*Z A F A F A B I Y A R 2023* *_DANDANO DAGA LITTAFIN_* *_A RUBUCE TAKE k'addarata_*📖📖📖✍🏽✍🏽 *S a f i y y a H U G U M A* A nutse ta bude k'ofar toilet din ta fito daure da babban towel fari sol,lallausar farar fatarta mai santsi da sheqi tana ta daukan idanu. Gaban dressing mirror din dake dakin ta isa,ta ja kujera ta zauna tana kallon fuskarta a ciki,gaba daya jin ranta da jikinta takeyi babu dadi,fuskarsa ke gilma mata cikin idanuwanta,sam jikinta bai bata ba,ta kasa nutsuwa gami da gamsuwa da wannan tafiyar da ya qirqirar mata bagtatan lokaci guda,tana tsaka da hidindimunta,tun daga yanayi fuskarsa da kuma yadda ya dinga tuqi daga bauchi zuwa katsina takejin kamar ba abbas dinta ba,tabbas akwai abinda ke faruwa,akwai wani muhimmin abu dake gudana,tayi tunani har babu iyaka,ta laluba dalilin tas tun daga randa ya sanya qafa ya fita daga gidan zuwa dawowarsa da kuma isowarsu katsina......tayi zagaye cikin tunani da abubuwan da suka wanzu kaf! Ta kasa gano abu guda daya farun. A iya saninta sun rabu suna masu kewa da kuma shauqin juna kamar ko yaushe,hakanan koda safiyar ranar sun jima ita dashi akan waya suna hira,wata irin hira irin wadda ke fallasa sirrin zuciyar masoyi zuwa ga dan uwansa,yana ta mata qorafin a takure yake acan din tare da mita tana lallabashi tana kuma masa dariya,har suka rabu kyawawan kalamai ne bisa fatar baki da zuciyar kowannensu,to amma me ya canza hakan? "AKWAI WANI ABU" ta fada murya qasa qasa tana motsa tausasan lips din bakinta tare da zare idanunta daga kallon da take qarewa fuskartata,ta dauki lotion dinta mai taushi da qamshi ta fara shafawa fatarta cikin kasala taraddadi da kuma damuwa. Duk bayan wasu mintuna saita kalli wayarta dake gefe tana tsammanin kiransa,saboda ta sani haka suka sabarwa juna,duk inda zashi cikin nigeria..... matuqar tafiyar mota zaiyi itace abokiyar hirarsa har ya isa inda zashi,idan kuma hakan bata kasance ba.....zaiyita kiranta har ya isa din,amma wannan karon ko gilmawar miscall dinsa bata gani ba bare kiransa,a qididdigen da tayi a yanzun kuma, tabbas koda baije gida ba yana gab da isa "Waishin meke faruwa?" Ta sake jefawa kanta tambayar wata irin damuwa tana tabata tun daga qasan zuciyarta. Cikin dauriya ta shirya kanta cikin doguwar rigar atamfa,ta fidda ainihin kyanta da surarta sosai,duk da yanayin da take ciki sai data tsaya gaban mudubi ta kalli kanta,lokutta da dama takan dubi kanta da kanta tana tuna WACECE ITA A SHEKARUN DA SUKA SHUDE,a yanzun sai taga kamar ba ita ba.....komai yana zuwa yana shudewa da wani irin sauyi mai ban mamaki. Lausasan slippers ta zurawa qafarta,sannan ta isa bakin qofa ta kama handle din ta bude tabi siririn corridor din da zai sadaka da ainihin falon gidan. Tun bata qarasa ba ta hangeta zaune cikin falon,halittace mai girman matsayi a wajenta,halitta dake sahun farko cikin halittu mafi soyuwa a wajenta,a duk lokaci irin wannan da zatayi balaguro ta taho takanas saboda kasancewa da ita.....duniyarta kan cika da farinciki,takanji a duniya yanayi irin wannan bashi da tsaara a wajenta. A jikinta taji tahowarta,saita dauke idanunta daga kan tv din da take kalla ta maida kanta,kusan lokaci daya suka sakarwa juna murmushi,ta kuma rigata magana "Wannan nauyin wankan naki dai yana nan,affan ya fara kuka har sai da aka fitar dashi" cikin karaya da rauni da takeji cikin gangar jikinta da zuciyarta ta qaraso dab da ita ta zauna,tana shirin amsa mata.....kamar me kiran yana jiran dai dai lokacinne kira ya shigo wayarta,a hanzarce ta daga wayar tana duba me kiran, zuciyarta cike da fata da burin ganin wanda ranta ke darsa mata. Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba hadi da fitar siririyar ajiyar zuciya ba "Ina zuwa" tace da mommie,ba zata iya amsa wayarshi a gabanta ba,ita kadai tasan hottest words da suke gayama junansu,kuma muddin aka samu mishkila mommie taji daga ita har shi sun gama tafka abun kunya. Kai tsaye dakin ta koma,ta samu gaban madubin data tashi dazu ta zauna tana yunqurin daga wayar "Assalamualaikum" ta fada a shagwabe tana karyar da wuyanta gefe,abu mafi soyuwa kenan da tasan yana so tattare da ita,har yau kallonta yake cikin madubin da yake kallonta shekarun baya da suka shude,bata canza a idanunsa ba "Wa'alaikumus salam" mummunar faduwa gabanta yayi daka jin sautin muryarsa me taushi da sanyi da yake mata magana da ita koda yaushe ta juye zuwa wata iriyar murya,irin muryar da yake magana da cirminals a yayin da aikinsa ya biyo ta kansu.....irin muryar da yake magana da juniors dinsa a yayin da suke hurumin aiki......irin muryar da yake magana da ita a duk sanda ya shiga qololuwar bacin rai da fushi,muryar da bata taba jin yayi mata magana da ita ba. Kowacce gaba ta jikinta tayi sanyi,tayi namijin qoqarin tattaro nutsuwarta da juriyarta tace masa "Ka sauka lafiya?,ya kaje gida" "Me yasa zaki aikata min haka?" Ya fada muryarsa tana ninka ta da kaushi da ban tsoro,daga cikin wayar tana iya jin hucinsa,da alama a matuqar bacin rai da kuma fusata yake, tambayar tasa kuma ta dilmiyar da ita kogin tunanin ina ya nufa ne?,kafin ta lalubo amsa kunnuwanta sun fara isar mata da saqo mafi muni cikin rayuwarta,daga bakin halitta mafi soyuwa a gareta "Ashe haka kike?,ina miki kallon saliha ashe mayaudariya ce ke?,maciyar amana ce?,macuciya ce ke?,na baki dukkan yarda,na damqi miki rayuwata ashe zaki wasa da rai na da lafiyata?" Wani irin tashin hankali ne ya sauko mata,me abbas ke fada ne "Me nayi maka?,abban affan me ya faru?,kasan me kake fada kuwa?" "Na sani!,nace miki na sani, tsahon yaushe tsahon kuma wanne lokaci kika dauka kina cin amanata kina kuma ha'intata WIDAD?" Kasa zama tayi,ilahirin jikinta ya dauki tsuma,sai ta miqe tsaye qafafuwanta suna rawa "Kana cikin hankalinka kuwa abban affan?,a ins kake yanzu?" Ta tambayeshi don ta tabbatar da cewa he's safe,ba gusar masa da hankali akayi ba yake gaya mata hakan "Har kinyi wayon fara bin maza?,ki kwana a hotel?,hakan bai isheki ba har sai kin dauko gardi kin kawomin gidana?,kin kuma kaishi har gadona na sunna widad?,wane laifi na aikata miki haka dana cancanci irin wannan hukuncin?" Yayi maganar ta qarshe muryarsa a wani mugun karye,saidai zafi da kaushin nan suna nan taf a muryarsa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada a bayyane,qafafuwanta suka hau rawa,gabanta yayi wani irin bugawa da zuciyarta ta hasko mata abinda yake magana a kai. "Hotel kuma?" Ta tambayeshi muryarta na wata mugun rawa,irin rawar dake bayyanar da zallar daburce wa a sanda aka ritsaka bisa wani abu na rashin gaskiya "Bakije bane?,ko zaki shiryamin irin qaryar da kika saba?" "Naje,tabbas naje....amm......" "Ya isa!!!!" Abinda ya fada kenan a tsawace "Abinda nakeson ji kenan kuma naji,kije ke da Allah,bazan taba yafe miki ba,amanata da kikaci ubangiji ne kawai zaiyimin sakayya,Allah ya isa ban yafe miki ba!!!" Kit! Wayar ta katse "Abban affan,daddy!!!" Ta fada a gigice,saidai tuni ya katse layin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta sake maimaitawa jikinta na wani irin kyarma tana yunqurin binsa,saidai a take kamfanin sadarwa suka gaya mata is switched off,saita saki wayar ta sulale a wajen tana sakin wani azababben kuka,wani abu mai tauri da zafi yana tokare mata qirji. "Waye ya ganta?,waye ya gaya masa?,waye???" Ta soma nacin gano daga inda maganar ta fita "Hafsah" taji an bata amsa daga can tsakiyar zuciyarta,kukanta ya tsaya cak na wasu sakanni,sai ta sake rushewa da kukan tana jin kanta yana sara mata,tana son miqewa amma ta kasa,idan tayi kamar zata tashi sai jiri ya maidata ya kayar,a haka aka turo qofar dakin,ta daga idanunta da taji kamar basa dauko.mata hoton komai da kyau ta tsurawa qofar idanu tanason tantance mai shigowar. *_A RUBUCE TAKE KADDARATA_* *DAGA TASKAR ZAFAFA BIYAR* *TARE DA ALK'ALAMI SAFIYYA HUGUMA* *TAFIYA CE MAI DAUKE DA DUMBIN* @ILIMI @ZAZZAFAN KISHI @SOYAYYA @KIYAYYA @SHARRI @MAKIRCI @KIRSA DA KISSA _________________________________ *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +22799643131 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *_A RUBUCE TAKE!!!_* (Kaddarata) *HUGUMA* Free page 02 *MAAB LUXURY HOME* *_idan kaji gangami akwai labari_* *_SABUWAR DUNIYA CE_* *ALFAHARIN UWAR GIDA* *FARINCIKIN AMARYA* *MAIDA TSOHON GIDA SABO* *DUNIYAR QYALE QYALE* *KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA* *_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_* *nasan zaku tambaya ina ne nan?* *MAAB LUXURY HOME* 😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya* *_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_* *Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu* *Kayan gado dana parlor* *Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida* *Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a* _adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_ *Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram* @maabluxuryhome *Facebook* @maabluxuryhome *Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka* 08034631010 *Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝 ____________________________ waiwayowa yayi yana dubanta bayan ficewarsu gaba daya,maficin da ummu ta tashi ta bari ne riqe a hannunta tana tsige adon jiki,fuskarta a dinke tsaf,yakanyi.mamakin yadda take masa,kamar wata qatuwar budurwa,ya rasa dalilin da sam bata son su zauna waje guda ko su hadu,saidai har yanzu zuciyarsa na bashi nutsuwar cewa quruciya ce kawai da rashin sanin ciwon kanta,da zarar ta sake hada hankalinta zata fuskanceshi? "Amma sai yaushe?,lokaci qara quracewa fa yake" zuciyarsa ta gaya masa,sai ya dan gyada kai "Soon in sha Allah" ya fada yana bawa kansa qwarin gwiwa,qwarin gwiwar da kusan kullum itace madogararsa "Widad" ya kira sunanta "Na'am" ta amsa a cunkushe ba tare data kalleshi ba,murmushi yayi "To kidan kalleni mana?,ummm,ke da zaki zama matata?,so nake ki saki jiki da yayan naki" manyan fararen idanuwanta ta daga tana kallonsa,wani haushi da kuma tsanarsa suka saukar mata,lallai yaaya mahfood ta tabbata dan iska ne,ita yakewa zancen ta zama matarsa?. Yadda ta zuba masa fararen idanuwan nata sai yaji dadi cikin ransa,don takan jima bata tsaya ta kalleshi ba,wannan ya bashi qwarin gwiwar janyo ledar daya shigo da ita wadda ke shaqe da kayan kwalliya,kasancewar ya santa da son kayan ado da gayu ya tura gabanta "Ga kayan kwalliya nan 'yammatan ummu,sai ayita shafawa ko?" Dauke idanunta tayi daga kansa ta mayar kan kayan,saita dalla wa kayan harara,ita zaiwa wayo?,ya dauka bata da hankali kenan,haka kawai,bayan ummu tasha gaya mata ko zama tayi kusa namiji ciki zatayi,shine zai wami bata kayan kwalliya?,to bai isa ba,tana gama wannan tunanin ta miqe abinta ta nufi qofa da saurinta. "Zo mana widad.....widad"ya fara qwala mata kira,gudun kada latifa ko ummu dake daki su jiyo shi,su kuma sanyata dawowa dole saita fella da gudu ta qarasa ficewa,don ta lura shi kadai ne zaifi mata saurin barin sassan. Bata tsaya ko ina ba sai sassan anty madina,taja birki tana zabga haki,dai dai lokacin da dukka yara yaran gidan da suke da shekaru irin nata ke zaune a falon anty madina,kaf cikin matan gidan ta fisu qarancin shekaru,tana da faran faran da son mutane,tana yawan jansu a jiki gami da biyewa shirmensu,wannan yasa kafatanin yaran gidan kowa ke sonta,yake kuma son zama a sassanta. Dago kai tayi tana duban widad,muhassana ce kwance a cinyarta diya ga qanwar mahaifin widad tana mata tsifa "Lafiyarki widad?,irin wannan cin burki haka?" Guri ta samu kusa da khalisa ta zauna tana maida numfashi,sai kuma ta bata rai, idanuwanta sukayi rau rau suka ciko da qwalla "Yaya mahfood ne" "Mahfood kuma?,biyoki yayi?" Kai ta girgiza tana turo baki gaba,ita sam sam ma batason maganarsa,yanzu su mahassana zasu fara tsokanarta "Wai cemin yayi matarsa" tana fadin maganar qwalla na gangaro mata,qaramin murmushi anty madina ta saki,ta rasa wanne irin rashin haduwar jini ne haka tsakaninsu,duk wanda ya kwana ya tashi yasan yadda mahfood din ke qaunar widad,hakanan kowa yasan yadda take gudunsa,bata qaunar hada inuwa dashi "To banda abinki mene ne don yace miki matarsa iyi widad?,bakiga su zahira ba aure za'ayi musu?,kuma daga su sai ku?" Kafin anty madina ta kammala bayaninta widad din ta saki kuka harda turje qafafu,baki anty madina ta sake tana kallonta gami da jan salati,yayin da su muhassana suma ke kallonta suna dariya "Tsaya,bakya sonshi ne shi yayan naku?" Kai ta gyada "Wallahi ni bana sonsa Allah" "To ya isa,ki share hawayenki,an gama maganar,ba wanda zai baki shi" dif kukan ya tsaya,ta tashi ta zauna dai dai tana goge qwallarta tana kuma hararar su khalisa kan dariyar da suke mata "In sha Allahu sai su abba sun baku dauda" dariya sosai anty madina ta tuntsire da ita,duk da quruciyarta wani lokaci idan tayi wani abun kamar babba,dauda shike wankin gidan,na kowanne sashe,daga qauye yazo a gidan aka riqeshi "Bakinki ya sari danyen kashi" khalisa ta fada tana dariya "Saidai naki bakin" widad ta fada tana sake harararta,dole anty madina ta shiga fadan ta raba,ta kuma janye musu hankalinsu da wani abu na daban. Qememe taqi komawa sassan ummun,duk da ummun ta aiko latifa har kusan sau uku amma taqi komawa,zatonta mahfood yana nan bai tafi ba,wayo ummun keso tayi mata don ta dawo,har abbanta yazo ya tafi bata koma din ba,son samunta ma tayi kwananta nan wajen anty madina cikinsu farisa,amma kuma tana tsoron kyankyaso,kada yayi mata irin yadda yayi mata daxun,har sai data fara barci sannan latifa tazo ta tafi da ita bayan ta tasheta ta sakata a gaba. Tana shiga dakin ummu ta haye gadonta taja bargo ta duqunqune sosai harda cusa kanta cikin pillow,tun tana kasa kunne taji shigowar ummu har bacci yayi awon gaba da ita. Washegari ummun bata ce komai da ita ba,saidai ta bata ledar kayan kwalliyar tace ta dauketa taje ta adanata,aifa kamar jira take,saita dire cup din da take shan tea dashi ta saki kuka "Allah ni bana so,banaso ummu" tana turje qafarta a qasa "Hukumullahu" ummun ta fada a ranta tana zuba mata idanu,wannan abun na widad din kuwa na qare ne?,kullum abu kamar ma sake ci gaba yakeyi?,kafin takai ga sake cewa komai akayi sallama falon,ta dauke kanta daga widad ta maida gareshi taba amsa sallamar. Babban mutum ne ko ace magidanci,wanda kallo daya zaka masa kasan danta ne daga tsatsonta ya fito,a nutse ya qaraso falon yana kallon widad da fuskarta tayi sharkaf da hawaye "Ke kuma da baki rabo da rigima me akayi miki?" Ya fadi yana neman wajen zama,baki ummu ta tabe tana girgiza kai "Don anyi maganar mahfood ne" saita zarce da gaya masa abinda ya faru jiya. Maida dubansa yayi gareta yana nazartarta na wasu daqiqu,shima kallon quruciyarta yakeyi,yasan ita ke dawainiya da ita,don idan a wani gidanne ko zancan aurar da yayunta da za'a aurar yanzu ba'a fara ba bare ita,to amma haka tsarin yake,a haka kuma dukka suke tafiya "K'aniyarki" abba ya fada yana tsuke fuska "Don gidanku mahfood ba babanki bane kike masa irin wannan?,maza tashi ki dauki kayan ki adana su" fuskarta jiqe da hawayen ta miqe ta dauki ledar,sai tayi hanyar fita da ita "Ina zaki?,nan ne dakinki?" Cikin muryar kuka ta waiwayo "Anty madina zan kaiwa...." "Eh itace ke iya jurewa shirmensu ai" ummu ta karba zancan tana qarashewa abba bayani,sai baice komai ba,wannan ya bawa widad damar ficewa. Tana tafe ita daya tana sharar qwalla,maimakon sassan anty madina,sai tabi siririyar hanyar da zata sadata da parking lot na gidan,tasan can ne babu kowa,don duka samarin gidan masu fita kasuwa kawo yanzu sun fita din,sai su 'yan makarantar da suke shirin komawa ranar litinin,sune daliban da aka yaye daga primary school zasu wuce zuwa qaramar secondry jss one. Dan bencin da ake ajewa a wajen lokaci lokaci ta haye ta zauna a kai,sai a sannan ta buda ledar tana duba abinda yake ciki,kayan makeup ne sosai irin wadanda takeso,batayi mamaki ba,don uncle mahfood din ya jima da sanin zabinta da kuma duk wani abu da takeso. Sai data fiddosu tsaf ta qare musu kallo,sai kuma ta tabe baki,motsin da taji daga parking space din ya sanyata fara tattara kayan cikin hanzari,tana gudun ko abba ne ya fito zaya tafi,ta tabbatar idan ya ganta a wajen fada zata sha. Wanda ta gani a wajen yana niyyar fitowa daga motar tasa ya sanyata sauke ajiyar zuciya,tasan cewa kome zatayi ba kulata zaiyi ba bare ya hanata,don kuwa tsahon tasowarta ta sanshi amma ba zata iya tuna rana daya da magana ta taba shiga tsakaninsu ba. Kamar yadda ta zata din kuwa,ko a yanzun ma dauke kansa yayi ya soma rufe motarsa sanna ya jefa key din a aljihu ya kuma soma takawa yabar wajen. Da kallo ta bishi tana tabe baki gami da jifansa da harara,har sai da ya bacewa ganinta sannan ta dauke dubanta daga wajen,a hankali take tattare kayan tana maidawa cikin ledar,qasa qasa take magana ita daya "Wallahi banaso,bayarwa zanyi,ni ba wani aurensa da zanyi,dan iska kawai" dif maganar tata ta yanke,sai kuma tahau zaro idanu cikin tsoron kada wani ya jita,sai data tabbatar babu motsin kowa sannan ta qarasa kwashe kayanta ta kuma fito. Isowarta farfajiyar gidan yayi dai dai da budewar gate din gidan,qaramar motar qirar 406 ta danno kai ciki,sai ta dakata daga yunqurin isa sassan anty madinan tabi motar da kallo,sai kuma ta saki murmushi har dimple din dake kwance saman kumatunta hagu da dama ya lotsa,saita cilla da gudu gudu sauri sauri zuw wajen motar,cike da zumudi da kuma murna. Sanda ta isa daura da motar tuni mamallakiyar motar ta kasheta tana yunqurin fitowa "Anty dina sannu da zuwa" waiwayawa tayi sashen da widad din take tana niyyar dauko jakarta daga back seat na motar "Widad rigimammiyar ummu,ya na ganki a gida kuma?" Murmushi tayi tana leqen cikin motar da alama akwai abinda take nema "Anty secondry zamu tafi fa,muma mun zama manya kin manta?" "Au anyi haka fa,kice zamu sake samun qarin 'yammata cikin gidan namu....." "Anty wai ina aysar ne?" Ta tambayeta cikin katsar numfashinta "Gashi nan a daure" ta fada tana nuna mata shi a kujerar dake kusa da tata cikin baby car seat,zagayawa tayi da hanzari "Don Allah anty kwantomin shi" "A'ah widad......ke kanki yaushe ummu ta daina goyaki?, barshi yanzu zan fito na kunceshi" bata rai tayi,wai me yasa kullum suke maidata baya,bayan ita kanta tasan girma take?,to idan ma har yanzu yarinyace ita a wajensu me yasa suke mata zancan uncle mahfood?,dole daga bisani anty dina ta ciro yaron ta miqawa widad shi,sannan suka nufi sassan mahaifiyarta tana ankare da widad din. "Ke kuma wanne tsautsayin ne ya sanyaki daukar yaronki ki bawa wannan yarinyar?" Cewa momma mahaifiyar anty dina bayan shigarsu babban falon sassan nasu. Kafin anty dina tace komai widad din ta rigata magana "Momma Allah na iya fa,gash.i nan ma ni na daukoshi tuyn daga parking space" ta fada tana turo baki,wanda ke sake nuni da zallar quruciyarta,abinda ya sake batawa momma rai,taja tsaki tana miqa hannu gami da yunqurin karbar yaron "Miqomin shi nan,me kika iya?,yarinyar da ko pant dinta har yanzu batasan ta wanke ba" momma din ta fada tana jifanta da harara,zallar quruciya ya hana widad fahimtar kuma,bugu da qari kuma,akwai wata irin wankakkiyar zuciya da take da ita,ba kasafai ta fiya damuwa da abubuwan da suke faruwa cikin gidan ba,duk da ta soma girma,hankalinta ya fara fahimtar wasu abubuwan "Allah na fara koya momma" "Naji,jeki da Allah" ta fada tana sake harararta kamar idanunta zasu fado,sai dauke dubanta daga fuskar momma din tana nufar hanyar kitchen dinta. Wata tsawa ta kwatsa mata,wadda sai data sanyata ta kusa tuntube da kujerar dake gefanta "Ina kuma zaki?" Ta fada tana fidda idanu "Wajen Aafiya zani" "Kiyi mata me?" Ledar hannunta ta daga tana nuna mata "Kayan kwalliya na kawo mata ta zaba" "Uhnnnn,salon kije kisa ta bata aikin dana sakata,to zauna nan har sai ta fito,kada ki shiga ku hadu ayimin shirme" narkewa tayi tana duban momma din,da alama tanason ta roqeta ne ta barta ta shiga,tana kuma tsoron tsawarta,don ba abinda ta tsana sama da tsawa da kuma fada. "Ki barta mana momma,idan yaso tana shiga saita fito kada ta zauna" dina ke fada qasa qasa,saboda tausayi da widad ta bata,waiwayowa momma tayi ta kalleta tana dan juya aysar a hannu kamar zata masa rawa "Wannan yarinyar?,tsab zasu iya barnatar min da guri,kuma baka da damar yi maya fada balle duka,tunda tana da uwa a bakin murhu" "Kiyi haquri momma,yanzu zata fito" "Naji,amma indai ta shiga din duk barnar da tayimin ke zaki biya" "Na yarda" sai.anty dina din ta daga kai ta dubeta "Shiga kikai mata kizo na aikeki sassan anty madina" "Tohm" ta amsa da zumudinta tana shigewa,deena ta bita da kallo,bata fiya yin fushi ba don mutum ya bata mata ko ya tsangwameta,bata sani ba ko tsabar quruciya ce?,ko sai nan gaba zata fahimta komai idan hankali ya gameta?. *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *_A RUBUCE TAKE!!!_* (k'addara ta) Page 03 *MAAB LUXURY HOME* *_idan kaji gangami akwai labari_* *_SABUWAR DUNIYA CE_* *ALFAHARIN UWAR GIDA* *FARINCIKIN AMARYA* *MAIDA TSOHON GIDA SABO* *DUNIYAR QYALE QYALE* *KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA* *_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_* *nasan zaku tambaya ina ne nan?* *MAAB LUXURY HOME* 😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya* *_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_* *Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu* *Kayan gado dana parlor* *Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida* *Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a* _adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_ *Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram* @maabluxuryhome *Facebook* @maabluxuryhome *Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka* 08034631010 *Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝 ____________________________ Koda ta shigan bata zauna ba kamar yadda anty deena tace tayi sauri,ta sameta tana yankawa momma albasa,sai zabga gumi taje gami da hawaye,duk da cewa kitchen din kitchen ne irin na zamani,da ya wadatu da iska da manyan windows,dukka a qoqarin momman na koya mata girki,kada ta tashi kamar widad,wadda bata cas bare as a gidan,abinda ya damu wasu cikin gidan,yake kuma basu haushi sosai,suna gajun gatan da ummu ke nunawa widad din yayi yawan da ya kamata ta rageshi ta sanwa wasu cikin jikokinta. Budewa Aafiya kayan tayi tana cewa "Zabi duk abinda kikeso a ciki" kanta ta leqa cikin ledar tana cewa "Ummm,yar gatan ummu,inda nice nace mata ta siyon kayan nan qi zatayi,sai tace naje na tambayi yayuna maza" "Yaaya mahfood ne nima ya kawomin" daga kai tayi ta kalli widad,dududu itama Aafiyan ba zata wuce sa'ar widad din ba,saidai ta danfi widad din girman jiki kadan "To me yasa ba zakiyi amfani dasu ba?" Tura baki tayi tana tsuke fuska "Banaso,ni bana son sa,banason ana min zancensa,ki dauka anty deena zata aikeni" ido ta fidda "Yaushe tazo?" "Yanzu" saita ajjiye wuqar tana zura hannu a ledar,ta zabi abinda takeso tana cewa "Aiko na godde wlh,bari nayi sauri na gamawa momma aikinta na fito" tana dan lila ledar ta fice abinta ba tare data tsaya sauraronta ba,ta samu anty deena a falo,ta bata leda tace ta kaiwa anty madinan,ta amsa ta fice da dan guntun gudunta. Ta dan samu yaran sassa sassan gidan da dan dama a sashen anty madinan,kasancewarta mai fara'a haba haba dasu da jan kowa a jiki,kowa nata ne,hakanan kowa yana jin dadin xama dasu,bayan sa'anninta masu kamar shekarunta data samu,harda yayyensu da ake dab da bikinsu,kuma suna tare da anty madinan,da alama akwai abinda take koya musu,sauran sa'annin nata suna daga gefe sun buda tasu chamber din. Bayan ta miqa mata ledar sai ta kalleta "To wannan dayar kuma fa?" "Kayan kwalliya ne na kawowa su rafi'ah" "A ina kika samu kayan kwalliya masu yawa haka?" Basma cikin 'yammatan dake shirin amarcewa ta fada tana dubanta bayan ta dago kanta daga danna wayar da takeyi,kanta tsaye ba kwana kwana ko damuwa tace "Yaa mahfood ne ya kawomin" "Shine kuma zaki rabar?" Anty madina ta tambayeta tana bada hankalinta sosai a kanta,kamar zata saki kuka tace "Banaso anty wallahi,ni banaso" "Barta don Allah ta rabar,miqomin na zabi nawa" basman ta sake fadi tana miqa hannu,ba wani damuwa tattare da ita ta miqa mata ledar ta qara gaba tana cewa "Anty basma idan kun gama su na'ima zasu zaba" anty madina data bita da kallo tana kallon zallar quruciya ta saki ajiyar zuciya "Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi,baaba mahfood dai kam to" "Uhmmm,wai laifin widad kuke gani?,ni nafi ganin laifin baaba mahfood din ai,kamar maye,yarinya tun tana 'yar tamilo kake faman mata hidima,jikinka da aljihunka basu huta ba,ta fara wayo ta nuna baka so basai ka haqura ba,dui gidan ita dayace 'ya?,ko ita kadai ce jika?" Kai anty madina ta girgiza "A'ah fa basma,har yanzu widad akwai quruciya tattare da ita,ai ba'asan maci tuwo ba sai miya ta qare" "Uhmmm,anty madina,yarinyar nan fa daurin gindi ta samu,Allah kuwa,kuma sai yaushe?,bayan mu kadai ne muka haura zuwa SS,mu dinma gashi SS one kawai aure ya tashi,bare su da jikinsu da alama mai saurin girma ne,Allah yasa su gama JS ma" "Allah ya shiga lamarin" anty madina ta amsa mata "To Ameen"basman ta fada tana maida kanta ciki ledar,don tuni marwa ummee da nujood suka gama zabar nasu,anty madina nata musu tsiyan girma ya fadi,raqumi ya shanye ruwan 'yan tsaki,su da za'a kawo musu akwati me zasuyi da toshin qanwarsu. Widad kam bata sake bi takan kayan ba,a nan suka gama gantalewa,duka ta rabar,dan abinda yayi saura ya gangarar dashi anan wajen anty madina,tayi komawarta sassansu. Sanda ta koma tuni abbanta ya tafi,sai ummu kawai "Ina kikakai kayan?" Ta tambayeta tana tallafe da kuncinta tana dubanta,maimakon ta amsa saita narke fuska,ta kuma shige cikin kujera abinta ta lafe taba mus mus da baki,juyin duniya ta gaya mata inda takai kayan taqi,dole ga qyaleta,tasan indai cikin gidanne zata ji. Tun tana zaman likimo har bacci yayi awon gaba da ita,bata tashi ba sai kusan azahar,sanda latifa ta kammala abincin rana,ta kuma tattaro panties da undies din widad din zata wanke. Sai datayi sallar azahar kamar yadda ummu ta horar da ita,ta karba abinci,saita zagaya baya inda latifan ke mata wankin,ta zauna tana ci suna hira da latifan... *********** Kamar kowacce safiya a ranakun makaranta,school bus din gidan ke tattara kan duka yaran gidan zuwa makaranta,wanda kusan yawancinsu makaranta daya suke zuwa,wadanda kuma suke mabanbantan makarantu sai ta miqa su sannan ta dawo gidan zuwa lokuttan tashinsu. Daga can sassan ummu widad ce zaune saman kujera,sanye da sabbin uniform dinta kamar yadda komai nata a ranar yake sabo a matsayinta na dalibar da ta shiga secondry school a ranar,ummu na zaune daga qasan carfet hannunta riqe da plate tana miqawa widad din plantain din ciki "Maza maza kici kafin 'yan azalzalar nan su biyo sawunki,idan ba haka nayi miki ba haka zaki tafi,yanzun latifa zata kawo miki lunch box dinki" fuska a nake a kuma sakalce take duban ummu "Wallahi na qoshi ummu,ya isa haka" "A'ah,qarashe wannan dai" ta fada cikin nuna kulawa,hakanan ba don taso ba ta daga cup din hannunta dake cike da tea tana shanye ragowar na ciki,dai dai lokacin basma ta shigo,sanye take da kayan gida,kasancewar ita din a yanzun sai daina zuwa,saboda kusantowar bikinsu,bawai don sun gama bane,haka al'adar gidan take,alhajin salim mai fata tsoho mai ran qarfe,kaka kuma uba ga ahalin gidan wannan sbine tsarin da ya dora dukka yara da jikokinsa,mutane da yawa 'yan bani na iya da kuma 'yan gaza gani kance 'Gidan me fata ai da wuri suke aurar da yaransu,da sun ga mai kudi sai su cire yarinya daga makaranta,basa ko gamawa,don sunga suna samun masu danshi ne,suma masu kudin da shegen kwadayi,suna ganin kyawawan mata sai su rude' duk da wannan jita jita na dawo musu kunne amma sunyi banza da zantukan mutane,abu daya tsoho kuma dattijon ya sani shine,mutuncin mace dakin mijinta,hakanan duk wadda tayi katari da samun mijin dake da ra'ayin karatu tana ci gaba da karatunta ne cikin dakin mijinta. "Goyon kaaka,sai a fito ko?,kin tsaida mutane kina bata musu lokaci" ta fadi tana harararta,ganin yadda ummu ta zauna dafa'an tana bata abinci kamar wata yarinyar goye,waiwayowa ummun tayi tana danqara mata harara "Ke kuma da bake za'ayi tafiyar wa ya sakoki a maganar?" "Yo fisabilillahi ummu saita makarar da kanta fa makarar da wasu?" Tayi maganar tana miqa hannu gami da fusgar sabuwar school bag din widad din dake ajjiye kusa da ita,kafin su sake cewa komai.muryar dattijon ta ratso falon "To....to,ya akayi?" Ya fada yana qarasowa a hankali zuwa cikin falon,kafin ya samu waje ya zauna yana dubansu. Russunawa basma tayi ta gaidashi,dai dai lokacin latifa ta qaraso dauke da lunch box din widad din "Gashi an gama" ta fadi tana ajewa gabanta "Ko muje motar na rakaki dashi" latifan ta sake fada tana kuma dauke lunch box din daga gabanta,tabe baki basma tayi sannan tace "Tabdi!,gigin primary,kina shiga dashi ansan burbushin primary ce,meye hadinki da wani lunch box tsabar sangarta?,Allah latifa ke kike sake taya ummu ana sakalta yarinyar nan" ta qarashe maganar tana hararar widad din "Wato kedai anyi babbar banza ko?" Alhj salim ya fada yana duban basma "Allah alhaji bata sanin ta fara girma" "Wuce ku tafi ga iliya can yana horn" ya fada yana daga musu hannu,sai a sannan widad ta sauko daga kan kujerar,ta maida takalmanta suka fice ummu tana muta addu'ar dawowa lafiya. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tabbatar da fitarsu,ta maida dubanta ga alhj salim din "Yaran nan sam basu da zurfin hankali,ta yaya zan banzatar da widad ta gaza samun kulawata?,yarinyar da tun tana watanni a duniya mahaifiyarta ta tafi ta barta?,idan ban kula da ita ba waye zai kula da ita?" Murmushi dattijon yayi yana qarashe janye ragowar carbin da ya rage a hannunsa sannan ya ajjiyeshi gefe "Iya tasu fahimtar kenan,amma duk da haka saboda gudun ci gaba da samun sabani da yadda suke jin haushinta ganin kamar kinfi sonta,kiyi qoqarin boyewa da rage wasu abubuwan" Dan sunkui da kanta ummu tayi "In sha Allah" ta amsa masa cike da ladabi,duk da bata da tabbacin yiwuwar hakan. "Kunun za'a kawo maka ko dumame?" "A fara kawomin kunun da qosai tukunna" ya amsa mata yana gyara zamanshi sosai saman kujerar,ta yunqura ta miqe zuwa kitchen da kanta,duk da tsufanta hakan bai hanata yi masa tasa hidimar da kanta ba,koda zata bawa latifa tata hidimar tayi mata,amma ta alhajin ita keyi. Awannin da tayi a makaranta a ranarta gane banbamcin secondry school da primary,sosai makarantar tayi mata dadi,lokacin tashinsu da yayi tun a cikin motar suke hayaniya,labarin sabon aji da kuma sabuwar makaranta "Don Allah kuyi mana shuru,kun cika mana kunne ha'an" ramziyya wadda take cousin a wajen widad ta fada,ita din gaba take dasu,don a qalla ta basu shekara kusan biyu,ita dinma wannan shekarar ta shiga js three,kuma akwai yiwuwar shekara mai zuwa a karba kudin aurenta kamar 'yan uwanta,dole suka rage hayaniyar,saita maida hankalinta ga iliya driver "Ko ka wuce damu gidan baaba mahmud?,muga lefen najwa tunda yau babu islamiyya" "To shikenan,babu laifi" ya amsa mata. Kicin kicin widad tayi,ko kusa ko alama bata qaunar zuwan gidan nasu,koda hutun makaranta akayi kuwa,gidan ba gurin zuwanta bane,zata iya cewa banda mahaifinta bata da kowa a cikinsa,sai yayanta wanda.ba kasafai kake samunsa cikin gidan ba,yawancin lokutta yana makaranta,duk da yadda mahaifinta ke nacin ta dinga zuwa din amma ummu ta hana,idan ta kama saidai ta wuni ta dawo. Tun daga harabar gidan matan gidan suka fara jiyi hayaniyarsu,babu wadda ta motsa,don kowacce dan data haifa kadai shine nata,har suka qaraso cikin ainihin babban falon gidan "A'ah,kada dai kucemin daga makaranta kuke?" Ta tambayesu tana tafa hannuwa cike da yaqe da kuma riya,saboda mai gidan na nan,daga inda yake din kuma zai iya jiyo komai "Ga alama kuwa umma" najwa dake fitowa daga dakinsu ta fada tana dariya gami da qoqarin daura dankwalinta "Lefe mukazo gani" widad ta fada tana dan dariya,ganin yau yau umman ta sake mata fuska,ramziyya ta harareta "Shegen son kallon kayan lefe,caraf ta bada amsa" "Da gaskiyarta,gaba su za'a kawowa ai" umman ta amsa bayan ta qwalawa me aikinta kira kan ta zubo abinci, murmushi widad tayi maganar tana bata mamaki da dariya,yanzun wataran itama sai a ciko akwatuna da kayan lefe ace nata ne?. A nan suka ci abincin rana suka kuma baje suka kalli kaya son ransu,alhaji mahmud ya fito a shiryensa,suka hau gaisheshi ya amsa musu cikin fara'a da jin dadin ganin 'ya'yan 'yan uwansa,ya bisu da kyautar dari bibbiyu sababbi,duka harda widad din bai banbantata da kowa ba a cikinsu,sannan ya fice yabar gidan. "Ni kunzo a dai dai ma,ku taimakamin na fidda kayan da zan kai dinki" ramziyya ce ta dinga tayata zabin,widad na hade mata su waje daya "Basuyi yawa ba wadan nan kayan anty najwa?, duka zaki kai dinkin?" Inji widad dake zaune daga gefe "Saina ma qara wasu,kin manta haka amare keyin dinki da yawa?" Kai ta jinjina kawai tana ci gaba da kallonsu,bayan sun gama najwa tace "Ki kwana anan widad,saiki rakani nakai dinkin,gobe saina maidaki gida". Cikin murna da zumudi ta amsa da to,ko ba komai zata yita kallon kayan lefen dake burgeta sin ranta,don haka ta baiwa su Aafiya jakarta suka wuce mata gida da ita. Sanda ummu taji shigowarsu sai tayita sanya idanu taji shigowar widad din amma shuru,har ta gaza daurewa ta aika latifa sassan su marwa ko sassan anty madina ta dubo mata widad din me ta tsaya yi bata shigo taci abinci ta sake wanka ta canza kaya ba. Da latifa ta dawo mata da batun sun barta gidan baaba mahmud shuru tayi,cikin ranta duka babu dadi,don bataso ko kadan widad din tayi nisa da ita,to amma tasan mawuyacine itama ta yarda ta kwana din,ta tabbatar da wahala bata nema a kawota gida ba. Sanin hali yafi sanin kama inji hausawa,don kuwa tun bayan sallar magariba bayan sun dawo daga wajen dinkin ta lafe a kujerar falon gidan tana raba idanu,ta cika tayi fam,gida kawai takeson komawa,har umma ta fahimci haka,itama hakan ya mata dadi,don duk randa yarinyar ta kwana a gidan ko yaya ne sai sunga wani abu na bacin rai daga mai gidan dangane da yadda yake nuna mata kulawa "Rabu da ita umma,kin ganta fa ta fara girma,Allah har qirga dangi naga ta fara,amma.har yanxu bata girma da kwana a bayan ummu ba,yau dai a gidan nan zaki kwana,idan bikin nawa yazo ma ba zaki iya kwana ba kenan?" Itadai batace komai ba har zuwa sanda baaba mahmud ya dawo,tare suka zauna da ita suna cin abinci amma sam taqi sakewa,qarfe takwas na dare ta fara musu hawaye,dole ya tashi driver ya maidata gida "Maidata,kada ta hanamu barcin dare" cewar abban nata. Karfe tara saura suka isa gidan,sanda motarsu ta tsaya daidai sanda motar uncle haisam abban su marwa qani ga mahaifinta ta tsaya "Aah,wa nake gani haka da daren nan kamar widad?" A ladabce drivern ya amsa shi "Itace,taqi zama ne abba yace a dawo da ita" "Ikon Allah,to muje ciki" ya fada yana kulle motarsa,sukayi sallama da drivern yabi widad din zuwa sassan iyayensa. Ummun da kuma alhaji suna falo a zaune,sai a sannan yake cin abincin dare sunadan taba fira sama sama da ummun. Bataji sallamar widad ba sai fadowarta jikinta data ji,tana shirin dagata sallamar uncle hisham ta biyo baya "Tare kuke ne?" Ummu ta jefa masa tambayar,yana rage tsahonsa gami da neman wajen zama yace "A'ah,can na ganta drivern gidan yaaya mahmud ya sauketa" "Yar nema,shine kike biyo dare kika gudo?,ba zaki qyalemin mata dai ta huta ba kenan?"cewar alhaji yana tsokanarta,daga ummu tayi tana turo baki "Bakaji dadin gani na ba?,bayan ko cigiyata ma bakayi ba..... shikenan" tayi maganar tana miqewa daga jikin ummu tana wucewa daki "Ahaf......me kika sani banda takura?". Bata ansa ba har ta isa daki ta tura ta shige abunta,dariya suka saka gaba daya, alhaji ya girgiza kai "Quruciya me dadi" ya fada a hankali,sai ya maida dubansa ga hisham yana tattara hankalinsa zuwa gareshi. *_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥 *_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥 *FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥 *JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA* *_'YAN BIYAR DIN NAN NE FA_* *_SARAKAN LABARUN_* *NISHADI* *CAKWAKIYA* *GWAGWARMAYA* *BARKWANCI* *TSANTSAR DARASIN RAYUWA* *TARE DA* *ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI* *SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!* *KIN SHIRYA MADAM?* *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA* *DAUD'AR GORA* Billynabdul *KI KULANI* Missxoxo *IDON NERA* Mamuhghee *RUMBUN K'AYA* hafsat rano *A RUBUCE TAKE* Huguma *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN* 0022419171 Maryam sani Access bank Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number 09033181070 *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU* 09166221261 *Yan nijer kuwa zasu tuntubi wannan number* +227 90 16 59 91 *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾 *HUGUMA* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addara ta) Page 04 ---------------------------------------------------- *MAAB LUXURY HOME* *_idan kaji gangami akwai labari_* *_SABUWAR DUNIYA CE_* *ALFAHARIN UWAR GIDA* *FARINCIKIN AMARYA* *MAIDA TSOHON GIDA SABO* *DUNIYAR QYALE QYALE* *KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA* *_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_* *nasan zaku tambaya ina ne nan?* *MAAB LUXURY HOME* 😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya* *_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_* *Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu* *Kayan gado dana parlor* *Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida* *Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a* _adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_ *Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram* @maabluxuryhome *Facebook* @maabluxuryhome *Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka* 08034631010 *Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝 ____________________________ *Widad* Alhaji salim musayyib mai fata shine cikakken sunan,mazaunin maiduguri da wanda aka haifa a can,ya taso ya girma ya kuma yi gwagwarmayar karatunsa dukka acan din,nau'in jinsin nan da mutane ke kira da suna SHUWA_ARAB,saboda asalin iyayensu da kuma kakanninsu dukka ba'a maiduguri aka haifesu ba,ba kuma anan sukayi rayuwarsu ba,rayuwar da sukayi a maidugurin duka duka 'yar taqaitacciya ce,sanadin kasuwanci,asalin tushensu sun fito ne daga qasar mali zuwa yemen,kuma har yanzu danginsa da tushensa suna can gaba daya ko nace mafi yawa daga cikinsu,iyali ga mahaifinsa musayyib suke ta yado a nan,da kuma nashi ahalin shima daya tara. Matan aurensa biyu dukka 'yan asalin qasarsa wadanda suka hada masa tarin zuri'a da kuma yara masu yawa,dansa na farko da matarsa ta fari wadda ta kasance balarabiyar qasar yemen shine mahmud,wanda yake mahaifi ne ga widad data kasance ruwa biyu,balarabiyar mali kuma bafulatanar usul daga katsina ta gefen mahaifiya,wannan shi ya taru ya bata wani irin sassanyan kyau daya banbanta da kyawun dukka cousin dinta da kuma sauran 'yan uwanta,domin ita daya mahaifiyarta ta haifa ta barta a gidan,sai tarin 'yan uba da kuma cousins da take dasu. Yanayi na rayuwa da kuma kasuwanci ya maido alhaji salim qasar kano da zama,ya fara tara iyalinsa shima,bayan ya aurar da mahmud arziqinsa ya qara ninkuwa fiye dana da,wanann ya siya manya manyan filaye ya hadesu waje guda,ya kuma yanki wani sashe na gidan ya fara ginin matsugunnin da zai zauna da matansa da kuma yaransa,bayan ya kammala suna gab da tarewa matarsa ta biyu ta rasu,sai mahaifiyar mahmud ce kawai Allah ya qaddara mata zama a gidan. Mahmud ne kawai ke rayuwa a wajen gidan,girman gidan ya sanya duk yaronsa daya tashi yin aure,za'a fitar masa da tsarin ginin da zai dace da gidan a gina masa ya tare a ciki,wannan yasa sannu a hankali gidan ya zama babban family house dake dauke da sassa sassa guda biyar,kuma kowanne sashe cike yake da albarkar zuri'a wadata da kuma kwanciyar hankali. Widad ta kasance ta musamman a wajen ummu,saboda ummun ta bude idanu ta gani a matsayin uwa kuma mahaifiya a wajenta,don itace ta raineta tun tana tsumman goyonta har kawo yanzu da shekarunta suke goma sha daya da watanni a duniya. Soyayyar da ummun itama kewa widad din ta banbamta data kowa,saboda itama tana jinta da matsayi biyu ne a wajenta,d'iya kuma jika,ta manta da raino sanda ta amshi widad da nufin rainonta,don a sannan ta aurar da autarta ma anty halima tuni,kasancewar su din basa zurfafawa karatun boko,kina gama primary ma kika samu miji to tabbas alhaji salim zai bada aurenki ne, matuqar ya yarda da addinin mutum da kuma mutuncinsa,ruwan miji ya barki kici gaba,ruwansa yace a'ah. Ko kadan rashin uwa bai wani taba widad ba,saboda ta samu dukka kulawa da 'ya ke samu ga mahaifiyarta daga wajen ummu. Mahfood d'a ne ga baaba maisara,wanda suke 'ya'yan wa da 'ya'yan qani da mahaifin widad,tun kafin ta kawo haka yake nuna yana da interest a kanta,amma ko daya widad din taqi sake masa balle ya samu fuskar da ko hira ta zauna tayi dashi,saboda ita din wata irin mutum ce,tana da wahalar sabo,hakanan idan kanason ganin kazar kazar dinta da hirarta to cikin gidansu ne,musamman sassan ummu ko na anty madina,indai akace maka baqon guri ne zaka tsammaci cikakkiyar magana ma bata iya ta ba. Abu na biyu tana da masifar tsoron maza,saboda kullum hudubar ummu shine,idan ta sake ta yarda ko hannunta namiji ya kama zatayi ciki,idan kuma ta samu ciki mutuwa zatayi,wannan yasa sam sam bata yarda ko inuwa su hada,bama shi ba,dukka samarin gidan da suke a matsayin yayye a wajenta haka dabi'ar ta take. _wannan kenan_ *Bayan shekara uku* Tun daga daren juma'ar da ya kama gobe sallah gaba daya yanayin gari ya canza daga yanayin azumi zuwa yanayin daren sallah,ko ta ina al'ummar musulmi sai hada hada ake,tituna zuwa layuka,gidajen kitso qunshi zuwa shagunan masu dinki ko ina cike yake danqam da jama'a kamar rana. Haka ce ta kasance gidan alhaji salim musayyib,babban gidan dake dauke da family masu yawa,a dabi'ar gidan babu tsawwalawa,koda salla ce kowanne sashe yana yin kalar girkin da mace ko matan sashen suka tsara yi,saboda kowanne part akwai store da kuma kitchen din su tare da me aikinsu,saidai idan an gama ranar sallah dukka suna zubawa abincin mai dan dama su aike sashen surukarsu hajiya ummu,duk da ita dinma ba zama take ba, takanyi abinci har kusan kala biyu,sabida karbar baquncin jikokinta dama surukanta matan 'ya'yanta maza guda biyar da Allah ya bata,su da 'ya'yansu da kuma 'ya'yan wajen diyarta halimatu,hakanan su kansu jikokin dake cikin gidan suma kusan a nan suke zuwa su karba nata,sukance yafi dadi. Dai dai lokacin da sassan anty madina yake a cike da yara yaran matan gidan,wanda ake ta faman saka musu qunshin salla daga mai qunshin da ummu da kanta ke daukowa ayi musu,sannan kuma ga me kitso itama tanata kitse musu kansu duk da baiwar suma da yalwar gashi da suke dashi tubarkalla,babban falon da anty madinan ta ware musu saboda irin wannan hidimar a kacame yake. Daga gefe daya widad ce zaune,tsahon shekaru ukun data qara kyawunta ya sake bayyana muraran,hakanan alamun girma sun fara bayyanar mata,duk da cewa har yanzu gabunta sakarci da kuma wautarta tana nan,cikakkiyar GOYON KAKA,Qunshinta yafi na kowa jan lokaci,saboda ummun tace na musamman za'ayi mata kamar yadda aka saba,masu zumbura baki nayi masu qorafi nayi,to amma kusan idan da sabo an riga an saba,haka sukayi suka gama suka kuma haqura. "Aafiya ciremin lallen nan" widad ta fada tana yamutsa fuska saboda jimawar da tayi a zaune "ke kam kin huta,sauranki kitso" afiya ta fada tana matsowa hadi da fara sabule ledar da aka rufa hannun,harara widad ta jefa mata "Tabdijan,wa za'ayi wa kitson?,Allah ya kiyaye" ta fada tana bata fuska,kitso babban abokin gabarta ne,sam bata qaunarsa,tun daga quruciyarta kawo yau tsaf zata iya irga adadin sau nawa aka taba yi mata kitso,mutane kance saboda tana da suma me kyau ne da tsaho,kusan sumarta ta zarta dukka ta yaran gidan,tamkar zabarta akayi,hakan kuma baya rasa nasaba da gado da tayi ta wajen uwa da uba,don idan ta ware sumarta tana iya saukar mata har tsakiyar gadon bayanta. Dariya afiya ta saki tana ci gaba da tsokanarta "Nikam naga lokacin da zaki daina gudun kitso" "Babu rana"ta amsa mata tana Allah Allah a gama cire mata ta tsallake ta gudu ma daga falon. "Tubarkalla ma sha Allah 'yammatan ummu,lallai dole mu caji 'yan samari kudi,irin wannan kyau haka?" Anty madina dake shigowa dauke da babban farantin data yanka musu fruit ta fada tana murmushi,cikin yanayi na nuna jin kunya abinda ke nuni da soma girman widad dim ta boye fuskarta tana dariya "Bafa wasu samari anty Allah" "Aah fada kike wallahi,kowa fa ya sani" wuf tayi ta tashi saboda yadda sauran 'yan uwanta ke juyowa suna kallonta,wasunsu suna mata dariya ne da gaske har zuciyarsu,yayin da wasunsu kallon hassada qyashi da baqinciki ne suke.jifanta dashi,abu guda daya da bai taba dadata da qasa ba,itakam indai zata jita wajen ummunta to komai lafiya lau,takan manta da dukka wasu qananun abubuwa dake tasowa ko kuma faruwa cikin gidan. "Ina zaki sauranki kitso ai" anty madina ta fada,sai ta tsaya tana duban anty madina,fuskarta dauke da zallar quruciya ta narke fuska,abinda ke nuna gab take da fara tara hawaye "Don Allah anty a barshi,nayi bayan sallah" haba ta kama tana kallonta "Anya widad?,ke wannan sumar bata damunki ne?" Dariyar yadda anty madinan ta saki baki ya kamata "Ai shikenan,ki biya ta kitchen,ki cewa yalwa ta baki abincin ki kaiwa ma'aruf" sunan da anty madinan ta ambata sai taji kamar tace mata ba zata aiken ba,amma anty madina tafi gaban haka a wajensu,dukkaninsu suna mata kallon babbar yaya, kasancewar dukka manyan yayyansu mata suna gidajen aurensu,a kaf surukan gidan kuma ita dince mai qananun shekarun da suke iya sakewa suke komai tare da ita,itama kuma ta riqesu tamkar qannen nata. Ba'a son ranta ba ta biya kitchen din ta dauki abincin,ta fito tana dariyar yadda yalwa keta koda kyan qunshin nata,tsakaninta da dukka ma'aikatan gidan qauna ce da soyayya,koda kuwa ba masu aikin sassan nasu ba,idan ka ture wautarta da quruciya da tabara ta goyon kaka,ita din yarinya ce mai matuqar girmama wanda ya girmeta,zaiyi wuya ka sameta da laifin rashin kunya,kai koda laifi akayi cikin gidan da wahala ka samu sunanta a ciki,idan kaji an ambaci sunanta to wata wautar aka tafka,ko kuma ta taba sakalcin nata data saba,wannan ya sanya ummu bata ragawa duk wanda ya tabata,takan ce "Nasa halin kayata fes,duk wanda yace tayi wani abu idan ma sharri ne zan gane ato,nasan me zata aikata,hakanan kuma nasan abinda ba zata aikata ba". Har ta isa qofar dakunansu taji hayaniyar mutane a dakin nasa,da alama baqi yayi abokansa,tsaki taja,ta koma da baya cikin takun da basu fi goma ba,ta tsaya dab da motarsa. Sai data qarewa motar kallo sannan ta matsa kusa da boot din motar ta dora masa abincin a nan,ta kama gabanta hankali kwance ta wuce sassan ummu. Saidai tana sallama a sassan taji nadamar dawowa sassan ta kamata,babu wanda ya gaya mata yazo gidan,da babu abinda zai sanyata dawowa yanzu,sun riga da sun ganta gaba dayansu,harda na'eema diyar anty halimatu da tazo gidan sallah,saboda haka duk wata dama ta komawa ta qwace mata babu ita,sai taci gaba da takawa cikin falon tana tsuke fuska,hadi da sake gayyato bacin rai saman fuskarta,uwa uba dama ga yunwa dake cin hanjinta,taqi abincin wajen anty madina saboda ba cimarta ta dafa ba,tace sai ta dawo wajen ummunta. *_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥 *_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥 *FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥 *JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA* *_'YAN BIYAR DIN NAN NE FA_* *_SARAKAN LABARUN_* *NISHADI* *CAKWAKIYA* *GWAGWARMAYA* *BARKWANCI* *TSANTSAR DARASIN RAYUWA* *TARE DA* *ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI* *SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!* *KIN SHIRYA MADAM?* *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA* *DAUD'AR GORA* Billynabdul *KI KULANI* Missxoxo *IDON NERA* Mamuhghee *RUMBUN K'AYA* hafsat rano *A RUBUCE TAKE* Huguma *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN* 0022419171 Maryam Access bank Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number 09033181070 *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU* 09166221261 *Yan nijer 🇳🇪🇳🇪kuma zasu tuntubi wannan number* +227 90 16 59 91 *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 05 *MAAB LUXURY HOME* *_idan kaji gangami akwai labari_* *_SABUWAR DUNIYA CE_* *ALFAHARIN UWAR GIDA* *FARINCIKIN AMARYA* *MAIDA TSOHON GIDA SABO* *DUNIYAR QYALE QYALE* *KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA* *_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_* *nasan zaku tambaya ina ne nan?* *MAAB LUXURY HOME* 😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya* *_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_* *Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu* *Kayan gado dana parlor* *Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida* *Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a* _adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_ *Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram* @maabluxuryhome *Facebook* @maabluxuryhome *Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka* 08034631010 *Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝 ____________________________ Idanu ya zuba mata yana kallonta,kullum sake canza masa takeyi,tana dada girma tana kuma sauyawa,yana kuma sake jinta a ransa,a haka ta qaraso wajen,amma ko sau daya taqi kallon sashen da yake zaune ma. "Ina yini?" Ta gaidashi tana rusunawa kadan,saidai bashi take fuskanta ba,wani sashe na daban take fuskanta "Lafiya lau widad,ya shirye shiryen sallah?" "Lafiya" ta amsa masa a cunkushe tana duban ummu "Ummu yunwa nakeji,me aka dafa?" Abinda ta tsana ummun ta fara yi wato miqewa,da alama zata basu waje kenan,gamin haka sai tayi wuf ta riga ummun miqewa,daga kai tayi ta kalleta "Ki zauna, na'eema zata kawo miki abincin yanzu" yadda ummu tayi maganar babu wasa saman fuskarta ya sanya ta koma jiki a mace ta zauna tana tara hawaye a idanunta,tana kallonsu suka fice daga falon. Ajiyar zuciya ummun ta sauke bayan barinta wajen,wanan wanne irin abune haka?,me yake faruwa ne?,har yanzu komai yaqi ya canza tsakaninta da mahfood din?'. Cikinsu shi da ita ba wanda ya iya cewa komai,har na'eema ta kawo abincin ta ajjiye ta juya ta fice,a hankali yasa hannu ya jawo abincin gabansa sannan yace "Kamar yunwa naji kince kina ji ko?,matso kici abincin kada ya huce" ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata cin,yayita fama amma qememe tayi biris,dole yaja ledar da yazo da ita zuwa gabansa "Ga kayan sallah nan,da fatan za'ayi kwalliya me kyau" sosai ya sake quleta,don tana da son kwalliya da gayu sai ya maidata wata qwalamammiya?,bashi da aiki sai kawo mata kayayyaki,yadda taji haushinsa sosai a yau din har taji tana qwarin gwiwar gaya masa abinda bata taba gaya masan ba,daga fararen manyan idanuwanta tayi ta azasu a kansa "Nifa bana so,banason komai naka,sannan ma ni ba wani auren dangi da zanyi,ni ba yanzu ma zanyi aure ba,don Allah ka rabu dani,ni.....bana sonka" dai dai lokacin da alhaji mahmud salim mahaifinta yayi sallama cikin falon ya kuma sanyo qafafuwansa. Idanu yake bin widad din dashi,yaji kalamanta guda biyu na qarshe,zallar bacin rai ne kwance akan fuskarsa,ita kanta suna hada ido da abban nata ta sadda kanta qasa gabanta yana tsananta faduwa,mahfood kuwa miqewa yayi yana masa sannu da zuwa "Zauna mahfood......me naji kina fada widad?" Tsoro da firgici suka hanata yin koda qwaqwqwaran motsi bare ta amsa shi,cikin tsawa ya sake maimaita mata tambayar,saita ida rikicewa gaba daya,ta kuma saki kuka a lokaci guda,saboda sam sam bata saba da irin wannan tsawar ba. "Dan uwanki kike gayawa bakiso saboda baki da kunya?,wato kin fara girma kenan widad?" Ya fada cikin mugun fada da kuma daga murya,sautin muryar tasa da ya isarwa da ummu saqon akwai abinda ke faruwa a falon,taji kuma ta kasa nutsuwa saboda kama sunan shalelenta da taji anyi,saita yunqura ta miqe tana duban na'eema "Ki qarasa hada muku kayan waje guda ki maida daya dakin kafin gobe gidan ya sake cika,ina zuwa" ta fada tana takawa a hankali saboda dan ciwon qasa da take fama dashi lokaci lokaci. Isowarta wajen kadai tafahimci abinda ya faru,fada sosai abban yake zuba mata,da alama ransa ya baci sosai "Mahfood dan uwanki ne,da kike cewa kuma bakya sonshi gwara ki koya tun wuri,don baki da miji sai shi,shi zaki aura ki jini da kyau" ya fada yana kama kunnensa da hannunsa guda daya "Tashi ki bani waje" ya fada a tsawace,ta gudu ta miqe tayi hanyar dakinsu fuskarta jiqe da hawaye,saman gadonta ta fada wanda ba kasafai ma take kwana a dakin ba,koda yaushe tana maqale da ummu,a dakinta take kwana,koda tana wajen alhajin to itakam tana dakin nata,haka zata hada duka filallukan dake saman gadon ta qudundune a ciki saboda shegen tsoron da take dashi,bare ma ba kasafai ummun ke barinta ba,wani lokaci ma bata sanin bata dakin idan baccinta yayi nisa ko kuma nauyi. Kan mahfood a qasa sanda abba ke bashi haquri "Nasan harda quruciya abba,har yanzu shekararta sha hudu" "Da kuma sakarci ba" "Ayi haquri" ya sake fada kansa a qasa,sannan ya miqe yayi musu sallama ya fice daga sassan ummun yace zai shiga cikin gidan su gaisa da sauran mutane. "Ka dinga bin al'amarin nan a hankali mahmudu,wannan fadan duka ba shine ba" ummu ta fada bayan dukkaninsu sun zauna "Ummu abunne yake dauren kai,anata cewa quruciya ce,to amma tana sake girma tana sake qinsa?" Kai ummun ta jinjina,ita kanta bataga na meye abba din sai ya matsa har haka ba,shi zumuncin da yakeson a qarfafa a kuma sake qullawar ai ba dole sai ta hanyar hada aure ba,inda akwai wata diyar gareshi wadda tadan tasa kamae widad din ma ita zaifi mata sauqi ya maida alqawarin kanta,bata qaunar wannan rikicin da aketa yi da widad din "Kasan haduwar jini ne,idan kuma Allah bai sanyata tsakanin bayinsa ba babu yadda za'ayi" "Haka ne,Allah yayi mana mafita" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" ummun ta amsa masa,sai ya miqa mata babbar jakar da yasa aka shigo da ita,wadda ke shaqe da kayan sallah na mutanen da ya saba yiwa duk shekara,wanda yaran gidanne 'ya'yan qannensa da suke sa'annin widad,wasu kuma qasanta a shekaru,ga kuma nata na musamman ita da widad din da alhaji "Alhajin baya gida ne?" "Kasan yau daren sallah,suna can fadar mai martaba,har sai an sanar da ganin wata sannan" kai ya jinjina,don kusan al'adar sa ce duk shekara "To Allah ya dafa mana" ya amsawa ummun. Kuka take sosai da hawayen daya fara jiqa pillow din da take kwnace akai,juyin duniya na'eema tayi ta tashi tayi haquri ta dauki abincinta taci amma ko kulata batayi ba,sosai take jin qin mahfood din cikin ranta,ko sau daya bata taba jin tana sonshi ko yana burgeta ba,yana da kirki ta sani,amma ita ba wani magana datayi kama data aure a tsakaninsu da take jin zata yiwu. Har abbanta ya tafi tana kwance tana kuka,ummu na falon bata motsa ba,duk da na'eema ta gaya mata,bataso taje taga yanayin da take ciki zuciyarta ta karye ta gaza bata qwarin gwiwar yiwa mahaifinta biyayya,wannan yasa tayi zamanta a falo,duk da zuciyar da hankalinta na kanta. Duk wanda ya shigo nemanta sai tace masa kawai tayi bacci,wasu su zauna suyi hirarrakinsu wasu kuma su wuce,tana nan zaune har qarfe goma na dare,zuwa sannan juriyarta ta qare,sai ta miqe ta shiga dakin da kanta. Tana kwance rub da ciki har yanzu,saidai ba zaka iya tantance bacci take ko idanuwanta biyu ba,ta qarasa a hankali tasa hannu tana taba kanta gami da kiran sunanta,sheshsheqar data sauke hadi da ajiyar zuciya ya tabbatar mata idanuwanta biyu "Meye haka wai widad?,tashi mana" ta fadi tana qoqarin dagota ta zaunar da ita,sanda ta kalli fuskarta sai zuciyar ummun tayi rauni,kallon marainiya takewa widad shine dadin abinda yasa batason komai ya sameta mara dadi,yarinyar da batasan dumin uwarta ba?,gaba daya fuskar tata ta tashi ta kuma yi jazur da ita abinka da farar fata "Kukan kike har yanzu kamar wadda akace mata zata mutu?,tashi ki wanke fuskarki kici abincin naki" "Ni banaci" ta fada muryarta na rawa hawaye yana sake barke mata,sai kawai ta fada jikin ummun tana sakin sabon kuka,har cikin ranta ummu takejin kukan,sai ta fara lallashinta,da qyar ta ciyo kanta taje ta wanke fuskar ta sanyata a gaba taci abincin,da qyar tayi cokali biyar tace ta qoshi,ummun taso sanyata a gaba su wuce dakinta ta kwana kamar yadda ta saba amma tace anan zata kwana,tunda ga na'eema,sannan Aafiya ma yau a nan zata kwana,dole ta rabu da ita tabar musu dakin bayan ta ja mata kunnen kada ta sake irin wannan kukan,ta kwantar da hankalinta kuma. *_W A S H E G A R I_* Kamar yadda suka saba kusan kowa da kowa ake tafiya sallar idi a gidan,akwai wadatar ababen hawa,kowa zai diba iya mutanen da motarsa zata iya dauka,tun sassafe kowanne sashe suke tashi yaran suyita shiri,iyayen kuma suna qoqarin qarasa abincin sallah wanda idan an dawo saga udi za'a dira akai a fara ci da kuma rabo,to hakanma wannan karon ta kasance,har sassan ummun hayaniya ce ke tashi,saidai banda widad dake nannade a bargo,ko motsawa batayi ba bare ta shirya,sunyi sunyi ta tashin amma taqi kula kowa,ummu kuma tunda ta fito da asuba ta tadasu sallah bata kuma fitowa ba,sai alhaji ya gama shirin idinsa. Karo na biyu latifa fa dawo,wadda itama ta shirya fes da ita cikin dinkin sallarta,duk sallah sai an mata dinki kamar kowanne yaro ko jika dake gidan,dinkinta masu kyau da tsada har kala hudu ko uku "Widad din ummu,kiyi haquri ki tashi ki shirya,kinga kowa ya gama shiryawa,yanzun nan zakiji an fara tafiya"ta fada cikin lallabawa,bakam tayi kamar bata a wajen,duk iya dabara da hila ta latifa haka tayi ta haqura,daga qarshe dai haka suka tattara suka tafi sallar suka barta. Bayan ficewarsu ummu ta fito "Ja'irai,tunda naji shuru nasan sun tafi,kafin su dawo su hana mutun sakat" tayi maganar tana tura qofar dakin,sai idanunta ya sauka kan tudun bargon dake kan gado,cikin ranta zuciyarta ta bata mutum ne,sai ta qarasa tana yaye bargon. Salati ta saka ganin widad din kwance tana sharbar kuka "Na shiga uku ni laila?,wai dama baki haqura ba widad?" Hankalin ummun ya tashi sosai,haka ta sanyata a gaba sai data tashi tayi wanka ta kuma zuba mata abincin safe taci,tana gama cin ta koma ta kwanta "Falo zaki fito ki kwanta,bazan barki ki sake kwanciya ba" "Ki qyaleni kawai ummu,tunda abba baya sona" ta fada da yanayi na quruciya tana kuma sake sakin kuka,baki ummun ta saki,tana magana kamar wata babba?,duk yadda taso ta fiddota amma taqi sai kwanciya. Koda aka fara dawowa daga idi tuni gidan ya fara cika da jama'a kamar yadda aka saba duk shekara,jikoki sun fara hallara,kowa fuskarsa da zuciyarsa cike da walwala da kuma farinciki,lokacin sallah lokacine na farinciki,amma wannan shekarar banda widad din,don kuwa duk budurin da akeyi tana kwance a qule a daki,da yake tana da kirki qwarai da son yara qananu,kowa yazo sai yace ina widad,saidai ummun tace bata da lafiya tana daki tana bacci. Duk yadda jikokinta ke karakaina a falon amma rashin walwala da fitowar widad din sai taji komai ma baya tafiya dai dai,maganar mahfood din taji itama ta soma fita mata a kai,gwara abar zancan,idan yaso a gwada bata wani,duk da abban nata ya gaya mata ita din bata son auren zumunci,to amma maiyuwuwa ta haqura idan aka gwada mata wani indai jininsu yazo daya,da wannan maganar a ranta tayita dakon shigowar alhaji don suyi maganar ita dashi. Bai samu shigowa gidan ba sai yamma liqis,zuwa lokacin manyan yayyensu maza dake sa mota sun debi yaran gidan da yawa zuwa guraren wasannin sallah da shaqatawa,gidan sai yayi shuru,sai dai daikun yara dake shigowa su fita,har sannan widad din tana daki a kwance,duk da tulin kayan sallar da take dashi bata sanya ko guda daya ba bare ta fito. Sai data gabatar masa da abinci yaci ya qoshi sannan ta fara magana dashi,yayi shuru yana sauraren ta har ta gama bayananta gaba daya,sannan yayi gyaran murya yana dubanta....... *_TOFA,TAFIYAR BA'A FARA BA,KO SHIMFIDA BAMU GAMA BA_* *_INA SAKE TUNA MUKU,IDAN KIN KARANTA HANGEN DALA,TO TABBAS SHAFAR MAI NE,WANNAN TAFIYAR TA FISHI ZAFI AMFANI DA KUMA DARUSSA_* *_LABARI NE DAYA QUNSHI TSANTSAR KISHI,KAIDI MUGUNTA DA KUMA SIHIRI_* *_MUGUN TAKU IRIN NA BAQAR KISHIYA_* *ZALLAR RAYUWAR GIDAJENMU TA GASKE* *MADARAR SOYAYYA MAI TSUMA ZUCIYA BURGEWA DA BARWA RAYUWA DARASI* *GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN* 0022419171 Maryam sani ACCESS bank *Saiku tura shaidar biya ta nan* +234 903 318 1070 *Masu tura katin waya kuma zasu tuntubi wannan number* 09166221261 *Yan nijer zaku tuntubi wannan number*🇳🇪🇳🇪 +227 90 16 59 91 *Thanks for choosing us* *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 06 "Gaskiya ne,kema kinzo da naki hanzarin,sannan a zahiri cikin musulunci babu auren dole,duk da shi mahmudu yana ganin kamar gata ne zaiyi mata,kuma hakan shine dai dai,to amma kuma duk da haka tana da damar da za'a bata zabi,iyaka idan aka duba ya zamana akwai kuskure ko rashin dacewa a ciki sai a soke lamarin",tana tausayin widad,tasan akwai maqiya da magauta fal cikin rayuwarta,shi ya sanya take a tsaye ga duk wani abu da zaya cutata mata. Bangaren widad kuwa haka ta yini ta kwana,ummu nata dakon zuwan mahaifinta suyi magana da alhajin,bai shigo gidan ba sai a washegarin da azahar,akayi sa'a alhajin shima yana nan amma yana shirin fita. Shuru abban yayi sanda alhaji ke masa maganar gami da bashi umarnin janye wancan qudurin nasa "Alhaji,naso ace an hada abun nan saboda a qarfafa zumunci,sannan yanzun bansan da wanne ido zan kalli isma'il ba(mahaifin mahfood)" murmusawa alhaji yayi "Akwai dangi da yawa,ba lallai sai mahfood ba tunda jininsu baizo daya ba,kada azo ayi abinda za'a zo daga baya ana dana sanin aikata shi,isma'ila kuwa shi da mahfood din kabar komai a hannuna zan magana dasu" kansa a qasa amma ransa a matuqar bace ya amsawa da alhaji,gami da yi masa godiya da fatan samun qarin shekaru masu albarka da lafiya me dorewa. Ummu da kanta ta shiga dakin inda widad keta fama kwanciya don yi mata albishir,a kwancen ta sameta,ta janye rufarta tana cewa "Tashi......ruwa sarkin kwanciya" sake curewa tayi waje daya tana turo baki gaba,don har ta gaji ma da kukan "Nace ki tashi hakanan, kwanciyar ta isa,maganar aure ce an janyeta an fasa" da sauri ta waiwayo tana kallon ummun gami da jin fitar maganar daga bakinta kamar almara,ko kuma tayi hakanne don ta tashi ta sake?,babanta fa?,wanda baya fadin abu ya canja,wanda baya magana ya sabata,tsayayyen akan duk abinda ya sakawa ransa zai aikatashi,to amma kuma......ummu bata qarya sam sam tasan halinta,fadi da cikawa ce,sannan yadda take qaunarta ta tabbatar ita da alhaji ne suka aikata hakan,sai kawai ta bugo wani tsalle ummu bata ankara ba sai jinta tayi a jikinta ta dane mata wuya cikin madaukakin farinciki. Murmushi ummu keyi tana jin farinciki cikin ranta itama,tasa hannunta tana banbanreta a jikinta tana cewa "Zaki qarasani 'yar nema,ashe duka iskanci ne,mitsitsiyarki dake wai kinsan meye auren dole,maza saiki sauka ki shiga bandaki ki wanka ki shirya ki shiga cikin 'yan uwanki" ummu kuwa bata kai qarshen zancan ba ta dire sai bandaki,tayi wankanta sarai,akwai kayan dama da taketa cin burin sakasu,yau kuwa zata gwangwaje kwalliyarta,latifa ta zuba mata abinci taci da kyau,sannan ta tsala kwalliyarta cikin wani lace mai azabar kyau da tsada da ummu ta dinka mata ita kadai,ta zauna ta tsara kwalliyarta dai dai da shekarunta da kuma iyawarta,sai gata ta fito dagwas dagwas gwanin kyau. A falo ta samu ummu tare da baqin da suka fara zuwa mata yawon sallah,wanda duka 'yan uwa ne da surukai,batulu ce matar baban widad din,haka suke rabawa duk sallah,wata zata fara zuwa gaida ummu dayar ta zauna a gida,washegari ko wata washegarin sai dayar tazo. Jakarta ummu ta kaba ta zuba mata sababbin kudi 'yan biyar biyar,duk da tasan halin kayarta,qila sai a gama yawon sallar a ci a cinye bata kashesu ba,daga qarshe dasu da wadanda ta samu duka dawo mata dasu zatayi "Ga barka da sallah ta nan" rungume ummu tayi tana dariya cikin farinciki "Na gode ummu" sai a sannan ta waiwaya ta rusuna kadan tana gaida batulu. Can qasan zuciyarta maqare fal da baqinciki da takaicin yarinyar,amma a saman fuskarta kadaran kadaham,tayi qoqarin gyara mood nata ko don ummu dake wajen ta amsa mata "Yammatan ummu,lafiya lau sai ina?" "Wajen anty madina zani" ta amsa mata tana yin gaba,duk da qarancin shekarunta,amma kwanyarta na iya tuna wasu abubuwan da suke gudana tsakaninta da matan baban nata,suke kuma kan gudana din,shi yasa dai dai da wuni guda bata marmarin zuwa gidan nasu bare ayi batun kwana,ummu ma ba zata bari ba,koda kuwa babanta yana da muradin hakan. Kamar ko yaushe chamber ta hadu a sassan anty madina,shigarta wajen kallo ya koma kanta,masu tankwa da yabawa nayi,masu baqinciki suna nasu aikin,ko meye saman fuskarka kusan ta saba dashi,uwa uba ga quruciya da bata sanyata daukan abubuwansu da muhimmanci,fatanta da burinta kawai ta shiga cikin 'yan uwanta ayi mu'amala da ita kamar kowa. Wunin ranar gaba daya cikin walwala ta yita,sai takejin kamar wadda aka daddaure ayau ta samu 'yanci,sai dare ta dawo sassan umnu,tana gefanta tana bata labarai na abinda suka faru,kowa cikin jikoki na zaune saman carfet suna cin abinci amma ita na nanuqe da ummunta,tare suka ci abinci kafin dare ya miqa su wuce dakin kwanciya. Sai bayan isha'i a ranar alhj mahmud ya koma gida,har lokacin akwai sauran damuwa da bacin rai a tattare dashi,yayi wanka ya canza kaya,umma dake da girki ya gabatar masa da abinci,sannan ta zauna a gefansa tana sake karantarsa,bakinta cike fal da tambayoyi da kuma son jin qwaqwafi,don tunda ya shigo ta karanci akwai wani abu daya faru. Ganin shuru yana ta cin abincin baice komai da ita ba,sai ta danyi gyaran murya tana gyara zama "Amma abbansu fuskarka kamar akwai damuwa,Allah yasa lafiya?" Tsaki yaja yana ajjiye cokalin hannunsa,ya kalleta "Bari kawai hauwa'u,yarinyar nan ce ta watsamin qasa a idanu,takeson ta kunyatani a dangi" "Wa fa?" Ta tambaya tana yamutsa fuska,duk da zuciyarta ta gama gaya mata wacece "Widad mana,qiri qiri yarinyar nan ta fandare taqi mahfood,har sai da alhaji yasa baki a maganar ya dakatar da abun" baki hauwa ta riqe tana sakin salati cikin sake kambama abun,lallai yarinyar shafaffa da mai ce,tana cewa su din akwai yaransu da aka yiwa haka?,kuma suna zaune lafiya lau a gidajensu har kwanan gobe sai tashin zancen "Yanzu abbansu,lamarin da aka faro zancansa tun yarinyar nan bata cika mutum ba,amma yanzu saboda idanunta sun fara wayewa zata ce bataso?,kuma alhaji shima ya biye mata?,wannan wacce irin tabara ce?,ah to lallai abu ya girmama,billahillazi idan ba'a yi wasa ba gaba sai abinda tace za'a yi mata,idan ba haka ba ran kowa ya baci harda mu iyayenta" fushin abba ne ya motsu sosai akan widad din,kuma dama abinda hauwan keso kenan "Haba ita din banza?,wallahi bata isa ba,ita ta haifemu ma ashe kenan" "To tana ganin haka tana faruwa tun yanzu gaba basai abinda taga dama ba?,aure kuma dama ai uba ya isa da diyarsa budurwa ya zaba mata miji,bare wannan da ko minzalin budurwa bata kai ba" shuru yayi yana juya zancan,abun ma sai yanzun yake sake bata masa rai,tabbas bazai barta haka ba,duk da ya sani rayuka zasu iya baci,don ummu ba zata lamunci takura ga widad din ba. A wannan daren da taimakon zugar hauwa ya kwana cikin tunani,washegari.batulu da hauwan ta bincina mata abinda ke faruwa itama ta dora da tata zugar,sai ya sake hawa sosai "Banason wannan maganar,ku qyaleni haka" yace dasu daga bisani,ya riga ya gama yanke matakin da zai dauka akan maganar. Widad kuwa walwalarta takeyi sosai abinta hankali kwancw,tunda ta samu akwa kwance ta daga daurin talala na auren mahfood,bikin sallarta take abunta gaba gadi,koda abbanta yazo gidan bayan kwanki biyu bata kawo komai a ranta ba,batasan cewa yazo da sabon alqawarin bada ita ga ma'aruf,ma'aruf dai,ma'aruf din da kalmar zo na kasheki bata taba shiga tsakaninsu ba,ma'aruf din da tsakaninta dashi saidai ido,saidai bata da labarin wannan alqawarin,domin ummu ta rufe zancan don kada a katseta daga walwalar data samu cikin bikin sallar,ta sakaya zancan bayan ta cewa abba "Mahmudu ni bazan dakatar dakai ba daga baiwa yarinyarka duk wanda kakeso ba,amma muddin babu haduwar jini ko taji bata sonsa bazan lamunci a kaita inda zafa quntata ba,don ina kallonta ne kamar amana a hannuna,idan tasu tazo daya da ma'aruf zanyi farinciki da hakan,don atika(mahaifiyar ma'aruf,jika ne shi cikin gidan,d'an mace ne)tamkar 'ya take a waje na". Ci gaba tayi da sabgoginta abinta,ta.maida kanta ga islamiyyar da take zuwa,don tunda aka koma hutu boko bata koma ba,alhaji yace ya isa hakanan,su maida hankalinsu ga islamiyya,ita dasu Aafiya,yayin da zancan bada ita ga ma'aruf ya fara yawo cikin gidan. Zancan ya zowa anty madina ta bakin mijinta uncle mulhim,ta jinjina lamarin sosai "Tirqashi" ta fadi,saboda tasan irin rashin jituwar dake tsakaninsu,duk sanda widad ta shigo tana binta da kallo yadda take sabgoginta da alama batasan abinda yake faruwa ba,tana tausayinta itama,tana yarinyarta amma sai abubuwa ke zuwar mata kamar wata babba?. Bata tashi sani ba sai wata rana suna dawowa daga islamiyya,a hanyarsu ta zuwa gida sun biyo ta wani layi,tun daga nesa suka hangi ma'aruf din yana tahowa shi da wani abokinsa,kunnensa maqale da earpiece suna hira kadan kadan da abokin nasa,kafin su qaraso Aafiya tasa hannu tadan bugi widad,wai tanason mata nuni dashi,saidai ko daya ita widad din bata ma fahimci me take nufi ba har suka qaraso dab dasu. Aafiya ce ta gaisheshi tana rusunawa,ya amsa mata suka wuce,widad kam da idanu ta bisu har suka wuce din,sai taja tsaki "Yanzun ya kusa zama angonki ma ba zaku fara magana ba widad?" Wani kallo tayi mata cikin quruciya da sakalci "Waye angon nawa?,ni ba wanda zan aura na gaya miki ina wajen ummu na,tare zamuyita zama" "Tabdijan,ni kuwa ana cewa aure za'a yimin zan yarda,bakiga kayan lefen da aka kawowa su anty ramziyya ba?,ga kayan girki da gadajen da aka siya musu masu yawa fa,ke don har yanzu bakije gidajensu ba,baki gani ba gwanin sha'awa,su dafa abinda sukeso,suyi kwanxiyarsu a gadonsu,ba duka ba aike ba fada,ke.....hmmmmm" Aafiya ta fada da alama abun yana burgeta,fuskar widad ta dan sauya zuwa fara'a "Su ai sun girmemu,ko auren za'ayi mana ba za'a yi mana irin nasu ba" kama baki Aafiya tayi tana fidda ido gami da kallonta "Inji wa?,wallahi momma tace qila ma mu samu abinda yafi nasu" "Allah?" "Wallahi" sai widad din tayi shuru tana jinjina kai,hadi da tuna yawan kayan da aka fitarwa kowacce cikinsu ramziyya daga gidan aka sa amota zuwa jeren gidanta. Sam ta manta ma da wani zancan ma'aruf,har suka isa gida suna zancan kayan auren,a harabar gidan suka rabu kowa ya shige sassansu. *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 07 Bata fahimci zancan da gasken gaske bane sai da ummu ta fara hadata da walid qaramin dan anty madina yana rakata kaiwa ma'aruf din abincinsa,ta maida wannan aikin na kullum kullum a kanta,a nan ne hankalinta ya fara tashi,duk a qoqarin ummu na kawo kusanci da fahimtar juna a tsakaninsu. Tun ranar farko kamar tasan manufar yin hakan bata shiga dakin ba,daga bakin qofa ta tura masa ta juyo tayi tafiyarta,hakance taci gaba da kasancewa,duk sanda aka aiketan turawa take daga qofa ta wuce abinta sassan anty madina ko sassan wani daga cikin kawunnanta. *_RABON ZA'AYI_* Sun tafi tiryan tiryan da walid kai abincin,tana ta qunci da dacin rai,amma ba zata iya qin zuwa ba,har sun kusa da qofar dakin taji akwai alamun baqo,sai ta koma da baya tana duban walid "Muje na aje masa akan motarsa,yazo ya dauka" yaron yana biye da ita har gaban motar ma'aruf,ta dora masa abincin sannan suka koma sassan ummu,ta fito ne suna kallon wani cartoon,dama kuma Allah Allah take ta koma ta qarasa kalla. Da kallon mamaki ummu ta bita sanda ta shiga ganin nan da nan ta dawo "Har kinkai?" "eh na kai", ta amsa kai tsaye tana komawa cikin kujera ta lafe hankalinta duka yana kan cartoon din,jim ummu tayi kamar tana tantama,sai kuma ta dauke kanta taci gaba da sabgarta. Bayan minti goma sai naadir ya shigo ya cewa ummu "Yaaya ma'aruf yace ba'a gama abincin bane?" "Wanne abinci kuma bayan wanda aka kai masa,ko qaro musu za'ayi?" "Anya?,yace dai yunwa yakeji abincin yake jira" waiwayawa ummu tayi ga widad data lafe sosai gabanta na faduwa,amma sai tayi kamar bata a wajen,ta rufe idanunta kamar mai bacci,kallo daya ummu tayi mata tasan ba bacci takeyi ba,sam qarya bata mata kyau,tun dazun ta fahimci akwai lauje cikin nadi a maganarta "Widad a ina kika aje masa abincin?" Manyan fararen idanunta ta bude kamar zata saki kuka ta bawa ummu amsa "Yana kan motarsa" baki ummu ta kama tana kallonta "Kai jama'a" maama batulu ta fada cikin bacin rai,yayin data tsaya tana jiran jin irin fadan da ummu zatayi mata,idan ya kama da duka ma ta doke ta,yarinyar ta tsayewa rayuwarta gaba daya,gata qauna da kulawar da ummun ke bata nata yaran basu samu wannan ba,duk da suna samu dai dai gwargwado daga wajenta,amma ita butulu ba irinta takeso ba "Yanzu tsabaragen iskanci a aikeki widad kije ki dorawa mutum.abinci saman mota?,ta yaya to zaisan kin kai?,idan wani ya kifar kuma bai sani ba fa?" Ta qarashe maganar tana maida kallonta ga ummu wai ko ummun zata kama mata,amma sai taji tace "Ubangiji ya shiryeki,wannan quruciyar da shirme da kike fama dasu Allah ya maganta miki" ta juya ga naadir "Jeka dauka daga kan motarsa ka miqa masa" amsawa yaron yayi ya juya yana ficewa,ita kuwa batulu dole ta kama bakinta jin ummun bata kama mata ba,taso taci gaba da maganar tana sake zuga abin,sai abun ya tsaye mata arai,sosai.haushi ya cikata,yarinya sai nema mata mazan aure ake tana iya shege?,wa tafi goshi?,idan kyau ne yaransu gaba daya babu wanda bashi da dai dai nashi,rashin uwa kuma a kusa ai ba farau kanta ba,dukka yaran dake can gida tare dasu kowanne ba uwar gareshi ba,amma babu wanda ummun ke shagwaba haka kamar widad din,kai hasalima ba wanda ummu ta kama ta riqe sai widad din?. Da wannan takaicin ta baro gidan,saidai kuma ta qudire a ranta ba zataji takaicin banza ba,don haka da daddare bayan dawowar alhj mahmud ta zauna tayi masa famfo sosai,ta bashi labarin qarya da gaskiya kan abinda ya farun. Sosai kuwa ya tunxura,ransa ya baci,abun na yarinyar ya fara kaishi bango,zuciyarsa dama yaketa danna,abinda ya faranta ran batulu kenan ta gyara zama "Diya mace dai 'yar gidan wani ce,gwara a gyara mata zama tun yanzu,sannan idan tace shima ma'aruf bata sonshi kuma bansan wa takeso ba,gashi sai dad'a girma suke,kuma ita din ba wata budurwa ba bare ace akwai irin mijin da take hari,duka duka ma yaushe tasan rayuwa ma?". Shuru kawai yayi yana jinjina kai, tabbas zai dauki mataki,bazai bari yana ji yana gani ba gata ya lalata ba,duka sauran yaran da ake riqo a nan gidan ai ba haka suke ba,idan ma ummu ke daure mata gindi lallai gobe sai ya nuna mata kuskurenta. Har widad din ta kwanta ummu ta tasheta "Widad,karki sake aikata abinda kika aikata dazu kinji?,baki gani ma'aruf yayanki ne?,kuma shine zai zama mijinki a nan gaba?" Baki ta sake tana kallon ummu a sakarce,hawaye na shirin fara taruwar mata a idanu "Miji?,ni wallahi bana sonshi ummu" sai kuka ya kufce mata sosai,ta kuma birkicewa ummun gaba daya "Samu guri ki kwanta" kawai ummun tace da ita bayan ta gaji da koke kokenta,tana jinta daga kwancen tana jan sheshsheqar kuka har bacci yayi awon gaba da ita,wannan al'amari na widad......to wa take so?,Allah shine mafi sanin gaibu shine amsar da ummu ta bawa kanta daga qarshe,ta rufe idanunta tana fata ko meye zaizo yazo da sauqi. *W A S H E G A R I* Tunda ta tashi da fushin zancan ma'aruf ta tashi,ummu tayi tayi ta kulata taqi,ko larifa mutuniyarta yau babu 'yar hirar da suke tsakaninsu,da take zata kwaso undies dinta da uniform ma zata wanke mata nuna mata inda ta zubasu kawai tayi,amma abinka da zuciyar yaro qarfe goma na safe sai ta fito falo ta zauna,ummu na zaune kan one sitter,sai ta koma kan two sitter ta kwanta tana kallo a MBC3,duban sashenta ummu tayi taci gaba yankan farcenta ba tare da tace komai ba,daga nan suna jiyo hayaniyar yaran gidan a farfajiyar gidan,wanda ta tabbatar da ranta fes yake da tuni ta fice,idan ba harabar gidan ba to wajen anty madina. Sallamar abban nata ya sanyata miqewa ta zauna suna kusan hada baki ta da ummu wajen amsa masa,haka kawai taji gabanta ya fadi,kallo daya tayi masa ta shiga nutsuwarta. Bai jira sun gama amsa sallamar tasa ba ya qarasa wajen kayan kallon dake falon ya zaro wayar USB dake jin wuta ya nufo widad da ita,baikai ga isa ba kiran sunansa da ummu tayi da qarfi ya dakatar dashi,don tuni ta fahimci abinda yakeson aikatawa,saboda ya taba aikata hakan a baya "Kayi hauka ne mahmudu?,da raina da lafiyata?,ina zaune a falon zaka shigo ka dauki mabugi ka dakarmin ita?,to daketa nace?,wallahi wallahi kana dukanta saina rama mata,idan kuma kana shakka to bismillah" ummu ta fada ranta a mugun bace,abinda yasa ya yarda wayar hannun nasa kenan,yana qoqarin saita kansa,tare da qoqarin gano rashin dacewar abinda ya aikata din,wannan ya bawa widad damar miqewa da gudu ta isa ga ummun,ta fada jikinta gami da qanqameta tana sakin kuka,abinda ya taba zuciyar ummun,ya kuma saukar mata da tausayin widad din,saita dora hannunta saman kanta tana lallashinta. Gaban ummun ya qaraso ya russuna yana gaisheta,harara ta jefa masa "Bana buqatar gaisuwarka" saita zare widad daga jikinta tana umartarta data wuce daki,ta miqe tana sharbar hawaye,sannan cikin kaffa kaffa da mahaifin nata ta gewayeshi ta wuce. "Kiyi haquri,ni banyi haka don na bata miki rai ba,abinda yarinyar nan takeyi yayi yawa,kowa sai tace bata so?,har a aiketa taje ta dora abinci akan mota?,sa'anta ne shi?,fisabilillahi haka za'a zuba mata idanu?" Duk da taji sallamar halimatu a falon amma hakan bai dakatar da ita daga bashi amsa ba,ta gano daga inda tushen zancan ya fita "To cewa akayi lallai lallai sai ta sosu?,ko kuma fadar Allah ce?,uwayensu ba sai da kukaji kuna sonsu ba kuka auresu?,to ahir wallahi,a sakar mata mara hakanan,ita kadai kunbi kun sata a gaba?,da kai da masu zigoka din ka gaya musu,wallahi tallahi su fita a idona akan lamarin widad,ba wanda ya haifeta ko yayi wahalarta,saboda haka su kama kansu" qas yayi da kai "Allah ya bada haquri,ya huci zuciyarki" "Ameeen" ta amsa a fusace,sai ya miqe,yana son tambaya yaji alhaji yana kusa amma fushinta ya sanya don dole ya juya ya fice, halimatu ta bishi da kallo sannan ta dawo da dubanta ga ummun bayan ta tabe baki "Allah ya kyauta amma dai ummu ai da kin bari ya hukuntata,icce tun yana danye fa ake tanqwarashi"ta fada tana duban ummu da kyau "Ya kyauta abinda yafi haka,iccen qaniyarki,duk cikinku wa aka yiwa hakan iyee?" Ganin fadan zai dawo kanta saita zame itama "Allah ya bada haquri,ni ba haka nake nufi ba". Wunin ranar kamar an dawo mata da zancan mahfood ne,saboda yadda taga abban nata yazo afujajan kamar yadda yayi mata kan auren mahfood,uwa uba bayan sun kebe ummu ta fara tausarta a hikimance,wannan yasa gaba daya ta shiga damuwa da 'yan koke koke,har sai da alhaji ya fahimta ya kuma bi ba'asi. To da yake shi dinma mai sauqin kai da fahimta ne sai yace "Ba ta haka ake bi da yaro ba matuqar anason ya fahimci abu,ta lallashi da siyasa ake binsa,gaba daya al'amarin mahmudu bansan me yake damunsa kan batun yarinyar nan ba" "Me yake damunsa kuwa banda matansa dake zugoshi?" Kai alhaji ya girgiza "Allah ya kyauta,amma kedai karki saka haka a ranki,mubi komai a sannu da kuma addu'a,zan sake magana da shi mahmudu din" "Allah ya rufa asiri" "To ameen,munyi waya dazu da muhsin,yace ko gobe ko jibi zai shigo garin" dan murmushi ummu ta sake "Ma sha Allah,ayyukan sunyi sauqi kenan?" "Eh da alama kam tunda har ya samu sukunin zuwa" "To Allah ya taimaka,ya ara mana rai" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" alhaji ya amsa mata,sai kuma suka shiga wata hirar ta daban. *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 Page 08 Cikin dakinta take tsaye,sanye da uniform na islamiyya,farin riga da wando da kuma hijab ne,sai baqar abaya da suke dorawa a sama,idan ta saka kayan sai ka dauka ita daya aka kebe aka yi uniform din don ita,tana da wani irin kyau da yasha banban da na yaran gidan dukkansu,innocent face ne da ita,duk da cewar a zahirance din ma bata fiya hayaniya ko rigima ba,bata da abokin fada idan bawai taso ba ko quruciyar ta motsa. Dukka jakar tata ta zazzage saman gadon tana kwashe tarkacen dake ciki gami da kauda su gefe daya,ta maida alqur'aninta ciki,tana shirin rataya jakar ummu ta leqo "Kin fasa zuwa islamiyyar ne?" Da fuskarta dake da qarancin walwala ta waiwayo tana dubanta,ssnnan ta buda baki a nutse "Zani" "To ai gwara ki hanzarta kada ki makara" ummu ta fada tana sakin labulen gami da juyawa,har cikin ranta bata jin dadin rashin walwalar widad din sam,gaba daya tun ranar ta koma wata sukuku. Plate takalmanta masu igiya ta daura,baqaqe da suka zauna suka yiwa fararen qafafuwanta kyau,saita fito a dakin,ta yiwa ummu dake zaune a falon sallama sannan ta fito farfajiyar gidan. Tana tsaka da tunanin ta tsayawa koda Aafiya ne su wuce tare ko kuma tayi tafiyarta hon din mota daga waje ya cika harabar gidan,ba tare da jinkiri ba baba awwa ya miqe ya bude gate din,baqar motar dake daukan idanu da sheqi ta sako kanta zuwa cikin gidan,hankalin widad ya dauku kan motar,kamar taso ta gane motar waye?,tunaninta yazo dai dai sanda baba awwa ya qarasa ga motar bayan ya rufe gate din yana fadin "Barka dai da sauka,barka da sauka mai gida muhsin" wani murmushi ne ya qwace mata,uncle muhsin?,uncle muhsin ne yazo?,mutumin dake cikin jerin sahun mutanen dake da girma da matsayi a rayuwarta,mutumin dake nuna mata kulawa kamar yadda yaga ummu nayi mata,gaba daya ta sha'afa ma da batun makaranta ta fito,gaba daya hankalinta ya tattara ga uncle muhsin din,wanda ko second daya bata qara a tsaye ba ta nufi inda ya faka motar tasa harda sassarfarta. Suna tsaka da gaisawa da baaba awwa din ya tsinceta a wajen,bakinta har kunne "A'ah,yammata sai ina?, islamiyya za'a je?" Farincikinta ya gaza boyuwa,ta gyada kai tana dariya gami da fadin "Uncle muhsin ka shammaceni,dama zaka zo?" "Gani kuwa widad,bakiji wajen alhaji ko ummu ba?" Kai ta girgiza still dai tana dariyar. Kafarta kafarsa suka shige gidan,sai daya fara shiga sassan 'yan uwan nasa suka gaisa,tana biye dashi qafa da qafa,duk da hararar da take samu daga wajensu amma bata damu ba,anty madina ce ma ta tsokaneta "Batun tafiya makaranta ya tashi kenan?". Dariya widad din tayi,sai uncle muhsin din ya juya ya kalleta "A'ah,ai ba za'a fasa zuwa makaranta ba saboda zuwa ne,kije ki dawo,ina nan ai" cikin shagwaba ta narke fuska "Don Allah uncle,yau kadai.....kuma ma lokaci ya wuce,na makara,idan ma naje bulala zaayimin Allah" kai ya jinjina kawai,widad din ta daukeshi da wani matsayi sosai,haka suka wuce sassan ummun tare. Ina ka saka ina ka ajjiye ummu keyi da dan autan nata,wanda take lelensa kamar kowanne auta a wajen iyayensa,duka su ukun suna falon suna hira,ita widad da kuma uncle muhsin din,sai da ummu ta korata tace ta fidda uniform din daga jikinta tunda taqi makarantar sannan ta miqe da jakarta a hanzarce ta wuce daki. Dauke dubansa muhsin yayi daga dubanta sanda ta bacewa ganinsa ya maido ga ummu "Me ya samu widad ne?,ko tayi ciwo baya bayan nan?" "Me ka gani?" Ummun ta tambayeshi itama "Ramewa naga tayi,ko girma ne ya kawo hakan?" Kai ummun ta girgiza tana tabe baki "Batun aurenta ne yaketa zuwa da mishkiloli kawai" "Aure fa ummu?,widad din?" "Eh baqon abu ne?,naga kusan duka 'yan bayanta ma haka aka musu" zamansa ya gyara,har cikin ransa bayaso a aikata wannan dabi'a ga widad din,yana jin yarinyar har ransa,saboda baya mancewa da yadda mamarta ta daukeshi a sanda take auren dan uwansa,saboda da shaquwa ne sosai tsakaninsu da ita,ta daukeshi kamar qaramin qaninta "Amma ummu sunfi widad datawa ai,duka duka ita din shekararta nawa ne?,sha hudu fa?" "To mahaifinta dai ya tasamma aurar da diyarshi,mahfood ne akayita gwagwarmaya akan lamarinsa tace bataso,muka saka baki ni da alhaji aka ajiye zancansa,ya dauko ma'aruf to yanzu akan batunsa ake,shima din kuma ba so take ba" sosai fuskar uncle muhsin ta sauya "Amma ummu shikam yaaya meye haka?,tunda bataso duka basai a qyaleta ba?,nawa widad din take?,naga batayi girman da zai daga hankalin kowa ba saboda batayi aure ba ko?" "Duk yadda nake da iko dashi da ita dole akwai huruminsa na uba daya zama dole na bashi,nidai abu daya na sani bazan bari ayi mata auren dole ba" dan qaramin tsaki yaja abun yana bashi haushi,ko da shi dabi'arsa ta daban ce,bare a yanzun da ya zama riqaqqen dan boko "Wannan maganar a barta kawai,indan tace taji ta gani tana so ne ma shikenan sai ayi zancan aure,amma ni sha'awar karatu nake mata,karatu nakeso tayi,bari zamu hadu da yayan,ya bani ita kawai mu wuce gida tare" "Bazan iya baka widad ba,zan maka lamuni dai taje zuwa sanda komai zai lafa" murmushi yayi "Zahra ta dade tana nacin a bata widad ummu,su kansu su nujood zancansu yaushe zatazo,tunda anyi haka kawai ki haqura ku barmin ita" "Banyi alqawari ba" ummu ta shaida masa kai tsaye. Sanda widad din ta dawo falon bayan ta sauya kaya ummu ta shiga ciki ta duba dashishin da za'a girkawa alhajin,har yau har kwanan gobe tsufa jin dadi ko wadata bai hana dattijuwar matar aikin abincin mijinta ba. Cikin hikima uncle muhsin yake bugun cikin widad kan batun,tuni ta fara share qwalla,sai ya ajjiye spoon din hannunsa "Kinga share hawayenki,ba wanda zai miki auren dole,dake zan koma ma na kaiki wajensu nujood,ai zaki je ko?" Duk da nisa da ummu shine abu da tafi tsana,amma a yanzun sai takejin shine mafi dacewa,kawai tabi uncle muhsin din,tayi nisa da garin ko abbanta zai haqura da qudurinsa,bata da zabin da ya wuce wannan,don haka ta gyada kai hadi da cewa "Zanje uncle" "To shikenan,share hawayen ki bani labarin izifinku nawa yanzu a islamiyya" hira ce ta barke tsakaninsu,harma ta manta da fargabar tafiya tabar ummu,saima zumudin matsawa daga garin,ko banza ta gujewa wani ma'aruf abbanta dama auren da ake shirin qaqaba mata. Uncle muhsin shine auta ga ummu a maza,daga shi sai halimatu kenan,kuma qani ga abbanta da suke uwa daya uba daya,shi din ba mazaunin kano bane,yanayin aiki ne ya kaishi bauchi,da farko ma kamar bazaije ba,saida ummu ta qarfafa masa gwiwa,ta kuma nuna masa aiki ba inda baya kai mutum,yanzu haka shekararsa kusan goma sha uku da aure,yana da yara hudu,diyarsa ta farko widad ta girmeta da shekara kusan daya,dan boko ne sosai,yana da sauqin kai som mutane da kuma kirki,widad na ji dashi cikin dukka tulin qannen da mahaifinta ke dasu,saboda yadda yake nuna mata kulawa da kuma janta a jiki. Da kansa uncle muhsin din ya zauna da yayan masa mahmudu,ya sha fama sosai kafin ya gane abinda yake kwatanta masa,don daga bisani dole ummu da alhaji suka sake shiga maganar sannan ya janye qudurin nasa,ba kuma wai don ya haqura da maganar bane gaba daya,wannan ya sake qarfafawa uncle muhsin gwiwar tafiya da widad din "Taje dai ta huta,amma ban bar muku ita ba,kada ma kazo kace min ga zance ga magana". Kamar wasa sai ga widad tana murnar tafiya,har ta fara hada kayanta da kanta ma,latifa ita da anty madina sunata dariya "Ba cinya ba qafar baya,Allah dai yasa a qarke qalau kada ku dawo ranar da kukaje" suke tsokanar uncle muhsin sanda sukaga widad din nata shiri. Kwana uku kacal ya qara suka tattara sai bauchi,ranar da zata tafin gaba daya 'yan rakiyarsu har bakin motar uncle muhsin din,latifa ke riqon jakarta,tana ta tsokanarta "Uwar dakina kada dai zama yayi dadi a manta dani" widad dake sanye da atamfarta dinkin doguwar riga tayi dariya tana qwamewa gaban motar uncle din "Bazan manta dake ba inna latifa,kedai ki zuba ido zakisha tsaraba" dariya ta saki "To Allah yasa" itama ta amsa tana dariyar,suna dakon uncle muhsin ne,yana rabawa yaran gidan da sukayo masa rakiya kudi,'yan dari dari ne sababbi qar,baya rabo dasu,ya kammala ya dawo cikin motar ya zauna yana sake waina injin motar sosai,ummu ta zagayo ta durqusa tana musu addu'ar sauka lafiya,sannan ta zura hannu saman cinyar widad ta ajjiye mata kudi "Gashinan,kada kije baqon guri hannunki babu komai" murmushi uncle muhsin yayi bayan ya kalli kudin "Banda abinki ummu me zatayi da kudi?" "Ina ruwanka kai dai?" Ta amsa shi,tana gyara yafen mayafin dake saman kanta "Nidai bance a riqemin yarinya acan ba,aro na baku" ta sake jaddada masa abinda yake ranta,sai yayi dariya kawai yana tayar da motar,dai dai sanda widad kema ummun godiya,duk da itama din batasan amfanin me kudin zasuyi mata ba. Har motar ta fice daga harabar gidan suna waigen juna ita da ummun "Zauna sosai kada ki baro kan naki a gida kije bauchi da iya gangar jiki" uncle muhsin ya tsokaneta,sai tayi dariya tana zama sosai din,saidai tun a lokacin taji ta fara kewar gida,taji kamar ta koma,to amma idan ta tuna abinda ta gujewan sai taji dadi,hankalinta kuma yadan kwanta,ko ba komai za'a daina zancan,tana saka ran maganar ma tabi ruwa ta huta. Suma shirin ficewa a unguwar motar ma'aruf din ta sako kai,uncle muhsin yadan dakata kadan,sai ta lafe sosai ta kwantar da kanta saman cinyoyinta ta yadda bazaya ganta ba,ma'aruf din ya gaidashi sukayi sallama,uncle muhsin yaja motar sukayi gaba yana dariyar widad din cikin ransa,quruciya sai abarta. *ZAFAFA BIYAR 2023* IDON NERA Mamuhghee KI KULANI miss xoxo A RUBUCE TAKE Huguma RUMBUN K'AYA Hafsat rano DAUDAR GORA Billynabdul Account number 0022419171 Maryam sani Access bank Saiki tura shaidar biyanki ga 09033181070 VTU OR MTN RECHARGE CARD 09166221261 AL'UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER +227 90 16 59 91 Thanks for choosing us *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 09 Suna tafe a hanya uncle muhsin din yana janta da hira,ta saki jiki sosai sunata hirarsu da yake abokin hirarta ne dama,a nan ya fahimci interest dinta itama game da karatu,da yadda take da kaifin basira,tun suna hirar har suka gaji kowa yayi shuru,saita maida hankalinta ga kallon titi da yadda suke wuce dazuzzuka,can qasan ranta ta dinga jin wata kewa tana shigarta,zuciyarta ta karye,suna dada yiwa kano nisa. Tun tana iya bin hanya da kallo har baccin ya soma fusgarta,babu jimawa kuwa yayi awon gaba da ita,ta saki jiki sosai tana barcinta abinta. Bata tashi farkawa ba sai da uncle muhsin ya iso qofar gidanshi ya tsaya yana jiran mai gadi ya bude masa qofa,idanunta ta bude a hankali tana murzasu hadi da budesu da kyau tana qarewa wajen kallo. Tun a sannan tasan ta shigo baqunta,ta kuma shigo sabon waje,quaters ne dake da qarancin jama'a tare da qarancin gine gine,saidai kuma duka manyan gidaje ne ta wajen,tana nan zaune har ya buda gate din gidan ya dawo ya shigar da motar. Sanda ya kashe motar waiwayo yayi yana tsokanarta "Yar qauyen kano yau gata a bauchi" kasa magana tayi saboda kewar ummu data fara shigarta,sai murmushi kawai data saki,dai dai nan matar gidan ta iso. "Kai kai kai.....abba wa nake gani haka?" Ta fada tana dariya gami da murza bdanunta,saboda baice mata da widad din zasu taho ba "Wa idanunki suka gani?" Shima ya fada yana dariyar "Tabdi,wai Allah na,anya kuwa ba gizo idanuwa kemin ba?" "Shafa kiji dai" ya sake fada yana dariya gami da qoqarin fitowa daga motar yana duban widad din "Fito mu shiga ciki" yace da ita yana fita daga motar "Gaskiya na ciri tuta,abba wacce irin addu'a ne ka yiwa ummu ta baka widad?" Ta sake fada tana karbar jakar hannun widad din tare da sake bude mata qofar motar sosai. Tare suka jera zuwa ciki hadiyya matar uncle muhsin da yaranta ke kira hajjaa nata mamakin zuwan widad din "Saurin me kike ne?,zakiji komai fa" cewar uncle muhsin. Tunda suka shiga falon gidan ta gane yaran gidan basa nan,da yake ranar makaranta ce,har dakin yaran hajjaa ta rakata sannan tace da ita "Ki alwala ki sallah,ki shiga kitchen da abinci ki diba kici,su nujood din sun kusa dawowa,yanzun nan zaki gansu" a nan dakin ta barta ta koma wajen mijinta. Tun bai gama kintsawa ba ta sashi a gaba,yana shiryawar yana bata labarin dalilin tahowa da widad din,gyara zamanta tayi tana sauke ajiyar zuciya "Gaskiya abba gwara daka taho da ita,duka duka nawa take da za'a dameta da batun aur,baya ga haka ma naga ko yayyen nata da aka yiwa auren duka sun fita datawa,tunda a qalla suna kaiwa sha bakwai sha takwas,sai ita tun tana 'yar sha hudu?" "Nafi tunanin farinjinin da yaaya yaga tana da shi ne fiye dana 'yan uwanta ya daga masa hankali yakeso yayi ya kawar da ita,amma gaskiya ni dama nafi mata sha'awar karatu,da zan samu ummu tabarmin ita karatunta zatayi sosai" "Gaskiya dai abba,Allah yasa ummu ta bari" "Ba tabbas" ya amsa mata yana zura jallabiyyarsa "Ki dauko system dita ki sakamin ita a charge,nabar ayyuka da yawa ban kammala ba,inaso na rage kafin gobe" ta amsa masa da to tana miqewa,shi kuma yana fita don zuwa masallaci sallar azahar. Hankalinta duka yana kan widad tunda ta barta a dakinsu nujood,widad din ba baquwarta bace,tasan yadda take da wahalar sabo da rashin sakin jiki,qilan yanzun tana can zaune a takure,kamar yadda ta zata kuwa haka ta sameta,tayi sallar dai amma tana zaune,cikin dariya tace "Anya widad za'a zauna mana a bauchin nan kuwa?,taso muje kuci abinci kafin su qaraso,yau sunyi delay ma,Allah yasa ba school bus din tasu ce ta sake basu matsala ba,don haka tayi musu jiya". Tare suka fito tana biye da ita,a falo suka samu uncle muhsin din,shima shirin cin abincin yake,sai hajjaa ta zuba musu tare,tana daga gefe suna hirar kano da uncle muhsin din,jifa jifa suna sanya widad,har ta fara sakin jiki,da yake daga uncle din har hajjaa mutanenta ne. Basu ko kai ga gama cin abincin ba sukaji ana taba gate din gidan "Tohm,ga 'yan makaranta nan"Hajjaa ta fada hayaniyarsu na ratsowa falon tun kafin sukai ga qarasowa. Tsam widad ta dauke hannunta daga plate din abincin cikin hanzari,kafin sukai ga qarasowa ita ta fita suka hade a farfajiyar gidan. Cikin murna nujood ta riqeta tana ta ihun murna kamar wadanda wani abu ya sama,banda uncle muhsin sun san abinda ke faruwa babu abinda zai hanasu tsorata,amma sai ya kada kai yana murmushi "Allah ya shirya,kamar basusan sun fara girma ba" "Banda abun abba ina hankali a nan,ai saidai aikin quruciya". A nan falo ranar aka wurgarwa da hajjaa kaya da jakar makaranta,sauqinta daya ranar babu islamiyya ta tabbatar da babu abinda zasu,baga nujood din kawai ba,har duka sauran 'yan uwanta sunji dadin zuwan widad din. Cikin kwanakin da basu da yawa taji ta qagu ta koma wajen ummunta,duk da cewa gidan yana mata dadi amma sam batason garin,hakanan take,ta fiya baqunta da rashin saurin sabo,abu daya ne yake sanyawa taji komawar ta fitar mata a ka,batun ma'aruf da kuma mahfood da taji rannan uncle muhsin suna zancan da hajjaa hadiyya sunayi cewar har yanzun bai haqura ba,yace idan Allah yayi rabonsa ce shikenan. Zumbura baki tayi gaba ba tare data baiwa zancan muhimmanci ba,duk da qarancin shekarunta amma ta fuskanci zallar nacin da mahfood ke dashi,ta rasa da wanne suna ya dace ta kirashi,takan kirashi da maye a ranta,taja tsaki ta dauki marker din zanen da tazo dauka suna wani zane ita da nujood ta fice zuwa farfajiyar gidan inda suka sanya kujeru suka zauna. ******* Baqar mota ce wuluk qirar BMW take ratsawa a hankali ta saman titin,daga cikinta tana dauke ne da mutane uku,dukkansu sanye suke da police uniform (kakin d'an sanda,matuqin motar akkauran dan sanda ne baqi dake hakimce a mazaunin driver yana sarrafa sitiyarin motar cike da qwarewa,yayin da wanda ke zaune a gefansa ya kasance siriri sosai,hakanan kuma dogo ne,duk da cewa a zaune yake zaka fahimci hakan. Na ukun nasu kuwa yana zaune daga bayan motar,tashin farko zaka iya kiranshi da matashi,don duka duka shekarunsa na haihuwa ba zasu haura talatin da biyar ba,mara hasken fata ne da zaka iya kiransa sa chocolate color,irin fatar dake da tsada da kuma daukan hankali,saboda yadda take a kwance kadai zai nuna maka zallar jin dadin da ma'abocin fatar ke samu. Yana da matsakaicin tsaho,wanda inda ace siriri ne kai tsaye zaka iya kiransa da dogo,saidai murjewar jikinsa ta shanye tsahon nasa ta sanyashi a sahun matsaikatan maza,manyan idanu gareshi masu daukan hankali,girmansu bai hanasu lumshewa ba a duk sanda yaso hakan,kamar yadda yake da wasu irin lips kai kace na mace ne. Sosai uniform din suka zauna masa a jiki,kai kace saboda jikin nasa aka qerasu,qafafunsa da yayi crossing nasu socks ce kawai,boots dinsa na aje gefan qafafun nasa. Duk da hirarrakin da mutum biyun dake gaban motar sukeyi shi sam ko sau daya bai tsoma musu baki ba,hasalima tafin hannunsa ne shimfide saman fuskarsa kamar mai wani tunani,abinda kuma zai iya hanaka ganin ainihin fuskar tasa sosai kenan,sai kyakkyawan agogon Rolex dake daure a tsintsiyar hannunsa. Yanayin zaman da yayi kamar na mutumin daya gaji tubus,sam zaka zaci baya cikin motar ne,duk da hirar da sukeyi din ta shafi aikinsu,dukansu cikin zuciyoyinsu suna muradin ya sanya baki,saidai sunsan abune mawuyaci,shi yasa cikinsu ma babu wanda ya sanya rai da hakan suka ci gaba da hirarsu ba tare da sun daga sauti yadda zasu dameshi ba. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana zame hannun nasa daga saman fuskar tasa,kyakkyawar zagayayyar fuskarsa dake cike da wani irin kwarjini gami da haiba ta bayyana,ya dan bude idanunsa kadan da nauyin gajiya ya cikasu. "Samuel" ya furta cikin muryarsa dake da kauri da nauyi "Yes sir" mamallakin sunan wanda shike tuqin motar ya amsa a ladabce "Ka saukeni gidan hajiya tukunna" "Consider it done sir" ya sake amsa masa cikin nuna qarfin bin umarnin sa. Kafin wani a cikinsu ya sake cewa wani abu wayar dake tsakanin seat din gaba guda biyu ta dauki tsuwwa,mutumin dake zaune a kujerar dake zaman banza ne ya miqa hannu yana dubawa,kana yadan waiwayo kadan dai dai sanda yake qoqarin maida boot din qafarsa "Sir,dan jaridar nan ne" shuru kamar bazai amsa ba,da alama ba ma'abocin son magana bane,sai kuma yace "Ka katse kiran ka tura masa saqo,gobe qarfe biyu su sameni a zone one" "Yes sir" shima ya amsa yana juyawa cikin qoqarin idar da umarninsa. Dai dai sanda ya gama sanya takalman yana gyara zamansa motar ta soma gangarawa cikin unguwarsu,sai ya juya gefansa yana daukar tarkacensa dake zube akan seat din gami da maida hularsa saman kansa yana dakon motar ta isa qofar gidan. *ZAFAFA BIYAR 2023* IDON NERA Mamuhghee KI KULANI miss xoxo A RUBUCE TAKE Huguma RUMBUN K'AYA Hafsat rano DAUDAR GORA Billynabdul Account number 0022419171 Maryam sani Access bank Saiki tura shaidar biyanki ga 09033181070 VTU OR MTN RECHARGE CARD 09166221261 AL'UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER +227 90 16 59 91 Thanks for choosing us *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 10 K'ofar wani madaidaicin gida mai fenti ruwan toka da qaramin gate ruwan madara motar ta tsaya,ya sanya hannunsa cike da nutsuwar nan tasa dake zmaa mabudin nasara ga dukka aikin da ya sanya a gaba zai buda motar,saidai kafin yakai ga aiwatar da hakan Samuel ya rigashi,ya kalleshi yadan kau da kai sannan yace "Thank you Samuel,you can go,zan koma gida da kaina" kai ya girgiza "No oga,zamu jiraka,daga nan station zamu koma,babu wani aiki da zamuyi kuma". Baice masa komai ba ya sauka daga motar ya nufi gidan yana takawa cikin tafiya ta tsayayyun maza. Da sallama ya tura qofar ya shiga,yar farfajiyar gidan babu kowa saidai qal take,fes kamar babu wanda ke rayuwa cikin gidan bare ya bata ba,yana hango takalma daga qofar falon,wanda zaka fara taka wata qaramae baranda kafin ka cimma falon,sai yaci gaba da takawa har ya isa baranda yana maimaita sallamar sa,hadi da yunqurin zame takalman qafarsa kafin yakai ga shiga falon "A'ah qaraso da takalmanka abinka" daga can cikin falon aka fadi,sai ya miqe murmushi daga qasan zuciyarsa na kubce masa,har ta hangoshi kenan,duk da shi bai hangota ba,ya yaye labulen yana sanya kansa ciki tare da jaddada sallamarsa. Daga can saman kujera mai cin mutum biyu take a zaune,babbar macace wadda aqalla ta doshi shekara sittin,zaune sanye da atamfa dinkin riga da zani,kanta lullube da kallabi mai santsi irin na asalin tsaffi a qasar hausa.kyakkyawae bafulatanar bauchi,wadda bata qi dibar komai nasu ba,illa hasken fata,bata cika fari sosai ba irin wanda akasan fulani dashi ba,fuskarta na nuna zallar kamala da nutsuwa da kuma mutuntaka irin ta cikakken dan adam. "Wa'alaikumus salam,maraba...yanzu kake tafe?"tayi tambayar tana gyara zamanta cikin kujerun "Eh hajiya" ya amsa mata dai dai sanda take duban 'yar budurwar dake kwance cikin kujera "Tashi ki bashi waje" tun kafin ma hajiyar takai qarshen maganarta ta soma yunqurin tashi tana lalubar dan kwalinta daya fita,cikin sauri ta fara gaidashi "Ina yini uncle" "Lafiya lau" ya amsa mata yana zama cikin wata kujerar ta daban,bayan ya dan ture kayan da suke kai "Shiga kitchen ki samo masa ruwa" "Tom" ta amsa tana ficewa daga falon. Sai a sannan ta tattara hankalinta a kansa,cike da girmamawa ya zamo qasa yana gaidata,ta amsa masa cikin kulawa da kuma qauna "Alhmdlh.....ashe kun dawo" "Shigowata bauchi kenan nace bari na fara zuwa na gaidaki" ya amsa mata yana komawa mazauninsa "Ma sha Allah,Allah yayi jagora" "Yayi hajiya,saidai fatan Allah ya dada yi mana,duk abinda akaje yi din Allah ya dafa mana an samu nasara" murmushi ya wadaci fuskarta,duk sanda zaiyi tafiya irin wannan sai ya shaida mata abinda zaije yi din,duk da cewa kusan komai din da zaiyi ma cikin rayuwarsa ita yake fara sanarwa,ita yake fara shawarta,takan tsaya tuquru da addu'a koda bai nema addu'arta ba,domin kuwa shi din na dabanne a zuciyarta,yana da wata irin tarin biyyaya me wahalar samuwa ga yaran yanzu. "alhamdulillah, alhamdulillah,Allah abun godiya,to Allah yaci gaba da kula mana da rayuwarku" "Ameeen ya hayyu ya qayyumu hajiya" ya amsata yana sake cire hular kansa kamar tana damunsa ne ya ajjiye a gefansa yana duban tarin kayanta dake ajjiye "Ya akayi maisara ya kawo miki kayanki haka babu guga?" Dan duban kayan tayi "To wallahi dai bana ce ba,kamar dai kallon qwallo suka tafi" fuska yadan tsuke "Qwallon me?,idan bazaya iya aikinsa yadda ya kamata ba sai yayi magana" murmushi hajiya ta saki,shikam akan dukkan abinda ya shafeta baya wasa dashi,baya bada uzuri,hakanan baya daga qafa "Yana qoqari ai,kasan su da son qwallo,kuma yau da gobe ma sai Allah" shuru yayi ya sanya hannu yana karbar cup din da muneera take miqo masa mai cike da ruwa. Sai da ya shanye ruwan sannan ya dubi hajiyan "Saura kwana nawa ne bikin gidan kawu hassan?" "Na zaci zaka leqa ma,yana gida kamar bai fita ba yau" "Sai idan na dawo,na yiwa auwal magana zai fidda kudin gudunmawar nan,zai kawo miki sai a bashi" "To to madallah,Allah yayi albarka,ya qara budi" "Ameen ameen" ya amsa mata yana sanya hannunsa a aljihun uniform dinsa ya fiddo kudi ya ajjiye mata yana cewa "Zan dan huta gobe,may be bazan fito ba" "Baka gajiya abbas?" Murmushi kawai ya saki ba tare da yace komai ba,baijin zai gaji da yiwa hajiyan tashi hidima bakin ransa,domin baya da kamarta a fadin duniya "Allah yayi albarka" "Ameen ameeen" "A gaida gida,a gaidamin kishiyoyin nawa" kamar tace kwana biyu sunqi gidan sai kuma ta fasa fadin hakan,ita din mutum ce mai son zaman lafiya,batason rigima sam,saidai a duk sanda ka qureta bata da dadi. A bakin mota ya samu su Samuel sunata hirarrakinsu,kafin ya iso ya bude masa qofar motar ya shiga,sannan suka zagaya suka shiga suma ya tada motar suka bar layin. Duka duka tafiyar minti talatin da 'yan kai motar ta sake sanya signal sannan suka shiga wani madaidaicin titi mai burji,wanda zai sakada da ainihin unguwar da suka nufi shiga. Basuyi tafiya me yawa ba motar ta fara slow,da alama sun cimma inda suka nufa,ba jimawa ta faka qofar wani madaidaicin gida. Daga girman gate din gidan zaka fahimci girman gidan,idan nace girma bawai ina nufin girma na sosai ba,saidai kana gani kasan yalwataccen gini ne daga ciki,hakanan ya qawatu ga idanun me kallo,yana dauke da tsayayyun katanku masu tsaho da qarko,wadanda ke dauke da fenti ruwan madara har jikin gate din,wanda aka yiwa ratsin zaiba(gold) a jiki. Wannan karon kafin su bude masa ya rigasu budewar,ya zuro qafafunsa dake saye cikin baqin boot zuwa waje yana duban gaban gidan sannan ya sanyo gangar jikinsa zuwa waje "Thanks Samuel" yace dasu bayan yadan waiwaya da kyau "You deserve it sir"ya fada yana saluting nashi cikin girmamawa,jinjina kansa kawai yayi yana nan tsaye har suka tada motar suka fara barin gaban gidan,sannan ya qarasa a hankali yasa hannu yana knocking. Daga ciki wata kakkaurar murya ta bayyana ana tambayar waye,bai bada amsa ba har zuwa sanda mai tsaron gidan ya bude qofar,da sauri yaja da baya cikin matuqar girmamawa yana masa sannu da zuwa "Yauwa sule,mun sameku lafiya?" "Lafiya lau oga" "Ma sha Allah" ya furta yana takawa zuwa cikin gidan,hannunsa guda daya saye a aljihun wandon uniform dinsa,daya hannun kuma riqe da hular tasa. A hankali yake takawa zuwa cikin gidan yana nazartar yanayin gidan,daga farfajiyar gidan ko ina fes yake cikin hankali da nutsuwarsa,duk da bashi da tabbacin abinda zai tarar a ciki amma hankalinsa ya dan kwanta kadan,yaci gaba da takawa cikin taku na qaqqarfan namiji wanda horon aikin damara ke yawo cikin jiki da kuma jininsa. Qofar falon ya murza,yayi sa'a ya sameta a bude,sai ya tura yana sanya kai ciki,bakinsa dauke da sallama. Kamar jira akeyi,yara biyun dake wasa a falon saman dan keken wasan yara suka waiwayo zuwa gareshi,babbar me wayon wadda ke tura qanwarta ta saki keken da mugun gudu ta nufeshi "Abba....abba!" Take fada cikin daga murya dake cakude da sautin zallar farinciki,yayin da daya yarinyar keta kiciniyar saukowa daga kan keken itama don ta iso gareshi. Wani qawataccen murmushi ne ya subuce masa,ya duqa a hankali yana jiran isowar yarinyar,tana qarasowa ya dauketa caraf yana sanyata cikin jikinsa,saidai kuma me?..... janyeta yayi da sauri yana duban kayan jikinta sakamakon qarnin da baisan na meye ba daya daki hancinsa,ya sauke idanunsa kan gaban rigar yarinyar,rigar da idan bai manta ba naira dubu shida ya sanya ya siyeta kafin tafiyarsa wannan aikin,kwanaki goma baya da suke wuce kenan. Jirwaye ne na abubuwa kala daban daban a gaban rigar,wanda shi kansa bazai tantance na meye ba,ya dauke idanunsa ya maida kan fuskar yarinyar dake dauke da jirwayen busassun hawaye,kafin yayi magana yaji ana jan hannunsa hade da gwaranci,sai ya mayar da kallonsa kanta,tana tsaye a gabansa tana ta babbaka masa dariya,da alama akwai abinda takeson gaya masa cikin gwarancin nata,sai ya miqa hannu daga tsugunen da yake ya dauketa cak yana azata saman cinyarsa,saidai ita din ma babu sauqi,tsami ko kuma warin pampers dinta ne ya kaima hancinsa ziyara,ya miqa hannu yana taba pampers din,sai ya jishi a cike,tausayin yarinyar ya kamashi,take kuma ranshi ya baci "Abba,ka siyo man teddy din?" Kumatunta ya kama yana qoqarin hadiye fushinsa,abinda kusan ya zame masa jiki koda yaushe "Mimi teddy,bari na huta tukunna" bai sake jiran komai ba ya sanya hannu ya sunkuci yaran duka su biyun,sunata zuba masa shirmensu yana biye musu ya doshi sassanshi dasu,don bazai iya sake zama a wannan sashen ba a yadda idanuwansa suka ganshi a hargitse kamar an shekara ba'ayi masa shara ba. Sashe ne daya tsaru matuqa cikin kalolin light blue da fari,tun daga babban falonsa dake manne da window size da hotunansa da yawancinsu cikin uniform dinsa ne na police zuwa bedroom dinsa wanda aka zubawa kayan gado masu matuqar kyau da tsari. Yayi zaton zai samu sassauci a sashen nasa,tunda yabar key ya kuma buqaci a gyara masa,amma sai ya samu waje shima sammakal,sauqin daya ne baikai jagalewar can ba,ya hadiye wani abu mai tauri yana sauke yaran gefan gadonsa,sannan ya fara cire uniform din nasa,ya rage daga shi sai wata farar shirt mara nauyi ko kadan mai gajeran hannu,wanda hakan ya bayyana cikar zati da siffar jikinsa,muscles tako ina dake nuni da siffar qarfi da kuma yanayi na motsa jiki da daga qarfe da yakeyi a kowanne lokaci,wandon jikinsa ya fidda ya rage iya boxer,sannan ya shige toilet dinsa ya hada ruwa mai dumi sosai ya dawo dakin ya fidda musu kayan jikinsu ya wuce toilet din dasu ya sanyasu a bathtub. Fes yayi musu wanka dukka su biyun har gashin kansu,sunata qyalqyala dariya hadi da cikashi da duminsu,shi kuma yana ta biye musu,dukka a qoqarinsu na hadiye damuwa da kuma bacin ransa,bayan ya gama ya sanya kayan daya cire musun a leda ya jefa a dustbin,duk da kudin da ya sanya ya siyesu,mutum ne shi mai tsananin tsafta hadi da tsantsami,don hakan baima san ta ina zai fara tsaftace kayan ba,don haka ya gwammace yayi musu hakan. Anan dakin ya shafa musu mai ya gyara musu gashinsu,sannan ya buda jakar da yazo da ita,a duk sanda yayi wata tafiya indai dama ta samu baya gajiya da yiwa iyalinsa tsaraba,ya fidda wasu gown na wani cotton material iri daya guda biyu ya sanya musu,sannan ya feshe jikinsu da turare. Murna suke abinsu kawai,walwalarsu ta dadu saboda yadda sukaji jikinsu yayi musu dadi,ransa a bace ya daga kai yana duban agogon bango,a qalla ya kusa minti talatin da shigowa,amma batasan ya dawo din ba,abar ta tashi ma,yaran data bari a parlor fa?,haka take tafiya ta qyale yaran qofa a bude kusan awa guda ba tare data leqa su ko ta bibiyi halin da suke ciki ba?. *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 11 Iska mai zafi ya furzar daga bakinsa yana miqewa tsaye,kafin yakai ga aiwatar da komai mimi ta kama cikinta "Abba......yunwa nakeji,tun dazu mommy tace zata dafa mana indomie......bata gama bane har yanzu?" Idanunsa ya zubawa yarinyar,a nutse yace "Bakuci abinci bane yau?" Kai ta gyada masa "Eh,momy tace tana jin bacci,kada mu dameta,musha tea,idan ta tashi zata dafa mana,har nawwara ma ta zuba ruwan tea din a qafarta,tayita kuka" lumshe idanunsa yayi,wani abu ya taba ransa,sai ya duqa a hankali tana laluben qafan yarinyar yana son ganin wajen,dai dai sanda yaji an murda qofar an kuma budeta,sanin waye ya sanyashi qin waiwayo yaci gaba da duba qafar nawwaran. Matashiyar macace,wadda a qalla zata doshi shekara ashirin da takwas ko kuma da tara,wankan tarwada ce wadda kalar fatarta ta kusa juyewa ta baqaqe,banda hutu da jin dadin data samu,mai matsakaicin tsaho ce,tana da 'yar qiba kadan da tudun hanci,idanuwanta basu fiya girma ba,saidai tana da 'yar cikar gira da kuma fararen haqora da suka sake bayyana duhun fatarta. Sanye take da kayan bacci a jikinta,kanta saye cikin wata hular zaren lilo da qabilu sukafi amfani da ita,zaka tsammaci qarfe bakwai ne na safiya a lokacin,saboda yadda fuskarta ke nuna alamu na bacci,uwa uba kuma sleeping dress din da take sanye dashi. Tsaye tayi daga bakin qofar tana qare masa kallo,fushi takeyi dashi sanda ya tafi,ta kuma ci alwashin sai yaga fushin nata,saidai tun bai jima da tafiyar ba kewarsa ta dameta,idanuwanta kuma suka damu da son ganinsa,ta ajeshi qololuwar matsayi a rayuwa da kuma zuciyarta,shi din na musamman ne,tunda har yana da qarfin ikon juyata da sauya mata ra'ayinta zuwa wadanda yakeso,abu mafi girma kenan dake haddasa sabaninsu,kowa da alqiblar da yake kalla tsakanin shi da ita,hakanan kowa yana ganin akan dai dai yake. Ci gaba tayi da kallonsa har ya gama duba qafar yarinyarshi,ya kuma tofa mata addu'o'i,tayi tsammanin zai waiwayo gareta ne tunda yaji shigowarta,amma sai taga yana yunqurin miqewa hadi da sake baiwa qofar baya,don haka ta saki hannayenta data rungume tana qarasowa cikin dakin,bayan ta dan bata fuska "Dama kuna nan kuka sanyani inata bulayin nemanku cikin gida?,sai dana fita gate sule yacemin ya ganku tare?" Maganarta ta qarshe ta sanyashi waiwayowa,idan ba gizo idanunsa yayi masa ba yaga shacin kayan bacci a jikinta,tana nufin haka ta tafi wajen sulen nemansu,mutum ne shi mai tsananin kishi,ko kusa ko alama baya daukan sakaci ko ganganci akan iyalinshi "A hakan kike tafi cigiyarsu har waje?" Ya jefa mata tambayar a nutse,saidai kuma wani bacin rai na daban bayan wanda yake ciki ke bijiro masa. Sai a sannan kwanyarta ta ankarar da ita zallar wautar data tafka,duk yadda taso taja zarenta itama har sai ya gane yayi mata laifi ya bata haquri take komai ya rushe mata,saidai cikin sa'a ta kama zaren qaryar da takejin zata qwaceta "Ta yaya zan fita a haka?,na cire hijab dina a falo" tana gama fada ta kauda qwayar idanunta daga cikin nasa,tana jin yadda yaketa kokawar ganin sun hada idanun,hanya guda daya da yake iya karanto qarya ko gaskiyarta,ta saara masa ta wannan fannin,kuma tasan ba banza ba,tunda aikinsa ne. Bayason ya sake dagula al'amuran,dole shima ya janye nasa idanun "Koda wasa,koda ganganci kada ki sake hakan ta faru" ranta ya baci,ta zumbura baki gaba,daqyar kamar wadda aka yiwa dole tace "Tom" saita maida dubanta ga yaran ba tare data wani damu da yi masa sannu da zuwa ba ko tambayarsa hanya "Kuka sani dafa muku indomie ashe ma ba yunwa kukeji ba kuka katsemin bacci na" sai taja dan siririn tsaki "Saiku tashi muje kuci,idan kuma bakwaci a bayar da ita" mimi ce ta maqale kafada "Nidai mommy banason indomie" ta hasala sosai,dama ga fadan da yayi mata "Baki isa ba tunda na dafa sai kunci" "Ji mana" ya dakatar da ita,saita waiwaya tana dubansa,ya ritsata da idanun nan nasa dake kassarata,bata buqatar ta sauko don haka ta kauda kanta "Babu lallai yaro sai yaci abincin da ya riga ya ginsheshi,ki deba musu cikin abinda kika dafa min,sauran ki kawomin shi falo na" fuska ta bata,cikin jin shakka murya ciki ciki tace "Ni ban dafa maka komai ba" ya zuwa yanzu mamakin hafsat ne ya kamashi,cikin son danne bacin ransa yace "Saboda me?" "To ai bakacemin ka taho ba" "Bakisan yau zan dawo bane?"ya jefa mata tambayar cikin salo na tsitsiye,saita rasa amsar bashi,saboda wayar qarshe da sukayi bayan sun gama ya tura mata tex na date da time na dawowar tashi,kawai ta share ne saboda tana jin haushinsa,tazo kuma ta raba dare tana kallo,shi yasa da safen ta dinga barci kamar matacciya,sai da yaran suka dameta da kukan yunwa sannan ta rarrafa ta dora musu indomie,ta rage wutar ta koma baccinta bayan ta zuba komai da komai,da nufin ta sake matsewa kafin ta dahu,a wannan tsukin ya shigo,kuma har ya kwashe yaran bata snai ba,uwa uba ma kuma manta shaf da batun dawowar tashi. Idanunsa ya lumshe yana jinjina kai,ya taka zuwa gaba kamar bazaice komai ba,sai kuma ya dakata ba tare da waiwayo ba yace "Ki gyaran sashe na,sannan ki dafa min abinda zanci kafin na gama" daga wannan ya wuce bandaki. Da kallo ta bishi har ya kammala wucewar ya rufe qofa,janye idanunta tayi tana sauke gauron numfashi,sai kuma tsaki ya biyo baya,bata dauka zai dauki abun da sauqi haka ba,duk da tasan halinsa,yakan iya share laifi yayi kaman ba'ayi masa ba,amma horonsa kuma sai yafi miki ciwo fiye da komai,a duniya babu namijin da ya taba yi mata abinda abbas din yake mata,batasan wanne irin so take masa ba daya samu dama da yawa yake juyata har haka ba,saita dakata da tunanin ganin bata da isashen lokaci,ta tarkata kan yaran ta sauka dasu zuwa sashenta,ta juye musu indomie din duk da sunce ba zasu ci,ta kunna musu kallo ta wuce kitchen tana tunani me zata dafa wanda bazai jaa mata lokaci ba. Sai data kwashe mintuna kusan biyar tana dawurwurar abinda zata dafa masa cikin kitchen din,daga bisani ta yanke dafa masa jallop din taliya,duk da tasan cewa kwata kwata bata cikin lissafin abincinsa,hasalima saboda ita da yara yake ajjiyeta,banda haka tasha zamanta,to amma kuma bata da wani sauran option,hakanan bata da idea din wani abu me sauqi da sauri baya ga taliyar,kuma koma meye dai oho,indai ta dafa ta bashi ai ta fita ko babu sabulu. Sai data wanke tukunyar da zata dafa abincin a ciki,saboda tun jiya datayi baqi qawayenta ta bata su gaba daya,ta kuma jiqasu sa zummar yau idan ta tashi aiki ta tsaftacesu,sai gashi kuma yayi mata dawowar ba zata. Tana hada girkin tana mita cikin ranta,taja tsaki yafi a qirga "Dole ne ma na samo 'yar aiki gaskiya,haba dame zaka ji?,kashe kanka zakayi?" Ta dinga gunaguni ita daya,tuntuni takeson daukar mai aiki,amma saboda wani banzan ra'ayi nashi da kuma kafiyarsa yaqi aminta,alhali kuma aiki yayi mata yawa,ga yara gashi karan kansa. Sanda ta gama ta juye masa a plate ta sanya wani ta rufe ta fito,a falon ta samu su mimi duka sun sheme barci ya daukesu,bacci dama sukeji,amma yunwa da rashin kyawun tsaftar jikinsu ya hanasu yin baccin,ga indomie dinta nan sunci wadda zasuci sauran sunyi wasa da ita sun sake d'aid'aita falon,sai a sannan ta lura da wankan da yayi musu,baki ta tabe "Kwado sarkin tsafta,ni wallahi bazan kashe kaina da wannan shegen son tsaftar taka ba" daga haka ta sanya kai tana ficewa zuwa sassansa. Zaune ta sameshi saman kujera riqe da remote yana kallon labarai,armless white shirt ce a jikinsa da three quarter wine color,ya miqa dogayen qafafunsa saman center table din yana kadasu a hankali. Kallo daya yayi mata ya amsa sallamarta yana maida dubansa ga tv,ta qaraso dab dashi ta janyo daya table din ta dora plate din abincin ta matso masa dashi,a gajiye take jinta tubus don bata sanyawa ranta wannan aikin ba,don haka ta koma kan daya daga cikin kujerun ta zauna "Sannu da zuwa" hankalinta ya bata tayi masa a sannan,sai daya sauke qafafunsa qasa ya zauna sosai sannan ya isa amsa mata,ya bude abincin yana kallonsa yayin da ita kuma take kallonsa tana jiran me zaice,kamar bazaici ba,sai kuma ya sanya fork a ciki ya debo yakai bakinsa. Idanunsa ya ragewa girma yana tauna taliyar cikin bakinsa,kamar mai tauna mutuwa haka yaji,baisan ya zaima hafsat ba,baisan sai yaushe zata nutsu ta gyara tukunyarta ba,kudade da yawa ya kashe wajen ganin ta iya abubuwa da dama saboda inganta rayuwar aurensu amma har yau babu riba,tana sane?,mugunta ce ko kuma meye?,idan kishi ne da nuna masa zallar soyayya a baki ita din tana kan gaba,amma ya rasa abinda yake damunta. Salin alin ya maida murfin ya rufe sannan ya miqe ya wuce bedroom dinsa,binsa tayi da kallo tana jiran taji me ya faru?,ba jimawa ya fito sanye da jallabiyya mai santsi dinkin qasar morocco mai gajeran hannu "Ina key din mota ta?" Ya tambayeta yana sanya qaramar hula saman kansa,maimakon ta amsa masa saita miqe ta wuce gaba zuwa dakin nasa,ta jawo locker inda ta zuba muqullan ta dauko ts miqa masa,saiya karba "Banaso na dawo na samu wajen nan a haka" ya fadi yana yin gab,tana son tambayarsa ina zashi amma bai bata damar wannan ba,tun daga fuskarsa har yanayin yadda yayi mata ya fice ba tare daya bata hanzari ba. *_ASSALAMU ALAIKUM_* _Barkanmu da dare da fatan kowa yana cikin qoshin lafiya_ _Akwai abinda muka turo tallansa na WOMEN EMPOWERMENT PROGRAM(KUDI KE KIRA),so please duk wadda batayi pyment ba ta jira tukunna kada tayi,akwai wani CONFIRMATION da mukeso mu samu a kansu_ *Idan komai ya daidaita zamu sanar muku* *_idan kikaci gaba da pyment kuma bada yawunmu ba_* *Muna godiya sosai* *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 12 *Widad* Dole qanwar naqi ta fara sakin jikinta,duk da cewa gaba daya hankalinta yana kan gida,abu daya ke mata burki ya sanya mata ko kwanto da kuma qaunar komawa idan ta tuna case din data bari a gidan. Satinta guda uncle muhsin ya maidata makarantar dasu nujood ke zuwa,baiyi shawara da kowa ba,hakanan bai gayawa kowa ba,yayi dai karambani ne,yana fatan karambanin nasa ya samu nasara. Makarantar boko ce hade da islamiyya,qarfe hudu ake tashi zuwa biyar yawanci duka yara suna gida,sosai widad tayi murna,don ita dinma akwai son karatu,cikin sati guda ta sake sosai abinta,zaka dauka tsohuwar daliba ce. ********** K'arfe takwas da rabi na dare ne,bayan su widad sun gama cin abincinsu su wuce daki,daga hajjaa sai uncle muhsin kawai a falo din,ta qaraso tana ajjiye masa zobon data dafa masa,ya dauka yana mata sannu ya fara kurba,sai ta gyara zamanta "Abba na cike foam din nan fa" ba tare da ya dubeta ba yana ci gaba da aikinsa bayan ya tura glass dinsa baya kadan yace "Ma sha Allah,to Allah yasa a fara a sa'a" fuska tadan bata kadan "Amma fa abba akwai matsala" sai a sannan ya waiwayo ya kalleta "Matsala wacce iri?" "Yara abba,bansan ya zanyi dasu ba,babu kowa a gida bare nace driver ya kawosu nan su zauna tare,kuma daga qarfe hudu zamu dinga farawa zuwa shida" ajjiye cup din hannunsa yayi yana dubanta "To yanzu ya za'a yi kenan?" Shuru ta danyi tana juya hannunta,sannan daga bisani tace "Eh to,da wai cewa nayi ko gidan hajiyan gida dubun zansa driver ya dinga ajjiyesu,tunda babu nisa wajen namu daga nan,idan yaso in mun tashi qarfe shidan sai na shiga na daukosu mu zarto gida?kaga kwana biyar kawai an gama" Kai ya jinjina "Qwarai kuwa,hakan ma yayi" "To abba ko zaka gaya mata kada suga yara kawai?" Dan dubanta yayi "Ke hajiya,ai fada zatayi tace don zasu zo sai an gaya mata?,ta wuce duk yadda kike zato,kamar uwa take a wajenmu,ba damuwa idan kinje kyayi mata bayani" "to shikenan ba matsala,godiya nake oga" "Baki da damuwa" ya fada yana murmushi tare daci gaba da aikinsa,ita kuma ta soma tattara kayan abincin da ya gama dasu ta wuce dasu kitchen,sannan ta biya ta dakinsu nujood din ta gaya musu gobe kowa ya dauki kayan gida cikin jakarsa zata saukesu ne gidan hajiyan. *********** Yau din tun safe da ya tashi dukka wayoyinsa na akashe,bashi da niyyar fita sam sam sam kamar yadda ya qudurta tun jiya,zaunawa yaso yayi a gida ya huta,saidai ra'ayin hutun ya kau daga ranshi daga sanda gari ya waye,sai kawai ya hau sanitation na gidan da kanshi,yana yi su mimi na biye dashi yana tayashi da aikin surutu,surutunsu bai dameshi ba,duk da kasancewarsa mutum marason hayaniya,sai surutunsun ya zame masa tamkar abokin hira. Sanda ta tashi ta taddashi yana aikin sai tayi kamar bata ankara da me yakeyi ba,ta qaraso inda yake tsaye saman wata stool yana cire yana,rungume take da hannayenta,tadan rusuna kadan tana fadin "Ina kwana" kansa yadan sauke kan,ya dubeta da manyan idanunsan nan masu kwarjini,a dai dai wannan lokacin kamata yayi ace ta kammala gyaran gidan gaba daya,ta kuma shiryawa iyalinta abun buda baki,shike kwance yana hutun da takeyi amma reshe ya juye da mujiya "Lafiya lau" ya amsa mata yana maida kansa ga aikin da yakeyi,sai taji sam sam ba dadi,tunda ya dawo babu wannan tarairaya da soyayyar tasa mai tsaya mata a zuciya,gaba daya fushin ma data tanada zatayi kamar ma ya fita yin fushin "Dame zan taimaka maka?" Tayi qarfin halin fada,batason ya soma nuna mata halin ko in kula din nan nasa dake mata ciwo,bai iya miskilanci ba ko kadan,idan ya fara sai kinji babu dadi "Inajin yunwa yara sukeji,ki sama musu abinda zasuci" ya amsa mata,sai ta sauke hannunta dake wuyanta,ta wuce kitchen dinta,tunda tuni ya gama da sassansa ya dawo nata. Tea ta hada musu da bread ta soma basu,amma da yake sun gaji da cima daya sai suka watsar suka kama gabansu "Ubanku ya bataku da cima,bazan iya wannan bautar ba,idan na gama kwaci gaba daya" ta fada tana nazarin abinda zaga dafa. Da yake tasan ita din mai laifi ce,duk da batajin tayi laifin har cikin ranta,saita zage ta bata lokaci ta shirya breakfast mai kyau,gasashen kifi tayi da chips,ta dafa masa ruwan tea din da yafiso,sanann ta dama masa kunun gyada still. Sanda ta gama bata gansu falon ba,sha biyu saura,sai ta jere komai a dining sannan ta wuce dakinta. Wanka tayi ta shirya kanta da kyau cikin wata atamfa,ta feshe jikinta da turarukan da tasan yafiso,wadanda takan jima batayi amfani dasu ba,duk da ya siyo su din amma sun zama kamar decoration saman mudubinta,takan ce bata da time na wannan qaqale qaqale din,bata shafawa fuskarta komai ba illa mai,ta taje kanta tana bata fuska saboda yadda yadan dunqule waje guda,ta manta when last data tajeshi,tunda yasa qafa yayi tafiya ta sauke 'yan gyaran da takeyi saboda matsawarsa da kuma qoqarin ganin ta hanashi qorafi a kanta. Daurinta ta kawo gaban goshi saita zari wayarta ta fito. Har yanzu babu kowa a falon,don haka ta zarce sassansa,tana tafe tana duba saqonnin wayarta har ta isa sashen. Ita kanta sai data shaqi iska ta fesar,yadda ya gyara sashen yayi matuqar burgeta,komai yayi fes yana fidda qamshi,tun bai iya wasu aikace aikacen ba har ya zamana ya koya ta dole,yanayin aikinsa karatu uwa uba yanayin matarsa,mutum ne shi sa baya shiri da qazanta sam,duk yadda yakai gason abu ko zama a waje yakan iya haqura idan yanayin baiyi masa ba. A falo ta samu su nawwara,sunyi fes dasu yayi musu wanka ya canza musu kaya,hakan yayi mata dadi sosai,ko banza ya rage mata wani aikin,dama tunanin yadda zata gyarasu takeyi a yadda ta gaji din nan,shi yasa bataso yayi tafiya wasu lokutan,duk da cakudewar aikinsa da yawan ayyuka wasu abubuwan shike dauke mata "Bari na fito da abban muje muci abinci,ku zauna anan" ta fada tana sanya kai zuwa bedroom dinsa. A nutse ta tura qofar ta sanya kanta bakinta dauke da sallama,idanunta suka sauka a kansa,yana tsaye gaban mudubi daure da guntun towel iya qugunsa,faffadan bayansa dukka yana a waje hadi da murdadden dantsensa,ya amaa mata ba tare saya waiwayo ba,jikinsa yake gogewa da wani qaramin towel din,saita maida qofar ta rufe a hankali ta soma takowa zuwa inda yake tsayen,tana jin qaunarsa da kewarsa na motsa mata. Ta baya ta rungume shi,ta kwantar da kanta a tsakiyar bayansa tana sauke ajiyar zuciya "Fushi kake tayi dani abba?" Kansa ya kalla a mudubi,tana bashi mamaki idan tayi wata maganar,kamar batasan komai ba,sai ya girgiza kai kawai yana qoqarin zareta daga jikinsa,don baya son ta bar masa wani feeling da zai dameshi,ya tabata kuma zance ya canza salo "Me kika gani?" "Abun ya motsa" ta fada a ranta,sai taqi bashi damar matsar da itan daga jikinsa ta riqesa gam gam "Nidai don Allah kayi haquri koma meye,duk da kasan kaine kayimin laifi,amma a barshi ya wuce" ta fadi tana qanqamesa gam a jikinta. Rainin hankalinta ya isa,baisan sai yaushe zata fara hankali,ta kuma fara gyaran kurakurenta ba,baisan sai yaushe zata gane haquri yake da ita ba,baisan sai yaushe zafa fahimci yawan uzurin da yake bata ba,sai ya sanya hannunsa ta baya ya jawota zuwa gabansa ya zaunar da ita saman kujerar mudubi yana kallon fuskarta,cikin tattausar muryarsa wadda a boye daga bayanta take cike da bacin ran da yaketa qoqarin binnnewa ya soma mata magana "Saboda nace bazan biya bashin dubu talatin da kika ciyomin ba a matsayin ankon da bansan da zamansa ba bayan sati biyu da suka wuce na miki dinkunan da suka tasamma dubu tamanin shine na zama mai laifi?,wannan shine dalilin da zai sanya ko sau daya ki kasa daga waya ki kirani kiji ya nake bayan kinsan aiki na tafi mai hatsarin gaske?,banda ina da uwa kenan babu wanda ya damu dani?" Yadda ya aza mata idanunsa sai taji sun mata nauyi,cikin jininta ta dinga jin rashin kyautawa na tsarga mata,amma bataso tayi giving up da sauri,saboda tsabar qi fadi dake damunta. Idanun nata ta zare tana kauda kanta gefe guda sannan ta soma magana "Amma dai tsakani da Allah,a wadatar da Allah yayi maka meye a ciki?,ka zabi ka kunyatani cikin qawaye na akan fiddani kunya kenan?,idan yaso duk fadan da zakamin ma kayimin shi daga baya" kai ya girgiza,mai hali baya taba fasa halinsa "Bazan karba abinda bani nace kiyi ba,bayan nasan ban gazawa gidana da iyalina da komai ba,suturar da zasu sanya ko mai matsayin mijin mace iyaka kenan,bazan yarda ki dinga daukomin basukan da basu da tushe bare makama ba,har yanzu wuyana baiyi wannan kaurin ba" ya fada muryarsa na qara nuba bacin ransa,dole tadan sassauta muryarta "Yanzu dai tunda na mayar kuma baka siya din ba ba shikenan ba?" "Eh shikenan,amma kada ki qara,ko meye kike da buqata ki gayamin,idan naga akwai sarari nayi miki,idan babu ki jira sai zuwa sanda ya samu" "To ai shikenan" ta fada tana kauda kanta gefe,ranta yana suya tana qoqarin dannewa,shuru ya ratsa dakin,yana ci gaba da shiryawa,yasan abu ne me wahala ta buda baki ta bada haquri,ba yau ya fara ganin hakan ba,yanason mata magana kan yadda take watsar da kula da gidan dama jikinta amma kuma yasan koda yayi dinma kamar busa ce a iska,babu lallai ta dauka,don haka yayi mata zance mafi muhimmanci yanzu a wajensa "Banga kina shirin komai ba,ko babu abinda zaki tafi dashi?" "Zuwa ina?" Ta fada tana waiwayowa da sauri,kafeta yayi da ido kafin ya dauke ganinsa,ya soma gajiya da wannan kayan takaicin,saboda tsabar rashin damuwa tana nufin har ta mance da maganar su dashi kafin ya tafi?,ko tsabar rainin wayo ne?. Bai amsa mata ba saboda baya jin akwai buqatar yi mata tuni,sai yaci gaba da shirinsa kawai,ita dinma ta tuna,duk da ba mancewa tayi din ba,amma tayi zaton zai bar maganar ne,tunda ta gaya masa ita babu inda zata bishi,ba zata iya barin bauchi ba. Tana zaune ya gama shirinsa tsaf cikin qananun kaya,binsa ta dinga yi da kallo,ba banza ba take tsakanin kishinsa,tasan ko kusa ko alama babu marching ko kadan tsakaninta da abbas,tako ina ya zarta mata,sau tari qawaye da 'yan uwa kan furta kamar ba mijinta ba,kalmar data tsana kenan,wadda duk wanda ya fadeta sai sun haura dashi,idan kuma tana ganin mutuncinka ta bika da harara ko baqar magana. Tsayawa yayi yana jifanta da wani kallo hannayensa zube a aljihun wandonsa,ya lura da yadda take binsa da wani mayen kallo "Zan samu abincin ko na zauna kiyita kallo na?" Ya fada da dan tsokana kadan cikin muryarsa,duk da fuskarsa bata nuna hakan ba,dama kuma yawanci ita daya ke ganewa wasan tsokanarsa, mmurmushi ya subuce mata,ta miqe tana cewa "Kaci abincin tukunna sai na zauna nayita kallon naka". Har yanzu dai still taste na girkinta bai kai masa yadda yakeso ba,amma hakanan ya kama yaci,yana mai bata uzurin wataran zata qware,tunda a yanxun abincin yana ciyuwa alhamdulillah. *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 13 Kusan suke cin abincin,ita dai tana ta biye musu ne amma cokalin kawai take juyawa cikin plate din,tuntuni sun jima da raba plate din cin abinci dashi,tare dai suke ci,amma kowa kwanonsa daban,tunaninta gaba daya yafi karkata kan yadda zata sake jaddada masa ba zata bishi kaduna ba. Har ya kammala cin abincin ta rasa kalmar kamawa,ganin yana qoqarin tashi sai tayi gyaran murya,ya dakata da shirin tashin da yakeyi ya aza mata hankalinsa "Abban mimi,nifa gaskiya ba zan iya binka kadunan nan ba,don Allah ka janye tafiyar nan dani" ta fada tana jin nauyin maganar,a mamakance yake kallonta,tsahon wasu sakanni sannan yayi gyaran murya "Nayi tunanin mun gama maganar nan dake ko?" Kai ta girgiza "Bamu gama ba gaskiya,bazan iya tafiya wata kaduna ba" ransa ya sosu,ta yaya yana son kare mutuncinsa da martabarsa ya tafi da iyalinsa don samun kariya daga sharrin shaidan amma tanason ingizashi zuwa ga hallaka?,kadunan bariki zai tafi shi kadai alhalin da iyalinsa ba gauro bane? "Koda bakiso hakanan zaki tafi,kuma bama kaduna ba,duk inda aiki ya jefani hafsat haka zaki bini muje,wannan shine tsarina" yana kaiwa nan ya miqe tsaye yana shirin sauka daga dining din,sai itama ta miqe,wai me yasa ya fiya kafiya da taurin kai ne?,haka kawai tana cikin garinta cikin dangi da 'yan uwanta zai cizgeta ya tafi da ita wata uwa duniya?,itakam sam bata ga dalili ba "Gaskiya babban mimi bazan iya barin dangina da kowa nawa da dan business dina dana fara ba na bika garin da bansan kowa ba,babu kowa nawa ba" ta fada adan hasale,kallonta yayi sai ya dauke kai ya gewayeta ya wuce,bashi da lokacin tsaiwa tanka mata ga yara zaune a wajen,sannan ma shi din ba mutum bane mai yawan son magana,banda Allah ya hadashi da ita mutum ne marason hayaniya,yafi qaunar zaman shuru da kadaici wani lokacin,shi yasa ko sabani suka samu bai fiya damunsa ba,yakan kebe yayi zamansa yana karance karance,idan kuma yara suna nan yayi sabgarsa dasu. Binsa tayi har cikin falon tana maimaita maganar,yasan idan ya zauna ciwon kai zata sanya masa a banza,don haka sai ya dauki key din motarsa dake gefan tv stand ya fice abinsa kawai,yana amsa adawo lafiyan da mimi ke masa. Komawa tayi ta zauna jabar saman kujera tana tuje daurin dankwalinta tayar gefe,wannan wanne irin maqalallen aiki ne da basu da aiki sai sassauyawa mutum gurin aiki?,daga can sai nan?,yaushe ma duka duka sauka dawo bauchin tana ta murna ta dawo gida?,to itakam wallahi ta gaji,tana son abbas matuqa tana tsakanin kishinsa,to amma aikinsa zai zama babban tarnaqi a rayuwarsu. Tana nan zaune tana saqawa gami da kwancewa,mimi nata gaya mata nawwara na wasa da abinci amma hankalinta bai wajen,har sai da yarinyar ta fado da tea flasks dinsu ya fashe a wajen sannan ta farga,sai a sannan ta miqe tana banbamin fada ta nufi wajen,sai data durma mata dundu sau biyu a baya sannan tahau aikin gyara wajen,tanayi tana mita,yarinyar kuwa ta fashe da kuka,mimi ce ta matsa ta ruqo yar uwar tata tana goge mata fuska. *********** Ranar da driver ya ajjiyesu gidan hajiya tayi mamakin ganinsu,ta danji fargabar ganinsu da uniform ba kayan gida ba,tana zaune a falonta tana lazumi bayan ta idar da sallar la'asar,da yake takan kwashi awa guda kafin ta kammala,ta amsa gaisuwarsu tana maida idanunta ga widad da take baquwar fuska a wajenta,saita dauke dubanta tana tambayar nujood ko lafiya "Mommy ce tace muzo nan mu zauna,qarfe shida zatazo ta daukemu,makaranta ta shiga" "To alhamdulillah" hajiyan ta fada tana jin hankalinta yana kwanciya. "Bari muneera ta zuba muku abinci kuci" "Zanyi alwala banyi sallah ba" widad ta fada,wadda tun dazun take jinta a takure,saboda yau nujood ta matsa musu basuyi sallah a makaranta ba. Dubanta hajiya tayi,sai taji yarinyar ta burgeta,a shekarunta amma tasan kiyaye sallah,duk da tasan idan bata fara haila ba kadan ya rage ta fara,amma ko su muneera da suke 'yammata sosai wani lokaci sai tayi fama da su kan sallar,kiran muneera hajiya tasa nujood tayi,ta kaisu dakin baqi tace suyi sallar sai su fito suci abincin,duka suka miqe suka bita. Ba jimawa suka gama sallar suka fito,muneera ta kawo abincin,hajiya na zaune daga gefansa tana lazuminta,jifa jifa tana kallonsu sanda suke cin abincin. Yaran uncle muhsin din suna da nutsuwa da tarbiyya,amma sai taga nutsuwar widad ta fita daban,ita tafara tsame hannunta daga abincin,ta kuma gyara wajen takai kwanon kitchen,wannan duka aikin ummu ne,duk da bata aikin komai irin ta horas da ita qananun abubuwa irin wadan nan da kyau,kwata kwata widad din ba maison jiki bace,da karambani ma ta iya wasu abubuwan sosai,wanda take koya wajen anty madina,ko idan ta shiga sassansu Aafiya ko ramziyya. Sunata sabgarsu amma tana zaune waje daya,ita gaba daya jinta take a takure,bata son baqon waje,tana da wahalar sabo kuma,wannan yasa ta qara tsumewa waje daya,Allah Allah take momy ta iso su tafi gida. Zaman daya isheta sai ta fara taya muneera ninkin kayan hajiya,sun kusa rabi muneeran ta miqe tayi kwanciyarta,widad din ita ta qarasa muneera ta kwashe takai mata daki. Shida da mintuna hajjaa ta iso a motarta,suna jinta suka fita da sauri tararta,widad ko murmushi tayi tana gyara zamanta,tana jin zama yazo qarshe sai gida. Da sallama ta shigo falon hajiya na mata sannu da zuwa fuskarta da murmushi "Hajiya ai ke za'a yiwa sannu,yau na hadaki da hayaniyar yara" "O'o,o'o,aini deben kewa ma sukayi,yau babu zaman shurun nan" murmushi hajjaa tayi tana maida dubanta kan widad "Kamar kiyi tsuntsuwa ki janyoni ko?,gani na iso sai gida" dariya ta danyi,hajiya ta dubeta "Da alama kam,don tunda sukazo ta kasa sakewa,tana zaune waje daya" "Ai akwaita da baqunta da rashin sabo,duk da dai dama bata da hayaniya sosai,ga oganni nan" dariya hajiya tayi sannan suka fara gaisawa,ta gaya mata aikin da zasuyi na kwana biyar din,tare da alfarmar zama da zasu dinga yi har na kwana hudu a wajenta "Kin jiki hadiyya,banda abinki ba jikokina bane,har sai kin nema alfarma,ai nan dinma gida ne,Allah ya taimaka yayi jagora" "Ameen hajiya,Allah ya qara girma". Hajiyan nata tsaidata suyi sallar magariba amma tace sayi a gida,ta tattara yaran suka wuce gida suna yiwa hajiya sallama tare da cewa sai gobe,don dama su nujood gidan zuwansu ne su,suna kuma jin dadin zuwa gidan sosai saboda kirkin hajiya. ********* Yammaci ne sosai daya kamata ace a lokacin yana cikin gida yana hutawa,tare da shirye shiryen barinsa bauchi zuwa kaduna,saidai bai samu wannan sararin ba,saboda fitinar da hafsat din keson tsirowa dashi,tun batun zuwanta kaduna da yace lallai sai tayi,ko a yanzun ma ya fito gidan ne saboda yadda ta tasashi gaba da nacin roqo harda qwallarta kan ya barta a bauchin,shi baisan wanne irin tunani ke gareta ba,baisan me yake damun kanta ba,kin gwammace kibar mijinki ki zauna da dangi?. Wasu lokuta matsalolinta caza masa kai suke,sai ya samu ya kebe tukunna yake samun kwanyarsa ta huta,don haka ya zabi fitowa daga gidan. Tun asali ba mutum bane shi mayawaci,idan ka ganshi a waje dalilin aiki ko kuma wata lalura ce ta kaishi,sau tari abokan aikinsa na yawan tsokanarsa,sam dabi'unsa kamar ba na dan sanda ba,saidai ya murmusa kawai,ba kasafai yake basu amsa ba. A hankali yake tuqin nasa,kwanyarsa cike fal da tunani,sannu a hankali har ya qaraso junction mai bada hannu ya tsaidasu,motarsa na sahun gaba,yana iya wucewa idan yaso,to amma sanin doka da qa'ida ta sanyashi tsaiwa kamar yadda ya dace ace kowanne mutum ya tsaya din. Hankalisa nakan radio din motar yana son kamo daya daga cikin tashoshin gidajen radio da yakan saurari labaran yamma,baisan me ya faru ba yaji tashin hayaniya,ya daga kansa da sauri yana duban gefansa inda hayaniyar ke tashi. Matashin saurayi ne tsaye kusa da motarsa qirar 206 yana zazzagawa wani tsoho dake saman mashin masifa,yayi tsai yana duban matashin yadda yake haqilo kamar zai kaiwa mutumin duka,mutane har sun fara taruwa ana bashi haquri,ci gaba yayi da nazarin matashin dake dukan saman motarsa yana fadin shifa sai an biya shi,daga gefe daya wani jami'in dan sanda ya fara ratsowa cikin mutanen yana fadin a bashi hanya,abbas din ya bisu da kallo yana son ganin abinda zai faru. Yana daga wajen yake nazartar komai,yadda dan sandan ya shiga maganar suka hadu da matashin suna son bauwa dattijon rashin gaskiya,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fito ya nufi wajen. "Assalamu alaikum.....lafiya me yake faruwa?" Yayi tambayar yana duban matashin da yaketa faman daga jijiyar wuya "Wannan tsohon ne ya gogar ma mutane mota da wannan tsohon mashin din nasa,dubi yadda ya gogewa mutane fentinsu" idanu ya lumshe kana ya bude kusan lokaci guda yana duban inda yake fadin an goge masan,duka duka gugar ba wata me girma bace "Kayi haquri kayi masa uzuri kuma,tunda nasan yana sane bazaiyi haka ba" "Wallahi dan nan tun daxu ma naketa bashi haquri,bansani ba,sauri nakeyi ina da uzuri a gida" "Baba ina ganin mutuncinka fa da tuni na zageka,da haqurin ya mutu sadakar nawa ka bayar?,ka biyani kawai" dunqule hannunsa abbas yayi cikin aljihunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa "Kayi haquri tunda shima ya baka haquri" "Kaga malam bazan fa haqura ba,idan ma tsaiwa kayi a nan don ka bani haquri gwara kayi gaba abinka" "Is okay,nawa ne kudin gyaran?" Ba kunya ba tsoron Allah ya karkace ya tsuga kudi,kallonsa abbas yayi na tsahon wasu mintuna yana karantar zallar qaryar dake qwayar idanunsa,sai ya saka hannunsa a aljihu ya ciro kudi,ya irga ya miqa masa. Kunya da haushi suka kama matashin,bai taba zaton zai iya biyan kudaden ba shi yasa ya saka da nauyi,cikin borin kunya yace "Ni ba kudi nake buqata,muje a gyaran motata" "Ko ka karba ka tafi,ko kuma kayi asara ba kudin ba gyaran" "Wai kai waye da zakazo kana cikamin baki malam?,bazan karba ba gyaramin mota nakeso ayi" matsowa dan sandan yayi kusa da abbas ba tare daya lura da waye ba a tsaye "Kai meye naka ne a ciki zaka zo kawai ka shiga rigimar kan hanya?,ka qyale mut....." A nutse abbas ya juya suka hada idanu da dan sandan,gabansa yayi mummunan faduwa,yayi baya babu shiri,gumi ya fara yanko masa,abbas din baice komai ba ya maida dubansa ga matashin "Ina me shawartarka ka karba" "Idan kuma naqi fa?" Wani qaramin murmushi na gefan baki abbas ya sake,hankali kwance ya maida kudinsa aljihu gami da fito da wayarsa a madadin kudin,ya danna kira. Baice komai ba illa adreshin titin da suke kai daya bayar ya maida wayar aljihunsa,ya kuma harde hannuwansa yana kallon yadda yake ci gaba da zuba rashin mutunci,jikin dan sanda yana rawa ya matsa kusa dashi "Bawan Allah kayi haquri ka tafi,zaifi maka alkhairi,tunda nasan zuwa yanzu ko kudin ma ka rasasu ba samunsu zakayi ba,gwara ka tsira da lafiyarka da mutuncinka" "Dalla malami sakeni,wallahi yau sai naga wanda ya tsaya masa" ya fadi yana kumfar baki,maganar tasa ta sake hasala abbas,saidai bai nuna hakan ba koda a saman fuskarsa,yana ji ya zama wajibi ya bashi tarbiyya da bashi da ita,sai ya juya ga tsahon "Kada ka sake bashi haquri baba" hannu ya saka a aljihunsa ya fidda dubu uku ya miqa masa "Hau mashin dinka ka tafi,Allah ya tsare" zaburowa yayi yana fadin "Idan ka barshi ya tafi rigimar nan ta koma kanka wallahi" "Na karba"ya amsa masa yana sawa tsohon muqullin babur dinsa ya kunna masa,dai dai sanda motar 'yan sanda ta iso,hakan ya baiwa tsohon hanyar wucewa,yana tafe yana jerantawa abbas din addu'o'in samun albarka da gamawa da duniya lafiya. Matashin bai fahimci waye abbas din ba sai da jami'ai suka cika hannu dashi shi da dan sandan dake goya masa baya,sai a sannan ya nemi russunawa ya fara roqon ya saka a sakeshi,ko kallonsa baiyi ba ya dubi Samuel "Ku sakayamin su a bayan kanta saina nemesu,mato ya tuqa motarsa a kaita station a ajjiye" "Consider it done sir" ya fada yana saluting nashi. *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA* *DAUD'AR GORA* Billynabdul *KI KULANI* Missxoxo *IDON NERA* Mamuhghee *RUMBUN K'AYA* hafsat rano *A RUBUCE TAKE* Huguma *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN* 0022419171 Maryam sani Access bank Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number 09033181070 *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU* 09166221261 *YAN NIJER ZASU TUNTUBI WANNAN NUMBER* +227 90 16 59 91 *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *_Arewabooks:huguma_* Page 14 Ta tsakiyar mutane da suka cika a wajen 'yan kallo ya samu ya ratsa ya koma motarsa,yabar mutane suna ta tattauna maganar,da yawansu hakan da yayi ya sake burgesu saboda diban albarkar yaron tayi yawa,yan bani na iya kuma na ganin baiken hakan,suna ganin kamar yayi amfani da qarfin ikonsa ne. Abinda ya faru akan hanyar ya qarawa kansa zafi,ransa ya dinga sosuwa duk sanda ya tuna girman shekarun mutumin da abinda qaramin yaro yayi masa,a nutse yaci gaba da tuqinsa har ya shiga unguwar tasu,qofar gidansu yayi parking,yana shirin fita a motar sukaci kacibus da qanin mahaifinsa suka tsaya suna gaisawa,wannan yaja masa jinkirin shiga gidan,sai bayan la'asar sa wasu 'yan mintuna bayan sunyi sallar la'asar a masallacin qasan layinsu sannan suka taho tare da kawu hassan din,yanata masa godiyar uban gudunmawar daya bayar na auren diyar kawu hassan din,har suka iso gida,kawun ya shige gidansa dake jikin gidansu abbas din. Tun a harabar gidan ya fuskanci kamar gidan yau ba iya mutanen gidan bane kawai a cikinsa,muneera dake wanke alayyahu cikin famfon dake baiwa shukokin da suka qawata harabar gidan ruwa ta amsa sallamar tasa gami da gaidashi ya amsa mata,har yaa taka zuwa gaba sai ya tsaya cak ya waiwayo ga muneera "Hajiya na ciki ne?" "Eh sallah takeyi" fasa shigar yayi,saboda hayaniyar daya danji,a yanzun kuma ba abinda yake buqata sai zaman shuru,don haka ya juya akalarsa zuwa sitting room din baqi dake harabar gidan daga gefe "Idan ta idar ki gaya mata na shigo,amma zan dan kwanta kadan" "To uncle" ta amsa masa tana daukan kwandon alayyahunta tayi ciki,shi kuma ya murza key din daya gani a jiki ya bude falon ya shiga. Yasan tsaf falon yake,duk da ba shigarsa akeyi akai akai ba,babu inda hajiyarsa ke bari da qazanta cikin gidanta,koda kuwa ba'a amfani da wajen,bata lamutar datti ko qura,wannan yasa babu haufi ya nufi daya daga cikin kujerun Three sitter ake falon yayi kwanciyarsa,ya miqe bayansa sosai saman kujerar yana lumshe idanunsa hadi da sakin ajiyar zuciya,yanason baiwa kwanyarsu hutu,bayason tuna komai da zai dameshi. Minti kusan goma yana a haka,yanata kokawa da tunane tunanen dake kwanyarsa,saidai surutai da 'yan iface ifacen dake gilamawa kadan kadan ta wajen nadan damunsa lokaci bayan lokaci,bai wani dameshi da yawa ba,wannan ya sanya yaci gaba da barin idanuwansa a rufe. Gigitaccciyar qarar data cika harabar gidan ta sanyashi durowa daga saman kujerar ba tare daya shirya ba,muryar nada matuqar kaifi da zaqin da zata iya huda kunnuwan duk wanda ke wajen,zaman dirshan yayi saman kujerar yana rufe idanunsa jin yadda qarar taqi tsagaitawa,ya rintse idanunsa yana jin yadda kansa ke sara masa sanadiyyar qarar,tsaki yaja dabmugun qarfi ya kuma miqe a fusace ya nufi qofa yaje yaga wanda ke qarar kamar wanda ake cirewa rai. A hankali ya yaye labulen ranshi a bace idanuwansa a farfajiyar gidan yana son ganin wanne tashin hankalin ne haka yake faruwa,idanunsa suka sauka a kanta,a lokacin ta jima da fara tsalle tana runtuma ihu hadi hadi da hawaye face face saman fuskarta,tuni 'yar hular dake saman kanta tayi nata waje,gashinta da koda lafiya lau yake sabulewa daga jikin ribbom ya baje abinsa iska tana daukarsa. Idanunsa ya zube mata,yana qare mata kallo,me ya sanyata wannan tsallen a gigice?,kunama ce ta harbeta ko maciji ta gani?,saidai kunamar,don ya tabbatar cikin gidan nasu ba za'a samu maciji ba,sai ya rasa me ya kamata yayi,ihunta yana sake cika masa kunne,baikai qarshen tunaninsa ba hajiya ta iso wajen da hanzarinta ita da muneera,a rude take qoqarin kama widad tana tambayarsu nujood me ya sameta?,sai ya harde hannayensa a qirji,ya zauna a hankali saman hannun kujerar dake daura da qofar yana kallo da sauraren abinda yake faruwa "Kyankyaso ne ya shigar mata riga" idanunsa ya lumshe yana jin wani haushinta yana cikashi,kyankyason takema wannan kamar wadda taga mutuwa?,bai bude idanun nasa ba yayi shuru yana sauraren muryar hajiya tana cewa "Kyankyaso?,riga kuma?,garin yaya?" "Musaddiq ne ya saka mata(qanin nujood dake binta)" "Ashsha musaddiq baka kyauta ba" hajiya ta fada tana qoqarin kakkabe mata rigar. Hannu daya ya sanya ya sauke labulen,ya kuma tura qofar da qafa sannan ya koma saman kujerar ya kwanta kamar dazun yana sake jan tsaki,ko a ina hajiya ta samo su suka cikawa mutane gida da hayaniya?. Still idanuwansa suna rufe,yana jinta cikin sheshsheqar kuka tana gayama hajiyan yadda abun ya faru,ta yima musaddiq fada sosai sannan ta hada kansu suka wuce cikin gidan. Ana kiran sallar magariba ya wuce masallaci yayi sallah sannan ya shiga cikin gidan,zuwa sannan babu kowa daga hajiyan sai muneera "A'ah,shigowar magariba kuma yau kayi abbas?" "Ina nan tun sanda wannan tsanyar ke ihu" dan shuru tayi na sakanni,sai kuma ta saki murmushi "Wai widad?,aikin musaddiq ne wallahi" "Musaddiq din muhsin wai?,dama sune?" "Sune,a nan hajjaa ke barinsu,idan ta taso daga makaranta take daukansu,widad kam ai bata da hayaniya ko kwaramniya,shaqiyancin musaddiq dinne,yasan yadda take tsoron kyankyason ya saka mata shi" kai ya jinjina kawai ba tare da yace komai ba,sai a sannan hankalin hajiya kuma ya dauku ga fuskarsa,ya akayi har ya shigo gidan tun yamma bai nemeta ba,fuskarsa ta nuna akwai damuwa tattare dashi "Allah dai yasa lafiya" ta fada bayan sun gaisa,furzar da iska yayi daga bakinsa,ya motsa baki zaiyi magana ta datsi numfashinsa "Kada kacemin babu komai" shuru ya ratsa falon na wasu sakanni,sai ya buda baki a hankali yana gayama hajiyan zancan tafiyarsa kaduna da hafsat tayi tutsun ba zata je ba. Ran hajiyan ya dan tabu,tun ba yau ba tasan matsalar dake cikin gidanshi,ba yau ta fara gani da fuskanta ba,saidai batason shiga lamuran gidansa sam,hakanan a matsayinta na uwa bata da abinda zata masa illa addu'a da kuma bashi shawara na gari "Kayi haquri ka tafin,kada ka matsa mata,duk sanda ka samu sarari ka dinga zuwa kana ganinsu,ta wani fannin tana da hanzarinta daya kamata a duba,ko don karatun mariya(mimi) da yanzu ta farashi kada ya samu tangarda,zama da iyali dan haquri ne,mahaifanku dukka haquri sukayi damu har zuwa sanda Allah ya rabamu,komai yayi farko kuma yana da qarshe" ajiyar zuciya ya saki,maganganun hajiyan sai suka sake kwantar masa da hankali da sanya masa nutsuwa,kalmominta masu tsada ne da baiwa zuciya da kuma ruhi nutsuwa,take yaji gaba daya dukka wani kwadayinsa na tafiya kaduna da hafsat din yakau a take "Na gode hajiya" ya fada yana bude abincin data saka aka kawo masa,ya fara ci a hankali suna hira da hajiya,hirar da ako yaushe ita ke debe masa damuwa. Basu jima suna hirar ba babban yayansa ya shigo,wannan yaja hirar tasu,har yakai qarfe tara na dare,sai da zai tafi yace ya saukeshi a hanya,ya ajjiyeshin sannan ya wuce gida shima. Tun k'arfe takwas da rabi duka yaran sukayi bacci,ta kwashesu ta kaisu dakinsu ta kwantar dasu,ranta a jagule,kishi fal ranta,zuciya nata mata saqe kala daban daban kan inda ya tsaya din,don ba kasafai yake kaiwa dare haka a waje ba,koda zaikai din yana kiranta ya gaya mata zai kai dare din,tunda babu ta yadda aikinsu baya kamawa. Dakinta ta wuce bayan ta rage hasken falon,tanaso qwarai tayi wanka amma kuma tana gandar zuba ruwa a jikinta,saita zarme da zama gefan gadonta kawai taja wayarta ta fara chart. Batasan lokaci ya ja haka ba sai data ji qarar shigowar motarsa,ta sauke wayar tana duba lokaci,sai taci gaba da chart dinta,don tasan yawanci bai fiya dawowa shi kadai ba,kuma idan hakan ta kasance sai ya sallamesu kafin ya shigo cikin gidan. Duk da yasan babu lallai ya samu kowa a falon amma bai fasa yin sallama ba,ya dan bi falon da kallo,babu laifi,bai wani kacame can da yawa ba,duk da bai masa tsari yadda rai da zuciyarsa sukeso ba,kai tsaye dakin yaran ya wuce,ya tura qofa ya shiga,wutar dakin tana kunne,yabi yaran da kallo,ba alamun an musu wanka da zasu kwanta bare ayi maganar brush,kowanne cikinsu yana da kayan bacci qasa da kala goma goma,amma bazaice ya gansu dasu sau biyar ba,baima san inda take kaisu ba. Yadan jima a kansu yana musu addu'ar daya tabbatar bata musu ba,ya shafesu da ita,ya sake gyara musu kwanciyar ya lullubesu sannan ya kashe wutar dakin ya fito yaja musu qofar. Yana fitowa tana fitowa a nata dakin,kallon kallo sukayi a tsakaninsu,tanason ta karanci har yanzu ranshi na abace ne ko ya haqura?,duk da ba yau suka saba irin wannan ba,yayin da shi kuma yake kallon dressing din jikinta,kayan daya fita ya barta ne dasu,wanda tun safe suke jikinta,duk da yalwar suturu da take dasu masu tsada da kyan gaske,to amma fa idan ka gansu a jikinta wani babban sha'ani ya tashi da zata shiga dangi ko qawaye tayi bajinta "Sannu da zuwa" ta fada tana dan basarwa" "Yauwa,ya gida ya yaran?" "Alhmdlh" ta amsa masa tana mamaki,a yadda ya fita bata taba kawo saukarsa a nan kusa ba,amma sai taga kamar babu abinda ya faru "Anan zaka ci abincin naka?" Ta tambayeshi sanda taga yana takawa yana barin wajen "Zan danyi wanka,kamar nan da minti goma ki kawomin sashena" dan yatsina fuska tayi can qasan ranta tana mita,bayan wahalar girkin da tasha kuma sai ya sanyata wahalar diban cooler din abinci ta bishi dasu?,me yasa bazai zauna a nan yaci ba?,bata amsa masa ba har ya fice,sai ta juya ta koma daki abinta taci gaba da charting dinta. Da sauri ta miqe sanda taji agogi ya buga,minti goma sai data ninkasu wajen sau hudu,ta qara ya zama minti arba'in da kusan biyar ba tare data ankara ba,ta jefa wayar gefe ta miqe tana gyara daurin dankwalin atamfar dake kanta sannan ta fito tana gyara daurin zaninta daya dangale tana qoqarin daidaita tsahonsa. Har ya gama shirinsa tsaf ba ita ba alamunta,ba wani yunwa yake ji ba ya riga da ya take cikinsa wajen hajiyarsa,don haka bai wani damu ba can,dama kuma idan da sabo ya riga ya saba,sai ya dauko luggage dinsa ya fara shirya kayan da zai tafi kaduna dasu. Ya gama hadasu tsaf ya debo wasu takardu nasa yana dubawa,sai ya koma kan sofa dake dakin ya zauna yana dubawa cikin nutsuwar nan tasa. *_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥 *_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥 *FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥 *JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA* *_'YAN BIYAR DIN NAN NE FA_* *_SARAKAN LABARUN_* *NISHADI* *CAKWAKIYA* *GWAGWARMAYA* *BARKWANCI* *TSANTSAR DARASIN RAYUWA* *TARE DA* *ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI* *SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!* *KIN SHIRYA MADAM?* *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA* *DAUD'AR GORA* Billynabdul *KI KULANI* Missxoxo *IDON NERA* Mamuhghee *RUMBUN K'AYA* hafsat rano *A RUBUCE TAKE* Huguma *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN* 0022419171 Maryam sani Access bank Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number 09033181070 *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU* 09166221261 *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾 *Arewabooks:huguma* *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 15 Qwayar idanunsa ya daga kan takardun yana dubanta sanda take shigowa dauke da kwanukan,ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana qarewa dressing dinta kallo,baisan sai Yaushe hafsat zata canza ba,baisan me zaiyi da zai canza ta ba,duka wani burinsa a kanta ya dade da tarwatsewa,wani lokaci sai ya dinga gani kamar ba hafsat dinsa ba. A gabansa ta ajjiye abincin sannan ta koma gefansa ta zauna tana maida idanunta ga takardun da yake dubawar shima "Ga abincin" ya daga takarda daya yana juya bayanta ba tare da ya kalleta ba "Shi zai zubamin kansa da kansa?" Jim ta danyi sannan ta tabe baki,wani lokaci ya fiya jin kai da izza,hutsu ne na gaske,sai yayi kamar ya sauko ko ya canza sai kuma ya sake hargitse mata,ita kanta tana sarawa kanta yanda take haqurin zama dashi,sai ta sauka tana zuba masa ta ajiiye gabansa tana komawa mazauninta. Sai daya qara minti kusan biyar sannan ya ajjiye takardun ya sauko,tana ta satar kallonsa,tana son masa maganar motarta data fara bata matsala tana shakka,dazun sun rabu ba ta dadi ba,yanzun kuma taga yana hada kaya,ta tabbatar kayan tafiya KD ne,wala'alla ya haqura ne ya janye qudurinsa?,idan hakanne ita tafi mata nono fari,saidai tafi kowa sani,shurunsa bashi da sauqi,mataki ne zai dauka daga baya ta ruwan sanyi,koma dai yaya ne idan har ya janye din shikenan its buqatarta ta biya,a hakan ta daure dai tayi gyaran murya kadan. Ya jita sarai yayi kamar baiji ba,sai data gaji da gyaran muryarta sannan ta magantu "Wai kayan tafiyar kake hadawa?" "sune" ya bata amsa a taqaice "Allah yasa a koma a sa'a,mudin ko weekend ma dinga zuwar maka,kaga bazai shafi karatun mimi ba" ta fada har qasan ranta tana jin ta fada ne kawai don ta wanke kanta,bawai don zata iya wannan jigilar ba "Yayi" ya amsa mata a taqaice kawai,don baison doguwar magana. Shuru ya sake ratsa tsakani,tana ta tauna yadda zata gaya masa zancan motar,don so take kafin bikin qawarta din nan ya sauya mata,taje a hajiyar ta da sabuwar mota,ba wannan qaramar motar da kowa ya sanya da ita ba "Nace ba" ta fada a darare "Uhmmm,kikace me?" "don Allah ba.....abban mimi motata...wallahi matsala take ta bani,sannan ma tayi tsufa da yawa,kada kunya na dinga shigarta bayan mutane sunsan matsayinka" shuru kamar bazai amsata ba,yaci gaba da cin abincinsa,yayin data kasa ta tsare ta kafeshi da idanu tana jiran ta cewarsa,har sai data gaji da jiran amsa ta sake magantuwa "Bakace komai ba abban mimi" plate din hannunsa ya ajjiye,ya waiwayo ya dubeta "Bani da kudi a yanzu" fuska ta dan bata "Abban mimi baka da kudi fa kake fada?,ko allowance dinka ya isa ka canza min babbar mota bama qarama bafa" "Kudina a yanzun bana canza mota bane,ina da abu me muhimmanci da ya fishi" daga haka ya miqe yaci gaba da aikinsa hankali kwance,cikin bacin rai taci gaba da zama wajen,tana ta baqin rai ita kadai,zantukan yayarta take tunawa "Kada fa kiga mijina ya canzamin mota ki dauka kema wannan mijin naki me ra'ayin riqau zai canza miki mota ta sauqi,mafi kyau ki haqura da maganar zancan mota yanzun,nasan halinsa sarai ba canza mikin zaiyi ba" a sannan baki ta tabe tana dan kada qafarta "Kiyi haquri umman walida,amma banjin yadda abbas ke kashemin kudi da yadda yakeji dani kina samun haka wajen baban walida....." "Ke kinga dakata,karki gayamin baqa mana" ta dakatar da ita,duk da cikin wasa suke maganar "Kowa ya san abbas yana jiqaki,amma kuma duk cikinmu babu wadda juya miji ke mata wahala irinki koba haka bane?" Ta fada tana duban sauran sisters dinta dake wajen,dariya suka danyi suna gasgata maganar maman walida din da suke kira da anty balaraba,wannan ya hasalata,ta kuma ci musu alwashin kawo sabuwar mota don ta nuna musu ta isa da mijinta kamar kowacce mace. Har yaci qarfin aikinsa tana zaune a wajen bata sake tofa tata ba,ta tattara fushin duniya ta azama ranta,me yasa koda yaushe abbas din sai ya kunyatata yakejin dadi?,kafin ya kammala aikin ta tattare tabar masa wajen,sai kawai tayi komawarta sashenta,tayi kwanciyarta acan. Shima daya gama komai kwanciyarsa yayi,bai wani tsaya bi ta kanta ba,bayason rainin wayo da kuma rashin hankali,ta kuma fi kowa sani abinda baya tolerating kenan. Washegari haka tayita kumbure kumburenta,sai ya nuna baisan ma abinda takeyi ba,ayi masa laifi kuma a fishi fushi?,yayita hidimarsa da yaransa,yana kuma yin breakfast ya shirya zai fita,mimi ta maqale masa sai ta bishi,ya kaita gidan hajiya,hafsat din nata danqara masa mata harara amma yarinyar batasan tana yi ba,ya shiga dakinsu ya shiryata da kyau cikin sabbin kayanta dake danqare a cupboard ba'a sanya musu,baisan uban me takeyi da kayan ba,yasan dai wani lokaci takan diba ta rabar,duk cikin fariya da alfaharin shi din wuyansa ya isa yankan da yake danqaro musu suttura ya ajjiye. Yana fita ta bishi da tsaki ta kuma miqe abinta saman doguwar kujera tana gunaguni,duk yadda take sonshi yana sanyawa yana fita a ranta gaba daya,bata isa ta sashi yayi abu ba sai abinda yayi niyya ya kuma tsarama kansa,kallo ta kunna abinta tana daga kwance,nawwara da yau suka samu albarkar wanka tun safe tana ta kaikawo tana wasanta qasan carfet,har bacci ya dauketa ta bingire a nan. Har biyu ta buga tana kwance tana kallo bata da niyyar tashi ta kintsa gidan,sai da taji sallama daga qofar falo sannan ta miqe tana sauke qafafunta qasa. "Anty ummee,ni banma dauki murya ba wallahi" "Ina zaki dauka kin tasa tv a gaba" ta fadi tana duqawa ta dauke nawwara daga qasa ta maidata saman kujera sannan ta zauna daga gefanta tana cewa "Yanzun da banzo ba a qasa zaki barta har tayi barcinta ta tashi" baki ta tabe,bacin ranta da ya dan lafa yana motsa mata "Hmmm,a qufule nake anty ummee,ubanta yaja mata,shi ya qunsan takaici" "Ke kam damuwarki da abbas bata qarewa,gashi dai baki rasa komai ba amma ko yaushe cikin complain?" "Na rasa ya zanyi dashi anty ummee,dan bada umarnin nan da mata kewa miji ni bansanshi ba" baki ta tabe tana jingina sosai da kujera "Ke kikaso hafsa" bata motsa daga wajen ba ta zayyanewa anty ummee din komai,itace wadda take bi a dakinsu,uwarsu daya ubansu daya,sai data gama tas sannan ta dubeta "A cikin banza ma ke banza ce wallahi hafsat,ke ko asiri kike fa saikin hada da kissa da kisisina yake ci maka yadda kakeso,ke dan makircin nan na mata ma ace baki iya ba?,ko da yake ko an doraki ma sauka kike" ta qarashe maganar tana yaada kanta gefe cike da takaicin 'yar uwartata. Matsowa tayi sosai kusa da ita "Zanyi wallahi anty ummeee" sai data qare mata kallo sannan ta zauna sosai tace da ita "Ki tattara kayanki ki bishi kaduna kamar yadda yakeso,yaran idan ta kama ko gida ko hannun hajiyarsa basai ki barsu ba?,bama mimi bace ita kadai?,idan kuka tafi can daga ke saishi,ba 'yan uwansa akusa ba 'yan sanya idanu,Allah ne kadai yasan nawa zaki tatsa daga jikinsa,masu aikin damarar nan fa ba qaramin iya soyayya sukayi ba,amma ke gaba daya komai naki a rikice?ki bishi ki kwantar da kai,dadin yadda kika faranta masa ma wallahi baisan sanda zai sauya miki motar ba babu wanda yaji ba wanda ya gani" Fuska ta bata,don ta dauka wata mafitar zata bata ba wannan ba,sai itama anty ummee din ta zuba mata idanu tana dubanta "Ba zakije ba kenan?" Cikin tsuke fuska tace "Ni anty ummee,kaduna fa wa na sani wa ya sanni?" "To ai shikenan saikiyita zama bauchi ki tsanana uwar da zaki tsinana" ta fada tana buga cinya. Shuru tayi na wasu sakanni tana nazari,yayin da anty ummee ke qarewa qawataccen falon nata kallo yadda ta barshi komai a zaune da duwawunsa,babu tsari bare kintsi "Shikenan anty ummee,an gwada aiki da shawarar taki,zanje" "Yadaifi miki" ta bata amsa sannan ta maido dubanta kanta "Yanzu kika tashi a barci ne wai?" Kai ta girgiza tana dubanta "A'ah,me kike gani?" "Bakiji bashi bashin da jikinki yakeyi ba?,sannan wannan uwar bolar da kika barwa falonki ta mece?" Shinshina jikinta ta soma yi,sannan ta bata fuska,don ita bataji komai ba "Ni ba abinda jikina yakeyi,hancinki ne dai,falo kuma wallahi yara ne suka bata su da ubansu kafin su fita,don jiya da daddare fes na shareshi kafin na kwanta,yanzu kuma ina shirin tashi na sake gyarawa kika shigo" "Allah ya sawwaqe" kawai tace da ita,tasan halinta ba yau ba ba jiya ba,koda ta tsaya gaya mata qarancin tsaftarta ma uzurin yara zata yita kawo mata,kamar ita tafi kowa haihuwa a duniya. Suna taba hira tana gyara falon har ta gama,ta shiga kitchen tana tunanin me zata dafa harda abbas din,don ba zata iya girki biyu ba,tayi yanzu tazo tayi musu na dare?,sai kawai ta dora.taliya da miya,suka wuce uwar dakan hafsat din anty ummee na sake jaddada mata muhimmancin binsa kadunan,tare da dabaru na kissa na yadda zata samu yadda takeso. Ita ta tayata suka hada kayanta dana yara,don tasan iya wannan sai ya zame mata aikin gabas,cikin kayan nata taga wasu night gown,tasan kudinsu saboda ta gansu wajen wata qawarta kwanaki da tayo order dinsu "Kai....wadannan nighty din fa?" "Sunyi kyau ne?" Ta amsata tana zuge qaramar jakar data zuba undies dinsu "Sosaima,ke bakisan kudinsu ba?" Baki ta tabe "Bana ce ba gaskiya,shi ya siyomin su kwanaki,ni kuma Allah ya gani bazan iya sanyasu ba,kamar waga kafira,shi yayita wani aiki kamar dan iska dan iska,ko kunyar yaranshi biyu baya ji" galala anty ummee ke kallon hafsat din,idan tayi wani abun kamar batayi karatu ba,ita yanzun just shekara ashirin da takwas zuwa da tara har tayi tsufan da bazatayi gyara ba?, Amma da yake itama kayan takeso sai bata bata shawarar komai ba,ta ninke abinta ta sanya a jaka,ita tasan darajarsu. Da ta tashi tafiya ta sake tambayar wasu designers turare da ya siyo mata,guda uku ne,guda biyu dubu ashirin da bibbiyu ya siyosu,guda daya dubu talatin,hakanan yake,mayen qamshi ne,shi yasa baya siyan banzan turare,ko su mimi zai siyawa turare baya siya musu na qaramin kudi,bata damu da su ba shi yasa.batasan daraja ko tsadarsu ba,tace ta dauka wanda takeso,ta kuwa dauke dan dubu talatin dana ashirin da biyun guda daya tayi tafiyarta,dama yawa yawan zuwanta gidan abinda ke kawota kenan,don ta qaru da 'yar uwarta,duk da tana bata shawarwari na gaskiya a wasu lokuttan,rashin daukan shawara ke damun hafsat din,data fara saita tattara ta zubar,tafi ganewa yawan qorafi da kai k'ara. *_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥 *_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥 *FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥 *JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA* *_'YAN BIYAR DIN NAN NE FA_* *_SARAKAN LABARUN_* *NISHADI* *CAKWAKIYA* *GWAGWARMAYA* *BARKWANCI* *TSANTSAR DARASIN RAYUWA* *TARE DA* *ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI* *SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!* *KIN SHIRYA MADAM?* *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA* *DAUD'AR GORA* Billynabdul *KI KULANI* Missxoxo *IDON NERA* Mamuhghee *RUMBUN K'AYA* hafsat rano *A RUBUCE TAKE* Huguma *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN* 0022419171 Maryam sani Access bank Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number 09033181070 *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU* 09166221261 *Yan NIJER 🇳🇪🇳🇪zaku tuntubi wannan number* +227 90 16 59 91 *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾 PAID BOOK 12/2/2023 Afuwan dan Allah banyi editing ba, idan kunga typing errors. Duk irin hauka da surutan da take zubawa, Aliyu baibi takanta ba yana jinta, ya shirya Tsaf cikin jeans and t-shirt Wanda sukayi masa masifar kyau, yana baza ƙamshi, ya ɗauki tickets ɗinsu ya saka cikin aljihun jeans ɗinsa, ya nufo ƙofar fuska ba wasa, yana takunsa anatse. Yana buɗe ƙofar suka haɗa idanu, ya sake tamƙe fuska yana kauda idanunsa daga kallonta, yana shirin tsallakata ya wuce,ta zabura ta miƙe cikin kuka tana cukuikuiye shi, tace. "Idan an isa akaini kwatano abarni ba Nigeria ba, Allah ya tsinan bazan yardaba kawai ka sakeni yanzun nan na kama gabana...." Ta faɗa cikin fitina da rikici mai ɗaga hankali, tana dukansa. Dariya ya yi yana manneta da ƙofar ɗakin. Rungumata ya yi yana rufe mata baki cikin taushin murya ƙasa-ƙasa yake faɗin. "Astagfirullah na yafe miki My zumaty kuma bazan sake ba, haka bazan kaiki Nigeria ba, Ni dake mutu ka raba Takalmin kaza." Ya faɗa yana sumbatar goshinta. Kuka take tana dukansa tare da faɗin. "Ni bana sonka Aliyu sai fa ka sakeni ko kai maye wallahi...." Finkiceta ya yi cikin ɓacin rai yajata ya wurgata saman kujera kafin ya yinƙuro yasa kai ya fice ya murza mata key ta waje ya tafi. Aguje ta miƙe tana faɗin. "Ni kakeson nakasawa sabida nace bana sonka? Toh wlh kaje ka dawo ina jiranka, Ni wlh bazan zauna mijin ƙanwata ba." Ta faɗa tana komawa ta zauna tana kuka dan taji ya rufeta ta wajen. Aliyu fitowa Alhj Ahmed da yake kiransa cikin mota ya shiga suka tafi. Wajen cira tickets suka tafi, aka masa canji zuwa Cotonou, Wanda jirgin sai zuwa dare zai tashi zuwa Cotonou. Daga can Aliyu pharmacy ya biya ya siyi wani magani...🐱 ★★★ *Nigeria* Tun safe su Auwal Jawad Hassan Hussaina su Mubina Anwar Yasmin, suka zo ganin little Aliyu, fafur yaƙi yarda dasu, sbd bai sansu ba haka suka ƙari zamansu bayan sun gaisa da Aalimah suka tafi. Jawad sai neman Aliyu yake awaya baya samunsa. Abie ma tun jiya yake nemansa awaya baya samunsa hankalinsa duk atashe. Aalimah kwance cikin ɗakinsu ta yi ƙarya ciwon kai, dan ta samu ta huta ita ɗaya, magani Baabah Bintu ta bata ta sha. Aliyu yana jikinta, yana zuba mata surutu, yana dariya sai turmusarta yake,. Aalimah taja hancinsa wanda baida maraba da JAANA ɗinta, tana zubar da hawaye, tausayin kanta take, sbd yadda takejin kishin mijinta, ta kuma san wacece Auntie Asmy bazata iya kishi da ita ba, tasha gabanta a komai. Cikin ƙarfafa zuciyarta tace. "Astagfirullah, yq ya Ubangiji Sarkin sammai da ƙasai ka bani ikon amsar ƙaddarata, na jure nayi tawakali na amshi ƙaddaramu auren miji ɗaya nida Auntie Asma'u, Allah ka bani juriyar ɓoye damuwata, haƙiƙa Auntie dasu Baabah sunfi ƙarfi komai awajena, sunmin halacci sun riƙe ba nuna banbanci sai ma nace sunfi sona akan sauran yaran anya idan sun gane ina kishin mijina ban butulce musu ba?' Ta faɗa tana share hawayen fuskarta tana rungume Aliyu da yake tambayarta. "Momy kukan me kikeyi? Kiyi shiru kinji" Aalimah batasan me yace ba, ta yi dai murmushin yaƙe tana sumbatar kumatunsa, tace. "I love You." Shima ya sumbaceta yace. "I love You Momy." Sukayi dariya suna rungume juna. Dai-dai lokacin Baabah Bintu da Ammie suka shigo da sallama, dan duba jikin nata. Aalimah ta amsa tana murmushi tana gyara zamanta da cewa"Kai sai son Jiki koh Aliyu?" Baabah Bintu tace. "Aalimah ya kan naki?" "Da sauƙi Baabah ina ƙoƙarin fitowa wajan Aliyu ya maƙaleni." Ammie da Yaren Mali tace. Aliyu taso muje kaci biscuits kabar Momy ta huta koh?" Da yake Ammie ce bai musaba ya miƙe yana dariya ya kama hannun Ammie suka fice. Aalimah cike da mamaki tace. "Baabah kinga baya ƙin Ammie ko me tace masa oho ya bita." Baabah Bintu ta zauna kusan Aalimah tana kamo hannunta tace. "Aalimah! Ina me ƙara baki haƙuri akan abinda ya faru..." Baki Alimah ta rufe mata da tafin hannunta, tace. "Wlh Baabah banajin daɗin haƙurin da kuke bani, hakan ɗazu yaya Murtala ya yi ta bani haƙuri wai shine ya matsa akayi auren ganin halin da Auntie Asma'u take ciki. Toh wa ya isa yaja da hukuncin ALLAH, wlh Ni ban riƙeku ba Baabah." Baabah Bintu ta rungumeta tana saka mata albarka. ★ Acan G.R.A Granny ta bugewa Abie hankali harda kuka, sai an nomo mata Aliyu ta waya idan kuma wani abun ne ya samesa a faɗa mata. Daƙyar ya samu ya lallaɓata sai fatar majina take. ★ Aliyu sai da sukayi ɗan yawo da Alhj Ahmed kafin ya dawo gida, bayan ya gama shirya mata tuggu ahanya yadda har su isa Cotonou bata wani kuzari bare ta yi masa masifar da ta saba. Zaune take a falon ƙafa ɗaya kan ɗaya tana hura hanci, ya shigo fuskarshi babu wasa, yana riƙe da leda ƙasa² ya yi sallama. Kallon ƙasa da sama ta masa ta kauda kanta tana amsa sallamar acikin zuciyarta. Tsabar neman magana ya ajiye ledar akan table cikin kakkausar murya yadda zai ƙufular da ita ta yi abinda yake son yace. "Malama karki kuskura ki shamin drinks ɗina, ban siyo da rabonki ba, tunda bakya ganina da daraja, masifa kika saka gaba, da tashn hankali." Ya faɗa yana zungurinta akai ya nufi Bedroom Yana danne dariyarsa, sabida ganin yadda ta harzuƙa tana zazzaro masa idanunta, amman batace komai ba. Yana shigewa ta buɗe ledar tana faɗin. "Sai an sha ɗin kayi abinda zakayi." Ta faɗa tana ɗaukan Apple ta fara ci ta miƙe ta nufi kitchen ta ɗauko cup ta buɗe drink ɗin ta cika cup ta shanye ta ƙara wani, sai da taji kamar cikin zai fashe tabar ɗan guntu, ta kama Apples ɗin duk ta saka musu haƙuri ta ɓatasu sauran drink ɗin ta juyeshi cikin cup ta barsa ta koma ta yi kwanciyarta, tana kallon Tv. Aliyu duk abinda take yana kallonta ya laɓe bayan ƙofar, dariya kawai yake ƙasa-ƙasa yadda bazata jisa ba. Sannu ahankali Asma'u ta dinga jin wata irin fitinanniyar kasala da bacci sai hammma take tana miƙa tana lumshe idanunta. Ganin hakan ya saka Aliyu fitowa falon. Daga nesa yace. "Kai-kai-kai! Waye me wannan ɓarnar haka?" Ya faɗa yana zama kusanta yana kallonta. Idanunta alumshe cikin wata irin murya kamar ƴar maye tace. "Nice me ka isa kayi? Ko zaka ramane?" Aliyu ya ƙyalƙyale da dariya yana kwantowa jikinta yana riƙe ƙugunta ya ɗago kanta da hannunsa ɗayan yana kallonta ƙasa-ƙasa yace. "Buɗe idanunki maras kunya yanzu dai dan kin isa kiyi tijarar, ɓarnarki ta ja miki ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya My Honey wife Aunt Asmy darling masoyiya ya dai? Zakiyi bacci ne?" Ya faɗa yana lasar wuyanta zuwa marabar ƙirjinta. So take ta tureshi ta kasa, tace. "Baby jikina ƙaiƙayi yake min bacci nakeji, Baby ka ciremin kasala wayyo ƙaiƙayi ko ina yake min" Ta faɗa cikin wata irin murya kamar ƴar maye, tana rungumesa tana hawaye, tana sakin nishi. Aliyu sai yaji matsakaicin tausayinta ya kamshi, ya shiga shafa jikinta yana sosa mata cikin wani irin salo, yana manna bakinsa akan kunnenta, anutse yace. I'm sorry my Asmy darling my wife ke ɗin ce Zuma sai da wuta, fitinarki ta yi yawa idan ba haka na miki bazaki bari mutafi lafiya ba." Ya faɗa yana cire mata kayan jikinta baki ɗaya yana bin jikinta da wata irin susa yana kissing nata anutse. Numfashi take saukewa cike da shagwaɓa ga mayen da take ciki ta fara miƙa tana kiransa. "Aliyu Babyna! Ina sonka zaka bani Babies? Ina son na haifama yara dayawa, dan Allah karka sakeni kaji Baby Baban Babies Nah kaba Aalimah haƙuri kace nima bansan lokacin da na kamu da matsanaiciyar ƙaunarka ba, tamin uzuri ba laifi na bane ta kamo so ta basa kashi kaji Babynah?" Aliyu yace. "Yaa Ilahi! WOW! Mah Asmy masoyiya zumata, irin wannan ƙauna, Alhamdulillah ai kuwa zanyi ta banka wannan magani a juice kiyi ta sambaɗo Wannan kalaman soyayyar masu neman su zautani, muahhhh my Asmy darling masoyiyata." Ya faɗa yana kallonta tana sauke numfashi ta yi bacci. Lisp ɗinta ya tsotsa kaɗan ya saki yana bin jikinta da wani irin fitinannan kallo yana shafata ahankali, ya cicciɓi abarsa ya shige Bedroom, ya sakata mata rigar bacci ya rungumeta yana sakin murmushi na zallar farin ciki... Har dare Asma'u suna shirin tafiya bata dawo hayyacinta ba sai yadda Aliyu ya yi da ita tana maƙale jikinsa tana zuba masa sambatu maye. Shi ya shiryata Tsaf cikin shirin tafiya kafin Alhj Ahmed ya iso ɗaukan su. Shima ya shirya ƙarfe tara da rabi suna Airport. Aliyu yama Alhj Ahmed godiya sosai da fatan alkhairi arayuwarsa da irin yadda ya karramasu ba kowa bane awannan zamanin zai maka irin wannan mutuntawar ba dangin iya bare na Baba. Asma'u tana jikin Aliyu a cikin jirgi, daƙyar Aliyu ya samu taci abinci da aka raba musu acikin jirgin, ta koma bacci tana masa sambatun akan kar ya maidata Nigeria zata zauna da shi. Aliyu murmushi kawai yake... Tsakiyar dare suka shigo garin Cotonou. Taxi Aliyu ya ɗauka har gida. Asma'u har yanzu bata saku ba, bacci take abunta, ajikinsa akan bed ɗinsa shima agajiye yake baccin ya ɗauke shi. ★ Washegari bayan ya yi sallar asuba ya takura Asma'u ta tashi dana yin sallah. A lokacin, ta fara sakuwa, sai dai batada ƙarfin jiki, batayi masa rashin mutunci ba, har tayi. Zaune take tana azkhar yunwa takeji kamar zataci babu,, cikin sanyin murya ya waigo tana kallonsa ashagwaɓe "Ni yinwa nakeji sosai." Aliyue zaune saman bed ya kunna wayarsa wadda ya kasheta tun shekaran jiya a Mali tunda layin ba yayi acan. Kallonta ya yi cike da ƙaunarta anutse yace. "Ok zo nan Mah Darling Asmy." Kafaɗa ta maƙale tana hararensa tace. "Bazan zo kawai ka tashi ka samomin abinda zanci, kuma azo amaidani ƙasata." Aliyu ya yi dialing number Mama Barira cikin ikon ALLAH tana fara ringing ta ɗaga tare da Sallama. Aliyu ya amsa yana gaisheta. "Mama ina kwana? Ya mutan gidan? Zanzo in Sha Allah anjima nida Asma'u." Daga can mama Barira tace. "Kai masha ALLAH naji daɗi toh sai kunzo." Katse kiran ya yi yana dialing number Abie. Bugu ɗaya Abie ya ɗaga daga can yana faɗin. "Haydar! Kana lafiya kuwa, yau kwana biyu ina nemanka ba dare ba rana, nida mahaifiyarka ga Umma ta tayar min da hankali sai rigima take harda kuka." Aliyu ya kwantar da murya ƙasa, yace. "Abie don Allah kayi haƙuri munje Mali ne neman Aalimah ashe sun taho Nigeria nima yau nake zauwa Asma'u batada lafiya ne bazata iya zuwaba..." Ya faɗa yana saukowa ya fice da sauri ganin ta miƙe ta nufosa tana masifa duk da bata kuzari. Key ya murzawa ƙofar ya nufi falo. Abie yace. "Subahanallahi Allah bata lafiya ya jikin nata? Alhamdulillah fa ga Aalimah da Aliyu ƙarami masha ALLAH, kayi ƙoƙari ka taho dan Allah yau ɗin tunda akwai me kula da Asma'un ko tana matsa ne?" Aliyu yace. "A'a da sauƙi Abie." "Ok toh kayi ƙoƙari yau ka taho yarinyar nan taban tausayi wlh, da gani ƙarfin hali takeyi, tana son ganinka kai da ƴar uwata tunda batada lfy ka barta kai ka taho ka duba matarka da ɗanka wanda komai naka bai bari ba." Aliyu cikin zallar farin cikin labarin mahaifinsa yace "Ok Abie in Sha Allah yau ina tafe." Hira sukayi sosai da mahaifinsa ya sauka downstairs, ya kaiwa Granny wayan, sukayi magana ya lallaɓata yace yau komin dare zai sauka Nigeria. Granny cikin jin daɗi tace. "Yawwa dan Allah kazo Allah ya.kawoka lafiya, ka gaishemin da Asma'u." Haka suka sha fira ya mata sallama ya su kayi sallama, ya kira MAAMAH, wacce take ɗakinta bata jima da idar da sallah ba. Ganin kiran Aliyu MAAMAH ta ɗaga tana faɗin. "Aliyu kana lafiya kuwa?" Aliyu yace. "Afuwan MAAMAH nayi tafiya ne, zuwa Mali yau in sha Allah zan taho Nigeria anjima zanje nayi booking din ticket, MAAMAH yasu Mubina?" MAAMAH tace. "Kowa lafiya lau Aliyu Alhamdulillah tunda kana lafiya, toh me kaje yi Mali?" Aliyu bai ɓoye mata komai ba ya faɗa. Tace. "Alhamdulillah! Kaga yanzu sai ka saketa tunda ta dawo hayyacinta, kuma matarka ta bayyana harda tsarabar zankaɗeɗan saurayi." Aliyu yace. "MAAMAH idan nazo zamuyi magana bari na sha tea cikina sai murɗawa yake..." Ahaka ya samu sukayi sallama ya katse kiran, yana shafa kansa. Ƙofar ya buɗe tana tsaye bakin ƙofar ta faɗa jikinsa tana sakin kuka tace. "Aliyu ka cuceni me ka bani jikina ba ƙwari haka? Aliyu yinwa nakeji." Ɗaukanta ya yi yana faɗin. "I'm sorry my Zuman Haydar muje na dafa miki tea kisha please bari kukan zakije Nigeria uhmm?" Asma'u tana kwatar da kanta ƙirjinsa ta ɗaga kanta... Da kasan ya dafa mata tea ya soya mata ƙwai, tana gama breakfast sai bacci ya hana bacci ta hanyar cire mata kayan jikinta, ya shige bathroom da ita. Wanka sukayi tana cikin jikinsa irin abubuwan da yake mata ya sakata wartsakewa ta biye masa tana amsar saƙon nasa... 11 am, ya lallaɓata suka tafi gidansu mama Barira, Amma sai da ya biya ya yi booking ticket ɗinsa. Zazzaune suke Asma'u tana kallon Mama Barira ita dai bata santaba sun dai gaisa. Aliyu yace. "Mama Asma'u fa ta warke kina ganin tana nuna miki rashin sani." Mama Barira tace. "Abinda zan faɗa kenan Aliyu masha Allah naji daɗi sosai, wlh Allah ya kiyaye gaba." Aliyu yace. "Mama! Daman zanyi tafiyane inason ki koma can gida ku zauna kafin nazo mu wuce Nigeria." Asma'u ta ɗago tana kallonsa tace. "Wlh bazan zauna ba kawai malam kaini ƙasata...." Mama tace. "Haba! Asma'u! Babu kyau miji yana magana kina maida masa, kefa ba yarinya bace. Aliyu kuje zanzo anjima da yaushe zaka tafin?" Aliyu yace. "Anjima ƙarfe biyar jirgin zai tashi." Mama tace. "Ok zanzo anjima bayan sallar azuhur, Asma'u! Inada fira dake dayawa idan nazo amman sai Aliyun ya tafi." Asma'u kamar zata fashe da kuka tace. "Tom Mama." Aliyu yaji daɗi sosai ya kama hannayenta ta miƙe yace. mun tafi sai kinzo." Mama Barira tace. "Allah ya muku Albarka..." Ko ahanya Asma'u masifa ta kama masa tana faɗin. "Akan me zaka min haka kuma ina ne ma zakaje ka barni?" Murmushi ya saki yana murza tafin hannunta yace. "Ghana zanje ganin wata mota na dawo, sai mutafi Nigeria Mah Asmy masoyiya zumata ki rage rikici kuma dan Allah ki nutsu ki saurari abinda Mama zata faɗa miki." Baki ta zumɓuro gaba batayi magana ba. BOWOOODEE jiya iyau duk yadda ake mata alluran bacci, bai hanaba ta sake jirɗe kayar, wanda ayanzu ya kai wajen baya ɗoruwa, cikin ƴan kwanakin da tayi asibitin har likitocin sun ce sun gaji a canza mata asibiti, bazasu iyaba, sabida kafar ta fara ruɓewa. Koda sukazo gida ganin zata fara masa iskanci ya lallaɓata ya banka mata maganin kasala da bacci, ya samu ya yi romantic ɗinta mai wuyar faɗa har yakai ya kusanceta ta gama gigice masa tana masa kuka tare da surutai sosai Aliyu ya kashe arna yana mata kalaman soyayya tare da sambatu. Koda suka nutsu Asma'u ta yi bacci daƙyar ya samu ya mata wanka Tsarki ya saka mata rigar bacci ya kwantar da ita, ya shiga shirya kayansa bayan ya kammala ya cire sim ɗinsa ɗaya dan barmata wayan da zai kirata, sai ya tuna akwai fa matsala gwara ya kirata awayan Mama Barira suna magana. Kamar yadda mama Barira tace bayan sallar azuhur zata zo ƙarfe uku tazo Asma'u na bacci sun taɓa hira da Aliyu ya zayyane mata komai akan tafiyar da zaiyi can Nigeria. Mama tace. "Tabbas kayi tunani hakan ya yi kafin ka dawo in sha Allah komai ya daidaita tsakaninku kasan dabarar da zan shiryama?" Aliyu yace. "A'a mama sai kin faɗa." Dariya ta yi tace. "Kawo kunnenka ɗana." Aliyu ya beƙa mata kunnensa ta masa magana. "Idanu ya zaro yana dariya yace. "Kai mama amman na gode fa sosai idan haka ta faru bansan irin farin cikin da zanyi ba..." Bayan sun gama shirya komai, ya miƙe. Ɗakin ya shiga ya ajiye mata kuɗi masu yawa ya kwanta ya rungumeta ya kissing bakinta kamar zai cinye mata baki. Sukayi sallama da mama Barira ya bata kuɗaɗe masu yawa, yace sai sunyi waya, har wajen mota ta rakashi kafin ta dawo ciki ta zauna tana jiran tashin Asma'u... Isma'il ya kai Aliyu airport ya dawo da motar gida. Ƙarfe biyar da rabi Jirginsu Aliyu ya ɗaga zuwa Nigeria.... _ƘADDARAMU CE AUREN MIJI ƊAYA Mallakin Rahma Oum Farisah NE...🖊️_ Littafin kuɗi ne *09030159301* *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: huguma* Page 16 Tunda ya fita yaso miqa mimi wajen hajiya sai ya wuce,idan ya dawo ya dauketa su wuce gida,amma tun baiyi nisa ba ogansa yayi kiransa,yayi shigowar ba zata yankinsu,don haka ya wuce da ita,sai ya ajjiyeta wajen rose abokiyar aikinsu ce,babbar macace haka,tana da matuqar kirki da son yara,sai yamma sosai sannan suka gama,ya dauketa suka yo gidan hajiyan. A qofar gida yayi parking,ya buda murfin motar ya fita ya zagaya ya fiddo mimi,yana riqe da hannunta suna shiga cikin gidan,tana basu labarin rose da irin abubuwan data siya mata,yana saurarenta yana murmushi,yaransa sune ke debe masa mafi yawa daga damuwae hafsat. Dai dai lokacin da widad ke daura alwala bakin famfon dake farfajiyar gidan,ta gama wanke qafafuwanta kenan tana gyara daurin dankwalinta gizo gizo ya taho,fallatsin ruwa yasa ya qara gudu,take ta rude,sai taga kamar kanta zaiyo,wannan yasa ta saki qara sannan kuma ta buga tsalle tana komawa gefe,bata dora ko ina ba sai a gabansa ba tare data lura da waye ke tsaye a wajen ba,saboda hankalinta gaba daya yana kan gizo gizon. Baya yaja yana bata fuska gami da dubanta,baya iya ganin fuskarta,sai sassalkar sumarta data yiwa kanta rumfa,sanadin dankwalinta da ya zame yake kuma riqe a hannunta tana ci gaba da kallon gizo gizon "Allah yasa bai tabani ba" yaji ta fadi tana ci gaba da maida daurin dankwalinta,wannan ya alamta masa ma batasan me tayi ba,sai ya kama hannun mimi suka shige cikin falo. "Yau kice a gidan kishiyata,ko batan kai kikayi?" Hajiya ta fada cikin dariya,yayin da su nujood dake falon suka fara gaidashi,yana amsa musu wayarsa ta dauki tsuwwa,sai ya fidda wayar yana dubawa,kawun sa ne,wanda shima gidansa ke jikin gidan kawu hassan,gida daya ne daa gaba daya,bayan rasuwar mahaifinsu aka raba gado aka fitarwa da kowa shiyyarsa ya gyara ya maidata gida me zaman kansa. Hajiya dake faman tsokanar mimi ya kalla "Hajiya bari naje,kawu imrana ke nemana,yace yaga motata a waje" "To ba laifi saika dawo" sai ya juya ya fice. A harabar gidan ya hangeta waje daya ta shimfida dankwalinta tana sallah,ya dauke kansa a hankali ya doshi gate din,ina hajiya ta samo wannan?,duka sauran yaran muhsin ne ya sani,amma wannan mai tsalle tsallen fa?. Dan tsaki yaja yana ture tunanin gefe guda ya doshi qofar gidan kawu imrana. Koda ta gama sallarta tattarawa tayi ta shige ciki,don ita ko sau daya ba wanda ta gani,tun daga shigowar tasa har fitarsa ta yanzun,bata jima da shiga ba hajjaa ta iso ta hada kansu suka wuce gida tana sake yima hajiya godiya da ban gajiya. Sai bayan magariba ya dawo,yaci abincinsa sukayi hira da hajiyan,sanda ya tasamma tafiya mimi tayi bacci,don haka ya barta a gidan "Babu matsala abbas kuwa idan ka barta?" Hajiyan ta tambaya a fakaice,saboda tasan halin hafsat,tana da tsananin nuna son 'ya'ya,bata iya boyewa gaban kowa,idan ka gansu sun kwana wani guri to tare da ita ne. Wani abu yaji ya tsaya mas a wuya,jikinsa yayi sanyi,mahaifiyarsa ke shakku da kokwanton kwanan diyar da shi ua haifeta a hannunta?,tabbas da saake,akwai kuma gyara "Ba komai hajiya,idanma kina buqatar wasu qarin kwanakin sai na debo miki kayanta" murmushi ta saki tana shafa kan mimin "A'ah,kwana dayan ma yayi alhmdlh" boyayyar ajiyar zuciya ya sauke,sukayi sallama ya fita. Yana tuqi a hanya amma tunani ne fal kwanyarsa,qarar wayarsa ce ta taimaka masa ta katse masa tunanin,ya duba mai kiran,sai ya dan saki miskilin murmushin nan nasa,ya miqa hannu ya daga "Allah ya taimakeka ranka ya dade,tuba nake,kwana biyu an zubda ni,naji tsoron kada hakan ya zama silar watsewar zumunci nace bari na kiraka" "Wallahi ko yau naso shiga na gaida umma,kawu ma'aruf ne ya tsaidani,sai kuma na sha'afa,ta yaya zan manta da kai,ayyuka ne suka taru sukayimin yawa,that's why na ajjiyema governor ADC dinsa saboda na ragewa kaina wasun sabgogin,so kuma maimakon su barni na huta,wallahi kaga sun sake cillani KD" "Naji labari,ina nan ina tunanin me yasa ka ajjiye appointment din?,bayan kana da sauran lokaci?" Kansa ya shafa da hannunsa "Mu hadu kawai gobe idan kana gari" "Ina nan,babu damuwa zan sameka gida" "To sai na ganka" sukayi sallama ya ajjiye wayar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa,hadi da sanya idanunsa kan hanya yana duba shagon dake masa aski,ya samu suna nan don haka ya gangara yayi parking ya kashe motar ya fito. Babban kanti ne na matasa masu aji,masu j da jini a jika wadanda duniyar ke garawa,suna qaruwa ga jikinsa sosai,sun kuma san matsayinsa,don haka tarbar musamman sukayi masa,ya zauna yana duba jaridar da suke ajewa kafin a gamawa wanda ka samu. Goma na dare ya baro wajen,ya tsaya ya siya fruit ya wuce gida,don yaga kaman nasun ya qare,to amma babu lallai ta gaya masa babu ya sanya a kawo kamar yadda aka saba,qila sai ya tashi amfani dashi sannan tace masa babun. Kulle ko ina yayi sannan ya wuce sashenta don ya duba lafiyarsu kamar yadda ya saba,ko me sukayi da ita baya fasa wannan,ko bai shiga don ita ba zai shiga don yaransa. Abun mamaki yau zaune ya sameta a falon,saidai fuskarta gana daya babu annuri,yau din ba laifi,wani lace ne a jikinta peach color dinkin riga da zani,fuskarta tas babu digon komai,sai daurin ture kaga tsiya da tayi. Tana daga zaunen tayi masa sannu da zuwa,ya amsa mata yana wucewa dakinsu mimi,yaga nawwara sannan ya fito,sai ta miqe tana cewa "Ina kaje wai?,sanda ka shigo gidan nan fa goma ta wuce" hannayensa zube a aljihun wandonsa ya waiwayo ya zube mata manyan idanunsa yana kallonta,a nutse ya buda baki "Ina wajen hajiya,daga nan na wuce aski" ya bata amsa yana kafeta da kallo me alamta sai kuma me?,kasa jurar idanuwan nasa tayi,sai ta kauda kanta,cikin salo na mita tace "Amma yanzu dai tsakani da Allah duk inda kaga dama kake zuwa,kama daina gayamin kana waje kaza" hannunsa ya fidda daga aljihunsa ya juya kawai yaci gaba da tafiya ba tare daya tanka mata ba "Ina mimi?" Ta fada tans leqe leqe,don sai a sannan hankalinta ya bata ba tare suka shigo ba "Tana wajen hajiya,zata kwana can" wani abune yayi mata tsaye a maqoshi,har ta bude baki zatayi magana sai kuma ta hadiye data tuna da maganganun anty ummee,ranta a bace amma tayi qoqarin rage kaifin bacin ran nata daga samsn fuskarta ta sake cewa dashi "Ga abincinka" ya riga ya qoshi sosai,amma yana cewa bazaici din ba sabuwar magana zata balle da ita,abinda bai buqata "Me kika dafa?" "Tuwon shinkafa ne" kai ya jinjina,ba kasafai tuwon shinkafarta ke shiga ba,koda bata jima da gamashi ba kana gutsura yana wargajewa,ga uban gaari da zaka yita cin karo dashi a ciki wanda ta d'aure tuwon "Babu wani abun sai shi?" Sai a sannan ta tuna ta yiwa anty ummee dafadukan taliya,wadda har shi ta dafa amma anty ummee din tace ta daure ta canza masa abincin da tasan yafi so,hakan zai sake sassauto dashi "Sai jallop din taliya" kai ya jinjina,duka babu wanda zai iya ci,sai yace da ita "Hadomin black tea kawai,ki saka kayan qamshi please sosai a ciki" "Tom" ta amsa takaici na cikata,baisan tana yi ba ya sanya kai ya fice,saita daga kai tana kallon agogo,takaici goma da shirin,ta zauna ta wahala tayi masa tuwon amma ya watsa mata qasa a ido,ita anty ummee idan tana bata wasu shawarwarin rashun sanin halin abbas dinne yasa take gaya matan,sannan yanzun qarfe goma harda kusan rabi a sanya mutum wani shig kitchen,ko uwarta bata taba bata wannan aikin ba,tana qananun motoci haka ta shige kitchen din,rabi da rabin hankalinta yana kan mimi dake wajen hajiyar,taja tsaki yafi a qirga,wai duka duka nawa mimin take da tsohuwar zata nace sai ta kwana wajenta(ni kuwa nace uhmmm,sai kace ke din wata uwar kike iya musu). Saman tray ta kammala komai ta wuce sassanshi dashi,sanda ta shiga bedroom din taji motsin ruwa a toilet,da alama wanka yakeyi kenan,sai ta dora masa saman madubi tana tabe baki,shi mutum Allahn da yayishi bashi da wani aiki saina wanka kamar kwado?,da wannan tunanin ta koma nata sassan don ta kashe wutar ta kuma dauko nawwara,don a nan yau tayi niyyar kwana. Nawwaran kawai ta dauko,wata zuciyar na cewa ta dauko turare da night gown amma taji ba zata iya ba,ta rufe sassan ta koma nashi. Har sanda ta koma din bai fito ba,sai ta kwantar da yarinyar saman gadon,ta zauna saman sofa bed tana danna wayar ta. Ringing wayarsa dake saman madubi ta fara,saita miqe da hanzari kai kace ita ake kira,haka dabi'arta take,duk wanda zai kira saita duba waye idan baya kusa da wayar,idan kuwa yana kusa kunnuwanta gaba daya tafiya suke ga wayar,sai ta tantance me yakeyi kafin taci gaba da harkarta,ta nufi wayar tana duba me kiran kamar yadda ta saba,sai taga sunan rose. *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 17 ____________________________ *_KAMSHI!_* *_KAMSHI_* *_KAMSHI_* *TABBAS K'AMSHI RAHAMA NE. INA MASU NEMAN INDA ZASU SAYI TURARUKAN WUTA MASU KAMA GIDAH! DA TURAREN KAYA, TURAREN TSGUNNO, TURAREN WANKA DANA WANKI DA JIKI?