[12/12/2017, 5:59 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* MRS NN ONE *Bismillahir Rahmanirrahim* Yaa Allah yadda ka bani ikon farawa lafiya Allah kasa na gama lafiya batare da na kauce hanya ba ALLAHUMMA amin Bawan Allah labari ne da ke cike da tsantsar tausayi tawwakali talauci da kuma soyyaya wanda bawan Allah labarin wani matashine wan da iya yensa basu karfi yatashi shine ak'ark'ashin kulawar mahaifiyarsa, Ku biyoni domin jin ya labarin zai Kasan ce ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page1⃣ Zaune yake akan dakalin k'ofar gidan su ya jingina da jikin gini daganin alama yana cikin tsananin damuwa hakan yasa har wani yazo yaita sallama bai jishi ba sai da ya dafa kafad'ar sa sannan yace " Haba Abdallah wannan wani irin tunani ne ina ta sallama baka jini ba " Wanda aka kira da Abdallah yace"uhum Umar kenan ba dole kaga ina tunani ba kafi kowa sanin halin da nake ciki dole nayi tunani " "Hakane aboki na amma ya kamata ka rage Dan kar ka haifar wa kanka da wata matsalar "cewar Umar "Ina k'ok'arin ragewa Umar abin ne yafi k'arfi na wallahi" "Allah ka iya mana ka kawo mana mafita" "Amin" cewar Abdallah Umar ne ya ce"ya naga ka zauna ko ba muda wurin zuwa ne yau? Murmushi Abdallah yayi Wanda da gani bata wuce fuskarshi ba yace" akwai gurin zuwa mana sai dai ba kud'i , dama tunani ni na idan na samu kud'i da safen nan in saima su inna abin da zasu CI , to gashi kuma duk k'ofofi sun kulle" Umar shiru yayi yana nazarin abokin nashi sannan yace "tashi muje" "Ina kenan? Cewar Abdallah "Bakin titi zaka raka ni" "to" kawai yace sannan ya mik'e sukA d'au hanya, Suna tafe suna firarsu irin ta abokai kuma aminai suka k'arasa , k'ofar shagon wani me shayi Umar ya ja birki , Abdallah ya kalleshi ya ce"me za muyi anan?" "Tsaya ka sha kallo "ita ce kawai amsar Umar, ya zagaya yayi ma mai shayin magana ya dawo ya ce mawa Abdallah "bismillah" ya nuna masa wata kujera da ba kowa akai ,. Bai musa ba ya zauna suna zaune a wajen kusan minti biyar ba Wanda yayi magana cikin su , sai ga mai shayi ya kawo musu , tea ne aka had'a musu dai-dai shan talaka da bread , Abdallah ya bud'e baki zai yi magana kenan Umar ya katse shi"da kata ustazu bana son wani k'orafi CI abin cin ka" Umar ya k'arike maganar yana janyo nashi kofin Ba yanda Abdallah ya iya domin baya son ganin b'acin ran abokin nasa Sam ya ja kofin shi tare da bismillah ya fara aikawa cikin shi Wanda rabon shi da abinci tun safiyar jiya , Bayan sun natsa ne Umar ya sallami me shayi tare da karb'ar wata Leda a hannun shi sannan suka kamo hanya "Umar bansan da bakin da zan gode maka ba , nagode da taimakon da kake yi min Allah ya saka maka da alheri Allah ka Nuna min ranar da zan faran ta maka kaima " "Amin , Abdallah bana buk'atar godiya daga gare ka taya za'a yi na samu kud'i har na iya kashe wa ba tare da kai ba wannan ba mai yuwuwa bane" "Dole na gode maka aboki na daga kai sai mahaifiya ta kuke gane meke damu na" "Uhum" kawai Umar yace domin ya san gaskiya Abdallah ya fad'i , Da haka suka k'arasa k'ofar gidan su Abdallah dukan su atare suka shiga gami da sallama , Mama ce a tsakar gidan tana zauna ita da wata matashiyar yarinya suna zaune akan tabarma kowa da hijab ajikin shi da alama sallah suka idar(salatul duha) Yarinyar ce ta amsa musu domin Mama addu'a take yi "Ina kwana yaya Umar?" Cewar. Yarinyar "Lafiya lau hafsa ya gida?" "Lafiya lau"inji yarinyar da aka Kira da hafsa Dai-dai nan Mama tace" maraba da Umar" murmushi yayi sannan yace "yauwa Mama , kun tashi lafiya ?", Mama ta bashi amsa da "lafiya lau " Sannan ya juya ya ce ma hafsa " ke karb'a wannan kije Ki had'o" Hafsa ta karb'a ledar ta wuce D'an k'aramin kitchen d'in su. Sai alokacin Abdallah yayi magana " haba Umar kaima fa ba kud'in nan kake da shi ba amma sai kai ta wani wahala" "Umar ya turb'une fuska yace "yan zun Dan nayi ma Mamana wani Abu shine wahala to ni Neman albarka nake nema " yadda ya k'arike maganar kamar yayi fushi basu yi aune ba sai jinshi suka yana fad'in " nabar Ku cikin amincin ubangiji" Aiko Abdallah ya zabura ya bishi , da k'yar ya shawo kanshi ya tsaya ya saurare shi , nan ya bashi hak'uri tare da tambayar ina ya samu kud'i "Acikin Raguna nane tun jiya d'aya bata da lafiya yau da safe da naga asara zanyi shine na yanka ta na kai kasuwa abanza mahauta suka siyeta dubu tara "ya k'arike maganar cikin takai CI "To amma Umar ai kana da hidima"Cewar Abdallah "Kaga gida uku na raba kud'in biyu naba umma narik'e d'aya nida aboki na " Ajiyar zuciya Abdallah yayi sannan yace "Allah ya Sanya ma kud'in albarka" "Amin" cewar Umar sannan suka bazama cikin gari For comment 08165728746 [12/13/2017, 8:32 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE*💋 Dedicated to PURE MOMENT OF LIFE WRITERS ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 2⃣ WAYE ABDALLAH Abdallah d'ane ga Abdallah asalin mahaifin shi D'an wani k'auye ne ahanyar jos ya baro gida sakamakon rasuwar iyayen shi kuma shi kad'ai iyayen shi suka Haifa , alokacin da ya baro gida yana da matar aure me suna Hindatu itama auren zumunci akayi musu da ita , Abdallah ya tattara yan k'wandalolin da ya ke dasu ya taho garin zazzau domin Neman kudi , yasamu wani D'an k'aramin gida yasiya suka zauna shi da matarshi Wanda har zuwa wannan lokacin bata da ciki , yakan fita kullum ko zai samu abin yi amma babu rannan kawai sai ya yanke shawarar bari yaje bakin kasuwa ko dako yayi , to ahaka yake samu yana ciyar da matar sa duk da ba kullum ake samu ba, Kasan ce warsa shida matarshi basu da hayaniya yasa suka zauna lafiya da mutanen unguwar , gidan da ke kallon gidan Abdallah gidan wani malami ne mai suna Malam Kabiru mai almajirai wani lokacin idan Abdallah ya dawo k'adugo yakan zauna yayi karatu awajen shi Kasan cewar shi mutum mai son karatu , akwana a atashi ba wuya sherar su Abdallah biyar agarin Zaria , suna rayuwar su yau samu gobe rashi , Akwai wani mak'ocin Abdallah wani tsanin gidan shi Dana mak'ocin gida biyar ne sunan sa Jafar shima dai rufin asirine kawai gareshi shiyasa abotar su tazo d'aya da Abdallah , Wata rana sai suka yanke shawarar suje su nemi aiki gidan bulo ko ruwa ne surunk'a d'ebowa , aiko basu sha wahala ba tunda sunsan me gidan bulo d'in , Kwanci tashi ba wiya har suma aka koya musu yadda Zasu had'a bulo wata , Wata rana Hindatu ta tashi da zazzab'i ciwon kai da jiri sai ranar sanyi take , akwai wani PHC asaman layin su nan ya kaita gwanjin farko aka tabbatar mai da tana da ciki murna kuwa ba'a fad'uwa tunda ga lokacin ya koma bata kulawa na musamman Dan duk wani aikin gidan shi yake yi Alokacin da cikin Hindatu yakai wata takwas ya shigo mata da wani madai-daicin rago tayi murna sosai tare da godiya , bayan sati biyu Abdallah yaje gurin aikin shi sai man injin d'in ya k'are be jira kowa ba ya d'auko mai ya shiga d'urawa yana cikin haka ne wani noti ta k'asan injin d'in ya fita yana gama d'ura man ya cire rigarshi ya kwanta ta k'asa saida ya lek'a ya ga Ashe ma notin ba d'aya bane kafin ya gama tunanin da zai yi injin d'in ya fad'o masa a k'irji bai sake sanin inda kanshi yake ba sai dai ya farka ya ganshi gaban Hindatu ta na ta faman kuka k'irjin shi duk an d'aura mai su da farin bandeji da k'yar ya iya d'aga hannu ya bubbuga mata bayan ta , sai sannan ne ta juyo tace mishi sannu Malam d'aga mata kai yayi dan ya kasa magana k'irjin shi ya mishi nauyi sosai , tunda ga ranar baya iya komai idan ya fara tari haka yake fitar da jini guda guda , ranar wata juma'a kuwa Abdallah ya rasu , Allahu Akbar mutane sunji mutuwar shi sosai musamman ma abokan shi guda biyu Malam Jafar da Malam Kabiru, Bayan rasuwar Abdallah da sati d'aya Hindatu ta haihu tare da taimakon matan Malam Kabiru da Jafar , matar Jafar lokacin tana da goyon yaron ta Umar D'an wata biyar , Hindatu ta haifi d'anta namiji yaro sak kamar shi da Baban shi dangin ta da suka zo sunso su maida ta gida amma fir ta k'i hakan yasa suka hak'ura suka barta mak'otan nan nata su ke ciyar da ita , ranar bakwai yaro yaci suna Abdallah . Haka rayuwa ta cigaba da garama Hindatu idan mak'otanta sun samo su bata randa basu samu ba kuma kowa ya sha ruwa ya kwanta , Lokacin da Abdallah ya kai shekara bakwai Malam Jafar ya had'a shi da Umar ya sasu amakaran tar boko ta gwamnati , Abdallah da Umar sun taso cikin son junan su da tausayin iyayen su wani lokacin da Kansu suke zuwa bakin kasuwa suyi dako su sami 'yan kud'i su kaima iyayen mata sukuwa suyi ta sa musu albarka Tun suna k'anana suke zuwa d'aukar karatu wajen Malam Kabiru har suka sauke bayan sun sauke sai ya sa musu littafai Suna SS3 mahaifin Umar ya rasu anan karatun su na boko ya tsaya , Abdallah da Umar suna iyakar bakin k'ok'arin su wajen ganin sun ciyar da iyayen su amma abin yana fin k'arfin su wataran gwanda ma Umar mahaifin shi da aka raba gado Maman shi ta fara sana'ar k'ulla-k'ulle dashi suke rufa ma Kansu asiri Lokuta da yawa Malam Kabiru yana musu nasiha akan suji tsoron Allah kada talauci ya sa su rasa imanin su da irin wad'an nan nasihohin kullum Malam ke musu Da temakon Malam suka samu koyar wa a wata islamiya da ke wata unguwa babbar makaranta ce sai dai albashin ta mai K'aranci ne baya isarsu d'awai niyar su Wannan shine BAWAN ALLAH kamar yadda mahaifiyar shi me kiran shi dan bats fad'in sunan sakamakon sunan mijin ta kuma sunan d'anta na fari For comments 08165728746 [12/13/2017, 5:36 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *I dedicated this page to you , masoyana a koda yaushe ina jin dad'in yadda kuke k'arfafamin gwaiwa na Gode Allah ya bar k'auna AMEERT Nd FATIMA (K'awwali)❤* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 3⃣ *CIGABAN LABARI* Haka suka k'araci zaga gurare da kasuwwani ba su samu komai ba har la'asar ta gabato , hakan ya sasu koma wa gidan ba Dan sun so ba , Da sallama ya shiga gida Mama da hafsa ne suke hirarsu jefi-jefi , suka amsamai sallamar ne ya shiga Cikin sanyin jiki ya nemi guri gefe ya zauna sannan ya juya ya kalli mahaifiyar sa ya ce "Kun wuni lafiya Mama?" "Lafiya lau ya k'ok'ari bawan Allah?" Ta kalli D'an nata cike da tausaya wa "Alhamdlillah Mama" cewar Abdallah daya ke k'ok'arin tashi , domin kiran sallar da yaji , Bayan sunyi sallah shi da aminin nashi islamiyar da suke koyar wa suka je , Abdallah shine malamin k'ur'an da tajweed , Umar kuwa yana daukan ahdari da tauheed Suna zuwa kowa yake shiga ajin shi Bayan sun dawo daga islamiya k'arfe takwas na dare suke zuwa d'aukar karatu wurin Malam Kabiru , Yauma kamar kullum sunje karatu Malam ke musu fad'a " wai yanzun Ku haka zaku zauna ba zaku yi aure ba Ai aure shike sa aga mutum da daraja kullum" "Insha Allahu idan lokaci yayi za'a yi "cewar Umar Shiko Abdallah shiru yayi Malam ya ce "Bawan Allah baka ce komai ba " Ajiyar zuciya Abdallah yayi sannan ya ce " yanzun Malam a yadda muke d'in nan wa zai d'auki d'iyar sa ya bamu , bayan bamu da abinda zamu ciyar da ita dashi balle kuma sauran buk'atu na duniya " Malam ya ce "hakane Abdallah amma ai ba'a rasa na Allah" "Hakane Malam " cewar Umar "Kuma ni gashi har na fara nema muku aure Dan zaman Ku ahaka baya min dad'i " Cikin sauri Umar yace " Malam kad'an yi hak'uri zuwa nan gaba kad'an" Malam yayi murmushi ya ce "Allah ya kaimu " Abdallah kuwa cewa yayi "duk yadda kayi Malam dai- dai ne" Nan Malam ya sa musu albarka sannan suka tafi , Suna fitowa Umar ya kalli Abdallah ya ce "Ustaz naga kamar kayi na'am da maganar Malam ne " Kallon shi Abdallah yayi sannan ya ce " Malam tamkar Uba yake aguri na Dan haka babu zab'in da zai min na bijire masa dole Sana'a zannema " Umar ya zaro ido"wace irin Sana'a kenan?" " zanyi tunani idan na yanke shawara zan gaya maka zuwa gobe da safe" cewar Abdallah yana k'ok'arin shigewa gida "Allah ya jisshemu alkhairi " Umar ya fad'a da D'an k'ar fi , Suka yi sallama kowa ya shige gida *DA SAFE* Yauma kamar kullum ba komai agidan suna zaune sai ruwa da suke D'an sha jefi-jefi , Shiko Abdallah yana can d'akin shi kwance kan shamulokin katifar shi yana ta tunanin sana'ar k'arfin da zaiyi , idan yace wannan ya ce A'Ah daga k'arshe dai ya yanke shawarar yin sana'ar wanki da guga , wannan shawarar ya tsayar Dan haka ya mik'e ya saka rigar shi ya fita tsakar gida Bayan sun gaisa ne sai ga Umar ya shigo da kwanon sha , a hannun shi ya d'ire a gaban Mama ,bayan sun gaisa Mama tace "Umar me muka samu ne?" "Murmushi yayi yace "koko ne Mama " Mama tace "an gode Allah ya saka da alheri" "Amin " dukkan su suka ce Bayan sun gama shan kokon ne Umar yace " Abdallah wai wace Sana'a zamu fara ne" Abdallah yayi gyaran murya yace "wanki da guga" Umar ya zaro manyan idanun nan nashi ya ce "wanki da guga?" "Eh, Kasan dalilin da ya sa na zab'e ta?" Umar yace "A'ah" "Saboda ita kad'ai ce samu yi ba tare da mun kashe ko sisi ba " "Hakane Abdallah Allah ya taimake mu " Dukan su suka amsa da "Amin" Mama ma fatan alheri ta musu , Cikin sa'a kuwa suka samu kasuwa , da yake gidan su Abdallah akwai rijiya kuma ba yara nan suke taruwa suyi sana'ar su , Da yake basu sa ha'inci a sana'ar suba hatta masu hannu da shuni na kewayen su suna kawo musu , Hafsa ce zaune tana tsintar wake zata dafa musu garau-garau , nan k'awarta Ummi ta shigo tare da sallama , Ummi akwai ta da son barkwanci ta cewa hafsa "Ah k'awata yaushe aka fara shiga kitchen?" Wata harara hafsa ta aika wa Ummi sannan ta ce "kefa 'yar rainin wayau ce wallahi yau kika fara ganina nayi girki?" Ummi tayi dariyar mugunta tace "to aike hafsa abinshi naki ne na ganin dama sai Mama tace kiyi kike yi" Hafsa ta tuntsire da wata dariya tace " kamar ko kin sani" Suka tafa Ummi tace "AI na sanki ne k'awata, ina Mama ," Hafsa tace "Mama taje gidan su yata Umar Gwago ce bats jin dad'i" "Subhanallah Allah ya bata lafiya "cewar Ummi Hafsa ta amsa da "amin" Nan Ummi ta taya ta suka gama sukayi shirin islamiyya [12/14/2017, 9:58 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *Dedicated to Rabi'atu Baba Paki😘 ina yinki mumcy irin dayawa d'in nan* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 4⃣ Lokaci ya ja su Abdallah nayin wankin da guga suna samun na rufin asirin su , daga baya wani k'anin MAMAN Umar ya saman ma Umar tsaran shagon abokin shi acikin kasuwa , to daga nan Umar ya bar wanki da guga sai Abdallah kad'ai keyi , da haka idan ya cire kud'in da zasu CI abinci sai ya saka sauran a asusu saboda wasu idan yayi musu aiki over payment suke mishi, Yanzun watan Abdallah shida yana wanki da guga wata , wata rana Malam ya aika a Kira shi , bai b'ata lokaci ba ya je, Bayan sun gaisa Malam ya ce" Abdallah ya maganar aure?" Wata irin muguwar fad'uwar gaba yaji amma sai ya d'aure ya ce"yanzun Malam akwai Wanda zai iya bani 'yarsa na aura yadda nake d'in nan?" Malam yayi murmushi yace "sosai ma kuwa Dan an dad'e ma da baka sadaki kwai ake jira a d'aura aure" Cikin firgici Abdallah ya d'ago ido ya kalli Malam Malam yace " sosai ma kuwa idan kana da naira dubu bakwai ka kawo amatsayin sadaki , " Gaba d'aya Abdallah ya diri-rice ya rasa me zai ce , Malam yace cikin sanyi murya "Abdallah dalilin da yasa na matsu kayi aure shine na dad'e ina lura da yanayin ka , sannan kuma ahalin yanzun da kake cike kana buk'atar mace ta gari da zata zamo natsuwa a gareka shiyasa kaga na damu" Ajiyar zuciya Abdallah yayi Dan yasan zancen Malam gaskiya ne "Insha Allah bazai gagara ba , nagode Malam Allah ya saka da alkhairi ya k'ara girma " "Amin "cewar Malam Sannan sukayi sallama akan zai kawo sada kin gobe , Abdallah na koma wa gida ya sanar ma da Mama yadda suka yi da Malam , tayi murna sosai hafsa na d'aki na kwance ta fito tana "Mama lafiya?", Abdallah ya turb'une fuska alamar be son raini yace" ke waye sa'anki a nan? dallah can koma d'aki" "Haba Bawan Allah wannan ba 'yar uwar ka bace ai ya chanchanci taji abin alherin da yake shirin samun mu" "Mama ni dai raini ne bana so" yana gama fad'in haka ya nufi k'ofar d'akin shi ya tura ya shiga ya fad'a kan shamulokin katifar shi yana tunani , "Shin ta ina za'a kawo wani mahaluki d'akin nan ya iya zama , ballan tana kuma Amarya?" Mik'e wa yayi zaune yace "ya Allah ga Bawan ka nan mak'ask'anci daga cikin bayin ka ya Allah ka taimake mu ya Allah kafi kowa sanin halin da muke ciki " wasu k'walla masu zafi da tuk'uk'i a zuciya suka zubo mai , Da k'yar ya had'iye wani Abu mai kama da dutse a wuyan shi ya koma ya kwanta , Chan kuma yayi zumbur ya mik'e ya nufi gana most go d'in kayan shi ya ciro wani gwangwani , nan ya bud'e kud'i ne a ciki , nan ya hau k'irgawa , naira dubu takwas da d'ari biyar ne , ajiyar zuciya yayi sannan ya mai da kud'in ya ajiye , da yamma bayan sun had'u da Umar a islamiyya yake gaya mishi yadda suka yi da Malam Umar sai da yayi dariya mai isarsa sannan ya ce " wato kai yanzun aure za'a maka ?, auren ma na dole"ya k'ara k'yalk'yale wa da wata dariya har yana rik'e cikin shi Abdallah da yaga abin na Umar da rainin wayau aciki kawai sai ya mik'e ya fice ya bashi wuri , Umar ya biyo shi yana "ustaz tsaya mana ya muna magana zaka gudu kuma" Abdallah be kula shi ba sai ma ture hanun Umar da yayi a kafad'ar shi cikin fushi ya k'ara sauri, Umar na ganin haka ya ce "yau maza sun yi fushi , sai naje biko" Abdallah kuwa yana shiga afusace ba kowa a tsakar gidan sai wani bokiti da aka cika shi da ruwa aka aje , Aiko ya suri bokitin yayi bayi dashi , haka ya ringa watsa ruwan a kanshi yana ajiyar zuciya , Hafsa kuwa ta fito d'aki daga ita sai zani tana 'yan wak'e- wak'en ta da sosan wanka a hannun ta ta k'arasa inda bokitin yake yace d'aukeni inda kika aje ni , Ta ringa zagaye a tsakar gidan tana fad'in" anan fa na ajiye shi " Mama da ta fito da buta za tayi alwalar magrib tace"ke hafsa ke dawa kike ta surutu kamar kanki be miki dad'i" Hafsa cikin muryar kuka tace "Mama ruwa na na ajiye a bokiti zanyi wanka na fito ban ganshi ba" Mama tace "yanzun hafsa ba na hana Ki wankan magrib ba?" "Mama to AI wankan tsarki zanyi gashi lokacin sallah ya kusa " "Uhum" kawai Mama tace "Duk ma aljanin da ya d'auka ya fito dashi kafin......."hafsa bata k'arasa maganar ba taji an buga mata wani Abu akai ta baya , tana juya wa taga Abdallah ne ya buga mata bokitin da take nema , AI sai ta hau kame -kame "Dalla ni rufe min baki mare kunya kawai" ya sakar mata bokitin a k'afa Aiko tayi tsalle tana "wayyo Mama ya karya ni" Mama kam bata bi ta Kansu ba ta gama akwalar ta ta shige d'aki *DA SAFE* Abdallah yakai ma Malam sadaki bayan ya nuna ma Mama tasa albarka , na n Malam ya sa ranar d'aurin aure kwana goma kuma ya ce baya buk'atar komai , Abdallah yayi godiya sosai ya tafi [12/14/2017, 8:13 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *Dedicated to BAWAN ALLAH fans group ina jin dad'in comments d'inku so let's keep it up*❤ ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 5⃣ Kuyi hak'uri readers wasu na k'orafin ban fad'i wacece hafsa ba Hafsa yarinyar wan Mama ce taje garin su dai-dai lokacin aka hafsa ta isa yaye sai aka bata ita ta taho da ita , da wan nata yaga ta nuna sha'awar a bar mata hafsa sai ya amince wannan ne dalilin zaman hafsa agurin Mama Cigaban labari Da biki ya rage saura sati d'aya Mama ta shirya domin zuwa k'auyen su Dan ta sanar ma 'yan uwa su , kud'in aikin da Abdallah yayi na ranar shi ya d'auka ya bata ta tafi , Alokacin da taje musu da zancen sun ji dad'i sosai har ma wan nata ya ce da lokaci be k'ure ba da sun zo sun ma Malam godiya , kwanan ta biyu ta ce zata koma aikuwa aka shiga had'a mata kud'i da kayan abinci Allah Sarki da taga abinda aka had'a mata sai da tayi kuka hatsine buhu guda aka mata sai kuma kud'i nai ra dubu hamsi , Mama tayi kuka har tace ba zata amshi kud'in ba sunyi yawa , Baban hafsa ne ya ce mata "idan ba kin raina bane Hindatu Ki karb'a" da haka ta karb'i kud'in tare da godiya ta dawo gida cike da murna da jin dad'i, Abdallah ma kanshi ya ji dad'in ganin kud'in Ranar talata da safe suna zaune sai Mama ta ce "Bawan Allah ya kamata ka gyara d'akin chan naka tun da dai ba wani sai shi " "To " kawai yace "Ke hafsa shiga Ki d'auko min lalita ta a d'aki" Mama ta fad'i tana nuna hafsa Bayan hafsa ta kawo lalita Mama ta kwance ta Ciro kud'in nan ta mik'e mai ta ce ya k'irga Ya gama k'irga yace "dubu hamsin ne Mama " Tace"to ka dauki yadda zai isheka ka gyara d'akin chan kafin dangin Amarya su buk'aci sa wani Abu " Nan ma "to" yace "Haba bawan Allah ina ta magana kayi shiru sai dai ka Bini da to" Cikin sanyin jiki Abdallah ya ce "Wallah Mama jiki name duk a mace gani nake duk yarinyar da aka had'a ta dani an cuce ta domin ba zan k'are ta da komai ba sai k'uncin rayuwa" "Kayi hak'uri Bawan Allah , Allah da yayi mu ahaka bai manta da mu ba , wani hanin ga Allah baiwa ne sai dai kawai muyita gode ma Allah," Mama ta fad'i tana share k'wallar da ta gangaro mata Abdallah kuwa ji yayi tuk'uk'in da yake ji sai k'aruwa yake Umar ne ya shigo da sallamar shi , duk suka amsa , bayan gaishe-gaishe Mama ta ce "To kaga ga Umar nan yazo tashi kuje Ku hanzarta lokaci na tafiya " Nan dai ya mik'e jiki ba k'wari suka fita , suna fita Umar Umar ya dasa shak'iyyan cin shi ya fara " Ango Ango kasha k'amshi " Ni irin kallo Abdallah ya masa sai Umar ya had'iye yawu , daga nan ya tsuke bakin shi be k'ara cewa komai ba Siminti suka siyo da katako sai kuma net da penti suna dawo wa suka hau aikin abin su , Ba su suka gama ba sai dare sannan Abdallah ya bi Umar d'akin shi Dan ya kwana Da safe Misalin k'arfe shad'aya na safe wasu mata su biyu shigo gidan da sallama Mama na tankad'an gari , hafsa na hura wuta ,suka amsa musu sallamar sannan suka k'ara sa shigowa wasu yara ne yan matasa biyu suka shigo da da wasu manyan ledoji guda biyu D'aya k'anwar Malam ce d'aya kuma yayar amaryar Malam d'in ce Da fara'a a Mama tace "ah 'ah sannun Ku da zuwa yaya ma'u" "Yauwa"suka amsa suma cikin fara'a , Hafsa ce tayi sauri ta d'auko tabarma ta shimfid'a musu suka zauna , Bayan gaishe gashe suka ce sunzo gyara d'akin Amarya ne , nan Mama ta nuna musu d'akin suka hau gyara , Leda duka shimfid'a ,suka sa labule , Suka rufe d'akin suka Mama makullin kwadon suka yi sallama Hafsa ce ta ce ma Mama "Mama komai yana son gyara kinga yadda aka gyara d'akin yaya kamar ba shi ba " Mama tace " shiyasa aka ce mana tsafta cikon addini" Hafsa ta ce" lallai kam , Mama bari naje na duba Ummi kwana biyu bana ganin ta a islamiyya" "Aiko nima ta kwana biyu bata zo gidan nan ba ko lafiya ?je Ki dubo ta" Hafsa ta suri hijab d'inta ta fita *Wace ce Ummi* Ummi ita kad'ai ce 'ya mace ga Malam wadda Amarya sa ta Haifa masa asalin sunan ta ZAINAB k'awar Hafsa ce tare suka taso *cigaban labari* Bayan sun gama d'aukar karatu a wajen Malam Abdallah yace "Malam lafiya Ummi bata zuwa makaranta kwana biyu?" Malam yace "Ummi bata jin dad'i ne amma dai ta ji sauki " Dukkan su suka yi mata fatan alkhairi suka kwashi littattafan su suka k'ara gaba *Ranar d'aurin Aure* Yau take juma'a kuma da an idar da sallar juma'a ne za'a d'aura auren Abdallah da Amaryar sa , Abdallah kuwa yau tun safe da ya tashi yake fama da wani matsanan cin ciwon kai ga jiri da yake gani , Umar har fita yayi yaje ya siyo mai magani ya sha amma a banza , sai da Umar yayi ta mai addu'a sannan ya samu yayi barci , Umar kuwa da yaga Abdallah yayi barci wanka yaje yayi sannan ya shirya cikin yadin shi mai sauk'in kud'i ya fita wajen daurin auren amma me kafin ya k'arasa har an d'aura , Malam ne ya k'araso wajen da Umar ke tsaye yana mamakin har an d'aura aure "Umar ina abokin naka yake?" "Wallah Malam yana can d'akina kwance yana fama da zazzabi amma dai yanzun yayi barci" Umar ya bada amsa Cikin tausayi Malam yace " subhanallah Allah ya sawak'e" Nan suka zauna suka CI gaba da tattaunawa Gidan su Mama cike yake da mutane 'yan biki , yamma nayi kowa ya fara watse wa Dan 'yan garin su ma motar da ta kawo su tana jiran su , Dan Baban hafsa yace ba zasu zo su d'ora mata d'awai niya ba , Hafsa ce ta shigo a guje ta ce ma Mama " Mama ga Ummi can an sata a napep za'a kaita asibiti ciwon ta ya tashi" "Hasbunallahu wani'imal malwakil , Ummi Allah ya yaye miki wannan lalura" Mama ta fad'i cikin jimami Hafsa ta k'ara cewa" Mama bari na bisu" "Ah'ah hafsa baki San asibitin da zasu je ba kiyi hak'uri ki jirasu" Hafsa ba Dan taso ba ta hak'ura , domin tasan ciwon k'awar tata idan ya tashi har suma take yi Allah Sarki Ummi Allah Sarki Abdallah😥🤫 [12/15/2017, 11:17 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *wannan page d'in ma naku ne ina matuk'ar k'aunarku kamar yadda kuke k'aunar BAWAN ALLAH*❤💋 ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 6⃣ Abdallah be farka ba sai wajen k'arfe shida na yamma , yana duba agogon wayar shi yaga lokacin sallah yayi yamik'e cikin sauri ya d'auki buta yayi cikin gidan , Maman su Umar ma bata nan , tana can gidan biki , alwala yayi ya fara jero azahar da la'asar bayan ya idar yayi addu'oi sannan ya fito ya kulle gida ya gangara Neman Umar , Yana cikin Neman shi ne yaji ana kiran magrib , kawai sai ya wuce massalaci , sai da aka idar da sallah yazo zai fita yaji an dafa kafad'ar shi yana juya wa yaga Ashe Umar ne , Murmushi ya masa , Shima Umar murmushin yayi sannan ya ce "Aboki ya jikin naka?" "Alhamdulillah"abdallah ya amsa , Sannan suka jero suna tafiya , Anan ne Umar yake gaya ma Abdallah Malam yana Neman shi , daga nan kai tsaye gidan Malam suka nufa , amma da suka je aka ce Malam yaje asibiti duba Ummi , Cikin hanzari Abdallah ya kira wayar Malam , ringing biyu aka d'aga , banji