*RAYUWAR MAKARANTA* *© Zahra Royal Star* THRILLER *K'AUYEN RIMAYE, GOVERNMENT SECONDARY SCHOOL RIMAYE KATSINA STATES NIGERIA.* "Hauwa! na ce ki duk'a k'asa ko?" Kallonsa ta d'anyi tana tab'e baki cike da jin tsanar Mlm Aliyun, tabi shi da harara k'asa-k'asa. A hankali tayi k'asa, tasa gwaiwowinta a k'asan. Muryarsa cike da b'acin rai ya kai dubansa ga D'alibansa y'an mata dake wajan, K'awayen Hauwa ya ce "kuma ku duk'a k'asa marassa jin kawaii" K'unk'uni suka kama yi kamar baza su duk'a ba, sai kuma suka kai kasa kamar yacce Hauwa tayi, sun kai su had'u. Ya dube su yana d'aga wata y'ar k'aramar waya dake rik'e a hannunsa. Kamin a hankali ya ce "wacece mai wayar nan a cikinku?, wato an hana zuwa da kowacce waya, amma tsabar bakwai jin magana shine aka kama ke Hauwa da ita kina jin wak'a Mlm na cikin aji?, an tabbayeki kin ce wai ba taki ba ce, ta uban wacece to?". Murgud'a baki Hauwa tayi kanta a k'asa tana jin zuciyarta na bak'i tsabar yadda sauran Malamai ke binsu da kallo wa'inda ke cikin Office d'in. A hankali kamar bata son magana ta ce "eh Mlm ba tawa ba ce ta wata Aunty na ce, ta ban ajiya" Zai sake magana Malama Rahma ta shigo Office d'in. Kamar kullum taci uban gayu na kece raini sai k'amshi ke tashi a jikinta, wani matsiyacin leshi tasa wadda yaji d'inkin gayu mai tsadar gaske, ta yafa wani mayafi wadda yayi dai-dai da kalar leshin. A hankali take taku dai-dai tana wata yanga kai kace bata son taka k'asa ne. Gaba d'aya Malaman dake a wajan, sai kallo ya koma kanta bakinsu kamar zai tsage, kowa sai binta yake da sannu da zuwa, Kai ka ce zata raba masu Lada ne idan sunce sannu d'in. Itama cike da yanga take amsawa tana washe baki. Su Hauwa dake d'uke a k'asa wani kalar kallo na tsana suke bin Mlm Rahma dashi, kai daka kalli yanayin irin kallon da suke jefa mata zaka san na tsantsar tsana ne. Zama Mlm Rahma tayi akan wani table tana ba wasu al'majirai umarnin cewa. "Kuje ku shigo da kululin nan gaba d'aya please, sai ku aje su a inda ya dace" Amsawa sukai suka juya. Mlm Aliyu dake ta jefanta da murmushi ya ce "Ohh Hajiya yauma abincin akayo mana, ai kina taimakon mu da kike mana abincin saidawar nan, dama sai mun fita cikin gari muke samu muci" Murmushi ta sakar masa wadda yaji kamar ya tashi ya taka rawa tsabar farin ciki. Ta ce "kai kam Mlm Aliyu kullum saika mai-maita wannan maganar, ai shi yasa domin ku nake yi, harma da d'aliban wadda yaji zai iya saya" Tab'e baki Hauwa tayi, ta tsaki wani tsaki wadda yajawo hankali jama'ar wajan. "Wannan sakarkarun miye suke a nan kuma?" Mlm Rahma ta fad'a tana nuna su Hauwa. Hauwa ta had'e wani miyau ji take kamar ta shak'o wuyan Mlm Rahma. "Wallahi fa wai waya ce suka zo da ita shine na taho dasu nan" Cewar Mlm Aliyu. Kallon banza ta jefa ma su Hauwa tana sake cewa "to miye kuke jira dasu ku amshe wayar mana ku yanke masu hukunci dai-dai da abunda suka aikata. Wai tsayama wayar wace a cikinsu a nan?" Mlm Aliyu ya ce "waifa duk abun nan wayar y'ar uwar Hauwa ce ta bata ita wai, kinji shashanci tana babba" "Ohhhoo wannan yarinyar wai wacce ke SS3" Mlm Rahma ta tabbaya Kai tsaye. Mlm Saminu dake kusa da ita shima ya hamshe da cewa "Kware fa ita ce, ai nasan yarinyar ba ita ce wacce kullum take tara maza a bakin wonder kujerar da take zama, but idan aure take so ke kece ayi mata mana, tazo tana tara mana Maza bata da aiki sai haka" Wani tuk'uk'in bak'in ciki ne ya turnuk'e Hauwa kallon Mlm Saminu take, yauce ta k'ara jin tsanar wani Mlm bayan Mlm Aliyu da Mlm Rahma. Can suka ji muryar Mlm Rahma na cewa "to sakarci kenan ma, idan son maza zatai danmi yasa ta fara karatu, su sanar da iyayanta aure take so mana" Kamin su sake magana Hauwa tsabar b'acin rai ta kalli Mlm Aliyu tana k'ok'arin magana ya rigata da cewa. "Zaku iya tashi kuje sai wayar nan tayi sati kamin na baku ita. Wai ku bakwai jin wahalar rik'e k'aramar waya ne?". Banza Hauwa tayi masa tana tashi harta juya baya kawai taji muryar Mlm Rahma akanta. "Kee tsaya na ce" Juyowa gaba d'aya Hauwa tayi tana duban Mlm Rahma data taso inda suke. Kallonta tayi kallo irin na rainin wayo da wulakanci kamin ta ce "Kee ban hana yo acuci Maza a school d'in nan ba?". Hauwa kallon takaici take bin Mlm Rahma dashi, kamin a hankali ta kai hannunta ta tab'a k'eyarta dake d'aure da gashi babu abunda tasa ta d'aure shi bare tayi acuci Maza dashi, tsabar gashin ne kawai tasa ta nannad'e shine sai ya bada kamar tayi acuci Maza. Ganin rainin wayon yarinyar yayi yawa Mlm Rahma zatai magana rai a b'ace Hauwa ta rigata cewa "Ni ai ba acuci Maza nayi ba" Tana gama fad'ar haka zata juya domin barin wajan taji Mlm Rahma ta kamo mata Hijab, da k'arfi har Hijabin na shak'e mata wuya. Dawowa baya tayi taga-taga kamar zata fad'i Mlm Rahma na cewa "Keee dan Ubanki har ni zanyi magana ban gama ba ki wani juya ki tafi?, tsabar dama kun raina mutane. Ki cire acucin nan na ce idan ba haka ba kuma inci Ubanki a nan wajan hmmmmm" Ko ci kanki Hauwa bata ce ba, kawai ta tsaya ne tana kallonta, Mlm Rahma kuma har yanzu tana rik'e da bak'in Hijabinta. Ganin yarinyar fa y'ar rainin wayo ce ta gidan gaba, yasa Mlm Rahma cike da son yarfa ta da son ci mata mutumci kawai Hauwa batai tsammani ba batai zato ba taji an jawo mata Hijab da mugun k'arfi wadda yasa gaba d'aya Hijab d'in daga kanta ta zame. Gashin kanta ne ya bayyana ta yadda mutanan dake wajan suka zaro ido waje, hatta su Atu K'awayen Hauwa ido suka zaro suna bin Uban gashin Hauwa da kallo, domin duk abotarsu basu tab'a ganin gashin Hauwa a waje ba sai yau. Tsananin yawansa harya zarce yadda basa zato, gashin kan nata har sai da ya sakko k'unk'uminta, yana niyar tab'o mazaunanta, gashi bak'ik'k'irin ga sulb'i kamar irin na k'asar Indiar nan. Wani kalar Mayan kallo Malaman dake wajan suke bin Hauwa dashi. Ita ko Mlm Rahma cike da tsananin hassada dajin haushi, inama ace batai haka ba, gashi duk taja hankalin Malamai sun koma akan y'ar k'ank'anuwar yarinya, ga wata irin tsanar yarinyar daya k'ara cika mata zuciya, bata tab'a tunanin haka zata gani a gashin nata ba, ai tayi zaton bai wuce iya k'eyarta ba, tayi mata hakan ne domin ayi mata dariya kuma ta yarfu a gaban samarin Malaman dake a cikin Office d'in. Ita ko Hauwa kallon Mlm Rahma take cike jin haushi tsantsarsa, sai wani murmushin gefen baki data sakarma Mlm Rahma wadda ta gansa Kuma ta shak'a. Tsabar ta k'ara jan hankalin Malaman Hauwa ta wani juya gashin har tashi sama yake fuskarta ta k'ara fitowa kyakykyawa da ita dama gata da hasken fata irin hasken nan na Fulanin asali. Tasa hannunta ta d'aure gashin nata ta maida abunta cikin Hijab, k'asa-k'asa yadda Mlm Rahma zataji ta take cewa. "Uhum wani ko ya d'auka gashin kowama kamar nashi ne?, gashi kamar hamtar d'an iska......... _____________________ RAYUWAR MAKARANTA. Hmm idan na ce rayuwar makaranta kowacce rayuwa akwai kalar nata k'alubalen, akwai darasi a rayuwar makaranta akwai rayuwar da ake gudanarwa a cikinta wacce baka tab'a mantawa rayuwace mai tsayawa a zuciya, labarin RAYUWAR MAKARANTA ya k'unshi b'angarori da dama, Malama da d'alibai na fuskartar k'alubale, shin wane irin k'alubale ne?, bare akace maka rayuwar secondry wacce d'alibai basu da y'ancin kansu, haka ma Malamai na fuskantar rashin kunya ga d'aliban, shin a tsakaninsu suwa keda laifi?, suwa ke janyo hakan?, ga Malaman ne?, ko ko d'aliban ne?, akwai shiga rai a wannan labarin. Bazance komai ba kai dai mai karantawa kawai ka biyo ni, kasan mai karatu bana rubuta labarin banza wadda baida fad'akarwa da shiga rai, masoya kune zaku bada shaidar Hakan. Find out in RAYUWAR MAKARANTA (LOVE STORY). RAYUWAR MAKARANTA zai fara zuwa maku a sabuwar shekara 2025 insha Allahu. #Zahra Royal Star #Bakatsiniya #Rayuwar Makaranta #Hauwa #Atu #Aunty Sa'adha #Mlm Rahma #Mlm Fiddausi #Mlm Aliyu #Mlm Bahari #Mlm Muhammad #Abdallah *RAYUWAR MAKARANTA* *©Zahra Royal Star* *GOVERNMENT SECONDARY SCHOOL RIMAYE KATSINA STATES NIGERIA* Page 1 A hankali take tafiya tana yi tana kallon shataletalen dogowar hanyar data mik'e wacce zata kaita zuwa school, da a yau zata fara zuwanta, tun bayan gama primarynta. A hankali ta saki wani k'aramin tsaki tana jin haushin Day d'in da aka sata, taso akaita boding school ba wai Day ba, gashi ba k'aramar tafiya suke sha ba kamin su iso school d'in, saboda tayi nesa daga cikin garin nasu, a can k'arshen gari kana gaf fita garin school d'in take. Da yawan d'alibai Maza da Mata wasu a k'asa suke zuwa, wasu kuwa akan Keke suke tahowa, wasu idan y'an gata ne har cikin mota ake kawo su, gashi duk tafiyar daka sha idan kazo k'arfe takwas ta gota, koda da ace da minti biyar tofa saika sha dukan makara. Juyowa tayi jin an dafa ta ana cewa "Hauwa please ki tak'o k'afa dan Allah, kinga na gabanmu har sunyi nisa, ina hangen wa'inda suke gaf shiga school d'in kamar sun had'a da d'an gudu, yanzu haka an fara bugun makara ne please musa k'afa muma ko mun isa, kin san bana son abunda zai tab'a min jiki bare duka" Tsaki Hauwa ta kuma bugawa tana tab'e baki tana cewa "Ke ni fa babu gudun da zanyi wallahi Atu, idan ke zaki iya to Bismillah, haka kawai nifa shi yasa nasu a kaini makarantar kwana wallahi ba wai wannan Day d'in banzar ba" Ta idasa maganar had'e da sakin wani tsakin. Kallonta Atu ta d'anyi tana tafiya da sauri har yanzu, tasa hannunta na dama ta kamo hannun Hauwar tana janta sosai yadda tafiyar taso zata zo d'aya domin taga Hauwa bafa saurin zatai ba, idan ta biye tata tofa yau sai sunsha jifgar makara. "Da alama Hauwa har yanzu baki san micece makarantar kwana ba, ke miye ake a Day school, ai in gaya miki mugunta da bugu da komai ba na kalar azaba tofa tana Makarantar kwana, dan haka banga laifin Abbanki ba daya ce kinyi k'arama ma da kaiki Makarantar kwana, gara a nan idan yaso kika k'ara girma a sadda zamu kai SS 1 mun wuce Boding school d'in" Murgud'a baki Hauwa tayi tana fisge hanunta tana cewa "Kinga cika ni, ai gashi nan ma har sun fara Taran makarar, kuma tunda na shigo Day d'in nan kin san Allah bazanyi wata Boding school ba kuma..... "Innallihi, Hauwa mun shiga uku, kinga dukan da suke yi kuwa, ki gani wayyo Allah" Atu ta katse maganar da Hauwa keyi mata, had'e da nuna mata yadda suke dukan d'alibai duk wadda ya k'araso yanzu. Tsaki Hauwa tayi tana kallon dai-dai bakin inda ake taran makarar, ga Siniyoyi nan manyan school d'in y'an SS3 suna tare duk wadda ya shigo yanzu bugu suke na Innallihi, ba tausayawa, wasu an sasu tsallan kwad'i wasu shara suke a house d'insu. School d'in ta cika tayi maki's amma duk da haka idan ka waiga baya wasu ne ke k'ara tahowa, idan ka dubesu da yawa hankalisu a tashe yake, bare sabbin zuwa, wa'inda suka giga kuwa irin y'an SS2 haka ko a jikinsu, domin ana bugunsu suke tashi su kakkab'e jikinsu, su tafi wasu harda tsakin tsaki. Atu ta kalli Hauwa tana had'iyar miyau tana cewa "Kefa dama ba tsoron bulala kike ba, duk ke kika ja min, Allah daga yau bazan sake jiranki ba, tahowa ta zan rink'a yi, yanzu gashi kinja mana, ni gaskiya sai dai nayi tsallan kwad'o bazan bari a duke ni ba, ko kuma a sani wankin toilet" Ta idasa maganar tana zare ido saboda sun kusa k'araso inda ake bugun makarar, ganin yadda suke hantarar d'alibai had'e da mugun dukan da suke ma Yara, gyeza ce suke sawa mai kauri ga tsawo suke bugun da ita, nanfa hankalin Atu ya sake tashi. Tana gani da Siniyoyi y'an SS3 sun iso koda sun makara wuce kawai suke abunsu, wani ma a nan zai tsaya ya amshi bulala ayi taran makarar dashi. Hauwa ta dubi Atu tana cewa "Allah ya kiyaye ni da wankin toilet daga zuwa na school d'in nan, kin san babu abunda zai hana aljanu shiga jikinka idan kana zuwa toilet d'in makaranta, garama kiyi shara ko su bige ki, amma karki sake a saki wankin toilet ko a saki tsallan kwad'o na gaya miki, tunda ke matsoraciya ce, daki tsaya ayi miki bulalar tafi " Hauwa ta idasa maganar