[5/3, 4:20 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *Nanameera ce#* *ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!! I'm so grateful to Allah subhanahu wata'ala for giving me the privilege to finished my book SHEIKH HEESHAM, I'm so grateful to my lovely fans I really luv you from the bottom of my heart nd my Role model Na'ima Sulaiman Sarauta(Nimcyluv) my regards to yhu Aunty nimcy. Now I'm back with another unconditional love book FATTOMAH don't miss it dears* Page 1-2. Hadari ne haɗaɗɗe a sararin samaniya banda guguwar iska babu abinda ake iya ji dubbannin mutane suna tattara kayansu domin kada ruwan saman ya iskesu domin a wannan lokaci ana tsaka da damuna ne babu tabbacin idan ruwan ya sauka ya dakata da wuri, cikin wannan yanayin take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a jiki, bakinta sai rawar sanyi yake da alama tana matuƙar jin sanyin da yake tashi. Yarinya ce ƙarama dan bazata shige 15-16yrs ba amma yanayin halittar jikinta zaka ɗauka takai irin 18yrs ɗin nan, tsayawa tayi da tafiyar ta durƙushe nan wajen tana riƙe ƙafarta sosai takejin ciwo a cikin ƙafar gashi kuma bata kusa zuwa gida ba babu kuɗi a hannunta bare tayi tunanin hawa ko keke napep ne dazai kaita gida, tana nan wajen durƙushe kusan 8mins wani mutum yazo shigewa har ya yi gaba sai kuma ya dawo ya tsaya yana kalllonta batareda ta san yana yiba "Keee me kike yi anan kina ganin hadari ya haɗo?" Sai a sannan ta ɗago runannun idanuwanta ta kalleshi amma ta gagara furta koda kalma ɗaya domin zuwa wannan lokacin jikinta banda rawa babu abinda yake wanda ke nuni da cewa ciwonta na gab da tashi, girgiza kai mutumin ya yi ya ce "ke kam kurma ce ko bebiya?" ba tare da ta ce komai ba ta miƙe tana dafe kanta wanda yake barazanar tsagewa a kowane lokaci. Gaba tayi mutumin ya bita da kallo yana mamakin hali irin nata to kodai bata ji ne???? ɗaga kafaɗarsa ya yi alamar bai dameshi ba sannan ya cigaba da tafiyarsa. Da sallama ta shige tsakar gidan nasu wanda bashi da girma ko kaɗan tana zuwa ta zauna gefen mahaifiyarta tana lumshe idanuwanta wanda take jin suna yi mata nauyi a kowane lokaci, "Fattum jikin ne?" Hawaye na gangarowa kan kuncinta ta ɗaga mata kai ajiyar zuciya ta sauke cikeda damuwa ta ce" sannu kinji Allah ya baki lafiya ya rabaki da wannan ciwon da yake damunki" shiru Fattomah ta yi ta kwanta kan cinyar mahaifiyarta nan da nan bacci ya ɗauketa. Zaune suke akan tabarma suna cin abinci cikeda kulawa ya ce" Faɗimatoh ya jikin naki?" tana kallonsa ta ce" Abbana da sauƙi kawai ƙafar ce har yanzu tana yi mini ciwo sosai" "Allah ya yaye miki gabaɗaya in Sha Allah" jinjina kanta tayi ta ce" Allah yasa Abba" ganin ba cin abincin take ba yasa ta ce" Fattum bafa kya cin abincin" turo baki gaba tayi cikeda shagwaɓa ta ce" koba na ƙoshi ba Ammi" girgiza kai Ammi ta yi ta ce"A'a me kika ci da zaki ƙoshi?, ki daure ki ci ko kaɗan ne kinga zaki sha magani" ranta a haɗe ta kalli Ammi sai kuma ta ɗauke kanta tana ƙunƙuni wanda basu san abinda take cewa ba "Faɗimatoh ki ɗauki abinci ki ci kinji" Kwaɓe fuska ta yi cikeda zallar shagwaɓa ta ce" ayyah Abbana wlh na ƙoshi sosai I'm full fa" numfasawa ya yi ya ce"kin tabbata?" da sauri ta gyada masa kai ya ce" shikenan ki je kisha magungunanki sai ki kwanta ki samu hutu" babu musu ta miƙe ta shige wani ɗaki wanda ya kasance ɗakinta ne. Tana shiga ta zauna kan katifar da take shimfide a ɗakin wata leda ta jawo ta buɗe tana ƙarewa magungunan ciki kallo sachet ɗin PCM ta buɗe ta ɓalla har ta kai bakinta sai kuma ta yi saurin yarda shi tana ƙoƙarin yin amai, yana ɗaya daga abinda Fattomah ta tsana a rayuwarta kenan wato sha magani duk irin lalurar da take tofa bazata sha magani ba kuma bazata yarda ayi mata allura ba saidai idan Abbanta ne zai kai ta ko kuma ya zaunar da ita ya bata maganin toh shine zata yarda tasha shima kuma tana kuka. Harhaɗa magungunan tayi duka cikin ledarsu ta ajiye daga gefen katifar ta koma tayi kwanciyarta. Kalle-kalle ta shiga yi ganin yanda ko'ina na tsakar gidan nasu ya jiƙe ta tabbata jiya da daddare ba ƙaramin ruwan sama akayi ba, wata ƙara ta fasa ta tsuguna nan bakin ƙofar ɗakinta ta rushe da kuka da sauri Ammi ta taso daga wajen gawayin da take kunnawa daidai nan shima Abba ya shigo daga waje, sosai take kuka kamar wacce aka cewa iyayenta sun mutu Abba ya ce"lafiya Faɗimatoh?" sake rushewa tayi da kuka ba tare da ta basu amsaba girgiza kai Ammi tayi ta ce" kodai jikin naki ne?" kallonsu duka tayi sai kuma ta fashe da wani sabon kukan tana ƙoƙarin birgima a ƙasa, tsayawa sukayi duka suna kalllonta dan ita Ammi ma ta ɗauka aljanu ne suka shiga jikinta Saida tayi mai isarta sannan ta fara sauke ajiyar zuciya "Yanzu faɗa mana ke dawa?" Kallon Abbanata ta yi cikin sheshsheƙar kuka ta ce"Ab... Abba.. Abbana koba takalmina bane ya jiƙe a tsakar gida da ruwan sama...." Sake rushewa tayi da wani kukan ita kuwa Ammi tsabar baƙin ciki kasa magana tayi kawai ta juya ta koma kan Abinda take, cikeda nuna kulawa da kuma rarrashi ya ce" shikenan kiyi haƙuri zan siyo miki wani sabon takalmin amma fa sai kinyi shiru da bakin ki, kuma kinje kinyi sallah" goge fuskarta ta shiga yi tana gamawa ta miƙe tana sake kallon tsakar gidan dan ita idan da abinda ta tsana tofa bai shige ganin waje a jiƙe ba shiyasa kullum takalmanta suna cikin ɗaki dan duk randa akayi rashin sa'a suka jiƙe tofa sai hankalin kowa ya tashi, a hankali kamar wacce ke taka kashi haka ta ƙarasa ta ɗauki takalmin nata ta sanya sannan ta ɗauki buta, girgiza kansa ya yi ya ce" Allah Ubangiji ya shiryeki Faɗimatoh". Shiryawa tayi cikin uniform ɗinta ta fito tana kallon Ammi ta ce" nikam Ammi tafiya zanyi karna makara Kinga yau nice da duty" kallonta Ammi ta yi ta ce"amma dai kin tsaya ki fara cin abinci ko Fattum?" Girgiza kanta ta yi tana sanya takalminta ta ce"kawai saina dawo zanci ai yau bazamu kai 4pm ba" shuru Ammi ta yi dan tasan tunda ta ce haka ko za'a kasheta bazata ci abincin ba, Saida ta gama sanya takalminta ta ɗauke jakarta tana kallonta ta ce"zan tafi ki yimin addu'a Ammina" murmushi ta yi ta ce" Allah ya kiyaye hanya ya tsaremin ke ya kareki daga dukkan abun ƙi Faɗimatoh" murmushinta mai kyau tayi ta ce" Ameen Ammina saina dawo" bye bye tayi mata sannan ta juya ta fita tanajin nutsuwa na saukar mata tabbas tana matuƙar so da ƙaunar iyayenta kamar yanda suma suke nuna mata soyayya. Malamin Geography ne ya shigo musu dole kowa ya yi shiru domin ko kaɗan baya ɗaukan nonsense shiyasa duk irin surutun da suke da zarar ya shigo kowacce zata shiga taitayinta banda Fattum dan daman ita duk wani malami da ake jin tsoronsa tofa ita shine abin rainawarta kwata-kwata bata ɗaukesa mutum ba shiyasa kullum cikin hukuntata yake amma kamar abanxa dan hazaka ɗauka ita yake yiwa wannan hukuncin ba. Yauma kamar kullum yana shigowa ta kwanta kan desk ɗinta wanda suke zaune su uku tanaji ya ce kowa ya ɗauko littafinsa kuma karya zo ya tarar dakai baka rubutu amma tayi kwanciyarta abinta, desk ɗinta taji an daka cikin baccin daya fara ɗaukanta ta buɗe idanunta tana murzasu ta kalleshi, yanda ya haɗe fuska kamar wani mala'ika sai abin ya bata dariya, cikin kakkausar murya ya ce "Get out!!" Kallonsa ta tsaya tanayi kamar ma bata gane abinda yake nufi ba, kalllonta ya yi ganin yar ƙaramar yarinya na neman raina masa hankali ya ce cikeda masifa" I'm talking to a doll?" shuru ta kuma yi masa for the second time, a fusace ya fincikota daga kan desk ɗin ta waɗo nan ƙasa amma ko kaɗan babu alamun zatayi kuka dukda saurin kuka irin nata, dawowa ajin ya yi da wani sanda na bishiya yana zuwa ya dinga ɗaukanta da ita ko ta'ina amma ko tari batayi ba sai sauke ajiyar zuciya ta dinga yi Saida ya gaji dan kansa sannan ya rabu da ita ya koma gefe yana sauke numfashi, duk ɗaliban da suke cikin ajin sunyi shuru sai binta suke da kallo ganin yanda tayi shuru amma fuskarta tayi jajawur wanda shine zai tabbatar maka da cewa taji dukan a jikinta kawai dai taurin kanta yasa bazata yi kukan ba. Kusan 5mins suna haka sannan ya ce "Daga yau i mean as from today idan na shigo class to ki tashi ki fita idan kuma ba haka ba wlh watarana sai nayi miki dukan dazan illataki shashashar yarinya kawai" Yana gama faɗin haka ya juya ya fita sai a sannan ta fashe da wani irin kuka mai gunji, da sauri duka su kayo kanta dan har bayanta ya fashe babu irin rarrashin da basuyi mata ba amma taƙi yin shuru suna cikin haka Form mistress dinsu ta shigo ajin. Komawa kowa ya yi wajensa yayinda take zaune nan wajen har sannan tana kuka kalllonta malamar tayi sai kuma ta kalli yan ajin ta ce" what's wrong with her?" Aysha ce wacce ta kasance seatmate ɗinta ta miƙe ta sanar da'ita duk abinda ya faru tundaga farko. Girgiza kai Maa Zainab ɗin ta yi sannan ta ce" Fateema bakijin magana ko kaɗan duk abinda za'a faɗa miki bazaki ɗauka ba kinfison yau wannan malamin ya dake ki gobe kuma wani ya dake ki, kullum cikin laifi kike gashi har kina SS3 amma babu alamar zaki daina haka ki keson kije University kina faɗa da lecturers?" Shuru Fattomah ta yi tana cigaba da kukanta dan ita kaɗai tasan abinda takejin a jikinta gashi batason shan magani kuma batason taje gida Abbanata yaga alamun an daketa, goge idanunta tayi batareda ta cewa kowa komai ba ta miƙe ta fice daga cikin class ɗin da idanu Maa Zainab ta bita sai kuma ta girgiza kai cikin ranta ta ce"Allah ya shiryeki Fattomah". Ɗakinta ta shige a hankali gudun kada Ammi ta fito tsakar gidan ta ganta tana shiga ta zare hijab ɗin jikinta sannan ta zauna kan katifarta tana ƙarewa jikinta kallo sosai jikinta ya kumbura duk ya yi Ja dukda ita ba fara tass bace amma tanada haske sosai, hawayene ya shiga biyowa kuncinta tana tsinewa malamin aranta dan ita ba taga abinda tayi masa ba dazai daketa "Fattum!! Fattum!!" Da sauri ta kalli ƙofar ɗakin jin Ammi na kiranta ko yaushe taga shigowarta????, Jin yanda take ƙara kiranta yasa ta miƙe a hankali ta maida hijab ɗinta sannan ta fito tana kalle kalle, "shine ki ka shigo babu sallama sai takalmanki na gani ko?" turo baki ta yi ta ce" koba nayi sallamar ba" girgiza kai Ammi ta yi ta ce" a yaushe ki kai sallamar banason ƙarya" zumɓura baki ta yi ta ce" shikenan naji ban yiba ay mantawa nayi" taɓe baki Ammi ta yi ta ce" ke kika sani ki shige ki cire kayan nan kizo zan aike ki" da sauri ta kalleta sai kuma ta langwaɓar da kai ta ce" ayyah Ammi ina zaki aikeni kina ganin yanda ake rana a garin nan" sakar baki Ammi ta yi tana kalllonta har takai ƙarshen maganarta Sannan ta ce "Ohhhh nufi kike bazaki ba ko me?" Girgiza kanta ta yi ta ce"Ni ba cewa nayi bazani ba ai zani mana" harararta ta yi ta ce" Allah ya baki sa'a Fattum karki daina rashin jin magana" bata sake cewa komai ba ta juya ta shige ɗakinta ita kuma ta tura baki gaba sannan ta koma ɗakin dan cire kayanta. Shiryawa ta yi cikin wata doguwar riga ta yadi wanda akayi ɗinkin straight gown milk colour ta sanya mayafi baƙi sannan ta fito tana tafiya kamar bataso daman indai ƙiwa ce tofa Fattomah number 1 ce a wannan fagen. Tsugunawa ta yi gefen Ammin tana kallon rai a haɗe ko kallonta Ammi batayi ba ta miƙa mata leda tana cigaba da aikinta ta ce"kije ki kaiwa Adda kice mata wai ankon bikin Hafsa ne" ƙoƙarin buɗe ledar ta shiga yi Ammi ta ce "Wai ke mene ne yake damunki ko ajiya kika bawa mutane da kike ƙoƙarin buɗewa?" Rufe ledar ta yi sannan ta miƙe tana kallon Ammin ta ce" Ammi kuɗin mota" a fusace ta ce" kuɗin jirgi zan baki bana mota ba a gidan ubanki zakiga masu mota a hanyar" da sauri ta fita waje tana zuwa soron gidan ta fashe da kuka, da gudu tayi waje ganin Ammi ta nufo soron haka har ta fita layin nasu tana haki tana juyowa taga ko ta biyota abaya. Ita kuwa Ammi addu'ar neman shiriya ta roƙa mata wajen Ubangiji dan lamarin Fattomah har tsoro yake bata yarinya kamar wacce ke mu'amala da aljanu *FATTOMAH isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 8106571862* *Nanameera ce#* [5/3, 4:20 PM] Nanameera: * FATTOMAH* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION. * PAGE 3-4* *Nanameera ce#* Tafiya take kamar bataso har ta ƙara so bakin layin gidan da Ammi ta aiketa "Fattum!" Da sauri ta juya dan ganin wanda yake kiran sunanta, murmushi ta saka tana washe baki ta ce"laaa yaya Aslam ina yini" murmushin shima ya mayar mata ya ce" lpyklao Fattum ya Ammi?" "Tana nan klao gidanku ma zani" waro idanunsa ya yi ya ce"dagaske?" gyaɗa masa kai tayi tana wasada ledar hannunta ya ce" okay tom dama nima can zanje sai mu tafi tare" toh ta ce masa sannan suka cigaba da tafiya yana janta da hira har suka iso gidan nasu. Murmushi Adda ta yi ta ce" Faɗimatoh yaushe rabonki da gidan nan?" sunkuyar da kanta Fattomah ta yi tana ɗan murmushi Aslam ya ce"wlh kam Mama rabonda naga Fattum har na manta ta ɓuya abinta" turo baki ta yi ta ce"ayyah yaya naga mun haɗu dakai rannan" "a makaranta ba" dariyarta mai kyau ta yi ta ce"ai dai mun haɗu ko Mama?" murmushi Mama ta yi ta ce" nikam nayi fushi dake" kwaɓe fuska ta yi ta ce"Hajiya Adda Mamata nasan ai kin haƙura zaki dafamin dambu ko?" Tuntsirewa sukai da dariya Mama ta ce"shikenan zan dafa miki amma ai kwana zaki yi ko?" girgiza kanta ta yi ta ce" A'a Mama ban faɗawa Abbana ba kuma kinsan faɗa zai yimin" haɗe rai Adda ta yi ta ce"saboda baisan gidan wa kika kwana ba?" shuru Fattomah ta yi Aslam ya ce"kawai kiyi zamanki kinga yanzu su Abla zasu dawo daga makaranta" narai-narai ta yi da idanu dan kwata-kwata hankalinta bai kwanta data kwana ba domin batason abinda zai ɓatawa Abbanta rai ko ya yake, Da gudu tazo ta rungumeta tana dariya ta ce" oyoyo sister sai yau?" murmushi Fattomah ta yi ta ce"wlh fa kowa ya ɓuya ina Khaltum?" Zama Abla ta yi gefenta ta ce"wai laifi suka yiwa Sheikh ɗinsu shine ya ce bazai tashesu ba sai anyi magrib kinsan kwata-kwata ƴan ajinsu basaji" jinjina kai Fattomah ta yi ta ce"okay bari ta dawo" "amma dai kwana zakiyi?" girgiza kanta tayi, tsaki Abla tayi ta ce"lailai ma ƴar nan mu amma muke zuwa gidanku mu kwana ko?" murmushi tayi ta ce"kiyi haƙuri sister in Sha Allah zan dawo na kwana soon kinga akwai makaranta gobe kuma zamu haɗu wajen biki" "saboda haka ne bazaki kwana ba?, dan Allah ki kwana kinji Fattomah" ajiyar zuciya Fattomah ta sauke sannan ta ce" amma gobe da wuri zan tafi gida" murmushi Abla ta yi ta ce"Eh to Allah ya kaimu", tashi tayi tana kallonta ta ce"toh uwar san jiki sai ki tashi muje ɗaki" murmushi Fattomah ta yi sannan ta miƙe ta kama hannunta suka shige ɗakin nasu. Haɗe rai tayi tana kallon Khaltum ta ce"toh mene ne amfanin kula saurayi bayan kinsan ba aurensa zakiyi ba?" wani irin kallo Khaltum tayi mata ta ce" lailaima Fattum wato ke zama zakiyi babu wanda zaki kula?" murmushi Fattum tayi ta ce" Allah ya kiyaye wlh babu ruwana da kula wani mutum bayan nasan ba aurensa zanyi ba kuma ba aurenma za'ayi min yanzu ba kinga kuwa babu amfani" harararta Abla tayi ta ce"ai sai kiyita zama hajiyata" tuntsirewa tayi da dariya tana kallonsu ta ce"Allah ya kaimu lokaci musha biki" "Ameen Ameen" suka amsa mata atare. Washegari tana tashi bayan sun gama shiryawa ta fito tana gyara mayafinta, kallonta Khaltum ta yi ta ce" wai ina zaki ne?" murmushi ta yi ta ce"gida mana" sakar baki tayi ta ce" ke kuma sai kace ana korarki zaki tafi ƙarfe nawa yanzu?" Mama ce ta shigo tana kallonsu ganin yanda sukayi curko-curko a tsaye ta ce" lafiya dai?" Khaltum ce ta ce"wai tafiya zatayi da wannan safiyar sai kace muna korarta" murmushi Mama tayi ta ce" haba Fattomah sai kace baki sanmu ba?, kibari anjima zai ki tafi" shuru Fattomah tayi amma har cikin ranta bataji daɗi ba domin tafi son tafiya gida fiye da zama anan kuma taji hankalinta bai kwanta da zaman ba. Misalin ƙarfe 2pm ta shigo cikin layin nasu da mamaki sosai take ƙarewa motocin data gani a bakin layin kallo domin kana gani kasan masu tsada ne bata ƙara tsorata ba saida taga wasu mutane masu kamada samudawa tsaye ƙofar gidansu kowanensu da bindiga atare dashi duk sun sanya wasu baƙaƙen kaya da glasses, da sauri ta shige gidan nasu tana waiwayon mutanen ta gani ko biyota suka yi. Da mamaki ta tsaya daga bakin ƙofar shiga tsakar gidan nasu tana kallon mutanen da suke zaune kan tabarmar sai kuma Abbanta wanda yake kwance daga gefe shima, kasa ƙwaƙwƙwaran motsi tayi daga inda take dan ita bata ganewa wannan abun ba bata taɓa ganin mutane irin haka ba kuma bata taɓa ganin Abbanta a kwance irin haka ba "Fattum" Kallon Ammi tayi wacce ta faɗi maganar ganinta da tayi kamar a tsorace da hannu tayi mata alama da tazo ta tafi cikin tafiyarta ta sanyi kamar kowane lokaci, zama tayi gefen Ammi tana kallon Abbanta wanda idanunsa suke a lumshe juyawa tayi kuma tana kallon manyan mutanen da suke zaune kan tabarmar suma kana ganinsu kasan masu arziƙine kuma jinin sarauta kowanne sun yana ji da kansa kuma ba yara bane domin Zasu iya girman Abbanta dukda kasancewarsa mai yawan shekaru, sunkuyar da kanta ƙasa tayi dan ita bata gane mene ne abinda yake faruwa ba kuma batasan wnada zai mata bayani game da hakan ba, tsinkaya tayi yana cewa "Wannan ita ce yarinyar taka?" Gyaɗa masa kai Abba ya yi har sannan kuma idanunsa a rufe suke ita kuwa Fattomah kallo kawai take binsu dashi ya ce" ya sunanki?" "Fattomah" ta bashi amsa a taƙaice"Masha Allah nice name dear" shuru tayi ta juya ta kalli Abbanta sai a sannan ta ce "Abbana mene ne ya sameka?" Riƙe hannunta ya yi cikin nasa yana magana da kyar ya ce" Faɗimatoh ki kula da kanki kinji ki riƙe tarbiyarki ki zama mai jin magana ga kowa ki daina rashin jin magana dan Allah Faɗimatoh" bakinta na rawa ta ce" Abbana bazan sake ba kaji kayi haƙuri wlh Adda ce tace saina kwana amma ban ƙarawa" tallafo fuskarta ya yi ya ce ahankali kuma cikin rauni" bakiyimin laifin komai ba Fattomah Abbanki yana matuƙar ƙaunarki kuma yana son ki kula da rayuwarki kinji" gyaɗa masa kai kawai ta iya dan duk ta rikice ganin haka yasa ɗaya daga cikin mutanen wanda ba shine ya yi mata magana ba ya ce"inaga zamu tafi da ita sai ta zauna a gidana" da sauri ta kalleshi amma ta kasa magana dukda tanajin babu inda zata iya tafiya tabar Abbanta a wannan halin duk inda yake toh itama nan zata zauna. Kiran sallar la'asar da akayi yasa ya ce" yanzu idan mun idar da sallah za'a koma asibitin in sha Allah" gyaɗa masa kai Abba ya yi sannan ya yi waje suka bishi abaya, wajejen ƙarfe 6:45pm aka fito dashi daga ward ɗin bayan an bashi ɗaki Fattomah na zaune gefensa sai Ammi wacce duk ta fice hayyacinta cikin lokaci kaɗan, cikeda damuwa Fattomah ta ce "Ammi wai mene ne ya samu Abbana?" Kallonta Ammi tayi ta ce"nima bansani ba Fattum kawai gani nayi anshigo dashi wai awajen aikinsu ya akaga ya waɗi shine fa yasa na kirawo masa Hakeem sai kuma naga waɗannan mutanen sunzo ashe sune yayyensa wanda suka banzatar da rayuwarsa Saboda bashi da kuɗi amma a zahiri suma ba su suka aikata ba iyayensu ne shine suka zo suka kaishi asibiti hankalina ya tashi sosai Fattomah" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Allah ya bawa Abbana lafiya" Ameen Ammi ta amsa mata. Tana idar da sallar magrib ta sauko daga benen kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Abba ta nufa babu ruwan kowa da kowa a cikin asibitin kasancewarsa asibiti mai tsada duk wani abu da kake buƙata tun daga mai jinya har wannan yake kulawa dashi zasu baka dan yafi wasu gidajen, tana shiga ta tarar da mutanen ɗazu su uku juyawa tayi zata fita ya ce"zo nan" batare musu ba ta komo da baya tana zuwa gabansa ta tsuguna tana kallon ƙasa, murmushi ya yi ya ce"meyasa baki shigo ba Fateema?" sunkuyar da kanta ƙasa tayi ya cigaba da faɗin" daga yau ki ɗauke mu matsayin iyayenki domin mahaifinki ɗan uwanmu ne I'm General Ibrahim Baira shikuma wannan Dr. Mansur Baira sai kuma Dr. Kabeer Baira muɗin mun kasance yaya ga sarkin Kano His highness Mukhtar Baira wanda yanzu Allah ya yi masa rasuwa yanzu haka ƙanina shine wanda yake matsayin sarkin Kano na wannan lokaci kuma mun kasance Cousins ne da Abbanki saboda haka muma ki ɗauke mu tamkar Abbanki kinji" jinjina masa kai tayi ta ce"toh Abba" shafa kanta ya yi ya ce"Allah ya yi miki albarka dear" Ameen ta amsa sannan ta tashi a hankali ta fita. *Fattomah isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 09121033575 or 08106571862 WhatsApp only* *Fattomah* *Nanameera ce#* *Idan har kin karanta to kiyi sharing ɗinsa sister* [5/3, 4:21 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION. *Nanameera* PAGE 5-6. Wajen ƙarfe 9pm suka shigo ɗakin saida likita ya sake duba shi sannan ya fita kallonta Daddy ya yi ya ce" Fateema taso mu tafi" da sauri ta ɗago tana kallonsa amma ta kasa cewa komai murmushi ya yi ya ce" gidana zan tafi dake kinji" sunkuyar da kanta ƙasa tayi Ammi ta ce"tashi kuje" tashi tayi tana sake juyowa tana kallon iyayennata haɗa ido sukai da Abba ya gyaɗa mata kai hakan yasa taji ɗan sanyi cikin ranta, sallama suka yiwa su Abba sannan suka fito suma, tsaya suka tadda ita gefen wani ɗaki tayi shiru da alama wani abun take tunani kallonta Daddy ya yi ya ce" Fateema me kike tunani haka?" girgiza masa kai tayi ya ce"tom muje" gaba ya yi tana biye dashi abaya har suka ƙaraso wajen da aka jere motocin nasu saida sukai sallama da ƴan uwansa sannan ya ce tashiga motar shima ya shiga. Cikin unguwar tudun yola ɓangaren satellite town gidan yake gidane iya ganin ka wajen girma da kuma haɗuwa kana ganinsa kasan da kuɗi aka gina gidan ko'ina na gidan zagaye yake da securites wanda zai tabbatar maka da babban mutum ne mammalakin gidan, a parking lot ɗin gidan sukayi parking sannan suka fito banda kallo babu abinda Fattomah takeyi domin tunda uwarta ta haifeta bata taɓa ganin gida ma girma da kyau irin wannan gidan ba idan ba sani kayi ba to tabbas za'a iya ce maka a ƙasar waje ne kuma ka yardar domin ginin gidan ba irin na ƙasar nan bane, sosai ta shagalta da kallon gidan dan batasan sanda Daddy ya ce mata ta shiga ba lura da ba saurarensa take ba yasa ya ce"Fattomah me kike kalla?" saurin ƙasa tayi da kanta dan saida taji kunya murmushi ya yi ya ce" kibari idan Allah ya kaimu da safe sai kiga ko'ina na gidan kinji" gyaɗa masa kai ta yi ya kama hannunta suka shiga ƙofar entrance ɗin parlon wacce itama kaɗai abar kallo ce, babu kowa a parlon sai sanyin AC dake tashi tare da wani daddaɗin kanshi ko'ina tsaf kamar a zubar da abinci a ƙasa ka ci ganin ta tsaya a tsaye yasa ya ce"zauna mana" a hankali kamar me tsoron wani abu ta zauna gefen royal cusion ɗin dake zagaye da parlon zama shima ya yi not to long ta fara jin ƙara saukowa daga kan stairs da sauri ta juya tana kallon matar da take sakkowa farace tass kuma doguwa kana ganinta kasan ba bahaushiya bace domin tafi kamada ƴan yankin saudia arabia murmushi ɗauke a fuskarta take kallon Fattomah har ta ƙaraso tana zama kan kujerar dake gefenta mijin nata ta ce" wannan ce yarinyar?" gyaɗa mata kai Daddy ya yi tace "Masha Allah she's beautiful" murmushi ya yi ya ce" sosaima naga kamar kunyarmu takeji" kwaɓe fuska ta yi tana kallon Fattomah ta ce mata" haba daughter ki ɗauka nan gidanku ne kuma mune iyayenki kinji karki wani ji kunyarmu koda yake nasan ma zaki saba nan bada jimawa ba" shuru Fattomah tayi tana wasada fingers ɗinta, tasowa Mommy tayi tana zuwa gabanta ta tallafo fuskarta tana sakar mata murmushi ta ce" taso muje ciki ko" murmushin itama ta mayar mata sannan ta miƙe tana kama hannunta suka haura stairs ɗin gidan. Kallon ɗakin Fattomah take Saboda yanda ya haɗu ya yi kyau har ya gaji komai na ɗakin purple and white ne sai tashin ƙamshi yake kallonta ta yi ta ce" yawwa sai kiyi wanka ki shirya akwai wasu kaya da aka kawo ɗazu ki sanya sannan sai ki fito kici abinci" gyaɗa mata kai tayi sannan ta ce"tom" shafa kanta ta yi ta ce"gud gurl" sannan ta juya ta fita. Kayanta ta cire sannan gas shige toilet ɗin dan yin wankan kamar yanda Mommy tace mata, kusan 3omins sannan ta fito daga toilet ɗin tana zuwa ta tsaya jikin dressing mirror ɗin dake maƙale a ɗakin tana kallon fuskarta murmushi ta yi sannan ta hau shafa mayukan data gani ajiye a wajen, tana gamawa ta buɗe wardrobe ɗin data gani a hankali ta dinga kallon duka kayan ciki kana ganinsu kasan they're expensive yawancinsu duk abayas ne sai riga da wando saida tagama dube-dubenta sannan ta ɗauko wata Turkish abaya black colour ta sanya komawa tayi gaban madubin ta kalli fuskanta sosai abayar ta haskata farinta ya fito sosai duk da ita ba fara can bace veil ɗin abayar ta saka ta ɗaure kanta sannan ta fito daga cikin ɗakin tana ƴan kalle-kallenta, murmushi Mommy tayi ganinta tana sakkowa daga benen tabbas Fattomah kyakkyawa ce dukda kasancewarta yarinya zaka fahimci hakan kuma tanada dirin halitta irin wadda wata ƴar shekara 20 ɗinma bazata fada mata ba komai nata cikin nutsuwa take gabatar dashi sannan kuma ga kunya wacce daman ita gadonta ce, lumshe ido Mommy tayi haka kawai taji wani tunani ya kawo zuciyarta ko hakan zai yiwu?????? Sallama Fattomah tayi ganin kamar hankalinta baya wajen, kallon Fattum tayi sai kuma tayi murmushi ta ce" sorry kinji" girgiza kanta tayi ta ce" babu komai Mommy" tashi tayi ta ce" bari nasa akawo miki abinci kici kinji" jinjina kanta tayi sannan ta zauna kan kujerar tana kallon wani movie da ake haskawa a Bollywood. Mamaki ne ya ishe ta ganin yanda ake kawo abinci kala-kala tana tunanin itadawa zasu waɗannan abincin wnada ya isa mutane biyar su ci su ƙoshi, saida aka gama jerasu kan Centre table sannan Mommy ta fito kallonta ta yi ta ce" A'a Fattomah me kike jira naga baki fara cin abincin ba?" Murmushi ta yi ta ce" babu komai Mommy" girgiza tayi ta ce" ki saki jikin ki please I'm ur Mom ok?" gyaɗa mata kai tayi ta ce" yanzu kigama cin abincin sai muyi magana" daga haka ta shige sama, da kallo Fattomah ta bita sannan ta juyo ta kalli abincin gabanta. Juyi kawai take kan makeken royal bed ɗin amma bacci ya gagari idanunta tunanin Abbanta kawai take ko wane irin hali yake ciki??? wannan tunanin yasa ta kasa Bacci domin da tana kusadashi dole zataga yanda yake da jikin amma yanzu babu wannan damar wannan tunanin ne yasa ta fashe da kuka ita kaɗai, saida tayi mai isarta sannan ta miƙe ta shiga banɗaki ta wanko fuskarta sannan ta ɗauro alwala prayer mat ta shimfiɗa ta sanya wani hijab ta tada sallah dan neman sauƙi wajen Ubangiji. Da sassafe Mommy tazo ta tasheta dan Daddy ya ce zata makaranta shiryawa tayi cikin sabon uniform ɗinta wanda batasan sanda aka ɗinka mata ba tana fitowa ta zauna breakfast not too long kuma driver da guard suka tafi rakata makaranta, da mamaki kowa yake kallon Fattomah bayan ta fito daga cikin motar domin kowa yasan a keke napep take zuwa makaranta yau kuma a mota harda masu tsaronta bayan sun shiga aji Aysha ta ce" wai Fattum wane ya kawoki yau?" tsaki tayi ta ce"nikam kinsan banason munafurci ko?, sai shegen gulma kuka ajiye to yayan Abbana ne shikenan" murmushi Aysha ta yi ta ce" toh hajiyar bala'i daga tambaya" "Eh kema kinsan banason irin haka ay" shiru sukai duka dalilin malaminsu daya shigo. Ganin yanda tayi shuru yasa Mommy ta ce" Fattomah lafiya?" kwaɓe fuskarta ta yi kamar zatayi kuka ta ce" Mommy wajen Abbana nakeson naje" murmushi Mommy ta yi ta ce" keee Fattum ki bari sai zuwa gobe nima zani dubashi sai muje tare kinji ai Daddy ya ce min zai shiga wajen nasu" badan ranta yaso ba ta ce" Tom shikenan Allah ya kaimu Mommy" murmushi ta yi ta ce" Ameen ya rabbi". Dariya Khaltum tayi tana kallon yayan nata ta ce" tab ɗijan yanzu yaya ka rasa wacce zakace kana so sai Fattomah tab wlh kuwa kana tare da wahala dan ka rigada kasan halinta kuma yanzu ma bata gida ɗazu Mama tace Ammi ta faɗa mata a asibiti" zaro ido ya yi ya ce" dan Allah ina ta tafi kuma?" "Wai yayan Abbanta ne ya ɗauketa tana gidansa a tudun yola" numfasawa ya yi ya ce" nikam babu ruwana dole sai naje inda Fattomah take domin har cikin raina ita ce wacce nakejin zan iya rayuwar aure da na daɗe inason yarinyar cikin raina bazan bari na rasata ba in sha Allah" kallonsa kawai Khaltum take dan ita batasan sanda ya koma haka ba shida magana ma bata damesa ba amma duk yabi ya rikice akan Fattomah, saida yagama fadar duk abinda yakeso sannan ta ce" yaya wlh ka cire ranka da Fattomah kaga yanzu ta koma gidan yan gayu kuma daman ita tafi kala da masu kuɗi idan kace zaka zira jiki ranka zai zo yana ɓaci abanza kawai kayi haƙuri ka rungumi Hafsarka itace take daidai dakai nidai a tawa shawarar" girgiza kansa ya yi ya ce "wlh bana daina son Fattomah ba har ƙarshen rayuwata kuma in Sha Allah sai na aureta ta zama mata agareni" rasa abinda zata ce masa tayi dan taga abin nasa ya fara sauka daga kan layi kuma duk irin shawarar da zata bashi ba ɗauka zai ba yasa ta ce" Allah ya taimaka yaya" miƙewa ya yi ya ce" Ameen Ameen shine abinda yafi dacewa ki faɗa" gaba ya yi ta bisa da kallo tana tausayin halin da yake ƙoƙarin sanya kansa. Har wajen ƙarfe 10pm Daddy bai shigoba ita kuma taƙi kwanciya tana zaman jiransa babu yanda Mommy batayi da itaba tace ba bacci take jiba dukdan yadawo taji halinda Abbanta yake ciki, kallonta ya yi ganin yanda take bacci akan kujera kana gani kasan baccinne ya ɗauketa ƙarasawa ya yi gabanta yana kallonta sosai yaga tana bacci hakan yasa baiyi tunanin tashinta ba ya ɗauketa tamkar Baby ya shige da'ita saman. Yana shiga ya kwantar da'ita sannan ya jamata duvet ya lulluɓeta addu'ar bacci ya yi mata sannan ya ƙaro gudun AC ya juya ya fita kai tsaye kuma ɗakinsa ya nufa. *Fattomah isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 09121033575 or 08106571862 WhatsApp* *FATTOMAH* *Nanameera ce#* IDAN HAR KIN KARANTA TO KIYI SHARING ƊINSA SISTER.