me aka ce a d'ayan b'angaren ba naji Abdallah ya ce "to Allah ya kawo ku lafiya " Banyan sunyi sallar issha sai suka Kama hanyar gida , Anan suka had'u da Malam shima ya dawo massalaci Dan basu ganshi a can ba , Bayan sun gaisa malam yace "Abdallah ya jikin naka?" "Alhamdulillah Malam na samu sauk'i , ya jikin Ummin?" "Jiki yayi sauk'i tana gida ma yanzun haka " "To Allah ya k'ara lafiya" "Amin" Malam ya amsa , sannan ya buk'aci su biyo shi rumfar k'ofar gidan shi , Bayan sun k'arasa sun zauna Malam ya fara magana, "To Abdallah yau dai Allah ya nuna mana ranar da ka zama cikakken mutum , domin shi aure shi ne yake cika kamalar D'an Adam , ina fatan zaka yi hak'uri ka zauna lafiya da duk macen da ta Kasan ce matar ka , kuma kayi hak'uri da halin yarin tarta , na zab'a maka ita ne saboda nasan cewar zaku zama natsuwa a tsakanin junan ku, inai maka fatan alkhairi , Allah ya Sanya albarka acikin wannan auran yaba ku zaman lafiya da zuri'ah mai albarka Amin" Tunda Malam ya fara koro bayani jikin Umar da Abdallah yayi sanyi lak'was , Abdallah duk jarumtar shi sai da k'walla ta zubo mai , Umar kuwa bubbuga bayan shi yayi Abdallah ya fara magana cikin rawar murya " insha Allah Malam bazan baka kunya ba , zab'in ka shine nawa tamkar mahaifi kake agurina nagode Allah ya saka da alkhairi " "Ba komai Abdallah da kai da Umar kun chan-chanci fiye da haka aguri na , Allah ya jikin iya-yen ku ya k'ara kyautata mak'wancin su" "Amin "dukkan su suka ce nan Malam ya k'ara yi musu nasiha , sannan ya ce su tashi su tafi dare na dad'a yi , har sun mik'e sai Malam yace , "Abdallah sun kai maka Amaryar ka tun d'azun ba kowa ma agidan" "To" d'in da ya saba fad'i ita ya fad'i yanzun ma , suka yi sallama suka fita Suna fita Umar ya shek'e da dariya " yau abokina zai angwance kai Allah ya samu a danshin ku" Abdallah Ya kawo hannu zai kai masa duka kenan Umar ya gudu yana fad'in "Aboki karka rufe k'ofar gida zan kawo ma Mama sak'on ta" Bai bi ta kanshi ba ya kulle k'ofar gidan ya shige abin sa , Yana shiga yaga Mama da hafsa suna kwance a tsakar gida suna fira Kasan cewar ana D'an zafi lokacin Da sallama ya shiga , duk suka amsa masa ya janyo bokiti ya zauna yana fad'in "Ina wuni Mama ?" "Lafiya lau " ta fad'i yana k'ok'arin mik'e wa zaune Sannan ta k'ara cewa "ya jikin naka?" "Alhamdulillah naji sauk'i" Nan suka D'an tab'a fira sannan Mama tace mishi" su zasu shiga su kwanta dare yayi " Mik'e wa yayi yaje kusa da hafsa ya shure ta da k'afa sannan yace " ke baki iya ma mutane sannu bako?" Cikin murya me kama da ta barci tace "yaya barci fa nake" "Dallah rufe min baki tunda ga waje nake jiyo hirar Ki Ki ce min wai barci kike yi" Mama kuwa tunda suka fara ta kakkab'e tabarmar ta ta shige d'aki Yana ganin mama ta shige ya juya ya kalli hafsa "to uwar gulma ko anan zaki kwana ne?" Pillow d'inta d'auka ta runtuma d'aki aguje. Tsaki yaja , ya nufi k'ofar d'akin shi , yana isa ya d'aga labulen tare da sallama , mutum ya gani kwance cikin hijab cire takalman sa yayi ya k'arasa shiga d'akin , Azuciyar shi yace "lallai ma wannan baccin ta ma take sha" Pillow ya ja ya kwanta ak'asan Leda , can dai yaji bazai iya hak'uri ba yana son ganin wace ce amaryar tashi , zaga ya wa yayi ta inda fuskarta ke kallo , ganin ko wace ce ya sa shi yin taga-taga zai fad'i Masu karatu kunsan wa ya gani 😱 Cikin tsananin mamaki yace"Ummi?!" To fa muje zuwa Dan jin yadda zama zai Kasan ce tsakanin Ummi da Abdallah [12/16/2017, 9:38 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 7⃣ Jingina da bango yayi yana k'are ma Ummi kallon mamaki , bawai baya son Ummi bane , Ummi macen rufin asiri ce , yasan halin Ummi akwai hankali natsuwa da sanin yakamata uwa uba kuma tarbiyya , Ummi mace ce San kowa k'in Wanda ya rasa , tana da kyawu dai-dai gwar-gwado ba za'a kirata da mummuna ba , ita ba fara bace kuma ba za'a ce mata bak'a ba zamu iya kiran ta chocolate colour , ba tada tsawo sosai kuma ba gajera bace sannan yatsunta suna da tsawo , tana da dogon hanci da yalwatattun idanuwa ba tada fad'in fuska sosai, gakuma D'an k'aramin bakin ta , kai masu karatu Ummi kyakyyawa ce ba laifi🙅🏾‍♀ Wani gwauron numfashi ya ja ya zame agurin ya zauna yana kallon ta kamar wata sabuwar hallita , Ya kai kusan awa biyu a wurin yana kallon ta azuciyar shi yace "tabbas Ummi kyakyyawa ce amma me yasa yau naga kyanta ya fita daban, ? mutane suna ciwo suyi muzai-muzai , amma Ummi kyau ta k'ara ko ita din ta daban ce ko kuma ido nane ?" Duk wad'an nan tambayoyin ba shida amso shin su Dan haka kawai mik'e wa yayi , ya fita yayo alwala ya raya daran da sallah , Ummi kuwa juyin barci tayi ta farka wani irin mugun fitsari taji ya matse ta , ga tsoro tana ji ba zata iya fita waje ita kad'ai ba sai matse matse take , Abdallah kuma alokacin ya idar da sallah yana jiran yaji an kira sallar asuba yana jingine idon shi a lumshe amma ba barci ya ke ba , Ummi kuwa da taga idan bata je tayi fitsarin nan ba to tabbas zata malale sabuwar katifar ta da fitsari , A hankali take kiran sunan "yaya Abdallah ? Yaya Abdallah? Yaya Abdallah?" Shi kuwa ya na ji kasa amsawa yayi sakamakon wani Abu da yaji yana sukan zuciyar sa , ana ukun da ta kira shi ne ya daure ya ce mata "Na am" "Fitsari nake ji" "To kije kiyi mana " Cikin d'auriya da matse fitsarin tace "wallahi tsoro nake ji " Azuciyar shi yace " ko a gida wake raka ta oho?" Afili kuma sai cewa yayi" kiyi addu'a ki fita babu abin da zai same Ki da yardar Allah" " wayyo Allah yaya zai zubo" Dafe kanshi yayi a zuciya ya ce "ni kam naga ta kai na " Azahiri kuma yace " tashi muje " "To kayi gaba"ta fad'i cikin shagwab'a Gaba yayi ya barta a baya tana tafe tana hard'e k'afafuwa , har ta isa nesa da bakin bayin ya tsaya tare da mik'a mata buta , sannan ya ce" adai yi addu'a " "Uhum" kawai tace ta k'ara sa bayin aciki ma ta k'ara sa addu'ar , Bayan ta fito ta gan shi yana alwala cikin sauri ta fara duk Dan gudun kar ya gama ya barta a wajen , shiko tsaya wa kawai yayi yana kallon ikon Allah , har ta gama ta shige d'aki , nan shima yayi ya koma d'akin Dan ya dauki hular shi Ita kuma ta tada kabbara sai ce mata yayi " wato ni da na raka Ki Dodon ya cinye ni ko?" Bata ce komai ba , shikuma ya d'auki hular shi , ustazu ka fiye naci ya saka ya fita , Bayan sun idar da sallah ne ya so ya D'an kwanta a massallacin ya D'an yi barci amma Umar Sam ya hana shi sai tsokanar shi ya ke yake " Ango Ango sai wani k'yalli kake kamar tauraro" haka dai yayi ta masa shak'iyyan ci, Abdallah kuwa tashi yayi ya barshi nan zaune yana dariya da dai ya ga da gaske fita zaiyi sai ya taso ya biyo shi dai dai kunan shi ya rad'a masa "ya kama ta kaje ka ji d'umin 'yar k'anwar ka" ya k'ara sa da kashe ido d'aya Abdallah ko da abun ya bashi haushi sai ya ce " ka manta ne ba d'umin ta zanji ba jikin ta Zan shige " "Yauwa mutumi na Ashe ka gane " Dai-dai nan Abdallah ya shige gida ya bar Umar a tsaye yana dariyar mugunta Dan shi gani yake kamar an had'a Abdallah da aiki ne , Yana shiga gida ya CI karo da Hafsa tana alwala , wata harara ya watsa mata sannan yayi sallama d'akin Mama suka gaisa take tambayar shi ya Ummi da jiki ya ce mata taji sauki suka Dan tab'a hira ya ji yana jin barci sai ya mik'e ya ce mata "Mama ina zuwa" D'akin su ya koma , Ummi kuwa tana jin motsi tayi sauri ta rufe idon ta , ko da yayi sallama yaji ba Wanda ya amsa mishi , ya yaye labule kutsa kai , Yana shiga ya ganta tana barci , ya koma inda yaga dadduma a shimfid'e ya kwanta nan wani barci yayi awan gaba da su duka ,, Mama kuwa da taga har takwas tayi Abdallah be futo ba , sai ta aiki Hafsa ta siyo kayan tea a bakin titi, ta na dawo wa ta d'aura ruwa zafi ta had'a citta da kaninfari da Lipton ya dahu sai k'amshi yake , , ta juye a wani tsohon plas d'in ruwan zafin su ta juye aciki ta d'iban musu nasu saura kuma ta had'a da bread tayi k'ofar d'in Ummi Sai da tayi sallama sau uku taji ba Wanda ya amsa kuma ba ta ji motsin kowa ba , murmushi tayi sannan ta d'aga labulen kad'an ta ajiye kayan ba tare da ta kalli d'akin ba , gudun kar tayi mugun gamo,🤣🤣 Ummi ce ta farka lokacin Tara tayi cikin sand'a ta mik'e gudun kar Abdallah ya tashi bata San shima ya tashi ba baya son yayi motsin da zata ji ne , Jakar kayan ta ta bud'e ta Ciro brush da MacLean ta d'auki butar ta ta fita bata lura da kowa a tsakar gidan ba ta tafi chan inda suke wanke wanke tayi brush d'in ta sai da ta gama ne d'ago kai suka had'a ido da Hafsa , aiko me Hafsa za tayi in ba dariya ba , Ummi kuwa murtuk'e fuska tayi Mama ta gansu amma sai tayi kamar bata ma gansu ba . Jiki a sanyaye Ummi ta k'araso ta zauna kusa da Hafsa , cikin jin kunya ta gaida Mama , ta amsa cikin sakin fuska Dan Mama tana son Ummi sosai Hafsa ce ta ce"Aunty Ummi ya jiki" Ummi da mamaki ta ce "yau kuma Hafsa nice Auntyn Ki?" "Eh mana AI tunda kin auri yaya Abdallah kin zama Aunty" Wata hara ra Ummi ta zuba mata ta gefen ido "Ummi tashi Ki je Ki karya kinji Ki k'yale wannan " "To Mama" Ai sai Ummi ta d'auki kofin shayin Hafsa tana fad'in "Mama AI wannan ma ya ishe mu ni da k'awa ta" "Malama bani shayi na naki na d'akin ku" cewar Hafsat tana zumb'uro baki Mama dai bata tanka musu ba Ummi ta ce cikin k'asa-k'asa da murya "K'awa ta je Ki d'auko min nawa tea d'in , zan aje miki naki," "Tab AI ko ba zan je b....." Bata gama fad'i ba Ummi ta make mata baki Mama kuwa murmushi kawai tayi "Ke hafsa nan matsalar Ki ba wayau je Ki d'auko min Ki zo musha fira" "Eh sannu uwar wayau..." Ummi ta k'ara make mata baki "Wallah Aunty Ummi kika sake duka na sai na... ." ta sake gwabje bakin , Hafsa ta mik'e "Mama kina kallon ta ko ?" Mama ta ce 'ai ni na gode gwanda ta min maganin Ki , wuce ki je Ki d'auko mata" Cikin zumb'ura baki ta tafi [12/17/2017, 8:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *Wannan page d'in na sadaukar dashi ne ga masoya novel d'in BAWAN ALLAH aduk inda kuke Wanda na sani da Wanda bansani na gode Allah ya bar zumunci, ❤* *BAWAN ALLAH fans wallahi ina matuk'ar jin dad'in comments d'in ku ku sani dani da ku muna mak'ale da juna🤞🤙* *K'awwali ta da Ameenert gaisuwar ku da bance 💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 8⃣-----🔟 Sai da tayi sallama sau biyu ba'a amsa mata ba , ana ukun ne ya amsa had'e da cewa, "Mene ne?" "Aunty Ummi ce tace na zo na d'auko mata shayin ta da magani" Chan dai yayi shiru kamar ba zai bada amsa ba sai kuma yace "kije Ki ce mata tazo ta d'auka da kanta" Har ta juya zata koma sai kuma yace "zo nan" Ahankali ta d'aga labulen d'akin ta shiga , "Kwashe gasunan inda kika ajiye su" Ba musu ta d'auka sannan ta fita jikin ta duk kyarma yake , Tana zuwa ta dangwarar da kayan a gaban Ummi " gashinan burinki ya cika kin tura ni wurin wancan zalimun mijin naki" "Oho ko ma dai mene ne buk'ata ta tabiya tunda kin min abin da nake so" cewar Ummi tana murgud'a baki , "Idan kun gama wasan kwai-kwayon sai ku mayar mai da kayan shayin " Mama ta fad'i yayin da ta d'au buta tayi hanyar bayi "To"dukan su suka ce , Mama na tafiya musu ya kaure tsanin Ummi da Hafsa akan Wanda zai mai da kayan shayi Ummi na cewa "ke kika d'auko ke zaki mai da " "Hafsa na cewa ke kuma ba mijin Ki bane ni ba runa wallah ba zan mayar ba" Dai dai nan Abdallah ya fito ya , duk yaji me suke cewa , amma sai yayi kamar ma bai San suna wajen ba , Ya fara brush kenan Mama ta fito daga bayi , anan suka k'ara gaisawa alwala tayi ta shige d'aki shima alwalar yayi ya shige d'aki , duk da yana wurin musu tsakanin Ummi da Hafsa be k'are ba sai dai wannan karan a hankali suke yi , yana shiga ya tada sallar mai rabo (salatul duha), Ummi ta gama tsumul- mulan shan shayin ta Dan Hafsat tuni ta gudu ta barta, Hakanan tayi shahada ta d'auki kayan shayin ta nufi d'aki da shi sallama tayi sannan ta shi , ta same shi akan dadduma yana addu'a , kawai sai ta tsaya tana kallon shi da taga ya gama addu'ar sai tayi sauri zata fita kamar daga sama taji yace "ina zaki je?" Sai ta hau kame kame, "Yau ko gaisuwa ba zan samu ba kenan?" Yawani tsare gidan shi Cikin sauri tace" yaya ina kwana?" "Ah'ah Ki rik'e gaisuwar Ki indai sai na rok'a" ya sake murtuk'e fuska Nan da nan ta tuna da nasihar Malam da ya ke cemata "ta guji b'acin ran mijin ta Dan zai iya kaita ga azabar Allah" AI yana tuna wannan sai tayi sauri ta dawo kusa da shi ta zauna Ta marai-raice murya "yaya Dan Allah kayi hak'uri , Malam yace idan kayi fushi dani zan iya shiga wuta" Abin ya bashi dariya amma da yake bata so ya gane sai ya tsare gidan sa , azuciyar shi kuma cewa yayi "wato tanan kika b'ullo? Muje a haka game d'in zai fi dad'i" Wani murmushi yayi sannan ya ce "idan kina so na daina fushi da ke kin had'a min shayi" "Yo AI wannan mai sauk'i ne "cikin minti biyu ta had'a mai tea d'in ta bashi Tana zaune a gurin ya gama karyawa sannan ya kalleta ya ce " ya jikin naki?" "Alhamdulillah , naji sauki" "To masha Allah , kinsha maganin Ki?" Kai ta girgiza alamar bata sha ba "Ummi Ki daina wasa da shan magani , tashi Ki d'auka Ki sha" Ba musu kuwa ta mik'e ta d'auko maganin ta bud'e wata k'aramar randar ta ta d'ibi ruwa kamar abun arzik'i zata sha , Ga maganin ta Tara a gaban ta amma ta kasa sha , Shikuwa sai ya bita da na mujiya , wani abun mamaki bai wuce da ya tana zubar da k'walla ba , tana hawaye tana kallon maganin , "Lafiya? Ki sha maganin mana" "Wallah yata magungunan ba dad'i " "Ki daure Ki sha shi dama magani ba Dan dad'i ake shan shi ba" Mik'e wa tayi tare da d'aukar ledar maganin zata fita , "Ina kuma zaki je Kuma?" Cikin shagwab'a Ummi tace "zan je gurin Ummi name ita kad'ai zata iya bani nasha ba tare da nayi amai ba" Shiru yayi na 'yan sakwanni sannan ya ce "zo na baki Ki sha" "Ummi na fa lallab'ani take" Wani murmushi yayi sannan yace" nima yayan Ki zan lallab'aki" Jin hakan yasa Ummi kwasar ledar maganin tayi wurin shi , Zaman dirshan tayi a gaban shi sannan ta mik'a mai maganin , ya karb'a yace "Ya Ummi take baki?" Sai alokacin itama Ummi ta faki idon shi ta saki wani shu'umin murmushi azuciyar ta tace "anzo gurin ya ustaz" "Ina magana kinyi shiru saifa kinsha maganin nan yau" yana magana yana d'aure fuska "Dama sai ta gutsura maganin gida biyu sannan ta ta saka min d'aya a baki da ruwa , tana Shafa baya. Na har sai ta gama bani kuma tana yi tana fad'in , kiyi hak'uri Ummi na kisha , haka take ta fad'i" 😂😂😂😂😂 Bawan Allah sai da ya zaro ido sannan yace "to naji matso" [12/18/2017, 1:47 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 1⃣1⃣++++1⃣2⃣ Matso wa tayi daf da shi sannan ya bud'e ledar ya Ciro magungunan ya b'ab'b'alla su , ya ce "bismillah " D'an k'aramin bakin ta ta bud'e ya saka mata tare da bata suwa tana jira taji ya shafa bayan ta sai taga yayi mursisi , ai ba shiri ta fara kakarin aman k'arya fita waje tayi da gudu ta tofar da maganin , ta shigo tana fuskar tausayi, tace "Yaya ka gani ko ba zaka iya bani ba kamar yadda Ummi na take bani" "Me yarinyar nan ta mai da nine amma zan nuna mata nafi Ummin iyawa"wannan duk azuciyar shi yake fad'i Azahiri kuma cewa yayi " ayya sannu na manta ne zo asake wani" Ta sake zuwa ta zauna sai cewa yayi "cire wannan hijab d'in ko shima ya shak'e maganin yak'i wuce wa" "Me ka ce yaya"ta zaro ido Ya k'ara k'asa da murya dai-dai kunnan ta yace "nace Ki cire hijab d'in" "Yaya ai ba zai hana ni sha ba" B'ata rai yayi ya tura mata maganin ta , "shikenan tunda ba zaki cire ba, ni ba zan baki kije kiyi amai ba" "Ayya yaya da gaske bana son Fushin ka bari na ciri" Yaye hijab d'in tayi dai-dai wuyan ta sannan ta ce "na cire " Hannu ya sa ya yaye hijab d'in , wata vest ce ajikin ta mai santsi da leshi agaban ta ta kwanta tayi luf ajikin ta , kayan arzik'i ne ya tsaya kallo har yana had'iye wani yawu mak'wat gaba d'aya imanin shi ya tafi awajen k'irjinta , ga dai su ba masu girma bane amma akwai d'aukan hankali, Sai da Ummi ta kira Abdallah sau uku be jita ta ba , sam ita bata lura da inda yake kallo ba, Tab'ashi tayi tana fad'in "yaya ina ta magana shiru" Bece mata komai ba , ya sa mata maganin abaki dan gani yake ko magana yayi za'a gane halin da yake ciki Ruwa ya sanya mata a baki sannan ya k'ara janyo ta jikin shi , tana jin ya tab'a ta tayi sauri taja baya , madadin ya kyale ta sai ma k'ara janyo ta da yayi ta kwanta a k'irjin shi yana shafa bayan ta ahankali cikin wani irin salo yana fad'in Yazo dai-dai saitin kunnan ta ya na rad'a mata"k'iyi hak'uri Ummi kishanye ko kya samu lafiya" Sai da suka kusa minti goma a haka Abdallah dauriya kawai yake yi amma ga ba d'aya notin jikin shi ya kwance Ummi kam har ta fara bacci abunta bata ma San yana yi ba , "Ummi , Ummi"Abdallah yake kira a hankali Cikin yanayin bacci tace "uwum Ummi na Ki barni ban gaji da jin d'umin jikin Ki ba " ta sa hannun ta biyu ta zagayo dasu ta bayan shi tare da dad'a cusa kanta cikin k'irjin shi "Inalillahi wa 'inna ilaihirraji'un"abinda Abdallah ke mai-maitawa kenan Acikin ranshi ko fad'i yake" wannan yarinyar zata kashe ni" Sun jima a haka bai kwantar da ita ba domin zaman ta a jikin nashi na rake mai wata damuwar , Ana haka ya tsinkayi muryar Hafsa tana fad'in "eh yana ciki" Sallamar Umar da yaji duk ta dagula masa lissafi shiko sai rafka sallama yake , A hankali ya lallab'a ya kwantar da ita , sannan ya fita, Umar na ganin shi ya saki wani murmushin rainin wayau , yace "kayi hak'uri fa na katse maka hanzari" "Ba hanzari ka katse min ba gudu" ya ja tsaki , yayi hanyar fita , binshi Umar yayi yana fad'in "ai dai ka tsaya kaji me ya kawo ni ko ?" Cikin murtuke fuska Abdallah yace" Umar muddin kana son zaman lafiya tsakani na da kai to dole daina min shakk'iyancin nan naka , wallah har cikin raina bana jin dad'i shiya sa kaga gaba d'aya na fita harkarka domin b'ata min rai kake" Umar yace "uhum Bawan Allah kenan indai wannan ne mai sauk'i ne , amma babu yadda za'ayi na ganka a cikin irin yanayin da na ganka a yanzun ban yi dariya ba" "Mtsww yanzun dai gaya min meya kawo ka?" "Dama Alhaji bello ne ya kirani yana ta Neman wayar ka be shiga shine ya bada wankin shi na kawo maka , amma wai gobe yake so da safe zaiyi tafiya" "Shikenan ba damuwa , ina wanki suke?" "Suna nan tsakar gida na barsu " Nan dai suka D'an yi fira sannan Umar yace " bari naje kasuwar nan kaji" Sukayi sallama , Abdallah ya koma gida , Mama da Hafsa ne keta kiciniyar d'aura tuwon rana , yayi musu sannu ya wuce d'aki , kaya ya chanja zuwa wata tsohuwar T-shirt , ya nannad'e k'afar wandon sa ya hau sana'ar shi ta wanki , Ummi kuwa ba ita ta farka ba sai d'aya saura , lokacin har Abdallah ya gama wankin shi yayi wanka yana shirin fita masallaci tana kwance tana kallon shi sai da ya gama shirin shi ya fita sannan ta mik'e ta d'auki bokitin ta da buta ta nufi rijiya , a nan waje ta tarar da Hafsa tana kwasar tuwo Ummi cikin tsokana tace "yau manya ne a kitchen d'in " Hafsa ta juyo ta watsa mata wata harara sannan tace " kuma dole aci ko be dahu ba ba" "Yi hak'uri maida wuk'ar" ta duk'a ta d'ibi ruwan ta sannan ta wuce bayi tayi wanka da alwala tayi sallah sai da ta idar ne ma ta lura da kwanon abincin nan ta D'an yafita ta barshi , Hirar su Mama da Hafsa ne da taji ya sata fita don ta gaji da zaman shirun, [12/20/2017, 9:27 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *Dedicated to* *MAMAN Tahir* *Maman Hanan* *Maman mamy* *Maman adhil* *Meenat* *Rukkaya maijega* *Amne* *Aisha Muhd Namadina* *Sadiya Illa* Agaskiya sunan ku ba zai lissafu ba I really appreciate your kind and support *Ina mugun k'aunar ku*❤💋 *Thanks for your well wishes*💋 ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 13___14 Shiko Abdallah tunda ya fita be dawo ba sai dare yana dawo wa ya shiga d'akin Mama ya gaishe ta sannan ya fita ya kwashe kayan wankin da yayi gashi yayi sa'a akwai wuta , kai tsaye d'akin su ya nufa , yayi sallama ya shiga , Ummi ya samu kwance tana baccin k'aryan da ta saba , be tanka mata ba ya shimfid'a sallaya ya hau gugan shi , Ita kuwa Ummi kallon mijin ta take yi cike da tausayi , azuciyar ta tace "shi ko gajiya baya yi?" Abunda bata sani ba shine shima Abdallah hankalin shi yana kanta kuma sarai ya gane ba barci take yi ba kawai sai ya fuske yaci gaba da gugan shi , har wajen shabiyun dare , Ummi ce tayi wata mik'a tamkar me yin bacci sannan tace "yaya fitsari nake ji" Fuske wa yayi ya ce "kije kiyi mana" "Wallahi tsoro nake ji" "Duk tsoron da kike ji da zaran kinyi addu'a zai tafi, ko baki iya addu'ar bane?" Ya k'arasa maganar kamar zeyi dariya Zumb'ura baki tayi cikin shagwab'a tace"na iya mana" " to sai kije kiyi kafin Ki min shi anan" Ai sai ta hau shura k'afafuwa ita ala dole sai ya raka ta, "Ya isa haka Sarkin shagwab'a tashi muje " Zumbur ta mik'e tama manta da d'aukan buta Dan fitsarin ya matseta sosai , Abdallah ne ya d'auki butar ya bita da shi, Bayan ta gama ta fito alwala ta d'auro sannan yayi gaba tana bin shi a baya kamar rak'umi da akala Tana shiga d'aki ta hau katifar ta tayi addu'oi ta shafe jikinta dashi sannan ta kwanta , nan kuwa bacci yayi awon gaba da ita , Shiko Abdallah bayan ya gama gugan shi alwala yayi , yayi nafilfili sannan ya kwanta ak'asa , bayan ya kwanta kuma me ya tuna oho ya mik'e kamar an tsikare shi ya lallab'a ya kwanta kusa da Ummi ya D'an janyo ta jikin shi kad'an , ita ko mage Sarkin son jiki ai sai ta k'ara shige masa , Can acikin baccin ta take jin wani Abu yana ratsa ta , tadai ji kamar ana mata waiwayi , har wani D'an zillo take , bata k'ara dawo wa hayyacin ta ba sai da taji yana k'ara mulmula ta, cikin fargaba ta cire hanunshi da ke kan k'irjin ta , Shi kuma kunya ce ta kama shi yaji kamar k'asa ta tsaye ya shige , kawai sai ya juya mata baya , Ummi ta kira shi a hankali " yaya?" Da k'yar ya iya cewa "uhum" "Dan Allah kada kayi fushi dani da gaske tsoro nake ji" Abdallah najin ta ce haka a zuciyar shi sai yayi hamdala yace "bari na buga sabon wasa" ya k'arike da murmushi Juyo wa yayi ya kalle ta sannan ya ce "idan bakya so nayi fushi da ke to Ki barni na gama abinda na fara" "Yaya da zafi fa" "Karki damu zanyi miki a hankali ba zaki ji zafi ba " Da haka ta yarda yana ta wasa da ita a hankali har bacci yayi awon gaba dasu , Da safiya tayi Ummi kunya Abdallah kunya , shi atunanin shi zata gaya ma Hafsa abinda yayi mata shi yasa yak'i sake wa , ❤❤❤❤❤❤❤❤ Lokaci yana ta tafiya yanzun auran Abdallah da Ummi ana Neman wata biyu , kullum zaiyi 'yan wasanninshi da ita domin wai a cewar shi tausayi take bashi k'aramar yarinya ce , Ummi ce kwance akan cinyar Abdallah yana yi mata tsifa duk da ba iyawa yayi ba amma tasa daru ita sai ya mata , Bayan ya gama na ta ce "yaya juya bayan ka kaga wani Abu " Shi ko yace "a ina?" "D'an duk'awa za kayi wani Abu zan cire maka" Juya wa yayi yace" gani cire min" AI sai ta d'are bayan shi tana fad'in "na mishi wayau" harda gwalon ta Murmushi yayi yace "sauka min abaya ke kullum ba kya girma" Nok'e kafad'ar ta tayi a lamar A'ah "Ummi kin cika rigima kamar wata 'yar yaye" Dariya tayi tace "ka manta yaye na aka kawo maka" Juyo da ita yayi yace "yarinya karki damu naku sa yaye Ki" ya k'arike yana kashe mata ido d'aya Duka ta kai mai abaya tana fad'in" wallahi ni bana so" Dire ta yayi yana dariya yace "wannan kuma ke kika sani ni na tafi masallaci" Cikin dare suna cikin barci manne da juna kamar tip da tyre sai Abdallah yaji motsin Ummi yayi yawa , janyo ta yayi ya sake k'ank'ame ta yana fad'in "Ummi Ki natsu mana" Sai da tayi wani D'an k'ara tace "wayyo yaya cikina zan mutu" Zumbur ya mike ko da ya duba ta Ashe ta galabaita sai murk'usu take yarik'e ta yana fad'in "ina ne " amma ta kasa magana , kwantar da ita yayi sannan ya hau Neman maganin ta cikin kaya be sha wahala ba ya gansu cikin hanzari ya d'ebo ruwa ya d'aga ta ya na bata yana shafa bayan ta ahaka har ta shanye , Ahankali taji ciwon na sauka tare da wani bacci , a haka ya k'arasa baccin da ita a nannad'e ajikin shi, Da safiya tayi ya je ya gaida Mama ya ke gaya mata ciwon Ummi ya tashi Dan haka zai je kasuwa ko zai samu dako , ya kaita k'aramin asibiti , Mama tayi mishi fatan alkhairi ya fita a hanya ya gamu da Umar shima kasuwar ya nufa bayan sun gaisa Umar ya D'an tab'a shakk'iyyancin shi sannan yace "ustaz sai ina haka" Nan Abdallah ya gaya mishi dalilin fitowar shi gida Dama inda ya yanufa "Allah Sarki Allah ya bata lafiya" "Amin "Abdallah ya amsa "Dama yau za'a sauke ma Alhaji Bello kaya a store d'in shi , yanzun ya kirani kayan sun iso muje mu rok'e shi ya bamu kayan mu sauke sai ya biya mu" "To" kawai Abdallah yace Dan shi mafita kawai yake nema Da suka je suka samu Alhaji Bello be hana su ba ya ce suyi domin shi mutum ne tausayi Suna cikin kwashe kayan ne , wayar Abdallah ta hau ruri , bak'uwar number da ya gani sai da gaban shi ya fad'i Yana d'aga wa muryar Mama tayi mai sallama tana fad'in " Abdallah ka dawo gida Ummi ba lafiya" Mama tayi maganar cikin muryar kuka sannan ta katse wayar Juyawa yayi a dabur ce yace "Umar jikin Ummi ya tashi" AI sai ya kwasa a guje Shima Umar ya runtuma ya bishi 🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀ [12/21/2017, 1:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *Dedicated to Bawan Allah fans , kusani ina sonku ina k'aunar kuma saboda ku nake rubuta wannan labarin , Allah ya bar zumunci ya k'ara mana dank'on soyayyah❤🏹 one luv*🏌‍com ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 15+++16 Koda suka k'ara sa gida Ummi a sume take bata San ma inda kanta yake ba , Mama na rik'e da ita ita kuma hafsa tana duk'e gaban Ummi tana kuka tana fad'in "Dan Allah Aunty