tana k'arasawa dai-dai inda wani Siniyo yake yana bugun wasu, ana gama masu ta duk'a ya fara zafga mata bulala, wani bugu daya kai mata saida da runtse idonta da k'arfi saboda taji bugun har tsakiyar bayanta. Yana gama mata ta tashi idonta sunyi jawur ji take kamar ta shak'e masa wuya shi kam bai ma san tana yi ba, jifgar wasu kawai yake idonsa a rufe. Tashi kawai Hauwa tayi tana kallon Atu da aka sasu tsallan kwad'o abunda take mata gudu kenan. Wani dogon tsaki ta ja wadda yasa wata y'ar SS3 ta juyo tana dubanta, a wulakanci take kallonta tana cewa "Kee tsaya" Tsayawa Hauwa tayi gabanta na d'an fad'uwa. Dakewa tayi tana kallonta itama, ganin irin duban da take mata Can ta ce "Ubanwa kike ma tsaki a nan wajan dan Ubanki?" Wani abu mai d'aci Hauwa ta had'i a mak'oshinta jin yadda ta zagar mata uba cikin isgilanci Kuma" Saukar maganarta ta k'ara ji tana sake cewa "Ba magana nake miki ba, kun raina mutane ke y'ar k'arama dake duka ba yau ne kuka baro primary ba, to bari kiji na gaya miki a nan ba'a mana haka, uban mutum zamuci wallahi, dan har yanzu yarintar primary bata sake ku ba, duk'a na ce dan Ubanki" Kowa na wajan kallonsu yake amma babu wadda yayi gigin mata magana, a yadda take zagin Hauwa son ranta. Hatta Malamai suna zuwa su wuce amma ko a jikinsu daga ganin alama ma suke ba Siniyas d'in Okay d'in cin uban yaro ko waye shi. Tana k'arasowa gaban Hauwa ta amshi bulala ta fara jifgar Hauwa baji ba gani dan har hijab d'in Hauwa na dagewa sama amma haka ta rink'a bugunta kamar ta sami Jaka. Sai da wata K'awarta tazo ta amshe bulalar dake hannunta tana cewa "Haba Lamratu ki barta haka mana, kefa muguwa ce dama wallahi, yara da yawa suna kuka dake idan kika kamasu bakya masu ta sauk'i" Tsaki Lamratu ta saki tana hararar Hauwa dake d'uke a k'asa tana mata kallon banza. Ta ce "dalla can tashi ki bar nan wajan, karki sake wani laifi yasa mu k'ara gamo da ke shashanci banza kawai" Tashi Hauwa tayi idonta sunyi ja sai jan ajiyar zuciya take tana k'ara tausar zuciyarta, da zata biye ta zuciyarta da yanzu wata maganar ake ba wannan ba. A hankali Lamratu ta juyo wajan Hindatu tana d'an harararta tana cewa "Kefa shi yasa ba'a son zuwa dake wajan taran makarar nan, miye haka yanzu Fisbilillahi? Karfa kisa Yara su fara raina ni wallahi, domin zaki sa na tsani yaro yayita shan jifgar banza a waje na wallahi, idan bazaki iya gani ba ki zaman ki a class mana please" Dariya kawai Hindatu ta saki tana cewa "Kin manta da acan nake zaune kece kika taso ne dole saina raka ki kinyi bugun makara, haka kawai Allah kuna bani haushi wannan muguntar da kuke ma yaran mutane, ku guji ranar da iyayan Yara zasu kawo k'arar ku wallahi" "Ahaye, yo ai da alama kin manta irin buguwar da mukasha muma ko?, har kin manta irin iftila'in rayuwar da muka shiga a school d'in nan, ai yanzu ma ana masu da sauk'i wallahi, ai yanzu banza suke sha, yo a lokacin mu mun ma isa na gaba da kai yana magana ka kalli tsakiyar idonsa, ranar baka ci ubanka ba harda ma uwar. To dan haka kinga ki barmu muma mu bigi banza dan wallahi saina rama abunda akai mana, duk da nasan bazamu tab'a rama irin abunda akai mana ba, sai dai mu kwatan ta kawai" Dariya kawai Hindatu tayi tana samun waje ta zauna akan wani dutse tana kallon yadda ake dukan Yara. "Washhh Allah na wayyo na k'afata" Cewar Atu tana zama d'aya daga cikin kujerun class d'in nasu bayan an gama aikatuwa an shigo aji, d'alibai sai shigowa suke suna zamun kujerunsu suna zama kamin kuma Malami ya shigo. D'an matsawa Hauwa tayi har yanzu ranta babu dad'i akan abunda akai masu d'azo ta ce "Ga waje nan ki zauna na zab'ar mana gaba-gaba bana son zama baya kin sani" D'an yamutse fuska tayi da kyar ta zauna tana dafe cinyoyinta tana cewa "Gaskiya dole mu sake waje bana son zama a gaba kin sani nima, saboda komai za'a fara damu za'a fara, ni kuma gaskiya bana so, kina ganin yadda y'an SS3 nan suke bafa mutumci suka cika ba, har cikin aji suke bi su bigi mutum son ransu ko Malami idan anyi masa laifi ya fara daga ta kanmu to bazata sab'o ba gaskiya ki duba magana ta" "Eh kuma Atu kina da gaskiya fa, tashi mu koma na bayan k'arshe. Amma ma wai miye kiketa yatsine baki kina tafiya a tale da kyar?" "Hmmm wai kin manta tsallan kwad'o aka sani a wajan taran makara ne?, to shine jikina kemin ciwo fa" Tashi sukai a tare suna tafiya bayan class d'in domin samun wani wajan zaman, suna tafe Hauwa na tikar dariya tana cewa "Sai da na gaya miki karki sake a saki tsallan kwad'o, ai gashi nan tukunna ma yarinya saima gobe jikinki yayi tsami Allah ma yasa ki iya tashi goben" Dai-dai sun iso kujerar baya ta ukun k'arshe suka tsaya, suna duban wasu y'an Yara wa'inda basu kai su ba sun kama kujerar mutum uku ne ko wacce kujera. Atu ta kalle su tana cewa "Kai ku tashi daga nan kuje ga wata can ku zauna, daga yau ta zama tamu wannan kujerar" Wata y'ar figaggiyar yarinyar idonta a tsaye yake ta tashi tana rik'e k'ugunta tana kallon su Hauwa tana cewa "Tabd'i jam, kamar ya mu tashi mu baku waje?, wannan ai mugunta ce da son kai, mune fa muka fara zamanta" Atu zatai magana Hauwa ta d'aga mata hannu tana kallon yarinyar kamin ta ce "Zaku tashi daga kujerar nan ko kuwa, yanzu jikin yarinya yayi tsami, na rantse yadda nake cike da yaushin nan k'ila akanku zan sauk'e shi wallahi" Hauwa ta k'are maganar tana maka masu wata uwar harara, Dole tasa ba shiri suka kwashe jakukunan su suka k'ara gaba suna tafe suna k'unk'uni. Zama Hauwa tayi tana cewa "Kaga y'an banza naga alamar makarantar nan sai ka zama d'an iska marar kunya tukunna zaka zauna lafiya da kowanne shege". Atu zatayi magana Malami ya shigo ajin, gaba d'aya suka mik'e suna gaisar dashi. Bayan sun zauna ya fara gabatar masu da lasin English zai rink'a d'aukarsu had'e da gabatar masu da sunansa Mlm Buhari. Ana cikin Lasin Hauwa ta d'an saki dariya k'asa-k'asa tana ma Atu rad'a a kunne tana cewa "Atu dubi yadda yake koyawa yana wani mik'e hannu yana rangwada kamar wani d'an daudu wallahi, ga iyaye a turancin nasa sai kace Nasara a gari" D'an matsawa kad'an Atu tayi tana magana a hankali tana cewa "Kinga Hauwa babu ruwana karya jiki wallahi, ke naga alama har yanzu bulala bata koya miki hankali ba dan....... "Heeyyy you" Da mugun sauri Atu ta kai dubanta inda Malam Buhari yake tsaye a gaban allo yana kallonsu fuska a murtuke. Wani miyau Atu ta had'e tana magana k'asa-k'asa yadda Hauwa kad'ai zata jita ta ce "Shikenan mun shiga uku yau zamu lallasu wallahi, ko miye ke ke ja mana wallahi Hauwa, na kusa daina zama tare da ke" Tsaki Hauwa taja tana d'an tab'a tana nuna mata inda Mlm Buhari ya nufa. Sauk'e ajiyar zuciya Atu tayi tana kallonsa ashe D'aliban dake kujerar bayansu dasu yake. Suna ji yake cewa "Surutun uban miye kuke min a cikin aji, kuzo ku fice min daga class ba'a min surutu a cikin aji dan uban mutum" Fara masa magiya sukai suna cewa "Dan Allah Malam kayi hakuri wallahi ba surutu muke ba, tabbayata take kawai na bata amsa kayi hakuri dan Allah" "Ku fice min daga class na ce ko?" Sumi-sumi suka fice daga class d'in su uku. Bin bayansu yayi yana cewa "You a nan zaku tsaya ku duk'a k'asa" Kamar zasu fashe masa da kuka suka duk'a suna sake basa hakuri amma ko kallonsu baiyi ba ya koma class d'in ya ci gaba da gabatar da lasin nashi. Yana gaf gamawa lasin d'in Malam Add'au ya biyo ta wajan class d'in ganin Yara a d'uke a k'asa yasa shi biyowa ta wajan. Kallonsu yayi fuska babu wasa ya ce "Kai ubanmi kukayi da aka fito daku waje?" Zasu bada amsa Malam Buhari ya fito yana cewa "Wallahi Malam Add'au surutu suke min a cikin aji, gasu nanma ka d'an lallasa min su kamin na gama lasin d'in nan" Yana fad'ar haka ya koma class d'in su Hauwa na kallon abunda ke faruwa a waje ta window d'in class d'in. Suna ganin yadda Malam Add'au ya zage sai jifgar Yara yake sai da yayi masu bulala goma-goma tukunna yana gamawa ya ce "Ku tashi kunga wannan filin tsakiyar ajin naku ku share min shi tass ya sharu idan baiyi ba kuma zaku k'ara jama kanku wani dukan". Da sauri suka mik'e suna kuka d'aya ce kad'ai batai hawaye ba a cikin su sai idonta dake gaf cika da hawaye. Da azama suka shiga ajin suka d'akko tsintsiyar shararsu suka fito suka fara shara baji ba gani. Bayan Malam Buhari ya fita ajin ya kaure da surutu. Hauwa ta ce "gaskiya wasu Malaman suma akwai mugunta, ki duba ki gani tun d'azo suke sharar wajan can fa da alama wallahi sun jigatu" "Uhmmm ai daga yanzu idan Malam Buhari ya shigo kinga sai kowacce ta kama kanta tayi shuru, ta rufa ma kanta asiri ai, tunda yanzu ansan halinsa ya tsani yana aji kana ma y'ar uwarka magana, kana masa surutun banza" Hauwa zatai magana kenan suka ji ajin yayi wani shuru kamar mutuwa ta gifta da wajan. Da sauri Atu da Hauwa suka kai dubansu a gaban Allo. Ganin y'an SS3 ne suka cika ajin sunkai su biyar Maza biyu mata biyu. A hankali wata daga cikinsu ta ce "Surutun uban mi kuke mana?, kun cika mana kunne da surutu" Shuru akai bamai iya bata amsa. D'ayar ta sake cewa "Ina shugabar class d'in nan take" D'aya daga cikin y'an ajin ta ce "Babu ba'a nad'a ba" Wani namiji daga cikinsu ya nuna wata Binta dake zaune a gaba ya ce "Kee daga yau ke ce shugabar ajin nan, daga yau idan muka zo muka taradda ajin nan ana surutu tofa kin shiga uku domin ko wanne hukunci a kanki zamu d'auka, dan haka da mun fita ki rubuta mana duk wacce tayi surutu a takarda, kin gane?" Binta jikinta na kyarma badan tana son wannan shugabancin da aka bata ba ta amsa da eh. Suna ficewa daga class d'in Binta ta zauna tana fashewa da kuka. K'awarta Fiddausi ta dafata ta ce "Kiyi hakuri yanzu dai ki yago faida ki fara rubutu duk wadda yayi surutu karma ki jama kanki". Hauwa zata mik'e domin zuwa inda su Binta suke Atu ta rik'e mata hannu tana cewa "Kee Hauwa mi kuma zakiyo wajansu?" "Kinga ki cika ni na je na amshi faifar ni na rubuta mata, tunda naga ita da alama bazata iya ba" "A'a fa Hauwa irin haka fa ne yasa na ce mu dawo baya da zama, da yanzu muna gaban da k'ila ni ce ko ke ce za'a nuna a matsayin shugabar class d'in nan, haka kawaii a d'ora maka nauyin da bazaka iya dashi ba, duk irin haka nake gudu" Badan Hauwa taso ba ta koma ta zauna, tana hararar Atu tana mitar tana shigar mata hanci a kudundine wallahi. Atu ta ce "eh na dai ji komi zaki ce, ki ce dai saura kije kiyi abun ya k'are kanmu, dama sai tsaya iya ke kad'ai ne to" Su Binta suna d'akko Faifa ta mik'e a tana cewa "To wallahi yanzu zan fara rubuta masu surutu duk wadda ya bari sunansa ya shiga a nan cikin faifar babu ruwana nayi gargad'i karma ka ce na fara ban sanar ba" Tana gama fad'ar haka ajin yayi shuru, sai marassa jin ajin wasu dake magana k'asa-k'asa suna rad'a duk tana kallon kowa tana halkance da kowa, duk wadda ta ci karo da bakinsa na motsi rubutasa take kawai........ *RAYUWAR MAKARANTA* *©Zahra Royal Star* Page 2 A hankali aka buga k'araurawar fita break, gaba d'aya ajin ne ya d'auki surutu kowa ya d'auki y'ar jakar sa had'e da kular abincin sa yayi waje. Hauwa ta kalli y'an bayansu dana gabansu ta ce "Sorry amma ya sunanku ne?" Harara Atu ta makama Hauwa tana k'ok'arin janta su fice waje amma ta dake tana kallon wa'inda ta tabbaya. Murmushi suka saki, d'aya daga cikinsu ta ce "Ni sunana Hadiza, wannan kuma Ammama sai kuma Fatee" "Masha Allah, ko zamu iya zama K'awaye" "Eh man babu damuwa ai, kuzo mu fita waje, inda muke zama muci abinci, naga kamar yau kuka fara zuwa ku hakane?" Murmushi Hauwa ta saki tana cewa "Eh yau muka fara zuwa" Ficewa sukai a tare suna raha kamar sun dad'e da sanin juna, ba abunda Atu keyi sai kunbure-kunbure danmi Hauwa zata jawo masu wasu a cikinsu. Zama sukai akan wasu duwatsu su duka. Atu na kallon yanayin makarantar kota ina d'alibai ke wucewa wasu na tafiya gida break, suna bi ta cikin daji su wuce. School d'in akwai girma sosai ta yadda zaka iya fita ta bayanta ta cikin jeji, ka dawo kowa bai sani ba, shi yasa da Malamai suka gane har nan wajan ana zuwa taran makara, saboda wasu y'an iskan school d'in suna biyowa ta cikin daji da safe. Maganar Hauwa ta katse d'an shurun daya gifta jin tana cewa "Wow Hadiza kwad'on tuwo kikazo dashi?, kai wallahi ina son kwad'on daddawa kuwa" Murmushi Hadiza tayi tana kallonta tana yayyaka tuwon data zo dashi tana niyar kwad'awa ta ce "Eh da shi nake zuwa, ku ai naga y'an gayu ne ku, da indomi da kawai fa kuka zo dashi" Hauwa ta tab'e baki cike da jin haushin abunda ya faru d'azo bayan fitar su aji, kamin su shigo class sun aje kayansu sadda zasu dawo an bud'e kular su an sace Kwan guda biyu ba'abar ko guda ba, anci rabin indomin anbar masu sauran. Tab'a ta Fatee tayi tana cewa "Hauwa ga kwad'on mai da yaji ni kuma na Yi, Bismillah. Tunanin mi kike naga kinyi shuru?" Tsaki Hauwa tayi tana cewa "Wallahi abinci muka bari a cikin aji d'azo da safe muka tafi house d'inmu domin yin aiki da shara, sadda za'a shigo aji an samu wani d'an iskan ya bud'a mana abinci ya cinye rabi" Dariya Ammama ta saki tana cewa "Kashh dan yau ne zuwanku na farko shi yasa, amma ai wake barin kayansa a cikin aji ya tafi yawo, ai in gaya maku ba'a yin haka nan, daga yanzu ko jakarku karku sake ku k'ara barinta a class idan zaku fita, ku rink'a sagala abunku ku fita da ita" Atu data fara cin indominta ta kalli Ammama bakinta cike da abinci ta ce "Tofa ashe class d'in namu akwai b'arayi tabd'i jam" "Ai ko b'arayi ma idan kinji b'arayi, baka da damar aje abunka mai mahimmanci a class ka fita, baka dawo kaga anyi ciki dashi ba" Cewar Hadiza ta idasa maganar tana kai kwad'on tuwo a bakinta bayan ta gama kwad'a shi. Wani faranti ta d'akko ta zubama Hauwa ta mik'a mata. Amsa tayi ta fara ci. Atu dake kusa ta ce "Ni dai na k'oshi ga Indomi idan zaku ci, ke kuma Hauwa baki cin indomin ne?" Hauwa ta cinye kwad'on data d'ebo zata kai bakinta bayan ta had'iye ta ce "A'a ni bazanci ba gaskiya ki basu idan zasu ci to, amma ni abun ne ya fice min a rai tunda aka bud'a aka cinye rabi na ce dama wallahi bazanci ta ba" Tab'e baki kawai Atu tayi tana juyowa gasu Ammama dake ta d'arkar abincinsu, zatai magana ta kalli Ammama, sake da baki ganin yadda ta wani cire hijab ta d'aureta a k'ugunta sai faman cin kwad'onta take babu abunda ya sha mata kai. Atu ta kasa hakuri ta ce "Ammama miye haka Kuma Fisbilillahi?" Ammama bakinta cike da kwad'on tuwo bata had'esa ba ta ce "Mi kuma nayi?" Atu ta nuna ta da yatsa tana cewa "Dube ki dan Allah kin wani yaye hijabinki kina cin abinci, kuma ga mutane Maza na wucewa ta wajan nan" Dariya Ammama ta saki tana duban Atu ta ce "Ke nifa haka nake cin abinci na, dan yau kuka fara zuwa shi yasa zaku yita ganin sabbin abubuwan da baku saba gani ba, ke dai ci abincinki kawai, ai wajan ba hayaniyar mutane ma, shi yasa muka zab'i zama bayan gidajan Malamai arna da ake kawowa daga wata uwa duniya" Zaro ido Hauwa tayi tana amshe zancen da cewa "Kee dan Allah wai a nan wajan wasu ke kwana Malamai?" "Kware da gaske kin dai gani, a nan suke kwana" Hadiza ta bata amsa Hauwa ta gyara zamanta akan dutsin da take zaune ta d'an gaji da zama a samansa kad'an ta d'an yatsine baki tana cewa "Tabd'i jam, basu gudun dare yayi, yanzu Fisbilillahi ai bazan iya zuwa koda hanyar school d'in nan ba ce cikin dare bare ace na shigo cikinta, duba ki gani miye zai hana Tanbotse a school d'in nan, kota ina daji ce fa, gabas Kudu yamma arewa ki duba fa" Ta k'are maganar tana faman nuna yanayin school d'in da hannu. Hadiza zatai magana aka buga k'araurawar komawa class. Da mugun sauri Ammama ta fara had'a kayanta data babbaje a wajan. Su duka tashi sukai suna saurin had'a kayansu. Hauwa ta dube su da d'an mamaki tana cewa "Kubi a hankali mana wannan sauri haka?" Hadiza ta kalleta da mamaki, sai kuma tayi murmushi tana kauda mamakinta ta ce "Har yanzu da sauranki Hauwa, yo ai nan idan ba saurin mukai ba aka rufe mintina ashirin ko goma yanzu nan zakiga y'an SS3 sun fara jifgar mutane, danmi baka koma class cikin lokaci ba, bugu suke nake gaya miki duk wadda aka gani a waje bare idan ba'a dad'e da komawa break ba, gara muje ajin mun idasa acan, bana son abunda zai tab'a lafiyar jikina" Atu data yi gaba tunda taji abunda Hadiza ta ce domin tama fi Hadiza rashin son a tab'a lafiyar jikinta. Da sauri suka take mata baya a haukace kamar sabbin mahaukata suka idasa class d'in, domin har sun fara bugun duk wa'inda sukai saura a waje, ko kuma asa mutum tsallan kwad'i har sai ya idasa class da tsallan kwad'in. Suna shiga suka baje akan kujera da yake kujerarsu tana kusa da juna ce, a haka suka fara uban surutu suna yi suna idasa cinye abincin da yayi saura. Suna cikin haka suka ji class ya d'au shuru, ba shiri har Ammama na niyar kifar da sauran kwad'onta dake akan cinyarta ta kusa cinyewa ta tashi tsaye. Da sauri kuma ta koma ta zauna tana rufe kular da sauri ta sata a k'ark'ashin kujera. Y'an SS3 ne wa'inda d'azo suka bada umarnin a rubuta masu, masu surutu. Jikin kowa yayi sanyi sai binsu ake da kallo. Wata daga cikinsu tana yatsine baki ta d'an dod'e hancinta tana cewa "Ohhh My God, class sai warin daddawa yake, dubeku k'azamai da'aAllah" Wata ta dafa mai maganar tana cewa itama "Ke kam Salma ai dole suyi k'azanta baki ganin har yanzu yarintar primary bata idasa sakinsu bane, duk sun cikama mutane aji da warin daddawa" Itama ta idasa fad'ar haka cike da isgilanci suna watsa masu wani mugun kallo. Ba wadda ya isa yayi koda tari ne a cikin ajin suna dai kallonsu kawai. D'aya daga cikin Mazan ne ya ce "Ina shugabar class d'in take?" Da sauri Binta ta mik'e tana cewa "Gani nan" "Yawwa ki fiddo da faifar da kika rubuta mana y'an surutu ki fito gaban allo ki kira sunan kowa, kowacce taji sunanta ta fito nan gaban allo" Ya idasa maganar yana kallon y'an class, da yawansu tsoro ya cika masu zuciya kowa na addu'ar Allah yasa dai baiyi surutu ba, Allah yasa dai ba sunansa a ciki. Wato sunan data fara kira ne ya ba y'an class mamaki ba kad'an ba, wato Hauwa Rabi'u. Da mugun mamaki Hauwa ta mik'e tana kallon Binta kallo irin na zaki ci uwarki ne idan na kamaki wallahi. Atu ma dai mamaki take, ta ina Hauwa tayi surutu?, domin ita ce ta hanata yinsa da ba abunda zai hanata tayi komai ta fanjama fanjam. Da haka tayita kiran sunaye ta kira ya kai mutum goma Sha. Ba tausayi ko tausayawa a tafin hannunka zata ware a nan suka rink'a bugun wa'inda sukai surutu, bulala goma-goma. Tabbas bulalar ta shigi Hauwa ba kad'an ba, domin tafin hannunta sunyi jawur. Bayan ta koma kujera tana ta kallon Binta tana ayyana miya kamata tayi ma yarinyar nan ne ma?. Bayan sun fita harda bada umarnin a sake rubuta wasu y'an surutun. Hauwa ta mik'e bata sauka a ko ina ba sai a gaban kujerar su Binta. Gaban kujerar ta buga da hannunta tana kallonta ido cikin ido ta ce "Keee dan Ubanki ubanmi nayi miki da har zaki saka sunana a cikin y'an surutu, al'halin kuma banyi surutun ba?" Shuru Binta tayi tana faman murgud'a baki. Hauwa ta ce "kan Ubancan" Ta shak'o wuyan hijab d'in Binta, y'an class na kallo babu wadda yayi gigin shiga fad'an, kowa na kallo, wasu ma so suke suga anci uban Binta, bare wa'inda ta rubuta sunansu cikin y'an surutu. Hauwa ta sake cewa "Zaki gaya min uban mi na tsare miki, ko kuwa saina gurji bakin shegiya yanzun nan?" Binta ganinfa idan ba dagewa tayi ba itama tofa zata bata kunya ne a gaban y'an class mutumcinta ya zube. Itama taci kular hijab d'in Hauwa tana cewa "Naje na saka kiyi duk abunda kika ga zaki iya, da bakiyi ba zan saki ne?" "Kutumar uba kaii yau zanci uban wata a nan wajan wallahi, har yanzu ban nuna maku kala ta ba wallahi a cikin class d'in nan, dole na fito da kalata ko an zauna lafiya, domin naga idan ba haka nayi ba bazan zauna k'alau da kowa ba" Hauwa na k'are maganar ta daddage iya k'arfin ta kaima Binta wani naushi a tsakiyar bakinta, ai ko nan take bakin ya fashe ya haye yayi suntum ba kyan gani. Wata uwar kururuwa Binta ta saki tana kuka tana cewa "Wayyo Allah na shiga uku na, ta fasa min baki, na rantse da Allah bazan yarda ba, idan na yarda Allah ya tsine min" Hauwa data sake ta tana rik'e da k'ugunta tana wata girgiza ta tsallar neman fitina tana makama mata harara ta ce "Ai ko yau sai dai Allah ya tsine miki yarinya, kuma wallahi na sake naji wata magana ta fito daga shegen bakin nan naki akaina saina miki abunda yafi wannan kin san hali na yanzu sarai ba sai na tsaya na sake miki wani dogon bayani ba, gobe ma dan Allah ki sake rubuta sunana a cikin y'an surutu kin ji?" Kuka kawai Binta ke yi domin ta lura Hauwa idan ta biye mata tofa dukan banza zata ci, dan bata da k'arfin k'arawa da Hauwa. Dole tasa ta koma ta zauna y'an class sai faman mata dariya suke k'asa-k'asa wai danma suna tsoron kar su fito fili da dariyar taci uban shege wajan sa sunansa a cikin y'an surutun aji. Ai ko kamar sun sani duk wadda taga bakinsa na murmushi ko alamar dariya sunansa kawai take dafkawa a cikin faifar dake gabanta. Kuma sai akai sa'a babu malamin daya sake shigowa har Hauwa tayi ta'asarta ta koma ta zauna. Ammama har saurin cewa take "kai amma wallahi kin birge ni, da kika yi ma shegiya haka, dama haushi take bani, sai wani iyayin tsiya cike da ciki, kinyi maganinta ai" Atu ta harari Hauwa tana cewa itama "Keee dai Hauwa kinji dad'i wallahi, ke dai idan baki nemi magana ba baki jin dad'i a rayuwarki" Kallonta Hauwa tayi rai d'an b'ace ta ce "Dakata Atu miye nayi na jan magana a nan wajan kuma?, ita duk abunda tayi min baki gani ba kenan?, sai ni kike ganin laifi na, saboda dama na saba haka ko?". "Hmmm" Kawai Atu ta ce tana gyara zamanta a cikin kujerar da suke tana fuskantar Hauwa kamin ta ce "Ko kad'an ba haka bane, itama batai dai-dai ba, domin Allah d'azo banga ko naji kinyi surutu ba, amma ai bai kamata kiyi mata haka ba ko?" D'aga mata hannu Hauwa tayi tana cewa. "Kinga kefa na lura bak'i k'i na barta taci bulis ba, kuma kema kin san bazan tab'a bari ba, idan ba'a tab'a ni ba ai bazan tanka ba, dan haka ki kama bakin ki kiyi shuru kawai yafi miki" "Ai shikenan ina gudar miki ranar da zaki tab'o wacce tafi ki iya rigima ranar ta gurji baki babu abunda zanyi kuma ba" Hauwa zatai magana kenan Malam ya shigo class d'in, dole tasa tayi shuru suna mik'ewa gaba d'aya suna gaisar dashi. Har ya fara goge allo da kansa sai kuma ya juyo inda su Binta suke yana cewa "Ina shugabar class d'in nan ta zo ta goge min allon nan?" Nuna masa Binta akai dake rik'e da bakinta har yanzu yana mata wani zugi, daurewa kawai take. Kallonta yayi sosai yana cewa "Ke mike faruwa ne da bakin naki?" Da kyar ta bud'e bakin maganar ma da kyar take yinta ta ce. "Malam bigewa nayi da bango ban lura ba, shine yasa ya kunbura haka" Daga can baya Hauwa ta saki wani murmushin gefen baki, tana duban Atu data saki baki tana maganar zuci. Wato kenan dai Hauwa taci bulis, yarinyar nan ta fara tsoronta. "Allah ya shirya ki Hauwa" Atu ta fad'a a hankali yadda ita kad'ai zata ji ta. Murmushi ta saki itama tana ce mata. "Amin idan da gaske kike" Hararar wasa Atu ta maka mata kawai tana girgiza kanta, suka maida hankalinsu ga Malamin da yake ba Binta amsar cewa. "Ayyah sannu fa, sai a rink'a kula daga yanzu, kije wajan y'an SS3 ki tabbaya ina Health take za'a nuna miki ita ki ce ta baki magani, zata baki" Girgiza kai tayi da sauri domin bata son abunda zai had'a ta da y'an SS3 ita a yanzu ta ce "A'a Malam idan naje gida zansha kawai" D'aga k'afad'arsa yayi yana d'an tab'e baki ya juya ya ci gaba da lasin nashi............. *RAYUWAR MAKARANTA* *©Zahra Royal Star* Page 3 "Dan Allah ki tak'o k'afa mu wace dajin nan, kinsa an tashi school mun biyo ta cikin daji haba dan Allah, kuma kin k'i kiyo sauri" Cewar Atu dake tafiya da sauri, domin dajin tsoro ma yake bata. Hauwa dake kallon wasu dondozen y'an mata su uku dake