[5/3, 4:21 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITER'S ASS. BOOK ONE PAGE 7-8. Kallonsa Mommy tayi ta ce" babu yanda banyi da'ita ba amma taƙi yarda taje ta kwanta wai batajin bacci dukda nasan daman ta gaji" murmushi ya yi ya ce" Allah sarki kawai ta damune akan halinda mahaifinta yake ciki in sha Allah gobe zakije ki dubashi sai ki tafi da'ita" okay tace masa sannan ya shige toilet dan watsa ruwa. Kalle-Kallen inda ta kwanta ta hauyi dan ita dai tasan ba anan wajen tayi bacci ba hasalima batasan sanda ya yi bacci shuru tayi na wasu mintuna sai kuma ta sakkoda ƙafarta a hankali ta miƙe ta shige toilet ɗin, shiryawa tayi cikin uniform ɗinta ta fesa turare wanda har Saida ya fara yawa murmushi tayi ita kaɗai sai kuma ta ce" I'm Fine gurl" tuntsirewa tayi da dariya Ni kuwa nace Fattum anajida yarinta. Kallon wanda yake zaune a parlon takeyi har ta ƙara so ɗaga kansa ya yi aikuwa cikin sa'a idanunsa ya shige cikin nata saurin ɗauke nata idanun tayi tana sunkuyar da kanta murmushi ya sakar mata ya ce" Hello!" sunkuyawa tayi ta ce" ina kwana?" "Lpyklao ya kike?" tana zama kan ɗaya daga cikin royal cusion ɗin parlon ta ce" ina lafiya" shiru sukayi duka na rashin abin faɗe dan ita bata taɓa ganinsa ba kuma shima haka tsinkayar muryar Mommy sukai tana faɗin " Jawaad yaushe ka shigo?" Murmushi ya yi yana shafa kansa ya ce"kina can ciki Mommy daman banason na tashe kine that's why nayi zamana anan sai kuma naga wata baƙuwa" ya ƙarashe maganar yana kallon Fattomah, murmushi Mommy tayi ta ce" kai kam bakada dama toh ba baƙuwa bace cousin ɗinku ce" sake kallon Fattomah ya yi sai kuma ya kalli Mommy yana dafe kansa ya ce" sai yanzu na lura Mommy wllh tana kamada Family" zama Mommy tayi tana murmushi ta ce"kadai ji dashi, Fattomah kin ci abinci?" girgiza mata kai tayi Mommy ta ce" ok bari na saka akawo miki amma ki dinga shiryawa da wuri saboda lokaci kinga yanzu ma kusan 7:25am ne" Tom tacewa Mommy sannan ta cigaba da wasada fingers ɗinta. Murmushi ɗauke a fuskarta ta ce" Abbana sannu kaji ya jikin naka?" Shafa fuskanta ya yi ya ce" nasami sauƙi Faɗimatoh ki daina damuwa kinji" goge mata hawayen fuskanta ya yi da hannunsa ta sakar masa murmushi, murmushin shima ya mayar mata ya ce a nutse "Allah ya yi miki albarka Faɗimah" "Ameen ya Allah Abbana". Saida aka idar da sallar isha'i sannan suka baro asibitin wanda azahirin gaskiya bada son ran Fattomah suka baro ba dan tafi ƙauna zama wajen Abbanta da Amminta, murmushi Mommy tayi ganin yanda take ta cin magani a hanya suna zuwa wajen wani mall tacewa drivern ya tsaya, parking ya yi sannan ta kalli Fattomah ta ce" Baby zo muje ki rakani ciki" gyaɗa kanta tayi sannan Mommy ta kama hannunta suka fito Da motar dan shiga cikin mall ɗin, duk irin yanda take moody saida ta saki jikinta tana zaɓar duk abinda taga ya burgeta awajen domin Fattomah batada rufi indai abu ya yi mata tofa sai ta ɗauke shi har suka gama siyan duk abinda suke buƙata aka kai musu mota sannan suka shige gida. Murmushi tayi ganinsa zaune a parlon da alama kallo yake yi zama tafi kan kujerar cikeda gajiyawa ta ce" washhhh!!" Kallonta ya yi ya ce" keee Fattomah yaushe kika gajin?" dariya tayi tana kallonsa ta ce" ayyah yaya Jawaad wllh nagaji sosaima" harararta ya yi ta gefen ido ya ce" babu wani nan"tuntsirewa tayi da dariya ta ce"kaga yanda kayi kyau kuwa yaya?" waro idanunsa ya yi yana kallonta dan yagama fuskantar raina masa hankali take ƙoƙarin yi ya ce" zan kamaki ne yarinya zaki gane ne" gwalo tayi masa lokacin tana hawa kan stairs ɗin benen ya kalli Mommy wacce take tsaye tana dariya ya ce" Mommy watarana sai nayiwa wannan yar taki duka tunda batajin magana" dariya tayi ta ce" aikuwa baka isa ka taɓa min ƴa ba sai dai can ku ƙarke amma ba duka ba" gyaɗa kansa ya yi ya miƙe yana gyara zaman t-shirt ɗin jikinsa ya ce" shikenan tunda kince haka ni zan tafi dan Daddy yana nemana" okay tace sannan ya juya ya fita. Tsaye suke ƙofar makarantar tasu dan tashinsu kenan, Aysha ce ta kalleta ta ce" Nifa zanyi tafiyata wllh" marairaice fuska tayi ta ce" Ayyah bestie ki ɗan jira mana na tabbata suna hanya wlh banason abarni anan ni kaɗai nasan ke kaɗai zaki iya yimin haka please" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta murmushi Aysha tayi ta ce" to kuka zakiyi ne?" tuntsirewa sukai da dariya atare kamar haɗin baki su kansu ba susan abinda suke wa dariyarba, wata ɓakar mota ce ta tsaya ƙirar Accord sport sai sheƙi take kana ganinta kasan bata ƙananun yara bace tsayawa kowa ya yi yana kallon motar ganin tunda tayi parking babu wanda ya fito kusan 2mins. Murmushi tayi ganin Jawaad ya fito daga motar yana nufo inda take, kallonsa tayi tana murmushi ta ce" yaya kai ne kazo ɗaukana?" gyaɗa mata kai ya yi yana rike hannunta bye bye tayiwa Aysha sannan tabi bayansa. Da sauri ta ja baya ganin kamar mutum daga ɗaya side ɗin mai zaman banza na motar "Ki shiga baya Fattum" Kallonsa tayi sai kuma ta buɗe back sit ɗin ta shiga, yana shiga ya tada motar suka bar harabar makarantar. Duk yanda Fattomah taso taga wanda yake gidan gaban kasawa tayi domin koda wasa bai yarda y juyo ba kuma bai ɗago fuskarsa ba har suka ƙarasa gida, yana gama parking ɗin ya ce" yawwa Fattum ki shiga gida za muje unguwa kinji" gyaɗa masa kai tayi sannan a hankali ta sauka daga motar kamar me tsoron wani abu, shiga motar ya yi yay reverse yabar cikin gidan da kallo tabisu duka har suka ɓacewa ganinta ko wane wannan?????? abinda zuciyarta ta faɗa mata kenan ɗaga kafaɗarta tayi alamun ko'a jikinta sannan ta kama hanyar entrance ɗin shiga gidan.. *Manage this lover's abubuwan ne sun min yawa☹️☹️🥰* *Fattomah isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 08106571862* *Kina sane da cewa free pages ya kusa ƙarewa ko kuwa A'a, kindly make ur payment sister 🤝🥰* *Nanameera ce#* [5/3, 4:21 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION. PAGE 9-10. Kallonta Mommy ta yi ganin yanda take Kalle-Kalle ta ce" Fattum lpy?" Shafa kanta tayi ta ce"babu komai Mommy bari na cire kayana" daga haka ta haura sama, da kallo Mommy ta bita sannan ta girgiza kai, zama tayi gefen royal bed ɗinta tana sauke ajiyar zuciya hannayenta ta saka ta tallafi haɓarta tana tunane-tunane, ko waye wannan mutumin??, tsaki tayi tana cewa "ko ina ruwana ma oho" tashi tayi ta shige toilet dan gabatar da sabgar gabanta. Zaune yake kan ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da parlon hankalinsa gabaɗaya yana kan system ɗin da yake dannawa yayinda Jawaad yake ta faman zuba da magana, kallonsa ya yi da lumsassun idanunsa ya ce" wai kai baka gajiya da magana?" murmushi Jawaad ya yi yana kallon abokin nasa kuma gudan jininsa ya ce" ina zan gaji da magana Imaad ma ya gaji da magana?" tsaki ya yi ya ce" Allah ya shiryeka kai kam" murmushi ya yi yana zama kusadashi ya ce" Footballer guda yana danna system" rufe system ɗin ya yi yana kallon Jawaad ɗin ya ce" mr talktive nifa na gaji da magana wlh ka tashi mu tafi gida" ok Jawaad ya ce sannan ya miƙe daidai lokacin wata mata ta fito daga cikin kitchen kallonsa ta yi ta ce" naga ka tashi?" Shafa kansa ya yi yana kallonta ya ce"wlh wai tafiya zai yi kinsan halin gogan" kwaɓe fuskarta tayi ta kalli Imaad ta ce" please yallaɓai ka zauna kaci abincin kaga na kammala" tashi Imaad ya yi yana murmushi ya ce" I'm sorry wani lokacin zanci kinji dear yanzu inason na tafi gida" shuru tayi na wasu sakwanni sai kuma ta ce" amma kasan ba haka mukayi dakai ba ko?" Dafe kansa ya yi ya ce" wayyo ni Imadudden na shiga uku da Ayrah shikenan naji zanci" murmushi tayi ta ce"yawwa ko kaifa bari na zubo muku" komawa tayi kitchen ɗin shi kuma ya zauna yana tallafar haɓarsa zama Jawaad ya yi gefensa ya tuntsirewa da dariya ya ce" yadai Footballer?" hmurmushi ya yi ya ce" wlh nifa babu macen da zata wahalar dani jifa yanda take shagwaɓa kana ƙoƙari" tuntsirewa ya yi da dariya harda riƙe ciki ya ce" shiyasa kenan matarka bata yi maka irin haka, dan baka samu wacce kake sobane wlh" tsaki Imad ya yi ya ce" kawai dan ina sonta saita dinga wahalar dani wlh bata isaba" girgiza kai ya yi ya ce" one day one time zakace na faɗa maka sai mace ta wahalar dakai fiye da tunaninka wuyarta ka samu wacce kake mutuwar so" numfasawa ya yi lokacin da Ayrah ke ajiye musu plates ɗin abincin kan Centre table ɗin dake tsakiyar parlon. Saida tagama jera musu tsaf sannan ta kallesu tana murmushi ta ce" yawwa yanzu ku sakko kuci abinci" ok suka ce sannan suka zauna dan cin abinci. Kallonsa ya yi ya ce" bakaza shiga ba?" girgiza kai Jawaad ya yi ya ce"kasan nidai bana shiga harkar matarka coz batada kirki kawai kayi tafiyarka sai gobe yanzu zanje wajen Fattum ne saina wuce gida" wani irin kallo Imad ya yi masa ya ce" wace Fattum kuma?" harararsa ya yi ya ce" yarinyar da Daddy ya ɗauko fa munyi da ita zan rakata shopping mall" "ƴar wace yarinyar?" kallonsa y yi ya ce" nima bansani ba amma naje na duba baban nata Daddy ya ce ɗan uwanmu ne" okay Imad ya ce sannan ya ce" shine kai kuma kake shishshige mata?" dariya Jawad ya yi yana girgiza kai ya ce" bangane shishshige mata ba banason iskanci" shuru Imad ya yi ya ce" kai kasani, saida safe" ok ya ce sannan sukayi sallama. Murmushi tayi tana rungumeshi ta ce"oyoyo dear sannu da zuwa" zameta ya yi daga jikinsa ya ce" thank you" shigewa ya yi ta bisa da kallo batasan mene ne matsalar Imad ba kwata-kwata bai iya soyayya ba ko kuma itace baya yiwa ohooo. Tsaye yake jikin dressing mirror ɗin dake kafe a bangon ɗakin sanye yake cikin wasu pyjamas blue colour sunyi matuƙar amsar farar fararta gashin kansa ya tufkeshi ya sakko har gadon bayansa sai a sannan na sake ƙare masa kallo Imad haɗaɗɗen matashin saurayine wanda yake ji da kuɗi da kuma kyau game da sarauta wacce take yawo cikin jinin jikinsu bashi da hayaniya ko kaɗan kuma bayason yawan magana ko cikin abokansa halinsa ya fita daban domin shi miskiline na gani kasheni kwata-kwata mata basa gabansa dan yarintar da yake aurema Daddy ne ya aura masa ita batareda saninsa ba, furzar da iska yayi daga bakinsa yana zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa sannan ya fito daga ɗakin. Kallonta yake ganin yanda take ta nishaɗi, murmushi ya yi yana sake jin so da ƙaunar yarinyar cikin ransa da sauri ta tawo wajensa ta ce" yaya Jawaad kazo muce ka sha ice-cream ɗin akwai daɗi wlh" murmushi ya yi ya ce"nikam na yafe Fattomah dan Allah kiyi ki gama kinga dare ya kusa ya yi" kwaɓe fuska ta yi ta ce tana jan hannunsa " please Yaya kazo mujeeee" rasa abinda zai yi yasa ya bi bayanta tana murmushi, saida suka gama cin cake ɗin wanda Fattomah ta tilasta masa ya ci suka tafi, Kalle-Kalle ta shiga yi sai kuma ta ce" yayaaaa!" da sauri ya kalleta ya ce"lafiya Fattum?" langwaɓar da kanta tayi ta ce" ka siyamin kantu please" waro idanu ya yi ya ce" mene haka?" " gashi can waɗancen suna siyarwa" kallon inda take nuna masa ya yi ya ce" ok bari yazo nan" murmushi tayi ta ce" thank you yayana" murmushi ya yi ya ce" Allah ya shiryeki Fattum" dariya ta yi ta ce "Ameen yaya". Wata irin shaƙuwa sukayi cikin yan lokuta ƙalilan ta saba da Jawaad fiye da tunani kulawa yake bata tamkar ƙanwarsa komai tace tanaso tofa sai ta samu duk inda yake saiya nemo mata haka ɓangaren Daddy da Mommy kulawa suke bata tamkar ƴar da suka haifa lokaci zuwa lokaci suke zuwa dubo Abbanta wanda ya samu sauƙi sosai amma asibitin basu sallameshi ba Saboda irin lalurarsa. Rayuwa take mai cikeda tsafta cikin Family ɗin sarki Baira mutum ɗaya ne wanda bazatace yana bata kulawa ba kuma daman bata damu dashi ba tunda batasan shiba, Imad baya shiga harkar kowa banda Daddy, Mommy, Jawaad sai uncles ɗinsa hatta matarsa ba wani shiga harkarta yake ba aƙalla yake shekaru 5 baya cikin ƙasar kasancewar professional footballer wanda ƙasar America ke ji dashi domin ya kasance asalin ɗan ƙasar dan ƙasar mahaifiyarsa ce da mutane kaɗan yake hira Kamar babu gobe ciki kuwa harda Jawaad wanda yake matsayin amininsa kuma ɗan uwansa domin Jawaad ɗan sarkin Kano ne. Shi kuwa Jawaad zuwa sannan babu wacce yake burin aure matsayin second wife ɗinsa sai Fattomah ya yarda zai jirata har tsawon sanda zata isa aure ya aureta domin yanada niyyar ƙara aure kuma daman su jininsu jinin auren mata ne. Fitowa tayi tana dafe bango saboda wani ciwo da kanta yake mata, zaune ta tarar da Mommy tana kallo wani show da ake haskawa a Mbc max dan tana matuƙar ƙaunar dramar kallon Fattomah tayi wacce ta zauna daga ƙasanta tana runtse idanunta shafa kansa Mommy tayi taji zafi ta kalleta ta ce" subhanallahi Baby meya sameki?" kwaɓe fuskarta tayi ta ce" Mommy kaina ciwo yake min ki kiramin yaya Jawaad" langwaɓar da kai Mommy tayi ta ce" Ayyah sorry dear bari na kira doctor ya dubaki sai na kirawo yayan naki kinga maybe yanada ayyuka a office" fashewa tayi da kuka tana girgiza kai ta ce" A'a nidai yaya Jawaad nakeson ya dubani ki kirawon shi please" okay Mommy ta ce sannan ta ce" zauna anan toh bari na ɗauko wayata" gyaɗa mata kai tayi sannan ta kwanta kan three seater nan da nan bacci ya ɗauketa. Kusan 5 missed call tayiwa doctor Amma bai ɗaga ba hakan yasa ta dawo parlon ta zauna dialing number Jawaad tayi amma itama bata shiga, tsaki tayi ta miƙe ta isa inda Fattum ta kwanta sake taba jikinta tayi taji har sannan zazzaɓin yana nan kamar ma ƙarashi akai, sallama ya yi yana shigowa parlon amsa masa Mommy tayi ya zauna kan kujerar yana kallonta ya ce" good afternoon Mommy" "katashi lpy?" "Alhamdulillah ina Daddy?" "baya nan" okay ya ce sannan ya kalleta ganin tana zaune gefen Fattomah shuru ya yi shikam baice komai ba ta ce" Imad please ka dubamin yarinyar nan batajin daɗi" kallonsu ya yi ya ce" what wrong with her?" "ciwon kai take" okay ya ce sannan ya miƙe ya isa gabansu, taɓa jikinta ya yi yaji yanda y ɗauki zafi hannunsa ya zame yaji ta riƙo hannunsa kallon fuskarta ya yi yaga arufe take cikin sambatun zazzaɓi ta ce" nikam ku rikeni zan mutu zafi yake mini wayyoo" kallonta kawai suke ya riƙe hannayenta ya shafa kanta ya ce" sannu" sake riƙe shi tayi ya kalli Mommy ya ce" zan tafi da'ita zuwa asibiti anjima in sha Allah zan dawo da'ita" okay Mommy ta ce sannan ya sunkuya ya ɗauketa tamkar Baby ya fice daga parlon. Kai tsaye gidansa ya shige da ita lokacin Salma tana zaune kan kujera tana kallo dan shine kaɗai sana'arta sallama kawai ya yi sannan ya haye sama da kallo ta bishi dan ta taɓa ganin yarinyar time ɗin da taje gida gurin Mommy amma me ya kawo ta gidansu kuma harma ya yi mata irin wannan ɗaukar???, ƙawarda tunanin tayi daga ranta ta cigaba da kallonta. Wani ɗan ɗaki ya buɗe tamkar chemist haka yake komai na buƙatar asibiti akwai cikin ɗakin cikin gaggawa ya kwantar da'ita sannan ya sanya mata drip ya yi mata allura, ruwan sanyi ya ɗebo ya zauna gefenta ya dinga shafa mata nan da nan zazzaɓin ya sauka sakamakon Ac ɗin daya kunna da fan Saida yaga bacci ya ɗauketa sannan ya fito daga ɗakin, tsaye ya tarar da Salma tana ƙoƙarin shigowa ɗakin baya tayi tana kallonsa baice mata komai ba ya ratsa ta gefenta ya shige master bedroom ɗinsa. Tsayawa tayi wajen tana kallon hanyar da yabi amma ta kasa shiga ɗakin dan batasan me zata tarar ba, buɗe ƙofar tayi ta hangota kwance tana bacci numfasawa tayi Sannan ta juya ta sauka. *Nanameera ce#* [5/3, 4:22 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION. PAGE 11-12. Buɗe dara-daran idanuwanta tayi tana kallon inda take kwance itadai tasan ba anan ta kwanta ba, buɗe ƙofar ɗakin akai yasa ta kalli ƙofar dan ganin wanda yake shigowa cikin sassarfa ya ƙaraso gare ta yana kama hannayenta duka biyun ya ce" ya jikin naki Fattum?" kwaɓe fuska tayi cikeda shagwaɓa ta ce" da sauƙi yaya, ina nake nan?" ajiyar zuciya ya sauke wacce shima bai san ya yi hakan ba ya ce" Allah ya ƙara lafiya ya kiyaye gaba Fattomah" shuru tayi tana kallonsa ganin kamar a dame yake ta ce" yaya ina Mommy?" murmushi ya yi ya ce" tana gida kema yanzu zamu tafi" "to ina muke nan?" dafe kansa ya yi ya ce" wayyo Fattum magana dai?, gidan Imad ne toh shine ya ɗauko ki" sosai taji gabanta ya faɗi dan harga Allah tsoro yake bata kwata-kwata batasan haɗa shirgi dashi lura da yanda ta tafi duniyar tunani yasa Jawaad ya ce" keeee!" a ɗan firgice ta ɗago tana kallonsa tana langwaɓar da kai ta ce" yaya kabani tsoro" yanda tayi maganar ne yasa shi tuntsirewa da dariyar da baiyi niyya ba murmushi itama tayi daidai nan Imad ya shigo ɗakin, kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai yana zuwa ya zare mata drip ɗin hannunta batareda ya kalleta ba fashewa tayi da kuka dalilin zafin da taji shi kuwa gogan ko a jikinsa dan bama zaka ɗauka yana ɗakin ba "Kayi mata a hankali mana" Wani irin shegen kallo Imad ya watsa masa sannan ya cigaba da abinda yake, saida ya gama tass sannan ya juya yayi fitarsa bai sake bi takansu ba, riƙe mata hannu ya yi ya ce" sorry dear zo mutafi gida kinji zan siya miki abin daɗi" dakyar ya lallaɓata tayi shiru sannan suka fito daga ɗakin yana riƙe da hannunta. Babu kowa a parlon sai tv dake aiki hakan yasa kawai ya yi waje tana biye dashi, tsaye suka taddashi jikin mota yana magana da wani maid ɗinsa suna zuwa bai ce komai ba ya shige motar ya fuskanci abinda yake nufi yasa ya kalli Fattomah wacce har sannan bata wani jindaɗin jikinta ya ce" shiga baya kinji" gyaɗa masa kai tayi sannan ya buɗe mata backseat ɗin ta shiga shikuma ya shiga ɗaya side ɗin ya rufe motar, bakinsa ɗauke da Bismillah ya yiwa motar key suka bar gidan. Saida sukayi nisa sosai sannan Jawaad ya ce" wai yaushe ne zaka koma America?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" randa Ubangiji ya hukunta" murmushi Jawaad ya yi ya ce" tom Allah ya yarda" lumshe idanunsa ya yi dalilin wani uban traffic da aka haɗa ahanyar, kusan 5mins kafin su samu su shige daga wajen yana shan kwanar round about ɗin ya ce" nikam halin ƙasar nan na ɓatamin rai komai babu tsari abunfa it's too much" dariya kawai Jawaad ya yi ya ce" dole kaga haka tunda ka daɗe rabonka da ƙasar amma da kasa ba zakaji ba komai ba" tsaki Imad ya yi ya ce" Allah ya kyauta" "Ameen". Da sallama suka shiga ɗakin yana kallon yayan nasa, zama ya yi gefensa yana kallonsa ya ce" yaya ya jikin naka?" gyaɗa masa kai kawai Abba ya yi domin yanda jikinsa ya yi zafi ko magana ma ya gagara ya yi, tashi Daddy ya yi ya ƙarasa wajensa yana zuwa ya rike hannunsa cikin rauni da kuma dashewar murya yake cewa" kulamin da Faɗimatoh ka aurar min da'ita inda zata samu kwanciyar hankali ka riƙe mini ita amana karka bari wani abu mara kyau ya samu rayuwarta ina matuƙar ƙaunarta dan Allah ka cigaba da kulawa da rayuwarta daga inda na tsaya na tabbata Faɗima bazatayi maraiciba indai kana tare da'ita kuma...... Salƙafewa maganarsa tayi lokaci ɗaya ya hau wani irin tari kamar zai fasa ƙirjinsa, da sauri duka suka taso sukayo kansa Daddy Kabeer ne ya ce" sannu kaji yaya Allah ya baka lafiya" ƙam Abba ya rike hannunsa yana magana dakyar ya cigaba da faɗin"dan Allah ku riƙe min Fateema amana ku aurar min da'ita inda za'a kula da rayuwarta domin na sani yarinyar tanada rauni kuma bataji amma tanada tarbiyya daidai tata dan Allah ku tai....... tai. La'ilaha illallahu Muhammadu rasulullahi Sallallahu alaihi Wasalla.." "Doctor!!! Doctor!!! Doctor!! Yaya!! Yaya!!" abinda Daddy yake faɗa kenan yana jijjiga ɗan uwan nasu hankalinsa ya yi matuƙar tashi Ammi kuma mutuwar tsaye tayi dan tama kasa ƙarasawa inda yake, da sauri likitocin suka shigo suka rufa akansa hakan yasa su Daddy suka fito daga ɗakin jikin kowa asanyaye sai addu'a suke a zuciyarsu, kusan 35mins sannan likitocin suka fara fitowa, da sauri Daddy ya tafi yana zuwa ya riƙe wani doctor ya ce "ya jikin nasa?" kallonsa kawai doctorn ya yi sai kuma ya ce"I'm sorry sir mun rasashi Allah ya karɓi abinsa saidai haƙu..... bai tsaya sauraren abinda zai ƙarasa faɗa ba ya shige ɗakin da sauri turus ya yi ganin Abba kwance sun rufe masa fuskarsa jikinsa na wani irin kyarma ya ƙarasa gabansa yana zuwa ya riƙe hannunsa a hankali ya zame gyallen, kifa kansa ya yi akan jikin Abba ya na hawaye rabonda ya zubarwa hawayensa har ya manta sai yau dalilin mutuwar Abba tabbas Abba ya yi kyakkyawan ƙarshe sai fatan Allah Ubangiji ya jiƙanshi da Rahama 🤲🤲. Convey ɗinsa ne suka fara shigowa sannan suma suka shigo lokacin Fattomah na kitchen tana taya maid aiki dan idan batada abinyi kitchen take shiga, miƙewa Mommy tayi ganin an shigo da wani abu kamar mutum arufe kasa magana tayi dan duk tarasa abinda zata yi, Uncle Mansoor ne ya zauna gefen kujerar saboda wani irin sarawa da kansa ke masa Kalle-Kalle ta shiga yi ganin babu wanda yake komai cikinsu duk sunyi shuru, Imad ne ya shigo da sallama Jawaad na bayansa sai matarsa wacce suka tawo tare da niyyar gaisheda Mommy. Da mamaki Jawaad yake kallonsu sai kuma ya kalli gawar dake kwance nan ƙasa cikin rawar baki ya ce" Dad...Daddy..D.. Daddy waye wannan?" kallonsa sukayi duka atare sai kuma sukai shiru, ahankali kamar me tsoron taka ƙasa ya ƙarasa gaban gawar ya tsuguna tamkar an tilasta masa ya buɗe fuskarsa dan gani waye haka, wata irin ƙara da ta saka yasa duka suka juya suna kallonta kafin su ƙarasa ta waɗi ƙasa sumammiya..... Allah Sarki rayuwa ayau akai sadaƙar bakwan mutuwar Abba wanda ya yi daidai da ranar juma'a, zaune take ta ɗora kanta kan cinyar Ammi banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa domin kukanma ya gagara kasawa take duk ta rame ta fice hayyacinta kamar ba Fattomah ƴar rigima ba tunda randa aka sallamota a asibiti bata kula kowa ba duk irin maganar da zaka yimata kuwa sai kuka dan ko abinci taƙi taci hatta Ammi ta gaji ta rabu da'ita domin duk irin yanda taso ta shawo kanta kasawa tayi, yanzuma tayi shuru tana tunanin Abbanta wanda shine abinda take kwana tana yi Mommy ce ta shigo ɗakin da sallama tana zuwa ta zauna gefen Ammi tana kallon Fattomah ta ce "Dan Allah dan Annabi Faɗimatoh kiyi haƙuri ki yiwa Abbanki addu'a kinji wannan kukan bashi da amfani ki daina dan Allah" kamar wacce ta zugata haka ta sake fashewa da kuka kamar ranta zai fita rungumeta Mommy tayi tana shafa kanta ta ce" ya isa haka stop crying Baby kiyi masa addu'a" cikin kuka Fattum ta ce" Mommy Abbana ya tafi ya barni Mommy inason Abbana dan Allah Abbana ya dawo wajena kice masa karya tafi ya barni zanta yin kuka bazan daina ba ni inason Abbana Fattomah tanason Abbantaaa" hawaye suma sukeyi domin yanda take kukan sai ta baka tausayi tabbas Fattomah ta saba da mahaifinta kuma tana matuƙar ƙaunarsa kamar yanda shima yake nuna mata wannan soyayyar dan tafi jinsa azuciyarta fiye da Amminta gashi yanzu ta rasashi rasawa irinta har abada. Baccine ya ɗauketa tana cikin wannan kukan Mommy ta kwantar da'ita sannan ta kalli Ammi ta ce" dan Allah A'isha ki ƙara haƙuri karki dinga damun kanki addu'ar ku yafi buƙata yanzu fiye da kukan please" ajiyar zuciya Ammi tayi tana share hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata ta ce" Nagode Hajiya amma bazamu taɓa mantawa dashi ba domin shiɗin ba kamar sauran maza yake ba yanada halaye wanda ba kowane namiji yake dasu ba ya kula da rayuwarku cikin walwala dakuma tsanani, yana ɗaukan iyalansa tamkar duniyarsa bashi da damuwa indai yana tare damu kuma muma da haka muka tashi wlh har abada bazamu taɓa mancewa dashi ba Allah Ubangiji ya jiƙansa da Rahama" dafata Mommy tayi ta ce" nasani amma dole sai kun cire tunaninsa cikin ranku sannan zaku cigaba da gudanar da rayuwarku Allah ya gafartamasa" "Ameen ya rabbi". Da murmushi a fuskarsa yake kallonta har ya ƙaraso inda take, zama ya yi kan kujerar dake facing wanda take kai ya ce" princess naji kinyi shiru lpy?" kallonsa tayi ta ce" yaya wai sai naga kowa yanada waya a school ɗinmu amma banda ni nima ka siyamin waya yau kuma" dariya ya yi yana kallonta ganin da gaske she's vert serious ya ce" toh Fattum zan siya maki idan kika yi graduation" wani irin kallo tayi masa sai kuma ta ɗauke kai tana kallon wani wajen daban, murmushi ya yi ya girgiza kai sannan ya ɗauko wata leda wacce take bayansa yana murmushi ya ce" kalli kiga" kin kallonsa tayi tana tura baki gaba, Jawaad ya ce" idan na mayar shikenan bazan baki ba shikenan kin rasa" satar kallon hannunsa tayi taga leda amma batace ga abinda yake cikin ledar ba, gyaɗa kansa ya yi sannan ya ɗauke ledar yana shirin mayarwa da sauri ta juyo ganin kamar waya ce cikin ledar tana washe baki ta tafi wajen tana zuwa ta karɓe ledar ta buɗe sakar baki Jawaad ya yi yana kallonta, tana gama ware wayar idanunta ya sauka kan iphone 11pro wata irin ihuuu ta saka tana ƙanƙameshi tana dariya ta ce" thank you so much Yaya nagode sosai Allah Ubangiji ya bikaya da gidan aljanna I'm so happy yayana" murmushi Jawaad ya yi yana kunshe idanunsa dan daman farin cikinta shine muradinsa ya ce" Ameen princess nima nagode" ledar kawai ta ɗauka ta fita daga garden ɗin da gudu da kallo ya bita sannan ya miƙe shima yabi bayanta "Mommy kinga Yaya Jawaad ya siyamin" waro ido Mommy ta yi ta ce" enyeeee yarinya ƴar gidan yaya Jawaad to kince kin gode?" gyaɗa mata kai tayi tana washe baki daidai nan Jawaad ya yi sallama a parlon, gaisawa sukayi da Mommy ta ce" wato na fuskanci kaine kake shagwaɓata yasa take abinda taga dama ko Jawaad" shafa kansa ya yi yana murmushi ya ce" A'a Mommy" murmushi Mommy tayi ta ce" kai da ita ni nan babu ruwana wlh" dariya ya yi ya ce"wai ina Footballer ne kwana biyu?" tsaki Mommy tayi ta ce" nima ina na ganshi sai ɗazu naji babansa ya ce wai ya tafi Spain shine amma ko ya sanar dani" murmushi