Ummi kar Ki tafi Ki barni inkika mutu bansan yadda zanyi ba " Hankalin Abdallah yayi k'ololuwa gurin tashi , kasa yin komai yayi , Umar ne yayi k'arfin halin fita waje a guje cikin sa'a kuwa yaci karo da me Napep nan ya tsayar da shi ya gaya mishi asibitin da zai kaisu sannan ya juya dashi suka koma , inda Umar ya bar Abdallah nan ya dawo ya same shi , dafa kafad'ar shi yayi yace "aboki ga me Napep can na samo a waje ku kama ta ku saka" Haka nan jiki ba k'awari suka saka ta a napep suka nafi wani primary health care da yake kusa da su , Suna zuwa wani likita ya duba ta yace musu ba zasu iya yi mata komai anan ba saboda ba suda kayan aiki , nan likitan ya rubuta ta musu transfer zuwa A B U teaching hospital dake tudun wada , hakalin kowa ya k'ara tashi sai alokacin ne Umar ya d'aga waya ya sanar ma Malam abinda yake faruwa yace gashinan zuwa shiko Abdallah ya zama kamar photo domin D'an zaman da yayi da Ummi ta riga ta zama wani jigo na rayuwar shi, tunanin shi d'aya idan ya rasa Ummi ba Wanda zai k'ara bashi 'yarshi ya aura , shi yasa kullum idan ya tuna da Ummi yake k'ara sonta gashi ita kuma halin da take ciki , Dai-dai nan Mama tazo ta tab'ashi tare da cewa " kamata muje" Kasan cewar wurin ba'a rasa abin hawa yasa suna fita suka samu napep sai tudun wada , Suna zuwa akayi emergency da ita nan ma likitoci suka shiga aikin su , bayan awa biyu wani likita yazo ya tambayesu sune 'yan uwan Zainab Kabir? Suka amsa masa yace su biyo shi office d'inshi Bayan suje office d'inne ya basu izinin zama sannan ya fara bayani cewar "wani k'ari ne ya fito mata a gefen k'odar ta kuma yayi girma Dan haka dole ayanke , amma kuma ba zamu iya yi mata aikin nan ba dole zamu tura ta Babban asibitin mu dake *Shika* Dan haka ku shirya" Tunda doctor ya fara maganar Abdallah ke karanto "Inalillahi wa inna ilaihirraji'un" Bayan fitowar su daga office d'in Mama tace suje suyi sallah , Hafsa kuma ta koma gida tunda sun bar gidan ba kowa , Bayan Abdallah da Umar sunyi sallah ne sai Umar yace "ustaz bari naje gida na dawo ba jimawa zanyi ba" Kai kawai Abdallah ya d'aga masa , sannan Umar ya tafi , Yana zuwa gida ya fasa asusun da yake Tara kud'in auren shi duk da dai beda budur war🤪🤪 Ya fito kenan zai fita sai Maman su ta kirashi "ina zaka je ne haka?" . Nan ya Sanar da ita meke faruwa , ita tace bata ga ta zama ba, Ko da suka koma asibiti sun tarar da Malam da uwar gidan shi can Wanda har yanzun ba'a basu ikon ganin Ummin ba Daf da la'asar wani likita yazo yace ga Ambulance cen suje su shiga za'a wuce da Ummi Shika , Umar ne yaje yayi clearing komai ba tare da sun sani ba ,nan suka d'unguma suka wuce asibitin Nan ma wani gwajin aka sake yi likitoci suka tabbatar da lallai saidai ayima Ummi surgery gobe domin abin yana gab da fashe wa kuma idan ya fashe mutuwa zatayi , Abdallah najin hakan yayi sauri yace "likita kuyi duk abinda ya kamata ni zan biya kud'in" Kowa ya juya ya kalleshi tare da mamakin abin yace Doctor yace shikenan ba damuwa , Abdallah ya sake cewa "kud'in zasu kai kamar nawa ?" "Zaku iya kashe kamar dubu d'ari da goma " "Shi kenan doctor kuyi duk yadda ya kamata" Mama dai suman tsaye tayi da jin kalaman D'an nata , Umar kuwa cewa yayi "Allah yasa abokina ba haukace wa kayi ba" Juyawa yayi ya kalli Umar yayi masa wani murmushi me wuyan fassara Malam ne yayi k'arfin halin cemai "Bawan Allah Kasan me kake fad'a kuwa ?" D'aga kanshi yayi alamar "Eh" "To ina zaka samo wannan mak'udan kud'in" Cikin sanyin murya yace"wallah nima bansan inda zan samu ba amma ina rok'on Allah ya bud'a min hanyar alkhairi kafin safiyar gobe" Malam ya jinjina kai Tunda Abdallah ya shiga masallaci sallar magrib ya duk'ufa sallah da addu'ar Allah ya kawo masa mafita dashi da Umar kwanan tsaye suka yi , Bayan sun idar da sallar asuba ne Abdallah ya tuna da wani Abu bashiri ya mik'e kamar an tsikare shi yace ma Umar bari yaje ya dawo 🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔 [12/22/2017, 12:23 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN* *KULLU NAFSIN ZA'IK'ATUL MAUT ( dukkan wata rai sai ta d'and'ani mutuwa)* *AMADADINA DA SAURAURAN 'YAN UWANA WRITERS NA PURE MOMENT OF LIFE WRITERS MUNA MIK'A SAK'ON TA'AZIYYAR MU GA 'YAN UWAN ZAINAB MUHAMMAD (ZEE SOBA) ALLAH YAJIK'ANTA YAYI MATA RAHMA ALLAH KA GAFARTA MATA ALLAH KA KYUTATA MAKWANCIN TA ALLAH KA WANKE TA DA RUWA MAI SANYI DA K'ANK'ARA ALLAH KA GOGE MATA ZUNUBAN TA KAMAR YADDA KAKE GOGE FARIN TUFA DAGA DATTI , KA MUSANYA MATA GIDA MAFI ALKHAIRIN GIDAN TA , DA IYALAI MAFI ALKHAIRIN IYALAN TA ALLAH KASHIGAR DA ITA CIKIN AJANNAR KA , KAKARETA DAGA AZABAR WUTA . AMIN YA ARHAMARRAHIM*😰 ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 17++++18 Abdallah na fita be zame ko ina ba sai tasha cikin sa'a saura mutum biyu motar ta cika , wata mace ce tazo ta shiga sannan driver ya ja suka wuce k'auyen su Abdallah, Yana sauka gidan Baban Hafsa ya wuce yana zuwa yayi sa'a ko ya sameshi a gida bayan gaishe-gaishe ya gaya masa abun da ke damun sa sannan ya ce yazo ne ya bada jinginar gonar mahaifiyar su ta gado domin su samu kud'in da zasu biya ama Ummi aiki , Bamusu kawun nashi ya amince sukaje wurin me gari aka samu Wanda zai amshi gonar aka buk'aci Abdallah ya fad'i ko nawa yake so abashi , yace dubu d'ari uku nan akayi yarjejeniya aka mik'a mai kud'i daganan yayi godiya ya kamo hanyar zaria , Ya shigo Zaria bayan la'asar gida ya wuce Hafsat kad'ai ya tarar a gidan tana ganinshi ta taso "yaya ya jikin Aunty Ummi?" "Da sauk'i "kawai ya iya ce mata ya karb'i mukullin d'akin su ya shiga, dubu d'ari da hamsin ya d'auka sannan yayi sallolinshi a gida ya kulle d'akin ya tafi da mukullin , yana fita mashin ya hau har k'ofar asibitin ya k'arasa shiga ciki , Umar ne ya hango shi yayi sauri ya k'araso yana fad'in "ustaz ina kaje ne har yi ma Ummi aiki baka nan" Murmushi yayi yace "naje Neman kud'i ne " "Abdallah Dan Allah karka je ka sama kanka damuwar da ta fi k'arfin ka , kaga yadda ka koma kuwa daga jiya zuwa yau?" "Umar damuwa dole ce agareni , kanaganin 'yar mutane zata mutu ta dalilin gazawa ta dole na shiga tashin hankali " "Hakane amma Kasan rayuwa da mutuwa duk na Allah ne idan kwanan mutum ya k'are ba tsumi ba dabara dole sai ya tafi" "Allah kasa mudace " Cewar Abdallah yana rik'e hannun Umar suka k'arasa ciki Har a lokacin bacci take yi Mama ce kad'ai AD'akin ta zabga uban tagumi ga carbi tana ja , har suka shigo ma bata sani ba , Sai da yace "sannu Mama " Da sauri ta d'ago kanta tana fad'in "Bawan Allah ina ka jene?" "Mama naje Neman kud'i ne kuma Alhamdulillah na samu" "Ina ka samo kud'i?" Cewar Mama tana zare ido "Bashi na samo kuma Dan Allah karki d'aga hankalin Ki nan bada jimawa ba zan mayar musu da kud'in su" Shiru Mama tayi tana tunanin ina d'anta zai samo wad'annan kud'in harya ya biya , azahiri kuma saita bishi da fatan alkhairi, Mik'e wa yayi yace ma Umar suzo suje su biya kud'in su dawo dayake akwai receipt a hannun su direct bank din cikin asibitin suka je suka biya kud'in , tare da siyan magunguna suka dawo , Satin su d'aya a asibitin aka sallame su duk wannan lokacin Abdallah be gayama mahaifiyar shi cewar gonar ta ya siyar Dan ya sama matar shi lafiya ba , Ummi kuwa kyakyawan kulawa take samu awaurin mijinta da Mama Hafsa ma ba'a barta a baya ba domin kullum ita ke kai mata ruwan wanka , bayan sati biyu da sallamo Ummi Abdallah yaje ya samu mahaifiyar shi ya sanar mata da gaskiyar inda ya samu kud'i , amadadin ya tayi fushi sai yaga murmushi a fuskarta tace " Abdallah banida wani magaji aduniyar nan sai kai duk abinda na mallaka halalin ka ne , Allah yayi maka albarka , ita kuma Allah ya bata lafiya , " "Amin Mama na gode" "Yanzun ina sauran kud'in suke?" "Suna d'aki" "To Sana'a ya kamata ka fara" "Eh hakane Mama ni anawa tunanin me zai hana inrunk'a zuwa kano ina saro kayan provision " "Hakane amma shago fa ?" "Insha Allah ba matsala zan ma hadi me shago magana naji yace zai saida nashi zai koma k'auyen su". "To shikenan Allah ya bada sa'a " "Amin , bari naje na nemi Umar naji ya tafiyar zata Kasan ce mana" "To adawo lafiya " "Allah yasa" nan ya fita , Ya samu Umar yana shirin fita kasuwa inda yake tsaron shago, Nan suka sauna suka tattauna suka tsaida ranar laraba zasuje kano , danan suka wuce gurin me shago suka fara ciniki Wanda da k'yar ya karb'i dubu ashirin , *LARABA* Da safe bayan sun gama karyawa ,Abdallah yayi wanka , Dan sunyi da Umar karfe goma zasu bar gida , Abdallah ne ya d'aga waya ya kira Umar yake sanar masa da ya shirya Dan haka yafito su tafi , Bayan ya aje wayar ne Ummi dake kwance jikin Abdallah tace"yaya ji nake kamar karka tafi" Murmushi yayi yace"bakiso naje Neman kud'i ko?" "A 'ah ba haka bane kawai dai..."sai kuma tayi shiru "Kawai mene ? K'arasa mana" "Kawai inajin jikina ba dad'i ne? Cikin sauri yace"bakida lafiya ne?" "Lafiya ta k'alau yaya kawai dai tafiyar taku ce bana jin dad'in ta a raina" "Kiyi hak'uri Ummi na nima yau tunda na tashi nake jin jikina duk ba k'wari kiyi min addu'a" Wata k'walla ta share idon ta sannan tayi masa addu'ar fatan alkhairi , suna fitowa d'aki Umar yana shigowa gidan , yana ganin su ya saki wani murmushi, nan suka gaisa da Ummi sannan suka lek'a d'akin Mama fatan alkhairi tayi musu sannan suka fita Ummi sai da ta raka su k'ofar gida sannan Abdallah yace mata ta koma amma ta nok'e kafad'a ita baza ta koma ba Azaure ta tsaya tana hangen su har sai da suka b'ace ma ganin ta sannan ta koma gida jiki a sanyaye , bata tsaya fira ba ta wuce d'akin ta tana ta juyi a gado irin wasan da suka yi jiya da Abdallah ne ya ke ta mata yawo a k'wak'walwa sai murmushi take tana dad'a matse pillown data rungumo Abdallah da Umar kuwa bayan sun rabu da Ummi Umar yace ma Abdallah akwai mutumin da Alhaji Bello yake siyan kaya awajen shi a kantin kwari Dan haka suje chan d'in , Sun isa kano azahar tayi kawai sai suka tsaya wani masallaci suka yi sallah sannan suka k'arasa cikin kasuwa dayake Umar yasan shagon kai tsaye chan suka nufa, Alokacin da suka isa ana sauk'e ma Alhaji Mati kaya Dan haka ya rok'esu da sujira agama Dan kar lissafi ya kwace masa , Bayan ya gama ya hau sallamar mutane sannan ya waiwayo kan su Abdallah lokacin had la'asar ta wuce , siyayyan kayan ciyaciye na yara su suka fi yawa sannan su omo da sabulai kaya dai sosai ya had'o , ko kafin su gama magrib tayi Umar ya kalli Abdallah ya ce "ustaz dare fa yayi mu kwana a garin nan da safe sai muyi sammako" "Gaskiya bazan iya ba yau duk dare gida zan kwana " Umar yayi dariya yace " kafiso kullum ka jika gaka ga 'yar k'anwar ka" "To ya San ranka , dalla Malam wuce muje" 'Yan dako biyu suka samu suka d'aukan musu kayan sannan suka fita kasuwa suka hau adaidaita suka nufi tasha suna shiga wata motar Zaria tana tashi Dan haka dole sujira ayi sabon Lodi , Sai k'arfe Tara sannan motar ta cika akayi duk abinda ya dace mota ta tashi bayan sunyi kamar tafiyar awa d'aya kawai sai motar ta mutu da kanta , nan fa driver yayi duk iya dabarun shi tak'i tashi gashi sunyi nisa da gari gasu a k'ungurmin daji, Sunan nan tsaye masu salati nayi masu zagin driver nayi wai lefinshi ne da bai duba mota ba ya kwaso su , Abdallah kuwa shiru yayi kamar ruwa ya cishi, Kwai sai suka ga ana ta kashe musu ido da wani haske me shiga k'wak'walwa , wata razananniyar murya suka tsinkaya ana ce musu "sit on your kneels!" AI sai kowa ya hau salati Ashe 'yan fashi ne, Haka suka ruk'a rashin mutumci harzuwa wannan lokacin Abdallah yana cikin motar be fito ba sai da wani yazo ta jikin window ya hasko ko shi yace "oga kaga wani D'an iska ana magana ya zaune , " Ogan yace fito min dashi na ragaje shi kawai zagayowa yayi ya damk'o wiyan Abdallah ya fito dashi dai dai lokacin idon Abdallah yakai kan Umar dake kwance jini yana ta zuba a hancin shi da alama suma yayi fincikewa yayi daga ruk'on da suka mai ya tafi wajen Umar aguje yana fad'in "Umar meya same ka ta...." Wani irin zafi yaji Wanda saida jini ya fito ta hancin shi Ashe bakin bindiga suka buga ma a kai "Muzaka yi ma taurin kai to ba irin mu ake yima ba" haka suka yita dukan Abdallah duk da ya suma basu k'yale shi ba , saida suka tabbata sunyi mishi babbar illa sannan suka k'yale shi Matan kuwa Dama su biyu ne nan suka tasa k'eyar su suka tafi dasu mazan kuma suka barsu kwance tare da k'wace duk wata dukiya dake tare dasu [12/26/2017, 8:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *This page is mine💃💃 💃💃happy anniversary to my self I hope you ga _ys will wishes me*_ 😘🏌‍♀ ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Kasan cewar dare ne kuma wurin ba wurin tsayawar mutane bane shiya sa basu samu temako ba sai da safe , wani me mota ne yazo wuce wa yaga mutane kwance kamar mattatu , nan da nan ya d'aga waya ya kira 'yan sanda , ba b'ata lokaci aka kwashe su sai asibitin Aminu kano , direct emergency aka wuce da su , Da bincike da bincike kowa D'an uwan sa ya runk'a zuwa amma banda mutum biyu , wato Umar da Abdallah , Umar ya farka sai dai be San inda kanshi yake ba , Abdallah kuwa har yanzun bema ko motsa ba, likitoci suna iya k'ok'arin su akan shi domin duk ciki ya fisu shan a zaba, *ZARIA* Ummi , Mama da kuma Hafsa kowa yayi cirko-cirko a tsakar gida , kowanan su da a binda yake sak'awa acikin ransa , iya k'ololuwar tashin hankali suna cikin su , "Ummi sake Kiran wayar muji" Mama ta fad'i cikin wata murya me ban tausayi Ummi jiki ba k'wari ta danna number Abdallah , still a kashe wasu hawaye ne suka sake yi mata ambaliya a fuska , "Aunty Ummi swich up ko?" Ita dai Ummi d'aga kawai tayi domin Sam ta kasa bada amsa , Haka suka zauna a wajen har kusan k'arfe biyu na dare , Ummi ce taga kukan ba zai fisheta ta ba ta mik'e ta d'auki buta yau ko tsoron ba ta ji , ta nufi bayi , tana fitowa ta d'aura alwala duk sai suka bita da ido , Mama a zuciyar ta tace "wannan ita kad'ai ce mafita" Duk sai sukayi alwala suka shige d'aki, kowa ya kai kukan shi ga Allah Wanda shi kad'ai ne buwayi gagara misali mai biyan buk'atun bayin sa, Koda safiya tayi suna zaune a tsakar gida sunyi jigum gidan tamkar ba mutane , A haka Maman Umar ta shigo da sallama Wanda da ganinta ita ma Kasan batayi kwanan dad'i ba , bayan sun gaisa sama-sama sai tace "Wai yaran nan basu dawo bane? " Mama cikin jimami tace"wallahi bamu gansu ba jiya kwana ne kawai ba muyi a tsakar gidan nan ba " "Inalillahi wa inna'ilaihir raji'un, ya Allah ka sa muji alkhairi" cewar Maman Umar "Amin " duk suka amsa Hafsa ce tace "Mama ya kamata aje a fad'a ma Malam ko da temakon da zai iya yi" "Hakane Hafsa kinyi tunani me kyau , yanzun tashi kije Ki sanar mishi " "To Mama" ta mik'e jiki ba kwari ta fita , Ummi kuwa wata alwalar ta sake yi ta nufi d'aki , Mama ta kalli Maman Umar tace " ina jin tausayin kaina ina jin tausayin yarinyar nan jiya haka ta kwana banda kuka da sallah babu abin da take yi " Maman Umar tace "wallah jibi yadda duk ta susuce , Ya Allah ka bayyanar mana da yaran" "Amin" dukkan su suka amsa Bayan Hafsa ta sanar ma da Malam halin da ake ciki ba shiri ya bazamo ya taho gidan Dan jin cikakken bayani , Mama ta fara magana "wallah Malam tunda suka fita jiya babu su ba labarin su har yau" "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un , ai ni Da naga ban gansu a masallaci ba da asuba inace ko gajiyar hanyace , Allah ka bayyanar mana da su" "Amin" kowa yace Dai-dai nan Ummi ta fito daga d'aki Dan ta jiyo muryar mahaifin nata , ahankali ta tako gefen Hafsa ta zauna tare da gaishe shi , bayan ya gaisa ya fara yi musu nasiha tare da kwantar da hankali , gami da cewar" Idan har dare yayi basu dawo ba to gobe shida wasu almajiran shi zasu tafi kano Neman su" Nan dai sukayi godiya ya tafi , Mama ta kalli Hafsa ta ce "je Ki dama ma Ummi koko tasha magani" "Mama nak'oshi"Ummi tace tana kifa kanta akan gwuiwoyinta "Baki CI komai bafa Ummi rabon Ki da abinci tun jiya da rana shi d'in ma ba wani ci ka kayi ba kina ta jagwal-gwalawa , " Ummi dai shiru tayi Maman Umar tace " haba Ummi Ki yi hak'uri ko kokon Ki sha kinga ba lafiya ce ta wada ce Ki ba " "To"kawai tace "Ke Hafsa je Ki damo mata" Wasa-wasa har dare ba wani chanji hakan yasa Malam ya nemi biyu daga cikin manyan almajiran shi da su raka shi kano , safiya nayi kuwa suka bazama, *_kano_* Tunda likitoci suka yi iya bakin k'ok'arin su akan Abdallah cikin ikon Allah numfashin shi ya dawo amma kuma gashi nan kwance kamar gawa , wani Babban Doctor suka kari yazo ya duba shi , koda yazo yaga Abdallah Sam ya kasa d'auke idanun shi a kansa , wani Doctor ne ya matso kusa yana magana "Ka sanshi ne Doctor?" Shiru yayi yana tunanin abinda zai ce sai kuma yace"ina 'yan uwansa suke?" Nan wancen Doctor din ya kwashe duk tsautsayin da ya faru da su Abdallah ya fad'a masa , Cikin tausaya wa Doctor ya ce "wannan yaron wani mak'oci nane , ayi masa duk abinda ya dace", Suka chanja Abdallah d'aki , ana fita dashi Umar ya farka , babu Wanda ya fara kira sai Abdallah , Bayan ya D'an huta suka fara yi mishi tambayoyi kamar haka Wani Doctor Usman ya fara cewa "ya sunan ka?" "Umar" a tak'aice ya bashi amsar "Inane garinku?" "Zaria" "Mekazo yi a kano?" "Munzo Sarin kaya ne nida d'an'uwa na Abdallah" Doctor Usman ya maimaita Kalmar "D'an uwa fa kace?" "Eh" inji Umar yana dad'a kallon Doctor d'in "To gaskiya duk cikin Ku ku goma da aka kawo babu Wanda 'yan'uwan shi basu zo ne manshi ba sai kai" "A'ah likita indai ina cikin asibitin nan to na tabbata Abdallah na ciki iyayen mu d'aya da shi " "To mudai kai kad'ai ka rage mana anan " Wani mugun fad'uwar gaba ne ya ziyarci Umar shidai yasan last seen d'inshi da Abdallah ya ganshi cikin mota tsaye kuma yaji sanda d'aya daga cikin 'yanfashin yayi magana akan Abdallah afili ya furta "innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, Allah kasa ba sun tafi min da d'an'uwa na ba" "Maybe sunzo basu gane ka bane dubi yadda ka chanja kammani gaba d'aya" Doctor ya fad'i yana nuna masa wani d'an k'aramin madubi Daya kalli fuskarshi sai da gabanshi ya fad'i tabbas yasan ba kowa zai gane shi ba Dan ko shi kanshi badan yasan shine ajikin madubin ba daya k'aryata kanshi, Doctor ne ya tsinke mishi tunani da cewa " idan ka haddace number d'aya daga cikin 'yan uwan ka kabani sai na sanar musu" Shiru Umar yayi sannan ya tuna number Malam nan ya bada , alokacin Malam suka shigo garin kano wayar shi Nokia rakani toilet ta fara ruri , ganin bak'uwar lamba yayi cikin sanyin jiki ya amsa tare da sallama Ad'ayan b'angaren ma aka amsa tare da fad'in "suna na Doctor Usman ina aiki a asibin Aminu kano dake cikin garin kano , muna da wani patient me suna Umar yace kai D'an'uwan sane" "Alhamdulillah dama yanzun su muka zo nema" Nan Doctor yayi ma Malam kwatancen inda zai same shi idan yaje asibitin , basu b'ata lokaci ba suka isa Kasan cewar asibitin yana farkon gari ne , koda suka k'arasa asibitin basu sha wahala ba suka samu Doctor Usman tunda akwai waya nan yayi musu jagora zuwa d'akin da Umar yake nan ya kaisu Malam cikin razani da tashin hankali ya k'arasa inda Umar ke jingine , gaba d'aya halittar shi ta sauya nan suka jajanta ma juna Malam ya tambaye shi labarin abinda ya faru , shi kuma ya kwashe ya sanar masa "To ina Abdallah?" Abinda Doctor dai ya gayama Umar shi ya gaya musu game da Abdallah nan hankali ya k'ara tashi har dare ana Neman Abdallah amma babu bayani Washe gari da safe aka sallami Umar , suna ji suna gani suka kamo hanya ba tare da Abdallah ba kowa da zullumi acikin zuciyar shi , "me zasu ce ma Mama akan *Bawan Allah* ?????" [12/27/2017, 8:23 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *To readers ina Wanda ya shirya zuwa kano Neman bawan Allah Sadiya neman bawan wa Allah Wanda rashinsa Sam baiyi mata d@d'i ba cikin sa'a ko ta samu abokan tafiya Maman sa'a tace ba'a barta a baya ba dole su nema wa Ummi farincikin ta , aceeya kuwa cewa tayi jirgin ya tsaya ajigawa ya d'auke , Amne kuwa da yake 'yar black stormach ce 🤪cewa ta ba inda za'a je saboda man fuel yayi tsada , Aunty axland ma tace ba'a barta a baya ba*🤣🤣🤣 ❤ *Gaisuwar fatan alkhair agareku masoya masu bibiyar littafin bawan Allah sakon ku na fatan alkhairi yana isowa agarene nagode agaskiya bansan da bakin da zan gode muku ba amma kusa ni har cikin raina inajin dad'in yadda kuka amshi wannan litttafin nagode sosai Allah ya had'a fuskokin mu a aljannatul firdaus Amin ya Allah*❤❤❤. *one luv*😘 *Ameenart Nd fatima (MAMAN Sadeeq) wannan page d'in naku ne dama d'aukacin yan Bawan Allah fans , I really like your comments❤* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 21----22 Haka nan su Malam suka tattara suka koma Zaria ba tare Abdallah ba zuciyoyin su cike da zullumin me zasu gaya ma mahaifiyar shi da kuma matar shi , ahaka suka sauka a tasha suka hau napep , direct gidan su Umar suka wuce , Aiko Maman Umar na ganin shi sai kuka domin yadda ta Ganshi ba k'aramin firgita tayi ba nan k'annen shi suka hau ihu " yaya Umar oyoyo !" D'an autan su ne ya fita da gudu yaje gidan su Abdallah Ummi na alwalar la'asar Mama na kofar d'aki Hafsa kuma tafito daga bayan gida , Yaron ya k'arasa kusa da Mama cikin zumud'i yake ce mata "Mama yaya Umar ya dawo " Cikin zafin nama Ummi ta waigo tana kallon shi Mama ko cewa tayi "da gaske ?!" "Eh Mama amma ya dawo kanshi a d'aure da wani Abu" AI nan Ummi ta yarda butar hannun da dama already akwai hijab ajikin ta AI sai ta nufi k'ofar gida , "Ke Ummi ina zaki je ?" Mama ta fad'i yadda taga Ummi zata fita kamar zautacciya "Ina zuwa Mama "kawai Ummi tace tasa kai Hafsa da sai yanzun ta k'araso waje sai k'wala kira tayi "Aunty Ummi jira ni" AI ina AUNTY Ummi gudu-gudu sauri-sauri ta runk'a had'a wa , 💔💔💔💔💔💔💔💔 *Kano* Yau kwana bakwai kenan ana fama da Abdallah amma Sam be san ana yi ba gashi zuciyar shi tana aiki amma kuma gangar jikin shi bata motsi , duk sun sare da al-amarin shi, Yauma kamar kullum likitoci ne zaune awani k'awataccen office suna tattaunawa akan Abdallah , wata nurse ta shigo cikin sauri ta fara gaya musu patient din room no 18 ya farka kamar jira suke nan suka mik'e cikin sauri suka k'ara k'ofar d'akin , A zaune suka same shi akan gadon ya sakko da k'afafun shi k'asa , ya rik'e kanshi dake tsananin Sara masa , Koda suka bud'e k'ofar suka shigo kallo kawai ya bisu dashi domin be tab'a ganin su ba , Doctor d'in nan ne da ya ce ya sanshi ya matsa kusa da shi ya fara magana "Ni sunana Dr Ahmad , zan iya sanin naka sunan?" Shiru yayi bece komai ba , Dr Ahmad ya sake cewa "ko zan iya sanin naka sunan?" "Ban sani ba" ita ce amsar da ta fito daga bakin Abdallah Dukkan su likitocin suka kalli junan su Dr Ahmad ya sake jefa mashi wata tambayar "ya sunan garin ku?". Girgiza kai yayi nan ma alamar be sani ba Nan likitoci suka sake firgita wani likita ne ya ce mai "nan ina ne ?" K'are ma d'akin kallo yayi tas sannan ya runtse idon shi gami da matse hannun shi kamar zai kai naushi Dr Ahmad ne yace su k'yale shi ya huta , nan suka yi mai allurar barci ya koma 💔 [12/28/2017, 7:26 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* 🌹 *ZURI'A D'AYA*🌹 *BY UMMU BASHEER* 🌹 *Congratulation sister for successful completing your amazing book ZURI'A D'AYA more grace to your powerful elbow*🌹 🌹 *KEEP SHINING DEAR*🌹 ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ #PMLWRITERS@GMAIL.COM # WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 2⃣3⃣ 2⃣4⃣ Akwana bakwan nan kuwa babu abinda su Ummi suke sai addu'a , Malam sai da yaje kano sau uku amma duk bawani cigaba Wata safiya ce Malam ya yi sallama gidan su Abdallah aka bashi izinin Shiga , bayan 'yan gaishe-gaishe da k'ara jajanta ma juna , sai ya k'ara da cewa "Nayi istihara akan b'atan yaron nan alamu sun nuna yana nan da rai kuma cikin kyakyawan masauki sai dai akwai k'unci a tattare da shi" Mama ta share k'walla ta ce " to Malam yanzun ya za'ayi?" "Addu'a , Addu'a ita ce kad'ai mafita" Nan dai suka cigaba da tattaunawa , Ummi kam tana d'aki duk tunani ya gama addabar ta shi yasa ma bata ji zuwan Malam d'in ba , *KANO* Dr Ahmad ne zaune a office d'in shi tunani duk ya da meshi ya kasa samun solution akan damuwar shi, Nan ya d'aga waya ya kira Dr Usman ba b'ata lokaci sai gashi ya iso , Bayan ya zauna ne Dr Ahmad ya fara, "Dama akan maganar patient d'in nan ne yaron mak'oci na , ina so zan maida shi zuwa k'asar London domin duba lafiyar shi" Ido Dr Usman ya zaro" you just say London?" "Yeah ,any think?" "No sir" "OK yanzun ina son kuyi discharging d'in shi domin in samu gudanar da shirye shirye na cikin sauki ?" "Ok sir insha Allah ba damu wa" Nan suka yi sallama ya tafi , Kamar yadda Dr Ahmad ya buk'ata haka aka sallami Abdallah alokacin da ya tashi aiki ya shiga d'akin shi domin tafiya dashi Yauma kamar kullum azaune ya same shi yayi shiru ba tunani yake ba domin ba shida abinda zai tuna Da sallama ya shigo d'akin , Abdallah ya amsa mai sannan ya k'arasa shiga d'akin d'auke da murmushi a fuskar shi , "Abdallah tashi mu tafi gida " Sunan da yaji an kirashi da shi sai da ya razana ya kasa tuna inda ya San sunan amma tabbas sunan yana da muhimmaci a wajen shi , Dr ne ya katse mai shirun shi da cewa "ko kafi so ka CI gaba da zama a nan ne kayi ta barci?" Kai ya girgiza alamar baya so "To tashi mu tafi" Cikin natsuwa ya mik'e ya bi bayan shi , Suna fita daga d'akin suka CI karo da Dr Usman rik'e da wani file a hannun shi , yace . "Yawwa sir ga records din " Nan ya karb'a tare da godiya nan Dr Usman ya raka su har bakin mota sannan ya juyo , shikuwa ya tada motar