biye da su suna tafiya suna nuna su kamar masu neman rigima dasu yasa Hauwa d'an tsayawa tana cewa "Kee tsaya dan Allah kamar fa Binta nake gani tare da wasu, miye take nufi ne, badai jawo wasu tayi ba domin su rama mata abunda nayi mata ba?" Da sauri Atu ta waiga tana d'ora hannunta a saman kanta ido a waje take cewa. "Shikenan mun shiga uku, yanzu miye kika ja mana ne haka?, da munbi su Hadiza da duk haka bata faruwa ba, da yanzu na sani mun shiga cikin gari ma" Tsaki Hauwa tayi tana rik'e k'ugunta tana sake kallon y'an matan da suka k'araso kusa dasu yanzu. Binta dake kallon Hauwa ta makama mata harara tana nunata da yatsa ta ce "Yawwa anti Amina ita ce ta bige min baki a cikin aji babu uwar dana yi mata Kuma" Wani kukan kura Amina tayi sai gata a gaban Hauwa tana k'ok'arin shak'o wuyan hijab d'inta tana cewa "Kutumar uban miye tayi miki da har zaki fasa mata baki?" Da sauri Hauwa ta matsa gefe hakan yasa hannun Amina bai kai jikinta ba, ta dubeta a wulakanci babu tsoro akan fuskarta ta ce "Kinga Malama karki sake k'azamin hannunki yayi gigin tab'a min jiki wallahi, kuma na fasa mata bakin ko akwai abunda zaki yi ne a akai?" "Jar ubancan kayyasa, ke Amina kika tsaya wannan k'aramar al'hakin take gaya miki magana son ranta baki ci uwar shegiya ba" Cewar wata dage gefe mai d'an jiki domin da kyar take tafiya ma tsabar y'ar kibar da taima jikin nata yawa. Atu dake gefe ta matso cike da tsoro ta ce "Kuyiwa girman Allah kuyi hakuri, bazata sake ba nan gaba in..... Da mugun sauri Hauwa ta katse Atu da cewa. "Kaiii amma dai Allah ya isa tsakanina dake wallahi, miye ruwanki a cikin fad'an nan, wa'innan zan ba hakuri? Ubangiji ya kiyaye ni, dan haka kiyi min shuru da bakin nan naki" Hauwa na rufe bakinta Amina ta ribaceta ta duk'a ta kamo k'afarta kawai sai dai Hauwa taji anyi zama da ita an fyad'a da k'asa. Ihu Hauwa ta saki tana sakin wata uwar kururuwa mai k'arar gaske, juye-juye ta farayi tana birgima a k'asa kamar macijiya, tana yi tana wasu surutai kamar wacce aljanu suka shafa. Zaro ido su Amina sukai suna duban Binta cike da tsoro Amina ta koma gefe tana cewa. "Mun shiga uku ke Binta ba dai mai aljanu kika kwaso mana ba, kinfa san ina tsoron mai aljanu?" Binta da y'an cikinta ke kuka itama ta ce. "Wallahi ban sani ba, yaufa suka fara zuwa makarantar" "Shegiya amma shine kika bari muka haye masu da rigima haka kawai, baki gama fahimtar wace ita ba, ki ja mana masifa" Cewar mai k'ibar cikinsu sai zufa take sharcewa ganin yadda Hauwa ke wata irin lankwasa kamar macijiyar gaske. Atu dake gefe itama bala'in tsoro ne ya rufe ta duk d'aukarta ko aljanun gaske ne suka shigi Hauwar a yanzu. Basuyi aune ba Hauwa ta mik'e ta rarumo Amina ta kad'a da k'asa ta haye ruwan cikinta ta fara kai mata yakushi a fuskarta kota ina. Ihu Amina take tana k'arawa tana cewa. "Wayyo Allah na shiga uku nah dan girman Allah kuyi hakuri na rantse banzan sake shiga harkar god'iyarku ba, ku yafe min dan Allah" "Wuuyihohooo sai ni d'an gidan sarkin aljanu, ubanwa yasa ku tab'a min masoyiya Abar k'auna ta, yau sai kun gano duniyar aljanu yau sai kun d'and'a kud'arku wallahi" Cewar Hauwa tana yi tana ihu had'e da lauyar da harshe kamar mai aljanun gaske, idan kaga yadda take baka tab'a cewa ba aljanun gasken bane. Mai k'ibar nan ce ta daddage iya k'arfin ta banga je Binta dake nanik'e da ita ta zura da uban gudu ko waige bata yi, tana cikin gudu wani dutse ya tab'e ta, ta zube a k'asa rikijahh, ihu ta saki tana tashi da kyar duk ta ji ciwo a hannunta da gwaiwarta amma tsabar tsoro haka ta mik'e ta ci gaba da tik'a gudu kamar wacce mutuwa ta biyo. Duk da irin halin tsoron da Atu take ciki hakan baisa ta kasa dariya ba, tana kallonta yadda take gudu da kyar. Sai da Hauwa ta tabbatar Amina ta bugu iya buguwa sai kawai ta sauka kanta tana faman sakin tashiwa. Haba kamar jira take tana ganin ta sauka akanta, Amina ta mik'e duk da irin dukan data sha, ta fanska da gudu itama, ganin haka Binta ta take masu baya. Hauwa na ganin sunbar wajan ta mik'e tana kakkab'e jikinta tana sakin wata uwar dariya har tana d'aukewa k'asa harda su kwanciya tsabar dariyar mugunta. Kallonta Atu take cike da mamaki tana cewa. "Wai tsaya ba dai aljanun k'arya kikai masu ba?" "Ke duk zama da nake tare da ke na tab'a tayar da aljanu ne?, ai kema kin san banda wasu aljanu" "To amma ke dai kam baki da mutumci wallahi, kinga Hauwa ki kiyaye kanki da k'arya irin wannan, sai na gasken sun shiga jikinki haka kawaii su shiga jikinki a banza, sufa ba'a masu haka wallahi in fad'a miki" Da sauri Hauwa ta mik'e ta fara tafiya Atu ta take mata baya tana cewa. "Kefa matsalata dake yima mutum mugun fata wallahi, yanzu miye nayi wadda ba dai-dai ba iyee?, baki ga mutanan data d'ebo min bane, idan na ce zan tsaya tofa jifgata zasuyi la'ada waje wallahi ai sarkin tawa yafi sarkin k'arfi, yanzu wannan rusheshiyar dana gani tare dasu idan ta haye ruwan cikina ai na shiga uku na, amma yanzu dana yi masu haka baki ga yadda suke gudu ba kamar wa'inda mutuwa tayi ma sallama" Atu ta sauk'e ajiyar zuciya tana cewa. "Tsakani da Allah Hauwa kinfi k'arfin kaina, kowaye ya shigo komarki ya bani ya shiga uku wallahi" "Yo a'ato kinga laifi na ne?, idan ba haka kayi ba naga alamar bazaka zauna da kowa lafiya ba, yanzu da irin hakurin da kike badawa nayi masu ai da yanzu wata maganar ake ba wannan ba yarinya, gobe ma su sake shiga harkata, ke basu bama wallahi hatta y'an SS3 ko Malamai suka ce zasu k'ara min muguntar da bata gimshe ni ba mataki kawai zan d'auka da bazai masu dad'i ba". Atu da d'an daka ta da tafiya tana cewa. "Kinga Hauwa ina jiye miki ranar nadama, kinga ki rufa ma kanki asiri abun naki ya tsaya iya d'alibai kad'ai banda Malamai, D'aliban ma banda y'an SS3" Wani uban tsaki Hauwa ta saki tana hararar Atu ta ce. "Kefa baki da wayo wani lokacin, babu abunda zan fasa wallahi, su y'an SS3 uban waye su da baza masu hakan ba, mi yasa suke jifgar yaran mutane, so kawai nake su k'ara shiga gonata wallahi". Har suka isa inda zasu rabu ko wacce ta wuce gidansu Atu bata k'ara magana ba, sai da Hauwa zata wuce ta santar gidansu taji Atu na cewa. "Dan Allah gobe ki fito da wuri, dan wallahi bazan sake bari na makara ba, kisa nayi tsallan kwad'i ko wankin toilet, kin san dai bazan bari a dake ni ba, ki rufan asiri ki fito da wuri" Da to kawai Hauwa ta amsa tayi gaba abunta. Tana gaf shiga gidansu taji wani yaro ya kwashe da dariya yana kallonta. Da mugun sauri ta kai dubanta gare sa a d'an mamakance take dubansa tana nuna kanta ta ce. "Kai da ubanwa kike?" Dariya yaron yayi yana nunata yana cewa. "Wai kin ganki kuwa kamar wacce tayi birkid'a cikin k'asa wahoho ku dubeta kamar wata biranya" Yara suka taro a wajan suna mata dariya. Cije baki tayi tana ware k'afa tabi yaran da gudu tayi sa'ar cafko wadda ya fara janta fad'an. Kwalar rigar yaron taci tana cewa. "Yau ba abunda zai hana banci ubanka ba wallahi, kaga d'an iskan yaro, ni sa'arka ce iyee?". "Ni ki cika ni na ce dan..... Wani uban bugu ta kai ma bakinsa wadda yasa shi ba shiri had'e maganar da yayi niyar k'arasawa. Ta k'ara kai masa wani mari a fuska tana cewa. "Naga ubanda ya tsaya maka a garin nan, daga yau idan ka ganni ka jani fad'a" Kuka yaron yake sosai ta sake shi zata juya ta tafi taji muryarsa ya baza da gudu yana cewa. "Kuma wallahi Allah saina gaya ma Umma ta, kuma Allah ya isa ban yafe ba" "Ba uwarka zaka fad'amawa ba ko ubanka ne ina jiranku" Ta idasa maganar tana idasa shigewa gidan nasu. Inna dake d'uke tana wanke shinkafa ta kalleta rai a d'an b'ace ta ce. "Da waye kuma kuke fad'a a waje?, wai ke dai kullum baki girma sai na jikin ki Fisbilillahi Hauwa?" Zunburo baki Hauwa tayi tana zama akan wani banci tana kallon Inna ta ce. "Inna kinfa san bana fad'a sai idan an tab'a ni ko?" "Ke dan Allah ni rufe min baki, zaki tashi ki cire kayan makarantar nan kizo ki wanke so ko kuwa sai kin gama sani maganar da kika saba?" Inna na rufe baki aka kwad'a sallama a k'ofar gidan, Inna na niyar amsa sallamar kawai taga mata rik'e da yaro a hannunta. Inna ta dubi Matar jin tana cewa. "Ina matsiyaciyar jikar taki mai jawo miki magana?, wannan y'ar iskar yarinyar ita ce zata zama ajalinki k'ila, tsabar masifar ta, Kuma wallahi sai an biyani kud'in maganin da zan je Kyamis na saima D'ana magani, kuma kiyi mata gargad'i karta sake tab'a min yaro wallahi, dubi kiga yadda ta fasa masa baki ya haye yayi suntum" Tashi tsaye Hauwa tayi tana cewa. "Kinga baiwar Allah shi yaron naki bai sanar dake irin abunda yayi min bane, ko kuwa kema irin iyayen nanne wa'inda basa ba Yaransu tarbiyya, daga gani Allah ba'a basu tarbiyya daga house ba" Inna ta matso kusa da Hauwa bata ankara ba Inna ta gwafje mata baki tana cewa. "Baiwar Allah dan Allah kayi hakuri hakan bazata sake faruwa ba, kuma kud'in magani ga naira d'ari biyar nan, ki sai masa maganin, amma shima yaron naki ki rink'a masa fad'a, bai kamata yana jan manya wa'inda suka girmesa ba" Matar tana hararar Inna ta ce "Kinga baiwar Allah bani kud'i kawai na wuce dan naga alamar baki son laifin jikar ki" Inna ta k'ank'ance Ido na matsifa domin matar ta fara bata haushi yanzu ta ce. "Bari na fito miki a mutum baiwar Allah idan baki ma D'anki Jan kunne ya daina shiga harkar Hauwa ba, to kuwa wallahi babu abunda zance mata, zan bari ta ci ubansa ta saita masa tarbiyya, tunda ke naga alamar baki tashi bashi ita ba" "Au hakama zaki ce?" "Haka na ce ko akwai magana ne?, bar min cikin gida, ko yanzu nasa Hauwar tayi min maganinku ku duka daga ke har yaron naki marar kunya" Inna ta k'are maganar had'e da wurga mata d'ari biyar d'in. Ta duk'a k'asa ba kunya ta d'auke kud'in tayi waje tana mitar dama Inna ita ke d'aure ma Hauwa gindi take duk abunda take so a cikin garin nan. Matar na fita Inna ta dawo da dubanta inda Hauwa take sai faman kunbura baki take. Inna ta ce "wato Hauwa baza ki daina d'aukar min magana ba ko?, hala yauma a makarantar kin jawo min abun magana ko?". "Nifa Inna babu maganar dana jawo miki a makaranta" "Yi min shuru na ce, ai nasan halinki kad'an daga aikin ki, yanzu idan ba jan maganar ba, miye na daga dawowarki ki kama yaro ki mammake Fisbilillahi?, so kike ayita zagin iyayenki suna kwance a kabari basu ji ba basu gani ba haba Hauwa" Turo k'aramin bakinta ta d'anyi tana bubbuga k'afa cike da shagwab'ar da Innar kawai take ma ita ta ce. "Inna fa kin san bana jan fad'a haka nan kawai saifa anja ni" "Ke dallah tafi can, to idan anja kin mi yasa bazaki iya hakuri bane?, ke bazaki iya hakurin zama da mutane ba dai ko?" Inna ta sake cewa. "Ai bari dai K'anin Ubanki ya dawo na gaya masa yayi min maganinki wallahi" Da sauri Hauwa ta ce "dan Allah Inna kayi hakuri, karki sanar da Abba, kina ji shine ya hana a kaini makarantar kwana da yanzu na tafi ba mai k'ara kawo miki k'arata ma bare ace nayi wani abu" "A haka kina uban rashin ji zai d'auke ki ya kaiki Makarantar kwana?, zab'ar baki da tunani ko, ai yayi min dai-dai abar min ke a nan yafi min kwanciyar hankali kina nan d'in ma walaAllah cika bare an kaiki Makarantar kwana, ai abun naki k'aruwa zaiyi, da ma dai kamar da makarantar kwanar take da sai na bari a kaiki, amma yanzu itama ta lalace kwata-kwata ba abunda ake a cikinta sai shashanci"............ *RAYUWAR MAKARANTA* *©Zahra Royal Star* Page 4 "Dan Allah kayi sauri Kinga k'arfe bakwai ta kusa haba Hauwa dan Allah" Cewar Atu dake tsaye a k'ofar d'akin Inna tana jiran Hauwa dake shafa mai kamar wacce bata son tashi. Inna dake jin radio ta aje radion dake hannunta ta kai ma Hauwa dak'uwa da hannu tana cewa. "Zaki mai da hankali kiyi abunda ke gabanki ko kuwa?, Atun tayi tafiyarta ta barki. Shashashar yarinya kawai. Ke Atu da zaki biye ta tawa da kinyi tafiyarki kin rabu da wannan sharmammar wallahi, idan dan ita ne bata k'i kullum taja maku bugun makara ba". Turo baki Hauwa tayi dai-dai ta idasa shafa man ta jawo Koko da k'osanta ta zata fara ci kenan, Inna ta warce farantin da aka zuba k'osan, tana cewa. "Zaki tashi ki fara saka kayan makarantar ne ko so kike yanzu jikinki yayi tsami?" Bubbuga k'afa Hauwa ta fara yi, ta mik'e tsaye tana d'an hararar Atu dake mata dariya k'asa-k'asa. Inna ta kalli Atu tana cewa. "Yawwa jikata, zauna ke ki fara cin k'osan kamin ta gama sa kayan" Zama Atu tayi ta fara shan kokon, ba'a d'au lokaci ba Hauwa ta fito da jakar school d'inta had'e da Hijab d'inta a hannunta ta zauna kusa da Atu suna cin abincin a tare. Hauwa ta d'akko k'osai zata sa a bakinta sai ta d'an dakata ta ce. "Inna please ba dai Dankalin Hausa kika soya min ba dai ko?, kin san baci nake ba, ni ina wadda Abban Kano ya kawo min na turawan nan shine nake so" Ta idasa maganar tana turo baki had'e da tusa k'osai a bakinta ta taune. Inna ta d'an harareta ta ce. "Ke ni ki mai da hankali ki ci abinci ko kun tafi, ga kular abincin can idan kinje makarantar kin gani" "To Inna yaushe Abban Kano zai zo ne garin nan?" "Son ganinsa kike ne?, ke da shekaran jiya ya kira ya ce a baki waya kika ce ke baza ki amsa ba, saboda bai kaiki Makarantar kwana ba" Hauwa ta mik'e tana zare hannunta daga cin abincin da take tana cewa. "A'a Inna nifa ina son ganin Abba, kawai na tsani zuwansa da Y Abdullah, dole ace idan zaizo garin sai dashi yake zuwa ni kuma na tsani wannan Y Abdullahn mugu ne fa" Harara Inna ta makama mata tana tab'e baki ta ce. "Kanki ake ji dai, da da kike cewa shine za'a aura miki fa" "Subhanallahi Inna, haba Inna Fisbilillahi wane irin fatane wannan kike min?, Ina zan kai irin izzar Y Abdullah da jin kai irin nashi, kofa kallon arzik'i bai maka bare naje na aure shi, yo duka nawa nake ma ina zan kai Y Abdullah tab yanka ni zaiyi ya cinye nama na d'anye Dan....... Inna ta katse ta ta ce "keee ni da'aAllah kimin shuru, kin cika zuba da yawa yarinya sai ka ce mai suna zubaida haba dan Allah, a haka Y Abdullahn zai soki kina surutun banza da wofi fad'i ba'a tabbaye ki ba?" K'ara zunburo baki tayi gaba tana sa Hijabinta ta ce. "Kefa Inna yarfa mutane gare ki Allah" Ta k'ara kai dubanta inda Atu take tana tusa k'osai bakinta har yanzu bata idasa ba ta ce "Ke kuma sai kiyi sauri kizo mu tafi mayyar k'osai kawai, yanzu duk zancan da nake yi hala ke kunnanki baiji bane hala?" "Mi kike cewa?" Atu ta fad'a tana mik'ewa bakinta cike da k'osai, sai da ta cinye sa tas, domin Allah ya sani tana bala'in son k'osai ba d'an kad'an ba. Tsaki Hauwa tayi tana k'ara mata kallon banza ta ce "Ba'a sani ba kinji?" Murmushi Inna ta saki tana kallon Atu ta ce "Rabu da mutuniyar taki, kuje Allah ya tsare hanya" Da amin suka amsa suka fice bayan Hauwa ta d'auki kular abincinta a kitchen d'in Inna. Suna hanyar school Hauwa tana ma Atu mitar Y Abdullah da irin girman kansa. Atu ta d'an juya idonta tana rik'e baki had'e d'an mamakin Hauwa ta ce "Wai tsaya ma Hauwa duka nawa kike, kike ikirarin Y Abdullah ya so...... "Ke Kinga dakata kinji na ce ina sonshi ne uwar shirri?" Hauwar ta katse Atu da sauri. "A'ato alamu nake gani mana, ke idan banda abunki ina zaki kai wannan uwar gidan tasa uwar bak'in kishin tsiya?, Ina gani fa idan aka zo da ita garin nan yadda take miki wani kallon banza, ke koda mace ta gani tana kallon mata miji ranar saita gane bata wayo, ke kam mi zaki dashi ma?" Wani abu Hauwa taji ya tsaya mata a zuci ita fa sai yanzu ne ma ta tuno cewa fa ashe Y Abdullah yana da mata. "Mtswww aikin banza kawai nina manta da shegiyar matar nan tasa Lubna wallahi, y'ar banza kawai" "Hhhhhh yo yada haka da zagi kuma Hauwa" Atu ta k'are maganar had'e da dariya. Wani bugu Hauwa ta kawo ma Atu, ai ko da sauri ta goce tana k'ara sakin dariya son ranta, Hauwa ko ta cika tayi fam, da haushin Atu. Da haka dai suna gaf k'arasawa school d'in suka hango y'an SS3 na gaf k'arasowa wajan taran makara, da gudu suka idasa shiga school d'in, shima sai da Atu taja hannun Hauwa sukai saurin shiga, domin suna k'arasowa suke rufe bakin shigowa school zasu fara tarban makara. "Waii waii Allah ya taimake mu, yau dai ba'a tare mu ba, yau bamu da rabon shan wahala" Harara Hauwa tayima Atu tana cewa. "Nifa da kin barni bafa zanyi gudun nan ba, haka kawai na tabbata ko kwas d'in bata idasa ba wallahi tsabar mugunta ce cike da cikin wa'incan bayin Allahn" Hauwa ta k'are maganar tana banka masu harara. Jawota Atu tayi suka nufi cikin school d'in suna k'arya wata kwana domin zuwa house d'insu, da yake house d'insu d'aya da Atun. Suna idasawa kota ina shara ake Yara da manta y'an SS1-SS2. Fatee ce ta k'araso wajan tana cewa. "Hauwa kuyi sauri ku d'akko tsintsiyarku, ku fara shara, domin idan suka ga mutum a tsaye bugunsa suke wallahi, koda irin mik'ewar nan yayi danya d'an huta, wallahi babu ruwansu sai dai kawai gaji bulala a gadon bayanka" Atu ba shiri ta aje jakarta tana d'aukar tsintsiya tabi ayarin masu shara. Hauwa ma tana turo baki tabi bayansu. Ba k'aramar shara sukai ma filin house d'in ba, da yake yau A'lhamis ana duban tsafta house to house. Bayan an shirya house d'in an jera D'alibai akan layi, Malamai nabi house to house suna duban tsaftar house da ta D'alibai. Fatee dake kusa da Hauwa ta kai dubanta a y'an yatsun Hauwa ta d'an rik'e baki da mamaki ta ce. "Kaii kaii kaii Hauwa yau zaki ci duka, mi yasa baki yanke farcenki ba?, kin san yau A'lhamis ana duban tsafta?" Zaro ido Hauwa tayi tana kallon y'an yatsun hannunta dake cike da farce zak'o-zak'o. Ta ce "d'an girman Allah baki da Reza na yanke kamin su k'araso inda muke?" "Wallahi tana can nesa damu cikin Jakar school d'ina" Fatee na rufe baki kawai Malamai da y'an SS3 suka shigo house d'insu Hauwa, suka fara duba yanayin tsaftarsa, had'e da duba tsaftar D'alibai. D'aya bayan d'aya ake bi ana duba jikinka da hannuka idan ka yanke farcenka. Duk wadda bai yanke ba k'asa ake duk'ar dashi. Tofa kusan Hauwa kad'ai ce aka sa duk'ar k'asa. Bayan Mahukunta sun wuce sunsa making d'in da house d'in yaci, kawai Hauwa bata san hawa ba, ba taba san sauka ba, ta fara jin bulala kota ina a jikinta. Ta rud'e ta rasa inda zata sa kanta, domin kota ina jin bulala take a jikinta. Sai can taji saukar muryar wacce har abada bazata mance da ita ba wacce ta fara bugunta, a wajan taran makara Lamratu ashe ita keda house d'in da suke. Lamratu na jifgar Hauwa tana cewa. "Kaga y'ar iska k'azama dake, a kanki ke d'aya kinja mana rage maki a house d'ina, ai ko yau ba abunda zai hana banji uwarki ba wallahi" Kallonta Hauwa kawai take tana kawo mata bugu tana tarewa da hannunta. Miye zatai ma wannan matar ne domin ta kiyayeta?. Lamratu a zuciye ta ce "Kee wai bake bace na ce karki sake wani abu ya k'ara had'a ki dani bane?, ai ko yarinya kin bani kin shiga uku tunda Allah ya kawo ki house d'ina, idan bazaki daina jakkanci ba ni kuma bazan daina kilarki ba son raina" Ta idasa maganar tana d'aga bulalar dake hannunta tana kai mata wata shaud'a a gadon bayanta. Wata irin gantsarewa Hauwa tayi kawai ta zube a k'asa ta fara wani juyi, tana yi tana wani irin gurnani kamar zakanya. A mugun tsara ce wasu suka fara ja baya. Lamratu kuwa murmushi ta saki tana cewa. "Ai wallahi ba aljanu ba ko kukar bulishiya ce a kanki yau saina sauk'e miki ita a kanki" Tana k'are fad'ar haka ta k'ara k'aimin kaima mata jifga baji ba gani. Wata shegin juyi da Hauwa tayi sai gata ta kamo k'afar Lamratu ta fyad'a da k'asa sai gata rashe-rashe a k'asa a zube. Mi d'alibai zasuyi idan ba dariya ba. Wani mugun haushi da tsananin kunya ne ya rufe Lamratu. Hauwa kuwa ta haye ruwan cikinta ta fara kai mata naushi ta hanci ta baki baji ba gani tana wasu surutai tana cewa. "Keee dan uban da ya haifeki kin isa ki tab'a mana godiyarmu ki zauna lafiya, daga yau idan kika sake sai mun zubar miki da hak'ora, mun tsiyayar miki da idonki ko mu maida ke kurma" Kuka Lamratu ta saki tana cewa "Dan Allah ba wadda zai kwace ni ne daga hannun wannan mahaukaciyar, wayyo Allah na zata kashe ni" Fatee dake gefe tsaye ta saki wata dariyar mugunta tana cewa k'asa-k'asa "Wahoho dole K'anwar nak'i, ai na d'auka girman kai bazai bari ki nemi taimako ba, ai wallahi masu aljanun nan sune dai-dai daku" Atu ko tana daga gefe ta rik'e baki tana kallon Hauwa dake jikin Lamratu tana gurzarta kamar wacce ta samu kayan wanki. Da gudu wasu Malamai suka k'araso wajan da kyar da sub'in goshi aka b'anb'are Hauwa a jikin Lamratu tana yi tana wata jijjiga tana ihu tana cewa. "Ku cika mu muka ce, ku barmu da ita yau sai mun sumar da ita tunda ta tab'a mana godiyarmu mu, ku gaya mata ba'a tab'a mana godiyarmu a zauna lafiya" Addu'a Mlm Bahari dake kusa da Mlm Shamsu, dama Mlm Shamsu Malamin Arabic ne, nan take ya fara tofa mata wasu addu'o'i. Wata irin y'ar iskar mik'a Hauwa tayi tana sakin wata uwar atishawa mai k'arfi, kai ka ce aljanun gaske ne suka fice daga jikinta. Har wani baccin munafurci ya d'auketa, Mlm Bahari ya bada umarnin a kaita zuwa class a kwantar da ita kamin ta farka. Bayan an wace da Hauwa Mlm ya kalli Lamratu yana cewa. "Ya kamata ku daina irin wannan hukuncin da bugun Yara a tsakar rana ko sanyin safiya irin haka, komai na iya faruwa dama, dan Allah a kiyaye gaba please" Wata muguwar harara Lamratu ta raka Mlmn da yayi maganar da ita. Uwar kunya duk ta isheta tana tashi ta fara zagin sauran y'an house d'in nata, tana hucewa a kansu....... *RAYUWAR MAKARANTA* *Zahra Royal Star* Page 5 *No. 12, Kawo Bos Stop, Kano Nigeria* Kirrr kirrr kirrr Ringing d'in wayarsa ta karad'e gaba d'aya parlon. Lubna dake zaune akan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, ta d'ago tana jefa masa wani kallo irin na zargi. Ko kallonta baiyi ba ya tashi domin d'aukar wayar. Da wani mugun sauri ta sha gabansa tana rik'e k'ugunta tana masa kallon tuhuma. Da kyar Abdullah ya iya bud'e baki domin ransa ya fara b'aci ya fara gajiya da halin Lubna ya ce. "Miye haka Lubna?, kinzo kin shiga gabana ki bani waja na wuce na ce" Wani kallon uku saura ta jefama Abdullah, duk cewar tana mugu-mugun shakkarsa ba kad'an ba, to amma indai akan kishinsa ne hankalinta ma barin gangar jikinta yake bata wani shakkar masa tujara akan hakan. Ta ce "dole na tare gabanka mana, miye dan an kira ka, zaka wani tashi kaje d'aki ka d'auki waya?, mi yasa baza'ayi wayar a gabana ba, idan ba wani abun kake kullawa ba, wallahi Honey ka sani bazan tab'a iya had'a kowacce mace da kai ba" Hannunsa na dama yasa a fuskarsa ya d'an kama kansa da ke neman fara masa ciwo, saboda hayaniyar da Lubna ke masa. Idonsa masu kamar mai jin bacci had'e da muryar nan tasa mai cike da isa da izza ya ce. "Lubna karki sake na d'au mataki a kanki, wadda zakiyi nadama a nan gaba, dole ne aka ce miki sai nayi waya a gabanki, ko kuwa ke kullum d'an k'aramin tunaninki bai da aiki sai kitsa miki cewa ai da mace nake waya?" "Ai dole ka ce haka mana, ya za'ai hankali na ya kwanta, kana koyarwa a wannan shegiyar school d'in taku kaine fa shugaba a cikinta, gaka da kyau da izza, da komai ka had'a na rayuwa ya za'ai y'an matan makarantar nan bazasu haukace akan ba, gasu dama ance sai shegen rawar kan tsiya ne dasu, ga son Mazan mutane, ni kuma wallahi naga y'ar iskar data isa da shigo min cikin gida, bance ub....... D'aga mata hannu Abdallah yayi yana cewa. "Stop kinga, I'm tired of hearing your words, kullum sai kin mai-maita min su, kuma kin san baki isa kin hanani hud'd'a da D'alibai na ba, so give me a place to pass" Yana idasa fad'ar haka wayar dake hannunsa ta sake d'aukar k'ara. Kallon wayar yayi yana rab'awa ta gefanta ya wuce. Da d'aki zai nufa taga kawai ya fice waje yana gaf fita parlon ya d'auki kiran da aketa masa a wayar. Bayan ya fito ya can cikin wayar aka ce "Abdallah wai sai yaushe ne zaka samu time zamu je rimaye ne?, ina buk'atar ganin uwata fa kai idan baka buk'atar ganin Kakar taka" Murmushi