[3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part 1 ⏩ 5 Bismillahir Rahmanir Rahim. Ina farawa da sunan Allah, ina rokon Allah yasa yanda zanfara littafin nan lafiya Allah yasa ingamashi lafiya. GARGADI..... Banyarda wani ko wata su canza mani littafi ba, ko su juya manishi ba, duk wanda yayi haka nabarshi da Allah. Kuma banyi wannan littafin domin incima wani fuska ko kuma dan inbata mashi rai ba, nayishi ne domin fadakarwa ga mutane. SADAUKARWA!!!! Na sadaukar da wannan littafin nawa ga dukkanin mata da maza, domin wannan littafi nakune, Samari da yan matan zamani. GODIYA!!!! Ina mika godiyata ga dukkanin masoyana, Allah yabar zumunci, nagode da addu,arku agareni. Wannan littafi nawa kowace irin fassara aka mashi ze bada amsa dede,domin kalmar tana da amsoshi dayawa. KOWA YA TAKA DOKAR ALLAH????? Nabar maku sauran, ku amsa da kanku😘 Wata motace medauke da samari da yanmata su shida ta kwaso da gudu sun kure kara suna jin sauti acikin motar, babu abinda yake fitowa aciki se shewa da dariya. Tafiya suke cikin dare da misalin karfe 1:00 na dare, sun taso daga partyn da daya daga cikinsu ya shiryama budurwarshi na murnar zagayowar shekarar haihuwarta. Gaba daya ba acikin gari sukayi partyn ba, saboda basa son asa masu ido, kasancewarsu yan garin Bauchi hakan yasa suka tafi can kauyen Bununu dake wajen gari. Awata gona sukayi partyn, mutane dayawa sun halarci gurin, anyi shagali sosai, ansha kayan maye anyi rawa, ganin dare yayi yasa suka tashi, kowa yakama gabanshi. Wannan motar itace ta karshe, kuma itace ta masu partyn, ko kula da dare basu yiba haka suka kure kara suka kulle glass suna shara gudu, acikin motar ma rawa suke suna shewa. Dede sun fito daga kauyen, sunzo wani karamin daji, motar tafara hayaki, ganin abinda yake faruwa yasa driver yayi saurin taka burki, gaba dayansu suka fito daga motar. Daga gaban motar sukayi ashe ruwa ne, yakare nacikin lagireton motar, dubawa sukayi sede kuma babu ruwa ko kadan amotar. Kafa daya daga cikinsu yasa yadaki tayar motar, dafa kafadarshi wani yayi yace lafiyade Nabeel? Tsaki yaja yace wlh babu ruwa amotar nan Najib, Daya daga cikin matan mesuna Sumy tace munshiga 3 yanzu honey yazamuyi gashi kowa yatafi, gashi adaji muke, wlh tsoro nakeji. Jawota Nabeel yayi ya rungumeta yana shafa bayanta yace kiyi hakuri Dear babu abinda ze samemu, kawai kushiga mota ku kwanta muzamu tsareku, tunda yanzu 2 takusa babu inda zamu samu ruwa, idan asuba tayi semu nemi ruwa. Sumy tace nashiga 3, Khairat, wlh Babanmu besan zanzo nan ba, Mamanmu ce kawai tasani, kuma seda taja mani kunne kada indade, nasan halin Babamu wlh ze iya dukana. Wadda aka kira da Khairat tace haba Sumy meyasa kincika tsoro, kinsan fa Mamanki tana goyon bayanki bazata bari Babanki yasan kinzo nan ba, nasan zata kareki, kuma wannan party saboda ke mukazo nan. Amma idan kina ganin akwai matsala ki kirata kice mata motarmu ta lalace, zaki kwana agidanmu. Sumy ta kalli dayar kawarsu tace Zuby bani wayata acikin jaka. Nabeel yace Sumy kiyi hakuri gurin nan babu network waya bazata shiga ba, kawai kiyi hakuri mubarma Allah gobe. Kallon dayan abokinshi yayi yace Saif miko mana dadduma acikin mota muzauna. Saif yajuya ze dauko dadduma sukaga mutane sun zagayesu kamar daga sama aka turosu, wasu bakaken mutane ne, masu kama da arnan daji, gaba daya fuskarsu babu alamar imani aciki. Babu riga ajikinsu, gajeran wando ne, kawai se wani tsumma dasuka daure kugunsu dashi, kowa se zaro idanuwa yakeyi, suna lashe harshe. Kuka matan suka sa, kowa takama saurayinta suka rike juna jikinsu yana bari. Gaba daya har mazan tsoro yakamasu, wata irin dariya daya daga cikin mutanan yayi, Kallon sauran yayi beyi magana ba, suka nufosu suna zare ido, haka suka tasa keyarsu suka nufi wata hanya. Tun suna kukan tsoro har suka koma na gajiya, domin bakaramar tafiya sukeyi ba. Ga duhu dan hasken dasuke haskawa beda wani haske, kuma duk sun anshe wayarsu sun wurgar da ita acan gurin motarsu. Cikin wani daji suke shiga babu alamun gida agurin, zuwa yanzu matan gaba daya sun fita ahankalinsu, domin tafiyace takusan awa daya da rabi. Se gurin karfe 3:30 suka isa tsakiyar dajin da bazasu iya gane gaba ba, bare baya, wasu mutane yan uwan wadan da suka taho tare suka gani, sun hura huta suna ta shagali. Da murna suka tarbi yan uwansu, ganin sun samo masu mutane, domin sun dade basu kama kowa ba, domin mutanan dasuke kauyen Bununu sun gane tarkon dasuke samasu. Hakan yasa suka dauki matakin dena bin hanyar idan akace karfe 10 tayi, domin da 12 tayi suke fara shawagi atsakanin gurin, dominsu aikinsu kama mutane, su kashe, ko kuma su maidasu bayinsu, matan kuma suyi amfani dasu. Mutanene masu kama da arnan daji, sam basusan meye imani da tausayi ba, acikin wannan dajin suke zaune, idan sungaji kuma su kara gaba, a wannan dare sukayi sa,ar cafke su Nabeel. Babu bata lokaci aka turasu cikin wani akurki dan,karami, dan atakure suke, Sumy dasu Zuby se kuka sukeyi, suna dana sanin zuwansu wannan party, mazan kuwa se hakuri suke basu. Wani katon mutum ne, yafito daga wata bukka, daga ganinshi babu alamun imani atare dashi, dukawa kasa sukayi suna kwasar gaisuwa, hannu yadaga masu, wani yashiga gaba ogan yana binshi abaya sauran suka take mashi baya. Hanyar inda aka rufe su Nabeel suka nufa saurin bude kofar sukayi fito dasu akayi, Sumy kamar zata saki fitsari dan tsoro, haka sukayi layi se rawar sanyi sukeyi saboda tsoro. Kallon Zuby yayi yana lashe baki, kallon daya daga cikin yaranshi yayi, nan take suka fahimci abinda yake nufi, hannun Zuby suka kamo, aikuwa saurin kai hannu Saif yayi yariketa, Fuskarshi a daure dan Saif akwai zuciya, tsawa wani yadaga mashi yana wani irin yare wanda basu san abinda yake fada ba, amma Saif yaki sakinta. Wani katon karfe dayake hannun wani yasa yabuge hannun Saif da karfi wanda seda Saif yafadi kasa saboda tsananin zafin dayaji hade da sakin wata kara, seda yan uwanshi suka tausaya mashi. Haka yarika burgima agurin yana rike hannunshi, sunaji suna gani wani yadauki Zuby yanufi bukkar Ogansu da ita tana kuka gwanin ban tausayi, wani ya tura sauran cikin akurkinsu, da kyar su Nabeel suka kama Saif suka shiga ciki. Zuwa lokacin hannunshi ya kumbura sosai daga gani yasamu buguwa agurin, kwanciya yayi agurin idanuwanshi se zubar da kwalla sukeyi. Nabeel yace sannu Saif, hakika Allah ya jarabcemu da dede laifinmu, mun saba mashi gashinan tun aduniya mun fara karbar sakamkonmu, dama kuma duk WANDA YATAKA DOKAR ALLAH BAZEGA DEDE BA. Yanzu gashinan munshigo inda babu wanda yasan ranar fitarmu, bamu sani ba ko zamu fita da rai, daga ganin mutanan nan wlh basuda imani, yanzu kalla sun dauki Zuby Allah kadai yasan mezasuyi mata. Sumy tace baiwar Allah, wlh nasan baze kyaleta ba, domin yanda yake lashe baki kamar tsohon maye, ni tsoro ma nakeji kada ya goga mata cuta. Khairat tace mu de munshiga 3, mun cuci kanmu, mun cuci iyayenmu mun dauki muguwar rayuwa mun sama kanmu, muna aikata sabon Allah babu tsoro azuciyarmu, acikinmu babu wanda yataba tunanin wata rana zamu mutu. Najib ya goge hawayen fuskarshi yace ina ganin addu,a itace abinda yakamata muyi ba wannan surutunba, babbar damuwata yanda ko sallar azahar zuwa isha,i babu wanda yayi acikinmu, Gaba daya saboda wannan dan iskan partyn daya jaza mana bala,i mun dauki lokacinmu gabadaya na yau mun bama wannan partyn, gashi daga karshe abinda yajawo mana. Wlh kudi Abbana yabani dubu dari biyar inkaima abokinshi a kaduna, kuma zuwa azahar zeyi amfani dasu, Abba hada bani mota dan kawai in isa da wuri,kunsan yau babu banki, gashi Abba beda kudi a account shiyasa bemashi transfer ba. kuma gashi tunda asuba nayi sallama da gida akan natafi Kaduna, Amma na ha,inceshi nakashe wayata nataho party, yanzu kudin suna cikin motar, gashi motar tana daji, ga kudi aciki shikenan nasan dole asamu wadan da zasu dauke motar. Nabeel yace inaganin naku me sauki ne, ni tunda nataso agidanmu nake aikata sabo, Ummi na bata taba hanani ba, gani dan gata agidanmu, ni daya ne, babu abinda nake nema inrasa. Allah kadai yasan iyakacin matan dana batama rayuwa, nasa Abbana kuka yafi akirga, yayi addu,a haryagaji amma bancanza halina ba, kuma har gobe yana sona,ayau ina matukar dana sani da irin wannan rayuwa dana saka kaina. Ummi na itace mutum ta farko data bada gudummuwa wajen lalacewar rayuwata, gashi yanzu zan mutu batare dana nemi yafiyar Abbana ba, wlh bazan iya cemaku ga ranar danayi sallah 5 arana ba. Sannan babban tashin hankalin duk gatan da Ummina tamun wlh yau kusan wata 2 kenan banganta ba, banje na duba jikinta ba, tana cikin tsananin rashin lafiya, wanda Abba ya kaita asibitoci da dama amma bata warke ba. Daga karshe ma gajiya yayi ya wareta yasa mata masu kula da ita, ko gurinta baya zuwa, gashi yayi aurenshi sede haryanzu beda wani da seni. Ina tsoron kada alhakin Ummina ya kamani, duk da itace silar lalacewata amma nasan UWA UWA CE. Kaichona Ihun Zuby dasukaji ne yasa gaba dayansu hankalinsu yakara tashi, Saif dayake kwance shima seda yatashi, dan kara yasaki daya fama hannunshi. Khairat tace shikenan Zuby Allah kadai yasan abinda suke mata, kilama fyade zasuyi mata. Cike da bacin rai Saif yace dan Allah kada kucika mana kunne da kuka, Ai gara ita taga abunda zasuyi mata, mufa? Babu wanda yasan abinda zefaru dashi, saukinta ma daya dama yar hannuce da senafi tausaya mata idan virgin ce. Tsaki yaja, ya kalli Nabeel yace dan Allah ni kama mun hannun nan kila zan rage jin zafin danakeji, murmushi Nabeel yayi yace kai mutumina, kana cikin bala,i amma baka dena wanna halin naka na bakar zuciya ba. Wlh kabi ahankali da mutanan nan idan kace zakayi masu zuciya zasu iya kasheka, Saif yace naji, kawai kama mani, Wani irin kara Saif yasaki da aka kama mashi hannun, dariya Sumy takusayi ganin wanda yake fada ancika mashi kunne gashi yanzu yana ihu. Ganin shiru ba,a maido Zuby ba, yasa suka kwanta cike da firgici, Zuby kuwa tana can seda Ogan yagama amfani da ita son ranshi ya mika ma sauran yaranshi, yace abar sauran seda safe yanzu bacci zeyi. Seda Zuby ta sume masu sannan suka kyaleta, sunso ace Oga yasa andauko sauran matan, amma sanin halin Ogansu yasa suka hakura, agefe guda suka jefar da ita ko motsi batayi suma suka kwanta. CIKIN GARIN BAUCHI Kuka kawai Maman sumy takeyi, yanda Baban Sumy yadage yana mata fada, domin tun tana mashi karyar anjima kadan Summay zata dawo har karyarta ta kare, Malam Haruna yace shikenan Zainab, tunda de bazaki fada mani, inda Sumayya ta tafi ba, shikenan, amma iname tabbatar maki zancire hannuna kome zefaru da ita babu ruwana, Dama na dade da sanin kece kike goyan bayanta akan duk wani iskanci datakeyi, amma idan nayi maki magana seki kareta, yanzu kince kin aiketa gidan yayarki, Kuma agabanki nakirata tace rabonta da Sumayya anfi wata guda, amma bakomai, idan kinfison incigaba dasamaku ido tarika kawo maki abun duniya kinaci shikenan. Dukawa kasa tayi tana kuka tace dan Allah mal. Kayi hakuri, nasan na cutar da diyarmu, na ha,inceka na dade ina boye abubuwan da Sumayya take aikatawa, Wanda duk nice silar shigarta halin datake ciki saboda tsabar son abun duniya irin nawa, amma wlh yanzu nayi danasani, tunkafin kashigo gidan nan hankalina yake tashe, Domin tamun alkawarin bazata kai magriba ba, amma nakira wayarta bata shiga, daga karshe ma senaji wayar akashe, ni nasan duk inda Sumayya take tana cikin wani hali, Dan Allah mal. Kada kayi fushi da ita, ayanzu Sumayya addu,ar mu take bukata, dan duk yawonta bata taba zuwa wani guri ta kwana ba, kayafe mana. Zama mal. Yayi yana jinjina kai, gaba daya tausayin matarshi yakamashi, hannu yasa yakamo hannunta yace ya isa haka, yanzu abinda nakeso insani wane guri ta tafi? Maman tace wlh bansan inda suka tafi ba, abinda nasani de partyn zagayowar haihuwarta wani saurayinta yahada mata, amma bansan inda zasuyi ba. Shiru yayi yana goge zufa. Babban yayan Sumayya dayake tsaye shima kukan yakeyi ya duka kasa yace Baba yanzu kuyi hakuri, yanzu dare yayi, mubarma gobe, se inje innemi wadan da sukaje partyn nasan zamu samu labari daga garesu. Wata matace kwance adakinta, banda kuka babu abinda takeyi, idanuwanta harsun kumbura, asalinta fara ce amma ayanzu tayi duhu sosai. Fuskarta wasu kuraje ne suka fito mata, jikinta duk ya yamutse saboda tsanin cutar da likitoci da dama sun kasa gane kanta. Hatta da mijinta ya kebe mata daki ya zuba mata masu aikin dazasu rika kula da ita, sam bayason ganinta idan bame dauriya ba babu wanda ze iya kusantarta domin dakin kanshi wari yake, duk yanda yake samun gyara amma hakan be hanashi wari ba. Kawarta ce Lawisa tace ya isa haka Ummin Nabeel, kidena kukan haka nan, asirinki baze taba tonuwa ba, domin mun toshe duk wata kofar dazata sa Alhaji yasan abinda kika aikata shekara da shekaru. Dago kai Ummin Nabeel tayi tace haba Lawisa, nikam nagaji da wanana zunubin danake daukarma kaina, na aikata sabo, nataka DOKAR ALLAH, kinsan kuwa Allah baze barni ba. Idan ma mutuwa nayi dole akwai wanda zan bari aduniya kinga dole asirina ya tonu, gara tun inada damar tuba, nayi amfani da ita, bazan damu da jin kunyar duniya ba, Inde Allah ze yafe mani, banida damuwa, ko yanda Allah ya maida Nabeel kadai ya isheni ishara, yaro kamar wanda shedan yayima fitsari akai, duk da hadani cikin wadan da suka bada gudummuwar lalacewar rayuwar Nabeel, Amma wlh hada zunubin dana aikatama Allah,kina ganin Babanshi ya guje ni, shima kanshi se inyi wata banganshi ba. Idan ma nasamu yazo dubani ko kofar dakin be karasowa daga waje ze gaisheni. shiyasa na kiraki domin infada maki zanje intona asirin da nadade ina boyema Alhaji, idan ma rabuwa zeyi dani banida damuwa matukar ze yafe mani tunda yanzu meyayi saura, tamkar yacireni daga matanshi ne, kina ganin kwanan nan yayi aure, amma ni ya ajeni abanza, wama yasani ko asirin danayi na aureshi yakare. Lawisa tace naji, kuma nima maganarki tasa jikina yayi sanyi, insha Allah nima daga yau nadena aikata abinda nakeyi, amma babban abin damuwar kince rabonki Nabeel kusan wata daya da rabi bedawo gida ba, Kuma kinsa akira abokinshi Auwal yace sunje party dashi kuma sun barosu ahanya suntaho, amma gashi haryanzu bedawo ba. Umman Nabeel tace wama yasani koyadawo tunda bazuwa wjena yake ba, kullum yana tare da Babanshi daya dauki so duniya ya dora mashi, sede besan asalin gaskiyar ba. Da zanga Babanshi ma dana sa anfada mashi yasa aduba shi koyadawo. Lawisa tace inaso kibar wannan maganar zuwa gobe, kisa aduba maki koyana shigowa wajen Babanshi, idan ance beshigo ba seki sa afadama Alhajin. Ummin Nabeel tace shikenan, Allah yadawo dashi lafiya, amma wlh tun dazu gabana yake faduwa. Lawisa tace insha Allah babu komai, Allah de ya kaimu safiyar. ASALIN LABARIN KOWA YATAKA DOKAR ALLAH............. Kubiyini domin jin labarin. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part 5⏩ 10 Lawisa!Lawisa! Na'am ina, jinki fa kike kwala mani kira kamar tsohuwar data shekara 100. Dariya wadda takira Lawisar tayi tana fadin, amma kin cuceni, kina kallona yarinya meji da kuruciyarta kihadani da me shakara 100. Zama Lawisa tayi tana gyara daurin dan kwalinta tace haba Maimuna, masuji da kuruciyarsu de sunaji, ke kam ai kinzama saura,duka takai mata sukasa dariya tana fadin haryanzu banyi auren farko ba amma kike mani maganar tsufa. Lawisa tace to a auren meye baki sani ba? Maimuna tace zaki fara ko? Aide dadin abun nida ke duk sana'armu daya. Lawisa tace toyi hakuri kema kinsan wasa nake maki. Yanzu de kitashi mutafi tunda angama komai, wanda ze dauki abincin ma ya dauka harya kai mana shago mutafi kada mutane sufara zuwa ba muje. Maimuna tace muje, dama ai kece kike bata mana lokacin kin tsaya kina kwalliya kamar wadda ta aje wani. Lawisa tace ke kuwa wannan sana'a tamu ai seda kwalliya, kinsan fa mu na mutane ne musamman maza. Kema ai kina kwalliyar dande kina riga ni shiryawa ne. Haka suka kulle gidansu suka tafi shago. Maimuna kenan da kawarta Lawisa. Yan cikin garin Darazo ne dake jihar Bauchi, kuma kawaye ne, sede Lawisa ta girmi Maimuna da kadan, kuma Lawisa yar tsintuwa ce, wata rana wani mutum yadawo daga cikin gari da dare ya sameta zaune aksan wata bishiya tana kuka. A lokacin bazata wuce shekara 9 ba, tsayawa yayi yana tambayarta me yafaru take zaune ita kadai da dare haka? Dago kai tayi tana kuka tace mashi mamarta. Dukawa yayi yana cewa ina mamar taki take? Cikin kuka tace ta tafi. Ganin dare yana karayi yasa ya jata suka nufi gidanshi. Koda yaje yayima medakinshi bayanin abinda yake faruwa ce tace malan nifa ina tsoron temako a zamanin nan, kasani ko mamar ta ta zuwa tayi tadawo kai kuma zaka shigo da ita, idan kuma tadawo bata gantaba fa? Zama yayi yana fadin dan Allah kiyi hakuri, ke daga ganin yarinyar nan kinsan bawai unguwa suka fito da mamarta ba. Kibata abinci taci duk da bata da wayau sosai nasan zamu samu wani abu daga gareta. Bayan taci abinci suka sata gaba suna tambayarta, ya sunanki? Tace Lawisa, to ina mamarki? Ba itace kullum seta dukeni ba, kuma kullum seta zageni tana cewa wai banida Baba. Cike da mamaki suka kalleta. Mutumin yace to me mamarki takeyi? Yarinyar tace abinci take saidawa, shine naga wani yazo wajenta senaji yace mata ze aureta. Shine da safe tayita dukana tace sena tafi nabarta tunda ita kadai take wahala dani. To waya kawoki nan? Tace mamana ce tace inzo mutafi unguwa, shine muka hau mota mukazo nan, shine tace inzauna injirata, ni kuma naga bata dawo ba shine nabita, tun dazu nake nemanta banganta ba, shine nazauna acan da dare yayi. Salati suka sa jin abinda yarinyar tace. Mutumin yace kinsan unguwarku? Lawisa tace ai mu idan za'aje garinmu se an hau mota 2 Kuma akwai nisa. Girgiza kai mutumin yayi yace Asabe kinsan abinda na fahimta da labarin yarinyar nan? Duk yanda akayi ba cikin garin nan suke ba, kila de a kauyen garin nan suke, domin tace se an hau mota 2, kuma kinga idan aka shigo cikin garin nan unguwarmuce farko dole ita zata fara sauka, kinga zefi mata sauki ta ajeta tayi saurin juyawa. Asabe tace ni kuma ina ganin yarinyar kamar bada aure aka sameta ba. Jinjina kai yayi yace toyanzu ya kikeso ayi? Kallon yarinyar tayi yanda ta kwanta lamo ajikinta tace malan inde ka amince kawai mu riketa, idan mutane sunganta muce masu diyar dan uwanace muka daukota daga kauye. Kallonta yayi yana murmushi yace gaskiya naji dadin wannan shawara taki, Allah yayi maki albarka, kuma yabamu ikon riketa da amana. Hannu yarinyar yakamo yana fadin Lawisa tunda mamarki bata sonki daga yau ga mamarki nan. Kin taba ganin babanki? Girgiza kai tayi yace yauwa to nine Babanki, dama wajena zata kawoki shiyasa tabarki anan, saboda haka zaki rika kwana anan gidan, kuma zan saki makaranta ai kinaso ko? Dariya tayi tana daga kai. Yauwa to inaso idan safiya tayi duk wanda ya tambayeki kice daga kauye muka daukoki kinji? Daga kai tayi, yace yauwa tashi kiyo fitsari ki kwanta. Tashi Asabe tayi tana fadin mukam Allah yakawo mana diya daga sama, dama gidan yana mun shiru tunda Jamila tayi aure. Malan yace ai ga diya kinsamu daga sama dama Jamila ita kadai Allah yabamu. Tashi sukayi suka shiga ciki suna me cike da murna. Tun daga ranar rikon Lawisa yadawo wajensu, kuma yanda sukace haka suka fadama jama'ar unguwarsu daga kauye suka daukota. Haka suka sata makarantar boko da islamiya. Sosai suke kulawa da ita, sede Allah yasa Lawisa batajin magana, akwaita da tonon fada duk ta addabi yan unguwar. Da haka ne suka hadu da Maimuna. Wadda ita kadaice a wajen iyayenta, suna sonta sosai, kuma suma sunada rufin asiri dede gwargwado. Tunda suka hadu da Lawisa jininsu yahadu, duk da Lawisa ta bata yan watanni amma baka ganewa domin Maimuna tana da jikin girma. Haka suka taso da kawacensu, har suka gama primary suka shiga secondary. Dayake makarantar dasuke hade take da maza hakan yasa Lawisa tafara shige masu, kujerarsu daya da Maimuna kuma kusa da wasu maza suke. Wannan daliline yasa take jansu da fira, ko break aka fita seta cema Maimuna taje tasiyo masu abinci su zauna cikin aji suci tare da mazan, daya sunanshi Babawo, abokinshi kuma Sani. Haka zasu zauna a aji suci abinci sunayi suna yan tabe tabe. Tun maimuna bata kulasu har itama tafara biyema Sani sunayi, ko tashi akayi basa tafiya gida da wuri, kuma basa bin hanyar da sauran dalibai suke bi. Haka suka taso tun abun yana faruwa kadan kadan har ya girma. Lokacin dasuka shiga aji 3, sosai suke soyayya dasu Sani, Maimuna da Lawisa sun saba da abubuwan da yan mazan suke masu. Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya iyayensu basu fahimci abinda suke aikatawa ba. Alokacin da suka shiga aji biyar kuwa sun zama manyan yan mata, har wani waje suke zuwa inda kango ne na Baban Sani. Zuwa wannan lokacin babu abinda basu aikatawa na lalata, sede haryanzu basu yarda sun wuce gona da iri ba. Wata rana da safe Lawisa ta biyama Maimuna zasu tafi makaranta, lokacin iyayenta sun fito zasuje unguwa. Bayan sunyi sallama da ita suka fada mata kafin su taso daga makaranta ma zasu dawo ba dadewa zasuyi ba. Kudi mahaifin Maimuna ya dauko yabasu yace sutafi kada su makara. Bayan suntafi suma suka nufi tasha dan su hau mota. Lokacin da su Maimuna suka dawo gida haka tasamu kofar gidansu cike da mutane. Saurin karasawa tayi wajen kanin mahaifinta wanda yake ta kuka. Kamata yayi suka shiga ciki, suna zuwa tasamu mata dayawa aciki. A nan yafada mata iyayenta sunyi hadari kuma duk sun rasu. Bakaramin tashin hankali Maimuna ta shiga ba. Tasha kuka ita da Lawisa. Haka aka cigaba da zaman makoki. Bayan kwana bakwai, suka zauna domin asan wanda ze dauki Maimuna tunda ita kadaice awajen iyayenta, gashi mamanta yar Minna ce. Kanin mahaifinta shine yace ze dauketa tunda takusa gama karatunta data gama se ayi mata uare kawai. Da wannan shawarar Maimuna ta koma gidanshi da zama. Bayan wata guda aka hada komai da iyayenta suka bari aka saida domin araba gado. Kasancewar kanin mahaifinta su biyu ne kuma basuda iyaye yasa shida Maimuna ne suka samu gadon mahaifinta. Ita kuma aka hada mata dana mamanta. Duk da yan uwar mahaifiyarta sun so idan tagama karatu abasu ita amma sam kanin mahaifinta yace beyarda ba, idan tagama zata kawo masu ziyara kafin tayi aure, idan yaso seta cigaba da zumuncinta a gidan mijinta. Lokacin da suka shiga aji shida idonsu ya gama budewa ita da Lawisa, domin matar kanin mahaifin Maimuna irin matan nan ne marasa kula, sam ba ruwanta da damuwa da yanayin da Maimuna take. Wannan dalilin ne yasa suke abinda suke so, domin shima mijinta neman kudinshi kawai yasa gaba. Wata rana sun tashi daga makaranta Babawo yace Lawisa ina alkawarin da kikayi mani? Murmushi tayi tace to wai kai idan ma na amince maka ina kakeso muje muyi abinda mukeso inda baza'a ganmu ba? Sani yace kawai kuzo muje dakina tunda a zaure yake kuma mamana bata nan yau dan abinci ma tunda safe tamun tabani na aje acikin dakina. Biki taje kuma seda dare zata dawo. Babawo yace yauwa gama guri munsamu muje muna kara batama kanmu lokaci. Lawisa tace Maimuna muje. A sanyaye Maimuna ta kalleta tace nide tsoro nakeji. Kina ganin muna SS 2, aka taba kama wata tayi ciki aka koreta kuma kowa seda yaganta. Babawo yace haba Maimuna sekace baki waye ba, hannu yasa a aljihu yaciro wata takarda yace kinga wannan maganin hana daukar ciki ne, nima awajen Ummata nasanshi domin ta dade tana aike na chemist ina siyo mata. Ada bansan amfaninshi ba, amma wata rana naji tana fadama kwarta shine take sha dasun kwanta da Babanmu yana tafiya bandaki take daukarshi tasha, kuma gashinan haryanzu bata kara haihuwa ba nine autanta. Murmushi Lawisa tayi tace wato kai harma ka shirya ko? Yace emana, kinsan me chemist din ya sanni shiyasa jiya da Umma ta aikeni dama inada kudi nace yabani guda 4, na bata 2, nataho da 2, kuma duk daya na kwana 10 ne, kafin yakare zan kara sama mana wani. Da wannan dadin bakin sukaja Maimuna suka nufi dakin Sani. Tare da temakon shedan suka samu damar kawar masu da budurcinsu. Sun sha wahala sosai, hakan yasa Lawisa tace ma Maimuna tana tsoron kada taje gida mamansu ta ganeta, sutafi gidansu Maimuna tunda ita ba'a samata ido. Cikin sa'a basu sameta agidan ba, haka suka shiga suka dafa ruwan zafi suka gasa jikinsu sukayi wanka, seda Lawisa ta huta sannan takoma gida, tana zuwa tasa kuka, mamanta tace meyafaru ko yauma dukanku akayi? Lawisa tace wani mugun malami aka kawo mana, wai dan bamuyi shara ba shine yace idan antashi duka ajin kada mutafi seya hukunta mu. Mama haka yasamu tsallan kwado bakiji duk cinyoyina ciwo suke ba, bantaba yin tsallan kwado ba ashe haka yake da zafi. Dariya Maman tayi tace ai dama idan kana aji shidda ba ruwanka da kowa sede malamai, haka zakuyita hakuri kowama haka yayi, damma ba makarantar kwana kikeyi ba ai da sekinfi haka shan wahala. Ai kun kusa gamawa se hakuri. Tashi kije kicire kayan ga ruwan zafi can kiyi wanka inbaki robb kishafa zakiji sauki. Da wannan karyar Lawisa ta kauda kan mamanta dan kada tagane tafiyarta ta canza. Tun daga lokacin suka zama yan hannu, sosai suka kara dinkewa dasu Babawo, duk sanda suka aikata lalatarsu Babawo ne yake basu magani suna sha. Da haka suka gama makaranta. Kuma a wannan lokacin ne marikin Lawisa yarasu, sun sha kuka, haka suka cigaba da zama ita da Asabe. A yanzu basa haduwa dasu Babawo sosai, shiyasa sukace zasu koma islamiya ita da Maimuna, wannan damar ce tasa suka cigaba da aikata abinda suke so da sunan zuwa islamiya. Tafiyarsu Babawo makarantar gaba da secondary ce tasa suka rabu dasu Maimuna. Kuma a wannan lokacin ne kanin mahaifinta yace ta fiddo miji yayi mata aure. Lokacin data fadama Lawisa ita ce ta zigeta akan kada ta yarda, idan ma ze matsa mata to yabata gadonta su shiga gari sukama sana'a. Sam Maimuna bata yarda da shawarar Lawisa ba, haka suka rabu bata amince ba. Tundaga ranar kullum Lawisa seta yimata maganar gadonta. Ita ko Maimuna har lokacin bata amince ba. Ba komai bane yasa Lawisa takeso subar garinsu ba se dan tunda malan yarasu rayuwa tafara yimasu wuya shiyasa take son barin gidan. Shikuwa kanin mahaifin Maimuna ganin shiru bata fiddo miji ba yasa yace ma wani abokinshi yazo suhada yaransu aure, bayaso ya mutu beyima diyar Yayanshi aure ba, dan besan wane irin hali zata shiga ba, sam bayason takoma wajen dangin Mamanta. Domin shi beyarda da rikon su ba. Jin haka yasa abokinshi yace ya amince, yana yima danshi magana shima yace ya amince. Lokacin daya fadama Maimuna kuka tasa tace ita wallahi bataso tayi aure yanzu. Haka yayi ta faman lallashinta amma sam bata amince ba. Lokacin data fadama Lawisa tabata shawara akan tace ta amince amma da sharadin za'a fara bata gadonta kafin a daura auren. Maimuna tace to idan kuma yabani kuma akayi auren shikenan kin kwareni? Lawisa tace kede kije kifadi haka, yana damka maki kudinki zamubar masu garin. Maimuna tace gaskiya bazan iya barin mahaifata ba. Lawisa tace to naji, ammade kinsan Bauchi babban gari ne ko? Bakiso mushiga birni muga rayuwa? Dan haka semu shiga can cikin gari muyi rayuwarmu me dadi. Shiru Maimuna tayi batace komai ba. Dafata Lawisa tayi tace kiyarda dani, idan muna nan babu abinda zamu sani na rayuwa. Yanzu tunda kike kintaba zuwa cikin garin bauchi kika ga duniya? Girgiza mata kai tayi. Lawisa tace to idan muka shiga garin acan zamuga manyan yan gayu, kuma muyi abinda mukeso. Amma munzauna nan komai se abinda akace mana zamuyi, yakamata muma mu zauna da 'yancinmu. Haka Lawisa tarika yima Maimuna kalamai har seda ta amince. Haka taje tasamu Kawunta, bayan ta gaishe shi tace Kawu dama wata magana nazo da ita. Kallonta yayi yace to Maimuna ina jinki meke tafe da ke? Dukar da kai kasa tayi tana wasa da hannunta tace dama inaso kafin adaura mani aure afara bani kudin gadona a hannuna. Kura mata ido yayi alamar tuhuma. Kara kasa tayi da kanta. Murmushi yayi yace Maimuna kin tabbata wannan shawarar daga zuciyarki tafito? Kai tadaga mashi. Jinjina kai yayi yace shikenan, bazan hanaki gadonki ba. Domin kin kai minzalin hankali zaki iya zama da kanki, asalima aure zakiyi. Amma meze hana kibari idan yan uwan mamanki sukazo wajen biki inbaki kudin agabansu dan suzama sheda? Saurin dago kai tayi tace nide Kawu yanzu nake bukatarsu. Kuma ai zamu iya yin rubutu shima ai sheda ne. Murmushi Kawu yayi yace Maimuna niba zanyi wani rubutu ba, idan kuma kinaso muyi to zan kira mutane 3 muyi agabansu, domin komai yana bukatar sheda. Maimuna tace to ka kirasu se ayi. Haka Kawu yakira abokinshi, da makwafcinshi tare da wani a bokin kasuwancinshi. Agabansu yadauko takardar da akayi rabon gado da ita, bayan yagama karanta masu abinda kowa yasamu yabasu suka kara dubawa. Wata jaka yadauko yace wadannan sune duk kanin kudaden Maimuna na gado data samu, domin komai na gadon kudi aka maidashi sannan aka raba. Allah yasani tunda aka bani kudinta nazo na boyesu. Kome dakina bata taba sanin inda na ajesu ba, kuma bantaba daukar ko naira nace zan juyata ba. Gashi nan malan ku kirga idan sun cika amika mata hakkinta. Bayan sungama kirgawa kudi haka suke. A bayan takardar da aka raba gadon Kawu ya rubuta sunanshi, da kwanan wata, kuma ya rubuta yamika ma Maimuna hakkinta na gado. Bayan yagama itama ta rubuta cewar ta amsa, haka yan sheda suma suka rubuta cewar sun tabbatar. Bayan kowa yasa hannu Kawu yace ze aje wannan takarda idan dangin Mamanta sunzo yabasu. Haka aka fara hidimar biki, Maimuna kuwa tunda ta amshi kudin ta kaima Lawisa domin ta aje masu. Ana saura sati daya biki cikin dare Lawisa ta biyoma Maimuna aranar suka gudu daga gida. Washe gari haka matar Kawu ta duba ko ina bataga Maimuna ba, Kawu tafada mawa, nan suka fara nemanta. Gidansu Lawisa sukaje, sede suna zuwa Asabe tace itama yanzu take niyar zuwa ta tambaya ko Lawisa taje can. Dakin Lawisa aka duba babu kayanta. Murmushi Kawu yayi yace tabbas dama zuciyata tafara zargin akwai wani abu dayake shirin faruwa. Babu ko tambaya yaran nan guduwa sukayi bayan sunyi sa'ar amsar kudin gadon Maimuna. Dafe lirji Asabe tayi tana salati. Kuka tasaka tana fadin dama ai tsintacciyar mage bata mage, kuma barewa bazatayi gudu danta yayi rarrafe ba. Hakika Lawisa kinyi mana butulci. Amma bakomai, Allah yagani mun rikeki tsakinmu dashi. Kawu ya kalleta yace Asabe dama Lawisa ba diyar dan uwanki bace? Girkiza kai tayi tana share hawayenta......... Labarin abinda yafaru tabasu. Sosai sukayi mamaki. Kawu yace lallai kunyi kokari, kuma Allah shine ze baku ladar temakon da kukayi. Wannan hali na butulci da yayi yawa a wannan zamini shine yake jama sauran masu gaskiya, domin a yanzu kowa yana tsoron temako saboda ba kowa ne na Allah ba. Lallai Maimuna tayi rashin wayau data biyema shawarar Lawisa. Bakomai, ki kwantar da hankalinki, duniyar da suka shiga suna tunanin tafiye masu zama agabanmu zasuje su iske dede dasu. Kuma insha Allah seta koya masu hankali. Asabe tace, nima bazan cigaba da zama garin nan ba, gara inkoma wajen yan uwana zefi mani. Dama nikadai ce nake anan, shima aure ne yakawo ni, tunda wanda nazo danshi yatafi ai gara inkoma kauyenmu. Kawu yace bazan hanaki ba, domin kazauna kusa da yan uwanka yafi, kome ze sameka kana gabansu, kuma sunfi kowa sanin muhimmancinka. Haka sukayi mata sallama suka koma gida. Da yamma dangin maman Maimuna suka iso. A nan suka iske tashin hankali, sunyi kuka sosai kuma sun godema Kawu abisa irin rikon da yayima Maimuna. Kwanansu daya suka juya, suma abinda sukace bazasu nemeta ba, idan duniya ta koya mata hankali zata nemesu da kanta. Haka Kawu yasamu abokinshi wanda danshi ze auri Maimuna yabashi hakuri. Tunda su Lawisa sukatafi haka suka shiga cikin garin Bauchi, suna zuwa suka sami wani mutum sukace dan Allah suna son kama gidan haya ne. Mutumin yace to gaskiya ni bansan wanda yake bada haya ba, amma akwai wanda nasani shine yake nema ma masu neman hayar gida. Haka ya kaisu wajen wani mutumi, suna zuwa sukaci sa'a akwai wani karamin gida me daki biyu da bandaki se kitchen da wata mata ta tashi. Kallonsu yayi yace dubu 50 zaku bada. Lawisa tace to mungode, amma dan Allah munaso muje kasuwa musiyo kayan amfani. Yace ai bakomai, akwai wani yaro zan hadaku dashi ya kaiku kusiyo abinda kuke so. Haka suka bashi kudin yabasu mukullin gida. Bayan sun shiga sun aje kayansu yaron yazo suka tafi kasuwa. Duk wasu kayan amfani seda suka siyo, haka suka gyara gidansu. Bayan kwana 3 da zuwansu Lawisa tace Maimuna zama hakanan fa baze mana ba, dole mukama sana'ar dazatasa muyi saurin yin suna awajen maza. Maimuna tace wace irin sana'a kike ganin zamuyi to? Lawisa tace meze hana muje kasuwa mudauki hayar shago murika dafa abinci muna akaiwa can? Maimuna tace kumafa kin kawo shawara me kyau. Koba komai zamurika fita kullum muna ganin gari. Lawisa tace kinsan yanda masu saida abinci suke, yawancinsu kazamai ne, inaso namu salon yazamo daban, mushiga kasuwa musiyo kaya masu kyau, da kayan kwalliya. Kinsan ance da kudi ake neman kudi. Maimuna kina da kyau duk wanda ya kalleki dole yasoki, kinga ai zamuyi saurin samun shiga. Dariya sukasa, Maimuna tace ammafa girki da wahala, bare kuma a icce. Lawisa tace ai zamu fara ne, idan komai yayi dede kinga semu dauki masu aiki, su dafa mana su kai mana shago, aikin mu muje murika zubawa, me wanke wanke tanayi. Maimuna tace haka ma yayi, tashi mutafi. Cikin sa'a suka samu shago a kasuwa, haka suka fara abinci, kulolin da suke zuba abincin kansu masu kyau ne, hatta da plate din zuba abinci bana roba ba ne, se robobin ruwa da suke zuba zobo ko kunun aya. Duk abinda zasu zuba basa barinshi abude, komai nasu cikin tsari yake. Haka suka fara zuwa saida abinci akasuwa, idan kagansu bazaka taba cewa masu saida abinci bane. Domin bakaramin ado sukeyi ba. Dama Maimuna akwai kyau, gata fara, duk wanda yagansu se sun burgeshi. Aranar dasuka fara zuwa kasuwa aranar suka fara samun customers. Gashi sun iya abinci, kuma suna canza kalar abincin dasuke saidawa, harsu dambun shinkafa sunayi. Kafin kace me, duk wani namiji dayake sayen abinci awani waje ya koma kansu, komai nasu atsari sukeyinshi. Cikin lokaci kankani arziki yafara zauna masu. Kuma da haka,ne, suka cigaba da sana'arsu ta neman maza. Dan wani lokacin mazan har kwana sukeyi. Dama unguwar dasuke bawata me taro bace, kuma gidansu abaya yake, babu taron mutane awajen. Tun daga lokacin su Lawisa suka dage da saida abinci, har suka samu masu aikin da suke tayasu kuma su kaimasu kasuwa. Wannan shine takaitaccen labarin su. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part 10 ⏩ 15 Haka su Lawisa suka isa kasuwa, babu bata lokaci kamar kullum haka mutane suka siye abincinsu har ana neman kari. Bayan me wanke wanke tagama ta hada kayan tayi masu gaba da kayan su kuma suka shiga cikin kasuwa domin siyayya. Duk abinda zasu siya sun siya, haka me dako ya dauko masu zuwa bakin titi. Duk inda suka wuce se sun gaisa da mazan wajen domin sun sansu sosai. Dede zasu fita daga kasuwar Maimuna taji an bige mata ledar hannunta. Kayan shafar da tasiyo duk suka zube, saurin juyowa tayi caraf idanuwanta suka sauka akan wani babban mutum kyakkayawa dashi, gashi dogo fari, sede ga duk kan alamu yadan manyanta. Saurin dukawa yayi yana fadin dan Allah kiyi hakuri ina amsa waya ban kula dake ba, Maimuna kuwa batama san yanayi ba, ta shagala wajen kallonshi,dariya Lawisa tayi ta tabo Maimuna tana mata nuni alamar ta tayashi kwasar kayan. Saurin dukawa tayi tana fadin haba dan Allah kabarshi zan kwashe ai bakomai. Bayan sun gama kwashewa yakara bata hakuri tace bakomai, Lawisa takama hannunta tana fadin mungode, muje kada yaron yayita jiranmu. Haka suka wuceshi, shikuma yabi Maimuna da kallo. Suna tsaye bakin titi Maimuna tana fadin haba Lawisa, kinsan yanda yatafi da imanina kuwa, shine zaki wani jawoni ko gama gaisawa bamuyi ba, kika sani ma koyace inbashi number ta. Lawisa zatayi magana sukaji ance haryanzu baku samu abin hawa bane? Saurin juyowa sukayi, Lawisa tana fadin wallahi kuwa. Murmushi yayi yace to muje in aje ku mana. Haka suka saka kayansu Lawisa tashiga baya Maimuna tashiga gaba, haka suka rika nuna mashi hanya har suka isa. Murmushi yayi yace nan ne gidanku kenan? Lawisa tace wallahi kuwa kaga dan gidanmu nan, shima haya mukeyi. Jinjina kai yayi yace amma naga gidan akulle ku kadai ne aciki? Lawisa tace mukadai ne aciki yanzu ma daga shagon mu da yake kasuwa muke kasan muna saida abinci ne. Kallonsu yayi cike da tausayi yace Allah sarki. Gashi yanzu ina sauri, amma idan kun bani dama zanso indawo domin inji kadan daga cikin labarinku. Lawisa tace lah! Ai bakomai, amma idan zakazo sede kazo da dare koda yamma sosai, domin da rana bama nan. Yace toshikenan, nagode, ni sunana Alh, Lamido Saraki, ku kuma meye sunanku? Ni sunana Lawisa, ita kuma Maimuna, murmushi yayi yace Maimuna sarkin yin shiru ba, da alama batada hayaniya. Murmushi tayi tayi kasa da kanta batace komai ba, bude kofar Lawisa tayi tana fadin to sekazo mungode. Maimuna ta bude kofar tana fadin mungode fa. Murmushi yayi yace bakomai, amma samun number dinki kada inzo inrasa yanda zanyi. Bayan tasa mashi sukayi mashi sallama suka shige gida. Suna shiga suka saka dariya tare da rungume juna. Lawisa tace se kawata, ai dama nafada maki wata rana semun shana, ke kinga yanda wannan Alhajin yamace a kallonki? Maimuna tace wallahi ya hadu, ai da naji haushi da kika jawoni. Lawisa tace ai nasan seya biyomu shiyasa na jawoki. Zama Maimuna tayi tabuga tagumi tana fadin Allah de yasa beda mata. Dariya Lawisa tayi tana fadin haba kawata. Meye naki na saurin karaya? Ai koyana da ita wallahi se tabar gidanshi, mune fa? Haba idan har na barki kika zauna da kishiya ashe iskancina be kai ba. Haba munga jiya, munga yau, gobe ma insha Allah semun ganta. Kede kibari yashigo hannu. Maimuna tace amma de ba aure zamuyi ba ko? Zama Lawisa tayi tana fadin bangane ba? Kema kinsan daga ganin wannan mutumin beyi kama da yan duniya ba, da ace dan hannu ne, yana kawomu seya shigo. Dan haka inaso ki aureshi kawai. Maimuna tace ni bazan iya aure in kyaleki ba. Lawisa tace aiko dole kiyi aure, idan kikayi aure nima zan ji dadi, ni kobanyi aure ba zan iya zama haka, domin kullum sabuwar kyankyasa akeyi ta yara maza. Kinga idan har kikayi aure dole a sama mani babban gida inzauna aciki, domin bazan iya biyoki muzauna tare ba, domin bazan iya kawo maza gidan matar aure ba. Ni kuma nafi karfin inbi namiji inda yake, sede shi yazo gidana yagama yatafi yabarni. Allah de yasa yace yana sona. Lawisa tace dole ma ze fada, kede kibashi daga nan zuwa kwana 3. Ina me tabbatar maki baze wuce gobe bezo nan ba. Dariya suka sa Maimuna tana fadin Allah yasa. Alh, Lamido Saraki. Haifaffen garin bauchi ne, shi kadai iyayenshi suka haifa, bayan yagama karatunshi a jami'ar garin bauchi iyayenshi suka rasu, kasancewar beda wasu yan uwa yasa yacinye gadon iyayenshi. Haka yafada harkar kasuwanci, cikin lokaci kankani yazama me arziki, ya gina katon gidanshi a unguwar Tambari sede ba cikin estate din yake ba, babban fili yasamu yayi gininshi me kyau yana da gidajen mai guda 3, sannan yana da mayan super market guda 2, haka kuma yana siyen manyan motoci yana badasu ana mashi haya dasu. Manyan DAF dinshi 2, suna legos ana aiki dasu, harkar kasuwanci babu wadda bayayi, yana da manyan store kayan abinci ne kawai aciki. Alh, Lamido ya dade beyi aure ba. Babu abinda yake tsoro se halin matan zamani. Domin yaso ace yayi aure tun kafin yayi arziki haka, amma ayanzu yasan duk wadda zata aureshi to saboda dukiyarshi ne. Shi mutum ne meson temako, duk juma'a seya kai ziyara gidan marayu da asibitoci. Mutane da yawa abokan kasuwancinshi suna mashi tallar 'ya'yansu, sede sam yaki amincewa da tayinsu, domin yasan suma saboda kudinshi ne suke so su hada zuri'a dashi. Mace ta farko daya aura diyar wani me kudi ce, ganin mahaifinta yana da kudi yasa yayi tunanin kudinshi bazasu tsone mata ido ba har taso cutar dashi. Aurensu ko shekara beyi ba yago tana mashi sata. Kuma ba kana nan kudi take dauka ba, lokacin daya kamata rana ta karshe, aranar ne ya saketa, dama bata da ciki. Ya dauki tsawon shekara 3 bayan rabuwarsu bekara kula kowa ba. Wata rana yadawo daga unguwa yaga wata yarinya budurwa tana bara. Bayan ya tsaya yabata sadaka seyaji yarinyar ta kwanta mashi, gatade budurwa amma kuma tana bara, haka yanemi gidansu, seya gano talakawa ne sosai, nan yasa aka gyara masu gidansu ginin bulo, kuma yabama mahifinta jari, shida mamanta. Bayan wata guda aka daura aurensu, babban dalilin da yasa ya aureta saboda talaucinsu, domin ya auri yar gidan masu kudi beji da dadi ba, shiyasa yace bara ya auri talaka yasan tasan wahalar rayuwa bazata taba bari tayi wasa da damar data samu yanzu ba. Kamar gaske suke zaune da ita lafiya, bayan shekara 1 da aurensu ta fara canza hali, babu abinda bata satar mashi, tun daga kayan abinci, kudi har suturarshi dauka takeyi, idan yau ya cika store din gidanshi da abinci bayan kwana 2 idan yaduba seyaga an kwashe rabi. Haka yarika binta har ranar da yakamata kuru kuru, yafita kasuwa se yayi mantuwa yadawo, yana zuwa ya iske ana loda kayan abinci za'a tafi dasu. A nan hankalinta yatashi tafara kuka tana rokonshi. Babu bata lokaci ya sallameta ita da megadinshi domin hadashi ake hada baki. Godiyar da yayima Allah ma bata da ciki. Haka yashiga daki kamar karamin yaro yarika kuka, babban abinda yake damunshi shekaraunshi sekara tafiya suke amma haryanzu beda da. A ranar yasha kuka. Kuma tun daga ranar aure yafitar mashi arai, haka ya maida hankalinshi kan kasuwancinshi, ahaka ya shekara 2 babu mata. Gidanshi dagashi sewani mutum dayake zaune a BQ din gidanshi, kuma shine yake kula mashi da gida. Sunanshi Babaye, sun kai shakara 2 dashi, shima beda iyali dan asalin wani kauye ne dayake Darazo.Wata rana Alh, Lamido yadawo daga unguwa da dare dede zeshigo cikin garin bauchi ya hadu dashi abakin titi kwance kamar matace. Harya wuceshi yadawo, domin akwaishi da temako. Babu bata lokaci yadaukeshi yasashi a mota suka shigo gari, wani karamin asibiti ya kaishi, bayan likita ya dubashi yace yunwace da tsananin wahala sukasa shi suma, amma zuwa da safe ze farfado. Haka yatafi yabarshi wajen likitan bayan yasiyo mashi tea da madara da biredi yace idan yatashi abashi kafin yazo da safe. Kwananshi 3 ya warware, bayan ansallameshi suka nufi gidan Alh, dashi. Bayan yayi wanka yabashi wasu kaya daga cikin nashi yasa. A nan ne yake fada mashi labarinshi, da kuma yanda yafito daga kauyensu yayita tafiya har Allah yate makeshi wasu masu motar kaya suka daukoshi suka kawoshi Darazo, daga can ne yarika tafiya har yakusa shigowa bauchi yafadi ya suma. Kuma yasheda mashi beda iyali tunda barayi suka kashe mashi matar be kara aure ba, hakan ne yasa da barayin suka matsa mashi yabaro kauyensu. Sosai Alh, ya tausaya mashi,kallonshi yayi yace Babaye idan zaka iya zama dani babu damuwa, sede banida mata............Labarinshi shima yabashi, sosai ya tausaya mashi, Babaye yace bakomai nizan zauna da kai bisa gaskiya da amana. Alh, yace shikenan akwai wasu dakuna acan bayan gida, zaka iya sauka acan, akwai komai na bukata, ka iya girki? Murmushi yayi yace sosai ma, Alh, yace to akwai kitchen zan hada maka kayan girki, ina ganin zefi maka sauki karika girki da kace zaka siya. Dan ni a waje nakecin abinci, idan kuma kafison na siyen badamuwa zan rika baka kudin abincin. Babaye yace a'a nafiso nayi girkina. Alh, yace to ai shikenan, kayan sawa kuma suma zan kawo maka. Kafin kasamu wata kaga semusha biki ko? Dariya yayi yace ai Alh, tunda narasa iyalina aure yafitar mani arai, nafiso na zauna haka. Alhaji yace to Allah ya rufa mana asiri,zaka rika kular mani da komai na gidan nan. Dama ni banda megadi tunda na kamashi yahada kai da matata suna satar mani avinci shima na koreshi. Dan haka zaka rika kula da komai, ina fatan zaka rike amana? Babaye yace insha Allah bazaka sameni da cin amana ba. Alh, yace bakomai muje inkaika masaukinka. Godiya Babaye yayi mashi suka fita. Tun daga wannan rana Alh, yasamu abokin zama acikin gidanshi, sosai yakejin dadin Babaye. Yana kula da gidan sosai, har cikin gidan yake shiga yashare ya goge komai, dakin Alh, ne kawai baya shiga, idan kashigo gidan zaka dauka akwai mace. Idan Alh, yadawo da wuri haka zasu zauna suyita fira kafin kowa yatafi makwancinsa. Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya cike da aminci, babu abinda Alh, baya siyama Babaye, kuma duk wata yana bashi albashin dubu 50, idan kasan Babaye abaya idan kaganshi yanzu bazaka iya ganeshi ba, da haka suka shekara 2 atare. Wannan shine takaitaccen labarin Alh, Lamido Saraki. Kamar yanda yace zezo domin yaji labarinsu haka tafaru, bayan yazo yakira Maimuna tafito tayi mashi jagora zuwa ciki. Lafiyayyen girki suka shirya mashi da zobo me dadi. Bayan ya shari girki ya kallesu yace to nazo acika mani alkawarina. Maimuna zatayi magana Lawisa tayi saurin fadin to kamar yanda kasan sunanmu, to mudin yan gida daya ne, wannan yayatace, daga ita se ni. Lokacin muna secondary iyayenmu suka rasu. Yayata Maimuna tayi aure da wani maci amana, ashe dama saboda gadonta yakeson aurenta. Gashi bamuda wasu yan uwa sosai, ni kadai nake zaune agidanmu lokacin da tayi aure, seda yayi mata wayau ya cinye komai, sannan yayi mata dukan tsiya ya saketa saki 3, Allah yaso batada ciki. Haka muka zauna cikin kunci, ganin rayuwar garin Darazo baya mana dadi yasa muka saida gidanmu na gado muka dawo nan dazama muka kama haya da kudin hannun mu, sauran kuma muka fara sana'ar saida abinci domin munfiso mu dogara da kanmu. Sosai labarinsu yabama Alh, tausayi har seda yayi kwalla, kallon Maimuna yayi cike da tausayi yace kiyi hakuri kinji, Allah ze saka maki, lallai kinga rayuwa kamar yanda nima nagani........... Labarin rayuwarshi yabasu, sosai suka tausaya mashi. Lawisa tace gaskiya Yaya kaima kaga rayuwa, bansan meyasa yanzu duniya ta baci haka ba. Kayi hakuri Allah ze saka maka. Murmushi yayi yace yanzu kam yasaka mani, domin inaji ajikina haduwata daku alkhairi ne, inafatan zaku daukeni dan uwa? Lawisa tace zamufi kowa farin ciki kasancewar munsamu Yaya daga sama. Allah yabamu ikon rike amana. Sun dade suna fira kafin ya aje masu kudi masu yawa yayi masu sallama yatafi. Bayan yatafi Maimuna tace lallai kanwata kin iya sharota. Wai ya akayi kika iya shirya wannan labarin haka? Dariya Lawisa tayi tace aike yarinyace shiyasa baki fahimci komai ba. Maimuna tace kemafa da watanni kawai kika girmeni. Lawisa tace nade girmeki ko? To bara kiji, jiya banyi bacci ba seda na shirya duk abinda zan fada mashi. Kinga na farko de kinsan harkar da mukeyi, idan har mukace mashi bakitaba aure ba dole ze gane, kuma daga ranar ze tsaneki. Amma yanzu yasan asalin halinki kinga baze zargeki da komai ba, idan kuma yasan mudin yan gida daya ne, kinga zefi daukata da daraja, dalilin da yasa nace mashi ke yayata ce kuma saboda nace kinyi aure. Dan haka nasan abinda ze biyo baya dole yace yana sonki, domin naga hakan a idonshi. Maimuna mun riga da munsan labarinshi da irin yanda matanshi sukayi mashi. Dole zaki koyi zama dashi medadi. Zakicire son kudinshi aranki, shida kanshi zerika maki mahau kaciyar kyauta, zaki tsare mashi komai na gidanshi, da kular mashi da harkar kasuwancinshi. Nasan a yanzu duk macen daze aura seya gwadata, koda ze rika aje kudi afili kirika adana mashi idan yazo kibashi, kada kibari kirika tambayarshi komai. Ko kyauta yabaki kada ki amsa da wuri, iname tabbatar maki sekinga abun arzikin dazaki samu, kuma ni bazan taba yarda yace indawo gidanshi da zama ba. Nasan baze rasa gidaje ba, ze iya bani daya izauna. Amma kafin kishiga gidanshi dole zamu cire mashi son duk wata diya mace, domin yanda yakeda kudin nan dole mata surika rubibi akanshi. Kibar mani komai a hannuna, ni nasan yanda zanyi. Sede ina fatan bazaki juya mani baya ba? Hannunta Maimuna tariko tace haba Lawisa, tun muna yara muke tare, har abada bazan taba juya maki baya ba, bazan taba aikata komai ba seda shawararki, kinzamar mani yaya, kuma uwa. Kima dena tunanin haka zata faru. Rungume juna sukayi suna dariya. Lawisa tace, ina fatan duk lokacin da Allah ze hadani da mamata ace lokacin nayi kudi sosai. Badan komai ba, sedan taga abinda tayarda yanda yazama. Maimuna tace wai dama Umma Asabe ba yar uwarki bace. Dariya Lawisa tayi tace kiyi hakuri duk tsawon taranmu bantaba baki labarina ba. Nidin yar tsuntuwa ce, amma inada kananan shekaru alokacin bazan wuce shekara 9 ba, sede ina da wayau, bazan taba manta fuskar mama na ba, nasha wahala a wajenta, sede naji Umma Asabe tace tana tunanin bada aure aka sameni ba. Sana'ar mamana saida abinci, shiyasa kikaji nakawo shawara akan murika saida abinci. Bansan waye Babana ba, kuma bana fatan insani, ayanzu wanna rayuwar tafiye mani komai dadi. Jinjina kai Maimuna tayi tace lallai kinada zurfin ciki. Allah ya kyauta, kuma insha Allah babu wanda zeji wannan labarin. Lawisa tace shiyasa kikaga naki yarda indauki ciki, domin bazanso inyima dan dana haifa irin abinda akamun ba. Koda ace nasamu ciki kafin na haifeshi zan zubar dashi, bazan taba bari in haihu batare da aure ba. Haka suka cigaba da labarinsu har sukayi barci. Tun daga wannan rana Alh, ya hanasu zuwa kasuwa saida abinci, duk wani abu na bukatarsu yana masu, soyayyar Maimuna tayi nisa a zuciyarshi, babban abinda yake burgeshi da ita duk yanda yayi mata kyautar kudi bata amsa, sede yakira Lawisa yabata. Wannan dalilin ne yasa ya yanke shawarar ze aureta. Bayan yafadama Babaye shima yayi murna, dajin zeyi aure, haka yaje yasamu Lawisa da maimuna yafada masu yana son auren Maimuna, amma zasu shirya domin suje can garinsu ya gaishe da yan uwansu kuma yanemi auren ta acan. Jin haka bakaramin data masu hankali yayi ba. Lawisa tace to ai hakan ma yana da kyau, amma kabamu nan da sati 1, semu shirya mutafi. Da haka yayi masu sallama yatafi. Cike da tashin hankali Maimuna tace yanzu meye dabara? Murmushi Lawisa tayi tace dole mufara zuwa wajen boka, domin aurenku dashi baze yuwu ayishi anan ba,domin Alh, yanason yaga yan uwanki. Amma idan mukaje wajen boka zamu sashi ya kawar mashi da tunanin zuwa Darazo, kuma yasa mashi bin umarninki. Da haka zamu samu ya aureki, sauran kuma sekiyi yanda nace maki. Rungumeta Maimuna tayi tana dariya tana fadin shiyasa nake kara sonki, kina son cigaba na. Yanzu ina zamu samu boka? Lawisa tace ai boka baya wahala, kede kibari zuwa gobe, akwai wata mata inda muke saida abinci kinsan muna mutunci da ita, to naga alamar yar bin malamai ce zanje gurinta seta rakamu. Da wannan shawarar suka aminta, suna fatan zuwan gobe domin suje wajen matar. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part 15 ⏩ 20 Kamar yanda Lawisa tace haka ne yafaru, wajen matar sukaje tayi mata bayani, bayan tagama matar me suna Gaje tayi murmushi tace lallai Lawisa kin kawo kukanki inda za'a share maki hawayenki. Kin ganni nan, ba dan narike boka nakan tudu ba dayanzu bana wannan sana'ar ta saida kayan mata, kina ganin de yanda mata suke tururuwar zuwa wajena domin su sayi kayana. Duk da bani kadai bace nake siyarwa anan amma dole duk wadda tazo gurina zata siya. Nafi karfin shekara 5 a wajen nan, nasayi gidaje da yawa da wannan sana'ar tawa, kuma ba kowane ya tsaya mani ba se boka nakan tudu. Hakika kin burgeni yanda kika zo mani da wannan maganar. Kuma zan temakeki, kizo gobe da safe wajen karfe 9 semutafi ina tabbatar maki da bukatarku zata biya, kuma idan har kuka rikeshi to baku ba sauran bacin rai. Sede yanada doka, inafatan duk abinda yanema awajen wadda zema aiki bazata hanashi ba? Lawisa tace haba ai duk abinda yakeso zamuyi mashi. Gaje tace toshikenan Allah ya kaimu goben. Washe gari haka su Lawisa da Gaje suka nufi wani kauye mesuna Bununu, can cikin wani daji saman wani dutse anan bokan yake dazama. Zaune suke acikin bukkarshi. Tun kafin Gaje tayi mashi bayani yace yasan abinda yake tafe dasu. Kallon Maimuna yayi yace kinaso a hana Lamido Saraki zuwa garinku ko? Surin daga mashi kai tayi, dariya yayi yace kuma kinaso acire mashi son kowace mace aranshi se ke kadai ko? Nan ma daga mashi kai tayi. Wata irin dariya yayi yasaka hannunshi cikin wata kwarya sega hoton Saraki yafito, nuna masu yayi yana fadin koba shi bane wannan? Lawisa tace shine. Dago kai yayi yace tabbas aikinki me sauki ne. Sede ayanzu zamuyi maki daya, amma na biyun baze yuwu ba harsekin aureshi, akwai abinda nakeso insaki. Wani garin magani ya dauko yana fadin ki tabbatar kinyi mashi abinci dashi kuma yaci ayau din nan, idan yawuce yau maganinki baze yi ba. Kuma lomar farko kece zaki bashi ita, duk yanda bayaso kisan yanda zakiyi kibashi so daya, idan ba haka ba, maganin bazeyi ba. Se sharadi na biyu zaku bamu waje domin zanyi rubutu a babban alkalamina in batashi. Murmushi Gaje tayi domin ita ta fahimci abinda yake nufi. Rada tayima Maimuna da sauri ta kalleshi. Gaba daya kyamarshi ce takamata, yanzu wannan kazamin zata bama kanta? Dariya yayi yace ba'a mani musu a cikin aikina, idan bakishirya ba, zaku iya tafiya. Lawisa tace habade, wallahi tashirya, tashi sukayi ita da Gaje tana fadin afito lafiya muna jira daga waje. Maimuna kuwa idanuwanta ne suka cika da kwalla, amma data tuno aikin daza'ayi mata kuma setayi saurin goge idonta. Haka boka ya shure awa daya shida Maimuna suna aikata masha'a, seda ya moreta san ranshi sannan ya kyaleta. Bayan ta maida kayanta tafito tana sinnar da kai, Gaje se dariya take mata kasa kasa. Dariya boka yayi yace aikinki zetafi yanda kike sonshi, nagama nawa saura naki, kada kimanta kada yawuce yau, kuma ki tabbatar kinbashi abakinshi. Godiya sukayi mashi tare da aje mashi kudi dubu 50 suka tafi. Bayan sun koma gida Saraki yakira Maimuna yana fadin haba Gimbiyata ina kikaje yau haka? Nakira wayarki yafi a kirga amma bata shiga, hankalina duk yatashi, haka nazo gidanku nasameshi a kulle. Murmushi tayi tace ran Saraki ya dade, Allah ya huci zuciyar abin sona, wallahi munje gaishe da wani kawun mu a Bununu shiyasa baka jini ba, kuma nakiraka infada maka bansameka ba. Ajiyar zuciya yayi yace har naji dadi, amma kada asake mani haka. Maimuna tace angama Sarakina. Yanzu de inaso kazo kaci abinci da rana, na shirya maka abinda kake so. Murmushi yayi yace kai amma nagode, amma meze hana kibari seda dare? Maimuna tace gaskiya banyarda ba, haka nan idan dare yayi kacemun kagaji, nide da rana nakeso idan kuma bazaka zo ba inji? Dariya yayi yana mamakin yanda Maimuna ta sake dashi yau, Maimuna tace bakace komai ba? Saraki yace, to Gimbiya duk abinda kikace ai shiza'ayi. Allah ya kaimu anjiman zanzo, murmushi tayi tana fadin yauwa abin sona, Allah yakawo ka lafiya. Tana kashe wayar Lawisa tace iye, ashede yayar tawa ta iya soyayya? Maimuna tace yanda nakeson Saraki ai dole na nuna mashi soyayya. Lawisa tace ammafa wannan sunan yayi. Maimuna tace shiyasa zanrika kiranshi dashi, amma arika kiranshi da wani Alhaji sekace tsoho. Dariya suka sa Lawisa tace gaskiya kam, tashi muje mudora mashi abincin kada yazo bamu gama ba. Ammafa duk yanda zece kici kice bakicin abun, kindafa wani abu kinci. Zaune suke afalo an shirya mashi kayan abinci, Maimuna taci kwalliya tayi kyau sosai, Saraki se kallonta yakeyi yana murmushi, shide Allah yasa mashi sonta, tunda yake betaba jin son wata mace kamar nata ba. Bayan sun gaisa tazuba mashi abinci da zobo a kofi, hannu tasa tadauki kofin tana fadin yau banaso Sarakina yasha wahalar komai, ni na girka kuma nice zan baka. Dariya yayi yana fadin kice yau nidin dan gata ne? Kofin tasa mashi abaki tana fadin kullum ma zaka kasance dangata. Murmushi yayi yana fadin nagode, haka tafara bashi abinci abaki yanaci yana lumshe ido, kallonta yayi yace to kema kawo in baki. Murmushi tayi tace aini tun ina yarinya banason dambun shinkafa, ko mama ta dafa sede ta dafa mani wani abun. Jinjina kai yayi yace ina matukar sonshi, kuma ina fata idan kinzo gidana inkoya maki cinshi? Maimuna tace idan har zaka iya koya mani to ni kuma zanyi kokari inkoya badan komai ba sedan yana cikin kalar abincin da kakeso, ni kuma ina matukar son inso abinda kakeso. Haka sukayita fira har yagama cin abincin, bayan yayi sallar la'asar yace zetafi. Lawisa ce tashigo tana fadin yauwa Yaya, ina ganin maganar tafiyarmu Darazo kawai muje jibi. Kallonta yayi yace wace Darazo kuma? Murmushi Lawisa tayi tana fadin wajen kawunan mu mana, ai kace kafiso a daura maku aure acan, ni kuma naga ko limami ze iya daura maku aure base anje can ba. Kallonta yayi yace kawai kibar wannan maganar. Tunda kunce bakuda wasu yan uwa sosai. Kawai zan samu liman din unguwarmu yazama waliyinta se a daura mana aurenmu. Lawisa tace amma yazakayi da yan uwanka? Tsaki yaja yana fadin, Kawuna ne kawai zan fadamawa tunda shine waliyi na, kuma nasan beda wata matsala shide kawai yaji kudi. Murmushi sukayi, Lawisa tace to ai shikenan duk abinda kakeso shizamubi Yaya. Kallon Maimuna yayi yace Gimbiyata nifa inaso ayi aurenmu da wuri banaso ku wahalar da kanku, duk abun bukata akwai agidana ke kadai yake jira. Murmushi tayi batace komai ba, kallon Lawisa yayi yace zan baku kudi kushiga kasuwa kuhado kayan lefe, kema kisiyo duk abinda kike so, zanje nasamu Kawu muyi magana nan da sati 2 za'a daura mana aure. Lawisa tace sati 2 yaya basuyi kadan ba? Murmushi yayi yace habade, kinsan yanzu nakosa inga Gimbiyata akusa dani, ada sam aure be dameni ba, amma haduwata da ita yasa nakeji ko sati daya wahala yakemun batare da ita ba. Lawisa tace toshikenan Allah yakaimu yasa alkhairi, yace amin, Kema seki hada kayanki dan bazamu barki anan ba. Zaro ido tayi tace gaskiya Yaya kayi hakuri bazan iya bin ku ba, nafiso nazauna nikadai zefi mani. Kallonta yayi yace haba Lawisa nifa bawai zama nacika yiba, kinsan dan kasuwa. Idan kina tare da ita ai zaki debe mata kewa ko? Lawisa tace tonaji, duk ranar dazaka bar garin nizanje intayata zama harka dawo, amma gaskiya bazanje inzauna daku ba. Jinjina kai yayi yace shikenan tunda kince haka, amma zaki tashi daga gidan nan, akwai wani gidana dayake Yalwan tudu zaki koma can dazama. Godiya sukayi mashi yace ai bakomai,gobe zan aiko maku kudi zansa Babaye yazo ya kaiku duk inda zakuje. Sukace to sungode. Bayan yatafi Lawisa tace Maimuna kinje de abinda yace, yanzu ya zamuyi gashi dazu boka ya lalata mana aiki. Tagumi Maimuna tayi tana fadin wallahi nima shinake tunani, ko yaya de ace kaje ma mutum da kwari yafi. Lawisa tace bara ayi magrib muje wajen Gaje, nasan zata temakemu. Maimuna tace yauwa hakan zefi, ko nawa ne zamu bata inde zata hada mana kayan mata. Haka suka je wajen Gaje, dubu 50 suka aje mata haka ta hada masu kayayyaki masu kyau, tabasu. Haka suka tafi Maimuna tafara amfani dasu. Washe gari Saraki yabama Babaye mota da kudi masu yawan gaske yace yakawo masu kuma ya kaisu kasuwa. Haka sukarika shirin biki, duk wani abu da suke bukata wajen Gaje suke zuwa, sun maidata uwar dakinsu, kasancewar suna sakar mata kudi yasa ta rikesu hannu biyu, Maimuna takara kyau, gyara ya ansheta. Medinki yagama mata dinkinta, haka suka shirya komai, ana saura kwana biyu biki Saraki yazo ya daukesu da kayansu yakaisu gidan da Lawisa zata zauna, duk abubuwan bukata yasaka mata, haka suka koma sukaci gaba da shirin bikinsu acan. Babu wasu kawaye abikin, Gaje ce kawai se mutanan ta data gayyatar masu sukaje, sunyi abinci merai da lafiya Saraki ya kawo masu lemuna kala kala. A masallaci aka daura aurenshi inda Limamin yazama waliyin Maimuna shi kuma Kawunshi. Manyan mutanan da sukazo daurin auren suna da yawa, kowa yana tayashi murnar auren da yayi, duk wanda yaga Lamido Saraki yasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa. Haka aka gama daurin aurensu akan sadaki dubu 50. Bayan kowa yaci yasha mutane suka fara tafiya. Aranar da dare Saraki da kanshi yaje dauko amaryarshi, motar matan Kawunshi kuma daban, haka suka shiga gidan, wajen Gaje Lawisa ta kaisu, bayan sun gaisa tayi masu fatan alkhairi, dan sun dauka itace mamar Maimuna. Haka aka fito da Maimuna aka sata motar Saraki, sauran Jama'ar Gaje kuma suka shiga sauran motocin. Bayan an kaita Saraki yabasu tukuicin dubu 100 haka sukayita godiya sukayi mata sallama, Daki suka shige ita da Lawisa, se kuka sukeyi, Lawisa tace tabbas ayau nasan zanyi kewarki, amma bakomai nasan arzikinki ne yakirawoki, kada kimanta da abinda nafada maki, banaso Yaya yagano wani halinki marar kyau. Wannan sabon layi ne nasiyo maki, kicire wancan ki karya kisa wannan, banaso kowa yasan kina da wannan layin, kome kenan zamuyi waya, kuma kada kisake ki kirani wayar sirri idan mijinki yana gida, kome zakiyi kirika bari se baya nan. Haka tayi mata sallama suna ta kuka haka suka rabu. Ango da amarya semuce asha amarci lafiya👫. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part 20 ⏩ 25 Haka Saraki da Maimuna suka sha amarcinsu, gaba daya Saraki ya susuce akan Maimuna, be taba cintar kanshi cikin farin ciki ba seda ya auri Maimuna. Domin Maimuna ta iya kula da miji, tasan duk wata hanya da zata sa miji farin ciki. Gashi ta iya girki kala kala, tunda sukayi aure bata taba bata mashi rai ba, yau satinsu 2 da aure komai na gidan ya canza, hatta da Babaye ta hanashi yin girki itace take bashi, cooler guda ta ware mashi, duk abinda ta dafa seta zuba mashi. Sam girki baya damunta, kuma baka taba ganin tayi abinci so daya arana, haka kuma ta hana Saraki cin abinci awaje, ko baze dawo gida da rana ba, seta bama Babaye abincinshi ya kai mashi office dinshi. Yanzu kam hankalinshi ya kwanta, kowa yaganshi yasan yana cikin farin ciki, ga harkar kasuwancinshi se kara habaka takeyi. Babaye yasa ya koyama Maimuna mota, haka ya dauki wata babbar mota me tsadar gaske yabata amatsayin kyautarshi. Duk halin da Maimuna take ciki kamar a gaban Lawisa akeyinshi, domin babu abinda take boye mata, duk wata kulawa Maimuna tana bama Lawisa, kuma kome ta girka inde na dadi ne seta aiki Babaye ya kaima Lawisa. Tunda Babaye yake zuwa gidan Lawisa idan taganshi gabanta yake faduwa, shikam sosai take burgeshi, ko Maimuna bata aikeshi gidan ba haka nan yake zuwa mata fira, ita ko sam jikinta yaki yarda dashi, shiyasa ma tace ma Maimuna zata rika kulle gidanta idan ta aikoshi setayi mata waya. Babu yanda ya iya haka ya kyaleta, domin so 2 yana zuwa yayita buga gidan amma seyaji shiru, ko ya kaimata sako data amsa take kulle gidan yatafi. Cikin siyasa Lawisa tasa saraki ya siya mata mota, domin duk abinda ta tambayeshi yana mata. Yanajin dadin yanda take kiranshi da Yaya, haka kuma bata taba zuwa gidan idan yana nan, har magana yake mata na rashin zuwanta wajen Maimuna, haka kuma tahana Maimuna tasashi yayi mata wani abu. Wannan abun da sukeyi bakaramin kara masu kima yake a idonshi ba. Kuma sosai yake ma Lawisa aike, a yanzu Lawisa tazama babbar mace, duk inda zata shiga a garin bauchi to acikin mota take zuwa, yanzu harkarta ta cigaba, harda kana nan samari takeyi, sede kuma itace take biyansu, idan kuma manyan Alhazai ne sune suke biya. Ko wane namiji sede yazo gidanta, dan ita bata zuwa gidan kowa, haka zalika bata kwanciya ita kadai, kasan cewar gidanta ba cikin mutane yake ba, hakan yasa takeyin abinda taga dama, duk wannan hidimar da sukeyi basu manta da Gaje ba, domin yanzu tazama yar uwarsu. Watan Maimuna 5 ta aure amma haryanzu shiru babu komai, sosai Saraki yafara damuwa, domin ya kwallafa ranshi akan samun haihuwa, gashi yanaso yaje asibiti sede yana tsoron abinda zeje yajiyo, hakan yasa ya kara hakuri. Ana cikin haka tafiya ta kamashi zuwa China, kuma tafiyar sati 2 ce, bayan ya fadama Maimuna zasu tafi unguwa seta tuno da zuwansu wajen boka, kallonshi tayi tace gaskiya banajin dadin jikina kawai katafi tunda sati 2 ne, wani lokacin idan zakaje semu tafi tare. Murmushi yayi yace kode zan samu da ne? Murmushi tayi tace kawaide inajin gajiya ne a jikina shiyasa, kaga kada mutafi naje na kwanta na hanaka aikin daya kaika. Jinjina kai yayi yace sannu, aikece ba kya gajiya,ko aikin gidan nan ya isa