* _KAI BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA TURAREN KHUMRAH KALA KALA DA KULACCAMS NA KECE RAINI._ _AROOS_SCENTS_ _AROOS_SCENTS_ _AROOS_SCENTS_ _KUNJI SUNAN KO? *AROOS_SCENTS*_ _*AROOS SCENTS* SUNA GARIN *KADUNA* SUNA KUMA TURA KAYAN SU A FADIN NAJERIYA DA KETARE_ _LAMBAR WHATSAPP DIN SU :07067786384_ _INSTAGRAM : aroos _scents_ _SCENT HEAVEN😍SMELL RICH! LEAVE DEM WONDER WHAT YIU USED…😍A SCENT LIKE NO OTHER. SCENT THAT WARDS AWAY SMELLS_ _KYAU! INGANCHI DA KAMSHI MAI SANYAYA ZUCIYA SAI KAYAN TURAREN_ *aroos scents* ____________________________ "Rose?" Ta maimaita sunan da qarfi tana fidda idanu,abu na farko da zuciyarta ta sawwara mata ire iren sunayen soyayya ne da namiji ke sanyawa masoyiyarsa mace,take duk wani jini dake jikinta ya fara tafasa,ta fara fidda huci daga bakinta,mugun kishinta nan ya motsa,ta warfci wayar ta daga ta kara a kunnenta. Sallamar da akayi da kuma muryar mace ya tunzurata,bata jira komai ba ta fara zunduma mata ashar da zagi "Shegiya karuwa,riqeshin da kikayi yau duka bai isheki ba,saikin biyoshi da kira yana cikin iyalinsa?,to wallahi billahillazi abbas yafi qarfinki,nawa ne ni kadai,ba wata mace data isa ta rabeshi na bart......." Bata qarasa ba taji an warce wayar daga hannunta,tabi inda taji an fusge wayar da kallo bala'i yana cinta,don bata gama fadar tarin tulin qazaman miyagun kalmomin dake bakinta ba,sai taga abbas ne,daure da towel yana duba wanda yayi kiran nasa,tun yana bandaki ya fara juyo sautin muryarta,baisan da waye take wannan hayagagar ba gashi dare ya fara yi,sai daya fito ya fuskanci a waya ne,wayarma kuma tasa. Already an katse kiran daga can,sai yabi kiran yana sake kara wayar a kunnensa,idanuwansa da suka hautsine saboda baqinciki suna kan fuskar hafsat dake huci,jin alamun yabi kiran sai ta fara matsowa "Kiranta ma ka sakeyi,kuma a gabana?,wal......" Mugun kallon da ya watsa mata yasa ta danyi laqwas tana dubansa shaidan na sake ingizata. Murya a sanyaye rose tayi sallama kafin yace komai ta rigashi "Sorry sir,na kiraka da dare ko?,a baiwa madam haquri" "No,kada ki damu,wani abunne ya faru?" Cikin gurbatacciyar hausarta ta fara masa bayani "Eh....dazun da kuna meeting mimi tayi bacci a office ta yar da dan kunnenta ne,dana duba kuma naga kaman gold ne,so don kada ayita nema hankali ya tashi shi yasa nace bari nayi maka magana" ajiyar zuciya ya sauke yana qoqarin cooling temper dinsa "Is okay,ba damuwa,ki aje wajenki,idan na shigo gobe zan karba,idan ban shigo ba zansa ko samuel ki bawa sai ya kawo" "Okay sir" "Sorry rose,am sorry" "No sir,babu komai fa,nasan bata ganeni bane" "Good night" ya fada yana datse wayar,ya cillata saman gadonsa,sannan ya waiwayo gareta. Bacin ran data gani cikin idanunsa ya sake sanya jikinta yin laushi,bayan ta gane wace rose din "Indai rashin hankali da rashin nutsuwa zaki saka a gaban hankalinki zakita aikata abinda zai kaiki ga nadama mara amfani,tsabar banzan kishinki yasa idanunki sun rufe ki kasa gane wace tayi kiran,rose dince baki sani ba?,kiyi a hankali dani ki fita idanuna hafsat,idan kika kaini bango zan baki mamaki wallahi" can qasan ranta taja tsaki,ya jima yana fadin zai bata mamaki,wanne mamaki kenan,amma a saman fuskarta saita yamutsa fuska tana nuna rashin jin dadi "Ai kasan bansan ita bace,inda na sani ai bazanyi mata haka ba,kuma itama ta yaya zata kira.mutum da aurensa a irin wannan lokaci?" "Bakiji dalilin da yasa ta kira bane?" Ya fada a tsawace ransa na sake baci,har abada kenan ita ba zata gane tayi laifi ba saita kawo nata uzurin? "Ina jaddada miki ki shiga hankalinki,bani da lokacin kule kulen mata,amma idan naso ke baki isa ki hanani ko ki tsaidani ba" ya fada yana nunata da yatsa. Maganar ta doketa itama,to me yake nufi?,taso hasala amma sai ta bagarar,tasan ya fada ne kawai don ya tunzurata ya bata haushi itama,tafi kowa sanin waye abbas din,bata da wannan damuwar don ya fada. Yadda ya banzatar da ita yana shiryawa taji duk ta takura,saita taka a hankali ta isa inda yake tsaye,ta rungume faffadan bayansa da yake shirin lullubewa da riga "Kayi haquri don Allah,kuma na shirya zan bika kadunan" maganar tata tazo masa a bazata,wannan yayi nasarar saukar da fushinsa cikin qasa da second biyar,ya ajjiye rigar hannun nasa,ya waiwayo ya kama hannyenta ya zaunar da ita gefan gadon sannan shima ya zauna. Cikin qwayar idanunta ya sanya nashi sannan ya fara mata magana a tausashe "Bansan me yasa kika kasa fahimatata ba har yanzu,tsahon shekara biyar cikin ta shida,bani da burin da ya wuce naga gidana da iyalina cikin walwala fahimta da kuma qaunar juna,wannan rayuwar ba itace mafarkina ba a rayuwar aure na,inason gidana ya zama very romantic place,matata ta zama tafi kowacce mace iya soyayya tsafta tattali da iya kula dani,wannan shine nawa qarfin gwiwar da zai bani damar tafi da ayyukana yadda ya dace,ya kuma qara kusancinmu,ban takuraki zuwa kaduna saboda radin kaina ba,nayi hakanne saboda na jawo kusanci a tsakaninmu,kusancin da zai sake haifar da sabuwar soyayya da shaquwa tsakanina dake,ni abbas babu wata mace a gaba a yanzu,duk sanda kuma kikaga wata mace ta shiga rayuwata ba shakka gazawarki ne,daga gareki ne,na baki wannan satar amsar,ruwanki ki tare ko ina kiyi gadin qofar,ruwanki ki bada dama a shiga,amma kiyi qoqari mu zauna lafiya" a daren dai anyi abun arziqi,duk da daurewa kawai takeyi,abubuwa biyu ne sukayi mata tsaye a rai,maganarsa ta qarshe da kuma taraddadin barin bauchi ta koma rayuwar kaduna. A dukka hasashenta bata ga wata qofa da ta baiwa wata mace ta shiga rayuwarsa ba,tana kishinsa irin kishin dake matsewa kowacce mace qofar shiga rayuwar mijin wata,tana kaffa kaffa da shigarsa da fitarsa,a gida gwagwadon abinda zata iya tana masa,saidai shi da baya gani ma,amma tana takura a abubuwa da yawa duk don sabodashi,batasan kuma me ya rage ba,me yakeso kuma?. _wannan kenan_ Kwanaki biyu suka qara suka gama shirinsu,har zuwa lokacin yana mamakin abinda ya sauya mata ra'ayin binsa kadunan,saidai bai matsa da sai ya sani ba,tunda zurfafa binciken a wadansu lokuttan ba alkhairi yake haifarwa ba. Ana gobe zasu tafi ya sanyata ta shirya don suje su yiwa hajiya sallama,daga nan kuma ya sauketa a gidansu,tana ta qoqarin danne zuciyarta ne,da kuma bin dukka abinda yakeso,saboda bataso ta bata hanyar data fara sharewa kanta,don antyn ummee tana ta jan kunnenta kan sai tayi juriya,kuma saita kula,don haka ta shirya ta bishi. Hannu bibbiyu hajiyan ta karbeta kamar yadda ta saba,cikin kirki da karamcin nan nata,ba laifi hafsat din kadaran kadaham itama,har suka gama gaisawar suka taba hira sama sama,saita miqe tana duba agogo gami da kallonsa "Inaga ya kamata ka saukeni a gidan,lokacin yana tafiya" kansa ya dauke daga kan jaridar da yake dubawa ya kalleta,har ya buda baki zaiyi magana hajiyan ta rigashi "Gaskiya kam,kuma sallama zakuyi ya kamata ace kinje da wuri don ki samu isashen lokaci,tashi ka sauketa abbas" baice uffan ba,saboda maganar hajiya gaba take da maganar kowa a fadin duniya,banda haka xamanta a gidan yayi kadan sosai,duka duka ko awa guda bata rufa ba,sai ya ajjiye jaridar ya miqe yana daukan key din motar sa ya fice,ta yiwa hajiya sallama,ita kuma tasa muneera ta bita da kayan amfanin kitchen data tanadar musu,kamar su kuka kubewa daddawa kanwa da yaji da sauransu,saboda tasan abbas din ma'abocin son tuwo ne,a halayya kuma irin ta hafsat din babu lallai ta tsaya tunanin tanadarsu,ta bisu da addu'a suka lafiya,qwaqwalwarta fal mamakin yadda hafsat din ta sauya ra'ayi,duk da bata tsaya tambayar abbas din ba. *********** Gab da sallar magariba hajjaa ta iso gidan hajiyan,cike da gajiya da kuma farincikin gama cooking classe din da sukayi na kwanaki biyar,wanda dai dai yake da na kwanaki sittin a wata makarantar,ita kanta tasan ta qaru over da abubuwa masu yawa. Tana shiga ta miqawa nujood jakarta ta daura alwala kawai sannan ta shige falon hajiyan,ta zauna suka gaisa hajiyan tayi mata sannu,sannan ta kira muneera kan ta zubo abincin dare suci kafin su wuce "Hajiya da kin barsu,yauma kafin na fito sai da nayi girki" "Me yasa kike nuna wa gidan nan kamar ba gidanku bane hadiyya?,kinga muneera zubo,idan ba zata ci ba yaran zasu ci,xakuci ai ko widad?" Tayi tambayar tana kallon widad,wadda keta faman hada kayansu a jaka tana kammalewa. Murmushi ta saki tana sadda kanta qasa,ba tare data amsawa hajiyan ba "Au,babarki zaki goyawa baya kenan,sai faman hada kaya kike,kamar dama kin gaji da zuwa gidanmu " wannan karon har sai da haqoranta suka fito tana dariya cike da kunya "Ba haka bane hajiya,muna ta saki aiki fa kwama biyar din nan,kema zaki huta" maganar yarinyar saita burgeta,ta kuma sake saka mata qaunarta a zuciyarta,haka kawai cikin kwanakin taji yarinyar ta kwanta mata,tana kuma burgeta,saboda taga bambancin dabi'a tsakaninta da sauran yara,sau tari takan zauna nan kusa da hajiyan suyita hira abinsu,widad din najin hajiya kamar ummunta,idan tana tare da ita sai taji kamar ummu,tana debe mata kewarta sosai. "Ni ai ban gaji da ganinku ba widad" "To mu zauna hajiya?" Ta tambayeta cike da quruciya,murmushi hajiyan ta sake,ta waiwaya tana duban hajjaa dai dai sanda ta sallame daga sallar "nikam da zaku bani widad da nayi murna na kuma gode muku" dariya hajjaa ta saki,ba tare daga fahimci abinda hajiya ke nufi ba,ta zare hijabinta tana cewa "Widad hajiya?,wannan mara sabo din da rashin sakewa da mutane?,idan muka baki widad ai mun gayyatowa kanmu ummu,takanas zata tahi bauchi ta dauke kayarta,dama 'yar aro ce" kai hajiya ta kada "Ni ba aro nakeso a bani ita ba,inaso a bani ita na baiwa abbas dina,kinga shikenan ta zama diyata babu zancan aro kuma" a yadda hajiyan tayi maganar yasa hajjaa maido hankalinta jikinta,ta kalli fuskar hajiyan da kyau,sai taga gaskiya baro baro kwance saman fuskarta,kalamanta sunyi kama da kalaman da suke fita daga can qasan zuciya,babu alamun wasa ko kakaci a ciki. Daurewa hajjaa tayi tayi murmushi,don zancan gaba daya sanyayar mata da jiki yayi,abbas hajiya ke magana,dan gayun matashin nan, mahaukacin damarar nan da kwanan nan aka qara masa rank?,abbas din dake da mata da yara biyu?,,abbas fa "To ai hajiya idan kinaso sai a bakin ai" "So kai,saboda inaso dinne ma na sako zancan,amma dai zan sake tuntubarki,ki shaidawa muhsin din" "To hajiya ba matsala" ta fada tana murmushi,zuciyarta na bata da wasa hajiyan tayi maganar,saita maida dubanta ga widad wadda tuni ta matsa gaba suna magana da nujood,don haka batasan ma wainar da ake toyawa ba. Sanda suka tashi tafiyar kayan ciye ciye ta hada musu da yawa a leda,hajiyan 'yar gatan tsohuwa ce,babu abinda ta rasa a gidanta,wannan ya sanya babu abinda zakaje baka samu ba a gidan. *BAYAN SATI DAYA* Tsaye take hadiyya take cikin kitchen din tana hadawa uncle muhsin abincinsa,gefe daya yaranne gaba daya sun cika mata kunne,hayaniya suketa yi suna tsokanar widad,wadda gaba daya cikin satin ta fara birkice musu,tunda tayi waya da ummun ta gaba daya hankalinta ya karkata zuwa komawa gida "Ya isa don Allah kuyi mana shuru" waiwaya tayi ga widad "Zan gayawa uncle dinki kada ki damu,zai kaiki kiga ummun da kansa indai free yake bashi da aiki" kai ta gyada tana danjin relief a ranta,a kwanakin nan ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta gaban ummun,bata taba zaton akwai abinda zai kawo rabuwarsu haka na tsahon lokaci ba,tama yi qoqari,don ko kwana guda batayi gidan kowa indai ba tare da ita ba,sai gashi yau ta doshi wata kusan guda cur. Sanda hajjaa ta isa yana amsa waya ne,saita zuba masa komai ta kuma jera a gabansa,tana niyyar tashi don ta koma kitchen din ta sallami yaran yayi mata nuni da hannu kan ta zauna,saita koma ta zauna din,ya kammala wayarsa ya kashe yana dubanta "Wanne saqo hajiyan abbas ya baki baki gayamin ba?" Cikin mamaki don ita sam ta ajjiye wannan batun tace "Saqo kuma?,anya kuwa?" "Gashi yanzun ta kirani tana tambayata,tace idan kin kammala gayamin din zata sake kirana" sai a sannan hankalinta yakai,tadan dafe kanta tana fadin "Ya salam,wallahi sai da kazo da maganar na tuna" kansa ya girgiza "Bai kuma.kamata ba,hajiya kamar uwa take a wajenmu gaba daya" "Ba haka bane abba,zancan ne naji kamar zolaya take yi,hankali na bai kama ba" ta fada tana kada kai "Wanne irin zance ne haka?" Uncle muhsin da ya fara cin abincinsa ya fada yana kallonta "Widad takeso a basu ta baiwa abbas aurenta" *_AREWABOOKS: Huguma_* *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:huguma* Page 18 Shi kansa zancan yazo masa a bazata,sai ya ajjiye spoon din hannunsa yana duban hajjaa "Abbas....abbas nawa fa" kai ta gyada "Eh shi" kamar me jiran hajjaa ta tabbatar masa da batun sai ga kiran hajiya ya sake shigowa wayarsa,ya kalli wayar na wasu sakanni zuciyarsa na gaya masa da gaske hajiyan take,tunda har ta kasa sakat saita samu tabbacin isar saqon kunnensa,ya dauka wayar a nutse ya kara a kunnensa "Ina fata saqon nawa ya riskeka?" Kai ya gyada kamar tana gabansa "Eh hajiya,yanzun take isarmin dashi" "To alhamdulillah" ta fadi tana sauraren ji daga gareshi "Amma hajiya....wani hanzari ba gudu ba,kina ganin babu matsala daga wajen shi abbas din?" Yayi tambayar saboda sanin halin abokin nasa,sun jima a tare tun zuwanshi bauchi,duk da cewa ya girmewa abbas din,amma suna tare dashi,don itama dama abota ba sai da sa'anka ba,takan iya zuwa ta kowacce fuska,Itama hajiyan kai ta kada kamar yana wajen "Bani da haufi akan abbas ko kadan,bamu ita din shine mai wuyar" sosai hajiyan ta aza masa nauyin da bazai iya kufcewa ba,tana masa kallon mazaunin uba a wajen widad,tasan kuma ya isa ya zartar da hukunci a kanta shi yasa ta nemeshi kai tsaye,uwa uba kuma abbas din wani irin mutum ne mai kima da daraja a wajensa,yafi kowa sanin irin qaunar da yakema mahaifiyarsa,kamar yadda ta dauki shi shima a mazaunin d'a,bai kyautu ya dubi tsabar qwayar idanunta yace mata bazasu bada auren widad ga abbas din da yana sahun farko farko na wadanda zasu bada shaidar kyawun hali da nagartarsa,bayan gajeran nazarin da bai wuce shurun sauraren hajiyar ba ya amsa mata "Hajiya ai abbas nawa ne,babu damuwa,an bashi widad,zan kuma sanar da can gida in sha Allah". Irin addu'ar da yaji hajiyan tana kwararo masa sai da abin ya bashi mamaki,wanne irin so take mata haka?,lallai da bai amsa ba Allah ne kadai yasan rashin dadin da zataji,duk da ba zata nuna masa ba. Wayar ya ajjiye gefe,ya daga kai yana duban hajjaa data tsareshi da idanu,kafin yace komai ta rigashi "Abbaa,aure fa kake bayarwa,auren widad din da ummu ta baka aronta?,ba tare da sahalewar ummu ko yaaya mahmud ba?" Dan gajeran murmushi ya saki "Yadda zan bada auren nujood kai tsaye babu haufi haka zan bada na widad,ina da wannan license din" "Amma kana ganin aurenta da abbas yayi dai dai?" Ta sake tambayarsa cikin jin d'ar d'ar da fargaba "Yana da wani aibune da musulunci yace idan namiji yana dashi bai cancanci ku bashi auren diyarku ba?" Kai ta girgiza da sauri "Ko kadan,abbas nagartaccen mutum ne mai kyawawan dabi'u abun kwaikwayo,amma abba kada fa ka manta yana da mata,sannan matarsa din nan ko kwanaki na danji ana kuka da ita,bata da kirki abba,zamansu da widad mai qananun shekaru a mazaunin kishiya zai yiwu?" "Duka ba wannan bane abun dubawar ba,tunda ba ita zata zauna da ita ba,indai ya cancanta magana ta qare" sai ya dauki spoon dinsa yaci gaba da cin abincinsa,dama tasan haka zaya fada,su maza nasu hangen daban dana mata,gaba daya hanakalin hajjan bai kwanta ba,bawai don abbas bai cancanta bane,aah,tana duba wani abu na dabanne,don haka ta gaza barin maganar "Gaskiya abba bazan tayaka gayawa ummu wannan maganar ba wallahi,kada ka sani a ciki" dariya yadan saki "Matsoraciya,yo waye ya sanya dama dake?" "Amma zataga a gidana aka shirya fa,gashi widad dinma ta matsu tana son zuwa gida,ya za'a yi kenan?" "Dama ina tunanin next week qarshensa taje taga ummu din,saboda ita kanta ummu kwanan nan maganar na dawo mata da yarinya taketa yi" shuru ya ratsa tsakaninsu,har uncle muhsin din ya fuskanci kamar ta shiga damuwa ne,don haka yayi gyaran murya "Ni banji komai game da haka ba hadiyya,abbas yana da nagartar da ko nujood yace yana so zan bashi,zai riqe mana widad da amana, sa'annan kuma ina da tabbaci hundred percent karatunta bazai yanke ba,zataci gaba da karatu har zuwa inda takeso,so kinga babu wannan haufin" "Gaskiya kam" ta amsa masa tana dan jin nutsuwa kadan,to amma batun zama da kishiya tasan ba abu bane mai sauqi,koda ga babbar macace bare yarinya irin widad,GOYON KAKA. ********** Tunda hajiya ta samu tabbacin samun widad daga wajen uncle muhsin wata nutsuwa da farinciki ta dinga saukar mata,haka kawai ta dinga jin nutsuwa da gamsuwa da al'amarin,ta dinga ji kamar ta daga waya tace yazo tana son ganinsa,to amma tasan zuwa qarshen wata zai zo ganinta,babu buqatar ta daga masa hankali ta sanyashi biyo hanya,sai tayi amfani da wannan damar ta yawaita addu'a kan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa akan lamarin,yasa ayi a sa'a,ya kade dukkan fitina. ************ Dukka shirin da yakeyi tana zaune gefan gado tana kallonsa,a yanzun da zai tafi bauchi tana jin inama yace ta shirya ta bishi,zaman garin ya gama kai mata ko ina,daurewa kawai take tana cijewa,ita kam duk inda zama zai kaita indai ba cikin garinta ba bataso. Bugu da qari taga sabon key din mota garin bincike bincikenta,tana sake dauriya akan dauriya ne cike da fatan wannan motar ta zamana tata ce kamar yadda anty ummee data baiwa labari tayi mata hasashe. Tsaf ya shirya cikin yadin kufta,wanda yayi matuqar masa kyau,ya fidda kwarjininsa da kuma kyan zubi da Allah ya bashi,saita sake karkata kai tana qare masa kallo,sau tari ita kanta takan gayawa kanta tabbas abbas wani rabo ne nata da Allah ya tsaga mata sai ta sameshi,amma ita kanta idan ta tsaya ta kalli kanta tana gano tarjn banbance banbance tsakaninta dashi,shi yasa take qara matsa qaimi wajen kishinsa,saboda tana tsoro.....tana tsoron kada idanun wata ya fada kansa,ta kuma sani wasu 'yammatan indai suka baza komarsu sai sun samu,bata fiya damuwa dashi ba,tasan sam mata basu a lissafinsa,amma shi din yana cikin lissafin gomayyar mata da suke kwana su kuma tashi da soyayyarsa,koda cikin danginsa kuwa tana da wannan information din akansa. Hure mata idanu yayi da sassanyar iskar bakinsa,abinda ya sanyata ja da baya da sauri,sai kuma ta saki murmushi "Har ka bani tsoro" ta fada tana dan harararsa "Ni kika bawa tsoro,wannan kallon kamar zaki cinyeni?" Murmushi ta saki "Da da hali cinyekan zanyi,don banason kowacce mace ta kalleka kota rabeka,ni kaina bansan adadin kishinka da nake ba" daga kai yayi ya kalleta daga daura agogon da yakeyi,har launin fuskarta ya sauya,sai ya maida kai yaci gaba da daura agogonsa ba tare da yace da ita komai ba. Ya rasa wanne irin dan banzan kishi take dashi,wanda kullum baya raguwa saima daduwa da yakeyi,abun takaicin har yau batasan yadda zata tsare masa komai ba,inda yadda take kishinsa haka ta tsaya masa wajen komai da lallai ya gama yin sa'a. Ganin bai bata amsa ba tasan bazai ce komai ba,don haka ta sauya akalar maganarta "Nidai da zaka barni Allah wannan watan zan bika,kamar na shekara banje gida ba haka nakeji" "Sai next month kamar yadda nace" ranta tadan bata kadan,har ya gama shirinsa ya fito bata sake magana ba. "Rakiyar ta isa daga nan" ya fada yana dakatar da ita daga qofar falon,saboda akwai driver daga waje da zasuyi tafiyar tare,mutum ne shi mai tsananin kishin iyalinsa,yakai bakinsa saman goshinta yayi kissing dinsa yana fadin "Sai na dawo,ki kula da gida da yaran" "A dawo lafiya" ta fada a taqaice tana dubansa har ya fice,tana tsaye ta window tana leqensa har motarsu ta fice,taja da baya ta zauna saman kujera tana jan tsaki "Babu biki ba suna ba barka,an takure a baqon muhalli" ta sake fadi a fili,sai kuma ta miqe ta nufi dakinsa,ta buda ta shiga ta isa inda taga key din motar,ta jawo da zummar sake duba motar wacce ce?. Wayam taga wajen babu muqullin,ta shiga birkitawa kamar wadda ta bashi ajiya,saidai babu shi ba alamarsa,da alamu ya dauka kenan,to amma me zaiyi dashi?,ta tambayi kanta tana zurfafa tunaninta,to ba tata bace kenan?,amma kuma motar da suka fita cikinta ai tasan motar,ba sabuwa bace,gaba daya sai ranta ya baci,ta jawo waya kamar zata kirashi ta tambayeshi sai wata zuciyar ta hanata,ta shawarceta ta bari ya isa gida tukunna. *_RUMBUN K'AYA_* *_IDON NERA_* *_DAUDAR GORA_* *_KI KULANI_* *_A RUBUCE TAKE_* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 19 Kafin ya iso tuni hajiyan ta sanya an tanadar masa abincin da yafiso har kala biyu,irin abincin da tasan zaiyi wuya ya samu a gidansa,duk da qaunar da yake masa,ta kuma hada masa lemo shima kala biyu,zobo da kuma ginger drink da aka dan matsa lemon tsami kadan a ciki qamshinsa ya fito. Da yake tun karfe tara na safiya ya taso,ana azahar yana shiga layinsu,jakarsa kawai ya bayar aka shiga dasu shi da drivern nashi da yake usulmi ne suka wuce masallaci. Ana idar da sallah yace masa zai juya ya koma kaduna,yasan akwai aikin da ya baro,saboda haka bai matsashi ba,yadai karba abincin wajen hajiyar ya hadashi dashi,yace yaci a mota,ya kuma fidda kudi masu dan nauyi yayi masa ihsani,wannan yana daya daga cikin abinda yasa abbas din ke samun biyayya da qauna gami da daukaka a wajen aikinsu,duk da biyayya dole ce a tsarin aikunsu,amma suna masa soyayya ne ta har cikin ransu saboda kyawawan dabi'unsa. Cikin nutsuwa ya shiga gidan nasu,yana jin farincikin ganin hajiyar tasa,jtama tana falo a zaune tana ta dakon shigowarsa,ta amsa sallamarsa ya sanyo kai falon fuskokinsu dukka dauke da murmushi. Kamar kullum ya duqa a qabanta ya gaidata,ta amsa masa cikin kulawa addu'a gami da tambayar lafiyarsa data iyalinsa,ya tabbatar mata da komai lafiya lau,ya kuma isar mata da saqon gaisuwa daga hafsa din,wanda a zahiri bata samu hakan ba,shi ya qirqira abinsa saboda sama mata soyayya da kuma kare martabarta a idanun mahaifiyarsa. Da kanta tayi serving nashi,yana cin abincin suna hira,wanda kusan abubuwane da suka dan faffaru da baya nan,ciki harda ciwon da diyar babbar yayarsu tayi "Zanyi qoqari na shiga in sha Allah" "Ya kamata,don ka kwana biyu bakaje mata ba,tana ta min qorafi rannan" "In sha Allah". Sai da aka kira la'asar sannan ya fita a falon,yace ma hajiyan zaije wajen Suraj,amma bayan magariba zai dawo "To Allah ya tsare,akwai maganar dama da nakeson nayi dakai" "To bari na zauna mu gama sai na wuce" "A'ah,jeka abunka,idan ka dawo mayi maganar,Allah ya tsare". Tsahon lokaci suka dauka shi da suraj din,saboda kwana biyu basu hadu ba,yanayin ayyuka da canjin muqamai da abbas din ke samu a kufi a kufi,anan suraj din ya samu damar masa qorafin "Naji mamaki sanda naji ka ajjiye appointment dinka,dama cefa da 'yan sanda da yawa suke jira" kansa ya shafo kadan yana duban suraj din "Nafi nutsuwa da hakanne suraj" "To kuma gashi sun biyoka da asp ba" "Gwara wannan kam,qarin matsayi ne,a tayamu da addu'a Allah ya bamu wuyan dauka da saukewa" "Ameen ya rahman". Bayan sun idar da magariba suka sake fita da suraj din a mota ya rakashi wani waje,a hanya ya tsaya qofan wani suya spot yana kashe motar "Kadan rakani ciki na yima hajiya siyayya mana" "Ba damuwa muje mana",tare suka jera xuwa cikin,suna tafe suna hira har suka isa,suka wuce kai tsaye inda zasu bada order din abinda sukazo siya din. Sun samu 'yammata biyu tsaye gaban kantar,wanna yasa abbas din ya bada taqi a tsakaninsu,ya tsaya daga baya baya suna ci gaba da magana da suraj din,irin hirar da ta shafesu. Tunda suka tsaya din gaba daya hankalinta ya karkata a kansa,ba qaramun daukan hankalinta abbas din yayi ba,shigar qananun kayan dake jikinsa sun taimaka wajen fidda surarshi ta qaqqarfan namiji,har suka gama biyan abinda zasu siya din,saita bude da duba wayarta tadan matsa gefe kadan tana cewa qawarta "Ina zuwa". Hankalinsa nakan suraj yana saurarensa yana saka order din abinda yakeso,har yaso yayi mistake ma saida waiter din yayi masa magana,aka hada masa komai ya irga kudin cikin wallet dinsa ya aje musu,saidai garin daukan ledan bai ankara ba ya dauki tata ledar,tana sane ta barshi har sai da isa gaban motarsa sannan yaji ana fadi cikin siririyar muryarta dake nuna zallar yauqi da gwalli "Hi.....hi,ranka ya dade" cak ya tsaya,don har ya bude murfin motar,ya waiwayo don ganin ko dashi ake. Da murmushi ta dinga jifansa har ta iso,cikin tausasa muryarta tace "Yallabai ledata ka dauke" ledar hannun nasa ya daga ya kalla,sai sannan ya lura,ya sauketa gami da miqa mata yana cewa "Sorry" "Ba laifi ai,hakan yayimun,kaga ko babu komai leda zata qulla mana zumunci" bai amsa mata ba illa amsar tasa ledar da yayi "Sunana rafi'ah" tayi saurin fada ganin yana shirin shigewa motarsa "Good,thank you ko" matsowa ta sakeyi don fa fuskanci rufewa zaiyi "Ko zan samu digits naka?" "Am sorry to say no" ya fada yana maida murfin motar a hankali ya rufe,sannan ya tashi motar yayi reverse suka fice daga wajen. "Har yanxu kana lokaci mutumina,bansan me yake fusgar hankalinsu ba haka,adan bani sirrin mana" ya fuskanci sarai abinda suraj yake fada,fuskarsa kadaram kadaham ya waiwayo kadan ya dubeshi sannan ya maida kansa ga titi "Kai har yanzu baka girma na suraj,ana ta neman na abincin da za'a kaiwa iyali kuma wa yake ta wannan" ya fada yana shafar habarsa dake zagaye da gemun daya samu wadataccen tsafta da gyara "Banga alama ba,don duk sanda muka fito irin haka sai wata ta taya" "To ai sai suyita yi,ta gidanma ya ka cika da ita bare ka sake daukan wata,kayita hadama kanka rigima da zafi,bazan iya daukan wannan ba" "Fada dai kake,bari ayi katari da wadda zata sace maka zuciya" "Haka kake gani" abbas ya maida masa amsa,hankali da idanunsa naga titi. Dariya kawai Suraj yayi,bai sake cewa komai ba suka shiga wata hirar. Sai daya fara sauke suraj a gida bayan ya hadashi da tashi ledar sannan ya koma gidan hajiyan. Bayan isha'i ya zauna sukaci abinci,kusan tare da hajiyan,saidai kowa kwanonsa daban,bayan sun kammala ya dauke kwanukan da kansa ya tattare wajen sannan ya dawo ya zauna yana fuskantar hajiyan "Hajiya kince zamuyi magana ko?" Gyara zamanta tayi sosai "Eh tabbas" "To ina jinki,Allah yasa ba wani laifi nayi ba" murmushi ta sake "Laifi abbas?,a'ah ko kadan,wani alkhairi na hango maka,na kumayi karambanin zartar maka dashi ba tare dana tuntube ka ba" qaramin murmushi ya saki "Hajiya...ai kinfi qarfin ki yiwa rayuwata karambani,kome kika ga dama ki zartar dashi kanki tsaye kawai" kai ta dan jinjina sannan tace "Aure na nema maka,'yar uwa ko 'yar muhsin" sosai gabansa ya fadi,abinda ya jima baiji irinsa ba tsahon rayuwarsa "Hajiya nujood?" Ya fada cikin fargaba,don ko da ya kasance itace bazai iya musawa hajiyan ba,haka zai auretan,yarinyar dake kallonsa a mazaunin ubanta "A'ah,widad" ajiyar zuciya ya sauke,sai yaji tashin hankalin da yake ciki din ya ragu,ya samu 'yar nutsuwa,duk da fahimci wa take nufi din ba,amma dai ya fahimci wata ce daban ba nujood ba "Inason kaje ka ganta,duk da ina zaton zuwansu gidan nan kamar ka taba ganinta,amma wannan zuwa ne na musamman,kaje ka gabatar mata da kanka" kai yadan sunkui qasa "In sha Allah hajiya zan saka rana sai na sanarwa muhsin din sai naje" har cikin ranta ta sake qaunar abbas din,tasan dama bashi da matsala kome kuwa tace yayi,saidai ta dauka zaiyi jayayya ko ya qalubalanci wannan danyan hukuncin nata. Duk yadda yaso ya fidda damuwa ya zauna suyi hira sosai amma ya kasa,jiki da zuciyarsa dukka a takure suke,dole bayan qarfe tara ya yiwa hajiyan sallama ya wuce gidansa. A kan hanya yana tuqi amma tunani ne fal kwanyarsa,aure?,wacece widad din ma?,oho shi bai ganeta ba,amma me hajiya ta hango masa?,sai Allah,bazai iya mata wannan tambayar titsiyen ba,da wannan damuwar da kuma tunanin ya isa gida. Bashi da hadi da sassan hafsa,don haka sassansa ya wuce,yabude ya shiga yana tsaye tsakar falon kamar maison tuna abinda ya kamata yayi wayarsa ta dauki sassanyan busar sarewar dake a mazaunin ringtone dinsa,don bayason ringtone mai hayaniya da yawa,mafi yawan lokutta ma yafi barin wayar tasa a vibration. Cikin wata kasala da gajiya da maganar hajiya ta saukar masa ya zaro wayar yana duba me kiran,hafsat dince,sai ya daga kiran yana neman kujera daya cikin falon ya zauna "Ina ka shiga ne inata kira baka daga ba" ta fada muryarta a tsaye carrr,alamun qagauta da son samun mutum,shuru yayi yana nazartar muryarta "Lafiya?" Ya fada da nutsatsiyar muryarsa mai nauyi,wadda ta dawo da hafsat din cikin nutsuwarta kadan,ta kuma fuskanci yanayin data masa magana baiyi dai dai ba,kishi ne keta cin ranta,har idanunta suka so rufewa,gani take kamar yana tare da wata ne shi yasa yaqi daga wayarta, "Ah....uhmm lafiya qalau,kawai hankalina ya dan tashi da naga inata kira baka daga ba" "Oh.....am fine,kufa?" "Lafiya qalau muke,yara gaba daya sunyi kewarka" "That's my babies.....kefa?" Ya fada yana danne damuwarsa,murmushi ta saki wanda ya jiyo sautinsa "To nima nayi" ta fada tana danjin nauyi,idanunsa ya lumshe yana kuma budesu,she's not romantic woman at all,ya rasa yadda zai canzata,kamar irin matan da soyayya bata damesu ba sam,dai dai da greetings cards da yake siya mata time to time,musamman idan yayi tafiya ya dawo bata wani daukar abun da muhimmanci,wani lokaci ma idan ya kawo cards din bata ko budesu bare ta karanta,karba take ta ajjiye bayan ta bishi da SANNU. "I miss you more than you can imagine" ya fada with softness,wanda har sai data ji tsigar jikinta ta tashi,wani abu ya tsarga mata,amma sai tace "Allah ya qara zumunci" "Zumunci dai?" Ya maimaita a ransa,even kalmomin da zatayi appreciating nasa bata dasu,har ya fara sabawa. Shurun da ya gilma tayi amfani da wannan daqiqun "Magana da zamuyi ko ince tambaya zanyi" "Am sorry ranki ya dade,yanzun nan na shigo gida,bari na gama shiryawa saina kiraki,inaso yau ayimin hira sosai,na gaji da yawa" "Kai da kaje hutu?,me kayi daya gaji da kai?" Ta fadi da salon tambaya,ita sam hankalinta bai kwanciya idan basa tare "Yawo" ya amsa mata a taqaice,sai ranta ya sosu,anya ba abinda take zato bane "Yawo kuma abban mimi?,don Allah ka daina banso wallahi" "It's okay" ya fada fuskarsa na fidda miskilin murmushin da bai shiryawa ba,yasan meke damunta "Ka kira da wuri,don bacci nakeji inason na kwanta" "Okay" yace da ita yana katse wayar gami da ajjiye ta gefe "Hafsat hafsat,ko sai yaushe zata canza?" Yayi maganar shi da zuciyarsa,sai ya miqe yana wucewa bedroom. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so,zasu fara fita a gobe da izinin mai duka_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 90 16 59 91 *Zafafa biyar kadai keda sinqin nau'ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci guda*🤝😄 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 20 Sai daya gama duk abinda yakeyi ya kwanta yaja bargonsa zuwa qugu bayan ya rage hasken dakin sannan ya kirata. Har tayi ringing ta gama bata dauka ba,ya sake kira karo na biyu sannan ta miqe daga kwanciyar da tayi,ta jawo wayar tana sakin hamma,dan qaramin tsaki taja,banda maganar da takeso suyi nada muhimmanci da bazata daga ba,batason zancan motar yayi nisa kada taje ta zama rabon wasu,abinda kawai bataso yanzun zaice saita tsaya sunyi hirar soyayya,batasan me dame zata ce masa ba,daga qarshe kuma ya tada mata feelings ko ya isheta da fitina idan ya dawo. Cikin qaramin sauti tayi masa sallamar wanda baccin data fara ji ya jawo hakan,saidai shi din abun ya tabashi,har ya tada masa tsigar jikinsa,ya rufe idanunsa yana amsa mata "Am sorry,na tasheki halan?" "Ummm,babu komai" "Thanks" da hanzarinta ta katsi numfashinsa "Abban mimi ina cikin maka gyara ne shekaran jiya naga key din sabuwar mota,to yau kuma mimi ta tabo wajen ta zubda kaya,da na maida kayan banga key din ba,nace Allah yasa ba wani wajen ta jefa maka ba" "Noo,ni na tafi dashi,motar dama ta hajiya ce,so sai na baiwa samuel nace gobe ya biyoni da ita a kawo mata,kinsan motar da ake fita da ita ta samu matsala" idan tace ga irin bacin ran da taji ya saukar mata ma ta yiwa kanta qarya,abinda taketa hasashe kenan,take kuma gudu,yanzun motar ya dauka ya baiwa hajiyan bayan yasan tana da buqata,tana ta kuma gaya masa ya canza matan bai canza ba?,ta yaya zata nuna masa ma zallar bacin ranta? "Abban mimi amma dai kasan ina da buqatar motar nan ko?,sati nawa ina maka naci ka hanani?,amma a gabana ka siya......" "Hafsatu" ya kirata da sunan da mafi yawa jama'a ke kiranta ba tare da ya bari ta idar da maganarta ba,kiran kuwa ya ratsa mata ko ina,yana da wata murya dake da kwarjini "Baki gane wacce na siyawa motat bane?,hajiyata mahaifiya ta nake magana" boyayyar ajiyar zuciya ta sauke,tana kuma qoqarin sassauta harshenta "Bance bakayi dai dai ba ai,amma nafi buqatar motar,da sai ka karba ta wajena ayi mata gyara ka bata,tunda hajiya bako yaushe ta fiya fita ba,sai ta dade a gida bata fita ba,zata iya manage da ita" "Hajiyan tawa za'a bawa ragowar motarki tayi manage?" Cikin zallar mamaki ya jefa mata tambayar, jikinta daga can yayi sanyi,saidai bacin ran da takeji a zuciyarta ya hanata gayawa kanta tana fadin abinda bai kamata bane "To menene a ciki?" "A wajena wani abunne,idan bakisan darajarta ba ni nasan darajarta,tafi qarfin cin ragowar kowa a duniya bare taki ragowar,karki kuskura ki kaini bango da banzayen maganganunki,idan ba haka ba zaki gane kuskurenki,ki adana maganganunki basu da wani amfani a wajena,kudi dai nawa ne,zan kuma wahaltawa mahaifiya ta a duk sanda naso ba tare da shawara ko yardarki ba" "Amma dai kasan nima ina da hakki ai a kanka ko?,tunda nima matark......" "You are very stupid" ya fada da zafi yana datse kiran,bayason yaci gaba da saurarenta kada ta tunzarashi,idan ya tunzura baisan me zai biyo baya ba,yana kallonta tanata kiransa amma yaqi dagawa,sai ma ya maida wayar silent ya maida kansa ya kwanta yana ta furzar da iska a bakinsa ko zai samu zuciyarsa ta rage zafin da take masa. Bayan kiran ya tsagaita da shigowa sai kuma wani haske yayi blinking,alamun shigowar tex,wayar ya jawo da niyyar kasheta gaba daya,saidai saqon ya fito saman screen din _Tunda ni bankai wani bigire na abu mai muhimmanci a tare da kai ba,nima bazan zauna ina aikin da ba'a gani ba,zan dawo garinmu inda akasan darajata_ "Mtsweew,shirme kawai" ya fada qasa qasa,ya danne switch button ya kashe wayar gaba daya ya dorata saman bedside drawer,ya sake jan duvet yana rintse idanu,saidai gaba daya baccin yaqi daukarsa,muraja'a kwanyarsa ta shiga yi masa kan halaye da dabi'un hafsat,tun daga kan aurensu kawo yau,tun kafin aurensu ya fahimci wasu baqin halaye daga gareta,banbancin ra'ayi da kuma wasu abubuwa masu yawa,ya dauka idan sukayi aure zai iya canzata,ashe yayi kuskure,babu wani sauran canji,saima abubuwa da suke ta'azzara kullum. Gefe daya kuma tunaninsa ya cilla kan maganarsu da hajiya,sai ya sauke ajiyar zuciya yana ambaton sunan Allah ya kawo masa agaji. ********Washegari bai tashi da wuri ba,saboda ya sanyama ransa babu inda zai fita yau din,sai wajen sha daya da rabi sannan ya shiga kitchen ya dafa irin tea dinsa ya soya qwai hudu ya dauki slice of bread ya hada dashi ya dawo falonsa ya zauna yaci,bayan ya gama ya kalli labarai kadan kafin ya canza wani program da akace masa jiya anyi da senior dinsu bai samu gani ba,bayan ya gama ya buda qofa ya karbi news paper wajen yaron dake kawo masa ya karanta,sai yayi wanka ya sanya wata jallabiya mai sulbi,wadda ta karbeshi sosai,ya daura alwala ya wuce masallacin dake gaban unguwarsu wanda suke sallah qarfe daya na rana,a qa'ida idan zai hau abun hawa zuwa masallacin zai biya 30naira amma ya zabi takawa a qafa,don tafiyar qafa ba baqon abu bane a wajensu. Bai dawo gidan ba sai qarfe biyu da rabi na rana,don yadan tsaya da mutane,yaron dake masa aike aike ya aika ya samo masa masa me kyau ko tuwo,sai daya buda fridge yasha ruwa mai matsakaicin sanyi sannan ya samu waje ya zauna yana qoqarin kunna wayarsa. Saqonni ne suka soma shigowa,kamar bazai bude ba don yana tsammanin hafsa ce,kada ya karanta abinda zai bata masa rai,sai kuma ya buda din,ba ita bace,ire iren 'yammatan dake crushing a kansa ne,yana mamakin ta inda suke samun numbers dinsa,bai ma batawa kansa lokaci ya karanta din ba ya goge saqon,yana tuna sanda yake barinsu ga wayarshi,irin tashin hankalin da sukeyi da hafsa din a kansu a lokacin,shi kuma rashin muhimmancinsu da rashin damuwa da masu saqon yasa yake mantawa ma dasu cikin wayar bare ya share kada ta gani din,yayin da kishi ke sanyata taga kamar yana sane ya barsu. Number hajiya ya nema ya kira,suka gaisa,ya shaida mata yau bazai fito ba yana gida kada taji shuru,fatan alkhairi tayi masa sukayi sallama,kamar ya ajjiye wayar sai yaga akwai kuma wani haqqin bisa wuyansa,don haka ya nema number hafsa din ya kira. Tsaf ta qaraci ringing dinta ta katse ba'a daga ba,sai ya sake kira amma sai aka gaya masa a kashe take,yayita qoqarin kira ana maimaita masa a kashe take,sai ya ajjiye wayar ya haqura,dai dai lokacin yaron da ya aikata din ya dawo ya karba saqon ya sallameshi. Sai da yaci abinci ya nutsa sannan ya kira suraj,suka gaisa suka taba hirarsu sannan ya buqaci ganinsa "Yau bana gari,na danyi balaguro azare,amma yau din zan dawo,zan sameka gida gobe" "Yayi,babu damuwa,saina jika" sukayi sallama. Wunin ranar a gida yayita shi kadai,yanata juya maganar auren da hajiyan ta nema masa,saida yamma ne ya fita farfajiyar gidan ya motsa jikinsa,ya danyi strolling cikin layinsu zuwa baya sannan ya dawo ciki. A farfajiyar gidan ya sanya musu kujeru shi da suraj,sannan ya dafo musu black tea wanda yasha kayan qamshi da ganyayyaki masu dadi,ya zubo musu a wata buta me hade da wasu irin cups ya zuba ya miqawa suraj,sannan yaja kujera yana zama "Kai....abbas badai iya dafa tea ba wallahi" "Zaka fara ko?" Kai ya girgiza yana dariya "Kasan Allah?,sai an tara mata da yawa basu iya dafa tea kamar haka ba" baice komai ba illa kai nasa cup din baki da yayi,saboda yasan haka dinne,koda a cikin gidansa ma,don yawancin lokutta ya gwammaci ya tashi ya dafa tea dinsa da kansa akan yasa hafsat ta dafa masa,indai kaga ya sha nata to lalura ce babu yadda zaiyi. Suna shan tea din suna taba hirar da bata qarewa tsakaninsu,suraj din aboki ne na tun lokacin quruciya har zuwa girma,kuma har yanzun kusan shine babban abokinsa sannan muhsin ya biyo baya. "Kace kana son ganina,me ya faru?" Cup din abbas ya ajjiye,yana hade yatsun hannunsa guri guda,sannan yayi crossing qafafuwansa suma yana duban suraj din,sai kuma yadan shafi goshinsa kadan sannan ya fara magana "Bansan ta ina ma zan fara maka bayani ba suraj,hajiya ce ta nema min auren 'yar yayan muhsin" "Ummm,kaga dan gata...kai yanzun ma auren sai an nema maka,bana fari ba ba komai ba?" "Akwai matsala suraj" da dan mamaki saman fuskarsa yake dubansa "Matsala ta meye?,matar ce bata yi maka ba ko kuwa?" Kai ya girgiza "Ba wannan maganar ake ba,don ko fuskarta ban sani ba,suraj cikin gidana akwai matsala sosai,ban kuma gama solving matsalar ba ta yaya zan qara aure suraj? Da shegen kishin hafsa zanji ko kuma da sabon auren da nayi?,beside ma kwata kwata banajin ina da cikakken lokacin fuskantar matsalolin mata bayan wadda nake ciki" Murmushi suraj din yayi cikin kwanciyar hankali,ya kuma gyara zamansa da kyau,shi kam kamar hajiya ta shiga tunaninsa ne,wannan abun da tayin shawarar da ya dade yana son bawa abbas din,amma kasancewarsa ba mai magana ba,ba kuma me fadan sirrinsa ba yasa ya qyaleshi ya zuba masa idanu,duk da cewa mutumin da yake da matsayi a wajensa kamar suraj dake shiga gidansa lokaci bayan lokaci zai fuskanci akwai damuwa a gidan,daga fannin tsafta kawai zakasan akwai nakasu,tunda tsafta da qazanta basa boyuwa "To ai kai abinda baka sani ba,wannan auren shine hanyar gyaruwar duk wata matsala taka da damuwa" "Kamar yaya?" Ya tambayeshi yana dan yamutsa girarsa "Bari nayi maka gwari gwari,yawancin mata suna qoqarin ganin sun gyara tsakaninsu da mazajensu ne a sanda suka qara aure,gudun kada kishiyar data shigo taga gazawarsu,ko ta qwace musu miji ka fahimta?,to sai kaga itama ta zage damtse don kar a barta a baya,gefe guda kuma ga kulawa daga amarya kana samu,kowacce qoqari take taga itace star a wajenka" shuru abbas yayi kawai yana jin suraj,mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,baya tunanin qarin aurensa zai zama gyara ga hafsat,amma bai san ikon Allah ba,kawai abu daya ya sani,ko ransa hajiya tace ya cire ya bayar zai iya,bare wannan buqatar da bata fi qarfin ikonsa ba,ya sauke ajiyar zuciya yana zama sosai cikin kujera manyan idanun san nan akan suraj "Hajiya tafi qarfin komai a wajena suraj,batun rashin karba ma bai taso min ba,kawai inason jin yadda za'ayi" dariya yayi ya koma ya jingina da kujera "Ya kuwa za'a yi,kawai ka shirya kaje kuga juna kai da ita,sai mu fara shirin biki". *********Tunda hajjaa ta gaya mata saura kwanaki biyar ta tafi kano take murna da zumudi,kullum cikin shirya kaya take,ko ta shirya sai ta fiddasu ta sake shiryawa,kowa a gidan dariya yake mata yana tsonakarta,ranar da nujood ta tsokaneta da cewar "Dama abba yace an fasa" fada suka kusa yi,taqi kula nujood din wunin ranar,saida hajjaa ta shiga batun ta musu sasanci. Saura kwanaki uku ta tafi da yamma suna kitchen suna ma hajjaa yanke yanken kayan miya,da yake tun zuwansu hajjan ke hadasu su shiga kitchen tare,ko daya widad din bata da son jiki,kuma tana sha'awar yin girkin dama,ummu ke hanata tana ganin kamar zata qone ko kuma wani abun zai sameta. Uncle muhsin ne ya shigo,dawowarsa kenan daga aiki,kai tsaye ya wuto kitchen din ya tsaya bakin qofa ya leqo yana tsokanarsu "Manyan 'yammata ne ke girki yau kenan" murmushi hajjaa tayi "Aiko dai yau su abba za'a ci dadi" "To Allah ya taimaka,dan zo mana minti uku" "To abba" ta fada tana tsame hannunta daga abinda take tabi bayansa. Sai da suka shiga bedroom dinsa,ta tayashi ya rage kayan jikinsa sannan yace mata "Widad fa gobe zatayi baqo,hajiya da kanta ta kirani ta gayamin gobe abbas zaizo suga juna" baki hajjaa ta kama tana murmushi "Ikon Allah,abu kamar wasa yana shirin zama gaske,to Allah dai ya doramu akan 'yar rigimar hajiyan,tunda dai abbas ba shine na farko ba" "Ba komai in sha Allah,idan sun gama girkin ki turon ita nayi mata magana da kaina" "Yafi dai abba" sai yayi dariya "Na fuskanci tsoro dai kike" "Wallahi abba,Allah dai ya tabbatar da alkhairi,ya kauda fitina" "Ameen ya rahman" ya amsa mata yana nufar bandaki,ita kuma ta baro dakin da zummar zuwa ta kawo masa abun sha kafin girkin ya kammala. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 90 16 59 91 *Zafafa biyar kadai keda sinqin nau'ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci guda*🤝😄 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 21 Sai da suka gama cin abincin ma sannan uncle muhsin ya shigo,ya zauna suka gaisheshi,widad ta miqe zata tattara kwanukan uncle muhsin yace "Dawo widad muyi magana,nujood debe kwanukan ke da musaddiq" da zumudinta ta dawo ta zauna,tana tunanin labarin tafiya gida zaiyi mata "Widadun ummu" uncle muhsin ya fada yana murmushi "Na'am uncle" ta amsa masa itama ta amsa masa murmushin,tun da tana son uncle muhsin sosai,kasancewar yana saya daga cikin jama'ar da suke nuna mata qauna da kulawa "Akwai wani abokina,sunanshi abbas,yacemin yana son yarinya mai hankali da nutsuwa zai aura,nasan widad dina nada hankali da nutsuwa,ina kuma alfahari da ita,wannan yasa nace masa yazo ya ganki kema ki ganshi" gabanta ne yadan fadi,saita dan rage fara'a kadan,uncle muhsin din ya karanci haka,don haka yayi murmushi "Kada ki damu,indai kika ganshi baiyi miki ba shikenan,babu wanda zai takura miki kinji ko?" Kai ta gyada "To uncle" "Yauwa,Allah yayi albarka widad" "Ameen uncle" ta amsa masa tana miqewa,jikinta yayi wani irin mutuwa,kamar zata daki sai kuma ta fasa tabi bayan nujood data tsaya a kitchen. Wanke wanke ta samu tana shirin yi,saita tsaya gefenta nujood din ta waiwayo "Menene?,na dauka zan ganki kina tsalle zaki gida,ko abban cewa yayi an fasa tafiyar?" Kanta ta girgiza "Wai wani abokinsa ne zaizo gobe ya ganni yanason yayi aure" murmushi nujood tayi "Ke wanne irin farinjini ne dake,amma abokin abba?,na sassan abokansa,wa yace miki?" Idanunta tadan juya alamar tunani na wasu sakanni sannan da sauri tace "Wai abbas" "What?" Nujood ta fada tana ajjiye plate din hannunta "Wai uncle abbas abba yake nufi?" "Oho,inajin shi dinne ko?" Ruqunqume widad nujood tayi,tana dan ihun murna "Wayyo widad,don Allah kada kice baki sonshi, uncle abbas yayi mugun haduwa,saima idan yasa uniform din nan nasa,ga miskilanci ga tsafta ga gayu,idan yazo gidan nan har ya tafi qamshin turarensa yana nan,don Allah kice kin yarda" ture nujood widad tayi tana tura baki "Dalla malama,ni ba wani nan,na barmiki ke ki cewa uncle kina so" dariya sosai nujood ta qyalqyale da shi tana cewa "Ni ai babana ne,banda haka ni abba zai bawa,tunda kika ga bai bashi ba kuwa babana ne din" ita dai widad bata sake cewa komai ba,sai ta hau saman kantan kitchen din ta zauna,tana sauraren nujood nata bata labarin uncle abbas din. Musaddiq ne ya shigo yayi kiran widad bayan kaman awa daya,yace tazo hajjaa nason magana da ita,ta sauko.tabi bayansa. A bedroom dinta ta sameta tana daga wasu kaya "Shigo mana widad" hajjaa ta fada ganin widad din ta dan rab'e,qarasa shigowar tayi,hajjan ta dan tsokanarta kan kayan tafiya kano take hada mata,don ta samu ta sake sosai tayi maganar da ta sanya aka kirata din dominta,ganin ta sake din sai tace da ita "Kinji abinda abbanku ya fada ko?" Kai ta gyada mata ba tare da ta amsa mata ba "Karki damu,abbas nada matuqar kirki,sannan shi din dan hajiya ne,hajiya dai wadda kuka zauna gidanta wancan satin" maganar data fada na cewa dan hajiyan ne ya sanyata sakin jikinta sosai,cikin dabara hajjaa keta janta da zance har ta saki jikinta,sai a sannan ta sallameta. Da yamma lis ta kama widad din duk rashin son kitso irin nata ta sake wanke mata kai,tana ta qi tana turjewa,sai data sanya su musaddiq suka dinga yi mata dariya ,tare da waqar me kukan kitso sannan ta nutsu,ta raba kanta tayi mata manyan kalaba da suka jelarsu masu tsaho zubo gefe da gefan fuskarta,saura kuma suka sauka a bayanta,kasancewar ba kasafai ta fiya kitso ba saboda qin da take masa,sai kalbar ta haska fuskarta tayi mata kyau sosai,hajjaa ta qawata qarshen kowacce jela da duwatsun kitso masu yawa da suka qarawa kalbar kyau suka taimaka kuma ta kwanta mata sosai a fuskar da bayanta. Itakam widad gaba daya murnar tafiya gida ya sanya ma bata damu ko ya dauki batun zuwan abbas da muhimmanci ba,siyayyar da uncle muhsin yayi mata taketa shiryawa abinta,tana ta zancensu Aafiya da sauran 'yan uwanta,da wannan batun ta kwanta bacci. ************Washegari a gida yayi breakfast wajen hajiya,ya kuma shaida mata yau din suraj zai rakashi gidan muhsin din. Har cikin zuciya da ruhinta take jin farinciki,tayi addu'a sosai tare da fatan samun dacewa da albarka mai yawa cikin lamarin. Sai Azhar ya wuce gida bayan yayi salla a nan,yana komawa bacci ya kwanta,bai farka ba sai gab da la'asar,tun bai tashi daga kan gadonsa ba ya janyo waya yana sake lalubar number hafsa,saidai yau din ma har tayi ringing ta gama bata dauka ba,a qa'ida idan yayima mutun kira daya baya qarawa,amma wannan karon ita din sai daya kira sau uku bata dauka ba,sai ya maida wayar ya ajjiye ransa yana baci,ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala ya wuce masallaci. Yana dawowa dakin kira na shigowa wayar tasa,suraj ne yana dagawa ya soma zolayarsa "Sabon ango,Allah dai yasa ka shirya" ido ya lumshe yadan saki murmushi,surja badai zolaya ba "Haba duk zumudin na meye?,bayan la'asar fa mukayi dakai,kuma yanzun nan ma aka gama sallar" dariya suraj din yayi "Na qagu ne naga wacce mai sa'ar ce zata sake samunka,bama ni kadai ba,kaga zainab a nan ita kanta so take naje na dawo na gaya mata wacece" "Ita da hafsat kuwa" "To sai me?,kayi qoqari ka shirya,gani nan fitowa,abinci kawai zanci" "Saika qaraso" ya fada yana katse wayar,dole ya fidda hular da ya sanya ya aje,ya shiga bandaki ya don yin wanka. Yana tsaye yana tsane ruwan da yayi lumm cikin gargasar jikinsa yana duban madubi,karo na barkatai ya sake kallon wayarsa yana tuna adadin wayar da ya yiwa hafsat din bata dauka ba,sai ya jinjina kai yana qiyasta yadda zai fita daga bauchi jibi da sassafe zuwa kaduna. Ya gama shirinsa tsaf yana gaban mudubi yana kallon kansa,hannunsa riqe da hularsa yana karyata,yana jin wani banbarakwai,wai yau shine a karo na biyu zashi zance,zancen ma wajen wadda baisan wacece ba,ya dora hularsa sannan ya dauki sassanyan turarensa dake fallasashi a duk inda ya shiga ya feshe jikinsa dashi. Kiran suraj da ya shigo ya shaida masa isowarshi,saiya kara wayar a kunne ya tallafeta da kafadarsa saboda takalman da yake sanyawa a qafarsa bayan ya zauna kan dressing chair yana fadin "Ka qaraso ciki mana" "A'ah,ina cikin mota fito kawai" bai musa masa ba,ya zame wayar ya qarasa sanya wasu rufaffun takalma masu kyau da asalin tsada da wasu sake fidda shigarsa,ya dauki wayar ya mayar aljihu ya dauki keys din gidan suma ya saka sannan ya fito. "Kai mutumina,kamar yau ne zan rakaka wajen maman mimi?" Harara ya watsa masa bayan ya rufo murfin motar sannan yace "Kunna mota mu wuce,so nake muyi mu dawo,ina da wani uzuri" "Yanzu kuwa yallabai" ya fadi yana dariya,sai ya tada motar suka wuce. Suraj nata jansa da hira amma shi hankalinsa ya rabu kashi kashi,dubansa yayi sanda yaga yana qoqarin parking qofar wani qaramin mall "Bari mudan samo abinda za'a kai mata,ai bama shiga hannu rabbana ba" "Share kawai suraj mu tafi please" "A'ah,nikam ba za'ayi haka dani ba,ko banza fa ta zama matarka,tunda an riga an tambaya an kuma baka" maganar sai yaji tayi masa nauyi,bace komai ba har suraj din ya fice,bai kuma dade ba ya dawo da tarin alawoyi da chocolates masu tsada da dadi,ya ajjiye ledar ya kunna motar sukaci gaba da tafiya. ~~~~~ "Kai,tubarkalla ma sha Allah,diyata din nan badai kyau ba" hajjaa ta fada bayan ta gama shirya widad,cikin wata sabuwar dark blue din super vilisco,dinkin doguwar riga,ta fidda jelar kalbarta tayi ta fito ta qasan daurin dankwalin data yi mata,ya zauna das a kanta,sannan ta bata siririn mayafi da ya dace da atamfar. Murmushi widad kawai keyi tana kallon kanta a cikin mudubin,badan badan ba da sai tace bata taba ganin tayi kyau haka ba,ummu ta tabo daa,bata iya zama tayi mata wadan nan qyale qyalen,saidai ko yaushe zaka samu widad din fes cikin tsananin tsafta da kuma sutturu masu tsada,saidai ita da kanta take zama tayi kwalliyarta wansa a wajensu Aafiya da yayyansu su ramziyya take kwaikwaya,ko latifa da take mutuniyarta ita dinma bawai ta yanzu bace,ba wani iyawa tayi sosai ba,amma da yake hajjaan gwanar ado ce,a yau din ta qawata widad din sosai,har abun yayi mata dadi ya kuma burgeta ita kanta,farincikin yadda taga tayi kyau yasa bata jin wani fargaba ko bacin ran zuwan baqon,Allah Allah ma take yazo ya tafi tazo hajjaa tayi mata hotuna masu kyau ta turawa daya daga cikin 'yan gidansu su nunawa ummunta kafin ta isa gida. Musaddiq ne ya shigo dauke da ball a hannunsa yana gayawa hajjaa ga uncle abbas nan "Bude musu setting room,ka kunna ac kadan kada tayi yawa,sai kazo kakai musu ruwa" da to ya amsa ya juya yana ficewa. Sai da hajjaa ta tabbatar an kai komai sannan taja hannun widad ta zaunar da ita "Na sanki da hankali da nutsuwa,to ki qaro wata a kai,idan kin shiga ki gaishesu kinji?" "Tom" ta fada tana gyada kai,sai hajjaa ta kira nujood,ta sanyata ta saka hijab tace ta raka widad,har sun fita ta kirayeta "Karki ce zaki zauna,nasan halinku da shirme,kina rakata kuna gaisawa ki dawo ciki" "To" tace tana ficewa,suka rankaya kuwa ita da widad din zuwa setting room. Setting room din yabi da kallo,duk da ba baqonsa bane,don yawanci idan yazo a nan suke zama da muhsin din,kamar bazai zauna ba,haka kawai ya samu kansa da qaguwa na ganin wacece,wayarsa da aka kira ya duba kuma yaga ogansa ne ya sanyashi zama dole,don suna da wani irin respect na ga gaba dasu,ya fara amsa wayar cikin nutsuwa da kuma girmamawa. Suna cikin yin sallama da ogan nasa yaji suraj ya dan taboshi,sai ya maida dubansa ga suraj din don,signal yayi masa da ido yana masa nuni da hanyar shigowa setting room din,ya qarqare wayar yana ajjiyeta gefansa,sannan ya maida dubansa ga inda suraj din ke masa nuni. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 22 Nujood da widad dake tahowa yake nuna masa,baiji abinda yace ba,yadai ci gaba da kallonsu,suna sarqafe da hannun juna,widad din tana jin gabanta na faduwa ne gami da sanyin jiki haka kawai,yayin da nujood ke tsokanarta,har ta daga qafa zata dan bi nujood din da gudu sai kuma ta tuna taga qofar setting room din a bude,wannan yasa takai idanunta ciki,bata hango wadanda ke ciki tar,saidai ta tabbatar suna iya kallonsu. Da sallama suka shigo,suraj ne ya amsa musu fuskarsa da murmushi,nujood din na riqe da hannun widad suka qarasa cikin falon. Nujood dince ta fara gaida abbas,fuskarsa kadaram kadaham ya amsa,already ta san halinsa,bai fiya fara'a ba don haka bata damu ba,ta maida akalar gaisuwar ta ga suraj "Lafiya lau,ya karatu?" Ya amsa mata cikin fara'a da murmushi "Alhmdlh" tuna abinda hajjaa tace da ita ya sanyata miqewa "Saikin shigo" ta fada tana duban widad cikin salo na tsokana,wanda iya ita da ita ne kawai zasu fahimta. Maganar nujood din taja hankalin abbas harma da suraj,tunani iri daya ya darsu a ransu lokaci guda,kowanne dubanta yake,abinda ya sanyata taji kamar an aza mata wani nauyi,gaba daya ta jita kamar a daure,kallon da suke mata yana neman daburtata,tana takure a gefe tsakanin kujeru tana wasa da gefan mayafinta,saita nannadeshi ta wareshi,suraj ya fuskanci hakan,don haka yayi gyaran murya,cikin murmushi kuma yace "Barka da fitowa 'yammata" muryar suraj din saita ankarar da ita mantuwar da tayi bata gaidasu ba,don haka ta daga kai in ta fara gaida suraj din,cikin sakewa da fara'a da kuma kulawa ya amsa mata,sa'annan ta koma ga abbas,idanu saika hada,take taji ya fiya kwarjini da yawa,tunda suka shigo kuma ta karanci fuskarsa bashi da yawan fara'a,sannan koda bata dade a wajen ba alamu su nuna yana da yawan shuru shuru,don ko daya bataji muryarsa ba tun bayan daya amsa gaisuwar nujood "Ina yini" ta fada tana kaida kanta,sai daya lumshe idanunsa ya bude sannan ya amsa mata,'yammatan daya fada sai abbas yaji kamar gatse ne yake masa,zaqin muryarta kuma me cike da zallar quruciya na zaga kwanyarsa "Kada dai ya kasance ita hajiya ta zaba masa?,anya kuwa?" Kamar suraj yasan tambayar dake yawo a ransa kenan,sai ya tsinceshi yana cewa "Allah yasa kece wadda hajiya tace muzo mu gani?" Kanta a qasa kawai ta gyada kanta,amsar data tilastawa abbas maida bayansa jikin kujera ya jinginar kawai idanunsa a lumshe. Yana iya jin yadda suraj keta janta da hira,tana amsa masa da qyar,muryarta cakude da kunya da kuma tsoro hadi da rashin sabo,tunda suraj din ya kalleshi ya karanci yanayinsa,wannan yasa ya karbe hirar abinsa ba tare daya sanyoshi ba,kamar ma shi abbas din ya yiwa rakiya. Jinnta take a takure kota ina,musaman idan ta waiwaya inda abbas din ke zaune abinsa ya sanya musu kunne "Wannan abokin nasa,ko me yasa yazo dashi?" Abinda tayita fada kenan a ranta "To widad mu zamu wuce,sai kuma wani jiqon?" Suraj ya fada yana duba agogonsa,maganar data yiwa widad din mugun dadi,don kafin ma ya miqe ita ta miqe tana cewa "Ku gaida gida" saita kada kai abinta tayi hanyar ficewa,a lokacinne abbas ya bude manyan idanunsa yana binta da kallo "Minti daya mana malama widad" suraj ya fada yana miqewa da ledar siyayyarsa a hannu yana yiwa abbas sign din ya tashi mana,sai ya kauda kai kamar bai gani ba,don haka ya taka ya isa inda take tsaye ya miqa mata ledar,cikin ransa yana fadin siyayyar kuwa ta dace da ita "Ga wannan ko babu yawa" sai data dora idanunta kan abbas dake zaune daga bayan suraj din taga ita yake kalla sannan ta saka hannu ta karba gabanta na faduwa "Na gode" ta fada tana ficewa a dakin da hanzari gabanta na wani irin faduwa. Da baya suraj ya dawo a hankali yana hararar abbas "Duk alamar da nake maka ka tashi ka miqa mata don ta fuskanci ma waye abbas din a cikinmu amma kayi banza dani?" "Wai kanason kacemin wajenta mukazo zancan?" Abbas din yayi tambayar hankalinsa kwance,sai haushi ya kama suraj,ya watsa masa harara "Ban sani ba,next time dama idan zaka zo kada ka sake ka kirani,idan kazo kai kadai zaka gane wajen wa kazo din,tashi mu tafi,ka barni ni kadai sai zuba nake". Cikin mota gaba daya kansa ya kwance,me yasa hajiya ta dauko masa wannan?,ta yaya zai samu sauqi ko kulawa daga wajenta,kansa kada,gaskiya bazai iya sake zuwa zance ba,yaje yace mata me?. Yana jin suraj yana ta hirarsa amma bai saka baki ba,saboda gaba daya tunaninsa na ata wani waje,suffarta da kamanninta yaketa qoqarin maidowa idanunsa ya hadasu waje daya,babu qarya.....tana da kyau,ita din kyakkyawace ta gasken gaske,to ko kyawun hajiya ta gani?,sai ya sake girgiza kansa,yasan hajiyan,tasan abun qwarai sarai,bai gano me ta hango masa ba,amma ya tabbatar akwai abinda ta hanga din. Saida suraj ya ajjiyeshi a gida sannan shima ya wuce,abbas din ya masa ban gajiya da godiya "Ai babu wannan tsakaninmu,kawai dai next time ka tafi kai kadai,saboda ka samu ku fahimci juna sosai, she's too young,dole sai kana janta a jiki da dabaru sannan zata saki jiki da kai,amma kuma ina me tabbatar maka indai aka samu shaquwa sabo da kusanci tsakaninka da ita,ina me tabbatar maka.....ina sake fadi ina mai tabbatar maka anan zaka fahimci komai basai an gaya maka ba" abinda suraj ya gaya masa kenan,wanda ya tsaya masa a rai,ya kasa fahimta kuma,da wannan maganar ya kwanta. Ita kuwa widad tana fitowa ta qara da dan gudu gudu,wani irin tsoro takeji da faduwar gaba sosai,don sai data tsaya a hanya tadan saisaita numfashinta tana dafe qirjinta da hannu,batasan me yasa batason wancan abokin nasa yana kallonta ba,to amma itafa wallahi mai wanna zubar maganar indai shine wanda uncle muhsin ya turo mata baiyi mata ba sam,saita tabe baki tana buda ledar daya bata,murmushi ya subuce mata da taga masoyiyar wato chocolate,saita zabura tayi cikin gidan tana qwalawa nujood kira. "Iyyeee,yammatan ummu,da alama ciniki ya fada tunda naga kin dade da yawa" hajjaa ta fada cikin salon tsokana tana murmushi,baki ta tura gaba tana ajjiyewa hajjaa ledar,kanta tsaye cike da zallar wautar quruciya tace "Ni gaskiya indai wannan mai surutun ne bana sonsa" dariya nujood ta sheqe da ita,kafin tace komai hajjaan da uncle muhsin ya bata aikin tuntubar widad din idan ta dawo aji ta bakinta tace da ita cikin tattara hankalinta "Saboda me?" "Ya cika siranta,kuma ya fiya magana" wannan karon nujood dariya harda fadowa "Bafa uncle abbas take fada ba,uncle suraj ne wallahi take nufi" sai hajjan itama ta saki dariya,tasan suraj din,duk da ba sosai ba,amma sai da nujood ta fada sannan ta tuna tabbas yana da kirki yana kuma da hira "To alhamdulillah,indai hakane uncle abbas yayi kenan?" Ta fada tana kallon widad,yadda suka tsareta suna jiran amsarta ya bata kunya,saita dauki filo ta cusa fuskarta a ciki tana dariya cike da jin kunya "Allah nidai hajjaa...."kunya ta sanyata tashi da gudu tayi dakinsu,sai suka bita da dariya,hajjaa taja chocolate din ta ajjiye da nufin idan uncle muhsin ya dawo ta nuna masa kafin su taba,ta kuma hada da gaya masa yadda sukayi da widad din. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 23 Duka dai yanata juya yadda abubuwan zasu kasance har ya gama abinda yakeyi yazo kwanciya,sai ya kauda wanann tunanin ya sake maimaita kiran hafsat amma kamar dai ko yaushe,sai abun ya shiga daure masa kai da kuma bashi tsoro,don haka ya sauya akalar kiran zuwa ga wani constable dake area din nasu,ya aikashi yaje gidansa ya duba masa lafiyarsu,cike da girmamawa ya amsa masa ya kashe wayar ya zauna yana jiran feedback. Bai haura minti biyar ba yayi kiransa "They're fine sir" "Are you sure?" "Yes sir" ya sake tabbatar masa,sai yaji ransa ya baci,ya kashe wayar ya ajjiye yana gyara kwanciyarsa gami da lumshe idanunsa yana furzar da iska daga bakinsa "Dole ya dauki mataki akan hafsat din,abun nata qara gaba yake,wannan zallar raini ne" ya fada a ransa. Washegari daga strolling ya wuce gidan hajiya a qasa,duk da 'yar tazarar dake tsakaninsu sai gashi yaje,saidai ya hada gumi sharkaf kafin ya isa din,hajiya nata masa sannu da fadan bai ganin nisa yayo wannan tafiyar a qafa?, qaramin murmushi ya saki "Hajiya kin manta aikina ne?,tafiya tsaiwa wahala da yunwa duka an koyamana juriyarsu"kai ta jinjina kawai "To Allah ya bamu dacewa" muneera ce ta hado masa breakfast kamar ko yaushe,yau din hajiya bata iya bari ya gama cin abincin ba ta jeho masa tambayar "ya ake ciki?,kaje kuwa?" Kai ya jinjina "Naje hajiya" "Ina fatan komai yayi?" Me zai iya cewa hajiya,bashi da wata amsa data wuce cewa "Alhamdulillahi" ya amsata yana kurbar tea dinsa,sai ta saki murmushi tana jin dadi har cikin ranta,ta sauke ajiyar zuciya "Inaso ayin auren nan a nan kurkusa abbas indai zai yiwu" da qyar ya hadiye bread din dake bakinsa,sannan ya daga idanunsa yana duban hajiyan "Kamar nan da yaushe kike so hajiya?" "Zuwa yaushe zaka shirya dai?" Shuru ya danyi,tunda ta magantu lallai da gaske tanaso ayi a kusa din,koda yaushe babban burinsa shine ya cika umarninta "Kada ka damu,kayi tunani a hankali,ko bayan ka koma ne sai ka fadi zuwa lokacin da kake ganin ka gama shiryawa" "To hajiya" ya fada cikin girmamawa,saidai tuni kwanyarsa tayi nisa wajen tunanin yadda abubuwa suke ta sauyawa suna zuwa masa a bazata. ~~~~~~~~ Sai la'asar ya koma gida,kai tsaye ya shiga bandaki yayi wanka,bayan ya fito ya fito zuwa sassanta don ya samu Black tea,cikin mintuna ya hada ya dawo falon da zummar zama,amma sai ya dinga jin kamar hayaniya hayaniya daga qofar gidan,sai ya miqe ya yaye laluben window din da ya bulla har harabar gidan,harabar gidan fes babu kowa hakanan babu komai,amma qoramar qofar gate din gidan a bude take,ya kuma tabbatar hayaniyar a qofar gidan sosai take tashi,don haka ya ajjiye cup din ya zura slipper dinsa da ya cire ya doshi qofar fita. Tun kafin ya qarasa ya dinga ji kamar muryar hafsa,amma sai ya qaryata kunnuwansa,tunda yasan bata nan,saidai yana dosar waje kunnuwansa na sake ji masa muryar tata. A hankali ya buda qofar ya fita,take idanuwansa suka gasgata masa abinda kunnuwansa suka ji,zallar mamaki ya kusa kasheshi a wajen "Hafsa a bauchi?" Ya yiwa kansa tambayar da bai san amsarta ba,yana sake zubawa hafsa din idanu,wadda bata ma fahimci ya fito ba,ta taqarqare sunata sa'insa ita da wani,nawwara na hannunta,mimi na tsaye gefanta tana riqe da hannunta,maqotansa biyu keta bada baki,yayin da wasu matasa dake sana'ar business center a wani dan container irin na mtn gaban gidan kadan suma suka iso wajen. Yana fitowa daya daga cikin maqotan nasa ya ganshi,da sauri yace "Yauwa alhmdlh,ga mai gidanta nan ma ya fito,mun dauka ai baka nan shi yasa tun dazu bamu yimaka magana ba" dukka idanu suka waiwayo suka zuba masa,take yaji ya muzanta,ya aro jarumta da juriya ya qaraso wajen yana riqe da hannun mimi,wadda tunda ta ganshi ta sheqo da gudu ta maqale ubanta. Qarawa yayi ya miqa hafsa din ita yana cewa "Wuce gida" saboda ganinta cikin mazan ba qaramin quntata masa rai yayi ba,ga kuma baqincikin tahowar da tayi babu izini ko shawara dashi. "Alhaji kayi haquri,amma babu inda zata saita cikamin kudina,zata gane ni din matsiyaci ne na ainihi" fuska a daure abbas ya juya yana dubansa "Kaga,barta ta tafi,za'a biyaka koma nawa ne" "To shikenan alhaji" sai daya tabbatar ta shiga gida ita da kayanta sannan ya juyo ga mutumin "Me ya faru?" Gyara tsaiwarsa yayi yana sake riqe qugunsa "Tun daga tashar kawo na daukota alhaji ita kadai qwallin qwal da sunan shata tayi,mukayi ciniki ita akan dubu sha biyar,sai da mukazo nann sannann zata hadani da dubu goma,wai nayi haquri bata da kudi,kudinta basu kai ba" cikin matuqar bacin rai ya fara laluba aljihunsa "nawa ne cikon kudin naka?" "Dubu biyar ne ranka ya dade" mai motar ya fada cikin matuqar jin dadi ganin hakkinsa zai fiti,sai ya irga ya miqa masa,yasa hannu ya amshe yana godiya,ya juya yana komawa motarsa "Lamarin mata sai haquri,tun dazu muketa qoqarin raba rigimar mu bashi kudin amma taqi saurararmu,Allah dai ya kyauta" maqotan nashi suka fada,gaba daga kunya ta gama baibayeshi,kamar shi matarsa tana fada dame mota akan cikon dubu biyar,bayason tsaiwa bare suja wata doguwar magana,duk da sunyi qoqari kuma alkhairi sukayi masa,sai ya basu hannu sukayi musabaha yana musu godiya,ya juya ya shige cikin gidan,xuciyarsa da rayuwarsa na wani irin quntata,wannan wanne irin kwance zani ne a kasuwa tayi masa?,me ma takeyi a bauchi?,wa ya bata ikon tahowa?,da wadan nan tambayoyin ya saka kai cikin gidan,kai tsaye ya zarce sassanta. Yana sallama cikin falon su mimi suka taho da gudu suka rungume qafafunsa,ya duqa ya daukesu gaba dayansu yana musu oyoyo,ba tare da ya zauna ba yake qarewa falon kallo,bata a ciki,saidai kayansu da suka taho dasu watse a falon,yawan kayan ya tabbatar masa gaba daya kayansu ta debo daga can,ya jinjina kai ya sauke yaran yana kunna musu tv "Ku kalli cartoon ina zuwa" ya fadi yana shafa kansu,mimi dake da wayo ta gyada kai ya wuce ciki. Daya shiga tana toilet,don yaji motsin ruwa,sai ya harde hannayensa a qirji ya jingina da jikin madubinta yana qarewa dakin kallo,a hargitse dakin yake,babu kintsi kwata kwata,da alama tun sanda zasu tafi kadunan haka ta barshi. Tana motsa qofar ya mayar da dubansa kai,sai gata ta fito da alama alwala ta daura,ko sallar la'asar dinma bata samu yi ba kenan,suna hada idanu ta daure fuskarta da kyau,batason ta karaya ko yayi mata kwarjinin da zata kasa fadin maganganun dake cikinta,ta dauke kai kamar bata ganshi ba tana nufar inda abun sallarta yake a watse a qasa zata dauka "Yaushe kika nemi izinina da har kika baro kaduna kika taho bauchi?" Dagowa tayi,tanason dubansa kai tsaye amma tasan tayi qarya,a kaikaice take duban gefansa "Saina nema izininka?,tunda bani da amfani ai ya kamata na shaida hakan,na baka waje,mutumin da bashi da kimar da za'a bashi sabuwar mota kaga wacce daraja gareshi?" Idanunsa ya lumshe yana ambatar sunan Allah,wani abu ya tsaye masa a wuya,tabbas inda shi madokin mata ne yau din nan sai ya tsitsinkawa hafsa mari,banda tsabar hauka a yanayin da ake ciki na matsalar tsaro da aka fara fuskanta tana matar ASP zata debo yara har guda biyu su kamo hanya ita kadai?,sannan duka ba tare da wata hujja mai qarfi ba illa dai kawai yaqi canza mata mota?. "Kinsan abinda kikeyi kuwa?" Ya fada bayan ya bude idanunsa yana dubanta "Na sani mana" ta amsa shi kanta tsaye,sannan ta dora "Ai babu dole,yadda ban maka dole ba nima bazakamin ba,kowa yayi abinda ransa yakeso,Kaduna ne bazan zauna ba,ka nemo wadda zata zauna da kai cikin wadanda kake baiwa kyautar" sosai maganar ta dakeshi,wani bacin rai ya lullubeshi,ya bude bakinsa a zafafe mimi ta turo qofar riqe da.hannun nawwara,dole ya hadiye abinda ke taso masan,sannan yabar jikin madubin yana dosar qofa "Hakane,kiyi abinda ranki yakeso,nima zanyi abinda raina yakeso,zan baki mamaki tabbas wannan karon hafsa kamar yadda nasha fada,zan kuma nemo mai zama dani din" daga haka ya fice ba tare da yaja mata qofar ba. Da kallo ta bishi,haka kawai cikin jikinta taji jikinta yayi sanyi,yadda yayi maganar kamar he's serious,amma kuma data tuna ya saba fada dama sai ta tabe baki kawai,tasan ya fada ne kawai saboda yayi mata barazana,don haka ta karkade abun sallarta ta shimfida tana cewa "Mu bawa juna mamaki dai" ta sanya hijabinta ta tayar da sallar. Sanda ta idar yaran nata mata rigimar yunwa "Ba uban da zai sakani wani shiga kitchen na kwaso gajiya" saita laluba jakarta ta fito da biscuit da lemon roba guda daya ta miqa musu,maimakin ta tashi ta gyara koda dakin nata ne daya cika da shara da qura,sai ta koma saman gadonta ta miqe abinta,ta dauki wayarta ta fara chart. Hankalinta kwance take chart dinta,yaran nata basu qoshi bama babu wanda ta kula,ba jimawa kira ya shigo wayarta,data duba sai taga yayarta ce,ta gyara kwanciyarta tana saka wayar a kunnenta. Bayan sun gaisa take ce mata "Ana hada gudunmawar bikin nafisatu ne,nace bari nayi miki magana,don an kusa gama hadawa" take ranta ya baci fara'arta ta janye,bata qaunar abinda zai sanyata fidda kudi,itafa abu indai ba abbas bane zaiyi mata shi to ta gwammace ta haqura da yinsa koda ita zata amfana,a yanzun kuwa da suketa uwaka ubaka dashi ba zata ma dosheshi da wata buqata ba,da sai ta lallaba ta karba wajensa,ta zabge rabi ta basu rabi "Nifa gaskiya anty shamsiyya bani da kudi" takaici da haushi ya kamata,suna ganin yanzun mijin hafsatun ya fara danshi danshi amma ko daya yarinyar bata banbaruwa "Ke dama kullum cikin babu kike,to ba kyauta nace ki bani ba,contribution ne na biki,idan zaki bayar ki bayar,idan baki bayarwa ki fada ki daina batan lokaci" murya a cunkushe tace "Nawa ne kudin?" "Dubu goma goma ce ba wani kayan gabas ba,kuma ko atika da bata da wani qarfi tuni ta bada nata" "Shikenan zanyi shawara,zan kiraki idan sun samu" bata amsa mata ba ta kashe kiran,hafsa taja tsaki tana gyara kwanciyarta,gaba daya sunbi sun dameta ba gaira ba dalili. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 24 Kai kawo ya dinga yi cikin dakin,ransa na masa suya,me zaiyi ya huce takaicin hafsa?,yasan dai tabbas bazai qyaleta ba,anzo gabar da dole ya koya mata lesson kamar yadda yasha fada. Idanunsa suka sauka akan wayarsa,sai ya jawota da hanzari ya fara kiran layin hajiya,bugu biyu ta daga "Abbas ya akayi?" Ta tambayeshi da mamaki,ganin bai wani jima da barin gidan ba,qoqarin dai daita muryarsa yayi,don bayason ta fuskanci akwai wata matsala ne ta tashi hankalinta "Lafiya lau hajiya,cewa nayi zai yiwu a gabatar da neman auren cikin satin nan?" Kai ta jinjina cike da mamaki,anya babu walakin goro a miya? "Eh to,saidai na nema kawunnanka naji" "Idan zaiyuwu hajiya kawai ayi,na shirya" tana saurin gano damuwa da kuma fushinsa,yadda yayi maganar a jikinta taji akwai damuwa,amma zata tambayeshi a hankali "Shikenan,zanyi magana dasu,duk yadda ake ciki zaka ji" "To hajiya na gode,gobe da yamma zan wuce,zan shigo ta nan kafin na wuce din in sha Allah" "To ba damuwa,Allah yakai mana rai" daga haka sukayi sallama. Cikin mamaki take sauke wayar,saidai kuma ta samu kanta da sakin murmushi tare da fadin "Alhamdulillah" zuciyarta na gaya mata wataqila akwai alkhairi mai tarin yawa a abun,shi yasa Allah ya kawo komai a kurkusa haka ya sauqaqe matsala da damuwa. "Tofa,ta samu kenan hajiya?" Faccalarta da suke tare a falon,ita da yayar abbas din mai suna mabruka suna hira ta fadi,wayar ta ajjiye gefe tana cewa "Aure ne ya tasowa danki" da mamaki ta kalleta "D'ana,wa kenan?" "Abbas mana" kallonta sukayi gaba daya cike da mamaki,abbas din da kowa yasan dabi'arsa,mutumin da ko auren hafsa dinma kamar bazaiyi ba saboda tsabar I don't care manner irin nashi da rashin baiwa lamarin soyayya muhimmanci? "Abbas din yaushe har yaga wata yanaso?" Faccalar tata da yara ke kira da gwaggwo fanteka ta fada "Tayani tambaya gwaggwo,na dauka ma bashir ko yaya sa'id zata ce,ko kuma Sunusi" kai ta girgiza tana murmushi "Abbas ne" kai suka jinjina su duka,mabruka tace "Ya cancanci ya qara aure dama tuni,wannan rayuwar da akeyi a gidansa bata da ma'ana sam,naga qoqarinsa ma,ganin baida wannan ra'ayin yasa ban taba tuntubarshi da maganar ba,ga 'yammata nan cike a dangi,ya zabi wata ya qara ko zai samu sassauci,haba abun na hafsa yayi yawa" kai gwaggwo ta gyada itama "Gaskiya dai,yammata kyawawa fa gasunan masu hankali,ita wannan din a ina ya samota?,cikin yan uwansa ne?,amma banji batun ba sai yanzu?" Gwaggwo ta fada cike da son jin wace?,tana fata ya zamana cikin yaranta ne,duk da tasan zaiyi wuya,don inda cikin nasu ne da tuni ta fahimta,amma rabonta da abbas a gidan tun sanda tayi wata rashin lafiya ya shiga ya dubata "Ba cikin dangi bane,wata yarinya ce diya take a wajen muhsin abokinsa,dukkanku ai nasan kunsan muhsin?" Ta fada tana kallon fuskokinsu, gwaggwo da tuni fuskarta ta sauya tace "Qwarai kuwa" sai hajiya ta dora "Yarinya ce ma,amma nutsuwarta da hankalinta ya bani abbas din xai samu nutsuwa a gidansa,zai kuma ce ayi ayi,a bari a bari" "Turqashi" gwaggo fanteka ta fada ba tare da tasan kalmar ta fita a bakinta ba,wani bacin rau na motsa mata,yaron da dukkan alamu suke nuna zaiyi arziqi cikin dangin nasu,taketa qulafucin ganin ta samu ta jogana diyarta,lokaci daya hajiyan ta wargaza fatanta da burinta ta dauko wata bare ta maqala masa?. "Banda abun hajiya ruqayya,gida bata qoshi ba za'a baiwa dawa?,gamu da yaran yammata duka sun tasa saiki dauko bare ki bashi?,duk da itama hafsan akwai alaqa amma ai baiyi alaqar sa da yaran kawunnansa ba ko?" Gwaggo fanteka ta fada tana dora murmushin yaqe kan fuskarta "Gaskiya nima wannan tunanin yazo min" mabruka ta fada tana gyada kai, murmushi hajiya tayi "Auren dangantakar ai bai amfana komai ba gwaggwo,gwara a gwada baren ko a nan za'a dace ko?" Kai ta kawar tana tabe baki,bacin rai iya bacin rai yana cikata,wanann babbar dama haka za'ayi asararta?,suna ji suna gani "Da dai kin sake tunani gaskiya,duk yadda bare yake da dadi ai baikai dadin dan uwa ba" "Hakane" ta amsa mata a taqaice,tasan halin gwaggwon da mita,ita kuma dama can bamaison dogon magana bace,gwggwon na daya daga cikin masu kushe aikin dan sanda a sanda abbas ya samu aikin "Dan sanda?,me na sama yaci ballantana ya baiwa na qasa?,kayan cin hanci da rashawa" wannan shine abinda taji tana fada sanda hajiyan taje gidan da kanta tana shaidawa kawunsa mijin gwaggwon cewa ya samu aikin,tun daga matakin constable saai yanzun da daukaka ta fara zuwa masa ake kwadayin hada zuri'a da ita?,duk haqurinta da kawaicinta ita din ba mahaukaciya bace. Hirar duka saita fita akan gwaggwo fanteka ta zama mara dadi,don haka bata jima ba ta miqe ta yiwa hajiyan sallama ta fice. *WIDAD* Sanda ta bude ido ta ganta qofar gidansu sai taga kamar wasa,kasa jira tayi drivern da uncle muhsin ya daukar mata shata har qofar gida ya fidda mata kayanta,ta sauka daga nan ta nufi gate din da gudu gudunta,ji take kamar zata bude ido ta ganta ta koma bauchi. Cikin sa'a kuwa tana buda gate din ummun ta hanga tsaye a farfajiyar gidan ita da kawunnanta,sanye da atamfa da kuma hijabi,hannunta riqe da carbi,da alama salla ta idar suka tasota,akwai zancan da sukeyi. "Ummunaaa" ta fada da qarfi sannan ta kwasa da gudunta,ta isa gabanta ta fada jikinta tana ruqungumeta. Sai da ummun tayi taga taga zata fadi kawu ya tareta "Ashsha,ashsha,zata kada mana uwa" sai ta saki dariya tana sakin ummun suka miqe tsaye dai dai ummun itama tana dariya idanunta akan fuskar widad din,kamar fa shekara bata ganta ba. "Ke dawa?,yanzu kike tafe?" Ummu ta fadi tana dubanta "Ni kadai yanzu yanzu na qaraso" "Iyeee,muhsin din barmin ke yayi ke kadai kika kamo hanya?,tabdijan ,zamu hadu dashi kuwa"kafin ta qarashe drivern uncle muhsin din ya shigo da jakankunanta,suka gaisa yace zai koma,ummu tace a'ah sai yaci abinci,suka wuce ciki ita da widad tace taje ta kawo masa abincin,su kawu kuma suka fice bayan an bashi wajen zama anan farfajiyar gidan. Zuwa wani lokaci sai ga sassan ummu ya dan cika da sauran yaran gidan,su Aafiya rafi'ah fareesa da sauran wadanda suke shekaru kusan daya,sun baibayeta tana ta basu labarin bauchi. "Kano fa tafi dadi Allah" ta fada daga qarshe tana yamutsa fuska,dariya sukayi mata "Daga baya kenan,bayan kin gama kwanakinki" dariya tayi tana cewa "Da gaske nake muku,bari kuga" sai ta wuce daki ta janyo jakarta,ta fidda jakar ledar kayan makeup din da hajjaa ta damqa mata tace inji abbas,tunda ta taho kayan suke daukan hankalinta,komai na ciki ya burgeta ya kuma yi mata kyau,harda takalmi me tsini irin nasu basma da aka sako musu a lefe,tayita maitar takalmin sai basman ta jefa mata harara "Ba baki zanyi bafa,kiyi addu'a kema Allah ya kawo me siya miki" fushi tayi tana tura baki tabar gurin,sai gashi ta sameshi sama ta ka,bayan shi harda mayafi da hand bag qarama mai matuqar kyau,a nan ta zazzage musu kayan,suka dinga santinsu,daga baya ta daukarwa kowa wani abun daga cikin kayan kwalliyar. ************* Kwana biyu a tsakani tana kitchen tana cin abinci suna hira da latifa,ta ajjiye warmer din data zuba abincin alhaji a ciki tana cewa "Ashe dan bauchi kika samo mana kuma" kallonta tayi tana ci gaba da cin abincinta,don ita har ga Alla ma ta manta da wani batu "Dan bauchi?" "Eh mana,naji abba mahmudu yazo suna zancan da alhaji ai" "Auho,wai abokin uncle muhsin" "Shifa" sai widad din tayi shuru kawai,don batasan me zatace ba,itadai ba sanin soyayya tayi ba bare ta tantance tana sonsa ko bata sonshi,kawai dai taji bata damu ba bata takura ba kamar sands ake zancan mahfood da ma'aruf. Sosai ummu ta dinga juya zancan bayan da mahaifin widad ya zartar da cewa an bawa abbas widad don,amma bata taba kawo cewa zasu nema aurenta a nan kusa ba haka,taji abun sosai a ranta,a yadda ta lura kuma shi mahmudu din a shirye yake da auren diyarsa,tasan watarana komai tsahon zaman da zatayi da qaunar da takewa widad su rabu dole ta aurar da ita,so a yanzun bataga nata hurumin da zata hanashi bada auren 'yarsa ba,tunda dukkan bincike da shaidu sun tabbatar da nagartar me neman auren kamar yadda musulunci yayi umarni. Amma babban abun shine,kishiya daya tabbata widad din nada ita,ta yaya yarinya kamar widad din zata iya fuskantar abu me wahala da zafi kamar kishi?,bata sani ba,saidai tana fatan ko mai zaizo da sauqi fiye da yadda suke zata. Kwanan widad din biyu da dawowa maneman auren abbas din suka iso kano qarqashin jagorancin uncle muhsin,sunga karamci irin na kanawa,duk da cewa su din ba kanawa bane usul,amma tunda an haifi 'ya'ya da jikokinta suna amsa wannan sunan. Cikin girma da mutunci gami da karamci suka gabatar da neman auren abbas ga widad din,aka sake jaddada basu,suka nema alfarmar karbar kudin aurensu harda sadaki,take alhaji yasa aka karba komai,suka karbi roqonsu na daurin auren sati mai zuwa. A ranar zancan auren widad ya fara yawo a dangi,abinka da family house,kowa idan yaji zai gayawa na kusa dashi,bugu da qari widad din 'yar gatan ummu,mai masoya da kuma tarin abokan adawa. "Uhmmm,sunje sun zaba mata miji ba,ai dama wannan yadda akaci buri a kanta nasan sai me abun hannu zasu bata" wannan shine abinda wasu suka dinga fada,musamman da suka samu labarin muqamin da ya riqe a gwamnatin bauchin,da kuma wanda yake kai yanzu,gani sukeyi uncle muhsin ya dauketa ne dama kawai don ya aikata hakan. Ita kuwa sam batasan ma me akeyi ba,don har ta koma islamiyya,wadda tun tafiyarta qaunar makarantar bata bar ranta ba,sanda ta koma din sai ta samu basu wani tsere mata ba,tunda ta dora daga inda ta tsaya a bauchin. **********Karfe shida saura na yamma suka iso gidan ita da Aafiya rafi'ah da widad din,bayan tasowarsu daga islamiyyar,gab da zasu shiga gate din gidan Aafiya ta kalleta "Nifa zancan bikinki naji ummanmu tana yi,wai nan da sati daya" "Nifa abinda yake hadani dake tsokanarki" widad ta fada tana watsa ragowar alawar data siya cikin jakarta "Wallahi nima haka naji,don kafin mu tafi islamiyya naji umma tana waya a karbo atamfofi akai mana wajen mai dinki" "Mahaukata,sai kuyi ai" widad din ta fada tana yin gaba abinta tana dan waqenta. Bata ma tsayasu ba ta zarce sassan ummu abinta,tana sallama a falon ta soma zare hijabinta daya dameta,gashinta mai santsi ya ware,don dama ita din ba ma'abociyar saka dankwali bace,tafi sanya hula,itama ba ko da yaushe ba,sai ummu tayita fama da ita. Ummu da anty halima ne a falon "Anty halima ina nabiha?,kikace idan zaki sake zuwa tare zaku zo?" Widad ta fada tana barewa alewan ta tura bakin yaron anty halima dake kan cinyarta. Da kallo anty halima ta bita,tana dan jin tausayin widad din "Oh ni sadiya?,wannan wacce irin amarya ce ummu?" Dan murmushi ummun tayi,ita kanta tausayin widad din takeji,har yanzu ma bata zauna tayi magana cikakkiya da ita ba kan auren da tasan widad din batasan meye shi ba,bata kuma da labari cikakke akan yinsa. "Au ina yini?" Ta fada tana dariya bayan ta tuna nata gaidata ba,ba kuma tare data maida hankali ga maganarta ta farko ba "Lafiya lau widad,nabiha zasuzo,sai satin biki in sha Allah" "Allah ya kaimu" ta fada tana gyada kai hankalinta kwance,saita dubi ummu a shagwabe "Yunwa wlh nakeji ummu,dazu banci abinci ba Aafiya ta matsamin na taho mu tafi" "ki wuce latifa tana kitchen ki karba" "Tom" ta fadi tana wurga jakarta ta zarce kitchen din,yayin da dukka su biyun suka bita da kallo. Ummu ce ta fara dauke idanunta tana sakin ajiyar zuciya,anty halima tace tana dariya "Wai,wa yaga widad amarya" kai ummu ta kada "Tausayinta nakeji halima,ban taba kawo rabuwarmu a nan kusa ba" tabe baki anty haliman tayi "Kaji ummu,to mu da aka rabu damu din tun bamu kai haka ba me ya samemu?,gamu ragal damu?,itama zata ware ne kamar kowacce mace" kai ummu ta girgiza "Ba zaki gane ba halima,dukkanku kunfi widad wayo sanda aka muku aure,kawai don lokaci yayi ne ba yadda zanyi,amma ban shirya kaita wani uwa duniya ba" "Tunda dai babanta ya bada ita,alhaji kuma ya goyi baya dole saidai ayi haquri,yanzu kawai yadda za'a tattarata akaita bata iya komai ba,kunbi duk kun shagwabata,bata iya komai ba,komai yi mata akeyi" anty halima ta fada tana mele baki,ta rasa wanne irin so ummun takewa widad?,tamkar ma ba mahaifin widad din ta haifa ba,ita ta haifa,ko ita diyarta ta cikinta bata jin tana mata son da takewa widad din. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 25 Murmushi kadan ummu tayi,qarara ta hango kishin widad a idanun halima,ta rasa me yasa haliman ta kasa sabawa da hakan,sai ta gyara zama "Mu dinma uwayenku da sanda aka aurar damu banajin munkai ya widad din,a gidan muka iya abubuwa,tun mun kwamacala har muka qware,yanzu gashi ba'a ce mune muka haifeku ba" kauda kanta anty halima tayi,tasan dama duk yadda takai bakai isa ka fadi wallen widad ko ka kusheta ga ummun ba. Yau din tun qarfe takwas ta qudunduna a bargo cikin dakin ummu,bayan ta gama qarewa kayan data gani jibge a dakin ummun kallo,tun shekaran jiya taga ummun nata jibge kaya a dakin nata,itadai bata ce ga dalili ba,ta dan tura baki taja bargo abinta,bacci yau takeji da gaske,don ko sassan anty madina da aka cika ana hira yadda aka saba taqi zama,bugu da qari kuma yadda suketa faman kiranta da sunan amarya,wanda ta dauka duka tsokana ce irin tasu yau ta sauka a kanta suka tasota gaba,ita kuma bataso. Fakare tayi tana jiran bacci ya iso,gefe daya tsoro tsoro takeji saboda ummun tana wajen dattijon mijinta,buda qofar dakin akayi a hankali,sai ta tada idonta tana kallon me shigowar ba tare data tashi ba,ummun ce,hannunta dauke da babbar baqar leda "Yauwwa,gwara ma da bakiyi baccin ba,tashi" kai tsaye ta miqe din,don itama tanason yiwa.ummu tambayar "Ummu...wai wannan kayan,na wanene duk sun cika miki daki?" "Kayan aurenki ne" ta amsa mata gaba gadi tana kallon fuskar widad din,cike da fargabar yadda zata kalli zancan,kada ta watsa musu qasa a ido. Idanun ta fitar,fuskarta babu wani emotion saina mamakin "Aurena ummu?,duka wadan nan kayan?" Kai ta gyada mata "Eh,harda wasu ma" ta fada tana bude mata ledar "Wannan babanku yace ki zaba iya wadanda kikeso za'a dinka miki" da mamaki ta sake duban ummu "Wai duka nawa ne?" "Kadanma kika gani shalele ta,za'a kawo lefe a kawatuna duka naki" murmushi ya subucewa widad,kawai taji farincikin na kamata "Harda kayan kwalliya ma irin nasu anty ramziyya?" "Sosai,inajinma yafi nasu" ta fada tana murmushi ganin bata dauki zancan da zafi yadda ta saba ba,da wannan hirar ummun ta dinga hilatarta tana jaddada mata zancan auren,quruciya ta sanya widad din bata wani damu ba,saima cika da tayi da zumudin zuwan ranar da za'a kawo mata kayanta,wanda ummun tace mata sai ranar daurin aurenta. ********Wasa gaske saiga shirin biki nata kankama daga bangarensu widad,sam bata wani damu ko daga hankalinta ba,abinda ya baiwa kowa mamaki,yayin da wasu kuma hankalinsu ya kwanta ganin bata qi yadda ta saba ba,'yan adawa kuma fadi suke "Shegiya dama da guntun wayonta,gashi tayi luff kamar ba ita taqi 'yan uwanta har mutum biyu ba" oho,ita dai sabgar gabanta takeyi kawai,tana lissafin ranar da za'a kawo mata kayan kwalliya. Daga bangaren su abbas kuwa maganar ta fara yawo,da yawa daga cikin dangi wadanda sukaci burin zuwan wannan rana,ranar da abbas zai qara aure labarin baije musu a dadi ba,wadanda suka jima suna addu'ar hajiyan ta sanyashi qara aure saboda halayen hafsa,duk sai gwiwarsu tayi sanyi,hajiyan ta musu ba zata,irin abbas din shi kowa ke kwadayin samu,saboda alamun wadata da aziqi dukka sun fara bayyana a tattare dashi. Tabbas hajiyan tasan da wannan,shi yasa tayi musu wannan ba zatar,ta kuma zartar da wannan hukuncin,fatanta daya abbas din ya samu inuwar da zai huta,ya kuma samu sanyin idaniyarsa. Har a sannan hafsat din bata da labari,gidanta ba gidan zuwan 'yan uwan abbas bane,bama su kadai ba,hatta da nata dangin,saboda wata iriyar jarrababbiyar rowa da take da ita,muguwar sa'a ka taka idan kaje gidan ka samu tarbar pure water bare abinci,kusan anty ummee ce kawai ke samun wannan daga gareta,shi kuwa abbas,bayan ya ajjiye wa hajiya dukkan wani abu da yasan zata iya nema daga gareshi,komawa yayi kaduna,amma yace mata cikin satin daurin auren zaiyi qoqarin zuwa da wuri,da fatan alkhairi ta bishi,domin kuwa ita ya gama mata komai,sai fatan dacewa bisa niyyar alkhairin data nufaci rayuwarsa dashi. ************ Daga can tsakiyar 'yan jaridar dake dauke da nau'ikan kayan aiki daban daban,ASP ABBAS SARKI ne tsaye,sanye da uniform din 'yan sanda daga dace da structure na jikinsa,ya kuma yi masa kyau ainun,iya yadda yake tsayen kadai ya isa ya gaya maka cewa jajirtaccen police ne,wanda ya qware a aikinsa "Wannan shine abinda ya faru a taqaice,we will let you know when the investigation is completed". Sai ya zare hannunsa daga aljihu yana shirin wucewa,amma suka sake yunquro masa da tarin tulin tambayoyinsu,rasa wacce zai amsa yayi,saidai akwai wani cikinsu da yafi kowa matsa masa da tambayar "Amma yallabai,labari ya iskemu cewa kai da kanka ka gudanar da wannan aikin,kuma kaine ka samu nasara cafko su,shin meye gaskiyar wannan al'amari?,don dama jama'a sun dade da saninka da kuma ficenka wajen gudanar da aiki?" Wani miskilin murmushi yayi wanda yake cike da tarin gajiya,murmushin da har yau hafsa ta gaza gane irinsa har sai ya buda baki ya magantu,yasa hannu ya cire hular police din dake kansa mai zubin P-cap,cikin muryarsa mai zurfi da kwarjini ya fara amsa tambayar tasa,bayan tarin jama'ar dake wajen sunyi shuru suna jiran amsa "Ko ni nayi wannan aiki,ko bani nayi ba nasara ce,nasarata kuwa nasarar dukka jami'an tsaro musamman na 'yan sanda dake wannan qasar ne,muhimmin abu aci gaba da yi mana addu'a,fatan nasara" ya fada yana saluting nasu,sannan ya juya sa sassarfa ya shige ciki gudun kada su sake tsaidashi,sai wajen ya rude da muryoyinsu cikin farinciki kowanne na bawa kafar yada labaran nashi cikakken jawabi. Tsaye yayi gaban table din office dinsa bayan ya ajjiye hular hannunsa a kai,saiya zare agogonsa ma ya dorashi saman hular,ya furzar da iska yana duba lokaci,ya riga yayi alqawarin barin Kaduna a yau zuwa bauchi,lokaci yanata quracewa ba tare da ya shaidawa hafsa komai ba,yanason ta fara ji daga bakinsa shi yasa ya hana kowa ya gaya masa,duk haukar da zatayi ta yita ta gama,yasan tabbas akwai case babba Uwa uba kuma mai girma gwamnan bauchin yanason ganinsa,ya bashi appointment gobe da yammaci,zai sameshi gidan gonarsa,to dole tafiya ta kamashi a yau,saidai yana jin komai ma zaizo masa da sauqi da yardar Allah,tunda aikin da yake kwana ya kuma tashi dashi ya kammalashi,duka suspect dinsu suna hannu. Wayarsa ya ciro da sirritaccen layinsa da ba kowa ya sanshi ba,ya kira wata number yayi confirming samun flight daga kaduna zuwa bauchi sannan ya aje wayar,ba kasafai ya fiya zirga zirga a jirgi ba,yafi ganewa yayi driving da kansa wani lokaci,yana tafe yana karantar hanya da inda tsaro yayi qaranci ko kuma inda komai yake tafiya dai dai,amma a yau din bashi da zabi illa yabi jirgin. Taku biyu ya qara kamar zai fita,sai kuma ya fasa,ya sake daukar wayar yayi kira na sakanni ya ajjiye,ya shiga toilet ya kama ruwa sannan ya fito,ya duba dukka wani abu da yake da buqata cikin office din ya hada waje guda,bayan yayi wasu rubuce rubuce a wasu files sannan ya fito. Daya daga cikin juniors dinsa ne yake driving nasa zuwa gida,yana a motar ya kira hafsat din don ya shaida mata tahowarsa,mimi ce ta fara daga wayar,sai data gama shirmenta sannan uwar ta karba wayar "Kuna lafiya keda yaran?" Ya fadi don yasan zaiyi wuya ta fara tambayarsa lafiyarsa kota gaisheshi "Lafiya qalau muke" ta amsa masa cikin ranta tana mamakin yadda ya sauko daga laifin data masa haka da wurwuri,duk da dama shi din bai cika riqo ba,amma a yadda taga ransa ya baci jikinta yayi sanyi,ta kuma aza zai mata hukunci mafi tsauri ne "Am on my way to bauchi in sha Allah,two to three hours" "Tooo....basai Friday ko Saturday ba?" Goshinsa ya murza kadan,ya salam,a nashi zaton tayi murna da yace zai dawo din ko?,amma saita buge da tuna masa ranar dawowarsa batayi ba? "Na sani,inda muhimmin abu ne da zanyi a nan" "Okay to,a taho mana da tsaraba" "Yayi.....me zan samu?" Ta fahimci sarai me yake nufi,amma sai tayi kamar bata gane din ba "Kamar me kenan?" Ta fada tana dan bata fuska,duk da ba ganinta yakeyi ba,zai dawo yanzu zai fara damunta da tsarabe tsarabensa. "In so samu ne tuwo nakeso" tanason musa masa amma kuma batason bata saukowa da yayi daga fushin da yayi da ita ba tare data bashi haquri ba "Xan qoqarta" ta fada cikin ranta tana jin ba zata iya yi ba "Alright,saina qaraso" ya amsa ta ba tare da yaja doguwar hira da ita ba. Bai wuce hutun awa yayi cikin gidan nasa ba,ya shirya ya wuce airport,gab da sallar isha'i cikin gidansa tayi masa, samuel ne yaje ya daukoshi ya ajeshi,ya shiga gidan nasa dauke da jakarsa,wata a hannu wata a kafada,sabida baya barin kowa da kowa ya shiga masa gida. Yana shiga falon yanayinsa ya canza gaba daya,saboda qarancin tsafta da falon yake da,babu wani alamun qamshi ko qanqani da zaka iya ji daga falon,wala'alla ma idan ka taki mummunar sa'a hancinka ya iya shaqo maka qauri mara dadi dake ratsowa tun daga kitchen din dake falon zuwa hancinka. Wannan ba baqon abu bane a wajensa,yayi fada yayi nasiha amma jiya iyau babu wani ci gaba,saidai yaci gaba da haquri kau da kai da nusashe ta,duk da hakan tana ganin kamar gazawarta yake gani,tunda dai tana iya nata bakin qoqarin a ganinta. Yaran da suka garzayo suna masa oyoyo ya daure ya duqa ya rungumesu cikin jikinsa,ko daya babu wani kyakkyawan yanayi a tattare dasu suma,ita kuwa saita aje wayar hannunta tana dan sosa kai irin na marasa gaskiya,tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa. Amsawa yayi yana kallonta,wani hargitsatsen kaya ne a jikinta,atamfar dake jikinta ya soma gajiya da ganinta,idan zai iya tunawa da ita tazo gidan,kuma har yau ta gaza bada ita kyauta saboda tsabar baqar rowa,sau tari yakan tambayi kansa menene amfanin karatun da hafsa tayi?,tabbas da yasan haka zata ci gaba da kasancewa,baiga abinda zai sanya ya barta ci gaba da karatun ba,don wadan nan dabi'un nata babu wanda zai gani ya dauka yasan bihim a boko. "Muje ku rakani na shirya" ya fada yana kada kan yaransa,saita bi bayansu da harara "Agwagwa sarkin wanka" tafada,don tasan zuwa zaiyi ya hada ruwa ya musu wanka,ita duka ba wannan bane ya dameta,yadda dafa dukan shinkafar da tayi masa ta kama ta kuma yi qauri da kyau,ta yadda zata masa bayani take tunani,tasan halinsa,sarai baya wasa da cikinsa,ya baiwa abincinsa muhimmanci sosai. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 26 Koda ya shiga sassansa sai yaji dama dama,duk da cewa akwai qura data dan shishshigo masa amma kuma babu wannan dattin da annakiyar ta sassan hafsat,bai gaji sosai ba kasancewar tafiyar jirgi ta banbanta data mota,don haka ya ajjiye yaran saman kujera sunata masa hira,yahau kakkabe sashen nasa da goge goge,sai da yaga komai ya dauki haske,sannan ya hada ruwa yayi musu wanka da kyau,yana wasafa yadda zai samu lokaci yakai mimi a wanke mata gashinta. Sai da ya gama shiryasu sannan yayi nasa wankan,ya shirya cikin kayan barci saboda tara ta gota a sannan,kamar ya kirata yace ta kawo masa abincin nan amma sai ya fasa,ya tasa yaran a gaba suka koma can. Tana kitchen tana ta kaca kacar yadda zata hada masa koda coleslaw ne mimi ta shigo tace tazo inji daddy, saita maida.kayan hadin data debo din kawai,ta kwashi warmer da plate din ta biyo bayan yarinyar,tana dan hade ranta,wai koda hakan zai sanya yaji shakkar mata magana ko fada. Saidai kuma ya bata mamaki,saboda yadda yakecin abincin yana yiwa yaransa hira ba tare da yace da ita komai ba,can qasan ransa yana ji ne kamar ya furzar da abincin daga bakinsa,duka dai yana daurewa ne saboda muhimmiyar maganar da zaiyi mata. Koda ya gama cin abincin bai tashi a wajen ba,sunta hira da yaransa yana biyewa shirmensu,duk da hirar babu wani armashi,ita kuwa gogar tana zaune a gefa tana danna waya,abinda tafi kauri kenan,bata wani damu da hira da miji ba sam,lokaci lokaci takan dan sanya musu baki a hirar,a haka har nawwara dake saman cinyarsa tayi bacci,jimawa kadan mimi ma ta soma gyangyadi "Gwara ki kaisu daki ko?" Yace da ita yana dubanta,saita aje wayarta tana dan bata rai "Sai da nace ma mimi ta wuce daki idan ta fara jin bacci fa" "She's too young da zata gane hakan ai" qarasowa tayi ta soma tashinta cikin hararrami,ya dakatar da ita cikin dabara ya daga yarinyar,ta kama hannunta suka wuce daki. Ba jimawa ya miqe,ya nufi kitchen don dafa tea,saboda ba wani sakin ciki yayi yaci abincin ba. Da kallo yabi kitchen din saboda uban wanke wanke da ya fara cin karo dashi,kana gani kasan ba iya kwanukan yau bane,saboda wasu ma sun fara bushewa wasu kuma sauran abincin ciki ya fara rubewa,kai ya girgiza takaicin na cinsa,ya matsa ya duba ma'ajiyar tukwanenta,cikin taimakon Allah ya samu wata wankakkiya,ya hada komai da komai ya tsaya ya jira ya tafasa ya juye ya dawo falon ya zauna ya fara kurba a hankali yana kallon labarai da ake haskowa a tashar alhadath,saidai sam ba ta nan hankalinsa yake ba,yana jiran jin fitowar hafsa ne,amma har ya gama babu ita ba dalilinta,wannan yasa ya miqe ya nufi dakin kansa tsaye. Yana tura qofar suka hada ido,tana kwance tsakiyar yaran,ya qarasa shiga ciki a hankali hannayensa zube a aljihun wandonsa yana nazarin dakin a fakaice,komai babu kintsi,ko ina ba'a gyare yake ba,sai ya kauda kai ya maida gareta "Zan wuce daki,wa zan daukar miki a cikinsu,coz na fara jin bacci,inason kuma muyi magana dake" fuska tadan yamutsa kadan "Kawai ka kwanta a nan mana,ni bansan me yasa bakason kwana a dakina ba,saidai ni kullum ina yawon binka?" Ta fada yau dai tana dan karya murya,jingina yayi da madubin dakin yana qoqarin controlling kanta,gaba daya dakin its not well organized,komai a birkice yake ba bisa tsari ba,duk sanda zai kwana a dakin komai sai ya nemi inda aka wulla masa,wannan dalilin ya sanya zaiyi wuya kaga wani abu nasa mai muhimmanci a dakin. Kafada ya dage "Well,zanje na shirya" "Yauwa,thank you"tafada tana dan jin dadi,saiya juya a hankali ya fice a dakin. Sai da yayi shafa'i da wutirinsa,ya kuma dauka duk abinda yasan zai iya buqata sannan ya rufe sashen ya koma,ya isa dakin ya dora kayansa saman madubinta yana fadin "didn't you sleep?" Saita motsa kadan tana cewa "Uhmm" "Okay,tashi,dama muyi magana dake" dan muskutawa tayi kadan,sai kuma ta miqe a hankali ta zauna tana dan murza idanu,zuciyarta na bada Allah yasa samuwa ce tazo. Kujerar gaban madubi yaja ya zauna dab da ita,har gwiwoyinsu na gogar na juna,ya goye hannayensa a qirji yana duban fuskarta da manyan idanun nan nasa da suke saurin kassarata,tsahon wasu mintuna baice komai ba,har sai data qosa tace masa "Wannan kallon fa?,kana azamin nauyi fa,ka tasheni bakacemin komai ba" kai ya gyada siririn murmushi yana kufce masa,saiya saki hannayen nasa ya hade yatsunsa waje guda "Har yanzu motar da kikace min kinaso ita dince baki canza ra'ayi ba?" Wani madaukakin murmushi ya kubcewa hafsat din,abunda bata taba kawowa shi xai mata maganarsa ba,duk da dama abbas din ya iya bazata,ba daga nan ba "Eh itace" ta fada cike da zallar zumudi "Shikenan,nan da two to three weeks zata iso.....sannan kuma.....inaso ki duba kayan dakin da kikeson canzawa,ki turonsu ta watsapp,amma kada su d'ara 1mil,sai nasu mimi su kuma kada su wuce 50000k" wani irin mamaki da farinciki suka cikata,cikin muryar zumudi tace "Da gask kake abban mimi?" ta fada idanunta a waje tanason ta samu tabbaci. Kai ya jinjina mata yana sakin qaramin murmushi cikin bata tabbaci,hannunsa ta kama ya riqe da kyau tana dariyar farinciki gami da yi masa godiya. Hannayen nasu yabi da kallo,yadda ta riqe masa.hannun dama bata aikata hakan idan ba wani abun farinciki ya sameta ba,idan bai manta ba rabon data riqe masa hannun haka tun lokacin da ya shaida mata ya biya mata hajji,sai ya zame hannun a hankali yana cewa "Yauwa,dama nace zamuyi magana ko?" "Ai mun gama magana,irin wannan manya manyan albishir haka?" Ta fada tana washe baki,sai ya kada kai "Saura abu daya" "To ina saurarenka" ta fadi ba tare data bada wani muhimmin ba "Hafsa" ya kira sunanta,sai ta amsa tana murmushi "Komai muqaddari ne daga Allah ko?,hakanan rayuwarmu da dukka qaddarorinmu suna hannunsa,yadda ya tsara haka bawa zaibi,hakanan fadarsa ne daga qur'ani ku auri abinda yayi muku dadi daga mata bibbiyu uku uku da hurhudu....." Statement dinsa na qarshe yasa fara'ar fuskarta taja baya,wani tunani kuma ya gilma mata,saita zuba masa idanu gabanta na wani irin faduwa,zuciyarta kamar zata fasa qirjinta ta fito "Hafsat,Allah ya nufeni da qara aure,wanda za'a daura shi cikin sati mai zuwa" "Meeee!!!" Ya fada da wata irin shaqaqqiyar murya,wadda tuquqin bala'i yasa ta gaza fita da kyau yadda ya kamata "Relax,calm down please,hakan ba yana nufin matsayinki ya canza daga yadda kike a zuciyata ba....." "Wallahi qarya ne!......qarya ne abbas......qarya ne wannan" ta fada ya qaaraaji tana nunashi kamar wata mahaukaciya sabon kamu "Shine ka zaunar dani kana yimin wadan nan kyaututtukan?,to banaso,ka riqe kyaututtukan ka!,wallahi baka isa kuma ka qara aure ba!,ni kadai ce matarka!,ni kadai zaka zauna da ita duniya da lahira!!" Ta fadi da wani qaaraajin tana dubansa da idanunta da sukayi jazur suka kuma firfito kamar wadda aka shaqawa borkono. "Cool down,karki bari ranki ya baci kinji......zauna muyi magana ta fahimta dake" ya fada with softness yana yunqurin kamota ganin tana shirin miqewa,fusgewa tayi tana jifansa da wani mahaukacin kallo,ta bude bakinta cikin madaukakin sauti ta fara gaya masa dukkan maganganun da suka zo bakinta,miyagun kalamai na aibatawa da kuma tunzuri,sai ya koma kawai ya zauna,ya harde hannayensa a qirji yana kallonta a nutse. Ya sani ita aka tabo,kasancewa batun lamari na kishiya a wajen mace babban al'amari ne da ba kasafai suke iya daukan wannan mummunan labarin ba,wannan dalili ya sanya ya bata dama taketa fadin dukkan abinda taga dama ba tare da yayi yunqurin dakatar da ita ba,duk da kalamanta akwai wuce gona da iri da kuma zaqewa da yawa,amma yayi haquri ne ya jura saboda yasan wani ciwo ne da radadi daga zuciyarta,wanda shine ya dasa mata shi yanzu yanzu. "Shine ka zauna kana kallona?, wallahi abbas baka isa ba,wallahi nace bazaiyiwu ba" sai tayo kanshi,tana rarumo kwalaben turaren dake saman madubinta ya soma qoqarin jifansa dasu. Cikin qwarewa ya dinga sanya hannu yana cafe duk wadda ta jefo,ganin ko daya bata sameshi ba sai tayi kukan kura ta jawo bed lamp ta wurgota. Bai samu tareta ba,amma ta dakar masa hannaye,glass din jiki kuma ya yankeshi ba tare daya lura ba,saita tsugunna inda take ajjiye takalmanta ta fara daukansu suma daya bayan daya tana masa ruwansu. Miqewa yayi cikin zafin nama da mazantaka ya isa gareta,ya kama dukka hannayenta ya hade cikin hannunsa guda yana kallon fuskarta,ransa ya soma baci,ya dubi sashen dasu mimi ke a kwance,Allah yasa babu daya cikin abinda take wurgowa daya samesu "Ki nutsu hafsat!,ki nutsu!"ya fada shima da murya sa mai kaifi da zurfi,saita dakata din ta kece da wani irin kuka "Macuci azzalumi,Allah ya isa tsakanina da kai,kuma wallahi wallahi baka isa kayi wannan auren ba,idan ba haka ba sai na baka mamaki nima dakai da munafukar da zaka auro,ka fita ka barmin dakina,ka fita bana son ganinka!" Ta fada da mugun qarfi,saiya sakar mata hannaye,ya kuma taka a hankali zai fice,sautin amon muryarta ya dakatar dashi "Kazo ka kwashesu,suma bana son ganinsu,ka debesu daga gabana!" Dawowa yayi a nutse yadan tsaya gabanta yana kallon yadda ta birkice gaba daya,jikinta banda tsuma babu abinda yakeyi,yasa hannu ya kwashe dukkan yaran ya fita dasu. Ya jima yana mamakin baqin kishi it n na hafsat din,ashe abun ya wuce yadda take tsammani?,wanne irin hauka ne wannan?. Bai lura da hannunsa dake zubar jini ba sai daya kwantar da yaran saman gadonsa yaga stains na jinin a jikin blue bedsheet din nasa "Ya salam" ya fada sanda yake duba wajen,sai yaga ya yanke sosai,don haka ya koma dakin yaran dake sassanta don ya dauko first aid kit. Tun daga falonta yana iya jiyo gunjin kukanta,irin kukan da mutum yake zama dirshan ya bude dukka muryarsa yayishi,tausayinta sosai ya saukar masa a rai,sai ya kasa wucewa ya sake komawa ta dakin,sai biyu yana murda handle din yana jinsa a riqe da alama ta kulle ne daga ciki,ya sassauta murya yana kiran sunanta "Open the door please, don't hurt yourself fa" "Ka tafi ka bani waje abbas,na tsaneka,banason kallon fuskarta,ka tafi nace tun ban bude na lahantaka ba!!" Duk yadda yaso ta bude din taqi,sai ma wasu miyagun kalmomin da zagi da yake antayo masa,hannunsa nata digar jini,dole ya haqura ya dauki kit din ya koma dakinsa ya gyara wajen. Daren ranar baccinsa ragaggene,haka yayita kai kawo tsakanin dakinsa zuwa sassanta,yasan halinta da muguwar baqar zuciya,yana fargabar kada ta illata kanta ita daya kulle a dakin,saidai duk sanda yaje din zaiji motsinta,wannan ke bashi 'yar nutsuwa kadan. *Arewabooks: Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 27 Washegari yaran da suka tashi suka gansu wajen babansu sam basu damu ba,murna suka dinga yi abinsu,shi ya dinga tiri tiri dasu,ya shiga kitchen da kansa ya hada musu breakfast mai kyau,da yake ya iya abubuwa masu sauqi hakanan cikin abinci,saboda yanayin karatun da yayi. Sunci kuwa sosai kamar ba gobe,sai ya zauna yana kallonsu,zuciyarsa na gaya masa basa samun kamarsa,duk da store dinsa cike yake da cima kala kala,wani abun har ya rube ko ya lalace batayi amfani dashi ba bata kuma bayar ba saboda baqar rowa,yayi nasihar yayi nasihar har ya koma fadan amma a banza,mutum ne shi mai bajintar wadata iyali tun samunsa baikai haka ba,tun rank dinsa bai kai haka ba,baya son iyalinsa suga wani abu a wani gidan da babu shi cikin gidansa,to amma kusan duk wannan qoqarin nasa a yawancin lokuta a banza yake tashi. Ruwan tea kawai ya iya sha bayan ya tabbatar sun qoshi,duk ransa a jagule in yake,saboda har sanann hafsat bata bude qofarta ba,yayi knocking yayi har ya gaji,ya ajjiye mata nata breakfast din bakin qofa amma baiga ta bude ta dauka ba. Bayan duka sun gama ya maida kwanukan kitchen,ya zage kamar yadda ya saba yawa yawan lokutta ya soma gyaran sassan nasa,yayi masa qal yadda yakeso,ya canza bedsheet da sauransu,ya hada duk abinda ya cire da kayansu mimi da yayi musu wanka cikin laundry basket,ya aje inda mai wankinsu zai dauka,sannan shima ya shirya kansa sannan suka dawo falon hafsat din,koda wai zataji motsinsu ta bude qofar. Saidai har suka gama zamansu ba ita babu dalilinta,a taqaice dai har zuwa azahar bata fito ba,yanason fita masallaci sallah amma kuma bazaiyiwu yabar yaran su biyu cikin gidan ba,don ita mimi din ma ba wani cikakken hankali ne da ita ba,dole ya hada kansu suka wuce sassansa,acan yayi sallar,sai la'asar daya dawo dora musu abinci yaga babu plate din daya ajema hafsat din,da alama yunwa ta korota,ta bude qofa ta dauka kenan,sai ya saki qaramin murmushi ya wuce kitchen din. Har dare suka kwanta babu wanda yaga qyallinta,a taqaice dai washegari kusan abinda aka maimaita kenan,don haka a kwana na ukun ya shirya yaran da kayansu ya wuce gidan hajiya dasu. Kallon farko data masa tasan hatsaniya ke tashi a gidan,ta kuma san bata rasa nasaba da batun aurensa,bata matsa da jin ba'asin kawo yaran ba,saboda tasan shi da zurfin ciki,zaiyi wahala ma ya iya zama yana fadin cikinsa,ta daiyi murna da zuwan nasu,don ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ta faru ba. Ya jima a gidan,sai yammaci sannan ya wuce,a sannan tuni nawwara tayi bacci a jikinta,ta baiwa muneera ta kwantar da ita,sai data dawo ta zauna gefan hajiyan "Hajiya da alama anty hafsat fa......" "Na sani muneera" hajiyan ta katseta,saita rausayar da kai "Shima uncle,ya haqura kawai hajiya suyi zamansu mana,irin wannan babu dadi fa don Allah" kallonta hajiya tayi,batasan ko taji abinda uwayenta ke fada ba,har mamaki suke bata yadda suketa goyon bayan hafsat akan auren nan,wanda tasan tsabar son zuciya ne,amma babu wanda baisan halinta ba da dabi'arta,idan sunce basusan yadda abbas yake samun careless daga wajenta ba wannan kam ba zata musa ba,don babu da wanda yake zancan,amma kuma sauran dabi'unta da abbas din ya dinga yaqi ta gyara fa?,ita hajiyan tasna wasu,saboda takan bashi shawari idan ta fuskanci yana cikin damuwa ne "Ke yarinya ce,ba zaki fahimta ba,sannan keba namiji bace,nan ma ba zaki gane komai ba" amsar da hajiyan ta bata kenan,sai tace "K'nnnn,ai shikenan" base on her experience tayi maganar,saboda taga halin da mamanta ta shiga sanda babanta yace zaiyi mata kishiya,a sannan hajiyan ce ta shiga batun(muneera 'yar dan hajiyan ce),duk da.bai fasa ba anyi,amma abubuwan da sauqi,to amma yanzun hajiyan da kanta takeson ayima anty hafsat din?. Yayi tunanin zata kaishi qara wajen hajiya ko daya daga cikin yayunsa maza kamar yadda ta saba a duk sanda wani rikici data kasa jurewa ya hadasu,amma sai yaji shuru batayi ba,bazai iya tuna rana daya rak da ya kai qarar hafsat din ga danginta ba,duk da tarin matsaloli da laifukanta,shi wanann ba dabi'arsa bace kwata kwata. Kwanaki biyar hafsat din tana a haka,cikon kwana na biyar din Allah ya jeho qanwar mamanta ita da naty ummee,matar data jima rabonta da gidan,yanzun ma.suna sukazo ta bayan layin,anty ummee ta roqeta su biyo. Yana farfajiyar gidan shi kadai yana duba jarida,suka gaisa dashi suka wuce ciki,ba jimawa anty ummeee ta dawo "Don Allah yallabai ka duba mana,hafsatun tana ciki kuwa?" Jaridar ya ajjiye ya miqe tsaye yana gyara shirt din jikinsa,yasan tana ciki,kawai taqi budewa ne tana zaton shine yake bugun,kuma a yau ya yanke zai balle qofar zuwa dare muddin bata bude ba,sai ya gewaye anty ummin yayin cikin gidan,ta bishi da kallo tana jaddada miskilancin sa,har yanzu yana nan dai ba abinda ya sauya. "Ki bude qofar, ummee ce" ya gaya mata kai tsaye,bai qara minti guda ba sai ga motsinta,ta murza key dun data sawa dakin ta bude. Wani irin scent ne mara dadi ke fitowa daga dakin,saboda qarancin iska me kyau,duk da akwai ac da fanka ta cikin dakin,amma baya zaton tana kunnasu,jikinta tun kayan daya dawo daga kaduna ya sameta dasu ne,da alama har wanka ta yiwa yajin aiki,ta nan inda yake tsaye yana iya jin sauyawar yanayin jikinta,sai ganshin kanta dake cuccure waje daya da alama bata tajeshi,fuskarta gaba daya ta kumbure,kamanninta sun dan jirkita. Harara ta watsa masa sannan taja tsaki,tsakin da yakai har kunnen anty uwani dake falonta,tadan kama baki tanason tabbatar daga inda tsakin ya fito. Ya tsani tsaki a duniya,ta kuma san hakan,shi yasa ta bishi dashi,ko zata samu ta fanshe bacin rai da quntata rayuwarta da yayi kaso daya cikin dubu na abinda takejin yayi mata. Bacin ransa ya daure,ya juya yana barin wajen,saita biyo bayansa a hankali har ya fita a falon,ita kuma ta qaraso ciki,suna hada idanu ta zube a nan ta saki kuka,ciwon dake danqare a ranta ya motsa mata,don a kwanakin ita daya ke fama da baqincikinta cikin daki,kwata kwata basirar ta gayawa wani bata zo mata ba,hasalima wayar tana kashe tun ranar,saboda abbas din ta kashe,bataso yayi kiranta ma. "subhanallahi meye haka hafsatu?" Anty uwani ta fada cikin firgici tana dago hafsat din,sai ta dan dauke kanta kadan saboda abinda ke tashi a jikin hafsat din,ta jata ta zaunar kan kujera sannan ta zauna dan nesa kasan da ita "Lafiyarki kuwa?" Anty ummee itama ta jefa mata tambayar tana kallonta,cikin muryar kuka kamar wadda akace wa'adinta ya qarato ta soma magana "Na shiga uku na lalace anty ummee,anty uwani wallahi mutuwa zanyi,abbas ne yace zai qara aure" ta qarasa fada tana rushewa da kuka,haushi da takaici ya qume anty uwani,yadda taga hafsat din ta aza hannu aka ta zauna dirshan a wajen tana musu irin wannan kukan na tashin hankali "Mutuwa fa kike fada hafsatu,kinsan mutuwar kuwa?" Anty uwani ta fada tana harararta "Sai an bita a hankali ai anty uwani.....sannu yi haquri tashi ki daina kukan" anty ummee ta fada yana dagota daga zamewar da tayi daga kan kujerar. Da kallon takaici anty uwani ta bisu su duka,ta da jin labarin abinda hafsatun keyi a gidanta,qazanta baqar rowa,ga rashin iya mu'amala da mutane,kuma ko a yanzun ta sake shaida tabbatar qazantarta,saboda yadda jikinta yake tashi ba kowa ne zai juri xama kusa da ita ba,da alama kwana biyar din kenan batayi wanka ba. Tana jinta sanda take rattabowa ummee labarin yadda komai yake wakana,tasani wanda suka fita ma sun gaya mata ba daukan shawara takeyi ba,ko a yanzun ma tasan idan tace zata gaya matan bata baki ne,don haka sai ta miqe "Kin gama ko na wuce kya taho?" Dubanta anty ummee tayi "Aah ki bari mu wuce tare mana" "Um um,yi zamanki,nikam ina da uzuri,saikin taho,hafsatu sai a qara haquri,ki duba dukka iya kurekurenki da abubuwan da kikasan bayaso ki gyara tun yanzu,Allah ya bada haquri" badon tasan anty uwanin bata da wasa ba,bata kuma daukan wargi da ashar zata maka mata,amma hakanan ta hadiye bacin ranta tace mata ta gaida gida da shaqaqqiyar muryarta data ci uban kuka. "Yanzu me kika yanke ke?" Anty ummee ta fada bayan ta dawo daga raka anty uwani,ragowar hawayen dake fuskarta ta share,tana jin gaba daya rayuwarta ta juya mata baya cikin kwanakin nan "Babu wata shawara ko dabara da nake da ita,kawai dai abinda na sani,koda tsiya ko da bala'i wallahi bazan bar wata mace ta rabi abbas ba,bazan iya zura ido ina raye ba abbas ya auro wata mace da sunan matarsa ba" jinjina kai anty ummee tayi "Amma ina ganin wanann ba dabara bace,kwata kwata ragon azanci ne,kinfi kowa sanin halin mijinki,idan yace yes babu wanda ya isa yasashi yace no,tunda ya niyyata babu wanda zai hanashi....." "Niko naci alwashin koda ta qarqashin qasa saina hana shi auren nan anty ummee" ta fada idanunta na sake kadawa suna kuma sake cika da hawaye. Ajiyar zuciya anty ummeen ta sauke,sannan tadan gyara zamanta "Niko sai nace wannan din ba hanya bace mai bullewa,face hanya mai wahala da kuma sanya kashe kudi,a matsayinki na mace,mai yasa ba zakiyi amfani da KISSARKI ba?" A hagunce hafsat din take kallon anty ummee,saboda bata fahimci me tafi nufi ba gaba daya,mafita kawai take nema,saboda haka tace "Kamar yaya kenan anty ummee???" **********Tun daga ranar bata sake kulle kanta ba,saidai kuma sabgarta takeyi kawai ba tare data shiga sha'aninsa ba,bai damu can can ba,don ko sanda suke shirin ma ba wani abu take dauke masa ko takeyi masa ba,kusan ya saba....fiye da rabin hidimominsa shikewa kansa,saidai ya dan samu nutsuwa,tunda aqalla bata sake tada wata fitina ba,har abun yaso ya bashi mamaki sosai. ********Karfe biyar na yamma tana kitchen tana hada abincin dare taji knocking,ta fito a kitchen din tana gyara daurin zaninta daketa kwancewa tun dazu,don bata daurin baya sai daurin gefe,a cewarta yana damunta ne. Tana bude qofar sukayi arangama da yaron gidan wanda ke musu aike aike,sai ya danja baya kadan cikin jin nauyi saboda ganinta babu mayafi "Madam oga ne yace a kawo,masu kayan gado ne da furnitures,zasu kwashe wadancan su saka sabbabi,yace muzo dasu suyi aikin" ta zuba masa ido ne taga zaiyin ko bazaiyi ba,duk da zancan kullum yana ranta dashi take kwana take kuma tashi,duk da ranta a bace yake matuqa har komai ma baya burgeta,to amma kuma tana son alqawaruran da yayi mata din. "Su bani minti goma ina zuwa" ta fada tana juyawa,ya rusuna cikin girmamawa ya amsa mata da to. Dakinta ta koma ta fara kwashe abubuwanta masu muhimmanci waje daya,aikin nada dan yawa,don sai ta shiga dakinsu nawwara ma ta hada nasu kayan,tanason ta samu dan tayi,to amma tasan a dai dai wannan lokacin koda tayi waya gida babu lallai a samu me zuwa ya tayata,saboda kowa yasan halinta da dna banzan rowa,saidai kayi mata wahala,dole ta koma kitchen ta kashe gas din girkin,dama ba wani girkin arziqi ta aza ba,tafi sati ma basa abincin saidai yayo musu takeaway,ita kuma ta nema wani abun taci. Sai da ta kusa awa guda sannan ta gama,duk ya hada gumi saboda ba maison aiki bace,sanann ta koma kitchen tana maida numfashi,su kuma suka shiga aikin gyara dakunan. Ana idar da sallar magariba suka gama kafa kayan gadon,da yake ba mutum daya ko biyu bane,sun kusa su biyar,suna fidda wadancan kayan ta fito "Su kuma wadan nan za'a kaisu?" Ta tambayi shazali yaran gidan "Yace a fiddasu compound a ajjiyesu" kai ta kada "Ka bawa masu kayan gadon idan suna siyan second hand,tunda wadan nan ba wani dadewa sukayi ba,kuyi ciniki su baka kudin ka kawomin" kamar yace ba haka oga yace ayi ba,to amma sai yaga meye nasa?,tunda kayanta ne,kuma matarsa ce?,don haka ya amsa mata da to yana ficewa,ita kuma ta juya ta shige dakunan tana jan tsaki a ranta,kudi takeso ta tara mai yawa daga jikinsa,ko banza ta rage wani radadin. Sosai dakunan sukayi mata kyau,dukka ya zaba favourite colors dinta ne,dakunan sun canza gwanin sha'awa,duk da ranta a bace yake amma sai data danji ta sauka kadan. Ba'a rufa awa ba kuwa ya dawo mata da kudin kayan cas,ta karba ta soke abinta taci gaba da sabgarta hankali kwance,ranar baya nan,yaje azare,zai kuma kwana sai washegari zai dawo,don haka hankalinta kwance ta gama tsara abinda zatayi da kudin,koda kuwa ya dawo ya tambayi yadda akayi da kayan,barema tasan halinsa,zaiyi wuya ya tambaya din,don bashi da wannan,amma koda yana da niyyar ma ta shirya abin fada masa. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 28 *********Washegari tana dakin yaran tana sauya musu kaya bayan tayi musu wanka taji ana sallama a falon nata,qaramin tsaki taja,ita gaba daya batason baqi a rayuwarta tun asali,bare a yanzu da take cikin wannan yanayin,mimi ta aika ta dubo waye?,sai ta dawo tana ce mata baquwa ce,tadan harari yarinyar,har yanzu taqi tayi wayo irin yadda takeso,irin wayon da zata iyayi mata bayanin duk abinda takeson ji,saita ajjiye kayan nawwara da bata kai ga sanya mata ba,ta miqe tana cewa "Bari muga wanne munafukinne" tayi waje yaran suna biye da ita. Tun kafin ta qaraso ta hangi wacece,rabi'atu ce,cousins suke da abbas din,takan jima bataga rabi'atun ba,bama ita kadai ba,danginsa ma yawancinsu ba wani zuwa sukeyi ba,saidai idan an hadu a wani sha'ani idan ta samu zuwa saisu gaisa,suna girmama ta dai dai gwargwado,amma ta dauki hakanne a mazaunin don anga mijinta yana da rufin asiri ne. Fuskarta kadaram kadaham ta qaraso ta samu kujera daya ta zauna tana dan satar kallon rabi'atun,saboda daga nesa taga yadda take satar kallon falon,zuciyarta kuma ta raya mata gyaran da akayi mata take kallo "Dangin miji irin jaraba" ta fada a ranta,babu dama suga sakakken abu a gida ko a jikinka sai sun nuna a fuska ko a kalaminsu(nace uhmmm,inama suka hadun ko sukazo gidan bare hakan ta faru?). Ba yabo ba fallasa suka gaisa da rabi'atun,sai kuma shuru yadan biyo baya,sai ita din da taketa qoqarin yiwa su mimi wasa,wadanda suka qi sakin jiki da ita saboda rashin sabo da basuyi da su ba. Kai rabi'atun ta dago tana cewa "Wai nan bayanku nazo suna,kinsan a nan qanwar mijina take aure" "Uhmmm,Allah sarki" ta fada a taqaice "Sai nace nari na qaraso mu gaisa,na kuma yi miki murna ko jaje zance,ashe kuma yaa abbas aure kishiya zai miki?,kuma a rasa wadda za'a rakito miki sai 'yar wani garin,kuma ma yarinya qanqanuwa wadda a haife ya kusa haifarta" da fari cin mutunci hafsat ta shirya yuwa rabi'atun,amma jin ta fara bata hint akan abubuwan da batasan dasu ba saita maida wuqarta tana gyara zamanta "Ya kusa haifarta fa kika ce?" "Wallahi haka inna ke gayamin,tunda kwata kwata bata wuce shekara sha uku zuwa sha hudu ba" wani abu ne ya tsargawa hafsat,saita nema tashin hankalinta kaso talatin cikin dari taji babu shi,ta aro sakin fuska ta dorawa fuskarta "Kin ganta ne rabi'ah don Allah?" Kai Rabia ta girgiza "Ban dai ganta ba,amma inna tacemin ta taba ganinta gidan sau daya,badai 'yar nan bace 'yar kano ce" gabanta yadan fadi kadi jin abinda ta fada daga qarshe,ana wata ga wata,ko zakayi kishi yafi kayi da 'yar garinku,kar tasan kar ne,bawai kayi da bare hayin wani gari ba,garin ma da tasha jin masu kishiyoyi daga wannan nahiyar suna qorafi,to amma 'yar shekara sha uku zuwa sha hudu kishiya ce ko 'yar raino?. "Ni irin wannan auren banda abin hajiyarsu,mutum na zaune da matarsa ya dauko aure,a kuma tsallake gida a tafi dawa?" "Da gidan da waje duk dai kishiya ce,ko daga dakinki aka fiddo miki da ita sunanta kishiya" hafsat din ta amsa mata rana dan hade rai,saboda tasan yadda 'yan mata da yawa cikin familyn ke sonshi,kamar shi kadai ne namiji a family din nasu,sai data dinga murje idonta tana yanka musu rashin mutunci ta samu salama. "Gaskiya dai" rabi'atu ta waske ta hanyar fadin haka,bata jima sosai ba saidai hafsat din tadan samu wani haske akan lamarin,da yadda hajiyansa ke maraba da abun,daga qarshe sukayi sallama,ko pure water rabi'atu bata samu daga wajenta ba,haka tabar gidan tana tsine mata cikin zuciyarta,saidai duk da haka sudai suna adawa da wannan auren,tunda nasu basu samu ba 'yan qannensu da suka zama 'yammata gwara a bata goma daya bata gyaru ba gaba daya. Rabiah tana fita hafsat ta wuce daki cikin hanzari,ta dauko wayarta ta soma neman number din anty ummeee ta labarta mata labarin data samu,saidai duk saurinta ya zama nawa saboda babu kati a wayar tata,dole ta koma ta mobile app din bankin da take amfani dashi,ta saka card din dari biyu ta kirata. Sai data kusa tsinkewa anty ummee din ta daga,hafsat na daga tsaye ta gaza zama,sai kai kawo takeyi "Anty ummee....kina jina?" Ta fada da matuqar zaquwa,har kana iya jiyo haka cikin muryarta "Ina jinki hafsatu,lafiya?" Guri ta samu saman bedside drawer dinta ta zauna sannan ta soma magana "Yanzun nan rabi'atu cousin din abban mimi tabar gidan nan,kinsan yarinya qarama yaje ya dauko?,ko shekara sha biyar bata cika ba?" Ta qarashe maganar tana tabe baki,takaici yana cikata. Dariyar da anty ummee ke qyalqyalawa tayi kasake tana saurara,sai daga bisani tace "Kai haba?,kice raino ya dauko?,tirqashi,to ke ai ta fadi gasassa,babu kuma wani sauran kishi da tashin hankali daya rage miki" "Kamar yaya?,haba anty ummee,idan za'a maka kishiya ma ai sai ayi maka isassa,wadda zaku goga da ita,ba wata can qasan qasanka ba" "Tabdijan" anty ummee ta fada sannan ta dora da cewa "Amma bansan baki da hankali ba sai yau,ke!,kishiyar da zata shigo ta goga da ke ai masifa ce,me yayi miki zafi?,to idan baki sani ba bari na gaya miki,Allah sonki yake shi yasa ya hadashi da qwaila,a yanzun ne za'a fara wasan ma da kyau,dama dukka tana hannunki,idan kika dauki.maganganun da mukayi dake rannan kikayi amfani dasu da kyau to ina me tabbatar miki yadda zaki bawa su mimi da nawwara umarni itama haka ne,ba boka ba malam,komai zaizo miki da sauqi,kina daga kwance kina sarrafa gidan a hannunki,yanxu saurara nayi miki wani sabon karatu......." Gyara zama tayi sosai tana bada hankalinta ga anty ummee din,tana hasashen qamshin gaskiya cikin msganganun anty ummee,sai taji ranta ya fara yin fes "Ina jinki" ta cewa anty ummeen...... *********Can quryar gadon ummu take kwance abinta,ta duqunqune waje daya,duk kuwa da cewa gidan a cike yake da baqi jikoki da surukan gidan,wanda a baya duk lokaci irin wannan tana tare dasu sunata sabgoginsu,sabanin yau da gaba daya take jinta wani iri,musamman da aketa mata abubuwa daya banbanta dana 'yan uwanta,aka kuma tsameta daga cikinsu. Tana daga kwancen tana kallon yadda ummu ita da warisha qanwar abbanta suketa hada kaya cikin manyan buhunhuna da kwalaye,wanda gaba daya kayan ummu tace nata ne,gidanta za'a kai mata ayi mata jeranta,itama ta samu nata gidan na qashin kanta,duk sanda ummu ta fadi hakan dadi takeji,amma yau gaba daya jikinta ya sanyaya,gwiwarta ta fara sagewa. Ana tsaka da wannan latifa tayi sallama ta shigo dakin ummun,ta tsaya daga bakin qofa yana gayawa ummu game gyaran jiki tazo,tunda widad din taji haka ta runtse idanunta tahau baccin qarya,ita kwata kwata batason wannan kwabe kwaben da aketa shafa mata yau wajen sati guda kenan,tana jin sanda ummun ta waiwaya tana qwala mata kira,amma sai ta sake lafewa cikin bargo tayi kamar bacci take,har ta gaji da kira ta juya ga latifa "Inaga kawai abar aikin nan haka,dama yau da gobe ne kawai ya rage" "To shikenan,bari na sallameta,yauwa......anty madina tace na gaya miki,kayan miyar ya za'a yi dasu,a markada gaba daya azubasu a freezer baya?" "Eh hakan yayi,don kada su lalace kafin jibin" "To shikenan" sai latifan ta juya ya fita,su kuma sukaci gaba da hada kayan,tana labe cikin bargo tana satar kallonsu,tana jin anty warisha na cewa "Banda abun ummu nawa ma jikin widad din yake,me ya sameshi ma da za'a mata gyara,ita da dama fatarta me kyau ce,a haka ma a karon banza daukan ido takeyi" "Wallahi madina ta matsa sai anyi mata,to ya na iya,itakam dama ta iya biyewa shirmensu,yanzu haka ta gama tsara musu komai,har kudi tasa muhsin ya karba musu wajen ango wai zasuyi walima" dariya warisha ta sanya "Kai,Allah mai iko,widad amarya" sai ummun ta murmusa kawai,don dauriya kawai takeyi batason aga rauninta. Tun tana labe tana kallonsu har baccin gaske ya dauketa,bata farka ba sai dab da la'asar,sanda ta tashi dakin babu kowa,sun gama aikinsu sun fice,bandakin ummun ta shiga ta daura alwala,ta shimfida abun sallar tayi sallarta,saita dan zauna tana jin hayaniyar su nabiha da sauran jikokin gidan,daga bisani ta gaza daurewa ta fito. Ido kuwa yayi mata caaa,mutane anata kiranta da amarya,saidai ta tura baki tayi gaba abinta,itafa shi yasa tunda aka fara baqin ma batason fitowa,a haka dai ta samu ta wuce sassan anty madina,a canne ta sake sosai abinta,harta manta da komai ma,har sai da anty madina tace lallai gobe za'a tsefe kai ayi kitso,a nan fa suka raba gaari da ita,saboda ta ambato maqiyinta wato kitso. *RANAR DAURIN AURE* Cikin jerin gwanon motoci na alfarma suka taso,tun daga garin bauchi zuwa cikin garin kano,qarqashin jagorancin jami'an tsaro da matakai masu tsauri,a ranar tamkar dai wani shugaban qasa,duk yadda ya dauki daurin auren sai ya wuce masa haka,tamkar dai dama ya dade da shiryama hakan,shi kansa cikin sabuwa dal din motarsa yake,yana seat din baya shi da suraj,sanye da wata danyar shadda wadda koda gari aka baka ka canki kudinta ba zaka ajeta nan kusa ba. Tunda suka taso fuskar hafsat ke masa yawo,tunda zancan ya tsiro bai taba jin tausayinta irin na yau ba,yana hangen yadda fuskarta ta sauya a sanda yake shiga motarsa cikin shigar dake jikinsa a yanzu,saidai zuciyarsa cike take fal da mamakin mene ya sauya hafsat?,me kuma ya kawo wannan sauyin?,yasan halinta ciki da bai,meye ya sanyata zub da makaman yaqinta?,wannan amsar ce har yanzu ya kasa lalubota,sai tarin wasi wasi da yake fama dashi kullum kwanan duniya. Tun daga titin farko zuwa abinda yakai layin da zao sadaka da ainihin gidan alhj salim mai fata cike yake tanqam da jama'a,idan akace maka jama'a ina nufin jama'a na gaske da zakayi tsammanin daurin auren wata hamshaqiyar budurwar data ci ta qoshi da karatu da wayewa akeyi,gaba daya unguwar a hargitse take sakamakon halartar daurin auren da manyan 'yan siyasa gwamnoni da kuma qusoshin gwamnati da abbas yake hulda dasu sukayi,jama'a dake tsaye a gefe guda suna ci gaba da lissafa gwamnonin da sukaga suna shiga unguwar tasu,sai da suka lissafa shida casss!. "Bisa dukkan alamu wannan karon babban kamu akayi a gidan nan,lallai yau sun jawo babban kai,kai kaga motocin dake ta gilmawa kamar daurin auren 'yar shugaban qasa?" Ire iren maganganun da matasa 'yan zaman banza a bakin layi keyi kenan,sunayi suna ci gaba da dorawa a lissafin su. Daga can cikin gidan kuwa a shaqe yake da jama'a,ko ina idan ka kalla hada hada akeyi,zaka tsammaci an dauki shekaru ne ana yiwa bikin tanadi,saidai hausawa suna cewa,kowanne aure da arziqinsa yake zuwa,wanna haka yake,domin kuwa a lokacinne aka baje lefen widad wanda ya iso ne tare da 'yan daurin aure,akwati mai sunan akwati,akwati na alfarma guda goma sha biyar,kowanne maqare da sutturu masu daukan hankali,duk wanda ya daga idanu ya kalla koda baiso magana ba sai bakinsa ya subuce ya furta "Ma sha Allah"mafi yawan mutane cikin family da wadanda ke cikin gidan dake zuba idon suga wani abun kaico ya bulla sai jikkunansu suka fara yin sanyi,musamman da labarin irin manyan mutanen da suka halarci bikin yajewa kunnuwansu.......... KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 29 Qarfe biyu na rana bayan sallar azahar aka daura auren asp abbas da amaryarsa widad mahmud salim akan sadaki naira dubu dari,dubban jama'ar da suka halarci wajen suka haida,labarin kuma ya kai har cikin gida ya fara yawo a tsakanin mata. Dai dai lokacin widad na zaune tsakiyar anty deena da anty warisha,sai sharban kuka takeyi,duk yadda sukayi da ita tayi shuru bare a samu ayi mata kwalliyar daurin aure taqi,sai suka sakata a gaba kawai suna kallonta. Anty madina ce tayi sallama ta tana turo qofar dakin,dakin da babu kowa sai su ukun kawai,warisha ta amsa sallamar anty dina dake danna wayarta kai kawai ta daga ta kalli anty madina "A'ah,na zata zanzo na tarar kun gama,an gama daurin aure fa,angwayen ma yanzun zasu shigo za'ayi hotuna" "Inafa akayi kwalliya,kin ganta nan ko kayan taqi ta saka ma,ni bansan me yake damunta ba" anty deena ta fada tana ajjiye wayarta a saman madubin dakin. "Ashsha,haba widad,mene hakan?" Hawayenta taketa qoqarin tsayarwa ta hanyar shareshi da hannuwanta amma hakan ya gagara,wani irin bacin rai tsoro da kuma takura takejin kanta a ciki,wanda ita kanta batasan dalili ba,kawai batason barin gida ne,hakanan shi uncle abbas din ta yaya za'a wani ce shine mijinta tana zaman zamanta?. Anty madina ce ta cewa su deena din su basu waje minti biyar kacal,nasu musa ba suka miqe,anty deena ta dauki mayafinta mahadin lace din jikinta ta fara yin gaba,don dama ta fara gajiya da zaman lallashin widad din,wadda bata da alamun daina kukan. Cikin mintuna goma sai ga hawayen ta tsaya tas,anty madina kuma ta shiryata da kanta,hatta da undies ita ta bata ta saka,tana jin kunya tana nonnoqewa,ta shiryata cikin wani lafiyayyen lace fari da ummu ta kashe maqudan kudade wajen siyansa,aka kuma shirya masa nutsatsen dinkin doguwar riga,gashinta da yasha gyara ta tufke mata,sannan ta qawata mata kanta da sarqa ruwan gold da aka sanyawa saman ka,wanda kusan al'adace ta asalin yarensu,hannayenta sun sha warware masu kalolin gold masu asalin tsada,haka yatsun hannunta kowanne zobe ne bibbiyu daga tsakiya. Fes widad din ta fito,asalin quruciya da qaranci shekarunta na sake bayyana kansu,wanda ya cakuda da qyallin amarcin da akewa kowacce mace feshinsa,komai kyau ko muninta,indai sunan nan na amarya ya hau kanta. Kiransu anty deena tayi sanda taji hayaniya ta fara cika gidan,muryoyin maza na tashi,alamu dake nuna tawagar angwaye ne suka shigo gaisawa da surukansu,daga inda take sai ta dinga jin kamar an daureta,gabanta ya tsananta faduwa,wani tsoro yana shigarta,kanta a qasa,nutsuwa ta musamman irin wadda duk wanda yasan widad din bai santa da ita ba ta saukar mata. Shi daya ne cikin motar kwance a seat din gaba,ya dage dukka baqaqen gilasanta,da hular da kuma babbar rigar duka ya ciresu ya jefa seat din baya,ta cikin motar yana iya hagen kai da kawon jama'a,ciki harda gungun abokansa da suka masa karar da ko auren farko bai sameta ba. Amatsayinsa na jimi'in tsaro,duba daya yayi musu yana daga kwancen ya fahimci shi suke nema,yasan zancan bai wuce ace su shiga cikin gidan,abinda sam bashi a tsarinsa kenan,saboda yana kallon haka a mazaunin keta haddin shari'a,tu dazu ya shigo ya kwanta,ya kuma gargadi Samuel kada ya gayawa kowa yana ciki. Idanunsa ya janye a hankali daga inda yake kallo sanda yaji ana knocking qofar motar,fuskar suraj yake hangowa wanda yayi wujiga wujiga saboda yawan al'ummar dake wajen,sai yasa hannu a nutse yana daga kwancen ya buda murfin motar,suraj ya sunkuyo yana sako kansa. Ajiyar zuciya ya sauke "Gaskiya baka kyauta mana ba,kaifa ake nema tun dazun,zaa shiga gaida iyaye da kakannin amarya,ga masu hotuna suna jira suma zasu wuce" kamar wanda baya son yin magana ya buda bakinsa "Duk da wannan uban jama'ar zamu kama mu shige musu gida suraj?" "To ya za'ayi,al'adace" kai ya girgiza "Ba dani za'ayi wannan aikin ba,idan ya zama dole ka sallamesu su tsaya iya waje,mu shiga koda mu uku ne muhsin yayi mana jagora iya sashen ummu kakarsa mu gaisa mu fito" dan hade rai suraj yayi,sai kuma ya saki dariya "Kai mutumina,anya ba kishin matarka ka fara ba?" Wani kallo ya watsawa suraj din "Waikai me yasa baka da girma saina jikinka,yarinyar da idan auren qauye ne na haifi kamarta?" "Allah yasa motsin gado ce,bar ganin allura,duk qanqantarta qarfe ce,any way.....banga laifinka ba,bari ina zuwa" ya fadi yana maida murfin motar ya rufe. Sai da yayi settling komai yadda abbas din yakeso sannan ya sanar dashi,hularsa ya dauka ya mayar saman kansa,ya riqe babbar rigar a hannunsa,yana jin ta masa nauyi,saboda rashin sabo da sanyata,tunda gaba daya aikinsa yafi alaqa da qananun kaya. Kamar jiransa maroqa da masu buga kakaki suke suka fara busarsu suna wasa shi,baisan a inda suka san muqaminsa da kuma muqaman da ya riqe a baya ba,duk da juniors dinsa da suke masa bodyguard hakan bai hanasu binsa da kide kidensu ba "Ka sallamesu don Allah" yace da suraj,saboda yadda yakejin kidan na haura masa har saman ka,sai da suraj din kuwa ya sallamesu da kudi masu tsoka sannan suka ja suka tsaya daga nan suna ci gaba da yagar rabonsu a hannun duk wamda suka fuskanci dan gaban goshin bikinne. Babban falon ummun cike yake da jama'a,saidai da yake yana da yalwa babu laifi ba'ayi cushewar da zaka fuskanci yawan jama'ar dake cikinsa ba. Duk da fargaba da kuma alhinin rabuwa da widad din tata hakan bai hanata qure ado fiye da duk wani bikin jikarta da za'a yi ba,ta cake cikin wani danyen lace purple color daya haska farar fatarta dake dan bayyana yanayin shekaru da suka soma hawa kanta. Muhsin ne ya gaya mata ga abbas nan zai shigo,don haka ta kira hauwa'u da batulu(matan baban widad) tace su rage mata jama'ar falon. Duk da jikinsu a mace yake saboda ganin irin hidimar da akeyi amma wannan aikin kam cikin karsashi suka yishi,saboda suma suna buqatar ganin mijin widad din sosai,cikin lokaci qalilan falon ya sake fili,ya zamana sai manya a cikin dangi suka rage,dai dai lokacin sukayi sallama suka shigo cikin falon su uku. Kamar yadda a tsarin zubi da halitta gami da kwarjini ya fita daban......hakanan adonsa da shaddar jikinsa ta banbanta data kowa,sai ya fito kamar wani wata a cikin taurari,qanwar ummu da sauran jama'ar dake wajen ke marabtarsu,har suka samu waje qasan carfet suka zauna bisa tsari na tarbiyya,sannan aka soma gaisawa. "Da gani babu tambaya,wannan na tsakiyar shine surukin namu ko?" Batulu da wani malolon abu ya tsaye mata a wuya ta fada,fuskarta kwance sa murmushin yaqe,kusan kowa a wajen sai da yaji banbarakwai,saboda ba ita ya dace tayi tambayar ba,ko banza ya kamata ace akwai kunya tsakaninsu,saboda a yanzun sune kamar copy na mahaifiyar widad. Murmushi suraj ya danyi,baisan dangantakar ta da widad ba,ya dauka abokiyar wasa ce,tunda suna irin haka,dalilin da yasa ya maida mata kenan cikin salo na wasa "Aah,nine fa,kingi batan dabo" "Allah ya sanya alkhairi,yasa anyi kenan,jikanyar tamu qaramar yarinya ce qwarai,sai anyi haquri da halayen quruciya da za'a yita gani,Allah ya bada zuri'a dayyi ba" qanwa ga ummu tayi hanzari katse doguwar maganar da batulu keson taja,falon sai ya game da addu'ar ameen ameen. Abbas din na shirin miqewa muhsin yashigo yana fadin ina widad din afito da ita,azo ayi musu hoto "Ya salam" yafada a ransa,me yasa muhsin zai masa haka,bashi da zabi illa yayi jiraye. Anty madina da anty deena ne suka fito da ita ta can backyard din gidan,basa so kowa ya tsaidasu bare kwalliyar tata ta baci,suna tafe anty madina na jaddada mata kada ta sake tayi kuka,zata bata fuskarta "Ke maison kwalliya,kinga yadda kikayi kyau kuwa widad,baki taba kyau irin na yau ba" takanji dadi idan akace kwalliya tayi mata kyau,musamman daya zamana ita din mai son kwalliyarce,to amma kuma bata samunta sai lokaci lokaci,yau din da anty madina ke cewa tayi kyau sai bata ji wannan dadin da takanji ba,ta daiyi qoqarin dakewa,tanason farantawa anty madina rai,saboda kirkinta da yadda take sonta. Sallamarsu cikin falon ya ja hankalin jama'ar dake falon,badawiyya abokiyar wasa ga widad din,wadda shigowarta kenan falon ta saki guda data ratsa falon gaba daya. "Ma sha Allah.....ma sha Allah,widad Allah yasa anyi a sa'a,Allah yasa mutu ka raba" bakunan masoyanta dake wajen ya cika da addu'a,yayin da kishi hassada da kuma qyashi ya cika zukatan wadanda ke qin jininta hakanan. Gaban ummu suka so kaita,amma saita musu nuni dasu ajjiyeta gaban abbas din ba tare da tayi magana ba,sun fahimta,saboda haka suka nufi gaban abbas din da ita,ganin haka yasa tun kafin su qaraso suraj da muhammad da suka masa rakiyar suka janye baya,suka basu fili sosai. A hankali suka tsugunnar da ita a gaban nasa,rabin fuskarta yana rufe,saidai hakan bai hana kayan adon dake jikinta bayyana ba,suka ja da baya,sai falon ya dauki hayaniyar abokan wasa da suketa yiwa juna tsiya tsakaninsu da uncle muhsin,abinda ya dan janye idanun mutane kenan daga kan abbas da widad din. Tana zama awajen wani irin qamshi ya soma fita daga jikinta,sassanyan qamshi mai fusgar hankali da kwantar da zuciya,irin qamshin dake saurin sakawa zuciya karaya da wani irin sassanyan yanayi,ya daga idanunsa a hankali,fararen hannayenta da suka jan lalle irin na asalin yamalawa su ya fara gani,a hankali yaci gaba da kallonsu kafin ya daga kai zuwa ga fuskarta,dai dai sanda itama ta daga kanta zuwa gareshi don ta gaidashi kamar yadda anty madina ta gaya mata,fuskarta ta fito tarwai da wani irin haske data qara "Ina yini" ta furta,bugun zuciyarta na bayyana har saman harshenta,ya kuma biyo ta sautin gaisuwarta ya sanya lafazinta fita a rarrabe,amma hakan sai ya qarawa sautinta mai cike da quruciya kyau,sai ya dan lumshe idanunsa kadan yana amsawa "Lafiya qalau" yana ganin fuskarta a yau ta sake zama ta manya fiye da ranar da ya ganta a gidan muhsin,a yau din ta dan sake zama babba kadan ba kamar ranar ba "Sir.....me hoton ya gama dauka,saura na tsaye da wanda za'ayi muku da hajiya ummu saboda tarihi ko?" Sam baima san zaman da tayi wai hoto akeyi ba,muhsin ya cuceshi,yanzun idan baiyi wasa ba kafin la'asar hoton ya riga rana fadawa cikin kafofin internet,ko a haka baisan yadda akayi labarin bikinsa ya karade duniya ba,ko ina ka duba tsakanin whatsapp twitter facebook da instagram zancan da akeyi kenan "Dagota mana please,yanzu yanzu aka gama baka amanarta fa suna kallonka" suraj ya rada masa,no more option sai bata hannunsa da yayi "Taso" ya fada yana kallonta,labbansa daya furta taso din take kalla,tsoro da mamaki fal idanunta,dama shima dan iska ne?,abinda take fada kenan a ranta,a gabansu ummun yake bata hannunsa?,bashi da kunya ashe shima?. Bata gama wannan tunanin ba taji ya kama lallausan tafin hannunta,ba shiri ta miqe ta kuma zame hannunta da sauri hawaye suka fara taruwa a idanunta,lallai saita gayawa ummu abinda yayi mata,so yake ta mutu?,bayan ummu ta hanata tsaiwa kusa da kowa ma?. _to masu karatu,gafa amarya widad mai cike da tarin wauta quruciya gata kuma goyon kaka,ba'a fara wasan bama,muje zuwa dai_😂😅👏🏽 KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 30 Anty deena ta ankara da yadda taketa narai narai da idanu,kadan take jira ta fara sakin ruwan hawayen nata,murya qasa qasa ta yadda ba wanda zaijisu tace "Haba mana widad,so kike ummu ta gani hankalinta ya tashi?" Kai ta girgiza tana kallon idanun anty deena da golden eyes dinta "Okay,maza hadiye,hadiye kinji qanwata" kai ta sake gyadawa,sannan aka fara daukan hoto. Gaba daya ji yayi ya qosa ayi a gama,murya can qasa yace da muhsin "Please muhsin,am tired wallahi" murmushi yayi,sau tari yana bashi dariya,bai taba ganin dan police wanda bai jure hayaniya ba irinsa "Okay" ya fada yana dagawa widad hannu,a hankali ta qaraso wajen tana kauda idanunta daga kallon abbas,haka kawai idan ta kalleshi sai taji gabanta ya fadi "Maza kusa ayi muku ku biyu" wani irin tsoro ya kamata,gabanta ya tsananta faduwa,sai ta narke cike da tsoro tana kallon uncle muhsin,wanda shi sam baima san me takeyi ba "Matsa widad lokaci na qure musu" anty deena ta fada,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta fara takawa zuwa kusa dashi,nesa kadan dashi ta tsaya,saida mai hoton yayita magana da taimakawar gargadin da anty deena ke mata da idanu ta sake matsawa aka dauka "Enough please" ya sake fada "Dama ai an gama" suraj ya amsa wannan karon yana dariya,sallama sukayi dasu ummu,akwai yiwuwar su kwana a kano,duk da babu tabbas, uncle muhsin keson hakan,saboda akwai walima daya shirya musu. Tun daga wannan lokacin gaba daya ta sake zama sukuku,ita gaba daya komai ya kwance mata,hakanan banbarakwai take kallon komai,daga qarshe dai a daki ta qule ta qarasa yininta,duk kuwa da sabgar da ake cikin gidan. Da daddare kuwa bata yarda ta kwana da kowa ba sai a bayan ummu,kowa tsiyar ai dole su rabu yake mata,wannan ya sanya zuciyarta karyewa ta kuma soma kuka sosai,da qyar ummu ta rarrasheta. ********Washegari tun da safe anty madina ta aiko kiranta,tana sanye da dogon hijab da ummu ta fidda mata,ganin cewa a yanzun wani nauyi ya hau kanta,kuma gidan akwai 'ya'yan baffaninta maza,ga kuma baqi maza still 'yan biki da basu kai ga tafiya ba. A kitchen ta taddata tana ta hidimar hada abincin safe,sai ta waiwayo tana kallonta "A'ah,ya haka?,bakiyi wanka ba dama?" Baki ta turo gaba a shagwabe tace "Anty madina duka duka yaushe garin ya waye?,kuma Allah an fara sanyi fa" rai anty madina ta bata sosai "A'ah,daga yau sai yau,kada na sake gani,idan akace mace tana da aure da wuri take wanka ta gyara jikinta kinji ko?,ta fidda kayanta tayi kwalliya sosai" kai ta gyada a sanyaye,ita dai komai sai ace aure aure,duk an takurata da kalmar nan. "Shiga dakina a hankali kada ki tada min abba,akwai turarenki da kika bari jiya saman mirror,ki dauka ki feshe jikinki sosai,sai kizo zan aikeki" amsawa tayi da to,don ita badai qauna da turare ba,ta wuce dakin anty madinan. Ba jimawa sai gata ta dawo,tana ta zanga qamshi kuwa,ta nuna mata wani baske tace "Dauki maza kikai sitting room din kawunnanki" ba tare data kawo komai a ranta ba ta amsa da to,ta dauki kwandon tayi ficewarta,tana tafe tana tsayawa magana da mutanen dake mata magana a hanya,cikin sauran baqi na gidan,har ta isa qofar setting room din. Jim tayi tana duban baqin half cover din dake qofar setting room din,wanda keta sheqi "Waye ma to a ciki?" Ta tambayi kanta,bata sani ba don haka ta tabe baki,cikin wannan d'arin d'arin nata da rashin sabo da maza ta saka kai ciki tare da yin sallama. A lokacin kansa yana duqe a qasa,yanata trying number hafsat ce,wadda tunda ya taho basuyi waya ba,duk kiran da zaiyi sai ace masa is switched off. A hankali ya daga kansa yana motsa labbansa tare da amsa mata sallamar,idanuwansa suka fada a kanta sanda take takowa kamar mai takatsantsan kada ta taka kwalba,baby face dinta dake tsakiyar blue black din hijab dinta ta fito fes,qananun gashinta masu santsi dake kwance gaban goshinta sun sake qawata fuskar,dan qaramin bakinta me red lips ta dan tsukeshi waje guda,fuskarta sam babu fara'a,sai ya lumshe idanuwansa kana ya maidasu qasa ga hannunsa inda wayarsa ke riqe,shidai baisan me hajiya ta hango ba data zabi ya auri qaramar yarinya har haka,kyau?....ko kuwa me hajiyan ta kalla?,shi kansa bai sani ba. Tazarar wasu inches ta bayar a tsakaninsu ta ajjiye kwandon,tana daga tsugunne ta gaidashi da siririyar muryarta "Ina kwana?" "Kin tashi lafiya?" Ya amsa mata yana sake daga kanshi gareta a karo na biyu,bata amsa masa ba sai miqewa da tayi tsaye ta soma shirin ficewa a setting room din,saboda gaba daya a tsorace take,already ummu tayi mata horon tsoron maza sosai da shan inuwa daya dasu,a yanzun kuma bata gama sanin muhimmancin abbas din ba Da kallo yabi bayanta,dariya ta taso masa can qasan ransa,ta yaya cikakkiyar budurwa mai shekaru da wayo ta aikata haka?,sai ya gyara zamansa kadan yana lalubo sunanta "Widad" ya furta a tausashe,tsayawa tayi cak gabanta yana faduwa,dama yasan sunanta wai?,ta tambayi kanta "Zo mana" ya sake fadi,abinda yasa ta waiwayo kenan,suna hada idanu duk wani kuzarinta yayi nasa waje,sai ta narke fuska "Ummu zata yimin fada idan na dade" kai ya girgiza yana lumshe idanunsa kamar yadda yake a al'adarsa "Ba zaki dade din ba,yanzun nan zaki tafi" kallonsa takeyi,sai ya jinjina mata kai alamun tabbatarwa,don haka ta dawo a hankali,ta samu nesa dashi ta zauna. Tattara dukka hankalinsa yayi ya zuba mata idanu,yanzun ta ina zai fara mata bayani ma?da wanne harshe zai mata magana ta fahimci abinda yake cewa quruciya duk ta baibayeta?,a qa'ida babbar budurwa ce yanzun zaune a gabansa,sai yafi sanin yadda zai dinga handling abubuwa har su saba da juna. Motsawa tayi kadan tana hade rai saboda yadda yake kallon nata ya sake takurata,ya fahimci haka sai ya aje wayar hannunsa,a bisa tilas ya arawa fuskarsa murmushi sannan ya fara magana "Ummu ta gaya miki an daura miki aure ko?" Kai ta gyada tana kallonsa "Good,daga yanzu na zama yayanki,na zama kuma abbanki,zamu tafi dake can zan kaiki gidana,zamu tafi tare,kema gidanki ne duka,zakiyi duk abinda kikeso a ciki,kina so?" Idanunta masu tsananin haske da ratsin gold color ta fara rarrabawa a tsakanin nasa idanun,sai ya kafeta da idanu sosai yana kallon yadda suke juyawa,yadda ta mele baki ta kuma tabe fuska hadi da lumshe idanunta,eye brows dinta masu tsayi suka hade waje guda sannan ta sake bude idanun warrrr a kansa yasa tsigar jikinsa ta zuba "Bazan dade ba zaka dawo dani wajen ummu?" Ajiyar zuciya mai nauyi ya sake yana dan murmushi kadan "In sha Allah,nima daga yau na zama yayanki ko?" "Uncle dina dai ko?,naji nujood na cewa sunanka uncle abb...." Kasa qarasa sunan nashi tayi,tana jin kada tayi abinda bata kyauta ba,murmushi ya subuce masa ba tare da ya shirya ba,har fararen haqoransa suna bayyana,ya fuskanci nauyin kiran sunan nasa take "Uhnnnn,uncle abbas" sai ta gyada kanta tana hade hannayenta waje guda,yakai duba ga hannun nata,tsararren jan lallen nan nata yana nan tas saman hannunta,ya zuba masa idanu kamar mai karnatar taswirar zane,lallai akwai hikima mai yawa ga masu yin lalle,har da suke iya tsara zane haka ya bada wani kala da nau'i mai kyau. Rai ta hada sosai ganin yana ta kallon hannun nata, saita zare hannuwan nata zuwa cikin hijabin tana sake qudundunewa waje guda,ya dauke kansa yana maidawa ga dan qaramin leda yar mitsitsiya daya shigo da ita,sai ya dauka ya tura mata "Wannan waya ce,ki cewa ummu a kunna miki,akwai komai a ciki,zan dinga kiranki,sauran kuma kudi ne,duk abinda kikeson siya ko kike son amfani dashi ki dauka a ciki,kada ki sake tambayar kowa yayi miki wani abu" murna farinciki da kuma mamakin bata waya da akayi ya lullubeta,to amma kuma tana tsoron kaiwa umnu kayan tace wani ne ya bata,duk yadda take zumudin wayar saita noqe "Wallahi ummu zata dakeni,zatace waye ya bani" murmushin dole ya sake subuce masa "Kice uncle abbas ne,idan ma bata yarda ba kice a kirani,bazata miki fada ba" sai ta matso kadan,ta dauki ledar tana cewa "An gode,Allah ya saka da alheri" girma yaji addu'ar tayi masa,sai ya bita sa kallo kawai harta fice,ya maido dubansa cikin falon yana sauke gauron numfashi,tsahon zamansa da hafsa bata taba fadin haka ba,duk girman kyauta idan yayi mata 'An gode' shine iya abinda ta iya fade kenan,bata buqatar cin komai,so yake kawai yaga sun dauki hanyar bauchi,to amma babu dadi su kawo suga baici komai ba,gashi ya baro baqi a masauki,don haka ya fidda qaramin flask din tea dake cikin kayan,ya hada tea. A gaggauce yake sipping,yana tsaka da kurba uncle muhsin yayi sallama "Aah ya haka bakaci komai ba?" Ya fada bayan sun gama gaisawa yaga abbas na ajjiye cup din "Sauri nake ne,ya kamata mu dauki hanya da wuri,saboda kamar gobe nakeson komawa kaduna,akwai gyare gyare da za'a yi acan,a office ma kuma ina da ayyuka da ban gama settling nasu ba bare na dora da nawa,ban taba aiki a kaduna ba sai wannan karon,kaga ina buqatar maida hankali na sauke nauyin al'umma dake kaina" kai muhsin ya jinjina "Gaskiya ne,to shikenan,muje kayi sallama dasu saimu fita tare,zaka saukeni a al-hamsad tower zan shiga wani shago akwai abinda nakeson dubawa,zuwa azahar an kammala walima in sha Allah saiku wuce kafin la'asar" Sai data gama nuqu nuqu da fargabar nunawa ummu kayan daya bata,da taga ba zata iya ba saita wuce sassan anty madina,ta sameta ta fito a wanka,don haka ta zauna cikinsu walid dake falo suna kallo harta gama shiryawa ta fito ta sameta "Widad,har ya tafi baqon?" Kai ta gyada tana miqa mata ledar "Wannan ya bani,sai da nace bazan karba ba ummu zatamin fada,yace wai ba zata min komai ba" dariya ta subucewa anty madina "Taso nan" tace da ita bayan ta karba ledar,suka matsa gefe can inda yaran ba zasu jiyosu ba,zama tayi ta zaunar da ita a gefanta "Shi wannan ai ba baqo bane yanzu,mijinki ne kin gane?,kamar ni da abban walid,kamar ummu da alhaji,kin gane?" Tadai jita,amma bata gane mai take nufi ba,ita kallon abban walid da anty madina takeyi a mazaunin yayanta ne,ummu kuma alhaji babanta ne "Bari muga me miji ya baiwa matarsa kyautar farko?" Ta fada tana dariya,ta zazzage ledar,kwalin kyakkyawar waya qirar samsung ta fado hade da sabbin kudi a miqe fil dasu "Lalalala,ah lallai wannan diya tamu da goshi take,tun yanzu?" Dariya ta kubcewa widad,haka kawia taji kunya ta kamata,saita sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta anty madina na tayata dariyar "Zankadi,bude idonki ki gani" saita bude idon da sauri,ba qarya wayar ta hadu,take taji murnarta ta qaru,qaunar wayar kuma ta shigeta,suna shirin kunnawa momma tayi sallama falon "Wa'alaikumus salam,qaraso momma,duk sun cika falon" anty madina ta amsa tana qoqarin tattare kudaden waje guda "Wannan sabbin kudi fa,ko na liqi ne da kikayi canji?,aisai ki adana abunki,bikin da babu ko kidan qwarya bare DJ,kamar wata amaryar buzuzu" "Uhmmm,momma kenan" anty madina ta fada tana dariyar yaqe "Albarkar aure ai ake nema,bare widad ma nawa take?,ina qawayen ma bare ace za'a zauna yi mata irin wannan bidi'ar?,ni ban canzo kudin komai bama,angonta ne ya bata hade da wayar?" Sai a sannan idanunta yakai kan wayar "Kai!" Ta fada cikin ranta,tasan wayar fes,irin wayar da deena tace yallabai(mijinta) ya kawo mata tsarabarta ne daga india a wannan satin daya dawo daga course daga can "Tofa,da gamo da kasawa,kada fa muna nan mun shanya baki muna kallonta yarinya qarama amma ace har tasan komai,kodai ta bada wani abune aka bata wannan tukuicin haka?" Momma din ta fada tana kama baki, zuciyarta cike fal da qyashi da baqinciki,don ko yanzu data baro sassanta maganar da suka gama kenan da batulu matar babanta da 'yan uwanta da basu tafi ba,duka dai akan widad din,suna ganin komai anyi mata fiye dana 'yan uwanta,ana kuma wuce makadi da rawa a kanta saboda tana da daurin gindin ummu,sun manta kowanne aure da irin nasa nasabin yake zuwa,labarin lefe data samu,manyan mutanen da suka halarci daurin auren da kuma kayan da aketa hadawa za'a tafi jere dasu kawai sukeyi,banbamcin da ake nuna mata akan nasu 'ya'yan yayi yawa. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 90 16 59 91 *Zafafa biyar kadai keda sinqin nau'ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci guda*🤝😄 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 31 Maganar ta qonawa anty madina rai sosai ta kuma bata haushi,sannan sai taji.maganar kamar tayi girma a kunnen widad,tana girmama dukka faccalolin nata saboda dukkansu sun girmeta,ita kadaice qarama a cikinsu,shi yasa take musu kallon yayunta,don haka ta tattara wayar da kudin ba tare data gama saita wayar ba ta miqawa widad "Kaiwa ummu ta gani ta adana miki,anjima zan shigo saina qarasa gyara miki" karban kayanta tayi ba tare data ma fahimci maganar me momma takeyi ba,ko baqincikin dake manne a ranta ba ta qara gaba cikin doki da zumudi. Da kallo momma ta bita sannan ta tabe baki "Kinga yarinya sai rawar kai take,Allah yasa bai lasa mata zuma a baki ba ya barmu da....." "Kai.....kai momma" anty madina ta fada tana kama kai fuskarta na nuna zallar rashin jin dadi "Wannan maganganun sunyi girma da yawa fa" "Wanne girma?,a wajen wa?, yarinyar da yanzu keda ita dukka matsayinku daya?,tabdijan,kina wasa da yaran yanzu,ni da rannan naji tana gaya musu zata tafi gidanta itama ta dinga girki irin nasu anty dina,tayi.bacci a gadonta?,to billhuwallazi kada ma kiyi mamaki idan akace miki ya gama lallatseta kafin ya tafi,ko ya fara buda hanyarsa" "To haka muke fata,aiba haram bane,me zan baki?" Tayi mai gaba daya saboda maganar ta soma isarta "Yauwa,mai zaki zuba mana,nawa ya qare gaba daya jiya suka zube shi a dambu" karbar robar tayi kawai ta miqe ta wuce store dinta dake manne a kitchen, cikin ranta tana tur da Ala wadai da irin wanna dabi:ar tata,banda abinta meye abun kishi da widad?,me za'a yiwa baqinciki akanta,yarinyar da bata da maraba da marainiya?,bata taka muku ba bata zubar muku ba amma kunbi kun qwarzabi kanku a kanta,batama san me suke ba,bata wani ganewa halinsu idan ba takurata sukayi da kyara ko hantara ba,shine zaka ga ranta ya baci saman fuskarta,ko kuma ta janye jiki daga gurin ba kuma zata dawo nan kusa ba. °°°°°°duk yadda take ta so ta tursasata kanta da zuciyarta.....ta tafi da zuciyar tata da ruhinta bisa doron shawarar da anty ummee ta dorata akai amma abun yana ta neman yaci tura,daga sanda labarin AN DAURA auren mijinta abbas sa wata gaba daya ta birkice,zuciyarta nata gaya mata anya mafita ce anty ummee ke bata?,ta tsaya kawai tayi masa hauka,tayi tawaye ta tada masa hankali har ya aje auren,wannan shine shawarar da mafi rinjayen sashe a zuciyarta ke bata,yayin da wani sashen yake gaya mata ta haqura taci gaba da tafiya a haka,saboda taga alfanun hakan,ta samu alkhairai masu yawa daga jikin abbas din. A ranar ita daya ce a gidan,ta tura yaran gidansu,ko wankan arziqi bata samu yi ba bare ta kintsa gidan,sai ta zauna dirshan,ta soma bin status din dukkan wanda tasan ya tafi kano daurin auren. Irin kyan da taga abbas yayi cikin dukka hotunan,da yadda taga fuskarsa shimfide da qayataccen murmushin nan nasa sake matuqar burgeta da daukar mata hankali sai taji ta sake birkicewa,saidai kaf hotunan bataga fuskar amaryar da taketa lalube ta gani ba. Jefa wayar tayi gefe tana rufe fuskarta da tafin hannunta,kuka ya subuce mata,abbas ya cuceta,kuma ko meye zaiyi mata bazai taba wanke kanshi ba,ba haka tasan abbas ba,bashi sa kallon mata ko kadan,bai shiga shirginsu kwata kwata,ya akayi wata mace ta gilmawa idanunsa har ya qyasa yaji yana son yin tarayya da ita?, macen ma yarinya qarama kamar yadda aketa bata labari?,ya zuwa yanzu ka ta fara tantamar anya yarinyar ce kamar yadda aka ce?,tasan tsarika da zabin abbas,ta yaya zai aura yarinya?. Wayar ta jawo da sauri ta cireta daga flight mode din data saka mata tun jiya,dai dai lokacin da saqon abbas ya fado wayarta bayan ya gaji da kiranta yana jin wayar a kashe,tsaki taja tayi fatali da saqon ta shiga duba number anty ummee. Bugu daya ta daga,kamar mai jiran kiran nata dama,kuka kawai ta saka mata,tayita yi har kudinta ya qare kiran ya katse,anty ummee daga can inda take zaune a falonta taja tsaki "Kuka ma yanzu kika fara,kishiya wasace,shegen son abun duniya irin naki,inda kin bada dama 'yan uwanki sunzo gidan an dan zauna dake aida an debe miki wannan damuwar,amma don kada mutum yazo yaci abinci da nama kika hana kowa zuwa,kyaci takaicinki ke kadai" ta fada tana bin kiran nata daya katse. "Anty ummee anya zan iya?,wallahi bakiji abinda nakeji a qirjina ba" ta fada cikin muryar kuka "Ke dole ki daure fa,saboda ribar ciki tafi rashin ribar yawa,wannan ce kadai hanya guda daya da zaki zauna salamun salamun a gidan,kuma kowa yayi miki.biyayya ba tare daya shirya ba,wannan itace kadai hanyar da zaki tankwabar da auren ma gaba daya ba tare da kowa ya zargeki ba,amma fa saikin jure sai kuma kin daure,in kikai haka gaba zaki godemin" Shuru tayi tana nazarin maganganun a kanta "Ki kwantar da hankalinki,idan kin samu lokaci kizo zan sake shirya miki yadda komai zaici gaba da tafiya" ta sake gaya mata bayan sunyi maganganu masu yawa da suka dan saka hafsat din sake aro dauriya,duk da yadda take jin zuciyarta kamar wuta "Zanzo gobe ko jibi ma" "To shikenan,amma lallai lallai karki nuna masa wani banzan hali ko daya,kiyi kamar ba'ayi komai ba,zakiga yadda zai sake bude miki bakin aljihunsa" "To shikenan" ta amsa mata tana sake share sauran hawayenta. Suna gama wayar saita koma ta duba saqon daya turo matan,gaisuwa ce yana kuma shaida mata suna kan hanyar dawowa gida,wani mugun tsaki taja,kamar zata ajjiye wayar sai kuma ta tuna da zancansu da anty ummee,tayi ta maza ta danne zuciyarta ta kirashi. Bugu biyu ya daga wayar,dai dai lokacin da har sun fara yiwa kano nisa,suna bayan motar da ake tuqasu shida muhammad da suraj a tsakiyar escort dinsa,sai ya gyara zamansa yana kara wayar a kunnensa. Tun daga sautin muryarta ya fuskanci akwai damuwa,duk da yadda tayi namijin qoqarin boyewa,to amma a yadda taji ta masa magana ba wani mummunan lafazi sai yaji hankalinsa ya sake kwanciya,da ya tambayeta mai ya sami wayarta tun jiya yake kira a kashe "Kamar da gaske an damu dakai" ta fada a qasan ranta bayan tayi tsaki,amma a zahiri sai yace "Nawwara ce ta jefamin ita bayan freezer,ruwa ma ya tabata,yanzu nakeson bada ita game gyara" "Ya salam,shikenan,ki jira na dawo zan bayar a duba miki da kaina" tuni zuciyarta ta gama hasko mata abinda zatayi da wayar don haka tace "A'ah,ai yaronma yana waje jirana ma yakeyi na bashi wayar" "Is okay,yayi,saimun qaraso" "Ala tsare" ta fada tana gintse wayar,saita maidata flight mode din,gobe ko jibi idan zata gidan anty ummee zata biya ta saidata ta sake hade kan kudadenta,ya sake kashe wani kudin ya siya mata wata,don ba imani ko daga qafa yanzun tsakaninta dashi. Zuciyarta nata gaya mata ta shiga kitchen tadan samar masa wani abun da zaici,amma sai tayi fatali da wannan tunanin,taja tsaki ta miqe kan kujera abinta tana cewa "Bazan iya ba wallahi,wannan pretending dinma da nakeyi duka ya fara isata" ta sake jan wani tsakin tana rufe idanunta tanajin yadda ranta ke mata suya. Awanni kusan biyu tana zaune a wajen,sai data gaji don kanta,sannan ta miqe ta kom bedroom dinta,yanayin da jikinta yake ciki itama ya fara damunta,don haka ta hada ruwa ta shiga wanka,gaba daya hatta da yaran batason motsinsu ko bari bari da zasuyita sakata,don haka tun da safe ta aika gidansu dasu,wannan ne kadai zai bata damar zama tayi jinyar kanta da kyau. A nutse ya fita a motar bakinsa dauke da addu'o'i,samuel ya zagayo yayi saluting nashi sannan ya miqa masa key din cikin girmamawa,hannu yasa ya karba yana masa ban gajiya,sannan samuel din ya juya ya fita a gidan,zasu qarasa a ragowar motocinsu dake cikin layin. Jefa key din yayi a aljihun rigarsa,sannan ya juyo yana nufar gidan bayan ya sauke ajiyar zuciya,zuciyarsa na gaya masa ko me zaya tarar cikin gidan kuma?,sanin gaibu sai Allah,haka yaci gaba da takawa da kuzarinsa da qarfin gabban nan nasa da ya zama kamae signature dinsa. Da sallama a bakinsa ya yaye labulen falon yana qarewa falon kallon,as usual yana nan kamar kowanne lokaci,kamar yadda ya saba tarar dashi, matuqar sa'a ce zaici yayi wata tafiya ya dawo ya samu falon a kintse,har ya zame masa jiki,bawai ya dawo ya sameshi a hargitse ne abun mamaki ba a gareshi,babban abun mamakin ya sameshi neat,sai ya saki labulen ya kutsa kai zuwa ciki. Shurun da yaji yayi yawa sai ya dauka ko bacci yaran sukayi bayan ya kalli agogo,bakwai sa rabi na dare harda wasu mintuna,kansa tsaye ya tunkari dakinsu,amma daya tura sai yaga wayam babu kowa,dakin dai shima kamar ko yaushe,saiya maida qofarsa ya rufe ya sauya akalarsa zuwa dakinta. Tana tsaye bayan ta fito a wankan,daure da zanin jikinta wanda tayi masa daurin gaba(daurin qirji),tana ta qoqarin taje gashinta yana cije mata saboda taurin da yayi,ya turo qofar suka hada idanu,saita amsa masa sallamar ta maida kanta wajen taje kan nata,kamar ma batasan wayeshi ba. Kofar ya saka yana zare idanunsa daga saman gashinta yana takowa zuwa ciki,yasan kafin ya tafi ya ajjiye mata kudaden gyaran jiki da gyaran kai,yafi tsanar qazantar gashi fiye da qazantar komai,amma ita kwata kwata ba damuwarta bane,to ina takai kudin?,me kuma ya hanata zuwa gyaran kan?,jikinma baiga alamun an gyarashi ba, tun yana sanyata a gaba ya kaita har ya daina bata lokacinsa da kudinsa,tunda ya siya mata mota kudin kawai yake bata,cikin kaso goma kuma kaso biyu kacal take zuwa,kaso takwas din saidai ta adana kudinta,duk da shi baisan me takeyi dasu ba. Cikin juriya ya isa bayanta,ya kuma rungumota ta baya zuwa cikin jikinsa, hannayenta biyu ta saka da dukka qarfinta tana son janyeshi a jikinta,yasan zata aikata hakan,shi yasa bai mata qaramin riqo ba "Am sorry" ya fada da muryar da yasan tana matuqar tasiri wajen karya lagonta,turjiya da tijara takeson masa koda zata rage zafin dake danqare a ranta,mugun guguwar baqin kishin da anty ummeen tasa ta danneshi bisa salo na kissa,amma sautin muryarsa data sauka a kunnenta ta karya dukka lagonta,sai ta sakar masa kuka,kuka kuwa sosai wanda ke bayyana ftsananun zafin da zuciya ke fuskanta. Ya sani,kishi yana da zafi,don haka ya fara lallashinta cikin wani salo da yasan yana saukar da zafinta,a hankali sai ya soma birkice mata,abinda yaja hankalinta kenan ta soma zame masa tana tureshi,cikin ranta tana mita,sai an fara abun arziqi dashi sai kuma ya canza hanya,shi din babu dama a hada jiki dashi sai wani zance na daban. Sosai yayi mata riqon tsauri,baisan meye damuwarta ba,bata taba iya karbar damuwarsa hannu bibbiyu ta bashi hadin kai ya sauketa ba,kamar bata da wani feeling,kuma qarya ne!, tabbas tana dashi,saidai ta sanyama ranta wani baqin rai da girman kan banza. Duk yadda taso tayi avoiding nasa amma ta kasa,dole ta bada kai bori ya hau,duk da ba wani hadin kai ya samu ba,ya saba da hakan,har kusan ya zame masa jiki,bayan komai ya kammala kuma ta shiga quncinta kamar yadda ta saba,baibi ta kai ba,hasalima kafin tayi wanka sai daya tabbatar ta wanke kanta da kyau,ya hadata da hand drayer sannan ya fito,ya wuce sassansa don ya shirya. Ko da ya gama shirinsa ya fito kitchen ya duba saboda yadda cikinsa ya rarake kamar an masa yasa,babu alamun an girka komai,sai kawai ya dauki key ya fita don yi musu takeaway ba tare da ya tsaya jiranta ba,yasan ba abinda zata dafa a wannan lokacin,a hanya yayi kiran hajiyarsa,har kuma ya qarasa wajen sunata wayar,yace mata gobe zai shigo da wuri kafin ya wuce,don a gobe yakeso ya koma kaduna. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 32 Yana daga tsaye yake shanye tea din dake cikin cup din,yana yi yana hadawa da qonannen cake din da hafsat din tayi,dai dai sanda ita kuma ke sanye da kampala dinkin tea bubu,fuskarta a wanke tas babu digon kwalliya kamar kullum,hakanan fuskar tata a dinke take babu walwala sam sam. A duk lokacin data kalli abbas....ta kuma tuna a yanzun bawai ita daya ce mutum dake amsa sunan matarsa ba,sai taji kamar ta shaqe kanta,kota zauna tayita zunduma ihu har sai dukkan jama'ar dake kewaye da ita sun fuskanci irin zafi radadi gami da qunar dake cikin ranta,tsantsar bacin ran da babu halin nuna shi,baqinciki da tashin hankalin data zabi lullubeshi da kissa da kuma nuna halin ko in kula da lamarin aurensa,wanda ko kusa ko alama ba haka bane cikin ranta. Cup din ya dire saman fridge din yana furta "Alhmdlh" da Peace voice dinsa dake dauke da wani calmness da bai cika son hayaniya ba,idanunsa ya zube saman fuskarta yana kallonta,saita janye nata idanun daga kallonsa,batason zuciyarta ta karye ko sonshi ya motsa mata har tayi wani misbehaving,tsaki yana subucewa daga bakin nata,saidai Allah yasa baiji ba "Zan wuce" ya fada murya can qasa "Allah ya kiyaye hanya" ta amsa masa a taqaice tana folding hannayenta a qirji,matsawa gabanta kadan ya sakeyi yana rage kusancin dake tsakaninsu "Me da me kuke buqata?,ko kuma shikenan?,ba wani taro da zakiyi?" Kusan duk abinda takeso ya dire mata,ta wanki aljihunsa yadda ya kamata,to amma duk da haka batasi tace masa shikenan din, tunda zataje wajen anty ummee,batasan me zasu tattauna ba,don haka tace masa "Idan akwai wani abu zamuyi waya" kansa ya jinjina,ya sauke mata soft kiss a goshinta,sannan yaja da baya ya juya yana barin wajen,dole ta kama masa qaramar jakar tabi bayansa da ita tana qoqarin gyara yanayin fuskarta,don komai ya sake hawa kan saiti,ya kuma ci gaba da tafiya yadda suke tsarawar. Da murmushin yaqe ta bishi sanda yake waving mata hannunsa,motarsu tana fita ta koma ciki da sauri,ta dauki jakarta mayafi da key din motarta,har takai bakin qofa ta koma ta rage yawan kudin dake cikin jakar ta adana a locker dinta,cikin ranta tana raya "Kada bacin rana ya gifta ta kansu" duk kuwa da cewa gidansu zataje,acan zasu hadu da anty ummee din. Tunda ya tafi kusan ayyuka suka cunkushe masa,bashi da wani cikakken lokacin kansa bare na sauran abubuwan,haka ya dinga qoqarin handling komai,ga gida babu mace,idan ya dawo kusan wasi hidimomin da ya cancanci ace matar aurensa ce tayi masa kafin isowarsa gidan shi zai gabatar dasu,wanann ya sanya shi yanke hukuncin ajjiye widad a nan kadunan,ko babu komai gidan bazai zamana shuru babu dan adam a cikinsa ba. Yana daga nan ya sanya aka sake gyara part guda daga cikin parts din gidansu na bauchi,a nan kadunan ma yayi wasu qananun gyare gyare,mutum ne shi koda yaushe mai tsananin kyautatawa ga duk mutumin da Allah ya dashi zama dashi,hajiya tafi kowa sanin hakan,shi yasa zamansa da hafsa ya tsaya mata a rai qwarai da gaske,tako ta ina abbas din inda rubutawa bawa qaddararsa akeyi ya cancanci samun mace ta gari,wadda zata kula dashi matuqa gaya. ************K'arasa zuba jewel's dinta data debo tayi cikin qaramar jakarta ta zuge,sannan ta dubi alhaji salim mai fata dake zaune kusan awa guda saman kujerar madubi dake dakin widad din "Alhaji na gama" ta fada tana murmushi "Da kyau jikata,sai tafiya kenan" kai ta gyada masa tana dariya "To muje na rakaki da kaina,kada ma mutsaya sauraren kowa su bata mana lokaci" sai ya miqe yana daukar mata jakar,yayin da ta lulluba mayafinta abinta,suka jera ita da kakan nata dake nuna mata zallar qauna hadi da kulawa kamar yadda tsohuwar matarsa ummu ke gwada mata. Hankali kwance alhaj salim ya bude mata gaban baqa wul don motar qirar range rover,daya daga cikin motoci mallakin ASP abbas muhammad bello "Shiga abinki ki zauna kafin su fito" sai a sannan ta kalleshi,tadan narke fuska "Amma alhaji,kace dakai da ummu duka kuna nan tahowa ko?" Kai ya gyada mata yana murmushi,saidai can qasan ransa kewa da kuma tausayinta ne fal zuciyarsa,farincikinsa guda daya zuwa biyu ne......sun aurar da widad din cikin aminci zuwa ga hannun mutumin da basu da haufi a kansa,nagartarta da ingancinsa sunkai,na biyu duk yadda suketa juya yadda za'a fidda widad din daga gidan salin alin bata tara musu taron jama'a ba,sai gashi da qafafunta ta fito zuwa motar da zata daga dasu bauchi,Allah ya bashi hikima da basirar da taketa shauqin tafiyar zuwa gidanta "Idan bamuzo ba waye zaizo?,kedai sha kuruminki,abinci zaki dafa mana mai dadi nida ita a kitchen dinki" murmushi ne ya sake kubce mata,itakam widad har ta isa macen da zata shiga kitchen tayi girkin baqi kenan,saita kama murfin motar ta kuma shige,alhj salim ya miqa mata jakar,sannan ya tsaya daga bakin motar yana mata hirar dake sake dauke hankalinta. A gajiye anty deena ta tura qofar dakin ummu tana sauke ajiyar zuciya "Allah ummu nidai nayi iya dubana banga widad bafa" cikin mamaki ta dubeta "Har wajen alhajin ku kin duba basa tare?" Kai ta girgiza "Ban duba ba" "Yi qoqari ki dubota,kinga kada suyi dare a hanya" "Gaskiya dai,nima banason muyi tafiyar daren nan saboda sanyi" tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin. Har zata gota jerin gwanon lafiyayyun motocin da aka shirya su saboda daukar widad din ta hangi alhajin tsaye jikin daya daga cikin motocin,saita dawo da baya,abinda ta gani ya sanyata kusan faduwa saboda dariya,widad ce zaune gaban motar ta qwame abinta,sunata hira da alhajin tana ta qyalqyala dariya,kome yake gaya mata oho,saita tsagaita dariyar tana kallonsu,murmushi na kubce mata,qasan ranta itama tausayin widad din na tsarga mata "Kuruciya me dadi" ta fada a hankali hawaye nadan tsatstsafo mata,ta tabbatar inda ace babba ce yanzun haka ake shirin tattarata zuwa gidan miji,gidan mijin ma wata duniyar ba duniyarta ba,ba duniyar data rayu a cikinta ba,ba shakka da tuni tana nan hankali tashe,saita juya kawai zuwa cikin gida don ta sanar musu,tafiya ta tabbata tunda amarya har takai kanta cikin mota,murmushi ya sake kubce mata. Dab da bakin falon sassan ummu sukayi kacibus da inna batulu momma "Har yanzu ba'a ganta ba?" Ta fada a fuska alhini ne fal,yayin da qasan zuciyarta wani fata ne na daban,ba tare da anty deena ta kawo komai a ranta ba tana danne dariyarta tace "Wa?,ai widad tuni tayi landing a mota" ido batulu ta zazzaro "Kamar yaya deena?" Dariyar da take riqewa ta kubce mata "Wallahi alhaji ya raka amaryarsa,kodan kishin nan ma bayayi,tana can tana jiran 'yan kawo amarya" dogon salati taja tana tafa hannu,sai kuma taja burki ta juya da sauri har tana tuntube ta koma zuwa cikin falon,da kallon mamaki anty deena ta bita,saita take mata baya tabi bayanta itama. Tana shiga falon batulu na kwazawa 'yan uwan abbas dake zaune a falon suna jiran fitowar widad din don su wuce "To ai bayin Allah zaman jira da qoqarin bikon da akeyi ya qare,amarya dai takai kanta cikin mota mu take jira" ran anty deena saiya sosu,duk da cewa akwai quruciya ga deena bai kyautu batulu ta kawo saqon a haka ba,fuskarta na nuna zallar alhini kamar ta aikata wani babban sabo a musulunce. Inna uwa qanwa ga hajiya ta tura wayar hannunta cikin jaka tana sakin dariya "La la la,lallai yaron namu badai farinjini ba,niko na godewa wannan diya tamu wallahi,ta hutashe shemu,saimu tashi shirin tafiya ta kammala" anty deena ce ta karbe cikin dariya "Aiko dai batason wahal daku biyan kudin biko,ai shikenan" dariya aka dauka a falon,kowa yana fadin albarkacin bakinsa,kusan yadda batulu taso a juya zancan ya zamarwa widad abun fada abun baizo a haka ba,kusan kowa dariyar quruciyar yakeyi. Sannu a hankali jerin motocin dake dauke da mafi yawan 'yan uwanta suka fara barin farfajiyar gidan alhj salim mai fata,motar da take ciki itace mota ya qarshe,duk da a tsarin tafiyar zata kasance cikin tsakiyar motar securities din da zasuyi musu rakiya har zuwa garin bauchin. A hankali tasu motar ta fara motsawa,yayin da taketa dagawa su Aafiya hannu tana fadin "Sai kunzo,karku damu,alhaji yace kamar wancan lokacin da naje gidan uncle muhsin,wannan lokacin har zuwa zasuyi shida ummu saimu dawo tare,idan zai taho ku taho tare dashi don Allah" ta fada tana kallon afiya,tans jin ba dadi itama,zuciyarta najin wani irin yanayi wanda.bata saba jinsa ba,irin yanayin dako sanda zataje gidan uncle muhsin bata sanshi ba,wannan shi ake kira da yanayi na rabuwa......rabuwa da gida..... rabuwa da muhallin da qaddara ta wanzar maka a haifeka a ciki......rabuwa da bigiren daka rayu kayi kuma gwagwarmaya a ciki.....fadi tashi tsakanin masoya da maqiya,zuwa wani bigiren da RUBUTACCIYAR QADDARARTA ta zana mata......BIGIREN dake qunshe da tarin qaddarorin rayuwarta.....qaddarorin dake da tsananin zafi quna da kuma barwa rayuwa tabo me cin rai. Tun suna tafiya tana biye da hirar wadanda suke tare cikin motar wato anty deena,anty madeena anty madeeha da inna uwa,wani bangaren na zuciyarta kuma nata hasaso mata kayayyakin da dukka ummu ta nuna mata ta kuma shaida mata nata ne gidanta za'a kai mata,yadda zata sarrafasu ta more kayanta,irin yadda taga su anty deena anty ramziyya basma da sauran yayyunta keyi,zatayi iko irin nasu kenan itama,zata saka wasu wanke wanke idan sunzo gidanta,sai qaramar dariya ta qwace mata ita kadai,tana fasalta yadda zata saka su rafi'ah aiki,kuma dole suyi,saboda jiya jiya taji anty madeena na cewa ita din yanzu dukka ta girmesu,duk kuwa da cewa sun babbata wasu watanni. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 33 Table guda ya kama shi kadai,sanye da fara sol din shirt me gajeran hannu,sai wani lafiyayyen trouser daya dace da boots din qafarsa,coffee kawai yake sha,duk da yana da buqatar abinci,loneliness yake da buqata,yayi hayaniya har baisan iyakar adadinta ba,abinda ba dabi'arsa bace,yana tsoron hakan ya haifar masa da ciwon kai,wannan yasa ya zabi ya kebe shi daya ba tare daya gayawa kowa inda yake ba idan ka dauke suraj. Tun jiya suke karbar baki,ko kusa ko alama bai dauka wani sabon bikin zasuyi ba,sai da yaje gidan hajiyarsa yaga yadda ta tashi gagarumin biki,ya koma gida bisa ga mamakinsa hafsat ta zauna tayi masa lissafi ta kuma karba kudade sosai daga hannunsa tana shaida masa itama taro zatayi "Ko yaya ma dai nakai ga qinta,tunda har an daura ta zama matarka,ina da ikon maida abinda ya faru ya zamana ba wanzajje ba?" Kai ya gyara cikin gamsuwa,ransa na masa dadi,yana sake samun nutsuwa,mamakinsa na sake daduwa akan hafsat din,fatansa da burinsa na dorewarta a haka na sake hauhawa,wanann abun yasa ba haufi ya ajjiye mata abinda ta buqata harda ma qari. Kusan komai mamaki yake bashi,auren yazo masa a hagunce,yanata kuma zuwa da abubuwan mamaki,bai dauka wani aure bane na azo a gani ba,amma sai gashi anata shirye shiryen daga kowanne bangare. Wayarsa dake yashe saman table din ta soma haske,saboda tuni ya maidata silent,idan kira ya shigo sai.ya duba ya tabbatar mai muhimmanci ne kafin ya daga,a yanzun ma suraj ne don haka ya danna green ya kuma maidata handsfree ba tare daya dauki wayar a hannunsa ba ya barta nan saman table din. "Baka dawo bane?,kana ta ina?" "I will be back......akwai damuwa ne?" "Babu,kusan ma an kammala komai,har presidential lodge din da za'a zuba sauran baqin ya zama ready" "Good,thank you suraj" "What are friends for" murmushi ya saka ya kashe wayar. Har ya daga coffee din zai sake sipping tunanin kiran Samuel yazo masa,ya lumshe manyan idanunsa kadan sannan ya budesu yana tuna yadda hajiya ke bashi amanar yarinyar,tun ranar da aka daura aurensu har yau din nan,ba ranar da zata fito ta fadi bata ambata masa cewa amana ce ta iyayenta ba,sannan amanace ta ita kanta hajiyan,farincikin da yaga hajiyar nayi da auren kawai ya isheshi shima,bashi da burin daya wuce ganin walwalarta,da kuma farincikinta,wannan ya qara masa qaimi ya danna number samuel din. Cikin girmamawa da kuma nuna respect yake amsa kiran ogan nasa,ya tambayeshi hanya yace komai lafiya,ya gaya masa a inda suke a yanzun,ya kashe wayar yana irga adadin mintunan da suka rage musu su qaraso bauchin,sai ya shanye sauram coffee dinsa ya miqe yana maida wayarsa aljihu,ya dauki key dinsa ya nufi parking lot na gurin shan coffee din. °°°°°°°Cike gidan yake da 'yan uwanta da abokan arziqi har zuwa compound na gidan,wani abun mamaki ko kuma rashin sabo ga duk wanda yasan gidan ko kuma ya saba wucewa ta gaban gidan,ko gari banza da wahala kaga tayi baqo,don ita din mutum ce mai tsananin rowa da tsumulmula,rashin kyauta rashin faran faran da rashin iya tarbar baqo. Daga cikin gidan kuwa,cikin bedroom din,hafsat din ce zaune a gefan gadonta,sai anty ummee da tayi tsaye gaban cupboard dinta tana zaqulo mata kayan data saka,sai mita takeyi cikin masifa "Duk wannan uban suturar bansan me kike dasu ba,ke baki saka ba ke baki bayar ba,duk kayanki na fadan kishiya kuma bansan gidan uban da kika kaisu ba,kudin dinki da gyaran daya baki suma ina kika kaisu oho" "Don Allah anty ummee kawai ki dauko kayan da zaki dauko ki barni naji da abinda nakeji" hafsat ta dago kanta da takejin kamar zai cire ta fadawa ummee din,sai ta waiwayo ta dubeta,idanunta har sun kada sun canza kala,tabe baki tayi,ta juyo hannunta riqe da wani lace,wanda a ido yayi mata kyau sosai,tana kuma saka ran zai zaunawa hafsa din "Da wannan raunin naki da kuma rashin juriyarki bana jin zakici nasara maganar gaskiya,yau kawai.....tun bata kai ga shigowa gidan ba?,ina ga ta shigo?,ta wanzu a cikinsa?,zakici nasara kuwa?,wannan siradin ba na raguwar mace mai raguwar zuciya bane,hanya ce mafi sauqi ta mallakar kowa da komai......saidai.....tana yiwa yawa yawna mata wahala,ciki harda ke da alama" Hannunta dake dafe da kanta ta saki,ta sake daga kanta tana kallon anty ummee da kyau,muryarta a mugun karye,ita kadai tasan me takeji tsakanin zuciya da qirjinta "Wanne qoqari zanyi anty ummee bayan wannan?,kinsan me nakeji kuwa?,har na fara nadamar daukan shawararki,qila da ace abinda zuciya ta ke gayan nayi na aikata.....wala'alla da ban fuskanci zafin da nakeji a yanxu ba....." "Da kuma kinyi biyu babu ba.....da baki samu darajar da kike ganinta a idanunsa ba,da nutsuwar da kike qaryatawa a yanzun a yadda kike ganin babu ita tayi qaura dake kwata kwata..... tashi kiyi abinda zai fishsheki,ki yiwa zuciyarki qarfa qarfa,kici galaba a kanta,don ki cimma muradinki" ta qarashe maganar tana watsa mata kayan data debo din,sannan ta juya ta fice tabar mata dakin don ta bata damar shiryawa. Bin anty ummee tayi da kallo harta fita,sanann taja gauron numfashi ta miqe ta soma daga kayan tana kallonsu,tana jin qirjinta na mata wani zafi,tana jin kamar ta cinnawa gidan wuta gaba daya,sauqi sauqi daya takeji a ranta,idan ta tuna qaramar yarinya za'a kawo mata,tana da ikon juyata duk yadda takeso,amma ta wani bangaren tana jin zafin yadda ya dauko yarinyar da ta kusa haifarta, tabbas banda gidansu ana zaman karatu ta haifi yarinyar,idan ta zauna ta lissafa shekarunta da nata. Bata damu da canza undies ba,tunda a nata ganin basa cikin abinda zaka damu da canzasu koda yaushe,ta riga data saba,sometimes abbas ke sakata canzawa,idan ta tarasu zaiyita fada sai ya tilastata ta wanke,idan kuma yana free ma baya jin qyashin wanke mata su. Tana gama shiryawa mimi ta shigo da gudu riqe da hannun nawwara,bin yarinyar tayi da kallo,tunda aka fara hidima a gidan taga jama'a taketa murna,rabonta da ganin mutane haka a gidansu tun haihuwar nawwara,a sannan kuma bata da wani wayau sosai "Anty jamila tace ki canza mana kaya,wai anty amarya tazo,yanzu motarsu ta shigo" gaban hafsat yayi mummunar faduwa,tabbas dirin motoci takeji daga harabar gidan,hakan yana gaya mata MUGUN IRIN ta shigo gidanta kenan,zuciyarta na wani irin zafi ta rufe mimi da fada "Anty amaryar ubanki,kike rawar qafa a kanta,ki cewa jamilan ba za'a canza miki kayan ba,tafi ki bani waje tun banyi ball dake ba" tsoro ya kamasu duka su biyun,bama kamar mimi da tayi tsilli tsilli da ido tana shirin saki kuka,dai dai nan anty ummeen tashigo,a bayanta kuma anty atika ce yayarta da suke uba daya "Yauwa,kin gama shiryawa ko?,maza fito gasu sun iso,fito" fuskarta tamkar wanda aka yiwa bushara da rasuwar wani makusancinsa "Na fita nayi musu me?" Kafin anty ummee ta amsa anty atika ta rigata "Ki tarbeta,ai haka akeyi" ta amsa mata tana shigewa toilet din hafsan,don fitsari ne ma ya shigo da ita,banda haka saitayi zuwa dari bata shigo dakinta ba,duk da dama bawai zuwan takeyi ba. Cikin wani madaukakin murmushi take takawa zuwa bakin motocin da sai yanzu suka gama tsaiwa,dai dai sanda anty deena ke tsaye a bakin qofar motar tana karantowa widad addu'o'i tana maimaitawa "Sannunku da zuwa,ma sha Allah" hafsat wadda ta lullube jikinta da kyakkyawan mayafinta kalar lace din jikinta ta fada,fuskarta wadace da fara'ar da takejin dai dai take da kukan mutuwa. Anty madina anty deena anty halima batulu da momma dake wajen dukkansu suka waiwaya suna duban inda maganar ta fito,hafsat din da mutum takwas dake tare da ita,anty ummee da anty uwani ne kawai 'yan uwanta,sauran duka 'yan uwan abbas ne "Yauwa sannunku" "Kun sha hanya barkanku da sauka" qanwar hajiyan abbas din mace mai yawan fara'a karamci da sanin ya kamata ta fada,don kwata kwata takun hafsatun bai mata ba,hausawa sukance wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,sai ta matsa tana kamo hannuwan widad da anty madeena ta jawa mayafin ta lullubewa fuska sosai,banda kuma tayi mata hakan ita ba sanin anayi tayi ba,ba lallai ta kula da wannan ba "Lale maraba diyarmu,taso a hankali" ta sake fada tana tayata tasowar,ta cikin mayafi widad take mita ita kadai,kawai an qunshewa mutum kai?,wannan ai rashin gaskiya ne,ita me tayi daga zuwanta ba za'a barta bama taga hasken garin daga baya sai a rufe mata kan,da wannan tunanin tabi bayan gwaggwo mero qanwar hajiyan zuwa cikin gidan,duka sauran jama'ar suka bi bayansu. Kusan hafsatun ce a qarshe qarshe,tana biye dasu, idanunta da zuciyarta kamar zasu fado,sai data cewa anty ummee ba zata fito ba ta tilastata,ta fuskanci akwai munafukai cikin 'yan uwan abbas dake murna da wannan auren,amma koma meye zatayi maganin kowa,bata ta yarinyar,don kallon farko tun bataga fuskarta ba ta tabbatar yarinyace din sosai kamar yadda akace. A babban falon hafsat da abbas yasa aka gyara mata shi duka don ya danni zuciyarta aka fara yiwa widad masauki,hafsat din ta shigo sai idanu sukayi kanta,wasu nason ganin launin fuskarta ne,yayin da wasu ke mamakin shigowar ta a qarshe,tayi ta maza ta aro dakiya da juriya tana sake musu sannu da zuwa da kuma sannu da hanya. Duk da cewa AKWAI WATA A QASA amma SANIN GAIBU sai Allah,hakan sai ya yiwa su anty deena dadi,ya kuma dan sanyaya musu zuciya,ko banza awajensu tayi abinda mata dubu suka gaza yi,a irin wannan lokacin wasu suke fara rabar da halinsu. Kanta tsaye ta wuce daura da inda aka zaunar da widad tana murmushi,tana zama sassanyan qamshin da fata da kuma sutturar widad din ke fitarwa ya ziyarci hancinta "Sannunku da hanya" ta sake fadar kalmar da tun dazu ita take maimaita wa,sannan ta dora "Sannu qanwata" idanunta nakan fuskar widad ta cikin mayafi,don har yanzu bata samu nasarar kallon fuskar tata ba,bata amsa ba kamar yadda bata motsa ba,anty halima data gama qarewa hafsat kallo a fakaice ta motsa,tace ayi salati ga annabi. 'yan addu'o'i aka yi sannan suka gabatar mata da amanar widad din. Wani murmushi ta saki,inda ace ba akan plan take komai ba....ashar shine abu mafi dacewa ga wadda tace ta riqeta amana,amma babu komai,akwai lokaci,a juri zuwa rafi... "Ai Allah ne ya hada zamana da ita,ita din koda baku fada bama ai tamkar qanwa take a gareni,ai babu komai,in sha Allah,zaku yaba,Allah dai ya bamu aron rai" ta qarashe fadi tana kuma fadada murmushinta,cikin zuciyarta tana ayyana kwana nawa zata gudu da qafarta,ko su dawo su kwashe ragowarta. Addu'a aka sake rufewa da ita,sanann suka dunguma sassan widad,sassan da a lokacin aketa kaya kayan shigar da kayan jerenta,wanda motoci uku ne manya suka iya daukesu,irin kudin da ummu da alhaji suka fitar basu tana fidda makamancinsa ba akan bikin jika,gefe daya kuma ga abbanta shima da yayi tasa bajintar,abun da ya bugar dasu batulu sosai,suka kuma sake tabbatar da cewa hae yanzu yana qaunar fatima,daga yadda ya aurar da autarta cikin girma,saboda bai taba irin wanna hidimar ga sauran yaransa ba,da sukayi qorafi sai.ya gaya musu,ita din nesa za'a kaita,duka yaransa kuma babu wadda aka taba kaiwa nesa,bugu da qari duk wata dama da wani alfanu da mutumin dake kusa da gida zaya samu ita banda ita,sunyi mita sunyi qorafi har suka gaji suka godewa Allah. Babban falo ne dake dauke da dakuna guda biyu,sai kitchen dining area da kuma ventilation ta baya,ginin yayi kyau sosai gwanin qayatarwa,komai kuma a wadace babu matsi. Basuyi minti talatin ba hafsat tasa aka kai musu coolers din abinci da tasa akayi musu,suna fara ci kusan suka ajjiye,nujood wadda aka taho da ita tace kuma sai 'yan kano zasu koma zata wuce gida ta ajjiye nata plate din itama "Nifa wallahi dana sani masauki nabi su na'eema,wannan abinci haka?" Ta fada tana yatsina fuska,harararta hajjaa tayi "Bamason abun magana daga zuwa baqunta malama,idan zaciki kici,idan bakici ki ajjiye musu kayansu" "To nima dai shuru kawai nayi,abun dai to....." Latifa ta fada yana yatsina fuska,duk sai aka kwashe da dariya,ashe kowa shuru kawai yayi yake kaiwa cikinsa,kada ya fara magana aga gajen haqurinsa,musamman da yake inna laila qanwar ummu tana wajen,ita kuma ba kasafai ta fiya son ire iren wadan nan abubuwan ba. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 34 Batulu dake zaune gefe tunda suka shigo gidan ta tabe baki,itakam ba haka taso ba,abubuwa da dama ta samesu ba a yadda take fata ba "To da alama dai uwar gidan nan tayi sake da yawa" ta fadi can qasan ranta,babu abinda take tunawa illa zamansu da fatima kafin su samu tabar musu gidan,koda yaushe mahmud ya tashi fatima dai.....fatima ce,basu samu salama ba saida tabar gidan,ko yanzun sun san cewa bawai tanar zuciyarsa bane gaba daya,rayuwarsa dai ta bari. Basuci da yawa ba suka ture abincin,can bayan awa daya saiga wasu sabbin coolers din,suna shigowa hajjaa ta gane daga gidan hajiyan abbas ne "Yanzu zakuci abinci ku ture" ta fada tana dariya sanda take bude coolers din,lafiyayyen abinci ne sosai,harda wani na daban tace na widad ne,sai ta miqawa nujood "Kai mata daki taci" nujood ta sutumi qawatacciyar warmer din dake fidda qamshi tun kafin ta bude ta wuce dakin da suka baro widad din. Su kuma a sannan suka sake sukaci suka qoshi. Saman katifa ta sameta,tana ta daddanna wayarta,wadda har yanzu batasan amfaninta ba idan ba game ba,dab da zata taho dai anty madeena ta saka mata numbers din mutane,ta kuma koya mata yadda zatayi wasu abubuwan "ga abincinki inji surukarki" nujood ta fada tana dariya,mayafin kanta tana gefe ta galla mata harara "Wai meye haka don Allah nujood" "Allah da gaske hajiya ce tace naki ne" ta zauna gefan widad din tana bude warmer din "Kedai kinji dadinki,kowa sai tattalinki yakeyi,kinga gidanki widad?,kinga kitchen dinki?,mtsewww,inda abbana zai yarda nima auren nan zance ayimin" kallonta kawai widad din keyi,ita kuma ji take dama itace su,tun sanda ummu ta fara mata fadan komai yace tayi tayi ta soma jin wani abu mai kama da takura ya sauka arayuwarta,kullum zancan ummu "Mijinki ne,babu musu a tsakaninku,ki girmamashi kamar yadda zaki girmama babanki da alhaji dani,ya fini matsayi yafi babanki matsayi" to wai banda abun ummu ta yaya zatace ya fisu matsayi?,idan tace tayi girmamashi tayi masa biyayya ta yarda da wannan,amma banda finsu matsayi (hankalinta baikai wajen ba). Tare suka soma cin abincin da nujood,tana ta bata labarin kayan da aketa jera mata, murmushi kawai takeyi,ita.mamaki abun yake bata,wai duk girman abu sai ace nata ne,har nan ma wai gidanta ne?. Koda suka gama saita labe ta cikin labule tana ganin yadda ake shirya falon,nujood na sake zugata ta tsaya ta kalla,har sai data gaji sannan ta koma ta zauna "Wallahi idan nice ko?, tabdi,sha'anina zansha babu takuramin" ta fada tana fadawa saman katifar,sai suka qyalqyale da dariya a tare. Da daddare aka sake kawo musu wani,muneer qanin abbas ya shigo da kansa bisa wakilcin abbas din,yayi musu sannu da zuwa,ya kuma tabbatar basa buqatar komai,sannan ya ajjiye musu kudi yace injishi. Sai wajen sha daya da rabi na dare ya shigo gidan,zuwa lokacin ya tabbatar kusan kowa yayi bacci cikin gidan,idan ma akwai wanda baiyi ba d'ai d'aiku ne,don haka kai tsaye ta wuce sashensa. Ya sameshi yadda yakeso,harma yayi mamaki,cike da tantama da kuma shakkar hafsa dince ta gyara ko sakawa tayi a gyara masa,bai sani ba,sai ya aje wannan tunanin,ya soma rage kayan jikinsa ya zubasu a laundry basket,ya wuce bandaki ya soma tara ruwa mai dumi sosai a bathtub,sai daya cikashi taf sannan ya fada ciki yana sauke ajiyar zuciya,bayan ya cikashi da turaren wanka mai sanyin qamshi. Luf yayi a ciki,idanuwansa a lumshe,yana jin hayaniyar daya wuni yana debowa tana sauka daga kanshi,sai daya kashe minti kusan talatin sannan ya wanke jikinsa daya tsumu da qamshin turaren wankan da kuma dumin ruwan daya jiqa kansa a ciki,ya zari daya daga cikin lausasan towels dinsa wanda qamshin shower gel da body mist dinsa suka kamashi da kyau,koda kuwa an wanke ya daura ya fito. A bakin madubi ya tsaya ya dauki wayarsa yana laluban layin hafsat,duk da bashi da hope kan zata daga,saidai cikin sa'a gab da zata katse ta dauka din "Ka dawo ne?" Abinda ta fara tambayarsa kenan,hakan kuma sai yayi masa dadi,saboda ya jima baiji magana cikin nuna kulawa kamar haka daga bakinta ba "Yeah,can u come to my room?" Ya fada da lallausar muryarsa da sauti can qasa "Why not?,gani nan zuwa" ta fada tana ajjiye wayar tata,sai ta miqe kanta tsaye ta soma canza kayan jikinta zuwa night gown,sannan ta shiga kitchen ta hada masa abinci ta kulle sassan nata,don taci alwashin yau din acan zata kwana ta fito. Duk da dare ne,hakanan babu cikakken haske a sassan widad din sai data zubawa part din nata harara,taja wani mugun tsaki kamar zata cire harshenta "Zakici ubanki da kyau,saboda tsaurin ido yarinya kamar wannan wai tasan soyayya?,tasan aure?,auren ma mutum kamar abbas,zaki gayawa aya zaqinta" ta sake fada tana jinjina kai tare da tabbatarwa da kanta hakan. Sanda ta shiga yana shafa mai ne,saita ajjiye abincin,fuskarta kadaran kadaham,ta koma gefan gado daga bayansa ta zauna,ya waiwaya kadan yana duban fuskarta,sai kuma ya dauke kai ya maida dubansa gabansa yana daukar body mist dinsa "Kinyini lafiya?,ya yaran" sai data dan yamutsa fuska kadan bayan ta tabbatar bazai ganta ba,tayi qoqarin saita muryarta,don tana jin kamar wani abu ya mata tsaye ne a hanyar shaqar numfashinta "Lafiya lau,yara kuma suna gida" ta cikin mudubin yadan dubeta kafin ya kawar da qwayar idanunsa "Har yanzu?,for now ya kamata ace sun dawo gida ko?,i missed them alort" baki ta tabe,bataga alamun hakan ba,ya shiga hidimar qara aurensa abunsa zai gaya mata haka?,da daa ne da tuni ya aika da mota ko kuma ya taka da kansa ya debo yaransa,amma yanzu saboda dalilin aurensa baiyi hakan ba,sai zancan a dawo masa dasu kawai yakeyi "Sai gobe idan Allah ya kaimu,zasu taho tare da nazeera,zata tayani hada abincin baqi" ajjiye body mist din hannunsa yayi ya waiwayo gaba daya yana kallonta,ya harde hannayensa aqirji,da gaske fa tana bashi mamaki,kamar ba hafsa na. Taji a jikinta sarai ita yake kallo,idanunsa ba normal idanu bane irin na kowa,zaiyi wuya ya kalleka dasu bakijisu har cikin qashinka ba,saita kauda kanta gefe,bataso su hada idanu,bare ya karanci komai ta cikin idanunta da wannan qwarewar aikin nasa da yake amfani dasu wani lokaci a kanta. Batasan tahowa yake ba sai da hancinta ya shaqi mayataccen qamshin nan nasa dake kashe mata jiki da zuciya,saman sofa bed ya zauna dab da ita,har gwiwarsa tana gogar tata,ya kamo hannuwanta sosai ya riqe cikin nashi,sai taji hawaye na shirin sauko mata,saboda yadda zuciyarta ta karye da tuna a yanzun abbas din sunan mijin mace biyu yake amsawa,so samu ta fusge hannunta,ta kalli idanunsa ta gaggaya masa magana,amma kuma hakan ya bata da tsarinsu,dole tayi laqwas,tana jin yadda azababben sonshi yake motsa mata. Da wata irin murya mai laushi yake mata magana,har yanzun bai saki hannunta ba "Idan nace miki banjin dadin wannan karamcin da kika yimin ba nayi qarya,kinyimin abinda babu wadda zaiyimin sai ke din,kin bani nutsuwar cikawa da sauke wannan nauyin,bansan da bakin da zan miki godiya ba hafcy" sunan da ya kirata dashi,wani suna ne mai dadadden tarihi a tsakaninsu,wanda ya jima bai kirata dashi ba,kuma kusan itace silar faruwar hakan. Dukka wadan nan maganganun da yake gaya mata gani take kawai rainin hankali da rainin wayo ne,maganganu masu zafi takeson gaya masa amma saita buge da janye hannunta daga nashi "Tunda dai ka samu yadda kakeso kuma ba shikenan ba?" Ta fada tana duqawa qasa ta soma serving dinsa,tasan idan ba haka tayi zata fallasa kanta ne kawai,saboda ta soma tsarguwa da irin kallon da taga yana binta dashi "Bismillah ga abinci nan"ta fadi tana matsawa gefe "Kiyimin alqawari zaku zauna lafiya ke da ita" "Banyi ba" ta fada a zafafe,saboda yadda takejin ta fara kaiwa maqura,haqurinta ya fara qarewa,ya zuwa sannan takai bango. Ita ta fara janye idanunta daga kallon qurillar da yake mata "Zanyi iya bakin qoqari na,zan mata yadda zanwa qanne na,amma idan ka taimakawa hakan ta hanyar nuna mata mutunci da kimata" ta qarashe zancan hawaye yana sauko mata. Karamin murmushi ya sake,sai ya bude mata hannayensa,with coolness yace "C'mon,is okay". Yadda taso din hakance ta faru,a sassan abbas din ta kwana,ya sake tsumata da muguwar soyayyar nan tasa data sake dasa mata matsanancin kishinsa,ta kuma sake cin buri da alwashin hana kowacce diya mace lasar wannan tsadadda zuma daga gareshi. Tare suka kintsa sukayi alwalar asuba,abinda ya dade bai faru ba,shi ya sanya jallabiyya yadau hula da carbinsa ya wuce masallaci,ita kuma bayan ta idar ta maqale daga gefan gado,zuciyarta nata lasafta mata irin abubuwan da zasu ci gaba da biyowa baya cikin gidan bisa tsarinta da kuma yadda taso,tana jin bacci,tana kuma son komawa,amma tana son ta sake yin wani abun da zai qara wanke ta a wajensa,ya kuma share mata filin da zata aiwatar sa qudurinta hankali kwance. Sanda agogo ya kada shida saita miqe tana fita a sashen zuwa nata,ta kuma fada kitchen tanata qunquni da surutan hanata rawar gaban hantsi,tsahon rayuwar aurenta batajin ta tana shiga kitchen sau uku a irin wannan lokacin,koda abbas kuwa yana da fitar sassafe,saidai ya hadawa kansa komai,kafin ta tashi ma ya fice abinsa. Daga masallaci sai ya wuce sassan widad din don ya gaida baqi,yasan cewa dole akwai manya a cikinsu,duk da rabinsu suna masaukin da gwamnan bauchi da kansa ya bayar yace a sauki baqin. Yadda ya gaidasu cikin girmamawa da dattako ya qara shiga ransu inna laila,dukkan wata haiba da nutsuwa tasa gami da sanin darajar dan adam ta bayyana,widad ita da nujood da anty madeena suka kwana a dakinta,anty madeena tunda tayi sallah ta fito nan wajensu ta barsu a dakin,don haka cikin hikima inna laila tasa aka taso nujood a dakin,saura widad kawai. Har ya miqe zai juya inna laila tace dashi "Tana ciki ai" sam bai kawota cikin ransa ba,to amma ya kamata ya dubata,tunda yanzun dole tana qarqashin kulawarsa,bugu da qari kosa yaushe akwai wani sashe na zuciyarsa dake sake tunasar dashi muryar hajiya cikin sautin dake gaya masa amana ce ita a wajenka,ka riqeta amana. Da qanqanuwar sallama a bakinsa ya tura qofar ya shiga,qamshin sabbin furniture da turarukan wutan da aka ajjiye cikin dakin saman mirror suka cakuda suka bada wani kalar qamshi suka daki hancinsa. Sake maimaita sallamar yayi amma ba'a amsa masa ba,ya dan sake takawa zuwa ciki kadan,sai ya hangota daga gefan gadon,kwance saman lallausar sabuwar dadduma,ta qudunduna sosai cikin hijabinta jakar daddumar,da alama dasu tayi sallah,tana kuma idarwa baccin ya dauketa a wajen. Takawa yaci gaba da yi har ya isa gabanta,yadda ta cure sosai kamar maijin sanyi ko jariri a cikin mamarsa yasa ya fahimci kamar sanyi takeji,saiya waiwaya inda ac din dakin yake,sun qureta ne da yawa,ta kuma hadu da sanyin asuba,ya laluba remote saman bedside drawer ya kasheta,sannan ya maida dubansa ga fuskarta da rabinta ne kawai ya bayyana. Idanun nasa ya dauke,yaja da baya ya nufi qofar fita,dai dai lokacin da hancinta ya cika sa qamshin wani tutare na daban,saita buda idanunta da sauri,take ta hangi bayansa sanda yake ficewa a dakin,saita miqe da sauri ta zauna tana jingina bayanta da gado tana kuma raba ido "Me yasa ya shigo?,haka kawai tana baccinta" saita kalli jikinta "Allah ma dai yaso hijabine a jikina" ta fada tana sake jan hijabin tana rufe qafafuwanta,kamar ce mata akayi zai dawo. *AREWABOOKS:HUGUMA* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 35 Tun gari bai kammala wayewa ba suka tashi da aikin qarasa kintsa gidan,saboda suna son wucewa a ranar,saidai hakan bata samu ba,don abbas ya sake dakatar dasu yace su sake kwana,wannan ya basu dama suka buqaci mota,ya kira samuel daga office yazo ya kawo musu tare da yi musu jagora,inna laila,batulu anty deena anty halima da hajjaa suka sada widad da gidan hajiyan abbas. Fadin irin dadin da hajiyan taji bata baki ne,bata zaci zuwanta ba sam,saboda taga ba kasafai ake hakan ba,tunda ba unguwa daya suke ba,yadda ta dinga nan nan dasu zai baka mamaki,farincikinta ya gaza boyuwa,ta kirayi gwaggo fanteka donta tayata karbarsu. Duk abinda akeyi fantakea din da kallo take binsu,saidai ta saci ido ta tabe baki,idanuwanta qir akan fuskar widad "Ashe.....ba banza ba,ashe sadakar yalla ya kwaso,kai jama'a,kashin hafsatu ya bushe,ba abinda ba zata gani ba,idan Allah ya tsare ma bata fiddata gidan ba" wannan ta dinga maimaitawa a ranta tana binsu da kallo,musamman da taga kowanne a cikinsu daga yanayin fata zuwa halittarsu da sumar kansu batayi kama sam da hausa fulani ba. Duk da batasan da zuwansu ba haka ta cikasu da abinci kala kala,kasancewarta mace mai karamci,baka rasata da abubuwa irin wadan nan. Tun basu bar gidan ba ta kira abbas ta shaida masa,shima yaji dadin yadda suka karrama masa mahaifiya,yasan zasu fita,tunda muhsin ya gaya masa,don hajjaa tace ya gaya masa,amma baisan can zasu kaita ba. Sai yamma lis suka dawo gidan,a sannan hafsa tana daga jikin window dinta tanata leqe,har yanzu batakai ga ganin fuskar widad ba,sai giftawarsu data gani kawai. Dan kwalinta ta cire ta jefar,ta koma ta zauna jabar saman kujera tana fidda wani hucin azababben kishi dake cinta,tunda zancan nan ya bullo har kawo yau bata sukuni ko qanqani,gaba daya a birkice take jinta,hatta da yaran tace kada a dawo dasu sai gobe ko jibi,sai kawai tasa hannunta a fuska ta fashe da kuka mai cin rai,tana tsananin son abbas tana kuma kishinsa,batasan yadda zata jurewa wannan al'amarin ba,abu mafi dagula mata hankali shine sadakar yalla da akace ya auro,tana sane da yadda suke fidda mace da yaranta daga gidan,ta yaya zata kaucewa wannan?,saita tayi cikin bedrooms dinta gudun kada wani yaji gunjin kukanta,don kukan take da buqatar yi sosai. Su biyu ne a dakin ita da nujood,sun nutse abinsu saman gadon da yasha shimfida da lafiyayyen zanin gadon da yake tafiyayye tun daga yemen,sai hira suke abinsu suna dariya,babu abinda ya damesu,ita sam bata wani tuna wai amaryace,nan din gidan aurenta ne,zamansu a haka dasu anty madeena yana mata dadi,hankalinta kwance,bata tuna tafiya zasuyi su barta. Dai dai nan anty deena data gama hada kayanta tsaf ta tura qofar dakin ta shigo,saita saki baki kawai tana kallonsu,gadon da aka gama gyarewa aka sa masa zanin gado mafi tsada suka haye tsakiyarsa abinsu? "Qaniyarki nujood,sauko" anty deena ta fada tana mata daquwa "Gadon amaryar zaki kama ku haye?,ke baki mata fada ba ita batayi miki ba?" Nujood din tana dariya ta sauko,sai widad tayi tsam da ranta tana kallon anty deena,itakam batason ana nuna banbamcin nan sam,yanzu meye laifi don sunyi kwanxiyarsu ita da nujood din a nan "Ke kuma bakiji inna laila na kiranki ba tun daxu mijinki ya shigo kizo ku gaisa?" Kanta ta dauke sannan ta tura baki gaba,ita wannan miji da aketa cewa,ita an takurata fa da zancansa "Ni banji ba" "Bakiji ba amma na gaya miki ana kiranki a falo ko?" Nujood ta fada gudun kada tayi laifi "Ya isa naji,jeki falo nujood" anty deena ta fada tana wucewa ciki,ba musu ta miqe ta fice,ita kuma ta isa babbar wardrobe din widad,ta bude tana duba kayan dake ciki. Wata lafiyayyar gown ta atamfa ta dauko mata hade da mayafinta ta ajjiye mata,kusan duka kayanta a tsume suke da wani irin turaren kaya na itace mai matuqar qamshi da daukar hankalin duk wanda ya jishi,ta duba inda suka adana mata kayan ado ta fidda mata sarqa dan kunnen da abun hannu masu matuqar kyau,sannan ta dauko mata sabbin undies,saita juyo tana kallonta ganin wata guntuwar pad "Kin taba yin period ne?" Gaban widad ne ya fadi,saita daburce lokaci guda,saboda bada kowa take magana irin wannan ba idan ba ummunta ba,ganin ta rude sai anty deenan tayi murmushi "Ni kikejin kunya?,to ai kowa ma yana yi,kin taba yi ne?" Kai ta gyada.mata a hankali,sai anty deena din ta sauke ajiyar zuciya,duk sanda ta daga idanu ta kalli widad din sai taji fargaba da tausayinta,babu tabbacin zata yita zama a haka ba tare da komai ya hadasu ba,tasan halin mazan yanzu sarai wajen rashin haquri,duk da cewa yana da mata,amma sometimes masu matan sunfi fitina,saboda sunsan yadda abun yake "Sau nawa kikayi?,kuma yaushe ne yinki na qarshe?" "Sau biyu inayi,yau sati biyu" kai ta jinjina,saita koma gefenta ta zauna,cikin dabara take mata tambaya kan jinin haila da kuma wankan tsarki,cikin ikon Allah komai ta sani,saboda ba baya bace ita din wajen zuwa islamiyya,sannan ummu ta zauna da ita ta mata bayanin komai. Sosai anty deena taji dadin hakan,saita dubeta "Shiga bandaki ki sake wanka kizo ki shirya zaki je ki gaida mijinki,tunda mukazo baku gaisa ba,ko kun gaisa?" Bata kawo komai a ranta ba ta girgiza kai alamun a'ah,saboda dazun tana bacci ya shigo,sai fitarsa ta gani,yanzun kuma tana nan suna hira da nujood "Amma anty deena sanda zamu gidan hajiya fa nayi" "Wannan daban yake,duk sanda kikasan zaki wajensa ko kinyi wanka ki dinga sakewa kinji?,ki dauko kayan kwalliyar nan da aka kawo miki kiyi kwalliyarki ki saka sababbin kaya,maza tashi qanwata ta kaina" murmushi kawai tayi,ta tashin ta shiga bayi ta hada ruwa kamar yadda ta umarceta,tayi wankanta da kyau. Kusan ita ta shiryata,wani irin tururin qamshi na fita a jikinta "Muje na rakaki,amma zan dawo,kya taho ke kadai" kai ta gyada mata,bata wani damu ba,kawai tana jin dadin yadda tayi kyau abinta,suka jera da anty deena din tana mata wani karatu cikin hikima widad din na jinta. Daga dan nesa kadan da part din nasa ta juya,ita kuma widad din ta wuce tana dosar wajen. A darare,cike da baqunta da kuma tsoro,kasancewar a sannan sha daya kusan na dare ta murda handle din falon,saidai a kulle ta jishi,sai ta saka hannu tadanyi knocking,tana rayawa a ranta indai ba'a bude ba tafiyarta zatayi,to amma me zata cewa anty deena?,tunda tayi mata alqawarin zuwa,kuma bata iya qarya ba bare tace taje ta dawo ne. Dai dai lokacin da yake zaune qasan carfet,ya bude babbar farar takarda mai girma wadda ke dauke da map na garin kaduna,system dinsa na kunne hakanan akwai wani dan madaidaicin allo dake tsaye a gefe,yayi wasu zane zane da qananun rubuce rubuce da shi kadai yasan ma'anarsu,akwai babban aikin da yake tunkara,wanda yakeson gabatar dashi a sirrance,kamar yadda ya saba,kusan nasarar aikinsa kenan,a duk sanda zai gabatar da aiki na kama masu laifi da sauransu,yakan shirya komai a boye ne,dagashi sai amintattun sa irinsu samuel,sai lokacin gabatarwa yayi sannan. Idanunsa daya tsurawa takardar yana karantar map din ya daga yana duban qofa,yana tunanin hafsa ce,saboda ta kirashi taji ya dawo ba jimawa,to amma kuma knocking din ba irin nata bane,sai ya miqe a hankali ya juya allon,ya kuma kifa takardar,ya matsar da butar coffee din da yaketa sha a madadin abinci ya nufi qofar. Tuni fuskarta ta soma narkewa da tsoro,ta sake daga hannu cikin saarewa zatayi bugun qarshe ya buda qofar,iska mai sanyi da taushi dake kadawa a gurin ta yayibo dukka qamshin dake jikinta ta jefo zuwa hancinsa,dai dai sanda ya sauke kallonsa ga baby face dinta,fararen idanuwanta tarwai a haske wajen hadi da hasken falon daya sake haske fuskarta. Idanu ta zuba masa kamar zata saki kuka,shima idanun ya zuba mata,sai kuma ya janye gefe yana bata hanya,tsaiwa tayi kamar ba zata wuce ba,ta wurga idanunta ta gefensa tana hango cikin falon,tanaskn tava da mutum ko su kadai ne?,hango system dinsa da tayi sai ranta ya bata bashi kadai bane,wannan ya bata sukunin rabawa ta gefansa sosai ta wuce zuwa ciki,tun daga ranar da ummu ke gargadinta da kebewa da duk wani namiji ko kusantar inda suke bata qara bari sun hada inuwa da kowa ba,nan nan kusa kuma data sake tsawatar mata fiye da baya,watanni uku baya sanda ta fara period,ta sake jadda da mata batun. Wata ajiyar zuciya ce ta subuce masa,yayi tsaye a wajen kamar mai jiran wani,saidai yana shaqar qamshin ne da yayi masa dirar mikiya,hannunsa ya miqa ya maida qofar ya turata,widad dake zaune a darare a qasa tadan fidda ido waje kadan,kai.....ya zai rufesu su biyu?,saita tsirashi da idanu sanda yake takowa zuwa ciki,tana masa kallon tuhuma. Yana shirin zama suka hada idanu,farare sol din idanuwanta suka hadu da nasa manyan idanun,sai yadan lumshe nasa kadan,ya janyo computer dinsa gabansa yana cewa "Bakiyi bacci ba?" Kai ta gyada a maimakon ta amsa masa,sannan tace "Ina wuni?" "Kin yini lafiya?" Ya amsa mata yana daddanna system din ba tare da ya sake dubanta ba "Lafiya lau,dama anty deena ce tace nazo na gaisheka,wai bamu hadu ba dazu" yadda tayi maganar cike da quruciya da kuma sakalci shigen na yaran fari ya tilasta masa daga kai ya kalleta,suka sake hada idanu a karo na uku,qaramin murmushi ne ya subuce masa,kallonsa take kanta tsaye kamar mai masa kallon tuhuma,ya karanci me take nufi a cikin zancanta,amma yana sa yaqinin ita din bata fahimci komai ba,ta taho abinta ne gaba gadi "Anty deena ta kyauta,kinga ta fiki kirki,sai ita tayi tunanin kizo ki gaida mijinki" ya bata amsa yana sake maida hankalinsa ga system din nasa "Uhmmm" ta fada cikin rashin sabo da kuma baqunta. Coffee din gabansa ya tura mata yana sake kallonta,saita girgiza kai alamun a'ah,saboda ummu ta hanata karbar abun hannun maza,yana nan kuma daram a kanta bata manta ba,bai sake cewa komai ba sai kawai ya miqa hannunsa,ya jawo allonsa yaci gaba da aikinsa,abun da ya dauki hankalin widad kenan,ta dinga binsa da kallo "Dama malamin makaranta ne?,amma kuma nujood tace mata har bindiga ce dashi,to amma wa yake koyawa karatu bayan shi kadai ne a dakin?,inama zai dinga koya mata,tayi missing makaranta da karatu sosai,tanason karatu" ire iren wadan nan tunanukan ta dinga yi,har sai da taga aikinsa yakeyi sosai cike da qawa zuci,ta dan fara motsawa,so take ta koma,amma kuma tasan ba zata iya fita ita kadai ba,saidai ya rakata,amma kuma ta kasa buda baki ta gaya masa. Marker din hannunsa ya ajjiye yana fesar da iska daga bakinsa,yayi taku biyu baya a hankali,sannan ya duqa dab da ita,idanu suka sake hadawa,sai ya kauda kai ya soma zuge jakar dake aje a gefanta,wasu tsofaffin takardu ne da yasa samuel ya kawo masa su zai duba wani abu a jiki,yasoma zarosu,sai tsanya tayi tsalle ta biyosu har guda biyu,daya ta fada gefe dayar kuma kai tsaye ta fada jikin widad. Gigitaccen ihu data saki ya sanyashi watsar da takardun hannun nasa,kafin ya ankara tayo kansa tana tsalle gami da kiran wayyo Allah,wayyo ummu,taso rudashi amma ya tattara hankalinsa waje guda,saidai duk yadda yakeson dawo da ita nutsuwarta widad batasan yana yi ba,mayafi tuni ta cillar dashi,dankwali ma ya zame,lafiyayyen baqin gashinta dake fitar da qamshi ya tarwatse. Suciyarsa tayi wani mugun bugawa sanda ta shige jikinsa tana,sassalkan gashinta ya wanzu a fuskarsa,ihu take da zazzaqar muryarta dake cike da tsoro tana fadin ya cire mata "Calm down,ki nutsu,tsanyace fa kawai" ya fada muryarsa na dan rawa kadan,saidai ko daya bata jishi ba,tsoro ya cika kwanyarta a lokacin. *AREWABOOKS:HUGUMA* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 36 Yadda ta shige masan tamkar zata koma cikinsa,gaba daya ta kasa gane me yake fada,sai kawai ya buda hannayensa,ya kuma rungumeta sosai a jikinsa,yayi mata riqon tsauri ta yadda ba zataci gaba da tsalle ba. A hankali ta fara samun nutsuwa,kukanta ya fara ja baya,sai a sannan kuma ta tuna ajikin wani take,tayi wani irin zillo ta zame daga jikinsa,cikin tashin hankali hadi da wani sabon tsoron,tunda take tsahon rayuwarta ko yatsarta ba wanda ya taba riqewa,amma yau gata a jikin wani?,ta shiga uku?,yanzu shikenan ta zama 'yar iska?,idan ta samu ciki ta mutu fa?,bata kyautawa ummu ba,sai sabbin hawaye suka barke mata,jikinta har rawa yakeyi "Tafiya zanyi" ta fada bakinta yana rawa,kafeta yayi da idanu yanason gane me ya tsoratata kuma dai?,kafin ya gama wannan tunanin aka fara knocking qofar,ya maida kallonsa ga qofar,kafin ya bada izini an murda handle din an shigo. Hafsat ce dauke da jug da cup,da farki idanunta naga abbas,sai kuma sabon qamshin da taji ya baibaye falon yaja hankalinta,a hankali idanunwanta suka sauka kan widad dake tsaye tana tsuma,jikinta yana rawa,kanta babu dankwali bare mayafi,dukka suna watse a qasa,ga hawaye shabe shabe kan fuskarta,gabanta yayi wani mummunan faduwa,abubuwa biyu suka bugeta lokaci daya. Zallar madarar kyau data gani kwance saman fuskar widad din,duk da shekarunta qananu,da kuma tunanin daya darsu a ranta a take a lokacin,abbas ya nemi tarayya da widad din,tunanin daya kusa sanyata zubar da kayan hannunta,jikinta duka ya dauki rawa. A nutse ya amsa mata sallamar,ya dauke kansa ya maida ga widad data fara yin gaba zata fice,har yanzu tana hawaye "Dakata" ya fada cikin salo na umarni,cak ta tsaya amma har yanzu jikinta rawa yake,tasan tata ta qare,tana shiga su anty deena zasu gane wani ya tabata. Inda ta yasar da dankwali da mayafin ya qarasa,ya dauko mata ya tsaya gabanta ya miqa mata yana kallonta,sannan yace da ita "Daura" jikinta na rawa ta karba din,amma ta gaza daura dankwalin,sai mayafin ta yafa kawai "Muje na rakaki" ya fada sannan ya waiwaya ga hafsat wadda ta yiwa kanta mazaunin dole don kada ta fadi "Ina zuwa" yace da ita suka fice shida widad din. Kuka sosai ta fashe dashi kamar qaramar yarinya,da gaske abbas neman tarayya da yarinyar yayi?,har zuciyar abbas ta fara qawata masa ita?,duk qoqari da jajircewar da taketa yi kenan tana neman tashi a banza?,ya akayi tayi saken da har yarinyar tasan tazo sashensa?,ba shakka sanyata akayi,tunda 'yan uwanta suna nan,tabbas ba zata ba haka ta sake faruwa ba,sai ta miqe tana barin flask din kawai ta fito ba tare data bi ta kansa ba,idanuwanta har basa gani sosai saboda tashin hankalin da takejin kanta a ciki,a daddafe ta dinga laluba hanya har takai kanta sassanta. A gaba ya sanyata yana biye da ita har suka isa sasssan nata,ita ta fara knocking,tayi tayi shuru ba alamun za'a bude,sai yace ta matsa shima ya shiga tayata,amma shuru kakeji,saiya waiwayo yana dubanta "I think duka sunyi bacci fa" kai ta langabe tana kallonsa,idanunta na fidda ruwan hawaye "To a ina zan kwana kenan?,don Allah ka tashesu mana" ido yadan zuba mata na wasu sakanni kafin ya kawar da kansa,quruciyarta ta gaske ce "Ki koma ki kwana a can,da safe saina rakoki,lokacin sun tashi ko?" Ya fada cikin sigar lallami,saboda yadda yakejin kansa yayi week,bacci ma dai a taqaice yaji yana saukar masa. "Amm....." "Ba'a musu da babba right?" Ya fadi cikin sigar tambaya yana ritsata da kallonsa,karon farko taji idanunsa sun dan mata nauyi,saita sadda kanta qasa,ya sake sakata a gaba kamar dazu suka koma,jikinta duk a mace, hankalinta a tashe,anty deena ce ta jawo mata,ta yaya zata kwana daki daya dashi?. Yayi mamaki sanda ya dawo yaga babu hafsat din ba dalilinta,sai ya tsugunna ya tattara komai waje daya ya adana,har a sannan widad na zaune a takure a waje daya,ac din dakin ya kashe gaba daya,ya rage fitilun falon,saiya kalleta "Muje ciki ki kwanta" fuska ta tattare waje daya,tanason cewa a'ah amma kuma batason yaga kamar ummu bata koya mata cewa ba'a yiwa babba musu ba,tunda gashi dazu ya fada,haka ta miqe tana biye dashi har cikin bedroom din nasa. Da ido take kallon komai,bedroom din nada wani irin weather mai saukar da nutsuwa,sassanyan qamshinsa ya kama dakin sosai,komai fari ne qal,kuma komai yana kan tsari a killace,saita haye kan sofa bed ta dunqule,shi kuma ya wuce bandaki. A ciki ya shirya cikin wasu silk pyjama sky blue,yayi brush ya feshe jiki da bakinsa da turarukansu "Zaki canza kaya ne?" Ya fada yana dan duban gefanta,cikinta ne ya bada qululu saboda tsoro,yana nufin ta cire kayan jikinta ta sauya wasu?,a dakinsa?,saita damqe jikinta waje guda kamar wadda ya taho zai rabata da suturarta,ta jijjiga kai da qarfi "A'ah,wadan nan nakeso na jikina" dariya taso qwace masa amma ya danne,a yadda take acting yasan lallai batasan meye cikakken ma'anar aure ba,to amma me yasa take tsoro haka,sai ya rabu da ita,ya jawo wayarsa da nufin kiran hafsat din yayi mata sai da safe,duk da baisan me ya fiddata daga dakin ba,ya tsammaci zatace zata kwana kamar jiya. Sau uku yana kiranta tana katse kiran,abun yadan daure masa kai,amma saiya tattara ya watsar,dare yayi,hutu yake buqata "Ki koma gado ki kwanta" ya sake fadi,kamar dazun dai a firgice tace masa a'ah,sai da yayi da gaske sannan ta kuma taga ya yibi filo da bargo yana shirin bar mata dakin sannan taji ranta ya sake. K'ofar tabi da kallo sanda ya fita,sai kuma ta fara baza idanu,dan banzan tsoron nan nata ya dawo,ji tayi kamar ta bishi,amma ba zata iya ba,curewa tayi waje daya ta lulluba har kanta,saita saki kuka,anty deena ce.....duk ita tace sai tazo,gashi nan sun rufe mata qofa,bayan sunsan ta fita,kewar ummu ta taso mata,ta dinga hawaye ita daya cikin filo,har bacci barawo ya saceta. A hankali ya bude qofar dakin,duk da akwai qarancin haske amma yana iya hangenta a cure waje daya,sai ya kada kansa ya wuce bandaki. Alwala ya daura ya dawo dakin,ya feshe jikinsa da turare ya sauya jallabiyyar jikinsa,ya taka a hankali zuwa gefan gadon,hannu yasa ya bubbuga saman filon a tausashe,ta motsa kadan kamar zata tashi,sai kuma ta sake qudundunewa,cikin muryar barci tace "Don Allah ummu,ba'a idar ba,yanzu aka tayar" shuru ya danyi yana nazarinta,ta kwabe fuska gaba daya tana tura baki gaba a shagwabe,har kuma a hankali ta saki bakin nata,da alama ta koma bacci sosai. Kai ya girgiza kawai,bai hango komai ba banda zallar quruciya a tattare da ita,shikam baisan ya al'amuran zasuci gaba da tafiya ba,bai hango sauqi ba,sai nauyi daya sake hawa kansa,sai ya juya a nutse ya nufi qofa,yana kama handle din zai.bude ta bude idanunta a hankali, saboda yadda taji cikin jikinta ba'a gida take ba,saboda duk sanda tayi irin haka ummu saita takurata akan sai ta tashi koda ba'a tayar da sallar ba. Tana qyallara ido ta hangoshi,saita zabura ta miqe tana rarraba idanu,a nutse ya waiwayo ya kalleta,sai baice komai ba ya sanya kai ya fice. Sai data daina jin motsinsa sannan ta miqe a hankali cike da tsoro ta tura bandakin ta shige tayo alwalar itama ta dawo ta gabatar da sallar,har Allah Allah take ta idar ta fice zuwa wajensu anty madeena,tana idarwa bata ko tsaya addu'a ba tayo waje. Cak ta tsaya a qofar falon kamar zata saki kuka,ganin garin da duhu har yanzu,gashi dukka fitilun harabar gidan an kashesu,dan banzan tsoronta kuwa bazai barta ta wuce sashenta ba,saita koma.bakin qofa ta rabe tana maida qananun hawayen dakeson sauko mata,ba zata koma cikin dakin ba kuwa,a nan zata yita zama har sai gari yayi haske. Baiyi zaton zai sameta zaune a bakin qofa ba,don haka cike da kuzari da kuma hanzarinsa ya buda qofar falon "Subhanallah" ya fada da sauri yana kama murfin qofar ya riqe a hannunsa,sai kuma yadan dai daita yanayin fuskarsa yana kallonta "Me kikeyi a nan?" Mele baki tayi fuskarta a yamutse,da alama qiris take jira ta fashe "Ina kwana?,can zan koma,kuma wajen da duhu bazan iya fita ba" sai daya juya ya sake kallon harabar gidan,shi yasa aka kashe fitilun saboda yaron gidan yace sunata wasa da wutar kada su lalata qwayayen,qwayaye ne masu tsada da daraja "Basu bude ba suma,ki koma ciki sai rana ta fito" kai ta maqale a kafada,sannan ta miqe kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,ta koma saman kujera ta takure waje daya,bai sani bama ko hawaye take sharewa. Dakin ya wuce,bai jima ba ya dawo,ya haye saman doguwar kujerar daya kwana a kai,yaja bargonsa zuwa qugu ya rufe, lokaci lokaci yana dan daga idanu ya dubeta,yadda take curewa waje daya ta kwanta shine ke bashi mamaki,amma baice da ita komai ba. Wantsalowa tayi daga saman kujerar sanda agogo ya gama buga qarfe bakwai dai dai,suna hada idanu sai kuma ta koma dai dai ta zauna,fuska a narke take dubansa,cikin salo na roqo da magiya tace "Don Allah.....ka rakani,gari yayi haske fa?" Ido ya tsura mata na wasu sakanni yana kallonta,sai ya janye idanun nasa yana zame bargon jikinsa,daki ya sake shiga,bai jima ba ya fito yana gyara button na rigarsa "Muje" da saurinta ta sauko muryarta tabi bayansa,don kafin yakai qofa har ta kusa cimmasa,yadan sake binta da kallo sannan ya buda qofar suke fice. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 37 Cak ta tsaya sanda suka isa bakin part din nata,ta juya tana fuskantar sa,fuskarta a narke,tana wasanda yatsunta,da alama magana takeson masa,amma ta kasa sai motsa yatsunta da takeyi,shi kuma ya kafeta da idanu,ganin ta kasa magana sai yayi gyaran murya,ta daga idanu ta dubeshi,kafin yace wani abu ta magantu "Don Allah kada ka shigo" mamaki maganar tata ta bashi,sai ya kafeta da idanu yana neman ba'asi,bata gane ba,murya a narke tace "Kaji?" Saiga qwalla ta biyo bayan maganar,bai shirya ba amma dole ta sanya qaramin murmushi ya qwace masa,sai ya kauda kansa gefe na sakanni yana danne murmushin kafin ya dawo da dubansa gareta,ya gama gano abinda take nufi,don haka yace "Is okay" sai ya juya a hankali yabar wajen yana nufar sashen hafsat. Ajiyar Zuciya ta sauke tana binsa da ido,sai taji dadi a ranta da ya tafin,don idan da ya tsaya ba shiga zatayi ba,da wanne ido zata kallesu?,me zatace musu?,ta samu relief don haka ta juya tana dosar qofar falon nata. Kamar wata munafuka haka ta dinga rarraba ido tana rabewa a bango,jikin labulen bakin qofa ta tsaya tana leqen falon,inna laila ce saman dining ita da batulu,sai nujood zaune saman kujerar falon,Momma na zaune daga qasa,dukkansu kowa sanye da hijab,da alama tun tashin asuba ne basu koma ba. Tana daga tsayen ta hangi anty deena ta fito dauke da wata jaka ta ajjiye saman kujera,ta kalli nujood tana cewa ta tashi su sake gyara falon,latifa ta riga ta gyaro ciki,saita matso ta wajen bakin qofa zata dauka mopper dake ajiye a wajen. Motsin mutum ya sanyata waiwayawa ta dubi wajen,cikin mamaki take kallon widad "Ke kuma me kike yi a nan a tsaye ke daya?" Rau rau tayi da idanu,a yadda anty deena ta kafeta da idanu saita fara hawaye kawai "Meye haka widad?" Tambayar da ta sanya jikinta rawa,saboda tana ganin kamar anty deena din ta hangi abinda ya faru jiya,hankalin anty deena yadan dauko kadan,ta zaci ko wani abun ya gudana tsakaninsu,sai kuma taji hankalinta yadan kwanta kadan da taga yanayin tafiyarta bai canza ba,tana tausayinta,koda wani abun zai faru ma ta gwammace basa nan. Sai data mata da gaske tabar kukan ta shigo,momma dake zaune ta bita da harara "Ja'ira,zakiyi bayani ne" kasa hada idanu tayi da kowa,sai ta wuce ciki sum sum sum. Dakinta ta murda ta fada tana sauke ajiyar zuciya mai qarfi,sai a sannan ta nutsu,ta soma bin dakin da kallo. Sosai ya qayatar da ita,an gama shirya mata komai sai qamshin sabinta yakeyi,ta waiwaya ta dubi bandaki inda anty deena tace akwai ruwan zafi,ta shiga tayi wanka,ta kuma zabi kaya masu kyau ta sanya,ta juya zata shige sai aka turo qofar,anty basma da anty ramziyya da anty marwa suka shigo,kowanne riqe da yaronsa,marwa dince kawai mai ciki bata samu rabo da wuri ba. Nan bakin gadon suka zauna sunata tsokanar widad tare da da son jin me ya faru jiyan,kuka ta saki sosai "Ni wallahi ku daina banaso,bayan ummu ta hana,babu kyau,wallahi ba ruwana" haka ta dinga fada tana sharar qwalla,su kuwa ganin abun suke kamar almara,wai yau widad din ummu ce aka aurar?,a wata uwa duniya?,ta tafi tabar ummu duk qaunar dake tsakaninsu?,Allah ne ya kawo anty madina ta korasu,sannan ta kada kan widad zuwa wanka,bayan ta fito kuma ta shiryata da kyau cikin wani lace da yayi masifar karbarta,ya fidda kyau da hasken fatarta,ita kanta ta dade tsaye gaban mdubi yana kallon kanta,tana ta zuba shirmenta na kyan da tayi,anty madina na binta da murmushi gami da goge qwalla a fakaice. Daga bakin gadonta take zaune riqe da waya a hannunta,lokaci lokaci tana saka hannu ta share hawayen fuskarta,duk furuci daya da zatayi da anty ummee tana jin kamar zuciyarta zata tsinke saboda baqinciki bacin rai da zallar kishi kai daci "Har kusan qonewa nayi garin saurin na hada masa tea nakai masa,amma wallahi acan na sameta,namiji dan babansa......alamun dana gani ma sunsha dambene,saboda ko dankwalin kanta gashi nan watse a qasa,don Allah anty ummee mai zaiyi da wannan mitsitsiyar yarinyar,banda tsabar cin fuska?" Tayi maganar tana jin kamar zuciyarta zata fito ta bakinta. "Kinga ki ajjiye wannan a gefe,matuqar zakici gaba daga inda kika tsaya,zaki nuna komai ba komai bane.....hatta kusantar tata ma saikin hanashi gaba daya,meye a cikin ido ne banda ruwa?,ai nasara tana tare da jajircewa" "Wannan nasarar anya kuwa tana tare dani?" "Kin saare a dare daya kenan?" Anty ummeen ta tambayeta tana jinjina zallar gajen haquri irin na hafsa din "Shin ba'a gabanki komai ya dinga gudana tsakanina da amaryar abban sayyid ba?,yanzu tana ina?" "Banqi ta taki ba.....amma akwai nisan tazarar banbanci mai yawa tsakanin abbas dashi.....abbas anty.....yana da ra'ayin riqau kafiya da kuma magana daya,yana da wuyar sha'ani,yana da wuyar canza ra'ayi,idan yace eh.....tofa a haka zata yita tabbata" "Uhmmm,mace fa tafi gaban tunanin dukkan wani mai tunani,saidai idan ba zaki iya ba" "Zan iya" ta fada tana son sake bawa kanta qarfin gwiwa,ji take kamar ta rufe idanu ta kuma bude taga komai ya tarwatse,komai yazo qarshe,ta rufe idanunta kana ta budesu duk kusan lokaci daya sannan tace "Na rasa ta yadda abbas yaga yarinyar nan anty ummee......abbas fa?,mara damuwa da abubuwa masu yawa,wanda wani abun ma sai kinta cewa kalli....ko ka gani" ta jefawa anty ummeen tambayar da taketa damunta tare da yi mata yawo a kai,har yanxu kums bata samu amsarta ba "Namiji yafi gaban haka,kedai ki maida kai ga mission dinki....." "Ina zuwa" ta fada da sauri tana sauke wayar daga kunnenta sanda fa jiyo alamun taku ana nufowa dakin,ta kuma san babu wanda zai shigo din sai shi. Da hanzari ta ajiye wayar,sannan ta fada bandaki ta maida qofar,da tattausar muryarsa yayi sallama ya tura qofar ya shigo,sai ya tsaya daga bakin qofa yana qarewa hargitsatsen dakin kallo,komai baya kan tsarinsa,baisan kuma sai yaushe zata gyara ba. Ajiyar zuciya ta sauke,ta matsa gaban babban madubin dake bandakin wanda ya cika da jirwayen ruwan wankan da ba'a wankewa,ta debi ruwa ta wanke fuskarta,saboda batason ya gane ruwan hawaye ya fita a idanunta,taja zaninta da tayi daurin qirji dashi saman t.shirt dinta ta gyara daurin,sannan ta goge fuskarta da towel ta fito. Suna hada idanu ta cika fuskarta da fara'a,sai ya dan lumshe idanunsa ya kuma budesu lokaci daya yana kallonta,qasan zuciyarsa kuma yana masa sanyi na yanayin da ya ganta a ciki,ba wata damuwa "Yanzu nake shirin fita mu gaisa da baqi,gashi ka tarar dani" ta sake fada tana murmushin da ita kadai tasan ciwon da yake mata. Agogo ya kalla kafin ya amsa mata "Kaman yayi wuri,gwara ki kwanta ki sake hutawaYou are very tired, you need a rest maman nawwara" ya fada yana sauke mata murmushi. Duk da cewa bata kalleshi ba amma tana jin saukar murmushin nasa har tsakiyar zuciyarta,murmushi ne da ita kadai tasan tsadarsa "To ya za'a yi,kamawa takeyi ai,gashi na kasa hada musu breakfast" ta sakeyin maganar tana zaqulo hijabinta cikin hargitsatsun kayan wardrobe dinta wadanda yana daga tsaye yake tayata kallon yadda suke a hautsine,haka suke koda yaushe,idan kayi magana tace su nawwara ne tana bacci suka aikata,ko kuma suna neman teddy dinsu ne "Ba matsala,kinyi qoqari sosai,zan saka a kawo musu breakfast" "Da dai yafi,na gaji da jegon jaka" ta fada qasan ranta tana zura hijabin a jikinta,sannan ta matso tana cewa "Bari naje mu gaisa kada suga rashin kyautawa ta,mun tashi gida daya ban leqasu ba" da kallo ya bita,duk da qoqarin sakewarta amma yana hangen wani.abu can qasan qwayar idanunta,zuciyarsa na alaqanta hakan da kishin da takeji a kansa. Hannayensa ya bude mata,cikin taushin nan nasa "Zaki wuce bamu gaisa ba madam" kallonsa tayi saita kauda kai tana qoqarin kawo murmushi kan fuskarta,tabbas idan tace zata shiga jikinsa a wannan yanayin kuka zata barke dashi,kukan kuma zai zame mata tonon silili ne. "Ina kwana oga?" Ta fada tana ci gaba da tafiya,sai ya maida hannayensa yayi folding nasu a qirjinsa yana kallonta,qaramin murmushi na sauka saman labbansa,irin gaisuwar da yafi qauna daga wajenta kenan,amma dama yasan zaiyi wahala ya samu yadda yakeso din "Alhmdlh madam,a dawo min da yarana mana?" "Zasu dawo dole yau" ta bashi amsa ba tare data juyo ba "Alright" ya amsa mata yana kallota ta cikin madubinta "Bari naje na dawo" ta fada tana jan masa qofar,tana so taje ta saje tantance widad din,yadda ta ganta a jiyan haka take ko idanuwanta ne da kuma sharrin dare?. Idanuwanta nakan dukka wani kayan qawa na falon,da qyar ta iya riqe kanta saboda yadda zuciyarta ke wani irin tsalle,ko ba'a gaya mata ba auren 'yar gata ne daga dukkan alamu,saboda yadda aka shirya gami da qawata sassan nata gaba daya,babu ce kadai babu,jere mai aji da nutsuwa. Ta basu fuska sosai ta gaidasu inna laila dasu momma,har tadan zauna suna dan taba hira,tana ta baza ido taga ta inda widad din zata fito,saiga nujood,kamar inna laila tasan buqatar ta tace da ita "Kira widad,kice tazo ta gaida yayarta" "To" ta amsa tana okomawa ciki da mopper din hannunta data goge inda ruwa ya zuba. "Yaaa latifa" widad din ta fito tana fada,hannunta riqe da dankwalin lace din nata da yaqi dauruwa,anty deena dake wanka kuma tace lallai saita daura. Hankalin hafsa ya fara kaiwa wajen,tana tafe da dankwalin fuskarta a kwabe tamkar shagwababbun 'ya'yan fari,gashinta dake wani irin sheqi da walqiya a daure cikin ribbon jelarsa na reto a bayanta, yanayin qirar jikinta kadai abar kallo ce,sai kace wata babbar budurwa,tun a yanzun coca-cola shape dinta ya fita sosai,kallo dayan data mata ya kusa tafiya da numfashin ta,ta dinga qoqarin riqe kanta da kyau,kada ballinta ya watse a wajen. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 38 "Don Allah ki dauramin,na kasa wallahi" tayi maganar tana miqawa latifa dankwalin ba tare data lura da hafsa dake zaune a gefe ba,tana jin kamar ta mutu,abbas ya gama cutarta,yaje ya auro yarinyar data kusa haifa?, sannan kumata fita komai da komai na siffa?,duk da tana qoqarin qaryata kanta da kanta,tana qoqarin gayawa kanta idonta ne yake ganin hakan "Kawo,Allah ya gyara min ke,bansan sanda zaki koyi daura kallabi ba" dariya tadan saki "Ni nauyi Allah,banda anty deena ta takura" "Ga antynki nan baku gaisa ba" latifa ta fada bayan ta karba dankwalin tana lanqwasashi. A sakarce ta waiwaya ta dubi hafsa din da irin kallon da takewa kowa,ba tare da ta bawa matsayinta muhimmanci ko matsar dashi gaba daga matsayin da take bawa kowa data fara saninsa ba "Ina kwana?" Ta furta cikin girmamawa kamar yadda ta saba gaida dukkan wanda ya girmeta "Lafiya lau qanwata,ya kwanan baqunta?" Hafsat ta fadi da wani murmushi da takejin kamar na sossoka qayoyi ne cikin bakinta. Murmushi ta danyi tana maida dubanta ga latifa,saboda batasan amsar da zata bayar ba,don batasan amsar da ake bayarwa din ba,ta dan ranqwafa kadan latifa ta soma daura mata dankwalin. Cas ya zauna a kanta,ta daga kai latifan tana kallonta "Ehen.....yauwa,yanzu kikai dauri" latifa ta fada cikin tsokana. Idanunta hafsa takai kai,cikin sakanni taji ba zata iya ci gaba da zama tana kallon yarinyar ba,wani irin mugun kyau da kwarjini daurin yayi mata,saita miqe cak tana cewa "Bari na koma,yau jiki yayi nauyi ban samu dafa muku komai ba,kuyi haquri" murmushi inna laila tayi "Lah,babu komai fa,yaran ma suna gab da kammala dafa abun karyawan,ai ansha hidima wallahi,mun gode,Allah dai ya qara hade kanku,ya kade fitina,gata nan sai ayita haquri da ita,har yanzu akwai quruciya sosai a tare da ita,sai ana yi mata nuni,ana kuma gyara mata inda tayi kuskure,ayi haquri da ita don Allah" ta fada zuciyarta na danson naqaltar mata fuskar hafsatun "Aiba komai wallahi" ta fada a taqaice,can wani sashe na zuciyarta yana jin kamar ya zundumawa inna laila ashar,babu zancan quruciya uzuri ko daga qafa ga duk wadda ta aurar mata miji,koda kuwa widad din qyanqyasar yau ce,tunda har ta iya sanin meye so?,ta banbance tana sonshi,ta kuma iya sanin meye aure ai magana ta qare,babu daga qafa babu ragi babu kuma rangwame,haka ta dinga jefa qafarta zuwa sassanta idanunta basa gani sosai,fatanta Allah yasa abbas ya wuce sashensa,ya kamata ta rage kukan dake damunta a qirji. Cikin awannin da suka biyo baya suka sake shiga qalqale sassan nata da kyau,duk sauran abubuwan da ba'a gama kintsawa ba suka kammalasu,sun gama kuwa da wuri,saboda wadanda ke presidential lodge din da aka kaisu motoci sun kwasosu sun dawo dasu gidan,nan da nan sashen ya dan qara cika,anata hira da barkwanci,kusan kowa gidan widad djn ya tafi dashi,saboda babu ce kawai babu. Duk da wannan jikinta ya mata wani mugun sanyi,babu wannan hayaniya ko kazar kazar din,tana lafe a waje daya kusa da inna laila,itace ta zame mata kamar ummun nata,mugun kewar ummun take,gaba daya zuciya da jikinta babu dadi,duk da yadda suketa qoqarin janta da hira da kuma wasanni. Qarfe sha biyu har sun fidda jakankunansu harabar gidan,sun kuma fito waje,zuwa sannan idanun widad fararen nan sun fara kadawa suna tara ruwan hawaye,hakanan ta riqe hannun inna laila gam. Sanda suka fara shiga motocinsu dai dai lokacin ya iso,shi ya fara qarasowa wajen sannan hafsat wadda keta yashe baki tana sake binsu da murmushin yaqe. Cikin nutsuwar nan tasa yake tsaye gaban motocin,yana sanye da wani soft yard na maza gray color da yayi matuqar kwantawa a lafiyayyar fatarsa,jikinsa na fidda soft scent mai kwantar da hankali. Tsaf kowa ya shige,saura inna laila da latifa,a sannan tuni ruwan hawaye ya gama wanke mata fuska tsaf,zame hannunta da inna laila ta soma yunqurin yi ya sanyata fashewa da kuka sosai "Don Allah inna zan koma,karku tafi ku barni" ta fada tana sanya hannunta saman fuskarta,saita karya zuciyar kowa,inna lailan ta dubeta "Ga latifa nan widad,zaku zauna tare kafin wani lokaci,kiyi haquri" daga haka sai ta matsa gaba,ta kuma shige motar da sauri,gaba tayi zata matsa hafsat ta rigata,ta kuma riqota,a zuciyarta tana jin kamar ta rufe widad din da duka sannan ta hadasu su wuce kanon tare,amma sai ta shanye ta kuma hadiye wannan,cikin sigar lallashi tace mata "Haba mana widad,kiyi haquri,ai saiki karya musu zuciya,ba gani ba?,ga yayanki ma,sannan ga latifa an bar miki,kome kikeso ki gaya mana kinji,babu mai takura miki, kiyi shuru mana haba,yanzu inda su nawwara na nan ai sai su tsaya kallonki antynsu tana kuka" ta fada tana rungumota jikinta,ta rintse idanu tana jin kamar ta kara wuta ne a jikin nata. K'asa k'asa take kukan har zuwa sanda motocin suka gama ficewa a gidan,shikenan sun tafi sun barta.....shikenan sun rabata da ummun ta...... shikenan bata da kowa.....haka zuciyarta ta dinga gaya mata. Hafsat dince ta matsa gaba da ita wajen latifa tana miqa mata ita "Ki kaita ciki ta zauna ki lallasheta" sai latifa ta gyada kai tana kama hannunta tare da jawota jikinta suka fara barin wajen tana yiwa widad din magana qasa qasa,saidai da alama ba zata iya jurewa ba,saboda qarfi da kukan nata ya fara yi. Da kallo hafsat ta bisu har suka shige,tsinuwa da zagi kaka kala cikin zuciyarta akan widad din,sai data tabbatar sun shige din sannan ta matsa gaba inda abbas ke tsaye suna magana da rabi'u yaron gidan dake musu 'yan aike aike da aikace aikace na filin gidan. Hannunsa zube a aljihun wandonsa har ta qaraso Inda yake tsayen,musayar murmushi sukayi,wanda murmushin dake kan fuskar hafsat din tasa ma'anar ta dabance "Sannu da qoqari madam" ya fadi har cikin ransa,don duk abinda je faruwa kan idanunsa ne yana gani,sai ta saki qaramin murmushi tana jin yadda zuciyarta keta mata ciwo "Yauwa sannu,amma kaima ya kamata ka shiga ka bata baki fa,kuka taketa yi,abun tausayi" ta fada tana canza yanayin fuskarta zuwa kalar tausayin. Da ido ya kalla sashen sannan ya maido kanta "Tunda kin rarrasheta aikin wakilceni" wani sanyi yadan sauka a ranta,ta juya idonta kadan "A'ah,ai matsayinka daban,inaga kaje din da kanka sai yafi" baice komai ba,sai ya kalla agogon hannunsa kawai sannan yace "Zan dan fita,inajin zan iya kaiwa magariba kafin na dawo,rabi'u zai kawo cefene komai da komai,ki duba abinda babu saiki gaya masa ya hado dashi" fuskar ta a wadace da fara'a,duk da sanda take ita daya ba haka takeyi ba,duk sanda yace za'a kawo cefene cikin bacin rai take,saboda tasan yana buqatar sauyin abinci kenan,zai kuma yita mata tsirfar kala kalar girki,tafi jin dadi idan cefanensu ya qare,zata girka abinda duk ranta yakeso babu wahalar da kai. Ita ta masa rakiya har bakin motarsa,ya shiga ya kunnata ya fice,ranta yayi mata dadi sosai,ganin ya share batun shiga sashenta "Wannan abun yana aiki,sai dan banzan wahala" ta fada a ranta,bata taba kawo zai fice bai shige ba,to amma auren soyayya ne kuwa hakan?,anya ba hadin hajiyar bane kamar yadda taketa jin qishin qishin tana qaryatawa?. Duk yadda latifa tayi kan widad tayi shuru amma abun ya faskara,yadda suke hanya suna ta cin kwalta har zuwa garin kano,haka ta lafe cikin kujerun ta ta dinga rera kuka,tun tana zaune tana aikin lallashi harta haqura ta zuba mata idanu,sallah kawai ta tashi tayi ta koma fa kwanta taci gaba da kukanta,koda latifan ta gama girkin rana wajen qarfe biyu da rabi na rana tayi mata maganar ta tashi taci qin tashi tayi,tayita lallabarta amma tayi funfurus,har akayi la'asar,ta sake lallabata amma taqi koda kallon abincin sai ruwan hawaye,bayan wasu mintuna ta gwada bata baki,saita tarar bacci yayi awon gaba da ita cikin kujerun "Gwara ma kiyi baccin kya samu salama,wanann kuka haka?" Ta fada tana jin tausayinta cikin ranta,saita samu dama ta shirya abincin dare mai rai da lafiya,tunda bata ga alamun girki daga wajen hafsat ba,tunda rana ma da jama'ar kano suka tafi bata sake jin duriyarta ba,tana sanya ran a nan zaici abinci indai abun ya tafi kamar yadda yake a tsare a shari'a,don haka ta tsara abincin da kyau. Dab da sallar magariba widad din ta motsa kadan,sai ta tsaya cak tana qarewa falon kallo tana daga kwance,kwanaki biyun nan mantawa take ba'a gida take ba,duk sanda tayi bacci ta farka saita zata zata farka ne ta ganta a dakin ummu. Tuna komai da tayi cikin yinin yau sai ta fara tara sababbin hawaye,sannan ta miqe daga kwanciyar tana zuro qafafunta qasa,dai dai lokacin latifa ta fito daga daya dakin da ta zabi zama a ciki "ai gwara da kika tashi,kwanciyar tayi yawa" ta fada tana qarasowa inda take zaunen,sai kuma ta dubeta "Aah,kukan dai widad?,to kiyi haquri mana,tashi kiyi sallah kizo kici abinci" kamar jiran me tanka mata takeyi wasu sabbin hawayen suka fara sauka,da qyar latifa ta lallabata ta shiga bayinta ta dauro alwala tayi sallar,amma qememe taqi daukan abincin ko cokali daya taci,sai dan banzan kuka da takeyi,abinda ya daga hankalin latifa kenan,tayi lallashin duniya amma widad din taqiyin shuru,tana kuma tsoron kira mata ummu taje ta birkice mata fiye da yanzu,a haka suka zauna ta sakata gaba har aka idar da sallah isha'i. Koda ya dawo a masallaci ya tsaya,sai da aka gama sallar isha'i sannan ya qaraso gidan,yau din shi daya ne,shi yayi driving abinsa,ya tsaida motar a parking lot na gidan ya kashe motar ya fito. Tsayawa yayi yana duban sassan guda biyu,baisan yadda akeyi ba,baisan wanne zai shiga ba,tsahon wasu mintuna kafin ya zare hannayensa daga aljihu,ya soma takawa zuwa sassan hafsa,tunaninsa ya bashi ya fara da babba tukunna. Yana tura qofar falon muryar mimi ya fara ji,sallamarsa ta ja hankalinsu,suka watsar da kayan wasan dake hannunsu suka nufoshi a guje,kowacce na kiran "Daddy oyoyo" dukka su biyun ya hada ya rungume a jikinsa,yana kallon yadda sukayi fes dasu suka canza,da alama suna samun kulawa da tafi ta mahaifiyarsu "Yaushe Kuka dawo?" Ya fad yana barewa nawwara chocolate "Dazu anty maamaa ta dawo damu" dai dai sannan hafsat dake kitchen tana ta faman yadda zata hada masa abinci me kyau da zai janye hankalinsa ta fito. "Sannu da zuwa" ta fada tana goge hannuwanta a jikin zanin jikinta,ya kalli zanin,kayan jikinta ne tun na safe,ya kuma tabbatar bata sake wani wankan ba,ya dauka zaiga canji ko yaya ne,amma ba wani abu daya canza,hatta da falonta a birkice yake,har da sauran maqalallun dattin yinin bikin da tayi da ba'a gama tsaftacewa ba,duk da haka ya danne shima,yana kallon yadda itama taketa qoqarin danne komai,duk kuwa da irin mugun baqin kishinta "Yauwa madam,kun yini lafiya ya yara?" Ya fada yana kashe mata ido,saita dauke kai tana jin wani zafi a ranta,duk sanda ta tuna akwai wata cikin gidan fa wai itama matarsa ce,sai taji kamar ta shaqeshi "Lafiya qalau" ta bashi amsa a gajarce tana nufar kitchen din "Bari na kawo maka abinci" ajjiye nawwara ya fara qoqarin yi,shekaru kusan bakwai ta kasa haddace me dame yakeso idan ya dawo "Noo,zan fara zuwa nayi wanka tukunna,kin kunna min heater dinne?" Da zaiyiwu ashar ya kamata ta qunduma,saidai tasan ko giyar wake tasha wannan shine kuskure mafi muni da zata aikata,me yakeson maidata?, baiwa?,wai da wanne ma zata ji?,da hidimar yara ko da ta kitchen ko kuma da tasa hidimar? "Ban kunna ba,banma shiga sashen ba yau kwata kwata" kai yadan kada,yanzun kenan yadda ya baro sashen haka zai koma ya tadda shi,babu shara ba komai,duk da cewa dama ya saba da hakan,sai ya sake kada kansa yana nufar qofa "Okay,ki shirya abincin,sai ki shiga ki kira qanwar taki kafin na fito" da harara ta bishi,sai taja tsaki bayan ya fice "To ubana,ga jaka tayi mata girki ko?" Buguzum buguzum tayi hanyar kitchen din tana mita hade da bala'i kamar zata fashe "Ni gaskiya na gaji,na gaji wallahi,dama hausawa sunce abun aro baya rufe katara,wannan attitude din dana ara ya fara isata,pretending din ya fara kaini bango" ta qarashe fada tana jan kwanon data gama hada coleslaw,bata kula ba santsi yasa ya subuce a hannunta ya fadi qasa ya tarwatse,abinda ke ciki yayi nasa guri "Innalillahi,kai jama'a" ta fada qwalla na cika idanunta,sai gasu kuwa sun gangaro,ta duqa a wajen ta fashe da kuka,dukka yaran da suka biyota sai sukayi carko carko suna kallonta. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 39 Cikin girmamawa latifa dake zaune gaban widad wadda ke lafe cikin kujera kamar wata 'yar mage tana hawaye ta amsa sallamarsa,idanunsa a kanta ya qaraso shigo wa,sai ya janye idanuwan nasa ya tsaya tsakiyar falon yana rungume da hannayensa. Gaidashi latifan tayi,ya amsa a mutunce sanann ya sake maida dubansa ga widad tare da tura tambayarsa ga latifa "Lafiya dai ko?,ba wani matsala?" Gyara tsaiwarta kadan tayi "Uhmmm,wallahi gata nan,tunda suka tafi take kuka,nayi nayi da ita amma taqi yin shuru,yau ko abinci bata ci ba" "Ya salam" ya fada yana lumshe idanunsa hadi da. Budesu lokaci guda "Matsala kan matsala" ya furta qasan ransa,saiya sauke hannuwansa ya fara takowa zuwa inda take kwance,ganin haka sai latifa ta juya ta nufi daki. Dab da ita ya tsaya yana dubanta,ita kuma saita cusa kanta cikin pillow tana sake sakin sabon kuka,batason ganinsa kwata kwata,saboda shi ya jawo mata,qila da tuni yanzu suna wajen anty madina suna hirarsu abinsu,qila da tuni yanzu suna falon ummu suna kallo da hirarrakinsu,da tuni yanzu ba cikin pillow take kwance ba,da tuni kanta yana kan cinyar ummu tana sosa mata kai,a hankali ya rage tsahonsa ya tsugunna a gabanta,saiya sarqafe hannayensa guri guda yana kallonta,ta takura sosai a kwanciyar da tayi,amma baisan ta yaya zai gyara ta ba,yana jin tashin sautin kukanta,amma baisan ta yaya zai fara lallashinta ba,idan nawwara ce ko mimi chocolate zai hadasu da ita,to amma ita din aita dara a rarrasheta da chocolate. Duk yadda ya kamo zaren lallashinta ya kasa daidaitashi da tunaninta,bayason qarya sam a rayuwarsa,kuma ba maqaryaci bane duk rintsi,amma a yanzun da aka hadashi da rainon yarinya dole sai ya hada da canza maganganunsa "Tashi muje" ya fada a hankali,abu na farko da yazo kanta shine gida zai kaita,don haka ta daga kanta da wani mugun hanzari,ta sauke manyan fararen idanunta da suka sauya launi saboda kuka tana dubansa "Gida zaka kaini wajen ummu?" Sai ya gyada mata kai,yana kallon yadda farar fuskarta tayi pink sosai saboda kuka,kafin ya gama tunanin sa tuni ta diro daga kan kujerar,ta nufi hanyar daki tana kiran sunan latifa ta dauko musu kayansu "Wait....zo mana kiji" ya kirata yana miqewa da sauri,saita tsaya cak,sannan ta saka hannunta tana maida gashinta baya,saboda ya rufe mata idanu bata ganinsa da kyau "Hijab kawai zaki dauko,kayan sai daga baya kinga suna da yawa,itama ki barta a nan zata biyomu" "To" kawai tace masa,saita qara wuta zuwa daki harda hadawa da sassarfa. Tafin hannunsa yasa ya dafe goshinsa,ya Allah.....a sanda kake buqatar ka huta......wannan wanne sabon raino ne ya sameshi?. Tunda latifa ta ganta afujajan ta kuma gaya mata me yace sai tayi murmushi kawai ta miqa mata hijab din tana cewa "Allah ya kiyaye hanya,saina taho" ta zura hijab din tayi gaba abinta. "Na shirya" ta fada a shagwabe tana karya wuya sanda ta dawo falon,kallon fuskarta sosai yayi,hijab din ya qara mata kwarjini,sai ya juya a hankali ba tare da yace mata komai ba ya soma ficewa,tuni tayi tsalle ta dafa masa baya,don kafin ya fice ma harta tarar dashi,jinta a gefansa ya sanyashi waiwayawa,dai dai sanda itama ta daga kai ta kalleshi,sai suka hada idanu,wani abu mai nauyi taji ya saukar mata,sai tadan dakata har sai daya gota mata da kusan taku uku sannan tabi bayansa. Da kansa ya bude mata seat din gaba ta shiga,sannan ya zagaya ya shiga shima ya tada motar,ta sauke ajiyar zuciya wadda ke hade da sheshsheqar kukan da tasha,sai taji hankalinta ya kwanta sanda suka hau kwalta,zata koma wajen ummunta. A hankali yake tuqin,ya rage speed na motar sosai,sai widad tayi relaxing sosai jikin kujera tana kallon yadda suke wuce titunan garin bauchi a hankali,kamar zata masa maganar cewa baya sauri,amma sai taga sannu sannu dai tunda sun fito zasu isa wajen ummun. Cikin nutsuwa da salo na janye hankali ya dinga bi tituna tituna da ita,tun tana zuba idanu taga sun dauki hanya dodar harta haqura taci gaba da bin unguwannin da suketa wucewa da kallo,wani waje ya burgeta,wani gurin taga kamar kano,wani gurin kuma taga kano tafi wajen kyau. Agogon hannunsa ya kalla,dai dai sanda ya nuna masa sha biyu saura na dare,saiya juya kan motar yayi reverse,ya koma asalin titin da zai maidasu gida. Tun tana zaune saman kujera tana chart su mimi na wasa a saman carfet,har bacci ya daukesu,sai a sannan ta lura da yadda lokaci yaja,to a ina ya tsaya?,ta tambayi kanta bayan ta gama kwantar da yaran,qirjinta ya buga sanda zuciyarta ta raya mata yana can da yarinyar yana neman hadin kanta qila kamar yadda ta samesu ran nan,tunanin da ya sanyata fara neman spare key din gefen nasa,wanda ta jima rabon da tayi amfani dashi,jikinta har rawa yake,bata ankara da rigar jikinta ta bambanta da zanin jikinta ba ta zaqulo muqullin ta fito da wani irin sauri. Cike da qwarin gwiwa ta sanya key din ta buda sashen nasa,wayam ba kowa a falon,wata zuciyar ta gaya mata suna can kan gadonsa yana cin amanarta,saita qara hanzari ta cusa kai bedroom din nasa,nan ma babu kowa,ta tsaya jim tana tad'i ita da zuciyarta,sai taji ranta yana raya mata qila yana sassanta acan suka yada zango,ta sake juyowa a birkice tana fita a sassan nasa. Tunga taja ta tsaya ganin alamun qofar falon na kulle ta ciki,wannan ya sake tunzurata,zarginta kuma ya fara hauhawa,ta fara bugun qofar da qarfi. Da hanzari latifa ta taso,wadda tuni bacci ya dauketa,gabanta ya dinga faduwa din irin qarfin bugun da akewa qofar "Allah yasa lafiya,Allah yasa ba wani abu bane ya faru" ta dinga fadi cikin zuciyarta sanda take kan hanyar zuwa ta bude qofar. Kallon kallo suka yiwa juna na sakanni kafin latifa ta tuna wace,saita sake fuska "Barka da dare" ta fada tana duban fuskar hafsat,bata amsa ba illa cewa da tayi "Tana ciki ne?" Kai ta girgiza "Sun fita,tun dazu kuwa,nima su nake tsimaye" saura kadan tayi subutar bakin sako ashar,Allah ya taimaketa ta danneta can qasan ranta,wani abu mai zafi da quna ya soma mata suya a qirji,wata mace abbas ya saka a gaban mota suka fita?,me yake nufi?,zai daidaita matsayinsa da yarinyar da ita take mata kallon bata da maraba da babu?,don cin fuska tana can tana zaman jiransa,bai gaya mata ma cewa ya fita din ba saidai taji a bakin wata?,saita juya ba tare da tace mata komai ba ta fara barin wajen,latifan ta bita da kallo ranta cike da tambayoyi,daga bisani ta maida qofar ta sakayata,ta koma falon ta zauna saman kujera tana hamma tare da duba lokaci,bataso ta koma bacci suzo kuma suyita bugu. Dab da zata isa sashenta qarar bude qofa da kuma hasken motarsa ya risketa,saita tsaya cak tana motar,kafin ta fara takawa zuwa wajen,tanason taga idanun abbas,da wanne baki zai mata bayani kuma?. Yana kashe motar tana isowa saboda saurin data kwaso,ya sauke Glass din motar a hankali yana dubanta kafin yace "Bakiyi bacci ba?,inata so na kiraki kuma saina sha'afa" hakan daya fada ba abinda yayi mata illa sake tunzurata,ya manta ma kenan da ita?,takai dubanta ga widad wadda jikinta ya gama yin la'asar,ta kwantar da kanta a seat din motar,bacci gaba daya ya cika mata idanunta,duk da haka ta hadiye "Qanwarki keta rigima nadan fita da ita" sosai tayi namijin qoqarin danne wani mulmulallen abun daya taso ya tsaya mata a wuya,bataso sam ya tabata da niyyar dagata ko taimaka mata ta fito,don haka tayi saurin zagayawa side din ta bude mata qofar tana cewa "Ayyah.....haba widad?,banda abinki da haka kowa yake sabawa, kowacce mace a matsayin baquwa take zuwa gidan aure,amma yau da gobe sai kiga ta saba" ta qarashe maganar tana bude murfin,tana jin kamar ta fincikota,amma hakanan ta tsaya harta fito din "Ka wuce ka huta,bari na rakata" ta fada tana kallonsa. Wani narkakken kallo yake binta dashi,gaba daya ta gama bashi mamaki ta kuma kwance masa kai,hafsat dinsa ta sauya fiye da yadda rai da zuciyarsa suke raya masa zata iya sassauta kishinta,kodon tana duba qananun shekarunta ne?,yana nan a tsaye har sukayi nisa,tana riqe da hannunta tana lallashinta da bata maganganu,saiya maida murfin motar ya rufe,ya sanya key din a aljihunsa ya soma takawa zuwa sashen sa yana jin gajiya nabin dukka gabbansa,babu abinda yafi buqata a yanzu irin ya watsa ruwa a jikinsa ya kwanta. Sai data tabbatar tayi nesa da widad daga inda abbas yake sannan ta fito tabar sashen,bayan ta gama mata lallashin qarya da nuna kulawa,wanda qasan zuciyarta cike yake fal da tsana da kuma qiyayyar yarinyar,tana jin kamar ta budi idanu taga babu ita kwata kwata cikin gidan. Latifa ce ta sakata a gaba kan sai taci abinci,da yake a gajiye take,kuma yunwar take ji da gaske saita zauna taci din,tana tsaka da cin ma baccin ya kwasheta ko.hannu bata wanke ba,sai tatifa ce ta gyara wajen ta kuma tasheta ta koma dakinta. Washegari tunda wuri latifa taga kiran ummu,bata yi jinkiri ba ta daga,don dama tana da niyyar kiran nata,bayan sun gaisa widad ta fara tambaya,bata boye mata ba ta gaya mata yadda suka wuni jiya,muryar ummun ta canza,da alama ita kewar widad din tata takeyi,sai tace takai mata wayar. Bacci takeyi amma sanda tace mata ummu ce sai gata ta wartsake sarai,ta karba wayar tana kiran sunanta hawaye na shirin balle mata,tausayinsu duka ya kama latifan,sai ta fice tabar mata dakin bayan taja mata qofar. *Arewabooks: Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 40 Kuka sosai ta sakarwa ummun,da qyar ta samu ta shawo kanta,cikin hikima da dabara irin ta manya ta dinga lallabata,har sai data gamsu ta kuma ji alamun sakewa da tayi sannan ta fara tambayar ta inda wayarta take,sam ta ma manta da wani batun wayarta,sai a sannan ta tuna tun randa suka iso da nujood ta gama game da ita tace ta saka mata a bedside drawer dinta. Kusan awa guda suka shafe da ummu a waya,har alhaji ma ya karba,Aafiya da rafi'ah da suka shigo suma dukkansu suka karba,sai da kudin ummu ya qare tsaf kiran ya yanke da kansa. Maganganun da sukayi da ummu yasa ta samu sassauci,sai walwalarta kadan ta dawo,ta sauko daga saman gadon da wayar riqe a hannunta da niyyar kaiwa latifa. Tana shirin bude kofar dakin aka turo qofar,sai ta danja da baya tana kallonshi yana shigowa dakin,sanye yake da wani yadi mai taushi,a ido kawai zaka fahimci bashi da kauri,saboda kana iya hangen fara qal din vest din dake jikinsa. Baya ta sake ja tana rakubewa,gabanta kuma yana faduwa,har ya qaraso cikin dakin,ya taka a hankali ya qarasa gaban madubinta ya tsaya "Ina kwana?" Ta gaidashi tana dan russunawa,sai ya maida dubansa a kanta,gaba daya a darare take, baisan me yasa ba,amma ya gama karantar dabi'unta tsaf na rashin sakewa da jama'a,da alama tana da wuyar sabo,shikam tako ta ina baiga ta inda wannan hadin zai zama me alfanu ba,saidai ya sani cewa,abinda babba ya hango,yaro ko ya hau dala da gauron dutse bazai hangoshi ba "Lafiya lau,ya kwanan baqunta?" Ya fadi yana gyara daurin agogonsa,bata san ya zatace ba sai tayi shuru kawai ta sadda kanta,ita kawai Allah Allah take ya fita mata a daki,kada latifa tazo ta gansu su biyu. Sai daya gama gyara agogon sannan ya maida kallonsa a kanta "Shikenan babu wani abu da kuke buqata?" Kai ta gyada masa da sauri,sai ya jinjina kai,ya sanya hannu a aljihunsa ya fidda kudi ya ajjiye mata,don dabi'arsa ce,haka yakewa hafsan,koda suna da komai baya taba fita ya barta hannu babu komai. Ido ta bude sosai ta zarosu waje tana kallon kudin,har ya kusa fita daga dakin sannan ta ankara,da hanzari tace "Don Allah ka dauke,kada latifa ta gani,ni banaso" qaramin murmushi ne ya subuce masa duk da bai shiryawa hakan ba,ya waiwayo yana kallonta da manyan idanunsa "Ba zata komai ba koda ta gani din,daga yanzu duk abinda na baki babu wanda zai miki fada don kin karba,right?" Jikinta a sanyaye ta gyada kanta,don dai ita ta sani ummu na fada sosai gasu basma ma idan wani ya musu kyauta suka karba,tana kallonsa har ya fice daga dakin,sai ta matsa kusa da kudin tana kallonsu ba tare data taba ba. Ja baya tayi kadan jin an sake buda qofar an shigo,latifa ce,idanunta nakan fuskar widad din "Kun gama wayar ne?" Kai ta gyada mata "Eh tun dazu,kinga kudi wai ya bani" ta fada a shagwabe cike da sakarci tana dubanta "Kuma Allah bani na roqshi ba" ta sake fada qwalla na cika mata idanu,dariya kufcewa latifa,ta yarda widad bayan quruciya ma harda sangarta irin ta goyon kaka ke damunta,qarasawa tayi inda take tsaye ta kama hannunta ta riqe "Don ya baki kudi ba komai bane,mijinki ne kinji, komai zai baki hakanan kome zaiyi miki ba haramun bane kin gane?", Kai ta gyada kawai bawai don ta fahimci me take nufi ba "Kuma ya akayi ya fita baki masa rakiya ba?" "Mu jera tare?" Ta tambayi latifa tana fidda idanu,saita jinjina mata kai "Eh mana,bakiga ummu na raka alhaji ba?" Shuru ta danyi tana tunowa,ta gyada kai a hankali "To daga yau kema haka zaki dinga yi masa kinji ko?" Fuska ta noqe,itadai wannan ai iskanci ne,batason irin wadan nan maganganun,haka dai ta gyadawa latifan kai,sannan ta sakata a gaba suka wuce kitchen. A ranar latifa ta fara gwada mata yadda zatayi wasu abubuwa cikin kitchen,kamar tsaftaceshi da inda zata dinga ajjiye komai a muhallinsa cikin kitchen din,yadda zata wanke kwanuka da sauransu. Da yammaci tana falonta a zaune bayan sun gama komai ta dinga jin hayaniyar yara,sai tayi mamaki don bata dauka akwai yara a gidan ba,daga nan ta yaye labulen falon nata,sai ta hangi su mimi suna wasa,tana son fita amma ita komai na gidan d'ari d'ari takeyi dashi,don haka taci gaba da kallonsu ta nan,har suka gama wasansu suka bar wajen. Tun qarfe shida ta gama lafta shinkafarta da miya,ta zubata cikin food flask,bata damu da jimawar da zaiyi kafin ya dawo ba,ko kuma gumin abincin da zai iya komawa cikin flask din ba. Fuskarta ta dauraye kawai,ta cire zanin jikinta ta nemo mahadin rigar ta saka,sannan ta tasa su mimi a gaba suka wuce sashen widad,tayi hakanne saboda ta hanashi dadewa acan,kada ya shiga yaje ya zauna,ko abinda ya faru jiya ya maimaita kansa,cikin ranta tana jin ko a jiyan ma kirsa ce kawai irin tata,ta sani cewa mace duk qanqantarta kaidi ne da ita,kada tazo tana tufka ta baya tana warware. Kan widad na saman cinyar latifa tana kitsa mata kalba tana warewa saboda santsin gashinta,sa'annan kuma ba wani kama mata takeyi da kyau ba,tana mata ne shigen yadda ummu ke mata idan tanason tayi baccin rana,latifan na bata labarun ban dariya,wanda ya sake sanyawa zuciyarta ta kuma saki. Koda tayi sallama hannu bibbiyu latifa ta karbeta,widad kuwa kamar ko yaushe binta tayi da kallo kafin ta zamo ta gaisheta kamar yadda take gaida dukan wanda ya girmeta,hakan kuma sai ya yiwa hafsat dadi,ta sake jin lallai itace a sama,ta dinga bin falon da kallo a fakaice,kafin ta koma satar kallon widad din,bata da matsala da komai,tana kuma jin komai zai tafi dai dai,damuwarta daya irin kyawun da yarinyar take dashi,tana tsoron kada wannan ya zama mabudin nasarar jan hankalin abbas... "Inaaaa,bazan bari ba" ta tabbatarwa kanta da kanta cikin zuciyarta,zatayi dukkan mai yuwuwa ta hana wannan kyan tasiri a fuska da idanunsa. Kusan da latifa suke hirar,ita widad ta maida hankalinta gasu mimi,kasancewarta mai son qananun yara,duka sai suka ja hankalinta,tana ta duban fuskar nawwara da taga tana mata kama da fuskarshi "Ke dawa kike kama?" Ta tambayi yarinyar tana dan murmushi,mimi tayi wuf tace "Da daddynmu mana,ni kuma da mommy na,wai shine su anty bara suke cewa ta fini kyau,wai daddy yafi mommy kyau" daga idanunta widad tayi ta dubi fuskar hafsat dake magana da latifa,eh itama taga wannan duk da qarancin shekarunta,amma dai tasan kyau "Eh wallahi,ya fita kyau" widad ta fada hankalinta kwance cikin yanayi na quruciya. Rigime mata mimi tayi ta soma qwalawa uwar kira "Mommy,kinji anty ma tace daddy yafiki kyau,kuma nawwara ta fini kyau?" Dariya latifa tadan saki tana kama baki,widad din tayi wauta,amma da alama ma ita a wajenta ba komai bane,yayin da hafsat ta kafe widad da idanu,wani abu mai kama da bacin rai yana motsa mata qasan ranta,sai kuma ta buge da murmushin yaqe "Tsokanarki takeyi,kuma ni nafi daddynku kyau,saidai ya nunamin manyan ido kawai" cikin murna mimi ta waiwaya tana duban widad "To kinji ko?" Dariya ta saki tana jawota jikinta "Wasa nake miki,kema kina kama da daddyn naki ai" kau da idanunta hafsat tayi daga kansu, zuciyarta na raya mata wani abu. Yau dinma kai tsaye sassan hafsat din ya fara isa,bai taras da kowa a falon ba,don haka ya sanya kai bedroom dinta,yana taka lallausan sabon carfet din daya sauya mata dab da bikin nan,amma har datti ya fara cikashi laushinsa ya ragu ainun. Dakin yaran ya fara budewa,komai a hargitse a zaune da duwawunshi,ash and baby pink ne color din dakin,amma pink din har ya dauki hanyar zama ash din shima,ya taka a hankali yana tattare kayan sawarsu dake watse a qasan dakin,sun cakude waje daya,ba zaka banbance wankakke da wanda baida wanki ko kuma guga ba,ya kwashe gaba daya,ya buda laundry basket dinsu da niyyar zubawa,sai ya sameshi a cike fam da kaya. Ransa ya sosu,baiga amfanin yaron da ya aje saboda ya dinga musu wanki ba,bayan duk wata sai ya ajjiye kudinsa,to kudin ake bashi a banza ko kuwa,ya daga kayan da niyyar zubasu a haka yaci karo da undies din hafsat din,harda brassieres. Kishinsa ne ya motsa,ransa ya sake baci fiye da dazu,sai ya watsar da kayan yaran gefe daya,ya soma birkito kwandon,nan ya dinga cin karo da undies dinta,ya dinga tarasu a gefe,har ya gama kwashesu tsaf,sannan ya zuba kayansu mimi din,ya buda toilet dinsu ya leqa,dole ya dawo baya da sauri,saboda abun babu kyan gani,mutum ne shi me masifar tsantsami,idan kanaso kaga fadansa to yaga qazanta. Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,yana dai tunanin me aikin da bayaso daga qarshe daqyar idan ba ita zai sa a daukowa hafsat din ba,ya gaji da ganin wannan qazantar gaba daya,to amma kuma hakan kamar daure mata qarqashi ne,kada ta sake sangarcewa ta miqe qafa,tun a baya yaqi a kawota dinne saboda gudun ta sake tabarbarewa,amma a yanzu dukka alamu suna nuna daukotan ya kusa zame masa wajibi. Dakin ya janyo musu ya wuce nata dakin,shima dai kamar dakin yaran,shikam natan harda tsami tsamin kayan wanki,bai saka kai da yawa ba ya dawo da baya yana ambaton sunan Allah,sai kawai ya juya ya fice daga sashen gaba daya. Duk da ransa babu dadi haka ya daure ya nufi sashen widad din,tunda dai itama matarsa ce kamar hafsat din,tana kuma da haqqi a kansa kamar ita. Sanda yayi sallama a falon yayi dai dai da sanda widad ke maimaitawa mimi karatun makarantar bokonta,yarinyar kuwa nata kamawa tana amsawa cikin jin dadi,don baqon abune a wajenta,mamarta bata taba tsayawa ko sau daya ta duba assignment dinta ko ta bibiyi karatunta ba,abbas din keyi mata assignment idan yana gari,idan baya nan kuma haka zata koma da litattafan ta, aunties dinsu sunsha rubuto letter suce ta kawo gida,hafsat ke karba,tana gama karantawa take yagawa,ta rubuta reply da cewa ayi haquri,mamanta ba mazauniya bace amma za'a gyara,har sun gaji da rubutun sun qyaleta,saboda suna ganin kudin ubanta ke tafiya,su basu da asara. Rige rigen zuwa yi masa sannu da zuwa sukeyi,widad ta bisu da kallo tana jin damuwarta da kewarta na raguwa,dan zaman awannin da sukayi dasu sun debe mata kewa matuqa. Tunda ya shigo din take bibiyar dukka motsinsa da idanuwanta,tana son taga shin ko zai kalli sassan da widad din ke zaune?,ko kuma zai saci kallonta ko sau daya ne?. *Arewabooks: Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 41 Latifa ce ta fara gaidashi,sannan ta kauce ta basu waje,falon ya zamana iya su yasu. Cikin baqunta tadan motsa kadan tana gyara zamanta gami da hade jikinta waje daya,kamar yadda ummu ta koya mata duk sanda wani baqo ya shigo sassansu,koda kuwa cikin mazan gidansu ne yayyenta 'ya'yan kawunnanta "Sannu da zuwa" itama fa fada kamar yadda su mimi suka fada,ba wani sakin jiki ko alamun sanayya a tattare da ita, yanayin da yayiwa hafsat dadi qwarai,ta kuma sake sanya idanu a tsakaninsu,tana kuma karantar yadda kowannensu ke nuna baqunta ga dan uwansa "Sannunki,kin wuni lafiya?" "Lafiya lau" ta amsa masa idanunta na a qasa,yayin da nasa hankalin yake kansu mimi,sai ya miqe dasu yana bare ma nawwara chocolate din daya shigo musu da ita. "Babu wani abu ko?" Yayi tambayar a wannan karon yana watsa idanunsa a kanta,ta girgiza kai da sauri "Ma sha Allah" ya fada yana kama hannun yaran,a sannan hafsat ta miqe,fuskarta fal murmushi "Amarya ki dinga sakin jiku mana kinji?,ba haka ya kamata ki marabci angon naki ba" sakato widad din tayi tana jin nauyin maganar hafsat din,zancan kuma yana mata girma "Ina zuwa bari.naje,ki shirya xamuci.abincin dare tare kinji ko?" Hafsat din ta fada tana danne dariya,yadda widad din tayi wuri wuri yayi mata dadi,bata amsa mata ba har ta fice. Sam batasan yana tsaye a wajen ba sai da tazo giftawa tana sauri don ta cimmasa saiji tayi an damqo hannunta,ya kuma jawota xuwa gabansa. Hannayensa ya sanya ya zage bayanta dasu,suka tsaya dab da juna suna ma juna kallon cikin idanu,ita ta fara janye idanunta,sabida bata fiya jurewa kallonsa ba,akwai wani irin kwarjini mai yawa cikin idanunsa,shi kuwa ci gaba yayi da.kallonta,irin wannan kallon yana tada masa feelings sosai a kanta,yana kuma karantar abubuwa masu yawa dake kwance a zuciyarta ta cikin idanun nata,saidai ya fuskanci ta koyi dabi'ar kaucema idanunsa din. Dan gyata tsaiwarsa yayi yana sake matsota kusa da jikinsa,duk da cewa ba irin wannan yanayin da scent din yake son samu daga jikinta ba.......zaya so ace tana fidda kalar launin qamshin daya daga cikin turarukan da yafi so,yake kuma siya ya ajjiye mata komai tsadarsu "Wai kin daina kishina ne?" Ya fada da wata irin cool voice,ita kadai tasan abinda ya saukar mata a zuciya,inda yasan yadda takejin zuciyarta a duk sanda yake magana kawai da wata macen,da wala'alla har ya mutu bazai sake kallon kowacce diya mace ba baya ga mahaifiyarsa "To amaryar taka ce naga bata iya komai ba,kaima kuma baka iya rainon da aka kawo maka ba" yadda tayi maganar yadan sansano sautin kishi a ciki,duk da yaso jurewa amma saida murmushi ya subuce masa,sai ya saketa kamar yadda taketa kiciniyar qwacewa daga hannunsa,yasan zata ce masa kada yara su gansu "Tunda gaki basai ki tayani rainon ba" baki ta tabe "Saboda ni ka aurowa ita?,yanzun ma......" Maganarta ta yanke sanda ta fuskanci gangancin da take shirin aikatawa,saita waske "Yanzun ma tausayinta nakeji,an aura mata tsoho" ta qarasa fada tana yin gaba,taku uku ya cimmata,sannan ya bata amsa "Tsohon ashe yayi.kasuwa,tunda har ya samo qaramar yarinya ko?" Cikin Zuciyarta sai taji kamar.magana ya gaya mata,don haka taja bakinta ga tsuke,bata sake saka.baki.akan magabar ba,gudun kada ta tafka shirme tana samu tana tsallakewa da qyar. Yana shiryawa yana mata magana cikin hikima akan ya kamata ra gyara dakin yaran dama nata dakin da kyau,baki ta tura,shi kome qoqarinka me yasa sai ya cika gyara?,sai yayi challenge naka?,duka ba hidimar dafa masa abinci ke cinye mata lokacin ba?,ita sai taji har ta qagu ya koma Kaduna,ta yadda zata samu ta miqe qafarta da kyau. Tana gama sallar isha'i ta shiga wanka saboda tuna alqawarin data daukarwa anty deena,data fito ta shirya cikin kayan bacci kai tsaye,wasu riga da wando ne kalan pink da suketa burgeta cikin kayan lefanta,dama Allah Allah take ta sakasu,tana gamawa ta maida hijab dinta tabi lafiyar gado tana hamma,yau ma a nan dakin zata kwanta tare da latifa,idan suka kwana tare sai tayita jin kamar ummu. Dai dai sanda take rufe bakinta sabida doguwar hammar bacci da taketa saki latifa ta turo qofar dakin,shigowarta kenan bayan ta maida kwanukan da sukaci abinci daki "A'ah,me zan gani?,yauma?" Ta fada tana kama baki,sai widad din ta waiwayo tana dubanta "Me nayi?" "Ke da zaki wuce ki tafi dakin mijinki?" "Dakin miji kuma umma latifa?,kamar wata 'yar iska?" Tayi maganar tana maida kanta saman pillow ta dora da cewa "Yanzu da kanki kike cewa ma naje dakin wani" dariya taso qwacewa latifan,lallai da gasken gaske wauta da quruciya sun yiwa widad din yawa,saita qaraso gefan gadon ta zauna tana qoqarin fahimtar da ita. Sam widad din ta gaza kai hankalinta kan abinda take nufi,sai ma tubure mata da tayi kan babu inda zata,dai dai lokacin hafsat tazo kiranta tazo suci abinci,nan ma tace ta qoshi ba zata ba,ran hafsat din ya mata dadi,amma duk da haka a gaban latifa dashi kansa abbas din saita nuna bataso haka ba "Rabu da ita,yi serving dina" ya fada kansa tsaye sanda yake dan diban abincin kadan kadan yana baiwa nawwara a baki,wadda tayi dare dare saman cinyarsa,saita soma zuba masa abincin,amma bata rabu da zancan ba,don lallai ta nuna masa ita ba'a son ranta ba,har sai da yace "Will you keep quiet madam?,ko sai na saka gum dina na rufe miki bakin?" Ya fada yana jifarta da hararar wasa "Kai bakasan na fika farinciki da haka ba" ta fada cikin ranta,amma a zahiri bakin nata taha ta rufe,bata sake tashin zancan ba. *********sannu a hankali kwanaki suka fara tafiya,widad cikin gidan har a sannan tana matsayin baquwa,baquwar dake ganin kulawa da damuwa daga idanun hafsat,harma taje ganin matuqar kirkinta fiye dana ja'afar,yadda su mimi ke kiranta da mommy haka nan itama take kiranta dashi,tana mata kallon da takewa anty madina ne,tana kallonta a matsayin uwa ko wata babbar yayarta,gefe guda kuma sabo ne ya shiga tsakaninsu dasu mimi da nawwara,musamman mimin,a nan sassanta suke kusan yini. Idan ka samu widad din dasu mimi zakayi tunanin yayace da qannenta,kusan ko yaushe suna tare,sosai suke debe mata kewa,idan lokacin da zasu shiga kitchen yayi ita da latifa zasu shiga tare,to amma kusan fiye da rabin hankalinta yana kan yaran,don haka ba wani abun arziqi take tsaiwa ta koya ba. Ta bangaren abbas shima tana masa kallo daya ne,matsayin uncle muhsin take kallonsa,saidai wani bangare na zuciyarta haka kawai yake cika da tsoronsa,ta kasa sakewa dashi kwata kwata,babu fashi,a kullum zai shigo da safe yaji basu da matsala,ya sake dawowa da dare ya tabbatar da komai lafiya,zaman cin abinci dasu kuwa ko sau daya bata taba yarda ta zauna din ba,hakan yana yiwa hafsat dadi matuqa,yadda yarinyar je tattare kanta waje daya,take kuma dari dari da komai nasa,wannan shike haska mata lallai komai zai tafi mata a sauqi. To hakanan duk yadda latifa zata lallabata taje sashensa kona awa daya ne sai ta dawo taqi,sai tayi mata kamar bata ji ba,ta kwanta ta hau barcinta,tare suke kwana da latifa din a daki daya,gado daya,wannan yana debe mata kewar ummu qwarai da gaske. *******A nutse cikin takun nan nashi dake nuna zallar karsashi da lafiya da tsiyayyar qirar jikin da yake dashi yake takowa zuwa harabar gidan,kunnensa maqale da waya yana amsa kira,hannunsa daya riqe da key din motarsa. Sanye yake wani yadin kuftan mai kyau da daukar ido,anyi masa aikin hannu mai tsadar gaske,sosai kayan suka zauna masa,abbas din ba daga baya ba wajen iya saka manyan kaya,kowacce shiga daukansa takeyi,saika gaza tantance wadanne kaya ne suka fi masa kyau. A hankali ya zare wayar daga kunnen nasa yana katse kiran, hankalinsa yana kaiwa kansu, suna daga gefan farfajiyar gidan,mimi ce da widad,widad din na daga zaune gefan wata tukunyar fulawa,sanye take da wata doguwar riga mai santsi mai dogon hannu,tana hade da hula ne daga bayanta,bata saka hular ba,tadai saketa,lallausan gashinta mai santsi da tsaho yana matse cikin qaramin band,jelar ta buya ta bayanta,fararen qafafunta na slipper blue din slippers,color din dake matuqar fidda hasken fatarta. Mimi kedan garo mata ball,itama tana daga zaunen sai ta sanya qafarta ta maida mata,yau din tunda ta tashi bata da wani cikakken kuzari,shi yasa ma tace wa latifa ba zata shiga kitchen kallon girkin yamma ba,itama bata matsa mata ba,ta barta suka fito da mimi din,wadda hafsat ta tafi unguwa ita da nawwara,ta barta a nan,don qememe taqi binta,ba kasafai ta fiya damuwa da bin hafsat din unguwa ba,tafison zama da widad. Idanunsa ya janye dsga kanta ya nufi parking space,yana hangosu har sannan ta cikin mirror din,shi kansa a yau sai yaga babu wannan kuzari da kazar kazar din daya santa dashi,idanunsa ya kuma daukewa yana rufe motar ya tayar da ita ya fice daga gidan a hankali. A nutse yake tuqinsa kamar kullum,yana tafiya yana lura da abubuwan dake faruwa saman hanya,gidan hajiya ya nufa kai tsaye,don dama a yau din can yayi niyyar zuwa,sai dare kuma ya tsara zai fita daga unguwar. A hanya ya tsaya ya siyama hajiyan abubuwan da yasan tana sha'awa kamar yadda ya saba,sannan ya wuce,mintuna qalilan ya iso unguwar tasu. Tun daga farkon layinsu matasan da suka ankara da shigowar tasa suka biyo bayansa, mutum ne shi mai matuqar kirki tausayi da kuma taimako,wannan ya sanya masa farinjini sosai ga al'ummar unguwar,kamar ko yaushe,bai shiga gida ba sai da ya gama sallamarsu. A bakin qofar dakin hajiyan ya duqa ya cire Black cover shoes din dake qafarsa mai matuqar tsada da kyau,sannan ya yaye kyawawan labulayen falon dattijuwar bakinsa dauke da sallama. Su biyu suka amsa sallamar,hajiyarsa da kuma yayarsa yaaya bara'atu,fuskar hajiyan kwance da fara'a tayi magana "Tun dazu akacemin kana qofar gida,a raina nace qila jama'a ne suka riqeka" yana qoqarin zama a gabanta saman carfet yace "Sune hajiya,da qyar na qwato" ya qarasa maganar tsadadden murmushin sa kwance saman fuskar sa yana duban mahaifiyar tasa,saita jinjina kai "Ma sha Allah,mafi alkhairin mutane shine wanda yake amfanar da mutane,Allah ya qara tsare mana ku a duk inda kuke" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" ya amsa,yaaya bara'atu tana tayashi. Sai da suka fara gaisawa da hajiyar sannan ya gaida yayar tashi,yana tambayarta mai gidanta,sannan suka shiga hira,kafin hajiya ta kira muneera ta kawo masa ruwa da lemo. "A qoshe nake hajiya alhmdlh,saidai kafin na wuce" "To shikenan muneera jeki", tsaiwa tayi ta gaidashi cikin girmamawa,sannan ta koma kitchen taci gaba da aikinta. "Nace sai yaushe zaka koma kadunan ne ango?,ko cin amarcinne bai qare ba?" Yaaya bara'atu ta fada tana gyara zamanta sosai cikin lausasan royal chairs din hajiyar. K'aramin murmushi ya subuce masa,banda yaaya bara'atun babu wanda zasuyi irin wannan maganar dashi "Jibi nake saka ran wucewa,hutun da suka bani ya qare" "Sun kyauta ma ai, duka duka yaushe ka koma kadunan ma,Allah ya sanya albarka sun kyautata maka kam" "Sosai hajiya" ya furta yana gyada kansa. "Tafiya dai ta kama hafsat zuwa yanzu,tunda dai ai ba zasu tattare gaba dayansu su zauna anan kai kana can ba" anty bara'atu ta sake fadi tana dubansa,duk da bata da tabbacin samun cikakkiyar amsa daga gareshi,ta sani ba kasafai ya fiya son hirarraki irin wadan nan ba. Kaman hajiyan ta fuskanci bashi da niyyar yin magana din,sai tayi amfani da wannan damar ta isar da saqon da take ta son isar masa din "Hafsat ai dama bauchi ta zaba,widad itace abokiyar tafiya Kaduna,ita ta riga ta yankewa kanta hukunci,bana jin kuma zata janye" tsaf ya gama karantar saqon hajiyan,saidai can qasan ranshi yana tunanin yadda zai dauki rigimammiyar yarinyar da bata da maraba dasu mimi har zuwa wata uwa duniyar da sunan matarsa "Amma hajiya sai nakega ba zataji dadi ba,daga zuwan wata sai a tafi da ita ita kuma tana zaune?" "A'haaannn,to daa waye yayi mata?,ita ta yankewa kanta wannan hukuncin,ta kuma bada zabin ya samo mai zama dashi,meye laifi yanzun dukka a cikin wannan lamarin?" Shuru bara'atun tayi,sai ta dan jinjina kanta "Allah ya sawwaqe" . Shigowar fanteka ya tasheshi,ya miqe yana zuba hannayensa a aljihun wandonsa "Bari na danje bayanmu na dawo" "Allah ya kiyaye,sai ka dawo" hajiya ta fada kanta tsaye,tashin da yayi yayi mata,don batason wata magana sam a gaban fantekan,tunda ta karanci inda ta sanya gaba. Ba haka fanteka taso ba,amma saita rakashi da yaqe tare da addu'ar a dawo lafiya. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 42 Sanda ya dawo gidan babu kowa sai hajiyan tashi,nan yayi zamansa bayan ya fito daga sallar isha'i,yana cin abinci tana qara masa suna hirarsu "Nidai don Allah zan riqo alfarma guda daya a wajenka abbas" tayi zancan tana ajjiye dan bowl din data qara masa miya,sai ya tattara mata hankalinsa gaba daya,har yana ajjiye spoon din hannunsa "Hajiya badai alfarma ba,saidai umarni ko?" "Ko alfarma koma umarni,nidai burina ka cika......don Allah ka kula da yarinyar nan kamar yadda zaka kulaa da hadiyya da kuke fito ciki daya" kai ya jinjina,can qasan ransa yana jinjina tarin qaunar da hajiyar kema yarinyar "Na daukar miki alqawari hajiya" "To Allah ya taimakeka,yaci gaba da dafawa al'amuranka" "Ameen ya raheem,Allah ya qara lafiya da nisan kwana" sai ta bishi da murmushi kawai,kafin ta amsa masa da ameen. Yau din sassan Widad din ya fara isa,saidai latifa na bude masa qofa taja baya cikin girmamawa,har ya sanya kansa sai ya dakata "Kuna lafiya?,baku buqatar komai?" Ya tambaya,kai ta girgiza,tana tsananin yabawa da irin kulawar da yake nunawa akan widad din "Lafiya qalau alhmdlh,babu komai" "Itafa?" Ya tambaya kai tsaye "Tayi bacci tun dazu" "Lafiya dai ko?" Ya tambayeta yana dan ritsata da ido,kusan bai taba zuwa ya sameta tana bacci ba,yafi samunta a daki,data ganshi zata fara tattare jiki waje daya,ta kuma sanyawa bakinta kwado da linzami,har sai ya gana zamansa na mintu biyu zuwa uku sannan ya fito "Eh bata dan jin dadin jikinta ne wai" "Subhanallah,amma me yasa ba'a kirani an kaita asibiti ba?" "Ba zazzabi ko ciwon kai bane,kawai bata da kuzadi ne kamar yadda ta saba" sai yadan kada kai kadan "Allah ya sawwaqe,ammmm..... Please,koda akwai wani damuwa,a kirani ko ta wayarta ne" "In sha Allah" ta fada cikin girmamawa,cikin ranta tana yaba kulawa da sanin darajar dan adam irin nasa. Sanda ya shiga falon hafsa a zaune ya sameta,yaran na kwance a wajen saman carfet kowa d'ai d'ai,itama saman carfet din take a zaune,hannunta riqe da waya,plates din abinci ne da abincin da sukaci suka zuzzubar kaca kaca,saman kanta ba dankwali,gashinta dake samun qarancin kulawa qwarai da gaske daure a kyauro. Idonsa ya dauke daga kanta yana qarasawa wajen yaransa,saita janye qafafunta tana masa sannu da zuwa,qasa qasa ya amsa mata,yana dauke yaran daga qasa ya nufi dakinsu dasu. A hargitse ya samu dakin kamar ko yaushe,sai a gadon nawwara ya fara ajesu,ya karkade gadon mimi ya maidasu kai,sannan ya gyarawa nawwara nata gadon itama ya maidata kai,bayan ya duba cupboard dinsu ya canza musu wankakken zanin gado,ya tattara karikicen kayan wasansu dake tsakiyar dakin ya killace a drawer dinsu ya hade kayan wankinsu a laundry basket. Yana gab da kammala mopping na dakin ta turo qofar ta shigo,zuwa yanzu daurin dankwalin ture kaga tsiya ne a kanta,dinkin atamfa ce doguwar riga data bude sosai daga qasa,saidai idan ka kalli kayan sosai a jikinta zakasan ta dan sha jiki. "Ya daga shigowarka kuma dear?" Ta fada tana jin wani iri a ranta,shi ya fiya qaqale qaqale,banda hakan bataga wani shahararren datti da dakin yayi wanda zai hana mutum yin bacci ba,taga ko daxun kafin ta fita sai data tattare kayan wankin gefe daya,amma shi baima gani ba. Idanu ya aza mata kafin ya janye yaci gaba da qarasa goge wajen,sai jikinta ya dan mata sanyi daga kalar kallon da yayi mata,don haka ta saki qofar tana qarasowa ciki. Kafin ta qaraso ya gama,ya ajjiye mopping stick din,sannan ya goye hannayensa da tuni ya nade hannaun rigar xuwa sama yana kallonta,yadda ya aza mata kallon mayatattun idanuwan nan nasa duka sai taji nauyinsa ya sake kamata,don haka ta daburce gaba daya "Samu guri ki zauna" ya bata umarni kai tsaye,sai tadan ja tunga,gabanta yana faduwa,bata qaunar fadansa gaba daya,yanzun nan zai sanya ka ka rasa abun fadi,bayan tasan bata da kalar kowacce hujja da zata kare kanta da ita,dole ta samu gefan gadon nawwara ta zauna. Daya daga cikin kujerun dake hade da teburin karatunsu ya jawo,ya ajjiyeta dab ds ita ya zauna akai. Shuru ya ratsa dakin,tana ta kasa kunne taji me zayace da ita,yayin da shi kuma bai furta komai ba,sai kallo da ya ritsata dashi,kallon dake sake sanyata jin cewa da gaske ita din mai laifi ce "Hafsat" ya kira sunanta kai tsaye,wanda abune mawuyaci kaji ya kirata din "Na'am" ta amsa masa ba tare data iya kallon qwayar idanunsa ba "Ki gayamin me kika nema kika rasa a gidan nan,wanne nauyi ne nawa da bana sauke miki?" Motsawa tayi,kamar wadda ke zaune saman wuta,kasa bashi amsa tayi,har ya gaji da jiranta,sai ya sauke hannayensa qasa ya dafe kujerar da yake kai yana ci gaba da kallonta "A iya sanina babu wani abu da yayi saura wanda bana miki shi,ci sha suttura,kudin kashewa,hatta da lighter da za'a kunna gas a gidan nan alhmdlh ban bari ko yarda ki siya ba,me kika rasa hafsat?,amma kin kasa tsaida hankalinki ki tsaftace gidanki,ki kula da yaranki,ki sauke hakkina dake kanki,zaki iya tuna when last da kika kawo kanki gareni?" Ys jefa tambaya mafi girma da taketa tsoron yayi mata ita "Don Allah kada ka kawo wannan zancan,ka san dai ina iya bakin qoqarina ai......" Wani miskilin murmushin takaici ya saki "Well......am listen to you" da qyar ta tattaro dukka jarumta da qwarin gwiwar ta,duk da cikin ranta har yanzu bata jin kanta a matsayin mai laifi "Ina fa kwatantawa,ina qoqarina dear,aikin gida fa ba is not easy at all,sauqinta ma ace ina da 'yar aiki,amma yanzun komai fa ni nakeyin abina,ga yara,ga makarantar mimi,dole wania abun fa sai ana haquri" ta fada tana dan tsuke girarta fuskarta qasa qasa,ita ala dole bataji dadin gyaran da yakeson mata ba. Shuru yayi kawai yana kallon fuskarta, reaction din da ta nuna saman fuskarta ya isa ya gamsar dashi cewa bata dauki kanta a tana aikata wani abu na ba dai dai ba,an dade hakan tana faruwa a tsakaninsu "Idan aiki ya hanaki gyara muhallin mijinki dana yaranki.....shi kuma kitchen da kika tara kwanukan wanke wanke fa?, harda na tuwon jiya?" "Yau ai fita nayi,kuma ka sani dear,ban zauna gaba daya a gidan ba,amma gobe in sha Allah da aikinsu zan tashi,idan na gyara gobe zaka ga kamar ba'ayi ba,ba shikenan ba?" A hankali ya lumshe idanuwansa gaba daya yana kiran sunan Allah,mata nawa ne keda nauyin da yafi nata amma zaka samesu su da gidansu da iyalinsu tsaf?,wannan muguwar qazantar baisan ta yaya zai raba hafsat din da ita ba,tafi komai ci masa tuwo a qwarya,ya yiwa qazanta wani mugu tsana da har baisan iyakarsa ba,abinda hafsat din har kwanan gobe ta kasa ganowa,mai aiki dai mai aiki dai.....shikam ba sakaran namiji bane da zai daukoma hafsat mai aiki,ya tabbatar daga qarshe ita zata koma yin komai.na gidan,qarshe harda abincinsa da zaya ci. Miqewa kawai yayi,ya zura hannayensa a aljihunsa "Duk abinda ya kamata nayi miki na miki shi,ya kamata ki canza for now.....yaranki suna girma,zasu kuma dauki jalar kowacce dabi'a daga wajenki,dama sau daya tak take zuwa ma mutum a rayuwa" yayi maganar yana daga yatsansa guda daya,sanann ya juya yana barin dakin. Gabanta ya fadi,binsa tayi da kallo har ya fice,to me yake nufi?,abbas din yana da wuyar fahimta wani lokacin,ta janye idanunta daga kallon qofar da tuni ya jima da wucewa,ta dawo da dubanta cikin dakin,komai yayi fea gwanin sha'awa,ta tabbatar koda ita tayi wannan gyaran bazaiyi kyau haka ba,to itadai bataga laifi ba,idan ma yayin ba duka yaransu bane shi da ita?. Taso sharewa itama,amma sai zuciyarta ta gaza nutsuwa da hakan,wannan dalilin yasa ta bashi kusan awa guda,sannan ta tattara kayan abincin tana ta mita a ranta na wahalar da ya bata na diban abincin tayi sashensa. Da sallama ta tura qofar bedroom din nasa,sassanyan qamshinsa ya fara mata maraba,babu wadataccen haske a dakin sosai,yana daga gefe saman dan table din da yake dora system dinsa yayi wasu ayyuka da suka shafeshi yana duba wasu takardu. Kallo daya ya mata ya maida kansa ga takardunsa,kallon da ya bata mata rai sosai taji kamar ta koma ita da abincinta,amma ta hadiye ta danne,tana da burika da yawa da takeso ta cimma,kuma anty ummee ta tabbatar mata sai ta iya mallakar kanta da kuma fushinta. Wani table qarami na glass ta jawo ta aza kayan a kai,tana shirin zama tace masa "Ga abincinka nan" "Am okay,ki kwashesu" ranta tadan bata,ta zumbura baki,kamar zatayi magana sai kuma tayi shuru,taci gaba da kallonsa,yayin da shi kuma ya aza dukka hankalinsa akan takardar dake dauke da wani zane mai kama da map,ya sani ba zata iya bashi haquri ba,abune mai wahala kaji kalmar haquri daga bakinta. Sai da ya gama abinda yakeyi ya ninke takardar sannan ya miqe "Jibi zamu wuce kaduna in sha Allah" ya fadi mata don ya fita hakkinta,gabanta yadan fadi "naji kace zaku wuce,kai da wa?" "Widad" ranar farko da ya fara ambatar sunanta,idanu ta qanqance cikin mamaki da ba zata tace "Na dauka a nan zaka barta ko" "Saboda ke ba zakije ba,kowa ma haka ne?" Wani tashin hankali ne taji ya ziyarceta,me abbas yake nufi?,ita zai barta a nan,ya tasa qanqanuwar yarinya a gaba su tafi garin da yake aiki?,ita tana nan tana me?. Sai da tayi yaqi da zuciyarta sannan ta hadiye maganganun da su taji sunfi dacewa ta gaya masa "Amma idan kun tafin me zata tsinana maka?,ka barta kawai a nan ta saba da dangi mu tafi tare" kai ya girgiza yana nufar wardrobe dinsa ya budeta sannan ya amsa mata "Ai bana magana biyu,kinfi kowa sanin hakan,zancan tafiya kaduna mun rufe wannan babin dake har abada,abinda yasa na gaya miki yanzun ma don na fita hakkinki,duk weekends zan dinga shigowa in sha Allah" wani abu ya taso ya tsaye mata a wuya,wannan karon taji ba zata iya shuru ba,ta yaya zai sanya yarinya qarama a gaba su tafi har wani gari,ita din tana jingine a gefe,sai qarshen sati sannan yazo mata?,me ma tayi kenan?,abinda take gudun afkuwarsa tabbas zai afku "Gaskiya ni ban yarda ba,saboda nice babba ni ya kamata ace na bika,ko ka bani zabi....." "Wanne zabi zan baki?,ki manta tun kafin wanzuwarta kika yiwa kanki zabi?,hafsat kinga..... please bana son ciwon kai,zancan ya isheni haka.....ina underwears dina?" Ya jefa mata tambayar yana ritsata da ido "Ban wanke ba" ta amsa masa tana miqewa cikin hucin bacin rai "Good" yace da ita yana maida murfin wardrobe din ya rufe zuciyarsa na masa zafi,duk sanda yake da buqatar neat underwears saidai ya zauna ya wanke abinsa da kansa,ko kuma ya diba yakai mata,ya kuma jaddada mata amfani zaiyi dasu,wataran ta diba wasu daga ciki ta wanke masa,wataran kuma ta wanke duka idan taso. "Abban mimi...." Ta kirayi sunansa da kaushi, ganin bai qara bi ta kanta ba,ya nufi ma qofar toilet dinsa "Duk haquri da kuma kawaicin da nake maka hakan bai hanaka gaza yimin adalci ba ko?,to wallahi bazan yarda ina zaune a tauyemin hakkina ba" zuba mata idanu yayi sosai fiye da dazu yana kallon zallar ainihin rashin kunya daga wajen hafsat din,eh rashin kunya mana,banda haka ta manta abinda tayi masa "Tunda kika zabi zama a bauchi baki isa ki bini ko ina ba,kince na nema mai zama dani a kaduna kuma na samu fine....na dauka hankali kikayi kika fara gyaro kura kurenki,ashe ba haka bane,to a wannan karon ina mai gaya miki da kakkausar murya,kibi a hankali,don bazanci gaba da lamuntar halayenki ba,if not kuma.....mu zuba dani dake" daga haka yayi gaba ya bude qofar toilet din ya shige abinsa. Wasu qwalla masu zafi ne suka biyo kuncinta "Wallahi zankai inda za'a qwatar min hakkina,nima na gaji" ta fadi tana juyawa da gudu gudu ta fice daga dakin. Sanda ta gifta sassan widad dake kulle sai taji kamar ta koma ta shiga ta shaqeta ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma wata zuciyar ta hanata,ta wuce da sauri sauri zuwa sashenta tana kuka sosai. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 43 Gefan gadonta ta zauna hannuwanta rufe da fuskarta tana kuka sosai,me yasa abbas bazai fuskanceta su zauna lafiya ba?,yasha gaya mata zai bata mamaki,bata taba zaton irin wannan mamakin zai bata ba,ba ruwansa da harkar mata,kamar ma baida damuwa dasu,wannan yasa ta saki jikin cewa duk wani mataki da zai dauka a kanta bazai wuce ya qaurace mata ba,ita kuma bata da wannan damuwar,bata da yawan buqata,tasa buqatar ma damunta takeyi. Wayarta ta jawo dake gefan gadon ta soma laluba number kyawunta zatayi abinda ta saba wato kai qara,saidai tana kallon agogo taga dare yayi,wata zuciyar na ingizata ta kirashi,wata zuciyar na cewa tayi haquri ta barwa safiya,saita aje wayar,amma kuma yadda zuciyarta ta cika ta tumbatsa da bacin rai da kuma fushi,sai taji ba zata iya kwana ita daya da wannan baqincikin a cikin ranta ba,don haka ta sake daukar wayar ta kira number anty ummee. Cikin sa'a ta shiga,tana shiga din kuma ta daga "Ke lafiyarki a wannan tsohon daren?" Ta jefa mata tambayar jin ta fashe mata da kuka "Anty kaduna zai dauketa jibi su tafi" "Ita wa?,au amaryar taki?" Kalmar tayi mata ciwo,amma saita gyada kai kamar tana wajen "To sai kuma me ya faru?" "Na gaya masa ni.ban yarda ba,shine yake wani gayamin wai aini na zabi haka, mukayi fada dai dashi na baro masa dakin" wani tsaki anty ummee taja "Dadina dake wallahi baki da qwaqwalwa kwata kwata wani zubun hafsatu,ke da zaki nuna murna,kice hakan da yayi shine dai dai,zasufi sabawa da juna?" Ido hafsat ta zaro,kukanta ya tsaya cak "Anty?,suje su kebe su biyu wani abun ya faru kenan fa?,kaduna fa nake gaya miki,gidan da daga shi sai ita" "To ubanme ma zakije kiyi a garin da baki da ko kashi?,kibar kowa naki asalinki da tushenki a nan,suje sai sun dawo,sannan ma kuma sai akace miki haka zaki barta idan sun tashi tafiyar?,tsaya kiji,bude kunnenki da kyau" tarawa anty ummee nutsuwarta tayi,duk da tanajin babu wata mafita data wuce tayi masa bore,ko ya tafi da ita ko ya aje yarinyar a gida,saidai cikin minti biyar da fara sauraran anty ummee fuskarta ta washe da farinciki. **********Tun daren jiya bai kwanta ba sai daya tabbatar ya hada duk kayan da zaiyi tafiyar dasu ranar asabar din,idan da sabo kusan ya zame masa jiki,a shekarun da sukayi da hafsat zai iya irga sau nawa ta taba hada masa kaya wai don zaiyi tafiya ko zai koma bakin aiki. Bai kwanta ba sai kusan biyu na dare,a nan ma tunani ya hanashi sakat,yayita juyi from side to side,yanata bitar halayen hafsat,ya yarda matar aure ta qwarai dace ne,bai taba kawowa hafsat din zata sauya haka ba,bai taba kawowa cewa haka halaye da dabi'unta suke a zahiri ba,bai samu bacci ba sai wajen uku da rabi na dare,asuba nayi yayi alwala ya wuce masallaci. Bai shigo gidan ba sai wajen qarfe tara na safe,ya tsaya taron magidanta da akeyi a unguwar duk qarshen wata,kafin sannan hafsat takai ta kawo a sassansa ya kusa sau uku,so take ta aiwatar da shirinta tun da wurwuri,plan din anty ummee yafi kwanta mata fiye da nata plan din,saboda idan tanason barin garinta to tana qaunar mutuwarta. Sunyi sabani,tana komawa sassanta yana shigowa gidan,kamar ko yaushe a matsayin widad na baquwa sai ya fara da sashenta. Dai dai lokacin suna bedroom din widad din,latifa ta gama musu breakfast,harma sunci,don basa iya cin abincin hafsa,wanna yasa ma basa jiranta,itama kuma ana kwanaki biyar ta daina kawowa,saidai ta aiko a kirata tazo suyi dinner,sai akaci sa'a widad din mai wahalar sabo ce bata zuwa. Sabbin kaya latifa ke ware mata,saboda ta soma shirin komawa kano,amma dai bata bari widad din ta sani ba,don kada ta birkice mata "Wadan nan kayan dasu zakici gaba da kwalliyar,kinji dai abinda anty deena ta gaya miki?" Kai ta gyada "Bakiga kullum sai nayi abinda tace din ba" "Eh amma har yanzu baki qara zuwa wajen uncle din naki ba,kuma na gaya miki a can ake kwana" ido ta fiddo,waisu basa jin kunya suke mata zancan ta kwana da namiji?,bayan ummu ta gaya mata ko hannunta aka riqe ciki zatayi kuma mutuwa zatayi?,kafin tace komai anyi knocking qofar,latifan tasan ba wanda zai.shigo kansa tsaye saimai gidan,don haka ta zube kayan hannunta tana yiwa widad nuni da.hannu akan ta bude qofar. Itakam bata gane komai ba,ta sauko daga saman gadon,ta isa bakin qofar ya buda a hankali manyan idanuwansa suka fada cikin manyan fararen nata idanun,ta saki qofar cikin rashin sabo da d'ari d'ari taja baya tana cewa "Ina kwana?" "Lafiya qalau" ya amsa mata yana duban kayan jikinta,kayan bacci ne riga da wando masu taushi da kauri,wandon iyakarsa qauri,rigar ce ma mai dogon hannu,ya kauda ganinsa yana sanyo kansa cikin dakin,sai tahau raba idanu tana duban latifa dake jiran ya gama shigowa su gaisa ta basu waje,gabanta tana dan faduwa. Gaidashi tayi ya amsa,sai ta juya ta nufi qofa,widad din batayi qasa a gwiwa ba tabi bayanta zata fice itama cikin jin tsoro "Zo nan" ya kirata a hankali,saita waiwayo fuskarta a narke kamar zata saki kuka,ya kalli siraran labbanta jajaye data tabesu "Bari na dauko hijabi na" ta sake fada tana sanya jelar dankwalinta tana faman boyon na shanunta da suka fara bayyana kansu ta cikin rigar jikinta. Dariya taso bashi acan qasan zuciyarsa,ya fuskanci me take boyewa,ko me zasu sakashi ji wadannan qananun abubuwan oho,ya fada a ransa,saiya sanya hannu ya jawo hijabin da ya gani a gefansa ya miqa mata,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,tana ta faman cukuikuye gaban rigarta ta qaraso ta sanya hannu ta karba hijabin ta zura,sannan ya nuna mata waje ta zauna. "Kice ta shirya miki kayanki,gobe in sha Allah zamu tafi kaduna" da farko daya fara zancan hada kaya harta fara murna,ta dauka zaya ce gida zasu,amma sai taji yana kiran wata kaduna,ta fiddo manyan idanunta waje da suka fara hada hawaye "Kaduna?....."sai ta kasa qarasa maganar,kai ya jinjina mata yana nazartarta,ta fiya tsoro, tsoronta yayi yawa,kuma ya lura maza kawai takewa haka "Eh,gobe da safe" shuru tayi tayi qas da kanta qwalla na zuba,bai lura kuka take ba,yamiqe yana cewa "Bakwa buqatar komai?" Saita jinjina masa kai kawai,ya taka a hankali ya fice,cikin ransa yana ayyana yadda zasuyi rayuwa a kaduna da ita ahaka a yadda take,itama din bata wuce raino ba. A haka latifa tazo ta tarar da ita,ta sata a gaba da tambaya,sai ta gaya mata,sannan ta dora da cewa "Ni gida zan tafi ba wani kaduna,wajen ummu zamu tafi" zama sosai latifa tayi tana kwantanta mata lamarin aure,ta kuma gaya mata gaskiyar ta taho kenan,ita da gida saidai ziyara,saita rude mata,ta dinga rusa mata kuka tana lallashinta,daga qarshe dai sai data kai ga kiran alhj mahmud. Cikin hikima irin ta d'a da mahaifi ya dinga bata baki,tare damata alqawurin zaizo can din,kuma ta fadi kome takeso zaisa a kawo mata "Ni banason komai,kawai komai a gidan,kullum shima sai ya tambayeni idan inason wani abu" wannan magana tata ta sake kwantar masa da hankali,ta kuma qarawa abbas martaba da bayyana asalin nagartarsa,abban nata bai barta ba har sai da ta sake sosai sannan sukayi sallama. Tsaf latifa ta hada mata kayan da dukka tasan ya kamata ta tafi dasu,itama ta faka nata kayan a boye. Bayan fitarsa sassan hafsat din ya wuce don yaga yaransa,a falon yayi sallama,sunata wasa da kayan bacci a jikinsu,babu alamun an musu brush da alwala ba bare wanka,fuskarsu duk jirwayen bacci da sauransu. Tana tsaye a dining area tana gyara kayan breakfast din data hada tun safe,bayan ta hana idanunta barci. Satar kallonsa takeyi,ya mata wani irin kwarjini da kyau,wani irin annuri ke fita daga fuskarsa,abinda ke qara mata soyayyarsa kenan da kuma kishinsa,kome ya sanyawa jikinsa karbarsa yakeyi. Cikin nutsuwar nan tasa ya duqa yana tarbar yaran nasa,suka shige jikinsa kowa a cikinsu yana son masa hira shi kuma yana biye musu,ta gaji da tsaiwa ganin baiko waiwayota ba,ta soma baro wajen zuwa inda suke tsugunne "Ina kwana" ta fada ranta yana suya,a dakeka a hanaka kuka?,wanne irin al'amari ne wannann "Lafiya"ya amsa a taqaice,ranta ya sake sosuwa,halin nasa ya motsa kenan,shi duk abinda ya faru kenan bai ga nasa laifin ba sai nata?. "Ga abincinka nan an gama" "Am okay alhamdulillah" ya bata amsa yana miqewa dauke da nawwara,sai itama ta miqe,zuciyarta na tafasa amma tana yunqurin danneta "Amma kada ka yimin haka,tun dazu na tashi saboda kai fa?" "Nace na qoshi" ya amsa mata bayan ya zube mata manyan idanunsa,abinda ya sage mata gwiwa ta koma baya ta jingina da kujera "Abinda ya faru jiya ne kenan har yanxu bai wuce ba?" Waiwayawa yayi yana sake kallonta,shi take ma tambaya kenan?,bai amsa mata ba sai ta baiwa kanta amsa "Kayi haquri,inasonka dole nayi kishinka,kishin ne ya sanya idanuna suka rufe,amma ya riga ya wuce,Allah ya tsare hanya" ta qarashe maganar tana jin kamar ta saki kururuwa,ita kadai tasan me takeji a zuciyarta,wani irin kisan mummuqe ne takewa zuciyarta,wadda bata saba da boye boye irin haka ba,komai nata gaba gadi take yinsa. Lokaci daya xuciyarsa yaji zuciyarsa ta karye,ta kuma sassauto,amma baiji gamsuwa akan lamarin hafsat din ba,ya santa,kamar hawainiya take akan wasu al'amuran,bashi da tabbacin ta fada din da gasken gaske "Kaji?,nace kayi haquri" ta kuma fada,a wannan karon duk yadda taso tare qwallar baqincikin dake idanunta sai da suka sulmiyo,abinda ya qarasa karyashi kenan,son sam baya qaunar kuka,sai ya sauke nawwara yacewa mimi taja nawwaran suje dakinsu su dauko brush dinsu. A tausashe ya sanya hannunsa ya jawota zuwa jikinsa,tun baice komai ba ta saki kuka mai nauyi,wanda ke dauke da saqonni da yawa da zuciyarta keson fesarwa,baki da ruhi sun gaza amintuwa da hakan saboda burin cikar wani buri. Baice komai ba sai hannu da ya sanya a bayanta yana dan bubbuga wa kadan kadan,har zuwa wani lokaci,ya dagata yana duban fuskarta "Is okay,wipe your tears" ya fada bayan ya miqa hannu ya yago mata tissue din dake kusa dashi,bata musa ba ta karba ta fara goge fuskarta ta,saidai zuciyarta har yanzu tana jinta kamar an fusgeta daga qirjinta an jefa gidan bread. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 44 "Ma sha Allah" shine abinda latifa ta fada bayan ta gama feshe widad da turaruka masu taushin qamshi "Duba ki gani" ta fada tana matsar da ita gaban madubi,murmushi ne ya subucewa widad bayan ta kalli kanta da kanta ta madubin,tayi kyau irin yadda takeso,yau latifan tana da nutsuwar data mata ado haka "Gaskiya nayi kyau" ta fada tana dariya hadi da kallon latifa,sai dariya ta kama latifan "To sai a bani tukuici ai" "Duk kudin da uncle yake ajjiyewa ki dauka" ta fada tana murmushi,girgiza kai latifa tayi "A'ah,ba ruwana da kudin miji da mata,tashi kije qila sun fito,sai kun dawo" tana murmushin maganar da latifa ta fada da kuma farincikin yadda tayi kyau a saman fuskarta ta fita zuwa farfajiyar gidan. Dai dai lokacin da gafsat ke tsaye gaban motar abbas,sanye da baqar doguwar riga mai sulbi da jan mayafi babba data yafawa kanta,fuskarta kamar ko yaushe,babu alamun kwalliya ko d'is,sai maiqo maiqo da takeyi,don tana tsaka da barci mimi ta tasheta akan ta fito inji abbansu zasu wuce shopping. Sam bata ankara da widad ba sai data kusa gab dasu, qamshin ta dake kadawa cikin iska shine abu na farko daya fara jan hankalinta ta gane akwai baqo a wajen,sosai ta zuba mata idanu,sai taji gabanta ya fadi,wanne irin kyau yarinyar nan ke dashi?,ta tambayi kanta da kanta,take taji gaba daya ta muzanta,duk da cewa dama ba wani ado tayin ba,rigar da ita ta kwanta baccin,ganin bata jima da sanyata ba kuma a motar gida zasu fita su dawo yasa batayi wani sha'awar canzawa ba. Kafin ta dawo daga duniyar tunanin data lula widad ta iso wajen,sunata kakaci ita dasu mimi suna qyalqyala dariya abinsu "Ina yini momy" ta fada fararen jerarrun haqoranta suna bayyana,sautin siririyar muryarta ta karade kunnenta,ta kuma dawo da ita hayyacinta "Lafiya.....lafiya lau" ta fadi tana bude bayan motar da sauri "Ku shiga ku zauna,mimi ku shiga" ta fada tana duban idanun widad,kama hannunsu nawwaran tayi,ta fara saka mimi sannan itama ta shiga tana ci gaba da jansu da wasa. Wata ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,har yanxu qirjinta bugawa yakeyi,kyawunta yana damunta,yana kuma son ya zame mata barazana,tafi yarda dari bisa dari kyawunta na daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin abbas dinta,ta yaya zata gusar da wannan abu dake shirin zame mata barazana?. "muje ko" ta tsinci muryarsa dab da ita,sai ta dan bishi da kallo har sai daya kusa shigewa motar,ta taka jiki a mace ta isa gaban motar ta buda daya side din ta shiga. Wani baqon qamshi ne ya ziyarci hancinsa,ya soma shirin tada motar yana zuqar qamshin,sai daya tada ita sannan ya waiwaya ya kalli hafsat "Yaushe kika sayi wannan turaren?" Kishi ya kamata,bataso tace ba ita bace ya farga da yarinyar,idan kuma tace itace tayi qarya,duk da haka ta gwammace wa qaryar,sai tadan murmusa "Eh,cikin bikin nan na siya" "Yayi dadi sosai" ya sake fada yana dan waiwaya sashen da take,duk da baiji yana busowa daga nan ba,murmushin yaqe ta saki tana basarwa,zuciyarta na bugawa,tana addu'ar komai ya tafi dai dai. Sun dauki hanyan babban super market din suke siyayya lokaci bayan lokaci,motar shuru,bakajin komai sai muryoyinsu widad mimi da nawwara,a hankali muryarta ke shiga kunnensa,itama ta saje dasu abinta,zuciyarsa cike fal da tunanin ita din fa wai matarsa ce,sai kawai ya gyada kai qaramin murmushi yana qwace masa,saboda shi kansa yasan akwai jagwal,baisan kuma ya zata kasance masa ba. Murmushin da yaja hankalin hafsa,ta dan juya kadan tana kallonsa,sai shima ya kalleta ya basar yaci gaba da tuqinsa,ita sam irin hirar nan ta debe kewa don kana driving ma bata iyata ba,sai suyi tafiyar awanni amma saidai kowa yaci kansa,imma ya kunna radio imma ya zubawa hanya idanu kwanyarsa ta cika da tunane tunane har su iso inda zasu. Su suka fara yin gaba zuwa cikin super market din,cewa widad tayi ta tsaya dasu mimi zata dauko mata duk abinda ya dace,bata wani damu ba ta jasu gefe suka zauna,haka tayita zagaye,tana hada duk abinda ranta ya mata a kwandon data dauka,ba wani abun azo a gani take zaba ba,don ba iya zaben tayi ba,majority tare suke shiga da abbas din,shike zabar mata abinda yaga ya dace da ita,takanyi mita a fili da zuci "Wannan asarar kudine kawai,ni da kudin ka bani da yafi" dubanta kawai yakeyi "Abinda zaki sakamin din ko kimin amfani dashi na kalla naji dadinne asarar kudi?" Takan basar kawai,itama batasan tana wannan subutar bakin ba a wani lokacin. Sai data gama zane zabenta sannan suka hadu a wajen biyan kudi,yaga abinda ta diba,takaici ya hanashi cewa komai,ya biya kudin kawai suka fito,baisan yaushe zata koyi siyan abubuwa masu amfani ba,sa'annan kamar ita zata biya kudin,ta saka tsaiwa ta dauki kayan daya dace. Kai tsaye gidan hajiya ya wuce dasu,tunda hafsat taga titin da yahau tasan can zasuje,sai ta bata rai,amma dai batace komai ba,don batasan bata wasan nata. Yana tsaiwa a qofar gidan widad tayi zaraf ita dasu mimi suka fice,yadan bisu da kallo kafin ya dawo da dubansa kanta,itama shi take kallo,ranta ya sake baci,sai take ganin kamar widad din yake kalla "Amma zaka jiramu mu gama ne saimu wuce gida ko?,don inason nadan kwanta,bana jin dadin jikina yau" dubanta yayi kawai,tunda suka fito din batace masa bata jin dadi ba saida sukazo nan,saiya soma zare seat belt dinsa,har ya bude murfin motar sai kuma yace da ita ba tare daya waiwayo ba "You know what?.....idan zakaso saniya ka sota har qahonta,domin kuwa no matter what ba yadda za'a yi su rabu,mahaifiyata itace duniyata,silar nasarar rayuwata" a birkice ta juyo tana kallonsa,bataso ya fahimci emotion dinta ba,ta buda baki zata jefa masa tambayar rainin wayon ya buda motar ya fice ya barta a ciki. Katsam hajiya taga shigowarsu,farinciki ya cikata,murmushi ya wadaci fuskarta,tana marabtarsu tana duban widad,tare dason gano wani canji tattare da ita. Ta sake haske dai ta kuma sake fresh,amma girman da taso taga tadan qara babu shi,alamu dake nuna babu komai kenan daya wanzu tsakaninsu. Tana tsaka da wannan tunanin yayi sallama da muryarsa mai zurfi ya shigo,idanunsa suka sauka a kanta sanda take zaune gaban hajiyan hankalinta kwance kamar tana gidansu,fuskarta ta wadata da murmushin da zai iya cewa tsahon satin biyun da tayi gidansa bai taba ganinsa ba,ba wani alamun surukuta a tare da ita,yo ina ta gama saninta ma. "Maraba lale,saiga baqin yamma" hajiya ta fada sanda yake duqawa gabanta daura da widad din yana gaida hajiyan,dai dai sanda hafsa ta sanyo kai cikin falon,sai idanunta suka qara kusancin dake tsakanin widad din da abbas,bugun zuciyarta ya dadu,wani abu ya kama wuyanta,tayi ta maza ta kauda kanta tana zuqar numfashin wahala,sannan ta qaraso falon tana sakin sallama da shaqaqqiyar muryarta. "Ah,kacemin tare kuka?" Ta fada har cikin ranta tana jin dadin ganinsu gaba daya "Eh munje sunyi siyayya ne,saboda gobe in sha Allah zamu wuce" "To yayi kyau,ma sha Allah" hakanan ta duqa itama ta gaidata don ganin idanun abbas din,ba komai a fuska ko zuciyar dattijuwar ta amsa tana tambayar ta yara,bayan lafiya lau data ce bata sake cewa komai ba,taja gefe daya ta zauna ta tsuke bakinta,amma idanunta yana kan komai dake wakana cikin falon. Yadda taga hajiyan ta maida hankalinta gasu widad din ya qona ran hafsat sosai,ta yita mutsu mutsu cikin kujera cikin bacin rai,tana jin kamar ta tashi ta fice tabar musu falon,sauqinta daya harda yaranta take ja da wasa,don su mimi suna kan cinyarta suna ta harkokinsu,amma ita wannan sam baiyi mata ba,daga qarshe ta buge ta amsa waya ta fice harabar gidan. Huci ta dinga yi tana fidda iska mai zafi daga bakinta,zuciyarta kamar zata fito,bata iya jurewa ire iren wadan nan abubuwan,akan abbas zuciyarta na gaya mata komai zata iya yi. Ana idar da sallar magariba suka baro gidan,a hanyar komawa ma tamkar kurame,shi ya riga ya saba da irin wannan zaman,uwa uba kuma dama shi din ba mutum bane mai son magana,yayin da hafsat din keta cin daci,gaba daya zuciyarta babu dadi. Qaramar leda ta dauka ta debi wasu abubuwa d'ai d'aiku ta bawa widad,bata damu ba don ba damuwarta din bane,tasa hannu biyu ta karba tana godiya,shi kuwa baisan me ya faru ba,an masa total dai ya biya kudi,yana tsammanin kowa ya dauki abinda ransa keso. ***********Kuka take sosai tsahon awa guda cur da sukayi suna tafiya bisa hanyar bauchi zuwa kaduna,duk yadda zai mata tayi shuru yayin amma kamar ma bata san yana magana ba,har ransa ya baci ya shareta taci gaba da kukanta. Tun sanda motar samuel ta daga da latifa kano,su kuma tasu ta dauki hanyar kaduna ta birkice da kuka,bata taba tsammanin latifan tafiyarta daban da tasu ba. Sai data kusa rufe awa biyu sannan kukan ya fara ja baya,jikinta ya fara saki,sanyin yammaci gajiya da kukan data sha suka saukar mata ds bacci,a hankali ta langabe kanta gefe tana sauke ajiyar zuciya mai nauyin,alamun taci kuka ta godewa Allah. Dubansa yakai gareta kadan kafin ya dauke kansa yaci gaba da tuqinsa,cikin ransa yana sauke ajiyar zuciya,wannan aure ne ko rigima sabuwa ta sameshi?,ya tambayi kansa. Karo na biyu ya sake maida dubansa gareta,sai ya rage speed na motarsa ya gangara gefan titi ya tsaidata,ya miqa hannunsa a hankali ya sauke mata kujerar yadda zata ji dadin kwanciyar,ya koma seat dinsa ya zauna dai dai,sannan ya sake kunna motar suka ci gaba da tafiya. Yammaci lis suka shiga garin kaduna,kofar wani babban gida ya tsaya,ya danna hon,babu jimawa mai gadin ya iso ya bude gate din,fuskarsa cike fal da murmushi,da alama farincikin ganin dawowar abbas dinne,aiko yana sako hancin motar zuwa parking lot na gidan ya biyo bayan motar da sassarfa yana fadin "Barka da zuwa oga" qaramin murmushi ya saki,yana hangoshi ta madubin,mutum badai barkwanci,ya tsaida motar dai dai sanda ya qaraso gefan window dinsa. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 45 "Barka da dawowa oga,tun wancan satin muketa zuba idanun dawowar ka,har mai gida yana tambaya" miskilin murmushi ya fita a fuskarsa "Naso dawowa,to amma ban gama shirye shirye bane,mun sameku lafiya?" "Lafiya sumul oga,ya hanya?,ashe an samu qaruwa?,to Allah ya sanya alkhairi,yasa abokiyar arziqi ce" bala mai gadi ya fada yana murmushi "Ameen"ya amsa masa a taqaice,sai ya zagaya da sauri ya soma budewa widad qofa yana fadin "Madam barka da rana" nauyi ya saukarwa abbas,da alama bala baisan qaramar yarinya bace yake gaidata,duk da ya bude motar bai damu ba yaga ta sake maimaita gaisuwarsa,sakato widad tayi cikin rashin sabo,wai yau ita ake gaisarwa?,ita da take gaida jama'a? "Ana magana" abbas ya fada yana cire belt seat dinsa,maimakon ta amsa saita maida masa gaisuwar,saboda rashin ganin dacewar ta amsa din,amsawa yayi ya kuma bisu da addu'ar zama lafiya da zuri'a ta gari,ita dai tana jinsa ba tare data amsa ba. Muqulli abbas ya miqa masa sannan yace "A shigo min da kayan qofar parlor bala" "An gama oga" ya fadi yana karba da hannu biyu "Muje" ya sake fadi yana duban inda widad taja ta tsaya,tana kuma bin gidan da kallon baqunta. Wata siririyar hanya suka bi,sai gasu qifar wata qaramar baranda mai kyau dake dauke da wata qofa mai dam fadi,yasa key ya bude qofar ya shige,ta bishi a baya,kamar za'a ce kettt ta zura da gudu. Madaidaicin falo ne amma ya qawatu matuqa,akwai qofofi guda uku a cikinsa na bedrooms guda biyu,daya qofar kuma ta kitchen ce sai dining area,sai qaramar qofar da zata fiddaka bayan gidan. Qarasawa yayi gaban daya daga cikin dakunan ya buda daya "Ki shiga nan kiyi wanka ki huta" bata iya amsa masa ba,sai gaba datayi zuwa qofar dakin tana raba idanu,turqashi,yau fa ake yinta,a wanann dakin zata zauna ta rayu ita kadai?,abinda yake nufi kenan?,ga gidan ta fahimci babu wadatar hasken rana,duk da cewa yammaci ne amma alamu sun nuna hakan,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta sanya kanta cikin dakin,dab da zata shige yace "Ki rubuta duk abinda kikeso,zan aiko a karba sai a kawo miki" sai a sannan ta samu daga masa kai,qwalla tana cika mata idanu,har yayi gaba ya dakata,ya juyo a nutse ya sanya idanunsa cikin nata "Me ya faru?"ya tambayeta yana kallonta,cikin jajircewa tayi qoqarin maida qwallar data cika mata idanu "Tsoro nakeji"ta amsa masa kai tsaye "Tsoron me?"ya tambayeta cikin mamaki, maimakon ta amsa masa saita maida dubanta ga dakin da ko qwan wutarsa ba'a kunna ba,saboda haka ya danyi duhu,gyara tsaiwarsa yayi,tana jin tsoro,to amma kuma baisan me zaiyi mata ba,hakan yana nufin saidai suyi sharing daki ita dashi?,kai ya girgiza kadan "NO" ya amsawa kansa,sai yanzu ya tuna da dan banzan tsoron da take dashi,ya manta the first time he saw her...ihun kyankyaso taketa yi,harda cire dankwali,takawa yayi ya matsa zuwa inda take tsaye,ganin ya nufota ta tuno da wani abu,tayi hanzarin jaa da baya a tsorace,har abun yaja hankalinsa,yadan dubeta kadan sannan ya dauke kansa,wannan bayan tsoron su kyankyaso hala harda tsoron mutane ma tanayi?. Qwan wutar dakin ya kunna,haske ua gaurayeshi,abinda ya rage mata tsoron dakin kenan,ya fita a dakin ya bata waje yana cewa "Sai anzo an share dakin,akwai qura" saboda sanda hafsata ta tashi tafiyarta a birkice ta barshi,shi kuma takaici yasa ko takan dakin bai sake bi ba tunda ta fita daga ciki. Sai data tabbatar yabar wajen sanann ta saka kai cikin dakin,ta tsaya tana duban komai,a hautsine yake,ji take yi ba zata iya zama ba,don kafin tafiyar latifa ta koya mata yadda ake gyaran bedroom xuwa falo,kuma babu laifi hannunta yadan fada,ta janyo jakarta zuwa tsakiyar dakin tayi mata waje. Zama tayi tana qarewa dakin kallo,idanunta fal hawaye,ta rasa qwarin gwiwar gyaran dakinma gaba daya,tana jin kamar an dauketa daga duniyar ta an kawota wata duniya ta daban. Bata tashi ba sai da aka kira magarib,ta miqe tana kame jikinta waje daya,saboda dakin ya mata datti,kasancewar bata taso ta saba zama cikin dauda haka ba,koda yaushe zaka samu sassan ummu qal qal,ko tsinke bata bari ya sauka,shi yasa basa shiri da jikokinta,don da zarar kazo ka zauna ta fuskanci kai dan bata guri ne yanzu zata koraka,widad dince kawai keyin yadda takeso a sassan ba tare data hanata ko tace mata komai ba. Toilet din ta shiga tayi alwala,tazo ta shimfida dankwalinta ba tare date nema abun sallah ba ta tada sallah,ko da ta idar tana zaune a wajen,har zuwa sanda aka turo qofar dakin,ta waiwayo a tsorace,saita zuba masa ido sanda yake shigowar,tsoro na kamata,a yanzun ya canza shiga,shirt da trouser ne a jikinsa da suka dace da jikinsa,suka fidda qirar jikinsa dake tafe da tsaho da murjewad jikin kadan,don ba zaka kirata qiba ba. Ido ta lumshe,tana jin dadin qamshin turarensa har qololuwar ranta "Kinyi sallah ne?" Kai ta gyada masa ba tare data iya kallonsa ba,sai ya dauke idanunsa daga kanta ya kalli agogon hannunsa "Zan dan fita....." Tun kafin yakai qarshe ta daga manyan idanunta ta watsa a kansa,haka kawai yaji nashi idanun suna lanqwashewa zuwa lumshewa,kafin ya budesu ya azasu a kanta,har zuwa sannan manyan fararen idanunta suna kanshi,ta yaya zai fita ya barta a wannan gidan ita kadai?,duk da bata da tabbacin ita daya ce cikin gidan gaba daya,amma itakam ko dakin ummu bata yarda ta zauna ita kadai,inaga gidan gaba daya "Bazan dade ba zan dawo,za'a knocking za'a kawo abinci,saiki bude ki karba,idan kuma wani abu ya taso ki kirani a waya" wani mugun tsoro ne ya shigeta sanda ya juya yana ficewa,kuka sosai yazo mata,ta cure waje guda tana cusa kanta tsakanin qafafunta "Wayyo ummu"ta fada muryarta can qasa wadda ke cike da kuka,sun kawota inda bata da kowa,kamar basa sonta,itakam meye tayi musu?,sai taci gaba da rera kukanta a hankali,har zuwa sanda taji kiran sallar isha'i ta miqe ta bada farali,ta sake komawa yadda take. Tana jin anata knocking kamar yadda yace amma ko yunwa zata kasheta bata jin zata iya miqewa zuwa falon har ta bude,tana jinsu har suka gama bugunsu suka tafi,saita sake sakin kuka tana takurewa waje daya. Lokaci lokaci tana duban agogo tare da fadin "Allah kasa ya kusa dawowa" saita sake maida kanta tana sharar hawaye,har kusan awanni uku babu shi babu dalilinsa. A karo na barkatai ta sake daga kanta don kallon agogo,saidai hasken farfajiyar gidan ya hasko mata mage dake tsaye jikin window din dakin nata tana kada jela,wani mugun tsoro da razani ya shigeta,take jikinta gaba daya ya fara rawa,hawayen idanunta suka ninku,ta fara karanta ayatul kursiyyu a rarrabe saboda yadda bakinta yake rawa,a duniya babu abinda ta tsana take mugun tsoro irin magen,don saboda ita kowa na gidan ya haqura da ita,sabod koda ka kawota sai ummu ta sanyaka ka maidata inda ka daukota. A hankali magen ta soma kankarar glass din jikin window din kamar me neman hanya tana kuka mieeeuuuu mieeeuu,ba abinda yaxo kwanyar widad illa ga magen har ta shigo ta fada mata a ciki,take ta saki wata qara hade da kuka. Sautin muryarta yakai kunnuwansa sanda yake tsaye yana knocking qofar falon,kusan sau biyar kenan amma baiji motsinta ba,har ya fara tunanin ko tayi barci ne?,sai kuma saqon muryarta ya riskeshi. Sosai yaji hankalinsa ya tashi,to meye ya sameta?,cikin hanzari da kuma gaggawa ya fara laluben keys din dake aljihunsa,ya fiddosu ya fara gwadaw jikin qofar cikin hanzari da zafin nama,har sannan ihunta na tashi saidai da yake harabar gidan tana da yalwa,babu lallai wanda ke can nesa kamar malam bala ya jiyota. Cikin sa'a ya samu key din,ya bude ya tura sannan ya shige da sassarfa zuwa dakin nata. Motsin bude qofar dakin ya zake dagula kissafinta,ya kuma sakata ta sake gigicewa gaba daya,a nata zaton magen ce ta bude window din "Calm down mana,ki nutsu,menene?" Ya jefa mata tambayar yana riqe da dukka kafadunta,idanunta da suka jirkice ta daga ta kalleshi,batayi wata wata ba ta shige jikinsa ta qanqamesa kamar yadda ta saba yiwa ummu,sannan ta daga yatsanta tana nuna masa window. Mutuwar zaune yayi,a yadda ta shige masa jiki gaba cikin ba zata,wani irin sanyi ya sauka a gabbansa, tashin farko kamar an zare masa laka,don matasan tudun qirjinta gaba daya sun hade da nashi qirjinsa,yana iya jinsu sosai,ya daga kansa kamar mai ciwon wuya ya waiwaya ga window din,dai dai sanda magen tayi tsalle ta sauka daga window din,take ya fahimci ainihin dalilin rudewarta,sai ya dawo da dubansa kanta yana qoqarin zareta daga jikinsa,tare da fadin "Am beside you,calm down, mage ce fa,look there,she's already gone" ya kuma fada yana qoqarin tsaida fuskarta tsakiyar tafin hannunsa tare da qoqarin lalubo qwayar idanunta don bata qwarin gwiwa. Sam taqi ganewa abinda yake fadi din,sai ya tuna abinda ya faru washegarin randa tazo gidan,don haka ya buda hannayensa ya sanyata cikin qirjinsa ya rufe,wata qatuwar ajiyar zuciya tana subuce masa. Dukka idanunta ta fidda waje kamar zasu zazzago,gabanta yayi mummunar faduwa,zai kuma?,irin ta ranar nan?,me yasa shi din dan iska ne?,take wata huduba data baro bauchi da ita ya fado mata,cikin dan qaramin qarfinta da bai taka kara ya karya ba ta saka hannayenta duka biyun tana qoqarin tureshi,ko kusa ko alama baiyi gezau ba,amma yaji abinda take shirin yi din,haka kuma yake buqata,sai yaja da baya yana kallonta. Kuka sosai ta fashe dashi,kukan takaici da baqincikin rungumeta da yayi,wannan wanne irin iskanci ne,haka kawai sai ya dinga taba ta? "Ya isa,ta tafi nace" ya fada calmly yana kallon yadda sumar kanta ta biyo ta gefan fuskarta,kamanninta suka fita sosai,fuskarta tayi jazur saboda kuka. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 46 Space ya bata,ya zauna daga nesa yana kallonta har sai data gamsu don kanta ta tsagaita kukan,don ya fuskanci kukan da take harda na sakalci ma,sanann ya miqe yana duba dakin ko zaiga abincin da yace a kawo mata amma baiga alamunsa ba,waiwayawa yayi yana dubanta "Ina abincin da nace a kawo miki?" Baki ta tabe sosai irin na yaran da suka gwanance wajen shagwaba "Naji ana knocking,inajin tsoro ne bazan iya fita ba" dan qaramin bakinta me dauke da jajayen lips yabi da kallo,wannan da alama ba abinda ta sani sai sangarta da sakalci,ya janye idanuwansa yana laluba aljihunsa ya fidda wayarsa,a nan ya samu tarin miscall na wanda ya aika din,yana kiransa kafin yace komai ya gaya masa yayita bugu ba'a bude ba "Ba matsala,am back,zaka iya kawowa" ya fada yana nufar qofar dakin da zummar ficewa,saidai tun bai sanya qafarsa a falo ba ta miqe ta rufa masa baya. Tsayawa yayi bayan ya zame wayar daga kunnensa sannan ya waiwayo yana kallonta,saita dauke kanta gefe tana turo baki gaba gami da tabeshi "Ina zaki?" "Ni binka zanyi,Allah ba zan zauna a nan ba" saiga hawaye yana biyo bayan maganarta "Saqo zan karbo" "Zan bika" ta sake fada wasu hawayen na sake zubowa "Yanzu zan dawo,just a compound din gidan nan ne" wannan karon maqale kafada tayi saboda kuka ya riga da ya subuce mata "Oh god" ya fada yana dan lumshe idanunsa hadi da budesu duka lokaci guda,kafin ya sake cewa wani abu anyi knocking,sai kawai yayi gaba,ta kuwa take masa baya yana dauke qafarsa tana saka tata. Takeaway na abincin ya karba ya maida qofar ya kulle,daya juyo sai kuma tayi tsaye tana jin banbarakwai,ya tako taja baya hadi da yin gefe ta bashi hanya,ya isa tsakiyar falon "Dauko plate a kitchen da spoon" ya fada yana ajjiye ledar,hadi da zama saman kujerar sannan ya fara qoqarin cire agogon hannunsa. Jin shuru bata amsa ba,bata kuma motsa ba ya sanyashi dago kansa,tana tsaye ta marairaice fuska kawai tana kallonsa "Bakiji bane?" Ya tambayeta da kaurin murya "Tsoro...." "Subhanallah" ya furta a hankali,sai kawai ya miqe ba tare da yace komai ba,nan ma batayi qasa a gwiwa ba ta rufa masa baya,tana tsaye ya dauko plate din,ya hado da spoons da bottle water da drink na kwali guda daya sannan suka rankayo suka fito. Wannan karon a qas ya zauna sosai,ya bude ledojin ya hada komai da komai kowanne plates d'ai d'ai ya tura mata hade da ruwan da kuma lemon,ya sanyawa nashi palate din spoon ya fara diban abincin yana ci bayan yayi bismillah,hannunsa daya riqe da wayarsa yana dannawa. Shuru tayi tana kallon plate din nata,tun asali ita din bata saba cin abinci ita kadai ba,tun tasowarta,saboda ta taso mutum ce mara son cin abinci,wannan yasa kowanne lokaci da ummu sukeci,suna ci tana hilatarta har sai taci me yawa,idan kuwa tana azumine ko kuma tana makaranta taci kafin ta dawo wanda zaiyi wuya ma ta rigata ci din,saita hada mata da wani cikinsu Aafiya,ko ta tafi sassan anty madina taci cikin jama'a,shine fa take ci da dan dama,ko zuwanta bauchi kullum da latifa sukeci,to a yanzun saita kasa tabuka komai,har yayi nisa da cin nasa abincin. Bai kula ba sai da yayi nisa sosai,ya daga idanunsa ya kalleta,itama shi take kallo,ta narke fuska kamar wadda kukan da tayi bai isheta ba tana neman qari ne "Dauki kici" ya fadi yana mata nuni da abincin da ido,saita girgiza kai "Na qoshi" mamaki ya kamashi,baici ace bata jin yunwa ba,yasan tun sanda suka fito rabonta da abinci,saiya rasa yadda zai mata taci.abincin,don daga qarshe ma baya taja ta rungume qafafunta kamar wata marainiya. Ajiyar zuciya ya sauke yana ajjiye nasa plate din,shikam ya gamu da gamonsa,da alama rainon zaiyi da gaske,suraj da suke chart dashi a lokacin ya turawa gajeran saqon tambaya _"If you want a child to eat and he refuses, what will you do for him?,ina buqatar taimakon,its urgent please"_. Sai daya tura masa sticker din dariya sannan ya amsa masa _"yar rainon taka hala?,ka lallabata,malam ka kuma koyi magana,wannan ba hafsat bace,ita din ba zata gane shuru ba,be a child like her for a while,sannan ne komai zai daidaita"_ _"thanks,i will tray_" ya amsa masa sannan ya kashe data dinsa ya ajjiye wayar "Oh God, give me courage" ya fada can qasan ransa yana kallonta "Let's share the food,come closer" ya fada yans miqa hannu yaja plate din,makarantar da tayi mai tsada ce sosai,don haka ko a iya js data tsaya tana jin turanci fes tana kuma iya mayarwa,don haka taji sarai abinda ya fada,to amma fa ita tsironsa takeji,ta sani tun a gida cin abinci da maza ba abu bane me kyau,uwa uba hudubarta tana nan a kanta fes bata bace ba,ya zataci abinci da wani?,to amma kuma yunwa takeji,idan kuma bai tayata ci din ba tabbas tana iya kwana da yunwa "Uhnnn,bismillah" ya sake fada yana juya spoon dinsa a ciki,jiki a mace,a kuma mugun darare ta matso,nesa da plate din ta zauna,saidai tana kai hannu tana diban abincin,tana yi kuma tana satar kallonsa,amma sai taga sam shi hankalinsa baya wajen,wannan yasa ta dan sake sakewa ta soma cin abincin a nutse. Duk da ya qoshi hannunsa kadai ya zame amma bai tashi daga wajen ba,har sai da yaga ta cire nata hannun,takai goran ruwan mitsitsin bakinta ta fara sha,har cikin ransa yaji ya sauke nauyi,zuciyarsa tayi wasai,sanda ya dawo ya samu bataci abincin ba ji yayi kamar yaci amanar hajiya,ya kasa sauke nauyin amanar daya karba ya kuma dauka tun ba'a kai ga kwana ba. Zaman kurame sukayi a falon,shi yana aikace aikacen sa a waya,ita kuwa tana takure gefe daya duk da tv tana aikinta,saidai ita hankalinta ya kasu kashi biyu,duk wani motsi da taji saita waiwaya da sauri taga meye,shi kuwa ya zauna ne don ya debe mata kewa ya kuma rage mata dare,duk kuwa da yanason tashi,yana nan a zaune sai kiran hafsat ya shigo wayarsa,abinda ya bashi mamaki kenan,ya kuma yi hanzarin dagawa yana tunanin ko wani abunne ya faru?,qila ita ko wani cikin yaranne babu lafiya,saboda sam ba dabi'arta bace ta kirashi don yayi tafiya,komai nisan zangon da zaiyi,koda da nufin jin yadda ya sauka,saidai idan shi din ya sauka ya kirata ya shaida mata ya sauka lafiya,ta kuma bashi yaransa suyi magana,indai kaga kiranta to wani abunne ya faru,ko kuma wata buqatar ce ta taso. A tsanake ya daga wayar yana mata sallama da lallausar muryarsa data saukar mata da wani zazzafan kishinsa,zuciyarta nata ayyano mata kasantuwarsu da widad a dai dai wannan lokacin,duk kuwa da tana da wani yaqini da kuma qwarin gwiwa abinda ta dasa zaiyi tasiri sosai,saboda saran da tayi akan gaba. Muryar data amsa masa sallamar da ita ta sake sanyashi a mamaki,ya manta rabon da yaji wannan tune din daga gareta,tun wani zamani can baya,suka gama gaisawa yana jiran yaji ta kawo complain ko wani damuwa sai baiji wannan ba,sai hira da taketa qoqarin jansa dashi. To anan dai ya biye mata,don shima yana da buqatar irin wannan kulawar,yana yunwar samun kulawa irin wanann amma ta zame masa jidali a wajen hafsat din,ya kishingida kadan yana sauraren hirar da take masa,duk kuwa da cewa qarfin hali kawai takeyi,daga can harta gundura,bawai don ta gaji dajin muryarsa ba,muryarsa na daya daga cikin abubuwan da bata taba jin ta gaji dasu ba. "Wai ina qanwata ne?" Ta jefa masa tambayar fa tun dazun so samu ta zama ta farko,to amma he is very smart,zai iya sansano wani abu,shi yasa ta kaita tsakiyar zancansu "Bata mu gaisa mana,nayi mata ya gajiyar hanya?,ina fata ba zaka sake tara mata wata gajiyar ba" maida idanunsa yayi kan fuskarta da a yanzun ta bada hankalinta ga tv,saboda wani cartoon da suka juya haskawa,hasken tvn ya haske fara tas din fatarta da kyau,haka kawai zuciya ta d'arsa masa abinda hafsat din ta fada akan widad,ya danyi imagination akai na wasu sakanni,sai yayi sauri ya ture daga ransa yana fadin "She's too young" "Hello" muryar hafsat dake tawa ta ratsa ta tunaninsa,saboda raya mata da zuciyarta tayi tana jikinsa ne yana debe kewa da ita "Ina jinki" "Tana ina?" "Bata kusa.....sai wani lokacin" haka kawai taji zuciyar ta bata yadda da abinda ya fada ba,don haka ta bishi da "Okay" taja qaramar keypad dinta ta soma trying number widad din,amma aka sanar mata a kashe wayar take,take tajin hankalinta ya tashi,abbas baya son barin waya a kunne a sanda suka kebe,haka yake,koda tata wayar karba yake ya kashe,yakance "I need a rest,ina buqatar kadaicewa da iyalina" bai fiya barinta kunna waya ba idan yana gida weekend a sanda suna tashen buga soyayyarsu. Haka kawai taji hirar duka ta fice mata a kai,don haka ta nema suyi sallama,bai matsa ba,don yaga qoqarinta,abun shekara da shekaru,shi yayi mata sallamar,yama rigata kashe wayar ya ajjiye,abinda ya sake saka mata zargi a ranta kenan,tayi jifa da wayar gefanta,ta koma da baya yaraf ta kwanta tana duban ceiling,dole ta kira yarinyar taji.me ya faru a yau,dole ta kirata ta dora mata bita. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 47 Komai nasa ya tattare a falon,abinda yasa widad ta fahimci ya gama zamansa a nan kenan "Muje na rakaki daki,zan kwanta" jiki a sabule ta miqe din,yana gaba tana binsa a baya har zuwa dakin,tana zaune a gefan gado ya zuzzuge dukka glasses na window din sosai,ya kunna ac ya daidaita mata temperature dinta,duk abinda yake tana binsa da kallo,duka jikinta babu dadi,dan wankan da takeyi ma data yiwa anty deena alqawari bata samu yi ba,ta kuma riga ta saba da yinsa zuwa yanzu,ya tako a hankali yana ajjiye remote din acn sannan yace "Kin iya addu'ar kwanciya bacci?" Kai ta gyada masa "Da kyau,kiyi kafin ki kwanta" ta sake gyada masa kai,ba wannan bane a gabanta,tana qiyasta yadda abubuwan tsoro zasu kawo mata farmaki cikin dakin idan ta kwana ita kadai,babu abinda ranta da zuciyarta basu kawo mata ba,batasan sanda tayi wuf tabi bayansa ba sanda taga ya nufi qofa. Tsaiwa yayi yana kallon ta,hawayen nan da basu da wahala a fuskarta suna fita "Mene kuma?" "Tsoro nakeji" "A'ah....wai meye abun tsoron ne?" Kasa amsa masa tayi,illa d'ari d'ar da taketa yi,shuru yayi ya zuba mata idanu,yanason tuna abinda ya dace yayi "Yanzu me kike so?" Saita kalleshi da dara daran idanunta masu haske sosai,bakinta yana dan rawa,ta kasa cewa komai,ganin haka sai yace da ita "Muje dakina ki kwana" da sauri ta girgiza kai tana fidda ido waje "To ki koma dakinki ki kwana" ya sake bata second option,nan ma ta girgiza kanta da sauri. Ranshi ne ya baci,har yaja tsaki a fili,wacce irin yarinya ce ita?,duk option din da aka bata bai mata ba? "Ba zaki dakina ba,bazaki dakinki ba,to zaman gadinki zanyi?" Ya tambayeta emotion din fuskarsa yana sauyawa zuwa bacin rai. Maimakon amsa saita sakar masa kuka sosai,abind ya hasalashi ya sakar mata tsawa,tsawar data sanyata durqusawa a wajen tana kuma sakin wani kukan tare da kiran sunan ummu. A take jikinsa yayi sanyi,yaga kuma rashin kyautawarsa muraran "Sai ka dinga haquri da ita,kana kwatanta mata abubuwa,bata zama cikakkiyar budurwa ba,da quruciya har yanzu a tattare da ita,to zaka yita ganin yarinta,sai kayita haquri kana gyara mata,amma data gane abinda kakeso da wanda baka so,zakaji dadinta fiye da kowa" maganar da sukayi da hajiyansa ta qarshe ta dawo masa,wannan yasa temper dinsa ta sauka,ya tako a hankali ya tsaya a gabanta "Get up....tashi" ya fada a tausashe,saita miqe din tana sanya gefan dankwalinta tana goge fuskarta,duk da hawayen sunqi tsaiwa "Yanzu ya kikeso ayi?" Ya tambayeta yana narkar da idanunsa cikin nata,itama kallonsa takeyi,ya fuskanci ko a jikinta bata jin nauyin kallon qwayar idanunsa,ta gaza bashi amsa sahihiya,ya kuma gane tsoron hada daki takeyi kawai dashi,kamar kuma yadda take tsoron kwana ita kadai,tsahon wasu sakanni da shuru ya biyo baya sai ya gyada kai "Shikenan,ki kwanta a daki,zan zauna a falo har kiyi bacci" a hankali ta gyada kanta,hakan yayi mata,yafi ace ya koma dakinsa ya kulle ba kowa a kusa,duk da dakunan kusa da juna suke. A gaba ya sanyata har dakin nasa,ya dauki duk.abubuwan da zai dauka ya ajjiye a falon,ya maidata dakin ya tsaya harta kwanta sannan ya ja mata qofar ya dawo falon ya zauna saman kujera hadi da jingina filo bayansa da gefansa don yafi jin dadin zama,sannan ya buda wani qaramin littafi ya soma dubawa. Fakare tayi cikin bargon data lulluba har kanta tana rarraba ido,lokaci lokaci tana dan jiyo motsinsa daga falo,wannan ne ya sanya mata nutsuwa,har sannu a hankali bacci ya saceta ba tare data sauya koda kayan jikinta ba. Awa guda y bayar sannan y shigo dakin,ganin qarar qofar dakin bai sanyata ta motsa ba ya fahimci tayi bacci,sai ya koma da baya yana sake rufe mata dakin,ya koma falon ya kwashe kayayyakinsa ya wuce nasa dakin "Case closed" ya fada a ransa,amma yana tunanun haka zasu maimaita da ita gobe?,kenan wani sabon duty dinne ya sameshi "Ya rabb" ya furta yana furzar da iska daga bakinsa,ya ajjiye komai a muhallinsa y wuce bandaki don yayi wankan da rigimarta ta hanashi yi. Tunda gari ya waye ta dawo falon ta zauna,bayan ta dafa ruwan zafi kamar yadda latifa ta koya mata,ta hada da cup da tea flask din ta dora saman table,tun daxu take jiyo motsinsa cikin dakin,amma bata yi qoqarin shiga ba,saidai ta zubawa qofar dakin idanu tana qiyasta sanda zai fito. Yana taba handle din ta sake zubawa qofar idanu,ya fito a hankali cikin police uniform,sun masa wani irin kyau kai bakace uniform na ya sanya ba,haiba da kwajininsa sun fita sosai,tsayayyen namiji da siffar qarfi ke bayyana a halittarsa,qafafunsa saye cikin baqaqen boots,yana shirin rufe qofar ya lura da ita,sai ya waiwayo yana dubanta da mamaki kan fuskarsa,da yaji shuru yayi tunanin har yanzu tana daki baccin takeyi,dalili kenan da bai tasheta ba. Sosai ya sake mata kwarjini,wani tsoronsa ya sake shigarta,sai ta dauke idaninta ganin yadda yake kallonta,tura baki gaba, itafa duk wanda yake kallon mata dan iska ne a wajenta,ta sauke qafafunta qasa sannan tace "Ina kwana?" Bai amsa ba sai daya rufe qofar dakin,sannan ya tako zuwa wajen yace "Lafiya lau...." Ya fada yana duban kan dining din,sannan ya sake dubanta "Kinci abinci ne?" Kai ta girgiza "Akwai kayan tea a cupboard na kitchen din,zan fita anjima za'a kawo kayan cefane,ba wata damuwa?" Kamar jiya yauma fuskarta kamar ta fashe,yana nufin ita kadai zata wuni a sassan kenan?,wai Allah,ya zatayi,lallai zata mutu da tsoro indai yace zai sake kaiwa dare,ganin batace komai ba sai ya dora "Akwai mutane cikin gidan nan,zaki iya shiga ku gaisa,ko kuma idan na dawo saiki shiga" ya fidda kudi ya ajiiye mata "Sai na dawo" ya fada yana nufar qofar,binsa tayi da kallo,kamar ta zura da gudu ta bishi "Don Allah kada ka sake kaiwa dare irin na jiya" ta fada muryarta tana rawa,waiwayowa yayi yana kallonta,ba tare daya shirya ba murmushi ya subuce masa,shi kam ya jima baiga matsoracin mutum ba irinta "In sha Allah" yace mata sannan ya fita. Ta kusa minti talatin a wajen tana jin yadda gidan yayi mata shuru,sai da cikinta ya fara kiran yunwa sannan ta miqe,kana kallonta zakasan a tsorace take,duk da akwao motsi jifa jifa daga harabar gidan,kitchen ta shiga tana neman inda kayan tea din suke,tsahonta bazai kai ba,sai tasa kujera ta taka ta dauko ta dawo dining din ta doma qoqarin hada tea din,gana daya ta rude,saboda ummu ko latifa ke hada mata,koda ta gama hadawa ta dandana sai taji test din baiyi mata ba,ta bare baki kamar zata saki kuka,haka ta runtse idanu tana kurba har ta kusa shanyewa,dai dai lokacin da wayarta ta dauki tsuwwa,ta firgita da ringing din wayar daya soma fita,don a bazata yazo mata,saura kadan cup din hannunta ya subuce,ta ajjiye kofin ta nufi dakin da sauri. A can qasan gado ta gano wayar,a lokacin ana sake kira karo na uku MOMMY ta gani,shine sunan data sakawa hafsat,ta saki murmushi tana jin dadi,itace ta fara kiranta,cikin zumudi ta daga "Hello.....ina abban mimi?" Abu na farko da hafsat ta fara fadi kenan,ba tare data damu tayi sallama ba "Mommy ina kwana?,inasu mimi?" Ta maida mata da tambaya,ba tare data bawa tambayarta ta farko muhimmanci ba,saboda ba wannan bane damuwarta ba "Lafiya lau....ina abban mimi?" "Ya fita mommy" "Jiya a ina kika kwana?" "A dakina" "Shi kuma abban nasu fa?" "Ban sani ba,na rigashi yin bacci" gaban hafsat ya fadi "Da kika farka kenan a dakinki kika ganshi?" Kai ta girgiza kamar tana gabanta,gabanta kuma yana faduwa cike da fargabar kada ta karanci ya rungumeta,babban abun kunya kenan,tana kuma tsoron kada zancen yaje kunnen mutane a dauka ita din 'yar iska ce "Daga dakinsa naga ya fito sai ya tafi office" "Karkimin qarya fa widad?" Kai ta langabe muryarta nayin sanyi "Allah ki tambayeshi ma" ta furta zuciyarta na addu'ar Allah yasa kada yace ya rungumeta idan ya tashi bata labari. Ajiyar zuciya ta sauke,hankalinta yana kwanciya "Shikenan,ina fata baki manta komai ba?" "Eh momy" "Da kyau,ki kula da kyau kinji ko?,ki kula" "To mommy.....mommy amma ki bani mimi ko...." Bata tsaya jinta ba ta gintse wayar,iya abinda takeson ji kenan,sauran koma meye ba damuwarta bane,ta aje wayar gefan gadonta tana furzar da iska "Shegiyar yarinya,kike cewa wani wai na tambayeshi,abbas din zan yiwa wannan tambayar?,ko ke ban isa na miki makamanciyarta a gabanki ba" sai kuma murmushi ya subuce mata "Anty ummee kinyi a rayuwa" ta fada a fili,ta duqa tasa qaramin muqulli ta bude drawer din jikin gadonta da take bawa kulawa ta musamman,kudade ne a ajiiye a ciki,ta fiddosu ta fara rigasu tana hade kansu waje guda,ranta na mata fari sol,yau sai taji gidan ya mata dadi,musamman idan ta kalli sassan widad din ra ganshi a rufe,sai taji kamar ta tafi kenan. Tana cikin maida kudin kira ya sake shigowa mata,ganin sunan mai kiran saita hade ranta,taja tsaki ta dauke kai,anty shafa ce yayarta,tasan kiranta baya rasa nasaba da zancan kudi,kullum zancanta na ta kawo wani abunne,ita kuwa kudinta bana tabawa bane,don haka ta maida wayar silent ta miqe tana kallon agogo. Sha biyu saura na rana,ko brush batayi ba bare ayi zancan breakfast shara ko gyaran gida,tana son abbas tana son ta kasance ko yaushe dashi,to amma idan suna tare irin wannan sakewar ce bata samu,shi yasa ba kasafai take damuwa da nisantar juna a tsakaninsu ba. Tunawa tayi tabar yara a falo,har tayi hanyar toilet saita sauya akalarta zuwa falon,tana addu'ar Allah yasa basuyi mata barna ba. Tun daga nesa ta hangi mimi tayi dafa'an a tsakar falon,ta fasa kwalin cornflakes ta cika madara kwano ta dama da ruwa tana ta durawa nawwara,tsawa ta kwaza mata,sannan ta fidda danu tana duban kwanon "Innalillahi" ta fada da qarfi,sannan ta nufi mimi da sauri, batayi wata wata ba ta gabza mata mari,gaba daya yarinyar ta jawo mata asara,kudin da ya bayar a siya wadan nan kayayyakin ta lankafesu,ta fitar da tsohuwar madarar daya taba siyawa yaran tasu tashan tea,ta ajjiye a dining tace suyi amfani da ita kafin ya dawo,yanzu ta daga madarar dukanta ta zazzage musu. "Uban wa yace ki taba?" Ta fada tana kama kunnen yarinyar,cikin kuka tace "Mommy,nawwara ce takejin yunwa" sai lokacin ta tuna bata basu komai ba ashe,ta saki kunnen nata tana huci "Ba sai kizo ki gayamin ba,kin tashi kin cuci mutane kin musu barna,matsa ki bani waje" haka ta sanya tsintsiya da ta gyara gurin,tana yi tana mita,yaran na rabe a gefe,mimi na hawayen murde mata kunnen da tayi. *Arewabooks: Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 48 Tana cikin wannan mitar aka buga qofar falon "Waye na?" Ta fada cikin fada fada,ranta fal quncin mimin ta karya mata budget "Nine,sale ne" "Shigo" ta fada kanta tsaye bayan taja tsaki,duk da tasan abbas baison haka,don baya bari a shigo masa har inda iyalinsa suke kai tsaye. Da sallama yaron ya shigo yana sunkui da kai,don bai saba shigowar ba,ga hafsat din da daurin qirji,sauqinta akwai t-shirt a jikinta,a samanta taja zanin ta daura "Ina kwana hajiya" "Lafiya lau ya akayi?" "Eh dama me yiwa engine service ne yazo,za'a bada kudin a siya kayan aikin,sai mechanic din da zai dauki motar oga ya kaita garage za'a mata service itama" tsuke fuska tayi,don tasan kudaden daya wara ya bata saboda a duba motar da engine din suna da yawa "Bakaniken ya dauki motar,amma shi me yiwa engine service kace ya barshi kawai,sai mai gidan ya dawo" "To....amma engine din yana bada matsala fa,jiya ma....." "Abinda nace kayi zakayi ko raayinka zanbi?" "Sorry madam" ya fada yana juyawa yabar falon,cikin ransa yana Ala wadai da dabi'arta,sarai yasan an bata kudaden,fitar dasu ne ba zata iya ba. Tsaki taja tana duban yaran "Ku wuce muje na dafa muku abinci" jin xancan abinci sai mimi ta ware,sukabi bayanta zuwa kitchen din,saidai tana ganin ta buda kwalin indomie yarinyar ta bata rai,ta gaji da ita,don jiya da daddare ma ita ta dafa musu "Indomie mommy?,bana ci nidai" cikin takaici ta kalla yarinyar,ubansu ya batasu da kala kalar abinci,ita kuwa ba zata iya dorama kanta wannan wahalar ba "Ba zakici ba ubanme zakici?" "Irin abincin gidan hajiya" "Meye abincin gidan hajiyan?" "Tuwo ko dambu" "Nabi tuwon da gudu,zakici ubanki wallahi,idan bakici ki zauna haka,yunwar cikinki" saita bare kwalin ta dauko guda biyu ta zuba a tukunyar. Kusan dai a gantale suka tsakuri taliyar,bata tsaya ta mata ma dahuwar arziqi ba bare darajar hakan ya sanya suci da yawa,daga qarshe ma.idan ta debo ta baiwa nawwara sai ta tankwabe hannunta,da yake ita din tafi mimi fada,sai ta tattarasu ta barsu ta shiga sabgarta,dole da yunwa ta ishesu suka dawo suka ci a haka bayan tayi sanyi. ¢¢¢¢¢¢¢¢¢ Hirar da suka sha da ummu da abbanta na kusan awa biyu ya sanya tajita tadan sake,sai kuma dan motsin da take jiyowa lokaci lokaci cikin gidan ya sanya bata matsu da yawa ba,ta dan saki jiki ta soma kade dakin da gyarashi kamar yadda latifa ta koya mata,sannu a hankali sai gashi ta gyara dakin fes,sadai fa tadan dauki lokaci,ta shiga toilet ta wanke fes,ta kama qugu tana dariyar farinciki na ganin yadda ta gyara dakin kamar ba ita ba,ta kama baki tana murna "Ashe dai na iya,amma ummu ke hanani,bari na kira umma latifa na bata labari" ta koma gefan gadon tana kaffa kaffa kada ta bata zanin gadon data d'ameshi da kyau,ta fara duba number latifa wadda basu jima da gama waya da ita ba itama,Latifa na daga wayar ta fara bata labari "Iyeee shalelen ummu,girma yazo,haka akeso,kiyita tsafta kamar ummunki,saura girki" dariya tayi tana sake bata labarin wahalar data sha,latifa na biye mata,ummu ja gefansu tana murmushi,duk da rabin hankalinta nakan shalelen tata. Wunin ranar bata wani ji yunwa ba,koda taji yunwa dinma tea ta hada tasha ta kwanta abinta. Kafin magariba tayi wanka,ta shafe jikinta da turarukan da latifa ta hado mata a kayanta,kusan sai data shafa kowanne turare,har ya soma yawa ya fara hawa ka,kowanne mai sanyi da dadin qamshi ne,amma yawan da yayi yasa ya jirkita,amma ita ko a jikinta,wata dubai abaya ta saka,ta dawo falo ta maqale jikin window tana leqen harabar gidan,gabanta yana dan faduwa kadan kadan,saboda ganin magariba ta gabato babu shi ba alamarsa. Ana qwala kiran sallar magariba motarsa tana shigowa cikin gidan,samuel ne ya kawoshi,shi ya koma shi kuma ya shigo ciki. "sannu da zuwa" ta furta tana jan dankwalinta daya zame saboda santsinsa daya hadu da sulbin gashinta,ta miqe tsoron nan nata yana bayyana,tanason karbar masa ledar daya shigo da ita kamar yadda ta saba duk sanda taga kaya hannun babba,amma tana shakka matsawa inda yake,a haka har ya qaraso ya ajjiye,ya zauna yana tube takalman qafarsa "Lafiya kika wuni?" Kai ta gyada masa,sai yadan lumshe idanu yana gyada kai,qamshin jikinta gaba daya ya cika falon,kamar anyi barin turare "Samomin ruwa nasha" hanyar kitchen din ta kalla,baiyi duhu sosai ba,don haka da sauri tayi hanyar,a nufinta tayi sauri ta dawo kada wajen yafi haka duhu. Binta yayi da kallo,ko yaushe ya kalletan sai ya dinga jin mamaki na shigarsa,wai matarsa ce wannan,ta dawo da ruwan ta russuna ta miqa masa kamar yadda ta saba yi tun a gida. Hannu yasa zai karba,yadda tayin yana burgeshi,duk da abub mamaki bane,duba da gidan data fito,muhsin kadai ya ishi a shaidesu,don ko cikin abokansu daban yake,wani abune da zai iya cewa baisan lokaci na qarshe da hafsat tayi masa ba wai don zata bashi abu. Sakin ruwan tayi da sauri sanda hannunsa ya sauka akan nata,jikinta ya dauki rawa,taja da baya tana yarfe hannu jikinta yana rawa,hawaye na shirin tarar mata a ido,shi bai kula bama,don ya duqa zai dauke ruwan bayan ya furta "Subhanallah" sanda ya dago harta samu waje ta rakube,ya bita da kallo yana mamakin yadda take matuqar tsoron tarayya dashi,kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya bude gorar ruwan ya fara sha,sannan ya miqe yana cewa "Zanje sallah,idan na dawo zaki shiga ciki ku gaisa da mutanen gidan,ga abinci nan a leda ki dauki naki" kai ta gyada masa gabanta na faduwa,bata samu nutsuwa ba har sai da yayi alwalar ya fice,ta bishi da kallo tana hararar hanya qwalla na gangaro mata,yanzu idan ummu ko mommy suka ga wannan abun da yakeyi fa?. A falo ya tsaya jiranta,ta fito yafe da mayafin abayar bayan ta cire hijabin da tayi sallar dashi "Koma ki samo babban mayafi,akwai mutane a waje" yayi maganar sanda yake dage labulen falon yana sake duba farfajiyar gidan,jikinta ta kalla,itadai bataga wani aibu a haka ba,amma sai batace komai ba ta koma ta lalubo mayafi cikin kayanta ta fito,suka jera zuwa cikin gidan. Babban gini ne,don yadan fi nasu girma da kayan alatu,sanda ta shiga ta samu matar gidan a falo,ta karbeta da fara'a,saidai tunda ta gaidata ta rasa me zata cemata. "Ban gane fuskar taki ba,ko kanwar amaryar abbas ce?" Qas tayi da kanta tana jin nauyi yana kamata,saita girgiza kai alamun a'ah "Ko amaryar ce da kanta?" Saita daga kai alamun eh,matar ta maida kanta sosai tana kallon widad din sosai,abbas data sani,abbas dake da.babbar mace kamar hafsat yaje ya auro wannan qwailar?,lallai Allah mai iko,sau tari mazan da suka fiya izza da kuma jin kansu daga qarshe haka suke qarewa,har gwara wannan din,kyakkyawa ce data amsa sunanta,komai nata mai ban sha'awa da daukan hankali,nan gaba kadan idan ta ida zama cikakkiyar mace lallai ba shakka sai an kalleta an qara,dole hankalin hafsat din ya tashi,amma a fili sai tace da ita "Ma sha Allah,Allah ya bada zama lafiya kinji amarya" bata iya amsa mata ba,sai shuru data sakeyi kawai kanta a qasa,gaba daya bata jinta a sake,tun asali dama ita din bamai saurin sabo bace,tana da wuyar sakewa da baqin fuska,don haka bata wani jima ba ta miqe tace zata tafi "To ina zuwa" ta fadi tana miqewa ta shige ciki,ranta da zuciyarta fal mamaki,ba jimawa ta fito da wasu kayan barci set uku ta bata,hannu biyu widad ta saka ta karba sannan ta fito. A inda ta barshi ta sameshi,ya sake mata jagora suka koma ciki,tana ta kallon gate,ji take kaman ta fita ta miqe qafarta,suna shiga falon ta miqa masa kayan kamar yadda takewa ummu a gida idan an mata kyautar abu "Gashi" ta fada tana ajjiye masa kusa dashi,dai dai lokacin da ledar ta zame,matan dake jikin takardar sanye da irin kayan baccin dake cikin ledar suka fito. Kusan tare suka dauke idanunsu shi da ita,taja baya da sauri qafafunta na sarqewa zata wuce ciki "Zonan" yayi kiranta yana karantarta,da baya da baya ta dawo,ita a lallai ba zata iya kallonsa ba,har abun yaso bashi dariya,ya dake da yanayin dakiyarsa da kuma miskilancinsa "Dauke abinki ki tafi dasu" "Banaso" ta fada kai tsaye tana maqale kafada,a mamakance yake kallonta "Bake ta bawa ba?" "Ni ta bawa,amma banaso,bana saka irinsu" dariyar da yaketa riqewa ta subuce masa,amma saita fita ta sigar murmushi "Zauna" yace da ita yanata kokawa da dariyar tasa,ta baya ta zauna har yanzu taqi yarda su hada ido dashi. "kinsan amfanin wadan nan kayan?" Fuska ta qara daurewa,tana sake tabbatarwa basu hada ido ba,kai ta girgixa masa ba tare da tayi magana ba "Oya....open your mouth,ban jiki ba" "Ban sani ba,kayan 'yan iska ne fa" tayi maganar tana narke fuska,kamar zata saki kuka. Wannan karon duk yadda yaso boye dariyarsa sai data fidda sauti,yayi qoqarin daidaita kansa,da gaske ta jahilci aure,da alama aiki je jajur a gabansa a kanta,bai tsawwala sai ya samu komai daga gareta ba,amma aqalla ta gama sanin meye auren kansa,don da alama batasan meye shi ba. "Kwashesu ki tafi" ya bata umarni a taqaice,ta baya ta zuro hannunta ta jawo ledar zuwa gabanta,sannan ta miqe da sauri sauri tayi dakinta. Tana shiga ta jefa ledar saman sofa bed tana zumbura baki kamar zata fashe,ledar ta qarasa yayewa kayan suka fito sosai,bata gama kula da hotunan jiki bama sai yanzu,ta qarasa tana daga kayan saita jefar zuciyarta a a cushe "Lallai matar nan ma 'yar iska ce ashe itama,don me zata bata wadan nan kayan?" Hadasu tayi ta cukuikuye ta jefa cikin sif,ta koma saman gado ta lafe a cikin bargo abinta,idanunta ta rufe,tana fata bacci ya dauketa tun tana iya jin motsinsa,basai waje yayi shuru ba. °°°°°°°°°Washegari ma haka ya fita,bai tsaya yin breakfast ba,yauma ita dinma kamar jiya,bayan ta gama 'yan gyare gyarenta da zata iya,saita dawo bakin window din falon ta zauna,lokaci lokaci tana yaye labulen tana leqa farfajiyar gidan,abinda ya tayata zama kenan,duk da yace mata tana iya shiga cikin gidan ta zauna a can,kota debe kewa,amma kasancewarta mara saurin sabo taji gwara tayi zamanta a nan har zuwa sanda ya dawo gida. To tsahon kwanaki biyar kusan haka rayuwar ta dinga gara musu,da safe idan zaya fita aiki zai sameta ne a falo,sabida yafi dakinta haske,zatayi masa a dawo lafiya bayan ta gaidashi,ya ajiye mata kudi ya kuma tambayeta bata da matsala,sannan ya mata sallama,takan bishi da idanu tana jin kamar ta bishi,wani lokacin yana ankare da ita,wani zubin hankalinsa yayi gaba,zata gyara dakinta data fara sabawa dashi,ta gyara falo ta goge shi tasa,duk da cewa tana daukan lokaci kafin ta gama,amma yana kintsuwa,kyan sharar nata da gyaran nata yake gani,saboda tafi hafsat nesa ba kusa ba, at least ita bata barin qura ko datti,sabanin hafsat din da ko ina a birkice yake,duk da suna da komai a store,to amma bata taba dora girki ba,yana sawa a kawo mata abinci,idan ya dawo tana cikin falon,amma wata qurya ta daban,a can zata zauna ba um ba um um,tana kallonsa kawai,duk da tana buqatar hira da wanda zatayi hira dashi,sai idan yaga tana gyangyadi kota gaji zai rakata ta kwanta ya dawo falo yaci gaba da sabgoginsa kafin ya tattara shima ya wuce nasa dakin. Duk sanda tsautsayi yasa ta farka cikin dare kuwa da qyar da sudin goshi take komawa baccin,saboda dan banzan tsoro,a rayuwarta bata taba kwana daki ita daya ba sai a wannan karon. Bangaren hafsat kuwa kullum a rana saita kirata,ta tambayeta me ya faru a jiya,me yake faruwa a yanxu,amsa kawai take buqata,tana ji zata katse wayarta,saidai idan weedad dince tabi bayan kiran tace a bata su mimi. Zuwa sannan fa fara jin dadin wayarta,da kanta da kanta ta koyi yadda ake sarrafa abubuwa da dama a cikinta,ta dauko games kala kala da suke debe mata kewa sosai,wannan yasa dogon wunin kadaicin da takeyi ya ragu sosai. _wannan kenan_ *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 49 Awanni kusan hudu kenan tana abu guda,baya ga kitchen din data yiwa kaca kaca kota ina,kamar wadda ke girkin mutum ashirin,sannan daga bisani ta samu ta kammala tuwon shinkafa miyar kubewa iya yadda taga latifa tana yi,ta zuba cikin sabbin warmer masu kyau da aka hado cikin siyayyar cefanen da aka kawosu jiya. Dafe bayanta tayi bayan ta kammala gyare kitchen din "Shi tuwo dama haka yake da wahala?"ta fada tana yatsina fuska,duk da can qasan ranta farinciki ne fal,wai yau itace da yin girki cikin kitchen dinta,ba kwaba ba hantara babu bakiyi dai dai ba,ta juya ta soma diban warmers din takai saman dining,ta jeresu da kyau,tana kallonsu tana murmushi,har cikin ranta dadi take ji idan ta tuna wai yau ance tayi girki. Dakinta ta koma tayi wanka,ta shafa powder a kyakkyawan fuskarta mai santsi da sheqi dauke da tambari na quruciya,dubai abaya wine color da tasha adon duwatsu masu walwali ta fidda ta sanya,ta daura dankwalin saman kanta,ta kuma shafa turarukanta kamar yadda ya taba gwada mata yadda ake sanyasu,tun daga ranar kuwa ta dauke tsaf,yadda ya kwatanta matan haka take sakawa,ita kanta sai taji tafi jin dadinsu. Sosai abayan ta haska jar fatarta,kamanninta suka fito sak na ainihin tushen yankin data fito,ta koma gefan gadonta bayan ta dauko wayarta dake saman madubi,ta bude ta shiga wata game da taketa daukan hankalinta ta fara bugawa cikin qwarewa. Hankalinta yayi nisa sosai a game din,har bataji qarar motarsa zuwa shigowarsa cikin gidan ya kuma tura qofar dakinta ba,sai ya tsaya riqe da handle din qofar dakin,zai iya lissafa adadin shigowarsa dakin,idanunsa saman fuskarta,tattausan siraran labbanta sunata qyallin lips balm,tana ta juyi saman gadon,duk sanda taci game din sai tayi dan tsalle kadan na murna sannan taci gaba. Idanunsa ya dauke sannan yayi gyaran murya kadan ya hada da sallama,daga idonta tayi daga kan wayar zuwa kansa,saita aje wayar gefanta tana masa sannu da zuwa,sannan a dabarance tana laluba maballan gaban rigarta taji sun rufu da kyau?,ta kuma tsareshi sosai da ido taga ko.yana kallonta?. Sarai yaga abinda takeyi,amma sai ya kauda kai ba tare da yakai idanuwansa kan qirjin nata da yake ganin basu da maraba da qirgar dangi a wajensa ba "Tare da baqo nake,ki kawo abincin" kai ta gyada masa,ya saki handle din qofar ya juya zuwa falon,yana duba wayarsa daketa ringing. Ba kowa ke kiransa ba sai hafsat,tunda satin ya wuce taga baizo weekend ba hankalinta ya gaza kwanciya,gaba daya zuciyarta cike take da wasi wasi da kuma fargaba,duk kuwa da bayanin da yayi mata na cushewar aiki da ya samu a kaduna fiye da dukka garuruwan da yake zuwa aiki,amma zuciyarta ta kasa aminta da hakan,duk inda yake baya wuce satin nan dai baizo bauchi ba ko don hajiyarsa,sai wannan karon?,sai wannan lokacin daya tafi da wannan sadakar yallan?,anya ba holewarsa yakeyi ba?,anya bai samu wani abu bane daga gareta?. A kullum kwanan duniya kira uku zuwa hudu ne sai ta yiwa widad shi,ta tambayi ya suka kwana?,ya suka tashi?,ya suka yini?,ya dawo gida kuwa?,me ya faru a tsakaninsu?. Sam widad din bata boye mata komai,rashin wayo da qarancin shekaru yasa bata dsuki wannan din a mazaunin komai ba,face ma qauna soyayya da kulawar da mommy hafsa din ke nuna mata,wannan yasa ta sake ganin kimarta,ta kuma sake ganin girmanta,hakanan taji tana qaunarta,shi yasa dukkan abinda zata umarceta dashi take aiwatarwa kanta tsaye,wannan dalilin ne kuma yasa tayi riqo da hudubarta yadda ya kamata,don ya zame mata kamar tishi ne akan tarbiyyar ummu,sai faduwa tazo dai dai da zama,tana nisantarsa iyakar iyawarta,tana kuma qauracewa duk wani abu da tasan mommy hafsa ta gargadi akai. Ta sani ta kuma fuskanta,sam qarya bata cikin dabi'ar widad,da gaske haka take tun a gida,duk da samun wannan tabbacin,hakan bai sanya zuciyarta da ruhinta sun aminta sun kuma kubuta daga zargin abbas ba, don haka taketa kiransa,tanason taji yaushe zai zo din. Ajiyar zuciya ya sauke,yau inda ace buqata ce da hafsat din dole.ya ajjiye dukkan abinda yakeyi yaje ya sauke mata ita,to amma yafi kowa sanin wacece ita,tana iya share wata guda koma fiye bata buqaci komai daga gareshi ba,saidai shi din ya nema,a yanzun ma.ya tabbatar ba wani qwaqwaqwaran dalili ne da ita ba na kafewar ya taho din,ya bata dukkan wata dama da zata fadi uzurinta amma amsa daya ce "Kawai son ganinka nakeyi" "Kiyi haquri,indai ba babbar buqata ce dake ba......akwai aikin da nakeyi a nan din,banason kuma na matsa daga kaduna sai na kammalashi,aikin yana buqatar sirri kula da kuma takatsantsan" amsar daya bawa hafsan kenan,ta furzar da iska dgaa bakinta,zuciyarta na raya mata ta shirya ta tafi Kaduna kawai,to amma sanin girman laifin data aikata masa wanda yayi silar haramata mata Kaduna kwata kwata yasa ta sake jaddadawa kanta wannan ba mafita bace,zata bi ta hanyar da tasan dole yazo gida koda baiso ba. Sai data nema yalwataccen mayafi ta yane jikinta dashi sannan ta wuce falon,idanun abbas din a kanta,hakanan yaji abinda tayin ta burgeshi,bai gaya mata ta yafa din ba,amma tasan ya kamata,ta tsugunna har qasa ta gaida ameen abokinsa,sannan ta wuce ta soma dauko warmers din tana jera musu bayan ta shimfida table mat a qasan. Ta tsara komai yadda ya dace,har cikin ransa yaji abinda tayi ya burgeshi,ruwan sha dana wanke hannu duka akwai a wajen,abinda hafsat bata taba yi ba,dai dai da tissue daya dace ko yaushe a sameta saman dining sai ya nema,ita kuwa ta koyo hakanne daga wajen ummu,haka taga tana yiwa alhaji. Har ta juya zata wuce daki,sai taga ana hasko wani cartoon da take mugun so,fasa shiga dakin tayi,ta dawo ta zauna fuskarta cike da fara'a,kadan abbas ya waiwaya ya kalleta,kamar zaiyi magana saiya fasa,ganin irin excitement din dake kan fuskarta na ganin cartoon din,ya maida kansa ga warmer din,ya bude ya sanya hannunsa ya dauko malmalar tuwon farko. Tun baikai ga budeta ba ya fahimci an samu babbar matsala,duk da haka bai fasa ba,ya wareta yana sakinta saman plate,take kuwa tuwon ya dare biyu,suka hada ido da ameen din,sai abbas din ya basar,ya bude warmer din miyar,koriyar kubewa shar,wadda aka qarantawa kayan hadi ta bayyana,bama kayan hadi ba,harda kayan dahuwa,wake yayi tsuru tsuru yaja gefe,ga danyan manja a sama ya hade rai. Serving spoon yasa ya kwaso musu ita da qyar ya zuba akan plate din,ya maidata ya rufe ya saka musu cokula yana cewa da ameen "Bismillah" dukka dauriyarsa amee din ya gayyato,ya matso ya dauki cokalin,suka sanya lomar farko a tare da abbas din. Spoon din ya ajjiye sannan ya miqe yana duban abbas "Kasan nayi mantuwa a office,zan koma,daga can gida zan wuce" yadda ameen din keta rattaba bayani ya bawa abbas dariya,amma sai.ya qushe abarsa,gulma ce da ganin qarshen mutum tasa yace zaya biyoshi "Okay....sai na fito" ya amsa masa,sai ameen din ya juya yana cewa "Amarya,ni zan koma ko,ina godiya sosai,sauri nake.ban samu naci abincin ba,amma...... next time" "Ka gaida gida" ta furta a sanyaye sanda ta kalli abincin taga kamar babu abinda ya dandana,idanunta nakan plate din har ya fice a gidan. Dukkan alamu sun nuna.girkin nan nauyi dadi ko ma'ana ba sam,jikinta a sanyaye,ta tabbatar shima ajiye mata abincinta zaiyi,ba iya ci zaiyi ba,musamman data hangi yadda tuwon ya baje abinsa,ya koma kamar shinkafar da bata samu wadatacciyar dahuwa ba. A mamakance ta maida dubanta ga fuskarsa,sai kai abincin bakinsa yake,kamar babu wani abu da baiyi dai dai ba a girkin,karo na uku suka sake hada idanu tana masa kallon mamaki "Zonan" ya fada a tausashe yana yafitota da hannunsa,saita aje filon data dora saman cinyarta,ta miqe a sanyaye ta nufeshi. Idanunta na tara ruwan hawaye. Gabansa ya nuna mata,ta zauna a hankali tana sake ja baya kadan,qaramin murmushi ya subuce masa yana kallon qwayar idanunta,sannan ya tsame hannunsa daga abincin bayan yaci wani adadi mai yawa "Tuwo yayi fa dadi,gyaran kadanne" da farko shuru tayi tana dubansa,fuskarta dauke da alamun mamaki,daga baya kuma sai murmushi ya subuce mata,cikin wani irin zumudi da sakewar da bata tabayi dashi ba "Allah?,ashe dai na iya girki" ta fada cikin murna,kai ya gyada mata yana kallonta "Kin iya,amma na fiki iyawa ai" ido ta fidda waje tana dubansa "Namiji dama ya iya girki?" Ya jinjina mata kai qaramin murmushi na fita daga fuskarsa "Iyawa kai,ki shirya daga gobe zan fara koya miki irin nawa" sosai taji dadi da fadin hakan da yayi,ita din tanason taga ta iya girki irin na anty madina da anty deena. Cikin ransa yakejin dole haka zai samu lokaci cikin lokutansa ya ware ya koya mata wasu abubuwan kafin ya laluba makarantar koyon girki ya sakata,at least koda girkin ta iya zai rage wani abun. Washegari da safe shi yayi mata knocking ta fito,ta rusuna ta gaidashi tana sanye da kayan bacci masu kauri riga da wando da wando,tana biye dashi suka isa kitchen,ya sama mata kujera yace "Zauna a nan ki gani" murmushi ta sake tana kallonsa,sanye da wani wando na sojoji da farar shirt,ta zauna din sannan ta jefa masa tambayar dake cinta tun daxu "Wai kai police ne kuma soja ne?" Sai daya juyo ya kalleta da manyan idanunsa,sai tayi tsuru tsuru kuma tana dafe bakinta,tana jin kamar tambayar tayi yawa,kai ya girgiza yana sakin fuskarsa "Ni police ne me kama masu laifi" saita jinjina kai tana murmushi kawai. Cikin kitchen din taci gaba da zama,kome zaiyi sai ya nuna mata,saidai tana daga gefe tana d'ari d'ari dashi,bata bari tazarar dake tsakaninsu tayi kusa,ya lura amma dariya kawai take bashi,daga baya bayan ya gama hada komai,ya bata yanke yanke yace tayi masa tana daga zaune. Cikin awa daya da rabi suka hada breakfast mai kyau tare,ta dinga murna tana jin dadi,shi kam saidai ya bita da ido,bayan sun kammala yabar mata kitchen din ta gyara,shi kuma ya wuce dakinsa yin wanka,ta gyara ta kwaso komai ta kawo falon,saita zube saman kujera tana maida numfashi,don tadan gaji,sai data huta sannan ta wuce itama dakin don yin wankan. A ranar ma ya samu sauqin aiki,don haka da rana ya dawo gida,ganinsa a gida da rana ba qaramin dadi yayi mata,ashe mutum rahama ne,cikin zuciyarta ta dinga jin wani dadi,duk da babu abinda ke hadasu daga sannu da zuwa zai wuce dakinsa ne,bayan ya fito suka sake shiga kitchen tare,ta dinga murna da zumudin son ganin me zasu dafa,abinci sassauqa sukayi,itadai tana ta mamakin yadda namiji ya iya girki haka,bayan sun gama kowa yaci nashi ya sake shiryawa ya koma. To da daddare ma haka,sabon girki sukayi,duk abinda yakeyi idanunta na kanshi tana biye,haka ce taci gaba da kasancewa,cikin satin gaba daya aiki biyu ya dinga yi,yayi na office ya dawo gida ya koya mata abinda ya sawwaqa,wani lokaci idan bai samu dawowa da rana ba,to da daddare akeyi. Cikin satin sai gashi an samu ci gaba,ta riqe wasu abubuwan,da yake widad din badai kai ba,kuma tana da qaunar yin girkin,sai gashi a satin ta iya hada breakfast,hakanan abincin duk daya koya mata ta fara gwadawa,yana kuma yi,saidai hannun baikai ga fadawa sosai ba. Ranar wata alhamis bayan sun gama girkin dare ya fiddo foam yace ta matso ta bashi bayananta zai cike,foam ne na wata makarantar secondry ta 'yammata daya samar mata zata ci gaba da zuwa,tsananin murna yasa ta fada jikinsa ta qanqameshi tana godiya,sai kuma ta sakeshi da sauri taja baya,jikinta nayin wani irin sanyi,kada fa mommy ta gane ta rungumeshi,tayi tsuru tsuru,har sai daya fahimta,ya dade da fahimtar wannan,koda a kitchen da suke ayyuka tare duk abinda zai kawo haduwarsu waje guda tana daga baya baya,ko abu zai bata sai ya ajjiye take dauka,hakanan suna gama komai take qulewa daki ta kulle abinta,shikam dariya take bashi,kamar yanzun,baisan me take tunani ba,shikam indai abinda take tunani ne idan yayishi yace yayi me?,saiya girgiza kai kawai yana boye murmushinsa cikin fuskarsa ya fara cike mata foam din,bayan ya gama ya miqa mata yana cewa "Idan zan fita gobe zan karba na fita dashi,and....ki shirya jibi zamu je bauchi" ta karba foam din jikinta a mace,sai taji inama ace kano yace mata zasuje?, tabbas da ranar ba zata iya bacci ba. *Arewabooks: Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 50 Blue black abaya mai sulbi ce a jikinta me rubi biyu,qafafunta saye cikin wasu slippers masu kyau qirar kamfanin DKNY light blue,mayafin abayar kawai ta yafa,bata wani tsaya rolling ba,tana janye da qaramar akwatunta har xuwa bakin motarsa qirar BMW. Yana jingine jikin motar yana amsa waya,a hankali idanunsa suka sauka a kanta,yana matuqar son ado da kwalliya,wannan dalilin yasa baya rabo da siyawa hafsat kayan qyale qyale na mata,saidai baya ce ga inda take kaisu ba,bata saka ba bata kuma bayar ba,a yanzun data saka abayar favourite color dinsa,sai yaga tayi masa kyau sosai a ido,karon farko kenan. Gabansa ta tsaya da akwatin,ta langabe kai gefe tana mele baki,tanason gaya masa ba zata iya daga akwatin bane,janye idanunsa daga kanta yayi,ya karanci me takeson fada,sai ya zaro key din motar daga aljihunsa ya soma takawa a hankali. Zagayawa yayi ya bude booth din motar,yasa hannu daya ya daga akwatin cak ya saka ya maida booth din ya rufe. Bismillah yayi yana daura seat belts dinsa,yadan saci kallonta,yana mamakin yadda take qaunar turare,gaba daya qamshinta ya cika motar,ya lumshe idanunsa a hankali,yana jin wani yanayi cikin jikinsa,he missed his wife alort,yayi qoqarin,more than two weeks rabonsa da ita,shi yasa yakeso yayi surprising dinta,yau ba mita ko qorafi duka sun qare,abu daya ke sanyaya masa gwiwa,yasan ba lallai ya samu wata tarbar arziqi,infact baisan ma a yanayin da zai cimmata ba,may be su buge da samun sabani kamar yadda ya zame ma hafsat din sunna,duk sanda ya dawo daga tafiya goma,to bakwai a ciki a ranar daya iso sai wani abun ya hadasu,duk kuwa da cewa shi din mutum ne mai yawan kawaici,wanda bai fiya qorafi akan abu ba idan ba cikashi kayi ba. "Kiyi addu'a" yace da widad yana shirin tada motar,kafin ya gama rufe bakinsa wayarsa ta dauki kuwwa,sai ya qarasa kunna motar ya barta tana daukan zafi ya duba me kiran. Hajiyansa ce,nutsuwa yayi sosai ya daga wayar a ladabce yayi sallama,ta amsa masa cikin nuna kulawa da qauna,ya soma gaisheta gami da tambayarta lafiyarta,duk da jiya ma da yammaci sunyi waya da ita "Yaushe zaka zo gida ne?,ka manta kabar wata iyalin naka a nan?" Tambayar yaji banbarakwai,saboda ba al'adar hajiya bane yi masa irin wannan tambayar "Yanzun haka ma muna cikin mota zamu fito daga Kadunan....." "To alhmdlh ma sha Allah" haka kawai yaji zuciyarsa da ransa basu kwanta masa ba "Hajiya lafiya dai ko?,ko wani abunne ya faru?" "Babu komai,Allah ya tsare hanya" "Hafsat ce ta kawo miki maganar?" Ya sake dai tambayar hajiyan "Nace babu komai,Allah ya tsare hanya,ina widad din?" Waiwaya yayi yana kallonta,ita sam hankalinta ma da alama baya wajen,yana farfajiyar gidan inda mai gadin gidan yaketa gyaran flowers,dauke kansa yayi ya maida gabansa "Tare zamu taho in sha Allah" "To hakan yayi,sai kun iso" "Madalla hajiya,Allah ya saka da alkhairi" sukayi sallama kowa ya aje wayar. Iska ya furzar yana tada motar,idan ya rantse ko kaffara bazaiyi ba hafsat ce takai qararsa wajen hajiyan,don ya sansano hakan daga muryar hajiyan,yasan ta boye masa ne kawai saboda kare martabar hafsa a wajensa,wai me yasa ita din bata jin kunya ko nauyin kaishi qara?,yanzun wannan abun har ya isa takai qararsa gaba?, just one week daya qara baizo ba?,bayan he explains to her?,baisan sai yaushe zata fahimci illar wannan muguwar dabi'ar tata ba,baisan sai yaushe zata gane zubarwa da kanta kima da daraja takeyi a wajen iyayensa ba. Ya danyi gudu,hakanan banda sallah basu tsaya sunyi komai ba a hanya,don haka awanni biyu da rabi suka kawosu bauchi daga kaduna. Ba'a jima da idar da sallar la'asar ba suka shiga unguwarsu,ya faka motar a harabar gidansa,kafin ya sake wani abu tuni widad ta balle murfin motar ta fice saboda hangosu mimi da tayi,suma tuni sukayo wajen,saboda sun shaida motar daddyn nasu. Binta yayi da kallo kawai,har zuwa sanda ta isa garesu suka rungume juna,sannan suka iso bakin motarsa suna dakon fitowarsa. Tare suka rankaya zuwa ciki,mimi da nawwara kowacce na bada nata zancan,fuskar widad fal fara'a,har suka isa falon hafsat din. Kallo daya ya yiwa falon yaji bacin rai ya saukar masa,kullum jiya i yau,dukka gyara da qyale qyalen daya zubawa falon daga bikin widad din tafiyarsu kaduna zuwa zuwansu yau gaba daya sun fara dakushewa,sai ka rantse kayan sunyi shekaru bakwai da sakasu,kai koda shekaru bakwai dinne indai ba qazamar mace ta ainihi ba bai kamata suyi wannan dafewar ba,ko ina tarkace ne dake nuni da cewa babu wadatacciyar sharar da falon yakeso,uwa uba turkish carpet dinta ruwan madara ya fara yin qaura daga aihinin kalarsa zuwa brown, qawataccen center table din daya zuba kudade ya siya mata an soma kwanceshi,ba wasu sassa a jikinsa. "Ina Mommy din?" Widad ta tambayi mimi "Tana kitchen,wanke wanke take" "Muje ki rakani" ta kama hannun mimi din suka wuce kitchen din. Bata a kitchen din,amma qofar backyard na kitchen din a bude yake,sai suka sanya kai can. Turus widad tayi tana duban iyayen kwanukan dake yashe a wajen tamkar anyi taron biki ko siyasa an watse,kusan dukka wasu kwanuka na kitchen dinta suna wajen,tana tsakiyar su ta hada kumfa a babban baho tana wankewa,tanayi tana maganganun qasa qasa,daurin qirji ne a jikinta na zanin atamfa,sai rigar shirt,kanta dankwalin zanin ne data masa daurin gaban goshi,daga qasa kana iya hango qananun gashinta sun burtso. "Mommy sannu da aiki" widad ta fada tana murmushi,hafsat ta waiwayo da sauri suka hada ido da widad din,a take taji ta muzanta,bata taba kawowa a yau idan hajiyan ta kirashi zai taho ba,dukka ta dauka sai gobe,don haka yau taci burin qarar da yininta tana gyaran kitchen,tasan shi da falo da toilet sune abu na farko da yaqi jinin ya gansu ba'a kintse ba,yau din kuma alhamis,ta zaci zai taho gobe juma'a ne. Sake juya idanunta tayi akan fuskar widad karo na uku kafin ta samu sukunin amsa sannun tata data yi mata,idan idanunta ba gizo yayi mata ba yarinyar qara haske da kuma qiba tayi,ga wani dan banzan qamshin turare da taketa bulawa hancinta,wani abu mai qarfi ya taso ya kama zuciyarta, muryarta ta sarqe,har sai da hakan ya bayyana cikin sautinta,ta jefa mata tambayar muryarta a cushe "Dake da waye?,da yammar nan?" "Ni da daddynsu mimi" tayi maganar tana kallon qofar da zata sadaka da kitchen din,saboda tuni hancinta ya shaida mata wanzuwarsa a wajen,sassanyan qamshinsa daya fara yo gaba. Idanun widad na kansa haka na hafsat,yayin da nasa idanun ke kan hafsat din da tarin kwanukan wanke wankenta,wanda ko ba'a gaya masa ba yasan halin nata tayi,wato tayi girki ta jiqa kwanon,gobe ta bare sabo ko wankakke ta sake wani girkin a ciki. Tuni idanusa suka cika taf da bacin rai,banda wanda ya shaqa daga falo,da kuma dattin daya hanga akan sumar yaransa,ga qurajen zafi da suka fesowa nawwara,tabbacin ba'a kunna musu gen kamar yadda ya bar sallahy,bayan ya aje kudin komai da komai. "Sannu da zuwa" ta fada tana miqewa hadi da sauke zaninta data yaye cinyoyinta "Yauwa" ya fada yana komawa da baya,cikin sa'a ko rashin sa'a,sai ya taka sauran rubabben abincin data kwakwkwafe a kwandon shara,Allah yasa boots ne a qafarsa,yaja da baya ya murje qafar tasa ya fice daga wajen. Cikin shan jinin jikinta ta soma takawa zata bishi,har tayi taku uku saita waiwayo tana duban widad,zuciyarta na cika da kishin kwalliya da sutturar jikinta "Zauna ki kamamin wanke wanken nan ina zuwa" "To" ta amsa mata,babu gardama,ta soma ratsawa ta cikin kwanukan tana tattare hannun rigarta,ta zauna kujerar data tashi,ta fara jan kwanukan tana wank su,mimi na mata hira. Har ta doshi hanyar sassansa saita tsaya,ta kalli jikinta da kyau,ita kanta ta shaida tsami takeyi,sai tayi ribas,ta koma da baya zuwa bedroom dinta,ta kunna heater a gurguje ta saba sabulu ta dauraye da ruwa,ta tsaya gaban mudubin ta ta balbala turare sannan ta zura wata doguwar rigar baqar atamfa,ta dora daurin dankwalinta sannan ta fito. Har zata wuce ta tuna tabar mimi a can,saita koma ta tsaya daga qofar kitchen din tana qwala mata kira,yarinyar ta taso,ta kama hannunta suka bar wajen,tana jefawa widad harara a fakaice "Saikin gane Allah daya ne wallahi yarinya,muje zuwa wai mahaukaci yahau kura". A falo ta samu nawwara,tasha chocolate har ta godewa Allah,ta aje mimi a nan ta wuce kai tsaye bedroom dinsa. Yana tsaye gaban mudubi yana maida maballin wata jallabiyya mai azabar kyau,hade take da wandonta da aka yima aikin zare daga qasa, lallausan qamshinsa daya karade dakin ta zuqa,tana son turarensa matuqa,saidai ko ya bata bata iya jurewa shafawa kullum da kullum Sarai ya hangeta ta cikin madubi sanda take shigowa,amma bai fasa abinda yakeyi ba,hakanan bai waiwayo ba,jikinta ya qara sanyi,ta tako a hankali kanta a qasa,tayi mazauni a kujerar bayansa "Sannu da zuwa ya hanya?" Ta sake fadi "Lafiya" ya amsa mata a taqaice,ya dauki comb yana sake taje kansa,sannan ya daura agogo ya dauki daddumaersa a qagauce "Zanje sallah na dawo,ki gyaramin sashe na" daga wanann ya juya ya fice a dakin,yana jin yadda shegen turarenta daya tsana yake cika dakin,baisan ita din wace irin mace bace,duk abind yake so tofa sunyi hannun riga,kamar ma tana jira yace ga abinda yakeso ta qalubalanceshi,duk wani abu da zaiyi mata don gyara da kyautata rayuwarta yayi amma ita kamar bata maraba da hakan. Da kallo ta bishi,kafin ya gama ficewa,tabi qofar da harara tana jan tsaki "Mutum sai shegen izza da tsari,daga dawowarsa gaba daya ya batamin duk wani lissafi ba,banda ya taho da waccar yarinyar yaushe na gama wanke wanken,na gyara nawa sashen,na gyara nasa?,sannan daga qarshe yacemin abinci yake jira na dafa masa kamar wata jaka,Allah yau saidai kowa yaci takeaway" ta fada tana sake jan tsaki,ta miqe tana kade zanin gadon da tun kafin ya tafi yake shinfide akai ba'a daga ba,kuma ko yanzun bata da niyyar dagawar. *Arewabooks: Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 51 Tun tana wanke wanken na marmari har ta soma ji gaba daya hannayenta sun fara mata zafi,sannu a hankali gajiya gaba daya ta saukar mata,hannunta yayi jazur saboda wankin kwanukan da kuma zafin detergent,tunda tunda uwarta ta haifeta bata taba wanke wanke mai yawan haka ba,da qyar ta samu ta kammala,ta gyara daurin dankwalinta daya sabule ta baro wajen. Babu kowa a falon,bama alamar suna nan,hakan yasa ta wuce zuwa sashenta kai tsaye,bayan ta ciro key din da ya bata a qaramar purse dinta. Idanu a narke ta shiga sashen nata,sai zuciyarta ta karaya,taga kamar zataga latifa,ta tuna wayon data yi mata ranar da zasu bar bauchi,komai yana nan a killace yadda latifa ta barshi,ba wani datti sai 'yan qananun qura dake shiga wajen sanadin babu giftawar kowa,ta zube saman kujera tana share qananun qwalla,itakam tana jin kamar tsanarta akayi,kowa yana gida banda ita?,hakanan ta gaji da zaman,ba motsin kowa cikin gidan,ba alamun kuma zata samu wani abun da zata ci,ta miqe cike da shegen tsoron nan nata cikin sanda ta isa kitchen,ta duba store dinta ta fidda indomie,cikin tsoro da fargabar kada ta cabe irin ta rannan ta kunna wuta ta dora. A kitchen din ta zauna harta dahu,ta juye a plate,tasa fork ta debo ta dandana,sai murmushi ya subuce mata,tayi dadi fiye da yadda ta zata,har abun ya burgeta ita kanta,ta dauki plate din da hanzarin tayo hanyar falo,tana fitowa sai tayi turus da plate din a hannunta,ta manta ba'a kaduna suke ba,ta yaya zata wuce momy hafsat dake gargadinta koda yaushe ta tafi dakinsa?,saita koma ta zauna jiki a salube,ta sanya cokalin ta fara diban taliyar tana ci,ko TV ta kasa kunnawa saboda tsoro,sai taji kamar ana tafiya daga bayanta. Duk da ba'a nutse take ba amma hakan bai hanata jin dadin taliyar ba da gaske,tana ci idanuwanta suna mata nauyi,don haka kafin ma ta kammala bacci ya kwasheta a wajen,ko hannu bata samu wankewa ba. Daga yanayin da ya samu gidan yasan cewa babu wani abinci da zaya samu,don haka koda aka idar da sallar magariba bai shigo gidan ba sai da akayi isha'i,daga nan kuma ya dauki motarsa ya wuce yayi musu takeaway,bai bi ta halin hafsat din ba,don ko kaffara bazaiyi ba yasan ba wanda ya qoshi a gidan ciki harda yaranta,don haka ya hado dasu. Afalo ya sameta ta kammala mopping,tana ta fada dasu nawwara,fadan da bashi da dalili,yasan dai duka bazai wuce akan aikin sharar daya sanyata ba,yaran suka masa oyoyo ya daukesu yayi hugging dinsu,sanna ya ajjiyesu hade da ledar hannunsa yana cewa "Bari naje na dawo muyi dinner ko?" Suka daga kai cikin zumudi da jin dadi. "Ina kuma zaka je?" Ta tambayeshi cikin d'ar d'ar ganin ya kama hanyar fita da leda daya,waiwayowa yayi ya dubeta,bai bata amsa ba yaci gaba da takawa "Kawo nakai mata ka zauna kai kaci naka abincin" ta furta tana matsowa,saidai kafin ta iso ma ya fice abinsa,baisan me yake damun kanta ba,ita idan tayi laifi ma bata yarda tayi bare ta kamo hanyar gyarawa. Sau hudu yana knocking yaji shuru,sai kawai yayi amfani da spare key dinsa ya bude ya shiga. Sassanyan qamshin turarukan da latifa ta tsuma sassan dashi har yanxu yana nan,kamar ma a yanxun ake turara wajen,turaruka masu tsada da kama jiki na asalin shuwa. A yashe ya hangeta saman carfet ta cure waje daya,ya taka a hankali zuwa cikin falon,ya dauki remote ya sanyin ac din,ya ajiye remote din ya maida dubansa gareta,ko pillow babu a kanta,ya ajjiye ledar a hankali a gabanta,sannan ya durqusa yana tunanin yadda zai gyara mata kwanciya. Pillow din ya miqa hannu ya dauko,sannan ya zauna sosai,ya sanya hannuwansa duka biyu ya dagota,sumar kanta data baje ta watsu saman baby face dinta,sosai pink lips dinta suka dauki hankalinsa,bai taba kallonsu da kyau irin yau ba,wani irin sexy lips masu daukan hankali,girarta da suka kusa hadewa da juna ta sake qawata fuskarta da kyau. Ji yayi sunyi mugun kusanci da juna,kamar wanda aka sawa electric shock ya saketa da sauri,ta farka a firgice sanadin sakinta da yayi,jinta kusa da mutum kuma ya sake sakawa ta tsorata da gaske,saboda tasan dai already kafin ta kwanta ta rufe qofarta. Ihu ta sanya sosai a tsorace,yasa hannunsa da sauri ya rufe mata bakinta yana cewa "Ke....meye haka,it's me" jin muryarsa ya sake kad'a mata cikinta,ta tattara qarfinta tana tureshi,dai dai lokacin da hafsa wadda ta saka zama ta biyo bayansa ta turo qofar falon da sauri ta shigo. Da yadda za'a fadi yadda taji a lokacin ya wuce haka,gaba daya ji tayi wani tashin hankali ya rufto mata,widad din a jikin abbas dinta?,sam batasan gabansu take nufa ba,har sai data isa,gaba daya zuciya ta gama gaya mata ta fincikota daga jikinsa ta rufeta da mugun duka ne,saidai tana isa din abbas din yana buda hannayensa widad din ta fice tana sakin dan qaramin kuka,gaba daya a tsorace take, jikinta sai rawa yakeyi tana kallon fuskar hafsat wadda ta ritsata da idanu,hantar cikinta ta gama kadawa kamar wadda aka kamata da kwarto,yanxun me zata cewa mummy?,duk yadda take kiyayewa da yin takatsantsan yau ta kamata a jikin wani. Mugun kallon data watsawa widad din ya sanyata cikin sauri da kuma rawar murya tace "Wallahi mummy ina cikin bacci,bansan ya shigo ba...." A nutse abbas dake tsaye ya waiwaya ya kalli hafsat din,da sauri ta dauke rikitaccen kallon da takewa widad ta maida ga abbas din cikin rudewa,yarinyar tana son balle mata liqin da tayi,sukayi kallon kallo na sakanni,kallon data hangi ayoyin tambaya masu yawa a idanun abbas din,ta hadiye wani yawu mai tauri,cikin qasa da second goma dabara ta fado mata,ta maida dubanta ga widad din "Ni Matsalata dake shegen tsoro,kinsan dai gidan nan babu wanda zai shigo,dagamu sai mu,ki dinga addu'a idan zaki kwanta kinji" tayi maganar cikin karyar da harshe,saita matsa tana zaunar da widad din sosai,amma qasan zuciyarta a mugun matse yake,kada fa ya zamana abbas ya fara latse d'iyar mutane,ta miqe sosai ta tsaya tana dubansa "Abban mimi.....ka dinga haquri,kaga dole ayi mata uzuri,akwai quruciya sosai a tare da ita" lumshe idanunsa yayi bisa fuskar hafsan,shi baima gane abinda take fada ba,gaba daya bugun zuciyarsa ne yake neman sauyawa,saiya maida dubansa ga hafsat din dake matsar qwalla "Ga dinner dinki nan,ki taso ki rufe qofar" ya furta yana juyawa cikin mutuwar jiki,sai hafsat ta biyo bayansa tana cewa "Kisa key ki rufe qofan falon kinji,saiki rufe ta bedroom din ma,sai da safe" "To Mommy" ta fada,cikin ranta tana jin tazarar son da hafsat din ke mata abbas din bai kama koda kwatarsa ba,haka tasa muqulli ta rufe qofar sannan ta dawo falon,tsoro ne fal ranta da zuciyarta,tana jin kamar ta bisu,amma kuma haushinsa takeji,don me zai dinga taba mata jikinta,a gurguje ta tattare komai ta wuce bedroom dinta,shima sai data saka key ta rufe da kyau sannan ta canza kayanta zuwa na barci ta haye gado,yau ko.wankan ma bata tsaya yi ba. Ta jima tana juyi ciie da tsoro, duqunqune cikin duvet,wannan gidan yafi na kaduna girma,hakanan gidan kaduna dakunan kusan a kusa da juna suke,tana jin kusancin abbas dake dakinsa a jikinta,sabanin wannan da kowa bangarensa daban,cusa kanta ta sakeyi cikin duvet din,hancinta na zuqo mata qamshin turarensa,wanda ya kama rigar jikinta radam,sai taja tsaki,haushi na cika mata zuciya "Dan iska" ta fada tana murguda baki. **********washegari bata bude qofarta ba har sai dasu mimi sukazo suna buga mata,taji dadin ganinsu,suka dinga wasansu a falonta,ita kuma ta shiga kitchen ta dafa musu jallop din taliya. Da dan gyare gyare cikin girkin,to amma da yake ba wani cimar kirki yaran suke ba sai abincin ya musu dadi sosai,suka zauna sukaci kaman ba gobe,itama cikinsu ta zauna,sunaci suna surutu tana tayasu,sai da suka qoshi sannan mimi tace "Mummy ce ta aikomu,tace kiyi mana wanka,bacci suke wai basu tashi ba" bata ji komai ba,don zamanta da yaran ita dadi yake mata,sannan ita kallon hafsat din take kamar anty deena,don haka ta kunna heater,ta tara ruwa mai dumi sosai,tayi musu wanka kuwa fes,ta shafa musu manta sannan ta dubesu "Ku karbo kaya wajen mommy din a saka muku" da gudu suka fella suka fita,saidai basu jima ba sai gasu sun dawo da kayansu a jikinsu "Mommy tace kizo" jikinta ta kalla,da da hali wanka zatayi kafin ta fita din,don gaba daya bata jin dadin jikin nata,saboda bata samu yin wanka jiya ba,amma kafin ta gama tunanin maganar mimi ta katse mata "Yanzu yanzu wai tace" mayafin doguwar rigarta ta zura tabi bayansu suka fice. Sallamar widad din ta sanyata ninke kudin da take irgawa ta daga bayan pillow dinta ta xubasu tana amsa sallamar,kudin da abbas din ya bata ne ta bawa widad din,anyi rasuwa yana sauri ya fita bai samu leqata ba. Sanda ta karba kudin kamar zuciyarta tayi tsalle ta fito,ita din gotai gotai da ita zai raba musu kudi dai dai da yarinyar da ta haifeta kota kusa haifar ta? "Badai ya fita din ba,meye abun damuwa" zuciyarta ta gaya mata,wannan ya sassauta fushinta,don tayi imanin sisin kwabo ba zata bata ba a cikin kudin. Har qasa ta tsugunna ta gaidata kamar yadda ta saba,saita koma gefe tayi tsaye a darare,ba tare data kalleta ba tace "Kitchen zaki shiga ki gyaramin,idan kin fito saiki fara da falo, bedroom dina kuma idan na gama abinda nakeyi zan miki magana saiki gyarashi,zan gyara dakin yaran da kaina" ta qarashe maganar tana debe kudinta,sannan ta wuce dakinta abinta. Hakanan widad ta zage ta cashi aikin da zata iya cewa bata taba kamarsa ba,ta gyara kitchen tayi wanke wanke,ta dawo falon ta gyarashi tsaf,sannan tayi knocking qofar bedroom din. Tana kwance abinta daga saman gado ta amsa da "Shigo" a darare ta shigo da sallama,a kashingide take tana chart "Mommy na gama" "Gyara abinda ya samu,idan na tashi kya gyara gadon,ko na gyara da kaina" cikin d'ararewa ta fara kwashe tarkacen dake zube a qasan dakin tana hadesu waje guda. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 52 Har ta gama gyaran dakin kwance saman gadon tana chart "Na gama" ta fada jikinta yana amsawa da wani irin ciwo,saboda wannan shine karo na farko data fara aiki mai yawa haka "Akwai 'yan kayan da zaki daurayemin.....amma,bari nayi kiranki idan na tashi" da to ta amsa,ta juya tana fita a dakin,tana jiyota tana cewa su mimi "Ku bita da Allah kuban waje na huta" da saurinsu kuwa yaran suka biyo bayanta. A falo ta barsu,ta shiga bedroom ta zarce toilet ta hada ruwan zafi tayi wanka,ta hado da alwala,farkon mkhtarin sallar azahar din ya shiga,sai kawai tayi sallarta,tana shafa mai gajiya tana bin jikinta,da qyar ta qarasa,ta shiga kitchen ta hada tea ta hado da bread ta dawo ta zauna tana ci,bata iya shanyewa ba taji ya fita a kanta,sai ta dire cup din ta wuce daki tabi lafiyar gado,bata jima ba kuwa bacci yayi awon gaba da ita,saboda uban gajiyar data tarawa jikinta. Tana tsaka da baccin taji ana dan dukan qafafunta,idanunta a rurrufe saboda nauyin da sukayi mata ta budesu kadan,mimi ce da nawwara "Nawwara ce tayi pupu,mommy tace ki wanke mata" idanu tadan runtse,baccin sam bai isheta ba,amma tana jin ya zame mata dole ta tashi,hakanan ta miqe ta cirema nawwaran pampers ta wanke mata,ta maida mata wandonta,lokacin sallar la'asar ya shiga,don haka ta daura alwala ta bada farali,sanda ta idar cikinta yayi wayam,dole ta shiga kitchen,ta rasa me zata dafa,ta jima a tsaye tana tunani,daga bisani ta raya gwada dafa jallop rice. Nutsuwa tayi sosai ta fara hada jallop din,sai data gama hada komai ta rufe Sannan ta koma ta zauna cikin kitchen din tana taya su mimi wasa,wayarta dake daki ta dauki ringing,sai ta fito tabar kitchen din ta wuce bedroom din,ta dauko wayar dake saman madubi ta duba me kiran. Anty deena ce,saita saki murmushi ta koma bakin gadon ta zauna,daxun da safe da sukayi waya da ummun take cigiyar anty deena di,tace an dauke mata waya ne "Shalelen ummu" baki widad ta tura gaba "Ni wallahi ba haka bane anty deena,duk ku manta dani,kun kawo ni nan kun ajjiyeni" murmushi ta saka "Banda abinki widad,ashe muma ba'a sonmu kenan, kowacce mace 'yar wani gida ce daman ai" "Amma ku ai kuna kusa da gida,kuma ana zuwa,ni kam ba wanda yazo,ummu ma taqi zuwa" "To daga aure weedad sai muhau zirya?,kiyi haquri kinji?" Kai ta gyada kamar tana a gabanta ne,saidai anty deena ta fahimci ta amsa ne tunda taji shuru "Komai lafiya ko?" Ta jefa mata tambayar,sai taji kamar ta tsokano ta,idanunta suka hada qwallar da itama ba zatace ga dalili ba. Ta bude baki tana shirin yin magana aka buda qofar dakin nata,ta daga ido tana duban bakin qofar dakin,hafsat ce ke shigowa,sanye da bubu na wani material,ta qulle kanta da dankwalin lace. Zubawa juna idanu sukayi dukka su biyun,abinda yasa hafsat din taji ta tsargu,bata kuma yarda da wayar dake kunnen widad din ba,ita kuma widad din taji wani mugun tsoro ya saukar mata,hafsat din tayi mata wani mugun kwarjini,tana ji anty deena na sake cewa "Hello weedad lafiya ko?" Hadiye wani yawo tayi mai cike da tsoro "Eh anty" muryarta ta sauya ba kamar dazun ba,tabi hannun hafsat da kallo wadda ta miqa hannu kai tsaye tana zare wayar daga kunnenta,ta duba me kiran sannan ta saka a nata kunnen,dai dai lokacin da anty deenan ta sake cewa "Idan da wata matsala ki fada kinji,in sha Allah zan baki shawarwari,basai kin kira ummu kin daga mata hankali ba,ba kuma sai kowa yazo ba" idanu hafsat din ta sauke mata,sai ta dan daga wayar daga kunnenta nesa kadan sannan tace "Bani mana mu gaisa" tamkar a lokacin ta karbi wayar,sannan ta mayar kunnen tana sallama. A sake suka gaisa da anty deena din,don basu manta da yadda ta tarbesu ba sanda suka kawo widad din ba,sun tafi suna yabonta,fargabarsu kuma na shigar widad din gidan kishiya tana raguwa "Da fatan qanwar tamu dai bata da matsala?" "Ah wallahi tana da hankali ga nutsuwa,komai lafiya alhmdlh" cikin jin dadi anty deena tace "To ma sha Allah,muna godiya sosai" "Aiba komai,yiwa kaine ai,bari na baku guri ku qarasabmaganarku" ta fada tana miqawa widad din,jiki a mace ta karba wayar,maimakon ta fita din kamar yadda ta cewa anty deena,sai kawai ta samu waje ta zauna nan saman madubin widad din tana qarewa dakin kallo,kunnuwanta kuma suna sauraren abinda take fadi,shegiya......shuwa ko sadakar yalla,sharrinsu yawa gareshi,yarinya mitsitsiya amma dakinta yana qamshin da nata dakin bai taba yi ba tun zamanin amarci?,take kishi ya kamata,ta maida dubanta ga widad din sanda suke sallama da anty deena. "Wani abu kika gaya musu?" Ta tambayeta tana hade rai tsam kamar tana magana ne da mimi,da sauri ta girgiza kai "A'ah wallahi mommy,muna fara waya ma kika shigo" kai ta jinjina sannan ta sake cewa da ita "Ko.meye yake damunki ni ya.kamata ki fara gayawa kina jina?,tunda yanzun mune muke gida daya dake kinji ko?,dani zaki dinga shawara" kai ta daga,sai hafsat din ta sako qasa tana sake nazartar dakin "Wannan turaren kuma da kike bulbulawa dakin,so kike.aljannu su tare miki a daki su dinga hanaki bacci suna zuwa da daddare suna tsorataki?" Dukka manyan fararen idanuwanta weedad ta fidda waje,iya maganar da hafsat din kadai tayi ta tsoratata matuqa,tsoro sosai ya shigeta,ta fara kada kai "To ki daina sakawa,kibar dakinki a hakama" "Ba sakawa nake ba,haka dakin yake ai" ta furta muryarta tana rawa,a fakaice ta jefa mata harara ta yatsina baki, shegiyar yarinya sai shegen sanabe da kidifiri "To shikenan,ki taso ki wanke uniform din mimi,idan ya bushe kiyi ironing dinsa" tana gama bada umarnin tayi gaba abinta,ai kafin ta kammala fita ma ta biyo bayanta,saboda zancan aljanun yayi mugun bata tsoro,a tsaitsaye ta kashe girkinta dake kitchen,bata ko tsaya dubawa ba tayo sashenta. Sai data gama komai kamar wata 'yar aiki,harda tsarabar sake goge mata falo dasu mimi suka bata,kafin dare ta gaji tubus,tana son komawa amma tana jan jiki,don har yanzu tsoron maganar mommy hafsa dince a ranta,saidai dole ta koma din,tunda a nan din ba wani sakin jiki takeyi ba sosai,kasancewarta mutum mara saurin sabo. Komai da takeyi da takatsantsan take yinsa,ta shiga kitchen ta juyo abincinta ta wuce daki dashi,sai da ta zauna taci mai yawa sosai,don har ita kanta tana mamakin yawansa,amma ba abun mamaki bane,saboda kusan yini tayi da yunwa,data gama din saita tube kayan jikinta ta daura towel ta wuce toilet. A parking lot na gidan ya tsaida motarsa,ya fito hannunsa dauke da ledar da uncle muhsin ya bayar yace a kawowa widad din,don jiya ya dawo daga kano,saqo ne daga mutanen gida,kowa da abinda ya bayar a kawo mata,amma shi abbas din baisan meye da meye a ciki ba,kawai dai ya karba ya taho dashi. Yau din tunda ya fita bai zauna ba,daga gidan hajiya ya dauketa sukayi ziyara sosai bayan sunje gidan makokin,basu dawo ba sai magrib,daga nan kuma yayo gida. Koda ya kashe motar kansa tsaye sassanta ya nufa,hankalinsa yana can,daya fita hajiya na tambayarsa lafiyarta,sai yaga kamar bai kyautawa hajiyan ba,don baisan ya tata tashi ba,wannan dalilin yasa hankalinsa ya dauko da zuwa sashen. A nutse ya buda qofar da sallama abakinsa cikin wannan kwantacciyar muryar tasa mai taushi,falon ba kowa,saidai wannan sassanyan qamshin da ya zaunewa falon daketa faman kadawa,jikinsa ya bashi tana dakinta,don haka kai tsaye ya nufi dakin. Sanda take fitowa daga bandakin lokacin shima ya turo qofar dakin ya shigo,bata ganshi ba saboda ta juya a hankali tana jan qofar toilet din tana rufeta,don ko kadan bata qaunar wani babban motsi,saboda yadda zuciyarta keta rawa,a tsorace take sosai,ta sauke ajiyar zuciya ta fara takowa tsakiyar dakin,sai a sannan idanuwanta suka gano mata shi. Baisan me ya tsaidashi ba daga bakin qofa ya kasa qarasowa ciki,yasan dai tunda ya dora idanuwansa a kanta yaji kamar an tsaidashi a wajen..... widad kuwa baya taja da sauri sanda sukayi ido hudu,jikinta ya fara rawa, idanuwanta suka fara tara hawaye,abu na farko daya zo mata a rai aljanine ya shigo mata part yayi mata suffarsa,fararen kaya ne a jikinsa na wani lallausan yadin filtex,hakanan jakar hannunsa itama farace....an kuma gaya musu a tatsuniya aljanu suna son shigar farare,don haka ta fara hawaye tana fadin "Wayyo ummu na.....don Allah kayi haquri,wallahi na daina,don Allah kada ka yimin komai" haushi dariya da kuma takaici suka qumeshi,yau kuma shine abun tsoron?,lallai abun nata babba ne,quruciyar tata ta gaske ce,rasa abunyi yayi,ta kuma tubure sosai tana masa kuka da magiya,ya lumshe idanu hadi da sauke numfashi ya kuma furzar da iska,ganin yadda yaketa qoqarin yi mata bayani amma ta gaza fahimta. Idanunsa ya sanya cikin nata ya kira sunanta da qarfi,tamkar numfashinta zai fita daga qirjinta ta sandare a tsaye "Kina motsawa anan inda kike zan batar dake,ki tsaya na iso gabanki saina tafi na baki waje" kai ta shiga kadawa,kamar zata saki fitsari a wando,qasan ransa kamar dariya zata qwace masa amma takaici ya hanashi,ya ajjiye ladar hannunsa saman madubi,ya soma takowa idanuwansa a kanta. Yana zuwa gabanta ya hade tazarar dake tsakaninsu,ya buda hannayensa gaba daya ya lullubeta tsam cikin qirjinsa,qamashin shampoo data wanke kanta hadi da shower gel dinta ya nutsa can cikin hancinsa,ya lumshe ido wani numfashi na fusga daga qasan zuciyarsa mai wani irin nauyi "Ya Allah,what's happening?" Ya fada can cikin ransa,jin yadda gaba daya jikinsa ya saki,abun mamaki baiyi abinda ya zata zatayi din ba,a maimakon haka saita tsaya cak a jikin nasa,wani irin nutsuwa taji tana saukar mata, tsoron yana gushewa,ta lullube idanunta sosai,kukan yana dauke mata,ajiyar zuciya tana maye gurbin kukan. Sun jima a haka,kusan mintuna biyar ba wanda ya zame jikinsa daga dan uwansa,dole tasa ya fara neman rabata da jikinsa,saboda yadda dumin jikinta ya fara ratsa nasa jikin,tudun matasan qirjinta ya fara masa barazana,har numfashinsa na qoqarin sauyawa,baiyi mamakin faruwar hakan ba,saboda yasan yana cikin wani irin situation,bako da yaushe yake samun yadda yakeso daga hafsat ba, saboda dan uban qazantarta dake hana masa rawar gaban hantsi koda kuwa ta bashi dama,lokuta mafi yawa kuma takan tsuqe,tare da kawo masa qorafe qorafen "Ni na gaji yau wallahi......bacci nakeji......bani da lafiya fa....." Ko sau daya bai taba waiwayawa yabi ta kanta ba,ya gwammace ya kama kansa,don baijin zai iya begging dinta akan abinda yake halalinsa,sannu a hankali ta fara cire masa sha'awar ta kwata kwata daga zuciyarsa,sai ya dauki lokaci bai waiwayeta ba,abun har ya fara zame masa jiki. Kamar raqumi da akala haka ya zaunar da ita gefan gadon,ya jawo kujera ya zauna yana fuskantar ta. Nazarinta ya fara,ya zuba mata idanu yana kallonta tun daga santala santalan cinyoyinta zuwa jiqaqqiyar sumar kanta da ta fara tsanewa,idanunsa suka tsaya ga fafaren kafadunta dake cikin farin towel,a lokacin ne hankalinta ya dawo jikinta,ta soma curewa waje daya sabbin qwalla suna cika mata idanu "Mene ne?" Ya tambayeta ganin yadda hankalinta ya tashi lokaci guda "Kaga fa....bani da riga" furucin ya qaraso fitowa da hawaye masu dumi daga idanunta,karon farko da yajin haushi ya kamashi "To sai menene?" Kuka ta fashe masa dashi tana nuna masa hijab dinta "Don Allah ka bani hijab dina na saka,Allah ummu ta hanani" "Tace miki harda ni kada na ganki a haka?" Ya jefa mata tambayar,yau kam sai ya qure tunaninta,kai ta kada "Ban sani ba,ka daina kallona don Allah" ta sake fada tana kuka,shuru yayi yana duban baby face dinta dake jiqe da hawaye,ya gama karantarta,a haka ta taso ba tare da tasan cikakkiyar ma'anar aure ba,kuma ko a yanxun indai yanason ta fahimci abinda zai gaya mata saidai ya bata hijabin yadda takeso,baisan dalil ba,sanda ya miqa mata hijab din,sai yaji baya buqatar ta saka,amma haka ya lumshe idanunsa harta gama sakawar,sannan ta tsareshi da ido tana jan majina. Shima ita din yake kallo,kafin daga bisani ya kauda dubansa,ba lallai ma ta gane meye miji ba bare aure,sai ya ajjiye wannan maganar ya soma mata wadda yake ganin tafi muhimmanci akan wadda da farko yaso yayi mata ita. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Page 53 "Daga yau,duk sanda kike ke daya a nan,ki kunna tv din falo,ki kamo saudi qur'an.....kinjini ko?" Ya furta yana kama kunnensa,saita gyada masa kai "Good.....sannan,baki iya addu'a ba sanda mutum yaga abinda ya tsoratashi?" "Na iya" ta fada a sanyaye "To daga yau ita zaki dinga ya,kada na sake ji ko ganin kina ihun nan......ki fahimta?" Nan ma kai ta gyada masa,ya jijjiga kai,shuru ya ratsa na second biyu "Kin yini lafiya?" "Ina wuni" ta maida masa da gaisuwa da muryarta dake dan rawa har yanzu "lafiya lau" ya amsa mata yana miqewa "Ga saqo can daga kano" fadin kano din da yayi ya sanyata warwarwwa ta farat daya,ya bita da kallo sanda yaga ta doshi kedar fuskarta na haske da murmushi,sai ua juya ya fice daga dakin,yanata juya al'amuranta a ransa,raino ne hajiya ta bashi,raino kuma me wuya da baisan sanda zai gamashi ba. Sanda ya isa sassan hafsat yayi mamakin ganinsa a tsaftace,zai iya cewa ya manta lokaci na qarshe da yaga komai a muhallinsa a sassan nata,baiyi dai magana ba,amma kuma hakan ya masa dadi, zuciyar sa kuma ta sauka,akaci sa'a a yau din ta danyi wankan dare,ta kuma qure adaka da daya daga cikin tsadaddun suturun da yake mata,don tana son ta sake amintar dashi,ta kums kore kowanne zargi daga ransa,uwa uba kuma akwai kudaden da takeson karba daga wajensa a daren. *********To tsahon kwanaki ukun da sukayi a bauchin widad ita kewa hafsat din dukkan wasu aikace aikacen sassanta,kama daga wanke wanke shara da wankan yara da dyk wata lalurarsu,koda bata shigo sashen ba zata shigo da kanta ta fiddota,idan abbas yana gida yafi zama sashensa,takanntattara ta bishi can,bata fita sai idan yasa qafarsa yabar gidan shima. Baisan meke faruwa ba,tunda ya sani akwai alamun tsoronsa sosai tattare da yarinyar,bayason ya dinga matsa mata ko takura mata,ganin yadda taje sakewa walwalarta take qaruwa idan tana tare dasu mimi sai ya saki komai shima,wuni take hidimar sassan hafsat din,girki kawai hafsat din keyi,itama widad din taje tayi nata. Quruciya qarancin shekarunta da rashin wayo ya sanya bata dauki hakan a bakin komai ba, saidai wasu lokutan tana jin aikin kamar yayi mata yawa,amma bata fasa yi mata ba,don a ganinta gaba take da ita,sannan tana samun sassaucin mugun tsoron da hafsat din ta dasa mata a ranta,tsoron abbas din da koda yaushe take zayyana mata abu kaza babu kyau....abu kaza babu kyau,ki tsare mutuncinki,dukka wani halali ta haramta mata shi,tayi amfani da wayo da dabararta da shekaru data daranma widad din. Ranar lahadi da yammaci suka tattara suka bar bauchin,kamar wancan karon,wannan karonma wani abune ya tsaya mata a rai,ta zubawa motarsu idanu sanda take fita daga gidan,zuciyarta a mugun quntace,saidai taci alwashin tafiyar tasu babu abinda zata bari ya sauya,data koma cikin gidan kuma ta sake qarewa sashenta kallo taga yadda ya fara komawa hayyacinsa,sai taji inama widad din a kadunan take,ta tuna gobe fa itace zatayi dukkan hidimar da widad din ke mata,ga shirin makarantar mimi,ranta sai ya baci,haka ta wuni tana qunci tana kuma jibgar yaran,saboda kwanaki biyun bata saka hannu a hidimarsu,duk wata lalura tasu widad dince,wanka tsarkin kashi abinci da sauransu,su kansu yau din duk sai suka zama sukuku,kada ma mimi taji labari,minti daya biyu saita kira sunanta,saida hafsat din ta fara doke mata baki sannan ta samu salaama. Tun a mota widad in ta dinga bacci,baccin gajiyar data debo a kaduna na ayyukan wahalar hafsat,koda suka isa gida ma sai daya tasheta,ta murza idanunta ta buda motar ta fito a kasalance tayi sassansu. Sallar magariba da isha'i kawai tayi ta sake kifewa a dakinta,sanda ya shigo gidan tayi nisa a duniyar bacci,sai ya maida mata qofar dakin nata ya rufe kawai ya sanya ledar takeaway din a fridge don kada ya lalace,mamaki yana dan kamashi da irin baccin da takeyi,kamar wadda bata samun baccin kirki. Washegari da zai miqa ta makaranta ma kusan a makare suka fita,don sai daya shiga dakin ya tasheta sannan ta samu ta shirya a gurguje,don ko gyaran gidan bata samu yiba sai da aka taso daga makarantar,samuel ya aika ya daukota a motarsa ya ajeta gidan,tana shigowa suna cin karo da maami matar gidan,wadda yaranta duka maza ne,shi yasa ba wanda ke shigowa sashen "Yaushe kuka dawo haka babu sanarwa?" Ta tambayi widad tana qare mata kallo cikin uniform din da suka bala'in karbarta "Jiya da daddare ne,uncle yace na shigo na gaisheki ma daman idan an taso daga makaranta" "Oh....makaranta kenan aka fara zuwa,aji nawa?" Ta sake tambayarta "S.s one" kai ta gyada,lallai namiji,shan koko daukan rai,banda qalata irin tasa,itadai bataga abun daukarwa kai wannan dawainiyar ba,amma wataqila kyan yake rudarsa "To Allah ya taimaka" "Ameen,a dawo lafiya" ta fada tana yin gaba zuwa cikin gidan,ita kuma ta amsa tana shigewa motarta,idanuwanta akan widad din,kamar zata gayawa hafsat sai kuma ta share,don bataga abinda yarinyar tayi mata bama,kawai dai hali irin na mata,taya kishin da bai shafeka ba. Sallar azahar kawai tayi ta fara gyaran gidan,duk da muguwar gajiyar da tayi,ta tuna sanda take dawowa daga makaranta,ummu tasa an hada mata komai,saidai tayi wanka taci abinci tayi shirin islamiyya,take qwalla ta kawo a idanunta,taji kamar ta watsar amma ba zata iya zama a datti ba,tsahon rayuwarta ko kadan batasan dauda qazanta ko datti ba,ummun nada wata irin mugu muguwar tsafta,kowa ya shaida,hakanan duk matan gidansu babu qazama. Tana gama mopping taji ana saka key za'a buda qofar sashen,ta tsaya a dan tsorace tana kallon qofar,har ya kammala budewa ya tura ya shigo. A kanta idanuwansa suka sauka,yayin da kuma ta sauke ajiyar zuciya tana jin tsoronta na zagwanyewa,baisan yadda akayi murmushi ya subuce masa ba,don ya gane tsoron nata taji da taba qofar da yayi,itama sai murmushin ya kubcewa fuskarta,ta kuma ji yar kunya ta kamata,tayi qas da kanta tana tambayar kanta me yasa ta fiya tsoro haka "Matsoraciya kawai" ya fada a hankali,murmushi ta danyi sannan ta turo qaramin bakinta gaba a shagwabe,kwatankwacin irin yadda takewa ummu,sai ya samu kansa da binta da kallo,batace komai ba shima haka,ya zauna hannun kujerar falon yana goye da hannayensa a qirji,lumsassun idanunsa nakan dan qaramin bakinta "Me kika ci?" "Ni?" Ta tambayeshi tana fidda idanu waje hadi sa taba lips dinta kamar mai tsoron wani abun, murmushi ya sake subuce masa "Eh me kikaci baki ajjiyemin ba?" Fuskarta ta narke a shagwabe "Nifa banci komai ba uncle,yunwa ma nakeji" ta fada tana shafa cikinta,shafaffen cikin nata yabi da kallo, idanuwansa suka kai har kan qugunta daya fito sosai ta cikin skeet din material na jikinta,ya janye idanunsa yana sauke numfashi,hirar da abokan aikinsa moses jackson da andrew sukayi yau ta fado masa a rai,har a lokacin suka cika shi suka kuma dameshi ya nemi tashi ya basu guri,sai suka dinga masa dariya suna tsokanarsa,ya sansu sarai,su din mayun mata ne,daya daga cikin abinda yasa ko kusa baya bari sukai ga ganin iyalinsa "Ina zuwa,bari na fito sai naga yau me za'a koya" sosai taji dadi,don har hakan ya bayyana saman fuskarta,tana son taga ta iya kalolin girke girke,saboda zumudi a falon ta zauna tayi jiransa,ba jimawa sai gashi ya fito. Sauri tayi ta dauke kanta sanda ya fito din,boxer ne a jikinsa sai wata armless shirt farare,kayan sun masu kyau sosai,saidai sun fidda qirar jikinsa. Har ya kusa isa kitchen din yaji bata biyoshi ba,sai ya waiwayo yana dubanta,tayi hanzarin sake dauke kanta gefe tana turo baki,shi wasu abubuwan idan yayi kamar baijin kunya wai?. "Ko baki shirya ba?" Ya tambayeta yana tsareta da idanunsa da suka rusuna yau din qwarai,kai ta girgiza ta kuma amsa masa ba tare data kalleshi ba "Na shirya.....amma.....amma" sai kuma ta kasa qarasawa "Amma me?" "Ka saka kaya don Allah mana" murmushin da bai shirya bane ya qwace masa,ya kalli jikinsa sannan ya dawo da dubansa kanta "Wannan meye a jikina idan ba kaya ba?" "Amma uncle,kalli gafarka kalli hannunka fa,ummu idan su yaa ma'aruf suka fito haka fada take musu fa" ta fada a shagwaben nan nata kamar zata saki kuka. Lallausan murmushi ya subucewa fuskarsa,for now yana ganin ya kamata ace ta fara sanin bambancin mutanen gidansu dashi,wannan yasa ya fara takowa a hankali cikin lallausan carfet din falon,bata lura dashi ba sai ganin mutum tayi dab da ita. Gabanta ya fadi,sai taja baya kadan,bai damu ba ya zauna a gabanta saitin qafafunta yana kallon idanunta dake cike da quruciya,ta kuwa bata fuska sosai,gabanta yanata faduwa "Akwai bambanci tsakanina dasu yaaya ma'aruf da sauran duk 'yan gidanku,ni mijinki ne,na biya sadaki an daura min aure,ni dake ya halatta muga komai na junanmu,mu taba juna,mu kwana guri daya....muci abinci tare,na ganki a duk yanayin da kike....koda tsirara kuwa....." "La ilaaaaa" ta fada da qarfi hade da wani irin kuka,idanunta a kansa, tsoronsa yana shigarta,ta kwashe qafafunta ta mayar saman kujerar kamar mai shirin zurawa da gudu. Wata dariya ta bashi,wadda a wannan karon ya kasa riqeta sai daya dara,hannunsa saman bakinsa yana qoqarin controlling na dariyarsa,he don't know what to do next kuma.....he don't know how to explain her, tabbas goyon kakace ta gaske,kuma symptoms ne na cewa ta samu tarbiyyar qwarai. "Shikenan,is okay,ya isa,bazan kalli jikinki ba,amma sorry for saying that.... shikenan?" Da qyar ya shawo kanta suka shiga kitchen din,yana hada girkin yana nuna mata kamar yadda suka saba,saidai sam taqi sakewa dashi,yana matsowa take komawa baya,gashi shi ba gwanin hira ba,biyu ta hadu,da haka dai ya dinga nuna mata har suka kammala. Ita ta zuba abincin a warmers takai dining,ta gyara kitchen din,ko kafin ta fito har yayi alwala ya leqo yace mata ya wuce masallaci,don haka itama tana gamawa alawar tayi,tayi sallah sai kuma ta dawo falon ta zauna, maimakon taci abincin amma sai taji ba zata iya ci ba har sai ya dawo,hakanan ta zauna zaman jiransa,wayarta na hannunta tana game tana dakon shigowarsa. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 54 Tana tsaka da game din taji mararta ta murda,ta dakata tana zare idanu jin wani abu mai danshi ya fara fitowa ta jikinta,gabanta ya fadi,kada dai ace wannan jinin ne da bataso yazo mata?,yanzu ya zatayi?,yi na qarshe da tayi suna tare da latifa,hankalinta a kwance yake,ta dinga kula da ita da ciwon mararta. A tsorace tadan miqe don duba jikinta,sai tayi sauri ta koma ta zauna saboda mararta data murda mata,ta dafe marar tana jin yadda danshin ke biyo jikinta,hankalinta ya tashi sosai,kawai sai kuka yazo mata,tana ganin kamar ba zata iya ba. gumi ya fara yanko mata ya gauraye da hawaye,ta soma jan majina tana raba ido. Sallamar da yayi cikin falon ya sanyata sake tsorata,sai taji kamar ta tashi ta zura da gudu,idanunshi a kanta,cikin mamakin yanayin da ya ganta a ciki,itama shi take kallo kamar wacce ta aikata wani mummunan abu. A nutse ya qaraso,hannayensa zube a aljihun wandonsa "What's happening?,lafiya?" Tsareshi taci gaba dayi da idanu,saidai qwalla ta cika idanunta fal,har bata iya ganinsa sosai,kallonsa take kai tsaye,kamar mai tsoron wani abu dake a jikinsa,maimakon ta amsa masa sai hawayen ya fara saukowa,ta sake dora hannunta saman mararta dake qara murda mata. "Me ya faru ne?" Ya sake maimaita tambayar yana sake qoqarin karantar fuskarta,hawayen dai taci gaba da fitarwa,a hankali idanunsa ya sauka saman hannunta,yadan kalli wajen na tsahon wasu mintuna,sai ya matsa gaba a hankali yana qoqarin miqa hannunsa,sai kuma ya janye yana duban qwayar idanunta "Ciwo cikin yake miki?" Kai ta gyada masa,Hawaye na sake saukar mata,sai ya sake matsowa yana cire hannunsa guda daya daga aljihunsa "Oh sorry....sannu,tun yaushe?" "Yanzu" ta fada a narke, zuciyarta tana karyewa,saboda komai yayi mata tana kallonsa banbarakwai,don ba haka ummu ta saba mata ba,indai tace bata da lafiya gaba daya komawa take kamar jinjinniya a wajen ummu,ta yita tattarota tana langabe mata a jiki,takanyi kamar ta maido ciwon a jikinta "Muje kici abinci,sai mu fita na kaiki kiga likita ko?" Kai ta girgiza da sauri,don ita bata qaunar ma abinda zai sanya ayi mata zancan asibiti,bata qaunar magani sam sam sam,babban abinda yake saka a gansu a rana ita da ummu kenan "Why.....zaki zauna ne a gida cikin yana miki ciwo?" "Ai zai daina" ta fada muryarta na rawa,saboda yadda ciwon ya fara mata azaba da gaske,wannan shine karo na biyu daya taba mata haka,duk da cewa duka duka period din nata ma wannan shine yinta na hudu. "it is not possible ki zauna da ciwo,oya......taso kici wani abun ko kadanne idan ma ba zaki asibitin ba" ya furta yana miqa mata lallausan hannunsa mai dumi,wanda ya wadatu da sassanyan qamshinsa. Hannun ta kalla sannan ta rintse idanunta da gaske tana jin yadda ake kartar mararta,yadda tayin sai ya tuna masa koda wasa ba zata taba yarda intentionally su hada hannu ba,don haka kansa tsaye ya miqa hannu ya kamo.hannunta guda daya,ya kuma dagota gaba daya. Luuuuu ta tafi jikinsa ba tare data shirya ba saboda wani azabar murdewa da marar ta sakeyi fiye da dazun,kamar numfashin ta zai bar gangar jikinta,take ta zabi bin gangar jikinsa ta yiwa kanta madogara,tana gama samun kyakkyawan masauki saita saki kuka tana kiran sunan ummu,hannayensa ya saka gaba daya ya rufeta da kyau cikin jikinsa. A yadda ta samu masauki me kyau cikin jikinsa ya sanya hatta da bugun zuciyarta da kai kawon numfashinta tana jinsa sosai cikin jikinsa,kamar jininsa suke bi cikin kowacce bugawa da zaiyi. Sunkuyo da tasa fuskarsa yayi ta gefen fuskarta dake kwance kan qirjinsa da yake ya fita tsayi sosai ya cusa tasa fuskar yana leqata,wani irin kuka take a hankali hade da sheshsheqa,hucin numfashin ta ya daki fuskarsa,sai ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na tashi,ya sake riqeta sosai zai motsa,saita kuma qanqameshi tana sake sakin kukan,abinda ya sanyashi kusan daskarewa a wajen,gaba daya ta manna masa jikinta da kyau,lallausar fatarta takai ko ina a jikinsa ba tare data sani ba,ita din kuma tayi hakane saboda batason su motsa daga wajen,ta tabbatar ta bata wajen da jini,bataso kuma ya gani,kunya takeji,da wanne ido zata kalleshi?. "Let's move from here,mu koma daki ki kwanta na fidda mota kiga likita,jikinki shacking yakeyi" yana fada ya sunkuya kawai ya dauketa cak,bata da sauran zanbi sai kawai ta boye kanta cikin jikinsa,bayan ta saka hannu ta riqeshi da kyau. Bai lura da komai ba sai daya shimfide ta saman gadonsa sannan yaga hannunsa ya baci,ya daga kai ya kalleta,sake saka masa kuka tayi,abinda taketa gudu kenan,ta rintse idanu tana jiran jin fada ko duka daga wajensa,kamar yadda yaa ma'aruf ya taba mata saboda kawai ta kawo abinci ya bata flask din ya riqe hannunsa ya baci. Maimakon taji abinda ta zata saima jiyo sautin ruwa da tayi a toilet,ba jimawa ya fito da alama wankewa yayi,suna hada ido ta dauke kanta hawayen naci gaba da sauka,ciwo da kunya duka suka hadar mata,ya qaraso gabanta a hankali ya tsugunna "Dama kina period ne?" Wayyo Allah,ji tayi kaman zata nutse a wajen,ta jawo filo ta cusa kanta tana sake sakin kuka,wannan abun sam bai kyauta mata ba,inda ta san zaizo gida zata dage sai ya kaita. Sake maimaita mata tambayar yayi amma shuru, ganin da gaske ba zata amsa mishi da komai ba,taqi daga kai ma ta fuskanceshi,sai kawai ya miqe yana murmushi ya fita a dakin. Da kansa ya gyara wajen data bata din a falo,wajen bashi da wani yawa sosai,ya dauki waya ya kira na 'yan mintuna ya kashe. Da pad ya dawo mata,ya ajjiye mata yace ta shirya zai fiddo mota suje asibiti,yana zaune a falo ya dora qafa daya kan daya yana amsa waya ta fito tana rab'e rab'e,kunya kamar qasa ta tsage ta shige,wayar na a kunnensa ya waiwaya ya dubeta,can qasan ransa fal dariya,duk da babu ko alamun hakan a saman fuskarsa,ya jima baiga yarinya mara wayo mai tsananin tsoro da kunya irinta ba,iya period kawai data fara ya gani?,inda ace ya karba budurcinta ne fa gaba daya?, Shi kansa daya raya zancan a ransa sai daya sake maimaitawa,sai kawai qaramin murmushi ya kubce masa,ya cije lips nasa na qasa kadan saboda yadda yaji jikinsa ya amsa gaba daya,baisan lokacin da hakan zai faru ba,amma tabbas duk sanda ya kasance qila saita kusa mace masa saboda tsoro. Wayar ya kashe ya mayar aljihu sannan ya miqe,ya tako kadan gabanta "Zaki iya tafiya?" Kai ta jinjina masa ba tare da ta iya kallonsa ba "Muje to na gani idan zaki iya din" ya matsa gefe yana kallonta,ta rabashi a hankali ta fara takawa tana hada hanya,taku uku ya cimmata,ya riqo kafadunta suka ci gaba tafiya,tanason zare kanta,amma hakan da yayi mata saita dinga jin kamar relief yake bawa ciwonta,a haka suka qarasa,ya buda gaban mota ya sanyata ya kwantar mata da kujerar,sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 55 Da numfashinsa da idanunsa ya dauke lokaci guda sanda taja zanin nata sosai qasan marar tata,har jan pant dinta yana bayyana "Ya Allah" ya furta yana sake rintse idanunsa,har suka gama bai bude ba sai da yaji nurse din na magana "Zaki iya tashi?" Ta tambayeta,ya bude idanunsa a hankali ya maida kanta,sai ya taka a hankali zuwa gabanta,ya miqa mata hannunsa,idanunta a qas, karon farko da kunya tayi mata mugun kamu fiye da ko yaushe ta miqa masa hannun nata,ya dagota a tausashe. Sosai ta zauna saman gadon tana gyara daurin dankwalinta, likitan ya shigo yana qarasawa gaban computer scanning din yana duba scan din data bari a jiki "Ba wata matsala,zan rubuta mata magunguna,zata samu relief in sha Allah". Koda suka fito dinma tana riqe a hannunsa,gaba daya ta narke masa,tana ta sharar qwalla,ummu take tunawa da yadda take kula da ita idan bata da lafiya,dan riqetan da yayi sai takejin kamar tana tare da ummun ne,don haka ta narke masa sosai kamar yadda takewa ummu. Tun a pharmacy din cikin asibitin ya siya magungunan,fruit kawai ya tsaya ya siya a hanya suka wuce gida. Dakinsa kai tsaye ya wuce da ita,ya shiga kitchen da kansa ya dauko gorar ruwa da cup,ya zuba abinci a plate ya zauna da kansa a gabanta yana dubanta "Kici abinci,magani zaki sha" kai ta girgiza,fuska yadan hade kadan,ya zama serious,ya debi abincin da kansa yakai bakin bakinta "Oya....karbi" haka ta dinga bude bakinta yana saka mata abincin,har yanzu hawayenta yaqi tsayawa,duk ta narke,kamar yadda takewa ummu,bai saba daukan shagwaba irin wanna ba,sai ya rasa ta inda zai bi da ita,a haka ya samu tadanci,ya balla mata magungunan ya bata tasha,sannan ya miqe yana kallonta "Ki huta kadan,sai na rakaki ki kwanta" ya fada muryarsa can qasa,saita gyada kai tana rintse ido,kawai yadda zata tafi dakin ta kwanta ita kadai take hasasowa. Toilet ya shiga,ya sauya kayansa zuwa jallabiyya mai sulbi saqar qasar india,ya daura alwala,ya dawo cikin dakin ya shimfida abun sallah yana dan duban sashenta,ta sanya pillow daga bayanta,idanunta na a lumshe,amma da alama idanunta biyu,sai ya juya ya kabbara sallarsa. Tun tana satar kallonsa da kadan da kadan har bacci ya soma rinjayar idanunta,tayita dagewa batason hawa gadon sosai,yana fusgarta tana qwacewa,har yaci qarfinta,ta kwanta riris saman gadon,bacci mai dadi yayi gaba da ita saboda sassaucin ciwon data samu. Da murmushi akan fuskarsa yake dubanta sanda ya idar da sallar yaga tayi bacci,ya qarasa addu'o'in sa ya sauya kayan baccin sannan ya matso dab da ita,ta ranqwafa saman kanta yana kallon fuskarta sosai da sukayi gab da juna,siraran tausasan labbanta masu kama da an shafa musu ban lebe suka dauki hankalinsa,ya miqa hannu a hankali ya dora saman lips din nata yasa yatsunsa ya shafasu kadan,saita motsa,ta turo baki gaba cikin shagwaba "Ummu na.....ummu don Allah fa ni...." Ta fadi tana yin juyi,abinda ya sake kawo kusancin dake tsakaninsu sosai har suka fara musayar numfashi,ta haye kusan rabin cinyarsa,ya kalleta yadda tayi relaxing a jikinsa,jikinsa ya bashi idan yace ma zai tasheta ne wata really rigimar ce,don haka kawai sai ya zame ya kwanta,hakan kuwa sai ya zamar mata kamar wata hanya data samu ta shige jikinsa sosai,harda curewa waje daya kamar kwanciyar yaro a cikin mahaifiyarsa,taja hannunsa kuma ta riqe gam tana cewa "Ummu......na....gode" ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke,da alama mafarki takeyi,hakanan ya samu kansa da sake kusanto da ita cikin jikinsa suna musayar dumin juna,ya lumshe idanunsa a hankali yana jin wani abu yana bin jinin jikinsa,zuciyarsa ta fara sauya tsarin bugunta,sannu sannu numfashinsa ya fara sauyawa,ya dinga fita a jejjere,mode dinsa ya canza gaba daya,yasan me jikinsa yakeso,amma bayajin wannan buqatar zata samu,ta yaya ma daga samun kusanci da yarinyar zuciyarsa zata bijiro da wannan babbar buqatar?,bashi da sauran zabi illa qoqarin zameta daya fara yi daga jikinsa,saidai ta riqeshi qam,daga bisani ma da yayi nasarar zameta din,juyi daya tak tayi ta dawo jikinsa,idanunta a rufe amma kukan shagwaba take saki,yayi shuru yana sauraren siririyar muryarta dake fidda wani irin kuka a shagwabe,wanda yake qara sanya tsigar jikinsa zubawa,ya sake rufe idanunsa da kyau yana sake qoqarin zameta a karo na barkatai,amma saita riqo hannunsa,ta kuma cusa kanta cikin qirjinsa sosai. Duk yadda yaso yayi controlling kansa ya kasa,komai na jikinsa ya gama amsawa,qwaqwalwarsa kuma ta dauki chargy fiye da kima,dukka hannuwansa ya sanya ya jawota cikin jikinsa,shi da ita suka sauke ajiyar zuciya a tare,a hankali ya nutsa hannunsa cikin sassalkar sumarta dake fidda qamshin man kitsonta mai hade da sinadarin menthol me sanyi,cikin sanyi taushi da nutsuwa ya fara yamutsa shi yana jin dukkan wata gaba ta jikinsa tana sake amsawa,abinda ya sanya widad sake sakankancewa cikin baccinta,zuciya da ranta suna bata tana tare da ummu. A nutse hannunsa ya biyo tsahon gashin nata daya sauka har zuwa gadon bayanta,yana kaiwa qarshe hannunsa ya zarce ta cikin rigarta dake da faffadan baya,lallausan tafin hannunsa ya hadu da fatar bayanta mai santsi da dumi,ya zura hannunsa a hankali yana shafota,idanunsa suna sake nauyi da kyau,zuciyarsa na sake dugunzuma da dokantuwa da samun biyan buqatar ransa,bai gushe ba yana ci gaba da murza fatar bayanta,duk inda yayi qasa da hannunsa zip din na bashi hadin kai wajen zugewa,har yakai can qasa,ya dora hannunsa numfashin sa yana sake gudu kamar wanda yayi tsere,wannan ya sake sanyashi matsa qaimi,ya birkitata a hankali ya soma sabule rigar tata,ya sake dora hannayensa saman wuyanta,hancinsa yana kaiwa wajen,sassanyan qamshin daya zamewa jikinta kamar dabi'a ya zuqa,qamshin da zai iya cewa tunda yake bai taba jin irinsa a jikin hafsat ba,sai yaji bashi da muradin daya wuce yayi sharing qamshin nata da tasa gangar jikin,don haka yasa fuskar sa sosai saman fatar wuyanta,ya kuma fara gangarowa ga qirjinta a hankali yana sauke wani irin birkitaccen numfashi. A hankali ya fara isowa ga tudun saman qirjinta,abinda ya sanya shi da ita sukaji tamkar an sanya musu wani irin electric shock,ya qanqameta da kyau yana sake zuqar qamshin turaren,yayin da ita kuma taji kamar ance mata tashi!!!,cak kwanyarta ta tsaya waje daya tana son rarrrabe abinda yake faruwa,sanyin daya fara ratsa fatar jikinta ta fahinci saura kadan rigarta ta sauka qasan qirjinta,yunqurin riqe masa hannu tayi cikun matuqar tashin hankali amma ta gaza,saboda yadda jikinsu take rawa gaba daya ita dashi "Don Allah.....don Allah" ta fara fada cikin mugun rawar murya da kuma kuka,cak ya tsaya kamar wanda aka sanyawa sarqa,ya zame hannunsa daga jikinta a hankali ya mirgina gefe yana fadin "Hasbunallahu wani'imal wakil" can qasan maqoshinsa,yayin ruf da ciki yana cusa kansa cikin katifar tare da qoqarin dawo da nutsuwarsa cikin jikinsa. Tuni takai bango,ta tattare dukka jikinta guri daya,tana riqe da rigarta a hannu qam qam,hawaye sun yiwa fuskarta ado,kuka take sosai cikin tsoro da kuma tashin hankali. Dakin ya dauki shuru na wasu sakanni,har yanzu kansa na cikin katifar,yana sauraren kukan da take rerawa,wanda ya dinga jinsa har tsakiyar kansa,wani tunani yazo mata,ta soma maida rigarta da sauri sauri,saidai ta gaza zuge zip din,sai kawai ta sauke qafafunta qasan gadon ta miqe ta nufi qofa. Cikin jikinsa yaji alamun takunta,ya daga rinannun idanunsa da har yanzu basu gama komawa dai dai ba yabita da kallo,duk da dakin ba wadatar haske amma kuma yana iya ganin bayanta daya bayyana sosai saboda rashin zuge zip din,wani irin baya dake dauke da wani shape mai jan hankali daya taimaka wajen fidda shape na mazaunanta da qugunta. Bayajin koda yayi magana zata fita daga maqoshinsa,don haka ya miqe kawai cikin wata iriyar kasala da mutuwar jiki,kamar wanda yasha abun maye,taku uku ya cimmata,ya isa jikin qofar,ya murza key sannan ya waiwayo ya zube mata idanuwansa gaba daya yana kallonta "Koma ki kwanta" ya fada da dakusashiyar muryarsa,saita janye gefe tana maqale kafada,bai sake mata magana ta biyu ba,illa hannuwansa daya sanya ya dauketa cak,bai direta ko ina ba sai saman gadon,ya kwantar da ita saman pillow,yaja mata duvet sannan ya sunkuya yana kallon qwayar idanunta sosai "Sleep......banason na sake jin kukanki,idan kuma kika sake tashi....tom" ya fada yana gyada kansa,alamun akwai abinda zai biyo baya,sai ya matsa yaja da baya,sannan ya juya ya shige bandaki. Runtse idanunta kawai tayi tana qoqarin danne kukan nata,wani haushinsa da tsanarsa takeji,ashe dan iska ne sosai haka?,tunda take ba wansa ya taba yi mata abinda yayi matan sai shi,boye kanta ta sakeyi sosai cikin duvet din tana share hawayen daketa bulbulowa daga idanunta. Ya jima cikin toilet din sannan ya kunna ruwan zafi dana sanyi ya daidaita temperature dinsu,ya sakarwa kansa shower,bai taba zaton yarinyar zata kunnashi haka ba,akwai wani irin magnet tattare da ita dake saurin jan zuciya da kuma gangar jiki,yayi shuru ruwan yana gangara a sassan jikinsa,yana tuna qamshi da dumin fatarta,da wani laushi kamar fatar jariri,irin yanayin da yakeso tattare da matarsa,irin yanayin daya jima yana fasaltawa,hannu yasa saman kansa ya sharce sauran ruwan da bai gama diga ba sannan ya fita daga qasan shower din ya samu babbabn towel ya daura ya fito daga bandakin. Koda ya fito turare kawai ya samu ya shafe jikinsa dashi ya sauya wata rigar,ya koma can daya side na gadon ya zauna yana kallonta yadda take nade waje daya,batayi motsi ba ko kadan,saidai duk da haka ya karanci bacci ya fara daukarta,saidai baccin baiyi nauyi ba,ya sauke ajiyar zuciya ya jingina bayansa da fuskar gadon yana sauke idanunsa kan agogon dake saman bedside yana duba time da date,yana buqatar zuwa bauchi lallai,saidai yau din Monday,zai iya jira har sai ran Friday kuwa?, tambayar da ta masa nauyi,kwanakin kuma yaji sunyi masa nisa da yawa,sai kawai ya jawo wayarsa,ya yanke bari ya kira hafsat din,at least ko hira da zata sake bashi nutsuwa ya samu daga gareta. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 56 Sanda yayi kiran farko har ta katse bata daga ba,bai qosa ba ya sake kira,dab da zata katse aka daga. Sallama ya fara yi mata,cikin muryar bacci ta amsa "Badai bacci ba?" Ya tambayeta da muryarsa da ta sake sanyi sosai "Uhmmm....bacci mana,isan banyi bacci ba me zanyi,ka wuni hidimar gida data yara,kiranka ne ma ya tasheni,da banjin zan tashi har zuwa nan da asuba" idanunsa ya ragewa kaifi kadan,sarkin qorafi da mita,ya kauda wannan a kasalance yace "Sannu da qoqari" "Yauwa" ta fada a gajarce "Ina yaran duka sunyi bacci?" "Eh" ta sake amsa masa a tsaye "Good......Allah yayi musu albarka" "Ameen" ta kuma amsawa a gajarce,shuru na sakanni ya ratsa,ya zaci daga sound dinsa zata karanci wani abu,amma baiga alamun hakan ba,don haka yace da ita "I missed you, that's why I call you,ko zan samu wani abu special haka who will cheer me up da daren nan" baki ta tabe daga can,zuciyarta na mata zafi,ya ma raina mata wayo ne kawai,me zata masa tunda ya zabi ta zauna a nan?,ai sai kowa ya zauna da lalurarsa "Kai da kake da amarya?,me zaka nema a wajena?" Duk da baiso ba qaramin murmushi sai daya qwace masa,there is jealousy in her words,bai kuma shirya gamsar da ita ba,don haka yace "Sister din taki yarinya ce qarama,she can't take all my needs,so dole ki tallafa mata kamar yadda kikacemin zakiyi" idanunta ta runtse tana jin wani ciwo,kamar da gayya abbas din yake gaya mata hakan,yanason ce mata yana samun kulawa daga wajen yarinyar kenan? "It is better to go back to her" ta fada cikin haqiqancewa "She's sick" shima ya amsa mata a gajarce,ba dacewa bane ya bata qofan da zata karanci me yake gudana tsakaninsu,wannan wani abu ne daya shafesu su biyu. Bata shiryawa tashi ta zauna ba amma sai gata a zaune,qirjinta ya buga sosai,me ya sameta?,kodai ya aikata?,indai da gaske bata da lafiya to tabbatar suna tare a yanzu haka,tafi kowa saninsa,yana da tsananin tausayi da kulawa akan iyali,idan baki da lafiya kulawarsa ta musamman ce "Tana ina?" "No need ki sani..... just relax me madam" a yadda hankalinta ya daga bata jin zata iya masa komai "I feel sleepy....so i can't do anything" Maimaita words din data fada din yayi a kunnuwanta sannan yace "Alright.... good night" sai ya kashe wayar ya ajjiye ta a gefe yana shafa kansa zuwa fuskarsa hadi da furzar da iska,tunani kala daban daban cikin ransa da zuciyarsa,yana ganin kiranta amma sam bashi da interest na dagawa,saboda yana da yaqinij ba ta kirashi don tayi masa abinda yake da buqata bane,wala'alla ma ta kira ne ta bishi da qorafi ko kuma mita. Kamar yadda ya zata kuwa saiga gajeran tex bayan ta fahimci bazai daga kiran ba _Na gode da wulaqantani da kayi,ka daga wayar ka bani ita zamuyi magana,i called her,but bata daga wayan itama_ Tsaki yaja ya ajjiye wayar,mamakin halayen hafsat har yau basa barinsa,she call her to tell her what?,a wannan daren?,she refused to do what he wanted amma kuma tana son magana da weedad for what?,baisan sanda zatayi hankali ba da gaske,duk sanda tayi masa irin wannan sake fita takeyi daga ransa,daga qarshe qur'ani ya rungume sannan ya samu bacci ya daukeshi. *_W A S H E G A R I_* Ta jima da gama shiryawa cikin uniform dinta,amma ta kasa fitowa,tayi zaune gefan gadonta tana duban fuskarta time to time ta madubi,batasan yadda zata fuskanceshi ba,haushinsa takeji a zahiri,a badini kuma idan ta tuna abinda ya farun jiya sai taji kamar ta nutse a qasa,da qyar ta samu hawayen ta ya tsaya. Tana jin an taba qofar za'a bude ta runtse idanu,idonsa a kanta,qaramar dariya tana cinsa,yasan wannan rufe idanun duka nasa ne "Kin fasa zuwa school dinne?" Kai ta girgiza da sauri alamun a'ah,sai ta tashi tana juya masa baya,ta rataya jakarta tayo bakin qofa,a lokacin tuni yabar wajen. Tayi tsammani Samuel ne zai kaita kamar jiya,sai data shiga motar sannan taga shine ashe,ya tada motar suka fara tafiya,babu wanda ke cewa da dan uwansa komai,har suka isa makarantar,ya cira kudi ya bata "Ga kudin break,idan an tashi ki jira,idan ban samu zuwa ba samuel zaizo" bata iya hada idanu dashi ba tasa hannu biyu ta karba "Na gode" ta fadi qasa qasa sannan ta juya da hanzari tana yin hanyar class,yana zaune cikin motar yana kallonta har ta shige sannan ya tada motar yana kada kai da qaramin murmushi kan fuskarsa yayi reverse yabar makarantar. Wunin ranar sukuku tayishi,don ma 'yan ajin nasu suna da saurin sabo da jan mutum a jiki,nan da nan tadan fara sabawa dasu bayan tasan sunayen wasunsu,da azahar aka tashi,bata tsammaci ganinsa ba still sai gashi,yana sanye da uniform dinsa din nan dake qara masa wani mugun kwarjini haiba da kamala,da suka isa gida ta dauka zaya koma aiki ne,sai taga ya canza kaya ya kirata suka shiga kitchen. Koda suka gama kowa ya diba nasa,dakinta ta wuce dashi taci a can,bata sake jin motsinsa ba kamar yadda ta wuni a kwance,sai da yamma ya leqo yace tasha magungunta ta shaida masa tasha,hakanan tun bayan magariba daya leqo ya tabbatar tasha maganin dare bata sake jinsa ba. Wanka tayi tayi shirin bacci kamar yadda ta saba,saidai bacci yaqi zuwan mata,data gaji ta dauki wayarta ta duba,taga tana da kati a ciki sosai,kusan katin tun sanda aka siya wayar yake cikin layin,batasan na nawa ya loda mata haka ba,though dai bata fiya kiran waya ba,mostly saidai ayi kiranta. Mutanen gida ta dinga kira,ummunta ta fara kira,sai abbanta,anty madina hajjaa sai anty deena,wadda sunfi jimawa da anty deena din,tana ta mata hannunka mai sanda da jirwaye mai kama da wanka akan kula da miji,saidai hankalinta baima wani kawo mata ba,tadai jita ne,sai kusan tara na dare sannan sukayi sallama. Sam bacci ya qauracewa idanunta,ta dinga juyi ita daya tana tuna daren jiya,rabon da tayi cikakken baccin mai dadi irin na jiya har ta manta,saboda ita din mutum ce da tayi sabo da kwana a jikin ummu,shi yasa a kullum idan zatayi bacci da qyar yake zuwa mata tun bayan tafiyar latifa. Karar wayarta ta katse mata tunaninta,har tadan tsorata ma saboda ta manta da ita,sunan mommy hafsat data gani ya sanyata tashi ta zauna ba shiri,gabanta yayi mugun faduwa,hakanan takejin mummunan faduwar gaba a duk sanda taga wani abu daya danganceta,kamar sunanta muryarta da sauransu. Muryarta na dan rawa ta daga wayar tana sallama tare da yunqurin gaisheta "Kina ina?" Ta tambayeta kanta tsaye ba tare da tabi takan gaisuwar da take mata ba "Ina daki" "Wanne dakin?" Ta tambayeta daga can gabanta yana faduwa "Dakina" "Abbansu mimi yace baki da lafiya jiya,me ya sameki?" Gabanta ya yanke ya fadi data tuna cewa a dakinsa ta kwana jiya,kuma koda ra farka cikin jikinsa ta ganta,ta fahimci hakanne?,kota gane? "Ciwon mara" ta amsa mata muryarta nadan rawa kadan,abinda ya sake sanya shakku a zuciyar hafsat din,tsoronta ya ninku "Kodai wani abun kukayi ke dashi?" Tambayar daketa mata yawo tsakar ka ta subuce ta fito daga bakinta,da sauri ta hau girgiza kai kamar tana a gabanta ne,hawaye kuma suka jiqa mata fuska "A'ah mommy....wallahi ba komai,ciwon mara ne kawai Allah ki yarda gaskiya na fada miki" boyayyar ajiyar zuciya ta saki,sanin weedad din bata qarya sai hankalinta yadan kwanta,amma saita fuske saboda ta samu nasarar sake dasa tsoron hakan a zuciyarta "Ohon miki idan ma wani abun kika yarda yayi miki,mutuwa zakiyi.....ina ruwan wani,nima ina gaya miki ne don ina sonki banaso ki mutu" "Allah mommy ba komai" sai kawai hafsan ta kashe wayar donta qara tsoratata. Sosai hankalin weedad din ya tashi,tana shirin bin kiran taji ya turo qofar,ta daga kai tana kallonsa,har qasan ranta tana jin haushinsa,ya danji wani iri ganin tana kuka,yana fargabar ko wani abunne ya sameta,yasan yau bai leqota da kyau ba,duka yau ya kulle kansa ne a daki yana aikin tracing din wani criminal a sirrance,abinda yasa ya baro office kenan,bayaso kowa yasan abinda yakeyi "Yaaya?.....jikinne?" Kai ta girgiza tana turo baki,ta kuma tura masa qeya taqi kallonsa "To ma sha Allah"ya fada duk da ya fuskanci kamar cikin fushi take,shuru ya ratsa tsakani na sakanni kafin ya miqe "Ki ajjiye komai ki kwanta" sai ya juya yana shirin barin dakin,binsa tayi da kallo,tana jin kamar ta bishi,amma da ta bishi ya tabata gwara ta zauna a dakinta. A jikinsa yaji kamar tana kallonsa,don haka ya dakata ya waiwayo,suka hada ido saita dauke kai,kamar xaiyi magana sai kuma ya fasa,ya saka kai ya fita. Tun bai kai tsakiyar falon ba yaji ihunta,ya juyo da sauri,sai gata sunyi kacibus a hanya har tana fadawa jikinsa,taja baya da sauri jikinta yana rawa "Mm....mage" "A ina?" "Bakin window" ta fada tana duban qofar dakin "Muje na gani" ya fadi yana sakata a gaba,kafada ta maqale tana sakin kuka,kome zaiyi mata bata jin zata yarda ta bishi,haka tayi tsaye a wajen ya shiga dakin,bai jimaba ya fito "Bata shigo ba,infact ta wuce ma,zaki iya komawa" waiwaya tayi inda yake,taga da gaske tafiya yake zuwa dakinsa,ta daga qafarta da sauri tabi bayansa. Batasan ta cimmasa ba sai da suka tsaya suna kallon kallo shi da ita,yana riqe da handle din qofar yana dubanta,itama shi take kallo saidai batace komai ba sai aukin hawayen da take faman zubarwa "Don Allah...zan karka tafi ka barni" "Bacci nakeji" ya amsa mata a taqaice,saita sake fashe masa da kuka,hannu ya sanya ya dafe goshinsa "Oh my goodness" ya furta a hankali,saiya maida manyan idanunsa kanta "Me kike so?" Shuru tayi kamar ba zata amsa ba,sai kuma tayi qasa da kanta "Zan kwana a nan" ta fada a hankali gabanta yana faduwa,zuciyarta na gaya mata girman laifinta,ta yaya zata hada dakin kwana dashi?. Qaramin murmushi ya saki "Silly girl" ya fada qasa qasa,ga dan banzan tsoro ga shagwaba da sakarci harda na siyarwa,sai ya matsa gefe daya "Bismillah" ya furta a hankali,ta rabeshi sosai ta shige dakin,ya rufe qofar ya sanya key sannan yabi bayanta. Ta jima a zaune har ya gama komai na shirin kwanciya bacci tana binsa da idanu,pillow ya dauka ya jefar a qasa sannan yabi pillow din ya kwanta idanuwansa a rufe yana karanto addu'an bacci,ya gama ya shafe jikinsa,ba tare daya bude idanun ko ya dubeta ba yace "Ki kwanta kiyi kuma addu'a" a takure take sosai saman gadon,duk kuwa da cewa ita daya ce,duk juyin da zatayi idanunta a kansa,har sai data ji saukar numfashinsa a hankali alamun bacci yayi awon gaba dashi,sannu a hankali itama jikinta ya saki,wani bacci me dadi wanda babu fargaba a ciki ya sureta. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 Da yake private hospital ne basu samu wani layi ba suka samu ganin likita,duk tambayoyin da yayi mata kusan shuru tayi,tanajin kamar ta narke,maza biyu a daki guda suna mata tamba game da period dinta,abinda ko acikin gidansu boyewa take ba kowa yasan ta fara ba, murmushi likitan yayi ganin lokaci lokaci tana satar kallon abbas "Yallabai,da alama kai din ba yayanta bane na hannun dama,ko zaka bamu waje qilan tafiyin bayani" haka kawai cikin ransa yaji bazai iya barinsu su kebe ita dashi ba,don yaga baima fahimci matar aure bace,yayi yunqurin miqewa da nufin matsawa daga koda zuwa bakin window ne,saiji yayi caraf an kamo hannunsa,ya waiwaya a hankali,itace ke kallonsa tana qwalla "Kada ka tafi please" hada ido sukayi da likitan,sai ya saki dariya sannan ya miqe "Ta gaya maka abinda takeji,sai kayimin bayani,ina zuwa bari na samo nurse,za'a yi mata scanning,tunda kace ciwon mara ne" sai likitan ya cire abinda ya saqala a wuyansa ya ajjiye ya fice daga office din. Cikin kunya ta soma qoqarin zame hannunta daga nasa,amma saiya qara matsowa yana sanya dukka tafukan hannunsa a ciki da saman nata,ya rahe gap din dake tsakaninsu sosai yana dubanta "Uhnnnn.... tell me,kinga idan ya dawo baki fada ba zan tafi na barku tare" qoqarin tsaida kukan nata take tayi,taja majina sannan tace cikin muryar kuka "Marata ce take ciwo sosai" ta fadi cikin mugun jin kunya "dai dai ina?" Ya tambayeta yana kallon qwayar idanunta,sai ta motsa hannunta dake mararta kadan,kamar mai tsoron kada ya taba hannun nata. Idanunsa ya mayar kan hannun nata,sai yasa yatsansa ya nuna wajen "Wajen nan kenan?' ta gyada kanta a hankali,sai ya dauke dubansa daga wajen yana fidda numfashi,ya miqe a hankali,yayi taku biyu kenan saiga likitan ya dawo,bayansa wata nurse ce,zata kusa shekaru talatin,ba yarinya bace. Yana dariya ya tambayi abbas me tace?,ya zube hannayensa a aljihun wandonsa yana duban likitan "Ciwon maranne dai" "Ba damuwa,da Allah ki mana scanning,bari naje mota na dawo" ya sake fada yana diban wasu takardu ya fice. Sanda taga an gama saitan scanning machine din tace kuma tahau sai ta fara zare idanu,ganin alamun tana jin tsoro sai nurse din ta dubi abbas "Yallabai ko zaka taimaka mata" a nutse ya maida dubansa ga widad din,itama shi take kallo,idanun nan har yanzu qwalla ce kwance a ciki,ya cire hannayensa da tun dazun ke aljihunsa,ya tako a nutse ya iso gabanta. Sosai ua tsugunna a gaban nata,cikin murya qasa qasa, yadda ba wanda zai iya jinsu ya fara magana "Kije ta dubaki,few minutes ne ta gama miki,ba ciwo ba zafi,just relax...." Baki ta kwabe tana dubansa "Tsoro nakeji" "I promise you ba abinda zakiji,muje na rakaki" yadda take a tsorace yasa bata damu da kama hannunta da yayi ba,ya kaita har kan gadon sannan ta kwanta. "Dage rigar taki" nurse din ta fada tana dauko cream din da zata shafa mata saman cikinta,sai ido ya sake raina fata,matsawa yayi dab da gadon,yasa hannunsa a hankali ya fara janye rigar jikin nata,da hanzari ta riqe tsintsiyar hannunsa,sai suka hada idanu,ya tsareta sosai da manyan idanunsa masu wani irin kaifi da tasiri,ya girgiza mata kai murya kuma can qasa yace "Nooo,i said just relax" sosai taji idanun nasa sun mata nauyi,saita kauda kanta gefe,hawayen da suka cika idanun nata suna gangarawa ta gefe. Kamar wanda aka zarewa laka haka ya dage mata rigar har zuwa saman cikinta, kyakkyawar farar fatarta mai sulbi ta bayyana,ya koma a hankali da baya yana jin kamar iska na yawo dashi,ya jingina da wani qaramin locker dake wajen idanunsa nakan saman fatar cikin nata. *Arewabooks:Huguma* KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:huguma* Page 57 To tun daga wannan rana kwananta ya dawo dakinsa,saidai tana kammala sallar asuba take komawa dakinta ta shirya shirin makaranta,wani lokaci shike kaita,wani lokacin kuma samuel ko daya daga cikin yaran dake qarqashinsa. Aikin da yakeyi yasa a yanzun zamansa a gida yafi yawa,wannan ya fara haifar da shaquwa a tsakaninsu,duk da baya barin kowa ya rabi inda yake wannan aikin amma yawancin lokuta suna tare,badai hira sukeyi da ita ba,amma zata dauki littafinta ta zauna a wajen,ko ba komai tana jin motsinsa bata da kewa,lokaci bayan lokaci tana barin karatunta tadan zuba idanu tana kallonsa,idan sun hada ido kuma sai ta basar,murmushi kawai yakeyi ko yayi kamar bai gani ba yaci gaba da abinda yakeyi,aikin nasa ke bata sha'awa yake kuma burgeta,tanason masa tambaya amma kuma tana jin nauyi,don har yanzu bata gama sakewa dashi ba. A lokacin yayi qoqari matuqa ya koya mata abubuwa da dama,har ya fara sakar mata,don majority ita ke dafa musu abincin rana,kuma ya ciyu saboda gyaran bashi da wani yawa. Wannan karon ma bai samu zuwa bauchin ba sai bayan sati biyu,tanata hada kaya ta zaci da ita zaya je,sai yace a'ah,tayi zamanta,ta dinga masa kuka amma daga baya dole ta haqura,ya yiwa mai gidan magana matar gidan ta bata 'yar tayin kwana suke kwana tare,friday ya tafi ya dawo sunday da magariba,saita samu kanta cikin murna da farinciki ranar daya dawo din,wanda ita kanta batasan dalili ba,tunda dai ya tafi taji gaba daya bata da sukuni. Zuwansa bauchi a yawancin lokuta bacin raine,yana zuwa ne kawai don ya sauke nauyin da Allah ya dora masa,ya kuma kwatanta adalci,amma baya ga haka baiga wani alfanu da yake samu ba,hafsat din ta yita mita da nunqufurcin bai taho da weedad ba,don ta tara ayyukanta jingim suna jiranta,gidan ya hada mugun datti da qura yadda ya kamata,to koda yaje ma kusan washegarin ranar a aikin kintsa gidan ya qarar dashi,daga qarshe sassan weedad din ya bude ya kwanta yayi baccin gajiya a falonta,ki sashen nata da babu dan adam baiyi wannan qazancewar ba,da yamma ya fice wajen hajiyarsa,wadda ta dinga jajjabin abinda yasa baizo da weedad din ba,a haka dai ya qare weekend din nasa a gantale babu wata kyakkyawar maraba. Haka kawai ta samu kanta da son masa gwaninta,yana fita sallar magariba din a gurguje ta shiga kitchen,ta hada masa simple spaghetti jallop,da murmushi yake kallonta sanda ta dire masa ita,taliya ba cimarsa bace,amma kuma sai yaji ta burgeshi dari bisa dari,ko babu komai tafi hafsat din wadda a qalla nata shekarun sun ninka na weedad din,amma ko irin hakan batasan tayi masa ba,don haka yaji bazai iya watsa mata qasa a ido ba,yaja taliyar ya soma ci,taste dinta sai ya bashi mamaki qwarai,har ya kasa jurewa "Yammata irin wannan abincin fa?,a ina kika koyo shi?" Sunan daya kirata dashi ya bata kunya,saita kifa kanta saman pillow tana dariya,batasan sanda suka fara irin wannan wasan dashi ba "Kaine ka koyamin" kai ya girgiza yana sakin murmushi "Wannan kaman ba aiki na ba" kuma ya fada dinne har zuciyarsa,saboda dandanon ya zarta yadda ya koya mata din. Daya tashi komawa bauchi da ita ya tafi saboda hajiyarsa dake ta tambaya,hakan ya yiwa hafsat dadi,ta sake miqa dukka wasu ayyukan gida ga weedad din,bata samun zama ko hutu saita gama dukka wasu aiki na sassan hafsat din,hakanan hidimar yaran gaba daya ta dawo hannunta,wankansu wanki cire pampers,basu abinci da sauransu,tun tana jin gajiya da wahala har ya soma zame mata jiki ta saba. Wani zuwa da sukayi,ranar asabar da azahar,tana kitchen din hafsat din tana gogeshi bayan ta gama wanke kwanukan da suka cika babban sink din kitchen din,cikin ranta cike fal da mamakin yadda take barin kitchen ya hada wannan uban datti da kayan wanke wanken kamar na gidan biki ko suna,mimi da nawwara na falon data gama gyarawa suna wasa,ta kadasu can don su barta ta gyara nan din a nutse,a dole ta sake qwarewa ta samu kuma experience sosai akan harkar kitchen da kula da yara. Sau biyu anty ummee na sallama sai surutansu mimi,har sai data bude qofar falon ta shigo,tabi falon da kallo zuciyarta cike fal da mamakin yaushe hafsta ta koyo tsafta?,yaran da suka ankare da shigowarta suka watsar da kayan wasan suka taho da gudu suka rungumeta "Ina babarku?" "Tana dakinta,ta kwanta tace kada a tasheta" "Babanku yana nan ne?" Kai ta girgiza "Ya fita a mota" "Muje cikin" ta fada tana kama hannunsu,har yanzu tana mamakin kintsuwar falon,duk da tazo kwana hudu da suka wuce amma ba haka ta samu falon ba. Tana kwance male male saman gadonta tana sana'artata wato chart,harta bude baki data ji an bude qofar zata hau masifa,a zatonta weedad ko yaran ne saita maida maganar dake cikinta tana murmushi ta miqe ta zauna saman gadon ganin anty ummee ce "Daga ina haka ba kira ba sanarwa?" Harara ta balla mata tana samun gefan gadon ta zauna "Kedai baki da hali,don zanzo gidanki saina gaya miki?" Dariya tayi "Allah ya baki haquri ba haka nake nufi ba" bedroom din nata anty ummen ta sake kalla "Nace ba,wai yaushe kika fara tsafta ne?,don nidai banga haka a jikinki ba" tafadi tana kallon jikin hafsat din,wadda ko brassiere babu,sai wata t-shirt data mata yawa da zanin atamfa,kanta kuma tsifa ce rabi da rabi. Fuska ta tsuke tana kallonta,tasan halin anty ummee idan ya motsa in ba cin mutunci tataba mata ba bata jin dadi "Ni dadina dake wlh cin fuska,aidai jikin nawa babu qazanta ko?" "Nima bance akwai ba" ta amsa mata tana boye dariya,sai hafsat din ta gyara zama tana cewa "Yarinyar nan ce sunzo weekend,ai na gayamiki indai sukazo bani da matsala,nima nawa weekend din nakesha" "Kina shan weekend dinki amma na ga kanki rabi da rabi,a haka mai gidan yazo ya sameki?" Kan nata ta shafo "To mene?,kitso naso azo ayimin kuma na kasa qarasa tsifar tun shekaran jiya" "Allah ya tsinewa qazantarki" anty ummee ta fada cikin ranta,amma a fili saita mirgina kai kawai,tasan kome zata gaya mata abanza,tunda ba yau farau ba,indai akan tsaftane "Amma dai ya kamata kiyi amfani da damarki duk sanda yazo weekend ya zamana kin qara kawo kusanci tsakaninki dashi" "Manta da wannan anty ummee,kome zakiyi masa baki taba burgeshi" baki ta tabe "Ai shikenan,Allah ya kyauta" daga haka ta maida kallonta ga dakin,ta fara bin ko ina da kallo tana neman abinda zata rabauta dashi,ganin haka sai hafsat din ta tsuke fuska da kyau,tasan yanzun zata rabata da wani abu,don haka ta zamo daga gadon tana daura zaninta "Muje falo anty ummee,kada a shigo gidan babu kowa a daukemin wani ita tana ciki tana aiki bata sani ba" ta fahimceta sarai,bata ce komai ba tadauki jakartata suka dawo falo,amma cikin ranta taci alwashin sai fa ta fita da wani abu daga gidan "A banza zan dinga baki shawari" ta fadi a ranta. "Nifa dadina dake rowa wlh,ko ruwa ki kasa bawa mutum?" Anty ummee ta fada ganin sunata zuba zance amma ko ruwa bata mata tayinsa ba,kusan wannan din dabi'ar hafsat ce,bawai wani abu bane a wajenta "Kai anty ummee,kedai kin cika qorafi wallahi" "Ahto ai gaskiya ce" daga nan inda take zaune ta qwalawa widad kira tace ta kawo ruwa,ajjiye mop stick din hannunta tayi,ta samu plate ta hado ruwa da kuma lemo babba da qarami me sanyi da cup,kamar yadda ta saba gani a gidansu ummu nayi,ta nufo falon. Idanun anty ummee a kanta harta qaraso,ta tsugunna ta ajjiye kayan sannan ta gaidata ta miqe ta koma ciki. Sai data koma sannan ta dauke idanunta daga kanta ta maida ga hafsat "Hafsatu,ya naga yarinyar nan tana girma ne?,kinga yadda take canzawa?" Baki hafsat ta tabe "Na gani,nima abun yana dan damuna,duk da dai nayi mata dashen dana tabbatar bazai barsu suyi kowacce irin sakewa ba,kai qarshe ma idan ya matsa nasan rikici za'a yi ba dan qarami ba,namiji kuwa kinfini sanin ba haquri gareshi ta wannan bangaren ba" kai ta jinjina "Eh da haka kam,amma dole mu sake lalubo wata hanyar kafin ta fahimci duk gaibu kike gaya mata" mugun tsaki hafsaa din taja "Kuma dai?,ni na fara gajiya,haka kawai kana zaman zamanka banda namiji matsiyaci ne ya dauko abinda zai hanaka sakewa,shi bai amfana ba kai baka sake ba,aikin banza kawai" ta sake fada tana jan mugun tsaki, idanunta har sun sauya launi,da kallo anty ummee ta bita tana fasa lemon da aka kawo mata,a baqin kishin hafsat dinma bata dauka za'a kai warhaka gayyar bata watse ba,saidai tana alaqanta dadewarta akan plan din da morar yarinyar da takeyi. Bayan ta shanye ta dauki dayan ta jefa a jakar hannunta,don tunda ta samu wannan damar ba zata barta ba,hafsat din kuwa ta bita da kallo cikin ranta tana fadin "Kwadayayya hadamammiya" yayin da anty ummee din ta waske da cewa "Karki damu,kafin lokaci ya qara turawa za'a samo wata mafitar". Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,watanni suka fara shudewa,tsakanin widad da abbas yanzun akwai sakewa da sabo ba kamar baya ba,duk da cewa ba wata mai yawa bace,don bata bari ya kusanci inda take sosai,idan ka gansu zakayi tsammanin yaya ne da qanwarsa da yake matuqar bawa kulawa,zuwa sannan weedad din ta fara girma ita a karan kanta tana ganin wasu sauye sauye,ta fannin girki ta iya abubuwan da baza'a rasa ba,sosai kuma takejin dadin makarantar ta,ta fara sabo da mutane,ta kuma fara karantar rayuwa da yadda mu'amala take tsakanin mutane KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *_Arewabooks:huguma_* Page 58 Tsakanin shi da itan zamu iya cewa wasu irin mutane ne da miskilanci yake gudana a jininsu,saidai duk da wannan hakan bai hana sabo da sakewa a tsakaninsu ba,kamar ko yaushe,safiyar ranar juma'a ce,suna kitchen ita dashi,tana sanye da abaya mai santsi peache color me turuwa kadan,wanda daga cikinta riga da wando ne straight leg,duk da basu matseta ba amma sun fidda aihinin shape nata,shi yasa ya dora abayan a kai,haka kawai tayi sha'awar sanyasu,taga hotunansu cikin wayar wata 'yar ajinsu yayarta ke sayarwa,data duba kayanta taga tana da irinsu,kaf ire iren wadan nan kayan nata suna hade ne a waje daya,bata taba gwada sakasu ba,tana ganin kamar kayan 'yan iska ne. Manyan kalba da aka yi ma kanta guda hudu masu kauri da tsahon jela,biyu suka zubo gefe da gefen fuskarta,suka kuma sauka mata har kafada,sauran biyun kuma suka sauka a gadon bayanta. Yau din abbas na saman cupboard a zaune kawai yana latsa waya,saboda tunda suka tashi da safen tana gaidashi tace,saita langwabe kai gefe guda tana wasa da yatsun hannunta "Yau babu abinda zaka koyamin,I want to surprise you" she is always like a baby,haka take maganarta cike da quruciya,daya daga cikin abinda yasa yakeson yaga tana magana,kota dake da gasken gaske tana zuba wautarta,amma ita a nata ganin a dai dai take komai. Yadda ta ritsashi da idanu bayan ta gama maganar ya sanya dole murmushi ya qwace masa,irin miskilin murmushinsa da ko haqoransa baka fiya gani ba,ya dage girarsa dukka biyun sama yana kallon tsakiyar qwayar idanunta "Really?" "Yes" ta amsa da amsa amo cike da qwarin gwiwa,sai ya girgiza kai yana qaramar dariya "Zamu gani,in zauna yau abina kenan?" "Eh mana,na baka hutu" ya fidda sauti kadan,yayi tsalla daya ya haye sama yayi zamansa,saita bishi da ido tana fidda manyan idanunta waje,wasu irin fararen manyan zagayayyun idanuwa da suka dauki hankalinsa a karon farko,har baisan yayi subutar bakin tambayar ta "What?" Ya fadi yana jin wani abu nason masa tasiri,qaramar dariya mai cike da sakalci tayi "Tsallae daya fa kayi uncle ka haye?" Murmushi ya sake subuce masa,ya girgiza kai "Shine kika bude dukka wadan qwala qwalan idanun naki zaki cinyeni dasu?" Baki ta tabe kamar yadda qaramin yaro keyi idan zai saki kuka,abinda ya sake shagaltar dashi da kallonta kenan,siraran labbanta kamar ta shafa musu jambaki "Qwala qwala fa kace uncle" "I don't mean qwala qwala marasa kyau,u have a beautiful eyes dear" ya fadi yana duban qwayar idanunta,kawai sai taji wani irin kunya ta kamata,ta saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta,hirar 'yan ajinsu ta fado mata,daya daga ciki dake basu labarin yadda saurayinta yake kodata,haka akeji dama data taba ce musu kunya takeji?. Zara zaran yatsuntsa data rufe fuskarta dasu yabi da kallo,farare tas,hatta da farcenta fari ne qal babu digon komai a jiki "Me kike tunani?" Taji ya sake fada "Ba komai" ta amsa masa da sauri tana sauke hannuwanta daga fuskartata,gani take kamar zai karanto abinda ke cikin zuciyarta "Kin manta am a police,da tsalle daya muna iya hayewa saman gini dake da tsahon da yafi na wannan,kin tuna?" Kai ta gyada tana murmushi,saita kasa ci gaba da cewa komai saboda yadda yake kallonta tsakiyar idanunta yana sanyata tana jin wani iri. Shuru kitchen din ya dauka,yayin data buda wayarta tana duba recipe na abinda zata dafa din,tana daukowa daya bayan daya tana ajjiyewa,har ta kammala ta fara aikinta. Haka kawai ya samu kansa da daga kai time to time yana kallonta,hakan ya sanya duk kai kawonta take yinsa cikin idanunsa ba tare data ankara ba,aiki yayi aiki,taja igiyar rigar ta daureta don tafi jin dadin yin aikin,saidai abinda bata sani ba,gaba daya ta fidda shape na mazaunanta qugunta da kuma qirjinta. Ya sake dagowa yaga a inda girkin ya tsaya idanunsa sukayi kyakkyawan gani,yaso janye idanun nasa amma sai ya kasa,karon farko kamar an zare masa laka daga jikinsa,yaso ya maida kai ga wayarsa amma sai yaji ya kasa,dole ya kashe abinda yakeyi din,ya aje wayar a gefe,ya jingina da bango ya harde hannayensa a qirjinsa ya zuba mata idanu. Sam batasan yana kallon ta din ba,saboda ta bada hankalinta gaba daya ga abincin,tanason yayi dadin da zai yaba mata,ta waiwayo zata dauki chopping board har ta juya ta fara yanka albasa jikinta ya bata kamar kallon ta yake,tana juyawa sukayi ido hudu,sai gabanta ya fadi,ta juya da sauri ta saki igiyar rigar tata,ta koma shapeless kamar yadda take idan ba igiyar a jiki,jikinta yadan dauki rawa kadan,ta sunkui da kanta tana yankan da sauri sauri. Bata son kallo ko kadan,bare shi da a duk sanda ya kalleta sai taji nashi idanun kamar sun banbanta dana kowa,ta fara nisa a tunani,don haka har ya sauko daga inda yake zaunen,ya tako a hankali ya tsaya a bayanta bata jishi ba. Sosai ya zuqi qamshin splash da jikinta ke fitarwa kadan kadan yana kadawa hagu da dama gaba da bayanta,taku biyu ya qara ya sake rage kusancin dake tsakaninsu,sai a lokacin taji kamar iskar dake bayanta ta canza da wani kalar qamshi na body mist na daban. Cikin hanzari ta waiwayo,ta manta da wuqar dake hannunta tana datsa albasa,tariga ta dora ashe saman yatsanta ne,tayi wurgi sa wuqar tana yarfar da hannunta gefe daya,saidai duk da zafin da taji kusancin shi da ita yafi daga mata hankali,ta kafeshi da idanu qirjinta na wani irin bugawar da bai taba yiba,ta kuma ja baya sosai har ta qure da jikin kitchen cabinet din. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin shi da ita,a hankali ya sanya hannunsa ya lalubo hannunta data yanke din ba tare daya janye idanunsa daga cikin nata ba,sai daya sanya hannun cikin tafin hannunsa sannan ya maida dubansa akai. Kusan lokaci daya suke duban hannun shi da ita,sannan suka kalli juna "Kinga abinda kikayi ko?" Ya tambayeta da wata shaqaqqiyar muryar,kamar jiransa dama takeyi sai ga hawaye ya cika mata idanu "Kaine fa ka bani tsoro" dariya taso bashi amma ya dake,saiya langabe kai kamar yadda yaga tayi "Banda ke banga wadda take tsoron mijinta ba" kamar ya tunzurata,don batason kalmar miji,sai ta fara qoqarin zame hannnunta daga cikin nashi "Ni ba mijina bane kai" "To waye ni?" Ya tambayeta yana dage girarsa sama "Uncle" kai ya girgiza kawai yana sake sakin boyayyen murmushi "Riqe uncle dinki,banaso,let me treat your wound first" ya fada yana sake kamo hannunta. Kujera ya saka mata ta zauna akai,sannan shima ya jawo wata ya zauna,har gwiwoyinsu suna haduwa da juna,ya bude first aid kit din ya fada wanke jinin,yana yi tana rintse idanu,ya daga idanunsa ya kalleta,idanuwansu suka hadu waje daya,sai taji hakan ya mata nauyi sosai,ta kauda nata idanun numfashin su yana gauraya da juna. Har ya gama mata babu wanda ya sake cewa komai,ya sakar mata hannun yana hade kayan waje daya "Jibi idan Allah ya kaimu zanje bauchi" kallonsa tayi da sauri,hakanan kwanakin nan sai ta dinga jin batason zuwa garin "Zanje nayi one week,zamu taho da hajiya,the next day zamu wuce umara ni da ita in sha Allah" zuwan da yace hajiyan zatayi taji yayi mata dadi,har zumudinta ya bayyana a fili "Amma wata daya ya kamata tayi,ko ka dawo da ita nan kawai" ta fada tana langabar da kanta,cak ya tsaya yana kallonta,yaji mamakin jin furucin daga bakinta,abinda bai taba ji daga bakin hafsat ba tsahon zamansu da ita "Hajiya ba zata zauna ba" ya amsa mata yana miqewa riqe da kit din. Koda ya dawo sai ya fara rolling hannun rigarsa zuwa sama,tana daga zaune tana kallonsa har ya gama,idanuwanta suka sauka kan lallausar gargasar dake lullube da hannunsa,abar da take yawan burgeta ba tare da tasan dalilin ko kuma amfaninta "tell me what you are cooking sai na qarasa" idanu ta narke "Zan iya qarasawa uncle,don't spoil it" girarsa ya daga ya watsa hannayensa "I will finished it anyway idan ma baki gayamin ba" ya fada yana qarasawa,ya bubbada tukwanen "Kin kusa gamawa ai" ya fada ba tare daya juyo ba,yana mamakin qoqarin da tayi,kai ta gyada masa. A nutse yake ci gaba da aikin,har ya kammala,duk inda ya motsa idanunta suna biye dashi,yana ankare da ita amma bai nuna ya ganta ba,har ya kammala,zata karba gyara kitchen din shima ya hada ya gyara komai,mamakinsa sake cikata yakeyi kullum,shi kam baya jin aiki ne?. ************Tana nade saman kujerar falon,tayi lamo kamar 'yar magen data samu waje mai laushi,sanye take da atamfa dinkin riga da skert na atamfa,ta yane saman kanta da dankwalin atamfar,jikinta na fitar da tattausan qamshin turarenta,daga gaba kadan kujerar ta uku daga gefanta,abbas ne a tsaye yana qarasa zuge jakarsa ta tafiya,yanayi yana amsa waya daga office,har ya kammala,ya kashe wayar ya sanyata a aljihu,ya dauki jakar ya rataya a kafadarsa. Sai a sannan ya waiwayo inda take zaunen,yadan zuba mata idanu yana karantar yanayin fuskarta,duk sanda zayaje bauchi indai bada ita bane sai yaga wannan damuwar a tare da ita,saidai a wannan karon damuwar kamar tafi ta kowanne lokaci. Yadda tayin kamar wata marainiya ya bashi tausayi da kuma dariya,ya taka a hankali ya tsaya a gabanta,ya miqa mata dogayen lausasan hannunsa. Hannun tabi da kallo kafin ta mayar saman fuskarsa dake dauke da wani irin haiba da wani sirritaccen kyau da ba kasafai kake iya hangensa farat daya a fuskarsa ba,har cikin zuciyarta takejin wani iri babu dadi,saboda wannan ne karon farko da zaije yayi sati daya,kwana biyu rak yake ya dawo duk sanda ya tafin,idan da itane ma suke kwana uku. Sake miqa mata hannun yayi,saita noqe hannun nata tana lumshe idanunta hadi da kwantar da kanta tsakanin cinyoyinta. Murmushi ne mai sauti ya kubce masa,cikin taushin murya yace "Get up,tashi muyi sallama" curewa tayi waje daya,saita saki kuka kawai "Ya rabb"ya furta yana sauke jakarsa daga kafadarsa ya ajjiyeta a qasa,sannan ya duqa saman gwiwarsa a gabansa "Na gayawa hajiyane baki barni inje na daukota ba?,ko na gayawa maman mimi baki amince naje muyi sallama ba?" Furta sunan mommy hafsat da yayi ya sakata zabura,ta kuma daga kanta da sauri,sunanta kawai na sanya gabanta faduwa,hajiya kuwa tana jin nauyi da kuma kunyarta fiye da yadda baki zai furta,dukkansu babu wanda zataso ya gayawa abinda yace zai gaya musun. Kai ta girgiza masa da sauri,ya lumshe idanunsa ya kuma budesu duka a tare "Wipe your tears" hannu biyu tasa ta goge hawayen yana kallonta, cikin ransa yana jin wani irin yanayi daya gaza tantance wanne iri ne,a yau apart from hajiyansa,yau ga wata halitta dake amsa sunan matarsa tana jin babu dadi wai don zaiyi nesa da ita,a wajen mutum guda yake ganin hakan..... hajiyan sa,babu na biyun sai a yanxun da yake gani daga wajenta. Sai daya hilaceta ta dan saki jiki,sannan ya miqe ya dauki luggage dinsa yayi mata sallama ya fice,tana tsaye a jikin window har motarsu ta tashi suka fice daga gidan. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 59 Ranar gaba daya wunin falo tayi,tayi kwance cikin kujera ta kasa hasala komai,,haka kawai take jinta wani sukuku,jikinta duka babu dadi,sai bayan sallar la'asar tana kwance kiran anty deena ya shigo "Lafiya kike?" Ta tambayeta jin muryarta tayi qasa da yawa,sai ta kama mata hawaye kafin daga qarshe ta gaya mata ya tafi bauchi ya barta ne,abun ya baiwa anty deena dariya,wohoho...... widad har yanzu quruciyar dai tana nan,sai data bata baki sannan tayi mata zancan da yasa ta kirata "Akwai watsapp groups da za'a saki,inason kowanne idan an sakaki ki tsaya kibi duk hirarrakinsu kinji ko?,akwai qaruwa sosai qanwata" "To anty" ta fada tana gyada kai,sun jima da anty deena din suna hira,sai data debe mata kewa sosai sannan sukayi sallama. Washegari haka ta tashi jikinta babu qwari har ta gama shirin makaranta,bayan kowanne minti daya saita kallin dukka wajen da yafi zama ko tsaiwa,sai taji hawaye sun cika mata idanu,tasa hannu ta share da sauri,sannan ta dauki school bag dinta zata fice a dakin,qarar wayarta ya dakatar da ita,ta waiwaya ga inda ta ajjiye wayar saman madubinta,ta koma ta zuba mata ido tana kallon number wayar,sai kuma ta miqa hannu ta dauka. Lallausar muryarsa ta bayyana cikin wayar,gaba daya kamar wadda aka bigewa gwiwoyinta haka taji,ta koma da baya ta zauna tana qoqarin amsa sallamar tasa,yana jin sautin muryarta ya saki boyayyen murmushi "Ina kwana?" Ta gaisheshi muryarta na rawa "Kin tashi lafiya?" "Lafiya qalau" shuru yadan ratsa sai yace "Baki kirani kinji yadda na sauka ba,tsakani da Allah ba amana,ni ina nan ina tunaninki" wata irin kunya ce ta saukar mata,har taji kamar gata a gabansa,saita saki murmushi tana qunshe fuska "Kayi haquri" ta samu kanta da fada,don ko kadan ta kirashin baizo kanta ba,hasalima ita batace ga number dinsa ba "Yayi kyau,yanzu me kikeyi?" "Makaranta" ta bashi amsa a taqaice,daga nan inda yake ya kalli agogon dake gefansa "To a dawo lafiya" "Allah yasa" ta fada cikin dan karsashin data samu "Babu komai ko?" Shuru ta danyi,da kamar tace masa gidan babu dadi,kamar tace masa jiya da qyar tayi bacci,kamar tace masa ya dawo don Allah,amma kuma saita kasa ta amsa masa da babu,sukayi sallama ta kashe wayar ta barta saman gado sannan ta fito ta cimma driver suka bar gidan,tana jin ta samu wani karsashi Cikin jiki da zuciyarta. Wayar yabi da kallo bayan sunyi sallama ya kashe wayar,hafsat data fito daga wanka tayi zaune gaban madubi tana shafa jambakin dole ta sake binsa da kallo ta cikin mudubin,tunda ya fara wayar gaba daya ta tattara hankalinsa a kansa,kusan wannan dabi'arta ce,tanaso ta cinye amma ta kasa,tadan gyara zamanta tana matso jambakin ba tare data shafa ba tace "Dawa kake waya ne?" Kansa ya daga yana kallon fuskarta ta cikin mudubin,maimakon ya maida kai ga amsa tambayarta,sai duka tunaninsa suka koma daren jiya tsakanin shi da ita "Hasbunallah" ya furta qasan ransa,bacin ranta ya motsa masa amma sai ya kori shaidan "Wanka kikayi?" Ya mata tambayar data bata mamaki,a mamakance ta amsa masa "Eh,baka gani ba?" Kai ya jinjina "I see,but.....zo muje in nuna miki wani abu" ya fada yana yaye lallausan duvet dinsa sabo fil da dole ta sanyashi daukoshi,saboda yazo ya tarar da nashi anci ubansa,tun kafin yayi magana ma tace masa nawwara ce,haka ya tattarashi a daren ya bawa mai gadinsu yace ya yar,shi kuwa ya kaishi baya cikin murna ya jiqashi zai wanke,saidai shi dinma yana wankewar yana tsinewa qazantar hafsatun a ranshi,saboda wani irin gamayyar hadakar dauda ne a jiki harma da guntun kashi dana fitsari. Kai tsaye ya shige bandakin,ta ajjiye jambakin ta bishi da kallo,itafa ba wannan takeso ba,bai amsa mata tambayar ta ba,abun yayi mata tsaye a rai tunda taji suna waya da yarinyar,abinda bata taba ji yayi da ita ba,to amma kuma dole ta lallaba a yanzun,bataso suyi tashin hankali,kada ta barar da umrarta,don tunda taji labarin tafiya umarar ranta ya raya mata harda ita a ciki,qilan bai fada mata bane,saboda ya saba,yana da wani irin miskilanci da shan qamshi ta wannan bangaren,ba kasafai idan zai maka abu yake gaya maka ba,har sai dab da faruwar abun,dole ta miqe ta bishi bandakin,zuciyarta nq raya mata dole ta kira yarinyar tabi ba'asi,ta kuma sake kada mata warning,dama ranta a bace yake tunda taga yazo babu ita,don ta hada himilin qazantarta,mai wankinsu ya gudu amma yace mata yana qauyensu,tana ta jira fa taji wayam,dole ta tattara duk wasu tarkacen kayayyakinta takaisu store din bayan gidan ta kulle saboda abbas din,ta tabbatar idan ya gani sai yayi fada,ita batasan uwar daya sanya yanzun sai yayi zuwa biyu baizo da ita ba,ko a yanzun wannan kusan zuwasa na biyun kenan,idan ta bigi cikinsa sai yace mata makarantar ya sanya haka. Tana shiga bandakin yana tsaye da clipper a hannunsa yana daurata,ya daga tsimammun idanunsa dake motsa mata soyayyarsa koda bata shirya ba ya kalleta "come closer" ya fada yana kallonta,kamar zata musa masa kota tambayeshi dalili sai kuma ta fasa,ta matso din kamar yadda ya buqata,bata kawo hakan a ranta ba kawai taji ya sanya hannu zai ware towel din jikinta,da mugun qarfi ta kama towel din ta riqe tana kallon idanunsa "Me zaka yimin da safiyar nan kuma?" Ta tambayeshi ranta a bace,mamakinta ya sake cikashi,yana sane yace mata "I want to be with you" ido ta zare ranta a bace "Haba don Allah,duk abinda kayi jiyan bai isheka ba?, al'amuranka are getting worst gaskiya abban mimi, jiyan kamar zan mutu fa" bai amsa mata ba illa hannu daya daya saka ya fincikota,ya ware towel din,ya kunna clipper din ya daga hannunta ya fara kwashe mata gashin hammata,sai tayi shuru tana kallonsa,fuskarsa a hade,kunya ta kamata,ta rasa yadda zata nade masa tabarmar kunya da hauka,har ya gama sannan yace mata "Kwanta na qarasa miki sauran,tunda bakisan yadda akeyi ba"yafadi ba tare daya kalleta ba yana goge gashin daya bata jikin clipper din, fuska ta bata "Kawai da ranar Allah saina yaye maka jikina,kai ba zaka ji kunyar kalla ba?" A nutse ya daga kai yana kallonta,ko yaushe mamakinta kasheshi yakeyi,kamar wata jahila ko wadda batasan meye aure ba,ya zuba mata idanunsa da suka sanyata tadan daburce,sai tahau quna quni "Zanji kunya mana,wannan uwar gayyar da kika tarawa wajen ai dole aji kunyar kallansa" batasan abinda zai maida mata dashi ba kenan,sai zancan nasa yayi mata ciwo "Me kake nufi?,daga fadin gaskiya zaka mayar min da baqar magana?" Baice mata komai ba,ya qarasa gefanta inda take tsaye ya ajjiye clipper din ransa ya suya,kome zaka.mata a duniya baka iya ba,bakuma zaka fita ba "Kada ki fito baki kwashemin wannan go slow din da kika tarawa wajen ba" ya fada adan zafafe ya qarasa sink ya wanke hannunsa da detergent ya fita yabar mata toilet din. Binsa tayi da kallo idanunta na hada qwalla,to wai ina ruwansa da sumar wajen?,badai ta bashi abinda yake nema ba?,why not zai dameta harda baqar magana?,banda tasan halinsa sarai tana kuma tsoron hukuncinsa da ba zata aske ba,tasanshi hukuncinsa bashi da dadi idan ka kaishi bango. Ko kafin ta fito ma shi tuni ya gama gyaran sassan nasa,suna falo suna breakfast shi da yaransa,wucesu tayi tana shan qamshi,ita ala dole ya bata mata rai,can qasan ranta kuma kunya ce fal bayan ta gama askewar taga uban tulin gashin data tara,taji kuma iska tana ratsata, baibi ta kanta ba shima,don idan da sabo ya saba da irin wadan nan dabu'un nata. Wankansa yayi ya shirya ya kuma shirya yaran,ya aikasu ta saka musu kaya,taja tsaki "Wato baima san tanayi ba,ficewarsa zaiyi kenan,me yasa ne duk fushin da zatayi baya iya lallashinta?" Ta tambayi kanta zuciyarta na quna,haka ya figi yaran ta watsa musu wata shadda ta kadasu daga dakin. Sanda suka shigo sai daya dakata daga taje sumarsa da yakeyi,ya juyo yana kallon kayan jikin nasu sosai,gezner ce mai mugun tsada daya siya musu kwanan nan da aka qara masa girma su da mamarsu,ya kuma biya kudi mai yawa aka muau dinki mai tsada,ita mamartasu tun randa suka fita a hannunsa bai taba ganinta a jikinsa ba,su kuma bai tashi ganinta a nasu jikin ba sai da wannan muguwar kamar,gaba daya ta fita hayyacinta,kamar ma ta soma dafewa,ga wata muguwat squeezing da sukayi "Allah ya kyauta"kawai ta fadi bayan ya taba shaddar ya tabbatar itace "Daddy mu tafi,daddy tare zamuje ko?" Mimi ta fada,saiya gyada mata kai,tausayinta na cikashi,sam bata damu da yanayin da kayan jikin nata suke ba "Muje na canza muku kaya tukunna" ya fada yana hada kansu suka wuce sashen hafsa din. Gaba daya dakin a qazance yake sannan a hautsine,dama kusan kaso casa'in na gyaran dakin shike musu,idan ya gama nasa gyaran saiya hada da nasu,yana saka ran kuwa ba'a sake bi ta kansa sai idan ya sake zuwa wani weekend din,baya qaunar yadda taje barin rayuwar yaransa cikin qazanta,yara mata ne,wataran dole gidan wani zasu,uwa uba ma lafiyarsu,yana tsoron wata cutar a tattare dasu,haka ya dinga hadiyar bacin ran bayan ya bude cupboard dinsu,duka kayan ma baya ganesu,baya gane masu wanki da wadanda babu wanki,ga kaya cike da cupboard din amma babu na zabe,ya zubo dasu duka,ransa a mugun bace,wai me yake damun hafsat ne?,kayan yaranki kamar na mahaukata?,banbancinsu kadanne?. Wayarsa ya zaro yayi kiranta,don bayason su hada fuska ma ta qara tunzurashi,tana ganin kiran taqi dagawa,har ya gaji ya tura mimi tayi kiranta. Sai data mula sannan ta taso,ta tura qofar suka hada ido,saita kauda kanta saboda yadda taga bacin rai baro baro saman fuskarsa,tayi gefe da kanta tana jiran jin tashin boma boman fada,saboda ta hangi himilin kayan yaran daya watso qasa "Meye matsalar me muku wanki?,bai iya bane?" Ya tambayeta calmly yana qoqarin dannar kansa,duk da can qasan ransa wani irin bacib raine kecin zuciyarsa "Kawai yaron bashi da mutunci ne,ba kasafai nake bashi wanki ba" ya jinjina kai kawai,saboda yasan ta fada ne kawai don ta kare kanta "Shi kuma engine wankin gidan fa?" "Ya lalace wata hudu kenan" wani abu mai tauri ya hadiye,ransa na baci, engine ma ya lalace amma ta buda baki ta gaya masa ba zata iya ba? "Yayi" kawai yace da ita,saita saki handle din qofar ta juya ta fice abinta "Ka qaraci jarabarka kai kadai" tafada can qasan ranta tana buga tsaki. Wayarsa kawai ya zaro ya kira hajiya "Ka iso ne?" "Ina dai hanya,muneera zaki turomin gida yanzu" "To gata nan" ta fadi ba tare data tambayi ba'asi ba,amma cikin ranta tana addu'ar Allah yasa lafiya. Babu dadewa kuwa sai gata,ya sakata ta zauna ta ware sababbin da rashin tsafta da kulawa yasa suka lalace,sauran kuwa yace dukka ta samu manyan buhu ta duresu ta fita dasu,hakan kuwa tayi,yasa takai waje ta baiwa mai gadi,sauran masu kyan ta saka masa a booth din motarsa ya sakasu a gaba suka fito a dakin. Jin motsi ya qaru a gidan da surutun yaran yasa ta kasa zaman dakin,tayita kai kawo tsakanin dakinta da kitchen tana kallon qofar dakin nasu tanaso taga waye yazo,dai dai sanda ta fito daga kitchen din muneera ta fitowa da jakar kayan dasu mimi, cikin girmamawa ta rusuna tana gaidata. Fuskarta kadaran kadaham ta amsa mata tana kallon jakar kayan a hannunta,shikam tuni yayi gaba,sai itama muneera tayi mata sallana tabi bayan uncle din nata. Baqinciki kamar tayi me,tabi yarinyar da kallo,tabbas shike sake wulaqantata tare da basu damar da zasu gaya mata magana su kirata da qazama,ya kira yarinya har cikin gidanta cikin dakin yaranta ta kwashi kaya an fita dasu,tome za'a je ayi mata da kayan yara?,da wannan bacin ran ta dinga mita da.surutu ita kadai a cikin gidan,banda tana shakkarsa saita tsaidasu tabi ba'asi,kai da babu ma mai daukar mata kaya ya fita mata dasu a cikin gida,saidai ta sani,bacin ransa bashi da dadi,dole tana jiyo qarar motarsa ya tasheta suka fita a gidan. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 60 Wuni tayi takaici yana cinta,amma kuma da sukayi waya da anty ummee ta tilastata sakin jikinta "Ke da kike jira kiji albashiri din tafiya dake,me ya kaiki dukka wadan nan abubuwan,dole ki taushi zuciyarki ki nuna masa komai ba komai bane,kuma kiyi dako kar kiyi gaggawar tambayarsa,ha sai in shi ya gaya miki da bakinsa" da wannan shawarar tayi qoqarin gyara dakin yaran,ta kuma tsallaka taje ta gyara nasa,dukda gyaran nata ba wani na azo a gani bane,amma bahaushe yace da babu gwara babu dadi. Cikin kwanakin kuwa ta dunga qoqarin yun dukma abubuwan da tasan yanaso,sai abunuwan nata gaba daya suka zama wanu banbarakwai saboda ba saba yi tayi ba,ita kanta da qyar take kai labari saboda rashin sabo,a wajensa shima abun ya zameasa wani iri,saidai shi din hakan yakeso inda ace zata sauya din. ***********Kwana daya rak amma gaba daya jikinta ya zama week kamar wata mara lafiya,randa ta dawo daga makaranta ma wannan dogon wunin kwanciyar tayi,don haka da dare bacci bacci yayi mata qaura,sai taja wayarta kawai ta soma bin charts na groups din da anty deena ta saka a sanyata,tun abun bai wanu burgeta ko mata dadi har ya fara jan hankalinta,a hankali ta dinga bin topics din da suke tattaynawa daya baya daya,tarin uban saqonni saidai dukkaninsu msu amfani ne ga macen auren dake neman gyara rayuwar aurenta,saidai ga widad fa abun kunya ya zame mata,tana karantawa tana jin kunya ita kadai,musamma idan ta tuna anty deena na ciki. Bayan tayi nisa ta soma fahimtar wasu abunuwa da suka sanyata cikin nqzari da lissafi,an gadi abubuwa masu yawa da ita bata sansu ba,kuma kallon iskanci take musu,amma kuma taji suna batun lada,dama akwai lada cikin iskanci banda tarin zunubi?,saita maida wayar ta ajjiye gefe tana tuno wasu abubuwa,ta dinga saqa tana warwarewa,wa zata tambaya wanda zaiyi mata bayanin da zata gane da kyau,ta kuma fita daga shakka?,ita kanta anty deena maganganun da taga tayin sai suka weedad ke tunani a kanta,tasan dai anty deena ba 'yar iska bace,to amma....... Katsewa tunanina yayi sanda wayarta ta soma wani qaramun ringing mai dadi,ta kalli wayar,kamar ta gane number din,ta jawo wayar ta daga ta sakata a kunnenta. A nutse muryarsa a qasa yayi mata sallama,ajiyar zuciya ta kubce mata ba tare data shirya ba,ajiyar zuciyar data sauka a kunnensa,ta kuma sanya tsigar jikinsa zubawa "Bakiyi bacci ba?"kai ta gyada sannan ta amsa masa "Eh" "Me yasa?" Rasa amsar bashi tayi,saboda dai ba zata iya ce masa ga abinda take karantawa ba "Me tayin kwanan ta shigo?" "Eh" ta bashi amsa,don sai da sukayi sallama da ita sannan ta shigo dakinta,saboda ita a falo take kwana,taqi yarda ta kwana dakin widad din "Yayi,yanzu gaya min dame dame kikayi yau?" Ya tambayeta yana hangen hafsa daga inda yake zaune cikn falonsa,tana nannade wandon kashin da nawwara tayi tana cusashi qasan kujera,ya dauke kallonsa daga kanta ya maida wani gefin,don bayason ransa ya baci. Sosai ta narke cikin pillow din,zuciyarta tana narkewa,kewa tana sake cikata "Bayan kaine....kaine kayi tafiyarka ka barni" ta fada a wanu kugun shagwabe,abinda yayi masifar tabashi,tsigar jikinsa ta zuba sosai,ita kuwa ko a jikinta,saboda tana ganin tayi maganarta ne sak "Am sorry......bazan sake ba" ya samu kansa da fadin hakan ba tare daya shirya ba,dai dai sanda hafsat din ta qaraso wajen,sai taji kamar kunnuwanta basu jiye mata dai dai ba,waye yake baiwa haquri wai?,ta tambayi kanta,ta tsaya cak tana dubansa,yayi kamar bai ganta ba,yaja cup din coffe daya hada kafin ya zauna ya kurba kadan "Yanzu kiyi addu'a ki kwanta,akwai school gobe" "Tom.....sai da safe?" Ta tambayeshi a sanyaye,saboda har ga Allah hirar ta mata dadi,bataso yace ta kwanta ba. Murmushi ya sake kubce masa,a hankali ya furta "Goodnight" sai ya zame wayar daga kunnensa yana kasheta,dai dai sanda hafsat din ta kasa tsaiwa,ta zame ta zauna a kujerar dame kusa dashi "Wai da waye kuje waya haka?" Sai daya kashe wayar ya ajjiye sannan ya dago yana dubanta,yadan zuba mata ido na wasu sakanni sannan ya saki murmushi "Qanwarki ce" "Qanwata ko kishiyata"shine abinda bakibta taji ya kamata ta furta,to amma tana tsoron kada ta barar da tafiyarta,don haka ta hadiye maganarta,sai gefw da tayi da kanta ta tabe baki "Dole yarinyar ta dinga tsoronka,ya zaka dinga gaya mata maganganun da sukafi qarfi kanta,a haife fa ka kusa haifarta,tunda ka ninka shekarunta harda doriya" ta qarasa maganar tana dawo da dubanta kansa. Fuskarsa a sake,saima murmushi daya saki,ya shafa kanshi zuwa kyakkyawan hanarsa dake dauke da gashi baqi sidik daya sha gyara "Kinason ki gayamin na tsufa kenan fa" "Kusan haka ne" ta fada tana tabe baki,a nufinta na zare masa karsashinsa da sha'awar komai,murmushi ya sake saki,abu daya ya sani,komai zatayi ba zataji komai daga bakinsa ba,ta manta wayeshi din wajen riqe sirri "Ki zaro wancan andon kashin ki fita dashi ki wanke,and please.....kada na ganshi a dustbin" ya maida zancan zuwa wani topic din na daban. Kunya da haushi suka cikata,ba wannan batyn takeso suyi ba,ita batasan ma ya ganta ba,maganar gaskiya babu agender din wanke kashi yanzu a gabanta,amma dole ta miqe rana cewa "Kadai dinga mata a hankali tunda yarinya ce,bawai wani abu zata fahimta daga gareka ba" da kallo ya bita yana son tantance da wanne irin sound tayi masa maganar,sai ya maida nayansa jikin kujera,ya lumshe ido yana maimaita maganarta,abubuwa da yawa sunzo kansa a sannan wadanda suka sanya dole murmushi ya qwace masa. Dukka abinda ta karanta a daren washegari ta dunga bitarsu a makaranta,kwatsam ranar sunyi missing periods har biyu,sai ajin ya zamana na surutu da hira,abinda ya sake sanyata daukar wayarta taci gaba da dubawa,saidai tana tsaka da dubawar hirar da 'yan bench din bayansu keyi yaja hankalinta,bata suaje wayarta ba amma ta bada kunnuwanta tana saurarensu,hirace ta aure da yawanci ba'a rasa matasan 'yammata da suke ganun sun fara zama seniors da yinta,fiye da rabin hirar ta zame mata kamar wani mabudi kuma amsa na dukka tambayoyinta,ta dinga saurarnsu tana ciro abubuwa masu yawa tana hadawa cikin maganganun data ji a groups daban daban. Koda aka tashi daya daga cikin qawayenta ta bata ajiyar hausa novels "Ki ajjiyemin don allah widad,yayana yazo gutu,doke sai ya koma zan karba,hanani karatun yakeyi,kada yaje garin bincike bincike ya ganosu na shiga uku" a karba din ta tafi dasu gida,da daddare ta buda jakarta bayan ta gama wani assignment zata maida jakar don kada ta manta idanunta suka gano mata litattafan,saita jawosu ta buda tana kallo tare da mamakin meye a ciki da za'a hanata karabtawa,don ita kallon normal kowanne littafi take masa,taji sha'awar duba meye a ciki,ta dauki daya part one ta buda ta fara karantawa. Ko page daya bata dauka da niyyar karantawa ba,sannu sannu sai gashi har tajai page na wajen biyar,ta saki murmushi saboda labarin yaja hankalinta,saita kife littafin,ta wuce kitchen ta zuba abinci ta dawo taci gaba da dubawa. Sannu a hankali sai gashi ta raba dare tana karatun,sam batasan dare yayi haka ba,don hatta da wayarta ta manta da ita,taje ta samu miscall na abbas kuwa harda sms guda daya,dare yayi don haka bata kirashi ba,sai tayi addu'a ta kwanta,amma kuma bacci ya qauracewa idanunta,tanata bitar abinda ta karanta din cikin kwanyarta,da gaske akwai soyayya irin haka?,soyayyar jaruman littafin ya tafi da ita,ta dinga kwantanta kanta dasu,kunya ta kamata ita akdai cikin dakin,saita kifa kai tana murmushi. Washegari babu makaranta good friday ce,wuni tayi tana karatun,wanda a ranar ta gama da part 02 ta shiga 03,sai data qare littafin a ranar ma sannan ta kwanta,nan dinma dai dukka labarin ta dinga tunawa,yadda jarumar ke gudanar da rayuwarta "Kamar ni da uncle kenan?" Ta ayyana a ranta,da sauri ta girgiza kai,kai anya?,ita kanta wasu abunuwan cikin labarin kunya suka dinga bata,first night dinsu ya dawo mata a rai,sai tsoro ya shigeta,itama wataran haka uncle din nata zaiyi mata?,amma wannan ai iskanci ne,to amma dama akwai ranar da wannan abun zai tashi daga sunan iskanci?,ta tuna haihuwar da jarumar tayi,suna nufin kowacce mace ta haka take haihuwa?. A daren qwaqwalwa da tunanin yarinya kala kala ta dinga yi,abubuwa da yawa ta watsar dasu tana ganin bazai yiwu ba,ta rungumi abubuwa da yawa da syka dinga burgeta,har ta dinga kwantata gwadawa. Da safe kuwa ta gwada abunuwa da yawa da ta karanta din,duk da tana wasu qarawa tayi,ta gama komai ta hada breakfast dai dai cikinta,din me tayata kwana gari na wayewa take komawa cikun gida tayi ayyukanta,bata dawowa sai wani daren,ko idan bata da abinda zatayi ta leqota su gaisa sannan ta koma,mayar mai gadin gidan ce,tana da matuqar kirki sosai. Tana cikin yin breakfast taji sha'awar kiransa kamar yadda taji jarumar littafin tana yi,gabanta ya dinga faduwa sabida rashin sabo,ta dinga jin tsoro tana ganin kamar ba wani abun burgewa bane,saidai duk da haka bata fasa kira ba. Lokacin ya shiga wanka,hafsat na zaune daga gefan gadon nasa tana dakon fitowarsa,da sauri kamar wadda aka kirayi wayarta ta dauki wayar tana duba mai kiran "Weedad" ta maimaita sunan data gani a rubucen cike da mamaki,kanta ya daure da kyau,ita dince ke kiran ko kuma dai idanunta ne,ko wata ce mai irin sunan,saita daga kawai kai tsaye. Shagwababbiyar muryarta data zame mata jiki,ta kuma saba magana da ita,da ita tayi sallama "Ke tsaya" hafsat ta fada da sauri dai dai sanda take ficewa a bedroom din don kada ma ya jiyota. Wani mugun faduwa gaban widad yayi jin muryar mommy hafsa "Ina kwana mommy" "Da ban kwana na zaki jini?,wa ya sakaki kiransa ko shi din sa'anki ne?" Mamaki ya bayyana a fuskar widad din,ta dauka ba komai,ta dauka momy din zata ce ta kyauta,saita kasa gane yadda abun yake "Kiransa nayi mu gaisa mommy,jiya ya kirani ban dauka ba" tashin hankali!!, Ta fada a ranta tana jin yadda fuskarta ta dauki wani irin zafi,zazzafan kishinta da taketa qoqarin dannewa ya taso mata "Yanzu ke har kisan ki kira d'a namiji kusan sa'an babban wanki koma babanki,ashe baki da kunya kwata kwata,to ba sa'anki bane,idan kika sake kiransa ko kuma ya sake kiranki kika daga saina miki mugun duka,ke bakya tsoron abinda zai sameki?,na gaya miki ba'a sakar musu fuska ko jiki,so kike yayi miki ciki ki mutu ko?" Karon farko taji maganar mommy hafsa din banbarakwai,sai taji kanta ya kulle "Karna sake ji kuma kada na sake gani,kina jina?" Ta tambayeta a tsawace "Tom" ta amsa mata jiki a sanyaye,sai hafsat din ta katae wayar tana jan tsaki,taso yarinyar na gabanta,amma bari ya fita,zata sake kiranta ta sake jadda da mata. Jiki a sanyaye ta ajjiye wayar, kwanyarta ta shiga rububin lissafin maganganun hafsat din,zuciyarta taqi amincewa da hakan jikinta yaqi karba kuma ranta yaqi gamsuwa,saboda aduk abubuwan data karanta bataga ta inda aka nuna abune mara kyau ba da har mommy hafsat din zata dinga mata fada haka ba,kusan minti goma ta kasa samun nutsuwa,sai tunani yazo mata,sai kawai ta kira anty deena tace bari ta tambayeta. KI KULANI miss xoxo DAUDAR GORA Billynabdul RUMBUN K'AYA hafsat rano IDON NERA Mamuhghee A RUBUCE TAKE huguma _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_ _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_ 0022419171 Maryam sani Access bank Saiku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan* 09166221261 *Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number* +227 96 09 67 63 *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:huguma* Page 61 Kiran farko aka gaya mata user busy,tadan dakata na wasu mintuna sannan ta qara kiranta,cikin sa'a kuwa ta shiga "Aah,kaga amaren kaduna" anty deena ta fada cikin tsokana,da yake idan taso tsokanarta haka take ce mata,dariya ta danyi ta gaidata tambayarta yaranta,ta amsa mata da suna lafiya,suka dan taba hirar data shafi gda sannan daga bisani shuru ya biyo baya,sai anty deena dince tace "Kina bibiyar kuwa karatun da ake a groups din nan,kinsan kudi na biya kada ki sakani nayi asarar kudina" dariya ta danyi "Inabi Allah anty,a ciki ma naga wani abu,nayi kuma to mommy hafsa tanata fada,nace anty ko banyi dai dai bane?" Ta qarasa fada a shagwabe "Me kikayi kuma?" Antu deena ta tambayeta,bata boye mata ba ta gaya mata komai,anty deena tayi shuru tana nazarin maganar cikin ranta,zuciyarta na hasaso mata wani abu,amma kuma nataso ta dora nata tunajun ko tunanun yarinyar akan hakan,tunda dukka dan adam ajizine,zai yiwu ajizanci ne da kuma yanayi ma kishi da zai iya motsawa kowacce mace a kowanne lokaci "Bakiyi abu mara kyau ba widadun ummu..." "Ba wani widad din ummu yanzun fa anty deena ta daina sona,su Aafiya tafiso,kullun mukayi waya sai tace zatazo amma taqi zuwa" murmushi ya kubce mata "Zatazo weedad,kullum ummu cikin zancanki take,amma kafin sannan.....inaso kome kika gani ance ayi kiyi qoqarin yinsa,zaki yi?" Ta tambayeta,saita gyada kai "Eh anty deena" "Yauwa widad dinmu,sannan ko meye kika gani baki gane ba ko ya faru ki kirani,koni ko anty madeena ki tambayemu,ba komai ne idan mommy hafsa tace kiyiwa uncle din naki zaki dinga yi ba kinji ko?" "Tom anty deena" sun dan jima suna waya tana sake wayar mata da kai a fakaice sannan sukayi sallama,koda suka gama wayar litattafan ta debo ta sake zabo wasu a ciki ta dora da karatunta,itama tama manta d batun mommy hafsa da duk matsalolinta. Rai bace hafsat din ta goge kiran da widad din tayi masa,sannan ta koma dakin ta maida wayar ta ajjiye ta kamar yadda ta ganta taci gaba da zaman jiransa,amma kuna qasan ranta a quntace yake da abinda ya farun,tana zargi da kuma tuhumar kanta,kwana biyu ta watsar da kiran yarinyar bare taci gaba da saita mata hanya,amma fa tana tsoro,kada ya zamana ta hadu da gogaggu kima wayayyun da zasuyi mata karatun da yafi nata shiga,tunda kaduna badai hadakar gamayyar mutane daga gari da qabila kala daban daban ba,amma zata kira ta binciki hajiya amina taji dawa dawa take hulda. Koda ya fito daga wankan baisan anyi kiranshi ba,saboda qarar shower ta hanashi jin ringtone din,yana goge ruwan jikinsa tana binsa da kallo,jikinsa luwai luwai, fatarsa mai santsi da taushi sai daukar idanu takeyi, muscles din a hade alamun ya samu kyakkyawan training,ta hadiye wani abu da qyar saboda kishinsa daya tsarga mata. Waiwayawa yayi suka hada idanu da ita,saiya dauke kansa yana cewa "Ya akayi?,me yake faruwa?" Qaqalo murmushi tayi sannan tace "Har yanzu banji kace na fara hada kayana ba" "Zuwa ina?" Yayi mata tambayar bayan ya isa gaban madubi yaja lotion dinsa zai fara shafawa,wani abu ya tsarga mata amma ta dake "Umara mana" sai daya kalleta ya kuma ci gaba da shafa mansa sannan yace "Ban shirya wannan zuwan dake ba,babu kudi a hannuna,ina cewa ma ko wata shida bamuyi da zuwa ba ko?" "Eh amma ai musulmi baya gajiya da zuwa" kai ya gyada "Haka ne,amma yanxun bani da kudin da xamu iya tafiya mu duka,ke ni da hajiya" ranta ya baci sosai, zuciyarta tayita qissimata mata abubuwa da yawa da zata gaya masa,a fakaice dai hajiyan kusan duk shekara saiya kaita kenan,tunda itama ai baara iwar haka taje "Aure ya cinye maka kudin kenan?" Ta tambayeshi tana tsareshi da ido,ya sake waiwayowa ya kalleta,ya kuma karanci yanayinta cikin sakanni,sai ya kuma dauke kansa ya maida ga abinda yakeyi,bayason doguwar magana,hakanan baya qaunar mita da qorafi "Idanma hakanne ba mamaki bane" tofa,baki yasan me zai fada amma baisan me za'a mayar masa ba,saita miqe a mugun fusace "Allah yayi mana arziqin da zamuyi ta zuwa babu mai hanamu" sai tayi waje fuuuu kamar zata tada iska. Ransa ya sosu,amma ko iskar data kwasota bai kalla ba,yaci gaba da shirinsa,kafin ya sanya kayansa ya tsaya ya tsaftace sassansa,ya kuma dafa coffee yasha sannan ya qarasa shiryawa ya fice abinsa,yasan bazai rasa abinci gidan hajiya ba. Tun daga wannan maganar ta dauke masa wuta gaba daya,shima kuma ya tattarata ya watsar ya baiwa banza ajiyarsa,yana ganin guga koda baiyi tsiran komai ba yayi na igiya,ta yaya zatayi kishi da mahaifiyarsa ko nawa kuwa zai kashe mata?,ita din ai ba tsararta bace. Duka kwanakin da yayi kowa sabgarsa yake,amma hafsa din ta fishi damuwa,saboda tana da buqatar kudi a wajensa,baya ga haka tanason ya dawo da widad din har su dawo daga tafiyar,a wata dayan da zasuyi tasan zata moreta sosai,zata kuma dora mata karatun da zai zauna daram a kwanyarta,amma girman kai da jin tafi qarfin tayi qasa yasa taji gwara tayi shuru duk abinda ma ya yanke shikenan. Ta bangaren widad kuwa cikin kwanaki qalilan karatun hausa novels ya shigeta sosai,idan tana karantawa tana jinta ne kamar a wata duniyar ta daban,yana debe mata kewa,tana kuma ganin abubuwan da suke bata mamaki,duk kuwa girki ko drinks din data gani saita gwada,a lokacin kitchen dinta yaga rayuwa,saidai duk abinda ta gwada din idan taga yayi farinciki cikata yakeyi,mai aikin maama(hajiya amina) ke tayata wani bin,tana ganinta kamar latifa saboda kirkinta. Ranar da zai baro kadunan zai biya ta gidan hajiya ya daukota su wuce,har ya kammala shirinsa tsaf a sassansa tana nata sashen tana baccinta,don tun daga waccan ranar basu qara hada makwanci ba,tana sashenta yana nasa,yaci alwashin ko meye zatayi badai shi da qafafunsa ya bita yayi begging nata ba,yasan abinda takeso kenan. Tare dasu mimi suka fito,a wajensa yaran suka kwana,tsaf dasu don su kansu sai daya shiryasu ya kuma gyara sasssan,suna riqe da hannunsa ya tura ya shiga,falon a hargitse kamar wanda aka tashi taron biki,harsa pampers din nawwara da yayi imanin idan bana shekaran jiya bane na jiya ne "Ku zauna nayi sallama da mamanku" ya fada yana kallonsu,sai suka amsa suna hayewa saman kujerar,ya ajjiye luggage dinsa ya nufi qofar bedroom dinta,don ko takalminsa bai fidda ba saboda tsaftar tiles din ma bata gamsheshi ba,duka yayi rod'i rod'i kamar an watsar da ruwan tea ya fara bushewa samansa. Sau uku yana knocking sannan yaji ana tambayar waye da cunkusashiyar muryar bacci,gyaran murya kawai yayi,ta taso tana turbune fuskarta daya kacame saboda bacci ta buda qofar. Ido hudu sukayi, doguwar rigar wata kodaddiyar atamfa ce a jikinta da aka yiwa adon net,net din har ya soma bubbulewa alamun dake nuna ya fara gajiya da aikinsa,kanta gashinta ne him daya hautsine kamar ciyawar da aka tara za'a ciyar da dabbobi,abinka da baqar fata idan bai shafa mai ba....duk jikinta yayi fari fari,dakin yana fidda irin abinda jikinta ke fiddawa,da alama ya kama ko ina. Kansa ya dauke,don takaicinta bazai kasheshi ba,ya fara gajiya da al'amuranta da kullum babu gyara sai gaba da abun yakeyi,ya sanya kai cikin dakin,dole ta kauce masa ya rabe ya shige,sai ya kasa zama,yana kallonta ta tsince pant dinta da bra dake watse a qasa "Ina kwana?" Ta gaisheshi murya a cushe "Lafiya....mu zamu wuce" ya bata saqo a gaggauce,saboda qagauta da yayi da wanzuwarsa cikin dakin,ya zura hannunsa a aljihu ya fiddo rafa na kudi ya matsa gefanta ya ajjiye mata yana cewa "jibi zamu tashi,zamuyi sati uku idan ta kama har hudu ma,saboda inaso zamu tsaya egypt hajiya zataga likita,duk yadda ta kama dai....shikenan babu wani abu?" sai a sannan ta dago ta sake kallon sa "Daa ka sani ma baka shigo ba,inda wucewarka kayi da hakan yafi" tsareta yayi da idanunsa yana mamakin furucinta "Hafsa.....magana nake miki ta zanyi tafiyar da babu lallai na sake dawowa fa" gaba tayi tana qoqarin komawa cikin bargonta "Allah ki yaye hanya" ta fada cikin nuna halin ko in kula taja bargo ta rufa abinta,saidai tuni idanunta sun cika da hawaye,banda qin Allah,da kudin da zataga likitan basai ta haqura ba a biya musu tare,idan suka dawo taga likitan a nan ba,ai duka daya ne,to amma a'ah,wai dole sai an nuna maka iyakarka. Sai daya bata kusan mintuna a tsaye yana kallonta ta cikin bargon,zuciya na hasalashi amma ya hadiye ya juya a hankali ya soma fice daga dakin. Wuf tayi ta yaye rufar ta kuma sauko daga gadon,da gudu tasha gabansa "Au tafiyar zakayi?" Ta fada hawaye yana layi kan fuskarta,kallo daya yayi mata ya kauda kansa,saboda yadda zuciyarsa ke azalzalarsa "Tun ba yau ba nasan baka damu da damuwata ba dama,ba abinda ya shafeka da baqinciki na ko walwalata,to kaje,amma ka sani akwai hisabi tsakanina dakai,Allah bazai taba yafe maka ba idan ka zalunceni" ido ya runtse yana jin zafin maganganunta,ya budesu a hankali sai suka kan yaransu,mimi da nawwara suna tsaye daga bayanta sunyi carko carko,da alama sun fahimci wani abune mara dadi yake faruwa. Maganganu ne da yawa a ransa da amsoshin da zai bata,amma sai ya hadiye,muryarsa a sarqe yace "Naji,Allah ya saka mikin,matsa ki bani hanya" jagale tayi tana kallonsa,sai kuma ta saki qofar ta koma ciki da gudu ta fada gado tana sakin kuka,baiko waiwayeta ba ya matsa zuwa gaba,ya sunkuya yayi kissing goshin yaran sannan ya kama hannunsu zuwa falo ya kunna musu cartoon yayi musu dabara ya fice. Har suka kama hanyar kaduna ransa a bace yake amma yaketa dannewa saboda kada hajiya ta fahimta,yasan yanzu zata gaza nutsuwa. Sai da suka shiga garin kaduna sannan ya fara tunanin yadda zasu samu widad ita kuma,abinci da zasuci da sauransu,yau dai ba makaranta yasan tana gida,to amma abinci bashi da tabbacin zasu samu,tunda ga wadda a haife ta haifeta ma bata da wannan tunanin,ina ga ita?,ya yanke kawai idan sun isa yana kai hajiya ciki ya koma ya siya musu abinda zasuci ya hada musu da order din abincin dare,gobe kuma ya samu time yayi musu,da wannan tunanin suka shiga unguwarsu. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:huguma* Page 62 Tun jiya da ya kirata yace mata gobe zasu taho da hajiya,tayi murna sosai saboda zaman kadaicin ya isheta amma bata kawo wai ta tanadi komai ba,ta dauki littafinta taci gaba da karatunta,tana tsaka da karatun taga inda jarumar littafin ke shirye shiryen dawowar mijinta daga tafiya,abun sai ya burgeta sosai,ta idar da sallah azahar tana saman abun sallah abun ya sake fado mata,saita dauki wayarta ta kira anty deena tana labarta mata "Kema irin hakan zakiyi, bakiga abincin da aka kiya jiya ba a group?" Kai ta gyada "To haka zakiyi,ki shirya shi kamar yadda aka koyar ana shirya abincin mutum" daga kan abun sallar kuwa bata koma yin komai ba ta fara practicing abincin,datayi kuma yayi mata yadda takeso,suna da komai ba abinda zata buqata,saita fara shirya komai tun a ranar. Washegari gari yana yin haske ta gyara gidan,dama ta saba wannan ya fara zame mata jiki,saidai yau har dakinsa ta gyara kamar yadda anty deena tace mata,tana yi tana kiran anty deena ita kuma tana qara mata haske,tana aikin suna video call da anty deena ta watsapp,sannu sannan sai gashi har girkin ta gamashi tsaf,ta kuma zuba a warmer,ta jera,anty deena ta kalla ta cikin wayar,cikin farinciki tace "Well done qanwata,yanzu saura abu daya" langabe kai widad tayi "Allah anty na gaji sosai" "Aikin gama,sauranki wanka,ki dauko kayanki na zuwa gidan biki ki saka,yau duka kayan kwalliyarki ki juyesu a fuskarki" ido widad ta zaro tana dariya "Kai anty....suna da yawa fa" dariya itama tayi "Ai wai ina nufin ayi kwalliya da kyau,a saka turaren gida dana jiki ako ina" dan turbune fuska tayi "Wai anty duk uncle akewa haka?" "Kai,ai yafi gaban haka ma,ba kinje min litattafai kika samu kina karantawa ba?,bakiga yadda akeyi bane?" Batason tacewa anty deena din eh,saboda wasu guraren cikin litattafan kunya suke bata(tsarkakakkun litattafai wadanda babu batsa a ciki sai qaruwa),kai ta gyada mata a kunyace "Good,maza kije ki shirya to" cewar anty deena,daga haka suka katse kiran,ta dauki wayar ta wuce bedroom dinta,tana tafe tana hangen dining din kamar wani zai bata mata aikinta,saidai murmushi kawai takeyi najin dadin yau ta qure adaka tayi abinci,gidan kansa yadda yau ta gyarashi ita da kanta yana bata mamaki. Sai data bata lokaci a daki tana zaben kayan da zata saka,anty deena dai tace mata atamfa,ita kuma babu abinda tafiso irin doguwar riga abaya,don kusan kullum itace shigarta,kamar kuma sunsan zabinta sun sakota da yawa sosai a lefenta,tana kallon abayar ta haqura,ta ciro atamfa riga da skert,blue black mai adon maroon,sannan ta shige bandakin ta hada ruwan wanka ta fara wanke jikinta. Tana wankan tana 'yan waqe waqenta qasa qasa,saboda yau din nishadi takeji cikin ranta,ta gama cuda jikinta ta shige asan shower ruwan yana ratsata,saita tuna gida,ummu na hanata shiga shower saboda wasa takeyi da ruwa, kuma tana jiqewa har kanta ne,sumarta nada tshao da yawa,yawancin lokaci saidai a saka hand Drayer a busar mata da ita,saita saki murmushi,tana jin ba dadi cikin ranta,ko sai yaushe zata ga ummu?,bata tabq zato a rayuwarta zatayi nesa da ummu har haka ba ta kuma haqura ba. °°°°"alhamdulillahi" hajiya ta fada tana fitowa daga motar bayan tsaiwar motar tasu a farfajiyar gidan,murmushi abbas yayi "Yau gaki a kaduna dai" sai tayi murmushi "Eh nufin Allah kenan" yana janye da trolly dinta, muneera na dauke da jakar hannunta suka doshi sashensu. "Assalamualaikum mutan gida" hajiya ta fada tana murmushi idanunta cikin falon,wani boyayyen ajiyar zuciya abbas din ya sauke,saboda hango warmers da yayi saman dining din,uwa uba yadda fakon yake a tsaftace ya qawatar dashi,duk da dama bai tana ganin wani abu na qazanta ko qanqani a tattare da ita ba,hasalima yana mamakin yadda bata son taji ta taka datti "Ki zauna hajiya,inajin tana daki" ya fada yana janye mata pillow din kujerar,tayi bismillah ta zauna,haka kawai taji ranta yana mata dadi,ya juya ya dubi muneera "Ki samo muku ruwa da lemo" "Aah,bari dai matar gidan ta fiti tukunna ta shaida xuwanmu ko?" Murmushi abbas yayi "Peace maker" shine sunan da sau tari yake kiran hajiyarsa,bata qaunar tashin hankali ko kuma husuma ko kadan. Kayan daya gani baje saman gado yasa hankalinsa yadan tashi,bai kuma ji motsinta ba,ba tare da tunanin komai ba ya murda handle na bandakin ya tura ya sanya kansa. Dai dai lokacin da take tsaye babu komai a jikinta,sai towel a hannunta tana tsane gashin kanta,mugun zabura tayi ta kuma tsorata matuqa,saidai data waiwayo suka hada ido sai taji kamar zata narke a wajen,saboda tsorata saita jefar da towel din,ta kuma sulale a wajen ta duqe tana cure jikinta waje daya,ko ina na jikinta rawa yakeyi,take ta fash da kuka. Shi din ma kamar an jona masa lantarki haka yaji,ganinta a hakan ba qaramin al'amari bane a zuciyarsa da kuma gangar jikinsa,ya rintae idanunsa ya koma baya days saut yana mayar da qofar yadda ya ganta,saidai ya kasa sakin hannun qofar,yayi tsaye riqe da handle din yana maida mumfashi. A hankali yaci gaba da sauke jumfashun nasa ta baki data hanci,ya bude idanunsa a hankali yana jiyo sautin kukanta,yasan yau kam ya taro match,sai ya matsa jikin qofar cikin kasala yace "Am sorry" shuru bata amsa masa ba,sai ya sake daga murya "Am very sorry" cakin muryar kuka tace "Kana sane ka budeni,ai kasan wanka nakeyi" murmushi ya saki tsigar jikinsa na sake zuba a,daga dawowarsa ta masa wani irin kunnawa da yasan bashi da maganinta "I swear bansan kina ciki ba.....am sorry.... please kiyi shuru mana" "Allah tunda ka ganni tsirara bazan yadda ba" ta fada bayan ta miqe tana daura towel dinta da sauri,tana tsoron kada ya dawo. Murmushi mai kama da dariya ne ya kubce masa,shagwabarta tana kasheshi ainun "To shikenan,let me come inside,sai na cire kayana kema ki rama,kinga shikenan anyi one one" "Wayyo ummuna....Allah karka shigo,idan ka shigo saina gayawa ummu" ta fada tana gunjin kuka jin yana taba qofar kama zai bude,dariya sosai ta kamashi har sai daya dan sunkuya "Alright.....alright,shikenan,khalas.....ya isa,am sorry,ki qarasa ki fito,hajiya na falo tana jiranki" ya danja da baya har yanzu fuskarsa murmushi ne kwance akai ya baro dakin,gaba daya bacin ran daya taho dashi babu kaso hamsin cikin dari. Da sauri ta miqe ta qarasa wankan jin cewa hajiya ta qaraso,ta shirya a gurguje,bata saka komai kan fuskarta ba,saisai jikinta ya wadata da turare,sanon turare ne ta bude cikin kayan lefenta. Rungume hajiyan tayi abinta tana jin dadi,sai take ganin kamar ummunta ce tazo,ta ma mance dashi a wajen,suna gama gaisawa ta gabatar mata da lemuka da ruwa "Hajiya na kawo miki abinci?,ni na girka da kaina" ta fadi tana murmushi,ta qagu taci taji me zata ce,dariya tayi "Bari nayi sallah tukunna widad,nunan bandaki" Dakinta ta kaita ita da muneera duka harda kayansu,sukayi sallah sannan suka dawo falon ta fara zuba musu abincin,a sannan abbas daya fita salla masallaci bai dawo ba. Hankali kwance suke cin abincin suna hira,duk yau sai widad takejinta free kamar a gida,babu wanna kadaicin ba komai,har suka gama bai dawo ba,sukaci gaba da hirarsu hajiya na jinsu,yanayin da taga widad yayi mata dadi sosai,saboda ta qara wani irin haske akan wanda take dashi,hakanan ta murje sosai,duk da ba qiba tayi ba,amma fatarta tayi kyau. Yamma liqis ta sake shiga kitchen ya gwada yin tuwo miyar kubewa,tanata taraddadi kada tayi kwaba,cikin ikon Allah sai gashi tayi shi fes,abinda ya faranta mata ranta,ta gama suka gyara kitchen din,muneera tayi mata wanke wanke sannan ta gabatarwa da hajiya bayan sunyi sallar magariba. Farincikin da hajiyar ta tsinci kanta a ciki ba dan kadan bane,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba cin.abincin gidan abbas din ba sai wannan karon,karamcin da yarinyar ta nuna mata ya qara dad'ad'a abincin a bakinta,ya kuma qara mata qaunar widad din a zuciyarta. Tana ta so tayi wanka amma kuma sai takejin nauyin hajiyan, saboda ba zata iya tube kayanya cikin dakin ta shirya ba,sai ta basar kawai sukaci gaba da hira abinsu. Ana idar da sallar isha'i dukka suna falo,a sannan yayi sallama ya shigo,hannunsa dauke da leda,dukkan alamun gajiya sun bayyana a tare dashi. Kusan a tare sukayi masa sannu da zuwa,ya amsa yana zubewa gaban hajiyan yana mata barka da dare "Ina ka shiga haka?,tun dazu nake taraddadi" "Wallahi na leqa office ne,akwai ayyukan da nakeso na rufe file dinsu kafin mu wuce,kuma zan dauki excuse ma.na tafiyar tamu".kai ta jinjina "To Allah yayi.jagora ya dafa" "Ameen ameen hajiya,kunci abincin dare?" Sai da tayi murmushi sannan ta amsa "Munci abinci kuwa,tuwo ma,mun qoshi kuma alhmdlh" "To ma sha Allah" ya fada ransa na masa fari,bai taba zaton zai tadda hakan ba,ya saci.kallonta kanta yana a qasa tana wasa da zaren dankwalinta,har yanzu haushinsa takeji,kunyarsa kuwa kamar ta bace a wajen,musamman idan ta tuno a yadda ya ganta,ko ummu bata zaton ta taba ganinta a haka da wayonta. "Na gaji fa sosai,inajin kwanciya zan shiga nayi" hajiyan ta fada tana miqewa,sai muneera itama ta miqe,don itama a gajiyen take "Ya kamata" "To Allah ya bamu alkhairi,sai da safe" tayi musu sallama suka wuce dakin ita da muneera. A hankali ya tattaro dukka.hankalinsa a kanta,ya xuba mata idanuwansa yana kallon ta,da gaske ba zata kalleshi ba,har yanzu baku dankwalinta yana hannunta tana ta murzasu,cikin sakanni jikinta ya bata saqon cewa ana kallonta, tasan kuma shine,saboda rashin wanzuwar motsinsa kadai ya isa amsa. Dan daga kai tayi,sai suka hada idanu, karon farki taji ba zata iya jurewa ba,ta saki gefan mayafin ta yunqurq zata miqe "Ina zuwa?" Ya jefa mata tambayar,qeya ta juya masa,ya kuma tura baki gaba "Zanje na kwanta,nima baccin nakeji" yadda tayin ya bashi dariya,amma ya maze "Haka zaki tafi ki barni,ni baki bani abincin ba yuwa nakeji" ya fada yana karyar da wuya kamar qaramin yaro,shi kansa baisan yayi hakan ba. Dan jim tayi,sai maganar anty deena ta dawo mata "Idan ummu taga yayi miki ba dai dai ba ko nuna rashin kulawa,kinsan zataji babu dadi ko?,to kema idan kika masa hakan hajiyarsa ba zataji dadi ba" da wannan tunanin ta juya zuwa dining area don kwaso masa abincin,yabi bayanta da kallo,sosai skert din ya zauna mata das das,ya fidda qugunta dake juyawa sanda duk tayi taku,kamar da gayya takeyin hakan,ya janye gajiyayyun idanuwansa a hankali ya lumshesu yana furta kiran sunan Allah. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 63 Koda ta hado kayan abincin ta dawo bata sameshi a falon ba,amma taga qofar dakinsa a bude,da alama yana ciki,tadan bata fusja kadan,itafa batason haduwarsu sam,ya gama kalle mata jiki ta yaya zata iya fuskantarsa,amma dai babu yadda ta iya,haka ta taka zuwa dakin nasa roqe da tray din data shiryo komai akai. Sanda tayi sallama ta shiga ya gama fidda kayan jikinta,daga shi sai pant na maza iya cinya,a yadda ta ganshi tayi masifar tsorata,don bata taba ganinsa koda singlet ba,hakanan tsahon rayuwarta bata taba ganin wani namiji haka ba sai a kansa,saura kadan ta zubda kayan hannunta,taja baya da sauri tana neman qofar fita amma sai ya rigata isa wajen,yasa hannu ya maida qofar ya rufe,ta bude baki ya tabbatar ihu ko kuka zata masa,sai yasa hannunsa saman bakinta ya rufe da kyau,sannan yasa daya hannun ya karbe tray din daketa tangal tangal a hannunta zai kife ya aje a qasa. Dab da ita ya matsa,har jikinsa yana dan gogar nata,sai taji kamar numfashinta zaiyu qaura yabar gangar jikinta,manyan idanunta gaba daya sun fito waje kamar zasu fado. Magana yakeson mata amma ta maqale masa a maqoshi,qamshinta dake tashi daga jikinta keson rikita masa lissafi,idanunta masu haske da ruwan hawaye ya cikasu suka soma fusgarsa,yayi ta maza cikin taushi da raunin murya yace "Keep silent please..... hajiya tana ciki fa,so kike tace na miki wani abu?,zata batamin rai idan haka ya faru" ya qarashe zancan a narke kamar yaron dake tsoron duka daga mamansa. Sake sanya idanunsa yayi sosai cikin nata,itama shi take kallo,wasu irin idanuwa da suka dinga tilasta saukar nutsuwa a jikinta,a hankali yaci gaba da aike mata da wani saqo ta cikin idanuwansa,har hawayenta suka fara bacewa,nutsuwarta ta fara daidaita,kunya ta maue gurbin tsoronta,sai ya sauke hannunsa a hankali daga kan bakinta daya gaji da motsawa yayi laqwas,yaja da baya a hankali ya dauki babbaj towel ya rufe jikinsa sannan ya doshi bandaki,doke sai yayi da gaske,ya cire tsoronsa daga ranta muddin yanason su zauna zama na auratayya mai dadi,sai ya sake kawo kusanci sosai a tsakaninsu,sai ya zama komai nata ya kusanta kansa da rayuwarta,tana da kima da darajar da yake jin dole ya sama mata gurbi a rayuwarsa,saboda ita din kamar isharar mahaifiyarsa abar soyuwarsa ce,ya zama dole ya kimantata ko don farincikin mahaifiyar tasa. "Ka rufe qofar fa" ta fada bayan ta hadiye wani abu muryarta tana dan rawa,har ya sanya kai a toilet din sai ya fasa ya waiwayo "Ki jira na fito daga wanka tukunna" sai ya shige. Jikinta babu kuzari ko kadan ta sulale ta zauna a wajen,wani abu ya fara mata yawo cikin kwanyarta gangar jiki da kuma zuciyarta,a yau daya kusanta kanshi da ita bawai tsoro kadai taji ba,kunya nauyi da kuma wani irin yanayi da batasanshi ya mamayeta,saidai akwai wani irin tsoro nasa danqare a zuciyarta,hakanan yana mata mugun kwarjini mara misali. Yana goge ruwan jikinsa yadan kalleta,ta takure waje daya,ta kuma qi yarda su hada idanu,ya saki boyayyen miskilin murmushi,yasan me yake damunta,ya matsa gaban mudubi ya fara shafa mai "Kina sane kenan kika shigomin daki ko?,kin rama nima kin ganni babu kaya" yayi maganar yana kallonta ta cikin mudubin,kai ta daga da sauri,suna hada ido ta mudubin kuma saita maida kan nata ta fara qananun hawaye harda rantsuwa ita batasan ya cire kayansa ba,ita bata kalleshi ba,dariya kamar yayi me,wanann wautar tata da quruciyarta wani bangare ne dake sanyashi nishadi,ya gama shirinsa cikin wata armless fara qal din shirt,sai wando daya tsaya masa iya qaurinsa "Ai shikenan......" "Budemin to zan tafi" ta katsi numfashinsa "To zubamin abincin naci tukunna" da sauri ta zuba masa komai ya zauna zai fara ci sai ya kalleta "Zauna muci" kai ta gyada "Na qoshi" "Bakison tafiya kenan?" Kai ta kada da sauri,saita matso ta sanya hannu suka fara ci. Suna ci yana kallon idanunta,saidai ko kadan taqi yarda ita din ta kalleshi,yadda cin abincin yayi masa dadi saboda ya saba ci dasu mimi a gida nan kuwa saishi daya.....haka abincin ma yayi masa dadi "I can't believe ke kikayi girkin nan" abinda take son ji dama taji ya yaba kenan,har batasan sanda ta kalleshi ba tana dan murmushi "Allah nice nayi,yankan kubewa kawai muneera ta tayani" "Wow...wow,,nan gaba ina da great cook kenan,na shirya cin abinci da kyau" murmushi ya subuce mata,tayi qasa da kanta,tana jin dadi sosai har cikin ranta. Ganin ya gama cin abincin yana shirin sake zama sai tace mishi "Kace idan ka gama zaka rakani fa" "Oh yeah,muje to" ya furta yana sanya bedroom slippers dinshi,yana gaba tana binsa a baya. Murda qofar kadan yayi,sai ya waiwayo yana dubanta da alamun damuwa kan fuskarsa "Ayyah....sun riga sun kulle qofar" kallon qofar tayi sannan ta kalleshi "Wayyo Allah na" "Ko ayi knocking ne?" Ya fada da sigar jarrabata,taci kuwa jarrabawar da karon farko.ta qara mata kima da daraja mai dimbin yawa a idanunsa,don kai ta girgiza "A'ah,ummu ta hana,tace ba'a tashin babba idan yana bacci,hajiya ta gaji tun dazu na gani.....amma saidai....." Sai kuma tayi shuru tana kallonsa. Wani qawataccen murmushi ya saki,idanunsa cikin nata yana jin kamar suna narkewa ne zuwa sassan jikinsa "Saidai me?" "Saidai na kwana a falo?" Kai ya girgixa "Qwarai kuwa" ya fadi sounding seriously,sannan ya fada takawa yana nufar qofar dakinsa,da hanzari ta taka ta bishi,harda riqo masa hannu ba tare data sani ba "Da gaske tafiya zakayi ka barni a nan?" Kai ya kada,yanata qoqarin danne dariyarsa "Yes,da ina zaki bini?" Marairaice masa tayi,harta fara guzurin hawaye "Please mana,kaji tausayina" badon yayi da gaske ba wannan karon dariyar saita fito "Oh.... okay,me kikeso yanzu?" "Ka barni na kwana a dakinka,nan din tsoro nakeji Allah" ido yq zaro kamar gaske "Dakina kuma?" "Eh" yadanyi shuru kamar mai tunani "Matsalar ni gaskiya ba za'a hanani kwanciya a gadona ba,kuma idan muka kwanta gado daya ina da juye juye,zan.iya danneki ban sani ba,saidai ki tasheni idan kikaji haka saina dagaki,kin yarda?" Kai ta gyada da sauri,saboda kukan mage data fara jiyowa "Fine,muje" tuni tayi gaba suka jera kafada dashi, dariyar kamar yayi ke haka ta dinga cinsa,yana sane yayi mata wannan hikimar,banda haka tubura zatayi masa. Ta rigashi kwanciya amma idanunta biyu,yana kallonta ta ninka duvet dinsa guda daya ta raba gadon dashi,taja daya ta lulluba, murmushi yayi qasa qasa "Zanyi maganinki yau kam" ya fadi yana maida dubansa ga takardun da yake dubawa,sai daya gama komai,sannan ya haye gadon,ya jawo wayarsa ya kunna sound na kukan mage,ya saitashi wajen kanta ya koma ya kwanta abinsa. A hankali kukan magen ya fara ratsata daga baccin daya dauketa,dama kuma ba wani nisa can sosai baccin yayi ba,rudewa tayi gaba daya saboda jin kukan a kusa da ita sosai,batasan sanda tayi cilli da katangar data gina a tsakaninsu ba, hankali kwance yaji ta shige jikinsa hadi da qanqameshi,wanan lallausan jikin nata ma'abocin qamshi ya nutse cikin faffadan qirjinsa,sai ya saki wani tattausan murmushi,cikin sanyi ya kamota zuwa jikinsa sosai ya mata kyakkyawar runguma da har sai da zuciyarsa ta gamsu da hakan,ya dora hannunsa a gadon bayanta yana dan bubbugawa "Shshhhhhhh.....,zata tafi fa.....yanzu" maganar tasa ta rarrabe saboda yadda ta raba tsakanin cinyoyinsa da qafafunta tana sake shige masa kamar zata koma jikinsa "Tana qasan gadon,ka koreta uncle" cikin tsoro take fadar haka,tuni ta soma rikitashi,sai ya dora bakinsa saitin kunnenta "It will be alright"furucin da ya sanya jikinta wani zubawa,abinda bata taba jiba tsahon rayuwarta,yanayin da yasa ta sake maqale masa da kyau,ta kuma sanya fitar numfashin sa sake jirkita,ya nutsa hannunsa gadon bayanta ya hade da ainihin fatar jikinta mai santsi a maimakon rigar dake jirkitanta,taji hakan har cikin qashi da bargonta,to amma kuma tsoro ya hanata motsawa,ji yayi kamar kada ya kashe kukan,amma yadda yaga ta tsorata dole badon yaso ba ya zura hannunsa ya kashe wayar gaba dayanta. A hankali a hankali ya fara fitar da numfashi da gudu gudu,tun tana tunanin ba komai bane har hankalinta ya kawo kan canzawar da taji yayi,hakanan bugun zuciyarsa sosai yake shiga zuwa ga kunnuwanta dake kwance saman qirjinsa dake shimfide da lallausar gargasa,a hankali ya daga kanta tana duban fuskarsa "Uncle.....baka da lafiya?" Murmushi ya qwace masa,gumi na saukowa ta saman goshinsa kadan kadan "Am fine,kwanta kiyi baccinki" ya qarashe maganar yana cije labbansa,saboda yadda mararsa ta murda masa "Gumi fa kake uncle" "I know,na sani" "Ka bari na taso hajiya" "Aah" "To akwai magani na dauko maka?" "Kece maganin" ya fada muryarsa tana rawa,sam bata fahimci me yake nufi ba,don batasan ainihin abinda yake damunsa ba "Ni kuma uncle?" "Yes,but.....ki kwanta kawai nace" ya fada da dan kaushi,saboda ciwon da cikinsa ya fara,jiki a sanyaye ta zame kanta daga jikinsa zata kwanta gefe,sai yasa hannunsa ya tarota "No,don't leave me,stay here,i will be okay" gaba daya sai taji bata da kuzarin musawa,ba wani sauran tsoro tattare da ita,tana jin sanda ya matso da ita zuwa jikinsa sosai,sai taji tausayinsa ya kamata,tana da saurin kuka da karyewar zuciya akan mara lafiya,don haka tasa dukka tafukan hannuwanta biyu a kuncinsa hagu da dama tana masa sannu da muryarta can qasa,abun sai ya zame masa kamar fami,don haka yasa hannayensa ya cire hannun nata,ya kuma jawota jikin nasa still yana cewa "Kiyi bacci,good night". *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 64 Shi kadai yasan yadda yayi surviving wannan daren,ya azabtu da yawa,daga baya da yaga ba sarki sai Allah dole ya zareta daga jikinsa bayan yaji saukar numfashinta tayi bacci. Ya dade yana kai komo,zuciyarsa na gaya masa ya aika abinda zai samu sassauci,to amma yana tuna abinda zaije ya dawo,har yanzu ya tabbatar bata gama sanin meye aure ba,bugu da qari rainon zuciyarta yakeyi,baida tabbacin soyayyarsa a ranta,beside ma hajiya na gidan,bai kamata haka ta kasance ba a karon farko. Sai wajen biyu na dare ya samu kansa da qyar,da kansa ya zabi kwanciya a qasa,zuciya da ruhinsa cike fal da tunani,wannan din ba komai bane sai kasawa da gazawar hafsa,bai taba zuwa mata weekend ko tafiya irin wannan ya samu irin tarbar da yakeso ba,bai taba dawowa sun rabu lafiya lau da ita ba,duk yadda kuwa zaikai gakai zuciyarsa nesa da dauke kansa,ya tabbatar inda ya samu ko yana samun yadda yakeso daga gareta,duka hakan ba zata faru dashi ba,saidai kuma ajizanci irin na dan adam. Kusan tare suka tashi sallar asuba shi da ita,abu na farko data fara tambaya tun batayi alwala ba shine lafiyarsa,ya jikin nasa,ya saki murmushi yana jin dadi hat xikin ransa,saboda baisan da kalar wannan kulawar ba,yana iya yin ciwo har ya warke hafsat din bata sani ba saboda tsabar rashin kulawa irin nata "Na warware alhmdlh" "Sannu uncle,Allah ya sawwaqe" "Ameen" ya amsata yana murmushi,da gaske yarinyar ce,wadda aka raineta bisa tsaftataccen tarbiyyar da har batasan meye ainihin ma'anar aure ba,batasan sha'awa ko wani abu daya danganceta ba,abu kadan ta sani wanda baikai girman da zai shiga tunani ya lalata mata rayuwa ba, tashin farko da yaji rashin sanin meye aure da batayi ba bai wani dameshi sosai ba,saboda wannan shine yake basji guarantee na cewa ita din mai tsaftataccen tunani ce da batasan komai ba,zaiyi dashensa yayi shukarsa ya kuma yi girbinsa yadda yakeso kenan. Tana kan abun salla tana tunanin me zata dafa da safen,wayarta da tayi qara ta katse mata tunaninta,ta tashi ta dauko wayar tana duba me kiran "Mommy hafsa da safen nan?" Ta tambayi kanta gabanta yana faduwa,sai a sannan ta tuna a dakinshi fa ashe ta kwana,ko wani ya gaya mata ne?,wannan tunanin ya hanata daga wayar har ta katse. Iska mai zafi hafsa dake tsaye cikin dakinta ta furzar,ta daura alwalar amma ta gagara tayar da sallar,ta manta gaba daya gidan daki biyu gareshi,hakan yana nufin hajiya na daki daya,ita da abbas dinta zasu kwanta daki guda shimfida guda?. Ko yanzun data kiratata bata daga ba, zuciyarta na kissima mata qila a daren jiyan ya samu yadda yakeso ne,babu yadda take shi yasa ta gaza daukar wayarta,wannan tunanin ya tashi hankalinta,ta koma gefan gadon ta zauna ta shiga jera mata kira ba qaqqautawa. Abin da ya sake tsorata widad kenan ta kasa daga kiran,lallai tasan a dakinsa ta kwana,kuma tambayar da zata mata kenan tunda taketa kira,sai ta ajjiye wayar tana kallonta gabanta yana ci gaba da faduwa,har zuwa sa'ar da abbas ya dawo daga sallah,ya buda qofar dakin ya shigo. Idonsa akan wayar,don itama ita take kalla,hannunsa zube a aljihunsa ya qaraso,ya dauke idonsa daga kan wayar ya maida kan fuskarta,saita dan dauke kai tsoron kiran da ake mata,da kuma kunyarsa suka hadar mata "Ina kwana?" "Kin tashi lafiya?" "Lafiya lau ya jikin naka?" Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu yana sakin murmushi, lallai quruciya na damunta da gaske "Da sauqi,na warke" kai ta jinjina masa,sai ya sake duban wayar "Ba kiranki akeyi ba ki daga" fuska ta kwabe sannan ta girgiza kanta,bai sake cewa komai ba ya matsa wajen kujerar da yakan zauna yayi karatu da asuba ya jawota ya zauna,sai widad din ta miqe a hankali ta nade abun sallar nata,ta nufi qofar fita a dakin "Ina zuwa?" Waiwayowa tayi "Xanje gaida hajiya" sai ya gyada mata kai kawai. Daga inda yake zaunen yana hangen hasken da wayar taketa yi,yadda aketa kira ba qaqqautawa ya bashi mamaki,ba tare daya shirya ba ya miqe,ya isa ga wayar ya dauko,sai yaga sunan mommy hafsat,abun ya daure masa kai,ya juya yana duba wayarsa waiko zaiga miscall dinta,may be ta kirashi ne baya kusa bai daga ba,wani abun kuma ya faru,amma sai yaga babu kiranta ko daya,ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da yin sallama. Jin muryarsa ya qarasa fadar mata da gaba,jikinta gaba daya yayi laushi,ta saki abun sallar a qasa,da gaske suna tare,tare suka kwana,kasa motsawa bakinta yayi,ta riga data samu amsar abinda take nema,don haka ta kashe wayar tare da sulalewa a wajen ta saki wani irin kuka mai tsananin zafi da cin rai,shikenan,ta faru ts qare. Jin alamun an katse ya sashi daga wayar ya kalli screen din wayar,sai yadan tabe baki ya maida wayar ya ajjiye,har ya taka zai bar wajen sai hoton fuskar wayar ya dauki hankalinsa,ya koma ya sake dauka,ya koma saman kujerar ya zauna,ya buda gallery ya soma kallon pictures din a hankali har baisan sanda murmushi ya dinga kubcewa daga fuskarsa ba,kowanne hoto da kalar quruciyar da za'a nuna a jiki. Hannunsa ya miqa,ya dauki wayarsa ya buda,yayi marking wasu daga ciki ya tura. Ranar kaf qin yarda tayi ta sake komawa dakinsa,ko hanya qin yarda tayi su hada dashi,tana tsakanin dakin hajiya da kitchen,bayan sun hada breakfast ita da muneera suka shirya komai a falo,tare sukayi break din har hajiyan,sunayi ana taba hira,da suka gama suka sake gyare gidan tare,shi da hajiyan suna dai falo suna hira,a nan sukaci abincin ranar tare da hajiyan,sannan ya koma daki ya shirya ya fice. A daren ranar yana zaune daga bakin gadon sa,qaramin littafin addu'o'i ne a hannunsa yana karantawa,ya gama komai,kammala addu'arka ne kawai ya rage masa,amma sam baiji motsinta ba,lokaci lokaci yana daga kai ya kalli bakin qofar dakin nasa a haka har ya kammala addu'ar,ya aje littafin gefen bedside ya zuro qafafunsa ya zura bedroom slippers dinsa ya miqe a hankali ya fito daga dakin. Babu kowa a falon,amma yaga dakinta a bude,yasan suna ciki,yayi gaba zuwa dakin,ya tura qofar bakinsa dauke da sallama. Dukkansu suka amsa,hajiya na zaune gefan gado,muneera da widad na saman qaramin carpet din dake shimfide qasan dakin,muneeran na maidawa weedad kalbar kanta da santsin kan ya sanya ta ware kamar ba'a taba yinta ba,bataso a taba mata kai tana ta qorafi muneeran na fadin saita yi mata,hajiya na goyuwa da bayan weedad din. Kadan ya kalli sashen da suke,ya qaraso ciki,ya samu gefan hajiya ya zauna "Bakiyi bacci ba hajiya?" Sai tayi murmushi "Banyi ba,ina dai shiri" "to yayi kyau,kin hada komai naki waje daya ko?, saboda gobe sha biyu zamu fita" "Komai a kammale yake" "Ma sha Allah.....shikenan,dama zuwa nayi nai miki sallama,sai da safe" "To Allah ya bamu alkhairi ya tashemu lafiya" sai ya juya yana ficewa a dakin,minti biyu hajiyan ta kalli widad "Maza tashi ki tafi ki kwanta kin baro mijinki,nikam sai da safenku" dif widad tayi,don ita gaba daya ta gama tsarin kwana a nan din,ta dan dubi muneera taga itama ta fara shirin kwanciyar,dole ta miqe,ta dauki siririn gyalen abayarta ta dora saman kanta,ta bude closet dinta ta dauki rigar bacci tayi musu sai da safe ta fita. A sanyaye ta tura qofar dakin tashiga da sallama,yana zaune daga bakin gado yana amsa waya,haka kawai yaji sanyi har cikin ransa sanda yaga ta shigo din,bandaki ta wuce,ta fidda kayan jikinta tayi wanka,don zuwa yanzu tayi mugun sabo da wankan dare,ta shirya cikin kayan baccin ta fito. Dim light ne a dakin,yana iya hangen sanda ta fito da kuma hawanta saman gadon,taja duvet ta kwanta ba tare data ce komai ba,qaramin murmushi ya saki,abinda ya faru jiya yana dawo masa,sai ya samu kansa da janyo wayarsa,ya duba wajen music ya lalubo kukan magen jiya ya saka. Curewa tayi waje daya,tun tana iya ganin zata jure harta kasa,sannu sannu sai gata cikin jikinsa ta cukuikuye shi,ya saki murmushin nasara ya sanya hannunsa ya lullubeta cikin qirjinsa yana sakin murmushi,ita kuna tayi lamo tana sauraren bugun zuciyarsa da nata da kowannensu ke fita da sauri da sauri. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 65 "Tom.....zamu tafi" abbas ya fada yana duban qwayar idanun widad din,hannunsa zube a aljihun wandon lallausan yadinsa da aka yiwa wani irin dinkin girma. Daga kai tayi da nufin kallonsa,duk yadda taso ya hadiye abinda takeji a qasan ranta amma ta kasa,dole haka ta saka qwayar idanunta a tasa,dai dai sanda hawayen da take riqewa ya sulmiyo daga idanunta,maganar da zatayi ta riqe mata a maqoshi,sai ta saki kuka sosai,abind aya tilasta mata saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu. Duka idanunsa ya fiddo,ya ciro hannayensa yana matsowa inda take tsaye "What's happening weedad?" Kai ta girgiza masa,saidai kukan take har yanxu "Noo....noo,kada muyi haka dake mana uhnnn?" Ya fadi a tausashe,sai ya sake matsawa gabanta,ya saka duka hannuwansa ya zare nata tafukan hannayen daga fuskar tata yana kallonta "I will be back in sha Allah.....ki daina kukan nan,yana qona ni,zuciyata tana zafi.....ko kinaso nima nayi kukan?" Ya fadi yana jin wani irin rauni da bai taba jin kamarsa ba,kanta ta girgiza amma ta gaza tsaida hawayen "It's okay,i promise you bazamu dade ba,shikenan?"saita sake jinjina masa kai,haka kawai takeji wani tashin hankali da rashin sukuni a tattare da ita,sai takejin kamar zai tafi ya barta,kamar bazai dawo ba,tana jin kamar an dauke wani muhimmin sashe ne a jikinta,batasan wanne irin feeling bane wannan,tsahon rayuwarta bata taba fuskantar irinsa ba. Tas yasa soft handkerchief dinsa ya goge mata hawayen,sannan ya bude tafin hannunta ya saka mata shi,ya maida ya dunqule hannun nata cikin nasa,sai yaja da baya kadan yana gyara zaman rigarsa data cukuikuye yana kallonta,cikin ransa yakejin wani shauqi yana saukar masa,ganin wani yana kewarka.....ya shiga damuwa saboda zaiyi rashinka a kusa dashi......wani irin dadi kima da daraja gareshi a zuciya,wani irin yanayi da bazaice ga lokaci na qarshe daya ganshi tattare da matarsa ba,sai ya buda dukkanin hannayensa yana kallonta da idanunsa masu girma da zuwa yanzu suka rusuna,girmansu ya ragu "Oya.... give me a hug" jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi,qaramin miskilin murmushinta ya subuce zuwa saman labbanta,a yau din sai taji bata shakkar yin hakan,ta fara takawa a hankali kamar wadda aka sakawa wani kida na musamman,yayin da idanunsa yaji sun fara narkewa a kallonta,cat walking takeyi,irin tafiyar da sai wance da wance cikin isassun mata,bai taba lura da hakan ba sai yau,ya qaraso gareshi a hankali,ta shige jikinsa kuwa gaba daya,harda qoqarin saka hannuwanta ta zagayo dasu ta bayansa,sai ya tallafa mata,ya durquso ya sakata sosai a jikin nasa,yana jin kamar ya maidata cikinsa. Sun jima sosai a haka kafin ta fara janye jikinta,ya danyi baya jikinsa a mugun mace yana maida numfashi,kusan minti hudu kafin ya dai daita kansa "Ayimin rakiya mana" kai ta girgiza tana murmushi,duka idanunsa ya bude a kanta "Why?" "Hajiya fa.....so kake ta gane ka rungume ni,sannan tun dazu muka shigo daki ni dakai fa,nidai kunya nakeji" ta qarasa maganar tana turo baki,bai shirya ba bai kuma zata ba dariya ta kubce masa,yasa hannunsa saman bakinsa ya dara kadan sannan ya janye "Ok, come closer" ya fada yana daga mata hannu,bata musa ba tasake matsowa,ya sukuya a hankali ya bata wani irin hot and deep kisses saman goshi da kuncinta,sannan yaja baya yana cewa "Na bawa Allah amanarku,ki kula da kanki" ta gyada kai a hankali,sannan ta motsa bakinta "A dawo lafiya,Allah ya kiyaye yasa ku dawo lafiya" lumshe idanu yayi har ya fice,ji yayi a duniya kamar ba'a taba masa addu'a ba, siririyar muryarta ta dinga masa amsa kuwwa a kunne,har suka isa airport yana wassafa wasu abubuwa da yawa a kanta. Kafin jirginsu yakai ga tashi yayi kiran hafsat,ko ba komai yana son ya sauke nauyin dake kansa,yanason kuma yayi magana da yaranshi,sai daya kira sau uku,ana hudu yaci sa'a aka daga,saidai muryar yaran ce,ya biye musu sukayi surutu sosai har sai da yaji ya siqe "Ku bawa mommynku" ya fadawa mimi,shuru na sakanni ya ratsa,sannan yaji mimi tace "Tace bacci takeyi" idonsa ya rufe sannan ya budesu lokaci guda, irin yadda yakanyi wajen hadiya fushi idan ransa ya baci,baya so tana saka yaransa a ire iren wadan nan abubuwan nasu,yanzu ko ba komai ta koyawa yarinyar qarya "Alright....idan ta tashi kuce nace ta kula daku,daddynku zaiyi kewarku" "A dawo lafiya daddy,ka siyo mana jirgi" murmushi ya kufce masa,yana fatan wataran dukkansu ya kaisu umara ko aikin hajjin suma "In sha Allah mimi na,i love you" "I love you too daddy" ta amsa masa,dai dai lokacin hafsat da haushi ya cikata tayi fam ta warce wayar,ta jefi yarinyar da harara "Uwar kinibibin tsiya,i love you too daddy" tayi maganar tana kwata muryar yarinyar "Koni ban fada ba sai ke,saikibishi ai uwar son uba" taja tsaki tana jefa wayar gefe,harta koma zata kwanta sai kuma taji ta fasa,ta miqe ta fada bandaki ta watsa kwaskwarima,ta fito ta fara shirin fita,su mimi kuwa kaya kawai ta fidda musu tace su debo wasu ta saka musu,gida zasu,idan sun qarasa can a samu wani yayi musu wankan, yaro ba hankali,da murnarta ta shiga dakinsu ta debo musu kayan,uwar ba tare data tsaya wani dubawa ba ta karba ta saka musu,ta hado kansu ta sanyasu a motarta suka fice daga gidan,gidan kamar mazaunin bola,saidai hankalinta a kwance yake,tasan me sanya damuwar saita gyara din baya qasar ma gaba daya,duk sanda ta samu chance ta gyara din,hankalinta yayi gidan,tana son su hadu da anty ummee taji sabbin shawarwari,tana jin kamar tafiyar ta ta fara baudewa. A daren ranar daya sauka ya sake kiran hafsat din don ya gaya mata sun sauka lafiya,amma harta qaraci ringing dinta bata daga ba,har a lokacin ma tana gida bata koma ba,mamarta ta sake cewa da ita "Shareshi,wani abunma duk laifinki ne,ace mijinka baya shakkarka me akayi kenan" . Yasan dai ba yadda za'a yi ya mata irin wanna kiran tace bata gani ba,kuma koda a daxun baccin take da gaske ai yaci ace tayi kiransa bayan ta farka,ransa yakai qololuwar baci,yaji kuma a ransa bazai sake kiranta ba indai shine,sai ya maida akalar kiran nasa ga widad. Dukkaninsu wata irin sakewa sukayi shida ita,sunyi hira mai tsaho,duk abinda tayi a yau din sai data zayyane masa shi kuma yana kwance saman gadon hotel din da suka sauka yana biye mata,a nan take bashi labarin taga tallan wajen wani koyar da girki a kaduna tanaso "Iyeee .... dole wai so take ta fini iya girki...... alright,zansa Samuel ya yiwa rose magana" da murnarta sosai ta shiga masa godiya,har yaga godiyar kamar tayi yawa,ita kuwa a wajenta normal ne,kamar yadda aka horeta kenan a gida. Kwana daya da zancan kuwa saiga rose tazo har gida samuel ya kawota,haduwar farko jininsu ya hadu da rose din,saboda tana da matuqar kirki da kuma ban dariya,wannan ya sanya saurin sabo a tsakaninsu duk da rashin saurin sabon da widad ke dashi,shiryawa sukayi ita da muneera da aka bar mata suka wuce wajen sukayi register da komai da komai sannan suka dawo gida,tun daga ranar rose ce ke zuwa ta kaita ta kuma dawo da ita gida,cikin lokaci qalilan sukayi sabo,itama tana son widad saboda kirkinta,don idan sun dawo din sai ta tsare rose ta zauna taci abinci,harma suyi hira da ita,sau tari ma idan ta gwada abinda ta koya saita ajema rose din,komai tabgwada din kuwa sai yayi kyau exactly kamar yadda ta koyo,abun yayita bawa rose mamaki da sha'awa,wata irin gifted ce weedad din. Ganin yadda widad din keda sha'awa girke girke,sai rose din ta ware wasu ranaku take koya mata irin girkin nasu qabilar,idan sukayi wasu daga ciki takance "Oga yanaso wannan" tsaf widad ta dauke wadanda tace yafiso din,ta dinga practicing nasu da kyau,har suka zauna mata,ita a karan kanta dadi takeji,tana jin dadin yadda a yanzun ta fara iya kalolin girke girke da dama, yadda ta maida hankali a kitchen yanzun bata maida haka kan karatunta ba,gefe guda ta matsawa anty deena, kullum saita qara mata bayani akan abincin ainihin qasarsu,duk da wannan dama tana ganin ummu tana yinsu sosai,saidai bata taba cewa zatayi da kanta ba. Cikin wata daya ta koya abubuwa da yawa ta fannin girki,ansha barna,don kullum da abinda za'a girka,saidai ta samu experience sosai. Tun saura kwana uku su dawo take ta practicing abinda zata dafa musu shida hajiya,sunyi hira da anty deena da anty madeena sosai,sun kuma bata shawarwari cikin hikima,ana ya jibi zasu dawo muneera ta taimaka mata suka gyare gidan tas,sukayi goge goge sosai,washegari kuma rose tace mata "Madam ko za'a kaiki saloon?" Fadin da rose din tayi sai ya zama kamar tuni a wajenta,tace ta kaita. Waje ne mai kyau da zaka yiwa kallo daya kasan sun iya aikinsu,cikin yarensu sukayi magana da rose bayan sun gama gaisawa,mutum biyu aka gamawa sannan aka kama kanta. Sosai matar tayi mamakin yanayin kan widad din,da kanta matar mai suna ada tace bata buqatar relaxer. Wani irin gyaran kai akayi mata,wanda ita kanta widad din sai data tsaya ta kalla kanta da kyau a madubi bayan sun koma gida,muneera tace "Wallahi matar nan ta iya gyara matar uncle,inama idan bikina ya taso nan zanzo tayimin" "Kizo wallahi,saina rakaki" ta fada tana sake kallon kanta dadi yana cikata. Isowar yammaci sukayi a washegari,kafin isowar tasu komai ya kammala kamar wata babbar mace,cikin atamfa ta shirya dinkin riga da skert,saidai ta gaza daura dankwalin sai yafashi tayi saman kanta,tana maqale jikin window din falonta har zuwa sanda motar data daukosu ta sako kai harabar gidan. Bin motar tayi da kallo,tana zuciyarta na bugawa da sauri da sauri,farincikin da batasan dalilinsa ba takeji yana ratsa zuciyarta,taci gaba da kallon motar har ta shige parking lot "Sun iso,bakiji shigowar motarsu ba?,kizo muje mu taraso" muneera dake sanya hijab dinta ta fada tana kallon widad, waiwayo tayi tana duban muneera,sai takejin kamar qafafunta ba zasu iya kaita wajen ba,ta girgiza kai "Kije yanzu ai zasu shigo" kai ta kada tana dariya "Oh,wai kunyar hajiya kenan kikeyi,to nidai nayi nan" ta fadi tana yin gaba da sauri,ta bude qofaf ta fice. Sanda ya shigo ta dauka zata iya dakewa,sai tsintar kanta tayi a gabansa,shima yayi tsammanin zai iya jurewa amma sai ya kasa, hannuwansa gaba daya ya bude mata,batayi wata wata ba ta fada ciki,ya maida ya rufeta gam a cki yana sauke wata wawiyar ajiyar zuciya,yayin da ita kuma ta fashe da kuka sosai cike da wani tune na shagwaba,sai ya gaza jurewa tsaiwar,ya sulale ya zauna a wajen,hakan ya bata damar zama sosai a jikinsa. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 66 Sun dauki mintuna a haka sannan ta daga kanta suka hada idanu,shima ita yake kallo,haka kawai taji wata kunya ta kamata,saboda kallon da yake matan ya mata nauyi sosai a gangar jikinta da zuciya,hakanan bata saba ganin kalar kallon ba a tattare dashi,saita cusa kanta a qirjinsa tana shaqar wani bala'e'en qamshi da fatarsa ke fiddawa "Eheenn.....baby na ta fara sanin kunya ne?" Tambayar data sakata ji kamar zata nutse,sai kuma ta janye jikinta da sauri tana fadi cikin fidda idanu waje "Hajiya!" Dukkansu bin falon sukayi da kallo,ba hajiya babu burbushinta,sai suka kalli juna a tare,kafin yayi komai ta rigashi miqewa tana narke ido "Hajiya fa uncle" amsar da shima bai santa ba,yasan dai yana gaba tana biye dashi,komawa tayi ko ciki ta shige. Tare sukayi hanyar dakinta,suna zuwa widad din ta lafe daga bakin qofa,shi ya tura ya leqa,saiya samu hajiyan zaune cikin dakin daga qasan carfet ta miqe qafafunta "Oh,hajiya kina ciki kenan" ya fada cikin jin kunya da nauyi yana shafa kansa,mazewa tayi kamar ba abinda ya faru "Wallahi,kasan ko yaya tafiya take ba'a rasa jiki da gajiya,kaima ya kamata ka shiga ciki ka huta hakanan,sai Allah ya kaimu anjima" "To hajiya a huta lafiya" ya fadi cikin jin nauyi,sai data murmusa sannan ta amsa mishi,ya maida qofar ya rufe sannan ya juyo suka hada ido da widad din. Qwalla ce ta cika mata idon tana dubansa a shagwabe "Ban mata sannu da zuwa ba" "Tace ta yafe,naje na huta,anjima saina rakoki ko?" Kafada ta maqale alamun bata yarda ba,sai ya qara taku ya matsa ya buda qofar kadan "Shiga to ku gaisa" nan ma ta sake maqale wuya,sakin qofar yayi ya koma da baya ya rungume hannayensa yana kallonta "To ya kikeso ayi?" Hawayen dake maqale ne ya sauko mata "Ba kaine ba......kaine ka jawomin Allah" dariya ta taso masa,ya murmusa yana kallonta "Ni me nayi tsakani fa da Allah" kuka ta sake masa,da sauri ya kalli qofar dakin sannan ya dawo da dubanshi kanta,ya tako da hanzari ya iso gabanta "Sorry..... sorry,kiyi shuru mana please,kafa hajiya taji,nayi alqawari zan rakoki,zan kuma gayawa hajiyan laifin nawa ne shikenan?" Kai ta gyada masa,sai ya saka hannu a aljihunsa ya fidda handkerchief ya soma dauke mata hawayen,idanunsa na manne da manyan fararen idanun nan nata dake yawan daukar hankalinsa,ya jima baiga abu mai daukan hankali kamarsu ba,daga bisani ya sauke dubansa kan mitsitsin labbanta jajaye da taketa motsasu kamar zatace wani abu,tsigar jikinsa ta zuba,ya dauke idonsa daga nan yana cije labbansa,ya gama yaja baya jikinsa na wani irin mutuwa,ko a ina ta samu irin wannan fitinannen turaren?. Kasa jurewa tayi ta jashi zuwa dining tana buda masa abubuwan data dafa,a mamakance yake kallonta,baiyi shakka ba saidai mamaki,yasan halinta a dan zamansu bata qarya,at last ya rasa me zaice mata "Bari na huta,ki zaba duk abinda kikeso idan na bude jakata a matsayin gift na wannan abincin" murmushi tayi "Ni hajiya nayiwa fa" "Ya salam" ya fada a qasan ransa yana lumshe idanu, yarinyar ta gama dashi,yasan ta fada ne har ranta da kuma quruciya,batasan hajiyarsa itace weak point dinsa ba "Yes.....i know, that's why nace ki zaba duk abinda kk so,hajiyata duniya ta ce,itace komai nawa" kai ta gyada masa tana murmushi Wanka kawai ya sakeyi,ya shirya cikin toilet don kada ma tace zata masa bore,lallabawa yakeyi,yana da buqatar ta a kusa dashi sosai,ko bata kawar masa da qishirwarsa ba dumin jikinta zai masa amfani ko yaya. Gadonsa ya haye yana lumshe idanu,qamshin da bedsheet din ke fitarwa har cikin jininsa,idanun nasa a lumshe yace "I hope ba muneera kika bari ta shigo dakin uncle ba" kai ta gyada tana murmushi "Anty widad ce" sosai ta bashi dariya,har sai daya bude idanuwansa a kanta yana kallonta,tana da wani irin salo da yake sauke masa komai na daga gajiya da bacin rai,yayi mamakin yadda ta iya duka wadan nan aikace aikacen,komai na gidan ya zama akan saiti "Anty?,su anty manya" ya furta cikin salon tsokana idanuwansa suna lumshewa sakamakon dankwalin dake yafe a kanta ya silale ya fadi,sassalkan gashinta da aka masa wani irin nadi jiya a saloon ya bayyana kansa. Da fuskar shagwaba ta kalleshi,abinda ya qarawa cute baby face dinta kyau matuqa "Ni din ko?,ni ba anty bace?" "Wait....kinaso a dinga kiranki anty?" Kai ta gyada "Good,zan koya miki wani abu,indai kika tsaya kika iya kike yimin,ba anty ba.....har mommy za'a ce miki" ya qarasa fada yana lumshe idanunsa,cikin zumudi take kallonsa "Yes,na yarda uncle" "Good.....bari na huta sosai tukunna.... Amma,zo muga wannan gyaran kan naki" ya fada yana yfitota da hannu muryarsa na qara yin laushi,bata kawo komai a ranta ba ta rarrafa zuwa gabansa,ta kuma miqa masa kan tana jin dadin yabawar da yayi "Anty rose ce ta kaini fa,tacemin ka taba cewa zaka kawo madam ayi mata irinsa dama" "Yeah" ya fada da qyar kamar mara lafiya,ya tuna lokacin,hafsa yaso kaiwa,tace bata da wannan lokacin, infact ma tace zaman banza ne da bata lokaci,saboda koda anyin zai yamutse shine da zarar sun dawo,ya kuma sakata zuba ruwa akan,shikenan ya tashi a aiki,gwara ya bata kudin taje ayi mata kitso ko wani gyaran mai sauqi. Ajiyar zuciya ya sauke,ya saka hannayensa gaba daya ya birkitota jikinsa,a dan tsorace tayi yunqurin tashi,muryarsa a kakkarye yace "Don't.....do me a favor please,bacci nakeji ki tayani,ko kin fita ma na tabbata ba kowa,just one hour kawai" wani irin abu taji yana mata yawo cikin jikinta a sanda yake maganar wanda ya zare mata duk wata laka ta jikinta,sai kawai ta maida kanta saman dantsensa dake cike da muscles ta kwantar,a hankali ya nutsa yatsun hannunsa cikin sumarta, numfashin ya fusga da kyau kamar zai qwace ya samu ya nemoshi,sai ya cure jikinsa waje guda,yayin da widad din tayi lamo tana jin faduwar gaba da fargaba. Tafiyar tsutsa yaci gaba da yi mata saman kanta yana yamutsa gashin da kyau,qamshi da santsinsa yana bashi wani salon nishadi,bai farga ba sai ji yayi tana sauke numfashi a hankali,daya duba yaga bacci ne ya dauketa,ya saki murmushi a hankali yana gyara mata kwanciya cikin jikinsa,ya tabbatar itama akwai gajiya a tattare da ita,don iya ayyukan daya gani tayi ba qaramin qoqarin gasken gaske tayi ba,baima taba kawowa kansa zata iya ba,ko makarantar da rose din ke kaita ya barshi ne kawai suna fita saboda rage zaman kadaici bawai don a koyo komai ba,ashe abun ya wuce yadda ya daukeshi. Basu hadu da hajiyan ba sai washegari,saboda ya riqeta a dakinsa,tunda hajiyan ta shiga dakin itama bata fito ba, muneera ce ta debo musu komai takai daki,shima ya dauki sauran yakai musu dakin,daga qarshe sai daya kira hajiyan a wayarsa,tace ta bari sai goben sannan ta haqura,saidai fa gaba daya jinta take cikin wani sabon yanayi,ko yaya ta motsa idanunsa yana kanta,duk bayan wasu mintuna sai ya jangwalo abinda zai bada connection a tsakaninsu,tanata zamewa amma kamar sake diga danqo take a tsakaninsu,shi kansa baisan me yake faruwa ba. Tare sukayi breakfast a falon, muneera da widad nata gyaran wajen hajiya ta dubeshi "To nifa yau sai gida" da mamaki ya kalleta "Ah...haba hajiya,ki bari ki qara koda kwanaki uku ne mana,sai mu wuce tare ko?" Kai ta girgiza "A'ah abbas,ai tunda komai ya kammala zaman me kuma za'a yi?,gwara na koma gida na nima nafi hutawa sosai" kafewa tayi tace bauchi zata tafi,da qyar ya sha kanta ta bari sai gobe,idan yaso sai su wuce gaba daya,da wannan maganar da sukayi ya wuce daki yace zaiyi wanka ya fita headquarter ya bada report na dawowarsa,zai kuma sake daukan excuse na three to four days. Ya fidda dukka kayan jikinsa yana daure da towel wayarsa ta dauki ringing,ya dawo da baya yana duba me kiran hannunsa a qugunsa,hafsat ce,yayi mamakin ganin kiran nata,tun randa yayi alqawarin bazai sake kira ba bai kuma din ba,hakanan itama koda wasa bata kirashi ba,komawa yayi ya jingina da mirror din dakin ya daga kiran tare da yin sallama,sannan yayi shuru yana jiran jin dame tazo. Kamar ba zata tanka ba bayan ta amsa sallamar sai kuma tace "Au ashe kun dawo" "Eh" ya amsa mata a taqaice,abin ya sake bata ranta "Yanzu kayi tafiyar wata guda,ka dawo qasar amma ka kasa gayamin ka dawo abban mimi,adalci kenan hakan?" Maimakon ransa ya baci baisan murmushi ya kubcewa fuskarsa ba,rainin wayonta ya fara yawa,idan tayi wani abun kamar zautacciya "Ai baki da buqatar jin komai daga gareni,so kinga baki da matsala dani" "Haka ma zaka ce?,duk abubuwan daka yimin kai baka gani?,kullum nice mai laifi a wajenka,kayi tafiyarka daga wajen wata,ka tashi dawowa ka sake sauka a wajenta ba tare da nasan ma ka dawo ba sannan ace ana kyauta min" saita fashe masa da kuka kawai,shuru yayi yana saurarenta,tasan weak point dinsa ne,amma bazai yarda ta raina masa hankali ba,don haka ya aje wayar saman mudubi kawai ya rabu da ita,duk da yana saurarenta. Jin tanata faman sharan majina baice mata komai ba ya kuma tunzura mata zuciya,kukanta banza shirunta banza kenan?. "Laifi nane da nayi kiranka" ta fada tana shirin kashe wayar "Wait.....am on my way tomorrow" baiji ta amsa ba,tadai yanke kiran,duk da haka ya tura mata gajeran saqo saboda ya fita hakkinta yana sake jaddada mata,ya aje wayar saman mudubin yana fidda iska daga bakinsa,hafsat.....hafsat.....ya yarda jarrabarsa kenan a rayuwa,ya taka zai shige bandakin sai yaji an turo qofar,yadan tsaya daga bayan labule kadan saboda yasan me shigowar,kuma tabbas idan ta ganshi a haka komawa zatayi qila harda gudu ma. Tana 'yan waqenta ta shigo,ta cire hular data rufe sumarta,ta zare underwear dinta,ta soma tattare doguwar rigarta zata cire ya motsa,don yasan matuqar ta cire qarshe idan ta ganshi tace shi ya jawo mata kuma ba zata yarda ba. Da sauri ta saki rigar, saidai saura data rage ta tattare saman qirjinta dake tsaye cas,idanunsa suka sauka a wajen,yaji wani abu ya tsarga masa,tun daga saman kansa har yatsun qafarsa,kamar sunfi yadda ya taba lura da girmansu. Kallon da yake mata da kuma a yadda ta ganshi ya sakata juyawa zata bar masa dakin,taku uku ya isketa,ya jawota cikin jikinsa yana jin yadda jikin nasa ya fara rawa,duk yadda yaso yayi controlling kansa kada yakai hannunsa saman jikinta a yau ya kasa,karon farko a rayuwarta da hannu ya taba kaiwa saman qirjinta,suman tsaye tayi da farko,don yayi mata mugun ba zata,yayin da shima yayi kusan mutuwar tsayen,saboda saqon da suka bayar zuwa ga kowacce gaba ta jikinsa,sun masa ba zatan shima,ya samesu fiye da yadda idanunsa ke wassafa masa. Motsa hannayensa daya fara yi ta wajen ya maido mata dukka wani tunaninta,kamar yasan ihu take shirin masa ya birkitota ya hade bakinsu waje guda, hannayensa kuma naci gaba da abinda kwanyarsa ke qawata masa. Wani irin tashin hankali ta shiga,ya matseta gam,ba damar ihu ko motsin ceton kai,sai kawai hawaye suka balle mata,tun tana sanya ran yanzu zai saketa harta saare, yaci gaba da aike mata saqon daya dinga sanyata jin kamar zata mutu *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 67 Kusan a manne fuskokinsu yake,yanajin saukar hawayenta,amma kuma bazai iya dakatawa ba,saboda wannan ce kadai hanya guda daya zata rage masa zafi,ya gwammace yayi duk wani kalar rarrashi da zaiyi daga baya. Ya kusa minti goma w offsha biyar a haka sannan jikinsa ya saki gaba daya har ta samu ta qwace kanta tana masa kuka sosai. Da qyar idanunsa ke buduwa,yana zube a wajen yana kallonta,ta koma gefe ta rakube tana kuka sosai,saboda qirjin nata dake mata zafi,haushinsa sosai ya cikata,taji kaman ta bude ido ya ganta a wani wajen ba a nan ba. Sai da energy dinsa ya dawo sannan ya tattara qarfin nasa ya miqe a hankali,ta runtse ido sanda yake gyara zaman daurin towel dinsa,ya tako qafafunsa a nutse ya iso gabanta ya tsugunna dab da ita,ta qurewa bango amma baya takeson ta sake ja "Relax.....am sorry kinji" harara takeson balla masa amma kuma yayi mata kwarjini da yawa, maimakon haka saita maida fuskarta tsakanin qafafunta ta boyeta,tun yana tsugunne sai daya zauna sosai yana lallashi,daqyar ya ciyo kanta,ya hada mata ruwan wankan ta shiga bandaki ta fara yi,data fito sanye da zumbulelen hijabinta tana ta qunci,tace ita ba'a nan zata shirya ba,salin alin ya bude mata qofar dakin ta fice dakinta. Da baya ya sake komawa ya zauna yana murmushi,wani nishadi ya samu kansa a ciki,ya yamutsa sumarsa sosai kwanyarsa na dawo masa da duk wani wani second daya daya shude sanda take cikin jikinsa "Oh my goodness" ya furta a hankali,ko a yanzun yana iya jin qamshinta cikin fatarsa,wani irin softness jikinta yake dashi irin wanda bai taba jin kamarsa ba,ya buda dukka tafukan hannayensa yana tuna santsi da laushin gashinta,saiya maidasu ya cure waje daya zuciyarsa tana jin inama zai sake samun wannan chance din. Kusan awa guda ya bata a zaune a wajen yana karanta tunanin baya,da qyar ya miqe yayi wanka,amma sai ya kasa fita,ya koma falo ya zauna ya tsiri hira da hajiya,hakan kuma ita sai ya takurata,saboda abinda ya faru a tsakaninsu ba mahalukin daya taba mata irinsa,duk giftawarta idanunsa a kanta,daga qarshe ta haqura tayi zamanta a kitchen tana tsara me zata dafa musu yau da abinda zasu tafi dashi hanyar bauchi gobe,bai fita daga gidan ba sai da akayi sallar azahar sannan ya wuce headquarter din tasu. Daren ranar qiri qiri taqi yarda ta kwana a dakin,hajiya nata mata hannunka mai sanda, har ta fahimci bata gane ba tayi mata quru quru "Zan tafi hajiya,bari mu gama hada kayan naku" haka ta yita cewa hajiyan,tun tana idanu biyu.har bacci ya dauke hajiya,hakan ya bata damar yin kwanciyar ta hankali kwance saman babban bargon data dauko ta shimfida a qasa,don sun barwa hajiya gadon. **********K'arfe tara na safe sun kammala shirinsu gaba daya,suja farfajiyar gidan ana shiga da kayansu booth din motar da zasuyi tafiyar,widad da muneera na tsaye daga gefe har aka gama,motar nada wajen zama biyu,sai wajen zaman driver,hajiya ce ta fara shiga seat din da yake da maqotaka dana driver "Bazan shige ciki ba abbas saboda qafata" "Ba matsala hajiya yayi hakan" yana shirin yima muneera magana kan ta shiga gefan hajiya sai weedad ta fara takowa,tsaf ya fahimci abinda take shirin yi,jiya kawai dama kawaici yayi mata,a yanzun sai yayi kamar bai ganta ba,sai da tazo daf dashi ya sanya hannunsa ya riqe hannunta da kyau,baiko waiwaya ba bare kayi zaton ya riqeta din,cikin sauri ta daga kai tana kallon fuskarsa,yasha muur da kyau,baiko kallon sashen da take kamar bashi bane ya riqeta. Gyaran murya kadan yayi sannan ya kira muneera yace ta shiga gefan hajiya "Saura ki saki baki kima mutane bacci ki barta da kallon hanya" murmushi ta danyi "Bazanyi ba uncle in sha Allah" hannu yasa ya rufe murfin motar,ya bude seat din baya sannan ya waiwaya ya kalleta. Cikin sa'a itama shidin take kalla, idanuwansu suka hadu waje daya,har cikin jininsa sai da yaji wani abu mai kaifi ya saukar masa,ya kuma baza saqonsa zuwa kowanne sashe na jikinsa,ya sake dawo masa da sweet memorie dinsu na shekaran jiya,wannan ya sake sanyawa gaba daya jikinsa ya amsa "Shiga" ya fada da mugun sanyi,narke fuska tayi sannan ta matsa ta shige yabi bayanta,ya maida murfin ya rufe sannan ya yiwa samuel da suka saba yin tafiyar dashi magana kan ya tashi motar suje. Gefe daya na motar ta rakube,gaba daya fuskarta a narke take,kamar wadda ke jiran qiris ta sanya masa kuka,yi yayi kaman bai fahimta ba,sunata hirarsu shi da hajiya,har taji shurun widad din yayi yawa "Widad ko.tayi bacci ne?" Hajiyan ta tambaya ba tare data waiwayosu ba,sai sannan ya juya inda take zaunen,tausayi ta bashi da kuma dariya amma ya danne,suna hada ido sai hawayen da take maqalewa ya sauko,ya miqa hannunsa ya lalubo tafin hannunta,duk da yadda take faman boyonsa ya sanya shi cikin nasa,sannan a hankali ya janyota zuwa kusa dashi ya hade duk wata tazarar dake tsakaninsu sannan ya amsawa hajiyan a ladabce "Idonta biyu hajiya" "Au to madalla". Tun basuyi nisa da tafiyar ba bacci ya dauke hajiya,muneera ce kawai ta rage wadda taketa game da wayar hajiyan,har a sannan tafin hannunsa yana cikin nata yana yamutsawa,santsi da laushinsa ke haifar masa da wata kasala ta daban,maqoshinsa gaba daya ya bushe,ya kalleta ta gefe "Bani ruwa" ya fada a taqaice,kamar jira dama takeyi ta zame hannunta daga cikin nasa,saidai kafin ta gama zamewa ya maida hannun cikin nasa,ta juyo suka hada ido ya kada mata kai "Zan dinga hukuntaki fa" yayi maganar can qasa da wata irin gajiyayyar murya,sai tayi narai narai da ido tana kallonsa,ya girgiza mata kai da sauri "Kinayimin kuka zan cinye idanun" yadda yayi maganar with seriousness ya sanya mata dan jin tsoro,sai ta kifa kanta saman cinyarsa,abinda ya sanya numfashinsa yin qaura na wucin gadi,ita kuma ta tura kanta da kyau tana son goge hawayen daya fara fita kada ya gani. Da sauri ya saka hannunsa ya daga fuskartata,idanunsa suna rurrufewa,bugun zuciyarsa na fita da sauri "Ya isa....banaso.....idan nace ki bari ki dinga cewa to,understand?" Kai ta gyada masa "Good,bani ruwa" a hankali ta dauko masa ruwan,duk da yadda jikinta ke rawa,shima ya lura da hakan,sai ya sakar mata hannun ya karba ruwan,ya balle gorar ya sanya bakinsa bayan yayi bismillah ya soma sha. Tas ya shanyeta,ya maida numfashinsa,ya juya kadan suka hada ido,tunda ya fara shan ruwan ta zuba masa ido tana mamakin yadda yakeshan ruwan,kamar wanda ya jima baiga ruwa ba,suna hada idon ta dauke kanta,ya saki murmushi,ya gama karantar komai daga qwayar idonta "Zo kiji" ya kirata can qasa kamar yadda suke maganar tun daxu, saboda muneera da hajiya da suke cikin motar,bata musa ba ta matso dab dashi,sai yasake hade hannayensu waje daya yana kallonta "Menene auratayya?" yayi mata tambayar kai tsaye,tambayar da ya jima yanason mata ita,tambayar data sakata rufe idanunta gam lokaci guda,zuwa yanzu koda batasan ainihin me yake nufi ba,daga karance karancen data fara ta fuskanci wani abune mai girma,wani babban alaqa ce babban gini da kuma qatuwar dangantaka tsakanin namiji da mace,zuwa yanxu kuma tambayar ta girmi tunaninta,ta kuma haifar mata da wani jin nauyi da kuma kunya. Yadda ya rutsata da ido haka tabar idanun nata a kulle,wayyo Allah kawai take fada a ranta,itadai wannan iskancin ya fara isarta,inda ya barta kusa da hajiyar da duk haka bata faru ba,sai ya saki murmushi yana sakar mata hannyenta,bai sake cewa komai ba,haka itama,a haka har baccin ya soma fusgarta,sai yayi mata makari da manyan kafadunsa,sanda baccinta ya fara nisa kwance tayi bisa kafadun nasa ba tare data sani ba,wannan ya bashi wani irin yanayi mai dadi sanda suke keta dazuzzuka,yayin da tayi wani bacci mai dadin gaske bisa kafadun nasa. Cikin ikon Allah suka iso bauchi lafiya,yayi yayi da hajiya ta fara sauka gidansa amma tace sammm a gidanta zata sauka,dole haka ya wuce da ita gida,sanda suka isa gidan akwai mutane,yaranta matan su uku duka suna gidan su da yaransu,sun gyare gidan sunyi duk wani abu na tarbarta,kowa kallon widad yakeyi,cikin watannin ta sake girma da cika,tayi wani fresh,abinka da farra fata idan ya samu hutu,cikin girmamawa ta gaida kowannensu,tunda dui cikinsu babu sa'arta,sun haifeta ma,qaramar cikinsu ce take ganin zasuyi sa'anni da anty deena. Ina ka saka ina ka aje suka dinga yi da abbas din,shima da yake mai.kirki ne kuma na mutane sai yadan zauna shima a cikinsu kusan awa daya,lokacin har maqota da sauran matan kawunnansa sun fara shigowa yuwa hajiyan barka da zuwa,kusan kowa ya shigo idonsa akan widad "Amaryar abbas ce?" Haka suke tambaya,kowa da abinda ke cikin ransa,ya kusa shafe awa daya sannan ya miqe da zummar tafiya "Dauko mayafinki ku wuce widad kinji,sannunki kema da qoqari ansha hidima,Allah yayi albarka ya bada zuri'a ta gari" baki baba usaina ta tabe,matar daya daga cikin kawunnansa,wadda suna da 'yar alaqa da hafsat din,fuska ta marairaice wa hajiyan,qasa qasa take gaya mata "Don Allah hajiya a barni a nan na kwana" can qasan ranta tana fargabar yadda yake liqe mata,a yanzun baya jin shakkar tabata,idan mommy hafsat ta gani tace mata meye?,gwara tana nan din,basu hadu ba bare ta gani. "Yaa abbas,ka barta zuwa anjima din kamar haka takeso tace ko?" Qanwarsa ta fada wadda ke kusa da hajiya,ta kuma ji abinda take fada din "Idan ka fito saika biyo ku tafi,idan ma baka zo din ba zan sanya a rakota" hajiya ta qara masa bayani. Idonsa ya maida kan widad din data wani lafe a gefan hajiyan,suka hada ido sai ya dauke kansa,itama janye nata idanun tayi cikin ranta tana jin kamar ta tsira,ya gyada kai "Shikenan hajiya,a huta lafiya" "To Allah yayi albarka,a gaida kishiyoyina" a hankali ya juya ya fice daga falon "Tirqashi" baaba usaina ta fada,yaaya bara'atu ta daga kai ta kalleta "Baaba usaina lafiya ko?" Baki ta tabe a fakaice,amma a zahiri sai tadan murmusa "Ina ganin rashin kunya irin ta yaran zamani,kema banda abinki hajiya kibar masa matarsa su wuce mana" "A'ah gwara ta zauna a gaisa sosai,aita kwan biyu dama bataxo ba" hajiya ta amsa mata cikin bagarar da zancan,don batason dogon zance. Sai da suka tsaya a hanya ya sake yin siyayya sannan suka wuce gidan,ba wani zumudi ko kadan a tattare dashi,abu daya ke sanyawa yaji dokin zuwa gidan,yaransa da yayi kewarsu. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 68 A farfajiyar gidan ya cimma yaran suna wasa,ya tsugunna suka dafeshi gaba daya ya miqe dasu,yau din ba yabo ba fallasa,basuyi datti ba amma kuma bai samesu fes yadda yakeso ba,dukkansu kansu a tsefe yake a daure da band,yana rungume dasu a jikinsa suka sanya kai cikin falon dake sassan hafsat din. Shima yau dai falon babu laifi,saboda babu dattin,amma bawai kar kar yake ba,yaji dadin hakan har qasan ransa,ya kuma tsinci kansa da fatan samuwar canji daha gareta da kuma dorewar dabi'unta. Bata parlor din,don haka ya zarce bedroom din nata kanshi tsaye,har yanzu yaran suna kafadarsa suna masa surutu,ya tura qofar dakin,dai dai sanda ta waiwayo suka hada ido,tana tsaye gaban mudubi,saita dauke kanta tana amsa sallamar,jikinta sanye da wata koriyar atamfa riga da fallen zani "Sannu da zuwa" ta fada cikin careless,kamar wanda yaje qofar gida ya dawo,bai amsa mata ba sai daya sauke yaran a qasa,ya saka hannu a aljihunsa ya fidda chocolate ya miqa musu "Ku jiremin falo maza mimin daddy" da gudu suka falla sukayi falon kuwa,sai ya maida dubansa gareta,har kullum idanuwansa ba zasu gaji da gayawa zuciya da kwanyarsa yadda yakeson ya ganta ba haka ya ganta ba,kamar yanzun,kai zaka ce matar qauye ce,koriyar atamfar da aka tashi aka yima wani sungul dinki,ba wani abun jan hankali a jikinsa nare style din zamani,daurin kanta kamar na matar qauye,amma duk da haka baiji ya wani tunzura ba,ko tsananin buqatar da yake ciki ce ta kauda duk wani aibu daga idanuwansa?,idanma hakanne harda tasiri 'yar tsaftar daya isketa a ciki. Duk duniya ta shaida auren soyayya sukayi da hafsat din,amma dabi'unta nata nesatata daga zuciyarsa,ya taka a hankali yayi tsaye a bayanta yana goye da hannayensa "Tsakani da Allah haka akewa miji maraba?,mijin da yafi wata guda baya tare da iyalinsa?" Waiwayowa tayi ta watsa masa wani kallo,a yau taci alwashin gwada mishi amfaninta,tunda kare ma ai yana da ranarsa,tasan a buqace zai dawo,zuciyarsa cike fal da tarin buqatun da babu wadda zai dosa da nufin saukewa idan ba ita ba "Bayan marabar daka samu daga wajen wadda ta fini?,ina cewa bani kadai bace iyalin naka" "Na fiki sanin hakan,amma yanzun taki marabar nake da buqata" ya fada yana rungume ta ta baya,saita fara qoqarin tureshi amma ya hana mata wannan damar,har ta gaji ta haqura,sannan ya saketa don kanshi "Kome zakiyi ki dinga qoqari kina zurfafa tunaninki,ina yawan gaya miki,ki dinga sanya hankalinki a gaban fushinki" "Eh ai dama kullum ni nake da laifi,kaikam baka aikatamin komai,duk wani rashin kulawa da kake nunamin ina hadiyewa baka gani ba" "It's okay.....na sameku lafiya?" "Gamu lafiya lau" ta fadi kamar wadda aka cusawa tsumma a baki "Ma sha Allah" ya fada yana shafa sumar kansa sannan ya juya zuwa falon,don sam tarbar da yake da buqata ma bata iya taba har kwanan gobe. Abinda ya fara dawo masa akai yadda widad tayi welcoming nasa,duk da cikin quruciya take komai.....amma komai nata burgeshi yakeyi,yaga zallar kewarsa a idanunta,irin kewar daya rufe mata idanu ta gaza ganin koda hajiya da take kunya da kuma marmarinta,kewar data gaza boyuwa daga idanunta......irin yanayin da yayita begen samu daga hafsat tsahon shekarun da sukayi a tare amma abun ya faskara. Wannan tunanin ya haifar da murmushi saman fuskarsa,bai zauna a falon ba ya dauki yaran suka wuce zuwa sashensa,can dinma ba laifi an dan gyarashi,duk da dama sashensa baya barinsa yayi datti. Ba jimawa ta shigo da kayan abinci,ta zuba masa ta koma gefe ta zauna tana danna waya,fuskarta kadaran kadaham,amma bata tsoma bakinta a hirarsa da yaransa ba,sai daya ci rabin abincin,taga babu alamun widad tare dashi sannan ta magantu "Ina ka baro antyn tasu?" Hankalinsa nakan zarema yaran uban qayar dake jikin kifin data dafa,bata damu data tsaya ta gyarashi da kyau ta cire qayar ba ya amsa mata "Na barta gidan hajiya" haushi ya cikata,saboda ba qaramin aiki ne yake jiran yarinyar ba,taci buri sosai wannan karon,don ta dauki alwashin daga shi har widad din saita fito musu da sabon taku,zuwa weekend din da ya dinga yi babu ita kafin tafiyarsu ta taso ba qaramin qona mata rai yayi ba,saboda ta riga ta saba da ayyukan widad din,wani lokacin tun ranar laraba zata fara hada dalar qazantarta ta jirayi zuwan widad din,tasan idan tazo kamar anyi ruwa an dauke ne,fes ko ina yake komawa. Bata sake tambaya ba don kada ya ramfota,amma cikin ranta addu'a take Allah yasa kada tace zata kwana,a badini ji taje kamar ta tafi gidan hajiyan ta janyo widad din tayi mata shegen duka. Suna qoshi suka bigire da bacci a wajen,dama kusan lokacin baccinsu ne,hannunsa riqe da yatsar nawwara ya saki ajiyar zuciya sannan ya kalli hafsat "Ki kaisu dakinsu kizo ina son ganinki" yayi maganar a tausashe yana duban tsakiyar qwayar idanunta,dauke kai tayi,don batason ya karya mata zuciya kwata kwata,taja tsaki qasan ranta sannan ta yunqura zata miqe wayarta ta dauki tsuwwa,saita dakata ta daga wayar ta sanyata a kunnenta "Hello.....kin qaraso?,kina falo?, okay gani nan" sai ta katse wayar,ta sunkuya ta dauki mimi ta fita a falon. Miqewa yayi ya shige bedroom dinsa ya zarce toilet,yayi brush ya sake alwala,sanann ya fito ya rage kayan jikinsa ya dawo falon,har a sannan bata dawo ba,bai dauka zata dauki tsahon lokaci haka ba,sai ya kunna tv ya kama labarai ya fara kalla,duk kuwa da cewa hankalinsa baya wajen. Kusan minti talatin ba ita babu labarinta,kamar ya shareta sai ya fasa,ya koma ya dauko jallabiyya mai santsi saqar qasar oman ya zuba,ta masa masifar kyau ta qara fidda wannan sirritaccen kyansa,ya dawo ya dauki nawwara suka baro sashen. Ba kowa a falon,amma da alama anyi baquwar ta tafi,dakinsu ya kai nawwara sannan ya dawo ya wuce dakinta. A gaban mudubi ya sameta tana hada kudi,suka hada ido,tasha jinin jikinta amma ta basar,ya zube hannayensa a aljihun jallabiyyar jikinsa yana mata duban da yasan yana ratsa qashinta da kyau "Gani na biyo sahu" ya fada cikin wani salo,ta lumshe idonta, muryarsa ta tabata da kyau,amma girman kanta sai ya motsa "Baquwa nayi,kuma yanzun ma wata baquwar gareni tana hanya" bai sauraren ta ba ya taka zuwa bayanta ya kuma rungumeta da kyau ta bayan,baiyi qasa a gwiwa ba ya fara aike mata da wasu saqonni masu nauyi da tsuma zuciya,sun isketa da kyau kuwa,ita kanta tasan waye abbas din fiye da kowa a duniya,ta wannan fannin idan ana taron bada award.....ba award ba idan akwai abinda ya fishi ya cancanci a bashi,tun tana dojewa har sai da ya zaqulo dukka wani qwarin gwiwarta yayi watsi dashi,ya gigita tunaninta da kyau ya kuma yi mata masauki saman gadonta ba tare data ankara ba,sadai tafiya nayin nisa,yana gab da kaiwa inda yake da muradi hudubar shaidaniyar zuciyarta ta dawo mata,ta tattara qarfinta gaba daya ta tureshi ta koma gefe tana cika tana batsewa. Da qyar ya daga kansa ya kalleta,idanunsa sun canza launi sosai,a sannan idan ka kalleshi zakayi tsammanin barkono aka watsa masa "Me kikeyi haka?" Baki ta turo masa "Sai yanzu kasan ina da amfani?,bakasan fushina ba balle damuwata ba" "Kinsan me kika aikata?,kinsan matsayin yin hakan har a wajen Allah?" Qeya ta juya masa tana kada qafa,tana jin itama a yanzun lokacinta ne da zata murza kambunta,batasan ma me ta tsaya jira ba da har yake mata haka take daga masa qafa,bayan tasan tana da wannan makamin a hannunta "Kai bakasan naka hukuncin ba saini?,meye naka hukuncin tukunna" shuru ne ya biyo baya,yayi qas da kansa yana dafe da mararsa data fara yi masa ciwo,hafsat itace musababbin samuwar ciwon mara a wajensa,a baya kafin yayi aure bashi dashi,duk da yana da qarfin sha'awa,to amma a lokacin baisan meye aure ba,bai kuma qwallafa ransa akan mata ba,hasalima basa cikin tsarinsa kwata kwata,har sai daya samu halalinsa. Shurun da taji bai sanyata ta juyo ba,abu daya take jira ya roqeta ya lallasheta,tana jin a sannan ne zata iya haqura ta san masa,shima saita shimfida masa dokoki ya kuma tafe mata kudin da take so wanda zata qara jari a business dinta,duk da zuciya da ruhinta suna d'ar d'ar, zuciyarta na gaya mata zaiyi wuya abbas din ya roqeta. Wata babbar ajiyar zuciya ya fidda,kamar zai hada da zuciyarsa,ya motsa ya miqe ya jawo jallabiyyar sa ya maida jikinsa,tayi tsit tana sauraren motsinsa,a yadda ya kamu da yawa bata dauka zai iya motsawar bama,ya tsaya qyam saman qafafunsa,cikin mamaki ta waiwayo tana dubansa. Kallo daya ta yiwa fuskarsa gabanta ya fadi,tayi hanzarin dauke kai tana gayyato dakiya "Ina da qarfi da ikon da zan iya danneki nayi dukkan yadda naga dama dake.....amma bazan aikata hakan ba,bawai don kinfi qarfina ba...... a'ah,saidai dalilai guda uku,na farko auren soyayya mukayi dake ba qiyayya ba,na biyu ban haquri da lallashi kikeso daga wajena......wallahi wallahi muddin wadan nan dabi'un naki zaki ci gaba dayi,ba zaki taba samun wannan daga gareni ba har abada.....abu na uku kuma.......bake kadai bace Allah ya halattamin ba,sannan kuma bake bace autar mata,ki jiqa abinki ki shanye,indai abbas ne na haifu,kuma dan halak ne ni gaba da baya" daga wannan ya fara takawa a hankali yana ficewa daga dakin,yana tafiya yana cije labbansa saboda yadda yakejin mararsa kamar zata tsage. Gaba daya maganganunsa sun gigita ta,babu zance mafi gigita kuma a ciki daya ce mata ba ita kadai Allah ya halatta masa ba......yana nufin widad?,shi yanzu sai ya kusanceta?,bazaiji kunya ba?,yarinyar da ya kusa haifarta?,zumbur ta miqe,tana jin kamar taje ta dawo dashi yayi abinda yayi nufin yin.....don da ya aikata abinda yake nufi a zancansa gwara ta bada kanta ta dawo dashi,amma kuma tana taku uku wata zuciyar ta dawo da ita "Zaki zubda mutuncinki da ajinki a wajensa" sai taci gaba da gamsar da kanta cewa abbas din bazai iya ba,yarinyar tayi quruciya da yawa,bazata taba iya gamsar dashi,kai ba zata daukeshi bama,ko ita da yaya suke qarewa bare widad din dako qasusuwanta basu gama yin qwari ba,ta tabbatar bashi yiwuwa "Namiji nefa,idan komai bai kawoshi ba buqatarsa zata dawo dashi,basu da haquri ta wannan fannin" ta sake tabbatar wa da kanta,sai taja tsaki ta koma tayi zamanta,har fana tuhumar kanta "Kin faye rawar kai akan abbas din nan,shi yasa ya rainaki,ya kasa ganin kimarki" wata zuciyar ta sake gaya mata,da wannan taja mugun tsaki ta miqe ta dauko wayarta dake ringing tana duba me kiran,baquwarta ce da zata kawo mata biyan bashi,saita aje wayar ta shiga bandaki tayi tsarki da alwala ta fito,saidai har a sannan itama tana ji a jikinta,don ba qarya tayi missing abbas din,sannan tarkon daya dana mata banda akwai wani quduri a ranta.....ta kuma yi da gaske ta dace da zuciya mai tauri bata isa ta tsallake ba,a ranta taji tana fatan tattaurar zuciyarsa ta sauko da wuri ya karyo ya nemeta,don itama a buqace take. Tunda ya zube a dakinsa bai iya tashi ba,a nan yayi sallar magariba ya kuma yi isha'i ya koma ya kwanta saman abun sallar,rub da ciki yayi tun tsahon awannin yana fatan ya samu sassauci na zuciya da kuma gangar jiki,gaba daya ya manta zaije dauko widad,sai da yaga kiran hajiyarsa. Bayaso yace mata baya da lafiya,yanzu zata daga hankalinta,kuma yasan babu driving din da zai iya,sai yace mata yana zuwa. Number k'aninsa umar wanda daga shi sai auta ya kira yace yazo ya karba key din motarsa ya kawo widad din,idan hajiya ta tambaya ya gaya mata baqi yayi,a ladabce ya amsa masa,ya katse kiran,ya aje wayar yana cusa hannunsa cikin fuskarsa. Ita kuwa hakimar tana falonta a zaune,duk sanda taji wani motsi saita leqa taga waye,so take taga shigowar widad din ta tsareta da ayyuka,idan da hali ma yau kwanan dakin su mimi zata sakata yi,taso acema key din part dinta yana wajenta tace mata ya bata,batasan me yasa bata saka mata dokar ajeshi a wajenta ba,amma daga wannan zuwan abinda zatayi kenan,ta dinga barinsa a hannunta,idan suka dawo ta dinga karba. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 69 A idanunta akayi sallar magariba bataga gilamawarsa ba,akayi isha'i ma haka,sai jikinta ya bata lallai ciwon cikinsa ya tashi ne,indai kuwa hakanne babu inda zai iya tafiya dauko yarinyar,hankalinta taji ya kwanta,ta kuma sake abinta,gwara yarinyar ta kwana a gidan hajiyan akan ta dawo cikin gidan yana cikin wannan yanayin,ta sanshi sarai,tamkar mayunwacin zaki yake,haram ce kadai baya iya dosa a irin wannan yanayin,saita koma ciki taci gaba da lissafin kudinta da kuma sabgoginta. Ta riga ta gama saddakarwa,wannan ya sanya shigowar umar da fita da motar duka bata jisu ba,ta gama abinda takeyi ta dawo falo ta kunna kallo abinta,saurana abincinsa da bai cinye ba shi ta zubawa yaran sukaci abincin dare dashi,hakanan suka tsakura,saboda sun gaji daci,shi sukaci tun rana sukaci da babansu yanzu ma kuma gashi shi dinne,sunata wasansu tana chart, hankalinta ma baikan tv din,tana bawa anty ummee labari ita kuma tana cin dariya _shegiya,wannan mafa hanyar samun kudi ce a wajen mace bana wasa ba_ anty ummee ta gaya mata _wallahi a wani group wata hamshaqiyar hajiya ta bamu sirrin,ina nan ina zuba ido,idan ya gaji ya kawo kansa ya kuma biya price sannan a bude masa gate_ Daga can anty ummee tana ta dariya,cikin ranta kuma tana gulmar hafsat din,sai kace wata hamshaqiyar mace,banda ma abin namiji,ai ita qoqarin abbas take gani,duk da tsananin tsaftarsa amma yake iya tarayya da hafsat din,harda qulafucinta haka?,lallai abar rai da abinda yakeso kawai. Sun jima suna hirar anty ummee na sake dorata akan keken bera,don itama tanaso idan ta yagi kudin ta yagi nata kason itama,tanason canza kayan kwalliyar falonta, hankalinta ya dauku ga hirar ta wuce kitchen dauko lemo,tafison tana yi tana korawa dame sanyi,dai dai sannan motarsu widad din ta shigo,ya tsaidata a parking lot. "Matar yaaya,yace ki sameshi a bangarensa,ga key din motar,saiki tafi masa dashi" "To,sannu na gode" dariya ya danyi kadan,itakam halinta dabanne,duk da sun girmeta,bai taba jin hafsat ta aikesu tayi musu ko sannu ba bare godiya. Tare suka fita a motar,shi ya doshi gate ba tare da yayi tunanin zuwa su gaida da hafsat ba,don sai suyi zuwa dari ba wanda ya kalli sashenta,sai dai idan sunga idanun abbas din,ko shi yace su shiga su gaisheta. Kallon sashen hafsat din tayi,gabanta yadan fadi,ta tuna kiran data dinga mata bata dauka ba,wanda shine tun daga ranar bata sake kiranta ba,saita dauke kanta,ta doshi sashen abbas din da dan hanzari,tana Allah Allah ne ta shiga ta bashi ta fito ta wuce sassanta. Tayi mamakin ganin wutar falon gaba daya a kashe,babu hasken komai sai na wutar bedroom dinsa,sarkin tsoro tsoron nata ya motsa,duk da bawai duhu can can yayi ba,don hasken fitilun waje suna ratsowa ta labulayen falon,ta fidda wayarta ta kunna torche sannan ta doshi dakin. Da siririyar muryarta tayi sallama tana shiga dakin,bata lura dashi ba har sai daya dan motsa daga kwancen yana amsa mata sallamar,ta danja baya adan tsorace,sai ya koma rigingine yana kallonta da rinannu idanunsa "Uncle.... Lafiya?" Ido ya lumshe sannan yayi qoqarin miqewa yazauna yana cije bakinsa kadan "Lafiya lau,ina umar din?" "Ya wuce,ga key din yace na kawo maka" ta qaraso gefansa ta duqa ta ajjiye,qamshinta ya huro masa har inda yake,sai ya maida idanunsa ya rufe "Yunwa nakeji,zan samu abinci?" Da mamaki ta kalleshi "Mommy hafsa fa?" "Zan samu abinci?" Ya sake maimaita tambayar tasa ba tare da yabi takan maganarta ba,sai ta gyada kanta da sauri "Okay,dafamin wani abun mai sauqi mai ruwa ruwa" sai a yanzun ta lura da yanayin fuskarsa,gaba daya ta nuna bashi da lafiya,jikinta yayi sanyi,ta matso sosai kusa dashi,tasa hannu tana dan taba fuskar tasa "Uncle kamar baka da lafiya fa" ji yayi kamar ta zuba masa wani abu me sanyi a gangar jikinsa,ya rufe idanunsa ya budesu a kanta "Bani da lafiya weedad" sosai fuskarta ta nuna damuwa qwarai,ta tsugunna gabansa tana ajjiye jakarta "Amma uncle ne yasa ba zakasha magani ba?" Ido ya zuba mata sosai,yana ji a ransa inama zata iya dauke lalurarsa,inama tace zata zame masa maganin?,ya sani matarsa ce.....amma yasan halittar da Allah yayi masa a shekarunta yana ganin indai ya fuskanceta da wannan zai iya cutar da lafiyarta "Zansha weedad......bani wani abun tukunna" da saurinta ta miqe ta zame mayafinta da jakarta duka ta aje a wajen,suman zaune ya kusayi,dogon sassalkan gashinta na kwance a bayanta,tunda ta shigo daman dankwalinta yana jakarta,ba kasafai take daura dankwali ba don basa shiri, skert din ya fidda shape dinta sosai,ta baya zata dauka takai shekaru ashirin da wani abu,sai a lokacin yaga girman da yaji 'yan uwansa na fadin tayi,ya koma da idanunsa luuuuu ya rufe yana kiran sunan Allah. Faten dankali ta shirya masa,duk da yadda yayi dadi amma gaba daya baya gane taste dinsa akan harshensa,zamanta kusa dashi yafi komai dagula masa lissafi,ita kuwa ta zauna ne bilhaqqi tana matsa masa yaci "ko baiyu dadi bane na sake maka wani uncle?" Ta fada a shagwabe saboda sam bata jin dadin yadda taga baya ci din sosai,kansa ya girgiza dankalin yana wuce masa wuya da qyar,sai ya aje plate din ya zuba mata idanunsa gaba daya yana mata wani mayunwacin kallo "Maganin zaki bani" ya furta da wata birkitacciyar murya,itama shi take kallo,karon farko da taji kallonsa ya saukar mata da wani abu mai nauyi a jikinta da zuciyarta "Ina maganin yake saina dauko maka" tayi masa tambayar tana janye qwayar idanunta daga kansa,saboda wani nauyi da taji ya saukar mata lokaci guda. Kanta ta daga sanda taga ya miqo mata hannunsa,ta kalli hannun ta kuma kalleshi,bata fahimci komai ba "Zo na gaya miki inda yake" a mamakance ta miqa masa hannunta,bata kai ga tuna komai ba ta samu kyakkyawan masauki a jikinsa daya dauki dumi,cikin qirjinsa ya lullubeta gaba daya yana sauke wani irin numfashi a jejjere,komai ya fara koma masa sabo,tunaninsa ya fara nisa ya fara daina gane komai. Yamutsa ta ya fara yi,abinda ya tsorata ta ta fara kiran sunanshi tare da qoqarin kama hannuwansa dake yawo a sassan jikinta,ko harafi daya bai gane ba cikin maganganunta,illa dai yana jin sautinta kamar mutumin daya sanya bakinsa cikin kofi yana magana(sama_sama),a yau ya ware dukka hannayensa a kanta,duk inda suka kai bai musu shamaki,haka nan bakinsa. Sanda ya hade fatar jikinsu waje daya daukewa numfashinsa yayi cak na wucin gadi sannan ya samu ya qwatoshi da qyar,qasan da suke yaji tayi masa kadan,ya dagata zuwa tafkeken gadonsa ya shimfidar da ita,zuwa sannan tsoro ya kusa halakata,abinda bata taba gani ba,bata kuma taba zata ko tsammani ba.....yayin da abbas yayi nisa a wata duniya, duniyar da tunda yake bai taba tunanin ana kaiwa har can ba,tun daga tsarin lallausar fatarta zuwa daddadan qamshin jiki dana sumar kanta komai ya sake kwance masa,ya rasa ta inda zai juyata,ko ina ya juyatan sai yaji yayi masa kadan. Kuka mai qarfi ta saki sanda taji ya soma rabata da sutturar jikinta,ta shiga roqonsa da kyau akan kada yayi mata komai......ummu ta hanata......idan yayi ummu zata kasheta,amma ina samm samm baiji ba,abu daya ne ya maidoshi duniyar sa,daukewar numfashi daga gangar jikinta bayan taja wani dogon numfashi sanda ya soma buda hanyarsa zuwa sabuwar rayuwa da sabuwar duniya.... dole ya zare jikinsa daga gareta ba tare da yakai ga cimma gaci ba,ya koma qoqarin ganin daidaituwar numfashinta. Tun da safe ta tashi da sha'awar cin awara,sai da yaran sukayi bacci sannan ta fita da 200 zuwa bakin gate dinsu,ta bawa yaron gidansu ya siyo mata "Ka riqemin kudi na da kyau,don idan ka yarmin sai ka biyani" kudin ya kalla sannan ya dubeta "Hajiya dari biyu ce fa" ya fada qasan ransa fal mamaki,kaf unguwar kowa yasan waye ASP abbas din,amma ita sam bata jin kunyar yin aike da qaramin kudi "Na sani,ko bani na baka ba?" Sai ya gyada kai "Hakane" daga haka ya juya yana fita daga gidan,cikin ransa yana tur da irin halinta. A hanyar dawowa ta kalli motarsa,har yanzu bataji motsinsa ba,wani sashen na zuciyarta yana mintsinarta kan ta shiga ta duboshi,wani sashen yana fadin ki shareshi,zai kawo kansa da kansa,kulawa ma yabawa ce ai. Kamar giftawar iska taji fitar sautin qaramin ihu,wanda banda hankalinta dama akan sashen yake babu lallai taji,birki taja ta tsaya,gabanta yayi wani mugun faduwa,ta tsaya cak tana duban sashen nasa,muryar tayi mata kama da muryar widad,to amma yaushe ta shigo gidan?,tunda dai ita bata ji shigowar kowa ba,hakanan bataji fitar kowa ba,ta zubawa sashen idanun sosai ko zata sake jin wani motsi amma bata ji komai ba,sai hankalinta ya rabu biyu,wani sashen na zuciyarta na bata shawarar ta shiga ta duba,wani sashen kuma yana cewa tsarguwa ce kawai tayi,duk da haka saita kasa gamsuwa,ta dawo farfajiyar gidan ta zauna saman fararen kujerun da abbas din ya zuba a wajen saboda baqi,idanunta nakan sashen tana nazartarsa. Babu ma alamun haske gaba daya,wanda wannan sign din da take gane abbas din yayi bacci,don baya kwanciya da haske a kanshi,sai taji zuciyar dake gaya mata tsarguwa ce tafi rinjaye,amma duk da haka zata jira dawowar yaron,tasan zaiyi wuya wani ya shigo ko ya fita baya wajen. Bai jima ba ya dawo da awarar a farar leda karrr kana hangota quru quru,tasa hannu ta karba tana dubansa "Babansu mimi ya fita ne dazu?" Kai ya girgiza "Anya?,tunda ya dawo dai banga ya fita ba" "Bayan shi fa ba wadda ta shigo gidan nan?" Kai ya jinjina "Babu gaskiya" saita gyada kai tana sauke ajiyar zuciya "Shikenan jeka" sai data qara wasu sakanni sannan ta miqe ta koma ciki,tana tafe tana waigen sashen, zuciyarta taqi gamsuwa,amma ranta ya aminta da abinda yaron ya fada,tsaki taja daga qarshe,ta maida qofa ta rufe sashenta. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 70 Duk da cewa baikai ga cimma gaci ba,duk da cewa buri da muradinsa bai cika ba......amma ta kaishi wata duniya data sake haukata tunaninshi,ta sake ninka burinsa......ta sake kwadaita masa ita,ta kuma haifar da wani yanayi da kai tsaye zaka kirashi da ZAZZAFAR K'AUNA a karon farko,cikin jininsa ya dinga ji cewa eh weedad din ta dabance,zata iya zamowa ta musamman cikin mata..... za'a iya kiranta da 'yar baiwa,ya samu wani irin nutsuwa da tarin ni'imomin dake hutar da zuciya su kuma sanya ma ruhi nutsuwa tattare duka a iya jikinta kadai,tun baikai ga afkawa waccar duniyar ba. Wani irin ciwo yakeji har cikin zuciyarsa sanda take rera wani irin kuka,ciwo ciwo takeji daga can qasanta duk da baiyi yawa ba,saidai hankalinta a mugun tashe yake,me ya aikata mata kenan?,da wanne fuska zata kalli mutane?. Yayi lallashi yayi ban bakin amma a banza,har sai da bacci ya taimakeshi ya dauketa,sai ya zareta daga jikinsa a hankali ya shimfidar da ita,ya kunna bedside lamp ya matso da ita kusa da fuskarta sosai. Kallo na haqiqa ya zauna yana qare mata,baisan da wanne suna zai kirata ba,baisan kuma a wanne matsayi zata iya tsayawa cikin zuciyarsa ba daga ranar da ya maidata tashi,a yanzun Allah ne kadai yasan me yakeji a kanta,qauna soyayya tausayi da kuma shauqi gaba daya, mintuna qalilan amma sun canza matsayinta daga wani bigire zuwa wani bigiren na daban. Ya jima zaune kamar mai karanta littafi yana kallon baby face dinta da tayi jazur da ita,sannan ya sauke ajiyar zuciya,ya zura qafafunsa ya sauka daga saman gadon ya shige bandaki. Tsarkake kansa yayi sannan yayi wanka,ya fito ya tsane jikinsa da kyau ya sauya kaya sannan ya koma saman gadon,bai jishi dai dai ba har sai daya jawota jikinsa,tunane tunane ne masu tarin yawa ke masa yawo a kai,shi kansa idan yace ga dai dai lokacin data ma zuciyarsa wannan muguwar illar yayi qarya,wani abu mai qarfi akanta ya dinga shigarsa,sai ya dinga jin gaba daya duniyarsa ta ta'allaqa da ita. Kiran sallar asuba ne ya tasheshi,har ya gama shirinsa na fita masallaci bata ko motsa ba,bacci take sosai tana kuma sauke ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci,har sunkuya saman kanta zai tasheta yaji ya kasa tashin nata,yaja mata bargon ya rufeta bayan yayi kissing goshinta,ya fita yana waiwayawa kamar wanda akace za'a dauketa kafin ya dawo. Sanda ya fita sallar yayi mamakin ganin cunkoson jama'a a layin nasu,ya qarasa a hankali ya fara musabaha da mutanen dake wajen "Munyi tunanin baka gari ai yallabai" daya daga cikin dattawan layin ya fada yana duban abbas "Me yake faruwa alhaji audu?" Abbas din ya tambaya yana dubansa "Wallahi daren jiya 'yan fashi suka shigo gidan maqocina alhaji isah" "Subhanallah" ya fada cikin alhini "Kusan kowa yaji abun,don tun wajen karfe daya na dare suka shigo unguwar,basu fita sai qarfe uku" "Ya salam,Allah bai sa naji ba,amma aka rasa wanda zaiyi kiran koda wayata?" "Wallahi Allah ya daukewa kowa wannan tunanin" matsawa gaba ya fara yi zuwa gidan alhj isah din,inda mutane suka fara dandazo "Badai wanda suka raunata ko?" "Eh to,sun harbi yarinyar sa,suna hanyar kaita asibiti" "Kun kira jami'an tsaron?" Cikin alhini alhj audu ya girgiza kai "Kusan awa guda kenan amma babu su ba dalilinsu" sosai ran abbas din ya baci,ya tambayi police din wanne area dinne alhaj audu ya gaya masa,sai ya fidda wayarsa yayi kiran dabai wuce na minti uku ba cikin bacin rai "you must be there before thirty minutes" abinda ya fada kenan ya kashe wayar ya mayar aljihu "Kada kowa ya shiga cikin gidan,sannan suma mutanen gidan a gaya musu su nisanci inda abun ya faru.... alhaji muje muyi sallah tukunna" tare suka rankaya da alhaji audu zuwa masallacin suna sake tattauna yadda abun ya faru,bashi da nauyin bacci sam,kamar yadda bai saba dogon bacci ba,amma yayi mamakin yadda jiya har akayi aka gama abun baiji ba,lallai da gasken gaske 'yar qaramar yarinyar ta gigita masa rayuwa da kyau a jiyan,ta kuma shirya janshi zuwa wata rayuwa ta daban,baisan sanda wani siririn murmushi ya kubce masa ba. Wannan case daya faru a unguwarsu ya hanashi komawa gida da wuri,sunata bincike kan abun har sai da suka samu nasarar tracking barayin cikin taimakon Allah da kuma qwarewar da yake da ita,sai wajen qarfe daya na rana sanann ya gama nasa aikin,ya danqawa wadanda alhakin kula da area din yake a hannunsu,ya zare safar hannunsa ya miqawa daya daga cikin police din,gaba daya hankalinsa yana kanta tun dazun,dauriya kawai yakeyi. Sama sama ya amsa gaisuwar yaron gidan nashi ya wuce zuwa cikin gidan,kai tsaye sashensa ya wuce,ya tura qofar falon ya shiga,bata falon bata bedroom din,sannan bata toilet,sai zuciyarsa ta raya masa ko tana sashenta,don haka ya juya akalarsa zuwa can. Kaf ya gama dubawa bai ganta ba,sai abun ya shiga bashi mamaki,baya da niyyar shiga sashen hafsat din yau gaba daya,amma dole ya shiga ya gani ko tana can. Dukkansu suna falo ita da yaran,tuni falon ya koma 'yar gidan jiya,tana saman kujera zaune abinta,ta cika tayi fam da fushi,daga abbas din har widad din kowanne da nasa laifin a wajenta,donme yarinyar zata tafi gidan hajiya tayi zamanta?,uban waye zaiyi mata aikin da tafi kowa sanin itace zata yishi?,sannan abbas din me yake nufi da ita?,har azahar tayi amma ya kasa leqowa yaga lafiyarsu?,jikinta ya soma sanyi amma wani sashen na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwa,tare da sake kambama mata laifukansa,duk da haka ta soma rasa qwarin gwiwarta,tasanshi....yana da danne zuciyarsa da hanata saurin fushi,amma kuma idan yayi fushin bashi da dadi sam. Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke sanda taga shigowarsa,ya tsugunnawa yaran suka haye bayansa,fuskarsa na fidda murmushi,zuciyarsa dauke da tausayinsu,da babu alamun an musu wanka "Ina antynku?" "Daddy ta dawo?,ka kaini wajenta" mimi ta fada,abinda ya tabbatar masa kenan bata shigo ba kwata kwata "Ina kwana?" Ta fada ganin yana niyyar miqewa ba tare daya kalleta ba "Lafiya" "Ga breakfast dinka har ya huce baka ci ba" "Na qoshi" ya amsa mata yana ficewa riqe da yaran. Hankalinsa yadan tashi,ina ta tafi to?,ya tambayi kansa,sai ya jawo wayarsa ya kira layinta,a kashe layin yake,ya sauke wayar yana fidda iska daga bakinsa,gidan hajiya ta koma?,wata zuciyar ta gaya masa,har ya danna kiran layin hajiya sai ya kashe,idan ta tuhumeshi dalilin komawarta baisan me zaice mata ba,don haka ya kira layin umar. "Kana gida ne?" "Eh hajiya za'a baka?" "Weedad tazo?" "A'ah yaaya,tun jiya dai dana kawota gida" "Okay,karka cewa hajiya ga abinda na tambayeka" "To yaaya" umar din ya fada ,kafin ma ya qarasa abbas din ya katse kiran,sai yaji hankalinsa ya sake tashi. Muhsin ne ya fado masa,baiyi qasa a gwiwa ba yayi kiransa bayan sun gaisa kafin abbas dinma yace komai ya rigashi magana "Jiya jiya muke zancanku,inajin madam fa gobe ko jibi zata shigo ganin diyarta,nace ban da tabbacin kunxo weekend wannan satin" "Jiya mukazo,amma kuma banajin zamu jima zamu koma,yanzun ban fiya sakewa a bauchi ba,ayyuka sunyi yawa a kaduna" hira kadan suka taba sukayi sallama,don shima muhsin din fitowarsa kenan daga gida yana kan hanya yana driving. Wayar ya ajjiye,ya koma gefen gadon ya zauna hannuwansa cikin sumarsa yana murzata a hankali,yanason qwaqwalwarsa ta hasaso masa mutum na gaba da zai kira ya bincika ko can taje,ya akayi ta iya fita daga gidan har ta fita ba tare da wani ya ganta ba?. Kasa zama yayi,sai kawai ya miqe ya dauki key din motarsa,tsoronsa daya kada yarinyar mutane ta bata cikin garin daba nasu ba,don yana da tabbacin zaiyi wuya ace shigowa akayi aka dauketa,don ya duba duk wani abu da zai iya bada alamun hakan bai gani ba,sai ya fita da yaran ya zubasu a motar suka fice daga gidan. Layi layi titi titi ya dinga bi yana dubata amma sam babu ita ba alamarta,har wajen azahar,ya tsaya a wani restaurant ya siyama yaran takeaway,ya dawo cikin mota ya zauna kenan wayarsa ta dauki tsuwwa,ya duba me kiran sai yaga muhsin ne "Kasan matarka ta tafi kano?" "Kano?" Ya tambayi muhsin din cikin mamaki qwarai,duk da dama yana cikin dimuwar son sanin ina tayi "Eh,yanzu muka gama waya da ummu,ta kirani tace na shaida maka,don tafiyar batayi mata kama data nutsuwa ba" qatotuwar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata nutsuwa na saukar masa "Alhamdulillah" ya fada a fili "Ka ganni a gefan hanya,tun dazun nake checking ko batayi nisa ba,ina shirin kira headquarter ma su bani mutane muyi aikin tare" "Subhanallah.......wanne irin sakarci ne wannan?,halan bata gaya maka ba bakasan da tafiyar tata ba" qaramin murmushi ya subuce masa,yasan sarai muhsin ba wasa,yanzun nan idan yace zai gaya masa gaskiya sai yace zai taba masa mata,shi kam a yanzun a yadda widad takai har cikin ruhinsa,baya jin ko ruwan sama zai lamunce masa ya taba masa ita "Me na tone tone?, tunda ka isar da saqon ummu shikenan,zan kirata" "Please abbas......kada kace zakayi kawaici,ka gayamin gaskiya" "Amma dai kasan indai kace zaka shiga tsakanin miji da mata zakaji kunya ne ko?" "I know.....but....." "But what?,shikenan kawai,ka qyalemu tsakaninmu ne" "Alright,Allah ya sawwaqe" daga wannan sukayi sallama ya aje wayar. Mamaki ya sake kamashi,yayin da qaramin murmushi ya subuce masa,rigimammiya ce yarinyar ta ajin qarshe,ya akayi har ta iya kai kanta kano?,da gaske batasan wannan rayuwar ba,batasan meye ma'anar aure ba at all "I will teach her......bazan bari ki subuce min ba,zan koya miki abubuwa masu zafin da zuciyarki zatayimin riqon tsauri da kyau" ya fada shi daya kamar me sambatu,abinda yake ji a ransa game da ita yafi qarfin a kirashi so,saidai wata irin zazzafar qauna da bai taba jin kamarta ba. Aje wayarta ummu tayi tana sauke dubanta ga widad data cusa kanta cikin pillow tana ta sheqa kukanta,kukan da tunda ta iso kano take kwararashi,tayi tambayar duniya amma taqi daga kai ta kalleta ma bare akai ga amsawa. Abu daya ne yasa hankalin ummu bai wani daga ba,widad din tata tayi fes tayi fresh,ta sake murjewa,ga kuma girma data qara,ta fara zama budurwa sosai,aure ya kwarzantata "Widad" ta sake kiran sunanta,shuru bata amsa ba sai kuka,tana tsoron su hada ido da ummun,tana ganin kamar zata gane abinda yayi mata a daren jiyan "Kinga idan ba zaki amsa min ba,ki daina kukan kada kanki yazo yayi ciwo" ummu ta fada tana miqewa "Ki samu waje ki kwanta" ta sake fadi bayan ta isa gaban wardrobe dinta ta fidda hijab,tayi sallar azahar sannan ta dauki wayarta ta fita tabar mata dakin,cikin ranta tana juyayin abinda ya faru,kodai ita da kishiyarta ne?,tunda muhsin ya sake kiranta yace abbas din yace babu komai,amma kishiya kuma......nawa widad din take da har kishi zai hadasu tayi wannan tafiyar afujajan. Da wannan tunanin ta isa falonta,ta iske latifa tana aje abincin rana "Batace komai ba ummu?" Latifan ta tambaya cikin damuwa "Uhmmm.....bata ce ba,nifa banga wani alamun damuwa tattare da ita ba,nafi zaton shirmenta ne kawai ya motsa,idan kuwa haka ne zataci qaniyarta,ta yaya zata dauko qafa daga bauchi ta taho kano ba tare da izinin mijinta ba?,baya ga haka kuma ita kadai a wannan rayuwar da muke ciki?" Ajiyar zuciya latifa ta sauke "Ayi mata dai a hankali ummu,ai ruwa baya tsami banza" "Kin manta widad din ne ashe" ummu ta amsa mata,wanda tana rufe bakinta momma tayi sallama "Barka da rana ummu" ta fada tana 'yar fara'ar da batakai zuci ba,da kallo ummu ta bita "Ke kuma daga ina da rana haka fatsar fatsar?" Murmushi ta danyi tana wuwwulga idanunta wai ko zataga himilin kayan widad din da akace an ganto ta shigo ita kadai "Zan fita ne nace bari na leqo,idan kina da canji ki aramin" "Canji?" Ummu ta maimaita cikin mamaki,saboda irin wannan ita baya hadata da surukanta "Eh....eh" dan shuru tayi tana karantar momma din,sai kuma tace "Allah ya kyauta,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta baki" amsa mata tayi sannan ta nufi kitchen din tana kalle kalle a falon ta gefan idanunta. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 71 Har ta karbi kudin ta dawo da baya,tunda dama.ba karbar kudinne a zahiri ya shigo da ita ba "Wai niko latifa,akace widad tazo ita kadai da tsakar ranar nan,kuma na shigo banganta ba,ko tana bandaki?" Kallonta latifa tayi,banda tana ganin girmanta cewa zatayi tana cikin masai ba bandaki ba,amma saita dauke kai tana ci gaba da aikace aikacenta "Kinsan ni bana shiga hurumin wasu,iya matsayina nake tsayawa a gidan nan,inaga da kin koma wajen ummu da kika wuceta a falo,zakifi samun bayani" ta gane sarai magana takeson gaya mata,sai kawai tace mata "Eh,kuma haka ne" ta juya ta fita tana tabe baki a ranta tana fadin "Koma dai meye idan tayi wari maji,oh.....yau ga 'yarso a gida,da alama ma dai auren ne ya balle,dama waye zai dauki wannan sakalcin nata,shafaffa da mai". Tun tana kukan har bacci yayi awon gaba da ita ba tare data sani ba,bata farka ba sai wajen qarfe uku na rana,ta miqe ta zauna tana murza idanunta,ta manta shaf a dakin ummu take,komai ya dawo mata,tabi dakin da kallo,dai dai lokacin ummun ta buda qofar ta shigo,tazo ne dama fa dubata kota tashin. Qin yarda tayi su hada ido,sai ta kauda kanta tana kallon qasa "Ki tashi kiyi wanka kici abinci" kai ta gyada,sannan ta zuro qafafunta qasa ta miqe,har yanzu wajen tana jinsa wani dundurus,duk da zafin zuwa yanzu ya baje. Ruwa me zafi ta hada sosai tayi wankan,wajen yin tsarki taji ruwan dumin ya mata dadi a wajen,ta dinga kwararashi har sai data ji wajen ya saki gaba daya sannan ta fito,ta samu ummu ta aje mata doguwar riga cikin ire iren kayanta da bata gama kwashewa ba daga gidan,ta sakata tayi sallar la'asar da aka soma kira sannan ta daure ta fito falon ummun. Su biyu ta samu,ita da anty madina,madinan batasan da zuwanta ba,don bata gidan,yanzun ta dawo ta biyo kawowa ummu sallahu data bata,baki ta riqe cikin madaukakin mamaki da kuma farinciki "Widad din ummu..... innalillahi,yaushe kika zo,babu sanarwa bare nayi miki kyakkyawar sauka?,saida kika bari ranar da bana nan fisabilillahi" murmushi ya qwace mata,karon farko kenan tunda tazo gidan. Tabe baki ummu tayi tana duban anty madina "Waye ma yasan da zuwan nata?,koshi mijin nata ai baisan zata zo ba,muma ganinta kawai mukayi" gaban anty madina ya fadi "Kamar yaya?,widad me ya faru?" Tambayar dai dai take da sukar bulalai a jikinta,ta yaya zata iya ce musu ga abinda yayi mata?,sai kawai ta fara hawaye bayan ta zauna a wajen. "Kici gaba da kukan,karki bude baki ki fadi abinda ya kawoki,mahmudu kawai nake jira ya dawo,ai jibi yacemin zai dawo,yana hanya" cewar ummu bayan tayi qwafa,da alama ranta ya baci wannan karon akan widad din,a tausashe anty madina tace "A'ah,ai baza'ayi haka ba,ki bita a hankali ummu don Allah" "Yo madina meye ban mata ba?,indai ba so take na tsugunna tahau gadon bayana kuma na goyata ba,shine kawai abinda ya rage". A nan suka sanyata gaba da tambaya harda latifa amma ta kasa cewa komai,har ummu ta qulu ta tashi ta barsu,daga baya suma hakanan kowa ya haqura ya qyaleta. A ranar duk wanda ya shigo gaida ummun cikin yaranta maza kawunnan widad din sai ya kirata ya tambayeta,amma ta kasa cewa komai sai kuka,haka washegari akayita fama taqi magana,tace duka su qyaleta, mahmudu ne dai dai da ita,a goben kuma ko jibi zai dawo,abinda ya sake ruda cikin widad din,amma batajin zata iya ce musu ga dalili. Yaran gidan nata shigowa murnar zuwanta amma ta kasa sakewa,haka su Aafiya,saidai suyita hirarsu tana kallonsu,don ita a cikin damuwa take,tana tsoron gamuwarta da babanta,amma kuma tayaya zatace musu ga abinda yayi mata daya sanyata guduwa?. Abbas kuwa umnu ce tasa muhsin ya gaya masa basai yazo ba,yayi zamansa,abinda ya bashi mamaki yadda yakejin damuwa sosai a ransa,har ya taba kuzarinsa,ya kira number dinta kuma sau babu adadi amma kullum wayartata a kashe take,inda don ta tashi ce da tuni ya tsufa a kano,kwana ukun kacal amma yana jin kamar wasu kwanaki ne masu dimbin yawa,hafsat ta lura da hakan,duk da kusan ba wani sabgar juna suke shiga ba,ta kuma ji qishi qishin zancan tafiyar widad din kano,duk da bata da tabbacin meye ya kaita,amma ko babu komai taji dadin hakan har qasan ranta,tunda dai tasan ba lafiya bace ta kawo hakan,fatanta ma ta tafi kenan,kada ta sake dawowa har abada. Abu daya ne ya tsaye mata a rai,damuwar data fuskanci abbas din kamar ya shiga,ta rasa gane ma'anar hakan,ya fara son yarinyar kenan?, tambayar data yiwa kanta kenan,sai kuma ta qaryata kanta da kanta,ta yaya abbas din zai fara son diyar cikinsa?,banda kyau babu wani abu data ga yarinyar tana dashi,samun kanta tayi da duqufa addu'ar kada Allah ya bata ikon dawowa. **********Dukkaninsu suna falon ummu,mahaifinta da ya kasance babba da kuma qannensa gaba daya,ummu da widad na gefe,yayin da widad din tayi kamar ta shige cikin ummun "Tunda taqi cewa komai yaaya,me zai hana a sake kiran abbas din aji" girgiza kai alhaji mahmud mahaifin widad yayi cikin takaici "Ya riga yace min babu komai,kuma tunda yace din babu,ita dai tana kwaso wadan nan siraran qafafuwan nata tazo,ita zata bude baki tayi mana bayani ko na tashi na babballata a wajen nan na zubar" ya fada cikin tsananin fushin da tun dazu idanun ummu yasa yake cinyewa. Duka kallo sai ya koma kanta,cikin hargagi kamar zai kai mata duka yace "Zaki bude baki kiyi magana ko saikin daku?" Kamar an rufto mata duniya haka taji,ga wani mugun tsoron yadda abban nata ya juye da yake ratsata,tayi qas da kanta tana hawaye, abinda ya tunzura alhj mahmud,ba wanda ya ankara sai gani sukayi ya isa kanta da wayar tv daya ciro ya fara sauke mata ita. Kuka ta saki sosai,don zata iya cewa wannan shine karon farko da aka taba mata irin wannan dukan kaf rayuwarta,kafin a samu a qwaceta kuwa ta daku yadda ya kamata,latifa ta karbota tana boyeta cikin hijabinta ta fice da ita daga sassan ummun cikin jimami da alhini. Kai tsaye sassan anty madina tayi da ita,tana kwance a falo ta miqe tana salati "Dukanta dama yaaya yakeyi dana jiyo muryarta daga nan?" Anty madina ta fada kamar zatayi kuka "Wallahi,taqi ta fadi komai ne,shi kuma ransa ya baci" rungumeta anty madina tayi tana lallashinta "Inda kin fada widad ai magani za'a yi miki na koma meye da yake damunki" a nan hannunta latifa ta barta "Kada kice musu tana wajena please" anty madina tace da latifa ta juya ta fice,ita kuma ta jata zuwa bedroom dinta. Shuru ne ya ratsa falon bayan fita da widad din,zuciyar ummu duka ba dadi,dukan da mahmud yayi mata saita dinga jin kamar ita aka daka,amma kuma babu wani sauran abinda za'a yiwa widad din "Inajin ruqiyya zan sanya azo gida ayi mata" ummu ta fada cikin karyewar murya,kai kawu maisara ya gyada "Eh to,ya kamata a bincika ta wannan fannin ma,saboda suna iya sakata yin hakan,kuma ba kasafai hankali yake kaiwa can din ba,sai abu ya ta'azzara sannan ba fata ake ba" Miqewa abban yayi "Ai magana ta qare,gobe in sha Allah zanzo na dauketa da kaina muje,idanma sune sayi bayani" "Da kanka yaaya,ka bari wasu cikinmu su kaita" "Gwara ayi komai a gabana sa'idu don qaniyarta" har dariya taso subucewa ummu,mahmud din badai zafi ba,duk cikin yaranta ya fisu zafi,musamman al'amarin aure,baya wasa dashi. A hankali anty madeena ta turo qofar dakin "Kinyi bacci ne widad?" Widad dake zaune qasan carfet tana duba wasu litattafai data gani a dakin anty madinan ta amsa "Ban kwanta ba maman walidi" "Au na dauka mai gidan ya koya miki baccin wuri" ta fada tana duban fuskarta "Uhmmm" kawai ta fada tana maida kallonta ga littafin,maganar da anty madinan tayi saita tuna da abbas din,yana da kirki matuqa,yana da tausayi,tanajin dadin hira dashi amma duka ya bata wannan ta sanadin abinda yayi mata. Kaya ta zuba cikin cupboard sannan ta dawo gefen widad din ta zauna tana kallonta "Ki shirya gobe inji yaaya abba(haka matan gidan suke kiran babanta),gobe da safe zaku gidan mai ruqiyyar cire aljanu" a tsorace ta kalli anty madina idanunta a waje "Aljanu kuma?" Kai ta gyada cikin nuna halin ko in kula "Eh,haka abbansu walid ya gaya min" tuni hawaye suka cika idanun widad,ta narke sosai tana kallon antyn "Don Allah anty kice kada su kaini wallahi ni ba aljanu bane dani" "To menene widad?,tundi kinqi gayawa kowa aka sani ko sune?,ai gwara aje can din,qila su zasuyi magana" yadda taga ta rude tana roqonta taji a ranta zasu samu bakin,sai ta gyara zamanta tana dubanta "Kinga daga ni sai ke,ki gayamin me yasa kika taho kinji" "Ni bana sonshi anty madina" baki anty madinan ta riqe tana kallonta cikin mamaki,lallai wani halin sai widad din,amma a yadda ta fadi maganar ta fuskanci akwai wani abu,don haka ta hadiye mamakinta tace da ita "Bakya sonshi?,to me yasa bakya sonshi?" "Dan iska ne" ta amsa mata kai tsaye hawaye na sauka a idonta. Dariya ce taso qwacewa anty madeena,to amma tanaso su qarqare qarshen zancan "Dan iska kamar yaya weedad?,me yayi miki na iskancin?" Kallon anty madeena tayi,idanunta kamar zasu fado,kunya da nauyinta takeji,amma.indai bataso a kaita wajen mai aljannu dole tayi bayani "Tattabani yakeyi" ta qarasa fada muryarta tana rawa. Zuwa wannan gabar dole dariya ta kufcewa anty madina,yayin da sautin dariyar ya sanya widad cikin rudu,ta dauka zataga ta saki salati tana tafa hannaye,kota rufeta da fada ko da duka ma akan ta bari ana tabata din,sai kawai taga tana dariya. Kusan minti biyu sannan anty madeena tayi shuru tana nazari,ba shakka kuskure nasu ne,duk yadda akayi ummu bata zaunar da widad ta gaya mata meye gundarin aure ba,suma kuma bata jin wata a cikinsu tayi hakan,duk da kusan abun ma qurarren lokaci yazo,amma duk da haka alhmdlh da aka gano bakin matsalar. A ranar dukka wata kunya anty madeena ta cire ta dinga gayawa widad komai gatso gatso,jikin widad har rawa ya dinga yi saboda mamaki,ta dinga kallon anty madeena tana mamakin haka take? "Eh kalleni da kyau,wannan abun da kika gudowa,kowa yana yi indai mata da miji ne an daura musu aure,harni kaina da kike gani" kunya ta sanyata cusa kanta a cinyoyinta ganin anty madeena din ta danganta abun da kanta,ta kasa daga kanta,sai kuma kwanyarta ta shiga mata research,me yasa mommy hafsa ta dinga jaddada mata kada ta yarda ya taba ko yatsarta yadda ummu take gaya mata sanda tana gida,meye dalili?,tambayar data rasa gano amsarta,sai kawai ta daga kai ta fuskanci anty madeena taga gwara ta tambayeta....... *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 72 "Umman walidi.....amma abinda mommy hafsat take fadamin ba gaskiya bane kenan?,naga itama babba ce kamar ku,amma bata taba gayan abinda kika gayamin yanzu ba" "Me take ce miki?" Anty madeena ta tambayi widad din tana kallonta,cikun fargabar kada ta koya mata dabi'ar banza "Ta gayamin abinda ummu ta jima tana gayamin har nabar gidan nan,tace idan ya kama hannuna Allah zai qona ni,idan na yarda ko kusa dani ya zauna sabon Allah ne,kuma Allah zai iya qonani,kuma koda wasa ya tabanin tana ganewa,har waya take tana tambayata" "Ke kuma idan ta tambayekin sai kike gaya mata?" Anty madina tayi hanzarim tambayar widad tana datsar numfashinta,kai widad din ta gyada,haushi da takaici ya saka anty madina sakin salati,sai yau ta yarda kaf gidan babu wanda yakai widad din rashin wayo,da gaske ne,ada da ake fada tana ganin ba haka bane,kawao miskilanci ne yayi mata yawa,ashe harda rashin wayon "Yaushe duka ta gaya miki hakan akan uncle din" "Kullum saita kirani,ta tambayeni dame dame nayi,dame dame yayimin" wanu malolo ya tsayawa anty madina,sai yanzu ta gane.....hafsat din tayi amfani da rashin wayon widad,da kuma tarbiyya me kyau data samu na girmama na gaba da kai da bin umarninsa ta kitsa mata wannaj baragurbin tunanin,tayi kuma sara akan gaba,suma sun manta basu fayyace mata irin rayuwar da ake nufi da rayuwar aure ba. Zama na dirshan anty madeena tayi ta fara dora mata bayani akan matsayin hafsat din a wajenta,ta fayyace mata wace kishiya fes,sannan ta rufe da cewa "Ba cewa akayi ki rainata ko kiqi yi mata biyayya ba,amma babu ruwanta da ko mene tsakaninki da uncle dinki,matsayinku daya a wajensa ke dashi,ki rufe sirrinki,karki yarda ki sake gaya mata komai dake tsakaninku". Sai kusan sha biyu na dare sannan anty madeena tabar dakin ta wuce dakin mijinta,tabar widad a zaune tanata saqa da warwara,komai ya yiwa kanta girma,tana ta jujjuya maganganun da sukayi da anty madina,tun daga farko har zuwa qarshe, yanzun itama data tafi dakin kawu abinda sukeyi kenan?,abinda ya fado.mata a rai kenan,kunya ta kamata ita kadao cikin dakin,saita cusa kanta a cikin filo tana sake hasashen abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninta da abbas din. Bayan sallar asuba anty madeena ta zayyanewa daddynsu walidi yadda sukayi da widad din,tana dariya dariya tace masa "Kaga babu sauran batun zuw wajen ruqiyya,a gayawa yaaya abba yayi haquri" kai ya jinjina yana murmushi "Na yarda widad din muguwar sakaliya ce,ku daman baku fada mata komai ba?" "Wallahi sam ban kawo haka a kaina ba,saboda naga yawanci yaran yanzun ma kafin a gaya musu sunsan komai,amma ita din shekarun nata sunyi qanana da yawa a sanda akayi auren,kuma dai dama widad din gaskiya ko cikin yaran gidan nan tana cikin 'yan ba ruwa na,gatan da qaunar dake tsakaninta da ummu ne kadai yasa ake ganin ta sangarce da yawa,amma tana da dadin zama ainun" "Shikenan,bari gari ya qara haske,zan shiga na yiwa ummu bayani,sai a shaidawa yaayan kafin yakai.ga fitowa,don nasan da abun ya kwana,da wuri zaki ganshi ya shigo" anty madeena dai tana dariya ta fice daga dakin. Tare suka shiga kitchen da anty madeena din,saidai yadda taga widad din tana hada breakfast din cikin qwarewa yasa ta tsaya tana kallonta,sosai abun ya daure mata kai ya kuma bata mamaki,widad dince da iya sarrafa abinci haka? "Me ya faru anty naga kina kallona" murmushi tayi tana sakin habarta "Hmmmm,ba dole ba,irin wannan delicious haka da ake hada mana yau,lallai aure me gyara mutum,su Aafiya suzo suyi kallo,yau widad din da ummu ke hanawa dosar kitchen yau itace da hada breakfast tsaf mai rai da motsi" dariya tayi kawai,ita kanta a yanzun shiga kitchen na daya daga cikin hobbies dinta. Kamar yadda daddynsu walid ya fada kuwa da wuri abban nata ya shigo da shirinsa,yana parlor yana breakfast ummu na ciki tana gyara dakin alhaji da ya tafi umra daddyn walid din ya gayawa abban komai. Kofin hannunsa ya ajjiye yana girgiza kai "Ashsha.....ashsha" sai yaja tsaki "Zataci qaniyarta,wanne irin shirmen banza ne wannan?,dama wannan shirmen da shashancin tazo yi mana?" "Har yanzu quruciya ke damunta yaaya,sai anyi a hankali" abban bai tanka masa ba,illa wayarsa daya ciro yayi kiran uncle muhsin. Widad kuwa batasan me akeyi ba,tana can tare da anty madeena tanta karanta mata abubuwa,da azahar saiga anty deena,kamar tayi kuka haka ta dinga yiwa widad fada "Me yasa kika taho,bance komai ya shige miki duhu ki gayamin ba?" Haduwa sukayi suka dinga wayar mata da kai,anty deena bata bar gidan ba sai bayan sallar magariba. Washegari dai taga an hau mata shirye shirye,sai da azahar anty madeena ke gaya mata gobe zasu maidata kaduna,hawaye fal a idanunta take qorafi "Tunda na tafi fa anty banzo ba ba'a jemin ba,kuma yanzu kwana hudu kawai sai ace na koma?ko alhaji ban gani ba" "Eh ai wannan zuwan da kikayi mu ba irinsa mukeso ba,ki bari kizo cikin dadin rai da yardar mijinki,babu me cewa ki koma sai idan ranki yaso" dole tana ji tana gani taja bakinta tayi shuru,sai cika kawai da take tana batsewa. Washegari samuel ya iso,tana ta kukanta kamar ranar za'a fitar da ita zuwa gidan miji,ita umma batulu,anty halima da anty madeena,anty deena ma taso zuwa,amma kuma a ranar mai gidanta zai dawo daga tafiya. *_BAYAN WATANNI HUDU_* *********A nutse motar ta cusa kai cikin gidan,bata saurara ba har sai data dangane da muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,ya dai daita tsaiwarta sosai sannan ya kasheta,ya zare key din daga jiki yana fadin "Alhamdulillah". Waiwayawa yayi gefansa,tana kwance,ta lafe sosai cikin kujerar tana baccinta hankali kwance, murmushi ya subuce masa,bai dauka da tace baccin zatayi da gaske shi din zatayi ba,a hankali ya sanya hannu ya zare littafin dake kife saman cikinta wanda ya fadi bayan bacci ya dauketa,yadan duba page din da take ya saka mata alama sannan ya rufe ya dorashi a gaban motar. Idonsa ya sake mayarwa kanta,ya zubawa baby face dinta ido,baccin da alama yayi mata dadi,ya saki murmushi,koda yaushe idan ya kalleta saiya tunata da wata wauta da quruciya data tafka,kome tayi ganinta take dai dai ne,har suyita rikici idan yace ba haka bane. Hannu ya saka yadan bubbuga seat din,a hankali ta bude idanunta,ta zubesu fes cikin nasa,ta kafeshi dasu tana dubansa,he look gorgeous,kaftan din da ya saka sun bala'in amsarsa,ta gani tun daga gida kafin su fito,harma ta yaba,a yanzun kuma sai ta sake gani ya mata fresh sosai "Yadai...." Ya fada yana dage mata girarsa cikin salon tsokana,murmushi ya subuce mata, kunyarsa ta kamata wanda a 'yan kwanakin nan haka take ji a kansa "Ba komai......"sai ta saka hannu ta bude murfin motar ta fito zuwa harabar gidan. Iska ta shaqa tana duban harabar gidan,daga tafiyarsu last two weeks harabar gidan har ta canza,akwai datti da qura sosai,ita ke sawa a gyara duk sanda sukazo din,bayan ta karba hidimar sassan hafsat data tabbatar ko a yanzun akwai aiki jingim yana jiranta,a yanzun zuwa bauchin ya fara fita mata a ka saboda wannan dan uban aikin bautar da hafsat ke hadata dashi. Waiwayawa tayi zuwa inda yake tsaye,ya fitar musu da kayansu daga booth "Shikenan?,i have done?" Ya fada yana dubanta,narke fuska tayi sannan ta marairaice masa "Uncle taimako please,ka qarasa min da luggage din mana" yadda tayi maganar a mugun shagwabe yayi masifar taba ransa,tun daga wancan ranar data dawo daga gudun hijirar da tayi,ba abinda ya sake bari ya hadasu,ko riqe hannunta,wannan yasa ta sake abinta sukaci gaba da mu'amalarsu,amma ya zuwa yanzun yadda kullum taketa canzawa da koyar abubuwa masu yawa ya sanya yaji ta fara taba zuciyarsa. Kansa ya gyada,ya kama hannun jakar zuwa sassanta tana biye dashi tana masa hira. Sai daya bude mata ya saka.mata jakar yana duban sashen nata da.har abada badai kaga datti ba saidai qura "Can you help me?" "Dame uncle?" "Idan kin gama gyara sassanki please" murmushi ta saki,ko bai qarasa ba tasan me.yake nufi,kuma tana da wannan nufin a wannan karon,saboda magana da hajjaaa tayi mata tun wancan zuwa sun tsaka da waya "Za'a yi in sha Allah uncle" "Thank you" murmushi ya subuce mata,komai.qanqantar abu idan kayi masa sai ya gode maka,tana kallonsa ya juya a hankali ya fice,yabar mata sauran qamshin turarensa data zuqa da kyau ta fesar tana sake sakin murmushi,sannan ta taka zuwa cikin falon nata tana kallon ko ina,tare da tsara yadda zata fara aikin. Sassan hafsat din ya wuce kai tsaye,yana son saur nauyin alqawarin sweet daya daukarma su mimi. Yana dosar sashen yana jin dan tashin hayaniya,sai abun ya daure masa kai,saboda iya saninsa ita din bamai sakewa mutane bace,bata da fuskar da za'a zo gidanta a zauna ana hira haka,suma mutanen kowa ya gane don haka zaiyi wuya kaga tayi baqo. Yana sake dosar sashen yana fahimtar tashin sautin maganganun ba na arziqi bane,yanayinsa yadan canza kadan da fargabar abinda yake faruwa,a haka ya isa qofar falon,ya tura ya shiga da sallama,dai dai lokacin da matar dake tsaye take cewa "Yanzu dai ki fito da shinkafa kawai,tunda ke waye yazo gidanki ma bare ya dauka" ta buda baki zata bata amsa maganar tata ta maqale a maqoshi,tana tsaye tsakar falon,fuskarta har maiqo takeyi,kayan jikinta wari da wari ne na rigar wani lace nata da har ya fara tashi tashi saboda dadewa,sai zanin atamfa,ta yane jikinta da wani tsohon mayafinta milk color "Sannu da zuwa" ta fada muryarta tana dan rawa,itama matar dake tsaye dauke da wata babbar roba blue ta miqa masa tata sannu da zuwan,duka ya hada ya amsa musu,sai ya wuce zuwa dakin hafsat din kai tsaye. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 73 A dan tsorace ta kalli matar,ganin kuma ita take kalla saita dake,don ita bata yarda ta fadi ba ako menene "Bazan bayar bafa,ladan wahalar aikin da mukayi mata,nima idan tawa haihuwar tazo duka biyun haka takeyimin" dubanta matar ta sakeyi sosai,cikin bacin rai da daga harshe tace "Haka ake taya aiki a kwashe maka abincin suna?,cooler guda saboda dan ke kafadai akayi girkin?,ku haka kukeyi?,don kun taya aiki sai kowa yace anan zaici abincin rana?" "Sai kuma kiyita yi,don Allah ki fita kiban waje,mijina ya dawo" "Au haka kika ce?,to wallahi saikin fito da abincin nan kuwa" nan sa'insa ta barke a tsakaninsu,tun sunayi iyasu har hayaniyarsu ta kaiwa abbas dake tsaye yana nazartar dakin hafsat din,yadda likkafara qazantarta taci gaba,ko ina pampers din nawwara da aka cire an kasa kirashi dust bin,ga zanin gadon dake saman gadonta a iya saninsa sanda ya siyoshi milk color ne mai kyau,amma yanzun ya tasamma zama ash color,naira dub ashirin da biyar ya siyeshi,kyansa da taushinsa ne ma ya burgeshi ya siya din,amma bazai iya tuna wani amfanarsa da yayi ba. Jin hayaniyar tana yawa ya sanya dole ya ajjiye bag din hannunsa dake dauke da sweet din,ya juya zai fita a dakin yaga me yake faruwa,sai cabal qafarsa ya taka wani abu,yaja baya da sauri tsigar jikinsa tana tashi ya duba meye a qasan, kashi ne harda fitsari,yaja tsaki yana girgiza kai,dole ya juya akalarsa zuwa vabdakinta saboda ya wanke qafar tasa. Da qyar ya samu ya hadiye yawu a bandakin,saboda urun bidirin daya gani,zarni tako ina,ga uban kashi cike cikin toilet din ba'ayi flushing ba, zuciyarsa ta fara tashi,yaji nadamae shiga bandakin,saboda qazantar bandaki tana daya daga cikin qazantar dake damunsa,baya qaunarta sam,haka ya wanke qafar ya fito yana qoqarin controlling kansa saboda sosai zuciyarsa take tashi. Dif hafsat din ta dauke wuta sanda suka hada idanu bayan ya fito,baibi ta kanta ba,ya maida dubansa ga matar "Me yake faruwa ne?" "Yallabai,shinkafar suna ce,bayan sun gama aiki ta kwasota da yawa ta taho da ita,mutane nata zuwa babu,shine na biyota nace tadan rage a samu a sallami wasu, shikenan fa......." "Okay,shikenan" ya dakatar da matar daga rattabo masa bayanin da takeyi,shi kadai yasan abinda ya tsaye masa a wuya,bacin ran ya nuna har idanunsa "Ina abincin?" Ya jefa mata tambayar murya a kausashe cike fal da bacin rai,muryarta a cushe tana ayyana irin rashin mutuncin da zata yiwa maqociyar tata tace "Yana kitchen" baice komai ba ya juya akalarsa zuwa kitchen din. Nan ma uban wanke wanke ne jibge a sink dinta,har wani tsami sukeyi,ya laluba da qyar ya gano wata warmer,ya janyo ya budeta saiga qudundunanniyar shinkafar a cuccure irin ta gidan suna tayi fuska abinta,ya daga warmer din ya juyashi,nasa ne da ake zuba masa abinci,wato tana nufin shi ta dibarwa?,shi zaici?,abincin gidan wani?,abincin da wani ya nemo a gidansa?,ba zata iya zama ta girka masa ba kenan saboda tsabar qwarewa a qyuya da kuma iya cin fuska?,ransa ya baci sosai,waye yasan tun yaushe take haka?,waye yasan irin b'arar masa da mutuncin da tayi,haka maqota suke kallonsa kenan tsirara?,ya jawo warmer din ya fito da ita. A tsaye ya samesu matar na riqe da qugu,wani bacin rai ya sake tokareshi,shinkafar da ko masu aiki cikin gidansa sunfi qarfinta yau saboda ita aka shigo masa cikin gidan ake wanna tijarar "Gashi" ya miqa.mata gaba daya,ta karba tana qoqarin juyewa ya daga mata hannu "Jeki kawai" "Flask din naku ba" "Tafi dashi" sai ta saka flask din cikin robar ta juya tana bari wajen. Ganin da gaske tafi mata zatayi da warmer dinta me tsada saita yunqura zatayi mata magana kan ta dakata ta juye ta bata abarta,wani kallo ya watsa mata wanda ya sakata dawowa da baya,ta kuma yi laqwas babu shiri "Ina yarana?" "Naga fa warmer din nan me tsada ne,sai kacw tatafi da ita?,idan kuma taje ta bata fa,kasan gidan suna" ta shigar masa da qorafinta a maimakon amsa masa tambayarsa "Ina yarana nace?" Ya sake tambayarta wannan karon a kaurare "Suna......a gidan sunan sukace na barsu" "Kika barwa wa su?" Saita dan sosa kai "Mai aikin gidan maman husna,tace zata kawosu idan......" "Idan sun gama cin abincin gidan sunan suma?,saboda yunwacw fal a gidan ubansu?,maza maza kirata a dawomin da yara na,na baki minti biyar" yayi maganar yana murza yatsunsa,sannan ya juya yayi gaba yana barin mata sassan. Da harara ta bishi,ai kuma shikenan ya dawo babu zaman lafiya ba sakewa,dole ya suri wayarta ta laluba number talatu tace ta dawo dasu abbansu ya dawo,tace tahe bayan layinsu da yaran amma gata nan "Kiyi sauri don Allah" "To" ta amsa mata,saita cire wayar daga kunnenta tana jan tsaki sannan ta wuce dakinta. Sai data taka kashin daya taka ta tuna ma yadda dakin nata yake,ta dauki salati,tasan ya gani,kwata kwata ta manta a haka tabar dakin,harta fara gyarawa ta tuna qila da widad sukazo,sai ta yanke tayi kiranta "Tazo ta kama aikinta,nima na samu na tsugunna na huta" daga haka ta figi mayafinta ta nufi sashen widad din. Ta gama kintsa ko ina,sai fidda qamshi yakeyi,tsumman towel ne a hannunta tana goge nayan kallo da sauran glasses da abubuwan da suke. Daukan qura a falon,hafsat din ta turo qofar da dan qarfi,dama.ba kasafai ta fiya sallama ba har sai ta shigo falon, saboda tsabar zargi da ranta ke raya mata ko zata kama abbas a wajen(kamar wani kwarto ba matarsa ba). Kamshin data shaqa ya riqe maya maqoshi da irin kishi ta gaza sallamar,widad ta daga kai tana dubanta,karon farko da taji ranta ya baci na yadda ta shigo mata ba sallama,ta riga ta saba,duk yawansu a gidansu,duk kuma yadda suke da ummu bata isa ta shiga waje kai tsaye ba sallama ba. A yau itama saita riqe gaisuwarta,tana kallon yadda hafsat din kebin sassan da kallo kafin ta sauke dubanta ga widad,hatta sassan ya sauya mata,bare widad din dake qara wani irin girma da haske "Sannu isassa, shigowar da kike nasan kinzo yau ban isa ba kenan,shine kikazo nan kika kama.naki aikin ni kin barni da tulin aiki,to ki gayamin waye zaiyi miki aikin?" Maganar ta dan baiwa widad din haushi,sai kace ita ta hada mata dattin ko tace ta dinga barinsa,ci gaba tayi da goge gogenta sannan tace "Gani nan zuwa" tsaki hafsat din taja,ganin yadda taketa qalqale komai na wajen,ta danyi jim sai kuma ta juya ta fita,ta tsani ta shigo sassanta taga tana wannan qaqale qaqalen "Wannan dole na sake matsa miki lamba tare da sanya idanu sosai a kanki,idan ba haka ba fin qarfina gaba zakiyi" ta raya haka a ranta. Haka kawai yau saita samu kanta da jujjuya abinda mommy hafsat din tayi mata a rai,sai taji bataji dadin abinda tayi mata ba,amma sai ta danganta hakan da rashin sallamar da batayi mata bane yafi bata ranta. Koda ta gama saita wuce bedroom dinta,ta canza kayan jikinta zuwa wata smocked gown me skinny straight skert da yasha tsaga ta baya,ta daure sumarta mai tsaho da santsi cikin dankwalin kayan. Sassan abbas ta wuce,don bata manta ba sunyi dashi zata gyara masa,zuwa yanzun kuma tasan umarninsa da aikinsa sama yake dana hafsat din,kamar yadda ta taba yiwa anty madeena tambaya,ba kamar a baya ba,da takejin umarnin mummun hafsat din sama yake dana abbas dama kowa dake cikin rayuwarta. Sanda ta shiga yana zaune saman kujerar parlor yana amsa waya,ya kasa dauke idanunsa daga kanta,saboda taja hankalinsa sosai,ta sakar masa murmushi ganin waya yakeyi,ta kuma masa nuni da hannunta kamar maganar kurame akan ta ina zata fara?. Idonsa ya lumshe sannan ya budesu a kanta,ya mata nuni da falon,he wants to keep his eyes on her,saita tako zuwa ciki a hankali ta soma kintsa wajen. Duk inda ta motsa idanuwansa suka biye da ita,kamar yadda duk sanda ta gifta saita bar masa qamshinta,wani irin yanayi ya dinga sauka a jikinsa,da qyar ya samu ya kammala wayar,sai ya ajjiyeta daga gefansa yayi folding hannayensa a qirjinsa yana kallonta sanda mopping parlor din da mopping mist dinta data taho dashi,lallausan qamshin daya saba ji a sassanta ya fara game nasa falon,yana sin qamshi yana son qamshi har baisan iyaka ba,tsafta na daya daga cikin abubuwan dake bashi nutsuwa a rayuwarsa,sai ya samu kansa da miqewa a hankali,ya isa gareta,ya kama mop stick din ya riqe,hakan ya sanya hannayensu gamuwa waje daya,ta daga manyan fararen idanuwnata suka sarqe da nashi waje daya. Har cikin jikinta taji wani abu ya tsarga mata,sai ta sakar masa sandan taja da baya tana murmushi "So kake ka tsoratani?,banji tahowarka ba Allah" tayi maganar tana yarfe hannunta kamar wadda ta riqe wani abu me zafi "So nake na samu ladan sunnan taya matata aiki" kalmar tasa ta bata kunya,saita sunne kai cikin dankwalinta,ya daga kai yana murmushi,yana son yaha reaction na fuskarta da yadda ta karba maganar. Tana biye dashi yana mopping din,kuma shine yace ta dinga binsa din,wajen da bai gogu ba ta gaya masa,yayi hakanne kawai saboda nutsuwar da zuciyarsa ke samu kasancewarta a kusa dashi. Tare suka gama aikin,har cikin bedroom da toilet dinsa,ta kwashe zanin gadon kai ta sauya masa da wani bayan ta turarashi a kabbasa,ta maida komai muhallinsa,sai ya dinga jin zuciyarsa wasai,gyaran yayi masa fiye da yadda ma yake so. "Ga tukuici" ya fada yana miqa mata wani siririn agogon silver da aka masa ado da dan wani dige digen gold a jiki,yana da tsada sosai,hafsat ya taba siyawa gift dinsa,amma har yau ya kasa bata,saboda ta kasa bada kyakkyawan yanayin da zai gabatar mata da kyautarsa,duk sanda yazo da niyyar bata sai wani bacin rai ya gifta da zai sashi ma mantawa da hakan. Ido ta fidda sanda ta ciro agogon,yayi masifar burgeta "Uncle.....duka nawa ne?" Ta fada da wani irin accent dake nuni da zallar quruciya,kai ya jinjina yana murmushi "Yes,kin manta abincin da kikayimin last three days?,dama nace miki akwai gift,na hada miki harda na ranan" dan tsalle tayi,ta isa gabanshi ta riqeshi tana cewa "Thank you uncle,na gode sosai" ajiyar zuciya ya saki saboda riqon data yi masan yasan yanzun zai bada reaction a jikinsa "Is okay" yana kallonta tana ficewa a sassan riqe da agogon,fara'ar fuskarta ta gaza daukewa. Da baya ya koma ya zauna saman gadon,tana ci gaba da haifar da wani yanayi mai girma da nauyi a zuciyarsa,how can he continue looking at her a mazaunin matarsa?. Sai data koma sassanta ta ajiye agogon sanann ta wuce part din hafsat,tana hanya tana tunanin inasu mimin da bataji motsinsu cikin gidan ba. Dai dai lokacin da hafsat ta cika ta batse rashin zuwan widad din,zuciyarta ta fara mata saqe saqe,lallai tayi sake,har ankai matsayin da zata taka ta kirata ammaa ta bata kusan awa guda batazo ta fara mata aikin data sakata ba?,anya kuwa bai aikata wani abu da yarinyar ba wanda ya sanya ta fara rainata ko qoqarin yi mata gani gani?,baiko daidaita matsayinsu ba a shimfida?,amma tana tantamar hakan,tasan abbas tasan lalurarsa tass.....ko dai itace ta fara sanyi da saken daya fara kawo wannan canjin daga yarinyar?. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: huguma* Page 74 Tana zaune saman kujerar dake fuskarta qofa yana kada qafartaranta cunkushe da tunani kala daban daban,warmer dinta da abbas ya bayar yafi komai bata mata rai a yanzun,don bata dauki widad din a wata matsala da zata kasa saitata ba,wannan kuma sai yazo ya hadu da rashin shigowar widad din ya qara tunzurata. Widad din nayin sallama ta watsa mata wani irin kallo mai hade da harara "Sai yanzu kikaga damar zuwa?" Ido widad din ta dauke yana qarasowa cikin falon "Gefen uncle na fara gyarawa tukunna" miqewa zumbur tayi,har batasan ashar ta subuce mata ba "Kina nufin dakinsa kika shiga kika gyara?,waye ya baki wannan izinin?" Kallonta take danyi da mamaki,sai kuma ta janye idanunta,saboda bata saba kallon babba haka kai tsaye idan yana mata fada ba "Shi yace nazo na gyara" maganar ta sake tunzurata,ba bata lokaci ta nufi qofa ranta na suya,wannan wanne irin zubda mata da mutunci yayi shirin yi?,me ya hanashi kiranta ita tazo ta gyara masan,kawai sai ya kama ya kira yarinya taga makwancinsu?. Har takai qofa kuma ta dakata,saboda tunawa da tayi ita din me laifi ce,sai tayi qwafa ta dawo ta zauna,koma meye akan widad din yau zata saukeshi "Me kika tsaya kina kalla da baki wuce kin kama aikinki ba?,ki fara da kitchen idan kin gama ki wanke bandakina,akwai kayan nawwara data bata a toilet dina,saura kiyimin ha'inci" idonta ta bude a hankali daga rufesun datayi tun sanda tayi mata tsawar farko,bata ce mata komai ba ta doshi kitchen,tana jin wani abu me kama da bacin ran da bata taba ji ba yana son fara tana zuciyarta,me tayi mata da zata dinga binta da irin wannan tsawar?. Tana ta cika tana batsewa ita daya a falon tayi baquwa,baquwar kaman customer a wajenta,tana siyan pieces na laces da hafsat din ke kawowa daga Lagos tana siyarwa,dadewarsu tare ya haifar da qawance a tsakaninsu,ta jima batazo gidan hafsat din ba,saboda dama ba kowa bane yakejin dadin ziyartar gidanta ba,saidai idan cikinka a cike yake da abinci,hakanan baka da qishirwa. Already ta gaya mata idan ta shigo bauchin zata qaraso taga wasu lace,tasan kudi zata samu a jikinta,wannan yasa ta karbeta da fara'arta,ta kuma ajjiye duk wani bacin rai dake damunta. Suna tsaka da gaisawa talatu ta dawo dasu mimi ta koma "Ma sha Allah,mimi ta fara girma" baquwar me suna hajiya habiba ta fada "Wallahi,aikin kwana biyu baki shigo ba,saidai aike" "Bari kawai,abubuwa ne suka cushemin" daidai lokacin da mimi ta matso kusa da hafsat din tana gaya mata zatayi toilet "Sarakan saka mutane aiki,baiwar taku ai ta dawo" sai ta sanya baki ta qwala kiran sunan widad din har sau uku. A lokacin tayi nisa cikin tunanin dabi'un hafsat din,me yake damunta da take tara wanke wanke haka ba zata iya kintsawa ba?,ko ina na gidanta bashi da dadin shaqar qamshi har sai sanda tazo?,muguntar zatayi mata ne?,ko haka dabi'arta take?,itadai tunda ta taso a rayuwarta bata tana ganin kalar qazanta irin wannan ba. Yadda take kiran sunan nata ya fargar da ita,ta ajjiye plate din hannunta da sauri,garin saurin wuqar dake ajiye a wajen tadan yanketa a dan yatsa,ta runtse ido tana jin zafin yankan yana ratsata,ta yarfe hannun tana bude idon nata sanda muryar hafsat ta sake iskarta cikin wani amo na gigitar kira. Dukkansu su biyun suka zuba mata idanu,hafsat din ta jifanta da wata muguwar harara,yayin da hajiya habiba ke mamakin ganin widad a gidan,tunda bata santa ba "Me kikeyi kina jina ina kiranki?" Ta fada cikin nuna isa taqama da gadara,tanaso ta yarfata sosai gaban hajiya habiba "Banji ba sai daga baya" "Kin fara canza hali ko?,indai kuwa hakane zakisha mamakina,zaki kuma sha wahala ne kawai,ki dauki mimi ki dorata a poo tayi toilet,kafin sannan ki kawowa baquwa ruwa" batace mata komai ba sai kama hannun mimin da tayi,tuni dama yarinyar ta iso wajenta tana mata sannu da zuwa,ita kanta yarinyar cikin walwala take,saboda me basu kulawar da mahaifiyar data haifesu ma bata iya basu ta dawo,surutan mimi ya rage bacin ran da a yau taji tana jinsa har cikin zuciyarta. Sai data dorata a poo din sannan ta shirya ruwan da lemo a tray ta dora cup a kai ta fito Parlor din. Sai da widad ta bace hajiya habiba ta dauke kallonta daga kanta sukaci gaba da cinikinsu,amma kuma maganar dake ranta tana ta cinta,har ta kasa Shuru "Wai nace ba.....me aiki kikayi ne?" Ta jefawa hafsa tambayar,dai dai sanda widad ke fitowa dauke da tray din. Duban widad din hafsat tayi,bata kuma tashi bada amsar ba sai data iso tsakiyarsu tana ajjiye tray din "Tayi kama dame aiki ko?" Ta fada a wulaqance tana tabe baki,amsar hajiya habiba shine ko daya babu kama da 'yar aiki a tare da ita,amma data fuskanci akwai magana a bakin hafsat din sai bata amsa mata ba,har zuwa sanda tace "Wai nan haka kishiyace aka yimin" "Kishiya?!" Ta amsa da amo mai qarfi tana sake bin widad data juya zuwa kitchen da kallo "Wallahi hajiya" "Kan ubancan....ah banga laifinki ba,amma ke kuma kina meye har aka miki kishiya?" Wannan shine iya abinda widad din ta iya ji. Ko data koma dakin hafsat din,tsaye tayi a gaban mudubi kalmar 'yar aiki tana dukan ranta,meye tayi da tayi kama da 'yar aiki?,tasan meye 'yar aiki,amma har yanzu bata fuskanci ainihin ma'anar kishiya ba,a cikinsu wanne yafi zafi?,ta samu kanta da tambayar kanta da kanta,kunnuwanta na iya jiye mata yadda hajiya habiba ta maimaita kalmar kishiya da wani irin nauyi da girma,me yasa kalmar kawai tayi girma haka?. Kallon hafsat hajiya habiba taci gaba dayi tana sauraren bayanin da take mata,da irin qoqarin da tayi take bautar da widad din "Kinyi qoqari qwarai,amma kuma ina jiye miki ranar da maigidan zai fuskanci bautar da ita kikeyi,ina mai tabbatar miki yana son kayarsa,saidai wala'alla yana ganin tayi qanqanta ne kawai shi yasa.mautara bata fito fili a kanta ba,ke.....baya ga haka ma mijinki me kamewa ne,idan wani ne ko jaririya ce yadda take da wannan mugun kyau wallahi tuni aikin gama ya gama,waima kina kallon fuskar yarinyar nan da kyau kuwa?"tayi tambayar tana kama haba,idanunta akan fuskar hafsat data bawa hajiya habiba dukka hankalinta "Girma ya fara zuwa mata fa,duk da dai ban santa a sanda aka kawota ba,kuma ke kin sani,ko makaho idan ya shafa ki ya shafata yasan ta fiku kyua nesa ba kusa ba,ta fiki diri,ke koni bazan yarda mijina ya dinga kallon wannan surar ba wallahi tallahi....." "Yanzu me kikeso kice?" Hafsat ta katseta daga yadda take kuranta kyan widad,saboda a yanzun a duniya babu abinda ta tsana irin taji an fada ko an yabi kyanta,ko tunawa ta fita kyau bataso tayi tsakanin ita da zuciyarta bare har a furta mata "Yauwa,idan kana da kyau ka qara da wanka,kudi zaki saka ki shiga malamai su sake kauda idonsa da zuciyarsa daga kanta,sannan a sake kama miki ita sai abinda kika ce" shuru hafsat tayi tana nazari,nan fa daya,an kuma zo wajen,ita indai zancan ta fidda kudi ne to babu ita a wajen,sannan ma kuma me take da buqata wai,komai da anty ummee ke tsara mata yana tafiya yadda ya kamata,ko canzawar da widad din ta fara yi hakan baya rasa nasaba da raga matan da takeyi kwana biyu qila shi yasa ta fara sakewa,kuma ko yadda anty umnee ke gudanar da gidanta ya isheta ishara,babu boka ba malam,amma ko meye ta fada ya zauna,kowa juyashi take a cikin gidan ta ruwan sanyi. "Gaskiya banajin a yanzu ina da buqatar wani malamin tsubbu hajiya,saidai ban sani ba ko nan gaba bana ma fata" jinjina kai kawai hahiya habiba tayi,tana ganin ta gaya mata iya abinda zata gaya mata,sauran dabara ta rage game shiga rijiya "Yanzun nawa ne balance dina a hannunki?" Hafsat din ta dawo dasu kan maganar kudi,abinda tafi qauna kenan. Gaba daya ta dinga jin sassan kamar a kanta yake,sai taji batason qara koda minti biyar a cikinsa,akwai tambayoyin da take da buqatar amsoshinsu,saboda haka sauri sauri ta gama mata duk abinda zatayin ta fito,sai mimi ta maqale zata bita,dama neman kai hafsat din take dasu tace su bita,amma sai nawwara taqi bin nata "Sai kiyita zama ai"ta fadi tana jifan yarinyar da harara,so take tadan samu ta dafa ma abbas wani abun,kafin yazo yahau kanta da qorafi. Ruwa me zafi ta hada tayi wanka,ta yiwa mimi ma,take walwalar yarinyar ta qaru,don har gashin kanta ta wanke mata. Cikin abaya ta shirya kamar yadda take zabinta,zataso shiga kitchen ta dafama yarinyar wani abu,to amma a gajiye take jinta,sai ta fidda snacks din da tayi ta zubo a jaka,ta zuba mata ta hada mata da lemo,sai gashi tana ci hannu baka hannu qwarya,don yafi mata indomie din da ta zame musu 'yar kullum safe rana dare,sai randa Allah ya cishesu suka fita unguwa ko taso ta dafa wani abun. Snacks kuwa irin haka ba samunsa sukeyi ba,muddin ba daddyn nasu bane yazo bauchin ya fita dasu wasu gureren ba. Tana saman kujera a zaune tana sauraren hirar da mimi ke mata,gaba daya kuzarin jikinta babushi,sunayen da hajiya habiba ta kirata dasu su suketa mata yawo akai "Kishiya/'yar aiki",so take yamma ta qarayi ta kira anty deena ko anty madeena ko hajjaa tayi musu tambaya. Tare da sallama ya tura qofar falon nata ya shigo,ya canza shiga zuwa wasu qananun kaya da sukayi masifar karbarsa,suka kuma fidda zatinsa sosai. Idanunsa a kanta sanda mimi ta kamo hannunsa tana cewa "Daddy zo muci,anty ce ta bani,yayi dadi sosai daddy,kace mommy ta dinga yi mana irinsa" biyewa yarinyar yayi,yaje ya tsugunna gaban plate din ya dauka ya gutsura yana yaba dadinsa,wasa wasa sai gashi yana ta ci,ya daga kai ya kalli widad dake zaune gefe tana kallonsu "Ya akayi?,yau babu sakalcinne?" Ya tambayeta da sigar tsokana, murmushi ya kubce mata,itadai batasan me yasa yake mata kallon quruciya sosai da sosai ba,itakam tana gani zuwa yanzun ma ai ta isa mace "Ga wayarki da kika manta" ya.miqa mata wayar yana kallonta,hannu biyu tasa ta karba,tama manta da ita "Adan qara mana snacks din mana baby doll" sunan da ya fara kiranta dashi kenan,tun last week da akayi wani taro na matan police,rose ta kawo me kwalliya har gida tayi mata,ya dinga tsokanarta wai ta zama kamar 'yar tsana,da wayo da wayo ma ya hanata zuwa taron,yace tayi kyau da yawa,bazai barta taje ba,data saka masa kukan shagwabarta sai yace "Wa yace kiyi kyau haka?,bazan iya barinki ba kije,but i promised you zan fita dake anjima kiga gari" da wannan ya fanshi kansa. Koda ta zuba musu snack din ta dawo zama tayi shuru,baice mata komai ba amma yaci gaba da karantar ta cikin qwarewa ta gefan idanu,ya fahimci kamar damuwa ce da ita,sannan tana yawan taba yatsarta "Me ya samu hannun?" Ya tambayeta a tausashe bayan ya miqe yana kallonta,kai ta girgiza da sauri "Ba komai" ta amsa masa tana dunqule hannun nata,baice komai,ya taka a hankali ya isa gabanta,ya kama yatsan yana dubawa,yanka ne,ga wajen yayi ja abinka da farar fata,sai ya daga kai ya kalleta "A ina kikaji wannan?" Shuru ta danyi sannan a hankali tace "Kitchen" "Me ya kaiki kitchen daga dawowarki?" Rasa amsar da zata bashi tayi,saita zabi tayi shuru "But na shigo sau biyu ban sameki ba kina wajen maman mimi" "Eh na dan shiga ne" shuru yayi yana tattara maganganunta guri guda,ya fahimci tana yawan zama a wajen hafsat din,to amma a idanunsa na zahiri baiga wani hali ko wani abu da take mata da zai sanya ya hana ko ya tuhumi zuwanta ba,sannan yafi ta'allaqa zuwan nata can akan su mimi,yasan halinta sarai nason yara,saidai sauyawar yanayin nata a yau yasa yaji bai gamsu da yadda ya ganta ba "Zanje na dawo indai da qarfe kika yanke sai an miki anti tetanus" narai narai tayi da.idanunta jin batun allura,yayi murmushin gefan baki,idan ya biyewa wannan sakalcin nata tabbas yasan ba za'a yi ba. Har yakai qofa ya waiwayo yana kallonta,idanunsa qasa qasa,kasa jurewa kallonsa tayi tadan kauda kallonta gefe "Ko zaki rakani,gidan suraj zanje na dubashi" kai.ta girgiza alamun a'ah,yau din tana jin gajiya sosai a jikinta,bugu da qari ma kuma tana son yin waya. Kai ya mirgina hagu da dama sannan yace "Alright,take care" yayi maganar yana aza mata nauyin kallon nan nasa,saita jinjina masa kai,ya juya ya fita. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 75 Kamar yadda ya saba ko yaushe bayan sallar asuba yana shigowa ya tabbatar da lafiyarta yauma haka "Gidan hajiya nakeso naje yau" ta fadi masa bayan sun gama gaisawa "Ba damuwa,jiya ban samu zuwa ba,ki shirya na fita dake idan zan fita anjima kadan" saita gyada kai,tana maida idanuwanta ta lumshesu,kwata kwata daga jiya zuwa yau batason zaman gidan. Karfe goma na safe ta gama komai a bangarenta,ta gyarashi ta hada breakfast dan dai dai cikinta,ta kuma shirya cikin atamfa dinkin doguwar riga,tana zaune a falonta tana buga game a wayarta tana jiran fitowar abbas,hatta mayafinta yana gefe. A nutse ya tura qofar falon,yana sanye da shadda butter color da aka tsarama wani lafiyayyen dinki me aji,a kanta idanunsa suka fara sauka,sai yayi tsaye riqe da handle din qofar yana kallonta idanuwansa suna lumshewa,tayi masa kyau har baisan iya yadda zai musalta ba,atamfar ta karbeta ainun,har ya gaza gane doguwar riga da kuma atamfa wanne ne yafi mata kyau,ya dan rufe idonsa yana shafar qirjinsa da hannunsa,yana jin tana sake saka kai sosai cikin zuciyarsa tana samun kyakkyawan mazauni,illa take masa a kowacce rana,kullum yaqi yake da zuciyarsa,yana ganin kamar ya fiya zaqewa da yawa,yanason canzata,yana son sake kawo kusancin da yafi wannan a tsakaninsu,baisan ta yadda komai zai zo ya kuma kasance ba. Batasan da tsaiwarsa ba,saboda hankalinta yayi gaba a game din da takeyi,sai da qamshinsa ya fara kawowa hancinta ziyara,ta daga manyan idanuwanta a hankali,idanuwansu suka sarqe waje guda,siririn murmushi ya subuce mata,ta shagwabe fuska "Ka tsoratani uncle" ta fada tana tura baki gaba,yabi dan qaramin bakinta da kallo,wanda yau yasha jambaki pink,hakan ya qarawa lips dinta color akan ainihin color dinsa. Hannu ya saka ya yafitota yana jin jikinsa na mutuwa,ta miqe a hankali tana dubansa tare da takowa inda yake "Uncleee.......na gama fa na dauko.mayafina?" Kasa amsa mata yayi har ta iso gabansa,yasa hannu a tausashe ya kamo qugunta janyota gabansa,suka zama very close sosai a tsakaninsu. A tare suka lumshe idanu sannan suka bude,suka zubawa juna idanu kamar shiri,kowa da abinda jiki da zuciyarsa ke gaya masa,ya motsa labbansa da salon miskilancin nan nasa "Kinyi kyau baby doll" murmushi ya kubce mata tana kallon manyan idanunsa da suka qara masa kyau a idanunta,kafin tace komai sautin muryar hafsat ta tunkarosu,da alama sassan take nufowa,tana ta hayagaga da mimi da nawwara,sai ka dauka wasu manyan 'yammata ne. Hannunta ta sanya da sauri ta zare hannayensa daga qugunta taja da baya,idamunsa a lumshe yana jinta,sai data matsa ta tsaya daga can baya sannan ya bude idon nasa fes a kanta yana kallonta "Meye hakan?" "Mommy" ta fada a tana yin narai narai da ido, kafin ya bata amsa hafsat din ta iso cikin saurinta kamar me shirin tashi sama,amma ganinsa a tsaye daga bakin qofa goye da hannayensa yana kallon ciki ya sauke mata duk wani fada da cin mutunci da tazo yiwa widad din nayin rana batazo tayi shara ba balle wanke wanke. Ta gefansa ta raba ta shiga ciki,da widad din ta fara cin karo,wanda ke tsaye rataye da qaramar jaka a kafadarta tana qoqarin yane kanta da kyakkyawan mayafin daya dace da kayan jikinta. Zuciyarta ce ta tsinke da irin kyan da yarinyar tayi,zuciyartata ta fara rawa,ta kuma fara ayyana mata tsaiwar da yayi widad din yake kallo,saita tsaya cak,ta fara raba kallonta tsakanin fuskokinsu su biyun,gabanta yana luguden faduwa. Fes yake kallon widad din kansa tsaye ba tare daya nuna kara ko alkunyar wanzuwarta a wajen ba,abinda ya sake dimautata kenan,bakinta har rawa yakeyi sanda jefa musu tambaya kamar wasu 'ya'yan cikinta "Ina kuma zaku da safen nan.....naga har kun shirya" maganar ta ta tuna masa inda zasu,ya sauke hannayensa dake goye a qirjinsa yana daukar mimi da tafi kusa dashi ya juya zuwa waje yana cewa "Ki sameni a mota,rana tana yi" da kallo hafsat din ta bishi har ya fice,saita dawo da dubanta ga widad,kamae zatayi kuka saboda wani malolon kishi daya riqe mata wuya "Izinin wa kika nema da zaki shirya fita unguwa?kin fara rainani fa widad,ki shiga hankalinki" karon farko da taji maganar banbarakwai,tunda dai ita ce mata akayi ta tambayi abbas ne a duk sanda zata fita bawai hafsat ba,to amma tana jin shakkarta ba zata iya tsaiwa mata bayani ba,don batason fada ita sam a rayuwarta. Hon din motarsa ya hana kowa a cikinsu magana,da wannan yake maka sign idan yana jiranka,duk da haka sai hafsat din ta kalli widad a gaggauce "Ina zakuje?" "Gidan hajiya" "Shine kika saka wadan nan kayan?,bana gaya miki ki dinga killace kanki ba karki bari ya dinga ganin tsiraicinki?" Ta fafa gajiya da soki burutsun hafsat,ita kawai so take taga ta fita a gidan "Aiba haram bane,tunda miji da mata ne ni dashi" ta amsa mata ba tare da kawo komai a zuciyarta ba,tunda dai tasan da wannan salon anty madeena tayi mata bayani. Mummunar faduwar gaba ta saukar mata,yaushe yarinyar ta fara fahimtar kalmar MIJI da MATA?,lallai akwai qura,liqi yana shirin balle mata kenan,kasa ce mata komai tayi,saita juya kawai ya fita,widad din ta bita da kallo,akwai abubuwa da yawa.na mommy hafsat din dake bata mamaki,takowa tayi ta kulle sassan nata ta wuce zuwa motar tasa. Ranar wuni tayi ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga qarshe ta dauka waya ta kira anty ummee don ta labarta mata,kiran duniya wayar taqi tafiya,sai taji tana ds buqatar fita taje gidanta zaifi mata sauqi,wannan ya sanya ta yita kiran abbas ta gaya masa zata fita amma bai dauka ba,ashe yabar wayar cikin mota. Ta kuwa cika tayi fam,zuciya ta dinga raya mata suna can suna holewarsa da yarinyar,lallai biri yayi kama da mutum,ba banza ba yarinyar ke iya kallon qwayar idanuwanta ba ta maida mata magana haka gatsal. Ji tayi kamar ta rataya mayafi ta fice abinta,to amma tana shakkarsa,tasan ko zai dauki komai banda wannan,bazai lamunta ba,haka tana ji tana gani ta haqura da fitar,taci gaba da kiransa amma saita daina shiga ma daga qarshe. Basu dawo ba sai dare,suna isowa kuma fa shige sassanta ta kulle abinta,abbas din ya bita da kallo, quruciya har yanzu taba dawainiya da ita ba ruwanta da zancan yau kwananta nw,baya mantawa akwai ranar da a gaban hafsat din ya zolayeta akan a sassansa zata kwana,kamar zata hadiyi zuciya haka hafsat taji amma ta dake tana tuna wasu daga cikin karatuttukan anty ummee,ta dake tana tayashi tsokanartata akan anan zata kwana, qarshe sulalewa tayi ya gudu abinta. °°°°°°°Tun daga wannan ranar ya zamana fiye da rabin weekend dinta agidan hajiya takeyi,wani lokacin tun a hanya taje cewa ya wuce da ita,sai ya wuce gida bayan ya ajjiyeta,baya musu, saboda hakan shi kansa yana faranta masa rai,saboda yadda take nunawa hajiyan qauna da kulawa,ita kanta hajiyan hakan yana mata dadi,don duk sanda widad din tazo saita gaji da kala kalar girki,saiya zamana shi kansa zaiyiwu wuya baka sameshi a gidan ba,a nan zaici abincin rana har na dare,kai wani binma da safe yake fitowa da jallabiya yazo yaci breakfast ya koma hafsat din na bacci,idan taga bai nema abinci ba saita share taci gaba da sabgarta tana ganin sauqi ta samu. Abu daya ke qonawa hafsan rai,yadda widad din ke guduwa tana barinta da tulin ayyukanta,tuni ungulu ta koma gidanta na gargajiya,qazanta sai wadda ta qaru,saboda gyaran weekend din data qwallafa rai akansa yanzu ba samuwa yake ba,idan widad ta shigo gidan sai daren da ana ya gobe zasu koma kaduna. *_MAFARI RAYUWA DA SOYAYYA_* Tun daga daren jiya daya daukota daga katsina gidan mahaifiyarta,har kawo yanzun da yake shigowa gidan jikinsa gaba daya baya jin dadinsa. Ya jima a parking space bayan dawowarsa daga aiki,yana zaune cikin mota,shi bai shiga ba shi bai fita a motar ba,daga nan inda yake yana iya jiyo daddadan qamshin turaren wutarta daya zama tambarinta,qamshin da duk sanda zasu bar kaduna zuwa bauchi yake kewarsa,haqurinsa ya fara gazawa,yana dab da hanata weekend gidan hajiyan,tunda ko ba komai idan tana gida,iya qamshinta kawai na saukar masa da nutsuwa. Cikin tattara qwarin gwiwar sa ya buda murfin motar ya fito,dai dai sanda ake qwala kiran sallar magariba a garin kadunan,sanye yake da uniform dinsa masu matuqar daraja da kuma qara masa kwarjini,yana iya hangen mai gadin gidan amma ya ratse yayi kaman bai ganshi ba,saboda yana jin kamae qafafuwansa ba zasu daukeshi ba. Da sallam ya shiga parlor din,dai dai sanda take fitowa daga kitchen dauke da wani tray data jera lemon zobo da abarba data koya ta gwada,ya kuma bata ma'ana sosai har fiye da yadda ta zata. Murmushi ne shimfide saman fuskartata,batasan dalilin da ya sanya kwata kwata batajin dadin gidan ba har sai sanda ya dawo,yayin da abbas din ya zube mata.manyan idanunsa yana kallonta,qafafunsa.na sakeyin laushi kamar bazasu iya daukarsa ba. Sanye take da wata baqa wul din gown wadda kwata kwata tsahonta iyakarsa qasan gwiwarta,hannunta gajere ne don kana iya hangen hammatarta da kuma tundun qirjinta da cikar da suka fara yasa suke bayyana kansu. Kanta babu komai sai lallausar sumarta baqa sidik mai laushi data yiwa kalba guda daya tak a kan nata,jelar ta sauka gadon bayanta taba reto,zata tsammaci relaxer ta sakawa kan nata. Tray din ta ajjiye,saita fara takowa gabansa tana juyawa gaba da baya "Uncle kalla ka gani,nayi kyau?,don Allah kwalliyata ba tayi kyau ba?" Ta fada bilhaqqi har cikin ranta tanason yace tayi kyau din,saboda ire iren kaya ne da mamarta mahaifiya ta hada mata su masu yawa da kyan gaske bayan ziyartarta da tayi,tsaraba tayi mata mara iyaka,don bata samu halartar bikinta ba,hasalima sai ana gobe daurin auren widad din ta sani,wannan yasa tayi fushi kwata kwata ta koma gefe,saidai zuwantan yasa tayi mata kyakkyawar tarba,ta kuma hada mata nau'in dukka wani kaya da tasan uwa zata yiwa diyarta,ta hada da nasiha mai kama da hannunka mai sanda "Kar na sake jin sirrinku ya fito keda mijinki,idan ba haka ba zamu bata dake,kome ya umarceki kiyi kiyishi indai kinaso muci gaba da shiri" a duniya idan akwai abinda ta tsana wani yace sun b'ata,waninma mahaifiyarta da take mata wata irin qauna take jinta har ranta. Bai ankara ba har ta iso gabansa,juyi daya tak tayi ta fada jikinsa,sai ta riqeshi tana dariya dariya "Uncle.....ba kace wannan rigar ba zata yimin kyau ba?,shi yasa itama na gwada maka ka gani.....bakace komai ba" ta furta tana tsareshi da ido. Tuni maqoshinsa ya bushe,ya tattaro yawu ya hadiye yana dan ja da baya "You look so good baby doll" dan tsalle ta saki a jikinsa tana cewa "Thank you uncle" cikin dabara yadan ja baya yana zare jikinsa saboda yadda yaji jikinsa ya fara dauka gaba daya,saita sake matsowa ba tare data lura da yanayin da gake ciki ba tana karbar jakar hannunsa "Sannu da zuwa,na manta" ta fadi tana dariya sannan tayi gaba tana cewa "Yau wani kalan abinci nayi maka,mommmy ce ta koyamin,tace irin abincinmu ne idan mun dawo nayi maka" duk maganar da takeyi yana tsaye cak yana kallon yadda qugunta yake juyawa ta cikin rigar,kusan rabin bayan rigar an debeshi,farar fata cikin baqar riga......abun ba qaramin qaawa yake bayarwa ba. Kasa riqe kansa yayi,har jikinsa yake jin bazai iya jurewa ba,saiya ja baya a hankali ya fice daga falon salin alin,sai waiwayowa tayi taga wayam,mamaki ya cikata,tahau kiran sunansa tana leqawa dakinsa,har nata dakin zuwa kitchen bashi anan,saita koma saman kujera ta zauna tana hawaye,me yasa zaiyi mata haka?,ta gama wahalar shirya masa abincin kuma kawai saiya fita bai gaya mata ba?. Tana qananun hawayenta ta miqe ta shiga daki itama ta daura alwalar sallar magariba ta tada sallar,tana sallar tana goge qwalla. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 76 Tunda akayi sallar magariba bai motsa ba a masallacin,yaci gaba da zama yana sauraren masu karatu dakeyi tsakanin magariba da isha'i,idanunsa a lumshe amma ita yake hangowa a ciki,yasan dai yau zaisha daaru da qorafi,to amma hakan yafi masa sauqi akan abinda zaije yazo,a yanayin da yake ciki yasan ko hafsat saidai idan zata nuna juriya ne kawai,bawai don qarfinta zai iya dauka ba. Har aka gama karatun aka yi sallar isha'i ba abinda ya canza,ya kalli agogo tara saura na dare,yasan a yanzun tana shirin kwanciya saboda akwai makaranta gobe,sai ya tashi yayi Shafa'i da wutiri sannan ya baro masallacin,bai koma gidan ba sai daya biya ya siya fruit. Tana lafe cikin kujera tana qananun hawaye,ga kukan mage daketa zarya yau tsakanin sassansu da ainihin main gidan,ya tura qofar da qaramar sallama maqale a bakinta,ga mamakinsa sai ya hangeta cikin kujerar,yayin da ganinsa ya bata qwarin gwiwar miqewa da gudu tayo wajensa,tana zuwa ta fada jikinsa ta sakar masa kuka Lips dinsa ya cije,ya dora hannunsa saman sumarta dake tsole masa idanu tun shigowarsa ta dazu yana shafa sumar daga saman kanta har zuwa inda jelar kalbar ta tsaya,bakinsa ya kasa furta komai,sabosa yadda komai ya dawo masa sabo bayab kasancewarta cikin jikinsa. Sun jima a haka,yanata karbar feelings yana mazewa har zuwa sanda ta lafa da kukan "To mene na kukan?" Cusa kanta tayi a qirjinsa,itama qamshinsa yana qayatar da ita,sai data tura baki gaba kamar yana kallonta sannan tace "Ba kaine ba,na dade inata shan wahala,nayi maka girki kuma daga shigowa saina nemeka na rasa" Murmushi ne ya subuce masa,ya hadiyi yawu da qyar sannan yace "That's all?" Kai ta gyada masa a hankali "To ya isa,yanzu bari nayi wanka nazo naci abincin,ai bance bazanci ba ko?" Hakan daya fada yayi mata dadi,ta rakashi dakin ta hada masa ruwan wankan da kanta,amma sanda taga ya fara balle botiran rigarsa saita miqe zata gudu. Hannu daya yasa ya dawo da ita gabansa,ya futa tsaho sosai,saiya sake janyota zuwa jikinsa suka hade waje daya,ya bata saman qafafunsa ya taka,hakan ya qara mata tsaho,yana riqe da ita da hannu daya,daya hannun kuma yana cire maballan. Saura hudun na qasa,saiya saki,ya kamo hannunta a tausashe ya dora akan qirjinsa "Qarasamin" ya fada yana saka daya hannun nasa ya zagaye bayanta dasu,hakan ya bata damar tsaiwa sosai,saidai dukka hannayenta biyu rawa suke,fatanta kawai ta cika umarnin mommmy data gaya mata duk abinda yace yanaso daga yau ta tabbatar tayi. Fuskarta yaci gaba da qarewa kallo sanda taje cire masan,tun daga cikakkiyar girar idonta,qaramin lallausan kabbanta,tana da wani irin kyau me sanyi da tsayawa a rai,duk da har yau yaga alamar batasan wannan baiwar da take da ita ba. Duk second daya da zasu qara a haka sake qayatar dashi tsaiwar take,rawar da hannunta keyi yasa ta dauki lokaci kafin ta gama,duk da cewa saman qafafunsa take a tsaye,amma hakan baisa yaji gajiya ba ko kadan "N.....na gama"ta fada muryarta tana dan rawa,saiya sukunya gishinta yayi kissing dinta,zuciyarsa nata tunzurashi ya zarme amma yana mata waigi,two step back yayi yana sauketa sannan yace "Thank you" ya furta hade da wani siririn murmushi ya wuce ta saman labbansa,saiya fara zare rigar,ta juya da hanzari ta fita a dakin, murmushi ta qara saki yana girgixa kai,ya dauki towel da widad din ta yiwa waje na musaman ya rataya ya shiga wanka,wannan ya bata damar guduwa daga dakin. Komai ta shirya masa a table mat,sai data tabbatar komai yayi sannan ta wuce daki ta debo books dinta na makaranta da aka basu assignment ta dawo dasu parlor din,don dama kusan ko yaushe tare sukeyin assignment,saita koma koma ta zauna saman kujera tana jiran fitowarsa,wayarta na hannunta tana chart. Ba jimawa sassanyan qamshinsa ya soma isowa parlor din,ta daga kai a hankali tana dubansa,yayi kyau cikin wasu light blue din kaya,fuskarsa tayi fayau kamar wanda yayi aikin wahala,saidai yayi fresh ya kuma yi kyau. Tana murmushi ta miqe tana cewa "Kazo kaci uncle please" tayi maganar tana karyar da kai gefe,sai ya sakar mata murmushi,komai nata burgeshi yakeyi,duk da tana komai ne ita bilhaqqi da gaske,ya tako a hankali har yanzu jikinsa babu qwari ya zauna. Tana serving dinsa tana zuba masa surutu, yana daurewa ne kawai yana biye mata, saboda yadda gaba daya qamshinsa ke tafiya da hankalinsa,uwa uba rigar ta mugun fidda surar qirjinta da suka fara cika suna bin girma da jikinta ya fara yi,ta gama zuba komai ta tura masa tana cewa "Aci a bani mark" kai ya jinjina ya fara diban abincin yana ci,shuru yayi yana jinjina dadin taste dinsa,baisan sunan abincin ba saboda bana hausa fulani bane,amma tako ina ya tafi dashi. Itakuwa tana zaune gabansa ta tsira masa ido tana jiran jin abinda zai fada,kusan minti biyar shuru,saita fara bubbuga qafafunta "Uncle..... uncle.....baiyi dadi bane?" Idanunsa ya zube mata ya lumshesu kadan sannan ya jinjina mata kai "what a wonderful taste!.....na kasa magana ne don kada nayi shirme,I have never eaten food that tastes like this" dadi sosai ya cikata,dariyar farinciki ta kubce mata,saita matso tana dauko pillow zata saka masa a baya tana cewa "Bari na fara da saka maka waigi kada ka fadi" hakan da tayi ya bawa tudun qirjinta damar gogar jikinsa,nan take ya qware da abincin da yake qoqarin hadiyewa yahau tari. Da sauri ta tsiyaya ruwa ta bashi tana masa sannu,duk fuskarta ta nuna damuwa qwarai,idanunta sukayi narai narai da hawaye,tayi tsai tana kallonsa gami da jero masa sannu har tarin ya lafa "Sannu uncle,ko na qaro maka ruwan?" A tausashe ya dubeta,wani kimarta da mahaukaciyar soyayyarta tana ratsashi,he never thought that she would care about him so much duba da qananun shekarunta da kuma yadda wadda ta girme mata ta ninka shekarunta ma ba haka take masa ba. He wonders how she shows concern for him,ko yaya yayi dare ko ya gaggara cin abinci duka sai tabi ta damu kanta,bare taga alamun bashi da lafiya,saita zauna ta dasa masa kuka har sai yayi da gaske wajen qarfafa jikinsa da nuna mata ya warke,ko iya wannan kulawar ya samu alhamdulillah,ko iya haka ya fuskanci manufar hajiya akan yarinyar.....ko haka aka tsaya ya samu tarin abubuwa da yawa daya rasa daga wacce suka debi shekaru tare,ko a iya wannan ya samu abubuwan da ada baisan namiji yana samu daga wajen matarsa ba,saidai yana buqatar qari.....zuwa lokacin ya fara gano muhimmancinta me girma cikin rayuwarsa,yana son ya maidata tashi.....halak malak......yanason su sake zama.abu daya,yana son dandana mata soyayya mai zaqin da dandanonta bazai iya fita daga halshenta ba,yanason ta zama tasa ta har abada. Sai data tabbatar ya nutsu sannan ta debe kayan abincin,ta kuma gyara wajen tas yana daga zaune cikin mutuwar jiki yana kallonta,daya daga cikin abinda yake burgeshi da ita,bata yarda tabar waje a hargitse ba. Dab dashi ta zauna har cinyarta tana gogar tasa,cikin jikinsa ta aike masa da wani saqo me nauyi ba tare data san tayi ba,a kwanakin nan da sabo ke sake shiga tsakaninsu haka take masa,ko meye zatayi tana maqale da jikinsa kamar mage,ya fuskanci ta saba ne tun a gida,tana da son jiki,kuma hakanan dama takewa ummu. Saman cinyarsa ta dora littafin da hannunta duka,sannan a shagwabe tace "Uncle..... assignment fa" jikinsa gaba daya ya dauki rawa,yasa hannu cikin zafin nama ya janye hannayen nata duka biyu daga jikinsa,tsoro yadan shigeta ganin yadda ya sauya lokaci daya, muryarta a narke kamar zata saki kuka tace "Uncle bazaka yimin ba?"kai ya girgiza muryarsa na dan rawa "No" "Amma shine ka ture ni?" Ta sake fada hawaye na cika mata idanu,zuba mata ido yayi wani abu na zaga jininsa,tana sake shiga rayuwarsa da wani mugun gudu da kuma gaggawa,bayason tana shige masa a irin wannan situation din da yake ciki,idan taci gaba kuwa bashi da tabbacin abinda zai iya biyo baya "Banaso kina hawa jikina" kunya ta saukar mata,itace ma ke hawa jikinsa?,sai ta miqe da sauri har tana zubar da litattafan cikin borin kunya tana hawaye ta shige daki. Da kallo ya bita har ta bace,sai.ya dawo da dubansa nan inda ta tashi yana sauke wawiyar ajiyar zuciya hadi da rufe idanunsa,bazai bita ba don kusancinsu da ita zai iya haifar da komai,ya miqe a hankali ya wuce dakinsa yana jin yadda komai na jikinsa ya daddaure. Saman pillow ta kifa fuskarta kunya na cikata,me yasa take yawan zama a jikinsa?,itama bata sani ba, yawancin lokuta ma batasan tayi ba banda yanzu daya fada,ta jima a haka tana jin kunyar kanta da kanta kafin ta miqe ta shige toilet,tayi brush ta dawo gaban madubi ta fara shirin kwanciya. Haka kawai ta zauna ta bata lokaci tana duba duka turarukanta,na gefen kunne na gabobi na matse matsi da sauransu,tana karantawa tana shafawa "Bari dai na gwada naga da gaske da qamshi" ta fada a sakalce,ita kanta da kanta sai data dinga bin jikinta tana shanshanawa ta lumshe ido "Hmmmm,aikuwa kullum saina shafa,ashe dai da gaske da qamshi" duka ta gama wannan,saita wuce cupboard dinta ta bude tana 'yan waqenta,leda ce ta biyota ta fado,a dan tsorace taja baya ta zubawa ledar ido,saita tuna ledar da matar gidan da suke ciki ta bata kyauta ce ranar data fara shiga,ta dauka ledar ta bude tana zazzage kayan ciki. Murmushi ya subuce mata sanda ta tuna abinda ta cewa abbas randa aka bata kayan,ya zuwa yanzu ta karanta amfani da muhimmancin kayan "Bari dai na gwada mu gani" ta furta tana dauko daya daga ciki,wine color ce mai wani matsiyacin ado na fararen furanni a jikinta,ta net ce mai wani irin sulbi kamar silk net,ta zura rigar harda pant dinta,sannan ta isa gaban madubi tana canza tafiya. Dan ihu ta saki tana fidda ido ganin komai nata ya bayyana muraran,ta rufe bakinta za hannayenta tana sake kallon kanta da kanta tare da jin kunyar kanta,saidai ta dade bataga abinda yayi mata maqurar kyau irin rigar ba. Wani abu ya darsu a ranta,gata gaban uncle abbas,saita fara jujjuyawa yadda ta taba gani a wani littafi tana gwada shine a gabanta. Kamar jira maqalalliyar magen gidan takeyi ta soma kuka tana kusur kusur jikin window glass dinta,mummunan faduwa gabanta yayi,ji tayi kamar ma ta shigo dakin saboda daya side na window din a bude yake,sai net kawai,ai bata tsaya tunani karo na biyu ba ta kwasa da gudu ta fita a dakin,bata kuma nufi ko ina ba sai dakin abbas cikin mugun tsoro. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 77 Bedroom slippers dinsa ya zura a hankali ya sauko daga gadon da nufin zuw kitchen ya samo lemon tsami ya matse yasha ko zai samu relief,ya isa bakin qofar ya dora hannunsa kenan da nufin bude qofar yaji an rigashi. Kamar wadda aka jefo haka ta fado jikinsa ta koma qanqameshi sosai tana sakin kuka. Cak komai na jikinsa ya tsaya ya daina aiki na wucin gadi kafin qwaqwalwarsa ta koma bakin aiki "Mage ce ta shig uncle,ni Allah a koreta daga gidan nan" ta fada cikin kukan shagwabar daya qarasa qwace dukka wani saiti da yayi saura tattare dashi,numfashinsa ya fara wani irin kai komo,babu abinda yake ji a tasa lallausar fatar sai tudun jikinta tako ina,tare da dumi da santsin tata fatar kasancewar jikinsa babu riga saboda wani mugun zafi da yake ji duk da akwai cikin dakin,hancinsa cike da wani tattausan qamshi mai tafi da hankali,irin scent din da bai taba jin irinsa ba,yayi mutuwar tsaye,ya zama kamar wani zane,hatta da gashin kanta daya maqale a habarsa yake isar da saqon qamshin hair mist dinta ya kasa cireshi. Shige masa ta sakeyi jin kukan kamar dakin yake matsowa,abinda ya sanya gaba daya jikinsa daukan rawa kamar wanda ake kadawa gangi,dukka wani sanin kamata nashi ya gushe,abu daya kwanyarsa ke karanta masa,ya kasance da ita,saiya zareta a hankali daga jikinsa ya sulale ya duqa saman gwiwoyinsa yana qare mata kallo. Komai na jikinta ya bayyana kansa,komai yana tsaye yadda zai dauki hankali fiye da kima,wata irin sura mai matuqar fusgar hankali da gusar da tunanin me tunani,wata irin halitta da idanuwansa basu taba ganin irinta ba. A lokacin gaba daha tsoron magen ya rufe mata ido,matsawar da yayi daga jikinta saita dinga jin she's not secure,magen zata iya shigo ne kawai ta haye jikinta,don haka hawaye ya balle mata,tana ganin kamar guduwa yayi "Uncle" kafin ta qarasa fada ya bude hannayensa,bata bata lokaci ba ta isa jikinsa ta fada,yayi mata wata wawiyar runguma kamar zai maidata cikinsa,ya tattaro dukka qarfinsa ya miqe saman qafafunsa,ya dauketa cak cikin jikinsa ya azata saman gadon dakin. Ko ina na jikinsa rawa yakeyi,da qyar ya laluba makunnin ac dana fitilar dakin ya kashesu,duhu ya mamaye dakin,babu abinda yayi saura sai siririn hasken dake ratso labule daga wajen farfajiyar gidan,ya kuma sassauta kaifin duhun dake dakin. Cikin jikinsa yayi mata kyakkyawan masauki ya fara sansana kowanne loko da saqo na jikinta yana jin kamar ya zuqe dukka qamshin,duk inda yakai hancinsa scent na daban yake bayarwa,irin wannan yanayin......irin wannan abun ya jima yana mafarki yaji daga jikin hafsat,amma tun satin farko na amarci bai sake jin hakan ba. Sosai ya haukace ya hautsine,ya koma real abbas dinsa dake bawa hafsat tsoro especially a lokaci irin wannan,widad dake da qarancin shekaru kuma batasan komai ba sai abun ya girmi tunaninta da kuma iyawarta,tun tana daukae ya lullubeta ne yana rarrashinta har ta gane wani karatu na daban yake mata,tashin hankalin da bata taba jin kamarsa ba ya sauko mata,ta kasa koda motsi bare ta zare jikinta,saboda ya cukukikuyeta tako ina,ya mata wani irin namijin riqo mai wahalar qwacewa,kiran sunansa ta dinga ji a jejjere,amma ko alamun muryarta baiji ba bare ya fuskanci magana takeyi,kansa da jikinta da yake sarrafawa kawai yake iya fahimta cikin duniyar daya shiga. Tako ina yayi mata riqon tsaurin da ba zata iya qwacewa ba,yayin da shi kuma yake jinsa a wata duniyar da baisan yadda zai kirata ba. Kuka sosai widad din keyi,irin kukan da ake kira na neman agaji da ceton rai,ceton da babu mai iya yi mata shi,tun tana ihu da iya muryarta har sautinta ya fara dakushewa. Duk da yanayin da yake ciki hakan bai hanashi karanto addu'ar nan da ma'aiki ya hori ma'aurata da karantata ba,sai yaji wata nutsuwa tana saukarwa qwaqwalwarsa,ya riqe fuskarta cikin tafukan hannayensa yana duban qwayar idanunta da suka bayyana tsoro da tashin hankali "Am sorry.....i love you" ya fada da wata shaqaqqiyar murya,daga haka ya fara neman hanyarsa zuwa maida widad din cikakkiyar mace kuma mallakinsa tahar abada,kamar yadda ya jima yana buri. Batasan yadda zata musalta azabar data ziyarceta ba "Ummmuuuuuuu......."ta kirayi sunanta da wata shaqaqqiyar murya,wanda daga sannan ta fara daina gane komai. Sanda yazo gangara kuka ne ya subuce masa,ya qanqameta sosai kamar zai tsagata gida biyu,tabbas banda hankalinta ya gushe sai tayi matuqar ji a jikinta,ya kifa fuskarsa cikin gashinta,idanuwansa na fitar da wani hawaye yana sake riqeta sosai cikin jikinsa,a lokacin wani abu mai girma da qarfi ya sake dasuwa a tsakaninsu,a lokacin ya dinga jin a shirye yake ya tunkari kowa da komai a kanta,ta wafce wani tsagi mai girma a rayuwarsa. Kusan mintuna hudu sannan ya dawo hayyacinsa ya fara qoqarin rabata jikinsa da ita,yadda jikinta ya saki gaba daya a hannunsa yasa ya fahimci babu numfashi a gangar jikinta. Sosai zuciyarsa ta kada ganin irin yadda wajen ya baci da jini,ya zare ido qirjinsa yana harbawa,kada dai ace ya kashe musu yarinya ne?,la haula wala quwwata illa billa. Cikin wani mugun kuzari da diro daga saman gadon ya doshi qaramin fridge dake dakin,hannunsa yana rawa ya dauko ruwa mai madaidaicin sanyi ya balle murfin har hannunsa yana jin ciwo ba tare daya lura ba,ya dawo ya zauna cikin jinin yana jawota jikinsa,ya bude ruwan ya soma shafa mata,amma harya kusa rabin robar bata motsa ba,wannan ya tashi hankalinsa,saiya sona tuttula yana zuba mata sosai har cikin gashinta. Doguwar ajiyar zuciya ta saki,suna hada ido ta maida idanun nata ta rufe tana sakin kuka wanda ko sautinsa ba'a ji saboda tuni muryarta ta dakushe,ko ina na jikinta wani azababben ciwo yake mata,ba zata iya tantancewa ba,amma daga can qasanta tana jin azabar data zarta tako ina. Saman qafarsa ta kifa fuskarta,sai ya rasa da wanne baki zai lallasheta,sai kawai ya cusa hannuwansa cikin sumarta yana shafawa a hankali "Am sorry.....kiyi haquri.....na tuba"shine abinda yaketa fadi,a qalla sun kusa mintuna talatin sannan wani baccin wahala yayi awon gaba da ita,kafin sannan wani zazzafan zazzabi ya rufeta ruf,tausayinta ya cikashi fal,shi kansa yasan yayi barna ba'yar qarama ba. A hankali yasamu yazameta cikin lallabawa kamar me riqe da sabon qwai ya kwantar da ita sannan ya tula mata duvet,don a yadda take cure waje daya ya tabbatar sanyi takeji,don ba qaramin zazzabi bane a jikinta. Qasan shower ya tsaya ya sakarwa kansa ruwa ba tare daya damu da rashin duminsa ba,don shi kansa wani zafi yakeji ta cikin qashinsa,kamar wanda zazzabin cikin qashi ke shirin kamashi. Kamar wani zautacce haka yabar ruwan yana sauka a jikinsa,yakai qololuwar tunani,sai furzar da duk ruwan daya shiga bakinsa da yakeyi,bai taba yarda da maganar nan da ake cewa mata suna suka tara ba sai a yau,iya yau kawai....iya yau kawai amma ta aje masa wani muhimmin tarihi cikin rayuwarsa. Tsaf ya gama wankansa sannan ya fito ya dawo dakin,ya tsane ruwan jikinsa,yana yi yana waiwayenta yaga ko ta motsa,amma har ya gama ya zame zanin gadon bata sani ba,bai damu ya maida wani ba,haka ya koma saman gadon tsurarsa babu shimfida. Sanda yake qoqarin sake maidata cikin jikinsa don ya rage mata sanyin zazzabin ta farka,kuka ta sakar masa sosai,don wannan karon muryarta ta bude ba kamar dazu ba,ido ya rintse yana jin sautin kukanta kamar saukar ruwan dalma a zuciyarsa,ya matso dab da ita,muryarsa tayi wani irin laushi,kamar ba abbas usman tafida ba(idan kunga sunan mahaifi ya banbanta kuyi haquri,na manta ainihin sunan mahaifinsa dana ambata a baya),jarumin kuma jajirtaccen dan sanda "Kina buqatar wani a kusa dake,let me help you please" qoqarin tureshi takeyi da hannu,don ko muryarsa batason ji "Banaso,ka qyaleni,ai ba sona kake ba,shi yasa kayimin haka,saboda ka ganni qarama ka girmeni" duk da yadda hankalinsa yake a kanta da damuwa da yanayin daya sanyata a ciki saida dariya taso kubce masa,har yanzu dai.....har yanzu dai ba zata bar wannan sakalcin nata ba "Naji... Kiyi haquri,ki bari na taimaka miki,idan kinji sauqi saiki rama". Kanta ta mayar ta kwantar a hankali ba tare data sake cewa komai ba,sai qwallar azaba kawai da take fitarwa daga idanunta,cikin d'ari d'arin kada tace aah ya sake matsawa kusa da ita ya sanyata a faffadan qirjinsa yayi mata rumfa,sai ajiyar zuciya ta kubce masa mai nauyi,ya dora habarsa saman lallausar sumarta data hargitse,hankalinsa nakan dukkan wani fitar numfashinta. Yadda zazzabin jikinta ke sake qaruwa ya hana masa runtsawa,akwai paracetamol a gidan,amma ko yaya ya motsa saita saki wani marayan kuka saboda zafin da radadi da jikinta yake mata,a haka kusan suka kwana yana gadinta,tana baccin rabi da rabi,tayi ta farka,bakinsa ya kasa hutawa da yi mata sannu. Da dabara ya samu yayi alwalar sallar asuba,ya hau gadon ya isa inda take,sai ya ranqwafa yana kallon fuskarta wadda ta fada sosai,ta kuma qara haske tafi fayau. Murmushi ne ya kubce masa,wanda tun daga qasan zuciyarsa ya ratso,sai a lokacin ya dan dinga tuna sunayen data dinga kira saboda neman agaji,ummu ta kiranyu har babu adadi,uncle muhsin,alhaji,latifa anty deena anty madeena harda mommynta,yau kam ya tabbatar kashinsa ya bushe,tabara ma tayi ta banza bare an tabota,saiya duqa a hankali ya hade tsinin hancinsu waje daya,take suka fara musayar numfashi,hakan kuma ya bawa danshin fuskarsa dama sauka a fatarta mai sulbi da taushi. A hankali taji yanayin numfashin da take shaqa ya canza,wannan yayi sanadin katsewar numfashinta,ta soma bude idanunta a hankali har ta budesu tar,basu sauka kuma a ko ina ba sai a tashi fuskar dake dab da ita. Da sauri ta maida idanunta ta kulle,sai taga kamar a sannan komai yake faruwa tsakaninsu,duk yadda yaso ta waiwayo ta kalleshi taqi,daga qarshe sai hannunsa ya miqa mata "Oya.... shikenan na haqura,taso kiji" shuru tayi kamar ba zata motsa din ba,sai kuma ta motsa a hankali ta miqa.masa zara zaran yatsunta ya kama ya dagata a hankali tana cije lebe,kasa zama tayi sosai saida ta karkace,bata ankara ba taji ya nemi gefanta ya zauna "Komai ya faru unexpected,abubuwan daya kamata na tambayeki kafin faruwar komai ban tambayeki ba,but now i will ask you.....ya ake wankan ibada?" Ta fahimci sarai abinda yake nufi,don tsohon karatune da suka jima da yinsa a islamiyya,amma sai taji tambayar tayi nauyi fiye da yadda zata jita a bakin kowa,sai tayi qas da kanta hawaye yana son saukowa. Ya fahimci da gasken gaske ya tabota yau,kuma hatta da 'yan muslikancinta sun motsa,ya saki qaramin murmushi na gefan baki,sannan ya zamo qasa ya tsaya kan gwiwoyinsa,yasa hannunsa masu taushi da sukayi wani sanyi da batasan na meye ba ya riqe dukka hannuwanta yana kallonta "Ayimin afuwa widad din ummu.....a gayamin naji,saboda wani nauyi ne da yake kaina da ya zama wajibi na saukeshi" a hankali ta motsa qafarta,saita cije lips dinta ta gefe saboda yadda taji ta kamar ba'a jikinta,saita motsa bakin nata ta fara yi masa bayani daki daki. Idanu ya zuba yana kallon yadda dan qaramin bakinta ke motsawa yana fidda sautin siriryar muryarta mai zaqi,duk bayanin da takai qarshensa sai ya gyada kai,ransa yana sakeyin fari tas,yana kuma sake godewa Allah "Ma sha Allah, alhamdulillah" ya furta murmushi yana subuce masa,ta fadi komai dai dai babu wani gyara a ciki,sai ya tuna wasu shekarun baya kamar haka shida hafsat din,gyara da yayi mata ya kusa na rabin bayaninta,amma yau sai gashi yarinya qarama tasan wajibin dake kanta. Miqewa yayi a hankali yana fadin "Get up dear" ta tattara dukka dauriyarta ta miqe din tana runtse idanunta,saidai taku daya tayi ta gagara yin na biyu kuka sosai ya qwace mata,dukka qafafunta suka dauki rawa da ilahirin jikinta,gumi kuma ya fara yanko mata,zata koma ta zauna ya tarota zuwa jikinsa da sauri ya riqeta da kyau "Is okay,ya isa....ya isa,you will be okay in sha Allah,am sorry,nasan duk nine na jawo" ya fadi abinda yake da tabbacin zaiyi wuya bata fadeshi ba,ya karanci komai tsaf cikin idanuwanta,haushinsa ne fal da kuma bacin rai,yanzun kuma zai qara mata wani fushin akan wanda takeyi,don kuwa daukarta yayi cak ya wuce bandaki da ita,ya kuma fara rabata da kayan jikinta. Gaban rigar da tuni ya tashi a aiki ta riqe sosai tana hawaye,kai ya girgiza mata alamar a'ah fuskarsa a hade ba alamun fara'a,dole ta saki rigar,yasa hannu yana qarasa zameta daga jikinta,ya kuma jefata gefe, don tuni ta tashi daga sunan riga zuwa tsumma,zamewa tayi kawai cikin bathtub din tana rufe idanuwanta dake fitar da qwalla,itakam ya gama da ita,tasan ya gama lalatata,iya zafin da takeji kadai ya isheta amsa. Tana ciki ya dinga tara ruwa me dumin gaske,tun bai cimmata ba har ya fara ratsata,a lokacin tayi yunqurin miqewa amma ina tuni ya rigata,da wani irin zafin nama ya xare rigar jikinsa ya shige cikin bathtub din,ya kamata zuwa jikinsa ya riqeta sosai saboda ruwan ya ratsata. Tana jin zafin tana jin komai amma ta kasa katabus,saboda dukka wani qarfi nata ya tafi, kukan ma ta kasa,saboda hatta bakinta tana jin kamar shima ciwon yakeyi,eh....batayi qarya ba, don idan ciwon ma yakeyi ba mamaki, tsahon lokacin da bakin shagwabar tata ya dauka yana tsone masa idanu,a jiya sai daya fanshe dukka wani haushinsa a kansa. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 78 Bakinta ya mutu murus,sai rawa da jikinta kawai yakeyi,abun ya bashi tausayi sosai,baiyi experiencing haka daga wajen hafsat ba a wancan lokacin,shi yasa a yanzu yake ganin komai daban,amma daya tuna banbancin shekarun sai ya fahimci dole a samu irin hakan,widad din yarinya ce sosai,dole tafi hafsat shan jiki. Sau uku yana sauya musu ruwa mai dumi sosai,kusan duka dashi akeyin gashin,har sai daya kintaci lokaci sannan ya canza ruwa me kyau "Zaki iya wankan da kanki?" Duk.yadda takejin nauyin ganinta da yayi a haka bata jin zata iya wankan da kanta indai toilet din takeso bari,don ko ina na jikinta rawa yakeyi,saita girgiza masa kai. Da kansa ya wanketa tas kamar su mimi,ya nadota a towel ya fito da ita,wajen shiryawa ne ta riqe towel din tace zata iya da kanta,ya saki boyayyen murmushi,don dariya ta bashi,abunda take fa boyon a yau ya gansu ya ta kuma taba halalinsa son ransa,saidai inda ta bashi damar da haka zaiso,don bai gaji ba,yana jin kamar ma ba'a yi komai ba. Bai matsa da yawa ba ya dauko mata komai ya aje mata kusa da ita ta yadda basai tayi tafiya me yawa ba sannan ya fice. Kitchen ya wuce da kansa ya fara hada musu breakfast,duk bayan sakanni sai wani murmushi ya subuce masa,ya koma kamar wani zautacce shi kadai,wani irin wasai yake jinsa tamkar angon da yayi kwanan farko a gidansa,ji yakeyi kamar an canzashi,kamar ba shine abbas ba. Lafiyayyen breakfast ya hada,ya shirya komai saman tray abun sha'awa kamar ba girkin namiji ba,ya jima da koyawa kansa girki,tun bai iya ba har dolen dole ta saka ya koya din,banda ya iya din ya tabbatar da tuni yunwa tayi masa illa indai don ta hafsat ce. A cure waje daya ya sameta tana ta rawar sanyi,ya ajjiye tray din ya isa inda take ya fara qoqarin dagota cikin damuwa,sai ya samu kuka takeyi "Ya rabb....." Ya fada cikin tsananin damuwa,gaba daya jikin nata ya rikice da zafi,ga complain na ciwon da takeji "Kiyi haquri kici.wani abu,sai muje kiga likita" ya fada a tausashe cikin sigar lallashi,gaba daya yayi wani mugun laushi. Kafada ta maqale cikin salon rigima hawaye ya ziraro mata,sai da ya murde ya koma ainihin abbas dinsa sannan ta yarda ta tsaya,ya hada tea ya zuba komai a plate ya saisaita zafinsa,sannan ya matso kusa da ita hannunsa dauke da mug din "Ehennnn.....oya,take it" da kadan da kadan take kurba bakinta yana rawa,bata wani sha mai yawa ba ta fara kelaya amai,sai data dawo da komai na cikinta. Tsaf ya gyara wajen da kansa,sannan ya dauki waya yayi kiran samuel yace ya bincika asibiti mafi kusa dasu yayi musu booking,idan so samu ne asibitin Dr jessica "Yes sir....zanzo na daukeka ne?" Sasssan da widad ke kwance ya kalla,sai ya girgiza masa kai hadi da cewa "Nob,idan ka gama abinda nace maka shikenan,you can go" "Yes sir" ya sake fada cikin girmamawa,wayar ya ajjiye ya soma takawa zuwa inda take kwance,ba samuel ba,koma waye bazai iya bari yayi driving widad din ba,yana jin kamar tsokar zuciyarsa ce ke rayuwa a wajen jikinsa. Gaban gadon ya koma,a tausashe ya duqa gabanta,ya saka hannu ya nutse ya janye gashin kanta daya rufe rabin fuskarta baya,idanunsa a kan fuskartata daya wani taushi ta kuma canza lokaci guda. A hankali ta bude idonta suka sauka cikin nashi,sai tayi saurin maidasu ta rufe,wani mugun kyau yaga ta qara masa a hakan "Zaki iya tashi muje asibiti?" Fuska ta narke,ita kam gaba daya bata qaunar abinda zai sanya ta motsa,amma hakanan yayi mata dabara cikin lallabawa ya sanyata tashi ta saka hijab dinta suka fito. Yana driving amma duk bayan wasu sakanni sai ya juya ya kalleta,ta tattare gu daya cikin seat din motar,sai ya miqa hannu ya kashe ac din motar,yadan qara speed don su isa da wuri. Already samuel ya gama komai,dr jessica ce da kanta,cikin girmamawa ta nuna musu seat,ya zaunar da widad wadda taketa bi da kallo,cikin zuciyarta tana ta yaba kyanta,shi kuma ya tsaya daga bayanta kamar wani bodyguard. Akwai sanayya tsakaninsu,don haka ta fara gaidashi cikin girmamawa,ya amsa mata tare da tambayarta aiki "me yake damunki madam?" Dr jessica ta tambayi widad tana murmushi,idanu a narke ta maida dubanta ga abbas,saboda batasan kalar amsar da zata bata ba,sai ya share kamar bai gane tana kallonsa ba "Uhmm,inajinki madam,fell free,kiyi bayani" ta fada tana jan takardar dake gabanta. Bai ankara ba sai sheshsheqar kukanta da yaji,ya daga kai da sauri daga danna wayar da yakeyi yana dubanta,sai yaja kujerar kusa da ita ya zauna har gwiwoyinsu na gogayya dana juna "Listen widad?,me kuma ya faru?" Muryarta a shaqe a kuma shagwabe qwarai tace "Kaine" sosai sound dinta ya taba zuciyarsa,ya saki murmushi "Okay,to ya isa,dr......she had her first night,she feels that the place is hurting her" kai dr jessica ta gyada sannan tace "Muje na duba" bata gane me take nufi ba sai data hau gadon da take duba marasa lafiya bayan abbas ya taimaka mata,nan ta fara raba idanu,ta kuma narke masa tana hawaye sosai,don kunya takeji ta buda gurin kuma a sake gani?. Da qyar yasha kanta yana riqe da tafin hannunsa cikin nata ha dr jessica ta gama dubawa ta koma kan kujerarta "It's bruises,you hurt her a lot sir,but ba damuwa,she will recover in a few days" ta fada tana jan takarda "Saika qara haquri sir, she's too young,dole ta samu ciwuka haka musamman idan ya zamana anyi gaggawa,but with time zata saba" tura baki widad tayi gaba,itama dr din nan bata da kunya,zata saba dame?,yayin da abbas yadan saci kallonta ya saki boyayyen murmushi "Allah yasa" ya fadi qasa qasa,cikin ransa yake hasashen lokacin da widad din zata sallama masa ruhi zuciya da kuma rayuwarta,lallai da ya shiga jerin maza mafi sa'a a duniya. Magunguna ta rubuta mata masu kyau,sannan ta basu wasu shawarwari har hakan yasa widad din tadan sake,saidai kunya kamar qasa zata tsage ta shige,tana ganin kawai abbas din ya gama kunyatata. Ko a hanya da wani irin nutsuwa da takatsantsan yake driving din,dukka hankalinsa da kulawarsa yana kanta,haka da suka koma gida,ya sanyata gaba da tambayar abinda takeson ci,saidai taqi sawa bakinta komai don bata da appetite,gaba daya taste din bakinta ya gama daukewa,tana ta faman koke koke,ta narke masa qwarai,dama hausawa sukace mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki,tsohuwar rigima da kuma shagwaba gaba daya ranar bawan Allah abbas aka juyewa,shi kuwa ya sanya hannu bibbiyu ya karba,saboda a yanzun jinta yake dai dai da ruhinsa. Girki kusan kala uku yayi mata amma tace bata ci,daga qarshe sai daya hade girar sama da qasa ya zaunar da ita ya dinga bata da kansa sannan ya samu taci,ya bata maganungunan tasha bayan ya tilasta mata ta shiga ruwa. Saman cinyarsa ya dora kanta,taso ta zame amma ya hanata,yanason kawo kusanci sosai a tsakaninsa da ita,ya kuma fidda dukka wani tsoro nasa daga zuciyarta daya dasu a daren jiya,sai tayi likimo ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya,ita kanta tana matuqar son kwanciya a jikinsa,bata taba jin wani guri da take jin wani nutsuwa da kwanciyar hankali idan tana gurin ba irin cinyar tasa,amma for now tsoronsa takeji, tsoronsa takeji sosai,gani take kamar idan tayi bacci zai sake maimaita mata abinda ya aikata mata jiya. Sannu a hankali bacci mai dadi yayi awon gaba da ita,ya sauke ajiyar zuciya yana gyara mata kwanciya sosai yana kallon fuskarta, murmushi ya sake subuce masa,yakai.hannu zai shafi lips dinta sai kuma ya janye hannu da sauri gudun kada ya tasheta. Wuni guda ranar suna tare cikin gidan,kwata kwata ma ya manta da wani batun aiki,sai da aka nemeshi a gurin aikin sannan ya bada excuse din yana da patient. A daren duk yadda taso bijirewa kwana dakin haka ya mata dole ta kwana a dakin kuma cikin jikinsa,dukkansu shi da itan wani irin ni'imtaccen bacci ne yayi awon gaba dasu. Ko cikin duniyar baccinsa ya tabbatar da cewa wani gagarumin ci gaba da sauyi ne ya tunkaro rayuwarsa,sauka da shigar numfashinsa cikin wata irin nutsuwa. Washegari bayan sun idar da sallar asuba,dukkansu shi da ita suna saman abun sallah,kowanne jinsa yake kamar a wata sabuwar duniyar,musamman abbas da yakejin jiki da qirjinsa wasai,babu komai a ciki sai wata irin mahaukaciyar soyayyar widad din. "Ina kwana?" Ta fada qasa qasa kanta a qasa tana murza tafin hannunta. Gaba dayansa ya waiwayo,sai ya saki murmushi,ya cira hannunsa a nutse ya miqa mata yana cewa "Zo nan mu gaisa da kyau" manyan idanunta da suka dan fada kadan ta daga ta kalleshi,sai ta noqe kafada,don gaba daya tsoronsa takeji "Please mana baby doll" ya fada da wata irin kwantacciyar murya,qas ta sakeyi da kanta tana tuna kalaman mommynta,sai ta miqe a hankali ta fara takowa zuwa gabansa. Da idanu ya bita,yana jinta tana tsarga masa har cikin jinin jikinsa,yabi takunta da kallo,akan tsari take ajiye qafafun nata kamar wadda ake qirga ma adadin takunta. A gabansa ta tsugunna tana watsa masa qamshin jikinta,lumshe idonsa yayi zuciyarsa na bugawa,duk yadda taso daurewa ya kauda kai ya gaza,sai yasa hannunsa ya fusgota a tausashe yayi masauki a jikinsa. A tausashe ya maida hannuwansa ya rungumeta "Kin tashi lpy my baby?,ya jikin?" Ya rada mata a hankali cikin kunnuwanta,har sai da duk wata tsiga ta jikinta ta tashi,ta lumshe idonta gabanta yana bugawa da sauri da sauri "Da sauqi" "Ma sha Allah......haka nakeson ji,Allah yayi miki albarka" har cikin zuciyarta taji sanyin addu'ar,ya motsa bakinsa zaiyi magana,kafin yace komai wayarsa dake gefe ta dauki ringing. A nutse ya sauke idanunsa yana duba mai kiran,hafsat ce,sai ya tsaya yana kallon wayar kamar mai son karanto dalilin kiran nata ta cikin wayar. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 79 Kaman wanda aka yiwa hani da daga wayar har ta katse sannan ya miqa hannu ya dauki wayar,yana shirin binta kiran ya sake shigowa,sai ya gyarawa widad zama a jikinsa sosai,yana sake riqeta a jikinsa cikin wani taushi da salo "Ina ka shiga ne inata kira" abinda kunnuwansa suka fara jiye masa kenan,sai ya lumshe idanunsa ya kuma bude lokaci guda "Assalamualaikum" ya furta a nutse,a tunaninsa zata ankara da kuskurenta ta kuma gyara "Wa'alaikumus salam......inata kiran wayarku baku daga ba duka ku biyun" ta sake maimaitawa tare da amsa sallamar duka guri guda. Danne zuciyarsa yayi kadan,idan da sabo yaci ace ya saba da duk wata dabi'a ta hafsat din,to amma kullum baqin halayenta sake qaruwa sukeyi "jiya gaba daya ko ka nemeni,sannan itama inata kiranta bata daga ba" ta kuma fadi cikin azalzala da ci da zuci "Tana ina ka bani ita" ta kuma fadi dai still,sai ya buda idanunsa gaba daya kamar tana gabansa "Wai me yasa koda yaushe ki bakisan abinda ya kamata ba?,da sassafen nan kin kirani kina jeramin tambayoyi kamar wani yaronki?,me yake damunki ne?,baki ji ya na kwana ya na tashi ba?" Fuska sosai ta bata,ita ba wannan bane ya dameta,hidimar bikin qanwarsu da suka fada kwana biyu bata kirata ta jaddada mata jan kunnen data saba mata ba shine damuwarta,uwa uba yadda ra'ayoyin mutane da kuma hirarrakin da aka sha akan kishiya gidan bikin ya dugunzuma mata lissafi gaba daya "Jiya kadai ban kiraki ba kinji babu dadi....kinyi tunanin yadda nakeji?,ke da sam idan ban kiraki ba saidai a zauna a haka idan ba buqatar kanki bane ya taso?" "Nidai don Allah,kai me yasa ba'a yi maka abun arziqi?,yanzu gashi dana kiraka ka hauni da qorafe qorafe?, widad nace ka bawa tunda naji muryarka ai nasan lafiya lau kake" "Bacci takeyi" ya amsa mata kai tsaye,zuciyar hafsat ta buga,bacci a dai dai wannan lokacin?,ya akayi ma yasan tana bacci idan dai ba tare suke kwana ba? "Bacci kuma kamar tare kuke kwana?" tayi subutar bakin fada,sai tambayar tayi masa banbarakwai,kulata sam bashi da amfani,don haka ya sauke wayar kawai ya kashe. Sosai hankalinta ya daga,ta saka lalubo number dinsa da tayi saving da abban mimi ta soma.kira ba qaqqautawa,har abun ya sake daure masa kai,daga baya sai ya kashe wayar ma gaba daya,ya sauke ajiyar zuciya yana sake gyarama widad kwanciya cikin jikinsa. Sau tari idan hafsat din tayi wani abun....sai ka rantse da Allah bata da maraba da masu tabin hankali idan ta aikata wani abun,kuma a wajenta wannan dai dai ne?. Kasa zama tayi,ta dinga kai kawo a dakinta,tana ganin kamar ta fara sakewa fa da yawa,kamar abbas din yana son canza hali da dabi'a,indai hakanne bai kamata taci gaba da sakewa yarinyar ba,bai kamata taci gaba da ganin haqorinta a waje ba,lallai dole tasa tsananin rashin wasa da rashin sakin fuska a tsakaninsu,amma ta ina zata fara?,duk shi ya cuceta da haramta mata zuwa kaduna,tasan halinsa kuma,yana da wahala kaga fushinsa,amma a duk sanda ya taurare lallai babu mai sakashi ya sauko,sai wata zuciyar ta bata shawarar ta kaiwa hajia ko kawu hassan qorafinta,to amma kuma hakan bamai yiwu bane,tasan babu abinda hakan zai haifar sai tashin tashina,abun qarshe yazo ya juye a kanta,amma kam tabbas ba zata dauki wannan dokar nashi taci gaba da tafiya a haka ba. Qarfe goma na safe ta motsa,ta bude idanuwanta a hankali ta zubesu kan fuskarsa,ta lumshe su tana sake budesu,wata bala'e'iyar kunyarsa tana saukar mata,sanda ya motsa yana ajjiye magazine din hannunsa ta maida idanunta ta kulle ganin yana niyyar fahimtar ta farka,batasan ya akayi ya gane ba,tadai ji fitar murmushinsa sannan ya sukunya yayi mata rumfa,ya sakar mata lallausan kiss saman tausasan labbanta dake matuqar jan hankalinsa "Good morning baby doll" cusa kanta tayi cikin cinyarsa cikin wani yanayi najin kunya,yaja numfashi mau nauyi saboda yadda ta sanya kan nata tana sauke masa numfashi mai dumi yana ratsa fatar cinyoyinsa ya tabashi sosai, hannuwansa ya saka ya dagata gaba daya ya sauketa cikin jikinsa,ya mamayeta da hannuwansa duka ta shige jikinsa sosai cikin wani lallausan riqo. Kasa kasa yake mata magana cikin kunne,kamar wani na a wajen zai iya jinsu "Yanzun ke babba ce babyn uncle,don Allah ki daina kunyar nan,tun jiya uncle dinki baiji muryarki ba,mommy tace banda musu...... mommmy tace ni mijinki ne......mommy tace ki kula dani kin manta?" Kai ta gyada a hankali,karon farko qaramin murmushi ya qwacewa fuskarta daya tuna mata da mommyn nata "That's good mommy's girl,say something please,i wanna hear your sweet sweet sweet voice" "Ina kwana uncle?" Ta fada a mugun shagwabe,zaka dauka tana sane tayi hakan,saidai ko kusa,kawai sound din ya fita a haka ne. Hannunta guda ya riqe cikin nasa tana murzawa a hankali "Lafiya lau baby.....ya jikin?,hope kin warware?" Kafada ta maqale masa a narke tana mele baki kamar yadda qaramin yaro keyi duk lokacin da yake shirin sakin kuka,hakan ya bashi damar ganin baby face dinta da kyau,ta sake wani fresh sossaaii,ko wannan shi ake kira da qyallin amarcin da ake fada?,ya raya hakan a ransa "Har yanzu gurin da ciwo" "Sosai?" "Ba sosai ba" ta amsa mishi tana kallon qwayar idanunsa,abinda ya haifar masa da wani sabon feeling mai qarfi a kanta "Kinsan me za'a yi?" Ya sake fada yana gyara mata zama sosai a jikinsa "A sake guda daya zaki warke" wani shagwababben kuka daya tasheshi a aiki ta saka,ta fara tuttureshi tana shura qafafuwa,irin yadda takewa ummunta duk sanda rigimarta ta tashi "Iyeeee,eh lallai babyn uncle ta warke,let's try again" shigewa jikinsa tayi ta qanqameshi tana sake sakar masa kuka,irin wannan shagwabar yakeso ya gani.....irinta yake da buri.....a matsayinsa na police.....He knows hardship,he knows hardness,duk wani nau'i na tsawa bada umarni da seniority shi ya sani yake gani, at least a gidansa yana buqatar soft and cool attitudes which can make him peaceful and calm. Shuru yayi ba tare da ya lallasheta ba,ya lumshe ido yana jin yadda muryarta ke fita da da wani irin taushi sakalci da kuma quruciya,har sai da yaga bata da niyyar tsagaitawa da gaske ta tsorata,sai ya saki murmushi,ya sunkuya a hankali,ya cusa fuskarsa ta gefan fuskarta ya lalubi kunnenta,cikin rada yake gaya mata wasu.maganganu da suka sanyata jin kunya "Uncle..... uncle" abinda ta fara fada kenan tana riqe gaban rigarsa da kyau wai zata boye fuskarta a ciki,sai ya saki siririyar dariya ya dagata gaba daya yana cewa "it's bath time". Sai da sukayi wanka gaba dayansu ya hada musu breakfast a gurguje sannan ya bata magungunanta tasha. Komai ya hanata yi,tana daga kwance tana kallo,saidai duk giftarawar da zaiyi saiya bar mata abinda zai sanyata dariya,inda zaka ganshi a lokacin,zaka rantse ba ASP abbas bane,miskilin da ganin haqorinsa ko murmushinsa ke zama wani babban aiki,zaka zaci wani mutum ne can na daban mai kama da abbas din. Cikin kwanaki biyun gaba da babu inda yaje,suna tare cikin gidan,komai na gidan ya dauke mata,yayi wani irin mugun sakewa da ita matuqa gaya,ya kuma jata jikinsa sosai,a yanzun babban burinsa ya gina rayuwa mai.inganci ya gina rayuwar da zata zame masa madubin gobensa,duk wani abu da yasan tana so,ya kuma fuskanci yana sakata nishadi da walwala shi yakeyi,wani irin tattali da kula yake nuna mata,wani abunma baisan yanayi ba,don yana tasowa ne daga qasan zuciyarsa komai yake tasowa,wani irin yanayi dashi kansa baisan a ina zai ajjiyeshi ba. Kudi yake zuba mata sosai a waya,tana daga zaune tayita kiran 'yan gida tana shan hira,musamman ummunta da mommynta,kusan ko da yaushe maganar mommyn tabi mijinta,banda musu ko taurin kai,sabawa umarninsa da sauran dukka abubuwan da bayaso,koda yaushe tana gaya masa "Ki kula dashi,kiyi masa dukkan abinda yakeso,banason na sake jin kowa yaji wani abu da yake gudana a tsakaninku,ko meye zaiyi miki ko ke zakiyi masa,mai dadi ko mara dadi,sirri ne tsakaninku,ki zauna kiyi tunani ki koyi warwarewa da kanki,idan kin gaza ki nemeni" kusan rabi da rabin hirarsu da ita kenan cikin hikima. Hutun satin ya dauka ganin ba wasu tarin ayyuka sosai a office,saidai lokaci lokaci ya leqa office din yayi awa daya ko biyu ya dawo gida a daddafe,don baya iya haura hakan,sai yaji gaba daya nutsuwarsa da hankalinsa sunyo gidan. Ita dinma komawa take kamar wata mara lafiya muddin xai fita ya barta a gidan,saidai idan ta fita makaranta,wanda zuwa yanzun da kansa yake jigilar kaita da daukota,bai sake yarda wani ya kaita koya dauko masa ita ba,bayajin zuciyarsa zata iya dauka wannan. Cikin sati guda ta warware,ta warware da wani irin soyayya da shaquwa dashi sabuwa data ginu a ranta,ya bar mata wani babban tambari da ya kame ilahirin zuciyarta gaba daya ba tare data ankara kota fuskanci meye ba,tasan dai a wannan lokacin tana matuqar son kasancewa tare dashi,tana jin wani farinciki duk lokacin daya zamana yana kusa da ita,suna hira aikin gida ko kuma assignments,tana jinta sukuku cikin rashin sakewa da walwala a duk lokacin da ya zamana ya nesanta da ita. _cikin wannan yanayin sati biyu da suka biyo baya ya shirya ma zuwa gida weekend,yace ta shirya su wuce tare,don baya jin zai iya barinta har tsahon kwanaki uku ba tare da tana kusa kusa da rayuwarsa ba_ *_muje zuwa dai masu karatu,yanzu takun zai fara daukan zafi_* *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 80 Tsaye yake gaban mirror yana taje kansa,shirye yake cikin mulberry silk da ya kwanta sosai a jikinsa,ya kuma fidda kyan fatarsa data wadata da tsafta da kuma hutu,jikinsa na fidda sassanyan qamshin turarensa. A nutse take takowa zuwa qofar dakin nasa,tura qofar a hankali saita tsaya tana kallonsa ta cikin madubin ba tare data saki hannun qofar ba,hakanan bata koma ba bata kuma shigo dakin ba. Idanu ta zuba masa sosai tana kallonsa,yayi bala'in yi mata wani sassanyan kyau,a yau din quruciya kyansa da haduwarsa sun sake fito mata muraran fiye da ko yaushe, shigar ta karbeshi,duk da dama zaiyi wuya ya saka kaya a jikinsa basu karbeshin ba,ta'ammali da uniform saboda yanayin aikinsa ya sanya yafi mu'amala da manyan kaya akan qanana,saita saki qofar a hankali ta goye hannunta a qirji taci gaba da kallonsa. A nutse ya sauke idanunsa a kanta,shi dinma shigarta ta yau ta fusgi hankalinsa sosai,abaya ce a jikinta ruby color,saita dora dan qaramin Vail a kayanta dusty rose,dan siririn pink lips dinta na fidda qyallin lipstick data shafa musu, fuskar ta ta kwanta da color din powder din data shafa "Ma sha Allah" ya fada ta hanyar motsa labbansa,ya ajjiye comb din hannunsa a hankali,yana so yau ne ya kamata real tana satar kallonsa,abinda ya lura fa koya kenan cikin satin nan,idan kuma ya fada saita waske harda qananun hawayen ita ba kallonsa take ba. Batayi zato ba taga ya waiwayo gaba dayansa,idanunsu suka sarqe cikin na juna,kunya ta kamata,tayi taku biyu baya zata koma ya dakatar da ita "Don't move baby" yayi maganar muryarsa nadan sarqewa,ganin da yayi mata a yanzu da idanu sai yake ganin kamar madubin ashe ya rage kyan da tayi,turarenta da ko yaushe yake tsaye masa a rai ya iska na kadoshi kadan kadan yana cakuda da nasa yana bayar da wani kalar qamshi na musamman,sai ya cira qafarsa ya soma takawa a hankali zuwa inda take, qafafunsa na nutsewa cikin lallausan carfet din daya malale dakin dashi,bazai iya kauda kai ba a yanzun,yana qishirwa wadan nan labban nata,yanason yaji duminta sosai.......wanda rabonsa da hakan tun randa ya maidata tasa halak malak,duk kuwa da cewa gado daya suke kwana,amma bai sake neman komai daga gareta ba, saboda yana son fidda duk wani sauran tsoro nasa dake ranta. Qugunta ya kamo da dukka hannayensa biyu ya matso da ita jikinsa sosai har jikin nasa yana gogar nata,gabanta ya fadi sosai ta lumshe ido tana son hadiye tsoronta "Bude idon na gani..... please my baby" ji tayi ba zata iya tsallake umarninsa ba,sautin muryarsa gaba daya ta kashe mata jiki,ta bude manyan idanuntan fes a kansa,sai yaja numfashi da kyau,yasa yatsunsa biyu ya kama kumatunta yadan ja kadan "Inason wadan nan idanun,inajin kamar na hadiyesu" ido ta fidda fuskarta na washewa "Ana cinye idon mutum uncle?" Ta fada a sakarce,sai ya saki murmushi kawai yana tunanin yaushe widad din tashi zata gama girma ne,ya girgiza kansa a hankali,yana jin komai na jikinsa yana amsawa "Ba'a cinye ido,amma ana iya lasheshi,ana lashe kunne,ana lashe baki ana lashe harsh........" "Stop uncle,wallahi kunya nakeji" ta fada a narke kamar zata sanya kuka,yadda fuskarta tayi ta sake tafiya da imaninsa,mitsitsin bakinta data turo gaba ya kalla,zuwa yanzun gaba daya burinsa ya tattara a kai,a tausashe yace "Bari na nuna miki ki gani" bai qara ko second biyu ba ya hade bakinsu waje daya,cikin wani irin lallausan salo da kuma qwarewa yake aike ma qwaqwalwarta saqo ta hanyar bata zazzafan french kiss daya birkita tunaninta gaba daya,ya kuma zare mata kowanne kuzari da qarfin hali da take jin tana dashi. Ba inda bai aika da harshensa cikin bakinta ba,ya lasheshi tsaf ciki da waje sannan ya saketa yana jan numfashi. Taga taga tayi zata fadi saboda yadda jikinta yayi laushi gaba daya,yayi hanzari da sauran nasa kuzarin ya tarota yana kallon qwayar idanunta,sai ya jinginata da jikinsa,hakan kuwa ya mata,don boye fuskarta tayi a qirjinsa,wata kunya tana dawainiya da ita. Qaramar dariya mai hade da ajiyar zuciya ya sake "Good baby.....da alama kin fara daukan haske ko?" Ya fada yana leqa fuskarta,saita kebe masa baki ta soma 'yar sheshsheqar kuka,har cikin jininsa ta aike masa da wani saqo daya huda zuciyarsa,sai ya dinga jij sheshsheqar tata kamar da manufa,yadan janye jikinsa kadan don bayason abun yaci gaba da tafiya,amma saita riqe hannunsa tana sake neman wajen buya a jikinsa,don gaba daya ya gama aza mata nauyinsa,amma ta lura shi ko a jikinsa,abinda yayi mata a yanzun tana jin kamar ba zata iya sake kallonsa ba har abada "Ohhh.....kina buqatar qari kenan?" Kai ta girgiza da sauri,saita sakeshi taja da baya tan lalubar qofa ta fice da sauri. Da kallo ya bita kamar wani sakarai harta fita din,ya koma da baya ya zube gefan gado,wannan din wani dadadden mafarkinsa ne da a yau ya cika,he loves kisses sosai,yana bala'in so body contact da iyalinsa qwarai,amma hakan bata samuwa sam sam a gareshi,saidai yayita fama da hakan a tarin mafarkansa,yayi loosing abubuwa masu yawa da yasha tsarawa kansa a tsarin rayuwar gidansa,saidai da daya da daya komai yake rugujewa ya rushe,tsarinsa da ra'ayinsa yayi nisa qwarai dana hafsat,wasu abubuwan ma tana kallonsu as bata lokaci,ko kaiwa maqura,yana jin kamar a yanzun zai gina dukka mafarkansa ya kuma rayasu in reality. Gaba daya ta saka jikinsa yayi laushi,bayajin zai iya driving dinsu daga kaduna zuwa bauchin,bashi da wannan qarfin kwata kwata,don haka ya ciro wayarsa ya kira samuel yace yazo zasu wuce bauchi yanzu yanzu. Minti goma kacal samuel ya kirashi kan ya iso,already motar dama a wanke take,hakanan dukka kayansu suna ciki,sai ya miqe yana gyara rigarsa,ya dauki agogo da hularsa duka ya sanya,ya sake fesa turarensa,sannan ya kwashi wasu documents dake cikin wata folder ya fito. A gaban fridge ya sameta tsaye tana shan ruwa,ya taka a hankali ya tsaya a bayan nata yana dora hannunsa saman nata hannun da ta riqe ruwan dashi tana sha,hannun ya qawatu sosai cikin wasu siraram banguls kusan guda goma ruby color da duka haska farar fatarta datayi wani fresh. Qwarewa tayi, saboda gaba daya bata ji takunsa ba,ya sanyata a kafadarsa yana dan dukan bayanta harta daina tarin sannan ya janye jikinsa kadan "Ki dauko komai?,samuel yazo xamu wuce" kai ta jinjina masa alamar eh,sai ya miqa mata document din hannunsa,ya ja mayafin dake kanta ya soma nada mata shi. Baya ya danja ya kalleta,she looks very gorgeous,sai yaji kishinta yayi bala'in kamashi,har yaji kamar dama bai kira samuel ba. Hannunta ya kama ya isa da ita gaban wani dan fashion mirror dake maqale cikin falon, murmushi ya subuce mata,ya akayi ya iya rolling haka?,ta cikin idanunta ya karanci tambayar dake cikin zuciyarta,sai ya saki murmushi "Mimi da nawwara" a taqaice ya amsa mata amma ta gane,saita kauce gefe daya saboda kallon da yake jifanta dashi ta madubin yana mata nauyi da yawa. Kafin su fita ya kira samuel ya masa aiken dole,wai fita dan kantin dake kusa da gidan ya karbo kasa biro,kafin ya dawo suna cikin motar,yana isowa yace ya aje masa wajensa zai karba,don kada ma.ya juyo har ya ganta,ya amsa masa a ladabce ya kunna motar suka fice daga gidan. Tun basuyi nisa ba bacci ya soma fusgarta,sai yayi mata majingina da kafadarsa sosai,ya lalubo hannunsa ya sanya a tafin hannunsa ya hadesu waje daya. Kusan awa biyu ta kwashe tana bacci,sanda ta farka saita janye jikinta daga nasa cikin jin nauyi,ya murmusa kadan yana dubanta "Kin more min kafada,sai naci tararki" kafada ta noqe tana dariya cikin jin kunya. Awa biyu da rabin suka shiga garin bauchi,sai tadan dubeshi har yanzu hannunsa yana cikin nata "Gidan hajiya zaka saukeni" ta fada qasa qasa,don sam sai taji bata qaunar zuwa gidan. Waiwayowa yayi ya zube mata manyan fararen idanunsa yana kallonta qasa qasa,cikin zuciyarsa yake son qiyasta yadda hakan zata faru,sai kuma ya girgiza kansa a hankali kafin ya dauke idamunsa a kanta "Ba yau ba" ya fadi kansa tsaye,don baya jin zai iys nesa da ita "Don Allah uncle" ta fada a mugun shagwabe kamar zata saki kuka "No,Baby" komawa tayi ta lafe jikinta a sanyaye tayi shuru,tafison gidan hajiyan,tafi qaunar zama a can,saita fara sharar hawaye kafin ta sake masa siririn kukanta. Idonsa ya lumshe yana jin wani abu mara dadi yana taba zuciyarsa,irin abinda bai tana jin kamarsa ba,duk da dama shi din kusan weak point dinsa kenan "Is okay" ya fada yana sanya hannunsa cikin nata,sannan ya bawa samuel umarnin canza titi zuwa titin da zai kaisu unguwar gida dubu. Ajiyar zuciya ta sauke,ta sake lafewa tana dan sakin murmushi "Na gode" waiwaya yayi a hankali ya kalleta,sai ya sanya hannu yaja hancinta "Karkiyi saurin godemin,don idan munje ba lallai bane na barki ki kwana ba" baki ta tura gaba,sai ta kwantar da kanta ba tare da tace masa komai ba,ya sake sakin qaramin murmushi yana kallon hanya hadi da matse hannunta sosai kuma a tausashe cikin tafin hannunsa,can qasan zuciyarsa yana jin wani abu mai qarfi a kanta yana sake ginuwa. Ita ta fara shigewa gidan hajiyan cike da karsashi, zuciyarta fal farinciki,don kusan wata guda kenan bata zo ba,zuwanta na qarshe har suka koma batazo gidan ba. Su biyu ne falon,ita da gwaggwo fanteka suna taba hira,sun gama cin abinci kenan tayi sallama,sosai farincikin dake fuskar hajiyan ya bayyana,ta amsa sallamar tana cewa "A'ah,mutan kaduna.....irin wannan ba zata haka?" "Aiko dai,haka amaryar abas din ta fara canzawa,ah lallai yarinya taji kiwo" gwaggwo fanteka data kama haba cike da jin wani abu a ranta me kama da qyashi qyashi ta fada,maganar da ta yiwa widad din nauyi,karon farko da kunyar hajiya ta kamata,musamman da ta tuna abinda ya wanzu tsakaninta da abbas din,sai take ganin kamar ma kowa yana iya karantar hakan,don haka tun daga dan nesa dasu ta zube tana gaidasu. Cikin kulawa hajiyan ta amsa, gwaggwo fanteka kuwa ta zuba mata ido tana kallonta,sosai widad din ta canza,ta fara cika ta kuma yi kyau abinta,ta amsa tata gaisuwar tana sauke numfashi hadi da gyara zamanta "Kundai tafi kunbar uwar gida da jiran gida ko?" Ta jeho widad da batasan ma kan asalin abinda kae faruwa ba tambaya "Uhmmm,ina ruwan widad,ita da batasan komai ba akai" hajiya tayi saurin karbar zancan "To ai shikenan,Allah ya kyauta" ta sake fada tana gyara zamanta,dai dai sanda abbas yayi sallama ya shigo parlor din,qaninsa muneer yana biye dashi da babban ledar da muddin da ransa da lafiyarsa baya gaza shigowa da hajiyan tashi ita. Washe baki gwaggwo fanteka tahau yi tana sake gyara zama,lallai yau din ta shigo a sa'a,tasan cewa shar da ita zata fita,harda ita wajen marabtar abbas din,ya duqa ya gaidasu cikin girmamawa sannan ya koma ya zauna sosai daura da hajiyan tasa. Miqewa gwaggwo fanteka tayi tana cewa "Ni bari na wuce gida,naga la'asariya ta kusa" "Ki tsaya mana ki karbi tsarabar taki?" "A'ah haba,kya dai aiko muneera ko muniru ya kawomin,yallabai Allah ya huta gajiya" hannu abbas ya sanya a aljihunsa ya fidda sabbin 'yan dubu dubu ya miqa mata,tasa hannu kuwa ta amshe babu tayi tana zuba godiya. Nan falon hajiyan yayi zamansa suna hirar yaushe gamo,duk danda widad dake kitchen tare da muneera ta gifta sai taji ranta ya mata sanyi,ta kuma sake godewa Allah,kallo daya ta yiwa abbas din harma da widad din ta karanci akwai wani gagarumin sabon canji cikin rayuwarsu,walwalar abbas din ta qaru,idan ma ba idonta bane ke mata gizo har 'yar qiba taga yadan qara,abinda bata taba gani a tare dashi ba,sannan duk sanda widad din zata gifta idanuwansa suna biye da ita,kamar yadda itama duk sanda ta ratso ta falon saita saci kallonsa. Ana idar da sallar la'asar yayi shirin wucewa gida,yace ta fito su wuce,amma saita sakar masa darunta tana maqale wuya,idan zata shekara tana masa wannan shagwabar yanason gani,ba kuma zai gaji ba,tilas ya haqura ya barta bayan hajiya ta sanya baki,ya wuce gidan shi kadai,amma cikin jikinta da zuciyarsa duka sai yakejin wani iri babu dadi,kamar ya baro wani b'ari ne na zuciyarsa a wani waje. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 81 Kamar ko yaushe a harabar gidan ya cimma yaran,sunata wasan qasa sunyi futu futu dasu,qasa har saman kansu,amma hakan bai hanasu murnar ganin juna ba,ya tsugunna ya kwashe abinsa sunata masa surutu yana kerbewa. Dab da zai shiga sashen nata ta fito,sanye da atamfa dinkin doguwar riga,tayi daurin ture kaga tsiya,duka gashinta da ba kasafai ta fiya son kitso ba ya fito abinsa ta qasan daurin,hannun brassiere dinta daya fito ta kafadarta ya sake muzanta shigar tata,atamfar anko ce da sukayi biki tun shekaran jiya,kuma tun shekaran jiyan take jikinta bata cire ba,sam batayi tsammanin zuwansa a yau din ba,shi yasa ta saki jiki ya sheqi baccinta,bata jima da tashi ba ta biyo sahun su mimi jin shuru ba motsinsu tun dazun. Tare hanya tayi tana masa sannu da zuwa hadi da karbar jakar hannunsa,bata son ya shiga sashen nata,saboda ita kadai tasan irin badaqalar daya kwasa ba,don hatta da uniform din mimi yana zube a falon da school bag harma da tsadajjen lunch box dinta daya siya mata "Mu qarasa sashen naka,dama fitowar da nayi gyarawa zanje nayi" ta fada tana sake kankane hanyar. Bai musa mata ba,don a yadda takeyin din yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,bataso ya shiga yaga ba dai dai ba ya gyara mata ko yayi mata fada,ko shi din yasan idan ya shiga babu lallai ya samu sashen a yanayin da zai iya zama,so no need ya matsa sai ya shiga din,don haka ya juya da yaran suka wuce sashen nasa. Tun daga qofa yaga abinda aka saba,a yau dinma sashen nasa babu gyara,yadda ya barshi kusan wata guda haka yake a yanzun,sai ya basar,ya ajjiye yaran ya zauna shima saman kujerun falon,ta yiwa jakarsa mazauni sannan ta juya tana kallonsa "Bari na fara dora maka wani abun sai nazo na gyara nan din" manyan fararen idanunsa ya daga ya kalleta "No,a bani abinda kuka dafa kawai da rana". Da sauri tadan kalleshi,sannan cikin yanayi na rashin gaskiya tace "Ba zaka iya ci ba,infact ma inajin sun cinye....." "Eh daddy,indomie ce mommy ta dafa mana,kuma saida nawwara ma tace tana jin yunwa s......" Yarinyar bata qarasa ba saiji kake fafff ta doke mata baki,take kuwa bakinta ya fashe "Shegiyar maganar tsiya,muna magana uban waye ya sako bakinki a ciki?" cikin bacin rai abbas ya kama leban yarinyar yana dubawa,sai da ya gama ganin iya wajen da ya fashe din,ya goge mata wajen ya dorata kan cinyarsa yana lallashi sannan ya dubeta cikin bacin rai "A gabana zaki fasawa yarinyata baki?,kece me abun duka ba ita ba,amma waye ga dakeki?,na rantse da Allah kinyi na farko kinyi na qarshe,bance kada ki hukuntasu ba,amma ba ta irin wannan hanyar ba". Ranta ya baci sosai,ta dinga jefawa yarinyar harara,tanason bata mata budget gaba daya,amma tasan maganinsu,tattarasu zatayi kaf kwanakin wajen widad. Saboda tana da plan sai bata tanka masa ba,illa bata fuska sosai data yi,ta juya tana ficewa daga sassan ranta a bace. Kai tsaye ta nufi sassan widad,gwara ta fito da ita tun yanzun ta kama mata ayyukan,saboda yau aikin nata suna da yawa,ko gyaran sassansa zuwa abuncinsa aiki ne babba a wajenta,ga nata sashen da tasan zaici tsintsiya ruwa da klien,saidai tun kafin ta qarasa taga kaman babu mutum a sassan,kasa gasgata idanunta tayi,ta dinga ganin kamar gizo,har dai data taba qofar,takuma yi knocking taji shuru. Sak tayi,ta tsaya yana jinjina kanta,baizo da ita bane?,ko kuma ta wuce gidan hajiyarsa yadda ta tsiri wannan iskancin wani lokacin?,bata da amsa,don haka sai ta wuce sassanta,ta dauki wayarta ta kira muneera. Tambayar farko tace mata gatacan ita da hajiya a falo suna hira,ta zuqi iska ta fesar,lallai kan yarinyar ya fara wayewa,ita za'a mayar 'yar iska?,aqalla wata guda da wani abu kenan bata saka yarinyar a idonta ba,ko zuwanta na qarshe kwana guda kwata kwata tayi a gidan suka koma. Sake fitar da iska me zafi tayi daga bakinta,maganganun anty ummee suka dawo mata,ai kuwa ba zata bari hakan ta faru ba,tare ta karantawa yarinyar karatun manya,dole tabi da ita,dole tabi hanyarta,dole ne kuma ta fara gane banbancinta da ita,sai ta fara dora abinci sannan ta kwashi kayan shara ta wuce sashen nasa tana sake saqa abubuwa da yawa da take da shirin aiwatarwa. *_W A S H E G A R I_* Karfe goma na safiya ya fito tsaf dashi,cikin lallausan yadin filtex na maza mai asalin kyau da tsada,komai yana yinsa ne a wani kasalance da rashin kuzari,duk kuwa da cewa a jiyan ya samu yadda yakeso daga hafsat din,to amma sai yakejin wani irin mugun banbanci mai tazarar yawa,banbancin da zai iya kiransa kwatankwacin nisan dake tsakanin sama da qasa,gaba daya ma zai iya cewa wani irin bacci yayi mara dadi cije da kewar widad din,duk juyin da zaiyi sai ya dinga ganin kamar itace a gefansa,amma dole ya tattara dukka wadan nan ya danne can qasan zuciyarsa da qarfin gaske gudun shiga hakkin me hakki. Yana daura links a hannunsa tayi sallama ta shigo dakin,hannunta dauke da plate din data soya plantain wadda ta qone tayi baqi abinta,yadan bita da kallo kadan,tana nan gayanta,bayan wankan ibada da tayi kafin sallar asuba babu wani abu data qara,koda da turare kuwa,wanda zuwa yanzu zamansa da widad hancinsa ya saba da shaqarsa. Yana yiwa turare wani mugu mugun so,amma ita nata ra'ayin sunyi hannun riga da ta'ammali dashi,sai randa ranta yaso,ko kuma aka taki sa'a ranar tana da ra'ayinsa. "Fita zakayi kenan" ta fada tana zama gefan gadon da har yanzu ta kasa gyarashi,don tuni dama yayi sallama da kwana a sashenta "Eh,akwai wani abu?" Ya fada yana takawa gaban mudubi,ya dauki cup din coffe din da yace ta hado masa dashi yakai bakinsa. "Aah,inason zuwa gidan hajiya ne" dire mug din coffe din yayi saman madubin bayan daci ya ziyarci bakinsa,sannan ya zarce da dubanta yana nazarinta. A ka'idarta zaiyi wahala taje gidan hajiyan haka siddan,shi yasa maganar ta bashi mamaki ko a yanzun ma,amma taqi yarda ta kalleshi bare ya karanto gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta,har ya gama kallonta,ya jawo qonanniyar plaitain din ya fara kokawa da ita "Saikin dawo" ya amsa mata daga baya,yana tsame hannnunsa daga plate din,yaja tissue yana goge maiqon daya bata masa hannu. Sarai taga yadda ya cakali abincin,abu na farko da ya kamata tayi taji dalilin da yasa bai maida kai yaci ba,tunda fita zaiyi,amma inaaaa,ba wannan bane a gabanta,sai kawai ta kwashe kwanukan bayan fitarsa,ta hada da kudin cefanen daya ajiye mata,duk da babu abinda zasu siya,ta soke a lalitarta,sannan ta shiga bandaki tahau shiryawa a gurguje,don tana da tabbacin zaiyi wuya idan ba gidan hajiyan ya nufa ba,tanason kuma ta cimmasa a can ayita ta qare. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 82 Qwafa taja sanda ta gama parking motarta kusa da tashi,ranta ya quntata sosai,duk sauri da taga yana yi dama nan ya nufa,tafison hakan dama,gwara ayi komai a gabansa,ta kashe motar, saidai kafin ma ta zare key din daga jiki tuni mimi ta bude murfin motar ta fice abunta. Da harara tabi bayan yarinyar,ta tsani yadda take rawar qafa akan wannan tsohuwar,amma tana qara wayo zataci ubanta ne,ba zata dauka wannan ba. Da gudunta yarinyar ta fada falon tana kiran sunan anty widad da hajiya,abbas ya bita da kallo yana hade ransa "Koma kiyi sallama" da sauri ta koma tayo sallamar ta sake shigowa,saidai hakan bai rage mata karsashinta ba,tana shigowar ta fada saman cinyar hajiyan,kafin su sake cewa komai hafsat tayi sallama ta shigo "Ikon Allah,ashe tare kuke" hajiya ta fada tana ma hafsat din sannu da zuwa. Idanunta akan kwanukan daya gama cin abinci, qamshin abincin yana nan daram a falon,kana shigowa kuma zai buwayi hancinka,haushi da kishi suka cikata,abind aya sassauta ma abinda takeji a ranta rashin ganin gilmawar widad din kwata kwata. Saman kujerar dake daura da hajiyan ta zauna,a maimakon zama a qasa kamar yadda ta samu abbas din "Hajiya ina kwana?" Ta gaidata tana sake qarewa falon da kwanukan abincin kallo,a mutunce ta amsa mata cikin nuna kulawa gami da tambayarta yara da kuma gida,duka ta amsa mata da lafiya lau,sai kuma shuru ya biyo baya,dai dai lokacin da baba usaina tayi sallama ta sako kai "A'ah yau kece a gidan?" Baba usaina ta fada tana zama itama,fuska hafsat din tadan saki,saboda saboda alaqar dake tsakaninsu ta amsa mata tana gaidata,suna tsaka da gaisawan mimi ta dami hajiya da batun anty widad "Tana daki,leqa kice idan ta gama tazo su gaisa da umminki,a kwashe kayana abincin nan ma a wajen" ta kuwa falla da gudu tayi dakin,abbas yabi yarinyar da kallo,yana jin shima kamar yabi bayanta. Sauke idanunsa yayi yana miqewa tsaye hadi da daukar wayarsa dake aje gefe "Kada ka fita fa,inason zamuyi magana ne ai" aninda ya dauke wutar magana cak a falon,kowa yayi shuru sai sautinta daya fita dake yawo,da mamaki ya kalleta,wacce magana ce da basuyita ba kafin ya fito sai a nan? "Hajiya wajenki nazo akan abbansu mimi" "Tooo.... ikon Allah,koma to ka zauna" hannuwansa ya sauke,ya koma hannun kujerar daya tashi a kai ya zauna,can qasan zuciyarsa nason darsuwa da bacin rai amma yana kaudarwa,tunda har yanzu baisan dalilin zuwan nata ba,saidai kwanyarsa nata son hakaito masa abinda ya faru da zai sanya tayi tattaki qafa da qafa har gaban mahaifiyarsa ta kawo qararsa,duk da bawai yau aka fara ba. Kafin takai ga cewa komai widad ta fito,riqe da hannun mimi sunata dariya abinsu,cikin wani lace sky blue da ratsin farin zare da aka yiwa dinkin tea bubu,bata daura dankwali ba sai siririn mayafi data dora a kanta mara nauyi kalar sky blue din. Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana sake zubesu a kanta,yaji wata nutsuwa na maye gurbin abinda keson motsawa daga zuciyarsa. Tare da qamshin nan nata ta iso,ya buwayi falon kuwa gaba daya,cikin ransa yake raya tabbas itama da qaunar turare cikin jininta,ta duqa cikin girmamawa ta gaida baba hassana. Kadaram kadaham ta amsa mata,tana qare mata kallo a fakaice "Tirqashi" ta fada qasan ranta ganin yadda yarinyar take sake juyewa,kyakkyawar siffarta da kuma kamanninta suna sake ninkuwa da bayyana kansu,idan akace za'a hadata da hafsat ko a yanzun ratar me yawa ce,balle kuma ace nan gaba?,ai sai abinda idanu suka gani,ita kuwa lami(mahaifiyar hafsa) tana aikin me?. Sanda widad din take gaida hafsan sai data tattaro dukkan qarfin halinta sannan ta iya amsa mata,gaba daya yarinyar tayi mata ba zata,tsahon wata dayan da bata ganta ba sai taga ta cika sosai,ta kuma fara zama cikakkiyar mace,gabanta yayi.mugun bugawa sanda zuciyarta ta laqana mata tambayar shin me zai kawo wannan sauyin?,ita kadai ta girgiza kai,bata yarda komai zai faru ba,a yadda abbas din yazo mata a zafafe jiyan ta tabbatar bai samu komai daga gareta ba,inda ya samu din ta tabbatar bazai zo mata a birkice haka ba,bataga wani sauyi daga wajensa ba duk sanda yayi mata zuwa irin wannan,saima qaruwa da abun yayi,duk da cewa taga wasu qananun sauye sauye,kamar mitar rashin shaving da turare a jikinta,saidai basukai mizanin da zata dorasu a komai ba,tunda batasan da zuwansa ba ai,ganinsa tayi katsam,bai kuma gaya mata yana da buqata ba ballantana ta shirya,kai koda ya gaya matan ma iya abinda zata iya shi tayi shi kuma zata ci gaba da yi. Motsawa baba usaina tayi "Bari na baku waje,naga kamar magana zakuyi" "Haba,kiyi zamanki,duka ba 'ya'yanki bane" hajiya ta fada da kyakkyawan nufi,dama haka takeso,don haka ta koma ta zauna din tana cewa "Hakane,ia bakaqi ba,kada aga kamar bakasan matsalar kowa ba sai taka,d'a ai na kowa ne, bare abbas da kowa yakecin moriyarsa?". "Ina jinki hafsatu,mene ya faru?,ina fata ba matsala bace" fara matsar hawaye tayi sannan ta magantu "Matsala ce hajiya, matsalar kuma abban mimi ne da kansa yakeson haifar da ita cikin gidansa" "Tofa!,tirqashi!" Baba usaina ta fada da madaukakin sauti bayan ta kama haba,yayin da abbas ya bude dukka idanunsa a kanta yana kallonta,tare da sauraren wanne kalar sharrin kuma zatayi masa "Mene ne ya faru?,gayamin" gyara zaman "Hajiya,kwata kwata abban mimi bambanci yake nunawa tsakanin da widad muraran,bayason huldarmu ni da ita,qiri qiri sai suzo weekend har su gama bazanga fuskarta ba bare ta zauna a gidanta ba,wasu ma basai suyimin sharrin na hanata zama ba?" "Laahhhh,da gudu kuwa,mutumin yau da baka iya masa?,tabdi" baba usaina ta karbe zancan "To bama haka ba,ta yaya zamu shaqu mu fahimci juna da ita hajiya tsakani da Allah,sannan su kansu yaran nan bakiga yadda sukeson zama da ita ba,amma gaba daya basu samun ganinta,a haka kan iyalinsa zai hadu?" Shuru hajiya tayi tana jinjina kai,maganarta ta qarshe ce kawai taja hankalinta,har takega tayi magana me ma'ana,baba usaina nason tsoma bakinta tace wani abu,amma kuma kwarjinin abbas din ya hanata,banda "Gaskiya ya kamata a aduba,saboda gobesu dana yaran" shi taketa maimaitawa "Kinzo da magana me kyau da ya kamata a duba,ki kwantar da hankalin ki, za'a gyara lamarin in sha Allah, Allah yayi muku albarka,ya qara hada kanku,ya wanzar da zaman lafiya a tsakaninku" "Ameen ameen.... yauwa,hakan dai yafi gaskiya,ta nan ne zasusan darajar juna,ita tasan darajar uwargidanta". Taso ta sake qirar wani abun,amma hada idon da sukayi dashi yasa ta kasa cewa komai,sai kawai ya miqe ya fice afalon ransa yana masa suya,fita yasoyi amma sai ya kasa,yana daya daga cikin kujerun dake harabar gidan ya zauna kawai,qafarsa daya kan daya yana dan jefata a hankali,bacin ransa yakeson dannewa,ba kasafai ya fiya son barin bacin rai yana masa tasiri ba. Ba jimawa baba usaina ta fice,daga bisani hafsat din ta fito yaran suna biye da ita,hajiya a bayansu tana rabawa yaran alawa da manyan biscuits data saba basu,daga inda yake zaune yana kallonsu,yasan babu lallai su ganshi,har suka fice daga gidan ya kasa motsawa sai rakiya da yayi musu da idanu. Sai da aka kira azahar ya fita masallaci yayi sallah,daya dawo sai ya bude setting room din gidan dake farfajiyar gidan ya kwanta,har yanzu abun yana masa yawo a zuciya,shi har yanzu baiyi girman da za'a daina kawowa hajiya da kawunnansa qararsa ba?,har yanzu baiyi girman da kunnuwan hajiya zasu daina jin matsalarsa da damuwarsa ba?,har yanzu hafsat batayi hankalin da zata zauna dashi su fahimci juna su warware matsalarsu ba shi da ita ba tare da duniya taji ba?,kansa ya kada a hankali yana kiran sunan Allah,ya rasa yadda zai rabata da wannan halin,bayan shi din har yau bayajin zai iya tuna wata rana da ya taba kai qararta gidansu ba. Wayarsa dake saman kansa ya dauko,ya lalubo number dinta dake rubuce da sunan BABY DOLL ya kira, ringing daya aka daga,muneera ce,ta gaya masa sallah takeyi,yace idan ta idar ta gaya mata ta sameshi a setting room,ya ajjiye wayar yana gyara kwanciyarsa. Minti biyar cikakku qamshinta ya fara marabtarsa,ya rufe idanunsa yana budesu,suka sauka a kanta,hannunta dauke da madaidaicin tray data dora wani glass jug akai da qaramin cup guda daya. Ido ya zuba mata yana qare mata kallo son ranshi,kamar kowanne lokaci sai yaji damuwarsa tana raguwa,a nutse ta iso ta sunkuya a gabansa tana ajjiye masa jug din,sai ya fara yunqurin tashi,ta miqe zata ja baya ya samu nasarar riqota,yayi mata mazauni saman cinyarsa,kunya ta sanyata boye kanta a kafadarsa,taqi yarda su hada ido "Ki kalleni please baby.......zuciyata ba dadi,nasan zan samu relief" har cikin zuciyarta taji wani abu ya tabata da fadin hakan,saita daga kanta da sauri,kodai qarar da mommy hafsat ta kawowa hajiya ce ta bata ransa?,ta tuna kalaman mommynta na qarshe "Banda kai miji qara,abune mara kyau,koni bance ki kawomin qararsa ba,idan ya bata miki rai ki gaya masa ku fahimci juna" sannan ta tuna da kalaman ummunta "Kome mijinki yayi miki ya isa ne,banason qorafe qorafe dakai qara" sannan tana tuna yadda take sanya yayyensu a gaba da fada duk sanda kika kawo mata qorafi akan mijinki,musamman idan bai gamsheta ba "Kayi haquri" ta furta da tausasan labbanta da ko yaushe suke burgeshi,har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,ya rabb......ba ita tayi laifi ba,amma ita take bada haquri,ya tabbatar idan zai dige indai ba wuya ce tayi wuya ba zaiyi wahala wannan kalmar ta fita a bakin hafsa "Zan haqura,amma saikin yarda na taba nan" ya fada yana mata nuni da qirjinta da yadan sake cika,da sauri ta kama hannunsa da yayi mata nunin dashi tana fidda ido waje,saidai kafin tace wani abu ya langabe mata kai kamar ba shine babansu mimi ba "Don Allah,kiji tausayina mana" kafada ta noqe masa itama tana shagwabe masa "To na kwanta agun ko na minti daya ne,idan kikace aah fa zanyi kuka" dariya yaso bata,amma tsoro tsoron da takeji ya danneta,kafin ta bashi amsa ya kama dukka hannayenta biyu ya riqe cikin nasa,ya kuma cusa fuskarsa da kyau tsakanin qirjin nata. Sosai ya zuqi numfashi ya kuma fesar,ta lumshe idonta tana jin yadda dumin numfashin yake ratsa ta tun daga rigarta zuwa brassiere dinta,ya kuma tarar da fatar wajen. Wani irin abu data kasa daurewa ya zarce dayi mata yana sake cusa kansa a wajen,ta zame hannuwanta daga cikin nasa ta riqe kansa da kyau,sai ya tsaya cak jin yadda jikinta ya dauki rawa,ya kuma zare fuskar tasa,ya sauke idanunsa da suka kada sukayi jaa saman fuskarta. Sai daya dauki wasu sakanni yana kallonta sannan ya motsa bakinsa cikinn shaqaqqiyar muryasa yace "Ina da buqatarki baby.....ina da buqatarki gaba dayanki,rayuwata na da buqatarki fiye da yadda ruhi yake da buqatar numfashi" kalaman sun mata nauyi sosai,saita kifa kanta kawai a qirjinsa bugun zuciyarta na qaruwa. Sun jima a haka kafin ta zame jikinta ta sauka qasa ta bude jug din,smoothie ne na banana da yasha madara data jefawa qananun ice cube a ciki yayi madaidaicin sanyi,ta tsiyaya ta miqa masa a cup. "Na gode" ya fada yana karba,kunyarsa tasa ta sakin murmushi kawai,ya kurba ya lumshe ido,dadinsa yana ratsa kunnuwansa "Yaushe kika koyi wanann?" "Jiya,yayi dadi" sai daya jijjiga kai sannan yace "Over!" Yadda ya fada din ya bata dariya *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 83 "wait.....amma fa da matsala" saita tsaya tana kallonsa da idanuntan nan dake cike da quruciya da rashin wayau a wasu lokuttan,muryarsa ya sassauta sosai "Eh mana,wannan abun da gani zai haifar da tashin hankali.......idan nasha ya zamemin matsala babu me saukemin hayaqin da zai tashi a kaina,gashi kedin raguwa ce,first night saida kika ziyarci asibiti" curewa tayi guri guda tana cewa "Wayyo Allah ummu na" "Wayyo Allah hajiyata,sonta zai kashe miki danki" ya fada cikin murya mai taushi qasa da tata jikinsa yana saki gaba daya. Kasa jurewa tayi,saboda bugu da zuciyarta keyi,saita zane ta fice da sauri,ya bita da kallo hade da murmushi,haka auren me quruciya yake da dadi?. Wayarsa dake ringing ce ta dawo dashi daga tunanin da ya lula,sai ya daukota yana duba me kiran. Suraj ne,yadan shafi kansa kadan kafin ya daga,don yasan sai yasha qorafi. Suna gama gaisawa qorafin kuwa ya biyo baya "Ban san ko widad din ce ke boye ka ba kuma,tunda dai daa ba haka kake ba" murmushi ya saki yana kurbar smoothie din "Yanayin aiki ne kawai" "Anyway,next week zamu shigo kadunan da madam" "Yayi,aikin ya biyo ta garinmu kenan" abbas ya fada,sai kuma suka fada wata hirar. Ranar bai bar gidan ba sai bayan magariba,yana isa unguwarsu ana sallar isha'i,ya tsaya a masallacin layinsu yayi sallar sannan ya isa gidan. Kamar ko yaushe,koda meye tayi masa baya fasa shiga sassanta idan ya dawo,ba don komai ba sai don yaransa,ya samesu kwance qasan carfet bacci yayi awon gaba dasu,ya tsallaketa tana zaune tana waya yasa hannu ya kwashesu ya kaisu dakinsu,duk da dakin ba'a kintse yake ba,amma kuma yafi falon data barsu,ya gyara zanin gadon ya kwantar dasu,ya duba laundry basket dinsu da yake cike taf da kaya da uban bedsheet dinsu masu kyau da tsada,amma sunyi datti kuma bata da lokacin da zata tsaya ta hadasu ta zagaya baya inda washing machine yake ta wanke ba,ko ta bayar wa sale yaron gidan ya wanke su ba "Allah ya sawwaqe" ya fada a fili,yana raya a ransa gobe zai zauna da kansa ya gyara musu dakin nasu ya fidda kayan ya bayar a wanke musu kafin ya koma,don yaci alwashin ya daina mata gyaran sashe,tunda abun nata sake ci gaba yakeyi. Kafin ya fito ta hattama wayar,saita sauke qafafunta dake saman center table tana fadin "Sannu da zuwa" "Yauwa" ya amsa sama sama yana zama hannun kujera,yayi imanin zaiyi wuya ya zauna cikin kujerar baici karo da danshin ruwa lemo ko fitsari ba "A kawo maka abinci?" Ta tambayeshi tana danna waya,sai ya girgiza kai sannan yace "Ajjiye wayar nan zamuyi magana" dan kallonsa tayi sannan ta aje wayar tana kallonsa "Nace shekararmu nawa yanzu da aure?" Dan jim tayi sannan tace "Kamar shida cikin ta bakwai" "Good......me yasa har yanzu kika kasa fahimtar zahirin rayuwa hafsa?,me yasa har yau kika kasa gane kina tafka kusakurai da hankalinki ya kamata ace yakai kai kin kuma gyara" fuska ta bata sosai "Wanne kuskure kuma nayi?,wai don Allah me yasa bakason zaman lafiya abban mimi?" Da ido ya tsareta,saita kauda nata idon daga kansa,ta sani nashi idanun yafi nata kaifi nesa ba kusa ba,ta hade rai sosai,ya janye idonsa yana miqewa hadi da saka hannunsa a aljihun wandonsa yana kallonta,baisan me yake damun kanta ba,gidadanci ne ko rainin wayo?,komai ka gaya mata ba zata gane ba, batasan maslaha ba batasan fada ba,duka dai dai take daukan kowanne,tunda taqi fuskantar alqibla,bari ya bita da zafi zafi tunda ya fahimci tafi ganewa hakan "Tunda baki ganewa kuskure ko laifi......fine,gobe banason na tashi na samu wannan tulin qazantar dake sassan nan,idan ma ke tana miki dadin zama ne a cikinta,to karki sake na samu daki da jikin yarana a yadda na sameshi yau" ya qarashe maganar a zafafe,sannan ya juya da dan hanzarinsa ya fice daga sashen. Kamar idanunta zai fado saboda kallon data bishi dashi,kallon da inda yana tsaye ne a gabanta bata isa tayi masa shi ba,taja dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta,ta rasa wanne kalar miji Allah ya hadata dashi,taurin kai kafiya da kuma tsatstsauran ra'ayi,dole ta tattare komai.nata ta wuce daki,gwara ta kwanta da wuri ko ta samu ta tashi da wuri ta gyara iya abinda take ganin zata iya,a goben ma idan widad din bata dawo ba to tabbas zata dauki mota taje ta daukota da kanta ta dawo da ita cikin ruwan sanyi da kwantar da kai,ta yadda babu wanda zai fahimci manufarta. **********Ranar lahadi,ranar daya zamana saura kwana guda suraj da matarsa suzo,yana gida ranar,don haka duk wasu ayyuka shi ya kama mata sukayi tare,suka gyara kowanne daki yadda zai dace da zaman kowa a cikinsu. Dakinta ne na qarshe,sun gama komai tare,ta tsaya hannayenta riqe a qugunta tana kallon yadda ya sauya fasalin dakin tana murmushi. Sanda take kallon dakin shi kuma ita yake kallo,wani short rubber wando ne a jikinta,wanda da kadan ya wuce gwiwarta,sai kuma rigar kayan mai gajeran kayan data fidda shape dinta sosai. Da wani siririn rubber band kalar kayan jikinta ta daure gashin kanta,hakan ya baiwa doguwar jelarta mai santsi damar reto a bayanta. Kusan yaune ranar farko data fara irin wannan shigar saboda aikin da zasuyi,amma iya yau din gaba daya ta hanashi sukuni,duk inda ta motsa idanuwanta suna biye dashi "Finished uncle" ta fadi tana dubansa tana murmushi,sai ya mayar mata da murmushinta,yanason ya gaya mata ta debi wasu kayan nata da zatayi amfani dasu ta maida dakinsa amma kuma bayason plan dinsa ya rushe,gwara ya barta a hakan,sannu sannu bata hana zuwa. *W A S H E G A R I* K'arfe uku na rana su suraj suka iso kaduna,bilkisa matar suraj akwai fara'a kirki da kuma saurin sabo,tun ba yau ba suna hira sosai da widad din ta watsapp,wannan yasa ba wani baqunta can me yawa a tsakaninsu ba. A nan falo suka zauna bayan abbas ya shiga musu da kayansu ciki,suka koma balcony din sashen suka zauna sukabar su widad din a falo. Basu rufa mintuna ashirin ba aka kira sallar la'asar,saida dukkansu suka bada farali sannan suka zauna zaman cin abinci,su suna balcony din saman lallausan carfet,ita da bilkisa suna zaune a falon,suna ci suna taba hira. K'arfe takwas na dare ta shigo dakin da bilkisa ta sauka,rigar bacci ce a jikinta wadda ta sauka har kusa da idon sawunta,saita dora hijabi a kai wanda bai wuce qugunta ba. Da murmushi bilkisa dake gaban mudubi tana fa shafe shafen turaruka ta waiwayo tana amsa mata,widad ta qaraso tana hayewa saman gadon gami da jan pillow "Na zaci har kin kwanta" kai ta girgiza "Ina ni ina bacci mai gidana bai dawo ba" qaramin murmushi widad ta saki tana rayawa a ranta "Kamar wani qaramin yaro" duk da cewa ita dinma tun dazu take leqawa ta window idan taji motsi taga ko uncle din nata ne,tunda suka fita bayan sun gama cin abinci basu dawo ba. Duk da sun sha hira sosai da balkisa,ta kuma debe mata kewa amma sai takejin gidan gaba daya wani iri babu dadi "Nima har na fara jin kamar bacci bacci" ta fada tana maida pillow din saman gadon zata kwanta,sai bilkisa ta juyo da sauri tana dubanta "Aah.....shi kuma abbansu ahmad din na kaishi ina?" "Zasu kwana tare da uncle fa" ta fada adan shagwabe "Aah wlh ban gayyato ki ba,haka kawai kisa nayi baqinjini wajen yallabai yana ganin mutuncina?,daga zuwana na rabashi da amaryarshi" "Mom Ahmad wallahi kema kin faye tsokana" widad ta fada tana gyara kwanciyarta,bilkisana qoqarin saka wandon sleeping dress dinta tace "Banda quruciya dake dawainiya dake..... yaci ace kin karanci irin kallon da yake binki dashi duk sanda kika gifta ta gabanshi,ina tsoro nan gaba kada yallabai ya fara tafiya yana kiran sunanki,idan haka ta faru kam hafsat inajin hadiyar zuciya zatayi ta mutu" "Kai mom Ahmad kai anty bilkisa" widad ta fada tana dariya sosai,don ita dariya ma maganar ta bata "To ita kuma mommy hafsat me zai sakata mutuwa don kawai uncle na kiran sunana?" Tambayar data sanya bilkisa maida dubanta sosai ga widad,da alama dai har yau batasan wace kishiya ba,batasan kuma kishi ba,uwa uba batasan wace hafsat sani na badini ba,kallon zahiri take mata "Kishiya irin hafsat ba zasu taba son suga miji irin uncle dinki.yana sonki ba,ba zasu taba so suga kina masa wani abu da zaiji dadi ba" "Amma mom ahmad,ni bata taba nunamin komai ba" kallonta sosai ta sakeyi "Ta gama yi miki komai din ai ba tare da kin ankara ba,saboda tasan ba lallai tunaninki ya kawo miki komai ba a kai" Shuru widad tayi tana juya maganar,zancan da suka taba yi da anty madeena ya dawo mata sanda take gaya mata ba gaskiya bane abinda hafsat din ta dinga gaya mata tana tsoratar da ita,to me hakan ke nufi?,wannan shine kishin?,idan kuwa shine yafi kama da HASSADA kawai "Idan kina tantama daga yau ki sake mata dukkan aikin da kike mata.....ki kula da uncle dinki,don nasan har yanzu idan ta samu dama sakaki aiki takeyi" maganar bilkisa ta saka widad a tunani sosai,kafin tace komai muryoyinsu sun bayyana a falon alamun sun dawo. Tare suka fita da bilkisa din,saidai suraj din kawai suka samu yana shirin shigowa ciki,dole widad ta yiwa bilkisa sallama ta wuce nasu dakin. Ta tura dakin ta shiga,baya ciki amma ga kayanshi nan saman gadon,sai ta qarasa a hankali ta debesu,ta ninkesu sannan ta zubasu a laundry basket,takalman ma tayi musu waje,sai ta koma kan sofa bed ta zauna ta kunna data dinta ta shiga watsapp tana duba saqonni. Qofar bandakin ya bude ya fito,daure da towel da ya daurashi daga qugunsa,duka duka tsahonsa kuma iya gwiwa,duk wata qirar jikinsa ta bayyana a waje sosai,qaqqarfan jiki daya ginu da excercise. Bata zaci a haka ya fito ba....wannan yasa ta daga kai,saidai suna hada ido tayi saurin maida idanunta kan wayar tana raba idanu. Karamin murmushi ya saki,har cikin zuciyarsa yana jin dadin yadda ta kasance,amma a fuska bai nuna ba,yadan basar duk da yadda taketa fusgar hankalinsa,don already ta cire hijabin ta ta ajjiye don tasha iska,yadda ta nannade gashinta yayi masifar jan hankalinsa. Sannu da zuwa tayi masa tana ta babbasarwa,ya amsa mata yana janta da hira,yayi kaman bai gane ba,ya tsaya gaban madubi yana shiryawa yana satar kallonta ta ciki,cikin dace ya dinga kamata itama tana satar kallonsa,amma duk sanda ya gani din saita bagarar,abin ya dinga bashi dariya sosai,amma ya dinga cinyewa cikin miskilancinsa,har ya gama shirinsa tsaf cikin dakin ya kuma zauna ta zuba masa abinci ya soma ci. Yana cin yana kallonta da lumsassun idanunsa har ya kammala,cin abincin da da wankan sun ja masa kusan awa biyu,zuwa sannan jikinsa ya gama saki,gaba daya muradinta yakeyi,sai ya miqe,ya zare kayan jikinsa,yabar iya boxer kawai,ya koma saman gadon ya kwanta rub da ciki yana lumshe idanunsa. Shuru ya ratsa dakin,sai ya bude idonsa a hankali ya zube a kanta,daga yadda take zaune yasan itama kwanciya takesonyi amma tana shakkar rabarsa "Baby...." Yayi kiranta a tausashe,muryarsa can qasan maqoshinsa,saita daga fararen idanuwanta ta kalleshi, idanunsu suka gauraya waje daya,wani abu taji ya taba zuciyarta sosai "Am very tired........zo kiyimin tausa please baby" ya fada yana narkewa hadi da yin fuskarsa tausayi,idanunsa suna lumshewa saman fuskarta,yana jin kamar yakai gareta ya fusgota. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 84 Yadda yayi din sai ya bata tausayi,don haka ta ajjiye wayar tana cewa "Wai tausa da dadi ne?" Dariya ta taso masa amma a yanayin da yake ciki batayi wani tasiri ba,ya maye gurbin ta da murmushi don ta bashi dariyar sosai can qasan ransa "Sosaima" ya furta a hankali yana lumshe idanunsa sanda tattausan tafin hannunta ya sauka a tsakiyar bayansa. Tun tana dari dari har ta sake,ta dage ita bilhaqqi da gaske tausa take masa,yayin da idanunsa suka kasance a rufe,yana jin yadda hannuwanta ke kai komo a bayansa,shi kadai yasan abinda yake ji cikin ruhi da gangar jikinsa. Kasa daurewa yayi,cikin wani irin zafin nama yayi mata wani irin juyi ya maidata gurbin daya tashi shi kuma ya maye nata gurbin ta hanyar mamayeta gaba daya,hadi da yi mata rumfa da mayalwacin qirjinsa. Tsoro ya gani a rubuce cikin idanunta,ta soma rarrabasu tana kallon gajiyayyar fuskarsa dake cike da shauqi da mayen so da qaunarta,da kuma burin kasancewa da ita. A tausashe ya rungumota cikin jikinsa,fatarsu ta hade guri guda,dumin jikin junansu ya gauraye waje daya,ya sanya kansa cikin wuyanta ta soma gaya mata wasu kalamai da suka saukar mata da nutsuwa,suka kuma sakata narkewa a wajen ba tare data sake qwaqwqwaran motsi ba. Cikin salo da kuma qwarewa ya fara aike mata da wasu saqonni da dukkan jikin da jini ke gudana a cikinsa zaiyi wuya ya tsallake musu,saqonnin da suka dinga bin dukka wata jijiya dake aike da tunani da kuma tantance abu suna tsinketa,suka dinga dilmiyar da ita zuwa wani bigire na daban,bigiren da dukka wani tsoro nata ya gushe yayi nasa waje. Saida komai ya kankama sannan ta fara gani kuskuren data tafka,tuni aikin gama ya gama,ya sake tabbatar wa zuciyarsa da gangar jikinsa cewa ita din mallakinsa ce halak malak. Kamar wancan karon,wannan karon ma yanayi ya shiga sosai,ya riqeta sosai cikin jikinsa yana sauraren siririn kukan da take fitarwa,wanda kusan fiye da rabinsa shagwaba tafi yawa a ciki,yasan yau dinma dole zata jigata ta kuma ji jiki,don shi kansa yasan halinsa ta wannan fannin,amma kuma bazai kai karonsu na farko ba,baiji komai ba ya biye mata ya dinga lallashin abarsa,yana kuma dauke kowanne hawaye nata da harshensa. Jinta yake takai masa ko ina,koma meye zai iya yi mata,haka ya lalace wajen rarrashinta. Har sukayi sallar asuba suka idar taqi duban fuskarsa,ta gaidashi kanta a qasa,ya saki murmushi,ya matso kusa da ita ya zauna sosai har gwiwoyinsu suna haduwa,yasa hannu a hankali ya janye hijabinta baya,kyakkyawar fuskarta ta bayyana,ya sanya hannu ya kamo tafin hannunta ya saka cikin nasa yana ci gaba da kallonta "Fushi ake dani baby?" Ya tambayeta yana narkewa kamar shima zai sakar mata kukan,kamar jira takeyi ita saita rigashi,ta sakar masa nata kukan qasa qasa "Ba kaine ba......shine ka yimin wayo,saboda kaga ka girmeni" tayi maganar tana mele baki,kaman zaiyi dariya amma sai ya danne "Am sorry,nima fa ba'a son raina ba,bansan nayi ba sai daga baya" "Kuma fa gidan nan kasan akwai baqi,yanzu idan mom ahmad ta gane me zance mata?" Dariya sosai ta sake kamashi kamar yayi me,amma ya tabbatar idan yayita yanzu zai jama kansa jagwal "Waye yace miki ana ganewa?, ba'a fa ganewa kayi,kuma ma....." Sai yayi qas sosai da muryarsa,ya sake matsowa da fuskar sa dab da ita kamar zai shige cikin hijabin ".....kowa yanayi,itama nasan sunyi jiya......." Bata barshi ya qarasa ba ta cure waje daya cikin hijabinta "....don Allah uncle" a wannan lokacin kasa boye dariyarsa yayi,ya dora fuskarsa saman qafafunta yayi dariyarsa sosai yana jin nishadi yana wanzuwa a rayuwarsa. **********Sati guda daya rak amma dai dai yake da wasu shekaru a wajensa,sati guda daya daya canza rayuwarsa da tunaninsa,tayi wani mugun tsayawa cikin rayuwarsa,ta kuma barma zuciyarsa wani babban tambari da yakejin har duniya ta nade bazai taba goguwa ba. Jinta yake sosai a ransa,wani irin ji da yake ratsa zuciya matuqar ratsawa,tattali qauna da soyayya yake nuna mata irin wadda idanuwa basu saba gani ba,wasu abubuwan shi da kansa baisan yana yinsu ba,ta mantar dashi dukka wata damuwa tasa da matsalar da yakejin yana ciki. Duk da bata gama sakewa dashi gaba daya ba,amma zai iya cewa ya samu fiye da rabin abinda yakeso,ya sani cewa da zarar ta sake sanin darajarsa ta kuma sake hankali da wayo,zai shiga sahun mazan da sukayi sa'ar matana aure a duniya,wani irin qauna da kimar hajiyarsa ke sake kwaranya a zuciyarsa,uwa uwa ce......uwa daban take,ashe irin wannan take ta kwadayin samar masa shi yasa ta dage cikin qanqanin lokaci sai data shigo da widad din cikin rayuwarsa?. Ta fannin widad din ta sake zama wata tabararriya ta gaske,shagwabarta take zubawa yadda taga dama,biye mata yakeyi,ta koma tamkar su mimi,ko tari tayi sai ya tambayi ba'asi,duk wani koke koke da take masa a duk sanda ya samu yadda yakeso sam basa damunsa,yasa hannu ya karbe ya kuma shnaye dukka rigimarta,hasalima shagwabarta na daya daga cikin abubuwan dake saurin kunnoshi da rura wutar soyayyarta a zuciyarsa,wannan ya sake haifar da shaquwa tsakaninsu shi da ita,duk da har a lokacin yana tantamar tasan kalmar so?,abu na qarshe da yakeson ya gina gini mai ingancin da bazai rushe ba cikin zuciya dama rayuwarta gaba daya. A qarshen watan ya gama yanke shawarar meye mafi girman tukuci da zai bawa rayuwarta?,yana tsaka da wannan tunanin saiga kyautar kujerar hajji har guda biyu daga wajen tsohon governor ya bashi kyauta,yayi masifar jin dadin aiki da abbas din,kuma har yau yana yaba masa,wannan yasa time to time yake tabo abbas din,inda tason ran Excellency dinne da tuni abbas din ya koma aiki qarqashinsa,saidai shi bashi da wannan interest din,dole ya haqura ya qyaleshi,amma lokaci lokaci yana taboshi akan wasu harkokin tsaro da suka shafeshi,kamar yanzun da zaiyi tafiyar,yaji ba wanda ya dace ya tafi dashi da yafi abbas din. A lokacin babu wanda yaga ya dace da wannan tafiyar sai widad din,don haka ya karba daya yasa sunanta a daya ba tare da tasan ma da kujerar ba,aka soma processing na tafiyar,wadda zasu yita ne in group cikin tawagar his Excellency din. Cikin sati na gaba suka shirya zuwa bauchi,tun bayan zuwan da sukayi suraj da matarsa sukazo musu basu sake zuwa bauchi ba sai a yanzu. *********Karon farko data zauna ta hadawa abbas din kayan tafiya bauchin,a lokacin ya fita office,baisan ma ta hada din ba,sai daya dawo daga aiki,ya buda akwatin,ya jima tsugunne yana kallon luggage din, murmushi yana kubce masa,yadda ta shirya masa komai kamar shi da kansa ya shirya kayan nasa,ya girgiza kai ya miqe yana jin qaunarta tana sake ninkuwa cikin ransa,tasan buqatarsa,tasan choices dinsa tun yanzu. Kai tsayr toilet ya shiga ya gama wanka ya fito,yana tsaye gaban mirror yana tsane ruwan wankan dake jikinsa,wanda ke fidda qamshin daddadan turaren wankan daya cakuda dana shower gel dinsa,fuskarsa yake kalla,cikin kwanakin har wani canzawa yaga yayi,kuzarinsa ya qaru,kamar yadda yaga yadan sake cikowa,fatarsa kuma ta qara haske kamar mai amfani da wani mai na daban. Ana taba qofar ya maida idanunsa ga bakin qofar,ya kasa ya tsare yana jiran shigowarta. Da sallama ta shigo cikin siririyar muryartan nan,sanye take da wata fara sol don smoked gown,kanta babu dankwali sai farin ribbon data matse sassalkan gashinta,fuskarta fes yau babu digon komai saina man lebe da ya sanya siraran lips dinta suketa qyalli,ba shiri ya saki comb din ya waiwayo harde da hannayensa a qirji yana qare mata kallo. Shigar yau ta fidda asalin tushenta wato larabawa,kamar diyoyin larabawan da suka samu kyakkyawan kulawa,rigar ta karbeta,haka gyaran data yiwa gashinta wanda gaba daya wani abune da bilkisa ta koya mata kafin su tafi "Bakison kiga uncle din yafi ji dake akan kowa?,to haka zaki dinga yi,ma sha Allah,inda nice da wannan jikin naki da wannan gashin.....ai da tuni na kori hafsat" ta fada tana qyalqyala dariya,don dama sam babu jituwa tsakaninta da hafsat din,duk da amintakar dake tsakanin mazajensu, bilkisa bata daukar raini ko wulaqanci,hakanan dama tun usul ita bata jituwa da marowacin mutum,wadan nan siffofi kuwa dasu hafsat tafi shuhura,wannan dalilin yasa matan abokansa da suke manyan mutane masu manyan muqamai iri daban daban a gwamnati suka janye jiki daga matarsa da gidansa,don babu wadda kejin dadin mu'amala da ita,idan sunzo gidan sai dole,kamar haihuwa da sauransu. Dukka hannayensa ya bude mata,yana mata alamar ta taho,saita tsaya daga bakin qofar ta noqe kafada tana tura baki gaba,tana tuna azabar da tasha daren jiya a hannunsa "C'mon mana baby doll,nayi alqawari fa bazan sake ba har sai kin yarda" "Promise?" Kai ya jinjina yana murmushi sannan yace "Amma kada ki manta,kema kinyi alqawarin zaki barni nayi komai banda wannan abun dai....." Yadda yayi maganar a narke shi kansa zaka dauka yarone dan shekara tara ko goma,abun ya bata kunya sosai,ta sanya zara zaran fararen yatsunta ta lullube fuskarta tana dariya,sannan ta fara takowa a hankali zuwa gabansa,yayin da shi kuma ya kafeta da ido yana jiran ta qaraso,bugun zuciyarsa na daduwa,yanajin kamar tana ja masa aji ne,kamar bata sauri. Taku biyu ya qara ya cimmata a hanya,ya durqusa gabanta ya lullubeta cikin ingarman qirjinsa dake cike da muscles da gargasa suka yiwa tufa,haka qirar jikinsa yake tun asali,wannan ya qara masa interest na shiga aikin police. Cikin abinda baifi second goma da shiga jikinsa ba dukka jikin nasa ya dauki rawa,ya cusa kansa a wuyanta yana shaqar qamshinta da har yanzu bai sake jin wani qamshi da yake burgeshi kamarsa ba,yadda bugun zuciyarsa ya qaru haka speed na fitar numfashinsa,banda girman alqawarin daya dauka babu abinda zai hanashi karyashi. Tayi lamo a jikinsa ita kanta,tana jin yadda numfashinsa ke kewaye fatarta yana ratsata har cikin qashi,ko qwaqwaran motsi batayi ba,wani yanayi yana sauka a jikinta,har ya haqura don kansa,ya daga kansa a hankali zuwa ga fuskarta yana riqe da fuskartata a tsakanin hannuwansa "Ki rage tsoro don Allah baby.....i love you" murmushi ta saka a kunyace tana son sake boye kanta,sai ya miqe yana cewa "Nooo.....wannan kwalliyar na siyeta har fuskar,zan biya.....don Allah a barni na kalla" cak ya dagata ya azata saman madubin,ya jawo dressing chair ya zauna akai ya buda lotion dinsa ya fara shafawa,yana shafawar yana duban fuskarta hadi da tsokanarta ta hanyar tuna mata da abinda ya faru daren jiya. Kukan shagwaba ta sakar masa tana bubbuga qafafunta "Nidai Allah uncle......Allah.....Allah" dariya ta dinga cinsa,irin abinda bata taba gani ya sake haka yana dariya ba "Shikenan.....wasa nake miki,na daina,amma bakiji bane?,nima fa na kira hajiya har bansan adadi ba,na dauka mutuwa zanyi,yarinyar nan haka kike da......" Ba tare data shirya ba ta saka hannunta ta rufe masa baki idanunta dukka a waje,tana jin kamar qasa ta tsage ta shige,sai kawai ta nemi silmiyowa daga saman madubin,cikin zafin nama ya tareta da cinyoyinta,sai gata zaune sosai a samansu "Yarinya kin kawo kanki" ya fada a tausashe murmushi na kubce masa. °°°°°°°°°Karfe goma na safe suka fito shi da ita,kallo daya zakayi musu kaji sunyi mugun burgeka,kamar hadin baki,shi da itan duka shigar sky blue sukayi,shi shadda ainihin gezner ya saka,ita kuma wani lace ne cotton mara nauyi. Yau din bai nema wani dan rakiya ba,shi da kansa yayi driving nasu daga kadunan zuwa bauchi,duk da jirgi ma yaso subi,amma sai yaji yana da muradin awannin da zasuyi a tare cikin motar waje guda kafin su isa kadunan,don yasan dole kuma ya bawa hafsan lokaci kodon fita hakki,amma for now ya fara tunanin yadda zai dinga raba musu kwana duk lokacin da suka je bauchi,musamman idan zaiyi kwanakin da yafi biyu. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 85 Yau din tunda suka tashi daga kaduna basu tsaya ba,don bata jima ba bacci ya dauketa,don dama yawanci saboda ita yakan tsaya din,ya samar mata wani abun da zataci,to har suka je inda yakan tsaya din suyi sallah da sauransu tana baccinta,don haka ya wuce abinsa kai tsaye,lokaci lokaci yana waiwayawa ya kalleta,yana monitoring baccin nata. Bata farka ba sai da suka shiga unguwarsu,tadan kalleshi,suka hada ido,yasan me takeson cewa,gidan hajiya takeson zuwa,to amma bayajin zai iya barinta,tunda duka duka kwana hudu zasuyi su juya,suya saki murmushi kawai ya shafi gefan fuskarta "Ba kwana gidan hajiya wannan karon,i need you by my side" shuru tayi kawai,ta langabar da kanta gefe guda ba tare data ce komai ba,duk da ba haka taso ba cikin ranta. Yana gama parking kusa da motar hafsat din data dauki qura mimi na shigowa ita dame daukota daga makaranta,ganin motar babanta ya sanyata tahowa da gudunta tana kiran sunansa,ya dagata ya rungumeta yayi kissing dinta,saita zame daga jikinsa ta koma wajen widad. Ta yima widad din nauyi,amma saita riqe hannunta tana tsokanarta hadi dayi mata waqar 'yar makaranta,tana ta dariya,dadi ya cika yarinyar,ko banza tana samun nishadi kulawa da kuma canjin rayuwa a duk sanda baban nata da antyn nata sukazo. Kamar sama sama take jiyo muryar mimi din tana kiran sunan baban nata,sai taja tsaki ta share,a ranta tana jin haushin yadda yarinyar keda qulafucin ubanta,tana tsoron gaba kadan ma zaiyi wahala idan batafi sonta akan uban ba,saita ci gaba da lissafin kudinta,amma kuma jin shiru bata ji motsin mimin ba,saita ajjiye wayarta da take lissafin a ciki ta miqe tana gyara daurin zaninta,ta sako kai zuwa harabar gidan. Dai dai sanda sale ke cire kayansu a booth din motar,abbas din yana gaya masa kada yayi nisa zai kaishi kasuwa. Cikin wani mugun mutuwar jiki ta sauke hannuwanta data tokare bakin qofa dasu "Kanbun bal bala'in bala'i!" Bakinta ya furta duk da batasan yaushe hakan ta faru ba,daga inda take tsaye tana iya hangen widad wadda ke riqe da hannun mimi,fuskarta kwance da murmushin daya qarawa fuskar tata kyau da kuma kwarjini "Wanne irin girma ne haka cikin wata guda kacal?" Ta tambayi kanta da kanta,har yanzu idanunta na saman fuskar widad din,ko sau daya ma bata waiwayi inda abbas din yake ba. Takawa ta soma yi zuwa inda suke tsaye a hankali tanason sake gasgata abinda idanunta ke nuna mata,saidai duk taku daya idan tayi bugun zuciyarta sai ya qaru,kyau da yadda girma ya fara nunawa a jikin widad din suka soma bata mamaki. Qaramar jakarta abbas ya dora mata saman mota bayan ya kulle motar "Keda mimin banga marabarku ba" yayi maganar yana kafeta da idanu hannayensa duka biyun cikin aljihun rigarsa. Dariya ya bata,tadan juya ido cikin irin nuna mamakin nan,saidai hakan batasan mugun kyan da ya qara mata ba "Uncle kace na girma fa?" Har tsakiyar zuciyarsa ta aike da saqo,bayason yayi saurin bada kai tun yanzun,tunda dai nan ba kaduna bace "Yes.....amma ga jakarki nan,ki dauka sai mu gani" ya fada tsadajjen murmushin nan nasa yana fita daga fuskarsa. "Uncle itama wannan din da nauyi don Allah....." Widad ta fada cikin shagwabar data saba yi masa "Ya salam" ya fada yana miqa hannu hadi da dauke jakar,yayin da hafsat taji tana shirin faduwa,sai takai hannu tana neman abinda zata riqe gudun faduwa,hannunta ya sauka kan kyakkyawar luggage din widad guda daya da tayi saura sale bai dauke ba. Hannunta ta janye,mamaki yana sake kasheta,gata kusa da wajen amma cikinsu ba wanda yama lura da wanzuwarta a wajen,wani tunani yazo mata,tayi qoqarin saita kanta ta hanyar yin gyaran murya kadan,abinda yasa duk suka waiwayo "Sannu da zuwa,saukar yaushe?" Tayi maganar tana tsare gida hadi dayin kicin kicin da fuska,sannan ta miqa hannu tana son karbar jakar widad dake hannunsa a zuwan tasa ce "Yanzu ne,ko kayanma ba'a gama daukewa ba" "Fitar wuri kukayi kenan" ta sake fada tanason calling attention dinsa,sai ya dan gyada kai,abun nata nayau yana dan bashi mamaki "Ina wuni" widad ta fada ba tare data dubi sashenta ba,haka kawai takejin wani abu mara dadi yana dan taba zuciyarta,taji kuma.ba zata iya gaidata yadda ta saba ba,sai hafsat din ta waiwaya tana kallonta,sai a lokacin ta sake ganinta sosai "Oh..... amarya lafiya lau" can qasan ranta tana dan mamakin yanayin data gaisheta dashi,ba haka ta saba gaisheta ba dashi,ta saba ta gaisheta tana fara'a bayan ta rusuna mata,sa'an nan idan tayi kamar bata ji ba sai ta sake maimaitawa "Ba jakata bace ta qanwarki ce" ya fada yana kulle motar sanda yaga tana nufar sashensa da jakar "Oh, okay" ta fada tana dawowa baya inda widad ke tsaye da mimi,kai tsaye ta miqa mata jakar,don dama abinda takeso kenan ta karba kayarta. Ba tare da nufin komai ba ta kalli abbas din a shagwabe "Allah uncle da nauyi,kuma kace zaka kaimin fa" "Bance na fasa ba ai" ya fada yana miqawa hafsat hannunsa,kamar sakarya ta sakar masa jakar,xallar mamaki yana cikata,ta bishi d kallo sanda yake cewa "Muje na ajjiye miki" Su ukun suka juya zuwa sassanta,mijinta..... diyarta ta bisu da kallo,me yake shirin faruwa ne wai?,ko kuma tace meye ne ya farun?. Kamar wadda aka tsikara saita kasa tsaiwa,ta daga qafarta da hanzari tabi bayansu,ta cimmasu ya karba keys din ya saka yana bude mata qofar sassan nata,sai ya waiwayo yana duban hafsat din da tayi tsaye a bayansu,ta kasa ta tsare tana dubansu,ya dauke kai ya qarasa buda qofar ya matsa mata gefe ta sanya kai ta shige ita da mimi da suketa surutunsu ko a jikinsu. Cikin falon ya ajjiye mata jakar,sannan ya juya ya fice daga falon yana tsokanar mimi,a sannan hafsat din tana qifar parlor din bata shigo ba,saidai tana jin zuciyarta na mata wani iri,ta kasa tuna komai bare tayi tunanin me ya kamata tayi,jikinta yayi mugun sanyi,zuciyarta kuma tana bata akwai wani abu. Kallonta ya sakeyi sanda ya fito,tana tsaye qyam kamar wadda aka bawa gadin qofar falon,yadan kalleta sai kuma ya wuce,ta taka ta bishi a baya,zuciyarta kamar sata fito daga qirjinta,tanason masa qorafi to amma kuma tace masa meye?,haka taci gaba da binsa a baya har zuwa sashen nasa. Sanda ya bude waiwayowa yayi yana kallonta,qura fal sashen,wannan abu yana masa ciwo,baisan sai yaushe zai fara dawowa yana samun sassan nasa a tsaftace ba,suna hada ido ta kauda kai,tasan qorafi yakeson yi,amma ba zata bashi dama ba,zata gyara tunda ga widad tazo,wasu ayyukan zasu ragan mata ai,sai ta karba jakarsa ta wuce bedroom dinsa da ita. *_BAYAN AWA BIYU_* Yana zaune saman kujera take gyaran falon,tana aikin tana gyara daurin zaninta dake kwancewa,fuskarta sam babu walwala,tunani ne cunkushe fal a ranta. Nawwara na zaune saman doguwar kujerar da yake kai,yanata bare mata chocolate tana sha tana masa surutu,lokaci bayan lokaci yakan daga kai ya dubeta,tun daga tsefaffen gashinta da yayi cibiri cibiri har zuwa qafafunta dake cike da kaushi,babu digo lalle ko kadan bare su samu arziqin suturta kaushin qafartata,brassiere dinta ta saki sosai,don kana iya hangota ta gadon bayanta. Ya lumshe idon takaici yana cikashi,duk wani abu da diya mace zaga gyara a jikinta ya bada sha'awa hafsat din ta kauda shi da kanta da mugun qazanta da rashin sanin ciwon kanta,tattausan qshin widad ya tuna,babu sanda zata giftashi bakaji tashinsa ba daga jikinta,sabanin hafsat din da saidai yaji wani na daban bawai qamshi ba. Ta gama gyaran tana jin tayi wani gagarumin aikin azo a gani,gaba daya qugunta har ya riqe,saita taka zuwa qofar fita,tanason kiran widad din tazo ta gyara mata kitchen hade da kayan miya zata dora girki,sannan ta kama sauran gyaran falonta zuwa sassan part din nata "Zo mana" ya kira hafsat din yana sauke lallausar qafarsa a qasa tsigar jikinsa nadan xubawa,haka kawai yake ji gyaran data yiwa sassan nasa bai gamsar dashi ba,saboda ya riga ya saba.....muddin widad din tayi gyara to sai ka rantse da Allah wani engine akasa aka kauda qazantar waje. Dan jim tayi don ta qagu ta kira yarinyar,tanason jin abubuwa da yawa daga bakinta ko zata samu haske kan zarginta,amma ganin ya kafeta da idanu yasa ta kasa bashi uzurin cewa tana zuwa din,ta juyo ta dawo ta samu waje ta zauna "Meye da meye a kayan amfaninki ya qare?" Ya tambayeta yana hada hankalinsa sosai a kanta with seriousness,don shikam Allah ya sani,bayason ya zalunceta,amma muddin za'a ci gaba da tafiya a haka komai zai iya faruwa,zuciyarsa zata gaza daurewa hada waje da ita. Sosai ta kalleshi,saita girgiza kai "Babu komai" shuru yadanyi yana jinjina amsarta,sai ya miqe ya kama hannun nawwara "Ban yarda ba,muje na gani", kamar zata fasa kuka haka ta miqe,shigarsa sassanta tasan ba abinda zai dadeta dashi wani bacin rai,bata da damar musu,haka ta miqe tabi bayansa. Suna fitowa daga sashen sukaci karo da wata iska mai qamshi dake kadawa dukka ilahirin harabar gidan,yaja iskar sosai cikin hunhunsa ya fesar,a wajen mutum daya yakejin wannan qamshin,kuma ko yanzun ya tabbatar yana fitowa ne daga sassanta,kewarta yaji ta saukar masa,tamkar sun dauki wani lokaci mai tsaho ne basu tare,yayin da hafsat ta dinga shaqar qamshin itama,tana tunanin daga ina yake haka?,da bata gane ba saita watsar,ta raya a ranta qilan daga maqota ne. Suna ratsa falon yana qare masa kallo,yadda dukka yabi ya haukace,harda kayan wanki zube saman kujera,ko meye ya kawo.kayan wanki falo oho,suna isa bedroom dinta ta qarasa tsinkewa da al'amarinta,anya hafsat bata da ciwon qazanta?,wani lafiyayyen zani da bashi bashi ne yake fitowa daga bandakinta yana baiwa dakin wani irin yanayi mara dadi,katifarta gayanta ce kawai,babu zancan bedsheet akai,dukka qofofin wardrobe din nata a bude suke hanhai,ga kaya wasu a qasa wasu a ciki. Iska ya shaqa ya fesar yana lissafa yadda zai kutsa kai bandakin,yaja iska sosai cikin hunhunsa sannan ya saka kai tana biye dashi,ranta dukka a bace,inda ya bari widad ta gama gyarawa ai kome zai shigo yayi sai yayi. Da daya da daya yake bude kowacce locker dake bandakin,dukka kayan da yake siya da sunanta na gyara kama daga shaving cream,shower gel, mouth fresh,relaxers,hair mist hand and foot cream dukka gasu nan jibge,wasu har ya manta daya siyesu ma saboda tsabar dadewa da sukayi,da ya saka hannu ya dauko da yawansu ma sun gaji da zama sun bushe a ciki,wasu sunyi expire,haka ya dinga tarkatosu gaba daya ya zuba a wani qaramin bucket ya fito dasu daga bandakin. A bedroom din ya tsaya,ya sake wangale qofofin wardrobe din nata yana duba kayanta daya bayan daya,yanaso yaga ta inda ya gaza,yanason yaga ko daga shine,saidai dukka sutturunta suna nan danqare,ya buda bangaren kayan baccinta dake jibge masu uban yawa,kasancewarsa ma'abocin son nighties baya rabo da siyansu komai tsadarsu,su dinma suna nan kar kar dasu,wasu ma a cikin ledarsu bata bude ba,sai ya juyo yana dubanta,idanunsa fal bacin rai da kuma soma gajiya da halayenta "Ta ina ne na gaza hafsat?,me kikeso nayi miki ne?,wanne hakki naki ne ban sauke ba?" Yaune kadai ta danji nauyi,amma girman kai da qi fadi yasa taqi hari hakan ya fito,sai ta bata ranta kadan tana cewa "Nifa bance ka gaza ba,sannan kuma nima ya kamata ana dubawa anamin uzuri,aidai kasan ba haka ka auroni ba,kuma ba haka nakeyi ba tun farko ba,yanxun yarane da hidimar gida ta yimin yawa" ransa ya baci sosai,a qalla tunda taga laifinta quru quru ko accepting ai ya kamata tayi ko?. "Ina yaran suke?,ni ban gansu ba,yara qwaya biyu kacal?" Ido ta fidda "Aikai raina hidimarsu kekeyi?" "Eh na raina,tunda koni ija iya hidimarsu,meye bana iya musu?" Baki ta tabe tana riqe qugunta,shikam ya fiya jidali da daga hankali,batasan meye damuwarsa ba da rayuwarta,yanzun nan ta gama gyaran sashensa ko hutawa batayi daga wahalar aikin ba ya tasota a gaba yana son tozartata. Wani bacin rai dake taso masa ya hadiye,cikin danne fushinsa yace "Am tired.....na gaji da wannan halayen naki hafsat,anzo gabar da dole ki gyara,bazan ci gaba da lamuntar haka ba" maganarsa ta farki zuciyarta ta kawo mata fassararta,zuciyarta na sake qarfafa mata gwiwa ba shakka akwai wata a qasa,bai taba gaya mata wannan kalmar ba sai yanzu,anya yarinyar can kuwa bata fara zamewa rayuwarta barazana ba *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 86 "Ka gaji?,ka gaji dani kenan kake nufi?,saika dauki mataki ai k......." Kafin ta qarasa ta daka mata tsawa,dukkan yadda yakeson ya taushi kansa haqurinsa ya gaza "Kada ki gayamin maganar banza da wofi,kin dauka ina tsoronki ne da bazan iya daukan mataki a kanki ba?,to ki shiga hankalinki wallahi,saboda idan nace hukuntaki zanyi abun bazai miki da kyau ba" yana kaiwa nan yayi gaba abinda har yana yin ball da botikin daya ciko da tarkacen kaya masu tsada daya wulaqantar. Da kallo ta bishi zuciyarta na suya,mamaki kuma ya cikata,wai yau ita abbas yakewa haka?,sai zuciyarta ta karye qafafunta sukayi sanyi,hawaye ya fara sauka daga idonta,ta koma ta zauna gefan gadonta tana share hawaye. Zuciyarsa na zafafe sosai sanda ya baro mata sashen,ya isa sashensa kai tsaye ya wuce bedroom dinsa,wannan karon bazai qyaleta ba,ko yaya zaiyi magana da wani magabacinta ko za'a samu sassaucin wani abu,yana tsoron faruwar abubuwa da yawa a nan gaba daga gareshi,baisan me zamansu zai zama ba a gaba,ga yara mata da yake dasu da yasan dolen dole wataran gidan wani zasu je,uwa uba kuma yanayi na lafiya,ta yaya muhalli babu cikakkiyar tsafta za'a samu ingantacciyar lafiya?. Saman sofa bed dinsa ya zauna yayi waya ta a qalla mintuna goma,koda ya gama wayar riqeta yayi a hannunsa yana jin banbarakwai babu dadi,yau ya aikata abinda bai taba aikatawa ba wato kai qarar hafsat din, tsahon zamansu tare na wasu shekaru. Ta bangaren widad tuni ta gama tsaftace sassanta, hankalinta bai kwanta ba saida ko ina ya dauki qamshi,ta fiddawa mimi uniform dinta ta sake mata wanka,akwai ragowar kayanta a sassan tun wancan zuwan da tayi,ta saka mata su,saita tsaya tana kallonta. Yarinyar kyakkyawace,kawai rashin tsafta da gyara ne yake dakushe duk wani kyau nata "Anty ki kaini wajen daddy yaga kwalliyata,dama inata cewa mommy tayimin tana cewa bata da lokacin wannan" murmushi ta sake "Wanka zanyi nima,ki bari idan nayi saina kaiki" marairaicewa tayi "Don Allah anty,nidai yanzu" ba yadda zatayi,dole haka ta dora qaramin mayafinta ta kama hannun mimin suka fice tana cewa "Duk chocolate din da daddyn ya baki kin yarda zamu raba?" Tana dariya ta gyada mata kai. Babu shi a parlor din sanda suka shiga,saita cewa mimi "Bari na duba shi a daki" ta gyada kai yarinyar ta zauna saman kujera cikin zaquwa. A nutse ta tura qofar dakin,daidai lokacin da yake zaune cikin sofa bed din,ya kwantar da bayansa sosai a jikin sofa din,idanunsa da suka rusuna ya daga yana kallon fuskarta sanda ta tsaya daga bakin qofar tana riqe da handle din tana kallonsa kamar yadda shima.ya zuba mata ido,duk sai taga kamar ya sauya daga zuwansu bauchin. Hannunsa ya daga yayi mata nuni da tazo,ta saki qofar ta soma takawa a hankali kamar mai tausayin qasa,ya zuba mata ido yana jin nutsuwa tun gabanin ta iso gareshi. Hannunsa ya bata sanda ta iso kusa dashi,ta saka nata hannun a ciki,sai ya fincikota cikin jikinsa a tausashe,ya mata kyakkyawan masauki a qirjinsa,yasa labbansa masu taushi yayi kissing goshinta,sai ta dan saki ajiyar zuciya "Mimi na rako zata nuna maka kwalliyarta" ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba yi masa magana,birkitota kadan yayi yana kallon fuskarta "Ina taki kwalliyar.....ita tafi muhimmanci" kunya ta kamata ta sauke fuskarta a qirjinsa tana shaqar daddadan qamshinsa "Banfa yi wanka ba,aiki na gama yi,gurin duk yayi qura" girarsa ya dage sama duka biyun "Iyyee,abun 'yar haka ne?,shine kika share iya wajenki banda nawa ko?" Kai ta girgiza da sauri tana 'yar dariya "Ba haka bane uncle,nasan mummy hafsat ta gyara maka fa" kai kawai ya jinjina "Yanzu yaushe ne za'a yimin kwalliyar,ta musamman nakeso,i will pay" dariya ta saki,tanajin dadin yadda yake yaba komai nata "Za'a yi maka uncle" ta furta tana rufe fuskarta da hannunta "That's my baby doll" shima ya amsa mata yana jan dogon hancinta "Muje naga mimi' ya sake fada yana dagata a jikinsa,gaba daya sai ya rasa kaso hamsin na bacin ransa, shigowarta kawai ya tafi da komai,ta miqe ya sanya hannunsa cikin nata ya riqe gam suka fara takowa xuwa falon. Babu irin abinda bata saqa a ranta ba sanda take tsaka da kukan,sai datayi me isarta sannan ta dauraye fuskarta,bata da wata mafita,komai ya tsaya mata cak,batasan me ya kamata tayi ba,saita dauki wayarta ta soma lalubar number anty ummee ko xata samu wasu shawarwari. Abun takaicin tana kira taji suna sanar mata kudinta ya qare,dama already taci bashin mtn na kusan dubu uku,duk kuwa da cewa duk wata sai abbas din ya saka mata kudin credit ta account dinta bama credit din ba,taja tsaki ta sauka ta koma bank dinta ta sakawa layin bashin da suke binta,bonus din da suka bata tayi amfani dashi ta kira anty ummee din. Shuru tayi har ta gama bayaninta sannan ta dora "Ina tsoron kada yarinyar nan ta fara shiga rayuwarsa anty ummee,ni zuwan nan da sukayi ma sai naga kamar ta fara budewa ta zama mace,harda kai mata kayanta sashenta fa,duk da na sanshi bashi da girman kan wannan wa iyalinsa,amma yarinyar ai bata cancanci wannan kulawar ba" baki anty ummee ta tabe,tana jin kamar ta jawo hafsat din tayita jibga "Nidai da farko saidai nayi miki addu'ar Allah ya yaye miki wannan baqar qazantar,bansan irin ribar da kike samu da ita ba" maganar ta bata ran hafsat,don duk yadda kake da ita kace mata qazama ce to sai an ganku a rana "Meye haka anty ummee?,nifa ba akan wannan na nemi shawararki ba,tunda dai ni ina iya bakin qoqarina,abubuwane sukeyimin yawa,kuma nayi nayi ya daukon mai aiki yaqi,to bazan kashe kaina ba" kai anty ummeen ta jinjina,gwara ta bita a yadda suka soma,kada ta yiwa kanta rasa rasa "Ke gaskiya ce baki so,na daina kuma gaya miki,amma indai kansa kike san shawowa dole kidan gyara inda idanunsa zasu ganki tsaf,tunda da tsafta aka jarabceshi ke kuma ea qazanta.....muddin kinason ganin dai dai dole ki sauko daga ra'ayinsa kibi nasa ko yaya ne,koni da kikaga ina yadda nakeso,wasu abubuwan ra'ayinsa nake bi kafin na murda idan naga ya biyu yadda nakeso na koma kan nawa ra'ayin" sun dan dauki lokaci suna fafatawa ma kafin hafsat ta fahimci abinda anty ummee take nufi,dole ta yarda tadanyi gyara a ranar ko zata cimma manufofinta ta ruwan sanyi. Suna gama wayar ta miqe tana tunanin ta inda zata fara,sai ta yanke ta shiga da kanta ta kira widad din,can qasan ranta tana mamakin yadda ko motsinta bata sake ji ba bare ta shigo taga abinda ya kamata tayi mata. Tun bata qarasa ba taga sassan nata a kulle,ta juya cike da mamakin ina taje?,ko gidan hajiyan da aka rufe babinsa ta koma?,harta dawo da baya.....amma tana kallon sashen abbas din akalar tunaninta ya canza,saita nufi can,duk da zuciyarta na gaya mata bata ciki,to amma mafi rinjaye na tunaninta yana rinjayarta ga zuwa sashen nasa. Tana buda qofar falon abbas dake riqe da hannun widad yana bude ta bedroom din,idanunsa na kallon gefansa yana magana da widad din,cak hafsat din ta tsaya kamar an dasata,qirjinta yana harbawa,ta zuba masa ido tana son ganin waye yake biye dashi. Wani mugun ashar ne taji ya taso mata,saidai abinda yazo ya tsaya mata a wuya ya hana kowanne kalma fita daga bakinta,widad fa take gani,widad yau a dakin mijinta?,riqe da hannunsa?,baqar zuciya da kuma fushin dake cin zuciyarta ya sanyata cikin zafin nama ta harbo zuwa cikin falon. Takunta yaja hankalinsa sanda yake tsokanar mimi tayi kyau,ya tashi daga durquson da yayi,ya zuba mata idanu,don kallo daya yayi mata zuciyarsa ta bashi akwai wani abu na daban. Kafin ta qaraso idanunsu suka sarqe cikin na juna,wani irin baiwar idanu gareshi masu tsananin kwarjini,abinda yayi mata tasiri kenan,kallonsa ya ratsa zuciyarta ya karya duk wani zafi data debo da kima qissime qissime da zuciyarta keyi mata na irin abinda zata aiwatar,saurin data kwaso ya canza zuwa nawa. Kallon kallo suka ci gaba da yiwa juna,sai taji zuciyarta kamar zata fashe idan bata ce komai ba,a sannan ta tuna ita din me laifi ce,ta kuma tuna gargadin da anty ummee tayi mata "Kissa saida kwantar da kai"maganar data gaya mata ta qarshe kenan "Nace me za'a dafa maka?" Ta maye gurbin dukka wani bala'i daje qasan zuciyarta da wannan tambayar,tambayar da yaji sam bata dace da yanayin da ya ganta a ciki ba,to amma koda ta tambaya dinne da gaske,yanajin ya zuwa yanzu ya kamata ya nuna mata fushinsa,saiya dauke idonsa daga kanta ya maida kan 'yarsa "Bana buqatar komai" ya amsa mata a dake yana duqawa yana gyarawa mimi kwalar rigarta. Wasu irin hawaye ne masu dumi suka cika mata idanu,ta zubawa widad ido,wadda sam idanunta baya wajen,ta tattareshi akan tv,haka kawai takejin wani irin itama cikin ranta, yanayin gidan a yau ya sake mata rashin dadi,ta tabbatar a lokaci irin wannan a kaduna ita dashi din suna kitchen tare suna girki,ko suna backyard dinsu suna wankin undies,ko suna karatu ko kallo. Qwafa taja can qasan ranta tana danne hawayen,batason ta zubdashi a gaban widad din,ta juya tana barin falon,kamar zatayi bindiga ta fashe haka takejin kanta,nadama da dana sanin ma tambayarsa me za'a girka din ya cika Zuciyarta,gashi ya yarfata a gaban qaramar yarinyar da a haife ta haifeta. Hanyar data fita yabi da kallo,yaja dan qaramin tsaki sannan ya koma ya zauna kusa da mimi "Hadamin coffee ko black tea" ya bata umarni yanason danne shima nasa fushin,tadan kalleshi da wani irin yanayi,cikin zuciyarta takejin akwai wani abu dake damunsa,don ba haka yake ba,kamar zatayi magana saita fasa,ta miqe tana nufar qofa. Tana sanya qafarta a falonta taji an biyo bayanta,ta tsorata sosai,taja da baya tana dubanta,sai data gane hafsat dince saita saki ajiyar zuciya tana lumshe idanunta hadi da budesu tana kallonta. Wani irin kallo take bin widad dashi,tana jin kamar ta fincikota ta rufeta da duka,yarinya qarama amma tana neman dagula mata lissafi,tanaji a jiki da zuciyarta abbas ya sake canzawa ne sosai ta sanadin aurenta,a baya idan ya fiya cika masa ciki tattarawa yake ya koma inda ya fito,sanda suna gari guda kuma saidai ya tsiri zaman gidan hajiya,ko kadan bata damuwa,saboda tasam ba wani wajen yaje ba,kuma shi din ba mai kula kulen mata bane,asalima sam basa cikin tsarinsa,don haka ba kasafai ta fiya damuwa,idan ya qare fushinsa zai dawo yaci gaba daci abincinsa ko yaya ta dafa kuwa,idan yaji bai masa bama zai shiga kitchen ya dafa da kansa (Hmmmm,duk a lokacin bata taba kawowa miskilanci bane irin na mijinta,ta aza hakan akan babu yadda zaiyi da itane,kamar dole yayi duka abinda yakeyi din). "Uban me kika shiga yi dakin abban mimi" kamar daga sama furucin yazowa widad,mamaki ya kamata,for now dai ta fahimci matsayinta daya da hafsat din,ta kuma fahimci me kalmar aure take nufi,indai haka ne bataga muhallin wannan tambayar ba,duka wannan ba damuwarta bane,abinda yafi bata mata rai kalmar UBAN WA data fada,wanda dai dai yake da zagi a wajenta "Dake nake!" Ta sake fada cikin tsawa kamar zata kai mata duka,amma ga mamakinta sai taga widad din ta tsireta da manyan idanunta "Ai ba haramun bane tunda kema naga kina shiga" ta fada a sakalce abunta tana dubanta. Zallar mamaki ya saukowa hafsat din,tayi sakato tana kallonta "Ni kike gayawa wannan maganar?" Ta fadi tana jin wani zafi har cikin ranta "Me nace mommy?" Ta tambayeta kanta tsaye,a karo.na biyu ta sake shiga mamaki,anya kuwa?,anya abinda take tunani bai faru ba?,yaushe yarinyar tabfara fahimtar abubuwa haka?.,da tayi wani qaramin tunani sai tabar wancan maganar tace "Ki wuce kije kiyi aikinki,suna can suna jiranki" "Tom,bari na dafawa uncle tea" tea?,har tea yake sakata dafa masa saboda zallar jawo mata raini?,wanne girki ta iya da zai buqaci tea daga wajenta "Ni kike.maidawa magana widad?" Juyowa tayi tana kallon hafsat din,ita gana daya sai taji ta sire mata daga zuciyarta,tunda ta fahimci akwai qaryayyaki da yawa data taba gaya mata,a dabi'arta kaifi daya ce,ko meye za'a yi mata bata qarya haka ta taso tun quruciyar ta,dalilin da ya sanya ta sake shan wahala kenan sosai a wajen 'yan uwanta da cousins dinta "Me nayi mommy?,aikinsa shine gaba da kowanne aiki fa,ba kyau miji ya saka kaqi" zuwa lokacin gaba daya hafsat din ta gama sarewa,lallai qaryarta ta fara qarewa,tund har yarinyar ta fara sanin ma'anar kalmar miji,ta kuma fara tantance bin umarnin wata a gaba da nata umarnin,basu taba musayar magana da ita ba koda da sau daya,amma yau da ita suke musu?,tana ce mata ga yadda za'a yi itama kuma tana fadin nata,ah wannan babbar musifa da babbar guguwar canji ce ta tunkarota,wadda take buqatar zama na musamamn da shawarwari don sanin meyenmatakin dauka na gaba,daga wannan sai bata sake cewa komai ba,ta juya tana barin wajen tana jin kamar duniyarta tazo qarshe gaba daya. Tsakin da batasan yazo bakinta ba shi ta fitar,tadan harari hanyar data wuce din "Kawai kawai ni...."sai kuma tayi shuru tana quna quni,ita tunda taga yadda taketa wani tsare mata uncle dinta da kallo taji tana jin haushinta,bata taba ma kula da haka take zuba masa ido ba sai yau din,haka ta shiga kitchen din,ta fara duba kayan hada tea din da tasan yana matuqar so ta fara hada masa,lokaci lokaci tana dan jan tsaki. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 87 Wayar anty ummee ta sake kira cikin mugun rudani da tashin hankali tafara gaya mata yadda ake ciki,ita kanta abun ya bata mamaki sosai "Wannan maganar bata waya bace,ki daure ki cinye komai kiyi masa duk abinda yakeso,zuwa jibi in sha Allah zamu dawo daga bikin 'yar yayar babansu khadija(mijinta),gaata in sha Allah da wurwuri zaki ganni,idan ban samu fita bama zan miki magana saiki shigo mu hadu. Wannan maganar ta tayar da hankalin hafsat din sosai,ganin jibi take tayi mata mugu mugun nisa "Don Allah ki katse bikin nan anty ummee,kizo mu samu mafita,ina cikin mugu yanayi,ji nake zuciyata ba zata iya dauka ba,kamar zata fashe nakejinta" "Indai bakiyi juriyar dana gaya miki ba kikace zakibi son zuciyarki to komai zai lalace miki ne" abinda tace da ita kenan. Tayita kwatanta yadda zata fuskanceshi da fuskar komai ba komai ba amma ta kasa,kwata kwata zuciyarta bata da irin wannan juriyar da jarumtar irin ta anty ummee din,ta gama cusguna ma rayuwarta kuma tayi masa abinda yakeso?,babu abinda idanunta ke hango mata sai sanda suke fitowa daga dakin,yau hannun abbas dinta ne cikin na wata macen?,turakarsa da duk duniya ita kadai tasan kalarta yau sai ga wata mitsitsiyar yarinya ta fito daga ciki?,wa yasan ma me suka aikata suka ajiye mata yarinya a falo?. Duk yadda ta juya ta kasa aiwatar da komai,kawai saita kulle kanta a dakin ita kadai,saqa da warwara ba irin wadda batayi ba akan yadda zata bullowa al'amarin,kota kan yaranta ba ma bata bi,suma yaran dawowar widad yasa basu sake nemanta ba,suna can wajenta,wadda bayan ta gama hada masa tea din ta koma yin wanka ta wuce dasu,ta sake yiwa nawwaran ma wanka,don ita kanta ba cikakkiyar tsafta a jikinta. Zamansa a sassan nasa sai zuciyarsa ta kasa jurewa rashin ganin gilmawarta,ta saba masa da qamshinta,girkinta da a yanzu duk duniya babu girkin da yakejin taste dinsa idan ka dauke na hajiyarsa bayan nata,ya dinga qoqarin danne xuciyarsa,don a qa'ida awannin na hafsat ne,bayason kuma ya fara sabawa jiki da zuciyarsa da aikata wani abu da zai jagoranceshi ga zamowa kasashen namiji mara adalci,dole yayi wanka ya shirya ya biya ta sashenta don a qalla cikin su biyun ya kamata wata a ciki tasan inda zashi kada a nemeshi,hafsat ya dace ya soma fadawa,amma yaci alwashin bazai shiga sashenta ba,zai mata horon da zata sake shiga hankalinta. Tana tsakiyar su mimi din suna assignment,ta dora abinci a kitchen,gown ce a jikinta na chiffon material butter color da zanen green flowers qananu "Zan fita amma bazan dade ba zan dawo" ya furta jikinsa na amsawa,don daga inda yake tsayen yana iya jiyo qamshinta mai dadi,ga kuma qamshin da sashen kansa yakeyi wanda ya cukude da qamshin girkinta. Marairaice fuska tayi tana kallonsa da farare sol din idanuwanta "Uncle.....don Allah kada ka dade" murmushi ya subuce masa, ya jinjina kai yana kallo labbanta "In sha Allah" kusan a tare sukayi masa a dawo lafiya,har ya isa bakin qofa yaji bazai iya wucewa ba,ta gama kashe masa jiki,yana qishirwar lausasan labban nan nata,sai yadan waiwayo ya mata sign din tazo. Miqewa tayi tana sakin murmushi,tana kaiwa bakin qofar ya jawota cikin labule yadda yaran ba zasu iya hangosu ba,baiyi wata wata ba ya mannata da qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya,ya dago fuskarta yana dubanta,idanunsu suka sarqe waje daya,sai suka hau yiwa juna kallon kallo,cikin zafin nama ya hade bakinsu waje daya. Da qyar yayi controlling din kansa,ya zareta daga jikinsa yana sake kissing goshinta "Allah yayi miki albarka,take care" ya fada yana ficewa a hankali,sai ta kasa motsawa ta bishi da kallo,yayin da wani lafiyayyen murmushi ya dinga fita daga fuskarsa,yana ji a jikinsa kallonsa take,wannan dalilin ya hanashi waiwayo,don ya bata damar kallon nasa sosai yadda ranta yakeso,ya hangi wasu abubuwa sosai daga zuciyarta,wanda ba lallai ita din ta fahimci shigarsa rayuwarta ba. Sai data daidaita kanta sannan ta koma cikin yaran tana tana labbanta da yatsunta, batasan me yasa duk sanda yayi mata irin wannan abun take tsintar kanta a wani yanayi ba "Kema kin zama yar iska ko?" Ta tambayi kanta da kanta,sai ta bushe da dariya ita kadai,har yaran suna kallonta dukansu,mimi ta tambaya "Mene ne anty" dan zubawa yarinyar ido tayi har yanxu murmushin dake saman fuskar ta bai bace ba,sai ta kama kumatunta "Babu komai mimi,kawai inason daddy uncle...." Ta furta maganar ba tare data shirya ba. Farinciki ya kama yarinyar,ta washe bakinta tana dariya "Shima yace yana sonki" ido ta fidda "Yaushe?" " rannan dinnan" murmushi ta kuma saki,tana juya maganar yarinyar a ranta,saita miqa mata pencil din sukaci gaba da rubutun,zuciyarta wasai cike da tunaninsa,abinda bata taba tsintar kanta a ciki ba akan wani halitta. Dole saboda yunwar cikinta ta fito ta shiga kitchen,ta fara tunanin me ma zata dafa musu?taja tsaki yafi a qirga,ta rasa dame zata fara,saita matsa ta window gaban window din kitchen din nata ta zugeshi saboda iska ta shigo. Tana gama budewar iska me dadi mai hade da wani hadadden qamshin abinci ya cika mata ciki,ta hadiyi yawu da kyau tana tunanin ta inda qamshi kala kala yau yake cika mata gida,tabi wajen da kallo tana qaramin nazari,sai ganinta ya tuqe a sassan widad. Gabanta yadan fadi,kada ya zamana yarinyar ke girkin dake bada irin wannan aroma din,kai ta kada,ko jikinta kunne ne ba zata yadda da haka ba,yarinyar da aka kawo ko ruwan zafi bata iya dafawa ba,yaushe akayi dare har garin zai waye ta iya girki haka?. Tun tana aikin tana basarwa har ta gaza,sai ta ajjiye abinda takeyi ta juyo ta baro sassan nata ta doshi sashen widad din,tana kusantar part din iska da kums hancinta suna tabbatar mata daga can ne qamshin abincin ke fitowa,sai tayi tsaye daga bakin qofa yatsanta a baki,ya akayi haka ta faru?,bata da abinda zatayi,dole haka ta juya ta koma gwiwa a sanyaye,amma kuma ta cika da mamaki tare dason gano yadda akayi haka ta faru. Tana girkin amma gaba daya tunani ya cika mata kanta,ranta a jagule yake,bata qaunar ganin wani ci gaba sauyi ko walwalar rayuwa daga yarinyar gaba daya. Sallama taji da muryar mimi,a mamakance ta waiwayo tana kallon yarinyar "Mommy kizo inji daddy" "Ke.....waye ya koya miki sallama?" Daria ta saki cikin jin dadi "Anty amarya ce,tace duk inda za'a shiga sai anyi sallama,ba kyau shiga guri idan ba'a yi sallama ba" haushi takaici da kuma baqinciki suka cikata,wanne irin sanabe ne haka za'a fito mata dashi akan diyarta,sai taha qwafa "Shi kuma me zanyi masa,har ya gama fushin nasa ne?" Ta fada tana kallon yarinyar kamar itace zata bata amsa,ita dai batace komai ba,sai taja tsaki ta kashe gas din ta fito zuwa dakin baqi da tace yana can. Tunda tayi sallama taga kawunta gabanta yayi mummunar faduwa,saboda tasan cewa lallai ruwa baya tsami banza,ta saci kallon abbas dake zaune daura da kawun nata suna taba hira,wadda duka akan abinda ya shafi security na qasa ne,baiko dubi sashenta ba,haka ta daga kai ta isa ga kawun nata ta zube tana gaidashi kanta a qasa. Shuru tayi ta nutsu sosai kamar da gaske tana sauraron kawun nata sanda yake mata fadan tsafta,iya abinda yafi abbas din yakai qorafinta akai kenan,amma ji take gaba daya ya gama tozartata ya wulaqantata,hausawa sukance wai wanzami bayason jarfa. "Nifa kawu kawai baya ganin qoqarina ne,amma ai inayin duk abinda naga zan iya bakin gwargwado" "Oh.....qarya yake miki kenan?,nace qarya yake miki,to ko ni da nake namiji ai gashi ina gani" ya fada yana nuna dakin baqin da ya hada qura sosai,sai kawai ta saki kukan takaici,kawun ya qara da cewa "Duk qoqarin da abbas yakeyi babu wanda bai san dashi ba,don bai taba kawo qararki ba tsahon zamanku tare sai yau,kuma bazai taba tiwuwa ace shekarun duka da kuka kwashe ke dashi baki taba yi masa laifi ba,saidai kece d baki gani" "Nima kawu ai yana yimin" "Rufen baki,me ya hanaki ki fada" ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,yayi mata fada sosai ya kuma tursasata ta bashi haquri. Kamar wadda aka cusawa tsumma a baki kanta a qasa haka ta furta kayi haquri,gaba daya ma abun sai ya jishi banbarakwai,don zaiyi mugun mugun wahala kaji kalmar ban haquri daga bakinta,daga qarshe dukansu kawun ya hadasu yayi musu nasiha sannan ya wuce gida,abbas ya fita ya rakashi har bakin mota sannan yayi masa alkhairi,duk da cewa da qyar ya karba. Daya dawo tana ta kumbure kumburenta sai ya watsar yayi kaman bai gani ba,ya tattara ya fita sallah,bai kuma dawo ba sai bayan isha'i,don ya tsaya ya saurari karatun da ake a masallacin duk bayan sallan isha'i zuwa qarfe tara na dare. Silk sleeping dress ce a jikinta baby pink mai gajeran hannun net,duka tsahonta iya qaurinta yake,ta lullube kanta da wata qaramar hular net mahadin kayan,ta cusa duka gashinta aciki,idan kayi mata kallon farko saika dauka batasan ko zo na kasheka da hausa ba,dakin babu wadatar haske sosai,sai na screen din wayarta dake hannunta. Gaba daya bata jin dadin chart din da takeyi,zuciyarta duka babu dadi,wani irin kewarsa ce take taba zuciyarta a hankali,tun dazu daya shigo yace zai fita bata kuma ganinsa ba,kuma dazun taji shigowar motarsa,taji mimi tana masa oyoyo,amma bai shigo ya sake ganinta ba?,wani abune da bata saba dashi ba,duka sai taji qirjinta da zuciyarta sun quntata,wayar ma ta fita a kanta,ta maidata gefa ta ajjiye tana zamewa ta kwanta,idanunta suna hada ruwan hawaye. A gajiye yake jinsa,don haka ya nufi sashen widad yayi mata sai da safe,ya murda qofar ya jita a kulle "Sarkin tsoro" ya fadi yana sakin murmushi,ya saka nasa key din ya bude ya shiga. Falon nata neat kamar ba'a zauna ba,qamshinsan nan yana nan,amma akwai qarancin haske,da alama ta gama shirin kwanciya. Lumshe idonta tayi sanda taji sallamarsa,sai taji wani abu da ya tokare mata a qirji yana sauka,ta bude idonta tana amsa masa sallamar,dai dai sanda ya shigo dakin,ya saka hannu ya kunna fitilar haske ya gauraye ko ina. A kanta idanunsa suka fara sauka,suna hada ido sai taji zuciyarta ta karye,ta sake narkewa tana jin idanunta suna tsatstsafo da hawaye "Bakiyi bacci ba?" Ya tambayeta yana takowa inda take,maimakon ta amsa masa saita cusa kanta cikin pillow tana sakin kuka,yaji a jikinsa kukan take,saboda haka ya tako da sauri ya iso inda take "Wuud(qauna/soyayya,sunan da ya kuma fara kiranta dashi kenan)" sake cusa kanta a pillow din tayi,sai ya haura gadon gaba daya,ya birkitota jikinsa yana leqen fuskarta "Me ya faru?,kuka?" Gaba daya ta saki kukanta,ta kuma qanqameshi tana saka kanta a qirjinsa,cikin narkakkiyar muryar kukan tace "Ba kaine ba?" "Nine?,nayi me?" Ya fada tana fidda idanunsa "Tunda ka fita baka sake shigowa ba kayi tafiyarka,kuma daka dawo ka shiga wajen mommyn mimi ni kuma sai yanzu ka shigo,bayan ma a can zaka kwana" "Kishi?!" Ya fada a zuciyarsa yana zaro idanunsa waje,wani lafiyayyen murmushi kwance saman fuskarsa,maganarta dai dai take da albishir a gareshi na rainon da yakewa zuciyarta ya fara kaiwa ga gaci,albishir ne a gareshi na zai fara tarbar sabuwar rayuwar daya raina,sabuwar zuciya da jaririyar soyayyar data fara ginuwa. Rungumeta yayi gaba daya a jikinsa,cikin taushi da laushin harshe ya fara gaya mata wasu kalamai da suka sata jin kunya,tun tana ya bari yana qi har kunya ta sakata ta shige jikinsa gaba daya,sai daya tabbatar ta nutsu sannan ya sakata ta kwanta,ya rufeta da duvet da kyau,ya saita mata sanyin ac dana fanka guri daya,ya kuma rufe mata dukka windows dinta dama sashen gaba daya. Tana jinsa yana fita kamar tace masa ya dawo,to amma ta samu dakiyar zuciya tunda ya gaya mata goben a nan zai kwana,ta rufe idonta tana sake bawa kanta qwarin gwiwa,duk da zuciyar dai babu dadi. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 88 *W A S H E G A R I* Ture plate din da ya gama cin chips din yayi gefe guda bawai don ya qoshi ba,a'ah sai don babu wanu taste a tattare da dankalin,salam dashi,yakai dubansa ga yaransa daketa cin abinsu hankali kwance,saboda rashin sabo da kuma rashin sanin dadin bakinsu. Kallonta yayi itama tana ta cin abinta kamar yaran,tun kayan daren jiya ne a jikinta,duk da tayi wanka a hakan,ya danyi gyaran murya "Yau din ba sai kinyi shirin komai ba,zan kwana wajen qanwarki,jibi sai na dawo wajenki,idan mun koma jibin shikenan,idan bamu koma ba sai a dora da haka" maganar taxo mata a mugun ba zata,ta daga kanta da sauri tanason ganin da gaske abbas ne ke mata zancan rabon kwana tsakaninta da widad din,tsabar mamaki da tsorata sai kuwa ta qware,dankalin ya shaqe mata wuya,tahau tari babu qaqqautawa,take idanunta duka suka firfito,ya tsiyaya ruwa da sauri ya miqa mata yana mata sannu. Ko data gama shan ruwan numfashinta ya dai daita sai taji kamar ta kurma ihu,abbas din yayi wani mugun baqi a idonta,duk qoqari da jarumtar da tayi a jiya bai gani ba?,shine da safiyar Allah zai zo da wani zancan na daban,banda rainin wayo da rainin hankali,su gama satittikansu a can,sannan a nan ma a cinye mata weekend dinta?. Bala'i ke cinta sosai tana kuma son ta saukeshi akan abbas din,amma kuma batason tayi wani abu da anty ummee zata ce ta bata plan din gaba daya,duk da haka ta kasa haqura,ta kafeshi da ido sosai tana kallonsa "Abban mimi.....ni kake cewa zaka yiwa rabon kwana da widad diyar cikina?" Cikin second uku kacal ya gama qare mata kallo,a nutse ya jingina jikinsa da kujerar da yake kai sannan ya gyada mata kai yana lumshe ido hadi da budesu,sai ta janye nata idanun,ranta yana qoqoluwar baci,daya daga cikin yanayin da zaka gane hankalinsa a kwance yake,kuma ransa bai baci ba kenan idan yayi maganarsa,kuma sign dake nuna tabbatacciyar magana ce da babu canzawa,sai kawai ta miqe da sauri ta nufi daki,batason hawayen da suka taso mata su zubo a gabansa yaga rauninta. Tana kuka tana kiran anty ummee,wadda tuni ta saba da ganin kiranta,kiranta babu alkhairi kamar yadda kiran nata ba samuwa bace damuwa ce,haka siddan idan bata da matsala ba zata taba nemanta ba,tana dagawar kuwa taji sautin kukanta "Anty ummee ni yau abbas ke gayawa wai kwanan widad ne?" "Abbas din?" Anty ummeen ta fada abun yana girgiza ta itama "Eh,shifa" shuru tayi mamaki na ratsata,wanne irin kafaffen namiji ne abbas din,duk hanyar da aka bullo masa sai ta warware?,tsahon minti biyar suna kan wayar hafsat na mata kuka,taja dogon numfashi tana cewa "Kinga,kiyi shuru da bakinki,inaso kiyi kamar baki damu ba,kada ma ki bari ya gane kinyi kuka,amma yau bai isa ya kwana a dakin yarinyar nan a gaban idonki ba,ke har su koma wallahi,ki kwantar da hankalinki,indai kinbi abinda zan gaya miki yanzu" sosai taji qunci da takurar da zuciyarta ta shiga yana warwarewa,ta goge hawayenta fes tana sakin dariya "Bansan wacce irin godiya zan miki ba 'yaruwa,bansan dame zan saka miki ba" "Ni dubu hamsin ma nake nema,inda zaki bani ita da komai lafiya lau" "Ki bari zamuyi maganar kawai anty ummee" ta katse zancan "Shegiya uwar son abun duniya,duk bala'in son abun duniyar taki wallahi Allah sai naci dake,duk wayon amarya sai an sha manta" anty ummeen ta fada a zuciyarta "To shikenan,sai na jiki" daga haka sukayi sallama,saita miqe ta shiga bandaki ta gyara fuskarta,ta dawo tahau gyaran dakin nata,cikin ranta tsanar widad na sake shigarta,gyaran dakin da a baya saita manta ma ya akeyinsa,don ita ke komai,koda brassiere dinta ta yasar duka zata kwashe ta kuma wanke,amma gashi cikin qanqanin lokaci komai yana shirin canzawa?,ba zatayi sake ba kuwa,ba zata bari haka taci gaba da faruwa ba cikin gidanta,zata bi kowacce hanya don ganin komai ya dawo bisa kan tsari yadda ta shirya. ************washegari wajen sha biyu na rana saiga nujood ita da sauran qannenta,dadi ne sosai ya kama widad,ta rungumeta kana taja baya tana cewa "Hajjaa fa?" A shagwabe,nujood daketa baza hanci ta dubi widad din batace komai ba,har sai da widad din tadan daki kafadarta "Kina jina ina tambayarki don wulaqanci" "Aina kasa magana ne,wani shegen qamshi kikeyi widad,ke bakiga ma yadda kika canza ba gaba daya,kinga wani shegen kyau da fatarki tayi?,wai dama haka auren yake amma naji abba na maganar saina gama secondry na shiga university ki higher institute?" Harara widad ta watsa mata,tana ji a ranta nujood din bata da hankali "Ke kike ganin haka dalla malama" dariya suka saki a tare,sannan suka zauna saman kujerun falon,suka hau surutu har wani bayajin muryar wani. Nan suka wuni a tare,saidai rabi da rabin hankalinta yana kan abbas din,yace mata zaije yakai hajiya dubiya,idan sun wuce ziyarce ziyarce zataji shuru,idan kuma sun gama da wuri he promised her zai dawo gida da wuri. Zuwa azahar ta gama yanke abinda zata dafa masa,taja nujood kitchen din,nujood nata tsokanarta "Uhmmm,kaga matan aure,Allah har mamakin girkinki nake widad,yaushe kika qware haka?" Murmushi tayi "Online classes ne dani sun kusa guda goma,kuma kowanne da irin abinda suke koyawa,dukkansu kuma expert ne,idan suna miki classes kamar a gabanki akeyi" "To ya girkin mutuniyarki?,har yanzu yana nan jiya iyau,hala kina dan sanmata idan kika dafa?" Nujood ta fada tana dariya,saboda tuna girkin da aka tarbesu dashi ranar da suka kawo widad din. Shuru widad din ta danyi tana nazari,sai kuma ta tuna,da sauri ta daki bayan nujood tana dariya kafin ta tsagaita "Oho,da yake ni bacin girkinta nakeyi ba" "Ah dole uncle abbas yaji dake wallahi,irin wannan delicious haka,lallai kwanan nan mommyn mimi za'a shiga uku" ta fada tana feshewa da dariya,tana kunna gas ta kalleta "Kaman yaya?,saboda girkina yafi nata sai uncle yafi ji dani?" Harara nujood ta balla mata "To zauna nan,ke bakisan maza mayun abinci bane?,ki dinga kula daga yau,yadda yakecin abincinki da yadda yakecin nata" nan kuma sai hira ta balle. Nujood tadan girmi widad da kadan,ta kuma fita wayo da shiga cikin jama'a,don takanje gidajen qannen hajjaanta hutu,kuma dukansu yaran mata ne,wasunsu suna da abokan zama,tana ganin yadda suke abubuwa,uwa uba qawayenta na makaranta suma kusan suna da yayye aurarru,kuma suma suna zuwa gidajensu,to idan aka hadu hirarsu bata wuce ta aure da gidan miji,musamman yanzun da suka shiga ss,kowacce tana ganin kamar ta zama senior. Shuru widad tayi tana biye da hirarrakin nujood,mamaki ya dinga kamata, zuciyarta ta dinga kawo.mata abubuwa da yawa game da hafsat,kenan matsayinsu daya da ita duk da qarancin shekarunta?,duk da ta girmeta amma matsayinsu daya kenan?,duk da bata tambayi nujood komai ba,amma ta tsinci abubuwa da yawa cikin hirar da sukayi. Nujood ce ta kama mata aikin,ta shurya lafiyayyar wainar shinkafa da miyar agushi data zuba naman rago wadatacce,don da safiyar abbas din ya aiki yaron office dinsu yayo cefane na duka kayan buqata na gidan,ita dama yawanci idan yasa akayi irin wannan siyayyar kadan yake diba mata,tunda basa wuce kwanaki hudu a bauchin suke komawa,saidai idan wani abunne ya taso. Ta taba ganin ya aika an siyo masa wainar,saita gwada yi masa sau daya,duk da bata tashi ba amma tayi dadi ba laifi,ya kuma ci sosai,data tambaya muneera sai taji ashe tana cikin favorite foods dinsa,yanzun kuma ikon Allah sai bata bata kunya ba,ta tashi tayi kyau sosai,tayi saqa saqa a ciki,ta kuma yi laushi,anty madeena ce ta bata wannan recipe din ta gwada,ta kuma sake tambaya a classes din da takeyi. Bayan ta gama suka gyare gidan fes tare, nujood ta soma hada kan yaran "Yamma tayi yanzun zakuga bala ya iso daukarmu" fuska widad din tadan bata "Haba mana nujood,ku bari zuwa magriba" baki ta kama "Waaa....niiii?, rufan asiri bazan iya.kallon love din da za'a balle yau ba, bakiji wai irin qamshin daya cika gidan na ba?,har waje wallahi,ina ganin kishiyarki yau saita hadiya yawu ya kusa sau saba'in" ta sheqe da dariya,hakanan maganar nujood ta bawa widad dariya "Ki daina sharri wallahi,ba lallai ma ta jiyo qamshin ba kike abunki" ido nujood ta zaro "Lallai yarinyar nan bakisan kishiya da kishi ba" harara widad ta watsa mata "To yaya babba" sai suka saka dariya. Kayan makeup ta hadawa nujood da sauran qannenta,sannan ta bata turare tace ta kaiwa hajjaa,ta rakasu farfajiyar gidan,saida drivern ya iso suka shiga mota sannan ta juya zata koma ciki. Kacibus sukayi da hafsat din,ido ta zubawa widad,itama saita zuba mata nata idon,dauke kai widad din.tayi ta wuce abinta,abun da ya qara daurewa hafsat din kai,tabi da kallo mamaki yana cikata,sai kuma ta ja qwafa cikin ranta tana sakin murmushin mugunta "Yaro man kaza,yaro baisan wuta ba sai ya taka" ta fada a fili,nishadi yana cika Zuciyarta. Ganin duhun magriba ya kawo jiki sai ta lafe a falon tanata duba agogo,sanda taji shigowar motarsa saita narke cikin kujerar tana tsumayin shigowarss,ba jimawa kuwa yayi knocking,ta taso a hankali tana tura baki gaba ta bude masa. Ko gama buduwa qofar batayi ba ya shigo ciki,cike da zaquwa ya sanya hannu ya dagata cak ya rungumeta cikin jikinsa yana sansanar kowanne sashe na jikinta,idanunsa a lumshe kunnuwansa na karbar daqon shagwabarta,ya tattara dukka qarfin halinsa ya taka zuwa ciki da ita,suka zube saman kujera,muryarsa na rawa yace "Me ya faru baby doll?,kukan na meye?" "Uncleeee......" Ta kirashi a narke "Ba kai bane,baka dawo da wuri ba,tun da rana nake jiranka" muryarta har tsakiyar kwanyarsa,tattausan murmushi ya subuce masa,ya cusa kansa cikin gashin kanta bayan ya zame dankwalin "Uhnnn......inda na dawo me zaki bani?" Ba zato yaji bakinta a kunnensa,da zazzaqar muryar ta din nan ta rada masa wani abu da ya sakashi qanqameta cikin jikinsa "Wayyo Alla na" ya fada cikin taushi,saita qyalqyale masa da dariya cikin matsananciyar kunya tana boye fuskarta,hannuwansa duka biyu ya saka ya daga fuskartata yana kallonta cikin tsakiyar idanunta da nashi idanun da suka canza launi "Gani na dawo,ko yanzun baby banyi late ba,don Allah kada ki fasa" ido ta lumshe sosai tana sake sakin murmushi,cikin hirarsu da nujood ta tsinci wannan,ashe haka uncle din nata keso yaji ta furta hakan? "Naje nayi sallah na dawo?" Ya tambayeta a narke shima,kamar qaramin yaro,saita gyada masa kai,ya miqe cikin qarfin hali yana dubanta "Bari nayi alwala.na fito" "Na rakaka uncle?" Ido ya zaro "Bakyason alwalar tawa ta tsaya kenan?" Saita saki qaramar dariya tana kwantar da kanta a hannun kujera. Kafin ya dawo ta gama sallarta itama,haka kawai yau ta tsinciki kanta cikin zumudin kasancewa tare dashi,wani irin sabo kullum zuciyarta ke sake yi dashi,saita miqe ta hada masa ruwan wanka,ba'a dade da.idar da sallar isha'i ba ya sake shigowa. Zaman cin abincin yayi bayan ya gama wankan,ya shaqi daddadan qamshin da miyar ke bayarwa,take tsohuwar yunwarsa ta tash,sanda yakai abincin bakinsa kansa qarasa kuncewa yayi,kamar kullum qarawa hannunta zaqi akeyi "Ki zabi dukka tukuicin da kikeso na baki na dafa min abinda nafiso da kikayi" murmushi ta saki "Kace Allah yayimin albarka,haka ummu ke yimin idan nayi mata wani abun kirki" kai ya jinjina yana sake samun gamsuwa da yarinyar a ruhi da gangar jikinsa gaba daya,tun daga tarayyarsu zuwa yau ya tabbatar ta samu cikakkiyar tarbiyyar da irinta tayi qaranci ga yaran yanzu,shikam zai iya cewa ya tsincik diamond ne a cikin tarin duwatsu marasa daraja can can. Cikin lallausar muryarsa data karye ya fara mata addu'a,addu'ar data dinga amsawa tana murmushi,saboda da gaske tayi mata dadi sosai. Karar sautin wayarsa ya katse musu daddadan yanayin da suke ciki na wata irin hira me tafi da hankali da tunani,daya duba sai yaga hafsat ce,ya danyi mamaki kadan,duk da dazun daya shiga ya sameta tana sallah,sai kuma bai qara komawa ba,ya bari sai yazo rufe gidan,ransa bai kawo komai ba ya jawo wayar ya daga. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 89 Sallama yayi sannan yayi shuru na wasu seconds "Okay' taji yace,ya sauke wayar yana sakin ajiyar zuciya sannan ya kalli widad "Baby.....ina zuwa" kawai sai taji ranta yayi mata babu dadi,a sanyaye ta gyada kai,ya sunkuya a hankali yayi kissing goshinta sannan ya fice. Tashi tayi ta tattara kayan abincin da ya gama ci,ta gyara wajen sannan ta dawo saman kujera ta kwanta tana maida idanunta ga tv,saidai kuma fiye da rabin hankalinta yana kan abbas,ko yaya taji motsi sai ta daga kai taga ko shine. Tun tana kallon agogo da marmari har ta sare,tun tana danne zuciyarta har ta kasa ta fara sharar hawaye ganin sha daya ga sha biyu itama ta gota an tafi qarfe daya na dare,saita fashe da kuka tana curewa cikin kujera,tsoro haushi da takaici hadi da baqinciki suka mamayeta,me yasa uncle zaiyi mata haka?,daga cewa gashinan yanzu yanzu?. Hada kai da gwiwa tayi tsakanin cinyoyinta ta saki kuka sosai,zuciyarta na wani irin tafasa,ya tafi wajen mummyn mimi ya barta ita kadai?,bayan shi yayi mata alqawarin a nan zai kwana yau. Tun tana kukan da qarfinta har ta soma jin babu dadi,zuwa uku na dare kukan ya isheta ita kanta,a hankali kuma wani wahalallen bacci mai hade da bacin rai ya dauketa nan cikin kujerun falo. Cikin mamaki yake saka kanshi cikin falon,wayam babu kowa,sai tarkacen kwanukan da suka gama cin abinci da sauran datti wanda dama falon baya rabo dashi,haka ya dinga tsallake shirgi har yakai qofar dakinta. Yana murda handle tana sakin wani irin nishi,abinda ya sanyashi buda qofar da dan hanzari ya saka kai ciki. Male male ya sameta,kwance qasan tiles tana juyi daga wannan bangon zuwa wancan,tana ganinsa ta dago masa hannu,idanunta jagab da hawaye. "Subhanallah" ya fada yana qarasowa da sauri inda take kwancen,ya saka hannu yana dagota,gaba daya jikinta sharkaf yake da gumi,ya dorata saman cinyarsa yana tambayarta "What's going on?,me yake damunki?" "Cikina abban mimi......cikina zai fashe.....wayyo Allah" ta sake fada da qarfi tana wani irin murdewa. "Relax,ya isa" ya fada yana riqe hannunta dake saman cikin nata "Mutuwa zanyi,mutuwa zanyi,ciwo yakeyimin" ta sake fada tana riqeshi da kyau "Ba abinda zai sameki,ki nutsu,bari na fiddo mota sai mu wuce asibiti" gan ta riqe hannunsa cikin nata "Don Allah kada ka tashi,wallahi kana fita zan iya mutuwa" "Just a minute......yanzu zan dawo,saina kira widad ta kwana da yaran kafin mu dawo" kai ta jijjiga masa tana fashewa da kuka "Don Allah nidai kada ka tafi,ka mayar dani kan gado,sanyin wajen nan kamar zai fasamin qashi" duk yadda zai motsa ta hanashi,ko waya da yakeson kira taqi bari,haka ya miqe ya dauketa ya azata saman gadon,tana ajjiyeta ta kanainaiyeshi da hannuwanta tana ci gaba da matagugun ciwo. Da qyar ta bari ya saka hannu ya kade shimfidar gadon saboda datti datti da yake ji akai,ya jawo mata pillow dinta da pillow case din ta gaji da haduwa da dattin dauda,sai tasa hannu ta kare "Ka barni a jikinka please,ina samun relief" ta fada tana hawaye,hakanan ya zauna jingine da makarin gadon yana fatan ta samu sauqi,duka hankalinsa akan agogo yana mamakin yadda lokaci yaja haka,widad na ransa,ya dauki wayarsa ya fara kiran layinta. Har wayar ta qaraci ringing dinta ba'a dauka ba,ya sake kira nan ma ba'a daga ba,ya danji relief,saboda ranshi ya bashi cewa bacci ne ya dauketa. Jin shuru abun ya lafa sai yadan motsa da nufin sa mata pillow yaje ya duba yaran ya wuce sassansu,ji yayi tayi caraf ta riqeshi,cikin kuka kuka tace "Yanzu ba zaka iya zama dani ba daddyn mimi?" Tayi maganar tana sake riqeshi d kyau "Ya isa shikenan,yara zan duba,kuma.nabar qanwarki batasan me ake ciki ba" banza tayi taci gaba da sharba kukanta kamar ma bataji abinda yace ba. Duka duka baccin minti arba'in yayi aka qwala kiran sallar asuba,ya zame jikinta ya kwantar da hafsat dake baccinta sosai,har ya buda toilet dinta yaji bazai iya shiga ba,ya koma ya buda dakin yaran. Sai daya duba lafiyarsu sannan ya shiga nasu bandakin dake da sauqin qazanta yayi alwalar ya wuce masallaci idanunsa akan sassan widad. Tun kiran sallar farko ta tashi,ta farka tana sauke ajiyar zuciya na kukan data sha,ta kalli agogo saiga wasu hawayen,ranta ya motsu qwarai,kawai sai ta miqe ta wuce dakinta tana jin bacin rai yana cikata. Alwala ta daura,ta dawo cikin dakin ta jawo akwatinta guda daya ta fara sauke kayanta kaf tana lodawa a ciki,tana yi tana sharar qwalla,itakam yau ta gama kwanan bauchi. Akwati biyu ta shirya cike da kaya,ta jawosu falo sannan ta koma dakin tayi sallah,sai ta shiga wanka kawai,bayan ta fito ta shirya cikin atamfa dinkin riga da skert,ta zabi hijabin daya dace da atamfar jikinta ta dawo falon riqe dashi tayi zaune kusa da akwatunta tana share qwalla lokaci bayan lokaci,jiran shigowarsa kawai takeyi. A gurguje ya kammala azkar dinsa ya baro masallacin,gaba daya hankalinsa yana kan widad din,key dinsa yayi amfani dashi ya bude qofar falon,ya tura a hankali yana mamakin ganin qwan wutar falon a kunne "Subhanallah" ya fadi sanda yayi tuntube da akwatin widad,sai yaja baya yana kallon akwatunan guda biyu dake maqare da kaya,sannan ya maida dubansa ga widad din. Fuskarta a dinke tsaf,sai qananun qwalla da take sharewa,ta dauke kanta daga gareshi gaba daya,sam taqi yarda su hada ido,ya fahimci laifi ya tafka a jiyan,kuma da alama laifin babba ne a wajenta,ya zube hannayensa a aljihun rigar jikinsa yana qare mata kallo gami da sakin murmushi,wata qauna da soyayyarta mai kaifi tana hudashi,sai ya fara takawa a hankali zuwa gabanta. Yana isa ya tsugunna saman qafafunsa yana qoqarin leqa fuskarta,amma kuma ta hana hakan faruwa,mamakin hawayen dake kwance saman fuskarta ya kamashi "Is that serious?,kuka take da gaske?" Ya tambayi kansa "Assalamualaikum" ya fada a tausashe,amma maimakon ta amsa saima hade rai data sakeyi tana share qwallar dake kwarara "Ya salam,baby kuka kuma?" Shuru nan ma tayi masa "kinga,ya isa,yi shuru ki gayamin menene?" Sai ya miqa hannunsa a nutse ya kamo hannuwanta,saita zame hannuwan nata ta fashe da kukan da take dannewa "Ba kai bane, kayimin alqawari,shine kuma ka tafi can ka kwana" "Ya salam......kishi?" Ya tambayi kansa cikin mamaki hadi da tsareta da idanu,saidai kuma wani abu mai sanyi na kwarara cikin zuciyarsa "He won.......ta fara sonshi" ya bawa kansa amsa yana jin duniyarsa na cika da farinciki,ya gyara tsugunnon da yayi a gabanta zuwa zama sosai yana sake kama lallausan hannunta "it was not intentionally.......naje na sameta bata da lafiya ne,i called you ki duba wayarki" sam ji tayi bata nutsu ba,gaba daya garin ya gama fice mata aka,sai ta sake zame hannuwanta "Ni tafiya zanyi" ido ya fidda cikin fargaba,ya kuma tambayeta cikin hanzari "Ina?" "Kaduna,bazan sake kwana a nan ba" ta fadi tana sake sakin kuka. Ajiyar zuciya ya sauke yana kama kunnuwansa da kyau "Am sorry please forgive me" "Allah ni tafiya zanyi,bazan sake kwana a nan ba". Duk yadda zaiyi yahi mata akan tayi haquri su qarasa weeknd dinsu amma ta tubure tace sam,itafa a yanzun saiya shirya sun wuce,daga bisani yace mata ta bari zuwa yammaci nan ma ta tubure masa,sam taqi zama suyi magana da nutsuwa da fahimta dashi,gaba daya ta birkice masa,saiya sauke ajiyar zuciya yana kallonta yadda take kuka riris,zuciyarsa na wani irin suya,kukanta a yanzun shine abu.mafi girma da zuciyarsa bata qaunar ji,ba kuma zata iya jurewa ba,sai ya sanya hannu ya jawota cikin jikinsa yayi mata kyakkyawar runguma yana shafa bayanta a hankali cikin sigar lallashi. Da qyar yadan shawo kanta ta tsaida kukan,dole ya soma hada kayansa sannan ya wuce toilet ya fara shiri. Ta bangaren hafsat kuwa yau ranta fes ta tashi,anty ummee ce mutum ta farko data soma kira ta zayyana mata komai,sunci dariya abinsu kamar ba gobe "Na gaya miki indai zaki iya jura wannan yarinyar juyata ba wani babban aiki bane,nawa take gaba dayanta?,da kanta zata ja qafafunta ta koma gidan ubanta". Sun jima suna hira da ita sannan sukayi sallama,tanaso tadan sake gyarawa kodon abbas din amma kuma tana tunanin idan tayi hakan kamar zaiyi saurin dago plan dinta,don haka ta narke taci gaba da kwanciyar ta. Tsaf ya gama shiryawa yau din cikin qananun kaya,trouser da shirt na kamfanin Armani masu asalin tsada da aji,ya waiwaya a hankali cikin kamewa da nutsuwa ya dubi widad da har yanzun ranta yake a hade,suna hada ido ta sake dauke kai,dariya ta taso masa,ya saki qaramin murmushi yana girgiza kai "Am done qanwata" kalmar qanwar tawa daya fada ta sakata waiwayowa tana kallon idanunsa,dama abinda yake da muradi kenan,abinda kuma yayi kewa kenan,ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na zubawa,yayi missing nata har baisan adadi ba "Zan iya zuwa nayi sallama dasu mimi?" Ya fada da wata kasalalliyar murya,saita gyada kanta a hankali,har ya taka zuwa gaba ta bude baki a hankali "Kada kuma ka sake zama irin ta jiya" cak ya tsaya yana dariya qasa qasa,wow......at her age amma ta iya kishi haka?,what if idan ta sake girma da wayo?,haka yayi gaba yana murmushi shi daya bayan ya amsa mata da "Yes ma'am I will be back quickly" cikin ransa yana raya girman mulki irin na diya mace,banda haka widad din da ya haifeta amma kai tsaye take bashi command,kamar ba shine ke bawa manyan zaratan police order ba kuma subi cikin hanzari da gaggawa "Mace ta wuce haka" wata zuciyar ta raya masa,ya jinjina kai yana sake sallamawa lamarin mata. Da murmushin da ya jima bai gani ba saman kuncinta ta tarbeshi "Ina kwana?" Ta gaidashi tana kallonsa da kyau,yayi mata kyau over,sai taji wani kishinsa yana ratsata,abbas din ba daga nan ba,mutum ne mai wani irin class da iya ado da gayu,ko yaya ne sai ya dauki hankalinki idan yayi kwalliya,sassanyan qamshinsa ya cika dakin gaba daya "Lafiya alhmdlh,ya jikin naki?" Sai ta sake sakin murmushi tana cewa "Da sauqi,naji dadin jikin" "Ma sha Allah,Allah ya qara lafiya" "Ameen" ta bashi amsa tana ci gaba da qare masa kallo "Su nawwara fa?" "Basu tashi ba......kayi kyau daddynsu" da dan mamaki ya kalleta,don kalma ce baquwa a kunnensa da bakinta,har widad da tazo daga baya bayanta ta fita iya fadinta,har baisan adadin sau nawa ita din ta fada ba "Thank you,na gode" "Amma wannan kwalliyar da safen nan fa?" Gyara tsaiwarsa yayi,don gaba daya bayajin dadin wanzuwarsa cikin dakin,iskar da take kaikawo a dakin bata masa ba at all "Inajin zamu wuce Kaduna ne" cikin mamaki ta qanqance ido "Kaduna kuma fa kake cewa,yanzu yanzu?" Yasan dole sai taja magana,bai kuma san sanda zasu gama ba,don haka ya taimaki kansa ya matsa window din dakin ya yaye labulen ya kuma bude glasses din Windows din ya bawa iska damar shigowa,kafi ya gama aikin ya amsa mata ta sake sakin qorafi,har qasan zuciyarta bata gamsu da wannan tafiyar ba ta gaggawa irin haka "Amma dai gaskiya daddynsu wannan tafiyar......kalli fa qarfe nawa gaba daya?" "Uzuri ne na gaggawa ya taso,so dole a tafin yanzu" shuru ta danyi har zuwa sanda ya ajjiye mata dukka kudaden da ya saba aje mata idan zai tafin,sukayi sallama tana daga kwance bata motsa ba,ya saba da wannan idan da sabo,don haka ba wani damuwa ya wuce dakin yaran,sunta bacci ya tofa musu addu'a ya fito,ga mamakinsa sai ya sameta zaune hannun kujera a falo,ta dubeshi sannan tace "Muje na rakaka mota" baice komai ba ya juya yayi gaba tabi bayansa. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 90 Tun kafin su qarasa gaban motar tasa idanuwanta akan widad,a lokacin bata kula dasu ba,sai da suka kusa da ita,iska ta fara debo mata qamshinsa,saita lumshe idanunta tana sauraren bugun zuciyarta tare da dakon isowarss,qamshin nasa na daya daga cikin ababen da ko a bacci zata iya tantancesu. Data waiwaya sai ta gansu su biyu,haka kawai taji ba dadi,saita dauke kanta ta dauki wayarta kafin su qaraso ta fara dannawa,hakan ya bawa Hafsat daman qare mata kallo da kyau,wani bahagon kishi na dukanta "Kada fa dan hakkin data raina yazo ya tsone mata ido" ta fadawa kanta da kanta sanda take qarewa gefan fuskar widad din dake kwance da wani gashi mai santsi "Anya kuwa batayi kuskure ba data gaza rabasu tun a farkon tafiya?" Ta sake tambayar kanta,da qyar ta hadiye wani abu mai tauri,taja ta tsaya kafin su qarasa tana yin magana da abbas din "Kasan dai akwai ragowar kwanaki na akanka" dubanta ya danyi, mamaki ma take bashi idan tana zancan kwana,kamar ta wani bashi muhimmanci,ya furzar da iska daga bakinsa "Na gaya miki amma uzuri ne ya taso ko?" Kai kawai ta gyada tana maida dubanta ga widad daya hakimce a gaban mota,zuwa yanzun ta zura earpiece a kunnenta ma. Mintunan agogon wayarta take ta kalla tana lissafa mintunan da sukayi a tsaye shida ita,tanata qoqarin danne abinda yake taso mata harta gaza,ta daga fararen idanunta masu girma,ta sake sauke glass din motar,a shagwabe ta kira sunanshi "Uncle......don Allah ka taho mu tafi......naaaa gajji" "Kambu" Wasu tagawayen duka qirjin hafsat yayi,sautin muryar widad din sai ya zame mata kamar saukar ruwan dalma a kunnenta,yayin da ta fusgi hankalin abbas sosai,har dai daya sauke wata qaramar ajiyar zuciya da hafsat din ta jiyota har tsakiyar kanta,wannan ya sabbaba mata maida dubanta kansa cikin sauri ba tare data shirya ba. Wani irin kallo da ita daya ta sanshi cikin idanunsa ta hanga kwance cikin idanuwan nasa yana yiwa widad din shi,wani malolon abu ya tokareta,dukka juriyar da takeson gwadawa ta gushe "To uwarmu,saiki saurara mana,ko sallamarma bazamuyi ba?" Ta fada da madaukakin sauti tana duban widad din da wani irin kallo,kallo daya widad din tayi mata ta dage glass din motar,gab da zata kammala rufewar ta daga yatsunta tayi masa sign na i love you,hafsat din bata gane me ake nufi da hakan ba,taga dai ya saki siririn murmushi,sannan ya maida dubansa ga hafsat din da takejin kamar ta taka zuwa gaban motar ta fusgo yarinyar. Cikin nutsuwa ya miqa mata tattausan hannunsa alamun musabaha,wannan kusan dabi'arsu ce shida widad,sai tabi hannun da kallo "Amma dai kasan ni ba namiji bace ai" murmushin da bai shirya ba ya qwace masa,ya manta ba widad bace,sai ya matsa gabanta kadan yayi kissing goshinta yaja baya yana mata sallama,yayin da widad daga cikin motar tana hangesu,saita tura baki gaba tana jin haushin abinda yayi mata. Har abbas din ya shiga motar ya tayar hafsat tana tsaye tana kallonsu,sai da suka fice daga gidan sannan ta koma sassanta da sauri kamar zata tashi sama,yau tabbas dole ta hadu da anty ummee,koda ba anty ummeen ba dole ta nema abokin shawara,tana jin alamu da qamshin lalacewar komai anan kusa idan bata sake daura damara ba,ta gaji da wanna pretending din,gwara ta fito sak a mutum ko zatafi qwatar 'yancinta tare da nunawa yarinyar ita ba kanwar lasa bace,ba kuma sa'ar yinta bace ita. Juyawa yayi yadan kalleta kadan jin tayi shuru,tunda ya shigo motar batace komai ba,sai yaga titi kawai take kalla,ya motsa kadan ya saka tafin hannunsa cikin nata ya riqe da kyau cikin taushi "Ba dai shikenan ba,kin hanani zama ko?" Daman jira takeyi,saita turo baki "Bayan harda kiss dina ka yiwa mummyn mimi" sosai dariya ta kamashi,ya dan daki sitiyarin motar yana dan dubanta "Wato kiss din ma naki ne.....wai.....yaushe kika koyi qorafi haka ne babyn uncle?" Fuska ta hade bata ce komai ba,ya sake sakin murmushi "Yaushe kika koyi kishi ne baby?,Ita kiss dinki nayi mata,ke kuma uncle din kika dauke gaba daya,ba shikenan an raba ba?" Murmushi tadan saki ta jijjiga kai "Good,yanzu bani labari,me dame za'a yimin idan mun koms,kinsan nayi missing dinki.....nayi missing abun nan....." Ya fada ba tare daya qarasa ba,saita juya tana kallonsa,girarsa daya ya dage mata tare da kashe mata ido,abun ya bata kunya sosai,sai ta rufe fuskarta da hannuwanta tana dariya,shima ya tayata dariyar idanunsa na kallon titi. Ko wanka bata tsaya yi ba,saboda tana ganin kamar zai bata mata lokaci ne kawai,ta canza kaya ta canzawa nawwara pampers,ta kada kan yaran ta zubasu a motarta suka wuce gidansu. Kallonta kawai mamanta takeyi sanda take gaya mata duk irin abubuwan da suke faruwa "Amma su uwa sun ha'inceni,keda duk da wadan nan matsalolin cikin gidanki amma kike zaune haka kina amfani da gurguwar shawarar ummee?,don ta kai mata ke lallai ne takai mikin?,bari na kira hajiya shuwa naji wanne malamin zata hadaki dashi" ta cire wayarta dake kusa da ita a chargy ta soma neman number din. Kamar hafsat tace abarsa,duk ds yadda matsalar take damunta,amma dai sai ta kanne tana sauraren mamar tata sanda suke gaisawa da hajiya shuwa din. Tana zaune tana sauraren umman nata tana yiwa hajiya shuwa bayani,bayan ta gama suka shiga tattanawa,kusan minti talatin sannan sukayi sallama,ta dubi hafsat "Baki da wata matsala,itama kanta fadan zaman da kikeyi takeyi,tace yanzu ai ba'a zama,kada kiga wai yarinya qarama,idan batayi ba magabatanta zasuyi mata,bare sadakar yalla?,ai sai addu'a kawai,shu'umai ne" kai ta jinjina tana jin abun yana damunta har cikin zuciyarta "Yanzu kudi kawai zaki fito dasu,sai mu saka rana mu sameta,tunda baya gari ma komai zaizo da sauqi" "Kudi kaman nawa?" Ta tambaya tana duban umman nata "Daga dai dubu dari zuwa sama" "Za'a kaiwa malamin?" Hafsat ta tambaya tana dan riqe da habarta "Eh,har miliyoyi ma ai kashewa akeyi,ita ranar biyan buqata rai ai ba'a bakin komai yake ba" janye hannunta tayi tana gyara zamanta,itakam bata jin ko naira dubu goma zata iya fitarwa,kudin da take fadi tashin tarawa rana daya ta wafci wani abun a ciki ta fara kaiwa wani suna raba dai dai,koma ya fita ci "Shikenan umma,ki bari idan na shirya sai ayi mata magana sai muje" wani kallo uwar ta watsa mata,dama tuni labarin yadda ta baci da son abun duniya yake zuwa mata "Kudin ne ba zaki iya fitarwa ba kenan?,ko a jikinsa ba zaki tarasu ba hafsatu?,gwara ki zauna da damuwarki kenan?" Kai ta girgiza "Ni ba haka bane umma,kawai dai matsalar batayi girman da zan kashe wadan nan kudaden ba,mu bari kawai anty ummee din tazo nasan tabbas akwai mafita daga wajenta,basai an kashe komai ba" haushi takaici da baqinciki suka cika umman,saita dauke kanta gefe tana cewa "To ai shikenan,sai kici gaba da zama har sai sanda matsalar ta girmama ta zama babbar". ***********Tunda suka koma ta tattara ta watsar da batun mommy hafsat din ta shiga sabgoginta,sosai ta maida hankalinta ga karatunta koyon girke girke online da kuma practical classes da akeyi cikin garin kadunan. Cikin lokaci qalilan ta zama expert,hannunta ya sake fadawa,ta kuma qware da kalolin abinci masu dama. Zamu iya cewa batason so ba,amma tana jin wani abu mai qarfi akan uncle din nata,wanda inda da cikakken wayo kai tsaye zata fahimci soyayyarsa ce ta fara kafa kanta a zuciyarta,sam bata iya wuni guda cikin nutsuwarta muddin baga ganshi ba,kowanne lokaci burinta shine tayi abinda zaice "That's my baby.....ma sha Allah baby wannan yayi......baby doll inason abu kaza,babyn uncle wannan yayi dadi ko yayi kyau" wannan ya sanya ta sake zagewa da dukan iyawarta ta haddace abinda tasan yafiso yafi muradi,gefe guda anty deena da anty madeena harda hajja sun zage sosai suna wayar mata da kai dai dai gwargwado. Ta gefan abbas kuwa abun har baya faduwa,wani irin wawan kamu soyayyar widad tayi masa,ta yadda shi kansa yake mamakin kansa,zuciyarsa ta koma sabuwa,tamkar bai taba qaunar wata halitta ba cikin rayuwarsa,yarinyar ta tafi da dukka zuciyarsa,ta kuma shiga rayuwarsa fiye da kima,har bayason wani abu da zai kawo su nisanci juna,duk da yana fama da shagwabrta sakalci da kuma wauta amma hakan sai ya zame masa kamar wani abun debe kewa,ya kuma zame mata ado,kasancewar bai saba ganin wannan ba. A koda yaushe hafsatun na masa magana ne a tsaitsaye,tana kuma nuna masa ita din me wayo ce,bata da lokacin shagwaba ko karya murya,kamar yadda take ganin bai kamata ace mutum yana da wani choice a rayuwarsa ba na tsafta abinci turare sutura da sauransu ba,banbancin ra'ayi me girma da kuma tarin yawa ne a tsakaninsu. Sabanin widad,da komai nata nashi ne,komai zatayi tana duba zai burge uncle?, uncle zaiji dadi?,hatta da shopping tana yinsa ne base on his choice,komai ta dauka saita tambaya cikin shagwabar nan tata "Uncle yayi?" Wani lokaci yace baiyi ba,wani lokaci kuma ya barta da zabinta,ya zuwa yanzu bayajin akwai wani abu da zai iya shiga tsakaninsa da widad din,ta shiga rayuwarsa fiye da kima,ta samu gurbi a zuciyarsa sama da yadda kowa yake hange. Tun daga wancan ranar ta rage binsa weeknd bauchi kwata kwata,koda ta bishi ma raba kwanan take tsakanin gidan hajiyan da kuma gidansu,dukkansu shi da hajiyan da suka fuskanci hakan yafi samar mata da nutsuwa sai suka rabu da ita. Hafsat na gama kwananta baya iya jurewa,haka zai je gidan hajiyan da kansa yayita raragefen daukarta saboda kunyar hajiyan,abinka da uwa,takan bishi da murmushi ne kawai sannan ta sanya widad din shiryawa ta kuma bishi,a yanzun duk duniya tafi kowa samun farincikin canjin da abbas din ya samu,idan ka kalleshi da kyau zaka fahimci hakan,don har wata murjewa yayi,yayi 'yar qiba,ba shakka ko ta iya fannin abinci kawai dole rayuwarsa ta sauya,saboda shi din mutum ne da baya wasa da cikinsa,sai Allah yasa widad din bata da wani fatinciki itin ta ganta cikin kitchen tana sarrafa wani sabon abu da basu saba ci ko basu taba ci ba,koda yaushe hajiyan godewa Allah takeyi da sauyin da abbas din ya samu,nutsuwa sosai tazo masa,duka matsalolin hafsat ma sai suka rahe damunsa,tunda ko ba komai akeai gefen da yake samun nutsuwa gamsuwa da kwanciyar hankali,inda widad din yakeso takai wanda bata qarasa kaiwa ba yanata qoqarin horar da abarsa cikin soyyaya qauna kulawa da kuma nutsuwa. Gefe daya hafsat din itama bata sake tayar da zancan ba,saboda anty ummee ta kwabeta kan ta barta haka,kada a fahimci takunta,saidai akwai sabbin hanyoyin da zasu sake dubawa. _wannan kenan_ *Masu karatu muje zuwa,akwai sinqi sinqin CAKWAKIYA a gaba* *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 91 Sassanyan qamshi parlor din yake fitarwa baya ga wani kwantaccen yanayi da duk wanda ya shigo ciki sai ya burgeshi,awa guda kenan da gama dukka aikinta,ta kuma shirya kanta cikin wata gown ta yadin chiffon mai qaramin hannu,plain ne black babu digo ko adon komai a jiki,ta matse gashinta da jiyan abbas ya kaita da yammaci aka gyara mata shi,yana daya daga cikin abinda yakeso,shi yasa shima yake bashi kulawa har fiye da yadda ita ke kula da sumartata,duk sanda take kwance a jikinsa zaka samu hannunsa saman kanta yana yamutsa sumartata mai tsaho da santsi,abinda yake yawan haifar mata da kasala,saita lafe a jikinsa. Hankalinta ya dauku ga wayarta sosai,tana karanta wani hausa novel mai suna HANGEN DALA,labarin ya tafi sosai da hankalinta,ya kuma fara ankarar da ita matsayin hafsat a wajenta. Ya dauki mintuna kusan uku tsaye a bakin qofar yana qare mata kallo ba tare data sani ba,hancinsa kuma yana shaqar daddadar iskar da parlor din yake fitarwa. Tayi masa wani mugu mugun kyau,cikin kwanakin gaba daya wani kyau take qarawa,ga wani irin fari data sakeyi kamar ka sanya hannu jini ya fito,ta kuma qara qibar data sakata murjewa,alamun hankali da girma sun fara nunawa a jikinta,qibar tayi mata wani irin kyau dake dimauta masa tunani,shi kansa wani lokaci yakan tuhumi kansa "Abbas anya baka zauce akan yarinyar nan ba?" Bai sani ba ko zaucewar yayi,amma shi kansa yasan yana mata wani irin so da bazai misaltu ba,baya gajiya da kallonta,baya gajiya da ganin shirmenta,baya gajiya da sauraren hirarta,ko ba komai zai samu nishadi irin wanda duk duniya idan ba wajenta ba babu wajen wanda yake samunsa. Yaga alamun hankalinta yayi nisa sosai,don haka ya sanya qafarsa cikin tattausar muryarsa yayi mata sallama,suna hada ido ta miqe da sauri bayan ta watsar da wayar gefe,ta kuma tako da sassarfa yadda ta saba yi masa ta dane shi,ya sanya dukka hannayensa ya tarbeta,ya kuma dauke abarsa cak ya aza a jikinsa yana aika mata kisses ta ko ina,laushin fatarta da qamshinta kamar zai zautashi. Kamar ko yaushe ta sunne kanta tana jin kunyarsa,ya saki qawataccen murmushi yana shiga cikin falon sosai da ita hadi da cewa "Gayamin.....me zanyi na qarasa cire kunyar nan baby......tana qwarata wani lokacin fa" ya fada murya qasa qasa kamar su da wani ne a falon,saita sakar masa murmushi tana shigewa jikinsa. A hakan yana dauke da ita suka shige bedroom dinsa tana masa sannu da zuwa "Yau anyi zafi,wanka zan fara yi baby,ba wani abinci yau" dariya ta sakar masa,sannan ta wantsalo daga hannuwansa zuwa qasa,ya tareta da sauri yana cewa "Yi a hankali,wai bakiga kin fara zama 'yar lukuta ba?,inajin na kusa fara kasa daukarki" baya taja tana bata fuska "Ka kusa daina daukata kuma uncle?" Ta fadi tana bubbuga qafa a shagwabe,yasan yanzun zai ballowa kansa ruwa,sai yayi saurin yin kwana "Wasa nake miki fa babyn uncle.....amma fa wait.... seriously kin fara zama 'yar lukuta,ban yarda ba akwai abinda yake faruwa,me kike ci bakya sanmin?" Siririyar dariya ta saki "Uncle ka fini ci fa,saidai wanda nake ci da daddare kana bacci" kai ya gyada yana dariya "Harda rabona kike ci ai,kuma ban bayar ba,saina fanshe abuna,zo nan" ya fada yana takawa gabanta idanunsa a narke a kanta,ta saki dariya taa fadawa toilet da gudu. Tsayawa yayi ya bita da kallo har ta shige,qugunta ya bude sosai,qirjinta ya fara cika irin yadda yakeso,abinda yake sake dimautar dashi a kanta koda yaushe,saidai har yau 'yar shagwabar tasa kukan amarci takeyi bata daina ba,hakan baya damunsa,hakan ma burgeshi yakeyi,ya zauna ya lallashi kayarsa. Gaban mudubi ya taka ya zuge jakar daya shigo da ita yana duba takaddun daya shigo dasu,ya sake sakin murmushi yana tunanin irin yadda zataji idan ya gaya mata komai na tafiyar ta saudiyya ya kammala,yana tsaka da dubawar kuwa ta fito tana goge ruwan hannunta da qaramin towel "Uncle ka shiga na hada" ajjiye su yayi,ya matsa zuwa gabanta,a tausashe ya kamo qugunta ya hade da nashi yana duban qwayar idanunta,itama shi take kallo,tana samun kanta cikin wani irin yanayi a duk sanda irin hakan zata faru,tana ji da ganin wani abu na musamamn cikin idanuwansa "Amma dai na gaya miki,indai kina yin wankanki bakya jirana,zaki dinga wanka biyu ko?" Fuska ta narke masa sannan ta turo masa dan qaramin bakinta "Uncle saina zauna ka dawo kaga qazantata?" Bin siraram lips dinta daketa qyallin lip gloss yayi da kallo tsigar jikinsa na zubawa,sannan ya dauke ya maidasu cikin manya kuma fararen idanuwanta,har cikin zuciya da ruhinsa yana yaba mata,yadda bata qaunar ya ganta ba wanka,naturally haka take,sometimes kafin ya dawo daga salla tayi wankanta "Okay,tunda haka ne zaki biya ladan qin jin maganar uncle" bai barta ta samu damar cewa komai ba ya hade bakinsu waje daya ya shiga aika mata da wani zazzafan kiss da ya sanya taji kwanyarta tana yamutsawa,cikin lokaci kadan ya sauke mata wani saqo mai nauyi daya sanya jikinta saki gaba daya,yayin da ilahirin nashi jikin ya dauki rawa gaba daya,kusan ta saba da wannan yanayin nasa,tun tana tsoro harta saba gani,ta saba ganin wannan romance din mai zafi daga wajensa,fice mata a hayyacinsa yakeyi cikin lokaci qalilan,wannan yake rudata itakuma tayita masa kula,kukan da baya samun damar lallashinta sai bayan komai.ya kammala. Yau dinma daga bata ladar rashin jin magana ya zarme,shi kamsa baisan me yakeyi ba,illa dai zuciyarsa da qwaqwalwarsa yaji sun kasa jurewa,bai kuma barta ba sai daya isa ga muradinsa duniyarsa qarshen farincikinsa. Tana a jikinsa tana masa 'yan koke koken data saba,hannunsa cikin sumarta yana yamutsata,idanunsa a rufe,lips dinsa kawai ke motsawa suna fidda sautin wasu kalmomi masu zaqi da kwantar da rai,yayin da zuciyarsa tayi nisa wajen son gano iya matakin matsayin da widad ta tsaya a ransa,ko yaushe yana jin kamar a ranar ya fara saninta,tana da wata irin baiwa da bai taba tsammanin za'a sameta jikin kowacce diya mace ba,a duk sanda ya kasance da ita burinsa na sake kasancewa da ita baya raguwa saidai ya qara hauhawa "Uncle wayo" ta fada a shagwabe da siririyar muryarta, murmushi ya kubce masa,hakan take yawan gaya masa duk sanda irin hakan ta faru "Kiyi haquri dani babyn uncle,na jarabtu dake har bansan iyaka ba,am sorry....but I have something special for you,muje muyi wanka ki gani". Tare sukayi wankan duk da tana dan zuzzulle masa,suka shirya ta gabatar masa da abinci yaci cikin nutsuwa da kwanciyar rai,best taste for ever a wajensa. Bayan ya kammala ya jingina bayansa da kujera qafafunsa a miqe harde wajen guda,yatsun hannunsa ma a hade yana dubanta,kamar cin abincinta yadan ragu,tun ranar nan ya gani,amma kuma bai sakashi damuwa sosai ba,ganin bata canza ba,saima murjewa da jikinta yakeyi,hannu ya miqa mata alamun ta taho,saita maqale kafada "Uncle wayo" ta fada tana dariya,bai shirya ba dole shima dariya ta kubce masa,a baya yakan jima baiyi dariya irin haka ba,amma a yanzu.widad ta maidata abu mai sauqi a wajensa idan yana tare da ita,dukka tsare gida shan kunun nan da kamewa sun koma office da sauran guraren aiki "Kizl ki karba albishir din naki,ba wayo bane yanzu" matsawa jikin nasa tayi,ya kuwa riqeta gam yana fidda takaddun ya fara mata bayani. Ruqunqumeshi tayi da kyau cikin farincikin da batasan yawansa ba tana sake tambayarsa "Uncle da gaske?" "Na taba yi miki qarya?" Kai ta girgiza "Baka taba uncle" ta fada hawayen farinciki yana sauko mata,saiya bata fuska kadan "Kuka?,noo baby,don't cry mana" ya fada yana janta jikinsa hadi da dan bubbuga bayanta alamun lallashi. Irin godiyar data dinga masa sai daya ji qwalla ta sauko masa,godiya ce da bai taba jin irinta daga bakin hafsat ba,duk kuwa da ya kaita gurin da yanzun widad din zata je a qalla sau uku kenan,sai ya saka hannuwansa yana sake lullubeta cikin jikinsa da kyau,yana sake jinta tana shiga rayuwarsa da gasken gaske. A ranar ta dinga kira waya tana shaidawa kowa,ummunta mommynta da abbanta sune farko,sannan uncle muhsin anty madeena anty deena dasu hajja,kowa yaji dadi ya kuma yi farinciki da wannan labari,ya kuma tayata murna qwarai, uncle muhsin ya kirashi yayi masa godiya,kai kawai ya girgiza "Bakasan wacece widad a wajena bane muhsin,she meant alort to me,bansan ya zan fasalta maka ba" yayi furucin tun daga qasan zuciyarsa. Murmushin jin dadi uncle muhsin ya saki,amma a fili sai yace "Easy sir.....surukinka nake fa kaketa fallasamin sirrin zuciyarka" sai suka sanya dariya a tare. Cikin satin yace ta shirya zasu wuce bauchi,batajin son zuwa bauchin sam,amma tana son ganin hajiya dasu mimi,don ta kwana biyu bata je ba,bata nuna masa komai ba,cikin karsashi ta shirya musu dukka jakankunansu,ta kuma siyawa su mimi da hajia tsaraba,bayan tace ya turo rose ko samuel su kaita kasuwa,sai gashi ya kashe aikinsa da kansa yazo ya kaita ta siya duk abinda takeso,don yanzun ba kasafai yake bari wani ya kaita wani waje ba,idanma ta kama to saidai ya turo mace. **********Tunda sale ya bude gate din gidan ta gane motarsa ce,amma data fahimci bashi kadai yazo ba saita ci gaba da zamanta saman plastic chair din da take zaune a kai,ta jibge kayan da take siyarwa tana faman lissafi,gefenta su mimi ke wasa kamar ko yaushe futu futu abinsu,kai bakace akwai interlock cikin gidan ba. Widad dake bacci abinta cikin motar ko shigowarsu cikin gidan bata san dashi ba,ya waiwaya yana mamakin nauyin baccin da takeyi a 'yan kwanakin nan,fuskarta tayi wani mugun fresh hasken fatarta ya kashe masa idanu,ya daga hannu da nufin tashinta,saidai mimi da nawwara sun rage masa aiki,don tuni suka fara kiran sunanshi suna rige rigen isowa,muryarsu ta sakata bude idanunta a hankali,ta saki murmushi tana kallon yaran har suka iso garesu. Ita dashi aketa rige rigen tarbarsu,tayi nasarar riqe mimi shi kuma ya dauki nawwara,daga inda hafsat din take kamar zuciyarta zata fado,ta janye idanunta tana jin kamar zuciyarta xata fashe,ta gaji da jiran da anty ummee tace tayi,sai take gani kawai ta soma gajiya da lamuranta,tunda ta nemi aron dubu dari biyu bata bata ba. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 92 Kasa ci gaba tayi da lissafa kudin,idan tayi gaba sai ta dawo baya,dole ta zube kudin tana jin kamar ana sukar zuciyarta da mashi,ta miqe tana gyara daurin zaninta da dan qaramin cikinta wanda ya fara fitowa kadan,duk da duka duka bai wuce wata uku ba,amma saboda tana da tumbi har ya fara bayyana kansa. Tana doso su tana qare musu kallo,dukkansu daga shi har ita sun canza,kamar wadanda ke rayuwa a wajen nigeria ba "Hafsatu kina me?,kina me kika zauna kina gadin gida?,kina meye kika zauna?" Zuciyarta ta fara raya mata,take taji ranta yayi mugun baci,kamar ma kada ta isa inda suke,tunda tun tsaiwarsu babu wanda ya fahimci wanzuwarta a wajen. "Sannu da zuwa" ta fada ciki ciki,qamshin turaren widad wadda ta tsaya daura da ita na cika mata hanci yana kuma qara iza wutar kishinta a zuciyarta. Waiwayawa yayi ya dubeta,har ya daga hannu zaiyi welcoming nata kamar yadda suka saba da widad,sai kuma ya tuna yanzun zata ce yara,ko ta canzawa abun akala,yayi qoqarin sakin qaramin murmushi yana kallon yadda ta canza,cikin tun baiyi nisa ba ya fara birkitata "Sannu mom mimi,ya gida ya jikin?" Ya tambayeta,duk da kullum sai ya kira yaji jikin nata "Alhmdlh" ta furta tana qoqarin saisaita kanta,saboda wani mugun muzanta da taji tayi tsaiwar da tayi kusa da widad din,ta glass din motar da suke tsayen take satar kallon mugun tazarar banbancin dake tsakaninsu da ita,saita zama kamar wata mai aikin gidan,don haka ta janye jikinta a dabarance zuwa gefe sanda widad din ke gaidata,gaisuwar data qona mata rai,don duka hankalinta nakan mimi tana janta da wass,ta amsa mata ciki ciki. Motar ya rufe yana ci gaba da riqon nawwara a hannunsa,ya juya zuwa sassansa yana yiwa naawara waqar da ya saba yi mata hafsat din tabi bayansa da sauri "Uncle" widad tayi kiransa da narkakkiyar muryarta,ba abbas da aka kira sunan shi ba,hatta da hafsat sai da ta tsaya cak,yaji kiran har jikinsa duk kuwa da ya saba,amma yau sai yaji kamar muryarta ta qara zaqi "Kayana please uncle,nagaji part dina zan shiga na huta" "Hutu" hafsat ta fada a ranta "Bai kamata acena qyale ta har tana samun damar hutawa cikin gidan nan ba"hafsat din ta fada a ranta,batasan ya akayi ta barta harta ajjiye dukka wani aiki da take mata ba "Munyi haka ne dake?" Ya fada yana narke mata shima da salon da ita ta koya masa,sai hafsat din ta daga kai da sauri ta kalleshi cike da mamaki,abbas din ke abu kamar wani qaramin yaro?. Baisan me akeyi ba,don idanunsa na ga widad "Alqawari ne zan cika Allah uncle" ta fada tana maqale kafada "Alright" ya amsa mata yana miqawa hafsat nawwara da nufin ta riqeta "Ajjiyeta mana" ta fadi cikin zafin zuciya, ganin yadda ita yakewa maganar,amma duka hankalinsa na kan widad din,baice komai ba ya juya da nawwara a kafadarsa ya daukar mata luggage din yana biye da ita a baya har zuwa sassanta. Da idanu ta rakasu,wai me yake faruwa ne?, yaranta ma farinciki suke da zuwan yarinyar ne?,ga wani abu me girma data lura yana gilmawa cikin idanuwansu shi da ita. Ko kafin ya dawo tuni ta tsufa cikin falonsa,tunani yayi mata katutu,koda ya shigo falon ta daga kai ta dubeshi sai taji gaba daya ta raina kanta,ga laulayi daya sanyata ta kwantsame ta fita hayyacinta,gefe guda rashin gyaran da bata daukeshi a bakin komai ba shima ya taka rawa wajen lalacewar tata. Kusan yinin ranar cikin qunci ta yishi,tana aikace aikacen da ba kasafai ta fiya yinsu ba sai abbas din yazo tana fama da qunci,itakam widad koda ta isa sashenta zagewa tayi ta gyarash fes,yaran na biye da ita har ta gama,ta kama yaran bisa radin kanta tayi musu wanka,tana jin dadin yadda yaran ke qaunarta,a nan falonta ta barsu bayan ta dora aninci mai sauqi,ta shiga itama ta sake wanka. A gaban madubi ta tsaya daure da towel tana kallon kanta,ko ina na jikinta ya fara cika,abinda yaketa bata mamaki kenan,hasken data qara ya ninka nata nada,tasan bata canza mai ko sabulun wanka ba bare tace ko sune suka saka,don kanta ta gaji da kallon kan nata,bata kuma gano dalilin wannan canjin ba saita tabe baki kawai taja manta ta fara shafawa. Hafsat din na gyaran sashen shi kuma yana gyaran closet dinsa,duk da yasan zaiyi wahala gobe widad din bata gyara ta ba,amma kuma yana tausayinta,yana ganin kamar aikin yana mata yawa,don sanitation irin wanda yakeso take a sassan nasa bayan hafsat ta gama jiqa jiqarta. Baisan ma ta gama ta fice ba sai daya gama wanka yana neman wasu qananun kaya nashi,ya tuna suna cikin akwatin widad din,dole ya dora jallabiyya saman towel din dake daure a qugunsa ya wuce sassan nata don ya ciro kayan. A falo ya tambayi su mimi antynsu,sukace tana ciki,ya wucesu bayan ya sake canza musu channel zuwa mbc 3. Sanda ya buda qofar dakin nata ta zame towel dinta tana saka brassiere,tsaf ya qare mata kallo ta cikin mudubin yana jin numfashinsa yana sauyawa,don komai ya fito masa muraran,komai na widad din sake daukan hankalinsa yakeyi kowacce rana,sai yaji ya kwadaitu da son jin duminta cikin jikinsa,don haka ya taka a hankali har ya isa gareta,yayi caraf ya riqe towel din sannan ya fincikota a tausashe zuwa jikinsa. Tare suka sauke ajiyar zuciya shi da ita,ya zaci zata nema qwacewa ko zame jikinta,sai yaji tayi luf cikin qirjinsa,qamshin sabulun wankansa yana mata dadi sosai har zuciyarta,wannan ya bashi damar aiwatar da abinda zuciyarsa ke kwadaita masa hankali kwance,har sai da taji yana niyyar zarmewa sannan ta zare jikinta tana tuna masa su mimi dake parlor. Da jirkitattun idanunsa da suka sauya launi yake dubanta tare da tayata daura towel dinta da ya zame,daurin gaba yayi mata,ya cukuikuye towel din a tsakiyar qirjinta yana duban wajen,sai tasa hannunta guda daya ta rufe,daya hannun kuma ta jawo hijab dinta dake gefe ta soma yunqurin sakawa,ya saki siririyar dariya yana cewa "Please mana,minti kadan fa zan dan kalla saiki rufe". Ya soma kicin kicin qwacewa ita kuma tana nade kanta a ciki tana dariya,da wannan har ta sake komawa jikinsa. Ganin aikin take kamar zai kasheta,ga laulayi gaba daya jikinta babu cikakken qwari,don haka ta tsame hannunta daga yankan salad da takeyi ta nufo sassan widad din. Tun a hanya take kwatanta da yadda zata fuskanceta do kada ma taga sassauci a fuskarta ta nema kawo mata wargi. Bin ko ina na falon ta dinga yi da kallo,ko ina fes kamar yadda abbas yakeso,ya koya mata kenan,tsinanniyar tsaftar nan tasa,taja mugun tsaki tana tambayar su mimi widad din "Tana daki,yanzu abba ya shiga kiranta" wata mummunar faduwa gabanta yayi,abbas kuma?,me yakeyi a dakin?,bayan yau din kwananta ne?,ta gama masa wahala daga kaucewarta har ya baro sassan?,cikin mamaki zafin zuciya da kuma kishi ta doshi dakin,batayi wata wata ba ta murza handle din ta tura da qarfi ta shiga,shigar da batayi mata dadi ba sam,shigar da sai da taji kamar kanta zai tarwatse,abbas dinta widad din kwance a jikinsa suna qyalqyala dariya,duk sun yiwa shimfidar gadonta squeezing. Tare suka daga kai suka dubeta,saita kasa jurar ganinsu ta soma girgiza kai,ga widad kuwa mo gezau batayi ba,tadai ci gaba da janye hijab dinta daga hannunsa tana cewa "Laaa,mummyn mimi wallahi bamuji sallamarki ba,uncle ne,yana nan yana......." Ido ta runtse da sauri taja baya,ta kuma buga qofar da kyau,gudu gudu sauri sauri ta fice daga sassan kuka yana kubce mata. "Yana nan yana me uncle din?" Abbas ya fadi yana jefa mata hararar tsokana,can qasan ransa a bace na yadda ta kutso mata har bedroom dinta ba tare da sallama ko neman izini ba, dariya ta qyalqyale dashi,duk.da qasan ranta taji haushi,ta riga ta saba da dabi'ar yin sallama kafin ta shiga waje,amma ita hafsat din qatuwa da ita batasan tayi ba? "Ba komai" ta amsa masa tana dariya,saiya tsaya kawai yana kallonta yanajin wani farinciki yana wanzuwa cikin rayuwarsa,tsahon seconds sannan ya miqe yayi kissing goshinta,ya qarasa akwatin ya dauki kayansa yana tsokanarta ya fito. Yana dosar dakinsa ya jiyo sautin kukanta,ya girgiza kai kawai yanajin takaicin hafsat din,yana saka kansa cikin dakin ta daga kai tana dubansa,idanunta sharkaf da hawaye,tasan halinsa sarai,miskili ne na qin qarawa yaso,ganin yayi.kamar.bai ganta ba ya nufi dressing mirror dinsa saita buda baki a zafafe "Na gode,na gode sosai da cin fuskar daka yimin,yau kacal amma harka fara satar kwana na kana kai mata?" Kamar bazai.amsata ba har ya gama fesa turarensa bayan ya fidda jallabiyyar jikinsa,sai a sannan taga towel kawai yake daure dashi, zuciyarta ta sake fusata qwarai,ya juyo ya dubeta "Ina kwanan yake?,ina cewa rana ce yanzu?,da kika shiga kuma wani abun kikaga munayi?" Tambayoyin nasa sai taji gaba daya na rainin wayo ne "Kayi laifi amma kana yin kamar bakayi komai.ba abban mimi?" Ta fadi tana nuna qirjinta da yatsanta,zare towel din ya qarasa yi yana sanya kayansa,sai da ya gama tsaf har sannan tana zaune tana dubansa,ya dawo gabanta ya tsugunna yana kallon qwayar idonta,ya sauke idanunsa zuwa ga hannuwanta da farcenta ya dan soma taruwa,ga 'yan qananun datti nan sun fara shiga qasan farcen,sun nuna kansu ne saboda yadda hannun da farcen suka kode dalilin rashin digon lalle ko kadan a jikinsu,abinda yafi tsana kenan ya gani,shi yasa sanda yake bauchi da kansa yake daukarta ya kaita gidan qunshu ya ajiyeta ya kuma bar mata kudi masu dan yawa akan ayi mata,amma da wahala idan ya kaita sau goma ayi sau uku saita kawo uzuri tace layi yayi yawa bata samu ba,wani lokaci ma kafin yazo daukarta ta hayo motar haya ta dawo gida,yasan kuma tabbas kudinta kawai take karbewa daga wajen mai qunshin,a yanzun yanason kama hannun nata amma yanajin wani iri,tun daga ranar da widad ta fuskanci me son lalle ne bata sake zama hannunta haka ba,hasalima bata rabo da sargen da take sawa yatsunta idan bata samu lallen ba,abinka da farar fata,mugun kyau yakeyi mata,wani zubin har tukuici sai ya ajjiye mata. Duk da haka ya kama yatsun hannun nata yadan ja kadan yadda zata fahimci zancan yace "Dani dake waye yafi wani laifi?,Allah da kansa fa cikin qur'ani yake cewa 'yaku wadanda kukayi imani,kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini kunyi sallama akan ahalin gidan,wannan shine mafi alkhairi a gareku,idan ma baku samu kowa ba a cikinsu gidajen kada ku shiga har sai an muku izini,idan kuma akace ku koma ku koma' kinga anan kin sabawa koyarwar qur'ani da sunnah" tunda ya fara maganar ta zuba masa ido tana hawaye,yau gidanta ake cewa ba zata shiga duk inda taso ba saita nema izini saboda ya ajjiye wata "Yanzu abbas gidana kake kafamin wadan nan sharuddan a kansa?" "Ya salam"ya fada yana lumshe ido takaici yana kamashi,wacce irin qwaqwalwa take da ita,yana gaya mata Allah da annabi tana gaya masa molanka da son zuciyarta, kafin ya buda idanun ta dora "A jikinka fa na sameta,ranar kwana na,kaci amanata kanason juya laifin kaina,wallahi sai yanzu na gane dalilin da ya sanya yarinyar nan ta fara rainani,kana raba mana kwana,kana duk abinda kakeyi dani da ita,tana shirme kana biye mata shi yasa take kallon kowa a banza.....". Tsam ys miqe "Excuse me"ya fada a taqaice yana rabata ya wuce,don bazai iya ci gaba da daukar rainin hankalinta ba,kamar yadda ya fuskanci gaba daya ba zata taba gane abinda yake nufi ba. Gaba daya ranar ta bata ta da kuka da takaici,taji a ranta ta riga ta gama yin sake,saidai har yanzu akwai sauran dama da zata nunawa yarinyar ita ba kanwar lasa bace. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 93 Widad kuwa sabgarta take a sassanta,don ko leqowa batayi ba bare ma su hadu,su mimi suna wajenta,sukaci lafiyayyen abincinta suka qoshi,daga qarshe ma bacci a nan ya dauki mimi,nawwara kawai ya dauka sanda yazo yi mata saida safe,tace yabar mata mimi din ta kwana a nan. Uwar bata wani damu ba,a lokacin kawai kallon raguwar hidimarsu bisa wuyanta takeyi,bayan ta kwantar da nawwara ta cimmasa a bedroom,ya gama shirinsa cikin kayan bacci,sassanyan qamshinsa ya cika dakin,yana zaune yana amsa waya hankalinsa kwance,saita bude closet dinsa ta duba doguwar riga cikin kayan baccin da yakan ajjiye a dakin,ta tube rigar lace din jikinta ta aza kayanta tayi fuska,babu batun sake wanka,tunda dai an tsira da wankan safe,ta dawo ta zauna,lokaci lokaci tana kallonsa har ya gama wayar ya aje yana dubanta "Ya akayi?" Ya fada yana kallonta, don yasan halinta,ungulu ce bata jewar banza,zaman da tayi lallai akwai magana a bakinta "jari nake buqata ka bani,jari na yayi qasa" yana daga kwancen yake kallonta,ya rasa me takeyi da kudi,ashana baya barin mace ta siya masa,ko yaushe cikin tura mata kudi yakeyi,suttura har wardrobe dinta baya rufuwa saboda yawansu kuma gashi ba sanyawa akeyi ba,hakanan ba bayar dasu akeyi ba,bata taba cikakken sati ba tare data nema kudi a hannunsa ba,sai ya lumshe idonsa sannan yace "Kamar nawa?" "Fice hundred thousand only" "Only?" Ya maimaita zancanta na qarshe,ba tare da ya jira amsarta ba yace "Allah ya hore" wani kallo tayi masa sheqe qe,amfanin da zatayi da kudin ta gama kasafta zasu fita ne a jikinsa,don ba zata iya fiddasu daga cikin kudinta ba,amma zaizo mata da wannan zancan "Allah ya hore,saidai idan ba zaka bayar bane?" Miqewa yayi ya zauna sosai yana kallonta cikin idanu "Kullum me yasa babban burinki da jin dadinki ki kawo sabani a tsakaninmu?,me yasa zaman lafiya baya miki dadi?" Maganganunsa sai taji kamar gugar zana yake mata,take ta cika tayi fam ta fara zubda maganganu "A hakanne banason zaman lafiya?,duk da tarin haqurin da nakeyi kai baka gani ba?,ina cewa makaranta ka maida waccan yarinyar kana kashe mata kudi,ko ka dauka bansan private ka kaita mai tsada ba?,itama taci kudinka ballantana ni,ita din da duka duka kwananta nawa a rayuwarka,duk kawaicina baka ganshi ba kenan tunda ni dama a wajenka babu abinda na iya na alkhairi" Ido ya maida ya rufe kamar me shirin bacci,saidai ba baccin zaiyi ba,yana sauraren bugun zuciyarsa ne da duk bugawa take bugawar da zallar qaunar yarinyar tare da ambato sunanta,she means alort to him,batasan wace widad cikin rayuwarsa ba,yana dai qoqarin dannewa ne kawai,bai baiwa soyayayyarta kaso daya cikin goma damar fitowa ba saboda kada ya bada kafar barna ko baraka a tsakaninsu,a wannan yanayin yasan duk bayanin da zaiwa hafsat din a banza,ba zata fahimceshi ba sam,idan idanunta suja rufe kan abu kamar cin qwan makauniya,burinta kawai ayi mata abinda ranta yakeso,yana jinta tana ci gaba da zayyano dalilai marasa tushe bare makama,da ya gaji da jinta sai ya miqe tsam kawai ya dauki pillow ya yada a qasa ya kwana abinsa,abun da ya sake tunzurata kenan,ta miqe ta cire rigar baccin jikinta ta maida rigar lace dinta data cire,ta buda qofar tayi ficewarta,yadan bude idanunsa a hankali yabi bayanta da kallo harta fice,sai ya gyara kwanciyarsa yana rufe idanunsa,sam baiji wata damuwa ba don ta fita din,tun yana tunane tunane har bacci yayi gaba dashi. A ranar kwanan kuka tayi ta godewa Allah,gaba daya tsanar widad ta gama cika mata zuciya,abubuwa da yawa basa faruwa saita sanadin zuwanta,gaba daya ta hargitsa mata gida ina dalili?,cikin ranta da zuciyarta takejin matakin data dauka shine dai dai, hukuncin data yanke kuma yayi dai dai,domin a yanzun babu wani abu da zai saurin sadata zuwa ga cimma burinta idan ba ta wannan hanyar ta biyo ba. Washegari widad din ta shirya ita dasu mimi,tun da safe tayi musu wanka,ta cire kaya cikin wadanda abbas a taho musu dashi ya manta su cikin kayanta tayi musu kwalliya da kyau suka wuce gidan hajiya. Taji dadin ganinsu matuqa,ta rasa inda zata sanyasu,a nan akayi mata jan lalle har bayan hannunta,hatta hajiya sai data yaba, idanunta na buye da Widad din tana ji a ranta anya ba juna biyu widad din ke dashi ba?, quruciya ta hanata ganewa,shi kuma uban gayyar hankalinsa baikai ba?,amma da yake hajiyan bata cika sanya baki a lamuran surukanta ba duk da tana jin widad sosai cikin ranta,kamar diyar data haifa a cikinta,duk da haka sai tayi shuru,cikin ranta ta bisu da addu'a. Da yamma tace masa zata koma taje tayi girki,suna shirin tafiya sai gashi,tayi mamaki don bata tsammaci zaizo ya dauketa ba,haka kawai yaji duka gidan babu dadi bayan fitarsu,amma hakanan dai ya daure suka wuni da giwar tasa a haka😂,duk da babu abinda ya tsinta a zaman,don gaba daya babu fara'ar arziqi a tattare da ita bare hirar arziqi,to dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka?. Tunda ya shigo shima yake binta da kallo,lallen ya sake fito da ita sosai,ya kasa daurewa har sai daya bita kitchen yasha dumin jikinta sannan ya samu nutsuwa,suka tattare sukabar gidan hajiyan suka wuce gida. Tare yau sukayi girki kamar yadda suka saba a Kaduna,gaba daya yau sai takejin kasala,har yana tsokanarta "Kindaiyi qiba baby kawai" saita hau bubbuga qafa "Niba wata qiba,Allah banaso" dariya mai taushi ya saki,ya dauketa cak ya dorata saman kantar kitchen din "Ni kuwa bakiga yadda kikayimin kyau ba,komai ya fito yadda nakeso.....fiye ma da yadda nakeso,sannan kin qara dad......." Hannu tasa ta toshe masa baki,don tasan qaarshen zancan,kalmar tana matuqar bata kunya,amma taga shi kansa tsaye yake fadarta. A daren ya same tantancewa,ya kuma sake nutsuwa da gamsuwa da cewa Allah ne kawai ya dubi zuciyarsa ya bashi widad din a lokacin da bai shirya ba,zuciyarsa kuma bata taba kawo masa ya aikata hakan ba. *W A S H E G A R I* Tunda sukayi sallar asuba tace masa tana son zuwa saloon,daga can zata wuce gidan uncle muhsin,kallonta yayi "Baby.....salon yawo ko?,kinsan banason kina yawan fita,jiya me yasa baki gayamin an hada duka ba?" Kai ta langabe gefe,kwata kwata batason zaman gidan,sannan haka kawai takejin haushin hafsat duk sanda ta kalleta,shi yasa batason ma hada waje da ita,bare yau tasan can zai kwana,may be tana kallonsa zaua tafi can ya barta ita kadai a sassanta,sai mimi dake tayata kwana,ta narke fuska "Don Allah uncle,na dade fa banje ba" ido yadan zuba mata,sai kuma yadan saki murmushi "Shikenan" qanqameshi tayi tana fadin "Thank you uncle" ido ya lumshe yana murmushi,jikinsa na amsawa saboda yadda ta manna masa jikinta sosai,hannunsa yasa ya dagota yana duban qwayar idonta,kamar me rada yace mata "In dan qara?" zamewa tayi tana dariya hadi da boye fuskarta cikin hijabinta,duk sanda ya buqaci kadaicewa da ita a fargaba yake sakata,har yanzun bata saba da abun nan ba "Ni uncle....banason nayi ciki,mutuwa zanyi idan nayi ciki fa" ta fada a shagwabe,tattausan hannunta ya kamo ya riqe,duk da qarancin shekarunta amma yasan tana da matuqar juriya dashi,shi kansa baisan me yasa baya gajiya da ita ba "Bana gaya miki ba wannan abun ne yake sawa a samu ciki ba?,sai kinsha ruwa kin qoshi sosai idan aka gama shine ake samun ciki" kai ta gyada a hankali alamun gamsuwa,ya bita da kallo can qasan ransa yana danne dariyar daketa cinsa,yana mamakin yadda ta yadda da wannan dabarar daya shirya mata,quruciyarta tana bala'in tafiya dashi,wani abune da yake kallonsa na musamman tattare da ita,don tana debe masa damuwa sosai,tana barinsa a nishadi duk sanda ta tafka wani babbar wautar da quruciyar. Tada da himma sosai,duk da tana danjin kasala da nauyin jiki amma sai data gama gyara gidan tsaf,ta shirya breakfast sannan sukayi wanka,tare suke wanka daman,indai ba wani babban uzurin fita bane ya taso masa,wannan yasa suka gama da wuri ya rigata fita parlor ya fara yin break din,ita kuma tana ciki tana qarasa shiryawa. Cikin baqa wul din abaya mai wani irin aiki da stones masu sheqi ta shirya,wani irin kyau tayi mai daukar hankali saboda yadda abayar tabi lafiyayyar farar fatarta ta kwanta da kyau,ita kanta sai data kalli kanta har sau babu adadi,ta juya gaba da baya sannan ta rola mayafin sama kanta,ta dauki wata 'yar mitsitsiyar hand bag mai hade da takalmi ta jefa wayarta a ciki sannan ta fito. Mug din da yayi niyyar kaiwa bakinsa ya sauke,ya bita da kallo tamkar yau idanuwansa suka saba ganinta "Ma sha Allah!" Ya furta yana kallonta,yana ji kamar ya buda zuciyarsa ya sanyata ya huta da radadin sonta da yake ji. Sama sama tayi break din,yanata tsokanarta da zumudin zuwa gidan uncle ya hanata cin abinci,suka fito tare "Bari na sallami antynki" ya fada yana buda mata motar ta shiga,sannan ya wuce sasssn hafsat din,tadan bishi da kallo saita dauke kanta zuwa gaban motar,ta jawo wani littafi ta soma buda shafukansa don ta ragewa kanta damuwar da take ta ji,da kuma wata irin faduwar gaba data tashi da ita tun dazun da safe. Suna zaune da yaran suna breakfast suma,wanda ba komai bane sai ruwan tea da tsurar bread,ya dauki yaran ya musu wasa yayi kissing dinsu sannan ya ajjiyesu,ta gaidashi fuska a cunkushe ya amsa mata,har batason kallonsa musamman idan ta tuna daga inda ya fito,wajen waye ya kwana,ya ajjiye mata kudi yadda ya saba,zai fita mimi tace ya tsayata zata gurin anty weedad "Antynku fita zatayi" jin haka yasa hafsat din tasha jinin jikinta kan tare zasu fita,don haka ta miqe sa nufin masa rakiya,abun yadan bashi mamaki don ba sabonta bane,amma.bai hanata ba,suka jero tare suka fito. Cikin jikinta taji kamar yana tahowa,ta daga kai sai ta hangosu a jere da juna,tashin farko taji wani abu ya tsaya mata a wuya ganin yadda suka jera din,ta maida dubanta kan fuskar hafsat din,wani haushinta ya cikata,saita dauke kanta ta mayar kan littafin tayi kamar bata gansu ba. Har suka iso wajen idanun hafsat din na kan widad,wani irin zafi me tsanani takeji a ranta game da yarinyar,kyan da tayi ya tsaya mata a rai,ta fito sakkk balarabiya,to amma tana samun sassauci ta wani fannin idan ta tuna gab take da yin maganin matsalarta,kowanne lokaci ne daga yanzu,don haka tayi masa a dawo lafiya tan juya zuwa ciki ranta yana mata suya da yadda yarinyar ta nuna halin ko in kula da ita,gaisuwar ma da take mata yau bata sameta ba,lallai ta yarda raini ne yake ci gaba da tsirowa a tsakaninsu,sai kuma ta saki wani irin murmushi tana jan qwafa "Zakisan ni ban sa'ar yinki bace yarinya" ta furta tana shigewa sassanta. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 94 Tunda ta isa gidan uncle muhsin sai ta sake sosai abinta cikinsu nujood,bayan sun gama hira da hajjaa a kebance,ta tabbatar babu sauran abinda yake damunta,saidai lokaci lokaci gabanta yana yawaita faduwa,saita tsaya da abinda takeyi idan ya lafa kuma taci gaba da sabgarta. Da yamma ya kira ta yaji kota wuce saloon din,tace eh gata ita da nujood sun fito zata rakata,abun mamakin saita taddashi acan,zaune cikin mota yana jiran isowarsu. "Gaskiya gaskiya nima cewa abban zanyi ko ya samo min police na aura,ko ya samomin cikin abokansa,irin wannan kulawa widad ba kowacce mace ke samun irinta ba,just saloon ma sai an miki rakiya ko anzo an jiraki harki gama a maidaki gida don kada ki shiga motar haya?" Idanun widad din akan abbas din sanda nujood ke maganar,duk da basu qarasa ba suna kusa da qarasawar amma idanun kowa yana kan dan uwansa,saita saki murmushi kawai ba tare data amsawa nujood ba, saidai can qasan ranta ita kadai tasan ya takeji akan uncle din nata,har wani lokacin takan zauna tace wai shin wa tafi ji dashi,wa tafi so tsakanin shi ummu ko mommynta?(quruci dangin hauka,kowanne so akwai kalarshi,na iyaye daban na miji daban). Fitowa yayi ya taka mata har zuwa bakin qofar wajen,sannan ya gaya mata abinda ya saba fadi "Ki fada mata tayi miki mai kyau,irin wanda ba'a taba yiwa kowacce mace ba" dariya ta kamata itama kamar kullum,shidai yanason gayun nan,yana son kwalliya,duk sonta da kwalliya ta samu wanda ya fita,tana murmushi ta shige,yayin da nujood ta rigata yin gaba tana jin kunya,saboda tamkar mahaifi take kallonsa. Sanda aka gama sai suka sauke nujood a gida,bayan ya bata kyautar dubu biyar,ta shiga ta yiwa hajjaa sallama,wadda ta hada mata kayan miya,kamansu kuka daddawa kubewa mai kyau da sauransu, saboda itama tasan abas din dason wannan cimar na gargajiya,tayi musu sallama ta fito. Suna tafe a hanya suna hira,duk da uncle din nata shine jigon hirar,kadan kadan take saka baki,saboda yadda faduwar gabanta take qara yawa fiye da dazu,a wani shopping mall ya tsaya yana dubanta "Zaki rakani?" Ya fada a tausashe,ta sake masa murmushi tana ajjiye jakarta ta fito tabi bayansa. Tana biye dashi ne kawai,shi ya dinga daukan kalar kayan da yakeso,wanda duka qananun kaya,irinsu mini skert leggings shirt shirt na masu daukan hankali da kuma lalatattun sleeping wears,kusan wannan din al'adarsa ce,yanason wannan shigar a wajen matarsa,a lokacin da hafsa kadai yake da ita,duk sanda yayi siyayya irin wannan asarar kudinsa kawai yakeyi,don ba sakawa takeyi ba,a yanzun kuwa kusan tare suke zabar kayan da zata saka masa duk rana shi da widad din,musamman idan suna Kaduna,sai wanda ya zaba zata saka masa,bata wani damuwa saboda kayan sunfi mata dadin sakawa a yanzun,idan tana cikin gida zaiyi wuya ka ganta da atamfa bare lace ko shadda,kayanta kenan,wani mugun kyau kuma sukeyi mata,bama kamar idan ta raba gashinta biyu,kota musu manyan kalba,yakan lalace wajen kallonta ne,itakam da batajin nauyin jikinta tayita tsalle tsallenta abinta. Chocolate ya hada dasu masu dan yawa saboda su mimi ya biya kudin suka fito,ya miqa mata ledojin yana cewa sanda yake shirin kunna motar "Ta kayan taki ce,ta chocolate kuma ta sha zumamu mimi ce" qaramar dariya tadanyi, tanason zaqi kam yarinyar,sai ta buda ledar kayan nata tana diban wasu tana zubawa a ledar su mimi,yadan kalleta yana yin reverse "Me kikeyi haka?" "Mommyn mimi na sakawa wasu kayan,baka siya da ita ba,naga kudin da yawa" kai ya girgiza suna haurawa kwalta "Kinason kiyimin asarar kudina na kawai....." Sai kuma yayi shuru ba tare daya qarasa ba,sannan ya sake cewa "Duka naki ne,jibi nakeson ki zaba me kyau a ciki.....wadda tafi kowacce kyau ki sakamin,ita kuma duk sanda muka fita ko tace tanaso saina siya mata nata daban" bata kawo komai cikin kanta ba ta gyara ledar ta mayar dasu yadda suke. Ana kiran magariba suka isa gida,wasu masallatan ma har sun tayar,ya kashe motar ya rakota,gudun kada sallar ta qwace masa saiya tsaya daga qofar falonta ta bude ta shiga shi kuma ya koma da dan sauri don ya riski sallar. Duhu falon saboda ta kashe dukka qwayaye kafin ta fita,tana tsoma qafarta gabanta yayi mummunar faduwar da har sai data dora hannunta a qirjinta,wani irin mahaukacin tsoro ya saukar mata,saita saka hannu tayi hanzarin kunna wutar sassan nata. Duk da haske ya wadaci wajen amma abinda ya gushe na tsoron daya saukar mata din bashi da yawa,ta fara takawa a hankali kamar mai sanda ta nufi dakinta,duk inda ta tsoma qafarta ta dauke sai taji kamar ana biye da ita,wannan ya sakata qara hanzari,ta fada dakinta ta tura qofar tayi zaune bakin gado tana wuwwurga idonta cikin dakin,cikin sa'a bakinta ya kama kalmar "Hasbunallahu wa ni'imal wakil,ni'imal maula wa ni'iman nasir" sannu a hankali saita fara jin tsoron yana raguwa,ta rufe idonta tayita maimaitawa kafin ta bude idon a hankali,sai taji tadan samu nutsuwa,ta ajjiye ledar da mugun takatsantsan saboda qarar ledar tana jinta har cikin kanta,ta cire mayafinta ta shige bandaki tana fatan mimi ta shigo mata ko ta rage zaman shurun. Alwalar data yo ta qara mata nutsuwa,ta dawo ta tayar da sallah,sanda ta idar sai tayi zaune saman abun sallar,gidan shuru ba motsin kowa,sai qarar babban generator dake aiki a farfajiyar gidan,yana daya daga cikin abinda yasa ta tsani bauchin,wannan zaman,inda a kaduna suke da yanzun tana jikin uncle dinta,suna karatu k suna wani abun tare,komai ma tare sukeyi ita dashi,ba wani abu da suke rabawa,kama daga wanka bacci cin abinci,sallar ma wataran jam'i sukeyi ita dashi,ya tsefe mata kai ya yanke mata farce,wani zubin ma har ya gwada mata kalba,amma a bauchi fa,duka time dinsa yana rabasu ne a tsakaninsu. Tana nan zaune har akayi kiran isha'i ta tashi ta gabatar,ta sake komawa ta zauna,tun yamma rabonta da abinci,amma kuma bata jin yunwa,batasan me yake damunta ba,wani lokacin ta tashi da mahaukaciyar yunwa,wani lokacin kuma ta tashi bata sha'awar cin komai,duk da haka dole ta tashi ta shiga kitchen bayan ta leqa window ko zataga wulgawar mimi amma ba ita ba alamarta,ta tsaya ta dafa indomie guda daya ta soya qwai biyu,tana yi tana takatsantsan,duk duk wani motsi da zatayi da kwanukan firgita takeyi,tana gamawa ta dawo daki ta zauna ta tasa abincin a gaba. Tana fara ci taji bataso,saita ture plate din,zuciyarta na mata wani qunci,kawai sai ta fashe da kuka sosai tana curewa waje daya,gidan gaba daya ya fice mata akai. Yana zaune da wayarsa a hannu yana amsa saqonni,su mimi na gefe suna wasansu,yayin da hafsat din ke hada masa abincin dare "Yau ba zuwa wajen anty mimi?" Ya tambayi yarinyar yana aje wayarsa bayan hafsat din tace ta gama zubawar "A wajen mahaifiyarta zata kwana" hafsat dake shirin zama tayi caraf da maganar,duba daya yayi mata ya kauda kansa gun yaran yana gayyatarsu suzo suci abinci,kusan al'adarsa ce wannan,tunda mamarsu bata iya cin abinci dashi ba,tare dasu yake cin abinsa,tun bai saba ba har ya zame masa jiki. Tana daga zaune a gefensu,bata ce komai ba,suna cin abincin suna hirar su da yaransa yana dariya abinsa,abinda yake sake qule hafsat kenan,sai abu mai ciwo ya faru,tana ganin abun yakai munzalin bacin rai,amma sai yasa yaransa a gaba suyita sabgarsu,taja qwafa can qasa tana jijjiga kai,idan komai bai faru ba ashe bata cika hafsatu ba. Suna gama cin abincin ta kada kan yaran zuwa dakinsu,basa jin bacci a sannan amma haka ta tilasta musu kwanciya,ya fahimci me take nufi,bayason suje wajen widad din,sai shima ya watsar da ita,ya wuce toilet yayi wanka hade da brush,ya shirya cikin wasu silk pyjama sky blue,ya dauki wayarsa ya wuce sassan widad din don ya mata sallama,ta bishi da harara ba tare da yasan me takeyi ba,cikin ranta fana fadin "Na kusa maganin matsalata naga qarshen wannan rawar kan". Tun kafin ya qarasa yaji ya qagu ya isa din,ya buda qofar da sallama a bakinsa,yadda yaga falon komai a kashe yasan tayi shirin kwanciya ne,don haka ya zarce bedroom dinta kai tsaye. Buda qofar da taji anyi har tsakiyar kanta,ta zabura ta daga kanta da sauri hantar cikinta na kadawa,wani mugun tsoro yana mamayarta,suna hada ido ta miqe da sassarfa ta isa gareshi hadi da fadawa jikinsa ta rushe da kuka "Ya salam......ya Allah" ya furta a tausashe hannunsa a bayanta yana dan bubbugawa "Menene baby?,mene?" Ya tambayeta yana sunkuya dai dai fuskarta,hucin bakinsa dake bada qamshin blueberry mouth spray yana sauka saman fuskartata,saita cusa kanta wuyansa tana sake sakin wasu hawayen. "Tom,abun ya motsa kenan" ya fadi can qasan zuciyarsa yana dan sakin murmushi,ya riqeta sosai suka koma gaban gadon suka zube a qasa,ya sanyata a jikinsa yana sake lallashinta. Sun jima a haka sannan ya samu ta tsagaita kukan,ya zaunar da ita sosai saman qafafunsa yana kallon fuskarta da tayi jajur saboda kuka "Me ya faru?" Sai tayi masa narai narai da ido xata sake sake masa kuka,yayi saurin cewa "Noo....ya isa, kinci abinci?" Sai sannan ta maida dubanta ga abincin data zuba din,shima ya tayata kalla,yasa hannu ya jawo plate din ya motsa abincin yana kallon qwayar idanunta "Zakici wannan din ko na canza miki wani?" Kai ta girgiza alamun zata cin,ya sake daukan cokalin ya fara diba a hankali tana zaune saman qafafunsa yana bata hadi da sako mata irin hirar da yasan zata sanyata ta sake. Babu laifi tadan sake din,don kafin ya gama bata tana murmushi,duk da qasan ranta wani irin tsoro ne keta mata tasiri,bayan ta gama ya tabbatar ta kammala komai na kwanciya,yayi tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa yana kallonta "Shikenan?,saida safe?" Kanta ta kawar gefe,tana jin ranta ya motsu,yanzun tafiya zaiyi wajen mummyn mimi,saita gyada masa kai a sanyaye,sannan tace "Mimi ba zatazo tayani kwanan ba?" Dan jim yayi kafin ya amsa "Sun wuce dakinsu kafin na fito,don't worry ki kwamta ki rufe idonki,yanzun nan zakiga safiya tayi, okay?" Saita gyada masa aki a hankali,tausayinta sosai yaji,yasan ko yaya batason rabuwa dashi,bare yanzun data saba da zama jikinsa kamar wata 'yar mage,ya sunkuya a tausashe yayi kissing dinta,ya juya zai kashe mata hasken dakin tace "Ka bari zan kashe" don batason duhun da zata zauna a ciki kafin bacci ya dauketa "Okay" ya furta can qasan maqoshi,ya juya a hankali ya fice a dakin yana waigenta. Idonta ta mayar ta lumshe tana jin ficewarsa,wani abu na tsaya mata a wuya,ta gwammace taci gaba da barin idon a rufe maimakon ta bude ta kalli hanyar da yabi ya fice din. Cikin mintunan da basufi qwaya biyu ba taji yanayin dakin ya fara sauyawa,kamar komai na dakin motsi yakeyi,ciki harda kujerar data kwanta a kan,zuciyarta tayi mugun bugawa, madaukakin tsoro ya mamayeta,kafin takai ga bude idanunta taji dukka wata gaba ta jikinta tayi nauyi,kamar wadda DANNAU ya danneta,ta kasa motsa koda dan yatsanta bare tayi yunqurin tashi daga inda take kwance.......... *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 95 Tayita qoqarin motsa wata gaba ta jikinta amma ta kasa,wata mummunar shaqa taji an yiwa wuyanta,abinda ya sabbaba mata numfashinta ya soma wahalar fita kenan,cikin gigita firgici da kuma tsoro ta soma bude idanunta a hankali tanason ganin waye a dakin?,waye yayi mata wannan aikin. Wayam......babu kowa a dakin,daga ita sai kayan gado labulaye zuwa frames a dakin. Idanunta ta wulga gefe,sai ya sauka ga bangon dakin da take fuskanta,wani irin motsi taga yana yi,yana kuma darewa a hankali,wani dogon hannu yana ratsowa har zuwa inda take kwancen,ta motsa bakinta da nufin addu'a amma komai ya gaza fita,idanun nata yana kan hannun da yaci gaba da ratsa bangon dakin yana qara shigowa hadi da ci gaba da shaqe mata wuya. Ci gaba tayi da kokawa da numfashinta tare da qoqarin ganin ta kira sunan Allah,tsahon wasu mintuna kafin ta samu ta fusgo addu'a da qarfi daga bakinta "Ya Allah..... innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada da qarfi,kalmar da tayi sanadiyyar yankewar komai,jikinta ya sake, bangon dakin ya koma dai dai,motsin da dakin yakeyi ya tsaya cak,ta miqe da mugun hanzari,ta nufi qofar dakin da gudu tana sake kiran sunan Allah da mabanbantan sunaye. Kai tsaye ta fada dakin abbas din ta maida qofar ta rufe sannan ta zube a wajen tana tokare bayanta da qofar kamar me shirin hanawa wani shigowa dakin,ya sulale ta zube a wajen tana riqe da wuyanta,saita fara karanta ayatul kursiyyu da qarfi,ko ina na jikinta yana wani irin rawa kamar me shirin ficewa daga hayyacinta. Ta jima a wannan yanayin tana karanta ayatul kursiyyu da dukkan addu'ar tsari da tazo bakinta,har sai da dukka yawun bakinta ya dauke,Allah ya saukar mata da wata nutsuwa,saidai har yanzu jikinta rawa yakeyi,tsoron dake tattare da ita ya ragu sosai,saidai a firgice take qwarai da gaske. Kusan awa guda kenan kafin ta samu kuka yazo mata,ta tattare guri daya cikin wani irin yanayi na tashin hankali,tana jinta ne tamakar a tsakiyar wani daji da babu gida gaba babu gida baya,ita daya qwal a sashen,ta ina zata iya fita tabar sassan?,ta baro wayarta a dakin da batajin zata iya taka koda qofar dakin ne bare tayi kiran abbas,cikin wannan yanayin taci gaba da zama a bakin qofar dakin,rabi kuka rabi addu'a,a haka ta qare darenta tsaf a zaune dungurgur har aka kirayi sallar asuba. A jikinsa ya dinga jin tunaninsa ya karkata a kanta,don haka ana idar da sallar asuba ya baro masallaci ya wuce sassanta. Kamar numfashinta zai tsaya haka taji sanda taji motsi yana buda sassan nata da key dinsa,ta qanqame jikinta guri daya tana sakin kuka sosai tana kiran sunan Allah,har ya buda ya shigo falon ya kuma duba dakinta bai ganta ba tana zaune a wajen ta kasa motsawa,mamaki ya cikashi ganin har bandaki ya duba,babu ma alamun ta shiga,don a bushe bandakin yake,sai tunaninsa ya bashi ya duba dakinsa,don haka ya fito ya nufi qofar dakin. Daya murda handle din yaji alamun a kulle take sai hankalinsa yadan kwanta,cikin ransa yana murmushin ya akayi ta canza daki ta koma nasa dakin?,sai ya gyara tsaiwarsa yana rayawa a ransa lallai yau zaiyi mata tsiya. Knocking yayi,widad dake zaune jikin qofar ta runtse idanunta tana jin kamar numfashinta zai dauke,ya sake qwanqwasawa murya can qasa ya kirayi sunanta,abinda ya bata qwarin gwiwar miqewa da hanzari ta bude qofar,batayi wata wata ba ta fada jikinsa,ya tareta da sauri cikin mamaki da tashin hankalin jin irin kukan data fashe dashi. A rude yake ta jero mata tambayar me ya sameta?,me ya faru?,menene?,amma ta gaza amsa masa tambaya ko guda daya,sai sake riqeshi da tayi da kyau kamar mai tsoron kada ya subuce mata,a haka tana jikinsa ya jata zasu koma dakin amma ta turje taqi,dole sai parlor suka dawo saman kujerar tana kwance a jikinsa tana gurzar kuka. Kusan minti talatin suna a haka sanann ya soma lallabarta,yace tayi sallah?,tace a'ah "Kije kiyi sallah sai kizo ki gayamin abinda ya faru" ko motsawa daga jikinsa qi tayi,sai a sannan ya sake experiencing tsoron dake tattare da ita,mamakin abinda ya haifar da irin wannan tsoron daga wajenta ya saukar mishi,duk da ya sani ita din matsoraciya ce,to amma tsoron nata baikai haka ba,hasalima ta fara sabawa da gidan,ta rage tsoron sosai. Sai shine da kansa ya rakata bandakin ya kuma tsaya tayi alwalar ta kuma yi sallar,ta hanashi motsawa ko ina,tana kwance a jikinsa wani irin zazzabi ya fara saukarwa jikinta,dole yaja duvet ya lullubesu ita dashi, hankalinsa gaba daya ya tashi,gashi tambayar duniya ta gaza ce masa komai,sai dan uban kukan da take masa.. Wani irin tsoro ke dawainiya da ita shi yasa ta kasa gaya masa,tana ji kamar idan ta fada masa abun zai sake dawo mata,don haka ta kasa cewa komai sai kukan,hankalinsa dukka a tashe yake,yayi lallashin duniya tayi shuru tunsa taqi fadin abinda ya faru amma ta kasa yin shurun,sai hawaye da taketa fitarwa,a haka har rana ta fara fitowa tana kwance a jikinsa saman gadon,a haka yayi azkar dinsa yana duban fuskarta wadda a sannan bacci ya fara fusgarta,wani irin zazzabi yana sake lullubeta. A hankali bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,sai a sannan ya samu ya zare jikinsa ya tula mata pillows yadda zata tsammaci shine,ya miqe ya soma bincike gidan wai ko wani abun ta gani,tun daga dakinsa zuwa nata dakin,bandakunansu qasan gado kitchen ventilation dinta dako ina amma baiga komai ba,dole ya haqura ya wuce kitchen ya hada ruwan zafi yasha zuciyarsa cike da wasu wasi da tunane tunane. Sanda ta farka zazzabin ya riga yayi qarfi a jikinta,dole ya zare mata rigar jikinta ya jiqa towel ya soma rage mata qarfin zazzabin,ba yadda bai lallabata tayi wanka ya kaita taga likita ba amma taqi,yace zai kira Dr gida nan ma tace bataso,sai kukan da taketa masa,wanda ya qarasa rudashi gaba daya. Ta bangaren hafsa hankali kwance take hidimarta,ta gama shirya breakfast suka ci abinsu da yara,tana ta kai kawo tsakanin falonta zuwa farfajiyar gidan hankalinta na sassan widad din,har sha daya na rana bataji motsinsu ba,don ta tabbatar yana sassan widad din,tunda ga motarsa ba fita yayi ba,saita koma ciki ta dauki wayarta tayi kiransa. A lokacin ya sanya widad din a gaba yana bata tea,da qyar take karba sai sharar hawaye take,sai da yayi da gasken ma ya samu take amsa din "Naji shuru daga sallah baka dawo ba,ga kuma break dinka" ido ya lumshe yana jin zuciyarsa babu nutsuwa gaba daya,a yanzun ma shi baijin wata yunwa,bare ma yasan ba wani break din arziqi ta tanada ba,idan tayi wutar duniya......ta qure adaka ta soya chips da fried egg "Ina cikin gidan,widad ce bata jin dadi" baki ta tabe,ranta fes ba tare da taji wani abu ya dameta ba "Inason fita ne,umma bata jin dadi xanje na duba jikinta" "Ki gaisheta" kawai ya fada a taqaice ya katse wayar,yasan dama kiran bawai don baici abincin bane main purpose ba,ya ajjiye wayar gefansa ya sake maida hankalinsa ga widad din. Ido ya zuba mata,gaba daya dare daya duka ta fada ta birkice masa,ya lumshe ido yana jin wani abu yana taba ransa "Me ya faru baby..... please tell me ko raina zai nutsu" kamar ko yaushe sai hawaye suka fara taruwa,ya tareta da sauri "Ya isa, shikenan" ya miqa mug din bakinta yana cewa "Qarasa shanye wannan" cikin ransa yana tunanin yadda zai lallabata taga likita,bazai iya zama yana ganin uban zazzabin nan a jikinta ba. Wayarsa ta sake qara,sai yaga hafsat ce,ya sake daga wayar ya sakata a handsfree "Na tura mimi ka bata kudin mai zan saka mai a motata" takaici ya cikashi,ya lumshe idanunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa "Kada tazo,ba kudi a jikina,kije zan tura miki ta account idan kinje gidan man kya basu ATM dinki su cira" "Tom" ta fada hankalinta kwance yana ajjiye wayar,ko kunya sam.bataji ba,ita dashi duka sun dani full tank yakewa motar tata,bama motarta kadai ba,hatta motar da zaya bari a gida idan zai koma kaduna.baya barinta haka,yaja qaramin tsaki qasan ransa yana fadin "Astagfirullah" sau tari idan hafsat din tayi masa abu,sai yaga istigfari kawai ya dace yayi,wala'alla yayi wani laifi ma Allah ne daya kasa gane me ya aikata din. Wunin ranar gaba daya tana maqale a jikinsa,duk inda zai motsa zata bishi,kwata kwata tsoron gidan ya kamata matuqa da gaske,tana jin kamar ta bude ido ta ganta a kaduna,ga zazzabin da ya hanata sukuni wunun ranar,taqi yarda kuma taga likita sam,sai gige mata jiki daya dinga yi da ruwa mai sanyi,ya bata paracetamol tasha sannan aka samu sassaucin sa,sai daga baya ya sake dawowa. zuwa dare ta dinga masa kuka saboda yadda wata muguwar tsanar gidan ta shigeta,ta dinga kuka sai sun koma kaduna,ba shiri cikin daren ya soma hada musu kayansu,bai kwanta ba sai daya gama shirin tafiyar tasu. Da safen ta tashi da 'yar walwalarta saboda jin zasu tafi,kafin ya gama nasa shirin ita tuni ta gama,sanda ya kammala shiryawar kuwa zaije ya sallami su hafsat farfajiyar gidan ta fito ta zauna tana jiransa,sam bata doshi wajen hafsat din ba,haushinta takeji musamman duk sanda zasu kebe da uncle din nata,ko zata ganta kusa dashi,idan wani abu ya kawo ga ta tabashi kuwa saidai tabar wajen tana goge qwalla,ita kanta batasan manufar hakan ba,batasan kuma abinda yake kawo mata jin hakan a zuciyarta ba (kishi😄, Allah sarki,quruci dangin hauka,ta fara kishin uncle din nata ba tare data sani ba). Tana tsaye daga bakin window din falonta tana hangensu sanda ya gama sallamarta ya fice,bayan ta gama mita da qorafin akwai sauran kwana daya daya rage ai bai cika shi ba,bai biyewa qorafin ta ba,don koma yaya yayi dai sai ta yishi,ya zama kamar cikin jininta abun yake. Murmushi ta sauke sanda suka fice din,cikin wata walwala da jin dadi ta fada saman kujera tana tunano abubuwa masu yawa a zuciyarta,lallai a baya ita taso har aka kai wannan matsayin ma da ake kai yanzu kamar yadda ummanta ta gaya mata,ashe wannan hanyar itace hanya mafi sauqi da sauri ta maganin matsalar ta ta tsaya tana biyewa hasashe da hanyoyin anty ummee masu tsauri?. Assalamualaikum Yanzu an wuce lokacin da za'a dinga novel na qaryar soyayya tsura kawai a ciki da uban tarin dukiya daga qasa zuwa qasa,dole mu fuskanci reality na abubuwan da suke faruwa yanzu suke damunmu,akwai darasi sosai da nakeso mu cimma cikin labarin nan,kuyi haquri muje harmu cimma gaci Sannan tun asali duk wanda ya sanni labaraina ba gajeru bane,daga bayan nan ne nake gajeru,to wanann salon labarin yazo a haka ne,sanann raguwar tsahon pages din yasa numbers din sukayi yawa,amma in sha Allah i will try my best naga pages din sun dan qara tsaho ta yadda numbers din zasu ragu, thanks for choosing me. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 96 Wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki tana samun nutsuwar ruhi da gangar jiki sanda taga sun dauki hanyar kaduna,duk da jikinta babu wani qwari sosai saboda zazzabin daya gallabeta,amma at least ta samu wani sassaucin. Dan waiwayo yayi kadan ya dubeta,sannan ya cire hannunsa guda daya daga kan motar ya kama dogon hancinta yadan ja "Hankalinki ya kwanta ko?" Saita sakar masa murmushi, murmushin da yayi masifar kewarsa,yaketa kuma struggling na ganin tayi shin amma bai sameshi ba sai yau. Tun basuyi nisa ba ta soma bacci,wani irin nannauyan bacci da shi kansa abbas din ya dinga kallonta,ko sau daya baiyi.marmarin tashinta ba,baccin ma datayin dadi yayi masa,aqalla yasan zata rama bashin baccin da batyi ba kwana biyu,sai ya kunna radio station yana sauraren labarai,da sauran programs da suka jibanci harkokin tsaro,da ya gaji ya maida karatun qur'ani,wanda ya qarawa baccinta dadi sosai,baccin da bata farka ba sai da suka isa kaduna. Tun daga wannan ranar bata sake binsa bauchi ba,don ko cewa yayi zasu weekend yanzu zata rage walwala,gaba daya garin ya fita a ranta,shima bai takurawa, don asalinsa ba mutum bane mai takura da tsanani akan abu bane,sai ya barta yaje yayi kwana biyu ya dawo,har kusan watanni uku. Cikin hakan bikin diyar yaaya bara'atu ya taso,ya gaya mata,duk da bataso amma ta gaza nuna masa,yana da tsananin kirki da karamci,yana mata kyautatawar da duk duniya baya ga ummu bata ganta a wajen kowa ba,wannan ya sanya duk wani abu da tasan bayaso ko zaiji babu dadi take nisantarsa(bawai don tasan muhimmancin hakan ba,kawai saboda yadda kyautatawarsa taje da nauyi a idanunta). Kaya ta fitar ta bayar akayi mata dinkuna masu kyau, zuciyarta duka babu dadi,cike da tsanar bauchin amma haka ta dinga shirya,duk da tana boyewar amma ya karanci akwai abinda ke faruwa,don kuzarinta ya ragu,a sanyaye take komai. Ana gobe zasu tafi da daddare,yana zaune kan sofa bed yana shan black tea din data hada masa ita kuma tana rufe wata qaramar jakarta data zuba qananun abubuwan amfaninsa da tasan zai buqata,duk inda ta gifta idanunsa yana biye da ita,baya gajiya da kallonta,barin yau din da tayi kwalliya ciki wani mini skert da wata riga da sukayi matuqar karbarta,zuwa lokacin komai nata ya cika yayi yadda akeso ya zamana a jikin diya mace,ta zama wata 'yar duma duma da ita,haske da laushin fatarta ya qaru,hakanan tsahon gashinta cikarsa dama baqinta,lips dinta ya qara zama pink sosai haka idanunta sun sake fitowa,ta fannin mu'amalarsu ya sake zama wani mayenta,shi kansa baisan yadda akayi ya sake horancewa ba,baiqi duka dare ya dinga kasancewa da ita ba,baya gajiya da ita,wata baiwa ke gareta ta musamman mai dimauta tunanin mutum,saidai widad din tashi har yanzu raguwa ce,batayi qwarewar da yakeso tayi ba,kullum hakan ta kasance sai yayi zaman lallashi,shagwabarta da sangarta take zube masa,shima sai ya biye mata. Ajjiye mug din hannunsa yayi yana fakon isowarta,aikuwa tana zuwa giftashi ya sanya hannu ya fincikota jikinsa,yayi mata kyakkyawan masauki saman cinyarsa dake bayyane a waje cike da gargasa,hannuwansa ya saka ya zagaye qugunta dasu ya sake matso da ita sosai,ya saka fuskarsa a tsakiyar dukiyar fulaninta yana shaqar qamshin dake fita a wajen. Hannu ta saka ta riqe kansa,tana jin tsigar jikinta tana tashi saboda yadda labbansa suka sauka a wajen,ta saki dariya tana janye jikinta baya,ya daga idanunsa da suka fara sauya launi yana murmushin shima ya kalleta "Kamar baki shiryawa zuwa bauchin nan ba" kanta ta langabar gefe,a zahiri batason zuwan,amma bai kyautu ta nuna masa ba,saita girgiza kai "Aah,kawai kasala nakeji kwana biyun" "Nayi noticing canji da yawa,kin koyi bacci,sannan ga overdose kyau baby da kike qarawa,overdose dad......" Hade bakinsu tayi waje daya yau da kanta,don batason ya qarasa fadin kalmar,bala'in sakata jin kunya takeyi,hakan da tayin saita tafi dashi wata duniyar ta daban,tasa ya dimauce ya mance dukka maganar da zai fada din,sanda zata qwace kanta kuma yace baisan zance ba,sai da ya cimma gaci sannan ya samu nutsuwa. Washegari da wuri suka isa,don sha biyun rana ma a can tayi musu,sassanta ta wuce kai tsaye,gidan duk bai mata dadi ba saboda su mimi basa nan,hajiya tasa anzo an daukesu,an musu kitso da qunshi kamar yaran kowa,an kuma dauki kayansu sai bayan biki zasu dawo. Wannan karon hafsat din bata hana ba,bata ma isa ta hana din ba don tasan abbas din ko zai jure komai banda wannan,kuma kai tsaye shi yayi kiranta yace ta bada yaran,ta hada musu tarkacen kayansu,gasu dai a ido masu kyau da tsada ne,amma dauda da rashin kula duk sunci mutuncinsu. Tsaye hajiya tayi kawai cikin takaici tana qarewa kayan kallo,banda ma gidan yana samun feshin maganin qwari da kuma gyaran da uban kewa dakin nasu duk sanda ya samu chance....ta tabbatar ba za'a rasa wani qwaron a ciki ba,hajiyan nada masifar tsafta,sai tattara kayan tasa akayi aka bayar,banda ma masu tsada ne da kuma sauran qwarinsu qazanta ce ta cinyesu,a wajen hajiyan bola ce tafi kamata dasu. Har ta fitar da kudi ta bayar za'a sake musu sabuwar siyayya mimi tace akwai wasu kayansu a wajen anty widad. Hajiyan da kanta ta kira widad din tace mimi tace suna da kaya a wajenta,ta fiddo musu dasu umar zaizo ya karba,tana shiga sassanta kayan ta fara hadawa,a killace a tsaftace a kuma goge,umar din ya karba ya tafi dasu. Tunda ta sauka gidan ranta yayita baci,gaba daya kamar an tattaro dukka bacin rai an aza mata,haka ta dinga dannewa,ta hau gyaran sashen nata,sai data tabbatar komai yayi neat din ta sake wanka ta canza kaya,ta dauki wayarta ta kira abbas don tanason zuwa saloon da qunshi,na qafafunta duka sun fita,kuma batason shiga mutane haka,abinka da farar fata, babban adon hannayensa da kyan ganinsu ayi musu qunshi. Lokacin yana tsaye a qofar toilet yana amsa wayar Jasmin yana jiran hafsat dake ciki ta gama wanke masa zai shiga saboda dan uban qurar daya hada,bata damu ta shiga ta gyara ba,sai ya bawa Jasmin excuse ya katse kiran nata ya daga na widad din. Cikin shagwabar nan tata dake sake narkar dashi tace "Uncle" "Babyn uncle" ya amsa mata tattausan murmushi yana subuce masa,sunan da hafsat taji ya kira saita miqe tsaye dafe da cikinta ta kasa kunne tana sauraren hirar "Zanje saloon da qunshi,kaina da hannuwana duka ba dadi" "Ba laifi,amma baby......ina kishi fa gaskiya,ki zaba duk inda kikeso zan sa a kira miki su har gida special services mana" kafada ta noqe,ita zaman gidan ne bataso har ga Allah "Don Allah uncle,yaushe rabon da nazo bauchi" ta fada da wata irin narkakkiyar shagwaba da har data sakashi lumshe ido ba tare daya shirya ba "Shikenan,ki shirya zan fita headquarter yanzu,sai mu biya" "Thank youuuuuuu" ta fada tana dariya "You are welcome" ya amsa yana sauke wayar sannan ya sake kiran Jasmin yace mata zai shigo nan da minti talatin. Sauri sauri tayi ta gama wankewa ta fice ta bashi waje,ya shiga ya hada ruwan wankansa da kansa,abinda bai sani ba kenan muddin suna tare da widad. Sassanta ta nufa tana sakin ashar cikin zuciyarta,ita ta dauka ma wannan karon shi kadai yazo,ashe sai data sake biyoshi,akwai sauran rina a kaba kenan?,saita jinjina kai,ta buda wardrobe dinta ta fiddo kayan sawa,sannan ta buda bandakinta ta shiga ta fara kwaskwarima. Cikin wata doguwar rigar atamfa da tayi mugun budewa daga qasa ta shirya,brown ce mai adon blue black,tayi amfani da blue black hand bag veil da kuma takalmi,kalar ta haska farar fatarta da kyau, daurin da tayi wanda ta kawoshi gaban goshi ta fidda gashinta ta qasan daurin ya qara mata wani irin kwarjini,ko yaya ta motsa jikinta qamshi yake fitarwa. Saboda saurin da take ta fita a gidan ta rigashi isa parking lot,tayi tsaye jikin motar tana jiran fitowarsa,wayarta sabuwa da ummu ta aiko mata da ita a hannunta suna hira da bilkisa ta watsapp,tana ta kwasan dariya,don bikisa din ba daga baya ba,ko yaushe qoqarinta taga ta dora widad din kan hanya,ta kuma ganar da ita wace hafsat. Cikin wasu lafiyayyun indian blazers ya shirya blue black din shima,tamkar yasan color din da zata saka kenam,tun daga nesa kwalliyarta ta tsone masa ido,ya zuba mata dukka idanun nasa yana takowa a hankali,ko qifta idanunsa a kanta qyashin yi yakeyi. Cikin jikinta taji yana wajen,saita daga kanta ta sauke a kansa,kamar shi,itama kwalliyar sa tatafi da ita ainun,yayi wani mugun kyau,ya koma yaro sosai da bai wuce sha tara zuwa ashirin ba,murmushi ya subuce mata,bakinta ya dinga motsawa tana jiran ya qaraso ta tsokaneshi,saidai dab da zai qaraso din hafsat ta bayyana,ta kwaso sauri cikin baqar abaya data saka ta yafa baqin mayafi wanda ya kasa zama a kafadarta saboda sauri dason ta cimmasu kafin sukai ga fita. Ganinta sukayi kawai tana kiciniyar bude gaban motar tana cewa "Banajin dadi abban mimi,ka miqa ni asibiti don Allah" tayi maganar tana shigewa gaban motar. Da kallo dukkansu suka bita,widad ce ta fara dauke kanta kamar bata ga abinda tayi ba,sai ta matsa ta dauke handbag dinta dake saman motar ta juya zuwa cikin gida "Ina zuwa kuma?" Dan dakatawa tayi da tafiyar "Na fasa zuwa ne" iska ya furzar "Aah,kizo Muje na fara sauketa saina qarasa dake" kai ta girgiza "Um um.....naje ko gobe ko jibi" ta fada tana qoqarin boye damuwa sa fushinta,kawai ba zata iya hada mota da hafsat din ba,kallo daya tayi mata tasan neman rigima ya fiddota,dazun da umar yazo karbar kayansu mimi taji yana wayar jiya yakai hafsat din asibitin awo "No....,wuce muje" ya fada yana takowa inda take tsaye,yana karbe jakarta daga hannunta "Uncle....." "Wai ba magana ake dake ba!.....yara suyita musu da na gaba dasu,kaga abban mimi just leave her mu tafi kawai" hafsat ta fada cikin tsawa,bayan baqincikin yadda taga yana lallabarta hadi da riqe mata jaka ya saukar mata ya tsaya mata a qirji. A sukwane widad din ta waiwayo tana jin wutar dai dai take da ita a yau tana tashi cikin kanta,fes ta kalleta ido cikin ido,cikin lallausar muryarta a nutse ta amsata "Sorry mommy....bafa dake nake ba......da uncle dina......au mijina na,da mijina nake magana" *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 97 "Sorry mommy.....bafa dake nake ba,da uncle dina,oh mijina,da mijina nake magana" widad din ta fada kanta tsaye,idanunta cikin na hafsat. Wani abu mai nauyi hafsat din taji kamar an aza mata,kanta ya buga har tana jin wasu sautuka cikin kunnuwanta,ita widad din yau take kalla kai tsaye.....kuma kai tsaye,ido cikin ido take gayawa haka?,a gabanta take kiran abbas da mijinta?. Kafin ta yanke abun yi har widad din ta soma qoqarin zame jakarta daga hannun abbas din,saidai yaqi cika mata,ganin yaqi cika matan saita juya ta fara takawa tana nufar sassanta,tana jin zuciyarta na mata qunci,batasan me yasa mommyn mimin keson shiga harkarta ba,bayan ita ko ganinta batason yi,batason su hada inuwa guda da ita, infact haushinta ma takeji,musamman lokuttan da zata gansu tare da uncle dinta. Sanda hafsat din ta yunqura da nufin fita a motar tabi bayan widad din abbas yayi gaba,sai tayi mutuwar zaune tana binsa da kallo tare da son ganin inda zaiyi,zuciyarta na wani irin bugawa,tana fatar ba bayan widad din xaibi ba,yadda ta zata hakance ta faru,sassan widad din ya shige. Tana shiga ta zare dankwalinta ta aje saman kujera,itama ta haye kujerar wayarta na hannunta tana ci gaba da chat dinta,duk da ranta a bace yake sosai amma batason tabar idanunta da suka tara hawaye su zubda qwalla. Daga bakin qofa ya tsaya hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya zuba mata ido yana kallonta,qamshinsa ya sanyata gane ya shigo,ta daga kai sau daya ta kalleshi ta maida kanta ga chat dinta,qaramin murmushi yaso subuce masa,yana saurin karantarta fiye da kowacce mace a duniya,ya gane fushi takeyi amma batason nunawa,amma kuma shi bashi yayi laifin ba amma abun yana son qarewa a kansa,sai ya tako ya iso gabanta,ya zame a hankali ya duqa saman qafafunsa,ya riqe hannayenta da take chat din dasu yana duban qwayar idanunta "Tashi mu tafi weedad......" Ya kira ainihin sunanta a tausashe,kawai tana daga kai suka hada ido dai kuka ya kufce mata,ya matse hannayenta gam cikin nasa yana jin wani abu na masa suka cikin zuciyarsa,bayason kuka sam,kukan ma kuma nata,bai hanata ba sai datayi kusa minti goma tana yi,sannan ta zare hannunta daga nashi ta dauki dankwalinta ta nufi bedroom dinta. Binta yayi da kallo,bai taba zaton zata bisun ba,amma ga mamakinsa sai gata ta fito,ta wanke fuskarta fes ta sake shafa powder da lip gloss,ta zizarawa fararen idanuwanta kwalli "Muje" ta fada fuskarta babu walwala,yi yayi kamar baiji ba amma idanunsa suna kanta,har zuwa sanda ta tako tazo dab dashi xata wuce sai ya matse mata hanya,ya kuma sanyata cikin jikinsa "Bakya kyau da fushi baby doll,smile please" ya rada mata a kunne,a hankali murmushi ya kubce mata tana dan boye fuskarta. Tuni ta gama cika ta batse,duk inda bacin rai yakai ranta yakai qololuwar zuwa wajen,sau biyu tana aika mimi tayi kiran daddynsu sai tace qofar na a rufe ne,gashi tashi yanzu wuya yake mata,har sai data yunqura zata fita taje da kanta ayi wadda za'a yi,sai gasu sun fito. Sanda ta kalli fuskokinsu ji tayi qafafun ta sun riqe,haka abbas din zaiyi mata?,fuskar widad din kamar ma komai bai faru ba,ta shaqa iya shaqa,sai taji kamar numfashinta xai dauke,dole ta kauda kai daga kallonsu,wata zuciyar na bata shawarar ta fice a motar kawai tace ta fasa zuwa,amma sai wani sashen na zuciyarta ke gaya mata,idan tayi hakan ai kamar taci galaba a kanta kenan. Fuska fs muryarta duka wasai tana tsokanar mimi daketa shirya beads masu dauke da alphabet nawwara na watsa mata,ta buda gidan bayan ta shige,taja yarinyar jikinta ta kama hannunta tana tayata saka beads din tare da warning nawwara cikin wasa kan kada ta sake ta taba musu. Tsantsar baqinciki da bacin rai ya hana hafsat din magana har suka isa asibitin aka sauketa,taso bar musu yaran duka amma nawwara taqi sai mimi ce tabi widad din. Abinda bata sani ba kwata kwata yara basa damun widad,hasalima ita din mayyar yara ce,ko hana mimi zuwa tayata kwana da takeyi hakan baya mata dadi kwata kwata,ita kadai tasan yadda taji,baya ga dan uban tsoron dake bibiyarta harda kewar yaran. Kamar ko yaushe zama yayi a waje ya jirasu har aka gama,wannan karonma mimi ta samu albarkacin widad din,an wanke mata kan tsaf,yarinyar sai murna take tana shafa sumartata tana kallon widad "Anty ashe da dadi" sarai widad ta fahimci me take nufi,tana nufin kanta yayi mata sawai,kuma ta tabbatar iska mai dadi yanzu tana shiga kan. Tunda suka iso gidan,tun basu shiga ba gaba daya aka saukar mata da bacin rai da baqinciki,taji kamar ta cewa abbas don Allah kada ya shiga ya koma da ita,haka ta dinga qoqarin dannewa har ya saka kan motarsa cikin gidan. Tana tsaye daga bakin window tana hangen komai dake faruwa cikin gidan,don haka tana hangen sanda ya ajjiyeta ya koma,ta jijjiga kai tana sakin labulen falon. Da daren ranar ta dinga tsoron kada abinda ya faru xuwanta na qarshe bauchi ya sake maimaita kansa,idan ta runtse ido saita bude,ba motsin komai ko alamu na faruwar wani abu,daga baya tayi dukka addu'o'inta don haka ta samu relief sosai,saidai gidan gaba daya taji ta tsaneshi,tsananin tsana ta gasken gaske,a lokacin taji bata da wata buqata data wuce tabar gidan,bata da wata buqata data wuce ta ganta ba cikin gidan ba,haka ta dinga yawo tsakanin falonta zuwa bedroom,sai tayi kamar zata fita saita koma bakin qofa ta zauna ta fashe da kuka,kusan awa uku tana a wannan halin kafin daga bisani bacci yayi awon gaba da ita a nan bakin qofar a yashe a qasa. *W A S H E G A R I* Yadda parlor din yake fitar da sassanyan qamshi mai dadi,hakanan jikinta yake fidda nashi salon qamshin daban,girkinta ne ko ba girkinta ba,wannan duka bai dameta ba,kusan qamshi da tsafta sun zame mata gaado idan ana gadonsu,tun daga hannun ummu kawo yanzu. Ita daya ce a parlor din,kwance cikin doguwar kujera mai cin mutum biyu,wani doguwar rigar material onion color ne a jikinta mai gajeran hannu,kanta babu dankwali sai sassalkar sumarta mai tsaho baqi da santsi data dameta cikin robber band,sai qyalli take saboda gyaran kan da taje shekaran jiya, hannunta wayarta ce,sunata hira da balkisa,bata jin dadin zaman ita daya,yau gaba daga ko dauriyarsa mimi ba,abinda bata sani ba hafsat dince ta hanata shigowa kwata kwata,ita kuwa koda wasa batayi gefan hafsat din ba,indai ba dalili bane ya hadasu a farfajiyar gidan,suna iya gama kwanakinsu duka basu hadu ba,hatta da gaisuwa da take zuwa mata a yanzun ta ajjiyeta gefe,idan sun hadu su gaisa,idan basu hadu ba fine,ta bawa bilkisa labari, bilkisan tana ta tsokanarta "Sanda nace ki daina gani kikayi kamar sabo nayi ko?,yanzu fa?" Dariya kawai tayi,its har ga Allah zafin hafsat takeji,batason ma su faye haduwa,data gayawa balkisa dalili sai da tayi dariya sosai "Anya widad,anya kuwa?,wannan zazzafar soyayya mai cike da kishin tsiya da akewa uncle?" "Kishi kuma anty?" "Qwarai da gaske" ta jima a ranar tana son gane banbanci tsakanin kishi da kuma abinda takeji akan hafsat din. Sake gyara kwanciyarta tayi tana jin yadda gaba daya cikinta yake a cushe,duka cikin kwanakin nan bata jin dadin cikinta da jikinta sam,sai tajishi kamar a kushe,mararta babu dadi,amma saita danganta hakan da rashin zuwan period dinta da take saka ran ko yaushe zata iya ganinsa,tun tana lissafi da xuba ido harma ta share taci gaba da harkokinta hadi da cewa cikin ranta "Wai meye ma don baizo ba zan damu?,nima na huta da takurarsa" har zata gayama abbas saita fasa,tana tsoron kada yace suje asibiti,daga nan ace sai anyi allura. Tsayawa tayi da replying massage din da takeyi sanda sassanyan sound din data sama wayarta na musamman saboda shi ya shigo "Baby uncle" shine sunan da tayi saving dashi, qaramin murmushi ya kubce mata saman fuskarta,bata gajiya da ganinsa,duk sanda zata bar kwana sassansa hafsat ta karba tana jin raunin zuciya sosai,tana jin kamar ta riqeshi ya barta tayita kwana,amma bata iya hakan. Karbar jakarsa data gani daxun hafsat tayi ta kuma bishi sassansa ya fado mata a rai,saita tura baki sannan ta daga wayar a shagwabe tayi masa sallama. Hannu yasa ya buda qaramar qofar dake jikin sashensa,wadda take bullo dashi zuwa parking lot na gidan,shi daya yake amfani da ita time to time,ya soma takawa a hankali yana fita daga sassan,sanye cikin wani yadin kaftan na maza,qafarsa sanye da lafiyayyen baqin half cover na maza qirar kamfanin aldo mai asalin kyau da tsada,kansa babu hula sai gyaran da yasha,komai nashi fes yana zuba qamshin nan nasa mai aji da daukan hankali. Ya tabbata don hafsat bata nan ne,don bayan ta ajjiye masa abinci ta fita sashenta,kafin ta dawo ya shirya ya fito ko abincin bai tsaya ci ba,don gida zashi,akwai dan zama da zasuyi meeting shi da yayansa da yayyensa mata. Idonsa ya lumshe,wani abu na tsarga masa sanda tayi masa sallama da shagwababbiyar muryarta,kwanaki biyun da zai cikashe a yau ba tare da ita ba sun masa mugun nisa,jinsu yake kamar shekaru biyu "Kina ina baby?" "Ina parlor" "Okay,ki sameni ta qofar bayan part dina,fita zanyi" "Okay sir" yadda ta fada cikin shagwaba da kuma salo na girmamawa dole yabar murmushi saman labbansa,ya zare wayar ya jingina da motarsa da ya saka sale ya wanketa kusan tun safe,idanunsa akan hanya yana jiran fitowarta. Dakinta ta shiga tayi fitsarin daya cika mata mara,tana ta mamakin yawan fitsarin da takeyi yanzu akai akai,har ta gota madubinta ta dawo da baya,ta dauki turarenta ta sake fesawa sannan ta dawo parlor din ta zura slipper dinta ta fito ba tare data nema dankwali ba. Tar harabar gidan take da wadataccen haske,wannan ne ya bashi damar hangota tun daga nesa,ya zuba mata idanu kamar ko yaushe yana kallonta,wani abu mai sanyi yana ratsa zuciyarsa,canji yake gani daga widad din da gasken gaske,murjewa takeyi tana sake ninka kyau da farinta "Fatabarakallahu ahsanul khaliqin" ya samu kansa da furtawa yana shafa qirjinsa da hannunsa saitin zuciyarsa. Dab dashi ta tsaya,ta langabe kai tana kallonsa, murmushi ya saki yana gyara tsaiwarsa,irin wannan kallon nata,duk sanda ya gani yasan zaisha rigima ne "You look so good baby.....You look so cute,bansan yadda zan fasalta miki ba" dan murguda masa qaramin bakinta kadan tayi "Duk ban yadda da wannan dadin bakin ba, kwalliyar ka kaima yau tayi yawa,ina zakaje?" Mamaki da dariya suka tuqeshi,yau itama zata rama kenan?,gefe daya kuma tana nufin kada ya fita yaje wajen wata?. "Wajen hajajju zani ranki ya dade,na rantse babu inda zani daga nan" yadda ya rantse mata din yana daga hannuwansa sama alamun surrender ya bata dariya,ta tuntsire da dariya shima yana tayata,kafin daga bisani ya gyara tsaiwarsa yana dubanta "Me zaki kaima yaa baraka na gudunmawa?" Fararen idanunta dake dimautar dashi ta juya sannan tace "Na baka zabi,ko zabamin kome kaga ya dace,sai nakai din" folding hannayensa yayi yana kallonta, sosai ta bugeshi kimarta tana sake cika masa zuciya,sai ya tuna yadda sukayi da hafsat dazun da safe,kai tsaye ta nuna kudi zai bata,ya bata din kuma ta karba abinta,yasan halinta farin sani,bashi da tabbacin kuma zata kai abinda yakai kimar abinda ya batan,kansa ya jinjina ya buda baki zaiyi magana,saidai kafin yace komai hafsat ta bayyana a wajen from no where,daga shi har widad babu wanda yaga tahowarta bare isowarta wajen,tana isowa kuma babu inda ta nufa sai kan widad gadan gadan,batayi wata wata ba tasa hannu takai mata shaqa tana fadin "Yau sai kinci ku******mar ubanki,zaki gane ke qaramar 'yar iska ce" cikin sauri da kuma tsananin tsoro widad din ta kauce,saita sake kai mata cafka,dai dai sanda abbas yayo kanta yana daka mata tsawa "Ke hafsa,meye haka?,kina da hankali kuwa?,me kike yi haka" ko sau daya bata nuna ma ta jishi ba bare ta dakatar da abinda take shirin aiwatarwa,burinta kawai ta cimma widad din ta ida nufinta,cikin wani irin zafin nama ya isa garesu ya kuma shiga tsakiya yana duban hafsat din cikin wani irin mummunar bacin rai da zaka jima baka ganshi kan fuskarsa ba. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 98 "Matsa daga gurin nan hafsa tun raina bai baci ba" ya sake fada cikin kausashiyar murya,shammatarsa tayi sai kawai ga hannunta jikin widad,ta shaqeta sosai tana dura mata ashar,kai zaka dauka mahaukaciya ce sabon kamu. Cikin qasa da second biyu,cikin wani irin bacin rai fushi da kuma qarfin hali itama widad ta shaqetan "Ya salam" abbas din ya fada da qarfi yana kama hannun hafsat ya fincike daga jikin widad,sannan ya janye widad din gefe yana riqe da hannunsa tsam cikin nata "Wuce cikin gida tun kafin raina ya gama baci!" Ya fada a tsawace "Bazan wuce ba,ba inda zani, wallahi wallahi yau saina koyawa yarinyar nan hankali don ku****mar ubanta,ni za'a dinga rainawa hankali ana cin amanata?" "Ba ubana kike zagi ba,naki kika zaga wallahi" widad ta fada cikin bacin rai,tana jin kamar abbas ya saketa ta sake komawa kan hafsat din. Sake yunqurawa tayi a zafafe jin raddin da ta mayar mata "Ni kike gayawa haka?,ka barni nayi mata dan banzan dukan da ba zata sake magana ba" kafin ta qaraso ya buda qofar bayan sashensa ya sanya widad wadda itama takeson qwacewa ya maida qofar ya rufe sannan ya juyo yana kallon hafsat da idanunsa da suka canza launi saboda bacin rai,ranshi a mugun bace yace "Ki shiga hankalinki, banason rashin mutunci da hauka" "Nice mara mutunci?,nice kuma mahaukaciya?,ai dole ka fadi haka,kun hada kai kuna cin mutuncina,kuna cin amanata,Allah ya isa wallahi ban yafe ba,Allah ya isa na" ta fada da qarfi,saidai......tun kafin ta kammala rufe bakinta ya kwasheta da wani kyakkyawan mari a kuncinta. Cak wuta ta dauke mata,yayi mata mugun ba zatan da bata taba tunanin zai iya aiwatar wa ba,itace yau abbas ya daga hannu ya mara saboda widad? "Stupid!" Ya fada yana huci,wani irin fincikar jikinta tayi tana dosar qofar "Wallahi yau sai na daketa naga abinda zakayi" dab da zata qarasa ya isa gabanta yana nuna mata hanya,amma burinta ta qarasa ta bude qofar ta fiddo widad "Ka matsa ka bani waje azzalumi kawai" "Kibar wajen nan hafsa na gaya miki" "Saina shiga,saina shiga azzalumi" wani lafiyayyen marin ya sake sauke mata hagu da dama,gaba daya sai wuta ta dauke mata,taci burki tana kallonsa kamar wata zararriya riqe da kumatunta "Don kina iskanci da rashin mutuncinki kina ganin kamar bazan iya daukan mataki a kanki ba kin yaudari kanki,sassauci na da dauke kan da nake miki inason na zama mafi alkhairi ne ga iyalinsa,amma ke gaba daya tosashiyar kwanyarki ta kasa gano miki hakan,to wallahi wallahi kinyi na farko kinyi na qarshe,bazanci gaba da dauka ba,ki bacemin daga wajen nan tun ban bi ta kanki ba!!!" Ya fada da wata irin rugugin tsawa,ba hafsat dake tsaye a wajen ba,hatta da widad dake daga cikin falon saida cikinta ya juya, tsoron sosai ya kamata,ta koma ta zauna saman daya daga cikin kujerun dake dab da qofar,karin farko da taji sautin fushi da bacin rai daga gareshi kenan. "Ko meye zaka ce, kuma ko me zakayi bazan fasa fadin cutata da kakeyi da cin zarafina ba,yarinya qarama ta mallakeka sai yadda tayi dakai,sai abinda tace,kanata zalunta ta,bazna yafe ba wallahi,sai Allah ya sakamun,kai da ita dukanku bazan yafe muku ba" cikin fushi ya sake daga hannu sai kuma idanunsa suka sauka kan cikinta,ya janye hannun yana qoqarin hadiye fushinsa,bai taba dora hannu a kanta ba sai yau,sai ya kama hannunta ya saita mata hanya yana gaya mata cikin tsawa ta bace masa a wajen. Jinta take kamar ba'a tsaye take saman qafafunta ba kamar akan iska take haka ta juya ta fara barin wajen, hannunta har yanzu akan kuncinta,idanunta na malalar hawaye masu zafi da quna,yau ita abbas ya mara?,wannan shine mummunan abun tarihi na farko daya faru a iya zamansu da ba zata mance dashi ba. Ido ya zuba mata cikin fushi har ta bace a wajen,sannan ya juya ya bude qofar,wanda tuni widad dake zaune saman kujera ta miqe tana dakon isowarsa,saidai zuwa yayi ya wuceta abinsa yana wani irin huci,kaman zai zauna akan kujera amma sai ya kasa,ya dinga kai komo widad din tana kallonsa tana kuka qasa qasa "Shut up" ya fada mata da wata irin tsawa data sakata qanqame jiki waje daya hadi da runtse idanunta,bayason jin kukanta ne kwata kwata,tana qara hasala masa zuciyarsa ne ba tare data sani ba,a cikin yanayin da yake kuma a yanzun bazai iya lallashinta ba,sai kuma ya koma ya zauna bayan ya sakar mata tsawar,jikinsa yana mutuwa,qaramin sautin kukanta yana sake ratsa falon. Kusan minti talatin suna a haka,ta kasa shuru shi kuma ya kasa lallashinta,sai da suka doshi minti arba'in sannan ya miqe ya fice,ba jimawa ya dawo dauke da hijab dinta da wayarta ya miqa mata,sannan ya isa gaban freezer dinsa ya ciro ruwan gora mai sanyi ya bude ya miqa mata,tasa hannu ta karba tana satar kallonsa,idanunsa ba'a kanta yake ba,wani gurin daban yake kalla,sai takai ruwan bakinta ta fara sha,ya fara sauka cikin cikinta yana ratsa qirjinta dake suya,yana kuma rage mata radadin da takeji. Kusan rabi tasha sannan ta miqa masa,sai ya sake saka hannu ya karba ba tare daya kalleta ba,bakinsa yakai ya shanye sauran yana yin gaba,ya cillar da robar yana cewa "Wuce muje" bayansa tabi ba tare da tasan ina suka nufa ba,motar sa ya bude tun kafin su qarasa da remote control,ya isa seat din gefan driver ya bude mata ta shiga ya mayar ya rufe,sannan ya zagaya shima nasa bangaren ya shiga ya tayar da motar suka bar gidan. Lamo tayi cikin motar,ta kwantar da kanta a makarin kujerar tana 'yar sheshsheqar kuka,idonsa ya dinga runtsewa,sautin kukanta yana qonashi da yawa,basarwa ya dinga yi yana zaton zai iya daurewa amma sai ya kasa,tausayinta ya lullubeshi,yadan daki kan motar,sai ya gangara gefan hanya yayi parking ya juyo sosai ya zuba mata ido yana hadiye bacin ransa da qyar "Why widad.....why.......me yasa kika biye mata?" Idanunta dake jiqe da hawaye ta daga ta kalleshi "Amma uncle.....itace ta fara fa" kai ya jijjiga "Na sani,amma kina zaton zan tsaya ne a wajen ina kallo ta cutarmin dake?" Kai ta kada a hankali alamun a'ah "So kike ki koyi irin abinda takeyi?,kinaso na daina samun walwala gaba daya?" Kai ta girgiza nan ma sabuwar qwalla na sauko mata "Kayi haquri uncle......am sorry" a hankali ya lalubo hannunta da hannunsa guda daya ya hadesu waje daya yana hadiye wani bacin rai daya tsaya masa "Am sorry too baby,na miki tsawa,it was not intentionally.......hankalina ne a tashe,raina a bace,banason kema ki koma wani abu daban" "Bazan sake ba uncle" ta kuma fada hawaye na sake balle mata "Kina qonani baby doll,kina qona zuciyata,ki daina wannan kukan" ya fadi yana kamo fuskarta cikin hannunsa,tare da zaro handkerchief dinsa ya soma goge mata fuskar cikin wani irin salo na tausasawa da nuna zallar qauna,hausawa sukance gaida mai gaidaka ko bazai amsa ba,ko meye zai mata idan tana cikin bacin rai bai fadi ba,widad ce kadai ke fahimtar ransa a bace yake ko yana fushi,saita tabbatar tayi abinda zai samu sassauci kota saukeshi daga fushinsa,duk da kusan ba itace sila ba. Saida suka shiga unguwar ta fahimci gidan hajiya ya kawota,bashi da wani solution illa hakan,saboda yasan kwana zatayi kuka ita kadai,babu lallai ta saki jikinta,a nan ne kawai zata sake tayi baccinta. Mamaki ya kama hajiya lokacin data gansu tare,baice ma hajiyan komai ba ya barta a nan ya koma setting room din qofar gidansu suka shiga meeting din da suka shirya yi din. Itama batace komai da hajiyan ba,saidai hajiya ta fuskanci sanyi jiki kadan tattare da ita,tanata kallon widad din,canzawar da tayi tayi yawa,ta kasa cinyewa wannan karon bayan sun gama meeting din ya shigo gidan,widad din ta tafi kawo masa abincin da bai samu ci ba tace dashi "Anya abbas ba juna biyu yarinyar nan take dashi ba?" Ido yadan lumshe yana sakin qaramin murmushi,hasaso 'yar rigimar tashi da ciki kawai yakeyi,inda hakan zata kasance da yafi kowa farinciki,amma fa yasan daru ne za'a shashi "Banjin haka hajiya" "Bata amai bata yawu,ba zazzabin dare?" Dan jim yayi sannan ya girgiza kansa "Babu hajiya" "To ma sha Allah,Allah ya kawo nagari masu albarka" "Ameen ameen" ya fada cikin dan jin nauyi. Muneera ya nema yace ta gyara daki daya widad din zata kwanta a ciki,ba jimawa muneera ta gyara din,don dama ba dakin da hajiyan ke barinsa da dauda. Yana zaune ta wuce dakin,hajiya tace taje ta kwanta,taga kamar tana alamun bacci a idanunta,ta yima hajiya sai da safe,ta juyo zata masa sallama suka hada ido,sai ta basar tace "Sai da safe" "Allah ya bamu alkhairi" ya amsa ta yana binta da kallo,inda suna kaduna waye zai shiga tsakaninsu a irin wannan lokacin,kaf rayuwarsa yana qaunar dare yayi,saboda lokacine da zai rabi jikinta sosai ya kuma kwana yana jin duminta hadi da shaqar tattausan qamshinta. "Ba yanzu zaka wuce bane" hajiya ta tambayeshi ganin goma da rabi na neman gotawa,agogo ya kalla sannan yadan dubi hajiyan "Wannan program din nake jira su gama saina wuce" ya bata amsa yana maida dubansa ga tv din,saidai a zahiri gidan ne baya qaunar komawa,idan ya tuna abinda hafsat din tayi sai yaji ransa ya baci,yana so ya sake hucewa ne kafin yakai ga shiga gidan,bayason komawa da zafinsa shaidan ya ingizashi ya yanke mummunan hukunci. "To bari na shiga na kwanta nidai" sukayi sallama da hajiyan,amma yace idan ya gama zai wuce zai mata magana. Ido yabi hajiyan dashi har ta shige daki,sai yayi zumbur ya miqe yana zuba hannuwansa a aljihun rigarsa ya wuce dakin widad. Tunda ta shiga dakin tana kwance ne kawai amma bacci bai zowa idanunta ba har sannan,har yanzu zuciyarta a bace take kan abinda hafsat din tayi mata,tunda take ba'a taba yi mata makamancin abinda hafsat din tayi mata ba,gaba daya kimarta babu ita a idanunta,duk wani sauran mutunci nata da take gani a yanzu babu shi,to me tayi mata da har take yunqurin dukanta?, tabbas inda ta dora hannunta a kanta babu abinda zai hanata ramawa kowa kuwa gemunta na jan qasa ne saboda girma da shekaru,tunda ai bataga abinda tayi mata ba. Sallamarsa tasa ta daga idanunta zuwa fuskarsa,ta zuba masa ido na wasu sakanni,haka kawai taji tausayinsa ya kamata,tausayin da batasan na meye ba,ya tako a hankali zuwa gaban gadon,sai ya matsa jikin switch na fankan yana rage gudun fankan dakin,sannan ya dqwo gefan gadon ya zauna yana cewa "Wannan iskan ai tayi yawa" "Zafi nakeji" ta fada muryarta qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta cikin mamaki,don garin a sake yake da iska, baice komai ba yakai hannunsa jikinta ya taba,da gaske gumi takeyi,sai yasa hannu ya dagota gaba daya yana zare mata rigar jikinta,ya barta daga ita sai farar vest me siririn hannu, idanunsa suka sauka a qirjinta da suka cika suke a tsaye kyam,sai tayi hanzarin jan bargo zuwa qirjin nata ta koma da sauri ta kwanta tana boye fuskarta. *H A F S A T* Kuka ta zauna tana yi sosai kamar zata fidda zuciyarta,ba zafin marin ne yafi damunta ba,wadda aka mareta ta sanadinta ne damuwarta,hannun abbas yau da yakai fuskarta ya daketa saboda widad din?,takai ta kawo,ta kasa zama tana jin kamar abinda yake cikinta zai fito a yau. Tana tsaka da wannan taji tashin motarsa,da sauri ta daga labulenta tana leqensa har ya fice, zuciyarta ta dinga qissima mata abubuwa da yawa,shi da waye?, abinda yafi tsaya mata a rai kenan,sai kawai kuka ya qwace mata,ta dauki wayarta da hanzari ta danna wa mamanta kira,tana jin baqinciki kamar zai kasheta,ba zata iya hadiyar wannan bacin ran ita kadai ba. Ashar mamanta ta dinga zundumawa "Saboda baisan darajarki da mutuncinki ba?,cikin daren nan,da tsohon ciki a jikinki zai kamaki ya daka?" "Ni umma anya wannan hanyar tana aiki kuwa?" "Bana shakka akai,saidai kice wani abu da ya kawo tasgaro ya faru,amma koma meye ki daga waya ki gayawa uwarshi abinda yayi miki,yadda yasa kika tasheni a bacci itama ki tasheta" akan wannan suka rabu,ba tare da wani dogon tunani ba kuwa ta laluba number hajiya ta kirata. Dai dai lokacin da dattijuwar ke saman abun sallah tana shafa'i da wuturi taji qarar waya "Subhanallah" ta furta bayan ta gane number wadda ke kira,tabbas matsala ce ta faru ta tabbatar,don ba zata iya tuna sanda taga kiran hafsat din a wayarta haka siddan ba tare da komai na matsala ya faru ba. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks:Huguma* Page 99 "Hajiya ina wuni" "Lafiya alhmdlh,ya nauyin jiki?" "Lafiya lau" ta fada a gaggauce,sannan ta zauna ta fara rattabo mata abinda ya faru. Fiye da rabin maganar ta canzata, hajiyan tayi shuru tana saurarenta har ta gama fada sannan ta rushe da kuka "Ya isa,kiyi shuru haka ki daina kukan ko don abinda yake jikinki,zan laluba gaskiyar maganar,indai na sameshi da laifi saina bata masa,ki kwanta kiyi bacci zan nemeki in sha Allah" a haka suka rabu da hajiyan,can qasan ranta tana jin haushi haushi,wai zata bincika taji,itama ta fara canza hali kenan. Ajiyar zuciya hajiyan ta saki "La haula wala quwwata illa billa" ta fada a fili,qaddarar abbas kenan shi kuma,kalar tasa jarrabawar rayuwar kenan,yunqurawa tayi ta miqe tana fatan ta sameshi a falo,duk da sha daya na dare ma ta gota,amma yace zai mata magana idan zai wuce. Murmushi ya bita dashi sanda ta koma ta kwanta tana boye fuskarta,sai yaja mata bargon sosai,ya sunkuya yayi kissing dinta lightly,sannan ya motsa bakinsa zuw kunnenta cikin rada yace "Kiyi bacci mai dadi babyn uncle" a dole murmushi ya subuce mata,hakan yayi masa dadi,sai ya rage mata hasken dakin sosai,ya sake lullubeta ya fice yaja mata qofar. Dai dai lokacin hajiya ta fito a dakinta,sai sukayi kacibus,kunya ta dan kamashi,sai hajiyan ta kauda kanta "Yanzu nake shirin shigowa muyi sallama" ya fada yana shafa kansa "Gwara da baka wuce din ba ai,zo ka zauna muyi magana" tuni jikinsa ya bashi tayi halin,ya dawo gaban hajiyan ya zauna "Matso" tace dashi,sai ya dawo saitin qafarta "Wanne abu ne ya shiga kanka da zaka saka hannu ka mammari matarka da tsohon ciki?" Kansa ya saddar qasa na wasu sakanni,sannan ya dago "Hajiya na fara gajiya da hafsat,na gaji da halayenta,inajin taqi kadan ya rage mu rabu" "Aah,kada ka sake fadin haka,yanzun me ya hadaku?" Bai boye mata komai ba ya gaya mata,tayi shuru abun na tsumata,ko yaushe abun na hafsat gaba yake ba baya ba? "Iya qoqarina hajiya inayi,ina dannewa,ban taba kai qararta ba,amma kome nayi ita bata gani,da qyar wani lokacin nake iya tanqwara zuciyata akanta,tana kaini bango,bani da guarantee din abinda zai iya faruwa gaba" "Haquri zaka ci gaba dayi,ko don albarkacin zuri'a data ratsa tsakaninku" Duk da ita kanta hajiyan abubuwan sunata kwance mata,to amma ita din uwa ce,duk yadda uwa take da juriya aka santa,ba yadda zataso abbas din yayi wani abu na rashin dadi ko kyautatawa,har abada da naka yayi cuta gwara shi a cuceshi,baki ta dinga baki da nasiha cikin hikima ta dattawan mutane masu hankali da sanin ya kamata,taga bacin rai da damuwa masu yawa a idanunsa "Ku shirya gobe ku koma inda kuka fito kawai abbas,banason wannan tashin hankalin,mun yafe bikin" statement din hajiya na qarshe kenan,don shine kawai mafita. Kamar dama ta shiga xuciyarsa,don darajarta ce kawai take sanyashi yawancin lokutta yake zama a garin har yayi kwanaki idan yazo. Sha biyu da minti goma ya isa gida,tana falo zaune don ta kasa runtsawa,ta kuma ji shigowarsa,sai taci gaba da zama tana tsammatar shigowarsa ganinsu mimi,amma har aka qara mintuna talatin shuru babu shi babu bayaninsa. Shikam sashensa ya shige,ya fidda kayan jikinsa yayi wanka,sannan ya shirya kayansa waje daya kafin nan ya kwanta. Har qarfe daya na dare tana zaune shuru,ranta yana sake baci,zuciya na mata saqa iri daban daban,yana nufin har kwanan nata ma ya saraya kenan?,idan bai shigo yanzu ba ta tabbata da safe zai shigo,zata ga da wanne ido zai kalleta. Daga sallar asuba ya zarce da wanka,kafin qarfe shida ya gama shirinsa tsaf,ya fidda luggage dinsa ya saka a mota. Sale ya barwa envelope yace ya bawa matar gidan,kudaden hidimar gida ne a ciki,ya zare dukkan wasu kudade daya saba bar mata wanda suke kyautatawa ce kawai bawai na haqqin dake wuyansa na shari'a ba. *********Da farko ta watsar dashi kamar yadda ya watsar da ita,don ba qaramin shaqar takaici tayi ba sanda ta karba saqon ta hannun sale,ya rasa wa zai bawa aiken kudin amfanin gidanta sai salen?,bata sake shiga rudu ba sai dataga kowanne kudi ya fadi na meye,babu ko qarin sile akan abinda ya saba bata,gashi buqatar kudin take da gaske saboda fara adashin asara data yi,ko cikin satin ummanta tace lallai lallai ta tanadi kudi,saboda ba zasu taba bari sakaci ya shigo cikin aikin da aka fara ba,wannan ya sanya ta sake qullatar widad din qwarai,a duniya idan aka bata bindiga akace ta kashe mutum daya widad din zata fara harbewa. Yadda ya dauke mata wuta abin ya fara damunta,gashi tana fuskantar EDD dinta yana sake matsowa,wata zuciyar tana ta kirashi wata tana ta shareshi,a haka kwanakin suka fara tafiya, dole daga bisani ta karya billent ta kirashi,ta kuma maida komai ba komai ba,don lallai tana buqatar kudi. *B a y a n wa t a u k u* Bayan watanni uku hafsat din ta sauka,ta sake samun baby girl,zagayowar kwanaki hudu abbas ya dauki excuse don zuwa ganin baby,dole widad ta soma shirin binsa itama,don rabonta da bauchi tun wancan lokacin da suka samu sabani da hafsat,duk sanda zaije weekend tabar binsa,saidai yaje yayi kwanaki biyu ya dawo Kaduna,hakan yafi mata kwanciyar hankali,har ya zamana koda wasa batason taji ya ambaci xuwa bauchi da ita,yanzu zataji hankalinta ya tashi. Ta shirya tsaf tayi sabbin dinkunanta,gyaran gashi zuwa lalle suka wuce bauchi,ranar ta shiga sassan hafsat din,wanda rabonta dashi har ta manta. Ba wani mutane bane sosai, kasancewar ita din dama bata mutane bace,mai zuwa mata sha'ani sai wanda ya dubi Allah,anty ummee ce sai wasu baqi mata biyu sai 'yar yayarta data dauko saboda aikace aikacen gidan,sai hajiya habiba. Ciki ciki hafsat din ta amsa mata barkan data mata,itama sai bata saka kanta can ba,ta zauna daga hannun kujera,anty ummee ta miqa mata baby da aka gama yiwa wanka tana qarewa widad din kallo tsafff tana kaduwa da yadda taga ta sauya,ta karbeta tana jin sha'awar yarinyar har cikin zuciyarta,kasancewarta mai son yara sosai. "Uhmmm.....ko a bar miki ita ne?,naga kin kasa daina kallonta" hajiya habiba ta fada tana wani munafukin murmushi tana kallon widad,sai ta saki murmushi kafin tace komai hafsat ta rigata,taja wani mugun tsaki tana gyara zamanta "Ki daina irin wannan wasan hajiya habiba......haihuwa wasa ce da zaka dauki yaro danka ka baiwa yaro,wanda ko ciwon kansa bai sani ba?,tab..... garinsu da nisa ai,idan fitsari banza ne kaza tayi mana" tsaf ya fahimci abinda hafsat din take nufi,don haka ta miqe tsam ta miqawa anty ummee babyn tana cewa "Allah ya rayata" ta fice a nutse a falon ta wuce sassanta,don saukarsu kenan ta fara shigowa nan din. Tare hajiya habiba da anty ummee suka dauke kai daga kallon widad bayan ta bace musu,suka maida kan hafsat data fara qananun motoci tana sakin tsaki kamar ta tsinke harshenta "Banso kika sanya baki ba,kallon me juna biyu nakewa yarinyar,naso na bugar mana cikinta muji akwai ko babu" hajiya habiba ta fada tana duban hafsat "Ai banza ce,nima kallon da nakeyi yarinyar kenan tunda ta shigo,kamar me yaron ciki,canzawar tayi yawa,ni tsorata ma nayi dana ganta wallahi,ta zama wata babbar mace?" Anty ummee ta fadi tana kama bakinta. "Allah ya kiyaye Allah ya sawwaqe,ni kuwa ina me zan zauna na barta tayi ciki?,haba don Allah,bazai yiwu ba" hafsat ta fada tana girgiza kai,cikin zuciyarta tana jin wani irin zafi kamar ma ance cikinne,tana qiyasta yadda zata cakuda 'ya'yanta da 'ya'yan wata matar?,ba zaiyuwu ba,ba zata iya ba,barin widad din ta samu ciki harta haihu shine babban kuskuren da zata tafka "Idan ba mataki kika dauka ba sanda zai narka mata cikin sani kikayi?,kina nan kina bacci saidai ki tashi ki ganshi" hajiya habiba ta fada tana miqewa tsaye gami da daukar jakarta "Bafa wannan maganar hajiya,matakin nasa aka dauka,shi yasa nake cika miki baki" "To yanzu naji magana.....hmmm aikin hadu da alaqaqai ciwon zamani mai wuyar magani" "Ko tunata banason yi wallahi hajiya,ban taba kawowa yarinyar nan zata shiga rayuwata tayimin karen tsaye har haka ba" hafsat din ta fada yana sauke idanunta a sassan widad din tana jin ranta yana mata ciwo. Duk da jego take amma hakan bai sanyata ta barwa widad din kwananta ba,haka take diban jiki tabar masu tayata zama ta wuce sassansa ta kwana,ko daya widad din bata bari taga damuwarta ba,saita shiga sabgar gabanta kawai. Da kansa yace me take buqata na taron suna,tace zata kirasa idan ya fita,saita dauki waya sukayi magana da anty madina "Kiyi komai naki ta yadda ba ruwanki da abincin taronta,wanda ya shigo miki ki bashi,wanda ma baizo na ya hutasheki" da suka gama wayan saita kira hajjaa ita kuma ta gaya mata yadda suke komai na taron suna,ta yiwa abbas din waya ta gaya masa,ya ajjiye mata komai,da taimakon hajja takai aikin abincinta,masa da sinasir sai soyayyiyar shinkafa (fried rice). Ana gobe suna ta yiwa uncle muhsin waya ya bar nujood tazo suka kwana tare,washegari aka tashi da suna. Kwalliya ta dinga yi sosai,tana canza shiga cikin kayan da abbas din ya dinka musu,duk da na hafsat din ya dara nata,da kadan da kadan saiga mutane sun cika sashen nata, don duk wanda ya shigo din ga abinci nan zaici ya qoshi,sashen mai jego kuwa babu bayani,don kudinta ta adana,ta sada mutane da wata irin jallop din shinkafa data hadu da taqadiriyar dahuwa mara tsaro,dukka lemon roban da yasa aka jibge ta debesu,ta musanya da zobo dan dauri. Daga qarshe dai sassan widad sai ya zamana kaman a nan akayi haihuwar,duk wanda ya shigo din kuwa saiya qoshi da abinci me kyau,hafsat na daga sassanta amma labarin abinda ke faruwa a sassan widad din tuni yaje mata,ta cika tayi fam,musamman matan abokan abbas din da suka yada zango a can bayan sun mata barka,don ba wadda ta zauna a cikinsu,saboda ba wani kyakkyawan mu'amala bace tsakaninsu,tsananin kirkin abbas din ne ma ya sanya suka kasa qin zuwa,dama kuma idan ka gansu a gidan to saifa irin hakan ta kama. Kasa zaune bare tsaye hafsat din tayi,da yammar ta canza kaya na biyu shima bisa takurawar anty ummee "Kiyita zama,suttura iya sutura an miki amma kin jibgesu,ga kishiyarki can kowa fadin shigar ta yakeyi,keda ake taron don ke amma kamar saboda ita akeyi" sannan ne ta sake saka wata atamfar. Sanda ta fito falon tayi baqi ta hangi fitowar widad din ta window din falon nata da aka dauke curtains dinsa,ta yima matan abokan nasa rakiya,tana sanye da shadda 'yar mali,baqa ce da aka yiwa adon mustard yellow,zo kaga baqar shadda jikin farar mace,an tsara mata wani mugun dinkin bubu,ido kawai ta runtse hafsat din tana dauke kanta daga wajen tana jin Zuciyarta kamar zata fashe. Kwana biyu da suna suka koma inda suka fito,tabar hafsat din da tarin ciwo a zuciyar ta,da kuma K'ULLACI hadi da ALWASHI iri daban daban akan widad din. Duka duka sati uku da komawarsu bauchi tafiyarsu ta taso,zasu tashi ta kano,don haka suka shirya zuwa bauchin yayi sallama da hajiyansa,ya kuma sallami gida sannan su wuce kanon. Kamar ko yaushe,cikin tsoro da wani mugun bacin rai da qunci ta sauka a sassan nata,yau din tana jin tsanar gidan sosai fiye da ko yaushe,cikin qafafunta takejin kamar ba lallausan carfet take takawa ba,kamar qayoyi ne zube a sassan nata gaba daya,haka ta dinga qoqarin dannewa ta fara gyaran sassan nata tayi ta kammala ta samu waje ta kwanta,wata muguwar kasala da nauyin jiki suna mamayeta,wanda a kwanakin nan sai sake gaba abun yake,har abbas din yace muddin sukaje hajjin suka dawo babu wani sauyi to ko bataso dole taje taga likita. Kamar wancan karon,wannan karon ma har bacci yadan fara fusgarta taji kamar an soma shaqeta,ta farka da sauri tana ambaton sunan Allah,sai numfashin ta ya ware ya koma dai dai,ta miqe a hankali tana sauke ajiyar zuciya,tana jin kamar ta fice a gidan kota yaya,sai ta zura slipper dinta kawai ta bude qofarta ta fito. *H U G U M A* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) *Arewabooks: Huguma* Page 100 A hankali take taka harabar gidan,tana jin kamar magnet ke janta zuwa waje,har ta kusa da gate din ta taka wani dan qaramin dutse mai tsini,zafin da ya soketa ya sanyata furta "Subhanallah" ta tsugunna tana dub qafar,Allah ya taimaketa bata huje ba,banda zafi da radadin da takeji kawai,koda ta dago sai ta tsaya tana duban qofar fita daga gidan dake kulle,tare da tunanin meye ya fito da ita a wannan daren?,saita girgiza kai ta juya tana komawa ciki. A hankali yake takowa zuwa dakin solar na gidan,don ya duba yana tunanin kamar sale bai kulle ba,cike da mamaki yake kallonta sanda take takawa zata koma sashenta,to daga ina take?,da alama ma bata ganshi ba,sai ya canza akala ya dosheta. A tausashe ya kamo lallausan tafin hannunta ta baya,tadan firgita kadan sannan ta waiwayo suka hada ido,ta saki waya ajiyar zuciya mai nauyi "Ina kikaje haka" "Babu ko ina,kawai na gaji ne" qarara ya karanto zallar gajiya da qin da takewa garin na bauchi a idanunta,sai ya jinjina kai "Muje kidan motsa,dama kin fara qiba ba dole ki dinga gajiya haka kawai ba".ya fada cikin salon tsokana yana lakuce mata kumatu,sai ta shagwabe masa tana tabe baki kamar mai.shirin sakin kuka,sakato.yayi yana kallonta tana sake tsumashi,don dama duka.yau din baiga wannan narkakkiyar shagwabarta ta ba,sai tsomoshi da shigar data dinga yi a sunan data dinga yi,duk sanda zai.shigo kuma sai yayi tozali da ita,ya dinga jin kamar ya dauketa subar gidan ya samu ya rage zafi,amma sanda yaga yawan jama'ar dake sashenta dole ya haqura ya hadiye,hafsat kuma ko a yanzun a dakinsa ya barta,ko kwana daya bata yarda ta bariwa widad din ba. Sassanyar iskar daren dake kada jikkunansu ta dinga haifar musu da wani yanayi cikin zukatansu,kada ma abbas din yaji labari,ya sake matsowa ya.kama hannunta suna ci gaba da strolling "Jibi zamu wuce,gobe ki kammala komai naki" da mamaki take dubansa har batasan murmushi ya subuce mata ba,bata dauka zasu koma da wuri haka ba,saboda taji yana cewa babu cinkoson aiki sosai,ya waiwaya a hankali ya sauke mata narkakkun idanunsa "Oh......murna ma kikeyi?" Nata fararen idon ta juya,lallausan murmushin dake qara fidda quruciyarta ta saki tana maida dubanta gefe "Dole ne ai......zan sake da uncle dina" murmushi mai dan sauti ya saki yana kallonta cikin mamaki,sannan cikin tsokana yace da ita "La la la.....eh lallai zan gayawa uncle muhsin,yarinyarsa tasan dadin mijinta" ya fadi qasa qasa dab da fuskarta,sai ta saki dariya tana zame hannunta daga nasa cikin jin kunya "Don Allah uncle karka fada" ya bita da sauri yana son cimmata yana sake tsokanarta kan sai fa ya gaya masa. Kamar yadda yace din kwana daya suka qara suka tattara suka koma kaduna abinsu,hafsat din tana ta cika tana batsewa,don ko fitowa batayi ba,daga daki sukayi sallamarsu suka gama. Ajiyar zuciya mai nauyi widad ta sauke sanda motarsu ta fita daga qasar bauchi tahau ta kaduna,har sai da abbas din ya juyo ya kalleta. *********Cikin wata muguwar zabura ta farka tare da miqewa zaune saman gadonta tana rarraba idanu,gumi sharkaf ya jiqa mata ilahirin rigar atamfar da take jikinta yana zartarwa cikin jikinta,kadan ya rage ta danne baby yusra dake bacci a gefanta,ji tayi kamar alqiyamarta zata tsaya,wannan wanne irin mafarki ne mai muni mara dadin gani?,me mafarkinta yake nuna mata kenan,widad dauke da baby tana miqo mata ita?,me hakan yake nufi?. Wayarta ta jawo tana dubawa kamar me neman wani abu,a sannan tayi ido hudu da number abbas,waddda itace kira na qarshe a jerin lambobin da aka kirata ko tayi kiran,awanni hudu da suka wuce,yake gaya mata jibi zasu iso bauchin,duk da sai da suka kusan dan samun sabani saboda a maganarsa ta fahimci da widad din xasuzo,abinda duk duniya ta tsana kenan a yanzu,take kuma neman hanyar da zata kawo qarshen faruwarsa. "Anya ba ciki ne da yarinyar ba?" Wata zuciyar ta gaya mata,saita hau girgiza kai da sauri kamar hauka sabon kamu,kai kace ita da wani suke magana a dakin "Inaaa,inaaa,bazaiyiwu ba" ta fada a fili,ba zata taba barin haka ta faru ba muddin tana raye,cikin abbas ace ya tabbata a jikin wata?,da kuwa lallai ta rako maya duniya,ta kuma cika hasararriya,iya qiyasta hakan kawai da tayi sai taji kamar zuciyarta zata tsinke tabar qirjinta,haka fa na nufin ya hada shimfida da ita?,ya santa a matsayin diya mace "Aah..... a'ah" ta sake fada tana girgiza kai da sauri. Ji tayi kamar ta kirashi tace su taho gobe,lallai kuma yazo da widad din, saboda tanason ganewa idanunta,shin da gaske ne abinda zuciyarta ke raya mata?,ko hasashe ne hadi da shirmen mafarki?. Wanann daren sai ya zame mata baqin dare,don tunda ta farka ta gagara komawa,saidai ta zauna idan ta gaji takai ta kawo har asuba ta risketa a haka. ********Sau biyu yana duba agogonsa sannan ya maida dubansa ga qofar fitowa daga sassanta,kusan minti goma tace tana zuwa,amma har yanzu bata fito ba,bata saba hakan ba,ba halinta bane,duk sanda zasuyi tafiya ko zasuje waje bata fiya bata masa lokaci ba,idan yace qarfe kaza kome takeyi ta kammalashi kafin wannan lokacin. Fitowa yayi daga motar hannunsa sanye a aljihun wandon yadin cashmere mai asalin kyau da tsada,wanda ya karbeshi qwarai,ya tunkari sassan nata yana fatan samunta lafiya. Saman kujera ya sameta zaune,tayi likimo a ciki kamar bamai shirin tafiya daga kaduna har bauchi ba,sai daya isa kanta sanann ta daga idonta ta kalleshi,saita miqe cikinmu mutuwar jiki tana sauko da qafafunta qasa hadi da gyara rufin veil dinta tana cewa "Sorry uncle,yanzu nakeson fitowa" "Me ya sameki?" Ya tambayeta kansa tsaye yana tsare sosai da idanu,qas tayi da kanta,batason gaya masa amai tayi kuma jiri take ji,batason hankalinsa ya tashi "Me yake faruwa dake ne?,ki gayamin gaskiya,karki yadda kicemin ba komai,jiya da daddare na ganki,tashinki nawa kina shiga toilet,na tambayeki kuma kikacemin lafiya qalau" yadda yayi tambayar cikun seriousness sai ya koma mata ASP abbas sosai,miskilin nan mai tsare gida da baiwa masu laifi tsananin tsoro,dole ta buda baki a hankali tace "Amai nayi,sai jiri,sai kuma fitsari da nakeji,idan naje yi kuma sai naga dan kadan,marata tayi kamar an saka dutse" shuru yayi yana kallon fuskarta,wani abu ya darsu a ransa,amma sai wata zuciyar ta kawar,don ba haka ya saba gani ba,ya miqa hannnunsa a hankali ya taba wuyanta ya janye hannun jin babu zazzabi "Subhanallah,amma shine kike ta cewa ba komai baby?" Kai ta langabe batace komai ba,sai qishirwa dake damunta,kamar ya gane me take nufi,ya isa fridge ya ciro mata ruwa mai madaidaicin sanyi ya bude ya miqa mata,tana tsaka da sha ya nema gefanta ya zauna yana murza agogon hannunsa "Banajin tafiyar nan zata yiwu......" "......don Allah uncle" tayi saurin katsar numfashinsa,tunda taji zasuje ayi mata vaccination na tafiyarsu wadda duka duka saura kwanaki biyar ta matsu suje din,ido ya lumshe yana dariya "Bance wai an fasa ba,nima inason zuwa naga hajiyata,bazata yiwu ya mota ba,bari na duba mana rocket ko zamu samu koda evening flight ne" ido ta rufe tana dariya,kunya kuma tana kamata na yadda tayi saurin yanke masa hanzari "Kayi haquri uncle"daga kansa yayi daga danna wayar ya kalleta yana murmushi,bai taba zaton bada haquri abu bane mai sauqi wajen diya mace ga mijinta ba sai daya zauna da widad,kalmar haquri kalma ce mai matuqar tsada da wahalar furtawa a wajen hafsat,tsahon shekaru bakwai,adadin lokuttan da ta taba buda baki ta bashi haquri tsaf zai iya qidayesu da yatsun hannunsa. Kafin su fita daga gidan zuwa airport ta qarfafa jikinta,duk don wai ya sake yadda ba wani ciwo take ba,ya kuma janye maganarsa na suna sauka yau din gobe zai kaita a dubata. Sau uku tana kiransa wayarsa a kashe,ta qagu su iso tayi ido hudu da widad din kamar yadda ummanta tace ta fara tsaiwa ta tabbatar da gaske da cikin?,ta duba idan taga wani canji tattare da ita,idan akwai alamunsa to zasu bincika su dauki matakin da duk hafsat din taso. Tana parlor tana shayar da baby yusra,su nawwara sunata sabgarsu cikin falon,sassan dai kamar ko yaushe sauqi sai wajen Allah,duk da ta dauko diyar anty ummee ta tayata zama har zuwa sanda zatayi arba'in,to amma itama yarinyar aikij ya mata yawa,abinda taga zata iya shi takeyi. Ko kusa ko alama bataji alamun shigowarsu ba,don mota ya dauko daga airport,ba kamar yadda ya saba ba,idan flight zai biyo yana kiran umar yazo ya dauka motarsa dake nan ya daukoshi ya kawoshi gida. Yusra ta cire daga shayarwar da takeyi,idanunta a kansa sanda yaran suketa rige rigen isa wajenshi. Mummunan kishi ya kama zuciyarta,duk sanda zaizo mata weekend sai taga ya canza,sai taga ya qara fresh ya qara murmurewa fatarsa tayi wani lumaui,komai nasa fes kamar wanda akewa wankan inji. Qarasowa yayi ya duqa yana shirin karbar yusra,dai dai sanda take masa sannu da zuwa,ya amsa yana dan dauke numfashinsa hadi da daukan yarinyar yana kallonta,tausayinta yana cika zuciyarsa,ba alamun qamshi jikinta bare na mahaifiyarta,yadan ja kumatunta yana mata wasa duk da ba gane komai takeyi ba,yayin da hankalin hafsat ke kansa,tanason jin tare suka zo?. Amsarta ta fito kuwa sanda mimi ke tambayarsa ina anty widad?,yauma batazo ba?. Murmushi ya sake,qauna ce sosai da shaquwa me yawa tsakaninsu da widad din,tamkar ma itace ga haifeta ba hafsat din ba "Tazo,muje ku gaisa" sai ya sanyasu a gaba suka fice,suka bar hafsat da lissafin yadda zata shiga ta ganta din,don yarinyar ya canza hali,wani irin canji da tafi zaton akwai masu zugata na gasken gaske daga gefe,tasan tsaf daga halinta ba zasu hadu ba sai ranar da zata koma Kaduna. Ya sameta harta cire kayan jikinta,ta saka wata black rmless gown A shape,tabi lafiyayyar farar fatarta ta.kwanta,ya bita da kallo tsigar jikinsa na zubawa,yana jin wani abu mara dadi na masa yawo a rai,yasan yau da gobe duka zaiyi missing dinta,saidai yasan zasu hade a kano,kuma tabbas zaya fanshe kafin su tashi. Bakinta har kunne ta karba yusra tana mata wasa,ita da mimi da nawwara duka sun zagaye yarinyar,tana mata waqa suna mata amshi,sai ya koma gefe ya harde hannayensa yana kallonsu murmushi yana qwace masa,yana hasashen yaranta kamar haka. Daga kai tayi suka hada ido,sai ya kashe mata ido daya yana mata murmushi,ta maida masa martani,Allah ya zuba mata son yara,baisan wanne irin son yara gareta ba,abinda ko uwarsu data haifesu bata damu da yi musu ba amma ita saita bata lokaci tana wasa dasu hadi da kula dasu. Anan yabar mata duka yaran ya wuce sashensa, pampers din yusran da widad din taga ya cika da kashi ta cire mata cikin jin tausayin yarinyar "Tun dazu da take kuka na cewabmommy kashi tayi sai tace ba yanzu zata cire mata ba" duban mimi widad tayi cikin mamaki,itadai ta sani,yayyenta da matan gidansu duk sanda yaro yayi bayan gida cire masa shi sukeyi,takanji sunce yana cin jikin yaro sai wajen yayi ja ya zama ciwo. Wanka tayi mata da ruwa mai dumi sosai,ta shafeta da farar powder ta goyata ta fara gyaran sashennata,tana aikin yarannna biye da ita,yau daya nishadinsu ya canza,sashen ba aiki sosai don ba datti bane sai qura,nan da nan ta gama ta cikashi da wannan qamshin da ya zamewa gurin jiki. Ko kafin ta gama ma yarinyar tayi barci,saita kwantar da ita tayo wankan itama ta sauya kaya ta zura hijab ta tayar da sallah. Tana idarwa hafsat tana sallama,ta shigo idanunta akan widad din kamar zata cinyeta,bata lura ba don zuciyar a wanke take,ta gaidata ba yabo ba fallasa,ta amsa tana sake qare mata kallo. Tabbas tayi qiba,ta kuma yi fari sosai fiye da farinta nada,amma kuma sanda ta miqe zata dauko mata yusra dake bacci bataga tudun komai a tare da ita ba,wannan shi ya saka mata shakka a ranta,ta debi yaran suka baro sashen tana lalubar number ummanta. Bayani tayi mata na canjin data gani din daga wajenta,sannan ta dora mata da "ta danyi watanni umma da wannan canjin,idan ciki ne ya kamata zuwa yanzu ya fito,amma banga alamar komai tare da ita ba" shuru ta danyi tana nazari,ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Ba'a nan take ba hafsatu wai an dannewa bodari kai,zanyi magana dashi,kome meye yake akwai su basa rasa ganinsa". Yana zaune daga bakin gadonsa,hannunsa dauke da tab,yana bibiyar statement na wasu masu laifi dake tsare a hannunsu,hafsat na daga gefe tana lallaba yusra tayi bacci fuskarta aa hade ranta a bace,tunda abbas din ya gaya mata kafin ta iso gadon tayi wanka take kumbure kumbure harta gama ta maida kayan jikinta ta dawo gadon,yayi haka na bawai don yana da bauqatarta ba,kawai ya fuskanci idan ba wanna titsiyen ya fara yi mata ba haka zata ci gaba da tafiya,sau daya ya kalleta bai sake dubanta ba,baisan me yasa har abada take sha'awa shigo masa bedroom da kayan data wuni dasu cikin gida ba,baisan sau nawa zai kwatanta mata bayason hakan ba,a yanzun da yake ganin sauyi daga wajen widad,sai abun ya daina bata ransa,tunda at least yana samun sassauci idan ita din taqiyi masa yadda yakeso,sai mamaki kawai da take bashi,sau tari tafi ganewa ta kwana da tufafinta,atamfa ko shaddar da tasha kwaramniyar yini guda da ita. Dakin shuru kamar ba kowa har ya gama aikinsa,koda ba aikin yake ba haka zaman yake dama,ita bata iya hira da miji ba,shi kuma dama tun asali miskili ne,yayin da take kallon miskilancinsa a matsayin zallar wulaqanci ne kawai (bata iya tsaiwa ta karanci ya yake). Tab din ya ajjiye a bedside drawer yana jan duvet dinsa zuwa qugunsa yana kallonta "Kiyi qoqari gobe da sassafe ki rubuta duk abinda kuke da buqata na kamar wata biyu haka,idan Allah ya kaimu ranar alhamis zamu wuce hajji ni da widad". Kamar wadda wuta taja ta kalleshi da sauri "Kai da wa?" Ta sake tambayarsa ba tare data bi takan sauran bayanansa na baya ba,sunan daya fada sai taji kunnenta kamar baiji mata dai dai ba "Widad" ya sake fada yana kallonta hankalinsa kwance idonsa yana dan lumshewa saboda baccin daya fara ji. Cikin zafin nama ta miqe ta zauna sosai, kaman zata bige yarinyar saboda yadda ta tashin da sauri "Kasan me kake cewa abbas?,da widad zaka tafi hajji?" Dubanta yayi "Me na fada da yake alamta ba cikin hayyacina nake ba?" Yadda yayi maganar cikin bagararwa kamar ba wani mummunan abu ya aikata mata ba,ta tsareshi da ido,wani yayyafin zafi yana sauka daga zuciyarta yana ratsa kowanne sashe na jikinta,tafasa sosai zuciyarta ta dinga yi,ta rasa wacce kalma ce ta dace dashi,saita kuka kawai.ya balle mata,ta miqe tana sauka daga kan gadon cikin hargagi masifa da daga murya ta fara sake masa maganganu marasa dadi,ya rufe ido yana jinta har zuwa sanda tace "Kuma duk munafukan da suke sake shirya wannan abun Allah ya tsine musu albarka idan basu fasa ba,ni dasu shege ka fasa" Wata gigiyacciyar tsawa ya daka mata,yana dubanta da idanunsa da suka fito waje "Shirmenki ya isheni haka,fita ki bani waje shashasha mara hankali,a gabana zaki tsaya kina furta tsinuwa munafukai da sauran shirmenki!,zaki fita ko sai na baki mamaki?" Hannu tasa tana son dauke yusra daga kan gadon,tsananin bacin rai yasa ya janye yarinyar gefe,saita koma ta tsaya tana cewa "Mamaki kuma na nawa?,aika gama bani mamaki,wallahi tallahi inda nasan haka kake da bazan taba aurenka ba,amma kaje na barka da Allah" ta juya da gudu tana kuka da qaqqarfan sauti ta fice a dakin. Hannunsa gaba daya qaiqayi yake,tabbas inda wani ne a waje yayi masa hakan yau sai ya gane shayi ruwa ne,bayason shaidan ya dinga tunzarashi ta sanadinta ya zama madoki,sai ya dinga ambatar Hasbunallahu wani'imal wakil. *********Karfe goma na safiya ta gama shiryawa,tun jiya cikin zumudi ta kwana,tayi zaune a parlor tana jiransa. Da sallama ya shigo falon,muryarsa tayi laushi sosai saboda baccin da bai samu ba isashe daren jiya,ya zama wani so cool yayi kyau cikin shigar qananun kayan da ba kasafai ya fiya sanyasu ba,yau din yayi amfani da sun glasses wanda zai hanaka gane ainihin qwayar idanunsa,sai ya qara masa wani mugu mugun kyau,har widad ta kasa dauke dubanta daga kansa. Duk da yadda ya sakaye qwayar idanunsa amma hakan bai hanata ganin canzawar mood dinsa ba "Oga zumudi..... let's go,banaso rana tayi mana sosai,inason na dawo gida na huta"ya fada yana duba agogon hannunsa. Tare suka jero zuwa harabar gidan yana riqe ds hand bag dinta tana gyara rolling na mayafinta tana masa shagwabar don Allah idan anzo yin allurar ya tsaya a wajen. Murmushi ya sake,ko yaushe tabararta na nasarar korar bacin rai ko damuwarsa,wannan ya sanya koda daga office wani abu ya bata ransa,tattara komai yake ya dawo gida,yana da yaqinin zai samu magani sa sassauci,koda batasan me yake damunsa din ba,koda batayi komai da nufin korar bacin ransa ba. Da kansa ya bude mata seat din motar ta shiga,ya tsugunna ya tattare mata rigarta data fito sannan ya miqa mata hand bag dinta. Hadawa tayi da hannunsa ta riqe tana kallon qwayar idanunsa "Me?" Ya tambayeta ganin yadda ta bata fuska "Smile mana uncle,kayi kyau yau,amma kaqi kayimin dariya.....haba mana uncle" ya qarasa fada a shagwabe. Don dole bai shirya ba siririn murmushi ya kubce masa,ya duqa a tausashe yayi kissing goshinta sannan ya zagaya ya tayar da motar. Suman zaune hafsat dake kallonsu ta dakin solar dinsu dake daura da wajen tayi,taji jiri kamar yana dibanta,har sai data samu waje ta zauna ta wucin gadi,kafin kuma kuma ya qwace mata,ta jima zaune a wajen tana kukan,har sai dataji shigowar sale sannan ta miqe tana barin wajen don kada ya sameta a haka raini ya shiga tsakani,saidai tana jin zuciyarta ta tsike gaba daya,zuwa yanzun komai ta fanjama fanjam,don haka wayarta kawai ta dauka ta fara neman number ummanta ba tare data damu da kukan da yusra ke tsalawa ba, wadda ta tashi daga bacci tun dazun taji ba'a Kula da ita ba. Idanunta fal tsoro,ta waiwaya tana dubansa sanda zata shiga dakin da ake bada rigakafin tana kallonsa "Please uncle,don Allah ka rakani" "Muje" ya fada yana maida wayarsa aljihun wandonsa suka shiga dakin a tare. Yadda taga suna gaisawa da likitar ya tabbatar mata akwai sabo tsakaninsu,tadan kalleshi,abbas din badai miskilanci ba,ya sansu amma ya maze mata,suka hada ido ta masa sing na zan rama,ya dage mata girarsa daya kawai. Fitsarinta suka fara buqata,tayi ta kawo mata aka bada gwaji. Gyara zaman glass din fuskarta likitar tayi sannan ta dago kai tana duban abbas din "Sir,bakasan madam nada juna biyu bane?" Sosai ya kalli likitan,sai ya zare gilashin idanunsa "Juna biyu?,Kina nufin,she's pregnant?" "Yes sir.....alamu ma sun nuna kamar yafi wata biyu" "Ya salam ya Allah"ya fada zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin farinciki,kamar wanda aka yiwa albishir da samun haihuwa karon farko bayan wasu shekaru daya diba yana neman haihuwar ba tare daya samu ba,ya bude idanun nasa fuskarsa na fidda wani irin murmushi yana sauke dubansa ga widad. *H A F S A T* Kamar zata zauce sanda taketa kiran ummanta ba tare data daga ba,muryar umman kawai takeson ji ta isar mata da saqon abubuwan da takeso a gabatar mata akan widad din,tana jin idan bata d'ai d'aita rayuwar yarinyar,ta gigita mata rayuwa ba tabbas mata ta rako duniya,indai bata dauki mataki mafi muni a kanta ba bata cika hafsatu ba,yarinyar tayi mata abubuwa masu.muni dake da yawan gaske,ba zata yaba qyaleta ba itama,ta rabata da abu mafi soyuwa a wajenta,halittar da duk duniya ba wadda take qauna sama da ita ABBAS dinta. Sai data yi mata kira biyar a jere,ana shidan ta dauka,kafin hafsat din tace komai ta rigata "Yauwa,nima ke naketa nema ai,ina hanyar dawowa daga gun aiki ne......,akwai gagarumar matsala hafsatu,akwai matsala" kalmomin umman nata da kuma tashin hankalin dake cikin nata kwanyar suka hadu suka kusa fasa mata kwanya,saita sulale ta zauna sosai a wajen tana jiran jin gagarumar matsalar dake tunkarosu din. *A L H A M D U L I L L A H* *_Masu karatu..... bakuji komai ba,baku karanta komai ba,kawai abinda zance daku shine......kuyi jumirin bibiyata,muje zuwa bayan hutun azumi,in sha Allah ina tafe da kashi na biyu na labarin A RUBUCE TAKE k'addarata,nima ba haka naso ba,amma yanayin yadda labarin ya dauko tunda farko,bazai taba qayatarwa ya bada ma'ana ba sai an cimma gacinsa,zanyi qoqari da ikon Alalh bayan sallar pages din sunfi wadan nan da muka gama tsaho in sha Alllah,fata na Allah ya bamu aron rai da lpy_* ina muku fatan ALKHAIRI AREWABOOKS FOLLOWERS dina,wadanda baku gajiya da bibiyata, alkhairin Allah ya kaimuku a duk inda kuke,ayi ibada da bukukuwan sallah lafiya,na barku lafiya *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_* *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *A RUBUCE TAKE* (K'addarata) *Book 02* Page 01 Cikin mugun mutuwar jiki kasala da kuma fargaba ta hada kalmomin "Wacce irin matsala kuma umma?,na shiga uku" "Malam baiga komai akan yarinyar ba,komai ya rufe masa,bai hangi ciki ba,kamar yadda babu tabbacin babu shi". Goshinta hafsat ta dafe,tana jin yadda zuciyarta ke tafasa,a zahiri tayi mugun tsanar yarinyar,ta zame mata qarfen qafa sosai,tanason kuma ta zama barazana ga rayuwarta,cikin tsananin fusata tace "Umma,yayi mata koma meye,duk abinda ya dace da ita da zai d'ai d'aita rayuwarta ayishi,banason ganinta kwata kwata cikin gidan nan,yanzu haka fa abban mimi ya biya mata hajji,aikin hajji zasu tafi" ta qarashe maganar tana barkewa da kuka,don abun yayi mata ciwo ba kadan ba. Salati umman tata ta sake kamar tana gaban hafsat din "Kina raye kina kallo?,lallai sai munyi da gaske,sai mun tashi tsaye akan yarinyar nan" *A B B A S* "Ya salam" ya fada zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin farinciki, kamar wanda aka yiwa albishir da samun haihuwa karon farko bayan wasu shekaru daya diba yana neman haihuwar ba tare da samu ba,ya bude idanun nasa fuskarsa na fidda wani irin murmushi yana sauke dubansa ga widad. Ido suka hada shi da ita,ta narke fuska sosai,dab take da sakin kuka,suna hada idon kuma sai rauninta ya bayyana muraran,yasan tabbas yau akwai daru,amma koma meye a shirye yake daya shanyeshi,ciki a jikinta?,cikin da yasha yi mata wayo yana gaya mata ba tarayyarsu ce zata saka tayi ciki ba,shan ruwa a qoshi ne?,yasan lallai zai sha tuhuma. Hannu ya miqa mata alamun ta taho har yanzu murmushi kwance bisa fuskarsa,amma sai ta kauda kai hawaye na ziraro mata,yasan za'a rina,yau saita Allahu,ya dinga danne dariyarsa sannan ya.miqe tsam ya isa gabanta,ya tsaya daga gefanta yana riqe da hannunta yana murzawa a hankali cikin nasa,idanunsa akan na dr "Yanzu ya za'a yi?,ina fatan bazai bada matsala ba wajen tafiya" "Bana jin gaskiya,zanyi qoqari ayi mata komai ku wuce tare,tunda bai nuna ba" ta fada ita kanta tana mamakin watannin cikin,da kuma yadda ya boye kansa da kyau,iya ganinka ba zaka hangeshi jikinta ba. Komai da akeyi kawai tana binsa da ido ne, hankalinta gaba daya bai jikinta tunda akayi zancan ciki,tsoro da fargaba gaba daya sun hadu sun lullubeta,har suka gama komai yana riqe da hannunta,ya bude mata gaban mota ta shiga ya maida murfin ya rufe ya zagaya mazauninsa shima. Ai yana shiga tana fashe masa da kuka,kamar wadda ke jira,ya dakata daga kunna motar ya waiwayo yana dubanta "Ya salam ya Allah.....menene kuma?,ko wani abun na miki ciwo?" "Wallahi idan abba yaji ka yimin ciki sai ya kashemu ni da kai" duk yadda yaso ya riqe dariyarsa amma wannan karon ya gaza,dariya ta kubce masa,har sai da yasa zara zaran yatsuntsa ya toshe bakinsa kada cibi ya zama qari,sai yaushe zata gama girma ne?,ashe har yau da sauran quruciyar nan tana nan?,ta yaya zai bullo mata,sai kawai ya juya fuskarsa zuwa kalar alhini shima yana dubanta "Innalillahi......yanzu ya kike ganin za'a yi?" Da farko dariyarsa ta qular da ita,amma yanzun maganar da yayi saita wanke wancan "Nima ban sani bafa....duk kaine ka jawo,saida nace banaso,kace wai idan nasha ruwa ne zaizo" ta fada yana harararsa,saiya narke fuska kalar tausayi ya langabar da kai "To ai nima na zata hakanne,kuma ma kinsan me?" Kaita girgiza tana sharar qwalla,sai ya juyo yana fuskantarta sosai "Sanda kika gudu kano?" Saita gyada kai tana dubansa "Abba da kansa ya kirani yace nayi wannan abun fa da bakiso din" dukka idanunta ta fidda waje kamar zasu fado tana kallonsa a tsorace,ya jijjiga mata kai "Da gaske nake" ya sake fada yana danne dariyarsa,bai ankara ba ya takai masa duka tana sake fashewa da wani kukan a sakalce "Allah abbana ba dan iska bane da zaice maka haka" sosai yau din take sashi dariya,ya kare dukan da daya hannun yana dariya tare da fadin "Allah.....Allah kinji nace Allah" ta sanshi farin sani,kaifi daya ne,baya qarya,yana fadin hakan sai kunya ta kamata,ta kifa kanta a cinya tana juya yadda abban nata zaice haka,yanzu.kowa.kenan yasan abinda suke aikatawa?,tana jinsa yanata magana amma bata dago ba bare ta amsa,yana dariya qasa qasa ya tashi motar sukabar asibitin,ransa fes,zuciyarsa qal,wani farinciki daya jima rabon da yaji irinsa ya cika masa zuciya,har hakan yana bayyana kansa saman fuskarsa. Saida sukayi nisa a tafiyar yace "Kona ajjiyeki gidan hajiya?" Ya fadi hakanne saboda yadda yaga sam.batason zaman gidan nasu,saita girgiza kai da sauri "Aah,nidai ka kaini gida" murmushi ya subuce masa,ya gane mai take gudu,kada hajiya ta gano tana da ciki,daga haka yabar zancan ya dauke kan motar suka nufi gida. Sanda ya tsaida motar da kansa ya dauki hand bag dinta yana riqe da ita zuwa ciki,ta langabe kai tana kallonsa "Ka bani,zan iya dauka" kai ya girgiza idanunsa cikin nata,yana jin wata qaunarta tana fusgarsa "Ban yarda ba baby,dama naji a jikina,wannan rashin lafiyan akwai dalili,muje kawai,ko na daukeki?" Ya fadi shima yana langabar dakai,kunya ya bata,ta kauda kanta gefe tana gulmarsa cikin ranta,wai shi kam bayajin kunya ne ma wai?,kamar ba ciki yayi mata ba?. Kamar yasan maganar da takeyi ya saki murmushi kadan,ya kama hannunta ya matsa kadan yana cewa "Muje baby". Sanda suke shiga din akan idanun hafsat dake tsaye bakin window,tunda suka fita ta kasa zama,zuciyara nata qiyasta mata gurare daban daban da zasu iya zuwa,tana goye da shukra dake ta faman rigima,ji take kaman ta yago yarinya ta ajjiyeta,qunqunin yarinyar har tsakiyar kwanyarta,idanunta suka sauka kan handbag din widad da hannayensu dake sarqafe waje guda. Wani matsanancin qunci zuciyarta ta shiga,duk yadda taso daurewa amma ta kasa,ta saki ashar,kasheta mutanen nan sukeson yi?,bayan abinda abbas din ya aikata mata shine zasuci gaba da sabgarsu kamar ma ba'a yi mata komai cikin gidan ba?,ba zata iya dauka ba,dole kowa yasan an tabota,sai kawai ta kunce yarinyar ta aza saman kujera ta nufi qofa da wani irin mugun sauri. Idanunsa ya lumshe kadan,yana tsaye saman kanta yana mata wani duba dake cike da shauqinta,ko yaya ta motsa sai taja hankalinsa "Zan dan fita,amma bazan jima ba zan dawo,me kike buqata?" Ya qarashe fada yana ritsata da idanunsa masu matuqar kwarjini da jan hankali,sai tadan rufe idanunta kadan ta girgiza kai "Babu komai" "Really?" Ya tambayeta yana dubanta,kai ta sake gyada masa "Okay.....zan tafi" ya sake maimaitawa,saita sake lumshe idonta,tasna me.yakeso,amma jikinta a mace yake murus,ta gyara zamanta sosai ta nutse cikin kujerar sannan tace "A dawo lafiya" "Au 'yar hakace yau?" Murmushi tayi kawai tana boye fuskarta,saiya saki wani murmushin,ya duqa kadan a tausashe yayi kissing goshinta sannan yace "Take care of yourself" kai ta jinjina,sai daya juya sannan ta bishi da kallo,zuciyarta na gaya mata wai da gaske ba abun kunya sukayi ba,ta dora hannunta saman cikinta a hankali tana shafawa cike da mamaki da kuma tsoron cewa wai ciki ne a jikinta. Dai dai sanda muryar hafsat ta ratso har cikin falon nata da wani irin amo,sai ta bude idonta a hankali tana saurarenta sanda take magana cikin rawar murya "Wallahi bazan yafe wannan zaluncin ba,sai Allah yayi min sakayya" wani mugun tsaki widad din taja tana tabe baki gami da gyara kwanciyarta cikin kujerar,ita gaba daya mutuncin matar ya gama zubewa a idanunta,tunda take bata taba ganin yadda akema babba rashin kunya ba kamar yadda itadin taga tana yiwa abbansu mimin,ko babu komai aiya girmeta,kuma ko ummu da take tsohuwa ai tana ganin yadda take girmama alhaji,har tabar gidansu bata taba gani ta karba abu daga hannunsa daga tsaye ba,ko ya fada tace a'ah, miqewa tayi cak tana daukar jakarta ta wuce bedroom dinta,haka kawai taji batason jin wata hayaniya kusa da ita. Hannu daya abbas ya sanya cikin zallar bacin rai ya fincikota,ya riqeta gam yana tafe riqe da ita,bai tsaya ko ina ba sai da yakai sassanta ya watsar mata da hannun cikin falon,da yatsa ya nunata "Wannan ya zamana shine lokaci na qarshe da zaki qara gangancin cewa zaki shiga sashenta ko zaki tabata,daga lokacin da kikayi wannan kuskuren zaki fahimci baki da wayo,tunda na fahimci sauna ce ke shashasha wadda batasan girmanta ba" sosai maganarsa ta doketa kamar saukar mashi saman zuciyarta,ita din abbas yake cewa sauna shashasha? "Kowanne suna kakeso ka kirani dashi,daidanka ne,amma bazan fasa neman haqqina ba" "Idan kika fasa neman haqqinki kin raina Allah" kalmar da tasa ta bishi galala da kallo har ya fice,sai ta sake fashewa da kuka,dole tayi iya yinta taga ta tarwatsa farincikinsu,ba zata zauna ita kadai bacin rai ya hallakata ba. Yana tafe zuciyarsa cike da bacin rai,mahaifin hafsat shi daya yake tunawa,mutumin kirki da kowa ya yaba halayyarsa kafin barinsa duniya,yana sonsa yana girmamashi,har yau yana tuna haquri na qarshe daya bashi a kanta kafin barinsa duniya da 'yan awanni,yaja wani dogon tsaki,xuciyarsa na ayyana masa hukunci kala daban daban da zai iya dauka a kanta. A hankali kuma yaji yana sauka musamman daya tuna kyautar da Allah yayi masa a yau daga wajen halitta mafi soyuwa cikin rayuwarsa,sai yaji dukkan haukan hafsat din wani abune mara muhimmanci da zai iya tattarasu ya watsa kwandon shara,idan ta gaji ta sauke kamar yadda ta saba. *******Cikin kwanakin da sukayi cikin gidan kafin tashinsu saudiyya dan qaramin yaqi aka dinga gwabzawa tsakanin abbas da hafsat din,kullum cikin kuka qorafi da masifa,dai dai sanda 'yan abun nasa suka motsa(miskilanci),yayi watsin tsiya da ita,tamkar ma ba dashi take ba. Ta fannin widad ma sai tayi kamar batasan me ake ba,dama ita dimma ba baya bace wajen miskilancin,bare a yanzun da take mugun jin xafin mummy hafsat din haka kawai,ta tsani ta ganta tare da uncle din nata,tana dannewa ne tayi kamar bai dameta ba tunda batasan ainihin me yasa takejin hakan ba,uwa uba ko meye zatayi saidai ta jiyota daha sashensa sashenta ko.farfajiyar gidan,bata doso sassanta,wannan yasa bata dameta ba,a kullum tunaninta da zuluminta sanda kowa zaisan tana da ciki,cikin wata irin wauta dake sanya abbas din ya qunshe kansa yayita mata dariya,a fuska kuma ya tayata jimami da alhini kamar gaske. A lokacin hafsat din ji take kamar zata mutu,yaqi kulata sannan widad din da taso rage zafi da ita ya mata shamakin da ko giyar wake tasha ba zata doshi sassanta ba,ta sanshi farin sani,yana da kawaici yana da alkunya,amma duk sanda ka sake ka turashi inda bai kamata ka turashi din ba.....to kuwa abinda zai biyo baya bashi da sauqi. Duk haukar da hafsat din keyi hakan bai canza komai ba,don kuwa kwanakinsu biyar suka wuce kano,kai tsaye kuma sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na mallam aminu kano. Sosai widad din tayi mamakin ganin 'yan gidansu acan suna jiransu,tayi farinciki sosai amma kuma abinda tasan tana tattare dashi ya hanata sakewa,sai qumbiya qumbiya takeyi,duk kuwa da cewa cikin abaya sakakkiya take da hijabin daya tsaya mata iya qugu saqar qasar indonesia,wanda ya sake fitar da zallar kyanta da kuma yadda ta sake cika ta kuma sake yin kyau. Duk wani motsinta yana kan idanun abbas har sukayi sallama da 'yan gidan nasu,suka kuma bi ayarin tawagar mai girma governor din bauchi wadda kusan duka iyalinsa ne da manya manyan qusoshin gomnati da matayensu. A darare take gaidasu saboda rashin sabo,uwa uba kusan duka sun girme mata,sa'annin yayyenta ne aurarru,saidai suna da tsananin kirkin daya gaza boyuwa,kallo daya zakayi musu kuma kasan wayayyun mata ne da suka goge da sanin rayuwa,idan akace wayewa bawai wayewa ta rashin kunya rashin da'a da rashin kamun kai ba,a'ah.......wayewa ta ma'ana da sanin darajar kai da kimar kai wadda ke gauraye da ilimin zamani. Yadda yaga taqi walwala kafin tashinsu sai yaji duk ba dadi,tana tsaye batasan da isowarsa wajen ba "Suma fa duk sunayi..... qila jiya da daddarema duk sai da sukayi kafin mu taho nan" abinda taji an fada kenan a kunnenta,da mugun hanzari fararen idanunta a waje ta waiwaya,duk da tasan duk duniya babu mai gaya mata hakan kanshi tsaye sai uncle din nata.....uncle abbas dinta,shi dinne,tsaye a bayanta dab da ita,hannayensa zube a aljihun wandon wata lafiyayyar suit da tunda ya sanyata ta gaza dauke idanunta daga kansa har suka iso nan,murmushi ne kwance saman fuskarsa yana jifanta da wani kallo da su kadai sukasan ma'anarsa,saita langabe kai a shagwabe tana dubansa gami da yi masa nuni da mutanen dake gabansu kadan tana masa alamar kada suji fa,kafadunsa duka biyu ya daga ya watsa hannayensa in i don't care manner,ya sake matsowa kadan yana yin qasa da muryarsa "Wannan tsoron naki xai sa kowa ya sani" ya furta yana duba agogon hannunsa "Feel free,u are safe dear,okay?" Saita gyada a hankali,ya aika mata da wani murmushi na musamman sannan ya juya,saita sauke ajiyar zuciya ta bishi da kallo. Batakai ga waiwayo ba taji maganar daya daga cikin matan mai suna hajiya sha'awa "Badai har kun fara kewar juna ba?" Kunya sosai ta kamata,saita girgiza kai da sauri,kafin ta amsa mata sauran sun iso,cikin mintuna qalilan ta shige cikinsu ta kuma fara sakewa,saboda yadda suketa qoqarin janta a jiki tare da sakata a hirar su,hirar data dinga jin kamar ta girmeta,saboda hira ce ta manyan mata,amma ta qarfi da yaji haka suke sanyata a ciki. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *A RUBUCE TAKE* (K'addarata) Book 02 Ta hadu da mutane masu karamci,don haka bata wani jima ba ta sake sosai a cikinsu,zamu iya cewa tafiyar ta zame mata wani mabudi na alkhairi tare da sake sanin wacece ita,wanne aiki ne a gabanta?,wanne muhimmanci abbas ke dashi a rayuwarta wanda abaya duka hankalinta bai taba mata hasashen hakan ba,duk kuwa da yadda take jinsa sosai a jikinta zuciyarta da ruhinta. Abun ya fara ne daga yadda suka maidata kamar qanwarsu,koda a aikin hajjin kowa qoqarin tallafarta tare da nuna mata abubuwa yakeyi,musamman daya zamana ita daya ce farkon zuwa wajen,cikij taimakon Allah sukayi hajjinsu lafiya suka gama,sai ya zaman lokacin komawa gida nigeria kadai ya rage musu. A sannan taga kowacce hankalinta ya tattaru kan mijinta da sukazo tare,a lokacin suka lura da yadda ita din bata maida hankalinta sosai akan hakan kamar yadda su sukeyi,hajiya sha'awa ita ta fara fahimtar hakan,wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,tuntuni suka gane quruciyar dake dawainiya da ita,wadda wasu abubuwan take gaza yinsu,babu wadda taji kunyarta acikinsu,dukka suka hadu kamar yadda zasu yiwa qannensu uwa daya uba daya suka fara dorata akan sabon saiti.....sabon karatu da sabon darasi. Bata taba jin kunyar wasu mutane kaf rayuwarta ba irin yadda suka sanyata jin kunya,amma ta dole sukayi mata ta sake ta kuma soma bin karatun nasu. Abinda bata sani ba kusan kowannensu tasan halayyar hafsat ciki da bai,wannan yasa hatta gidan babu wadda tayi masa zuwa uku, lokacin da sukaga widad din a mazaunin kishiyar hafsat qaunarta da tausayin yadda zata iya zama da ita ya shigesu,wannan yasa suka samu qarfin gwiwar dora mata abubuwa masu nauyi da yawa,wadanda sukasan koda bayan rabuwarsu zai zauna a kanta ya kuma bi jikinta. Ranar farko kuma karo na farko da taji itama tanason kasancewa da mijinta kamar kowacce mace,ta dauki waya ta kirashi,a sannan suna tare da sauran abokansu da basu taho da matansu ba,saidai dukka kewarta ya isheshi,bayason ya fiya takura mata ko matsanta mata ne kawai,duba da situation din da take ciki,amma he really needs her,kullum kwanan duniya sake shigewa rayuwarsa takeyi. Cikin karsashi ya daga kiran,saidai muryarta kawai ya kashe masa jiki,ya jingina da kujerar yana saurarenta sanda take magana dashi cikin narke murya "Bakayi kewata ba ko uncle?" Maganar tata tadan tabashi,har sai daya murmusa "Har bansan yadda zan misalta miki ba babyn uncle,kawai dai baison takurawa maman baby dama babyn" har ranta taji dadin amsarshi "Indai hakanne to kazo mu tafi,yau a wajenka zan kwana" mutuwar zaune yayi yana mamaki,widad dinshi ce ke fadar haka da bakinta?,ya rasa amsar da zaya bata har sai data sake cewa "Hello" "Than you baby,gani nan zuwa" abinda ya iya fadi kenan jikinsa yana dan rawa kadan,wanda ba lallai ne kai ka fahimta ba "Ina zuwa" kawai yace musu yana barin wajen. Kiran wayarsa ya shigo wayarta sanda ta fito daga wanka,tana tsaye jikin madubin dakin nasu tana mulke jikinta da wasu oil perfumes da hajiya fanna ta bata sanda zasu fice subar mata dakin,hajiya khairi ke tsokanar hajiya fanna "Allah dai yasa ba kyautar turaren banza kikayi mata ba,wala'alla ki dawo ki sameta nade a gado ma tayi baccinta" "A'ah ai ba za'ayi haka ba,na tabbatar karatunmu yana shiga,nidai ina ganin canji" qas tayi da kanta tana murmushi,dukkaninsu kunyarsu takeji,tunda sun girmeta,tana jinsu suna tsokanarta har suka fice. Wayar ta daga tace masa gata nan fitowa,ta gama shirinta a nutse,ta dauki duk wani abu da takega ya dace da wanda taga suna dauka suma idan zasu fita din,ita kanta tana jin banbanci da canji a tattare da ita,ta kammala komai a nutse ta fito. Ko sau daya baiji ya qosa da jiranta ba har ta iso,kasa magana yayi sanda qamshinta ya gaurayeshi,sai ajiyat zuciya mai nauyi daya sauke kawai,suna shiga dakin ya maida qofar ya rufe da wani irin zafin nama,ko ina na jikinsa yana daukan rawa. Zaucewa ya kusa yi sanda widad din ta miqa masa kanta yadda yakeso,ta kuma hada da bashi gudunmawa,sai kansa gaba daya ya kunce,jikinsa ya dauki rawa tako ina ya fita mata a hayyancinsa. Bawai shi ba,ko ita din a yau ta gane da banbanci,ta fahimci kuma maganganun su hajiya fanna,bayan komai ya kammala wata kunya ta kamata,yayin da shi kuma ya hanata sakat,bakinsa kuma ya kasa yin shuru,ya dinga zuba sumbatu ya kasa tsuke bakinsa,domin kuwa ta shammace shi fiye da kima,ta kuma kaishi wata duniya da tunda hajiya ta kawoshi sararin duniyar nan bai tana zuwa can din ba,ko sanda yake kidansa yayi rawarsa shi kadai yaya ya qare?,bare yanzu data bashi tallafi ta kuma miqa masa kanta kacokam. Wannan canji na widad ya tabashi fiye da kima,ya sake kuma cusa wata irin zazzafar soyayyarta a zuciyarsa,ya sake susucewa,har abun yake bawa widad din mamaki,yadda ya dinga cire kudi yana mata siyayya abun sai ya dinga daure mata kai,wanne irin so uncle din nata yake mata haka?. Ranar da suka fita siyayyar data sake sanya widad sallamawa abbas rayuwarta da jikinta......ta sake yaqini da yadda yake yawan fadin yana sonta,cikin shagon gold ya mallaka mata wata sarqa da farashinta yakai naira dubu dari tara da hamsin. Kanta ya daure sosai,a wauta da quruciya irin tata tace ba zata karba ba,sai bayan taje dakinsu da ita su hajiya sha'awa suka dinga mata dariya "Karki qara cewa ba zaki karba ba,tunda ya siya baifi qarfinsa bane,kuma tukuici ne tabbas yake baki,lallai soyayyar da yake miki tana da girma da fadi,saiki sake kula ki kuma tabbatar duk abinda yakeso kina aikatashi sau da qafa,tabbas gaba saikin mallaki abinda yafi haka muddin zaki sallamawa mijinki tare da tsare duk wani abu da yakeso,ki kuma guji wanda bayaso" ta jima a kwance tana tariyo rayuwarta ta baya,da kuma abubuwa da suka faru a yanzu,ko addu'a ce da ummu da mommynta suka yita jaddada mata ta yiwa kanta mijinta da kuma rayuwar aurenta?,ba shakka akwai tasirin addu'ar data dinga yi tuquru,sai gashi tanata ganin abubuwan da ada bata iyasu ba batama san dasu ba. Ranar da suka qara fita siyayya gefe ta koma kawai tana kallonshi,yadda ya zage yana siyan kayan babies kamar yasan me za'a haifa,har sai data gaji da ganin yadda yake diban kaya kamar baisan ciwon kudinsa ba tayi magana "Uncle" ta fada a narke "Baby" ya amsa bayan yabar dukkan abinda yakeyi ya waiwayo yana duban idanunta farare masu haske sosai,wanda suka dan qara girma kadan "Wai don Allah bakajin kunya?,ciki fa ka yiwa mace" dariyar da bai shiryawa ba ita ta kubce masa,nutsatstsiyar dariya mai wani irin siririn sauti da tasa fararen haqoransa bayyana,sakalci da shirmen quruciya dai a cikin jinin widad qilan yake,sai tayi kaman ta daina sai wataran ta sakankance ta yanko maka wata wautar,kallonta yake kawai yana dariyarsa,yama rasa wacce amsa zai bata. Turo baki gaba tayi ganin yadda yaketa mata dariyar yana kuma kallonta "Kaiko a jikinka,ka yiwa mace ciki kuma kana siyan kayan jarirai,bakajin kunya ma mutane su gane". Takowa yayi gaba kadan ya tsaya a gabanta yana kallonta,ko yaushe qara kyau takeyi tana zama wata balarabiya,ba wanda zai kalleta ya yadda ta iya hausa,hakanan babu wanda zai kalleta ya yarda akwai ciki a jikinta "To ko mutanen duniya zasu fara boye kawunansu ne?" Kai ta daga ta kalleshi don bata gane me yake nufi ba,saiya kashe mata ido daya "Ai kowa ma ta yadda wannan cikin ya samu ta haka yazo,ciki harda ni dake da......." Da sauri ta rufe masa bakinsa bayan ta danyi dage kadan,saita janye hannunta da sauri "Kuma me ya kawo wannan maganar?" "Kece mana" ya amsata yana qunshe dariyarsa "To naji,amma bakasan fa me za'a haifa ba kake diban kaya" "Ko meye kika haifa wuud(qauna/soyayya matsananciya) inaso,idan ana haifar rabin mutum ma kika haifamin zan karba hannu bibbiyu" ido ta zaro tana kama haba "Rabin mutum?,wai?" Yadda tayin ta bashi dariya,sai.ya janyeta cikin hikima sukaci gaba da zaban kayan unisex a tare,ya kuma tura mata option na zabar favourite colors dinta a dabarance,ta zaba din sosai,duk da tanayi tana waiwaye kamar wadda ke aikata wani abu ba dai dai ba. **************Karfe sha biyu da mintuna na dare motarsu ta tsaya qofar gidansu na bauchi,a sanyaye widad din ta maida bayanta jikin kujera tana kallon gidan,wani mugun tsanar gidan na shigarta sosai,tana jin kamae ta balle murfin motar ta fice ta kama hanyarta,inda zai bata zabi....da salin alin zatace masa ya kaita gidan hajiya ko gidan uncle muhsin,to amma koda ta fada din tasan ba lallai yayi hakan,don zaice mata ne dare yayi,ko baya ga haka ma.....iya kusancin da suka samu a yanzu a tsakaninsu,bata tunanin zai bari tayi nesa dashi. Shi ya fara fita daga motar yana cewa "Ina zuwa" saita gyada kai kawai,tana jin yadda qirjinta yake bugawa,tana iya hangensa daga inda suke zaune a motar ita da umar qaninsa daya daukosu,yanata knocking. Tun yana qwanqwasa a hankali har ya koma bubbugawa da dan tsauri,wasa wasa sai gashi sun kwashe mintuna masu tsaho yana bugawa,amma qofar ko gezau,babu alamun za'a bude musu gidan,har umar dake zaune cikin motar ya miqe ya fita ya soma tayashi bugun. Tun ransa bai baci ba har ya soma baci,don ba cikin gida ba......muddin dai ba wani abu bane ya samesu ba a irin bugun da yakeyi yasan har maqota sun jishi,sannan ma ba ita daya bace a gidan,idan ita bata ji ba saboda tayi ciki......shi kuma lawal fa dake kusa kusa?(dan dan uwanshi daya dauko sanda zaiyi tafiya). "Kira number lawal ka hadani dashi" ya fada yana duba agogon hannunsa,umar ya fidda waya ya fara kiransa,amma wayarsa na a kashe,sabanin ta hafsat daketa ringing kuma ba'a daga ba,a handsfree take don haka yaji me computer ta fada, kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai sunji motsi ana tambayar waje,abbas ya tsaya kam yana riqe da qugunsa yana kallon qofar,umar ne ya amsa mata da "Mune" sai aka fara buda qofar gidan a hankali kamar mai ciwon hannu *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *A RUBUCE TAKE* (K'addarata) *Book 02* Page 03 Sakin qofar tayi tayi gaba,abbas din yabi qofar da kallo sannan ya taka zuwa cikin gidan,ya cimmata sanda take juyawa abinta zuwa ciki,daure da zanin atamfa saman wata kodaddiyar rigar baccinta daya jima yana ganinta jikinta,jin takunsa ya sanyata dan dakatawa kadan ta waiwayo,suka hada ido. Duk da dare ne da kuma qarancin haske,amma tana iyabhangen yadda taga yayi wani mugun fresh,qamshinsa ya cika wajen,ya mata kyau,amma data tuna a yanzun tare da wa yake sai taji komai ya gushe mata,kishinta ya motsa sosai,wanda tunda umar yazo ya dauki motar da zummar daukosu tahau kan zafinta,ita tunda suke tare dashi bata taba ganin yayi kyau da gogewa irin hakan ba,kuma ba wannan bane ai zuwansa aikin hajji na farko ba "Me kikeyi mintuna kusan nawa muna tsaye muna bugu?" Ya fada ransa a dan bace "Bacci ne fa ya daukeni" ta fada murya a cunkushe tana bata rai,sai ya janye idanunsa yana dan jan qaramin tsaki "Ta yaya zaki kwanta kinsan muna hanya?, at least dai ai kya tsaya kiga shigowata" ya fada yana qoqarin buda gate din gidan da kansa yana yiwa umar maganar ya shigo da motar ciki dare yana qara yi. Ranta ya sosu,ta tura kayan baki gaba tana jin kamar ta maida masa magana,ason ranta ta shige ciki,amma sai taji tana son tsaiwa taga yarinyar,ta sake tabbatarwa babu cikin da a kullum ta kwanta cikin mafarkinta take ganin kamar tana dashi. Tana tsaye daga gefan har umar ya shigo da motar ya fakata a parking lot na gidan,ya kasheta sannan widad ta buda murfin motar ta fito tana jin ranta da zuciyarta duka babu dadi. Rawa qafafun hafsat suka danyi,ta kadu sosai da yadda taga yarinyar ta sake canzawa,sanye take da wata lafiyayyar abaya baqa sidik mai sulbi, balarabiya sakkk!! Haka ta koma,hasken fatarta sai daukan ido yakeyi,ta sake cika sosai,ta zama cikakkiyar mace,kai bazakace widad din da aka mata aure da qananun shekaru bace,duka cikin watannin da basu wuce biyu da tafiyarsu ba irin wannan gagarumin sauyin na babu zato bare tsammani?. Kasa amsa gaisuwar da take mata tayi,gaba daya a rude take har umar yayi musu sallama ya fice daga gidan bayan abbas ya masa izinin tafiya da motar ya kawo masa ita gobe. Gajiya gami da tsanar data yiwa gidan ya sake kashe mata jiki,ta kallai abbas "Uncle bacci nakeji fa" yadda tayi maganar a mugun shagwabe ya taba ran hafsat sosai,saidai a wajen widad din hakan ba komai bane,don kusan a haka yanzun ta saba magana dashi "Muje sashena,nasan bangarenki akwai qura kam yanzu,dare kuma ya riga yayi bare ki gyara" ya amsa mata a tausashe yana mata wani irin sassanyan kallo da ya riga ya saba yi mata shi,har baisan yana fidda kansa da kansa daga idanunsa ba. Turqashi!.....me abbas din yake nufi?,taje sashensa ta kwana?,aiko sama da qasa zata hadu ba zata bari hakan ta faru ba,wannan ba komai bane ba face zallar rainin hankali,ta gama fadi tashin gyaran sashen saboda shi sannan yace wata ce zata kwana?,uwa uba ma watansa nawa basa tare,hakan yana nufin zai karbe kwananta na yau ya bawa yarinyar?. Taku biyu sukayi tasha gabansu,dubansu takeyi kai tsaye "Ba inda zata ta kwana wallahi,bazan dauki wannan rainin wayon ba" ta fada tana fidda idanunta. Ido yadan qanqance yana dubanta "Me kikeyi ne haka?" "Abinda idonka ya gane maka" kafin abbas din ya sake cewa komai widad ta zame hannunta a hankali ta fara takawa zuwa shiyyar sashenta,shi da hafsat din dukansu suka bita da kallo,sai ya motsa da sauri yabi bayanta,yayin da hafsat ta rakasu da ido qirjinta kamar zai qone saboda zafi da tsananin kishi. A qofar sassanta tana gwada keys din hannunta ya cimmata "Me zakiyi a ciki?" Murmushi ta sake masa a nutse "Zan shiga na kwanta ne uncle dare yana sake yi" ta fada a narke "Amma ai ba'a gyare yake ba,nace muje part dina ki kwanta a can kafin safiya" a nutse ta girgiza masa kai,fuskarta still da murmushi "Zan kwanta a nan din uncle,awa nawa ne gari ya waye?,kada ka damu,kana buqatar hutu,kaje ka huta" gaba daya saita gama kwance masa kai,abinda ya kamata ace hafsta dince tayi ita ta gaza sai 'yar cikinta,wani irin qauna da kimar yarinyar ya sake qaruwa a idanunsa,ya santa gwanar tsoro ce,kawai dai tayi hakanne don ta samar masa da kwanciyar hankali da nutsuwa,ya fuskanci wannan din kusan a dabi'arta yake,batason hayaniya sam,sai ya rasa me zaice mata,ya matsa ya karba keys din ya gwada na qofar ya bude sannan ya tura yayi gaba tana biye dashi. Sosai wajen yayi qura,da kansa ya dinga saka tsintsiya yana kade mata hanya har zuwa bedroom dinta,sai daya tabbatar ta gama komai ta kwanta sannan ya baro sashen. Runtse idanunta tayi zuciyarta na matsanancin bugu da tsoron dake shigarta kamar zuciyarta zata faso qirjinta ta fito,tana ji har cikin Zuciyarta kamar ana tunkudata ta fice,amma can qasan zuciyarta tana kiran sunan Allah kadan kadan,abinda ya kawo sauqin yanayin da takeji din wanda keta azalzalarta kamar ana gaya mata cikin kunnuwanta. Bai samu Hafsat din a wajen ba,sai bai wani damu ba,har yanzu Zuciyarsa tana cike da mamakin halayenta, kullum babu sauyi?, sai sake ta'azzara al'amuranta sukeyi?,da wanann tunanin ya isa sassansa. Ba laifi babu datti hakanan babu qura,yaci gaba da takawa har dakin gadonsa,yana tura kansa,sautin sheshsheqar kukanta yana masa maraba. Dauke kansa yayi kamar bai ganta ba,baqinciki yana cika masa zuciya,baiga me akayi mata ba da zata zauna a daren daya dawo yana buqatar ya huta ta tusashi da koke koke ba,idan ita bai rufeta da fada ba bazata sashi gaba tana masa kuka ba,sai kawai ya fara rage kayan jikinsa ba tare da yabi ta kanta ba,rabin hankalinsa yana ga widad da yadda yaga taqi sakewa,lallai tsoronta ya dawo,irin tsoron daya ninka na baya,sai wani bangare na zuciyarsa ya bashi ko juna biyun da take dashi ne,qaramin murmushi ya kubce masa sanda ya tuna da ajiyarsa dake jikinta,dai dai sanda muryarta ta ratsa kunnensa cikin sautin kuka "Da wannan wulaqancin da kakeyimin gwara kacemin ka gaji da zama dani na tafi gid......." "Hey..... stop it dallah!" Ya katseta da mugun sauri cikin bacin rai yana dubanta,bacin ran data gani a idanunsa sun ninka nata don haka dole tayi shuru tana binsa da kallo "Banason rainin wayo da wulaqanci cikin daren nan,hutu nake da buqata,idan qorafi ya shigo dake ki tashi ki fita ki bani waje,idan kin fita idan kinga dama ki wuce gidan ban riqe miki qafa ba" sosai.maganar ta daga mata hankali sannan ta bata mata rai,ta sake fashewa da kuka ta miqe tana daukan yusra ta fice a dakin,yaja tsaki yabi bayanta ya kulle qofarsa ya dawo ya wuce bandaki,gaba daya ta gama fita a kansa,fushinta ko kukanta ya daina damunsa sam. Wannan abun daya faru a daren ya sake tunxura zuciyarta,ta kasa kuma bacci sai data kira ummanta,cikin daren suka qulla abubuwa masu yawa da suke saka ran zasu aiwatar,ko akan widad ko akan abbas din,duk wanda nasararsu ta fada a kansa. *********Da qyar ta wayi gari da wani irin matsanancin tsoro daya haifar mata da ciwon kai,inda Allah ya taimaketa washegarin saiga su nujood harda hajjaaa sunzo mata,ta samu tadan sake,daga qarshe hajjaa ta tafi tabar mata nujood ta tayata kintsa sashen da sauran gyare gyare,wannan ne ya sanyata tadan warware,saidai komai a darare takeyinsa,koda abune yayi babban faduwa yanzu zata firgita,har nujood ta fahimta ta tambayeta "Hakanan nakejin haka,nima bansan dalili ba" "Saikiyita kiran sunan Allah da addu'a" "Inayi,daqyar nayi bacci jiya" "Zan karbo miki addu'ar yawan firgita a wajen ya sayyadinmu" da haka suka fada wani zancan,tana ci gaba da addu'a cikin ranta duk sanda taji irin hakan,da haka ta dinga samun sassauci cikin ranta. Dawowarsu daga saudiyyan sai komai ya sake canzawa,gaba daya hafsat din ta tattara sanya idanunta da komai ta aza akan abbas da widad wadda bata sakata a lissafinta ba kwata kwata,don abinda yake gabanta shi ya dameta,saidai duk wata tijara da abubuwan da zatayi tana jinta daga farfajiyar gidan,ko idan guri ya hadasu,ko daga kai ta kalleta batayi bare akai ga jallin tanka mata,tunda bata taba tararta gaba da gaba ta kama sunanta ba tun sanda abbas din yaja kunnen hafsat,ita a yanzun kawai burinta abbas yace ta shirya su koma kaduna,gaba daya ta tsani garin wani muguwar tsana,duk ranar da ba girkinta bane da qyar take iya bacci saboda wani irin tsoro da yake shigarta,da qyar take hana kanta fita a wasu dararen,saidai ta zauna bakin qofar falo tayita kuka tana jin fita kawai takeson yi. A WANI DARE karfe sha biyu da rabi na dare,har ya shiga sassansa ya kwanta ya tuna kamar yau din da daddare batasha magungunanta na anti natal ba,ya sauko daga gadon hafsat na gefe tana kwasar baccinta ya fito. Kamar mutum ya dinga hangowa daga nesa,sai ya sauya yanayin tafiyarsa cikin hikima da dabararsu ta jami'an tsaro,bai wani jima ba ya gane widad dince ke nufar qofa,cikin wani irin zafin nama ya cimmata cikin takun da basu gaza biyar ba,saiji tayi caraf an riqota,ta waiwayo suka hada ido,cikin matuqar kaduwa yace mata "Ina zaki da daren nan?" Kamar jira takeyi ta fashe da kuka "Fita nakeson yi,banason gidan nan uncle" mamakinsa ya qaru,to duka me yake kawo haka?,wannan shine karo na biyu daya taba ganinta zata fita din. A tausashe ya kama hannunta yana son maidata ciki,saita kuma saka kuka "Don Allah uncle" shuru yayi ya zuba mata ido,yadan lumshe idanunsa hadi da budesu "Muje ciki magana zamuyi" dole ta sakar masa hannun ya riqeta zuwa ciki. Bakin gado dukansu suka zauna yana dubanta "Me yake faruwa?" "Banason gidan nan" ta amsa masa kanta tsaye tana qwalla "Me yasa?" "Tsoro nakeji" shuru ya danyi,ya ciro wayarsa yana son kiran dr,saidai yaga dare yayi,amma duk da haka yanajin ya zama dole ya kirata din. Bugu daya ta daga ya nema afuwan tashinta,tace batama jima da shigowa daga aiki ba sannan yayi mata tambayar "Kwai matan da ciki yake sakasu jin zaquwa gajiya da tsanar waje" saita fara masa bayani,yana fahimtarta yana kuma nazartar widad dake zaune a gefansa ta cure waje daya,ya karanci bayananta,to amma a abinda yake gani a tattare da widad din kamar nata yanayin ya dan sha banbam da wadda dr take qoqarin masa bayani "Amma ba komai,with time zata daina ne" daga baya sukayi sallama yayi mata godiya,sai ya miqe yana kallon widad "Bari na kawo miki mimi,hakan yayi?" Kai ta gyada masa a hankali sannan ya juya a nutse ya fice,ta bishi da kallo tana sauke ajiyar zuciya,rabon da yarinyar ta kwana a wajenta harta manta,gaba daya uwar ta hanata kwana a wajenta. Yana buda qofar hafsat din na farkawa,ta bishi da kallo ganin ya shigo ne daga waje,ina yaje?,badai satar kwana aka fara yi mata ba?,saita miqe ta zauna tana kallonsa sanda ya duqa zai dauki mimi daga gadonsu dake gefe,don yau din a nan bacci ya daukesu,sai yace ta barsu kawai "Bacci take fa" "Na sani,zata tayata antynta kwana" ya amsa mata ba tare daya kalleta ba,wani abu ya darsu a ranta "Me ya samu antyn nata?,naga yanxun ita daya take kwana bata ko nemanta ko?" "Basai wani abu ya sameta zasu kwana wajenta ba ai,tunda yaranta ne itama" ya amsata yana rufe yarinyar da dan qaramin lallausan bargonsu,wanda zamansa a dakin ne kawai yasa bargon ya tsira da mutuncinsa ya kuma dade da kyansa. Bai sake ce mata komai ya juya ya fice,sai ta bishi da kallo qaramar dariya tana qwace mata,ashe har yanzu da sauran abun nan bai gama sanewa ba,tanason wannan aikin tabbas!, jaddada shi takeson ayi kafin a wuce zuwa matakin gaba,bata qaunar hada inuwa daya da yarinyar kwata kwata. Sai da kwanciyar tace tayi mata sannan ya tashi yana kallonta "Ki shirya kayanki jibi zamu koma" wannan shine albishir din da yafi faranta mata rai,duk da ason ranta bataqi ma yace gobe zasu tafi ba,amma babu komai,goben ai a wajenta zai kwana,bata da damuwa. *H U G U M A* *Arewabooks: Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 04 Batasan ma tsautsayin da ya sanyata ta yarda da shawarar zama a bauchin ba ta barsu shi da ita a kaduna,sai a yanzu da mamarta ta zauna ta lissafa mata abinda ka iya faruwa acan alhalin ita din tana nan zaune batasan meke gudana ba,ciki kuwa zata iya tara dukiya da abun duniyar da ita da suka kusa haura shekara bakwai bata sameta ba. Sai yanzu ta yarda komai na babba yafi na yaro,ta kuma gasgata dukkan abinda babba ya hango yaro ko yahau bishiyar rimi bazai hangoshi ba,don haka ta hadiye dukka maganganunta taci gaba da zare pampers din data cika ta tumbatsa "Ai basai ka kashe kudinka kayi wata siyayya ka ajjiye a nan ba,nima wannan karon dani za'a tafi" cup din hannunsa ya ajjiye ya miqe a nutse "Wannan tsohuwar magana ce da muka jima da gamata,ki rubuta list ki turamin" ya qarshe maganar yana aje mata kudin cefananta "Allah bazan zauna ba" ta fada kanta tsaye,shi kuma daya fita baima ko nuna yaji ba ya fice abinsa. Yadda yayi matan ya qona mata rai sosai,ta tabbatar akwai gagarumin dauki ba dadi da zai biyo baya kafin ta samu bauqatarta ta biya,sai ta dauki wayarta kawai tayi kiran ummanta ta gaya mata yadda sukayi "Ai gaba da gabanta,baba ma da babanshi,ki kira babarsa ki gaya mata,itace dole zata turasashi kuma yabi" fuska hafsat din ta yatsine "Nifa matar nan ban yarda da ita ba,sonshi take fiye da kowa cikin yaranta,munafuka ce kawai,umma....na gaji da kaishi qara,don Allah don annabi ayi a kammala aikin nan,nafison idan nace eh ta zauna kawai" ajiyar zuciya ta sauke "Hafsatu.....da mijinki da kishiyarki aikinsu dole sai an dinga binsa a hankali,idan kuma ba haka ba yace za'a yi hasara masu yawa" "Ko hasarar mecece can ta matse musu ayita indai buqatata zata biya" "Aah.....ke bari kiji,daga bangarenmu ne hasarar,shi yasa nace abi a sannun,inda daga gurinsu ne ina ruwan wani?,da tuni aikin gama ya gama ai" sun jima akan wayar suna tattaunawa,duka saqa ca a mugun zare da yadda zasu ida mugun nufinsu. Har ta ajjiye wayar ta tuna da yaya baraka,dabarar kiranta takai mata qara a wannan karon ta fado mata,kai tsaye tayi kiran nata,bugu uku ta daga. Suna gama gaisawa ta fashe mata da kuka,sannan ta rattabo mata abinda yake faruwa,bayan ta qawata zancan da qarya da gaskiya,yaaya barakan ba komai ta sani akan lamarin gidan abbas din ba,tunda itace babba a dakinsu itama ba shiga zancan takeyi ba,a yadda hafsat din ta gaya mata maganar sai taji ranta ya baci sosai,saboda rashin adalci zalla data hango,sannan hafsat din tayi sara akan gaba,don bata jima da jin tsegumin da ake na tafiyarsu widad din hajji akabar hafsat a gida ba "Zan sameshi nayi magana dashi,basaima hajiya taji ba,ki kwantar da hankalinki,wannan ma ai rashin adalci ne,ita widad din da gwal aka yita da zaiyita yawo da ita gari gari ke ya barki tsugunne da 'ya'ya?,ya ajjiyeta a tafi dake wannan karon,ko kuma ya hada kanku duka ya tafi daku,shi yaga zai iya" maganar tayi mata dadi,don haka sai tahau shirinta abinta,duk da shirin ya hadu da cikas,kusan kowanne kaya nata suna da naqasu,da qyar take tsintar wanda zata iya dauka a ciki. °°°°°°°°°Yana daga zaune saman carfet tana kai kawon dire masa abincinsa,duk inda ta gifta sai ya bita da ido,yana jin wani abu yana tsarga masa dangane da ita,a yanzun data sallama masa kanta yadda yakeso,sai.yakejin kamar shi kadai yayi sa'ar mace a duniya,komai na matsalolin hafsat a yanzun baya musu kallon da yake musu ada. Boom Short ne a jikinta da wata armless turtle neck shirt wadda ta kama jikinta,dukka kayan black ne,wannan ya qara fitar da haskenta sosai,ga wani kyau me jan hankali,ya kasa dauke idonsa daga kanta,ba wanda zai kalleta yace akwai juna biyu a jikinta,yabi tsaho da kuma qibarta ya boyeshi tsaf. Zuwanta na qarshe ta ajjiye masa strawberry juice data hada masa,zata miqe ya kamo hannunta da kyau ya kuma jawota jikinsa a tausashe yayi mata mazauni saman cinyarsa yana cewa "Na gaji da wannan qwalelen da aketa min tun daxu,ko yaya dai ai kyazo naji duminki ko?,kinsan kuma nayi missing dinki fa" ya fada yana saka hannunsa ya ware gashin kanta,ya cusa fuskarsa cikin wuyanta yana shaqar azababben qamshinta daya sauya daga aihinin wanda ya sani "Ya sub....hanallah.......babyn uncle so kike ki kasheni.....wannan qamshin......" Sai ya kasa qarasawa ya sake cusa kansa sosai a jikinta,sumarta tana yiwa kansa da fuskarsa rumfa, yayin da ita kuma ta saki siririyar dariya tana riqe kansa da kyau saboda saukar hucin numfashinsa. Basu ce komai.ba sukaji an tura qofar falon da mugun qarfi,a firgice weedad ta maida dubanta ga qofar,shi kuma ya zaro kansa daga inda ya boye fuskarsa yana kallon bakin qofar da idanunsa da suka sauya launi. Hafsat ce,baya tayi.kamar zata fadi,tunda take bata taba mummunan gani irin wannan ba, widad ce saman cinyar abbas din?,ko ita ba zata iya tuna when last da tahau cinyarsa kamar haka ba,wani abu me zafi ya taso ya riqe mata qirji,ta fada zuqar numfashi da qyar. Motsawa widad din tayi da nufin zamewa daga kan cinyarsa,sai ya janyota ya gyara mata zama sosai akam cinyar tasa yana zagaye qugunta da hannayensa,yayin da idanuwansa ke kan fuskar hafsat yana kallonta cikin bacin rai,ita kuma widad din take kallo,tana jira taga ta sauka,amma sai taga ko motsi batayi ba,saima shirin jingina da take da jikinsa,saboda yadda ya hanata sauka daga cinyar tasa,kunyar yadda ta gansun kuma tana tabata,duk da haushi da taji na yadda ta shigo musu babu ko sallama "Wajenka nazo" ta fada murya a tsaye,tana fatan widad ta sanya baki a maganar ko zata samu hanyar da zata dake ta fa huce takaicinta "Fita waje ki jirani" "Yaaya baraka ce tace na kawo maka waya tanata kiranka baka dauka ba" ta fada a kausashe tana jin yadda hawaye keson kunno kai cikin idanunta tana hanasu zuba,wannan cin fuska da rainin da yarinyar tayi mata har ina,tana zaune sosai saman cinyar mijinta kuma tana kallon qwayar idanunta?. "Ki fita nace ki jirani" ido ta zuba masa kamar zuciyarta zata fado,ita yake kora a gaban qaramar yarinya?,saita jinjina kai ta fice fuuu kamar zata tashi sama. Da sauri ya sanya hannu ya sake tarota sosai cikin jikinsa,ya maida gashinta gefen kafada yana sake zura kansa gefen wuyanta "Un..... uncle" ta kirashi murya a rarrabe, fuskarsa kawai ya dago dab da tata yana kallon fararen qwayar idanunta "Kace mummyn mimi ta jiraka a waje fa" "Ba zata jirani ba,tafiya zatayi" "Amm....." "Shshshs......" Ya fada yana dora yatsarsa akan labbansa yana duban qwayar idanunta "Kada kicemin komai,sannan daga yau,duk sanda ta sake shigo miki waje irin haka muna tare kikace zaki matsa ko zaki tashi,zan hukuntaki ne,ai bata nema izininki ba kafin ta shigo miki waje.........ko ban fada miki ba nasan dole ki sani,a nan ne kadai wajen da nake samun nutsuwa da kwanciyar hankali,kawai sai na bari lissafina ya dagulemin?,nayi wasa da damata kamar yadda tayi wasa da tata?,come-on.....forget her, let's continue to enjoy" ya fada yana sake shige mata. Sai daya gama rage zafinsa sannan yace ta dauko masa wayar,ta dauko ta miqa masa cikin girmamawa,ya saki murmushi yana cewa "Thanks" sannan ya buda wayar yana duba me kiran. Yaya baraka dince,sai kawu hassan,kowanne miscall bibbiyu yayi masa,baibi takan yaya baraka ba,tunda har sunanta ya fita a bakin hafsat yasan akwai wata a qasa,bare yana sane da maganarsu ta daxu,sai ya fara da kiran kawu hassan. Cikin girmama juna suka gaisa,sannan ya shigar masa da zancan baraka ta sameshi da batun iyalinsa kan komawa kaduna,ya yiwa kawu hassan din bayanin komai,yayi shuru yana nazari "Duk dadai mun gama magana da hajiyarku,kusan abu daya muke gani,kayi.haquri ta biku kada duniya ta zageka,kuma ita kanta kada ta sake daukar cewa kana hakanne don rashin adalci,don rashin kyautawa bata kyautata ba,amma ko yanzun ma baka da tabbas din zata zauna idan taje din,tunda mai hali baya fasa halinsa,don haka ka zuba mata ido,taje din". Koda suka gama waya da kawun hajiya ya kira,itama kusan abinda tace dashi kenan,dole ya sauko daga dokin naqin da yahau,saidai baice mata zataje ko bazataje din ba,ya barta tana ta raba ido da taraddadin zai yarda ko zaiyi halin nasa na kafiya,saida asubahin ranar da zasu tafi tunda girkinta ne yace ta shirya da wuri zasu wuce. Jikinta na rawa take kintsa abinda zata iya,qarfe goma na safe sale ya gama fidda kayansu duka an zuba a booth din motarsa,dole ya canza motar komawa saboda wadda suka saba zuwa da ita kamar zasu matsu da yawaga yara biyu ga hafsat din ga widad gashi. Ta riga kowa fitowa ita da yaran,ta buda gidan gaba ta shige ta watsa yaran a baya "Kya zauna a cikinsu,dama nan ne yafi dacewa dake" ta fada a ranta,don dama ko sama da qasa zasu hadu batajin zata yarda ta barwa widad din gidan gaban. Batasan ma me yake faruwa ba,ta fito abinta a shirye tsaf cikin wata atamfa dinkin A shape budadde sosai,duk da yadda hafsat din take ganin ta qurewa ado sai data raina kanta,sai dataji ta muzanta,ta zuba mata ido.tana fatan Allah ya kawo wani mummunan sanadin da zai dakushe wannan kyan da kullum kwanan duniya yake mata barazana cikin idanunta. Tun bata qaraso ba taja hankalin abbas dake tsaye jikin motar yana amsa waya ba tare da yakai ga shiga ba,ya bita da kallo tun daga can harta kawo bakin motar,yaran duka suka fito suna mata oyoyo tasa hannu ta rungumesu cikin jikinta,mimi tace "Anty qamshi,qamshi kike,ki sakamin turaren nima" "Yanzu kuwa.babbar qawa" ta fada tana zuge hand bag din dake maqale a hannunta,ta fidda qaramar kwalbae turare mai kyan gaske ta fara fesawa yarinyar "Ranki ya dade.....mu baza'a san mana qamshin ba?" Abbas data gama kashe masa jiki da adonta ya fada yana turo hularsa gaban goshinsa. Zata iya cewa hatta kalar murmushi hajiya fanna sun koya mata,daya daga ciki ta aro ta aike masa dashi tana juya fararen idanunta,saqonta kuwa ya isa,don kasa takawa yayi ya koma a dole ya manne bayansa da motar yana jin qafafunsa sun saki "Idan ba'a fesa maka ba wa za'a fesawa" sai ta tako a hankali ta matsa gabansa ta fara fesa masa turaren daga wuyansa zuwa qirjinsa,sanyinsa da qamshinsa ya ratsa fatarsa,ya saki ajiyar zuciya,sai ya kama hannunta ya riqe cikin nasa yana cewa "Kada fa ki jawo hannun agogo ya koma baya,zan iya kasa tuqin nan f........" Bai qarasa ba uban horn din motar ya karade gidan,a tare suka juya zuwa ga motar,yayin dasu mimi suka tsorata saboda yadda ta danne horn din har baka iya jin abinda wani ke fada. Hafsat ce da komai ya faru a gaban idanunta,abinda suke fada ne kawai kunnuwanta basa iya jiyowa,sabida Glass din side din a rufe yake,ta cika tayi fam kamar zata fashe,ita zasu rainawa hankali su shanya a cikin mota?,zame hannunsa yayi ya tako a nutse ya buda murfin motar yana kallonta "Idan tafiya tafiya,idan zama zama,ya zaku tsaya gaban yara kuna abu iskanci iskanci?" Ta fada tana huci,tana jin kamar ta fita ta kamo widad ta shaqeta. Kamar ransa zai baci sai kuma murmushi ya kubce masa,ashefa ita duk irin wadan nan abubuwan a rayuwar ma'aurata iskanci ne a wajenta,kuma shi har ga Allah ya manta da ita "Yi haquri mommy" yana fadin haka ya maida.murfin ya rufe,bai dai fasa ba,sai daya koma ta fesa.masa turaren sannan suka dawo cikin motar,xuwa sannan tayi nisa wajen juya kalmar.mommy daya jefeta da ita,aiba haka yake gaya mata ba,yanzun kuma daya fada me yake nufi kenan?,babu me amsa mata,haka suka cika motar da karadinsu widad na biye musu tana kume jefo abbas a ciki shima yana shiga sabgartasu,har ta dinga jin kamar sunyi watsi da ita ne kawai,kamar babu ita ne a cikin motar gaba daya, abun da ya isheta saita dakawa mimi tsawa "Banason shegen surutu,ki kama min bakinki a wajen" yarinyar tayi tsuru tsuru,sai ta bawa widad din tausayi,ta lura tana yine saboda ita,taja yarinyar jikinta ta fara mata hira qasa qasa,sai gashi ta ware,abbas da yaji shuru yace "Wai me aka gayawa mamana ne tayi shuru haka?" "Daddy labari ake bani me dadi" mudubin gefansa ya saita yadda zai hangesu da kyau,suka hada ido ya kashe mata ido daya "Retired za'a yimin?,ba haka mukeyi dake bafa" baki tadan murguda masa,abinda ya fusgi hankalinsa kenan,don bai taba gani tayi ba sai yau,har sai da murmushi ya subuce masa ba tare daya shirya ba,yayi mata sign na tuba yakeyi saita dauke kai tadan qara volume kadan na muryarta,motar ta dauki shuru suna biye da ita. Tarihi take basu na daya daga cikin sahabbai,kusan ya zauna sosai a kanta saboda alhaji na yawan yi.mata shi,sosai tarihin yake shigar abbas din yana mamakin yadda ta riqe komai exactly,hafsat da takejin muryar widad din kamar tana watsa mata ruwan zafi taja tsaki karo na kusan goma "Nifa gsky an shiga hakkina" "Da akayi me?" Ya jefa mata tambayar ta sigar ko in kula "Lallai ne kowa sai yaji abinda take fada?" "Ba lallai" ya fada yana zura hannunsa aljihun motar,ya ciro wata mini laptop da earpiece ya xube mata ba tare da yace da ita komai ba,sai tabi kayan da kallo kafin ta maida kansa,saidai tuni yaci gaba da abinda yakeyi kamar ma baiyi komai ba. *H U G U M A* *Arewabooks: Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 05 Kafin sukai kaduna zuciyarta kamar xata fashe,bata samu sauqi ba saida bacci ya daukesu mimi,widad kuma ta sanya earpiece abinta ta kunna data tahau watsapp. Saidai duk da hakan hankalinsa yana kanta,bini bini ya juya ya gani,ta rasa da wacce siga zata masa magana juyawan da yakeyi tana jinta kamar a qahon zuciyarta yake soka mata abu mai tsini,amma yadda taga ya tsare gida tasan bata isa ma tace komai ba,haka ta dinga cinyewa kamar ta zuqo kaduna ta rage nisan tafiyar suyi su isa,saidai wannan abun ba zata barshi ba,dole taci uban yarinyar da kyau. Qarfe biyu da mintuna suna cikin gidan,kowa na gidan na maraba da dawowar abbas din,kasancewarsa mutum me kirki da kyauta,ma'aikatan gidan suka kwashe kayansu zuwa falon gidan. Shi ya buda musu parlor din ya koma don gyara parking,hafsat ce a gaba,tana tafe tan qarewa parlor din kallo,komai na parlor din ba wanda ta sani bane,an canza abubuwa da yawa da wani irin tsari me kyau,komai qal kamar basuyi tafiya sun bar gidan ba,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,tana tuna lokacin data sanya qafa tabar gidan,tana jin duk duniya babu yadda abbas zaiyi da ita. Awancan lokacin tana jin babu matakin da zai iya dauka,babu wata mace da zata iya shiga rayuwarsa,ashe babbar matsala ce zata biyo baya,yanzun gata ita kusan sa'ar diyarta ta fari inda auren wuri tayi zasu goga kishi. Gaba widad tayi abinta,ta buda dakinta ta shige,tunda komai nata yana ciki,lokuttan baya kafin kusanci ya samu tsakaninta da abbas din ta koma dakinsa a nan take kwana,da kallo hafsat din ta bita tana jin kamar ta jawota,ganin yadda ta barta tsaye a falon,wato ta samu dakin zama kenan,taja wani mugun tsaki tana kallon dakin nasa dake kulle,sai ya shigo kenan zai bude mata dakin,ta koma ta zauna saman kujerar tana sauke shukra dake bacci,yaran nata guje guje da murnar zuwa gurin da suka jima basu zo ba. Duka duka part din bedroom biyu ne,a dole abbas din ya budewa hafsat nasa bedroom din suka saka kayansu. Tana daga gefan gado tana bawa yusra yusra mama tana qarewa dakin kallo shima,komai neat,qamshin shegiyar yarinyar ya kama dakin da kyau,da qyar take iya hadiye yawu saboda wani abu daya tokare mata wuya,ta cirr yusra data koma bacci ta kwantar da ita gefe,sai hannunta ya fada saman wani.abu mai taushi,ta janye hannun tana dubawa da sauri. Baby pink rigar baccin widad ce wadda ta barta saman gadon garin sauri ranar da zasu bar kadunan,ta daga rigar tana qare mata kallo,bata da maraba da tsirara,saboda duk inda muhallin tsiraici yake neat ne a wajen da wani silk yard duka jikin rigar,nannade rigar tayi tayi wurgi da ita cikin tsananin bacin rai,ita za'a yiwa iskanci?,sai ta miqe ta fara bincike dakin,tun daga drawer dinsa zuwa toilet. Da qarfi ta buda murfin wardrobe dinsa,idanuwanta ba zasu juri ganin kayansu a cakude waje daya ba,brassiere dinta da qananun kayanshi,kai tsaye ta miqe ta fita a dakin da nufin zuwa ta gaya mata tazo ta kwashe kayan nata. A falo sukayi kacibus dashi yana shigowa riqe da hannun nawwara,ya bita da kallo "Ina zuwa?" Kallonsa tayi qirjinta kamar zai fado saboda radadin da zuciyarta keyi mata "Zuwa zanyi na gaya mata tazo ta kwashe kayanta a dakin" wani nutsatsen kallo ya bita dashi sannan ya gyara tsaiwarsa "Ki barni da kaina zan gaya mata,sannan ma dole ki samu kayanta cikin dakin tunda batasan da dawowarmu tare ba" galala ta bishi da kallo kanta yana daurewa,ita abbas ke cewa ba'asan da zuwanta ba?,to banda ma iskanci da fidda sabon salo,tana cewa ita din sanda tana nan dankwalinta baya bari a dakin,kome ta bari sai ya sanya ta tattarasu ta fiddasu a dakin kafin ya rufe ya wuce aiki,shine yanzu zata samu kayan yarinyar cike a dakinsa,kayan ma na rashin arziqi da rashin kunya?. Bai wani nuna ya lura da yanayin data shiga ba ya miqa mata nawwara "Ki dafa musu wani abun suci kafin ku gama kintsa gidan,yunwa sukeji" bai tsaya jiran amsarta ba ya wuce ciki yana janye da luggage dinsa. (Widad) Tun shigowarsu gidan tare duka taji gidan ya canza mata,batasan me takeji game da biyosu da mummyn mimi tayi ba,amma dai tasan har ranta hakan bai mata wani dadi ba,saidai idan ta tuna matarsa ce itama kamarta sai tayi qoqarin dannar zuciyarta,duk kuwa da cewa tanajin mugun qunci duk sanda taga wani kusanci a tsakaninsu,haka ta dinga qoqarin shanyewa,ta gyara dakinta zuwa toilet dinta tsaf,tanata son fitowa ta gyara sauran sassan gidan amma tana ta jin motsin yaran,batasan ko suna amfani da falon ba,sai dataji shuru sannan ta fito. Tuni falon ya fara watsewa da tarkace,bata saba ganinsa haka ba,duk sai taji wani iri,ta tattare musu shirginsu guri guda ta kintsa falon,tana gamawa hafsat din na fitowa daga kitchen dauke da plate din wata cakurkudaddiyar jallop din taliya yaran na biye da ita. Tsaki taja tana shigowa falon tare da kallon yadda ta gyarashi,itafa batason irin wannan sanaben tsiyan,daga dan tashinsu an wani hau shara?,saita watso dukka kayan qasa tayi abun zama dasu,ta ajjiye musu plate din a qasa suka fara cin taliyar,mimi na cewa "Anty kizo muci" harara hafsat ta maka mata "Tunda ita ta dafa man ba uwar iyayin tsiya" qaramin murmushi widad ta saki,itakam wannan taliyar ko matse bakinta akayi batajin zata iya hadiyarta,ko kadan bata bata sha'awa ba "Na gode mimin daddy" saita juya ta wuce dakinta,zuwa yanzun duk wani girma da mutuncin hafsat babu abinda yayi saura a idanun widad din,ta zare kayan jikinta ta shiga wanka. Yana shigowa daga sallar azahar ya zauna falon yana tambayarta abinda ta dafa,sanda ta zubo ta kawo gabansa sai yaji duk yunwar da yakeji.tayi qaura babu ita a cikinsa,ya kalli abincin da kyau ya girgiza kai ya kawar gefe,bazai iya saka wannan "Ina antynku?" Ya tambayi su mimi "Tana daki" shi kansa yau din gaba daya sai yakejin wani iri,ba da wannan yanayin suka saba dawowa kaduna ba,kewarta duka ta isheshi,a kadunan yake samun kanta fiye dako ina,don tafi sakewa sosai a nan din,sai ya miqe tsam ya nufi dakin nata,yayin da hafsat dake zaune a wajen tunda sukaci abinci bata motsa ba bare tayi haramar gyara kayan da sukazo dashi da kuma dakin ta bishi da kallo. Duk yadda taso ta daure sai ta kasa,ta buda baki cikin qunci "Ina zaka?,girkina ne fa?" A nutsensa ya waiwayo yana kallonta "Wani abun nace miki zanje nayi?,idan girkinki ne ki maida hankali wajen tunanin abinda zaki dafa mana da dare" tasan magana ya gaya mata a fakaice,sai tayi shuru tana sake rakashi da idanu,kamar ta tashi ta tari gabansa,har ya murda handle din ya waiwayo yace mata ta sama masa black tea ta hada masa da wani abun da zaici. Maida qofar yayi ya rufe a hankali ya jingina da jikin qofar yana sauke ajiyar zuciya,gaba daya dakin ya gauraye da qamshin shower gel air freshener spray dinta,ya zuqi iska ya fesar yana kallonta,tana daure da towel tana mulke lallausar fatarta da kyawawan mayukan gyaran jiki da suke qarawa fatarta kyau da glowing. "Ki daina kallona da wadan nan idanun naki don Allah,kada ki sa na kasa qarasowa mana madam" ya fada yana kallon yadda ta tsareshi da ido ta cikin madubi,ba shiri murmushi ya kubce mata,duk yadda kuwa takejin ranta a quntace,amma shi dinma a yanzun kallo daya tayi masa ta karanci kamar akwai 'yar qaramar damuwa a fuskarta. Dab da bayanta ya tsaya,ya dauki cumb yana taje mata kanta a tausashe,yadan ja kadan saboda yana son tsokanarta,fuskarta yakeson gani sosai,sai ta yamutsa fuska "Asshhh" ta furta tana shagwabe masa,ya saki siririn murmushi "Idan ba haka nayi miki ba naga alaman rowar fuskar nan akemin yau" siraran labbanta ta tura gaba "Idan baka gani ba ai zakaga ta mummyn mimi" farko bai gane me take nufi ba sai daga baya, siririyar dariya ta qwace masa,yaja kujerar madubi ya zauna,ya jawota cikin zafin nama zuwa saman cinyarsa ya zaunar da ita,dukkansu wani shock sukaji cikin jikinsu,ya dora hannunsa saman cikinta "Idan naga ta mummyn mimi sai akace naga taki?,sunanku ma aiba daya bane,matsayin taki daban matsayin tata daban" matsayin da yace din sai ya kumbura zuciyarta,ta fara qoqarin zamewa "Tunda itama mai matsayi ce ai duk daya ve da tawan" dariyar da yake riqewa ta qwace masa "La'ila....lallai yarinyar nan,zoki gayamin......kin iya kishi dama wai?,dama tun rannan nake ganin alamu,ashe nayi hasashe dai dai......yaushe kika fara son uncle din naki haka?" Duka hannuwanta ta saka ta zagayesu a qeyarsa tana kallon idanunsa sosai "Ranar da kayimin ciki mana" mutuwar zaune yayi,ya nutsa idanunsa cikin nata yana mata wani irin narkakken kallo,inama zata zauna a haka?,ta yakice sauran kunyar da tayi ragowa tattare da ita?,that's all he needs,yana buqatar kulawa da soyayya kamar ba za'a mutu ba,sai kawai ya sanya dukka hannuwansa ya mata masauki cikin jikinsa ya matseta gam yana sauke numfashi "Bansan lokacin dana fara sonki ba,kishin da nake naki kuma inajin zai iya kasheni......inaso kici gaba da kishina,kiyita kishina kiyita kishina,na miki alqawari wani abu na musamman" Murmushin jin dadin ya kubce mata,wannan satar amsar hajiya fanna ce ta bata ita,ta jima tanason gwadawa amma tanajin nauyi da kunyarsa,sai gashi.....yayi aiki,tana iya jin bugun zuciyarsa ya qaru sosai. Bugun qofar da akeyi shi ya tilastata zare jikinta daga nashi tana kallonsa,wani abu ne da basu saba dashi ba,muddin suna kaduna a irin wannan lokacin ba wani abu dake disturbing dinsu *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 06 Hannu ya miqa mata yana dubanta da idanunsa da sukayi laushi,saita noqe kafada alamun a'ah,ya sauke hannunsa muryarsa adan shaqe yana tambayar "Waye?" "Nice" kakkausar muryar hafsat ta bayyana,ya miqe cikin wata irin kasala hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya isa bakin qofar yasa hannu ya bude mata. Idanu suka zubawa juna shi da ita,ita din tanason karantar cikin wanne yanayi yake,yayin da shi kuma yakeson jin ba'asanin bugun qofar "Tazo ta kwashe kayan nata" sai daya lumshe idanunsa ya lumshe ya budesu lokaci guda sannan ya amsa mata a nutse "Meye damuwarki ne?,badai kinyi complain ba?" Mugun haushi ya cikata,yadda ya bata amsar sam shi bashi da damuwa ma kenan "Eh.....amma dai kasan yau din kwana na ne da zakazo har cikin dakinta ku rufe qofa" sai daya dubi bayansa wato cikin dakin ta gefan idanunsa sannan ya maida dubansa kanta "Stop it hafsat......kisan irin abinda zaki dinga fada,yara kin sani suna jinki" "Eh ai.hakkin......" "Dalla ya isa......bacemin agun" ya fada cikin bacin rai ganin bata da niyyar yin shuru,gasu mimi dake zaune daga falo ta fara calling attention dinsu. Ido ta zuba masa cikin bacin rai,saita jijjiga kanta da qarfi ta juya da sauri tana barin wajen saboda hawayen da suka ciko mata idanu,cikin bacin rai yaja siririn tsaki ya koma da baya cikin dakin,zuwa sannan har widad ta nema doguwar riga ta saka. Wani kyan yaga ta sake masa fiye dana dazu,yasa hannu ya dan shafi cikinta kadan wanda shima har yanzu yake mamaki idan ya tuna tuna akwai d'a a ciki "Ki shiga dakina ki dauke abubuwanki masu muhimmanci,mamansu mimi zata aje kayanta" ido tadan lumshe sannan ta kauda kanta tana jin wani abu ya soki zuciyarta,a taqaice dai an koreta daga dakinsa mummy Hafsat din ta tare kenan "To" ta amsa masa ciki ciki tana dan tura baki gaba,ya fahimceta sarai,qaramin murmushi ya kubce masa,yadda take kishin nan nasa yana nurgeshi sosai,sai ya.miqa hannu ya jawota jikinsa "Bamu rabu ba babyn uncle,ko yaushe ina cikin gidan nan,ranar girkinki kuma zamu kasance tare anan har sai kince kin gaji" da sauri tadan tureshi tana dariya "Nifa ba haka nake nufi ba,kuma ma bance komai ba uncle" dariya ya saki cikin jin dadi,Allah baya hadawa bawansa zafi biyu,idan ya rageka ta wani bangaren saiya sanyaya maka ta wani,sam bata daukar abubuwa da zafi,uzuri guda daya kacal ya isa ya wankeshi a wajenta. Shi ya taka mata har dakin gudun fitina,yana tsaye ta hada kayanta tsaf ta baro dakin,shima duk sai ya dinga jin ba dadi,har ya fara tunanin sauya muhalli wadatacce muddin hafsat din ta dage da zaman kadunan. Kamar jira take widad din ta fita a dakin ta fito daga bandakin data shige sanda taji motsin shigowarsu,gudun kada widad din taga hawayen da takeyi ta rainata, qorafi taso dasa masa kan wanda ta fara dazun amma bai bata fuska ba,hasalima sai ya fice daga gidan abinsa,dole ta tattara dukka wani quncinta ta adanashi waje guda,don ko widad dinma tana cikin dakinta tana sabgarta,bata ganta ba bare ta juye a kanta. Da dare shi ya kira widad din akan tazo suci abinci,hafsat din tanata wani cika tana batsewa kamar wadda tayi wani abun kirki,shinkafa ce da miya 'yar kullum,sai nama da bai gama rusuna ba cikin miyar. Wata armless chiffon gown ce a jikinta ruwan zama, tsahonta duka duka iyakarsa qauri,ko sauko mata batayi ba sosai,hafsat din ta bita da kallo ranta kamar zai fashe,ta cika tayi fam a rigar saboda cikinta da yabi jikinta sosai zuwa qirjinta,ita batayi don wata hafsat ba,tayine saboda sabo,ire iren shigarta kenan dama a kadunan,da wuya ka ganta da atamfa. Da qyar take zuba abincin,ta gama ta turawa kowa tabar widad da zuba nata,kadan ta zuba,don ko a ido ma ta dinga jin abincin bai mata ba tun batakai cikinta ba,aikuwa da qyar tayi loma biyu ta miqe,ya bita da kallo yana tambayar ba'asi "Na qoshi ne uncle" ta fada adan shagwabe,yasan inda matsalar take,shi kansa da ya saba cin wannan collabo din nata yana ci ne kawai don babu yadda zaiyi,bare widad din da bata saba ba. "Amma.....me zakici?" Tadan juya fararen idanunta cikin dan tunani "Zan duba wani abun ko cikin fridge ne" kai ya gyada "Make sure kinci wani abun kafin ki kwanta,karki sake ki kwanta da yunwa" ya fadi yana dan jin damuwa a ransa,ya dauko abinda ya zame musu damuwa duk su duka,kai ta gyada "In sha Allah uncle" sai ta fara takawa zuwa cikin dakinta,yayin da hafsat ta kasa daurewa taja wani mugun tsaki mai masifar qara "Ayidai mu gani" kallonta yayi baice komai ba yaci gaba da cin abincinsa ganin widad din ko waiwaye batayi ba bare tasan abun ya shafeta,sai yarinyar ta sake burgeshi,yasan ta tsani taja masifa aqi tanka mata,yanzu zata sake haukacewa "Sai wani rawar qafa kake a kanta,idan banda daurewa qarya qarqashi,ayi abincin tace wani wai bataci,sannan kai ka biye mata da zancan ta nemi wani abun taci tsabar ciwa mutum fuska" tayi maganar muryarta tana rawa. Sosai ya kalleta kafin ya aje spoon din hannunsa "Ki shiga taitayinki hafsat,ni ba haka na saba rayuwata a Kaduna ba,nutsuwa da kwanciyar hankali sosai nake samu,ba zaki zo ki hanamin wannan ba,indai kikace irin wanan halin zaki dauka to ki tabbatar ba zaki taba jin dadi na ba" daga haka ya miqe shima yabar mata wajen. *******Kwanakin girkinta guda biyun nan ta rasa inda zata tsoma ranta taji dadi,itadai widad bata fasa sabgoginta ba kamar yadda hajiya fanna ta bata shawara,illa iyaka ganinta ma wuya yakema hafsat din bare ta takaleta,wuni a daki baya yi mata wahal,tayi kallo ko tayi chart ko ta buga game,idan ta fita falo daukar abu tazo yi zata dauka ta wuce abinta,yaran suna son zuwa wajenta amma uwar ta kasa ta tsare,idan ta bari sun rabeta to uban yana gidan ne babu yadda zatayi tana shakkar hanasu. Abbas din yana ta qoqarin ganin tana fitowa ta sake a cikinsu amma taqi bada wannan damar,don ta sake sanin ciwon kanta zuwa yanzu,uwa uba kuma kishin hafsat din itama takeji sosai,musamman ta ganta ta fito daga dakin uncle din nata sai taji kamar zuciyarta zata fashe,tafi ganewa tayi zamanta a dakinta tayi sabgoginta,ko abincin darenma na washegari tsakura tayi tabar falon,hafsat din nata binta da harara kamar idanunta zasu fado,amma ita bata ma kalleta ba bare tasan me takeyi. ********Kwanansu biyu da dawowa widad din ta karbi girki,ranar tunda safe datayi wanka ta shirya cikin wata farar wide leg jumpsuit,sai baqar gatsby cap data dora saman kanta. Duk sa cewa tayi shigarta ne kawai normal bada wani manufa ba amma wani mugun kyau tayi,shigar ta karbeta sosai,saika dauka wata baturiya ce,musamman yadda sassalkan gashinta ya fita ta qasan hular kan nata. Ta lura da lalacewar falon kwanaki biyu kacal,saboda haka can ta fara fita bayan ta zura lallausan bedroom slippers dinta. Yadda take tsammani haka ta samu falon,a wargaje tarkace kota ina,haka ta dinga kawar da duk abinda tasan bai kamata ya zauna a falon ba tana killaceshi,cikin mintuna qalilan ya fara daukan saiti. Tana tsaka da aikin hafsat ta fito dauke da qaramin mug da plate dinsa,suka hada ido widad ta janye kallonta daga kanta tana ci gaba da aikinta,wata irin harara da widad din batasan tana yi ba ta zabga mata,taja wani dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta,gaba daya yarinyar ta gama shige mata rayuwa,banda tsabar raini me ya hadata da taba mata falo?,ko tana tunanin itama tana da power ne irin yadda ita take da ita? "Iyayin banza da wofi kawai" ta fada tana wuce widad din,wadda tabi bayanta da kallo,saita samu kanta itama da cillama bayan nata harara kafin ta maida dubanta ga qofar dakin uncle din nata,wanda a yanzu ya zama nasu shida hafsat din,wani zafi takeji a zuciyarta,tunda mommyn tazo komai ya sauya a tsakaninsu,a baya kullum suna manne da juna,amma yanzun ta shiga tsakaninsu,siririn tsaki taja data tuna uncle din nata yana dakin,tare suka kwana,kuma duk wani abu da yake mata itama mummyn yana mata kenan?,tana shaqar wannan daddadan qamshin nasa?,tana jin wannan lallausar fatar tasa?,yana bata wannan soft kiss din irin wanda yake bata?,sai taji ranta ya baci amma tayi saurin koren shaidan yadda anty madeena ta koya mata. A kitchen kuwa tsaki hafsat din tayita ja a jajjere,yau abbas din zai raba musu kwana da yarinyar?,saita zube cups din kawai ta fito tabar kitchen din. Wuceta ta sakeyi ta gefanta kamar zata gogeta,ko daga kai widad din batayi ta kalleta ba taci gaba da aikinta,ba jimawa aka turo qofar dakin,bata juya wajen ba,amma duk da haka lallausan qamshinsa ya gaya mata waye. Tsaye yake daga bakin qofar yana qare mata kallo cikin police uniform dinsa dake matuqar qara masa kyau da wani irin kwarji na musamman,hannayensa cikin aljihunsa fuskarsa ta wadata da murmushi,duk kuwa da cewa bata ma san da tsaiwarsa ba,tun tana basarwa hadi da qin kaon qofar har zuciyarta ta gaza,tana jin saukar idanunsa a dukka jikinta,yana kuma haifar mata da kasala sosai. A gajiye ta daga fararen manyan idanunta ta sauke masa,idanuwansu suka gauraye waje guda,sai shima ya gaza.....ya zaga da tsaiwa a nan ba tare daya iskota ba,ya fara takowa a hankali har yanzu ya kasa dauke idonsa daga kanta "Good morning babyn uncle" fuska tadan narke kadan ta karyar da wuya,kishi nason taso mata amma tana danneshi,uwa uba kuma ya mata wani irin kyau me taba zuciya "Morning uncle din baby" maganar tata ta sanya murmushi ya subuce daga labbansa,kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai hafsat din ta fito daga dakin,dauke da briefcase dinsa, idanuwanta a kansu har ta iso ta miqa masa jakar,ya karba yana gyara rufinta "Ina kwana?" Ta fada tana russuna masa cikin girmamawa "Lafiya lau baby,kin tashi lpy?" "Lafiya uncle" ta amsa masa a narke tana karyar da wuya,ya gyara jakar yana mata duban tsakiyar ido,yana jin kamar ya jawota ya rungume cikin jikinsa,shi wani mutum ne da muddin yana so ba kasafai yake iya boyeshi ba,ba soyayyar mutum ba,soyayyar komai ma "Ba wani matsala ko?" Kai ta gyada tana dan murmushi, idanunsa kawai sun wanke mata komai a ranta "To shikenan sai na dawo" "A dawo lafiya uncle,Allah ya tsare" "Ameen babyn uncle" tsaiwar mashi cak sunan ya yiwa hafsat a tsakiyar ranta,wanann zallar iskanci ne da wulaqanci,a gabanta suke irin wadan nan abubuwan?,sai kawai tayi fuuuu tayi gaba,hakan ya bashi damar qarasa sallamarsa a nutse ya fice yana qorafin tayi masa qauro,ai ba irin wannan sallamar suka saba yi,tana ta masa dariya hadi dace masa aiba ranar girkinta bane,yayita juya zancan cikin ransa,wato har ta fara rarrabewa da wani girkinta da ba girkinta ba,yadan daki sitiyarin motar kadan,shikam wannan tafiyar da hafsat ta tauyeshi da yawa. Aikinta taci gaba da yi,saidai sanda ta shiga kitchen ta gane hafsat ta jiqa mata aiki,komai a qazance,sak dai yadda ta saba barin sassanta na bauchi,saita zage ta shiga gyara haiqan,wanda tun batayi nisa ba taji cikinta ya wani cure kamar an sakar mata dutse,ta miqe tana dora hannunta saman cikin,tana mamakin wani dan tudu da take iya ji cikin nata yayi,idan ta kalli kanta cikin madubi kuma bata iya ganin komai,saita koma da baya ta huta kadan sanann ta qarasa. Duka abinda akeyi hafsat tana falo ta kasa ta tsare,wata irin dakiya ce ta zoma widad din,bata fasa aikace aikacenta ba kamar yadda bata bi ta kanta ba,da taga bata ko lura da zamanta ba saita fara zirya tana qananun maganganu daga kitchen din zuwa falo,burinta yarinyar ta tanka,ta samu ta likideta ta fake sa rashin kunya tayi mata. Tana jiyo su mimi daga falo suna nemanta ta daka musu tsawa ta zaunar dasu waje daya,saida suka fara kukan yunwar da suka farka da ita sannan ta wuto kitchen din daukar musu abinci,sannan harta gama kintsa kitchen din,tana adana kayan cefanen da tun randa suka dawo hafsat din ta karbi girki abbas din yayosu masu yawan gaske,amma haka nan hafsat din ta barsu,komai saidai ta farka ta diba yadda ranta yakeso ta barshi a wajen,hatta da kayan miyansu haka ta wurgasj fridge babu gyara. Zuciya tazoma hafsat din iya wuya,me yarinyar ke nufi,duk abinda ta fita a girki ta barshi ta sauya masa fasali daga yadda yake wai ita zata karba girki,har tazo fita ta dawo baya a zafafe "Ke nifa banason iyayin banza da wofi,duk kin kama abubuwa kin sauya musu waje kamar kinfi kowa iyawa?" Tana ware tomatoes din da suka lalace ta daga kai ta dubeta,ido tadan zuba mata ba tare da tace komai ba "Dake nake magana kika zuban ido,ba zaki zo gidana kice zaki isheni da kinibibi bafa" sai a sannan ta janye idanunta,qasa qasa tace "Gidanmu dai" "Qunquni kikemin?,me kika ce?" Ta tambayeta a zafafe "Gidanmu dai" ta amsa mata kai tsaye tana kallon qwayar idanunta. Wani abu ne ya saukar mata a kanta mai nauyi,mamaki yayi bala'in cikata,yanzu haka har tana da qwarin gwiwar maida mata magana haka kai tsaye?,lallai tayi sake,tayi kuma barci kwana biyu "Zaizo me daure miki gindin ya gaya min idan shine ya gaya miki gidan nan kema gidanki ne" sai tayi gaba widad ta rakata da ido tana tabe baki,sai kuma ta gwada yadda tayi maganar sannan ta saki dariya,ita abinda ke bata mamaki,mummy hafsat din babba da ita,amma kullum aikinta tsaiwa taja magana tsakaninta da ita,taja tsaki tana sake tabe baki taci gaba da aikinta. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 07 Wuni hafsat din tayi tana zirga zirga cikin gidan,bata falo bata kitchen,ita kuwa widad hakan bai hanata zagewa ta shiryama uncle abbas dinta abinci lafiyayye ba, hafsat din na zaune daga falo sanda qamshin ya fara mata sallama,ta baza qofofin hancinta, Zuciyarta na gaya mata ko daga babban sashen hajiya na gidan qamshin ke fitowa?,to amma data nutsu da kyau saita gane daga kitchen din gidansu ne,mamaki ya daskarar da ita a wajen,ta gaza daurewa ta nufi kitchen din kamar zata dauko wani abu. Qamshin da tayi arba dashi yafi na falon,ta gefan ido take kallon yadda yarinyar keta aikin girkinta komai da komai tsaf,kai bakace girki takeyi ba,zarcewa tayi da dauko ruwa zuciyarta na wani irin tsalle daga qirjinta saboda zallar kishi,ta dauka ruwan ta juyo ta fito,saita ajeshi kawai gefanta ranta yana baci. Tako ina yarinyar ta bata mata tsari,komai na yarinyar canzawa yakeyi ko tace tama canza totally,komai nata a yanzun na cikakkun matan aure ne,yaushe ta iya girki mai bada matsiyacin qamshi haka?,cikin wadanne watannin ne da bata banbancesu ba?. Tana tsaka da wannan nunqufurcin da tunanin harta gama komai ta kuma fito daga kitchen din zuwa dakinta,a nan yaran suka ganta,suka ruga da saurinsu suka bita dakinta,a sannan bata da kuzarin hanawa,don tayi nisa cikin tunani da lalubowa kanta mafita. Sosai yaran suka sake suna wasansu a dakin nata,ta fidda chocolates ta basu ta shiga wanka,ta fito tana baza qamshin shower gel dinta mai taushin qamshi,ta tsaya gaban madubi ta soma gyara kanta. Tunda wuri yake qoqarin yaga ya kammala duka aikinsa ya dawo gida,duk wani motsi da zaiyi tana maqale cikin ransa,haka yayita kokawa da ayyuka don ya samu dawowa gida da wuri ya kasance da ita,amma hakan bai yiwu ba,sai yamma liqis sannan ya samu ya ture wasu ayyukan ya fito. Sai daya tsaya ya siya dukka nau'in fruits din da yasan tana so,ha hadama yaran da kayan kwadayi sannan ya dauki hanyar gida,cikin ransa yana jin wani zallar nishadi da farinciki,wata walwala da baisan tushenta ba ita ke wanzuwa saman fuskarsa,lokaci lokaci yakan saki murmushi idan ta fado masa a rai,a haka har ya cimma gida,yadan dannan hon mai gadi ya dage masa qofar. Sautin hon din motarsa daban yake a kunnuwan widad,ta lumshe ido dai dai sanda ta gama shirya kanta tana duban kanta da kanta cikin madubi "Ga daddy nan fa ya dawo" tace da yaran tana dan dubansu,wani shauqi da qaguwar riskarsa tana ratsata,sai takejin kamar tayi shekara ne bata rab'i uncle din nata ba "Yau sai na riga kowa zuwa taro daddy" mimi ta fada tana tattare kayanta,murmushi widad ta saki "Zamuga waye zai riga wani" sai ta dauki turare ta sake feshe jikinta,sannan ta nufi qofa da sauri tana yiwa mimi gwalo,wannan ya sanyata zubda kayan ta miqe tana qyalqyala dariya "Allah anty saina rigaki" ganin yarinyar ta biyota sai ta dan saka sassarfa tana mata dariya tayo gaba mimi din ta rufo mata baya. Dai dai sannan hafsat da taji muryarsa daga waje suna gaisawa da ma'aikatan gidan ta fito falon,daga kujerar dake daura da bakin qofa ta zauna,ta yadda idan ga shigo idanuwanta zasu iya gane mata komai,uwa uba ma tasan babu wanda ya isa ya keta idanunta ya tsallaketa ya isa gareshi,ta baza dukka idanunta tana qarewa gyaran da aka yiwa falon zuciyarta kamar ta fito,lallai ba shakka sai taci uban yarinyar,sai tayi maganin dukka wannan kinibibin nata,taja qwafa tana karkada qafafunta. Yana doso part din ransa yana sake yin fari,tun bai isa falon ba ya tabbatar ya koma saitinsa yadda yakeso,qamshi mai sanyi ke hudowa ta tsakanin labule da qofar yana fitowa har harabar gidan,ya buda qofar falon a nutse bakinsa dauke da sallama,hafsat din ta miqe tana dan sakin murmushi tare da amsa masa sallamar. Taku biyu tayi zuwa gaba da niyyar amsar jakar hannunsa muryar widad hade data mimi ta karade falon. Hankalinsa da nata gaba daya ya koma kansu,sanda suke rige rigen tarbarsa kowa yanason ya fara isa a tsakaninsu. Sosai ta fusgi hankalinsa ta kuma tafi da dukkan nutsuwarsa,yadda take tahowa da sassarfa yaji ya masa kadan,ya fara takawa shima ha ruskesu,cikin sa'a ta riga mimi isa,ya bude hannunsa ta fada jikinsa tana fadi cikin dariya "Oyoyo daddyn mimi" sosai yake kallon fuskarta da narkakkun idanunsa dake kanta,yasa hannu ya daga fuskar tata yana murmushi wanda yafi kama da dariyar farinciki "Kinwa 'yarki wayo ko?" "Dama na gaya mata,sai na rigata" saita jefawa mimi gwalo,yarinyar ta tabe baki kamar zata saki kuka,sai widad din ta miqa mata hannu tana sakin dariya "Taho.....taho mimin dadd......" Sautin kuka shi ya maida hankalinsu duka ga hafsat,duk sai sukayi sak suna dubanta,har ga Allah abbas din ya manta da wanzuwarta a wajen gaba daya,widad tasan tana gurin amma batajin zata iya fasa abinda ta saba yiwa uncle din nata,uwa uba kuma dazu da taji yana cika baki da tinqaho akan uncle din,abun ya bata haushi amma saita qyale kawai,tana ji a ranta zuwa yanzu ko meye mommy hafsat din tayi mata ta daina qyaleta. Kuka sosai takeyi,kafin abbas ya samu damar cewa wani abu ta juya da sauri ta nufi dakinta,batason yarinyar taga hawaye har haka a fuskarta saboda gudun raini. Bayan wucewarta sai suka koma kallon kallon a tsakanin,a nutse ya zare widad daga jikinsa yana cewa "Ina zuwa" yabi bayan hafsat din,tabe baki widad tayi ta dauki.jakarsa daya aje a wajen suka wuce dakinta ita da mimi,yarinyar nata murnar tare daddy ya tarbesu,saidai sama sama widad din ke amsawa,don dukka hankalinta nakan abbas din. A nutse ya tura qofar dakin ya shiga,tana daga zaune bakin gadonta tana sharar qwalla,ya taka ya isa gabanta ya tsaya kawai kallonta hannayensa goye a qirjinsa "Me akayi miki?" Ya jefa mata tambayar data sakata dago kai idanu jiqe da qwalla ta dubeshi,wani baqinciki ya tokare mata wuya,wato baisan me yayi ba? "Bakasan me kayimin ba abban mimi?,ko yaushe baka da burin da ya wuce ka wulaqantani ka tozartani a gaban yarinyar nan,nice na fara welcoming dinka,amma tana fitowa ka kasa tarata ka koma kanta saboda tsabar cin fuska" iska ya furzar daga bakinsa yana gyara tsaiwarsa "Yanzu wannan shine abinda yakai ayi masa kuka?" Shuru tayi bata amsa ba tana ci gaba da goge qwalla,baisan yadda takeji ba a yanzun,da bai tsaya kanta yana magana fada fada ba "Dole sai kinyi haquri kin dauke kai,akwai banbancin shekaru a tsakaninku, infact ma ta riga ta saba ita kadai take rayuwa a gidan nan,wasu abubuwan sai a hankali zata dainasu" saiya fara takawa zai fita a dakin,ta bishi da kallon takaici,bataso ya shigo dakin ya fita haka da sauri,tana so ko yaya ne ta bata masa lokaci yadda zata dasa zargi a zuciyar yarinyar,tunda ta lura zuwa yanzu zaman kishi sosai takeso suyi,ta wuce wancan lokacin da zata dinga juya ta da raina mata wayo yadda taso. Sunansa ta sake kira,cike da qosawa ya tsaya ya waiwayo,saita taso ta iso gabansa ta fada jikinsa ta fashe da kuka sosai,ba yadda ya iya haka yasa hannu ya tallafeta,rigimar hafsat din tayi yawa,matsaloli kala kala marasa tushe balle makama,qanqanin abu saita hurashi ya zama babba,har yau ta kasa gane girmanta balle ta riqeshi. "Bansan me yasa kakemin haka ba,bakasan yadda nakeji a zuciyata ba" ta fada cikin kuka,tilas ya bata lokaci yana lallashinta tare da nusashe da ita cikin hikima,saidai abinda bai sani ba,duk abinda yake fada tana bi ta bayan kunnenta ne,burinta kawai ya jima a dakin. Ta samu yadda takeso kuwa,don ya jima yana jan hankalinta kafin ya baro dakin bayan ya umarceta data sake gyara dakin, saboda tuni ya fara fita daga kamanninsa a kwanki uku kacal,baya jin kuma zai jura,ba kamar bauchi bane,a yanzun bashi da wani dakin daban da zaice zai kebance a cikinsa. Bacci ya dauke mimi sai widad dake zaune gefan gadon,ta cika tayi fam,bata taba jin bacin rai irin wannan ba,shi yasa sam ko ganin mummy hafsat din batasonyi,tana jin wani zafi a zuciyarta duk sanda ta fahimci ko taga sun kebe,koda yayi sallama saita zumbura baki ta miqe ta nufi toilet kawai tana amsa masa ba tare daya tsaya a nan ba,qaramin murmushi ya saki bayan ya kalli agogo,sai a sannan ya fuskanci laifinsa,ya qarasa bakin gadon ya duqa ya dauki mimi ya maidata wajen hafsat sannan ya dawo dakin,ya jingina da mirror yana jiran fitowarta. Kamar bata ganshi ba sanda ta fito daga bandakin,ya bita da kallo yana sake tantance kyan da tayi,wani abu na motsa masa a ransa game da ita,a strong desire,idanunsa na zagawa bisa jikinta,bomshort din jikinta yayi masifar fidda shape na qugunta,kaman ana fusgarsa haka yaji,ya isa gareta cikin sassarfa ya jawota jikinsa. Abun yazo mata a bazata,wanann ya haifar da motsi a cikinta,abinda yayi matuqar firgitata tunda bata bata taba ji ba,a zabure ta saki ihu da ya sanya abbas riqeta da kyau yana lalubar abinda ya faru,hafsat kuma dake maqale a bakin qofa tana jiran jin taqaddamar da zata faru a tsakaninsu sanadin dadewarsa a dakinta ta sake gyara tsaiwarta da kyau,dadi yana cikata da jin ihun widad din,may be ta masa wani rashin kunyar ne yaji bazai iya jurewa 'yar cikinsa tayi masa haka ba ya kaiwa bakinta bugu. "calm down.....menene?" Kasa amsa masa tayi sai hawaye da ya fara bin idanunta,ta kama hannunsa ta dora saman cikinta,dai dai sanda motsin ya ratsa tafin hannunsa ya aika saqo kwanyarsa,sai kuma ya tsaya cak. Sosai ya shiga mamaki da tunani,ya dubeta cikin mamaki "Yaushe ya fara irin wannan motsin?" "Bai taba yi ba sai yau" ta fada tana sharbe hawaye,qaramin murmushi ya saki,saita saki baki tana kallonsa "Karki damu,zan kira dr yanzu nayi mata bayani,zauna a nan ki nutsu,don't bother". A nutse ya zaunar da ita sannan ya lalubi wayarsa ya fara neman number din dr maryam,daya daga cikin personal doctor dinsa. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 08 Bai jima yana kira ba aka daga,suka gaisa cikin yanayi na sanin juna,sannan yayi mata bayanin dalilin kiran nata idanunsa akan widad da dukka ta sauya lokaci daya tayi wani laushi,idanunta cike da tsoro. "Indai cikin yakai watannin da zaiyi motsi ai zaiyi dama,hakan kuma alamu ne na cikin lafiyayye ne,watansa nawa?" Kai ya girgiza "Bansan watanninsa ba" Dan murmushi ta saka mai sauti "An gaisheku gaskiya,ina ganin gobe ka kawota asibitin sai ayi mata scanning da komai da komai,har EDD dinta sai mu gani,amma kace mata kada ta damu,babynta ya fara rayuwa sosai cikin qoshin lafiya ne" godiya yayi mata ya ajjiye wayar,ya saka hannayensa a aljihun uniform dinsa daya kasa cirewa tun shigowarsa gidan, idanunsa a kanta yana sakar masa murmushi,duk da cikin tsoro take amma hakan bai hanata basar dashi ba,zata miqe ya kamo hannunta da sauri ya sakata cikin jikinsa yana sansanarta kamar wata 'yar mage,yunqurin tureshi takeyi amma yaqi bata dama "Ka koma wajen hafsa kawai" ido ya fidda yana dariya "Yau kuma?,hafsa zalla?" "Eh sunanta ne ai" ta fada tana dan murguda bakinta,har qasan zuciyarta tana jin kishi yana tsunkulinta,juyo da ita yayi suna fuskantar juna "Yanzu dai na gane,kishi ne kikeyi,to ayimin afuwa" kafada ta maqale "Ni ban haqura ba,saidai idan zaka kaini na siyo ice cream" kai ya girgiza bayan ya fidda ido "So kike ki debarwa babyna sanyi?,bayan dr tace da alama lafiyayye ne?" Fuska ta kwabe ta langabar da wuya,yadda tayin tilas tasa yace "Shikenan ki shirya,amma yau kawai" cikin farinciki ta amsa masa,tuni har ta manta komai ta fara shiryawa,shi kuma ya fara rage kayan jikinsa don ya shiga ya watsa ruwa,wanda already ta hada masa,yana shiryawa shima yana tsokanarta akan cikin,ita kuwa kunya takeji,saida tayi masa kamar zatayi kuka sannan ya qyaleta. Sai da qafafunta suka gaji da tsaiwa bata sake jin komai ba,uwa uba da taga lokaci yana matsowa na fitarsa zuwa masallaci,dole taja jikinta tabar gurin tsakanin kokwanto da rashin tabbas na samuwar matsala a tsakaninsu,saita koma dakinta tabar dan space tana leqensa,har ya fito daga dakin tsaf dashi ya wuce masallaci yana baza qamshi,saita koma bakin gadon ta zube tana riqe da kanta,idan akwai abinda ta tsana a duniya shine taga walwala da zaman lafiya na gudana a tsakaninsu,dole ta sake kashewa tsinanniyar yarinyar kudi,dole ta sake aiki a kanta. Sai da yasa yara suka kirata sau uku akan ta fito suci abincin dare sannan ta fito,dai dai lokacin da widad ta fito daga kitchen dauke da babban try data zuba. Kofta(ire iren abincinsu ne na 'yan yemen da ake sarrafashi da nama). Hafsat din na shirin zama sai taji qafafuwanta zuwa bayanta ya sage,da qyar ta danni zuciyarta ta zauna zuciyarta na wani irin tuquqi da suya,wannan zallar cin fuska ne kawai abbas din yaso yi mata,banda haka ta yaya zai kirata cin abinci jikin yarinyar da wadan nan kayan?,duk kuwa da cewa ta dora wata 'yar kyakkyawar farar riga mai budadden gaba,amma hakan baikai ga boye dukkanin adonta ba. Da ido kawai take bin abincin,sunata walwalarsu tsakaninsu,abbas din yana tsokanar mimi widad na tare mata,ta gama serving kowa suka fara ci a nutse. Har qasan zuciyarsa yakejin nutsuwa tana saukar masa,ba shakka lafiyayyen abinci mai daddadan dandano ma rahama ne a rayuwa,bashi ba,hatta mimi ta soma santin abincin,abun ya taru.ya yiwa.hafsat yawa,duk yadda qamshin abincin ya karade falon yake tsinkar da yawu amma sai taji ya fice mata aka,ta ture plate din ba tare da tace komai ba ta saba yusra a kafadarta,tana gyara zaninta daya tattare. Sai da yakai lomar kufta din bakinsa sannan ya daga kai a nutse ya dubeta "Ya haka?,ina zuwa?" "Bazan zauna a nan ba tarbiyyar yara na ta lalace ba,don ba wajen zama bane,ta saka wasu kaya fingil fingil yarana suna zaune suna kallonta?,ke nawwara......mimi ku tashi muje" ta fada a tsawace,haushin yadda yaran ke wasoson abincin yana sake qureta Bata fuska dukkaninsu sukayi,saboda sudai suna jin dadin abincin sosai "Mommy ki zauna kici,da dadi wallahi" mimi ta fada fuska a narke,abunda ya sake hasala hafsat din ta kwaza mata tsawa,sai abbas din ya daga mata hannu "Kinga ya isa,jeki abinki ke daya" yadda yayi maganar tayi mugun baqanta mata,nan da nan hawaye suka cika mata idanu,sai ta girgixa kai kawai tayi gaba da sauri hawayen nason subuce mata. Ko tunata babu wanda ya sakeyi,abunda yayi masifar baqanta mata rai kenan,don tayi tsammanin zai biyo bayanta kamar dazun,saidai a maimakon haka ma sai tashin motarsa da taji,koda ta fito Parlor din wayam babu kowa,saita zauna anan hawaye na qwace mata,ya wankin hula yake shirin kaita dare?,saita miqe zumbur ta koma dakinta tana lalubar wayarta. Cikin kwanakin girkin widad din gaba daya hafsat ta tsangwami kanta,ta rasa nutsuwa bare sukuni,bata daki bata falo,komai widad din zata aiwatar idanuwanta suna kai,hakan ko kadan bai damu widad din ba,don zuwa yanzu ta fahimci meye ma'anar kishiya da abinda zamansu yake nufi ita da hafsat din,ko daya idanunta bai sanya widad din ta fasa duk abinda ta saba yi ba,hasalima yi tayi kamar bata gane ba,kamar dai har yau wautar quruciyan ne ke dibanta,abinda ke masifar hargitsa hafsat din,tana ganin kamar abbas din yana biyewa duk abinda takeso ne,yana kuma fifitata a kanta,wannan ya sanya ya ta sake cin alwashin wargatsa komai da lalata duk wani farinciki na widad din kota tsiya kota tsiya tsiya,sam ba zata gajiya ba. Ta gaza shuru ta gaza haquri da yadda yarinyar ke gudanar da komai kamar wata babbar mace,cikin kwanakin komai na gidan tsaf yake a kammale,bata bari komai ya lalace ko a barshi wasarere,tun daga cikin kitchen zuwa parlor dinsu,duk kuwa da yadda hafsat din keta qoqarin ganin ta watsa komai,widad din taja yaran a jiki,ta koya musu yadda zasu bar waje da kyansa bai lalace ba,ta koya musu koda sweet suka sha inda zasu saka ledan,abun ya yiwa hafsat din ciwo,tayita jaraba tana fadan su yar amma qememe sai suqi,kada ma mimi taji labari,maganar anty widad awajenta kamar fadar Allah,hafsat tayi dukan tayi banbamin ta hanata zuwa duk inda take amma kamar turi,abun ya soma taruwa yana mata yawa,ta rasa inda zata taro,yaran ko abbas din?,dole ta zauna ta fidda kudi sosai ta turawa ummanta,tana hasashen samun mafita. *******Yammaci ne lis,inda suke zaune cikin falon ita da yaran suna kallo,duk da cewa girkin hafsat dinne,amma ko alamun shirin dora girkin dare batayi ba,hasalima tana daki kwance abinta. Hakan gaba daya ba damuwar widad bane,don dama da qyar take kaiwa labari da abincin hafsat,wani irin girki mara tsari mara fasali kuma,sam ko a ido bashi da wani qayatarwa bare kakai ga bakinta,Allah ya bata wani irin kurman ciki da har yanxu ya gaza nunawa a jikinta,saidai can cikin jikinta tana jin wasu sauye sauye da ita kanta tasan wani muhimman al'amari ne yake tunkarota,takan zauna tayita lissafin scanning din da dr tayi mata,wai cikinta watanni shida harda kwanaki,ta sha ganin ciki amma itadai ba haka taga ana ciki ba,tasha tsayawa gaban madubi amma bata ganin komai idan ba turoshi gaba tayi sosai ba,duk da yana motsa mata sosai amma yabi jikinta da kyau,ya qarawa breast dinta cika ne sosai,abinda ke matuqar daukar hankalin abbas kenan kamar zai zauce mata. Waya ce a hannunta tana duba wasu sabbin recipe da Chief deeja Berver ta basu,tana yi tana murmushi,saboda yadda take fahimtar komai kamar a gabanta akeyi,har ya fada hasashen yaddaa gobe zata tashi kan gidan da nau'in kalolin sabbin girke girke. Taji qarar bude qofad sarai,amma bata ko kalli bakin qofar ba,don tasan wacece,sai taci gaba da duba wayarta kawai ba tare da tako motsa ba. Idanuwan hafsat din a zube fes akanta,ko wacce rana tana kwana ta tashi da mamakin yadda yarinyar ta gaza tabuwa,duk kuwa da kudin data kashe akanta,sai wata 'yar qaramar nasara data samu,wadda har yau wannan nasarar bata gamsar da ita ba,don bata ga wata alama ta shiga damuwa ko qunci daga wajen yarinyar ba sam,duk kuwa da cewa a yanzun tana iya juya wasu abubuwa na gidan,wanda a kwanaki ko watannin baya bata isa ta juyasu ba. "Ke mimi..... nawwara,uban me kuke zaune kukeyi a nan?" Ta jefawa yaran tambaya tana zare idanu a kansu,cikin tsoron kada ta hanata zama mimi ke kallonta,yayin da nawwara tayi qirmisisi abinta "Baba me gadi ne ya kawo kayan abba,yanata buga qofa shine na bude masa" "Da kika bude masa kuma sai kika samu waje kika zauna?,ina kayan suke?" "Suna dakin anty widad". Wani abune yazo ya tsaya mata a rai,ta kalli widad da har yanzu bata kalleta ba koda sau daya,miskilancin yarinyar yana qona mata rai,tanaso tayi mata cin mutunci wasu lokutan,amma bata kulata ma bare ta bata dama "Ke.....ki tashi ki debo kayan wankin abbansu ki kawomin nan" cak ta tsaya da danna wayar,saita daga kai a hankali karon farko ta kalleta,daga samanta cukurkudadden gashinta data daura dankwalin atamfa,zuwa jikinta dake sanye da rigar atamfar da wuyanta ya yima yawa,ta sauko ga fallen zaninta wani kalar atamfar daban. Kamar zata fashe da dariya amma kuma bacin ran da take ciki ya zarta tayi dariyar,don cikin kwanakin kawaici kawai takewa hafsat din,ta dauka har yanzu wai widad din dai data sani ce?,cikin kwanakin gaba daya ta fito da wata sabuwar gadara cikin gidan,komai ta taba komai zata gyara ko zatayi amfani dashi sai ta tsoma mata baki,tana tutiyar cewa gidanta ne,yadda takeso haka za'a yi,yadda taga dama haka takeson ta gani. Koda ranta ya baci bata taba tsaiwa tabi ta kanta ba,abu daya ta lura kamar abbas ya kasa dai daita hakan,abinda ita kuma takejin tazo maqura,ba zata lamunta ba itama. "Dakina nima akwai wajen ajiya" amsar data bata kenan a taqaice taci gaba da danna wayarta,abinda ya harzuqa hafsat din kenan "Ba shawara nake baki ba,umarni ne" sake sauke wayar tayi ya dubi idanunta da kyau,ta gaji da rainin hankalinta,kusan fiye da rabin komai da komai na abbas yana dakinta,tunda shine asalin dakinsa,amma ko sau daya bata taba nuna damuwa ko tayi qorafi ba,shine yanzu "Ajiyar ce akace miki ni ban iya ba?,wai meye damuwarki?,naga dai kayan mijina ne ko?" "Miji?,ni kike cewa mijinki ne?,turqashi!,wallahi saina nuna miki isata,saina nuna miki ni wacece,kuma wadan nan kayan saikin fiddosu" ta fada tana nunata da yatsa,kamar ma batasan me take ba, saita bawa banza ajiyarta taci gaba da abinda takeyi,ita abinda bata sani ba,tana jin zafinta fiye da yadda ita takejin nata,tana kishin uncle abbas fiye da yadda ita take kishin nasa,saidai ita an gaya mata,matsayinsu daya hasalima gaba take da ita,dole tayi respecting nata,amma ko daya bataga alamun daukar girma a wajenta ba. Banbami tahau yi tana sauka akan yaran,ta tattarasu ta wuce kitchen dasu,widad ta tabe baki taci gaba da abinda takeyi,saidai can qasan ranta zuciyarta tana mata zugi,ta gaji da rainin hankali irin na hafsat din,ta kuma daina daga mata qafa. Ko daga kitchen din tana jiyo masifarta da kuma mitarta,ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga bisani ta kashe girkin data dora ta dauki yusra suka fito "Sai maganinki,bazan zauna qaramar yarinya dake kina maidamin magana ba kamar sa'arki" abinda ta fada kenan tana ficewa daga falon. Gyara kwanciyarta ma tayi tana maida hankalinta ga kallo,tsahon mintuna kusan goma sha biyar saiga maari matar me gadinsu tayi sallama,widad ta miqe ta zauna cikin fara'a da yake mutuniyarta ce sosai,suka gaisa sannan tace "Hajiya ce tace ayi kiranki" mamaki sosai ya kama widad din,hajiya kuma?,irin hakan bata taba hadasu ba illa iyaka gaisuwa "Bari na fito muje tare" ta fada tana miqewa tayi daki,maari tabi bayanta da kallo cikin tausayawa yarinyar,Allah ya hadata da BAK'AR KISHIYA. Tana sallama ta hangi hafsat daga zaune tana bawa yusra nono,a nutse widad din ta qarasa tana gidata,sama sama ta amsa mata fuska a hade,tun daga nan sai itama widad din ta kama kanta. "Kinsan alaqata da babanki?" Ta fada kai tsaye,saita dubeta sannan ta girgiza kai,tadai san suna da alaqa amma batasan wacce iri bace,kwanaki da ummu tazo mata suna yawan zama suna hira,hakanan itama tana aiko mata da abinci kullum "Kamar qanwa nake a wajen babanki,wannan dalilin ya sanya nayi kiranki,mummyn mimi ta kawo qararki,ki shiga taitayinki,banason rashin kunya da diban albarka,kizo ki sameta da mijinta da komai nata amma ki dinga qoqarin nuna kinfi kowa iyawa?,ki dinga yi mata isa da gida?" Wani abu ne ya taso mata,taji sam ba zata iya daukan zancan ba,don haka ta runtse idanu tayi nesa da tunaninta na tsahon wasu mintuna kafin daga bisani ta miqe "Ai bansan gidanta bane ba,amma yanzu na sani" abinda tace kenan ta soma takawa tana yin gaba,duk sai suka bita da ido,nauyi da kunyar yadda yarinyar tayi yana kama hajiya,yayin da hafsat ranta ya baci,ta kawo qarar wajenta ne saboda taji akwai alaqa a tsakaninsu,amma kuma haqarta bata cimma ruwa ba. Ranta yanatason ya baci amma tana qoqarin dannewa,tayi nasarar korar wannan,taci gaba da sabgoginta,bata ce ga sanda hafaat ta dawo ba,ta daiji motsinta cikin kitchen da kuma qananun mitocinta qasa qasa. Kwance tayi a dakinta har aka kira magrib,ta shiga toilet dinta ta sake wanka sannan tayi alwalar sallar magariba,wanna din sunnarta ne,ta riga ta saba koda bata da girki sai tayi wankan nan ta canza kaya,abinda hafsat din tayita son ganin ta hanashi faruwa,a cewarta ba ranar girkinta bane,don me zata dinga fitowa tana mata kwarkwasa da turare da kwalliya,saidai bata samu wannan nasarar ba. Ana idar da sallah taji alamun shigowar abbas din,duk sanda ya shigo gidan koda motarsa na anesa,ko motar office ce ta ajjiyeshi daga nesa sai taji hakan cikin jikinta,har zuwa sanda ya shigo sassan nasu, tanajin muryar su mimi suna masa oyoyo,taso tashi amma sai taji duka bata da interest akan hakan,kuma ma tasan bazai wuce minti uku bai qaraso dakinta ya dubata ba,don haka taci gaba da zama tana qarasa addu'o'inta da bata rabo dasu. Tun tana zuba ido harta soma qosawa,shuru bataji sake jin motsinsa ba,ta kalli agogo minti kusan ashirin kenan,tana sauke ido yayi dai dai da tashin muryarsa daga parlor yana kiran sunanta,duk sai taji banbarakwai,abinda bata saba dashi ba,amma kuma yau da gobe sai Allah,sai ta miqe a nutse tana gyara hijabinta sanan ta nufi qofa,gefe daya tana jin yadda cikinta yake qara tauri,wanda ita daya keji da ganin hakan. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 09 Yana zaune saman kujera sanye da uniform din nan nasa dake qara masa kyau da kuma kwarjini,ko boots din qafarsa baikai ga cirewa ba,hafsat na tsaye daga gefansa,hannayenta goye a qirjinta,fushi ne kwance saman fuskarta. Idanunshi a kanta,wani abu daya kasa tantance meye yana tsinkulin zuciyarsa,mabanbantan abubuwa guda biyu daketa faman gogayya da juna,har ta iso ta zauna gefan kujerar dake daura dashi tana masa sannu da zuwa. "Me ya hadaki da hafsat.....har kikayi mata rashin kunya?" Maganar tazo mata a bazata,mamaki ya kamata,ta dubi hafsat din suka hada ido,sai hafsat din ta aike mata da saqon harara,ta daure ta shanye sanann tace "Ni bansan yaushe nayi mata rashin kunya ba" "Kina nufin bakisan maganar kayan da kika kwashe ba?" Ta tambayeta kamar wata diyar cikinta,sai abbas din ya daga mata hannu "Ya isa.....me yasa kika kwashe kaya da aka dawo dasu daga laundry?" Cak ta tsaya ta zuba masa idanu,mamaki yana kasheta,duk yadda taso hana taruwar qwalla a idanunta amma ta gaza,saita gyada kai tana hadiye wani abu mai tauri daya tsaya mata,cikin rawar murya ta fara masa bayani "Baba mai gadi ne ya kawo su,tana.bacci yace a kwashe maka kada yara su tattaka,don ma debe shine nayi laifi?,ina cewa kusan kaso uku cikin hudu na kayanka suna dakinta a wajenta,na taba magana?" Sosai ta taba zuciyarsa yadda hawaye ke sauka saman fuskarta,tana kuma maganar muryarta tana rawa cikin sautin kuka,yanason yace ta tashi taje,tayi dai dai amma kuma kamar ana ingiza zuciyarsa,kamar kuma ana hura masa bacin rai haka yakeji. "Tashi kije ki debosu!" Yadan fada a kausashe,idanunta ta sanya cikin nasa mamaki yana sake daskarar da ita,totally uncle abbas din canzawa yakeyi cikin kwanakin,ba yau ya fara ba amma na yau yafi qona mata rai da tsaya mata a rai,ba yau ya fara ba,cikin kwanakin ko meye hafsat din tayi gaskiya yake bata,yana kuma qoqarin goyuwa da bayanta,sai ta miqe tsam cikin matsanancin bacin rai,ta dauke idanunta daga kansa ta maida ga hafsat,sai taga tuni yanayin fuskarta ya sauya zuwa madaukakin farinciki. Janye idanunta tayi daga kan fuskokinsu gaba daya,ta kuma juya da sauri ta nufi dakinta, abbas ya rakata da idanu yana jin kamar ya bita amma kuma wata zuciyar na gaya masa yayi dai dai,sai yaci gaba da kallon qofar da kuma tsammanin fitowarta. Cikin bacin rai ta fara tattara dukka wani abu da tasan nashi ne cikin daki,bata bar komai ba koda kuwa agogo ne,tana hade kayan hawaye na fita a idanunta,ta tsani rashin gaskiya,ta tsani a bata rashin gaskiya a rayuwar ta,ta tsani batayi abu ba ace tayi,tana jin kamar ta mutu idan akayi mata haka. Debo kayan ta fara yi hannu bibbiyu,ba ruwa ta da wadanda suke zubewa ta riqosu zuwa falon,tana zuwa batayi wata wata ba ta watsar dasu a wajen ta juya da sauri taci gaba da debo sauran tana zubarwa a wajen,ran hafsat ya sosu sosai,wanne irin raini ne wannan?,ta tsammaci zaice wani abu,sai taga bai ko motsa ba yana kallonta ne kawai,yana karantar zallar fushin dake fuskarta,wanda bai taba ganin irinsa ba a tattare da ita ba "Wai baka ganin abinda yarinyar nan takeyi?,kaga fa yadda take watso mana kaya?" Maganartata yayi da gama kwaso kayan,ta juya abinta da nufin komawa dakinta "Widad" ya kirata a tausashe,bata ko waiwayo ba bare ta saurareshi,don kuka takeyi sosai ta wuce daki abinta. Cikin qarfin ikon Allah ya miqe da wani irin zafin nama,zuciyarsa yaji kamar zata fashe da kukan da widad din keyi,ya tuna meye a jikinta,ta yaya zai barta tana irin wannan kukan?,sai ya nufi dakin da wani irin sauri wanda yasa hafsat ta zaci zuwa zaiyi yayi maganinta,ya dauki mataki akan abinda tayin yanzu,don haka ta saki wata qaramar dariya cikin nishadi da jin dadi,ta tako cikin rashin damuwa ta fara tsince kayan tana dibansu zuwa dakinta,sai a sanann ta lura da mimi dake sharar qwalla "Ubanki kike a wajen?,wato an saka uwarki kuka shine kikazo kika rabe a nan kina naki kukan,zaki tashi ki wuce ciki ko sai nayi ball dake?" Ba shiri yarinyar ta zame ta wuce daki tana tura baki gaba hadi da ci gaba da goge qwalla. Rub da ciki takeso tayi kukanta yadda takeso ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma tudun da takeji a cikinta ya hana,dole sai saman pillow ta dora fuskarta tana sakin kuka sosai. Jiki a matuqar sanyaye ya qarasa shigowa dakin,sai ya kasa qarasowa ya tsaya daga bakin qofa yana kallonta,shi kansa baisan me yake damunsa ba,baisan me yasa yake wasu abubuwan ba,duk da abinda yakeyi din bata taba nuna damuwarta ba,koda ta nuna mintuna kadan take sakin fuskarta kamar ba'a yi ba,sai ayau data nuna fushinta har haka. A nutse ya qaraso ya zauna gefanta,tunda ya buda mata qofar daki tana jinsa amma bata nuna tasan da shigowarsa bama,hannu yasa a tausashe ya zare pillow din ya maye gurbinsa da tattausan tafin hannunsa,sai tayi saurin kawar da fuskarta daga wajen kamar ya dora mata wuta,yasan halin kayarsa,ta iya rigima a duk sanda taso ko aka tabota,don haka yayi amfani da dukka qarfinsa ya azata saman jikinsa. Dukka qarfinta ta sanya ta zame a jikinsa,bai gaji ba ya sake maidota yana kiran sunanta tare da qoqarin son su hada idanu amma taqi bashi wannan damar. Kin zama tayi bare ta saurareshi ba,haka ya gaji da son yin magana da ita ya haqura ya fice yana sauke ajiyar zuciya,ransa gaba daya a jagule babu dadi. Da kanta ta lallashi kanta,saidai a ranar ta yiwa kanta hukunci qauracewa abbas din da dukka abinda ya shafi hafsat dama cikin gidan,ba zata iya gani ba bazata iya jura ba,duk jarumtar ta abun ya taba ranta,tana iya bakin qoqarin bashi farinciki da son ganin walwala da nutsuwarsa.....gefe guda yana bawa hafsat go ahead tayi duk abinda yake shine dai dai,yana kuma mara mata baya,ta yaya ita tata zuciyar zata samu nutsuwar bashi nutsuwa?. Washegari ranar girkinta ne,tun safe tana kwance a dakinta wanda tun dare ta saka muqulli ta rufe abinta,tana da abubuwan ciye ciye da yawa a dakinta da bata rabo dasu,don a lokacin abbas da ya shafe babin fita da iyalinsa zuwa wasu guraren shaqatawa a baya,a yanzu widad din ta dawo masa da wannan dabi'a tasa,ko rana daya hafsat din bata taba yunqurin binsu ba,sai mugun haushi da takaicin da take fama dashi,har zuwa sanda zasu dawo cikin gidan,takan ce ita tafi qarfin zuwa nan wajen. Zamu iya cewa borin kunya ne takeyi,don tun sand yake marmarin kaita take watsa masa qasa a ido,take nuna tafi qaunar ya bata abinda za'a kashe a wajen ta adana,har abun ya fita a kansa,ko ssnda ta haifi su mimi yana son kaisu amma bai samu wannan qwarin gwiwa daga wajenta ba,don haka sai a jima bai fita da yaran ba sai sanda ya samu hutu mai tsaho,gaba daya ita din opposition na rayuwarsa ne totally,bata kuma taba sawa a ranta ta sauya wani tsari yanayi hali ko dabi'a tata saboda shi ba,saboda a samu dai daito da zama me dorewa. Tana jin motsinsu daga parlor din amma bata ko motsa ba bare tayi yunqurin fitowa,ciye ciyen da tayi a daki ya dauketa fes,don dama bata iya cin abinci me yawa,yana zaune dining area amma hankalinsa yana kan qofar dakinta,jiya da abun ya kwana dashi ya tashi,duk kuwa da yadda hafsat din keta qoqarin mantar dashi da wasu salo da sam baibi jikinta ba bare ya dace da ita,don ba dabi'arta bane. Ya kammala shan tea din da babu qamshin komai a ciki saina Lipton da milo,ya ajjiye cup din ya miqe yana sauka daga wajen,hafsat din na zaune tana kallonsa batace komai ba,tanason ganin ya za'a qare,ya isa qofar dakin nata ya tsaya a nutse ya fara knocking yana amsa wayar data shigo masa a lokacin. Taso ta shareshi taqi bude qofar,saboda Wani mugun zafinsa da takeji har cikin ranta,amma sai taga hakan bai kamata ba,tunda tasan a lokacin kowa yana parlor,ta kuma tabbatar hafsat din tana ganin komai da zai faru,don haka ba'a son ranta ba ta miqe a hankali tana gyara zaman yaloluwar rigar jikinta ta zura bedroom slippers dinta ta nufi qofar. Tana bude masa ta saki qofar ta koma,yabi bayanta da kallo tsigar jikinsa tana zubawa,ko kadan baya gajiya da ita,baya qosawa da ita,kwanaki biyun da basu tare mugun yunwar ta yakeyi,yaci gaba da kallonta yana dan hangen cikinta daya turo kadan,wanda sai ka saka ido da tsananin kula zaka iya ganinsa. Guri ta samu ta zauna ta gaidashi ba tare data kalli fuskarsa ba,yanata qoqarin su hada ido amma taqi "Ya jikin naki?" "Lafiyata qalau" ta amsa masa a shashance,ya sake duban fuskarta sosai yadda taketa basarwa,sai ya ajjiye mata kudin cefane yayi mata sallama ya fice. Dashi da kudin gaba daya tabi da kallo, zuciyarta ta tsinke kuka yaso qwace mata amma ta danne,ta kalli agogo sannan ta miqe ta shiga bandaki ta watsa ruwa,ta fito taa shirya cikin dinkin doguwar ruga bubu gown ta yane kanta da madaidaicin mayafi ba tare data daura dankwali ba,fuskarta tayi kyau,ta sake wani fresh da haske mai daukan idanu,inda ya ajjiye kudin cefanen ta isa ta dauki kudin,sannan ta qarasa inda wayarta take ita dauketa tare da daukan wasu abubuwan masu amfani sannan ta fito falon. Babu kowa,sai ta zarce kitchen,ta dan samu abinda zataci wanda bazai mata wahalar narkewa ba,don yanzun matsalar da take fama da ita kenan. Ta gama ta dauraye cup din ta maidashi inda ta dauko tana kallon yadda kitchen din ya hargitse,kamar ba kwanaki biyu baya ya koma hannun hafsat din komai fes bisa tsari,saika dauka watanni aka dauka ba'a gyarashi ba. Baki ta tabe ta fice abinta,yau daga kitchen din har Parlor din babu inda zata sama hannu,itama tasan dadin jikinta,kawai dai tanayin komai ne don samun walwala da nutsuwarsa,tunda ta fuskanci babu abinda ke daga masa hankali a rayuwa irin qazanta,amma tunda bai gani itama ba zata dinga wahalar da rayuwarta ba,zata barsu shida hafsat din tasa. Tana isowa falon sukaci karo da mimi "Ina kwana anty?" "Oyoyo mimin daddy,kin tashi lafiya?" "Lafiya lau anty,yau duka baki fito ba" "Banajin dadi ne,ungo wannan ki kaima mommynki kice kudin cefane ne inji ni" ta hada dukka kudin da abbas din ya bata ta sanyashi a hannun mimi,sai da taga ta shiga dakin sannan ta fice abinta harabar gidan. Kai tsaye boys quaters ta nufa wajen maari matar baba mai gadi,sosai taji dadin ganinta kuwa,don bata taba zuwan mata ba,ko yaushe widad din tafi ganewa zamanta daki tayi kallo ko chart,ta marabceta sosai suka fara dan taba hira,tun widad din bata sake ba har ta saki jikinta suka shiga hira sosai,kasancewar hajiyan bata nan,babu wani aiki cikin gidan haka suka wuni tare. Maari din saita tuna mata da latifanta,cikin awanni kadan ta gane tana da kirki matuqa da jan mutum ajiki,har tafi tsohuwar me aikin hajiyan data dinga tayata kwana sanda abbas yake tafiya bauchi ba tare da ita ba. Tayi musu faten tsakin masara da yasha gyada da yakuwa,batayi zaton zata iya ci ba,sai gashi taci sosai sunata hira,kirkin widad da yadda take girmama kowa cikin rashin nuna qyama ya sanya maari ma taji ta shiga ranta,ba kamar hafsat din ba,dake dagawa izgilanci da wulaqanta na qasa da ita. Hafsat na tsaka da barci taji mimi na qwala mata kira saman kanta,da qyar ta bude idonta tana jan mugun tsaki,kafin daga bisani kuma ta buda hancinta sosai saboda warin bayan gida da take jiyowa,dole ta wartsake ta miqe sosai ta zauna tana duban mimi "Ban hanaki idan ina bacci ki dinga tashina ba don ubanki?" Kebe fuska yarinyar tayi kamar zata saki kuka "Ai ban tasheki ba harma su nawwara sukayi kashi,yanzunma anty ce tace na kawo miki kudin cefane" "Kudin cefane kuma?"ta tambayeta da mamaki,saita jinjina kai,ta miqa mata hannu ta saka mata kudin,ta waresu tana irgawa. To me yarinyar take nufi?,nufinta ta ajjiye girki kenan saboda abinda ya faru jiya?,aiko ba zata sabu ba,ita dinma ai ba jaka bace da zata zauna tayita girka musu suna ci. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 10 Kamar ta bawa mimi kudin ta maida mata,sai taga kada tayi asara,ta bata kudin kuma tazo batayi musu girkin ba,don haka sai ta ajjiye kudin tanata qananun mitoci. Tun tana saka ran ganin widad din ta shigo sashen har ta fidda rai,don yamma ta riga tayi,ga yunwa suna ji ita da yaran,dole ta shiga kitchen ta dora dafa dukan shinkafa. Tana kitchen din tana fama ga magrib ya kawo jiki widad ta dawo,dakinta ta wuce kai tsaye,bata bi ta kan jagulallen parlor din nasu ba,tana mamakin yadda suke iya hargitsa guri har haka suci gaba da zama a cikinsu abinsu hankali kwance. Ta taho da sauran faten tsakin daxu,da zafinsa don a wani warmer mai kyau da hajiya ta bawa maari yake a ajjiye,saita hada ruwa me zafi ta cire kayanta ta shiga toilet tayi wanka ta gasa jikinta sosai,ta dawo ta zura wata armless riga da iya tsahonta gwiwa,ta wadata jikinta da turare,ta sake jona humidifier sannan ta dawo tana laluben hijabin da zatayi sallar dashi wanda zai saukar mata har qasa. Sosai yau ya hado yunwa da kuma gajiya a jikinsa,ya tabbatar zai samu dukkan wani hutu da kulawa hadi da kwanciyar hankali daga gurinta,wannan yasa ya hada dukkan yunwarsa ta yinin ranar,bai wani tsaya yaci cikakken abinci ba,don yasan zai tarar da irin taste din da yake muradi,har fiye ma da yadda yakeso. Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya kashe motar tasa,ya waiwaya baya ya dauko ledar fruit din da ya siyo da chocolate nasu mimi ya fito,ya kashe motar sannan ya nufi cikin gidan. Tun kafin ya qaraso ya fara buda hancinsa yana tsammatar samuwa sassanyan qamshin nan dake masa maraba a duk sanda girkinta ya shiga,saidai babu shi ba alamarsa,duk da haka yaci gaba da takawa cikin hope da kuma karsashi. Sosai mamaki ya cikashi sanda ya yaye labulen falon ya sameshi a tarwatse,komai yana zaune zaman kansa,sai su mimi dake ta hada hada da kayan ciye ciye na leda irin wanda yake siyowa ya jibge musu,ko ina tarkacen kayan ledojin da tsinken sweet ne,dukansu suka watsar da abinda yake hannunsu suka nufoshi suna rige rigen qarasowa,ya tsugunna ya tarbesu gaba daya. Miqewa yayi yana dauke da nawwara mimi na hannunsa,yaji motsi a kitchen,don haka zuciyarsa ta bashi widad ce,sai ya wuce kitchen din dasu kanshi tsaye yana amsa tarin tambayoyinsu da suketa damunshi dasu. Tun bai gama shiga kitchen din ba idanu da hancinsa suka gaya masa ba widad bace,hafsat ce sanye da doguwar rigar wani material ruwan qwaiduwar qwai,sulbinsa ya sanya dinkin da aka masa a wasu sassan ya zazzame yayi zare zare,tana goye da yusra daketa mutsu mutsun son a sauko da ita,ya qarasa yana amsar yarinyar,ta sauke masa ita tana masa sannu da zuwa muryar a cunkushe. "Ina antyn nasu?" "Tana dakinta mana" hafsat ta amsa adan fusace tana juya dafadukan data fara kamawa "Lafiyarta qalau?" Juyowa tayi kamar ta banka masa harara,amma kwarjinin nashi idanuwan sun shallake nata "Aiba wannan ya kamata ka fara tambaya ba,kamata yayi ace ka tambayi wanda ya bamu abinci wunin yau,ta shige daki saboda ta samu daurin gindi tayi kwanciyar ta wuni guda ta barmu da yunwa ni da yara" sam hankalinsa bashi akan maganarta, zuciyarsa da tunaninsa sun karkata kan sanin lafiyarta da abinda ya hanata fitowa wunin yau,sai ya juya yana sabe da yusra ya fice a kitchen din. Ana fara knocking ta gane shine,ta riga ta saba da komai nasa,hatta takun takalminsa ya banbanta dana kowa,tana kuma iya banbancewa,ranta yadan quntata,itakam ko son ganinsa batason yi,space take da buqata, batason takura,to amma batason tayi wani abu na rashin girmamawa a gareshi gaban yaransa,dole ta ajjiye qaramar hular da take qoqarin sanyawa sassalkar sumarta daketa sheqi saboda yadda tayi oiling dinta da mai,tana tura baki da shagwababbiyar fuskarta ta isa qofar ta bude masa,sai taja ta tsaya daga bakin qofar,kamar wadda aka zo gayawa saqo take jira a gama gaya mata a fita ta kulle qofarta. Tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa wani abu ya tsarga masa,yadda batasaka brassiere ba amma hakan bai hana na shanunta tsaiwa kyam suna nuna kansu ba,lafiyayyun cinyoyinta sun fita sosai ta cikin tsingilalliyar rigar,yadda ta turo bakinta gaba kuma ya qarasa kunnashi,soft pink lips dinta daketa sheqin lip gloss,sai yaji kamar ya jata cikin jikinsa ya kama bakin ya tsotse,amma yusra na kafadarsa,tilas ya daure,ya qarasa gefan gadon ya zauna ya dora yarinyar saman cinyarsa "Sannu da zuwa" shuru ya ratsa maimakon ya amsa mata,ya tsareta da ido yana jin yadda kallonta kawai yake saukar masa da kasala "Banda na shigo na nemeki bakisan ma na dawo ba kenan?" "To me zanzo nayi maka?,bayan maganar matarka kawai kake ji" ta fadi haka cikin ranta,amma a fili saita sake tura baki gaba tana yamutsa girarta hadi da sarqafe yatsunta waje daya tana ballaqasu "Zonan" ya fada a tausashe yana nuna mata kujerar madubin dake gabansa,ta kalli wajen sannan ta kalleshi,ko yaushe girma da kimarsa ke sakata ta kasa masa musu ko wasu dabi'u da basu kamata ba,ta sauke hannuwanta ta dawo inda ya nuna matan ta zauna,wannan karon idanunta cikin nasa tanason jin abinda zai gaya mata kuma. Rage kaifin nasa idanun yayi kadan daga kanta sannan ya magantu "Ya akayi gidan ya zamana yau duk a hargitse,infact ma yau girkinki ne amma baki fito kwata kwata ba,ko yanzun ma antynki ce cikin kitchen din" wani haushi ya kamata,aiki?.....a nan tafi kauri kenan, idanunta ta lumshe kadan tana daukesu daga kansa,abinda ya sake fusgarsa da wani madaukakin shauqi zuwa gareta,duk da ba tayi bane don ta burgeshi ko kuma da wata manufa "Gida a hargitse?,ina cewa mummyn mimi tana cikin gidan,amfanin zaman mutum biyu kenan,idan dayan ya gaza ko ya gajiya sai dayan ya tallafa masa.......girki kuma ni na daina girki,na bar mata komai da komai harda kwanana" mamakin widad din sosai ya kamshi,yadda tayi maganar ya tabbatar da gamewar hankali a jikinta,don tana maganar ne with seriousness in her sound,baibi takan maganarta ta farko ba,maganarta ta qarshe tafi fusgar hankalinsa tare da tabashi,don abune da bayajin ko sama da qasa zata hadu zai amince da hakan "Kin daina girki?,meye dalili?,da kuma izinin wa kika dauki wannan matakin?" Sake tura bakinta gaba tayi sosai tana hade fuska,ta kuma kaucewa dubansa "Saboda gidan da mijin duka nata ne,so komai da yake cikin gidan yafi cancanta ya zama nata" sai yanzu ya sake gano inda ta dosa,can qasan ransa murmushi ya kubce masa,kishi take da gaske.....ta kuma ji haushin abinda yayi mata kenan fiye da yadda ma shi ya zata,amma bayason ta dore da haka don haka ya miqe yana dora yusra a kafadarsa "Ki shirya komai kamar yadda kika saba,banason dawo da zance,abinda ya wuce ya wuce" sai ya taka yana ficewa a dakin. Sam maganarsa bata bawa zuciyarta sassauci ba,saima tunzurata da yayi,bazai iya daukan mataki ba kenan kwata kwata?,indai haka ne itama bataga dalilin da zai sanyata saukowa ba,don haka yana fita sallar magariba ta sakawa dakinta key tayi sallarta ta jirayi isha'i ta bada ita sannan ta haye gado ta nutse cikin duvet hankali kwance. Sai daya dawo daga masallaci sannan ya zarce dakinta don ya samu ruwan nan nata me wani irin dumi da qamshi don yayi wanka,ruwan da ita kadai tasan yadda take hada masa shi,don koshi ya hada da kansa baya jin dadinsa kamar haka. A nutse ya tsaya yana knocking a bakin qofar,tana jinsa ta share,saita saka earpiece ma a kunnenta,don haka batasan adadin awannin ko mintunan da ya dauka yana bugun ba. Sosai ransa ya quntata,don yadda yayi tsaye yana bugun har mimi taji ta fito ya tabbatar tana jinsa,ya kirayi sunanta kusan biyar shuru,dole ya juya dakinsa dakin kuma hafsat,tana zaune a qasa ta tara kayan qazantar yusra tana waresu,ya wuce gaban cupboard dinsa yana rage kayan jikinsa. Binsa tayi da kallo ta tabe baki,ita da zasu tabbata a haka sai tafi kowa farinciki,duk bugun akan kunnenta akayishi,tana sane tayi bakam "Ba kwananta bane?,ya na ganka a nan dakin?" Ta jefa masa tambayar da tasan amsarta. "Na sani,hadamin ruwa zanyi wanka" ya fada muryarsa da wani irin laushi daya bata mata rai,komai na yarinyar tabashi yakeyi,saka masa damuwa yakeyi,duk qoqarinta na kau da hankalinsa amma baya wani tasiri yadda take da buqata,ita sau nawa suna irin wannan sabanin,amma ko a fuska bata taba gani yayi laushi irin haka ba,komai dadewar da zasuyi,sai yanzu akan qaramar yarinya kwana uku kacal amma duka ya canza?. Da tunani iri daban daban ya shiga wankan,sam ruwan baiyi masa ba,hasalima ya cika zafi da yawa,yaja tsaki ya saki famfo akai,sai kuma yaso salance masa,ya sake jan wani tsakin yana komawa cikin bathtub din ransa duka a jagule. Koda sukazo cin abinci ma yasa mimi ta bubbuga mata,duk da yadda hafsat ke faman hada rai tana ganin ya girkinta ne batayi ba ita ta zauna tayi kuma saboda gata wai a kirata taci,itama mimin haka ta qaraci bugunta ta haqura ta dawo jiki a sanyaye "Bata bude ba" sai ya shafa kanta "Inajin tayi bacci" a yadda yake jinsa koda lafiyayyen girki hafsat din tayi abincin bazai masa dadi a baki ba,bare tafashi kadan hafsat din wadda ta cuccure waje daya,kamar gidan da aka yiwa gorin man girki,bayan komai a wadace yake a store dinsu,zuciyar tata ce dai haka. Da qyar yayi loma hudu ya ture abincin,ya maida hankalinsa ga news da ake haskowa a channel din al_hadath,duk da a badini fiye da rabin hankalinsa yana kan qofar dakinta,duk bayan mintuna biyu saiya kalli qofar dakin,amma ko motsinta daga ciki baiji ba bare ya sanya ran zata bude ta fito. Har yaran sukayi bacci hafsat ta debesu takai daki ta dawo tayi masa sallama yana zaune a wajen,sanda sha daya na dare ta buga sai ya tashi yana sake gwada bugun,a lokacin tuni tayi bacci,bugunsa ne ya tasheta,ta sauko a hankali ta wuce toilet abinta,tayi fitsari ta sake alwala ta dawo ta kuma kwanciyarta. Wannan karon yaji motsinta shigarta bandaki zuwa fitarta,hakan ya nuna masa tana jinsa,bata kuma da niyyar bude masa,ya koma da baya ransa yana baci,ya juya yana nufar dakinsa. Dadi ya kama hafsat dake labe,saita koma bakin gado ta zauna tana kada qafa a hankali,itakam gaba ta kaita,dole yau ya kwana dakinta,sannu a hankali dai gida yana shirin dawowa hannunta sai yadda ta juyashi, murmushin nasara da farinciki ya kubce mata. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 11 Yana turo qofan dakin ta kalleshi,irin kallon mamakin nan wanda tuni ta shiryama hakan "A'ah,abban mimi ba kwanana bane" idanunsa ya zube fes akan fuskarta,yana iya hangen wani abu fake behind her face,sai ya lumshe ido kadan ya gyada kai "I know" sai ya qarasa ya dauki duvet dinsa da pillow ya juya ya fice yana ja mata qofa. Da kallon mamaki ta bishi,saita miqe ta nufi qofar yana leqensa,saman kujerun parlor din ya shimfidashi ya yada pillow din ya kwanta bayan ya rage hasken qwan falon,ranta yayi mummunar baci,wato ita bai isa ya kwana gurinta ba,saboda kwanan gimbiya ne?,har ta buda qofar zata iskeshi a falon wata zuciyar ta haneta,saita koma da baya ta maida qofar ta rufe. A wannan daren haka kowa cikinsu ya kwana,kowa da irin abinda ke kai kawo a zuciyarsa. *******Tun daga ranar suka koma 'yar haka dashi,sai sa'ar gaske yake iya sanyata a qwayar idanunsa,tuni ta ajjiye girkinta dama komai da komai,iyaka ta gyara bedroom dinta da kanta,idan tana da ra'ayin hira ta kira wanda takeso cikin 'yan uwanta,ummunta anty deena ko anty madeena koma mom dinta,ko kuma ta fice wajen maari susha hirarsu,ita kuma dake mata kallon me qaramin ciki tayita mata dafe dafe na abubuwan gargajiya,wanda da gudu widad din ke ci,don wasu abubuwan ma ta manta dasu sam,ummu ke musu lokaci lokaci a gida dama. Ba wanda ta taba gayawa abinda ke faruwa,don sai taji abun baya ma wani damunta gaba daya,yammaci tana yi dab da zai dawo zata koma dakinta ta kulle. Yadda hafsat take ganin damuwa qarara tattare da abbas din sai hankalinta yayi mugun dagawa,bata taba zaton baka ya damu da yarinyar ya kuma bata muhimmanci mai yawa cikin rayuwarsa ba irin wannan lokacin,ta auna ta auno......taga kaf zamansu bata taba irin wannan sakarcin ya damu da ita haka ko yabi ta kanta ba,hasalima wani lokacin saidai ta bude qofar ta tarar ya koma wajen aikinsa ya ajjiye mata dan note. Kishi sosai ya tasata a gaba,ta daina jin dadin gidan gaba daya,ba zata iya jure ganin soyayya da damuwar abbas akan wata diya mace ba a gaban idanunta tana raye ba,sai ya zamana bata da aiki sai mita da qorafi "Gaba daya qaramar yarinya na neman rikita maka lissafi,totally ka canza abban mimi,ba ita ta zabi haka ba,aiba wansa ya tilastata,saika qyaleta idan ta gaji ta watsar.....banda ma iyayin banza da samun waje,mema akayi mata?" Sai taja qaramin tsaki. A sannan yana shiryawa ne bayan ya fito a wanka,sanda take wannan maganar ma yanata bulayin neman wankakkiyyar singlet da zaisa duka babu,ya watsar dana hannunsa yana duban idanunta "Kin gaza ta abubuwa masu yawa,wannan ya sanya dole nayi kewar kebance kanta da tayi daga wajena,abubuwan da kika kasa ita din duka bata daukesu a komai ba.......ki jiqamin singlets dina da hypo zan wanke da kaina,na gaji da siyan sabbin undies,idan kin gama ki gyara parlor zuwa cikin dakin nan,idan Fresheners dinmu ne suka qare ki gayamin,idan na fita zan shigo da wasu,banason na dawo na samu gidan nan a yadda yake" daga haka ya juya yaci gaba da shiryawa. Turqashi!,ita yake kafawa misali da widad din?,daya kafa mata misali da ita gwara ya buga mata misali da mutuwarta,sai ta rikice masa gaba daya itama,tana ganin bata da wani amfani a wajensa,baya ganin kimarta sam a cewarta,gaba daya saboda yarinya guda daya jal ya rasa walwalarsa ya rasa sukuni,yanata qoqarin shawo kanta tana wahal dashi,ita kuma da take iya bakin qoqarinta a kansa baya gani,bai dauketa da daraja ba. A hankali sai damuwa ta fara yi masa yawa,tako ina ba dadi,widad itace sanyin idaniyarsa,ita ta zamewa rayuwarsa wani bango da zai jingina ya samu relief a duk sanda wani damuwa ta sakoshi gaba,ba damuwar hafsat kadai ba,hatta damuwoyi da matsalolin gurin aiki,don rigimar hafsat ya riga ya saba dasu,to amma a yanzun da suka hadu da juya bayan widad sai abun yayi masa tsauri da yawa,dole ya dauki hutun kwana biyu don ya samu ya gyara komai,bauchin da zasuje ma ya daga tafiyar sai satin gaba,bayason su tafi bauchi a haka,yasan bazai fahimci komai ba har suje su dawo. Ranar farko wuni yayi a parlor din gidan shi da yaran,salla ce kadai take fiddashi,gaba daya zaman yayishi ne a bisa dole,don yadda widad din ke bashi kulawa ta musamman a duk sanda zaiyi wunar musu a gida irin haka bai samu koda quater din wannan daga hafsat ba,saidai ya share ya maida hankali ga yaransa da kuma gyaran bedroom dinsa da hafsat din ta tasamma sauya masa kamanni da halayen baqar qazantarta,ya gama sukayi gyaran parlor tare da yaran,baiko nema sa hannunta ba,saita fake da girki a kitchen. Duk bidirin da akeyi widad din tana jinsu tana daki a kwance abinta,tunda ta fuskanci wunin gidan zaiyi sai taqi yarda ma ta bude qofan bare ya ganta,ta kunna data tayi chart sosai irin wanda ta jima batayi ba,daga baya ta koma youtube ta vidmate ta dauko K dramas da chinese masu yawa na soyayya ta shiga kalla abinta,abinda ya rage mata tsahon wunin sosai. Da mamaki ya kwana,washegari bayan ya tattara su dukka ya kaisu wankin kai,don ya gaji da kallon buyagin kan hafsat din da bata damu ta gyara ba,daga nan yace ayi mata harda manicure and pedicure "Amma dai.....da kudin yaran ka bari a hannuna,sai nayi musu su a gida" ko ta kanta baibi ba ya tashi motar yana cewa "Idan kun gama let me know,zanzo na daukeku" yaja motar abinsa,don tuni ya tura kudin komai ta Account din kamfanin, gurin da widad ke zuwa ne,kuma gyaransu yana da kyau,already yana da details nasu dama saboda yadda ta saba da zuwa wajen duk bayan wani lokaci. A masallaci ya fara tsaiwa yayi sallar azahar sannan ya qaraso da motar cikin gidan. Duk da yasan babu kowa cikin Parlor din amma hakan bai hanashi yin sallama ba,kai tsaye ya doshi dakinta,yana jin cewa yau zaiyi maganinta,murdawa daya ga mamakinsa qofar ta bude,ya tura ya shige,ajiyar zuciya mai tafe da numfashi mai nauyi ya sauke, sassanyan qamshin nan da yayi mugun kewa shi ya fara masa maraba,ko ina na dakin fes dashi yana bada qamshin nan daya cakude ta turarukan jikinta,he missed her badly..... He missed komai da ya shafeta. Ba kowa a dakin sai ya tura qofar toilet din,itama wayam ba kowa,saidai da alama ba'a jima da gama amfani dashi ba,farare qal qal din undies dinta shanye a ciki suna digarda ruwa fari tas da alama sun wanku da kyau,sai qamshi suke fiddawa dasu da toilet din gaba daya. Da baya ya koma yana tunanin ina zata,ya tabbatar ba zata fita daga gidan ba ba tare da ya sani ba,tunani ya fado masa,saiya koma da baya yayi boys quaters. Dai dai sanda tayi rashe rashe abunta a dan qaramin parlor din maari tana cin dumamen tuwo miyar kuka,har tsakiyar kanta takejin dadin tuwon,maari na daga bakin famfo tana dauraye kwanukan da baba mai gadi ya gama cin nasa abincin,suna dan hira kadan kadan taji sallama daga bakin qofa. Sam hankalin widad baikai kai ba,tuwonta kawai take azawa cikinta, maari ta aje kwanon taja mayafi ta leqa,sai taja da baya cikin matuqar girmamawa da jin nauyin abbas ta soma gaidashi,ya amsa mata a mutunce yana tambayarta widad din,tace masa tana ciki "Zaka iya shiga yallabai" ta fada tana rabeshi ta fice a sassan ta wuce sashen hajiya,don dama akwai gyaran da zata mata yau din,gobe ko jibi zasu dawo daga balaguron da sukayi,tayi hakane don ta karanci kamar akwai 'yar matsala ko sabani a tsakaninsu,batason saka baki ne a abinda bai shafeta ba,kuma ba'a yi mata tayin shiga ba. A nutse yake ratsa tsakar gidan nasu har ya isa qofar rumfar tata,idanunsa ya zube a kanta yadda take cin tuwon nata kamar ta samu nama,harma batasan ya iso wajen ba,ya qare mata kallo a nutse,kallon da bai samu yi mata shi ba tsahon sati kusan biyu,ta sake wani mugun cika,hatta da idanuwanta sun qara haske da girma,farinta ya sake daduwa kamar jini zaiyi tsartuwa a jikinta,duk da akwai madaidaicin hijab a jikinta,amma hakan bazai hanaka ganin yadda qirjinta ya cika fam ba,daga inda take zaune kuma baka isa ka nuna ciki a jikinta ba,abun yana mugun daure masa kai,yadda cikin yabi jikinta sosai,kamar bayason a ganshi,ya lumshe idanunsa kishinta yana cikashi,haka ta sake cika amma kullum take baro dakinta tana wuni a nan?,ko waye da waye suka taba kallon masa ita?. Tayi matuqar fusgar hankalinsa,wata kewarta mai zafi ta dinga taso masa,sai ya gaza jurar ci gaba da kallonta,ya tsugunna ya zare takalminsa,sannan ya miqe ya saka kansa rumfar maari,duk da ba haka yaso ba,amma yana jin kamar wani magnet ke jansa zuwa gareta. Sai daya kusa isowa gareta sannan turarensa ya ankarar da ita,tana dagowa idanunsu suka sarqafe waje daya,ta tsame hannunta zata miqe,ya saka dukka wani zafin namansa ya riqeta gam,ya kuma jawota zuwa jikinsa suka zube a wajen,bai tsaya wata wata ba ya hade bakinsu guri guda ya fara sauke mata french kiss mai zafi,wanda ya sanya cikin lokaci kadan jikinsa ya dauki rawa gaba daya,kamar wanda aka watsawa ruwan qanqara a lokacin hunturun sanyi,yayin da bugun zuciyar widad din ya qaru qwarai,har tana jin yadda abinda ke cikinta ya takure ya cure waje daya kamar yasan abinda ke gudana tsakanin mamarsa da abban nasa. Sai da yiwa zuciyarta laga laga,ya luguiguitar da ita,ya kuma sauke duk wani fishi dake maqare a zuciyarta sannan ya saketa yana maida numfashi,abun ya zame musu kamar wani faamin ciwo ne da tayar da tsohuwar soyayya da kewar juna da sukayi na nisantar juna da sukayi tsahon satittikan. Saida bugun zuciyoyinsu suka daidaita sannan ya sauke mata kallonsa da wani irin zazzafan kallo dake saka mutum a shauqi,tayita kauce masa tana jin nauyin yadda ta sake masa jiki haka ba tare data iya kare kanta ba,tabbas ta karbi saqo yadda yakeso,don yaga alamun haka a tattare da ita "Widad...." Ya fada muryarsa a mugun sanyaye,bata iya amsa masa ba,shima kuma bai damu ta amsa din ba ya dora da cewa "Fushi kikeyi dani?......wanne irin fushi ne haka widad?,so kike zuciyata ta buga?" Statement dinsa na qarshe ya sakata dago kai da sauri ta kalleshi,ya samu yadda yakeso,ya kuwa riqe qwayar idanunta da kyau ya hanata motsawa. Fuska ta narke cikin salon shagwabar nan tata da yayi mugu mugun kewa "Ba kai bane ba....." Kawai sai ta fashe masa da kuka,gaba daya ta ida rikitashi "Ya salam" ya fada yana matsowa gareta gaba daya yahau aikin lallashi baji.ba gani,har zuwa sanda zuciyarta tayi sanyi "Pardon me please,I assure you it may not happen again" ya fadi hannayensa hade da juna,shi kansa yana mamakin yadda ya dinga misbehaving nata a lokacin,baisan me ya shiga kansa ba,amma a wannan lokacin sai zuciyarsa ke bashi kawai hafsat keda gaskiya,yasan ya mata abubuwa marasa dadi da yawa wannan shine kusan na biyar ko goma,amma ko a fuska tana qoqarin cinyewa,iyaka ta tura masa baki ya kama bakin yadan ciza shikenan an wuce wajen,a wannan karon ne itama ta gwada masa tata matantakar. Kai ta gyada tana sharar qwalla,sai yakejin kamar tana yankar naman zuciyarsa ne "Don't cry mana,haba babyn uncle,It really hurting me when I see you crying" ya qarashe maganar yana tayata sharar hawayen. Fadan masoya hutu inji hausawa,cikin qanqanin lokaci ya wanke kansa a zuciyarta,daga qarshe dai jawa maari qofar sassanta tayi tabi mijinta. Tun daga parlor ya fara sauke mata dakon lodin soyayyarta daya dauka bashi,ta kuwa sakar masa kanta yayi yadda yakeso da ita,harma fiye da yadda ya zata,saboda sabon karatu data sakeyi wajensu fanna,kuka ya dinga mata saboda gaba daya ya gaza controlling kansa,duniyar da widad ke kaishi a duk sanda yake tare da ita......wata irin duniya ce mai nisan gaske da babu a inda yake nasarar zuwa nan idan bata bangaren widad din ba,'yar gaske ce ta wannan bangaren,mai madaukakiyar baiwa da ni'imar da ita kanta bata gama fuskantarta ba. "Me kuma nayi maka uncle kake kuka?" Ta fada tana tura baki gaba,fuskarta a tsakiyar tafin hannunsa,idanunsa jiqe da lema ya girgiza kai yana murmushi "Komai ma widad,komai ma kinyimin" saita zare ido,ya dora hannunsa saman lips dinsa yana fidda mata fararen mayanyan idanunsa "Shshshs.....ba zaki gane ba ko meye zance miki yanzu, I don't know how to stop my self from crying duk sanda na kasance tare dake,bazan iya misalta dad....." Tasan me zaice,kalmar kuma na masifar bata kunya,hakan yasa tasa tafin hannunta da sauri ta rufe lausasan labbansa tana boye kanta,sai ya dora nasa hannun saman nata yadan ciji tafin hannun nata kadan "Wayyo hannuna" ta fada tana janye hannun cikin shagwaba tare da yarfar dashi gefe,ya lakuce mata hanci "Shagwababbiya kawai" suka saki dariya a tare. Tare sukayi wanka,ta shirya cikin doguwar riga umbrella shape data bude sosai,mayyar dogayen riguna ce ita din,wanda hakan ya taimaka sosai wajen sake sirranta cikin dake jikinta,shi ya taimaka mata ta gyara shimfidar gadon da ya yamutsa,hatta da pillows a qasan gadon ya tsinto mata su,tanata tsokanarsa yasha mur cikin wasa yana basarwa "Duk aike kika jawo". *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 12 Sam ya manta da batun dauko hafsat daga wajen saloon,yana biye da widad din suna gyara parlor zuwa kitchen wadanda sukayi mugun kewarta,don duk gyaran da hafsat din zatayi bayayin kamar na widad,ya rasa meye dalili. Tayi masa kira ya kusa guda bakwai,ta cika tayi fam,cikin ranta tanata fadin inda waccar sadakar yallan yakai ai bazai manta ba,tilas ta tare musu drop na keke napep ta kawosu gidan. Dai dai sanda suke kitchen shi da ita,yau jin kansa yake fes,bai gane nauyin yadda yayi rashinta ba sai yanzu data dawo da kulawarta a kansa,ko cikin kitchen dinma taso ya zauna falo ne,amma sai ya kalleta sosai yana saka qwayar idanunsa cikin nata "Bazan iya ba.....kinsan yadda nayi missing kallon kyakkyawar fuskar nan?" Ya qarashe maganar yana shafar gefan fuskarta,inda wani kwnataccen baqin gashi mai sulbi ya mamaye wajen,sai murmushi ya subuce mata,ita da Allahnta ne kawai sukasan yadda ta dinga kokawa da zuciyarta a kansa,bata sake sanin yadda ya samu gurbi cikin rayuwarta ba sai a yanzu data sake riqeshi da muhimmanci......sai da su hajiya fanna suke ankarar da ita game da muhimmancin kula da mallakar hankalinsa ta kyakkyawar hanya irin wannan da take kai yanzu. Kusan tare suke aikin,yaqi ya zauna,saidai gaba daya a rikice yake,yayi yayi tabar aikin yau zaima kowa takeaway amma tace dashi cikin narkewa da karyar da wuya a shagwabe "Dole nayi belin kaina na biya bashin abincin da ban ciyar da kai ba" sosai maganarta ta burgeshi,ta kuma samu kyakkyawan gurbi a zuciyarsa,ya sakar mata wani tattausan murmushi,yana jin kamar ya bude qirjinsa ya maidata ciki,bai taba tunani akwai so mai zafi irin wannan ba. Dan qaramin ihu ta saki tana yarfe hannu,ya watsar da lettuce din hannunsa da yake gyarawa ya nufota, hannun ya kama yana dubawa "Taji miki ciwo?" Saita zame hannun a hankali "Ba sosai bane,na tsorata ne" ta fada a shagwabe,kai ya girgiza "No,ban yarda ba gaskiya.....ajjiye muje,na yafe girkin yau" maqale kafada tayi "Su mimi fa?" "Kowa zai qoshi,baki da damuwa" kafin ta ankara ya sanya hannu ya dauketa cak da hannu biyu "Wai wai wai......kilo dinki nawa baby?.....wait......waima......how many months baby na yake yanzu?" Ya tsaya cak yayi maganar cikin rada. Duk sanda zai mata maganar cikin sai kunya ta kamata,musamman idan ta tuna wautar data tafka,da irin wayon daya dinga mata a sannan na cewa sai ansha ruwa an qoshi ake samun ciki. Kanta ta boye a faffadan qirjinsa tana dariya qasa qasa "Bazan gaya maka ba,nima saina rama" dariya suka saki gaba daya a tare sanda suke shigowa parlor din,hakan yayi dai dai da shigowar hafsat ita da yara gaba daya. Mutuwar tsaye tayi,ta tsaya cak tana kallonsu,sanda ya zaunar da ita saman kujera one sitter ya tsugunna gabanta kan gwiwoyinsa hadi da dora kansa saman cinyarta bayan ya kama hannunta yana sake dubawa......sai taji gaba daya kamar rufin sama ne zai rufto a kanta,jakar hannunta data saka pampers na nawwara da sauran tarkace ta silale daga hannunta ta fadi,ta bada dan sauti abinda yaja hankalinsu kenan. Da sauri ya miqe yana nufarta hadi da fadin "Subhanallahi" sai yasa hannunsa ya kama kunnuwansa ya riqe duka biyun yana kuma fadin "Am so sorry......nayi laifi ko?,bansan za'a gama muku da wuri haka ba,me yasa baki kirani ba?" "Wanne irin nau'in kira kakeso nayi maka abbas?, miscall nawa kake buqata daga gareni kafin ka amsa wayata?" Ta jefa masa tambayar tana kallonsa da idanunta da suka fara zubar da ruwan hawaye,tanajin wani zafi a qirjinta kamar zuciyarta zatayi bindiga. Goshinsa ya dafe,shaf ya manta wayar na a silent "Ya salam.....i forget to......." "To what?!,kada kacemin komai,don babu abinda zaka gayamin da zai sakani yarda da kai,kawai ka shirya cimin mutunci ne,oho.....dama shi yasa ka turani gyaran gashi ni da yara don ka samu kebewa da matarka?,me yasa baka gayamin ba?,ai da ban dawo yanzu ba bare naga cin amanar da kuke aikatamin" "Cin amana kuma?" Widad ta fada cike da zallar mamaki, saboda nauyi da kalmar tayi mata,me yasa hafsat din take abu kamar kwancan hauka?, uncle abbas din kwartonta ne ko kuwa?,ita bataga dukka abinda yake faruwa a gidan ba,oh.....hala ma dadi abun ya mata kenan?,shi yasa a jiya fanna keta mata fada kan matakin da ta dauka,tace sam baiyi ba,zata sake nesanta kanta da mijinta ne hadi da kawo kusanci tsakaninsa da hafsat din,ta gani,ta gani kam "Ke ba dake nake ba,kiyimin shuru tun ban cimmaki na lallasaki ba" wani murmushi widad din ta sake,hankali kwance ta girgiza kai "Wuce nan......wuce nan wallahi,me jiya ma tayi ballantana yau?" "Ya isa....ya isa" abbas ya tsaidasu yana daga hannunsa,hafsat dake kallon widad kamar wata sakarya cike da madaukakin mamaki yadda yarinyar ke kallonta kanta tsaye,ba alamun tsoro ko shayi a tattare da ita,ta dauke dubanta daga kan widad ta mayar kan abbas "Kaga abinda ka jawomin ko a wajen diyar cikina?.....shikenan b......burinka......yac.....cika" tana kaiwa qarshe kuka ya kubce mata,sai tayi dakinta da gudu gudu ba tare data dauke jakarta a wajen ba. Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai mimi da nawwara suka shigo da gudunsu hannuwansu dauke da leda babba "Daddy.....kaga abinda abban kaduna ya bamu,yanata sallama bakaji ba,yace zai dawo anjima" idanunsa dauke dauke da damuwa da bacin rai ya bude yana kallon yaran,abban kaduna amini ne ga mahaifinsa,kuma shine a yanzu ya bashi part daya cikin gidan suke zaune,saboda yana kallonsa tamkar dan cikinsa. "Me aka samo mana" widad ta fada cikin qoqarin kawo raha da kawar da bacin ran data fuskanci ya taba zuciyarsa,ta karba ledar ta bude tana biyewa yaran tare da sako abbas din a ciki. Cikin mintuna qalilan tayi nasarar kore masa bacin ransa,shima ya zauna cikinsu ana rabon kayan wasan yara fal leda da chocolates masu yawa daya kawo musu,sai da aka kusa kiran sallah sannan ya nufi daki yace zai daura alwala,su shirya idan ya dawo zasu fita yayi musu takeaway. Murna yaran suka hauyi,nawwara tace baei ta gayama mommy sai mimi ta jawota "Kina gaya mata zata hanamu zuwa,don Allah kada ki gaya mata kawai kiyi Shuru" Tsaf ta shirya cikin gold laffaya data sake fiddata a jinin larabawa sosai,sanda ta fito parlor din narkewa abbas yayi a wajen yana binta da wani kallo mai nauyi,ko nawa ne.....kuma komai yawan kudi bayajin qyashin kashewa ya siya mata wasu kaya daya gani suka burgeshi ko kuma kayan gyara,saboda ya sani,komai ta saka yana dacewa da ita fiye da yadda ya gansu. Yatsunta ta murza saman fuskarsa tana murmushi "Yallabai" murmushin shima ya saki yana gyara tsaiwarsa "Wudd(so,qauna,soyayya mai zafi)" kai ta langabe gefe,tana jin dadin sunan sosai "Ka yima mommyn mimi magana sai mu wuce gaba daya,kada a dauko mata abinda batajin cinsa" "Saidai ke ki kirata" ya amsa mata yana shafa gefan sumar fuskarsa zuwa habarsa,gaba daya ta gana tsumashi,bai taba ganin mutumin da ciki ya boye sosai a jikinsa,ya kuma yi masa mugu mugun kyau ba kamarta. Kafada ta daga,ta kuma taka a hankali ta nufi dakin. A nutse tare da sallama ta tura qofar ta shiga,da sauri hafsat ta daga kanta tana mamakin jin muryar yarinyar cikin dakin,sai data shiga sosai yadda zata ganta da kyau sannan tace "Maman mimi..... uncle yace ki shirya ki samemu a mota,zamu dan fita shan iska" widad tayi maganar cikin wani salo me aji da gayu. Ashar hafsat din ta saki sannan ta miqe tsaye kamar kububuwa "Ga hanya nan ki ficemin daga daki tun baki raina kanki ba,ke har kin isa na shiga rigar alfarmarki don zan fita da mijina,idan kunje kada ku dawo" fuska tadan yamutsa cikin nuna yanayin alhini "Ayyah....me yayi zafi?,Allah ya baki haquri" widad ta fada qaramin murmushi yana qwace mata,wanda hakan ya sake tunzura hafsat, saita tako kamar zata yo kanta,widad din ta juya ta fice abinta. Ta samu duk sun fice daga parlor din babu kowa,don haka ta tsaya taci dariyar da taketa dannewa "Inda ta kamaki da kinci qaniyarki" ta gayawa kanta da kanta tana ganin tsaurin ido da qoqarin da itama tayi dariya na sake qwace mata. Ta jima tsaye tana duban bakin qofar bayan fitar widad din,ta hango soma wanzuwar raini qarara a tsakaninta da yarinyar,banda haka a baya yaushe ma ta isa ta isko falonta indai ba ita tayi kiranta ba sanda ta maisheta ma'aikaciyarta?,balle har ta samu sararin da zata shigo har daki ta gaya mata magana mai kama da jirwaye,saita koma ta zauna tana huci,ta sake tashi tana laluben su mimi,daga bisani ta fahimci dasu akayi tafiyar,domin kuwa ga kayansu nan tun na safe zube a falon,kenan har canjin kaya tayi musu,ta lailayo ashar ita daya ta dura "Zasu ci ubansu ne,gobe ko dakinta akace su kalla ba zasu sake ba" saita koma daki kwanyarta cike fal da tunani, itakam dai banda uwa uwace,da tace anya ummanta tana mata abinda ya dace da dukka iyayen kudaden da take turawa da sunan za'a yi mata aiki irin wanda takeso?. Widad da kanta ta zaba musu wani eatery suka sauka a can,kowa yayi order din abinda ransu yakeso,yau kam mimi kamar tayi me saboda dadi,don sam a gidansu bata saba ganin wannan rayuwar ba,shi kansa abbas din ba qaramin dadi yakeji ba duk sanda ya debo familyn nasa sukayi fita irin wannan,suna cin abincin suna raha a tsakaninsu,bayan sun kammala yayi musu takeaway suka tafi dashi,ya tsaya wani supermarket ya hado musu da sauran kayan qwalam. Tayi zarya daga dakinta zuwa falon bayan fitarsu sau babu adadi,jiran dawowarsu kawai takeyi,suna sallama tana fitowa daga dakin,sanye da wata riga ruwan madara mai dan qaramin hannu daga can saman kafada,a saman rigar ta daura fallen zani. A yadda taga abbas da widad din sun shigo a tare suna dariya ya sake hassalata,tana isa tsakar falon tasa hannu ta janyo mimi ta zuba mata mari "Gidan ubanwa kika tafi?, daga yau idan akace ki sake binta ba zakiyi marmari ba,saikin gayan uban wa ya baki umarnin fita....." Tayi maganar tana sake cakumo yarinyar kamar ta samu babba,ta kuma ware yatsunta zata sake zuba mata masu,abbas ya dakatar da ita a tsawace "Kina dukanta ba zaki sauke hannunki ba zan rama mata,kuma da izinin ubanta mahaifi ta fita" ya amsa mata cikin tsananin fushi shima. Idanunta dake cakude da bacin rai ta daga ta kalleshi "Me ka shawo a waje?,'yata zan hukunta kakemin shamaki?,to wallahi ba wanda a isa ya hanani hukuntata,tunda ba wanda ya haifa min ita" tayi maganar tana sauke kallonta akan widad da takejin inda za'a bata bindiga yanzu,a kuma bata damar kashe mutum guda daya tak a duniya ita zata harbe,bata sauke dubanta ba abbas ya zare yarinyar daga hannunta yana cewa "Idan kina haukarki kiyi ke daya,karki sake kice zaki huce kishin haukarki akan yarinyata,don abun bazaiyi miki kyau ba" sai ya miqata ga widad dake tsaye tana kallon zallar hauka daga wajen mummy hafsat din. Ganin ya miqata ga widad saita zabura "Karki sake ki tabamin 'ya don baki da iko da ita,idan kinji haushi kema ki haifi taki" waiwaya abbas yayi yayi mata alamar su wuce daki abinsu,kwnataccen murmushi ta sake masa a shagwabe "Take it easy sir.....banason ka qare da ciwon kai please" kai ya gyada yana lumshe ido "I Will handle it in sha Allah" saita kama hannun mimi suka wuce dakinta,suna tafiya tana shafa mata wajen tare da lallashinta,akwai qauna sosai tsakaninta da yarinyar,tana son widad din sosai,wannan yasa itama widad din duk cikin 'yan uwanta tafi sonta,uwa uba ma kama da takeyi da uncle abbas dinta. Shihewarsu daki da mimi ya sake hargitsa hafsat din,ta fashe masa da kuka tana masa hauka sosai,widad dake daki batasan ainihin abinda ke faruwa ba,don bata tantance abinda hafsat din ke fada,amma tashin muryarta da hayaniyarta ta tabbatar har harabar gidan ta isa. Batasna ya suka qarke ba,wajen goma da rabi ya shigo dakin,sosai kansa yake sarawa,qasan zuciyarsa yana ambaton sunan Allah,mutum ne da baya qaunar hayaniya ko kadan,ga hafsat kuma wannan din ba komai bane,ya duqa yasa hannu ya dauki mimin "Ka barta uncle ta kwana a nan" kai ya girgiza kadan "No.....i need space,i want to be with you..... only you" jin abinda yace sai bata qara magana ba,bashi ba,ita kanta tasan tayi tsananin kewarsa,tana kuma buqatarsa,ba zata bari kuma haukar hafsat ya bata musu wannan daren ba kamar yadda hajiya sha'awa tasha gaya mata "Akwai hanyoyi da yawa da kishiya zata iya sace miki kwana,bawai saita hanyar dauke miki miji ya kwana a dakinta ba". Ko inda take zaune tana gursheqen kuka bai kalla ba ya kwantar da mimi daketa baccinta saman gadon,ya gyara mata kwanciyar gami da tofeta da addu'a,ya tsaya sosai bisa qafafunsa yana duban qofa "Ko qwarzane na gani da safe a jikinta,wallahi wallahi ki kuka da kanki" daga haka ya fara nufar qofa "Ai da saika barta wajen uwar daka sake mata" Ta amsa masa tana sakin wani kukan baqinciki daga zuciya zuwa maqoshinta. Kamar yadda ta saba bata barshi ya kwana da wani bacin rai ko tunanin hafsat ba gaba daya,ta dauke dukka wani tunani da hankalinsa zuwa wata duniya ta daban,ta sakar masa ragamarta gaba daya,ya fanshe dukka wata gajiya bacin rai da kuma bashin daya dauka a kanta,shi kansa yasan ya bata aiki da yawa,bashi da wani sauran aiki sai lallabarta da tattalata da ya shiga yi tamkar wani sabon qwai. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 13 *W A S H E G A R I* K'arfe shida da mintuna na saafiya ya baro masallaci,bayan ya gama 'yan addu'o'insa. Daga bayansa yaji tafiya,kafin ya waiwaya an ambaci sunansa,tuni ya gane muryar sai ya rage tafiyar da yakeyi yaja baya kadan hadi da waiwayawa. Karasowa mutumin yayi fuskarshi qunshe da murmushi ya miqawa abbas din hannu,maimakon ya bashi hannun shima sai ya rusuna yana gaidashi cike da matuqar girmamawa. Kin amsa masa yayi har sai da sukayi musabahan,duk da har yanzu abbas bai miqe tsahonsa ba saboda bashi girma "Ban sani ba ko yara sun gaya maka saqona" yayi murmushi "Eh abba.....sunce kazo zamu gaisa" "Eh.....to ma sha Allah,na sake dawowa amma ban samu ganinka ba dai,mu qarasa gidan,inason magana da kai" tare suka jera da mutumin,suna tafe suna dan taba hirarrakin da suka shafesu,har suka isa cikin gidan. Bayan gaisawa da ma'aikatan gidan,kai tsaye suka wuce setting room dinsa. Sunansa abban ya kira yana duban fuskarsa "Nazo jiya sau biyu kamar yadda na gaya maka,saidai duk zuwan da nayi din na iske rikici ne da hayaniya tana fitowa daga gidan har harabar gidan nan,ya akayi kabar gidanka yake neman zama haka?,me yake faruwa?" Gyara zamansa abbas yayi yana sunkuyar da kansa,abban kamar mahaifi yake a wajensa,babu abinda zai boye masa,don haka ya gaya masa komai. Shuru yayi na wasu mintuna sannan ya sauke ajiyar zuciya "Ba yadda za'a yi ka ajjiye mata biyu a guri irin wannan sannan kayi zaton samun kwanciyar hankali,muddin kanason zaman lafiya saidai ka raba musu muhalli,wannan shine kawai hanya daya da zaka samu dai daito akan irin wannan matsalolin,daya bataga 'yaruwarta ba bare wani abu ya biyo baya" kai abbas yake jinjinawa yayi, masa godiya sosai,lallai shawarar abban tayi masa qwarai,ya kuma bashi mafitar da shi a kansa ma bai kawo hakan ba "Amma.....ita hafsatu meye ya dawo da ita kaduna idan ba zallar neman fitina bama?" Abban ya fada cikin mamaki, saboda fes yasan halinta ya kuma san abinda ya wakana wancan karon,abbas din yayi qasa da kansa,yama rasa wacce irin amsa zai bawa abban,Allah shine masanin gaibu,kuma shi daya yasan yadda yakeji a qirjinsa game da dabi'a da halayyar hafsat din,shi kadai yasan irin haqurin da yakeyi da ita "Kada ka damu,kaci gaba da addu'a,sannan kaci gaba da jajircewa,Allah ya kawo mafita ya shige gaba" Ranar bai fita aiki ba,gaba daya sai yaji bashi da kuzarin fita aikin, widad din ta gama kashe masa jiki da xuciya da soyayyarta,a irin abinda take masan,yaso ace gidan nasu kamar daa ne sanda suke daga shi sai ita. Rashin fitarsa aiki ya sake harzuqa hafsat din qwarai,ta sake birkicewa sanda ya fiddo kaf kayansa dake dakin widad da wanda yake dakinta,ya kuma raba komai yace kowacce ta dauka,ranar kamar zata ara hauka "Wallahi na yarda.......yarinyar nan mallaka da asiri takeyi mai matuqar qarfin da yafi nawa" hankalinta ya tashi sosai,tana ganin abubuwan kamar suna fin na baya lalacewa da jagwalewa,ta rasa inda zata tsoma ranta ranar taji dadi,tanason tayi waya kuma tana shakkar kada ya shigo ko wani ya jita,dole ta dinga hadiyar bacin ranta ita kadai zuciyarta kamar zata fashe. To tun daga ranar abbas din ya fara neman wani gidan ba tare da sanin kowa a cikinsu ba,satin gaba kuma da zasuje bauchi hutu,zuwansu na farko bayan tahowarsu dukka gaba daya kaduna. Daren da suka isa da qyar widad takai safiya cikin gidan,saboda wani birkicewa da tayi,an dasa ma zuciyarta wani mummunan tsoron gidan,kwanan zaune tayi tana rusa kuka,tana jin kamar ta fita da gudu tanar cikin gidan,wani irin qunci ne ya cika mata qirji,tana jinta kamar wadda aka jefa cikin dokar daji ita daya. Sosai hankalin abbas ya tashi lokacin da ya biyo da asuba dubata ya sameta firgai firgai,tana ganinsa ta fada jikinsa ta saki kuka,tambayar duniya me yake faruwa ta gaza yi masa bayani,abu daya dai take fada "Banason gidan nan uncle don Allah,ka kaini wajen hajiya ko gidansu nujood" ko fita a part din ta hanashi,bata wani damu da jarabar hafsat da zata iya biyo baya ba saboda zamansa a part din nata ranar kwananta,haka shima abbas din,ba wannan bane damuwarsa,abinda ya sauya widad din yasa ta firgice haka ke bashi mamaki,bayan yasan lafiya qalau suka baro kaduna. Ko part din bai bari ba ya sanyata ta shiga toilet tayi wanka,wankan ma da da tace tayi idan sunje gidansu nujood yace aah,kafin ta fito ya shirya mata jakarta da kansa,ta fito ta shirya agurguje kamar wadda ake jira suka fito ya kulle mata sashen da kansa,yanata binta da kallo cike da mamakin abinda yake damunta. Sai data shiga motar sannan yace mata yana zuwa,ya juya zuwa sashen hafsat. Da sauri ta bar bakin window din,ta koma saman dining tana ci gaba da gyara kwanukan data zuba akai,duk da ba wani abun kirki ta dafa ba,a cewarta ta gaji,ba zata iya wani dogon aikin abincin safe ba. Amsa sallamarsa tayi kamar bataga komai ba,ta daga kai tana dubansa,shima ita yake kallo, already ya saba ba kasafai yake gaidashi da safe ba,wani lokacin yayi mata gyara wani lokacin ya watsar da ita "Zan kai widad gidan muhsin kada ki jini shuru" "A dawo lafiya" ta amsa masa ba tare data dubeshi ba hankali kuma kwance,tana jin wani dadi yana ratsata,sai ya shafa kan yusra dake kwance cikin kujera sannan ya juya ya fice. Yana fita taja wani mugun tsaki sannan ta saki dariya "Habaaaaa yarinya,ki hanani sakewa a can a nan ma ki hanani?,Allah ya raka taki gona,da ikon Allah ma kin fita kenan ba zaki sake dawowa ba" ta sake rufe zancan nata da tsaki,tabar aikin da takeyi din ta koma saman kujerar tana karkada qafa,a duniya ita daya tasan yadda yarinyar tayi mata karen tsaye a rayuwa,duk yadda takai ga zuba iskancinta bata taba fuskantar matsala irin wannan daga wajen abbas ba sai yanzu,ta sake jan wani tsakin "In sha Allahu sai nayi maganinki,bazan gaji ba wallahi" ta fadi a fili kamar ita da wani suke magana. Kamar cirar qaya haka taji bayan fitarsu daga gidan,sai taji komai yana raguwa cikin kanta, nutsuwarta tana dawo mata a hankali a hankali. Sanda suka isa gidan ta shiga ciki mamaki ne ya kama hajjaa,koda ta tambayeta lafiya?,ce mata tayi ba komai,kawai ta gaji da zaman gidanne. Cikin mintuna qalilan ta sake sosai kamar ba ita ba,zuwanta ya yiwa yaran gidan duka dadi,ta ware sosai abinta,har zuwa sanda abbas dake setting room sunata hira da uncle muhsin,irin hirar da suka jima basuyi irinta ba ya tashi tafiya,ta miqe ta yafa mayafin abayarta ta fice don suyi sallama. Idanunsa qur bisa qofar,kamar daman jiran isowarta yakeyi,ta yaye labulen ta shigo a hankali,saiya miqa mata hannunsa,ta kama a hankali ya jawota a tausashe yayi mata masauki saman cinyarsa. Hannusa guda daya ya dora saman cikinta,kamar yasan me akayi yayi wani zillo,tadan motsa da sauri tana zare ido,don har yau ta kasa sabawa da irin wannan motsin,abbas da yaga irin yadda ta motsa sai ya saki murmushi "Kin gani ko?,shi kansa yana cewa zaiyi kewar babansa,amma mamansa kamar bata damu ba" ya qarashe maganar yana langabe mata kai kamar wani maraya me neman agaji. Yadda yayi din ya bata dariya,tadan saki siririyar dariyar data bayyanar da fararen haqoranta dake burge abbas sosai,ta saka hanuwanta duka biyu ta riqe kansa cikin tafukan nata tana dubansa "Mamansa zatayi kewarka fiye da yadda shi zaiyi......" "Amma me yasa kika zabi kibar gidan?,kinsan yadda nakeji duk lokacin da na juya cikin gidan naga babu ke a cikinsa?,widad.....duk gidan da babu ke a cikinsa shida kango daya suke a wajena. ,inji a zuciyata kina gidana wata babbar rahama ce a wajena,kallonki yana bani dukkan nutsuwa da zuciya da ruhi suke buqata.....ban taba kasancewa tare dake ba.....koda wata mu'amala bata shiga tsakanina dake baba tare dana samu nutsuwa ba" yadda yake tsara mata kalaman da yadda yake karanta mata su cikin kunnuwanta sai suka kashe mata jiki,ta matsa a hankali ta kwantar da kanta saman kafadarsa tana rufe idanunta gami da jin yadda bugun zuciyarta ya bugawa a nutse,irin bugun da bata samu irinsa ba daren jiya. Ita kadai tasan irin yadda take fighting da wani mugun tsoro..... tsoro irin wanda bata taba jin irinsa ba..... qunci da damuwa da wata irin qaguwa na tabar gidan,ta matsa a wajen,tana jin kamar tana taka qayoyi a qafafunta duk sanda take taka kowanne sashe na gidanta,amma batasan ya zata gaya masa ba,ya zatayi masa bayani,tunda ita daya takejin hakan,ta sani tana addu'a kuma tana samun sauqi lokaci lokaci. Sun jima a haka suna shan dumin jikin juna,kafin ya dagata yana duban fuskarta "Gobe ne kwananki,zanzo na daukeki,babu cin bashi" narke masa tayi,ya dora yatsantsa saman labbansa "I will bring you back,right?" Murmushi ta sakar masa sannan ta gyada kanta,tashin hankalinta dama yace zata ci gaba da zama har zuwa sanda zasu koma Kaduna. Kwana daya tak tayi yazo ya dauki abarsa,hajja nata tsokanarsa ko surukuta babu?,bai amsa ta ba illa binta da yayi da miskilin murmushinsa. Hafsat ta sake sosai ganin widad bata gidan,hankalinta kwancw tana ganin zata ci gaba da riqe abbas muddin suna bauchi saidai idan sun koma kaduna,a can dinma tunaninta ya fara karkata.....me zai hana tayi wani abu a kaine kwatankwacin abinda ke wakana yanzu?. Sosai shawarar ta zauna mata cikin kai,don a yanzun da take zaune ita daya cikin gidan sai takejin kamar bata da sauran matsala a duniya. Ba qaramin kaduwa tayi ba lokacin da ta fara jiyo qamshi na fita daga part din widad din,qamshin turaren wuta da na abinci duka lokaci guda,sam sam batasan sun shigo gidan ba,daga ita har abbas din,zuciyarta tayi wani irin nauyi,mamaki ya kusan kasheta "Wannan wacce irin musiba ce" ta furta a fili kamar zata zunduma ihu,duk ta inda take hangen nasara sai alamun nasarar sun fara bayyana kansu sai komai ya rushe. Kasa jurewa tayi ta aika yaran su gano mata abbansu yana nan,baya nan din don tunda ya ajjiyeta ya fita yace zaije ya dawo,saidai sun dawo mata da tsarabar lafiyayyen samosa da yaji nama carrot dankali da wadatacciyar albasa. Samosan yana daya daga cikin abinda take mugun so,qyuya son jiki da rashin maida hankali a koyi girki yasa bata iya ba,duk da suna da komai na amfani a gidan da zata iya yi da kanta,sa'annan son kudi da son abun duniya kuma baya barinta ta siya a wani waje,saidai idan anci sa'a ta fita wani gurin sha'ani ta samu a can taci. Duk sonta dashi yau din quncin zuciya da kuma tsanar widad din ya hanata ci,duk da yawan wanda ta bawa yaran,suka sanya abinsu a gaba suka cinyeshi tas suka sha ruwa,duk sai suka hau bacci. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *UCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 14 Tun daga ranar sai ya zamana duk sanda sukazo kadunan gidan hajja take sauka abinta,don a yanzun ta yiwa gidan hajiya qaura,mugun kunyarta takeji saboda cikin da yake jikinta,ranar da hajiyan tayi mata addu'ar Allah ya raba lafiya kamar zata mace a wajen saboda kunya,taso qwarai ma ya dinga barinta kaduna,amma yaqi,saboda hajiyan nayin fada duk sanda yazo babu ita,bugu da qari shi kansa bazai iya wadan nan kwanakin tana wani gari yana wani ba,a haka rayuwar taci gaba da juyawa,har suka share watanni uku,mugun nufin hafsat din bai cimma gaci ba yadda takeso take kuma tsarama ranta,saidai a wasu abubuwan da dama ubangiji kan yiwa bawansa talala ya barshi da zabinsa. *_B A Y A N W A T A U K U_* Sanye take da wata farar gown ta wani cotton material dake da wani irin ado mai qyalli na golden din zare,ta bude sosai daga qasan rigar,hade take da mayafinta mai dan yalwa,tana tsaye gaba madubin dakin nujood tana shafawa fuskarta farar powder,nujood din na saman gadonta daga bayan widad din,hannunta dauke da littafin da widad din ke karantawa,tana tsaka da karatun abbas yayi kiranta kan cewa zai shigo. Yadda widad din keta qalqale jikinta yasa nujood ta kasa yin shuru "Ni banga amfanin wannan qaqale qaqalen da kiketa yi ba,just yaushe kikayi wanka ma?,wannan skin din naki da baya riqe dauda kwata kwata?,a wannan kyan da cikinki ya sakaki kikayi indai baso kike ki matso muninki ba don Allah kibar face dinki haka" murmushi ya qwacewa widad din ta juyo tana kallonta "Uncle abbas ne fa zaizo,ke waya gaya miki ana wasa da lokuttan da za'a kebe da miji,kin mance kishiya gareni?" Dariya sosai nujood ta kece da ita sai itama widad din ta saki dariyar,ta tashi ta zauna sosai saman gadon "Ni wanna kishiyar taki ita da zero duk daya,kinsan Allah tun bankai haka wayo ba nake tunanin uncle abbas me aji,dan gayu wanda bai rasa komai ba.....me ya gani a tattare da wannan wai?,wai kinsan tun asalinta qazama ce?,da sallah abba yayi yayi muje gidan uncle abbas muqi,ya rasa dalili in gaya miki,baisan idan munje wuni muke da yunwa ba,bata iya dafa mana abinci saidai ta hadamu da kayan tarkace,ci banza ci wofi,ga uban wanke wanke da wankin undies da zata hadaka dashi" sauke hannuwanta data goya widad tayi tana jinjina kai,qazantar hafsat din ita kanta tana matuqar daure mata kai,harta kama jikinta,don ko kumbarta ka kalla kasan akwai burbushin qazanta a tattare da ita "Allah ya kawo mata sauqi" "Ai wannan ba zata daina ba har ta mutu" "Banason wulaqanci,mamar yaran masoyina ne fa" widad ta fada tana jifan nujood da hararar wasa,saita fidda ido "Wai yaushe kika zama rasa kunya ne?,komai naki uncle abbas,baki da aiki sai maganarsa?" Fararen idanunta ta juya kafin ta saukesu akan nujood "Kin manta shine rayuwata?,a kansa na fara sanin soyayya qauna kulawa da tattali,a kansa na fara sanin rayuwa, ga kuma d'a ko 'yarsa a jikina" baki sosai nujood ta kama tana gwalalo ido "Na shigesu,widad yanzu kinfi qarfina,Allah yasa dai nima gab nake da auren nan bare ki sani a uku" dariya suka sake qyalqyalewa da ita "Wai nikam......mamar mimi tasan da cikin nan?,banji har yanzu ta nuna kowanne reaction ba" baki widad ta tabe,har zuciyarta bata qaunar zancan matar,ita a yanzun ta mijinta kawai takeyi "Idan nace miki muna iya sati daya bamu hadu ba zaki yarda?" "Haba dai?" Juyawa widad tayi tana zizarawa idonta kwalli "Bata da aji gaba daya matar,da farko kallon mamata ma nakeyi mata,bana iya.musu ko qanqani da ita,ta cutar dani taso gurgunta rayuwata ta hanyar yin amfani da quruciyata,to a yanzun kuma meye yayi saura tsakanina da ita,ina kishin uncle sosai,shi yasa bana hada inuwa daya da ita,har muzo bauchi mu gama zamanmu bama sake haduwa sai a mota idan zamu koma,to me zai hada ni d........" Maganarta ta katse sanda kira ya shigo wayarta,ta duba fuskar wayar tana murmushi "Uncle dina ya iso....."kafin ta daga wayar kiran ya katse,dai dai nan hajjaaa ta turo qofa tana gaya mata tayi ta fito ga uncle abbas dincan a setting room "Saina dawo" ta fada rana zira wani plate white shoes na fata daya dace da qafarta "Allah ya kiyaye hanya Juliet matar romeo" "Babanki ne dai" ta amsawa nujood ta fice tana dariya,itama dariyar ta saki tana bin widad din da kallo,gaba daya rayuwarta da uncle abbas din burge nujood take,wata qauna da soyayya yake bata irin wadda bata iya boyuwa,duk inda kayi musu kallon farko zuwa.na biyu zaka fahimci hakan "Ashe dama uncle din nan dan duniya ne" ta fada qasa qasa a fili tana dariya, saboda ta tuna sanda yake zuwa gidansu,tsakaninsu dashi gaisuwa,sai qarancin fara'a da kuma tsare gida da yake dashi,amma fa duk da haka dama can din shi mai kirki ne da yawan kyauta. A nutse tayi masa sallama da sassanyar muryarta wadda ta tanadeta musamman sabodashi,kasa amsa sallamar yayi,saima ya miqe tsaye cak yana jiran isowarta. Hannuwansa ya bata duka biyun,ya kuma jawota zuwa jikinsa yayi mata kyakkyawan masauki,ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi yana tura kansa cikin mayafinta da kyau,tare da shaqar daddadan qamshin da take fiddawa. Ya jima a haka shi da ita suna jin dumin jikin junansu,kwana biyu tal amma yana jin kamar ya shekara ba tare da ita bane "Ka zauna uncle" tayi qarfin halin fada,saiya dago fuskarsa ya hade da tata "I missed you har bansan yadda zan kwatanta miki ba" "I missed you too uncle" ta fada tana qanqameshi sosai,sai ya saki murmushi tare da ajiyar Zuciya gaba daya,yana jin dadin yadda kullum widad din ke sake zama cikakkiyar mace data karanci abinda yafiso da wanda bayaso,tamkar yana mata sharinga wani part na qwaqwalwarsa ne. Ita ya fara zaunarwa sannan ya zauna a gabanta,ya dauko dukka qafafunta ya dora saman cinyoyinsa yana matsawa a hankali hadi da sauke mata wani narkakken kallo kamar zai cinyeta. Kusan ta saba da irin wannan yanayin,duk da yana azama zuciyarta wani sabon naiyi ne,amma ko tace ya koma saman kujera ya zauna bazai zauna ba,yakance yana matuqar jin dadin hakan,duk da tana zaune sai data rusuna da dukkan girmamawa tace "Barka da yamma yallabai" "Barka kadai yallabiya maman biyu" saita zaro ido "Uncle.....kanason na mutu ko?" Kai ya girgiza da sauri "No.....idan kika mutu babynuncle......na tabbatar a ranar nima zan biki,just kawai ina sha'awar twince dinne,amma tunda bakiso shikenan" ya fada yana dariya cikin ransa,ta wani bata fuska kamar shine mai bayarwa ko kuma yace lallai twince din zata haifa. "Ya bakaso dasu mimi ba?" Ta sake tambayarsa "Ban qarasa gida ba,daga sokoto direct nan nayo.....ba zama ma zanyi ba,ki koma ki dauko abinda zaki dauko mu wuce gida" fuska ta narke masa sosai tana kallonsa "But uncle.....a wajen mummyn mimi ya kamata ka sauka,kuma ma ka manta.....gobe fa na gaya maka zasu wuce kano anty madeena ta haihu,inason na bisu,i missed ummu alort,nayi missing kowa,abba na....su Aarifa da kowa" "I know.....i know,bance kuma ba zakije ba,amma ina buqatar ki cike ragowar kwananki,kwana daya nayi miki aka kirani sokoto,kin tuna?" Baki ta turo masa gaba,a kwanakin gaba daya ciwon mara ne yake damunta,abunka da rashin kan gado fa rashin sanin makama irin na masu haihuwar fari saitake ganin duka takurarsa ne ya jawo mata,don kamar wanda aka qarawa qaimi a kanta,baya iya daga mata qafa a dukka kwanaki biyun da zaiyi a wajenta,shi kansa yasan tabbas tana qoqari,wannan ya qara mata matuqar kima da martaba mai tarin yawa a idanunsa,abinda wadda ta linka shekarunta ta gaza qanqanuwa da ita tana iyayi,kai bama ita ba,hatta da muhsin yanzun ganin girmansa yake qwarai da gaske "Uncle a daina tuna baya fa" "Wannan tuna bayan ya zama dole ai" ya fada yana lumshe ido,yana zagaye lips dinta da suka dan qara tudu kadan da yatsun hannunsa "Nidai nidai" "Baki zuwa?,sai naje na kaima mummyn mimi kwanan naki" ya dauka zatace bata yarda ba,don ya gama sallamawa kan yadda take kishinsa,saidai kishi ne irin na hankali da sanin ya kamata,wanda zakayi zaton wasu shekaru gareta masu yawa,amma sai yaji yace ta yarda. Kicin kicin kuwa yayi,ya kasa ya tsare yace ta shiga ta fito yana jiranta,cikin sa'a Allah ya jefo da uncle muhsin,ya goya masa baya ya tayashi koro qaryarta,harda guzurin "Kada ka yarda gobenma ta wahalar dakai,zasu biyo ta nan gidan su dauketa basai tazo ba". A mota ta dinga masa fishi,bai damu ba ya biye mata kawai,ya yita yawo da ita ya cikata da qwalaman kayan toshiyar baki,bakin kuw aya tosu,ta tasa kayanta a gaba ta dinga ci,saidai a yau din bata wani ci da yawa ba taji ta qoshi. Yau dinma bayan widad din kawai hafsat din ta gani sanda shiga sashenta,mugun kishin da takeji a ranta ba kasafai ma yake barinta take iya mata wani kallo mai tsaho ba,don duk sanda tace zata zurafafa kallonta zuciya na ingizata ta aiwatar da abubuwa masu yawa,wanda ta tabbatar muddin ta aikata hakan sakamakon bazai mata kyau ba,takanji kamar ta samu wani ruwan guba da zai bata mata fuska ta watsa mata,ko tayita dukanta har dai ta galabaitar da ita,ko kuma ta shaqeta har sai ta daina motsi "Baqar matsiyaciya" ta fada a ranta,tana sake jin qwarin gwiwar ci gaba da jarraba sa'arta akan widad din har sai sanda ta cimma nasara. K'arfe sha biyu na rana suka sauka garin kano,cikin gidansu,gidan dake da tsohon tarihin a wajen widad,gidan da tayi wata rayuwa ta gata shagwaba da sangarta,batasan me kalmar matsala ke nufi ba,batasan bacin rai ko damuwa ba,a lokacin ko baka sonta bata jin zafin abun saboda zallar quruciya da rashin damuwa da ire iren wadan nan abubuwan. Duk yadda zuciyarta ke matuqar dauki da son ganin ummunta amma qafafunta da suka dan tasa saboda zaman mota sunqi bata dama,tana hanya kafin ta qarasa su nujood suka dinga wuceta suna mata dariyar sai sun rigata ganin ummu,ta kuwa kebe baki shagwabar ta motsa,hannunta riqe da bayanta dake dan motsa mata lokaci lokaci ta isa falon ummun,dai dai sanda nujood ke dariyar "Saida kowa ya gama gane miki ita sannan kika iso" tureta gefe ummu tayi ta miqe tana cewa "Ba wanda ya rigata gani na,ni na fara ganinta,kuma itama ni ta fara gani" sai widad din tayi qaramar dariya tana jefawa nujood harara hadi da cewa "Munafuki dai baiji dadin halinsa ba wallahi" ta fada jikin ummunta,ummu ta riqeta da kyau,farinciki ya cika zuciyarta gaba daya,widad dinta kullum girma takeyi,kullum kuma alamu suna nuna soyayyar mijinta a jikinta,ta zama wata babbar mace kamar ba ita ba,idan ka ganta zaka musanta shekarunta,ga kuma albarkar aure a tattare da ita,duk da batasan watanninsa ba amma tasan dai ya fara mata nauyi,Allah zai cika mata burinta na ganin dan widad a duniya?,saita share hawayenta cikin dabara ta zaunar da widad din a nutse tana fadin "Me yasa kikayi tafiyar mota ga qafafunki nan sun tasa" "Bazan iya jurewa ba ummu,a taho kano a barni?" Saita girgiza kai tana dariya,kai itama ummun ta girgiza "Ki shiga ciki to ki fidda kayan nan,ki watsa ruwa sai a dumama miki qafar ki shafa man zafi,kici abinci saiki kwanta ki huta" "Duk ita kadai ummu?" Aafiya dake shigowa ta fada,cikin madaukakin farinciki suka rungume juna ita da widad "Wai ashe dai da gaske mun kusa zama iyaye" ta fadi tana kallon cikin widad da wahalar tafiya tasa a yau din ya fito sosai,kamar damar ranar yake jira,kamar jira yake su shigo kano din. Da sauri ta kwabi Aafiya, saboda ita har ga Allah kunya takeji idan akace ciki ne da ita,sai taji kamar ta nutse "Ba abinda ummu fa zata miki,tafi kowa ma murna,randa aka gaya mata ko abincin kirki kasa ci tayi" ta fada tana sheqa dariya,don dukkansu sunsan danbarwar boye cikin data dinga yi,sai suka sanya dariya gaba daya qasa qasa. To wanka da hutu dai baiyiwu wajen widad ba,don gidan nasu cike yake da baqi kasancewar jibi sunan yarinyar da anty madeena ta haifa,baqi anata shigowa,yan uwa da abokan arzuqi gidan a cike yake,wannan ya shigo wannan ya fita,anata hirar yaushe gamo,sai widad din take jin ranta fes,kamar bata da sauran matsala,hatta da wayarta ta mantata a jaka gaba daya. Jin hajjaa zata fita ziyarce ziyarce danginta da nasu uncle muhsin din sai widad din tace zatace,ummu ta kasa ta tsare tace ba inda zata fita,ta marairaice mata da kyau "Don Allah ummu ki barni naje,yaushe rabona da kano,koda zamuje aikin hajji kwana nawa duka nayi,da muka dawo kuma ko gidan nan uncle bai barni na shigo ba muka wuce bauchi" "Ki barta taje ummu,ta dan tattaka ma,tunda acan nasan ba wani waje kike zuwa ba" anty halima dake wajen ta roqar mata ummun. Yawo sukayi sosai harda tafiyar qafa,kafin su dawo kuwa jikinta ya soma gaya mata,a ciwon mara da bayanta ya sake qaruwa time to time,a haka take cinyewa ganin idan ya motsa yana daukan wasu mintuna masu tsaho sai basake motsa mata ba. Basu suka dawo ba sai ana gab da sallar magariba,kai tsaye ta wuce dakin da ummu tasa aka gyara mata ta fidda kayan jikinta tayi wanka da ruwa me mugun dumi wanda mutuniyarta latifa ta hada mata. Tana fitowa daure da towel taji marar tata ta sake riqewa da kyau,saita lallaba ta zauna gefan gado tana cije lebe har zuwa sanda ya lafa mata,ta yunqura zata miqe don ta shirya ta sake ficewa, hankalinta yayi gaba saboda sautin hirarraki da take jiyowa daga falon ummu sai taji ringing din wayarta,ta dafe baki tana mamakin yadda yau wuni sur ta manta da wayarta,suna gama waya da mommynta kiran abbas ya shigo,tunda sukayi sallama ta maidata jakar,tasa hannu ta dauko jakar da aka aje mata saman pillow wanda duka tasan aikin latifarta ne,ta buda ta ciro wayar. Ido ta zazzaro ganin tarin miscall din abbas kusan guda ashirin,ta bude pattern din tana yunqurin kiransa sai gashi ya sake kira. Ajiyar zuciya ya fara sauke mata kafin yayi mata sallama,ta amsa tana jin kewarsa a take tana saukar mata "Kin dagamin hankali sosai,banda yanzun muka gama waya da naadir ya tabbatarmin lafiya da tuni na kamo hanyar kano" ido ta zaro cike da mamaki "Uncle?,da gaske?,kano fa kace?,don kawai ban daga wayarka ba?" Murmushi ya fidda mai sauti,ko yaya zaiyi mata bayanin girman matsayinta a idonsa ba lallai ta gane ba,saidai kwanyarta ta dauki iya abinda zata dauka "Wudd..." Ya kirata da sunan da kaf duniya shi daya yake kiranta dashi,ta amsa masa a tausashe "Matata fa.....da yarona ne suke neman bacemin,yaya zan saka wasa?" Dariya ta subuce mata mara sauti,saita jinjina kai "Allah ya qara maka lafiya da nisan kwana" "Inason hakan musamman ya zamana tare dake zamu mori lafiyar da kuma nisan kwanan" kunya tadan kamata,yadda uncle din yake mata kamar baya tuna cewa ya ninkata a shekaru,ita din sa'ar 'yar abokinsa ce,ba ruwansa da wanann,kwata kwata baya iya boye mata soyayyar da yake mata. Wata irin hira mai sanyi sukeyi shi da ita,sau uku latifa na leqota taga waya takeyi saita koma,basu rabu ba har sai da mararta ta tsikareta tace "Wayyo Allah" cikin matuqar kulawa yake tambayarta lafiya,data gaya amsa yace ta ajjiye wayar taje taci abinci ta kwanta ta huta sosai,gobe sur yakeso ta yini a gida kada ta sake fita,shima a goben tun asuba zai fita shida Samuel zasu sokoto,tayi masa kyakkyawar addu'ar nan tata dake qara masa qwarin gwiwa sannan suka rabu. Doguwar rigar da tasan ba zata takura ba ta sanya,ta zura hula ta sakawa qafarta socks sannan ta fito. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 15 Parlor din kuwa cike yake da surukan ummu da jikokinta,saboda wasu a nan zasu kwana sai ranar suna ko washegari zasu tafi,duka kowa baida matsalar wajen da zai sauka,don gidan nasu badai girma da yalwar masaukin baqi ba. Cikinsu ta zauna latifa ta kawo mata abinci akaci gaba da hira da ita,bataci mai yawa ba ta ture tana yatsina fuska,don ciwon mara da bayan kamar ma yafi na baya. Ummu dake ankare da ita tace "Lafiya?,mene?" "Baya na ne yaketa ciwo ummu" "Ehaan,kaji ba,shi yasa nace kiyi zamanki kika qi,saiki tashi ki shirya bari a yiwa wani cikin yaran nan magana ya dauko mota kuje asibiti" kai ta girgiza "Aah,kawai a bani man zafi na shafa har qafafuwana ma" "Basai taje asibiti sun jagulata ba ummu,tunda naga cikin kamar bai isa haihuwa ba ai,a bata.man ta shafa,zai ware,idan bai ware bama sai suje" anty halima ta fada cikin kulawa. Ummu da kanta ta shafa mata ta kuma tasata a gaba kan ta wuce daki ta kwanta ta huta hakanan,a hadu gobe,tunda hirar tasu bata qarewa,dole badon taso ba ta wuce dakin tayi musu sallama,su kuma suka rakata da sannu. To abu kamar wasa maimakon ciwo yayi baya sai yake qara gaba,tun tana daurewa daga kwance harta miqe ta zauna sosai,kafin wani lokaci mararta ta dauka itama,ta hada gumi sharkaf duk da ac din dake aiki a dakin. Cikin ikon Allah ummu ta leqa dakin da kanta ganin nujood da zasu kwana dakin tare bata gama tata hirar ba bare ta shiga,da sauri ummu ta qaraso tana mata sannu "Bayan ne?" "Harda marata ummu" ta fadi muryarta na karyewa tana dafe da marar saboda wani irin ciwo da take mata. Daga nan inda take bata matsa ba ta fara qwalawa latifa kira,kiran da yaja hankalinsu anty halima suka shigo. "Amma fa kamar mai naquda,kuma cikin kamar baiyi girman da zata haihu ba" Mmn muhassana matar uncle dinta ta fada "Shine nima abinda na gani,inaga ki shirya keda halima ku bita,kome mene zasu fada,Allah ya sawwaqe" ummu ta fadi tana dafe da widad din,kamar ta cire ciwon daga jikinta,ba jimawa naadir yace ya fidda motar,anty madeena na riqe da ita suka fice kowa na mata sannu. Babban private hospital ne daya hada qwararrun ma'aikata a cikinsa,kai tsaye sukayi amfani da file din mommyn muhassana tunda a nan suke ganin likita,kuma family file ne dasu,aka turata labor room bayan sun gama nata gwaje gwaje da tambayoyi. Idanu ta dinga rarrabawa sanda sukayi maganar ta cire pant dinta,bata fahimci me za'a yi ba,ta cire ta tsaya suka buqaci ta kwanta ta kuma bude su gwadata. Qwalla ta dinga yi sosai,ga zafin ciwon mara dana baya ga kuma budetan da nurses sukayi "Labor kikeyi,kuma nan da asuba zuwa wayewar gari zaki iya haihuwa,don yanzun haka kinkai 4cm" abinda suka gaya mata kenan,abinda ta gayawa su anty halima. Mamaki sosai suka dinga yi,don duk kowa kallon cikin suke baifi watanni biyar ba,tunda bai fito ba sosai,ba jimawa suka bata gado da daki,anty madeena kuma tayi waya gida ta gayawa su ummu,nan da nan saiga 'yan gidan sun fara zarya zuwa,itakam widad batasan ma me akeyi ba,don tana labor room private room da aka bata,basu sukabar asibitin ba sai sha biyu na dare,aka bar anty halima da anty deena. *_A R U B U C E T A K E_* K'arfe takwas na safiyar ranar Allah ya bawa widad ikon haifo santalelen d'a namiji mai kama da abbas SAK!,tamkar yayi kakin yaron ya ajjiye,ko kuma photocopy dinsa akayi yana yaro aka ajjiye,wannan kusan itace kalmar da kowa yaga yaron ke fada "Tabdi,wai don Allah a wanne waje wannan yaron yaje ya boye kansa?" Tambayar da anty haleema ta yiwa mommyn muhassana kenan "Kin rigani ne a fili,na rigaki a zuci halima,ciki a ido dan qarami amma yaro tubarkalla ma sha Allah?,wacce addu'a kikeyi ne widad?" Widad dake jingine da jikin gado idanunta a lumshe murmushi kawai ta saki cikin jin nauyi,babu abinda take tunawa sai iein gwagwarmayar da tasha,wai dama hakan kowacce mace keji a sanda tazo haihuwa?,amma duk da hakan duniya cike take da 'ya'ya?. A safiyar ranar asibitin yayi wata irin cika da 'yan uwa da abokan arziqi,duk wanda ke asibitin a ranar ya fahimci lallai haihuwa ce me kima da daraja aka yiwa wannan family,bata wani jima ba suka sallameta bayan sun tabbatar da komai nata lafiya. Ita a cikin jikinta take jin wani banbarakwai,idan ta dubi kyakkyawan jaririn mai fuskar uncle abbas dinta taga wai a yanzun danta ne itama,mallakinta. *A B B A S* Yana tsaye sakiyar parlor din yana saka links din hannun rigarsa,yanayi yana duba agogo gami da dubansu mimi da nawwara da suka sanya yusra a gaba suna mata wasa,su a lallai ga manyan yayye. Lokaci lokaci yana kallon qofar kitchen dinta,ya danja tsaki yana yarfe hannuwa,shikam gaba daya yayi dana sanin sanyata aikin ma,da yasan haka zata jawo masa yayi late da da kansa zai shiga ya hada breakfast dinsa yadda ya saba wasu lokutan,ta sani fa yau din zaiyi tafiyar,amma ta kwanta tana bacci abinta babu abinda ya dameta har sai da ya tasheta, just ruwan baqin shayi da soyayyen qwai amma ya gagara ta kammala masa,a lokacin widad ke ransa,yaji wata muguwar kewarta ta saukar masa,sai yake tunanin zaiyi wuya idan bai biya ya taho da ita ba idan ya tashi dawowa daga sokoto. Wayarsa dake aje saman briefcase dinsa ta dauki tsuwwa,ya sunkuya ya dauki wayar yana duba me kiran,ya dan saki fuska ganin muhsin ne,jiya jiya suka gama waya dashi,ya danyi mamakin kiran,to amma maybe wani abun ya taso ne,saiya daga wayar ya saka a kunnensa. Agurguje suka gaisa ya sanar masa da saqon kiran "Ni zan tayaka murna....ko kaine zaka tayani?,...ko duka mu taru mu taya juna?" Dan murmushi ya sake,fararen jerarrun haqoransa suka bayyana "Eheen......me ya faru?" "Kayi d'a,ni kuma nayi jika,widad ta haihu" unexpected maganar yazo masa,sai ya fidda idanu waje "Bama haka dakai muhsin" "Kuma yau ba zamu fara ba,ka samu d'a na miji alhmdlh" "Allahu akhbar,Allahu akhbar,Alhamdulillah, Alhamdulillah" shine abinda bakinsa kawai ya iya maimaitawa cikin wani irin yanayin madaukakin farincikin da shi kansa baisan adadinsa, uncle muhsin yayi masa barka don tabbas yasan ya fishi cancantar ayi masa barka,ya kuma ce yana jiran goron albishir dinsa sanann ya katse wayar don ya barshi yayi sharing farincikin wa danginsa. Wayar kamar zata fadi a hannunsa haka yaji,ya rasa da wa zai fara sharing wannan abun farincikin,sai kawai ya kamo.su mimi ya rungumesu cikin jikinsa yana ta maimaita hamdalar da tun dazu taqi barin bakinsa "Daddy menene?" Mimi ta tambayeshi tana kallon fuskarsa "Antynku ta haihu yanzu" wani irin tsalle ta buga cikin farinciki tana kallon nawwara "Nawwara mun sake samun baby,anty ta haihu,yanzu mun koma mu haka ko daddy?" Ta fada tana daga yatsunta guda hudu,kai ya jinjina mata murmushi yaqi barin fuskarsa,bakinsa kuma ya gaza rufuwa "Bari naje na gayawa mummy" tayi maganar tana zame jikinta daga na abbas din,ta kuma ruga kitchen da gudu. Ta gama zuba ruwan tea a flask kenan mimi ta fado kitchen din,ta juyo ta zabga mata harara "Ban hanaku wannan guje gujen ba?,saikun fadi ku ishi mutane da koke koken banza" "Anty ce ta haihu mummy" da sauri ta juyo tana dubanta "Wacce antyn?" "Antyn nan gidan,anty widad" wata mummunar faduwar gaba da tunda take zata iya cewa bata taba jinta ba banda randa abbas ya sanar mata qarin aurensa ba taji,ta zaro dukka idanunta tana kaiwa bakin mimi bugu "Kijimin yarinya da shegen jawowa kai masifa,shashasha wadda batasan ciwo da matsalar 'yan uba ba,baku da 'yan uba a cikin gidan nan,kada na sake jin kinyi wannan maganar" dafe bakinta yarinyar tayi duk da Allah ya taimaketa bata sameta da kyau ba "Wallahi mummy d........" Tsawa ta daka mata ba tare data barta ta gama fadin abinda zatace din ba "Fitarmin a kitchen masu shegen surutun da zai halakaka idan bakayi wasa ba"(subhanallah,yana da kyau mu dinga iya bakinmu akan yaranmu,komai qanqantar kalma mu kiyayeta mu guji fadarta akan yara saboda tsanani girma da kuma saurin tasirinta a kansu). Bin yarinyar tayi da kallo harta fice sannan taja tsaki kamar zata tsinke harshenta,ta kuma juya tana ci gaba da rufe flask din,saidai har a sannan qirjinta bugawa yakeyi. Komai ta shirya kan tray,duk da ba wani abun azo a gani bane,amma.bataso takai masa wani abun yace babu kaza ya sake sakata tashi "Maimakon ya wuce ya samu eatery akan hanya yayi breakfast dinsa shima" ta fada cikin ranta tana gunguni,har yanzu zuciyarta ba dadi idan ta tuna abinda mimi ta fada,dole ta kwabi yarinyar don kada ma ta sake magana irin wannan,kada wataran ta fada da bakin mala'iku,'yan ameen suna kusa su amsa. Cikin tray din ta dauko flask da cups din ta fito daga kitchen din,dai dai sanda suke waya da yaaya bara'atu bayan sun gama waya da hajiya "Yanzun ina shirin tafiya sokoto muhsin ya kirani ya gayamin" shuru ya danyi fuskarsa daukr da wani irin murmushi da zai fayyace maka farincikin dake zuciyarsa bazai misaltu ba,ya sake murmusawa sanann yace "Eh wallahi.....an samu baby boy". Cak komai nata ya tsaya da aiki na wucin gadi,kunneta yayi toshewar data kasa jiyo abinda yaci gaba da cewa,kalamansa zuwa ga yaaya bara'atu sai taji kamar ba hausa bane wani yare yake daban,sai ta dinga jinta kamar a duniyar mafarki ko kuma daga bacci ta tashi,daga bisani kuma kamar wadda babbar mota tazo ta daka haka taji kowanne sashe na jikinta ya saki,har kwanukan hannunta suka zame suka tarwatse a wajen,qarar faduwarsu da kuma fashewar flask din mai cike da ruwan zafi yaja hankalinsa daga wayar kan wayar da yakeyi,ya miqe da sauri yana katse wayar hadi da furta *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 16 "Subhanallahi, garin yaya?" Bayan ya iso yana duba kayan,komai ya tarwatse ya hade waje daya,saita duqa da hanzari jikinta yana dan rawa tanason boye hadiye tashin hankalinta,ya duqa shima yana tayata tattare wajen sannan yace "Qanwarki ta haihu......" Ya fada yana tattare wajen ba tare daya ko kula da yanayin da fuskarta take ciki ba "Ta samu d'a namiji ba......abinda ni hafsat na gagara baka har kaje ka qara aure don ka sameshi,burinka ya cika" ta fada da wata irin shaqaqqiyar murya sai kuma ta saki tarkacen data fara kwashewa ta wuce daki tana sakin boyayyen kuka mai bala'in cin rai,komai ya qarasa lalacewa kenan,yaushe akayi cikin?,yaushe harya girma?,sannan data tashi haihuwa ma ba mace ba?,namiji?,saita quma kanta da bangon dakin wanda har tsakiyar kanta taji zafin buguwar da tayin,amma radadi da zafin dake cikin zuciyarta ya zarta wanda taji. Da kallo ya bita sanda take wucewa dakin,mamakinta yana kasheshi,banda yasan bata da aljanu da tabbas wasu lokutta sai yaga ruqiyya ce tafi dacewa da ita,yanzun a batun haihuwar widad din meye abun daga hankali?,harda qirqirar batun d'a namiji da 'ya mace?,bashi karan kansa ba,ko a cikin danginsa ba wanda ya taba zancan mata take haifa,hakanan tsahon zamansu bai taba kawo wannan tunanin a ransa ba banda yanzu data furta,don shi a wajensa d'a duka d'a ne,yadda ake haifar namiji haka ma mace,sai wanda Allah ya sanya yafi wani albarka kawai. Yadda yaran sukayi carko carko suna kallonsa yasa bayan ya gama sharar wajen ya wuce dakin nata bayan ya zaunar dasu a falon,kuka ya sameta tanayi sosai hadi da safa da marwa,ta kasa zama waje daya,ya isa tsakiyar dakin a nutse hannayensa zube a aljihun wandonsa yana kallonta "Hafsat,ki nutsu mana,duka wannan abun na meye?" Sosai tayi qoqarin saita kanta, batason ya karanci yaron da aka haifa takejin buri da muradin mutuwarsa yana ratsata "Na nutsu fa kace,wai meye ka maidani abbas?, yarinyar tayi ciki harta haihu ban sani ba sai ranar data haihu din?" Mamaki ya sake kamashi,lallai idan mutum bashi da abun fada to fada yakeyi da kowa ma "To naji,amma relax please,kin saka yara duka hankalinsu ya tashi,yanzun dai tunda ta haihu ai ya wuce ko?,sai kiyi haquri" ya rufe da bata haquri duk don bayason tashin hankali. Kuka ta sake fashewa dashi ganin wani lafiyayyar nutsuwa da walwala shinfide saman fuskarsa "Ko yaushe cutata kake abbas,ko yaushe zaluntata kakeyi" abinda ta fada kenan,kalmomi biyun da ya tsana kenan a rayuwarsa,ko zai yarda da komai amma bazai dauki kalmar cuta ko zalunci ba akan wani,babban dalilin da yasa yake da abokan adawa sosai akan aikinsa, don baya yarda a zalunci kowa,mai gaskiya ne kai ko mai laifi,kowa sai an tabbatar masa da hakkinsa. Ganin yadda ta birkice ba bisa gaskiyarta ba sai kawai ya juya ya fice daga dakin ba tare daya sake bi ta kanta ba,ta sake tunzura ainun sanda tashin motarsa,data leqa falon ba kowa duka ya tattara yaran ya fice dasu banda yusra da tayi bacci ya kwantar mata da ita saman couch ya tareta da pillow don kada ta fado,saita sake rushewa da kuka,a fili tana cewa "Widad ta haihu?,kuma d'a namiji?" Ta fadi hakan ya kusa sau biyar,tanason idan wai mummunan mafarki takeyi Allah ya taimaketa ta farka,saidai still sake samun tabbacin cewa idanu biyu take tayi,musamman da taji muryar sagir dan yayansa daya dauko yake zaune a gidan,saboda samun security na gidan idan suna kaduna. Yana tuqi a hanya amma tunani barkatai yana zuwan masa,lamarin hafsat ya fara sakashi a kokwanto,ko a labari bai taba ganin mace mai baqin kishi irinta ba,ya maida dubansa gasu mimi dake ci gaba da murnarsu ta samun dan uwa,wanda a gidan basu samu sukuni ba saboda gargadin da hafsat din tayi mata,yaran fici fici dasu,ko wanka babu amma haka ya daukosu saboda yasan idan ya barsu a gidanma akansu zata huce idan ba'a yi wasa ba. Yana tsaida motarsa gaban gidan hajiya ya bude yace su shige ciki,da gudunsu kuwa suka fella,ya dauke idanunsa daga kansu yana murmushi bayan sun shige din,wayarsa ya ciro ya sake trying number widad amma taqi shiga, shikam bayajin yau zai iya kwana bai sanyata cikin idanunsa ba,don haka ya shiga kiran number din suraj karo na biyu "Yaya dai angon qarni" "Don Allah idan ba wani muhimmin uzuri gareka ba,ka ajjiye komai kazo kayimin rakiya kano" "Da zafi zafi haka?" "Kaima kasan bazan iya jurewa ba" ya amsa masa yana murmushi "Bani nan da awa daya" "Godiya mai kima" ya fada yana jin dadi,suraj din aboki ne na gari dake tsaya masa cikin kowanne irin yanayi. Suna gama wayar mimi ta fito da gudu tana kiransa "Wai ka shigo inji hajiya" "Gani nan mimin daddy" ya fada yana dariya hadi da kashe motar,ya fito suka jera zuwa cikin gidan tana riqe da hannunsa tana gaya masa zasuyi party dasu nawwara da qawayenta "An gama mimi na" ya bata amsa yana murmushi hadi da shafa kanta. Da waya a hannu ya samu hajiya,ya tsugunna yana sake gaidata duk da sun gaisa dazu ta waya. A nutse ta amsa masa tana kallonsa,cikin muryar nan dak cike da dattijantaka tace "Wai meye yake faruwa a gidanka Abbas?" Tayi maganar cikin qosawa,sai ta kasa jira yace komai ma "Me dame kake boyewa matarka" sosai ya dubi hajiyan,yasan kwanan zancen "Hafsat ce ta kawo qara ta hajiya?" Ya tambayeta a sanyaye,saita gyada masa kai,tana jin tausayinsa yana kama ta,ya hadiye wani abu mai tauri sannan yace "Wai na boye mata cikin widad,ni kaina ban dauka lokacin haihuwar yayi ba,saboda duka scanning dinta da awon da ake mata bata cemin komai" yayi maganar da sound na damuwa da takaicin dabi'ar hafsa. Zama hajiyan tayi a gefansa sabanin dazu da take zaune,sannan ta fara masa magana da harshe irin na uwa,tana tausarsa da kalamai masu kwantar da hankali da suka sanya jikinsa mugun sanyi,saboda yadda hajiyan ke masa magana kamar wadda ke bashi wasiyya ne "Kaci gaba da haquri,ibada kakeyi,kuma nasan tabbas Allah bazai taba wofantar da kai ba,bazai kuma tauye maka ladanka ba,wataran sai labari,kuma wadan nan abubuwan da dukka nake gaya maka ko bayan raina zaka tuna,nidai abu daya da nake godewa Allah,widad da Allah ya baka,ko babu ni nasan zata kula dakai....in sha Allah" "Hajiya ki daina fadin bayan ran nan don Allah" ya fada yana son katse zancan,sai tayi murmushi kawai "Bara'atu harta kirani tayimin zancan zuwa kano" "Eh nan da awa daya zamu tafi ni da suraj in sha Allah,su kuma ina ganin saisu bari ko bayan kwana biyar ne ko shida ko ranar suna" "Ba laifi hakan yayi,Allah ya tsare" Kaye kaye ta masu uban yawa hajiya ta hadama widad din,a yau tana jin zuciya da ruhinta fes,tana sake godewa Allah da ya bata iko tayi wannan hadin,ko ba komai abbas din ya samu wani sassaucin rayuwar gidansa ta wani gefen. Sun dauki hanyar kano a lafiyayyar motar abbas din,daga shi sai suraj,wanda suraj ke tuqin,hira sukeyi sosai a junansu,wanda kusan fiye da rabin zancan na widad ne, zaiyiwu wuya kawo yanzu muddin akwai shaquwa da aminci irin wanda yake tsakaninsa da suraj kuyi dogon zama baiyi maka maganar widad ba "Ka godewa Allah daya baka wani bangere da zaka dinga samun sassauci,amma koni.ina ganin qoqarinka,tabbas inda nine keda hafsat,da tuni na jima da qara mata mai" murmushi abbas yayi sannan ya miqe ya zauna sosai,ba daga bakun suraj kadai.yake jin wannan maganar ba,sai ya dan dubeshi kadan sannan ya maida dubansa ga titi "Saki ba shine hanyar maslaha kadai ba,bai kamata saki ya zama wani abu mai sauqi ga kowanne magidanci ba,idan hakan kuwa ta kasance al'ummarmu zata zama bata da wata makoma,tunda kowacce al'umma gidan aure shine tushenta,tunda daga can ake samar da nau'i na dan adam,nagartacce ko gurbatacce,wanda daga baya shi zai fito ya zama madubi na al'umma,imma malami jagora ko shugaba,mun ruguxa gidajen aurenmu da aure aure da sake sake,me muke tunanin zamu tsinta a gobemmu?,idan kayi qoqarin gyara ko canza matarka hakan bata samu ba,ba saki bane kawai hanyar da zaka samu gyara,infact idan ma bakayi wasa ba,sai ya bude qofar wata barnar,wani lokaci ya kamata mu dinga duba da wasu abubuwa kafin afkuwar saki,kamar makomar yaranmu,da wanne ido zamuyi musu bayani sanda suka budi idanu sukaga babu iyayensu a tare dasu?,wanne alkhairi matar nan ta taba yi maka a rayuwarta komai qanqnatarsa?" Kai suraj yake jinjinawa,ya jima baiga mutum kamar abbas dinsa ba,ko yaushe yana gayawa kansa da kansa abbas din na dabanne,samun irinsa sai an tona,inda hafsat zata gane waye take aure,lallai ba shakka zata fahimci a duniya tana cikin mata masu sa'ar da ba kowa ke samunta ba. Misalai kala kala yaci gaba da bashi,wadanda suka fahimtar da suraj abbas ya fishi gaskiya da kuma hangen nesa,saidai a halittarsa bazai fa iya daukan abinda shi yake dauka ba. Wayarsa da tayi qara ita ta katse zancan,ya daukota daga inda ya zurata yana duban me kiran, al'ameen ne abokin aikinsa,sai ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da sallama "Oga.......kasan an saki signal kuwa?" Abinda ya fara cewa dashi kenan bayan sun gama gaisawa "Ah.....haba,yaushe?" "Jiya cikin dare,ban kwanta ba sai dana duba list,saiga sunanka a farko farko,You have been promoted to DSP.....congratulations" sosai labarin ya tabashi,saboda baisan ma abinda ke faruwa ba banda al'ameen din ya gaya masa yanzun. Hajiya ya fara kira ya gaya mata,tayi masa addu'a sosai cikin zallar farinciki da fatan ci gaba da samun nasara,widad itace tazo ata biyu,don a yanzun a duniya bayan hajiya widad itace number two dinsa,ya gaza haquri har sai ya isa,tayi amsa addu'a sosai data burgeshi, shigen addu'ar da hajiya tayi masa,sai yaji zuciyarsa tana qara sanyi tare da samun nutsuwa a ransa. "Lallai muhammad yazo da alkhairi da albarka" suraj ya fada yana murmushi,kai abbas ya jijjiga sosai,yana tuna sanda ya samu promotion sanda maganar aurensa da widad din ta taso,haka Allah yake al'amarinsa,yana tsara komai bisa yadda yakeso ya kasance. Daga sanar masa haihuwar zuwa isarsu kano duka duka ba'a cika awanni uku ba, lokacin da sukayi ido biyu da widad din sai yaji gaba daya duniyarsa ta dawo sabuwa,tausayi girma da kimarta suna sake ratsashi,ya sanya hannu biyu ya karba yaron idanuwansa suna qishirwar ganinsa. Wata irin qauna da soyayyar yaron mai qarfi ta saukar masa sanda idanunsa suka sauka akan fuskar da marabarta da tashi shekaru ne kawai "Subhanaka rabbi.....maa a'azama sha'anik, Hasbunallahu wani'imal wakil" ya fadi zuciyarsa na bugawa da soyayyar yaron,ya daga kai yana duban widad da wani irin narkakken murmushi "Yau wannan babyn ta zama uwa.......wannan babyn ta zama maama,babyn uncle ta zama maman baby" kunya sosai ta kamata,ta kama hannunsa ta kifa fuskarta a ciki tana dariya qasa qasa. Tamkar abbas bazai bar gidan ba,yana jin kamar yayita zama yana kallon yaron nasa dama widad din gaba daya,saidai abisa tilas yayi musu sallama saboda tafiyarsa sokoto da dole ta koma washegari. Bai bar garin kano ba sai da ya tabbatar hatta da magi da widad zatayi amfani dashi ya tanadar mata,duk da cewa bata rasa komai ba a gidan,ga jibge mata komai na amfani,banda kayan sawa na barka nata dana baby wadanda musamman ya sake sabuwar siyayya banda wadda sukayi a saudiyya,wanda kowa ya gani sai ya shaida irin soyayya qauna da kuma yadda take da muhimmanci cikin rayuwarsa. A ranar ya yiwa yaron huduba da suna muhammad muhsin,wanda zabi ne ya baiwa widad kuma ta zabi sunan uncle muhsin din "Hakan yayi miki?" Saita gyada kai tana murmushi "Uncle muhsin ya bani komai a rayuwa da yayi silar wanzuwar rayuwata tare da taka,ya bani komai da ya bani kai" ta furta kalaman da wani irin sanyi,har cikin zuciyarta tana jinta cikin mata masu sa'a data samu abbas. Kalamanta sun sake gina mata matsayi mai girma cikin jiki da zuciyarsa cikin qanqanin lokaci,ya saki wani tattausan murmushi "Ni zan fadi haka widad,ya kawowa rayuwata alkhairi,ya kuma yarda ya kawowa rayuwata dauki a sanda take gab da dulmiyewa,samunki wani babbar tagomashi da baiwane daga Allah, ubangiji na ya gama yimin komai,babu abinda zance dashi sai godiya mara yankewa har ya zuwa qarshen numfashi na". ********JEGO widad takeyi sosai,irin jegon da ake kira jego ja ainihi,don hajiya umma kakarta ta wajen mahaifiya wadda ta haifi mommynta ce ta taso takanas daga katsina ta taho yi kata zaman dabaro,tace damar da ba'a basu ba lokacin bikinta ba yanzu zasu nuna tasu bajintar. Nan sashen ummu ta sauka cikin dakin da aka warewa widad din,zamansu gwanin sha'awa,gurin sai ya zama majalisar gidan,abinda ya qarawa widad dadin zaman gidan kenan,sai 'yan qananun abubuwa dake damunta,rashin sabo da raino,da kuma shayarwa da sai an tsaya a kanta take shayar da yaron saboda tsoro da rashin sabo. Gyara iya gyara widad tana shansa,jego take irin na da wanda a wajenta yake kamar takura ce,har sai da anty madeena tace da ita "Ki godewa Allah,ke yar gata ce gaba da baya,irin wannan gyaran da kulawar mata da yawa suka rasa,wanda daga ita ne kika samun sbauwar daraja da kima idan kin samu kula da gyara me kyau,daga itane kuma komai yake qwace miki ki kasa fahimtar inda mijinki ya dosa idan kinyi sakaci da ita". Ta sake yarda da haka bayan hajiya fanna tazo mata barka,daga cikin abinda ta kawo matan itama kayan gyara ne 'yan maiduguri masu shegen kyau,ta kuma jadda mata lallai lallai tayi duk abinda tsaffin suka ce mata,domin sun fita sanin me sukeyi,yadda taga kuma suna kula da ita itakam hakan ya burgeta. Fadin irin alkhairin data dinga samu ma bata baki ne,abun sai ya zamana kamar lokacinne aka yiwa abbas din haihuwar fari,abokan aikinsa kota ina,basajin tafiya daga bauchi zuwa kano ganin jariri,abun har mamaki ya dinga bawa kowa. To amma ba abun mamaki bane,duba da dabi'a da halayyar abbas din,mutum ne mai tsananin kirki kyakkyawar mu'amala da kuma budadden hannun alkhairi ga kowa,haka suka yita karbar jama'a,har akayi kwana biyar,aka fara shirin gagarumin suna. *********Ita kadaice a zaune a falon nata tana yankan farcenta da wannan karon da kanta tayi amannar yayi datti yadda ya kamata,don babu ko sirkin jan lalle a kansa ko baqi balle ya taimaka ya boye datti ko tsahon da yayi. Gaba daya tunda akayi haihuwar takejin wani gagarumin sauyi yana tunkarar rayuwarta,tana fuskantar motsin kowa,kowa cikin family kamar rawar jiki yake da haihuwar,abbas kuwa duk da dama can nutsatse ne,komai nasa kuma bisa tsari da dacewa da kuma mutuntaka yakeyinsa......amma walwalarsa ta qaru dari bisa dari,jifa jifa tana tsintar hirarsa da yaransa akan sabon qaninsu,abinda yake matuqar quntata mata,ya kuma jefata cikin baqincikin da yake sake sakata cin alwashin da takejin muddin ranta ba zata sauke ba,sai taga abinda ya turawa buzu nadi. Ko a yanzun ma da take zaune ita kadai a gidan sai yusra,ya kwashesu suna wajen tailor dinsu karbo dinkunan suna,sunan da batajin ko sama da qasa zata hadu zata bar yaranta suje,badai a gobe zai wuce kaduna ba saboda tasowar wasu ayyuka masu matuqar muhimmanci?,taga wanda zai tareta da maganar zuwansu kano. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 17 Sallamar anty ummee ce ta tsinkar mata da zuciya,a sanyaye ta amsa mata,anty ummee din ta shigo idanunta na dan shawagi cikin falon,cikin ranta tana Allah wadarai da halin qazantar ummeen da har yau ta gaza rabuwa dashi. "Ya naji gidan shuru,ina yaran?" Ta tambayeta bayan sun gama gaisawa,kamar jira takeyi sai kawai ta sakewa ummeen kuka "Ke meye haka?,ai sai a dauka wani abu nayi miki daga shigowata" kamar zuciyarta zata fito daga qirjinta sanda take gayawa anty ummeen damuwarta,sai data gama tsaf sannan ta tabe baki "Ai wallahi yanzu yadda kissa ke ci asirin bai isa yayi wannan aikin ba,ke ko masu asirin aida kissar suke hadawa bawai ki tsaya haka sungungum ba,ni ai tunda umma ta gwasaleni saina tsame hannuna,yanzu ki yiwa kanki hisabi,da lokacin da muke kan takunmu da yanzu wanne lokaci ne kikafi samun yadda kikeso?" Shuru tayi tana nazari,ko ba'a gaya mata ba tasan amsar,a wancan lokacin ta samu dukka wata dama da rashin haqurinta yasa ta gaza kaiwa ga gaci ta koma bin malamai,duk da suma nasu aikin tana samun biyan buqata duk kuwa da bamai yawa bace,amma babu jinkiri a hanyarsu,sha yanzu magani yanzu ne(wa'iya zubillah). "Nasan kin riga da kin baiwa kanki amsa,to koda zakibi malamai saikin hada da kissa,saboda haka idan kin shirya bismillah,duk da dai yanzun bani da lokaci isashe,muna shirye shiryen tashi zuwa sabon gidanmu,idan na hada hankalina waje daya saimu tsara yadda zamu gyara komai,muga kuma yadda Allah zaiyi". A ranar saita samu walwala sosai,daga ganin anty ummeen sai taji kamar matsalarta tazo qarshe,ta dan jima a gidan,wanda bata fita a gidan ba sai data yagi wani abu daga jikin hafsat,bata hanata ba,don itama yanzu taimakonta take nema,daga qarshe ma sai data bawa dan riqon gidanta dan yayan abbas din key din motar ta ya maida anty ummeen gida. Sau biyu tana fitowa tana shige kitchen amma tana ganinsa a zaune inda ta barshi,kusan awa guda kenan yana zaune a wajen,yaran suna kwance daga gefansa sunyi barci. Tunda ya dawo ya watsa ruwa ya zauna zaman cin abinci,ta dire masa abincin ta qara gaba,don tun ranar da widad ta haihu haka take masa,zafinsa takeji,saidai ko.sau daya bai taba nuna mata ma ya gane wai fushi take ba,don shidai kaf a abinda ya faru baiga abin yiwa fushi a ciki ba,shi yasa ya tattara ya bawa banza ajiyarta. Cikin zafi yake amsa wayar tsahon awa gudan kenan da gurbataccen turanci (brooking),da alama yana magana da wasu cikin yaransa ne akan abinda ya shafi aikinsu. Fitowarta ta qarshe daga kitchen din ya sauke wayar a kunnensa bayan yaja tsaki,sau da yawa ire iren abubuwan dake janyo musu bacin suna kenan daga wajen al'umma suke musu kallon abu daya,yanzun ya zama dole ya tafi kaduna a gobe "Zoki dauke yaran nan ki kaisu daki" kakkausar muryarsa da amonta babu wasa kwata kwata a ciki ta ratsa kunnenta,saita ratso ta tsakiyar kujerun ta fara daukesu daya bayan daya,shi kuma ya buda warmer din abincin yana qare ma abincin kallo. Bacin ransa ya sake daduwa sosai,ya maida murfin ya rufe,ya koma.ya jingina da kujera yana sauke ajiyar zuciya,ya dade da sanin irin muhimmancin widad cikin rayuwarsa,amma nisan da tayi dashi a yanzu ya sake haska masa girman da muhimmancin da take dashi ga rayuwarsa. "Idan kinkaita ki dawo" saita tura baki gaba tana cure fuska kamar wadda aka yabawa kashi,tana tsammanin yana buqatar wani abune daga gareta,indai.kuwa hakane yau a jikinsa zata fanshe abubuwa da yawa da ta qudirta,don haka koda takai nawwara sai da taja lokaci sannan ta dawo cikin falon,zuwa sannan ma har ya shiga kitchen ya hada coffe da kansa,don ya gwammace ya shashi ya kwanta akan yaci wannan qaddararren abincin nata. Gefe ta zauna tana hada rai, baice komai da ita ba sai daya gama sha ya dire cup din,ya jawo system dinsa dake cike da rubutu yayi saving ya kasheta,sannan ya bude briefcase din gefansa ya ciro kudade ya ajjiye mata. "Nasan hajiya ta gaya miki gobe zaku wuce kano suna,gashi nan,kudin transport ne dana amfanin gida,nasan zasu isheki harda ragowa ma" ya qarashe maganar ba tare daya dubi fuskarta ba,sai jakarsa da yake rufewa "Ni ba inda zani fa,saboda haka sai sun dawo" wani kallo ya watsa mata bayan ya miqe yana kallon cikin idanunta "Ba shawararki nake nema ba,umarni ne na baki, bijirewa magana ta kuma bazatayi miki dadi ba,banason doguwar magana,gobe zaku kano period" ya juya a nutse yana tafiyar nan tasa majestically kamar bashi da sauran damuwa,duk kuwa da cewa qasan ransa bacin rai ne fal,ga na shirmen da aka masa a office ga matsalar hafsa din da har yau babu alamun gyaruwa ko nutsuwa a tattare da ita sam sam. Dakinsa ya wuce ya ajjiye jakar sannan ya fara hadawa kansa ruwan wanka a mugun gajiye,abinda baisan dashi ba muddin kwanan widad ne,koda ya gama gado kawai ya haye,sannan yaja wayarsa ya kira widad din don ya tabbatar zai samu relief. Ya samu har fiye da yadda yakeso ma,ta sauke masa dukkan wani bacin rai dake ransa,daga qarshe ma video call sukayi ita dashi,ta nuna masa duk wata kwalliyar suna "Wannan ai tsomo ni kawai zakiyi,nayi missing......nayi missing sosai,ina da aiki amma banda haka ya kamata nazo naga kwalliyar sosai" "Za'a yi maka wadda tafi wannan,kada ka damu,ka maida hankali ga aikinka,wanda na tabbatar muhimmncin da kake bashi shine mabudin dukkan wannan nasarorin da kake samu" "Sirrin kuma nasarorin kece ba......nutsuwar da kike bani widad.......I don't know how to explain it to you,you become part of me". Irin wadan nan hirarrakin dake qara dasa kowanne cikin zuciyar dan uwansa su sukaci gaba da gudana,daga qarshe yace a karbo masa muhammad zai ganshi,dole ta ajjiye wayar duk da yadda takejin kunya don yana hannun 'yan suna,ta samu nujood ta lallabata ta karboshi. Ya jima yana kallon yaron ta cikin video call din sannan ya sauke ajiyar zuciya "Bazan iya hana wannan taron sunan ba,amma don Allah..... please na roqeki,ki kulamin da kanki,ki kuma kularmin da yaro na,kada ayita wannan shige da ficen da shi" dariya ma ya bata yadda ya marairaice,kuma yake maganar da gasken gaske "Oh...... dariya ma na baki?, seriously madam......am in pain na yadda za'a kallemin ke a gobe,don Allah ki kula" "Nifa taka ce,mallakinka ce ta har abada,infact ma saboda kai Allah ya halicci widad,no need ka damu,kayi aikinka hankalinka kwance don Allah" maganganu tayi masa masu kwantar da hankali,dole daga bisani sukayi sallama saboda yadda aketa kiranta daga falo. Suna gamawa ya ajjiye wayar yayi addu'ar kwanciya barci,yaja duvet abinsa ko takan hafsat baibi ba. Sanda ta gama baqin ran nata tana zaton zai biyota taga bai biyota ba saita shirya ta taho,koda ta iso tuni ya jima da yin baccinsa,abinda ya qara mata baqinciki da takaici,ta kasa kwanan dakin ta rufe masa qofa ta koma nata dakin. ********Tun asuba ya shirya ya fice abinsa,bai sake tada mata zancan zuwa kano ba alamun zabi kenan ya rage nata. Duk abinta tasan iya lokuttan da take iskancinta,ta sani sarai idan ya kafe bashi da dadi sam,dole ta fara shirin tafiya,bayan ta kira muneera taji qarfe nawa ne tafiyar. A ranar sai data fidda kayan sawarta daga cupboard dinta gaba daya amma ta rasa wanda ya dace ta saka,kowanne akwai nashi illar,sutura iya sutura masu tsada,don abbas baya siyan abun banza,saidai idan ita ya bawa kudin ta siya na banza ta soke sauran kudin,wannan kuwa ko ta kanta baya bi. Wata rigar tasha squeezing,wata bata ga dan kwalinta ba,wata na buga tsami,saboda an saka an maidata cikin kayan ba tare da an wanke ko an barta tasha iska kafin a maidata din ba. Bata taba jin haushin irin abun ba sai yau,so takeyi tayi shiga ta kece raini,amma maimakon taji haushin kanta sai haushin ya tattara akan widad da abbas,kamar dole sai taje sunan?,amma kuma data tuna maganar anty ummee da tace gwara taje ta ganewa idanunta barnar kudin da yayi musu sai taji babu case,taci gaba da bincikawa,da qyar ta dace ta tsamo wata ABC england dark blue,itama a yamutse take,saidai atamfa ce mai laushi cotton sosai,don haka ta fesa mata ruwa ta zauna akai ta samu tadan miqe. Duka mayafanta masu tsada da abbas ke siya sanyasu takeyi cikin kayan siyarwarta ta saida,a nan ma da qyar ta samu wani baqi ta dora,sanann ta laluba jaka da takalmi duka ta yamutsa abinta. Idan kika ganta zakiyi tsammanin amaryar 'yar talla ce daga wani qauyen ranar fitowa daga gidan miji na farko,ga jambaki ja ya kama ya haska baqar fatarta data rasa gyara bare tayi kyan da masu duhun fata keyi idan ta samu kula ba tare da canza launin fata,to amma da yake ba saban bace ta fannin ado da kwalliya,sai take ganin ta gama qure adaka,qarfe goma na safe motar da abbas ya sanya ta kaisu kanon ta iso ta dauketa suka wuce. Daga ita sai gwaggwo mero qanwar hajiyarsu,sannan muneera yaaya bara'atu,sai gwaggwo fanteka da gwaggwo hassana matan uncles dinsa,da kuma qanwar abbas wadda take binsa nasma. Tunda suka dau hanya babu wanda ta kula a cikinsu,saboda kowa fuskarsa babu alamun damuwa ko bacin rai sai ita kadai,har gwara gwaggwo hassana da yake suna da alaqa da ita,takan tabe baki lokaci lokaci ko tayi magana qasa qasa akan tafiyar. A can kano kuwa ko cikin family ranar kowa yasan sha lelen ummu ta haihu,gata tako ina a ranar ya nuna kansa,ba daga wajen mommy mahaifiyarta ba,ba kuma daga wajen ummunta ba,ba daga wajen tsoho mai ran qarfe alh salim ba ko mahaifinta Alhj mahmud da Allah ya dorama son jikan nasa,kamar a kansa aka fara masa haihuwar jika ba,ga kuma mai dungurungum din wato DSP abbas turaki. Wani kalar suna ake gudanarwa,irin sunan da tsiya da babu suke gudu da qafafunsu, komai a wadace,hatta da almajirai da mawadata ranar sun shaida sunan,tun da sassafe widad ke sanya sutura tana canzawa harta fara gajiya,qarfe sha biyu saiga motarsu hafsat tayi landing cikin tsakiyar harabar gidansu widad😂😂😂 _to mai karatu,ya zata kaya ne?,anya kuwa hafsat ayau zata iya cinye kishinta?,kuzo dai mu rakasu ciki mu gani_😂😂🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️ *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 18 Tun daga harabar gidan ta fara fahimtar daga wanne irin gida widad din ta fito,daga yadda taga abubuwa suna gudana tun daga farfajiyar gidan da aka cika da rumfuna jikinta ya fara sanyi,wani irin kishi da bacin rai yayi mata tsaye a wuya,a haka dai ta daure,ta fita a motar,suna biye da hajjaa data zame musu jagora cikin gidan. Tarba ta girma akayi musu bisa jagoranci anty deena,ta shirya komai yadda zai qawatar da baqin cikin girma da karamci,komai kasa cewa tayi,sai idanunta dake biye da komai na gidan,tun daga falo zuwa wani falon da aka tanada don su kadai,ko da mutum guda bata gaisa ba,sai ido da takebin mutane dashi,sannan ta watsar kamar babu ita a wajen. Komai dake gudana gwaggwo mero na ankare dashi,har zuwa sanda suka kadaita a falon,aka kuma turo musu widad dake shirye cikin wani dandasheshen lace da mummyn ta ta dinka mata,wanda kudinsa yakai dubu sittin. Lace dim shine abu na farko daya fara tsone ma hafsat din idanu,tasan kudinsa sarai tunda sana'arta kenan,wani tashin hankali ya rufto mata,har ta gaza dauke idanunta daga kan lace din,tana jin kamar ta tashi ta yageshi daga jikin widad. Duk yadda taso ta tausa zuciyarta ta amsa gaisuwar da widad din ke mata,ranta fes fuskarta cike da walwala amma ta kasa,daga qarshe ma sai tayi bandaki kamar wadda wata buqata ta kama. Kasa riqe kukanta tayi,sai data matsi hawaye sosai sannan ta fito bayan ta waske da dauro alwala,ta riga kowa tayar da sallah tun farkon muhtarin sallar azahar. Tana kan abun sallah ba tare data waiwayo ba,tana jinsu suna yaba yaron da aka shiryashi cikin wasu irin kaya masu asalin kyau da tsada na qasar saudiyya,kowa ya daukeshi sai ya fadi kyau da kuma tsantsar kamannin dake tsakaninsa da babansa,abinda ya sake dagula mata lissafi kenan. 'yan awannin da sukayi ta shiga quncin da sai data gwammace bijirewa zuwan tayi koma meye suyi da abbas din,idanunta sunga abubuwa kala kala,wadanda da wannan bacin rai tayi guzurinsu zuwa gida. Taro ya watse lafiya cike da tarin alkhairi da yaron ya zoma iyayensa biyu dashi,widad kuma ta shiga ci gaba da samun kulawa irin ta tsaffin da sukaga jiya sukaga yau,gefe guda ga gudunmawar yayyen zamani irinsu anty deena anty madeena,da matan abokai na qwarai irinsu fanna da sha'awa. *_DUKKAN ME RAI MAMACI NE_* Cikin sati biyu kacal muhammad da suke kira da affan ya fara wayo da wani irin girma dake alamta qiba zaiyi,daga shi har mamansa widad fatarsu ta qara gogewa,sunyi wani irin kyau na samun nutsuwa da kulawa,jegonta take hankali kwance,kulawa da soyayya tako ina,kusan ko yaushe suna manne a waya ita da abbas din,sukan shafe lokuta sosai suna hira,irin hirar dake debe kewa da sawa zuciya nutsuwa. Kwana biyu kacal yin wayarsu yadan ja baya,data tambayeshi yace hajiya ce bata jin dadi a kwanakin,a ranar sau biyu tana kiran hajiyan taji jikinta,cikin dauriya da murmushi take amsa mata "Da sauqi fa,kawai abbas ya tashi hankalinsa ne" kiran data mata a washegari da safe wanda shine kiran na kusan biyar hajiyan ta daga suka gaisa,ta tambayi dan jikallen nata wanda yake kamar shi daya ne jika a wajenta saboda yadda takejinsa a ranta "Allah yayi miki albarka widad,ya dafawa al'amuranki,kiyi haquri,kiyi juriya,Allah ya baki ikon kula da mijinki da dukka abinda ma zaki haifa a gaba" bata kawo komai a ranta ba,saima nauyin addu'ar hajiyan ta qarshe,duk da haka saita samu kanta da cewa "Ameeen" suka dan sake gaisawa sannan sukayi sallama da hajiyan. A ranar duka basuyi waya da abbas ba,tadan shiga damuwa amma daga baya ta bayar wataqila yanayin aiki ne,wanda wasu lokutan dama idan ya sakasu a gaba basu da wani sauran sukuni har sai sun gama sannan suke samun sauqi. Washegari affan yana saman cinyarta tana shayar dashi cikin dakinta,ita dashi dukkansu sunyi wankansu fes,sai qamshi suke fitarwa,so take ta gama bashi ya qoshi ta kaiwa latifa shi ta goyashi,kamar daga sama sai taji muryar uncle muhsin daga falo,cikin zumudi ta zare maman daga bakin affan ta sanyashi a kafada tana shafa bayansa,don yana shirin fara rigima ne,don da alama bai gama qoshi ba,tayo falon dashi. A tsaye ta sameshi shi da tsoho me ran qarfe da kuma ummu,yadda dukkansu suka bita da idanu haka kawai sai taji ta tsargu,saboda basu taba yi mata irin wannan kallon ba,duk sai taji qafafuwanta sunyi laushi,ta daure ta qarasa falon tana masa sannu da zuwa,ya miqa hannu yana cewa "Bani takwara na,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta tayaki hada kayanki zamu wuce bauchi" sosai maganar ta daketa,ta dubeshi da kyau "Bauchi kuma uncle?,ina cewa yanzu ka shigo?" Kai ya gyada mata "Eh,rakani zakiyi,flight zamu bi,kuma yanzun haka da nasa a siya mana ticket saura awa daya duka duka lokacin tashinmu yayi" kasa ci gaba da tambayarsa tayi,kawai saita juya tayi abinda yace din,saidai ko latifa dake hada mata kayan batace komai ba,bata tambayi ba'asin irin wannan tafiyar ta gaggawa ba,sai ta sake jin cewa lallai akwai wani abu dake faruwa. Samun kanta tayi da gwada wayar abbas don ta tambayeshi yasan wani abu akan tafiyarta?,ta kuma shaida masa tahowarsu amma amsa daya computer ke bashi wayar a kashe take,dukka.layukansa,da personal da na aikin gaba daya,saita jefa wayar jakarta kawai ta dauki mayafin abayarta ta roller ta fito. Sallama ta dinga yi da mutanen gidan,duk da tana gaya musu zata dawo sai tayi arba'in zata koma,ba wanda yace mata komai daga uncle muhsin har ummu,a haka suka fice a gidan ta cikin motar daya daga cikin samarin gidan da zai saukesu a airport. Tun saukarsu a garin bauchi taji gabanta yana wani irin faduwa mai tsanani,nutsuwarta tana neman barin gangar jikinta,ta dauka irin yanayin da take tsintar kanta ne duk sanda sukazo bauchin,amma saita karancin yanayin ya sha bambam da wannan da take tsintar kan nata a ciki,tayita kokawa da zuciyarta har zuwa sanda taga sun doshi hanyar gidan hajiya. Waiwayowa tayi tana duban uncle muhsin "Na dauka gidanka zamu sauka?" "Aah" ya fada a taqaice,daga haka shi da ita ba wanda ya sake magana,har zuwa sanda suka gangara gefan titi suka shiga faffadan layin dake malale da kwalta. Mummunar faduwa gabanta yayi lokacin da taga jama'ar dake zaune a qofar gidan,qarqashin rumfar tempol,qofar gidan cike yake jama'a,haka ta dinga ratsa mutanen qafafunta kamar ba'a jikinta ba, zuciyarta na wani irin bugu,ta kuma kasa tambayar uncle muhsin komai,burinta kawai ta isa cikin gidan ta gano abinda yake faruwa. Bata tsaya ba har sai data isa falon hajiya da shima yake tanqam da jama'a,sai surutai kadan kadan da kuma koke koke,kamar wata mutum mutumi ta tsaya tana qarewa kowa dake falon kallo,bakinta ya gaza cewa komai "Kamata ki zaunar da ita" taji muryar Gwaggo mero tana fada,sai a sannan ta samu qwarin gwiwar kallon hajja dake sama mata wajen zama bayan ta karba affan ta miqawa yaaya bara'atu "Waye ya rasu hajjaa" "Kiyi haquri ki zauna,hajiya ce Allah yayi mata rasuwa" kamar an qwala mata qarfe haka taji,kunnuwanta suka daina ji na wasu sakanni kafin su dai daita, bakinta da dukka ilahirin jikinta ya fara rawa,Allah ya taimaketa ta kama kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kuka mai tsananin qarfi ya qwace mata,sai kuma numfashinta ya fara sarqewa,ta fara kokawar qwatarsa,daga haka kuma saita daina gane komai. Sanda ta farka cikin setting room ta samu kanta ita da hajjaa nujood da bilkisa matar suraj,suna mata sannu amma sake tanbayarsu take da gaske hajiya ta rasu ko kuma mafarki tayi?. "Allahn da ya fimu sonta ya dauki abarsa,addu'a ce kawai zata nuna zallar soyayyar da muke mata ba koke koke ba" nasihar da suka dinga mata kenan cikin kwantar da kai, saita fashe da kuka sosai tana jerawa hajiya addu'o'i har kamar ba zata tsaya ba,a haka suka miqo mata affan daketa rigima ta soma shayar dashi,amma hawayen fuskarta yaqi tsayawa,duk sanda ta kalli affan din sai taji zuciyarta ta sakeyin rauni,yayi rashin kaaka,kuma masoyiyarsa,wanda tun yana ciki take qaunarsa da begen ganinsa amma Allah bai qaddara hakan ba. Ba shakka hajiyan ta dace,domin dukkan wata siffa dake alamta kyakkyawan qarshe hajiyan ta sameshi,kama daga yanayin yadda ta mutu da cikakkiyar kalmar shahada a bakinta,zuwa yabo data dinga samu daga wajen mutane,gidan kamar xai tsage da jama'a,har maqwafta a cike yake babu masaka tsinke. Ta idar da sallar la'asar tana zaune saman abun sallah,har a sannan qwalla bata bar fita daga idanunta ba,tuni kanta yake sara mata da matsanancin ciwo,husna 'yar nasmah qanwar abbas ta shigo mata da abinci,ta kalleta ta kalli abincin "Ina abbansu mimi ne?" "Ni tun safe ban qara ganinsa ba" hankalinta sai ya qara daukuwa a kansa,tasanshi sarai,tasan irin soyayyar dake tsakaninsa da hajiyan,ya kamata a duba halin da yake ciki,itama tunda tazo bataji an ambaceshi ba,don haka ta miqe ta goyawa husna affan sannan ta canza hijabin jikinta zuwa babban daya saukar mata har qasa ta fita a dakin. Da qyar aka gano mata shi a dakin su umar,sanda tayi sallama ta shiga dakin kasa ganinsa tayi saboda duhun da dakin yake dashi,ta laluba makunnin fitilar dakin ta kunna,haske ya wadaci ko ina,mamaki ya kamata ganinsa zaune saman abun sallar, idanunsu suka hadu waje guda,sai taji wani rauni ya ziyarceta,kuka take da muradin yi amma kuma zuciyarta na gaya mata ba haka ya kamata tayi ba. Takowa tayi a hankali zuwa inda yake zaunen har yanzu idanunsu na manne da junna,fuskarsa ta fada wuni guda,sai wani irin jigata da idanunsa sukayi,dab da zata iso ya shafa addu'a sannan ya miqa mata hannunsa,ta dora nata hannun akai,zai mata masauki saman cinyarsa ta zame ta zauna daga gefansa tana kallon qwayar idanunsa dake cike da wani irin tashin hankalin da ba kowa bane zai iya karanta,tsananin jarumtarsa ya boye komai "Yaushe kukazo?" Ya tambayeta da wata irin murya dake cike da sanyi da jigata,ta danyi gyaran murya kadan don kada ta fashe masa da kuka "D'a.....d'az......" Kasa qarasawa tayi,dukkan wata jarumta ta qare,saita fashe masa da kuka harda sheshsheqa,baice komai ba illa rungume kanta da yayi a qirjinsa yana shafa bayanta,yadda kanta ke qirjinsa haka take jiyo yadda Zuciyarsa ke wani irin bugawa a hagunce. Mintuna kusan biyar ta dauka a haka sanann ta fara qoqarin saita kanta,ta daga kai tana dubansa da idanunsa da suka sauya kala,hannu biyu yasa yana goge mata hawayen sanann yace "Nasan ba wannan ne kukan da kika fara ba,pls karki qara yin wani kukan,hajiya bataso,kiyi mata addu'a" kai ta jinjina cikin aro jarumta,ta gaidashi tare da yi masa gaisuwa,don ya fita cancantar ayi masa gaisuwa,duk kuwa da cewa itama kallon uwa takewa hajiyan,ba zata taba mantawa da gudunmawa da soyayya qauna da kariya data baiwa rayuwarta ba. "Amma uncle,me kakeyi a nan kai kadai a duhu?" "Sallah nayi,baki gani ba sanda kk shigo?" Kai ta jinjina "Na gani,amma idan ka shiga cikin jama'a kamar sai yafi,a nan din tunani zaiyi maka yawa ne" kai ya jinjina kawai "Kaci abinci?" Ya sake girgiza mata kai,saita ajjiye masa affan ta shiga cikin gida ta samo masa abinci me kyau,saidai gaba daya ya kasa ci,ya ture plate din yace "Samomin coffee kawai ya isa" haka ta koma ciki ta hado masa coffee din,a hanya ne suka hadu da hafsat tana shigowa goye da yusra,yadda ta dauke mata kai itama haka ta bawa banza ajiyarta ta shige. Coffee din ya shige cikinsa da qyar,ya kama hannuwanta ya riqe cikin nasa yana cewa "Allah yayi miki albarka" don badon tazo ba yanajin azumin yini biyu zaiyi,don shidai ko qyallin hafsat bai gani ba,duk da ya tabbatar tana gidan,don suna gaban gawar hajiya ta shigo gidan tana runtuma ihun da sai da akayi mata magana. Bata barshi shi kadai ba sai data sashi gaba ya fito daga dakin ya koma cikin mutane,duk bayan wasu lokutta kuma tana sawa ana duba mata shi da yadda yake. To rashin mahaifiya wani rashi ne mai mugun ciwon da fadin radadinsa bazai misaltu ba sai wanda Allah ya jarabta dashi, rasuwar hajiya rashine na dukka dangi dama mutanen unguwa,kowa yaga tsananin jarumtar abbas,don ba wanda baisan irin shaquwa da qaunar dake tsakaninsu ba. A gidan yake kwana shi da widad din,amma daki daban daban,hafsat kuwa yaran take diba su wuce gidan iyayenta su kwana,sai kusan azahar take zuwa har akayi kwana uku. Randa akayi sadakar ukun da safe ne tsananin ciwon kai na rashin bacci da kuma damuwa suka sanya abbas a gaba,dole ya buqaci tafiya gida don ya kwanta ya huta,duk da bashi da tabbacin yiwuwar baccin. Farko hafsat yasa widad ta nemo masa su wuce tare,don yasan gidan kansa yayi qura,sanann widad din tana jego ga kuma mutuwar itama yadda ta bugeta tilas tana buqatar hutu,to amma sama da qasa babu hafsat din ba alamarta,dole yasa widad ta shirya suka wuce gidan. Sosai ta gyara masa bedroom dinsa irin yadda tasan yana so,sannan ta shirya masa dan abinda zaici mai dadi da ruwa ruwa,ta kuma hada masa ruwan wanka mai dumi sosai da qamshi,yayi ya canza kayan,ta sashi a gaba yaci abincin ya kwanta sannan ta baro masa dakin bayan ta sanyashi yayi addu'a. Falon ta dawo taci gaba da gyaranshi,tanayi tana duba affan dake kwance yana watsal watsal da qafa,ya cusa yatsunsa biyu a baki. Doko qofar falon akayi lokaci guda ba zato ba tsammani,har affan dake kwance yadan firgita "Subhanallahi" widad ta fadi tana duban bakin qofar. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 19 Hafsat ce a wani birkice sanye da hijabi ruwan qasa,fuskar nan cike taf da bala'i,tun sanda ta dawo taji sunyo gida da abbas din hankalinta yatashi,kullum fatarta da addu'arta yarinyar ta tafi kenan,sai gashi ta dawo rayuwarta tsundum "To mayya natacciyar dole,da kika tashi dawowa ai saiki jira girki yazo kanki,bawai ki biyomin miji kihau aikin da ba naki ba" sosai maganar tata tayi mata ciwo,kamar ba zata tanka mata ba,amma saita dago daga gyaran throw pillows din da takeyi ta kalleta "Maita da naci ga miji inajin isace wannan,wadda bata isa ba ko tayi babu riba,mukan da mukeyi alhmdlh akwai riba, miji kuwa babu wata rana da na kebe da zan tsame hannuna daga bashi kulawa saboda na girkina bane muddin yana da buqatar kulawata,ke meye ya hanaki tsaiwa ki bashi kulawar idan har kin damu dashi?" Ta fadi kanta tsaye tana kallon idanun hafsat da mamaki ya kasheta. Turqashi!,anzo wajen,yau ta samu dama,tanajin babu abinda zai hanata cin uban yarinyar yau abinda ta jima tana buri,kamar widad din ta karanci hakan,kuma bataso tayi abinda zai tada abbas di daga bacci,don haka tayi hanyar kitchen da dan saurinta "Dawo mana qaramar mara kunya kiga yadda ake yinta yau a fidda raini" hafsat ta fada tana bin bayan widad,dama abinda widad din keso kenan,don haka tadan daga qafa,tana shiga kitchen din ta tsaya tana ajjiye plate din hannunta,dai dai sanda hafsat ta qaraso ta dora hannunta a kafadar widad da nufin damqota. Tankwabe hannunta widad tayi cikin fushi tana kallonta "Sakeni,karki sake gigin riqeni,idan raini kikeso a fidda ki bari ya gama baccinsa ya fita a gidan ya zaman dagani sai ke,a sannan zan nuna miki cewa jaa da baya ga rago ba tsoro bane,shashasha wadda har yau batasan ta girma ba" ta dire maganar da tsaki mai mugun qarfi. Tsananin mamaki ya sanya hafsat din mutuwar tsaye tana kallon widad,cikin fushi ta yunquro a karo na biyu kafin tace komai widad ta rigata yin magana "Kika sake kika dora hannunki a jikina.... wallahi tallahi sai nayi miki wanka da wannan ruwan zafin,sauna kawai,shashasha"tayi maganar tana fidda manyan fararen idanunta waje a kan hafsat din. Abu makamancin wannan bai taba hadasu da wida din ba,don haka furucinta ya tabata sosai,sai taja da baya tana tafa hannuwa "Ashe da 'yar kalare nake zaune?,dama kanawa 'yan sara sukane mazanku da matanku?,to shi wanda ya baki daurin qarqashin yimin rashin mutuncin bari na tasoshi" saita juya tana haramar fita a kitchen din. Ai widad bata barta takai qofar ba ta sanya hannu ta fincikota saiga hafsat warwas a qasa,ta isa bakin qofar kitchen din ta tsaya riqe da qugunta "Azzaluma mara imani,wanann baccin dai yau sai ya yishi wallahi duk baqincikinki da baqin halinki" sai kawai taja qofar kitchen din ta kulleta aciki,bata da wata hanyar fita kuma saidai tabi ta qofar baya ta kitchen din ta fice,saita isa qofar part din nasa shima ta kulle,sannan ta saki ajiyar zuciya tana jan tsaki a ranta. Sam ta daina ragawa matar,zata nuna mata ita din bakanuwa ce,duk da ba jininsu bace amma kuma cibiyarta na bunne anan,tana jjn surutanta da zage zagenta sama sama har ta daina ji,da alama tabi ta qofar bayan ta fice. Yayi bacci kuwa sosai,don bashi ya tashi ba sai dab da magariba,a sannan widad din tayi wanka a nan sashensa ta sauya shigarta da wani sky Blue din material me kyau,ta daure kanta da band ta kuma dora dan yalolon mayafin material din,affan na kwance daga gefe cikin farar overall yana bacci abinsa shinfide cikin farin towel. Tunda ya fito yaga dukansu sunyi masa kyau uwa da dan nata,karon farko da ya fara ganin mai jego mai tsafta irin haka,abinda bai saba gani ba,idan hafsat na jego idan kaji ana jaga jaga ko itace,duk wani kalar qarni da bashi bashi zaka jishi,idan anyi magana takance jego take,dama wannan ai shine jegon inji hausawa,sallamawa sassanta dama yakeyi gaba daya,saidai tazo nashi da ziyara ta wuce. Ta daga kai daga wayar dake hannunta tana duba saqonnin watsapp suka hada ido,ya sauke mata murmushi yana jin zuciyarsa tana yin sanyi,ya samu nutsuwa kaso hamsin cikin dari daga qunci da rudanin da zuciyarsa ke ciki,ya durqusa a hankali yayi kissing affan dake baccinsa cikin qauna, qamshin da jikin yaron keyi ya ratsa hancinsa,ya daga kai yana sake kallonsa "Kullum kamanninmu da muhammad sake fitowa takeyi" ya fada da sassanyar muryarsa,ta saki dan murmushi "Sosai.......kun nunamin son kai ai" ta fada tana dan masa hararar wasa,sai ya saki murmushi yana cewa "Ba komai,next time by now ya samu yaruwa,ita na tabbatar zatayi miki karar" ido ta fidda sosai tana kallonsa sannan ta langabar da kai "Habba mana uncle....." Kai ya jinjina yana tarar numfashinta "Yes.....inason yara da yawa babyn uncle,mutuwar hajiya tasa naji ina son in tara yara masu yawa sosai,just pray Allah ya bamu nagari da zasuji qanmu"sai ta jinjina kai tana cewa "Ameen". Bai fita sallar magariba ba sai da yaci abinci ya sake wanka,kafin ya dawo ta sake gyare komai,ta budade falon da qamshi yadda zai masa dadin zama. Sai da akayi isha'i ya dawo,ya zauna a falo suna taba hira,yana kan kujera tana zaune a qasa,qafarsa saman cinyarta tana matsa masa qafafunsa a hankali cikin wani salo da ya sake saukar masa da nutsuwa,kamar an jehota saiga hafsat ta sake shigowa falon tana kumbura. Kallo daya widad tayi mata ta dauke kai kamar batasan Allah yayi ruwanta ba a wajen tana ci gaba da tausawa abbas qafarsa,yayin da abbas din ya tsirata da idanu yana kallonta ba tare da yace komai ba "Daddyn mimi,zuwa nayi na gaya maka ka jawa matarka kunne sanna kayi mana tsakan........" "Dakata da Allah"ya fada da kakkausar muryarsa yana daga mata hannu "Bana buqatar wata hayaniya ko tashin hankali,idan ba zaman lafiya bane ya kawoki ba..... please stay away from here" yadda yayi maganar yana nuna kamar ta gundureshi yasa ranta ya quntata sosai "Adalcin da zakayi kenan?,ba zaka tsaya kaji abinda akayimin bama.....dama kaine kakar daure mata gindi shi yasa kullum take kallon mutane sa'aninta,to wallahi......" "Shut up" ya miqe tsaye a zafafe yana nuna mata hanya "Fita banason hauka" hawaye ne suka balle mata "Yanzu a gabanta kakemin haka abbas?,na rantse da Allah......" Wani mahaukacin mari yakai mata wanda widad ta tabbata inda ya sameta saita rasa haqoran gaba,Allah ya taimaketa ta goce,ba shiri ta juya tana fita daga falon,hannunta dafe da kuncin nata cikin kuka kamar wadda marin ya sameta. Hannunsa cikin kana ya zauna yana yamutsashi,ya samu ciwon kan ya ragu amma tana neman maido masa bara bana,miqewa widad din tayi tayi mazauni gefans kamar zata shige jikinsa,da kalamai da hikimomi data koya ta samu nasarar saukeshi,ya dinga sauke ajiyar zuciya yana matsa hannunta dake cikin nasa,ba shakka mace ta gari rahama ce,inda bai samu widad din ba ashe da haka zai qare rayuwarsa cikin wahala da baqinciki?. A daren tason ya barta ta kwana sashenta ta kira hafsat din ta kwana tare dashi,tunda ita din na abinda zata iya masa amma yace bata isa ba,muddin ta tafi ranta sai ya baci,shiba wani abu yake buqata ba a situation din da yake ciki ba,koda batayi masa komai ba kasancewarta a damansa yafi komai kwantar masa da hankali. Kwanan daga fuskanci widad din tayi ya sake ingizata sosai,wutar qiyayya ta sake ruruwa a zuciyarta,ranar tayi kukan fili tayi na boye,ta kuma tsinewa duk wata kishiya dake duniya. Washegarin da akayi addu'ar bakwai suka shirya komawa kaduna bakin aikinsa,yabar widad a nan don ta gama arba'in dinta,taso komawa kano amma muhsin yace tazo kenan,dan tsoho alhj salim ya goya masa baya,hakama abbanta,don dole ta zauna a nan,amma ta koma gidan hajjaa ne saboda yadda gidan har yau yake bata tsoro. ********To sannu a hankali kwanaki suka ci gaba da tafiya,al'amuran rayuwa kuma sukaci gaba da gudana yadda suke a baya,duk da ciwon rashin hajiya yana zukatansu,amma dole a yadda da hukuncin ubangiji a kuma rungumi rayuwa a duk yadda tazo. Zamanta gidan hajjaa taci gaba da samun kulawa,tana kuma sake gogewa da rayuwa da sanin makamarta. Sanda sukayi arba'in affan yayi wata qiba gwanin sha'awa,yaron kamar ka saceshi ka gudu saboda kyau da wani kwarjini da yake dashi,farat daya yake shiga ran kowa,hakanan itama widad din,kana kallonta zakasan lallai girma da hankali ya soma gameta,ta samu hutu da nutsuwar rai sosai a tattare da ita,ta zama wata big madam,ta kula da jikinta da kyau ciki da waje. Ranar da sukayi arba'in ranar abbas da yammaci ya diro,da safen sunyi waya da tace masa basuyi arba'in ba sai jibi,saboda batason yace mata zaizo,akwai abubuwan da takeson qarasawa,to ashe yana lissafe tsaf da kwanakin. Dariya nujood ta dinga yi mata sanda aka saukeshi a setting room,tana zaune dafa'an a qasan carfet sanye da wata riga me qaramin hannu mai kama jiki kamae robber,sai palazzo pants daya zauna mata sosai ya kuma bude yadda ya kamata daga qasa. Harara ta watsawa nujood din ta miqe tana cewa "Karki bari aji kanmu dake wallahi" tayi maganar tana zare ribbon dinta da yayi sakwa sakwa tana gayara gashinta,duk da cewa itama taji dadi qasan ranta,don ba qaramin kewarsa tayi ba,to amma kuma taso ta kammala komai ne "Bani nakar zomon ba" ta gama gyarawa tsaf ta duqa zata dauki affan nujood ta rigata tana cewa "Rufa masa asiri,kada a jawo masa a matse dan bawan Allah,ku gama gaisawar tukunna sai na kawo miki shi" ta fuskanci jan magana nujood din keji,sai bata sake ce mata komai ba ta juya ta fice. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 20 A tsaye yake yana fuskantar qofar shigowa falon,hannayensa duka zube a aljihun trouser din dake jikinsa,qananun kaya ne a jikinsa da sukayi matuqar dacewa da lafiyayyar fatarsa da kuma qirar jikinsa dake bayyana halittarsa ta qaqqarfan namiji. Tun kafin ta qaraso ya saka hannunsa ya zare baqin gilashin fuskarsa yana qureta da kallo,totally ta sake canza masa,kamar ba widad dinsa ba,a yanzun wata cikakkiyar mace yake gani,wadda komai nata ya cika goma cif cif,kama daga kyan halitta zuwa qirar jikinta,yanayin takunta mai daukan hankali wanda a baya yafi kama da na shagwaba,a yanzun ya zama wani irin taku me aji. Itama shi take kallo sanda ta shigo setting room din,uncle din nata ya canza,yadan rame kadan amma fatarsa tayi fresh sosai,manyan idanunsan nan masu matuqar kwarjini da fusgar hankalin suna tsaye kyam a kanta,sai kawai ya bude mata hannayensa,batayi qasa a gwiwa ba ta tafi a tausashe ta fada,ya maida dukka hannayensa ya kulleta gam yana sauke ajiyar zuciya yana rufe idanunsa "Welcome back abbas" ya furta da murya can qasa,saita daga kanta sa sauri tana duban fuskarta,dai dai sanda shima ya bude idanunsa ya zubasu cikin nata "Back from where?" Murmushi ya saki,ya kama tsinin hancinta yadan riqe sannan yace "from an unhappy life to a life full of joy and happiness" murmushi ya subuce mata,tayi juyi me kyau cikin qirjinsa,tana sake tuna kalaman sha'awa da tace indai mijinki yana jin kece rayuwarsa,indai mijinki yana jin bashi da sauran farinciki da walwala sai idan yana tare dake,lallai kincika mace,kin amsa sunan daya cancanci a hada miki da yabawa. Matseta yayi gam cikin jikinsa yana sansanarta da kyau,duk sai qamshinta ya ida rikitashi,ya fara kai hancinsa ko ina a jikinta yana sansanawa,kafin Wani lokaci sai ya nemi ya birkice mata gaba daya. Itama da qyar ta saita kanta,tadan tureshi tana cewa "Uncle,gidan surukanka kake fa" dauke fuskarshi yayi daga inda ya boyeta cikin jikinta,yana dan jan hancinsa kamar me mura,ya lalubo nutsuwa da qyar ya azama kansa "Oh.....haka.....ina fata kin shirya tafiya" noqe kafada tayi "Uncle,ban gama shiryawa ba,da saura fa" kai ya girgiza,ba zai iya tafiya ya barta ba a yau din,don shi kadai yasan yadda yakeji,shi kadai yasan irin azbtuwar da yayi watannin data dauka basa tare "Pack your stuff we will go home,ko mu wuce a kawo miki kayan daga baya" duk yadda taso ya bari ko zuwa dare ne amma yaqi,dole hajjaa ta kira uncle muhsin a waya ta gaya masa zasu wuce "Har sai an gayamin banda abinki?, shi da matarsa?,tunda ya tako da kansa yazo ya gaza haquri zuwa randa sukayi dashi ai kinga akwai dalili" "Amma uncle,akwai abubuwan da ba'a gama hada mata ba ko.kayanta ma bata shirya ba" "Kinga please stop it......ta bishi kawai,koma meye a aika mata dashi daga baya,tabar hada kayan sawar nata nujood takai mata su gobe ko jibi" hakanan aka bi umarnin uncle muhsin din,sukayi sallama sun cika da kewar affan tun kafin ma su qarasa barin gidan. Sanda suka isa gidan lawal ne ya buda masa gate yana masa sannu da zuwa,daga haka ya saka kai zai bar wajen,sai abbas din yayi kiransa,ya sanyashi debe dukka kayan da suka shigo dasu,yadan rusuna ya gaida widad,ta amsa tana mamakin yadda yau ya gaidata din ma,don dan dakin hafsat ne,ba wani magana bace take hadata dashi ba wanda ya wuce gaisuwa,gaisuwar ma da sai idan sunyi clashing sosai ba yadda zai wuceta. Ba kowa a gidan dama sai mai gadi,sai kuma lawal din da yana shirin fita suka dawo,don haka bayan ya fice gidan sai ya sake zama shuru. Tare sukayi aikin komai da komai,suka gyara part dinsa sannan suka koma suka gyara nata. Cikin lokaci kadan gidan ya koma fes,iska mai dadi hade da wani lallausan qamshi ya shiga kai kawo,ta gyarawa affan kwanciya saman dan qaramin gadonsa da abbas yasa aka hada masa,sannan ta fidda kayanta ta shiga wanka. Tana gama zare towel din jikinta ya tura qofar toilet din ya shigo,ta waiwayo a hankali suka hada idanu,kowa ya kafe dan uwansa da kallon nan mai cike da shauqi da wata irin qauna mai fusgar hankali tare da kewa,ya zame idanunsa a hankali ya saukesu kan qirjinta,wani abu ya jashi kamar lantarki,sai ya gaza ci gaba da tsaiwa a wajen,ya shigo ciki sosai,ya maida qofar toilet din ya rufe. Kayan jikinsa ya fara zarewa,har yanzu idanunsa yana kanta "Bari nayi joining dinki,ruwanki yafi nawa dumi da qamshi" ya fada yana fidda qaramin murmushi hadi da kashe mata ido daya. Kafada ta maqale a shagwabenta,kamar dai widad din nan da aka kawo masa lokuttan baya da suka shude wadda batasan komai ba "Allah uncle wayo dai,iri daya na hada mana fa,kaje toilet din naka ka dub......" Bata qarashe ba ta tsinceta manne da jikinsa,abinda ya kusa sanyata shidewar numfashi saboda yadda fatar jikinsu ta hadu guri guda,daga nan bakin dukkansu ya mutu ita dashi,wani irin feeling mai qarfi ya dinga kewaya cikin jini da zuciyarsu,sai gashi gaba dayansu kowa ya birkice tsananin ita dashi,wankan da ba'a ida gamashi ba,suka zarce zuwa gadonta daya samu kyakkyawan gyara. Kai tsaye zata iya kiran ranar da second first night dinta,don sai komai ya zame mata sabo kamar bata haihu ba,taci wuya a hannunsa,har shi kansa ya shaida hakan,tana rungume tsam a jikinsa,kwanyarsa cike fal da tunani,dama ana samun hakan bayan d'a ya tsaga jikin mace ya fito?,lallai da gaske mata suna suka tara,kamar yadda suka banbanta a abubuwa da dama haka suka banbamta ta wadan nan guraren. Sati guda sukayi a bauchi suna bare wani amarcinsu,irin amarcin da a baya ma bai sameshi ba,a yanxun ya samu fiye da abinda yakeso,ya samu fiye da yadda yake zato,ya kuma samu fiye da abinda yake tsammani,gaba daya widad din ta gama zama cikakkiyar mace ta kowanne fanni,yana samun fiye da abinda yake buqata daga wajenta,bata fannin kwanciya kadai ba..... a'ah,ta kowanne fanni ma ta cike masa dukka wani gurbi. Wannan yayi matuqar tasiri a rayuwarsa da zuciyarsa,ta sake shiga ransa da wani irin matsayi mafi girma da yakejin kaf kafin duniya a yanzu babu diya macen data takashi. Randa suka cika kwanaki bakwai ranar suka tattara suka wuce kaduna,kai tsaye kuma ya zarce da ita sabon gidan da ya kama mata,ya kama haya ne saboda bashi da tabbacin zasu yita zama a Kaduna,koda yaushe yanayin aiki yana iya canzashi daga kadunan zuwa wani gari na daban. Yayi mata ba zata matuqa,al'amarin kuma da ya faranta mata rai fiye da zatonsa,ko ba komai zata samu sakewa,ta rabu da wata matsalar,zata kuma tattara hankalinta ta kula da mijinta da kuma yaronta yadda ya kamata,gida ne two bedroom,kowanne da toilet a ciki,kitchen parlor da kuma dining area,sai madaidaiciyar harabar da zata iya dauke motar abbas din,yayi matuqar tsaruwa gidan,dole ya burgeka,an shirya komai bisa mizanin hankali da ilimi. *H AF S A T* Batasan cewa zata damu ba da gidan da widad ta koma din ba sai bayan ta koma din,tunda ita da kanta ta zaba cewar ba inda zata motsa daga nan gidan da suke,saidai ita widad din ta qara gaba ta barta,tunda itace babba,babu mai cire gwamnatinta. Murmushi kawai abbas ya saki sanda take wannan bayanin cike da izza fariya da kuma alfahari "Gwamnatinki saidai kuma wata,mai guri yazo mai tabarma dole ya nade abarsa" abbas ya fada cikin ransa,yana matuqar tausayin hafsat din amma ita sam bata tausayin kanta,yana hango mata rasa abubuwa da dama cikin rayuwarta amma ita bata gani,Allah ya sani,ko ra'ayin auren mata biyu baya dashi,ko meye ya faru tamkar itace ta bashi lasisin aikata hakan. Widad kam cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta tsara gidanta ta kuma ci gaba da tafiyar dashi,cike da qwarewa da kuma gogewar da take sake samu daga mutanen dake tare da ita,cikin ikon Allah ta hadu da maqota na qwarai,macace mai matuqar karamci dake kallon widad din kamar qanwarta,jininsu ya hadu qwarai tashi guda,wannan ya sanya widad din taja babbar 'yar matar da ba zata wuce shekara sha daya ba a jiki,aminatu yarinyar nada matuqar hankali,ta iya komai ita kewa mamanta ayyuka da yawa,amma yawan alkhairan widad a garesu ya sanya maman tabar mata ita,rainon affan da sauran 'yan aikace aikace ita take mata,wannan ya sake bata nutsuwa a zaman gidanta,tana dame debe mata kewa kuma ta rage mata ayyuka,saita samu cikakken lokacin tsara duk wani abu da zai faranta ran abbas ya kuma sake zaunar da ita a ransa. Gidanta yana dab da wajen aikin abbas,wanda ko a qafa zai iya takawa ya qaraso gidan nasa,abu na farko kenan daya soma hana hafsat sukuni,ta dinga tunani kala kala,a duk ranar kwananta bata da kwanciyar hankali harma ranar da ba tata ba,tana ganin a yanzu widad din ta fita samun kusanci dashi,kamar ko yaushe suna tare,kwata kwata a lokacin tunaninta bai bata hakan zai iya kasancewa ba,kawai a sannan tanaso ta nunawa widad ta koreta daga mazauninta ne don ta isa,ita kuma ta maye gurbinta,daga iya haka tunaninta ya tsaya. *F I T S A R I N F A K' O* Tunda ta dawo kusa ya daina cin abincin rana a ko ina sai gida,idan ayyuka sun masa yawa sai ya aiko yaransa su daukar masa,idan kuma ya samu chance da kansa yake dawowa yaci abincinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ya koma,wani lokaci ma idan akayi sa'a aminatu ta fita da affan ko suna dakinsa sai ya more lokacinsa sosai sannan yake komawa din,a wannan lokacin ya samu wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali daya jima bai samu irinta ba,don har wata qiba da murjewa ya sakeyi,gaba daya hafsat da matsalolinta ya sanyasu a mala,dai dai da abincinta ba damuwarsa bane yanzu,ita kanta ta lura da wannan sauyin daya sake daga mata hankali matuqa,har take ganin widad din ta fara aiki a kanta ne da 'yan tsubbu don ta janye hankalinsa daga kanta,ko sau daya a tsukakkiyar qwaqwalwarta bata taba shawartarta ta duba inda ta gaza ta gyara ba. **********Tunda ya sallameta a safiyar dazu data fita a girki ranta yake suya,komai nata yanzun ya koma yana shakulaton bangaro dashi,ta kalli inda ta ajjiye masa gantalallen breakfast din da ko ta kansa baibi ba ranta yana sake baci,zuwa azahar ta gaza daurewa,bayan mimi ta shirya kanta ita da nawwara ta zubasu a mota ta ajjiyesu a islamiyya duk da ba ita ke kaisu ba,sai kawai ta dauke kan motar tata tayi hanyar police college. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 21 Riqe yake da hannunta gam cikin nasa,yana sauraren shagwabarta da 'yar qaramar muryarta mai taushi,murmushi ne yake fita kadan kadan daga saman fuskarsa,har bayason ta dakata daga magiyar da take masa, sosai muryarta take masa dadi,ta narke masa sosai,ita kano takeson zuwa,shi kuma baya jin zai iya barinta a yadda yakejinta cikin rayuwa da zuciyarsa a yanzun tayi nesa dashi. Wata farar long sleeve blouse ce a jikinta fara sol,sai mini side button skirt a jikinta mai tsaga daya baya shima fari sol,ta kame gashinta mai tsaho da sulbi a tsakiyar kanta,jikinta ba abinda yakeyi sai fidda tattausan qamshin turarenta daya hade da kabbasar da takewa kowanne kaya nata da mabanbantan qamshin turare. Tuntuni ta gama haddace yadda yake mutuwar son yaga tayi shigar qananun kaya,wannan ya sanya ta mayar dashi al'adarta,don zata iya cewa ba zata iya tuna sau nawa ta saka atamfa kace ko material a jikinta ba muddin tana cikin gidan,walau ran girkinta ko ba ranar girkinta ba,har ya riga da ya zame mata jiki,hakanan fararen kaya na mugun yi mata kyau,da yake kuma ya hadu da mace mai tsafta idan ta saka saika dauka kowanne sabo ne bata taba sakashi ba. Gidan ba kowa shi yasa ta baje masa tabararta sosai,har yaji kamar bazai iya komawa gurin aiki ba,dama cin abincin rana ya dawo dashi,affan yana wajen aminatu,tun daxun gab fa zata gama abincin rana ta goyashi suka shiga gidansu. Waiwayowa yayi,har yanxu murmushi na bisa fuskarsa yana dubanta,sai ya zare hannunsa daga nata "Baby......wallahi kinason yau nayi satar kwana kenan,da irin wannan shagwabar taki zan kasa kaiwa yayarki kwananta fa" kai ta girgiza tana dan bubbuga qafa "Nidai ba ruwa na,abinda nace kawai inason naje kano,sanya ranar Aafiya za'a yi fa" "Ba yanzu ba baby.....idan bikin ya taso dai zakije" jikinsa ta shige tana fadin "Don Allah.....don Allah" dai dai sanda aka angizo qaramar qofar dake jikin gate din gidan aka shigo. Idanuwanta a kansu,zuciyarta na wani irin bugawa,wannan shine karo na hudu da zuciyarta ke raya mata yana gidan yarinyar,kuma idan tazo din take cimmasa,bata taba kuskuren zuwa bata sameshi ba. Waiwayawa sukayi gaba dayansu suna kallonta,widad ta janye idanunta tana jan tsaki can qasan ranta,ko daya bata sani ba,bata kuma gane dalilin wannan safarar da take musu a gida ba,bayan ita tunda tabar gidanta bata sake koda marmarin taka qafarta ba,idan ta shiga unguwar ma,mutanen da sukayi zaman arziqi tajewa jaje ko taya murna,daga nan kuma bata qarawa ko ina take dawowa gida abinta,duk da tanason ganin mimi amma haka take haqura. Dage tayi sosai,ta mannawa abbas din kiss a goshi a tausashe sannan tace "Allah ya kiyaye hanya,im gonna miss you baby" ta danyi rolling idanunta hadi da daga masa hannu,taja baya a hankali tana takawa zuwa cikin gidan,da gayya take juya mazaunanta da kyau,duk kuwa da cewa koda batayi hakan ba salon tafiyarta ne dake tafiya da abbas din ainun. Tare sukabi bayan nata da kallo shida hafsat din,nashi kallon na zallar qauna tare da jin wani iri,kwana biyu kawai da zaiyi ba tare da ita ba sai yakejinsu kamar shekara dubu,duk da zai leqota a qalla sau biyu a wuni kafin ya tashi a office,yayin da kallon hafsat ke cike da wani mugun baqin kishi,wanda a wannan lokacin inda zata samu dama tabbas saita nakasta wannan surar da akemata barazana da ita. Kasa jure ci gaba da kallonta tayi,sai take ganin kamar taqi sauri ta shige falonta ne da biyu,ta maido dubanta ga abbas din,saidai gaba daya hankalinsa baya kanta,kamar ma ya manta a inda yake tsaye,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,har taji ba zata iya magana ba,sai kawai ta juya da mugun sauri ta koma cikin motarta,wadda ko kasheta batayi ba saboda tsabar sauri ta shiga ta rufe murfin da mugun qarfi,taci ribas ta fice daga layin. Qarar buga murfin motar ne ya dauki hankalinsa,ya juya yana kallon qurar data tayar,sai a sannan ma komai ya dawo masa,yaushe sukayi da ita zata fita?,ya gyada kai ransa na mugun sosuwa,ya taka yana fita a gidan ya nufi tasa motar don ya koma office. Gudu kawai take shararawa a hanya,sauran masu ababen hawa dake bin hanyar sunata binta da kallo,wasu na kaucewa wasu suna Allah wadai da ita,kuka takeson yi amma idanunta sun soye,a bisa qa'ida ai ya shiga lokacin girkinta,karo na hudu kenan tana ganin irin haka,dama wannan shine dalilin da ya sanya ya canza mata gida ya kaita kusa da office dinsa?,zaizo zasu hadu,yau din saidai kowacce wacce. Batasan abbas din ya fita bacin ran fitar da tayi ba tare da izninsa ba,ba kowanne sakarci yake dauka ba ko kuma ya qyale,tunda suke da widad koda wasa bai taba kamata da laifin yin leqe bama bare har takai ga fita,fitarma irin tata mara tushe bare ma'ana,tunda me tazo yi gidan widad din a wannan lokacin?,abinda ta saba?,bin qwaqwafi da bin diddigin yarinyar da ta haifeta?,bai taba jin widad tayi zancanta ko ta damu da lamarinta ba,amma ita ko yaushe damuwarta widad,ko yaushe qorafinta yana kan widad din,sai yaushe ne zatayi hankali?,yaushe zata gyara halinta?. Lokacin da ya koma gida baibi ta kanta ba,hidimarsa ya shiga yi da yaransa,hatta da abincinta ma bai nema ba,ya shiga kitchen ya dafa musu wani bayan ya tambayi yaransa me sukeson ci. Banza ya bawa ajiyarta suka baje a qasan carfet da yaran suka hau cin abincinsu,kamar ma baisan da wanzuwarta cikin falon ba. Ta sake cika tayi fam kamar zuciyarta zata fado saboda yadda take mata ciwo,cikin sa'a za'a ce ko rashin sa'a mimi tace "Mummy ke bakyacin abincin?" "Zan tsinka miki mari,aiba a yunwace kika ganni ba ko?" Sauke idanunsa yayi a kanta a nutse,sannan ya motsa labbansa "Tashi kibar nan gurin" a dan fusace ta kalleshi,amma a kallo dayan ta karanci bacin ran dake kwance cikin qwayar idanunsa,saita miqe da wani irin qarfi tana kade jikinta,amma kuma ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Ki miqomin key din motarki yanzun nan" ya bata umarni nakai tsaye ba tare da ya ko dubeta ba " a mamakance ta juyo tana kallonsa,amma ko kallon inda take baiyi ba,ta dauke kai ta jinjina sannan ta taka zuwa ciki,ta dauko key din ta dawo ta ajjiye masa ta wuce daki wasu hawaye masu zafi suna qwace mata. Koma wanne karin magana bahaushe yayi akan kishiya,koma meye aka fada akan kishiya tabbas ya dace da ita,wasu baqaqen dabi'u da halaye da batasan dame zata kwatantasu ba abbas din ya koyo,saidai koma meye ita ba zata taba bari widad din taga faduwarta ba. *_A N K U M A M A C E T A H A I F I M A C E inji bahaushe_* Watan affan bakwai dai dai wanda yayi dai dai da samun qarin matsayin abbas din ya sake samun wani promotion din daga DSP(deputy Superintendent of Police) zuwa SP(superintendent of police) din gaba daya,wani irin ci gaba da budi yaketa samu tako ina wanda bai zaci samunsa haka a kurkusa ba. Randa aka saki signal sunansa ya fito widad din na falo a kwance,sanye take da wata armless chiffon gown,yatsunta na hannu da na qafa sunsha jan lalle jajir gwanin sha'awa,basu jima da dawowa daga wankin kai ba ita da aminatu,ta dauki affan suka fice sai ita kadai a gidan,gashinta mai tsaho santsi da baqi yayi kyau sai sheqi yakeyi,wannan gyara ne daya zame mata jiki jiddin zaka sameta cikinsa. Yau din ba ranar girkinta bane,sai a gobe zata karba girki,amma ta gama shirya tarbar abbas din tun a yau din,ta gama komai,zuwa yanzun yadda abbas din keyi a kanta ya daina damunta,ta riga ta saba,ya zamar mata jiki,hasalima tausayi yake bata,don ta tabbatar inda yana samun kulawa yadda ya kamata daga wajen hafsat itama zata samu sauqin wani abun,to amma ita daya ce ke iya kashe masa qishirwar komai,ita kadai ke tsaye a kansa take samar masa nutsuwa da kwanciyar hankali. Tunda ya duba sunansa yaga ya fito yaji har cikin jiki da zuciyarsa ita yafi dacewa ta fara sani,a nutse yake tuqa motarsa bakinsa dauke da hamdala da godiya ga Allah fili da badini,don yayi masa dukkan wata baiwar da rufin asiri,kuma dama a rayuwa baka taba samun komai cif cif dari bisa dari. A kofar gidan ya kashe motarsa sannan ya fito,yasa key ya buda gidan yana sanya kai,yau gaba daya aiki ya sashi a gaba,ko zuwa ya dubasun da yakeyi baiyi ba sai yanzun da ya samu break,amma da yake gwanar alkunya ce tare da yi masa uzuri,da sukayi waya ita ta fara bashi uzuri ma kafin ya bata. Lumshe idanunsa yayi sanda ya tura qofar falon,sassanyan qamshin nan na kullum da kullum dai shine a falon cakude da sanyin ac da aka daidaitashi dai dai da buqatar dan adam. A duniya gidanta ne waje na farko da yake fara saukar masa da nutsuwa a rayuwarsa,bazaiqi ya dawwama a cikin gidanta ba kaf rayuwarsa,yasan bazai rasa komai ba,ba kuma zaiyi kuka da Komai ba. Tana daga kwancen ta daga fararen idanunta masu girma ta.kalleshi,ta sakar masa murmushi tana miqewa daga kwancen ta zauna tana dubansa "Welcome home sir" tsaiwa yayi ya moqe kafadarsa kamar qaramin yaro yana kallonta "Ban yarda da wannan qwangen da akeson yimin ba" saita miqe da sassarfa ta isa gareshi,ya buda mata hannuwansa kamar yadda suka saba ta fada jikinsa,ya maida hannun ya lullubeta gam cikin qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya,kamar yaron da yayi kuka ya qoshi "Alhamdulillah ala kullin ni'am.......na samu promotion,now am SP abbas" wani irin qanqameshi ta qara yi cikin wata siririyar qara "Seriouse abbin affan?" "Da gaske nake sarauniyata" ya fada a tausashe yana shafa sumarta da taja hankalinsa sosai,qamshin jikinta kuma yana neman birkitashi,yana jin yadda bugun zuciyarta ya qaru saboda murna,zamewa tayi a jikinsa ta kama hannuwansa dukka biyun,ta dinga jera masa addu'ar samun nasara tare da fatan alkhairi mai yawa a rayuwarsa,har sai da qwalla ta cika idanunsa,zuciyarsa ta tabu sosai. Mutum daya...... mutum daya ke tsaiwa tayi masa irin wannan,hajiyarsa,zayaso ace yau tana raye taga abinda ubangiji yaketa yima rayuwarsa. "Zan samu abinci madam" ya fada yana langabe mata kai,a gabanta kawai yake komawa hakan,inda zaka ganshi a fagen aiki zaka dauka bashi bane. Kafada ta noqe tana tura baki gaba "Girkin mummyn mimi ne fa daddyn mimi" girarsa ya daga "Yes i know....amma kinsan banason cin abincin waje baya ina da mata har biyu,gida kuma yanzun yamin nisa,infact ma abincinki nakeson ci,in kuma ba za'a bani ba to shikenan" ya fada yana komawa kamar wani abun tausayi,dole ya sanyata ta saki wata shagwababbiyar dariya "Ni na isa na hanaka abinci?,zauna sosai na zubo maka" tayi maganar tana miqewa,saiya riqo hannunta ta baya,ya kashe mata ido daya "Zafi nakeji,hadamin ruwa nadan watsa tukunna,yau aiki zai riqeni inajin har wajen isha" kai ta jinjina masa,saita sauya akalarta zuwa bedroom dinsa ta hada masa ruwan kamar yanda ya buqata sannan ta fito ta gaya masa ta wuce kitchen. Tana tsaka da shirya masa abincin taji yana kiranta,ta ajjiye warmer din ta fito. Tana tura qofar toilet din unexpected kawai taji an fincikota,ko kula dashi ma batayi ba,bata zame ko ina ba sai cikin bathtub,ta jiqe jalaf har saman kanta,tabi jikinta da kallo sannan ta waiwaya tana kallonsa ta gefe,don tuni ya mata masauki cikin jikinsa "Daddyn mimi......" "Shshshs....."ya fada yana dora yatsantsa saman labbansa "Karkice komai,minti biyar kawai zakiyi ki tafi,ba abinda zan miki,kawai ina buqatar ki a jikina kamar haka" bata iya masa musu a wannan bangaren,saboda tasan koda ransa bai masa dadi ba bazai nuna mata ba,uwa uba kuma tasan ba inda zai samu hakan sai wajenta,saita lumshe ido kawai ta jingina da jikinsa. Sun kusa mintuna goma a haka sannan ta samu ta zame,haka ta fita da kayanta suna diga,sai data shiga bedroom dinsa sannan ta ciresu,ta dauki bababn towel dinsa ta daura ta nufi qofar fita don ta koma nata bedroom din ta saka wasu kayan. Gabanta yayi mummunar faduwa sansa ta bude qofar dakin,don kwata kwata bata tsammaci ganin mutum cikin falonsu ba,ta kafeta da idanu wani bacin rai yana taso mata,ita din wacce irin dabba ce?,don ta wuce a kirata mahaukaciya,haka kawai saika buda gidan mutane ka shigo babu sallama babu komai?,ba neman izini kamar naka gidan,yau kuwa zata nuna mata ta fita hauka da danyan kai,idan akace ta sake zuwa mata gida ba zata qara ba,saita fasa shiga nata dakin,ta tako a hankali ta nufi gurin tv dake aiki. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 22 Gifatatan da tayi shi ya fahimtar da hafsat dake zaune tana huci fitowar ta,ta bita da kallo daure da towel din daya bayyanar da kyakkyawar surarta da farar fatarta dake ta glowing mai daukan hankali saboda gyara da mai da sabulan wanka masu kyau data samu. Qamshinta ya cika mata hanci,ta gaza dauke idanunta daga kanta har zuwa sanda ta isa gaban tv din ta kasheta. Kashe tv din tayi sannan ta dawo ta sake wuceta kamar batasan Allah yayi wata halitta ba a wajen,ta sake nufar bedroom din abbas din cikin takun na isa,tana shiga ta maida qofar ta rufe hankalinta kwance. Gefan gadon ta koma ta zauna tana qissima abubuwa da yawa cikin ranta,bata taba ganin mace kidahuma irin hafsat din ba,sau tari idan ta zauna tana nazarin rayuwar abbas din tausayinsa kamata yakeyi,yana da matuqar kirki sanyin hali da qoqarin sauke haqqin da ya rataya a wuyansa,yana da mugun haquri,mutum ne mai nisan haquri sosai da kuma idan aka qureshi fushinsa yakanyi tsahon da ba kasafai yake sakkowa da wuri ba,tako ina babu digon match atare dasu,idan ka kalleta ka kalleshi ba zaka taba zaton miji da mata bane,to amma kuma kowanne bawa da kalar tasa qaddarar,TASHI QADDARAR KENAN. Yayi mamakin ganinta a zaune daya fito,yana goge jikinsa sa towel yana tsokanarta "Ko nazo na qarasa aikina ne kawai mu samu ladan me gaba daya?" Ya fada yana kashe mata ido,saita dan jefa masa hararar wasa yana karya wuya "Naqi wayon.....na yarda ka kashemin jiki,kazo dai ka rakani kitchen saimu debo kayan abincin gaba daya" "As you wish maaaa" yadda yayi maganar sai ya bata dariya,gefe guda kuma tausayinsa ya kamata,tasan yanzun nan jahilar matarsa zata jagula lissafi da kuma nutsuwar da ya samu. Tana gaba yana biye da ita daure da towel shima,yadda widad din ta tsara ma ranta kuwa haka ya kasance, idanun hafsat din a kansu ya fara sauka,saita miqe tsaye cak kamar wadda aka yiwa barin wuta,yayin da abbas ya dubeta cike da mamaki,take zuciyarsa ta fara tafasa "Da izinin waye kika fito?" Ya tambayeta da kakkausar muryar,maimakon ta amsa shi saita sauke dubanta ga widad "Shegiya la'ananniya,dama nasan yana wajenk......." "Dakatamin......karki qara kuskuren kirana da wannan sunan,idan ba haka ba wallahi zakisha mamaki na......tunda kike haukarki kinga na taba bi ta kanki?,saboda ni ba take nake ba,ta mijina nake,shine a gabana,ya samu farinciki da nutsuwa daga gareni,ta yadda zan tsaya gaban kowa na amsa suna na na mace,bawai muna mata ba,sannan zanji gamsuwa ba mata na rako duniya ba" ta qarashe maganar tana watsa mata wani banzan kallo,kallon da ya kusa fin maganar da widad ta yaba mata zafi,sai ta fige mayafinta ta watsar da jakarta "Yau saina nuna miki wace mace wace muna mata" "Karki kuskura ki sake taku ko guda daya idan ba haka ba yau zakiga abinda baki taba gani ba daga gareni" abbas ya fada idanunsa na sauya launi "Wuce" ya juya yana gayawa widad,saita fara taku a nutse fuskarta fes da murmushin d hafsat taji kamar ta watsa mata garwashin wuta a fuska. "Kana gani fa......kana kallon gaskiya kake taketa?,sau nawa ina kamaka a gidan nan abbas?" "Tunda kwartanci nazo yi saiki tsayarmin da haddi,da izinin wa kika fito nace miki!!!" Ya daka mata tsawar da sai da cikinta ya kada,amma taurin zuciya da tsaurin rai ya sakata ci gaba da tsaiwa tana dubansa "Dole ne ka fake a bayan na fita baka sani ba,tunda idonka ya rufe ka manta sanda na gaya maka bani da lafiya ko" kallonta yakeyi yana jin kamar ya yanke mata hukuncin da zuciyarsa ke raya masa ko zai samu sassauci daga abinda yakeji a ransa na zallar bacin rai "Idan kika qara minti daya tsaye a nan wallahi saikin raina wayonki" abinda ya fada mata kenan ya juya ya koma dakinsa. Tana kuka wurjanjan ta fita a gidan ta wuce titi ta samu abun hawa,bata jin zata iya jurar ci gaba da zama a garin kaduna,bata da sauran amfani a wajen abbas,ba wata soyayya ko qauna data rage tsakaninsu. Tsaf ta shirya abincin ta fito dashi bayan ta sauya kayan jikinta,da taga baya falo saita wuce bedroom dinsa. Ko towel din jikinsa bai cire ba,yana zaune a gafen gadon dafe da kansa,ta ajjiye abincin a nutse tausayinsa yana kamata,ta tako a hankali ta zauna gefansa tana dafa kafadarsa hadi da kiran sunansa a tausashe. Hannunsa dake dafe da kansa ya sauke, sannan ya dagashi zuwa gareta yana duban fararen idanunta da nashi idanun da suka rine "Kayi haquri....." "Na gaji widad.....na gaji,nayi duk iya bakin qoqarina,na kuma yi irin haqurin da nake ganin zan iya,shekara nawa?,shekara nawa amma har yau babu sauyi?,har yau jiya iyau,sai yaushe zata canza?" "Mai haquri baya taba tabewa daddyn mimi,kaci gana da haquri ko don yaranka" dan shuru yayi sannan ya fara magana a sanyaye "Ina da dubban hanyoyin da zan hukuntata,amma ta kowanne fanni idan na duba mafi yawan hukuncin da duk zan mata sai ya shafi yarana,inda ace bamu da zuri'a ko daya da ita,wallahi wallahi bazan zauna da ita ba" maganar ta daki widad sosai,don duk wanda yake wajen yadda maganar ta fita daga bakinsa zai fahimci tun daga qasan zuciyarsa ne. Sosai tayi qoqarin kwantar masa da hankali da dadadan kalamai da ban haquri,ta tayashi sukaci abincin tare duk da ba yunwa takeji ba,sannan ta taimaka masa ya sake shiryawa cikin wasu uniform din,don idan ya watsa ruwa da rana kamar haka baya maimaita kaya,takan tsokaneshi da cewa "Ban taba ganin police din da kayan aiki sukewa kyau irinka ba,hakanan ban taba ganin dan sanda mai tsafta kamar ka ba" murmushi yakeyi sannan yadan harareta "Kina nufin qazamai ne kenan?" Takan maida masa murmushin hadi da salute nashi "Afwa nake nema yallabai,ni na isa na fadi haka,kada kasa hukumar 'yan sanda ta kamani" "Waya isa,wane mutum,kina da Abbas turaki" ire iren hirarrakin da suke sakawa basa gajiya da junansu. Relief din da ya samu daga wajenta yasa zuciyarsa ta sauka sosai,ya kuma yi aikinsa cikin sukuni,sanda ya tashi komawa gida sai yaji kamar ya koma gidan widad din,amma hakan bashi yiwuwa,kodon yaransa da kuma hakkin Allah dake kansa. Daya koma din kamar wancan lokacin,baibi takan komai nata ba,hidimarsa yayi dasu mimi,gefan abincinta ma bai kalla ba,saida sukayi baccin ua debesu ya wuce dakinsa dasu,yabar musu gadon ya kwanta saman sofa bed. Da safe da wurwuri ya shiryasu ya wuce aiki,ya ajjiye mata kudin cefane,bayan ya zabge fiye da rabin abinda ya saba batan,yana sane yayin hakan,don yanason ko yaya ne ya horata taji a jikinta. Koda aka tashi daga aikin gidan widad ya wuce,bai koma ganinsu ba yadda ya saba,bai kuma kirata ba,baisan ya akayi ba washegari suna waya da lawal kawai yaji muryar su mimi,tsananin amaki ya cikashi "Suwa nakeji kamarsu mimi?" "Eh....eh sune" yadan fada a daburce,saboda yasan yadda akayi tahowar,baiso kuma yaji wani bayani daga bakinsa ba "Ok,shikenan yayi" abinda ya fadi kenan,don ba hurumin yaron bane suyi kowacce magana dashi ba,suka gama maganar da zasuyi ya kashe wayar. Duk yadda yaso yayi controlling fushinsa amma ya gaza,tattarawa tayi ta koma bauchi ba tare da izininsa ba kenan kwatankwacin abinda tayi masa wancan karon da yayi sanadiyyar haramta mata kaduna kwata kwata kenan?,sai ya sake daukar wayar ya fara kiranta. Sai da yayi mata miscal biyar bata daga ba,abinda bai taba yiwa wani dan adam ba,ya sauke wayar ya shiga gurin rubuta saqo ya aika mata da saqo kamar haka _Ki wuce gidanku har sai na nemeki_ Abinda ya aika mata kenan a taqaice,saqon da yayi mugun gigita mata hankali,ta fara kiransa babu qaqqautawa,amma sai shima yayi biris,daga qarshe ma da kiran yayi yawa sai ya kashe wayar gaba daya,widad dake zaune gefansa tana tayashi shigar da wasu bayanai system dinsa batasan abinda yake faruwa ba,sai da taji yana ta jan tsaki sannan ta kalleshi "What's...." "Shshsh....."ya fada yana dora yatsantsa saman labbansa yana dan lumshe idonsa,saita dage kafada da gira tana murmushi,bata sake cewa komai ba taci gaba da tayashin,yayi qoqarin shima tattara duk wata damuwar hafsat din ya watsar. Kwana uku rak kawu hassan yayi kiransa,yace a jirashi sai ya shigo weekend,weekend din da baije ba sai da bayan wata guda cif!. Widad sam batasan me ake ba,taga dai ya dawo gidan gaba daya,ta kuma sake samun wata sabuwar zazzafar soyayya da kulawar data dinga sakata jin kunya muddin cikin mutane suke,takan tambayi kanta wai wacce irin soyayya abbas din yake mata?,tasha tambayarsa amma shima baida amsa illa yace "Min indillah" daga qarshe itama haka ta barwa ranta daga Allah ne,saidai tabbas ZUCIYA TANA SON ME KYAUTATA MATA,TANA KUMA QIN ME MUNANA MATA KOMAI SOYAYYAR DA ITA ZUCIYAR KE MASA. Suna sauka a bauchi ya wuce gidan kawu hassan din,don akwai maganganun da zasu tattauna,yanason wannan karon su halarci bikin qara musu girman da akayi,itama bata zauna ba tace zata je gidan uncle muhsin,da fari ya hana don mugun kishinta yakeyi,yace ta jira ya dawo ya kaita. Amma ta kafe da roqo da nacin ya barta,don akwai abinda take shirya masa,batason kuma ya sani sai ranar,daga qarshe da qyar ya yarda idan ya isa gida zai turo umar ya dauki motarsa guda daya ya kaita,ta saki murmushi sanda yake fita "Uncle dina" ta fada qasa qasa cikin murmushi,wani kaffa kaffa yakeyi da ita,hatta da kayan sawarta yanzun ya hanata saka wasu muddin fita zatayi,yafi ganewa kowanne dinki ma ayi mata doguwar riga sakakkiya. Abbas sun tattauna sosai da kawu hassan harma da yaaya sa'id da Bashir akan batun hafsat din,sun tausheshi sosai sun bashi haquri,yace yaji,amma su qyaleshi,ko zai maidata ba yanzun ba,ya fara gajiya yana son shima ya huta,ba wanda ya tilastashi a lokacin,babban wansa yaaya sa'id ne yace "Shikenan,zan nema kawun nata zamuyi magana,amma dai ka daure kaci gaba da haquri ko don zuriar da Allah ya qaddara a tsakaninku" "In sha Allah" ya fada cikin girmamawa,sun qyaleshin,suka ajjiye batun suka shiga tattauna sauran maganganun da ya shafesu. Kafin yabar gidan ya bawa umar key din motarsa yace ya dauko masa su mimi,saboda yanason su koma kaduna tare,ko don makarantar yaran. Abinda yayi matuqar bata mamaki da daga mata hankali kenan,a dauko su mimi fa?,to me yake nufi?,kada fa ya zamana ta fita kenan a gidan gaba daya,kada yarinyar ta zama sanadiyyar fitarta haihata haihata a gidan,ta kadu don irin hakan bata taba faruwa a tsakaninta dashi ba,amma ummanta ta kwantar mata da hankali "Kada ki damu,ki bada yaran,kinsan muddin ina raye bazan bari irin haka ta faru dake ba" hakanan ta daure ta hada musu tsummokaransu. Kafin abbas din ya dawo ita ta rigasu dawowa,ta gyara bangarenta da nashi,ta dora abinci,sanda yaran suka iso ta gyarasu fes ta canza musu kaya,sai gashi sun sake sunata walwala abinsu,musamman mimi data dinga fadin "Nidai wajenki zan zauna anty", murmushi kawai widad tayi "Dama ta wajena ce ke" abbas na zaune yana binsu da kallo,sai yakejin gidan nasa ya sake masa dadi, widad nata kai.kawo tana hidima dasu,affan yana hannun su mimi suna masa wasa,wanda inda mahaifiyarsu na nan basu isa su samu wannan damar ba. Waya ta shiga daki ta amsa,koda ta fito sai ya tsareta da ido,daga bisani kuma murmushi ya kubce masa "Madam.......tsakani da Allah ban yarda dake ba,me kike shiryawa silently" dariya takeson yi amma bataso ta bashi qofar da zai gane plan dinta "Siyar dakai zanyi" tayi maganar tana kashe masa ido daya,wani qawataccen murmushi ya subuce masa yana jin kansa fes cikin wata irin walwala "Girmanki ne,don kin siyar da DSP,har IG ma zaki iya siyarwa,duka girmanki ne" sai dariya ta qwace musu su duka biyun. Washegari bayan ya fita ta kuma tambayarsa zasu fita ita da yaran gaba daya,ya langabe kai a inda yake zaune "Babyn uncle.....ki jirani zuwa dare na kaiki please,wallahi banaso...... inajin kishin ki fita a kalleki,banason kihau motar haya" "Allah uncle ba zamu jima ba,kuma inda zanje din basa fitowa ai da daddare,don Allah ka turon umar ko ko muneer,saika bamu aron daya motar taka ya miqamu ya dawo damu" "Shikenan nan,amma awa biyu kacal na baku" "In sha Allah bazan wuce haka ba" ta amsa masa a ladabce. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 23 Wankin kai da qunshi akayi mata,haka suma yaran duka,sunata murna don ba'a taba musu gyara da lalle irin wannan ba,bata wuce awa biyun ba ta dawo,koda ya dawo gidam ya samesu da gyaran bai kawo komai ransa ba,tunda yasan dama already ita kullum cikin gyara take ta saba (qalubale gareki, keda bakya komai sai sallah ko idan zakuyi biki ko wani sha'ani na taro ya kama,mai gida har ya gane hakan,yara suyita tambayar umma unguwa zamu?,umma biki za'a yi,ba lalle ba gyaran kai babu kitso). *******Karfe hudu na yammacin washegari tayi wata kyakkyawar shiga cikin wani tsadajjen crystal swarovski lace,duk inda ta motsa ko ta gifta daddadan qamshi ne yake fita daga jikinta da wani irin qyalqyali mai daukan hankali. Ta nutsu ita daya daga can bakin gate,ta yadda abbas data kirashi gida urgently bazai gane abinda ke faruwa cikin gidan ba har sai ya shigo. Daga waje ya kashe motar,ya bude ya fito ya kulle yana kallonta cikin mamaki,tace yazo gida yanzu yanzu,yazo kuna ya tarar da ita cikin ido me narkar da zuciya da idanunsa "Wow......amma kin kyauta da kika kirani naga wannan kwalliyar kada nayi missing nata" ya fada yana murmushi,batace masa komai ba sai kama hannunsa da tayi suka shiga cikin gidan. Mutuwar tsaye yayi sanda yaga yadda aka maida harabar gidan nasa kamar wani event center,har yaushe akayi hakan bayan fitarsa daga gidan duka duka bai wuce awa uku ba,ko ina ya daga kai manya banners ne masu dauke da hotonsa cikin full police uniform a tsaye,da wasu rubututtuka na nuna murnar tayashi qarin samun promotion da yayi,ga family saman kujeraru da shigowarsa ta saka kowa miqewa yana masa maraba,a lokacin wani irin sassanyan abu yaji yana tsarga masa akan widad din "Ya rabbb,wacce irin yarinya Allah ya azurtashi da ita?" "Surprise?" Ya fada yana sauke idanunsa a kanta yana lumshesu cike da wani irin shauqi,saita jinjina kai lallausan murmushi yana kubce mata,shima kan ya jinjina,ya kuma kama hannunta da kyau cikin nasa ya fara takawa zuwa ciki suna riqe da hannun juna ya nufi yan uwa dake dakon isowarsa don a gaggaisa kafin a fara ciye ciye na abinda aka tanada a wajen. Cikin wani yanayi me kyau da qayatarwa aka kammala taron lafiya,abu yayi masifar qayatarwa,ya burge masoya, abokan adawa kuma da masu taya hafsat kishi kamar su mutu "Yar qanqanuwar yarinya ta iya kidifiri da iyayi,ta kora sa'ar uwarta uwar gida cikin yaranta gida tazo tana shimfida abinda taga dama" ire iren abinda su gwaggwo hassana da gwaggwo fanteka suke fada kenan,saidai babu bakin cewa komai saidai gulma daga gefe,hakanan kuma sukaci suka sha suka watse. Sai data tabbatar an sallami kowa harabar gidan ta barwa su shazali zasu qarasa gyarawa sannan ta dawo cikin gidan duba yaran,tasan bata da matsala don suna tare da aminatu,tare suka taho wannan karon. Aminatun kam akwai hidima,ba qyuya sam,harta sake musu wanka,affan da nawwara sunyi bacci,ita da mimi ne kadai suna kallo a ipad din widad da abbas din yabar mata kwanan nan,don dama itace bata da ita,hafsat nada tata duk da ta bari yara sun tsoma tatan a ruwa. Bayan ta tabbatar sunci abinci sai ta dauki affan tayi musu sai da safe,don ta gaji tubus,ta kuma ji shigowar abbas din tun kusan dazun ma tana waje tana sallama da mutane. Tana tura qofar suna hada ido,waya yake amsawa,da alama kuma mai tsaho ce,don haka ta daga masa hannu kawai,ta ajjiye masa affan ta kitchen ta hado musu baqin shayi me kayan qamshi sosai,don ya koya mata itama,sanann ta wuce toilet ta hada ruwa mai zafi tayi wanka. Daure da towel ta fito,fatarta sai sheqi takeyi,ya ajjiye wayar gefe ya miqa mata hannunsa,batayi qasa a gwiwa ba ta miqo masa nata hannun,yayi mata mazauni saman cinyarsa yana sansanarta,yana bala'in son qamshinta,ba qaramin burgeshi yakeyi ba "Sannu da hidima madam" murmushi tayi tana saqalo wuyansa da hannunta "Kaine da sannu yallabai,don dukka aikinka ne wannan" da mamaki ya daga kai ya dubeta,don dai shi yasan sisinsa babu a ciki,hasalima baisan zata shirya ba sai daya shigo gidan. "Aikina kuma?" Gira ta daga tana murmushi "Sosai,mun samu kyakkyawar kulawa daga gareka,ka sauke dukkan wani haqqi naka dake wuyanmu,wanann yasa har a cikin zuciyata naji ka cancanci fiye da haka ma,donma ni din ba wata bace,da fin haka naso ya kasance" cikin jikinsa ya qanqameta yana cusa kansa tsakanin qirjinta,abinda ya sanya tsigar jikinta tashi,ya sauke mata zazzafan numfashin da dole ta riqe kansa da hannunta tana 'yar dariya "Ji nakeyi kamar na maidaki cikina na boyeki,zuciyata har wani irin zafi takemin saboda sonki" yana kaiwa nan saiji tayi ya watsata saman gadon ya kuma maye gurbin towel din jikinta. Washegari ta tsinci alert a wayarta da sunan mijin nata har na naira million daya,ta sameshi a bayan gidan shi daya da wasu takardu data tabbatar ayyukansa yake,da alama za'a baza komar kama wani mai laifi ne "Yallabai kudinka sunyi batan kan shigowa account dina fa,da saninka?" Takardun ya aje gefe,ita daya duk duniya yakema haka idan yana aiki irin wannan "Zonan" yace tana bata hannunsa,saita qaraso din ta zauna "Ba batan kai sukayi ba,sun shiga inda ya dace ne,nawa kika kashe jiya." Fararen idanunta tadan juya kadan "Bazance ba,amma dai bazai wuce three hundred thousand ba" kai ya jinjina "Kice duka tattalin arziqinki kika kwashe" saita saki dariya,kome zata bawa abbas din batajin zatajishi a matsayin asara "To yayi,kudin dana tura duka naki ne,inason ki zauna kiyi tunani ko kiyi shawarar sana'ar da kike sha'awa,inason ki fara kasuwanci cikin gida" sosai ya bata mamaki kamar yadda itama ta bashi mamaki jiya,ta sauko saman gwiwoyinta ta fara masa godiya,ya kamata ya tayar da ita "Ban miki komai ba,saboda ke din kin bani komai" *H A F S A T* Kai kawo taci gaba da yi,wayar hajiya habiba tana hannunta,duk hoto daya da zata bude tashin hankali ne yake sauko mata mara adadi,kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,abbas dinta mijinta da kuma yaranta,duka under control na widad,wacce irin asara take shirin tafkawa?. "Nidai gaskiya kin bani mamaki,am totally disappointed wallahi,ni duk sai kunya ta kamani ma da naga irin abinda akeyi a wajen,sai lawal ne ya bani address na gidan nan,shima yana daga gefe takaici ya isheshi,don dai bashi da yadda zaiyi ne". Kananun qwalla ce suka kubcewa hafsat,tana jin tata ta qare,duk wani abu da zatayi akan widad tayi amma jiya iyau "Aah,ai kuka bai ganki ba,mafita ya kamata ki nema" komawa tayi ta zauna,don gaba daya jikinta babu sauran qwari ko karsashi "Meye ma banyi ba,kissar nayi babu ci,malaman nabi amma sai abun yayi kamar zaiyi tasiri saiya wargaje" murmushi haj habiba ta saki "Malamai kika bi ko muna malamai?,hajiyata kiqi kudinki kizo na kaiki inda zaki mori kudinki,kissa kuma iri iri ce hakanan iyawa ce,ki fita batun yarinyar koda an miki aiki yayi,ko agabansa ki dinga nuna bata gabanki shine kawai" "Wallahi na shirya,ko nawa zan kashe a shirye nake,ai ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba" murmushi ta saki "Gwara da Allah ya ganar dake ai" (hmmm,kodai shaidan ya batar da ita,Allah yasa mufi qarfin zukatanmu,muje dai zuwa masu karatu,aci gaba da haquri,so nake mu sauke dukkan darasin dake ciki,saboda labarina yafi rinjaye da true life story) *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 24 Kafin su gama hutunsu a bauchi ta tattauna da mutanen da suka zame mata tamkar fitila a rayuwarta,su anty deena hajiya sha'awa dasu hajiya fanna,anty deena tace "Kina 'yar kano cibiyar kasuwanci ai baki da matsala,kaya kawai za'a yita kawo miki kina saidawa kina maido kudin ana sake miki sari" su hajiya fanna dake 'yan kasuwa ne suma sukace ba matsala zasu dinga karba,ta zauna tayi shawara da tunani ta zabi kayan da zata dinga saidawa,bata bar bauchi ba saida kayan suka iso,ta raba wasu suka wuce kaduna da wasu. Abu kamar wasa saiga kaya sunata shiga ana hada mata kudinta,hakan yayi mata dadi sosai,a cikin lokaci qalilan ta fara gane amfanin sana'a ga mace. Ta maida kanta sosai ga kulawa da mijinta da yaronta dake shiga watanni takwas,gasu mimi da takejinsu kamar yaran cikinta,bata da sauran matsala sai godiya ga Allah. Watansu daya da dawowa ya dauki su mimi ya maidasu bauchi kan mamarsu ta dawo,bata wani damu ba tunda zuciyarta babu wani mummunan nufi a ciki,saidai bataji dadin tafiyar yaran ba,don hatta mimi taso a barta amma hakan bai yiwu ba. *R U B U T A C C I Y A R K' A D D A R A* K'arfe hudu na yammaci,tana kitchen tana aikin abincin dare,affan yana goye a bayanta,don aminatu bata nan tana islamiyya,yau din ta dauko aiki me dan wahala,favourite foods na abbas din takeyi har guda biyu,don ma aminatu ta rage mata wasu ayyukan kafin ta wuce islamiyya. Knocking taji anatayi sosai,kamar za'a balla qofar,mamaki ya kamata,sam bata qaunar bugu me qarfi haka,taha tsaki ta share bugun ta qarasa juya miyarta sannan ta ajjiye ludayin ta nufi qofar tana tambayar waye da dan qarfi,saidai ba'a amsa mata ba har ta bude qofar. Tsananin mamaki ya kamata ganin abbas a tsaye,ya kafeta da ido kafin ya sanyo kai ciki,saita rabe gefe tana bashi hanya hadi da binsa da kallon mamaki,a hankali kuma ta taka ta bishi a baya jikinta na wani irin mutuwa. Sai da ya gama qarewa falon kallo tsaf sannan ya kalli wayarsa dake hannunsa ya maida dubansa gareta da murtukekkiyar fuskarsa "Ina kika je?" "Ni kuma?,ina zan fita ba tare da saninka ko izininka ba?,ina kitchen ina girki" "kina kitchen kuma?" Ya sake tambayarta cikin yanayi na rashin yarda sosai kwance a fuskarsa,abinda ya bawa widad mamaki sosai "Eh mana,uncle na taba yi maka qarya?" "Amma naketa kiranki baki dauka ba?,kamar kin fita ko kin tafi Wani wajen?" Idanu tadan zuba masa sannan ta sauke ajiyar zuciya mai qarfi,sai kawai ta kama hannunsa suka wuce zuwa bedroom dinta inda tabar wayar a ajjiye. Cak ta dauko wayar ta danqa masa a hannunsa,ya dubeta ya dubi wayar sannan ya bude "A silent take,ni na sakata saboda inason affan yayi bacci,kada kira ya shigo ya tadashi" wayar yadan juya a hannunsa kadan yana sauke ajiyar zuciya a jejjere,sai ya koma da baya ya zauna a bakin gadonta. A matuqar sanyaye ta fice,ta shiga kitchen ta bude fridge ta fiddo zobo me sanyi data hada masa da yaji kayan hadinsu abarba,daya daga cikin nau'ikan zobon data koya a class dinsu da deeja Berver (the best online class da na taba shiga da ya burgeni qwarai qwarai 0907 927 4454). Tason yana matuqar sonshi saboda taste dinsa na dabanne da ba ko wanne gida zaka shiga ka samu irinsa ba,shi yasa bata rabo da yi masa. Gabansa ta dawo ta durqusa ta soma zuba masa sannan ta miqa masa idanuwanta a kansa,bai musa ba ya karba ya kuma shanye tas ya miqa mata cup din,saita koma gefan gadon ta kwantar da affan sannan ta dawo gabansa ta zauna tana tattara nutsuwarta a kansa "Uncle,me yake faruwa?,kwanakin nan gaba daya idan ka kira wayata baka sameni ba sai hankalinka yayita tashi,sannan duka ka gaza nutsuwa a wajen aikinka,me yake faruwa?" Idanunsa ya lumshe yana kada kansa da yakejin ya masa wani nauyi,zuciyarsa kuma tana rabuwa gida biyu "I don't know,kawai dai.......ina tsananin kishinki" shuru tayi tana nazarin maganarsa,a baya yana kishin nata amma ba ta irin hanyar da yanzu yakeyi ba,ya canza kwata kwata,wasu irin halaye yake mata da suke sakata shakku,kamar zargi zargi,to amma tunda ya bata wannan hanzarin bata da hurumin masa hukunci kai tsaye "Ka kwantar da hankalinka uncle,ni taka ce har abada" qaramin murmushi ya subuce masa wanda baikai har zuciya ba,ya waiwaya yana kallon affan dake bacci abinsa hankali kwance cikin cikakkiyar tsafta da kulawa. Bayan wasu kwanaki da yammacin wata litinin,a yau din ba ita keda girki ba,don haka tun bayan kammala sallar la'asar ta gama komai.nata tana zaune,sai kiran ummu ya shigo mata,suka shiga hirarsu sosai tana wasa da hannun affan dake zaune saman cinyarta yana wasa da teether. A qalla sun kusa awa guda,suna gamawa kuma kiran anty fanna ya shigo,suka hau hirar kasuwanci da lissafin kudaden kayan widad din da aka saida wadanda suke hannunta. Daga qofar falonta taji ana knocking,ta dauki excuse tace zata kirata ta aje wayar ta miqe tana bude qofar,aminatu ce sanye da kayan islamiyya,hannunta riqe da waya "Aah,har an taso?" Widad ta tambayeta "Aah anty,yau korar school fees akeyi" dan bata rai tayi kadan "Amma sau nawa zan gaya miki,duk sanda wata ya qare ki dinga tunamin ina baki?" "Mamace tace na qyaleki hakanan,wancan watan kin kawo kayan abinci,yanzu kuma......" Sai maganarta ta katse saboda ringing da wayar hannunta ta fara,duka suka kalli wayar a tare "Wayar waye wannan?" "Wani ne,da uniform irin nasu abban affan,yace sunanshi samuel,oga ne yace wai a kawo miki wayar zakuyi magana" ta gane komai a dan bayanin aminatun,amma sai mamaki ya kamata,tasa hannu ta karbi wayar,kafin takai ga dagawa ta yanke,saita saki qofar ta juya cikin falon jikinta a matuqar sanyaye,abun na abbas har ya fara kaiwa haka?,meye haka mai qarfi ya shiga zuciyarsa dangane da ita?. Tana shirin zama amintu ta sunkuya ta dauki affan tana masa wasa sai gashi ya sake kira,batayi qasa a gwiwa ba ta daga wayar ta sakata a kunne tare da yin sallama. Maimakon ya amsa sai ya fadata da fada,ta runtse idanunta tana jin kakkausar muryarsa har cikin zuciyarta,sai ta miqe tsam ta wuce daki riqe da wayar tabar aminatu da affan a nan. "Ke dawa kuke waya?" Ya tambayeta bayan ya gama fadan rashin daga wayar da wuri "Nida ummu,sai kuma anty fanna" "Shine har kusan awa daya da rabi?" Mamaki ya sake cikata,to meye a ciki?,yasansu kuma dukkaninsu dama idan tana waya dasu tana dadewa "Eh lissafin kaya mukeyi da ita,ummu kuma dama kasan hirarmu ai" Shuru ya danyi sannan yaja tsaki ya kashe wayar. Duk yadda taso danne zuciyarta amma ta gaza saida hawaye ya silalo mata,wai meye hakan?,me yake faruwa?. Sai data dan koka kadan zuciyarta tayi sanyi sannan ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta shafa farar powder sannan ta fito. Har yanzu suna falo ita da yaron,ta bata wayar tace ta maida masa,sannan ta zauna ta dauki tata wayar tana dubawa. Tex ta rubuta masa na ban haquri,duk da abun naci mata zuciya sannan ta tura masa,saita koma ta zauna jikinta gaba daya babu qwari. Falon shuru saboda aminatu ta fita da affan,zuzzurfan tunani ta shiga tanason gano ainihin abinda ya kawo wannan lamarin tsakaninta da abbas din amma ta gaza gano komai,cikin haka ta kwashe awa kusa biyu,ta daga idanunta tana kallon qofa sanda taji ansa key ana qoqarin bude qofar. Tasan waye,don shi kadai keda key din gidan,miqewa tayi cak da nufin shigewa bedroom dinta,motsinsa da taji kadai ya karya mata zuciya,bata kuma so tayi kuka a gabansa,saidai ta makara,bata kai ga isa dakin ba ya shigo,kuma ya ganta,yana dauke da affan,da alama ya tsaya ya karboshi ne. Daga nan inda yake ya tsaya bayan yayi sallama yana kallonta,ta amsa amma bata juyo ba,sai ya tako a hankali ya iso bayanta ya rungume ta ta baya,saita sake masa kuka kawai. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 25 Kasa cewa komai yayi,sai zuciyarsa dake wani irin tsinkewa,sun jima a tsaye a haka har affan ya fara kuka,sai ya miqa mata yaron ya juya ya koma dakinsa yana jin wani yanayi mara dadi cikin ransa,yanason bata haquri ya kuma lallasheta ya kasa,sai bayan ya zauna cin abincin dare yake sake jadda mata "Ina tsananin sonki,ina kuma tsananin kishinki" bata da amsar bashi,amma batasan wanne irin kishi ko soyayya bane daya rikide yake son komawa ZARGI. Tun daga ranar data fuskanci haka saita daina doguwar waya don kada ya kirata bai sameta ba,hakanan ta daina nisa da wayarta,idan zaiyi kira dubu zata daga,don don kiyaye faruwar wata matsala da take gani kamar tana shirin kunno kai,da tayi hakan sai taga kamar abubuwan sun ragu,kira dai tana jurar dagashi,to amma ta barwa ranta hakan shine maslaharta. Ya koyi dawowa gida akai akai,sabanin baya da abincin rana kawai ke dawo dashi,a yanzu sai yazo gida sau hudu biyar kafin lokacin tashinsu a aiki yayi,tun abun yana mata wani iri har ya koma bata mamaki,tako ina ya koma wani irin tsauri da yake mata kama da ZARGI don yafi gaban kishi,amma tayi qoqarin dannewa,tare da bashi uzuri. Tafiya ta kamashi katsina ta kwana biyu,har sunyi sallama dashi kan aminatu zata dawo gidan ta zauna har sai ya dawo,amma bayan awa uku sai gashi da fahad,dan yayansa ne shima "Zai tayaki zama har na dawo" da to kawai ta amsa masa,don abubuwan nasa sun fada daure mata kai. A tafiyarsa ta kwanaki biyu ya dage da addu'ar Allah ya sassauta komai,ya kawo qarshensa,cikin sa'a daya dawo din sai taga abun ya ragu,satinsa daya da dawowar suka shirya zuwa weekend yadda suka saba,daga nan zasu maida fahad gida. *R U B U T A C C I Y A R K' A D D A R A II* Shigar yammaci suka yiwa bauchin,sanda motarsu take shiga gidan duka yaran suna farfajiyar gidan suna wasa saman kekuna,hafsat na tsaye da wata baquwa da alama sallama takeyi tayo mata rakiya ne. Dukka yaran suka kwaso a guje sukayo kansu suna murna tare da kiran sunan affan,harda yusra dake rarrafe,duka tyai budu budu da jikinta da qurar dake farfajiyar gidan,widad bata barta ta qaraso ba ta isa gaban yarinyar ta dagata tana mata waqa "Allah rayan.....rayan 'yar nan" sai kuwa ta bangale mata baki tana dariya,ta sanya yarinyar cikin jikinta itama tana dariya,duk da ajiqe jikinta yake,fitsari ne ko ruwa itama bata sani ba,yarinyar akwai fara'a sosai,shi yasa take sonta. Ga mamakin widad da hafsat ta dawo daga raka baquwar sai tayo wajensu "Sannu da zuwa daddy" ya daga kai da murmushi yana kallonta "Yauwa sannu da gida maman yara" ta saki murmushin jin dadi kadan,sai widad ta taka kadan ta gaidata. Ba yabo ba fallasa ta amsa mata sannan ta maida kanta ga mijinta suka fara hirarrakinsu,har widad taji tadan qosa da tsaiwar ta dauki qaramae jakarta ta cewa fahad "Shigomin da sauran kayan don Allah" sai tayi gaba ta barsu a wajen. Sai bayan kusan awa guda aka shigo mata da affan,a lokacin har tayi nisa wajen gyaran sashenta,ta karbeshi tana tambayar fahad ina duka yaran "Mamansu ta tafi dasu bagaren abbansu" saita gyada kai kawai tana cirema affan pampers dinsa,don ba kasafai take barinsa dashi ba don ba mai yawan fitsari bane. Ta kama kanta sosai game da lamarin hafsat dama tun ba yau ba,don sai ta gama zamanta a bauchi su koma bata bari hanya ta hadasu ba,to wannan zuwa hutun ma haka ya kasance,hatta dasu mimi ta janyesu,wannan bai damu widad ba,tunda koba komai itama Allah ya bata nata,affan ya isheta suyi sabgarsu a sassansu,ga kasuwancinta dake dauke mata hankali,wani lokacin saita share awanni tana lissafin kaya dana kudade. Uwa uba wannan zuwan ma da sukayi sai takejin jikinta duka babu dadi,yawan bacci da kasala gaba daya,ranar da ta karba girki washegari abbas din yana saman dining tana shirya masa breakfast yana riqe da affan yana masa wasa,ta kammala taja kujerar ta zauna ta fara saving dinsa,idanunshi a kanta harta gama ta daga kai suka hada ido "Lafiya yallabai?" Sai ya dage mata girarsa dukka biyun "Sonki nakeyi" maganar ta bata dariya har sai data murmusa "So na nawa kuma ranka ya dade?" "Na babu adadi,malala gashin tunkiya,ina sonki sosai,ina kuma kishinki widad,da ina da hali ko quda bazan bari ya sauka a kanki ba" ajiyar Zuciya ta sauke mai nauyi tadanyi rolling idanunta tana kallonsa,ta yarda kai idanma akwai abinda yafi yarda ta yishi akan irin soyyyar da abbas keyi mata "Amma jiya kinsan kinci bashi na,kikayi baccinki kina barni da kewa" murmushi ta sakeyi tana dan rufe bakinta "Amma yallabai,ina jinka fa ka rage zafi sosai fa" fuska yadan bata "Hakan bai gamsar dani ba madam.....bana wani ganewa rage zafi,na ji na kasance tare dake kawai shine magana,kwanan nan kin koyi lalaci da dogon barci,ko so kike na qara aure oho" ya fada yana dan shan mur kamar da gaske. Idanu ta fiddo,saita fara bubbuga masa qafa cike da shagwabar nan tata tana masa kukan qarya "Haka kace uncle?,haka kace?" Dariya ya saki "Wasa naki miki wuddu na" ya dora affan saman dining din yana cewa "Idan na biyewa mamarka bazan fita ba,ina da aiki masu yawa,gobe ma kuma sokoto zan tafi daurin aure,zai yiwu ma mu kwana can sai jibi" "Allah ya nuna mana"ta amsa tana qarasa tura masa sauran breakfast din. *W A S H E G A R I* Tunda wuri ta gama masa komai na tafiyan yana kwance yana bacci,hatta da breakfast da ruwan wanka,sai data kammala ta shiga dakin,suna cikin duvet shi da affan suna baccinsu hankali kwance,ta saki murmushi har qasan ranta tana jin dadi idan ta kallesu,su din sanyin idaniyarta ne,kamarsu kullum qara fitowa takeyi da juna,kana ganinsa basai ka tambaya ba kasan mahaifinsa ne,tadan dora hannunta saman pillow din da yake kai ta soma bubbugawa a tausashe,ya motsa kadan saiya dora hannuwansa saman kunnensa ya rufe. Murmushi ta saki,ta gane ya farka tashi ne bashi da niyyar yi,saita gyara zama ta zame duvet din gaba daya daga fuskarsa,ta kamoshi ya maida fuskarsa,ta sake zamewa,sai kawai ya cakumota gaba daga ya mirginata ya danneta da dukka qarfinsa,sannan ya kama fuskarta ya riqe a tafin hannunsa saitin tasa,ya fara bude manyan idanunsa da suka qara girma kadan saboda barci cikin nata qwayar idanun,suka kuma dan canza launi kadan. "Na meye zaki dameni da tashin sassafe,bayan ke kika gajiyar dani jiya?" Ya fada da muryar bacci wadda tayi mata dadi qwarai cikin kunnuwanta,saita saki murmushi tana girgiza kai "Banda sharri uncle,ka fadi gaskiya" girarsa ya daga mata "Wacce gaskiya ce da tafi wannan,ni wani irin zaqi naji kina......." "Wayyo uncle,don Allah kada ka fada" ba shiri murmushi mai kama da dariya ya qwace masa,sai ya hade goshinsu waje daya "Don Allah ki barni na fadi irin abinda naji,da gaske nake widad,kullum sake dad......" Bata da zabi illa hade bakinsu da tayi waje guda,shi kuma hakan ya zamana kamar ta sake bashi dama ne,sai kuwa ya manne mata da kyau. Da qyar ta qwaci kwanta tana sakin numfashi,ta nuna masa agogo da yatsantsa "Lokaci yana tafiya, everything is ready" tayi tsalle ta fice daga bedroom din don kada ha biyota. Binta yayi da kallo yana murmushi,sai ya waiwaua gefan inda affan yake,sun tula masa pillows basu sani ba,ya gyara masa kwanciya sosai sannan ya fada toilet. Komai ita ta taimaka masa ya gama shi,yayi kyau cikin Wani lallausan yadi ruwan zama,wanda ya sake fitar da haibarsa da kwarjininsa. Widad dake tsaye tana qare ma kwalliyar tasa kallo,tana sake jinsa har cikin jininta tayi.magana qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta bayan ya ajjiye tissue din da ya gama goge sauran maiqon abincin da yaci,saiya zube hannayensa a aljihun wandonsa ya fara takowa inda take idanunsa akan fuskarta "Me kika ce?" Dariya take qoqarin dannewa "Bance komai bafa" da wani irin zafin nama ya kamota ya sakata sosai cikin jikinsa yana sansanarta "Kayi kyau da kwarjini,idan ka fita kamar ba kai ba,kamar ba kaine ka gama danne 'yar mutane dazu dazu ba,ko ba haka kikace ba?" saita zaro ido sosai,batayi tsammanin yaji abinda ta fada ba,girgiza kai ta fara yi "Don't say no.....na riga naji" juyo da ita gabansa yayi "I love you,ina kishinki sosai" ido ta lumshe tana mamakin yadda yake jaddada maganar kishin nan koda yaushe "I love you too" ta amsa masa a sanyaye. Har gaban mota ya rakoshi,tana tsaye suka fice daga gidan bayan ya leqa ya yiwa hafsat sallama,ita din dama can batasan rakoshi ba,saidai idan wani abun zata amsa tayi mantuwa ta biyoshi,ko kuma abinda zata karba din yana cikin motar tasa. *B A Y A N A W A H U D U* Misalin qarfe hudu na yammaci,tana kwancw a falo tana chart,affan yana kwance saman cikinta yayi bacci kira ga shigo wayarta,data duba da kyau sai taga abubakar ne,dan uwa ga mahaifiyarta wanda yake kamar mazaunin uba a wajenta,yana da matuqar kirki,ya kuma dauketa kamar diyar cikinsa. Kwantar da affan tayi,ta zauna sosai tana amsa wayar,suka gaida dashi sannan yace "Muna garinku,amma bamusan inda zamu iso gidanki ba,don wannan shine shigowarmu ta farko bauchi" sosai dadi ya kamata,iya zuwan da takeyi wajen mummynta kawai ta fahimci yadda sukeson mommyn nata,bama ita kadai ba,har su da suka fito daga cikinta "Ta wanne guri kuke?" "FAAZ hotels" "Bansan gurin ba kawu,amma zan tambaya saina taho daku" ta fada cikin murna,karon farko wasu daga dangin mahaifiyarta zasu kawo mata ziyara gidanta. Suna gama wayar ta kira abbas din don ta gaya masa zata taho dasu,saidai cikin rashin sa'a dukka layukansa is switched off,ta kira rose tace ta yiwa samuel magana ko tare suke ya cewa ogansa ya kirata,to amma shima ba tare dashi sukayi tafiyar ba,ta kusa minti talatin tana kira bata sameshi ba,sai ta miqe ta gyara yafen mayafinta ta fito farfajiyar gidan. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 26 Hafsat da lawal ta hango tsaye jikin motar hafsat din suna magana,da alama fita zasuyi ko kuma sun dawo,ba kasafai takeson shiga sabgarsu ba,amma yanzun dole tayi tambaya taji ta inane wurin yake tunda ba garinta bane,saita sauya akalar tafiyarta zuwa wajensu. Dif sukayi sanda suka ganta a wajen,hafsat ta dauke kai kamar bata ganta ba "Don Allah lawal ta ina faaz hotels yake?" Tambayar data fusgi hankalin hafsat,saita waiwayo ta zubawa widad din ido "Faaz hotel kuma?" "Eh nayi baqi ne zan taho dasu" "Okay" ya fada sannan ya fara mata kwantance inda yake ya qarashe da cewa "Kibi ta nan ahmadu bello way" "Aah,ta sa'adu zungur road kaman yafi" hafsat ta tsoma bakinta,bata kawo komai a ranta ba,cikin tsarkakakkiyar zuciya tace "Yauwa na gode" kamar tace lawal din ya kaita ganin suna rufe motar sun gama uzurinsu da ita amma saita fasa,ta shige part dinta da sauri ga sauya kayanta zuwa abaya wadatacciya tayi rolling,saita saba affan a kafadarta ta dauki key dinta da kudin napep da zai kaita ta fita,tasan ba zata jima ba,duka duka da zuwa da dawowar ba lallai ta wuce awa daya tunda basu da wani nisa sosai. Wani irin duumm yaji kansa yayi,ya sake daukan wayar jikinsa yana rawa ya kuma buda hotunan,itace dai..... widad dinsa ce dai babu canji, itace dauke da affan dinsa,yaron dake tsananin kama dashi "Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" ya fada wannan karon har bakinsa yana rawa,kansa ya sara masa yasa hannu bibbiyu ya dafe,wani sashen na zuciyarsa yanata qoqarin kawo uzuri da kariya a gareta,amma wani sashen kuma yana qaryata haka hadi da sukan duk wani hanzari da zuciyarsa ke badawa,sashe mafi qarfi kuma mafi rinjaye kenan. A hankali sai zuciya ta fara ayyano masa irin abubuwan da suka faru a jiyan,ita tafara tashinsa a bacci,ta kuma shirya masa komai na tafiyar tun lokacin tafiyar baiyi ba,ta dameshi kuma ya tashi ya shirya kada yayi latti,hakan yana nufin dama akwai abinda ta shirya zatayi a ranar shiyasa take Allah Allah ya tafi?. Bayan nan yayi kiranta da yammar kusan miscal uku,bata biyoshi kiran ba,har sai cikin dare bayan bacci ya daukeshi,sai da safe yaga miscal,bata kuma sake nemansa ba,me hakan yake nufi,duka wadan nan abubuwan da ido yake gani ya zama gaskiya kenan?, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya sake fada kansa yana qara sara masa sosai yayi qas da kansa yana jin yadda zuciyarsa ke masa wani masifaffen zafi. Yafi awa uku cikin matsanancin halin da baisan dame zai kwatantashi ba,kafin daga bisani wata qaqqarfar zuciya ta yunquro masa,ya miqe ya fara hada kayansa,abinda sam baiyi shirinsa a sannan ba har sai zuwa gobe da safe. Bashi da kuzari ko qarfin halin da zai iya tuqi daga sokoto zuwa bauchi,dole ya nemi daya daga cikin yaransa da sukayi tafiyar tare ya bashi driving din. Tunda suka dauki hanya bai iya katabus din komai ba,sunci rabin tafiyar saiga kiran widad din ya shigo,ya kalli wayar sosai kamar widad dince a gabansa,zuciyarsa na wani irin bugawa,wani sashe na zuciyarsa na bashi izinin dagawa,wani sashen kuma yana hanashi tare da tuna masa girman laifinta a gareshi,daga qarshe daya sashen yayi rinjaye,sai yayi rejecting kiran,yama kashe wayar gaba daya,ya maida kansa jikin kujera ya kwantar yana lumshe idanunsa,kanshi yana ci gaba da sara masa "Widad fa,widad" abinda zuciyarsa keta maimaitawa kenan cike da wani irin zulumi tashin hankali tsoro da kuma fargaba. Cikin mamaki ta sauke wayar tana kallon fuskar wayar sosai,zuciyarta na gaya mata rejecting kiran nata yayi amma ta kasa gasgatawa,saita katse shakka da mamakinta ta sake yunqurin kiransa a karo na biyu,saidai computer ta gaya mata wayar tasa a kashe take. Jim ta danyi,to kodai wayar tasa babu charge ne,ya qare sanda take kiran nasa?,bata sani ba,amma daga qarshe saita barwa kanta cewa hakanne,don baka ta miqe ta soma aikace aikacenta lokaci lokaci tana gwada sake kiransa,saidai babu wani abu daya canza,a kashe din dai take. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 27 Yamma lis suka sauka a bauchi saboda gudun da yaron nasa ya tsula bisa umarnin ogan nasa "FAAZ hotels zaka kaini" ya fada a wani galabaice,kamar yau ya fara doguwar tafiya a mota "Yes sir" ya fada yana karya kan motar tasu ya dauki titin da zai sadasu da hotel din. Karon farko gabansa yayi mummunar faduwa sanda suka isa gaban hotel din,abind aya jima baiji ba kenan,duk irin hatsarin aikin da zai shiga kuwa,zuciyarsa ta dinga masa saqe saqen munana abubuwa,tana ayyana masa adadin xuwan widad wajen,kamar wanda allurarsa ta motsa ya zunkuda cikin zafin nama ya buda murfin motar ya fice,bayan ya yiwa yaron umarnin ya zauna cikin motar ya jirashi,yanzu zai dawo su wuce gida. Cikin rashin nutsuwa yake takawa zuwa makekiyar qofar hotel din,hannunsa cikin aljihun wandonsa yana qarewa qofar kallo,duk da irin qwarewarsa a wajen aiki,duk da qwarewarsa wajen iya bincike amma a yau kamar an bude kwanyarsa an kwashe dukka wannan qwarewar,komai ya kwance masa,a haka ya isa ga security din dake zaune daga bakin qofar. Sallama yayi masa ya bashi hannu suka gaisa,ya gabatar masa da kansa gami da nuna masa ID card dinsa,ya jinjina kai "To na shiga ciki ne na sanar da manager zuwanka?" Kai ya girgiza da sauri ransa yana masa suya,yau wai shine zai gwada aikinsa akan widad?,yau shine yazo bincike hotel akan widad?,halittar da duk duniya babu ta biyunta a wajensa?. "Ba buqatar haka,personal investigation ne,tambaya daya ce kawai zan maka,idan akwai buqatar shiga cikin sai na sanar maka" "To officer ba damuwa" . Wayarsa ya ciro daga aljihunsa yana rawa,ya buda hoton widad sannan ya miqa masa yana hadiye wani abu mai tauri a wuyansa,zuciyarsa kamar zata fashe "Zaka iya shaida wannan fuskar?,ina nufin ka taba ganinta a nan wajen naku?" Cira kai yayi daga kallon fuskar,ya shaidata sosai,matar da yayita jiya mamaki da yaji tana hausa,don bai zaci ta iya hausa ba "Tabbas jiya ma na ganta" "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ya furta yana saurin dafe qarfen qofar sanadiyyar jiri da yaji yana niyyar kayar da shi, idanunsa suka rufe na wucin gadi,da qyar ya samu ya daidaita kansa jin security din yana tambayarsa lafiyarsa lau?. "Na gode" ya fada yana karbar wayar daga hannunsa,sannan ya juya da wata irin tafiya yana nufar motar. Koda ya shiga sai ya saka kansa tsakiyar hannayensa yana jin kamar ana masa laguden tashin hankali,wani saqo can qasan zuciyarsa na gaya masa qarya ne,amma wani abu mai qarfi yana taso masa daga wani guri da baisan ina bane,yana gasgata masa abinda yake son ha zarga din "Idan hafsat kishiyace,bata qaunar ta,zata iya mata sharri,shi kuma wannan security din fa?,meye hadinsa da ita da zai mata sharri?,ga shaidu da suka tabbatar kuma da haka?" "Sir.......sai ina?" Muryar yaron ta kutsa tunaninsa "Kaini gida"ya furta ba tare da ya iya daga kai ya kalleshi ba. Farfajiyar gidan babu kowa,sai lawal dake zaune daga bakin gate yana yiwa hafsat CID din shigowar abbas din,ko karbar key din motar bai iya tsaiwa yayi ba ya wuce sashensa,yace lawal ya sallami yaron da kudi masu nauyi ya karba key din ya bayar cikin gida a ajjiye masa. Kansa a sama ya wuce sassan widad,hakanan yaji ko sassan nata bayason kallo bare ya hangeta. Da murnarsa ya kirga kudi ya bashin,ya karbi key din ya wuce sashen hafsat kansa tsaye baki har kunne,lallau yau ya warke,aljihunsa zai jiqe. Tana jin muryar sa ta fito da gudu gudu daga kitchen tana watsa hannaye idanunta a waje,irin na mutumin dake jiran wani kyakkyawan albishir "Ya ake ciki?" Dariya yadan saki "Da alama komai ya kankama fa,sassansa ya wuce yana tafiya da qyar,ga key dinsa nan" "Ma sha Allah,miqomin shi,ina zuwa" ta fada tana karbe key din,saura kadan ta fadi saboda yadda zaninta ke hardeta ya fice daga falon. Ba abinda ya iya cirewa daga jikinsa banda takalminsa,sassan fes wanda yake da yaqinin gyaran da widad din tayi ne randa zata fita a girki,abinda ya sake dagula masa lissafi,da qyar ya iya zama saman kujerar. Duk inda ya kwaso lissafin sai ya wargaje masa,yaji har cikin zuciyarsa yana qyamarta sosai,haske da tagomashin data samu cikin zuciyarsa wani qaqqarfan abu yana shirin tasowa ya lullubeshi fes!!! Ta yadda ko burbushinsa ba za'a samu ba. Sai data dan tsaya ta saita nutsuwarta a bakin part din nasa sannan ta tura qofar tayi sallama,bata ko duna yanayin shigarta ba dake a jikirce,wata rigar kamfala da sukayi anko ce ash color da aka yiwa dinkin half bubu,ta daura zanin atamfa a sama,sai dankwalin kamfalar a kanta data masa wani dauri kamar na 'yan talla. Sosai kamfalar ta fidda duhunta,don dama daqyar tayita,don kala ce dake nuna baqinta,wannan yasa bata cikason abu ash ba. Da qyar ya bude idanunsa ya watsasu a kanta yana amsa sallamarta,sai yaji kansa ya sake sarawa,ya zuba mata ido harta iso gefansa hannun kujerar da yake kai "Sannu da zuwa daddyn mimi" "Yauwa sannuku" "Ya hanya?" "Alhmdlh ya yaran?" "Lafiya lau,sun gaji da jiranka sunyi bacci,yau kayi delay na dawowa,hala ka tsaya wani waje ne?" Kai ya girgiza mata,haka kawai yaji baiso tasan damuwarsa,tunda dama asalan basu saba haka da ita ba,batasan damuwarsa ba,shi daya yake cinye kayansa yayi solving dinta,saiko hajiyarsa Allah ya jiqan rai,ita kuma ba kowacce damuwa yake gaya mata ba,saboda kiyaye lafiyarta "Sokoto to bauchi kinsan tafiyar ba kadan bace" saita gyada kai "Ummmm,kuma fa hakane" daga haka shuru ya biyo baya a tsakaninsu,tanason taji ya sake cewa wani abu, tanason taji koda kalma guda daya daga bakinsa amma yaqi magantuwa,daga bisani ma sai ya miqe yana shirin shigewa bedroom dinsa "Baka buqatar komai?" Bayajin zai buqaci wani abun,amma kuma idan baice komai din ba bazata qyaleshi ya huta ba,a yanzun kadaice kawai yake buqata ko zai samu sararin yin tunanin mafita ga gagarumin ibtila'i ko musibar data afko rayuwarsa "Ki kawomin black tea" "In sha Allah" ta fada da wani yanayi da sam bata saba ba,hakan ya sanya ma abun bai wani karbeta ba. Ta gama shirya komai tsaf sai zaman jiransa da takeyi,tayi shiga irin wadda tasan yana tsananin so,tayi kewarsa kwana dayan nan kacal,ya shiga rayuwarta da yawa,ko yaya suka nisanci juna dukkansu saisun galabaita,ta samu wasu satar amsoshi da yawa a group dinsu na hanyoyin da zaki sake tsayewa mai gida a rai da takeson ta gwadasu a yau din,ita ta yarda da kanta,ta kuma yi imanin ta tsaya a rayuwar uncle din nata yadda ya kamata,amma kullum tunaninta da burinta shine taci gaba da tsaiwa a wannan matakin ba tare data cutar da abokiyar zamanta ba. Har aka idar da magariba tana sake gwada wayarsa amma still a kashe,sai abun ya soma bata tsoro,tayi Shuru saman abun sallah,cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa lafiya,ta qiyasta wasu awanni,indai suka shude bai iso ba,bai kuma bude wayarba zata magantu,ba zata iya jurewa ba. Har isha'i shuru,don haka bayan ta idar da sallar isha din saita zura slipper dinta ta dora babban hijab saman qananun kayan jikinta sabbi fil data saka sabodashi,ta fito farfajiyar gidan tana neman fahad. Da motarsa ta fara yin ido hudu,mamaki ya cikata,sai taja burki kawai tana kallon motar,yaushe ya shigo?,shine tambayar da takewa kanta,amma saita bawa ranta qila tana tsaka da sallah ne yanzu yanzu shi yasa bataji ba. Muryar fahad taji a bayanta,saita waiwaya "Yaushe daddy ya shigo ne?" "Kai ai ya kusa awa biyu inajin" "Ok inajin ya leqo ina ciki" ta fadi yana qoqarin danne damuwa da mamakin nata dai,sai tayi gaba tana cewa yadan duba mata affan a falo kada ya tashi ya fara koke koke. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 28 Ba kowa a falon,saita saka kai zuwa bedroom dinsa,ta isa bakin qofar ta murdata ta tura tana saka kanta ciki. Dai dai sanda yake tsaye gaban madubu yana goge kansa da fuskarsa da qaramin towel,ya qurawa fuskarsa idanu da kyau,sai kace wanda yake karantar wani sabon abu daya tsiro masa a fuskar,saidai duka ba haka bane, zuzzurfan tunani da ya cika zuciyarsa fal. A hankali idanunsa suka sauka akanta ta cikin madubin dake gabansa,amma sai ya janye idon yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da goge jikinsa. Ko sau daya a tsahon zamansu bata saba ganin haka ba,don haka bata kawowa ranta wai ya ganta ba,saita fara takowa cikin shagwabar nan tata data saba masa tana cewa "Ya da haka uncle?" Ta fadi tana kebe fuska kamar zata sakar masa kuka,duk kuwa da cewa ranta cike yake fal da wasi wasi. Bayajin zai iya kallon fuskarta a sannan,saboda wasu abubuwa da zuciyarsa ke sake saqa masa a kanta,sai ya barta bai tanka mata ba,har ta iso bayansa,ta rungumeshi tsam ta bayan,tana dora hannuwanta saman ruwan cikinsa. Qamshin turarenta da abaya yafi qaunar ji fiye da komai,a yanzun sai yaji dadinsa yana sauyawa zuwa wani abu da yafi qyama hadi da tsanar shaqa "Uncle?" Ta sake kiransa a shagwabe,kanta kwance a gadon bayansa. Ajjiye towel din hannunsa yayi saman madubin,sannan ya saka dukkan hannuwansa biyu ya zare hannunta dake saman cikinsa,har zata fara masa tabarar tata ya waiwayo suka hada ido,sai tayi sak tana kallonsa. Wani abu take gani yana wulgawa cikin qwayar idonsa, irin abinda bata taba gani atare dashi ba,wani irin kallo da ya sanyata jin ta muzanta gaba daya,kallon da ya sakata ta daburce ta kuma rude,sai kuma ya dauke kansa daga dubanta ya taka gaba zuwa wajen drower dinsa don ya fidda kaya,ta taka da hanzari ta cimmasa,ta kama murfin drower din da nufin budewa ta zaba masa kayan kamar yadda ta saba masa amma sai ya dakatar da ita da kakkausar muryarsa "Stop,bashshi kawai" abinda yayi mugun sanyaya mata jiki,yau me ya samu uncle?,me ta aikata masa yake zuwa da baqin halayen da bata taba ganin irinsu tattare dashi ba. Tsabar mamaki yasa tayi sakato tana kallonsa,har ya ciro kayan ya dawo gefan gado ya fara fidda na jikinsa don ya saka wadan nan. Har yau bata iya kallonsa naked don haka ta russunar da idanuwanta,amma jin muryar hafsat daga falo tana doso dakin ya sanyata zabura ta isa gabansa,ta dauki rigar ta fara ware masa fuskarta qunshe da murmushi tana jira ya gama saka boxer din ya karba,a haka idan ka kallesu saika dauka soyayya ake bugawa a lokacin. Sak hafsat din tayi wani idin abu na bugunta "Kan jar uba!,kada dai ace wannan plan din ma score zero point," shine ya fara zuwa mata ka,da kuma irin kudaden xaga narka. kamar ta juya da tea flask din kuma saita fasa ganin ya ganta,ta tufa qofa ta shiga idonta akan widad da babu alamun akwai abinda yake damunta. Cikin son nuna bariki ta qaraso cikin daki "Gashi abban mimi,akwai wani abu da kake buqata kuma?" Kai ya girgiza mata,saita jinjina kai "Alright,idan akwai sai kayimin magana" "Thanks" kawai yace muryarsa can qasa, saita juya tana ficewa kamar babu abinda ya dameta dasu,saidai can qasan ranta tana jin kamar ta juyo ta dawo cikin dakin ta kora widad din. "Ehen......yauwa uncle,ni zan saka maka da kaina please,ka barni na samu wannan ladan" ta fadi a shagwabe da qarfi tana kallon bayan hafsat,dai dai sanda taga tana shirin ficewa a dakin. Aikuwa maganar ta daketa sosai,don da qyar ta iya cinyewa bata waiwayo ba,saita dan qara sauri cikin tashin hankali ta fice ta isa sassanta. Kallonta yake kai tsaye cikin idanunta,yasa hannu ya damqe rigar dake hannunta "Jiya ina kika je?" Gabanta ya fadi,wani tsoro da shakkar gaya masa ya kamata,saita saki murmushi "Jiya?,bako ina,ina gida" idanunsa duka ya lumshe "Ya Allah,ta tabbata......lallai ta tabbata" "Please do me a favor" ya furta idanunsa a lumshe ba tare daya bude ba,don bayason kallon fuskarta kwata kwata "Name uncle?" "Stay away from here,i need space" gaba daya sai jikinta ya hau rawa,to amma saita hanawa zuciyarta samun rauni "Ok shikenan" ta sakar masa rigar ta juya a sanyaye,harta kusa fita ta jiyo lallausar muryarsa yana cewa "Karki matsawa kanki,ki kwanta a sashenki kiyi baccinki" da qyar ta hadiye wani abu da ya taso mata,ta gyada kai ba tare data juyo ba ta fice da sassarfa. Sai daya tabbatar ya kulle sashen nasa sannan ya dawo ya zauna,wani baqinta na sake ninkuwa a ransa,zarginsa kuma na sake tabbata, widad da baisanta d qarya ba ko misqala zarratin yaushe ta fara qarya?,lallai akwai qamshin gaskiya a dukka abinda yake zargi. Wata baqar zuciya da baisan ta inda ta shiga qirjinsa ba ta dinga kambama abun tare da qara masa muni a idanunsa,wanda daga qarshe ta tayashi yanke mummunan hukunci akan widad din. Karon farko a rayuwar aurensu da Wani abu me suna bacin rai da batasan ta inda ya samo asali ba ya raba makwancinsu a ranar da yake girkinta ne,ranar da babu ranar da uncle din yake zumudin zuwanta irinta,ta rungume affan tsam a qirjinta tana ta juyi,ta lalubi bacci kaf a idanunta ta rasashi,ba irin tunanin da baizo kanta ba,amma saita taushi zuciyarta take gayawa kanta wata damuwa yake ciki wadda qila bayaso su sani,tunda a gabanta hafsat ma ta fice,amma bataso haka ba,batason ya dinga aje damuwa a ransa,tafison suci gaba da sharing problems dinsu tare suna samo solution yadda suka fara tun farko. Sai tsakiyar dare ta samu bacci ya dauketa,kiran sallar farko kuma ta farka a firgice saboda wani mafarki mara dadi da tayi,sanda ta idar da sallar asuba ta fuskanci saqo ya shigo wayarta,data duba saita saki murmushi,zuciyarta na saki daga damuwar data kwana cikinta,ranta yana mata fari sosai _ki shirya around 10 zaki rakani katsina,wani aiki ya tasomin,but basai kin shigo ba,idan kin shirya kawai ki fito gaba daya_ Dadin da taji a ranta yasa ta miqe tun lokacin ta fara shiri,ta fara da hada masa lafiyayyen breakfast,farfesun kaza da yaji spice masu dadi,sannan ta masa hadadden spicy tea,gefe daya ga wani irin chips dake cakude da qwai,sannan ta gyara sashen,tayi wanka,sai a sannan affan ya farka, yaron yana da haquri sosai,ba kasafai yake hanata aiki ba,ta dagashi tana masa miqa hadi da karanta masa addu'ar tashi daga bacci sannan ta rungume shi tana kissing dinsa hadi da tambayarsa "Ka tashi lafiya uncle dina na kaina?,yau kaji baccin ka daban ko?,munyi missing daddy dukkanmu,karka damu,we have a trip tare da daddy,na tabbatar we will enjoy it in sha Allah" saita saki murmushi tana shafan kan yaron,sannan ta miqe dashi ta masa wanka a toilet suka hau shiryawa. Kayan data sawa yaron ya dace sosai sa shigar atamfar da tayi,atamfar tayi mugun karbarta kamar don ita aka bude kamfani atamfa,ita kanta sanda ta tsaya a gaban madubi tana kallon fuskarta a tsakiyar mayafin kanta ruwan zuma sai data burge kanta,ta saki murmushi tana jin dadin yadda kullum take sake zama cikakkiyar mace me iya dressing me fusgar hankalin mijinta, cikakkiyar macen da duk inda ta shiga za'a waiwaya a kalleta,ta tashi daga sakaltacciyar widad din ummu,ta zama classy madam din abbas turaki. Fahad ne ya shigo yana gaya mata "Uncle yace ki fito anty" "Breakfast dinshi fa,kace a kawo masa na gama" "Okay bari na gaya masa" sai ya juya ya fita,ba jimawa ya dawo ya gaya mata yace he's okay,bazai iya cin komai yanzu ba,sai abun yayi mata banbarakwai,bata taba masa tayin abinci koda ba ranar girkinta bane ya tankwabar bare kuma ranar girkinta,don haka sai ta share wannan maganar ta shirya abincin cikin wani basket mai kyau da daukan hankali,na musamman ne da tasa akayi mata da dukka favourite colors na abbas din don saboda shi din, kome zatayi tana yin sa da colors ko yanayin da tasan zabinsa ne,bata taba duba nata choice din,wannan ya sake sawa ta kama zuciyarsa da kyau. Fahad ta bawa kwandon,ita kuma ta kulle sashen nata,ta saka affan a kafadarta ta fito. A seat din baya yasa fahad ya saka kwandon,karon farko da ya rasa duk wata sha'awa na cin abincinta,bama abincinta kawai ba,gaba daya yayi loosing komai da yakeji a kanta,sanda ya daga ido ya hangeta tana takowa,gaba daya ta haske farfajiyar gidan da wani irin kyau da qamshinta daya fara aika saqon tahowarta kowanne sashe na gidan,ita da yaron sunyi wani kyau na kusamman kamar fure,saiya dauke kansa ya maida gefe,yana jin zuciyarsa na masa matsanancin bugu kamar zaya fado daga qirjinsa,abubuwa hiyu suna gogayya cikin qirji guda daya lokaci guda SO YAYYA DA KIYAYYA,soyayyar nason tasiri,amma wani abu mai nauyi yana tasowa ya danneta yana baiwa qiyayyar damar wanzuwa a farfajiyar qirji da zuciyarsa,zuciyarsa na kwadaita masa ya sake kallonta,don ta fito a kamar da yakeso,amma tsananin haushinta ya danne wannan muradin da ransa ke dashi,don haka kafin ta qaraso ma ya shige cikin motar yana haki qasa qasa. Mamaki ya sake cikata,da kansa a irin wannan lokacin yake takowa ya karba affan daga hannunta ya bude mata motar ta shiga sanan ya miqo mata shi,jiki a sanyaye ta qarasa motar ta bude ta shiga ta zauna, qamshinta ya qarasa baibaye ilahirin motar "Ina kwana uncle" ta gaaidashi tana dan rusunawa,ya amsa a taqaice ya miqa hannu yana karbar affan,tsam ya rungumeshi a qirjinsa hana jinjina hukuncin da zai yanke wanda har yaron zai shafa,amma dai wannan shine maslaha a wajensa,don yana ji a zuciyarsa bazai taba iya zama da fasiqar mace ba "Why widad why?,ta ina na gaza?" Ya fada can qasan ransa yana jin wani ciwo,saiya sunkuya a sanyaye yayi kissing goshin yaron ya saka masa dariya kuwa,sai zuciyarsa ta karye,ya miqa mata shi ba tare daya sake kallon fuskarta ba,don kallon fuskarta na gaya masa wani fa ya taba tabata,wani ya taba rabar wanann jikin nata,wani ya taba kwanciya da ita yadda kakeyi,tunanin da yake sakashi jin kamar zaiyi bindiga. Duk yadda taso yaci abincin ya qiya,dole ta qyaleshi,tayita sako hira a hanyar tafiyar amma yana banzatarwa,ta jinjina kai tana mamakin wacce damuwa ce haka ke damunsa?,don kada fa takura masa daga qarshe sai tayi shuru itama, motar kamar ta kurame,tafiya mara dadi data fara yi dashi tsahon rayuwarsu dashi,har daga qarshe bacci ya dinga daukarta,dama yau din bata samu tayi baccin nata data saba ba. Lokacin da zasu gifta kano sai taji kamar ta sauka yaje ga ummunta,amma dole ta danne,koshi bata cewa komai ba,batason ta dameshi da magana,tunda ta fahimci a yanayin rashin son magana yake. Sai bayan azahar sannan suka isa magariba,ta ware idanunta sosai tana jin kewa da shauqin mommynta,tana jin dama ya ajeta wajenta duk da rakiyar aiki tayi masa,ga mamakinta sai taga ya dauki hanyar gidan nasu,ta kasa haquri sanda taga sun shiga unguwar su "Na gode uncle" kansa kawai ya daure ya gyada mata ba tare da yace komai ba. A qofar gidan yayi parking,cikin sa'a usama daya daga cikin qannenta maza da mamarta ta haifa a gidan ya fito,cikin zumudi da murna ya qarso wajen,suka gaisa da abbas sannan ya fidda mata kayanta "Kakaimin jakar kazo ka karbi affan" saboda yadda taji qafarta da mararta duka sun riqe mata gam. Yana shiga ya fito ya karbi affan din suka shige ciki suka barta,ta buda murfin motar,saidai har a sannan abbas din baice mata komai ba,sai ta dakata da fitar ta waiwayo "To sai yaushe kenan?,sannan a nan zaka sauka?" Kai ya girgiza mata alamun a'ah,ya bude bakinsa da yakejin kamar ya manne yace "Ki zauna kawai,sai lokacin dana gama aikin,zanzo na daukeki" duk da yanayin da yayi mata maganar yana saka mata rashin jin dadi a ranta,saboda ba yanayin daya saba mata mu'amala dashi bane,amma jin zata dan zauna a gidan ya mata dadi,tanason kasancewa sosai da mamarta,don tana jin dadin haka,uwa uba tana qaruwa da abubuwa masu yawa,sajta jinjina kai "Allah ya bada sa'a,yasa a gama lafiya, zamuyi kewarka nida affan" ta fadi a sanyaye da wani abu dake bugun zuciyarta wanda batasan meye ba "Ameen" ya fada muryarsa a qasa "Ba zaka shiga ku gaisa ba?" Tayi masa tayi,abinda bata taba ba kenan sai yau "Later" ya fada a gajarce,saita jinjina kai kawai,ta saka qafarta ta fice a motar jikinta a mugun sanyaye kamar wadda aka zarewa laka. *H U G U M A* Arewabooks:huguma A RUBUCE TAKE (k'addarata) Part 2 Page 29 A nutse ta bude k'ofar toilet din ta fito daure da babban towel fari sol,lallausar farar fatarta mai santsi da sheqi tana ta daukan idanu. Gaban dressing mirror din dake dakin ta isa,ta ja kujera ta zauna tana kallon fuskarta a ciki,gaba daya jin ranta da jikinta takeyi babu dadi,fuskarsa ke gilma mata cikin idanuwanta,sam jikinta bai bata ba,ta kasa nutsuwa gami da gamsuwa da wannan tafiyar da ya qirqirar mata bagtatan lokaci guda,tana tsaka da hidindimunta,tun daga yanayi fuskarsa da kuma yadda ya dinga tuqi daga bauchi zuwa katsina takejin kamar ba abbas dinta ba,tabbas akwai abinda ke faruwa,akwai wani muhimmin abu dake gudana,tayi tunani har babu iyaka,ta laluba dalilin tas tun daga randa ya sanya qafa ya fita daga gidan zuwa dawowarsa da kuma isowarsu katsina......tayi zagaye cikin tunani da abubuwan da suka wanzu kaf! Ta kasa gano abu guda daya farun. A iya saninta sun rabu suna masu kewa da kuma shauqin juna kamar ko yaushe,hakanan koda safiyar ranar sun jima ita dashi akan waya suna hira,wata irin hira irin wadda ke fallasa sirrin zuciyar masoyi zuwa ga dan uwansa,yana ta mata qorafin a takure yake acan din tare da mita tana lallabashi tana kuma masa dariya,har suka rabu kyawawan kalamai ne bisa fatar baki da zuciyar kowannensu,to amma me ya canza hakan? "AKWAI WANI ABU" ta fada murya qasa qasa tana motsa tausasan lips din bakinta tare da zare idanunta daga kallon da take qarewa fuskartata,ta dauki lotion dinta mai taushi da qamshi ta fara shafawa fatarta cikin kasala taraddadi da kuma damuwa. Duk bayan wasu mintuna saita kalli wayarta dake gefe tana tsammanin kiransa,saboda ta sani haka suka sabarwa juna,duk inda zashi cikin nigeria..... matuqar tafiyar mota zaiyi itace abokiyar hirarsa har ya isa inda zashi,idan kuma hakan bata kasance ba.....zaiyita kiranta har ya isa din,amma wannan karon ko gilmawar miscall dinsa bata gani ba bare kiransa,a qididdigen da tayi a yanzun kuma, tabbas koda baije gida ba yana gab da isa "Waishin meke faruwa?" Ta sake jefawa kanta tambayar wata irin damuwa tana tabata tun daga qasan zuciyarta. Cikin dauriya ta shirya kanta cikin doguwar rigar atamfa,ta fidda ainihin kyanta da surarta sosai,duk da yanayin da take ciki sai data tsaya gaban mudubi ta kalli kanta,lokutta da dama takan dubi kanta da kanta tana tuna WACECE ITA A SHEKARUN DA SUKA SHUDE,a yanzun sai taga kamar ba ita ba.....komai yana zuwa yana shudewa da wani irin sauyi mai ban mamaki. Lausasan slippers ta zurawa qafarta,sannan ta isa bakin qofa ta kama handle din ta bude tabi siririn corridor din da zai sadaka da ainihin falon gidan. Tun bata qarasa ba ta hangeta zaune cikin falon,halittace mai girman matsayi a wajenta,halitta dake sahun farko cikin halittu mafi soyuwa a wajenta,a duk lokaci irin wannan da zatayi balaguro ta taho takanas saboda kasancewa da ita.....duniyarta kan cika da farinciki,takanji a duniya yanayi irin wannan bashi da tsaara a wajenta. A jikinta taji tahowarta,saita dauke idanunta daga kan tv din da take kalla ta maida kanta,kusan lokaci daya suka sakarwa juna murmushi,ta kuma rigata magana "Wannan nauyin wankan naki dai yana nan,affan ya fara kuka har sai da aka fitar dashi" cikin karaya da rauni da takeji cikin gangar jikinta da zuciyarta ta qaraso dab da ita ta zauna,tana shirin amsa mata.....kamar me kiran yana jiran dai dai lokacinne kira ya shigo wayarta,a hanzarce ta daga wayar tana duba me kiran, zuciyarta cike da fata da burin ganin wanda ranta ke darsa mata. Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba hadi da fitar siririyar ajiyar zuciya ba "Ina zuwa" tace da mommie,ba zata iya amsa wayarshi a gabanta ba,ita kadai tasan hottest words da suke gayama junansu,kuma muddin aka samu mishkila mommie taji daga ita har shi sun gama tafka abun kunya. Kai tsaye dakin ta koma,ta samu gaban madubin data tashi dazu ta zauna tana yunqurin daga wayar "Assalamualaikum" ta fada a shagwabe tana karyar da wuyanta gefe,abu mafi soyuwa kenan da tasan yana so tattare da ita,har yau kallonta yake cikin madubin da yake kallonta shekarun baya da suka shude,bata canza a idanunsa ba "Wa'alaikumus salam" mummunar faduwa gabanta yayi daka jin sautin muryarsa me taushi da sanyi da yake mata magana da ita koda yaushe ta juye zuwa wata iriyar murya,irin muryar da yake magana da cirminals a yayin da aikinsa ya biyo ta kansu.....irin muryar da yake magana da juniors dinsa a yayin da suke hurumin aiki......irin muryar da yake magana da ita a duk sanda ya shiga qololuwar bacin rai da fushi,muryar da bata taba jin yayi mata magana da ita ba. Kowacce gaba ta jikinta tayi sanyi,tayi namijin qoqarin tattaro nutsuwarta da juriyarta tace masa "Ka sauka lafiya?,ya kaje gida" "Me yasa zaki aikata min haka?" Ya fada muryarsa tana ninka ta da kaushi da ban tsoro,daga cikin wayar tana iya jin hucinsa,da alama a matuqar bacin rai da kuma fusata yake, tambayar tasa kuma ta dilmiyar da ita kogin tunanin ina ya nufa ne?,kafin ta lalubo amsa kunnuwanta sun fara isar mata da saqo mafi muni cikin rayuwarta,daga bakin halitta mafi soyuwa a gareta "Ashe haka kike?,ina miki kallon saliha ashe mayaudariya ce ke?,maciyar amana ce?,macuciya ce ke?,na baki dukkan yarda,na damqi miki rayuwata ashe zaki wasa da rai na da lafiyata?" Wani irin tashin hankali ne ya sauko mata,me abbas ke fada ne "Me nayi maka?,abban affan me ya faru?,kasan me kake fada kuwa?" "Na sani!,nace miki na sani, tsahon yaushe tsahon kuma wanne lokaci kika dauka kina cin amanata kina kuma ha'intata WIDAD?" Kasa zama tayi,ilahirin jikinta ya dauki tsuma,sai ta miqe tsaye qafafuwanta suna rawa "Kana cikin hankalinka kuwa abban affan?,a ins kake yanzu?" Ta tambayeshi don ta tabbatar da cewa he's safe,ba gusar masa da hankali akayi ba yake gaya mata hakan "Har kinyi wayon fara bin maza?,ki kwana a hotel?,hakan bai isheki ba har sai kin dauko gardi kin kawomin gidana?,kin kuma kaishi har gadona na sunna widad?,wane laifi na aikata miki haka dana cancanci irin wannan hukuncin?" Yayi maganar ta qarshe muryarsa a wani mugun karye,saidai zafi da kaushin nan suna nan taf a muryarsa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada a bayyane,qafafuwanta suka hau rawa,gabanta yayi wani irin bugawa da zuciyarta ta hasko mata abinda yake magana a kai. "Hotel kuma?" Ta tambayeshi muryarta na wata mugun rawa,irin rawar dake bayyanar da zallar daburce wa a sanda aka ritsaka bisa wani abu na rashin gaskiya "Bakije bane?,ko zaki shiryamin irin qaryar da kika saba?" "Naje,tabbas naje....amm......" "Ya isa!!!!" Abinda ya fada kenan a tsawace "Abinda nakeson ji kenan kuma naji,kije ke da Allah,bazan taba yafe miki ba,amanata da kikaci ubangiji ne kawai zaiyimin sakayya,Allah ya isa ban yafe miki ba!!!" Kit! Wayar ta katse "Abban affan,daddy!!!" Ta fada a gigice,saidai tuni ya katse layin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta sake maimaitawa jikinta na wani irin kyarma tana yunqurin binsa,saidai a take kamfanin sadarwa suka gaya mata is switched off,saita saki wayar ta sulale a wajen tana sakin wani azababben kuka,wani abu mai tauri da zafi yana tokare mata qirji. "Waye ya ganta?,waye ya gaya masa?,waye???" Ta soma nacin gano daga inda maganar ta fita "Hafsah" taji an bata amsa daga can tsakiyar zuciyarta,kukanta ya tsaya cak na wasu sakanni,sai ta sake rushewa da kukan tana jin kanta yana sara mata,tana son miqewa amma ta kasa,idan tayi kamar zata tashi sai jiri ya maidata ya kayar,a haka aka turo qofar dakin,ta daga idanunta da taji kamar basa dauko.mata hoton komai da kyau ta tsurawa qofar idanu tanason tantance mai shigowar. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 30 Mummy ce dauke affan da yake faman tsala kuka,kukan nasa daya dinga shiga kunnuwan widad kamar a duniyar mafarki "Karbeshi ki bashi yasha,kamar bacci yakeyi" mummyn ta fada tana miqa mata shi,saidai ko motsawa batayi ba bare tayi azamar karbarsa,abinda yaja hankalin mummyn kenan "Ke widad.... widad lafiya?" A hankali ta ajjiye affan ta zauna tana jan widad din cikin jikinta gami da ambaton "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil" ganin kamar tana neman fita a hayyacinta,addu'o'i ta soma karantawa tana shafa mata a fuska,a hankali sai nutsuwarta ta fara dai daita,ganinta ya fara dawowa dai dai,ta zubawa mummyn idanu wasu hawaye masu zafin gaske suka fara zarya akan fuskarta. "Meyake faruwa?,me ya sameki?" "Mummy cikina ne yakemin wani irin ciwo" "Ya subhanallah" ta fada wani sashen na zuciyarta yana mata wasi wasi,yanayin da taga ta shiga baiyi kama da yanayin ciwo ba,yafi kama da wanda yaga wani mummunan tashin hankalin "Bari na kira saleem sai mu muje kiga likita,ai bai kamata a zauna ba" kama hannun mummyn tayi "Aah mummy,addu'a zakici gaba da yimin,ko yanzun da kika yimin na samu sassauci" kai ta jinjina badon ta yarda da widad da abinda yake damunta ba,a haka ta sakata ta shayar da affan saita sake karbarsa ta fita,saidai fiye da rabin hankalinta yana kan widad din,duk bayan wani lokaci saita leqata tare da tambayarta ya jikin?,akwai abinda take buqata?,saidai tace babu. A ranar yadda taga baqar rana haka taga baqin dare,baqin daren daya zame mata baqiqqirin,yayi mata kuma tsaho tamkar daren mutuwa,tayi dukka Wani qoqari na fahimtar da abbas abinda yake zato ba haka bane amma yaqi saurararta,ta kira har sau ba adadi,ta tura masa tex na bayanai har batasan yawansu ba amma ba abinda ya canza,kafin gari ya waye ta fige ta fita hayyacinta da tashin hankali,kamar yadda shima a nasa bangaren wani irin firgici tashin hankali da razani yaso da'ai d'aitashi,duk sanda ya tuna har lawal ya shaida fitar tata ya kuma bashi tabbacin zuwa take hotel din tana kuma kawo maza sai yaji kamar zuciyarsa ta fashe ya mutu. Sanda mummy ta shigo da safen ja da baya tayi tana salati ganin yadda fuskar widad din tayi jajur da ita ta tasa "Ke tashi,tashi ki gayamin gaskiyar abinda yake damunki" mummyn ta fada tan ajjiye kayan tea data shigo mata dasu,ta nemi gefanta ta zauna ta a nutse tana rutsata da ido. Batasan ba zata iya daukan wannan tashin hankalin ba,batasan zuciyarta ba zata iya jure wannan al'amarin ba sai data dora kanta a kafadar mummyn,a sannan ta sake gasgata uwa rahamace da babu kamarta a doron duniya,tayi kuka tayi kuka,har sai data zagwanye dukkan wasu damuwoyi data jima tana dakonsu a ranta,sannan a hankali cikin wani irin ciwo da zuciyarta ke mata ta furta ma mummyn abinda ke faruwa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta maimaita sau uku cikin mugun gigicewa tana daga widad daga kafadarta "Da wannan abun kike boyewa?,wacce iri ce ke widad?,to ni kaina wannan abun yafi qarfina,yafi kuma qarfin jina da kunnuwana,bazan iya jin wannan abun ni kadai ba,maza tashi"ta fada tana dauko ruwan tea din data shigo dashi "Tashi kisha wannan yanzun nan fita ta kamani,banga ta zama ba" haka ta dinga bata tea din,tana kurba tana jin kamar mutuwa takesha,mararta kamar zata fashe saboda tsananin ciwo,amma wannan ciwon bashi ke damunta ba,salama ne akan ciwon dake danqare cikin zuciyarta. Mummy na bata tea din tana sake maimaita innalillahin saboda yadda batun ya daki zuciyarta,ta sani ta kare kanta da mutuncinta tsahon rayuwarta,dai dai da rana daya kuma bata taba hutawa da yiwa yaranta da jikokinta addu'a kan samun kariya daga zina ba,tayi imanin addu'arta ba zata tashi a banza ba. Da cup din ta fice bayan ta sakata kwanciya sanda taga gumi yana yanko mata ko ina "Ki cire damuwa a ranki,Allah yana tare dame gaskiya muddin kinsan kedin me gaskiya ce,komai daren dadewa Allah bazai bar gaskiya ta tozarta ba" da wannan kalamin na mummy widad ta samu nutsuwa kadan,saidai duk da haka hawaye baibar fita daga idanunta ba,yadda abbas ya rufe idanu kamar yau ya fara saninta,yaqi ji yaqi gani,yaqi tsaiwa ya saurari gaskiyar ta. Shiryawa mummyn tayi tsaf suka fice zuwa gidan yayanta,tabarsu a gidan ita da affan da su saleem,tace su kula da ita su dinga yawan leqata,zasuje su dawo ita da usama. Shi kansa uncle bashir ya kadu da jin batun da mommyn tazo dashi,yayi Shuru yana jinjina maganar cikin ransa "Abinda nake gani,mu basu iska shida ita,shi din na tabbatar tunda jami'in tsaro ne bazai gaza bincike ba,zuwa sannan ya huce ba kamar yanzun da yake kan doron zargi ba,kuma wala'alla ya kammala bincikensa sai mu tuntubeshi muji daga gareshi,zan shigo naga widad din in sha Allah,kici gaba da tausarta komai zai dai daita in sha Allah" mummyn ta gamsu da shawararsa,da wannan kuma ta dawo gida ta shiga kula da widad din,dukkan qoqarinta ta sanaya akanta,bata barinta ta kebe kwata kwata saidai idan ya zama dole gudun kada ta shiga damuwa,saidai abar zuciya da abinda takeso,wata muguwar damuwa keta cin ranta ta can qasa,duk da tana ta qoqarin sakewa saboda yadda take ganin mummyn nata tana wahala da ita. Komai nata mutanen gidan sun bashi muhimmanci,kowa qoqarin ganin ya nuna mata damuwa da kulawarsa yake,amma har yau al'amarin abbas yaqi sakinta,mamakinsa ke cikata a duk sanda ta tunashi,a kowacce rana tana duba wayarta sau babu adadi waiko zataga kira ko saqonsa,kozai bayyana mata ya gano qarya ne sharri ne,ya gano kuskuren fahimtarta yayi,a kullum dakonsa takeyo ko zataga saqon ban haquri,amma shuruuuuu kakeji,babu shi babu dalilinsa. Idan tace zata kwatanta yanayin da rayuwarta ta fada a wannan tsukin ma bata baki ne,wata irin damuwa me cin gangar jiki da ruhi,duk yadda take wuni cikin jama'a idan dare yayi tazo bacci saita kasa,kuka kuwa ta yishi kamar hawayen idanunta zasu qare,wai yau ita uncle dinta ke tuhuma da laifin zina,zina fa?,saita rushe da kuka tana jin kamar ranta zai bar gangar jikinta ta huta. *H A F S A T* Duniya ta zame mata sabuwa,sai takejin kamar bata da sauran wata matsala kuma yanzun,duk sanda ta dubi sassan widad ta ganshi a garqame,ta tafi kuma ba'asan ranar dawowarta ba,tayi rawa tayi juyi duk ita kadai,ta kuma kira habiba tayi mata godiya mai yawa,tare da fadin zasu koma wajen malaminta nan kusa,amma abu daya dake damunta,irin yadda abbas din gaba daya ya canza,bashi da kuzari bare walwala, fara'a kam babu ita,tuni tayi nata waje,duk da qoqarin da takeyi taga ta gyaggara yadda widad keyi amma babu abinda ya canza,sai abubuwa suka fara mata wuya,ga qoqarin ganin ta dauki pattern din widad wanda dukka jiki da zuciyarta suka gaza saboda bata saba ba,ga sauyin yanayin abbas din. Shikam kome baisan yana yi ba,duk yadda yaso ya manta komai ya cisge widad daga rayuwarsa amma ya gaza,abun ya masa tsaye a rai,ya tsaya masa fiye da duk yadda ya zata,ko mutuwar mahiafiyarsa ya dangana amma ya kasa dangana da widad din,ya tsaya a gaban mudubi ya kalli kansa da kansa ya yiwa kansa fada amma ko gezau,yasha rasa bacci cikin dare idan abun ya taso masa amma abu guda zuciyarsa keta nacin bashi shawara "Ki saketa kawai ka huta,ka saketa zaka manta da ita" saidai sam hannuwansa sun gaza rubutu takardar sakin. Irin wannan maganar hafsat din tayi masa,bayan sallar isha'i yana zaune a falonsa yana kallon labaran duniya a tv,ga mai zuzzurfan hankali duba daya zaiyi masa ya gane tunani yakeyi bawai kallo ba,ta turo qofar ta shigo idanunta a kansa,ta dauke kai tana jan tsaki qasan ranta "Haka zakayita yi kazo kuma ka haqura,kun rabu kenan har abada billahillazi" kafin ta qaraso ta sauya fuskarta zuwa yanayi na tausayi "Daddyn mimi,nifa banajin dadin ganinka a haka gaskiya,wannan abun tunda ya riga daya faru,kawai ka sawwaqe mata,saika samu nutsuwar zuciya idan aka rabu gaba daya,badai affan ne zai hada ba?,ka dauko yaronka,na maka alqawarin zan riqeshi tare dasu mimi" kamar wanda wuyansa ya sage haka ya daga kai yana kallonta,wani irin duba ne da yafi kama da duban baki da hankali,duk yadda zuciyarsa ke bashi shigen wannan shawarar amma ai bata taba ma kawo masa ya rabo affan da mamarsa ba,sai kawai ya ajjiye remote din hannunsa ya miqe tsam ya wuce bedroom dinsa. Da kallo ta bishi cikin mamakin yadda abubuwan har yau suka kasa saitan mata yadda takeso "Wai me yake faruwa ne?" Ta tambayi kanta,sai ta miqe tabi bayansa,saidai ta sameshi ya wuce toilet,da alama kuma alwala yakeyi,dole ta fito,ta wuce sassanta ta kirayi habiba ta tsegunta mata damuwarta "Ai dama yace kibi a hankali,don har yanzu zuciyarsa na ga yarinyar,zuciyarsu guri guda take,rabasu sai anbi da nutsuwa da taka tsantsan,don haka kibi a sannu,a hankali komai zai shigeshi ya rabu da ita harma ya manta da ita ba tare da ya sani ba,a yanzun dai gidanne ta barshi har abada,malam yace bazai bari ta dawo miki ba" taji dadi tayi maya godiya,ta kuma koma sashen,saidai tana murda qofar ta jita a kulle,tayita knocking amma ba'a bude mata ba,abun ya mata ciwo yadda a yanzun yake banzatar da duk wasu al'amura nata fiye da yadda take gani a baya,to amma data tuna da zancan da suka gama yi da habiba sai taji zuciyarta ta wanke,ta juya tana cewa "A juri zuwa rafi da tulu da diban ruwa,baqar matsiyaciya yadda kika fiddani daga rayuwarsa,kin bar gidan nan har abada,kuma saikin fita daga zuciyarsa kema haihata haihata" ta fada a fili a hankali kamar me sambatu. Yana fitowa kira yana shigowa wayarsa,kamar bazai dauka ba amma sai ya koma saman sofa bed ya zauna yana daga wayar,daga can uncle bashir yayi sallama jin ya daga wayar,ya amsa masa da muryarsa data zama me sanyi sosai. Gabatar masa da kansa yayi,sai suka sake gaisawa cikin mutuntawa,sannan uncle bashir ya sanar masa da dalilin kiransa. Wani irin zafin tururi ya dinga ji yana taso masa a qirjinsa,ya dinga furzar da iska daga bakinsa,da qyar ya iya controlling kansa kafin ua fara magana "Na sameta da laifin cin amanata ne,tana zuwa hotel tana kuma kawomin maza har cikin gidan aurena,yanzu haka ina da shaida a hannu na,kuma ita kanta ta amsa da bakinta taje" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" uncle bashir ya dinga fadi "Yanzu babu ta inda kake gani za'a gyara lamarin?" "Sai nayi bincike shine abinda zan iya cewa" ya fada a taqaice,don gaba daya bai qaunar maganar,sai yaji numfashinsa yana riqewa. A sanyaye uncle bashir ya kalli mommyn widad "Ya kukayi dashi?" Bai boye mata komai ba ya gaya mata,ta sake maimaita innalillahin da tun zuwan widad bata bar bakinta "Ina zaki?" Ya tambayeta sanda yaga ta miqe "Kiranta zanyi naji waye din yazo kuma da gaske taje hotel din ita?" Daga haka tayi gaba,ta isa qofar dakin ta tura ta budeta, widad ta daha jemammun idanunta wanda ta manta rabon da suga kwalli tana duban mahaifiyarta,tana zaune saman abun sallah,ta hade tafukan hannayenta waje daya,da alama addu'a takeson yi amma ta rasa me zatace "Taso" mommy ta fada tana yafitota,saita miqe tsam tabi bayanta. A nutse ta amsa musu duk tambayar da sukayi mata "Dama shi baisan abubakar ba?" "Zuwansa na farko kenan shida baaba hamisu" duk sai sukayi shuru suna jinjina abun da yadda za'a warwareshi "Bari nayi kiran mahmuda,dole yasan abinda ake ciki,don na fuskanci abun babba ne" uncle bashir ya fada,ya sake fidda wayarsa ya zayyanewa abban komai. Shima dai kiran sunan Allah ya dinga yi "Ku kawomin ita kano" shine abinda ya fada,a washegari mummyn da uncle bashir suka yi mata rakiya zuwa kano,a gidan ummu suka sauka,suna shiga kuma widad din ta fada jikin ummu tana sakin kuma me tsuma zuciya. Wani mawuyacin hali ummun ta shiga,ta dinga goge qwalla zuciyarta fal tausayin widad din tata,ganin yadda tayi wata rama ta sake yin fari faaattt,hatta fatar bakinta a bushe take "Tun yaushe kika shiga wannan yanayin amma ba'a sanar min ba?,kiyi haquri ki kwantar da hankalinki,Allah yana tare dame gaskiya,kuma zai fiddaki ko ba dade ko bajima" haka ummu ta dinga fada cikin tashin hankali da yanayi na tausayi,zuciyarta kamar zata tsaga qirjinta ta fito,tasa aka gyarewa widad din daki,sannan aka shirya mata abinci kamar yadda aka shiryawa mommy da uncle bashir,amma komai widad din ta kasa tabawa,saboda bata iya cin komai,daga ruwa sai lemo,na fata kona gora,ita kanta mummyn tayi tayi ta dinga cin abincin amma baya wuce mata,kota kwatanta ci baya ciyuwa sai tayi amansa. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 31 Zuwa azahar abba mahmud ya iso,ba dadewa saiga uncle muhsin shima takanas,wanda sam baisan abinda yake faruwa ba sai sannan,suka zauna shida sauran qannensa biyu dake binsa dukka cikin falon ummu,ya dubi widad da fuskar nan tasa dake nuna tsantsar da gaske yake,ya kirayi sunan widad din,wadda duna daya ta yiwa fuskarsa yawun bakinta ya dauke tsaf!!,tasan waye abban,tasan halinsa sarai,baya daukan wasa ko raini,hakanan bayason rashin gaskiya kaf rayuwarsa "Ki gayamin tsakaninki da Allah me ya faru?" Bakinta ne ya fara rawa,cikin kakkausar murya yace "Ki nutsu kiyimin bayani,idan kuma baki da gaskiya ne kiyi gaggawar fadamin basai kin batawa kowa lokaci ba" ta rufe idanunta sosai tana son bawa zuciyarta haquri ta kuma dai dai tata,saita fara gaya masa komai daki daki harta kammala. "Wayeshi abubakar din?" "Abubakar dai fa daka sani" uncle bashir ya amsa masa,sake waiwayawa abba yayi ga widad "Wannan abun da kika fada ayanzun idan baki qur'ani zaki iya dafawa ki sake rantsewa da hakan shine iya abinda ya taba faruwa?" Da sauri ta jijjiga kai "Zan rantse abba wallahi zan rantse" "A bani number wayar abubakar din" ya miqawa uncle bashir wayarsa,ya saka masa number abubakar akayi kiransa. Yadda widad ta fada din haka shima ya fadi,abba yayi masa sallama ya kashe wahar yana duban widad idanunsa tsar a kanta "Ashe kece duk kika jawa kanki wannan,ki gayamin uban da yace miki koni na mutu zaki fita daga gidanki kafin ki shaidawa mijinki,kadin kuma ya baki izni ta hanyar amincewa?" "Nayi kuskure abba,kuma naga indai fita ta uzuri ya kama yana barina ko ban gaya masa ba,saidai idan ya dawo din saina gaya masa....... astagfirullah" ta fada a rude hawaye yana zirarowa saman kuncinta sannan ta fashe da kuka,har affan yana daga kai yana kallon fuskarta sosai,dukka saida kowa a wajen zuciyarsa ta karye, dukkaninsu sunsan halinta,bata qarya ko za'a yanka ne zata fadi gaskiya,tun tashinta haka take. Sosai ran abba ya sosu,ransa ya kuma baci har ya gaza jurewa "Wanne irin aure ne wannan kukeyinsa da zargi?,ina akace anayin aure da zargi irin haka,zina fa?" "Wai ba zargi yakeyi ba,har hujja yana da ita" "Idan ba zargi bane waye ya gaya masa?" "Abokiyar zamanta ce" wani balaeen bacin rai ya tasowa abban, musamman shi da ya taba fuskantar halin makirci irin na mata "Abokiyar zamanta?" Ya maimaita wani bacin ran yana ciyoshi,sai kawai ya kasa sake cewa komai saboda tsananin bacin rai,ya miqe tsam yana cewa ummu "Ta zauna a wajenki ummu" daga haka ya fice,kowa a wajen ya fahimci yadda ransa yayi mummunar bacin rai,na biyunsa kuwa uncle muhsin ne,wanda shima ya miqe ya fita,ya kuma lalubi number abbas din ya kira. Daidai lokacin da yake tsaka da aiki da dukkan qananun police dake qasansa da zasuyi aikin tare. Cikin uniform dinsa dake qara masa kwarjini sosai,fuskarsa a dinke tsaf,a yau din baya ga yanayin aiki da yake sawa ya koma hakan,harda wannan qulalliyar damuwar dake qasan zuciyarsa,wadda ta koma masa abokiyar rayuwar ruhinsa,ya saka hannu a aljihun wandon uniform dinsa ya fidda wayar,ganin sunan muhsin din sai yadan gyara tsaiwarsa,tunda abun ya faru ko sau daya basuyi magana ba,sai ya juya a hankali ya taka yana fita zuwa qofar dan qaramin hall din da suke ganawar sirri. Kan qaramar barandar dake wajen ya tsaya ya daga wayar,suka fara gaisawa kamar komai bai faru ba,sannan a nutse ya jefa masa tambayar abinda yake faruwa tsakaninsu da widad. Yadda ya gayawa uncle bashir haka ya gayawa muhsin din,ransa yabaci shima "Yanzun ka yarda da abinda ita ta fada?" "Bana ce ba,sai nayi bincike kawai,zan sake bincikawa yanzun haka ina katsina ne" kai muhsin ya jijjiga ransa a bace "Saika gaggauta,saboda ran yaaya mahmud ya baci,kuma nasan halinsa sarai" daga haka ya yanke wayar,abbas din ya sauke wayar daga kunnensa yana kallonta,daga can qasan zuciyarsa ana gaya masa bakayi dai dao ba baka kyautawa,wani sashen kuma yana gaya masa shine dai dai,ya rufe idonsa a hankali yana jin kansa yana masa nauyi,a hankali sai ya fara jinsa kamar iska na kadashi hagu da dama,jinsa ya fara yin qasa hayaniyar dake kusa dashi ta fara komawa nesa dashi,sai kuma yaji kamar qafafunsa sun lanqwashe an turashi,ya tafi luuuuu zai fadi,mutumin dake dauke da posting later dinsa ta sauyin gurin aiki daga kaduna zuwa katsinar ya isa gareshi yayi saurin tareshi yana fadin "Subhanallah, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" sai ya fara neman dauki,wadanda ke kusa suka qaraso suka tayashi riqe abbas din daketa qoqarin daidaita numfashinsa ya kuma miqe ya tsaya da qafafunsa saidai abun yaci tura,sunqi sakinsa don sun tabbatar zai iya faduwa,dole aka dauko motar aiki aka sakashi a ciki suka wuce asibiti dashi. Ummu tafi kowa saninta da sanin wacece ita,hatta da mahaifiyarta ba zata gaya mata wacece ita ba,zamanta wajen ummun an dan samu ci gaba kadan,ta lalubo abubuwan da takeson ci ta saka latifa na tanadar mata su,a yadda ummun ta lura sai taga kamar qaramin ciki ke sake wahalar da widad din,koda ta gaya mata a gigice ta daga kai ta kalleta cikin tashin hankali gabanta na wani irin faduwa "Ciki kuma ummu?" Yadda taga hankalinta yayi mugun tashi saita saki murmushi "Wai hasashe na ne,amma ba lallai ya zamana shi din bane" tabar widad din a haka,don ta fuskanci sanin tana da cikin kamar zai sake zame mata wata qarin damuwa akan wadda take ciki,sai kawai taci gaba da kula da ita a hakan. Kwanansa biyu a asibitin yana jin jiki,a kwana na ukun yaji dama dama,ya kuma nemi sallama amma likitan yace bazai bashi yanzu ba,sai ya huta sosai,saboda stress yayi masa yawa,so yana buqatar ya samu hutu sosai. Daga wajen aiki sun bashi kulawa sosai,sun kuma saka an saka komai a gidan da aka bashi zai zauna a zaman aikinsa,koda suka gaya masa shi sai yaji duka wannan ba damuwa bace a wajensa. Ciki ikon Allah a kwana na ukun yaji ya fara damuwa da yanayin da yake ciki,zuciyarsa ta fara tuhumarsa,ko yaya widad take ba zaka iya zama da ita ba?,ya sadaukar da komai dominka fa. Maganar da wannan raunannan sashen na zuciyarsa ke gaya masa kenan,ya tuna wayarsu ta qarshe da muhsin,wadda daga ita bai kuma kiransa ba,ya kuma tuna yadda ya gaya masa abban ya dauki zafi,mutum me mugun karamci da kirki,sai ya miqe zumbur ya zauna saman gadonsa ya jawo wayarsa. Kai tsaye ya kira kawu hassan,bayan sun gama gaisawa ya fara masa bayanin biko yakeso suje masa "Ikon Allah,hafsatun abun yakai har da sake tafiya gida?" Kai ya girgiza yana jin zafi a ransa "Ba ita bace,widad ce" "Widad kuma?" Kawun ya tambaya cikin mamaki "Eh kawu" shuru ya danyi sannan yace "Allah ya kyauta,amma ya zama dole ka sake zama mai nisan haquri,su mata indai kace ba zaka dinga haquri ba,kowacce ma ba zaka iya zama da ita ba,ko ka auro saisun tafi,kuma zo mu zauna zo mu saba" ya danyi masa fada sannan yace zaiyi magana da ko sunusi ne sai su shiga kanon ko zuwa gobe ne,ya yiwa kawun godiya sosai,yace zai sanya a tura musu kudin da zasu sha mai "Don qaniyarka muba iyayenka bane,har sai ka bamu kudin mai banda alkhairin da kake mana" wani busashen murmushi ya danyi kawai,ya sake masa godiya ya ajjiye wayar. Shuru yayi ya jingina da gadon idanunsa a rufe,wata zuciyar na gaya masa ya kyauta,wata kuma tana tuhumarsa,kanme zai dawo da ita bayan babban laifin data aikata?,bata cancanci ya zauna da ita ba,ya rasa wanne matsaya yake a cikin biyun?. Sai da yayi sallar azahar hafsat ta fado masa a rai,ya dauki wayar yana duba ko akwai kiranta amma babu ko daya tsahon kwana ukun,mamaki ya kamashi,sai ya fara neman layinta. Sai data kusa da tsinkewa sannan ta daga,murya a daqile tayi masa sallama,ya amsa sa muryarsa mai laushi "Sai yau ka tuna damu,ni kamar ma mu ka kama a hotel din nan" ta fada cikin gatse,sai yayi shuru yana jinta ransa na masa zafi,batayi dogon nazarin taji sauyi a muryarsa ba ta dora "Duk masifar ta dawo kanmu,kwana uku kayi tafiya amma ka kasa neman matarka daka bari da yaranka" kansa ya girgiza yana jin ciwo a ransa "Ke bakisan ki kira mijinki kiji ya ya isa ba?,idan kinji shuru bakisan ki karashi kiji me yake faruwa dashi ba?,bani da lafiya ina asibiti kwana uku amma rashin kulawarki yasa bakisan da hakan ba,da irin wannan halin naki wataran sai an kawo miki gawata unexpected" sai kuma jikinta yayi sanyi,ta danyi shuru sannan ta fara magana "Ni wallahi bansan baka da lafiya ba,sannu Allah ya sawwaqe ya baka lafiya" "Ameen" ya amsa can qasa,duk wani karsashinsa babu,sai yaji baya buqatar dogon magana da ita,ya tambayi yara ta hadashi dasu. Kusan su suka debe masa kewa,yayi hira dasu mai tsayi sannan yasa suka kaiwa mamar tasu wayar,ta tambayeshi wanne asibiti yake,daya gaya mata ya dauka zatayi batun zuwa ganinsa,amma sai tace masa kawai Allah yasa kaffara,akan haka sukayi sallama,sai ya kashe wayar,widad ta fado a ransa,yayi imanin inda itace da yanzun haka ta rude masa gaba daya,ya mirgina kansa gefe yana jin zafin zuwanta hotel,sai yaji ko sunansa bayason ji. *********Sai da ya gama shirin fitarsa kasuwa sannan ya fito gaba daya,ya samu baqin da akace masa suna jiransa a falon saukar baqi na gidan. Sukayi gaisuwar mutunci sosai,ya shaida kawu hassan don haka bai buqaci sanin daga ina suke ba,haquri suka bayar kan su din basusan me yake faruwa ba sai daga baya,suka kuma gabatar masa da buqatarsu na abasu bikon widad din tare da alqawarin hakan ba zai sake faruwa ba. Gyara zamansa sosai abba yayi "To naji dadin zuwanku,don dama inata shawarar neman daya daga cikinku,batun ya sake faruwa ko kada ya sake faruwa dama bazai sake din ba,saboda a yanzun bana buqatar kowa ya nemi bikon widad,abinda nake buqata don Allah,ku gaya masa ya rubuta takardar sakin diyata ya aikomin da ita,ko ya turomin ni tunda yana da number ta,magana ta biyu kuma,ku gayawa ita abokiyar zaman tata mai shaida da shaidu cewa,ta shirya shiga kotu dani uban widad bisa qazafin zinar data yiwa diyata,zamu shiga kotu har sai gaskiya tayi halinta,walau gaskiyarta ko kuma gaskiyar tawa diyar" dukkansu sun girgiza sun kuma ji babu dadi,don basu zaci wannan hukuncin daga wajen abban ba,sai suka fara qoqarin bashi haquri "Ai baza'ayi haka ba alhaji" "Me zai hana ayi haka?,na gama magana kuyi haquri bana maimaici,ya bayar da takarda ita kuma ta shirya shiga kotu,'yata ba mazinaciya bace,ba kuma zata sake zaman zargi ba" daga haka ya musu sallama cikin girmamawa yabar musu falon. Dole bayan sun gama jimanta maganganun a tsakaninsu suka fito,kowa sai da ransa ya baci dajin cewa wai hafsat ce ta gaya masa anyi haka harda bashi shaidu,kawu hassan bai rufeshi da komai ba,ya kirashi yayi masa tatas,ya kuma bashi saqon abban ya kashe wayarsa abinsa. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 32 "Hasbunallahu wani'imal wakil,ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" itace ya samu kansa da maimaitawa,jujjuya kansa kawai yakeyi yanajin kamar zai zauce,kamar hankalinsa na shirin yin qaura daga gangar jikinsa ne,wasu irin muryoyi ne daga qasan zuciyarsa ke karanta masa abubuwa iri daban dabanya kama kansa da kyau ya riqe,sai yaji hawaye na shirin fita a idanunsa,kewar hajiya ta mamayeshi,ita daya ce yake iya jingina da ita a duk sand aya shiga matsanancin hali irin wanna,ita daya yake raba yaji snayi ya kuma samu mafita cikin sauqi,gaba daya kansa ya gama kwancewa,yanason yayi wani abu amma sai yaji kamar ana dannarsa,a wannan gabar abu daya ne kadai tunda ya darsu ya kasa barin zuciyarsa,yana son widad ta dawo,koma yaya ne yanason ta dawo,idan ta dawo koma meye sai yafi gabatar dashi a nutse,nesantarsa da tayi sainyakejin kamar bashi da sauran komai da ya rage masa a rayuwa,gaba daya maganin da likita ke bashi da sauran treatment da yake bashi ana bashine kawai badon suna wani amfani ba,a wannan rana da kansa ya kira yace ayi masa allurar bacci,saboda daina gane komai da yayi,kowanne sashe na zuciyarsa da abinda yake umartarsa da ya aikata. Cikin kwana uku ya gaza samun sukuni,gaba daya a rikice yake,yanatabyaqi da zuciyar dake umartarsa da nisantar widad da dukkan wani abu da ya shafeshi,ya dinga naci wa su kawu hassan da basu haquri,ba yadda suka iya,shi din mai alkhairi ne da maida damuwarsu tashi,haka suma suka dinga ziryar zuwa kano neman bikon widad din,zukatansu suma duka babu dadi. Tun abba yana saurarensu tare da jadda musu cewa,shifa takardar sakin widad yake jira bawai batun biko ba,har takai yama daina sauraron kowa a cikinsu,ba abbas da har yanzu yake kwance yana jinya ba,hatta dasu kawu hassan abun ya daure musu kai,don basu tsammaci samun hakan daga wajen abba ba. A yanzun har takai ta kawo baya saurarensu,sai yasa a kaisu dakin baqi suyita zaman jiransa,har sai sun gaji sun tafi. Yanayin da yake ciki na jinya a asibiti ne kawai ya hana su kawu zame hannunsu daga batun bikon widad din,duk yadda suke zaton al'amarin daga wajen abban ya wuce nan,dole suka yanke shawarar tuntubar tsoho mai ran qarfe alhaji salim,suna da yaqinin shi kadai ne zai iya masa magana yaji,shi daya ne zai iya sakashi yayi. *******K'arfe takwas na safiya ne,tana zaune saman kujerar dining din ummu tana kurbar tea mai dumi sosai,a yanzun ta zama wata acici,ita da abinci bai wani dameta ba,amma yanzun tun farar safiya take fara neman abinci,ita kuwa latifa bata gajiya da bata duk kalar abincin da takeso. Cikin kwanakin ta gama amincewa juna biyu ne da ita,bata buqatar zuwa asibiti su gaya mata,don dukkan wasu alamu sun nuna mata,a yanzun ba kamar lokacin cikin affan bane,babu quruciya sosai a kanta bare ta gaza fahimtar komai. Hankalinta a tashe yake sosai da fahimtar hakan da tayi,duka duka watan affan nawa?,sai taji tana shakka da d'ar d'ar na gayawa wani,a wannan situation dinma da take ciki?, yanayin da take ciki na zargin zina daga mijinta,mutumin da ya kamata ace shine mutum na farko da ya fada bata yarda?,sai ya zama shine mutum na qarshe da zai gasgatata?,iya wannan tunanin ya sanyata taji ta qoshi da tea din,ta ajjiye cup din gefe tana ta kokawar yage tunaninsa ta ajjiye gefe kamar yadda ta daukarma ranta,cikin kwanakin ta dan samu nutsuwa albarkacin addu'a da kuma karbar qaddararta da tayi,ta jawo wayarta ta buda tana duba saqonnin customers dinta,don har harkar business dinta ta dawo kai yanzu sosai. Sallamar abban nata ya sanyata daga kai da sauri,ta kuma miqe tana masa sannu da zuwa cike da mamkin fitowarsa da safe haka,saita samu kanta da faduwar gaba,amma ganin baice komai ba sun gaisa kamar ko yaushe yana tambayar abokinsa affan saita saki jiki,ummu ta fito ya tsugunna ya gaidata "Alhajin ya tashi?" "Eh kai yake jira ma,yace zaka kaishi dubiya" "Na iso, za'a sanar mas ako za'a min iso" "Bari na shaida masa" ummu ta fada tana komawa ciki. Ba jimawa ta dawo ta gaya masa yace ya jirashi,minti goma basu cika ba tsohon ya fito a shirye tsaf yana qamshi cikin farin kaya da farin rawani,shigar da yafiyi,ko gaisawa bai tsaya sunyi ba yace suje sa gaisa a mota,ummu da widad sukayi musu fatan dawowa lafiya suka fice yana takewa tsohon baya. Sai da suka dauki hanya sosai sannan tsoho yayi magana "Mamuda an kawo min qararka,surukanka sunce kaqi haquri ka basu bikon diyarka ko?" Nauyi yadan kama abba kadan,mutanen sun masa shigar sauri sunyi kuma mugun shammatarsa,sam hankalinsa baikai zasu nema alhajin ba,da tuni ya musu kandagarki ko ya yiwa tufkar hanci,so yake ya hukunta hafsatun harma da abbas din gaba daya,ta yadda a gaba koda wasa abu makamancin wannan bazasu bari ya sake faruwa ba. Ya muskuta ya dan gyara zamansa zai bada uzuri tsohon ya tari numfashinsa "Kanaso ayi amfani dakai a ruguza auren widad kamar yadda akeso ta faru ko?,wannan abun da kake shirin yi ba komai bane face hanyar cikawa maqiya burinsu,koma waye ya shirya wanna,ya shirya hakanne na tabbatar don yaga bayan auren yarinyar,to inason ka bawa mara d'a kunya,ka turawa koma waye aniyarsa ka maida widad dakinta,sannan ina me baka shawarar ka barwa Allah,duk yadda zaka hukunta wanda yayi mata wannan qazafin baikai hukuncin da Allah zaiyi masa ba,qarshenta kasa a daure maka shi ko?,to daurin da Allah zaiyi masa har yakai wanda zakayi masa?" tunda alhaji ya fara magana gyada kai abba yakeyi cike da gamsuwa "Hakane,in sha Allah za'a yi yadda kace alhaji" "To alhamdulillah,Allah ya tsare gaba,ya basu zaman lafiya dawwamamme,ya kauda sharrin maqiya da mahassada" "Ameeen ya hayyu ya qayyumu" abban ya amsa masa. Sai bayan sun gama harkokinsu da alhaji ya maidoshi gida sannan yasa aka kira masa widad,a sannan bata jima da gama sallar la'asar ba,tana saman abun sallah tana cin popcorn,wai yunwa takeji bayan duka abincin da taci,tana jira latifa ta gama gasa mata kifin da take sha'awar ci,ta ajjiye popcorn din ta miqe tsam ta fita a dakin. A falon baqi na gidan ta sameshi shi daya zaune "Shigo mana widad din ummu" ya kirata da sunan da ake yawan kiranta,wanda bata taba ji ya kirata dashi ba sai yanzu,ta qaraso kanta a qasa ta zauna gefe. "Allah yayi miki albarka,Allah yayi miki albarka,ya sake tsaremin ke" "Ameeen ya hayyu ya qayyumu abba,na gode" "Kinsan dalilin da yasa na kiraki?" Saita girgiza kai alamun a'ah "Inason ki gayamin gaskiyar abinda yake ranki,banaso ki boyemin komai" "To abba" ta sake fada tana bashi dukka hankalinta "Kinason ki koma gidan mijinki?" A wani mugun ba zata maganar tazo mata,har sai data daga kai ta kalli abban nata sannan ta saukar da kanta qasa,tun randa taji labarin zaryar da su kawu hassan keyi wajen abban nata,bata sake bari anyi zance makamancin hakan a gabanta ba,don zuwa yanzun ita din bata jin akwai sauran gurbin abbas a zuciyarta,ta soma sabuleshi daga rayuwarta. Har sau uku abba yana sake maimaita tambayar amma ta gaza amsa masa da komai,sai ana ukunne wasu hawaye masu zafi suka zubo mata,yadda abban yake nanata tambayar kamar yana alamta mata ya bada kai bori ya hau,su kawu hassan sun rinjayeshi "Ni bana buqatar komawa gidansa abba,bana so,amma indai kai kana da buqatar hakan,zan maka biyayya abba zan koma" ta qarasa fada kuka yana qwace mata. Sake saka mata albarka yayi sosai tausayinsa yana ratsata,ya dora da cewa "Ni bazan cuceki har abada,bazanso kuma ki shiga takura da damuwa ba,burina dukkanku ku rayu rayuwa ingantacciya me kyau,inaso ki koma gidanki,zan kuma maidaki ne saboda maqiya susan cewa basu isa su raba aurenku ba,kiyi haquri idan hukuncina baiyi miki dadi ba" "Kafi qarfin haka abba a wajena,ka isa dani ta kowavce fuska" tayi maganar siririn kuka yana qwace mata,don tuni ta fara shiryawa kanta yadda zatayi rayuwa ba tare abbas din ba. Maganganu masu dadi da kwantar da rai yayi mata gami da nasiha da jan hankali,har sai da kukan nata ya ragu sosai sannan ya sallameta,bayan ta fita kuma ya kira kawu hassan ya basu bikonta a bisa sharadan da idan ya amince dasu widad zata koma dakinta,idan kuma bai amince ba a shirye yake da karbar takardar sakinta. Na farko abbas din bazai sake hadasu zama gida daya ba tsakanin hafsat da widad,kowacce ta zauna gidanta daban,yace sam zamansu bazai yiwu ba,baya ga banbancin shekaru,irin wadan nan abubuwan da suka fara bullowa a tsakaninsu ba'a san gaba me ta dauki aniyar aikatawa ba,saboda bazai iya dauka da jurar abinda zata bullo dashi a gaba ba idan wannan sun barta da Allah sun qyaleta,na biyu ta kiyayeshi,koda wasa ya sake jin labarin ta aikata abu makamancin wannan to fa duk duniya babu mai tanqwarashi akan matakin da zai dauka dangane da ita,dukkansu sun aminta da wannan sharadin,sun kuma gode masa da har ya nuna dattako ya haqura yayi kawaici akan shariar da yace zasuyi,sun zaunar da hafsat kuma sun gaya mata komai,wadda tuni cikinta yayi bala'in durar ruwa sanda taji batun kai qara kotu,tana tsoron kada ballinta ya tashi,ta tabbatar idan asirinta ya tonu ta ba makawa wannan karon ba asiri ba,ko meye tayi abbas din bazai qyaleta ba,tanason taji cewar kotun za'a je ko an fasa?,amma ta rasa amsa daga wajensu,saboda batason ta matsa da tambayar da zata alamta musu bata da gaskiya,ta wajen abbas kuwa ta kasa jin komai,don ko wayarsa ta kira bashi yake dagawa ba, samuel ne ko wani cikin yaransa,kuma duk sanda zasu daga din zasu gaya mata ne cewa bacci yakeyi,sai suka barta cikin duhu,duhun da ya tafi da dukka nutsuwarta,dare da rana tana zulumin da tsoron ta ina ballin zai tashi?,abu daya yadan kwantar mata da hankali,kudaden data aikawa habiba tace ta koma wajen malamin nasu,ya kuma shaida mata magana ta mutu,har abada abbas bazai sake iya tada zancan ba,kai hatta da komen widad ma,yadda tabar gidan ta barshi kenan yadda yaro ke fita daga cikin mahaifiyarsa,wannan yasa ta saki jikinta taci gaba da sabgoginta. Tana kuka tana komai haka ummu ta gyara mata komai nata ita da anty deena,daban anty deena suka kebe da ita ita da anty madeena suka sake mata lecture kan wasu abubuwan masu amfani,wuni guda,itadai jinsu kawai takeyi tana binsu da idanu,gani take a yanzun tsakaninta da abbas ai sai kallo. A washegari lafiyayyar motar security tazo ta dauki widad tare da affan zuwa garin katsina,sabon muhallin da gurin aiki ya bawa abbas,tanata kuka ganin alhaji ya hana kowa yi mata rakiya "Ku barta ta tafi ita daya,hakan zai bata damar sasantawa da mijinta da wuri,tunda na fuskanci kamar har yanzu akan fushi take". Tafiyar awa biyu da rabi ta sadasu da qofad kyakkyawan madaidaicin gidan,driver ya tsaya yayi hon aka buda qaramin gate din gidan ya saka motar a ciki,ya wuce qaramin parking lot na gidan da bai wuce yaci mota biyu ba ya tsaida motar "Rabbi anzilni munzalan mubarakan wa anta khairul munzilin" ta fada tana lumshe idanunta sannan ta budesu,bata taba zaton qaddara zata sake hadasu zama da abbas ba,hakanan a yanzu batasan wanne irin zama zasuyi dashi ba. Tana rungume da affan ta nufi qofar da ta tabbatar ta parlor ce,a hankali take takawa,sanye da wata irin doguwar riga 'yar morocco mai sulbi da tayi masifar dacewa da fatarta data fara sheqi tun yanzu saboda qaramin cikin dake jikinta. Yaji shigowarsu sarai amma ya gaza motsawa,yana zaune cikin doguwar kujera hannunsa daya maqale da carbi counter,wanda a yanzun zama tare da shi ne kadai yake bashi sanyi da nutsuwar zuciya,daya hannun nasa kuma wayarsa ce yake duba news akan abubuwan da suka shafi katsina da kewayenta kafin ya gama warkewa ya fara fita aiki. Idanunsa qyar akan qofar sanda yaji an tabata,tana bude qofar idanunsu suka gauraya da juna,kowannensu sai yayi qoqarin janye idonsa daga kan dan uwanta,tayi sallama da siririyar muryarta daga can qasan maqoshinta,wanda banda Allah yasa ya saka kunne da kyau babu ta yadda za'a yi yaji abinda take fada. Amsa mata yayi yana qoqarin fita daga page din da yake karatun,ya aje wayar hannun kujerar da yake kai sannan ya miqe ya nufota. Batasan ya taho din ba,don tunda suka hada ido dashi bata sake marmarin kallonsa ba,ya rame sosai har hakan ya bayyana a fuska da jikinsa,to amma sai taji sam bata damu ba yadda ta saba ji a baya idan bashi da lafiya, taci gaba da takawa zuwa cikin falon,sai ganin mutum tayi yasha gabanta. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 33 Ido suka kuma hadawa,ta sake janye nata idanun tana kuma hade fuskarta tsaf tamkar bata taba dariya ba,sai shima ya basar,yakai hannu kan kafadarta zai karba affan. Ji tayi sam ba zata iya bashi shi ba,don haka ta goce ta hanyar ja da baya,ya kalleta cikin tsantsar mamaki,ya sake takowa ya matso ta sake matsawa baya,sukayi haka har sau uku sai ya gaza daurewa,ya motsa labbansa da dan bacin rai a muryarsa "Yarona nakeson ki bani" "Sai yanzu ka tuna yaronka ne?,aina dauka shima a hotel nayo cikinsa" gam ya runtse idonsa yana jin saukar maganar kan qahon zuciyarsa kamar saukar mashi,karo na farko tsahon tarayyarsa da ita data taba gaya masa wata magana mai gautsi,ko kafin ya bude idanun nasa yaji giftawarta ta gefansa,ya waiwaya ya bita da kallo,ta doshi dakin data gani a bude ba tare data tsaya tambayarsa bedroom dinta ba. Tanata addu'a Allah yasa nata dakin kenan,ta kuwa dace don duka kayanta da aka shigo mata dasu suna ciki,wadataccen bedroom da aka saka komai na buqata daya dace da dakin kwana,ta qarasa a hankali ta kwantar da affan dake bacci saman gado,sannan ta jawo jakarta zuwa tsakiyar dakin,ta budeta ta fidda abubuwan da take buqatar cirewa,ta jefata dukanta cikin wardrobe na dakin,cikin ranta tana jin kamar ba wani zama zatayi ba,kamar na dan lokaci ne zata koma inda ta fito. Agogon hannunta ta cire ta ajiye saman madubi ta shiga bandaki tayi fitsari sannan ta daura alwala,tana fitowa ta hangeshi,tsugunne gaban gadon, hannunsa riqe da hannun affan dake bacci,ya sunkuya a hankali yayi kissing dinsa sannan ya miqe,suka sake hada ido ta kuma kau da kanta tana tabe baki,shima sai ya dauke kansa,amma duk da haka idanunsa na fusgo masa yadda ta wani murje,sai kishinta ya sake motsawa a zuciyarsa,yadan cije lips dinsa kadan,har yanzu zuciyarsa ta gaza samun nutsuwa akan abinda ya farun,kuma bayajin zata samu nutsuwar har sai ya sakeyin binciken qwaqwaf akai. Kamar yasan me take shirin aikatawa,har yasa qafarsa waje sai ya fasa ya dawo yana dubanta tana rolling mayafinta saman kanta tana jira ya gama ficewa ta saka sakata "Karki kuskura kice zaki kulle qofa,ki barmin yarona ya sake a gidan babanshi yadda yaso,inda ke daya ce sai nace bismillah,kiyita rufe qofar har Allah ya gajisheki" tabe masa baki tayi ta kauda kai ba tare da tako tanka masa ba,sai yaji haushi ya kamashi,yaso ko yaya ne tace wani abun,yaso ta magantu ko baqar magana ta gaya masa amma sai ta qiya,haka ya qarasa ficewa yana wani tsatstsare gida,yana jin Wani abu mai nauyi yana taba zuciyarsa. Bata kuwa fasa kulle qofarta ba,don batason ma ya wani shigo mata daki,don bata da buqatar ganinsa sam sam,zuciyarta wani irin zafi take mata idan ta ganshi,ta idar da sallar la'asar,zuwa sannan jikinta har yadan fara rawa,don bata jure yunwa kwata kwata,don dole ta fita ta laluba kitchen. Akwai komai a ciki,harda ruwan zafi a flask,ta shiga tunanin sassauqan abinda zata dafa kafin ya dawo gidan,sai kawai tayi amfani da ruwan zafin flask din ta tsaida ruwa,ta bare noodles ta zuba,ta kunna daya side na gas din ta soya qwai,cikin minti talatin kacal ta hada komai ta dauko ta wuce dakinta abinta. Tana murza key din yana shigowa,yaji qarar key din,yabi qofar da kallo,ransa ya baci,bata ji abinda ya fada kenan ba?,sai ya taka zuwa qofar dakin,ya daga hannu kamar zaiyi knocking me ya tuna kuma sai ya fasa Ya juya ya wuce kitchen. Wayam ya samu kitchen din,sai tukunyar data dafa noodles wadda ta cika da ruwa ta ajjeta a wajen,da spoon din da tayi amfani dashi wajen juyawa,bawon maggi dana vegetables din data zuba,sai yaji abun yayi masa banbarakwai,tsahon zamansu bai taba ganin tayi girki tabar gurin haka ba. Ci gaba yayi da duba kwanukan kitchen din,ko noodles din bata ajjiye masa ba,ransa ya sosu,haka ya jawo wata qaramar tukunya ya dora baqin shayi,don bashi da kuzari da kuma qarfin jikin dora komai a yanzu,girkinta yake marmari,ya kuma sanya ran ci,sai gashi ko ruwa bata dafa ta ajjiye masa ba. Jikin kitchen cabinet ya tsaya yana shan tea din,sau biyu ya kurba ya furzar,babu dadi sam bakinsa,sai a sannan ya ankara ashe ya cika komai yayi yawa,baisan kuma ya akayi hakan ta faru ba,haka ya kwarar da tea din ya fito yabar kitchen din. Parlor ya dawo ya zauna yana sauke numfashi saboda qirjinsa da yaji ya fara riqewa "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya soma maimaitawa a hankali yana qoqarin cooling down kansa,likita ya gargadeshi game da dorawa kansa stress da damuwa mai yawa,jininsa ya hau an samu kuma ya sauka da qyar,idan kuma bai kiyaye ba zai iya dawowa. Yana tunanin akwai yunwa tattare dashi,ya manta rabonsa da cin abinci cikakke,ta riga ta batashi da taste din abincinta mai dadi,damuwa da rashin samun kalar taste dinta yasa ya watsar da lamarin abinci,dole ya cire waya ya kira daya daga cikin yaransa ya gaya musu irin abincin da yakeso. Ko da aka kawo din ba wani mai yawa yaci ba,cikinsa gaba daya a cushe yake,sai ya ture abincin ya koma ya kwanta kan doguwar kujerar falon,tunani ya masa yawa,a yanzun yake jinsa cikakken maraya gaba da baya. Sau kusan biyar yana ganin kiran hafsat,saidai yabi wayar da kallo,harta gama ringing dinta ta katse,bayason damuwa a yanzu,don haka bashi sa buqatar daga wayarta. Daga bangaren hafsat din sai ta dinga jin fargaba da dar dar,amma indai abinda malam ya gaya mata haka yake,me zai hana abbas din daga wayarta,tunda dai lokaci irin wannan da baya da lafiya ta tabbatar yana gida bare tace ya fita Wani aiki na musamman "Basa qarya a zancensu,tunda ta gayamin hakanne,kawai ki shareshi" zuciyarta ta bata shawara,saita aje wayar taci gaba da sabgarta. Washegari kafin ya fito ta gama duk abinda zatayi a kitchen din ta dawo daki ta rufe abinta,bata kuma sake fitowa ba sai bayan isha'i data tabbatar ya tafi masallaci sallah,ta zube kwanukan ta debi wasu ta koma. Cikin kwanaki uku abinda da dawowarta abinda ya dinga faruwa kenan,wani irin zama sukeyi na shariya da fita sabgar juna,saidai widad din ta fishi daukan zafi sosai,don bata fita a dakin sai idan ya fita sallah,da yake har yanzun bai gama warwarewa ba,yana gida yana sake hutawa,ko aiki bai fara fita ba,da zarar ya fita zata fita ta dafa musu abinda zasuci ita da affan ta zuba a cooler ta koma daki,ko wanke wanke taqiyi,haka ta dinga tarawa kitchen din kwanuka itama. Sau daya da wasa bata taba saka tsintsiyarta ta share falon ba tunda tazo cikin gidan,iya dakin da take ciki kawai take tsaftacewa,tun bai lura ba har ya lura da abinda takeyi shigen na hafsat,don kitchen din ya fara canza launi,haka qura ta fara yiwa gidan yawa,hakanan duk da baida lafiya ya zage ya gyara kitchen din da gidan,yayi tsammanin zata dauki haske ta gyara amma a banza,don ci gaba tayi da batawa tana jibge masa kayan a kitchen din,tun yana ganin zai jure har haqurinsa ya gaza,ya dinga fakonta ta fito amma ko sau daya bata bari hakan ta kasance ba,har ya gama murmurewa ya koma bakin aikinsa. Randa zai soma fita din haka ya hadawa kansa baqin ruwan shayi a tsaitsaye,yana tsaye a falon yana kurba,gaba daya sai yakejin bashi da sukuni,idanunsa qyar bisa qofar dakin,yana jiyo hayaniyar yaron,bama rashin isashen abinci da baya samu ne damuwarsa ba,wata kewarsu da yaji ta fara shigarsa da gasken gaske,tun bayan da ya duqufa da addu'o'in da aminin mahaifinsa ya bashi bayan zuwansa dubashi,ya kasa jurewa ya ajjiye cup din ya taka zuwa dakin. Sai da yayi knocking kusan sau biyar sannan aka tambayi waye a daqile "Kinsan ko waye ai ko ban fada ba" ya amsa mata adan kaurare,sai tayi banza dashi kamar bataji abinda ya fada ba,har sai da ya qosa da tsaiwar ya sake bugawa,amma sai tayi biris dashi "Open the door malama" ya fada da dan hargagi "Dakin 'yar kwanan hotel din zaka shiga?,me zakayi da ita kai da kake da kamilar mace a bauchi?" Runtse idanunsa yayi yana jin zafin sunan data kira kanta dashi sannan ya bude a hankali yana aje numfashi "Stop it......ki budemin qofa kiban affan" "Affan kuma?,ai yarona ne ni kadai" "Widad!" Ya kirata da qarfi,sai taqi amsa masa "Ki budemin qofa nace" nan ma tayi masa shuru,har gwarancin da yaron yakeyi,da alama har yazo bakin qofar ne shima yaji.muryarsa,sai ya zame ya duqa a bakin qofar,yana jin kamar yayi zaana ya tsaga qofar ya shige,ba yaron kadai yayi missing ba,harda mamansa,yana son kallon wannan fuskar tata da ya jima bai gani ba,ya tabbatar ba zata sake ce masa komai ba,haka ya gama tsaiwarsa a wajen,ya juya a hankali ya dauki brief case dinsa ya fita a gidan. Rana ta farko a office dinsa amma bai iya wanzar da komai ba,shi kansa yasan baiyi tabuka komai ba,tunani fal kwanyarsa,gaba daya yana jin kamar an canzashi ne,kamar ba ainihin abbas ba,yaja tsaki yafi sau dubu,ya yarfa hannuwansa har baisan adadi ba,har cikin zuciyarsa yaji bazai iya jura ba,kawai sai ya dauki wayarsa yayi qundumbala ya kira muhsin. Kamar komai bai faru ba suka gaisa,sai abbas din ya samu kansa da bawa muhsin haquri "Ya wuce,amma tabbas saika dage da addu'a abbas,idan ba haka ba mata basu da kirki,zasuyita saka ka kana abu kamar Wani zautacce ko qaramin yaro" ajiyar zuciya ya sauke "Na gode" ya gaya masa "Alfarma nake nema don Allah idan zan samu" "Ba 'yar wannan a tsakaninmu,fadi kawai" "Maman affan nakeson ka yiwa magana,ta hanani ganin yaron gaba daya,ta takureshi a daki, at least ta sakeshi ya dinga fitowa yana samun wadatacciyar iska" ya fada a mugun karye,karayar da shi kansa baisan ya nunata ba,sai dariya taso kubcewa muhsin,ya fahimci wani abu a cikin muryarsa wanda shi kansa baisan yana bada wannan amon ba,ba affan bane,maman affan din yake kewa gami da qishirwar gani "Kada ka damu,zan mata magana in sha Allah" yayi masa kuwa godiya sosai sannan sukayi sallama,ya ajjiye wayar yana sauke ajiyar zuciya,sai yake jin wani sassauci cikin ransa,ya jawo system dinsa zai fara rage wasu abubuwan saboda wani dan karsashi yanzun da ya samu,sai kira ya shigo wayarsa,daya duba sai yaga number hafsat ce. Da kallo yabi wayar yana jin wani abu yana yawo a ransa kafin daga bisani ya daga wayar,cikin salo da kisisinar jin cewa a yanzun ita daya ce a duniyarsa tace "Barka da yamma,ya gida ya jikin?" "Alhmdlh,ya yaran?" "Lafiya lau suke,yaushe zaka shigo?, inaga ya kamata ka taho gida don nafijin dadin kula da kai,ga rashin lafiya sannan kuma kai daya kake zaune ai baiyi ba abun" inda ace yau ya fara sanin halaye da dabi'unta sai yace ta bashi mamaki,wato ita ba zata iya takowa ta iskeshi a inda yake ba inda ace cikin buqatar hakan yake,saidai shi ya dawo ya sameta kenan,bai shirya gaya mata komai a kansa a sannan ba,saboda zuciyarsa ta fara tsara masa wasu abubuwa a kanta,shi yasa ya hana a sanar da ita komai game da abinda yake faruwa,har kuma dawowar widad din "Bazan iya tahowa yanzu ba,sai na warke sosai sannan" "K'nnnnn,ai shikenan,nace pampers din nawwara,kudin makarantar yara duka sun qare fa,naji Shuru" "Zan miki transfer ki siya" ya fada a gajarce,dama abinda takeson ji kenan "To yayi,sai anjima" ta fadi a gaggauce kamar wadda ake jira. Wayar yabi da kallo na wasu daqiqu,sai ya tafi contact nasa ya fara lalubar number wayar umar qaninsa. A ladabce ya gaida yayan nasa yakuma yi masa sannu da jiki "Kana ina?" "Ina kasuwa,muna lissafin qarshen shekara zamu danje hutu" "To yayi,idan kun gama ka ajjiye lissafin a wajenka,zan karba idan na nutsu na duba" "To yaya" "Aiki nakeson na baka,amma banason kowa ya sani,inason ya zama sirri tsakanina dakai" "To yaaya in sha Allah" "Ka hada kayanka ka koma gida na,karka taho har sai ranar da na umarceka,anjima idan na koma gida zan kiraka nayi maka bayanin abinda nakeso kayimin" "To shikenan,in sha Allah" yayi masa sallama,ya ajjiye wayar,saiya sake komawa kan system din,maimakon yayi aikin dake kai,sai kawai ya fita,ya saka sunan FAAZ HOTELS ya fara wani sirrintaccen bincike a kansa. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 34 Tana kwancen saman gadon tana chart affan yana kwance a gefanta yayi bacci abinsa kira ya shigo wayartata,tadan saki murmushi ganin suna uncle muhsin ta zauna sosai ta daga wayar suka gaisa,cikin hikima ya sako mata zancan abbas din,yadda yaga tana kame kame ya fahimtar dashi gaskiyar zancan,sai ya fara yi mata fada cikin nasiha,nasihar data sanyata zubda qwalla,ya kuma umarceta ta buda qofarta,tabar uba da da suyi harkarsu,shi yaron ba ruwansa a fadansu,wannan tsakaninsu ne,bazai hanata hukunta abbas ba muddin zata huce,amma kada ta sako affan a ciki. Cikin share qwalla ta bawa uncle muhsin haquri tare da bashi tabbacin ba zata qara ba,ta ajjiye wayar tana sake jin zafin abbas a ranta,a daketa a hanata kuka?,har yana da qwarin gwiwar kaita qara?,saita gyada kai tana cije lebe,ya kirawa kansa ruwa kuwa,lallai ba shakka zata hukuntashi har sai ya gwammace kida da karatu,saita sake daukan wayarta taci gaba da abinda takeyi. Yayi aikin da yakeson yi sosai,ya kuma hada information masu yawa,wannan yaja masa lokaci,bai fita a office din ba sai da yayi sallar magariba,ko kafin yaje gida ana dab da kiran isha'i. Komai data saba yi a gidanta na kaduna ta miqe tayi,ta tsaftace gidan saboda ita kanta jurewa take,duk da bata rayuwa a falon amma tana jin ya dameta har ranta,sabo da qazanta masifa ne,kamar yadda sabo da tsafta yakebin jini shima,tayi girkinta amma iya cikinta dana affan,ta gama ta kwashe musu,ta gyara kanta da yaronta,saboda batason abbas din ya shigar mata daki saita dawo falon tana jiran shigowarsa ta bashi affan din ta wuce dakinta abinta,aqalla ai tayi qoqari,ta kuma bi umarnin kawun nata,bata watsa masa qasa a ido ba. Ya jima zaune cikin motar bayan ya shigo gidan,murfin motar a bude qafarsa daya a waje yana shaqar daddadan qamshin da tun daga harabar gdan kana jiyoshi, qamshin da gaba daya ya gama kashe masa jiki,bai fito ba sai da yaji ana kiran sallar isha'i sannan ya fita,ya daura alwala a famfon harabar gidan ya wuce masallaci. Rigima yaron yaketa mata,saita sakashi a kafada ta soma zarya dashi,sanye take da doguwar rigar wata atmafa mara nauyi,an mata budadden dinki daga qasa,saman kuma yasha tattara ya zauna dai dai qirjinta. Tana kawowa bakin qofar zata juya yana buda qofar,suka hada ido ita dashi,yayi wani irin kwarjini na musamman cikin uniform din, hular kayan na riqe a hannunsa,saita janye idanun nata ta juya zuwa ciki affan na qijrinta,yabi bayanta da kallo,ya tako a hankali zuwa cikin falon bakinsa dauke da sallama,ta duqa tana ajjiye yaron gami da amsa sallamar tasa muryarta can qasan maqoshinta,saita juya ta nufi dakinta ba tare da ta sake kallonsa ba,tana shiga ta tura qofar,ta koma saman gadon tayi kwanciyar ta gami da jan wayarta ta fara dubawa,saidai zuciyarta adan hargitse take kadan,don bugunta ma ya sauya ba kamar yadda yake a qa'ida ba,kuma ita kanta batasan dalili ba. Tsaye yayi kawai a wajen kusan minti biyu yana duban hanyar,sai ya dauke idonsa yana sauke ajiyar zuciya,gaba daya a wannan lokacin bazaice yana jin dadin duniyarsa ba,duk yadda yaso ga qaryata hakan da gayawa kansa komai dai dai yake,amma yasan ya fada dinne kawai bawai don dai dai din yake ba. Gurin affan ya qarasa,ya dauki yaron yayi masa wasa sosai sanann ya wuce dashi dakinsa,ya cikashi da kayan wasa ya shiga bandaki ya sake wanka, sanda ya fito harya bingire saman gadonsa yayi bacci,da alama dazun dama kukan rigimar baccin yakeyi,ya saki murmushi yayi kissing goshinsa a hankali ya gyara masa kwanciya yana jin qaunar yaron har cikin jininsa,sai ya tsaya gaban madubi ya shirya cikin qananun kaya,ya shafe jikinsa da turare sanna ya fito. A falo ya fara zama,amma kamar wanda magnet ke jan hankalinsa zuwa ga dakinta saiya kasa samun sukuni,bayason shurunta,kasheshi yakeyi,a qalla ko fada yana da buqatar su dinga yi,duk sanda tayi masa shariya irin wannan baya iya jurewa,bashi da juriya akan abinda yakeso,sai ya taka a hankali ya saka kai zuwa cikin dakin. Tana tsaye gaban wardrobe tana fidda wasu kaya,sau daya ta waiwayo ta kalleshi ta mayar da kanta kamar batasan da wanzuwarsa ba,ya tsaya daga bayanta yana dubanta "Ina abinci na?" Kamar ba zata amsa masa ba,saita zuqi numfashi ta fitar ta bakinta a hankali, zuciyarta tafasa kawai takeyi amma batason tayi wani abu da zai nuna bata ganin qimar uncle muhsin,ta saki kayan hannunta ta juya ta fice ba tare data tanka masa ba,yabi bayanta sai ya sameta saman dining tana serving dinsa. Kujera yaja ya zauna yana bin dukka motsinta da kallo,ko sau daya taqi duban inda yake,kamar ma ita daya ne cikin falon,wani irin fushi ne kwance saman fuskarta ba tare da ita kanta tasan da hakan ba,yaja ajiyar zuciya me nauyi ya sauke a hankali,dai dai sanda ta gama zuba abincin ta motsa da niyyar miqewa tabar wajen "Dawo ki zauna" ya fada a tausashe cikin muryar bada umarni,bata musa masa ba,kamar yadda bata kalleshi ba,ta kauda kanta zuwa wani sashen daban,yaja abincin gabansa ya fara ci,saidai gaba daya girkin kamar ba nata ba,ta cika masa yaji sosai,abinda tasan yafi tsana kenan,ya lumshe ido yana jin yadda yajin ke ratsa harshensa har kwanyarsa,ya sakeyin loma ya biyu ba tare da ya bari ta gane tsananin yaji da yakeji ba,saidai idanunsa suna kanta,ya tsatstsareta dasu ya hanata sakewa gaba daya,cikin jikinta takejin laifin data masa,amma zuciyarta taqi amsar haka. "Karomin" ya fada yana tura mata plate din,sai ta daga kanta da sauri cike da zallar mamaki ta kalli plate din ta kuma maida dubanta gareshi suka hada ido,idanun nasa da suka dan canza launi saboda tsananin zafin yaji,sai kuma ta janye idon nata ta basar,tasa hannu ta dauki plate din ta qara masa ta tura masa hadi da bashi qeya. Spoon ya sake sakawa ya kuma cinyewa,sanda ya sake cewa ta qara masa sai data zauna sosai ta dubeshi da kyau,bakinta yadan motsa kamar zatace wani abun sai kuma ta fasa,ta sake janyo plate din ta fara zuba masa "Wannan karon ki zuba yafi sauran yawa,muddin ta wannan hanyar zuciyarki zatayi sanyi......zan jurewa ci har sai kince na barshi haka" "Kayita ci,bazance ka barshi ba" ta gayawa zuciyarta hakan. Ta gefan ido ta dinga satar kallonsa ganin yana hanyar cinye uban abincin data sake loda masan,tun tana satar kallonsa harta koma kallonsa kai tsaye,ko sau daya bai kalleta ba yaci gaba da ci,ta kalli idanunsa zuwa sannan sun canza launi sosai,tasan yadda yajin abinci ke masa illa,musamman ulcer da yake da ita wadda idan ta tashi ba qaramar wahala take bashi ba,batasan lokacin data riqe hannunsa ba "Ka barshi haka" ta fada da sauri muryarta tana rawa. Jajayen idanunsa Ya daga ya kalleta dasu,sai ta gaza jurewa kuka ya qwace mata,ta saka dukka hannuwanta biyu ya rufe fuskarta dasu tana sakin siririn kuka. Tsam ya miqe daga inda yake zaune ya iso gabanta ya tsaya yana dubanta zuciyarsa na wani irin tafasa,kafin yace komai tayi hanzarin bude fuskar saboda wani irin amai mai zafi daya danno mata,yana qoqarin riqeta tana qoqarin zamewa,saboda tasan muddin yaci gaba da riqeta zata wankeshi da aman. Bata iya riqeshi ba kuwa ta fara kwararashi,bai damu da yadda ta batashi ba saboda gaba daya hankalinsa a tashe yake,dama bata da lafiya?,tun yaushe?,duka bashi da wannan amsar,ya riqe hannuwanta sosai daya hannun nasa ya dafe mata bayanta yana jera mata sannu kamar zai ari baki. Shi ya gyara wajen,ya hada mata ruwan dumi ta gyara jikinta da ta bata shima ya gyara nasa jikin,tana kwance tana maida numfashi idanunta a kulle ya qaraso dakin,ya canza kayan jikinsa, boxer ne kawai a jikinsa,qaqqarfar kuma lafiyayyar surarsa ta fita sosai,ya dawo gaban gadon ya durqusa dab da ita ya kama lallausan hannunta ya riqe cikin nasa "Tun yaushe ne baki da lafiya?" "Kada ka tambayeni" ta fada muryarta tana rawa "Why?" Ya tambayeta a mamakance,sai data zame hannunta daga nashi sannan tace "Saboda baka damu dani bama gaba daya bare lafiyata" Tashi yayi ya haye gadon gaba daya,ya jawota cikin jikinsa dukkaninta ya rungumeta tsam,bata da qarfin da zata qwace a jikinsa dole haka ta zauna,a hankali sai taji yadda zuciyarsa ke bugawa da Wani irin qarfi n da ya wuce qa'ida "Tun daga wancan lokacin da abun ya faru haka kullum zuciyata take bugawa,ban taba zaton zankai wannan lokacin ban kamu da ciwon zuciya ba,komai nina aikata miki shi,amma bisa wani umarni da bansan daga inda zuciyata take karboshi ba.......kiyi haquri da dukkan abinda ya faru,ki kuma yafemin,amma nayiwa zuciyata alqawarin bazan bar wannan abun ya wuce a haka ba, kowanne irin tunani nasan zaki iyayi a kaina,dai dai ne bazan hanaki ba,amma ki bani dama......i need a chance don Allah don kuma affan bawai don ni ba" daga wannan maganar ya zame jikinsa daga gareta,ya barta da tunani. Hijab ya dauko mata sannan ya dauko affan "Muje kiga likita,bai kamata ki kwana hakanan ba" shi ya taimaka mata har zuwa bakin mota,sai data shiga ya kwantar da affan a baya sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan,dukkaninsu zuciyoyinsu babu dadi. Idanunsa qyar akan allon computer din sanda likita yake mata scanning,yara biyu ne gasunan kwance a mahaifarta har zuciyoyinsu sun fara bugawa. Da sauri ta dauke kanta gefe hawaye yana sauko mata,ta yaya zata iya rainon cikin 'yan biyu?,bayan ko yaye affan batayi ba,a wannan yanayin da take ciki bata jin tana da qwarin gwiwar da zata iya rainon cikin ma gaba daya "Satin cikin sha biyu gashinan,congratulations" Dr anwar likitan mai matuqar kirki da barkwanci ya fada. Abbas dake jinsa kamar a duniyar mafarki ya miqa masa nasa hannun,Allah me yadda yaso a lokacin da yaso,cikin yanayin da yake na daukewar dukkan wani farinciki daga rayuwarsa sai ga hasken farinciki ya ratso daga ubangiji,ya maida dubansa ga widad hankalinsa ya tashi da ganin hawayen da take zubarwa,ya matsa saman kanta yana jera mata tambayoyin akwai abinda ke mata ciwo ne?,saita gyada kai "Bari ina zuwa" Dr anwar ya fada yana fita a office din,hakan ya bawa abbas damar dagata,ta zauna sosai yana riqe da hannunta,saidai ya kasa zama,yana tsaye ne tsakiyar qafafunta yana kallonta "Bani da qwarin gwiwar rainonsu da haifarsu" ta fada tana zubda sabbin qwalla,sai ya dora yatsantsa saman labbansa "Zan baki duk wani qwarin gwiwa da kika rasa,zan baki dukan hope,zamu rainesu tare na kuma tayaki naqudarsu,don Allah ki kwantar da hankalinki na roqeki,ina da buqatarsu,burin kuma hajiya kenan kullum taga tarin jikoki daga wajenki" furta sunan hajiya da yayi ya sake sanya damuwa da karyewar zuciya a zukatansu su duka biyun,sai ya matso ya sanyata cikin qirjinsa yanason saukar mata da nutsuwa. Tun daga wanna lokaci gaba daya ya maido hankalinsa akan widad din,ya bata dukkan lokacinsa ya rage ranakun fita aikinsa,ya hanata yin komai,komai shi yake mata,yayi nata yayi nasa yayi na affan,sai daya gama karantar komai da takeso naci sha da sauransu,wani lokacin har tausayi yake bata,duk da har yanzu ta kasa warewa yadda suke a baya,abinda yake qara masa damuwa cikin qirjinsa kenan,yake ganin kamar komai bai wuce a wajenta ba. Tun randa yaci wannan abincin qirjinsa yake yawan riqe masa da ciwo,amma sam bai nuna mata ba,don so yake ya dawo da dukkan farinciki da walwalarta. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 35 Wannan shine babban damuwarsa kafin ya tunkari abinda yake gabansa. *******Qarfe daya na tsakiyar dare ya farka da wani irin mugun gumi da yake karyo masa,saboda riqewa da qirjinsa yayi da wani irin mugun ciwo,da qyar yake iya jan numfashi,ya laluba hannunsa ya kunna fitilar gefan gado,haske ua gauraye dakin nasa,shi daya yake kwana,bai taba takurata ko sau daya akan su hada makwanci ba,hasalima ta lafiyarta yake,ya sauko daga gadon ya fita waje don ya samu ruwa mai sanyi yasha ko qirjin nasa zai sake,ya tabbatar ciwon da yaketa dannewa ne yau yaci qarfinsa. Haki ya dinga yi sosai bayan yasha ruwan,ya samu hannun kujera ya zauna yana riqe da qirjinsa,a hankali ya fara kiran sunan Allah ganin ciwon yana neman yafi qarfinsa. Tana yawan fama da qishirwar dare,tsakiyar baccinta ta tasheta,ta farka a hankali tana mutsitsike idanu sannan ta zauna sosai tana kallon sashen da abbas din ya zauna dazun,wayam babu shi,ya zauna ne yana karanto mata wasu laifuka cikin system dinsa da wasu suka aikata ya kamasu ya kaisu kotu da hukuncin da kotu ta yiwa kowannensu,batasan sanda bacci ma ya dauketa ba. Ba ruwa a dakin,dole ta gyara farar hular data dora kan sassalkar sumarta ta zura bedroom slippers dinta ta fito. Da farko tsorata tayi jin alamun mutum cikin parlor din,amma kuma sai sautin muryarsa dake tashi can qasa ta gaya mata waye,cikin tashin hankali sosai ta iso gareshi. Gaba daya ta rude da yadda taga ya fita a hayyacinsa,tana ta son ta kira wani cikin mutanensu na nan amma ya riqe hannunta gam ya hanata motsawa,batasan sanda hawaye ya fara zaryar saman fuskarta ba,yanayin yadda yake riqe da qirjinsa ta tabbatar ulcer dinsa data jima bata tashi bace a yau ta tashi,kuma ko bai gaya mata ba ta tabbatar abincin data bashi ne yaci. Sosai hankalinta ya tashi,gani take kamar mutuwa zaiyi a daren,kamar bazai kwana ba,indai hakan ta kasance kenan itace ajalinsa?,abinda ya sake daga mata hankali ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai. Duk da cikin ciwo yake amma hakan bai hanashi jawota cikin jikinsa ba yana dan bubbuga bayanta "Kayi haquri daddy,ni na jawo maka" "Shshshsshsh" kawai yace da ita,sai tayi lamo cikin jikinsa,cikin ikon Allah zufar jikinsa ta fara raguwa,kasa sakinsa tayi,har zuwa sanda taji numfashinsa yana sauka a hankali da alama bacci ya fisgeshi. Har zuwa lokacin bata bar share hawaye ba,ta sake qanqameshi cikin jikinta tausayinsa ya kamata a karo na farko,hajiya ce ta fado mata,tayi imani inda tana raye ko meye zai faru bazaikai tsananin wannan ba,ta tuna maganarta ta qarshe akan abbas da affan "Allah ya baki ikon riqesu gaba daya" har maganar ta bawa widad din mamaki,ashe kusan wasiyya hajiyan ke bata. Dukkansu kukan affan ne ya tayar dasu,da tafiyarsa daya fara koya ya qaraso wajen,sai abbas din ya miqa hannu yana daga kwancen ya daukoshi cak ya azashi saman ruwan cikinsa yana kallon yaron fuskarsa dauke da murmushi "Am sorry son.....na hanaku bacci kai da mamanka ko?" Ya fada a karye,saita miqe ta zauna sosai tana masa sannu kafin ta kalli agogo,an riga an idar da sallar asuba,dole sai hakanan suka yita a makare. Yau din musayar aiki akayi,ta hanashi yin komai tayi dukkan wani aiki kamar yadda ta saba a baya,yana kwance yana binta da kallo,duk inda ta gifta sai wani abu ya motsa ransa,zuciyarsa bata masa dadi da yadda ya zargeta ya dasa bacin rai a ranta,ashe yaransa har biyu suna kwance a mahaifarta. Wuni sukayi ranar a tare,har bayan la'asar tana ta hidimar hada musu abincin dare,affan yana kwance saman cikinsa,tayi tayi ya dagashi saboda qirjinsa amma yace "Ki qyaleshi,yayi missing dina shima" tasan akwai magana a bakinsa amma ta shareshi. Cewa yayi tazo ta dauke affan din,tana isowa yasa hannu ya janyota jikinsa,sannan ya sauke affan a gefe,sosai ya sakata cikin jikinsa yana kallon fuskarta "Da gaske widad....bagarar dani kiketa yi,yau kwanaki nawa da dawowarki,da gaske bakiyi missing dina ba?,hala kin daina sona?" Ya fada murya a karye,hannu tasa tana ture fuskarsa daga tata,saboda wani nauyi yake sakar mata da manyan idanun nan nasa "Daddy bamu da lafiya dukkanmu,ka barmu mu warke cikin salaama" ido yadan lumshe sannan ya budesu ya zubesu fes kan fuskarta,saita janye idanunta tayi kamar bata ganshi ba "Alright.....jibi nakeso na wuce bauchi" ta daga kai a hankali ta kalleshi,ranta yadan quntata kadan da zuciyarta ta tuna mata da hafsat,wajenta zaije kenan?,kamar yasan me take rayawa sai yace "Wani aiki ne mai muhimmanci ya tasomin" "Amma daddy,su office din basusan har yanzu baka gama warkewa ba?" "Saun dauka na gama warkewa sumul,tunda sunsan ina da jarumar mata dake bani kulawar dake warkar da zuciya da gangar jiki,basusan wannan karon ta zama raguwa ba" kanta ta kawar kawai,tasan jan magana yakeso,ya saki boyayyen murmushi,wannan boyayyen fushin nata ya barta ne kawai,yana jiran lokaci,zai sauke mata shi tassss,a yanzun taci albarkacin abinda yake jikinta ne,amma itama ta sani,yasan lagonta fiye da yadda take tsammani,ya kauda shurun da ya wanzu a tsakaninsu "Aikin yana da muhimmancin da bazai iya jikirtuwa ba,saidai kiyimin fatan nasara kawai" ya fada yana lumshe idanu,yana tuna wayar da sukayi dazu da umar dinsa,wadda a qalla ta kwashesu kusan awa guda. "Allah ya bada sa'a ya kuma bada nasara" "Ameeen ya hayyu ya qayyumu". Bayan ya kwantar da affan sai ya bita kitchen suka kama aikin tare,ba wata doguwar hira a tsakaninsu,amma lokaci lokaci tana kamashi yana satar kallonta,kallon da batasan na meye ba,daga bisani ya gaza jurewa,ya zagayo ta bayanta ya riqe qugunta sosai ya jawota cikin jikinsa, ya dora habarsa saman kafadarta "Wannan cikin yayi miki kyau fiye dana affan,ina fatan zaki bani baby girls masu kama dake this time around" murmushi ta saki tana jin saukar numfashinsa har cikin kunnenta,hakan kuma ya fara tayar mata da tsigar jikinta,saita zame a hankali "Eheeennnn.....gwara ma ka fadi gaskiyar ka,koda baby girls dinne masu kama dakai kakeso,ka dauka ba'a gayamin ba,sanda na haifi affan yadda ya deboka ya dinga maka dadi har baka iya jure fada" siririyar dariya ya saki,ya koma ya jingina da kitchen cabinet yana kallon kyakkyawar fuskarta "Bakisan kin fini kyau ba?,affan namiji ne,duk munina idan yayoni ba matsala,kinga kenan dama baby girls din ne yafi kamata su dauko ki ko?" Yadda ya kira kansa da mummuna ya sanyata dole ta daga kai tana sake dubansa da kyau,suka hada ido yayi wani kalar tausayi kamar ita zata zana masa yaran,sai dariya ta qwace mata. A sirrance ya sauka a bauchi,ba wanda yasan ya iso bauchi sai umar,ya kuma gana da manager din hotel din a ranar bayan ya kama daki a wani hotel na daban. Duk wani dauka na cctv camera dake hotel din saida yasa aka sauke masa,tun daga kwanan watan da kwanyarsa zata iya riqe masa na sanda suka fara zuwa weekend shi da widad,ya wuce dasu dakin hotel dinsa dasu. Sai da ya gama komai ya nutsu sannan ya fara bibiya,komai tiryan tiryan,bayan ya bawa umar wasu yace ya tayashi,amma ya tabbatar sai yana kebantaccen waje kamar haka. Aikin ba wani sabon aiki bane a wajensa ba,yana da kafiya da jajircewa akan aikinsa,idan yasa qahon zuqa akan abu sai ya ganoshi,saidai idan baiyi niyya bako bai sa kansa ba,wannan na daya daga cikin sirrin samun qarin girmansa akai akai,dom haka kuma zama bibiyat dukka motsin hotel din na watanni bai wani jigatashi ba,daren gaba daya ya sadaukar yayi wannan aikin,sai coffe kawai da yake makawa cikinsa. Ya tsaya ya jajirce yayi aikinne bawai don har a sannan akwai sauran zargin widad a ransa ba,a'ah,yayi hakanne saboda ya zamana shima yana da hujja kamar yadda tsarin aikinsu yake. Bai gama ba sai kusan azahar,zuwa sannan idanunsa sun kada saboda tsabar rashin baccin da kallon abu daya,amma duka wannan bai dameshi ba,sai wata nutsuwa data dinga saukar masa "Subhanallahi wabi hamdih,subhanallahil azeem" ya dinga maimaitawa yana lanqwasa yatsunsa,cikin tsakiyar kansa yana sake samun kansa da tuhumar kansa da kansa,tuhumar da tunda ya dawo hayyacinsa yakewa kansa,har yau kuma ya rasa dalilin da yasa ya fita hayyacinsa a wancan lokacin da har yau iya aminta da wannan mummunan zargin wa widad,wanda baisan me zaiyi da zai wankeshi ba,amma ya dora hakan bisa mizanin qaddara da jarrabawar rayuwa da rayuwar kowanne bawa bata rabuwa da ita. Ko kwana daya bai qara a hotel din ba ya hada kayansa gaba daya ya kira umar yace yazo ya kaishi gida,yawan baccin dake kansa bazai samu sakewa yayishi cikin dakin hotel din ba. Yana cikin mota ya kira Ezekiel,daya daga cikin yaransa dake bauchi,ya kuma bada umarnin ya hada yara suje su kamo masa lawal duk inda yake,amma bayason sunansa ya fito a ciki gaba daya,ko don saboda yaaya sa'id(mahaifinsa),ya masa bayanin kalar tuhumar da yakeso ayi masa,ya kuma aika masa da number wayar lawal din,yace kada su karbe wayarsa,muddin ya buqaci kiran wata me suna hafsat su bashi dama ya kirata,sannan ya kashe wayar,ya maida bayansa sosai jikin makarin kujerar yana karkata akalar tunaninsa kan next target. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 36 Har sun dauki hanyar gida ya cewa umar ya kaishi gidan hajiya,ya sakashi ya shiga da motar ciki ya karbi key din gidan ya bude ya shiga. Komai na gidan yana nan tsaf tamkar tana raye,ba qazanta ba komai,su umar suna kula da gidan yadda ya kamata,har ya bude parlor dinta zai shiga sai ya kasa daurewa,ya fito ya bude dakinsu umar din. Wanka yayi ya sanya boxer da farar riga armless,ya rage hasken dake shigowa dakin ya kwanta,a maimakon bacci sai tunani suka cika kwanyarsa fal,ya dinga bitar halaye da dabi'un hafsat din,yana kuma irgen shekarun da suka dauka a haka ba tare da wani sauyi daga gareta ba,har cikin zuciyarsa yana jin ya fara qosawa,haqurinsa kuma yana dab da qarewa,abu daya yake tunawa yake kuma tausayawa,mimi nawwara da yusra,bayason su girma su kalleshi a matsayin wanda ya gaza wajen samar musu da nagartacciyar uwa. Haka yayita saqe saqe,kansa kamar tsage saboda rashin bacci da tunani,dole ya jawo wayarsa yana dubawa,ya cika da mamaki fal na rashin ganin kiran widad ko sau daya daga jiya zuwa yau,wani abune da bai taba faruwa ba a tsakaninsu saida wannan ibtila'in ya fadowa rayuwarsu,ya gama lalubensa sai ya kirata kai tsaye. Tana zaune riqe da wani qaramin littafin addu'o'i da anty madeena ta hadota dashi tana dubawa tare da qoqarin haddace wadanda suke na ko yaushe suke fi kuma muhimmanci,tun jiyan yana ranta,amma kuma batason bada kanta ta kirashi,tanason ta auna yadda take da matsayinta a yanzu a zuciyarsa,akwai abinda ya sauya ne ko har yanzun tana nan dai a yadda take a wajensa bata motsa ba. Qarar wayar yaja hankalinta,koda ta duba taga sunan data saka masa akan wayar sai ajiyar zuciya ta qwace mata,ta kife littafin ta dauki wayar ta kara a kunnenta. Sassanyar muryarta ta sauka a kunnensa, abinda ya sakashi sakin ajiyar zuciya da sautinta ya shiga kunnuwan widad "Kina azabtar dani da yawa maman affan,na dahu haka na dahu,wallahi nayi laushi over,don Allah kiyi haquri ki sassautawa dan marayan da baida uwa baida uba......sai Allah saike......" "Sai kuma uwar gidansa,sarautar mata" ta tari numfashinsa tana qarasa maganar da ba ita ta daukota ba. Dif sukayi gaba dayansu shida ita,ita tana sauraren amsar da zai bata,shi kuma yana fama da wasu abubuwa data saukarwa zuciyarsa,sai yaji harshensa yayi nauyi,duk wani abu da yayi shirin fada ya kama gabansa,bashi da sauran zabi illa zame wayar daga kunnensa ya kuma kasheta gaba daya ya koma yayi rub da ciki yana sauke numfashi da qarfi. Taji lokacin da wayar ta tsinke,don haka ta cireta daga kunnenta tana kallon wayar,tausayinsa ya darsu a ranta,amma ya zatayi,ta kasa daina jin zafin wai hafsta ce zata hadasu?,har ta isa ta zama silar girgizar yadda tsaftatacciyar qauna shaquwa da soyayyar da suka ginata ita dashi?,wata zuciyar na raya mata ta kirashi,wata tana hanata tare da gaya mata ki barshi ya sake dandanar irin abinda kika dandana,duk da ranta ba dadi hakanan ta shareshi,ta dauki littafin addu'o'inta taci gaba da dubawa. Da qyar ya samu bacci ya daukeshi,saboda maganar data gaya masa tayi masa nauyi da yawa a qirji,ya samu baccin nasa yayi nisan zango,don har missing salloli biyu yayi,ya tashi da hanzari ya daura alwala ya bada su, kafin ya kammala wayarsa ta fara tsuwwa alamun shigowar kira. Miscall uku ne na ezekiel,kafin ya gama dubawa tex ya shigo masa akan idan ya samu miscall dinsa ya kirashi. Sai da ya gama 'yan addu'o'insa sannan ya zauna sosai gefan katifa ya kira Ezekiel din,bugu daya ya daga,ya gaidashi cikin girmamawa,sannan ya fara bashi feedback akan aikin da ya basu. Tunda ezekiel ya fara bayanin idanunsa a kulle suke yana saurarensa,babu abinda zuciyarsa keyi illa bugawa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai yake maimaitawa a hankali bakinsa yana motsawa,sai da ya gama bayanin tas abbas yayi saluting nasa,ya kuma tattara komai kama daga recording na muryarsa da video ya turawa abbas din ta email dinsa sannan sukayi sallama bayan ya gaya masa kwana biyu yakeso lawan yayi a cell,zaizo da kansa ya fiddashi. Duk da jikinsa yayita bashi hakan,duba da sanya idanun da yasa umar yayi masa kan yanayin mu'amalar dake tsakanin hafsat da lawan din,amma kuma ya girgiza matuqa,yadda har lawan ya iya aminta suka hada baki suka shiryawa widad din wannan tuggun,wanda kai tsaye zai iya cewa shi suka cutar bawai widad ba,duk abinda zai cutar da iyalinsa kai tsaye za'a iya cewa shi ya cutar,bare mummunan al'amari irin wannan,ya jima yana juya dalilin da yasa hafsat din ta sadaukar da lokacinta da kudinta ta sanya akabi widad din har hotel din akayi mata hotunan,me hakan ke nufi?,me takeson ta cimma,tace gyara,amma ta haka ake bin hanyar gyara?. Bai dauki komai ba illa key din motarsa ya fita a gidan ya nufi gida,yana tuqi cikin qarfin hali ne kawai,babu wani karsashi a tuqin nasa,har ya isa gidan,ya wuce parking lot ya ajjiye motarsa. Sashensa kawai ya nufa,don sai yaji gaba daya ya tsani kallon fuskar hafsat,mutum ne tsayayye ma'abocin gaskiya da kuma son aiwatar da ita,wannan ya sanya ya tsani qarya da maqaryacin mutum qwarai da gaske,ya buda sashen nasa ya shige ya maida muqullin ya rufe,sannan ya wuce bedroom dinsa kawai ya fada saman gadonsa qwaqwalwarsa na zayyano masa kalolin hukuncin da zai dace za hafsat,don ta lawan ya tabbatar ko iya haka ya barshi ya zuwa yanzu ya gane Allah daya ne,bare shi dinma bazai qyaleshi haka ba,yabar masa gidansa bari na har abada. *H A F S A T* Tun da rana data aiki lawan take jiran dawowarsa amma shuru wai malam yaci shirwa,tun tana bashi uzuri harta tunzura ta fara fada,ta kuma fara neman layinsa amma anata gaya mata a kashe layin yake,ta zauna tayita masifa tana kumfar baki,ragowar lace din da aka siya na anko ne a wajenta guda daya bai cika ba,ta bashi kudin kan yaje kasuwa ya cikaso mata dayan,gashi sun gaya mata suna hanya amma shuru babu shi ba dalilinsa. Sai data gama fadan ta godewa Allah ta koma taraddadi kuma saiga kiransa,sanda ta daga da niyyar yin sababi sai maganarta ta tsinke sanda taji muryarsa a shaqe kuma cikin tashin hankali yana magana da ita "Ina hannun police,sun kamani ne akan batun maman affan, wallahi bakiga mugun dukan da nakesha a hannunsu ba,yanzu haka basusan da wannan wayar a hannuna ba,sun gama dukana sun fita su hutane na kiraki,don Allah kizo kiyi beli na,ki fitar dani daga wannan masifar da kika jefani a ciki". Wata hajijiya ce ta kwasheta ta jefar,dama da gaske ne kenan?,ashe dai zancen bai mutu ba?,wannan wacce irin masifa ce,tana zaton komai ya lafa,tana zaton ta samu nasara ashe qura tana baya "Idan na sake nazo wannan wajen lawan na zama nama na tabbatar,ka jirani zan nemi abban mimi na gaya masa qarya da gaskiya,zaiyi magana kosu waye na tabbatar zaka fito" saita yanke kiran tabar lawan da waya a hannu cikin matuqar mamakin yadda takeso ta barshi shi kadai a masifar,bayan ita ya yiwa aikin. Sanda taketa yunqurin kiran wayar abbas din a kashe take,dai dai sanda ya kashe wayarsa bayan widad ta yaba masa maganar data masa zafi matuqa,tayita kira a jere amma amsar daya ce,haka ta fito wajen baqinta tana rarraba idanu,fuskarta a yamutse,gumi yana tsattsafo mata ta kowacce kafa ta jikinta "Don Allah ina zuwa" ta fada tana yin waje da hanzari zani a hannu kamar zata ci da baka ta fara kiran wayar habiba tana dosar sassan abbas da nufin fakewa a can tayi wayar,don can dinne bata da haufi dashi,tana da tabbacin babu kowa a ciki bare tayi shakka ko taji dar dar din wani zai iya jinta. Koda ta bude sashen abban din sai data tabbatar ta qule har cikin bedroom dinsa,tsabar hankalinta a tashe yake bata ma yi tunanin yadda akayi qofar bedroom din yake a bude ba,burinta kawai ta isa dakin habiba kuma ta daga wayarta. Sama sama ya dinga jin magana yana tsaye gaban madubin bandakin yana kallon fuskarsa,ya matsawa kansa da tambaya da kuma tunanin son sanin yadda akayi ya yankewa widad wannan hukuncin,ya akayi ya aminta da zancan hafsat,a irin baiwa da Allah yayi masa,a irin matsayi da yake dashi da rank a wajen aiki?, tabbas wannan babbar jarrabawa ce,kuma qaddara ce mai girma,wadda ya godewa Allah da ya taqaita masa komai,bai jarrabeshi da sakin widad ba. Sautin muryar hafsat da ya fara ji yasa ya tako a hankali zuwa gaban qofar,har ya sanya hannu zai bude qofar sai ya fasa,kalamanta cikin rudani da tashin hankali suka fara shiga kunnuwansa "Ina cikin tashin hankali habiba,komai yana iya faruwa dani,wannan maganar dai bata mutu ba yadda malam yace,yanzu haka lawan yana hannun 'yan sanda ba,na tabbatar zuwa yanzu indai sun gama bincikarsa to asirina ya gama tonuwa,don ba lallai ya iya iurewa dukansu wallahi sunana zai fadi,ki taimakamin habiba a sake danne maganar nan,dama hankalina tun ranar da sukayi maganar zuwa kotu ba'a kwance yake ba,ko baccin kirki bana iyayi wallahi,idan har abbas yaji maganar nan bani da sauran dabara kuma sai abinda y........" Gaba daya ya rasa karsashi da qwarin gwiwar tsaiwa yaji qarshen maganganunta,hankalinsa yayi mummunar tashi,bayan sharri makirci da qazafi harda bin malamai hafsat din ta hada dashi?,a yaushe?,kuma yana me?,sai kawai ya buda qofar da wani irin qarfi,qarar qofar taja hankalin hafsat har sauran maganar ta maqale mata a maqoshi. Batasan wanne yanayi ta shiga ba,suma tayi a tsaye ko mutuwa tayi ta dawo?,itadai ta bude idanunta taga abbas a gaban mudubi riqe da biro yana rubutu,ta dinga qoqarin zaqulo kalamai daga qasan maqoshinta amma kalma daya ta gaza fita daga bakinta,har ya kammala rubutun ya iso inda take ya ajjiye takardar a gefanta "Daraja daya zuwa biyu kawai zakici yau a hannuna,na farko iyayen widad tun sunan zallar tauhidinsu,sun miqa ki kotun ubangiji wadda babu wata kotu a gaba da ita,babu wani adalin alqali da yakai ubangiji iya hukunci,to kije ni dasu suka mun barki da wannan,na biyu kuma kinci darajar mimi nawwara da yusra,banason na fito na qara ganin fuskarki cikin dakin nan,idan kuma baki yarda ba......" Sai ya murza yatsunsa kawai ya gewayeta ya fice ya barta a wajen a tsugunne. Dukka hannuwanta ta saka ta kama kanta da kyau ta riqe,sai kuma ta saki kuka mai qarfi kamar wata zautacciya "Haba abbas......daddyn ya zakayimin haka?,ko meye nayi nayi ne saboda kai" sake rushewa tayi da kuka,tana jin abun tamkar a mafarki,yau ita abbas ya saka?,abinda bai taba giftawa ba tsahon zamansu sai a yanzu?,a dalilin wata?,wai shin saki nawa ma yayi mata?,sai ta zabura ta dauko takardar ta warware jikinta yana rawa kamar wadda zazzabi ya yiwa mugun kamu. Saki biyu ta gani a rubuce fes,ta saki takardar tana sake rushewa da kuka,duk da ta samu sassauci ganin akwai sauran igiya daya da tayi saura, saita miqe da sassarfa ta fita daga dakin nasa ta doshi sashenta. Wayam ta tarar babu kowa,ba yaran babu baqinta,ta shiga nemansu kamar zautacciya lungu da saqo na gidan amma babu su,a bakin gate shazali ya gaya mata yaga mai gida ya fita shi da yaran duka a mota,batasan sadda ta sulale a wajen ba ta sake fashewa da kuka,tsoro ya kama shazali ganin yadda take sheqa kuka yau a gabansa,gashi babu damar ya tambayeta ko kuma ya bata haquri saboda yasan cin mutunci irin nata,haka ya koma gefe yana satar kallonta,har ta gama me isarta taja qafafunta tayi cikin gida bayan tayi futu futu da jikinta a wajen. Baifi minti talatin ba sai gata da jakarta tana janta,ta buda motarta ta jefa jakar ta shige itama,ta dannewa shazali wani mugun hon,tuni ya durfafi gate din ya bude mata da hanzari gudun kada ta huce haushinta a kansa. Gidan yaaya bara'atu yakai yaran wadda ta cika da mamakin ganinsa,diyarta budurwa ta kira ta dauki yaran,tace ta hada musu abinci,tuni sukabi bayan mariya ta zuba musu abincin suka sake abinsu sunaci,don dama yunwa ce fal cikinsu,tunda tun rana rabonta da basu abinci,tana ta business dinta,sai kuma wannan tashin hankalin yazo ya ratso na kama lawan,hatta da yusra abinci taci sosai,suna gama ci ba dadewa dukkansu bacci ya kwashesu a wajen. A can falo kuwa Shuru yaaya bara'atu tayi kamar ruwa ya cita,jikinta gaba daya ya gama mutuwa murus,tausayi da kuma namijin qoqarin da abbas yayi na zama da ita har tsahon wadan nan shekarun duka sun gama kasheta,gidan abbas dama duka ba wajen zuwansu bane,don babu fuska daga wajen hafsat din,wannan yasa da yawan dangi suka janye jiki saidai idan an hadu a gaisa,wannan ya sanya da yawa basusan wanne hali yake ciki ba,sai idan taso kawo qorafinta a kansa ta hada qarya da gaskiya ta fada saboda ta bawa kanta kariya. "Inason yaran suci gaba da zama a wajenki kafin na gama settling komai" "Ko har abada zakace ka barminsu ina maraba da haka" ta fada tana girgiza kai zuciyarta tana karaya,tausayin yaran na sake kamata. Murmushi kawai ya saki,yana son yaransa sosai,bayajin zai iya kyautarsu. Daren ranar daga hafsat har ummanta babu wanda ya runtsa,sun raba dare suna jajanta abun,don basu taba zaton zai iya sakinta ba,sun masa mugun qullin da tun aurensa da hafsat din sukayi wannan shirin,tsohon shiri ne da ita kanta hafsat din ta manta anyishi,saboda a sannan zuciyarta najin zata iya zama da abbas ba tare da anji kansu ba,zata kuma iya sauke duk wani hakki nasa,tayi abinda yakeso tabar wanda bayaso,don sanda umman ke mata albishir din anyi abun ma ita bata wani daukeshi da muhimmanci ba. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 37 Tun bakwai na safe ya gama shirin barin bauchi ya wuce katsina,sai daya tabbatar yabar gidan hannun umar,yace ya kula da kowanne sashe na gidan,idan ya gama ya rufe gidan,ya kaiwa yaaya bara'atu key din,sannan ya dauki dukka wani abu me muhimmanci ya zuba a motarsa ya fice a gidan. Gidan yaaya bara'atun ya fara isa,tasa aka kawo masa breakfast ya taba sama sama,don shi yanzu kowanne abinci kallon hadarin kaji yake masa indai ba abincin widad ba,bayan ta sallami mai gidanta dake sammakon fita tazo suka zauna,a sannan su mimi na tare dashi,yaran duka babu wata damuwa a tattare dasu,ita mimi ma nata murnar "Daddy har anyi kana wanka munci abinci,daddy aiba yanzu zamu koma gida ba ko?" Sai ya gyada kai yana shafa kanta,tausayin yaran kawai yake damunsa,banda mutuwa babu abinda zai raba uwa da danta,amma da yake Allah ya jarabcesu da shashashar uwa bata wani shiga jikinsu da zasu damu can da ita ba,kawai yana baqincikin su girma su tuhumeshi da rashin samar musu da uwa ta gari,saidai yayi imanin Allah bazai taba tozartar dashi ba,tunda yayi dukkan iya bakin qoqarinsa bisa kyautatawa hafsat din zato ya zabeta a matsayin uwar 'ya'yansa. Duk da yaaya bara'atu tana dojewa amma bai bar mata wahalar yaran ta sisin kwabo ba,komai sai daya ajjiye musu kama daga na islamiyya har zuwa na boko,sannan ya bada wasu kudaden yace a canza musu suturar sanyawa,saboda ya lura da yadda kaf kayansu suka qarasa macewa,harda tsadaddun laces din da ya dinka musu,wanda ko shekara basu rufa ba,don shi baya jiran sai wani lokaci na daban zaiyiwa iyalinsa dinki,kusan ko yaushe cikin yi musu suttura yake. A nan ne tace ba zata karba sisinsa ba, dole ya maida kudin dinkinsu,ya mata sallama ya wuce. Tunaninsa a hanya kaf ya qare kan yadda zai doshi widad da yadda zai hukuntata,don ya gaji da maganar da take yaba masa a fakaice,yanaji a jikinsa muddin taci gaba da haka wataran za'a wayi gari ya samu matsalar hawan jini ko zuciyarsa ta tabu,ta shiga rayuwarsa da yawa,a yanzun kuma ta sake kutsawa nisan inda baiyi zato ba,wannana abun da ya faru sai sake qara mata kima da daraja a idanunsa,ya sake qaunar iyayenta tare da ganin zallar dattakonsu. Tun tana bagarar da batunsa daga ranta har tadan soma jin damuwar rashin jin wayarsa da kuma dawowarsa,amma hakanan dai taci gaba da daurewar tana yakicewa. Ko a yau data tashi duk jikinta babu kuzari sosai,ta gama komanta da wuri wajejen azahar,saita zauna shuru,sai kallo da kuma duba littafi zuwa waya da ta dinga yi,affan baya nan,wata maqociyarta ta daukeshi tun azahar din,babbar macace,dukka yaranta sun girma,shi yasa suke da son qananun yara. Karfe uku da kusan minti talatin da tara ya sauka a cikin gidan,ya sanya motarsa cikin parking lot ya kasheta,ya fito yana yiwa yaron gidan magana ya bude booth na motar ya fidda tsarabar da yayo a hanya ya aje masa qofar falon sannan ya wuce. Knocking yayi,ta dauke fuskarta daga kan littafin dake hannunta,sai ta aje littafin ta miqe a zatonta affan aka dawo dashi,tana gyara wuyan rigar wata bubu ta net da aka yiwa shafin wani irin yadi me kyau daga qasanta,rigar tayi mata kyau sosai,saboda ko ina na jikinta ya a cike yake,babu wani rami loko ko lobawa sai inda yake dama a halittar diya mace haka yake,fatarta lumui lumui,wiyanta ta saka wani ziririn zaren sarqa me qyalli da ya ake qawata wuyan nata,ta riga data saba,ya kuma zame mata jiki,ko yaushe a haka zaka sameta fes tana fidda qamshinta me laushi. A nutse ta bude qofar,ta buda siraran labbanta zatayi magana sai maganar tata ta maqale,yana tsaye gaban qofar falon hannunsa harde a qirjinsa,idanunsu suka gauraya waje daya,sai wani abu ya tsarga ma kowannensu,wani abu ya tasowa widad mai matuqar qarfi da tasiri. Ashe dai qarya ne idan kace ka daina son mutum?,ashe dai qarya ne kace baka damu da masoyinka ba saboda wani sabani ko bacin rai,saita juya da hanzari zuwa ciki,batason ta bada kanta. Baice mata komai ba ya dauki kayan duka ya shiga dasu ciki,ya maida qofar ya rufe,ya tsaya tsakiyar falon yana sauke ajiyar zuciya hancinsa yana zuqar lallausan qamshin da yake bayarwa,qirjinsa yana masa wani irin wasai,duk uban nauyin nan da yakeji cikin qirjinsa a yanzu babu shi,yana jin kamar ya sauke wani uban dutse daya danne masa zuciya. Ya wuwwulga idanunsa bata cikin falon,yasan ba zata wuce bedroom dinta ba,don haka ya wuce kai tsaye. Gaban madubi ta wuce kai tsaye, tayi tsaye kawai tana kallon fuskarta da qirjinta dake motsawa saboda bugun da zuciyarta ke mata,ta lumshe ido tana tuhumar kanta akan yadda take samun sauyi akan abbas din,duk wani alwashinta yana sulalewa yana yin nasa waje. Sam bataji shigowarsa ba,sai sautin muryarsa daga bayanta "Me bakin tsiwa,ina tsiwar taki ta tafi?,kin iya gasama mutum magana ko?,ki barshi da ciwon zuciya kiqi nemansa" ya fada yana kafeta da ido,gami da hukuntata da kallon nan nasa,haka kawai batasan ya akayi ta juye masa kalar shagwabarta data saba ba,saita tura baki gaba taja baya tana qara kusancin dake tsakaninsu "Qarya nayi?,ai banyi qarya ba k......." Kasa qarasawa tayi saboda yadda taku biyu kacal ya hade ratar dake tsakaninsu,yaci gaba da ritsata da kaifaffen kallon nan nasa "Uhmmm......qarasa mana" ya fada yana matsota. Ta hangi fitintinu bama fitina ba fal idanunsa,ta kuma tabbatar yau idan ya kamata zata ji jiki da kyau,don haka ta kulle bakinta taqi tanka masa,saidai duk da hakan bai fasa matsota ba,har ya danga da bangon dakin "Tunda kinji tsoro zan qarasa cire wannan rashin kunyar taki,kin dauka ni age mate dinki ne ko?" Kai ya shiga girgiza masa,saidai kafin tace wani abu yakai mata cafka,yayi mata wata wawuyar runguma har yana takure abinda ke kwance a cikinta,baiyi wata waya ba ya hade bakinsu waje daya,ya fara aika mata da wani zazzafan kiss,wanda ko sau daya ya gaza dauke bakinsa daga cikin nata. Cikin mintunan da ba masu yawa ba ya zare mata dukka wata laka ta jikinta,ya cire dukkan wani zafin rai taurin kai da kuma qwafar data yi masa,cikin qalilan din mintuna ya zautata,ya jefata wata duniya wadda ta mantar da ita wacece ita,ta sukurkuce gaba daya,ta kuma miqa masa kanta,irin miqawar da bata tashi gane cewa ta tafka abun kunya ba sai bayan da komai ya kammala,tana kwance a qirjinsa tana kukan da dai dai yake da nade tabarmar kunya. Tabbas taji jiki a hannunsa,ta kuma biya dukkan bashin soyayya da kewa da suka cima juna,yana maqale da ita tsam a jikinsa yana aikin lallashinta,hannunsa daya kan sumarta yana shafawa a hankali,zuciyarsa fes,nutsuwa tana saukar masa "Ka daina tabamin kai,bayan tunda na dawo baka nema komai a gurina ba,har dai kaje bauchi ka gama bincikenka" ta fada cikin kukan shagwaba tana turo baki gaba. Don dole dariya ta kubce masa,ya rungumeta da kyau jikinsa "Am sorry madam,bansan a matse kike ba ai....."kuka ta fashe masa dashi,ta dunqule hannunta tana dan dukan qirjinsa "To na daina,na fasa fada,nine a matse" ya fada yana kare dukan da take kai masa da hannayensa shima. Sai da ya tsagaita dariyar sannan ya sake gyara mata kwanciya sosai a jikinsa,ya kira sunanta cikin sautin muryar data sanyata daga kai ta kalleshi "Banqi neman komai a wajenki da gangan kodon saboda wata mafita ba,a lokacin kina cikin zafi da radadin abinda na aikata miki,na tabbatar idan na nemi wani abu a wajenki a sannan,abinda zaizo kanki shine jikinki kawai nakeso,ban fara sonki saboda jikinki ba ke shaida ce akan hakan,kuma bazan fara saboda hakan ba in sha Allah,koda baki da komai tattare da ke banajin zan daina sonki har gaban abada" sosai kalamansa suka kashe mata jiki,tayi shuru tana saurarensa,tana kuma sake gasgata zancan nujood da tace mata,abinda uncle abbas yayi din tabbas ba halinsa bane,tafi gasgata asiri ne yake dawainiya dashi,a lokacin tace mata hafsat,saidai ita din har yau bata kawota cikin ranta ba. Sake kiran sunanta yayi bayan ya hade hannayensu guri guda cikin wani irin taushi da sanyi,sai data sake shigewa jikinsa da kyau saboda yadda sautin muryar yaratsa kowacce gaba ta jikinta "Don girman Allah ki yafemin,yafiya irin ta har abada,banason ki sake tuna wani abu makamancin wannan ya taba faruwa a rayuwar aurenmu" Abbas ya cancanci yafiyarta,koba komai uban danta ne wanda ta haifa da wanda zata haifa ma a gaba,ba zata taba mancewa kuma da yadda ya tsayawa rayuwarta ba,ya dauki wautarta da shirmenta,ya raineta har ta zama abun kallo ga kowa ba "Na yafe maka har abada" wani farinciki yaji yana ratsa zuciyarsa,har baisan adadin godiyar daya dinga jera mata ba. Cikin kwanakin komai ya wuce ya kuma zama tarihi a rayuwarsu,ba wanda ya sake tada zance makamancin wannan a tsakaninsu,ta koma masa widad din nan dake rikita duniyarsa,ta sake shigewa rayuwarsa da zafafan sirrikan mallakar zuciyar miji tsaftatacciyar hanya babu boka ba malam,sai addu'a data duqufa da ita haiqan a kowacce sujjadarta akan Allah yaci gaba da mallaka mata abbas din. Da yake zuciyarta akwai haske da tsarki,sai komai yake zuwa mata yadda takeso,abbas din ya samu a gareta har fiye da yadda ta zata,ta sake gasgata cewa addu'a ba qarya bace,hakanan duk macen data sadaukarwa kanta wa mijinta,tabbas zai zama bawa a gareta ba tare daya ankara da hakan ba. Samun nutsuwa da kwanciyar hankalin da yayi daga widad yasa yake aiki tuquru cikin garin katsina,aikin da ya sake tamfatsa sunansa,ya kuma sake sanya sunansa a bakunan manyansa,suka kuma ji tabbas hazaqarsa da qoqarinsa sun girmi wannan matsayin da yake kai a yanzu. Budi sosai ya dinga shigo masa,hatta da kasuwancinsa kamar an qara masa albarka,cikin lokacin ya rasa wanne tukuici ya kamata ya bawa widad din,ba tare da saninta ko shawara da ita ba ya dallo mata sabuwar mota,ya kuma siya wani babban gida daban acan qasan layinsu dake garin bauchi ya ajjiyeshi reserve. Randa ya danqa mata motar tsananin murna ya sanyata kasa runtsawa,kyau da tsadar motar sai takejin kamae tafi qarfinta kamar ba tata bace "Madam,azo a kwanta hakanan murnar ya isa,ko kin manta bake kadai bace?,anya bazan fasa wannan kyautar ba?" Da sauri ta qaraso ta haye gadon tana dariya "Afwan yallabai,suma babies din naka taya ummarsu murna sukeyi" ya saki murmushi ya yaye rigar baccin jikinta yayi kissing cikinta sannan yaja mata duvets ya rufeta. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 38 Duk wajen wanda hafsat tasan zata ya yiwa abbas magana ya maidata taje amma abbas yayi biris,yaqi bawa kowa fuska yayi masa zancan hafsat din,suma din kuma suna kunya da nauyin yi masa maganar,saboda kowa yasan irin haquri da wahalar da yasha da ita,a yanzun sai yakejin ya samu wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali da ya jima baiji irinta a rayuwarsa ba. Duk yadda takai ga bugawa bataga alamun samun nasarar komawarta gidan abbas ba,cikin qasqanci mugun bacin rai da baqinciki mai tsanani ta dauki shawarar da ummanta ta bata "Tunda yanzun itace ke fada masa yaji,babu wata hanya data rage illa mu wanke qafarmu muje kanon,mu samu kakanta shi kadai nakejin yayi saura da zai gaya masa yaji,karkiyi baqinciki,idan kika samu nasarar dawowarki gidan,wannan karon ko komai nawa da naki zai qare saimun salwantar da ita,ko ta fita daga gidan d qafafunta,koshi ya koreta,ko kuma tabar duniyar gaba daya". Washegari suka shirya suka nufi kano ita da ummanta,ummu ta ganesu,ta kuma tarbesu kadaran kadaham,basu gaya mata abinda ya kawosu ba amma sun nemi ganin alhaji tsoho,ta sanar masa tayi musu iso ta kuma basu guri. Yadda ta dinga kuka tana gaya masa qaramin ciki ne a jikinta tana roqon alhaji ya sanya baki ya karyar masa da zuciya,duk da yana sane da komai da yake faruwa,ba kuma wai bayajin ciwo ba,to amma hausawa sunce d'a na kowa ne,kuma har yanzu shi akwai wannan jinin na karamci cikin jikinsa,wannan ya sanya ya tabbatar mata da cewa zata koma dakinta in sha Allah ta riqe yaranta. Murna kamar ta taka rawa ita da umman nata,ta yamutsa fuska bayan sun fito ta goge sauran ruwan hawayen dake fuskarta "Yadda kika qasqantar dani kika sanya na nemi alfarma daga wajen iyayenki,na zubda ruwan hawaye na duk ta dalilinki wallahi bazan qyaleki ba" hafsat ta fada cikin cin alwashi da buri. Sanda alhaji yayi kiran abbas din yana office,yabar dukka aikin dake gabansa ya saurari alhajin. Yayi mamakin jin ta inda hafsat ta bullo,bazai iya musu da tsohon ba koda wuqa ya dora masa a maqoshi,saidai yasan maganin hafsat,idan tasan wata batasan wata ba,don haka bai musa din ba yace ya karbi komen ya maidata,amma alhajin yayi masa alfarmar sanar da ita cewa,daga rana irin ta yau,duk randa ta sake yunquri ko ta daga masa hankali to a bakin aurenta. Alhajin baiso yayi wanna furucin ba,to amma kuma mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,duk mutumin da ya iya irin wannan hukuncin akan uwargidansa duk da zuri'ar dake tsakaninsu......shi kadai yasan irin abinda yake fuskanta. Saida alhaji ya nemi magabatan hafsa sukayi magana ta waya,ya kuma shaida musu sharadin abbas sannan yace musu ya maidata. "Alhmdlh,Allah ya qara girma,ya saka maka da alkhairi yasa a gama lafiya" kawunta da ya cire hannunsa daga lamarin saboda baqincikin hafsat da uwarta ya fada,yanason 'ya'yan yan uwansa,amma hafsat ta fita zakka ko a cikin marasa mutuncin gidan,dukka qoqarin da yakewa rayuwarta yana yine kawai don girman zatin Allah da kuma hakkin zumunta. A washegari ta tattara kayanta ta koma gidan,gidan da har ta debe haso da tsammani daga zamanta a cikinsa. Ranar data koma ta tsammaci zai maido mata dasu mimi,saidai har washegari shuru,washegarin ma data saka rai shima dai shuru,haka ta wuni gidan ita daya kamar mayya,zuwa dare ta kasa haquri,ta daga waya ta kirashi. Dai dai sanda suke zaune a falonshi shida widad da tsohon cikinta da take gab da shiga watan haihuwarta,tana saman kujera yana zaune a qasa,ya dora qafafunta saman cinyarsa yana matsa mata saboda yadda suke yawan kumburar mata,iya girman cikin kawai ya isa ya gaya maka cewa lallai twince dinne da gaske,labari yake bata kan gagarumin promotion din da yake sanya rai za'a yi masa koda wanne lokaci,muqamin CP wato commissioner of police,saidai akwai masu so da yawa,amma yana fatan indai zai zame masa rayuwarsa data iyalinsa alkhairi Allah ya tabbatar masa. A yanzun widad din itace abokiyar shawararsa da baya iya boye mata kowanne sirri nasa,duk abinda ya taso masa zai zaunar da ita yayi shawara da ita,Allah ya hore mata wani irin kaifin qwaqwalwa da basirar da muddin ta bashi shawara yana ganin haskenta. "Waye yake kira?" Ya tambayeta saboda tafi kusa da wayar,ta kalli screen na wayar sannan ta amsa masa tana miqa masa wayar "Mummyn mimi ce" qaramin tsakin da baisan ya fito ba yaja "Ki daga kice mata hutawa nakeyi" kai ta girgiza "A'ah fa,ba ruwana,kayi mata dai bayani" "Bazanyi ba,ke nace ki daga,idan kuma ba zaki daga ba ki gayamin kanki tsaye" "Allah ya baka haquri" ta fada tana girgiza kai,sannan ta daga wayar takai kunnenta Cikin kwantar da murya da kuma laushi tayi sallama ta dora da "Daddyn Mimi yanzu ba yafiya tsakanina da kai kenan" "Sorry,yana hutawa ne yanzun haka,saidai ki sake kira anjima" wata ashar ce ta tasowa hafsat din amma ta haqura ta danneta, zuciyarta kamar zata fito ta bakinta,saboda tsabar wulaqanci ita zai bawa wata ta daga mata waya?,a duniya yanzu cikin wadanda ta tsana babu sama da widad,sai taja mugun tsaki ta dauke wayar daga kunnenta,saidai ashe widad din ta rigata gimtse kiran. Safa da marwa kawai ta dinga yi a falon,da qyar ta taushi zuciyarta da dare ta sake kiransa amma bata sameshi bama kwata kwata,haka ta kwana biyar cikin gidan,ga kayan amfaninta duka sunyi qasa,sai takejin gidan gaba daya ya sauya mata tunda ba haka ta saba rayuwa a cikinsa ba. Tasan yaran suna gidan yaaya bara'atu,koda ta kira tace don Allah tasa a kawo mata su sai tace "Babansu yace zai kirani ya gayan duk sanda za'a kaisu din" kan bala'in ubancan,ita da yaranta ma sai an shata mata layin sanda zata gansu?,me abbas ke nufi da ita ne?,anya zata iya jura kuwa?. "Dole ki jure muddin kinason zama cikin gidan" haka anty ummee tace da ita,haka taci gaba da hadiyar baqinciki,cikin lokaci kadan ta fara rama. Sai da tayi sati uku da dawowa sannan umar ya shigo mata da kayan abinci zallarsu,bata ga alamun nama kifi fruits ko drinks da ya saba hadawa dasu ba,babu kuma kudin da yake dora mata akai,wannan karon ta kasa daurewa ta kirashi "Iya abinda zan iya kenan,idan zaki zauna ki zauna,idan ba zaki zauna ba qofa a bude take" amsar da ya bata kenan ya kashe wayarsa. Tana kuka sosai ta kira anty ummee tana gaya mata,don ta kasa samun ummanta "Ke kin cika gajen haquri,tunda bada yunwa ya barki ba saikiyi haquri ai" ta fada a mugun gajiye,saboda itama yanzun ta kanta takeyi,nata ballin kissar ya fara tashi,miji da sauran danginsa sun fara ramfota. Cikin aljannar kare abbas din ya sakata,dukkan wani abu da bai zama dole a addini ba ya janye mata shi,kudi da yake bata na kashewa da qari da yake mata da sauran wasu kayan alatu da basu zama tabbas ba gaba daya ya janye,yanason ya gani shin da gaske ta rusuna?,saidai a yadda ta fara rawa da kiraye kiraye zuciyarsa ta gaya masa "Mai hali fa baya fasa halinsa". Sai da tayi wata guda da komawa sannan ya shirya zuwa bauchi,wannan karon da widad din za'a je,abinda ta manta rabonta dashi,ta jima sosai rabonta da bauchin,gaba daya ma garin ya fita a ranta tun wancan lokacin,yanzun ma tsaowar bikin nujood ne zai kaita garin,don dole taje tayi kara duk da nauyin da tayi,abun kuma yazo dai dai da saukar 'yar yaaya bara'atu. Ya zame mata dabi'a,a duk sanda zaiyi tafiya bata qasa a gwiwa ita ka shirya masa komai,koda weekend din kuwa zaije bauchi,duk dadai ya jima rabonsa da bauchin,tun bayan kammala bincikensa da sallamar hafsat da yayi. Koda ta gama da qyar ta iya miqewa da taimakonsa hannunta riqe da bayanta tana cije lebe "Anya madam,kodai triples ne computer bai gano dayan ba?" Ya fada cikin sigar tsokana yana boye dariyarsa,harara ta balla masa "Ta ina zasu fito?,yallabai ka barni ma naji da wadan nan guda biyun,bansan ina zaka kai son yara ba" "Yaya ai rahama ne,banqi kowacce shekara na dauki sabon baby cikin gidan nan ba" kukan shagwaba ta sake masa tana yarfa hannu,tayi tayi qafa ta taku takai gareshi ya rufeshi da duka kamar yadda ranta keso amma ta kasa,wannan ya sake hasalata ta sakar masa kuka sosai. Shi da affan suka dinga mata dariya,duk da yaran baisan me akewa dariyar ba amma ya taya babansa,sai daga bisani daya fuskanci da gaske take sannan ya aje affan din yana cewa "Baka kyauta ba affan,kawo hannun taho ki rabu dashi" data samu kanta tana isowa kuwa abbas din ranqwasa saman kansa,ya dafe wajen yana shafawa a hankali,sai tasa hannu ta tureshi gaba daya yayi baya ya fadi. Motarsa ya ajjiye ya dauki tata motar,a ciki suka tsara tafiya bauchin dama,tunda already yana da wata motar a gida,idan sunje sai ya bata abarta tayi ziyarce ziyarce itama. Tunda suka idar da sallar asuba basu koma ba,sun gama shiri tsaf sai suka dauki hanya,sammakon da sukayi ya basu damar isa da wuri,taso ta masa magana kan ya sauketa a gidan uncle muhsin amma sai tayi Shuru gudun ta zama mai yawan qorafi,tasan dai yana sane da sharadin raba musu muhalli. Sun shiga layin sai taga yana fakawa qofar wani gidan na daban,tabi gidan da kallo,yakai girman nasu gidan,a tsare yake kamar dai nasun,ya fita ya bude qofar sannan ya tura gate din,ya dawo cikin motar ya jata zuwa ciki. A parking lot ya tsaya ya kashe motar ya waiwaya yana kallon widad din,ya sakar mata murmushi sannan ya fita a motar,ya zagayo side din da take zaune ya bude mata sannan yace "Welcome to your new home" kallonsa tayi da alamun son qarin bayani,sai ya dage mata dukka girarsa "Eh ga naki gidan.....kin dauka mance?,ni na isa nayi saken mantawa da sharadin abba?,ban shirya rasaki bafa kwata kwata koda kuwa da wasa" yayi furucin yana miqa mata hannunsa,saita dora nata akai murmushi yana qwace mata,ya taimaka mata fita a motar,ya fidda affan ya aza a kafadarsa suka wuce cikin gidan. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 39 Duk da kayanta ne na wancan gidan nasu amma gidan yayi bala'in burgeta,komai ya tsaru,an kuma shirya mata shi dai dai da ra'ayinta da kuma yadda takeson gida ya kasance,ta dinga satar kallon abbas tana mamakin yadda ya karanci komai nata,me takeso,meye bataso,walwala da damuwarta,sai taji zuciyarta ta karaya,ta samu kanta da addu'ar kada Allah ya kawo abinda zai sake rabasu ko ya saka shakka ko rudani a tsakaninsu har qarewar numfashinsu. Widad din mutum ce mai matuqar qoqari,a tsaye take kan hidimar gidanta,duk da komai a gyare yake amma sai da tayi goge goge,ta kuma samar musu da abinci duk da akwai taimakon abbas din yana kama mata,sannan suka sake wanka gaba dayansu suka shirya don wucewa gidan saukar yaaya bara'atu. Yana riqe da hannunta suka shiga motar tata "Inajin aminatu zanje na roqa abarmiki,wannan aikin yana miki yawa" dadi sosai ya kamata,ta murmusa tana cewa "Amma da ka kyautamin qwarai,inason yarinyar,tana da hankali,amma kuma ranka ya dade,naga kaman baka da ra'ayin daukan mai aiki" kallonta yayi sannan yayi murmushi "Wayon tsiya gareki,nasan me kikeso kice,na farko amintu ai bame aiki bace,qaramin qarfi garesu,daukotan zai zama kamar taimako,kamar yadda tasa aka dauko lawan yaso ya zame mana wani abu daban,na biyu kuma ina da tabbacin ko ire iren aminatu dubu zan cika miki gidanki dasu,ba zaki bari kowacce tayi hidimar mijinki ba,ba kuma zaki sakar musu hidimar gidanki gaba daya sai yadda sukaso suyi ba,munsan aminatu muna da tabbaci akan tarbiyyarta,ba zata batamin yara ba,kuma na tabbatar baki da sakaci da zaki kasa sanya ido a kanta,ko yaya motsinta ya canza nasan in sha Allah zaki kula,zaki kuma tsawatar" shuru tayi tana dan gyada kai,komai yayi wato yana sane,yana kuma da hujja akai "To Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" ya fada cikin nuna kulawa. Sai da ya ajjiyeta a qofar gidan sannan ya miqa mata key dinta yana jifanta da wani kallo,saika dauka sabon saurayi da budurwa ne "Drivernki ya gama aikinsa ranki ya dade" dariya ta tsuntsire da ita "Godiya nake,zan ninka maka salary dinka" "Da kuwa kin kyautawa dan marayan Allah" ta girgiza kai tausayinsa yana dan tabata "Allah ya jiqansu ya kyauta makwancinsu ya kyauta namu zuwan" "Ameen ya Allah,Allah yayi albarka" ta amsa da ameen ya fita a motar yana gaya mata zai qarasa gidan suraj da yake basu da nisa,idan sun shiga wata sabgar yasan zata iya maida kanta gida,idan kuma ya dawo da wuri sai ya maidata "Koka maidani dawowa zakayi,kasan dai kwanan waye ai" harara ya balla mata,tayi kamar bata gani ba ta wuce ciki tana qunshe dariya tana riqe da hannun affan da ya fara koyon tafiya,wannan yasa ta dinga takawa a hankali cikin kula da takatsantsan. Tun daga qofar gidan jama'a ne,ta dinga gaisawa da mutane sunayi mata sannu saboda ganin yadda tayi nauyi sosai da uban ciki a gaba,yan mata matan suka daukar mata affan din suka kutsa cikin gidan dashi ita kuma ta tsaya tana ci gaba da gaisawa da mutane. Hafsat din na tsakar gida anata rabon tuwon sauka,gaba daya ba cikin sukuninta take ba ganin yadda su mimi suka shiga sabgarsu cikin mutane,ko ta kanta basayi,yaran sunyi fes dasu sunyi haske sunyi qiba "La la la,da gani babu tambaya wannan yaron sir abbas ne" wata qanwar mijin yaaya bara'atu ta fada bayan an shigo da affan ciki "Tubarkalla ma sha Allah,yaro ya debo ruwa biyu,miqomin shi na ganshi" ta miqa hannu tana karbar affan dake fidda qamshi cikin navy blue din jeans da shirt dinsa. Sosai maganar taja hankalin hafsat,gabanta ya fadi ta waiwaya tana kallon yaron dake da yawan fara'a,abinda ya qara masa farinjini kenan,saita dauke kanta wani abu yana tsaya mata a wuya,shi da babansa sukazo lo shi kadai?, indai kuwa shi da babansa ne lallai abun abbas qara ta'azzara yakeyi,har yazo bauchi amma bata da mutuncin da zai gaya mata yazo din?. Bata gama wanann taraddadin ba widad ta danno kai,kamar kunna fitila cikin duhu haka ta haska gurin,da kyakkyawar shigarta me aji,dama tunda can din ita gwanar iya dressing ce,tunda quruciya ballantana yanzu data mallaki hankalin kanta,wata lafiyayyar atamfa ce a jikinta wadda tafi kama da material. Suna hada ido gaban hafsat din yayi Wani mummunar faduwa,faduwar da sai data rufe idanunta don tanajin sautin bugun zuciyarta har kunnenta,kamar ciki fa take gani a jikin widad din,ciki fa,cikin ma tsoho?,saita miqe tana laluben hanya,wanda banda Allah ya kare tayi hanzarin dafa bango da tuni ta timu a gurin ta fadi. Ba wanda ma ya kula da ita suna yiwa widad din maraba,kowa na qoqarin mata godiyar alkhairin da ya samu wannan karon daga wajen abbas din,wanda da yawansu sun tabbatar widad din ce sila,hakan yake kuwa,a wannan karon tayi shirin karbar soyayyarsu ne gaba daya,ribar kasuwancinta ta raba biyu,rabi ta dinga qarawa kowa akan abinda abbas ya saba bayarwar,har sai da suka qare,ita da fahad sukayi,batasan bakinsa bai iya shuru ba sai daya gaya musu,saboda shidai abun mamaki ya bashi,don koda wasa bai taba ganin hafsat din tayi musu haka ba,saidai tayi qoqarin ragewa ma. Mayafi da takalminta ta dauka ta sulale sai gidansu,tsananin bacin rai yasa da tashin hankali yasa ta manta da batun daukansu mimi da jiran zuwan abbas tayi masa kwance kwance ya bata yaranta. Tana shiga gidan ta dora hannu aka ta sakama maman nasu kuka,tayo wajenta hankali tashe "Wani cikinne da ita umma na shiga uku,ta kusa haihuwa fa?" "Ina fatan bakiyi wannan haukar a gabansu ba ko?" Ta fada cikin taraddadi,ta jinjina kai kawai don ta kasa cewa komai "Shikenan tashi muje ciki" yunqurin miqewa tayi amma sai jini ya soma bin qafafunta,ta fidda idanu waje ta qwala qara tana fadin "Wayyo Allah!.....cikina umma" sai kuma tayi baya luuuu ta sume umman tata ta tareta cikin tashin hankali. Kai tsaye asibiti suka wuce da ita,bayan an basu gado anyi gwaje gwaje aka tabbatar da zubewar cikin jikinta,kamar zatayi dan qaramin hauka koma ace qaramin haukan ta dinga yi a asibitin,har sai da haushi ya kama 'yan uwanta. Ta ciwa cikin jikinta buri sosai,tasan abbas din da matuqar son yara,ta gama tsara yadda zai zame mata makamin da zata yaqi abbas ta kuma dawo dashi tsundum cikin rayuwarta. Ba abinda abbas din baiyi ba na hidimar asibitin,hatta da ruwan da yan dubiya zasu sha bai bari kowa ya siya masa ba,ko dama can shi din tsayayye ne,baya dorawa kowa lalurar iyalinsa. Ranar da aka sallameta ranar suke komawa bauchi,don haka duk wani plan dinta ya gama rushewa,umman nata tace kada ta damu,ta bari ta gama jinin biqin nan,sai su shirya ma komai da kyau. ********Shirin haihuwa sosai abbas yake yiwa widad din,siyayya yakema twince din da basuzo duniya ba kamar ba gobe,abun yazo masa akan gaba,saboda wani irin budi yake samu sosai,harkokin kasuwancinsa da yake gudanarwa a gefe kamar ana musu yayyafin alkhairi,haka ta fannin aikinsa,ya tsare gaskiya da amana,hakanan koda cikin yaransa ya kamaka da laifin karbar cin hanci ko rashawa to ka kade,dukkansu sun sani kuma suna kiyayewa dokokinsa. Already likita ya gaya mata,tana cika watanni takwas to zata iya haihuwa daga sannan,kasancewar cikin twince,kuma ba haihuwar fari bace,don haka kullum abbas din cikin shiri yake,tayita dariya saboda yadda yakeyi din,kamar lokacin za'a fara yi masa haihuwa. Ranar da zaije bauchi weekend kamar kada ya tafi,tace sam sai yaje,watansa guda kenan baije ba saboda cunkoson aiki anan katsinan,hakadai ya tattara ya tafin ya barta da aminatu da yasa akaje aka dauko mata ita kafin ya wuce,sai da ya dawo sannan hankalinsa ya kwanta. ********Tun kafin su gama cin abincin dare bayanta da mararta ke ciwo,amma take daurewa tana cijewa,suna gama cin abincin tasa aminatu ta dauki affan suka wuce dakinsu,sai itama tace kwanciya zatayi,don bayan sun gama cin abincin fita ta kama abbas din ta gaggawa,don haka suka rufe ko ina,yana da key din kowacce qofa tasan idan ya dawo zai bude. Tashinta uku xuwa wani irin fitsari da yake takura mata,a zuwa na hudunne ta durqushe a bakin toilet din tana riqe da mararta da bayanta saboda wani mugun murdawa da tayi "Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" ta dinga maimaitawa,sai ta koma ta zauna sosai a wajen. Tun a can yaji jikinsa bai bashi ba,don haka ya katse meeting din,yabar mataimakinsa yace su qarasa,kome ake ciki su gaya masa. Yana buda qofar nishinta ya fara ji,a rude ya qaraso inda take yana tambayarta,amma babu baki,sai kawai ya fara sauko da kayan haihuwar data hadasu jiya jiya ya fidda cikin mota,ya kamata ya kaita mota,ya qwanqwasa dakinsu aminatu ta bude,ya gaya mata su kulle ko ina su kwanta,ya bata dukka keys din na gidan yace zasu asibiti,hankalin aminatun a tashe tayi musu addu'a ya fice. Kafin su isa ya kira daya daga cikin juniors dinsa,suka sameta a asibitin,bayan an dubata aka wuce labor room da ita. Addu'ar data dinga yi ba kadan bace,a wannan karon duk yadda ta zata ba haka bane,ana kiraye kirayen sallar asuba lokacin da abbas ya wuce masallaci cikin hukuncin ubangiji ta haife kyawawan twins dinta dukka maza. Yana kuma idar da sallar kira na shigowa wayarsa,ya daga yana sauraren bayanin da ake masa,tafiyar gaggawa ce ta taso musu shida matimakinsa da wanda abbas din ke bi,shine matsayar tattaunawarsu ta jiya,qarfe shida na safe,don dole ba yadda zaiyi haka ya amsa,don a qa'idar aikinsu ba sabawa umarni,ya baro masallacin yazo ya tarar da alkhairin da Allah ya saukar masa a wannan sassanyar asubar,baki da dukka zuciyarsa sun gaza daina furta godiya ga Allah,yaran kawai ya samu gani suma a gaggauce,haka yabar asibitin cike da kewar yaran da kuma mamarsu. Tun a hanya ya buga waya ya gayawa dukkan wanda ya dace ace ya sani,daga danginsa zuwa nata,gab da zai shiga gida ya kashe wayar don ya samu ya shirya,bai kunna wayar ba sai da suka dauki hanya. Yana kunnawa hafsat ya fara kira don ya fita hakkinta,ko basa tare indai zaiyi tafiya ya saba yana sanar da kowaccensu,bayan ya gama gaya mata tafiyar ya dora mata da batun haihuwar. Uffan kasa cewa tayi,saboda wani qaton abu da ya toshe mata qofofin maganarta,twince?,to maza ko mata?,ko Mace da namiji?,kai koma meye yarinyar ta haifa itakam ta shiga uku. Shurun da yaji yayi yawa sai ya mata sallama kawai ya katse wayar,ya amsa kiran yaaya bara'atu daya shigo masa. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 40 Jikinta yana rawa ta lalubi layin muneera don jin me widad ta haifa "innalillahi,na shiga uku" shine abinda hafsat ta samu kanta da fada bayan muneera ta tabbatar mata twins ta haifa kuma dukka maza,ta dinga safa da marwa cikin falonta kamar wata zautacciya,kamar kuma wadda ciwon naquda ya sameta,kuka takeyi wurjanjan,tana tsinewa widad a zuciyarta,yarinyar ta gama cutarta,cuta tahar abada,ta gama da rayuwarta gaba daya,haihuwa?,haihuwa tayi?,haihuwar kuma ta yara maza ma?,sai yaushe zata iya ruguza dukkan wannan ginin da widad tayi?,yaushe haqarta zai cimma ruwa?,rayuwa na qara tafiya,tana saqa widad din tana warware mata tana dawo da komai baya,ta gaji da wannan jiran gawon shanun,sai ta kira habiba ta fashe mata da kuka me cin rai ta fara gaya mata. Ajiyar zuciya ta sauke "Abinda nakeso dake kiyi haquri kawai,ko kowa ya kasa yi miki komai boka bagwaare ina mai imanin zai miki komai(wa'iyazubillah),saura wata daya kacal aikinka ya kammala,wallahi kinji na rantse miki,ko hajiya dake kabari inda zata dawo duniya tace masa yayi kaza wallahi wallahi naki zai dauka,kudade kika kashe bana wasa ba kin manta?, fiye da rabin jarinki kika bayar,ta yaya zan bari asara ta hauki?" Bayanan habiba sun sanyaya mata rai qwarai sun bata kuma qwarin gwiwa "Kedai abinda nakeso dake,kici gaba da lallabawa,ki sake ayi komai dake,yadda kome zaizo zaizo da sauqi" "Anya zan iya kuwa habiba?, zuciyata bata da wannan qwarin gwiwar" "Ke matsalata dake kenan, kwata kwata baki iya cinye jarabarki ba,wannan karon kuwa dole kiyi haka ko don amfanin kanki" "Zan jarraba in sha Allah". Wunin ranar haka ya yishi babu wata walwala ko jin dadi,ranta a mugun quntace,a zuciyarta tanata fatan taji wani mummunan abu ya samu yaran kowa ya huta,duk bayan mintuna saita tsine musu su da uwarsu,amma cikin ikon Allah lafiya sumul widad ita da jariranta. Wannan karon ummu ce ta kashe kunya da kanta ta yiwo tattaki katsina,gidan widad din sai ya kasance kullum cikin jama'a yake abokan aikin abbas na nan katsinan,gashi kuma a gida take,garin ummanta,dangi tako ina barkowa suke barka ,haka daga kanon ma,wasu na zuwa barka,wasu kuma sai ranar suna sannan zasu iso,yara dai sunyo goshi sosai kamar affan,kowa yasan yadda twins suke da farinjini daman,widad din taga gata tako ina. Ko yaushe suna waya da abbas din da yakejin kamar yayi tsuntsuwa ya dawo,an katse masa hanzarinsa sosai,don bai gama kallon yaransa,iya kallo guda dayan da yayi musu qaunarsu sosai yakeji cikin rayuwarsa da ruhinsa. Komai ya sakar musu dai dai bakin samunsa,don yanzu babu abinda zaice da Allah sai godiya,hatta da hafsat da yara bai barta ba,sai daya gwangwajesu da dinkunan fitar suna na alfarma har kala uku,ta kalli kayan taja mugun tsaki ta nadesu a waje daya,wannan karon kam koda ba'a ce mata ba tabbas zataje suna,zataje kallon sunan widad na qarshe a gidan abbas din,zata je kuma ko don ta sake ganin yadda zata qara sawa bokanta ya qara tsanantawa da aikinsa. _batasan tuni qaddara tayi mata nata tanadin ba,tanadin da tabbas da tana da masaniya a kansa......da babu abinda zai kaita garin katsina_ _hukuncin Allah,da kaf dube duben bokayen nata basu iso suka gano shi ba,hukuncin Allah TALALA mai kamar sake,lallai qaddarar kowanne nawa A RUBUCE TAKE_ Ana ya gobe suna gidan widad din ya qara cika sosai da jama'a,ba laifi gidan yana da nashi girman,don haka kowa ya samu masauki da wajen zama,duk da dakuna biyu ne,nata dana baqi wanda aminatu ke ciki don na abbas a rufe yake,sai wasu dakunan guda biyu da toilet ta baya. A ranar widad ta gama komai,gyaran kai kawai ya rage mata,tayi wani mugun kyau na fitar hankali saboda yadda jegon ya fara karbarta tun a sannan,da safiyar ranar sukayi waya da abbas din yace ta bari sai azahar taje gyaran gashin,abun mamaki zuwa azahar din taji wayarsa,yace ta fito qofar gida ya miqata. Na'eema da marwa ta dauka, kowacce ta dauki baby daya suka fito,tayi kyau cikin maroon din abaya, fuskarta tamkar madubi. Tunda ta fito ya zuba mata ido yana kallonta ta madubi,ya lunshe ido sannan ya bude,yana tuna muryarta lokacin da take naquda,addu'o'i da salati kadai ke fita a bakinta cikin wani hali,ya sake gasgata lallai haihuwa ba wasa bace,duk dan a baibi uwarsa ba ba shakka ya tabe,hakanan duk namijin da bai girmama matarsa ba kodon darajar yaransu lallai ya cika abun zargi. Buda motar tayi ta shigo,suka hada ido ta saki murmushi "Amma fa ka shammaceni,shine baka gayamin zaka dawo yau ba?" "Bakiji dadi ba da kika ganni kenan?" Shagwabe masa tayi "Sosai ma uncle, Surprise fa kayimin" "Good me jego" a ladabce ta gaidashi,sannan suka gaisa dasu marwa da suka zama 'yammata suma,ya tayar da motar yana tambayarta "To yaya?,meye labari?, Ya akaji da jama'a yan suna?,hope komai dai lafiya ko?". Qasa qasa suke hirarsu cike da wani irin kulawa da juna,kosu marwa dake baya basajin me suke fada kamar masu rada,abinda yayi matuqat burgesu ya kuma tafi dasu,don basu taba ganin irin wannan soyayyar tsakanin miji da mata ba,sunfi ganinta ga saurayi da budurwa,amma yau anty widad da uncle abbas din sun karya musu record. A saloon din ya ajjiyeta sannan yace "Zanje na karbo dinkina gaba da nan,idan na tashi dawowa sai na daukeku mu wuce" "Tom,godiya nake sosai,Allah ya qara girma" ta fada tana dunqule hannu cikin salon jinjina da kuma rusunawa, murmushi ya balle masa,tana bala'in respect dinsa,ko meye zai hadasu bata kasa ganin wannan girman nasa. Yana ci gaba da tuqi yana murmushi,halaye da dabi'un widad din yaketa tariyowa,tun daga aurensu kawo yau,tana da sauqin kai da dadin mu'amala over,bata da fushi ko tsaurara abu indai ba bango taje ba. Ya isa ya samu tailor din ya masa halinsu,don a sannan yake qarashe hade dinkin,yana ganinsa ya rude "Sir.....ayimin afuwa yallabai,tuba nake" sai ya jawo stool ya bashi "Yanzun nan za'a kammala sir" bai zauna ba,yadai harde hannayensa a qirji yana dubansa "Kome zakayi ka dinga qoqarin cika alqawari,shine cikar kamalar mutum,sannan sana'arka,duk yadda ka riqeta haka take zamar maka" "In sha Allah sir" yaci gaba da qoqarin hada masa kayan "Ka zauna mana sir" ya sake masa tayin zama "Karka damu,qarasa aikinka" ya fada a nutse,don shi bayajin tsaiwa duba da yanayin aikinsa. Wayarsa ce dake aljihun trouser dinsa ta dauki ruri,ya saka hannu a hankali yana qoqarin cirota,yana duba me kiran kiran ya katse,saiya fara qoqarin kira sai gashi an sake kiransa. Hafsat ce,ya daga wayar a nutse ya kara a kunnensa "Kana ta wajen ina?,gamu a park kazo ka daukemu" ta fadi kanta tsaye cikin son nunawa wadanda take tare dasu lallai har yanzu itace da gwamnati,fiye da rabinsu jama'ar widad ne ta fahimci haka ta yadda suketa hirarta da fadan alkhairinta tun a mota,hakan ya sake hassala zuciyarta da wani mugun bacin rai. Cikin mamaki yace "Me ya biyo dake titi bayan na tura kudin ticket a siya muku keda yara,yanzun haka fahad inajin yana airport yana jiran saukarkuya dauko ku" baki ta tura gaba hadi da tura dankwalinta ma,haka kawai ga mota tana gani sai ta bari ayi asarar kudin a wani siya musu ticket,kudi ba dubu biyar ba ba goma ba "Kawai haka nafiso,na karba kudin ticket din nayi saving mayi wani abun dashi" yadda take masa magana a tsaitsaye yadan bashi mamaki,don tunda tayi kome ta danyi laushi "Okay,to yanzu haka ina cikin wani uzuri,ki kira fahad din ki kwatanta masa inda kuke sai ya daukoku" daga haka ya datse wayarsa shima. Sai yaushe zata bar son kudi?,yaushe zai saka doka ta daina karya masa kanta tsaye?. Sakato tayi da wayar a hannu,ranta yana mugun baci,batakai yabar duk abinda yakeyi ba kenan saboda ita yazo ya daukesu?,cikin wannan bacin ran ta kira fahad ta gaya masa inda suke din,wanda saboda dan nisan dake tsakanin airport din da station din sai daya dan dauki lokaci,sauran wadanda basuga amfanin abinda tayi din ba sukace tunda ba abun hawa na haya available na zasu tsaya wani jira ba sai kawai suka dauki taxi drop suka wuce suka barta ita da su baaba hassana 'yan kanzaginta,sai da suka jima da wucewa sannan fahad ya iso,tayita masa bala'i amma yayi biris da ita bai kulata ba tunda ya riga yasan hali. Sai da aka gama hada masa dinkin sannan ya dawo ya dauki su widad,tuntuni an gama suna zaman jiransa ne ma "Ba komai,tunda dai ya gama alhmdlh" abinda tace dashi kenan sanda yake bata labarin abinda ya tsaidashi,shi kansa baiji dadi ba,don shima yana da baqi daga wasu garuruwan da sukazo masa saboda yana sanya ran zaiyi walima a goben kamar yadda ya saba kowacce haihuwa,haihuwar affan ce kawai bai samu yayi ba. Tunda suka isa gidan tana farfajiyar gidan a zaune ta kasa shiga ciki,kowa saidai yazo ya wuceta,tun a sannan hidimar da akeyi da yadda taga gidan ya fara tara jama'a ya tsaya mata a rai,kowa yana ciki yana huce gajiya harda su mimi,amma baqin kishi ya hanata sakat. Sanda motar abbas din ta shigo harabar gidan idanunta akai,baqin glass ne,bata lura da waye da waye a wajen a ciki ba sai da suka bude,su marwa suka fara fitowa sabe da yaran dake cikin wani lallausan blue din abun daukan yaran suka nufi cikin gidan,ta qurawa motar ido tanason ganin wadda zata fito,sai bayan kusan minti uku sannan widad din ta fito tana murmushi,da alama wata maganar sukayi da abbas din data bata dariya. "Kan abu ta kazar uba" hafsat ta fada cikin ranta,zuciya tayi mugun dibarta,batasan sanda ta isa gaban motar ba side din da abbas din ke zaune cikin wani mugun fushi "Ai dama odan bakayi haka ba ba kaine abbas ba,idan bakayi haka kai din ba namiji bane,dan kunama.....tabarmar qashi RIGAR K'AYA" ta da cikin madaukakin sautin da yaja hankalin mutanen cikin gida da sauran na farfajiyar wajen,ganin yadda hankula ke dawowa kansu bai saka ta fasa magana ba "Ni dana taho daga wata uwa duniya ka zubeni a station ka kasa zuwa daukata,amma ka dauki 'yar gwal da danyen jego a gaban mota kana yawo da ita,kabi ka tattare a gindinta ita da danginta,kana musu wahala kana musu bauta......wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni da.......". Tsawar daya daka mata ta yanke sauran maganar,yayi wata irin fitowa daga cikin motar,Allah ya kissimawa widad ba za'a kwasheta da kyau ba,cikin gaggawa ta shiga tsakani ta dora hannayenta kan qirjinsa tanason yaja baya,ta tabbatar gamuwarsu da hafsat din ba zata taba kyau ba,batason kuma zuciyar nan data taso masa ta sanya ya biye mata ga mutane a wajen. 'yan uwan abbas dake kusa ne suketa yima hafsat fada suna janyeta,ana tsaka da haka kiran dan auta a dakinsu baban abbas din ya shigo yana shaida masa sun bata kwatancen masaukinsu,sai ya kashe wayar yana huci ya juya ya koma cikin motar ya figeta ya fice daga gidan. Iska me zafi widad ta furzar,tabi hafsat da kallo wadda aka janyeta can bayan gidan "Barin hali sai mutuwa"ta fada tana mamakin halin halin tantagaryar hauka irin na hafsat din. Ranar gaba daya a birkice hafsat din ta yini,donma 'yan kanzaginta suna dannarta,da qyar takai ga shigowa falon,saidai gaba daya a hargitse take. A yanzun widad din tafi qarfin raini,kuma tafi qarfin ta keta idanunta ta gaya mata maganar banza,uwa uba kuma tana tsakiyar danginta da hafsat din bataga alamun daukan raini ko wargi daga wajensu ba,haka ta yini har dare a falon tana qunsar takaici,saidai idan abun ya qume mata da yawa ta fita ta matse hawaye ta dawo. Har tayi shirin kwanciya abbas din ya shigo,har yanzu fuskarsa babu walwala,ta kalleshi cikin langabar da kai a shagwabe tace "Angon qarni babu fara'a, gaskiya ba kanta,abunma ko kyau baiyi maka ba" dole ta sakashi dariya,sannan ta gyara zamanta "Kaci gaba da haquri uncle don Allah" "Wanne haqurin?,haqurina ai ya gama qarewa......akwai abinda kuke buqata?,zan tafi masauki wajen baqi na" kai ta girgiza,don babu ce kawai basu da ita,ya tsugunna yayi kissing yaransa duka,harsu mimi da tasa aka debo mata suka kwanta gaba daya su bakwai kenan harda ita,da yake gadon babba ne ba wanda ya matsi wani. Har ya fita tana juya abun a ranta, zuciyarta duka ba dadi,batason bacin ran nan nasa,fatanta ko yaushe mummyn mimi ta gyara halinta ko zai samu nutsuwa. Dakin da su gwaggwo mero suka sauka ya leqa don ya musu sallama,baima san hafsat din tana cikinsu ba sai daya shiga,ya gama yi musu sallama ya miqe ya fice,sai hafsat din tayi zumbur ta dauki jakarta ta biyo bayansa. A tsakiyar falon ta cimmasa,tana riqe da qugunta,zuciya kuma na ingizata tace "Muje masaukin tare,acan nima zan kwana" wani banzan kallo ya watsa mata,yaja mata tsaki yayi gaba,saita sha gabansa cikin kuka "Wallahi na gaji da wanna wulaqancin da kakemin,kamar nima ba matarka bace,yau saidai duk abinda zaka yimin ka yimin,na gaji da wannan rashin adalcin" sosai zuciya ya ciyoshi,ya finciki jakar hannunta yayi wurgi da ita sai gata a bakin qofa "Na fiki gajiya,na gaji dake gaba dayanki,kije na sakeki saki daya,badai shikenan ba?" Wutace ta kawo mata ta kuma dauke mata a take,saita aza hannu aka ta kurma wata uwar kururuwa data zama tamkar shele ga dukkan wani me rai da yake gidan,shelar tata kuwa ta iske kowa,take falon ya fara karbar jama'a dake cikin gidan banda na harabar gidan da kunnuwansu baije wajen ba,a lokacin abbas ya jima da ficewa daga gidan yana jin kamar an zare masa qaya. Faduwa tayi tahau tirje tirje a wajen, gwaggwo hassana ce ta riqeta tana kiran sunan Allah kafin sauran su tayata riqe hafsat,tanata abu kamar wadda ke shirin hawa bori ko kuma tayar da iskoki "Ku cikani,ai kuna gani,a gabanku ya sakeni,saki uku kenan yayimin,saki uku kenan fa". *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 41 Saita sake fashewa da kuka,tana jin kamar ranta zai fita,kamar alqiyamarta aka tsayar mata ita kadai. "Ikon rabbi sai kallo,wannan wanne irin musiba ce?,saki haka bagtatan?,wannan abu nu hassana yafi qarfina" gwaggwo hassana ta fada tana kama hafsat daketa zamewa tana tumuwa a qasa "Kiyi haquri tunda aikin gama ya riga ya gama" amma inaaaaa.....sai hafsat din ta hau zage zage,ta dinga debo ashar tana qundumawa widad "Sai naga bayanki,yadda kika hanani zaman lafiya saida kika cisgeni daga gidana wallahi tallahi kema ba zaki sake jin dadin abbas ba.....na rantse kinci bashi bazan qyaleki ba" gwaggwo mero ce ranta yayi mugun baci,ta sanya widad ta koma dakinta abinta ta dubi hafsat "Sakin nan dai ba ita tayi miki shi ba,hasalima batasan me ya hadaku ba,kuma zaman gidan aure dama kowa ya iya allonsa ya wanke ne,halinka kuma shike sai daka,indai bazakiyi haquri kija bakinki ki karbi qaddaraki ba har zuwa wayewar gari,to don Allah bamason hayaniya da tashin hankali ki wuce kitafi,mu taron farinciki ne ya hadamu" gwaggwo mero ta fada wadda ta jima dama tana juya maganganun da sukayi da 'yar uwarta hajiya na qarshe kan yadda take gasa abbas. Banda tsoron fita da takeyi da daddaren ba shakka saita yayyabawa gwaggwo mero maganganu,don tana ganin a yanzun ta zama munafuka ne, goyon bayan widad takeyi. Ranar wani irin dare mai mugun tsaho da baqinciki hafsat ta gani,ta dinga kuka kamar idanunta zai fado,idan ta tuna wai a yau ta rabu da abbas uban yaranta rabuwa ta har abada?,sai taji kamar mafarki takeyi,lallai namiji qanin ajali ne,namiji tabarmar qashi,namiji bashi da tabbas yau ita ta gani zahiran!!! (To masu karatu kunji fa,nidai nace uhmmmm). Ita kanta widad batayi cikakken bacci ba,idan ta kalli su mimi sai tausayinsu ya kamata,ta dinga kiran wayarsa yaqi dagawa,sai daga qarshe ya daga a dake yace da ita "Meye kike ta kirana?,idan zaki samu guri ki kwanta saboda baqinki na gobe gwara ki kwanta" kit ya kashe wayar,yasan magana zata masa akan abinda bakin alqalaminsa ya riga ya bushe,a daren yau sakayau ya dinga jin kansa,zuciyarsa tayi wani irin fes kamar an fito masa da ita an wanke,hankalinsa kwance yayi baccinsa,irin baccin ma da shi ya jima baiyi ba. Washegari kowa da harkokinsa na bikin suna ya tashi,sai hafsat da jama'arta dake qule a daki,wanda kowa ke mamakin abinda ya hanata tafiya tun sassafe,yadda ta dinga yi a daren jiyan basu zaci hantsi zai daga basu tafi ba. Widad na kitchen tana hada ruwan zafi suna magana ita dasu marwa dasu muneera gwaggwo hassana ta shigo,suka hada ido da widad din ta jefa mata Wani munafukin kallo,widad din ta basar ta gaidata a matsayin matar kawun abbas din,ta amsa mata kadaran kadaham,sai tahau neman abinci,sai data gama diban komai sannan tace "Mudai wannan bikin sunan ba damu za'ayi ba,dole muje mu raka diyarmu da aka kora......yarinya kin samu duniya,ku dama sadakar yalla wuyarta ku shiga gida,saikun fidda kowa,da biye biyen malamai duk sai kunbi kun ishi kowa". Ran widad ya baci da kalaman gwaggwo hassana,itadai tasan ba wani abu daya taba hadasu ballantana tace,akan hafsat din?,ita meye nata a ciki?,ita tayi sakin?. "Gwaggwo ni bansan meye sadakar yalla ba kwata kwata,saboda tsatsona ni balarabiya ce,kuma duk wanda ya kalleni ya kalli ahalina ya sani,malamai kuwa isa ce,kuma na gode da kika shaidamin aikina yayi,zanje na qarawa malamina kudi yaci gaba da aiki kada ya daga qafa" Kuka gwaggwo hassana ta saki tana jan salati wai widad tayi mata rashin kunya,duka kitchen din sai akahau kallon kallo,kowa yaqi tanka mata,don duk sunsan itace bata da gaskiya,haka ta fita tana fatar majina tana kaiwa gwaggwo mero qararta,a cewarta yanzu ita daya takejin maganarta. Suna tsaka da maganar abbas ya shigo gidan cikin wata danyar gezna fara qal,sai maiqo takeyi,ta fidda zatinsa da kwarjininsa gami da kyansa da wani irin kamala. Gwaggo hassanar tana ganinsa sai tayi shuru,ta wuce dakinsu sumi sumi,ya tsugunna yana gaida gwaggwo mero tare da tambayarta me ya faru "Fitina ce kawai sukeson ja kafin hafsatu ta fita a gidan nan" "Bata tafi ba?,zaman me takeyi?" Ya fada fuskarsa a hade,sai ya miqe ya nufi dakin, gwaggwo mero ce ta dakatar dashi "Ka barsu muga iya gudun ruwansu,neman wanda zai tayasu dama sukeyi" . Dole ya haqura da shiga dakin,amma ya kasa ya tsare yaqi barin gidan,daga qarshe ya zauna daga bakin gate yana amsa waya. Abinda baiyi zato bane ya sameshi,wato qarin matsayin da yaketa addu'ar tabbatuwarsa idan da alkhairi,hadi da tafiya course na watanni shida america. Dai dai sanda hafsatu ke fitowa da jakarta fuska qozai qozai ita gwaggwo mero,don gwaggwo fanteka tace ita fa babu inda zata sai an gama suna taci abinda tazo ci,idan sun koma dai tazo gida ta sameta ta sake jajanta mata,bayan sun fita taja tsaki tana gunguni "Yarinyar da ba mutuncin kowa take gani ba, zamanta da yaron nan har yai alkhairin da ita qanwar cikinta ya samemu ta sanadinta,ita da ya shekara kusan takwas da ita har ta gama zamanta bamu sameshi ba,yo na meye zan damu kaina?,saina gamacin qwai kaji da nama,ina gani an tirke sa za'a kayar kawai sai na yiwa kaina na tafi rakiyar sakakkiya?,da yake nice maqunshin gishiri"(😂😂,niko nace gaskiyar ki hajiua fanteka,shi mutum mai yawan alkhairi dama maqiyinsa ma wataran masoyinsa yake komawa,Allah kada ka jarrabemu da hannun 'yan dambe). "Alhamdulillah, Alhamdulillah,Allah ya tayaka riqo,kai nayi farinciki,inama ace yar uwata tana raye taga wannan rana da taketa roqa maka ita" gwaggwo mero ta fada zuciyarta a karye,abinda kuma ya shiga kunnen hafsat kenan wanda ya sakata tsananin rudewa,ko ba'a fada ba tasan wani promotion dinne ya samu,dai dai sanda take fita a rayuwarsa?,wannan wacce irin hasara ce ta tafka. Ko gwaggwo mero dake ban baki tare da musu fatan sauka lafiya basu kalla ba,suna fita wajen gidan ta damqi hannun gwaggwo mero "Na shiga uku mero,ya samu promotion,kuma wallahi babban matsayi ne ya samu wannan karon" ta fada qwalla na zubo mata "Eh to dai hakanan zakiyi haquri,duk wani abun rashin haqurinki ne sila,yqnzu gashi kin bar mata gidan kin bar mata mijin,kin bar mata yaran" maganar gwaggwo hassana saita zama kamar kamar wani fami ta yiwa hafsat din,taji kamar itama tana layin maqiyanta ne,amma dole haka ta danne don tana buqatar dan rakiya,bazaiyiwu ta tafi ziqau ba abun sai yayi mata yawa. Abinka da ba 'yan halak ba,isarsu keda wuya laifin yaso ya koma kamar na gwaggwo hassana ne ma,ummanta tana salati tana komai amma tana fadin su gwaggwon basu kyauta mata ba,ta yaya suna wajen zasu bari ya qarasa tsinke ragowar igiyar da tayi saura?. Abun duniya ya taru ya ishi gwaggwo hassana,ta kama baki kawai tana kallon qarfin halin umman hafsatun,wato shi dai abun arziqi bai karbi kare ba wato,hakanan matsiyaci ko a tandun mai aka sakashi haka za'a fiddashi qamas,haka ta karkade zaninta ta tashi ta wuce gida cikin takaici,abun arziqin da tasoyi ya koma na tsiya,can kuma ga daula da gagarumin bikin sunan da za'a yi ta yiwa kanta rasa rasa,sai ta yiwa gwaggwo fanteka barka da batayi biyu babu ba. ******Kwananta biyu cikin matsanancin hali na kuka da damuwa,har daga qarshe umman nata ta gaji da ji ta zaunar da ita "Nifa wannan koke koken naki ya fara isata,wai shin abbas shine autan maza koko ya aka fara?,kinga fa babu ta inda Allah ya rageki in gaya miki,kin samu a jikinsa kin tara abinda kika tara,ki gama iddarki ki gyagije ki fara zawarci me lasisi,wallahi da gudu zaki samu manema,ai sai wani ya yar wani yake dauka,abu daya zaki.masa ki rama,kema da zarar kin gama iddarki ki rattaba aurenki kawai,shine qarshen baqincikin da zaki cusa masa,yara kuma ya baki abinki,ta nan ma kadai zamu sake samun wasu kudin shigar". Da wannan shawarar suka dinga shige da fice saida aka saka baki aka bata su mimi,kallonsu kawai yakeyi,yasan manufarsu,don haka dukkan abinda ya tashi bayarwa na amfanin yaran qeqe da qeqe yayi musu,na watanni uku cas ba qari babu dadi,haka umman da hafsat din sukayita zaginsa sunayi dashi a gaban yaran,mimi da nawwara saidai su bata rai,babu damar yin magana,don tun randa nawwara tayi magana da yake ta danfi mimi tsiwa uwar ta gwabje mata baki basu sake cewa komai ba,saidai suyita bata fuska,takaici da baqinciki ya ishi hafsa,don ko widad aka zaga a gabansu sai fuskarsu ta canza "Shegu an goga musu baqin hali" haka hafsat din ke fada. Watanni uku aka bawa abbas din kafin tafiyar da zaiyi america, office zasu gama masa dukkan shirye shiryen tafiyar,sun bashi damar tafiya da mata daya da yara uku zasu dauki nauyinsu,idan yana buqatar qarawa kuma wannan saidai yayi a aljihunsa. Hankali kwance cikin wata irin nutsuwa yake dukka shirinsa,yanason tafiya da widad amma baisan ya zata kasance ba,saidai yana mata shirin ba tare data sani ba incase koda zai buqaci hakan,don bayajin zai iya nesa da ita na wadan nan watannin. Gefe guda kuwa widad din ta gaya ma kanta aikine sosai ya sameta,idan a baya su biyu ne yanzun ita daya ce dashi,uwa uba kuma riqe namijin da a baya yake da mata biyu yanzu ke daya ce dole saikin zage damtse kin ninka shirinki,duk da hafsat din akwai ya babu ce,amma dai duk tsiya macace itama. Ta tsaya ta gyara kanta da kyau,ciki da waje ta fara canzawa tana komawa yarinyarta danya shakaf,ta sake shiga classes kala kala da groups groups 'yan gaske na manyan matan da suka fita gogewa a komai, groups na hajiyoyi masu mutunci da tarbiyya da ake mugun qaruwa,ta shiga ne ta sanadiyyar su anty fanna da a yanzu suka zame mata madubi kuma makaranta,gefe guda kuma ga su anty madeena da anty deena da sauran yayyenta da kowannensu yanzu zaman lafiya sukeyi sosai,dama can widad din akwai sauqin kai da bin na gaba da ita koda tazarar shekarunku babu yawa,to har kawo aure bai canzata ba,saima sake riqe yayyenta da kyau datayi. Ga mummynta itama da bata jin kunyar yi mata bayanin komai,widad din kawai gareta diya mace,sauran dukka maza ne,don haka ta sake zage damtse tana gyare yarta tsaf,kama daga tarbiyyar jiki data zamantakewarta da mijinta. Cikin lokaci kadan ta sake gigita abbas din,idan sun zauna bashi da zance sai yace "Kina haihuwa kina sake zama mace,kina kuma sake dada wayo,kina kuma mallakeni wuudd" dariya yake bata "Allah ka daina fadan mallakar nan,banason jinta,kada wataran kayi subutar baki a dauka da gaske mallakar nayi maka". Murmushi kawai yake binta dashi,ta shiga kowanne lungu da saqo na rayuwarsa ta tsaye masa cakkk,yasha rayawa a ransa zama da hafsat da rabon haihuwar su mimi ne qaddararsa,bansa haka,inda ace widad din ya fara samu babu abinda zai sanyashi sake wani aure anan dai gidan duniya,saidai hurul'een na aljanna. Wata biyu kacal ta gama gyaran kanta,idan ka ganta ita da yaranta ko ke mace saita baki sha'awa ta burgeki,yaran su dukka ukun affan da sajid da sajjad (twince dinta)dukansu masu kyau ma sha Allah,sun debo kyau wani daga na widad wani daga na abbas,sai kyansu ya zama wani kala daban me ban sha'awa,bul bul dasu dukansu,idan ka gansu su ukun ba zakace ita ta haifa yara ukun nan ba(daya daga cikin sirrin auren wuri kenan,zaki tara yaranki tunda quruciyarki,baki san dadin jikinki ba,sanda zaki gama haihuwa da sauran qarfinki,sai ayita mamakin wadannan duka yaranki ne,ayita sha'awarku,Allah ya bamu haihuwa me albarka,ya albarkaci wadanda muke dasu). Sai da suka cika cika watanni uku sannan sukayi shirin shiga garin bauchi,suka shirya tsaf da tsarabar da widad din tayi da kudinta,ita da yaran da aminatu da fahad wanda a yanzun yake tare dasu,sun fara gaba ne,abbas din yace washegari zai biyosu,akwai wani case da zai rufe ne a ranar. Zuwa tayi ta tarar an yiwa gidanta sabon gyara,wancan gidan nasu kuma da hafsat ta kwashe kayanta duka anata masa aiki,an canza masa fasali da tsari gaba daya,wani irin gini ake masa na tashin kai. Washegari da azahar ya iso, yaran duka suna wajen aminatu ita kuma tana wajen mai gayya mai aiki tana kula dashi,sai da yayi wanka yaci ya qoshi sannan yace mata su shirya suje suyi gaishe gaishe,ta shirya yaran duk da dama ko yaushe tsaf suke,suka fita gaba daya a sabuwar dalleliyar motarsa daya canza,ita kuma yabar mata waccar. Sun zaga dangi sosai,widad kuma tasha sanya albarka sosai ita da yaranta,bayan sun taho hanya abbas ya kalleta "Waini hajjaju,jarin naki duka kike kwashewa kike kyauta dasu?" Murmushi tayi masa tana narkar da wuyanta,ta masa wani kallo na qasan ido "To yallabai ko me zan basu ai ban fadi ba,danginka ne fa?,abun tutiya wa yarana,kuma ka manta ribar da na samu a wannan shekarar?,ko ka manta ina shirin bude shago?" "Tuba nake,na manta fa da hajjajun gaske nake magana ba da jabun ba" sai suka saka dariya a tare tana dora kanta a kafadarsa bayan ta kaiwa bayan hannunsa duka. "Mu samu wani eatery din muci abinci,banason mu koma gida kice zaki shiga kitchen din nan girki,nidai yau na sauke miki" "Godiya nake" ya fada tana hade hannayenta guri guda,ya sakar mata murmushi,yasan duk da yayi hakan tabbas saifa ta shiga kitchen ba fashi,ko Black tea saita dafa masa hankalinta zai kwanta,dun rintsi duk tsanani bata taba bari rana ta fito ta fadi baici komai daga hannunta ba. Gaba daya ta tattara hankalinta akan baqin mutumin da za'a iya kiransa matashi,don bai qarasa shekarun abbas ba,aqalla abbas din yana iya bashi shekara biyar,tun wancan sati biyun da ta kammala idda ya fara zuwa wajenta,amma tun lokacin taji sam baiyi mata ba,a tsukin maza kusan uku sunzo mata,amma duk wanda ta daga kai ta kalla sai taga baikai mata zatin abbas ba,tana da buri.....tanason bawa mara da kunya,tanason tayi auren huce takaici,tanason tayi auren da za'a san bataci baya ba,zatayi auren da abbas zai ciji yatsa,widad kuma tasan cewa tayi mata nisa,ta kuma yi mata tazara da ratar da bazata taba iya kamota ba. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 42 Matashin ya sake gyara zamansa yana gyaran murya "Sunana AVM mu'awiya mani adam" da hanzari hafsat ta daga kai tana dubansa "AVM kuma?,air vice marshall kenan fa?,dama babban mutum ne shi din haka me muqami yaketa binta tana wulaqanta shi?,wato Allah yayi tana da rabo,da tayi wasa da damarta,saita gyara zama tana sakin masa fuska sosai harda murmushi "Ayyah,afwa yallabai,inata bata maka lokaci ko?,kasan komai sai Allah yayi" shima murmushin ya saki,da alama tarkon da ya dana yayi kamu "Ba komai,yau ai gashi zamu tattauna sosai" sakewa yayi yana bayyana mata waye shi da irin abinda yake dashi,cikin mintunan da basu gaza talatin ba taji ta gamsu ta kuma amince dashi,kuma lallai ta samu mijin auren da take fata wanda yafi abbas matsayi da dukiya,saidai ya nuna masa kyau,take ta bashi damar turo magabatansa,sukayi dan ciye ciye suka kuma sake tattaunawa,ganin shima din mawadaci ne sai bata boye masa komai ba ta gaya masa irin business din da takeyi,da kuma abinda ta mallaka yanzu haka,don ma tanata fama da ummanta dakeson ta hau kan kudin a dinga murqushewa,banda ta bade idanunta da toka zuwa yanzu Allah ne kadai yasan nawa za'a rugurguza,bayan kudaden abincinsu mimi da ake kawowa suke kashe mu raba,shi yasa taji ta matsu tayi aurenta ta samu inda zata sauke dawainiyarta ta daina facaka da kudinta. Sosai take kashewa kanta kudi,ita ala dole bataso aga ta canza bare ayi tunanin baqincikin barin gidan abbas ne yake damunta,idan tayi aure kuwa tunda ta samu mai farcen susa,zata tsula tsiyarta yadda taga dama,sai tasa widad taji ta muzanta. Ya jima wajen masu biyan kudi sannan ya qaraso wajen motarsa yana mita "Sai suce su basuson Dollar dole saida naira za'a biyasu,bayan ribarsu ne idan aka basu dollar din". Kanta ya sake fashewa ta saki murmushi "Rashin wayewa ne kawai yake damunsu" "Wallahi kuwa,duk da haka saida suka riqe canji na wajen 5k" kamar ta juya taje ta karbo,amma sai taga kamar ajinta zai zuba,haka ta kanne sukaci gaba da tafiya. Tana tsaye tana jiran ya bude mata ta ciki motarsu abbas ta faka daga gefansu,tunda motar ta tsaya hankalinta ya dauku a kanta,don ba qaramin burgeta motar tayi baba jimawa ya bude ya fito cikin wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin zamani. Mummunar faduwa gabanta yayi,abbas din ya canza yayi mugun fresh,ga qiba mai kyau daya hada,fatarsa ta qara haske,gaba daya qamshinsa ya cika wajen. Sanda madam widad kuma ta fito cikin wani fitinannen dinkin bubu sai yawun bakinta ya ida qafewa,abbas din ya sunkuya ya karbi sajjad daga hannunta,sajid yana wajen aminatu shida affan,sannan ya karba hand bag dinta ya riqe suka jera zuwa ciki. "Ina zuwa" tace da AVM mu'awiya tana komawa ciki da sauri saurinta kamar wadda tayi mantuwa,so take ta tabbatar da abinda idanunta ke gane mata,widad dince ta koma kamar wata basarakiya a fadar masarautun larabawa. Can ta gansu suna magana da receptionist din,tana dan jifan abbas din da harara,gurin zaben abinci ne,sun saba kuma irin haka,akwai saboda da fahimtar juna sosai tsakaninsu da ma'aikatan wajen,wani abu ya tsaye nata a wuya, tsabar hassada da baqinciki ya rufe mata ido,ta nufi gurin dason nuna musu itama cikin wadata take,kuma tare take da mijin zata aura "Hello" ta fada tana wani yatsina,tunda abbas ya waiwaya sau daya ya kalleta bai qara ba,a yadda yayi zaka tsammaci ranar farko ne daya taba ganin halitta me kama da ita,kuma basu da wata alaqa ko kusa ko alama,sai ya dauke kansa yanaci gaba da miqa musu atm dinsa kan su cira kudin "Takeaway zaku hada mana kawai,basai mun zauna ci a nan ba" abbas ya fada yana duban ma'aikacin,widad da ta yiwa hafsat din kallo biyu cike da mamakin yadda ta tsomale kamar dattijuwar kaza ta maida dubanta ga abbas tana mamaki,yace anan zasuci amma yanzu ya canza,batadai ce komai ba,dukkansu sukayi shuru sai.muryar hafsat daketa qoqarin mata kwaskwarima,ita ala dole ga ajebo. "Nice wadda muka zauna a wancan table din ni da AVM mu'awiya" "AVM mu'awiya kuma?" Ma'aikacin ya tambayeta cikin mamaki "Yes.....mijina da zan aura,akwai sauran 5k canjinsa dake wajenku.....idan ba damuwa zaku iya riqewa" junansu suka kalla cikin mamaki,saboda sudai sunsan indai wanda take magana akai ne da qyar ya cike musu balance dinsu ma,daya daga cikinsu ne ya girgiza kai "Aah,muba wanda muke riqewa canji,saidai idan bai fada miki dai dai ba,ko bakiji dai dai ba" fuska ta bata ganin suna niyyar yarfata "Me kake fada?,ya anyi muku alkhairi zaku saka ma mutane da sharri?" "hajiya wai me kike fada?,mufa ba wani canji a wajenmu,kije ki sake tambayarsa dai" "Okay,indai kuka sakani zuwa na dawo zaku gane kurenku,zaku gane da matar waye kuke musu" ta fada tana murza hannu,saita juya tayi hanyar fita tana taku dai dai,tanason murza power dinga a gabansu ko don yau ta hanasu barci. Jajantawa suke a tsakaninsu na abinda tayin,abbas dake tsaye yana jinsu yace "Inajin bata da hankali,ko damuwa ce tayi mata yawa" ya fada da salon shaqiyanci dariya tana cinsa yana dannewa,dubansa widad tayi da sauri ta galla masa harara "Hafsat dince bata da hankali?" "Oh.....wai dama kinsanta ne?" Yayi tambayar yana dubanta gami da dage dukka girarsa sama,sakato tayi tana kallon abbas din,sai kuma ta girgiza kai kawai,dai dai sanda suka juya suna barin wajen zuwa inda su aminatu ke zaman jiransu "Dama ai dole kace baka santa ba,kana kishi" wata dariya ce ta qwace masa sosai,ya dinga dariya yana duban widad din,bai tsagaita ba har suka shiga mota ya tayar da ita sannan yace "Bakisan tausayin wanda zai dauketa nakeyi ba?,niko a lahira horon da za'a yimin shine na sake zama da ita inuwa daya bare nan gidan duniya?,sam,haihata haihata,idan taso ta auri sarkin makka ma,ina mata murna,amma nikam abbas turaki har abada,ni kadai nasan me naji me na gani" shuru tayi tana girgiza kai cikin mamaki,wato mace na iya fidda kanta fit daga zuciyar namiji kenan,kamar yadda take iya kafa kanta kwatankwacin yadda ita tayi "Su mimi ne a raina,banajin zan iya ci gaba da bar musu yarana gaskiya,kullum haqurina sake qarewa yakeyi a kansu" "Yaushe zamuje ganinsu?" "Gobe......in sha Allah" "Yayi,Allah ya nuna mana" ta fada itama can qasan ranta da damuwa,Allah ya sani tana son yaran sosai,bataqi kuma a dawo dasu a mallaka mata su ba. Daren ranar kasa bacci gaba daya hafsat tayi,ta dinga zarya tana hango abbas da widad a idanunta,happy family,me zatayi wanda zai bata wannan jin dadin nasu?,bata samu hutu ba saida zuciyarta ta yanke mata abinda zata aikata musu,ta san yadda mata suka tsani riqo,musamman ma riqon dan kishiya,ba abinda zata cusgunawa widad din dashi saidai takai mata yaran,ta qara mata yawan aiki ta hanata hutu,wannan kuma tasan zaiyita hadata fada da abbas din,shikenan hankalinta ya kwanta. Da wannan shawarar ta kwanta, washegari kuwa tunda safe ta soma hada musu kayansu,har sun sanya uniform tace su cire,ummansu nata fada da mita "Dan hanyar samun alkhairin zaki toshe mana?" "Nifa aure zanyi umma,don haka yaci gaba da riqe yaransa,babu me masa wahala,yanacan yana holewa da matarsa mu ya barmu da raino" hakanan badon umman taso ba ta tasasu a gaba,ta sakasu a napep sai gidan abbas din kanta tsaye. Kusan kowacce safiya zaka samu gidan neat dashi,bama gidansu na katsina ba har na nan din,saboda basa kwanciya dama abar gidan da datti,har aminatu ta saba,ya zame mata jiki,duk inda takwas tayi ta gama komai,ta yi wanka ta yiwa affan din kansa wanka,saidai suyi wani abun daban kuma,kosu sake kwanciya bayan sunci abinci,ko suyi game na alphabet din arabic ko na english da dai sauran abubuwa masu amfani. Tsaye tayi a tsakiyar falon tana qare masa kallo,an tsara komai na falon daki daki bisa sha'awa da burgewa,hakanan ya samu cikakkiyar tsafta da kulawa,ba abinda yake fitarwa sai wani irin sassanyan qamshi da ya hade da sanyin ac din dake Parlor din. Muryarta ta ware cikin baqinciki ta kwarara sallama,aminatu dake daki ta jiyota,ta miqe ta fito tana riqe da hannu affan,hannunta daya kuma dauke da sajjad dake cikin wasu fafaren overall,ya cikata fam ma sha Allah,idan ka kalli yaran ba zakace twins bane ba. Tsaiwa tayi tana kallon hafsat din cike da mamakin ganinta a gidan,saita kalleta da harara harara "Ina mutan gidan?" "Antyn tana wajen daddynsu....." "Na sani,dalla malama kiramin shi mai gidan" ido aminatu ta fiddo,tunda take dasu bata taba buga musu qofa ba ai,ba zata iya ba,barema dokar widad dince,indai ba wani babban abu bane ya faru basa kiranta idan tana tare da daddyn "Ba'a kiranta idan tana wajen daddy,kiyi haquri ki zauna ki jirasu,bari na kawo miki ruwa" ta fada cikin nutsuwa irin ta yarinyar tana sakin hannun affan,wanda mimi tayi caraf ta kamoshi "Qani.....ka manta ni ko?,ya naga kana kumatu,muji ko bread ka boye" ta fada tana dariya gami da fara lallatsa masa kumatun,yaron bashi da saurin mantuwa,ya tunata sarai,sai kuwa yahau bagala mata dariya,dukkansu sai suka matso kuwa,abinda ya qarawa hafsat takaici ganin yadda suka yanyame yaron dukansu cike da qauna suna masa wasa,ta daka musu tsawa,duk sai suka koma suka lafe. Sosai aminatu ta cika plate da kayan kaiwa baka ta ajjiye gaban hafsat dake tsaye,tabi kayan da kallo,rai naso amma kuma zuciyar ta hana,baqinciki qyashi da kishi mara amfani ya rufe mata ido,taso ta basar amma ta kasa,saita faki ido ta dauki lemo ta jefa a jaka,ta dan rarraba ido taga hankalinsu bai kanta,ta sake zarar wani abun ta jefa,tana kan jefa na uku ne qofar bedroom din abbas ya bude suka fito shi da ita,sai tayi sauri ta saki abunda ta dauka,saidai tuni sun gani,amma sai sukayi kamar basu gani ba. Riqe suke da hannun juna,perfect match couples da kowa ya kallesu sai sun bashi sha'awa,sanye take da wata rigar wani material da aka yiwa wani kyakkyawan dinki da ya zauna mata sosai a jiki,kanta ba dankwali sai sassalkan baqin gashinta me yauqi wanda kullum bata gajiya da gyaransa da yi masa style kala kala harda nasu bead,yau matseshi tayi cikin band ta kuma yiwa jelar kitso guda daya ta barshi yana yawo a bayanta,jikinta ba abinda yake sai fidda sassanyan qamshin turarukan jiki dana hayaqi data tsuma kanta dasu. Shima abbas din shirye yake tsaf cikin qananun kaya wadanda suka sake qara masa kyau da quruciya, hannuwansu cikin na juna,tana riqe da wayarsa da kuma takalmansa da baikai ga sakawa ba da alama wata magana suke me muhimmanci,don kowannensu fuskarsa dauke take da walwala,duk da kusan ko yaushe haka suke su din,zaiyi wuya kaga sabani a tsakaninsu. Kanta ta dauke kamar zatayi aman zuciyarta,saidai a fuska kuma bata nuna hakan ba,amma wannan yanayin ya bayyana har saman fuskar tata "Oyoyo mimin daddy,oyoyo nawwaraty.....a'ah ga baby yusra" widad din ta fada cikin farincikin ganin yaran,suka taho da saurinsu suka rungumesu duka har uban,sai ta sanyasu cikin jikinta sosai,tausayinsu yana ratsata,inama ace abban nasu zai bar mata su. Yana zaune yana gaisawa da yaran nasa daya bayan daya yana bincikar lafiyarsu ba tare daya dubi ko sashen da hafsatun take zaune ba,widad kuma na tsugunne gabansa tana sanya masa takalmi a qafafunsa,sun share hafsat din kamar ba ita a falon,tun bayan sannunku da zuwa da widad tace mata ta amsa da qyar sai itama ta watsar da ita,don a yanzun kuma bataga wani alaqa tsakaninsu ba bare ta dameta. "Yaranka na kawo maka,don nima aure zanyi" maganar data fada kenan cikin gadara,dai dai sanda widad ta gama saka masa takalman,sai ya miqe tsam ba tare da yabi takan maganarta ba yana fadin "Allah yayi miki albarka,zan fita amma idan na taho zan kiraki,karkiyi nesa da wayarki" ido ta lumshe tana gyada kai "In sha Allah daddy" har ya daga qafa saita tsaidashi "Kamar kai mummynsu mimi keson gani" "Ohhhh....." Ya fada yana dan sosa girarsa "Yara ta kawo,kuma tayi abinda ya dace,shikenan ta ajjiyesu ta tafi,idan kuma akwai sauran wani damuwan ki wakilceni kawai dear,nasan zaki iya komai.....i trust you" ya fada yana jinjina kai fuskarsa kwance da murmushi. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 43 Sake baki kawai tayi tana kallonsa,ya gama kasheta gaba daya,babu kunya ko kara a lamarin nasa?,sai ya kashe mata idonsa guda daya ya juya ya fice abinsa a falon hankalinsa kwance. Yana gama fita ta waiwayo ga hafsat din "Ki zauna sai....." "Ba zama nazo yi ba,ga yara nan Allah ya karemin su ya kula dasu,idan kuma aka cucesu Allah ya isansu basu yafe ba" wani lafiyayyen murmushi widad din ta sakar mata hankalinta kwance,ta koma ta zauna saman kujerar ta dora qafarta daya kan daya tana kallon hafsat din "Ki kwantar da hankalinki,kowanne tsuntsu fa kukan gidansu yakeyi,mu namu kukan me dadi kyau da ma'ana ne,haka aka koya mana,yara kuwa sunzo gidan ubansu inda yafi dacewa dasu,inda zasu samu kulawar da suka rasa kaf iya tsahon rayuwarsu,na meye kuma zaki damu?,idan ka shuka alkhairi ai baka tsoron ranar girbi......oh......na manta,kina tsoron kada na maidasu 'yan wanke wanke ba?,ko masu yimin shara ko wanki,ko kina tsoron kada na dinga basu wankin kashin su affan ko su sajjad?" Saita girgiza kai "Allah ya tsareni,banason ranar girbi na ta zamemin ranar kuka da nadamar baragurbin shukar dana dasa da hannuna,don haka kije kiyi baccinki harda minshari,zasu samu kulawar da ke kanki kika gagara basu,idan iya abinda ya kawoki kenan sai nace ki gaida gida,na gode da kyautar dan mutum sukutum da kikayimin har rai uku ba tare da nayi naqudarsu ba" saita qwalawa aminatu kira tace ta wuce ciki dasu. A karon farko hafsat tabar gidan jiki a matuqar sanyaye,kalaman widad sun bugeta qwarai,anya batayi gwaari ba data dauka yaranta duka ya danqa mata su?,sai shaidaniyar zuciyarta ta jaddada mata tayi dai dai,dole yaran zasu dameta,kuma shine kawai abinda zatayi ta baqanta musu rai,batasan wannan abun da tayi shine abu na farko data yi wanda ya faranta ran widad ba,don kuwa cikin kwana uku kacal yaran suka fara hawa saiti,farincikinsu ya qaru,dadi kamar suyi me babu ma kamar mimi da taji a duniya an gama mata komai,ta dawo waje antynta. Wannan kawo sun shi ya bawa abbas damar fara musu shirye shiryen tafiya america din gaba dayansu,ya kashe kudinsa sosai amma baiji komai ba,farincikinsa shine kasancewa da iyalinsa,sai a yanzu yakejinsa cikakken namiji kuma cikakken mutum,widad ta hada masa kan iyalinsa gaba daya,idan ka shigo gidan kai kanka sai ya burgeka,komai a tsare bisa doka da tsari,yaran sun soma samun wata cikakkiyar nutsuwa da kuma tarbiyya. Ranar da suka bar nigeria ranar hafsat din ta daura auren da ta dinga fatan abbas din yana nan zata daurashi,to baisan ta daura din ba don tuni jirgi ya lula dasu,koda yaji dinma babu abinda zai dameshi,don a duniya bayajin akwai wanda ya fishi farincikin rabuwa da ita,ya yadda KADDARARSA ce zama da ita,a yanzun kuma yana kyautata zaton yaci jarrabawar da Allah ya saukar masa,shi yasa yayi masa tagomashin rabuwa dashi. Rayuwarsu a america tazo da sabon tagomashi qarin wayewa da kuma budewar ido,don a nan ne widad tayi amfani da result dinta tayi course akan kasuwanci na shekara daya,don sun samu qarin wasu watanni shidan,a nan ta hadu da mutane sosai kala kala data qaru dasu,ta fannin gogewar Rayuwa mu'amala da zamantakewa, nau'in girke girke harma da gyaran kai gyaran jiki da kuma kula da iyali da miji gaba daya,ta samu experience na rayuwa me tarin yawa,bayan sun cika shekara suka tattara suka dawo,dukka yaran sun canza,sunyi dima dima sunyi fresh dasu,sai suka zama wasu ababen kallo,widad business dinta ya kankama,don tayi business sosai tacan,ta kawo kaya a shekarar kamar ba gobe,ta rabawa yan uwanta duka harda dangin miji,kowa ya samu alkhairi yayi murna,don sun qaru da ita,wasu har qaramin jarinsu suka tayar,hannunta me albarka ne sosai da komai ta taba sai ya siyu da tarin alkhairin ubangiji,ne yiwuwa zuciya me kyau da take da ita ne ya zame mata silar hakan. Kai tsaye suka sauka a tsohon gidansu da suka bari ana yiwa sabon gini,wani irin tsari aka yiwa gidan me matuqar jan hankali kamar a turai,masu sannu da zuwa da zuwa ganin sabon gida aka yita tururuwar zuwa, widad nata jin kunya tana boyen qaramin cikin data dawo dashi,a lokacin duka duka shekarar su sajjad daya da wata shida,ita a ganinta sunyi qanqanta da ayi musu qani,duk da sanda ta haifesu affan ma baikai haka ba. kuka ta dinga yi tace ita bataso "Ya kikeso yanzu ayi dashi" "Nidai a zubar" "What!!!" Ya fada da mugun qarfi "Eh lallai na yarda baki da hankali,kuma har yau baki girma ba,bari kiji abun Allah ya kiyaye Allah ya tsare,ko cikin shege nayi miki ai baki isa ki zubarmin da ciki ba" cikin wannan rigimar tasu suka iso nigeria,yana shareta tana shareshi,kowa yana ganin yafi dan uwansa gaskiya. Yau tunda ta tashi batajin dadin jikinta sosai,don haka koda safe ma tana jinsu suna sabgoginsu daga can babban falon gidan amma bata leqo ba,tasan aminatu zataji da komai,ga adda mimi kamar yadda tasa suke ce mata,yarinyar akwai qoqari,duk wani aikin zaka sameta tana taya aminatu,widad din bata taba hanata ba,saboda tana tuna wahalar data ci sanadiyyar rashin iya komai a aikin gida,duk da gatane na goyon kaka,tafison idan ta tashi aurar da mimi din kamar yadda take fata wanda duk zai auresu ya qare rayuwarsa yana shi mata albarka. Tana kwance abbas din ya gama shirinsa,yazo kanta ya tsaya,saita dauke kanta gefe,yakai hannunsa ya taba wuyanta,sai ya sauke ajiyar zuciya jin bawai zazzabin da yake takurata ne a jikinta ba,yana mamakin yadda ta iya shareshi da gasken tsahon kwanakin,sai yasa hannu yadan shafi fuskarta kadan yana fadin "Sai na dawo" "A dawo lafiya" ta fada ciki ciki,sai kuma tabi bayansa da kallo,bayan ya fitanbta lumshe ido tana fidda numfashi mai sanyi. Abbas miji ne na musamman,idan tace na musamman tana nufin hakan,duk yadda sukakai ga fada ko sabani da juna saidai iya kan harshe kawai,amma duk wata kulawa basa fasa baiwa junansu. Agogo ta kalla,qarfe daya saura,ta yunqura zata miqe ihun sajjad ya kawo mata har nan inda take,tasa hannuwanta ta toshe kunnuwanta "Allah ya yiwa aminatu albarka" ta fada idanunta a runtse,batason hayaniya kwata kwata,banda akwai aminatu da mimi da batasan yadda zatayi ba,dole yanzun ta fita,tasan filin dambe aka bude tsakanin affan sajjad da sajid,wataqila yusra na gefa tana tilliqa dariya,nawwara na qoqarin shigarwa affan mutuminta,saita sauko kawai ta shiga bandaki ta wanke fuskarta da bakinta ta fito ta zura wata sassalkar abaya a jikinta,already da wankanta dama,don bata iya kaiwa haka batayi wanka ba sam,ta zura wasu lausasan slipper kalar abayar ta fito tana daura siririn dankwalin rigar a kanta wanda bai rufe komai a gashin kanta ba. Falon kuwa ya kacame gaba daya,duk sun ruda aminatu kamar tayi kuka,dama gata gwanar sanyi,saida widad tayi musu tsawa sannan suka dakata da abinda sukeyi,sai kowa ya fara shiga taitayinsa,suka matso kowa yana gaidata "Maami ya jiki?" Suka dinga cewa,mamaki ya kamata,oh wato abbas yace musu bata da lafiya kenan?,zai hada mata case,yanzun idan suka dinga mata sannu har sai ta gaji,har sai an fuskanci abinda ke maqale a jikinta "Jiki alhmdlh,na warke ai" "Allah ya baki lafiya maami" mimi ta fada cikin damuwa da kulawa "Ameen mimi na" tattarasu duka tasa aminatu tayi waje daya,ta kunna musu cartoon din da sukafi so,sai aka samu salama kowa ya nutsu,sai sajjad da sajid da lokaci bayan lokaci ake fama dasu ana bari bari. Dining ta wuce ta duba abinda aminatu ta dafa musu,saita zauna daga can saman ta hafa baqin tea tana dan kurba kadan kadan tana kallon yaran,rai shida dukka yaran abbas,ga na bakwai a jikinta,kome zata haifa kuma Alla masani,cikin ranta ta samu kanta da addu'ar Allah ya raya mata su taga girmansu,ya bata ikon ci gaba da tarbiyyantar dasu. Qarar wayarta dake gefe ya katseta,ta duba wayar saita saki murmushi,ummunta ce,ta gyara zama ta daga wayar cikin shagwabar da har yau bata iya daina yiwa mutum biyu a duniya ita,suma kuma har yau bata girma a wajensu,abbas da ummunta. Ta sakankance sosai suna hirarsu kusan rabin awa,sai taga aminatu ta buda qofar falon ta fita,sai gata ta dawo,ta hauro inda widad ke zaune "Maami baquwa kikayi,to mai gadi ya hanata shigowa waisai an gaya miki" mamaki ya cikata,bai tana hana kowa shigowa ba muddin ya yarda dashi sai yau?,da yake qarin matsayin da ya samu yana da me gadi cikin qananun 'yan sanda,hakanan an bashi driver da security "Koma wace a barta ta shigo" ta fada tana maida wayarta kunne,idanunta akan qofar falon har zuwa sanda labulen ya dage fuskarta data jirkice ta bayyana,saita zame wayar daga kunnenta tana cewa ummu "Zan kiraki ummu anjima" "To babu damuwa" ummun ta fada tana a gaida mata kishiyoyinta da masu gidan. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 44 Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn Whatsapp 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549 Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 _______________________________ Har yanzu kallon fuskarta takeyi,tanason tantancewa itace ko ba ita bace. Yadda itama take kallonta haka baquwar,kafin ta janye idanun nata ta maida kan yaranta dake zaune gaban tv sun bata hankalinsu,wasu hawaye masu ciwo suka tsatstsafo mata,dai dai sanda widad ta miqe tana cewa "Sannu da zuwa" gami da gangarowa daha step na dining din "Yauwa sannu" ta amsa mata murya a dakushe,widad ta qaraso wajen can gefe daga inda yaran suke tana fadin "Bismillah zauna" "Har ina iya zama?" "Ba damuwa ki zauna......mimi ga mummynku,nawwara yusra?,maza ku taso,aminatu a kawowa baquwa abun tabawa" duk sai hankulansu yayo kanta,duk suka tsaya suna kallonta da kyau,kamar basu ganeta ba. Itama ido ta tsura musu,hawayen da take riqewa ya silmiyo mata,sai suka miqe dukansu sukayo wajen uwar jiki a matuqar sanyaye,dadi ya kamata,ta bude dukka hannuwanta suna isowa ta rungumesu tana sakin kuka mara sauti. Sun jima a haka,tausayinsu yana ratsa widad,Allah alhakim,Allah mai iko,Allah me gaggawar hukunci mai sakayya da hisabi tun a nan gidan duniya,wai yanxu hafsat ce haka?,kamar wata almajira?,cikin shekara guda kacal,cikin wata mummunar kama da siffa. "Naji dadin ganinku haka mimi,duk da dama raina yana rayamin ba za'a samu wata matsala ba,kuna cikin aminci da kulawa,don na tabbatar ban barku a mummunan hannu ba" hafsat ta fada tana sharce hawaye "Na gode,Allah ya saka da alkhairi,Allah ya biyaki da yadda kika riqemin yarana" ta sake fada tana kallon widad kamar me kunyar su hada ido. Duk mamaki sai ya kama widad din,hafsat dince ke mata godiya har tana yabonta,lallai kaji tsoron duniya kaji tsoron ubangijinka "Ba komai,d'a ai na kowa ne,da dukiya da d'a babu wanda yasan me morarsu sai Allah" "Haka yake" ta fada tana jinjina kai,gami da tuna tata dukiyar data dinga salwanta daya bayan daya,har ta zamana a yanzun bata da komai bata mallaki komai ba. Ta jima da yaran a falo widad ta basu waje suna hira,sunata gaya mata abubuwan da suka faru da kuma zamansu a america,a ranar taji farinciki da nishadin data jima bataji irinsa ba,damuwarta ta ragu qwarai da gaske,ta sake gasgatawa lallai yaran sune sanyin idaniyarta. Data tashi tafiya cikin d'ari d'ari tace da widad "Don Allah zan roqi alfarma guda biyu a wajenki idan zan samu" "Babu wata damuwa,ki fada ko menene" "Don Allah ina roqarki ki yafemin duk abubuwan da nayi miki,sannan ki roqarmin babansu shima ya yafemin,duk da nasan saimai qarfin imani ne zai iya yafewar" "Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe,duk abinda ya faru ya riga da ya faru,shima zan gaya masa,zai kuma yafe din in sha Allah" "To na gode qwarai qwarai....alfarma ta biyu don Allah ki sake roqarmin shi,ya dinga barin yaran nan suna zuwarmin,koda ba kwana ba,ko basu yini bama don Allah" tausayinta ya sake kama widad,kaida yaranka amma saika roqi a baka su ka gansu "Xan gaya masa,kada ki damu kinji" godiya sosai ta sake yiwa widad din,sannan ta miqe tana musu sallama "Gashi ban kawo muku komai ba,kuyi haquri babu dama ne" cikin son kwantar mata da hankali tayi murmushi "Karki damu fa,suna da komai mummyn mimi" kai ta jinjina "Shikenan,na gode Allah ya saka da alkhairi" tsaidata widad tayi ta wuce bedroom dinta,cikin matuqar sanyin jiki da kuma tsoron halin duniya ta dauko hand bag dinta data dawo da ita ta buda,ta laluba kudin ciki,duka duka dubu goma ce tayi mata saura kudin nigeria,saita shiryasu ta fita dasu ta miqawa hafsat. Jikinta na rawa cikin mamakin yawan kyautar da tayi mata tasa hannu biyu ta karba qwalla tana cika idanunta,shekara guda kenan rabonta da riqe kudade irin wadan nan,godiya sosai ta dinga yi mata,sannan ta juya ta fice hawaye wani yana korar wani. Haqiqa duk wanda baiji tsoron Allah ba yana tare da wahala,duk wansa baibi duniya a sannu ba matsala bata qare masa ba,a yau yaran da take banzatarwa gasu tana ganinsu tana qaunar su rabeta,tana qaunar zama dasu amma sunfi qarfinta,don tasan ko sama da qasa zasu hade a yadda taga sun samu kwanciyar hankali da kulawa abbas bazai taba bata ko daya daga ciki ba. Gidanta da take ganinsa kamar mallakinta,ta kasa kula dashi,ta banzatar dashi gashi a yau yafi qarfinta,ta fita ta barwa wadda tazo gidan daga baya. Mijin da take banzatarwa,ta kasa tsayawa ta gyara kurenta,ta kasa tsayawa ta karanci abinda yakeso da wanda bayaso,ta kasa bashi abinda yake muradi cikin rayuwarsa.....gashi qaramar yarinyar da a haife ta haifeta,tazo ta sha gabanta,ta shiga rayuwarsa ta maye masa gurbin komai. Idanunta sun rufe,amma a yau suna bude kansu da kansu,tsantsar kishin banza da jahilci mara ma'ana yasa tabar gidanta, mijinta da yaranta dukka yanzu sun zama mallakin wata,saboda anyi mata kishiya ta kasa haqurin zama a gidanta,ta fita daga raminta ta fada ramin wata,tabar ramin data gina ta fada ramin wata,watar dake gallaza mata ita da mijin da baisan darajarta ba (babban qalubalen dake damun mata, mijinki da yasan darajarki,gidanki da kikasan ciwonsa,yaranki da basu da kamarki,dukka sanadin miji zai qara aure saiki watsar dasu kice saiya sakeki,bayan bai wulaqantaki ba,yayi hakanne saboda wani qarin auren a qaddararsa yake bai isa ya tsallaketa ba,babban abun mamakin kuma shine,sai ka ganta can ta buge da auren wani me matar,wai shin da ramin daka gina da kanka?,da wanda wani ya gina ka shiga zai zamto daya a wajenka gurin samun 'yanci da komai ma?,mata mu nutsu mu yiwa kanmu karatun ta nutsa,kishi yana da ciwo,yana da matuqar zafi,babu komai ke gane hakan sai masu zaune da kishiyoyin,to amma kuma ita addu'a maganin komai ce,sannan duk wanda ya miqa lamarinsa ga Allah,Allah ya isar masa,Allah yasa mu dace,yasa mufi qarfin zukatanmu amen). Widad ta dade tana juya abun cikin ranta,ta dade tana tuna fuskar hafsat,Allah abun tsoro duniya abun tsoro,sai jikinta ya sake sanyi,hakanan ta sake lafkewa akan kujera,tana tuna ko akwai inda ta sabi ubangijinta?,iya tunaninta bata tuna ba,amma saita samu kanta da istigfari,zuicyarta kuma ta sake tsarkaka,tare da sake daura aniyar kula da yaran tsakaninta da mahaliccinta,duk da dama ko sau daya zuciyarta bata taba bata wai ta zaluncesu ba. *H A F S A T* Sai data tsaya a soron gidan ta gyara zaman kudin sosai a jikinta cikin zaninta sannan ta sanya kai cikin gidan qirjinta yana dukan uku uku. Da ita kuwa ta fara hada ido,tana tsaye a gaban falonta,gaban hafsat yayi wata mummunar faduwa,tayi saurin janye idanunta,sannan da hanzari ta doshi dakinta kamar zataci da baka,tasa hannu ta tura qofar ta bude kai tsaye don dama bata kulle qofar ba,saboda bata ma da ikon don zata fita ta rufe qofar dakin nata. Falo ne falle da daki a ciki,kujerunta ne tun na aure,wanda su kadai ne suka tsira mu'awiya bai dauka ya siyar ba,maimakon ta samu guri ta zauna saita maqale jikin window din tana leqen tsakar gidan,tana kallon sahura dake mazaunin kishiyarta tana hararar qofar dakin nata,sai kuma ta daga zaninta ta ciro wayarta tecno keypad. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" hafsat ta fada jikinta yana rawa,tasan yau ta kade daga ita har ganyenta,dama tasan tunda ta fita batayi mata sallama tare da gaya mata inda zata ba yau ba ita ba kwana lafiya cikin gidan,tana jinta tana cewa "Ma'a,kazo gata ta dawo.....oho muku,can ta matse muku" sai taja mugun tsaki ta kashe wayar tana mita. Tunda uwar hafsat ta haifeta bata taba ganin bala'e'iyar mace irin sahura ba,bata gajiya da fada da bala'i,mita kuwa saita kwana tana zarya a tsakar gida tana yinta,dare baya mata kaifi haka rana bata damunta, bala'i idan ta kwan biyu bata yishi ba jinta take kamar mara lafiya,jikin hafsat ya dauki rawa,ta fada dakinta tana laluben kayan da zata sakawa jikinta da suka dan fi wannan kauri,tunda taji tana kiransa a waya lallai yau babu makawa jibga zatasha,babu kuma me qwatarta sai sarki Allaha. Ai hijabi kawai ta gama sawa taji anyi ball da kwanonta dake falon sannan ya fara magana da qarfi "Kina ina munafuka,fito nan nace miki" yayi maganar yana nade danqon dake hannunsa,jikinta na mazari ta fito ta qaraso gabansa ta durqusa,baiyi wata wata ba ya fara lafta mata "Ka tsaya don Allah nayi maka bayani,wallahi ba wani guri naje ba" "Qarya take munafuka,dama ta saba bin maza,kana fita take sanya qafafunta ta fice,saita dai daici kana dab da dawowa sannan takes shigowa gidan nan" . Baiko tsaya jin bayanin bakinta ba ya dinga laftarta,garin qoqarin zillewa kudaden da take maqale dasu suka zubo,sahura ta saki salati,ita da mu'awiya duka suka duqa lokaci daya suna qoqarin dauke kudin,sahura da ta fishi son abun duniya ta rigashi dauka,tahau lissafawa. Dubu tara da dari takwas cif,don tayi kudin mota a ciki "Ka gani ko,tabbacin bin maza ta koma,kaima Allah ya qara maka,ta yaya zaka dauko matar me kudi kace zaka iya riqeta,aiga irinta nan" "Miqon kudaden nan" ya fada yana miqawa sahura hannu,wani kallon banza ta jefeshi dashi "Uban kuturu ma yayi kadan bare na makaho,ka manta kudina daka dinga karba sanda zaka aurota?,ai da haka zan gama fanshe asarata,don ni wallahi mun raba hanya da asara,bana daukarta" daga haka ta soke kudin a brassiere ta fice abinta. Bulalar yayar cikin baqincikin rashin samun nasarar daukar kudin,ya zauna saman kujera yana huci "Tashi ki zazzage jikinki ko akwai sauran wasu kudin" haka ta miqe ta zazzage masa kanta,saidai ko sisi bai fado ba,yaja mugun tsaki "Ki rufewa mutane baki ki daina musu kukan banzan nan" "Wallahi bana bin maza,Allah maawiya sharri takemin" "Dalla rufemin baki,bazan taba yarda ni dake ba...." "Na'am" ya katse maganar yana amsa kiran sahura da taketa qwala masa kan ya fito yaja mata ruwa a rijiya,sai ya fice da sauri kamar wanda zai amsa kiran uwarsa. A wajen ta zube tana kukan baqinciki,dama haka qazafin zina yake da ciwo ?,haka widad taji lokacin data qulla mata sharri?,sau daya tayi mata ita,amma sai gashi ita kuma Allah ya hadata da kishiyar da kullum ta Allah daga fitowar rana zuwa faduwarta saita jefeta da wannan qazafin,saita rushe da kuka tana tuba zuwa ga Allah,tana tuna irin tashin hankalin data saka widad a ciki,bama ita kadai ba,hatta da abbas din,banda kiyayewar ubangiji da zuwa yanzu yana dauke ciwon zuciya ko kuma mummunan hawan jini,tati amfani da irin son da taga yana mata,ta saka an dasa zargi me qarfi a kanta cikin zuciyarsa,sannan ta jefeta da qazafin,ashe duk jifan da kayi wataran kanka zai dawo,bayan saki data rabauta dashi a wancan karon,yanzun kuma gashi tarihi ya maimaita kansa. Duk inda takai ga kaidi da jaraba da bin malamai sahura ta dameta ta shanye,a yanzunma ina taga kudin da zatabi malaman?,abinci ma wataran cikin gidan gagararta yakeyi sai tayi biyayya sannan sahuran zata san mata,tunda kusan fiye da rabin qarfin kula da gidan itace. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 45 Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn Whatsapp 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549 Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 _______________________________ Wanne irin hakki ne haka yake binta?,ta shiga uku,mu'awiya mutumin da yazo mata a matsayin air vice marshall,ashe kurtu ne,kurtun sojoji wanda akewa alfarmar daukarsu a aiki,suke dan aike aike wa manyansu,amma tsabar hakki da kuma ranar girbar abinda aka shuka da take dab da fadawa ta kasa ganewa,tun daga yadda yazo mata,ba wasu cikakkun suturu na alfarma da zasu gaya mata wayeshi,babu wasu securities da akasan dukka masu matsayi irin masa na yawo dasu ko da yaushe ko kuma motoci yaci ta gane amma idonta ya rufe, kwanyarta ta toshe, duka batayi wannan tunanin ba,matsayinsa ke mata kuwwa cikin kunne,ta tuna ranar da ya raina mata hankali yasa ta koma eatery karbar canjinsa,data koma masa da batun sunce ba'a binsu kudi sai yace "Ayyah,inatason tsaidaki,ai kina shiga ina ganin alert,sunmin transfer yanzu yanzu" da haka ya shashantar da maganar,ashe duka ya shirya aurarta ne ya cinye duk abinda ta tara da abinda ta mallaka,don yanzun haka bata da komai,ko wayar hannu tafi qarfinta,sai azabar da take qunsa daga hannunsa da kuma wajen kishiya. Watanni shida baya ummarta ta rasu,aka rabon gadon da mahaifinsu ya bari wanda a baya ba'a raba ba saboda ummar ta hana a taba,kowa kuma yana tsoro haka yayi Shuru,nata kason bata sani ba mu'awiya yayi ruwa yayi tsaki ya saida mata,yan uwanta kuma sukace babu ruwansu,sun dauka da hadin bakinta ne,hatta anty ummee yanxu tana gida tana zaman zawarci da nakasar ido daya da mijin ya tsiyayar mata,bayan ya gane dogon lokacin data dauka tana ha'intarsa tare da sanyashi yana cin zarafin uwar gidansa ta hanyar amfani da kissa,ita kanta yanzu ta zama abun tausayi,tayi nadama tayi nadama har babu iyaka,kissa bata amfaneta da komai ba sai dana sani da wahala a rayuwarta,ya karbe dukka yaransa dake wajenta ya danqawa uwar gidansa,ita kuma tana kulawa dasu cikin amana da kulawa (Babu inda ba na gari,babu kuma side din da babu baragurbi,daga iyayen gidan har amaren,saidai mata muji tsoron Allah,mu yiwa Allah mu yiwa muhammadur rasulillahi S A W mu daina wahalar da junanmu,ke idan zaki shiga gidan me mata kiji tsoron Allah,ki tsarkake niyyarki,ki shiga da niyya me kyau,wallahi wallahi idan kikayi haka bata isa taga bayanki kota tozartaki ko ta samu nasara a kanki ba,indai kinyi da zatin Allah,kiyi haquri da wasu abubuwan ki dauke kai a wasu,amma kada ki yarda da cin xarafi,kema uwargida ki sanyawa zuciyarki haquri,ansani kishi yana da ciwo,amma ki dauka haka taki qaddarar tazo,ki sanya Allah a gabanki,ki toshe kunneki daga 'yan gulma da yan bani na iya masu kawo miki labaran da zasu daga hankalinki,karki yarda ki cutar da ita bayan ta shigo koki qoqarin fiddata daga gidan,kada ki manta ko meye kikayi wallahi ba'a cin bashin Allah,duk wanda yaci sai ya biya ko 'ya'yansa sai sun baya,ko bakya raye kinga kin bar musu musiba,ki kama girmanki karki bada qofar da za'a rainaki,ki yawaita addu'a sai kiga Allah ya kwarjantaki an girmamaki ko ba'a so daga ita har mijin,ki dauki girman da Allah ya baki,Allah ya bamu haquri da juriya gaba daya). Tana tsaka da wannan tunanin cikin tsananin qunci da tashin hankalin yadda rayuwa ke gare gare da ita aka bankado labulen dakin,ta firgita ta miqe ta zauna suna kallon kallo da sahura "Badai kin aurar min miji ba?,wallahi babu ke ba sauran zaman lafiya,ki tashi kije ki wanke masa bangon bandaki,yace bai fita ba,bazai dauki wannan qazantar taki ba" daga wannan ta juya ta fita tana karkada mata mazaunai. Ko second biyar bata qara ba haka ta miqe ta fito tun kafin ya dawo yaci zarafinta,jikinta nata ciwo tako ina saboda dukan da tasha,ta qarewa bandakin kallo,babu qazanta ko dis,kawai tiles din jikin bangonne da bata wanke ba,tunda ta fara zaman aure bata taba yiwa bandaki bautar da takewa bandakin gidan mu'awiya ba,bama bandaki ba,gidan gaba daya,wata muguwar tsafta ce dasu daga shi har sahura,kamar masu aljanun tsafta,sanda tazo da qazantarta taci wahala,kyara tsangwama daga baya harda duka kamar diyarsu,sai ayi shara kusan goma a gidan,bandaki kuwa duk bayan awanni haka zata tashi ta wankeshi tasss,tasha wahala sosai,don bata saba ba,zuwa yanzu kuwa ya zame mata jiki,saidai hausawa sukace ba'a sabo da wahala. Tana farawa sahura ta dawo bayanta ta tsaya tana mata gyara cikin masifa,daga qarshe ta dauko kofin bandakin ta dinga sheqawa hafsat ruwan tana dirzawa,tana sane da gayya take hakan,don kusan rabin jikin hafsat din sai data jiqa mata shi,bacin rai yazo mata iya wuya,amma bata isa tayi magana ba yanzu suyi kamar zasu cinyeta danya ita dame gidan,yanzun zata hau mata gorin gidanta ne tunda filin da ginin gidan duka ita ta gina,shi kuma zai hau fadin eh dole ta bita,saboda gidanta ne kuma a gidan ta sameta,don mu'awiyan kamar qarqashin umarnin sahura yake rayuwa. Tunda hafsat ta fita tabar gidan ta barta cikin mutuwar jiki mamaki da kuma juyayi,lallai duniya rawar 'yammata ce,na gaba ya koma baya,muddin bakaji tsoron Allah ba ka shiga uku duniyarka da lahirarka. Sai zuwa yammaci ta samu ta qwarara jikinta ta shiga kitchen,don bata taba saukewa kanta kula da cikin abbas din duk rintsi indai suna a tare. Ita da aminatu ne,don haka cikin sauri ta kammala komai,tabar musu gyaran kitchen din ita da mimi dake da himmar aiki,sannan ta dawo parlor din gidan zuwa bedroom ta tabbatar komai yana kan order,ta kuma cikashi da qamshi ta yadda zai dace da yammacin sannan ta wuce bedroom dinta ta fidda kayan jikinta ta fada wanka. Ta jima a bayi sannan ta fito daure da towel,kome takeyi cikin mutuwar jiki take yinsa,baya ga lamarin hafsat akwai kasala sosai a jikinta,taja kujera ta zauna gaban mirror tana kallon lallausar farar fatarta daketa sheqi. A nutse aka turo qofar bedroom din,ta cikin mudubi suka hada idanu dashi,kamar an manne idanun nasu guri daya,sai kuma kowa ya janye idonsa daga na dan uwansa yana basarwa. Saman sofa bed ya zube kayan hannunsa,ta jawo mai ta fara shafawa "Sannu da zuwa" ta fada ciki ciki ba tare data kalleshi ba. Dubanta yayi kadan hannuwansa cikin aljihun wandonsa,kamar zai magana sai ya fasa ya amsa mata da yawwa,ya juya kadan ya fara cire kayan jikinshi. Mamaki ya kamata ganin yadda yau ya yada zango a dakinta,neman rigima ne ko kuwa?,daya gama din yaja towel ya daura saman gajeran wandon jikinsa daya tsaya masa iya cinya. A bayanta ya tsaya,ya saka hannunsa ta gefen fuskarta ya shafi wuyanta zuwa fuskarta da zummar jin ko da zazzabin a jikinta? "Alhamdulillah" ya furta qasa qasa harda sakin ajiyar zuciya,sai ya taka ya wuce bandakin,ta bishi da satar kallo,har sai da ya shige sannan ta dauke idanunta,ta saki ajiyar zuciya saita maida man shafawan nata saman madubin kawai ta sanya hannuwanta dukka biyun tayi tagumi. Komai ya tsaye nata a rai,da alama wannan karon abbas din ya fita fushi,hankalinta sam ba'a kwance yake ba,sai yanzu ta sake ganowa azabtar da miji ko sanyashi cikin baqinciki ko yaushe na iya jefa mace cikin jarrabawa,sai taji qwalla ta cika mata idanu,taji kuma ta damu sosai da fadan nasu,wanda bata taba damuwa kamar yanzu ba,don a baya tana ganin kawai wahala zata sha cikin dake jikinta. Sanda ya fito a haka ya sameta,sai ya dauke kansa kamar bai gani ba,duk da qasan Zuciyarsa shima cike take da damuwar fadansu,to amma kuma ya koyi darasi daga zamansa da hafsat,ba ko yaushe kake barin mace da zabin kanta ba,hakanan bako yaushe kake barin mace tayi abinda takeso ko kuma abinda yayi mata suger ba. Yadda ya kauda kai kamar bai kula da taguminta da qwallar dake cikin qwayar idanunta ba sai ya sake sanyaya mata jiki,ta gaza daurewa,sai kawai ta miqe tsaye da sassarfa ta nufeshi,ta fada jikinsa sanda yake ware towel din jikinsa ta ruqunqumeshi. Cak wutarsa ta dauke,saboda tayi masa ba zata,uwa uba kuma yadda fatarta me santsi da laushi ta manne a jikinsa,sai ya gaza ci gaba da riqon towel din ya sakeshi ya fadi a qasa, yasa hannu ya tarbeta cikin jikinsa da kyau amma kuma cikin dakakkiyar murya da kuma basarwa yace "Meye hakan?" Muryarsa na danson yin rawa yana qoqarin daidaitata "Kayi haquri don Allah uncle,wallahi bazan sake ba" "Laifin me kikayi?,ba haka kikeso ba?,so nake dama na gama shiryawa yanzu ina yin sallar isha'i muje a zubar din,kinga nan da next year na auro wata meson haihuwar harta haifamin babies" ji tayi maganar tasa ta soketa sosai,sai kawai ta kasa riqe kanta ta sakar masa kuka sosai tana kwantar da saman qirjinsa hadi da rungumeshi da kyau cikin jikinta tana cewa "Na tuba Allah bazan qara ba" sautin muryarta kawai yana sanya masa nutsuwa,wani bangaren kuma yana sakashi yaji ya buqatu da yawa da ita,sai ya dinga lumshe idanunsa yana jin yadda yanayinsa ke canzawa,saboda sautin kukantan sai ya zame masa kamar fami cikin kunnuwansa da kanta dake kwance a allon kafadarsa. "Ka yafemin don Allah" ta fadi tana qoqarin zamewa ta duqa,yayi hanzarin tattarota zuwa jikinsa,don ko daya bayason ta matsa daga jikin nasa,dumin jikinta ya masifar yiwa jikinsa dadi "Na yafe miki,na yafe miki har abada,but don Allah.....karki sake zancen zakiyi abortion,kalma ce me muni,don zaman aure mukeyi ba dadiro ba,inason kowanne qwayar halitta data fita daga jikina ta bayar da d'a,ko ana ciki sau goma nine ubansa,kuma inaso" ya fadi yana kallon tsakiyar qwayar idanunta ciken mayen so da qauna. *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 46 *_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_* *LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete* *GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA* _kama daga kan_ Furnitures Decoration Kitchen items & Boutiques _our tittle_ Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot Instagram@ Lifestyle_Nig Facebook@ Lifestyleng Tik tok@ Lifestyle_Nig Delivery nation wide _ku tuntubemu ta wannan number_ 08036414048 *Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah* _______________________________ "Na daina uncle" ta fada tana cusa kanta tsakanin qirjinsa tana shaqo qamshinsa mai kwantar mata da hankali,wani ciki ta samu a wannan karon meson qamshin jikinsa,sai ya saki murmushi yana shafa sumarta "Nima kiyi haquri,nasan kinyi missing jikina ko?" Ba kunya ta gyada kai tana sake cusa fuskarta cikin gargasar dake qirjinsa,tsigar jikinsa ta dinga zubawa,shima haqurinsa yakai qarshe,dama shima din kawai basarwa yakeyi tsahon lokacin,sai ya zura hannunsa ta baya ya kwance towel din jikinta ya sulale ya fadi qasa ta koma kamar yadda yake,ya maidata jikinsa sosai suka zama abu daya,kowannensu ya dauke numfashi na wucin gadi sannan suka zuqoshi da qyar,cikin rawar jiki ya dauketa cak ya wuce da ita saman tsaftataccen gadonta da baya gajiya da kwanciya a kai. Ranar dai sai a dakin sukayi sallar isha'i shi da ita,sunyi kewar juna ba kadan ba shi da ita,sun kuma gane yadda suka azabtar da junansu. Suna gaban madubi yana sharce mata gyara mata gashin kanta kafin ta saka kaya ta kalleshi ta cikin mudubin "Uncle" "Babyn uncle" ya amsa mata softly "Don Allah zaka iya yimin wata alfarma guda daya zuwa biyu?" "Kinki qarfin komai a wajena" ta dauki hair mist dinta ta miqa masa ya soma fesa mata sanann tace "Ka yafewa mummyn mimi don Allah,ta roqeni na roqar mata wannan alfarmar" "Na yafe mata,Allah ya yafemu gaba daya" ya fada kansa tsaye,donshi wani lokacin ma mantawa yakeyi ya taba aurenta,sai idan dalili ya ratso. "Na fadi ta biyun?" "Eheen,ina jinki" ya fadi yana buda mata doguwar rigar da zata sanya "Kasan tsakanin uwa da d'a sai Allah,ta roqeni na gaya maka don Allah ka dinga barinta tana ganin yaran nan....." Kallonta yayi da sauri sannan yace "Wait......wai zuwarmin gida ma takeyi ba tare da na sani ba?" "Relax uncle manaaaaa" ta fadi tana juyowa da sauri cikin wata narkakkiyar shagwaba hadi da zube masa fararen manyan idanunta,sai ya dan lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya "Uhmmmm.....u have all my ears" "Bata taba zuwa ba sai yau,kaima ka sani,tunda duka duka yaushe muka dawo qasar uhummm?" "Naji,ni banaso tana shigomin gida,kada ta cutarmin dake wataran,i will send her the kids duk sanda naga ya dace,ama bance zasu kwana ko daya ba,kada ta qara zuwanmin gida please" ido ta lumshe gami da gyada kai,ita komai ma mamaki yake bata,ta yaya zata samu miji irin abbas indai ba mummunar qaddara ba tayi saken da zai kufce mata?,the best husband ever. Sajjad da sajid ne suka fiddasu don dole,suka zauna dukkansu suda yaran a table mat suna cin abincin cikin wani irin yanayi da zai nun maka kyakkyawar rayuwa da mu'amala ta gari da kuma cikakkiyar tarbiyya da suke samu,kai kanka idan kana wajen sai familyn yayi mugu mugun burgeka. ***********Katafaren gidan da ya zama na daban cikin layin shaqe yake da jama'a,gida ne da ya zama mallakin IG(inspector general of police) ABBAS TURAKI,tako ina kana hangen yadda tun daga layin har zuwa bakin titin dazai shigo dakai ainihin kayin ke shaqe da al'umma da kuma ababen hawa na alfarma,ko ina shaqe yake da jama'a,yadda manyan riguna da kuma fararen kaya keta nuna kansu,na wannan yana wane wancan,da kuma yadda busar algaita ke tashi kadai zai gaya maka cewa wani katafaren daurin aure akeyi. Ta cikin microphone din dake fitowa daga masallacin,kana iya jiyo muryar wani qaqqarfan mutum na cewa "An bawa muhammad yasir matawalle auren Dr raheema(mimi) IG abbas turaki akan sadaki naira dubu dari lakadan ba ajalan ba......eh diya ga shugaban duk wani dan sanda dake nigeria" ya sake bayani cikin kambamawa irin na maroqa. Dai dai lokacin da IG abbas ke zaune daga can wani sashe na masallacin cikin shigar alfarma ta farar shadda da babbar riga me asalin tsadar,fuskarsa cike da wani irin haiba kwarjini da kuma cikar kamala,sanarwar data haifar da wanzuwar murmushi saman nutsatsiyar fuskarsa,ya sauke boyayyr ajiyar zuciya yana godewa Allah da ya fara nuna masa auren diyar cikinsa ta farko. *C I K I N G I D A* Wani kebantaccen falo ne dake da matuqar kimar da ba kowa take bawa damar saka qafarsa a ciki ba,falo ne na musamman da aka tanadeshi saboda hutawar IG,yake kuma samun kulawa qarqashin uwar gida sarautar mata wato hajiya widad,kamar yadda komai na IG din yake qarqashin jagoranci da kulawarta,duk kuwa da ma'aikatan dake gidan. Duk girman falon su biyu ne a ciki,ita da amarya mimi dake lullube cikin wata lafiyyayar alkyabba,hannunta dake dauke da Wani irin lalle yana sanye cikin tafin hannun hajiya widad da yasha lafiyayyen jan lalle da bata rabo dashi,wadda tana zaune ne a gabanta suna fuskantar juna,tana karanto mata wasu addu'o'i tana maimaitawa. Ta dauketa ne daga cikin taron hayaniyar jama'ar saboda yadda tunda satin bikin ya kama take fama da koke koke,ita batason tafiya tabar maami,ita ba zata je ba,hankalinta na sake tashi idan ta tuna a yau zatabar qasarta ta haihuwa,zata tafi wata uwa duniyar zaman aure ita da mijin da Allah ya bata wato muhammad yasir. Sai data gama karanta addu'o'in kaf yadda maamin tata ta karanta mata,sai suka hada ido,widad tayi qoqarin danne raunin zuciyarta don kada ta karya ma mimi qwarin gwiwar data samu "Basai nace miki komai ba mimi,bani da haufi a kanki,kowanne d'a namiji zaki iya zaman aure dashi,ki kuma mallaki zuciya da hankalinsa babu boka ba malam" kai mimi ta jinjina,ita shaidace yadda maamin nasu ke tafiyar da mahaifinsu,koke 'ya mace akewa haka sai an samu kanki fiye da zato,wata irin macace da batasan ya zata fasaltata ba,a taqaice ta zame mata wata role model dinta,tana kuma alfahari da ita,hakanan tana kiranta da uwa a duk inda ta shiga a duniya,maamin ta zamewa rayuwarsa alkhairi,dukkan mutumin da ya shigo rayuwarsu daga baya yana mata kallon mahaifiyarsu ce data tsugunna ta haifesu,ta basu abinda dukka uwa ke bawa yaranta,harma abinda wasu uwayen suka kasa bawa yaran nasu,koda wasa bakinta bai taba kiran widad a matsayin uwar riqo ba bare wani suna na kishiyar uwa,kullum kallon mahaifiya suke mata,duk da sunsan asalin wadda ta haifesun,amma ko ita kullum gaya musu takeyi widad dince babarsu,itakam kawao naqudarsu tayi ta kawosu duniya,amma idan suna neman uwa itace. Zamewa tayi ta tsugunna gabanta "Maami ki yafemin don Allah tsahon zamanmu idan na taba bata miki...." Da sauri ta kama kafadunta ta dagota ta zaunar da ita sosai "Bakiyimin komai ba mimi iya zamana daku,kun riqeni kamar mahaifiyarku,saidai nan gaba zakiyimin laifin" da sauri ta daga kai ta dubeta,saita sakar mata murmushi tana jinjina kai "Eh,muddin baki zauna lafiya gidan mijinki ba,muddin bakiyi haquri dashi ba,muddin ya kawo qararki gida ya zamana kece da laifi" "Bazan miki laifi ba kuwa har abada maami,saidai in har ajizanci irin na dan adam" ta fada kuka na qwace mata,idan batayi zaman aure bama ai bata yiwa maaminta adalci ba,ta basu dukkan misalai na rayuwa da zamantakewa a baki da kuma a aikace,su shaida ne sun gani. Juriya da jarumtar nan tata ce kawai ta hanata kuka,tayi qoqari ta saukar da mimi daga kukan da takesonyi tana tsokanarta,dai dai sanda khadijatou (diya mace qwaya daya da widad din ta haifa qanwa ga mimi) taturo qofar a hankali tana baza ido "Na shigo maami?" Ta fada a dan shagwabe tana leqo da kanta "Meye haka kamar munafuka?,shigo ki rufen qofa banason wancan me zuciyar matan(affan) yasan muna ciki yazo su hadu suyita ma mutane kuka kamar cewa akayi idan ta tafi ba zata dawo ba" murmushin yaqe khadijatou kawai tayi,don itama daurewa kawai takeyi,anty mimin she's the part of their lives,ta iya tafiya da qannenta cikin kulawa da qauna,bata fada amma ta iya hukunci,ta iya wasa da dariya amma idan gyara yazo babu wannan wasan,dukkansu sun dauketa kaman abokiyar wasansu,amma kuma suna girmamata sosai,itama ta iya zama da kowa a cikinsu da halinsa,sun taso da shaquwa da qaunar junansu qwarai,ba zaka taba cewa ga wadanda suke uwa daya uba daya ba,yanzun haka khadijatou tafi nawwara jin tafiyar mimin,har gwara yusra ma,itama duk da haka affan ya fita rauni,saboda anty mimin abokiyar sirrinsa ce,kuma abokiyar gulmarsa,sai mimin taji abunsa maami widad bataji ba. "Wai dangin angon sun sakeyin tuni,sha biyu zasu wuce airport din,jirgi qarfe uku zasu bi" ta fada qasa qasa tana satar kallon anty mimin nasu,kai widad ta jinjina "Yayi gamu nan" a sanyaye khadijatou din ta juya ta fice tana matse qwallarta. Hannun mimi maami widad ta riqe cikin nata, suka ratsa falon suka fita ta qofar baya suka wuce kai tsaye suka sashen da aka sauki mummy hafsatu da danginta. Da sallama ta shiga matsakaicin falon sashen,mummy hafsatu na zaune saman kujerun falon,sanye da wani lace wanda widad dince ta dinka mata shi da kudinta,tace koda bataci arziqin abbas na kai tsaye ba tunda tana da igiyar auren wani a kanta ba,amma zataci arziqi sa darajar yaranta su mimi. Da sallama ta shiga,hafsat da dangin hafsat din da suke tare da ita suka fara yiwa widad din sannu,don ko maqiyinta ya yaba mata,yaga yadda ta kasa tsaye ta kasa zaune kamar diyar data tsugunna ta haifa take aurarwa. *_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_* *LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete* *GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA* _kama daga kan_ Furnitures Decoration Kitchen items & Boutiques _our tittle_ Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot Instagram@ Lifestyle_Nig Facebook@ Lifestyleng Tik tok@ Lifestyle_Nig Delivery nation wide _ku tuntubemu ta wannan number_ 08036414048 *Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah* *H U G U M A* *Arewabooks:Huguma* *_A RUBUCE TAKE_* (K'addarata) Part 02 Page 47 END *_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_* *LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete* *GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA* _kama daga kan_ Furnitures Decoration Kitchen items & Boutiques _our tittle_ Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot Instagram@ Lifestyle_Nig Facebook@ Lifestyleng Tik tok@ Lifestyle_Nig Delivery nation wide _ku tuntubemu ta wannan number_ 08036414048 *Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah* _________________________________ Gaban hafsat taje ta tsugunnar da mimin sannan ta zauna daga gefe "Mummyn mimi,ga mimi tazo neman albarka,yau dai Allah yayi zata tafi nata gidan,sai ayi mata sauran nasiha a kuma saka mata albarka" hawaye hafsat din ta fara sharewa,farinciki ne fal zuciyarta na samun uwar riqo ta gari da sukayi,ta tabbatar inda a hannunta suke babu lallai mimi din ma ta samu miji irin muhammad yasir,wanda ba abinda ya fara burgeshi da mimi din sai tarbiyyarta da kuma nutsuwarta,shine babban abinda ya fara jan hankalinsa "Aikin gama gaya mata komai,nikam babu abinda yayi saura da zan gaya mata wanda baki gaya nata ba, abinda zata samu daga bakinki yafi wanda zataji daga gareni,abu daya zan gaya mata shine,tayi koyi dake,tayi koyi dake,tayi koyi dake,don kin zamewa rayuwata alkhairi,kin maida yarana abun kwantace abun sha'awa,kin gyatta tawa rayuwar nima a yanzu na dace da mijin da yasan darajata,kin rabani da mu'awiya,Allah ya hadani da mudassir kin kuma tsayawa rayuwata da jari da sana'a,wanda yayi maka wannan me zakace dashi?" "Babu...babu" shine amsar da yan uwanta da a yanzun suke zumunci ta kuma.kamasu da amana irinsu anty uwani amsar da suka bayar kenan,a yanzun suta riqe ta watsar da irinsu anty ummee duk da suma jikin ta qaura yayi la'asar, rayuwa ta gama karanta musu nata karatun. "Allah ya albarkaci rayuwarki,ya baki ikon yin koyi da babarki widad" shine maganar hafsat na qarshe,akayi addu'a sosai sannan suka miqe don sadata da dangin banbanta su gwaggwo mero sukayi sallama. Sanda akaxo sanyata a mota don su wuce kasa tsaiwa gurin widad tayi,don dukka dauriyarta ta qare,yaran duka affan sajjad sajid khadijatou nawwara yusra al'ameen harda auta fadil kuka sukeyi,sun riqeta kyam sai da IG yazo ya tsawatar musu yana hararar affan "Kai dai kam anyi yaayan banza,ita kanta yanzun mimi din ba kaine yayanta ba?" Akasa dariya gaba daya,sai affan din ya fara ciccijewa kuma yana qoqarin maida qwallar data cika masa ido,ya waiwaya gasu sajjad, identical twins masu kama daya "Ku kuma mage da bera.......kun gama cakar da ita sai yau kukasan yaaya mimin taku ce?, nawwara harda ke?,ranar fa ina jinki kina cewa gwara ta tafi ta barki ki shaqata,ba wanda zanwa jaje ma sai hadizatu" yusra ta yunquro "Daddy nifa..."kafin ya bata amsa al'ameen ma yace "Nima daddy" duk sai suka bawa kowa dariya,kowa so yake ya nuna mimin tashi ce,shi kansa IG a sannan qarfin hali da dauriya kawai yakeyi. Kusan duka motocin gidan aka dauka yiwa mimi rakiya airport,duk titin da suka ratsa sai ansan 'yar IG ce zata wuce,don qarqashin security suke har suka isa. Sai da suka isa din IG abbas ya juya ya juya baiga widad ba,ya saki murmushi qasan ransa,yasan tana can tana kukan data ci masa alwashin ba zatayi ba,basu bar airport din ba sai da jirginsu mimi ya tashi sannan kuma sukayo gida. Sanda ya dawo ya dinga bulayin nemanta cikin gidan amma bai ganta ba,daga qarshe acan part dinsa cikin qawataccen bedroom dinsa ya cimmata,ta gama kukan nata ta wanke fuskarta,tana tsaye gaban madubinsa tana laluben powder da takan ajjiye zata shafa. Sunan hada ido tayi saurin janye idanun nata,ta wani hade rai tasha mur,ita lallai kada yace ta karaya sai da tayi kukan,dariya ta qwace masa ba tare da ya shirya ba,dariyar tasa ta qara raunata zuciyarta,yazo bayanta ta tsaya yana duban qwayar idanunta,sai kawai ta sakar masa kukan shagwaba tana fadawa jikinsa,shagwabar nan da har yau ba abinda ta rage masa a cikinta,bata ganin girmanta idan tana tare dashi,kamar yadda bata ganin girma da shekarun abbas din,har yau tana ganin kamar jiya jiya suka hadu,kamar jiya jiya aka daura musu aure,shi dinma kullum kallonta yake a mitsitsiyar widad din nan,shagwababbiyar ummu,mai yawan tsoro wauta da sakalci. Ya zare babbar rigarsa ya ajjiye gefan gado yana murmushi,ya sanya hannuwansa duka ya ya lullubeta cikin jikinsa,ya sani daman,ba zata iya jura ba,kuma duk duniya a yanzu shi yafi kowa iya lallashinta,yadan hura mata iska a fuska kadan yana cewa "Ai dama na sani,you can't take it......ke kuma da son yara,ai dama na shirya aikin lallashi" sai da yaga kamar kukan bazai tsaya ba sanann suka zauna,ya kama dukka hannayenta yana bata baki,daga qarshe ta buge da murmushi cikin jin kunya tana boye fuskarta saboda wata kalma da ya gaya mata,ya miqe shima yana dariya "Nifa madam aiki yayi kira,ina tunanin nima yau da dare zanbi jirgi na koma abuja,ki taimakeni ki sallami baqinki kiyi qoqari ki biyoni,bana jin dadin gidan sam idan baki kusa" ta riga data saba,duk inda abbas din zashi sai ya ganta a gefansa hankalinsa yake kwanciya,duk inda zashi a nan nigeria ko a waje sai ya tafi da ita,tun tana zolayarsa harta gane haka tsarinsa yake,a jininsa qaunarta take,hafsat ta kasa fuskantar sa tun farko akan irin wannan tsarin nasa abinda ya fara kawo musu matsaloli kenan tun yana qaramin dan sandansa ana yawan masa musayar garuruwan aiki,shi mutum ne dakeson ko yaushe yaga yana tare da iyalinsa,bawai kasancewa ta auratayya ba, a'ah, at least ya dawo daga duk inda yake ya shigo gida ko masauki ya tarar dake,ita data fuskanci hakan sai ta bashi dukka rayuwa da lokacinta,shi kuma ya sakar mata ragamarsa. Bashi da tsanani ko takura sam,mutum ne mai wani irin sauqin hali kawaici da kuma yawan bada uzuri,shi yasa idan kaga yadda sukeyi da 'ya'yansa da yadda yake mu'amala cikin gidansa abun zai daure maka kai sosai,ba zakace shine wannan namijin zakin IG din ba "Zaki biyonin please?" Ya tambayeta cikin karya murya, dariya taso kamata "Habba uncle.......ka girma fa,yau din nan ka aurar da diya ko ka manta?" Mur yadan sha "Hakane fa,zaki biyonin?" Ya fada yana murtike fuska da murya,dariya ta qwace musu a tare saboda yadda yanayinma sam bai masa kyau ba "Zan biyoka uncle,kusan zuwa anjima dama kowa zai wuce gida,na nesan ma gobe zasu tafi,amma ayimin alfarma zuwa jibi saina taho,zan sauka na duba jikin ummu daga can saimu siya wani ticket din,banason ma mu wuce jibin saboda yara duka zasu koma school suma,banason faashin makaranta" fuskarta ya kama yayi kissing goshinta "Na gode,Allah yayi miki albarka,yadda kika kula dani da yarana da sauran dukka dangina,ina roqa miki aljanna madaukakiya tun daga duniya har zuwa lahira" murmushi mai sanyi ya qwace mata,ta kama button din rigarsa tana dan wasa dashi "Kaine sirrin komai uncle,ka cancani fiye da haka,don ka zamewa rayuwata wani alkhairi,tun bansan meye rayuwa ba har na santa,Allah ya dawwamar da farinciki a rayuwarka yaci gaba da yi maka jagora,ya doraka saman maqiyanka,ya tabbatar da nasara a dukka rayuwarka" "Ameen summa ameen wuddu na" ya fada yana jifanta da wani sassanyan kallo daya sanyata jin kunyarsa,saita fice tana cewa bari ya hado masa abinci,ta tabbatar jama'a basu barshi yaci ba,daga nan kuma ta duba komai ta samu yana tafiya yadda ya kamata,su amina su nujood Aafiya na'eema da muneera na kula da komai,don haka ta wuce kitchen ta dauki zababbun warmers din IG ta soma shirya masa abincin da kanta. *Komai yayi farko yana da qarshe!!* _Alhamdulillah,Alhamdulillah,Alhamdulillah,dukkan godiya ta tabbata ga Alla madaukakin sarki me kowa me komai daya aramin rai da lafiya har na kawo qarshen labarin A RUBUCE TAKE_ _thank you arewabooks followers for being with me all this while from beginning to end_🥰🥰👏🏽 _Godiya ga tarin masoya mabiya daga kowanne lungu da saqo na media,musamman wadanda basa gajiya da kasancewa tare damu da siyan rubututtukan zafafa biyar ta manhajar watsapp,Allah ya qara danqon zumunci da qauna mara yankewa,ubangiji ya kula da lamarinku_ *Abinda muka rubuta dai dai Allah ya bamu lada,wanda muka kuskure kuma ajizanci ne irin na dan adam,muna fatan Allah zai gafarta mana,ya yafe mana kusakurenmu mu daku gaba daya,sai Allah ya sake sadamu a rubutu na gaba da wasu ZAFAFAN LABARAN idan ubangiji ya bamu aron rai da lafiya* *Na gode na gode na gode* @team zafafabiyar _subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'atubu ilaika_👏🏽👏🏽