ya saki yana cewa. "Abba barka da dare" "Barka kad'ai, ko gaisawa ban bari munyi ba, kai d'in ne hidimar ka tayi maka yawa, idan bazaka samu zuwa ba gara ka bari kawai ni naje naga uwata" Murmushi Abdallah ya sake saki, wadda yasa kyakykyawar fuskarsa mai cike da kwarjini da haiba ta k'ara kyau da cikar zatii, murmushin da Abban ne kad'ai ke ganinsa, dan ko Lubna a yanzu bata cika ganin murmushinsa ba, saboda yanzu kullum cikin b'ata masa rai take, akan bak'in kishinta, ba damar taji yana waya sai ta ce ai da mace yake waya, ba damar mace D'alibarsa ta kirashi ko akan matsalar karatunta ne, yanzu sai ta fara nuna masa halin k'auyancin nata, a wacewarshi, abunda take yi da haukan da takeyi akansa haukane da k'auyanci da gidadanci. Sauk'e lumfashi yayi yana cewa. "No Abba insha Allah zamu je very soon, kawai so nake na samu time na tafiyarmu da wuri" Daga cikin wayar Abba ya ce. "Ya kamata dai, dan so nake naje naga Y'ata Hauwa nasan yanzu ta sake k'ara girma" Wata irin halbawa zuciyar Abdallah tayi, jin sunan da aka kira Hauwa, shifa har mantawa yake da wannan yarinyar marar hankali mahaukaciya, wani abu ya tuno kuma yasa shi lumshe ido yana hango irin rigimar da za'a sha a lokacin da abun ya fito fili. Sunyi magana sosai inda daga k'arshe yake cewa "Karka damu Abba itama tsohowa mai ran k'arfe saita gaji da ganinmu ne insha Allah" "Haka dai kake fad'a k'ila sai lokacin da muka d'ibar maka na tarewar Hau..... Da sauri Abdallah ya ce "Abba sai munyi magana" Ya datse kiran, yana kallon Lubna da fitowarta kenan ta rik'e k'ugunta. Sauk'e ajiyar zuciya yayi yana hamdala bata ji mi Abba yake cewa daga k'arshe domin wayar zaka iya jiyo mai magana, danshi akwaisa akwai iya k'ure k'ara yadda zaiji mutum sosai a cikin waya. Baiyi aune ba Lubna ta matsa kusa dashi ta warce wayar dake hannunsa tana jujjaya ta tana cewa. "Wato saboda baka da gaskiya shine dan kaga na fito zaka kashe wayar, idan ba wayar munafurci kake ba mi yasa ka katse ta, ka ci gaba da wayar mana idan kana da gaskiya" Abdallah harya d'aga hannunsa zai kai mata mari, sai kuma ya dunkulesa waje d'aya. Kallonsa take da mamaki ta saki wata shewa tana cewa "Ahayeee aren't you just slapping me?, kuma kaji in gaya maka wallahi daga yau bazaka sake waya da wata y'a mace a wayar nan ba" Tana idasa maganar ta buga wayar da k'asa nan take ta tarwatse. Zaro ido waje Abdallah yayi yana bin Lubna da kallo, ganin yadda ta fasa masa waya kuma ta shigewarta parlo ta barsa cike da baki. Tana cin galaba akansa ne dan taga bai da hayaniya, baya son yawan magana a rayuwarsa, shi yasa take anfani da wannan damar domin takurama rayuwarsa, akan bak'in kishinta da mugun zarginta akansa. D'aukar wayarsa yayi yana shafa sumar kansa wacce a kullum take a gyare, ya bud'e k'ofar parlon ya shiga ciki. *Government Secondary School Rimaye Katsina State Nigeria* Zama Atu tayi akan kujerarsu ta class, tana duban Hauwa data ware tana ta hidimarta bayan dawowarsu cikin class, yadda kasan ba ita ce ta gama bori d'azo a house ba. Atu ta ce "tabbas Hauwa kin shallake tunani na da hankali na, kin cika Hauwa hatsabibiya wallahi, ina dai raba ki Hauwa da yin k'aryar aljanun..... Da mugun sauri Hauwa ta toshe ma Atu baki da tafin hannunta tana zaro ido waje, tana wurga idonta tana bin y'an class d'in da kallo, ganin hankali y'an class ba kansu yake ba kowa ma harkar gabansa yake yasa Hauwa sakar mata baki tana cewa. "Gaskiya Atu bana son irin abunda kike min wallahi, haba dan Allah, yanzu da wani yaji ki fa? Shikenan kin tona min asiri kennan?, idan bazaki iya ganin yadda nake ba kiyi shuru da bakinki, domin wallahi ko ba k'aryar aljanu duk wadda ya tab'a ni nima sai na tab'a sa, kin sani kuma ai" Girgiza kai Atu tayi tana cewa. "Ni dai gaskiya nake fad'a miki" "Rik'e gaskiyar tak'i wata rana k'ila tayi anfani" "Au yanzu bata da anfani fad'ar ta kenan?" Gyara zamanta Hauwa tayi tana hararar Atu ta ce. "Da alamar haka gaskiya, nifa bana son shiga sharra ba shanu" "Au haka kike ce?, tom shikenan na daina shigar miki sharra ba shanu, idan hanyar da kika d'auka mai b'illewa ce ki ci gaba kinji Hauwa?" Turo baki tayi tana sa hannunta ta dafa kafad'ar Hauwa ta ce. "Nifa ba haka nake nufi ba, ba dai fushi kikai dani ba dai ko?" Wani murmushin gefen baki Atu tayi tana kallon Hauwa cike da sonta duk rashin mutumcin Hauwa ita kam bata mata shi, duk muguntar Hauwa bata ma Atu, bata ma son abunda zai b'ata ranta, daga Inna sai Atu sai Abba sune mutanan da Hauwa ke bala'in so a rayuwarta, sune kad'ai wani lokacin idan suka fad'a mata magana d'aya take daina shi. Atu ta ce "ni ko kad'an ba fushi nayi ba, ai kin sani fushi ba d'abi'ata ba ce" "Hakane kam na sanki ai ke y'ar Aljanna ce, ban tab'a gani ko tab'a jin labarin kina fushi ba" Atu zatai magana tana murmushi su Ammama suka shigo class d'in, domin duk yanzu ake dawowa ajin. Zama sukai Hadiza ta aje kular abincinta da jakarta, tana juyawa ta fuskanci Hauwa da Atu tana cewa. "Wai wani labari naji a cikin makaranta, na ce amma idan haka ne Ubangiji ya saka miki da alkhairi Hauwa" Zatai magana Atu ta wurga mata wani kallo shuru tayi tana turo baki gaba, Fatee ce ta amshe zancen da cewa. "Ai ko abinda kika ji dai shine gaskiya, domin ko yau Lamratu ta ci Jakin duka nake gaya miki harda su neman taimako" "Duk girman kan nan tana?, amma wallahi naji dad'i, inama house d'inmu d'aya da yau naci dariya, dan ba abunda zai hana banyi ta ba, sai dai ta kashe ni" Cewar Hadiza ta idasa maganar suna sakin shewa had'e da tafa hannu da Ammama. Shuru sukai jin Binta na cewa. "To y'an class d'in nan Malam Bahari ya ce a gaya maku gobe zaiyi texs had'e da amsar book d'in ko wannan mu domin zai duba note d'in mutum gaba d'aya, idan ma mutum yasan baya yi to yayi k'ok'ari yayi shi kamin zuwa gobe" Tana idasa fad'ar haka taje ta zauna a kujerarsu. Wani tsaki Hauwa tayi tana bin Binta da harara, Binta ko yanzu ko kallon saitin kujerar da su Hauwa take bata ma yi bare abunda zai had'ata da Hauwa. Atu ta kalli Fatee tana cewa. "Please Fatee kina rubutun Mlm Bahari duka ne?, ki bamu nida Hauwa muyi" Hauwa ta amshe da cewa "Ke ni fa bazan yi ba, text d'insa kawai zanyi, ni bazan iya rubutun nan ba, ya cika rubutu da yawa idan ya shigo wallahi" "Kar Allah yasa kiyi d'in, ke ce zaki ci jifgar banza ai ba ni ba ko?" Fad'ar Atu tana amsar book d'in da Fatee ta mik'o mata, fateen na cewa. "Kinga Hauwa ki rufa ma kanki asiri ki amsa kiyi rubutun nan, Mlm Bahari fa ba bugu yake ba, mugun Jakin aiki ne yake saka mutum, wadda sai ka gwammace dama bugun naka akayi wallahi ina gaya miki, shi zaki ga duk rashin jinmu muna kiyaye note d'inshi, idan ya shigo shida Mlm Add'au". Tsaki Hauwa taja tana tab'e baki ta ce "Nifa badan ina tsoronsa zanyi ba yawwa a'ato" Dariya kawai Atu tayi tana yin rubutun ta ce. "Da kar kiyi mana y'ar neman rigima" Bugun wasa Hauwa ta kai mata tana cewa. "Atu bana son abunda kike min fa" Hadiza ta kalli Atu ta ce. "Yawwa please idan kin gama ki d'an bani zanyi na shekaran jiya, da yayi ban idasa note d'in ba, wani waje ya goge, dad'i dashi idan baka da saurin rubutu bakwa idasa rubutu a tare dashi, dole ne sai ya wuce ka" Da to Atu ta amsa tana rubutunta. Hauwa ta ce. "Kinga Fatee zaki ara min book d'in idan naje gida zanyi ni, dan banzan iya yanzu ba gaskiya" To kawai Fatee ta amsa suna mik'ewa a tare jin an kad'a k'araurawar fita break, yau tunda suka shigo class ba Malamin daya shigo har aka kad'a k'araurawar........... *RAYUWAR MAKARANTA* *©Zahra Royal Star* Page 6 *Government Secondary School Rimaye Katsina State Nigeria* Class d'in yayi shuru sai muryar Mlm Bahari dake tashi yana kiran sunayen y'an class d'in, sai kuma magana k'asa-k'asa dake tashi ta y'an class d'in. Mlm Bahari dake tsaye rik'e da takardun text d'in da yayi masu jiya bayan ya amshe book d'in kowa, littatafan na aje gefansa, sai ya gama raba masu text d'in kamin yazo ga book d'in. A hankali yake kiran sunayen mutane duk wadda yayi abun kirki sai ya tsayar dashi an tab'a masa. Masu k'ok'arin ajin sai wani kankanba suke suna wani shan k'amshi. Ciki harda wata Hafsat da Asiya. Atu ta kalle su tana tab'e baki, dan Allah ya sani Atu ta tsani mutum mai nuna girman kai da son asanin shi wani ne, su kuma ta lura haka suke nuna isa da wata yangar banza a cikin makarantar. Tab'o Hauwa dake hidimarta tayi, ita ko a jikinta ma. "Wai ke tunda muka fara school d'in nan, baki lura da wa'incan su Hafsat d'in ba, sai jin kai da d'aukar kansu su wasu ne, baki lura bane?, dan naga basa ma shiga harkar y'an class d'in nan, sai mutum ya kai suke masa magana" Tsaki Hauwa taja tana shirin magana Mlm Bahari ya kira sunanta. A hankali ta mik'e ta fice gaban allon, y'an class d'in sai binta suke da kallo ganin yadda Mlm Bahari ke jifanta da murmushi. Tana k'arasowa ya mik'a mata takardar yana cewa. "Wow gaskiya kinyi k'ok'ari Masha Allah, da haka kike maida hankali a class ai da ba haka ba, kinyi k'ok'ari sosai, y'an class a tafa mata dan Allah" Sosai aka d'au tafi, ita kam Hauwa d'an k'aramin murmushi ta saki ta amsa ta koma ta zauna. Tana kallon su Asiya ta wutsiyar ido yadda suka bin ta da harara k'asa-k'asa. Zama tayi tana cewa. "Idan banda abunki Atu, ai basu tab'a shigowa gona ta bane shine yasa, ina nan ina jiran ranar da zasu tab'o ni zan nuna masu ko wacece ni" Ammama data amshe takardar Hauwa tana murmushi ta ce "Kaii ashe zamu ci wannan text d'in, duba ki gani duk abunda kika fad'a mana shine muka rubuta, kuma kinga kin cinye goma bisa goma fa Wow, ashe Hauwar tamu ba banza ba, kan nata yana ja" Dariya Hauwa kawai tayi. Tabbas akwaita da wasa da jan fad'a, amma ta b'angaran karatu, baka tab'a cewa tama iya wani abu, sai anzo fagen exam's ko wani abu, nan ne zaka ga takardunta sunyi kyau sosai, dan ko a class bata cika idan Malamai sunyi tabbaya ta tashi ta bada amsa ba, a'a a wajan exam's ko text ne kake gane Hauwa tana da shegen k'ok'ari" Atu ko murmushi itama tayi domin ita tasan Hauwar akwai kaii kawai dai bata nunawa saita kama ne. *Asalinsu Hauwa* Asalinsu Hauwa, iyayenta y'an katsina ne, Fulani ne gaba da baya. Inna su biyu ne ta haifa Rabi'u sai Nura Abba kenan, Mahaifin Hauwa wadda suke kira da Abbi. Abbinta mai kud'in gaske ne, sai Mahaifiyarta Hauwa'u, mace mai kirkin gaske, tunda ta auri Rabi'u basu tab'a samun haihuwa ba, har tsawon shekaru masu dama, har tsofa ya fara tasar masu, Mahaifiyar Rabi'u wato Inna, bata wani matsanta masa cewa ya k'ara aure ba, Abba ko shi ya riga Abbi aure shi yasa ya rigasa samun y'ay'a duk da haihuwar ta Allah ce, har D'an Abba yayi wayo wato Abdallah, Shuru kake ji, har Matar Abba Haj Nuriyya ta sake samun ciki, amma ta b'angaran su Abbi shuru, sosai Hauwa'u ta sake tada hankalinta, Abbi ne ke k'ara kwantar mata da hankali harda ma Inna, tunda Hauwa'u take bata tab'a ganin suruka mai kirkin Inna ba, da sanin ya kamata, domin harda ita ake sa baki domin tausarta da kwantar mata da hankali. Lokacin da cikin Nuriyya ya shiga wata Tara, dai-dai lokacin ne kuma Allah ya d'orawa Hauwa'u wani ciwo, kullum da zazzab'i take kwana, tak'i kuma aje asibiti da ita, Inna ce tayi mata jan ido harda Innar aka tasa ta a gaba suka je asibiti, an mata gwajeje, sakamako na fitowa doctor yayi masu kyakykyawan albishir d'in cewa Hauwa'u nada shigar ciki na tsawon wata uku. Wai wai wai karko so ganin irin tsananin murna da farin ciki da wa'innan ahali suka shiga, dan Abba da kansa yazo katsina aka had'a wata y'ar lifaya akaci aka sha. Inna a ranar ta ce a bata Hauwa'u ta tafi da ita Rimaye, Mahaifar su Abba, ta tayata rainon cikinta. Ba yadda Abbi ya iya shima ya tattara kayansa suka koma Rimaye kusa da Inna. Kota ina Hauwa'u gata take gani kulawa ta musamman Inna ke bata, sai abunda take so take ci, da ta motsa kad'an Inna zata fara tabbayar Ina ne ke miki