Jawaad ya yi ya ce" kinsan halinsa sai shi watarana sai naji kamar dai yanada almutsutsai akansa" tuntsirewa tayi da dariya suka juya duka suna kallonta, saida tayi mai isarta sannan ta ce" yaya Jawaad ka bani dariya wai almutsutsai" sake tuntsirewa da dariya tayi Mommy ta ce" Allah Ubangiji ya shirya mana ke Fattum" tana dariyar ta ce" Ameen Mommy". Haka Fattomah ta cigaba da gudanar da rayuwarta cikin gidan General Ibrahim Baira babu abinda ta rasa arayuwarta komai suna yi mata abu biyu ne kawai yake damunta na ɗaya rashin Abbanta wanda har sannan bai saketa ba sai kuma rashin Amminta kusada ita dan bayan arba'in ɗin Abba ta koma garinsu Katsina saidai suyi waya da'ita lokaci zuwa lokaci, banda waɗannan abubuwa batada wata damuwa rayuwarta tana tafiya yanda ya kamata hakana ɓangaren karatunta wanda yanzu taƙi kaɗan ya rage mata dan gab suke da fara jarrabar kammala karatu matakin secondary. Bangaren Jawaad ma yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya kyautata mata duk da zuwa sannan Mommy ta gama fahimtar inda ya dosa saidai babu wanda ta sanarwa hakan ta bari har sanda suma zasu gano hakan da kansu, Ayrah kuwa da batasan wainar da ake soyawa ba ta ɗauki Fattomah tamkar ƙanwarta duk abinda ta samu tofa natane itada Fattum har kwana takeyi gidansa idan Daddy ya barta. Yauma suna cikin kitchen tare inda suke dafa jallof rice sai chips da zasuyi da kuma pineapple nd coconut drink, Banda ƙamshi babu abinda yake tashi dan indai girkine tofa Ayrah number ɗaya ce tanada kwarewa ta wannan fannin ba'a taɓa kada ita a girka haka itama Fattomah wacce yanzu take koyan duk wani abu wand da bata iya shiba. Sallama suka ji a parlon hakan yasa Fattomah ta miƙe daga kan stool ɗin tana kallon Ayrah dake ƙoƙarin wanke hannunta ta ce" aunty Ayrah bari na duba" ohk ta ce sannan ta cigaba da abinda take ita kuma ta fito dan ganin waye, da gudu ta tafi ta rungumeta tana dariya ta ce". *Nanameera ce#*[5/13, 9:27 PM] Nanameera: *FATTOMAH* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* PAGE 13-14. "Aunty Salma sannu da zuwa" Murmushi Salma ta yi tana kallonta ta ce" Fattomah ya kike?" "Ina lpy muje ki zauna" okay Salma ta ce sannan tabi bayanta suka zauna kan kujera, Salma ta ce" Ayrah bata nan ne?" Tashi Fattum ta yi ta ce" muna aiki a kitchen ne bari na sanar da'ita" okay Salma ta ce sannan Fattomah ta juya ta shige kitchen ɗin, kallonta Ayrah ta yi ta ce" wace Fattum?" "Aunty Salma ce tazo" ok Ayrah ta ce sannan ta ce" ki ƙarasa haɗa drink ɗin please karki cika sugar Kinsan yayanki baya so" murmushi ta yi ta ce"toh in Sha Allah". Murmushi ɗauke a fuskarta suka gaisa ta ce"sannu da zuwa sai yau?" Murmushin itama ta mayar mata sannan ta ce" wallahi kinsan halin mutumin ban samu saƙafar faɗa masa ba sai yau shiyasa ma kikaga ganni yanzu da yamma ya ce anjima zai zo mu tafi" Ayrah ta ce "wallahi yaya Imad halinsa sai shi rannar fa dakyar ya tsaya ya ci abinci wai tafiya zai yi bayan ya gama saka ni aiki" dariya Salma ta yi ta ce"Allah dai ya kyauta" Ameen Ayrah ta amsa sannan ta ce" let me get you something". Harararsa Jawaad ya yi ya ce" bangane ba?"kamar bazai magana ba sai kuma ya ce"wannan abinda kake shirin yi isn't proper matarka ta ɗauki yarinyar nan matsayin ƙanwarta bata nuna mata wani banbanci da ƴan uwanta shine zaka ɓata alaƙar tasu kuma sannan ma ka rasa wa zaka aura sai ƙaramar yarinya ubanme zata yi maka idan zakayi aure ka ɗauko babbar mace shine Malam ba wacce zaka zauna raino ba" tuntsirewa ya yi da dariya yana kallon ɗan uwan nasa ya ce" a naka tunanin kenan amma ni kam babu abinda zai hanani auran Fattum sai ikon Allah naji zanyi rainon nata kai bakasan sunfi daɗi ba yaran" taɓe baki Imad ya yi ya ce" bakada hankali ne shiyasa sai ka ƙara girma" wani shegen kallo Jawaad ya watsa masa ya ce" lailaima wato kaine ka girma ko Abba" haɗe rai Imad ya yi ya ce" E, kasan ai daman ni ba sa'anka bane" fitowar Fattum ya sanya sukayi shuru da maganar tana zuwa ta kalli Jawaad tana haɗe rai ta ce" yaya muje ka mayar dani gida" da mamaki ya ce" lafiya princess?" turo baki ta yi ta ce" kawai nidai ka mayar dani mana" "Fattum!!! Fattum!!" Ƙin juyawa tayi Ayrah tazo tana murmushi ta rungumeta ta baya ta ce" I'm so sorry dear ban ƙarawa" ƙin kallonta Fattomah tayi dan ita daman riƙo gareta, murmushi Jawaad ya yi ya ce"me kika yimata?" murmushin itama tayi ta ce" wai dear daga nace mata ta cika sugar cikin drink shine fa wai gida zata tafi" dariya ya yi ya ce" rigima dai Fattum?" zumɓura baki ta yi ta ce" ni bazan sake zuwa gidan nan ba" Jawaad ya ce" dan Allah kiyi haƙuri Fattomah Kinga yanzu dare ya fara yi ki bari gobe in Sha Allah da kai na zan mayar dake gida okay?" girgiza kanta tayi bata ce komai ba, babu yanda basu yi da'ita ba amma Fattomah taƙi haƙuta ita a lallai sai ta tafi gida. Ji tayi an fizgota ta juya kafin tayi aune har ya kaita compound ɗin gidan, cikeda ɓacin rai yake cewa "Idan kika sake two minutes cikin gidan nan sai ranki ya ɓaci shashasha kawai" Da sauri Jawaad ya ƙaraso wajen yana kallonsa ya ce" haba Imad mene ne haka yarinya ce fa?" Afusace Imad ya juyo ya ɗaga masa hannu ya ce" enough!!, banason jin komai nd idan baki bar gidan nan ba I'll show you the other side of me" banda rawa babu abinda jikin Fattomah keyi Allah sarki duk tabi ta tsorata bata saba da irin wannan masifar ba domin kwata-kwata ba'a yi mata faɗa idan ka cire Ammi wanda shima a hankali take faɗa mata koda kuwa laifi tayi shiyasa duk tabi ta ɗimauce, ganin har sannan batada niyyar fita yasa yace da ƙarfi" ubanme kike jira ne?" jikinta na kyarma tayi hanyar fita daga cikin gidan veil ɗin nata ma ya waɗi saboda tashin hankali. Ganin ta kusa kai wai bakin gate yasa Jawaad ya bi bayanta ba tare da ya kalli Imad ba har zata fita dan gateman ɗin bai yi ƙoƙarin hanata ba ganin abinda ya faru, da sauri ya fice daga gidan yana bin bayanta ya ce "Fattomah!!" Ko juyowa bata yi ta cigaba da tafiya da sauri da sauri gudun kada ya cimma ta, kasancewar tafiyarta da tashi ba ɗaya ba yasa ya yi saurin shan gabanta yana kallon fuskarta wacce duk ta jiƙe da hawaye ya ce" Fattum!" kasa kallonsa tayi sai kawai ta rungumeshi tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi ba ƙaramin tsorata tayi ba har jikinta ya fara ɗaukan zafi, tsam ya rungumeta a ƙirjinsa yana jin yanda take kuka a hankali shafa kanta kawai ya iya yi dan bashida zarafin ce mata tayi shuru tabbas akwai buƙatar tayi kukan ko ta samu sauƙi cikin ranta. Saida tayi kukanta mai isarta sannan ahankali ta fara sauke ajiyar zuciya hakan yasa ya ɗago fuskarta akan hannayensa yana kallonta ya ce" I'm sorry kinji na baki haƙuri a madadin Imad" kwaɓe fuskarta ta yi cikin sanyin murya ta ce" yaya ka kai ni wajen Ammina please" sosai ta bashi tausayi jin wacce tskeson gani gashi yasan bashida wannan damar bazasu taɓa yarda ya kai ta ba, shurun da taji ya yi ne yasa ta ce" yayaaaa" lumshe idanunsa ya yi ya ce" na'am ƙanwar yayaaaa" murmushin da batayi niyya ba ta saki ta ce"Allah yaya ka daina banaso" okay ya ce sannan ya kama hannunta, sauri riƙe nasa hannun tayi tana kallonsa, kallonta shima ya yi ya ce" mene?" "bazan bika ba" haɗe ransa ya yi ya ce" bangane ba Fattomah ina ne bazaki bini ba?" sunkuyar da kanta tayi sai kuma ta share hawayen da yake ƙoƙarin fitowa kan idanunta ta ce"ka kaini wajen Mommy kaji Wlh bazan kwana anan ba" sosai ya yi mamakin jin furucin bakinta sanin kuma halin gaddamarta yasa ya ce"muje na ɗauko mota to" naɗe hannayenta tayi a ƙirji ta ce" kaje yaya ina jiran ka anan" girgiza kansa kawai ya yi sannan ya juya ya koma cikin gidan. Zaune ya tarar da Imad yana danna wayarsa haka ma Salma wacce take zaune tana jiransa, sallama kawai Jawaad ya yi musu sannan ya haye sama ko kallonsa Imad bai yi ba saida ya haye saman sannan ya miƙe without looking at her ya ce"muje" babu musu ta miƙe dan daman sunyi sallama da Ayrah ɗaga mata hannu tayi itama ta mayar mata sannan sukai waje, fitowa ya yi jikin wata jallabiya ash colour wacce ta amshi farar fatarsa da mamaki ya kalli Imad wanda yake ƙoƙarin shiga mota bayan guards sun buɗe masa, ƙara sawa ya yi jikin mota ya yi nocking hakan yasa ya sauke glasses ɗin yana kallonsa ya ce" ina zaka je kuma yanzu fa zan dawo?" ba tare da ya kalleshi ba ya ce" gida" shuru Jawaad ya yi na wasu sakwanni sannan ya ce" okay saida safe" gyaɗa masa kai Imad ya yi sannan ya zuge glasses ɗin. Komawa ya yi ya shige motarsa saida ya jira motocin Imad suka bar gidan sannan shima ya yiwa motar key ya fita, tsaye ya sameta daidai inda ya barta tana ganinsa ta tawo ta shiga motar sannan ya ci-gaba da tafiya, ganin yanda ta lumshe idanunta yasa ya ce" bacci ki keji?" buɗe idanunta waɗanda suka fara sauya kala ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce a hankali" zazzaɓi nake ji yaya" tsayar da motar ya yi yana taɓa jikinta ya ce"subhanallahi sannu bari na siya miki magani kinji" gyada masa kai tayi sannan ya ci-gaba da tafiyar. Wani pharmacy ya tsaya ya siya mata magunguna Sannan suka fito tafiyar 5mins ta kawosu wajen wani suya spot Banda ƙamshi mai daɗi babu abinda yake tashi a wajen fita ya yi ya karɓo kaza leda biyu sai chilli yoghurt daya siya sannan ya dawo, da idanu kawai Fattomah ta bishi har ya sake barin wajen. Zaune suka tadda Mommy tana danna system da alama wani abun mai muhimmanci take gabatarwa, sallama sukayi ta ɗago idanunta tana kallonsu zare glass ɗin idonta, kwanciya Fattum tayi akan cinyarta tana lumshe idanunta sosai take jin Mommy tamkar Amminta kodan saboda yanda itama ta ɗauke ta matsayin ƴa ne????, Zama ya yi suka gaisa da Mommy sannan ya kalli Fattum wacce take shirin fara bacci ya ce"keee zo nan" a hankali ta miƙe tana tafiya kamar bata so ta ƙara so wajensa hannunta ya kama ya zaunar da'ita gefensa sannan ya buɗe ledar da ya shigo da'ita, kallonsa ta tsaya tana yi har ya kutsuro kazar yana kallonta ya ce"haaaa" babu musu ta buɗe bakinta ya dinga bata kazar har Saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya bata maganin ya miƙe ya ce" yanzu kije ki kwanta saida safe" tashi tayi ta shige apartment ɗinta shi kuma ya yiwa Mommy sallama, Mommy ta ce"wai lafiya naga ka dawo da'ita da daren nan?" murmushi ya yi ya ce"rigima ta sanya sai na dawo da'ita kuma zazzaɓi take" okay Mommy ta ce sannan ya juya ya fita, nima da naga dare ya yi kuma ga Meeyrah ta sanyani gaba da kallo yasa na tattara alƙamin na ajiye naje na kwanta. *Nanameera ce#* *Ameenatou ce#* [5/13, 9:28 PM] Nanameera: *FATTOMAH* *MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* *PAGE 15-16* Kusan 5days kenan basu haɗu da Imad ba dan daman Jawaad ne mai nemansa sosai kuma shima ransa ya ɓaci, kasancewar yau Friday yasa da wuri suka tashi daga makaranta, tsaye suke itada Aysha tana mata hira wacce ita kaɗai take abarta dan Fattomah ba saurarenta take ba, tsaki Aysha ta yi tana kallonta ta ce"wai ke wannan wane irin wulaƙanci ne ina yi miki magana kin yimin shuru" langwaɓar da kai ta yi ta ce"bana cikin yanayi na magana ne Aysha please ki rabu dani" murmushi Aysha ta yi ta ce"shikenan thank you" gaba ta yi Fattum ta bita da idanu dan ko ajikinta. Har wajen 12:30pm babu wanda ya zo tafiya da ita hakan yasa ranta ya ɓaci duba jakarta ta yi taga tanada kuɗi hakan yasa ta tsayar da keke napep ta sanar dashi inda zai kaita sannan ta shiga, shiga parlon ta yi bayan tayi sallama babu kowa cikinsa sai tv dake faman aiki ita kaɗai hakan yasa tayi shigewarta apartment ɗinta dan a matuƙar gajiye take, wanka kawai tayi sannan ta shirya cikin wata doguwar riga ta lace ɗinkin bubu sosai ya yi mata kyau musamman yanda maroon colour ɗin ta haska fatarta, veil ta ɗauko fari ta sanya sai takalmi half cover shima fari yi tayi kamar amarya dalilin mayafin data ɗora akanta, wasu yari da sarƙa ne na gold wanda Mommy ta bata ta ɗauko ta sanya sannan ta saka agogo wanda yaya Jawaad ya siya mata lokacin da suka je super market, Masha Allah sosai Fattomah tayi kyau abinta bazaka taɓa cewa she's under 16yrs ba domin ko ƴar 20yrs ba zata gaya mata cika ido ba sannan kuma nutsuwarta dan idan ba magana tayi maka ba bazaka taɓa ganin yarintar tata ba da zarar tayi magana tofah zaka gane yarinya ce. Fitowa parlon tayi tana faman zuba ƙamshi murmushi Jawaad ya yi yana kallonta ya ce"enyeeee kinyi kyau sosai princess" rufe fuskarta tayi da hannunta cikin shagwaɓa ta ce"Allah yaya bansooo" yanda tayi maganar ya kwaikwaya ya ce" Allah kanwa inasoo" tuntsirewa da dariya ta yi shima yana taya ta ya ce"nima ai na iya shagwaɓar" turo bakinta wanda yasha lip gloss ta yi ta ce"Allah babu kyau" murmushi ya yi ya ce"shikenan muje lokaci na tafiya" gaba ya yi tana biye dashi abaya har suka fice daga cikin parlon. Kalle-Kalle kawai Fattomah keyi tunda suka shigo cikin gidan sarkin wanda bata taɓa zuwa ba kafin sannan, sosai gidan yake bata sha'awa dan tana shige shi idan zata tafi Makaranta, ko ina suka shige bayine ki tsugunawa suna gaishesu ita ce kawai take mayar musu da murmushi shi kuwa Jawaad ko kallon inda suke ba ya yi, a babbar fadar gidan suka zaune inda nan ne suka tadda mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammad Baira, murmushi ya yi yana kallon Fattomah ya ce"sannu kinji" yanda ya yi maganar tamkar Daddy ne ya yi yanayinsu ɗaya kana ganinsu kasan sarauta da arziƙi ya gama ratsa su, sunkuyar da kanta ta yi hakan yasa Jawaad ya ce"Dad wai kunyar ka take ji fa" murmushi mai martaba ya yi ya ce"wai haka Faɗeemah?" Saurin girgiza kanta ta yi tana kallon Jawaad, murmushi Jawaad ya yi ya ce"hakane mana"turo baki tayi amma batace komai ba saboda mai martaba da yake wajen, sosai ya dinga janta da hira tun tana sunkuyar da kai har ta saki jikinta itama tana bashi amsa. Sai wajejen ƙarfe 6pm sannan suka baro gidan sarkin kai tsaye kuma gidansa suka shige, suna shigowa gidan bayan ya yi parking ta kalleshi ta ce"wai yaya naga ka kawoni nan?" Yana kashe motar ya ce"E, meya faru?" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce"Ni fa gida zan koma" Jawaad bai ce mata komai ba ya sauka daga motar ya shige gidan da kallo ta bisa tanajin zuciyarta na tafarfasa wato yama mayar da ita ƴar iska, kwafa tayi sannan tabi bayansa tana turo baki, zaune ta tarar dashi yana magana da Ayrah wacce take zaune gefensa kamar ta shige jikinsa, sunkuyar da kanta ta yi ta shige bedroom ɗin ba tare da ta yarda ta kallesu ba. Murmushi ta yi tana kallon Daddy ya ce"Eh mana yaushe zaku gama ni kuma nayi alƙawarin kai ki kamar yanda nace" dariya Fattomah ta yi ta ce"sauran 3months kaga yanzu Waec zamu fara" Daddy ya ce"okay toh Allah ya bada sa'a dear" murmushi ta yi ta ce"Thank you Daddy", murmushi Daddy ya yi lokacin da Imad yake zama gefensa bayan ya yi sallama cikin parlon da sauri Fattomah ta miƙe tana shirin barin wajen Daddy ya ce"ina kuma zakije Fattum?" cikin rawar murya ta ce"Daddy zan ɗan duba abune a ɗaki"okay Daddy ya ce sannan ta fice daga parlon da sauri har tana ƙoƙarin tuntube. Taɓe baki Imad ya yi bayan yaga shigewarta, kallonsa Daddy ya yi ya ce"Imad daman inason magana dakai" kallonsa ya yi ya ce"ina jin ka Daddy" Daddy ya ce"in sha Allah next week zamu tafi Abuja kasan daman zama nake temporary anan, kuma akwai abubuwa dayawa" kallonsa Imad ya yi ya ce"Okay Daddy Allah ya kaimu" tashi ya yi ya ce"Ameen zuwa gobe zan sanar dakai abinda ake ciki" tashi shima Imad ɗin ya yi yana zube hannayensa cikin aljihun trouser ɗin jikinsa ya ce"Allah ya kaimu bari naje wajen Mommy"okay Daddy ya ce sannan shima ya yi waje. Shiru Fattomah ta yi tana zaune tsakiyar royal bed ɗinta banda tunani babu abinda take, hawayene suka fara sintiri akan fuskanta tunanin Abbanta take Allah sarki rayuwa tasan da yanzu duk inda yake daya nemata yafi a ƙirga sannan ga rashin Ammi wanda shima yake matuƙar taɓa mata zuciya dukda babu abinda ta rasa cikin gidan Daddy amma ko yaya da tana ganin gilmawar iyayenta zata ji daɗi gashi batasan wanda ma zata tambaya akan maganar ganin Ammi ba tabbas Amminta tayi mata nisa sosai tuna hakan yasa ta sake fashewa da kuka wannan karan har saida muryata ta fito, kwanciya tayi kan gadon tana rufe fuskarta jikin filo ta ci-gaba da kukanta. Tashi ta yi kanta nayi mata ciwo hakan yasa tana yin wanka ta fito a hankali kamar me tsoron wani abu haka ta buɗe ƙofar apartment ɗin nasa, wani irin ƙanshi ne ya daki hancinta lumshe idanunta ta yi sannan ta buɗe su cikin kyakkyawan parlon wanda ya gaji da haɗuwa, kallon parlon ta shiga yi kamar bata taɓa ganinsa ba koda yake a rayuwarta zata iya girƙa shigar ta ɗakin, domin Imad baya bata damar shiga ɗakin saidai su haɗu a nata ɗakin "Lafiya??" A ɗan firgice ta juyo suka haɗa idanu dashi, saurin sauke idanunta ƙasa ta yi ya ce a gajarce"mene?" haɗa nutsuwarta ta yi sannan ta ce"daman kai na ne yake min ciwo shine nace bari na sanar dakai please ka bani magani" ba tare da ya kalleta ba ya yi gaba yana faɗin" ki shirya ki fito" okay ta ce sannan tabi bayansa. Kallonsa Jawaad ya yi ya ce"amma Imad sai yanzu zaka kawota asibiti kenan?" haɗe ransa ya yi ya ce"bangane ba yaushe ka keson na kawota?" girgiza kai Jawaad ya yi ya ce"wannan fa ba daidai bane kaga jikin nata har ya fara worth da ka sanar dani ai sai nazo na dubata a gidan" wani shegen kallo Imad ya yi masa ya ce"toh babana Jawaad Allah ya baka haƙuri" murmushi Jawaad ya yi ya ce"ai gaskiya ka faɗa" harararsa ya yi bai ce komai ba Jawaad ya ce"nasa ansaka mata drip kuma sai ya ƙare za'a cire saboda haka kana iya tsayawa ka jirata" miƙewa Imadudden ya yi ya ce"no idan angama driver zai zo ya tafi da'ita ni inada wajen zuwa" da kallo Jawaad ya bisa dan ya kasa magana, ganin kamar ya tafi tunani yasa Imad ya daki table ɗin gabansa, da sauri ya ɗaga idanuwansa ya kallesa ya ce"sorry na tafi wani tunanin ne shikenan muje na rakaka" waje ya yi yana biye dashi har suka isa parking lot na asibitin, saida yaga ya bar asibitin sannan ya sauke numfashi yana jinjina hali irin na Imad tabbas halinsa ya banbanta dana mutane ko kaɗan mace bata gabansa idan ba haka ba ya ci ace Imad ya haifi ɗa ko ƴa saboda aƙalla ya kai shekara 5 da aure amma idan da za'a zauna to za'a iya ƙirga tarayyarsa da Salma, tun tana jin haushinsa har itama ta saba da rayuwa a haka wanda hakan babbar illa ce ga rayuwar ma'aurata. Shuru Ayrah ta yi tana nazarin maganganun da Ameesha ta faɗa mata tabbas sai yanzu abun yake kawowa kanta, ganin kamar tunani take yasa Ameesha ta ce"ke a tunaninki yana kawota gidan nan ne saboda tana matsayin ƴar uwarsa?, meyasa shi wanda babansa ne ya ɗaukota bai ɗauketa ya kaita gidansa ba, ke kuma saboda baki san ciwon kanki ba shine kike wani sakar mata fuska har take da zarafin shiga cikin bedroom ɗinki wanda ya kasance sirrinki keda mijinki Wlh kin bani mamaki Ayrah bansan yaushe kika zama haka ba domin nasan ba halinki bane" ajiyar zuciya Ayrah ta sauke tana kallon ƙawartata ta ce"ni Kawai na ɗauke ta matsayin ƙanwata ne ganin yarinyar marainiya ce kuma tanada hali mai kyau Fattomah batada matsala gashi naga yanda suke ji da'ita cikin family ɗinsu kinga nima idan inason zaman lafiya dolena na so abinda mijina ke so" da wani expression Ameesha ta kalleta har ta gama maganganunta sannan ta yi tsaki ta ce"amma wlh kin bani mamaki wato saboda kin makance cikin soyayyar mijinki ya sanya har zaki ɗauki wannan kasadar toh ki zauna wlh zaki ce na faɗa miki kina nan zaki je ana rangaɗa guɗa ankawo sabuwar amarya daga nan zai fara daina kulaki tunda ya samu ƴar yarinya under 18yrs Kuma ƴar uwarsa kinga ta ko'ina bakida amfani danginsa zasu koma san ƴar uwarsu ke kuma kinzama shara bola mara amfani" shuru Ayrah ta yi tana kallonta duk hankalinta yabi ya tashi idan da abinda tafi ƙauna a rayuwarta to mijinta ne kwata-kwata batasan abinda zai rabata dashi ko me ƙanƙantarsa, tana matuƙar kishin mijinta idan kuwa hakane to zata ɗauki matakin gaggawa ga Fattomah dan bata shirya rabuwa da mijinta ba kuma bata shirya zama da kishiya ba, katse mata tunani Ameesha ta yi ta hanyar faɗin "Ni zan tafi amma ki sake tunani akan maganar nan zaki ce na faɗi gaskiya sannan koda na kwana ɗaya ki saka idanunki akansu zaki fahimci abinda nake faɗa miki" Miƙewa Ayrah ta yi duk jikinta ya yi sanyi ta ce"shikenan I'll do so in Sha Allah nagode Ameesha" murmushi ta yi ta ce"karki manta babu wannan a tsakaninmu yi wa kai ne" ajiyar zuciya Ayrah ta yi sannan tai murmushi ta ce"sai anjima muje na rakaki"okay ta ce sannan suka fita a parlon, suna cikin magana bayan sun fito Fattomah ta fito daga cikin motar tana sanye cikin wata abaya black colour ta yi rolling kanta da veil ɗin abayar babu komai a hannunta sai wayarta ƙirar iphone 13pro Max wacce yaya Jawaad ya siya mata, kallonta suka tsaya yi domin yanda tayi wani siritaccen kyau kamar ba itaba kullum sake canza kama take abinta, da murmushi a fuskarta ta ƙaraso wajensu tana zuwa ta kallesu cikeda farin ciki da sakin fuska ta ce" laaaaa Aunty Ameesha kece a gidan?" wani kallon banza Ameesha ta watsa mata sannan ta ce"Eh" shuru Fattomah ta yi lokaci ɗaya murmushin fuskanta ya yi padding dukda batasan abinda ya sanya tayi mata hakan ba amma taji babu daɗi, kallon Ayrah ta yi taga ta ɗauke kai bata kawo wani abu ba ta shige cikin gidan with thousands of though on her mind, saida ta shige Ameesha ta bita da harara sannan ta kalli Ayrah ta ce"kinga munafuka ko?" kwafa Ayrah ta yi ta ce"karki damu ki barni da'ita dani take zancen" murmushi Ameesha ta yi sannan ta ce"bari naje mayi waya"okay Ayrah ta ce sannan ta shige motarta ita kuma ta koma gidan. *Nanameera ce#* *Ameenatou ce#* *Like nd share* [5/13, 9:28 PM] Nanameera: *FATTOMAH* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* PAGE 17-18. Zaune ta tarar da Fattomah idanunta akan wayarta da alama wani abu mai muhimmancin take yi a wayar, kallo ɗaya Ayrah ta yi mata ta ɗauke kai banda maganganun Ameesha babu abinda ke yawo cikin kwakwalwarta kallon Fattomah ta yi jin yanda ta yi shuru ta ce"Aunty Ayrah naji kin yi shuru ko wani abun ya faru ne?" batareda ta kalleta ba ta ce"babu komai" bata sake cewa komai ba ta miƙe ta haye sama, da idanu Fattum ta bita tana mamakin abinda ya sameta wanda ya sa ta canza lokaci ɗaya ita dai tasan ita ta kirata tazo zasu dafa wani kalar abinci amma gashi tazo ta rar da Ameesha wacce ada suke wasa da dariya ta haɗe mata rai yanzu kuma Aunty Ayrah tabbas akwai abinda ba daidai ba ko mene ne?????, Rashin sanin wanda zai bata wannan amsar ya sanya ta maida hankalinta kan wayar hannunta tana cigaba da chat ɗin da take da class mate ɗinta, tana shiga ɗakin ta zauna gefen gadon haka kawai taji har shi Jawaad ɗin haushinsa take ji dukda bata tabbatar da abinda Ameesha ta faɗa mata ba amma taji tana son Fattomah ta nisanta da'ita domin tabbas aka cigaba da tafiya a haka watarana sai Jawaad yaji yana son aurenta musamman idan tafi haka girma tunda kullum ƙara girma take hallitarta na sake fitowa tana sake zama cikakkiyar mace, da wannan tunanin har bacci ɓarawo ya ɗauketa bata saniba. Tsayawa tayi bakin titin tana jiran napep wanda zai kaita gida dan gaba ɗaya bata jindaɗi duk ta zama moody saɓanin yanda ta fito daga gida cikeda farin ciki, har ya yi gaba ya hangota ta cikin mirror ɗinsa hakan yasa ya komo baya kaɗan dan ssmun zarafin yi mata magana, ganin mota ta tsaya gabanta ya sanya ta ɗanyi baya kaɗan gudun kada ya takura mata wajen samun abun hawa, kashe motar ya yi sannan ya fito yana sanye cikin wata dakkakiyar shadda milk colour sai sheƙi take ya ɗora hularsa zanna bukhar akansa, hannun maƙale da agogo ya sanya gilashi a kyakkyawar fuskarsa haɗaɗɗen saurayine irin ajin farkon nan kana ganinsa kasan kuɗi ya zauna daram a wajensa, kallonta ya yi yaga kwata-kwata bata kalli inda yake ba hakan yasa y rufe motar tashi sannan ya tako cikin tafiyarsa ta isasshen namiji ya ƙaraso gabanta "Assalamu alaikum" Juyowa tayi tana kallon wanda yake mata sallama dan ita dai tasan ita kaɗai ta fito batareda wani ba kuma babu kowa a wajen da take, idanu biyu sukayi da Kamal wanda yake sakar mata wani kyakkyawan murmushi, shuru Fattomah ta yi ba tace komai hakan yasa ya ce"haba baiwar Allah ko bazaki kulani ya kamata ace kin amsa sallama a matsayinki na musulma ko?" shiru ta yi sai kuma ta ce "wa alaika salaam" murmushinsa mai kyau ya yi ya ce"yawwa nagode sosai" bata sake ce masa komai ba kusan 2mins hakan ya sa ya ce"dan Allah idan bazaki damu ba kibani number wayarki idan yaso sai nazo gidanku later" da sauri ta kalleshi taga ya kashe mata ido ɗaya saurin ɗauke kanta ta yi sai kuma ta ce a hankali"nikam karka dameni please" dariya Kamal ya yi ya ce"toh Madam ai girmanki ne yanda kika ce haka za'a yi" taɓe baki Fattum ta yi dan har cikin ranta ya fara damunta da magana gashi babu alamar napep a hanyar daman kuma titin ba'a fiye samunsu ba duk sai motocin gida, numfasawa ta yi sai kuma ta ce"nifa ka tafi please kada ma wani ya ganmu tare" Kamal ya ce"idan baki so aganmu a hanya kibani address naki sai nazo nima banason tsayar dake akan hanya ko kuma ki shiga motana na kai ki inda zaki sai mu ƙarasa maganar" wani kallon kayi hauka Fattomah ta watsa masa sannan ta ce" Allah ya kiyaye na shiga motar namiji har abada" girgiza kai Kamal ya yi sai a sannan ya fahimci cewa yarinya ce kuma daman auran irin su shine muradin zuciyarsa tabbas sai ya mallaketa matsayin matarsa. Ganin lokaci na tafiya yasa ya ce"ki bani number kin ji dan Allah" ajiyar zuciya ta sauke kusan 2mins sai kuma ta fara karanto masa numbern wayartata, "Fattomah!" Aɗan firgice ta juya inda sukayi 4eyes da yaya Jawaad sai taji gabanta ya faɗi dukda bawai tsoronsa take jiba kuma tasan babu abinda zai mata amma sai taji kamar bata kyauta ba, kallonsa Kamal ya yi sai kuma ya kalleta ya ce"Kinsan shi ne?" gyaɗa masa kai tayi tana sauke kanta ƙasa cikin sassarfa ya ƙaraso wajen without looking at her ya ja hannayenta kasa cewa komi Fattomah ta yi har ya sanyata amotar sannan ya shiga cikin ƴan sakwanni suka ɓace daga wajen, da kallo Kamal ya bisu har sukayi disappearing a wajen kallon wayarsa ya yi yaga ta gama sanya masa numbern hakan yasa bai damu ba ya koma tasa motar shima yabar wajen. Har suka je gida Jawaad bai ce mata komai ba amma kana ganinsa kasan ransa a ɓace yake, yana gama parking ya fice daga cikin motar bai ko kalleta ba samun kanta tayi da kasa fitowa daga cikin motar dan ko ba'a faɗa mata ba tasan yaya Jawaad fushi ya yi da'ita ga abinda ya faru ɗazu ita da Ayrah shiyasa ma tabar gidan bata jirasa ba, kusan 10mins tana cikin motar kafin a hankali ta fito daga ciki ta shiga cikin gidan kamar wacce kwai ya fashewa ajiki. Bataga kowa cikin parlon ba hakan yasa Kawai ta shige bedroom ɗinta dan daman batason haɗuwa dashi, har akayi sallar magrib Fattomah bata fito ba, kwata-kwata ta kasa fitowa parlon gudun kada ta haɗu da yaya Jawaad ga wata uwar yunwa da take ji dan rabonta da abinci tunda tayi breakfast ganin babu sarki sai Allah ya sanya ta sakko daga kan gadon ta ɗaura veil ɗinta sannan ta fito parlon tana ƴan kalle-kalle, gabanta taji ya faɗi ganinsa da tayi zaune kan kujera 2seater yana operating laptop ɗinsa kasa ƙarasowa gabansa tayi unlike da da take zama tana kallon abinda ya ke yi suna hira, ji tayi wasu hawaye sun zubo mata ta sanya hannuta ta share sannan ta shige cikin kitchen ɗin da sauri ta fito ganin Ayrah tsaye da alama abinci take dafawa, rasa inda zataje tayi hakan yasa a hankali kamar me koyan tafiya ta ƙarasa gaban Jawaad. Tsugunawa ta yi daidai wajen ƙafafunsa cikin rawar