shi ya d'au hanya , hanyar gidan shi ya d'auka da ke cikin G R A gidan Babban gida ne kuma da kagani Kasan Wanda ya mallaki wannan gidan ba k'aramar dukiya gareshi ba , Flat ne guda biyu a gidan tangama tangama , bayan yayi parking motarsa ya fito Abdallah ma ya mik'e ya fito d'aya daga cikin flat d'in suka nufa shi dai Abdallah tafiya kawai yake batare Da yasan inda aka dosa ba, , Key yasa ya bud'e k'ofar d'akin sannan ya ba Abdallah izinin shiga , tun da Abdallah ya d'aga kai bai sauke ba har sai da yaci tuntub'e da center table , shiko Dr murmushi kawai yake sannan yace , "Nan d'akin ka ne akwai duk wani abun buk'ata aciki bari nasa akawo maka abinci" Kai kawai ya gyad'a tare da zama acikin d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun d'akin, Tunani da yawa yake acikin ransa , wane ne shi?, waye kuma wannan mutumin? Waye Abdallah , sunan da yafi d'aga masa hankali kenan idan ya tuna, Yana nan zaune Dr ya shigo shi da wani matashi d'auke da tire a hannu , Cike da mamaki matashin ya tsaya yana kallon Abdallah , sai da Dr ya daka masa tsawa sannan ya aje kayan abincin ya fita , Kusa dashi Dr ya ya zauna sannan ya dafa kafad'ar shi yace"Babana tashi muje na nuna maka d'akin ka kayi wanka lokacin magrib yayi " Jin maganar sallah ya sashi saurin mik'e wa , wata k'ofa ya bud'e suka kutsa , bedroom ne na gani na fad'a tamkar a k'asar turai , duk kayan more rayuwa akwai gidan , directtoilet ya wuce da shi ya nuna masa yadda zaiyi amfani da komai sannan ya kullo masa k'ofar ya fita, Cikin tsoro Abdallah ke wanka har ya gama ya fito kayan da ya cire ne ajikin shi ganin wasu kaya yayi an aje mai su akan bed nan ya cire na jikin shi ya sasu , k'ananan kaya ne sunyi matuk'ar yi mishi kyau asalin kyanshi da talauci ya b'oye duk sun bayyana, masu karatu zanso kuga *Bawan Allah* Ko da ya fito pallor ba kowa , daga gefen kujera yata an shimfid'a mishi sallaya , nan ya hau ya gabatar da sallah *Waye DR AHMAD* Dr Ahmad bakano ne ciki da bai awata k'aramar hukuma da ake cema Rano , *Ahmad Abdallah* shine cikakken sunan shi su biyu ne awajen iyayen su shi da k'anwar shi *Fiddausi* Alhaji Abdallah d'an kasuwa ne yana da rufin asirin shi dai dai na Alhajin k'auye, matar sa d'aya ce *Maimuna* kuma ita ta Haifa masa yaran sa biyu da yake matuk'ar so da k'auna, Tun asalin Ahmad mutum ne me son taimakon jama'a hakan ya sanyan ya sanar mawa mahaifin shi yana son zama likita , mahaifin shi ya bashi kulawa ta musamman har ya kammala karatun shi, nan mahaifin shi yayi mishi aure da wata 'yar abokin shi *RAMLA* Bayan bikin shi da kimanin wata uku ya samu aiki a asibitin Aminu kano , bayan shekara d'aya Ramla ta sunkuto d'anta namiji yaci suna *Abdallah* suna kiran shi da Abba, Dr Ahmad ya samu nasarori masu d'imbin yawa ciki harda bud'e asibiti nashi mai zaman kanshi wato private sai da Abdallah ya shekara goma sannan Ramla ta sake haifo wani namijin yaci sunan Babanta *Abubakar* Abdallah yana da shekara ashirin da bakwai ya gama karatun shi na law a k'asar England saurayi ne ajin farko kamili, alokacin da ya dawo aka fara batun auran shi da wata yarinya *Aisha* amma kuma cikin ikon Allah bikin shi saura wata d'aya ciwan ciki ya murd'e shi ya rasu , K'ololuwar tashin hankali Dr Ahmad da Hajiya Ramla sunshige shi amma da suka sa tawwakalli sai suka hak'ura , , Masu karatu idan kuka ga *Abdallah Ahmad Abdallah* ba zaku banban tashi da *Abdallah Abdallah* ba Wannan ne mafarin taimakon da Dr Ahmad yake shirin yima Abdallah [12/29/2017, 7:53 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* 🌹 *ZURI'A D'AYA*🌹 *BY UMMU BASHEER* 🌹 *Congratulation sister for successful completing your amazing book ZURI'A D'AYA more grace to your powerful elbow*🌹 🌹 *KEEP SHINING DEAR*🌹 ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ #PMLWRITERS@GMAIL.COM # WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 2⃣3⃣ 2⃣4⃣ Akwana bakwan nan kuwa babu abinda su Ummi suke sai addu'a , Malam sai da yaje kano sau uku amma duk bawani cigaba Wata safiya ce Malam ya yi sallama gidan su Abdallah aka bashi izinin Shiga , bayan 'yan gaishe-gaishe da k'ara jajanta ma juna , sai ya k'ara da cewa "Nayi istihara akan b'atan yaron nan alamu sun nuna yana nan da rai kuma cikin kyakyawan masauki sai dai akwai k'unci a tattare da shi" Mama ta share k'walla ta ce " to Malam yanzun ya za'ayi?" "Addu'a , Addu'a ita ce kad'ai mafita" Nan dai suka cigaba da tattaunawa , Ummi kam tana d'aki duk tunani ya gama addabar ta shi yasa ma bata ji zuwan Malam d'in ba , *KANO* Dr Ahmad ne zaune a office d'in shi tunani duk ya da meshi ya kasa samun solution akan damuwar shi, Nan ya d'aga waya ya kira Dr Usman ba b'ata lokaci sai gashi ya iso , Bayan ya zauna ne Dr Ahmad ya fara, "Dama akan maganar patient d'in nan ne yaron mak'oci na , ina so zan maida shi zuwa k'asar London domin duba lafiyar shi" Ido Dr Usman ya zaro" you just say London?" "Yeah ,any think?" "No sir" "OK yanzun ina son kuyi discharging d'in shi domin in samu gudanar da shirye shirye na cikin sauki ?" "Ok sir insha Allah ba damu wa" Nan suka yi sallama ya tafi , Kamar yadda Dr Ahmad ya buk'ata haka aka sallami Abdallah alokacin da ya tashi aiki ya shiga d'akin shi domin tafiya dashi Yauma kamar kullum azaune ya same shi yayi shiru ba tunani yake ba domin ba shida abinda zai tuna Da sallama ya shigo d'akin , Abdallah ya amsa mai sannan ya k'arasa shiga d'akin d'auke da murmushi a fuskar shi , "Abdallah tashi mu tafi gida " Sunan da yaji an kirashi da shi sai da ya razana ya kasa tuna inda ya San sunan amma tabbas sunan yana da muhimmaci a wajen shi , Dr ne ya katse mai shirun shi da cewa "ko kafi so ka CI gaba da zama a nan ne kayi ta barci?" Kai ya girgiza alamar baya so "To tashi mu tafi" Cikin natsuwa ya mik'e ya bi bayan shi , Suna fita daga d'akin suka CI karo da Dr Usman rik'e da wani file a hannun shi , yace . "Yawwa sir ga records din " Nan ya karb'a tare da godiya nan Dr Usman ya raka su har bakin mota sannan ya juyo , shikuwa ya tada motar shi ya d'au hanya , hanyar gidan shi ya d'auka da ke cikin G R A gidan Babban gida ne kuma da kagani Kasan Wanda ya mallaki wannan gidan ba k'aramar dukiya gareshi ba , Flat ne guda biyu a gidan tangama tangama , bayan yayi parking motarsa ya fito Abdallah ma ya mik'e ya fito d'aya daga cikin flat d'in suka nufa shi dai Abdallah tafiya kawai yake batare Da yasan inda aka dosa ba, , Key yasa ya bud'e k'ofar d'akin sannan ya ba Abdallah izinin shiga , tun da Abdallah ya d'aga kai bai sauke ba har sai da yaci tuntub'e da center table , shiko Dr murmushi kawai yake sannan yace , "Nan d'akin ka ne akwai duk wani abun buk'ata aciki bari nasa akawo maka abinci" Kai kawai ya gyad'a tare da zama acikin d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun d'akin, Tunani da yawa yake acikin ransa , wane ne shi?, waye kuma wannan mutumin? Waye Abdallah , sunan da yafi d'aga masa hankali kenan idan ya tuna, Yana nan zaune Dr ya shigo shi da wani matashi d'auke da tire a hannu , Cike da mamaki matashin ya tsaya yana kallon Abdallah , sai da Dr ya daka masa tsawa sannan ya aje kayan abincin ya fita , Kusa dashi Dr ya ya zauna sannan ya dafa kafad'ar shi yace"Babana tashi muje na nuna maka d'akin ka kayi wanka lokacin magrib yayi " Jin maganar sallah ya sashi saurin mik'e wa , wata k'ofa ya bud'e suka kutsa , bedroom ne na gani na fad'a tamkar a k'asar turai , duk kayan more rayuwa akwai gidan , directtoilet ya wuce da shi ya nuna masa yadda zaiyi amfani da komai sannan ya kullo masa k'ofar ya fita, Cikin tsoro Abdallah ke wanka har ya gama ya fito kayan da ya cire ne ajikin shi ganin wasu kaya yayi an aje mai su akan bed nan ya cire na jikin shi ya sasu , k'ananan kaya ne sunyi matuk'ar yi mishi kyau asalin kyanshi da talauci ya b'oye duk sun bayyana, masu karatu zanso kuga *Bawan Allah* Ko da ya fito pallor ba kowa , daga gefen kujera yata an shimfid'a mishi sallaya , nan ya hau ya gabatar da sallah *Waye DR AHMAD* Dr Ahmad bakano ne ciki da bai awata k'aramar hukuma da ake cema Rano , *Ahmad Abdallah* shine cikakken sunan shi su biyu ne awajen iyayen su shi da k'anwar shi *Fiddausi* Alhaji Abdallah d'an kasuwa ne yana da rufin asirin shi dai dai na Alhajin k'auye, matar sa d'aya ce *Maimuna* kuma ita ta Haifa masa yaran sa biyu da yake matuk'ar so da k'auna, Tun asalin Ahmad mutum ne me son taimakon jama'a hakan ya sanyan ya sanar mawa mahaifin shi yana son zama likita , mahaifin shi ya bashi kulawa ta musamman har ya kammala karatun shi, nan mahaifin shi yayi mishi aure da wata 'yar abokin shi *RAMLA* Bayan bikin shi da kimanin wata uku ya samu aiki a asibitin Aminu kano , bayan shekara d'aya Ramla ta sunkuto d'anta namiji yaci suna *Abdallah* suna kiran shi da Abba, Dr Ahmad ya samu nasarori masu d'imbin yawa ciki harda bud'e asibiti nashi mai zaman kanshi wato private sai da Abdallah ya shekara goma sannan Ramla ta sake haifo wani namijin yaci sunan Babanta *Abubakar* Abdallah yana da shekara ashirin da bakwai ya gama karatun shi na law a k'asar England saurayi ne ajin farko kamili, alokacin da ya dawo aka fara batun auran shi da wata yarinya *Aisha* amma kuma cikin ikon Allah bikin shi saura wata d'aya ciwan ciki ya murd'e shi ya rasu , K'ololuwar tashin hankali Dr Ahmad da Hajiya Ramla sunshige shi amma da suka sa tawwakalli sai suka hak'ura , , Masu karatu idan kuka ga *Abdallah Ahmad Abdallah* ba zaku banban tashi da *Abdallah Abdallah* ba Wannan ne mafarin taimakon da Dr Ahmad yake shirin yima Abdallah [12/29/2017, 7:56 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *To readers ina Wanda ya shirya zuwa kano Neman bawan Allah Sadiya neman bawan wa Allah Wanda rashinsa Sam baiyi mata d@d'i ba cikin sa'a ko ta samu abokan tafiya Maman sa'a tace ba'a barta a baya ba dole su nema wa Ummi farincikin ta , aceeya kuwa cewa tayi jirgin ya tsaya ajigawa ya d'auke , Amne kuwa da yake 'yar black stormach ce 🤪cewa ta ba inda za'a je saboda man fuel yayi tsada , Aunty axland ma tace ba'a barta a baya ba*🤣🤣🤣 ❤ *Gaisuwar fatan alkhair agareku masoya masu bibiyar littafin bawan Allah sakon ku na fatan alkhairi yana isowa agarene nagode agaskiya bansan da bakin da zan gode muku ba amma kusa ni har cikin raina inajin dad'in yadda kuka amshi wannan litttafin nagode sosai Allah ya had'a fuskokin mu a aljannatul firdaus Amin ya Allah*❤❤❤. *one luv*😘 *Ameenart Nd fatima (MAMAN Sadeeq) wannan page d'in naku ne dama d'aukacin yan Bawan Allah fans , I really like your comments❤* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 21----22 Haka nan su Malam suka tattara suka koma Zaria ba tare Abdallah ba zuciyoyin su cike da zullumin me zasu gaya ma mahaifiyar shi da kuma matar shi , ahaka suka sauka a tasha suka hau napep , direct gidan su Umar suka wuce , Aiko Maman Umar na ganin shi sai kuka domin yadda ta Ganshi ba k'aramin firgita tayi ba nan k'annen shi suka hau ihu " yaya Umar oyoyo !" D'an autan su ne ya fita da gudu yaje gidan su Abdallah Ummi na alwalar la'asar Mama na kofar d'aki Hafsa kuma tafito daga bayan gida , Yaron ya k'arasa kusa da Mama cikin zumud'i yake ce mata "Mama yaya Umar ya dawo " Cikin zafin nama Ummi ta waigo tana kallon shi Mama ko cewa tayi "da gaske ?!" "Eh Mama amma ya dawo kanshi a d'aure da wani Abu" AI nan Ummi ta yarda butar hannun da dama already akwai hijab ajikin ta AI sai ta nufi k'ofar gida , "Ke Ummi ina zaki je ?" Mama ta fad'i yadda taga Ummi zata fita kamar zautacciya "Ina zuwa Mama "kawai Ummi tace tasa kai Hafsa da sai yanzun ta k'araso waje sai k'wala kira tayi "Aunty Ummi jira ni" AI ina AUNTY Ummi gudu-gudu sauri-sauri ta runk'a had'a wa , 💔💔💔💔💔💔💔💔 *Kano* Yau kwana bakwai kenan ana fama da Abdallah amma Sam be san ana yi ba gashi zuciyar shi tana aiki amma kuma gangar jikin shi bata motsi , duk sun sare da al-amarin shi, Yauma kamar kullum likitoci ne zaune awani k'awataccen office suna tattaunawa akan Abdallah , wata nurse ta shigo cikin sauri ta fara gaya musu patient din room no 18 ya farka kamar jira suke nan suka mik'e cikin sauri suka k'ara k'ofar d'akin , A zaune suka same shi akan gadon ya sakko da k'afafun shi k'asa , ya rik'e kanshi dake tsananin Sara masa , Koda suka bud'e k'ofar suka shigo kallo kawai ya bisu dashi domin be tab'a ganin su ba , Doctor d'in nan ne da ya ce ya sanshi ya matsa kusa da shi ya fara magana "Ni sunana Dr Ahmad , zan iya sanin naka sunan?" Shiru yayi bece komai ba , Dr Ahmad ya sake cewa "ko zan iya sanin naka sunan?" "Ban sani ba" ita ce amsar da ta fito daga bakin Abdallah Dukkan su likitocin suka kalli junan su Dr Ahmad ya sake jefa mashi wata tambayar "ya sunan garin ku?". Girgiza kai yayi nan ma alamar be sani ba Nan likitoci suka sake firgita wani likita ne ya ce mai "nan ina ne ?" K'are ma d'akin kallo yayi tas sannan ya runtse idon shi gami da matse hannun shi kamar zai kai naushi Dr Ahmad ne yace su k'yale shi ya huta , nan suka yi mai allurar barci ya koma 💔 [12/30/2017, 10:59 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 2⃣5⃣ *Cigaban labari* A b'angaren Dr Ahmad kuwa be b'oye ma iyalin shi komai game da Abdallah ba , Hajiya Ramla tayi farin ciki sosai har ta k'osa safiya tayi taga me kama da d'anta, *Zaria* Yau kusan sati uku kenen ba labarin Abdallah hakan bai sauya akalar damuwa acikin zuciyoyin dangin sa ba musamman ma mahaifiyar shi da matar shi , Ummi kuwa yanzun wani irin tsantsar son Abdallah ne ke damun ta gashi yayi mata nisa , Dan yanzun gani take bayan iyayen ta babu Wanda take ma so da k'auna tare da mararin gani irin Abdallah, Malam kuwa ya duk'ufa addu'oi ba dare ba rana , Umar kuwa Alhamdulillah ya ji sauk'i sai dai damuwar rashin d'anuwan shi amininshi, shi kad'ai ke tayar mai da hankali akoda yaushe Hafsa ce keta fama da Ummi akan taci abinci " haba Aunty Ummi yanzun ke kullum sai an ta fama da ke wajen cin abinci kamar k'aramar yarinya ?" Ummi dai bata ce komai ba iya kacin k'walla da keta gudu a kan kumatunta , Hafsa ta sake cewa , " ayyah k'awata Dan Allah ciki kinga rabon Ki da abinci tun jiya da rana gashi yanzun Kusan k'arfe uku" Kallon Hafsa tayi tace "zanci amma sai in zaki bani a baki " ta k'arasa maganar cikin shagwab'a "Naji duk wannan me sauk'i ne " Nan Hafsa tayi ta ba Ummi abincin tana ci , haka Mama ta fito ta samesu duk sai suka bata tausayi, *Kanon Dabo* Kamar yadda Dr Ahmad ya tsara acikin sati uku ya samar masu *Visa* shida D'an mak'ocin sa kamar yadda yake fad'i , basu bar garin ba sai da yasan yadda yayi ya masamar ma Abdallah takaddun makaranta sannan suka d'aga birnin *London* Sosai Abdallah yayi k'auyanci Kasan cewar bai tab'a sanin wani Abu makamancin k'asar ba , A wani hotel suka sauka , bayan sun D'an huta sannan Dr ya nema masa Wanda zai runk'a koya mai turanci Ba da jimawa ba ya saman mai admission a London university , inda zai karanci medicine, Sosai Abdallah ya maida hankali wurin karatun shi saboda bashida damuwar kowa acikin k'wak'walwar shi, Sai da Dr ya tabbar da Abdallah ba shida matsalar komai sai nan ya dawo Nigeria tare da barin shin amanar shi awajen wani Bature 💟💟💟💟💟💟💟 Wasa-wasa dai yanzun wata takwas da b'atan Abdallah ko wanda yaga me kama da shi basu gani ba, Abun da yake k'ara d'aga ma Ummi da Mama hankali bai wuce duk in sunyi istikhara suna samun natsuwa ba hakan ke nuna musu Abdallah yana cikin kwanciyar hankali, to amma yana ina ne? Mai ya sa yayi nesa da su? Shin baya tunanin halin da zasu shiga ne? Wad'an nan tambayoyi su suke ta yawo a k'ak'walen su amma kuma kaf babu mai amsa masu su, Wata rana Mama tashir ya taje gidan su Ummi domin su tattauna da mahaifiyar ta akan makomar auren Ummi da Abdallah, Bayan sun gaggaisa tace " Dama nazo ne akan maganar wad'an nan yaran , kinga yanzun wata takwas amma bawan Allah shiru , shine nace ko za'a raba auren Ummi idan ta samu wani mijin tayi aure" Maman Ummi tace " amma Maman Hafsa sai naga kamar yayi wuri afara wannan maganar balle ma muna sa ran insha Allah ba da jimawa ba zai dawo" Ajiyar zuciya Mama tayi sannan tace " to AI shikenan ni dama naga k'a'idar musulunci wata shida ne shiya sa kuma da naga babu rabo a tsakanin su" "Hakane Maman Hafsa my dai k'ara hak'uri" Nan dai suka gama maganar su ta tafi , Ummi na kwance a d'aki tunani duk ya isheta Mama ta d'aga labulen d'akin ta shigo da sallama amma Ummi Sam bata ma anayi ba , Sai da Mama ta dafa ta sannan ta waigo a firgice ta kalleta "yanzun Ummi ba zaki cire wannan yawan tunanin a ranki ba ,? Shi wanda kike yi Dan shi d'in yana chan hankalin shi kwance bema San kina yi ba , Dan Allah Ki rage tunanin nan kar ya haifar miki da wata matsalar kuma" Cikin jin kunya Ummi tace "to Mama" 💟💟💟💟💟💟💟 *BAYAN SHEKARA D'AYA DA RABI* *London* Wa ni had'add'en guy ne na gani na fad'a zaune a cikin library yana karatu fuskarsa d'auke da wani farin glass , kamar daga sama , yaji an ce mai "Hi" D'agowa yayi yakalli wanda yayi maganar shima matashi shi ne kyakyawa , "hi"kawai yace masa ya maida hankalin shi zuwa littafin da yake dubawa Matashin ya sake cewa " please can I have a sit?" D'aga mishi kai kawai yayi , , Shi kuma wancan ya zauna yana murmushi, mik'amai hannu yayi yace " I'm saifullah from Nigeria " Sai alokacin mai karatun ya aje littafin tare da cire glass d'in idonshi sannan ya mik'a masa hannu sai ya ce " Abdallah also from Nigeria" *Nikam nace lallai ma lallai Ashe Abdallah ne gaskiya ya k'aro wulak'anci* Cike da murmushi Saifullah ya ce "Ashe dai nasamu D'an uwa" Murmushi kawai Abdallah ya mai , Saifullah irin mutanan nan ne masu shegen surutu ba irin su Abdallah ba miskilai, Ba jimawa suka saba sosai har suka k'ulla abota [1/1, 6:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 2⃣6⃣ Mama ce zaune a tsakar gida ta zabga tagumi tana kallon Ummi da keta faman wanki , hak'ik'a yarinyar tana matuk'ar bata tausayi tayi aure amma bata San miye auren ba balle ta tantance dad'in shi , babu abinda ta tsinta a cikinshi sai wahala ita irin tata k'addarar auren kenan , can kuma ta mik'e kamar an tsikare ta , ta zari Hijab d'inta da ke sagale jikin k'ofa sannan ta juya ta ce ma Ummi "bari naje na dawo" "To Mama adawo lafiya" Mama na fita bata zame ko ina ba sai gidan su Ummi ta ci sa'a ta samu Malam yana nan bayan sun gaggaisa ta fara fad'in abin da ya kawo ta , "Dama Malam Maganar Ummi ne ya kawo ni" Malam yace "to Allah yasa dai ba laifi tayi ba" "Ko kad'an Malam Ummi bata laifi , sai dai mune muke k'ok'arin yi mata laifi" "Kamar yaya kenan?" "Malam tunda kaga har yanzun Abdallah bai dawo ba kuma gashi shekara har ta gota Dan Allah anema ma yarinyar nan sauk'i a raba ta da wannan auran" Shiru Malam yayi sannan yayi ajiyar zuciya yace "maganar Ki gaskiya ne amma kafin mu yanke hukunci ya kamata muji ta bakin Ummin , Dan haka idan kin koma Ki turo min ita " "To shikenan Malam mungode Allah ya k'ara girma" Nan suka k'ara tattaunawa akan maganar sannan Mama ta yi musu sallama ta tafi , Mama kuwa bayan sallar isha ta kira Ummi tace mata taje Malam yana Neman ta , sai da ta D'an ji gaban ta ya fad'i amma kuma ta daure ta tafi , Kai tsaye cikin gidan su ta nufa bayan gaishe-gaishe suna D'an fira da k'anan ta a tsakar gida sai ga Malam ya shigo , Maman Ummi ta shimfid'a mai tabar ma ya zauna suka gaisa sannan ya k'ara da cewa " Ummi dama ba wani Abu bane yasa nakira Ki akan auran Ki ne da Abdallah shin kin yarda a raba ko kuwa zaki iya hak'urin jiran shi?" Tunda Malam ke magana hawaye suke ambaliya a fuskar Ummi , ta kasa magana , Malam ne ya sake magana "ina jinki Ummi baki ce komai ba " Ummi ta fara magana muryar ta na rawa " Baba Dan Allah karku raba ku D'an k'ara mai lokaci Dan Allah Baba" Shiru Malam yayi domin ya fahimci 'yar tashi tana son mijin ta "shikenan Ummi mun k'ara mai shekara d'aya idan be dawo ba ko ba da yardar Ki ba za'a warware auren nan" "Baba na amince na gode" "Shikenan Allah yayi miki albarka shi kuma Allah ya bayyanar mana dashi" "Amin" Ummi tace sannan kuma tayi shiru "To tashi Ki tafi dare nayi ko kuma akwai Wani Abu ne " Shiru tayi kamar bazata ce komai ba sannan kuma ta fara magana bakinta na rawa "Baba dama alfarma nake nema" "Ki fad'eta ko menene indai bai sab'a ma addini na ba zanyi miki shi " "Baba dama so nake Dan Allah ka barni na cigaba da zuwa makarantar boko" D'agowa yayi ya kalli 'yar tasa cikin natsuwa sannan yace "Ummi ba nak'i kiyi karatu bane , ah'a imani ne yayi rauni a zukatan wasu , duk da cewar bani da kokwanto akan tarbiyyar da na baki , amma igiyar auran da ke kanki?" "Insha Allah Baba nayi maka alk'awarin kare mutunci na ko ina da aure ko banda shi , Dan Allah Baba ka amince min karatun shi zai rage min damuwa" Jinjina kai yayi tare da gamsuwa da zancen 'yar tasa sannan yace " kije zanyi shawara duk abin da na yanke zaki ji" Godiya tayi sannan suka yi sallama ta Shiga d'akin Ummin ta , sukayi sallama sannan ta Shiga d'akin abokiyar zaman Umman nata ta fito ta koma gida , Da sallama ta Shiga Hafsa da Mama ne a tsakar gida sai kuma Umar da ke zaune gefe d'aya yana sharb'ar tuwan dawa miyar kuka da taji daddawa , dukan suka amsa mata sannan suka gaisa da Umar , tayi ma Mama barka da dare ta wuce d'akin ta , Katifar ta tahau ta yi matashi da pillow d'aya d'aya kuma ta rungume shi tsam ajikin ta kamar za'a k'wace mata shi , wasu zafafan hawaye suka gangaro mata a fuska a hankali ta fara magana " mijina *KADAWO GARENI* ( by Rafee'at D/Dukko) suna shirin rabamu , hakan yana nufin rabuwa ta har abada domin duk randa na aka katse igiyar auran mu na tabbata bazan moruba" nan dai tayi ta Sumbatun ta har bacci yayi gaba da ita Kamar yadda ta saba karfe uku na dare take tashi ta gabatar da nafilfili har sai alfijir ya keto sannan ta had'a da raka'atanil fijri sannan bayan tayi sallah tak'ara da karatun littafi mai tsarki sannan ta fito tsakar gida Susan abinyi ita da sahibar ta, wannan itace d'abi'ar Ummi, A b'angaren Abdallah kuwa karatun shi kawai yasa gaba ba ruwan shi da kula 'yan mata , kuma har sun gaji da naci idan ma suka dameshi har mari yake had'awa dashi , sau dayawa Saifullah yana k'ok'arin tank'wara shi amma ina Abdallah kaifi d'aya ne baya tank'waruwa , haka rayuwa take cigaba da wanzuwa atsakanin su, Ab'angaren Ummi kuwa ranar wata juma'a Malam ya aiko mata da wata takarda a nannad'e a cikin Leda yaron yace mata gashi ita da Hafsa , Tana bud'ewa form ne na wata makarantar gwamnati ya sama masu , ai aguje ta ruga d'akin Hafsa tana k'wala mata kira , Saida ta Shiga d'akin sannan ta b'oye takardar tare da fad'in " nazo miki da albishir amma sai kin ban goro" Hafsa da ta farka daga bacci ta fara magana had'e da mik'a "lallai AUNTY Ummi wannan al-amarin mai girma ne tunda na ganki cikin farin ciki" "Ke nidai Ki daina b'ata min lokaci Ki bani goro nabaki albishir " Hafsa tace "to naji zan siyan miki biscuit d'in nera goma " Ummi ta bita da harara tare da fad'in " saboda kin maidani k'aramar yarin ya ko? To Ki bari lokacin da kika tanadi goron kizo Ki karb'i albishir d'in naki " ta kama hanyar k'ofa Cikin hanzari Hafsa ta bi bayan ta tana fad'in " haba Aunty Ummi tawa , Aunty Ummi ta yaya Abda...." Ummi ta katse ta tare da nuna mata form d'in dai dai nan Mama ta fito tana fad'in "hayaniyar me nakeji ne?" Ummi ta gayawa Mama ko mene ne , Mama taji dad'i sosai sannan ta bi Malam da addu'ar fatan alkhairi sannan ta ce ma su Ummi suje suyi mishi godiya @08165728746 [1/2, 7:22 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *Dedicated this page to you my k'awalli , Allah ya raya mana Sadeeq, kekuma Allah ya.....