ciwo?, shi kansa Abba daga can Kano kullum cikin aike yake masu na kayan dad'i, duk da babu abunda suka nema suka rasa. Cikin Abba da Abbi baka tab'a gane wanene yama fi wani Dukiya, idan kaga gidan da suka gina ma Inna a Rimaye zakai mamaki, babu alatun duniyar da ba'asa mata ba, shi yasa koda Hauwa'u ta dawo garin da zama bata ji komai ba, saboda babu ce kawai babu a gidan Inna. Bayan wasu kwanaki Nurriya ta haihu, Y'a mace, murna sunyi sosai inda Abdallah ne cikin Family yanzu dan har ya fara d'aukar wasu nauyi na Familyn nasa. Ranar suna akasa ma yarinyar sunan Inna wato Nana Khadija, suna kiranta da (NahNah). Duk da lokacin Hauwa'u tana laulayi hakan bai hanata zuwa sunan Nahna ba, har kwana biyu sukai a Kano ita da Inna, suka dawo. Cikin Hauwa'u na wahalar da ita sosai, wadda har Inna abun ya fara bata tsoro, domin idan suna zaune da Hauwa'u ta kama cewa "Inna anya wannan cikin bana tafiya bane kuwa?, ki duba kiga kullum cikin ciwo nake, yau lafiya gobe babu" Murmushin k'arfin hali kawai Inna tayi tana cewa. "Kufa yaran zamanin nan, kun cika raki da yawa, mu zamaninmu duk ba haka mukai renon cikin ba, kema dan haka lafiya lau zaki sauka, baga y'ar uwarki nan ba Nurriya ta haihu k'alau" Murmushin itama Hauwa'u tayi tana d'an gyara zamanta akan kujerar tsakar gidan da suka fito suna shan iskar hantsi, cikin nata yayi girma sosai haihuwa yau ko gobe, ta ce. "Hakane Inna, amma kin san ko wacce haihuwa da kalar nata salon" Ware y'an yatsunta Inna tayi tana kai ma Hauwa'u Dak'owa tana cewa. "Ungo nan Hauwa'u, ke kin tab'a haihuwar ne?, ba sai yanzu ba, baki san ya take ba, dan haka kisa ma ranki salama insha Allahu lafiya sumul zaki sauka" Inna ta k'are maganar cikin zolaya. Dariya Hauwa'u tayi tana sa tafin hannunta ta rufe fuskarta, domin idan irin wannan wasan ne ta saba da Inna, idan ka gansu ka rantse da Allah ba suruka bace, kai ka ce uwa da Y'a ne. Abdallah ya fara aikinsa ya zama cikakken mutum yanda yake koyar a wata makaranta mai suna School Of Hygiene dake cikin garin Kano, an basa babban matsayi, Abba ba dan yaso aikin ba, sai dan Abdallah ne ke so, Abba yaso yayi aiki a companynsa, amma ganin kota ina babu abunda Abdallah bayayi hatta aikin Companyn yana zuwa, kawai ya raba aikin biyu ne. A wata rana yaje shopping suka had'u da Lubna, D'iyar wani hamshakin mai kud'i ce itama, tunda ta d'ora idonta akan Abdallah Allah ya d'ora mata bala'in sonsa da k'aunarsa. Ta addabama rayuwarsa, har sai da ya amince da ita, aka kai maganar wajan manya, ba'a wani dad'e ba su Abbi sukai jagoranci aka d'aure auran, ba'a wani ja lokaci ba. Inda haka nan akai bikin Hauwa'u na gaf Hauwa'u haka ta d'aure aka gama hidimar biki, dan Allah kad'ai yasan abunda take ji, d'auriya kawai take. Anyi biki da kwanaki, halin Lubna wadda Abdallah bai san dashi ba ya fara fitowa fili, domin k'azama ce da ta sosai ta saba komai a gida yi mata ake, hatta gyaran gado bata iya ba, shi kuma Abdallah yafi so komai nasa ace matarsa ce ke masa shi, ba wai y'ar aiki ba, idan yayi mata k'orafi sai ta rink'a ce masa "yafa tuna ba y'ar Malam Shehu ya aura ba, da zata je tana masa bauta kamar wata jaka, to ita bafa mai aiki ya auro ba. Danma tana mugun shakkarsa domin ko a school d'insa baya d'aukar raini kowa ma ya sani, duk Malaman makarantar ana masu shaidar bin mata da son y'an matan tsiya amma banda Mlm Abdallah ya kame kansa, k'aryar yarinya ta ce ya tab'a mata wata maganar banza, babu fuskar ma yarinya da zata kawo masa raini, amma sai cikin gidansa, kodan taga gadon baccinsa ne, kuma bai d'auki y'ar aikin ba, sai dai ita Lubnar tasa aka samo mata daga gidansu, da kanta take biyanta duk wata, to amma wani lokacin y'ar aikin ba zuwa take ba, saboda itama akwai hidimomin Yara dake kanta, ta sake y'ar aiki yafi sai biyar duk batai dacen su ba, a haka dai da kyar ta sami wata y'ar yarinya, tun wata rana da ta kama yarinyar wai tana kallon mata Miji tana jifansa da murmushi, wai harda cewa tana kashe masa ido, shi a lokacin ma Abdallah dariya abun ya basa, ko wacce y'ar aikin da zata samo tsabar zargi da rashin yarda suke rabuwa da y'an aiki da yawansu, kwata-kwata bata son wata Y'a mace ta rab'i mijin nata ko misik'ala zarratin. Ranar wata Litinan, Hauwa'u ta tashi da nak'uda, ranar su Inna sunga tashin hankali, wadda basu tab'a gani ba, domin suma Hauwa'u ta rink'a yi tana rik'e da cikin nata, ba abunda take sai Addu'a a bakinta, domin Inna tana ganin yadda cikin Hauwa'un ke juyawa kamar D'an dake cikin nata zai fasa cikin ya fito duniya, tsabar yadda fatar saman cikin ke juyawa. Hankali a tashe Abbi ya d'auke su sai Katsina suka nufi asibiti, kamin su isa Inna ta d'auki waya ta kira Abba dake Kano shima hankali a tashe a ranar, duk da Yamma tayi, haka ya tasa Abdallah gaba da Haj Nuriyya suka taho Katsina, da Abdallah ya gaya ma Lubna sai cewa tayi Allah ya tsare ita fa ba zata wata katsina ba, yaji mugun haushin abunda ta ce, dan kawai suna sauri ne, hankalinsa kuma baya gareta yau da ya bata mamaki wallahi. Sadda su Abba zasu iso Hauwa'u ta wahala iya wahala, dan har Abbi yasa hannu za'a shiga da ita tiyata, a ciro abunda ke cikin nata, Inna ba abunda take sai kuka, zuwan su Abdallah nema yasa Abdallahn rarrashin Inna, yana kwantar mata da hankali, Inna ta lura da babu Lubna a tafiyar, taso ta ce wani abu, to amma ganin hankalinsu ba'a kwance yake ba yasa kawai ta shanye maganar. Shi ko Abba wajan Abbi ya nufa shima yana basa baki, Momy (Haj Nuriyya) itama ta kasa zama sai zarya take, ga Nahna dake hannunta yarinyar sai wani irin kuka take kamar wacce ake zarema rai, ta rasa inda zata sa kanta, kukan yarinyar duk shi ya k'ara rud'a masu tunani, domin har Inna sai da ta amshe ta amma yarinyar nan tak'i shuru kamar wacce ake mintsini. Ana gaf shiga tiyatar Hauwa'u da aka turo akan gadon asibiti ta ce ma doctors su d'an dakata. Kamo hannun Nurriya Hauwa'u tayi tana kallon Abba da Abbi tana cewa. "Ba lallai idan an shiga dani tiyar nan ba na fito da rai na, ina rok'on wata alfarma a wajanku?" Da sauri Inna ta k'ara rik'e hannun tana cewa. "Haba Hauwa'u ki fad'i komiye a wannan duniya kike so ayi miki kamar anyi an gama insha Allahu" Murmushi mai ciwo Hauwa'u ta saki, tana k'ara jan lumfashi, da take fitarwa da kyar, ga wata irin zufa da takeyi cikin k'arfin hali ta ce. "Ina so idan mace na haifa, dan Allah Abba da Abbi ku aura ma Abdallah ita" Ta waiga inda Abdallah yake zaune kansa a k'asa idonsa sun kad'a sunyi jawur, saboda yana bala'in son Hauwa'u, domin sun shak'u kamar ita ce ma ta yaye shi tun yana yaro yake zuwa katsina ya dad'e a wajanta. Ta mik'a masa hannunta ya taho a hankali ya rik'e hannun nata, da ta cire sa daga hannun Nurriya ta rik'e na Abdallahn. Ta ce "D'ana nasan zaki rik'e duk yarinyar dana haifa da daraja, dan Allah karka bari tayi kukan maraice, koda ace namiji na haifa karka bari yayi kukan rashin uwa kaji D'ana" Wasu hawaye ne suka soma gangaroma Abdallah, dole tasa doctors tura gadon da take da sauri aka shiga d'akin tiyatar da ita, saboda ganin yadda jikinta ya d'auki wata irin jijjiga. Inna zubewa tayi a wajan tana kuka marar sauti, Momy ma idonta sunyi jawur ga Nahna dake kuka kamar wacce aka gaya ma miye zai faru. Bayan tsawon awa biyu doctors suka fito suna share zufa, hannun wata Doctor rik'e da jinjiri a hannunta wadda aka nad'e da farin tawul. Da mugun sauri su duka har suna rige-rigen tabbayar Ina Hauwa'u take, ko wanne tabbayarsa ita ce ina Hauwa'u take, basu damu ma da abunda aka samu ba. Doctor cike da tausayin wa'innan ahali da kyar ta iya bud'e baki ta ce. "Sai hakuri, dama tun kamin ma mu shiga tiyatar da ita Allah ya amshi abunsa, tiyatar ma babu ranta mukayi mata, domin munga abunda ke cikin nata har lokacin yana motsi, shine yasa kawai muka ceto abunda ke cikin nata. Gata nan Y'a mace ce aka samu" Doctor na rufe baki Inna ta zube a sume, wani irin salati suka saka a tare, da gudu wani Doctor ya matso da gado aka sa Inna aka yi d'aki da ita. Ya tsaya yana ma Doctor d'in data gaya masu mutuwar fad'a yana cewa. "Danmi zata tsaya haka ta gaya masu mutuwa haka, ai ba'a sanar da mutuwa a tsaye haka, bare da irin su Inna a wajan", hakuri ta rink'a basu tana mik'a masu d'iyar. Abba ne ya amshi yarinyar, Abbi ko duk ya zama kamar zararre yana tsaye ne kawai hawaye masu d'umi keta masa zarya akan fuskarsa. Haka wa'innan ahali suka kasance a wannan rana cike da tashin hankali, da kyar Inna ta farka, domin sadda zata dawo hankalinta har ankai Hauwa'u gidanta na gaskiya, domin Abbi ne ya bada Umarnin haka, domin sunga alamar idan Inna ta tashi taga gawar Hauwa'u, ba k'aramin tashin hankali zata k'ara shiga ba. Inna tayi kuka sosai, aka bata yarinyar data haifa ta rik'e yarinyar sosai tana kuka tana kallon fuskar yarinyar, kamar su d'aya da Hauwa'u, a hankali Inna ke sauk'e ajiyar zuciya tana rungume da yarinyar. Kwanan Inna biyu aka sallamota daga asibitin suka taho Rimaye, a nan akai addu'ar uku. Madara aka fara ba yarinyar, kawai domin babu wacce zata shayar da ita. Tunda akai mutuwar Abbi bai sake lafiya ba, kullum cikin ciwo yake, sai ya rink'a wani tari wadda tun yana b'oye ma Inna harta fahimta, domin idan yana tarin har shid'ewa yake, jini na masa zuba ta baki ta hanci. A ranar da Inna ta ga wannan abu idan ranta yayi dubu Toya tashi, a ranar bata bari ba sai da ta kira Abba take sanar dashi, shima kansa Abba hankalin yayi mugu mugun tashi ba d'an kad'an ba. Da kyar suka lallab'a Abbi aka tafi dashi k'asar India, domin duba lafiyarsa, daga Abba sai Abdallah suka tafi aka bar Inna da Momy a gida Nigeria. Ba irin surutun da Inna batai ma Lubna, domin taga yarinyar bata da tarbiyya ko kad'an, ai ko Inna ta d'au alwashin su Abba na dawowa daga India zata sa a d'aura auran Abdallah da Yarinyar da Hauwa'u ta bari, gara ayi tun tana da rai, gara ayi auran ko hankalinta ya kwanta, domin taga matar Abdallah kanta rawa yake akan mijinta. Dawowar da Abbi baiba kenan da ransa a k'asar Nigeria, domin a can tun kamin su isa India Allah ya amshi abunsa. Abba yayi kuka, yayi kuka, kamar ransa zai fita shima, ji yayi kamar zai zare tsabar tashin hankali, Abdallah ne mai k'arfin halin kiran Momy ya fara sanar da ita yana kuka, inda suka yanke kar a sanar da Inna har sai an dawo da gawarsa. Kusan satin su biyu suna ciku-cikun yadda za'a dawo da gawar gida Nigeria, saboda sai da suka isa k'asar Indiar suka fahimci Abbi rai yayi halinsa tun a cikin jirgi. Idan Inna ta kira waya a Bata shi sai dai ayi mata wata k'aryar ko bacci yake ko wani abu. Tun Inna na yarda har jikinta ya fara bata ba lafiya ba. A ranar da zasu dawo haka Nahna ta rink'a wannan kukan kamar irin wadda tayi a sadda Hauwa'u zata rasu. Lokacin da aka shigo da gawar Abbi a cikin gidan Inna, lokacin da Inna tayi tozali da Gawar tasa, sai Allah yasa mata wata irin dangana da juriya, amma kam taci kuka kamar mi, a ranar ta k'ara rik'e Yarinyar da Hauwa'u ta haifa, tana kuka cike da tsananin tausayin yarinyar da zata taso babu uwa babu uba. Bayan anyi arba'in, Abba yaso amshe yarinyar wacce taci sunan Mahaifiyarta Hauwa, ya rik'eta a gidansa Kano, inda Inna ta murje ido ta nuna baza tab'a basa Hauwa'u ba, ita kad'ai take gani taji dad'i. Ba yadda Abba ya iya haka ya bar mata Hauwa, amma fa komai na rayuwa Abba bai bari yarinyar tayi kuka dashi ba, hatta dukiyar da Abbinta ya bari, shine yake juya mata ita, kuma bai bar garin ba sai da aka d'aura auran Abdallah da Hauwa, tun tana jaririyarta. Sosai yarinyar tunda ta fara tasawa bata jin magana kwata-kwata, ga jan fad'an tsiya, amma akwaita da shegen k'ok'ari kamar mi a makarantar Boko da islamiya, saboda tun tana y'ar shekara biyar ta sauk'e al'qur'ani mai girma. A sadda zata gama primary taso akaita boding school Inna ta hana, saboda bata son abunda zai raba ta da Hauwa. Hauwa ko tasha kuka