murya ta ce" yaya Jawaad" shuru ya yi mata babu reply badan bai ji abinda ta ce ba, sau uku tana kiran sunansa amma ya ƙi amsawa wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, cikin sanyin murya da kuma rauni take cewa "Dan Allah dan Annabi yaya Jawaad kayi haƙuri wlh ba laifina bane ko kulashi banyi ba dan Allah yaya" rufe system ɗin gabansa ya yi sannan ya zuba mata narkakkun idanunsa akanta, sunkuyar da nata tayi dan bata iya jure kallonsa, kusan 3mins suna haka sannan ya ce"wane shi?" girgiza masa kai tayi ta ce"wlh ban sanshi ba" "amma kike kulashi har kike ganin kin isa tsayawa da samari akan titi daman irin tarbiyyar da aka miki kenan?" girgiza masa kai kawai take dan ta gagara magana batasan da wani harafi zata yi masa bayani ya fahimceta ba sai faɗa yake mata akan abinda bata da laifi, cikeda masifa wacce batasan Jawaad ya iyata ba yake cigaba da faɗin "Wlh Fattomah duk ranar dana sake ganin kamamancin wannan abun ya faru nayi miki alƙawarin ɓata miki rai irin wanda ba'a taɓa yi miki ba, sai na tabbatar da ranki ya ɓaci daga ke har shi shegen wanda kike kulawar, har yaushe kika yi girman kula saurayi nawa kike?, You Are just 15yrs amma kina tunanin namiji kodan kin ganki da girman jiki?, toh ki sani ko nan da 2yrs baki isa barinki tsayawa da wani ƙato ba bare yanzu shashasha kawai get out of my side" Da sauri ta tashi har tana ƙoƙarin bigewa ta shige bedroom ɗinta tana zuwa ta waɗa kan gadon ta fashe da wani matsananci kuka, kallonsa Ayrah ta yi bayan ta ajiye food flask ɗin hannunta ta ce"doctor lafiya?" tsaki ya yi ya ce"babu komai" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce"haba dan Allah ai tunda naga kana wannan faɗan dole akwai abinda ta aikata dan Allah ka sanar dani" numfasawa ya yi sannan ya bata labarin abinda ya faru briefly. Ajiyar zuciya Ayrah ta sauke ta ce"toh akan wannan kake ta faman faɗa doctor macace fa dole daman ai maza su biyota musamman Fattum" wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce"Eh tunda ita mace akuyace da ake barinta sakaka ke kina kamar shekarunta aka fara barinki tsayawa da samari?" Murmushi ta yi ta ce"Allah ya baka haƙuri yallaɓai ni da wasa nake, saida na kammala secondary school na shiga University sannan Daddy ya fara barinmu" harararta ya yi ya ce"okay shine ita kike son abarta tun yanzu ko?" girgiza kai tayi ta ce"tuba nake dear" murmushi ya yi sannan ta fara serving nasa. Tashi tayi duk idanuwanta a kumbure dalilin kukan data kusan kwana tanayi, a hankali ta sakko daga saman without making any sound ta fice daga parlon, ko kallon masu gadin gidan bata yi taje ta buɗe ƙofa tayi fitarta, cikin Sa'a ta samu wani napep ya shiga ɗaukan ƴan makaranta ta faɗa masa inda zata ya ce to tahau suka tafi. Murmushi ta yi ta ce"kayi kyau sosai doctor" jan kumatunta ya yi ya ce"kema haka dear" dariya ta yi ta ce"mu tafi?" girgiza kansa ya yi ya ce" kirawo Fattum" haɗe rai ta yi sai kuma ta juya ta shige bedroom ɗin da take, kalle-kallenta ta gama ta fito tana kallonsa ta ce"dear bafa ta cikin ɗakin" da mamaki Jawaad ya ce"kamar ya?" ɗaga masa kafaɗa tayi alamar bata sani ba, da kansa ya shiga ɗakin dan tabbatar da gaske Fattomah bata ciki ɗin, tsaki ya yi sannan ya fita wajen masu gadi zuwa sannan hankalinsa ya fara tashi yana zuwa ya kalli gateman ɗin ya ce"kai ina kaga Fattum?" cikeda ladabi yake cewa" yallaɓai naga sanda ta fita ina yi mata magana taƙi kallona wajen 3hrs kenan" da mamaki Jawaad yake furta kalmar ta fita ɗin toh ina ta tafi da safiyar nan da sauri ya shiga motarsa Ayrah ma ta shiga sannan suka bar gidan. *Nanameera ce#* *Ameenatou ce#* *Like nd share*[5/13, 9:29 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION. PAGE 19-20. A hankali yake ƙarewa farfajiyar gidan kallo wacce ta kasance iya ganinka sosai ya yi mamakin ganin fadawa a wajen kenan mai martaba yazo???, kama hannun Ayrah ya yi wacce itama take kalle-kallenta suka shiga cikin gidan. Zama ya yi aƙasa bayan sunyi sallama cikeda ladabi ya gaida iyayen nasa kallona Uncle Kabeer ya yi ya ce"son meyasa ka makara Faɗeemah ta ce kuna bacci ta tawo?" Jawaad ya ce"Eh wlh Abba naɗan tsaya yin wasu abubuwa ne shiyasa"okay ya ce sannan ya kalli Imad wanda tunda ya shigo bai ce komai ba ya ce"kaifa goga?" ɗan murmushi Imad ya yi amma bai ce komai ba, mai martaba ne ya yi musu addu'a sannan ya fara cewa "Kamar yanda kuka sani mun tara wannan taron ne saboda sanar daku abinda ku baku saniba da kuma irin hukuncin da muka yanke a tsakaninmu" Shiru kowa na parlon ya yi dan jin abinda zasu faɗa Uncle Mukhtar ne ya cigaba da faɗin "Kunsan yaya zai bar garinnan zuwa Friday sannan kuma Fattomah tana karatu cikin garin nan bazai yiwu ya tafi da ita ba saboda haka muka yanke shawarar zata zauna gurin ɗaya daga cikinku wanda kuma Imad kaine wanda zata zauna cikin gidanka" Da wani irin expression Imad ya ɗago kai yana kallon Uncles ɗin nasa ba shi kaɗai ba harda su Adda da Fulani Jawaad kuwa mutuwar zaune ya yi, kasa magana Imad ya yi amma banda tafarfasa babu abinda zuciyarsa ke yi baya jin zai iya zama gida ɗaya da wannan mara hankalin yarinyar ba wacce batada nutsuwa ko kaɗan cikin lamuran rayuwarta tabbas saidai idan ta zauna gidan Jawaad amma ba nashi gidan ba, gyaran murya mai martaba ya yi sannan ya cigaba da faɗin "Kasan kuma bazai yiwu ace anbar yarinya budurwa ta zauna cikin gidanka ba kuma ba muharramar kaba tabbas anyi ganganci bawai dan ba'a yarda da kai ba a'a saboda ita rayuwa abar tsoro ce za'a iya zuwa mas'asal da ake buƙatar muharraminta awajen kuma babu, saboda haka muka yanke shawarar aura maka ita yanda duk abinda zai je ya dawo babu tashin hankali ko fargaba aciki" Wata irin zabura Imad ya yi ya miƙe tsaye yama kasa magana sai riƙe gefen zuciyarsa da yayi ba shi kaɗai ba hatta Jawaad Saida ya mike tsaye baisan yaushe ba kuma baisan meyasa ba kawai yaji wasu zafafan hawaye na gangarowa kan fuskarsa, kallonsu kawai iyayen sukayi da rashin fahimta, sosai parlon ya yi shiru kamar ba'a taɓa hallitar mutane cikinsa ba sai Imadudden da yake ta sauke ajiyar zuciya har sannan kuma bai zauna ba. Daddy ne ya kalli Jawaad ganin yanda yake kuka kamar ƙaramin yaro yasa ya kamo hannunsa zama Jawaad ya yi yana kallonsu kamar wani zararre Daddy ya ce"Jawaad meya faru?"kallon Daddy ya yi sai kuma ya fashe da kuka kamar ba shiba ya ɗora kansa kan cinyar Daddy yana kukan, da mamaki kowa yake kallonsa banda Mommy wacce daman tasan kwanan zance kwata-kwata basu yanke abinda ya kamata ba domin Jawaad shine wanda yafi dacewa da Fattomah ba Imad ba dukda tanason Fattomah ta kasance surika awajenta amma tasan bazata samu farin ciki ba indai tana tare da Imad dan ba tun yau ba ya nuna zallar ƙiyayyarsa ga yarinyar. Shafa kansa Daddy ya shiga yi dan yasan tunda har Jawaad ya zubar da hawayensa to tabbas abune mara daɗi ya sameshi, ita kuwa Ayrah da idanu ta bishi tama rasa murna zatayi ko baƙin ciki Mai martaba ne ya ce"wai Jawaad mene haka wannan wane irin abune mene yake damunka?" a hankali Jawaad ya fara rage kukansa amma har sannan bai ɗago fuskarsa ba Daddy ne ya ce"kai kuma akanme kake tsaye kan mutane?" A fusace Imad ya ce "Daddy wallahi bazai yiwu ba, ni bazan iya zama da wannan yarinyar matsayin wata matata ba banida wani interest nayin aure yanzu kuma koda zanyi auran to ni ban shirya auran ƙaramar yarinya ba bazan iya wahala ba banida wani feeling akan yarinyar kuma kunsan bazanyi abinda zan cutar da rayuwata ba banasonta kuma bazan taɓa sonta ba domin ita bata dace dani ba nima kuma ban dace da ita ni ba ajinta bane ni Imadudden Ibraheem Baira nafi ƙarfin auran wannan yarinyar shi dayake da buƙata kuma ya nuna yanaso kuna iya bashi aurenta amma ni.......har abada!!" Yanda yake huci yana maganar yasa duka suka zuba masa idanu suna kallonsa duk sunyi mamaki banda Daddy wanda daman yasan hakan zata iya kasancewa domin ya daɗe da lurada yanda yake mu'amala da yarinyar cikin gidan kuma yasan halin Imad da mugun taurin kai ga kafiya kamar mutanen farko koda yake barewa batayi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba dan shima Daddy number 1 ne wajen kafiya da gaddama. Uncle Kabeer ne ya ce rai a haɗe"ba shawararka muke nema ba Imad umarni ne kuma dolenka kayi biyayya ko kanaso ko baka so" Bai ce komai ba kuma har sannan bai zauna ba sai wani irin numfashi yake saukewa kamar wani zakin da yake a yunwace danma sun raina masa hankali shine sai shi zasu bawa auren yarinyar da ko a hanya baya fatan haɗuwa da'ita bare kuma ya zauna da'ita gida ɗaya matsayin matarsa never!!! Mai martaba ne ya ce anutse"Imadudden!" kallonsa Imad ya yi cikeda girmamawa ya ce"na'am Dad" da hannu ya yi masa alama da yazo ya karaso gabansa ya tsuguna kallonsa ya yi cikeda tausayawa ya ce"mene matsalar?" ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Dad wallahi bana so bamu dace da juna ba amma shi Jawaad yana matuƙar ƙaunarta dan Allah Dad ku mayar da auran kansa please ban shirya ba wlh" shafa kansa Mai martaba ya yi ya ce"ƴar uwarka ce Imad kuma munyi la'akari da cewa kaine kafi buƙatar mace ba Jawaad ba kaine kake da buƙatar second wife dan kamar wanda bashida mata haka kake kuma Fateema yarinyar kirki ce marainiya idan ka kula da rayuwarta Allah zai kula dakai kaima" girgiza kai Imad ya yi ya ce"Dad wallahi banajin zan iya domin zuciyata zafi yake min idan ina tuna cewa wannan yarinyar matsayin matata take ko a mafarki bantaɓa tunanin haka ba ko Jawaad daya nuna yana so banyi supporting nasa ba why yanzu kuma abun zai ƙare akaina Da?, wlh banason auren yarinya" murmushi mai martaba ya yi ya ce"itama yarinyar watarana girma zatayi sannan duk abinda ka ɗorata shine wanda zata aikata maka yarinya tafi daɗi wajen sha'anin aure kayi tunani Imad" shuru Imad ya yi badan ya gamsu da abinda mai martaba ya faɗa masa ba saidan bayason yawan jayyaya da iyayensa, Fulani ce ta ce"nikam dan Allah yaya idan abun zai zama faɗa kawai a haƙura" wani kallo uncle Kabeer ya yi mata ya ce"ku daman mata ai ƙaramin tunani ne daku karki sake cewa komai amaganar nan" shiru ta yi batace komai ba. Daddy ya ce"shikenan Imad kanason yarinyar nan ko baka sonta?" kallonsa Imad ya yi da idanunsa wanda suka canza launi ya ce"wlh Daddy bana sonta" jinjina kai Daddy ya yi ya ce"good, yanda kace haka za'ayi an rigada an ɗaura muku aure saboda haka dole sai ka saketa" Shiru duka suka yi suna sauraren maganar yayan nasu tunda suka ji ya magantu tofah tabbas akwai abinda hakan zai haifar kuma daman bada son ransa suka ɗaura musu auren ba "Zan raba auren dake tsakaninka da'ita amma bisa sharaɗi guda ɗaya" da sauri Imad ya ce"na amince koma mene ne Daddy zanyi"girgiza kai ya yi ya ce"ka fara tsayawa kaji abinda zance, zan bar garin nan ita kuma yarinya anan take karatunta kuma ta kusa ƙarasawa babu buƙatar a tsayar mata da karatu saboda haka Faɗeematoh zata zauna wajenka cikin gidanka a matsayin yarinyar da kake riƙo daga nan har zuwa sanda zata kammala karatunta wanda yanzu ya kasance watanni uku nan gaba har sanda wannan lokacin zai cika bazaka saketa ba daga ranar da suka gama jarrabawa zan aiko a ɗaukar min ita shikenan daga nan sai ka saketa" gorar ruwan da take gefensa ya ɗauka ya buɗe saida ya kusa shanyewa sannan ya ajiye ya cigaba da faɗin "Har zuwa sanda zan karɓeta zata zauna matsayin ƴar riƙo wacce zaka kula da rayuwarta matsayin ƴar uwarka banason jin wani tashin hankali ko wata magana tsakaninku Fattum batasan da wannan maganar ba kuma ba zata sani ba" kallon Jawaad ya yi wanda har sannan yake kwance kan cinyar Daddy ya ce"karka damu Jawaad nayi maka alƙawarin auren Fateema indai ina raye kuma kaima kana raye da zarar ta kammala secondary school zan ɗaura maka aure da'ita karka damu kanka kaji" sanin indai Daddy ya faɗi magana sai ya cikata yasa Jawaad goge hawayensa ya ce"thank you Daddy"shafa kansa Daddy ya yi ya ce"Allah ya yi maka albarka" Ameen kowa na parlon ya amsa. Mai martaba ya ce"Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi"Ameen suka amsa sannan ya kalli Imad ya ce"ka yarda da wannan hukuncin?" gyaɗa masa kai y yi y ace"magana zakayi Babana" a hankali cikin sanyin murya ya ce"na yarda Dad zan barta cikin gidana har zuwa sanda zata kammala karatunta amma zan dawo da'ita kuma kome za'a ce bazan zauna da'ita na tsayin rayuwa ba domin ni bana sonta" murmushi Daddy ya yi ya ce"ba Saika cigaba da faɗa ba mu muna sonta muna ƙaunarta kuma bamu kyamatarta Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya" Miƙewa Imad ya yi ya ce"zan tafi inada ayyuka" gaba ya yi kafin ya kai waje ya tsinkayi Daddy yana cewa "Amma ka sani koda wasa naji wani abu bayan zamanta matsayin ƴar riƙo ranar zaka gane bakada wayo kuma bakasan kanka ba, ranar zan nuna maka the other side of me saboda haka take note" wani irin murmushi Imad ya yi sannan ya fice daga parlon. Daddy ne ya kalli Jawaad ya ce"tashi ku tafi kaji karka damu kamar yanda na faɗa maka Fattomah matarka ce in sha Allah"murmushi ya yi ya ce"tom Daddy nagode sosai Allah ya ƙara girma" Ameen ya ce sannan ya miƙe yana kallon Ayrah wacce ta cika ta batse ya ce"tashi muje" miƙewa tayi ko sallama bata yi musu ba ta fice daga parlon saida ya yiwa su Mommy Sallama sannan ya fita shima. Murmushi Uncle Mukhtar ya yi ya ce"Allah ya nuna mana wannan ranar" murmushi shima Uncle Kabeer ya yi ya ce"aikam ranar akwai kallo dukda nasan babu lallai ma su rabu" miƙewa Daddy ya yi ya ce"kamar sun rabu sun gama saidai idan bana raye amma sai Imad ya saki yarinyar" shuru sukayi jin ya yi magana mai martaba ya mike ya ce"zan koma Allah ya tsare hanya" okay Daddy ya ce sannan duka suka tashi kowa ya tafi Daddy ya kalli Mommy wacce ta dawo daga raka su Fulani ya ce"jeki kiramin Fattum"toh ta ce sannan ta juya ta fita *Ameenatou ce#* *Nanameera ce#* *Like nd share* [5/13, 9:29 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION. PAGE 21-22. *Ameenatou I Ibraheem* *Nanameera ce#* Cikin yanayin na mutuwa Daddy ya fara cewa"Fateema zan bar garin nan ranar Friday kuma naso ace tare zamu tafi saida ke kinada makaranta kuma banason karatunki ya tsaya tunda har kinzo gangara, saboda haka zaki zauna gidan Imad har zuwa sanda zaki kammala karatunki daga nan zaki dawo wajena mu cigaba da rayuwa" Hankali tashe Fattomah ta ɗago idanunta ta kalli Daddy lokaci ɗaya hawaye ya game kyakkyawar fuskanta bakinta na rawa ta ce"Da..Dad.Daddy dan Allah ka barni anan gidan zan zauna ni kaɗai ko gidan yaya Jawaad kaji Daddy" yanda tayi maganar dole ta baka tausayi hakan yasa Daddy ya taso ya zauna gefenta ya kamo hannayenta cikin nasa ya ce"Fattum kiyi haƙuri kinji ki ɗauki Imad matsayin yayanki na tabbata zai kula dake koda kuwa bakuyin shiri sosai bazai yiwu ki zauna gidan Jawaad bane da can zaki zauna sannan bana son zamanki a fada shiyasa bance Muhammad ya tafi dake ba kiyi haƙuri zaman wata uku kawai zakiyi daga nan zaki dawo kuma Imad bazai cutar dake ba muddin baki saɓa masa ba kinji" cikin kuka ta riƙe hannun Daddy ta ce"Daddy wlh tsoronsa nake ji dan Allah karka barni wajensa wayyoo Allahna Daddy" rungumeta Daddy ya yi ahankali yake faɗa mata kalamai masu kwantar da hankali wanda duk suka saka jikinta ya yi sanyi, saida yaga tayi shiru gabaɗaya sannan ya ɗago fuskarta ya goge mata hawayen ya ce"karki damu kinji zan dinga kiranki mu gaisa kuma Imad zai dinga kawo ki one's in a tym saboda haka you don't need to worry dear"jinjina masa kai tayi ya shafa kanta ya ce"good gurl Allah ya yi miki albarka" a hankali ta ce"Ameen Daddy" miƙewa ta yi Mommy ta ce"ki je ki shirya zuwa anjima zamuje super market sai a siyamiki abubuwan buƙata"toh kawai Fattomah ta ce sannan ta shige ciki. Zama Mommy ta yi tana kallon mijin nata ta ce"wlh ina tausayinta" kallonta Daddy ya yi ya ce"akanme kuma?" numfasawa ta yi ta ce"bata saba da Imad ba kuma kasan Imad ko mutum ya saba dashi toh fa yanada wahalar sabo sannan gashi ita kanta matar tasa bawani alaƙa ce mai kyau tsakaninsu ba kaga kuwa kullum zata kasance lonely" tashi Daddy ya yi ya ce"babu wata mafitar ne sai wannan dole hakan za'a yi" "Allah ya rufa asiri" Ameen ya ce sannan ya yi waje. Tunda ta shiga ɗakin take kuka bata taɓa jin kewar iyayenta irin wannan ranar ba tabbas da suna kusada ita to makamancin wannan abun bazai faru da'ita ba, da yanzu tana wajen iyayenta suna rayuwa cikeda farin ciki kamar yanda suka saba kowane lokaci Allah sarki rayuwa batada tabbas ko kaɗan bata taɓa tunanin rayuwarta zata juye zuwa haka ba sai gashi cikin ƴan watanni komai ya koma upside down, tasan zamanta gidan Imad tamkar ƙarewar farin cikinta ne domin ko kaɗan baya ƙaunarta wanda take sa ran farin ciki daga gareshi yaya Jawaad ne kuma gashi ya juya mata baya haka tayi ta saƙe-sakenta har akayi sallar azahar sannan ta tashi ta shige toilet dan shiryawa. Kamar yanda Mommy ta ce haka ya kasance karfe biyar suka isa super market ɗin, siyayya sosai sukayi Fattomah tana tsaye wajen ɗaukan chocolate saboda ƙaunarta da'ita kamar daga Sama ta ji ya ce "Nima ki siya mini man" Aɗan firgice ta juyo idanunta suka sauka kan Kamal wanda yake kallonta da murmushi afuskarsa, sunkuyar da kanta tayi ya ce"sannu ya kike kwana biyu?" kallonsa ta yi amma bata ce komai ba ya sake cewa"I'm sorry rannar na saka anyi miki faɗa nasan kiyi haƙuri kinji" sai a sannan ta ce"babu komai" murmushi ya yi ya ce"me zaki siya?" kamar bazata yi magana ba sai kuma ta ce"chocolate zan ɗauka" "can i help you?"shiru tayi batace komai ba ya fara zaɓar mata chocolates ɗin masu matuƙar tsada ita kuwa Fattum tsayawa ta yi tana kallon ikon Allah juyowa ya yi suka haɗa ido ta tuntsire da dariya tsayawa ya yi yana kallonta ganin yanda dariya tayi matuƙar yi mata kyau tabbas Fattomah kyakkyawace ajin farko. Murmushinsa mai kyau ya yi ya ce"me kike yiwa dariya ne?" ta ce"wannan kayan na wane?" waro idanunsa ya yi ya ce"naki mana Fattomah" da sauri ta ce" a ina kasan sunana?" dariya Kamal ya yi ya ce "naji yayanki na faɗa rannan" jinjina kai ta yi sannan tabar wajen hakan yasa shima yabi bayanta. "Meyasa kake bina ne nida Mommyna muka zo fa" Kalle-Kalle ya shiga yi ya ce"tana ina mu gaisa please" sakar baki Fattum ta yi tana kallon ikon Allah ganin da gaske Mommy ɗin yake nema su gaisa, haɗe rai ta yi tana kallonsa ta ce"nikam please banason abun kunya sai anjima" gaba tayi ya yi saurin biyota hakan yasa ta ƙara tsayawa ya ce"chocolates ɗin naki fa?" "bana so ni wanda na ɗauka sun isheni" girgiza kai ya yi ya ce"ko ki karba ko kuma naje har inda Mommynki take na baki agabanta sai ki zaɓa" Fattum ji tayi kamar ta ɗora hannu aka ta fashe da kuka amma babu dama hakan yasa ta ce"Dan Allah idan ba so kake raina ya ɓaci ba kayi tafiyarka" murmushi ya yi ya ce"ki karɓa shine kawai zai ceceki" dafe kanta ta yi ta ce a shagwaɓe"idan Mommy tazo wajen nan kaida Allah wollah" dariya Kamal ya yi ya ce"kin shirya karɓa?" ganin da gaske ba rabuwa zai yi da'ita ba yasa ta gyaɗa masa kai a hankali, ya yi murmushi ya ce"good gurl". Saida ya biya kudin sannan ya koma ya cigaba da ɗaukan abinda ya kawo shi ita kuma ta koma inda Mommy take tsaye, sai gab da magrib sannan suka baro super market ɗin duk sun gaji saboda yawo, har suka zo gida babu wanda ya ce komai dan duk sunyi laushi.... Sosai Fattomah tayi mamakin irin kayan da Mommy ta siya mata dan ita bata ɗauka sunkai haka yawa ba kayana irin latest ɗin nan kuma unique kana gani kasan kuɗaɗe aka sa aka siyesu, duk yawancinsu ƙananun kaya ne sai abayas only fews ne traditional clothes saida ta gama ganin kayan sannan ta mayar ta ajiye ita kuma ta fito dan zuwa wajen Mommy, banda ƙamshi babu abinda parlon keyi ko'ina very cleaned and tidy, zama tayi kan royal cusion ɗin dake zagaye da parlon ta lumshe idanunta a hankali wata nutsuwa ke saukar mata, Cikin wani babban gida wanda ya kasance kamar lambu ko'ina iska mai daɗi ke kaɗawa wasu irin kyawawan furarrani ne ke zubowa kamar irin a film ɗin, da sauri Fattomah ta tafi wajen Abbanta wanda yake kallonta yana sakar mata murmushi faɗawa jikinsa ta yi ta fashe da kuka cikin shagwaɓa take cewa"Abbana meyasa ka tafi ka barni?, banajin daɗi Ababana gashi Ammi ma tayi tafiyarta sai ni kaɗai banida kowa Abbana dan Allah kadawo kaji" shafa fuskarta Abba ya yi ya ce"Faɗeematoh rigima, kiyi haƙuri kinji tabbas akwai ƙalubale sosai a rayuwarki amma inason ki kasance mai juriya akowane irin hali kika tsinci kanki kada kiyi ƙasa a gwuiwa, ki zama mai jin magana Faɗeemah domin shine farkon abinda zai haddasa miki matsala cikin rayuwarki ki daina rashin jin magana kome ya faru watarana zai yi ƙarshe kuma kece wacce zaki ci riba ki ƙara haƙuri akan wanda kike dashi Faɗeemah komai ya yi farko zai yi ƙarshe" "A'a Abbana kada kace haka Please ka dawo wajena dan Allah Abba!!!" Da mamaki Mommy take kallonta ta ce"Fattum kedawa?" A firgice ta buɗe idanunta tana zazzaresu, kallonta Mommy ta yi ganin yanda take haɗa gumi dukda AC dake faman aiki cikin parlon ita kuwa Fattomah ta kasa gane abinda yake shirin faruwa da'ita ashe daman mafarki take ba gaskiya bane?, da gaske Abba ya mutu kuma bazai dawo ba?, mene ne abinda Abba ke ƙoƙarin faɗa mata???, rasa abinda zata yi yasa kawai ta fashe da kuka tana riƙe kanta wanda take jin yana mata wani irin ciwo. Zama Mommy tayi gefenta ta dafata ta ce"Fattomah lafiya meya faru?" kasa magana Fattum ta yi sai kukanta data cigaba, rungumeta Mommy tayi ta ce"dan Allah ki yi hakuri ki daina wannan kukan karki zo kina rashin lafiya kinji kiyi shiru" sosai Fattomah tasha kukanta kafin daga bisani tayi shiru ta koma sauke ajiyar zuciya har bacci ɓarawo ya yi gaba da'ita. A hankali ta tura ƙofar bedroom ɗin ta shiga tana ɗan Kalle-Kalle, zaune ta ganshi kan kujerar dake gefen gadon da alama ya yi nisa cikin duniyar tunani dan bai ma san ta shigo ba, zama Ayrah ta yi kan gadon a hankali ta ce"Doctor!" ko kallonta bai yiba wanda ya sake tabbar mata dacewa tunanin yake har sannan sauke idanunta ƙasa tayi cikin sanyin murya ta ce"Doctor dan Allah ka daina wannan tunanin da kake please" ganin har sannan bai juyo ba yasa ta miƙe ta ƙarasa inda yake, saida ta taɓa shi sannan ya kalleta aɗan firgice ya ce"Ayrah lafiya?" numfasawa ta yi ta ce" ka tashi mu ci abinci please" gyaɗa mata kai ya yi ya ce"I'm coming" girgiza kai ta yi ta ce"kawai ka tashi muje idan ba haka ba zama zaka sake yi" murmushi ya yi sannan ya kama hannunta suka fita daga ɗakin. Banda kuka babu abinda Fattomah keyi ta ruƙunƙume Mommy sai kuka take kamar ranta zai fita ita kanta Mommy ƙarfin hali kawai take dan tana matuƙar jin Fattomah aranta, ganin abun nasu ba mai ƙarewa bane yasa Daddy yazo ya janyeta daga jikinta yana kallon Fattomah ya ce"ya isa haka dear zaki dinga zuwa you don't need to worry kinji"tana kuka ta ce"Daddy ku tafi dani" murmushi ya yi ya ce"shikenan next week Imad zai kawo ki kinji" kallon Imadudden ya yi ya ce"please ka kula da'ita yanda ya kamata tym to tym kana kawota"Okay kawai Imad ya ce sannan ya yi gaba, kallonta Jawaad ya yi ya ce"ki yi shuru mu tafi gida" gyaɗa masa kai tayi sannan ta bar wajen su Mommy akan idanunsu jirginsu Mommy ya tashi zuwa garin Abuja, wani sabon kukan taji yana neman kwace mata Jawaad ya riƙe hannunta suka fara tafiya, back seat ya buɗe mata ta shiga sannan ya shiga gaba Imad ya yiwa motar key bakinsa ɗauke da Bismillah suka bar Airport ɗin, a hankali ya gangara gefen hanya ya yi parking da mamaki Jawaad ya kalleshi kafin ya yi magana ya juya yana kallon Fattomah ya ce"whether you keep quiet or get out okay?" a hankali ta fara rage sautin kukan nata tsaki ya yi sannan ya ci-gaba da tafiya batareda ya sake cewa komai ba. *Ameenatou I Ibraheem#* *Nanameera ce#* *Like nd share* *Juma'at Mubarak to oll muslims Allah ya haɗamu da Alkhairan cikinta🤲🤲* [5/13, 9:29 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION. *Ameenatou I Ibrahim* *Nanameera ce* PAGE 23-24. Kallonsa Jawaad ya yi bayan ya tsaya da driving ɗin ya ce"zuwa gobe zan shigo in sha Allah" gyaɗa masa kai Imad ya yi, murmushi ya yi yana kallon Fattomah ya ce"sai da safe dear" kallonsa kawai tayi amma bata ce komai ba ya juya ya sauka daga motar, sosai gaban Fattum ya shiga faduwa ganin ya rage daga ita sai Imad cikin motar shi kuwa ko nuna alamar yasan da mutum bai yiba ya cigaba da driving ɗinsa har suka ƙarasa gida. Kashe motar ya yi ya fice daga ciki hakane yasa itama ta fito tana bin bayansa kamar wata mara gaskiya, a babban parlon gidan wanda yasha kayan alatu kala-kala ta ganshi tsaye yana magana da Salma wacce itama take tsaye jikin kujera da mamaki ta kalli Fattomah sai kuma ta kalleshi ta ce" baƙuwarmu har ta iso?