🤭 kindai gane ba sai na k'araso ba*🤣 ❤ *Much love dear*❤ ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 2⃣7⃣ Cikin sa'a Ummi da Hafsa suka fara zuwa makaranta , uniform d'in yayi musu kyau Kasan ce warshi Navy blue da white sunyi matuk'ar kyau a cikin shi , SSS1 aka sasu , Kasan cewar makarantar tana da d'an nisa da unguwar su amma sabo tsabar son ayi karatun haka suke takowa suje a k'afa su dawo a k'afa , babu ranan da zasu fita maza basu biyo su ba sunan Sam magana da su amma Sam basa sauraran su hakan yasa dole Ummi ta fara sa nik'ab amma duk a banza , Dan wasu ma da suka gane gidan nasu kai tsaye suke zuwa Susa yara suyi sallama , duk da Hafsa tasha gaya musu cewar Ummi matar aure ce amma Sam basa yarda , tun Malam be San meke faruwa har yazo ya sani amma dai ya zuba mata ido ne kawai lokacin da suka d'iba ya ciki, A b'angaren Dr Ahmad kuwa komai zai yi ma Abdallah tsakani da Allah yake yi mai baya la'akari da cewar bashi ya haife shiba duk wani Abu na more rayuwa ya mallaka mai tun daga kan suturar sawa har zuwa mota me tsada tare da sauran a bubuwan more rayuwa Dr baya k'yashin sai mishi , yanzun haka yana nan yana gina wani tamfatsetsen asibiti da niyyar idan Abdallah ya dawo ya mallaka mai shi, A b'angaran Abdallah kuwa karatun shi yake sosai ya madai hankalin shi , shima Saifullah ba baya ba yana da k'ak'walwa sai dai shi wani lokacin yana da barkwanci kamar Umar, a haka suke karatun su Wanda ko Hutu akayi basa dawo wa Nigeria, *BAYAN SHEKARA D'AYA* Ummi ce zaune gaban Malam , Ummin ta , Mama da kuma Inna a bokiyar zaman Babar ta duk sun tsura mata ido , ita ko sai faman k'walla take share wa , Cikin sanyi Malam ya fara magana "Ummi tun d'azun muke miki magana baki bamu amsa ba gashi sai kuka kike yi " Cikin kukan ta fara magana " Baba Dan Allah kar ku raba in da yaya Abdallah wallahi ni ina ji ajiki na yana Raye be mutu ba " Mama ce tace "to yanzun Ummi ai ba zaki zauna kiyi ta jiran shi ba yan zun kusan shekara uku fa , kiyi hak'uri Ummi " Ummi ta kalli Mama tace "yanzun Mama har da ke ake shirin rabani da Abdallah ?" Karin Mama tayi magana Inna ta amshe " Ummi muna sonki muna k'aunar Ki shiyasa mukayi wannan tunanin Ki fahimce mu ba muna nufin cizguna miki bane" Malam yayi gyran murya yace " shikenan Ummi na sake k'ara miki shekara d'aya amma kisani daga wannan ba k'ari ," Shiru tayi sannan kuma ta jinjina kanta alamar ta yarda , Sannan Malam ya ce ta tashi ta tafi , Tana Shiga gida Hafsa ta samu tana shara , Hafsa na ganinta ta shigo idon nan jajir ga k'walla suna sintiri a Kumatun ta ta saki tsitsiyar ta nufi kanta tana fad'in "Aunty Ummi lafiya ?, mai aka miki?" Cikin sauri Ummi ta k'arasa kusa da Hafsa tan rungume ta tana kuka tana fadin " Hafsa zasu raba ni da farin cikina da jin dad'i na ," Hafsa cikin d'aurewar kai ta ce "Aunty mene ne wannan abun da za'a rabaki dashi ?" Cikin kukan ta sake cewa "zasu rabani da yaya Abdallah bayan duk sun San ba mutuwa yayi" Cikin sigar lallashi Hafsa take shafa bayan Ummi tare da fad'in " kiyi shiru Aunty Ummi , babu Wanda zai raba ku , kuma insha Allah yaya zai dawo gare Ki" Sun kusan minti goma atsaye Hafsa tana ta faman lallashin Ummi sannan ta hak'ura ta tafi d'akin ta kan katifarta ta fad'a tare da dafe kanta da take ji kamar ana sa gatari ana Sara mata shi, ahankali kuma take fad'in "Yaya Abdallah meya ka nisanta dani? Shin baka San ina sonka bane ? Shin baka tunanin halin Dana ke ciki?, yaya rashin ka zai sa su guntule igiyar auran mu" Ta k'arasa tare da sakin kuka mai siririn sauti nan da nan jikin ta yayi zafi sai zazzab'i chan kuma ta hau rawar sanyi , Shiko Abdallah suna zaune a d'aki shi da Saifullah suna buga game sai Saifullah yaji abokin nashi yayi shiru juyawa yayi ya kalleshi tare da fad'in "bro's how far?" Kai Kawai ya girgiza mishi domin wani irin bugawa da ya wuce misali yake jin zuciyar shi tana mishi , Wanda har ya kasa magana, Sake tab'ashi Saifullah yayi sannan yace "ba kada lafiya ne aboki na ?" Cikin rauni ya kalli Saifullah ya girgiza gami da dauriya suka cigaba da game d'in . Hafsa kuwa data ga Ummi ko alwalar magrib bata fito tayi ba gashi har an idar da sallar Isha yasa ta d'auki kwanon abincin su ta bita ta d'aki tana Shiga ta same ta tana ta rawar sanyi , ahankali ta k'arasa kusa da ita tare da tab'a wuyanta zafi rau ga wani irin numfashi da take yi sama sama , a tsorace Hafsa tace "Aunty Ummi bakida lafiya ne?" Ummi kawai ido ta bita dashi sai wasu zafafan k'walla dake gangaro mata, Hafsa na ganin haka ta mik'e cikin sauri ta fita , fitarta yayi daidai da sallamar Umar ta amsa shi cikin firgice ta sanar ma da Mama halin da Ummi ke ciki, dukkan su suka d'unguma suka Shiga d'akin Cikin tausayin Ummin , Umar ya ce ma Mama ta D'an shafa mata ruwan sanyi bari ya he ya siyo mata magani ya dawo , Haka kuwa akayi ba'afi minti ashirin sai gashi ya dawo d'auke da ledar magani ,shafa mata ruwan sanyin da mama tayi yasa ta D'an ji dama-dama Cikin sanyin murya yace mata "sannu Ummi" "Yauwa "ta fad'i sannan ya mik'a ma Hafsa maganin tare da fad'in "ku bata ta sha idan taci abinci , no zan Shiga gida sai da safe" Godiya suka yi mai ,shiko rashin jin dad'in hakan yasa shi yamutsa fuska tare da fad'in"haba Mama yanzun Dan nayi muku wani Abu sai kun gode min idan kina gode min sai naga kamar kin ban-bantani da Abdallah Wanda bana jin dad'in hakan" Ajiyar zuciya Mama tayi sannan tace "Allah yayi muku albarka , Allah ya jib'inci lamuran ku ya kare ku daga sharrin masharranta ya sada ku da alkhairin sa" Cikin jin dad'in addu'ar mama duk suka amsa da "amin" Sannan Umar yayi musu sai da safe ya fita, [1/3, 3:37 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* *Readers bansan da bakin da zan gode muku ba akan addu'oin fatan alkhairi da kuke min nagode nagode Allah ya bar k'auna Allah ya sada mu a aljannatul firdaus*🤝 *Fiddausi (maman junior)*❤ *k'ungiyata abin alfaharina ina jidaku ina alfahari da ku da bazarku nake rawa REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS Allah ya k'ara mana hazak'a da basirar nishad'antar da masu karatu*🤝 ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 2⃣8⃣ Ummi kam kwanan ta uku taji sauki har ta fara zuwa makaranta sai dai damuwa da yayi mata yawa tana yawan tunani wani lokacin sai kazo kusa da ita ka gama duk abinda zakayi bata sani ba , Hafsa kam ta shiga damuwa ganin halin da k'awarta take ciki , Wata rana suna school antashi break Hafsa ta fita ta samo musu D'an abin da zasuci , tana fita Ummi ta dasa tunani har Hafsa ta dawo bata San ta dawo ba, saida ta tab'ata tare da fad'in "Wallah Aunty har za'a iya sace Ki baki sani ba " Harara ta balla mata tare da fad'in "tunda na zama gunki ko?" "A'ah ni bance kin zama gunki ba , nidai CI Waran nan Principal yana Neman mu a office d'in shi" D'an kwab'e baki tayi sannan suka fara ci , Hafsa tana tunatar da ita illar tunani , ahaka suka gama ci sannan suka nufi office din P C kamar yadda suke Kiran shi , ko da suka suka isa sun Tarar da students takwas gefen P C vice d'in shine yana rik'e da wani file a hannun shi , bayan sun gaida su P C ya fara magana kamar haka , "Lura da yanayin k'ok'arin ku a aji shiyasa muka zab'eku , kuna da k'ok'arin da yawuce ace kuna SSS2, Dan haka mun yi muku alfarma kuje ku sanar ma iyayen ku zasu biya Rabin kudin jarabawar W A E C sauran kuma gwamnati zata biya " Cike da jin dad'i d'aliban suka fara godiya gami da nuna farincikin su , Vice Principal ya ciro receipt me d'auke da iya yawan kud'in da zasu biya , sannan suka k'ara godiya suka koma classes d'in su , Ummi da Hafsa kuwa sai zumud'i ake akoma gida , Dan Ummi har ta manta da bak'in cikin da take tare dashi , Bayan an tashi kai tsaye gidan Malam suka nufa suka gaya mai shi kanshi yaji dad'i sannan yace musu suje gida ba wani damu wa insha Allah bazai gagara ba , da murna suka tafi, Gidan Mama kuwa da sallama suka Shiga Hafsa ce tayi turus ganin mahaifinta cikin sanyi ta k'arasa Ummi kuwa Dama bata San Hafsa ta tsaya ba nan duk suka gaishe shi tare da tambayar mutanan gida sannan Ummi ta nufi d'akin ta Mama ko tana band'aki basu sameta a tsakar gidan ba, Baban Hafsa ya kalleta cikin kula yace "ya makaranta ba dai wata Matsala ko ?" Bayanin da PC yayi musu shi tayi mai ,murmushi yayi sannan yace " to ai ba damu wa idan na koma gida zan turo Bello da kud'in " cike da jin dad'i Hafsa ta fara godiya Baban ya sake cewa " Hafsa Ki natsu Ki maida hankalin Ki kiyi karatun nan Dan nan gaba inyi alfahari da ke" "Insha Allah Baba ba za'a samu wata Matsala ba" Dai dai nan Mama ta fito tana fad'in " 'yan makaranta an dawo?" "Eh Mama ya gida ?" "Lafiya lau " Hafsa ta tashi ta Shige d'akin ta domin ta chanja kaya tayi sallah , Ummi kuwa da yake ba sallar take ba kwanciyar tayi har saida Ummi ta kawo musu abinci sannan ta tashi suka ci, 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 Ko wani Uba ya jajirce wajen Samar ma 'yar sa farin ciki kuma yanzun Alhamdulillah an dace Dan yanzun har sun gama zana exams d'insu both NECO , WAEC Nd JAMB, admission kawai suke jira, Cikin sa'a kuwa suka samu admission a A B U ,dukan su zasu karanci Medicine bak'aramin dad'i suka ji ba mu sammam ma iyayen da su kad'ai suka San kud'in da suka kashe, Bayan suyi registration da wuri ba har sai da aka fara lectures , sannan suka gama suka fara attending , Mutane da dama suna son yima Ummi magana daga mazan har matan amma rashin sakin fuskarta kesa su kasa zuwa wurin ta , ita ko bata San ma suna yi ba , Hafsa ce mai D'an sakin fuska har tayi k'awaye, Watanni sunja lokaci ya tafi wata rana umma na zaune a class d'in su sai ga wani lecturer ya aiko wai a kira masa Zainab Kabir , Wani fad'uwar gaba ne ya Ziyarci zuciyar ta kawai sai ta fara fad'in "INNALLILAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN" Hafsa dake gefen ta tace"Aunty Ummi kefa ake kira" Jiki a sanyaye Ummi tabi bayan shi har zuwa office d'in mutum , ita dai bata taba ganin shi ba amma , gashi kallon da yake mata kad'ai yana sa hanjin ta juyawa , Mutumin ya kalli Wanda suka shigo tare ya ce masa "you can go" "Ok Sir" matashin ya bada amsa tare da barin office d'in Juyawa yayi ya kalli Ummi wadda da ka ganta Kasan a firgice take "zauna mana 'yammata" yafad'i tare da nuna mata kujerar dake opposite d'in shi ya , Cikin sanyi ta zauna , Murmushi yayi sannan yace " Malam Zainab nasan baki sanni ba amma ni nasan Ki kuma ina bibiyar Ki , Ki bani dama in yaye miki k'unci da kewar dake addabar zuciyar Ki" Cikin zaro ido da firgici Ummi tace "Subhanallah nifa matar aure ce" Ido ya kanne mata irin nasu na 'yana duniya yace "karki damu Zainab dama ba aure zamuyi ba kawai zamu d'an huta ne mu mori junan mu " Ummi kam salati kawai take ta faman rafsawa Shikuwa k'aton banzan sai ya sake ce mata "karki damu babu Wanda zai San meke faruwa a tsakanin mu daga ni sai ke , kuma nayi miki alk'awarin samun nasara arayuwar duk abinda kike buk'ata indai kud'i nayin shi zanyi miki " Cikin hasala ta fara magana "kaico kaico shin da kake cewa babu mai ganin mu Allah da ya hallice mu fa? Idan ka manta bari na tuna maka , Allah ne ya hallice mu baki d'aya Dan haka ko k'asa muka hak'a muka shige Allah yana kallon mu kuma baka isa kai D'an Adam kayi Katanga tsakaninka da mahaliccin ka ba, kuma ka sani bana buk'ar taimakon wani abun hallitta balle kai azzalumi Allah ne gatana kuma shi na dogara shi kad'ai zai biya mun buk'atuna " Wata dariyar mugunta yayi sannan yace" duk kalaman Ki bazasu sa na chanja k'uduri na a kanki ba baby kin had'u , Ki taimaka min na lashi zumar nan" Wani bak'in ciki ne ya turnuk'e Ummi gashi tana so tayi kuka ta kasa kai sai ta mik'e zata fita , takai dai dai wajan k'ofa tajiyo muryar shi yana cewa "baby na baki kwana biyu kije kiyi tunani Idan baki amince ba kuma duk abin da ya biyo baya ke kika ja" Wani dogon tsaki taja tare da fad'in "Allah ya fika "ta fita Shiko jingina yayi yana jin sha'awar ta yana k'ara azazzalar shi, Ita kuwa Ummi kanta ne yake juyawa nan ta lallab'a wa tana tana tafiya a hankili Chan sai ta fara ganin duhu ba tare da tasan inda take ba ta duk'e awaje ta jingina da glass d'in da yake hanyar mutane basu cika wuce wa sosai Shiya sa ta d'au tsawon lokacin da ita kanta bata san lokacin da ta d'auka awajen ba, Kamar daga sama taji wata sassanyar murya tana fad'in "Baiwar Allah lafiya kike zaune anan ?" Ahankali ta d'ago kanta tare da sauke idanun ta akan matashin kallo d'aya tayi mai ta sake kauda kanta domin gaskiya guy d'in ya had'u ga iya dressing fa kyau kuma da ganin alama iyayen sa masu k'unbar Susa ne ba tare da Cewa komai ba mik'e wa tayi har ta juya zata tafi sai kuma taji ya k'ara cewa " Sis ga jakar Ki" Ba tare da ta juyo ba ta karb'a tare da fad'in "thanks" Murmushi yayi tare da biyo ta abaya yana fad'in "Suna na Aminullah Alhassan ina department of business administration ina two hundred level" Bata bashi amsa ba sai ma k'ara sauri da tayi , domin ita duk atunanin ta shima shed'anar yazo mata dashi, Sake jin muryar shi tayi yana cewa " tunda dai ba zaki yi sharing k'uncun Ki dani ba to Dan Allah ki saurareni bai kamata kitafi kina d'auke da fuskar shanu ba" ya k'ari ke yana murmushi , Ita ko kalaman shi na k'arshe yasa ta juyo wa daidai lokacin kuma ya saki murmushi "Me kake nufi da fuskar shanu?" Ta k'ara tamke fuskarta D'aga kafad'ar shi yayi sannan ya ce "ba abinda nake nufi ,amma da zaki runk'a yin dariya tauraruwar Ki sai ta fi haskawa" Ta bud'e baki zata yi magana kenan ta ji an tab'o ta ta baya rud'e ta juya , Hafsa ce tsaye sai nishi take kamar wadda tayi gudun famfalank'i duk da yana yin da Ummi ke ciki taso tayi dariya amma sai ta daure tace "Ke kuma fa lafiya? kinzo sai nishi kike kamar wata zakanya" "Eh dole Ki ce haka mana bayan duk kin gama ba mutane wahalar nemanki for more than an hour Ashe kina nan" "To ina ruwanki da nema na ko ni yarinya ce da zan b'ata?" Cikin b'acin rai Hafsa tace "naga Wanda ya fiki shekaru ma ya b'ata har yanzun ba labarin shi bare ke , to Ki sani ko kin b'ata ba zanje Neman Ki ba" Nan Ummi ta had'a girar sama da k'asa tsabar bak'in ciki ma ta rasa me zata ce Hafsa na ganin hakan tasan k'awar tata fushi tayi kawai sai ta rungumeta tana lallashi cikin sigar tsokana har sai da tayi dariya sannan ta jata suka bar gurin Shiko Aminullah tunda suka fara yake kallon su har suka tafi yana binsu da ido , ahankali kuma ya furta "I love your dramer" [1/4, 8:49 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 2⃣9⃣➕3⃣0⃣ Tunda suka koma gida Hafsa ta lura Ummi tana cikin wata damuwar da tafi tada tana so ta tambaye ta amma kuma ta kasa , wani tunanin ne kuma ya sake bijiro matashin saurayin da ta ganshi tare da Ummi meye tsakanin su?, ita dai takan Ganshi amma ba kullum ba kuma tana Ki k'ayenta na yawan yin zancen akan suna son shi, wata zuciyar kuma tana cewa karki zargi k'awarki domin kema kinsan ba halinta bane , daga k'arshe dai ta yenke shawarar zuwa ta tambayeta , Koda ta Shiga d'akin ta sameta a zaune atsakiyar katifa ta had'a kanta da gwuiwoyin ta tana kuka bilhak'i da gaskiya , Azuciyar Hafsa ko cewa tayi "ita kam Aunty Ummi kuka baya mata wuya" k'arasawa tayi kusa da ita cikin tausayi ta dafa kafad'ar ta , har wannan lokacin Ummi bata d'ago ba , Cikin sanyin murya Hafsa tace "k'awata me ke damun Ki ne ?, ko maganar da na fad'a miki d'azun ne?" Girgiza kai tayi alamar "A'ah " Hafsa ta sake cewar " to mene ne ? Kinji yadda jikin Ki yayi zafi kuwa?" Cikin kuka Ummi ta sanar ma da Hafsa abin da wannan lecturer d'in ya fad'a mata har had'uwar su a Aminullah , "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un lallai wannan anyi D'an iska , insha Allah ba zai samu nasara ba " Nan dai Hafsa tayi ta kwantar mata da hankali har ta D'an saki ranta , 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 *THE NEXT DAY AT SCHOOL* Bayan sun samu interval d'in lecture suka fito waje suna shan iska ita ko Ummi zuciyarta cunkushe yake da fargaba domin bata San me zai faru gobe tsakanin ta da wannan shed'anin ba, Hafsa ce ta gaji da shirun tace " Aunty Ummi ba dai tunanin wannan fasik'in kike ba ?" Ajiyar zuciya Ummi tayi sannan ta ce " dole inyi tunanin shi mana Hafsa kaidin wani mutum d'in yafi sharrin shed'an" "Hakane amma Allah ba zai bashi galaba a kanki da yardar Allah" Ummi ta bud'i baki zata yi magana kenan taji wani k'amshi ya doki hancin ta juyawa tayi ta kalli Hafsa taga ita ma ita take kallo a tare suka d'aga idanuwan su suka zuba kan Aminullah, nan da nan dukkan su suka d'auke Kansu , A cikin Takun da baifi uku ba ya k'araso inda suke tare da sallama , A dak'ile suka masa mai murmushi yayi sannan ya ce "sisters ya kuke ?" Ba samu amsa daga bakin Ummi ba sai dai Hafsa ce tace "lafiya " itama a dak'ile ta amsa , Kallon Ummi yayi yaga ta wani d'auke kai murmushi yayi yace "sis ba dai fushin jiya ya shafe ni ba?" Nan ma bata tanka mai ba sai ya koma kusa da Hafsa kujerar da ke kusa da ita ya zauna tare da fad'in "sis wai me ke damun k'awar Ki ne tun jiya nake ganin ranta a b'ace jiya da k'yar nayi bacci saboda halin da na ganta ciki" Hafsa ko baki ta saki azuciyar ta tace "lallai wannan bashida hankali " Daya ji shirun yayi yawa ne yace "au kema shiru zaki yi ?" Wata zuciya ce tace ma Hafsa Ki fad'a mishi abinda ke faruwa ko zai iya temaka muku, Nan ta bashi labarin komai daya faru , Cikin b'acin rai yace "ya sunan lecturer ?" Shiru tayi tana so ta tuna sunan da taji an fad'i jiya da k'yar ta tuna Ta kalli Aminullah tace "D'an Asabe" Murmushi mugunta yayi yace" hakane na tuna jiya akusa da office d'in shi na ganta dama kuma ina da case dashi double fire kenan " Matsawa yayi kusa da Ummi ya ce "karki damu sis insha Allah daga kanki bazai k'ara marmarin zina ba ", Da k'yar ta iya cewa "nagode" Sallama yayi musu tare da fad'in "ku jira result zuwa gobe "ya Shiga motar shi domin k'arasawa department d'in su Ummi ce ta juya ta ce ma Hafsa "ke banza ce wallahi ya kawai daga ganin mutum zaki zauna Ki saki baki kina ta surutu , to yanzun da kika gaya mishi me zai iya yi?" "Haba Aunty Ummi Ki fahimceni ni ba da wata manufa na fad'i mai ba kawai gani nake zai iya taimakawa amma idan banyi miki dai dai ba to Ki yafeni" Ajiyar zuciya Ummi tayi tare da fad'in "shikenan ya wuce" nan dai sukayi ta hirarrakin su daga k'arshe suka koma class , Shiko Aminullah tunda ya tafi yake shirya k'ulum botom da zai shirya ma D'an Asabe cikin murnar samun mafita yace "zaka ci ubanka" ya saki wata dariyar mugunta, 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 *AT NIGHT* Wata dalleliyar mota ce k'irar CRV ta faka a parking space din Quarters d'in lecturers da ke cikin makarantar b'arayin me zaman banza da b'arayin driver aka bud'e , wasu matasa ne guda biyu cikin bak'ak'en kaya d'aya yana zuk'ar segret d'ayan kuma yana tofar da miyau gami da toshe hanci yana fad'in "wallah kai banza ne nagaya maka bana son warin wannan abar amma saboda tsabar iskanci sai ka shata a gabana ". D'ayan yace "guy charge nake domin naji dad'in karta rashin mutum ci ", Dai dai nan suka isa inda suke son Shiga , tab'a k'ofar sukayi suka jita a bud'e , sai d'ayan ya cema mai shan segret d'in ya lek'a ta window'n' ko akwai matsala , bayan minti biyu ya dawo yace"ya sama kanshi jaraba ba dole ya manta ya bar k'oda bud'e ba yana chan yana shanawa" Cike da takaici d'ayan yayi k'wafa ahankali suka tura k'ofar suka Shiga tare da lab'e wa abayan wata kujera dake lungu , Sai alokacin na gane waye d'ayan Ashe Aminullah ne , tab Lokaci zuwa lokaci suna duban agogo suda suka zo tun k'arfe goma gashi gashi yanzun shabiyu , d'ayan ya bud'e baki zai yi magana kenan suka ji an bud'e k'ofa lakwaf sukayi wata budurwa ce ta fito cikin wasu tsinannun English wears sai wani taku take cikin yauk'i , sai da wuce da kimanin minti talatin sannan suka mik'e suka kashe kulle k'ofar har zasu bud'e k'ofar bedroom d'in sai abokin Aminullah yace tayani mu harmutsa d'akin nan sai da suka ma d'akin biji-biji sannan suka kashe globe d'in d'akin suka fad'a bedroom d'in 🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 [1/5, 9:22 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 3⃣1⃣ Ko da suka Shiga d'akin yana kwance akan gado ya lullub'e da alama barci ya fara yi , Aminullah ne yayi ma abokin shi nuni da ya zagaya ta d'ayan b'arayin koma ya nemi kan bedside drower ya zauna tare da d'ora k'afa d'aya kan gadon , sunsa D'an Asabe a tsakiya , Wata 'yar k'aramar wuk'a Aminullah ya Ciro a aljihun shi me kama da ta wanzamai , ahankali yake yawo da wuk'ar akan wuyan D'an Asabe , mak'wat ya had'iye wani miyau chan dai dayaji waiwayin ya isheshi sai ya kawo duka zafin da yaji a hannunshi shi ya sashi farkawa ciki magagin bacci azabar dake k'ara ratsa shi ne yasa shi bud'e ido me zai gani jini ne keta zuba a hannun shi cikin firgici ya d'aga kanshi yayi tozali da Aminullah wani wawan mari ya sakar mai yanda sai da ya daina gani na 'yan sakwanni , wata muguwar dariya ce yaji abayan shi yana juyawa yaji an sake d'auke shi da wani Marin cikin firgice ya fara fad'in, "Wayyo Allah na Dan Allah me na miki?, su waye ku?" Cikin wata irin murya Aminullah yace " zakasan ko mu su waye , zaka San ko me kamana amma sai kayi laushi tukun , oya come down my friend!" Jiki na rawa ya sakko a gadon kamar Wanda beda jini ajikin shi , Abokin Aminullah ya ce "maza kayi frog jump sau hamsin" Cikin zarana D'an Asabe ya ce "Oga ina da matsalar ciwon k'afa fa " "Keep quite sanda kake turmushe 'ya'ya da matan mutane kana tuna k'afarka na ciwo ne banza kawai" ya had'a mai da wani Marin , Chan kuka ga D'an Asabe yahau tsallen kwad'o , shiko Aminullah gefe ya koma ya barshi da gwaska A wahale D'an Asabe yayi frog jump ashirin shima yana yi ya tuntsurawa dukkan ninsu dariya suke ta cikin k'yallen da suka rufe fuskokin su , sai da wahala sannan Aminullah ya taso daga inda yake yace "guy tale min shi namai kaciya ". Nan D'an Asabe ya hau muzurai da ido jikin shi sai kyarma yake , Nan guy ya Fara kici-kicin cire mai wando , cikin magiya D'an Asabe yace "Dan Allah Dan Allah kar ku min wallahi anmin tun ina D'an shekara bakwai" Wata harara guy ya wurga mai sannan cikin k'arfi ya ja gajeran wandan ya yi k'asa , hankalin shi be k'ara tashi ba sai da yaga Aminullah yayo kanshi da Aska AI ba shiri ya zabura zai gudu gajeran wandon shi ya tad'iyeshi ya fad'i ji kake TIM!! , D'an Asabe yasha k'asa , da dai yaga har yanzun k'ara Mateo shi yake AI sai ya tak'ark'are yayi parlour a guje haba basai wani sabon satin ba ji kuke k'um! Gwaram !!, D'an Asabe ko na chan parlour yana cin karo da kayan d'akin da aka yamutsa idan yayi sai yaci karo ko ya hantsala , Sukam su Aminullah suna chan suna jiyo ihun shi , sukam sai dariya suke ci ma'ishin su sai da suka gama dariyar sannan suka fita parlour suka kunna switch d'in gloves d'in D'an Asabe ne zigidir a tsaye tsakiyan center table sai muzurai yake fuskar nan duk ta kumbura ga wata uwar zufa da ke ketomai kamar yayi gudun famfalank'i K'arasa wa suka yi kusa da shi sannan Aminullah ya fara magana "wato kai k'wallan D'an iska ko iskan cin naka ya koma kan matan aure ko to kad'an ma ka gani muddun zaka ci gaba da irin haka" Cikin rawar baki D'an Asabe yace "wallahi yallab'ai indai wannan ne na daina amma Dan Allah ku k'yale ni haka" Cikin tsawa guy yace "kai! Kana tunanin zamu tafi ne bamu tab'a lafiyar jikin ka ba to kayi k'arya "damk'o shi yayi turmushe yace "Man zo ka D'an sha jinin shi" D'an Asabe sai zillo yake amma ya kasa k'wacewa , yana ji yana gani ajikiyi mai siririn yanka ajikin shi sannan suka k'ara mai da gargad'in yaje ya ba Zainab Kabir k'uri in na haka ba next time kaciya zasu mishi Jiki na rawa yace" wannan duk mai sauk'i ne ai " Suka tafi suka barshi suna ta shek'a dariya 🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Washe gari da yake juma'a su Ummi basu da lectures d'in safe Dan haka sai k'are biyu suka je school suna Shiga class sai ga wani yazo ya ce" Zainab Kabir taje inji Malam D'an Asabe " sosai firgici ya bayyana a fuskarta , tana cikin tunani sai taji mutum akan ta Aminullah ne tsaye cikin manyan kaya brown d'in shadda ne ajikin shi anyi mata aiki da coffee din zare hular kanshi ma ratsin coffee da brown Kasan ce warshi fari sai abun ya k'ara sajewa farar fatar shi murmuahi kawai yake mata yayin da d'ayan hanunshi yake sanye cikin aljihun shi , ahankali ya matso kusa da ita yace " minti biyu please" yana gama fad'in hakan ya juya ya fita , Hafsa ce ta kalleta tace "Aunty Ki je mana maybe ya Samar mana mafita ne " Jiki a sanyaye ta fita yana hangota sai ya fara tafiya ahaka har sai da suka kusan office d'in D'an Asabe sannan ya tsaya tana K'araso wa ya fara magana a hankali , "Karki ji tsoro kije hak'uri kawai ze baki , na ruga da na gama da shi" ya k'arike maganar cikin murmushi Kallon shi tayi sannan tace "Anya wannan ba wani *SABON SALON YAUDARA* bane kuka zomin dashi?" Cikin sanyin murya yace "Ki yarda da ni Zainab bazan tab'a cutar da wata 'ya mace ba most especially ma ke da nake so kinga bazaki je ba shikenan dama hak'uri zai baki" Ummi wata fassara tayi daban cikin tsiwa tace" owoo dama badan Allah zaka taimaka min ba saboda na kub'uta a hannun kai na fad'o naka hannun ko , to bari kaji idan baka sani ba ni nan da kake ji da gani matar aure ce na wuce na tsaya kuna ball dani kuyi duk abin da kuka ga zaku iya ni *DA ALLAH NA DOGARA* " tana kai wa nan ta koma da baya tana tafe tana share k'walla har ta bangaje Hafsa da tazo Neman ta tafad'a ma anshiga ajinsu ita kuma ganin Ummi ta wuce a fusace kamar zakanya chan kuma ga Aminullah ya d'ora hannayen shi duk biyu akai sai abin ya d'aure mata kai Shiko Aminullah duka biyu ne Ummi tamai ga mummunar fassara gashi ta ce mishi ita matar aure ce , Cikin sauri Hafsa ta k'araso kusa da Aminullah tana fad'in meke faruwa ne ?" D'ago jajayen idanuwan shi yayi ya fara magana cikin sark'ak'yar murya "wai dagaske Zainab na da aure?" Ita ce tambayar da ya watsa mata. . With confidence Hafsa tace "Eh matar yayana ce" "To ina mijin nata yake ? Meyasa bata sanar masa matsalar ta da D'an Asabe ba?" Yasake jeho mata wata tambayar Ajiyar zuciya tayi tace " is a long story" Katseta yayi da cewar "I need to know" Bada b'ata lokaci ba tayi mishi briefing wace ce Ummi, [1/11, 1:06 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com *HAPPY ONE YEAR ANNIE PURE MOMENT OF LIFE WRITERS❤* *Dedicated to REAl PURE MOMENT OF LIFE WRITERS sisters we're the best ever , let's continue shining like a ster in the sky🌠🌠😍* *Readers ina mai Baku hak'urin rashin jina da kukayi kwana biyu wani uziri ne na musamman ya tsayar da ni amma insha Allah zaku rink'a jina akai akai*❤ *godiya mai tarin yawa gareku masoya na da fatan alkhairin da kuka yi agareni nagode Allah ya bar k'auna,*😍 *BAWAN ALLAH fans kullum burina shine nishad'an tar daku , Allah ya barmu tare*🤝 ❤ *k'awalli*🤪 ❤ 3⃣2⃣ Ummi kuwa bata zame ko ina ba sai gida , tana shiga gida Mama ta kalle ta da mamaki tace " a 'ah Ummi har an da wo?" "Eh Mama" Mama ta sake tambayar ta " ina 'yar uwar taki take ?" "Tana chan baya ni nayo gaba ne " Ummi ta fad'i tana tura k'ofar d'akin ta , Mama ta girgiza kai cike da al'ajabin hali irin na Ummi Ummi kuwa koda ta Shiga d'aki wurgi tayi da jakar makarantar ta fad'a katifar ta tana ta tuno kalaman Aminullah tabbas tasan da babu Abdallah ikon Allah ne