yasaki gajiya. Nace maki kirika abinci so daya idan yaso na dare semu fita muci awaje amma kince baki yarda ba. Murmushi tayi tace nifa bana son abincin waje, kama dena wannan maganar. Dariya yayi yana fadin kina tsoron kada wata ta kwace maki ni ko? Hararshi tayi tace ai babu wadda zata kwacemun kai. Bara na hada maka kayan dazaka tafi dasu, kallonta yayi yace amma gaskiya naso ace tare zamu tafi, amma idan naji nakasa hakura kawai zan dawo, murmushi tayi tace aikuwa fushi zanyi da kai matukar kadawo baka gama abinda ya kaika ba, kasande inason duk wani abu daze kawo maka cigaba. Dan haka kadena kawo wasa acikin harkar kasuwancinka. Jinjina kai yayi yace hakane, shiyasa kullum nakema Allah godiya daya bani ke, domin kinsan muhimmancin komai nawa, Allah yayi maki albarka. Zansa Babaye yarika kula da komai, har nadawo, kuma Lawisa zata dawo nan domin ta tayaki kwana. Haka tagama hada mashi kaya, kitchen ta nufa domin ta dauko ma Babaye abincinshi, hanyar waje ta nufa domin takirashi yazo ya dauka taga yau ya dade bezo ya karba ba. Cak ta tsaya tana kallon abinda yake faruwa, wata budurwace taga tafito daga bangaren Babaye shi kuma yana bayanta se dariya sukeyi, seda ya leko sannan yayi mata alamar ta taho, haka ya rakata har gate, ya bude mata tafita sannan yanufo gidan domin ya karbi abincinshi. Saurin komawa tayi tana mamaki dama Babaye yana kawo mata? Jinjina kai tayi se kuma ta tuna abinda Lawisa tace mata idan yaje seyayi ta kallonta. Bayan yashigo suka gaisa tace Babaye ai naleka inkiraka naga bakazo ka karbi abincinka ba se naga baka nan. Kanshi yafara sosawa yana fadin wallahi nashiga dakine nadan kwanta se bacci ya daukeni. Murmushi tayi tace Allah sarki, gashinan kadauka. Washe gari haka Saraki yakira Lawisa yace tadawo nan gidan dazama kafin yadawo, bayan sun gama yayimasu sallama ya ajema maimuna kudi masu yawan gaske, Babaye yatafi kaishi airpot. Zaune suke agaban boka suna sauraron abinda ze fada masu. Dariya yayi yana fadin amarya kinsha kamshi, shine ko akawo mana cincin din biki. Murmushi sukayi, Lawisa tace ai kasan bawani babban biki akayi ba, bamuyi tuya ba. Kallon Maimuna yayi yana fadin, kamar yanda nace maki idan anyi bikinki zan fada maki abinda zakiyi, abu na farko dazen fada maki, mijinki baya haihuwa. Kuma bazaki taba haihuwa dashi ba, kuma nasan mijinki yana matukar son haihuwa. Sede haryanzu betaba sanin laifin daga gareshi yake ba, ajiya kafin kuzo nayi bincike akanshi sosai, kuma matukar baki haihuba dole seya kara aure, dan haka zanyi maki aiki 3, na farko zansa mashi tsanar kowace mace da sunan aure. Na biyu kuma zan kauda mashi hankalinshi akan zuwa wajen likita domin yaduba lafiyarshi. Abu na 3, kuma wannan aikinki ne. Inaso kifada mani mutumin da mijinki yafi kusanci dashi? Shiru Maimuna tayi tana tunani. Lawisa ce tace gaskiya boka babu wanda muka sani wanda yafi kusanci dashi sama da wani mutumi dayake gidanshi, domin bamu san abokan aikinshi ba, amma shi wannan mutumin sunfi shekara 2 suna zaune agida daya. Wata irin dariya yayi yana fadin, hakika babu wanda yafi kusanci dashi kamarshi, dan haka dashine zamuyi wannan aikin. Saurin dago kai sukayi suna akallonshi. Daure fuska yayi yana fadin Babaye ko? Kai suka daga mashi. Wata kwarya ya dauko yana fadin, mijinki yayi tafiya ayau,kuma ze dawo nan da sati 2, amma bazan barshi yadawo ba se nan da wata 1,domin aikin dazan saki yana bukatar sati 4. Idanuwa kawai suka zuba mashi suna jiran abinda ze fada masu. Dago jajayen idanuwanshi yayi yace daga yau inaso Babaye ya maye gurbin mijinki harya dawo. A zabure suka mike tsaye kamar zasu fadi. Wata irin tsawa ya daka masu wadda seda tasasu gigicewa. Haka suka zauna kamar zasu saki fitsari. Kara kallonta yayi yana fadin, idan har kinaso mucigaba da tafiya dake, daga yau kada ki kara nuna tsorata akan duk wani aiki dazan saki, idan ba haka ba zansa aljanu suyi maki aiki. Cikin rawar murya Lawisa tace tuba muke. Wani garin magani ya dauko yabama Maimuna yace wannan shikadai zan baki, amma bazan te makeki akan yanda zaki shawo kan Babaye ba, sede idan kukayi kwanciya ta farko shine zaki dafa mashi abinci da wannan garin maganin, dayaci shikenan ze manta duk wani abu da kukayi dama wanda zakuyi daga yau har sati 4. Kuma daga wannan sati hudun da zakuyi atare shikenan bazaku kara aikata komai ba, domin bukata zata biya, kuma baze kara kallonki da kun aikata wani abu ba, komai ze wuce agurinshi, sede duk ranar da asirinki ya tonu dole ze tuna komai. Sannan adakin mijinki da kuke kwanciyar aure dashi anan nakeso kurika kwana kedashi har nan da tsawon sati 4. Idan har kika kasa shawo kanshi ayau to ina me tabbatar maki zaki rasa mijinki, domin ze karo aure wanda zesa soyayyarki ta rauna na azuciyarshi. ke macece kisan yanda zaki shawo kan Babaye. Idanuwan Maimuna cike da kwalla tace atemaka mani boka, idan narasa Saraki bansan yazanyi ba. Idan Babaye yaki amincewa da bukatata nasan zetona mani asiri kuma Saraki korata zeyi. Dariya yasa yana fadin shikenan za temakeki da abu daya, wata laya yamiko mata yana fadin, bazakiyi amfani da ita ba harse kinga yaki amincewa da bukatarki sannan zakiyi amfani da ita, amma kada kice daga kin gwada sodaya zaki danna. Domin ko kinyi bazatayi aiki ba, se kinga tura takai bango sannan. Hannu biyu tasa ta amsa tana godiya, dubu dari 2 suka aje mashi yace sena kara ganinki. Dariya yasa yana wasu surutai. Zaune suke a falo Maimuna ta buga tagumi, dafata Lawisa tayi tana fadin haba Maimuna, meye baki gani ba? Meye ze baki tsoro arayuwa yanzu? Kada kimanta tun kina secondary kika rasa budurcinki, duk wannan be baki tsoro ba se wannan karamin abun? Kuma fa Boka yace da kunyi na yau ze manta duk abinda yafaru da wanda ze faru wanda zaku aikata matukar yaci magani acikin abincinki. Maimuna tace Lawisa nasan mutuncina ze zube a idon Babaye. Murmushi Lawisa tayi tace lallai Maimuna bansan bakiyi kwari ba , domin idan har wannan karamin abun ze gagareki to wallahi gudo warki daga gida batada amfani. To bara kiji, idan dare yayi kiyi wanka, kiyi kwalliya da matsiyatan kaya masu jan hankali, sannan kileka ki kira Babaye. Yana zuwa cikin tashin hankali kice mashi kinajin motsi adakin mijinki, tunda kince mun Babaye manemin mata ne, nasan bazakisha wahala wajen kamashi ba. Yana shiga dakin kawai ki kulle kofar ki fada mashi. Babu wani lafiyayyan namiji da zejiki ajikinshi ya kyaleki koda shine ya yankema ustazanci cibi. Dariya Maimuna tasa tana fadin wallahi bakida dama Lawisa, Lawisa tace ba dole ba, keyanzu idan kika samu ciki kika haihu ai kinsan Yaya seya rasa irin kyautar daze maki, dan haka kawai kimanta dawani abu domin yanzu duniya seda kudi ake soyayya. Maimuna tace tonaji, amma yaushe zaki dauko kayanki? Lawisa tace rufamun asiri, yanda zaku bude sabon amarci agidan nan yaushe zanzo intakura maku. Kede kawai kuyi zamanku nima naje nayi harkata domin nasamu wani danyen yaro da ya iya harka sosai. Maimuna tace wallahi nide kinmun wayau, shikenan se inta tsayawa a waje guda. Lawisa tace aikuwa dole kicire wannan tunanin aranki, domin kece fitilarmu idan kika da kushe muma zamu da kushe, dan haka kicire komai aranki. Haka Lawisa tagama shirya mata komai, se dare tayi mata sallama haka Maimuna tacikata da kayan arziki da kudi masu yawan gaske sannan ta tafi. Bayan ta tafi wajen karfe 10 Maimuna tagama shiryawa, tafeshe jikinta da turaruka masu dadin kamshi, haka tafita da hijab a jikinta. Tana lekawa tafara kwalama Babaye kira cike da tsoro, a kidime yataho dagashi se singileti da gajeran wando, yana zuwa yace hajiya lafiya meyefaru? Kamar zatayi kuka tace shigo Babaye kaga wani abu, wallahi motsi nakeji acikin daki. Yana shiga ta kulle kofar falon, haka yashiga gaba tana binshi abaya tana fadin kashiga kagani bazan iya shiga ba, yana shiga itama tashiga tare da kulle kofar dakin, kafin yajuyo tacire hijab dinta, lokacin daya juyo se yayi arba da Maimuna cikin wasu matsiyatan kaya. Saurin runtse ido yayi yabude baki zeyi magana kawai ta fada mashi, basu sauka a ko inaba, se saman gado, kafin kace me Maimuna ta fara ruda Babaye, haka shedan yayi tasiri azukatansu suka cigaba da aikata alfasha, dama shima dan hannu ne. Washe gari Babaye kasa tashi yayi, itako Maimuna tunda wuri ta tashi tayi wanka taje kitchen ta dafa mashi abinci ta zuba maganin da boka yabata, kafin ta koma Babaye yayi saurin shiga yayi wanka yayi sallah. Tana zuwa ta aje mashi abinci tafita falo domin taci nata. Yana gama cin abincin sam ya manta da abinda yafaru, duk wani tsoro yafita daga ranshi, haka ya koma saman gado ya kwanta, Maimuna tana shigowa tayi murmushi, domin tasan magani yafara aiki. Haka tacire kayanta tahau saman gadon tana zuwa ya rungumeta suka cigaba da aikinsu. Tun daga wannan rana Maimuna da Babaye suka koma tamkar miji da mata, hatta da kayanshi daukosu yayi yadawo dakin Saraki da zama, kullum gate dinsu a kulle, dama Maimuna bata da wata kawa datake zuwar mata gida. Lawisa ce kawai take zuwa se kuma Gaje, itama kafin tazo seta sanar mata. Kullum suna waya da Saraki sede yakasa fadamata dalilin dayasa baze dawo ba, itama taki tambayarshi lokacin daze dawo. Haka suka jigaba da shan amarcinsu ita da Babaye, lokaci guda yakara haske da kiba. A ranar da suka cika sati 4 suna aikata masha'arsu aranar Saraki yakirata yace gobe ze dawo. Kuma tun daga ranar tacema Babaye daga ranar kada yakara zuwa inda take, daga ranar alakarsu tayanke. Babu bata lokaci ya amince, haka ya hada kayanshi ya koma dakinshi. Washe gari Saraki yadawo, sosai yayi murnar ganin Maimuna yanda takara kiba tayi haske, se tsokanarta yake yana fadin anya babu ajiyata ajikinki? Murmushi tayi batace komai ba. Bayan yayi wanka yaci abinci suka kwanta domin agajiye yake. Washe gari haka ya fiddo mata tsarabarta data Lawisa, Babaye ma ya ware mashi tashi. Bayan sati guda da dawo warshi Maimuna ta tashi da zazzabi da amai, cike da tashin hankali suka tafi asibiti, awon farko aka gano tana da ciki wata 1. Ai tun a asibitin Saraki ya rungumeta yana dariya, hatta da likitan daya fada mashi seda yasamu kyauta me tsoka. Haka ya rubuta masu magunguna suka tafi gida, Saraki yarasa inda zesa Maimuna saboda farin ciki. Haka yace sede Lawisa tadawo gidan dazama tarika tayata aiki, amma Lawisa tace ita kunyarshi takeji sede zata rika zuwa da safe tana tafiya da yamma, amma ya samo mata masu aiki, babu yanda ya iya haka ya amince, dayake akwai wasu dakuna agidan daga baya seyace masu aikin zasu zauna can. Haka yadauki son duniya yadorashi akan cikin Maimuna, duk wata kulawarshi ta koma kanta. Masu aiki 2 aka samo wasu dattijai domin surika kula da gidan, Lawisa idan tazo da safe da yamma take tafiya. A haka cikinta yakai wata tara, Saraki yaso ya kaita waje ta haihu amma sam takiyarda. Haka ya hakura domin bayason bacin ranta. Ranar asabar da safe Maimuna ta tashi da nakuda, haka suka nufi asibiti tare da Lawisa Saraki duk ya rude. Suna zuwa bata wuce minti talatin ba ta haifi namiji me kyau dashi. Saraki yama rasa wane irin farin ciki zeyi, besan lokacin da hawayen farin ciki suka zubo mashi ba, hakika Maimuna tagama mashi komai, besan da abinda ze biyata ba, amma aranshi ya aje wani babban abu da zeyi mata wanda ze sata farin ciki har karshen rayuwarta. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part 25 ⏩ 30 Fadar irin kayan da Saraki ya sayama Maimuna da danta baze yuwu ba, domin bakananan kudi yakashe masu ba, walima sosai yashirya wadda koda bikinshi beyita ba. Masu abinci na musamman aka dauko domin suyi abinda za'aci wajen walimar suna. Ranar suna takama asabar yaro yaci sunanshi Nabeel Lamido Saraki, da misalin karfe daya da rabi abokan Saraki suka halarci gidanshi domin suci abincin da aka tanadeshi saboda su. A harabar gidan aka kafa rumfuna. Mutanan da sukazo wajen basu kirguwa, haka kowa yarika taya Saraki murnar samun karuwa, anan kowa yazauna masu raba abinci suka fara aikinsu, se abinda kakeso zakaci. Lemuna gasunan kala kala. Acikin gida kuwa mutanan da sukazo basu da yawa, yawancinsu duk jama'ar Gaje ne, domin su Maimuna basuda wasu mutane, ko makwaftansu bata mu'amala dasu sosai, hakan yasa ba kowa ne yazo ba, sede wasu daga cikin abokanshi sunzo da matansu hakan yasa taron yakara armashi. An raba abubuwa mejego tayi kyau harta gaji ita da danta, Lawisa ma tayi kyau, haka kowa yaci yasha, masu diba suka diba suka tafi dashi, bayan taro ya tashi masu aiki suka fara gyaran gida, kasancewar sunada yawa cikin lokaci kadan suka gama,gida yadawo kamar ba'ayi taro ba. Haka suka cigaba da renon Nabeel cike da kauna, Saraki komai nashi ya maida sunan Nabeel ajiki, haka ya saimashi share a banki da kamfanoni, account guda ya bude mashi yana saka mashi kudi aciki duk wata. Babbar super market dinshi ma Nabeel ya barma ita. Duk wata riba da aka samu a account dinshi ake sakata. Haka yaro yataso cikin gata gaba da baya, kyanshi se kara fitowa yakeyi, yana kama da Maimuna, kuma yana dan kama da Lawisa, har mamaki Lawisa take tana fadin kinga yaron nan yana dan kama dani, Maimuna tace kinsan ai ni dake muna dan yanayi shiyasa zakiga haka, Lawisa tace haka ne, sede kunfi kama dashi sosai, kamar ma seya fiki kyau. Maimuna tace kinsan wani abu? Wallahi har tausayin Abban Nabeel nakeyi yanda yake nunama Nabeel so, yanzu fa komai nashi yamaidashi da sunan Nabeel, danayi mashi magana yacemun yayi haka ne saboda mutuwa. Yasan yana da kudi sosai, idan har ya mutu yan uwanshi zasu iya cutar da Nabeel, amma idan sukaga komai na kadararshi sunan Nabeel ne dole zasu hakura. Wata takarda ta mikama Lawisa tana fadin kinga nima kyautar da yayi mani saboda na haifa mashi da. Dariya Lawisa tayi tana fadin kina nufin yabaki gidan manshi daya? Kai Maimuna ta daga tana murmushi. Jinjina kai Lawisa tayi tana fadin dama nafada maki, zaki ji dadin rayuwarki, yanzu bagashi ba cikin lokaci kadan kinzama babbar hajiya. Ni daga yanzuma hajiya zan rika kiranki duk da bakije makka ba. Maimuna tace itama zamuje kuma hadake, yace sena yaye Nabeel zamu tafi gaba daya. Guda Lawisa tayi tare da shewa tana fadin, lallai bariki tayi mana rana, dole mu so Nabeel, domin ta sanadiyarshi gashi arziki yana fito mana ta ko ina. Dafa Maimuna tayi tace inaso ki bude kunnanki kiji abinda zan fada maki. Naji kina maganar wai Yaya yafara baki tausayi saboda Nabeel ba danshi bane. To wallahi idan ma zaki cire wannan tunanin aranki kicire. Domin babu abinda ze haifar maki se damuwa, arzikin da kikeso kisamu ya gagareki ci, duk duniya babu wanda yasan da wannan maganar se mu biyu, ko uban yaron besani ba, dan haka zamu bata matukar kika kara mani maganar nan. Maimuna tace insha Allah daga yau nadena. Dariya suka sa. Tun daga ranar Maimuna bata kara tada maganar ba, haka suka cigaba da more rayuwarsu, kudi masu yawa Maimuna tabama Lawisa tafara kasuwanci, sosai arziki ya wuce na da, ganin harkarsu tafara kwari yasa Saraki yakara mata jari tafara fita waje tana saro kaya. Gaje take bama wasu tana dora ribarta itama tana saidawa, kafin kace me, Gaje takara zama babbar hajiya, shiyasa take son su Maimuna, mutane da yawa sun san Lawisa saboda tana kawo masu kaya kala kala, kuma bata sama kayanta kudi dayawa, domin Lawisa tace tafison suna akan kudi. Lokacin da aka yaye Nabeel haka Saraki ya biya masu kujerar makka su biyar, suka tafi, gidan ma kulleshi akayi domin hada Babaye aka tafi. Bayan sun dawo suka cigaba da renon Nabeel cike da so. Lokacin da Nabeel ya isa shiga primary haka aka sashi private school me tsadar gaske, sede sam Nabeel baya maida hankali akan abinda ake koya mashi, sanin irin son da Babanshi yake mashi yasa babu me tabashi acikin malamansu. Haka Nabeel yataso cikin gata islamiyya ma malami Saraki yadauko mashi yana koya mashi agida, sede duk abinda zeyi malamin be isa ya dokeshi ba, domin Nabeel ko fada be sani ba bare duka. Babaye kuwa harkarshi ta bin mata se abinda yaci gaba, domin yanzu har kwana suke zuwa suyi agidanshi, kuma har yanzu Saraki besan yanayi ba, domin yasan lokacin fitarshi da dawo warshi. Umman Nabeel ce kadai tasan yana kawo mata. Lawisa kuwa yanzu abun nata yazarce tunanin me karatu, domin bata dauki aikata zina abakin komai ba, fitar da takeyi waje yasa ta koyo harkar mata, shiyasa yanzu tadena neman maza sede mata. Kasancewar sunada Gaje yasa take samun kayan gyara sosai. BAYAN WASU SHEKARU Abban Nabeel ne da Ummanshi sukaje graduation din Nabeel na gama secondary school dinshi, da gudu ya rugo ya rungume Abbanshi jikinshi sanye da rigar graduation, yayi matukar kyau, gashi fari kuma dogo. Bayan an kammala haka suka dawo gida cike da farin cikin kammalawar karatuni na gaba da primary. Wata sabuwar mota me tsadar gaske Abbanshi yabashi amtsayin kyautarshi. Sosai Ummanshi tayi farinciki, Nabeel kuwa rungumeshi yayi yana murna. Umma ce ta kalli Abbanshi tace amma de a waje zaka samar mashi gurbin karatu ko? Murmushi yayi yana shafa kanshi yace gaskiya yanda nakejin Nabeel bazan iya barinshi yayi tafiyar kwana daya batare dani ba. Kinga kuwa bazan iya kaishi waje yayi karatu na tsawon shekaru 4 batare da yana kusa dani ba. Duk da nasan akwai karatu a waje, amma gara yazauna kusa dani yayi karatunshi, ya kwana gida yaje makaranta nasan idan yagama gida zedawo komin dare ya kwana. Wannan dalilin ne yasa ban kaishi makarantar kwana ba. Murmushi Nabeel yayi yace nima Abba banason zuwa ko ina, nafiso kullum ina ganinka, kuma ni banason zama cikin turawa nafison hausawa yan uwana. Hannunshi yakama yana murmushi yace yauwa yarona, babu inda zakaje. Murmushi Umma tayi tana fadin nima ai nafiso yazauna kusa dani. Nabeel yace ammade Abba kaga abokanai na agidansu sunada part dinsu amma gashi nagama secondary zanshiga wata amma haryanzu ina cikin gida. Dariya Abba yayi yace kada kadamu, yanzu kam ai kazama babba dole arika yima komai na manyan maza, zansa a gyara maka wancen part din na gefen dakina amma kuma Nabeel kofarshi ta wajen gida take, kode insa a hadesu amaido kofar ta cikin falo? Shagwabe fuska Nabeel yayi yana fadin nide Abba abarshi haka, yanzu fa nazama big boy shikenan idan friends dina sukazo dole se sun shigo ta cikin gida, kuma idan kuna zaune falo haka zamuyita wuceku muna shiga da fita. Kagafa Saif agidansu part dinshi daban yake. Dariya suka sa mashi, Abba yace e da gaskiyarka, nima inason privacy, shikenan yanda kakeso haka za'ayi maka, amma abinda nakeso ka dage kayi karatu sosai, kuma malaminka me koya maka karatu zecigaba da zuwa kafin exams dinku ta fito, Idan kafara zuwa makaranta seyarika zuwa week end, nafiso kataso da iliminka duka biyun. Kallonshi Umma tayi tace haba Alhaji, yanzufa Nabeel ya girma ina yake da lokacin karatu biyu, abinda yasamu yana karami ai ya isa, so kake abokanshi surika mashi dariya ana zuwa koya mashi karatu? Nabeel yace e wallahi Abba, nide ya isheni haka, nasan abubuwa da yawa ina yaro, zamurika karatu dasu Saif idan mundawo daga makaranta. Kallonshi yayi Nabeel yace plsss Allah zamuyi karatun.Jinjina kai Abba yayi badan yaso ba, sedan bayason bacin ranshi ya amince. A washe garin ranar Abba yasa masu aiki suka gyara mashi part dinshi, duk wani abu na bukata seda aka samashi yanda kasan gidan me mata. Yayi kyau sosai, Umma da kanta tasa Gaje ta samo mata wata budurwa wadda zata rika gyara mashi part dinshi tana kula da komai nashi. Babu bata lokaci Gaje ta samo mata wata yarinya a kalla zata kai shekaru 16, wani daki dayake kusa dana masu aikin gidan aka bata, hatta da kayan sawa seda Umma ta siya mata da kayan kwalliya domin Nabeel yace bayason kazama. Sabuwar waya tabata tasa mata number Nabeel shima tabashi tata saboda idan yana nemanta, duk wasu sharudda seda Umma tafada mata, tun daga gyaran dakinshi, wankin bandaki, da gyara mashi kayanshi duk itace zata rikayi. Yarinyar me suna Sa'adatu ana kiranta da Ada,sosai tayi mamakin irin aikin da aka sata, a tunaninta namiji yakamata ace ansa wannan aikin amma aka sata. Sede kuma data tuna kudin da Gaje tace za'arika bata yasa tayi murmushin jin dadi, domin dubu 30 Umma tace zata rika bata duk wata. Kuma tace matukar tana kula da Nabeel sosai zata iya kara mata. Murmushi Ada tayi tana fadin wannan kudi sekace me aikin gwamnati? Ga sababbin kaya, ga kayan kwalliya, ga kwanciya aguri me kyau, ga abinci me dadi. Lallai nima nakusa shigowa gari. Me ake da zaman kauye. Tun daga ranar Ada tafara yima Nabeel aiki, duk abinda yake bukata idan bayason shiga cikin gida to ko karfe nawa ne haka zekira Ada takawo mashi koda tafara bacci, haka kuma hatta da ruwan wanka itace zata hada mashi, yanda kasan wani Yarima. A hankali Ada tafara burge Nabeel, cikin lokaci guda sha'awarta tafara darsuwa a zuciyarshi, sede alokacin yadauka ba wani abu bane shiyasa ya share domin duka alokacin shekararsa 22 domin yashiga makaranta da wuri. Ana cikin haka ne yasamu admission a ATBU bauchi ze karanci Micro biology. Lokacin daya fadama Saif shima yace abinda ze karanta kenan, sosai sukaji dadin samun course daya. Haka Abbanshi yabashi makudan kudi domin yaje yayi siyayyar abubuwan dayake so, dan yasa ayi mashi komai sede kawai yafara zuwa makarantar. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part. 30 ⏩ 35 A ranar monday Nabeel yafara shiga makaranta, lokacin daya isa bakin depertment dinsu gaba daya mutanan dasuke wajen seda kallonsu yakoma kanshi, tundaga tsayuwar motar kowa ya kosa yaga wanda zefito daga motar, domin motar kanta abun kallo ce. Ya dade befito ba, dayar kofar aka bude sega Saif yafito cikin kananan kaya masu masifar kyau da tsada,fuskarshi dauke da bakin glass shima daga ganinsa zeyi tsada. Nabeel ne ya bude kofarshi yafito, ai gaba daya sakin baki sukayi suna kallonshi. Shigarshi da Saif iri daya, yanda sukayi se sukayi kama da yan biyu. Murmushi yasaki suka rufe kofar, tare da takawa zuwa inda sukaga mutane suna shiga domin ganin malaminsu yashiga. Haka suka samu waje suka zauna, duk yan matan dasuke wajen rabin hankalinsu yana kansu Nabeel. Haka malaminsu yafara da introducing kanshi sannan yasa kowa yatashi yayi introducing kanshi. Bayan kowa yagama haka yacigaba ta gabar masu darasinsu. Bayan yagama kowa yafito, alokacin wata mota ta tsaya, murmushi Saif yayi yana fadin shegen kaya seyanzu ya iso. Nabeel yace wanene? Saif yace wannan friend din nawa danake fada maka munyi primary dashi Najib. Murmushi Nabeel yayi yace ok naganeshi. Najib yana fitowa yazo suka rungume juna shida Saif, hannu ya mikama Nabeel suka gaisa, jerawa sukayi suka nufi wasu kujeru suka zauna. Gabatar da Nabeel Saif yayi wajen Najib kara gaisawa sukayi, nan suka cigaba da firarsu. Saif ne yace Nabeel tsaya kaga wannan film da nake fada maka na kalla jiya, Najib yace Saif kaifa dan iska ne kada ka koyamashi kallon irin films dinka. Dariya Nabeel yayi yace kyaleshi ya nunamun yanzu ai seda kallo. Saif yace kai bafa irin film din daka sani bane, wannan bakowa zaka bari ya kalla ba, kuma yafi dadin kallo idan kayi shirin bacci kashige bargo. Nabeel yace wane irin film ne haka? Saif yace kaide tsaya ka gani. Mika mashi yayi yana dariya, saurin mika mashi wayar Nabeel yayi yana fadin wallahi nayarda kai dan iska ne, aini bantaba kallon irin wannan iskancin ba tunda nake. Saif yace wallahi abokina zakaji dadin kallonsu. Nabeel yace nikam bazan kalla ba. Ai ko Ada tafi wannan matar kyau wallahi. Najib yace wacece Ada kuma? Kada kace mani sunan babynka ce? Kallonshi Nabeel yayi yace Baby kuma? Adar? Lallai ma yarinyar da take mani aiki ce fa. Dagajin yanayin maganarshi zakasan akwai yarinta aciki da tsabar shagwaba sosai, domin su Saif sun girmeshi. Dariya Saif yasa yana fadin wallahi na lura su Umma sun shagwaba ka, wato har me aiki suka aje maka? Yatsuna fuska Nabeel yayi yace komai ita take mani, hatta da gyaran kayana itace takemun, kai har ruwan wanka itace ke hadamun. Najib yace kawai kace sun fara koya maka traning na megida. Dariya suka mashi, Nabeel yace kun maidani abin dariya ko? Dafashi Saif yayi yace ba haka bane, kawaide abunne da ban dariya. Kasan wani abu? Kanshi ya girgiza alamun a'a. Saif yace inaso idan muntashi daga nan muje inga Adar taka. Nabeel ya kalleshi tare da turo baki yace to meye nacewa Ada ta? Murmushi Saif yayi yace kawai dan ayi saurin ganewa, Nabeel yace shikenan bara nakirata nace ta hada mana abincin mutum 3. Bayan suntashi suka nufi gidansu Nabeel, zaune suke a falo ya kunna masu kallo, Ada ce tashigo dauke da tray tana sallama. Tana shigowa kamshi ya cika falon domin Ada akwai cika turare, dago kai sukayi suna kallonta, dukawa tayi ta gaishesu. Saif yace sannu da kokari Ada, tace yauwa sannunku da zuwa. Nabeel yace Ada zuba mana ki dauko mani casset dina a wajen Umma ki kawo mani. Najib yace kawai kabarshi bara indauko mana wani film a mota ta mu kalla. Bayan tafita Najib yakawo masu film din yasa masu. Kallon Nabeel Saif yayi yace amma wannan Adar tana da kyau, meze hana idan kagaji karika sata tanayimaka tausa. Nabeel yace kawai se inbari tarika tabani haba baze yuwu ba. Haka suka rika saka mashi abubuwa marasa kyau, suna nuna mashi films din banza, aranar sun dade suna kallo seda suka sama Nabeel ra'ayin kallonsu. Dazasu tafi Saif ya tura mashi films din a wayarshi sannan suka tafi. Da dare yana kwance yana kwallo haka yayita juyi asaman gado, wayarshi yadauka yakira Ada yace tazo ta hado mashi tea, bayan ta hado mashi takawo mashi, zaune take harya gama ya kalleta yace Ada jikina yana mun ciwo kozaki danna mani? Saurin kallonshi tayi yace ko bazaki iya ba? Saurin girgiza kai tayi yace yauwa cire hijab din kitaho, haka ya kwanta tafara mashi tausa, sosai yakejin dadin yanda take mashi, bayan tagama yace sannu Ada nasaki wahala ko? Murmushi tayi tace ai bakomai aikinane. Murmushi Nabeel yayi yace kema taho nayi maki dan naga alamar kingaji. Ada tace kabarshi kawai, Nabeel yace nide kitaho. Haka Ada ta kwanta yafara yimata tausa, tuni ta lumshe ido tanajin dadin abinda yake mata. Da haka yafara yimata irin abinda yagani a film din daya gani, sosai suka shagala daga haka har bacci ya daukesu, haka suka kwanta rungume da juna. Basu suka tashi ba se wajen 8. Atare suka tashi, Ada ta kalli jikinta babu kaya, saurin jan bargo tayi ta rufe jikinta. Murmushi Nabeel yayi yace gaskiya naji dadin baccin jiya, daga yau tare zamu rika kwana ina fatan zaki amince? Ada tace nide inajin tsoro kada inyi ciki. Nabeel yace kinga nayi maki wani abu bayan wanda namaki jiya? Girgiza kai tayi tana fadin ai wata rana zaka iya yimani. Nabeel yace ni babu abinda zan maki, amma kibari anjima zan nuna maki wani abu dana kalla awayata, tashi muje muyi wanka muyi sallah nasan yanzu Umma zata kirani. Bayan sun gama ta nufi part din Umma. tana zuwa tashiga kamar munafuka, Umma tasamu afalo, dukawa tayi tana gaisheta. Umma tace Ada ya akayi yau bakizo da wuri ba, kuma na aika Iya takira mani ke tace baki cikin dakin ki? Sosa kai tafarayi tace dama Yaya ne yakirani tunda asuba naje na kai mashi tea yace wai da yunwa ya tashi. Cike da damuwa Umma tace Ada ya akayi Nabeel ya kwanta da yunwa haka? Ada tace wallahi yaci abinci kafin ya kwanta. Umma tace idan kinsan bazaki iya kularmun dashi ba zan sake me kula dashi. Ada tace kiyi hakuri wallahi zan iya. Umma tace shikenan amma ki kara kula sosai, dauki abincinshi ki kaimashi. Haka ta dauki komai na abincinshi takai mashi, yana gamawa yashigo domin su gaisa dasu Ummanshi. A zaune ya samesu ita da Abbanshi, kusa da Abbanshi yaje yadora kanshi saman cinyarshi yana fadin Abba ina kwana, murmushi yayi yana shafa kanshi yace lafiya lau yarona, katashi lafiya? Yace lafiya lau. Umma ina kwana, tace lafiya lau, Nabeel meyasa bakaci abinci kafin ka kwanta ba? Dazu Ada tace mun ka kirata tunda asuba kace ta kai maka tea wai da yunwa katashi. Murmushi yayi yace Umma naci abinci kawaide haka natashi. Abba yace karika kula banaso wani ciwo yasameka, idan kuma bazaka kula ba zansa kadawo cikin gida murika kula da kai. Nabeel yace Abba zan kula, yace da kyau, tashi katafi makaranta kada ka makara kaga 10 ta kusa,Umma tace ko akwai abinda kake bukata? Nabeel yace bakomai, Umma tace kaide jeka dakina cikin jakata akwai kudi ka dauki wadan da zasu isheka. Nabeel yace Umma inada sauran kudi bana bukata, tace kaide kaje kadauka yanzufa kai babban mutum ne, kanaso a makaranta ko,abokanka su tambayeka wani abu kuma kace masu bakada hali? Abba yace tashi kaje kada kamakara, haka Nabeel yaje yadauki kudin da yakeso yafita. Zaune suke Nabeel yana basu labarin abinda yafaru jiya da dare, dariya kawai suke mashi. Saif yace ammafa abokina kayi kokari. Da ace kayi irin wasan da na nuna maka wallahi bazaka kara kwana babu mace ba, Nabeel yace ai tace tana tsoro kada tayi ciki. Najib yace bara in baka wani abu, nima awajen wani abokina na sameshi yace mun wai wajen yayanshi yagani. Shine ya kaima wani wanda suke tare yake fada mashi amfaninshi, tun daga lokacin nima nafara bama duk yarinyar dazan kwanta da ita, ai yanzu sakarai shine yake bari yayima yarinya ciki. Saif yace mugani idan irin nawa ne, karba yayi yace e yana da kyau wannan maganin. Amma duk lokacin da kaga yarinyar kamar bazata amince tasha ba, kawai kamata dabara kota cikin lemu ne kabata kuna gama harka idan ba haka ba kai zasu bari da aiki kuma ta tona maka asiri wajen iyayenka. Nabeel yace bani nima yau zan gwada, domin jiya kamar zan mutu marata tarika mani ciwo. Dariya suka sa mashi, Najib yana fadin kutashi mutafi naga anfara shiga class. Lawisa ce kwance adakin Umman Nabeel tana daga gefenta suna fira, Lawisa tace wallahi harna gaji da hawa jirgi, gashi wannan satin hajiya Samira tace zan rakata dubai. murmushi Umma tayi tace wallahi kina jin dadinki yanda kike rayuwarki asake. Wai mezesa baza kiyi aure haka nan ba Lawisa? Tasowa Lawisa tayi tadora kanta saman cinyar Umma tana murmushi tace yanda nakejin dadin wannan harkar tawa yanzu namiji baya burgeni,shikenan kulluma arika abu daya. Uhm kema baki shiga harkar bane shiyasa. Umma tace ko nashiga kina ganin wannan sarkin nacin zebarni inrika zuwa wani waje,kuma baze yuwu narika kawo kowa gida na ba saboda gudun bacin rana. Nasan Babaye baze taba fahimtar komai ba,tunda shima dan iskan kanshi ne. Hannu Lawisa tasa cikin rigar Umma tana shafa cikinta ahankali, lumshe ido tayi tanajin dadin yanda Lawisa take shafa mata ciki. Dago kai Lawisa tayi taga yanda tayi, murmushi tayi tace ina zuwa, tashi tayi ta rufo kofar dakin tana fadin yakamata kema kishigo gari, amma nizan fara koya maki, kafin nafara kawo maki abokan harka. Umma tace kai Lawisa kina ganin babu wata matsala? Jawota tayi tana fadin kede kawai kiyi shiru. Haka Lawisa ta fara koyama Umma harkar bin mata, shedan yasamu damar kara dulmiyar dasu. Tun daga wannan rana Lawisa da Umma suka kara zama aminan juna, sosai Umma ta kware a harkar, seda Lawisa tagaji sannan tafara kawo mata abokan harka, Abba besan abinda yake faruwa ba, domin Umma tace mashi Lawisa tana kawo mata kaya tana saida mata shiyasa mata suke zuwa siye, da wannan bayanin ta kauda mashi da duk wani tunani, dama kuma shi ba mazaunin gida bane sosai. Nabeel da Ada kuwa sosai harka ta cigaba, domin zuwa yanzu Nabeel ya kware a harkar banza, kulluma tare suke kwana da Ada, gaba daya son Nabeel yagama kamata har kosawa takeyi yadawo, shiko anashi bangaren bawani sonta yake ba. Haka acikin makarantarsu sun zama taurari, su 3 ne haka suke yawo, Saif shine ya farayin budurwa me suna Zubaida yana kiranta da Zuby, yar garin gombe ce iyayenta suna da hali, sede ita a cikin makaranta take zaune, tunda suka hadu da Saif suka fara soyayya, kuma tun daga lokacin tadena maida hankali a karatunta. Kuma shine mutumi na farko daya fara bata mata rayuwa, sede yanda yake sonta yasa baya kula kowace mace, kasancewar gidansu akwai kannanshi yasa becika kaita gidansu ba, sede suje gidansu Nabeel. Wannan dalilin ne yasa Nabeel shima yafara kula yanmatan da suke bibiyarshi, anan ne kuma Najib ya hadu da Khairat, itama 'yar gombe ce, kuma kawar Zuby ce, sosai suke soyayya, Nabeel ne kawai yake bin mata dayawa domin yace har yanzu besamu wadda zuciyarshi take so ba. Ganin suna yawan shigowa da mata gidan yasa Saif yace ya samu Abbanshi yace mashi yabashi mukullin wani gaidanshi dayake Nasarawa domin acan zasufi rayuwarsu batare da takura ba, amma anan wata rana Abba ze iya dawowa ya gansu. Haka yasamu Ummanshi yafada mata yanaso abashi makullin gidanshi na nasarawa. Umma tace Nabeel bade can zaka koma dazama ba, kasan bama son kayi nisa damu? Nabeel yace Umma ba haka bane kawaide inason inrika zama lokaci zuwa lokaci acan, kinsan wani lokacin mutum yana jin zama waje daya ya ishe shi. Umma tace toshikenan tashi muje nasan yanzu yagama wanka muje zan sashi yabaka. Jin jina kai Abba yayi lokacin daya gama jin bayanin Umma. Jin yayi shiru yasa Nabeel ya shagwabe fuska kamar zeyi kuka yace Abba bafa can zan rika kwana ba, kawaide inaso inga nima ina canza wajen zama. Umma ta dafa Abba tace haba meye abun damuwa, bafa kwana zerika yiba, kuma Nabeel shi kadai garemu mezesa bazamu bashi duk abinda yake so ba. Murmushi Abba yayi yace haka ne, amma ina tsoron halin yau, domin kinsan yanzu duniyar ta baci, samari basuda aikinyi se tara mata agidansu suna aikata alfasha. Umma ta daure fuska tace shikenan tunda kace haka, ashe dama baka yarda da tarbiyar da muka bama Nabeel ba? Bakomai tunda ka nuna kafara gajiya da Nabeel. Saurin kamo hannunta yayi yace haba Umman Nabeel yazakice haka? Duk son da muke ma Nabeel baze hana mu lura da rayuwarshi ba, domin abinda yake faruwa ne a zamanin yanzu nake fada, amma duk duniyar nan banajin akwai wanda ya kaini son Nabeel, amma bazanso ace na barshi ya baci ba. Murza ido Nabeel yafarayi kamar kamara min yaro kamar zeyi kuka ya tashi yana fadin shikenan Abba kabarshi kawai tunda baka yarda dani ba, amma har na fadama abokai na inada gida a Nasarawa kuma zamu rika zuwa can muna karatu idan mungaji, shikenan Abba. Murmushi Abba yayi yajawoshi yana fadin to meye na bata fuska kamar zakayi kuka, kada kamanta rabonka da kuka tun kana yaro? kuma nayi alkawarin bazan taba barinka kayi kuka ba matukar ina raye, shikenan jeka daki kadauko makullin, amma anjima zansa a gyara maka gidan a samaka duk abinda kake bukata. Dariya Nabeel yasa ya rungume Abba yana fadin nagode sosai Abbana. Haka Abba yasa aka gyara mashi gidan aka sa komai, tun daga ranar su Nabeel suka samu wajen hutawa da yan matansu, abokanshi har kirari suke mashi me yan mata buhu buhu, sosai Nabeel yake masu barin kudi, domin seda Umma tasan yanda tayi tasa Abba yabashi ATM dinshi domin Nabeel yace mata yanason abashi yarika cirar kudinshi kawai. Duk wani abu da yakeso Ummace takesa Abba yana mashi koda bayaso domin Abba yana tsoron kada su batashi,amma matukar Umma tace ayi mashi dole yakeyi domin baya son bacin ranta dana Nabeel Hatta da shiga lecturers ba sosai suke yiba, domin yawancin malamansu duk Nabeel yagama siyesu, cikin lokaci kankani Nabeel yazama babban dan duniya, hatta dasu Saif dasuka dorashi akan harkar yanzu yafisu, sede duk abunsu basa shaye shaye. Wani dattijo ne zaune atsakar gidanshi, zekai shekara 50, sunanshi Mal. Labaran, kusa dashi matarshi ce me suna Zainab, se babban danshi me suna Abbas, wata budurwace me kimanin shekaru 20, zaune akusa da Ummanta. Mal. Labaran ya dago kai ya kalli diyarsu ahankali yakira sunanata. Sumayya, Alhamdulillahi babu abinda zamu ce sede muyima Allah godiya, domin yau ya cika mana burinmu nasan ganin kinsamu damar shiga wannan makaranta ta jami'a domin kema kisamu damar karatu kamar yanda kikeso. Kina ganin waccan shekarar saboda rashin kudin registration yasa muna kallo damarki ta wuce haka kika zauna agida shekara daya, gashi yanzu cikin sa'a munkara nema kuma kinsamu damar kara shiga wannan makarantar. Ganin zaki kara rasa wannan damar ne yasa na saida gonata ta gado wadda ita kadai ta rage mani aduk abinda na mallaka daga mahaifina, Allah yasani banyi niyar saida wannan gona ba, domin ina samu daga ita, sede tunanin danayi idan Allah yasa kikayi wannan karatu zamu amfana daga shi yasa na saidata. Gashi har an danyi nisa da fara karatun, amma waccan malamin da muke karatu dashi a masallaci shine yashige mani gaba aka gama komai dayake acan yake aiki. Sumayya kinga de cikin ku biyu danake daku ke kadaice kika samu sakamako me kyau har Allah yasa gashi zaki shiga makarantar jami'a. Duk da yayanki iyakarshi secondary amma kina kallo shima bezauna haka ba yana kasuwancinshi, kuma dama kowa da inda Allah ya tsaga mashi wajen cin abincinshi. Yanzu ranar litinin zaki fara zuwa makaranta kuma banyarda ki koma can da zama ba. Nafiso kizauna agida kirika zuwa kina dawowa gabanmu domin yanmatan jami'a mutane da yawa sun san halinsu, kuma wasu da yawansu rashin zamansu agaban iyayensu ne yasasu suke aikata abinda sukaga dama, domin sun san kome sukayi cikin makaranta zasu koma su kwana. In Allah ya yarda bazamu rasa kudin motar dazamu baki kije makaranta ba, kuma inaso Sumayya ki tsaya matsayin ki, jami'a ba kamar secondary bace, nasan yanda kike da son shigema yaran masu kudi lokacin kina makaranta, kuma nasha yimaki fada akan hakan. To wannan makaratar tasha bamban da waccan, dan haka ki kula da kanki, kedin bakowa bace, mahaifinki ba kowa bane face me walda, mahaifiyarki ba kowa bace face me saida kayan miya acikin gida, kina kallon gidan damuke ciki inbadan ina gyarashi ba dayanzu ruwa ya dade da tafiya dashi. Dan haka kizauna tare da dede ke, idan kika bari shedan yayi maki muguwar huduba Allah yasani munfita hakkinki, domin yanzu tun aduniya Allah yake nuna ma mutum kuskuransa. Kuma kinsan KOWA YATAKA DOKAR ALLAH! Tabbas Allah baze kyaleshi haka ba shima seya takashi. Allah yabaki sa'ar wannan karatu dazaki fara yasa kishiga a sa'a kuma yakareki daga sharrin masu sharri. Magana ta karshe kuma dazan maki itace, banaso koda wasa wai dan kinshiga jami'a kice zaki fara samun gyale acikin gidana, idan ma hijabanki sunyi kadan zan baki kudi ki kara yanko wasu, kuma kamar girman wadan da nasiyo maki zakisa. Ina fatan kinji abinda nafada maki? Kara dukar da kanta kasa Sumayya tayi hawaye suna zubo mata azuciyarta tana fadin wannan wace irin takurace? Mamanta tace to Sumayya inafatan kinji abinda Babanki yafada, kuma nasan bazaki taba bamu kunya ba, domin nasan kina da kokari kuma kina kiyaye duk wani abu daze bata mana rai. Allah yayi maki albarka. Abbas yace amin Mama, nima babu abinda zance sede ince Allah yabada sa'a, abinda baki gane ba kuma kada kiyi shiru kirika tambayar wadansa suka gane, Allah yakare mana ke daga sharrin mazan jami'a. Gaba dayansu sukace amin. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263. Ina godiya da irin addu'arku agare ni, Allah yabar zumunci😘😘😘 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part. 35 ⏩ 40 A dede bakin gate din makarantar aka sauke Sumayya, haka tafito sanye da doguwar hijabinta me hannu har kasa, fuskarta a daure kamar zatayi kuka, domin tunda tagama shiri agida take bacin rai. Gashi gaba daya 200 Babanta yabata tayi kudin mota 100 zuwa da dawowa ta kashe 100, ganin ranta abace yasa mamanta ta karata mata 50, haka tafito tana ta bacin rai, ga haushin hijabin data zumbula kamar meshirin zuwa islamiya ga haushin kudin da aka bata kamar zataje secondary. Kara kallon gate din tayi yanda manyan yan mata suke wucewa kowa taci gayunta, wasu ma amota suke wucewa, wasu hawaye taji sun taho mata, ga haushinta daya tasan idan kazo jami'a baka hadu ba bakowane yake kula ka ba, gashi ita bata san ko ina ba. Ganin mutane suna ta wuceta yasa itama ta fara tafiya har tashiga cikin makarantar, tsayawa tayi tana kallon yanda kowa yake harkarshi, wasu maza ne tare da mata wasu kuma su kadai ne. Wata kujera tasamu tazauna tabuga tagumi, batasan lokacin da hawaye suka fara zubo mata ba, jitake kamar takoma gida tace tafasa karatun. Yanzu duk burin dataci na zuwa jami'a ahaka ze kare? Tun tana secondary Allah yayita da son shiga cikin yaran masu kudi. Tana da son taga itama ana damawa da ita, amma gashi yanzu Babanta yakafa mata dokar sa hijabi, ina ma laifin yabarta tasa koda karamace. Lokacin da aka ce tasamu admission waccan shekarar har asusu tafarayi badan komai ba sedan tasayi gyaluluwan shiga makaranta. Hannu tasa ta goge kwallar datake zubo mata,dariya taji daga gefenta, saurin dago kai tayi tana kallon masu yin dariyar, tana kallonsu taga ashe da ita suke, wasu samari ne zasu wuce suka ganta tana kuka. Daya daga cikinsu yace abokina da alama wannan sabuwar zuwa ce, dariya dayan yasa yace kai bakaga yanda tasha wata hijab ba kamar meshirin gabatar da da'awa. Kara kwashewa sukayi da dariya suka wuceta. Wasu hawayen ne suka kara zubo mata, saurin tashi tayi ta nufi gate domin gaba daya makarantar ta fitar mata a rai, muryar wani taji yana mata sallama, saurin juyawa tayi seta ganshi sanye da manyan kaya da hula akanshi. Hannu tasa ta goge idonta tare da amsa mashi sallamarshi. Karasowa kusa da ita yayi yana fadin sannu ko, kiyi hakuri naji duk abinda wadan can suka fada maki, kuma naga kintashi kamar zaki fita daga makarantar. Ajiyar zuciya tasaki tana fadin ni wallahi bazan iya wannan makarantar ba, daga zuwa na har an fara mani dariya, kawai zankoma gida ince ma Baba na hakura. Murmushi yayi ganin yanda take kuka sosai. Kara matsawa kusa da ita yayi yace dan Allah kibar wannan kukan kada kitara mana mutane, kinsan fa haka jami'a ta gada, idan har mutum yazo yana bako dole ya fuskanci kalubale, musamman idan shikadai ne, kuma besan kowa ba. Duk wadan da kikaga sun saba to suma da haka suka fara, kuma idan kika koma gida shikenan kinjama iyayenki asarar kudin registration din dasuka maki, domin de makaranta bazata maida masu kudinsu ba. Shin ya sunanki ma? Sumayya, Allah sarki kinga sunan kanwata kenan, ni kuma sunana Naseer, muga wane course suka baki? Mika mashi takardar hannunta tayi tana fadin micro biology suka bani, murmushi yayi yana fadin ai course din mu daya ma. Wannan course form ne, zamuje kifara kaiwa ayi maki singning seki kwafi time table. Amma wannan badamuwa bane, yanzu muna da class, muje idan muka fito zan rakaki ki kammala komai, se in baki time table domin kisan time din da muke da class. Murmushi tayi tana fadin nagode yaya, shima murmushi yayi yace bakomai ai duk wanda yatemaki wani shima Allah ze temakeshi. Haka suka jera suka nufi class. Suna shiga aka bisu da kallo, wasu daga cikin maza suka fara fadin kaga class capting yau da wata mace. Dariya suka sa wani yace ina jide kanwarshi ce,wani yace bawani