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce"kaita wannan apartment ɗin"okay ta ce sannan takalli Fattomah ta ce"muje Fattum" bin bayanta Fattomah ta yi bata sake yarda ta kalleshi ba. Tsaki ya yi sannan ya haura samansa, sosai apartment ɗin ya tafi da imanin Fattomah dan ya yi matukar haɗuwa kana gani kasan gidan manya ne, kallonta Salma ta yi ta ce"nan ne ɗakinki akwai komai cikinsa including kitchen idan kina son dafa wani abun okay?" gyaɗa mata kai Fattum ta yi sannan ta juya ta fita ajiyar zuciya Fattum ta sauke sannan ta shige cikin bedroom ɗin dan kwanciya ta huta. Tuntsirewa ya yi da dariya yana kallonsa ya ce"to kai yanzu ina zaka sake samunta?" murmushi Kamal ya yi ya ce"inada numbernta kuma ko ba haka ba ni nasan zamu sake haɗuwa da Fattomah saboda ita ɗin ta kasance mallakina ce kaga dolene mu kasance tare nasan zan sake ganin kayata" girgiza kai Saleem ya yi ya ce"sannunka romeo kace tama zama taka?" jinjina masa kai ya yi Saleem ya ce"Alhamdulillah finally dai Aboki zai yi aure Allah ka nuna mana lokacin nan ai ka zaunu"murmushi kawai Kamal ya yi bai ce komai ba. A hankali take sakkowa daga stairs ɗin tana ɗan Kalle-Kalle gudun kada ta haɗu da Imad har ta ƙaraso parlon, babu kowa cikinsa ko ina ya yi shiru gwanin daɗin zama, kamar wacce aka yiwa dole haka ta samu kanta da zama kan kujerar tana kallon wata drama da ake haskawa Mbc 3 ƙaunarta da cartoon yasa hankalinta duk ya tafi da ganinsa wanda hakan yasa har batasan sanda ya shigo cikin parlon ba, jin kamar mutum akanta yasa ta juya dan ganin waye a mugun tsorace ta mike daga wajen tana mutstsuke idanu, wani banzan kallo Imad ya watsa mata sannan ya ce"get out!!" yanda ya faɗi maganar ne ya sanya taji jikinta na ɓari ganin kamar bata gane abinda yake faɗa yasa ya daka mata tsawa ya ce"ba dake nake magana ba shashasha kawai!!" fashewa tayi da kuka ta tafi da gudu tabar parlon tsaki Imad ya yi ya ce"aikin banza kawai zanyi maganinki ne soon" yana gama faɗin hakan ya juya yana kallon tv ɗin tsaki ya yi ya ce"yarinya ko wahala". Kuka ta dunga yi ita daman tasan wannan zaman babu abinda zai ƙara mata sai wahala bazata iya zama da wannan mutumin ba ko kaɗan bashida mutunci, tunawa dasu Mommy ya sanya ta sake fashewa da wani irin kuka tabbas tasan ta shiga uku zamanta anan, haka ta dinga kukan nan ƙasan carpet har bacci ɓarawo ya saceta. Wani kallo ya yiwa Jawaad amma bai ce komai ba Jawaad ya ce"gaskiya na faɗa wlh dole sai kana sanyaya zuciyarka saboda yarinya ce ƙarama batada wayo idan da zaka jata jikinka ka nuna mata soyayya wlh duk abinda kace tayi shine zata yi amma indai zaka dinga nuna baka sonta tofah zata dameka ne gwara kayi tunani" murmushi Imad ya yi irin na rainin hankalin nan ya ce"idan ta fasa rashin hankalin, what do you think?, zan rabu da'ita ta ɓatamin rai ne?, wlh duk sanda ta yi min laifi sai na hukuntata i most punish her saboda haka ruwanta ne ta shiga hankalinta ruwanta ne tayi rashinsa nidai ina nan kan matsayata" shuru Jawaad ya yi yana tausayin Fattomah cikin ransa fatansa ɗaya yarinyar tayi masa biyayya domin duk abinda Imadudden ya ce tofah yana iya aikatashi batareda ya yi duban wani abu ba, cikin sigar lallashi ya ce"Allah ya baku ikon zama lafiya shine kawai abinda zan ce maka, yanzu yaushe zaka koma America?" tsaki ya yi ya ce"ina naga tafiya America yanzu ai dole sai nan da 3months idan ta koma wajen Daddy" Jawaad ya ce"please ka kiramin ita zamu gaisa" harararsa ya yi ya ce"ba'a gidan nan ba ka bari ta koma hannun magabatanta please" tuntsirewa da dariya Jawaad ya yi ya ce"ai kaima magabacinta ne yanzu malam ko bakada labari?" "Allah ya kiyaye" tashi suka yi atare Jawaad ya ce"dan Allah ka kirawo min ita" wani kallo ya yi masa ya ce"bakasan hanya bane?" murmushi ya yi ya ce"ai naga mutum da iyalinsa" kwafa Imad ya yi sannan ya bar parlon. Kallonta Imad ya yi ganin yanda take bacci a ƙasa duk ta takure jikinta, tsaki ya yi sannan ya sanya ƙafarsa ya ɗan shureta, a mugun firgice ta farka saboda daman cikin tsoro ta yi kukan, wani shegen kallo ya watsa mata sanda suka haɗa ido ya sa ta sauke idanunta ƙasa "Tashi ki fita" Abinda Imad ya furta kenan sannan ya yi waje, miƙewa tayi tana ɗan turo bakinta itama ta fita wajen. Da sauri ta ƙarasa wajensa tana murmushi ta ce"yaya Jawaad" mirmushin shima ya mayar mata sanda ta zauna gefensa ya ce"Fattomah" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce a shagwaɓe"yaya Jawaad ka tafi dani gida please nan babu daɗi" shafa kanta ya yi ya ce"Ayyah sorry dear ki bari kin kusa dawowa gidana forever" Fattomah bata gane abinda yake nufi ba ta ce"kawai mu tafi yau yaya" murmushi Jawaad ya yi yana kallon Imad wanda ya haɗe rai ko kallonsu bai yiba, cikin sigar rarrashi Jawaad ya ce"kiyi haƙuri ki zauna anan in sha Allah kina gama exams zan tafi dake amma yanzu kiyi haƙuri" raurau tayi da idanu ta ce"Allah yaya kayi alƙawari?" gyada mata kai ya yi ya ce"yeh! amma yanzu ki shirya gobe ki tafi makaranta" jinjina masa kai ta yi ta ce"toh yaya kai zaka zo ka tafi dani?" waro idanunsa ya yi yana murmushi ya ce" Fattum rigima to driver zai kai ki" haɗe rai tayi ta ce"toh ni bazani baaaaa" yanda tayi maganar cikeda shagwaɓa yasa ya yi dariyar da bai shirya ba, wani kallo Imadudden ya watsa musu da ya sanya tayi ƙasa da kanta shi kuwa Jawaad murmushi ya yi ya mike yana kallonta ya ce"saida safe dear ki shirya da wuri kinji" jinjina masa kai tayi ya ce"good gurl Allah ya yi miki albarka" murmushinta mai kyau ta yi ta ce"Ameen yayana" kallon Imad wanda yake danna wayarsa ya yi ya ce"saida safe Footballer" can ciki ya ce"good night dear, Allah ya tashemu lpy" Ameen Jawaad ya ce sannan ya juya ya fita. Miƙewa ta yi ta shige ciki yabi bayanta da wata uwar harara ni kuwa nace abanza 😂😂. Da sassafe ta tashi ta shirya saboda abinda yaya Jawaad ya ce mata, bayan ta ɗauko school bag ɗinta ta sakko ƙasa dan tafiya makarantar, tsayawa ta yi dalilin Imad data gani tsaye jikin dinning table hannunsa rikeda mug na tea, a ɗan duburbarce ta ce"ina kwana?" idan table ɗin dake gaban Imad ya yi magana to Imad ma ya yi magana ganin haka yasa ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba amma tana tsaye dan batasan wane wanda zai kaita makarantar ba. Kusan 5mins tana nan tsaye shikuma har sannan bashida niyyar gama abinda yake ko kuma kulata, fashewa Fattomah ta yi da kuka da ƙarfi, da sauri Imad ya juyo ya kalleta dan ganin abinda aka yimata Tsabar baƙin ciki ji ya yi kamar ya jawota ya yi mata duka, a matuƙar fusace ya ƙaraso gabanta yana kallonta ƙirjinsa sai ɗagawa yake dan idan da Abinda ya tsana a rayuwarsa bai shige kuka ba ya tsani yaga ana kuka musamman yanzu da take masa kukan na rashin dalili, cikin wata shaky voice ya daka mata tsawa ya ce". *Ameenatou ce#* *Nanameera ce#* *Like nd share*[5/13, 9:30 PM] Nanameera: *FATTOMAH* *MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* Ameenatou Nanameera PAGE 25-26. "Uban me aka yi miki?" yanda ya yi maganar afusace yasa ta ɗan yi baya tana kare fuskanta gudun kada ya kai mata duka, kwafa ya yi sannan ya ce"akwai ubanda ki ke jira anan?" turo ƙaramin bakinta wanda yasha lip gloss kamar ba school zata tafi ba tayi ta ce aciki-ciki "koba kuɗin makaranta zaka bani ba" wani banzan kallo Imad ya watsa mata sannan ya yi wani killer smile, juyowa ya yi gaba ɗaya yana sake ƙare mata kallo ya ce cikin rainin hankali ya ce"wane ya kawo ki gidan nan?" kallonsa Fattum ta yi sai kuma ta ɗauke kai tana zumɓura baki, murmushi Imaad ya yi ya ce"I'm asking you" can ƙasa ta ce"kai ne" ya ce"wane ya siya miki kaya sanda za kizo gidan nan?" asanyaye ta kalleshi sai kuma ta sauke idanunta ƙasa ta ce"Daddy ne" murmushi ya yi for the second time ya ce"da gaske?"gyaɗa masa kai ta yi ya ce"kuma amma shine bai haɗa miki da kudin makaranta ba?, ki ce Daddy baison kije da kuɗi makaranta" da Mamaki Fattomah take kallonshi dan har sannan bata fahimci abinda yake nufi ba. Lura da hakan yasa Imad ya ce"ki huce ki tafi dan ni bazan iya baki wani kuɗin makaranta ba tunda ba ni ne na sanya kiba kuma ba zamana kike ba saboda haka wuce daga nan" tunda ya fara magana Fattum take kallonsa with mouth agape yama za'ayi ta tafi makaranta babu kuɗi ai abinda bazai yiwu ba kenan, ganin har sannan tana tsaye ko motsawa ba tayi ba yasa ya ce"ba kiji abinda na ce miki ba?" cikeda shagwaɓa ta ce"ni wllh bazan tafi babu kuɗin makaranta ba to me zan siya??" baki buɗe Imad yake kalllonta har takai ƙarshen maganartata sannan ya ce"keee, I'm play with you?, kinga alamun Ina yi miki wasa???" shuru Fattomah ta yi dan ita ko kaɗan bai bata tsoro ba kuma yanda ta faɗa bazata tafi ba dole sai ya bata kuɗin school kamar yanda aka saba bata. Jinjina kansa ya yi sannan ya ce"Malama bar wajen nan ko ranki ya ɓaci" ƙin tafiya tayi ta tsaya tana kafeshi da manya manyan idanunta masu matuƙar ɗaukan hankali, riƙe ƙugunsa ya yi da hannayensa yana sake jinjina gaddama irin tata amma duk iya gaddamarta bata ko kawo ɗan yatsan sa ba. Agogon dake aiki jikin bangon ɗaki ta kalla wajen ƙarfe 7:45am kuma tasan Indai 8:00am tayi tofah baza'a barta ta shiga ba kamar zata yi kuka ta ce"dan Allah kabani wlh zanji yunwa kuma ba'a tashinmu sai la'asar" ko kallonta Imad bai yiba ya haye sama wanda hakan ke tabbatar mata da cewa bazai bata ba. Waje Fattomah ta yi tana fita taga drivern da zai kaita makarantar already ita yake jira shiga motar ta yi sannan suka bar gidan, saida taga sunyi nisa sannan ta fashe da wani irin kuka, kallonta drivern ya dinga yi ta jikin mudubi har suka isa makarantar tasu. Yana sauketa ta shige makarantar bata ko kalleshi ba, kasancewar ranar Monday ne yasa tana shiga ana assembly ƙin tsayawa tayi ta shige class tayi kwanciyarta ita kaɗai tasan abinda take ji gashi dama ko breakfast bata yiba cikinta banda ƙugi babu abinda yake saboda kwata-kwata arayuwarta bata saba da zama da yunwa ba, runtse idanunta tayi wasu zafafan hawaye suka shiga sintiri kan kuncinta. Shiru Daddy ya yi na wasu sakwanni sannan ya ce"yanzu me kike tunani?" ajiyar zuciya Mommy ta sauke ta ce"babu komai kawai dai ina missing ɗin yarinyar ne sosai akwaita da shiga rai, amma dai General tana kammala exams ɗin zata dawo ko?" murmushi ya yi ya ce"in Sha Allah haka nake fata daga nan sai ta shiga University ko anan garinne dan banason ta yi nisa damu" Mommy ta ce"Nima haka nake so wlh barima na kira Imad naji ya ya take" daga haka ta ɗauki wayarta dan kiran Imadudden ɗin. Ringing biyu ya ɗaga cikin sakin fuska ya ce"Mommy Barka da safe kun tashi lpy?" murmushi ta yi ta ce"lafiya klao Imad ya naka iyalin?" ya ce"sunanan klao" Mommy ta ce "Daman kira nayi naji ya Fattomah take kwana biyu kenan banji muryarta ba" Imad ya ce"wallahi tana nan klao Mommy yanzu ma driver ya tafi kai ta makaranta amma tana dawowa zan haɗaku da'ita itama tana ta nemanki" Mommy ta ce"Allah sarki yarinyar kirki kace mata ina matuƙar kewarta yaushe zaka kawomin ita Imad?" murmushi ya yi yana shiga cikin motar tasa ya ce"soon in Sha Allah Mommy", ta ce"Tom Allah ya yarda dear sai anjima" Ameen ya ce sannan ya kashe wayartasa. Kallonta Aysha tayi ganin yanda duk tayi kamar mara lafiya ta ce"Fateemah bakida lafiya ne?" shiri Fattomah ta yi dan ba komai take magantuwa akansa ba duk da tanajin yunwa kamar ta mutu ta ce"kaina ne yake ciwo kawai babu komai amma" cikin rashin jindaɗi Aysha ta ce"wayyo bestie sannu kinji zo mu ci abinci Kinga an fita breakfast sai mu karɓo magani a clinic" girgiza mata kai Fattum ta yi ta ce"ni bana ci na ƙoshi kije ke kaɗai please", wani banzan kallo Aysha ta watsa mata tana harararta ta ce"dallacan taso malama bana son iskanci"shiru Fattomah ta yi mata bata ce komai ba kuma bata da niyyar tashin, bank yanda Aysha bata yi da'ita ba sai haƙura tayi ta ta miƙe afusace ta ce"kije ki ci kanki da masifaffiyar gaddama"tsaki tayi sannan ta yi waje. Sake gyara kwanciyarta tayi tana riƙe cikinta wanda takejin yana barazanar fashewa akowane lokaci saboda matsananciyar yunwa. Murmushi ya yi yana kallon friend ɗin nasa ya ce"yanzu ya muke ciki dakai?", waro idanu Imad ya yi ya ce"nifa banason irin haka Kamal gaskiya ka daina yimin irin haka kai meya hanaka yin auren?" tuntsirewa da dariya Kamal ya yi ya ce"ai aure sai Allah ya yi kuma in sha Allah nakusa dan na haɗu da irin yarinyar da nakeson aura soon zakuji ance ku shirya" gyara zama Imad ya yi yana kallon abokin nasa ya ce"bani nasha friend" murmushi Kamal ya yi ya ce"ai aboki ba'a magana yarinya ce haɗaɗɗiya irin ta gaban motar nan na tabbata kaf TAWAGARMU babu wanda zai auri kamar ta excluding You" harararsa Imad ya yi ya ce"da ka haɗa dani mana ɗan rainin hankali" Kamal ya ce"kai ai nasan kanada mata kuma Salma kyakkyawa ce babu ƙarya amma fa wlh wannan tafi Salma kyau nesa ba kusa ba kawai ka zuba ido ta fashe min Friend zanyi ƴaƴa kyawawa zasu gaji ubansu ƴan ball nakeson su zama" dariya ya yi ya ce"toh Allah ya tabbatar friend kace zamu ƙara yawa time ɗin mu mun barwa yara Ball" ya ce"aikuwa dai gaskiya, yaushe zaka koma ne?" ya ce"kullum abinda ake tambayata kenan ni kaina nagaji da zaman 9ja kuma gashi sai nan da 3months" Kamal ya ce"Ayyah to Allah ya kaimu daman bamu gaji da zama dakai ba idan ka tafi sai anganka" tashi Imadudden ya yi ya ce"zanje na karɓi result ɗin" miƙewa shima ya yi ya ce"muje nima zan duba patient. Kallonta Aysha ta yi ta ce"kinga drivern naki yazo Fattum" gyaɗa mata kai tayi sannan ta saki hannunta ta ƙarasa inda ya yi parking ɗin, buɗe mata motar wani guard ya yi ta shiga sannan shima ya shiga suka bar harabar makarantar, tana shiga ta kwanta nan ƙasan carpet tana riƙe cikinta ta fashe da wani irin kuka, yanda take kukan zaka san a matuƙar wahale take dan ko muryarta ba'aji kuma babu hawaye Da sauri ta ƙaraso tana kallonta ta ce"lafiya Fattomah?" kasa magana ta yi sai miƙa mata hannu da tayi sunkuyawa Salma ta yi ta riƙe hannunta, sosai ta ji jikinta da zafi hakan yasa ta taimaka mata ta zauna kan kujera ta jingina da jikinta "Bakida lafiya Fattum?" Dakyar ta buɗe bakinta tana harhaɗa kalmomin ta ce"aunt.aun.aunty Salma yunwaaaa." ta ƙarashe maganar wasu hawaye na zubuwa kan fuskarta, da mamaki Salma ta ce"yunwa kuma Fattomah?, baki tafi da abinci ba?" gyaɗa mata kai tayi ta miƙe da sauri ta shige kitchen dan samo mata abinda zata ci. Saida tagama jera kayan kan wani ƙaramin Centre table sannan ta ce"taso ki ci" a hankali ta dawo kusada shi ta zauna Salma ta zauna gefenta ta buɗe plate ɗin, chips ne ciki sai wainar kwai wacce taji wadatacciyar albasa da kayan ƙamshi Fattomah da jikinta har wani rawa yake ta saka hannuta dan ko spooon bata nema ba ta fara cin chips ɗin da kwan har wani lumshe ido take saboda tsananin daɗi, mug ɗin tea Salma ta miƙa mata ta karɓa, tunda ta kafashi a bakinta bata ajiye ba saida ta shanye tass sannan ta ajiye mug ɗin tana sakin wata gyatsa ji kake "ƙettttttttttttttttttt😂" Murmushi Salma ta yi tana kallonta tabbas ba ƙaramar yunwa take jiba cikin yan mintunan da basu shige 10 ba ta cinye abincin tasss babu abinda ta rage, saida ta gama sannan ta kalli Salma wacce take kallonta tun ɗazu, rufe fuskarta ta yi tana murmushi ta ce"Aunty Salma ban ƙoshi ba" waro idanu Salma ta yi ta ce"da gaske Fattum?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce"keee Fattum wanne wane irin yunwa kika ji?" turo baki tayi bata ce komai, murmushi Salma ta yi ta ce"yanzu bari na zubo miki abincinki na lunch kinga daman wannan ai breakfast kika yi" gyaɗa mata kai Fattum ta yi tana murmushi. Wani irin gumi ne yake keto masa tundaga kansa har ƙafafunsa ya gagara furta wata kalma ko guda ɗaya, Kamal ne yaja hannunsa ba tare da yace komai ba suka yi waje, office ɗinsa ya mayar dashi yana zuwa ya zaunar dashi kan kujerar dake office ɗin shuru Imad ya yi dan baida abun furtawa shi kaɗai ya dinga sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya sha dambe zagaye parlon Kamal ya hau yi kamar wani wanda ya yiwa sarki ƙarya afili ya shiga furta "inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun" kusan 5mins suna haka sannan Kamal ya dawo ya zauna yana kallon abokin nasa cikeda tausayawa ya ce"dan Allah karka saka wannan abun aranka friend wlh babu abinda yafi ƙarfin Allah in Sha Allah kanada rabon haihuwar ƴaƴa bila adadin, wannan ba wani abun bane" murmushi Imad ya yi wanda ya kasance na takaicine yana kallonsa ya ce"idan haka Allah ya tsara min babu yanda na iya da ƙaddara kuma kaima shaida ne tun inada 20yrs aka faɗi wannan maganar amma gashi har yau bata sake zani ba kuma gashi nan har yau Daddy bai sake haihuwa ba ni ɗaya da aka faɗa masa ni ne kawai ɗan da ya haifa, wlh Kamal yana ɗaya daga dalilin daya sanya mata basa gabana Saboda babu wacce zata jure zama dakai da irin wannan lalurar hatta Salma tausayi take bani tanada matuƙar ɗauke kai kuma ta nunamin ƙauna tsawon lokacin da muka ɗauka tare saboda haka kawai zan rabu da'ita taje tayi aurenta ko tanada rabon samun ɗa ita a duniya" girgiza masa kai Kamal ya yi ya ce"wannan fa wani abu ne daban dan ance daga ɗa ɗaya bazaka sake haihuwa ba saboda bakada wadataccen sperm sai kaga Allah ya yi ikonsa akanka ka haifi ƴaƴa masu tarin yawa sannan tunda har ta iya hakuri wannan lokaci zata iya zama dakai koda da ɗa ɗayan ne ai ba duka bane ba zaka haihu ba, yanzu shi Daddy daya haifi iya kai kaɗai ya kasa rayuwa?, ko akwai abinda ya rasa arayuwartasa?, Please Friend karka saka wannan aranka kaje kuma wani ciwon na daban ya sameka kayi haƙuri watarana sai labari in Sha Allah sai kaga ƴaƴanka da jikokinka" murmushi kawai Imad ya yi ya ce"toh Allah yasa thank you friend" dafa kafaɗarsa ya yi ya ce"karka damu dear". Tana gama sanya kayanta ta zauna gefen gadon tana tunane-tunane, miƙewa tayi da sauri ta buɗe drawer, wayarta ta ɗauko ciki ta dawo ta zauna, data ta kunna tana shiga Whatsapp taga anyi mata magana da baƙuwar lamba amsa sallamar ta yi sannan ta cigaba da hira da ƙawayenta a group ɗin makaranta, murmushi ta yi bayan ganin reply ɗin da akayi dan ta ganeshi saboda pic ɗinsa ne kan dp nashi murmushi ta yi tana kallon abinda ya rubuta kamar haka "Hyyy Fattomah ya gida ya Mommy yaushe zan zo na gaisheta?" Dariya ta yi sannan ta mayar masa reply da imoji na mamaki, murmushi Kamal ya yi ya ce "Please beauty wlh so nake na ganki ya za'ayi?" Rasa abinda zata bashi amsa ta yi hakan yasa ta kashe datar tata ta kwanta tana kallon sama, sosai maganganun su Khaltum suka dinga dawowa fresh cikin kwakwalwarta tsaki ta yi ita kaɗai ta ce "Haukama kenan" Tana wannan tunane-tunane bacci ya yi awon gaba da'ita. *Ameenatou ce#* *Nanameera ce#* *Like nd share* [5/13, 9:35 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION. *Ameena I Ibrahim* Nanameera PAGE 27-28. Kallonsa Salma ta yi ganin kamar yana cikin damuwa amma batada ikon yi masa magana dan basu saba haka dashi ba, zama Imad ya yi kan ɗaya daga cikin royal cusion ɗin dake zagaye da parlon kusan 3mins sannan ya kalleta asanyaye ya ce "Salma!" Juyowa ta yi dan tabbatar da ita ce wacce yake kiran amma sai taga yana kallon wani abu daban, ahankali ta ƙaraso wajen ta zauna kujerar dake facing ɗinsa ta ce"gani" numfasawa ya yi sannan ya ce"please ki dafamana abinci banason na maids ɗin nan yau" Okay Salma ta ce sannan ta miƙe dan shiga kitchen zuciyarta fal farin ciki, cikin mintuna ƙalilan tagama dafa abincin banda ƙamshi babu abinda ke tashi dan Masha Allah Salma ta iya girki babu ƙarya musamman yanzu daya kasance Imad ne yakeson ya ci abincin nata hakan yasa ta ƙara baje basirarta. Tana kammala ta jera komai kan dinning table sannan ta haye sama dan shiryawa dan ta tabbatar yau zata kwana ɗakin mijinta, da mamaki Salma ta tsaya ganinsa tsaye jikin mirror ɗin ɗakin daga gani kasan wanka ya fito dan har sannan jikinsa na ɗigar ruwa shagala Salma ta yi da kallon mijin nata dan ganinsa take kamar wani sabon halitta tabbas Imadudden asalin kyakkyawane irin first class ɗin yanada wani irin hallitar jiki wanda ba kowa Allah ke horewa irinta ba sai kaɗan daga cikin mutane kallon gashin kansa ta yi ta ganshi luf ya kwanta gadon bayansa kamar na mace itama mai gashi sosai a Hausawa sai sheƙi kan nasa yake dukda ruwan dake jikinsa, kallon suffar jikinsa tayi wacce saida ta tsorata dan bata taɓa lura haka yake ba dukda wasu lokutan tana ganinsa babu kaya amma ba kamar yanzu ba da ya kasance bathrobe ce kawai jikinsa duk ƙirjinsa a buɗe yake wanda ya sha tatu wanda aka rubuta Imadudden amma sai ka ƙura idanu sosai sannan zaka gane sunan mutum aka rubuta tabbas da ace Imad ɗan dambene to fa babu wanda ya'isa ya kada shi dan kana ganinsa kaga asalin namiji mai ji da mazantaka "Salmehhhhhhh" Da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta saboda kunya dan har ga Allah batasan sanda ya zo gabanta ba, ganin taƙi ɗagowa yasa shi ya tallafi fuskarta da hannayensa masu matuƙar laushi cikin yanayi na gajiya ya ce"mene?" a hankali ta girgiza masa kai ta ce"babu komai kayi haƙuri" harararta ya yi ya ce"da aka yi me?" murmushi ta sakar masa shima ya tsinci kansa da mayar mata da murmushi ya ce"je kiyi wankan sallah I'm coming" toh ta ce masa sannan ta shige toilet ɗin tana sake waiwayonsa. Kai tsaye master bedroom ɗinsa ya nufa yana zuwa ya buɗe wata drawer bayan ya saka pin wani ɗan sachet na magani ne ya fito dashi, zama ya yi gefen gadon shi kaɗai ya dinga juya maganin kusan 3mins kafin ya mike ya isa wajen da freezer ɗin ɗakin take buɗewa ya yi ya ɗauko ruwa ya ɓalli maganin guda ɗaya ya saka abaki sannan ya kora da ruwan. Da sauri ta farka tana kallon agogon wayarta mamaki tayi ganin yanda tayi bacci har haka batareda ta sani ba, tsaki ta yi sannan ta miƙe tana murza idanunta ta shige toilet ɗin, tana idar da sallah ta fito dan yunwa take ji kitchen ɗinta ta shiga ta duba store ɗin ciki tsaki ta yi ganin babu komai ciki sai indomie da kwai wato kallon Baby ma suke mata??, turo bakinta ta yi sannan ta kunna gas ɗin ta ɗora ruwan dafa indomie ɗin. Tsaye ya tarar da'ita tana shafa mai ajikinta ba tare da tasan ya shigo ba ya ƙarasa gabanta yana kallonta from head to toe, juyowa ta yi da niyyar ɗaukan rigarta idanunta ya sauka cikin nasa da sauri ta juya masa baya tana murmushi dariya shima ya yi sannan ya dafa kafaɗarta ya juyo da'ita gabansa, ahankali kamar wanda ake forcing nasa haka ya dinga shafa jikinta kamar kwai ya fashe masa ajiki, ji tayi wani abu na tsirga mata tundaga kanta har ƙafarta da sauri ta riƙe hannayensa bakinta sai rawa yake amma ta gagara furta wani abu dan daman Indai Imad ne tofah ba daga nan ba yasan takan biyar da mace yanda ya kamata ganin tana ƙoƙarin kaiwa ƙasa yasa ya jata ahankali suka kwanta kan gadon yana cigaba da abinda yake, ahankali cikin salo ya fara zare towel ɗin jikinta ta lumshe idanunta dan ko kaɗan batayi ƙoƙarin hanasa ba dan itama a matuƙar buƙace take. Sai kusan 12pm sannan suka dawo hayyacinsu musamman Salma wacce takejin so da ƙaunar mijin nata na nunkuwa cikin zuciyarta Imad ya iya soyayya kawai baya nunawa ne ko kuma akwai abinda yake nufi, saida sukayi wanka sannan ta kalleshi murya can ƙasa ta ce" abincin fa?" kallonta ya yi da idanunsa wanda har sannan basu gama dawowa daidai ba ya ce" I'm full" shuru Salma ta yi dan bazata iya musu dashi ba ta koma ta kwanta, addu'a ya yi mata sannan shima ya kwanta nan da nan bacci ya ɗaukesu. Kusan 2weeks kenan da dawowar Fattomah gidan Imad wanda ko kaɗan batajin dadin zaman gidan muradin zuciyarta shine lokacin makaranta ya yi ta tafi dan anan ne kawai take samun hutu amma da zarar lokacin tashi ya yi tofah idan hankalin Fattomah ya yi dubu toya tashi tana samun sauƙine idan ya kasance Jawaad ya zo gidan sau tari tana yin kuka akan zata bisa amma koda wasa Imad bai basu wannan damar ba baya taɓa barinta ko gidan taje dan kwata-kwata ma idan ba school bata fita ko'ina kullum tana zaune cikin gidan, yau ya kasance Friday yasa suna tsaye da Aysha bayan an tashi daga makaranta, har ya yi gaba sai kuma yaga kamar Fattomah hakan yasa ya dawo baya dan tabbatar da ita ɗin ya gani. Fitowa ya yi daga motar tasa yana sanye cikin ƙananun kaya wanda suka amshi jikinsa ba karya ya yi kyau fuskarsa asake kamar koda yaushe ya ce"Fattomah!" kallonsa ta yi da mamaki sai kuma ta ce"kai ne??" gyaɗa mata kai ya yi ta ce"me kake yi anan kuma?"murmushi ya yi ya ce"zan wuce sai naga wata kamar ke shine na dawo ashe kuwa kece" dariya ta yi ta ce"naji toh shige ka tafi" yanda ta yi maganar serious yasa ya tuntsire da dariya saida ya yi mai isarsa sannan ya ce"toh Hajiya Fattomah" kwaɓe fuskarta ta yi ya ce"shikenan zamuyi magana a waya ko?" gyaɗa masa kai ta yi ya ɗaga mata hannu itama ta mayar masa sannan ya shige motarsa yabar wajen, da kallo tabi bayan motar. Aysha ce ta taɓota ahankali ta ce "Kee Fateemah ga Uncle dinkin can fa tunɗazu ya zo yana kallonmu" da sauri Fattomah ta juyo tana kallon inda take nuna matan, wani irin faɗuwa gabanta ya yi dan duk a zatonta yaya Jawaad ne ya zo ɗaukan nata, da sauri ta riƙe hannun Aysha ta ce"yaushe yazo?" ta ce"sanda kuke magana da wannan mutumin" shuru Fattomah ta yi na wasu sakwanni sannan ta ce"shikenan bye sai Monday" ok Aysha ta ce sannan tabar wajen. Kamar wacce akayi forcing nata haka Fattomah ke tafiya tana haɗa hanya har ta ƙaraso inda ya yi parking ɗin, buɗe motar ta yi ta shiga batace komai ba drivern yaja suka bar wajen, tunda taga irin kallon da ya yi mata ta sunkuyar da kanta har suka je gida bata ɗago ba. Drivern na gama parking ya sakko daga motar without looking at her ya kama hannunta ya jata har cikin gidan yana zuwa parlon ya watsar da'ita yana mata wani mugun kallo ya ce cikin ɗaga murya "Da ubanwa kike tsaye?" Girgiza masa kai Fattum ta yi dan batasan amsar da zata bashi ba, wata uwar tsawa ya daka mata wacce tunda uwarta ta haifeta ba'a taba yi mata irin ta ba, jikinta ne ya fara rawa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, kallon rainin hankali Imad ya yi mata sannan ya fincikota ta miƙe tsaya haɗe hannayenta biyu ya yi a hannunsa ya wanketa da wasu maruwa ji kake "Tassssssssss" Tsabar yanda ta ji marin kusan shiɗewa tayi lokaci ɗaya gefen bakin ya fara fitarda jini, yana mata wani shegen kallo ya ce"zaki faɗa mini ko kuma sai na kakkaryaki anan wajen?" ƙoƙarin magana take amma ta gagara yi sai ajiyar zuciya da take saukewa dan ko kukanma batada zarafin yinsa. Ganin batada niyyar magana yasa ya ɗorata kafaɗarsa ya haye sama da'ita, cikin bedroom ɗinta ya direta yana mata wani kallo ya ce"yau zaki gane bakida wayo wallahi sai nayi maganinki nan gaba koda sunana kika ji an ambata zaki shiga taitayinki" yana gama faɗin hakan ya juya ya fita ta kwanta nan wajen tana wani irin kuka mai ban tausayi kusan 2mins sai gashi ya dawo hannunsa riƙeda wata irin bulala irinta dukan dokin nan, bai tsaya sake faɗar wata magana ba ya Fara sauke mata ita a gadon bayanta, tun tana ƙoƙarin karewa har saida ta gagara yin hakan saida dan kansa ya gaji sannan ya rabu da'ita ya ajiye bulalar yana kallonta cikin ɗaga murya ya ce"daga yau na sake ganin kin fita daga cikin gidan nan bare har kiji zaki iya tsayawa da wani" wayarta ya ɗauke kan drawer ya ce "Wallahi daga nan har sanda zaki bar gidan nan babu ke babu ita ni bazaki raina min hankali na gyaleki ba shashasha kawai" yana gama faɗin hakan ya juya ya yi fitar yana huci kamar wani zaki. Allah Sarki Fattum kasa koda motsi tayi daga inda take tunda tazo duniya babu wanda ya taɓa yi masa koda kasan abinda Imad ya yi mata ayau ba duk ya fasa mata jiki da duka ko'ina ta shafa jikinta sai taga jini na biyo wajen tasan ko kaɗan baya ƙaunarta amma bata taɓa tunanin har dukanta zai iya ba gashi ya kwace mata waya, wannan takaicin ya sanya ta sake fashewa da kuka tana kwanciya kan carpet ɗin dake wajen. Murmushi Ameesha ta yi tana kallon Salma ta ce"Allah ya yi zamu haɗu yasa ban tafi ba yanzu nake shirin tafiya" Salma ta ce"dan Allah fa?, toh ya kike kwana ɗagawa kin ɓuya" dariya Ameesha ta yi ta ce"wallahi lafiya lao kema ai kin ɓuya ni kinga ina yawan zuna gidan nan" Salma ta ce"ina Ayrah?" "Ta shiga kitchen yanzu zaki ganta"okay Salma ta ce sannan suka ci-gaba da hirarsu. Ganin har sannan ransa a ɓace yasa Jawaad ya ce"dan Allah kayi haƙuri Imad kasan yarinya ce ƙarama komai ma zata iya aikatawa amma bai dace ace kana fushi da'ita irin haka ba dan Allah ka dinga sassauta zuciyarka kaji" tsaki ya yi ya ce"saboda ba kaine wanda kake zaune da'ita ba shiyasa kake faɗin haka akanme Daddy zai haɗani da wannan kucakar yarinya wacce batasan kanta ba wlh ji nake inama na fita da'ita can daji na yarda ita ko nma samu na huta duk tabi ta isheni" dafa shi Kamal ya yi ya ce"calm down please komai zai shige abinda ba zama ne na har ƙarshen rayuwa ba, kayi haƙuri da wautarta please" shiru Imad ya yi bai ce masu komai ba amma shi kaɗai yasan abinda yake ji cikin zuciyarsa gamewa wannan yarinyar. Ayrah ta ce"wallahi fa ni shiyasa nafison na dafa abinci da kaina bana wani tolerating ƴan aiki" murmushi Salma ta yi ta ce"nima abun yana burgeni amma kullum maids sune ke yi maka aiki cikin gida ai babu daɗi, ni Kinsan mene ne yake damuna?" girgiza mata kai Ayrah ta yi ta ce"sai kin faɗa" numfasawa Salma ta yi ta ce "Wallahi abinda Imad yake yiwa Fattum baya dacewa kwata-kwata bana jindaɗi bakiga yau irin dukan da yayi mata ba wlh gwara ya mayar da'ita wajensu Daddy da wannan zaman doya da manja kwata-kwata baya sonta ya tsaneta bakiga yanda ta dawo ba sai ta baki tausayi wlh ina matuƙar tausayinta" Tunda ta fara maganar suke kallonta baki buɗe har ta yi shiru sannan Ayrah ta ce"Allah ya kara daidai kenan maganin mai son auran mazajen wasu" da rashin fahimta Salma ta ce"mazajen wasu kuma?" Ameesha ta ce"kin bani haushi wallahi ke saboda mijinki na faɗa da kishiyarki shine Abinda zai dameki har ki dinga jin haushinsa tab" da mamaki Salma ta ce"bangane kishiya ba wace kishiyar?, Fattomah fa nace muku" dariya Ayrah ta yi ta ce"ashe baki nan baki san Abinda ya faru ba bakisan da kishiyarki kike zaune ba" labari Ayrah ta bata na abinda ya faru gidan Daddy tundaga farko har ƙarshe, miƙewa Salma ta yi tana huci ta ce"wai kina nufin Fattomah matar Imad ce yanzu?" miƙewa itama ta yi ta ce"Eh wlh matarsa ce ta sunna ma kuma" cize laɓɓe tayi ta ce"aikuwa saina nuna mata kuskurenta na bari ta auri mijina domin har abada Imam na wane ni kaɗai wlh, i must teach her a lesson" tana gama faɗin haka ta juya ta