kad'ai zai iya sa bata auri Aminullah ba domin yafi Abdallah'n' da ta sani had'uwa sai dai kuma bata San ya zuciyar shi take ba ga kuma zargin da take mishi , haka tayi ta juyi tana tunani , koda Hafsa ta shigo class Neman ta suka ce bata dawo ba tayi Neman har ta gaji daga baya dai ta yanke shawarar komawa gida ko ta koma , Ta fito dai dai bakin gate taga motar Aminullah yana ta zabga mata horn da dai kamar zata wuce sai kuma ta tsaya , Fitowa yayi daga cikin motar da kaganshi zaka gane hankalin shi ba'a kwance yake ba Dan har idon shi yayi ja cikin sanyin muryar shi yace "Hafsat ina zuwa ne ?" "Gida " ta bashi amsa atak'ai ce "To muje na sauke Keki mana kinga ana wuyar mota " "A ah ka barshi zan jira " "Hafsat kenan saboda na b'ata ma k'awarki rai shine zaki hau fushi dani ?" "Ko kad'an yanzun muka je gida dakai kuma Kasan laifin kaina zai dawo " "Babu Wanda zaisan Nina maidoki Idan kuma baki yarda da ni ba I can't furse you" Shiru ta yi na D'an lokaci tasan dai indai bata bishi ba to batasan ranar samun abun hawa ba nan tace mishi "shikenan muje" Nan da nan yaji zuciyar shi tarage suyar da take mai domin yasamu hanyar ba Ummi hak'uri , Bud'e mata motar yayi ta Shiga sannan ya rufe shima ya zagaya ya Shiga sai da ya hau titi sosai sannan ya juya yace mata " sis ina zamu je ne ?" Kwatan chan tamai cikin 'yAr dariyar shi da iyakarta fuska yace "Ashe ma bamu da nisa" "Uhum" kawai tace ta maida kallon ta titi , daga nan kuma babu Wanda ya k'ara magana , Dai dai sanda ya Shiga unguwar su ana ta kiraye kirayen sallar issha , agurguje yayi parking motar a k'ofar gidan da ta nuna mai ta fito daga motar kenan sukayi ido biyu da Malam yana ta sauri zashi masallaci , kallon da taga Malam ya mata ya sata shigewa gidan aguje , Aminullah ma nan bar motar shi ya wuce masallaci , Yadda Mama taga Hafsa ta shigo ba natsuwa yasa gabanta fad'uwa "ke lafiyarki kuwa kinwani shigo kamar an koroki " Hafsa ko sai zare ido take , Mata ta daka mata tsawa"ke Dan gidanku!? Zumb'ura baki tayi tace "ba komai fa Mama" Ta d'aga labulen d'akin Ummi ta fad'a ganin Ummin na sallah ne ya sata fita domin itama ta sauke nata faralin , Malam kuwa banyan sun idar da sallah ya tsaya bakin masallaci domin jiran saurayin da ya ganshi da Hafsa domin yana son yasan mene ne tsakamin su? Bayan Aminullah ya fito daga masallaci ya fara tafiya kenan sai yaji sallama a bayan shi , cikin natsuwa ya juya tare da amsa sallamar Dattijon ya k'ara da cewar "ka wuni lafiya Baba?" "Lafiya lau D'an samari , amma kai bak'o ne a unguwar nan ko?" "Eh Baba " Shiru ya biyo baya sai Malam ya sake cewa "na ganka tare da 'yata lafiya dai ko?" Aminullah shiru yayi sannan daga baya ya ce "ni D'an makarantar su ne ganin yamma tayi gashi babu abun hawa shi yasa na dawo da ita" Duk da cewar Malam ya yarda da nutsuwar yaron amma sai yaji hankalin shi bai kwanta ba musamman ma da yagan su su biyu ba tare da Ummi ba , Ya kalle shi yace" to ina 'yar uwarta?" "Baba Zainab ta dad'e da barin school ina tunanin yanzun haka tana cikin gida " Dai dai lokacin suka k'araso k'ofar gidan su Hafsa Aminullah ya juya cikin kulawa yace "Baba ni zan wuce a huta lafiya" "Ah d'ansamari ko ruwa baka sha ba bari nasa akawo maka ruwa " D'aya daga cikin almajiranshi ya yafito , sai gashi cikin sauri ya k'araso Malam yace " Shiga ciki kace Hafsa ta kawo ma bak'o ruwa" ya fad'i yana nuna gidan su Hafsa Sannan ya juyo ya kalli Aminullah ya ce "Bawan Allah zauna mana"yanuna mishi dakalin k'ofar gida sai da yazauna sannan yace "Baba suna na Aminullah" "Masha Allah suna me daraja " Alokacin da d'an Aiken Malam ya Shiga Mama ce kad'ai a tsakar gidan Hafsa na d'akinta tana shimfid'a Mama ta k'walla mata kira bayan ta fito taji sak'on Malam sai da gabanta ya fad'i nan dai ta daure tace "Mama ina Aunty Ummi ?" "Taje gida duba Sani yana zazzab'i " Jiki a sanyaye ta d'auki wani jug a d'akin Ummi ta kamfato ruwan randa a fita tana ta sak'e sak'e azuyarta, Tana fita tayi kicib'in da Malam da Aminullah suna ta hirarsu kamar dama sunsan juna , Gaban tane yayi mummunan fad'i amma sai ta daure ta gaida Malam tare da aje ruwan , ta juya kenan zata Shiga gida ta ga Ummi a k'ame tana mata kallon tuhuta , Ahankali ta furta "Aunty Ummi?" Cikin tsoro ta k'arasa maganar Sai lokacin su Malam suka lura da ita awajen , Malam ne ya kalleta ya ce " ke Ummi mekike awaje a irin wannan lokacin ?" Murya na rawa tace "Baba Sani naje dubawa " "Maza Ki shige gida " Zata wuce kenan Aminullah yayi zumbur ya mik'e "tare da cewa Baba Dan Allah ka min izini nayi magana da Ummi" Ummi najin haka ta fad'a gida aguje , kamar zai bita sai da Malam ya rik'oshi , Malam ya kalleshi cike da takaici yace "Bata gaya maka ita matar aure bace?" "Hafsa ta gayamin komai Baba laifi na mata shine nazo na bata hak'uri ne" Malam dai abin ya d'aure mai kai kawai sai ya daure ya tambayeshi "wani irin laifi ?" Nan dai Aminullah ya kwashe labarin farkon had'uwar shi da Ummi har zuwa yanzun ya fad'a ma Malam , Malam hankalinshi ya tashi jin wani yana farautar mutuncin 'Yarsa nan ya fara fad'a har yana cewa ma makarantar ta daina zuwa , Sam Aminullah baiji dad'in zanchan Malam ba nan ya fara fahimtar da Malam amfanin karatu da illar rashin sa ga al-umma musamman ma d'iya mace mai bada tarbiya Dan wani b'arayin dole anabuk'atar mata ,daga nanan yayi mishi alk'awarin kula da su matuk'ar yana numfashi , Gaba d'aya jikin Malam yayi sanyi da jin kalaman Aminullah kuma yayi na'am da zanchan shi Malam ya kalli Aminullah ya ce "Yakai *AMINTACCAN BAWA* na baka amanar Zainab da Hafsa kamar yadda ka buk'ata duk abinda ya faru da su dakai zanyi kuka" Duk da cewar gaban shi ya fad'i amma sai ya dake yace "insha Allah Baba babu abinda zai faru dasu sai alkhairi" Hafsa da Ummi dake mak'ale a zaure suka kalli juna sukayi tsuru tsuru Cikin mutumci da girmamawa Malam da Aminullah sukayi sallama bayan Aminullah ya ba Malam dubu biyu amma firr Malam yak'i amsa ahaka sukayi sallama [1/12, 5:43 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com *k'ungiya ta abin alfahari na😘* *DEDICATED TO ALL HAUSA NOVELs WRITERS ina mana fatan alkhairi Allah ya bamu ladan fad'akarwa ya k'ara mana hazak'ar tunatar da masu karatu Amen*🤞 *Readers ban manta daku ba muna godiya bisa soyayyarku ga littafan mu*😍 *Masu cewa na manta da Abdallah, ku sani ba yadda za'ayi na manta da Abdallah domin shine jigon labarin ku biyobi a hankali Dan jin ya zata kasance*❤ *Page*3⃣3⃣ Kwanci tashi ba wuya yanzun su Ummi suna Hutu Wanda da zarar sun koma zasu 200level , ba laifi tad'an saki jiki da Aminullah amma duk da haka bata tab'a bari suyi fira , sai dai Hafsa ce k'awarshi. *Umar* Umar kuwa ko da mahaifiyar shi taga yana D'an samun rufin asiri tace lallai sai dai ya fara Neman aure , da taga bashi da niyya sai ta had'a shi da Malam , nan Malam ya kirashi yayi mai nasiha sannan ya amince , zai yi auren amma D'an k'ara mishi lokaci domin ya d'anyi shiri, mahaifiyar tace ta amince . Wannan kenan Ummi da Hafsa kuwa yanzun ankoma makaranta karatun su suke tuk'uru basuda matsalar komai , Aminullah shi yake kula da al'amuran su na makaranta , lokuta da ma shi yakan maida su gida duk da Ummi bata son hakan amma idan Aminullah ya nace mata da magiya dole take binshi su tafi. 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 Yau shekara biyar kenan da b'atan Abdallah , Wanda ko me kama dashi ba'ace angani ba tun ana zuba idon ganin shi har an hak'ura da wannan *RUTACCEN ALAMARI* sun fawwalawa Allah komai . 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼 To masu karatu bari na lek'a birnin London Dan ganin meke faruwa . *W*asu kyawawan matasa ne na hango d'aya akwance d'aya kuma yana tsaye gaban wardrobe yana ta cillo kaya sama Dan k'areren gadon dake d'akin sai da ya d'ibi mai isarsa sannan ya rufe wardrobe d'in ya hau kitsa kayan shi awani kyakkyau sky blue d'in trolley , yana gama wa ya juya ya kalli na kwancen da keta faman lumshe idanuwan shi yace "Friend Kodai bayau zaka bar k'asarnan bane? Wanda aka Kira da Friend ya mik'e zaune tare da jingina da bango yace " Saif wallah bana jin tafiyar nan bansan mai yasa duk lokacin da naji sunan 9ja gabana ke fad'uwa ba , amma kuma wani b'arin na zuciya ta yana son koma wa ta bansan mai yasa hakan ke faruwa ba" Ajiyar zuciya Saifullah yayi domin ya fahimci abokin nashi Dan tunda yake dashi be tab'a jin yayi hirar Nigeria ba ko wani relative nashi sai yai yana ganin kamar akwai wani *B'OYAYYEN AL-AMARI*da abokin nashi yake b'oye mai . Cikin sanyi ya taka zuwa kusa da abokin nashi ya dafa shi tare da fad'in " ka kwantar da hankalin ka abokana mai yuwa wani alkhairi ne shiyasa zuciyarka ta aminta da komawar" Cikin yanayin damu wa Abdallah ya d'aga k'ana nan idanuwan shi ya kalli abokin nashi kallon ban fahimta ba amma kuma sai bai ce komai ba . Cikin tausasawa da lallashi Saifullah ya kwantar ma da Abdallah hankali yaryaji yana son tafiyar , nan ya mik'e suka cigaba da shirin su Kasan cewar yau zasu koma kuma flight di k'are hudu zasu bi . Cikin dare suka sauka a Abuja Dr Ahmad da kanshi yaje taryar D'an nashi cikin sauri ya k'arasa ya rungume Abdallah yana fad'in "welcome to Nigeria son " Da murmushi ya amsa masa sannan suka rungume juna . Saif kuwa dama agida yace karsu zo tarbar shi su bari sai gobe sabo rashin kyawun hanyar . Cike da fara'a Dr ya jawo Saifullah yana mishi sannu da zuwa . Daga nan ya jasu zuwa gurin motar shi suka Shiga suka wuce gidan shi dake maitama. Kusan raba dare suka yi suna hira Wanda Kasan firar Dr ne da Saifullah suke yi Abdallah ko jefi-jefi yake sa musu baki da ga baya dai ya gaji ya mik'e ya Shiga toilet ya d'auro alwala ya fara jero nafilfili , idan da sabo Saifullah ya saba da ganin hakan wannan d'abi'ar Abdallah Wanda shima yake k'ok'arin koyi da kyawawan halaye irin nashi . Bayan Dr yayi musu sallama ya koma d'akin shi tunanin Abdallah ne suka addabe shi Wanda ba tun yau ba yake jin hakan , yanzun kam dole ya nemi mafita don baya son hak'k'in 'yan uwan shi ya kama shi wata k'ila ma yana da mata da yara idan ko hakane ya zama azzalumi kenan , da irin wad'an nan tunanin yayi barci Wanda sun zame mai jiki duk in yazo kwanciya sai ya yisu , . *DA SAFE* Bayan sunyi wanka sun shirya sukayi break 9:30 suka d'auki hanya bayan Saifullah ya kira mahaifin shi ya sanar masa da Dad d'in abokinshi zai dawo dashi . Saifullah ne ya k'arb'i tukun suna tafe suna hira cikin nishad'i tun lokacin da suka doshi Zaria Abdallah yake ganin hotunan wasu abubu a idon shi sunan mai flashing tamkar video black white rutse idonuwan shi , duk wani moving d'in shi Dr yana gani sai bai kula shi ba Dan yana ganin wannan wani sign ne da Abdallah zai fara sanin koshi waye . Ko da suka Shigo Zaria Abdallah duk ya gama zaucewa musamman ma da suka biyo ta kasuwar tudun Wanda Kasan cewar Saifullah D'an cikin tudun wada ne abun da k'ara d'aga mai hankali bai wuce da yaga shagon ogan Umar ba nan kam gaba d'aya durkushewa yayi a waje nan take zufar da yake yi ta k'ara yawaita , shi kanshi Dr abin ya bashi tsoro matuk'a , janyo shi yayi jikin shi yana shafa bayan shi. Motsin da Saifullah yaji ana yi ne yasa shi kallon su tajikin mirror , yaga yadda abdallah jikinshi ke wani irin b'ari afirgice ya ce "Dr lafiya" Shi kanshi Dr ya firgita kawai sai cewa yayi su wuce asibiti, mik'e titi yayi street *SHIKA* yake son kaisu domin nan ne yake ganin za'a ba abokin shi kyakyawan kulawa. Kasan cewar basu had'u da cinkoson ababen hawa ba yasa acikin minti ashirin da biyar suka isa asibitin emergency aka kab'e shi aka wuce dashi wani private room nan likitoci suka duk'ufa akanshi . Iya k'ololuwar tashin hankali Saifullah ya Shiga mostly yana ganin Abdallah a irin wannan halin amma nayau yafi gigitashi , ringing d'in wayarshi ce ta katse mai tunani da ya keyi ahankali ya zaro wayar cikin pocket d'in shi sunan da yagani ajikin screen d'in wayar ya fad'i a hankali "DAD?" A nutse ya d'aga wayar gamida sallama bayan Anas sallamar maifin ke tambayar shi lafiya shiru har yanzun basu iso ba? Cikin natsuwa Saifullah yake sanar ma dad d'in shi abunda ke faruwa . Cikin mamaki dad d'in yace gashinan zuwa, [1/13, 8:00 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com *Wannan shafin rankatakaf naku ne masoya Bawan Allah na mallaka muku shi aduk inda kuke fad'in k'asar nan Allah yabar zumunci da k'aunar juna Amin ❤🤞* *Dedicated to Faty Axland🤪* 3⃣4⃣ Banda *SAFA DA MARWA* babu abunda Dr da Saifullah suke yi , sun d'ibi kusan minti arba'in a haka sai ga Dadyn Saifullah ya Iso cikin girmamawa suka gaisa da Dr sannan yayi masa ya mai jiki sai wurin ya d'auki shiru , chan Dr ya juyo ya kalle Saifullah yace "Saif kaje gida ka huta mana " Cikin sanyi yace " no Dr bazan iya zuwa ko ina ba har sai nasan halin da abokina yake" Dadyn Saifullah yace "gaskiya ne bari mu tsaya muga jikin nashi " Ana cikin haka k'ofar d'akin da aka kwantar da Abdallah ta bud'e wani Dr ne ya fito daga cikin ta cikin ta ya k'araso kusa dasu yace " ina Baban Abdallah?" Dr yace" gashinan " "Ina son ganin ka" Cikin sanyin jiki Dr Ahmad ya bi bayan shi suka D'an tab'a tafiya kad'an sannan suka k'arasa office d'in shi bayan sun Shiga sun zauna Dr ya fara yima Dr Ahmad tambayoyi akan rashin lafiyar Abdallah , Ba tare da b'ata lokaci ba ya sanar masa da duk abunda ya faru har zuwa yanzun , Ajiyar zuciya Dr yayi yace "this is serious, but Dr meyasa baka yi k'ok'arin dawo masa da tunanin sa ba kuma ka k'asa sashi cikin wata rayuwar rud'ani ? Wannan serious case ne amma da tun farko ne da yanzun memory d'inshi ya dad'e da dawo wa " Shi dai Dr Ahmad shiru yayi Dan duk abinda zai fad'a ya gama fad'i , Dr ya sake cewa "kuma abinciken da mukayi muna da tabbacin yana da connection da garin nan , Dan haka indai ka shirya nema masa lafiya to lallai sai dai ka barshi a nan zuwa wani D'an lokaci" Bayan guntun nazarin da Dr Ahmad yayi yace" shikenan ba damuwa indai zai samu lafiya komai me sauk'i ne" Dr yace "akwai yuwuwan hakan insha Allah" "Zan iya zuwa na gashi ?" "No har yanzun likitoci basu gama aikin suba ku k'ara musu lokaci" Nan dai suka k'ara tattaunawa akan matsalar sannan suka rabu , alokacin da Dr Ahmad ya koma wajen Saifullah shi kad'ai ya tarar a wajen nan yake tambayar shi "Saifullah ina Baban naka?" Saif cikin yanayin damu wa yace " yayi bak'i ne agida " "OK muje muyi sallah Gashi har la'asar tayi ba muyi azahar ba " Sai da suka d'anyi tafiya sannan suka fara tambayar inda masallaci yake akayi musu kwatance , Bayan sun fito daga masallaci ne ya Ciro wayarshi ya fara kiran wata number da aka rubuta "Bro" ajikin ta , acikin ringing na biyu aka d'aga kiran , Murmushi yayi sannan ya amsa sallamar da aka mai , bayan shiru da yayi na kimanin minti d'aya sai yace " duk naji k'orafin ka kafin nabaka amsa , kana school ne ?" Shiru yayi domin sauraran me za'a ce mishi sannan yace "to ina ina cikin hospital naku ka sama mana abinci mare nauyi na mutum uku " Nan d'in ma shiru yayi sannan daga baya yace "no don't worry ba ni bane friend d'ina na , kayi sauri fa na fara jin yunwa " kitt ya kashe wayar Dan yasan halin k'anin nashi ba k'i ma yatafi siyan abincin da wayar akunnen shi suna hira ba Bayan sun aje wayar ne Dr Ahmad yace "AI da ka bari ma akwai restaurant anan waje da sai muci achan kawai " "Wallah Sam bana son Barin cikin hospital d'in nan sai naga kamar wani Abu zai faru da Abdallah" Dafa kafad'arshi Dr yayi yace "babu abunda zai faru dashi a hirar ma da mukayi da Dr yace yaji sauk'i yanzun ma bacci yake yi " Ajiyar zuciya Saifullah yayi sannan yace " Alhamdulillah" Suna tafe suna hira jefi jefi har suka k'arasa bakin d'akin da aka kwantar da Abdallah suka zauna a d'aya daga cikin kujerun dake aje wurin. Bayan kimanin minti ashirin wayar Saifullah ta hau ringing ya d'aga tare da karawa akunne , k'anin nasa ya tambaye shi a inda suke , shi kuma ya mai kwatance , ba'afi minti Biyar ba sai gashi ya bayyana awajen . (Ni mai d'aukan rahoto Wanda Nagani wajen saida alk'alami na ya fad'i k'asa saboda mamaki Saifullah ne ya mik'a min tare da fad'in " yes he's my brother " 🤪 AI ba shiri na cigaba da d'aukan rahoto Dan kar ayi show bani) Aminullah ya k'arasa cikin sauri gami da ajiye ledar abincin kan d'aya daga cikin kujerun ya rungume D'an uwan sa cikin shauk'in bege yace " I miss you sweet bro " "I miss you too little bro" Sannan suka saki juna suna murmusawa . Ahankali ya kai Cuban shi ga Dr cikin girmamawa ya gisheshi Dr ya amsa tare da murmushi afuskarshi "Bros ga abincin nan fa kuci " Cin abincin suke amma kowa da abinda yake sak'awa a ranshi. Wasu doctor's ne guda biyu suka fito daga d'akin , d'aya daga cikin su ya ce musu ya farka zasu iya zuwa su Ganshi , cikin sauri suka Shiga d'akin shiko Aminullah mamaki ne fal acikin shi yanda yaga har riga-rigen Shiga suke yi AI shima sai ya bisu abaya. Akwance suka same shi hannun shi d'aya an samai drip tashi d'aya har yad'an fad'a kad'an , Cikin kulawa suka fara tambayar shi yajin nashi , kai kawai ya d'aga alamar da sauk'i , sannan ya kalli Saifullah yace. "Saif baka tafi gida ba?" Saif ya D'an harare shi yace " why should I go home when you are here" Murmushi yayi ya kawai sannan ya juya kalli Aminullah kallon Neman k'arin bayani akan shi , Said ya janyo Aminullah kusa dashi yace " Aminullah da nake baka labarin shi, " Sannan ya juya ya kalli Aminullah yace " Abdallah nasan ka gane shi " Aminullah ya rab'a ta gefen Saifullah ya k'arasa kusa da Abdallah sannan yayi mishi ya jiki , suna d'an fira jefi-jefi dai-dai nan wayar Aminullah ta hau ringing sunan da yagani jikin wayar yad'an murmusa , Saifullah na kallon shi ya sakar masa dundu tare da fad'in "D'an iska dariyar me kake " "Ba komai sister na ce ta kira " Zuwa lokacin kiran har ya katse D'an haka shi sai ya k'ara kira , Alokacin da aka amsa kiran yaji ance " haba Aminullah ka ce mujiraka kuma kayi shiru gashi har Aunty Ummi ta gaji ta tafi " Dafe kanshi yayi tare da fad'in "ya subhannallah yan ke kina ina?" "Ina inda ka barni " "OK gani nan zuwa". Ya juya ya kalli Saifullah yace "bros bari naje na dowa , kuna buk'atar wani Abu ne " "Ah ah ka gaida k'anwar tawa" Yamik'e tare da Sosa k'eya yayi musu sallAma har ya kai bakin k'ofa Dr yace " Aminullah kawuce da Saifullah gida ya D'an huta " Saif zaiyi magana Dr ya dakatar dashi ta hanyar nuna masa yaje kawai ba wata damu wa, Sai da suka Shiga mota sannan Aminullah ya juya ya kalli D'an uwansa yace "bafa gida direct zan wuce ba kuma kaga yamma tayi " D'an tsaki yaja yace "muje" Cikin makaranta suka koma , Hafsat na hango motar Aminullah ta taso ganin wani kyakkyawan saurayi cikin motar sai da yasa numfashin ta d'aukewa na wucin gadi , da k'yar ta iya Jan k'afafun ta zuwa kusa da motar , baya ta bud'e ta Shiga bayan ta rude motar sai nan ta gaida Saifullah a dak'ile ya amsa mata ya juyar da kanshi kan titi gami da d'aure fuska Tunani yake yi wannan wace yarinya ce take tare da k'aninshi? Meye dangan takar su , yana cikin maganar ya tsikayi muryar abokin shi yana cewa "Hafsa nakira wayar Aunty Ummi bata d'aga ba ko tayi fushi ne?" Sai da tayi dariya sannan tace " idan munje kaji" "Is that what you said?" Dariya kawai tayi domin tasan yanzun zai birkice Dan baya son ganin fushin Ummi Sam *sorry for this one [1/15, 1:55 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com *Readers bansan da me zan saka muku ba har kullum bakwa gajiyawa wajen sambad'o addu'oin fatan alkhairi agareni wallah har cikin raini ina ji daku ina k'aunarku Allah ya k'ara had'a tsakaninmu ya karemu daga sharrin dukkan abin k'i*🙏 *This page dedicated to you dearies* *k'awalli* *Maman hanan* *Nafi khan* *Fareeda* *Ameenah* *Mrs Abdulwahab* *Rahma Isma'il* *sa'adiya illa* *Calz me nuccy* *Maman Mimi* *Umulkhairi Jibril* *Ummulkhairi GJ* *kai wallahi kuna da yawa you're uncountable amma kusani ni d'in taku ce har gaban Abadan*❤😘😍 3⃣5⃣ Shikam Saifullah ta kaici Duk ya cika shi , tun kafin su k'arasa aka fara kiran sallar magrib , dan haka suna k'arasawa Aminullah ya gyara parking dai dai k'ofar gidan su Hafsa , ta na fitowa tayi musu godiya had'e da sallama , Aminullah ya kalli yayan shi yace "bros ga masallaci chan muje muyi sallah " D'an tsaki yaja sannan ya fito daga motar tare da fad'in " dama akan wannan abar ka b'ata min lokaci?" Murmushi yayi yace "uhum bros ba zaka gane bane amana tace dole na kula da su " Wata harara ya sakar mai sannan suka wuce masallaci . Ummi kuwa tana shigowa unguwar su madadin ta wuce gidan su Hafsa sai ta wuce gidan su sai dai ta aika k'aninta da jakar makarantar ta , sai da ta yi sallar magrib sannan tayi sallama da gida tafito. Dai dai lokacin su Aminullah suka dawo daga masallaci , yana ganinta yaja ya tsaya shiko sai tuni ya kame acikin motar Takaici ne duk ya isheta bata so suka had'u ba tasan yanzun zai dameta da surutun shi , tamau ta had'e ranta sannan ta k'araso wurin , Hannun shi biyu ya had'a alamun banhak'uri sannan ya marai-raice yace " ayya Aunty Ummi Ki gafarce ni " Dariya ne yakusa kufce mata dan yadda yayi maganar dole ne ma yabaka dariya, "Is OK sai da safe " tana k'ok'arin shigewa gida ya tsayar da ita tare da fad'in "Ga bros d'ina ku gaisa " D'an lek'awa tayi ta window motar k'yarrr suka had'a ido dashi yana waya , d'agowa tayi tace ma Aminullah "ka gaishe shi nina tafi sai gobe " Tana kaiwa nan ta shige gida , shi kuma ya bi bayanta da kallo yana murmushi Yana Shiga mota Saifullah ya tallabe mai kai yana fad'in " D'an iska arasa gane wace ce budurwar taka aciki" Tallabe k'eyarshi yayi yana cewa "wallah bro amana nane" Ahaka dai yaja motar suka tafi suna hirar yaushe gamo ****************** Wasa-wasa dai Abdallah yau kwanan shi biyar a asibiti yana samun kulawa sosai wajen su Dr Ahmad da Saifullah , Aminullah ma ba baya ba idan ya samu chance yana k'araso wa su sha fira , Abdallah har ya gaji da nacin asallameshi dan shi babu inda yake mai ciwo sai uban gwaje gwaje da ake mai da tare tambayoyi wad'anda suke k'ok'arin birkita mai tunani, Saifullah kuwa har yanzun baisan hak'ik'anin abinda yake damun abokin shi ba domin Dr Ahmad ya sakaye zancan daga shi sai likitoci suke aikin su, Tun lokacin da Saifullah yaga Ummi Sam hankalin shi ya kasa kwanciya fuskarta sai gizo take mishi duk iya k'ok'arin shi ya daure amma ya kasa , sai kawai ya yanke shawarar ya nemi k'anin shi suyi magana , bayan ya dawo asibiti da daddare ya nufi part d'inshi wanka yayi ya ci abinci sannan ya nufi part d'in Aminullah a kwance ya sameshi yana game d'in criminal case a tab d'inshi da alama yana jin dad'in game d'in , motsin da yaji ne abayan shi ya sashi juyawa Saifullah yagani tsaye bakin k'ofa ya jinga ya zuba mishi k'ananun idanuwan shi da suke alumshe kamar mai jin baccin , dama idan ka Ganshi cikin wannan yanayin to akwai abunda ke damun shi . Cike da kulawa Aminullah ya aje tab d'inshi sannan yace "what's up bro?" D'aga kafad'un shi yayi alamar babu sannan ya k'arasa shigowa d'akin ya zauna kan kujera ya sake zubamai ido Tasowa yayi yazo ya zauna kusa da shi yace " Bros wai meke damunka dan Allah ka sanar da ni idan zan iya taimaka maka idan ba zan iya ba kuma ko shawara na baka" Ba tare da b'ata lokaci ba Saifullah ya sanar ma Aminullah da k'udurin shi akan Ummi daga k'arshe kuma ya nemi shawarar shi Duk da Cewar Aminullah yaji wani iri akan maganar amma sai ya dake domin yana son ganin farincikin D'an uwansa , shima bai b'oye mishi komai ba game da wace ce Ummi , Tausayinta ne k'arara a fuskar Saifullah ya d'ago idanuwan sa da suka k'ara k'ank'ancewa yace "kana nufin har yanzun ba'a ga mijin nata ba ?" "Had yanzun ba'aga Wanda yaga me kama dashi bama" Jinjina kai yayi yace "gobe zaka rakani wajen mahaifin ta" D'an zaro ido Aminullah yayi yace" me zakayi?". With compidence yace "auren ta zan nema" "Bro haramun ne fa Neman aure akan aure " "Sam wannan auren nata bashida amfani kawai yarinya k'arama ana k'ok'arin d'aura mata wahala , yanzun haka ma wayasan inda yake ? Ko yana da rai ko bashida da rai oho?" "Tab mai da wuk'ar , but you have to control your anger " Bai cemai komai ba ya fita a d'akin , daren da k'ar ya samu yayi barci tunanin Ummi kawai yake yi dan yanzun wani tsananin sonta ke k'ara shigar shi duk ya k'agara gari ya waye Kasan cewar yau Saturday ne ba makaranta dan haka da wuri suka shirya suka je gidan Malam kasan cewar safiya ce sun same shi yana ta koyar da almajiran shi wuri suka samu gefe suka zauna saida Malam ya sallami almajiran sannan ya kalli Aminullah yace " Amintacce bawa Kaine da sanyin safiyar nan ?" Murmushi yayi yace "nine Malam" Cikin girmama juna suka gaisai sannan Aminullah ya gabatar da D'an uwanshi Saifullah awajen Malam Shikuwa Saifullah ya gabatar da k'udurinshi na son auran Ummi a wajen Malam Shiru Malam yayi kamar ba zaiyi magana ba Dan maganar tazo mishi a bazata Ya fara magana kamar haka , " kamar yadda D'an uwanka yayi maka bayani Ummi dai da aure a akanta sannan kuma bamu da ikon daura wani aure har sai an warware wanchan dan haka kayi hakuri duk yadda muka shawarta zan nemeka" Godiya sukayi suka tafi duk da cewar sa Saifullah baiji dad'i ba Kasan cewar bai samu k'wak'waran tabbaci daga Malam ba haka ya koma gida cikin zullumi Ranar wata talata ne wurin k'arfe biyar Ummi ta gama lectures d'in ta Hafsa kam bata samu zuwa va sakamakon wani irin ciwon kai da ta tashi dashi , hakan yasa yau ita kad'ai Aminullah zai mayar gida , bayan sun Shiga motar ya