattara wajen da ya 6aci dakyar take aikin saboda ba karamin buguwa tayi ba da alama wani abin ne ya faru da d'an lelen don ba haka Sabeer yake musu ba sai dai idan ranshi ya 6ace shi da Jiddah su kad'ai ne masu kirki a gidan. Kai tsaye bedroom d'in shi ya wuce yana shiga ya rasa me yake mishi dad'i gaba d'aya zuciyar shi da idanun shi Suhaima suke son gani muryar ta suke son ji. "Bana son ka Sabeer bazan iya auren ka ba " Muryar Suhaima yaji cikin kunnen shi tamkar a lokacin take furta mishi hakan, runtse idon shi yayi da k'arfi yace "Nooo Suhaima sai kin so ni!" Ya k'arasa fad'in haka yana zubar da kayan saman dressing mirror a k'asa nan perfumes wasu suka faffashe, nan ya dawo cilli da pillows d'in kan bed da na sofa cikin lokaci kad'an ya hargitsa d'akin cilli yake da duk abin da ya samu saboda ya rasa yanda zai yi kuwwar muryar Suhaima ce take mishi amo a kunnen shi. Yana kok'arin zubewa a k'asa ne yaji an rik'o shi kallon wanda ya rik'e shi yake sai yaga Alhj Ahmad ne ga Mumyn shi kuma a gefe tana kuka hankalin ta a tashe sosai me yake damun Sabeer d'in ta, kwace jikin shi yayi ya samu k'asa ya zauna cikin tashin hankali Alhj Ahmad yace "Sabeer me......? " D'aga mishi hannu Sabeer yayi tare da cewa "ku fita ku ban waje " "What! Kana nufin zamu tafi mu bar ka a wannan halin? " Idanun shi sun ja haka fuskar shi ma ga hawaye suna zuba ya d'ago kanshi ya kalle shi, sai da gaban Alhj Ahmad da na Mumy ya fad'i ganin yanda Sabeer ya koma tamkar ba Sabeer d'in da suka sa ni ba. Cikin magana da k'arfi yace "Leave me alone please don't disturbing me". Yana gama fad'in haka ya sanya hannun shi dukka biyun cikin gashin kanshi yana hargitsawa su kuma kallon shi suke tamkar wasu sokaye sun rasa abin yi dakyar Alhj Ahmad ya zauna yana goge hawaye don ya d'auka Sabeer ya haukace haka Mumy ma kuka take sosai, sun dad'e a haka kafin ya tashi ya shige bathroom ya sakarwa kanshi shower, ya dad'e sosai a ciki kafin ya fito d'aure da towel. Ko'ina an gyara tsab tamkar ba yanzu ya gama hargitsa d'akin ba, kwanciya yayi kan bed yana tunanin ta inda zai fara shawo kan Suhaima don yafi jin haka fiye da shawo kan iyayen shi... Ya kuka ji page d'in nan, Sabeer kamar sabon kamu 😹 ya koma, ni Mumy da Alhj Ahmad sun fi ban dariya 😂 da suka sashi a gaba suna kuka, ina fatan zan ga Comment's, idan na samu Comment's da yawa zan k'ara muku 1 page anjima 😹 Aishat A Muh'd ✍ A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 44-45 Yana nan kwance kan bed idanun shi a lumshe hawaye ne har yanzu suke zuba gaba d'aya brain nashi ya d'auki zafi har ya kasa tunanin abin yi, banko k'ofar akayi da k'arfi aka shigo Hajjah Hauwaa ce ta shigo a matukar kid'ime bayan ta Alhj Ahmad, Mumy da Daddyn Sabeer ne suka k'arasa shigowa cikin bedroom d'in. Cikin kuka Hajjah Hauwaa ta k'arasa inda Sabeer yake kwance idanu a lumshe suna zubar da hawaye, fyace hancin ta tayi da hankycif d'in hannun ta kafin ta zauna saman drower na gefen bed, hannun Sabeer ta kamo cikin tashin hankali tace "Sabeer me yake damun ka?, wane ya 6ata maka rai?, ka sanar damu yanzu kaga irin mataki da zamu d'auka akan kowanne d'an mara mutunci ne, ka sanar da mu yanzu kaji d'an lele na ba wanda zai ta6a min kai ya kwana lafiya kowa ne maza ka sanar da ni...?" Shiru Sabeer yayi mata tamkar baisan da mutum kusa dashi ba, "Bana son ka Sabeer bazan iya auren ka ba" Maganar Suhaima ce take ta amsa kuwwa a kunnen shi tamkar yanzu take fad'i, hannu shi yasa ya damk'o zanin gadon da k'arfi tamkar irin mace mai nak'udar nan kafin ya furta "Suhaima ki so ni bazan iya rayuwa bake ba please idan kika baki soni ba mutuwa zan yi " Wayyo tashin hankali a wajen iyayen Sabeer da su Hajjah ba kad'an ba najin abin da Sabeer yake fad'a, hannu Hajjah Hauwaa ta d'ora saman kanta ga hawaye kace kace saman fuskar ta tana cewa "Hussein kuyi wani abin kai na shiga uku Sabeer ya haukace ko wata aljannar ce ta shafe shi " Abin da Hajjah ta fad'i ne yasa Sabeer bud'e jajayen idanun shi ya watsa mata wani kallo, ai tuni Hajjah tayi wani tsalle ta koma bayan Alhj Ahmad tana rawar jiki tare da zare idanu tana lek'en Sabeer ta d'auka fisgota zai yi ya shak'eta don da gani kasan baya cikin hayyacin shi. Ganin haka ya sanya Daddy kallon iyayen shi da Mumy wadda take shar6ar kuka yace "Abba ku d'an bani wuri zanyi magana dashi " Jikin a sanyaye suka fita daga bedroom d'in kowanne na sak'e sak'e cikin zuciyar shi. Bayan sun fita ne Daddy ya samu waje kusa da Sabeer ya zauna tare da janyo shi cikin jikin shi yana bubbuga bayan shi na rarrashi, sun d'an dad'e a haka kafin Daddy ya raba jikinshi dana Sabeer kallon shi yayi sannan ya janyo wata bottle d'in faro ya bud'e ya sanya wa Sabeer a bakin shi, ba musu Sabeer ya fara sha kafin ya d'auke bakin shi alamar ya isheshi ajiye bottle d'in yayi, ta6a jikin Sabeer yayi yaji har jikinshi ya d'auki d'umi alamar zazza6i yana son rufe shi. Cikin nutsuwa Daddy ya kalle shi kafin yace "me yake damun ka Son ka fad'a min damuwar ka ko da abin da zan iya taimaka maka? " Sai da Sabeer yayi shiru na tsayin lokaci kamar bazai yi magana ba kafin kuma ya bud'e baki yace "Daddy ko na fad'a maka matsala ta babu abin da zaka iya akai saboda ba irin ra'ayin ku ba ne" D'an shiru Daddy yayi cikin mamakin abin da Sabeer ya fad'a, kawar da mamakin yayi ta hanyar yin murmishi na kwantar da hankali kafin yace "Ka sanar da ni Son idan abin da ka fad'a min abin da zai yiwu ne why not mu baka had'in kai " Kai tsaye Sabeer yace "Daddy aure nake son yi kuma Suhaima nake so Daddy " Abin ya bawa Daddy dariya sai kawai ya murmusa sannan yace "Toh Sabeer ban da abin ka mene na damuwa kuma?, wace ce Suhaima?, me akai akayi ta fad'a min sunan Baban ta a fad'in Nigeria a gobe za'a d'aura aure " Kallon Daddy kawai Sabeer yake cikin zuciyar shi yana cewa lallai Daddy bakasan wace Suhaima ba ita ba 'yar kowa bace amman ta fita daban da sauran mata sannan kud'in bazai iya siyan ra'ayin ta ba....... Katse mishi tunani Daddy yayi ta hanyar rik'o hannun shi yace "Son wace Suhaima tell me? " Cikin muryar damuwa Sabeer yace "Daddy bata sona bazata iya aure na tace min" "K'arya take yi Son dole ta soka kuma ta aure ka, fad'a min ita wace zata kalli idon d'ana tace batason shi, fad'a min wane Ubanta? " Daddy ya k'arasa fad'in haka rai a 6ace. "Daddy Suhaima ba kowa bace haka iyayenta bakowa bane infact ita a k'auye take renon k'auye ce" "What! Son me kace, kasan abin da kake fad'a? " Daddy ya fad'i hakan yana tashi tsaye, tashi Sabeer shima yayi tsaye babu alamar tsoro ko fargaba yace "Yes! Daddy nasan abin da na fad'a kuma ina cikin hayyaci na " "Bazai yiwu ba Son ka sake nemo wata amman sam wannan yarinyar bata dace da kai ba 'yar talaka ce kuma 'yar k'auye bata da ilimi ko kad'an bazan iya had'a zuri'a da ita, kai kad'ai Allah ya bani bazan iya zuba ido naga kayan takaicin nan ba don haka ka sake tunani! " Cikin tsantsar 6acin rai da abin da Daddy ya fad'a yasa Sabeer naushin dressing mirror da k'afar shi da k'arfi wanda sai da tayi k'ara tsabar had'uwar kafar shi da katakon dressing mirror wata k'ara mai razanar wa Sabeer ya saki da sauri Daddy ya juyo a razane da sauri ya k'arasa wajen Sabeer zai rik'e shi "Don't touch me! " Ya fad'a cikin wata irin voice, hankalin Daddy ya tashi sosai cikin rarrashi yace "Saboda na hanaka auren yarinyar nan zaka nakasta kanka Sabeer? " Idanun shi na tsiyayar hawayen kallon shi yake cikin ido kafin yace "Idan baku barni na aureta ba zan iya mutuwa ma Daddy!" A matak'ar razane Daddy yake kallon d'an nashi cikin wani irin yanayi na tsantsar tashin hankali. Sabeer bai k'ara kallon inda Daddy yake ba ya fara tafiya cikin d'ingisa d'ayan k'afar nashi wanda ya dakidaki dressing mirror da ita, yana runtse ido saboda azaba da haka ya shiga bathroom yana shiga ya kunna shower ya rasa yanda zaiyi sai kawai ya fashe da wani irin kuka yana bubbuga jikin bango da hannun shi ga ruwa yana zuba a kanshi da jikin shi. Ya d'auki lokaci mai tsayi kafin ya fito k'afar shi ta isheshi da zugi da azaba ji yake tamkar ya cireta dakyar ya iya sanya kayan shi ya kwanta saman sofa fuskar nan tayi ja da ita saboda tsabar kuka, a haka wani wahalallen bacci yayi awon gaba dashi. Azabar da k'afar shi ya dame shi da ita ne yasa shi farka wa daga baccin da ba wani jin dad'in shi yake ba, kallon k'afar yayi yaga ta kumbura sosai tamkar ba k'afar shi ba, tsura mata ido kawai yayi yana kallo, yana jin an bud'e k'ofar d'akin an shigo. "Subhnallah Son haka k'afar ka ta koma? " Bai kalle shi ba balle yasa ran zai amsa mishi, ganin haka yasa Daddy d'auko wayar shi ya kirawo mai gyaran k'afa tare da kiran family doctor d'in su Kafin ya ajiye wayar ya zubawa Sabeer ido yana kallon shi, ya hana kowa shigowa inda yake amman dukkanin su suna parlour a zaune Mummy da Hajjah sun sha kuka sun more yak'i sanar musu da ainahin abin da Sabeer ya fad'a mishi saboda yasan ba k'aramin ruguntsumi za'a sha ba. Suna zaune har mai gyaran k'afa yazo bayan ya shigo d'akin sun gaisa da Daddy zai ta6a k'afar Sabeer ya janye ta da sauri tare da cewa "Bana buk'ata a duba min" "Haba Son taya ga ciwo a jikin ka kak'i yarda a duba maka, kayi hak'uri a duba maka please " Duk wani rarrashi da lalla6a Daddy yayi wa Sabeer amman yak'i yarda har Doctor d'in da Daddy ya kirawo yazo amman duk Sabeer yak'i yarda gashi k'afar dad'a kumbura take, Daddy kasa jure ganin tilon d'an shi a haka yayi don haka ya bud'e baki yace...... Mu had'u next page fan's, naga Comment's naku na jiya sosai naji dad'i Allah ya bar k'auna. Aishat A Muh'd ✍🏻 A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 46-47 Daddy kasa jure ganin tilon d'an nashi a haka yayi don sam bazai iya ganin Sabeer cikin mawuyacin hali ba don haka ya bud'e baki yace "Ammm ku d'an bamu wuri zamu yi magana da Sabeer please idan muka gama zan kirawo ku" Tashi suka yi suka fita kafin Daddy ya matso kusa da Sabeer ya dafa kafad'ar shi da hannun shi d'aya, zame hannun Daddy yayi tare da juyawa ya kalli wani 6ari daban, d'an murmishin yak'e Daddy yayi wai yau Sabeer d'in shi akan soyayya yake juya mishi baya wannan wanne irin so yake mata, bar tunanin yayi ta hanyar cewa "Son look at me please" Fuska a had'e Sabeer ya jiyo yana kallon Daddy sai wani had'e rai yake. Girgiza kai kawai Daddy yayi kafin yace "Son bazan iya jurar ganin ka cikin wannan yanayin ba, na amince ka auri wannan yarinyar sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba tace maka bata son ka ya za'a yi? " Tuni fuskar Sabeer ta fad'ad'a da wani irin fara'a na tsantsar farinciki saboda jin abin da Daddyn shi yace, rungume shi yayi cikin dariya mai hawaye yace "Thank U Daddyna nasan kai mai k'aunar farinciki na ne duk abin da nake so kana kok'arin yi min, sannan zan tafi inda Suhaima take nayi rayuwa irin tasu don na sami soyayyar ta A SANADIN SON Suhaima zan iya jure duk wata wahala Daddy indai zan same ta " Kallon shi Daddy yake kawai cikin d'umbin mamakin abin da Sabeer ya fad'a ajiyar numfashi yayi kafin yace "Son kana nufin k'auyen zaka koma da rayuwa, kaci irin abincin su, ruwan su ka kwana irin d'akin su?" "Yes Daddy zan iya indai zan samu Suhaima " 6ata fuska Daddy yayi tare da cewa "ina Son bazai yiwu ba, kaje dai ka taho dasu ita da Family d'in ta zan basu gida da kud'i sosai sannan na bawa mahaifin ta aiki amman kaje k'auye kana matsayin jikan mafi soyuwa acikin family d'in d'an fillo kaje ka zauna a k'auye haba Son " D'an yatsina fuska yayi tamkar zai fashe da kuka yace "ni dai zan iya Daddy idan naje zanyi musu maganar dawowa nan da abin da zaka yi musu nasan zasu biyo ni " Girgiza kai Daddy ya fara alamar bai yarda ba, aikuwa Sabeer ya ta6e fuska irin ta shagwa6a66un yaran nan zai fashe da kuka da sauri Daddy ya rungume shi yana bubbuga bayan shi yace "Nooo Son don't cry please na amince Allah ya baka nasarar sace zuciyar ka kamar yanda ta sace maka zuciya lover boy" Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Sabeer, kafin ya saki wani murmishi cikin zuciyar shi yana cewa ganin tafe zuwa gare ki Suhaima, rungume Daddy yayi cikin farinciki yace "Thank U so much Daddy i am proud of U" Bubbuga bayan shi Daddy yayi kafin yace "Don't worry Son farinciki ka shine nawa all the best" "K'arya kake Sabeer daman akan 'yar talaka 'yar k'auye kake wannan haukan duk ka d'aga mana hankali, danasan saboda haka kayi wannan abin da wallahi bazan zo wajen ka balle har na zubar maka da hawayen tausayi " Gaba d'aya suka jiyo a matukar razani daga Daddyn har Sabeer d'in had'a ido suka yi da Mummy tana tsaye sai faman sauke numfashi take fuskar nan ko kad'an babu fara'a. "Nima ina goyan bayan ta bazan ta6a zuba ido ya auro mana 'yar matsiyata ba daman akan haka kake wannan haukar to ko zaka mutu baza mu ta6a yarda ba, amman Sabeer ka bani kunya da mamaki, kai ma Hussein ka ban kunya da ka amince da buk'atar shi " cewar Hajjoh cikin tsananin 6acin rai. Alhj Ahmad d'an fillo kuwa ya kasa magana ma saboda tsantsar 6acin rai har wani rawa fuskar shi take lol, saboda 6acin rai magana ma ya kasa yi. Had'e fuska Sabeer yayi alamar ba wasa ya mik'e tsaye yana d'ingishi ya k'arasa wajen Hajjah yace "Hajjah kada ki k'ara kiran Suhaima da 'yar matsiyata ni Suhaima nake so ba ruwana da kud'in su don haka sai na aure ta babu wanda ya isa ya hanani! " Tasss Sabeer yaji saukar zazzafan mari a saman kuncin shi wanda tunda Mumy ta haifo shi ba'a ta6a marin shi ba, marin ba k'aramin shigar shi yayi ba don sai da gefen bakin shi ya fashe kad'an jini ya fito, dafe kumatun shi yayi cikin mamaki ya d'ago kanshi ya kalli wanda ya mare shi ba kowa bane sai Alhj Ahmad d'an fillo sai huci yake zuba kamar wanda ya had'iyi kunama har da had'a gumi tamkar babu ac da fanka a bedroom d'in yayin da Daddy, Mummy da Hajjah suka kusan suman tsaye tsabar kid'ima da abin da akayi wa Sabeer. Yana dafe da kumatun shi yana kallon Alhj Ahmad kafin kuma ya lumshe idon shi sai gani suka yi yayi baya luuu zai fad'i k'asa cikin zafin nama Alhj Ahmad da Daddy suka taro shi ya fad'o jikin su. Daddy jiki na rawa ya d'auko wayar shi ya kirawo Doctor, Hajjah da Mumy kuma kuka suka sanya tare da zube wa kusa da inda Sabeer yake suna cewa "Sabeer ka tashi please " Daddy ne ya d'auke shi ya d'ora kan bed da taimakon Doctor ya shigo don Alhj Ahmad zube wa yayi a k'asa yayi zaman 'yan bori hannun shi yake bi da kallo wanda ya mari Sabeer dashi tamkar wani soko haka yake kallon hannun, wai shi yau ya mari Sabeer mafi soyuwa cikin zuciyar a gaba d'aya cikin jikokin shi, anya shine kuwa da hankalin shi ya aikata wannan abin ko dai mafarki yake yi ba gaske ba ne kamar wani mutum mutumi haka ya koma ya rasa me zaiyi ma. Dakyar Daddy ya lalla6a su Mumy da Hajjah suka fita don a bawa Doctor damar duba Sabeer haka Daddy yazo ya janye Alhj Ahmad dakyar suka fita tare da jan k'ofar bedroom d'in. Likita yana cikin duba Sabeer yaga ya bud'e idon shi tare da tashi ya zauna cike da mamaki Doctor yake kallon shi, kamo hannun likitan Sabeer yayi sannan yace "Doctor ina son abin da zan fad'a maka yanzu ka sanar da iyaye na bana son a samu matsala fah" Gid'a kai likita yayi kafin yace "Okay baza'a samu matsala ba insha Allah " A hankali Sabeer ya matso kusa da likitan kafin ya fara yi mishi magana cikin k'asa k'asan murya, bayan ya gama yi mishi maganar ne ya koma ya kwanta tare da rufe idon shi. Suna zaune jugum jugum a parlour kowannen su ya rafka tagumi suna tunani ba mai yin magana a tsakanin su, k'arar bud'e door suka ji da sauri suka mik'e tsaye tare da nufar Doctor da sauri kowanne na jefo mishi tambayar jikin Sabeer. D'an share zufa likitan yayi yayi shiru baiyi magana ba, cakumar wuyan shi Alhj Ahmad yayi tare da cewa "Kai wanne irin wawa ne muna maka magana ya jikin Sabeer zaka zuba mana ido kana kallon mu kamar ka samu tv" Ba k'aramin shak'a likita yasha ba dakyar Daddy ya cire hannun Alhj Ahmad daga wuyan shi, kafin yace "Abba mu bi a hankali please " Zama suka yi sannan likita ya shafa wuyan shi tare da jujjuya shi yace "A binciken da nayi damuwa ce tayi wa Sabeer yawa sosai wanda a yanzu yana d'auke da hawan jini, idan kuka cigaba da matsanta mishi da 6acin rai ko ku k'i mishi abin da yake so idan ranshi ya 6aci zuciyar shi zata iya bugawa na lokaci d'aya don haka ku kiyaye " "K'arya kake zuciyar Sabeer bazata ta6a bugawa ba " Cewar Alhj Ahmad cikin tsawa gaba d'aya hankalin shi a tashe yake, "a cigaba da kwantar mishi da hankali a bashi abin da yake so, zanje na kawo maganin da zai sha yanzu " Babu wanda ya kula shi haka ya zame ya tafi sannan suka shiga cikin d'akin inda Sabeer yake kwance, nan Alhj Ahmad ya zauna kusa dashi tare da rik'o hannun Sabeer yana mai nadamar abin da yayi mishi, a lokacin Daddy ya kirawo mai gyaran k'afa ya fara gyarawa Sabeer kafar shi kuka sosai Sabeer yasha shi a lokacin haka Hajjah da Mummy tare da Alhj Ahmad sun zubar mishi da hawayen tausayi Daddy ne kawai yayi dauriya ta rik'e Sabeer har aka gama gyara mishi kafin daga k'arshe wani wahalallen bacci ya sake d'aukan shi sai sauke ajiyar zuciya yake....... Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz Dis page is dedicated to my Biebie dee ina tayaki murnar k'arin shekara Allah ya k'aro shekaru masu albarka Allah ya baki miji nagari wanda zai kular mana dake muzo musha biki 💃🏻😍😅. _fan's kuyi hak'uri akan rashin yi muku typing kwana 2 akwai uzirin da ya dakatar da ni but yanzu insha Allah zan cigaba da yi muku daidai iyawata, inason ku oll my fan's_❣ *PAGE 48-49* Sai after mangarib Sabeer ya tashi daga wahalallen baccin da ya d'auke shi, lokacin da ya tashi zugin k'afar ya ragu babu laifi nan ya yunkura ya tashi bathroom ya shiga alwala yayi ya fito yana d'ingishi haka ya gabatar da sallahr la'asar da ta tsere mishi tare da mangarib, bayan ya idar ya zauna yin addu'o'in neman za6in Allah akan neman auren Suhaima, da haka har aka kirawo sallahr ishsha ya gabatar. Bayan ya idar ne ya tashi ya shiga bathroom wanka yayi da ruwa mai d'umi kafin ya fito ya shirya cikin sleeping dress koma wa yayi ya kwanta a ringingine ya fad'a kogin tunani, ta yanda zai tunkari k'auyen su Suhaima don neman soyayyar ta, yana cikin haka 'yan uwan shi da k'annen Daddy da kuma matansu suka shigo duba Sabeer, dakyar ya iya k'ak'alo yak'en dole ya sanya saman fuskar shi yana amsa musu sannun da suke mishi, kowanne fuskar shi da tausayin Sabeer ganin yanda k'afar shi ta kumbura sai wurin 9 na dare suka bar bedroom d'in nashi wanda har zuwa lokacin ba ga Mumyn shi ba da Hajjah. Bayan fitar su babu dad'e wa Daddy ya shigo bedroom d'in bayan shi kuma 'yar aikin Mumy ce da babban plate a hannun ta saman shi cike da kaya ajiyewa tayi saman k'aramin table d'in d'akin sannan tayi wa Sabeer sannu da jiki ko amsawa bai yi ba ta fita don shi ba wannan ne a gaban shi ba. "Son ya kake jin jikin naka?" D'an yatsina fuska yayi kafin yace "Daddy na samu sauk'i" D'an ajiyar zuciya Daddy ya saki tare da cewa "Allahmdullilah Son naji dad'in abin da ka ce, oya zo kaci abinci nasan rabon ka da abinci tun breakfast da kayi " Girgiza kai Sabeer yayi tare da cewa "Na k'oshi Daddy" D'an zaro ido yayi tare da cewa "What! Son kanason illata kanka ne? " Sai kuma ya sassauta murya cikin sigar rarrashi yace "Haba Son tun da na amince da buk'atar ka ya kamata kaci wani abin zan jure duk wata matsala da zan fuskanta a wurin Abba, Hajjah da kuma Mumyn ka duk don farincikin ka ". Kallon Daddy yayi sai yaga kamar ya fad'a a fuskar shi wani tausayin Daddy ne ya kama Sabeer har yana kok'arin fitar da kwalla duk don farincikin shi Daddy ya zama haka, yasan yanda bai ci wani abincin kirki ba yinin yau haka shima ya zauna. Tashi tsaye Sabeer yake kok'arin yi da sauri Daddy ya taimaka mishi ya tashi tsaye zuwa saman kujera wanda kujeru guda biyu ne kacal daga gefe tsakiyar su kuma table ne nan Daddy ya zaunar da Sabeer a d'aya daga cikin kujerar, sannan shima ya zauna a baki ya fara baiwa Sabeer abinci haka shima Sabeer yake bawa Daddyn shi a baki. Bayan sun kammala ci ne Daddy ya lalla6a Sabeer yasha maganin shi don sam baya k'aunar shan magani, k'ofar bedroom d'in aka bud'e aka shigo kallo d'aya Sabeer yayi mata ya d'auke kanshi gaban shi yana fad'uwa, Mumy ce ta shigo fuskar ta a had'e babu alamar fara'a bata yiwa kowa magana ba ta wuce bathroom babu dad'ewa ta fito hannun ta rik'e da wani d'an madaidaicin bowl ruwan d'umi ne a cikin shi sai wani small towel a hannun ta. Inda Sabeer yake ta nufa tana zuwa ta zauna kan carpet tare da d'aukan k'afar Sabeer mai ciwon ta d'ora saman k'afar ta, towel d'in ta sanya cikin ruwan d'umin ta fara gasa k'afar Sabeer, daga Sabeer har Daddyn babu wanda ya samu fuska wajen Mumy balle su yi mata magana, runtse ido Sabeer yayi wani rad'ad'i da zafi yana shiga cikin zuciyar shi gefe d'aya na cikin zuciyar shi kuma yana tunanin hanyar da zai bi ya shawo kan Mumyn shi ta hak'ura ta kar6i Suhaima matsayin surukar ta. Bayan ta gama gasa mishi k'afar ne ta d'auko wani cream ta shafa mishi a k'afar sannan ta sauke ta a hankali daga kan k'afar ta kafin ta yunkura ta mik'e tsaye ta kwashe kayayyakin da tayi amfani dasu zata wuce kenan. "Mumy! " Taji saukar muryar d'an nata mafi soyuwa cikin zuciyar ta, runtse ido tayi wasu hawaye na kok'arin zubo mata amman sai ta had'iye su ta wuce toilet da sauri ta ajiye bowl d'in da towel kafin ta fito tabar d'akin da sauri. "Kada kayi kuka Son zan rarrashi Mumyn ka" "Daddy Mumy tana fushi da ni " Cikin rarrashi Daddy yace "Mumyn ka bazata iya fushi da d'anta ba abin da yake sone baiyi mata shi yasanya ta 6acin rai but nasan zata huce bazata iya jure fushi da yaron ta ba kamar yanda nima na kasa jurewa" Gid'a kai Sabeer yayi kawai, suna cikin haka Alhj Ahmad d'an fillo ya shigo d'akin sannu yake yiwa Sabeer amman bai kalli inda yake ba da yaga yana kok'arin ta6a shi ma sai ya tashi yana d'ingishi ya bud'e kofar baya ya fita ko kallon shi bai yi ba. Da kallo duk suka bishi na mamaki kafin Alhj Ahmad ya zauna yana goge gumi na tashin hankali yace "Hussein anya yarinyar nan ba asiri tayiwa Sabeer ba? " D'an murmishi Daddy yayi kafin yace "Abba ba wani asiri asali ma yarinyar bata son shi " D'an zaro ido Alhj Ahmad yayi kafin yace "Batason shi kamar yaya? Kana nufin Sabeer ne kawai yake son ta? " "Ehh Abba so yake yaje neman soyayyar ta " Cire hular kanshi d'an fillo yayi yana firfita da ita don wani gumi da ya keto mishi na tashin hankali, daman ashe Sabeer son maso wani yake wanda ake ce mishi k'oshin wahala innallahi, tuni jikin Alhj Ahmad yayi mugun sanyi da yaji jarrabar da Allah ya d'orawa jikan shi na son maso wani gashi yarinyar 'yar k'auye shi yanzu mene mafita?. Shiru suka yi gaba d'aya babu mai yin magana a tsakanin su har wurin 10:30 suna zaune jigum jigum suna jiran shigowar Sabeer amman bai shigo ba haka suka tashi suka bar bedroom d'in kowanne zuciyar shi cike da tunani kala kala. Wasa wasa yanzu gaba d'aya Sabeer baya kula Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah, Daddy kawai yake kulawa kawai Mumy kuma bata shiga harkar shi sai dai zata zo ta gasa mishi k'afa sau biyu ta sanya mishi magani, tsakanin ita da Sabeer bansan wanda yafi wani ramewa ba a tsakanin su, ta 6angaren Daddy kuma yana ta kok'arin shawo kan Mumy ta amince don samin farincikin tilon d'an su amma tak'i yarda da maganar tashi ko baccin kirki bata iyayi saboda tunanin tilon d'anta ta rasa samun mafita don mafitar ta d'aya ta bari Sabeer auren Suhaima kuma sam abin da bazai ta6a yiwu ba. Alhj Ahmad d'an fillo kuwa ya rasa samun sukuni don Sabeer bayayi mishi koda shi yayi mishi magana bazai kalli inda yake ba balle ya amsa mishi k'arshe ma sai Sabeer ya bar mishi wurin, duk yanda ya so Sabeer ya saurare shi yak'i bashi had'in kai da wani cikin jikokin shi da tuni yayi watsi da al'amarin amman Sabeer kuwa na daban ne son shi cikin zuciyar shi mara adadi ne, tun kafin a haifi Sabeer yake nuna wa cikin so har aka haife shi a kullum son Sabeer k'ara yawa yake cikin zuciyar shi. Duk yabi ya rame ya fad'a ga mafarkin da yake da Sabeer da wata kyakkyawar yarinya duk mafarkin da zai yi da wannan yarinyar yake ganin su da Sabeer, gashi Sabeer yana kuka yana rok'an ta da ta so shi amman sai tayi tafiyar ta, gaba d'aya d'an fillo ya hankalin shi a matuk'ar tase yake don ganin irin mafarkin da yake. A haka aka d'ibi sati biyu cikin wannan yanayin alokacin Sabeer k'afar shi ta warke sosai duk babu kumburin ya koma tafiyar shi normal babu d'ingishi, har zuwa lokacin Mumy bata yi magana ba Daddy kullum cikin lalla6a ta yake. "Daddy tun da na warke kayi min izinin tafiya wajen Suhaima " Sabeer ya fad'i hakan cikin marairaice fuska, d'an shiru Daddy yayi yana tunani don rasa ta inda zai fahimtar da Sabeer cewa Mumyn shi bata amince da hakan ba da kuma Abbah da Hajjah, yana shirin bud'e baki yayi magana yaji ance "Hussein basai kayi tunani ba ni na bawa Sabeer izinin tafiya wajen masoyiyar shi neman soyayyar ta na amince Sabeer ya tafi domin samun farincikin shi " Da sauri suka jiyo suna kallon D'an fillo a tsaye yana murmishi daga ni na yak'e ne ba'a son ranshi ya fad'i hakan ba, ba har cikin zuciyar shi ya furta hakan ba amman Sabeer da Daddy saboda farinciki sam basu d'ago shi ba, da gudu Sabeer yaje ya rungume D'an fillo yana dariyar farinciki wata ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali D'an fillo ya sauke jin Sabeer rungume dashi yaushe rabon da Sabeer ya rungume shi, yaushe rabon da yaga dariyar shi haka duk so ya canja shi tamkar ba Sabeer d'in da ya sani ba. "Thank U so much kakanah! " Ya k'arasa fad'i yana bashi peck a kumatun shi, dad'i ya ishi D'an fillo jin Sabeer d'in shi cikin farinciki kamo hannun shi yayi ya rik'e tare da cewa "Ka yafe min marin da nayi maka Sabeer nayi regretting akan haka" Girgiza kai Sabeer yayi yana murmushi yace "Kada ka damu Abbah ya wuce " Sake rungume Sabeer yayi yana bubbuga bayan shi. "Ni an mance da ni da.... " Daddy ya k'arasa maganar da hannun shi na alamar shima ayi hugging nashi, da sauri d'an fillo ya janyo shi ya had'asu ya rungume su acikin jikin shi. Sun jima a haka kafin su rabu da juna nan Sabeer ya mak'ale jikin D'an fillo yana zuba mishi shagwa6a son ranshi shi kuma yana lalla6a shi, dariyar yak'e kawai D'an fillo yake yi, sun jima suna hira kafin kowa ya tafi ya kwanta zuciyar Sabeer fal farinciki a wannan daren yayi baccin da ya jima bai yi ba. Washe gari da safe ya tashi saboda d'oki da kanshi yake had'a kayan shi cikin trolley bags nashi saboda zumud'i saboda a yau yake son tafiya zuwa k'auyen su Suhaima ya fara fayyace mata abin da yake damun shi. Bayan ya gama had'a kayan ne ya d'auki phone nashi ya kirawo Jiddah maganar mintuna biyar yayi da ita ya kashe wayar, saboda tsananin mamaki Jiddah kusan sumen zaune tayi na jin inda Sabeer yake neman address a wurin ta na gidan su Suhaima, tura mishi tayi ta message saboda ita ma sauri take a yau jirgin su zai tashi zuwa yawan honeymoon wanda gama wayar ta da Suhaima kenan Sabeer ya kirawo ta kanta ya d'aure sosai amman ta bar komai sai sun dawo tukunna. Zaune Sabeer yake durk'ushe gaban Mumy cikin bedroom nata, gwiwar shi a k'asa ya sanya hannun shi saman k'afar ta idanun shi hawaye ne yake fitar wa, gama shiryawar shi kenan zai tafi ya shigo bedroom d'in ta cikin rawar murya ta kuka yace "Mumy nah! Ki yafe min kisa min albarka tare da yi min addu'ar samun nasara tafiya da fushin ki ba k'aramin barazana zai zame min ba" Juyar da kanta gefe tana share hawayen fuskar ta, Daddy da shigowar shi kenan shima yabi sahun yanda Sabeer yayi yana cewa "Sweetheart kiyi hak'uri ba laifin Sabeer ba ne so ne kiyi mishi fatan samun nasara please " Jiyowa tayi ta kalli Sabeer da Daddy da suke durk'ushe a gaban ta wani kwarjini da cika ido d'a da uban suka yi mata ta rasa me zata ce bakin ta yayi mata nauyi ta kasa bud'e shi tayi magana. Rarrashin ta da lalla6awa Daddy ya dunga yi wa Mumy sun dad'e a haka kafin Sabeer cikin dashashshiyar murya yace "Mumy ki taimaka wa rayuwata please kada na mutu" Kallon shi tayi da sauri gaban ta yana fad'uwa idanun shi sun yi ja suna fitar da hawaye, "please Mumy nah! " Ya fad'a can k'asan mak'oshi, Mumy ta gaji da jin wannan maganar a wurin Sabeer ta gaji da ganin fitar hawaye a idanun d'anta, hannun ta yana rawa kamar mai jin tsoron ta6a abu ta d'ora hannunta saman gashin kan Sabeer tace "Ka tafi Sabeer kaje Allah ya kare min kai " Basu yi tsammanin jin wannan maganar a bakin ta ba don haka sai suka tsaya suna kallonta kamar was7 sokaye, d'an murmishin yak'e tayi hawaye na fita a idanun ta tace "Ka tafi kada yamma tayi maka ka kula da kanka " Rungume ta yayi cikin farinciki shi da Daddy suna zuba godiya kafin Daddy ya rik'o hannun ta zuwa compound d'in gidan Sabeer na rik'e da d'ayan hannun Mumyn, gaba d'aya family na D'an fillo sun fito suna sallama da Sabeer, sai da Sabeer ya bisu one by one yana rungume na sallama, sannan daga k'arshe driver ya bud'e mishi kofa ya shiga mota idanun shi akan iyayen shi yana kallon yanda Mumy ta fad'a jikin Daddy tana kuka. Kauda kanshi yayi suna nan tsaye driver yaja motar suka fita daga gidan, kowa yana mamakin saukowar Alhj Ahmad d'an fillo har ya amince da buk'atar Sabeer wasu sun tausayawa Sabeer don sunsan Sabeer bazai jure zaman k'auye ba yayin da wasu kuma suka cika da farinciki daman a rayuwa dole ka samu mai tausaya maka idan kana cikin damuwa wasu kuma a lokacin zasu yi farinciki da ganin ka cikin haka..... Hmmm fan's ya kuka ga wannan page d'in? Anya Mumy da D'an fillo da Hajjah har cikin zuciyar su suka aminta da tafiyar Sabeer kuwa?. Sai ku biyo ni next chapter don jin yanda zaman shagwa6a66en nan zai kasance cikin karkarar k'auye koya zata kasance? Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey SaNaz Ina kike Khadijah Neenah cool wannan shafin naki ne kyauta na murnar taya ki kammala littafin ki mai suna WASU MAZAN.. Hak'ik'a kin fad'akar damu ya kuma nishad'antar Allah ya k'ara basirah da k'arfin ido, ina miki fatan Alkhairi! ❣ PAGE 49-50 Bayan tafiyar Sabeer Mumy kasa danne kukan ta tayi da gudu ta wuce side d'in su bedroom ta shige ta hau kuka sosai na tausayin halin da Sabeer zai shiga da kuma kukan takaici da bak'in ciki akan wata banza 'yar k'auye d'anta kamar Sabeer zai tafi neman soyayyar ta. Da haka Daddy ya shigo ya fara rarrashin ta bayan ya janyo ta jikin shi, dakyar ta shiru tana sauke ajiyar zuciya, sai da Daddy yaga tayi bacci sannan ya kwantar da ita ya fita duk jinshi yake babu dad'i na tafiyar Sabeer. Daddy yana fita daga bedroom d'in Mumy ta bud'e idanunta tare da sakkowa daga saman bed dama tayi hakan ne don Daddy ya fita ya bata waje, tana son ta samu nutsuwar da zatayi tunani na d'aukan mataki akan shegiyar yarinyar nan da zuri'ar ta don sam bazata ta6a amince wa Sabeer ya auro mata d'iyar talakawa ba, talakawan ma na k'auye wanda basusan komai ba sai nemo da kiwo inaaa abin da bazai ta6a yiwuwa ba, daman ta barshi ne don kafin ace za'a yi auren tasamu mafita haka ta tsunduma a tunani sosai na samun mafita kuma bazata yi abin da Sabeer da Daddyn shi zasu zargeta da hana wannan auren ba. ***** ***** ***** Suna tafiya a mota Sabeer kuma ya kwanta tare da tukunkune jikin shi waje d'aya tamkar mai jin bacci, hawaye ne suke fita a idon shi yana kewar iyayen shi yana kuma tunanin yanda zaman shi anan zai kasance shin Suhaima zata kar6e shi matsayin masoyin ta sannan ya 'yan uwanta zasu kar6e shi matsayin mai son 'yarsu, wannan tunanin shi yake dad'a dagula lissafin Sabeer kada su kore shi su hanashi Suhaima tsoron shi d'aya kada su hanashi neman soyayyar Suhaima. Sai da driver yazo wurin da suka ta6a had'uwa da Suhaima anan Sabeer ya bashi umarnin tsayawa, bayan yayi parking ne sosai Sabeer ya tsaya yana kallon wurin yana tuna wani al'amari da ya ta6a faruwa a wajen har wani murmishi ne ya su6uce mishi. Nan Sabeer ya yiwa driver magana akan ya fito mishi da kayan shi, bayan driver ya fito dashi ne nan Sabeer yace mishi ya koma gida, yana nan tsaye driver yaja motar ya tafi zuciyar shi fal tausayin Sabeer don yasan bazai ta6a iya zaman wannan k'auyen mai kama da daji ba nan cikin zuciyar shi yayi mishi addu'ar fatan dacewa. Sabeer ya d'an jima a wajen yana dad'a nazarin wajen gaban shi na fad'uwa saboda ganin garin ya fara d'an duhu don dab ake da akirawo sallahr mangarib. Wani d'an saurayi ne yazo zai shige Sabeer ya rasa ta yaya zai mishi magana da yaga yana kok'arin wuce shi ne yasa shi yin kar6in hali yace "Assalamu Alaikum" D'an jiyowa yayi ya kalli Sabeer kafin ya tsaya nesa kad'an dashi yace "Waalaikumussalam " "Ammm inason zan yi mata tambaya please " Saurayin cikin mamaki ya ke kallon shi don bai zaci Sabeer yana jin hausa ba ya d'auka bature ne ko balarabe yazo yin wani abin a k'auyen nasu. "Allah yasa na sani" D'an sauke numfashi Sabeer yayi tare da cewa "Don Allah ko kasan gidan wani uhm... " Ya d'an yi shiru kad'an yana tuna sunan Yayan Suhaima da Jiddah ta sanar dashi d'an murmishi ya saki tare da ya tuna sunan yace "Yawwa sunan shi Aliyu yana da k'anwa Suhaima kuma manomi ne " D'an murmishi saurayin yayi kafin yace "Na gane shi nasan gidan " Wani sanyin dad'i ne ya kwararanya cikin zuciyar Sabeer cikin murna yace "Yawwa don Allah taimaka min ka kaini gidan " "To shikenan " Nan saurayin yayi gaba Sabeer kuwa sai ya tsaya kamar an dasa shi ta ina zai iya d'aukar trolley d'in nan, ganin Sabeer ya tsaya yasa saurayin dawowa yace "Lafiya? ". "Ko zaka iya taimaka min da trolley d'in bazan iya d'auka ba please " Saurayin bai yi mamaki ba don kallo d'aya zaka yiwa Sabeer kasan cewa d'an hutu ne, d'an murmishi yayi tare da kinkimar jakar, nan Sabeer ya rataya jakar laptop d'in shi suka tafi, tun ana tafiya ba'ayi nisa ba Sabeer ya fara gajiya ga wani uban tsoro da ya mamaye zuciyat shi ganin babu gidaje sosai, amman suna dad'a gaba sai ya cika da mamaki da yaga sun shiga wata unguwa duk gidaje sosai ba kamar inda suka baro ba. A k'ofar wani gida yaga sun tsaya saurayin yace "Ga gidan nan " "Yawwa sannu thank U so much " Nan ya shigar mishi da trolley d'in cikin zaure ya ajiye, laluba aljihun shi Sabeer yayi na jeans ya zaro 1k ya mik'a mishi tare da cewa "Gashi abokina na gode sosai but ka kar6a don Allah " Hannu biyu saurayin yasa ya kar6a tare da zuba godiya har zai wuce da sauri Sabeer yace "Hmm jimana abokina ya sunan ka? " D'an murmishi yayi tare da cewa "Sunana Ashiru kuma ga gidan mu nan " Ya k'arasa fad'i yana nunawa Sabeer gidan su wanda gida d'aya ne tsakanin su da na Suhaima. "Ni kuma Sabeer " "Sunan ka mai dad'i irin na 'yan birni " Dariya ya bawa Sabeer wanda ya sanya sai da ya d'an yi murmishin dariya saboda ya kula zai yi abin dariya, daganan ya wuce ya tafi Sabeer kuwa babu neman isowa ya kutsa kai cikin gidan tamkar irin gidan nan nasu. Suhaima tana zaune kan wani dutse tana alwala ta sallahr mangarib, ga Aunty Aliya kuma tana kok'arin sauke miyar abincin dare kenan daga saman murhu suka yi wata sanyayyar murya tayi musu sallama. Amsawa Aunty Aliya tayi yayin da Suhaima ta tsinci kanta da bugawar zuciya na lokaci d'aya, kafin su ankare sunga mutum a filin tsakar gida a tsorace Aunty Aliya ta kalle shi yayin da Suhaima ta kusan zubewa a k'asa saboda tsabar kid'ima da tsorata na wanda ta gani a k'auyen su kuma cikin gidan su. "Malam lafiya wa kake nema " D'an murmishi yayi tare da d'auke idanun shi daga kallon Suhaima ya dawo dasu kan Aunty Aliya yace "Nazo neman Suhaima ne sunana Sabeer " "Suhaima kuma? " Aunty Aliya ta furta hakan tana kallon Sabeer kafin ta jiyo da kanta zuwa kallon Suhaima wadda jikin ta yake rawa na tsorata. "Eh Suhaima nake nazo nema, idan babu damuwa zanyi sallah sai nayi miki bayanin ko ni waye? " Aunty Aliya sai tsoron nata ya ragu don kallon da tayi wa Suhaima ta karance ta tsaf alamar tasan shi amman tayi mamaki sosai na yanda Suhaima ta iya 6oye mata abu, don haka sai tace "Toh ai babu damuwa " Nan ta je inda suke ajiye botocin gidan ta d'auko babbar butar Yaya Aliyu da bata rabo da ruwa aciki ta ajiyewa Sabeer a gaban shi, d'an murmishi yayi tare da cewa "Na gode " Murmishin yak'e Aunty Aliya tayi, tana nan tsaye ya ajiye jakar laptop d'in shi dake rataye a kafad'ar shi saman wani dutse sannan ya tsugunna yayi alwala, abin sallah Aunty Aliya ta bashi sabida masallacin da nisa daga gidan ba lalle ya gane ba yana bak'o, kar6a yayi ya shimfid'a ya fara sallahr har zuwa yanzu Suhaima na tsaye tamkar wadda aka dasa a wajen ko kwakkwaran motsi bata yi, ganin haka ya sanya Aunty Aliya janyo hannun Suhaima suka wuce d'akin ta. Cikin tsoro tace "Suhaima wane ne wannan? " Suhaima itama a tsorace tace "Na shiga uku Aunty yanzu sai da Sabeer ya biyo ni " "Ki fad'a min wane shi kafin Yayan ku ya dawo daga masallaci " Murya na rawa ta bud'e baki zata yi magana suka ji sallamar Yaya Aliyu daga tsakar gida, kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Aunty Aliya da Suhaima ko motsin kirki sun kasa...... Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 51-52 Murya na rawa ta bud'e baki zata yiwa Aunty Aliya bayani suka ji sallamar Yaya Aliyu daga tsakar gidan, kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Aunty Aliya da Suhaima ko motsin kirki sun kasa gaban su sai dukan uku uku yake na tsoron yanda Aliyu zai saurare su na shigowar wani kai tsaye gidan. A haka ma a tsakar gida kallon kallo aka tsaya yi da Aliyu da Sabeer wanda idar da sallahr mangarib d'in shi kenan, da fara'a Aliyu ya shigo gidan anman had'a idon da suka yi da Sabeer ya sanya fara'ar fuskar shi ta d'auke lokaci daya ya 6ata fuska gefe d'aya na cikin zuciyar shi yana mamakin wannan wane ya shigo mishi gida haka kai tsaye haka har yana sallah. Sabeer ganin Aliyu ya d'aure fuska sosai yasa shi tsorata gaban shi ya fad'i kada ya kore shi daga gidan, murya na rawa yace "Sannun ka ina yini? " Cewar Sabeer kanshi a k'asa don ya fara tsarguwa da wannan kallon da Aliyu yake mishi, tamkar bayason amsawa yace "Lafiya k'alau " D'an matsawa yayi kusa da k'ofar d'akin Aliyah yana mamakin da har yanzu babu wanda ya fito ya amsa mishi sallama tsakanin ta da Suhaima tunda ba haka suke mishi ba matuk'ar suna gidan kuwa. "Aliyah, Suhaima kuna ina? " Muk'ut Suhaima da Aliyah suka had'iye yawu lokaci d'aya, idanun ta saman fuskar Suhaima tace "Gamu a d'aki mun yi sallah ne " Alhalin babu wanda yayi yunk'urin yin sallahr har gwara Suhaima tayi alwala. "Ku fito ina son ganin ku " "Toh gamu nan " Fad'in Aliyah cikin dakiya don ita tafi ma Suhaima jarumtar amsawa, sun d'an d'auki mintuna biyu sannan suka yi shahadar fitowa gaba d'ayan su. Yaya Aliyu yana zaune saman tabarma kusa da k'ofar d'akin Aliyah, yayi da Sabeer yake zaune saman abin sallah a tak'ure hankalin shi a matuk'ar tashe saboda uban cizon da sauro yake galla mishi a hannu da k'afar shi ga kukan shi da ya dameshi cikin kunnuwan shi ga zafi don sai had'a gumi yake. Fitowa suka yi tare da zama kusa da Yaya Aliyu sai da ya kalle su na 'yan mintuna kafin yace "Na shigo gida sai na tarar da wani abin mamaki dana gani, shin wane? Kuma me ya kawo shi cikin gidana ba tare da yarda ta ba? " K'uwwww cikin Suhaima da Aliyah ya fitar da wannan sautin ganin yanda Aliyu ya d'aure fuska tamkar bai ta6a dariya, basu ta6a ganin shi cikin wannan had'e fuskar ba sai yau don haka suka tsorata. "Ku nake saurare ku yi min bayani " Fad'in Aliyu kenan ganin sunyi shiru kansu a sunkuye. Aliyah ce tayi k'arfin halin cewa "Uhm da....daman yanzu mu... muke son kiraka a... a waya mu fad'a maka, ya dai... dai ce sunan shi... shi Sabeer " Kallon baku da hankali yayi musu da sauri Aliyah ta sunkuyar da kanta ganin irin kallon da Aliyu yake jefan ta dashi, idan ba wannan kallon yayi musu me zaiyi taya ya kawai bakasan mutum ba ka barshi ya shigo cikin gidan ka kai tsaye namiji ma ba mace ba a yanda zamanin yanzu abubuwa suka ta6ar6are. Bai k'ara bi takansu ba ya juya wajen Sabeer da lokacin hankalin shi ya gama tashi saboda cizon sauro tamkar zai fashe da kuka ko yayi ta ihu ko yaji dad'i, Suhaima tana ankare dashi cikin zuciyar ta tace "Allah ya k'ara da uban wani iyayi ne ya kawo ka inda bazaka iya rayuwa mai dad'i ba kamar yanda ka saba rayuwar jin dad'i da hutu maganin iyayin mutum kad'an ma ka gani" duk da a d'an tsorace take sai da ta saki murmishi mugunta sauran kad'an dariya ta kubce mata ta mugunta. "Malam Sabeer muna son sanin kai waye? Me ya kawo ka kuma nan gidan? " Sabeer d'an had'iyar yawu yayi kafin ya motso kusa da Yaya Aliyu cikin sanyin muryar shi yace "Kamar yanda ka sani Sunana Sabeer Hussein d'an fillo Yaya ga k'awar Suhaima wato Jiddah " Nan take Yaya Aliyu yayi murmishi da jin Yayan Jiddah ne ko ba komai d'an uwan Jiddah bai cancanci wulak'anci a wajen su ba. "Masha Allah ashe d'an uwan Jiddah ne kai yarinya mai hankali da nutsuwa, toh Malam Sabeer muna son sanin lafiya kazo inda muke?". Sai da yayi shi na d'an minutes kafin ya bud'e baki yace "So da k'aunar Suhaima ne yasa ni zuwa nan domin na sami soyayyar ta, na kasance tun lokacin da na ganta naji inason ta so na tsakani da Allah kuma ba yaudarar ta zanyi ba wallahi auren ta zanyi " "Ikon Allah! " Fad'in Aliyu kenan, Suhaima da Aunty Aliya kuma sun baza kunnuwan su suna sauraren abin da yake fad'a. "Shine idan baza ku damuwa ba ina son ku koma can birni zan baku gida, mota da kuma aikin yi sannan zan...... " Kasa k'arasa maganar shi yayi ta mak'ale a fatar bakin shi ganin irin yanda fuskar Aliyu ta rikid'a ta koma wata iri na yanayin fusata ga wani d'an iskan kallo da yake jifan Sabeer jin yazo mishi da wani banzan magana. Sabeer kuwa kasa magana yayi yana kallon Aliyu yanda yake mishi wani irin kallo alhalin a girmi bazai girme shi sai ma watak'il ya bashi shekara biyu. "Gaskiya tun da ka biyo ta wannan hanyar ba lallai Suhaima taso ka koda ta so ka ni kuma bazan yarda ta aure ka, mu ba makwad'aita bane duk da mu talakawa ne muna rayuwa a karkara muna jin dad'i yanda muke rayuwar mu bama hangen wani abin don haka ka sake tunani Sabeer baza mu ta6a yarda da wannan maganar taka ba " Nan Aliyu ya cigaba da masifa don ya d'auka Sabeer ya raina musu arzik'in su ne, baisan Sabeer ko kad'an ba haka bane cikin zuciyar shi da yasan yayi wannan tunanin amman sai ya watsar daga baya tun da iyayen shi sun amince da auren Suhaima a haka amman sai Daddy ya sanya shi furta hakan wanda yayi dana sanin fad'in haka. Ana cikin haka sai ga Babaa Lantana nan da Baba Adamu sun shigo domin kwana biyu basu lek'o ganin jikin Aliyah ba, suka tarar da wannan hatsaniyar har Aliyu yana cewa Sabeer ya kwashi kayanshi ya koma inda ya fito, sosai hankalin Sabeer ya tashi tuni hawaye sun fara zuba a idanun shi. Aunty Aliya ya bata tausayi sosai Suhaima kuwa ko a jikin ta, nan Babaa Lantana da Baba Adamu suka shiga zancen dakyar Aliyu ya hak'ura sai lokacin kuma yaga hawayen da Sabeer yake fitarwa sai kuma jikin shi yayi sosai, bai kamata ya wulak'anta jinin Jiddah ba yanda taso su ba tare da kyamatar su ba. Suhaima kuwa dad'i ya kamata tasan yanzu Yaya Aliyu zai kore shi addu'a take cikin zuciyar ta Allah yasa kada Yaya Aliyu ya amince da dad'in bakinshi. "Kayi hak'uri idan ka bani dama zan zauna a gidan ka na nemi soyayyar Suhaima " Fad'in Sabeer yana goge hawayen fuskar shi. Nan jikin Aliyu ya Kara sanyi sosai mene laifin Sabeer anan Allah ne ya jarrabe shi da son Suhaima bai kamata yayi mishi haka ba kodan 'yar uwar shi Jiddah wadda ko d'azu da safe sai da sukayi waya da ita gaba d'ayan su don haka cikin sanyin murya yace "Nima kayi hak'uri da abin da nayi maka kuma na amince da hakan Allah ya taimaka" Wani sanyi dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Sabeer wanda har sai da ya rungume Aliyu yana godiya, yayin da Aliyu, Aliyah, Babaa Lantana da Baba Adamu suka yi dariyar farinciki, Suhaima kuwa wani bak'in ciki ne ya turnik'e ta sai kawai taja tsaki ta wuce d'akin ta da sauri duk suka bi ta da kallon mamaki. "To kai gaka d'an birni anya zaka iya cin abincin mu ka kwanta a irin d'akunan mu kuwa " Cewar Babaa Lantana, dariya Sabeer yayi kafin yace. "Me zai hana kuwa Babaa " Nan aka d'an ta6a hira cikin farinciki wanda a lokacin Sabeer ya shiga ransu saboda sauk'in kanshi. Tashi Babaa Lantana da Baba Adamu suka yi da zummar tafiya nan Aliyu ya dage sai sun ci abinci aikuwa k'in yarda suka yi tare da tafiya. Bayan sun tafi Aliyu ya umarci Aliyah da ta kawo musu abinci, babu dad'ewa ta shirya musu sannan ta wuce d'aki don yin sallah. Bud'e kwanon Aliyu yayi tuwan biskin gero ne da miyar taushe tasha gyad'a da manshanu sai tashin k'amshi yake, nan Aliyu yayiwa Sabeer Bismillah ba don Sabeer ko yasan mene ba ya tsunduma hannun shi ya fara ci dakyar ya iya had'iye lomar da yayi saboda rashin sabo da cin irin wannan abincin . Kasa cigaba da ci yayi fahimtar hakan da Aliyu yayi yasa shi girgiza kai yana tausayin Sabeer yasan wahala ce sai yasha don birni da karkara akwai banbanci musamman a irin gidajen da Sabeer ya taso. Ruwan Sabeer ya runtse ido yasa ba don yayi mishi irin yanda yake so ba gashi cikin shi sai k'arar yunwa yake don rabon shi da abinci tun breakfast na safe saboda zumud'i ma bai ci abinci sosai ba. "Zaka iya shan fura? " Cewar Aliyu yana kallon shi d'an sosa k'eya yayi kafin yace "Eh zan sha kasan mu ma family's d'in mu Fulani ne muna sha amman ni ba sosai ba " Gid'a kai Aliyu yayi yana cewa "yanzu don duhu yayi zuwa gobe sai mu fita kaga yanda garin namu yake " Tashi yayi ya shiga d'aki babu jimawa ya fito shi da Aliyah nan ta wuce kitchen tana kok'arin damawa Sabeer fura, babu dad'e wa ta dama shi ta kawo mishi a cikin k'ok'o da ludayi had'e da kofin roba ta ajiye mishi. "Sannu Aunty Aliyah na had'a ki da aiki " Murmushi tayi tare da cewa "laaa ba komai wallahi dafatan zaka iya shan wannan furar " "Zan iya mana " Murmishi tayi ta wuce d'aki, nan Sabeer ya janyo furar ya fara sha da ludayin gard'in gero da kindirmon nono ya ratsa shi sosai furar tayi mishi dad'i. "Da ka zuba a kofi koh" Yana lumshe ido yace "Barni kawai Yaya nasha a haka don na saba " Dariya kawai Aliyu yayi, bayan sun gama ne Aliyu ya shiga wani d'aki na kusa da zaure ya fara gyarawa nan Aunty Aliya ta fito itama ta bishi d'akin tana tayashi aikin, Sabeer najin dariyar su da magana suna yi k'asa k'asa lumshe idanun shi yayi sun birge shi sosai yana fatan su yi irin wannan zaman da Suhaima idan ya shawo kanta ta kar6i soyayyar shi. Tsaf suka gyara d'akin bayan sun share sun bud'e window na d'akin nan suka sanya labule na k'ofa dana window kafin su fito kuma su shiga d'akin Aliyah sai ga Aliyu ya fito da k'aramar katifa ta k'aramin gado ya sanya d'akin Aliyah kuma ta shimfid'a mishi zanin gado a jikin katifar ta kunna turaren wata na tsinke sai d'akin ya fito fes dashi, Aliyu ya d'auki jakar Sabeer ya shigar mishi da ita kafin kuma su d'unguma shi da Sabeer su tafi masallaci don yin sallahr ishsha.... Aishat A Muh'd 💃🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 53-54 Bud'e labulen d'akin Aliyah tayi tare da shigowa zama tayi kusa da Suhaim wadda ta kwanta rub da ciki a saman gadon ta, dafa bayan ta tayi kafin tace "Suhaima tashi mu yi magana " Tashi Suhaima tayi zaune tana goge hawayen fuskar ta da hannunta, kallon mamaki Aliyah take mata kafin tace "Me yasa kika yi mishi haka Suhaima?, haba Suhaima bansan ki da halayyar wulak'anta mutane ba, ki tuna saboda sanadin son ki fah ya bar gatan shi da komai nashi na jin dad'i ya dawo nan k'auye wanda bai ta6a rayuwa acikin irin wannan yankin ba ya aminta zai jure kowacce wahala indai zai same ki, koda da iya abincin mu ma kafin ya saba aiki ne zai hak'ura ya jure duk don A SANADIN SON KI, haba Suhaima ki tausaya mishi kada ki bashi wahala don na tabbatar Sabeer son ki yake tsakani da Allah ba yaudarar ki yake, idan yaudara ce ma bazai zo har nan ba don haka kiyi tunanin kafin ki yanke hukunci tukunna " Zum6ura baki Suhaima tayi tare da cewa "Ni gaskiya Aunty bana son Sabeer hasalima kinsan na tsani auren mai kud'i saboda gujewa wulak'anci, musamman gidan su Sabeer tunda na baki labarin abin da suka yi min" D'an shiru Aliyah tayi tana d'an tunani kafin tace "Kina da gaskiya don wannan amman ni ina mai baki shawara kiyi tunani sosai kafin ki yanke hukunci,tare da addu'ar neman za6in Allah kada ki yanke hukunci da gaggawa" Gid'a kai Suhaima tayi kawai tare da cewa "Ni bama zan so shi ba" "Hmmm na dai ji ki Suhaima kawai amman wannan zakad'ed'en sauryin ne kece bakya sonshi kawai ra'ayin ki ne ya hana ki tsayawa kiyi tunanin kin fad'a son Sabeer daga irin kallon da kike mishi d'azu " Wayyo aikuwa Suhaima ji take kamar ta rusa kuka jin abin da Aunty Aliyah ta fad'a mata, zum6arar baki tayi tare da kwanciya ta juyawa Aliyah baya, abin ya bata dariya tashi tsaye tayi tare da cewa "Abincin ki yana kitchen fah kije ki ci kada ya huce " Tana gama fad'in haka ta fito daga d'akin, nan ta tarar da Sabeer da Aliyu sun dawo bayan tayi musu sannu da dawowa ta yiwa Sabeer sai da safe ta wuce cikin d'aki. Sun d'an jima suna hira kafin Sabeer ya wuce d'akin da aka sauke shi bayan yayi wa Aliyu sai da safe, yana tafiya yana waiwayar d'akin Suhaima ko Allah zai sanya ya hango ta don kuwa yana son sake sakata cikin idanun shi kafin yayi bacci, Aliyu yana kallon yanda yake kallon d'akin Suhaima nan ya sake tabbatar wa Sabeer yana son Suhaima bana wasa ba, amman mene dalilin k'in amincewar Suhaima na ta kar6i soyayyar Sabeer?. Sabeer yana shiga d'akin sai yaji shi kamar wanda aka sanya shi a akurki duk da d'akin yana da d'an girma kuwa hakan bai hana sa Sabeer ganin k'ank'antar shi ba irin wanda ya saba kwanciya da shi ba. Zama yayi gefen katifar yaji ta tik'irk'ir tauri sosai, ga wani hucin zafi da d'akin yake fitarwa alamar dai ba'a yin amfani dashi a rufe yake sai shegen kukan sauro da ya addabi kunnen shi, ga ba wadataccen haske wata 'yar k'aramar fitila ce kawai a rataye jikin k'usa a bango mai irin mai batir d'in nan, zabga tagumi Sabeer yayi yana tunanin yanda ya tsinci kanshi inda bai ta6a tsammanin ganin a haka ba koda a mafarki sai gashi kwatsam lokaci d'aya ya tsinci kanshi aciki ikon Allah kenan. Zumbur ya mik'e kamar wanda aka tsikara sakamakon wani fitsari da ya matse shi, wayyo Allah nah yanzu ta ina zan fara shiga toilet d'in su, fad'in haka cikin zuciyar Sabeer yana faman matse k'afa, fuskar nan tashi tayi kalar tausayi tamkar wanda zai fashe da kuka kasa jurewa yayi kawai ya tashi da sauri ya fito daga d'akin zuwa tsakar gidan. Ba kowa a tsakar gidan ga duhu yayi tsit kake ji, yana nan tsaye sai ga Suhaima ta fito a d'aki zata shiga kitchen d'ebo ruwa suka kusan cin karo da Sabeer saboda duhu gashi babu wadataccen hasken farin wata, ba k'aramin tsorata tayi ba ta d'auka ko wani aljanin ne amman lokacin da ta fuskanci Sabeer ne sai kawai ta dake tare da d'aure fuska zata wuce daga sauri yasha gabanta ya tsaya "Malam lafiya? " "Uhm ina son ki nuna min toilet " Da hannu ta nuna mishi ba tare da tayi magana ba ta wuce shi ta d'auko ruwan ta shige d'aki ko kallon inda yake bata sake yi ba, buta ya d'auka ya wuce cikin toilet d'in a d'an tsorace, duk da a duhu ne hakan bai sanya shi gane tsabtar da band'akin yake dashi ba a tsorace yayi abin da zai yi ya fito yana share gumi sai kace wanda yayi tseren gudu duk gumin tsoro ne, da sauri ya wuce d'akin ya rufe kafin ya kwanta saman katifar. A cikin wannan daren ya zame wa Sabeer daren da bai ta6a tsammanin zai irin shi a wannan duniyar ba saboda yanda zafi da sauro suka hanashi runtsawa, idan zafin ya isheshi sai ya cire kayan jikin shi iya vest da 3quater ne kawai a jikin shi sai buge bugen sauro yake yi ko baccin kirki ya kasa samu ga wani tsananin ciwon kai da ya kamashi saboda gajiya ga rashin bacci. Washe gari kuwa jikin Sabeer yayi luhu luhu da cizon sauro abin ka da d'an hutu kuma farar fata duk tayi ja tundaga fuskarshi kuwa har jikin shi inda kaya bai rufe ba, idanun shi sun yi ja sosai ga wani zazza6i da ciwon kan ya saukar mishi dashi wajen asubah, har gari ya waye yana kwance a d'aki bai iya fitowa ba sai da Aliyu ya shiga ya ganshi kwance sai rawar sanyi yake ya tukunkune waje d'aya. Cikin tashin hankali Aliyu ya k'arasa tare da cewa "Subhanallah! Sabeer baka da lafiya ne? " D'an murmishin yak'e yayi hawaye na zuba a idanun shi na zafin ciwo yace "Zazza6i ne yake damuna da ciwon kai ko zaka taimaka min da paracetamol? " "Sannu Allah ya baka lafiya, bari na d'auko maka amman ka d'aure ka fito sai kayi brush kaci wani abin kafin ka sha maganin " D'aga kai kawai Sabeer ya iya yi sannan Aliyu ya taimaka mishi suka fito tsakar gidan bayan ya d'auko mishi maclean da brush nashi cikin bag d'in da ya taho da ita. Aunty Aliya da Suhaima suna zaune a kan tabarma ga breakfast a saman tabarmar da yake tare suke karyawa, Aunty Aliya batasan sand ta mik'e tsaye ba tana zaro ido tare da cewa "Innallilahi Aliyu mai ya cije haka " Zaunar da Sabeer yayi saman kujera kafin yace "Cizon sauro ne wallahi" "Allah sarki sannu Sabeer Allah ya baka lafiya " D'an murmishin yak'e yayi mata yana d'aga kanshi alamar amsawa, tun lokacin da Aunty Aliyah ta fara magana Suhaima ta d'ora idanun ta kan Sabeer ta k'ura mishi ido cikin wani yanayi wanda ni kaina na kasa tantancewa, sai da suka had'a ido tukunna ta janye nata idon daga kallon shi ta sunkuyar da kanta. "Suhaima zo ki samo ruwan d'umi a kitchen yayi brush dashi " Tashi tayi ta d'auki buta ta d'ebo ruwan d'umin ta kawo maimakon ta sirka shi sai kawai ta dire a gaban shi a haka gaba d'aya jinta take wata iri kamar ba ita ba. "Wash Allah! " Taji muryar Sabeer ya fad'a da sauri ta kallo inda yake sai taga yana yarfe hannun shi tare da yatsina fuska ga hannun yayi ja sai lokacin hankalin ta ya dawo jikinta ta mance bata surka ruwan da na sanyi ba. "Suhaima baki da hankali da zaki kawo mishi ruwan zafi ba tare da kin surka ba" Fad'in Yaya Aliyu kenan yana hararar ta bayan sun had'a ido. "Laaa Yaya na mance ne Allah kayi hak'uri " Da sauri ta mik'e ta d'auki butar ta nufi wajen da suke ajiye ruwa ta surka ta kawo mishi tukunna ta koma ta zauna, duk inda tayi idanun Sabeer suna kanta suna shawagi gaba d'aya ta kasa sakewa. A haka ya lalla6a yayi brush sannan ya dawo saman tabarmar zama yayi kusa da Suhaima sai ya jingina da bango, sannu Aunty Aliya da Yaya Aliyu suka yi mishi ya amsa muryar shi can k'asa, koko ne mai kauri yasha gasara Aliyu ya mik'a wa Sabeer hannun shi yasa ya kar6a tare da kaiwa baki ya kur6a. Ba shiri ya furzo dashi waje sai a jikin Suhaima ya 6ata mata jiki don duk ya tsatstsalu a jikin ta har da saman fuskarta, sannu suka k'ara yi mishi yayin da Suhaima ta cukune fuska takaici da 6acin rai fal zuciyar ta har a saman fuskar ta ya nuna. "Am sorry please " Ya fad'i cikin sanyin murya fuskar shi d'auke da damuwa dagani kasan ba'a son ranshi yayi mata ba. "Je ki canja kayan ki wanke fuskar ki" Fad'in Aliyu kenan ganin irin yanda Suhaima take jifan Sabeer da kallon tsiwa. A fusace kuwa ta mik'e ta wuce d'akin ta bata dad'e ba ta fito d'aure da zanin wanka tare da hijab a jikinta ruwan wanka ta had'a tare da wucewa toilet. Duk wannan abin da take Sabeer yana kallon ta ji yake tamkar ya tashi ya rungume ta cikin jikin shi ya rarrashi ta ya nuna mata hakan da ya faru ba'a son ranshi ba ne tsautsayi ne amman babu damar yin haka. "Me zaka ci a dafa maka tunda baka son kokon? " Fad'in Aunty Aliya kenan "Aunty idan na samu ruwan tea ma ya isheni don bana sha'awar cin komai" "Haba haba ruwan tea me zai maka ka fad'in abin da kake so kawai nan kamar gida ne " "Kin ga wuce kitchen mu je " Cewar Aliyu nan suka tashi suka tafi kitchen suna shiga Aliyu ya fita bai dad'e ba ya dawo, cikin mintuna kad'an Aunty Aliya ta dafawa Sabeer tea da yasha kayan kamshi citta da kaninfari sannan aka soya kwai suka kawo mishi. "Sannu da kok'ari Auntyn mu" D'an murmishi kawai tayi. A lokacin Suhaima ta fito daga toilet da harara tabi Sabeer kafin ta wuce d'akin ta. Nan suka karya har suka gama Suhaima bata fito ba nan Aliyu ya tafi siyowa Sabeer paracetamol, yayin da Aunty Aliyah ta wuce d'akin ta. Sabeer yana kok'arin mik'ewa don wuce wa d'aki ya kwanta Suhaima ta fito kallon shi tayi tare da cewa "Malam ba lallai ba dole idan baza ka iya zaman nan ba ka tarkata ka koma inda ka fito tunda babu wanda ya gayyace ka anan don bazai yiwu kana had'a mutane da wahala ba " Tana gama fad'in haka ta fice daga gidan gaba d'aya, nan tsaye take Sabeer yaji wani zazza6in yana neman rufe shi dakyar ya iya kai kanshi d'aki ya zube akan katifa yana wani irin numfashi...... Kuyi hak'uri da ni fan's, kun ji ni kwana 2 shiru abubuwa ne sai a slow but insha Allah zan nayi kok'ari wajen typing. Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz Dis page is dedicated to Faridah Bashir (Ummu Safwan) marubuciyar Tambarin sarautah, wannan shafin naki ne kyauta Allah ya raya mana Safwan ya k'ara zumunci Amin ❣ PAGE 55-56 Yana cikin wannan haline Aliyu ya shigo d'akin hannun shi rik'e da paracetamol da ruwa a cup na roba, ganin halin da Sabeer yake ciki ne yasa Aliyu ajiye maganin a gefe ya k'arasa wajen shi da sauri ya rik'o shi tare da cewa "Sabeer jikin ne? " Jan wani numfashi yayi wanda ya sanya Aliyu mugun tsorata, a hankali kuma ya sauke numfashin nashi tare da zaunawa saman katifar ya jingina bayan shi da bango kallon Aliyu yayi da idanun shi jawur dasu wanda yake afkin yi mishi sannu fuskarshi da tarin damuwa yace "Kada ka tashin hankalin ka bani maganin nasha " "Kodai zamu je asibitin nan na kusa damu su duba ka " Cewar Aliyu d'an murmishin yak'e yayi kafin yace "Basai mun je ba naji zazza6in ya sauka yanzu sauran ciwon kai bacci zanyi yanzu " Sannu Aliyu ya k'ara yi mishi kafin ya fita ya bashi gurin dob ya samu damar yin bacci, tunani kawai Sabeer ya fad'a na yanda Suhaima take wulak'anta shi ina laifin shi anan don kawai yace yana sonta da wannan tunanin bacci mai nauyi ya d'auki Sabeer. Tunda Sabeer ya farka daga baccin yaji da sauk'i ciwon kan ya ragu, tun daga lokacin Sabeer yake kok'arin koyan cin abincin su yana kuma bin Aliyu gona duk da baya kok'arin yin aiki idan sun je zai zauna yana kallon yanda yake yi ko kuma ya dunga zagaye gonar ko kuma Ashiru wanda ya taimake shi ya kawo shi gidan su Suhaima da yamma wani lokacin zai zo su tattaka zuwa cikin k'auyen, gashi yana kiran iyayen shi su gaisa sannan Aliyu, Aliyah da Babaa Lantana da Baba Adamu suna kok'ari wajen janshi a jiki ya sake dasu tamkar 'yan uwan na jini. Sai dai ta 6angaren Suhaima ne har yanzu babu wani cigaba don har yanzu tak'i bawa Sabeer fuskar da zai bayyana mata yanda yake sonta. Aunty Aliya kuma tayi nauyi sosai sai ya kasance duk wani aiki na cikin gidan Suhaima ke yi, yayin da Aliyu wani lokacin yake taimaka mata idan ayyukan sunyi mata yawa. Suhaima ce zaune saman kujera tana yankan salad tana sauraron freedom redio cikin shirin su na duniyar mu a yau wanda Usman Usman yake gabatar wa tana son shirin sosai batason ya wuce ta, Sabeer ne yayi sallama ya shigo gidan tun kafin ta amsa mishi, haushi ya turnik'e ta don haka sai ta fara gunguni tana cewa "Mutum sai kawai ya shigowa mutane gida kai tsaye tun kafin a amsa mishi sallamar a bashi izinin shigowa sai kace a gidan arna " D'an murmishi yayi yana girgiza kai don yaji ta tsaf sai kawai ya tashi ya koma zaure sannan yayi sallama mamaki sosai Suhaima taji da taji ya koma sai da ta d'an jima kafin ta amsa mishi sallamar sannan ya shigo yaja kujera ya zauna lokacin har ta gama yankan salad d'in. Shiru taji bai yi magana ba sai ta d'an d'ago kad'an ta kalleshi duk ya rame yayi d'an bak'i kad'an kamar ba Sabeer ba, gani tayi zai kallo inda take ya sanya ta kauda idonta da sauri zata tashi kenan taji muryar shi cikin sanyi yace "Baby taimaka min da abinci I'm very hungry wallahi please " Yi tayi kamar bata ji shi ba ta wuce kitchen kafin ta fito ta wanke salad d'in duk yana kallon ta don tayi mishi kyau cikin wata gown ta atampha duk da basu kamata ba d'inkin amman sun zauna cif a jikin ji yake kamar ya sanyata cikin jikin shi ya dunga fad'a mata irin son da yake mata ko ya samu sassaucin da yake ciki. Ya fad'a dogon tunani yana yi yaji kamshin turaren Suhaima a kanshi da sauri ya d'ago kanshi ya kalle ta tana tsaye hannun ta d'auke da plate na abinci tana mik'a mishi, hannun shi ya sanya ya kar6a hadda ta6o mata 'yan yatsun ta saboda tsokana yak'i kar6ar plate d'in aikuwa wani irin shock Suhaima taji ajikinta wanda bata ta6a jin irin shi ba da sauri ta saki plate d'in nan yayi saurin tarewa yana sakin murmishi ganin irin yanayin da ta shiga ajiye abincin yayi yana kallon shi shinkafa da wake ne sai salad da mai da yaji gefe d'aya a saman abincin ga kifi nan an sanya sosai abincin ya bashi sha'awa. "Uhm sauran ruwa Baby " Ya fad'i hakan a lokacin da Suhaima take kok'arin shiga d'akin ta ta huta don ta gaji tun safe take aiki, haushi ne yake kamata tun lokacin da Sabeer ya koyi ce mata Baby kuma ko a gaban su Yaya Aliyu haka yake fad'a mata, komawa tayi kitchen ta samu jug k'arami mai murfi ta d'ebo mishi na randa mai sanyi ta kawo ta dangwarar mishi a gaban shi. "Sannun ki Baby nah Allah ya bani ke " Ko kallon shi bata yi ba ta juya ta wuce d'aki sai kawai taji zuciyar ta tak'i aminta ta furta ba Amin ba daga addu'ar da Sabeer yayi. Cikin kwanciyar hankali ya fara cin abincin yayi mishi dad'i sai dai ko rabi bai ci ba ya ture shi saboda yayi mishi yawa yasan da gayya ta zubo mishi da yawa, yana nan zaune ya fara jiyo muryar Aliyah k'asa k'asa tana kiran Suhaima daman yinin yau a d'aki ta yini bata jin dad'in jikinta. Jin wannan kiran yasan Suhaima bazata ji ba ya sanya shi tashi ya nufi d'akin Suhaima ya shiga ba tare da neman izinin ta ba tana kwance saman bed tayi kwanciyar ringingine tana duba littafin addu'o'i. Tsayawa kallonta kawai ya tsaya yi don wannan kwanciyar ba k'aramin sanya shi a wani yanayi na daban, Suhaima ji take kamar ana kallon ta sai ta kawar da littafin daga saitin fuskar ta fuska a d'aure tace "Malam lafiya zaka shigo min d'aki ba neman izinin? " D'an sosa kai yayi kafin yace "Aunty Aliyah tana kiran ki " Yana gama fad'in haka ya fita, d'an tsaki taja kafin ta mik'e ta fita d'akin Aliyah ta shiga sai ta tarar da ita cikin wani hali don nak'uda ce ganga ganga ta taho mata da sauri ta k'arasa inda take durk'ushe ta rik'o ta tana kuka. Sabeer zai fita kenan yaji kukan Suhaima nan ya fara kiran sunan ta hankalin tashe gashi bashi da damar shiga d'akin, nan Aliyah dakyar ta fad'awa Suhaima taje ta kirawo mata Babaa Lantana. Tana fitowa taci karo da Sabeer wanda yake tsaye a bakin k'ofar hankalin shi a tashe kamar ya fad'a d'akin haka yake jin shi. Ganin Suhaima zata fita yasa shu rik'o hannun ta yace "Baby what wrong with U? " Kamar ta share shi sai kuma tace "Aunty ce zata haihu tana shan wahala " "Innalillahi bari naje na kirawo Yaya da Babaa Lantana ki zauna kusa da ita " Da sauri ya juya ya fita yayin da Suhaima ta koma cikin d'akin, babu dad'e wa da fitar shi sai ga Babaa Lantana da Aliyu sun shigo gidan tare da Sabeer nan suka shiga cikin d'akin ban da Sabeer wanda yake tsaye zuciyar fal tausayin Aliyah. Yana nan tsaye Suhaima ta fito tana kuka da Aliyu wanda idanun shi suka yi ja na tausayin halin da matar shi take ciki akabar Babaa Lantana a cikin d'akin "Ya kamata mu tafi hospital " Cewar Sabeer da ya matso kusa da Yaya Aliyu, d'an girgiza kai Aliyu yayi kafin ya bud'e baki yayi magana sun ji kukan jariri. "Alhamdullilah " Suka furta gaba d'aya suna nan tsaye Babaa Lantana ta fito fuskarta d'auke da farinciki tace "An sauka lafiya mun samu namiji " Nan fuskar su ta fad'ad'a da fara'ar farinciki, Suhaima mai kuka ta dawo dariya har da buga tsallen murna ta rungume Yayanta, kallon su Sabeer yake cike da sha'awa daman shima yana da k'anwa ko Yaya wanda suka fito ciki d'aya da shima ya nuna mishi irin son da yaga Aliyu da Suhaima da suke yiwa junan su. Suhaima ruwa ta d'ora kan wuta bayan ta hura itace bayan yayi zafi ne ta kwashe takai toilet sannan ta d'ebo wanda za'a yiwa jariri wanka ta kai d'akin Aliyah inda har Babaa Lantana ta gyara ko'ina fes ta sanya turaren wuta na kamshin d'akin. "Sannu Aunty Aliya " Suhaima ta furta tana rik'o hannunta fuskarta d'auke da murmishi, "Yawwa kanwata ke ma sannun ki " Kamata Babaa Lantana tayi ta kaita band'aki wanka tayi mata suka fito sannan tayi wa jariri lokacin da suka gama tsaf suka shirya sai ga Yaya Aliyu nan da taxi ya taro zasu je asibitin da Jiddah ta kaisu lokacin tana laulayin ciki. Suka tafi aka bar iya Suhaima a gidan tana dad'a gyarawa, bayan ta gama ne sai tayi wanka ita ma ta fito d'aure da zanin wanka ko hijab bata sanya ba da yake tasan a tunaninta Sabeer ya bi su hospital ne. Tsayawa tayi bayan ta fito daga wankan tana taje dogon gashin kanta ta sunkuyar da kan gashin yayi gaba tana taje shi, bayan ta gama irin ta d'ago kanta gashin yayi baya sai a fuskar Sabeer wanda shigowar shi kenan gidan, ya hango ta tana taje kanta. "Wash! kin sanya min gashi a ido da bakina fah" A d'an tsorace Suhaima ta jiyo jin muryar Sabeer a kusa da ita, suna had'a ido nan gabanta ya hau fad'uwa ganin irin kallon da yake jifanta dashi idanun shi har sun fara canja launi, na shiga uku ni Suhaima daman wannan mutumin bai bi su ba, ta fad'i hakan cikin zuciyar ta tana mai ja da baya shima yana bin ta da haka har bayanta ya jingina da bangon d'akin ta sai kawai ta runtse ido tare da k'ank'ame jikinta waje d'aya. Hannun shi ya sanya ya d'auke gashin da ya rufe mata face nata ya zuba mata ido musamman pink lips nata wanda ta d'an danne na k'asan kad'an da hak'orinta na k'asa ji yake kamar yayi ta kissing d'in su sai dai ba yanzu ba da sauran lokaci amman duk lokacin da ya mallake su sai ta gane kurenta sai ya ladaftar dasu ta tsiwar da suke mishi. "Baby open your eyes please " A hankali ta bud'e idanunta gabanta na cigaba da fad'uwa ta zube idanunta saman fuskar Sabeer wanda batasan lokacin da suka d'auki mintuna 2 tana kallon cikin idanun shi wanda daga k'arshe kasa jure kallonsu tayi sai kawai ta sunkuyar da kanta k'asa jikinta yayi sanyi wani irin abu ne yake fisgarta game da Sabeer amman tana kok'arin yaki ce shi don batason yayi mata tasiri akanta. "Baby mene aibuna da baki sona why Suhaima? " Shiru tayi babu amsa hannun shi ya sanya ya d'ago face nata cikin muryar shi da ta soma rawa tamkar wanda zai fashe da kuka yace "Saboda me baki sona ni d'an iska ne ko kuma ban cancanta a so ni ba? " Girgiza kanta tayi don bakinta yayi mata nauyi ta kasa magana. "Toh kina sona? " Nan ma ta girgiza kai, wani abu ne ya tokare wuyan Sabeer wanda ya sanya wasu hawaye fita daga idon shi. A hankali ya saki fuskarta jikin shi yayi sanyi sosai goge hawayen face nashi yayi tare da sakin murmishin yak'e yace "Ni kuma ina son ki kuma insha Allah zai kin zama tawa, ina son ki Baby " Yana gama fad'in haka ya juya ya tafi har yana cin tuntu6e da abu sauran kad'an ya fad'i saboda gaba d'aya ba'a hayyacin yake ba. Hankali Suhaima ya tashi da sauri ta ce "Sabeer kayi hankali kada kaji ciwo" D'an jiyowa yayi ya kalleta kafin ya juya ya bar gidan gaba d'aya zuciyar shi sam babu dad'i. Jikinta a sanyaye ta shige d'aki ta kwanta rub da ciki a saman bed wasu hawaye ne suka fara zuba a idanunta me yasa bata ta6a jin tausayin Sabeer irin na yau, me yasa ta fara jin wani yanayi game da Sabeer wanda bata ta6a jin irin shi ba, anya kuwa zuciyar ta bata fara son Sabeer ba kuwa?...... Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 57-58 Ta dad'e kwance a hakan don batasan iyakacin lokacin da ta d'auka ba jin dawowar su Yaya Aliyu taji daga hospital, nan ta tashi da sauri tana zira kaya tana mai mamakin dad'ewar da tayi don ma ta gama dukka ayyukanta, wani siket ta sanya pink colour mai turuwa sai T-shirt in black colour mai k'aramin hannu tana da tattara daga gaban rigar sai ta gyara gashin kanta tayi rolling da pink d'in veil kalar siket d'in batayi wani make-up ba daga powder da ta sanya sai lips gloss mai kamshin apple tayi kyau sosai duk da batayi kwalliya ba. Nan ta fito tsakar gidan babu kowa d'akin Aliyah ta wuce sai ta tarar da Babaa Lantana da Aliyu sai Sabeer a palour babyn na hannun Sabeer yana faman kallon shi addu'a yake cikin zuciyar shi Allah ya nuna mishi auren shi da Suhaima ta haifa mishi kyakkyawan babyn yanda yake shi d'aya yana rok'an Allah yasa ya haifi yara da yawa don bazai sassautawa Suhaima ba duk shekara yake son tana haifa mishi baby shi zaina yin zaman rainon su. Yana cikin wannan tunanin yaji sassanyar kamshin turaren ta sai da ya lumshe ido kafin ya bud'e su ya sauke su saman beautiful face d'in Suhaima sai akayi dace ita ma ta d'ago idanunta ta kalleshi nan suka fara kallon junan su, dakyar Suhaima ta iya controlling d'in kanta ta janye idanunta ta wuce ta samu ta zauna kusa da Aunty Aliyah, shima Sabeer d'auke idon nashi yayi yana wani shan kamshi ji yake tamkar ya lasheta don tayi mishi kyau. Duk wannan kallon da suke yiwa junan su Aliyah da Aliyu suna kallon su suna kyautata zaton Suhaima an fad'a tarkon Sabeer, wayar shi ya d'auko ya d'auki babyn pic's yana d'an yin hira da Babaa Lantana wadda yake zaune kusa da ita, sun jima a zaune a haka Suhaima tana son d'aukan babyn don bata ganshi ba gashi Sabeer yak'i ajiye shi gajiya tayi don haka cikin muryar shagwa6a tace "Wai ni Aunty Aliya baza'a ban na d'auki babyn ba ni fah tun da aka haife shi ban d'auke shi ba sosai " Rik'e ha6a Aliyah tayi tare da cewa "Ni zan hana ki d'auka ne ai gashi hannun mutumin na ki sai kije ki kar6a " D'an jim tayi kamar bazata je ba sai kuma ta kasa jurewa don haka sai ta mik'e a nutse ta nufi inda Sabeer yake zaune, kamar an tsikare shi ya mik'e tsaye da sauri ya mik'awa Babaa Lantana babyn tare da cewa "Nayi mantuwa Babaa rik'e minshi ina zuwa " Yana mik'a mata ya fice da sauri har yana mance wayar shi, baki sake Suhaima take bin shi da kallo tabbas akwai wani abin d'an ta6e bakinta tayi ko maye ruwanta ma, kar6ar babyn tayi ta rungume shi a jikinta k'aunar shi na ratsa cikin zuciyar ta. Wayar Sabeer ce take k'ara kira na biyu kenan da ake yi mishi gashi tun da ya fita bai dawo ba. "Suhaima ajiye babyn ki kai mishi wayar tunda bai dawo ba " Cewar Yaya Aliyu, Babaa Lantana ta mik'awa babyn ta mik'e tare da d'aukar phone d'in nashi ta fita daga parlorn, kallon phone d'in take sosai tayi mata kyau da gani mai tsada ce sosai bana kad'an ba. Bata ganshi a tsakar gida ba don haka tayi sallama d'akin shi sau uku ba'a amsa ba, sai kawai ta tura kanta cikin d'akin wayam bata ga Sabeer, abin ya d'aure mata kai ina ya shiga ne. Fitowa tayi ta duba don ta duba kofar gida tana lek'awa ta hango abin da ya kusan sumar da ita saboda tsanannin tashin hankali, tuni jikinta ya hau rawa zuciyar ta na bugawa da k'arfi nan da nan idanun ta suka rikid'a daga farare sol zuwa ja, ba komai ta hango ba sai Sabeer da yake zaune saman wani d'an reshen bishiya da ya karye ya fad'o k'asa sai ake zama a kanshi sai wata budurwa wadda bata gane fuskarta ba tasha uwar d'amara a kugunta a tsaye gaban Sabeer suna dariya hankalin su kwance ita kuma tana wani jan mayafi tana rufe fuskarta tamkar mai jin kunya. Shi kuma yana mata magana, tuni Suhaima taji wani mugun kishi ya tokareta wanda batasan tana da irin kishin nan ba, batasan lokacin da ta k'arasa inda suke ba ta tsaya ranta a mugun 6ace. Tun tahowar ta Sabeer ya hango ta yana kallonta ta gefen idon shi ganin yanda fuskarta ta koma yasa shi narke murya yana dad'a jan budurwar da hira wadda kasance k'anwa ce ga Ashiru. Ganin ta d'auki tsayin seconds a tsaye babu wanda ya kulata yasa taja wani mugun tsaki tamkar zata tsinke harshenta, da sauri suka jiyo suka kalleta. "Laaa Suhaima ashe kece " Cewar budurwar yarinyar tana washe baki, wata harara ta gallawa buduwar wanda batasan ta iyata ba, sauran kad'an dariya ta kubcewa Sabeer ganin abin da tayi. D'an wani tunani Suhaima tayi sai kawai ta k'ak'alo yak'en dole tace "Eh ni ce Sadiya ya kike? " Tana washe hakora tace "Lahiya lau wallahi yanzu tahowar da zanyi gidan ku zan shigo ganin jaririn Aunty Aliya sai wannan d'an binni ya tsayar da ni " "Hmmm " Abin da Suhaima ta fad'a kenan, sannan ta mayar da hankalin ta kan Sabeer ta mik'a mishi wayar shi ba tare da sun had'a ido ba tace "Kiran ka akai " Bata bari ma ya kar6a ba ta sakar mishi ita Allah ya sanya yayi saurin cafewa ba don haka ba da ta kwankwatse sai kawai ya bita da kallo har ta wuce cikin gida kafin ya sauke ajiyar zuciya ya mik'e shima ba tare da ya kula Sadiya ba ya wuce cikin gidan d'akin shi ya shiga ya rufe k'ofa tare da kwanciya saman katifa yana son fassara abin da yake kan fuskar Suhaima amman ya kasa tantacewa nan ya fara juyi kawai. Suhaima kuwa tana shiga gidan ta wuce zuwa cikin d'akin ta idanun ta sun rufe da wani irin abu da ta tabbatar da ba komai ba ne sai kishin Sabeer, fad'a wa tayi kan gadon ta tare da fashewa da wani irin kuka, tasan idan ka fara son mutum dole kayi kishin sa kenan ya ita ta fara son Sabeer tunda gashi daga nin shi da wata batasan dalilin tsayuwarta ba ta ji wani abu ya tokare mata wanda tasan ba komai ba ne sai kishin Sabeer!...... _ku cigaba da hak'uri fan's da ni, ga wannan ku yi manage da shi please_ Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 59-60* Tana kwance kawai taji an dafa bayanta a d'an tsorace ta d'ago kanta sauke ajiyar zuciya tayi don ganin Aunty Aliya ce ta dafata. "Tashi mu yi magana Suhaima" Tashi zaune tayi tana mai sunkuyar da kanta tana murza 'yantsunta batason ta kalli Aunty Aliya su had'a ido kada ta karanci wani abin akan fuskarta. "Hala Suhaima kin fara son Sabeer ne kike kishi dashi? " A razane ta d'ago kanta tana kallonta, gid'a kanta Aliyah tayi tare da cewa "Idan baka son mutum taya zaki fara jin haushi don kin ganshi a tsaye da wata?" "Ni fah Aunty bason Sabeer nake ba ni ba haushi naji ba fah dana ganshi da wata a tsaye" "Shikenan tun da ni ban isa ki fada min matsalar ki ba amman tabbas kwanaki biyun nan kin canja don ba haka kike ba, amman tun da kin ce ba haka ba" Tana gama fad'in haka ta juya zata tafi da sauri Suhaima ta sanya hannun ta ta rik'o na Aunty Aliya da D'an k'arfi ta matse hannunta "Ni kada ki ji min ciwo kawai ki cikani na tafi tunda ni baki d'auke ni matsayin Yayar ki ba kuma abokiyar shawarar ki, ni da nasan Suhaimar dana sani ba haka take ba bata iya 6oye min komai nata" "Aunty kiyi hak'uri ki zauna zan fad'a miki koma mene " Zama Aunty Aliya tayi kusa da Suhaima. Kamar bazata yi magana ba tayi shiru sai mutsu mutsu take da baki, d'an kallonta Aliyah tayi tare da girgiza kai kawai wani lokacin Suhaima tana bata mamaki idan tana wasu abubuwan. "Idan baza ki magana ba zan tafi ". Cikin rawar murya kamar mai shirin fashewa da kuka tace "Uhm... Uhm Aunty ni kaina na rasa mai yake damuna haka, cikin kwanaki biyun nan idan Sabeer yayi min magana ko muka had'u sai naji gabana yana fad'uwa, sannan kuma kawai d'azu dana ganshi da wata sai naji wani takaici wanda ya sanya ni kuka" "Kin fara son Sabeer kenan ". Waro ido waje tayi tare da dafe kirjinta da hannu kafin tace "Taya na fara son Sabeer Aunty bayan ni kuma sam baya gabana? ". "Ta yanda kika fara kishi dashi, Suhaima ina mai k'ara tunasar da ke da kada kiyi abin da zai sanya ki dana sani daga baya saboda na tabbatar idan kak'i Sabeer zaki zo kina nadama mara amfani don kafin ki samu wanda zai so ki kamar Sabeer zaki dad'e kina nema, kiyi amfani da damar ki Suhaima kafin ta kubce miki " Tana gama fad'in haka ta tashi ta fita saboda kiran da Babaa Lantana tayi mata, ta bar Suhaima cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa. "Nayi amfani da dama ta kafin ta kubce min, me Aunty take nufi.....! " Dafe kanta take wanda ya fara yi mata ciwo gaba d'aya ta rasa me ya kamata tayi shin zata bi shawarar Aunty Aliya ne ko kuwa zata bi abin da zuciyar ta yake kitsa mata na kada ta bari son Sabeer ya zauna mata cikin zuciya idan ba haka ba zatayi nadama don family d'in Sabeer baza su so ta ba a matsayin surukar su duba da wulak'ancin da tasha lokacin bikin Jiddah. *_After two weeks_* Acikin wannan satin ne bayan an sha sunan d'an Yaya Aliyu wanda aka sanya mishi sunan Baba Adamu, su Babaa Lantana sun so ya sanya sunan mahaifin shi Umaru amman Aliyu da Suhaima suka k'i aminta da hakan k'ememe don baza su ta6a mance abubuwan da mahaifin su ya aikata musu ba, Ameer Suhaima ta sanya yaron suna fad'a mishi saboda 6oye sunan shi da suka yi. Zuwa wannan lokacin Sabeer ya dad'a ramewa sosai sakamakon tunani da ya sanyawa kanshi gashi yaja baya da al'amarin Suhaima da yana da ikon da zai cire sonta cikin zuciyar shi da yayi, duk wanda yasan Sabeer a baya yanzu ya ganshi sai ya tausaya mishi musamman akasan A SANADIN SO ya zama hakan gaba d'aya ya fita hanyar Suhaima tunda ko ya kulata ba wani sauraren shi take ba, sosai Aunty Aliya da Yaya Aliyu suke tausaya mishi don yayi alkawarin bazai yiwa Suhaima auren dole ba sai dai kawai taji ana d'aura auren ta da Sabeer sosai Aliyu yana bashi tausayi. Ta 6angaren Suhaima ma duk ta wani rame saboda son Sabeer da kullum yake shiga cikin zuciyar ta yana nuk'urk'usa kowanne sashi na cikin zuciyarta, sai dai ta kasa bawa zuciyar ta aminta har takai da ta furtawa Sabeer cewa tana son shi zata aure shi sannan zata iya jure duk wani wulak'anci na family d'in shi zata jure shi indai Sabeer zai rik'e ta cikin mutunci bazai juya mata baya. Da wannan tunanin take kwana take tashi tana jiran Sabeer ya k'ara furta mata kalmar so a time d'in take son sanar dashi ita ma ta kamu da son shi, a lokacin da take kok'arin fad'a mishi ta kamu da sonshi a lokacin kuma ya canja mata ko magana bata had'a su yanzu ya zatayi kenan. Zaune take a d'aki tana wannan tunanin da ya zame mata kamar karatu don a kullum makamancin tunanin take yi, runtse ido tayi hawaye masu zafi suka samu sauka asaman face nata, zafi zuciyar take mata. Zumbur ta mik'e tsaye da zaunen da take ta fito tsakar gida nan ta fara shara gyara gidan tsaf tayi sannan tayi wanke wanke da wanke toilet kafin ta wuce d'akin Aunty Aliyah ta gyara mata shi tsaf ta sanya turaren wuta, kallonta kawai Aunty Aliya take saboda ganin yanda take rama gashi kana kallon face nata zakasan tana d'auke da damuwa, har ta gama sanya turaren wuta ta fita daga d'akin tana kallonta ajiyar zuciya ta sauke tana mai taya Suhaima da addu'a Allah ya yaye mata abin da yake damunta. Agurguje tayi wanka ta shirya cikin wasu kaya pakistan dogon wando white ne sai rigar da tsayinta wajen gwiwar ta ne itama farace rigar sai touch d'in flower's blue ajikin gaban rigar body spray ta fesa bayan ta shafa powder da man le6e, tayi kyau duk da ba wani make up tayi ba. Hijab dogo mai hannu blue colour ta sanya sannan ta zura flat shoes akafanta white ta fito ko d'akin Aunty Aliya bata shiga ba ta fita, a k'ofar d'akin da Sabeer yake ta tsaya tana son shiga tana kuma tsoro gabanta sai fad'uwa yake, ta dad'e a haka kafin dakyar ta iya d'aga kafarta ta shiga d'akin sai dai kuma wayam babu kowa sai dai da alama bai dad'e da fita ba don ga kaya a zube a k'asa wanda ta ganshi ya sanya da safe. Da sauri ta k'arasa shiga ta tattara d'akin ta gyara ta share shi tas sannan ta hango wani diary nashi akusa da pillow d'auka tayi ta fara karanta wa. Tun da ta fara karantawa take kuka a hankali har takai da ta bud'e baki sosai tana kukan tausayin Sabeer daman ashe haka yake sonta, me yasa ta wulak'anta shi da tasan haka yake sonta da a lokacin da ya furta mata so ta amince dashi, me yasa bata tsaya ta fahimce shi ba ita wacce iri ce da bata tsaya tayi nazari akanshi ba. "Wayyo Allah nah...! " Fad'in Suhaima hawaye na zuba a idanunta. "Allah sarki Sabeer ashe kai masoyina na gaskiya dole a yau ba gobe ba na bayyana maka zuciyata ta dad'e da kamuwa da son ka!, i luv U Sabeer with oll my heart! " Tashi tayi tsaye bayan ta ajiye mishi diary d'in ta fita daga gidan gaba d'aya ma, a k'ofar gidan ta tsaya tana kalle kalle ta inda zata hango Sabeer, amman ko mai kama dashi bata hango ba sosai tayi mamaki don bai fiye yawo sosai ba sai dai idan Yaya Aliyu zai je wani wajen ya rakashi shima ba koyaushe ba sai abokin shi Ashiru da suke d'an fita amman basa nisa kuma basa dad'ewa sosai. "To ina yaje!? " Cewar Suhaima a fili ta furta hakan tana furzar da iskar bakinta, cikin sanyin jiki ta juya zata koma cikin gida kenan ta hango Ashiru, wata ajiyar zuciya ta sauke kafin ta k'arasa kusa dashi da sauri tace "Ashiru don Allah ko kaga Sabeer? " Da murmishi a fuskar shi yace "Eh yana cikin gonar Yaya Aliyu a zaune yanzu na barshi acan na taho d'auko abu " ajiyar heart Suhaima ta sauke tare da hamdala jikin zuciyar ta kafin tace "Yawwa nagode Ashiru" Tana gama fad'in haka ta wuce da sauri zuwa cikin gonar Yaya Aliyu, yayin da Ashiru ya wuce cikin gida. Tana k'arasa gonar ta fara dube duben inda yake ta d'an jima tana dubawa kafin ta hango shi kan wani dutse mai d'an girma a zaune, kallo d'aya zaka yi mishi ka fuskanci yana cikin damuwa. Ta jima tana kallon shi hawaye na zuba a idanunta na tausayin Sabeer kasa k'arasa wa inda yake tayi kawai ta tsaya tana kallon shi, jikinshi ne ya bashi ana kallon shi yasa shi d'ago kanshi yana dubawa ya hango Suhaima a tsaye ta zuba mishi ido, d'an murmishi ya saki na yak'e kafin kuma lokaci d'aya ya zaro ido waje fuskarshi d'auke da tsantsar tashin hankali da k'arfi ya furta "Suhaima! " Bazato Suhaima taji ya kirawo sunanta fuskarta d'auke da murmushi itama ta furta "Sabeer! " Ganin batasan abin da ya hango ba ne bane yasa shi zabura ya mik'e da wani irin gudu da zafin nama ya k'arasa inda take tsaye bai yi wata wata ba ya ture ta gefe guda ta fad'i k'asa. Arud'e ta d'ago kanta ta kalle shi inda kuma a daidai lokacin Sabeer ya saki wata k'ara da k'arfin gaske ya fad'i k'asa yana wani irin abu kafin kuma jikin shi ya sandare kamar matacce ya zama, cikin hargitsi Suhaima ta mik'e tsaye ta taho inda Sabeer yake kwance, sauran taku d'aya tayi ta k'arasa wajen ta hango abun da ya matuk'ar firgitata ya tsorata ta lokaci d'aya jikinta ya hau rawa na tsoro ko kwakkwaran motsi ta kasa balle ta nemi agaji....... Uhm ga Sabeer a kwance kamar matacce ko mene ya same shi sai ku biyo ni don jin abin da ya faru, mu had'u a next page don jin yanda zata kasance, ku cigaba da hak'uri fan's. Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 61-62* Ba wani abu Suhaima ta gani ba wanda yayi matuk'ar razana ta sai wani k'aton snake baki wuluk dashi wanda batayi tantama ba shine ya harbi Sabeer, ganin yayi kanta ne yasa ta bud'e muryar ta gaba d'aya ta zuba wata k'ara ta firgita, gaba d'aya jikinta rawa yake yi saboda tsabar firgita rufe idanunta tayi kawai ta sadakar kasheta zai yi. Kafin ya k'arasa inda take ne Aliyu da Ashiru wanda suka taho gonar suka jiyo k'arar Sabeer a rud'e suka taho da gudu suna gaf da k'arasa inda suke ne suka sake jin k'arar ihun Suhaima da gudu suka k'araso ganin abin da yake kok'arin cutar da ita ne ya sanya su nufar inda yake nan Ashiru da Yaya Aliyu suka far masa da duka sai da suka kasheshi tsab tukunna suka k'arasa wajen da Sabeer yake kwance Suhaima tana rik'e dashi tana kuka kamar ta shid'e. Hankali a tashe suka k'arasa wajen sannan Yaya Aliyu da Ashiru suka d'auki Sabeer suka nufi gida, Suhaima tana biye dasu kamar tayi hauka saboda tashin hankali. Suna k'arasa gida suka shigar dashi gida nan aka kirawo mai magani na gargajiya ya fara aikin shi har ya cire dafin a k'afar Sabeer inda macijin ya cijeshi, sannan ya sanya magani a wurin nan yace musu zai iya farkawa a koda yaushe don ya auna arzik'i saboda macijin da ya harbe shi yana da dafi sosai, sannan ya ba da maganin da zai yi amfani dashi daga k'arshe kuma yace idan ya farka a kirawo shi sannan yayi musu sallama ya tafi. Aliyu da Aunty Aliyah hankalin su ba k'aramin tashi yayi ba kada d'an mutane ya mutu ta sanadin su haka kuma ta 6angaren Suhaima kuka sosai take tana zaune kusa da Sabeer idanun nan tamkar wad'anda zasu zazzago saboda kuka duk ta d'auki laifin ta d'ora wa kanta me yasa Sabeer bai bari ya harbe ta ba ya tureta, da dare wajen 11pm dakyar Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suka lalla6a Suhaima ta tafi d'akin ta sai dai sam babu bacci a idanunta balle kuma maganar abinci. Wanda rabon da taci tun da rana shima ba wani ci tayi sosai ba, ko yunwar ma bata ji baccin ma k'in yi tayi don gani take idan bacci ya d'auke ta kafin ta tashi Sabeer ya mutu tayi kukan har hawaye sun daina fita daga idanunta gashi sun kumbura sunyi ja sai zugi suke mata da rad'ad'i, daga k'arshe alwala ta d'aura ta shimfid'a abin sallah ta fara sauke sallahr mangarib da ishsha sannan ta fara nafila tana mai mik'a kukanta wajen Ubangiji ya tashi kafad'ar Sabeer tsayin daren nan a haka ta d'auka tana nafila sai da tayi sallahr asubah bacci yayi awon gaba da ita mai nauyi. *_ Washe gari 11am_* Firgigit Suhaima ta farka da baccin da yayi awon gaba da ita idanunta ta sauke kan agogo taga har 11 na safe mamakin nauyin baccin da ya d'auke ta take kafin kuma brain nata ya tunano mata abin da ya faru jiya da yammaci. Zumbur tayi ta Mike cikin kid'ima ta fita daga d'akin, babu kowa a tsakar gidan kai tsaye d'akin Sabeer ta nufa ta shiga ko sallama bata samu damar yi ba. Ta kutsa kai ciki a kwance yake sai Yaya Aliyu da yake sanya mishi magani a k'afar wajen harbin micijin daga gefe kuma Aliyah ce zaune ta zabga tagumi fuskarta d'auke da damuwa. Zubewa Suhaima tayi a k'asa kusa da Sabeer cikin rawar murya tace "Yaya bai farka ba har yanzu? " Cikin damuwa Yaya Aliyu yace "Eh Suhaima bai farka ba amman ki cigaba da yi mishi addu'a Allah ya tashi kafad'un shi " Wani marayan kuka Suhaima ta saki nan Aunty Aliya ta janyo ta jikinta tana rarrashin ta, ana cikin haka sai ga Babaa Lantana, Baba Adamu da kuma Ashiru sun shigo kowanne hankali shi a tashe Ashiru har da kukan tausayin Sabeer. Nan suka zauna kowa yayi jugum sai sautin kukan Suhaima ne yake tashi a cikin d'akin, sai da azahar tayi tukunna suka fita don yi sallah, Suhaima kuwa a d'akin tayi sallah ko wanka yau babu saboda tashin hankali (oh su Suhaima ashe dai ana son Sabeer ana tsoron kada ya margaya......lol ). Bayan ta idar da sallahr ne ta zauna kusa dashi tana mishi addu'a duk ta wani rame saboda tashin hankali, har yammaci dai Sabeer bai farka ba kuma still har zuwa yanzu Suhaima na zaune a d'akin babu abin da yake fitar da ita sai alwala. Sai bayan sallahr mangarib ne Suhaima na zaune kusa dashi taga ya farka a razane tare da yin magana da k'arfi yana cewa "Suhaima ki gudu maciji ne a bayanki Suhaima....! " Ya k'arasa maganar da fad'in sunan Suhaima da k'arfin gaske, da sauri Suhaima ta k'ank'ame hannun shi ana cikin haka Yaya Aliyu ya shigo da gudu bayan shi Aunty Aliya ce yana ganin Sabeer ya farka sai dai a razane yake cikin farinciki Aliyu ya rungume shi yana zubar da hawaye cikin zuciyar shi yana godiya ga Allah da ya sanya Sabeer farka wa. Nan dai aka kirawo mai magani ya duba shi ya bayar da wanda zai sha tukunna ya tafi, Suhaima tana zaune a gefe ta zubawa Sabeer ido hawaye farinciki na zuba a idanunta. Tun da Sabeer ya fara nutsuwa daga firgitar da yayi suna had'a ido da Suhaima da yayi mata kallon seconds ya d'auke kanshi bai k'ara kallonta ba, a hankali ta matso kusa dashi cikin sanyin murya tace "Sannu Sabeer " Ko kallon inda take baiyi ba ya d'auke kanshi, sau uku tana mishi sannu amman k'arshe sai ya kwanta kawai ya juya mata baya kawai. Tuni Suhaima ta tsure sai faman rarraba ido take gaba d'aya jikinta yayi sanyi, kallon ta Aliyu yayi tare da cewa "Suhaima tashi kije kiyi wanka kici abinci, yau fa ko wanka da abinci baki yi ba tunda ya farka kije ki huta " Cikin sanyin jiki da rawar murya tace "Toh Yaya " Tana gama fad'in haka ta mik'e jiki babu kwari ta fita yayin da Aliyu da Aliyah suka bita da kallon tausayi lallai Suhaima ta fara son Sabeer bana wasa ba. Tana fita Sabeer ya tashi zaune tare da cewa "Aunty ko zan samu ruwan d'umi nayi wanka " "Sabeer ka hak'ura da wanka sai gobe yanxu kayi brush kasha ko tea ne sai kasha maganin " Cewar Aliyu kenan. "Toh amman bazan ji dad'in jikina ba wallahi" Sabeer ya k'arasa maganar cikin shagwa6a abin ka da shagwa6a66e komai zai yi saiya sanyo shagwa6a murmishi kawai suka yi suna mai sake bashi hak'uri, daga nan yayi brush yasha tea sannan aka bashi magani dakyar yasha yana yatsina fuska saboda ya tsani shan magani balle wanda bai ta6a shan irin shi ba tunda Dr Faridah ta kawo shi duniya, a wannan daren dakyar bacci ya d'auki Sabeer saboda sharewar da ya yiwa Suhaima ta tsaya mishi a rai sam bai ji dad'in abin da yayi mata. Haka ma Suhaima dakyar ta iya yin wanka ta d'an ci abinci sannan ta kwanta bacci sai lalla6awa yayi ya d'auke ta. Abu kamar wasa Sabeer baya kula Suhaima duk da tana kok'arin shigowa sau biyu safe da dare tana duba shi wani lokacin har da rana tana kawo mishi abinci amman baya kallon inda take balle ya amsa sannun da take mishi, gaba d'ayan su ba k'aramin hora junan su suke ba har Sabeer ya warke ras yana fita amman bai daina share Suhaima ba duk da ya karanto tsantsar sonshi akan fuskarta da cikin idanunta, kullum itace cikin gyaran d'akin shi. Da sallama ta shigo d'akin hannunta da k'aramin flaks da cup wanda tayi mishi kunun gyad'a ta shigo d'akin, wani sanyin dad'i ne ya ratsa Sabeer jin sautin daddad'ar muryar Suhaima don rabon da yaji muryar tun jiya da safe saboda ciwon kan da ya hanata zuwa inda yake, amman sai ya maze ya amsa sallamar dakyar tare da d'auke kallon shi daga saitin k'ofar. Shiga tayi ta same shi zaune kan katifa yana danna laptop yana sanye da wani 3quater da T-shirt mai k'aramin hannu yayi kyau sosai ga gashin jikinshi sun kwanta luf dasu gwanin sha'awa, zama tayi a gefen katifar tare da ajiye abin hannun ta a k'asa tace "Wash! Na gaji yau, ya jikin ka? " D'an kallonta yayi na D'an second's tayi mishi kyau cikin wata gown light blue tayi rolling da black veil sai tayi kyau sosai duk ire iren kayan da Jiddah take bata ne, d'auke kanshi yayi cikin zuciyar shi yana cewa zai sanya a kawo wa Suhaima gowns masu kyau daga dubai don ganin yanda suke mata kyau sosai. "Uhm... Uhm ga kunun gyad'a nayi maka na zuba maka? " "Bana sha tafi da abin ki " Da d'an sauri ta kallo shi sai taga hankalin shi yana kan laptop, wani abu ne ya tokare mata makogaro muryar ta na rawa tace "Don Allah kasha tun d'azu nake aikin yi maka shi fah please " "Nace bana sha ana dole ne ko kuma na sanya ki " Hawaye ne suka zubo akan face nata kafin kuma ta fashe da kuka ta fara diddira k'afa a k'asa kamar wata small babe, hankalin shi a tashe ya ajiye laptop d'in tare da cewa "Toh ni me nayi miki da kike min kuka? " Cikin shagwa6a tace "Ba... Ba kai ne ba kace min baka sha kuma sai fushi kake dani bakason kula ni" Nan ta cigaba da kukan sosai ta bashi dariya hannun shi ya sanya ya rik'o hannunta don bazai jure ganin Suhaima a haka ba tana mishi kuka agaban shi, had'uwar hannun su waje d'aya shi ya saukar musu da wani yanayi a tsakanin su, sake runtse hannunta yayi da d'an k'arfi har sai da Suhaima tayi d'an k'ara kad'an. D'an sassauta rik'on yayi tare da cewa "Sorry! " Can k'asan mak'oshi yayi maganar. "Don Allah Sabeer kayi hak'uri bana jin dad'in baka min magana idan na duba ka " Girgiza kanshi yayi idanunshi cikin nata yace "Komai ya wuce Suhaima but zan tafi na bar muku gidan ku " D'an zaro ido tayi tare da cewa "Saboda me? " "Saboda wanda nazo domin ita bata sona gwara na hak'ura na koma inda na fito " D'an shiru tayi kafin ta d'ago kanta tace "Waya ce maka ba'a son ka " "Ke kika fad'a min " Ya k'arasa fad'i yana nunata da hannu. "Ni.... ni ba haka ba fah nake nufi ba kawai dai...... " Kasa k'arasa fad'a tayi don ganin yanda ya zuba mata ido tamkar wanda zai cinye ta da idanun shi...... Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 63-64* Kasa k'arasa fad'in maganar tayi ganin yanda ya zuba mata ido tamkar wanda zai cinye ta da idanun shi, jin tayi shiru ne kuma ta sunkuyar da kai yasa shi sanya hannun shi ya d'ago face nata kafin yace "Uhm ina jin ki Baby kawai dai me ". Kasa jure kallon cikin idanun shi tayi sai ta lumshe idonta, kallon eye's lashes nata kawai yake cike da sha'awar kissing nasu sai dai ba yanzu yake son aikata hakan ba, d'an bud'e idonta tayi suka had'a eye's nasu kafin cikin d'an jin kunya Suhaima ta janye idanunta saboda ganin har idonshi ya fara canja launi tace "Ya wuce fah, yanzu ka hak'ura zaka sha kunun ? Kada kace min a'a please " Mak'e kafad'a yayi cikin shagwa6a da langa6e kai yace "Nak'i wayon sai kin fad'a min idan ba haka ba bazan sha ba yarinya " Sam Sabeer ya mance da duk wani shiri da yayi na share Suhaima, lallai ba k'aramin so yake mata ba, maganar tace ta katse mishi tunanin shi da yaji tana cewa "Haba Yaya nah na zuba maka " Dariya ta bashi sosai jin sunan da ta kirawo shi. "Yaya na koma yau kuma?, wannan ai sunan Babban Yaya ne ni miji ne ba Yaya ba " D'an rufe hannunta tayi da tafin hannunta sai ta d'an wara yatsun tana kallon shi ta haka kafin tace "Ai kaima kazama Yaya tunda Yayan Jiddah ne kuma ka girme ni" Tana gama fad'in haka ta janyo cup ta had'a mishi kunun ta ajiye mishi a gefen shi. "Koh! " Ya fad'in hakan yana kashe mata ido d'aya wani kunya ne ya sake kama Suhaima sai kawai ta mik'e zata gudu har zata fice daga d'akin taji yace "Suhaima har zuwa yaushe zaki furta min kina sona ne?, ki tausaya wa rayuwata Suhaima ki amshi soyayyata nayi alkawarin kasancewa dake cikin tsayin rayuwata bazan ta6a wulak'anta ki ba ko na guje miki ina yi miki wani so wanda baki bazai iya kwatanta miki ba " Cikin sanyin murya ya k'arasa fad'in haka fuskar shi d'auke da damuwa. Jikinta ne yayi sanyi sosai har ta gaza d'aga k'afanta sai kawai ta tsaya itama zuciyar ta yayi rauni sosai ga wani sabon son Sabeer da ya k'ara shiga cikin zuciyar ta, gashi yanda ya sadaukar da rayuwar shi don ya ceci nata lafiyar da rayuwar koda iya hakan tasan Sabeer ba k'aramin sonta yake ba don haka bazata bar wannan damar ta kubce mata, don haka batasan lokacin da bakin ta ya furta "Ina sonka Sabeer nima bazan iya rayuwa babu kai ba " Tana k'arasa fad'in haka ta juya da gudu tabar d'akin cikin jin kunya. Sabeer kuwa zaune yake kamar mutum mutumi saboda tsabar mamakin abin da ta furta mishi, anya ba mafarki yake ba kamar yanda ya saba tunanin shi da ne ya katse a lokacin da hannun shi ya dangwarar da cup d'in kunun gyadar har yayi nasarar zubo mishi a hannun shi wata 'yar k'ara ya saki kad'an, kafin kuma ya wuntsala kan katifar ya fara juyi na jin dad'i tabbas ba mafarkin da ya saba ba ne, da gaske ne Suhaima tace mishi tana son shi, sai da ya gama juyin murna sannan ya d'auki phone nashi num d'in Daddy ya lalubo ya kira. Daddy yana picking ko sallama Sabeer bai yi ba saboda tsabar zumud'i cikin murna yace "Daddy ka tayani murna Suhaima tace tana sona zata aure ni Daddy! " Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Daddy fuskar shi cike da fara'a yace "Alhamdullilah congrats son, yaushe zaka dawo don muna kewar ka? " Yana dariya Sabeer yace "Very soon Daddy! " "Okay ya kamata ka dawo sai a fara maganar aure, uhm son za'a zama babba " "Kaiiii Dad! har da tsokana koh? " Ya fad'a cikin shagwa6a, dariya Daddy yayi kafin su cigaba da hira har zuwa lokacin da suka yi sallama, kwanciya Sabeer yayi ya lumshe idanun shi yana tuno lokacin da Suhaima take fad'a mishi tana son shi zata aure shi da wannan tunanin bacci yayi awon gaba dashi. Lokacin da Suhaima ta fito da gudu daga d'akin Sabeer sauran kad'an ta bige Aunty Aliya tayi saurin kaucewa tana cewa "Sorry Aunty nah" "Lafiyan ki kuwa Suhaima? " Fad'in Aliyah kenan. "Aunty lafiya qlau wallahi " tana gama fad'in haka ta wuce d'akin ta da sauri yayi da tabar Aliyah baki sake tana kallonta. Kan bed ta fad'a tana murginawa akai tana wani murmishi dagani murmishin farinciki ne take, jinta take sakayau kamar ta sauke wani babban abu akanta. "Ina son ka Sabeer, i luv U so much " Fad'in Suhaima a fili tana rufe fuskarta da hannunta kamar mai jin kunya wani na ganin ta. Tun daga wannan lokacin wata tsaftacacciyar soyayya ake gudanarwa tsakanin Sabeer da Suhaima, bawa junan su kulawa suke tare da tattalin juna, Yaya Aliyu, Aunty Aliya da su Babaa Lantana da Baba Adamu sun yi matuk'ar farinciki da kar6ar soyayyar Sabeer da Suhaima tayi. Yammaci ne irin na bayan sallahr la'asar Sabeer da Suhaima suna zaune a tsakar gidan saman wata babbar tabarma hira suke yi irin ta masoya. "Assalamu Alaikum " Suhaima ta tsinkayi sallama da muryar da bazata ta6a mance ta ba, don haka zumbur ta mik'e da sauri ta nufi k'ofa nan suka had'u da juna, wani ihun murna Suhaima ta saki tare da yin tsalle ta rungume Jiddah cikin tsananin farincikin ganin ta. Sai dai kuma jin abu ya tokare ta yasa ta sakinta tare da yin baya kad'an tana kallan d'an tudun da cikinta yayi, cikin dariya tace "Besty kaddai mun samu Baby " Dariya Jiddah tayi tare da kawo hannu ta d'an bugi kafad'ar Suhaima cikin k'asa k'asa da murya tace "To sarkin tonon silili kina son ki kunyata ni gaban su Yaya " Hannunta ta rik'o tare da juyawa da nufin su k'arasa wajen tabarmar su zauna, sai suka had'a ido da Aunty Aliyah wadda ihun Suhaima ya fito da ita daga d'aki ba shiri. Cikin farinciki Aunty Aliya tace "Jiddah yau kece a gari" Cikin dariya Jiddah tace "Ni ce wallahi Aunty ina Yaya Aliyu da Ameer ne ban gan....... " Sauran maganar Jiddah ta mak'ale a bakinta saboda had'a ido da Sabeer da tayi. Cikin mamaki tace "Yaya Sabeer! " Da murmishi kan face nashi yace "Sai yanzu kika kula dani kenan " Tana dariya tare da rufe bakinta tace "Yah Sabeer ba haka ba ne wallahi d'okin ganin Besty ne ya sanya ban kula da kai ba " D'an murmishi kawai yayi kafin ya wuce ya tafi, da mamaki sosai Jiddah take bin shi da kallo ko a mafarki bata zaci Sabeer zai zauna a irin wannan yanayin ba, kuma tayi farinciki da hakan don tun ba yanzu ba take sha'awar wani nata ya auri Suhaima saboda son da take mata, kama hannun ta Suhaima tayi suka zauna nan ta kawo mata ruwa kafin su fara gaisawa da Aunty Aliyah tana yi mata barka da samun Baby sun d'an ta6a hira kafin su wuce cikin d'akin Suhaima. Nan suna shiga hira ta 6arke tsakanin su Suhaima sai tsokanar Jiddah take yanda tayi k'iba, Jiddah na dariya tace "Yarinya sai kin yi uku nama don nasan Yah Sabeer zai baki kulawa ba kad'an ba" "A haba taya zan yi ukun ki da ban ganu ba" "Babyn kune ya sanya min wannan k'ibar don kiji yana zuwa nan duniya zan koma kamar yanda nake " Da haka suka cigaba da hirar su inda Jiddah take fad'awa Suhaima abin da ya sanya bata zo ba lokacin da suka dawo daga honeymoon laulayin ciki ne ya sanyata a gaba sai yanzu ta samu dama dama. Sai wajen mangarib Jiddah ta tafi cike da kewar Suhaima bayan ta ajiye musu tsarabar su har ta tafi dai basu k'ara had'uwa da Sabeer ba..... Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 65-66* Suhaima ta shigo gidan kenan daga rakiyar Jiddah k'ofar gida sai taji rik'o hannunta a d'an tsorace ta juya don duhu ya fara yi gaf ake da kiran sallahr mangarib. Had'a ido tayi da Sabeer yana mata wannan kyakkyawan murmishin nashi "Matsoraciya kawai " D'an sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace "Ni Allah kaban tsoro na kusa sanya ihun neman taimako " 'Yar dariya yayi kafin yace "Sorry Baby nah kin cika tsoro, haka jiya kika cika mana kunne da ihu don kinga lizard ya shiga toilet kina wanka " Murmishin dariya Suhaima tayi don ta tuna lokacin Allah yaso ta ko cire zanin jikinta bata yi ba ta hango shi manne jikin bango. "Baby ki rage tsoro please bana son ganin abin da zai na tsorata ki " D'aga kanta tayi alamar toh kawai nan ya cika mata hannu tare da cewa "Baby anjima zamu yi magana fah da kai lokaci yayi da ya kamata mu yi aure na bar rungumar pillow koh yah? " Ya k'arasa fad'in haka yana d'aga mata gira ya cigaba da cewa "Nasan kema kina buk'atar hakan koh? " Kunya ce ta rufe Suhaima don haka sai kawai ta ruga da gudu zuwa cikin gida tana 'yar dariya a hankali, bayanta Sabeer yabi da kallo yana murmishi kafin kuma ya juya ya fita zuwa masallaci. Suhaima tana shigowa tsakar gida ta nufi wajen alwala, nan tayi alwala ta wuce d'aki tana shiga ta shimfid'a abin sallah ta fara sallahr mangarib after ta idar ne ta janyo Qur'an ta hau karatu har zuwa sallahr ishsha bayan ta idar ne sai tayi addu'o'in ta daga k'arshe ta rufe addu'ar da neman za6in Allah tare da yiwa mahaifiyar ta addu'a kamar yanda ta saba, bayan ta kammala ne sai ta kwanta saman sallayar tana mai fad'awa duniyar tunani ta yanda zata iya d'auke kai daga duk wani wulak'anci da family d'in Sabeer zasu yi mata, ta jima tana wannan tunanin kafin kunnen ta ya jiyo mata kiran sunan ta da Aunty Aliyah take mata. Tashi tayi tare da kallon k'aramin agogonta taga har 8:32 na dare, da sauri ta rarumo hijab nata ta d'an fesa turare ta fito tunawa da tayi Sabeer ya fad'a mata zasu magana anjima, tana fitowa ta tarar da Aunty Aliyah a zaune tana bawa Ameer mama. Zama tayi kusa da ita tare da cewa "Aunty ga ni " Yawwa Suhaima daman Sabeer ne yake kiran ki yana k'ofar gida" Tashi tayi ta wuce ta fita a k'ofar gida ta hango shi zaune shi da Ashiru wajen ta nufa tayi musu sallama cikin sanyin murya, Sabeer sai da ya lumshe idanun shi kafin ya bud'e su akanta ya amsa sallamar ta. Ashiru ya gaida Suhaima ta amsa cikin fara'a kafin ya tashi yace "Toh Yaya ni sai da safe zan shiga gida " "Okay Ashiru sai goben" Yana gama fad'in haka ya wuce gidan su, sannan Sabeer ya dawo da hankalin shi kan Suhaima wadda take tsaye yace "Amarya ta zauna mana kada ki gaji da tsayuwa " D'an nesa kad'an dashi ta zauna saman wani dutse, nan ya fara tsokanar ta yana dariya ita kuma kunya yake bata don har yanzu ta kasa sakin jiki dashi musamman idan ta tuna abin da tayi mishi a baya. Bayan ya gama tsokanar ta ne sai kuma ya gyara zama cikin nutsuwa yace "Suhaima! " D'an d'ago wa tayi ta kalleshi kad'an saboda jin yanda ya ambaci sunan nata kafin tace "Na'am! " D'an ajiyar numfashi yayi kafin yace "Suhaima ina son gobe zan koma gidan mu fah" A d'an razane ta d'ago tana kallon shi don lokacin da ya fara maganar kanta a k'asa yake tana wasa da 'yantsunta. "Yes! Baby gida zan tafi zanje na samu Daddy yazo neman min auren ki, mun gama magana da Yah Aliyu dasu Baba don sam ban so awuce 2 month's ban mallake ki matsayin mata ta ba" "Wata 2 fah Sabeer haba me ma laifin nan da 2 year ". Cewar Suhaima kanta a sunkuye don bazata iya jurar ganin irin kallon da Sabeer yake mata, ji take kamar ta kwashe da dariya saboda tasan tsokanar shi take so take taga yanda zai yi don haka danne dariyar ta. Aikuwa wata harara ya dank'ara mata kafin yace "Sun yi kad'an ma 2yrs a barshi nan da shekaru goma ma yafi" Ba shiri dariyar da take danne wa ta kubce mata aikuwa ta fara kyalkyala dariya amman ta nutsuwa, sakin baki Sabeer yayi yana kallonta sai a time d'in ya lura tsokanar shi take, lallai kuwa idan ya kama Suhaima a hannun shi zata yi bayani. "Ya hak'uri mai da wuk'ar tsokanar ka nake a daina harara ta" D'an murmishi yayi tare da cewa "Lallai yarinyar nan kin rainani da yawa but zaki bayani idan kika shigo hannuna duk sai na rama abin da kike min " Marairaice fuska Suhaima tayi tare da cewa "Wayyo Allah kayi hak'uri ni fah tsokanar ka nake yi amman bazan k'ara ba" Mak'e kafad'a yayi tare da cewa "Nak'i wayon yarinya sai nima na rama " Ya k'arasa fad'i yana dariyar mugunta, baki ta murgud'a kafin ta turo shi gaba "Lallai ma yarinya ni kike murgud'a wa baki?" Girgiza kanta tayi sannan tace "Ni fah ba da kai nake ba ". "Toh naji dawa kike? " A shagwa6e tace "Ni kawai nayi ne". Murmishi kawai yayi kafin yace "Baby mu dawo maganar mu, mene ra'ayin ki? " Kanta a sunkuye tace "ni mezance toh Allah ya za6a abin da yafi alkhairi ". "Amin Baby nah, ko zaki rakani mu tafi tare? ". D'an zaro ido tayi tare da dafe kirji tace "waiii ni! rufa min asiri don Allah " D'aga kafad'un shi yayi kafin yace "to mene aciki " "Tabbb ni dai bazan iya ba wallahi " "Sarkin kunya kawai kin cika kunya Baby amman ina daf da cire miki ita kad'an zan rage miki ita" Waro idanunta tayi gaba d'aya tare da cewa "Tabbb daman ana cire kunya " "Eh mana sosai, idan kina so ma yanzu sai na fara cire miki " ya k'arasa fad'a yana dariyar mugunta Da sauri ta girgiza kanta tare da cewa "A'a bana so ina son kayata " Hannun shi ya sanya a gefen shi ya d'auko d'aya daga cikin phone's nashi, ya mik'o mata cikin mamaki take kallon shi ta kasa kar6a "Baby kar6i mana " Hannu tasa ta kar6a sannan yace "Ki rik'e wannan a hannun ki kafin kizo gidana mu je ki za6i wadda kike so " "A'a Sabeer baza mu yi haka gaskiya ka rik'e wayan ka, sai muna magana da wayar Yah Aliyu ". D'an 6ata rai yayi kafin yace "Baby bana son irin haka king kin 6ata min rai, idan kina son raina yayi sanyi ki kar6a " "Ayyah sorry na kar6a nagode sosai Allah ya saka da alkhairi naji dad'i " Wani sassanyar murmishi ya saki sannan yace "Baki k'arasa mana addu'ar ba fah Baby? " "Kamar yah fah" "Ki gane mana kamar kice Allah ya barmu tare Allah ya bamu yara masu kamar ku " Murmishi kawai tayi ta kasa magana daga k'arshe dai tattarawa suka yi suka nufi gida don dare ya fara yi, haka suka rabu cikin tsananin begen junan su. Washe gari wajen 10 na safe Sabeer yayi sallama da kowa ya fito Yah Aliyu ya d'auke shi a machine don fitar dashi titi, gaba d'aya kayan da yazo dasu ya bawa Ashiru su iyakar jakar laptop d'in shi sai phone nashi d'ayar kawai. Sun d'an jima a tsaye a titi kafin dakyar su samu taxi wanda zata kai Sabeer gida, shiga cikin motar yayi yayin da Yah Aliyu yaja driven taxi d'in gefe ya bashi kud'in motar Sabeer shi kadai zai dauka har gida ba tare da Sabeer ya sani ba, sai da Aliyu yaga tafiyar Sabeer tukunna ya koma gida zuciyar shi fal kewar Sabeer don su saba da junan su....... _Na gaishe ku masoya na ina jin dad'in yanda kuke bibbiyar labarin nan nawa_❣ _bazan mance karamcin ki ba my Momma nah (Aunty maijiddah musa), Ni Aishat ina matuk'ar kaunar ki kirkin na daban ne wallahi, Allah ya bar mu tare ya raya zuri'a, Amin ya rabbi_. ❤ Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 67-68* Wata sassanyar ajiyar zuciya Sabeer ya sauke a lokacin da driven taxi yayi parking a k'ofar get d'in D'AN FILLO FAMILY kallon gidan yake tamkar yau ya fara sanin shi, fitowa yayi daga cikin motar tare da rataya jakar laptop d'in shi a kafad'a sannan ya kalli d'an taxi yace "Malam nawa ne kud'in ka? " D'an taxi murmishi yayi kafin yace "Yalla6ai ai wanda ya rako ka d'in nan ya biya ni kud'ina " D'an zaro ido kad'an Sabeer yayi tare da cewa "Da gaske ne maganar ka" "Kwarai kuwa ya bani" Cikim tabbatar wa driven taxi d'in ya fad'a, gid'a kai Sabeer yayi cikin zuciyar shi kuwa wani son Suhaima da Yayan ta ne ya Kara ji sun shiga zuciyar shi gaskiya Aliyu yana karamci, amman duk da haka sai da Sabeer ya k'arasa d'an taxi d'in kud'i. Nan yayi ta godiya tamkar bakin shi ya tsinke saboda godiya yasan yau koda gida ya koma zai samu abin ciyar da iyalan shi na kwana biyu daga k'arshe yaja motar yayi gaba. Knocking d'in k'ofar gate yayi nan gateman ya bud'e, duk da ramar da bak'in da Sabeer yayi hakan bai hana shi gane d'an lelen family d'in D'an fillo ba ne ya dawo, washe baki yayi tare da bud'e k'ofar yana yiwa Sabeer sannu da zuwa, da D'an murmishi akan face nashi ya amsa mishi kafin ya wuce zuwa part d'in su. Yana shiga part d'in ya tarar Mumy bata nan haka ma Daddy don haka kawai ya wuce bedroom nashi, bude shi yayi ya tarar da ko'ina tsaf sai kamshin air freshener yake tamkar yana gidan, sai duhun da d'akin ya d'an yi sannan yayi zafi don haka k'arasa wa yayi ya kunna ac da fanka tare da kunna light d'in d'akin, ajiye jakar yayi saman sofa sannan ya hau cire kayan jikin shi. Yana gama cirewa toilet ya fad'a ya jima yana wanke jikin shi sosai a bathroom sannan ya d'aura alwala ya fito, lotion ya shafa tare da sanya white 3quater and T-shirt red colour mara hannu yayi kyau don kayan sun amshe shi, perfumes ya fesa different colours bayan ya taje kwantaccen gashin kanshi ya shafe shi da mayukan gyaran gashi tamkar wata mace. Bayan ya kammala gyara jikin shi tukunna ya shimfid'a abin sallah, nan ya gabatar da sallahr la'asar bayan ya idar ne yayi en addu'o'in shi sannan ya fito zuwa parlor. Tun daga kan steps d'in stairs ya hango Mumy zaune a saman dining table tana cin abinci, d'an girgiza kai yayi don ganin yanda Mumyn shi ta d'an rame alamar akwai abin da yake damunta cikin zuciyar ta, cikin tafiyar sand'a ya zagaya ta bayan ta ya sanya hannun shi dukka biyun ya rufe mata idonta yana murmishi. Mumy na cikin cin abinci taji an rufe mata ido da farko ta tsorata amman da taji wani kamshin turaren tilon d'anta sai ta d'an nutsu don fuskantar wane, don tasan dai Sabeer baya gidan sai dai ko Daddyn shine yake son zolayar ta sai ta sanya hannun ta saman hannun wanda ya rufe mata idon tana kok'arin zame hannun shi, amman ta kasa zame hannun sai kok'arin cirewa take but Sabeer yak'i bud'e idonta yana yin wata dariya k'asa k'asa. Cikin mak'e murya Sabeer yace "canki ko wane sai na bud'e miki ido " Jin muryar Sabeer tayi ta rikid'e mata kamar muryar Daddy don haka tace "My dear bud'e min ido please na ganka daman yau throughout ban ganka ba " A hankali Sabeer ya zame hannun shi a eye's nata ya jingina bayan shi da jikin bango yana sakin murmishi, juyawa Mumy tayi da nufin ganin Daddy sai eye's nata suka hango mata tilon d'anta, tsabar mamaki ne ya hanata gasgata abin da ta gani sai da ta mutsutstsuke idonta sannan tace "Sabeer! " Da mamaki da kuma rud'ewa da ganin shi ta sake ambatar sunan shi kafin wasu hawaye su fara zubowa daga idanun ta kallon shi take tamkar yau ta fara ganin shi. Shima wasu hawayen tausayin Mumyn tashi ne suka zubo mishi cikin sassarfa ya k'arasa ya tsugunna agabanta ya dire gwiwar shi a k'asa sannan ya d'ora kanshi saman cinyar ta, hannun ta take saman lallausan gashin kanshi tana shafawa ta kasa magana ma gaba d'aya. Muryar shi na rawa hawaye na zuba yace "Mumy baki yi murnar ganina ba koh, saboda ba'a son ranki na tafi ba, kina fushi da ni ne?" Girgiza kai take yi lokacin da yake magana, cikin sanyin murya tace "Bazan iya fushi da kai ba Son" "To gashi kin sanya damuwa a ranki kin rame ba" D'an murmishi tayi kafin tace "tunanin halin da d'ana yake ciki ne ya sanya ni ramewa da shiga tashin hankali,amman yanzu tun da nagan shi a gabana zan kwantar da hankali na " "Mumy kenan, nayi kewar ku ke da Daddy wai yana ina ne? " "I missed U too Son, Daddyn ka yana office bai dawo ba, yaushe ka dawo, zo kaci abinci " Duk ta rud'e da ganin tilon d'an nata sai faman tambaya take watsa mishi akan lafiyar shi don ta d'an razana da ramar shi da ta gani da duhun da D'an yi, hannun ta ya kamo yana kallon ta kafin yace "Mumy ki nutsu ni ina cikin lafiya sosai " "Okay zo kaci abinci, me zan zuba maka? " D'an shiru yayi kafin yace "ki ban duk abin da kika ci" Cikin farinciki tace "okay Son taso ka zauna " Haka ta kamo hannun shi ta zaunar dashi kusa da ita, kafin ta mik'e tsaye ta fara zuba mishi abincin, da kanta take bashi tana faman kallon shi tamkar wata sabon halitta a gabanta, ita kanta tasan tayi kewar d'an nata da yawa duk saboda matsiyar yarinyar nan d'anta yayi mata nisa. "Mumy tunanin me kike ne ba gashi na dawo ba" Da murmushi kan face nata tace "Son kawai ina tunanin irin wacce wahalar kayi a k'auyen da ko wutar nepa babu " "Haba Mum aikuwa suna da wuta sai dai ba'a fiye samu sosai ba" D'an ta6e bakin ta tayi sannan tace "kuma kana iyacin abincin su naga duk ka rame kayi bak'i " "Mum kibar wad'annan tambayoyin please " "Shikenan Son na bari " Tana gama bashi abincin suka koma parlor tana rik'e da hannun shi gane take tamkar zai sake guduwa ya barta, basu dad'e da zama ba Daddy ya dawo agajiye sosai yake, amman had'a ido da Sabeer yasa shi neman gajiyar tashi ya rasa nan suka yi hugging d'in junan su cikin tsananin k'aunar junan su. Nan babu dad'e wa Family d'in D'an fillo dashi kanshi Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suka samu labarin dawowar Sabeer, nan suka dunga shigowa ganin Sabeer kusan dukkanin su sunyi farincikin ganin shi, musammam Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah don rungume shi sukayi tamkar zasu mayar dashi cikin jikin su saboda tsabar son da suke mishi. Jiddah wadda agidan ta wuni ta d'ago kanta suka had'a ido da Sabeer wanda yake ta zuba musu shagwa6a su kuma sun shashance da lalla6a shi, dariya take son fashewa da ita amman ganin hararar ta da yake yi ne ya sanya ta kunshe dariyar ta, daga k'arshe sai ta faki idon shi tana mishi video don ta nunawa Suhaima ta shirya zama da shagwa6a66en miji..... Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 69-70* Tun bayan tafiyar Sabeer gida Suhaima ta shiga tsananin kewar shi ranar cikin kewar shi take duk ta sanyawa kanta damuwa ko abincin kirki ta kasa ci sai tunanin Sabeer, sam ta mance bata kunna wayar da ya bata ba duk a tunanin ta a kunne take. Sabeer kuwa duk ya shiga tashin hankali da ya kirawo ta yaji wayar a kashe yana son sanar da ita ya sauka lafiya sannan ya fad'a mata yanda yayi kewarta na tsawon yini guda, daga k'arshe dai sai kiran Yayah Aliyu yayi bayan sun gaisa yake fad'a mishi ya sanarwa da Suhaima ta kunna phone nata zai kirata tukunna suka yi sallama. Tana kwance still har yanzu har bacci ya fara fisgarta sai taji sallamar Yah Aliyu ya shigo d'akin, kallon ta yayi cikin kulawa kafin yace "K'anwata me yake damun ki duk kinyi wani iri yau kodai duk tafiyar Sabeer d'in ne ya sanya ki zama haka" Ya k'arasa maganar cikin zolaya, da sauri Suhaima ta rufe fuskar ta da hannayen tana 'yar dariyar jin kunya tace "Kaiiii Yaya! " "Eh mana gaskiya ce ina kula da ke fah ko abincin kirki baki ci ba sannan baki zo munyi hira ba " Kasa magana tayi don batasan da me zata kare kanta ba don kuwa maganar shi haka take, ganin haka yasa shi mik'e wa tsaye yana murmishi yace "Sabeer yace ki kunna wayar ki zai kirawo ki sai da safe " Yana gama fad'in haka ya fita, d'an waro ido tayi kad'an tare da cewa "Daman wayar a kashe take oops! " Bata tsaya 6ata lokaci ba ta janyo wayar ta kunna ta sannan ta zuba mata ido tana sauraren kiran Sabeer. Ko mintuna goma cikakku batayi da kunna phone d'in ba taji ta d'auki ringing, d'auka tayi ba tare da duba screen d'in ba saboda sauri da zak'uwan son jin voice d'in Sabeer. "Hello Baby nah ". Lumshe idonta tayi saboda jin saukar daddad'ar muryar Sabeer cikin kunnen ta har ta shagala ma sai da ta sake jin muryar shi yana mata magana sannan ta sauke ajiyar zuciya ta amsa mishi tare da gaida shi. Bayan ya amsa ne suka d'an ta6a hira ta tsayin wajen mintuna 30 sannan suka yi sallama da junan su don ganin dare ya fara yi, kowannen su cikin kewar d'an uwanshi suke. Bayan dawowar Sabeer da kwanaki uku ne ya buk'aci da iyayen shi su je neman mishi auren Suhaima, nan take Daddy ya aminta da hakan don haka ya had'a kan 'yan uwan shi maza suka had'u zuwa part din mahaifin su suka sanar mishi don ya tsayar musu da ranar tafiya neman auren Suhaima. Sam Alhj Ahmad d'an fillo ba'a son ranshi yayi magana ba don kana kallon fuskar shi zaka karanci hakan, don farincikin Sabeer kawai ya aminta da auren nan amman sam baya so Suhaima, nan ya yanke lokaci zuwa nan da sati biyu su Daddy zasu je, aikuwa Sabeer najin haka ya tubure bazai yadda ba don sati biyu sunyi mishi nesa shi fah da ason ranshi ne aranar a d'aura auren Babyn shi ta tare a gidan shi, ganin yanda ya tada rigima ne ya sanya shi tambayar shi yaushe yake son aje. Bud'ar bakin Sabeer yace shi gobe yake son aje kuma a tsayar da lokacin biki nan da sati uku, don fah shi har ga Allah satin ukun ya fad'a ne kawai amman sunyi mishi nisa, yanda ya buk'ata haka Alhj Ahmad d'an fillo ya amince ba don yaso ba sai don baya k'aunar 6acin ran d'an lelen shi, don haka ya kirawo 'ya'yanshi ya shaida musu gobe kowa ya tashi cikin shirin tafiya don zuwa neman wa Sabeer aure nan take suka amince da hakan. Sabeer ba k'aramin farinciki yayi ba da jin sun amince da abin da yake so, da dare Daddy yake sanarwa da Mummy yanda suka tsara shi da 'yan uwan shi ko uffan Mumy bata ce ba k'arshe sai juya mishi baya tayi ranta a k'untace batason Suhaima bazata ta6a son yarinyar da ta fito daga k'auye ba kuma 'yar talakawa ta had'a zuri'a da ita dole ta sami mafita ta tarwatsa auren kafin lokaci ya k'ure mata. *** *** *** Duk wasu shirye shirye sun kammala shi na saukar bak'in su, anyi musu lafiyayyen girki sannan Yah Aliyu ya siyo musu drinks na kwali da faro, d'akin da Sabeer ya zauna nan suka tsaftace shi aka sanya mishi turaren wuta aka shimfid'a tabarmi don nan zasu sauki bak'in su. Bayan Suhaima ta k'arasa gyaran gidan taje tayi wanka ta shirya cikin wani maroon less d'inkin riga da skirt sunyi mata kyau sannan ta zuba hijab agurguje ta fice daga gidan don tana kunyar su zo su sameta, ban da wani irin nishad'i da take ji a cikin zuciyar na daban a yau d'in nan gashi tana son ganin kyakkyawar fuskar Sabeer. Tana shiga gidan Babaa Lantana da sallama a bakin ta suna had'a ido da Babaa Lantana ta sanya dariya tare da cewa "Oh amarya Suhaima ai na d'auka bazaki bar gidan ma zama zaki yi da na ji ki shiru " Akunyace tayi 'yar dariya tare da zama a gefen ta tana cewa "Haba Babaa kinsan bazan iya zama ina jin kunya ne " "Ai na d'auka ku 'yan zamani babu wannan kunyar a wajen ku ashe da akwai masu ita " "Uhmmm" Kawai Suhaima tace kafin ta d'ora da cewa "Ni daga zuwa kin isheni da surutu ko ruwa baki ban balle ki kawo min abin dad'in da Baba ya kawo miki " "Lallai gidan bakon ki ne ko yau kika ta6a zuwa ai kinsan hanyar wajen ajiye ruwan" "Tabbb d'an tsohon nan naki yana kok'ari nasan shima idan ya dawo gida ko ruwan sha bakya kawo mishi " 'Yar hararar wasa Babaa Lantana tayi wa Suhaima kafim tace "Ku yanzu mai kuka iyama a yiwa miji hidima, wata ma miji ya dawo daga aiki ko sannu da zuwa babu balle aje batun kawo mishi ruwa mai sanyi ya jik'a mak'ogaran shi, wata ma ko kallon inda yake baza tayi ba balle yasa ran ayi mishi magana duk wata kulawar miji da hidimar shi ba'a fiye sauke mishi ba sai afkin kwalliya kamar ta aljanu da kyalakyalen da basu zu amfane su ba, wata ma ba don mijin nata zata yi kwalliya ba sai don zata fita anguwa gasu nan da yawa muna gani kuma muna jin labari, idan kika ga wata awaje ma fes da ita idan kika je gidan watak'il ko ruwan gidan baza ki iya sha ba sannan....." "Kaiii Babaa Lantana daga tsokana zaki d'auko dogon sharhi haka kamar wata ma'aikaciyar gidan redio sai zuba kike " Cewar Suhaima kenan bayan ta katse Babaa Lantana daga maganar da take. D'an hararar ta tayi kafin tace "Yo ai gaskiya nake fad'a da kin barni na cigaba sai ki d'auki abubuwa masu amfani ke da zaki tafi birni ga mijin ki kyakkyawa kamar balarabe don nasan baza ya rasa mata masu rububin son shi ba, don yanzu mun zo wani irin zamani da sam wasu matan basu da alkunya sai kaga mace har mace amman ta zubar da k'imar ta tana furta wa namiji so babu kunya wannan abin yana ban takaici " "Allah ya kyauta " Abin da Suhaima tace kenan tana jin wani abu yana mata tuk'uk'i cikin zuciyar ta da taji Babaa Lantana tace yanzu haka da akwai wasu matan da suke son Sabeer wad'anda suka fita kyau, wayewa da ilimi na boko tunda ita iyakar ta secondary kawai. "Yanzu me kika shirya mishi wanda zai ci idan yazo? " D'an yatsina fuska Suhaima tayi tare da cewa "Tabbb ni ban wani shirya mishi komai ba sai abubuwan da aka tanadarwa bak'in" Kama baki Babaa Lantana tayi sannan tace "Allah ya shirye ki Suhaima yanzu baki d'an yi mishi abu na musamman ba shi d'aya haka ake tar6ar saurayin" Cikin yanayin shagwa6a tace "Toh ni me zanyi mishi kawai yaci wannan na gaji tun safe nake aiki wallahi " "Ke tafi can tsaya sanyin jiki na kwace miki shi " Dariya Suhaima tayi kawai nan Babaa Lantana ta tashi ta fara kiciniyar aiki. "Babaa me zaki yi ne haka? " D'an hararar ta tayi kafin tace "Tsaya ki gani yarinya kiga yanda ake tar6ar bak'o " D'an ta6e baki Suhaima tayi tare da kwanciya tana ganin yanda Babaa Lantana take zirga zirga k'arshe ma fita tayi daga gidan, tayi mintuna goma da fita sai ga ta da kaji biyu yankakku ta cigaba da aikinta bata k'ara bi takan Suhaima ba. Phone nata ta d'auka ta bud'e data da yake tayi downloading what's app da Instagram sai fb da yake taga yanda Jiddah take charting shi yasa batasha wahala wajen iyawa ba, message's ne suka fara shigowa duk da iya Jiddah da Sabeer ne kawai take what's app dasu sai wani group na kitchen da na novels sai na make up wanda Jiddah ta sanya ta. Kan number d'in Jiddah ta shiga nan taga ta turo wani video tare a tsokanar ta amarya, bud'e videon tayi bayan ya gama bud'e wa sai ta fara kallo tun tana murmishi har ya sanya ta fara tuntsira dariya ganin irin shagwa6ar da Sabeer yake yiwa su Daddy sai kace wani d'an yayen yaro k'arami dariya tayi sosai har da hawaye, Babaa Lantana kuwa sakin baki tayi tana kallonta kafin kuma ta girgiza kanta tana cewa "Allah ya shirya " Ta wuce ta cigaba da aikinta. Bayan ta gama dariyar ta fad'a dogon tunani daman haka Sabeer yake duk da tasan daga yanayin shi zai yi shagwa6a bata zaci shagwa6ar zata yi haka wani murmishi kawai take saki wanda ita kadai tasan ma'anar shi. Wajen misalin karfe 2 na rana su Daddy suka k'araso tare da jagorantar Sabeer don yana son ganin Babyn shi, suna k'araso wa sun samu kyakkyawar tar6a daga wajen Yaya Aliyu, Baba Adamu da kuma wasu amintattun dattijai biyu abokanan Baba Adamu kuma mak'obtan su, su Daddy sunyi mamakin ganin irin wajen da Sabeer yaje neman aure duk da haka kuma k'auyen ya basu sha'awa gashi sun ji dad'in tar6ar karamcin da aka yi musu. Bayan sun yi sallahr azahar ne don a hanya ta riske su, sai aka yi zaman gaisawa kafin kuma a fara cin abinci, a d'an kyamace suka fara kai abincin bakin su amman da suka ji irin dad'in d'and'anon shi tuni suka zage suka fara ci. Ganin sun fara cin abincin ce yasa Sabeer zamewa zuwa cikin gidan suka gaisa da Aunty Aliyah sannan ta fad'a mishi a inda Suhaima take wani murmishi ya saki kafin ya fita kuma. "Wannan 'yar tsohuwar me kike girkawa ne duk kin cika min hanci da k'amshi yawu na sai tsinke wa yake " Cewar Suhaima tana shiga madafin Babaa Lantana wadda ke zaune akan kujera 'yar tsugunno tana faman yin aiki. "Tafi can ki ban wuri kina kallo ina faman aiki ko kizo ki taya ni da yake ci ne ai gashi kin taho, toh ko d'and'ane bazan baki ba na megidan nawa ne " Dariya Suhaima tayi tare da cewa "Yanzu duk wannan kamshin da nake shak'a ace baza'a sammin ba haba 'yar tsohuwa ta kaina " "Yarinya duk dad'in bakin ki bazan bayar ba ki bari idan yaci ya rage kyaci sauran " D'an turo baki tayi cikin sigar shagwa6a tace "Nayi ma fushi bazan ci ba " "Da naji dad'i kuwa " Cewar Babaa Lantana tana tattare kayayyakin zuwa cikin kitchen, nan ta shirya farfesun kaza da tayi mishi guda d'aya sai gashashshiya kaza d'aya tasha kayan had'i da mai sai shek'i da tashin k'amshi take, sannan ta dama mishi fura da ruwan randa mai sanyi ta zuba ta a dogon kofin silver, sauran kayan ma a cikin kwanan silver ta zuba sai ta d'ora saman farantin silver, bayan ta gama had'a su ne ta fito daga d'akin girkin tana cewa "Gashi nan na gama shirya komai sauran ya zo ki kasa kawo mishi don nasan an fad'a mishi kina nan zuwa kowanne lokaci zaki iya ganin shi ". Suhaima na dariya tace "Toh naji 'yar tsohuwa sannun ki da aiki don nasan yau kika kwanta sai kin kasa motsi saboda gajiya " Da harara ta bita kafin tace "An gaya miki jikina irin naki ne koda zan yini aiki ras zaki ganni, Allah Suhaima ki rik'e yaron nan sosai saboda yana son ki wallahi na tsakani da Allah " Tana gama fad'in haka ko rufe baki bata yi ba suka jiyo sallamar Sabeer aikuwa da gudu Suhaima ta fad'a d'akin Babaa Lantana, sosai abin ya bawa Babaa Lantana dariya. Kallonta Sabeer yayi had'e da cewa "Matar ke dawa kike dariya haka? ". Cikin dariya tace "Ni da wannan matar da kake kok'arin jajibowa ne daga jin sallamar ka ta kwasa da gudu sai kace wadda taga wani abin firgitarwa ". Murmishi ya saki tare da cewa "Babyn tawa ce kunya ce da ita Babaa, amman gashi ai kin hutashshe ta sai ki min sannu da zuwa " Washe hakora Babaa Lantana tayi tana cewa "Eh mana rabu da ita ni na kwace ka ai tun da babu abin da ta fini " Sosai maganar ta bawa Sabeer dariya, Suhaima na jin su a d'aki tana mirmishi ita kadai. "Ai sai ki fita ki kai mishi tabarma kyayi murmishin da dalili ba ki k'ule d'aki kina murmusawa ba ke d'aya " "Kaiii Babaa " "Ni dai ki tafi maza kin bar mutum a tsaye " Babaa Lantana ta fad'a tana mik'awa Suhaima sabuwar tabarma, kar6a tayi sannan ta fito daman Allah ya taimake ta da hijab d'in ta a jikinta. Fitowa tayi daga d'akin tana d'aga kai suka had'a ido da Sabeer sai kawai ta zuba mishi don yayi mata kyau sosai duk d'an bak'in nan da yayi da rama ya washe tsaf dashi, yana sanye cikin wani black jeans and T-shirt black mai kwala sai kuma ya d'ora wata yellown T-shirt mai dogon hannu daga sama, takalmin shi baki haka ma belt d'in shi sai agogon hannun shi k'irar Gucci shima bak'i, gashin kannan nashi yasha gyara sai shek'i yake gwanin sha'awa, shagala da kallon shi Suhaima tayi haka shima kallon ta yake don tayi mishi kyau ba kad'an ba. "Idan kun gama kallon junan naku sai ka zauna ni na wuce d'aki zanyi bacci ". Firgigit suka dawo hayyacin su tamkar wad'anda suka tashi daga bacci, saboda jin muryar Babaa Lantana da suka yi a kusa dasu duk kunya ce ta kama su ba irin Suhaima da take ji tamkar ta nutse a k'asa, wayance wa tayi da shimfid'a tabarmar yayi da Sabeer yake sosa kai, murmishi Babaa Lantana tayi ta wuce d'aki ta bar su. Bayan ta gama shimfid'a tabarmar ne cikin sanyin murya tace "Ka zauna mana " Zama yayi yana cewa "Baby ki k'ara kyau mene sirrin " Kunya taji ta sake tuk'unk'une wa cikin hijab, sai kawai ta fara gaida shi amsawa yayi cikin murmishi. Suna gama gaisawa ta tashi ta d'auko mishi abubuwan da Babaa Lantana ta had'a ta ajiye mishi tare da da ruwa da lemo wanda aka aka siyawa bak'i Babaa Lantana ta tura aka kar6o na Sabeer. "Baby nah yanzu baza ki bud'e min fuskar na ganki sosai ba? " D'an murmishi tayi har dimple nata ya lotsa kafin tace "Ni dai kaci abinci kawai nasan mybe ko breakfast baka yi ba " "Kamar kin sani Baby don ruwan tea nasha cup d'aya saboda kawai ina saurin nazo na ganki don nasan idan nazo baby nah zata had'a min irin abincin ta mai dad'i " D'an murmishi kawai tayi cikin zuciyar ta tana sake godewa Babaa Lantana da tayi tunanin dafa mishi wani abin. Zuba mishi tayi ya fara ci yana santi don gashin kazar yayi mishi dad'i sannan yasha furar sosai ba laifi, bayan ya gama ne suka d'an fara hira irin ta masoyan gaske. "Wai ina Sabeer ne? " Cewar uncle Aminu, nan suka dudduba bashi ganshi ba, Daddy ne yace "Mybe yana wajen Babyn tashi can nasan zai gudu " "Kaji ja'irin yaro shine yabar mu salon mu gama yanke magana ya dawo yana cewa ba haka ba " Fad'in Uncle Aminu dariya suka yi kawai irin tasu ta manya, Daddy sai kallo Aliyu yake don yaron ya birgeshi da gani yana da nutsuwa da kamun kai, yana fatan haka itama Suhaima Allah yasa haka take. Nan aka kirawo shi a waya, suna tsaka da hira yaji kiran nashi dole babu yanda zai yi ya tafi wajen su don shi fah gaskiya bai gaji da ganin Babyn tashi ba. Bayan ya je wajen nasu aka fara tsaida lokacin biki inda Sabeer ya nemi a sanya sati uku, su Baba Adamu suka nuna yayi kusa dakyar nan dai aka bar shi a 2 month's, nan suka zube kud'ad'an neman aure har da na sadaki, kasa kar6ar kud'in su Baba Adamu suka yi don gani suke tamkar siyar musu da Suhaima zasu yi, dakyar suka lalla6a su suka kar6a anan suka sake tabbatar wa lallai 'yan uwan Suhaima basu da son abin duniya. Cikin farinciki suka yi sallama da junan su, har sun shiga mota suka ga Sabeer zai bar wajen kamo hannun shi Daddy yayi tare da cewa "Son ina zuwa ne? " Yana sosa kai yace "Daddy zanje yiwa Baby sallama ne " Murmishi manya Daddy yayi tare da cewa "Mun baka 5 minutes kayi sauri don kada dare yayi mana " "Okay Daddy yanzu zan dawo " Yana gama fad'in haka ya wuce da D'an saurin sa don yiwa Suhaima sallama, bashi ya taho ba sai da ya kusan 30 minute's sannan ya dawo su Daddy sai tsokanar shi suke shi dai kawai murmishi yake nan suka yi sallama cikin farinciki suka tafi gida..... Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 71-72* Sai bayan mangarib su Sabeer suka k'arasa gida, yana shiga part d'in su ya hango Mumy kusa da dining table tana shirya abincin dare fuskarta d'auke da damuwa wanda mutum kallo d'aya zai mata ya karanci hakan. Yana zuwa ya rungume ta tare da bata peck a cheek d'in ta cikin farinciki yace "Mumy yau ina cikin farinciki sosai na kusan mallakar Suhaima ki tayani murna " Wani abu ne ya tokare mak'oshin Mumy wanda ya sanya ta d'an jimawa kafin ta bud'e bakinta tace "Son nasan ka gaji da yawa kaje kayi wanka da sallah tukunna " Ta k'arasa maganar cikin murmishin yak'en da yafi mata kuka ciwo, da yake Sabeer na cikin farinciki shi ya hanashi fahimtar yanayin Mumy, don haka kawai sai ya wuce up stairs. Bin bayanshi da kallo Mumy tayi kafin ta zauna saman kujerar dining table ta zabga uban tagumi, duk wannan abin da suke Daddy yana kofar shigowa parlourn yana kallon su. Ganin Mumy ta zauna ta zuba tagumi ya sanya shi k'arasa wa cikin parlourn hannun shi ya sanya ya janye tagumin da tayi kafin yace "Haba sweetie nah me yasa kike son shiga tsakanin farincikin d'anki, kinsani Suhaima itace farincikin Sabeer yana sonta rabuwa da ita ba k'aramin wani hali zai shiga ba, a matsayin ki na uwa kina mishi addu'ar fatan Alkhairi a wannan auren nashi, ni kaina da fari ban yarda ba da hakan ba, zama nayi tare da yin nazari kafin na amince mishi sannan da naje yau naga gidan da Son yake neman aure sai naji hankalina ya sake kwanciya da wannan auren don kuwa gidan gidan mutunci ne sosai, ina son ki kwantar da hankali kada wani ciwo ya shige ki matar mutum kabarin shi Allah yayi Suhaima ce zata kasance matar d'anki don haka kawai ki bisu da fatan alkhairi " Yana gama fad'in haka ya tashi ya wuce side d'in shi don kada a kirawo sallahr ishsha bai yi ko mangarib ba, Mumy tasan Daddy gaskiya ya fad'a mata but zuciyar ta tak'i amincewa da hakan. Bayan Sabeer yayi wanka tare da yin sallahr mangarib da ishsha ne, ya zauna saman sofa yana kok'arin kiran Suhaima hannun shi d'aya kuma yana rik'e da cup aciki fresh milk ce don baya jin zai iya cin abincin dare cikin shi a k'oshe yake ji Babyn shi ta cika mishi ciki. Lumshe idanun shi yayi jin sanyayyar murya Suhaima tana tambayar shi sun je gida lafiya, sake gyara kishingid'a yayi tare da cewa "Alhamdullilah Baby mun isa gida lafiya yanzu kin ganni a d'aki ni d'aya duk nagaji " "Ayyah sannu " Cewar Suhaima cikin tausayin shi. "Da munyi aure Baby nasan da ban da matsala zaki min tausa har na warware bama iya tausa ba har irin wanka da....... " Bata bari ya k'arasa maganar ba da sauri cikin jin kunya tace "Kaiii Sabeer baka jin kunyar fad'in wannan maganar? " "Keee Baby bana jin kunya indai da ke zanyi irin wannan maganar" Ya fad'i hakan cikin kwaikwayar maganar ta, dariya suka d'an yi kafin yace "Baby ina son ki da yawa kada ki wahalar da rayuwa, kada kiyi amfani da son da nake miki ki wahalar dani please " Ya k'arasa maganar kamar zai fashe mata da kuka, wani tausayin shine ya rufe Suhaima tare da wani irin son da yake k'ara shiga cikin zuciyar ta. "Sabeer don me zan wahalar da rayuwa bana fatan na kasance daga irin wadannan mutanen masu amfani da son da ake musu suke wulak'anta mai son su, ina maka son da bazan jure ganin ka cikin wahala ba balle ni na wahalar da kai, daga lokacin da ka zama mijina zan kasance mai yi maka biyayya dai dai iyawata" Wata ajiyar zuciya ya sauke wadda har sai da Suhaima ta jiyo shi kafin yace "Naji dad'in abin da kika ce Baby nah thank U very much" "Uhmmm " Abin da tace kenan, d'an murmishi yayi yana cewa "Baby ya neh koh bacci ya fara zuwa ne? " "A'a me kagani? " "Just naji kin ce uhmm" "Ba komai " "Okay bari na barki ki huta gud night and sweet dreams " "Same 2 U" A haka suka yi sallama kowa ya ajiye waya. Soyayya mai zafi suke nuna wa junan su tsakanin Sabeer da Babyn shi, duk wata kulawa wanda ya kamata suna bawa junan su, soyayya mai tsafta suke nunawa junan su, yayin da Daddy ya matsantawa Mumy da dole ita zata had'a lefen Sabeer saboda da fari da yayi mata maganar k'in amincewa tayi sai da yayi da gaske sannan ta yarda dakyar, ta 6angaren su Suhaima ma Yaya Aliyu da Aunty Aliya sai shirye shirye suke yi sosai na hidimar biki. Sabeer sai da ya nunawa Aliyu kada ya sha wahalar yi mata kayan d'aki zuwa kitchen don shi tuni ya gama shirya musu gidan su shi da Babyn shi, amman sam Yah Aliyu yak'i yarda ya kafe sai yayi dole tasa Sabeer hak'ura tunda baisan dalilin shi ba. *** **** *** *_After 2 week's_* "Hello Suhaima kina jina? " "Ehh Jiddah ina sauraren ki " "Yawwa Babyn Yah Sabeer gobe ina son zuwa zamu tattauna akan maganar bikin fah" Cikin rashin fahimta Suhaima tace "Kamar wanne shiri? " Hararar ta Jiddah tayi duk da tasan ba gani zata yi ba tun da a waya suke magana tace "Har kinsa na harare ki wallahi, da kin d'auka zamu yi biki lami ne kamar bikin Yah Sabeer da Besty na ai dole mu kwashi shoki " Dariya Suhaima ta tuntsire da ita kafin tace "Kinyi nauyin zaki kwaso shokin a haka? " "Dallah malama ina ruwan ki sai fah anyi duk wani zagaye zagayen ki yarinya " Suhaima na dariya tace "Toh sarkin masifa naji na yarda " "Yawwa ko kefa, kin ga zan d'auko mai gyaran jikin da zata yi miki ke dai kawai sai nazo don my dear ya dawo gud night " "Okay Allah ya kaimu " "Amin kiyi min d'an wake don Allah " "Zanyi miki kodan Babyn mu " Dariya suka yi kafin su yi sallama, sauke numfashi Suhaima tayi tare da gyara kwanciyar ta, wayar ta ne ya sake k'ara nan ta d'auka da sauri ganin Sabeer ne, hirar su ta soyayya suka sha sosai kafin su yi sallama, addu'ar bacci Suhaima tayi babu dad'e wa bacci mai dad'i ya d'auke ta.......... _Fan's kuyi hak'uri da page's d'in nan don ban samu damar yin editing ba dafatan za'a yi min afuwa duk inda aka ga error typing_ Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 73-74* Washe gari kuwa tun safe bayan ta gama had'a breakfast ta karya nan ta gyara d'akin ta tsaf da tsakar gidan zuwa wankin toilet da wanke wanke sannan ta fara yiwa Jiddah d'an waken da take buk'ata, wanda ta hada filawa da garin rogo kad'an a ciki. Bayan ta gama yin d'an waken ta ne ta daka mata yaji mai dad'i wanda yasha citta da garlic sannan ta yanka cucumber, tomatoes and onion, tana kammala wa ta wuce wanka, bayan ta fito ta shirya kanta cikin wani lace black and touch flower's pink colour d'inkin riga da skirt ne sunyi mata cif tayi kyau kam abinka da farar fata, tana cikin fesa perfumes ne ta jiyo muryar Aunty Aliya tana fad'in "Ashe kai ne tafe sannu da zuwa " D'an mamaki ne ya kama Suhaima ita dai tasan Sabeer baice mata zai zo ba, Jiddah ce ta sanar mata zuwan ta, amman bari taje ta duba ko bak'on Aunty Aliya ne, don haka sai ta janyo wani k'aramin veil pink tayi rolling dashi sannan ta fito. Kusan suman tsaye tayi ganin Sabeer da suka had'a ido dashi yana jifanta da wani sanyayyan murmishi har da wani d'aga mata gira. Tana kok'arin k'arasa wa inda yake ta jiyo sallamar Jiddah don haka sai kawai ta juya da sauri ta taro ta cikin farinciki, cikin tsokana tace "Maman twin's sannun ki da zuwa " "Yawwa Amaryar mu wallahi har kin fara kyallin amarcin gashi sai wani cika kike mene sirrin me Aunty Aliya da Yah Aliyu suke baki ne?" D'an murmishi Suhaima tayi tana sunkuyar da kai tare da cewa "Ke koh! Kin cika surutu" Ta k'arasa fad'i tana turo bakin ta, dariya Jiddah tayi kafin tace "Allah zan fad'awa Yah Sabeer idan ya kama wannan bakin kada yayi mishi ta sauk'i tunda aikin shi murgud'a baki da turo shi sai ya koya mishi h...... " Kafin ta k'arasa fad'in hankali sai kawai ta had'a ido da Sabeer yana faman kallon su, turus taja ta tsaya saboda mamaki kafin kuma ta wayance tana cewa "Ah Yah Sabeer kai ne?" Yana d'an hararar ta yace "A'a bani ba ne " Er dariya tayi tana k'arasa wa inda yake tana cewa "Ayyah Babban Yaya ban kula da kai ba ne " "Dole kice haka tunda gulma ta rufe miki idon tun da kika shigo kike gulmata ina kallon ki " "Kaiii Yaya ni ba gulmar ka ba fah nayi ba hirar mu muke ko Suhaima?" Ta k'arasa maganar da shagwa6a tana langa6e kai ta kalli Suhaima tana kifta mata ido alamar kada ta sanar shi abin da ce, batasan duk yaji ta ba d'auke kai kawai yayi yana murmishi shi dai kusan tsaf familyn shi sun d'an fi jituwa da Jiddah saboda kusan halayyar su d'aya, dariya Suhaima take kafin tace "Ni ba ruwana bansan me akai ba " "Auuu! Haka ma zaki ce shikenan " Tana gama fad'in haka ta mik'e fuuu tare da wuce d'akin Aunty Aliya, er k'aramar dariya Suhaima ta saki don Jiddah ta bata dariya, yayin da Sabeer yake binta da kallo cike da sha'awa don sosai dariyar tayi mata kyau dimples nata da yake so duk sun fito. Ganin yanda yake bin ta da kallo ne yasa ta d'an tsargu ta nutsu kafin tace "Au ashe bamu gaisa ba, ina kwana? " Ta fad'i tana rufe bakin ta da hannu, d'an murmishi yayi yana cewa "Baby bana cikin nutsuwata gaba d'aya " Gabanta ne ya d'an fad'i kafin tace "Subhanallah me yasa meka? " Fuskarta d'auke da damuwa ta furta hakan. "Baby abin da yake damuna lokacin auren mu yayi nisa da yawa, 2 month's fah aka sanya ni da nafison 3 week's, yanzu gaba d'aya fah 2 week's muka ci acikin wata 2 " Kallon shi take kawai idan banda abin Sabeer wata biyu nawa yake idan Allah ya basu aron rai, wasu ma shekara ake sanya wa ko wata 6 amman basu damu ba sai shi, amman sai ta danne mamakin ta saboda ganin yanda duk ya koma sai fitar da huci yake idanun shi har sun d'an canja launi saboda damuwa gashi ya wani kafeta da ido tamkar zai had'iye ta haka yake jin shi ga tsugunnawar da tayi ta k'ara wani sanya tunanin cikin zuciyar shi sai a lokacin ya sake tabbatar wa Suhaima yarinya ce k'arama. Anya bazai d'aga mata k'afa ba yana ganin tamkar zai iya cutar da ita a yanda yake jin shi, amman da wuya ya iya juriyar hakan don ma yau yaga ta k'ara cika kamar yanda Jiddah ta fad'i ga hips nata da boobs nata sun dad'a fitowa, wani had'iyar yawu yayi lokacin da ya kai idanun shi kai wanda ya sanya shi kusan kwarewa, da sauri ya kau da kai lallai Annabi yayi gaskiya da yace kada kana kallon matar da ba taka ba don bakasan inda idanun ka zasu kai gashi yau idanun shi sun ja mishi ganin abin da zai hanashi bacci cikin jin dad'i, daman can ba wani jin dad'in baccin yake ji ba tun lokacin da idanun shi suka fara ganin Suhaima. Muryar Suhaima da yaji ne yasa shi d'ago wa ya kalleta yana sauke ajiyar zuciya, sai da gaban ta ya fad'i da ganin yanda eyes nashi da face nashi suka canja, cikin kwantar da murya tamkar mai rad'a tace "Sabeer bana son kana sanya damuwa cikin ranka kada ya janyo maka wata matsalar please , wata 2 d'in kamar yau ne" D'an murmishin yak'e yayi kafin yace "Ba komai Baby na hak'ura amman ki tabbatar idan kika zo hannuna Hmmm.... " Yak'i k'arasa maganar tashi, cikin rashin fahimta tace "Kamar ya idan nazo hannun ka? " "A'a ba komai Baby " Ya k'arasa maganar da dariyar mugunta a d'an tsorace ta kalle shi don ta gama tsarguwa, ganin haka ya sanya shi danne dariyar shi don kada ya tsorata ta yace "Calm down Baby matsoraciya ba fah wani abun nake nufi ba, yanzu me zaki ba ni naci? " Ya fad'i hakan yana bagarar da zancen don baya son ta sanya shi a ranta. "Me kake so nayi maka? " "Baby fura ma ta isheni" "Ita kadai kawai? " D'an girgiza kai yayi kafin yace "Kaiii Baby anya zan iya shan furar nan kuwa kada ta dame ni fah " D'an zaro ido kad'an tayi sannan tace "Furar ce zata dame ka, me take maka? " D'an murmishi yayi sannan yace "zaki san kome take min amman ba yanzu " Ya fad'i yana d'aga mata gira kan ya cigaba da cewa "Eh Baby kiyi min kunun da kike min zan je na dawo " "To shikenan " Daga haka ya mik'e ya fita, ita kuma ta fad'a falon Aunty Aliya ta tarar da ita suna hira da Jiddah. Jiddah na ganin ta ta harare ta kan tace "Shine nace zan zo kika fad'a mishi yazo koh? " D'an murmishi Suhaima tayi tana cewa "Kinsan Allah Jiddah bansan da zuwan shi ba ko da safe munyi waya bai fad'a min, idan ya fad'a min zai zo ai zan fad'awa Aunty Aliya koh? " Murmishi kawai Aunty Aliya tayi, "Ni fah kinsan abubuwa zamu tattauna masu mahimmanci kin je kun wani lik'e kuna hira " Er kunya ce ta kama Suhaima don ga Aunty Aliyah a zaune a wurin, d'ago kanta tayi ta harari Jiddah tana tuna mata da akwai Aunty Aliya a wurin fah. Dariya Jiddah ta sanya kafin tace "Uhm sabon salo yau ke ake jin kunya Aunty Aliya fah " Dariya tayi sannan tace "Allah ya shirya ki Suhaima yau wani sabon salon aka fito dashi to wallahi tun wuri yarinya ki cire iyayin kunyar da kika yafa a toh" Cewar Aunty Aliya kenam dariya suka sanya kafin Jiddah ta k'ara cewa "Yanzu sai ki kawo min d'an wake na mu fara maganar da ta kawo ni koh yah amaryar mu? " "Ban yi ba kuwa don ki ji" "Tabd'ijam yarinya kinma isa tun wuri kije ki kawo min " Tashi tayi tana murmishi taje ta kawo mata duk ta zuzzuba ta yawun Jiddah har wani tsinkewa yake, tana gama hadawa ta mik'a mata, kar6a tayi tana cewa "Da kuwa baki yi ba da sai na kaiwa my dear k'arar ki kuma yau sai anganmu a rana " Dariya Suhaima tayi tare da cewa "Aci lafiya Maman twins" Mik'e wa Suhaima ta sake yi don tafiya yiwa Sabeer kunun da yake buk'ata, kallon ina zaki je Jiddah tayi mata duk ta wani tsatstsare ta da idanu abin ya bawa Jiddah dariya don haka tace "Keee Jiddah irin wannan tsatstsare ni da eyes haka " "Dole na tsatstsare da ido mana naga kin mik'e kuma kinsan ban da ishashshen time da wuri zan koma " "Had'a mishi kunu zanyi yanzu zan gama" "What! Wa zaki had'a wa kunu Yah Sabeer koh? " "Eh shi " "Tabbb aini tun da nagan shi nasan yau bazai barmu yin abin da ya kamata ba wallahi duk tak'ura mana zai yi ji har da wani cewa kiyi mishi kunu tsabar sanya mutum aiki " "Eh d'in ina ruwan ki tun da bake aka sanya ba " Ta k'arasa fad'i tana murgud'a bakinta tabar d'akin, Jiddah wadda ta saki baki tana kallon Suhaima da D'an k'arfi yanda zata ji tace "Eheyyy yarinya ni kike fad'awa haka lallai Aunty Aliya kinji Yah Sabeer zai shiga tsakanin mu " Dariya tayi sannan tace "Kun fi kusa don ba'a shiga tsakanin ku yanzu mutum zai ji kunya don anjima kad'an zaku jone ". Cikin shagwa6a Jiddah tace "au haka zaki ce Aunty? " "Eh mana idan na shiga ni za'a bari da jin kunya" Murmishi Jiddah tayi ta cigaba da cin d'anwaken ta suna ta6a hira da Aunty Aliyah. Suhaima kuwa bayan fitar ta a palon tana jin abin da Jiddah tace murmishi kawai tayi, nan ta fara aikin had'a kunun da yake tana da gyadar shi yasa aikin yazo mata da sauk'i don tana son shan kunun gyada shi yasa take ajiye markad'add'iyar gyad'a, bayan ta gama ne ta zuba mishi a dogon jug na silver sai k'aramin cup shima na silver ta ajiye mishi a kitchen sannan ta zuba musu nasu a cup ta d'auka ta koma d'akin Aunty Aliya ta mik'a wa Jiddah da Aunty Aliya nasu. "Yawwa tawan shi yasa kike birgeni kamar kinsan inason sha tun lokacin da kika ambaci sunan shi raina ya biya" "Ai daman nasan Babyn mu naso shi yasa na dama" Bata dad'e da zama ba Sabeer yayi mata text ya dawo ta kawo mishi, nan ta d'auki k'aramin tiren silver wanda ta shirya kunun akai ta kai mishi sun d'an ta6a hira har yasha kunun da yawa kafin kuma yayi mata sallama don akwai inda zasu je da Daddyn shi, mota ya shiga drive yaja suka tafi sai da taga tafiyar shi sannan ta dawo gida. "Lailah ina Majnun d'in? " Fad'in Jiddah wadda take zaune tana kallon Suhaima da take warware veil d'in kanta, d'an yatsina fuska tayi kafin tace "Auuu! Sunan da muka koma kenan? " "Kun ma fi haka " Girgiza Suhaima tayi tana murmishi ta zauna tana shan kunun ta, nan Jiddah ta bud'e k'atuwan bag d'in da tazo da ita ta fara fito da kayan ciki. Duk abubuwan kusan irin su dilka, kurkum da sauran nau'ikan kayan gyaran fata har dasu sabulu na wanka da cream da akayi mishi had'e had'e na abubuwan da suke sanya fata laushi da santsi da turaren da zata nayin amfani dashi idan zata yi wanka, sai kayan gyaran ciki masu kyau da nagarta sosai kayan suke da yawa kuma da ganin su kaya ne masu kyau da inganci amman fah za'a kashe kud'i ba karami ba. Daga Suhaima har Aunty Aliya sakin baki suka yi suna kallon kayan nan Jiddah ta fara yi mata bayanin kowanne yanda zata yi amfani dashi kafin daga k'arshe tace "Abin da ya sanya naje wajen mai mana gyaran jiki na auren mu nace ta had'a miki saboda kun yi nisa, shine nace ta bani wanda zaki amfani dashi kafin sauran sati d'aya biki tazo ta yi miki da kanki amman don Allah Suhaima ki d'aure kiyi amfani dasu suna da kyau wallahi don nagani akaina bama su cutar wa ba ne " Jiyowa tayi ta kalli Aunty Aliya sannan tace "Aunty don Allah ki sanya ido tana yi kullum don so nake Yah Sabeer ya rikice mana " Ta k'arasa fad'i da dariya, Suhaima dai da Aunty Aliya sai addu'a suke yiwa Jiddah don ta hanasu godiya, addu'a sosai tasha ta musamman ta rabuwa da cikin jikinta lafiya. Kayan suka d'auka zuwa d'akin Suhaima bayan sun ajiye Suhaima rungume Jiddah tayi kawai sai ga hawaye yana fita a idanun ta karamcin Jiddah na daban ba k'aramar masoyiyar ta bace batasan da me zata saka mata shi ba. "Haba tawan mene kuma na hawaye share hawayen ki, kin fi k'arfin komai a wajena tun lokacin da Allah ya nufa na ganki naji kin shiga raina, yanzu bari na fara gwada miki yanda zaki yi ki gani " Zama Suhaima tayi nan Jiddah ta fara had'a dilka da sauran abubuwa kayan had'in bayan ta gama ne sai ta fara mutstsuke jikin Suhaima bayan ta gama ne suka jira zuwa 30 minute's kafin ta murje shi sai kuma ta shafa mata had'in kurkum shima sai da ya d'auki 30 minute's d'in sannan tayi wanka da ruwa wanda aka sanya turare acikin shi, tun daga wajen wankan Suhaima ta tabbatar ta fara canjawar fatar jikin ta yanda take zuba santsi da k'amshi ga wani irin laushi da skin nata ya dad'a yi duk da kuwa fatar ta mai laushi ce amman yanzu ta k'ara laushi. Tana fitowa ne kuma Jiddah ta gama had'a garwashi tana jiranta tana zuwa ta zuba turaren jiki acikin wutar nan Suhaima ta shiga tana turare jikinta yayin da Jiddah ta fito ta barta a d'akin, sai da ta d'auki wajen 10 minutes sannan ta gama turaren kafinx ta zauna ta shafa cream d'in nan bayan ta gama ne ta zura wata yellow d'in gown har k'asa sai dai hannun vest ne da ita, wani irin mugun kyau na daban Suhaima ta k'ara yi ga gashin ta mai kyau na asalin fulani mai laushi da santsi ya zubo mata a kafad'unta tana cikin tajewa Jiddah ta shigo. "Wow! Suhaima kin ganki kuwa yanda kika koma tabbb gaskiya Yayana zai more " Ta k'arasa fad'i tana d'auko wayanta pic's ta fara d'aukan ta, cikin dariya Suhaima tace "Don Allah Jiddah ki daina d'aukan pic's nawa please kalli fah ki ga yanda rigar take" "Ina ruwa mijin ki zan nuna wa ya bani kyauta" Ta fad'i hakan tana daukan Suhaima lokacin da take dariya, ita kanta Jiddah pic d'in yayi matuk'ar birgeta ba kad'an ba. D'an waro ido waje tayi kafin tace "Haba Jiddah kada ki tura mishi please " Ta fad'i tana langa6e kai cike da shagwa6a, dariya Jiddah tayi kan tace "Toh naji dake da mijin ki bansan wanda yafi wani shagwa6a ba gidan ku da kallo kuwa duk an tara shagwa6a66u" "Yanzu dai tafiya zanyi don my dear yana hanya shi da driven da ya kawo ni, yace ya gaji da yi mishi mitar da nake yak'i zuwa su gaisa da Bestyna shine yau yace zai zo " Murmishi Suhaima tayi kan tace "Allah ya kawo su lafiya" "Amin " Fita Jiddah tayi bata dad'e ba sai gata da Aunty Aliya wadda ta saki baki tana kallon yanda Suhaima ta koma tamkar ba ita ba. Hannu tasa tana shafa hannun Suhaima tace "Wannan da fita kika yi da ita Jiddah da nace wankan inji kika yi mata " Dariya suka yi dukkanin su jin abin da Aunty Aliya ta fad'i. "Aunty kema kiyi don Allah " Cewar Jiddah, rik'e baki tayi tana cewa "A haba wannan ai na irin kune " "Kaiii Aunty aikuwa ya kamata kiyi " Cewar Suhaima. "Suhaima ki had'a mata tayi itama kafin Yah Aliyu ya dawo yaga yanda zata canja idan na dawo zan kar6i tukwicin kyauta ta " Suna nan zaune suna hira har mijin Jiddah yazo, shigowa har gidan yayi suka gaisa da Aunty Aliya da Suhaima bayan an ta6a hira ne suka yi musu sallama suka tafi har k'ofar gida Suhaima ta rako su sannan ta dawo gida bayan sun tafi. Bayan Suhaima ta dawo gida ne ta had'a wa Aunty Aliya itama tayi kamar yanda Jiddah tayi mata, sosai tayi kyau ba laifi bayan angama ne Suhaima tayi wa Aunty Aliya simple make-up tayi kyau kamar ba ita ba sai da Suhaima ta d'auke ta a pic's. Suna zaune tsakar gida suna hira sai ga Yah Aliyu ya dawo nan sauran sallamar mak'alewa tayi a fatar bakin shi ganin yanda matar shi ta koma kamar ba ita ba, kallon ta kawai yake yi don ya mance da wata Suhaima dake zuba mishi sannu da zuwa, duk kunya ta d'an kama Aliyah ganin kallon da yake mata. Yayin da Suhaima ta tattara ta arce d'akin ta don kada taga abin da yafi k'arfin idon ta, dariya k'asa k'asa take don kuwa Yah Aliyu ya bata dariya, phone nata ta d'auko data ta kunna sai gashi Jiddah ta turo mata pic's d'in da ta d'auke ta d'azu, zubawa pics d'in ido tayi ita kanta tasan tayi kyau. *_11:30pm_* Sabeer ne kwance kan bed yana zuba murmishi gama yin wayar shi kenan da Suhaima, duba wajen pic's nashi yayi sam bashi da pic's d'in Babyn shi yana shirin kiranta ne yaji alamar shigowar sak'o a WhatsApp d'in shi don haka ya duba sai yaga Jiddah ce ta turo mishi da wasu pic's guda 5 daga k'asa ta sanya "Yah Sabeer kada ka nunawa Besty na turo maka pic's d'in nan don inason kaga yanda Babyn ka ta zama kuma ka bani tukwici idan ba haka ba na daina turo maka " ta k'arasa da sanya d'an aljanin murgud'a baki, sannan ta kuma cewa "Asha kallo lafiya angon Besty " ta sanya aljanin dariya da gwalo. Tun kafin ya bud'e yake murmishin abin da Jiddah ta rubuta, sakin baki, hanci da ido Sabeer yayi yana ganin pic's d'in sai da ya sake murza eye's nashi kafin ya dad'a zubawa pics d'in ido, wannan anya Baby nace?, ya fad'i haka cikin zuciyar shi kafin maganar ta samu matsugunun tunani a brain nashi tuni ya gama hashasho Babyn shi ce. "Wow! Gaskiya Baby nah kin had'u ashe zan more woo" Ya fad'i hakan yana cigaba da kallon ta tuni ya tafi mafarkin ido biyu, baisan adadin lokacin da ya dauka yana kallon pics d'in ba, sai da yaji Jiddah ta turo mishi da text d'in taji shiru bata ga tukwicin ta ba. Cikin rawar jiki ya fara typing da cewa "Me kike so k'anwata ta kaina? " "Yah Sabeer komai ma " "Car or Money wanne kike so fad'i?" "Yah Sabeer Mota nake sooo" "Angama sister gobe za'a kawo miki key " Wani ihun murna Jiddah ta saki har phone nata na fad'uwa k'asa don tasan kyautar Sabeer baya k'arama, nan tayi mishi godiya tare da addu'ar Allah ya bashi Suhaima, na takaice muku Sabeer ranar har dasu mafarkin Suhaima suna tare don da asuba sai da Sabeer yayi wanka sannan ya iya yin sallah..... lol. *_Washe gari_* Sabeer ne ya fito daga bedroom d'in shi yana taka staircase anutse ya kusan k'arasa wa palour ne ya hango Mummy da Daddy zaune ga kayan bag's na akwatinan lefe nan barbaje a palourn tun daga kan akwatunan mutum zaisan basu da wani tsada ko kalar kyau basu dashi gashi guda 6 ne gaba d'aya kayan ciki kuwa ko arzik'in kyau basu dashi. K'arasa wa yayi cikin palourn yana kallon kayan a wulak'anci yace "Daddy Mumy kayan wane ne wannan?" "Nima jira nake ta sanar dashi bansan na wane ne ba nafi kyautata zaton ko gate man ne zaiyi aure ta bashi kyautar su " Cewar Daddy kenan, duk sun zubawa Mumy ido suna sauraren abin da zata ce dasu......... *_Ya kuka ji wannan page d'in Fans dafatan ya k'ayatar ku, inason ganin comment's, yau nayi abin kirki koh?_*😜 Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 75-76* Ganin Mumy tayi shiru tak'i magana yasa Sabeer yin magana cikin k'aguwa yace "Mumy ke fah muke jira ki fad'a mana ki zo ki bani abinci yunwa nake ji " Hankalin Mumy kwance ta bud'e baki tace "Lefen da Daddy yace na had'a ne sune na gama had'a wa " Cikin son sanin na waye Sabeer yace "Na wane kodai gaskiyar Daddy ne gateman ne zai yi aure?" Yayin da Daddy kuma ya saki baki yana kallon Mumy zuwa yanzu ya tabbatar lefen Sabeer ne da yace ta had'a shine ta had'a mishi wulak'antaccen kayan nan da ko wani talakan mai zuciyar nema idan ya sanya kanshi sai ya had'a wanda yafi shi had'uwa, ranshi ne ya soma 6aci yama kasa magana sai kallon mamaki da yake bin ta dashi,yana jiran yaji me Sabeer zaice kafin shima ya d'ora hukuncin da zaiyi don sosai wannan karon Mumy ta 6ata mishi rai, yana cikin wannan tunanin ne yaji muryar ta tana cewa Sabeer. "Lefen auren ka ne da wannan talakar yarinyar 'yar k'auye don nasan sun fi dacewa da ita kuma zata kar6a su cikin murna don basu saba ganin irin su ba" Wata 'yar dariyar ban yarda ba Sabeer yayi kan yace " are you serious Mumy maganar ki nasan da wasa ne ai? " "Sabeer kadaina sanya wasa cikin maganar nan da gaske nake duk abin da nace " Wata dariyar Sabeer yayi wadda tafi kuka ciwo yace "Yayi kyau Mumy " Ya fad'i hakan yana barin parlourn cikin 6acin rai da taiaicin abin da Mumy tayi na niyyar wulak'anta shi yake hawa staircase d'in da sassarfa, bedroom nashi ya nufa yana shiga ciki ya bud'e tafkeken wardrobe nashi ya fara watso kayan ciki yana barbaza su a ko'ina, shi Mumy take neman wulak'antawa saboda kawai yana son d'iyar talakawa wadda ta rayu a k'auye. "Why Mumy why shi talakan ba mutum bane, ba Allah ne yayi shi ba yaso ganin shi haka a rayuwa ba, Mumy kada k'ureni muzo muna yin abin da kowa zai yi nadama " Wani 'yar k'arar takaici ya saki yana sanya hannun shi cikin sumar kanshi wadda tasha gyara yana hargitsawa, can kuma kamar wanda aka mintsina ya mik'e zumbur ya fara cire kayan jikin shi ya canja da wasu jeans black da T-shirt maroon colour mai k'aramin hannu ya d'auko phone da car key's ya fito daga d'akin. Yana saukowa daga upstairs yaji muryar Daddy yana yiwa Mumy fad'a sosai akan abin da ta aikata, suna ganin sai kuma suka dawo da hankalin su nan, cikin damuwa Mumy ta fara cewa "Son ina zuwa baka ce min yunwa kake ji ba, ga breakfast fah na had'a maka favourite foods naka? " "Bana buk'atar su " Sabeer ya fadi hakan ba tare da ya kalli inda take ba ya k'arasa wajen Daddy yana cewa "Daddy zan fita " Rik'o hannun shi Daddy yayi tare da cewa "Ina zaka Son? " "Daddy zan je na nemi mai had'a min lefe wanda nasan baza su so na kunyata a rayuwata ba " "Da kyau Son but da ka nemi Jiddah da Yusrah (Yayar Jiddah wadda take bi itama dai bata da tsaurarawa sosai akan abu wanda ya danganci talaka tana da aure har da yara 2), nasan zasu fitar da kai kunya baza su so kansu ba da yawa, kamar wasu mutanen da basu d'auki talaka a mutum mai mahimmanci ba, wanda kuma agaba zai iyayi mishi wani abin alkhairi mutum ya dawo yana jin kunyar aikata abin da yayi" Mumy ta cika tayi fam sai huci take don tasan da ita yake don tuni ta tsargu. Sai lokacin hankalin Sabeer ya d'an kwanta don dama shi baisan wurin da zai je ba kawai ya fito da niyyar barin gidan ko yaji sanyi cikin ranshi. "Yanzu Daddy wanne k'asa zasu je? " "Ina tunanin su je dubai su had'a acan idan ma bai wadatar ba sai a dad'a neman wata k'asan, yanzu zan kirawo mazajen su na rok'i wannan alfamar a wajen su, ka kwantar da hankalin ka Son " Rungume shi Sabeer yayi cikin jin dad'i yace "Nagode Daddy nah hak'ik'a kai uba ne na gari wanda yake faranta ran d'an shi koda yaushe Allah ya barmin kai " "Amin Son nima ina alfahari da kai " Yana gama fad'in haka yaja hannun Sabeer suka fita daga side d'in, suka bar Mumy da baki a sake tana mai bin su da kallo cikin mamakin gasa mata maganar da suka yi sannan suka fitar mata da waje ko sallama babu gashi ba wanda yayi breakfast a cikin su, kuma saboda su ta shiga kitchen ta tsara girki shine suka watsa mata k'asa a ido, zubewa tayi kan kujera tana faman kallon kayan da ta sanya house girl d'inta ta had'a su, da yake er aikin dattijuwa ce kuma er k'auye ce sosai sai tace ta had'a mata lefe kamar yanda suke had'awa a k'auyen su, amman irin wanda mai kud'in k'auye zai iya had'awa amman sai tace mata akwatina 6 zata siya shine fah ta had'o kayan, ko lokacin da ta gansu sai da taci dariya ta more saboda abubuwan da aka zuba aciki. D'an ta6e baki tayi kan tace "Ni ban ga wulak'anci anan ba nasan da gudu zasu kar6a suna murna tun da basu saba ganin kayan lefe masu yawa irin wannan ba" Ta k'arasa fad'i tana kwanciya kan kujera wata tsanar Suhaima na k'ara shiga cikin zuciyar ta,tun kafin taga yarinya take jin tsanar ta kuma tabbas sai tayi nadamar auren d'anta don bazata barta tayi rayuwa cikin jin dad'i ba, (kun ji tunanin Mumy fah sai kace itace mai tsarawa mutum rayuwar shi). Tun da Sabeer da Daddy suka bar gidan basu dawo ba sai wurin 11 na dare suka shigo part d'in, tun after sallahr ishsha suke cikin gidan ba tare da Mumy ta sani ba don ko dinner a Muh'd part d'in Hajjah suka yi, Mumy kuwa batasan sun dawo gidan ba don haka ta k'ule iyakar k'uluwa akan abin da Sabeer da Daddy suka yi mata don ko abincin dare da kanta ta shiga kitchen ta 6ata lokaci sosai wajen shirya musu abinci, tun tana zuba idanun ganin su har ta hak'ura ta kwanta kan kujera 3 siter tana sak'a da warwara ina mijin ta da d'anta suka yi. Tana cikin wannan tunanin ne taji shigowar su palon don haka ta mik'e tana kallon su cikin mamaki yanda suke ta zuba fara'a abin su Daddy ya rik'o kafad'ar Sabeer tamkar wani abokin shi. Kanta ne ya k'ara d'aurewa ganin zasu shige upstairs basu kulata ba, yanda ma suka nuna ko alamun sun san da ita a palon basu yi ba, kasa jurewa tayi don haka tace "Hala baku kula da ni ba, ina kuka zauna har wajen 11pm baku dawo gida ba? " Tsayawa suka yi tare da juyowa suka had'a ido lokaci d'aya suka had'e fuska sannan Daddy yace "Ina ruwan ki da inda muka je wannan ba matsalar ki bace? " Gaban Mumy ne ya fad'i kaddai ace adalilin Suhaima mijinta da d'anta su juya mata baya, ganin har sun fara taka staircase ya sanya ta katse tunanin ta da sauri tace "Ga abinci nan fah na girka muku " "Mun koshi Mumy wata k'awar Daddy ta bamu abinci mai dad'i mun ci don haka ki bawa masu aiki su ci " Cewar Sabeer kenan wanda sauran kad'an dariya ta kubce musu shi da Daddy don haka da sauri suka fad'a bedroom na Sabeer suka rufe suna kyalkyala dariya, har da rufe baki da hannun su saboda kada Mumy ta jiyo sautin dariyar tasu. "Son ka razana Mumyn ka da yawa fah kada wani abu ya samu mata ta ina jin tsoro " "Haba Daddy daga wannan maganar sai wani abu ya faru da ita? " "Eh mana Sabeer kasan yanda Mumyn ka take da kishi kuwa ni bama zan jure ganin ta cikin damuwa ba bari naje na rarrashi abata " Daddy ya k'arasa fad'a yana kokarin fita a d'akin, da sauri Sabeer ya rik'o hannun shi tare da cewa "Nooo Daddy kyale Mumyn nan, nima kaina bana son ganin ta cikin damuwa but Mum batason ganin farincikina i swear" "Kada kace haka Son nasan nan gaba zata so Suhaima " "Anya kuwa Daddy, na fahimci Mum ta gama tsanar Suhaima " "Kada kace haka Son addu'a zaka cigaba da ni " Gid'a kai Sabeer yayi kafin kuma su zauna suna hira akan tafiyar da su Jiddah da Yusrah zasu yi nan da gobe da yamma jirgin su zai tashi zuwa dubai, kafin daga bisani Daddy ya wuce side d'in shi don dare ya d'an yi. Mumy kuwa tun lokacin da maganar Sabeer tayi mata dirar mikiya cikin kunnen ta, ta gama firgicewa kusan suman tsaye tayi tsabar kad'uwa da jin abin da Sabeer ya fad'a mata, wato dalilin da ya sanya su yin dare a waje kenan, aikuwa ba 'yar iskar da zata shigo gidan nan matsayin matar Hussein wallahi duk wadda tayi gigin shigowa kuwa sai tayi dana sani kuwa. Tana gama fad'in haka haka ta wuce side d'in ta tana shiga bedroom saboda tsabar takaici ta rushe da kuka kamar wata k'aramar yarinya, Allah yayi ta mace mai tsananin kishin sosai ji take har numfashin ta yana kokarin d'aukewa tsabar tashin hankali. Anutse Daddy ya shigo bedroom d'in jin kukanta ba k'aramin d'aga mishi da hankali yayi ba don shi yaushe rabon yaga kukan matar shi kamar haka har ya mance. Cikin sanyin jiki ya k'arasa inda take ya zauna kafin ya dafa kafad'ar ta yace "Yake matata kukan me kike haka? " D'ago kanta tayi ta kalle shi idanunta suna zubar da hawaye ta fad'a jikin shi ta k'ank'ame shi tare da cewa "Ina tsananin son ka Hussein ina kishin ka bana son wata mace ta ra6ar min kai but why da zaka yi min haka kaje wajen wata kai da Son har kuci abincin ta? " Murmishi Daddy yayi kafin yace "Haba Faridah kinsan bazan iya kallon wata d'iya mace da sunan ina sonta ba, banyi hakan tun k'uruciya ta ba sai yanzu da na girma kinsan ke kadaice cikin zuciyata daga ke babu dad'i, duk wannan maganar tsokanar ki Sabeer keyi" Kallon idanun shi take don son tabbatar da gaskiyar maganar shi, gid'a mata kai yayi tare da lumshe eye's nashi alamun haka maganar take. "Toh ina kuka je da Son har kukayi dare? ". Fuskar shi d'auke da murmishi yace "Muna part d'in Hajjah ana hira " Rungume Daddy tayi tana sauke ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali don sai yanzu taji ta a nutse nan kuma suka 6ige da nunawa juna kauna. Washe gari da yammacin ranar Jiddah da Yusrah suka d'aga zuwa dubai don siyayyar kayan lefe, sosai Daddy da Sabeer suka saki kud'i don a had'o kaya masu kyau da tsada. **** **** **** Satin su Jiddah 2 suka dawo Nigeria da tarin had'add'un kayan lefen da suka had'a, kaya sunyi ta ko'ina sosai kayan Daddy da Sabeer suka yaba za6en su ko Mumy sai da ta jinjina irin dukiyar da aka narka anan ko ita kayan sun birgeta duk hassadar mutum yaga kayan sai sun birgeshi, har da tukwici Daddy yayiwa Jiddah da Yusrah don sun mishi yanda yake so. Har zuwa lokacin Sabeer tsakanin shi da Mumy gaisuwa sam yak'i sake mata kamar da, don ba k'aramin 6ata mishi rai tayi ba akan lefen da ta had'a wai za'a kaiwa Babyn shi idan ya tuna hakan har ranshi 6aci yake. Duk wannan kayan da aka had'o sai da Jiddah ta kar6i kud'i na musamman hannun Sabeer ta siyawa Suhaima kayan da zata yi amfani dasu wajen biki komai sai da ta had'o yanda ya kamata. Bayan kwana 2 duk 'yan uwa sun gama ganin lefen sai zuzutashi suke saboda had'uwar shi but idan suka tuna 'yar kauye za'a kaiwa wannan duk sai ransu ya 6aci su fara jan tsaki da k'ananun maganganu, babu mai goyon bayan Sabeer akan wannan bikin sai Daddy don ko Dr Ahmad d'an fillo kadaran kadahan don farincikin Sabeer ya hak'ura. Shiyasa Sabeer da Daddy ne kawai suke kid'an su da rawar su, duk wadannan tarin kayan da aka had'a sai da Daddy ya k'ara da wata dank'areriyar sark'ar gold mai matuk'ar kyau da tsada ba kad'an ba da kuma key na mota, don Daddy tuni ya zubar da makaman yak'inshi na k'in talaka yanzu sosai yake tsayawa sauraren talakawa masu neman taimako yana taimaka musu kuma hakan ba k'aramin jin dad'i yake ba da kuwa daga iya fidda zakka shikenan. Wannan abun da Daddy yayi wa Suhaima ba k'aramin bak'anta ran Mumy yayi ba don ita aganin ta taya zai tsaya siyawa 'yar k'auye wannan gold d'in mai tsada bayan wad'anda aka zuba mata a lefe gashi har da wani kyautar mota ko'ina 'yar k'auye da tukin mota me zatayi da ita, banzatar dasu zata yi tunda batasan darajar su ba, Daddy sai da ya toshe kunnen shi don kuwa Mumy da Hajjah sai mitar abin suke yi, shi kuwa ganin farincikin tilon d'an shi yafi mishi komai. Ko ranar da za'a kai lefe motoci 3 Daddy yace za'a yi na mutane saboda bayason a had'a su da wahala kuma bayason ayi hatsaniya don sosai sai da ya gargad'i wad'anda zasu kai wanda suka kasance daga kanwar su Daddy sai k'annen matanshi da yaran su mata kad'an daga ciki, sai kuma motar Suhaima wanda aka zuba kayan lefen ta a ciki nan suka d'auki hanyar k'auyen su Suhaima. Sai wurin 3 na yamma suka k'arasa kowanne ya fito daga mota sai faman yatsina fuska da ta6e baki suke suna yiwa mutane kallon d'ai d'ai, koda suka shiga gidan su Suhaima sunsha mamakin ganin yanda gidan yake don kuwa Yah Aliyu ya kashe kud'i sosai wajen gyara gidan har da sabon fenti akayi, shi yasa ko'ina yayi kyau yayi fes ga an tsabtace gidan sai k'amshin turaren wuta yake. Anan tsakar gidan suka zazzauna saman tabarma, su Aunty Aliya da Babaa Lantana da wasu daga cikin 'yan uwan su Suhaima sun d'an zazzo kar6ar lefen, wasu kuma don ganin kwakwaf suka zo don sunji ance d'an mai kud'i Suhaima zata aura suna son tabbatar wa aikuwa da ganin irin motocin da suka zo acikin ta sun tabbatar da gaskiyar zancen. Babu wanda yayi gigin shiga toilet sai alwala da suka yi suna tsoron kada su shiga su ga abin da zai sanya su amai, dai dai da ruwan alwala da bottle na faro suka dunga yi saboda tsantsanin ruwan suke. Jiddah ranta ya 6aci sosai da wannan wulak'ancin da 'yan uwanta suka yi don an zuba musu ruwa a botoci suka k'i amfani dashi suka d'auko bottles na faro, kasa magana tayi don tsabar takaici, yayin da mutane suka saki baki da hanci suna kallon wannan sabon salon nasu, awurin sallahr ne kawai basu da yanda zasu yi suka yi akan tabarmar da aka shimfid'a musu bayan sun idar aka sake gaisawa sannan aka fara fito musu da abinci zuwa drink's da ruwa na bottles. Sunyi mamakin na ganin irin abincin da suka gabatar musu dashi don basu yi zaton samun hakan ba, basu san wannan duk aikin Jiddah ba ne don kawa batason a 'yanuwanta su wulak'anta mata Suhaima. Sun ci abincin bayan sun kammala aka gabatar da kayan lefen da car key sai kuma kud'in da ake d'ora wa saman kaya har 1 million, sakin baki, hanci sukayi 'yan kauye don ganin irin wannan abun da basu ta6a tsammanin zasu ganshi da ido ba nan kowa ya fara kokwanto cikin zuciyar shi anya ba siyar da Suhaima su Aliyu suka yi ba yo banda hakan ina za'a bayar da irin wannan kayan lefen haka har da mukullin mota da 1 million akai. "Kada ku damu wannan ba wani babban abu bane a wurin mu don mun bayar da wadannan 'yan kayan don haka ku dai na mamaki, kodan nasan dole kuyi mamakin don ido bai ta6a ganin irin kayan ba " Cewar Aunty Fadilah kanwar su Daddy tana wani yatsina fuska banda kallon raini da take bin su dashi, don 'yar gaban goshin Dr Faridah ce tana taya matat wan nata bak'in cikin wannan abu. "Haba Aunty Fadilah don Allah ki daina irin wannan maganganun babu dad'i " Cewar Jiddah tana turo baki wata uwar harara Aunty Fadilah ta aikawa Jiddah kafin tace "Daman ina zaki ga rashin dacewar hakan bayan an shanye mana ke da Sabeer har da Yaya Hussein, idan ban da k'addara ina mu ina neman aure a irin wannan wurin " Ta k'arasa maganar tana jan tsaki, cikin rashin kunya Jiddah tace "Allah Aunty kika sake magana sai na gayawa Daddy tun da har kin mance abin da Daddy ya fad'a kafin mu taho " Wata hararar ta sake zabga mata tamkar idanunta ya fad'o amman bata sake magana ba don tasan sarai halin Jiddah tsaf zata fad'awa Daddy kuma tasan tsaf zai ci mutuncin ta. Sai bayan la'asar da suka yi sallah suka taho da tarin kayan snacks da drink's d'in da Jiddah ta bayar akayi, sai kuma cikin kud'in da suka kawo aka basu tukwicin dubu d'ari biyar, a wulak'anci suka kar6a kud'in babu sallamar arzik'i suka tafi. Sai bayan tafiyar su ne aka saki jiki ana kallon lefen akwatina har 15 kowacce cike da kaya damk'an dakyar bag's ake zuge zipe saboda cikar kayan. Duk kwakwkwafar mutum dai ya hak'ura da ganin kayan, k'arshe bayan an gama gani Aunty Aliya suka tattara su aka zuba su cikin d'akin Suhaima, daman Suhaima bata gidan tana can gidan Babaa Lantana ita da wasu kawayen ta biyu wad'anda suke shiri dasu. Sai dare Suhaima ta dawo gida kasa kallon kayan tayi sabida kunya sai da Aunty Aliya ta dunga fito mata dasu tana gani a haka shima Yah Aliyu ya tarar dasu ya d'an kalla sama sama kafin yace "Masha Allah kanwar tawa tayi goshi sai dai gaskiya kayan sunyi yawa sosai wallahi" "Gaskiya kam sunyi kyau sai dai yawan su mu muke ganin haka amman su ba wani abun ne rabon ta ne" Cewar Aunty Aliya kenan tana bud'e bag d'in da aka zuba sark'ok'i, sannan ta d'ora da cewa "Yanzu ya zamu yi da motar ta? " Sai lokacin Suhaima tasan har da mota haka ma Yah Aliyu. "Tabd'ijam har mota fah kika ce Aliyah? " "Kwarai kuwa baka ganta a waje ba? " "Naga mota na d'auka ko lalace musu tayi " "A'a ta Suhaima ce " "Yanzu yanda za'a yi idan Sabeer yazo sai ya tafi da ita ya ajiye mata acan gidan nashi ko kuma Jiddah ta tafar mata da ita ta ajiye " "Haka za'a yi kuwa don shine mafita nan ba wajen zaman ta ba ne " Suhaima tana jin su duk wannan tattaunawar da suke bata ce komai ba sai tagumi da ta yi, bayan su Yah Aliyu sun fita daga d'akin har Yah Aliyu yana tsokanar ta da "ke fah yanzu Suhaima kin zama matar manya koh? " Murmishi kawai tayi ta turo mishi baki dariya yayi ya fice abin shi Aunty Aliyah na taya shi. Suna fita wayar Suhaima ta d'auki k'ara ganin Sabeer ne ya sanyata d'auka had'e da yin sallama, lumshe idanun shi yayi kafin ya bud'e su yana amsa sallamar ta throughout yau bai ji wannan muryarta ta ba. "Amarya ta kinsha k'amshi nayi missing naki fah Baby yaushe zan zo? " D'an murmishi ta saki mai d'an sauti sannan tace "sai nan da 4 week's zaka zo " D'an zaro ido yayi kamar tana ganin shi yace "Washsh! Allah nah kice Baby sai dai ki zo dubiya ta asibiti don nasan sai Doctor ya kwantar dani " Dariya ta kyalkyale da ita tana cewa "Haba lallai da ka cika rago kuwa" Da sigar tsokana ta fad'a. "Baby nine ragon koh, tabbb yarinya zaki bayani ne idan na rik'e ki a hannuna a time d'in ne zaki fahimci irin jarumta ta " Gaban Suhaima ne ya d'an fad'i har ta kasa magana duk da bata fahimci maganar tashi sosai ba, jin tayi shiru ya sanya shi murmushi ya basar da zancen da cewa "Baby kaya sun yi miki kuwa? " "Laaa sunyi kyau sosai sai dai Sabeer gaskiya sunyi yawa, bayan haka har da mota fah sai kace wadda za'a siyar " Dariya ya d'an yi jin yanda ta k'arasa maganar cikin shagwa6a. "Baby nah kenan toh ai motar ba ni na baki ba Daddy nane ya baki, kuma zancen yawan kaya ki daina zancen su don kin cancanci fiye da haka " "Ina godiya sosai a mik'a min godiya ta wajen Daddy " "Toh Baby yanzu mene tsare tsaren bikin ne, mai kuke son yi, don ina son zan zo nida friend nawa Musaddiq " "Daman kana da aboki ne? " "Baby ina da aboki mana amman duk acikin su da d'aya na aminta dashi wato Musaddiq sai dai shi miskili ne na ajin k'arshe shi yasa baki san shi ba " "Ayyah amman wannan kafin ya samu macen aure zai sha wahala " "Baby ai yana da aure matar shi Mufidah da yaran shi twins sai dai yana rik'on d'iyar Yayan shi wanda ya rasu" (dafatan masu karatu baku manta labarin littafin YAYI SAKE ba), nan Sabeer ya bata d'an labarin shi a takaice sosai Suhaima ta matuk'ar tausaya musu jin irin gwagwarmayar da Musaddiq yasha a cikin rayuwar shi. "Allah ya jik'an Abubakar Sadeeq" "Amin ya rabbi Baby, yanzu kije ki kwanta dare yayi ranar friday ko Saturday zan shigo" "Okay Allah ya kawo ka lafiya " "Amin Baby nah kiyi bacci mai dad'i da sweet dreams dani aciki " D'an murmishi kawai tayi nan suka yi sallama abin su zuciyar kowannen su cikin farinciki. **** **** **** Bayan kwana 2 da kawo lefe Jiddah tazo ta d'auki Suhaima don kai d'inkin kaya, kaya da D'an yawa ta zazza6o cikin kayan lefen ta had'a da wanda zatayi amfani dasu ranar bikin sannan ta had'a da wanda Yah Aliyu da Aunty Aliya suka yi mata, wajen tailor d'in Jiddah suka kai bayan sun gama za6ar irin style's d'in da suke so aka yi total na kud'i bana wasa ba nan take Jiddah ta biya su ko ragi babu don tana son su cika mata alkawari don nan da 2 week's zata dawo ta kar6e su dukka, duk wannan kud'in d'inkin a wajen Sabeer Jiddah ta kar6o, sannan suka zarce zuwa gidan Jiddah yini Suhaima tayi acan sai yamma driven Jiddah ya dawo da ita gida, motar Suhaima kuwa tana gidan Jiddah a ajiye don tun washe gari Yah Aliyu ya fad'a mata a waya ta turo driven ta ya dauka sai ya hau taxi drop har k'ofar gidan sai ya koma da motar. Sai shirye shiryen biki ake ta koina duk da family d'in D'an fillo basa maraba da shigowar Suhaima cikin su hakan bai hanasu shirya bikin ba fiye ma dana kowanne d'a a gidan,har dinner suka shirya ta family da suke yi har da yin ankon su kamar irin gasken nan, haka ta 6angaren Suhaima ma sosai Yah Aliyu da Aunty Aliyah suka zage wajen shirya bikin nasu dai dai gwargwadon iyawar su, Jiddah sun gama tsara event's d'in da zasu yi dinner, walimah, kamu sai kuma dinner d'in family d'in Sabeer wadda zasu yi ranar da aka kawo amarya........ Ku cigaba da hak'uri da ni Fan's. Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 77-78* *_AFTER 2 WEEK'S_* Duk wasu shirye shirye na bikin kusan an gama kammala komai sai jirab ranar lokacin wanda ya kama nan da next week zasu fara shagalin biki. Amarya Suhaima kuwa ta k'ara wani irin kyau da cika a jikinta duk wani gyara na saman fata da ciki yi mata ake yi amman masu kyau da inganci ake amfani dasu, har anje anyi mata jeren kayanta a gidan Sabeer, sosai Yaya Aliyu yayi mata kok'arin siya mata kayan d'aki zuwa na kitchen na zamani don Aunty Aliya da Jiddah sai Suhaima suka tafi zuwa kasuwa suka siyo duk abin da ya dace. Suhaima ce gaban dressing mirror tana taje dogon gashin kanta bayan ta gama taje wa ne ta d'aure shi da ribbon sannan ta mik'e ta zura wata black gown mai touch d'in red a jiki sai tayi rolling kanta da veil d'in gown d'in black shima, nan 'yar beautiful face nata ya fito gwanin sha'awa gata daman abin ka da fari cikin bak'in abu, bata yi wani makeup sosai ba simple make-up tayi daga powder sai red na jambaki da ta sanya ta taje kwantaccen gashin girar ta sai kawai ta fesa perfumes different colours ajikin ta masu sauk'in k'amshi. Black flat shoes ta d'auko ta sanya a k'afar ta, gama sanya takalmin kenan taji wayarta na ringing d'auka tayi tare da yin picking cikin sanyin murya tace "Hello! " "Hi! Mata ta kina ina gashi na k'araso" Fuskarta d'auke da murmishi tace "Gani nan zuwa kana ina? " Sai da ya lumshe ido kafin yace "Baby ina zaune cikin mota a k'ofar gida" "Okay gani nan zuwa" Tana gama fad'in haka ta kashe wayar, sannan ta fito zuwa tsakar gida Aunty Aliya ce tana zaune sai faman shirya Ameer tayi wanda tayi mishi wanka yanzu, kallon ta tayi fuskarta d'auke da smiling tace "Amarya tasha k'amshi hala angon ya k'araso?" "Eh Aunty Aliya ya k'araso" "Naga alama ai irin wannan kyau haka kada ki rud'a musu d'a ya kasa kai kanshi gida" Cike da zolaya Aunty tace, sunk'e kai Suhaima tayi cikin 'yar jin kunya tace "Kaiiii Aunty! " "Gaskiya ne ai, ki tafi kin barshi a waje shi kadai" Tashi tsaye tayi ta nufi k'ofar fita a gidan cikin tafiyar ta na nutsuwa, Aunty Aliya ta bita da kallo don kwalliyar nata ya birge ta. Tana fita suka yi 4 eye's da Sabeer wanda yake tsaye ya jingina bayan shi da mota ya hard'e hannun shi saman kirjin shi ya zubawa k'ofar fitowa ido yana kallon ta inda Babyn shi zata fito. Ajiyar zuciya ya sauke wanda Musaddiq da yake kusa dashi sai da yaji shi har ya d'ago daga danne dannen da yake a phone nashi suna charting da Mufidah ya kalli Sabeer sannan ya kalli inda yake kallo, ko ba'a fad'a mishi ba yasan wannan ce Suhaima amman yayi mamakin yanda sam batayi kama da en k'auyen ba anya ba zuwa take family d'in en uwanta hutu ba, sai dai kuma da ganin ta k'aramar yarinya ce sosai don bata fi 17 zuwa 18 ba, d'aga kafad'ar shi yayi alamar ba damuwar shi bane na sanin ko ita wace, don haka sai kawai ya cigaba da abin da yake. Kallon ta Sabeer yake tamkar ya had'iye ta haka yake ji ko kuma ya d'auke ta ya tafi da ita gaba d'aya ta kid'ima shi, gaba d'aya Suhaima ta rasa nutsuwar ta saboda irin kallon da Sabeer yake mata, kunya ce ta lullu6e ta kawai dakyar ta iya k'arasa wa inda suke tayi musu sallama amsawa sukayi kafin ta gaida su, nan Sabeer ya k'ara gabatar mata da Musaddiq a matsayin abokin shi na sosai, nan suka k'ara gaisawa tana tambayar shi iyalan shi. Sannan Musaddiq ya shige cikin mota don shi ba mai son magana ba ne, zama Suhaima tayi saman wani dutse mai d'an fad'i da tsayi ta kasa magana duk a tak'ure take, ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na biyu sannan yace "Baby nah ji nake tamkar na d'auke ki na gudu da ke, kinyi min kyau sosai " Ya k'arasa fad'i eye's nashi akan lips nata har sai da ya had'iyi yawu har ya hango shi irin shan da zai mishi bana wasa ba kuwa idan ya kama shi. "Baby kin yi shiru fah kin bar ni da surutu ni d'aya " D'an murmishi kawai tayi kafin tace "Ba haka bane ni na rasa abin da zance ne?" "Haba yarinya daman mata tana rasa abin da zata ce idan zasu yi hira ita da mijinta " Ya k'arasa maganar yana zama kusa da ita, d'an turo mishi bakinta kad'an tayi tukunna tace "Toh! Ni mai zance maka" "A'a babu komai kiyi ta kallona ma kawai " D'an hararar shi tayi ta gefen ido kad'an, ashe ya gani d'an girgiza kai yayi yana murmishi yace "Ni kike harara yarinya koh!?, ki cigaba komai da lokacin shi nima nawa ya kusa" Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da zoben azurfar hannun ta yayi da shi kuma ya tsurawa dogayen 'yan yatsun ta ido ji yake tamkar ya lashe su kai shi da yana da dama gaba d'ayan ta zai yi mata don yanda ta k'ara yi mishi wani kyau na daban. "Duk naji event's d'in da zaku yi Baby sun isa ko zaku k'ara? " "A'a sun ishe mu ni da ba wasu kawaye ne dani sosai ba, da Jiddah ma zata yarda iya walimah kawai zamu yi '' "Haba Baby ayi mana har da dinner saboda aboki nane ya had'a mana gashi family d'ina sun had'a mana wata ranar da aka kawo min ke" D'an shiru yayi yana kallonta kafin ya cigaba da cewa "Ni sai naga kamar zasu takura min yaushe har aka gama dinner mu dawo gida sannan mu bawa junan mu kulawa... Uhm kin dai gane? " Ya k'arasa maganar yana d'aga mata gira wata kunya ce ta sake lullu6e Suhaima daman haka Sabeer yake, ta rasa abin cewa tayi tsit da ita tamkar babu ita a wurin. "Ya dai Baby ko kin gaji ne? " "Uhmmm" Kawai ta iya cewa don tana tsoron ya Kara 6aru mata wani sabon rashin kunyar tashi, nan dai sai ya sako wani zancen na daban sannan ta saki jikinta suka d'an ta6a hira. "Washhh! Baby bari mu zo mu wuce gida kinsan wancen mutumin duk ya dame ni da kira yana tsoron kada matar shi ta rufe mishi k'ofa yak'i shiga gidan baya son yin nesa da matar shi sai dole " "Uhm ai ya kyauta gwara yana bata kulawa matsayinta na matar shi, don mazan da basa kula da matansu haushin su nake ji" "Eyyye Baby kice nima haka za'a na rik'e ni a gida " "Ai bani zan ma rik'e ka ba da kanka zaka zauna ma " ta k'arasa maganar da murgud'a baki. Er dariya kawai yayi yana cewa "Huh Baby rigima ni ake murgud'a wa baki koh, to bari nazo na tafi baza ki k'ara gani na ba sai ranar dinner " Nan suka yi sallama da junan su kamar kar ya tafi haka yake jin shi don gani yake 1 week d'in da ya rage musu ya mallaki Suhaima yayi mishi nisa, haka suka tafi duk jikin shi yayi sanyi har Musaddiq na tsokanar shi. Bayan kwana 2 Jiddah ta dawo gidan su Suhaima tare da mai yin gyaran jiki wanda zata yi mata na tsayin kwanaki 5, sannan ta taho mata da d'inkunan ta gaba d'aya, a lokacin duk suka fitar da wanda zata yi amfani dasu komai da komai aka had'e su bag guda 2, sauran kayan lefen kuma Jiddah zata tafi dasu ta kai su gidan Suhaima, bayan duk sun gama shirye shiryen su sannan Jiddah ta tafi baza ta dawo ba sai ana gobe za'a yi kamu zata kai Suhaima wajen lalle da gyaran gashi ta tafi ta bar mai gyaran jikin anan. Nan mai gyaran jikin nan ta cigaba da yiwa Suhaima duk da kyau da Suhaima ta k'ara wannan karon kuwa da Sabeer zai ga Suhaima mybe ya rud'e iya rud'ewa don kuwa wani irin laushi da santsi da fatar ta take yi na daban ne ga wani ni'imtaccen k'amshi da take fitarwa ta ko'ina a wajenta fatar ta har wani yellow yellow yake tsabar gyaran da tasha, ban da wanda Aunty Aliya take mata wanda fulani suke yi idan zasu aurar da yaran su. **** **** **** *KOMAI NISAN LOKACI....* Kamar yau aka sanya bikin Sabeer da Suhaima tsayin 3 month's sai gashi lokaci yazo kamar kiftawar ido, tun ranar talata da safe wajen 10am Jiddah tana gidan su Suhaima har Yaya Aliyu yana mata fad'an yawan zirga zirgar ta yayi yawa kada ta cutar da Babynta ko ita kanta don gashi cikin nata ya d'an fito kad'an ana ganin shi don ma dogowa ce shi yasa ya 6oye a jikinta, zum6ura baki tayi tana cewa "Ni dai Yaya Aliyu ka kyale mu nan da kwana 3 ma fah har angama bikin " Murmishi kawai yayi ya girgiza kai sannan ya fita daga gidan soyayya tsakanin Suhaima da Jiddah daga Allah ce had'in Ubangiji ne. Agurguje suka gama breakfast sannan suka tafi zuwa cikin gari har da mai gyaran jikin suka tafi zasu ajiye ta a gidanta, suna ajiye ta kuwa suka nufi wajen wani katafaren shago wanda ake gyaran gashi, kunshi da komai ma wanda ya kunshi gyaran jiki. Suna zuwa mai shagon musulma ce nan ta tar6e su cikin fara'a bayan ta basu wajen zama sun zauna suka gaisa sannan Jiddah tace "Sister gyaran gashi da lalle irin na amare zaku yi mata wanda zaku zage iyakar fasahar ta ku yi mata, don inason Yah Sabeer ya ganta ya rud'e da yawa " Dariya suka yi Jiddah da mai shagon tare da tafawa tace "Kada ki damu Hajia Jiddah kinsan mu ba yabon kai ba mun iya abubuwa na kwarewa a wajen nan don haka zaki sha mamaki da kaina zan yi mata ma don nasan Yalla6ai Sabeer ya cika miki bag da money" "Kamar kuwa kinsani don ba k'aramin ji da Babyn nan nashi yake ba" "Naga alama ai gashi sun dace da junan su kyawawa dasu " Daga nan aka fara yiwa Suhaima gyara tun daga wankin k'afa zuwa manicure and pedicure, sannan aka fara yaryad'a mata lalle ja da bak'i irin na amare, amaren ma 'yan gata. Bayan an gama yin lallen ne ya kama iya lokacin da ake buk'atar shi aka wanke shi, wow masha Allah kowa awajen haka yake fad'i ganin irin wani mugun kyau da yayi wa Suhaima tamakar lik'ashi aka yi ba zanawa shi aka yi ba. Daga nan aka fara yi mata gyaran gashi shima an d'auki tsayin lokaci ana yin shi Suhaima ta fito tsaf da ita gwanin sha'awa ko mace ta ganta zata birge ta balle uban gayyar ya ganta ai ba magana, itama Jidda sai da akayi mata lallen da gyaran gashin tukunna suka biya ta. Har sun fita Jiddah ta dawo tace "Sister gobe fah kizo gidan nawa wajen 4pm zaki mata makeup don gobe ne kamu bama son african time ne" "Kada ki damu Hajia Jiddah zan zo akan lokaci " "Okay sai anjima " Fitowa tayi daga shagon ta shiga bayan motar inda Suhaima take zaune nan driver yaja su sai gidan Jiddah , suna zuwa sallah suka yi sannan suka ci abinci suka zauna hutuwa. "Washhh! Allah na gaji Jiddah sosai " Cewar Suhaima tana yatsina fuska, dariya Jiddah tayi kafin tace "Yarinya ai agajiya baki yi komai ba sai an fara event's don ma ba wani event's da yawa zamu yi ba" D'an zaro ido Suhaima tayi kan tace "Ke ce sai k'asusuwa na sun kusa 6a66alewa" Tuntsire wa da dariya Jiddah ta sake sannan tace "Idan ma sun 6alle Yayana zai gyara su" Murmishi kawai Suhaima tayi nan suka suka cigaba da hirar su, kafin kuma suka k'ara fita zuwa wajen da zasu gabatar da event na kamu wajen yayi kyau sosai duk da ba'a yi mishi decoration ba sai gobe da safe wad'anda aka d'auko zasu yi, bayan sun gama ganin wajen ne suka dawo gida. Sai wajen 5 na yamma Suhaima ta fito drive zai mayar da ita gida, nan Jiddah tace "Gobe fah da safe za'a zo a d'auke ki ke da kawayen ki wad'anda zasu je nasan Aunty Aliya ma zata zo da Babaa Lantana ma duk su zo" Gid'a kai kawai Suhaima tayi ta rufe murfin motar suka tafi sai after ishsha su iso gida tana fita daga motar driver ya juya ya tafi yayin da Suhaima ta k'arasa shiga gidan agajiye take lik'is. Wanka kawai ta iya yi tabi lafiyar katifa ko takan abinci bata bi don a k'oshe take, bacci mai nauyi ne ya d'auke ta don ko kiran da Sabeer yayi bata ji ba, shima a nashi 6angaren yasan gajiya tayi kawai don haka shima ya kwanta amman yaso jin muryar ta kuwa. Washe gari da safe kuwa Suhaima kusan makara tayi ma don lokacin da take breakfast ma wajen 11 na safe a lokacin Jiddah ta kirata ta shirya driver ya taho, tana kashe wayar ne ta lalubo number Sabeer ta kirawo shi don taga kiranshi na jiya da dare, bai d'aga ba sai ya kashe kiran nata shi ya kirawo ta. "Amaryar ta ina son ganin beautiful face naki nayi kewar ki da yawa kodan anjima zamu had'u a wajen kamu zan ga yanda Baby na ta koma tsayin kwanaki 6 ban gan ki ba nasan kin k'ara girma ta ko'ina koh? " Shiru tayi mishi murmishi yayi don yasan bazata amsa ba, kafin kuma su d'an ta6a hirar su irin ta masoya daga k'arshe suka yi sallama da junan su, tashi tayi ta zura hijab nata fari mai hannu kawai ta fito don taji Aunty Aliya tana ce mata ga driven yazo. "Yanzu Aunty babu da wanda zan tafi ni kadai zan tafi" "Eh Suhaima ki tafi kawai zamu taho da yamma kafin a fara kamun kin ji " Gid'a kanta tayi cikin sanyin jiki ta fice daga gidan. Suna zuwa gidan Jiddah mota nayin parking Jiddah ma ta shigo gidan ita take driving d'in ma. "Amaryar mu kin ganni ko wallahi daga wurin da za'a yi kamun nake naje naga yanda suka shirya wajen yayi kyau " Cewar Jidda tana rik'o hannun ta suka k'arasa cikin gidan. "Ya banga su Aunty Aliya ba? " "Zasu taho anjima sun ce " "Okay Allah yasa su zo" "Amin, ni fah agajiye nake har yanzu fah " Fad'in Suhaima kenan tana hamma, dariya Jiddah tayi kan tace "Sai ki je ki kwanta kafin lokaci yayi " Nan ta wuce bedroom na Jiddah tayi kwanciyar ta babu dad'e wa bacci ya d'auke ta kuwa. Sai azahar Jiddah ta tashi Suhaima bayan tayi sallah suka ci abinci sannan Jiddah ta fara fito da kayan da Suhaima zata sanya suna yin er hirar su, bayan sun yi salllahr la'asar ne Suhaima ta shiga wanka tana shiga mai yin makeup ta zo don haka tana fitowa ta shafa wani cream mai kyau da k'amshi ta sanya underwears sannan ta zura wata gown har k'asa ash and silver, ash colour ne sai touch d'in flowers silver, bayan ta gama sawa ne ta zauna aka fara tsantsara mata makeup wanda suka kwashi tsayin lokaci suna yi sannan aka d'aura mata abin head silver sai takalmin ta hill ne ash & silver haka ma purse d'in hannun ta take, wow masha Allah tubarakallahu ahasanul kaliqeen duk hassadar mutum sai yasan Suhaima tayi kyau bana kad'an ba sannan aka d'ora mata wani veil mai d'an girma kad'an saman kafad'un ta. Nan ta fah Jiddah da mai yin makeup suka fara sumbatun kyan da Suhaima tayi nan Jiddah ma tayi gayun ta cikin wani maroon lace sai ta d'aura silver asaman kanta itama tayi kyau, suna gama wa lokacin har 5 ta wuce da wajen 10 minutes agurguje suka tafi wurin kamu, wajen yayi kyau sosai ga mutane nan sosai an zazzau haka families d'in Sabeer sun zo su ma da yawa Dr Faridah ce kawai ban hango ba ko Hajjah Hauwaa ma na hango ta anci gayu an cakare. Jiddah tana rik'e da hannun Suhaima a mazaunin da zasu zauna da Sabeer, sai da Jiddah ta zaunar da ita sannan ta bar wurin aikuwa tasha harara a wajen 'yan uwanta sai kawai ta d'auke kanta, slow music ne ke tashi a wurin kawai mai dad'in saurare. Babu jimawa ango Sabeer ya shigo yana sanye cikin wani d'anyen boyel ash colour hular shi ash da ratsin bak'i takalmin shi bak'i sai agogon hannum shi k'irar gucci black shima sai tashi wani k'asaitaccen k'amshi yake bayan shi friend's nashi 2 ne Musaddiq da Khaleel suma sun yi gayun shi sunyi kyau sosai, nan Sabeer ya zauna kusa da Suhaima sannan friends nashi suka zauna inda aka tanadar musu don zama. Kallon ta Sabeer yake har yaso ya mance ma a inda yake don gaba d'aya Babyn nashi ta canja mishi kamar ba ita ba, sunkuyawa yayi da kanshi dai dai kunnen ta yace "Baby nah kin had'u da yawa kinyi kyau sosai dama zamu dawwama a haka ni da kai " D'an murmishi ta saki tana yin k'asa da kanta don kunya hannun ta ya lalubo ya damk'e cikin nashi wani tattausan laushi yaji ya ratsa shi lokacin da ya rik'o hannun ta har sai da ya lumshe eyes nashi, yayi da Suhaima taji wani irin shock ajikin ta tana kok'arin zame hannun ta ya Kara damk'e su duk kunya ta gama lullu6e ta don kamar tana ganin mutanen wurin suna kallon hannun su sark'e cikin na junan su. Nan aka cigaba da gudanar da kamun har zuwa lokacin da su Aunty Aliya suka k'araso, Babaa Lantana da Hajjah Hauwaa ne suka fesa musu perfumes a jikin su nan aka saki gud'a sannan Sabeer ya mik'e ya fara zuba wa Suhaima kud'i a jikinta yana mata lik'i nan sauran friends nashi da en uwa suma suka taso ana ta zuba lik'i kafin daga k'arshe aka fara ciye ciyen abubuwan da aka tanada. Juyowar da zan d'an yi da kaina sai na hango my Sadeey da Biebie dee sun wage baki suna yagar naman kaji tamkar yau suka fara ci... lol, can gaba kuma na hango Mommana Aunty Jiddah da twins nata a zaune suna shan drinks a nutse nan na k'arasa na kwashi gaisuwa ta, juyawar da zanyi na hango gungun en group d'ina suna wawason shinkafa kaza duk sunyi dumu dumu da kayansu gaba d'aya 🤣😜 sai kawai na d'auke kaina don kada su ganni su nuna sun sanni su ba da ni a gaban en uwan Sabeer lols, duk fan's nasu Sabeer da Suhaima sun halaccin wajen sosai sunyi karar zuwa. Daga nan bayan an gama cin abubuwa ne aka d'ad'auki pic's sannan aka fara tafiya saboda har an fara kiran sallahr mangarib ma, dakyar Sabeer ya iya rabuwa da Suhaima don ji yake kamar ya tafi da ita gashi ko damar su dan ke6e ma basu samu ba, ko gidan Jiddah bata koma ba Sabeer ya sanya drive ya mayar dasu gida. Kayan jikin ta kawai ta iya cirewa ta watsa ruwa ajikinta tana sanya sleeping dress ta kwanta, tana cikin yin addu'ar bacci Aunty Aliya ta shigo hannun ta d'auke da wani cup ta mik'awa Suhaima bata tsaya tambaya ba ta kar6a ta shanye tana yatsina fuska ta mik'awa Aunty Aliya cup d'in sannan ta janyo blanket ta rufa itam Aunty Aliya fitowa tayi daga d'akin, bacci mai nauyi ne ya d'auki Suhaima. _gobe insha Allah zaku ga next pag fan's_ Aishat A Muh'd ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 79-80* Washe gari kuma shine ranar dinner d'in da friend d'in Sabeer wato Muusaddiq ya shirya musu don haka Suhaima ma ranar ma wajen azahar driver ya d'auke ta sai gidan Jiddah ita da wasu friends nata guda 5 wad'anda suka yi islamia dasu kuma kawayen ta na cikin unguwa, lokacin da suka k'arasa ma Jiddah bata nan ta tafi gidan su nan suka zauna a palour suna hirar su mai aikinta ta shirya musu abubuwa ci dana sha ta kawo musu sai after la'asar Jiddah ta yakice jikin ta dakyar ta taho gidan don sun yi waya da Suhaima sun zo. *_8:40pm_* Wata had'add'iyar mota black sai shek'i take da ganin ta kasan sabuwa ce tayi parking a compound d'in gidan Jiddah, ko mintuna biyar bata yi da parking ba sai ga su Suhaima sun fito wow masha Allah nace ganin yanda Suhaima tayi wani masifar kyau cikin wata gown har k'asa take ja sosai hannun rigar dogo ne har karshen hannu peach colour ne mai d'an haske tana da adon flower's manya shima kalar peach ne da kyallin duwatsu silver ajiki, sai abin nad'in kanta peach ne mai d'an duhu sai veil mai d'an girma an yafashi a saman kafad'un ta, tana sanye cikin shoes hill peach da purse nata itama kalar takalmin tasha wata sark'ar gold babba mai d'an girma a wuyanta haka ma hannun ta warwaron gold ne kowanne hannu guda hud'u hud'u tasha heavy makeup irin na bride, fuskar ta sai wani shek'i take kyau iyakar kyau Suhaima tayi shi sai tashin wani sanyayen k'amshi take yi ajikinta mai rikita mutum ya rasa irin perfumes d'in da akayi amfani dashi, tana tafiyar ta a nutse yayi da wasu kawayen ta biyu suke rik'e da karshen gown d'in ta inda yake jan k'asa suka nufi motar da ango yake, suma friends nata biyar sun sha gayun su cikin wani material pink da blue sun yi kyau kam ba laifi, Jiddah ma ta shirya cikin wata gown ta material pink colour tayi kyau itama hannun ta yana rik'e dana mijinta Khaleel shima yayi kyau cikin wata lallausar shadda fara. Tun da suka taho Sabeer ya saki baki da hanci yana kallon Babyn shi yanda ta koma tamkar ba ita ba, duk da yasan Babyn shi mai kyau ce ko batayi kwalliya but wannan kyan da tayi na daban ne har baisan lokacin da ta shigo motar ba sai jin daddad'an k'amshin turaren ta cikin hancin sh. Wata ajiyar zuciya ya sauke mai d'an k'arfi baisan lokacin da ya rik'o hannun ta ba d'aya ya d'ago fuskarta da d'ayan hannun yana mata wani irin kallo da eyes nashi wanda suke a wani lumshe lumshe, bakin shi yakai saman goshin ta yayi kissing d'in shi sannan ya cika fuskar ta yana cewa "Masha Allah " Abin da ya fad'a kenan a lokacin da suka bar harabar gidan Jiddah but still hannun shi yana cikin nata yana wani irin murza su a hankali, ita kuma Suhaima kunya ce ta kama ta sosai ganin abin da Sabeer yayi mata wanda bai ta6a kwatanta yi mata sai yanzu kuma tasan kwalliyar tace ta burgeshi sosai. Sabeer bakin shi yayi mishi nauyi ya kasa magana saboda wani irin abu da yake ji yana ratsa shi a cikin kowanne lungu da sako na jikin shi, da haka suka k'arasa wajen da za'a gabatar da dinner d'in kallon ta yake tamkar yau ya fara ganin ta. A d'an sace Suhaima ta kalle shi yasha wata shadda milk colour mai d'an duhu milk d'in sai aikin jikin rigar brown zare akayi amfani dashi har da babbar riga karo na farko kenan da Suhaima taga Sabeer cikin shigar manyan kaya sai taga yayi mata kyau ya k'ara mata wani girma da kwarjini a idanun ta har da hula milk and brown ne kai Sabeer ya had'u kawai ta ko'ina gaskiya Suhaima tayi dacen miji haka shima yayi dacen mata sun dace da junan su sosai. Motar su tana k'arasa wa wajen tayi parking but basu fito ba suna zaune aciki, sai da Jiddah suka k'araso sannan suka fito hannun su na sark'e waje d'aya suna gaba Jiddah da Khaleel, Musaddiq da Mufidah a bayan su sai kuma friends na Suhaima su biyar d'in nan a bayan su. Wajen yasha decoration na peach, red, pink and white ko'ina sai kyalkyali yake ga mutane duk an zazzau suna zaman jiran shigowar ango da amarya wani slow music ke tashi na wakar india ta Piya O Re Piya Tere....., itace ke tashi a wurin suna shigowa kallo ya dawo kansu sai fesa musu wani spray mai kyalkyali ga wasu furanni farare da ja da ake watsa musu a jikin su har suka k'arasa inda zasu zauna wata kujera ce d'aya mai d'an fad'i da zasu zauna daga bayan su kuwa wani k'aton frame ne yasha decoration an rubuta anyi zanen heart sai aka rubuta S-S ajiki wato Suhaima and Sabeer. Bayan an zazzauna ne kuma Jiddah ta bud'e taron wajen da addu'a sannan ta bayar da tak'aitaccen tarihin amarya da harshen turanci bayan ta gama Musaddiq ma ya tashi cikin tafiyar kasaita Mufidahn shi mak'ale dashi yaje shima ya bayar da tak'aitaccen tarihin ango Sabeer sannan kuma akan nemi ango da amarya su fito su d'an taka rawa. Suna tsaye wajen da aka tanada don yin rawa hannun Sabeer d'aya zagaye da kugun Suhaima d'ayan hannun kuma yana rik'e da d'ayan hannun ta ita kuma hannun ta yana zube saman kafad'un shi da haka suke d'an jujjuyawa don babu wanda ya iya wata rawa acikin su, sun birge mutane sosai yana mata magana kasa k'asa saitin kunnen ta bayyana mata irin tarin son da yake mata yake yi. Jiddah ce da Khaleel suka fara zuwa wajen suka fara yi musu lik'i nan Musaddiq da Mufidah suka taso suma daga nan sauran mutane suka fara yi musu lik'i, can na hango My Biebie dee, my Sadeey, Ummu Safwan, Zahra da sauran fan's suna faman lik'a musu 'yan five five a kunyace suke yi saboda babu mai lik'a k'asa da five hundred sai su lol 😂. Nan daidai aka cigaba da gudanar da dinner har zuwa lokacin da za'a yanka cake, Sabeer na rik'e da Babyn shi suka k'arasa wajen cake d'in wanda ya kasance hawa 5 ne yasha decoration sosai na white da peach, Suhaima ta rik'e knife na yanka wa Sabeer ya d'ora hannun shi saman nata nan suka yanka sannan Suhaima ta gutsuro cake d'in sai da ta d'an russuna k'asa sannan ta sanya mishi abaki a d'an kunyace tayi hakan tana yin murmishi. Shima Sabeer murmishin yake kafin ya sanya hannun shi ya d'ago ta tsaye tukunna ya d'an rungume ta a jikin shi ya bata cake d'in da d'an juice a cup daga k'arshe ya bita da kissing a cheek d'in ta sai d'an ihun birgewa mutane ke yi suna yi musu tafi daga haka suka koma wajen zaman su. Sannan aka fara ciye ciyen abubuwan ci da sha wanda aka shirya su na alfarma, Sabeer ne ya kallo Babyn shi cikin wani salon kallo yace "Baby nah i luv U, i really luv U bazan iya rayuwa babu ke ba ina fatan addu'ar Allah ya bar min ke har iyakar tsayin rayuwa ta " D'an murmishi Suhaima tayi kawai, hannun ta ya rik'o wanda ke rik'e da cup da juice aciki ya kai bakin shi ya d'an kur6a kad'an kafin yace "Baby baki ce komai ba fah, yanzu gobe kamar haka na zama ke kin zama ni babu zancen jin kunya kuma, kodan ma kunyar bin ta zanyi duk inda take na cire ta ko ba haka ba amarya ta? " Kamar k'asa ta tsage Suhaima ta shige haka take ji lallai Sabeer ya fitsare da yawa, yanzu ma yana mata haka balle gobe an d'aura musu aure sai kuma abin da yafi haka nan taji gaban ta ya fad'i, yana kokarin sake magana Musaddiq ya k'araso yana cewa "Ango kazo ayi pic's don dare nayi my wife ta gajiya zamu tafi gida" Tashi suka yi nan aka fara d'aukan picture's sosai da mutane, nan na d'an kutsa na samu aka d'auke mu pic's da ango da amarya sannan na samu wani table na zauna a gajiye nake lik'is, d'an waigawar da zanyi ba sai na hango su My Sadeey, My Biebie dee, Zahra, Ummu Safwan ana faman kiciniya da cinyoyin kaji bakunan su yayi dumu dumu da maik'o amman basu san da hakan ba, wani huci na saki mai zafi ganin zasu sanya ni jin kunya idan aka tambaye ni wadannan wane ya gayyace su idan aka nuna ni dole naji kunya kuwa don haka harara na dalla musu sannan na d'auke kai na lol🤣😂, gaskiya naji dad'i sosai ganin yanda fan's na ASANANDIN SON KI sunyi k'arar zuwa wannan bikin na Sabeer da Suhaima mun sha hira dasu sosai gashi har da ankon su na daban suka yi daga k'arshe muka yi sallama dasu don ni bayan amarya zan bi don na cigaba da d'auko muku rahoto yanda zata kasance nayi musu fatan komawa gida lafiya. Sai wurin 12am na dare aka tashi daga wannan dinner d'in Jiddah tayi tayi da Sabeer yabar Suhaima su tafi gida tare ya 6ata rai tare da cewa "Ke ni fah kin dame ni Jiddah ranki zai 6aci cinye ta zanyi kome, nace zan kawo ta har gida? " Zum6ura baki Jiddah tayi had'e da cewa "Toh gaakiya kada ku dad'e sannan ayi ahankali ba'a d'aura ba don naga rawar kanka ta fiye yawa" Fad'in Jiddah tana tafiya tana maganar k'asa k'asa kamar gunguni don bai ma ji k'arshen maganar ta ba. Sai wajen 12:40 na dare Sabeer da Suhaima suka taho don sai da ya gama sallama da friends nashi da suka zo tukunna suka taho, driver yana parking Suhaima ta sanya hannu zata bud'e k'ofar ne da sauri Sabeer ya rik'o hannun nata yana cewa "Baby wai har tafiya baki jira mun yi sallama ba? " Tana lumshe ido tace "Bacci nake ji Sabeer wallahi gashi na gaji " Ta k'arasa maganar tamkar zata fashe da kuka, d'an murmishi yayi sannan yace "Baby sarkin raki huh, bari na kyale ki don nasan kin gajin " Kissing d'in bayan hannun ta yayi sannan ya bud'e motar ya fito ya zagayo ya bud'e mata hannun ta ya kamo suka fito har zuwa k'ofar shiga parlourn gidan Jiddah, knocking yayi sau d'aya kamar wanda ake jikin k'ofa ana jira aka bud'e da sauri. D'ago kanshi yayi ya watsa wa Jiddah harara don yasan itace zatayi hakan, dariyar da ke neman kubce mata ta had'iye tare da cewa "Ni me nayi Yaya kuma kake harara ta? " "Bansani ba " Juyowa yayi ya kalli Suhaima yace "Baby kiyi bacci sosai gobe karfe 8 na safe zan aiko driver ya mayar daku gida " Ya k'arasa fad'i yana kissing goshin ta, d'an waro idon Jiddah tayi cikin tsokana tace "Yaya agabana koh? " Harara ya sake watsa mata sannan ya wuce Jiddah ta tuntsire da dariya sannan ta kama hannun Suhaima suka wuce ciki. Washe gari da safe wajen 8 na safe Suhaima, Jiddah da sauran friends nata suka taho k'auyen su Suhaima, friends na Suhaima jiya sun ga abin da basu ta6a gani ba sai jin labari sun rud'e sosai da ganin wannan dinner da akayi lallai kud'i suna wajen masu shi kowacce cikin su tana fatan Allah yasa ta a danshin Suhaima. Sai wurin 11am suka isa nan suka tarar gidan ya cika da 'yan uwa da abokanan arzik'i, suna gaisawa da en uwa tukunna suka tafi gidan Babaa Lantana can suka nufa, shima ba zama suka yi ba sai shirye shiryen walimah suke yi don kafin a d'aura aure zasu yi don ana gama d'aurin zuwa la'asar za'a tafi kai Suhaima gidan ta. Daman sun gama tsara inda za'a yi har malamar da zata yi lecture sun gayyato, don haka gyara wajen akayi aka shirya ko'ina yayi kyau sosai, zuwa karfe 12 mutane sun zo sosai har shahararriyar malaman nan My Momma Aunty Maijiddah tazo tare da tawagar ta don haka babu 6ata lokaci su Jiddah su zo wajen tare da amarya Suhaima tana sanye cikin wani ash da pink colour lace sai ta d'ora alkabba ash mai adon flower's pink da sliver ajiki tayi kyau sosai sai zuba k'amshi take zaunar da ita suka yi kan kujerar sannan kowa ya samu waje ya zauna. Sannan Momma ta fara da bud'e taro da addu'a kafin ta shiga yiwa amarya nasiha da shawarwari na zaman gidan aure, hak'uri, biyyaya, iya tsabta, kwalliya da tattalin miji kowanne sai da ta d'auke su tare da yin bayanin su sosai, taja hankalin mata sosai akan kishiya da zuwa wajen boka, kaiii gaskiya My Momma ba k'aramin nasiha da shawarwari ta bawa mutane ba don ba iya Suhaima bama har wad'anda suka halacci wajen sun k'aru sosai daga k'arshe aka yi aka sha tare da yin kyautittaka ga duk wad'anda suka zo karfe 1 aka tashi daga walimar kowa ya watse. Bayan an sako daga masallacin juma'a ne aka d'aura auren Suhaima Omar and Sabeer Hussein Ahmad d'an fillo akan sadaki mafi neman albarka aure ansha pics sosai tare da rabon kud'i don family d'in D'an fillo ba k'aramin bajinta suka yi ba, bayan an gama d'aura auren ne aka tafi yin walima ta maza wanda Dr Ahmad d'an fillo ya shirya don farincikin Sabeer. "Hello! Mata ta! " Cewar ango Sabeer kenan, shiru Suhaima tayi don gaba d'aya tun lokacin da aka d'aura auren jikin ta yayi sanyi sosai. "Baby nah yau ina matuk'ar farinciki wanda ban ta6a kasancewa acikin shi ba, yau ni Sabeer Suhaima ta zama mata ta ji nake kamar a mafarki ina godiya ga Allah da ya nuna min wannan ranar, anjima kad'an za'a zo d'auko min ke wanne tanadi kika yi mana Baby a wannan daren? " Kittt ta katse wayar nata, dariya Sabeer yayi don yasan kunya ce ta sanya ta hakan d'an lumshe idon shi yayi yau zuciyar shi fes yake jin ta wata k'aunar Suhaima ce take k'ara shiga cikin zuciyar shi. Suhaima tana kashe wayar kawai sai ta fashe da kuka wanda na kasa tantance kukan me take, Jiddah ce ta rarrashe ta sannan ta kama hannun ta suka tafi can gidan Yaya Aliyu, anan Aunty Aliya da Yaya Aliyu, Babaa Lantana suka yiwa Suhaima nasiha mai ratsa jiki sosai kafin 'yan uwa su zo suyi mata kowa idan zai mata nasiha sai ya ambaci kalmar hak'uri. Daga nan suka dawo gidan Babaa Lantana wanka Suhaima take amman kuka take har ta fito ta shirya cikin wani maroon lace da touch na silver ajiki d'inkin riga da siket ne sun yi mata kyau sosai, dakyar Jiddah ta rarrashe ta tayi mata makeup sannan ta nad'a mata laffaya bak'a mai kyalkyalin silver ajiki sai shoes black da purse black ita ma suna cikin shirin ma motocin d'aukan amarya suka k'araso. Kuka Suhaima take sosai tana rungume da Aunty Aliyah da Yaya Aliyu dakyar aka 6an6are ta daga jikin su tana kuka aka sanya ta mota shima Yah Aliyu sai da yayi hawaye Aunty Aliyah kuwa kuka ta fashe da shi sosai suna kallo har aka tafi da Suhaima, da gudu Aunty Aliya ta shige cikin gida tana kuka nan Yah Aliyu ya bita yana rarrashin ta don gaba d'aya mutane sun wuce kai Suhaima. Aljannar duniya abin da nace kenan don ganin tsararren gidan da Sabeer ya gina, kaiii tsayawa ba fad'in had'uwar gidan 6ata lokaci ne mai karatu kawai kayi hasashe da kanka, kud'i sunyi kuka a wajen ginin gidan, nan mutane suka fara santin gidan tun daga farfajiyar gidan, da suka shiga cikin gidan kuwa sakin baki da hanci suka yi suna kallo. Jiddah bata bari an shiga bedroom d'in Suhaima na ainahi ba don kuwa tsarin da tayi mishi sai amarya da angon ne zasu shiga, da yake bedrooms biyu ne na Suhaima sai aka wuce da ita d'ayan Babaa Lantana ce rik'e da hannun ta zaunar da ita tayi kan bed kafin kuma a fara fita daga d'akin zuwa kallon yanayin tsarin gidan. Sai bayan mangarib aka tafi mayar da mutane Suhaima k'ank'ame Babaa Lantana tayi tak'i cikata sai dakyar aka kwaci Babaa Lantana don ba k'aramin riko Suhaima tayi mata ba, Jiddah ce ta rik'e ta tana rarrashin ta yayin da su kuma suka tafi Babaa Lantana har da goge hawayen ta na kewar Suhaima. Gidan sai yayi tsit daga Jiddah sai friends na Suhaima gyaran gidan suka yi suna gama gyarawa kowacce ta fara shirin tafiya dinner na family d'in D'an fillo, Jiddah ta sanya Suhaima tayi wanka ta bata wata white gown ta material har k'asa take ja sosai sai adon flower's silver ajiki, dakyar ta tsayar da hawayen idon ta aka yi mata makeup sannan aka nad'amata net white akanta sai hill shoes and purse white sai d'igon silver ajikin su, sunyi mata kyau sosai kayan different perfumes Jiddah ta fesa mata kafin ta rik'o hannun ta suka fito zuwa compound na gidan. Suhaima na shiga cikin motar tun kafin Jiddah ta rufe murfin motar Sabeer ya rungume ta ajikin shi yana sakin wata ajiyar zuciya gaba d'aya yabi ya wani matse ta cikin jikin shi k'am tamkar za'a kwace mishi ita. "Kaiii Yah Sabeer agaba na ji yanda ka matse ta" Jiddah ta fad'a tana rik'e da murfin motar, wata harara ya watsa mata don bazai iya magana ba dariya ta kwashe da ita kan ta rufe motar. Kok'arin zame jikin ta take amman yak'i sakin ta sai faman shinshina wuyan ta yake yana wani sauke ajiyar zuciya da numfashi cikin murya k'asan mak'oshi yace "Baby ki barni mana kinsan dai yanzu kin zama tawa ta har abada hakan da nake miki babu haramci aciki tunda an d'aura mana aure, Baby kinsan tun yaushe nake mafarkin zuwan wannan ranar kuwa? " Ita dai Suhaima a tsorace take dashi ganin yanda Sabeer d'in ta ya rikid'a ya koma wani daban tamakar bashi ba jikin ta har ya fara 6ari na tsoro, da haka suka k'arasa wajen da za'a yi dinner, yana rungume da kusan rabin jikin ta suka shiga wajen. 'Yan uwan Sabeer gaba d'aya yawancin sun zo haka ma Hajja Hauwaa, Dr Ahmad d'an fillo, Daddy da k'annen shi Dr Faridah da sauran matan k'annen Daddy, haka ma yaran duk sun zo tun daga manya har k'ananu waje dai ya cika masha Allah gashi sun sha gayun su na kece raine, ga friends na Dr Faridah wato Mumy duk kusan sun zo manyan hamshak'an en boko da en siyasa da kuma likitoci gaskiya anyiwa Dr Faridah karar zuwa wajen bikin tilon d'anta. Amman fuskar ta sam baza ka iya karantar yanayin da take ciki ba farinciki ko akasin haka, kusan nace gaba d'ayan su Daddy ne kawai yake faman zuba murmishi cikin zuciyar shi yana yaba za6en d'an nashi don sai yanzu yasan Suhaima da ido, bayan ango da amarya sun yi rawa an musu lik'i ne sun yanka wedding cake ne suka bi ko'ina suna gaida en uwa da abokanan arzik'i da suka zo an ci ansha sannan aka watse da tarin gift's d'in da Suhaima ta samu a wajen friends na Daddy da k'annen sai na Dr Ahmad d'an fillo tasha kyautittaka sosai a wajen su, zuwa lokacin gaba d'aya jikin Suhaima ya gama yin sanyi ganin irin kallon da mahaifiyar Sabeer take bin ta dashi da sauran en uwan shi ita duk ma kallon da Mumy take binta dashi yafi hargitsa mata kai ko gaisuwar ta bata amsa ba sai tashi tayi da sauri tabar wajen tana amsa kiran karya a wayanta don kuwa ba kiranta aka yi ba. Sai karfe 11 da wajen rabi aka tashi kowa ya kama gaban shi, Suhaima ce take rik'e da hannun Jiddah k'am sai fitar da hawaye take tana cewa "Ni dai tare daku zan tafi gaskiya " Dariyar da take neman kubce wa Jiddah ta had'iye ta kafin tace "Haba Suhaima kiyi hak'uri ku tafi kin ga yanzu dare yayi gashi na gaji sosai amman nayi miki alkawarin gobe zan zo na kawo miki friends naki kuyi sallama dasu " Kasa magana tayi sai hawaye gaba d'aya hankalin ta a matuk'ar tashe, sosai Jiddah ta bata tausayi cikin sanyin murya da kwantar da hankali take rarrashin Suhaima tana rik'e da hannun ta har ta sanya ta cikin mota ji take kamar itama ta taya Suhaimar kukan sai dai ta daure. Sabeer yana shiga motar ya umarci driver ya dasu tafi don ya matsu ya ganshi su kadai da Babyn shi awaje daban, rarrashin ta shima Sabeer d'in yake har suka k'arasa gida cak ya d'aga ta sama ya d'auke ta suka nufi cikin gidan bai dire ta a ko'ina ba sai a tsakiyar bedroom nata. Hannun shi ya sanya ya fara warware mata net d'in kanta sannan ya dawo kan sark'a, d'an kunne warwaro zuwa takalmin k'afar ta, bata ankara ba taji yaja zipe d'in rigar tun daga sama har k'asa wani 'yar k'ara Suhaima ta saki tare da yin baya da sauri ta jingina da bango idanun ta taf hawaye take kallon shi. Shima ita yake kallo da wasu birkitattun eye's nashi da suka fara canja launi zuwa ja, matsowa yayi kusa da Ita murya a shak'e yace "Baby what wrong? " Girgiza kai kawai take tana hawaye ganin haka ya sanya shi cewa "Okay shikenan yanzu ki je kiyi wanka kinji " Da muryar rarrashi ya fad'a gid'a kanta tayi kawai, ganin tak'i tafiya ya sanya shi barin d'akin ya tafi side d'in shi yana jinjina yarintar Suhaima daga zuge zipe shine take k'ara. Yana fita Suhaima tayi saurin zare rigar ta shiga toilet wanka tayi da ruwan d'umi sosai ta gasa jikinta Saboda gajiyar da take tattare da ita sannan tayi alwala ta fito, lotion kawai ta shafa sannan ta fesa body sprays da shafa humra a jikinta sannan ta sanya wata red d'in sleeping dress mai siririn hannu ce tsayin ta iyakar gwiwa sai ta d'ora ta saman ta wanda ake d'aure ta da mad'auri a gaba kayan sun mata kyau, tana cikin gyara gashin kanta Sabeer ya turo k'ofar ya shigo, sai da gaban Suhaima ya fad'i shima yayi wankan shi cikin sleeping dress na maza farare ne sol masu laushi sosai, kallonta yake tamkar ya lasheta haka yake ji. "Baby zo mu yi sallah " Hijab ta d'auko mai hannu har k'asa ta sanya sannan suka tada sallah sai da suka yi sallahr ishsha sannan suka kawo raka'a biyu ta nafila ya dad'e yana musu addu'o'i na samun zaman lafiya da zuri'a mai albarka, ya dafa kanta yayi addu'ar da Annabi SAW ya umarci kowanne ango da yayi wa amaryar shi. Yana gama wa ya tashi ya fita bai dad'e ba ya dawo d'akin hannun rik'e da babban plate, ajiye shi yayi ya fara bata naman abaki kad'an ta iyaci ta girgiza kanta alamar ta k'oshi sannan ya bata fresh milk tasha, shima kad'an ya iya ci ya barshi don sun ci abinci a wurin dinner. Janyo ta yayi jikin shi yana rad'a mata "Baby ki saki jikin ki dani please bazan cutar da ke ba" Ita dai gaba d'aya jikinta rawa yake na tsoro, yana kok'arin had'a bakin shi anata yaji alamar shigowar message a wayan shi d'an tsaki yayi kad'an sai lokacin ya tuna da bai kashe ta ba. Janyo wayar yayi da niyyar yayi switch off d'in ta sai yaga message d'in Jiddah ce ta turo don haka sai ya bud'e shi " _Yah Sabeer ka canja bedroom zuwa d'ayan na Suhaima nasan idan ka shiga sai ya birge ka, asha amarci lafiya, kayi k'awata a hankali please_". Abin da Jiddah ta rubuta kenan d'an murmishi ya saki cikin zuciyar shi yana cewa lallai Jiddah ta raina shi idan ya kamata zata yi bayani har da wani ce mishi yayi hankali, batasan ya fita son Suhaima ba bazai yi abin da zai cutar da ita ba. Tashi yayi ya janyo hannun Suhaima suka shiga toilet brush suka yi, kafin Suhaima ta ankara ya d'auke ta cak suka fita daga bedroom d'in zuwa d'ayan na kusa dashi. Suna shiga wani sanyayen k'amshin turare ne ya fara yi musu sallama d'akin ya had'u komai kalar maroon and black ne gashi babu haske sosai sai wani hasken k'ananan bulbs kawai, d'akin yayi d'an duhu kad'an k'arasa wa Sabeer yayi kusa da bed yaga an jera wasu flowers na furanni jajaye anyi zanen heart an rubuta Suhaima and Sabeer ajiki, sosai d'akin ya birge Sabeer kuma ya k'ayatar dashi, cikin ranshi ya jinjinawa kok'arin Jiddah. Kwantar da Suhaima yayi saman bed d'in wadda itama bedroom d'in ya birgeta sosai duk da yanda take a tsorace sai da ta gane hakan, jin Sabeer ya kwantar da ita shima ya kwanta a gefen ta ya sanya ta dawo da hankalin ta kanshi, had'a ido suka yi nan suka shagala da kallon junan su, hannun shi ya sanya yana shafa saman gashin kanta cikin wani irin yanayi yace "Baby kin gaji ne, kina jin bacci? " D'aga mishi kanta yayi, a hankali ya janyo ta jikin shi ya rungume ta k'am yana wani shinshina gashin kanta da wuyan ta yana shak'ar daddad'an k'amshin turaren ta........ _Sorry Fan's jiya nayi muku alkawarin page kuma banyi ba sakamakon ciwon kan da na yini dashi_. Aishat A Muh'd ✍🏻 *A̺ S̺A̺N̺A̺D̺I̺N̺ S̺O̺N̺ K̺I̺* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aıʂɧąɬ A Mųɧɖ Dɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ Sąɖɛɛყ Sąŋąʑ *PAGE 81-82* Ahankali ya janyo ta jikin shi ya rungume k'am yana wani shinshina gashin kanta da wuyan ta yana shak'ar daddad'an k'amshin turaren ta, cikin nutsuwa Sabeer yake yawo da hannun shi cikin jikinta, yayin da Suhaima jikinta ya hau rawa gabanta na mugun fad'uwa amman bata yi yunkurin hanashi ba, saboda tasan hakk'in shine an fad'a musu a islamia sannan Aunty Aliya da Malama Aunty Jiddah sun sanar da ita hakan, amman fah a tsorace take don tasha karanata wa a novels taji yanda amarya take shan wahala a daren ta na farko. "Baby ki kwantar da hankalin ki bazan cutar da ke ba, wannan rawar jikin yayi yawa kin ji" Suhaima bata yi magana ba sai wasu hawayen da suke zubo mata sakamakon wani bak'on al'amari da yake kok'arin tunkaro ta yanzu, had'e bakin su yayi waje d'aya yana wani kissing d'in ta gaba d'aya jikin shi rawa yake tamkar yanda Suhaima nata yake rawa dukkanin su sabon shiga ne a wannan yanayin, tun da ya fara kissing nata bai sakin bakin ta ba sai da yaji numfashin ta na kok'arin fita, saboda tsayin lokacin da ya d'auka nason yaga wannan bakin cikin nashi shi yasa bai yi mishi da wasa da ya cafke shi. Cikin nutsuwa Sabeer yake aikawa da Suhaima zafaffan soyayyar shi mai ratsa kwakwalwa da tsayawa a rai, har zuwa lokacin da ya mayar da Babyn shi cikakkiyar matar shi ya zama ita ta zama shi, gaba d'aya Sabeer ya gama rud'e wa da kid'imewa awannan lokacin in banda hawayen farinciki babu abin da yake fitar wa yana rungume da Babyn shi tamkar zai mayar da ita cikin jikin shi wani dad'i ne yake ratsa jikin brain nashi da zuciyar shi na yanda ya riski Suhaima. Kuka sosai Suhaima ke yi idanun nan sun kumbura sosai saboda kuka na azaba don ta wahala hannun Sabeer ba kad'an ba sai da ya saukar mata da duk wani tanadi da ya dad'e yana shiryawa zuwan wannan ranar. "Baby nah Allah yayi miki albarka, Allah ya bamu 'ya'ya masu albarka, Allah ya barmin ke har k'arshe rayuwa ta hak'ik'a kin bani farincikin da bazan ta6a manta wa dashi a iyakacin rayuwa ta, zan ajiye wannan daren da yafi kowanne dare cikin tsayin rayuwata, Baby na mallaka miki kaina zuciya ta gaba d'aya sun zama naki sai yanda kika yi dasu i luv you Baby i luv U with all my heart sweet mata ta" Ya k'arasa fad'i yana wani sake hugging d'in ta cikin jikin shi tamkar za'a kwace mishi ita, duk da Suhaima bata cikin nutsuwar ta kalaman Sabeer sunyi matuk'ar yi mata dad'i sosai har sai da wasu hawaye suka zubo mata. "Sweet Baby sannu kiyi hak'uri nayi miki da zafi koh gaba d'aya bana cikin hayyaci nane am sorry " Ya k'arasa maganar kamar yayi mata kuka, ganin haka ya sanya ta aro jarumta ta girgiza mishi kanta alamar babu komai but still eye's nata na zubar da tears amman sai da ta k'ak'alo smiling na dole, kallon ta yake tamkar ya had'iye haka yake ji yasan tayi juriya sosai kuma yaji dad'in hakan, but baya son ganin wannan hawayen sai yana jin zafin fitar su cikin zuciyar shi sai yaga kamar bai kyauta mata ba. Sai da ya 6ata lokaci yana rarrashin sosai har ya samu ta bar kukan sai ajiyar zuciya da take saukewa, sannan ya tashi ya shiga toilet wanka yayi sannan ya had'a mata ruwan d'umi acikin bathtub sannan ya fita zuwa bedroom d'in yanda ya barta akwance haka yazo ya same ta, blanket d'in da ta rufe jikinta dashi ya sanya hannun shi zai cire da sauri ta rik'e hannun shi tare da marairaice face nata, cikin rarrashi yace "Baby nah wanka zaki yi nasan zaki ji dad'in jikin ki " Ya fad'a yana wani bin ta da mayen kallo ji yake kamar ya maimaita abin da yayi yanzu, ko had'a ido Suhaima tak'i yi dashi saboda kunyar shi da take ji sosai, bata ankara ba taji ya d'auke ta gaba d'ayan ta har da blanket d'in da take ciki yayi bathroom da ita, saboda tsorata sai da Suhaima tayi 'yar k'ara "Kaiii Baby kin cika tsoro da yawa " Ya fad'i hakan yana kok'arin cire abin blanket da ta kudundune acikin shi, dakyar ya iya warware shi ya sanya ta cikin ruwan d'umin, 'yar k'ara kad'an ta sake saki kafin kuma ta sauke ajiyar zuciya saboda yanda ruwan yake ratsata. Kukan shagwa6a ta sanya mishi sai ya fita daga toilet d'in, ba don yaso ba ya fita saboda yana son taimaka mata, gyaran kan bed sannan ya fita zuwa d'ayan bedroom d'in Suhaima ya d'auko fresh milk da cup ya fito ya dawo d'akin. Bayan ta gama gyara jikinta ne sai ta d'ora towel tana kok'arin fitowa daga bathroom Sabeer ya turo k'ofar ya shigo saboda jin ta shiru da yayi, d'aukan ta yayi ya had'e ta da jikin shi akan bed ya sauke ta, sannan ya zauna kusa da ita yana murmishi yau jin shi yake cikin nishad'i kamar yafi kowa farinciki ayau d'in nan. Ita kuma sai nok'ewa take tana sunkuyar da kanta tare da jan towel d'in jikinta wanda yake iyakar cinyar ta yanda take janshi tamkar zai k'ara tsawo akan tsayin shi, hannun shi ya sanya saman kan cinyar ta yana shafawa a hankali sannan yace "Baby nah ya jikin naki " Cikin sanyin murya tace "Ni.... Ni lafiya ta qlau " Mak'ale kafad'a yayi sannan yace "A'a Baby ban yarda ba, fad'a min gaskiya idan wani wajen nayi miki ciwo" Kamar zata fashe da kuka tace "da gaske nake ni kawai bacci nake ji sai jikina da kaina da suke ciwo " "wayyo sannu Baby nah nasan its all my fault, am so sorry " Yana maganar ne yana mammatsa mata jikinta fuskar shi duk tayi kalar tausayi. Fresh milk ya zuba a cup ya bata tasha da pain relief, kok'arin tashi take ya rik'ota tare da cewa "Baby ina xaki? " "zan sanya kaya ne " Rungumo ta yayi jikin shi had'e da cewa "Muyi baccin mu kawai Baby " D'an d'aga ido tayi ta kalli agogo sai taga har 4:35 na dare kafin ta mayar da eyes nata ta lumshe su, shafa ta yake tare da yi mata tausa a hankali wani bacci mai nauyi ya d'auke ta, yayin da Sabeer kuma ya zuba mata eyes yana kallon ta wani sonta na sake ratsa mishi zuciya da haka shima baccin ya d'auke shi yana rungume da ita cikin jikin shi. *_8:30ąɱ_* Ahankali take bud'e idanun ta sakamakon shafa mata fuska da ake, had'a ido da Sabeer tayi yana zaune kusa da kanta fuskarshi d'auke da murmishi har yayi wanka yana sanye cikin wata white t-shirt and trouser black kayan sun kar6e shi gashin kannan nashi yasha gyara sai shek'i take. "Baby gari ya waye fah" D'an lumshe eyes nata tayi sannan ta bud'e su, kafin ta fara kok'arin tashi zama tayi sannan tayi mik'a kallon Sabeer tayi sai taga ya k'ura mata ido sai wani mayataccen kallo da yake bin jikinta da kallo ganin haka ya sanyata bin inda yake kallo da eyes nata sai taga ashe towel d'in ne ya cire wanda batasan lokacin da ya fita ba, wani 'yar k'ara ta saki da sauri tare da k'udundune kanta da blanket tana mai tsananin jin kunyar shi, dariya abin ya bawa Sabeer sai ya shiga cikin blanket d'in yana dariya yace "baby mene kuma abin 6oyewa kuma bayan naga..... " Da sauri ta sanya hannun ta tare da rufe bakin shi k'am, d'an cizon hannun yayi kad'an da sauri ta janye shi tana yarfewa bayan 'yar k'arar shagwa6ar da ta saki. "Ayyah Baby nah mu gani da zafi ne?" D'aga kanta tayi alamar eh, kama hannun yayi yana busa mata shi daga k'arshe ya shagala da wani abin daban, dakyar ta kwace kanta ta shige toilet a daddafe, Sabeer kuwa kwanciya yayi saman bed jikin shi sam babu k'arfi idanun shi akan bathroom d'in. Bayan ta gama wanka ne da d'aura alwala ta fito daga toilet d'in, tana d'an d'ingishi kad'an bata ga Sabeer ba tana tunanin ko ya fita, don haka wajen dressing mirror ta nufa cream ta shafa sannan ta nufi closet ta janyo wata atampha white da touch na pink ajiki d'inkin riga da siket ne, bayan ta sanya underwears sai ta sanya kayan sunyi mata kyau tare da zauna mata ajikinta, hijab ta d'auko ta sanya tare da shimfid'a praying mat tayi sallah tare da yin addu'a. Zama tayi kan stool bayan ta jona hand dryer ta fara busar da gashin kanta, duk wad'annan abubuwan ta iya su ne wajen Jiddah, bayan ta gama ta shafa mishi mai tare da taje shi ta d'aure shi da ribbon, simple makeup tayi a face nata daga powder da ta sanya sai tayi gira tayi blending d'inta ta kwanta sosai gashi ta fitar da shape, sai jambaki pink da ta sanya kad'an a lips d'inta. D'aura d'ankwalin ta tayi style mai kyau tayi mishi then sai perfumes da tayi using dasu different color's wanda daga kan body sprays, humurah and perfumes na kaya, kallon kanta tayi jikin mirror ta tabbatar da tayi kyau yanda take so, sannan ta k'arasa kan bed tana gyarawa bayan ta gyara shi yanda take so sai ta share d'akin fes duk da kuwa dauriya take don duk jikinta babu dad'i amman bazata iya kallon d'akin a hargitse ba, tana gama wa ta sanya turaren wuta a burner sannan ta fesa air freshener tuni d'akin ya d'auke k'amshi, kan sofa ta kwanta tana mayar da numfashi tare da bin d'akin da kallo yayi mata kyau. Sabeer ne ya shigo bedroom d'in kallon d'akin yayi sosai yaji dad'i cikin zuciyar shi da ta gyarashi wani son ta ya sake shiga cikin heart nashi, k'arasawa yayi inda take kwance saman sofa har ta fara lumshe ido zata yi bacci ta ganshi ya kafeta da eyes. Cike da kunyar shi ta sauko daga kan sofa tsugunnawa tayi cikin sanyin murya tace "Ina kwana? " Zama yayi fuskar shi k'unshe da murmishi ya janyo ta jikin shi kan k'afafun shi yayi mata masauki kan yace "Lafiya k'alau Baby nah, ya kika tashi? " "Alhamdullilah " "Masha Allah naji dad'in ganin ki a haka Baby " Ya k'arasa maganar yana yi mata peck a cheek nata. "Kinyi kyau sosai Baby" Tana wasa da warwaron hannun ta tace "Nagode " Sakin layi ya farayi yana mata wasu abubuwa ita gaba d'aya a tsorace take da abin shi ya sanya jikin ta ya fara rawa, cikin 'yar rawar murya tace "Me zan dafa maka kayi breakfast " D'an murmishin yak'e yayi abin da ya kamata ace Mumyn shi zata yi ta aiko musu ko na kwanaki 3 ne, amman hakan yasan bazai yiwu ba. "Baby zo mu je kitchen d'in mu ga abin da za'a dafa but ni fah ko kunna gas ban iya ba sauran kiyi min dariya " Aikuwa ya bata dariyar musamman yanda ya wani d'an had'e face yana yamutsa fuska, don haka ta sanya dariyar ta amman ta sigar jan hankali a nutse tayi ta. "Auuu kika yi min dariya Baby nima sai na rama " Yayi maganar yana wani shagwa6e face har da bubbuga k'afa a k'asa ta shagwa6a, tunawa tayi da vidoen da Jiddah ta ta6a turo mata ya sanyata sake tuntsirewa da dariyar, kallon ta yake cikin sha'awa sosai dariyar tayi mata kyau d'an matse ta yayi ajikin shi har sai da tace "Wash!". Tana yamutsa fuska ta fad'i hakan. "Raguwa kawai don na d'an rik'e ki har da wani wash!, nima yanzu zan rama dariyar da kika yi min don haka ki shirya" Yana gama maganar ya sanya hannun shi zai zuge zipe, nan Suhaima ido ya raina fata ta fara rarraba ido na tsoro, dariya ya sanya kan ya gyara mata rigar yace "Kin cika tsoro Babe tashi mu tafi " Yana rik'e da hannun ta suka fito parlour direct kitchen suka nufa, sosai tsarin kitchen d'in da yanda aka shirya shi yayi matuk'ar birgeta sosai. Jingina bayan shi yayi jikin bango yana rik'e da hands nata yace "Baby gashi nan na kawo ki kitchen me zaki dafa mana naci girkin 'yar amarya ta " Murmishi kawai tayi kafin tace "Me zan had'a maka? " "Komai ma Baby zanci tunda ke zaki dafa min" Tana kok'arin kunna gas ne suka ji an danna door bell, kallon ta yayi sannan ya yamutsa fuska yana cewa "Yanzu haka Jiddah ce zata zo ta dame mu muna cikin hutawar mu ko lokacin da tayi nata auren wane ya tak'ura mata da zata dame mu" Dariya ta kusan kubcewa Suhaima amman sai ta danne don taga fuskarshi d'auke da damuwa, amman gaskiya har cikin zuciyar ta taji dad'i zuwan Jiddah har idan itace d'in. "Har kasan Jiddah ce ta zo? " "Of course don nasan itace zata yi zuwan wannan wurin " Tunawa da Suhaima tayi ko lokacin da zasu fito a d'aki da 11 na safe yayi shine zuwan wuri, Sabeer yasan ba mai zuwa cikin family d'in shi sai Jiddah shi yasa ya kawo ta cikin ranshi itace. Fita yayi tare da bud'e door d'in aikuwa tunanin shi ya zama gaskiya Jiddah ce da sauran friends na Suhaima wad'anda anjima kad'an zasu koma gidan su, shine suka zo yiwa Suhaima sallama. Wata harara da Sabeer ya watsawa Jiddah sai da dariya taso kubce mata amman ta danne ta tare da turo baki tace "Wai... wai kai Yah Sabeer indai muka had'u sai kayi ta harara ta ni me nayi maka? " Share Jiddah yayi yana amsa gaisuwar friends d'in Suhaima da suke mishi yana gama amsa wa ya basu hanya zasu wuce, aikuwa ya sanya hannun shi ya rankwashi kan Jiddah har sai da ta saki k'ara ta rik'e kanta nata wanda sauran kad'an ta zubar da basket d'in hannun ta. Jin k'arar Jiddah ya sanya Suhaima fitowa daga kitchen duk saurin da taso yi amman ta kasa sai a hankali ta taho, Jiddah na hango ta da sauri ta k'arasa wurinta had'e da rungume ta. "Lafiya naji kina k'ara? " Tana turo baki tare da kau da kanta daga kallon Sabeer tace "Ba mijin ki bane ya rankwashe ni akaina ba, duk abin da nayi mishi bai gani ba" Had'a ido tayi da Sabeer taga yana shafa bayan kanshi, d'an murmishi tayi tare da girgiza kai kawai wannan abu tsakanin su ne ita me zata iya yi akai, hannun Jiddah Sabeer ya kamo yana cewa "Sorry sweet sister ke kika ban haushi ina cikin hutawa zaki zo ki katse min hutu, yanzu me kika kawo mana? " Duk a hankali yake mata maganar, yayin da Suhaima ta k'arasar da friends nata cikin parlour suka zauna. "Yaya breakfast na had'awa Besty na da kai, ko an kawo muku daga gida? " Girgiza kanshi yayi cikin takaici ya furzar da numfashi, hannun shi ta kamo cikin jin tausayin shi tace "Yaya kayi hak'uri komai zai wuce insha Allah " "Nagode 'yar uwata " Dinning table suka k'arasa zama yayi sannan Jiddah ta fara jera kayan breakfast d'in kan table sai da ta gama sannan ta shiga kitchen ta d'auko su plate, cups, spoons and sauran abubuwan buk'ata na kayan tea, sai da tayi serving Sabeer tea ne sai pepper chicken and chip's da egg's, sannan ta had'awa Suhaima ta kallo inda take zaune acikin parlour ta d'an d'aga murya tace "Babyn Yah Sabeer kizo kiyi breakfast " Murmishi Suhaima tayi kan ta tashi ta taho zama tayi ta d'an fara shan tea d'in, da yake su Jiddah sunyi breakfast a gida sai kawai ta d'auko musu ruwa da drinks ta zauna a parlour cikin k'awayen Suhaima suna hira tare da kallo. Ganin yanda take cin abincin ne yasa shi cewa "Baby lafiya kuwa? " "Me yafaru? " Ta fad'a tana kai cup na tea bakin ta. "Bakya cin abincin sosai " Kamar zata yi kuka tace "Ni bana jin dad'in baki na ne " Tausayin ta ne ya kamashi cikin kulawa ya rik'o hannun ta sannan yace "Sannu Baby amman ki daure kici abincin zaki ji dad'in jikin ki" Fork d'in ya kar6a daga hannun ta bata yake abaki a hankali take kar6a har tace mishi ta koshi sannan ya rabu da ita, tashi suka yi daga dinning table d'in parlour ta dawo yayin da shi kuma ya shige upstairs. Cikin 30 minute's ya fito ya canja kaya zuwa wani black boyel takalmi ma black da watch d'in shi but bai sanya hula ba sai ya gyara gashin kanshi, sosai yayi kyau Suhaima ma binshi da kallo tayi kan ta d'auke kanta kuma tana yiwa Allah godiya da ya bata Sabeer a matsayin miji. Saukar numfashin shi taji kan face nata, d'ago eyes nata tayi suka had'a ido kafin ta janye nata, d'an murmishi yayi yana daf da k'arasa cire wannan kunyar. "Baby zan tafi gida wajen su Daddy mu gaisa " "Okay, ka gaida su Allah ya dawo da kai lafiya " Sai da ya lumshe idon shi yaji dad'in abin da ta fad'a, kafin yace "Amin Baby nah " Yayi kissing nata a kumatu sannan ya fita. Hira suka yi sosai har zuwa lokacin da 'yan uwa Suhaima suka zo, gara suka kawo kamar yanda al'adance ake yiwa amarya sai su dublan, alkaki da su cincin, wani abin dad'in a wajen Suhaima har da Baba Lantana da Aunty Aliyah aka zo. Don Aunty Aliyah kasa jurewa tayi sai da ta biyo su aikuwa Suhaima rungume ta tayi k'am tana kuka, dakyar dai aka rarrashe ta tayi shiru sannan Suhaima ta canja kayanta zuwa wani lace milk and touch pink ajikin shi sai mayafi pink da shoes nan Jiddah ta fesa mata perfumes masu sauk'in kamshi suka tafi gidan su Sabeer don damk'a amanar Suhaima a hannun su. Sakin baki da hanci suka yi suna kallon had'uwar gidan, inda Allah ya taimake su basu da yawa suka zo su 5 ne sai Suhaima, Jiddah da friends nata. Jiddah ce tayi musu jagora har zuwa part d'in Alhj Dr Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa suka tarar a parlour tana zaune ta wani hamshak'e kan kujera eyes nata d'auke da medical glass tana kallon tashar Arewa 24 suna yin film na india mai translation in hausa. Sai Dr Faridah da take gefen ta suna d'an ta6a hira jifa jifa a tsakanin su, a wani kyamace suka amsa sallamar tasu ko wajen zama ba'a basu, sai da Jiddah tayi magana cikin bak'inciki tace "Babaa Lantana Aunty Aliyah ku zauna " Nan suka zauna jikin su a sanyaye da irin tar6ar da aka yi musu, Jiddah fita tayi ta kirawo Umman ta da sauran matan gidan duk suka taho part d'in Hajjah Hauwaa sannan taje kitchen d'in Hajjah Hauwaa ta d'ebo musu soft drinks and snack's sai ruwa ta ajiye musu. Suna yamutsa fuska suka amsa gaisuwar su, sannan Babaa Lantana ta damk'a musu amanar Suhaima babu dai wanda yace komai saboda takaici Jiddah barin parlourn tayi, tana kyamar halin family d'in su. Ko drink's d'in da Jiddah ta kawo basu sha ba suka taso suka fito gaba d'aya gwiwoyi a sanyaye, sosai Jiddah ta basu hak'uri a hanyar dawowar su ta gidan Suhaima. Abinci ma sai takeaway Sabeer ya sanya akayi musu saboda lokaci ya k'ure zasu tafi, bayan sun gama ci suka yiwa Suhaima nasiha sosai Aunty Aliyah ta d'ora da bata shawarwari masu kyau. Suna yin sallahr la'asar suka ci abinci suka tafi, driver Sabeer ya aiko ya mayar dasu gida tare da kyautar kud'i da ya basu mai yawa, Suhaima tasha kukan rabuwa dasu sosai, har jikin ta ya fara d'umi alamar zazza6i ne zai rufe ta kwanciya tayi tana kuka musamman idan ta tuna family d'in Sabeer basa sonta sai Jiddah da Daddyn Sabeer kawai, rarrashin ta Jiddah tayi sannan ta gyara mata gidan tsaf, sai da tayi wanka Jiddah tayi mata kwalliya ta shirya cikin wata gown tayi kamata sosai duk wani sura na jikin ta ya fito da yake irin roba d'in nan ce, ita ma Jiddah shawarwari ta bata sosai sannan tayi mata sallama ta tafi. Kwanciya tayi kan kujera ga jikinta babu dad'i, ga abin da 'yan uwan Sabeer suka yi musu ga kewar gida da kad'aicin ita kad'ai agida sai kawai ta fashe da kuka aikuwa nan da nan zazza6i da ciwon kai suka tarar mata lokaci d'aya........ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ *PAGE 82-83* Tana nan kwance ta kudundune cikin bargo tana rawar zazza6i ga hawayen da suke zuba a idanunta, kanta ciwo yake mata kamar ya cire duk eye's nata sunyi ja sun kumbura, tana cikin wannan halin Sabeer ya shigo bedroom d'in nata. "Baby baccin yamma kike me yasa Jiddah bata zauna da ke ba har na dawo? " Yana maganar yana hawa kan bed d'in, yaye blanket d'in yayi tare da sanya hannun shi zai d'ago ta jikin shi, sai yaji zafi sosai jikinta da ya ta6a jikinta, a rikice da kallo ta sai yaga hawayen da take nan da nan hankalin shi yayi mugun tashi har ya rasa me zaice yana tsoron kada ya kasance ya illata 'yar mutane, jiki na rawa ya d'auke ta ya shimfid'e ta saman k'afafun shi cikin tashin hankali yace "Baby nah me ya same ki, ina ne yake miki ciwo, me yasa baki kirawo ni kin fad'a min na kirawo doctor ya duba ki ba, tun yaushe wannan zazza6in ya rufe ki haka? " Muryar shi da d'an rawa yake maganar, kasa magana Suhaima tayi sai hawayen da suke zuba kawai ita abin da yake sake firgitata da tsorata ta kada 'yan uwan Sabeer su rabasu, tabbas ta kamu da son Sabeer wanda tasan idan suka rabu su ba k'aramin tashin hankali zata shiga ba. "Kiyi min magana Baby please, ki daina kuka kin ga yanda idanun ki suka koma kuwa? " Ganin yanda ya d'aga hankalin shi ya sanya bud'e idanun ta dakyar ta kalle shi kafin tace "Zazza6i da ciwon kai ne kawai suke damu na" "Sai me kuma? " "Shikenan " D'an kallon ta yayi sannan yace "Baby fad'a min gaskiya abin da su Mumy suka yi muku shi ya sanya ki kuka ko? " Da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi cikin mamakin a inda yasan me akayi musu, d'an girgiza kai na takaici yayi then yace "Nasan komai Baby, idan don wannan kike damuwa don Allah ki daina sanya shi cikin zuciyar ki kada ya janyo miki wani ciwon please, sannan zan d'auki mataki " "Amman dai bai ka......." Hannun shi ya sanya saman bakin ta ya rufe tare da cewa "Baby kiyi shiru kawai, bari na kirawo doctor ya duba min ke " Langa6e kanta tayi cikin yanayin shagwa6a tace "Ni Allah bana son allura ne da shan magani, zan warke a hakan kawai " "Ke kinma isa amarya fah kike taya ciwo yazo bazan d'auki matakin gaggawa akanshi ba sai yayi k'arfi ya hanani cin amarci nah tabbb yarinya naki wasa ne " Sanya face nata tayi cikin kirjin shi tana d'an murmishi don ya bata kunya, tana ji ya kirawo Doctor Aishat wadda take babbar likitace ta gynecologist ce tana aiki a hospital d'in Dr Faridah wato Mumy. Tsayin 5 minutes suka d'auka suna waya kafin ya kashe ya kalli Suhaima wadda ta lafe ajikin shi dauriya kawai take amman kanta ciwo yake sosai, shafa kanta yayi da hannun shi yana cewa "Sannu Baby nah yanzu Doctor Aishat zata zo ta duba ki " "Amman bazata yi min allura ba koh? " "Eh zance kada tayi miki tunda bakya so" D'aga kanta tayi kawai. "Baby jikin ki yayi zafi sosai sannu dama zan iya dawo da ciwon jikina dana dawo dashi" Hannunta ta d'ora saman face d'in shi tana shafa kwantaccen gashin sajen shi zuwa gefen bakin shi, lumshe eyes nashi yayi yana jin wani abu na ratsa shi kai hannun ta yayi bakin shi yayi kissing d'in tsakiyar tafin hannun ta, wanda daga shi har ita da bata jin dad'i sai suka ji wani yanayi atattare dasu. "Kada ka damu zan samu sauk'i insha Allah" "Amin Baby nah " Sunan zaune suka ji door bell kafin ya tashi kuma ya bud'e yaji phone nashi na ringing, bayan ya d'auka ne Doctor Aishat take mishi bayanin gata a k'ofar parlour a tsaye. "Baby bari naje na bud'e mata door ta k'araso " Yana gama fad'in hakan ya fita daga bedroom d'in, yana shigo da ita ya koma bedroom ya d'auko Suhaima cak kamar wata Baby ya kawo ta parlour duk kunya ta kama Suhaima sosai sai wani sunkuyar da kai take shi kuwa gogan ko ajikin shi sai ma kok'arin had'a ta da jikin shi yake, yayi da Suhaima sai nok'ewa take. "Yalla6ai me yake damun amaryar taka? " Cewar Dr Aishat kenan ganin idan ta cigaba da shiru Sabeer zai bata kunya yanzu. "Uhm Dr Aishat zazza6i ne ke damunta da ciwon kai sai kuma..... Uhmmm kin dai gane bansani ba ko taji ciwo? " Ya k'arasa fad'a yana shafa bayan kanshi, kamar k'asa ta tsage ta shige ciki haka Suhaima taji a lokacin, yayin da Dr Aishat ta maze don tasan tatsuniyar gizo bazata wuce k'ok'i ba. "Yalla6ai na fahimta inason zan duba don nagane ko taji ciwo " "Okay ba damuwa " Kafin Suhaima ta ankara ya d'auke ta sai bedroom ya kwantar da ita saman bed yayi da Dr Aishat take binsu a baya, ganin ya tsaya bashi da alamar fita ya sanya tace "Yalla6ai ka taimaka ka d'an bamu waje kad'an" Ba dan yaso ba ya fita daga bedroom d'in, bayan ya fita ne Doctor Aishat ta duba Suhaima nan ta gane bata ji wani ciwo sosai ba idan tana amfani da ruwan d'umi ma zuwa nan da kwanaki biyu zata warke, nan ta fara kok'arin yi mata allura aikuwa Suhaima ta sanya kuka tare da rirrik'e hannun Doctor d'in, sai Sabeer ta kirawo dakyar ta yarda akayi mata da rarrashi da lalla6a tare da sanya ta ajikin shi aka samu akayi guda biyu sannan ta bata magungunan da zata sha, kuma ta basu shawarwari na yanda Suhaima zata kula da kanta har ta samu sauk'i. Tukunna tayi musu sallama ta tafi bayan Sabeer ya taka mata zuwa bakin k'ofar fita parlour, kitchen ya wuce ya bud'e frige fresh milk ya d'auko tare da cup ya dawo d'akin lalla6a ta yayi har tasha maganin da fresh milk d'in babu dad'e wa bacci ya d'auke ta da yake har da maganin sanya bacci aciki. Yana zaune kusa da kanta ya rik'e hannun ta yana aikin kallon ta kawai jinshi yake kamar a mafarki yau wai shine da Suhaima a matsayin ma'aurata, sannan abin da su Mumy suka yi yaji haushi sosai Jiddah ce take fad'a mishi a waya bayan tabar gidan Suhaima, da yaso yin magana dasu Mumy but Daddy ya rarrashe shi kan yayi hak'uri komai mai wuce wa ne wataran sai labari ya zuba musu ido kawai, shi ya cigaba da kula da matar shi don bata da kowa a kusa sai shi. Kiran sallahr mangarib ne ya tashe shi daga zaunen, addu'a yayiwa Suhaima sannan ya tashi ya fita side nashi ya shiga yayi alwala ya wuce masallaci sai after ishsha ya dawo gidan, yana shigowa farfajiyar gidan ya had'u da driven Jiddah bayan ya gaida Sabeer ne ya bashi sak'on Jiddah na basket mai d'auke da foodflaks 3 sai Jug kar6a Sabeer yayi sannan ya d'auko kud'i ya bawa driven, sosai driven yayi godiya kafin ya tafi, shiga cikin gidan yayi hannun shi rik'e da basket d'in cikin zuciyar shi yana jinjinawa Jiddah da matuk'ar kok'arin da take akan su, yaji dad'in kawo abincin nan daman yanzu yake shirin fita yi musu take away sai gashi na kuma ta hutar dashi, addu'a yayi mata cikin zuciyar shi na Allah ya sauke ta lafiya. Ajiye basket d'in yayi saman dinning table sannan ya wuce bedroom ya tarar har Suhaima ta tashi tana bathroom don yaji k'arar zubar ruwa, don haka sai yawuce nashi side d'in yayi wanka ya shirya cikin wani catton na kayam bacca and sky blue ya fesa different perfumes masu dad'in kamshi, tukunna ya koma bedroom d'in Suhaima ya tarar har ta fito daga bathroom sallah ma take. Shiga yayi cikin d'akin ya zauna kan sofa ya d'an lumshe idanun shi, bacci ne sosai cikin eyes nashi ga gajiya, tana idar da sallahr mangarib and ishsha ne bayan tayi shafa'i da wutiri tare da addu'o'in ta ne sai ta tashi ta cire hijab d'in jikinta. Tana sanye da wata sleeping dress white tsayin ta iyakar shi tsakiyar cinyar ta sai zanin da ta d'aura tayi sallah, batasan Sabeer ya shigo ba sai kawai ta warware zanin ta ajiye shi sannan ta k'arasa wajen dressing mirror ta taje gashinta tare da sanya perfumes ajikinta. Duk wannan abin da take Sabeer yana kallon ta yayi luf ne kawai ajikin sofa, tuni ya fara jin wani canjin yanayi a jikinshi don kuwa Babyn shi tayi mishi kyau amman sai dai ya had'iye abin da yake ji dole yabar ta taji sauk'i. Tashi yayi tsaye yana wani binta da kallon k'asan ido ya k'arasa inda take tana d'aure kanta da ribbon hannun shi ya sanya ya cikin gashin kan nata yana wani yamutsa shi, a d'an tsorace ta jiyo ganin Sabeer ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya........ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ *PAGE 83-84* Ganin Sabeer ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya tare da juya kanta, rungume ta yayi ta baya ya sanya kanshi cikin gashin kanta da wuyan ta yana shak'ar kamshin daddad'an perfumes d'in ta saukar d'umin numfashinshi a wuyanta shi ya saukar mata da wani irin kasala, hannun shi ya sanya yana shafa dogon hannun ta daga kafad'a zuwa 'yan yatsun hannun, kasa jure abin da yake mata tayi sai kawai ta juyo tare da fad'awa kan kirjin shi tsam ya rungume ta ajikin shi yana saukar da ajiyar zuciya, suna nan tsaye wajen 5 minutes ahaka kafin kuma ya bud'e baki yace "Baby muje kici abinci sai kisha magani " Hannun ta ya rik'o zuwa parlour har kan dinning table ya zaunar da ita kan kujera, sannan shima ya zauna yana zuba musu abinci, kasa barinshi tayi da ya zuba musu ta kar6i serving spoon tana zuba musu. Abaki suka dunga bawa junan su har suka k'oshe sannan ta tattara kayan ta kai kitchen, ta dawo ta gyara dinning table d'in, zama suka yi a parlour suna kallo tare da ta6a 'yar soyayya. Sai da Sabeer ya bawa Suhaima hutun kwanaki biyu sannan aka d'ora daga inda aka tsaya, soyayya, kulawa da duk wata kauna suke nuna wa junan su, cikin farinciki da kwanciyar hankali suke abin su, babu mai zuwa gidan sai Jiddah ce ke lek'o su, sai dai waya da take yi dasu Yaya Aliyu kullum Sabeer kuwa yana kok'arin zuwa gida gaida iyayen shi, amarcin su suke sha yanda suke so babu mai tak'ura musu ko house girl basu da ita Suhaima ta hana Jiddah ta kawo mata tace ba yanzu ba. Akullum cikin nuna wa junan su so suke biyayya sosai da kyautatawa Suhaima ke yiwa Sabeer yayin da shima yana kok'arin wajen sanya ta farinciki koyaushe, idan ka shiga gidan su kuwa sai ya birge ka saboda tsananin yanda suke kula da junan su. Motarta tuni Jiddah ta aiko mata da ita gashi Sabeer ma ya bata kyauta ta mota mai matuk'ar kyau da tsada da sabuwar tsadaddiyar phone, sosai Suhaima tayi mishi godiya ta nuna mishi dad'in da taji addu'a sosai yasha ta daga bakin ta, gashi yana koya mata driving duk weekend da yamma zasu fita yana koya mata, yanzu matsalar ta d'aya shine ta cigaba da karatu amman tun da tayi mishi maganar sau d'aya ya nuna ba yanzu ta hak'ura duk da tsananin son da take yiwa karatun ta cigaba da farantawa mijinta rai ta barwa Allah za6in alkhairi akan makaranta. _*After 3 Month's*_ Zuwa wannan lokacin idan kaga Sabeer da Suhaima sai kayi mamaki sun k'ara wani kyau musamman Suhaima ta k'ara cika sosai tayi 'yar kiba kad'an, bata fita ko'ina sai zaman gida kullum sau d'aya ta sake jarraba zuwa gidan su Sabeer amman har ta karaci zaman ta babu wanda yace mata ci kanki har gwara lokacin da Daddy ya dawo ya zauna sun d'an ta6a hira dashi amman ko a fuska bata nunawa Sabeer jin haushin abin da suka yi mata, Sabeer a lokacin tuni ya fara aiki da company d'in shi da Daddy ya bashi kyauta. Zaune suke a garden da wani yammaci lokacin damina ne garin yayi luf luf dashi sai iska mai dad'i da take kad'awa mai ratsa jiki da sanya mutum nishad'i. Suhaima tana sanye da wani wandon jeans iyakar shi rabin cinyar ta blue sai half vest white, yayin da Sabeer kuma yake sanye cikin 3quater kawai suna zaune kan wani babban carpet ga kayan fruits da juice da ruwa a gefen su. Sabeer ne yake danna laptop d'in shi da hannu d'aya, d'ayan hannun kuma yana rungume da Suhaima ta gefen shi, cikin shagwa6a ta bud'e baki tace "Ni Allah ka bar aikin nan kazo ka goya ni idan ba haka ba zanyi maka kuka " D'ago kanshi yayi ya kalle ta sai wani turo baki take murmishi yayi tare da jan hancin ta yace "Oh Baby rigima naji zan goya ki amman kiyi min afuwa na k'arasa aikin nan please " D'aga kanta tayi, da sauri ya rik'o d'ayan hannunta yace "Amman ban da kuka please" D'an murmishi tayi sannan tace "Toh bazan yi ba " "Yawwa 'yammata na " Cikin 10 minute's ya k'arasa aikin tare da rufe laptop d'in ya kallo ta cikin murmishi sannan ya sunkuya yace "Baby taho na gama " Cikin sauri ta taso tare da d'anewa bayan shi, yatsina fuska yayi sannan yace "Wash! Bayana Baby kin k'ara nauyi zaki karya min baya " Turo baki tayi cikin shagwa6a tace "Ni.... Ni Allah ban wani k'ara nauyi ba kai ne ka dad'a zama babba " "A'a Baby fad'i gaskiya " "Toh bakai ne kake d'ura min abinci ba da yawa " Dariya yayi yana cewa "a haba Baby fad'i gaskiya dai " Hannun ta ta sanya tare da d'an mintsinin shi a damtsen hannun shi, wata 'yar k'ara ya saki "Laaa Baby kika mintsine ne, aikuwa sai na rama " Kafin ta ankara ya kwantar da ita akan carpet ya bi jikinta ya kwanta gaba d'aya sai ya saukar mata da nauyin shi , dakyar take jan numfashi tace "Wayyo don Allah ka d'aga ni dear " Yana dariya yace "Nak'i wayon yarinya sai na rama ko kuma yau da dare na hanaki bacci kin yarda " Da sauri ta d'aga kanta dariya ya sake yi sannan ya d'aga ta, hannun ta ta zube su kan carpet tana sauke numfashi, janyo ta yayi kan k'afafun shi tare da had'e bakin su waje d'aya wani salo na daban yake nuna mata itama babu 6ata lokaci take mayar mishi da martani. Sunyi nisa cikin wannan yanayin ne yaji wayar shi na k'ara, ba don yaso ba ya d'auki wayar yana jan tsaki don an katse mishi jin dad'in shi. "Hello Yaya na haihu " "What! Da gaske kike? " Cewar Sabeer yana tambayar Jiddah, cikin dariya tace "Allah Yaya da gaske nake an samu Baby girl" "Masha Allah na tayaki murna 'yar kanwata Allah ya raya " "Yaya ka fad'awa Suhaima ita na fara kira wayan ba'a d'auka ba" "Okay babu damuwa " "Toh yaushe zaka kawo min Besty tun da kuka yi aure bata zo ba fah?" "Jiddah surutu huh, yanzu kina buk'atar hutu ne kije ki huta zan kawo ta ne" Cikin shagwa6a tace "Yaya ka kawo min ita gobe don Allah idan zaka fita office " "Okay naji " Nan ya kashe wayar tashi, kallon Suhaima yayi wadda take kallon shi tun fara wayar shi ya ce "Albishirin ki Baby " Matsowa kusa dashi tayi sosai tace "Goro fari k'al dear " "Mene tukuici na idan na fad'a " D'an dariya tayi kad'an sannan tace "Ka fad'i duk abin da kake so zanyi maka " "Jiddah ta haihu ansamu Baby girl " Wani ihun murna ta saki tare da rungume shi tana dariyar farinciki kallonta yake duk tabi ta birkitashi ta kashe mishi jiki. "Dear ka tashi mu tafi ganin Baby please " "No Baby yanzu mangarib ta kusa ki bari sai gobe don gaskiya yanzu kin gama birkita ni tashi mu tafi ciki before mangarib tayi " Sanin halin shi ya sanya ta biye mishi suka tafi, sai da suka sha soyayyar su tukunna sukayi wanka tare da yin alwala ya tafi masjid ita kuma ta shige bedroom nata don yin sallah, bayan ta idar da sallahr ne ta samu damar kiran Jiddah don yi mata barka kafin tazo sunsha hirarar su sosai kafin suyi sallama da juna. _*Washe gari*_ Tun asuba da tayi sallah take faman gyaran aikin gidan bayan ta gama ta had'a breakfast sannan ta jera saman dining table, bedroom ta wuce ta cire kayanta ta d'aura towel ta shige bathroom don yin wanka, acan Sabeer ya same ta suka sha soyayya then sukayi wanka suka fito shirya junan su suka yi, yana sanye cikin wata blue na suits sai necktie black da black shoes yayi matuk'ar yin kyau. Yayin da Suhaima kuma ta shirya cikin wani swiss lace brown da touch na red d'in flower's tayi kyau sosai, fita suka yi zuwa dinning table agurguje suka yi breakfast, sannan ta wuce d'aki ta d'auko mayafi babba red colour ta yafa sai flat shoes da handbag redred in colour perfumes masu sanyin k'amshi ta sanya sannan ta fito. "Wow! Baby na kinyi kyau sosai " Cewar Sabeer yana rungume ta ajikin shi. "Nagode Dear kai ma kayi min kyau " Kissing ya bata goshi sannan ya rik'o hannun ta suka fito zuwa compound. Suna zaune bayan mota driver nayin tuk'i suka fita daga gidan hanyar gidan Jiddah suka nufa. "Baby nima yaushe zaki haifa mana Baby? " Ya fad'a yana shafa flat tummy d'in ta, kunya ce ta kama Suhaima dakyar ta iyacewa "Duk lokacin da Allah ya bani sai na haifa mana " "Haba Baby ina kula fah dake tun daga kika zo gidan nan baki yi period ba yau 3 Month's har da 'yan kwanaki da auren mu, ai nasan da ajiyata anan shiru kawai nayi miki " D'an tunani ta fad'a yi tabbas rabon ta da yin period tun lokacin sauran 2 week's bikin su amman koda tana gida sai tayi 2 months bata ga period yazo mata shiyasa idan ta tashi yi take fama da menstruation pain mai tsananin zafi. "Kinyi shiru Baby ko ba haka bane? " Tana shirin yin magana suka shiga gidan Jiddah don haka sai ta mayar da bakin ta tayi shiru. Tare suka fito daga motar hannun su sark'e cikin na junan su, suna kok'arin shiga parlour ne aka bud'e kofa tare da fitowa, sai da gaban Suhaima yayi mugun fad'uwa ganin Mumyn Sabeer ce wadda ta jima da zuwa duba Jiddah da Babyn ta, idanun ta akan hannayen Sabeer da Suhaima fuskar ta sam babu alamar fara'a. Jikin Suhaima na rawa take kok'arin kwace hannun ta amman Sabeer ya rik'e k'am yak'i ya cikata don haka kawai ta tsugunna tana gaida Mumy, bata amsa ba sai kau da kai da tayi. Sakin hannun Suhaima yayi bugging d'in Mumy tare da bata peck a cheek nata, cikin sanyin jiki Suhaima ta mik'e daga tsugunnan da tayi. Kallon ta Mumy take yi sosai wanda ya sanya Suhaima k'ara rikicewa gabanta banda fad'uwa babu abin da yake, wani irin fad'uwa gaban Mumy yayi masifar yi a lokaci d'aya da ta hango wasu canji atattare da Suhaima wanda tasan tabbas sai mace mai ciki ne take canjawa irin haka abin ka da likita, wani mugun gumi taji ya karyo mata tun daga saman gashin kanta zuwa fuskarta da jikinta. Zame hannun ta tayi daga na Sabeer ta fara tafiya zuwa wajen motar ta hankalin ta a masifar tashe duk yanda zata yi sai tayi don ganin ba'a haifi wannan cikin ba, don bazata ta6a had'a zuri'a da 'yar kauye ba abin da bazai ta6a yiwuwa ba dole tasan yanda zatayi cikin ya fita idan yaso duk lokacin da ta samu ciki sai tana zubar dashi. Tasan halin Sabeer yanda yake masifar son yara dole ya rabu da ita daga lokacin da ya gane ita take zubar mishi da ciki duk da son da yake mata kuwa a wannan lokacin ne zata aura mishi yarinyar da take son ya aura wannan dabarar ta shine kawai zai kawo k'arshen zaman Sabeer da Suhaima, wani shegen murmishi Dr Faridah ta saki tare da shiga mota tabar gidan zuciyar ta fes take jin ta gani take kamar ma Sabeer ya rabu da matsiyaciyar yarinyar nan.......... _To fah reader's kunji tunanin Dr Faridah ko zata yi nasara akan Suhaima ta rabata da Sabeer, ina jiran comments naku yanzu labari zai fara, ƙų ¢ıɠąცą ɖą ცıŋą ɖơŋ ʝıŋ ყąŋɖą ʑąɬą ƙąʂąŋ¢ɛ_. Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ *PAGE 85-86* Da kallon mamaki Sabeer da Suhaima suka bita dashi kawai kafin kuma Sabeer ya rik'o hannunta yace "Sorry Baby nah akan abin da Mumy take miki bana jin dad'in haka ko kad'an " Cikin rarrashi ya k'arasa maganar gashi fuskar shi d'auke da damuwa, d'an murmishin yak'e Suhaima ta saki sannan tace "Kada ka damu don Allah komai mai wuce wa ne, mu tafi ka ga Baby kada ka makara a office ". "Thank U Baby nah da yanda kike da fahimta i luv U " Suhaima na shirin bashi amsa kenan Jiddah ta lek'o da kanta tana cewa "Don Allah Yah Sabeer mene haka tun d'azu kuna tsaye anan ka hanata shigowa " Hannun shi ya sanya tare da janyo kunnen ta d'aya yace "Jiddah kin raina ni da yawa zan miki duka na tsayar da ita d'in mata ta ce ai " D'an ihu ta saki na jin zafi kafin ta marairaice fuska tace "Sorry Yah Sabeer na tuba na daina " Yanda tayi d'in dole yasan ya shi murmishi ya cika mata kunnen, kamo hannun Suhaima tayi suka wuce cikin gidan. Masha Allah abin da Sabeer ya fad'a lokacin da ya kar6i Babyn fara ce tas har wani ja ja take yi kyakkyawa da ita ta d'ebo kamannin D'an fillo family, wani son yarinyar ne ya shiga zuciyar Sabeer har yana imagine gashi Suhaima ta haifa mishi Baby yana d'auke da shi. Kallon Suhaima yayi wadda take zaune kusa dashi tana lek'en Babyn don itama kanta tayi mata kyau ba kad'an ba. "Baby kema kina so koh, ki haifa mana mu ma please " D'an murmishi tayi kafin tace "Toh my dear kayi addu'a Allah ya bamu masu albarka " "Amin Baby " Jiddah ya mik'awa Babyn don ya makara ma sosai, tashi Suhaima tayi ta rakashi har bakin mota suka yi sallama ta dawo cikin gidan, bayan ta gama ganin Babyn ne sai ta gyarawa Jiddah bedroom nata sannan ta wuce kitchen don shirya abincin rana. Tana tsaka da girkin 'yan uwan Jiddah suka fara zuwa gidan kasa fita tayi su gaisa tayi don gabanta sai fad'uwa yake, dakyar ta k'arasa girkin ta zuba a foodflaks sai kawai taja kujera a kitchen ta zauna tare da had'a kai da gwiwa tana tunani. Awannan yanayin Jiddah tazo ta same ta tausayin Suhaima ne ya kamata, dafa kafad'ar ta tayi a tsorace Suhaima ta d'ago kanta ganin Jiddah ce ya sanyata sakin ajiyar zuciya. "Suhaima ki rage tsoron su fah wallahi, taya zaki zauna a kitchen bazaki fito ba saboda su? " "Uhmmm Jiddah wallahi bana son kallon wulak'anci da k'ask'ancin da suke min, ina jin tsoron fita mu gaisa dasu kada su gwasale ni kamar yanda suke yi min " "Kada ki damu Suhaima komai zai wuce amman baza ki tak'ura kanki ba saboda su don haka ki fito daga kitchen " Babu yanda zatayi haka ta fito hannunta rik'e dana Jiddah, wani kallo na wulak'anci suka bita dashi kamar yanda Suhaima ta tsani ayi mata, babu wanda ya amsa gaisuwar ta sai ta6e baki da suke Jiddah ma sai da ta samu alakoran harara a wajen su. Bedroom d'in ta Jiddah ta kaita ta zauna amman duk da haka a tak'ure take har so take lokacin tashin Sabeer daga office yayi yazo su wuce gida, duk da ya kirawo ta awaya amman ba'a kwanciyar hankali ta amsa ba mishi ba, har tunanin ranar suna take batasan irin wulak'ancin da zasu yi mata cikin mutane ba. Atak'ure take har zuwa bayan mangarib sannan Sabeer yazo suka tafi gida, kallo d'aya yayi mata ya fuskanci tana cikin damuwa girgiza kanshi yayi yana yana sauke numfashi dole ya takawa 'yan uwan shi birki akan abin da suke yiwa Babyn shi bazai jure ba ko kad'an ganin ta cikin damuwa. Duk damuwar da take tattare da ita sai da Sabeer ya cire mata ita ya mayar da gurbin farinciki a wannan daren sosai Suhaima ta k'ara jin wani son mijinta cikin zuciyar ta yanda yake faranta mata rai itama tana addu'ar Allah ya sanya ta haihu don cika mishi burin shi. Ranar suna tun safe Sabeer ya kaita don yak'i barin ta ta kwana ko komawa bata sake yi ba sabida yana gudun kada a sake 6ata mata rai duk da kuwa nacin da tayi mishi, sosai Sabeer da Suhaima suka kashe kud'i wajen had'a wa Babyn kaya da kuma ita kanta Jiddah don duk abin da suka yi mata baza su biyata abin da tayi musu ba ita kadai ce mai kaunar ganin su tare sai Daddy adukkan familyn Sabeer. Sosai Jiddah taji dad'i abubuwan da suka kai mata tayi musu godiya tare da addu'ar Allah ya basu suma yaran masu albarka, Sabeer yaji dad'in addu'ar da tayi musu sosai duk cikin 'yan uwanshi yafison Jiddah fiye da kowa don itace mai kaunar abin da yake so. Baby taci sunan Babar Khaleel wato Khadijah suna ce mata Islam, ansha suna sosai don har walima da yamma sai da aka shirya an kashe kud'i sosai, amman duk wannan abun Suhaima bata shigaba tana zaune waje d'aya kanta ma yake masifar ciwo sosai, gashi tasha kukan habaici da wulak'ancin da su kayi mata. Sai bayan mangarib 'yan uwa suka fara tafiya, zaune Suhaima take kan abin sallah idar da sallahr ishsha da tayi kenan tana addu'a cikin zuciyar ta tana mai tunanin inda Sabeer ya tsaya baizo sun tafi ba don kanta sosa yake ciwo kamar ya cire ga idanun ta da suka kumbura saboda kuka, ta kirawo phones nashi basa shiga dukka, gashi hadari ya had'u sosai sai walk'iya ake. "Munafuka har yanzu zaman me kike da baki tafi ba, mun gaji da ganin fah ya kamata kisan nayi " Cewar Aunty Fadilah 'yar autar su Daddy kenan tana wani hararar Suhaima, sunkuyar da kanta Suhaima kawai tayi idanun ta suna zubar da hawaye. "Wallahi na tsani yarinyar nan kyau kamar aljanna duk tabi ta asirce mana Sabeer sai yanda tayi dashi daman 'yan kauyen nan da shegen yin asiri" Dariya aka kwashe da ita irin mai k'ulawar nan suna cewa "Sai Auntyn mu fad'a mata dai munsan asiri tayi ta mallake mana d'an uwa don Yah Sabeer bazai ta6a son wannan talakar ba yana cikin hayyacin shi" Cewar Zahra kenan, bak'inciki da takaici ya ishe Jiddah cikin d'aga murya tace "Ke Zahra wallahi ki kiyayi kanki Allah zan fad'awa Yah Sabeer yaci uban ki matar shi kike fad'awa haka " Make mata bakinta Aunty Fadilah tayi tana cewa "Ta fad'a d'in ya kashe ta idan ya isa " Kuka Jiddah ta sanya saboda make mata bakin da tayi don da ba k'aramin zafi taji ba, yayi da Zahra take danna mata harara. "Ni na rasa abin da zamu yiwa wannan mayyar yarinyar ta rabu da Sabeer ba irin wulak'anci da bamu yi mata ba amman ta lik'e mishi " Dariya aka sake kwashewa da ita, sannan Khairat tace "Ina fah zata rabu dashi Aunty taga kyakkyawan saurayi sabon jini ga kud'i da ilimi inace ko aji ma ta ta6a shiga wannan shegiyar Jiddah ce ta wayar da ita " Wani irin kuka mai tattare da bak'inciki Suhaima ta saki saboda ta kasa rik'e kukan nata, aikuwa ganin haka suka kwashe da dariya tare da tafawa, sannan Aunty Fadilah ta bud'e bottle d'in faro da yake hannun ta sai kawai Suhaima jin saukar ruwa mai sanyi da taji ajikinta har sai da ta saki ajiyar zuciya mai karfin gaske. "Shegiya mara zuciya idan kin cika ke mai zuciya ce kare bai d'auke ba ki rabu da Sabeer daga yau " "Aunty mu taya ki " Cewar Zahra da Khairat sarakan tsiwa. "Ku taho mana 'yan 'ya'yana masu kishin 'yan uwan su " "Don Allah Aunty kuyi hak'uri kada ku min haka " Cewar Jiddah tana kuka da karfi tana kare Suhaima, ture ta Aunty Fadilah tayi nan Zahra da Khairat suka dunga bud'e bottles na faro suna shek'a mata a jikinta suna zaginta da yi mata rashin mutunci duk gaba d'aya sun jik'e jikinta jagab da ruwa gashi don mugunta da ruwan sanyi suke amfani. Yusrah yayar Jiddah da batason hayaniya tabar dakin bata jin dad'in abin da suke mata ba amman da yake miskilace sai kawai ta bar wajen. Jiddah tana cikin kuka ne d'ago kan da zata yi sukayi 4 eye's da Sabeer tsaye ya hard'e hannun shi a kirjin shi eyes nashi sunyi ja tare da fuskar shi, sai da gaban Jiddah yayi mugun fad'uwa ganin yanda d'an uwan nata ya rikid'a kamar ba Sabeer ba, bata ta6a ganin shi cikin makamancin irin wannan yanayin ba. Zahra ce ta fara arba da Sabeer ta ankara dashi tuni tayi cilli da bottle d'in hannun ta jikinta ya fara rawa na tsoro, haka ma Khairat itama ta cillar da robar tana rarraba ido Aunty Fadilah kuwa sai da gabanta ya fad'i da suka had'a ido da Sabeer don bata ta6a ganin shi a haka ba batasan lokacin da ta saki nata robar ba. Cikin wani irin taku na fusata ya k'arasa shiga d'akin bai kalli inda suke ba ya k'arasa inda Suhaima ke zaune jikin ta jagab da ruwa har tsiyaya yake d'ago ta yayi tare da kallon Jiddah yace "Kai ta wani bedroom d'in ki bata kaya ta canja " Muryar shi dakyar take fitowa saboda tsananin 6acin rai jikin shi har wani rawa yake, da sauri Jiddah taja hannun Suhaima wadda take kuka sosai suka fita. Aunty Fadilah, Zahra da Khairat kuwa suman tsaye suka yi ko motsin kirki sun kasa yi, Zahra bata ankara ba taji saukar wani zazzafan mari mai saurin kurmanta mutum wani ihun k'ara ta saki da karfin gaske ya fara dukanta yana ball da ita cikin zafin nama, Khairat tun kafin azo kanta take rusa kuka sosai tana dana sanin biyewa zuciyarta da Aunty Fadilah. Bata ankara ba taji saukar nata marin wanda har sai da bakin ta ya fashe, belt d'in jikin shi ya cire ya fara narkar su cikin tsananin 6acin rai har wasu hawaye ne suke zuba a eyes nashi zuciyar shi tana zafi. "Sabeer mene haka kashe su zaka yi ne akan wannan matsiyaciyar yarinyar ne " Bata gama rufe bakin ta ba taji saukan mari akan face d'in ta da mamaki ta d'ago kanta ta d'auka Sabeer ne ya mare ta sai taga ashe Daddy ne. Zaro ido tayi cikin tsorata tace "Yaya! " Sake kwad'a mata mari yayi tare da cewa "Rufe min baki mara kunya banza mara kunyar wofi " Cikin 6acin rai Daddy yake fad'in haka ashe Jiddah ce ta kirawo shi tana kuka tana yi mishi bayanin abin da yake faruwa shine ya taho. Dakyar aka kwaci Zahra da Khairat a hannun Sabeer aka fita dasu daga d'akin duk ya farfasa musu jikin su ko kuka sun kasa saboda azaba, zubewa yayi kan carpet tare da rik'e kanshi da hannun shi yana sakin wani ajiyar zuciya. Babu dad'ewa gaba d'aya kusan family suka had'u a gidan Jiddah har da Dr Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa wadda take kuka wiwi Sabeer zai kashe mata 'yan jikoki akan wannan shegiyar yarinyar amman ta kasa yiwa Sabeer fad'a saboda son da take mishi sai hucin da take saki. Dr Faridah ma ranta a 6ace sosai da kanta tayi treatment d'in su Zahra da Khairat a inda suka ji ciwo dole ta d'auki mataki akan wannan shegiyar, Aunty Fadilah kuwa tayi tsit da ita sai raba ido take saboda ba k'aramin tsoron Daddy take ba. Suhaima bayan ta canja kaya ne tana kwance wani zazzafan zazza6i ne ya rufe ta kuka take sosai yau taga karshen wulak'anci dole ta rabu da Sabeer duk da kuwa son da take mishi bazata jure wulak'anci da zagan mata da mahaifiya da suke wadda take kwance a kabari. Dakyar Daddy ya rik'o hannun Sabeer suka fito zuwa parlour kallo d'aya Dr d'an fillo yayi mishi yaji duk haushin dukan da yayiwa su Zahra ya kau hankalin shi ya tashi sosai ganin yanda d'an lelen shi ya koma dole yayi wa su Aunty Fadilah tatas don kawai Sabeer yaji sassauci ya nuna musu abin da suka yi basu kyauta ba daga karshe kuma yayi musu iyaka da matar Sabeer. Daga karshe tafiya suka yi gaba d'ayan su, Mumy kuwa aranta haka tace kowa ya gama nashi rashin mutuncin akan wannan yarinyar yanzu lokacin ta yayi dole tayi nasarar raba Sabeer da Suhaima rabuwa ta har abadaaa......... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ* *PAGE 87-88* Shiga cikin bedroom d'in da take a kwance yayi hawa kan bed d'in yayi yana kok'arin had'a ta da jikin shi duk da jikinta ba kwari sai da tayi kok'arin matsawa da sauri, cikin marairaicewa Sabeer yace "Baby please kada ki hora ni akan abin da akayi miki, bazan jure hakan ba " Kamar zai yi kuka yake maganar, cikin muryar ta wadda ta dushashe tace "Mu hakura da junan mu Sabeer 'yan uwanka basa sona sun tsaneni" "Nooo! Baby ki daina fad'in haka bazan iya rabuwa dake ba, ni ina sonki kuma ni zan zauna dake basu ba " Duk yanda yaso yanda yaso ya had'a ta da jikin shi don ya rarrashe ta tak'i yarda, gashi kukan ta yana ta6a mishi zuciya, bata ankara ba taji Sabeer yana fitar da hawaye. Kallon shi ta tsaya yi kawai ana cikin haka Jiddah ta shigo da sauri ya goge hawayen shi don bayason ta gani, cikin sanyin murya yace "Jiddah ki tayani rarrashin Baby tace bazata koma gidana ba" Cikin jin tausayin su ta zauna tana kama hannun Suhaima tace "Haba Suhaima mene hakan idan kika yi hakan ai abin da suke so kenan, taya zaki zalunci kanku bayan kuna son junan su kice zaku rabu, kiyi hak'uri don Allah kada ki rabu da Yah Sabeer yana son ki " Rarrashin ta sosai Jiddah take dakyar ta ciyo kanta ta amince, rungume ta Sabeer yayi don jin dad'in abin da ta fad'a. Har an fara yayyafi suka tafi gida, bayan sun je gida Suhaima tana yin wanka wani zazza6i mai zafi ya rufe ta sosai da ciwon kai sai kuma amai sosai ranar basu iyayin baccin kirki ba saboda yanda jikinta ya rikice sosai don Sabeer ba k'aramin tsorata yayi da jikin ba. Washe gari da safe ya kirawo Dr Aishat don ta dubata, babu jimawa tazo tayi mata gwaje gwaje nan ta hango ciki d'an wata 2 ajikin Suhaima sai kuma damuwar da ta saukar mata da zazza6i, ganin yanda ta gala6aita ne ya sanyata sa mata drip don taji kwarin jikinta sannan tayi mata allurar bacci. Nan tayiwa Sabeer albishir d'in cikin jikin Suhaima, dad'i da farinciki ne ya rufe Sabeer saboda tsakanin murna sai da yayiwa Dr Aishat kyautar mota, dad'i ya ishe shi Dr Aishat nan tayi ta zuba godiya da addu'a sannan tace da zarar Suhaima ta farka ya kirawo ta awaya tukunna ta tafi, Sabeer ya koma d'akin Suhaima kallon ta yake kawai wata zazzafar kaunar Suhaima take sake mamaye cikin zuciyar shi sai shafa cikinta yake Daddy ya iya kira yayi mishi albishir sosai Daddy ya nuna murnar shi. *** **** **** Dr Faridah ce zaune a katafaren office d'in ta sai jujjuyawa take cikin kujera idanun ta a lumshe, turo kofar akayi tare da shigowa. Bata bud'e ido ba taba da umarnin azauna, wadda ta shigo ce ta zauna kan kujera kanta sunkuye tana jiran abin da Dr Faridah zata ce. "Dr Aishat ina kika je bakizo office akan time ba? " Cikin girmama wa tace "Ranki ya dad'e naji gidan Yalla6ai Sabeer ne duba matar shi bata jin dad'i " "Okay me ya same ta " Cikin fara'a Dr Aishat tace "Ai abin farinciki ne ya same mu Doctor don Matar shi ciki ne da ita har tsayin 2 months " Wani shegen murmishi Dr Faridah ta saki mutum ya zaci murmishin farinciki ta saki har da wani cewa "Masha Allah Dr Aishat naji dad'i sosai da wannan albishir d'in " Bud'e bag nata tayi ta d'auko kud'in da batasan adadin su ba ta mik'awa Dr Aishat tace "Ga nawa tukuicin " Kar6a Dr Aishat tayi cikin fara'a tace "Kaiii wannan d'a da farinjini yake tun kafin yazo duniya nake samu alkhairi yanzu Yalla6ai fah ya bani kyautar mota " "Babu komai zaki iya tafiya " Tashi tayi tana godiya ta fice daga office d'in, wata shegiyar dariya Dr Faridah ta saki tare da cewa "Lokaci na yayi dole cikin nan ya zube ta kowanne hali " *** **** **** Bayan ta tashi daga bacci ne Sabeer yayi mata wanka tare da bata tea ta d'an sha kad'an da maganin da Dr Aishat ta bata, sannan ya kirawo Dr Aishat ya fad'a mata ta farka babu 6ata lokaci tazo ta sake dubata tare da bata shawarwarin yanda zata kula da kanta daga nan tayi musu sallama ta tafi. Kulawa sosai Sabeer yake bawa Suhaima don haka cikin kwana 2 ta d'an warware tunda cikin ba mai laulayi bane, tana cin abinci babu laifi, sai dai baccin da yake damunta don sai ta yini tana bacci ganin haka ya sanya Sabeer tunanin samin 'yar aiki don tana tallafa mata da wasu abubuwan. Suna zaune da Daddy a parlour yake gaya mishi yana son 'yar aiki da zata na taimaka wa Suhaima saboda yawan baccin da take yi, abin da Mumy ya kamata ya fad'awa hakan amman babu fuskar hakan. Suna cikin tattauna yanda zasu samu house girl ne can daddy yace "Sabeer ina tunanin ka nemi Jiddah ta samo mata" "Yawwa haka za'a yi Daddy " Yana kok'arin zaro wayan shi ne a aljihu yaji muryar Mumy tana cewa "Haba Son basai ka kirawo Jiddah ba, zan baka d'aya daga cikin house girl's nawa su taimaka mata " Kallon ta suke da mamaki sosai ganin yanda take fara'a, duk yanda suka so su fahimci akwai wani nufi cikin zuciyar ta suka kasa gane hakan da yake Mumy 'yar duniya ce baka gane gabanta balle bayanta green snake ce. Daddy duk da haka sai da yaji shakku da abin da tace bai yarda da ita ba amman sai yabar abin cikin zuciyar shi kawai, sai kuma ta zauna sosai ana hira da ita wanda rabon ta sakewa Sabeer tun lokacin da ya fara son Suhaima. Da ya tashi tafiya ta had'a shi da house girl d'in yarinya ce bata fi 18yrs ba suka tafi amman bata bi motar Sabeer ba sai drive ne ya kaita, Suhaima taji dad'in zuwan 'yar aikin sosai gashi kuma taga bata da rawar kai. Cikin kwana 2 ta tsaya tana aikin ta sosai yanda ya kamata gashi bata da k'iwa Suhaima najin dad'in zama da ita. Da wani yammaci ne Suhaima tana zaune a parlour tana ta6a charting ita da Jiddah ne, sai ga Larai mai aiki ta kawo wa Suhaima wani had'in so6o acikin jug ga cup nan ta ajiye su kan center table tace "Aunty ga so6o nan na had'a miki " D'an yatsina fuska Suhaima tayi kan tace "Anya zan sha so6on nan Larai bana sha'awar shanshi " Murmishi tayi kan tace "Haba Aunty ki daure kisha na 6ata lokaci ina shirya miki shi fah " "To shikenan zuba min " Cikin rawar jiki ta fara zuba mata har Suhaima taso d'ago wani abun atattare da ita ganin yanda take rawar jiki amman sai ta share zancen ta kar6i glass cup d'in ta fara shan sa6on, bata ji wani canjin wani yanayi aciki ba sai ma kamshin cocomber da kayam kamshi kawai taji sai zak'in sugar, taji dad'in so6on don har cup biyu ta shanye, tana gama sha ne Larai ta tattara ta d'auke gaba d'aya takai kitchen ta zubar cikin sink ragowar ta wanke jug da cup d'in tas ta goge su tare da jera su. Tana gama wa ta bud'e k'ofar baya ta fita garden, zaro waya tayi cikin zanin ta tare da lalubo wata number ta danna kira, babu dad'e wa aka d'auka. "Hajiya nayi duk yanda kika umarci ne nayi tasha har cikin so6o biyu " Daga can akayi mata magana banji dai abin da akace ba sai naga Larai ta washe baki tana zuba godiya tare da kashe wayar cikin tsananin farinciki ta koma cikin gidan. Suhaima kuwa ko 10 minute's bata yi da shan so6on nan ba taji cikin ta marar ta da bayan ta yana wani irin ciwo na daban tun tana daurewa har ta kasa ta fara kuka sosai tana kiran sunan Allah, zaro ido tayi gabanta yana bugawa mai tsanani ganin jini yana bin k'afar ta da yawan gaske saboda tsabar firgita da razana ga azabar ciwo ta fad'o daga kan kujera kanta ya bugu da center table lokaci d'aya numfashin ta ya d'auke........... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ* *PAGE 89-90* Sabeer yana zaune a office kawai yaji gaban shi yana fad'uwa sosai Suhaima ce kawai ta fad'o mishi arai don haka phone nashi ya d'auka tare da lalubo number d'in Suhaima ya fara kiranta, sai dai wajen 10 missed calls ba'a d'auka ba. Nan ya tabbatar babu lafiya don haka tashi yayi ya fito daga office hannun shi d'aya rik'e da coat nashi d'ayan hannun kuma jakar laptop da phone nashi, cikin sauri da sassarfa yake tafiya har ya k'araso compound na company d'in. Driver na hango shi yayi saurin shiga mota tare da yi mata ya kawo ta gabanshi bai jira ya bud'e mish ba kawai ya sanya hannu ya bud'e murfin motar ya shiga tare da cewa "Driver kayi sauri ka kaini gida " "Toh Yalla6ai " Tafiya suke cikin motar shiru gaban Sabeer ban da fad'uwa babu abin da yake yi lumshe eyes nashi yayi tare da jingina kanshi jikin kujera yana janyo addu'a cikin zuciyar shi. Tafiyar 20 minutes suka k'araso gida da yake driver yayi gudu ko gama parking bai yi ba Sabeer ya fito daga motar ya doshi cikin gidan. 'Yar aikin da ke la6e ajikin window na parlour wanda za'a iya hango farfajiyar gidan tana raba ido irin na munafukai tana hango Sabeer ne ya sanya ta saurin k'ak'alo kukan dole tare da nufar k'ofar parlour ta bud'e tana kuka sosai har da k'ara. Sauran kad'an ta bugi Sabeer tayi saurin ja baya ta tsaya cikin tashin hankali yace "Keee lafiya kuwa? " "Yalla6ai ka taimaka mana Aunty ce ina fitowa daga d'akina na ganta a parlour a kwance cikin jini kuma ta sume....... " Kan ta k'arasa fad'a tuni Sabeer yayi wurgi da ita gefe da gudu ya shiga cikin parlour yana rarraba ido ina zai hangi Babyn shi. Can idanun shi sukayi mummunan gani na ganin Suhaima a k'asa kwance saman carpet babu alamar numfashi a tattare da ita, da gudu ya k'arasa wajen tare da d'ago ta jikin shi yana cewa "Suhaima! Kada ki tafi ki barni ki tashi please" Wani irin kuka yake yana jijjigata amman ina batasan yana yi ba ma still har yanzu jini na zuba a jikinta. "Yalla6ai ko zamu kai ta asibiti " Cewar Larai mai aiki sai a time d'in Sabeer ya tuna da asibiti don tsananin rud'ewa ya hanashi yin wannan tunanin. Cikin sauri ya d'auke ta tare da fita daga palon duk jikin shi ya 6aci da jini da karfin shi yake kwallawa driver kira, nan ya taso a tsorace ganin matar Yalla6ai ahaka ya sanya shi saurin bud'e mishi mota ya shiga. Da gudu driver yake jan motar hanyar asibitin Mumy kawai driver yayi don yasan nan ne wurin zuwan su gaba d'aya 'yan gidan. Suna shiga compound d'in hospital d'in suka yi kici6is da Mumy ta fito daga ciki zata tafi don time d'in tashin ta yayi, ganin motar Sabeer tayi parking ne ya sanya ta sakin wani shu'umin murmishi don tasan komai ya faru a yanzu. Da sauri ta k'arasa wajen motar tun kafin ta k'arasa Sabeer ya fito daga motar cikin tashin hankali kamar gaske tace "Son me yasamu Suhaiman ne? " Idanun shi na zubar da hawaye yace "Mumy ki taimaka min kada Suhaima ta mutu please " Da sauri Mumy ta kirawo nurses suka taho da gadon daukan mara lafiya, kwantar da Suhaima Sabeer yayi nan suka nufi cikin asibitin da sauri, yayin da Mumy ta rik'e hannun Sabeer suka shiga ciki, saboda gujewa zargi ya sanya Mumy k'in shiga room d'in da Suhaima take don ta dubata. Sai kawai ta kirawo Dr Nabilah don ta tsaya akanta tunda Dr Aishat ta tashi, yayin da Mumy ta rungume Sabeer ajikinta tana shafa bayan shi idan ban da ajiyar zuciya babu abin da yake saki. Dakyar suka tsayar da bleeding d'in da Suhaima take duk yanda suka so cikin ya zauna amman hakan ya gagara sai da ya fita, gyara mata jikinta suka yi bayan sun samu nasarar dawowar numfashinta sannan suka sanya mata drip tare da yi mata allurar bacci don ta huta sosai. Fitowa suka yi daga room d'in Dr Nabilah ta nufi office d'in Dr Faridah sauran nurses d'in kuma suka nufi nasu office d'in, tura k'ofar tayi a hankali ta shiga Sabeer na ganin ta ya tashi da sauri ya matsa kusa da ita yace "Dr fad'a min awane yanayi Suhaima take, kada kice min ta mutu please" Kallon shi Dr Nabilah take cike da tausayi dakyar ta iya cewa "Yalla6ai munyi nasarar dawowar numfashinta yanzu haka nayi mata allurar bacci sai dai muna buk'atar jini don tayi bleeding sosai " Ajiyar zuciya ya saki tare da hamdala kafin ya kuma cewa "Cikin jikinta fah yana nan? " Kasa magana tayi tuni Sabeer ya shiga cikin wani yanayi na daban mara misaltuwa. "Am sorry Yalla6ai cikin ya fita duk iya kok'arin da muka yi bai zauna ba" Sauran kad'an Sabeer ya fad'i da jin abin da tace mishi jikin shi har rawa yake ya zauna kan kujera cikin rawar murya idanun shi tap da hawaye yace "Innalillahi wa'inna ilaihhir raji'un, Mumy.... Mumy shikenan d'ana ya tafi bazai dawo ba " Dr Faridah wadda ta sauke ajiyar zuciya na kwanciyar hankali jin cikin ya fita sai dai kuma ta tausayawa yaron nata, da hannu tayi wa Dr Nabilah alama da ta fita. Rungume Sabeer tayi wanda yake kuka sosai kafin daga karshe kuma ya daina kukan kiran Daddy yayi yana fad'a mishi kamar Daddy yayi wa Sabeer kuka haka yaji saboda yasan yanda Sabeer yake bala'in son ciki kodayaushe zancen shi Suhaima zata haihu ya samu Baby shima. Sabeer fita yayi zuwa room na Suhaima wanda aka kwantar da ita, kallonta yake duk ta rame tayi wani irin haske daga ni bata da ishashshen jini ajikinta, hannun ta mara drip ya rik'e gam yana kallon ta hawaye na fita a eyes nashi. Daddy ne ya shiga office d'in Mumy cikin fusata, kallon ta ya tsaya yi kawai har sai da Mumy ta tsorata sosai, kallon ta kawai yake amman sam bai yadda da zubewar cikin Suhaima ba sai da dalili don yasan halin Dr Faridah ciki da bai. Hannun ta ya damk'o da k'arfi har sai da ta saki k'ara tana cewa "Daddy da zafi fah " Idanun shi cikin nata yace "Faridah ki fad'a min gaskiya da sanya hannun ki cikin zubewar cikin matar Sabeer? " Afrigice Mumy ta d'ago da kanta tace "Ni..... Ni kuma Daddy ina ruwana da ita ne saboda me zan zubar mata da ciki gidanta nake zuwa kuma saboda irin haka na sanya Dr Nabilah ta tsaya akanta kada naje ace ni na zubar mata gashi nan ma duk da haka ban tsira ba " "Uhmm Faridah na sanki ciki da bai fah zan bincika dalilin faruwar hakan idan zargina ya tabbata gaskiya zakiyi nadama don daga ni har Sabeer zamu guje ki! " Yana gama fad'in haka ya tureta sauran kad'an ta kife akan table ya fice daga office d'in, Direct office d'in Dr Nabilah ya nufa. Bayan ya shiga ne ya samu waje ya zauna yana kallon ta sannan yace "Inason ki fad'a min gaskiya mene silar zubewar cikin matar Sabeer? " "Yalla6ai a iya bincike na na gano zamewa tayi ta fad'i a k'asa wanda ya zama silar zubewar cikin " "Kin tabbatar da hakan? " "Sosai ma Yalla6ai " Ta fad'a hakan tana k'ak'alo murmishin yak'e, don Dr Faridah ce ta tsara mata abin da zata ce idan ba haka ba zata koreta daga hospital nata. Murmishin mugunta Dr Faridah ta saki bayan ta gama kallon maganar da Daddy yayi wa Dr Nabilah ta laptop d'in ta, kwantar da kanta tayi jikin kujera tana juyi tace "Daddy duk binciken ka bazaka ta6a gane gaskiya ba dole Sabeer ya rabu da matsiyaciyar yarinyar nan " Ta k'arasa maganar tana dad'a sakin wani murmishin. Mumy ta mance da _rana dubu ta 6arawo rana d'aya ta mai kaya, za'ayi walkiya duk daren dad'ewa zaku ma a gane abin cikin dubu_ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ* *PAGE 91-92* Sabeer k'in yarda yayi a zubawa Suhaima jinin kowa sai nashi hakan ba k'aramin k'ara fusata Mumy yayi ba amman ta danne don batason nunwa. Jiddah itama tayi kuka ta tausayawa Sabeer sosai mutane sosai suka zo dubiyar Suhaima har dasu Yah Aliyu, Aunty Aliyah, Babaa Lantana da Baba Adamu duk sun zo, haka ma friend d'in Sabeer wato Musaddiq da matar shi Mufidah sun zo, kowannen su da abubuwan kayan duban shi. Sati d'aya Suhaima ta d'auka a hospital ta samu sauk'i sosai don kulawa sosai Jiddah da Sabeer suke bata gashi ma yak'i yarda Babaa Lantana ta zauna saboda shi yake kwana da ita dole ta hakura da zaman jinyar Suhaima, duk da har yanzu tana cikin takaicin zubewar cikinta bata sanya shi cikin ranta sosai ba ita take ma da k'arfin gwiwar rarrashin Sabeer da yayi hak'uri ya kar6i kaddarar da Allah ya d'ora mishi. Kwanakin ta goma a hospital aka sallame ta don ta warke garau da ita, bayan an sallame su gida suka dawo abin su sosai Jiddah ta gyara mata gidan tsaf sai da tayi mata girki na dare sannan ta tafi gida. Awannan daren Sabeer yayi addu'a Allah ya sanya kwallon shi ya fad'a raga, sun nunawa junan su so da kulawa sosai a wannan lokacin sai gabanin asubah suka samu damar yin bacci. _*After 4 Month's*_ Da dare misalin wajen 10 na hango Suhaima tana fitowa daga bedroom nata, tana sanye cikin wata white sleeping dress irin transparent d'in nan gashin ta yasha gyara sai kyalli yake ta zubo shi ga wani k'amshi mai dad'i da take fitarwa tayi kiba abin ta. K'arasa tayi inda Sabeer yake ta shige jikin shi, wanda tun tahowar ta yake kallonta kasa k'arasa aikin yayi a laptop d'in ya rufe ta tare da janyo ta jikin shi yana shinshina ta yace "Baby kinyi kyau sosai " "Thank U " "Ni fah ice cream nake son sha yanzu " D'an zaro ido kad'an yayi kan yace "Baby yanzu fa 10 ta wuce fah kiyi hakuri sai gobe please " "Allah idan bansha ba bazan iya bacci ba ka taimaka min Yah Sabeer please " Ta k'arasa maganar kamar zatayi kuka, bubbuga bayanta yake yace "Okay Okay naji Baby za'a kawo miki yanzu, amman ya akayi na koma Yah Sabeer kuma" Kashe mishi ido tayi tare da kad'asu tace "Abin sirri ne " Yana dariya yaja hancin ta sannan yace "Bari na dawo a fad'a min sirrin " Tashi yayi yana kok'arin fita tace "My dear a sanya min flavours na vanilla and strawberry " "Okay Baby na" Fita yayi ya samu driver da bai riga ya tafi gida ba ya tsaya hira da maigadi Sabeer ya aike shi siyo mata ice cream d'in sannan ya dawo ciki. "Baby fad'a min sirrin da ya sanya aka kirawo ni da Yah Sabeer " 'Yar dariya tayi tukunna tace "Kaiii my Dear baka mantuwa ni fah ba komai " "Aikuwa yarinya sai kin fad'a min " Nan ya fara yi mata cakulkuli tana tuntsira dariya shima dariyar yake sauran kad'an ta fad'o daga saman kujera ya rik'o ta tare da d'orata kan k'afar shi yace "Baby naga fah alamun Allah ya amshi addu'a ta don kin sake canjawa musamman hips d'in ki da boobs nake sun k'ara cika anya ban ajiye miki ajiyata ba, ga kwanaki biyun nan wani irin kwad'ayi kike ji dashi dama Doctor na karanta kamar yanda Mumy taso nayi da yanzu na gane " Sai da gaban Suhaima ya fad'i da taji ya ambaci sunan Mumy amman sai ta share tace "Nima bansani ba my dear amman nasan tunda na dawo daga hospital sau d'aya nayi period d'ina kuma yanzu muna 4 Month's fah " "Allah nagode maka insha Allah shine ma gobe zan kirawo Dr Aishat ta duba min ke " Suna cikin haka aka danna door bell Larai mai aiki ce ta bud'e k'ofar ta kar6i sak'on ta kawo wa Sabeer, kallonta Sabeer yake shi sam yarinyar bata kwanta mishi a rai ba shi yasa yake sanya mata ido aduk wani motsinta. "Hajiya na tabbatar da abin da na fad'a miki don naji suna hirar yanzu " Daga can 6angaren akayi mata magana nan ta dunga gid'a kai kamar k'adangaruwa alamar tana fahimtar abin da ake fad'a mata, sun d'an jima suna waya kafin ta ajiye wayar nata. Apalo kuwa bayan Suhaima ta gama shan ice cream d'in ne Sabeer ya d'auke ta suka nufi side nashi, a wannan lokacin kowannen su sai da ya zage wajen nunawa d'an uwanshi irin son da yake mishi, sunyiwa kansu alk'awarruka acikin wannan daren wanda har daga cikin alk'awarin su na zasu rayu da juna har abada bazasu rabu ba da junan su, soyayya sosai suka gwada wa junan su, sai bayan Suhaima ta samu bacci ne Sabeer yaje yayi wanka tare da d'aura alwala ya fito, shimfid'a abin sallah yayi ya fara nafila sai da yayi raka'a biyu sannan yayi addu'a sosai Allah ya sanya Suhaima ciki ne da ita ya dad'e yana addu'ar samun yara nagari tare da addu'ar Allah ya kad'e duk wata fitina da tashin hankali azaman su na aure, sai bayan yayi sallahr asuba bacci mai nauyi ya d'auke shi, ko da Suhaima ta idar da nata sallahr ta tarar ya koma bacci itama jikin shi ta kwanta suka koma baccin nasu da yake weekend ne. _*10:35 am*_ A lokacin suka tashi daga bacci suka yi wanka simple gown Suhaima ta sanya ajikinta shima Sabeer ya shirya cikin 3quater white da T-shirt white itama a palo ya zauna yayin da Suhaima a gurguje ta shirya musu breakfast. Kallon Larai tayi tace "Don Allah d'an had'a min kunun gyad'a cikin cup d'aya " Jiki na rawa tace "Toh Aunty " Sannan Suhaima ta fita daga kitchen d'in, ta kaiwa Sabeer breakfast d'in kan dining table ta had'a mishi komai, zama tayi alokacin ya k'araso inda take yace "Baby taho nayi feeding d'in ki " "A'a ni bana son cin komai kunu zan sha kawai " "Ayyah Baby gashi ni ban iya ba kizo mu je kitchen kina fad'a min nayi miki " "Kabar shi na sanya Larai ta dama min " D'an 6ata fuska yayi yana shirin magana Larai ta k'araso wajen gaida Sabeer tayi bai amsa ba sai ma kau da kan da yayi. Ajiyewa Suhaima cup d'in tayi cikin murmishi tace "Na gode Larai " "Ah ba komai duk abin da kike so ki fad'a min Aunty " Tana gama fad'in haka tabar wurin d'an hararar Suhaima yayi kan yace "Baby ni fah i hate dis gurl zata bar gidan nan soon a sama miki wata" "A haba dear me ta tsare maka? " "Ni bata kwanta min ba a rai " Murmishi tayi kawi ta fara shan kunun sam Sabeer kasa cin abincin yayi yana kallon ta don sai yaji zuciyar shi na ayyana mishi kunun nan bai yarda dashi ba, amman ganin bashi da wata hujja ne ya sanya shi kawai barinta tana sha. Bayan ta gama shane ta fara bashi abinci abakin shi ganin yak'i cin nashi, bayan ta gama bashi suka dawo parlour zama Sabeer yayi ita kuma Suhaima ta mik'e tsaye kallon ta yayi kafin yace "Baby ina zaki? " "Fitsari nake ji Dear bari naji na dawo " Shiga bedroom d'in ta tayi ya bita da kallo kawai, Suhaima na shiga bathroom ta tsugunna zata yi fitsari sai kawai ganin jini tayi yana zuba maimakon fitsari, a razane ta mik'e tsaye jikinta na 6ari lokaci d'aya taji marar ta tana k'ullewa kasa d'aga k'afar ta tayi sai kawai ta zube akasan tiles d'in bathroom ta kwallawa Sabeer wani irin kira da k'arfi. Sabeer da yake zaune yana kallon film d'in furious 7 a mbc 2 yaji kiran da Suhaima take mishi da sauri ya tashi ya nufi d'akin nata kai tsaye bathroom ya bud'e ganin bata cikin d'akin, idanun shi ne suka sauka akan tiles d'in toilet d'in wanda ya kasance fari jini gaba d'aya ya rina wajen, ga Babyn shi durkushe tana murk'usus tare da kiran sunan shi. Saboda tsabar tashin hankali sau ran kad'an Sabeer ya zube a k'asa jikin shi na rawa ya d'auke ta kawai ya fito daga d'akin da gudu ya nufi hanyar fita daga parlourn. Larai tana ganin haka da sauri ta shige bedroom d'in Suhaima ta sanya wasu abubuwa cikin drower ta fito. Gudu kawai Sabeer yake shararawa akan hanya har ya k'arasa hospital d'in Mumy, a rikice yayi parking tare da bud'e bayan motar ya d'auko Suhaima yayi cikin asibitin da ita. Da Mumy ya fara cin karo fitowar ta daga room d'in operation tana zame hand gloves d'in hannun ta, ganin d'an nata ne tare da Suhaima ya sanya ta kiran nurses suka kar6i Suhaima zuwa wani room na daban, yayin da Sabeer ya zube a k'asa yana kuka sosai, dafa kafad'ar shi tayi jiyowa yayi ya rungume ta had'e da fad'in "Mumy ina rok'an ki kada ki bari na sake rasa cikin nan please Mumy ki taimaka min " Tausayin d'an nata ne ya kamata amman tasan dab take da rabuwa su bazata bari tausayin shi yayi rinjaye cikin zuciyar ta ba. Da kanta ta jagoranci su Dr Aishat da Dr Nabilah zuwa room d'in da aka kwantar da Suhaima don tana son su zame mata shaidu, sunyi nasarar tsayar da jinin sai dai kuma tun kafin suzo asibitin cikin ya zube allurar bacci akayi mata tare da sanya drip suka fito domin neman jinin da zasu sanya mata. "Mumy ina fatan ban dad'a rasa shi a karo na biyu ba? " "Yalla6ai yanzu jini muke buk'ata da za'a sanya mata " Cewar Dr Aishat kenan, dole Sabeer ya hakura da tambayar yaje aka d'auki jinin shi duk yanda Mumy taso ta hanashi yak'i yarda ya biye mata. Bayan awanni biyar a lokacin Suhaima ta farfad'o in banda kuka babu abin da take yi haka ma Sabeer wanda yayi kuka ya more yana zaune agefen Suhaima ya kasa rarrashin nata. Shigowa room d'in akayi Daddy ne da Mumy suka shigo sai Jiddah, ko zama basu yi ba suka fita daga d'akin gaba d'aya har Sabeer da Suhaima tare dasu Dr Aishat mota suka shiga sai gida. Zama suka yi a parlour duk sunyi shiru kafin Daddy yace "Muna son sanin mene ne musabbabin zubewar cikin Suhaima tun da kune kuka dubata". "Yalla6ai mun gano inda matsalar take tablet d'in zubar da ciki akesha shine dalilin zubewar cikin " Ba Suhaima da Sabeer ba hatta Daddy sai da ya d'ago a matuk'ar razane yana kallon Dr Aishat, "Tabbas kuwa anyi hakan ko zubewar cikin farko ma shan maganin akayi Dr Faridah ce tace kada na fad'a a bari sai ta sake zubar da wani " "Okay mun gode kuna iya tafiya " Cewar Daddy kenan, tashi suka yi suka tafi, yayin da Suhaima, Sabeer, Jiddah da Daddy sun kasa cewa komai musamman Sabeer da Suhaima da suka ji abun wani iri. Cikin kuka Mumy tace "Innallilahi wa'inna ilaihi raji'un daman nasan za'a rina talaka bai iya samu wuri ba sai yayi rashin mutunci, daman bason Sabeer d'in take ba tun da har bazata iya had'a zuri'a dashi ba take zubar mishi da ciki " Girgiza kai tayi tana tafa hannu tace "Aikuwa tun da haka ne wallahi sai Sabeer ya rabu dake rabuwa ta har abada, yanda Allah shi kadai ya bani inason ganin ya tara min jikoki shine don bakinciki da munafarci irin naki kike zubar da cikin har sau biyu to wallahi baki isa...... " Bata gama maganar ba Daddy ya d'aga mata hannu dole tayi shiru cikin nutsuwa Daddy yace "Suhaima ki fad'a mana gaskiya shin wannan abin da ya faru da had'in hannun ki aciki?" Cikin wani irin kuka na tashin hankali tace "Wallahi Allah Daddy bansan komai akai ba ban ta6a shan wani magani ba na rantse da Allah " "Daddy Allah Suhaima bazata sha magani ba don ta zubar da ciki tana son Sabeer bazata iya aikata haka ba sai dai idan sharri akayi mata wallahi a fad'i wanda yake bata abu taci a lokacin sai cikin ya zube anan za'a gano munafikin da ya...... " Kafin Jiddah ta k'arasa maganar ta Dr Faridah ta kwad'a mata mari tare da cewa "Daman Jiddah baki da hankali yanzu sai ki bi bayan wata bare bayan kina ganin d'an uwanki take cuta tana zaluntar shi amman kin ban kunya wallahi" Basu ankara ba sai ganin Sabeer suka yi da sauri ya tashi a sukunye ya nufi bedroom d'in Suhaima ya fara hargitsa d'akin don yasan indai gaskiyar magana ne Suhaima na zubar mishi da ciki zai samu wani k'arin haske akai. Birkita d'akin yake komai sai da ya hargitsa cikin wardrobe duk ya zubo mata kayanta k'asa har katifa ya d'aga cikin toilet drawer d'in gefen gado duk ya duba bai ga komai ba a lokacin zuciyar shi ta fara aminta da maganar da Jiddah tayi sharri akayiwa Suhaima daman shi bai gama yarda ba. Har zai fito daga d'akin idanun shi suka sauka kan drower d'in jikin mirror da sauri ya k'arasa wajen yana bud'e su har ya janyo ta k'asan, lokaci d'aya jikin shi yayi wani irin sanyi ga66an jikin shi suka saki wata irin tsanar Suhaima ta fara mamaye cikin zuciyar shi ganin abin da idanun shi suka gane mishi. Kwaso kwalin maganin yayi gaba d'aya ya fito daga d'akin a fusace kamar wani zaki yana zuwa ya watsawa Suhaima maganin akanta cikin kzakkausar murya yace "Suhaima! Wannan mene? " Suhaima wadda sauran k'iris fitsari ya zubo ta ta zubawa maganin ido duk da batayi karatun likita ba jikinta ya bata wannan maganin shine wanda ake magana akan shi. "Alhamdullilah da Allah ya toni asirin munafuka" Cewar Mumy kenan tana jijjiga kafa hatta Daddy mamaki ne ya hanashi magana. "Yaya wallahi Suhaima bazata aikata haka ba " Cewar Jiddah tana faman kuka kamar zata shid'e, cikin 6acin rai yace "Jiddah close your mouth or I'll slap U wallahi " Juyowa yayi wajen Suhaima tare da cewa "Nagode Suhaima akan duk abin da kika yi min wannan shine sakayyar da zaki min A SANADIN SON KI mene banyi ba nayi fad'a da family na iyayena na bar inda suke na tafi wajen ki nasha wahala kafin ki kar6i soyayya ta ashe duk kallon wawa kike min bansan me nake ba, kin zubar min da cikin jikin ki sau biyu nasan baki sona dama don haka get out from my house i hate you Suhaima i hate you so much nasan bazan yi regretting wannan abin da nayi ba kuma da sannu Allah zai saka min " Yana gama fad'in ya nufi upstairs zuciyar shi na wani irin zafi, tashi Suhaima tayi tana faman kukan tashin hankali zata fita daga parlour tabar gidan taji muryar Daddy yana cewa "Suhaima kada ki tafi zansa ayi bincike ban yarda da wannan abun ba" Girgiza kai take tana cewa "A'a Daddy kabar na tafi bazan zauna ba " Tana gama fad'in haka ta fice daga gidan da gudu tana kuka, Jiddah ce tayi kok'arin bin ta amman Mumy ta rik'e ta gam tana faman hararar ta.................. Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 93-94* Suhaima gudu take tana kuka har ta samu ta fito daga gidan, sannan ta d'an tsaya tana yiwa gidan kallon k'arshe don tasan bazata ta6a komawa cikin shi ba har abada kuwa. Fara tafiya tayi tana goge hawaye da hijab d'in jikinta ko takalmi babu a k'afar ta, wani mai taxi taga ya sauke wata mata bata tsaya tambayar shi ta fad'a cikin motar tana kuka kawai, daga matar har mai taxi d'in suka bita da kallo kowanne fuskar shi ta d'auki alhini suna tunanin ko mutuwa akayi mata mai zafi yasanya ta haka dad'in dad'awa da suka ga ko takalmi babu a k'afar nata, canjin matar mai taxi ya bata sannan ya tada motar suka fara tafiya sai da suka hau kan titi sannan yace "Baiwar Allah ina zan kai ki? " Dakyar ta iya tsayar da kukan tayiwa mai taxi bayanin inda zai kaita, mai taxi bai zaci wajen da nisa ba sai da ta fad'a mishi sunan kauyen da zai kaita yaso yi mata maganar ba nan zai je ba but ganin irin halin da take ciki ne kawa yayi niyyar taimaka mata. ***** "Faridah ina jiye miki duk ranar da gaskiya tayi halinta, idan har da sanya hannun ki cikin wannan abun to kiyi gaggawar warwarewa tun kafin kizo kina nadama " Turo baki tayi kan tace "Wai ni duk kun tattara laifi akaina ina ruwana da ita da har zanyi yunkurin zubar mata da ciki kawai ta samu sake ne kasan halin talakan mutum bai iya samun waje ba, kuma nagodewa Allah da ya sanya suka rabu da d'ana yaje ya auri wadda zata haifa min 'yan jikoki na, yanzu kawai saki nake so naji yayi mata yanda zasu rabu har abada" "Allah ya shirya ki Faridah " Cikin wani irin murmishi tace "Amin my Dear " Tashi Daddy yayi zai fita itama ta mik'e tana cewa "My Dear ka tsaya mu tafi da Son mana kada mu tafi mu barshi shi d'aya " Cikin jin haushin abin da Sabeer yayi wa Suhaima tunda bai tsaya yayi bincike ba kawai ya yanke hukunci yace "Ai ba yaro bane shi kuma yasan hanyar gida " Yana gama fad'in haka ya wuce ya fita daga palon, Jiddah ma d'aukan Islam tayi ta wuce da sauri ta bi bayan Daddy da harara Dr Faridah ta bita tukunna ta wuce upstairs inda Sabeer yake. Agefen gado ta ganshi yayi ruf da jiki rabin jikin shi a saman bed rabin a k'asa sai wani irin shashshak'a yayi na kuka idanun nashi sunyi ja sun kumbura hatta face nashi tayi ja sai maimaita kalmar "Why! Why! Suhaima zaki yi min haka na tsane ki i hate U " . wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Dr Faridah jin yanda Sabeer yake furta ya tsani Suhaima kamar tayi tsalle da ihun murna haka take ji amman sai ta danne, zama tayi akan gadon ta tare da d'aukan kanshi ta d'ora kan k'afafun ta shafa mishi gashin kanshi take a hankali tana rarrashin shi but still Sabeer eyes nashi basu bar zubar da tears ba. "My Son kayi hak'uri mu tafi gida kaji bazan iya barin ka anan kai d'aya ba " "No! Mumy ki tafi ki barni zuciya ta yana daf da tarwatse wa, ina jin zafi acikin zuciya na idan na tuna Suhaima ta cuce ni taci amanata ta yaudare ni tayi min butulci Mumy! " Dafe saitin zuciyar shi yayi da hannun shi d'aya yana jan wani irin numfashi, wani irin zabura Dr Faridah tayi ganin yanda eyes d'in Sabeer suka kakkafe. Hannu ta d'ora saman kanta tana kuka tace "Wayyo Allah nah na shiga uku zan kashe d'ana da kaina! " ****** Sai bayan sallahr ishsha ne suka k'arasa kauyen su Suhaima har k'ofar gida mai taxi ya kaita har zuwa yanzu Suhaima bata bar kukan bak'inciki da takaicin hukuncin da Sabeer ya yanke ba batare da bincike ba aure ko shekara baiyi ba ace har an rabu daman ashe ba sonta yake tsakani da Allah ba yaudare ce yake mata irin ta mazan yanzu nima na tsane ka kamar yanda ka tsane ni Sabeer!. Maganar da d'an taxi yake mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunani fitowa tayi daga motar cikin dushewar murya tace "Bari na kar6o maka kud'in ka " Ko taku uku bata yi ba taji ta bige mutum d'agowar da kanta da zatayi suka had'a ido da Yah Aliyu cikin tsakanin mamaki yace "Suhaima! " ai Suhaima batasan lokacin da ta fad'a jikin shi ba ta saki wani irin marayan kuka, wani irin tashin hankali da fad'uwar gaba ne ya ziyarci Yah Aliyu tuni fuskar shi ta fara canja yanayi. "Yay... Yaya ka biyashi kud.... kud'in shi " Ta fad'a cikin kuka tana nuna mai taxi da hannun ta, zuciyar Yah Aliyu tana tafasa yace "Malam nawa ne kud'in ka? " Nan d'an taxi d'in ya fad'a hannu Yah Aliyu ya zura a aljihu ya d'auko kud'in shi ya bashi yana bashi ya rik'o hannun Suhaima suka shiga cikin gida. Aunty Aliyah da take zaune tana jijjiga Ameer yayi bacci taga shigowar mijin nata batasan lokacin da ta kwantar da Ameer saman katifa ba ta mik'e a razane tana cewa "Suhaima kece da daren nan? " Jikinta Suhaima ta fad'a tare da fashewa da kuka da k'arfi, ruwa Yah Aliyu ya d'ebo mai sanyi a randa zama yayi tare da zaunar da Suhaima akusa da shi ya bata ruwan da hannun shi, bayan ya gama bata ne sannan cikin nutsuwa yace "Suhaima fad'a min me yafaru kada ki 6oye min komai don baki da kamata a duniyar nan " Kallon Yah Aliyu tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta fara zayyana mishi abubuwan da suke faruwa gaba d'aya bata 6oye musu komai ba tana gama fad'in ta sake fashewa da kuka, Aunty Aliyah wadda take kukan tausayin Suhaima ta janyo ta jikin ta tana rarrashin ta. Yah Aliyu kuwa wani zafi zuciyar yake yi sai wani huci mai zafi da yake fitarwa zagaye tsakar gidan yake hannun shi goye a bayan shi ya ma rasa abin cewa can ya bud'e baki cikin kakkausar murya yace "Yau ni Aliyu za'a wulak'anta aci mana mutunci don kawai muna talaka, abin da Sabeer zai aikata mana kenan lallai yau koda bai sake ki ba ni ni Aliyu na sanya almakashi na datse igiyoyin da suke tsakanin ku dashi bake bashi har abadaaaa.......... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 95-96* Yana sauke wani irin huci Yah Aliyu ya k'arasa maganar ga wasu hawaye na bak'inciki da suke zubo mishi idan ya tuna yanda aka zubar wa k'anwar shi ciki har sau biyu, an cuci k'anwar shi cuta ba k'arama idan ya tuna idan kuma shine iya k'wanta aduniya fa, idan ya kasance iyakar 'ya'yan da zata haifa ne a iya duniya fah shikenan angama cutar k'anwar shi ba ita ba ganin 'ya'yan da zata haifa wasu can daban sun zubar mata dashi. "Inaaa! Bazai yiwu ba dole sai na d'auki fansar abin da akayi wa k'anwata koda zai kasance abu na k'arshe a rayuwashi, an cuce mu don abin da akayi wa Suhaima tamkar shi aka yiwa. Komawa yayi ya zauna tare da janyo Suhaima kusa dashi ya sanya hannun shi ya d'ago kanta suna kallon juna yace "Suhaima baki da kowa sama dani don haka wannan abin da akayi miki sai na d'auki fansar shi koda duk abin da na mallaka a duniyar nan zai k'are " Girgiza kanta Suhaima kawai take cikin kuka take cewa "Nooo! Yaya kada ka kula su na bar mutum da Allah duk wanda yayi min wannan abun shi da Allah " Idanun shi jawur yace "A'a k'anwata baza ayi haka ba sun zalunce ki da yawa bazan kyale su ba don suna tunk'aho su masu kud'i ko suna tunanin zan ji tsoron su to wallahi a'a sai na ja dasu kuma sai nayi nasara " Hannun shi Suhaima ta k'ank'ame tana kuka tace "Na had'a ka da girman Allah Yaya kayi hak'uri ka kyale su idan har kana son ganin farinciki na mu bar wanda ya aikata da Allah da sannu Allah zai saka min " Tsayawa yayi kallon ta na wasu 'yan mintuna kafin yace "Tabbas ina son ganin ki cikin farinciki k'anwata zan kyale su saboda ke kawai".. Rungume shi tayi tana cewa "Yawwa Yaya na nagode " Shafa kanta yayi sannan yace "Allah yayi miki albarka k'anwata, yanzu bari na kai miki ruwa kiyi wanka da sallah kici abinci" "Amin Yaya na " Har ta mik'e ya sake rik'e hannun ta sannan yace "K'anwata kiyi min alkawarin kin rabu da Sabeer har abada " Shiru Suhaima tayi tana mai sunkuyar da kanta ta rasa abin da zata ce ma, ta d'an jima ahaka sannan ta d'ago kanta ta kalli Yaya Aliyu wanda yake kallonta yana jiran me zatace, har ta bud'e bakinta zata yi magana da sauri Aunty Aliyah ta tari numfashin ta tare da cewa "Yaya abar wannan maganar don Allah taje tayi wanka tukunna " Aunty ta fad'i hakan ne don batason Suhaima tayiwa Aliyu alkawari don tasan irin soyayyar da Suhaima da Sabeer suke yiwa junan su rabasu abu mai wahala ne tasan kuma idan ya huce sai ya dawo inda Suhaima take, tasan mak'iya ne basa son ganin su tare musamman 'yan uwan Sabeer da tasan irin k'iyayyar da suke yiwa Suhaima saboda kawai don ta kasance talaka 'yar kauye, tana son Suhaima da Sabeer amman sai ya gane kuskuren shi na yanke hukunci kafin bincike. Sakin hannun ta Aliyu yayi sannan yace "Je ki kiyi wankan " Cikin sanyin jiki ta wuce yayi da Yah Aliyu ya bita da kallon tausayi yarinya k'arama an mayar da ita bazawara auren da ko shekara bai rufa ba, da ace ana dawo da abin da ya wuce da ya dawo rayuwar su baya ko dan ya goge Sabeer daga rayuwar Suhaima, amman ina kaddara ta riga fata Allah ya rubuta sai hakan ya faru dasu zasu rungumi kaddara su koma zasu cigaba da godewa Allah a duk halin da suka tsinci kansu aciki, wasu hawaye ne suka zubo mishi da ya tuna mahaifiyar su da irin bak'incikin da ta fuskanta awajen d'a namiji kafin ta mutu. Baisan ma hawayen na zuba ba sai da yaji hannun Aunty Aliyah suna goge mishi hawayen, cikin sanyin murya tace "Kayi hak'uri Yaya komai tsanani yana tare da sauk'i rayuwar Suhaima zata inganta agaba insha Allah " "Amin mata ta! Na gode da kulawar ki agare ni " Tashi yayi yana kok'arin had'awa Suhaima ruwan wanka nan Aunty Aliyah ta kar6a ta had'a mata sannan ta kai mata toilet. Shiga d'akin ta tayi ta tarar da Suhaima a zaune ko kayan jikin ta bata cire ba nan tayi zaman rarrashin ta kafin ta cire kayan ta d'aura zani ta fita wanka inda Aunty Aliyah take fad'a mata bayan tayi wankan ta zauna cikin ruwan d'umi sosai. Bayan ta gama wankan ne ta sai kayan Aunty Aliyah ta sanya saboda kayanta sunyi datti gashi tafiya bata kwanciyar hankali ba bata taho da wasu ba, abinci ma kasa ci tayi sai fura Aunty Aliyah ta dama ta Yah Aliyu da kanshi yake bata a baki, bayan ya gama bata ne sai tasha paracetamol saboda yanda kanta yake ciwo sosai ta kwanta kan 3siter d'in d'akin Aunty ta lumshe eyes nata hannunta d'aya dafe da kanta, tunanin kawai maganganun da Sabeer yayi mata take da yanda yace ta fice mishi daga gidan shi ya tsane ta, hawaye masu zafi ne suke zubo wa daga eyes nata. Yah Aliyu da Aunty Aliyah ne suka zage wajen gyara mata d'akin Suhaima na da gyara shi sukayi tas, suka share har zasu fito daga d'akin Yah Aliyu ya tsaya kallon d'akin na 'yan mintuna kafin ya sauke ajiyar numfashi yace "Aliyah ya kamata na gyarawa Suhaima d'akin ta yayi kyau sosai duk wani jin dad'i ma zan tanadar mata koda duk abin da na mallaka zai k'are, don haka cikin satin nan zan nemi mai siyan d'ayan gonata na siyar sai na bar d'ayar kawai ta ishemu zaman duniya dai " Gid'a kai Aunty Aliyah tayi kafin tace "Gaskiya kam ka kyauta Allah ya k'ara had'e kanku Allah kuma ya k'ara bud'i " Yana murmishi yace "Amin mata ta " Har zasu fito daga d'akin Aunty Aliyah tace "Ni kuwa ina maganar cigaba da karatun ka da kayi min maganar kwanaki naga baka k'ara cewa komai ba? " "Tana nan maganar don har na samu gurbin karatu na k'arasa secondary yanzu zan zana jarabawar wec da neco" Murmishi Aliyah ta saki tare da cewa "Masha Allah abu yayi kyau Allah ya taimaka ya bada sa'a " "Amin Amin " Daga haka suka fito daga d'akin zuwa d'akin Aliyah tarar da Suhaima tana kuka ne ya sanya su tsayawa suna rarrashin ta dakyar tayi shiru sannan suka rakota d'akin ta nan ma sun jima sannan suka yi mata sai da safe suka tafi. Cikin wannan daren ya zamewa Suhaima wani irin dare na bak'inciki musamman idan ta tuna jiya kamar yanzu suna tare da Sabeer suna nunawa junan su zazzafar soyayya, tayi kuka Suhaima awannan daren har sai da taji kamar kanta da idanun ta zasu zazzago da ciwon da zafin da suke mata. ************ Cikin nutsuwa yake motsawa tare da kok'arin bud'e eyes nashi dakyar ya samu ya bud'e su saboda hasken da yake dallare mishi ido, kallon d'akin yake cikin mamakin me ya kawo shi, duk ya rame bakin shi ya bushe kallo d'aya zaka yi mishi kasan cewa bashi da cikakkiyar lafiya. "Alhamdullilah Son ka farka? " Cewar Mumy da shigowar ta room d'in kenan, cikin farinciki ta k'arasa inda yake ta zauna tare da rik'o hannun shi tana goge hawayen idonta da d'ayan hannun, don sosai lalurar Sabeer ta firgitata sosai don yau kwanan shi 3 a kwance sai drip kawai da ake sanya mishi tunda yayi doguwar suman nan. Bai kulata ba duk yanda taso da yayi magana kawai sai ya kwanta tare da juya mata baya, runtse eyes nashi yayi yana tunano musabbabin abin da ya sanya shi cikin wannan halin, tar komai ya dawo mishi cikin brain nashi a hankali wasu hawaye masu zafi suka fara sauko mishi idan ya tuna yanda Suhaima ta cuce shi bai ta6a zaton Suhaima zata aikata hakan ba agare shi. Tashi ya yunkura yayi dakyar sai dai ko taku biyu bai yi ba sai yayi luuu kamar zai fad'i da sauri Mumy ta taro shi ya fad'o jikinta a kid'ime tace "Son ya zaka tashi cikin wannan yanayin kasan jikin ka babu kwari? " Cikin fusata yake cewa "Mumy ki barni na kai Suhaima k'ara akan abin da tayi min bazan kyale ta ba sai na d'auki fansa akanta na yanda take zubar min da yara na " Wani dad'i ne ya kwaranya cikin heart d'in Mumy amman sai ta marairaice tare da cewa "Haba Son ka kyale mata Allah sai ya saka maka yanzu samun lafiyar ka shine kwanciyar hankali na " Nan Sabeer ya birkice mata sai yaje ya sanya an kama Suhaima sai sumbatu yake daga kasan ba'a ciki hankalin shi yake ba, gani haka ya sanya Mumy yi mishi allurar bacci babu dad'e wa bacci yayi awon gaba dashi ta gyara mishi kwanciyar zuciyar ta fal farinciki.... ******** Cikin tsananin 6acin rai Yaj Aliyu yake cewa "Ki fita daga gidan nan Jiddah bana son ganin ki daga ke har 'yan uwan ki macuta " Cikin rikicewar kuka Jiddah take rik'e k'ofar shiga gidan saboda kok'arin rufeta da Yah Aliyu yake yi "Yaya Aliyu don Allah kayi hak'uri ba laifi na bane inason ku wallahi baza'a ta6a had'a baki dani a cuce ku ba ka tsaya nayi maka bayani" "Tun kafin naji miki ciwo Jiddah ki fita daga gidan nan nace zan iya illata ki idan baki tafi ba " "Allah Yaya Aliyu sai dai ka kashe ni bazan tafi ba, Suhaima Aunty Aliyah kuce mishi ya tsaya ya saurare ni Suhaima ki fad'a mishi babu hannuna wajen aikata miki haka " Jiddah ta fad'i tana kallon su Suhaima da Aunty Aliyah da suke gefe suna kuka ganin yanda Yah Aliyu yake korar Jiddah. Wani irin k'ara Jiddah ta saki da k'arfi saboda yanda Yah Aliyu ya rufe k'ofar da k'arfi har yana mutstsukewa da hannun ta, a rikice Suhaima ta k'arasa wajen tare da bud'e k'ofar Jiddah ta zame hannun ta har sunyi ja sosai tana kok'arin k'arasa wa wajen Jiddah Yah Aliyu ya damk'ota tare da rufe k'ofar gidan 6am har da sanya sakata, Suhaima naji kukan Jiddah tana bubbuga k'ofar sai dai bata da ikon bud'e wa wani kuka ta fashe dashi tare da shiga d'akinta da gudu........... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 97-98* Jiddah ta dad'e tana kuka anan sosai Babaa Lantana ce da Baba Adamu suke rarrashin ta don Yah Aliyu yak'i tsayawa ya saurare shi ranshi a 6aci yake sosai da abin da akayi wa k'anwar shi. "Babaa Lantana Baba Adamu ku taimaka min ku fahimtar da Yaya Aliyu wallahi ba had'in hannuna cikin abin da akayi wa Suhaima ni kaina yanzu binciken da nake yi kenan don gane gaskiya amman bai kamata Yaya Aliyu yayi min haka ba? " Ta k'arasa maganar tana goge hawaye. "Yanzu dai yanda Aliyu ya d'auki zafin nan ki bari har zuwa lokacin da ya huce don yanzu bazai tsaya sauraren komai ba ranshi ba k'aramin 6ace yake ba " Cewar Baba Adamu kenan. "Kiyi hak'uri Jiddah ki koma gida duk lokacin da ya huci zan sanya Aliyah ta kirawo ki awaya sai kizo " Gid'a kanta Jiddah ta iyayi kawai daga nan ta shiga mota driver ya jata, wani tsanar familyn su ya d'arsu cikin zuciyar ta yanzu da ba don sun aikata haka ba da tuni Suhaima tana tare da masoyin ta Yah Sabeer, dole zanyi iya yi na do ganin an kama wanda ya aikata haka bazan iya jure rashin Suhaima kusa da ni ba ina sonta, lallai Yah Sabeer ba k'aramin ganganci yayi ba na korar Suhaima don koda zata dawo gidan shi sai yasha wahala ba k'arama. Tun daga lokacin abubuwa suka fara canjawa don Sabeer sai da yayi wajen sati biyu a hospital kan a sallame shi, yayi wani irin ramewa sosai ko abinci baya iya ci sosai sai an matsa mishi ga wata k'asumba da ya tara yak'i yarda yaje aski agyara mishi ita sannan Mumy ma tayi kok'arin cire mishi ita da kanta amman yak'i yarda, gaba d'aya Sabeer ya canja ya koma wani iri kamar bashi ba yana zuwa aiki office amman daya dawo fah idan ya k'unshe kanshi a d'aki baya sake fitowa sai dai idan sallah zai tafi masallaci. Ya fara zama mafad'aci abu kad'an zai fara fad'a baya shiga harkar family d'in shi kamar da, har wani lokacin ita kanta Mumy tsoron kulashi take tana mai mamakin me ya canja mata d'anta lokaci d'aya haka, idan ya sake da wani suna hira har da murmishin shi to Daddy ne kawai don ko Dr Ahmad d'an fillo baya sake musu kamar da, sosai abin yake damun su a ransu Jiddah ma baya kulata sosai kamar da sai gaisuwa ce kadai ke tsakanin su idan ma har sun had'u, ita kanta Jiddah duk yanda take da son Sabeer tana jin haushin shi. Duk yanda yaso da ya fitar da Suhaima daga zuciyar ya kasa ji yake kamar ma k'ara mishi sonta yake, baya iya bacci kullum sai yaga pic's d'in ta, yayi kukan sosai wani lokacin ji yake daman zai iya cire zuciyar shi ya fito da ita ya goge son Suhaima aciki ko ya huta da abin da yake ji cikin zuciyar shi. Ta 6angaren Suhaima itama kusan haka al'amarin suke sai dai ita ta cigaba da zuwa makarantar islamia kullum da yamma duk da tayi saukar alqur'an but tana sake fad'ad'a karantun ta da sauran litattafai, gashi bata yi rama kamar yanda Sabeer yayi ba don ita sosai tana kok'arin yakice shi cikin ranta ga kuma yanda Yah Aliyu suke tsananin bata kulawa duk da har yanzu son Sabeer na mak'ale cikin zuciyar ta, kullum idan tayi sallah tana addu'ar Allah ya toni asirin wanda yayi mata wannan sharrin, har a makaranta tana fad'a wa Malamai su sanya ana mata addu'a Allah ya yaye mata abin da yake damunta, sai dai kuma tana shan zund'e akauyen shi don tasha surutai don ma Yah Aliyu yayi musu kyakkyawa warning duk wanda ya k'ara nuna k'anwar shi da hannu yana aibatata sai ya sanya an d'aure shi da wannan warning da yayi musu suka samun sauk'in abun don Yah Aliyu yana da arzik'i duk ta sanadiyyar noma da kiwon da ya rik'e hannu bibbiyu. Ko zancen Sabeer ba'a k'ara tayar dashi ba agidan ba kowa yabar abun cikin zuciyar shi, duk wani kyautata wa Yah Aliyu yana kok'arin yiwa Suhaima duk abin jin dad'i yana kok'arin bata shi. Ya sanya anyi gyaran gidan sosai ya kashe kud'i sosai agyaran, ginin zamani na dai dai talaka mai rufin asiri ya sanya akayi mishi, sai gidan Baba Adamu suka koma akayi gyaran, inda Suhaima ta samu yalwataccen d'aki babba guda d'aya har da toilet aciki ya sanya akayi mata, sai kuma palo babba da akayi da 2 bedrooms wanda ya kasance na Aunty Aliyah da nashi sai kitchen da toilet a waje, amman filin tsakar gidan ya ragu sosai gashi ko'ina yasha sumunti dak'unan tiles ya sanya aciki, hatta furnitures sababbin ya sanya na dai dai mai rufin asiri ban da kayan kallon da ya had'a musu duk wannan abin Yah Aliyu yayi shine don kawai faranta ran Suhaima saboda yana ganin tayi rayuwa ta cikin kud'i tsayin wasu watanni ta fara sabawa da jin dad'i shine dalilin da ya sanya yayi haka duk da ya san bai kai rabin rabin kyan da gidanta na da yake dashi. Suhaima taji dad'in abin da Yayan nata yayi mata kawai don ganin farincikin ta, nuna mishi farincikin ta da yayi ne a lokacin ya sanya shi cikin jin dad'i da walwala wanda rabon da ya kasance cikin haka tun kafin Suhaima ta dawo gida, acikin wannan lokacin ne yaje ya zana wec and neco a wata secondary ta gaba da kauyen su don makarantar ma ta shiga cikin gari sosai, Suhaima ba k'aramin jin dad'i tayi ba na komawar da Yayanta makaranta da zai yi, shima yace mata ta kwantar da hankalin ta zai nema mata wata university d'in ta d'ora karatun ta sai ya cikawa mahaifiyar su burinta insha Allah na ganin sun samu ilimi sosai, saboda jin dad'in wannan maganar Yah Aliyu sai da Suhaima tayi kuka ashe daman zata cikawa kanta buri na ganin tayi karatu mai zurfi. Bayan exam d'in su Yah Aliyu ta fito ne dakyar da sod'in goshi ya samu gurbin karatu a jami'ar Buk da taimakon wani Alhaji da yake kai mishi kwai da kaji duk karshen wata gidan shi a birni, duk da kyan da takardun Yah Aliyu sukayi inda zai yi karatun Mass com inda Allah ya taimake shi ma yana da machine d'in hawa sai dai cacar kud'in mai da haka ya fara karatun shi cikin nasara da kwanciyar hankali. *********** _*AFTER 7 MONTHS*_ Sabeer ne na hango yana fitowa daga side d'in shi duk yayi wani tamkar ba Sabeer d'an gayu d'an kwalisa ba yana sanye cikin wani jallabiya milk mai yankakken hannu, tafiya yake kamar zai fad'i saboda yanda jikin babu kwari, bedroom d'in Mumy ya nufa yana son fad'a mata yana son shan coffee a dafa mishi. Har ya d'ora hannun shi kan handle d'in bud'e k'ofar zai murd'a yaji muryar Mumy tana cewa "Ga wannan kud'in na sallame ki daga yau ki koma kauyen ku yanzu yanzun nan don na fahimci sosai Daddyn Sabeer ke zargin ki kuma naga yana sanya miki ido a duk wani motsin ki nasan idan ya cigaba da hakan asirin mu ne yake daf da tonuwa, tunda kinyi nasarar raba wannan shegiyar matsiyaciyar da d'ana aikin ki ya gama, idan kuwa kika yi kok'arin tona min asiri kinsan zan iya sanya wa a kulle ki har karshen rayuwar ki ko a 6atar min da ke " Cikin rawar jiki mai aikin tace "Wallahi Hajia bazan ta6a tona miki asiri ba baza ki k'ara ganina ba ma har abada " Wani murmishi Dr Faridah ta saki kafin tace "Good da ya fiye miki alkhairi kuwa tashi maza ki had'a kayan ki ina son yau kibar gidan nan " "Toh toh Hajia yanzu ma kuwa " Ta kwashe kud'in mai yawa da Dr Faridah ta bata ta fito zata fita daga d'akin. Jikin Sabeer wanda ke rawa kamar mai yin rawar sanyi yayi hanzarin barin bakin k'ofar ya 6uya a wani corridor yana kallon ta ta wuce can part d'in su na masu aiki. Cikin zafin nama Sabeer ya bita a baya da sauri aikuwa yayi nasarar ritsata zata shiga d'akin, kallon Sabeer take tuni cikinta ya d'auki k'ara yana hautsinawa ganin yanda ya rikid'a kamar wani zaki. Bata ankara ba ya dalla mata mari har guda biyu zata yi ihu yayi saurin sanya hannun shi d'aya a baki alamar tayi shiru yana zare mata ido wad'anda suka yi ja jikin shi yana rawa sosai, ba shiri ta mayar da bakin nata ta rufe shi k'am har da d'ora hannu ta damk'e bakin nata. Kafin ta ankara wani fitsari mai zafi ya kubce mata yana tsiyaya sai faman matse kafa take da sauri Sabeer yaja baya kafin yana yarfe hannu tare da duba jikin shi ko ta 6ata shi, belt d'in jikin shi ya cire ya fara zuba mata, sai rawar disco take gashi ba damar yin ihu, gani yayi belt d'in kamar bata shigarta sai kawai ya yar da ita ya nufe ta ya shak'e mata kamar zai kashe ta tuni idanun ta sun firfito kamar zasu zazzago ga dakyar take sauke numfashin ta, Allah ne ya kawo Daddy hanyar wajen zai tafi garden yaji kakari awajen ya nufo wajen, ganin abin da d'an nashi yake kok'arin aikatawa da sauri ya nufi wajen dakyar ya 6am6are ta daga hannun shi sai wani huci yake fuskar nan tashi tayi ja. Yana sakin ta ta zube tana jan numfashi cikin rud'ewa Daddy yake girgiza Sabeer yana cewa "Son me kake shirin aikatawa ne me tayi maka iyeeeee? "" Cikin rawar murya Sabeer yake nuna ta da hannu yana cewa "Dad.... Daddy kace ta tayi magana ita... itace ta... take zubar wa da Suhaima ciki " "What! " Cewar Daddy da sauri. "Keee fad'a mana uban da ya sanya ki aikata hakan? " Cewar Daddy a fusace, cikin rawar murya tace "Don Allah kuyi hak'uri wallahi sanya ni akayi " "Wane ya sanya ki? " Murya na rawa da jiki na 6ari ta kasa magana sai da Sabeer ya daka mata wata razananniyar tsawa sannan ta bud'e baki dakyar tace "Wallahi Hajiya ce ta sanya ni ba laifi na bane " "Wacce Hajia? " Cewar Daddy cikin zak'uwa. "Hajiya Faridah ce wallahi take sanya ni zubawa Suhaima maganai a abu tasha sai cikin ya zube " "What!? " Cewar Daddy da Sabeer a lokaci d'aya suka furta hakan cikin matuk'ar razana tare da firgita da jin abin da tace, sulalewa Sabeer yayi a k'asa tare da d'ora hannun akai shikenan Mumy ta cuce shi ta gama dashi wayyo Allah nah Suhaima daman ba laifin ki bane yanzu ta ina zan iya dawo da Suhaima a rayuwa ta. Wata zabura da yayi sai da ya firgita Daddy cikin tsananin fusata ya nufi cikin palo yana kwallawa Mumy kira, yayin da Daddy ya tura Larai cikin d'aki ya sanya key ya 6ame k'ofar don baza'a barta ta gudu a banza ba sai ta fuskanci hukunci dai dai da abin da ta aikata, kafin ya bu bayan Sabeer don yau za'a yi tashin hankali.............. Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 99-100* Mumy har ta fara gyangyad'in bacci acikin bedroom d'in ta bacci ne take son yi ko hospital bata lek'a ba sai da yamma, kamar cikin mafarki taji Sabeer na kwalla mata kira a firgice ta fito saboda tasan wannan kiran bana lafiya bane. Cikin sauri take taka steps na bene saboda har yanzu Sabeer bai bar kiranta ba, cikin sauri ta k'arasa wajen shi inda yake tsaye tsakiyar parlour yana faman kiranta ga hawaye da suke zuba a eyes nashi. "Son lafiya irin wannan kira haka? " Kallon ta yayi hawaye na kwaranya a idon shi yace "Mumy ashe bakya son bakya kaunata ko kad'an Mumy kin cuce ni kin cuce ni! " Gaban Mumy ne yayi wani irin fad'uwa sosai da sauri ta dafe kirjin ta da hannu tare da zaro ido irin na shiga rud'u tace "Son me kake nufi, me nayi maka har na cuce ka anya kanka d'aya ko wani abun kasha ne, ina matsayin mahaifiyar ka zan cuce ka ne ? " Idanun shi jawur yace " Mumy sam baki cika uwa mai bawa d'anta farinciki a rayuwa ba, kin rabani da 'ya'yana har biyu tun kafin su zama mutum kika zubar min dasu bayan haka kin rabani da mata ta Suhaima anya Mumy zan iya yafe miki kuwa? " Sauran kad'an Mumy ta kife a k'asa tsabar firgita da kalaman Sabeer, amman sai ta wayance da cewa "Haba Son wanne munafiki ne ya shirya maka wannan zancen kamar a mafarki, kada ka yarda da wannan shirmen zancen" Kallonta Sabeer yake ba don mahaifiyar shi bace da idan ya shak'eta sai ta kusan daina numfashi, kasa magana ma yayi saboda takaici da bak'inciki sai wani irin kallo da yake mata mai tattare da nuna kin cuce ni, wannan kallon da Sabeer yake yiwa Mumy shi yafi komai d'aga mata hankali. "Kada ki nemi ki raina mana hankali Faridah daman nasan duk wannan abun da ya faru da sanya hannun ki aciki" Cewar Daddy a fusace wanda k'arasowar shi palourn kenan. Kukan kissa da munafurci Mumy ta saki tare da cewa "Na shiga uku Daddyn Sabeer ni kuke cewa na aikata hakan ta ina, na ta6a zuwa gidan Sabeer ko kuma na ta6a bata wani abun da hannuna taci cikin ya zube? " Sam Mumy ta d'auka Larai tabar gidan kamar yanda ta umarce ta. Cikin fusata Daddy yace "Ta dalilin 'yar aikin ki Larai mukasan komai, wadda kika turata gidan Sabeer don tana taimaka wa matar shi ayyukan gida ina fatan ba sai na k'arasa miki maganar ba kinsan komai tunda ke kika shirya hakan" Da sauri Mumy ta dafa bango don ganin yanda take kok'arin fad'uwa kallon Sabeer da Daddy take tamkar wasu sababbin hallita agabanta yanda suka rikid'e mata kamar wasu zakuna, can kuma ta aro jarumta ita ma afusace tace "Nayi nayi d'in! Duk abin da kuka fad'a na aikata su saboda bana son yarinyar da Sabeer i hate her bazan iya had'a zuri'a da shegiyar matsiyaciyar yariny..... " "Stop it Mumy! Kada ki k'ara aibata min mata ta, nagodewa Allah da ban sake ta ba!" Sabeer ya fad'a cikin hargowa, kallon shi Mumy kawai take cikin mamaki yau Sabeer ne yake mata tsawa. "Son ni kake yiwa tsawa akan waccan 'yar iskar yarinyar " Kuka ya fashe dashi kan yace "Daddy! Daddy ka fad'awa Mumy ta daina danganta Suhaima da wad'annan kalaman" Hugging nashi Daddy yayi yana bubbuga bayan shi yayin da yake jifan Mumy da wani irin kallo, saboda tsantsar rashin gaskiya Dr Faridah sai wani had'a uban gumi take kamar wadda ta had'iyi kunama abin da bata ta6a zaton zai faru da ita ba ya faru a lokacin da batayi tsammani ba ganin Sabeer d'anta kwaya d'aya tal da masoyin ta kuma mijinta suna kok'arin kubce mata a lokaci d'aya. "Ni fah Daddy duk abin da zaku yi kuyi min amman gaskiya bazan iya kar6ar yarinyar nan ba matsayin suruka ta " Cikin dakewa tayi maganar nan, da gudu Sabeer ya haye upstairs yana kuka zuciyar shi tana wani bugawa da k'arfi, cikin tsantsar 6acin rai Daddy yace "Faridah da bak'incikin ki ya kashe min yaro gwara na rabu da ke! " "What Daddyn Sabeer! Kana nufin akan waccan 'yar kauyen zaka sake ni? " "Ofcourse Dr Faridah bazan zuba ido ki kashe min d'a ba wanda ya kasance shi kadai ne d'ana a duniya" Matse hannun ta yayi da k'arfi tare da murd'asu har sai da tayi k'ara kafin yace "Kina tantama ne bazan iya ba yanzu zakisan baki da wayo yarinya " Wani irin lugude kirjin Mumy yake kamar zuciyar ta zata faso kirjinta ta fito, ganin tana daf da rasa mijinta amman duk da haka tana nan kan bakanta tasan Daddy bazai iya rabuwa da ita ba koda ya sake ta sai ya dawo da ita, tunanin ta ne ya katse a lokacin da Daddy yace "Faridah ki tafi gidan ku na sa....... " Kafin ya k'arasa fad'a yaji anyi sauri an toshe mishi baki, d'ago kanshi da zai yi suka had'a ido da Dr AhmadAhmad d'an fillo ranshi a 6ace yace "Haba Hussein kamar baka da hankali taya zaka biyewa zuciyar ka ta aikata abin da zaka zo kana dana sani, ko da wasa kada ka k'ara yunkurin cewa zaka saki Faridah don duk cikin surukaina nafi kaunarta sakinta da zaka yi shine datse duk wani alak'a tsakanin mu da kai " Sakin baki Daddy yayi yana kallon mahaifin nashi cikin mamaki kafin yace "Abbah! Yanzu baka ga laifin Faridah anan ba?" Cikin irin I don't care d'in na yace "Yo wane baya yin kuskure Hussein tun da abun ya wuce ba shikenan ba a kiyayi gaba kawai " Haushi ne ya turnik'e Daddy kallon Faridah yayi kafin yace "Abbah! Duk da ka hanani sakinta amman ta tafi gidan su bazata dawo gidan nan sai Sabeer ya dawo da Suhaima matsayin matar shi " Yana gama fad'in haka ya wuce fuuuu a fusace zuwa wajen Sabeer don ya rarrashe d'an nashi, yayin da Dr Ahmad d'an fillo da Dr Faridah suka bishi da kallo kafin lokaci d'aya ta fashe da kuka ganin yanda komai ya jagule mata lokaci d'aya ta rasa d'anta da mijinta!........ _kuyi hak'uri da wannan fan's_ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 101-102* Kallon ta Dr Ahmad d'an fillo yayi cikin jin tausayin ta yace "Faridah kiyi hak'uri babu inda zaki je har idan ina raye, ki cigaba da zaman ki kamar da nasan ta inda zan 6ullowa al'amarin " Gid'a kanta take kamar k'aramar yarinya tana goge hawayen face nata, bayan ya gama rarrashin ta ne sai ya tafi yayin da ita kuma Mumy ta nufi upstairs zata fara hawa steps sai ga Daddy nan zai sakko. Suna had'a ido ya sakar mata harara kafin yace "Me kike har yanzu baki bar min gida na ba!? " Ko kallon inda yake Mumy bata yi ba ta wuce shi da sauri zuwa side d'inta da kallo ya bita kafin ya girgiza kanshi kawai, ya wuce zuwa 6angaren masu aiki ya bud'e Larai da take cikin d'akin wadda ta kasa zaune ta kasa tsaye tsabar firgita da razana. Jin an bud'e k'ofar nan ta jiyo a rikice ganin Daddy ne ya sanya ta zubewa a k'asa cikin tsorata tace "Don girman Allah Alhaji kayi hak'uri ka barni na tafi nayi alkawarin bazan sake maimaita abin da nayi ba wallahi " "Ya isa haka zan barki ki tafi amman kiji tsoron Allah a duk inda kike kisan yana ganin ki komai zaki aikata, ina son ki tafi kada ki k'ara dawo min gida " Abin da ya sanya Daddy kyale ta ganin ga babbar mai sanyawa a aikata laifi amman an hanashi d'aukan mataki akanta shi ya sanya rabuwa da ita, nasiha yayi mata kan ya bar d'akin.Aikuwa cikin rawar jiki ta sungumi ghana must go d'inta ta k'ara gaba da sauri ko waiwaye bata yi. Cikin kwana 2 gidan ya koma shiru babu walwala acikin shi kamar da, Sabeer baya iya zuwa ko'ina kullum yana cikin bedroom a kwance yana tunanin ta yanda zai tunkari Suhaima da wanne ido zai kalle ta yace ta koma gidan shi baya ga cin mutuncin da yayi mata tare da 'yan uwanshi tun da ta tafi wajen 7 months bai je inda take ba. Wad'annan tunanin ne idan yayi suke matuk'ar hargitsa mishi kai ya rasa sukuni cikin zuciyar shi, ta 6angaren Mumy da Daddy ma babu wata jituwa tsakanin su kowa yana side shi gashi babu mai shiga harkar wani acikin su, duk da Mumy kusan kullum sai tayi kuka a 6oye saboda ganin d'anta da mijinta sun guje mata amman bata ta6a nuna musu hakan a fili ba. Sabeer kasa hakura yayi sai kawai ya nemi Jiddah a waya dakyar Jiddah tayi picking wayar saboda haushin shi take ji ya rabata da Suhaima da tasan sanadin auren Yah Sabeer zai kawo matsala a tsakanin ta dasu Suhaima da bata bayar da goyon baya. Murya ciki ciki ta amsa mishi sallamar tashi, d'an murmishin yak'e yayi cikin zuciyar shi yana cewa, Jiddah da zaki fahimci halin da nake ciki yanzu da kin tausaya min amman a fili sai yace "Uhmm Jiddah kina fushi da ni koh? " "Ni kuma! Me kayi min da har zanyi fushi da kai? " "Saboda na rabu da k'awar ki mana alhalin kina sane da ban saketa ba saboda son da nake mata " "Tabd'ijam Yaya a haka kake son Suhaima bayan baka tsaya kayi bincike ba ka kore ta daga gidan ta? " Wani irin abu ne ya taso ya lullu6e mishi cikin zuciyar shi na tsananin nadamar abin da ya aikata kafin ya sauke numfashi mai zafi yace "Ina son Suhaima Jiddah har yau amman nasan bai kamata na kore ta ba, bincike ne farkon abin da ya kamata nayi sai na kasa controlling d'in zuciya ta har takai da na aikata hakan, amman yanzu na gane gaskiya " "Da gaske kake Yaya an gane wanda ya shirya makircin nan!? " "Ehhh Jiddah duk wannan shirin Mumy ne don kawai ta raba ni da Suhaima " No wonder ai nasan itace zata aikata hakan don kuwa ita nake zargi fiye da kowa, fad'in Jiddah cikin zuciyar ta kafin ta d'ora da cewa "Alhamdullilah nagodewa Allah da ya sanya k'awata ta fita daga zargi " "Yanzu ki fad'a min ta ina zan bi don na dawo da mata ta na kasa tunanin mafita komai ya hargitse min wallahi" "Tabd'ijam Yaya babu ruwana ni kaina ka shafa min laifi wajen Yah Aliyu sau biyu nake zuwa yake korata baya barina na shiga gidan haka nake dawo wa, bani na aikata laifi ba amman Yah Aliyu ya kasa tsayawa ya fahimci ne babu hannuna cikin aikata wannan abun wallahi " Ta k'arasa maganar cikin rawar murya hawaye na zuba daga idanun ta, wani fad'uwar gaba Sabeer ya tsinci kanshi aciki kafin ya iya bud'e baki dakyar yace "Yanzu kenan babu wani idea a wurin ki wanda zai sanya ni zuwa wajen Suhaima na dawo da ita? " "Ni dai shawarar da zan baka kawai ka je wurin Suhaima duk abin da Yah Aliyu zai yi maka ka hakura ka daure zuciyar ka har zuwa lokacin da zai sakko ya hakura, don Yah Aliyu mutum ne mai zafi amman yana da tausayi sosai amman ina mai baka shawara kada Mumy taji labarin tafiyar ka can don zata iyayin wani abun don kawai Suhaima kada ta dawo wajen ka " "Nagode k'anwata" "Babu komai Yaya Allah taimaka " Dakyar ya iya cewa Ameen sannan suka yi sallama, tunani ya fad'a sosai kafin daga k'arshe ya fito daga bedroom d'in shi. Parlour ya fito ya tarar da Daddy yana zaune yana aiki a laptop yayin da Mumy take ta shirya kan dinning table duk da ba cin abincin suke ba wani lokacin idan tana free tana kok'arin had'a musu abinci da kanta. "Daddy ina son zan tafi England akwai wani abu da zanyi mai amfani acan " Kallon shi Daddy yake cikin mamaki kafin yace "Son me zaka je kayi acan? " "Daddy abun sirri ne idan na dawo zan fad'a maka shi " Gid'a kai Daddy yayi kan yace "Okay bari na sama maka visa wajen friend d'ina " "No Daddy na gama komai nan da 2hrs jirgi zai tashi " Kallon ban yarda da kai Daddy yake yiwa Sabeer, yayin da ya d'an yi murmishi kawai yana kauda kanshi don baya son had'a ido da Daddy. "Shikenan Son sai kaje ka fara shiri, amman kwanaki nawa zaka yi?" "Daddy ni kawai sai an ganni huh don na gaji da zaman gidan " "Ni kaina Son na gaji da zaman don haka mybe na biyo ka can sai kawai mu huta " Murmishi Sabeer ya d'an yi hannun shi zube cikin aljihun shi yace "Okay Daddy amman ni sai na fara yin gaba " 'Yar dariyar farinciki Daddy yayi ganin yanda yau Sabeer ya sake yana hira har da murmishin shi, akwai abin da Son ya shirya yi dole na bincike shi, fad'in Daddy cikin zuciyar shi. Sabeer bai d'auki wani abu masu yawa ba kayanshi set 3 ya sanya cikin k'aramar bag sai laptop d'in shi ko atm card's nashi bai d'auka ba, bayan ya gama ne ya shiga wanka a d'an jima a cikin bathroom kafin ya fito ya shirya cikin wani lallausan farin boyel perfumes different colour ya sanya. Yana gama wa ne ya d'auki bag d'in tare da rataya ta saman kafad'ar shi ya fito hannun shi rik'e da phone nashi, Daddy shima har ya gama shiryawa don raka Sabeer airport har sun fito zasu tafi sai ga Mumy nan da car key a hannunta tana cewa "Son muje nayi maka rakiya airport " Ko kallon ta Sabeer bai yi ba ya wuce zuwa cikin motar da Daddy yake zaune, fita suka yi daga gidan gaba d'aya motar Mumy tana bin bayan tasu Sabeer. Bayan sun k'arasa airport ne nan Sabeer yayi sallama da Daddy don uwa uwace kawai Sabeer ya sanya shi yiwa Mumy sallama ya wuce su ya tafi zuwa cikin airport ne, dad'i ya ishe Mumy ganin Sabeer ya kulata tana tunanin ko ya fara sakkowa ne, cikin mota ta wuce ta shiga driver yaja ta don hospital zata tafi. Sabeer ya d'auki wajen 30 minute's azaune kan ya tashi ya fito daga cikin airport d'in zuwa waje, tsayar da taxi ya fara kok'arin yi yaji an dafa mishi kafad'a a razani ya juyo 4 eyes suka yi da Daddy wanda ke faman yi mishi murmishi, ajiyar zuciya ya sauke kawai. Hannun shi Daddy ya rik'o zuwa cikin mota bayan sun zauna Daddy ya kalle shi kafin yace "Son tunda ka fad'a min zaka tafi England nasan ba haka bane jikina ya bani akwai wani abun dalilin da ya sanya ni ban tafi ba kenan, ina zakaje? " "Daddy kauyen su Suhaima zan tafi don na dawo da mata ta " "Hakan yayi kyau Son ina goyon bayan ka, amman bai kamata ka 6oye min ba " "Am so sorry Daddy bana son Mumy tasan da inda zan tafi don kada ta hanani dawo da Suhaima cikin rayuwa ta " Hannunshi Daddy ya rik'o kan yace "Ka tafi Sabeer idan ta kama duk tsayin lokacin da zaka yi acan kayi shi amman kada ka dawo gida babu Suhaima don yarinya ce mai hankali, ka daure duk wani yanayi da zaka fuskanta acan don nasan dole ka fuskanci hukunci awurin su, Allah yayi maka albarka ya taimaka maka ya tsare min kai a duk inda kake" Rungume Daddy Sabeer yayi yana goge hawayen da suka zubo mishi sun d'an jima a haka kafin Daddy yace "Ka tafi Son kada kayi tafiyar dare, amman kada mance ka kashe wayar ka saboda Mumyn ka idan ta ji shiru zata iya bibbiyar layin ka har ta gane a inda take ", gid'a kai Sabeer yayi. Fitowa suka yi daga mota jikin Sabeer duk a sanyaye Daddy ne yayi k'arfin tsayar mishi da taxi ya biyashi kud'i masu yawa tare da ce mishi ya kai Sabeer duk inda yake so, sallama Daddy da Sabeer suka yi har taxi d'in ta wuce Daddy yana tsaye a wajen zuciyar shi fal tausayin d'an nashi kafin ya juya ya shiga mota driver yaja shi sai gida. Idanun Sabeer a waje yana kallon yanayin gari amman tunani da fargaba tsoro fal cikin zuciyar shi ta yanda za'a kar6e shi gidan su Suhaima idan yayi duba da abin da Aliyu yayiwa Jiddah wadda bata da laifi ko kad'an a wannan abu da ya faru. Har k'ofar gidan su Suhaima d'an taxi d'in ya sauke Sabeer, dakyar ya iya jarumtar fitowa daga motar gaban shi na dukan goma goma don baisan me zai je ya tarar ba. Yana fitowa d'an taxi ya k'ara gaba sake gyara jakarshi yayi ta saman kafad'ar shi ya doshi gidan, amman duk takun da zai yi sai gaban shi ya fad'i a haka ya k'arasa k'ofar gidan. Kallon gida yake da mamaki sosai cikin fuskar shi ganin yanda aka gyara gidan kamar a birni ba'a karkara ba, zauren gidan ya kutsa kanshi, dakyar ya iya bud'e baki yayi sallama cikin sanyin murya. Amsa mishi sallamar akayi babu tantama yasan muryar Aunty Aliyah ce. "Suhaima sanya hijab d'inki ki duba ko bak'on Yayan ki ne kice ya jirashi ya shiga wanka " "Toh Aunty " Suhaima ta fad'a cikin tsintar kanta da fad'uwar gaba, d'aki ta shiga ta d'auko hijab ta sanya tare da nufar k'ofar zauren still gabanta bai bar fad'uwa ba. "Ka d'an jira shi ya shiga wank........ " Suhaima bata k'arasa maganar ba da zatayi sauran ta maka'ale a saman fatar bakinta ganin mutumin da ta had'a ido dashi, rufe idonta tayi ta sake bud'e wa ko mafarki take but still Sabeer take gani cikin eyes nata, tsayawa kawai taji jikinta na rawa zuciyar ta na bugawa da k'arfi kallonta yake cikin wani irin tausayin ta da yake ratsa shi ga wani sabon sonta da yake sake kwaranya cikin zuciyar shi, ita ma kallon nashi take kawai cikin mamakin me ya kawo shi gidan su ko dai ya zo ya baki takardar saki ne wannan tunanin da Suhaima tayi ya sanya firgita da tsorata. "Suhaima wane ne naji kin tsaya lafiya " Cewar Aunty Aliyah, maganar da Aunty Aliyah tayi shi ya dawo da Suhaima hayyacin ta, da sauri tabar wajen da sauri Sabeer ya biyo bayanta yana cewa "Suhaima ki tsaya ki saurare ni please " A tsorace Suhaima tayi bayan Aunty Aliyah ta 6uya ganin sauran kad'an Sabeer ya cafkota, a firgice Aunty Aliyah take kok'arin cewa Sabeer ya gudu ya bar gidan amman kafin ta bud'e bakinta Aliyu ya fito daga toilet sanye da jallabiya ajikin shi. Kallon Suhaima da Aliyah yayi ganin gaba d'ayan su a razane yasa shi kallon inda suke kallo aikuwa suka had'a ido da Sabeer, kamar wani zaki ya nufi inda Sabeer yake tsaye wanda ko gezau bai yi ba na nuna tsoro hasali ma gaba d'aya hankalin shi na kan Suhaima............. Aishat A Muh'd Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 102-103* Afusace Yah Aliyu cakumi wuyan Sabeer ya matse da k'arfi idanun shi tuni suka yi ja ya fara wani irin tari, cikin fusata yake cewa 'Me kazo yi kuma, bayan ka koreta daga gidan ka ina fatan takardar sakin ta ka kawo min don k'anwata bazata ta6a komawa gidan ka ba? " Dakyar Sabeer yake jan numfashi don ba k'aramin shak'a Aliyu yayi mishi ba, cikin murya k'asa k'asa yake cewa "Nazo ne domin na baku hak'uri akan abin da ya faru na kuma dawo da Suhaima gidana " Dad'a shak'e shi Aliyu yayi kan yace "Kaiii asuwa da har zaka sanya Suhaima dawowa gidan ka, k'anwata ta barka har abada bakai ba ita " Sabeer na kok'arin magana Yah Aliyu yaja shi tare da watsa shi waje ya mayar da k'ofar ya rufe har da sanya sakata, kallon su Suhaima da Aliyah yayi ganin yanda suke kuka sosai hararar ya maka musu kan ya wuce d'aki yana huci. Suhaima ma da gudu ta shige d'akinta tana kuka da ta rasa na mene, yayin da Aunty Aliyah ta tafi wajen Aliyu ko zata rarrashe shi yayi hak'uri amman tana fara magana da ya buga mata wata tsawa batasan lokacin da ta tsallake Ameer ta wuce d'akin Suhaima da gudu ba, wanda har taso sanya Aliyu dariya amman ya matse dariyar. Afirgice Suhaima ta juyo jin an shigo d'akin ta da gudu ganin Aunty Aliyah ce ya sanya ta sauke ajiyar zuciya tana goge hawayen fuskar ta tace "Aunty lafiya kuwa " Zama tayi kan tace "Hummm Suhaima Yayan nan naki ya d'auka da zafi sosai wallahi don zuwa nayi na bashi hak'uri amman wata tsawa da kwantsama min bansan sanda na sanya gudu ba, ina tausayin Sabeer nasan ba laifin shi ba ne laifin shi d'aya da yace ki bar mishi gidan shi " Suhaima bata ce komai ba kawai sai ta zame ta kwanta tare da d'ora kanta saman k'afar Aliyah zuciyar ta a cunkushe take sam ta rasa abin da yake damunta. Sabeer kuwa tun lokacin da Yah Aliyu ya watsa shi waje kasa tashi yayi awajen kawai ya zauna tare da janyo bag d'in shi ya d'ora saman k'afar shi ya fad'a kogin tunanin yanda zai shawo kan wannan matsalar, gaba d'aya wuyan shi ya rik'e ko iya juyashi sosai baya yi sabida shak'ar da yasha a hannun Aliyu, wai shi Sabeer shine aka watso shi waje kamar shi da kud'in shi da gatan shi amman duk A SANADIN SO komai na rayuwar shi ya canja. Yana nan zaune aka yi kiran sallahr mangarib yana kok'arin tashi ya tafi masallaci ko zai samu ruwan alwala yaji an bud'e k'ofar an fito, sai da gaban Sabeer ya fad'i ganin yanda Aliyu ya tamk'e fuska tamkar bai ta6a dariya ba. Kallon Sabeer yake cikin mamaki kafin yace "Wai kai wanne irin mutum ne nace kabar min gidana bama buk'atar ba ana dole ne k'anwata ta tsane ka bata sonka ina son kawai ka rubuta mata saki ka bata tun muna mu biyu da kai kaji na fad'a maka " Yana gama fad'in haka yaja tsaki tare da wuce wa, wani bak'inciki ne ya lullu6e Sabeer ganin wanda a girme bazai girme shi ba yake fad'a mishi magana son ranshi, da zai iya cire son Suhaima ya ajiye shi gefe da yayi don kawai samun sauk'in halin da yake ciki da me zai ji abubuwa gaba d'aya sun hargitse mishi ya rasa samu mafita. Dakyar ya lalla6a yaje masallaci can ya samu ruwa yayi alwala tare da bin jam'in sallahr mangarib bayan an idar ne yana zaune a masallacin yana addu'ar Allah ya sassauta zuciyar Aliyu ya kyale mishi Suhaima kada ya rabasu, har aka kira sallahr ishsha bayan an idar da sallahr ne kowa ya watse sai shi kadai ya rasa wajen zuwa. Yana nan zaune har wurin 9 na dare ga wasu sauro da suke kai mishi cafka ga zafi da duhu dulum a wajen ga wata azababbiyar yunwa da take k'ulle mishi ciki, kamar a mafarki yaji ana kiran shi cikin mamaki da sauri ya tashi ya fito daga cikin masallacin. Baba Adamu ya gani tsaye da torchlight a hannun shi, tsugunnawa Sabeer yayi ya gaida shi amsa wa yayi kan ya kama hannun Sabeer suka doshi gidan Aliyu. Atsakar gidan ya tarar da Aliyu, Suhaima, Aliyah, Babaa Lantana suna zaune ran Aliyu a 6ace yake don sosai Aliyah ta shammace shi taje ta fad'a wa su Baba Adamu halin da ake ciki sai aika mata da harara yake yi saboda yaso ya kar6i takardar sakin Suhaima ya fatattaki Sabeer kafin su ankara, sai gashi Aliyah ta shammace shi. Zama Sabeer yayi gefen Baba Adamu sanann ya fara magana akan rashin kyautawar da Sabeer yayi na tsayawa yayi bincike kafin ya kori Suhaima, sanann ya d'ora da yiwa Aliyu nasiha tunda ya gane gaskiya bai kuma kyauta da abin da yayi ba har yazo domin ya nemi afuwar su ya kamata ya hakura kowanne d'an adam bai cika goma ba. "Baba ni kawai ya bata takardar ta kawai yayi tafiyar shi Suhaima bazata koma gidan shi ba" "Baza'a yi haka ba Aliyu a tambayi Suhaima tana son komawa tunda ya gane laifin shi har ya bada hak'uri kamata yayi ayi mishi afuwa " Kallon ta Baba Adamu yayi kan yace "Suhaima ina son ki fad'a min tsakani da Allah kina son komawa gidan Sabeer? " Da sauri ta d'ago kanta ta kalli Baba Adamu kafin ta mayar da kallonta kan Sabeer gaba d'aya ya wani marairaice fuskar shi ta koma kalar tausayi sosai yana rok'an ta da tayi hak'uri ta amince, d'auke idonta tayi akan shi ta mayar dashi kan Yah Aliyu sai taga yanda ya wani had'e fuska gashi ya tsattsare ta da ido, ta rasa yanda zata yi zata bi bayan Sabeer ko zata bi bayan Yayan ta idan bata mance ba Yayan ta shine uwa ubanta don bata da wanda ya fishi duk duniyar nan, idan matsala ta sameta shi zata tunkara taya zata dubi tsabar idon shi ta za6i miji wanda bashi da tabbas. "Kin shiru ke muke jira Suhaima " Cewar Babaa Lantana kenan. Kasa magana kawai tayi ta fashe da kuka sosai don batasan wanda zata bi bayan shi ba da gudu ta shige d'aki tare da sanya key. Wata ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yayin da Sabeer kanshi yake sunkuye wasu hawaye na zuba daga cikin su duk shi yajawa kanshi yayi wasa da damar shi gashi komai ya rikice mishi, tsugunnawa yayi tare da cewa "Ina rok'an ka Aliyu ka taimaka min kayi hak'uri akan abin da nayi wa Suhaima wallahi nayi nadamar korar ta da nayi bazan sake maimaita hakan ba insha Allah kuma zan sanya ido sosai tare da d'aukan mataki ga duk wanda yake kok'arin cutar min da ita " Tsaki Aliyu ya saki tare da d'auke kanshi yana cewa "Tun da Suhaima tak'i amincewa sai ka tashi ka koma inda ka fito " "Babu inda zanje har ina nan har sai lokacin da Suhaima ta yafe min ta amince zata koma gidana " Ta6e baki Aliyu yayi kan yace "Ba dai agidan nan ba kuwa " "Bashi da inda ya wuce nan Aliyu dole ya zauna tare da ku " Cewar Baba Adamu yayin da Aliyu yace "Baba ni bani da wani d'akin kwana anan gidan " "Ga d'akin matar shi nan " Fad'in Babaa Lantana kenan da duk tausayin Sabeer ya lullu6e ta. "Babaa kiyi hak'uri amman gaskiya ban amince mishi da ya kwana anan d'akin ba " Duk yanda yaso su Baba Adamu su taushi Aliyu yak'i basu had'in kai har sai da ran su Baba Adamu da Babaa Lantana ya 6aci sosai kafin dakyar ya amince da sai dai ya kwana a zauren gidan. "Kana ji Sabeer zaka iya kwana a zauren gidan? " Da sauri Sabeer yace "Eh Baba zan kwana nagode sosai Allah ya k'ara girma " "Amin Sabeer ba komai, yanzu Aliyah tashi ki zuba mishi abinci yaci " Aunty Aliyah da tunda aka zauna bata tsoma baki ba ta tashi ta nufi kitchen tana zuba mishi abinci, bayan ta zuba ta kawo mishi gaban shi ta ajiye tare da kawo mishi ruwa mai sanyi na randa ta ajiye mishi. Saboda yunwar taci ta cinye shi kad'an ya iyacin abincin yasha ruwa, zama yayi kawai tare da zabga tagumi abin duniya yayi mishi yawa, bayan su Baba Adamu sun gama ta6a hirar su ne suka yi sallama suka tafi nasu gidan. Tashi Sabeer yayi ya koma zaure saman wani dutse ya zauna wanda ake tokare k'ofa dashi duk kayan jikin shi sunyi squeezing gashi sunyi datti wanka yake son yi sai dai babu fuskar hakan, had'e kai da gwiwa kawai yayi ga wani zafi, kukan sauro da cizon shi da suka addabi Sabeer dashi. Yah Aliyu ne ya shigo gidan ya dawo daga rakiyar su Baba Adamu kenan, rufe k'ofar gidan yayi sannan ya wuce cikin gidan ko kallon inda Sabeer yake bai yi ba. Sabeer na zaune anan yaji motsi d'ago kanshi yayi suka had'a ido da Aliyah saboda akwai hasken farin wata, tabarma ta mik'a da pillow tace "Gashi nan Sabeer kayi hak'uri " Girgiza kanshi yayi kan yace "Auntyn mu nine da baku hak'uri don ku nayiwa laifi, nagode da kulawar ki agare ni ina rok'an ki da ki cigaba da bawa Suhaima hak'uri har ta huce " Girgiza kanta tayi cikin tsananin tausayin shi don kallo d'aya zaka yi mishi kasan yana tattare da damuwa sosai, kar6ar tabarmar yayi da pillown yayin da Aunty Aliyah tace "Insha Allah zanyi kok'arin daidaita ka da Suhaima da Yayanta " Tana gama fad'in haka ta wuce da sauri don fakar idon Aliyu tayi ta fito ta kawowa Sabeer tabarmar, kallon ta yake irin kallon tuhumar nan d'an 6ata fuska itama tayi kan tace "Lafiya kake kallo na haka kamar wadda tayi mata sata? " D'an girgiza kanshi kawai yayi baice komai ba ya kwanta, ajiyar zuciya Aliyah ta saki ganin bai fahimci inda taje ba, kwanciya ita ma tayi gefen shi tana tunanin yands zata 6ullo wajen ganin Aliyu ya sassautawa Sabeer............ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 104-105* Cikin wannan daren Suhaima bacci kasa d'aukan ta yayi ta rasa abin da yake damunta tun da Sabeer yazo ta rasa nutsuwar ta wanda har takai da yiwa kanta tambayoyi tana son Sabeer ne har yanzu, tausayin shi take ji ko kuma har yanzu zuciyar ta na son sake zama da shi a matsayin mijinta. Ta 6angaren Sabeer kuwa kusan kwanan zaune yayi saboda zafi da cizon sauro ga duhu dulum ko'ina sai buge bugen sauro yake ya rasa inda zai sanya kanshi yaji dad'i, yayi dana sanin abin da yayiwa Suhaima sau ba iyaka yayi nadama sosai akan tsayawa binciken da bai yi ba gashi ya janyo kanshi shiga cikin tashin hankali. Wajen k'arfe 3:25 ne gari hadari ya had'o sosai sai walk'iya da cida wato tsawa ake yi ga wata irin iska mai k'arfi da take kad'awa sosai, nan Sabeer ya shiga mugun tashin hankali sosai don yasan idan ruwa ya tsinke babu shakka sai yayi mishi jagab musamman idan mai feshi ne, kawai sai ya fashe da wani irin kukan tausayin kanshi, yana cikin kukan ne ruwa ya zuge kamar da bakin kwarya kafin Sabeer ya ankare ruwa ya jik'e shi jagab tunda kanshi har k'afafun shi. Tak'urewa yayi waje d'aya ya had'a kai da gwiwa yana faman shashshak'ar kuka da rawar sanyi, ga ruwan sai zubo mishi yake jikin shi amman ya kasa tashi daga wajen toh idan ma ya tashi ina zai je bashi da wajen zuwa a yanzu wanda ya shige inda yake zaune. Tun da aka fara walk'iya Suhaima ta farka tana zaune tsakiyar gado ta zabga tagumi duk ta rasa abin da yake mata dad'i, don tasan irin yanayin zauren gidan nasu ruwa zai jik'a mutum Yah Aliyu yana da niyyar gyaran shi cikin satin nan, amman tasan halin Yayanta sai yak'i gyara shi saboda Sabeer, kasa jurewa tayi ta sakko daga kan gadon ta nufi bakin window wanda za'a iya hango filin tsakar gidan zuwa cikin zaure. Hannu ta sanya ta yaye labulen window wani irin mugun sanyi tare da feshin ruwa ne ya ratsa ta, bata hango Sabeer sosai ba saboda duhu sai kyallin farin kayanshi da ta hango, sakin labulen tayi tare da dawowa ta zauna kan gado kusan har aka gama ruwan gabannin asubah Suhaima na zaune ta kasa komawa bacci, da yake tana da toilet aciki ya sanya ta yin alwala tayi sallah tana idarwa ta fara addu'a tana cikin yi ne wani bacci mai k'arfi ya d'auke ta. "Suhaima! Suhaima!! Ki tashi haka baccin ya isa " Cewar Aunty Aliyah tana bubbuga k'afar ta, cikin nutsuwa take bud'e idanunta akan agogo ta d'ora eyes nata taga har 10:40 da sauri ta mik'e zaune daman haka lokaci yaja lallai tayi bacci mai nauyi. "Aunty gaskiya nayi bacci mai nauyi haka lokaci yaja " "Naji shirun yayi yawa har mun karya shine nazo duba ki ko lafiya?" D'an murmishi tayi sannan tace "Lafiya qlau Aunty kawai bacci ne " "Kiyi sauri ki shirya kizo ki karya don ina son mu gama aiki da wuri zan fita suna da yamma " "Laaa Aunty zan raka ki don Allah " Cewar Suhaima cikin shagwa6a, 'yar dariya tayi kan tace "Waiii rufa min asiri sai dai ki tambayi mijin ki tukunna " Had'e fuska Suhaima tayi kan ta mik'e da sauri ta shige bathroom da kallo Aunty Aliyah ta bita kan ta girgiza kanta kawai fita tayi daga d'akin. Agurguje Suhaima tayi wanka ta shirya cikin wata blue d'in jallabiya ire iren kayan da Yayan ta ya siya mata ne tunda bata taho da kaya ko d'aya ba, bata yi wani kwalliya ba wet lips ne sai powder kawai ta shafa duk da haka tayi kyau kuwa, d'an perfume ta shafa kan ta had'e gashinta da ribbon ta fito daga d'akin. Hankalin ta akan hanyar zaure amman bata hango shi ba nan taji hankalin ta ya d'an tashi kaddai ya tafi, har tana yin tuntu6e saboda lek'e ashe Aunty Aliyah na kula da ita girgiza kanta tayi kawai tana murmishi don tasan Suhaima nason Sabeer haka shima yana sonta don haka zatayi bakin kok'arin ta wajen daidaita su. "Lek'en me kike har kina yin tuntu6e " Wani kunya ne ya kama Suhaima sai kawai ta sunkuyar da kanta tana shafa kai ta wuce kitchen don d'auko abin karyar ta tana cewa "Ni babu abin da nake kallo fah Aunty " Murmishi kawai Aunty Aliyah tayi, fitowa tayi daga kitchen ta zauna kusa da ita tana kok'arin zuba kunun tsamiya a cup tace "Aunty ina Yaya ne? " "Ya tafi makaranta yana da lecture d'in safe gashi zasu yi test ma " Suhaima tana bud'e wani k'aramin flaks wanda kosai yake ciki tace "Ayyah Allah ya taimaki Yayana " "Amin " Cewar Aliyah tana murmishi, kafin kuma tayi bismillah ta fara cin abincin cikin nutsuwa bayan ta gama ta wanke hannun ta tana kok'arin d'auke kayan da ta karya dasu don ta kaisu kitchen Aunty Aliyah tace "Bar wannan aikin Suhaima ki rik'e min Ameer don kuwa sauri nake son yi " Shagwa6e fuska Suhaima tayi kan ta ce "Kaiii Aunty nima fah na iya wannan saurin gashi ke kadai kika had'a abin kari " "Ni na isa na fad'i hakan ke dai zo ki rik'e min shi idan ba haka ba yana wannan rarrafen nashi zai hanani saurin aiki " D'aukan Ameer tayi tana cillashi tare da cafe shi tana dariyar shima Ameer d'in dariyar yake mata da 'yan hak'oran shi, tana cikin haka ne taji tsayuwar mutum akanta da sauri ta d'ago kanta ido 4 tayi da Sabeer wanda yake tsaye ya hard'e hannun shi yana kallon ta cike da so da tarin sha'awarta don sosai ta birgeshi ji yake kamar ya kamota ya gudu da ita, d'auke kanta Suhaima tayi daga barin kallon shi ta cigaba da yiwa Ameer wasa amman jikinta ya bata har yanzu bai tafi ba kallonta yake lokaci d'aya taji wata kasala ta lullu6e ta har takai ta kasa d'aga Ameer sama sai kawai wasan da take mishi. Fitowar Aunty Aliyah daga kitchen ne ya sanya shi katse kallonta, kallon shi Aliyah tayi kafin ta girgiza kanta ganin lokaci d'aya ya rame gashi kayan shi sunyi datti sosai tace "Sabeer kana buk'atar wani abun ne? " Cikin dashashshiyar muryar shi wadda mura tayi mishi mugun kamu yace "Auntyn mu wanka nake son yi sannan ina son bak'in tea da lemon tsami aciki " "To amman wannan murar taka ko chemist zaka je kada ta ssukar maka da zazza6i " Cikin murmishin yak'e yace "A'a basai naje ba zata warke " "Anya kuwa Sabeer za'a yi haka kada fa ta baka matsala? " "Auntyn mu kada ki damu zata warke nagode da kulawar ki, wadda ya kamata ta nuna damuwa akan ciwon bata damu ba sai ke don haka ki share zancen zuwa chemist " Da sauri Suhaima ta d'ago kanta ta kalli shi har zata yi magana kuma sai kawai ta d'auke kanta tana murgud'a baki, duk abin da take yi akan idanun Sabeer, yayin da Aunty Aliyah tace "Yanzu sai kayi wankan zaka sha tea d'in? " "Eh " Ya fad'i a takaice "Ka shiga d'akin Suhaima akwai toilet aciki sai kayi wankan ka aciki " Daga Suhaima har Sabeer da sauri suka d'aga kansu tare da kallon Aliyah, gid'a kanta tayi sanann tace "Kada ka damu kaje kayi " "Aunty amman...... " Cewar Suhaima sai dai bata k'arasa fad'in abin da zata ce ba taja bakin ta tayi shiru ta had'e fuska. "Aunty nayi kawai a wannan toilet d'in " "A'a bazai yiwu ba, Suhaima kije ki had'a mishi ruwa nace idan har na isa na sanyaki abu kiyi " Tashi Suhaima tayi tana 6a66ata rai zata wuce d'aki taji tana cewa "Dawo ki d'ebi ruwan zafi tun da garin da d'an sanyi gashi yana fama da mura ". Kitchen ta shiga ta d'ebo ruwan zafi ta wuce d'akin ta tana cika tana batsewa don me Aunty Aliyah zata ce yayi wanka a d'akin ta, ko ta mance da irin yanda ya koreta daga gidan shi ne. "Auntyn mu 6atawa Baby nah rai fah? " Ya fad'i hakan bayan wucewar Suhaima. "Kyaleta Sabeer sakkowar Suhaima daga fushin da take da kai shi zai sanya Yayan ta ya huci daga d'aukan zafin da yayi maka, kai dai kayi kok'arin shawo kan Suhaima " Gid'a kanshi yayi kan ya wuce zuwa zaure ya d'auko bag d'in kayan shi ya wuce d'akin Suhaima, yayin da Aunty Aliyah ta cigaba da aikinta bayan ta goya Ameer. Yana shiga cikin d'akin wani k'amshi ne ya fara mishi sallama mai dad'i har sai da ya lumshe eyes nashi, tsayawa yayi yana kallon d'akin cike da sha'awar shi yayi mishi kyau duk da ba wasu kaya ne masu tsada ba sosai amman yanayin yanda aka tsara d'akin ne ya birge shi, daga gado, wardrobe sai dressing mirror k'asan kuma carpet ne sai kayan kallo gashi d'akin babba ne sai labulaye masu kyan tsari gadon nan an gyarashi sosai tamkar ba'a ta6a kwanciya akan shi ba. Yana nan tsaye Suhaima ta fito daga toilet d'in ba tare da ta kalli inda yake ba ta fara kok'arin fita daga d'akin, hannun ta ya rik'o cikin sanyin murya yace "Baby nah kiyi hak'uri please ki daina fushi da ni " Bata ko kalle shi ba ta fara zame hannunta daga nashi sannan ta fice daga d'akin, da kallo ya bita kafin kuma ya nufi hanyar da ta fito ya shige toilet d'in. Suhaima tana tsaye kusa da Aunty Aliyah tana mata mitar yanda ta sanya Sabeer shigar mata d'aki, yayin da Aunty Aliyah take murmishi kawai yaro yaro ne idan ban da haka yaci ace ta yafewa Sabeer don ita kanta Suhaima ya kamata ta baiwa Sabeer shaidar yanda yake nuna mata so da kulawa abu ne ya gifta a tsakanin su wanda mak'iyan su da basa son su gansu tare suka yi amfani da abin da Sabeer yafi so suka had'a makirci shi kuma laifin shi d'aya da ya biyewa zuciyar shi ya yanke hukunci cikin fushi sai dai kuma yayi kok'arin controlling din zuciyar shi tun da bai sake ta ba. Sallamar da suka ji anyi ne ya sanya Suhaima da Aliyah zabura gaban su ya hau fad'uwa lokaci d'aya kafin su ankare ya shigo gidan, kallon su ya tsaya yi cikin mamaki ganin yanda suka zuba mishi ido kallo d'aya yayi musu yasan basu da gaskiya. Tsarguwar da suka yi da yanda yake kallon su ne ya sanya su sakin murmishin yak'e tare da yi mishi sannu da zuwa, amsa musu yayi kawai yana sake bin su da kallon ban yarda daku ba. Zuciyar Suhaima da ta Aliyah tamkar zasu faso kirjin su ta fito saboda yanda take bugawa sam basu yi tsammanin ganin Yah Aliyu yanzu ba sun sakankance sai da yamma, musamman Aunty Aliyah tafi kowa tsorata tayi dana sanin sanya Sabeer shiga cikin d'akin Suhaima yanzu idan ya fito daga d'akin batasan hukuncin da Aliyu zai d'auka ba akanta don itace da wannan shishshigin, gashi kafin ya fita sai da tasha gargad'i kada ta sake tsakanin Sabeer da Suhaima magana ta had'a su, nan ta fara addu'a Allah ya sanya kada Sabeer ya fito. "Wai lafiyar ku qlau kuwa? " Cikin sauri Aunty Aliyah tace "Me kagani? " "Gani nayi kunyi wani tsuru tsuru sai rarraba ido kuke kamar marasa gaskiya " "A haba ba komai, lafiya ka dawo yanzu? " "Nayi mantuwa ne " Yana gama fad'in haka ya wuce d'akin su da sauri don kuwa sauri yake, bai dad'e ba ya fito daga d'akin ya fice daga gidan, sai lokacin suka saki ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali. "Aunty kinga abin da nake tsoro koh da yanzu ya gane fah " Aliyah wadda jikinta ya mutu saboda tsoro ta aro dauriya tace "Kai dai Allah ya kiyaye kawai ba don haka ba da yau zanyi bayani don nice da laifi " Suhaima dariya ce ta kubce mata ganin Aunty Aliyah na goge zufa tace "Haba Aunty kinsan Yah Aliyu bazai iya ce miki komai ba sai dai kisha harara da mita " "Ke kyale Yayan nan naki kawai idan ya fusata " Cup d'in da ta had'a wa Sabeer tea ta mik'o mata tare da cewa "Gashi ki kai mishi da zafin shi yasha kada ya huce gashi jiya fah bai samu cikakken bacci ba don nasan ruwan nan ya jik'a shi sosai " D'an ta6e baki Suhaima tayi kan tace "Allah Aunty kina son wanann guy d'in ya rainani da yawa bakisan haushin shi nake ji ba wallahi " "Hakuri zakiyi Suhaima kinsan kowanne d'an adam da irin tashi k'addarar Allah ya riga ya tsara hakan sai ya faru tsakanin ku" Kar6a tayi kawai ta tafi tana zum6ura baki Aunty Aliyah ta bita da kallo tana murmishi kawai. Tana shiga d'akin ta ajiye cup d'in tea saman drower na gefen gado ta jiyo da niyyar fita daga d'akin taji an janyo hannun ta da d'an k'arfi wanda ya sanya d'an kwalin kanta mai santsi ya zame lallausa dogon gashin kanta ya tarwatse, bata tsaya ko'ina ba sai saman faffad'an kirjin shi har sai da d'an kanta ya bige kad'an, kallon shi tayi da niyyar yi mishi tsiwa sai dai suna had'a ido duk wani abu ya kunce mata kallon junan su kawai suka tsaya yi cikin wani irin shauk'i da tsananin kewar junan su............ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 106-107* Kallon shi tayi da niyyar yi mishi tsiwa sai dai suna had'a ido duk wani abu ya kunce mata kallon junan su kawai suka tsaya yi cikin wani irin shauk'i da tsananin kewar junan su tare da wata irin zazzafar kauna, sun d'auki wajen 5 minute suna aikawa da junan su kallo yayin da Sabeer ya kasa jure kallon da suke aikawa junan su ya fara matsar da fuskar shi saitin fuskar ta da niyyar yayi kissing d'in cute pink lips nata wanda yayi tsananin missing d'in su a lot. Jin saukar numfashin shi kusa da hancin ta sosai ya sanya Suhaima dawowa cikin hayyacin ta ta daddage ta fiske jikin ta daga jikinshi, sai dai yanda ta fisgi jikin nata ne ya sanya ta tafiya baya da d'an k'arfi kamar zata fad'i k'asa yayin da Sabeer wanda gaba d'aya kasala ta baibaye shi ya biyo ta shima. Sauran kad'an Suhaima ta saki ihu na tsoro sai taji ta fad'a saman bed yayin da Sabeer ya biyo ta shima cikin jikinta, lokaci d'aya suka sauke wata ajiyar zuciya sai dai kowannen su da banbancin ajiyar zuciyar tasu Suhaima ita ta jin dad'in bata fad'i k'asa ba shi kuma Sabeer na jin shi rungume da Babyn shi a jikinshi wanda ya d'auke tsayin lokaci da su had'u kamar haka. Kok'arin tashi take amman ya wani rik'e ta k'am kamar wanda za'a kwace mishi itaa haushi ne ya ishe Suhaima ta d'aure fuska cikin fusata tace "Malam wai me kake nufi ne haka ni ka d'aga ni wallahi ko nayi maka ihu " Murmishi Sabeer yayi kafin yace "Haba Baby nah kinsan nayi missing d'in ki da yawa ki barni ko na samu kwanciyar hankali da nutsuwa cikin zuciya ta " Haushi ne ya k'ule Suhaima don haka tace "Kada ka mance da bakin ka kace min ka tsane ni me yasa zaka zo inda nake nima kasani na dad'e da tsanar ka tun lokacin da ka furta min haka " Jikin Sabeer ne yayi wani irin sanyi wanda Suhaima har ta samu ta ture shi daga jikinta ta mik'e tare da d'aura d'an kwalin kanta ta wani kalle shi taja tsaki ta fice daga d'akin gaba d'aya. Tana fitowa suka had'a ido da Aunty Aliyah da take zaune can gefen kitchen tana aiki, sake d'aure fuska Suhaima tayi don duk ita taja gashi ba don tayi kok'arin yakice shi ba da tuni ta bada kai bori ya hau, don haka ta samu waje ta zauna kawai ko kula Aliyah bata yi ba, sauran kad'an dariya ta kubce wa Aunty Aliyah amman ta danne ta kada ta janyo tayi mata kuka da rigima don kad'an daga aikin Suhaima don haka taja bakinta tayi tsit ta cigaba da aikinta. Wani zafi da zugi ne yake ji cikin zuciyar shi kalaman Suhaima ne kawai suke fad'o mishi a rai da jan tsakin da tayi mishi don yaji ta ya dad'e kwance a haka yana tufka da warwara tare da yin d'unbin nadamar abin da yayi dakyar ya iya shiryawa cikin wani jeans blue da T-shirt fara mai k'aramin hannu ya d'an fesa perfumes kan ya zauna ya sha tea d'in da ya fara sanyi ma. Yana gama sha ya mik'e ya d'auki kayan shi ya rik'e mai dattin a d'ayan hannun ya fito waje kallon Suhaima ya d'an yi kan ya kalli Aunty Aliyah yace "Auntyn mu nagode bari na d'an fita waje ko zanga Ashiru don bamu had'u ba tun da nazo " "Toh Sabeer sai ka dawo, amman ina zaka tafi da kayan nan masu datti haka a hannu? " D'an murmishi yayi yana cewa "Anjima zan wanke su ne zan ajiye su a inda nake kwana " Tausayin Sabeer ne ya kama Aunty Aliyah tasan bai ta6a tsammanin zai yi irin wannan kwatankwacin rayuwa ko zuwan da yayi na farko baya yin wanki Yah Aliyu ne yake had'a wa ya wanke musu da nashi. Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 106-107* Kallon shi tayi da niyyar yi mishi tsiwa sai dai suna had'a ido duk wani abu ya kunce mata kallon junan su kawai suka tsaya yi cikin wani irin shauk'i da tsananin kewar junan su tare da wata irin zazzafar kauna, sun d'auki wajen 5 minute suna aikawa da junan su kallo yayin da Sabeer ya kasa jure kallon da suke aikawa junan su ya fara matsar da fuskar shi saitin fuskar ta da niyyar yayi kissing d'in cute pink lips nata wanda yayi tsananin missing d'in su a lot. Jin saukar numfashin shi kusa da hancin ta sosai ya sanya Suhaima dawowa cikin hayyacin ta ta daddage ta fiske jikin ta daga jikinshi, sai dai yanda ta fisgi jikin nata ne ya sanya ta tafiya baya da d'an k'arfi kamar zata fad'i k'asa yayin da Sabeer wanda gaba d'aya kasala ta baibaye shi ya biyo ta shima. Sauran kad'an Suhaima ta saki ihu na tsoro sai taji ta fad'a saman bed yayin da Sabeer ya biyo ta shima cikin jikinta, lokaci d'aya suka sauke wata ajiyar zuciya sai dai kowannen su da banbancin ajiyar zuciyar tasu Suhaima ita ta jin dad'in bata fad'i k'asa ba shi kuma Sabeer na jin shi rungume da Babyn shi a jikinshi wanda ya d'auke tsayin lokaci da su had'u kamar haka. Kok'arin tashi take amman ya wani rik'e ta k'am kamar wanda za'a kwace mishi itaa haushi ne ya ishe Suhaima ta d'aure fuska cikin fusata tace "Malam wai me kake nufi ne haka ni ka d'aga ni wallahi ko nayi maka ihu " Murmishi Sabeer yayi kafin yace "Haba Baby nah kinsan nayi missing d'in ki da yawa ki barni ko na samu kwanciyar hankali da nutsuwa cikin zuciya ta " Haushi ne ya k'ule Suhaima don haka tace "Kada ka mance da bakin ka kace min ka tsane ni me yasa zaka zo inda nake nima kasani na dad'e da tsanar ka tun lokacin da ka furta min haka " Jikin Sabeer ne yayi wani irin sanyi wanda Suhaima har ta samu ta ture shi daga jikinta ta mik'e tare da d'aura d'an kwalin kanta ta wani kalle shi taja tsaki ta fice daga d'akin gaba d'aya. Tana fitowa suka had'a ido da Aunty Aliyah da take zaune can gefen kitchen tana aiki, sake d'aure fuska Suhaima tayi don duk ita taja gashi ba don tayi kok'arin yakice shi ba da tuni ta bada kai bori ya hau, don haka ta samu waje ta zauna kawai ko kula Aliyah bata yi ba, sauran kad'an dariya ta kubce wa Aunty Aliyah amman ta danne ta kada ta janyo tayi mata kuka da rigima don kad'an daga aikin Suhaima don haka taja bakinta tayi tsit ta cigaba da aikinta. Wani zafi da zugi ne yake ji cikin zuciyar shi kalaman Suhaima ne kawai suke fad'o mishi a rai da jan tsakin da tayi mishi don yaji ta ya dad'e kwance a haka yana tufka da warwara tare da yin d'unbin nadamar abin da yayi dakyar ya iya shiryawa cikin wani jeans blue da T-shirt fara mai k'aramin hannu ya d'an fesa perfumes kan ya zauna ya sha tea d'in da ya fara sanyi ma. Yana gama sha ya mik'e ya d'auki kayan shi ya rik'e mai dattin a d'ayan hannun ya fito waje kallon Suhaima ya d'an yi kan ya kalli Aunty Aliyah yace "Auntyn mu nagode bari na d'an fita waje ko zanga Ashiru don bamu had'u ba tun da nazo " "Toh Sabeer sai ka dawo, amman ina zaka tafi da kayan nan masu datti haka a hannu? " D'an murmishi yayi yana cewa "Anjima zan wanke su ne zan ajiye su a inda nake kwana " Tausayin Sabeer ne ya kama Aunty Aliyah tasan bai ta6a tsammanin zai yi irin wannan kwatankwacin rayuwa ko zuwan da yayi na farko baya yin wanki Yah Aliyu ne yake had'a wa ya wanke musu da nashi. "Sabeer kabar shi Suhaima zata wanke maka " "A'a Auntyn mu kada na wahalar da Mata ta " Ya k'arasa maganar fuskar shi d'auke da murmishi wanda ya k'ara mishi kyau. 'Yar dariya Aunty Aliyah tayi kan tace "Mata manya ni ai ban ta6a ganin matar da take gudun mijinta ba akan wani abu da ya faru bisa kuskure " "Kaiii Auntyn mu kada mu yi haka da ke waya gaya miki tana gudun mijinta? " Ya fad'i yana satar kallon Suhaima wanda ta cika tayi fam, "Ai abin a fili yake K'anina " Daga jin dai yanda Aunty Aliyah ke maganar kasan ta tsokana ce, sai akayi sa'a Suhaima bata tanka musu ba, ajiye kayan Sabeer yayi kusa da k'afar Suhaima kan yayi wa Aunty Aliyah sallama ya fita daga gidan. "Allah Aunty ki daina yi min haka taya ina zaman hutawa na ki had'a ni da wanki don Allah "Cewar Suhaima cikin turo baki. "Haba K'anwata bansan ki da fushi mai yawa ba ki d'auka ki wanke mishi na tabbatar Allah zai rubuta miki lada tunda da auren shi akan ki " Cewar Aunty Aliyah cikin rarrashin Suhaima. "Aunty kawai naga alama yanzu kin fi son shi da ni " "Tabd'i kinsan dai Suhaima son da nake miki na daban shak'uwar mu da ke ma ba d'aya ce da ta Sabeer ba dukkanin ku matsayin k'annena ba don na girmi Sabeer ba, ina son ku had'a kanku da Sabeer ne da zarar Aliyu yaga haka duk fushin da yake dashi zai daina, Allah ya gani ina sonki da Sabeer wallahi gashi yana ban tausayi jiya da dare ji ruwa da aka tafka amman kusan akanshi ya k'are ga sanyin waje da duhu dalilin da ya tashi da mura kenan don tun da na tashi da asuba nake jin tarin shi da atishawa yana yi kuma duk wannan abun yana yi ne saboda A DALILIN SONKI Suhaima ya kamata kiyi tunani sosai kisan Sabeer masoyin ki ne na gaskiya " Tana gama fad'in haka ta tashi ta wuce don cigaba da aikin ta yayin da tabar Suhaima cikin wani irin yanayi wanda lokaci d'aya ta fara jin haushin Sabeer yana raguwa cikin zuciyar ta. Cikin sanyin jiki ta tashi ta fara wanke mishi kayan fes ta wanke su ta shanya saman igiya sannan tayi alwala ta tafi d'aki don yin sallah, bayan ta idar ne tana nan kwance saman abin sallahr Aunty Aliyah ta shigo cikin shirin tafiya suna tace "Suhaima ni zan tafi idan Yayan ki da Sabeer sun dawo ga abinci nan a foodflaks ki zuba musu " "Kaiii Aunty yanzu ki fasa tafiya dani? " "Kiyi hak'uri Suhaima bazai yiwu mu tafi tare ba saboda baki tambayi mijin ki ba amman zan dawo da wuri kafin mangarib insha Allah " "Toh Aunty adawo lafiya " "Yawwa K'anwata haka nake son ji kin fad'a " Tashi tayi suka fito har k'ofar zaure ta rakata ta tafi sannan ta rufe gidan ta wuce ta zuwa d'akin ta, kwanciya tayi kawai maganganun Aunty Aliyah ne suke dawo mata, da taga tunanin ba mai k'arewa bane ya sanya ta tashi taje ta had'a wuta a dutsen guga ta zauna ta gogewa Sabeer kayan shi tsaf ta d'auke su taje ta ajiye mishi saman jakar shi. Tana zama kenan taji ana buga k'ofar gidan tashi tayi taje tana tambayar wane sai taji muryar Yayanta Aliyu bud'e k'ofar tayi tana murmishi tace "Yayah sannu da dawowa? " Shima fuskar shi d'auke da murmishin yace "Yawwa Suhaima ya zaman gida ke kadai don nasan Aliyah ta tafi gidan suna koh? " "Eh Yaya ta tafi sai ni kadai duk tsoro ya kama ni " "Ai dama ke matsoraciya" Cewar Yah Aliyu yana dariya cikin shagwa6a tace "Kaiii Yayah aikuwa ni jaruma ce " Hannun ta ya kamo suka k'arasa cikin gidan yana biye mata, bayan yayi wanka ta zuba mishi abinci yana ci suna hira yana bata labari akan harkar karatun shi tana yi mishi addu'ar Allah ya taimaka, yana tsaka da cin abincin Sabeer ya shigo gidan bakin shi d'auke da sallama. Sanin muhimmancin sallamar ne ya sanya Yah Aliyu amsa mishi ko k'arasa shiga tsakar gidan bai yi ba ya juya zuwa cikin zaure ya shimfid'a tabarma ya zauna akai kawai, wani tausayin shine ya kama Suhaima wanda ya sanya ta binshi da kallon tausayi, ashe duk wannan kallon da take binshi dashi Yah Aliyu yana kallonta shima girgiza kanshi yayi kawa ya cigaba da cin abincin shi. "Ki zuba mishi abinci ki kai mishi " Ya furta hakan kamar bashi yayi maganar ba, aikuwa tsam ta mik'e da sauri taje kitchen ta zuba mishi tare da d'iban ruwa ta kai mishi, duk abin da take Yah Aliyu yana kallon ta yana kula da yanayin ta, bayan ta dawo daga kaiwa Sabeer abinci ta wuce d'akin ta kawai. Ahaka har aka kwashi tsayin sati biyu Sabeer na kwana a zaure har zuwa yanzu babu wata kyakkyawar fahimta tsakanin shi da Aliyu, ga wani irin tari da zazza6i mai zafin gaske da yake yi da cikin dare baya iyayin wani cikakken bacci duk yabi ya rame sosai yayi bak'i ga rashin aski duk gashi ya cika mishi fuska ko abincin kirki baya iya ci, gashi kirjin shi yayi mishi wani irin nauyi gashi tsakiyar damina akai ana samun ruwa akai akai sosai. Suhaima tana tausayin Sabeer ganin yanda ya koma har kuka take a 6uye, Aunty Aliyah tayi tayi dashi Ashiru ya rakashi chemist yak'i zuwa yayin da Yah Aliyu yake ce mishi ya tafi gidan su bazai iya zaman nan ba tunda shi ba d'an wahala bane kawai ya sakar mishi k'anwar shi, Sabeer idan yaji haka sai kawai yayi murmishi kawai shi ciwon da yake damunshi da k'in kulashi da Suhaima take yafi komai d'aga mishi hankali. Kamar yau tun kafin mangarib ake ruwa har zuwa bayan sallahr ishsha bai tsayaba sai dai idan lokacin sallah yayi ya d'an tsaya, Sabeer yana tukunkune a zaure yana rawar sanyi sosai ga tari da yake faman yi idanun shi sunyi ja sun k'ara fitowa sosai saboda tarin da yake yi zuwa can kuwa numfashin shi ya fara d'auke wa kafin daga bisani ya tuntsire a k'asa yana jan numfashi dakyar. Suhaima kuwa tana zaune a d'aki sai faman kukan zuci take tasan Sabeer yana can yana fama da dukan ruwan wani tausayin shine yake ratsa mata zuciya tana fitar da hawaye. Yah Aliyu kuwa da Aunty Aliyah sai fad'a suke tana fad'a mishi idan Sabeer ya mutu mai zai cewa iyayen shi wannan horan haka ya isa duk yaro yabi ya rame yayi bak'i ga rashin lafiyar da yake fama da ita nasan zuwa yanzu yayi horan da bazai sake maimaita abin da yayi ba. "Aliyah ana dole ne nace ya rabu da ita kuma bani na ce yazo ba fah ya zauna ra'ayin shine to ni mene ruwana " "Haba Yah Aliyu nasan ka da tausayi zuciyar ka mai kyau ce kayi hak'uri ka yafe mishi, baka ganin yanda Suhaima ma ta shiga damuwa kada ka shiga hakk'in su fah da yawa tana son mijinta shima yana son matar shi don me yasa baza ka hakura ka bashi matar shi ba kuma na tabbatar kana son Sabeer ya kasance da Suhaima har k'arshe rayuwar ta, bakasan abin da Allah ya 6oye ba kawai ni a shawara ta ka bashi matar shi don Allah Yah Aliyu " Cewar Aunty Aliyah tana kama hannun shi fuskar ta tab da hawaye, shiru Yah Aliyu yayi yau Aliyah ta tunasar dashi abubuwa da dama, take yaji zuciyar shi tayi sanyi ya kalli Aliyah yace "Naji na amince zan bashi matar shi " Wani dad'i ne ya ratsa zuciyar Aunty Aliyah tayi murmishi tana cewa "Ko kaifa Yah Aliyu naji dad'i sosai don Allah yanzu ka taso muje ka ce ya koma d'akin Suhaima " Hannun shi yasa ya ja hancin Aliyah yana cewa "Toh Mata tagari angama taso mu tafi " Ya mik'e tsaye yana murmishi tare da kamo hannun Aliyah suka fito zuwa zaure, sai dai suna shiga zauren hankalin su yayi masifar tashi ganin yanda Sabeer yake jan numfashi dakyar yana rik'e da kirjin shi ga kuma tarin da yake. Da sauri suka k'arasa inda yake Yah Aliyu ya tashe shi zaune tare da rik'e shi yace "Sabeer me yake damun ka? " Kallon Yah Aliyu yayi kafin yayi luuu da eyes nashi kamar wanda yasha kwaya bashi da k'arfin bud'e baki yayi magana ma, ganin haka ya sanya Yah Aliyu d'ago shi yana rik'e dashi suka k'arasa d'akin Suhaima. Da sauri Aunty Aliyah take buga k'ofar d'akin Suhaima tana kiran sunan ta, a firgice Suhaima ta duro daga saman gado tare da bud'e k'ofar nata. Kafin tayi magana Yah Aliyu ya shiga da Sabeer cikin d'akin tare da zaunar dashi ya juyo ya kalli Suhaima wadda sai rarraba ido take hanaklin ta atashe yace "Kiyi maza ki cire mishi kayan jikin shi ki canja mishi bari naje na samo mishi magani, Aliyah kije ki dafa mishi tea da kayan k'amshi ki dafa da lemon tsami a ciki " Yana gama fad'in haka ya wuce ya tafi da sauri yayi da Aunty Aliyah ma ta wuce zuwa kitchen da sauri duk da kuwa ana yin yayyafi, Suhaima kasa motsi tayi saboda ganin Yah Aliyu da kanshi ya kawo Sabeer har da cewa na cire mishi kayan jikin shi, ganin halin da Sabeer yake ciki ne ya sanya ta kok'arin cire mishi kayan shi dakyar ta iya cire mishi saboda gaba d'aya babu k'arfi ajikin shi balle ya mik'e tsaye, bayan ta gama cire mishi ta duba kayan nashi ta ciro dogon wandon jeans ta sanya mishi sai dai babu wata riga ta sanyi aciki wanda mutum zai sanya ya ji d'umi. Ahaka ta zura mishi T-shirt mai dogon hannu sannan ta lullu6e shi da blanket idanun shi har zuwa lokacin a lumshe yana jan numfashi dakyar gashi jikin shi yayi zafi sosai, jik'akk'un kayan ta d'iba ta fitar dasu waje ta ajiye sannan ta dawo dakin ta zauna kusa da Sabeer tare da rik'e mishi hannu tana kallon shi hawaye na fita a idanun ta........... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 108-109* Da sauri ta mik'e tsaye tare da matsawa can nesa da Sabeer saboda jin ana kok'arin shigowa d'akin, Yah Aliyu ne ya shigo hannun shi rik'e da magani sai Aunty Aliyah dake bayan shi tana rik'e da k'aramin flaks na tea da k'aramin cup na shan tea suka shigo cikin d'akin da sallama, Suhaima ce ta amsa musu sallamar. "Ya samu bacci ne? " Yah Aliyu ya tambayi Suhaima, girgiza kanta tayi kafin tace "A'a idanun shine a lumshe amman bai yi bacci ba " Juyowa Aliyu yayi tare da cewa "Sannu Sabeer zaka iya tashi kasha shayi da magani? " Ahankali ya bud'e eyes nashi tare da d'aga mishi kai, yunkura ya fara yi zai mik'e ya zauna amman sai ya koma ya kwanta don jikin shi babu k'arfi, ganin haka ya sanya Yah Aliyu taimaka mishi ya zauna bayan shi ya sanya mishi pillow biyu don yaji dad'in zaman. Shayin Aliyah ta mik'awa Aliyu nan ya dunga bashi da spoon yana sha da d'an zafin shi kad'an yanda bazai k'ona shi ba, sai da ya sha wajen cikin cup d'in don yaji dad'in tea d'in sannan Yah Aliyu ya bashi magani yasha, bayan ya gama shan maganin Yah Aliyu ya kalle shi tare da cewa "Sabeer na yarda na amince Suhaima zata koma gidan ka da zama, nasan kai masoyin ta ne na gaskiya Allah ya baku zaman lafiya " Duk da Sabeer jikinshi babu k'arfi sai da yayi kok'arin rungume Yah Aliyu cikin tsananin farinciki ga hawaye suna zuba a eyes nashi, cikin muryar mara lafiya yace "Thank U Babban Yayah bani da bakin yi maka godiya naji dad'i sosai Allah ya saka maka da alkhairi, kuma insha Allah zan rik'e Suhaima sosai bazan k'ara kwatanta hakan ba " Bubbuga bayan shi Yah Aliyu yayi then yace "Yanzu ka kwanta ka huta sosai gobe ma k'arasa maganar " Yana gama fad'in haka ya gyara mishi kwanciyar shi sannan ya kalli Suhaima wadda tayi mutuwar tsaye jin abin da Yah Aliyu ya fad'a, cikin murmishi yace "K'anwata ki cigaba da hak'uri tare da yiwa mijin ki biyayya Allah yayi miki albarka " Yana gama fad'in haka ya janyo hannun Aunty Aliyah suka fita daga d'akin tare da ja musu k'ofar d'akin su suka wuce kowannen su zuciyar shi fes musamman Yah Aliyu sai yake jin shi sakayau kamar wanda aka d'auke mishi wani gungumeman dutse akanshi. Jingina tayi da bangon d'akin ta d'aga kanta sama idanun ta a lumshe wasu hawaye ne suke fita cikin idonta wanda ta kasa banbance hawayen mene. Tun d'azu ya tsura mata ido yana kallonta ji yake da zai iya mik'ewa tsaye zuwa inda take zai yi ya rungume ta cikin jikin shi ta fad'a mishi dalilin zubar hawayen ta ya kuma rarrashe ta tare da nuna mata tsantsar k'aunar ta ya nuna mata yanda yake jinta cikin ran shi sai dai ba damar hakan sai ido ya zuba mata. Hannu ta sanya tare da goge hawayen face nata ta bud'e idonta a hankali tare da sauke su kan Sabeer had'a ido suka yi da junan su da sauri ta janye nata eyes d'in ta wuce zuwa wajen wardrobe nata ta bude shi d'ayan bargo ta d'auko ta shimfid'a a k'asan carpet sannan ta wuce ta rufe k'ofar d'akin da key kafin ta shiga toilet ta d'an jima a ciki ta fito. Wajen bed ta k'arasa ta gyara mishi lullu6ar jikinshi sannan ta d'auki pillow ta kashe fitilar d'akin sannan ta koma inda ta shimfid'a bargon ta kwanta tare da yin addu'ar bacci ta shafe jikinta ta juyawa Sabeer baya. Duk abin da take yana kallonta har lokacin da ta kwanta ta juya mishi baya, d'an murmishi ya saki kawai zuciyar shi fal farin ciki da haka bacci mai nauyi ya d'auke shi da yake cikin maganin da Yah Aliyu ya siyo mishi yasha akwai na mura aciki. Washe gari da safe Suhaima ta makara sosai wajen tashi daga bacci don har wurin 7am takai tana bacci, duk da shima Sabeer d'in ya makara amman ya rigata tashi ya lalla6a ya shiga toilet ya d'aura alwala yayi sallah bayan ya gama addu'o'in shi ne ya tashi domin ya k'arasa wajen Suhaima ya tashe ta. Tsugunnawa yayi a gabanta yana kallonta d'an murmishi yayi ganin yanda ta k'ank'ame jikinta alamar tana jin sanyi don har zuwa yanzu da sanyi garin gashi da duhun hadari, hannun shi ya sanya yana shafa mata face nata cikin nutsuwa. Far tayi ta bud'e eyes nata wanda ya haddasawa Sabeer wata muguwar kasala wanda ya sanya shi zama a kan carpet ya k'ura mata ido cikin wani yanayi daban, d'an hararar shi tayi tare da murgud'a mishi baki ta mik'e ta wuce toilet da kallo ya bita yana murmishi sannan ya girgiza kanshi har yanzu tsiwar tana nan ba'a daina ba. Bayan ta idar da sallah ne agurguje ta wanke toilet tsaf tazo ta gyara bedroom d'in amman ban da kan bed saboda Sabeer da yake kwance akai yana bin ta da mayataccen kallon shi, bayan ta gama ta fita zuwa tsakar gida ta tarar har Yah Aliyu ya wuce schl Aunty Aliyah kuma ta gama komai ta gyara gidan tsaf. Gaida ta Suhaima tayi tana tambayar ta mai jiki bata amsa ba ta wuce kitchen tana cewa "Aunty da akwai ruwan zafi zanyi wanka? " Murmishi tayi kafin tace "Da akwai na dafa muku don nasan zaku nema " D'an zaro ido kad'an Suhaima tayi gabanta ya fad'i kada Aunty Aliyah ta zargi ko sunyi wani abun bayan babu abin da ya faru tsakanin su, sai kuma ta share kawai ta d'ebo wanda zai ishesu wanka ta wuce d'akin bata k'ara bi takan Aunty Aliyah ba don ta bata kunya. "Idan ki kai ruwan ga abin karyawa nan kizo ki d'aukar muku " "Toh " Kawai tace ta shige d'akin, had'a mishi ruwan wanka tayi sannan ta fito tana kok'arin yi mishi magana yace "Baby nah kin tashi lafiya?" Kauda kanta tayi bata amsa ba sai kawai tace mishi "Na had'a maka ruwan wanka " Tana gama fad'in haka ta wuce ta fita zuwa waje, kayan breakfast d'in ta d'auko musu ta kawo d'akin ta tarar dashi har ya shiga wanka, gyaran kan bed tayi ta d'ameshi sosai yayi kyau. Kayan shi ta duba taga duk sunyi datti da squeezing sai iya wanda ya sanya jiya da dare masu kyau daman kayan gaba d'ayan su kala 4 ne ya taho dasu, tana nan tsaye tana tunanin mafitar wanne kaya zai sanya sai gashi ya fito daga toilet d'in yana daure da towel d'in Suhaima wanda dakyar ya ritsa shi d'ayan hannun shi kuma rik'e da kayan da ya cire su. Kallo d'aya Suhaima tayi mishi ta d'auke kanta kawai ta tattaro kayan shi masu datti ta k'arasa inda yake ta fisge masu dattin wanda ya cire tayi fita daga d'akin da sauri, da kallo ya bita yana murmishi kawai. Tana fita kayan ta had'a ta fara wanke mishi tana gama wanke su ta koma cikin d'akin har zuwa lokacin yana zaune gefen gado dashi da towel d'in kanshi a sunkuye yana ciccila k'afa. Had'a mishi tea tayi sannan ta zuba mishi jellop d'in da akayi na taliya a plate, kusa dashi ta ajiye mishi tare da maganin shi dakyar ta iya cewa "Ga breakfast d'in ka nan " Tana gama fad'in haka ta wuce toilet don yin wanka, a nutse yake shan tea d'in har yasha rabin cup sannan ya d'auki taliyar kad'an ya iya ci ya ajiye yasha maganin shi da ragowar tea d'in. Fitowa tayi daga toilet tana daure da zani ta dubi dressing mirror k'ara had'e fuska tayi ganin yana bin ta da mayataccen kallon shi, tana tsaka da shafa mai ne taji lallausan hannun Sabeer yana yawo a jikinta da sauri ta sanya hannun ta tana kok'arin cire hannun shi amman sai taga ya zube saman gwiwowin shi ya kama hannunta dukka biyun ya had'e dana shi yana kallon cikin idonta yace "Baby nah da farko ina neman yafiyar ki akan abin da nayi miki, ina rok'an ki da ki yafe min nasan nayi kuskure ban kyauta miki ba da na kasa gane makirci aka had'a mana don kawai a raba mu nayi nadamar hakan, wallahi Baby ina son ki sosai kullum sonki k'ara shiga zuciyata yake i luv U with oll my heart " Shiru tayi mishi hawaye ne zasu zuba daga idonta da sauri ya girgiza mata kanta kan yace "No Baby kada kiyi kuka please, kukan ya isa haka bana buk'atar sake ganin zubar hawayen nan " Dole ta had'iye kukan amman duk da haka sai da wad'annan hawayen da suka fara fitowa suka zubo, hannun shi ya sanya ya goge su yana cewa "Baby kice kin hakura kin yafe min zamu koma zama da junan mu kamar da " Rungume shi Suhaima tayi tana cewa "Komai ya wuce a wurina, sai dai ina tsoron komawa gidan ka " Ta k'arasa fad'a duk alamar tsoro ya bayyana a face nata, wani tausayin ta ne ya kamashi yasan da gaske take fad'in haka har cikin zuciyar ta, bubbuga bayan ta ya fara yi yana cewa "Baby anan zamu zauna baza mu tafi ko'ina ba har sai kin amince da kanki zaki koma gidan ki, kin yarda da haka? " Cikin jin dad'i ta saki murmishi wanda shine na farko da tayi mishi tun zuwan shi kauyen su tace "Na yarda da hakan sosai " Jan hancin ta yayi kad'an yace "Naji dad'in haka Baby nah zan kasance mai faranta miki rai har k'arshe rayuwata insha Allah " Ya k'arasa fad'a yana matse ta ajikin shi har sai da tace "Wash! You are hurting me " Sannan ya sassauta ruk'an da yayi mata kafin tace "Kaje ka kwanta tunda baka da lafiya " "Waya fad'a miki aini na warke daman ciwon so ne ya kwantar dani gashi kuma na samu maganin shi " D'an hararar shi tayi tana turo baki bata ankara ba taji lips d'in shi kan nata, sun d'auki wajen 5 minute a haka kafin su rabu da junan su suna sauke ajiyar zuciya kallon junan su suke cikin wani shauk'i. *********** Hango Dr Faridah nayi cikin katafaren palourn ta tana faman safa da marwa kallo d'aya zaka yi mata kasan hankalin ta a matuk'ar tashe yake, don yau kimanin wajen sati 3 bata samun wayar Sabeer daga dukannin number's d'in na k'asar waje wanda yake amfani dasu. Kullum tayi try numbers d'in a kashe harda ta gida 9ja ma, abin yayi matuk'ar d'aga mata hankali don kuwa hakan bai ta6a faruwa dasu ba, tananin wanne hali Sabeer yake ciki don ta tabbatar Sabeer baya cikin Nigeria tun da har da ita aka raka shi airport. To ina ya shiga?, dum gaban ta ya fad'i da tuna ko yana tare da wannan shegiyar yarinyar, amman kuma tasan Sabeer baya k'asar, da sauri cikin rawar jiki ta d'auko phone nata ta shiga searching d'in numbers d'in shi na Nigeria domin ta bibbiyi layin nashi ko yana nan Nigeria bai tafi ba yaudarar ta yayi. Sai dai har taga ma searching nata bata ga wata alama ba don nuna mata ake layukan suna kashe, jefar da wayar tayi tare da d'ora hannunta saman kanta gaba d'aya ta tallafi kan nata, gashi har zuwa yanzu Daddy baya bata fuskar tayi mishi magana balle ta fad'a mishi matsalar ta ina d'anta ya shiga, wasu hawaye ne masu zafi suka fara sauka kan fuskar ta na tsabar kewar d'annata da tayi ji take kamar ta shekara 3 bata ganshi ba............ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 110* Tana zaune a palourn tana wannan tunanin tunanin ga hawaye kaca kaca a face nata Daddy ya shigo parlourn kallo d'aya yayi mata ya d'auke kanshi kada ta karya mishi gwiwa don kwanakin biyun nan tana bashi tausayi ta sanya damuwa akanta saboda rashin jin muryar d'an nata, duk ta rame ta fara zama silent sosai, kok'arin hawa steps na bene yake yaji muryar ta na cewa "Daddyn Sabeer ina son magana da kai please " Ko kallonta Daddy bai yi ba ya fara hawa steps don har yanzu bai ga tayi laushi sosai ba na yanda zai sanar mata inda Sabeer yake. Ganin Daddy ya shareta ne ya sanya ta tashi da sauri ta bi bayan shi, har zai shiga side d'in shi tayi saurin rik'o hannun shi cikin muryar kuka tace "Don girman Allah Dear ka fad'a min inda Son yake? " Hannun shi ya sanya wanda bata rik'e nashin ba ya zame nata hannun yayi gaba kawai ya shige side d'in shi, nan Mumy aka durk'ushe tare da sakin kuka na tashin hankali. Daddy jingina bayan shi yayi da bayan door tare da runtse eyes nashi tausayin ta ne yake neman rinjayar zuciyar shi don yasan yana son Dr Faridah so bana kad'an ba, ba k'aramin wahala yake sha ba na wannan zaman da suke yi tare amman bashi da yanda za yi dole ya nuna mata kuskurenta na zubar mishi da en jikokin shi da tayi so yake tayu nadama sosai yanda a lokacin zai sanar mata da inda d'anta yake, amman fah kukan ta yana ta6a mishi zuciya sosai. Sai da tasha kukanta ta more sannan ta mik'e ta wuce side d'in ta hawaye na zuba a eyes nata, kamar wata mahaukaciya sabon kamu take faman gwada kiran number's d'in Sabeer na dukkan k'asar da tasan yake zuwa har da ta gida Nigeria amman dukka abu d'aya nau'ora take sanar da ita a kashe suke, zaman tayi kan bed tare da rafka tagumi dole ta fara binciken inda Sabeer ya tafi bazata zauna ba batasan halin da Sabeer yake ciki ba. *********** Zaune Suhaima take kusa da Aunty Aliyah suna aikin girki na dare suna er hirar su cikin nishad'i, Yah Aliyu ya fito daga palon Aunty Aliyah hannun shi rik'e da phone nashi kallon su yayi tare da girgiza kai kullum haka suke kamar abokanan juna ya fad'i hakan cikin zuciyar shi, mik'awa Suhaima wayar yayi ba tare da yace mata komai ba ya juya zuwa cikin palon. Da kallo ta bishi cikin mamaki wane yake kiranta haka, kawai sai ta sanya wayar a kunnen ta jin ana magana, wani zabura tayi tare da tashi tsaye ta buga tsalle da ihu murna tana furta "Jiddahhhh" Sabeer da yake kwance kan bed cikin d'akin Suhaima da sauri ya taso jin muryar Suhaima tana ihu, turus yaja ya tsaya da yaji ta ambaci sunan Jiddah, tsayawa yayi bai k'arasa fitowa ba daga d'akin tare da hard'e hannun shi dukka biyun yana kallonta yanda take tsallen murna, murmishi ya saki cikin zuciyar shi yana cewa "Baby nah har yanzu yarinta na damun ki halin nan yana nan bai canja ba " Ya fad'i hakan cikin zuciyar shi yana kok'arin komawa cikin d'akin suka had'a ido da ita hura mata kiss yayi sannan ya shige cikin d'akin. Murmishi Suhaima tayi da taga abin da Sabeer yayi mata nan ta cigaba da waya da Jiddah cikin farinciki taji dad'in sakkowar Yah Aliyu sosai kodan kewar Jiddah tayi sosai, bayan sun sha hirar su Jidda cikin d'oki take fad'a mata gobe zata zo daga k'arshe suka yi sallama cikin kewar junan su. Aunty Aliyah na zaune tana kallon ta murmishi kawai take ganin yanda Suhaima suke waya cikin d'oki, zama tayi tana cewa "Wallahi Aunty nayi kewar Jiddah sosai naji dad'in yanda Yah Aliyu shi ya kirawo ta da kanshi ya had'a mu " "Nima kaina naji dad'in hakan Suhaima Allah ya bar wannan kauna dai" "Amin Aunty, gobe ma tace zata zo " "Allah ya kaimu sai kiyi shirin yin dambu ko d'an wake don nasan halin Jiddah da son cin su idan tazo gashi an kwana 2 bata zo nan ba " Cikin murmishi Suhaima tace "Haka ne kuwa Aunty nah kin ma tuna min gobe da wuri zan tashi na fara hidimar taryan ta kinsan Jiddah da d'oki da wuri zaki ganta" D'an hararar wasa tayi mata kan tace "Wanne tashi wuri kuma kimsan dai mijin ki na nan gashi baya jin dad'i zama zaki ki kula dashi naji da hidimar Jiddah " Kwa6e fuska Suhaima tayi tare da shagwa6e wa har da karyar da wuya tace "Kaiii Aunty bayan ya warke kuma gaskiya ni zan yi " Girgiza kai Aunty tayi kafin tace "A'a Suhaima ki bawa mijin ki kulawa yafi koma ni zanji da komai" Bata son yin musa da ita don haka tace "Toh Aunty " "Yawwa tawan dad'i na dake bakya jayayya Allah ya bamu jikoki twins " Wata kunya ce ta rufe Suhaima musamman da taji Yah Aliyu ya amsa da "Amin Mata ta " Wanda ya fito zai fita yaji Aunty Aliyah tana wannan addu'ar, da gudu Suhaima ta mik'e ta wuce cikin d'aki kunya sosai ta rufe ta kamar ta nutse, yayin da Yah Aliyu da Aunty Aliyah suka sanya dariya har da tafawa da hannun su. Bayan ta yana jingine a bayan k'ofa eyes nata a lumshe tana murmishi bata ankara ba taji saukar kissing a wuyan wanda ya haddasa mata sauke ajiyar zuciya tare da bud'e idonta sauke su tayi kan na Sabeer wanda daman kallonta yake. Da sauri tayi niyyar wuce wa cikin d'akin ya sanya hannu tare da rik'e nata kafin kuma ya janyo ta gaba d'ayan ta jikinshi ya rungume ta tsam, wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke cikin kunnen ta ya rad'a mata " i luv U Baby nah " Murmishin jin dad'i tayi bata ankara ba taji ya d'auke ta gaba d'ayan ta bai ajiye ta ko'ina ba sai saman bed kwanciya a jikinta yayi hannun ta yana saman kanshi tana wasa da gashin yayin da shi kuma yake fad'a mata irin matsayin da take cikin zuciyar shi yana bayyana sirrin zuciyar shi wanda wasu abubuwan baza su fad'u a baki tsakanin shi da DANGARTAKAR ZUCIN shi ne wanda yana godiya ga Allah da bai sanya YAYI SAKEN sakin Suhaima ba wanda yasan sai ya fad'a kogin tsantsar nadama amman Allah ya takaita mishi K'ARSHEN WAHALAR shi, zai kasance mai godewa Allah har karshen rayuwar shi akan bashi Suhaima da yayi kamilar mace wadda ta had'a komai kuma wadda kowanne namiji yake fatan ajiye irinta a gida, yasan yasha wahala duk A SANADIN SON ta amman gashi komai ya wuce K'ARSHEN WAHALAR shi yazo yana fatan insha Allah babu abin da zai sake rabashi da Babyn shi sai mutuwa. Kiran sallahr mangarib ne ya katse su Sabeer ya tashi yayi alwala ya wuce masjid ya bar Suhaima na kok'arin shiga toilet don yin alwala. Bayan ta idar da sallahr ne ta tsaya karatun Qur'an har zuwa sallahr ishsha bayan tayi addu'o'in ta ne sannan ta sake gyara d'akin sosai ta fita ta sami garwashi ta kunna turaren wuta, sannan ta koma wajen Aunty Aliyah suna d'an ta6a hira duk da har yanzu tana jin kunyar ta akan maganar d'azu. Sai wurin 9 na dare suka shigo gidan Yah Aliyu da Sabeer nan inda suke zaune a saman tabarma suka zauna kowanne kusa da matar shi, nan Suhaima ta zuba abincin aka fara ci bayan an gama ci aka zauna er hira zuwa 10 na dare suka yi sallama kowa yaja matar shi suka wuce d'akin su. Duk yanda Sabeer ya so kasancewa da Babyn shi tak'i bashi had'in kai saboda tak'i mance ya tsane ta da ya furta mata, k'arshe da zai takura mata ta sakar mishi kuka dole ya hakura ya fara lalla6a ta har ya samu bacci ya d'auke ta, zuba mata ido yayi bayan bacci ya d'auke ta Baby rigima ya furta hakan kan ya sake rungume ta ajikin shi wani sonta na sake ratsa mishi cikin zuciya da haka shima bacci yayi awon gaba dashi. *_WASHE GARI DA SAFE_* Suna zaune gaba d'ayan su a tsakar gidan suna breakfast da yake Yah Aliyu sai da rana yake da lecture sai hira suke cikin jin dad'i da annushuwa. Sallama suka ji ana yi lokaci d'aya gaban Aliyu da Suhaima yayi mugun fad'uwa wanda har ya kasa yunkurar tashi don yaga wane, sai da aka kuma yi har sau biyu amman ya kasa tashi har sai da Sabeer yace "Babban Yaya ko naje na duba? " Da sauri Aliyu ya mik'e tare da cewa "Barshi bari naje " Fita yayi jikin shi a matuk'ar sanyaye, yana bud'e k'ofa ya fita ras ras gaban shi ya fad'i ganin wani tsohon mutum duk kanshi da gemun shi furfura ta mamaye su gashi kamar ka hure shi ya fad'i d'an siriri dashi duk yayi bak'i ya zama wani kala gashi yana rik'e da sanda da ita yake dogarawa kallo d'aya zaka yi mishi kasan bai dad'e da tashi daga wannan muguwar cutar ba ta paralyzed ba, jiyowa mutumin yayi suka had'a ido da Aliyu lokaci d'aya Aliyu ya d'ago hannun shi yana nuna shi bakin shi na rawa dakyar bakin shi ya iya had'a kalmar "Ba... Bab..... Babaaaa! " Sorry Fan's na kusan gama muku ku cigaba da yi min uxiri. Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 111* Cikin tsananin mamaki da razani Aliyu ya sake furta "Baba me ya kawo ka wajen mu kuma yanzu?" Dattijon ya fashe da wani irin kuka yana cewa "D'ana kayi hak'uri ku yafe min abubuwan da nayi kuma ciki har da tafiyar da nayi na barku sama da shekaru masu yawa ban waiwaye ku ba " Ran Aliyu ne ya k'ara 6aci da ya tuna saboda bak'incikin shi mahaifiyar su ta rasu da irin wulak'ancin da ya dunga yi musu, sam bazai ta6a yafe mishi akan abubuwan da ya aikata a gare su, don haka ya bud'e baki cikin rawar murya yace "Baba ni da k'anwata bama buk'atar sake ganin ka kamar yanda mu ma ka gudu ka barmu don haka kawai ka kyale mu zamu k'arasa rayuwar mu babu uba " Yana gama fad'in haka ya juya zai koma gida, yayin da Baba yake faman kuka yana furta "Ku yafe min Aliyu hakk'in ku ne yake bibiyata ku yafe min ko na ji dad'in rayuwata " Amman ina Aliyu bai saurare shi ba ya wuce gida tare da rufe k'ofar ya jingina bayan shi kan k'ofar duk dauriya irinta Aliyu sai da ya kasa rik'e kukan shi ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi har yanzu yana jin amon murya Baban nashi yana furta su yafe mishi. "Lafiya kake kuka? " Yaji saukar muryar Sabeer kusa dashi yana mai rik'e shi hankalin shi a tashe don a iya sanin shi Aliyu jarumi ne ba kamar shi ba dole akwai wani babban abu da ya d'aga mishi hankali. Girgiza kanshi yake kawai ya kasa magana, suna cikin haka Suhaima da Aunty Aliyah suka shigo zauren jin kamar sautin kuka, hankalin su ba k'aramin tashi yayi ba ganin yanda Aliyu yake kuka, nan take suka fara kukan ita Aliyah zuciyar ta ce ta bata Baban ta ko Babaar tane wani daga cikin su ya rasu. Da sauri Suhaima ta k'arasa wajen Yah Aliyu ta shige jikin shi tana kuka tace "Yaya me.... me ya faru kake kuka? " Ganin yanda hankalin su ne ya tashi sosai ya sanya shi bud'e baki dakyar cikin muryar kuka a shak'e yace "Suhaima Bab..... Baban mu ne ya dawo " Awani firgice Suhaima ta d'ago kanta ta kalli Yah Aliyu cikin tsananin tashin hankali da rud'ani kafin ta rushe da kuka tace "Yaya don Allah kace ya tafi ina tsoran shi wallahi kada ya kashe mu kamar yanda ya fad'a, Yaya zai dawo yana dukan mu da zagin mu ina tsoran shi..... " Ganin abin nata ya had'ar mata da tsoro, firgici da kuma sumbatu har ta rasa me zata ce ya sanya Sabeer ya janyo ta jikin shi ya rungume ta yana bubbuga bayan ta alamar rarrashi yayin da Aliyah ma ta k'arasa wajen mijinta tana bashi baki da ya bud'e k'ofar duk da kuwa da irin kallon da yake wurgata, gashi sai wani sauke huci yake kamar wani tsohon zaki. Suna tsaka da haka ne suka ji ana bubbuga k'ofar cikin sauri Aliyah ta sanya hannu zata bud'e k'ofar amman kafin ta bud'e Aliyu ya sakar mata wata harara bashiri ta hakura kawai ta zubawa mijin nata ido yanda ya rikid'a ya koma mata wani daban kamar ba Aliyun ta ba. "Aliyu, Aliyah, Suhaima, Sabeer ku bud'e k'ofar nan nasan kuna jin na" Suka jiyo amon muryar Baba Adamu yana kwalla musu kira, Sabeer ne yayi kok'arin janye Suhaima daga jikin shi ya samu ya bud'e k'ofar, yana bud'e wa Baba Adamu da Babaa Lantana suka shigo bayan su kuma mahaifin su Aliyu ne yana dogara sanda. Suna had'a ido da Suhaima ta wani saki k'ara mai rud'ewa wanda sauran kad'an ta wuntsila tsabar firgita da tsoran shi da sauri Sabeer ya taro ta ya rik'e ta k'am itama rik'eshi tashi sosai suka shige cikin gidan jikinta na 6ari don masifar tsoron shi take. Daman tabarmar da suka karya akanta tana nan a shimfid'e zama suka yi dukkanin su ban da Suhaima da ta gudu d'aki tana kuka sai Yah Aliyu da yake tsaye ya kasa zama. Tashi Sabeer yayi ya nufi d'akin ya tarar da Suhaima tana kwance a ruf da ciki tana kuka sosai, cikin sanyin jiki Sabeer ya k'arasa inda take ya zauna tare da janyota jikin shi ya d'orata saman k'afafun shi share mata hawayen face nata yake yi cikin sanyin murya yake rarrashin ta, dakyar ya samu tayi shiru sannan ya d'auko ruwa ya bata tasha, kad'an ta iya sha sannan yace "Baby nah ki nutsu mu je, amman na rok'e ki kada kiyi kuka ji yanda idanun ki da fuskar ki suka yi ja gashi sun kumbura saboda kukan da kika yi" Cikin sanyin jiki ta d'aga kanta alamar toh daga haka yaja hannunta suka fito zuwa tsakar gidan inda suke zaune jugum jugum kamar gidan makoki sautin kukan Baban su Suhaima ne kawai yake tashi, damk'e hannun Sabeer Suhaima tayi jikinta ya fara rawa don masifar tsoron Mahaifin ta take kallonta Sabeer yayi cikin zuciyar shi yana tunanin mai Mahaifin su yayi musu da har Suhaima take jin tsoron shi haka gashi ya karanto tsananin tsanar shi kan fuskar Aliyu da Suhaima. Gefe suka samu suka zauna sannan Baba Adamu yayi gyaran murya tare da cewa "Alhamdullilah dukkan godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da ya bamu aron rai har zuwa wannan lokacin da ya sanya ni ganin wai Umaru ne ya dawo gida" Baba Adamu ya k'arasa maganar tashi cikin tsananin mamaki da jimamin yanayin da suka ganshi aciki, cikin sanyin murya da tsantsar nadama Baban su Aliyu yace "Bani da bakin kare kaina a wajen ku don hak'ik'a na cika azzalumi mara imani kuma butulu a wajen iyalina, nayi nadama dana sani mara adadi nasan na cika mara tausayi wajen mata ta Fatima da yarana Aliyu da Suhaima, bansan ta inda zan fara neman gafarar ku ba ku tausaya min duk wani jin dad'i na rayuwa bana jin shi kuma nasan duk hakk'in ku ne ku yafe min 'ya'ya n........ " Bai k'arasa fad'in maganar ba saboda wani kuka da ya kubce mishi na nadama, duk wajen shiru akayi ana sauraren shi sai da ya tsayar da kukan dakyar yace "Ina Fatima ku kaini inda take na nemi yafiyar ta don Allah, Aliyu Suhaima ku yafe min ba don ni ba don girman Allah " Baba Adamu ne yace "Umaru sai dai kayi hak'uri amman Allah yayi wa Fatima rasuwa tun washegarin da ka tafi cikin ma dake jikinta shima ya rasu " Neman mik'ewa yake amman jikin shi babu k'arfi ya k'asa tashi sai kawai ya fashe da kuka yana cewa "Na shiga uku yanzu ya zanyi da d'unbin tarin hakk'in Fatima da yake kaina me yasa ma na tafi na barku Fatima ki yafe min " Babaa Lantana tana zubar da hawaye tace "Umaru ka godewa Allah kafin Fatima ta rasu ta yafe maka duk abin da kayi mata" Kallon Babaa Lantana yayi tare da kura mata ido kamar yau ya fara ganin ta yace "Da gaske kike Fatima ta yafe min? " "Tabbas Umman mu ta yafe maka don ita ba macuciya bace kuma ba azzaluma bace ta kasance mai hak'uri da yafe wa mutanen da suka zalunce ta komai girman laifin da suka yi mata " Cewar Aliyu kenan a fusace, matsowa kusa dashi yayi kan ya sanya hannun shi yana kok'arin rik'e Aliyu da sauri Aliyu yayi baya yana girgiza mishi kai tare da wurga mishi wani kallo yace "Kada ka sake ka ta6a ni " "Ka yafe min d'ana 'yata ki yafe ni " Ya k'arasa maganar yana kallon Suhaima kauda kanta tayi daga kallon shi sai dai zuciyar ta ta fara rauni tausayin mahaifin nata ya fara shiga cikin zuciyar ta amman tana tsoron kallonshi balle tayi mishi magana. "Haba Aliyu kada ka zama mutum mara yafiya, nasan ka da zuciya mai kyau kayi hak'uri ka yafe mishi mahaifin ka ne baka da kamar shi duk duniyar nan, Allah yana son masu yafiya idan an zalunce su, kayi duba ma da halin da yake ciki wannan kadai ma ya ishe shi " Nan Baba Adamu da Babaa Lantana suka dunga yi musu nasiha tare da nuna musu mahimmanci mahaifi agare su koda wanne laifi ya aikata a wajen ka yana nan matsayin mahaifi ba'a ta6a canja shi k'addara ce da son zuciya suka rinjaye shi ya aikata hakan, nan Sabeer ma ya fara ya fara lalla6a su akan suyi hak'uri su yafe mishi haka Aunty Aliyah ma ta sanya baki akan maganar dakyar da sud'in goshi Aliyu da Suhaima suka yafe wa mahaifin su saboda ganin girman mutanen da suka sanya baki cikin maganar. Yana kuka yana gode musu tare da sanya musu albarka Yah Aliyu dai tashi yayi kawai ya shiga d'aki baya tunanin ko makaranta zai iya zuwa yau wani abu ne yake nuk'urk'usar cikin zuciyar shi kwanciya yayi yak'i fitowa sai da yaji muryar Baba Adamu yana kira shi sannan ya fito idanun shi jawur ya samu waje ya zauna. Cikin kuka Umaru ya fara basu tak'aitaccen labarin shi bayan barin shi gidan..... "Tun da na d'auki jaka ta na tafi ban tsaya ko'ina ba sai cikin kaduna anan na tsaya cikin kasuwa ina buge buge na, na neman aiki ni ne dako da duk wani aikin k'arfi don kawai na samu kud'i na tara naji dad'in rayuwa ta,amman sai naga ko nayi aikin kud'in basa yi min albarka sai dai uban wahalar da nake sha da haka dai na samu dakyar na samu d'an rumfa ina siyar dasu kayan miya, ba laifi ina d'an ciniki akusa da inda rumfa ta take ne akwai wata mai siyar da abinci sunan ta Ladidi mai abinci 'yar duniya ce sosai awajen ta nake siyan abinci kullum, mun gaisuwar mutunci da ita gashi wani lokacin kyauta zata zuba min abinci ta aiko min shi har rumfata da haka muka d'auki tsayin lokaci ashe sona take sai daga baya take sanar min, da fari nak'i yarda ganin yanda idanun ta suke a bud'e sosai amman daga k'arshe ta shawo kaina na amince da ita, nan muka shirya yin aure nace mata banda iyaye ni maraya ne sai kawai na samu limamin unguwa ya zama wakili na ya d'aura mana aure daman agidan ta zamu zauna tun da tana da gida, farkon zaman namu munyi shi cikin kwanciyar hankali da jin dad'i amman da muka fara d'aukan shekaru komai ya canja ta fara yi min rashin mutunci kala kala na yau daban na gobe daban, gashi yanzu kasuwa taja baya d'an kayan miyar da nake siyarwa jarin ya karye mun cinye shi a abinci, daga nan fah wulak'anci take min kala kala har takai zaman gidan ya gagare ni saboda masifar ta duk wani hakk'i nawa na kanta bata sauke min na zama kamar matar ita mijin tunda ita take ciyar dani amman da sharad'in sai nayi mata aikace aikacen gidan ". Kallon shi Yah Aliyu yayi ya tuna lokacin da Umman su idan bata gama abinci ba da wuri zagi kala kala zai yi mata har da duka kuma ya dunga ball da duk abin da ya ci karo dashi agidan yana kiranta k'azama abubuwa dai kala kala babu irin wanda bai yiwa Umman su ba lallai Allah ne ya nuna mishi ishara akan zaluntar su da yayi. Ya cigaba da cewa "Haka nake yi mata aikin don kawai ta ban abinci, gashi tana tara maza agidan musamman 'yan daudu, ashe Ladidi 'yar bariki ce ta k'arshe daga baya nake jin labari har shaye shaye take agabana babu abin da na isa nayi k'arshe sai ta ware min d'aki a zaure aciki nake kwana azaba da wahala nasha shi kala kala nayi bak'i na rame sosai nayi nadama sosai gashi kullum cikin mafarkin Fatima nake da yara na, ita kuwa Ladidi bata haihuwa kwata kwata gashi na rasa me ya sanya na zauna nake bauta mata duk zafin zuciya ta kuwa gaba d'aya nayi sanyi kamar ba ni ba ni kaina nasan Ladidi ba haka ta bar ni ba don tana bin malamai sosai, da haka muka kwashe shekaru da ita ina cikin wannan wahalar, nan na fara rashin lafiya sosai dakyar nake iya tashi amman ko kud'in da zan siyi magana ban dashi, daga k'arshe dai Ladidi ta kamu da cutar HIV ban san tana da ita sai kawai........ " Wani kuka ne ya kubce mishi na tsananin bak'inciki da takaici, yayin da gaban Aliyu da Suhaima yayi mummunar fad'uwa kada Ladidi ta shafawa mahaifin su ciwon, kallon shi suke a tsorace don jin mai zai ce haka su Baba Adamu da Babaa Lantana, Aliyah da Sabeer suka tsorata suna addu'ar Allah ya sanya bata sanya mishi ba. Cikin kukan ya cigaba da cewa "Sai kawai ta yanke shawarar bazata mutu ita kadai ba sai ta goga min ciwon nata, bansan hawa ba ban san sauka ba wata rana kwatsam naga tana faman gyara gidan ta shirya lafiyayyen abinci ta kawo min amman ban iya ci ba saboda lokacin jikina babu sauk'i, na tashi zan shiga bandak'i ne naji tana magana da wata kawar ta a waya ashe abincin nan da ta kawo min duk sai da ta zuba musu jinin jikinta saboda yanzu ban da k'arfin da zan sauke mata buk'atar ta sai ta 6ullo ta wannan hanyar, ban k'arasa jin zancen ba na zube k'asa a sume don nayi matuk'ar kad'uwa da jin wannan maganar ta" Wata ajiyar zuciya Aliyu da Suhaima tare da sauran mutanen wajen suka saki jin bata yi nasara akan shi ba lallai Ladidi ta cika macuciya kuma muguwa, share hawayen fuskar shi yayi kafin ya k'arasa da cewa "Daga nan sa farkawa nayi naji ni agadon asibiti sai dai na had'u da lalurar shanyewar 6arin jiki wato paralyzed,nayi kuka nayi nadama sosai alokacin kullum cikin addu'a nake akan Allah kada ya d'auki rayuwata sai nazo na nemi yafiyar ku kullum da ku nake bacci nake tashi ina tsananin son naga na dawo wajen ku, naji ma ina jinya kafin na samu na 6arin jikina ya fara motsi da taimakon wannan liman d'in da ya d'aura ma aure da Ladidi da yake d'an shi likita ne, bayan na d'an fara magana ne na saki Ladidi saki uku wadda itama alokacin ciwon yaci k'arfin ta har ta kwanta, daga nan liman ya taimaka min da kud'in mota na taho gida na nemi afuwar ku don nasan hakk'in ku ne yake bibiyar ta dakyar na iya kawo kaina garin nan wannan shine tak'aitaccen labarina tun bayan bari na gida, ina sake neman afuwar ku 'ya'yana ". Suhaima kuka take sosai najin irin azabar da mahaifin su yasha a hannun muguwar matar nan, Cikin rad'a Sabeer yace "Baby ba kuka zaki yi ba godewa Allah zakiyi da ya tseratar da Baba daga hannun ta " Nan Aliyu ya dad'a saukowa daga fushin da yake da mahaifin shi jin irin azabar da yasha, sosai Baba Adamu ya dad'a yi musu nasiha kafin kuma ya nunawa Baba surukin shi wato Sabeer da kuma surukar shi Aliyah sosai Baba yaji dad'i da ganin yanda yaranshi suka dace da samun abokanan rayuwa nagari, bakin shi yak'i rafuwa saboda jin dad'in yanda su Baba Adamu da Babaa Lantana suka rik'e mishi yaran shi godiya sosai yayi musu da addu'o'i sun sha shi a wajen shi, daga k'arshe Baba Adamu yace "Idan Allah ya kaimu gobe Aliyu ya kamata ka kaishi asibitin birni ya dad'a ganin likita sannan kuma tunda babu d'aki anan wanda zai na kwana sai ya koma gidan mu tunda muna da d'akuna ya zauna aciki kafin ya warware asan abin yi " Kowa ya aminta da abin da Baba Adamu yace Aliyu da Suhaima sun rasa wace irin godiya zasu yi wa bayin Allahn nan tun suna yara suke d'awainiya dasu gashi har girman su basu kyale su ba, daga haka Baba Adamu ya tashi suka tafi don Mahaifin su Suhaima yaje ya kwanta ya huta. Bayan sun tafi ne Jiddah take kiran Yah Aliyu a waya bazata samu damar zuwa yau ba sai gobe, sun d'an ta6a hira da Suhaima duk da ba'a cikin nutsuwar ta take ba, kiran sallahr azahar ne ya tashe su daga nan kowa ya fara kok'arin haramar yin sallah. Bayan sallahr ishsha ne hadari ya had'u a garin sosai dole ta sanya Suhaima d'aukan abincin su ta shigo dashi d'aki saboda yau babu zaman waje ruwa daf yake da ya sakko, agurguje ta dafa ruwan wankan su ta d'ura wani a flaks ragowar kuma ta zuba a bokiti mai murfi ta wuce d'aki, cikin toilet takai ta ajiye sanann ta koma d'akin Aunty Aliyah wadda take zaune tana sanyawa Ameer kayan sanyi saboda yanda garin iska take kad'awa, zama Suhaima tayi tana jan kumatun Ameer shi kuma yana yi mata dariya. Hirar su suke yi inda Aunty Aliyah take taya Suhaima murnar dawowar mahaifin su, bayan ta gama sanya mishi kayan Suhaima ta d'auke shi tana mishi wasa, Aunty Aliyah ta mik'e ta shiga cikin bedroom d'in ta bata dad'e ba ta fito hannun ta rik'e da wata roba da abu aciki sai wani cup kuma a hannun ta, zama tayi kusa da Suhaima tana cewa "Kin ga tun safe na had'a zan baki amman dawowar Baba yasa na mance kinsan dama baki k'arasa sha ba koh? " Ta fad'i tana kallon Suhaima wadda ta ta6e fuska take son yin shagwa6a tace "Kaiii Aunty wallahi ni nagaji da shan irin wad'annan abubuwan fah? " 'Yar dariya Aunty Aliyah tayi kan tace "Yarinya yanzu kika fara sha kuwa wani abin ma sai kin haihu kuma ba abu ne wanda zai cutar da ke ba " Tana gama fad'in haka ta bata na cup d'in ta shanye sannan ta tsiyaya mata na robar ta shanye daman ragowar cup biyu ne dakyar ta k'arasa shan kamar zatayi kuka ita dai Aunty Aliyah dariya tayi cikin zuciyar ta tana cewa da kanki zaki dawo neman shi yarinya. Ganin an fara yayyafi ne yasa Aunty Aliyah fad'a mata ta tafi d'akin ta, haka ta tashi tare da yi mata sai da safe ta wuce d'akin ta, tana shiga d'akin aka saki wata tsawa batasan lokacin da ta fad'a kan bed ba ta tukunkune jikin ta na 6ari saboda tsorata. "Washhh Allah nah! Baby kin karya ni " Taji an fad'a a kusa da ita da wata irin murya da ta sanya Suhaima k'ara rikicewa ga d'akin da duhu, tana kok'arin sauka daga kan gadon taji an sanya hannun an kamota tare da janyo ta jikin shi, bud'e baki tayi zata saki ihu taji an rufe mata da bakinta ashe Sabeer ne ya dawo batasani ba lokacin tana d'akin Aunty Aliyah. Had'e lips d'in shi yayi da nata yana wani irin passionate kiss jikin Suhaima rawa yake sosai don ta tsorata walk'iya akayi wanda har haskenta ya ratso ta window d'in d'akin nan Suhaima taga ashe Sabeer wata ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kwace bakinta ta d'auki pillow tana bugun shi na wasa cikin kukan shagwa6a take cewa "Shine ka tsorata ni koh?, sai na rama nima" Kare dukan yake yana dariya yace "Haba sweetie nah sai dai ki rame kuwa " Gajiya tayi ta ajiye pillow tare da cewa "Bazan ma kwana a d'akin ba komawa zanyi d'akin su Yah Aliyu " Kok'arin tashi take ya sake janyo ta jikin shi ya rungume ta yana cewa "Ke yanzu aka ce kije sai ki tafi? " "Eh mana bama sai ance naje ba " "Lallai Baby da sauran yarinta akan ki, sai ki tafi ki bar mijin ki anan suma tak'ura musu zaki yi babba dake ki wani tafi d'akin su " Har ta bud'e baki zata sake magana ya sanya hannu ya rufe tare da cewa "Yunwa nake ji Baby " Sai lokacin ta tuna ko abincin rana bai ci ba saboda baccin da ya d'auke shi sai daf da la'asar ya tafi kuma ya tafi masallaci bai dawo ba sai yanzu gashi daman a makare aka gama abincin ranar. Hannun shi ta kamo ta zaunar dashi kan carpet sanann ta zuba mishi tuwon shinkafa miyar bushashshen ku6ewa tare da manshanu ga yajin daddawa mai dad'i agefe, langa6e wa yayi a baki zata bashi bata da yanda zata yi ta fara bashi da hannun ta shima yana bata, kad'an suka iya ci ya 6ata lokaci yana lashe 'yan yatsun nan nata dakyar ya saki ta bashi tea mai lemon tsamin da ta dafa mishi ya sha, kwashe kwanukan tayi ta ajiye su waje d'aya ba damar fita kai su kitchen saboda ruwan da yayi k'arfi, rufe k'ofar d'akin tayi tare da sanya key sannan ta saki labulen window bayan ta gama ta wuce toilet don wanke hannun ta sannan ta had'a mishi ruwan wanka. Tana tsaka da had'a ruwan ne ya shigo cikin bathroom d'in da sauri Suhaima ta juya taga Sabeer ne ya cire kayan shi sai k'aramin towel nata da ya d'aura a kugun shi wanda dakyar ya ritsa shi, hannu ya sa ya matsar da ita ya had'a musu ruwan dukka su biyun kafin ta ankara ya janyota jikin shi ya fara cire mata kaya zata yi magana kenan ya girgiza mata kai idonshi cikin nata, sunkuyar da kanta tayi kawai tana jinshi ya cire mata kayan nata tsaf. Bayan sunyi wankan ne sukayi brush sannan suka fito daga bathroom d'in, Suhaima ta shirya cikin wata doguwar riga ta bacci mai siririn hannu cotton ce ta shafa perfume da humrah ta had'e gashin ta cikin ribbon tayi parking d'in a gefe don kada ya hanata bacci, Sabeer kuwa yana sanye da boxer d'in shi duk abin da take yana bin ta da kallo jira kawa yake ta gama shiryawa yaji ta a cikin jikin shi. Kasa jira yayi ta gama shirin ya tashi ya d'auko ta saman bed ya sauke ta tare da kashe fitilar d'akin wadda take amfani da batir, kafin Suhaima ta fara yi mishi korafi ya had'e lips d'in su waje d'aya, nan fah Suhaima ta fara kuka tana zame jikinta aikuwa Sabeer ya rikice mata sosai wasu zafafan sak'onni yake turata mata wanda ya sanya Suhaima sakin jikinta ta biye mishi ba tare da ta sani ba. Wannan daren sun faranta shi ya zame musu tamkar daren su na farko, Sabeer ya nuna mata tsantsar son da yake mata yana kuka yana rokanta kada ta rabu dashi, bayan komai ya kammalu ne ta fara zum6ura baki tana k'unk'uni, abin ma dariya ya bashi sosai nan ya 6ige da aikin rarrashi kan su wuce suyi wanka suna kwanciya bacci mai dad'i yayi awon gaba dasu, zuciyar kowa fes da farinciki ga kuma yanayin garin da yayi dad'i suna rungume da junan su suka yi bacci............ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 112* Washe gari tun safe da wuri Aunty Aliyah ta kammala abin karin safe ta aikawa da Baban su Aliyu, har Aliyu ya fita schl bata ji motsin Suhaima ba, ganin ta gama komai ne ya sanya ta zura hijab ta d'auki Ameer suka tafi gidan su don gaida Baba Umaru. Suhaima wadda tsabar gajiyar da tayi ya hanata tashi da wuri tun sallahr asuba da tayi ta koma bacci ko shima Sabeer yana dawowa daga masallaci ya rungume kayar shi suka cigaba da baccin su hankali kwance. Suna tsaka da baccin su mai dad'i ne Jiddah ta k'araso gidan cikin d'oki da zumud'i take rafka sallama, kamar a mafarki Suhaima taji muryar Jiddah na sallama don haka da sauri ta sauko daga gadon ta fito zuwa waje, had'a ido suka yi da juna wani ihun murna suka saki tare da nufar juna da gudu suka rungume junan su cikin farinciki kamar wad'anda suka shekara basu ga junan su ba. Ihun sune ya farkar da Sabeer daga baccin da yake gane muryar Jiddah ne ya sanya shi jan d'an k'aramin tsaki yasan yanzu zata zo ta dame su bayan yau yana son kasance wa da Babyn shi kusa dashi, don ba k'aramin kewarta yake ba wannan Jiddah duk zata 6ata mishi planning d'in shi tashi yayi ya shiga toilet don yin wanka. Sakin junan su sukayi tare da k'urawa junan su ido na tsayin mintuna can Suhaima tace "Jiddah kin k'ara k'iba da kyau ko dai an samu k'anin Islam ne? " Dariya Jiddah ta saki tare da cewa "Tabbb lallai yarinya don bakisan wahalar haihuwar bane ai sai na huta sosai kafin na sake, ke dai muna jiran naki nan da 'yan watanni " Murmishi Suhaima tayi tare da juya eye's ball d'in ta tace "Ni dai yanzu amarci muke ci sai mun gama tukunna " Kama ha6a Jiddah tayi tare da cewa "Iyyyyeee! Lallai yarinyar nan naga alama Yah Sabeer ya koya miki rashin kunyar shi " Murmishi kawai Suhaima ta sake yi kan tace "Ina zamu zauna d'aki ko waje? " "Kaiii bari nasha iska a waje tukunna ina Aunty Aliyah da Yah Aliyu, hala ma yanzu kika tashi daga bacci? " Kallon kanta Suhaima tayi sai yqnzu ta tuna da sleeping dress d'in da yake jikinta don ma cotton ce kuma doguwa, "Sallamar ki ce ta tashe ni fah, Aunty Aliyah ina tunanin ta fita Yah Aliyu kuma schl ya tafi" "Yah Aliyu ya koma makaranta ne? " "Eh an d'an jima ma da komawar shi, wai ni ina Islam ne? " Dariya Jiddah tayi kafin tace "Zamu shigo kenan muka had'u da Babaa Lantana ta dawo daga wata barka shine ta kar6e ta " "Okay na d'auka baki zo da ita ba nace nayi fushi dake " "Haba ni na isa Besty na, na taho miki da ita " Murmishi Suhaima tayi tana cewa "Kin kyautawa kanki ba don haka ba da sai dai ki koma gida " Suna tsaka da hirar su Sabeer ya fito daga d'aki yayi wankan shi ya sanya wata T-shirt yellow da jeans black, suna had'a ido da Jiddah ya watsa mata harara abin sai ya bata dariya aikuwa ta kwashe da dariya tare da cewa "Ohh ni Yah Sabeer me nayi haka daga zuwa na sai harara " Kallon Suhaima yayi tare da cewa "Baby nah tashi kije ki wanka ki rabu da wannan mai zuwan sassafe gidan mutane " Murmishi Suhaima tayi ta tashi tare da wuce wa d'aki, sai da ta fara gyara d'akin tsaf sannan ta wuce toilet ta wanke shi sannan ta fara wanka. "Allah Yaya kana tak'ura min yanzu fah 11:50 kace nayi zuwan sassafe " Rage murya yayi kafin yace "Saboda zaki hanani hutawa da mata ta ne na tsayin yini guda " "Tabbb Yaya yanda nayi missing d'in Suhaima dasu Aunty Aliyah ai kwana zanyi anan sai dai ka koma kwanan zaure har na tafi " Ta k'arasa maganar da tsokana tana dariya, harara ya dalla mata kafin ya murd'e 'yan yatsun ta kad'an yana cewa "Kin fah rainani yarinyar nan amman zan sanya Khaleel yi miki kishiya ko zaki yi hankali " "lallai ma Yayan nan an fad'a maka ina tsoron kishiya ne tazo mana ba'a kaina zata zauna ba " Hirar su nan suka cigaba dayi har yana fad'a mata dawowar Baban su Suhaima tayi murna sosai da farinciki, da haka Suhaima ta fito har tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga ta atampha tayi kyau sosai sai tashin k'amshi take, tun da ta fito Sabeer ya kafeta da eyes, cikin dariya Jiddah tace "Yah Sabeer irin wannan kallo ai sai kasa ta fad'i " Murmishi kawai yayi indai Jiddah ce bakin ta baya shiru idan taga abu, zama tayi nan kusa dasu bayan ta d'auko musu abin karyawar su anan take taya Suhaima murnar dawowar mahaifin su, murmishi kawai Suhaima tayi tare da cewa nagode, nan suka karya bayan sun gama ne Sabeer ya fita bai dad'e da fita ba Aunty Aliyah ta dawo da Islam a hannun ta d'ayan hannun kuma Ameer ne ta rik'e mishi hannu da yake ya fara tafiya, kar6ar Islam Suhaima tayi tana fad'in Masha Allah ganin yanda tayi 6ul6ul da ita gwanin sha'awa, cikin jin dad'i Aliyah suke gaisawa da Jiddah, suna gama gaisawa ne Aunty Aliyah da Jiddah suka fara kok'arin girkin rana yayin da Suhaima ta baiwa hankalin ta kan su Islam da Ameer tana musu wasa suna dariya. Sunsha hira sosai tsayin yini guda don tun da suka ci abincin rana akayi sallahr azahar suka k'ule a d'aki suna fama zuba hira, sai wajen biyar driven Jiddah ya k'araso suka yi sallama dasu Suhaima ta tafi gida ko had'uwa da Yah Aliyu bata yi ba. AFTER 3 MONTH'S Acikin wad'annan watannin abubuwa da d'an dama sun faru daga cikin abubuwan da suka faru akwai warkewar mahaifin su daga lalurar da ta same shi da kuma samun cikin da Suhaima tayi, sosai Sabeer yayi matuk'ar farinciki da wannan cikin tsabar murna har kuka sai da tayi don yana masifar son yara, sai dai kuma wannan cikin akwai shi da laulayi fiye da na baya sosai Suhaima take shan wahalar shi duk ta rame tayi fari koda yaushe cikin amai abinci kuwa sai ta kusan yini batasa komai a bakin ta ba, duk abin da tayi sha'awar ci Yah Aliyu da Sabeer suna kok'arin nema mata shi kulawa sosai take samu daga mijinta, Yayanta da Aunty Aliyah ga su Babaa Lantana nan har Baban ta ma kullum sai ya shigo dubata kuma sai ya taho mata da d'an abin kwad'ayi gaba d'aya yayi wani sanyi kamar ba Umaru ba, Jiddah tayi farinciki sosai da albishir d'in da Sabeer yayi mata na Suhaima tana da ciki. "Baby nah yau me zaki ce ne? " Sabeer ya tambaye ta yana sanya kaya fitowar shi daga wanka kenan. Kallon shi tayi idanun ta tap da kwalla tace "Ni bana sha'awar cin komai " K'arasa sanya kayan yayi sannan ya zauna kusa da ita tare da d'ago ta ya d'aura ta kan k'afafun shi, kallon ta yake cikin tausayi yace "Bazan barki baki ci komai ba Baby ki fad'a min please " Shiru tayi na d'an mintuna kafin tace "Zan sha fruits toh sun ishe ni " D'an murmishi yayi kan yace "Yawwa Baby nah haka nake son ji bari naje na samo miki " Kwantar da ita yayi saboda jikin ba k'arfi, ya bud'e mata curtains d'in window da na k'ofa don ta samu iska tana shigowa, sannan ya dawo yayi kissing nata a goshi ya fita, ya dad'e tsaye a k'ofar gida yana tunani don duk kud'in da yazo dasu sun k'are ragowar d'ari biyar ce dashi yanzu ya siyowa Suhaima fruit's da ita sun k'are, gashi gobe ko anjima idan tana son wani abu baisan yanda zai yi ba kuma shi bazai ta6a neman kud'i wajen Aliyu ba wanda shima fama yake da hidimar karatu ga d'aukan ciyar su abin da yawa gaskiya gashi duk master card d'in shi da atm card's nashi duk suna gida bai taho dasu ba da wannan tunanin ya tafi. Wajen 30 minute's da fitar shi ya dawo lokacin Aunty Aliyah ta shiga duba ta kuma tana tambayar ta abin da zata ci, d'auko wani bowl na silver yayi da wuk'a bayan ya wanke fruits d'in zama yayi saman carpet din d'akin zai fara yanka mata Aunty Aliyah tace "Sabeer kawo na yanka mana " Murmishi yayi yana cewa "Mamin Ameer ki barni aiki nane kije ki huta kawai " Itama murmishi tayi kafin ta wuce ta fita, Suhaima na kallon shi har ya gama yanka rabi iya yanda zata iya sha anjima sai ya yanka mata sauran. Kusa da ita ya dawo tare da tashin ta zaune ya jingina bayanta da pillow ya fara bata fruit d'in a hankali take bud'e bakin yake bata, duk da Sabeer yana iyakar d'auke damuwa akan fuskar shi ta rashin kud'i da kewar iyayen shi da 'yan uwan shi ga kuma rashin lafiyar Suhaima duk dashi wannan laulayi ne sai anyi hak'uri na d'an wani lokaci amman lalurar ta tsaya mishi a rai har wani d'an rame wa yayi amman duk da haka sai da Suhaima ta gane akwai wani abin da yake damun shi koda ta tambaye shi baya sanar da ita abin da ke damunshi sai dai ya fad'a mata rashin lafiyar tace take damunshi kyale shi kawai tayi amman tasan da wani abin sai dai ta dage da addu'a Allah ya yaye mishi koma mene. Bayan ya gama bata ta shanye shi gaba d'aya cikin tausayin ta ya kalle ta tare da cewa "Na k'ara miki wani? " Murmishin yak'e tayi kafin ta girgiza kanta kawai. "Okay ni zan fita Baby zamu fita da Ashiru amman bazan dad'e ba" Cikin sanyin murya irin ta mara lafiya tace "Allah ya kiyaye hanya ya dawo min da kai lafiya " Cikin murmishi yace "Amin Sweetie nah " Ya k'arasa maganar yana bata peck a kumatu itama tayi mishi a saman lips d'in shi daga haka ya fita daga d'akin Suhaima tabi shi da kallon tausayi. Haka lokaci ya cigaba da tafiy har aka shiga watan ramadan zuwa wannan lokacin jikin Suhaima ya d'an warware zata ci kowann abinci sai dai har idan ita zata dafa da kanta ba zata iya ci ba, kulawa babu irin wadda bata samu, har azumin ma tun da aka fara take jarumtar yinshi batason tasha, Sabeer kam matsalar kud'i ta yi mishi sauk'i don Daddyn shi ya sanya Jiddah kawo mishi atm card nash duk lokacin da yake buk'ata zai je ya cira amman sai dai idan ya kasance muhimmiya ce saboda yana ganin Aliyu bazai ji dad'i ba zai yi tunanin ya raina duk kulawar da yake bashi. Da haka suka cinye wata ramadan aka shiga hidimar sallah, Yah Aliyu yayi matuk'ar kok'arin yi musu d'inkunan sallah haka aka cinye bikin sallah lafia, sosai cikin Suhaima yake girma zama dakyar tashi dakyar sosai cikin yake da girma. Sabeer ba k'aramin tausayin ta yake ji ba haka da dare zai sanya ta a gaba yana faman kallonta tare da shafa cikin kafin ya tashi ya d'aura alwala yana kai kukan shi gun mai dukka akan ya sauki Suhaima lafiya, har wata rama yayi ta fargaba idan ya tuna yasha jin labarin haihuwa akwai wahala, daman tana zuwa awo amman a asibitin cikin gari duk ranar awo shi yake kaita ya jira ta gama su shiga adaidaita sahu ko taxi su dawo gida. Cikin haka cikin Suhaima ya shiga watan haihuwar shi sai zuba ido ake ana jiran haihuwa shiru, yayin da Jiddah da siyo duk wani abin daya danganci kayan jariri unisex da duk wani abin buk'ata Sabeer ya bata atm card nashi taje ta ciri kud'i ta siyo, duk an gama shirin komai sai jiran haihuwa duk wani masoyin Suhaima yana mata addu'a ta Allah ya rabata lafiya da abin da yake cikinta saboda girman cikin kadai ya isa firgita mutum duk ta wani kumbura tayi wani iri kamar ba ita ba kaya sai dai ta zura dogowar riga saboda riga da siket ko da zani bata jin dad'in amfani dasu dogowar rigar ma irin buba nan mara shape, Baba Adamu kullum cikin yi mata rubutu yake na sauk'in nakuda tana sha. Sai da cikin Suhaima ya shiga wata goma cif cikin wata safiya ta monday ta tashi da azababben ciwon nakuda Allah yaso Yah Aliyu da Sabeer duk suna gida basu fita ba nan da nan aka samo taxi suka tafi asibitin da take zuwa awo, suna zuwa aka kar6eta cikin gaggawa suka wuce da ita labour room Sabeer ji yake kamar ya bita ciki amman Yah Aliyu ya rik'e shi gam ganin yanda jikin shi yake rawa yace "Sabeer addu'a kawa zaka yi mata " Nan ya zube akan benci kawai yana faman yin addu'ar duk wadda tazo cikin bakin shi. Suhaima kuwa abin ba'a cewa komai iyakar wahala tasha ta kamar bazata iya haihuwa da kanta ba ma, tasha kukan har hawayen suka daina fita daga idonta saboda azaba addu'a kowacce yin ta take tana fatan Allah ya rabata da cikin nan lafiya, tun safe ake abu d'aya har zuwa k'arfe 9 na dare sannan wahalar ta tazo k'arshe inda ta haifi kyawawa yaran ta guda biyu duk maza wanda suka kasance lafiyayyu masu koshin lafiya, tana gama haihuwar su da taja wani numfashi sai ta zube nan nurse suka yi kok'arin wajen farfad'owar ta sannan suka gyara mata jikinta tsaf bayan sun gama suka sanya mata drip na k'ara k'arfin jiki da kuma allurar bacci don ta samu ta huta sosai don ta wajugu ba kad'an ba. Sai da aka gyara Baby's d'in tsaf suka sanya musu kaya sannan suka duba lafiyar su, su kansu nurse's d'in yaran sun matuk'ar birgesu da basu sha'awa gasu identical twins ne masu kama da junan su sosai. Sabeer kusan suman tsaye yayi tsabar farinciki a lokacin da aka mik'a mishi yaran shi, kallon su yake cikin wani irin masifar kaunar su d'in nan had'e su yayi ya rungume su cikin kirjin shi yana jin wani irin farinciki da shaukin son yaran shi addu'a yayi musu kafin ya bawa su Yah Aliyu da Aunty Aliyah yaran. Room d'in da aka canjawa Suhaima ya nufa zama yayi kusa da gadon yana kallon fuskar ta yanda ta wani rame ta k'ara haske sosai, hannun shi ya sanya yana shafa face d'in ta wani irin kaunar ta ne yake ratsa mishi heart din shi, ta gama yi mishi komai tunda ta haifa mishi yara har biyu masu matuk'ar kama dashi da me zai sakawa Suhaima saboda farincikin da ta sanya shi, daren ranar Sabeer kasa bacci yayi idan yaran suka yi kuka ya d'auki wannan ya d'auki wannan Yah Aliyu ne kadai ya koma gida don Aunty Aliyah zama tayi saboda taimaka mishi da rik'o ln yaran. Sai wurin asuba Suhaima ta farka lokacin Sabeer ya tafi masallacin asibitin, nan Aunty Aliyah ta taimaka mata ta gyara jikinta sannan ta zauna kan bed wata mahaukaciyar yunwa ce take kwakwular cikinta kamar wanda aka kwashewa kayan ciki gaba d'aya, sai da Aunty Aliyah ta mik'a mata Baby's d'in nan sannan ta had'a mata tea tana firfita mata don ya huce. Kallon su take hawaye na zuba daga idonta suna d'iga kan fuskar yaran godiya take yiwa Allah da ya bata wannan kyautar da babu wani d'an adam da ya isa yayi maka ita, hakika ko a mafarki Suhaima bata ta6a tunanin zata haifi twince ba duk wannan wahalar ta haihuwar ta mance da ita ta rungume yaranta cikin tsantsar kaunar su. Duk abin da take Sabeer na jingine a bakin kofa yana kallonta cikin wani irin kaunar ta sun bashi sha'awa, a hankali yayi tattaki ya k'arasa kusa da ita ko kunyar Aunty Aliyah bai ji ba ya rungume ta yana faman yi mata godiya kok'arin had'a lips d'in shi yake da nata ta tuna mishi da Aunty Aliyah a room d'in dole ya hakura da abin da yayi niyya, kar6ar tea d'in yayi yana bata a hankali a baki har ta shanye shi tas sai wurin 10 na safe Doctor ya salllame su bayan ya dad'a duba su an tabbatar basu da matsala sannan suka taho gida har da Aliyu wanda zuwan shi kenan ya tsaya kar6ar kayan abin karyawar da Babaa Lantana tana bashi ya kawo musu. Tun kafin su k'arasa gidan Jiddah ta ruga su zuwa suna shigowa ta nufi wajen Suhaima da gudu ta rungume ta cikin farinciki har Sabeer na hararar ta yana cewa kada ta k'arasa mishi mata, kar6ar yaran tayi ji take kamar ta had'iye su don so gaba d'aya ta kidime sai taji tana son itama ta haifi twince sun bata sha'awa sosai. "Suhaima don Allah kika yaye su zaki bar min su " Fad'in Jiddah kenan harara Sabeer ya sake dalla mata tare da cewa "Yarinya kada ma kisa a ranki bazan baki yara na ba " "Kaiii Yah Sabeer kasan gaba nawa Allah zai baka watakila ma twince da twinkle zata yi ta haifa " "Innallilahi Jiddah rufa min asiri idan ba mutuwa kike so nayi ba wannan ma sun ishe ni rayuwa " Dariya aka kwashe da ita ganin yanda Suhaima gaba d'aya ta firgice, wanka Aunty Aliyah ta fara yiwa yaran yayin da Babaa Lantana kuma ta kama Suhaima tana kuka tana yi mata wankan ganye da tafasasshen ruwan zafi Suhaima ansha kuka fatar nan taji ja saboda dokan ganye jikinta, Sabeer kamar yayi kuka ganin yanda ake wahalar da Babyn shi. Sai da aka gama gyara su tsaf sannan Baban su Aliyu yazo ganin jikokin nashi yayi musu addu'a sosai, daga nan ya tashi ya tafi sai yamma lik'is Jiddah ta tafi kamar bazata tafi ba haka take ji a wayar ta Sabeer ya kirawo Daddy yake fad'a mishi Daddy tsabar murna kamar yayi tsintsuwa ya taho har da hawayen shi na farinciki daman yana addu'ar Allah ya sanya Sabeer ya haifi yara masu yawa saboda shi kadai ne gare su sai gashi haihuwar farko da biyu Allah ya fara basu. Washe gari kuwa sai ga Daddy yazo da kanshi saboda tsabar murna rungume Suhaima yayi yana mata godiya sosai har sai da taji kunya sosai nan ya d'auki yaran yana kallon su ya rasa ina zai sanya kanshi saboda murna. A lokacin Sabeer yake musu hud'uba Hassan yaci sunan Dr Ahmad d'an fillo kamar yanda Daddy yace ya sanya Hussein kuma sunan Baban su Suhaima aka sanya mishi Omar dakyar Daddy ya iya tafiya har yana tafiyar Sabeer yaushe zasu gidan su don ya sanya an gyara gidan an canja komai hatta da fentin gidan sai da aka canja. "Daddy sai lokacin da Suhaima taso dawowa har yanzu tsoron Mumy yana nan cikin zuciyar ta " Gid'a kai Daddy yayi tausayin d'an nashi fal cikin zuciyar shi kafin suyi sallama ya tafi. Suhaima da Aliyu tare da Mahaifin su sunyi matuk'ar murna da jin sunan shi aka sanyawa Hussein har kukan farinciki yayi sosai. Ranar suna anyi taron suna dai dai gwargwado Suhaima ta samu kyautittika tun daga kan uban gayya wato Sabeer, Yah Aliyu, Aunty Aliyah, Jiddah da mijinta Khaleel, Baba Adamu, Babaa Lantana, Baba Umaru, Ashiru abokin Sabeer na kauye, Daddy da kuma Musaddiq da matar shi wanda sai lokacin yake fad'a mishi komai da ya faru, kowannen su yayi mata kyauta daidai k'arfin shi anyi suna lafiya an gama lafiya, raguna 2 da sa 2 Sabeer da Daddy suka yanka duk wannan abin da yake faruwa babu wanda ya sani cikin family d'in d'an fillo sai da Daddy da Jiddah kawai, haka su Suhaima suka cigaba da yin wanka cikin kwanciyar hankali gashi Na'eem da Shaheed suka cigaba da girma kamannin su da Baban su na k'ara fitowa da haka har sukayi arba'in........... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 113* Bayan sun yi wata biyu da en kwanaki ne Suhaima babu inda taje duk kuwa da nacin da Jiddah take akan Sabeer ya barta taje amman yak'i yarda sai dai ita tazo, duk wani gyara da ya kamata ayiwa wadda ta haihu Suhaima ta samu wannan gyaran daga 6angaren Aunty Aliyah, Jiddah da Babaa Lantana, tuni tayi er kiba kad'an ta murje tayi kyau abin ta duk da kuwa rainon biyu babu sauk'i amman Sabeer yana matuk'ar taimaka mata haka Aunty Aliyah da Babaa Lantana suna taya ta rainon su sosai. Bayan ta gama yiwa Na'eem da Shaheed wanka ne da yake lokacin zafi ne ta sanya musu powder tare da kaya marasa nauyi gadon su taje ta kwantar dasu tare da yi musu addu'ar tsari ta bacci sannan ta wuce toilet tayi wanka, d'aure da towel ta fito d'an k'arami, had'a ido tayi da Sabeer wanda yake zaune kusa da gadon Na'eem da Shaheed yana lilasu a hankali murmishi suka sakarwa junan su cike da so, wani mayataccen kallo Sabeer yake bin ta dashi wanda tun safe ta kula da irin wannan kallon nashi, ita tsoron ma zuwa kusa dashi take hannun shi ya mik'a mata bata yi musu ba ta mik'a nata ya rik'e shi tare da janyo ta jikin shi ya fara shinshina wuyan ta zuwa bayan ta hura mata iskar bakin shi yayi cikin kunnen ta wanda ya haddasawa Suhaima kasala cikin muryar rad'a yace "Baby nah ki bani wannan damar please ina son kasance wa dake nayi missing d'in ki da lot " Duk da ta gane nufin shi amman da taji abin da yace sai da taji fad'uwar gaba amman ya zata yi tunda hakk'in shi ne wanda ya rataya kan wuyanta, don haka k'ara shigewa jikin shi tayi kawai tana cusa face nata a chest d'in shi. "Bari naje nayi wanka koh? " Ya k'arasa maganar yana d'aga mata gira, tashi yayi ya wuce toilet yayi wanka sannan ya fito ya tarar da ita har ta shirya cikin wata gown ta bacci iyakar rabin cinyarta (da yake Sabeer ya sanya Jiddah d'ebo mata kayan ta ba tare da wani ya gane ba) ta gyara gashin ta sai tashin kamshi take, kallonta yake kamar yau ya fara ganin ta. Agurguje ya shirya ya taho wajen ta ya rungume ta cikin jikin shi yana faman aika mata da zafafan sak'onnin shi cikin wani irin salo mai wuyar fassara, wannan daren sun raya shi sosai cikin wani irin kaunar junan su anan Sabeer ya gama tabbatar wa Suhaima itace rayuwar shi haka ita ma a 6angaren ta gwarzon nata shine jin dad'in rayuwar ta suna addu'a da fatan Allah ya barsu har karshen rayuwar su. Rayuwar su suke cike da jin dad'i da kwanciyar hankali suna kula da yaran su sosai da haka har Na'eem da Shaheed suka tasamma shekara d'aya yaran sunyi wani irin girma gashi suna wata goma suka iya tafiya gudun su suke ko'ina zuwa lokacin Aunty Aliyah tana d'auke da tsohon ciki itama, zumunci Jiddah da Suhaima kuwa kullum k'aruwa yake idan bata zo ba to za suyi waya junan su, tsakanin Suhaima da Sabeer kuwa kullum soyayyar su k'ara k'arfi take kula suke bawa junan su sosai, Daddy kuwa a weekend yake zuwa ganin jikokin shi. Suna watanni goma sha bakwai Suhaima ta yaye su, yayin da Aunty Aliyah kuma ta haihu aka samu mace sunan Umman su Suhaima aka sanya mata wato Fatima suna kiran ta da Ameerah, Yah Aliyu ma karatun shi ya d'auki zafi yana daf da had'a degree d'in shi a Buk. Wani zuwa weekend da Daddy yayi yace yana son Na'eem da Shaheed su bishi suyi mishi kwana 2 sunyi matuk'ar shak'uwa da Daddy sosai, a tsorace Sabeer ya barwa Daddy yaran shi don yana jin tsoron kada Mumy ta kashe musu yara, tsaf Daddy ya karance shi girgiza kai kawai yayi yana murmishi bai ga laifin shi ba yana da gaskiyar shi baisan yanzu yanda Mumy ta koma ba ne duk wannan ji da kan babu shi. ********** Duk wani jin dad'i gashi nan akwai shi sai dai babu kwanciyar hankali, duk tayi bak'i ta rame Dr Faridah kenan wato Mumy abin duniya yayi mata yawa wajen shekara 2 bata sanya tilon d'anta a idon ba tayi neman tayi binciken duk a banza tayi kok'arin tambayar Daddy akan inda d'anta yake but yace shima neman shi yake k'arshe ma rufe ta da fad'a yayi ai duk laifin ta ne gashi ta salwantar mishi da rayuwar d'an shi ba'a san inda yake ba. Ta 6angaren Dr Ahmad d'an fillo dasu Hajjah Hauwaa suma suna cikin wannan tsantsar tashin hankalin na rasa sanin inda Sabeer sunyi binciken iyakar iyawar su amman basu ji d'uriyar inda yake amman Dr Ahmad d'an fillo yaso d'ago Daddy yasan inda Sabeer yake ganin yanda hankalin shi yake kwance bai d'aga hankalin shi sosai ba akan 6atan Sabeer amman sai Daddy ya nuna mishi ba haka, tun daga lokacin Dr Ahmad d'an fillo ya kwanta rashin lafiya saboda 6atan Sabeer d'an lelen shi yayi kuka sosai yana mai nadamar da tun lokacin yayi magana matar shi ta dawo gare shi tun da dalilin ta suka neme shi suka rasa, Haka ma Mumy ta kwanta ciwo a tsaitsaye ko hospital bata iya zuwa jinin ta hau sosai damuwa biyu ce ta had'e mata rashin tilon d'anta da kuma juya mata baya da mijinta yayi duk a dalilin Suhaima, wadda zuwa wannan lokacin tayi nadamar abin da ta aikata yafi sau ba adadi tayi kukan sosai da bata aikata hakan ba da tuni d'anta na kusa da ita har da jikokin ta ma, har tana fatan ta d'an samu sauk'i ta nemi garin su Suhaima taje ta nemi yafiyar ta ko zata samu sassauci cikin zuciyar ta da rayuwarta gaba d'aya. Tun safe yau jikin ta ya rikice ga Daddy baya nan yafita tana kwance a falo wajen 4 na yamma ne jefi jefi tana kallon tv tana kallon African Tv suna wa'azi na marigayi sheik Ja'afar Mahmoud Adam (Allah ya jik'an shi da rahma Amin), lokaci zuwa lokaci gaban ta na fad'uwa. Sallama Daddy yayi ya shigo palourn hannun shi rik'e da Na'eem da Shaheed suna d'an tsalle tsallen su, wata zabura Mumy tayi ganin wasu kyawawan yara masu matuk'ar kama da junan su kuma abin da ya k'ara hargitsa ta ganin yanda suke matuk'ar kama da Daddy da kuma Sabeer, nan take wani tunani ya d'arsu cikin zuciyar ta ko Daddy aure ya sake bata sani ba matar ta haifa mishi yara. Da d'an gudun su suka k'arasa inda take tare da rungume mata k'afafun ta, sakin baki kawa tayi tana kallon su wani irin sanyi taji jikinta yayi ta zame ta zauna lokaci d'aya wani mugun son yaran ya ratsa mata cikin zuciyar ta da zuciya d'aya ta d'ago su zuwa jikin ta cikin murmishi take cewa "Ya sunan ku yara nah?" Na'eem da yafi surutu cikin muryar shi wadda bata kware ba yace "Ni sunan Na'eym wannan kuma Sha'eed" Ya k'arasa fad'i yana Shaheed da d'an yatsan shi, "Masha Allah sunan masu dad'i Allah ya albarkaci rayuwar ku " "Amin " Daddy ya amsa cikin zuciyar shi, d'agowa tayi ta kalli Daddy tare da cewa "Daddy yaushe ka sami yara masu kama da kai bansani ba? " Murmishi yayi yana tafiya Stairs yana cewa "Bana wa bane aron su aka bani na kwana 2 " Cikin d'okin murya tace "Da gaske kake Daddy?" "Ban ta6a yi miki wannan wasan ba gaskiyar kenan " Washe baki tayi duk yanda jikinta babu dad'i amma sai taji lokaci d'aya kamar an cire mata ciwon cikin farinciki take cewa "Nagode Thank U very much Daddy naji dad'in ganin yaran ji nake kamar my Son nake gani Allah ya biyaka " Ta k'arasa maganar hawaye na fita daga eyes nata sosai Daddy yaji wani mugun tausayin ta lokaci yayi da Dr Faridah ya kamata tasan ainahin inda d'anta yake yana gama wannan tunanin ya wuce stairs da sauri. Dad'i ya ishe Mumy ta rasa inda zata sanya yaran duk wasu kayan kwad'ayi na yara haka ta cika musu gaban su dashi, koya ta kalli yaran wani sonsu ne yake sake ratsa zuciyar ta ji take tamkar da Sabeer take tare lallai idan tasan iyayen yaran nan dole ta k'ulla zumunci dasu kodan suna zuwan mata, a baki ta dunga basu abinci bayan sun gama ci ne ta shiga bedroom d'in Daddy tana tambayar shi kayan yaran ce mata yayi bai taho musu dashi ba. "Don Allah ka barni muje wani mall d'in sai na siyo musu kayan har da na wasa kada kace a'a please dear " Murmishi yayi sannan yace "Okay, amma ke da baki da lafiya zaki fita? " "Zan iya wallahi " Ta fad'i hakan tana yin gaba da sauri kamar wata yarinya da kallo Daddy ya bita dashi kafin ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "Ina son ki Faridah naji dad'in yanda kika daina daukan kanki kamar kin fi kowa " Cikin farinciki ta shirya agurguje ta fito car key kawai ta d'auka tare da rik'o hannun su suka fito zuwa compound na gidan shigar dasu tayi ta zaunar dasu sannan ta rufe k'ofar, sit na drive ta zauna da kanta tayi motar key cikin kwarewa take driving d'in ta tana jin wani nishad'i cikin zuciyar ta. Bayan sun shiga wajen kayayyakin wasan yara nan ta sake su aikuwa da gudu suka tafi wajen kowanne na d'aukan abin da yake so, sosai ta kashe kud'i wajen siya musu kayan wasa, sannan ta siya musu kayan sawa masu kyau da tsada 6angaren kayan ciye ciye ma haka ta siya musu duk abin da suke so sannan daga k'arshe suka taho gida, idan kaga Na'eem da Shaheed tare da Mumy bazaka d'auka jikokin ta bane zaka fi zaton yaran ta ne wanda ta haifa........... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 114* Cikin kwanaki biyun da Na'eem da Shaheed suka yi Mumy tayi matuk'ar sabawa dasu sosai sai kace 'ya'yanta kaunar su take tamkar ita ta haife su tana musu wani irin so da baki bazai iya misaltawa ba, ko hospital bata zuwa kullum tana cikin basu kulawa da tattalin su, ganin yanda take kula su ya sanya Daddy jin sanyi cikin zuciyar shi duk wani fushi da yake da ita gaba d'aya ya daina koda ta rok'i ya yafe mata abin da tayi a karo na ba adadi a lokacin kasa jurewa yayi ya yafe mata don yaga tayi matuk'ar yin sanyi sosai, rungume shi tayi tsabar farinciki da jin dad'i. Kwana su biyu kamar yanda Daddy yayi alkawarin zai mayar wa dasu Sabeer yaran su don haka a ranar da safe ya sanarwa Mumy ta shirya su za'a mayar dasu gidan iyayen su, kuka sosai Mumy ta fashe dashi don ta shak'u da yaran acikin kwana 2 wani irin son su take, dakyar Daddy ya rarrashe ta tayi shiru nan ta shirya su tsaf tare da had'a musu kayan wasan su da ta siya musu su kansu Na'eem da Shaheed har da kukan su lokacin da zasu tafi, yini guda Mumy tayi a kwance saboda tsabar kewar Na'eem da Shaheed duk gidan yayi mata babu dad'i picture d'in Sabeer ta d'auko tana shafa face d'in shi cikin muryar kuka take cewa "Ina ka tafi ka barni Son, ina son ganin ka ina son jin muryar ka nayi kewar d'ana ka dawo wajen mahaifiyar ka zanyi maka duk abin da kake so Son zanje da kaina na dawo maka da Suhaima ku haifa min jikoki nima kamar su Na'eem da Shaheed " Wani kuka ne yaci k'arfin ta nan ta kife kanta akan bed tana yin kuka sosai cikin tsananin kewar d'an nata. ******* Kwance yake akan carpet yayi ringingine yau tsayin kwanaki uku kenan yana mafarki da Mumyn shi tana kuka tana ce mishi ya dawo gare ta, yanzu lokaci yayi da zai bayyana kanshi wajen Mumy shi kanshi yana cikin tsananin kewar ta yana son ganin mahaifiyar shi ya neme afuwar ta akan d'aga mata hankalin da yayi don yasan yanzu hankalin ta a tashe yake sosai, ga tsananin kewar yaran shi da basa tare dashi yanzu yanda ya kwana 2 kawai bai ga yaran nashi ba yana tsananin kewar su ina kuma Mumy da ta shafe wajen 2yrs bata sanya shi a idonta ba ko taji muryar shi dole ya gaggauta komawa gida wajen Mumyn shi. Yana cikin wannan tunanin ne Suhaima ta shigo d'akin ta jima tana kallon shi baisan ma ta shigo d'akin ba, cikin kwanakin nan tana kula dashi da yanda yake cikin damuwa, cikin sanyin jiki ta k'arasa inda yake ta kwanta cikin jikinshi lokaci d'aya suka saki ajiyar zuciya, k'ara k'ank'ame ta yayi cikin jikin shi, kallon face d'in shi Suhaima tayi tace "My dear har yanzu tunanin ne, ka fad'a min abin da yake damun ka please " Shafa face nata yayi kafin yace "Baby ina son ganin Mumy nah ne " Murmishi ta saki mai sanyi kan tace "My dear abu mai sauk'i kawai gobe ka shirya ka tafi, nima kaina ina son kaje kaga Mumy don nasan hankalin ta yanzu yana tashe " "Yawwa Baby nah ki shirya mu je zan yiwa Daddy waya kada a kawo su twin's gobe muka je sai mu taho dasu " "Lokaci yayi da zaka koma ka cigaba da rik'on company d'in ka my Dear kabar Daddy da nashi shima " "Allah Baby da gaske kike zamu koma gidan mu? " Mak'e kafad'a tayi cikin sigar wasa tace "A'a ni dai zamu zauna anan duk weekend sai kazo kana ganin mu " Ta6e fuska yayi yana son yin kukan shagwa6ar da aka kwana 2 ba'a yi ba yace "Haba Baby baza ki tausaya wa d'an mijin ki ba, idan muka zauna waje d'aya sai yafi min kwanciyar hankali please please Baby nah" "Uhm uhm wayo kake son yi min nak'i yarda " Da ya gane tsokanar shi take nan ya cafkota tare da cewa "Baby kin rainani da yawa don kin ga kwana 2 kin huta baki samawa su twin's k'annen su ba koh, bari yanzu zan baki ajiyar Baby nah " Dariya sosai Suhaima take yi ganin yanda yayi, tashi yayi da sauri ya rufe k'ofar d'akin sannan ya dawo kusa da ita ya shiga aika mata da sak'onnin shi bata yi musu ba itama ta shiga mai da mishi da martani, sun jima suna faranta ran junan su kafin su yi wanka kuma ya shirya ya tafi masjid don sallahr la'asar yayin da Suhaima kuma ta zauna gyara jikinta. Su Daddy na hanya dawo da Na'eem da Shaheed ne Sabeer ya kirawo shi a waya akan suyi zaman su gobe suna tafe zuwa gida don yaga Mumyn shi, sosai Daddy yaji dad'in haka nan ya shiga sanyawa Sabeer albarka daman da wannan niyyar ya taho na wajen rarrashin shi ya zo Mahaifiyar shi ta ganshi, bayan sun gama waya ne Daddy ya sanya driver ya koma gida sai ganin su kawai Mumy tayi cikin jin dad'i ta rungume Na'eem da Shaheed suma sai murna suke da ganin sun dawo wajen ta sai da ta gama murnar dawowar su sannan ta kalli Daddy tace "Yana ga kun dawo sun bar min su ne? " "A'a gobe iyayen su zasu zo sai su tafi dasu basanan yau ne " Yana gama fad'in haka ya wuce ya fita, dad'i sosai Mumy taji idan sun zo zata nemi alfarmar su barmata su don Allah idan yaso ta sanya su schl duk hutu sai suna zuwar musu hutu wajen iyayen su. Da daren ranar Sabeer yake yiwa Aliyu maganar zuwan su gobe gida nan Aliyu yayi mishi fatan alkhairi shi da Aunty Aliyah, cikin daren nan Sabeer kasa bacci mai nauyi yayi yana zumud'in gari ya waye ya ganshi a jikin Mumyn shi yana zuba mata shagwa6a son ranshi. Washe gari bayan sun gama breakfast ne Aliyu ya sanya aka taro musu taxi har k'ofar gida, basu dad'e ba suka fito cikin shirin tafiya Sabeer na sanye da wata shadda ash colour yayin da Suhaima take sanye da wani lace ash&pink d'in flower's sunyi kyau sosai nan suka yi sallama da kowa kafin su shiga motar mai taxi yaja su tafi, Suhaima murmishin yak'e kawai take amman gabanta sai fad'uwa yake batasan me zata je ta tarar acan ba don haka duk a tsorace take. Tun safe da Mumy ta tashi take faman zirga zirga a tsakanin kitchen da dining area tana shirya abincin bak'i, dariya ta bawa Daddy ma sosai ganin ko baccin kirki ta kasa don tana son kyautata musu Sosai su ji dad'i, don su ji dad'in bar mata Na'eem da Shaheed cikin zuciyar Daddy cewa yayi yaran ki ne zasu zo ba wasu bak'i daban ba. Sai da ta gama shirya komai sannan ta barwa en aikin ta gyaran palon da na kitchen, tattara Na'eem da Shaheed tayi suka tafi Upstairs d'akin ta suka shiga nan tayi musu wanka tsaf tare da shirya su cikin kayan su irin d'aya jean ne blue sai pink d'in T-shirt sunyi kyau sosai takalman su ma pink ne ta fesa musu perfumes masu k'amshi, zaunar dasu tayi saman bed tare da basu iPad d'inta bayan ta kamo musu game tace "Oya ayi game ban da fita kuma ban da rigima yanzu zanyi wanka " Gid'a mata kai suka yi don hankalin su nakan wayar murmishi tayi ta shafa kansu sannan ta wuce toilet, agurguje tayi wanka ta fito ta shirya cikin wata gown black mai adon silver tayi rolling kanta da veil d'in rigar sosai tayi kyau bakace ita ta haifi Sabeer ba bayan ta fesa perfumes ne ta kamo hannun su Na'eem da Shaheed suka fito zuwa downstairs a palourn suka zauna tana zaune ta zubawa k'ofar palo ido so take kawai taga iyayen Na'eem da Shaheed. Motar na tsayawa agaban gate d'in gidan sai da gaban Suhaima ya fad'i sosai fiye da lokutan bayan, hannun ta Sabeer ya rik'o ya rik'e k'am tare da cewa "Relax Baby na ki kwantar da hankali babu abin da zai faru insha Allah ina tare da ke " Jikinta a sanyaye ta gid'a kanta kawai don bakin ta yayi mata nauyi, fitowa suka yi daga cikin mota daman Yah Aliyu ya biya kud'in duk kuwa da Sabeer yak'i yarda da hakan amman sai da biya, mai taxi ya juya ya tafi kallon gidan Sabeer ya tsaya yi yana nan yanda yake sai gyaran shi da akayi sosai, tura k'ofar jikin gate yayi suka shiga hannun shi rik'e dana Suhaima jikinta ko'ina rawa yake na tsoro. Da yake atime d'in rana tayi sosai kowa yana part d'in shi, maigadi sakin baki yayi yana kallon d'an lelen gidan d'an fillo, murmishi Sabeer yayi mishi aikuwa nan ya k'araso wajen Sabeer zai tsugunna ya hanashi bakin shi yak'i rufuwa yake gaida Sabeer da Suhaima yana murnar dawowar shi. Sallamar maigadi yayi sannan suka wuce cikin gidan kai tsaye part d'in su ya shige dasu, door bell ya danna sau biyu zai danna na ukun ne aka bud'e k'ofar parlourn. Kallon junan su suka tsayi cikin wani irin shauk'in so na tsakanin uwa da d'anta kowannen su idanun shi taf da hawaye, ji suke tamkar a mafarki hawayen eyes d'in Mumy ne ya sakko kan face d'in ta tana cewa "My Son kai nake gani da gaske? " K'arasa shiga cikin parlourn yayi still hands d'in shi cikin na Suhaima, d'ayan hannun shi ya sanya yana goge mata face d'in ta cikin rawar murya yace "Mumy ni ne Sabeer d'in ki ba mafarki kike ba " D'aga hannun ta sama tayi tare da cewa "Allah Yah Allah nagode maka da ka dawo min da yaro na cikin koshin lafiya " Tsugunnawa k'asa suka yi daga Sabeer har Suhaima wadda bata kula da ita ba yace "Mumy I'm so sorry nasan na 6ata miki rai da yawa kiyi hak'uri ki yafe min please " Dafa kanshi tayi kafin tace "Son ni ce wadda ya kamata na rok'i ka yafe min don ni na aikata maka abubuwa da dama ka yafe min d'ana" Ta k'arasa maganar tana had'a ido da Suhaima, da sauri Suhaima tayi k'asa da kanta gabanta na fad'uwa jikinta na rawa sosai don batasan me zata yi mata ba. Cikin mamaki sosai Mumy tace "Son daman kana tare da Suhaima " "Yes! Mumy ina tare da Mata ta " "Alhamdullilah Allah nagode maka da ka dawowa da d'ana farincikin shi " Tashin Suhaima tayi ta rungume ta k'am ajikinta lokaci d'aya ta fashe da wani irin kuka tana fad'in Suhaima ta yafe mata, cikin hawayen farinciki da na tausayin Mumy Suhaima tace "Mumy komai ya wuce wallahi na yafe miki tuntuni, mu ma ki yafe mana " "Na yafe muku duk da babu abin da kuka yi min ni ce na zalunce ku" "No Mumy ki daina fad'in haka komai ya wuce please " Had'a su tayi ta rungume su sosai suna zubar da hawayen farinciki, Daddy ne yayi clapping hand's nashi duk suka jiyo suka kalle shi face nashi fal farinciki yace "Alhamdullilah wannan rana itace nake addu'a koda yaushe Allah ya nuna min ita ina raye, hak'ik'a naji dad'i sosai nayi farinciki da haka " Murmishi Mumy take duk da kuwa tears ne ke zuba daga eyes nata, nan Sabeer ya nemi yafiyar iyayen su suka yafe mishi tare da yi musu addu'o'i na fatan alkhairi acikin rayuwar su kowannen su cikin zuciyar shi fal farinciki. "Abbah! Mamee! " Suka jiyo voice d'in su twin's suna kwala musu kira da sauri suka taho inda suke da gudu suka rungume iyayen nasu suna masu farincikin ganin su, kusan suman tsaye Mumy tayi kallon Daddy tayi tana neman k'arin bayani a wajen shi. Murmishi yayi kafin yace "Jikokin ki ne yaran Son d'in ki ne da Suhaima " Wayyo dad'i Mumy rasa inda zata sanya kanta tayi don farinciki da tsabar murna kawai zuwa tayi ta rungume Daddy tana kuka, tapping hands nashi yayi kan bayanta yana cewa "Is okay Mata ta kukan ya isa hakan godewa Allah zaka yi " "Daddy bansan me zance ba " "Godewa Allah zaki yi kawai " Suna cikin haka ne suka ji anyi magana da bakin k'ofar parlour ana cewa "Hussein da gaske maigadi yake cewa Sabeer ya dawo gida " Da sauri Sabeer ya juya ganin kakan shi Dr Ahmad d'an fillo ne yake maganar daganin shi kasan bashi da cikakkiyar lafiya, da gudu Sabeer ya k'arasa wajen shi ya rungume shi yana cewa "Ni ne Sabeer d'an lelen ka na dawo gare ku kakanah " "Alhamdullilah naji dad'in haka sosai Allah yayi maka albarka da ka dawo gare mu kada ka sake yi mana irin haka d'an lele don ka tasar mana da hankali sosai " Cikin kaunar d'an tsohon da tausayin shi Sabeer yace "Insha Allah bazan sake ba " Ana cikin haka Hajjah Hauwaa tazo itama ta gama d'an kukanta na dawowar Sabeer, anan suke ganin Na'eem da Shaheed wai duk yaran Sabeer ne, Dr Ahmad d'an fillo baisan lokacin da ya rik'e hannun Suhaima yana zuba mata godiya ba Hajjah Hauwaa kuwa rungume ta tayi, nan family's na cikin gidan suka dunga shigowa zuwa ganin twin's da taya su Mumy murnar dawowar Sabeer gida. Dr Ahmad d'an fillo kwasar twins yayi suka wuce part d'in su dasu don bazai iya barin su ba son yaran yake har ma ya zarta son da yake yiwa Baban su, sai after la'asar ne su Suhaima da Sabeer suka samu zaman cin abinci bayan sunyi wanka, suna gama ci Mumy takai Suhaima bedroom d'in ta don ta huta komai ganin shi Suhaima take tamkar a mafarki wai yau itace Dr Faridah take rungumeta ajikinta tana mata godiya sannan kuma family's d'in Sabeer suke murnar kasancewar ta acikin su kowanne yana farincikin ganin ta lallai komai da lokacin shi duk tsanani yana tare da sauk'i hak'uri yana da riba babba a rayuwa haka kuma ka rik'e addu'a baza ka ta6a ta6ewa ba a rayuwar ka............ _Masu yi min addu'a ta samun sauk'i Alhmdllh na samu lafiya, nagode sosai Allah ya bar zumunci_Ameen Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 *A SANADIN SON KI* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *THE END* _Na sadaukar da dukannin shafin nan ga dukkanin masoya na da fan's d'in A SANADIN SON KI, ina gaida ku aduk inda kuke tare da yi muku fatan alkhairi cikin rayuwar ku_❣ *PAGE 115* Kwanakin su biyu agidan suna zaune cikin farinciki Mumy tattalin Suhaima sosai tana bata kulawa haka sauran en uwan Sabeer ma haka duk wad'anda suka yi mata abubuwa marasa dad'i sunzo sun bata hak'uri kuma ta hak'ura daman bata rik'e su ba cikin zuciyar ta, Jiddah tayi farinciki yanda en uwanta suka kar6i Suhaima a yanzu matsayin suruka ta gaban goshi kowa tattalin ta yake. Kwana su biyu agidan da dare Sabeer ya shigo side d'in Mumy ya gaji da kewar matar shi, kunya ce take sanya ta k'in zuwa side d'in shi koda ya nemi da ta zo inda yake, gajiya yayi da wannan abun ya tahi d'akin, yana shigowa d'akin tana fitowa daga bathroom d'aure da towel duk gashin kanta ya watsu a fuskar ta da wuyanta duk sun manne saboda ruwan dake jikinsu. Suna had'a eyes ne suka tsaya kallon junan su cikin tsananin kewa da shauk'in junan su, kallon ta yake kamar ya had'iye ta anutse ya k'arasa inda take tsaye ya zuba hands nashi cikin aljihun jeans d'in dake jikin shi, lumshe eyes tayi tana mai jin fad'uwar gaba kamar yau ta fara kasancewa dashi, kamshin perfumes d'in shi ya cika mata hanci yana k'arasa wa wajen ya cire hannun shi daga aljihun ya zuba su saman kafadun ta cikin tattausar murya yace "Baby haka zaki yi min koh? " Cikin shagwa6a tace "Me nayi maka kuma? " "Lallai Baby har kin mance koh, idan na kirawo ki kizo bedroom d'ina bakya son zuwa why? " "Ni Allah kunyar Daddy da Mumy nake ji amman kayi hak'uri " Murmishi yayi kafin yace "Okay tun da haka ne yau zamu koma gidan mu " D'an waro eyes tayi sannan tace "Wayyo my Dear dare yayi fah ka bari sai gobe please ". "Okay naji amman sai na rage zafi tukunna ". Kafin ta sake magana taji ya had'e ta da jikin shi sannan ya sanya lips nashi cikin nata wani soft kiss yake mata wanda yake ratsa kowanne jijiyar jikinta, kok'arin cire towel d'in yake ya mance ma a inda suke gaba d'aya ya tafi wata duniya ta daban sai ji yayi Suhaima ta kwace bakinta da gudu ta shige ta rufe, yayin da Sabeer ya bita da wani irin kallo jikin shi asanyaye ya k'arasa kan bed ya kwanta yana mayar da ajiyar zuciya. Kwanciyar kenan Mumy ta shigo bedroom d'in agajiye daga hospital take kallon d'an nata take cikin kulawa tace "Son ya haka lafiya? " Cikin shagwa6a yace "Mumy bakin rik'e min mata ba kunyar ku tasa ko side d'ina bata zuwa gaskiya gobe kisa a gyara mana gidan mu zamu koma nagaji " Kallon shi Mumy take har sai da ya k'arasa maganar sannan tace "Toh sarkin mara kunya kai kuma koh, babu inda zata je sai ta huta nan da koh 1month ne " Azabure ya tashi kamar wanda kunama ta d'ana yace "What! Mumy kashe ni zaki yi ne " "Ba'a mutuwa sai kwanan mutum ya k'are mara kunya " Juya kanshi yayi gefe yana k'unk'uni tare da turo baki, dariya sosai ya bawa Mumy don sauran kad'an ta kubce mata amman ta danne ta. Ana cikin haka Daddy ya shigo d'akin lokacin Mumy tana kok'arin cire lapcot d'inta, taimaka mata yayi yana tayata cirewa sai kuma ya hango Sabeer yana 6a66ata fuska yace "Ah! Son what wrong with U? " Kauda kai yayi bai yi magana ba kallon Mumy yayi yace "Sweetie nah me akayi wa Son ne? " Bashi labarin komai Mumy tayi ta k'arasa da fad'in "Shine fah ina gama fad'a mishi ya tsaya yana wani 6ata fuska " "Gaskiya Mumy baki kyautawa Son ba a bashi matarshi please ina rok'an mishi wannan alfarmar " Murmishi Mumy tayi kan tace "Okay Daddyn Sabeer an gama gobe sai su koma gidan amman gaskiya za'a bar mana twin's " Wani tsallen murna Sabeer ya doka tare da rungume Mumy yana cewa "Indai twin's ne Mumy mun bar miki nasan zamu samu wasu very soon " D'an bige bakin shi kadan Mumy tayi tare da cewa "Baka da kunya wannan yaron " Sosa kai yayi da d'an gudu ya bar bedroom d'in, dariya Mumy da Daddy kawai suka yi zuciyar su fal farinciki, Suhaima ma da take cikin toilet murmishi kawai tayi da yake duk tana jin su wani sabon son mijinta taji yana ratsa kowanne lungu da sak'o na zuciyar ta, sai da taji fitar Mumy da Daddy daga bedroom d'in sannan ta fito ta shirya. Washe gari kuwa da safe Mumy ta tura en aikinta tare da Jiddah suka gyara gidan tsaf Jiddah na kula da yanda suke gyaran gidan, zuwa bayan sallah issha suka koma gidan nasu amman ban da su Na'eem da Shaheed don su Mumy sun kar6e su sun zama nasu. Kula tattalin juna da kuma soyayya ta gaskiya ita tace jigon zaman lafiyar da Suhaima da Sabeer suka ginata cikin gidan su, zaman su suke cikin jin dad'i da kwanciyar hankali, Suhaima yanzu bata da wata matsala yanzu sai tason cigaba da karatun ta kuma tasan komai lokaci ne idan Allah ya nufa zata yi ne. *AFTER 2 YEAR'S* Abubuwa da dama sun faru acikin wad'annan shekarun ta 6angaren Yah Aliyu ya kammala karatun shi na mass com har ya samu aiki a freedom radio a 6angaren labarai, Sabeer kyautar gida yayi mishi don yafi samun sauk'in zuwa wajen aikin da kuma sabuwar mota amman sam Yah Aliyu yak'i kar6a sai dakyar aka shawo kanshi ya kar6a, tuni suka tashi suka dawo cikin gari wannan gidan nasu na kauye kuma suka barwa Mahaifin su bayan Sabeer ya k'ara gyarashi tare da gidan su Babaa Lantana da Baba Adamu, anan aka matsawa mahaifin su Suhaima da yayi aure babu 6ata lokaci ya sami wata mata wadda auren ta d'aya mijin ya rasu ko haihuwa bata yi ba don haka ya aureta suna zaman su cikin kwanciyar hankali. Haka kuma sun samu en uwan Umman su (Fatima) wad'anda suka zo kauyen suna neman su har suka dace wajen samun Baba Umaru, a lokacin aka nemo su Aliyu da Suhaima suka zo don ganawa da family d'in su wad'anda basu ta6a gani ba, sunyi mamaki sosai na ganin irin manyan mutanen da suka zo a matsayin en uwan Umman su, labari aka zauna yi bayan ansha koke koke da neman gafarar juna inda suke ba da labarin su en asalin garin kd ne, ashe Mahaifin su ne maraya ne Mahaifin Fatima ya d'auke shi aiki matsayin drivern shi so daga nan suka fara soyayya babu wanda ya sani bayan ta gama schl ne aka had'a ta aure da wani d'an uwanta wanda bama a k'asar 9ja yake aiki ba tak'i yarda sai tace sai Umar shine kadai wanda zata aura a k'arshe suka gudu sai neman su akayi aka rasa, shine en uwanta suka yi fushi da ita sosai har suka k'i neman ta sai kuma daga baya zuciyoyin su suka yi sanyi aka fara neman su amman ba'a gansu ba sai yanzu Allah ya tak'aita musu wahalar su. Atime d'in da suka ji Fatima ta mutu sunyi kuka sosai iyayen ta sun yafe mata abin da tayi musu, nan fah aka gabatar musu da Suhaima da Aliyu saboda tsabar murna rungume su suka yi, Suhaima da Aliyu sunji dad'in ganin family d'in su sosai, sai yamma suka fara shirin tafiya Aliyu yayi musu alkawarin zasu zo har kd d'in, nan suka tafi kamar kada a tafi haka suke ji. Daren ranar Suhaima take bawa Sabeer labarin komai ya tayata murna sosai, bayan sati d'aya suka shirya suka tafi kd sosai suka yi mugun mamakin ganin irin had'add'un gidajen su ashe manyan en boko ne, en siyasa da kuma en kasuwa da yake Umman su ita kadai ce mace duk maza ne yayyannin ta wajen su bakwai kuma suna raye har da yaran su manya ma. Tar6a sosai suka yi musu ji suke kamar su had'iye su don so tattalin su suke sosai har sukayi kwanak biyu aka zagaya dangi sosai sannan suka dawo gida Suhaima har da kuka ta na rabuwa dasu sun shak'u da Hajia mahaifiyar Umman su sosai. Bayan dawowar su ne Jiddah ta haifi d'anta namiji ansha suna sosai su Suhaima, acikin lokacin ne ita ma Suhaima ta samu ciki sai dai mai sauk'in laulayi ne ba kamar cikin Na'eem da Shaheed ba, Sabeer yaji dad'i sosai sai kula yake bata da tattali kamar shine cikin farko haka ma su Dr Faridah ba'a barsu a baya ba suma sosai suke kulata, haka ta cigaba da rainon cikinta cikin kwanciyar hankali. After 9 months ne Allah ya sauki Suhaima lafiya ta haifi twince d'inta dukka mata tsakanin Sabeer, Mumy, Daddy da Dr Ahmad d'an fillo bansan wanda yafi murna ba acikin su, bayan sun dawo gida nan fah gida ya cika da en uwa da abokanan arzik'i sai taya murna ake na samun wannan karuwar da akayi, washe garin haihuwar ne mutan kd suka taho da abubuwan arziki sosai sai lokacin Mumy take ganin en uwan Suhaima sosai tasha jinin jikinta don tasan bazasu nuna musu komai ba nan zuciyar ta ya dad'a kyashin halinta tabbas ba'a son wulakanta d'an adam don bakasan irin baiwar da Allah yayi mishi ba. Ranar suna yaran suka ci sunan Dr Faridah da kuma Fatima suna kiran su da Shaheeda da kuma Afnan, sosai ansha suna da walima an kashe kud'i sosai a wannan sunan sai fatan Allah ya rayasu. Haka lokaci ya cigaba da tafiya har sukayi arba'in duk family na Suhaima sai da suka je sosai sai da sukayi wurin 1week a kd Hajia sai da ta gyara jikarta sosai sannan suka dawo gida, twince na da 5months Aunty Aliyah ta sake haihuwar mace wadda taci Sunan Suhaima Yah Aliyu ya mayar da sunan k'anwar shi nan aka sha suna aka watse. Duk wani jin dad'i da kwanciyar hankali Suhaima tana samun shi wajen gwarzon mijinta Sabeer, itama ta bashi duk wata kulawa da ta kama zaman su suke cikin jin dad'i, Na'eem da Shaheed tuni Dr Faridah ta sanya su a tsadaddiyar wata prvt schl sai hutu suke zuwa gidan iyayen su don har islamia da tahfiz duk an sanya su ban da extra lesson da ake musu a gidan masha Allah kuma yaran brain nasu naja gasu nutsattsu basu da hayaniya sosai. Bayan wasu en shekaru Shaheeda da Afnan sunyi wayo sosai har an yaye su, a lokacin Sabeer ya samawa Suhaima schl a Buk tana karantar medicine sosai Suhaima ta nuna farincikin ta haka ma Yah Aliyu yaji dad'in barin Suhaima da Sabeer yayi ta cigaba da karatu har godiya yayi wa Sabeer. Ta 6angaren Yah Aliyu kuwa Alhmdllh duk wani bud'i yana samu ta 6angaren aikin shi, gashi sun had'a hannu da Sabeer sun bud'e wani tafkeken gidan gona a kauyen nasu Suhaima da kuma wurin hutawar su inda sunje sosai wajen yayi kyau sun d'ibi ma'aikata suna biyan su, sosai en kauyen sun ji dad'i hakan don an rage masu zaman banza babu sana'a. Duk sunje sunyi aikin hajji da Omarah sun yawata k'asashe sosai musamman Suhaima ma don Sabeer yace honeymoon d'in da basu yi ba suna farkon auren auren yanzu zasu yi shi nan suka zube Shaheedah da Afnan hannun su Dr Faridah suka wuce honeymoon d'in su, sai da sukayi wajen wata hud'u sannan suka dawo gida har da tsarabar ciki. Tun safe take faman zirga zirga a tsakanin kitchen saboda yau Sabeer zai dawo daga tafiyar da yayi ta tsayin wata 1, ta gama had'a mishi abubuwan ci dana sha ta gyara ko'ina sannan ta barwa er aikinta wanke wanke, upstairs ta haye ta shiga d'akin su Shaheedah wanka tayi musu ta shirya su cikin wasu English wears na gown sai dai tsayin ta iyakar gwiwar su ne sannan ta gyara musu gashin kansu style mai kyau tayi musu sunyi matuk'ar yin kyau gashi kayan iri d'aya komai da komai daman kuma komai iri d'aya ake yi musu peck ta basu a cheek nasu suma suka yi mata sannan ta mik'e tsaye tace "Wow! Emmatan Daddy kunyi kyau bari naje nayi wanka sai mu d'auki pic's before jirgin su Daddy yayi landing koh " Cikin tsallen murna suka ce "Okay Mumy " Nan ta wuce tayi wanka bayan ta fito simple makeup tayi da yake cikin ya fara girma sai ta sanya wata milk d'in gown tayi kyau tayi rolling kanta da veil d'in rigar tana cikin fesa perfumes ne taji tsallen ihun su Afnan suna kiran sunan Daddy da nasu Na'eem. Agurguje ta k'arasa shiryawa ta fito zuwa downstairs inda take jin hayaniyar su, ko kunyar samarin yaran shi bai yi ba ya rungume ta yana kok'arin kissing nata ture shi tayi tare da yi mishi nuni da yaran duk da kusan hankalin su nakan tsarabar kayan su. Marairaice fuskar yayi tare da cewa "Haba Baby na nayi kewar ki sosai fah " "Sorry Dear bari mu sallami yaran ka sai kayi koma mene " Ta k'arasa fad'i tana kashe mishi ido, murmishi yayi sannan ya huro mata da kiss ta iska dole yau ya tura su Shaheed wajen Mumy don zasu tak'ura mishi idan ya barsu. Bayan yayi wanka sun ci abinci sannan suka fita zuwa gidan su Daddy kowanne part suka shiga suka gaida su sannan suka dire a part d'in su Mumy ansha hira sai da sukayi dinner sannan suka bar gidan Shaheedah da Afnan ko bin iyayen basu yi ba daman haka Sabeer yake so. Awannan daren Suhaima ta yabawa aya zak'inta don sosai ta wahala a hannun Sabeer, zuciyar su fal farincikin kasancewar su da junan su bayan komai ya kammalu ne suna rungume da junan su Sabeer cikin muryar shauk'i yace "I luv U Baby nah " "I luv U too sweetheart " Daga nan suka wuce bathroom wanka sukayi sannan suka zo suka kwanta babu dad'e wa bacci yayi awon gaba dasu. _*Alhamdullilah!*_ Dukkan yabo ya tabbata ga Allah da ya bani ikon kammala wannan littafin nawa. _gaisuwar fatan alkhairi gare ku My Sadeey and my Momma nah (Aunty Maijiddah) hak'ik'a ku masoya na ne na gaskiya ina son ku sosai Allah ya bar mu tare Amin_. ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _Ina matuk'ar alfahari da wannan kungiyar tawa, ina yiwa sisters d'ina na cikin fatan alkhairi a duk inda kuke i really luv U guy's_ *MASOYA NA KUYI MIN UZURI DON AGURGUJE NA KAMMALA MUKU WANNAN LABARIN HAKA YA FARU NE SABODA GABATOWAR WANNAN WATAN MAI ALBARKA DA YAKE TUNKARO MU WATO RAMADAN, DAFATAN EN UWANA ZAMU HIMMATA GA AIKATA ABUBUWAN ALKHAIRI CIKIN WANNAN WATAN, MU DAGE DA IBADA MU KAURACEWA GULMA KALLACE KALLACE DA KUMA HIRA MARA AMFANI ALLAH YASA ZAMU GA WANNAN WATAN DA RAI DA LAFIYA, WAD'ANDA BASU DA LAFIYA ALLAH YA BASU LAFIYA, ALLAH YA JIK'AN WAD'ANDA SUKA RIGA MU GIDAN GASKIYA IDAN TAMU TAZO ALLAH YASA MU CIKA DA IMANI* _Masoya na baza ku lissafu ba amman ku sani Aishat A Muh'd tana matuk'ar kaunar ku tana muku fatan alkhairi sai mun had'u a wani sabon nvl d'in nawa after sallah indan Allah ya kaimu_.