fita ko gyale bata samu zarafin yafawa ba. *Ameenatou ce#* *Nanameera ce#* *Like nd share* [5/16, 9:55 PM] Nanameera: *FATTOMAH* *MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* *Ameenatou I Ibrahim* Nanameera PAGE 29-30. *I dedicated this page to yhu mabiyan FATTOMAH, Imad yana kallonku kuma duk yaji abinda kuka tattauna tawagar Nanameera's Library 😂ya ce a sanar daku yana nan babu gudu babu ja da baya he most teach her a lesson kuma babu yanda kuka iya 💪idan kunji haushi to kuce Daddy ya ɗauki abarsa mudai muna bayan Imadudden 🌝aikin hajjin bana damu team IMADUDDEN 😂😂much luv FATTOMAH na godiya wasu tashi sallar dare tana godiya da abin arziƙi 🙏* Dakyar take tafiyar saboda wani irin ciwo da jikinta yake mata tunda take babu wanda ya taɓa yi mata irin wannan dukan da Imad ya yi mata jikinta duk ciwo yake, ahankali ta zauna gefen gadon nata tana duƙunƙune jikinta saboda wani irin sanyi da yake ratsata kamar mai jin zazzaɓi cikin mintuna kaɗan jikinta ya ɗauki wani zafi sai shivering take sosai zata baka tausayi saboda yanda ta koma gashi babu magani kusa kuma batasan wanda zata sanarwa ba babu waya a hannunta bare ta kira yaya Jawaad inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun wannan wace irin rayuwace ta tsinci kanta wasu zafafan hawayene suka shiga rige-rigen sauka kan kuncinta. Jiki asanyaye ta miƙe kamar zata haɗi ta fara tafiya azaba sosai take ji da tafiyar amma batada wani zaɓi wanda ya shige ta nemi magani domin batajin zata iya kaiwa gobe idan har tana cikin wannan yanayin, Kalle-Kalle ta shiga yi aparlon ganin kamar babu kowa ƙofar bedroom ɗin ta kalla taji sanyi aranta, without knocking ta shiga ɗakin tana rarraba idanu Salma ce zaune gefen gadon ta zuba wani uban tagumi kana ganinta kasan tabbas wani abun yana damunta ahankali Fattomah ta ƙarasa gabanta dan Salma batasan ta shigo ba tana can tunani "Aunty Salma!" Sai a sannan ta ɗago tana yi mata wani irin kallo cikeda tsana ta ce"lafiya?" tuni ruwa ya kawo idanun Fattomah ta ce"wallahi Aunty kullum jikina ciwo yake bana iya bacci dan Allah ki bani magani ko ki kaini asibiti kinji" afusace Salma ta miƙe tana riƙe da ƙugunta cikin wani irin ɓacin rai ta ce"uban asibiti zan kai ki ba asibiti ba keeee harni zaki rainawa hankali?, wallahi duk ranar dana sake ganin ƙafafuwanki cikin apartment ɗina wlh sai kin gwammace baki zo duniyar ba sannan ni ba abokiyar wasanki bace ke ko fuskarki banason na sake gani acikin gidan nan duk sanda muka haɗu to wlh sai ranki ya yi mugun ɓaci shashasha ƴar matsiyata kawai" Tsabar shock Fattomah kasa magana tayi zazzaɓin jikinta na dawowa sabo kuma mai zafi fiye da na da, bakinta na rawa amma ta kasa furta koda kalma ɗaya infact ma batasan abinda zata ce ba "Dallacan fita awajen nan!!" Agigice Fattomah tayi waje har tana neman haɗuwa, tsaki Salma ta yi ta ce"gayyar tsiya wlh sai zaman gidan nan ya gagareki zaki san kin haɗa hanya dani" Wani irin raunataccen kuka ta fashe dashi tana sake ƙanƙame pilon dake hannunta wace irin ƙaddarace wannan ke bibiyar rayuwarta?, meyasa Abba ya mutu ya barta, meyasa Ammi ta koma garinsu without second thought na makomarta?, meyasa Daddy yabar garin nan ba tare da ita ba?, meyasa ba'a ce ta zauna gidan yaya Jawaad ba sai gidan Imad?, waɗannan sune tambayoyin wanda ta gagara samun mai amsa mata tabbas akwai ƙalubale sosai a rayuwarta kamar yanda Abbanta ya faɗa mata cikin mafarki batasan laifin da ta yiwa Salma ba amma tana jin idan babu ita bazata iya cigaba da zama cikin gidan ba domin watarana zuciyarta sai ta fashe saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali tuna irin waɗannan abubuwan yasa ta sake rushewa da kuka iya ƙarfinta amma babu wanda yake sauraronta har bacci ya saceta. Wani kallo ya yiwa Jawaad sannan ya ce"banfa gane abinda kake nufi ba" murmushi Jawaad ya yi ya ce"zama ka fahimta ne Footballer tunda kana abinda kaga dama yanzu zuwa yaushe zaka tafi??" Imad ya ce"Ehh tohhh nan da one week in sha Allah" okay Jawaad ya ce, miƙewa ya yi ya ce"ni fa zan tafi coz inada meeting around 3pm zuwa 5pm zamu fito sai mu ƙarasa maganar ko kazo gida da daddare" okay ya ce masa sannan sukayi sallama ya fita.. Tsaki Aysha ta yi ta ce"kawai muje gidanmu kiyi zamanki wallahi tunda babu kowa gidan kuma kina jin tsoro" girgiza kai Fattum ta yi ta ce"A'a Aysha idan Uncle ya tarar bana gida dukana zai yi kawai zan tafi saina zauna wajen gatekeeper har su dawo kinga daman gobe bamuda paper sai next week" haɗe rai ta yi ta ce"ke wllh kin fiye tsoro ai shikenan kuma ke ba waya ba bare muyi magana ta chat" murmushi kawai Fattomah ta yi bata ce komai ba, can kuma ta ce"ina wayarki please?" "Me zaki yi da'ita?" tsaki ta yi ta ce"please ki bani da sauri zanyi amfani da'ita ne" miƙa mata tayi ta ce"hope akwai card?" gyaɗa mata kai ta yi sannan ta ci-gaba da kallonta. Ringing biyu ta ɗaga wayar ta sanya akunnenta daga ɗaya ɓangaren akayi sallama ji tayi kamar duk wata damuwarta ta gushe hawaye na taruwa akurmin idanunta ta ce asanyaye "Ammina!" Wani irin yanayi ta jita ciki itama hawaye na cikowa idanunta ta ce"Fattum kina nan klao?" girgiza kanta ta yi amma ta ce"ina lafiya Ammi, kin tafi kin barni ko Ammi?" ajiyar zuciya Ammi ta sauke sannan ta ce"ban barki ba Fattum babu yanda zanyi ne shiyasa na barki karki damu nasan zaki zo ko kuma ni nazo inda kike Faɗemah" kuka Fattum ta saka tana jin wata sabuwar kaunar mahaifiyarta na shiga jikinta tabbas baka gane amfanin abu sai sanda ya yi nesa dakai ayau ji take inama Amminta na gefenta da bata dinga yi mata rashin jin magana ba, da ta zaunar da'ita tana yi mata hira mai daɗi har bacci ya ɗauketa. Jin tayi shuru yasa Ammi ta ce"Kina kan layi Fattomah?" gyaɗa mata kai tayi kamar tana gabanta ta ce"Eh Ammi yaushe zaki zo?" murmushi Ammi ta yi ta ce"in Sha Allah zan zo nan bada daɗewa ba, kina karatu dai?" ta ce"Eh Ammi ina yi yanzuma exams muke ta Waec mun kusa gamawa" Ammi ta ce"toh Masha Allah, Allah ya taimaka ya bada sa'a Faɗeemah ki cigaba da haƙuri" Ameen ta ce jiki asanyaye sannan sukai sallama, ajiyar wayar tayi kawai ta kifa kanta ta fashe da kuka sosai taka kewar iyayennata, dafata Aysha ta yi ta ce"kiyi haƙuri kinji Fateema dan Allah ki daina wannan kukan duk kin rame kinyi baƙi fa" dakyar Fattomah ta yi shiru sannan ta tashi tana kallon Aysha ta ce"zan tafi ni dai" "ke kaɗai zaki zauna?" gyaɗa mata kai ta yi dan bata yanayin da zata iya doguwar magana gaba tayi kaiwa Aysha ta bita da kallo cikeda tausayawa koda Fattomah bata faɗa mata halinda take ciki ba tasan tabbas akwai abinda yake damunta domin yanda duk ta fice hayyacinta cikin ƴan sattitika ƙalilan. Da mamaki Fattomah ke kallon motar tasa dan tama gagara ƙarasawa kar taje ba ita yazo ɗauka ba, tsaki Imad ya yi ganin ta tsaya tana kallonsa fitowa ya yi daga motar yana sanye cikin wata jallabiya blue colour ya tufke gashinsa ya zubo har gadon bayansa dukda yanda ransa yake a haɗa hakan bai hana ainihin kyansa fitowa ba kana ganinsa kasan yesssss akwai kyau babu ƙarya. Da kallo ɗaliban makarantar suka bishi ganin mutum mai kamada Larabawa yana tafiya toward direction na makarantar, duk yanda zuciyarta ke lugude haka ta danne ta cigaba da kallonsa har ya ƙaraso, wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce"kin bar kallona ko saina tsiyaye idon" sauke idanunta ƙasa tayi bata ce komai ba ya juya ya koma motar itama tana biye dashi. Kwafa Salma ta yi sannan tabar wajen tana jin baƙin ciki kamar ya kasheta wato daman son yarinyar yake shine dalilin daya sanya yake raina mata hankali kuma baya bata lokacinsa ko kaɗan, suna shigowa parlon ta yi sauri ta haye sama gudun kada ya yi mata magana ko kuma ya yi mata tsawa, da kallo ya bita sannan ya taɓe baki ya zauna kan kujerar yana kallon tv inda al-jazeera ke haska labarai. Tana fitowa daga wanka ta shige kitchen ɗinta, tsaki ta saka tunawa da tayi babu komai cikin kitchen ɗin sai indomie kuma ta gaji da cinta, juyowa ta yi zata fito suka yi karo da sauri ta koma baya tana ɗan yarfe hannu haɗe rai ya yi ba tare da ya yi magana ba ya miƙa mata wayar hannunsa karɓa ta yi tana sanya kunnenta tana ɗan satar kallonsa juyawa Imad ya yi yabar ɗakin tana murmushi ta ce "Mommy nayi missing naki sosai inason na ganku please" Murmushin itama ta yi ta ce"Fattomah rigima ki bari da zarar kin ƙarasa exams Imad zai dawo dake shikenan mu cigaba da rayuwarmu kamar da" sosai Fattum ta ji daɗin haka ta ce"toh Mommy daman mun kusa gamawa ai"okay ta ce sannan suka ci-gaba da hirarsu cikeda so da ƙauna kai ka ɗauka da gaske ita ce wacce ta haifeta. Wani irin sanyi taji ya daki hancinta ta lumshe idanunta dan daman tana matuƙar ƙaunar yanayi irin wannan shiru parlon yake babu alamar mutum ciki hakan yasa kai tsaye ta shige bedroom ɗin mamaki ta yi ganin yanda ɗakin yake da wani irin kyau kaf ɗakunan gidan ba taga wanda ya kai shi kyau da kuma tsaruwa ba, tsayawa ta yi tana kallonshi ganin yanda yake bacci hankalinsa ya kwance ya duƙunƙune cikin lallausan duvet ɗin harararsa ta yi ta ce can ƙasa"mugu shi gashi ya zo yana ta baccinsa ni kuwa kullum bayana ya yi ta yimin ciwo" tsaki ta yi sannan ta ajiye masa wayar gefen bedside drawer juyawa ta yi zata fita sai kuma ta dawo ta ce"nima bari na ɗan kwanta na huta anan kafin ya tashi"tana gama faɗin hakan ta haye kan gadon ahankali kamar wata ɓarauniya haka har ta samu ta kwanta daga can gefe guda ta ja bargon ta rufa wata irin ni'ima taji tana saukar mata ta lumshe idanunta nan da nan bacci mai daɗi ya ɗauketa. Wani irin azababben ciwo taji mararta na yi mata tun tana dauriya har ta miƙe daga kwancen duk ta haɗa gumi kamar wata wace take naƙudar haihuwa kuka ne ya kwace mata dan tasan irin azabar da zata sha nan gaba dan ita duk sanda zata yi period tofah sai duniya ta sani dukda Allah ya taimaka mata tana kaiwa wajen 4 to 5months bata yiba amma duk randa yazo mata tofah sai tasha baƙar wahala arayuwarta sau biyu ta taɓa yi sai kuma wannan karo na uku, ahankali ya buɗe idanunsa jin kamar sautin kuka ware idanunsa ya yi tass akanta ya miƙe yana kallonta da mugun mamaki amma ya kasa magana ganin yanda jikinta ke rawa sai zufa take yasa ya ƙara sa wajenta yana zuwa ya kalleta da sauri ta riƙe masa hannu bakinta na rawa tama kasa faɗa masa abinda take so ya sani ɗin, hannunsa ya ɗora kan goshinta yaji babu zafi kwata-kwata mamaki ya yi dan ya ɗauka zazzaɓin dare take, ahankali ya ce "What wrong?" Hannunsa ta kama ta ɗora daidai saitin mararta dan batajin zata iya yi masa bayani, kallon wajen ya yi sai kuma ya yi tsaki ya ce"toh ubanme zan miki nd me kika shigo yi ɗakin nan?" kuka kawai Fattomah ta sanya tana riƙe da hannunsa dan gani take kamar idan ta saki zata mutu ne, sauka ya yi daga kan gadon ya fita a ɗakin, bai wani daɗe ba ya dawo hannunsa riƙe da injection sai drip. Tana nan zaune inda ya barta ya gama haɗa allurar ya yima amma hankalinta baya wajen, yana sanya mata drip ɗin ya fice daga ɗakin ya koma parlon ya yi kwanciyarsa dan wani irin mugun bacci yake ji. Kiraye-Kirayen sallar asubar da aka fara shine ya farkar dashi da sauri ya miƙe ya shige toilet dan ɗauro alwala dan ko sallar dare bai samu damar yiba, yana fitowa ya tarar da ita zaune kan gadon sai nuƙurƙusu take kamar wacce zata haihu, tsaki ya yi sannan ya ƙara so gabanta yana kallonta ya ce"keeeee" dakyar ta ɗago ta kalleshi idanunta duk sun sauya kala sun kumbura, taɓa jikinta ya yi yaji zafi zau saɓanin ɗazu, ganin kamar tana neman sumewa azaune ya sanya ya ɗaukota tamkar Baby ya sakko da'ita yana fita ya sanya driver ya taso ya shiga mota shikuma ya shiga baya yana riƙe da'ita ajikinsa. *Ameenatou ce#* *Nanameera ce#* *Like nd share*[5/17, 9:24 PM] Nanameera: *FATTOMAH* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION. *Ameenatou I Ibrahim* Nanameera PAGE 31-35. Tsaki Imad ya yi ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita duk tabi ta dagula masa lissafi ranshi a ɓace ya ce"wai ba zaki yiwa mutane shuru ba?" ko kallonsa Fattomah batayi ba bare ya yi tunanin amsa ta ci-gaba da kukanta tana yarfe hannu, sai kusan ƙarfe 7am sannan ta samu ta yi bacci shi kuma ya fito dan komawa gida dan sai a asibitin ya yi sallah asuba. Tunda ya shiga parlon take kallonsa amma ta kasa yi masa magana har ya shige rai ɓace Salma ta miƙe daga kan kujerar wato saboda rainin hankali har wani fita suke abarta cikin gidan saboda batada amfani, goge hawayen dake ƙoƙarin zubo mata tayi sannan ta shige bedroom ɗinta tayi kwanciyarta zuciya babu daɗi. Ƙarfe 12pm ya shiga asibitin yana sanye cikin wani yadi black colour ɗinkin babbar riga da jamfa sosai ya yi kyau abinsa ya sanya face mask a fuskarsa gudun kada attention ɗin mutane ya zo kansa yana shiga ɗakin ya tarar tana zaune sai wata nurse dake ƙoƙarin cire mata drip ahankali ya yi sallama wacce idan ba kasa kunne ka yiba bazaka ji abinda ya ce ba, tsayawa ya yi yana kallonta har ta ƙarasa cire mata sannan ta juya ta fita, sunkuyar da kai Fattum ta yi ya zauna kan kujerar dake gefen gadon ya ce"ya jikin naki?" ahankali ta ce"da sauƙi"miƙewa ya yi ya fita ta bisa da kallo. Murmushi Doctor ya yi ya ce"sir hakan dana faɗa shine solution kuma kai ma kasan haka tunda kasan field ɗin" ajiyar zuciya Imad ya sauke yana jin abun kamar ba mai yiwuwa ba lura da hakan yasa doctorn ya ce"sir kadai duba maganar coz haka ne kawai mafita wallahi komai na iya ka sancewa da rayuwarta kuma kullum ahaka zata kasance cikin ciwo tunda dai akwai halin taimakawa please ka taimaki rayuwarta kayi trying ko sau ɗaya ne" miƙewa Imad ya yi ya ce"zanyi tunani akai" okay Doctorn ya ce sannan ya juya ya fita. Yanda ya barta haka ya tarar da'ita har sannan bata kwanta ba amma wannan karan ta haɗa uban gumi jikinta sai rawa yake ƙara sawa gabanta ya yi ya kama hannunta ya ce"keeee" kasa kallonsa ta yi tana kuka ahankali sosai yaji jikinta da zafi ta ɗora kanta kan cinyarsa koda wasa bai yi yunƙurin hanata ba yana jin yanda take fitarda zazzafan numfashi kan cinyarsa, kusan 5mins sannan ta fara sauke numfashi ahankali ya shafa kanta tana sauke ajiyar zuciya sallama Jawaad ya yi ya shigo aɗan rikice ya ce"ya jikin nata?" Imad ya ce" da sauƙi Alhamdulillah" kallonta Jawaad ya yi ya ce"sannu dear" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"yaushe za'a yi discharging naku?" Imad ya ce"har anyi gida zamu tafi yanzu"okay Jawaad ya ce sannan ya kalli Fattum wacce duk ta fice hayyacinta ya ce"tashi mu tafi gida" miƙewa Imad ya yi ya kama hannunta ta miƙe jikinta na rawa ta ce asanyaye"bazan iya tafiya ba ni"kallonta Imad ya yi kamar ya ce wani abu sai kuma ya yi shiru ya ɗauke ta kamar Baby suka fita daga ward ɗin. Waro ido Salma ta yi hankali atashe ta ce"kamarya Ameesha?" murmushi Ameesha ta yi ta ce"naga kin wani firgita ko daman baki shirya ba?" girgiza kai Salma ta yi ta ce"bawai haka bane Ameesha kawai banason zuwa wajen wani malami ne shiyasa kawai gwara Imad ya sakeni na kama gabana ni bazan iya kunsar baƙin ciki ba wlh" tsaki Ameesha ta yi ta ce"aikin banza ashema ke ƙaramar ƴar iska ce kenan kin haƙura da duk tarin dukiyarsa wacce zaki mallaka idan yana ƙarƙashin ikon ki har kike tunanin fita daga cikin gidansa" Salma ta ce cikeda damuwa"wai to Ameesha mene ne abinda zan yi kusan 5yrs muke tare dashi kuma Alhamdulillah na samu abinda na samu wajensa dan Imad bashida rowa ko kaɗan ni gaskiya bazan taɓa iya cutarda shiba lemme tell you" dariya Ameesha ta yi ta ce"da ni nace miki ki cutar dashi ne?, ko kuwa kina ganin zaki iya cutar dashi ɗin ne?, ai daman ba shine target ɗinmu ba ya kamata ace kina saurin fahimta Salma" da mamaki Salma ta ce"bangane abinda kike nufi ba, waye target ɗin toh?" murmushi kawai ta yi sannan ta ce"yarinyar dake gidan nan Fattomah da'ita zamu yi amfani wajen aiwatar da abinda muka yi niyya batareda kowa ya zarge muba idan har zaki iya yin abu yanda na tsara wlh zamu samu nasara kawai ki cire tsoro malama" numfasawa Salma ta yi ta ce"zanyi tunani akai Ameesha dan bazanyi abinda zai dawo kai na ba wlh nasan halin Imadudden bashida mutunci idan yaso kome zai iya aikatawa saboda haka bazanyi Abinda zan jawo a ɗaureni ba gwara na rabu dashi cikin mutuntawa" miƙewa ta yi daidai lokacin suka shigo cikin parlon bakinsu ɗauke da sallama, da kallo suka bisu har suka zauna sannan suka gaisa Jawaad ya ce"Ameesha ke ce anan?" murmushi ta yi ta ce"wallahi fa Doctor na ɗan shigo sada zumunci ne ya Ayrah?" "tana nan klao Alhamdulillah" "Masha Allah". Satar kallon Imad ta yi taga ko inuwarta bai kalla ba hakan yasa ta ce"yallaɓai ina yini" "Lafiya" Abinda kawai Imad ya ce kenan ya ɗauke kansa yana cigaba da danna wayarsa, shuru Ameesha ta yi dan daman tasan haka zata iya faruwa dan tun ba yau ba Imadudden baya wani ƙaunarta dan murmushin yaƙe ta yi ta ce"toh Salma sai anjima" miƙewa ta yi ta ce"muje na raka ki" okay ta ce sannan sukai waje. Kallon Fattomah ya yi wacce take kwance kan kujera 3seater ya ce"tashi ki tafi " ahankali ta miƙe daga kwancen ta fara hawa stairs ɗin kamar ta waɗo har Allah ya taimaka takai ɗakin nata, saida ta shige sannan Jawaad ya ce"wai what wrong with her?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce"wai menstrual pain ke damunta shine fa harda kwanciyar asibiti" Jawaad ya ce"ayyah to Allah ya ƙara sauƙi ya rabata dashi kuma" Ameen Imad ya ce sannan ya cigaba da abinda yake. "Kin gani ko Ameesha ke daga ganin irin kallon da Imad ke miki kinsan akwai wani abun a ƙasa nidai ki rufamin asiri ki rufawa iyayena idan zamuyi magana dake mu haɗu gidan Ayrah ko muyi chat idan ya zama worth akwai buƙatar na ganki ko park ne sai muje please" taɓe baki Ameesha ta yi ta ce"ke kam Allah ya yaye miki ai shikenan mayi wayar" okay ta ce sannan ta shiga mota ta fita ita kuma ta koma ciki, zaunar ta tarar dasu da alama wani abun suke tattaunawa hakan yasa tana yin sallama ta tafi zata hau sama "Salma!" Da sauri ta juyo jin ya kira sunanta, gani tayi ba ita ce wacce ya ke kallo ba amma tabbas da'ita yake hakan yasa ta dawo wajen ta zauna kan kujera "Gani" Ɗago dara-daran idanuwansa ya yi ya saukesu akanta, da sauri ta yi ƙasa da nata idanun haka kawai taji gabanta na faɗuwa tabbas akwai abinda ya sanya ya yi mata wannan kiran, kusan 2mins sannan ya ce"karna sake ganin wannan yarinyar cikin gidan nan okay?" gyaɗa masa kai ta yi ta ce"in sha Allah" kallon Jawaad ya yi ya ce"as i said before" ganin sun cigaba da maganarsu yasa ta miƙe ta haye sama tana dafe ƙirji. Cikin kwanaki uku data ɗauka tana period tayi matukar shan wahala duk ta rame kamar ba itaba dukda yanda Imad ya yi ƙoƙari wajen ganin ta samu duk wani abu da take da buƙata har ta kammala sannan ta cigaba da zuwa makaranta zuwa yanzu kuma sun kusa fara yin Neco, murmushi ta yi tana kallon Fa'eeza ta ce"ke kam ki dinga jin tsoron Allah wallahi duk irin amsar da kika kwafa" dariya Fa'eeza ta yi ta ce"wallahi ƙarya kike Banason sharri ayaushe ai wallahi sai na faɗawa Daddyna dama ya sani bai biyamin anan makarantar ba" dariya suka hau yi mata Aysha ta ce"abanza dai tunda har kin fara zanawa" Shuru Fattomah ta yi ganin motarsa tsaye bakin gate ɗinsu sai na guards ɗinsa kusan guda biyar, kallonsu Aysha ta yi ta ce"sai anjima anzo ɗaukana" bye bye suka yi mata sannan ta tafi. Zaune ta sameshi cikin motar yana danna system da alama wani abu mai muhimmanci yake gabatar dan duk attention ɗinsa yana can, shiru Fattomah ta yi bayan ta shiga tana jin wani sanyi na ratsata ga ƙamshin turarensa wanda ya haɗe da sanyi A.C ya bata wani irin sanyi mai ban sha'awa, lumshe idanunta ta yi tanajin duk wata gajiyarta na sauka kallonta kawai Imad ya yi ganin yanda ta fara bacci jikin motar ajiye system ɗin hannunsa ya yi ya ɗauko wata leda ƙarama a hannunsa buɗewa ya yi ya ɗauki wata injection saida ya gama haɗawa sannan ya matsa kusa da'ita ahankali cikin dabara ya yi mata allurar motsawa ta yi amma Saboda yanda baccin yake kanta ya sanya ta cigaba da abinta. Fitowa ya yi daga toilet ɗin yana tsane jikinsa, wayarsa ce ta fara ringing ya ɗauka cikeda ladabi ya ce"ina yini Daddy?" Daddy ya ce"lafiya Imad kuna lafiya?" ya ce"Alhamdulillah Daddy ina Mommy?" "Tana nan, ka bawa Fateemah zan yi magana da'ita" kallon Fattomah ya yi wacce take ta faman bacci ya ce"Daddy bacci take wallahi saidai zuwa anjima ko gobe" okay Daddy ya yi Sannan ya yi hangup na kiran. Ajiye wayar ya yi sannan ya cigaba da gyara jikinsa saida ya gama shiryawa sannan ya ɗauko wani tablet sosai ya dinga tunani kusan 5mins sai kuma ya zaro wayarsa dialing number Doctor ya yi ring biyu ya ɗauka bayan sun gaisa ya ce "Nifa ina ganin bazan iya ba she's to small" girgiza kai doctor ya yi ya ce "daurewa zaka yi saboda haka ne kawai taimakon da zaka yi mata kuma kaga yarinya ce beside kuma kai ɗin mijinta ne banajin akwai abinda ba daidai ba, dan Allah ka kwantar da hankalinka kayi komai anutse muddin kayi mata injection ɗin to bazata ji wani zafi ba kuma bazata fahimta ba tunda daman batasan komai ba amma idan ba haka ba wallahi zata dinga shan wahala ne daga nan har sanda zatayi auren tunda Allah yasa tana dashi kawai ayi amfani da dama please sir" numfasawa Imad ya yi ya ce"shikenan naji I'll try my best in Sha Allah" okay ya ce sannan sukai sallama. Miƙewa ya yi yana sake kallonta ganin yanda take baccinta hankali kwance light ɗin ɗakin ya kashe sannan ya hau kan gadon. Tsaki Kamal ya yi ya ce"kai ka fiye gaggawa to yarinyar yanzu tana kan rubuta exams ne so nake da zarar ta kammala sai naje muyi magana da iyayenta" dariya Saleem ya yi ya ce" na ɗauka ai yaudararka ta yi kamar sauran ƴanmanta naka" harararsa Kamal ya yi ya ce"banza kawai in Sha Allah sai na auri Fattomah sooner or later" murmushi Salem ya yi ya ce"Allah ya sa Friend nima haka nake fata". Murmushi Khaltum ta yi ta ce"yawwa yaya dan Allah idan zaka je nima ka tafi dani inason ganin Fattum please" murmushi ya yi ya ce"ke nima fa duk a tsorace nake gashi banason nabar garinnan bamu haɗu ba wlh inama su bani ita muje taga Ammi" Khaltum ta ce"wallahi ba zasu baka ba kaga ko Ammi babu yanda ba tayi ba suka hanata ƴarta bare kuma kai" Fu'ad ya ce"idanma suka bari na ganta ai sun yimin zanji daɗi" murmushi ta yi ta ce"Allah yasa toh" . Ahankali ta buɗe idanunta tana kallon inda take baccin ita dai tasan a mota tayi bacci amma yanzu ta ganta cikin bedroom wanda bata taɓa gani cikin gidan ba, tsorone ya kama Fattomah ta miƙe daga kwancen da take tana sake kallon ɗakin wani enlargement ɗin hotonsa data gani ya sanya taji relief to amma a ina ne nan?, yaushe tazo nan?, buɗe ƙofar akayi ya sanya ta kalli wajen kamar idanunta zasu fito shigowa ya yi hannunsa riƙeda drip yana ya ce"lafiya?" girgiza masa kai ta yi ya ce"tashi kije kiyi wanka" gyaɗa masa kai ta yi kawai sannan ta miƙe ganin yanda take tafiya ya yi har ta shige toilet ɗin sannan ya sauke ajiyar zuciya. Babu kowa a bedroom ɗin sanda ta fito sai kaya da taga ya ajiye mata gefen gado shiryawa ta yi cikin abayar black colour wacce tayi mata kyau Masha Allah tana ɗaura veil ɗinta ya shigo yana kallonta ya ce"idan kin gama ki fita parlon ki ci abinci" toh kawai ta iya ce masa sannan ya juya ya fita, da kallo kawai Salma ke binta irin kallon tsanar nan ita kaɗai tasan abinda take ji cikin zuciyarta kamar ta kamata ta shaƙeta ta mutu musamman yanzu da ya fara mayar da hankalinsa akanta hakan yana matuƙar ƙona mata rai. Fotwarsu kenan daga paper civic education wacce ta kasance ita ce paper ta karshe a Waec sosai suke farinciki da murna banda Fattomah wacce tayi shuru sai kallo da idanu, Aysha ce ta zo inda take zaune tana kallonta ta ce"wai ke ma aka yi miki ne?, kina gani anata hira amma kin zo nan kin wani zauna ke kaɗai" kallonta Fattomah tayi ta ce" ke ni ki kyaleni banajin daɗi wlh" harararta ta yi ta ce"to da waye yake jindaɗi kin fiye rainin hankali kefa" murmushi kawai Fattomah ta yi ta ce"wallahi da gaske nake banajin daɗi tun jiya duk jikina amace nake jinsa" Aysha ta ce"toh Allah ya baki lafiya yasa ki dinga jindaɗi" tsaki Fattum ta yi ta ce"kefa ƴar iska ce" dariya ta yi ta ce"ay addu'a nayi miki, sai ki tashi ki tafi gida" miƙewa ta yi ta ce"ko baki faɗa ba yanzu zan tafi Allah yasa driver yazo dan kawai so nake na jini akwance wallahi" taɓe baki Aysha ta yi ta ce"sannu ƴar hutu sai kije ki ta kwanciya har gobe ai daman ba wani aikin arxiƙi ki ke yi ba" murmushi ta yi sannan ta ce"byeeee" bye itama ta ce mata sannan tabar wajen. Tana shiga ta kwanta nan kan kujera a parlon nan da nan wani irin bacci mai nauyi ya ɗauketa, fitowa ta yi daga kitchen ta ganta kwance kan kujerar sai baccinta take hankali kwance tsayawa tayi akanta sai kiamtta juya ta koma kitchen freezer ta buɗe da ɗauki ruwa mai sanyi tana zuwa ta balle bottle ɗin ta sheƙa mata afuska a razane Fattomah ta miƙe kamar zata shiɗe take kallon Salma harararta ta yi ta ce"dan ubanki an faɗa miki nan parlon saboda bacci aka yisa?" shiru Fattomah ta yi ta cigaba da faɗin"duk randa na sake ganin kin zo kin kwanta anan wallahi sai ranki ya yi mugun ɓaci shashasha kawai" fashewa tayi da kuka ta miƙe daga kan kujerar ta haye sama tana cigaba da kukanta, tana shiga apartment ɗinta ta kwanta gefen gadonta tana cigaba da kukan har wani baccin ya ɗauketa. Kallonta ya yi ya ce"maybe next Friday ne tafiyar so get ready" zama Salma ta yi ta ce"ok Allah ya kaimu daman ni ashire nake" okay ya ce sannan ya cigaba da cin abincinsa, zama ta yi daga gefen kujerar tana kallonsa ta ce"Uncle" kallonta Imad ya yi ya ce"lafiya kuma?" shiru ta yi ya ce"keee I'm play with you?" girgiza masa kai ta yi ya ce"idan baki da abin faɗi tashi kibar nan" hawayene ya kawo idanunta cikin rawar murya ta ce"ko..koba aunty Salma bace ta watsa mini ruwa kuma banason ruwa ni" fashewa ta yi da sabon kuka kamar sannan aka yi abun, kallon Salma ya yi yaga ta ɗauke kai, kallonta ya yi ya ce" idan har ba zaki daina sheɗanci ba to za'a dinga yi miki abubuwa daban-daban karki nutsu ki zama kamar kowace mace ki cigaba da rashin hankali kinji" kallonsa kawai Fattomah ta yi hawaye na biyo idanunta bata taɓa zaton abinda zai ce mata kenan ba, miƙewa tayi jiki asanyaye zata koma sama "Dawo Malama" Dawowa ta yi ta tsuguna tana ɗauke idanunta, ya ce"ubanki ki ke kallo atanan?" da sauri ta kalleshi sai kuma ta ce"Uncle Abbana fa ya mutu ka daina zaginsa please" baki buɗe Imad yake kallonta sai kuma ya ce"ni kike faɗawa haka?" girgiza masa kai ta yi ya ce"tashi anan wajen ko nayi ball dake shashasha kawai mahaukaciya" da gudu ta tashi daga wajen tana zuwa ta faɗa kan gadon tana sakin wani raunataccen kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, sosai Fattomah take kuka har tana ƙoƙarin shiɗewa kullum sake tsaanr zaman gidan take, kullum ji take inama ita ce wacce ta mutu tabar Daddy araye da ta huta ganin irin wannan tsanar tunda take ba'a taɓa tsanarta arayuwa irin yanda Imadudden ya tsaneta ba kowa ƙaunarta yake batasan mene ne tsangwama ba saida ranar data fara haɗuwa da Imad gashi har yau bai daina nuna mata irin wannan tsanar ba, tunanin wani abun tayi aranta yasa ta miƙe daga kwancen ta goge idanunta sannan ta tashi wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗauko trolley ta fara jera kayanta ciki kamar wacce zata bar gari. Wajejen ƙarfe 12pm ne ta fito daga ɗakin nata without making any sound take tafiya kamar wata mara gaskiya, ahankali ta fita daga cikin parlon tana ɗan waige-waige gudun kada wani ya hangota, tafiya ta fara yi har takai bakin gate tana ƙoƙarin buɗewa gateman ɗin dake wajen ya ce "Keee