Tayar kenen wayarshi ta hau ringing Saifullah ne ya kirashi , bayan ya d'aga wayar yana sauraron me zaice bayan ya gama kawai sai ya ce "OK "ya kashe wayar Juyawa yayi yace ma Ummi "Aunty Ummi kimin hak'uri kad'an zan amshi sak'o wajen bro acikin hospital " Ta D'an b'ata rai tace "to" Suna isa asibintin yayi parking inda ake parker motoci sannan yace "D'an Allah muje Ki gaida yaya na yana da mutumcin shi be cika d'aure fuska irin na Saifullah ba" "Uhum muje" Haka suka taka sunan jera wa kowa ya gansu sai ya sake kallon saboda tsabar marching da sukayi Sai da sukayi tafiya me d'an nisa sannan suka k'arasa d'akin Ummi kuwa nan take taji zuciyar ta na bugawa kamar zatayi tsalle ta fad'o k'asa Tare da sallama ya bud'e k'ofar Kasan cewar gadon yana kallon k'ofar ya saya direct kana Shiga zaka hangi na kwance akan gadon yana baccin K'iiii taja wani dogon birki sakamakon arba da tayi da wata fuska da ta dad'e tana marmarin gani duk da dai sauyin da ta gani hakan bai hanata gaskata ko wa ta gani ba Aminullah ne ya juyo da niyar yi mata magana ita kuma alokacin ta juya ta kwasa aguje "Ummi! Ummi!! Ummi!!!?" Haka yayi ta kwad'a mata kira amma bata waiwayo ba haka yasa shima ya kwasa aguje yabi bayan ta ❤❤ [1/17, 3:57 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 3⃣6⃣ Tun da ta runtuma bata tsaya ba mutane sai kallonta suke , duk iya k'ok'arin Aminullah ya tsaida Ummi ya kasa , aiko yana ganin sun kai wurin wani kwararo da ba mutane ya figo hijab d'inta ta dawo baya , kamar zata bangaje shi , Ganin yadda take kuka harda majina gashi sai wani tittirjewa take kamar sabuwar 'yar bori ya sashi daka mata tsawa " ke Zainab!!" K'ara firgita tayi zata sake gudu sai ya sassauta muryarshi yafara magana cikin sanyi " Ummi Ki natsu mene ne ?, me ya faru ?, wani Abu aka miki,?" Duk ya gama jero tambayoyin shi amma kawai da ido tabishi Azuciyar ta ko fad'i take ina ma tana da halin amsa masa wad'an nan tambayoyi data amsa su Shi kuma ganin shirun da tayi ga hawaye yana ta sintiri a fuskarta sai ya fara tunanin anya Ummi kam kanta k'alau ? Bai sake cewa komai ba yaja hannun ta har gurin motar shi sannan yace mata ta Shiga , tana Shiga ya rufe sannan ya zagaya shima ya Shiga , sannan ya tada motar har a lokacin kuka take shak'a , Haka yayi ta tuk'i amma Sam zuciyarshi bata mishi dad'i saboda yadda yake jin kukan Ummi a zuciyarshi kamar ana d'iga mishi tafasasshen ruwa. Suna isa k'ofar gidan su ta hangame murfin motar ta fito ko tsayawa ta rufe batayi ba ta fad'a gidan su Hafsa , shi dai Aminullah kanshi duk ya d'aure ya rasa gane meke damun Ummi ayyah batada junnu, nan ya coge a k'ofar gidan. Ummi kuwa tun da tasa kanta a zauren gidan ta fara k'wala ma Mama kira Mama na d'aki abin da bata tab'a ji ba kenan afirgice ta fito tana "Ummi mene ne ?" Amma ina zubewa tayi ta dasa sabon kuka , Mama duk ta kid'ime , Hafsa dake d'aki tana fama da kanta tafito ganin yadda Ummi ke kuka bilhak'i da gaskiya sai jikin ta ya k'ara sanyi domin duk runanin ta wani mummunan abun ne ya faru . Duk suka rud'e da tambayoyi amma Sam Ummi tak'i magana sai kuka , cikin k'unci Hafsa ta koma d'aki ta d'auko hijab d'in ta ta fice , yanayin tashin hankalin da take ciki shi yasa bata lura da Aminullah dake zaune kan dakali ya zabga uban tagumi ba , shima kuma bai kula ta ba . Direct gidan su Ummi ta fad'a ba'afi minti biyar ba sai gashi sun fito tare da Malam. Malam ya ga Aminullah zaune turus ya zabga tagumi , shi kanshi Malam d'in sai da gaban Shi ya fad'i , cikin sanyi ya ce " Amintacce meke faruwa ne ?" Aminullah ya kalli Malam cikin damuwa sannan ya labarta mishi sukkan abubuwan da suka faru d'azun , Bai yi wata wata ba yace ma Aminullah zo muje , suna suga gidan Malam ya hau fad'a yana tambayar ta me ya faru ? Ko tayi hauka ne duk ta tayar wa da mutane hankali, Murya na rawa kamar ta mai koyon magana tace "Baba na...na..Ganshi" "Wa kika gani?" Zata k'ara wani kukan Malam ya yi jan ido yace takuma sai ya lallasa ta Da k'yar tace " *ABDALLAH* " Maman kam dab'as ta zauna a k'asa tayi zaman 'yan bori , tana tunanin to kodai mafarkin ta na jiya ya zama gaskiya ne? Hafsa ma sai da ta Zabura, Aminullah gaba d'aya ya firgice domin bai gane inda zancen ya dosa ba . Malam ma kanshi duk ya d'aure ya kalli Ummi da keta wik'i-wik'i da ido dan yanzun kukan ya tsaya ya ce "Ummi kinsan me kike fad'a kuwa?". With confidence ta d'aga kanta tare da fad'in "ku tambayi Aminullah AI shi ya kaini inda yake " Nan fa kallo ya koma kan Amintacce wanda duk sun k'ara birkita shi , Malam ya kalli Aminullah yace " Amintacce mene ne hak'ik'anin wannan zancen?" Cikin muryar rud'u Aminullah yace "kamar yadda na gaya maka a waje , abokin yaya na ne bai da lafiya shine yaya na yakirani na je na karb'i kaya na wuce mai dasu gida , shine na rok'i Ummi ta raka ni lafiya lau muka shigo asibitin amma tunda muka Shiga d'akin duk ta birkice kuma ni bata cemin komai ba shine na kwaso ta na dawo da ita" Malam ya kalli Ummi cikin takaici zai magana tayi sauri ta ce "wallahi tallahi Baba naga yayan Hafsa indan kuma baka yarda ba kuje dashi ka gani idan bashi ba wallahi na yarda daga yau na zama bazawara" ta k'arike maganar da wani kuka me tsuma zuciyar me saurare. Kowa awurin sai da ta bashi tausayi , Mama da k'ar ta tattaro natsuwar ta tace " Malam aje a duba ko Allah yasa za'a dace" "To"kawai yace ya fice Aminullah ya bi bayan shi , suna fita ya juyo ya kalli Aminullah yace " ka tsaya muyi sallar magrib anan sai muje ka kaini" jiki a sanyaye yace "to" Shikam Bawan Allah duk wainar da ake toyawa bai sani ba sharar baccin shi kawai yake yi sabo allurar da aka mai Saifullah kuwa tun da su Aminullah suka fita yabi bayan su amma cikin rashin sa'a ya sa bai gansu ba , tun lokacin ya ke kiran wayar Aminullah amma bai d'aga ba hankalishi duk ya tashi gashi shi kad'ai ne awajen Abdallah ballantana yabi bayan su . Sai 7:30 sannan Dr Ahmad ya dawo ganin Saifullah cikin rud'ani yasa shi tambayar meke damunshi amma ya rasa amsar da zai bashi kawai sai yace mai "ba komai " Bayan minti goma Abdallah ya farka gami da mik'a da salati , duk suka yi mishi sannu jiki a mace yakalli agogon da ke mak'ale a bangon d'akin zumbur ya mik'e ya fad'a toilet domin d'auro alwala , shigarsa bayin kenan Aminullah ya bud'e k'ofar d'akin tare da sallama suka shigo da Malam Cike da girma-mawa suka gaggaisa Malam yayi musu ya mai jiki , Saifullah ya kalli Aminullah domin Neman k'arin bayani suna had'a ido yayi sauri yuyar da kanshi , Murfin k'ofar bayin aka bud'in tun da Malam yayi arba da wannan fuskar gaban shi yayi mummunan fad'uwa ya tabbatar da ba'a zaune yake ba da sai ya fad'i k'asa warwars lallai Ummi tayi namijin k'ok'ari 😂😂😂😂😂😂😂😂 Da k'ar Malam ya had'o miyon bakin shi yace " *BAWAN ALLAH?*" Sosai sunan ya daki k'ok'on zuciyar Abdallah amma Sam Brain d'in shi ta kasa functioning , D'aga idanun shi yayi ya d'orasu kan Malam take tsigar jikin shi ya tashi , brain d'in d'in shi ta fara mishi flash back nan take ya runtse ido , Dr Ahmad na ganin haka ya danna k'ararrawar kiran likita zame wa yayi zai fad'i sukayi sauri suka tare shi. *sorry for this one wayata tana hucking*🤪👈 . [1/21, 12:18 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com *This page dedicated to you Bawan Allah fans , nagode da addu'oin fatan alkhairi da kuke agareni lallai Ku k'awayen arzik'i ne nagode Allah ya barmu tare ya sadamu aljannatul firdau*❤ *k'awa*🤪 3⃣7⃣ Gaba d'aya Abdallah ya birkice wasu irin hotuna yake gani black and white wa D'an da bai San inda suka samo asali ba . Ko da likita yazo tambayoyi ya runk'a mai amma yace bai San komai ba , haka suka sake masa allurar bacci ya koma . Har zuwa wannan lokacin Malam yana asibin mamaki duk ya cika shi . . Dr Ahmad ya maida duban shi ga Malam yace " Malam dama ka sanshi ne?" Murmushin takaici Malam yayi yace "Abdallah haihuwar shi ce kawai banyi ba , kuma har yau bana bamban tashi da 'ya'yan da na Haifa da ciki na" Shiru d'akin yayi Malam ne kawai da Dr Ahmad suka san mai suke cewa amma Saifullah da Aminullah gaba d'aya Kansu s juye yake . Malam ya kalli Aminullah tare da nuna Abdallah dake kwance yace "wannan shine mijin Ummi da ya b'ata shekara biyar da suka wuce " Wayyo Allah zo kuga tashin Hankali a idon Saifullah gaba d'aya yaji maganar ne tamkar saukar aradu , tabbas da za'a gwada jininshi alokacin da ansha mamaki , domin bai taba zato ba balle tsammani, Cikin murya mai cike da firgici yace " Malam mai kake nufi ne wai ?" Malam bai ce komai ba domin baisan kuma ya zaiyi ya fahimtar dashi ba . Dr Ahmad yace "Saifullah ka kwantar da hankalinkA gobe insha Allah za kaji komai yanzun dare yayi " Sannan ya juya ya ce "Aminullah ka maida Malam gida gobe zamu je gidan dukan mu in Allah ya kaimu" Nan suka mik'e Malam yaje wajen kan Abdallah ya tofa masa addu'oi sananan sukayi sallama amota kuwa Aminullah ne ya damu Malam da tambayoyi domin shi duk ya k'agu yaji gaskiyar al'amari, amma Malam yak'i Sam suyi magana . A can gida kuwa su Ummi sun kasa sun tsare , har da Umar ma da ya shigo gidan bayan fitar su Aminullah da Malam , tun suna tsaye har suka gaji suka zauna amma babu su babu labarin su, har 10:30am . Mama ta kalli Umar tace "Umar kaje gida mana kaga dare yayi " " Mama ko naje gida bazan iya yin bacci ba" Mama zatayi magana kenan sai sukaji k'arar tsayuwar mota , Umar yace "Mama Bari na duba nagani" Ummi kuwa zuciyarta sai k'ara bugu takeyi. Umar na fita Aminullah har ya ta tada motar shi yayi gaba Malam kuma ya d'auki hanyar k'ofar gidan shi, cikin sassarfa Umar ya k'arasa gurin Malam yana fad'in "sannu Malam" "Yauwa Umar " "Malam Abdallah ne kuka gani ko?" Murmushi Malam yayi sannan ya dafa kafad'ar Umar yace " ka kwantar da hankalinka gobe insha Allah zasu zo sai muji koma wane ne" Ajiyar zuciya ya sauke sannan sukayi sallama , shikuma Umar ya koma gidan su Hafsa dan sanar dasu yadda sukayi da Malam, Ranar dai kowa kwanan zullumi yayi musamman ma Ummi da take ganin ga k'oshi ga kwanan yunwa. *Da safe* Misalin k'arfe Tara na safe Abdallah ya fito wanka ya shirya cikin shigarshi ta k'ananan kaya maroon din T-shirt ce ajikinshi sa navy blue d'in jeans kalar yayi matuk'ar amsar jikinshi Kasan cewar shi faran saurayi kan kujerar robar da aka tanada dan masu dubiya ya zauna tare d'aukar wayarshi ya fara dannawa . Aminullah ne ya bud'e k'ofa ya Shiga tare da sallama , batare da ya juyo ba ya amsa sallamar , "Bros Dr yace mu same shi awaje " cewar Aminullah yana kallon Abdallah da ya kyab'e fuska "Ina zamu je ne?" Aminullah zai yi magana kenan wayar Abdallah ta fara ringing , cikin sanyi ya d'aga wayar gami da sallama , bayan D'an shiru kuma sai ya mik'e ya kashe wayar ba tare da yace komai ba , Aminullah ne ya d'auki wata 'yar k'aramar traveling bag dake gefen gadon suka fita A parking space na cikin asibitin suka tarar da Dr Ahmad da Saifullah suna jiran su Saifullah ya Shiga mazaunin driver , Abdallah ya Shiga b'arayin me zaman banza , yayin da Dr da Aminullah suka Shiga baya . Tunda suka d'auki hanya Abdallah ya tattare hankalin shi da natsuwar shi yaba titi amana, runtse idanun shi yake yi yayinda wasu hotuna keta masa yawo a kwanyar shi wasu kalamai suna ta mashi yawo a dodon kunan shi , hannu ya sa ya toshe kunan shi idon shi kuwa runtse shi yayi kamar k'aramin yaro , duk suna lura dashi amma Sam Dr ya hana su tab'a shi sai dai suka bishi da fuskar tausayi , har suka iso k'ofar gidan bai ma San sunzo ba , sai da Saifullah yayi mishi magana sannan d'ago jajayen idanuwan shi ya kalle shi "Mun iso fa" cewar sai ya bud'e murfin motar zai fita , shima murfin ya bud'e ya fita k'ofar gidan su ya ci karo dashi take wasu abubuwa daban daban suka runk'a yi mishi yawa akai gaba d'aya ya daina ganin zahiri sai bad'ini Malam dake ta karatu da almajirai ba shiri ya sallame su suka tafi sannan ya k'araso fuska d'auke da farinciki Umar ya fito daga cikin gidan su Hafsa sakamakon tsayiwar motar da yaji yana fitowa yayi arba da Abdallah jingine jikin mota aiko da gudu yaje ya k'wak'wu-meshi , shi dai Abdallah ji kawai yayi an rungume shi , shikam Umar ji yake kamar in yasaki Abdallah bazai sake ganinshi ba , rungumar da Umar ya ma Abdallah sai da yajiyo bugun zuciyar shi domin yi take zamar zata fasa k'irjin ta fito Cikin dauriya Abdallah ya b'amb'are Umar daga jikinshi , kallon juna suke ido cikin ido , da k'yar Abdallah ya k'ak'alo wani murmushi ya jefa asaman fuskarshi , Umar ya kalli Abdallah cikin kewa yace "nayi kewarka aboki na , kai kam ko nema na baka yi " Shikam Abdallah bubbuga kafad'ar Umar kawai yayi amma Sam bai ma San koshi waye be . Malam ne ya katsesu da cewa " mu Shiga daga ciki ". Hafsa da tafito ta basu izinin Shiga sai kallon Abdallah take kamar taga sabon hallita , suna had'a ido dashi ya balla mata harara azuciyar ta tace"bari na kama kaina tun kafin ya jizga ni dan naga ya k'aro wulak'anci" Juyawa tayi sukuma suna binta abaya tana tafe tana tuntub'e , shiko Aminullah sai dariya yake kwasa aranshi yace ya samu na tsokana [1/22, 5:11 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com 38 Hafsa na k'arasa Shiga gida ta runtuma aguje sai d'akin Ummi ko sallama bata tsaya yi ba ta yaye labule ta afka , Ummi dake ta cikiniyar sa kaya Wanda da alama yanzun ta fito wanka ta kalli Hafsa tace "ke dai banga ranar da zaki girma ba ke kullum aguje kamar y'ar gudun hijira " Hafsa ta had'a girar sama da ta k'asa tafara magana cikin hasala "ke fa gaba d'aya ba'a miki gwaninta daga zuwa yi miki albishir sai Ki hau gwasale mutum , to ni kinga tafiya ta nama fasa fad'a " ashagwab'e ta k'arasa maganar Cikin marai-raice murya Ummi tace "ayya *k'walli* ta yi hak'uri zo Ki fad'a min " Hafsa ta had'e rai tace " a nawa ?," Ummi tayi dariyar mugunta tace "a arba'in" Du Kansu suka kwashe da dariya . *Bawan Allah* kuwa tunda suka shigo gidan ya k'ara birkicewa musamman ma da yayi arba da Mama tana shimfid'a tabarma k'uri ya k'ura mata ido tamkar mai son ya fahimci wani Abu amma Sam ya kasa Saifullah ne ya jashi ya zaunar dashi, har wannan lokacin idonshi yana kan Mama , ko da Mama ta juyo suka had'a ido sai da taji gaban ta ya fad'i , azuciyarta tace "tabbas wannan bawan Allah ne" Bayan 'yan gaishe-gaishe Mama ta mik'e taje ta kira su Ummi domin ayi komai a gaban su , Ummi ce agaba Hafsa tana binta a baya ahankali take takun ta kamar me tsoron kar ta taka wani abun , dai dai lokacin Abdallah ya juyar da fuskarsa b'angaren , tundaga k'afafuwan ta yake kallon ta har sai da ya dire idanuwan shi cikin Nata Sam yakasa daina kallon ta wani Abu yake ji tamkar magnet yana fizgarshi zuwa gareta badan ya danne zuciyarshi ba to tabbas zai iya mik'e wa zuwa gareta , cikin natsuwa tagaishe sannan ta nemi wuri chan gefe ta rakub'e Malam ya kalli Aminullah da yayi shiru amma idanuwan shi k'yar akan Ummi yayi murmushi kawai ya maida duban shi ga Saifullah da kawai pretending yayi amma zuciyar shi Sam bata mishi dad'i , Malam ya Kali Dr Ahmad yace " Alhaji zamuso muji ya akayi ka had'u da Abdallah?" Cike da fahinta Dr Ahmad yafara magana sai alokacin Abdallah ya maida dubanshi wurin, Dr yace" akwai wata rana ina hanyata ta dawowa kano daga Kaduna Kasan cewar tafiyar asuba nayi k'arfe shida da Rabi nakusa Shiga kano ina daf da shiga gari sai naga cincirundon jama'a a gefen titi har zan wuce kuma sai naji zuciyata tana fizgata akan naje wajen koda na fita nayi parking mota ta a gefen titi na tsallaka abunda nagani ba k'aramin tayar min da hakali yayi mutane ne kwance kamar matattu cikin gaggawa na kira motar asibitin my nan da nan sai gasu sunzo akwashe su sai asibitin aminu kano , to nikam tunda na mik'asu cikin saurin likitoci ban k'ara bi ta Kansu ba domin ba b'arayi na bane , bayan yan kwanaki sai aka kirani ake sanar dani cewar mutanen nan duk 'yan uwansu sun gansu amma banda mutum biyu dan d'ayan ma bai farfad'oba likitoce nata aiki akanshi shikam d'ayan ya farka , tunda naji hakan na garzayo nazo asibitin , abunda na gani ba k'aramin rud'ani nashiga ba amma na dake duk dan kar agane , fuskar Abdallah iri d'ayace da fuskar d'ana Abdallah da yarasu shekara bakwai kenan da ace yana Raye to tabbas za'a kirasu da identical twince wannan dalilin ne yasa naji ina son taimaka masa" Tunda ga nan Dr Ahmad ya cigaba da bada labari har yau da suke tare . Malam yayi ajiyar zuciya yace "lallai Allah mai girma wato Abdallah Allah bainifi zakayi ilimi har ka zama wani abuba sai da basirarka ta gushi lallai Allah mai girma ne , Alhaji babu abunda zamu ce maka sai dai mu bika da godiya gami da fatan alkhairi Allah yasaka maka da mafificin alkhairi , Allah ya jik'an Abdallah" Nan dai Malam yayita kwararo addu'oi suna amsawa da Amin, Daganan Dr Ahmad ya buk'aci yasan wane ne Abdallah , tiryan tiryan Malam ya runk'a bashi labarin tundaga haihuwar Abdallah har zuwa ranar da suka rabu dashi da sunan zuwa kano saro kaya , maikaratu idan ya had'a da labarin Dr zai bashi cikkaken taruhin Abdallah, Ko da Malam ya gama bada labari gaba d'ayan su kowa da hawaye a idonshi musamman ma Saifullah da baitab'a tsamanin Abdallah zaiyi irin wannan rayuwar ba tsantsar tausayin abokinshi ne ya kamashi matuk'a . Shikam Abdallah kuka yake kamar yaro dan sai yau duk abubuwan da yake gani suka fayyace mishi gaba d'aya ya rasa bakin magana sai hawaye dayake ta faman yi . Ummi kuwa abad'aya farinciki ne ya mamaye mata zuciyarta Rana ji kamar taje ta rungume mijinta dan murna da jin dad'i . Duk dauriyar da Mama taso yi amma hakan ya gagara sai hawaye ya sub'uce mata . Umar , Saifullah tare da Aminullah su kaita rarrashin Abdallah *gareku readers shin me kuke tunanin dai Kasan ce bayan nan ? Shin Dr zai bar Abdallah hakanan duk da cewar ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar shi ? Shin ya alak'arshi da Ummi zata kasance , maiye makomar soyayyar Saifullah ga Ummi? Wannan da ma sauran wasu tambayoyi suna cikin page na gaba* Taku ce Maman Muhammad💓 @08165728746 [1/24, 4:46 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com *Wannan page d'in na sadaukar da shi ga dukkanin masoya labarin bawan Allah , tare da duk mai suna Zainab*💓 *Fatan alkhairi*❤ *Edited by Mum Mussadiq*😁 3⃣9⃣ Bayan natsuwa gami da gamsuwa ta ratsa zukatan su sannan Malam ya maida hankalinshi kan Abdallah yace " to Abdallah yanzun ka gane ko kai waye ko ?" Sai da ya ajiye wata nan nauyar ajiyar zuciya sannan yace "na gane Malam" Murmushi Malam yayi sannan yace " to wace ce waccen?" Ya nuna Mama Kallonta yayi tana ta sharar k'walla yaja gwuiwoyin shi ya tafi kusa da ita tare da rik'e hannuwan ta yana fad'in " Ki yafe min Mamana na saki kuka insha Allah ba zaki k'ara kuka ba daga yau" Dafa kanshi tayi tana Sosa gashin kanshi da ya kwanta yayi luf tamkar D'an India tama kasa magana tsabar farinciki , Dr Ahmad yayi gyaran murya yace " Allah ne k'addara zumunci tsakanin mu shiya sa bai bani ikon Neman danginka ba tunda farko kuma zumuncin mu ba zai tsaya anan ba " Rarrafawa ya sake yi yakoma gaban Dr Ahmad yana mai share k'walla yace " thank you soo much Dad bansan da bakin da zan godemaka ba hak'ika kai wani haske ne acikin rayuwata, ka bani ilimin da ina rayuwar zahiri banyishi ba sai gashi na samu alokacin da iyayena da dangi na suka cire tsammani da rayuwata, nagode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi Allah ya jik'an d'an uwana Abdallah yayi mishi Rahama" Duka suka amsa da "Amin" Kusa da Umar ya koma tare da rik'e hannun shi yace "ina cikin kewar d'an uwana wani lokacin nakanji zuciyata tayi min baki Ashe rashin abokin arzik'i ine irin ka" Murmushi kawai Umar yayi Dai dai kusa da Aminullah ya koma ya saiti kunnanshi yace " thanks for taking care of my wife I really appreciate you are indeed a real hero" Aminullah yace " you deserve it" Banza yayi da Saifullah kamar bai ganshi ba , Ashe shikuma abin ya bashi haushi sai ya mik'e afusace zai bar gurin , cikin sauri Abdallah ya rik'o hannunshi " where do you think you're going? ka kwantar da hankalinka ba sai na ambace ka ba you're always and ever in my heart" Nan duk suka kwashe da dariya haka sukayita hira har lokacin azahar yayi , Awaje haka mutane keta tururuwar zuwa ganin D'an gayu Abdallah wasu ma sai sun tab'a shi sunji . Mama kuwa haka mak'ota suka ta zuwa mata barka da taya murnar dawowar tilon d'anta cikin lafiya da aminci Bayan tafiyar su massalaci sai ga yara daga gidan su ummi d'aya Leda ce ahanunshi bak'a d'ayan kuma d'irkeken zakara ne anyanka shi an fige sukace gashi inji Malam , nan da nan suka fara aikin su , K'arfe 2:30 suka dawo massalaci , suko su Ummi har sun gama dafa jalof d'in shinkafa da wake ga naman k'aza k'amshi sai tashi yake , su jera kan tabarma . Bayan sun ci abinci sun k'oshi Dr Ahmad yace musu dama yau yake San komawa kano , Abdallah yaso ya bishi amma k'emadagas Dr yak'i yace ya zauna sai ya huta agida sunaji suna gani yayi musu sallama yatafi bayan ya yima Mama da Malam alkhair Nan fa suka zauna shida abokanshi suna ta hira Mama na gefe yana kallon D'an nata zuciyarta k'all. Ummi kuwa duk haushi ne da takaici ya cikata wato yasan da zaman kowa amma banda ita? lallai ma meyake nufi ? badai jiran banza tayi ba? Haka taita jero tambayoyi har Hafsa tazo ta sameta Cikin tsokana ta fara magana "Amarya angon naki ya dawo madadin na ganki cikin fara'a amma naga sai cin magani kike " Wani kallon shatara shatakwas ta aika mata dashi , tsabar takaici ma ta rasa me zata ce. Abdallah , Saifullah , Aminullah, tare da Umar suna tare har k'arfe Tara sannan Aminullah yayi hamma gami da salati yace "jama'a Bakujin bacci ne?" "Subhanallah" cewar Saifullah yayin da ya kalli agogon hannun shi Mik'e wa sukayi dukan su Mama na d'aki ta jiyosu ta lek'o cikin barkwanci tace " Amintacce inace pillows kawai zan mik'o muku". Dariya kawai sukayi sai da suka rakasu har bakin mota sannan suka Shiga suka tada ita suka tafi , yarage daga Abdallah sai Umar . Abdallah yace" kaima badai guduwar zakayi ba ko?" Kallon shi yayi da idanuwanshi da sukayi fici-fici saboda tsabar bacci yace " jiyafa saboda tsabar k'osawa da nayi inganka Sam nakasa yin bacci" Dariyar mugunta Abdallah yayi sannan yace " ayyah abokina " Umar tsaki yaja ya k'ara gaba yana cewa" ajedai a rungumi pillow" gaba ya abinshi Shikam dariya kawai yake yi ahaka ya Shiga gida . Ummi kuwa tunda magrib tayi ta fara kwasan kayan da zata buk'ata adare ta maidasu d'akin Hafsa dan chan take so taje ta kwana . Dai dai k'ofar d'aki taci karo dashi shikuma zai Shigo cikin hanzari ta fad'a d'akin Ummi kamar an wurgo ta , shikam abin ma dariya ya bashi d'akin ya nufa direct , yana ta k'are mai kallo komai nanan yadda yake da ba tarkace jakar kayanshi da Aminullah ya kawo mai ya tuna dashi fita yayi ya nufi d'akin Mama wadda har ta fara bacci a hankali ya d'auki jakar tare da sakayo mata k'ofa Kasan cewar yanayin sanyi ne , komawa yayi d'akin ya rage kayan jikinshi , sannan ya fito ya tunjumi ruwa arijiya ya nufi bayi , *kuyi hak'uri da wannan readers ina fama da ciwon kai*🤦‍♀🙏 [1/26, 4:53 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com Page 4⃣0⃣ Sai da ya watsa ruwan ajikinshi yaji wani sanyi yana ratsa shi , haka nan dai ya k'arasa wankanshi ya fito sai rawar sanyi yake yana Shiga d'akin ya fara Neman bargo chan gefen katifa yaga bargon Wanda da alama an ajeshine aka manta ba'a d'auka ba , aiko ba shiri ya d'auki bargon ya lullub'e har kai wanda duk da hakan bai hanashi jin sanyin da yake ji ba Wanda k'afafuwan shi da hannayen shi sukayi sanyi tarara sai wani kyarma yake. A d'akin Hafsa kuwa Ummi keta k'orafi sai Hafsa taje ta d'auko mata bargon ta , ita kuma Hafsa tace bazata ba . Da dai taga da gaske Hafsa take kuma ga dare yana dad'a yi ga sanyi yana k'ara sauka hakan ya sata fita ba shiri dan sanyi ya gama ratsata. Da sallama ta Shiga d'akin idon ta duk ya rufe bargon ta kawai take hange bata lura da Abdallah dake ta rawar sanyi ba ta kai hannu tafara yaye bargon , bata Ankara ba taji an janyota an wurga ta cikin bargon tare da k'udundune ta , tafa ihu kenan taji an toshe mata baki , cikin muryarshi dake rawa yace "Shhh ba abinda zan miki d'umin jikinki kawai nake so" Ruk'on da yayi mata ya sata kasa k'wacewa a hannun shi , tana ji tana gani ya runk'a murza duk wata gab'a da keda d'umi ajikin ta Ummi tun tana 'yan k'ana nan kukan ta har ta daina domin ta fara jin dad'in abin , dukkan su basu San iya lokacin da suka d'auka awanan yanayin ba ita dai Ummi taji Abdallah shiru ne sai wata sassanyar ajiyar zuciya da yake hakan ya tabbar mata da cewar yayi bacci . D'agowa tayi ta kalleshi yana ta sharar baccin shi azuciyar ta tace " kai maza kunyarsu ragagga ce " kayanta ta d'auka tasa sannan ta koma ta kwanta ajikinshi ta k'ank'ameshi tamkar zata farka taga bashi. Tofa masoya ansha bacci Abdallah ne ya fara farkawa yaga da kyakyawar fuskar abar k'aunarshi ya fara tozali murmushi yayi ya furta a hankali " you are always beautiful my Queen" ahankali ya zameta ajikin shi ya mik'e sai alokacin ya lura da yadda gari yayi tangaras , dafe kanshi yayi yana fad'in "ya subhanallah" Cikin hanzari ya zura jallabiya ya fita bokiti ya d'auka ya nufi kitchen dai dai lokacin Hafsa ta d'aga tukunyar ruwan zafi zata shek'a ma kama ya ce "Ke! Ke! Tsaya" tsaf ta gane me yake nufi dan ta d'ago ta kalleshi amma sai ta k'ara seta tukunyar da bakin bokitin Cikin kirne fuska yace " ina mai tabbatar miki kika juye ruwan nan duk zafin shi sai kin shanye shi" Yadda yayi