kanwarshi kila de shima yasamu kawa dama ai duk munafunci ne ustazancin nashi, dariya suka sa, duk abinda suke fada yana jinsu, banza yayi dasu yasamu waje yazauna tare da nunama Sumayya wajen zama. Haka tazauna ko kanta takasa dagowa domin gaba daya a tsarge take, haka malaminsu yashigo gaba daya class din akayi shiru. Tambayar abinda sukayi jiya yayi, Naseer ne yatashi yabashi amsa. Haka yacigaba da gabatar da darasi, yana cikinyi ya jefo tambaya, shiru ajin yayi babu wanda ya bada amsa, can malamin yaji an bada amsa a hankali, gaba daya ajin suka fara waigen wadda tayi maganar. Malamin yace wacece tayi magana? Naseer yace Sumayya ce malam, wacece Sumayya tashi tsaye, ai cikin Sumayya lokaci guda yafara kara, gaba daya jikinta yafara rawa, Naseer yace tashi mana babu abinda ze maki. Tana tashi kowa yabita da kallo, amma takasa daga idonta ta kalli malamin. Murmushi yayi yace mekikace? A hankali takara maimata abinda tace, malamin yace da kyau, kin bada amsa dede atafa mata. Gaba daya ajin ya dau tafi. Malamin yace amma ke bakuwa ce ko? Kai tadaga mashi, yace meye sunanki? Sumayya Labaran, yace da kyau, zauna. Nan fa ajin yafara surutai kasa kasa kowa da abinda yake fada. Ana cikin haka su Nabeel suka shigo. Zubaida da Khairat sun dauki wanka sunyi masifar kyau, suma mazan sun sha wanka, kowa yabisu da kallo, Sumayya kuwa sakin baki tayi tana kallonsu Zuby, sosai suka burgeta, jitake inama ace itace. Bayan sun zauna malam yaci gaba da darasinshi domin yariga yasaba da halin su shiyasa baya ce masu komai idan suka shigo yana ciki. Bayan yagama kowa yafita. Naseer shiya raka Sumayya har tagama abinda zatayi bayan sun dawo yabata time table ta kwafa, wani guri suka samu suka zauna, kallonta yayi yace lallai kanwata kina da maida hankali, duk da bada ke aka fara wannan course din ba amma gashi har kin fahimceshi, kinga nima zan karu dake kenan. Murmushi Sumayya tayi tace haba Yaya ai kaine zaka rika nuna mani abinda ba'ayi dani ba,dan naga semister har tayi nisa. Yace haka ne domin next week zamu fara test, Allah yaso kinzo da wuri. Haka suka cigaba da tattaunawa har lokacin shiga wata lecture yayi. Bayan sunfito sukayi sallar azahar, Naseer yace ma Sumayya suje suci abinci tunda karfe 4 zasu gama lecture, haka suka nufi wajen wata me saida abinci, dadi taji dabe kaita wajen yan gayu ba. Plate biyu yasa aka yimasu yabiya. Bayan sungama ta fara bude jaka tana tambayarshi nawa ne, murmushi yayi yace kibarshi kawai na biya mana, Sumayya tace anyi haka kuwa? Yace harma anyi, dariya suka sa yace muje mukara duba abinda aka mana kafin lokaci yayi. Haka suka gama lecture wannan rana Naseer ya rakota har bakin titi seda ta samu abin hawa sukayi musayar number sannan shima yatafi gida, domin shima dan bauchi ne. Sosai Sumayya taji dadin abinda Naseer yayi mata, duk da taso ace tafara haduwa da yan gayu. Tun daga wanannan ranar Sumayya tafara sakewa da makarantar, kullum suna tare da Naseer sede idan sukayi sallah take tafiya taci abinci dede kudinta domin ta lura idan suna zuwa tare shine zerika biya mata kuma tana jin kunya. Tun yana mata fada akan tadena tafiya ita kadai har ya kyaleta. Sede idan tagama su hadu wajen dasuke haduwa. Duk shige da ficen su Nabeel akan idanun Sumayya suke yinshi, sosai suke burgeta, wani lokaci setaji kamar tayi masu magana amma seta fasa domin bata ma samun lokacin ganinsu, wani lokacin suna cikin lecture suke fita. Kuma kafin sutashi sun bar makarantar, haka ta hakura tacire ran zata shiga cikinsu, a haka tafara samun kawaye acikin course dinsu, domin Sumayya akwai kokari duk abinda aka masu dan da nan take daukeshi, kuma ko assignment aka basu lokaci guda takeyinshi, idan bata gane ba Naseer ya nuna mata, shima idan be gane wani abun ba ita take temakonshi. Sosai shakuwa takara shiga tsakanin Sumayya da Naseer, suna mutunci sosai har gidansu yana zuwa, wasu da yawa suna tunanin soyayya sukeyi. A haka har suka yi mid semister test, kuma duk wadda sukayi Naseer da Sumayya suna cinyewa, sosai iyayenta sukejin dadin yanda take maida hankali. Lamarin su Nabeel kuwa abun ba'a magana, domin neman matan Nabeel yayi yawa, kuma yawanci duk abinda yakeyi Ummanshi itace take goya mashi baya, kuma take kareshi a wajen Abbanshi. Itama harkarta kawai takeyi ta neman mata, domin yanzu ta kware sosai, hartafi Lawisa domin ita ba kananan kudi take sakar ma mutanan ta ba. Abba ne a falo yana ta zagayen falonshi fuskarshi cike da damuwa, Ummace tayi sallama tana zuwa tace Alh, lafiya na ganka cikin yanayin da bantaba ganinka ciki ba? Juyowa yayi yasamu waje ya zauna yana fadin, dole ki ganni cikin wannan yanayin. Na dade inajin jita jita akan halin da Nabeel yake ciki, amma bantaba yarda ba, ayau naje kuma naganema idona, Nabeel da abokanshi sun fito daga gidanshi na Nasarawa tare da wasu yan mata, bakiga yanayin shigarsu ba. Daure fuska Umma tayi tace dakata Alh, dama tun ba yanzu ba nafara gane kana zargin danka,dama tun kafin kabashi mukullin gidan kafara korafi akanshi, dama ai bakin iyaye yana kama dansu, kuma kaine kafara yimashi bakin hakan. Kuma ni wallahi bazan taba yarda Nabeel yana neman mata ba. Kuma da kake maganar kaganshi sun fito da mata daga gidanshi wani abu kaga suna aikatawa? Kada kamanta ko kotu kaje dole seka gansu turmi da tabarya kuma dole seda shedu 3. Dama ai dole kaga Nabeel da mata domin ba makarantar maza zalla ka kaishi ba, kuma kada kamanta Nabeel cewa yayi zasu rika zuwa karatu agidanshi idan sun gaji, shikenan kuma sekace wai yana kai mata gidanshi, ai dole yayi abota da mata ko kaima zakace dakayi makaranta bakayi abota da mata ba? Dago kai Abba yayi yana kallon yanda Umma ta rufe ido tana ta masifa abinda bata taba yimashi ba. Hannu tasa kamar tana goge kwalla tace shikenan nagode Alh, tunda har zaka iya daukar maganar mutane, ashe dama baka san akwai masu jin haushin yanda kakeson Nabeel ba? Idan baka sani ba kasani akwai mutane dayawa dasuke jin haushinka kaida Nabeel. Kukan karya tasa,tana fadin yau ka nuna mani kafara gajiya damu, saurin rufe mata baki yayi yajawota ya rungumeta yana fadin kidena fadar haka, abinda nagani ne kawai na fada. Nabeel danmu ne, bantaba zuwa maki da maganar da mutane suka fada mani ba seda yau na tabbatar da kaina. Duk yanda mukeson Nabeel dole semun kula da tarbiyarshi, domin masu iya magana suna cewa kasa yaro kuka tun kafin yasaka kuka, kuma icce tun yana karami ake lankwasashi, idan ya bushe sede ya karye. Wannan dalilin ne yasa naki kai Nabeel waje yayi karatu. Domin ina tsoron turawa su bata mani yaro, to meyasa yanzu dayake gabanmu bazamuyi kokarin gyarashi ba? Gara ace bama sonshi yazama na kirki da ace son da muke nuna mashi ya kaishi ga halaka, yau kome Nabeel ze zama daga gare mune, idan yazama na kirki mune, idan yazama na banza mune. Idan har Nabeel zerika zama tare da mata suna karatu acikin gida, tabbas wata rana shedan zeyi tasiri azuciyarsu harsu kai ga aikata abinda ba'aso. Dan haka inaso kibani goyon baya muyi kokarin tsaida wannan barnar datake niyar shigo mana cikin gida, bawai dan bama son Nabeel ba. Tashi zaune Umma tayi takama hannun Abban Nabeel tace dan Allah Alh, kabar yaron nan yayi rayuwa me dadi, Nabeel fa ba mace bane, mezesa murikeshi agida mu hanashi more rayuwarshi, wallahi a wani wajen kamar Nabeel iyayenshi sun sallama ma duniya shi, domin shi namiji ko ina ze iya shiga aduniya, kuma kome yayi ado ne agareshi. Amma idan muka fara takura mashi tabbas zamu jawoma kanmu babbar matsalar da semunyi kuka da idonmu, kuma yanda yasaba jindadi rayuwarshi ze iya bijirema umarninmu matukar yaga munaso mutakureshi waje guda. Amma kabarni dashi zan san yanda nayi na hanashi kai mata gidanshi, idan zasuyi karatun zance surikayi a makaranta. Haka Umma tayita kwantar ma Abba hankali har ya hakura yabarta tayima Nabeel magana. Tun daga lokacin da Umma tafadama Nabeel Abbanshi yakusa karbe mukullin gidanshi Nabeel ya canza taku, sam babu wanda ze iya gane lokacin da suke shiga da kuma fita, alokacin ma yakara maida hankali wajen neman mata. Sumayya ce tashigo cikin makaranta tana ta sauri domin yau ta makara, sam bata kula dasu Nabeel ba da suke zaune saman motarsu suna fira, su Zuby suna daga cikin motar suna shan lemu. Garin sauri tayi tuntube litattafan dasuke hannunta suka zube. Kafin ta duka ta dauka iska ya figi wata takardarta, saurin kwashe sauran tayi ta ruga domin ta dauko takaradar, jikin wani icce takardar ta tsaya, dede kusa da inda Nabeel ya dora kafarshi yana zaune saman mota. Hannu ya kai ze dauki takardar yaga kota mecece, yana kai hannunshi Sumayya tayi saurin dauke takardarta. Tana dago kai idanuwansu suka sarke da juna, cak suka tsaya suna kallon kallo. Sumayya ce tayi saurin dauke manyan idanuwanta daga kallonshi ta juya domin ta tafi class, lumshe ido Nabeel yayi domin bakaramin tafiya dashi tayi ba. Dariya Saif yasa tare da dukan kafadarshi yana fadin to mayen mata kallon ya isa haka. Murmushi Nabeel yayi yace tahadu Saif, kaga yanda idanuwanta suke kuwa? Kara lumshe ido yayi yana murmushi. Najib yace to wannan de ustaziya ce garama kamaida zalamarka. Saurin saukowa Nabeel yayi yana fadin wallahi inasonta. Kama hanunun Saif yayi yana fadin da gaske inasonta, ni idan ma Abba ze aura mun ita wallahi zan aureta. Dariya suka samashi ganin yanda ya rikece masu, kamashi Saif yayi yana fadin haba abokina kazama namiji mana,kama dena maganar aure haryanzu fa baka kai shekara 25 ba. Zuby ce tafito tana fadin haba Nabeel duk yan gayun dasuke makarantar nan basu isheka ba seka jawo mana wannan kazamar? Yanzu daka tabata zata fara cewa Allah yace annabi yace, kai bakaga irin shigarta ba? Wani irin kallo Nabeel yayi mata hakan yasa tayi saurin hadiye sauran maganarta. Khairat ce tafito tana fadin haba Nabeel ai abun be kai haka ba, karka damu wannan yarinyar course dinmu daya da ita, kai baka taba ganinta ba? Girgiza kai Nabeel yayi, Khairat tace to kada kadamu insha Allah nizan shawo maka kanta. Murmushi Nabeel yayi yace nagode khairat, idan kikamun haka tabbas kin biyani, domin ina ganin nasamu matar aure dan yakamata nima nabar wannan shiritar nashiga sahun manya in kyaleku kucigaba da harkar ku. Saurin kallon juna su Saif sukayi, murmushi Saif yayi ya dagama Najib gira, lokaci guda suka saki wani mugun murmushi. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part 40 ⏩ 45 Shiga mota Nabeel yayi yana fadin zanje gida inga Umma se kun taho, Khairat dan Allah kimun wannan kokarin. Murmushi khairat tayi tace angama, Saif yace wai duk ganin ustaziyar ne yasa ka wannan saurin? Nabeel yace no, kawai inason ganin Umma ne. Najib yace shikenan semun hadu. Yana tafiya Najib ya kalli Saif yace lallai jindadin mu yakusa zuwa karshe, yanda Nabeel yake mana facaka da kudi kuna ganin idan yayi aure zecigaba da abinda yake mana? Kunaji de yace idan yayi aure ma kyalemu zeyi. Murmushi Saif yayi yace kai har wannan maganar tafara damun ka? To wai duka nawa Nabeel yake ma da har ze fadi magana kayarda, idan baka sani ba, Nabeel mota ne, ni kuma nine sitiyarin nashi, dan haka kabarni dashi, bazan taba barinshi yayi aure yanzu ba. Zuby tace haba dear kai kuma ina ruwanka da aurenshi? Hannun Zuby Saif yakama yana fadin nasan Nabeel da gaske yake yana son waccan yarinyar, matukar ya aureta nasan zata iya rabamu dashi, kuma kinga ku dukanku tare kuka gammu dashi. Murmushin gefen baki yayi yace bama zeyuwu ba, aure? Muna a 100 lvl yace zeyi aure, tabbas nasan iyayenshi zasu iya mashi auren gata domin suna matukar kaunarshi, amma nikam bazan bari yayi aure ba, idan har yana sonta ni nasan yanda zamu jawo ra'ayinta tadawo cikinmu, amma Khairat inaso kibi abun a hankali. Dariya Najib yasa yana fadin shegen kaya, wallahi kai mugu ne, nasan ma zataso Nabeel domin ya hadu, kuma kasan shawo kan mace ba abu bane me wahala. Haka suka rika tsara duk yanda zasu hana Nabeel aure. Saurin dago kai Umma tayi alokacin dataji abinda Nabeel yafada, Abba kuwa murmushi yayi yana shafa kanshi yace lallai yarona ya girma, kada kadamu nafada maka babu abinda zaka nema awajena banyi maka shiba matukar be saba ma Allah ba. Saurin kallonshi Umma tayi fuskarta adaure tace haba Alh, wace irin magana ce haka? Duka nawa Nabeel yake daze fara maganar aure yanzu? Idan kamanta bara na tuna maka shekarar Nabeel 22 yaushe kake tunani zamuyi mashi aure. Gaskiya nide banyarda da wannan maganar ba. Murmushi Abba yayi yace haba Umman Nabeel, tsoro kike kada ace kamarki kinfara aje jika? To meye dan munyima Nabeel aure yanzu? Kada kimanta babban abinda yake hana mutane aure shine rashin kudi. Meye Nabeel bedashi? Ko yanzu yace bayason makaranta yanada hanyar daze iya rike mace sama da 2, dan haka kibar wannan maganar, tunda kikaga yazo yace yana son aure toshikadai yasan abinda yakeji, kuma musulunci be hana muyi mashi aure dan yana da shekara 22 ba. Kamo hannun Ummanshi Nabeel yayi kamar zeyi kuka yace Umma dan Allah kibarni na aureta, wallahi yau kawai nafara ganinta amma bakiji yanda nakejinta araina ba, kinga idan nace sena gama karatu ita mace ce iyayenta zasu iya yimata aure a koda yaushe dan Allah Umma. Hannu tasa tana shafa kanshi tace shikenan Nabeel naji, banaso kabari hawaye su zubo maka saboda mace, kada kataba bari kazama rago akan soyayyar mace har ka bari tagane, domin zata wahalar da kai, kuma idan har kanaso naso duk macen dazaka aura to kada kabari son da kake mata yafito fili. Bazan taba bari wata mace ta maida mani yaro bawa ba. Kallon Alh, tayi tace naji ze aureta amma nima inada sharadi. Alh, yace fadi koma wane sharadi ne tunda kin amince da bukatarmu. Nabeel bazeyi aure yanzu ba harseya gama 100 level tunda yanzu sun kusa fara jarabawa. Murmushi Abba yayi yace dan wannan babu matsala kafin lokacin ma sun kara fahimtar juna, dafa kan Nabeel yayi yace yarona kada kadamu kamar gobe ne zakaga lokacin yayi, kaga kaima sekaje ku kara fahimtar juna da ita. Murmushi Nabeel yayi ya rungumeshi yana fadin nagode Abbana, nagode Ummana. Dariya suka samashi, Umma tace to mu baka fada mana sunanta bama. Sosa kai Nabeel yayi yace Umma nimafa yau nafara ganinta ammade tana da kyau sosai. Abba yace to idan kaje ka tambayo sunanta seka fada mana. Tun daga wannan rana Nabeel yadena fashin makaranta, kuma da wuri yake zuwa, haka yasa su Saif suma suka rika zuwa kullum sede idan sun tashi sutafi yawonsu. Sam yarage kula yan mata sede idan abunshi ya motsa. Kullum idanuwanshi akan Sumayya, sosai sonta yakara yawa a zuciyarshi, duk lokacin da yayima Khairat magana akan taje wajanta setace e taje amma taki kulata. Ganin Nabeel zeje wajenta da kanshi yasa Saif yace kai wasa fa take maka. Murmushi Nabeel yayi yace metace to? Saif yace tace kabari adawo next semister saboda yanzu karatun exam ne agabanta. Wani murmushi Nabeel yasaki yana fadin zanjira dan bana son in takura mata. Kuma ma su Abba sunce damun gama 100 lvl zamuyi aure. Dariya suka sa mashi Najib yana fadin lallai muna da babban biki. Saif yace yanzude tunda ta amince zata kula ka idan angama exams se kacigaba da harkar ka. Haka suka shiga mota tare da fita suna cike da nishadi. Sumayya kuwa kullum tunanin Nabeel take, tun ranar data ganshi taji tana sonshi, bare kuma da kusan kullum take kamashi yana kallonta, atunaninta ko sonta yakeyi amma ganin yanzu yama dena yawan zuwa makaranta tagane ba sonta yake ba. Haka suka dage wajen karatun exam ita da Naseer da wata kawarta Mansura, kullum da sun fito daga class suke tafiya library karatu, duk lokacin da Nabeel yaso ganinta haka zeshigo class ya zauna yasa bakin glass yayita kallonta batare da kowa ya gane ba. Da haka suka fara exams dinsu ta first semister cikin sa'a suka gama lafiya, sede ba kowace exam su ke zuwa ba, haka suka gama suka tafi hutun sati biyu. Aranar har gida Naseer yaraka Sumayya, sun dade suna fira kafin yatafi. Tunda suka rabu Naseer ya tabbatar ma kanshi son Sumayya yake da gaske, domin bayan rabuwarsu yaji kewarta sosai, kuma kullum seya kirata sun gaisa, yaso yafada mata yana sonta seyayi tunanin kada tace bata sonshi kuma alakarsu ta baci. A ranshi ya bari duk ranar data rage masu saura shekara daya su gama ze fada mata yana sonta. Nabeel ne zaune shida su Saif gaba daya ranshi abace yake, Saif ne yace abokina yaude ka kwantar da hankalinka na gano maka gidansu Sumayya, saurin kallonshi Nabeel yayi tare da sakin murmushi yana fadin dagaske kake? Saif yace wallahi da gaske nakeyi. A cikin abokanmu akwai wanda nasa ya dubo mani gidansu, Nabeel yace tashi mutafi yanzu dan Allah, Saif yace haba de, kabari seda dare ai zefi amma yanzu kawai semuje fira ido naganin ido. Nabeel yace shikenan nagode. Tsaye suke a jikin motar Nabeel sun sha manyan kaya sosai sukayi kyau bakamar Nabeel, domin baya sasu daga juma'a se juma'a, su biyu kadai sukaje shida Saif. Yaron da suka aika ne yafito yana fadin ance gata nan zuwa, kudi Nabeel yaciro yabashi. Tadan dade kafin ta fito, akofar gidansu ta tsaya tana jiransu su karaso domin Babanta ya hanata barin kofar dakalin gidansu idan zatayi fira, ganin bata karaso ba yasa Saif yace abokina muje kasan mata da sarauta, takawa sukayi suka matsa inda take. Da sallama suka isa, Sumayya kanta na kasa ta amsa tare da gaishesu. Nabeel se murmushi yake, Saif ne yace Malama Sumayya kiyi hakuri bakisan da zuwan mu ba gashi mun fiddoki. Murmushi tayi tace ai bakomai. Saif yace nasan kila baki gane mu ba kodan duhu ne yasa hakan. Ni sunana Saifullahi, wannan abokina ne sunanshi Nabeel, kuma muna karatu a makarantar da kike asalima course dinmu daya. Saurin dago kai Sumayya tayi domin tasan sunan Nabeel a wajen yan course dinsu, kasancewar akwai hasken wuta yasa ta iya ganin fuskarshi dauke da murmushi. Tsayawa tayi tana kallonshi, fuskarta dauke da mamaki, jitake kamar mafarki takeyi. Tafi Saif yayi ganin yanda suke kallon junansu, saurin kawar da kanta tayi cike da kunya, Saif yace nasan yanzu kin gane mu ko? Daga kai tayi tana murmushi. Saif yace to Sumayya gamu munzo gareki, duk da bamusan ya zaki karbe mu ba. Abokina tun ranar daya fara ganinki sonki yashiga zuciyarshi, munso muyi maki magana se mukayi tunanin kada mu hanaki karatu, shiyasa yanzu da aka gama mukace bara muzo, ina fatan bamuyi shishshigi ba? Dukar da kanta tayi tana murmushi, jitake kamar a mafarki wai Nabeel ne yake sonta? Lallai tayarda mahakurci mawa daci, wasa ta cigaba dayi da hannunta batace komai ba. Saif yace Sumayya nasan zakiyi tunanin yanayinki da namu ba daya bane,to kada wannan ya dameki, domin ni nasan abokina betaba ganin wata mace ya rude sama da ke ba, ke ko abinci sena matsa mashi yakeci, so dan Allah kada ki watsa mana kasa. Sumayya tace to nagode da zuwanku, amma Saifullahi kana ganin yanayin Nabeel da ni yadace kuwa? Kalli fa yanda gidanmu yake, kana tunanin banyi zari ba idan nace zan amince da soyayyarshi? Gyara tsayuwa Nabeel yayi tare da shagwabe fuska yace haba Sumayya, meye wani abun fadar haka? Kinsan ma wani abu? Abbana yace ze nema mani aurenki matukar muka gama 100 lvl, kuma Ummana ma tana sonki to meyasa zaki fadi haka. Dariya suka sa mashi ganin yanda yayi da fuska yana koro bayani. Dafashi Saif yayi yace ina ruwan dan Abba da Umma, kai kuma waya fada maka anama budurwa shagwaba? Ai itace yakamata ace tana maka shagwaba. Duka Nabeel ya kaimashi yana murmushi, yace ai gaskiya nafada ko Sumy ta? Murmushi tayi tana kallonshi. Saif yace da alama de munsamu karbuwa, wannan fara'a haka. Nabeel yace yauwa Saif kamanta baka fada mata ba. Kallonshi sukayi, yace Sumy Allah yasa baki kula kowa? Kinsan fa ina da kishi, kuma ni banaso arika hadani da wani. Dariya suka kara samashi, Saif yace to tajika, kaga dare yanayi kada ayi mata fada agida yakamata mutafi. Juyawa Nabeel yayi yaje yadauko wata leda acikin mota, kayan zaki ne kawai aciki, yana zuwa yace Sumyta ga sweet nasiyo maki, karba tayi tana murmushi tace nagode. Hannu yamika yana fadin muga wayarki in samaki number ta. Mika mashi tayi, bayan yasa mata yace gashinan nasamaki My King, zaro ido tayi tana kallonshi, gira yadaga mata yana fadin ko beyi ba? Idan beyi ba ki canza to. Ni kuma nasa maki Sweet Sumy. Karar wayarta ne ya katse mashi maganar da yakeyi, saurin kallonta yayi yana jira yaji waye, kin daukar wayar tayi, Nabeel yace waye ne? Murmushi tayi tace yaya Naseer ne. To meyasa baki dauka ba? Kawai nasan idan yafara mani fira seya dade shiyasa nabari idan nakoma gida se muyi waya. Saif yace babanku daya dashi ne? Girgiza kai tayi tana fadin class capting din mu nefa. Saif yace ok wannan ustazin zakice mani, na ganeshi. Nabeel yace saurayinki ne ko? Tace a'a kawai muna mutunci dashi shine guardian dina. Nabeel yace ai kuwa wallahi daga yau kun rabu, daga yanzu nine komai naki, yanda yayi maganar fuskarshi adaure yabasu mamaki, zatayi magana kenan Nabeel yace Sumy kishiga gida kada Baba yayi maki fada. Murmushi tayi tana fadin nagode, haka suka tafi Nabeel yana me cike da farin ciki. Sumayya kuwa tana shiga ciki Babanta yafara tambayarta waye, nan tayi mashi bayaninshi da abinda yace. Wani murmushi Mamanta tasaki tana fadin toshidin dan gidan waye? Sumayya tace naji de ana fadin dan gidan Lamido Saraki ne, washe baki Mamarta tayi jin abinda tafada. Amma ganin Babanta ya daure fuska yasa tayi saurin boye murnarta. Kallon Sumayya yayi yace kinajina? Inaso daga yau kicire tunanin kara tsayawa da wannan yaron, domin kwata kwata ba sa'anki bane, kilama kin girmeshi, sannan kuma ni bazan taba daukar diya ta in bama wannan yaron ba. Tabbas nasan mahaifinshi mutumin kirkine, amma mutane suna jita jitan ba'asan asalin Uwarshi ba, kanwarta da sukazo garin nan tare bata da aiki se bin maza, yanzu ma naji ance har mata take bi, kuma asalinsu yan tasha ne, domin akasuwa suke saida abinci. Mamanta tace malan kai waya fada maka haka? Murmushi yayi yace kada kimanta nidin meshiga cikin mutane ne, kuma sanin labarin masu kudi ba abu bane me wahala, domin basuda wani sirri komai nasu abude yake dasu da yan siyasa. Waye besan yaronshi mane min mata bane? Saboda haka komin kyan halin mahaifinshi ni bazan iya amincewa da tarayyarku ba, barema har kizo kifada mani wai mahaifinshi zezo nema mashi aurenki. To bara kiji Sumayya, yanda na saida gonar gadota na hakura da ita dan kiyi karatu, haka babu wanda ya isa yasa nayi maki aure batare da kingama karatunki ba. Dan haka kicire tunanin yin aure azuciyarki harsekin gama makaranta. Mamanta tace haba malan ya zakace haka, yanzu fa ba zamanin da bane, yanzu rayuwar tacanza, kana ganin kananan yarama aure ake masu, amma yazakace seta gama shekara 4 kafin kayi mata aure, idan kuma takasa daukar wannan hukuncin naka fa? Hannu yadaga mata yana fadin ya isa Zainab, banaso kiyima diyata mugun baki, ni nasan irin tarbiyar dana bama diyata, kuma nasan bazata taba aikata wani mugun abu ba, dan haka kisani wannan yaron da kuke karatu Naseer shi kadai nayarda kucigaba da alaka dashi, daga yau na hanaki fita fira da kowa, idan Naseer ne yazo ku gaisa yashigo zaure. Domin nasan dan gidan mutunci ne, kuma nasan yana temakonki akan karatunki, daga bashi ba banaso inkara ganin kowa a kofar gidan nan. Tashi kitafi. Haka tashiga daki cike da bakin cikin abinda Babanta yake mata. Tadade tana jin haushin irin takurar da yake mata, duk da yanda yasata saka hijabi amakaranta hakan be hanata samun saurayi dan gayu ba, gashi kuma yanzu yana so ya rabata dashi, saman katifar ta tafada. Wayar tace tafara kara tana dubawa taga my king, murmushi tasaki tare da gyara kwanciya tadauka, sun dade suna firar soyayya ita da Nabeel, cikin lokaci kankani yakara saye zuciyarta da muryarshi medadi da kalamanshi masu cike da shagwaba. Seda suka dauki kusan awa 1 da rabi suna fira kafin sukayi sallama, rungume pillow din ta tayi tana jin son Nabeel yana kara shigarta, hakika tasamu irin saurayin datake so, koba komai itama zata fara fasowa a cikin makarantarsu, domin duk wanda zeganta da Nabeel dole yakara ganin girmanta. A hankali tace Baba sede kayi hakuri, domin son Nabeel yadade azuciyata tun kafin ya furta mani. Tabbas zan san yanda zamurika kasancewa atare batare da Baba yasani ba. Juyi tayi tare da kara rungume pillow dinta. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part 45 ⏩ 50 JINJINA GA DUKKANIN MASOYANA, INA MIKA SAKON GAISUWA ZUWA GAREKU, NAGODE DA ADDU'ARKU AGARENI ALLAH YABAR ZUMUNCI😘😘😘😘 Tun daga wannan rana Nabeel da Sumy suka kulle, soyayyar gaskiya sukema junansu, acikin kwana biyu kadai amma jisuke kamar sunyi shekara da fara soyayya,duk yanda Nabeel yaso yazo gidansu Sumy ta hanashi. Daya gaji ya tambayeta dalili, setace Babanta ne ya hanata fita fira yace se tagama karatu, Nabeel yace amma baki fada mashi labarina ba? Tace se jiya nafada mashi shine yace to inbari sena gama second semister sannan mufara fira. Shiru Nabeel yayi can yace amma Sweet kinsan bazan iya hakurin rashin ganinki har mu koma makaranta ba ko? Jinjina kai tayi kamar yana ganinta tace wallahi nima my king bazan iya hakurin rashin ganinka ba. Nabeel yace kinga dole ki samo mana mafita, Sumy tace shikenan ai Ummana nasan zata kareni, anjima zance mata zani gidan kawata da yamma, zanje bakin gate din makarantarmu seka sameni acan. Kiss yayi mata ta waya yana fadin nagode sosai, lallai yau zamusha fira. Babaye ne suka fito shida wata yarinya me tallar gyada, a kalla bazata wuce shekara 17 ba, se washe baki yake haka suka fito daga bangarenshi, suka nufo hanyar gate. Ada ce tafito zataje kiran da Umman Nabeel take mata,domin tunda Nabeel yagama yayinta yadena kulata, sede idan yazo bacci yana bukatar ta sannan yake kiranta su kwana tare, shiyasa yanzu yake mata wahalar gani, sede taje tayi mashi aiki kawai. Tsayawa tayi tana kallon yanda Babaye yake kamo hannun metallar suna ta dariya, tsaki taja tana fadin wannan tsoho dashi amma besan ya girma ba, yarika neman diyar cikinshi. Allah yasa wata rana Alhaji yaganka. Wucesu tayi tashiga part din Umma, dede sun kai bakin gate yaji karar horn din Abba, a kidime ya ruga sam yamanta da yarinyar, bayan ya bude mashi yashigo yarinyar ta nufi gate tana ta sauri, bayan yafito yanufi Babaye da gaba daya hankalinshi atashe yake. Bayan sun gaisa Abba yace Babaye wannan yarinyar fa daga ina? Hannu yadora a kai yana sosawa yace wallahi me tallar gyadar datake kawo mani ce, to yau tazo bakin gate bata ganni ba shine tashigo, to nima nafito daga daki naganta tsaye abakin dakin gate shine nazo nasiya. Kallon tuhuma Abba yayi mashi yace, ammade kafada mata kada takara shigowa wajen dakin ka, kasan sharrin zuciya, kuma mutanan gidan zasu iya zargin wani abu. Babaye yace haka ne, ai bata taba shigowa bama, kawaide dan taga nasaba siye shiyasa da bata ganni ba tashigo. Abba yace Allah ya kyauta ya shige ciki. Yana shiga ciki yaji beji motsin Umman Nabeel ba, hakan yasa ya nufi bangarenta, ita kuma alokacin suna can wata yarinyar ta tazo suna shirin fara aikata masha'arsu, se yarinyar tace tana jin kishi, Umma tayi murmsuhi tace to bara na kawo maki ruwa, kiyi hakuri na manta ban kawo maki komai ba, wallahi duk kingama rudani ne da wannan kwalliyar taki. Haka tafito jikinta daga ita se towel, tana fitowa dakinta taci karo da Abba, saurin ja baya tayi cike da firgici, har seda towel dinta yakusa faduwa, saurin kamoshi tayi, shima Abba yayi saurin zuwa kusa da ita ya rikota. Idanuwanta a waje take kallonshi, janta yayi ganin a firgice take suka nufi dakinta. Saurin ja dabaya tayi tana kokarin seta kanta tace wallahi kabani tsoro, wanka fa zanshiga naji inason insha ruwa shine nafito kawai sena ganka. Murmushi yayi yace ai naga alama, muje dakin se inkawo maki ruwan kinga nima se ayi wankan dani. Saurin kamo hannunshi tayi tana fadin muje kawai insha da kaina, kallonta yayi yace towai meyasa bakiso inshiga dakin? Murmushi tayi tace bakomai nasanka idan kashiga hanani wankan zakayi kuma sauri nakeyi domin wata kawata zatazo karabar wasu kaya da Lawisa ta aiko mani. Murmushi yayi yace to muje kisha ruwan nima mantuwa nayi nazo in dauka, ajiyar zuciya tasaki tana fadin nide nasan ai ba lokacin dawowarka bane yanzu. Bayan ta sallameshi yatafi, seda taga Babaye ya kulle gate sannan tayi saurin komawa tana fadin Allah nagode maka daka rufa mani asiri, daban fito ba yau daya kamani dumu dumu, haka takoma suka cigaba da aikinsu. Kamar yanda Sumy tashirya haka ta fadama Mamanta, Maman tace to Sumayya kada kidade kinsan halin babanki, Sumayya tace kai Mama, yanzu shikenan ni arayuwata bazan rika fita ba, duk wani jin dadi kina gani Baba ya tauyemunshi kamar wanda beyarda dani ba. Tsaki Mamar taja tana fadin nima narasa wannan bakin hali irin na malan. Kina ganin yanda 'yar gidan Laure take tara manyan samari a kofar gidansu,rannan naje gidan bakiga yanda wani saurayinta yakawo mata kaya ba, itama kanta uwar dubu 5 yabata, amma shikenan ni se ya hanaki sauraren kowa. Idan kyau ne ai kinfita kyau, na tabbata dakina fita samarin dazaki samu se sunfi nata yawa, dan haka ni bazan hanaki fita ba, domin kowace Uwa tanaso taga itama ana kula 'yar ta, ai ba bokon zamu kai maki daki ba, idan kina kula samarin da haka zamu fara tara kudin kayan dakinki. Kitafi idan yazo nasan yanda zan ce mashi. Godiya tayima ta tafita cike da farin cikin samun goyon bayan Mamanta. Nabeel ne tare da Saif se faman duba agogo yake yana jan tsaki, dariya Saif yayi yace ka kwantar da hankalinka, tunda de tace zatazo zata zone, Nabeel yace kallifa har 4 da rabi da kusa, yaushe tazo har mukayi fira, kuma nasan da taga magriba tayi zatace zata tafi. Saif yace amma idan tazo kawai kutafi gidanka, domin idan kuka tsaya cikin mota wani ze iya ganinta kaga kada yafadama Babanta. Nabeel yace wannan ustaziyar ce zata yarda, Saif yace tana fa sonka, duk abinda kace mata nasan zata yarda matukar baka nuna mata son da kake mata yafi nata yawa ba. Kuma kasan halin mata, idan har kanaso soyayyarku tayi karfi to dole se kuna samun exchanging na feelings shine abunda ze kara sa Sumy ta mace a kanka kuma ka tsaya mata a zuciya takasa mantaka. Nabeel yace ina tsoron kada na tabata tacemun dan iska. Saif yace kanaji ko? Cikin dabara zaka fara taba hijabinta, kanayi kana kallon fuskarta, idan kaga bata canza fuska ba, to kayi kokarin kama hannunta, shima idan bata hanaka ba, to tabbas bazata hanaka komai ba, inaso ayau kasamu kadanyi romancing dinta ina me tabbatar maka bazata iya kwana daya bata ganka ba, daga haka kuma se ka cigaba da buga game kawai, dariya sukasa. Nabeel yace shikenan, karar wayarshi ce ta katseshi, saurin dauka yayi yana fadin haba sweet haryanzu? Dariya tayi tana fadin ina bakin gate din makaranta, murmushi yayi yace muma gamu nan cikin makarnatar ai, bara mufito. Suna zuwa Saif ya bude mata baya yana fadin kishiga kada yan sa ido suganki, dariya tayi tashiga, bayan sun bar wajen ta gaishesu, Saif yace haba Sumy yazaki sacema abokina zuciya kuma kirika hanashi ganinki? Dariya tayi tana fadin ai ba laifina bane shima yasani. Saif yace aikuwa tunda kuna son junanku dole kusamu mafita, kinga yanzu duk inda zakuje dole asamu wasu wadanda suka sanki, shiyasa nace kawai kuje gidanshi kusha firarku acan, kinga babu wanda zesan kuna tare. Shiru tayi gabanta yana faduwa, Saif yace ya naji kinyi shiru ko bakiyarda da abokina bane? Murmushi tayi tace haba de, shikenan hakan ma zefi, Saif yace yauwa kinga nima budurwata tana can tana jirana agidan semu hadaku zumunci ma, akwai budurwar Najib ma kinga akwai yan uwanki mata acan ma. Ajiyar zuciya tasaki jin ance akwai mata agidan, Saif yace waini abokina tun dazu ka kosa Sumy tazo amma tazo naga kayi shiru se murmushi kake, Nabeel yace ai kasan idan farin ciki yayima mutum yawa yana kasa magana, dariya sukasa mashi. Bayan sun isa gidan Saif yafita ya bude masu gate suka shige, haka Sumy tafito kamar tanajin tsoro, a bude suka samu kofar, suna shiga suka iske su Zuby sunata kallo suna dariya, Khairat da Najib suna zaune a kujera daya tana kwance a jikinshi. Zuby kuwa wasu kana nan kaya ne ajikinta ta bazo gashin doki, tana ganin Saif tayi saurin tashi ta rungumeahi, Sumy kuwa da kallon mamaki tabisu, gabanta se faduwa yake. Daure fuska Nabeel yayi ganin haka yasa kowa yakoma mazauninshi. Bayan sun zauna Saif yace Zuby, Khairat gafa Sumy yau tazo mana ziyara, murmushi sukayi Zuby ta tashi tadawo kusa da ita tare da kama hannunta tana fadin sannu da zuwa Sumy, hakika labarinki yarigaki sani a wajenmu. Kin sace zuciyar Nabeel, inafata bazaki kara bari yasha wata wahala ba? Murmsuhi Sumy tayi tace insha Allah, khairat tace sannunki da zuwa, inafatan zaki saki jikinki damu, domin daga yau munzama yan uwa, dadi Sumy taji zata zama kawar yan gayu, tace nagode da karramawarku. Najib yace sannu da zuwa Sumy, tace yauwa, Najib ko? Dariya suka sa yana fadin nasan Nabeel ze fada maki ai, tashi Zuby tayi tana fadin bara nakawo maki lemu, Saif yace abokina kuje daga ciki kusha firarku kada mu hanaku sakewa ga lokaci yana tafiya gara mu maidata dawuri domin gobe. Nabeel ya kalli Sumy seya sadda kai, tsoro yake kada yace suje daki tayi mashi wani zargin, murmushi Saif yayi yace Sumy tashi muje in rakaki naga alamar kunyarki yakeji, murmushi tayi ta tashi tabi bayanshi, suna tafiya Najib yace shegen kaya, wai yau kaine ake tayawa kula da mace. Murmushi Nabeel yayi yana fadin ba dole inji tsoro ba, kasanfa ustaziyace kada tayi saurin ganoni ta rabu dani, dariya sukasa yatashi yashiga daki, Zuby kuma ta kai mata lemu. Saif yace to asha fira lafiya nima zanje inyi tawa firar. Yana fita Nabeel ya matso kusa da Sumy ya zauna, kallonta kawai yake yana murmushi, hura mashi idonshi tayi tana fadin wannan kallonfa? Murmushi yayi yace nakine mana. Hannu yasa yadauko lemun da aka kawo mata yazuba akofi. Kallonta yayi yace to bude bakin in baki, dariya tayi tana fadin a'a nagode sekace wata karamar yarinya, yace emana agurina kin wuce haka ai, idan mukayi aure babu abinda bazan maki ba. Murmushi tayi ta bude bakinta yabata. Kallonta yayi yace hajiyar hijabi, waike ko zafi bakiji kiyita zama da wannna katuwar hijab din? Murmushi tayi tana fadin to yazanyi tunda Baba yace dole sena sa. Nabeel yace kice ba ra'ayinki bane? Ya mutsa fuska tayi tace kasan iyayenmu da tsoro. Hannu yasa yakamo hijab din yana fadin kuma gashi yadin akwai nauyi, tace wallahi kuwa waishi yafison irinshi, Nabeel yace ai yanada gaskiya, kinga kin boye mani jikina babu wanda ze gani seni. Amma idan muna tare seki rika cirewa sauran mutane kuma ki boye masu. Murmushi tayi tace kaima kana goyon bayanshi kenan? Yace sosai ma, ai haka akeso, gara inrika gani nikadai, hannu yasa yana fadin bara incire maki, haka ya cire mata dama daga ita se doguwar riga ko dan kwali bata saba. Gashin kanta ne yazubo harya rufe mata fuska, domin hada ribom din yafitar besani ba. Cak ya tsaya yana kallonta, itako ta dukar da kanta tana murmushi, kara matsowa yayi yana fadin Sweet, wannan gashin naki ne ko sawa kikayi? Murmushi tayi tace nawa ne mana, hannu yasa yana gyara mata yana fadin aikuwa, gaskiya babu abinda zan ma Allah se godiya daya bani ke, nasan zamu haifi yara masu kyau da gashi, ina matukar son mace me gashi. Kara kallonta yayi ganin tana murmushi yasa ya duko yana kallon fuskarta har jikinsu yana haduwa, murmushi sukasa gaba daya, hannunta yakamo yana murzawa, kara dukewa tayi tana murmushi, ganin bata hanashi ba yasa yakara matsawa jikinta yana fadin. Sweet dan Allah kina sona? Kai tadaga mashi, yace sweet wallahi idan narasaki nasan zan iya mutuwa, saurin dagowa tayi tasa hannu ta rufe mashi baki, dariya sukasa yafara yinata cakulkuli suna dariya da haka har suka kwanta cikin dabara Nabeel yafara yimata salonshi, sam Sumy takasa hanashi. Ganin har ankira magriba basu fitoba yasa Saif yatafi dan yakirasu, yana daga labule yaga halin dasuke ciki yayi saurin sakin,labulen yana murmushi, juyawa falo yayi. Najib yace ya kuma kafito kai daya? Dariya Saif yasa yana fadin shege abokina, yana can yana harka. Najib yace wai da gaske? Saif yace wallahi kuwa, ammade bansan wane irin game yake bugawa ba. Najib yace muje zuwa de wata rana dole yamanta da maganar aure sucigaba da morewa. Saif yace inaso Sumy tazo ta tafi gida saboda banaso Babanta yafara hanata fita, ni kuma nafiso kullum su kasance atare hakan zesa soyayyarsu takara zama makusanciya. Wayarshi yadauka yakira Nabeel, seda takusa katsewa ya daga. Murmushi Saif yayi yace idan kanaso gobe Sumy tadawo to yakamata kufito domin ankira sallah. Cikin lokaci kankani suka fito, Sumy se dukar da kai take, haka tayi masu Zuby sallama, suna fita su Zuby sukasa dariya suna fadin zaki dena kunya ma. Can daga farkon layinsu Nabeel yayi parking, atare suka kalli juna, kwantar da kai Nabeel yayi saman kujerarshi yana fadin bansan ya zan kasance yau ba, hakika sweet kin iya soyayya me tsayawa arai, ni nasan yau bade inyi bacci ba sede shi baccin ya daukeni. Lumshe ido tayi tana karajin kaunarshi tana ratsata, kallonshi tayi tace ni kaina nasan yau bazan iya bacci ba,tabbas ayau nasan ina matukar kaunarka, dan Allah my king kada kabari wata ta kwacemun kai. Hannunta yakamo yana fadin sweet daga ke bana tunanin kara kallon wata mace matukar zaki bani duk wata kulawa da nakeso. Kinsan nidin dangata ne, idan har bansamu kulawa daga gareki ba dole zan kalli wasu matan, Sumy tace ni kuma namaka alkawarin zan baka kulawa wadda babu wata mace data taba baka, sena sa kamanta da kowace mace bayan ni. Naso ace a hostel nake zaune da nabaka kulawa ta musamman, amma anan nasan Baba baze rika barina ba. Nabeel yace zaki iya sweet, kede kibari mu koma makaranta zamu bama kanmu lokaci sosai, saboda iyayenmu basu san yanda zuciyo yinmu zasu rika wahala ba idan basa tare. Murmushi tayi tace nakosa akoma wallahi, dariya sukasa, Nabeel yace bara na barki kitafi kada Baba yayi maki fada, turo baki Sumy tayi tana fadin wallahi kamar kada murabu. Murmushi yayi tare dasa hannu aljihu yaciro dubu ashirin ya dora a saman hannunta yana fadin gashi kibama mamata kice ina gaisheta. Godiya tayi mashi tafita tana daga mashi hannu. Da sallama tashiga gidansu, gabanta ne yafadi ganin Babansu a tsakar gida, Mamanta ce tayi saurin fadin yar halak amma kinyi sauri na dauka ma se anjima zaki dawo ya kika samu su Inna Bintar? Ajiyar zuciya Sumy tasaki tana fadin duk suna lafiya tana gaisheki, ai ina zuwa ko zama banyi ba nabata sakon na juyo ganin yamma tayi. Dukawa tayi tana fadin Baba sannu da kasuwa, murmushi yayi yana fadin yauwa Sumayya, ai da zan fara fada na dauka tun dazu kika fita? Sumy tace a'a ai bazan karya maka doka ba, nasan bakason infita unguwa da wuri kuma inki dawowa da wuri. Murmushi yayi yana fadin haka ne, Allah yayi maki albarka, tashi yayi yana fadin nizan fita fira bara na turo maku gidan, sukace seka dawo. Yana fita suka shiga daki, Sumy tace nagode Mama da yau bansan irin fadan daze mani ba. Mamar tace ai banfada mashi gidan kawarki kikaje ba cewa nayi kina gama sallar magriba Inna Binta takirani inabaki wani sako ki kaimata. Zama tayi tana fadin ai agidansu Mansura Nabeel yasameni muka sha firarmu, yace ingaisheki, kuma ga wannan yace akawoma mamarshi, hannu tasa cikin jakarta taciro kudin daya bata tamika mata. Sakin baki Mama tayi tana kallon uban kudin da Sumy ta bata, karba tayi hannunta har rawa yake tana fadin ke Sumayya, anya ba mantuwa yayi wajen girgawa ba? Murmushi Sumy tayi tana fadin habade Mama, ai kinsan kowaye Babanshi, kumafa shi kadai suka haifa. Hannu Mamar ta daga sama tana fadin Allah nagode maka, lallai ayau nasan haihuwa tayi mani rana, shiyasa akace daka haifi gwamna gara ka haifa mashi mata, domin mata Allah yayi mu dajin kai, da ace ke namiji ce komin kyanki sede ki amfanama wasu, ga yayanki nan Allah kadai yasan abinda yake kaima budurwarshi. Dafata tayi tana fadin kinajiko? Daga yau kada ki kara hanashi ganinki, tunda de akwai gidan kawarki da kuke haduwa kirika zuwa can, ni,nasan mezan rika fadama malan, kuma ai da kun koma makaranta zakufi haduwa ma. Amma tabbas bazan bari malan yayi mani bakin cikin samun abun duniya ba, tunda de Allah yasa na haifi mace aiko dole abarta muci arziki, domin haihuwar mace arziki ne. Allah yayi maki albarka kinji. Wannan kudin asusu zan sakasu, nasan kina bukatar kayan kwalliya da sauran na amfani, ke macece kisan yanda zaki fada mashi kinason kayan kwalliya, nasan ze kaiki kisiya amma wadan nan kudin gara mufara tarasu, tashi kije kidauko abincinki. Nabeel ne kwance saman cinyar Ummanshi tana shafa mashi kai yana bata labarin Sumy, kallonshi tayi tana murmushi tace kasan wani abu? Girgiza mata kai yayi, tace yanzu daka fara soyayya da ita bakaji dadi ba? Murmushi yayi yace naji mana sosai. Murmushi tayi tace to haka akeso, mutum yagama cin moriyar rayuwarshi sannan yayi iyali, kaganni nan banyi aure da wuri ba, kuma babu irin dadin daban jiba, kuma da lokacin auren yayi gashi nayi, da ace nayi aure da wuri nasan da yanzu na tara yara dayawa, shikenan kuma bazan karajin dadin rayuwata ba. Shima Abbanka abinda yasa yakiyin aure da wuri saboda bayaso yatarama kanshi damuwa tun yana yaro, amma kai gashi kana shekara 22 kake tunani aure, idan kuma ka kai shekarun Abbanka yazaka koma lokacin? Abinda yafi maka kabari kugama karatunku sannan kuyi aurenku, kaga yanzu lokacinku ne. Sekuyi soyayya son ranku, kuma aurenku seyafi dadewa saboda kowa yasan halin kowa. Murmushi Nabeel yayi yace haka ne Umma, nima ada nayi tunanin bazata amince muyi soyayya ba ganin ita ustaziya ce shiyasa nace zanyi aure. Amma ayau ta nunamun itama tana sona, sam hijabin datake sawa be hanata nunamun soyayya ba, murmushi Umma tayi tana fadin ai yawancin masu saka wannan hijabin kawai dansu kauda hankalin mutane ne daga zarginsu, amma bakowace mace bace take amfani da abinda take sawa. Wani lokacin abinda me hijabi zata aikata wallahi me yawo da kananan kaya bazata aikatashi ba, kuma naji dadi tunda kace ka hakura da auren se kagama, abinda nakeso da kai idan Abbanka yayi maka maganar auren kace mashi iyayen yarinyar da yarinyar sunce se tagama karatu zasuyi mata aure, dan haka kaima kafasa auren seka gama. Nabeel yace angama Ummata ta kaina, tace yauwa dan autana, tashi ka kaima Auntynka Lawisa farfesu gashi can angama tun dazu naso nabama Babaye ya kaimata na manta kuma banaso ya kwana bataci ba, tashi kafin Abbanka yadawo yana iyacewa Babaye yaje. A wannan rana Nabeel da Sumy basuyi bacci ba, haka suka rika waya kamar basune suka rabu dazu ba, se wajen asuba ya kyaleta, sam takasa bacci, son Nabeel kawai yake yawo a zuciyarta, bata taba tunanin wannan