ina ne inda zaki cikin daren nan?" Hannayenta guda biyu ta ce"dan Allah dan Annabi ka rufamin asiri ka barni na fita kaji dan Allah karka faɗawa Uncle ka barni na fita daga nan gidan dan Allah wallahi zan iya mutuwa idan na cigaba da zama agidan nan" murmushi matashin saurayin ya yi ya ce"kiyi haƙuri bazan iya bari ki fita ba kuma bazan faɗawa mai gida ba ki koma ki kwanta idan safiya tayi sai ki faɗa masa gaskiya kina son kibar gidan nan ina ganin kamar zai fi Fattum" hawaye na zubowa cikin idanunta ta ce"dan Allah ka taimakeni" girgiza mata kai ya yi ya ce"taimakon da zan iya yi miki kenan ki koma ki kwanta dare ya yi" gyaɗa masa kai ta yi sannan taja trolley ɗinta ta koma gidan. Inuwar mutum ta gani tsaye yana shan tea da sauri tayi baya zata koma, riƙe hannunta ya yi ya sanya ta fashe da kuka hannunsa ya sanya ya rufe mata baki sannan ya ɗauketa bai direta ko inaba sai parlonsa hasken data gani ya sanya ta sake ruɗewa fara zagaye parlon ta yi ta ce"dan Allah dan Annabi Uncle kayi haƙuri wlh bazan sake ba" ko kallonta Imad bai yiba ya shiga bedroom ɗinsa not too long ya fito hannunsa ɗauke da bulala wata irin razana ta yi ta fashe da kuka kamar ranta zai fita ya ce"dan Annabi kayi haƙuri wayyoooo Allahna Uncle......"kasa ƙara sawa ta yi saboda wata irin bulala daya shiga sauke mata tun Fattomah na bashi haƙuri har saida tayi shuru dan ta shiɗe ya fi sau nawa, saida yaga ya yi mata laga-laga sannan ya rabu da'ita, kama hannunta ya yi ya jata har cikin bedroom ɗin sannan ya kulle ƙofar da key ya fito ya koma master bedroom ɗinsa dan daman anan yake kwana. Dakyar take buɗe idanunta wanda sukayi mata nauyi sosai hasken data gani ya sanya ta runtse idanunta dan rabonda taga haske yau kwana 4 kenan, kallonta ya yi ya ce"tashi ki fita ko ranki ya ɓaci" kasa koda motsi Fattomah ta yi, kukanma na zuci take domin hawaye ya daɗe da ƙafewa daga idanunta, kama gefen gadon ta yi ta miƙe wani jiri taji yana ɗibanta komawa ta yi ta zauna kan gadon ta fashe da kuka ta ma rasa abinda zatayi ga ciwon da jikinta ke mata, ga yunwa, ga ciwon da cikinta ke mata goge hawayen idanunta ta yi sannan ta sake attempting na miƙewa akaro na biyu baya tayi zata faɗi taji an riƙe ta, kwantar da'ita Jawaad ya yi akan gadon sannan ya kalli Imad wanda ya shigo sannan rai a ɓace ya ce "Wannan abunda kake zalunci ne Imad, wane Irin rashin imani ne wannan har ka kulleta a ɗaki for almost 4days babu abinci baka damu wane hali zata shiga ba wannan ba adalci bane Imad kuma wlh sai Allah ya tambayeka, idan kana ganin bazaka iya zama da'ita ba ta kusa ƙarasa makarantarta ka bani ita na tafi da'ita gida idan ta ƙarasa sai na mayar da'ita wajen Daddy" Murmushi Imad ya yi ya ce"abinda nakeson naji ka faɗa kenan, wato na baka ita ka tafi da'ita gidanka to bazan bayar ba, kuma wlh ko yanzu zata sake gwada aikata sheɗanci wlh saina hukuntata daidai da laifin data aikata idan kuma tana ja dan Allah yau ma ta sake haɗa kayanta zata bar gidan nan taga" kallonsa kawai Jawaad ya yi dan shi arayuwarsa bai iya tashin hankali ba idan kaga yayi faɗa toh tabbas abinda akai ya kai abu, tsaki Imad ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Ƙara sawa gabanta ya yi yana kallonta ganin duk yanda ta rame ga jikinta duk tabon duka tayi duhu ba kamar da ba, runtse idanunsa ya yi sannan ya ce"sannu kinji bari na kai ki asibiti" juyawa ya yi zai fita ta riƙe masa hannu kallonta ya yi yana sanya hannayensa cikin nata ya ce"mene ne?" Murya can ƙasa ta ce"yaya karka tafi ka barni ka tafi dani" yanda take maganar zaka gane har cikin ranta haka take nufi, shafa kanta ya yi ya ce"kiyi haƙuri babu inda zani Fattomah asibiti zan kai ki" gyaɗa masa kai tayi sannan ya sake ya fita. Wani banzan kallo Imad ya watsa masa sannan ya ce"babu wani asibiti da za'a kai ta ko mene za'a yi mata ai mata a gida wlh babu inda zata je, kai bari kaji ma babu inda zata sake fita indai tana cikin gidan nan" murmushin takaici Jawaad ya yi ya ce"shikenan duk abinda kake dai ka dinga tuna akwai ranar sakamako akwai ranar da zakayi regreting abinda ka dinga aikata mata alokacin kuma ba zai amfane kaba, dan kana ganinta yarinya ko kuma marainiya wacce batada wani gata to ka sani Allah yana nan a madakata kuma wlh bazai barka ba Imad ya kamata ka daina wannan abunda kake I'm not force you kawai shawara nake baka a matsayina na ɗan uwanka" cikeda rainin hankali Imad ya ce"aikuwa nagode" gaba ya yi bai sake bi takansa ba. Sosai ta sami sauƙi saboda yanda yaya Jawaad ya kula da rayuwarta har yaga ya ta samu sauƙi sosai sannan dukda Imad ya hana akaita asibiti haka ya dinga jigilar zuwa gidan safe da yamma, zaune take kan kujera tana kallon dramar da ake a arewa 24 sosai ta bawa kallon muhimmanci dan batasan sanda ya shigo ba tsaki ya yi sannan ya kashe tv hakan yasa ta ɗago idanunta tana kallonsa, harararta ya yi sannan ya zauna kan kujera yana kallonta ya ce "Duk randa na sake ganin kina wannan kallon na asara sai ranki ya ɓaci wlh" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba ya ce"zan tafi Spain yanzu and bansan tsawon lokacin dazan ɗauka ba maybe one week maybe kuma yafi haka ina sanar dake ne saboda idan har na dawo na samu kina aikata wani abu daban wlh Fateemah sai ranki ya ɓaci ki kama kanki ki zauna idan safiya tayi ki tafi makaranta idan kin dawo babu ke babu yawo" raurau tayi da idanu tana kallonsa ta ce"Uncle ka kaini gidan yaya Jawaad tsoro inaji" harararta yayi ya ce"ki mutu" miƙewa ya yi ya fice daga parlon without looking at her, hawayene suka shiga sakko mata kan kuncinta tana sharesu wasu na sake zubowa. Convey ɗin da taji ya sanya ta mike taje jikin window tana kallonsu har suka shiga mota shima Salma sannan guards suka shiga suka rakashi, sauke idanunta tayi tana rufe bakinta saboda wani kuka daya tawo mata tayi saurin komawa parlon ta faɗa kan kujera ta rushe da kuka. *Ameenatou ce#* *Nanameera ce#* *Like nd share* [5/18, 9:52 PM] Nanameera: *💞 FATTOMAH 💞* MIKIYA WRITERS ASSOCIATION. *Ameenatou I Ibrahim* Nanameera PAGE 36-39. Da sauri ta gama shiryawa dan ta kusa makara ko kallon abincin da maid ta ajiye mata batayi ba tayi waje, bayan ta zauna a motar tana ɗan Kalle-kallenta drivern ya ce"Hajiya ƙarfe nawa zaku tashi dan sir ya ce azo a ɗauke ki da wuri" kallonsa ta yi ta mudubi sai kuma ta ce"sai 4pm sannan"okay ya ce sannan suka ci-gaba da tafiya ba tareda ta sake furta wata kalma ba. Fa'eeza ta ce"wai yanzu babu kowa a gidan sai ke kaɗai?" gyaɗa mata kai Fattum ta yi ta ce"kuma kika zauna tab ni ce ke wallahi bazan zauna ba ko tsoro baki ji" murmushi kawai Fattomah ta yi batace komai ba Aysha ta ce"kawai ki zo mu tafi gidanmu idan aka tashi sai ki dinga kwana acan" da sauri Fattum ta kalleta ta ce"ke bakida kai ne?, so kike Uncle ya kusa kasheni idan ya dawo?" tsaki ta yi ta ce"to ai bai saniba kuma baya nan yanzu ke kinfiye tsoro wllh" dariya kawai ta yi ta ce"ni babu inda zani kinji" harararta ta yi"to kar kije mara mutunci". Kallon noodles ɗin tayi wacce taji kayan haɗi kana gani kasan ba ƙaramin daɗi zata yiba, Aysha ta ce"kee Fattum nasan halinki wlh karki yi cin mugunta kinga mu ukune" harararta ta yi ta ce"saboda kin maidani kwaɗayayyiya?" ta ce"nasan halinki da indomie shiyasa" "to ni bama ci zanyi ba" kallonta Aysha tayi ta ce"dan Allah kiyi haƙuri da wasa fa nake" ta ce"nima wlh nasani kawai bana cine rabonda naci indomie har na manta ni mango ma zan siya" haɗe rai Aysha ta yi ta ce"shikenan Nagode babu matsala amma wallahi nima bazan sake cin abin hannunki ba har muyi graduation" dafata Fattomah tayi ta ce"I'm sorry dear wlh na ƙoshi shiyasa kema kinsan bama haka dake" doke hannunta ta yi ta ce"dallah rabu dani" dariya ta yi ta ce"bari naje na siyo Mango kafin sannan kun kammala cinyewa" ko kallonta Aysha ba tayi ba bare ta bata amsa ta cewa Fa'eeza"please muci na rabu da wannan yar iskar" dariya Fa'eeza ta yi sannan suka fara cin abincin. Ganin yanda take haɗe rai yasa Fa'eeza ta ce"wai Fateema lafiya?" ya mutse fuska Fattum ta yi ta ce"wlh Mangon babu daɗi kamar gwanda" tuntsirewa sukayi da dariya Aysha ta ce"A'a kin manta kamar abarba" harararta ta yi ta ce"na saka ki a maganata?" Aysha ta ce"ban sani ba" miƙewa tayi ta ce"nidai na tafi gida sai kuma Friday please ku shigo da wuri" Aysha ta ce"wai bazaki gidan namu ba?" girgiza mata kai Fattum tayi sannan tayi gaba dan ba wani son yawan magana take ba. Tsaye taga drivern da alama bai koma gida ba saida suka fara tafiya sannan ta ce masa"wai anan ka zauna tunda safe?" murmushi ya yi ya ce"Eh haka sir ya ce idan mun kai ki azauna a jiraki har ki gama sannan"taɓe baki Fattum ta yi aranta tana cewa"wato ashe har ma'aikatan nasa ma muguntar yake musu?????". Sosai tasha baccinta sai wajen ƙarfe 8pm sannan ta shirya cikin wasu riga da wando ash colour wandon iya gwuiwa yazo mata kasancewar ita kaɗai ce gidan yasa bata damu ba, murmushi tayi ganin yanda abincin ke turiri saboda tsabar dawuwar da ya yi zama tayi ƙasan carpet ta tankwashe ƙafafunta ta ajiye plate ɗin jallof rice ɗin gabanta wani ɗan bowl ta ɗauko wanda Aysha ta kawo mata yajin daddawa ta buɗe ta zuba akai har saida abincin ya fara yin wannan kalar sannan ta rufe ta fara ci, haka ta dinga cin abincin kamar mayya saboda yaji sai shuuuuuu take da baki amma hakan bai sa ta haƙura ba, saida ta jinye tasss sannan ta ɗauki wani ruwa mai mugun sanyi ta sha gyatsa tayi sannan ta ce"Alhamdulillah" tashi tayi ta kwashe plate ɗin ta kwanta kan kujera nan da nan wani sabon baccin ya ɗauketa Da gudu ta ƙarasa toilet ɗin tana zuwa ta zube nan ƙasa ta shiga gwara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta saida duk abincin ya fita sannan ta jingina da bango hannunta bisa cikinta tana sauke numfashi, dakyar ta samu ta mike ta ɗauraye bakinta da wajen Sannan ta fito tana bin bango sake kwanciya tayi amma kwata-kwata ta kasa baccin banda ciwo babu abinda cikinta ke mata gashi babu wani magani cikin gidan bare ta ɗauka tasha kuma batada waya bare ta kira yaya Jawaad tunanin hakan yasa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita. Haka ta gaji da kukan tayi shiru dan kanta tunda babu wani mai rarrashinta, sai wajen ƙarfe 12am sannan ta fito parlon tana riƙe cikinta wanda take jin kamar zai bar jikinta dakyar ta sauka daga benen tana dafe bango ta fita daga cikin gidan tana kallon compound ɗin gidan wanda ya wadatu da kayan ƙyale-ƙyale haske ta ko'ina wani guard ne wanda yake aikin night ya kalleta ganin yanda take tafiya, tashi ya yi ya ƙara sa gabanta ya ce"ina zakije ƴan mata?" kallonsa ta yi ta ce "dan Allah kabani magani cikina ciwo yake min zan mutu please" ya ce"ohh sorry zo muje na baki drug kisha sannu kinji" toh ta ce masa sannan ya yi gaba tana biye dashi abaya. Sosai Fattum ta gaji da tafiyar ganin kamar ma ba tafiyar suke ba, saida suka je daga bayan gidan inda babu haske sosai ya ce"yawwa zauna anan bari na ɗauko miki acan"toh kawai ta ce sannan ya juya ya bar wajen gajiya tayi da tsaiwar ganin kusan 5mins bai dawo ba, zama tayi awajen saboda ba zata iya cigaba da kasancewa a tsaye ba "Keeeee!!" Aɗan firgice Fattomah ta ɗago kanta tana kallonsa ya ƙaraso yace"me kike yi anan?" ta ce"dama..daman wannan ne ya ce zai ɗauko mini magani anan na jira shi shine na zauna cikina yana min ciwo" tsaki ya yi ya ce"ke wace irin shashasha ce?, bakida hankali ko ko ya ya?, mene ne ma abinda kika fito yi a wannan daren?" hawayene ya kawo idanunta ta ce"cikina ne yake ciwo kuma na kasa Bacci shine nake neman magani" girgiza kai ya yi aransa yana cin babu daɗi tabbas abinda Imad ya aikata ba daidai bane bai dace barin yarinya budurwa cikin gida ita kaɗai ba tareda wani wanda zai kula da'ita ba, ganin tana neman faɗuwa yasa ya ce"shige ki koma gida da safe sai kije asibiti a dubaki" gyaɗa masa kai tayi sannan ya ce"yi gaba" gaba tayi yana binta abaya daga yanda take tafiyar zaka gane tana matuƙar jin jiki dan dakyar take ɗaga ƙafarta a haka har suka fito compound na gidan, saida yaga ta shiga ciki sannan ya girgiza kansa ya koma wajen gate ɗin aransa yana tausayawa rayuwarta.Fattomah kuwa na shiga ta zauna a parlon nan tana kuka saboda wani irin zafi da cikinta ke mata ita kaɗai tasan masifar da take ji da wannan ciwon ciki, haka ta ƙarasa wannan daren ba tareda tayi bacci ba sai wajejen asuba sannan ta samu ya ɗauketa ABUJA Rai ɓace Daddy ya ce"when zaka dawo malam?" ya ce"in sha Allah ranar Thursday Daddy zanfara biyowa nan maybe" Daddy ya ce"Imad karka ce zaka rainami hankali"murmushi ya yi ya ce"Daddyyyy calm down wlh zan zo ko ban biyo ba ina komawa gida zan tawo" yace"nadai faɗa maka" kashe wayarsa ya yi yana kallon Mommy ya ce"ya kusa dawowa ai" Mommy ta ce"toh Allah ya dawo dashi lafiya amma dan Allah idan zai tawo ya tawo mini da Fattomah naganta" Daddy ya ce"why?, bai fi ba sauran 5weeks ta dawo nan duka ba please ki bar wannan maganar kawai"murmushi kawai tayi dan tasan saboda ransa aɓace yake ne ta ce"toh na bari yallaɓai" tashi ya yi bai sake cewa komai ba ya shige bedroom. KANO Tashi tayi wajen karfe 10am kalle-kallen inda ta kwanta ta shiga yi dafa cikinta tayi wanda har sannan yana mata ciwon amma ba kamar ɗazu ba, freezer ta buɗe da ɗauki ruwa ta sha sannan ta haye sama dan kintsawa. Kallonta gateman ɗin ya yi ya ce"yanzu ke dawa zaki je asibitin?" ta ce"nida ƴar uwarmu ka kaini gidanta please" girgiza kansa ya yi ya ce"bari akira yallaɓai dan ya ce kar a kuskura a barki ki fita wani waje idan ba makaranta ba" turo baki Fattum tayi bata ce komai ba ya ce"bari naje wajen oga" tafiya ya yi ta bisa da kallo. Saida taga ya shige sannan ta yi sauri ta kalli ƙofar, ahankali kamar wata mara gaskiya haka ta buɗe gate ɗin ta fice da gudu. Cikin wayar Imad ya ce"A'a kar wanda ya barta ta fita indai ba school ba kuma koda school ne idan an kaita kar a tawo abarta tare da'ita zaku dawo" toh kawai sukace sannan ya katse wayar, da mamaki gateman ɗin yake kallon wajen da yabar Fattomah tsaye dan yanzu bai ganta wajen ba, sosai ya duba bai ganta ba kuma babu alamun ta koma cikin gidan buɗe ƙofar ya yi yay waje ya fara tafiya cikin unguwar kwata-kwata babu mutane a titin kowane gida kuma arufe yake wani ƙofar gida ya gani da gateman zaune kan kujera da sauri ya ƙarasa bayan sun gaisa ya ce"dan Allah kaga wata yarinya ta shige tanan?" gateman ɗin ya ce"ai kuwa wata ta sanya abaya blue ko?" da sauri ya ce"Eh ita ce" ya ce"wallahi naganta ɗazu ta shige tana tafiya da sauri kamar tayi gudu ma, amma lafiya" cikin tashin hankali ya ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun meyasa yarinyar nan zatayi haka?' magana gateman ɗin yake masa amma ko juyowa bai yiba shi kaɗai yasan tashin hankalin da zasu fuskanta wajen Imad idan har ya dawo ya tarar bata nan fatan shi ɗaya Allah ya bata ikon dawowa da wuri duk inda taje,koda ya shiga gidan babu wanda ya sanarwa cewa bata nan ya koma ya yi zamansa dukda zuciyarsa fal take da tunani kala-kala. Da gudu Khaltum ta zo ta rugumeta tana sake kallonta cikeda murna ta ce"Fattomah ke ce dagaske?" murmushi ta yi ta ce"to dafa?" dariya suka yi tare ta ce"ina Adda?" "yanzu ta fita taje wajen biki yanzu zasu dawo" okay ta ce Sannan ta zauna kan katifar "Washhhh wlh nagaji sosai" Kallonta Khaltum ta yi ta ce"wai daga ina kike?" "daga gida mana, ina yaya Aslam?" ta ce"wallahi ya tafi Katsina mukaje gidan da kika koma muka tarar arufe shine ma ya tafi" miƙewa daga kwanciyar da tayi ta ce"dan Allah fa meyasa baku bugamin waya ba nag ...." shiru ta yi tunawa da tayi babu waya a hannunta Khaltum ta ce"wallahi mun kira ki amma wayar akashe shiyasa kawai muka haƙura muka dawo gida, kina waya da Ammi?" hawayene ya kawo idanunta amma ta ɓoye ta ce"rannan na kirata please kina credit wayarki kimin kiranta?" okay ta ce sannan ta ɗauko wayarta, ringing ɗaya Ammi ta ɗaga wayar tana yin sallama Fattomah ta ce "Ammina!!Ammina!!Amminaaa". Kukane yaci ƙarfinta tama kasa magana ita kanta Ammi kuka take domin tana matukar kewar ɗiyarta saida ta daidaita muryarta sannan ta ce"mene ne haka Faɗeematoh?" sake rushewa tayi da wani kukan saboda tunawa da tayi da Abbanta da yake yawan ce mata Faɗeematoh, cikin sheshsheƙar kuka ta ce"Amma.Amm...Ammina dan Allah ki dawo Kano kinji banason zama gidan uncle ki dawo mu zauna agidanmu kinji yafi daɗi Ammi" cikin raunin zuciya Ammi ta ce"kiyi haƙuri Fattum ina nan zan zo wajen ki in sha Allah karki damu ki daina kuka kinji ki daina rigima" Fattomah ta ce"Ammina inason naganki dan Allah" murmushi tayi wanda yake zuba da hawaye ta ce"Nima haka Fattum inason naganki amma in sha Allah zan zo nan kusa" "Ammi amma bazaki koma ba?" ta ce"ai nadawo gida Fattum nida rayuwa cikin Kano saidai hukuncin Ubangiji" sake fashewa ta yi da kuka Ammi ta ce"ya isa kiyi shiru banason kukan zan zo shikenan?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce"to sai kin zo Ammi kuma so nake ki dafamin dambun shinkafa da zogale da gyaɗa Ammina" dariyar da bata shirya ba ta yi tanajin zallar rigimar ɗiyar tata ta ce"in sha Allah randa nazo Kano duk zan dafa miki wannan abubuwan Fattum" murmushi ta yi ta ce"toh Ammina sai kin zo" ta ce"toh Faɗeema" murmushi ta sake yi ta ce"ina sonki Ammina" dariya ta yi ta ce"nima inasonki Fatyy na", sallama sukayi sannan ta miƙawa Khaltum wayarta. Dariya ta yi ta ce"naga randa zaki daina shagwaɓa arayuwarki" harararta ta yi ta ce"babu rana kuwa wollah" dariya Khaltum ta yi ta ce"ai shikenan" kwanciya Fattomah tayi gefen katifar nan da nan bacci wanda baya mata wahala ya sake ɗauketa. Murmushi Adda ta yi ta ce"aikuwa kin kyauta Faɗeematoh amma dai kwana zaki yi?" gyaɗa mata kai Fattum tayi tana murmushi dan daman haka ta shirya, Abla ta ce"kinyi kyau abunki amma duk kin rame Fattu"harararta Adda ta yi ta ce"ke kam da gulma Allah ya shirya" dariya suka yi duka sannan suka cigaba hira gwanin ban sha'awa, tun bayan rasuwar Abba sai yau ta sake samun farin ciki irin wanda ake kira farin ciki domin ji take kamar zata koma gidansu ta tarar da Abbanta da Amminta zaune suna jiranta "Fattomah kuka?" Da sauri ta taɓa fuskarta taji hawayene yake zuba, Adda ta ce"faɗa min lafiya kuwa?" murmushi ta yi ta ce"lafiya klao Adda kawai Abbana na tuna shiyasa" cikeda tausayawa Adda ta ce"ayyah Allah ubangiji ya jiƙan Ahmad" cikin asanyaye ta ce"Ameen ya Allah". Har wajen ƙarfe 12am ba suyi bacci ba suna hira idan wannan ta faɗa sai wannan ta ɗauke a haka har baccin ya ɗaukesu banda Fattum wacce take jinta cikin wata duniya tabbas rashin iyaye babu daɗi duk irin abinda zaka samu idan har babu iyayenka tofah bashida amfani haka ba kowane zai ƙaunaceka saboda Allah ba dukda ƙanƙantar shekarunta amma ta naɗe wannan cikin kwakwalwarta, ba ita tayi bacci ba sai wajen 2am a haka ma ɓarawone ya saceta. Da safe bayan sun idar da sallar asuba suka fito tsakar gida Abla ce ta shimfiɗa musu tabarma suka zauna suna cigaba daga inda suka tsaya jiya, Adda ce ta fito jin hayaniyarsu ta ce"tunda kun tashi sai ku nemi abun dafawa, Faɗeema me kike so?" sunkuyar da kanta tayi tana murmushi ta ce"Adda kunu nakeso da ƙosai please" murmushi irinna manya Adda ta yi ta ce"tom shikenan Khaltum ki tashi ki kunna wuta bari nima na fito"toh ta ce mata sannan ta koma ɗakin. Suna gama karyawa suka haɗa kwanukan wanke-wanke suka fara yanda suke yi da nishaɗi yasa basu wani ji wahalar aikin ba har suka gama gyara gidan wajejen 10am sannan suka koma bacci, da rana Adda ta dafa musu dambun shinkafa wanda yaji zogale Masha Allah Khaltum ce ta daka musu yaji mai daɗi suka zauna yanda suke cin dambun shinkafar ni kaina saida yawuna ya tsinke musamman Fattomah dan ba ƙaramin ci tayi masa ba dan saida ya fice kanta tsabar irin cin da tayi masa ni kuwa na ce ko dan saboda harta sammin ne☹️babu komai Imad namu zai bani nasan 😂. For a good three days data zauna gidan Adda taji daɗi sosai ta dawo asalin Fattomahnta kafin Abbanta ya rasu rayuwa mai daɗi cikin gidan Adda da taimakon su Khaltum wanda koda yaushe take sake jin ƙaunarsu aranta, kasancewar ranar Friday ƙarfe 7am suka gama aikin gidan, suna zaune tana kallo wayar Khaltum, shiru tayi sai kuma ta ce"yau yaushe ne wai?" Khaltum ta ce"Friday ko kin manta ma" afirgice ta miƙe ta ce"nashiga ukuna!" miƙewa itama tayi tana kallonta ta ce"lafiya Fattomah?" a rikice ta ce"gida zan tafi yau Uncle zai dawo" da mamaki ta ce"wane Uncle kuma?" "Bazaki ganeba kawai tafiya zanyi" waje Khaltum tayi dan kiran Adda dan ita bata gane abinda Fattomah ke nufi ba. Ahankali yake sauke ajiyar zuciya lokacin da motocin nasa suka fara parking cikin gidan, fitowa ya yi yana sanye cikin wata suit black colour gashin kansa atufke da ribom, sosai ya kara kyau da fari abinsa Salma ce ta fito cikin wata abaya black colour tayi kyau har ta gaji kana ganinsu kasan ahuce suke abinsu, da sauri ya ƙaraso wajen ya rungumeshi yana murmushi ya ce"welcome back I.I Imadudden" dariya ya yi ya ce"thank you bro fatan kana lafiya?" murmushi Jawaad ya yi ya ce"Alhamdulillah, ina Fattum kuma?" sakinsa ya yi ya ce"ai daman ba tare da ita na tafi ba ko ka manta exam take" da mamaki Jawaad ya ce"wai ita kaɗai ka bari cikin gidan nan?" gyaɗa masa kai ya yi Jawaad ya ce"amma kayi ganganci fa" murmushi kawai ya yi sannan ya ɗauko wata ƴar teddy bear milk da ratsin ja kallonta Jawaad ya yi ya ce"wowwwww amma tayi kyau doll ɗin wace?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce "*FATTOMAH*" da sauri Jawaad ya kalleshi dan tunda suke bai taɓa jin ya ambacin sunan ba sai yau, murmushi ya yi ya ce"tsaraba ka siya mata kenan?" ya ce"Eh naganta ne a wani mall dana shiga shine ta bani sha'awa shiyasa na ɗaukar mata"okay Jawaad ya ce sannan suka shiga cikin parlon. Saida suka huta sosai sannan ya ce"Salma ki ramin ita"okay ta ce sannan ta bar wajen, kusan 5mins sannan ta dawo tana kallonsu ta ce"bafa ta nan" ya ce"kamar ya?, have you check?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"to ina ne inda zata je da safen nan?" tashi ya yi zuwa apartment ɗinta Jawaad yana biye dashi, babu inda basu duba ba amma babu Fattomah babu ma alamun mutum yana zaune cikin ɗakin, da sauri ya fito zuwa compound ɗin gidan wani socket ya danna nan da nan jiniya ta cika gidan cikin 2mins duka maids ɗin gidan suka hallara, kallonsu ya yi ya ce"ina Fattomah?" shiru duka suka yi domin sai daga baya gateman ɗin yake faɗa musu cewa ta bar gidan, cikin faɗa ya ce "Ina magana kuna wani kallona nace ina yarinyar dana bari cikin gidan nan dazan fita?" shiru duka suka sake yi sai boss ɗinsu ne ya fito a hankali ya fara magana kamar haka "Sir daman yarinyar ta tambayi zata asibiti kamar yanda muka sanar dakai a sannan toh kafin ya koma ya tarar ta gudu tabar gidan kuma tun ranar bata sake dawowa ba" Wani irin kallo Imad ya ke binsu dashi kafin ya kalleshi ya ce cikin ɓacin rai"daman haka shine aikinka?, abinda na ɗaukeka kayi kenan?, yanzu ku tsaya ta ina kuke son nafara neman ƴar mutane daga ina zan fara?, Ko kuwa yawo zan shiga cikin gari ina nemanta?, saboda rainin hankali data ɓata aka samun wanda zai kirani ya sanar dani for almost 4days bata gida amma shine kuke zaune hankalinku kwance kuna cin abinci ku kwanta" kwafa ya yi ya ce"wallahi I'll teach you a......" maganar ce ta maƙale masa dalilin Fattomah da yaga ta shigo hannunta riƙe da jaka, banda faɗuwa babu abinda gabanta keyi tasan yau ubangiji ne kaɗai zai hanasa ya kasheta tsabar duka, yanda zuciyarta ke rawa haka ilahirin jikinta ma ke rawa tama kasa kallonsa, Jawaad ne ya zo zai je wajenta Imad ya jawo hannunsa ya dawo baya har sannan kuma bai ɗauke idanunsa daga kanta ba. Yanda kasan wani zaki haka yake tafiya toward direction ɗin inda take tsaye sosai bugun zuciyarta ya ƙaru tsananin fargaba da tashin hankali sune cikin idanunta tabbas tayi nadamar zuwa gidan Adda tayi wannan kwanakin batareda ta sanar dashi ba, hucin mutum da taji ya sa ta tabbatar da yazo gabanta runtse idanunta tayi ta tsuguna kan ƙafafunta tana haɗe hannayenta biyu alamar roƙo ta ce" *Ameenatou ce#* *Nanameera ce#* *Like nd share**💞 FATTOMAH 💞* *MIKIYA WRITERS ASSOCIATION* *Ameenatou I Ibrahim* Nanameera. PAGE 40. *END OF BOOK 1* *This page naku ne Nanameera's Library ina matuƙar jin daɗin sharhinku akan FATTOMAH 💞 kuna tashin kaina da yawa, Imadudden yace a gaisheku kyauta 😂team FATTOMAH idan za'a yi abu a dinga yi dan Allah Maganar gaskiya mun fasa halartar zaman Court ɗin tunda abun haka ne bamu son tashin hankali shiyasa bawai tsoro muka ji ba💪idan kunje ku sanarwa da judge I.I Imadudden baya ƙasar nan bazai samu damar halartar zaman ba🙏 FATTOMAH na godiya da nuna soyayya Nanameera's Library tana ganin saƙon abun arziƙi kuma ba zata baku kunya ba in sha Allah 😂much luv both Imadudden and Fattomah team❤️❤️* *Special thanks to my dearest friend Khadeejerth Sabi'u Yahya The Nainarh Kd ✍️ Ina matuƙar jin daɗin zamanmu tare🥰📚Allah ya ƙara haɗa kanmu✍️* Hannunta Imad ya kama bai ce komai ba ya koma cikin gidan da sauri Jawaad ya biyo bayansa, bai ganshi a parlon ba hakan yasa ya tsaya nan yana ɗan zagaye parlon shikuwa Imad master bedroom ɗinsa ya buɗe ya zurata sannan ya mayar da ƙofar ya rufe, cikin sanyin murya Jawaad ya ce"dan Allah kayi haƙuri karka yi mata hukunci mai tsanani please" "Lokaci na shigewa" Gaba Imad ya yi Jawaad yabi bayansa dan daman yasan ba lallai ya ɗauki abinda zai faɗa masa ba, har suka je gidan mai martaba suka dawo Imad bai ce komai ba kuma bazaka taɓa gane halin da yake ciki ba dan kai tsaye ba zaka ce ransa a ɓace yake ba haka bazaka ce farin ciki yake ba, tsayawar da drivern ya yi yasa Jawaad ya ce"dan Allah Imad kayi haƙuri nasan bata kyauta ba amma kayi la'akari da yarintar ta kar kace zaka mata hukunci da abinda yafi ƙarfin shekarunta dan Allah ka sassauta mata" kallonsa kawai Imad ya yi dan idan ya ce zai iya rabuwa da Fattomah shima yasan ya yiwa kansa ƙarya tabbas sai ya hukuntata hukunci mai tsananin gaske yanda koda nan gaba bazata taɓa yunƙurin aikata makamancin abinda ta aikata yanzu ba, numfasawa Jawaad ya yi ya ce"ko kuma muje na ɗauketa please idan yaso nan two days sai na dawo da'ita" wani kallon ka zama mahaukaci Imad ya watsa masa sannan ya ce"inada abubuwan da zan gabatar a gida dayawa please ka sauka" murmushi ya yi ya ce"wato korata kake?" gyaɗa masa kai ya yi dan yasan bazai masa ƙarya ba, murmushi Jawaad ya yi ya ce"shikenan sai anjima amma ina sake baka haƙuri yallaɓai" ko kallonsa bai yiba ya cigaba da danna wayarsa har ya sauka sannan drivern yaja motar. Shuru Fattomah tayi bayan ta idar da sallar la'asar ɗin ita kaɗai take tunani dan batasan irin hukuncin da Imad zai mata ba bata taɓa tunanin zai rigata dawowa ba da ko ƙarfe nawane zata iya tawo wa Saboda dai kar ya rigata gashi har yanzu bai shigo ba dukda taji sanda convey ɗinsa suka dawo, ko ruwa ta kasa sha saboda duk atsorace take, taɓa ƙofar da akayi yasa taji gabanta yayi wani irin faɗuwa lokaci ɗaya ta fara shivering dan tana tsananin tsoron abinda zai mata musamman yanzu da kwata-kwata bata jindaɗin jikinta, tamkar wani zaki haka Imad ya ƙaraso gabanta ji tayi kamar ta nutse a ƙasa ko hakan zai sa ya rabu da'ita, zama ya yi gefen kujera yana ƙare mata kallo from head to toe, hawaye ya fara sauka kan kuncin Fattum saboda two eyes da tayi da wata bulala saurin rufe bakinta tayi jin kuka na neman kwace mata, miƙewa ya yi yana zuwa inda take ya sanya hannunsa guda ɗaya ya ɗagota haɓarta ya tallafa akan hannunsa fuskar nan babu annuri ya ce "Keeee!" Sake runtse idanunta tayi saboda tsoro cikin faɗa ya