maganar ya bata tsoro shiyasa ta aje tukunyar , aje bokin yayi yace" zubamin" ta d'auki tukunyar ta zuba ruwan rabi , ahasale yace " wai ke kinraina nine ko to duka zaki juye " Sai alokacin tayi magana " to kokon fa?" "Ki dafa wani ruwan dallah ni juyemin " Ahaka tana k'unk'unai ta juye ruwan ba don ranta yaso ba . Wani bokitin ya d'auka ya raba ruwan zafin biyu duka ya tafi rijiya ya surka su sannan ya aje bokiti d'aya a k'ofar d'aki ya tafi da d'aya bayi . Hafsa ko baki ta saki kamar wawiya azuciyar ta tace "idan baka mutu ba baka gama ganin abun mamaki ba " hakanan ta sake d'aura wani ruwan kokon. Ummi kuwa tunda ya fita ba dad'e wa ta farka kunya ce ta hanata motsi Sam tana zaune har Abdallah ya fito wanka tana jin motsinshi tayi sauri taja bargon tafe har fuskarta da sallama ya shigo tana ji bata amsa ba A hankali ya fara magana " Ummi kije ga ruwa can a k'ofar d'aki kiyi wanka 8 ta kusa " Zumb'ura baki tayi ta yaye bargon ko kallon inda yake bata yiba, yadda ta d'aga labulen ta lek'a ba k'aramar dariya ta bashi ba aciki yake dariyar . Tunda ta lek'a ta hango ba Mama a tsakar gidan sai Hafsa da ke shara yasa ta fita ta d'au bokitin , me Hafsa zatayi inba dariya ba . Lokacin da tagama wankan Mama ta fito tsakar gidan Ummi tana tsaye a bayan k'ofar bayin ta na lek'e ita ala dole sai Mama ta Shiga d'aki zata fito . Kamar ance Mama ta kalli k'ofar bayin ta hango Ummi a tsaye ta d'aura hannu akai , murmushi Mama tayi ta mik'e ta Shiga d'aki Ummi na ganin haka ko tsayawa d'aukan bokitin batayi ba fella d'akin Hafsa .Hafsa ko sai shak'ar dariya take abinta . Ummi na Shiga ta chanja kaya ta tada kabarar sallah. Abdallah kuwa tunda ya jira Ummi bata shigo ba nan ya mik'e ya fito ba kowa a tsakar gidan hakan yasa kai tsaye d'akin Mama ya nufa ya sameta tana ta gyaran 'yar tsohuwar drower kayanta cike da tausayin mahaifiyar tashi ya gaisheta ta amsa mai fuska a sake , d'akin ya d'anyi shiru sai Mama ta katse shirun da cewa " abincin Ku nanan a k'ofar kitchen " to kawai yace ya mik'e dan gaskiya yana jin yunwa , yana bud'e kwanon yayi arba da d'umamen tuwon masara miyar busashen kub'ewa " oh my GOD" abinda ya fad'i kenan ya rufe kwanon ya fita machine ya hau yaje wani restaurant yaci abinci sannan ya kira number Umar ya tambayeshi yana ina , Umar yace" yana gida yanzun zai wuce kasuwa" "Kajira ni ganinan zuwa " ya kashe wayar Ko da yakoma gida yayi karo da motar Saifullah a k'ofar gidan su k'arasawa yayi ya gaida Malam da keta fama da almajirai , sannan ya bar gurin ya Shiga gida still bai ga Saifullah ba , nan ya kira wayarshi ringing biyu ya d'aga bayan sallama Abdallah yace "Aboki ya naga motarka ban ganka ba?" Dariya Saifullah yayi yace " gatanan aro na baka kafin kasiya taka amma ka sani idan ka tashi mayar min sabuwa zaka siyan mun" Abdallah ma dariya yayi sannan yace " to waya gaya maka ina San kwancen wasu " Haka dai sukayi ta barkwanci daga k'arshe Saifullah ya ce mai "key d'in motar yana bayan k'ofa a sagale a zaure " Da haka sukayi sallama irin tasu ta abokai. Fita ya sake yi dan so yake yaje ya siyo kayan abinci dan gaskiya ba zai iya cimar nan tasu ba ya saba da irin cimar turawa 😨 A b'angaren Ummi kuwa Sam tak'i fitowa saboda kunya sai da Hafsa ta kaimata abinci , sannan ta ce mata ta shirya suna da lecture anjuma , wannan dalilin ne ya fata mik'e wa daga inda take ta fara shiri , ahankali take fitowa sai da tazo dai dai k'ofar d'akin ta sukayi clashing da Mama ta fito band'aki , akunyace ya gaisheta Mama ta amsa sannan ta wuce ita kuma ta wuceta d'auko abunda take buk'ata ta fito , Lokacin da suka je makaranta suka samu lecturer yace bazai Shiga ba sai 4 kowa yana ta Allah wadaran halinshi , kowa ya fita ya kama sabgogin gaban shi , Hafsa kuwa Aminullah ta kira ya Zo shima suka zauna suka dasa shiriritar su , ita kuwa Ummi tsaninta dasu ido , ana haka suka tsinkayi muryar Saifullah yana cewa "to na mamajo" Aminullah na had'a ido dashi ya d'aure fuska dan yasan yanzun zaizo ya takura mai Zama yayi kusa da k'aninshi sannan ya ce ma Ummi" Madam d'in mu ina wuni?" Akunyace ta amsa da taso ace ita ta fara gaisheshi , Hafsa ta gaidashi a dak'ile shima a dak'ilen ya amsa mata , juyawa yayi ya kalli Ummi yace "Wai wannan k'anwarki ce " Ummi tambayar ya bata dariya amma sai ta kalli Hafsa taga yadda ta d'aure fuska itama sai ta tsare gidanta tace "eh k'anwa tace " Hafsa dan takaici kamar tayi kuka . Sai kuma ya sake jefo mata wata tambayar " k'anwarki ta jini ko kuwa" Tsaki Hafsa Hafsa tayi ta tashi tabar gurin , Aminullah me zaiyi inba dariya ba Ummi tace "ah ah k'anwar yata Abdallah ne shima kuma y'ar wan Mama ne" "That's great ina jin nan zan maida shek'ata" Da sauri Aminuallah ya juyo yace " what do you mean?" "Abinda kunannan ka yaji " " to da sakel inji Fulani , wai kai yayan nan duk abunda nace ina so sai ka yi k'ok'arin rabani dashi " ya ko had'e rai ya juyar da fuskarshi gefe Saifullah gyara zamanshi yayi yace " mekake nufi ?" " ina nufin ina son Hafsa haka sanda ina tsak'a da son Ummi ka fara k'ok'arin rabani da ita wannan kam bazan barma ita ba I have already win her heart , go and find your own" Ummi kam rufe fuskarta tayi ta runk'a shek'a dariya abinta.... Follow me readers* *Maman Muhammad d'inku ce*😎 [1/27, 9:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com *Nafi khan Nd k'awalli wannan page d'in nakune zamuga Wanda za'a yi ma gwalo kwando kwando*😜😜 *Amma fa kar ace nayi nayi son kai ehe*😉 *ina gefe ina cin daria*😁🤭 *edited by husnah beauty love you sis*😉 *page* 4⃣1⃣ Wani bak'in ciki ne ya tokare Saifullah amma sai ya dake ya ce " zo muje D'an k'anina musa contains kar Madam tayi mana dariya" Nok'e kafad'a Aminullah yayi yace "nak'i wayon " "Haba my little bro my best friend ever " Da k'yar ya lallab'eshi suka matsa gefe kad'an . Ita dai Ummi tana gefe tana cin dariya Can sai taji Aminullah ya na cewa " asshhh da zafi fa " ko da ta juya ta kalleso sai taga suna ta dariya har da rungumar juna , nan suka canja salon hirar tasu . Sai da sukayi sallar la'asar sannan suka Shiga lectures . Ba su duka Shiga gida ba sai k'arfe 7:30 , ga wahala ga yunwa agurguje sukayi sallah sannan kowa ta mik'e awurin don jiran sallar isha Ummi kuwa wani wahalallen bacci ne yayi awon gaba da ita Hafsa da taga tayi bacci saita fita ta tafi d'akin Mama , tana d'akin Abdallah ya shigo yana shigowa bayan sun gaisa yace ma Hafsa "Ke kira min Ummi" "Tayi bacci " "Baccin gaske ko baccin k'arya ?" "Wallahi tayi bacci tun d'azun " "Go and call her for me my Friend!" Sumi sumi ta mik'e ta fita , Ummi na bacci taji ana jijjigata ana kiran sunan ta , tana bud'e ido taga Hafsa ce taja wani wawan tsaki , Hafsa abun ya bata haushi tace "oh ga marainiyar wayaunki ko , to bani ke kiran Ki mijin Ki ke kiranki " Cikin muryar bacci tace "baki ce mai ina bacci bane ?" "Na gaya miki Malama Ki tashi kije kafin ya gaya wa mutane a matse yake dan naga yana gab" "Bafa inda zanje idan kinga na tashi awajen nan to Tara tayi " Baki a sake Hafsa tace " eyyeh haka kika ce , ni 'yar sak'oce , kar ya huce a kaina " Hafsa ta fita taje d'akin Mama baya nan sai ta tafi d'akin su sallama tayi ak'ofar d'akin sai da ya amsa sannan yace "ya akayi kuma ?" Kai tsaye tace " tace ba zata zo ba" Shiru yayi sannan yace "tana da waya?" "Eh" "Bani number ta" Nan da nan ta rattafo mishi numbers din sannan yace mata "jeki " ta tafi tana sauke wani nannauyan ajiyan zuciya,. Tana kwance taji wayarta na ringing da kamar ba zata d'auka ba sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta d'aga tare da sallama , Amsa sallamar kawai yayi sannan yace " kizo Ki sameni ad'aki ina jiranki minti biyar kawai na baki" k'itt ya kashe wayar , Wata zuciyar tana cemata taje wata zuciyar tana cemata kije ya sake rik'e Ki irin na jiya Ki kwashi abun kunya da safe shi ba ruwan shi🤷‍♀ Can kuma dai me tatuna oho sai ta mik'e ta fita , tana zuwa bak'in k'ofar tayi ta jero sallama bai amsa ba sai da ya mula ya mulmule sannan ya amsa be ce mata ta Shiga ba ita ma kuma bata Shiga ba takai kusan minti biyar awajen sannan ya ce "Idan baki gaji ba to kiyi ta tsayuwa " ba shiri ta banko labulen ta shigo ta nemi gefe ta rakub'e kamar wata bak'uwa, Juyawa yayi ya kalleta cikin tsare gidan shi yace mata " Ummi na lura Sam bakya murna da dawowa ta " Cikin sauri ta d'aga ido ta kalleshi kallo me tattare da alamar tambaya Shima kallonta yayi yace "yes da kin damu dani da zaki nuna farin cikinki gareni amma dayake ba damu wa da ni kikayi ba sai wa wasan b'oyo mukeyi " Ita dai ta kasa magana Wanda tasan har ga Allah ko mahaifiyashi da wiya ta kaita zumud'in ganin shi , tana cikin tunani taji muryar shi yana cewa " shikenan tunda ni ba bazaki iya magana ba kije kawai " Ba tare da tayi tunanin komai ba tayi waje abinta . Abdallah kam bak'in ciki ne ya isheshi wato ma ba zata iya zama kusa dashi ba me take nufi ? Irin wannan tunanin yayi tayi har dare ya raba sannan ya fita ya d'auro alwala . Ummi kuwa d'akin Hafsa ta koma ta k'udun dune cikin hijab d'in ta tana ta kuka azuciyarta tana fad'in " ina ma ace zan iya fad'a maka sirrin zuciyata , ina ma ace zan iya fad'a ma irin kewarka da nayi ina ma ace zan iya fad'a maka irin farin cikin da nashiga lokacin da ka bayyana agareni amma bazan iya ba dan duk sun wuce gaban kwatance sai dai a aikace mijina " Irin wad'an nan kalaman tai ta fad'i cikin mayan shauk'in soyayya har Hafsa ta dawo daga d'akin Mama ta same ta wajen tana kuka , A hankali Hafsa ta zauna gefen Ummi tace " Aunty Ummi lafiya ?, me ya faru?" Kamar jira take dama akulata sai ta zauna ta dasa sabon kuka , da k'yar Hafsa ta lallesata sannan ta sake tambayarta me ya faru cikin kuka take sanar da ita yadda sukayi da Abdallah . Hafsa ko mai zatayi inba dariya ba Ummi kam had'e rai tayi tace " saboda wulak'anci kice na gaya miki damuwata madadin Ki bani shawara sai tsaya kina yi min dariya ?" Cikin dariya Hafsa tace " yo Aunty Ummi AI ke d'in ce sai a hankali" "Da nayi me fa?" Murmushi tayi tace "Aunty Ummi yaya Abdallah kulawar Ki yake nema kin kasa ganewa yanzun haka ma k'ila ko D'an welcome kiss d'in nan baki mishi ba , au ko dayake bari nayi shiru naga jiya kun kwana d'aki d'aya " ta k'arasa maganar tana dariyar mugunta . Ummi kam abin ya k'uleta ta d'auki pillow ta makawa Hafsa tare da fad'in " wallahi baby bakiyi ba" Duk suka kwashe da dariya daganan Ummi ta mik'e ta d'auro alwalar sallar isha da batayi ba sai da tayi sannan 'yan hanjinta suka fara Neman agaji , ba shiri ta nufi kitchen shinkafa da miya ta tarar miyar taji soyayyen nama sai buga k'amshi take nan tazubo taci sannan ta koma ta kwanta. *DA SAFE* Kamar yadda Umar yake yi yanzun kafin ya tafi kasuwa sai yazo sunsha hira da Abdallah sannan ya wuce , yauma suna tsaka da fira sai Umar yace "Aboki nima fa na kusa Shiga daga ciki " Cikin sauri Abdallah yace " Allah mutumi na " "Wallahi kuwa , yau saura sati biyu" Had'e fuska Abdallah yayi sannan yace " amma gaskiya bana kyauta min ba sai yanzun kake gaya min" "Kayi hak'uri abokina na bari ka samu natsuwa ne sai muyi maganar " Ajiyar zuciya yayi sannan yace " shikenan Allah ya Santa alkhairi , a ina ka samu matar?" "A funtua 'yar k'anwar Mama ce" "Hakan yayi kyau , to ya maganar kayan aure an had'a ?" "Eh an gama komai " "Masha Allah na tayaka murna sosai , a ina zaku zauna?" "A nan d'aki na mana " "To ai kaji matsalar guy haya zaka nema idan ba haka ba ina mai tabbatar maka ba zaka mori amarcin ka ba" Umar ya kalleshi ya kwashe da dariya yace "ahankali dai abokina yanzun kam dole mu zauna a nan dan duk basira ta ta k'are Mama kanta bataso mu zauna wuri d'aya amma insha Allah ba da jimawa ba zan nemi hayar" "Tashi muje Umar " "Ina zamu? nifa kasuwa zanje " "Shikenan kaje amma kasani gobe ba inda zaka je " "Allah ya kaimu" Nan sukayi sallama [2/6, 10:54 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com *dedicated to you readers ina alfahari daku* *BAwan Allah fans much luv dearies Allah ya barmu tare*❤ Page4⃣2⃣ Su Abdallah anata shirye shiryen bikin Babban aboki , acikin kwana uku ya Samar ma Umar gidan haya me dan sauk'in kud'i . Alokacin da biki ya rage saura sati d'iya sai Mama ta kira Abdallah tana masa fad'a , ranar ba kowa agidan su Ummi duk sun tafi makaranta , "Kai ma ai ya kamata ka d'auki taka matar kusan inda dare yayi muku " Shiru yayi yana Sosa k'eya sannan yace "to Mama ina zamuje?" "Kai ma hayar zaka nema kuje can Ku bani guri in sarara" Sai da yad'anyi nazari sannan Yace " ni da Mama na bari ne idan na fara aiki na samu kud'i sai in siyan mana wadataccen gida sai mu koma gaba d'aya" "Eh tunanin ka yayi kyau amma dai yanzun kafin wannan lokacin ka nemam muku wani gurin da zaku D'an zauna" "Shikenan nan Mama bari a gama bikin Umar sai na fara Neman gidan" "A'ah *BAWAN ALLAH* ni so samu ma Ku tare rana d'aya da abokin naka" Kunya ce ta kamashi ya mik'e yana Sosa k'eya yace " to Mama sai anjima" "Mu juma da yawa" ta fad'i tana murmushi . Bayan ya dawo da daddare ya samu Malam ya fad'a masa yadda sukayi da Mama fatan alkhairi ya bisu dashi Sannan suka k'ara tattaunawa daga nan ya rok'i alfarmar kar asanar da Ummi komai har sai ta tare Malam dai murmushi kawai yayi, Daga nan ya koma gida bayan yayi wanka yayi shirin baccin shi tsaf sannan ya kira Dr Ahmad shima cikin jin kunya ya sanar masa , cike da jin dad'i da murna yayi masa fatan alkhairi Sannan sukayi sallama, Ajiyar zuciya Abdallah ya sauke sannan ya furta a fili "komai ya kusa zuwa k'arshe" murmushi yayi tare da jero addu'oi sannan yayi bacci, Washe gari da safe Umar yazo gidan dama sunyi da Abdallah zasu je funtua gidan Amaryar Umar d'in, bayan sun gama shirya wa tsaf suka fito. Abdallah ya sha kwalliya kamar wani sabon ango sai fara'a yake , Ummi dake zaune d'akin Hafsa tunda ta k'yallara ido ta ganshi sam ta kasa kauda idonta ba dan k'yafta ido dole bane to da Ummi bata yiba tasan Abdallah kyakkyawa ne amma bata tab'a ganin asalin kyanshi ba sai yau . Shikam tunda ya juya suka had'a ido sau d'aya bai k'ara waiwayar inda take ba , ya nufi k'ofar Mama , yana shirin yin sallama ita kuma tana fitowa, hakan yasa duk suka zauna a k'ofar d'akin kan tsaftacecciyar tabarmar dake gurin , Bayan sun gaisa Mama tace "Umar ina zuwa haka wannan shiri kamar yaune za'a kawo mana suruka " Caraf Abdallah ya amshe da " wata surukar za'a je nemo miki" Cike da mamaki Mama tace"wata suruka kuma AI ni na gama aurar da yarana maza sai dai na jira suruki kuma" Dariya Abdallah yayi sannan yace " to Mama suruka ta biyu za'aje ne mammiki" ya k'arishe maganar yana langab'ar da kanshi tare da had'e hannunshi guri d'aya alamar pleading , Mama ta gane zolaya yake ji sai tai murmushi ta ce "Hakan yana da kyau AI Allah ya sanya alkhairi " Duk suka amsa da "amin" Umar yace " Mama AI yarinyar ma k'awar Maryam ce " "Masha Allah Abu yayi kyau" nan dai sukayi ta barkwancin su sannan suka fita . Ummi kuwa tunda suka fara maganar take jin zuciyar ta kamar zata tarwatse , mekunanta ya ke jiye mata ne ?tun kafin ta tare Abdallah zai mata kishiya ? , wani kuka ta fashe dashi , Hafsa kam ya kwance a d'aki tana sharar baccin ta har Ummi taci kukanta ta gaji , har tayi shiru Shikam Abdallah ko ajikin shi fita ma yayi harkarta duk da hakan bai mishi dad'i shirye shiryen kawai yasa agaba A b'angaren Dr Ahmad kuwa zuzurutun kud'i ya turama Abdallah yace su sha shagali shida aminin shi Abdallah kuwa wani gidan haya ya samu unguwar me kyau gashi babu hayaniya Plat uku ne agidan da ya wadatu da manya manyan dakuna 2 bedrooms ne sai Babban parlor mai tare da dining area gefe kuma kitchen ne da madai daicin store aciki balaifi gidan yana da tsari mai kyau Wajen Ummi Mama da ummanta gyara suke mata sosai da tambayi dalili duk amsa d'aya suka bata suna so 'yarsu tafi ta kowa kyau , Babban abinda abinda ke damun ta kuwa shine yadda Abdallah ya d'auke k'afa agidan sai ya kwana bai shigo ba bata San yana can ya k'ok'arin karb'ar Amarya ba , Akwana a tashi ba wuya agurin mai rai yau ta kasance juma'a, Wanda gobe asabar za'a sha shagalin biki, Ummi na zaune ita da Hafsa ad'aki yayin da Mama tana tsakar gida tana Taryar bak'i daga danginta zuwa dangin Baban Abdallah , wata daga cikin k'annen MAMAN Ummi tashigo d'akin da sallama bayan sun amsa mata tace "Ummi yaya tace maza Ki tashi muje gidan su Habiba mai kotso da k'unshi ayi miki" Shiru tayi kamar bata jita ba da yake ba wani girman Ummin sosai tayi ba. Hafsa tace" ummi dake fa ake magana ," Azuciye ta juyo dan bak'in ciki duk ya gama cikata tace " naji sai mene ? Ni ku k'yaleni da kinibibin kU ba inda zanje" Zuwaira k'anwar Umma taji haushi ta fita kai tsaye Mama ta sanar ma duk yadda sukayi da Ummi , murmushi Mama tayi tace "muje gurin Ummin " Ummi najin sallamar Mama sai ta hau kuka ita bazata ba da k'yar da sid'in goshi Mama ta lallab'a ta ta tafi , Daren ranar kuka ta kwana yi sai ta d'aga waya zata kira Abdallah dan ta gaya mai irin dumbin k'aunarshi da take yi sai kuma ta kasa domin zuciyar ke gargad'in ta muddin tayi hakan to zaiga zak'ewar ta bare ma yanzun da yake rawar jiki za'a kawo mai sabuwar Amarya zai yi auren soyayyah acewar Ummi fa kenan🤣 [2/7, 10:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH* *MRS NN ONE💋* ® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_* _ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_ # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS* # https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com _Assalamu_ _alaikum_ _readers anan Zan tsaya da littafin*bawan Allah*sakamakon wasu dalilai ina fata zaku yi min uzuri🙏sai mun had'u a sabon novel dina mesuna RAYUWA TA ina fatan shima zai nishad'antar damu ngd_ *GODIYA* _Godiya ta musamman ga k'ungiyar REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS,like I said b4"sisters we are the best ever so let's keep shining like a stars in the sky🌠🌠_📚✏ *jinjina gareku readers* *Bawan Allah fans bansan ta inda zan fara ba duk fad'in social media bani tamkarku ina yinku irin sossai d'in nan Allah ya bar zumun ci* *my bestie I miss you (Ummu Sadeeq)* *Ameenert* *Rahma Ismail* *Sadiya illa* *acceya* *Maman hanan* *Ummu adil* *fareeda* *nafi khan* *matar me kake* *sadeeya* *MAMAN sa'a* *Binta mala* *aisha saleh idrees* *Kai aradun Allah kuna da yawa ba zaku lissafu ba Kawai Kudai Ku sani kuna mak'ale azuciyata*🤞🤸‍♀ *miss husnah*no more hawan water yanzun agayama likita bawan Allah yazo k'arshe dan haka ya ajiye ya ajiye makaman aikinsa agefe wannan ba fanni shi bane Maman Muhammad ce zata yi aikin ta🤣 *Maman Mimi* *MAMAN Abdul* *ummul khairi Gj* *ummul khairi Jibril* *hussaina sanee* *Rabi'atu paki* Love you guys😍 Kuyi hakuri readers idan nace zan lissafoku to kunfi k'arfin fige d'aya mai d'auke da read more goma fatan kun gane 🤣🤣🤣🤣🤣🤣 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Page 4⃣3⃣ Washe gari da safe haka ta tashi kamar an zare mata laka ajikinta komai cikin sanyin jiki take yinshi . Tana kwance a d'aki har 11:00am batayi wanka ba Sai ga Mama tashigo d'akin ta kalli Ummi da kwaNce tamkar mai bacci , gefen katifar Mama ta zauna sannan ta dafa kafad'ar Ummi dake kwance tace "kiyi hak'uri Ummi nasan dukkan kowace Mace dole tayi kishin mijinta bai kamata Ki nuna damuwar Ki acikin mutane ba aro juriya zakiyi Ki sanya ma zuciyarki , sannan kada Ki kuskura Ki nuna ma kishiyar kin damuwar ki domin idan tasan lagwan Ki ta runk'a k'untata miki kenan , Ki zama mai juriya ta fannin kishi, Ummi ?" Mama ta k'arishe da kiran sunan Ummi wadda tuni idonta yake ambaliya da ruwan hawaye Cikin sanyi Ummi ta d'ago ta kalli Mama tacw "na'am" "Kiyi hak'uri da duk wacce zaki gani amatsayin abokiyar zamanki ba bak'uwar Ki bace kin Santa farin sani dan na tabbata zakuji dad'in zama" Tunda Mama take maganar k'irjin Ummi ke dukan uku uku , kanta be k'ara kullewa ba sai da Mama tace mata tasan wadda Abdallah zai aure , mamaki take ita dai tasan bata San kowa Funtua ba to me hakan yake nufi? Haka dai Mama tayita mata nasihohi sannan ta lallab'a ta taje tayi wanka , Da daddare Hafsa tashigo d'akin ta samu Ummi na zaune ta zabga tagumi, cikin tausayin k'awarta ta , zama tayi kusa da ita sannan ta fara magana "Kiyi hak'uri Ummi nasan yaya bai kyauta miki ba , kin jajirce kinyi zaman jiran shi na shekara biyar duk da cewar bakida tabbacin cewar yana Raye ko akasin hakan amma kika jure, sai gashi da ya dawo babu abinda ya saka miki dashi sai kishiya, kiyi hak'uri Ummi wannan wata jarabawa ce daga ubangiji ya gwada kine don ya gane k'arfin imaninki, kuma nan gaba kad'an zaki samu *CHANJIN RAYUWA* tare da *RIBAR BIYAYYA* Kinji k'awata?" Cikin sanyi Ummi ta d'aga kanta alamar "eh" Hak'ik'a nasihar Mama da Hafsa ba k'aramar tasiri sukayi ba azuciyar Ummi har taji damuwarta ya fara raguwa. "Yauwa k'awata to tashi muje ance Amarya na hanya muje mu tarbeta" Harara ta juya ta watsa ma Hafsa sannan ta ce"to meye nawa kuma aciki?" "Haba Ummi ba yanzun muka gama magana ba?" "Eh amma Ki sani ba inda zani" "To shikenan dama Malam ne yace lallai muje Dake tunda kince bazaki ba bari naje na gaya mai" Bashiri Ummi ta mik'e ta sanya hijab d'inta tare da fad'in "Hafsa bomb " Koda suka firo k'ofar gida motoci biyu ne dalla dalla sai d'aukan idanuwa suke , Abinda yaba Ummi mamaki bewuce ganin yayyen mamanta biyu da k'annin Malam biyu tana cikin Mamaki taji anjata zuwa jikin d'ayar motar da Babu kowa aciki , itadai Ummi haka ta zama rak'umi da akala, har suka isa gidan , "Masha Allah gida yayi kyau " haka mutane keta fad'i lokacin da suka gama zaga Gidan, Hafsa da Ummi kuwa suna parlor Kamar suyi kuka dan takaici dan gidan ya tsaru komai ansa dadai na k'aramin mekud'e , Suna zaune su kad'ai a parlorn sai Ummi tace "ke nifa naji gidan shiru " Hafsa tace "nima haka" AI duk sai sukayi waje abin mamaki babu motocin da sukazo dasu babu Kuma matan da suka zo tare , nanfa suka fara salati kowa na bazai zauna ba , Suna zuwa bakin gate megadin ya taso yace "kuyi hak'uri 'yanMata an bani umarnin kar na bar kowa ya fita daga wancan b'arayin " ya k'arike yana nuna inda suka fito Nan suka hau magiya da bashi hak'uri amma Sam yak'i hakanan suka koma , Hafsa Ce tace "yauwa bari na kira Aminullah ya zo ya maida mu gida ," Ummi tace" dad'ina na da ke akwai basira wani lokacin" Alokacin da Hafsa ta kira Aminullah yace mata gasu nan a Hanya shida angon , Suna zaune tsumu kowa da abinda yake sak'awa azuciyar shi , suka jiyo k'arar tsayuwar mota, Nan da nan zuciyoyinsu ya tsananta bugawa , Hannun k'ofar aka murd'a tare da turo k'ofar gami da sallama , Nan take numfashin Ummi yayi sizing na wucin gadi sakamakon idanuwanta da sukayi tozali da kyakkyawan angon ta ahankali ta furta "Subhannallahil khalk'il azim" Abdallah ne a gaba sannan Saifullah sai Aminullah dake take masu baya , Abdallah kuwa direct kusa da Ummi yAje ya zauna yana fad'in "uwar gida sarautar mata" Ta kaici ne ya kama Ummi ta yunk'ura zata mike kawai sai taji an jawota , unexpected taJi ta fad'o ajikin shi , Dariya Saifullah yayi yace "au tun bamu je ko ina ba?, ke Hafsa tashi mu tafi", Shi dai bai ce komai ba harsuka kai bakin k'ofa , Ummi ko sai kick kici take tana son k'wacewa amma ta kasa Da dai taga dagaske tafiya zasuyi AI sai tace "ni ka k'yaleni zasu tafi subaRni," Ahankali ya rad'a mata. Dai dai saitin kunnanan Ta," ina zakije ne baby?" "Gida" ta bashi amsa a tak'aice Kallon yayi sannan yace " Ummi kina tunanin zanyi miki *Butulci* bayan *Hallacin so* da kikamin idan na miki haka banzama adali ba , Ummi kisani har *ABADAN* bani da tamkarki ke kad'ai ce Mata AI mutumiyar taku duk ya kashe mata jiki da k'yar ta iya cewa "Amaryar taka fa?" "It's just a plan"ya fad'i yana dariya Cizo ta daddage ta ganna Mishi a k'irji saida yayi 'yar k'ara ita ko mik'e wa tayi taruga bed room aguje ya bita yana fad'in " saina rama" Haka dai sukayita guje guje daga K'arshe dai sukayi abinda ya zamar musu wajibi bayan sunyi sunnoni sannan suka fuskanci junansu cikin soyayya da k'aunar juna , Tun daga wannan rana Ummi take samu kulawa ta musamman gami da soyayya *Bayan sati biyu* Saifullah ya aika aka nema masa auren Hafsa Kasan cewar da sannayya nan take aka bashi tareDa sa rana wata d'aya aiko Saifullah ya daka tsalle yace yayi yawa ina laifin sati biyu nan dai Aka sha kan Baban Hafsa ya hak'ura An ragargaji biki Ummi itace Babban k'awar Amarya Sosai akasha shagali , Bayan biki Dr Ahmad yakira Abdallah ya sanar masa ranar ranar wata litinin asibitin shi bashiri ranar Sunday ya wuce Kano , Aiki yake sosai , ,sai ya kasance shi da Zaria sai dai week end , Allah Sarki Abdallah bai manta hallaci ba mak'udan kud'i ya d'auka yA ba Umar domin YakAfa kanshi , Bayan shekara d'aya Da Rabi Tunda Nesa na hango shi yana Ta sunturi k'ofar labour room ya had'a zufa, Bud'e k'ofar da akayo ne ya sashi saurin matsawa Dr da ya bud'e k'ofar D'auke da murmushi afuskarshi yace"congratulation Dr Abdallah your wife delivered healthy Nd safely " Murnar Abdallah Sam tak'i b'oyuwa jiYake duk duniya ba Wanda ya kAI shi Sa'a, yana cikin murna sai ga Saifullah da Hafsa itama DA tik'ek'en cikinta, tare suka Shiga dakin saibarcin ta take , FArincikinSu bai Kara bayyanu wa ba sai da suka ga yara biyu kyawa wa Wayyo zokuga godiya ga ubangiji wajen Abdallah. Ranar suna yara Ahmad da kabir . Bayan wata uku Hafsa ta Haifo sankaceceyar yarta taci sunan Hindatu (Mama) Aminuallah kam yana chaina yana masters dinshi akan bussines *ALHAMDULLIH*