ranar ba. Takosa a koma makaranta kodan ta nunama mutane matsayinta. Tun daga wannan rana haduwar Nabeel da Sumy tazama farilla, domin yanzu bada yamma take fita ba, Babanta yana tafiya kasuwa shida yayanta Nabeel yake zuwa inda yake daukarta tafito sutafi. Haka zasu shiga gari wajen shakatawa suyi yawo su sha fira, wani lokacin kuma suje Yankari acan suke hutawa, a hankali Nabeel yafara canzama Sumy rayuwa, duk yanda tayi shiga haka zasuje gidanshi ta canza wasu kayan su shiga gari. Idan kaganta bazaka taba cewa Sumayyar daka sani bace, Naseer tun yana kiranta tana dauka tana amsa mashi sama sama har tadena dauka, daga karshe ma tayi diverting call dinshi. Duk wasu kayan bukata Nabeel yana sai mata. Haka ya bude mata account ya samata kudi masu yawa, duk kayan dayake sai mata babu abinda Babanta ko yayanta suka taba gani, daga ita se Mamanta, idan ma kayan dadi taje dasu haka zasu cinye kafin su dawo. Kasancewar basa dawowa se sunyi isha'i yasa basu taba kamata bata gida ba, domin duk inda akayi magriba ta dawo gida,duk wannan abun da suke Nabeel betaba neman Sumy da aikata zina ba, domin yana tsoron kada sanadiyar haka su bata. Bayan sati biyu suka koma makaranta, amma Sumy ko tafito daga gida bata zuwa makarantar suna tare dasu Zuby a gidan Nabeel, sosai suka saba dasu, seda akayi sati biyu da komawa makaranta sannan sukayi shirin shiga. Hatta da kawarta Mansura seda ta kirata taji ko lafiya bata dawo ba, dan Naseer duk yadamu shiyasa yace takirata tunda taki daukar wayarshi. Tana dauka tace mata lafiya lau kawai tana hutawa ne amma yau zata shigo, Mansura tace dama an lika result kuma kincinye duka dan kinada 3 point. Sumy tace amma naji dadi, sena shigo, Mansura tace Yayanki yana gaisheki, saurin kashe wayar Sumy tayi tana tsaki. Sosai Naseer yaji dadin dawowar dazatayi, aranshi yana fadin tana zuwa kawai ze fada mata yana sonta tun kafin wani yayi mashi shigar sauri. Saif ne da Nabeel tsaye ajikin mota suna jiransu Zuby domin Najib yaje gida Babanshi yana kiranshi. Kallon Nabeel Saif yayi yana fadin wai abokina har yanzu baka saka kwallo araga ba? Murmushi Nabeel yayi yana fadin rufamun asiri, kanaso nakawo karshen soyayyata da Sweet. Sumy ba kamar sauran matana take ba, shiyasa nake tsoron tun kararta da wannan bukatar. Murmushi Saif yayi yace lallai abokina da sauranka, kuma kwanan nan zaka tafka baban kuskure domin kayi shuka me kyau amma barruwa yanaso yabaka wahala. To bara kaji, matukar Sumy tasamu wadda yafika iya bada ruwa yanzu labari zesha banban, kana ganin nida Zuby, ayanzu bata iya kula kowa seni, domin nine mutum na farko dana fara bama flower ta ruwa. Matukar kanaso soyayyarka da Sumy ta dade dole seka fara bata ruwa idan ba haka ba wallahi shukarka zata mutu. Cike da damuwa Nabeel yace yanzu ya kakeso in bulla ma lamarin? Murmushi Saif yayi yace yanzu kuwa zan fada maka, kuma ayau nakeso agama komai, kawo kunnanka kaji. Dariya suka sa jin abinda Saif yafada, Nabeel yace haka nakesonka abokina. Su Zuby suna gama shiri suka fito, gaba dayansu kallon Sumy sukayi ganin yanda tayi shiga me kyau,domin kayan datazo dasu daga gida ciresu tayi Zuby tabata wasu tasa. Sosai tayi kyau, gashin kanta yasha gyara an mata daurin dan kwali kamar tasa gwaggwaro, doguwar rigace ta wani material me shegen tsada tasa, tarike wata jaka da takalminta masu tsada, gyalen ma a kafada ta ajeshi, tayi matukar kyau, kosu Zuby seda suka sara mata. Har suka karaso basu dena kallonta ba, tana zuwa kusa da Nabeel yayi saurin jawota ya rungumeta yana fadin ina matukar sonki sweety na, gaskiya badan inaso in nunama kowa tauraruwata ayau ba da bazaki fita haka ba. Amma daga yau kindena fita haka, gara kirikasa after dress, Saif yace haba Nabeel so kake abokanmu suyima budurwarka dariya, kasanfa kafi kowa iya wanka ya za'ayi ace budurwarka takasa yin wanka me kyau. Nabeel yace ina tsoron malaman mu, Zuby tace haba Nabeel, kama dena wannan maganar babu wani namijin daze iya kusantar Sumy matukar yasan kuna tare, shiyasa mukeso yau ka nunama kowa Sumy takace, ke kuma Sumy kada kiji kunya wannan itace damarku. Hannuta yakama suka shiga mota. Lokacin da suka isa harabar depertment dinsu mutane suka samu cike suna jiran malamin, bayan sun tsaya su Zuby da Saif da Khairat suka fara fita, can Nabeel yafito haka kowa ya zuba mashi ido domin aranar yayi kyau, kusan colour daya sukasa shida Sumy. Zaga yawa yayi ya budema Sumy kofa, kafarta daya tafara saukowa sannan ta fiddo dayar,hannu ya mika mata takama nashi tafito, tana fitowa yajawota tafada jikinshi yarike mata kugunta da hannunshi. Saboda tsananin mamaki babu wanda ya iya magana, wasu sun ganeta, wasu kuma kallon sani suke mata, Naseer da Mansura kuwa sun riga kowa ganeta, Naseer jiyayi kanshi yana juyawa, kara murtsike idonshi yayi domin ya tabbatar da Sumayyar daya sani ce? Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [3/18, 11:23 AM] nabilalady5: ☝🏻☝🏻KOWA YATAKA DOKAR ALLAH☝🏻☝🏻 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) www.NabilaLady5@gmail.com Facebook...Nabeela Ladeey Part 50 ⏩ 55 Samun waje Naseer yayi yazauna domin jiyake kamar zuciyarshi zata buga, da gaske wannan Sumayyarshi ce? Yarinyar da ko magana bata iya yi sosai, kullum cikin hijabi take amma itace yau tare da mutanan da sukafi kowa rashin ji. Dafe kai yayi yana addu'a. Nabeel ne cikin daga murya yace Assalamu Alaikum, inaso kudan bani aron hankalinku domin inaso nagabatar maku da matar dazan aura da zarar mungama school insha Allah. Bakowa bace se Sumayya Labaran, Sumy. Ina fatan zaku tayani da addu'a domin samun nasarar aurenta. Tafi aka samasu wasu daga cikin abokanshi suka rika ihu suna tayashi murna, wani ne yace agaskiya abokina ka iya zabe, domin kazabo tauraruwar cikin matan course dinmu. Allah ya nuna mana wannan rana musha biki na yan course daya, dariya akasa Nabeel ya ciro bandir din 200 yamika mashi, ai nan waje yakara rikicewa da tafi, kara kamo Sumy yayi batayi aune ba taji bakinshi cikin nata yana mata kiss. Gaba daya wajen yakara daukar ihu da tafi, yana cire bakinshi ta maida kanta saman kafadarshi, domin gaba daya kunya ta kamata, Saif yace mun duba munga gobe da misalin karfe 1 muke gama lectures, dan haka muna gayyatarku taron taya Nabeel da Sumy murnar fara soyayyarsu. Za'ayi taron ne a gidan Nabeel dayake Nasarawa idan mungama lectures duk wanda ze halarci wajen yazo ya karbi address din gidan da pass. Haka suka shiga class dan hango malaminsu yataho, a waje daya suka zauna Sumy ta hade fuska domin taga wasu se wani kallo suke mata shiyasa tacire kunya tadago kanta tana kallon kowa. Malamin yana zuwa yafara tambayarsu abinda yayi masu. Sumy ce ta tashi tabashi amsa, har tagama bayani malamin besan tagama ba, domin ya shagala wajen kallonta🤣. Wani irin bakin ciki ne yakama Nabeel, gaba daya ajin kuma aka sa dariya, can malamin ya ankara yayi saurin gyara glass dinshi yana kame kame. Tashi Nabeel yayi yana harararshi yakama hannun Sumy suka fito gaban aji, kallon malamin yayi yana fadin malan wannan itace matar dazan aura nan da wani lokaci. Kasa malamin yayi da kanshi, gaba daya kunyar abinda yayi takamashi. Jan hannunta Nabeel yayi sukabar class din. Haka ajin yakara daukar dariya, da kyar yasamu ya dedeta ajin yacigaba da darasinshi, ko lokaci be bari yacika ba ya sallamesu. Haka kowa yafito yana gulmarshi. Naseer kuwa zaune kawai yake yakasa tashi, idanuwanshi sunyi ja. Wani abokinshi ne yazo yadafashi yana fadin haba Naseer, meyasa zaka sama ranka damuwa akan wadda batama san kanayi ba? Ai yanzu ko Sumayya tace tana sonka wallahi kawuce da ajinta, domin babu wanda besan duk macen dataje wajen Nabeel tazama saura ba. Inaso kacire ma kanka damuwa akan Sumayya, rayuwarta ce, kowa yadebo da zafi bakinshi, dan haka taji zata iya ne shiyasa takarbi tayin soyayyarshi, dama can hijabin datake sawa saboda bata waye bane, kuma babu wanda besan irin wadan nan matan ba, dazaran sun waye zasu nuna ma kowa be iya ba. Naseer yace wallahi ina tausayinta, sam gidansu ba haka yake ba, sharrin Nabeel ne yamaidata haka, amma burin mahaifinta tazamo ta kwarai, duk lokacin da muka gaisa dashi yana fadamun inrika kula mashi da ita, nikadai ya yarda dani kada inbari samarin Jami'a su bata mashi diya. Nasha fada mashi halin kirki irin na Sumayya, da hazakarta a makaranta, duk lokacin dana fada mashi haka farin ciki ne yake bayyana a fuskarshi, ina matukar tausayin mahaifinta duk ranar dazesan halin da diyarshi tafada, ni na tabbata bawai yaune tadawo makaranta agidansu ba, nasan tana fitowa dasunan zuwa makaranta su tsaya ita dasu Nabeel. Amma zanje insamu Babanta infada mashi halin datake ciki, kasan icce tun yana danye ake lankwasashi, gara infada mashi yayi saurin daukar mataki tun kafin abun yayi nisa. Abokin yace Naseer kai asuwa? Meye dangantakarka da Sumayya? Kanaso kasa rayuwarka cikin hadari ko? Kana tunanin idan Nabeel yasan kanaso ka kawo mashi wargi akan Sumayya baze iya yin komai akanta ba? Dan Allah kabar wannan maganar. Naseer yace shikenan nabarta, insha Allah daga yau nabar Sumayya, zanyi kokarin cire sonta azuciyata, dama kyawun halayenta ne suke dibata, amma ayau data canza tabbas haushinta yacika zuciyata. Allah yakicire mun sonta. Washe gari bayan sun tashi daga makaranta haka mutane wasu daga cikin course dinsu kowa yarika daukar budurwarshi suna tafiya gidan Nabeel, da misalin karfe 2:00 mutane suka gama halartar gidanshi, bayan kowa yashigo suka kulle gate din. Wajen yayi kyau kamar za'ayi wani party na biki, fitowar Nabeel da Sumy ce ta katsema mutane surutun da sukeyi, masha Allah, fadin irin kyan da sukayi bazeyuwu ba, domin ko iyayen dasuka haifi Sumy da kyar zasu iya ganeta ayanzu. Tasha Dinner gown red colour, anyi mata kwalliya me masifar kyau, gashinta yasha gyara an bazoshi. Yanda kasan ba hausawa ba haka suka kasance, shima Nabeel yasha Black suit se ta cikin red, gashin kanshi yasha gyara yayi,masifar kyau, haka suka jero kamar ba musulmai ba, ba kamar Sumy ita datake mace, hatta da faratan ta sunsha fanti red. Inda aka tana dar masu nan suka nufa su Saif suna take masu baya, suna zuwa mutane suka hau tafi, Saif ne yafara bayani, muna mika godiya ga duk kanin Mutanan da suka samu halartar wannan engagement na abokina da masoyiyarshi Sumy. Wannan rana ta farin ciki ce agaremu domin taya abokinmu kuma dan uwanmu murnar samun abokiyar rayuwa. Kamar yanda Allah yataramu anan Allah yataramu ranar dazamu rakasu dakinsu amatsayin ma'aurata. Tafi aka dauka gaba daya. Bayan sun yanka cake, suka ciyar da junansu, Saif yamikama Nabeel zobe yasama Sumy, haka aka dauki tafi, itama Zuby tabata tasa mashi, rungume juna sukayi, gaba daya wajen yadauki ihu da tafi. Nan aka samasu kida suka fara takawa, kowa yafara fitowa yana takawa. Taro yayi kyau, anci nasha kuma an cashe, se karfe 6 sannan suka tashi, kafin kace me har hotunansu ya baza gari, bayan kowa yatafi Sumy tashiga tayi wanka tana fitowa Nabeel yashigo, shima wankan yayi lokacin daya fito tagama shafa mai da towel ajikinta tana kokarin sa kaya. Karasowa yayi ya rungumeta suka saki murmushi, Nabeel yace inama ace wannan taron da akayi na daurin aurenmu ne. Sumy tace wata rana ai zata kasance ta aurenmu. Nabeel yace gaskiya yau bazan iya kwana ni kadai ba. Sumy tace inama ace a hostel nake da nice zan zamo abokiyar kwanciyarka. Hannu yasa ya cire towel din jikinta yana rada mata wata magana a kunnanta, saurin ja baya Sumy tayi tana girgiza mashi kai, daure fuska Nabeel yayi yace dama nasan baki sona, wallahi babu abinda bazan iya mallaka maki ba, ke koda ace zaki kamu da ciwo zan iya sadaukar da wani shashe najikina asamaki matukar zaki rayu, bandamu da rayuwata ba inde ke zaki rayu. Amma dan na tambayi wani abu kadan zaki tureni, yayi kyau, kuma nagode Allah dakika nuna mani iyakata, kishirya inmaidaki gida, dama nasan ai bazaki taba iya daukar bukatata ba, zan nemo wadda zata iya kula dani. Juyawa yayi yana kokarin sa kayanshi, saurin matsowa tayi ta rungumeshi ta baya tana kuka tace kayi hakuri kada kayi fushi dani, wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba, zan iya kula da kai wannan alkawarina ne, dan Allah kada kaje wajen wata. Kasan komai nawa naka ne, kawai abinda nake tsoro kada inyi ciki. Murmushi yasaki tare da juyowa yana share mata fuskarta yace ya isa haka sweet banaso inga hawayenki, bazan taba bari kizubar dasu ba. Ina sonki kema kinsani bazan taba bari kisamu abinda ze takura mana ba, zan baki maganin daze hanaki daukar ciki, kuma wannan abun dazamuyi shine zekara dankon soyayyarmu, kuma bazamu taba rabuwa da juna ba, domin munriga da mun mallakama junanmu kanmu. Haka Nabeel yayita fadama Sumy da dadan kalamai har yayi nasarar amincewarta, shedan kuma yakara zigasu zuwaga aikata alfasha, aranar seda Nabeel yayi nasarar biyan bukatarshi awajen Sumy. Bayan sun gama komai sukayi wanka, sosai Sumy ta wahala, magani yabata tasha yana ta yimata godiya, kallonshi tayi tace dear ina fatan Mama bazata gane abinda yafaru dani ba ko? Murmushi yayi yace kece zaki bata damar fahimtar wani abu, amma idan kika cire damuwa daga ranki bazata taba fahimtar komai ba. Wannan maganin ciwon jiki ne, idan kinci abinci zaki kwanta kisha insha Allah da safe zaki jiki garas, wata durowa ya bude yadauko wata waya acikin kwali me kyan gaske, daga ganinta zatayi tsada, kamo hanunta yayi yace wannan kyautarki ce bisa wannan kyauta nima da kikamun. Kuma nayi maki transfer din million 1, nagode sweet, hakika yau kin biyani, Allah yabarmu tare. Sosai Sumy taji dadin wannan kyauta, godiya tayi mashi tasa kayanta suka fita, suna fita Saif yasaki wani murmushi, kallonshi Nabeel yayi tare da mashi alama da hannu angama komai. Alamar jin jina yayi mashi, haka tayimasu Zuby da Khairat sallama suka tafi, cikin sa'a bata samu Babanta agida ba. Nabeel ne zaune afalon Abbanshi ya jingina da jikinUmmanshi yana shan Kankana, kallonshi Abba yayi yace Nabeel wane irin taro ne kukayi yau agidanka? Ya mutsa fuska Nabeel yayi yace kai Allah kayi mana tsari da yan sa ido. Umma tace meyafaru kuma? Abba yace dazu wani yake fada mani wai yaga motoci suna shiga gidanshi kuma yaji anata ihu ga kida yana tashi. Tabe baki Umma tayi tana fadin kai Allah ya sawake, wallahi Alh, idan kana biya ta mutane se sun rabaka da danka. Nabeel yace Abba abokaina ne fa sukazo tayani murnar samun matar aure shine muka dan hada walima, kuma naga ai ba abu marar kyau muka aikata ba, iyakarmu harabar gidan. Jin jina kai Abba yayi yace ai na dauka kowani mugun abu ne kukayi yanda mutumin yazo yana fada mani. Kace mun kusa zuwa nema maka auranta? Nabeel yace Abba iyayenta sunce seta gama karatu zatayi aure, nima kuma da suka fadi haka naga yadace ace nima nagama karatuna sannan inyi aure haka zefi, lokacin ma nakara shekaru kuma mun kara fahimtar juna. Murmushi Abba yayi yace hakan ma yana da kyau, Allah yasa munada rabon gani, nide abinda zan fada maka kaji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka dage kayi karatu domin shine kadai gatan dazan maka, nafiso ko bana raye kada kayi maraicin komai, domin koda ban bar maka dukiya ba nabar maka ilimi. Domin dukiya zata iya karewa, amma ilimi har abada baze kare ba. Umma tace wannan haka yake, kuma nasan Nabeel yarone me haka zaka baze taba bamu kunya ba, kada ma kadamu ni nasan waye yarona. Abba yace Allah yayi maka albarka. Kallon Umman Nabeel yayi yace yakamata azo ayimashi kanwa ko kani haka nan, gaban Umma ne yafadi jin abinda yafada, saurin kallonshi tayi yana murmushi yace emana, kinsan inason inga gidana yacika da yara, idan kuma kin gaji ayo maki kanwa. Saurin tashi Umma tayi fuskarta adaure tana fadin mene? Dariya Abba yasa yana fadin yi hakuri kada idanuwanki su fado wasa nake maki, jawota yayi suka samata dariya shida Nabeel, kallonshi kawai take cike da tsoro, yace wasa nake maki kinji. Amma de gaskiya inason akara mani yara kamar 2 ko 3 ma sun isa ko bahaka ba Nabeel? Yace kwarai ma Abba, nima zanji dadi ace inada kannai, tashi Umma tayi tana fadin Nabeel tashi kabani waje, dariya yasa yana fadin Umma de bakiso ki tsufa dawuri shiyasa. Tashi tayi tabasu waje sunata mata dariya. Tana zuwa daki takira Lawisa tana fadin kizo akwai matsala. Lawisa tace bana gari dazu na kaima wata kawata ziyara a abuja, amma jibi zan dawo idan nadawo zanzo, ki kwantar da hankali banaso kibari kowa yafahimci damuwarki, idan nadawo zanji koma meye. Kashe wayar tayi, haka Umma tazauna cike da damuwa, kada de ace maganar bokace zata tabbata, domin yace mata idan har asirinta yafara karewa Alh, zefara mata maganar yara da kuma ta aure, lallai dole su koma wajenshi, dama tunda sukaje so daya basu kara waiwayarshi ba, domin bukatar ta tabiya. Washe gari tunda wuri Sumy tashirya tace ma Babanta yau sunada lecture din safe kuma bazasu dawo da wuri ba, haka yadauko 200 yabata yayanta yakara mata 100, kamar bazata karba ba se kuma ta tuna kada Babanta ya tambayeta ina take samun kudi, karba tayi tana masu godiya tafita da kwatuwar hijabinta. Murmushi Babanta yayi yana fadin nayi sa'ar yara ni kam. Aranar ko makaranta bata shiga ba, wuni sukayi ita da Nabeel suna aikata masha'a domin adaren jiya kasa bacci tayi, dan son Nabeel kara shiga ranta yayi, hakan yasa yau tafito dawuri dan su kasance tare. Seda ta jera kwana biyu bata shiga makaranta ba, kullum suna tare da Nabeel, sosai suka kara dinkewa, dan yanzu Nabeel becika kula kowa ba, Ada ce kawai idan yaso yake kiranta ta tayashi kwana. Sumy dasu Zuby sun kara zama kawaye, dan yanzu Sumy itace shugabarsu, domin komai se abinda tace, kuma ta dalilinta suke samun komai daga Nabeel, babu ruwansu da tunanin makaranta, Sumy ce kawai take dan magana, shima kuma Nabeel yace mata kada tadamu ko basuyi exam ba dole abasu result, bataga first semister basuyi exam ba amma aka basu result kuma babu wanda yayi carry over, haka yayita kwantar mata da hankali har ta amince ta kuma cire damuwar makaranta aranta. Tun acikin mota Umma take bama Lawisa labarin abinda yafaru, Lawisa tace haba kidena damuwa ai yace wasa yake maki ko, wallahi duk kin tada mani hankali, da se gobe zan dawo kawai ganin kintashi hankalinki yasa nataho, gashi daga zuwana ko hutawa banyi ba kika dauko ni. Umma tace dole indamu Lawisa, yau idan asirina yatonu ai gaba dayanmu mun shiga 3, Lawisa tace shiyasa nace maki kisamu Yaya yakara maki kadarori, domin nasan wata rana dole asirinmu yatonu, kinga alokacin muna da madafa, amma kintsaya soyayya, ai yanzu lokacin soyayya yawuce. Kin ganni nan nasamu wani yaro me masifar kyau, buzu ne irin yan cirani ne, kinsan nace maki na dena harkar bin maza, amma wallahi haduwata dashi yasa nakasa hakura,yanzu haka nace mashi ya hado kayanshi yadawo gidana. Ana gobe zan tafi abuja muka hadu dashi abakin titi yana saida lemu da ayba, na tsaya zan siya naga ya burgeni shine nabashi address dina nace yazo da dare, kinsan wani abu? Aranar tare muka kwana yaron ya hadu sosai ya iya harka, shiyasa zan maidoshi gidana in ginashi yazamar mani abokin debe kewa. Kafin infara koya mashi harkar kasuwanci kinga semu rika tafiya tare. Murmushin takaici Umma tayi tana fadin ke ana maganar matsala kina maganar wani yaro can. Dariya Lawisa tasa tana fadin ke kin cika tsoro, kibari muje wajen boka nasan komai ze warware duk da bamu kyauta ba da bamu kara waiwayarshi ba, amma yanzu semuyi mashi sallama me tsoka. Parking sukayi daga gefen wata gona suka taka da kafafuwansu zuwa cikin dajin da bokan yake. Koda sukaje basu sami komai ba, inda bukkarshi take ada yanzu babu komai se fili, cike da tashin hankali suka fara waige waige, Umma tace kode ba wajen bane? Lawisa tace wallahi nan ne, kamata yayi musamu wani mu tambayeshi ko Allah zesa yasan inda ya koma, gashi Gaje bata gari bare in tambayeta, kuma nan babu network bare akirata. Dafe kai Umma tayi tana fadin nashiga 3. Wani mutum suka hango yana dibar itatuwa, da sauri suka isa wajenshi, bayan sun gaisa Lawisa tace bawan Allah ko kasan wani mutum dayake zaune a wata bukka datake wajen can? Kallonsu yayi yace kice mani wani dan iskan boka. Lawisa tace eshi nake nufi. Dariya yayi yace Allah ya kashe tsinannan dayake lalata mana mata da yara da yan uwa musulmai, wallahi kun bani kunya gaku da cikar kamala amma kuke neman wanann la'anan nan Allah. To idan baku sani ba, yau kusan wata biyu da bokan yayi mutuwar wulakanci, mutuwa irin ta karnuka, kai wani karenma yafishi daraja, domin kila wani karen idan yamutu yasamu a gina rami arufeshi, amma shi wannan bokan babu wanda yaje kusa da gawarshi. Karnuka da tsuntsaye sune suka cinye namanshi, daga karshe aka sama bukkarshi wuta ta idasa cinye sauran kashinshi daya rage, dan haka yarage naku ku koma ga Allah ko kuma kunemi wani bokan. Daukar iccenshi yayi yatafi, zubewa Umma tayi tana fadin munshiga 3, shikenan asirina ze tonu. Lawisa tace kiyi hakuri kitashi mutafi gida kada wani abun yasamemu kinga babu mutane dayawa, muje gida ai bashi kadai bane boka, kuma Gaje tana nan nasan zata nemo mana wani. Haka suka tafi gida, bayan ta aje Umma tawuce gida domin yaronta yayi mata waya ya iso. Umma kuwa tana zuwa ta kwanta cike da damuwa, kafin wani lokaci zazzabi me zafi ya rufeta. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263