ce"gidan ubanwa kika je?" rawa jikin Fattomah ya fara yi tama kasa furta masa koda kalma ɗaya sai kuka take kamar wacce ke gaban mala'ika, kwafa ya yi ya ce"wato bakida bakin magana saboda kin fita yawon gabanki yar ficiciya dake har kinsan fita wani wajen ki kwana har tsawon kwanaki wato duk abinda za'a yi miki ayi miki bakida asara toh bari kiji Wlh sai kin gane Allah ɗaya ne, daga rana mai irinta yau bazaki sake aikata abinda kika aikata ba ke koda kuɗi kuwa aka ce za'a baki I'll teach you a lesson" fashewa tayi da kuka ta fara zagaye ɗakin tana bashi haƙuri sosai abin ya ɓatawa Imad rai musamman yanda take kukan kamar ranta zai fita baisan sanda zuciya ta ɗebeshi ya fincikota ta waɗo gabansa ba, bulalar ya shiga sauke mata ta ko'ina dan baya ma duba inda zai daka jikinta, kusan 10mins yana aikin dukanta tuni jikinta yagama saki gabaɗaya dan babu alamun tana numfashi duk jikinta ya fashe gwanin ban tausayi, tsaki ya yi sannan ya taka cikinta ya yi ball da'ita ya shige yana fita ya mayar da ƙofar ɗakin ya rufe ya sanya lock sannan ya fice daga gidan gabaɗaya dan baya jin zai iya cigaba da kallon yarinyar musamman idan ya tuna abinda Yusuf ya faɗa masa akanta shine ma abinda ya ƙara sawa ya yi mata wannan mugun dukan da bai taɓa yi mata irinsa ba. Kai tsaye gidan gonarsa ya shige dan nan kaɗai ne yakejin zai samu farin ciki zuciyarsa tayi sanyi, sosai gidan gonar zai baka sha'awa saboda irin abubuwan dake cikinsa kai tsaye wajen da peacock ɗinsa suke nan ya nufa, gamayyar ɗawisu ne aƙalla sunkai guda 50 maza da mata yanda suke buɗe jelarsu kaɗai ya isa ya sanya mutum nishaɗi zama Imad ya yi kan wata farar kujera yana kallonsu. Har aka idar da sallar isha'i Fattomah bata iya tashi ba duk da zuwa sannan ta farfaɗo daga sumar da tayi yanda fuskarta ta koma sai ta baka tausayi dan bazaka taɓa cewa ita ce ba duk fuskarta ta kumbura saboda irin marunka da ya yi mata sannan ko'ina na fatar jikinta ya fashe sai jini ne ke ɗiga ko kuka ta kasa yi sai ajiyar zuciya da take saukewa duk irin yanda tayi attempting na tashi amma abin ya faskara, kifa kanta wanda yake barazanar tsage mata tayi kan cinyarta tana jin wani irin jiri na ɗibanta dukda azaunen da take. Har wajen 10pm tana nan zaune ahankali kuma akaro na babu adadi ta yunƙura da niyyar tashi wata irin ƙara ta saki saboda wani irin kullewa da cikinta ya yi tana jin kamar ana zarar ranta kasa komawa ta zauna tayi sai tsayawa da tayi tana riƙe da cikin nata, buɗe ƙofar ya yi bayan ya yi unlocking nata ya shigo kallo ɗaya ya yi mata sannan ya kama hannunta ba tareda ya ce komai ba suka fita a ɗakin, janta kawai yake domin ba tafiya take ba har sannan kuma hannunta na kan cikinta yana shiga bedroom ɗin ya hankaɗata har saida ta waɗi nan kasan carpet cikin kakkausar murya ya ce "Daga yau nan ne wajen zamanki kuma ba zaki sake fita koda parlon cikin gidan nan ba saida kiyi rayuwarki anan tunda yar iska kike neman zama kuma koda school billahil Azeem ba zaki sake zuwa ba muddin kina cikin gidan nan saida bayan kin bar gidan nan" duk irin halinda Fattomah ke cike hakan bai hanata rike ƙafafunsa ba cikin dashasshiyar muryata ta ce"dan Allah Uncle kayi haƙuri ka barni naje makaranta wllh bazan sake zuwa ko'ina ba dan Allah Uncle karka hanani" janye ƙafarsa ya yi yana yi mata wani mugun kallo ya ce"idan kika sake riƙeni sai na gwaɗa miki mari" saurin ɗauke hannuta ta yi ya yi tsaki ya juya ya fita. Wani irin raunataccen kuka Fattomah ta fara yi kukane wanda yake tsuma zuciyar mai sauraro kukane wanda yake cikeda abubuwa daban-daban, kukane wanda yake tabbatar da maraicinta a wannan ranar tabbas da tanada iyaye toh haka bazata faru da'ita ƙaddara ce ta rabata da iyayen ta kawota rayuwa inda ake ɗaukarta tamkar dabba dan wani lokacin ma gwara dabba da abinda ake mata, gashi batada kowa wanda zai rarrasheta saida tayi kukanta ya ishe ta tayi shuru abinta haka ta zauna taci kukanta har Allah ya sanya mata dangana da haƙuri bacci ya ɗauketa a wajen. Kallonsa Ayrah tayi sai kuma ta ce"wai saurin me kake ne?" hular hannunta ya karɓa ya ce"bazaki gane ba ke kam kawai sai nadawo" kwaɓe fuska tayi ta ce"wai kana nufin ba zaka ci abinci ba zaka fita dear?" murmushi ya yi yaja kumatunta ya ce"I'm sorry wlh idan na tsaya makara zanyi kuma kinsan halin Imad dai" haɗe rai ta yi ta ce"ni daman nasan tunda naga kana wannan saurin toh shine ya kira ka shi ya fiye nuna isa wlh ko kai da kake ɗan sarkin baka...." ganin kallon da yake mata ya sa ta yi shuru da bakinta saida ya ɗaura wrist watch ɗinsa sannan ya ce" banason sake jin irin wannan maganar a bakin ki okay?" gyaɗa masa kai tayi ta ce"I'm sorry dear" murmushi ya yi ya ce"ya wuce saina dawo" "bari na rakaka toh" okay ya ce sannan suka fita suna rike da hannu juna. Rai ɓace Aysha ta ce"banda rainin hankali tasan yau akwai paper amma tayi zamanta haka ranar Friday ma tayi ko ubanme take nufi da kanta bansani ba" murmushi Fa'eeza ta yi ta ce"ke kuma kin fiye saurin fusata maybe akwai wani abun kinsan haka kawai Fateemah ba zata ƙi zuwa exam ba" Zainab ce ta ce"wlh kuwa amma mu kirata awaya mana naga kwana biyu bata hau online kwata-kwata" tsaki Aysha ta yi ta ce"ai babu waya a hannunta bare a kirata kuma gashi bamusan gidan da take ba balle muje muga ko lafiya" da damuwa Fa'eeza ta ce"gaskiya kam Allah dai yasa lafiya" Ameen Zainab ta ce sannan suka miƙe dan sannan zasu shiga biology. Dakyar ta idar da sallar asuba ɗin sannan ta zauna gefen gadon banda raɗaɗi babu abinda jikinta ke mata ko'ina babu daɗi ga bakinta wanda take jin yana yi mata wani irin ɗaci rabonta da abinci har ta manta dan bata iya cin komai ruwa ma dakyar take samu tasha kuma shima sai ƙishirwar ta ƙure kuma bata iya sha da yawa saidai kaɗan hakan yasa duk fatar jikinta ta fara yamushewa kana ganinta kasan babu wadataccen jini da ruwa ajikinta cikin sati ɗaya da tayi a haka koda sau ɗaya Imad bai leƙo da niyyar dubata ba saidai kullum taji alamun tashin motarsa idan zai fita idan har wanda yasan Fattomah watanni uku da suka shige zai ganta yanzu toh tabbas sai ya yi dagaske kafin ya iya gane itace duk tayi baƙi ga wata uwar rama da tayi idanuwanta duk sun faɗa ciki Fattomah wacce ta kasance mai yawan hira da wasa da dariya yau sai tayi kwanaki ba tace uffan ba idan har zata buɗi bakinta to saidai wajen karatun sallah amma ko kaɗan bata hira to dawa ma zata yi hiran???????? Ita ba uwa ba ita ba uba ba Allah sarki kaɗan daga cikin ƙalubalen maraici kenan. Cikin kwantar da murya da son faɗa masa gaskiya ya ce "Wallahi dagaske nake maka babu amfanin wannan abinda kake aikatawa, yarinya ce ƙarama batasan komai ba ko wace irin tarbiyya kake so zaka iya ɗorata kuma tabi amma wlh duk ranar da Fattum ta fara gane kanta bazaka taɓa iya lankwasa taba, duka baya taɓa sakawa yaro ya daina abu saima tunzurashi da yake wasu lokutan bare kuma Fattomah da batada saka magana ko kaɗan yarinya ce wacce bata damu da rayuwar kowa ba beside kuma batada laifi dan ba itace ta kawo kanta gidanka ba bata cancanci irin wannan rayuwar ba kamata ya yi ka tausayawa maraicinta ka kula da rayuwarta naɗan wannan lokacin ka daina dukanta domin hakan tamkar zaluntarta ka ke, ka dinga ƙoƙarin sassauta fushinka akanta kuma wani lokacin ba laifi tayi ba kawai saboda kanajin cewa ka tsaneta cikin ranka yasa kake mata haka, dan Allah Imad ka faɗa min mene ne lafin Fattomah daya sanya ka tsaneta dan Allah ka faɗa min?" Shiru Imad ya yi dan tabbas bashida amsar bashi kuma baisan dalilin hakan ba kawai yaji baya ƙaunarta ko kaɗan cikin ransa aduk sanda ya ganta ji yake tamkar ya shaƙe mata wuya ta mutu ko ya daina ganin fuskarta bai taɓa jin tsanar mutum cikin zuciyarsa irin Fattomah ba ko mene dalili ohooooo?????, Jawaad ya cigaba da faɗin"dan Allah ka buɗe yarinyar nan kuma karka sake rufe ta saboda alfarmar Annabi koda bazaka kula da'ita ba to karka cutar da'ita kabarta haka nan please Bro" ajiyar zuciya Imadudden ya sauke sannan ya gyaɗa masa kai a hankali ya ce"in sha Allah kodan saboda kai nasan bakason kaga matarka cikin damuwa right?" kallonsa Jawaad ya yi amma bai ce komai ba, da sallama ta shigo parlon tana sanye cikin wata atamfa Holland coffee color ta sanya farin mayafi ɗan ƙarami hannunta riƙe da mukullin mota, gaisawa suka yi da Jawaad sannan ta kalli Imad ta ce"daman zan fitan ne" okay ya ce mata sannan ta juya ta fita abinta. Kwance ya tarar da'ita ta duƙunƙune cikin duvet, ahankali ya ƙarasa gaban gadon ya tsaya yana kallon fuskarta wacce tagama sauya kammani gefen duvet ɗin ya daka hakan yasa ta buɗe idanunta saboda batada nauyin bacci da sauri tayi baya cikin tashin hankali ta fara faɗin "Da..Da...dan Allah Uncle kayi haƙuri da. n Allah" Kallonta kawai ya tsaya yana yi dan baima san abinda zai ce mata ba kuma daman ba shigowa ya yi dan ya yi mata maganar ba tsayawa tayi da kukan ganin ya juya ya yi fitarsa jingina tayi da jikin gadon tana sauke numfashi ahankali, saida ta nutsu sosai sannan ta miƙe tana tafiya a hankali ta shige toilet. Da mamaki ta ƙaraso tana kallonsa murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa amma kana ganinta kasan mamakine fal fuskarta, gaisawa suka yi ya ce"sannu kinganni gidanku ko?" gyada masa kai Aysha ta yi ta ce"Eh mana kamar na taɓa ganinka" murmushi kawai Kamal ya yi ya ce"Eh mana kece ƙawar Fattomah ko?" gyaɗa masa kai tayi nan ma ya ce"daman ina son na tambayeki ne" Aysha ta ce"Allah yasa na sani" gyara tsaiwarsa ya yi sannan ya ce "Daman Fattomah ce bana ganinta kwana biyu kuma na kira wayarta several times switch up to shine nazo school ɗinku jiya na tambayi wasu yan class ɗin ku suka cemin kece best friend ɗinta shine nazo na tambayeki ko lafiya?" numfasawa Aysha ta yi sai kuma ta ce"wlh nima abinda ke damuna kenan ina cikin tashin hankali yau kusan sati biyu kenan banga Fattum ba kuma bansan inda zan sameta ba bata zuwa makaranta kuma babu waya ahannunta duk na damu" da mamaki ya ce"kema bakisan inda take ba toh, kina ƙawarta bakisan gidan su ba?" hawayen da yake zubowa afuskarta ta goge sannan ta ce asanyaye "Ai bata gidansu saboda babanta ya rasu Mamanta kuma bata garin nan tana gidan relative ɗinta kuma ban sani ba" dafe kansa ya yi cikin ɗunbin damuwa ya ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun wlh ina matukar son ganin yarinyar nan yanzu babu inda zan ganta hasbunallah" kallonsa kawai Aysha tayi dan ita tama fishi son ganin Fattum tunda suke basu taɓa rabuwa irin haka ba koda kuwa hutu aka yi Aysha zataje gurinta su zauna suyita hira amma sai gashi cikin lokaci ƙanƙani ta nemata ta rasa, shuru ya yi na wasu mintuna sai kuma ya ce"shikenan zan tafi in sha zan sake shigowa naji ko akwai wani abu da kika samu" okay Aysha ta ce masa sannan ya zaro rafar yan ɗari biyu a aljihunsa yana kallonta ya miƙa mata ya ce"take this" girgiza kanta ta yi ta ce"A'a nagode sosai" murmushi ya yi sannan ya ajiye mata kuɗin gefenta ya bar wajen tana nan tsaye har taga tashin motarsa sannan ta ɗauki kuɗin ta shige gida. Tsaki Saleem ya yi ya ce"kai ma ai kayi ganganci har zaka bari baka karɓi address nata ba to yanzu gashi babu wayar kuma bakasan inda take ba" hannunsa ya sanya ya wargatsa gashin kansa sannan ya ce"idan har inada rabon aurenta nasan tabbas watarana zamu sake haɗuwa naji haka cikin rai na" gyaɗa kansa ya yi ya ce"Ehh Lallai to Allah ya tabbatar da Alkhairi" jingina ya yi da jikin kujerar ya ce"oh god!!" kallonsa kawai Saleem ya yi sannan ya girgiza kai. Kallonta kawai Jawaad yake har ta karasa sakkowa daga benen tafiya take kamar wacce kwai ya fashewa ajiki har ta ƙaraso wajensu, tsugunawa tayi tana cize laɓe saboda wata irin azaba data ziyarci kwakwalwarta, Imad ne ya ce"tashi anan wajen" toh ta ce sannan ta kama kujera tana niyyar tashi dakyar ta miƙe ta haɗa wani uban gumi ta zauna kan kujerar tana maida numfashi, Jawaad ne ya ce"bakida lafiya ne Fattum?" girgiza masa kai ta yi ya ce"A'a ki faɗa min gaskiya mene yake damunki" a hankali ta kallesa hawaye na taruwa a idanunta ta ce"yaya ƙafata ciwo take kullum haka" Jawaad ya ce"Ayyah sannu kinji bari zan kawo miki magani sai ki dinga shafawa okay?" gyaɗa masa kai ta yi Imad ya ce"have you eaten?" girgiza kanta ta yi ya ce"tashi kije ki ɗebi abinci" kwaɓe fuskarta ta yi bata ce komai ba, ganin yanda tayi yasa ya ce"ko maid ta kawo miki?" girgiza masa kai ta yi ta ce"A'a na ƙoshi ni" haɗe rai ya yi sannan ya kira wata maid cikeda ladabi ta ce"gani sir" "ki kawo abinci amma bamai nauyi ba something liquid haka" okay ta ce sannan ta juya tabar wajen. Juyi kawai take kan gadon amma ta kasa bacci banda ciwo babu abinda cikinta ke mata gashi daman wajen ya yi wani irin ja da kuma kumbura tun ranar da Imad ya daketa koda wasa bata taɓa nuna wani abu agabansa wanda zai sa ya fahimci haka ba dakyar take iya taka ƙafarta duk jijiyoyin wajen sun riƙe haka take kasancewa duk dare cikin rashin samun bacci wadattace, Fitowar ta kenan daga wanka tana tsaye tana ƙoƙarin shafa mai ajikinta batasan sanda ya shigo ɗakin ba har ta gama shafa man sannan ta zame towel ɗin da niyyar ɗaukan rigarta "Keeeeee!!" Afirgice ta juyo tana kallonsa dan batasan sanda ta karasa yarda towel ɗinba hankali tashe yake kallon cikin nata yama kasa furta komai ita kuwa fashewa tayi da kuka tana ƙoƙarin rufe jikinta batasan ko kaɗan tunanin Imad bai zo wajen ba, tsugunawa ya yi gabanta yana kai hannunsa kan cikin nata, sosai abun ya bashi mamaki haɗi da tashin hankali dan bai taɓa ganin irin abun azahiri ba saidai akaratu bakinsa na rawa ya furta "Keeee..keee...Mee..mene wannan?" Cikin kukan ta ce"dan Allah Uncle kayi haƙuri dan Allah karka dakeni wlh mutuwa zanyi dan Allah Uncle" miƙewa ya yi kawai bai ce komai ba ya miƙa mata rigarta sannan ya juya ya yi waje, rigar ta sanya har sannan tana ci-gaba da kukanta dan gani take kamar sake dukanta zai yi, shi kuwa rasa abinda zai yi, ya yi duk hankalinsa ya tashi ko yaushe ta samu wannan ciwon???. Suna shiga cikin asibitin aka shige da'ita emergency Imad kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye dan tashin hankalinsa ɗaya abinda zai cewa Daddy idan ya tambaye shi ya kuma san halin Daddyn nasa, Jawaad ne ya ƙara so yana kallonsa amma ya kasa ce masa komai dan ransa a matuƙar ɓace yake kusan 5mins suna tsaye kafin ya ƙaraso yana kallonsa ya ce"friend wane bashida lafiya?" asanyaye Imad ya ce"wlh yarinya ce kuma gaskiya abun ba karami bane please kaje ka gani" okay ya ce sannan ya kalli Jawaad da sauri ya sake kallonsa ganin kamar yaso ya tuna inda ya sanshi kallonsa shima Jawaad ya yi amma bai ce komai ba shima Kamal shigewa ya yi saboda ya duba mara lafiyar. Kusan mutuwar tsaye Kamal ya yi ganin Fattomah kwance an sanya mata oxygen bai taɓa tsammatar haka ba dukda ya yi mamakin ganin Jawaad amma bai ɗauka ita ce batada lafiyar ba tunaninshi ɗaya yanzu mene ne alaƙarta da abokinsa Imadudden har zai kawota asibiti shidai yasan shi kaɗai iyayensa suka haifa bare yace ƙanwarsa ce wannan tunanin shine abinda ya sanya duk ya zama moody har aka shiga da yarinyar domin dubata. Da sauri Jawaad ya fizge takardar hannun Kamal ɗin cikin son gazgata abinda Kamal ɗin yake faɗa ji ya yi numfashinsa na neman barin jikinsa lokacin daya gama karanta takardar bai taɓa tunanin haka ba koda kuwa cikin mafarki ne zama ya koma ya yi jin jiri na neman ɗibansa ba shi kaɗai ba shima kansa Kamal ya kasa magana ji yake inama ace mafarkine wannan abinda yake faruwa ɗin ba gaskiya ba, inama ya farka daga wannan mafarkin wanda yake neman tarwatsa masa farin cikinsa zuciyarsa da kwakwalwarsa duk a dagule suke kuma cikeda tambayoyi masu tarin yawa. Kamar wani zaki haka ya mike yana riƙeda takardar ya fice daga cikin office ɗin, shigowarsa kenan bayan yaje gida dan ɗauko mata kaya ganin Jawaad tsaye ya haɗe hannayensa a ƙirji yasa ya ƙara sa ya dafa shi cikin sanyin murya ya ce"Jawaad ya jikin nata?" "Ka kyauta Imad!! Ka kyauta wannan shine cika alƙawari haka shine daidai wllh ban taɓa zaton haka daga gareka ka koda kuwa a mafarki ne ban ɗauka zaka kasance mai son zuciya kuma mara imani har haka ba nasan kawai Kanada saurin fushi da fusata amma ban yi zaton kai azzalumi neba Imadudden kaci amana kayi yaudara kuma kayi zalunci wanda kai ma kasan Ubangiji bazai taɓa barinka ba kai ɗin azzalumi ne!!!" Kallonsa kawai Imad yake yi tunda ya fara maganar dan baisan abinda yake nufi ba kuma baisan akan me yake magana duk sai ya ruɗe gashi Jawaad sai surfa masifa yake ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba "Ka sanar dani wai mene ne abinda ke faruwa Jawaad?" murmushin takaici Jawaad ya yi sannan ya miƙa masa takardar hannunsa, ahankali ya warwareta ya fara karantawa anutse, wani irin gumi ne ki tsassafo masa tundaga tsakiyar kansa da sauri ya kalli Jawaad yaga shi yake kallo da alamar tuhuma, zama Imad ya yi kan wata kujera daya gani wajen dan ji yake kamar ya yi hauka ya rasa mene ne yake shirin faruwa farin ciki ya kamata ya yi ko kuwa baƙi ciki???, damuwa ce fal ransa da kuma tashin hankali dan baisan da wane idanu zai tari Daddy ba shine babban tashin hankalinsa, kallonsa Jawaad ya yi sai kuma ya ce "Imad why??why??why??, Dan Allah wace irin tsana ka yiwa wannan yarinyar?, mene laifinta daka yanke shawarar rabata da farin ciki?, me ta aikata maka wanda kake tunanin ta cancanci wannan hukuncin?, akan wane dalili ne Imad?" Dafe kansa ya yi dan bashida amsar da zai bawa Jawaad a halin yanzu dan kome zai faɗa masa bazai ɗauka ba. Miƙewa Imad ya yi bai ce komai ba ya yi waje yana haɗa hanya saboda ciwon da kansa ke masa, da kallo Jawaad da bisa yasan tunda ya yi haka bazai faɗa masa sannan bane shiyasa shima ya rabu dashi. Kallonsa Kamal ya yi jiki babu kwari ya ce"yarinyar matarka ce daman?" girgiza masa kai ya yi ya ce"A'a matar ɗan uwa nace" "wanne kenan?" "Imadudden" da sauri Kamal ya kalleshi sai kuma ya sunkuyar da kansa yana tunani yaushe Imad ya yi aure bashida labari?, kuma ina yaga Fattomah ya aureta?? "Zan yi maka bayani dalla dalla da zarar na samu lokaci" kallonsa Kamal ya yi dan duk a zatonsa azuciyarsa ya faɗi maganar bai ɗauka afili bane. Kamal ya ce"abinda ke jikinta ya ɗan daɗe gaskiya kuma bata samun kulawa yanda ya kamata that's why har ba'a gane ba cikin jikinta zai kai kusan 7weeks saboda haka tana da buƙatar kulawa sosai, sannan maganar abunda yake cikinta ciwone taji kuma gaskiya ya yi worth sosai dole saidai ayi mata aiki dan gyara wajen" ajiyar zuciya Jawaad ya sauke sannan ya ce"okay shikenan a shirya yi mata aikin" Kamal ya ce"to ai ba zai yiwu ayi mata aikin ba saidai idan har an cire cikin dake jikinta shine kawai zai bada wannan damar" shuru Jawaad ya yi sai kuma ya ce"dole saidai a cire cikin?" gyaɗa masa kai Kamal ya yi, miƙewa ya yi ya ce"taɓ bari naje wajen Imad sai muyi maganar" Okay Kamal ya ce sannan ya juya ya fita. Shuru Imad ya yi sai kuma ya ce"why ana bata magani ai hakanma zai yiwu ba dole sai an cire cikin jikinta ba, beside kaima kasan bazan taɓa yarda acire abinda ke cikinta ba saboda idan babu shi nifa bazan sake samun wani cikin ba har abada bazan iya wannan kasadar ba gaskiya" Jawaad ya ce"Imad magana fa ake ta lafiyarta idan batada lafiya ka faɗa min ta ina zata iya haifa maka ɗan?, sannan idan Allah yaso sai kaga nan gaba ka sake samun wani cikin daban yanda kayi da niyyar taimakon rayuwarta to wannan karanma haka zaka yi domin shine kaɗai mafitarka" girgiza kai ya yi ya ce"Jawaad bafa zan yarda ba shima kuma Kamal ɗin yasan da hakan wlh bazan taɓa yarda ba zan dai siya mata magani daga Naira ɗaya har abinda ya turewa buzu naɗi koda zan rasa duk abinda na mallaka bazan gaji da siya mata magani ba duk tsadarsa kuwa amma gaskiya i won't tolerate cire ciki bazan taɓa iyawa ba" miƙewa Jawaad ya yi ya ce" zan koma asibitin idan ka gama yanke shawara sai ka biyo ni dan zaka yi sign jikin file kafin a shiga aiki" miƙewa shima ya yi ya ce"Jawaad koda zamu shekara ɗari kalma ɗaya zan sake faɗa bazan yarda ba i won't tolerate Kuma nima yanzu zan je asibitin" gaba Jawaad ya yi yana binsa a baya. Cikin kwantar da murya Kamal ya ce"dan Allah Friend kayi haƙuri ka bari ayi mata aikin nan kaga wlh tana sake kaiwa matakin ƙarshe dan Allah ka duba maganar" ransa ne ya fara ɓaci ya ce"kunga please ku daina faɗa min irin waɗannan maganganun please wlh bazan iyaba okay ku rabu dani bance kowa sai yaji tausayina ba amma ni ina tausayin kaina Wlh bazan iya ba" cikin faɗa Jawaad ya ce"dole kace haka tunda kana tunanin ka gama da rayuwar yarinya kayi mata ciki ka yaudari mutane da dama da cewa baka sonta ka fake da cewa kayi ne saboda ta samu lafiya amma yanzu ka kasa yin abinda zaka taimaketa wlh Imad ka yi matukar bani mamaki kuma bari na faɗa maka idan har baka yarda an zubar da cikin nan ta daɗin rai ba toh wlh saina ɓallo maka ruwa sai na yi abinda ko kanaso ko bakaso dole ka bari a zubar saboda haka zaɓi ya rage naka" Wani banzan kallo Imad ya yi masa sannan ya ce "Idan ka fasa baka ƙaunar Allah da Annabi Jawaad wlh babu wanda ya isa ya sanya ni nayi abinda banyi niyya ba kuma Wlh kowane zaka faɗa wa bazan bari a zubar da abinda ke cikin yarinyar nan ba saboda haka karka fasa kaje duk inda zaka" Waje Jawaad ya yi bai ce komai ba zuciyarsa a matuƙar ɓace, kallonsa Kamal ya yi kafin ya yi magana ya ɗaga masa hannu ya ce"dan Allah Kamal" shuru ya yi bai faɗi abinda y yi niyya ba yace masa "ina take?" nuna masa ɗakin ya yi sannan yabar wajen. Zaune yake gefenta yana bata tea a hankali take karɓa ko rabi bata sha ba ta girgiza masa kai babu yanda bai yi da'ita ba taƙi karɓa hakan yasa ya ajiye, komawa tayi ta kwanta tana sauke numfashi kusan 5mins sai kuma ta ce"Uncle" da sauri ya ce"na'am" "ka siyamin mango please" shafa kanta ya yi ya ce"mango ki ke so?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"toh bari na siyo miki amma kar kiyi bacci" gyaɗa masa kai tayi sannan ya tashi ya gyara mata duvet ɗin ya fice daga ward ɗin, waro idanunta tayi dukda yanda sukayi ciki bakinta na rawa ta ce" Da..Da ..Daddy!" riƙe hannunta ya yi yana jin kamar ya fashe da kuka ya ce"Faɗeematoh" fashewa tayi da kuka tanajin numfashi, girgiza mata kai Daddy ya yi ya ce"daina kuka irin haka kinji Faɗemah I'm sorry ni ne duk na jawo miki kinji I'm so sorry Fateemah I'm....." Kasa ƙara sawa ya yi saboda wani kuka daya ci ƙarfinsa rabonda ya yi kuka a rayuwarsa har ya manta sai yau dalilin abinda Imad ya yiwa Fattomah, shafa kanta ya yi ya ce"don't worry dear karki damu zanyi abinda ya kamata zan kwato miki haƙƙinki" Kallon Jawaad ya yi ya ce"ɗauketa Jawaad" okay Jawaad ya ce sannan ya ɗauketa kamar yanda Daddy ya bashi umarni suka fita daga asibitin. Kai tsaye Airport suka shige inda jirginsu ke jiransu cikin mintuna kaɗan jirginsu ya ɗaga zuwa Abuja. Kalle-Kalle ya shiga yi a ward ɗin amma bai ga alamar ta ba, har toilet ya duba amma babu Fattum fitowa ya yi yana ganin wata nurse ya ce"hyyy please Kinga inda Fattomah tayi?" da yake sun santa ta ce"Eh sir General Ibrahim ya tafi da'ita tun ɗazu" ji ya yi gabansa ya yi wani irin mugun faɗuwa ya ce"yaushe?" ta ce"sun ɗan jima dan gaskiya yanzu sun kai Abuja" bai tsaya sake sauraronta ba ya yi waje cikin tashin hankali. Cikin yan mintuna ya gama haɗa komai zuwa rabin awa jirginsa ya sauka cikin garin ABUJA. Sosai yake kallon compound ɗin gidan ganin motoci dayawa yasa ya tabbatar da cewa ba Daddy ne kaɗai ya dawo ba, ko sallama bai yiba ya shiga parlon. Zaune ya tarar dasu da alama wani tattaunawa suke akan maganar, tsayawa ya yi daga gefen kujera yana kallon Mommy ko gaisheta bai iya yiba ya ce"Mommy ina FATTOMAH?" kallonsa kawai tayi amma batace komai ba ya kalli Daddy wanda yake kallonsa tunda ya shigo, Jawaad ne wanda ke zaune gefen Daddy ya kalla ya ce"tana ina Jawaad?" shiru shima ya yi masa ya yi tsaki sannan ya kalli Daddy ya ce"Daddy she's under medication Bai kamata ka ɗaukota daga asibiti ba kamata ya yi......" Wasu maruka da Daddy ya yi masa ya sanya ya riƙe kuncinsa kafin ya yi magana Daddy yara magana cikin tsananin baƙin ciki da ɓacin rai "Kai har kanada bakin magana?, har kanajin zaka iya zuwa ka tsaya a gabana Saboda bakada kunya kenan?, na baka yarinya amana kawai ka zauna da'ita na wata uku shine abinda ka kasa, har ka iya saka hannun ka dinga dukanta, ka zageta kaci mutuncinta duka bai isheka har ka iya yi mata ciki bayan lalurar daka sanya mata kuma shine yanzu ka iya takowa kazo nan wajen ko?" Shiru Imad ya yi bai ce komai ba Daddy ya cigaba faɗin"wallahi idan har sunana Ibraheem Baira babu kai babu Fateema har abada babu wata alaƙa da zata haɗaku sannan cikin dake jikinta sai an zubar dashi a yau ba sai gobe ba kai kayi kaɗan ka raina min hankali ba'a haifi ɗa ba, zan nuna maka true colour na yanzu" afusace Imad ya kalli Daddy da duk sauran mutanen dake parlon sai kuma ya ce "Daddy I'm sorry abinda ya faru zan kuma karɓi laifina duk inda za'a je amma wlh bazan taɓa yarda a zubar da abinda ke cikin yarinyar ba saboda daga shi bazan taɓa samun wani ba kamar yanda ka sani a baya yanzu ma haka take saboda haka na shirya karbar kowane irin hukunci amma banda na cire cikin dake jikinta I'm sorry" Murmushi Daddy ya yi sannan ya ce"Okay mu zuba mu gani tsakanin ni dakai zan ga mai gaskiya" Mai martaba ne ya mike yana kallonsu ya buɗe baki zai magana, ɗaga masa hannu Daddy ya yi ya ce"babu ruwanka Muhammad banason kowa ya shiga maganar nan kowa ya yi shiru" shuru mai martaba ya yi dan tunda yaga Daddy ya yi haka to ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci kuma abune ma wuyaci ya sakko. Kallon Imad ya yi ya ce"banason ganin cikin gidan nan ina the next 10mins kabar gidan nan" Imad ya ce"I'm sorry Daddy zan tafi amma ka fara kirawon Fattomah saboda tare zamu.........." Wasu tagwayen maruka Daddy ya ƙara sauke masa a fuskarsa zuwa lokacin fuskar tayi jajawur saboda kasan cewar sa fari cikin zallar ɓacin rai Daddy ya ce "Wlh na rantse da Allah baka isa ka ɗauki yarinyar nan ba har ƙarshen rayuwarka kuwa sannan kuma abinda ke cikinta tamkar an zubar dashi ne ka rubuta takardar saki ka turon kamar yanda na tsara" Cikin zallar ɓacin rai Imad ya shige cikin bedroom ɗin Mommy, da kallo suka bisa har ya fito hannunsa riƙe da Fattomah wacce take kallonsa sai rarraba idanu take, yana zuwa ya kalli Daddy ya ce"I'm sorry Daddy zan tafi da'ita saboda she's under medication kamar yanda na faɗa ba zai yiwu abarta haka ba" gaba ya zo zai yi Daddy ya sha gabansa yana yi masa wani irin mugun kallo mai cikeda ma'anoni daban-daban ya ce". *End of book 1* *Shin mene ne abinda Daddy zai ce?* *Shin wane hukunci zai yanke akan Imad?* *Shin dagaske za'a zubar da cikin dake jikin FATTOMAH ko A'a?* *Shin FATTOMAH zata auri yaya Jawaad ko A'a?* *Shin da gaske Kamal zai aureta ko A'a?* *Shin IMADUDDEN zai cigaba da zama da FATTOMAH ko kuwa za'a raba auren kamar yanda Daddy ya yi Alkawari?* *Shin Ammi zata dawo Kano ko A'a?* *Shin Aslaam zai auri FATTOMAH kamar yanda ya ci alwashi ko A'a?* *Shin FATTOMAH zata haife ƴaƴan IMADUDDEN ko kuwa.....?* *DUKA ZAKU SAMU AMSOSHIN TAMBAYOYINKU CIKIN LITTAFIN FATTOMAH💞 NA BIYU (2)WANDA YAKE KAN KUƊI NAIRA ƊARI BIYAR 500#* *Zakuyi making payment ta wannan account ɗin 9086030007 Hauwa lawan opay digital service evidence via 09086030007 or 07041901078 Whatsapp only* *DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁENI TA WANNAN NUMBER 09086030007 OR 07041901078* MUHAƊU A BOOK 2 DOMIN JIN YANDA ZATA KASANCE, TEAM FATTOMAH AND TEAM IMADUDDEN 💞💞. *Ameenatou ce#* *Nanameera ce#*