tana shagwab'ar Inna da Abba sun hana a kaita boding school, shine da Abba ya kira yana rarrashinta tak'i amsar wayar, tana turo baki, inda Abba yayi mata al'k'awarin sai siya mata Keke ko mota a rink'a kaita school d'in saboda yaga akwai nisa sosai makarantar daga cikin gari. Ai ko Hauwa nan take ta ce ita fa bata son komai a barta ta tafi da k'afarta, bata son asai mata komai, ba yadda Abba ya iya ya hakura da sai matan, ba dan yaso ba, sai dan farin cikin Hauwar, domin duk abunda take so shine yake mata. Tun kamin ta kai haka suka had'u da Atu, a makarantar Islamiya tare suke zuwa, da yake unguwa d'aya suke, layin gidansu ne kawai ba d'aya ba, sunyi mugun sabo da Atu wadda har idan Atu ta nuna b'acin rai ga wani abunda Hauwar keyi, take daina sa ba gardama, daga Atu sai Abba sai Inna kawai suke iya tankwasa Hauwa wani lokacin. Kuma har yanzu Hauwa bata san da auran Abdallah a kanta, hatta Lubna itama iya tsawon shekaru bata san dashi ba, inda har yanzu Lubna tak'i ta bari su haihu, Abdallah kuma yana son Yara ba kad'an ba, amma ya fuskanci matsalar tana daga wajan Lubna, dan ita cewa tayi bazata haihu yanzu ba, haka kawai aja mata tsufa da wuri....... *RAYUWAR MAKARANTA* *©Zahra Royal Star* Page 7 *No. 12, Kawo Bos Stop Kano Nigeria* Kwance take akan gado tayi d'ai-d'ai sai sharar bacci take. Tsaye yake akanta yana kallonta cike da mamakinta, a hankali yasa hannunsa ya d'an bubbuga k'afarta. A d'an firgice ta tashi tana mistsitsike idonta, kallonsa take cike da magagin bacci ta turo baki gaba tana cewa. "Fisbilillahi Honey miye haka?, zaka wani tayar dani ina baccina mai dad'i" Tsaki yaja yana cewa. "Kin duba k'arfe nawa kuwa?" "To ina ruwa na da k'arfe nawa, yanzu miye zanyi maka kuma?" Kallonta yake ransa ya soma b'ace ya ce. "Kin san fa da tafiyar da zamuyi zuwa Rimaye, kuma harda ke na ce zanje, dan mi zaki nemi waje ki kwanta, kuma kin san da tafiyar, tunda tun jiya na gaya miki" Tsaki taja ciki-ciki ta ce "Nifa gaskiya baza ni ba, bazanje wannan K'auyen ba haka kawai, kaima dan ba yadda zanyi ne na hanaka zuwan" "Mi kike nufi ne garin Iyayen nawa kike kira da K'auye?" Tashi tayi ta sakko daga gadon tana nufar toilet tana sake cewa. "Ni karka min wata fassara yawwa, amma gaskiya ni bazan biku ba, sai kun dawo gaskiya, domin yanzu idan ma na ce zan biku to tsayar daku zanyi kawai saika dawo" Tana idasa fad'ar haka tayi shegewarta toilet ta barsa nan a tsaye. Wayarsa sa ce ta d'auki k'ara, hakan yasa ya katse tunanin daya fad'a ya ciro wayar daga aljihon gaban rigarsa, yana d'aukar kiran, ganin Abba ne ke kira. "Yeah Abba gani nan zuwa insha Allah" Abinda ya ce kenan ya katse kiran. A hankali yayi parking motarsa a parking lot na gidansu. Mai gadi ya k'araso wajan yana mik'a masa gaisuwa, gaisawa sukai a mutumci, kamin yayi cikin babban parlon gidan nasu. Sallamarsa a parlon tayi dai-dai da sakkowar Nahna, daga kan bene. D'an kallonta yayi ganin yadda taci wani magani, kamar wacce take jira ace tak ta fashe da kuka. Tsaki ya saki yana duban su Abba da Momy dake a shirye dama shi suke jira kawai, hakan yasa suka mik'e a tare. Momy ta kalli Abdallah da d'an mamaki tana cewa. "Ah ina ita Lubnar take?" Sosa kansa Abdallah yayi yana d'an basarwa ya ce. "Momy wai bata da lafiya ne shi yasa, bazata iya zuwa ba" Kallon tuhuma take jefansa dashi kamin ta ce. "Na rasa wacce irin mata ce Allah ya baka Abdallah, amma komai ya kusa zuwa k'arshe da izinin Ubangiji, domin bazan zuba ido mace d'aya ta lalata maka rayuwa haka ba, ace tsawon shekara sha biyar, ko wadda zai irink'a maku addu'a baku aje ba, ace kuma matsalar komai da kake ciki matarka ce sila dol..... Da sauri Abba ya d'aga mata hannu yana yin gaba yana cewa. "Please Momyn Yara ki bar zancan nan muje kawai" "Uhmm" Kawai Momy ta amsa tana kallon Nahna dake turo baki gaba. Momy ta makama mata harara ta ce. "Ke kuma idan baki daina mana wannan bak'in halin naki ba, na rashin son jama'a da mutumta danginki, sai naci Ubanki wallahi, dan ubani garin Mahaifin naku kike ikirarin kefa baki zuwa K'auye, saboda kin raina mutane, haka naga kina ma Hauwa wani jijji da kai, ki kiyaye Nahna wallahi" K'ara zunburo baki tayi tana cewa. "Kiyi hakuri Momy" Ko kallonta Momy batai ba tayi gaba rik'e da jikarta a hannu, tana d'an latsa wayar dake hannunta. Abdallah shima ya jefa mata wani kallo daya sa Nahna Shan jinin jikinta ya ce. "Idan baki daina wannan halin naki na wulakanci ba, wallahi wata rana saina barki kwance, shashasha kawai" Shima yana fad'ar haka ya fice daga parlon yana tsakin tsaki. Da saurinta ta take masa baya, kamar tayi kuka haka take ji, dan Allah ya gani ta tsani zuwa K'auye a rayuwarta, duk sadda zasu je Rimaye kullum sai ranta ya b'aci. *Government Secondary School Rimaye Katsina State Nigeria* Ammama ta d'an kalli tsiraron mutanen da yau suka zo school d'in, sakamakon an gama exams ta first term, ana wasan sati d'aya kamin a bada hutu. Bobe zata kasance juma'a ne ranar da za'ayi hutu ce. A hankali ta juyo inda su Hauwa suke ta ce. "Please kuzo muje hanyar gidan mutum d'aya musha magarya mana, da zaman banzar da muke Yi" Da sauri ko Hauwa ta mik'e tana cewa. "Kuma wallahi kamar kin san zaman nan ya ishe ni haka, shi yasa jiya ban shigo school d'in nan ba, duk ga yarinyar data jamin zuwa nan yau" Ta k'are maganar tana nuna Atu, data mik'e tana kallon su Ammama da sukai radin tafiya shan magarya. Atu ta girgiza kai tana cewa. "Kai Kai Kai shan magarya har kuma wajan gidan mutum d'aya, gaskiya bada ni ba Hauwa kema bazan bari kije ba" Wata y'ar iskar harara ta jefama Atu tana yin gaba tana cewa. "Su Hadiza dalla can ku rabu da ita ni kunga tafiya ta, kuzo muje, dama idan aka biye take ai babu abunda za'ayi, matsoraciya kawai" Da d'an gudu Atu tabi bayansu tana cewa. "Dan Allah karku sa dole sai munje wata shan magarya, ni gaskiya tsoro nake ji wallahi" Hauwa ta d'an tsaya tana rik'e k'ugunta ta ce. "Wai tsaya Atu wani ya ce ki biyo mu ne?, kiyi zaman ki mana, dole aka ce ki biyo mu shan magarya ne?" Dafe kanta Atu tayi ta ce. "A'a amma ai kin san bazan tab'a zama na barki ki tafi ke kad'ai ba ai ko?" Ci gaba da tafiya Hauwa tayi su Fatee suna take mata baya, sai nausawa cikin daji suke, suka fito daga school d'in suka mik'e titi kamar zasu bar gari. Ba dan Atu na so ba ta bi bayansu, sai dan bazata iya zama ita d'aya a cikin school d'in ba, saboda duk yawanci babu yawan D'alibai. Sosai suke shiga cikin daji suna kutsawa duk inda suka ci karo da magarya sai sun tsaya sun tsiga son ransu, sai da suka cika leda ko wacce ta samu da yawa, Atu badan tana so ba ta d'an d'iba kad'an. har yanzu zuciyar Atu cike take da tsoro kar ace suga wani wadda suka sani a cikin dajin nan, ko su had'u da y'an SS3. Sun gaf isa gidan mutum d'aya, suka tsaya, sai da suka ci uban yawo kamin Atu ta bud'e baki ta ce. "Dan Allah Hauwa mubar tafiyar nan kizo mu wuce gida haka nan" Juyawa sukai su duka suka kama hanyar dawowa school suna tafe Hauwa na cewa. "Ban tab'a ganin matsoraciya irinki ba, ba gashi yanzu har munje mun dawo ba, bamu had'u da kowa ba, da har kina cewa zamu had'u da y'an SS3, idan ma mun had'u dasu ai suma shan magaryar ne ya kawo su, miye zasuyi mana?" Tana rufe baki Atu ta tab'a ta tana nuna mata hanyar dake gabansu idonta a zare. Gaba d'aya suka ja suka tsaya suna duban Y'an SS3 dake a gabansu suna masu kallon yau zaku ci ubanku" Wani miyau Atu ta had'e tana cewa. "Ai dama sai da na gaya maku shikenan yau mun bani mun shiga uku, Allah kad'ai yasan matakin da zasu d'auka akanmu" Tsaki Hauwa ta saki da ganin farko ta d'anji tsoro amma sai ta ce. "Ke dallah can karki wani damu babu abunda zasu iya yi mana" Ita dai Atu ba dan ta yarda ba suka k'arasa inda suke. Nan take ko, suka sasu duk'awa k'asa kan gwaiwowinsu. Su Hadiza ba abunda y'an cikinsu keyi sai kuka, cike da tsoro suka fara basu hakuri. Sai cewa sukai. "Kaii dan ubanku ubanmi kuke a cikin daji haka?, saura wani abun cutarwa ya sameku kuja ma makaranta b'acin suna ko?" Had'e hannu Atu tayi alamar ban hakuri tana cewa. "Dan girman Allah kuyi hakuri" "Ai ko yau zaki gane shayi ruwa ne, domin wajan Malamai zamu kaiku, su ai kunga sai kuyi masu bayanin abunda kuka je yi a cikin daji" Kuka Atu ta fashe dashi tana cewa. "Dan girman Allah karku kaimu wajan Malamai, kuyi hakuri kuyi mana hukunci a nan, ba sai munje wajan Malamai ba" Wani daga ciki y'an SS3 ya ce "Ke rufe mana baki, fad'a min sunayenku d'aya bayan d'aya" Ya idasa maganar yana sakko da jakarsa, ya yago faifa. Hauwa ko a jikinta saima ta fara fad'in sunanta, harda su Hararar Atu domin ji take duk ta zubar masu da mutumci harda wani yi masu kuka. Haka suka rubuta sunansu, suka tasa k'eyarsu a gaba zuwa cikin makarantar. Suna tafe Atu na sharb'ar kuka, Hauwa sai harararta take, Atu ko ji take kamar ta shak'o Hauwa. Suna gaf shiga makarantar Atu taga giftawar wata mota mai shegen kyau, dan kamar ta tab'a ganinta a wajan gidansu Hauwa da dad'ewa. Atu duk da halin da take ciki hakan baisa ta kasa cewa. "Lahhh Hauwa Kinga wata mota can ta wuce kamar nasan motar nan a gidanku, kamar y'an uwanku dake Kano ne suka zo Rimaye" Da mugun sauri Hauwa ta waiga, sai dai motar har tayi nisa kad'an take hango ta. Hauwa ta ce. "Ehh k'ila sune, domin dama Inna ta ce min yau ne zasu zo, kuma kamar can zanyi hutuna ma. Amma ni wallahi banso zuwansu ba" Ta k'are maganar had'e rai. Atu ta ce "Kamar ya baki son zuwa?, birnin ne baki son zuwa?" "Ke miye a birni to wadda K'auye babu?, ni haka nan bana son zuwa, saboda kinga wannan Nahnar na tsane ta, kamar yadda take nuna min bata son y'an K'auye, duk sadda naje Kano fad'a kawai muke da ita, sai wannan matar Y Abdullahn Lubna, dan ita tsabar wulakanci ta ce ma Nahna ban waje, shi yasa y'an Birni basa birge ni, wulakanci ne dasu wallahi" Atu ta sake rik'e baki ta ce. "Tabd'i jam mu kinga bamu da y'an uwa a birni gaskiya, idan ko hakane to basu da kirki" Hauwa zatai magana suka k'araso inda Malamai ke zama a bakin wata bishiya suna shan iska duk sun fito daga office nasu. Atu sai y'an cikinta suka k'ara hautsinawa. Ashe har Y'an SS3 sun rigasu isa sunyima Malaman bayanin komai. Suna zuwa Mlm Add'au ya banka masu wata uwar tsawa ya ce. "Wato ku y'an iska ne ko?, to maza ku nuna mana yadda ake hawan bishiya, tunda naga shan magarya kuka je maza ku nuna mana yadda ake shan magaryar" Su Hadiza sai hakuri suke basu, suna duk'awa k'asa gaba d'ayansu. Sauran Malaman suka sa Y'an SS3 d'in su d'ebo masu Daman bulali masu yawan gaske. Ai ko Atu tunda tayi tozali da yawan bulalin da aka d'ebo ta fara kuka kamar k'aramar yarinya. Ko wanne Malami sai da ya d'auki bulala biyu-biyu masu kauri da tsayi, Malaman dake wajan sun kai su biyar a zaune a jere. A tafin hannu suka fara bugunsu, Hauwa ce ta farko, ko wanne Malami dake zaune a wajan, sai yayi masu bulala biyar-biyar, idan ka had'a kusan bulala arba'in da biyar kenan. Iya buguwa sun bugu domin hannun Hauwa sunyi jawur jini har yana kwanciya, Atu da Ammama ne kawai kake jin kukansu a wajan, baya ma Atu tasha kuka kamar ba gobe, sai tsine ma Ammama Atu keyi, domin ita ce ta fara kawo maganar tafiya shan magarya. Tafe suke bayan an gama masu hukunci Atu sai jan majina take a hanci tana cewa. "Ai wallahi Ammama kin cuce ni bazan yafe ba" Murtukewa Ammama tayi tana murza hannunta daya duka tana cewa. "Haba Atu da wanne zanji ne?, kima kyale ni da dukan da mukasha" Tsaki kawai Atu taja tana kallon Hauwa ta ce. "Ke kuma gobe sai ki k'ara janmu muje shan magarya" Shuru Hauwa tayi tana murgud'a baki. Idasawa aji sukai suka d'au sauran kayan su, suka fito suka kama hanyar zuwa gida. Shigar Hauwa gidansu yayi dai-dai da sawo kai da Abdallah yayi, sai Allah yasa sukai k'aro da juna. A mugun zabure Hauwa tayi baya, amma duk da haka sai da Abdallah ya d'aga hannun ya sharara mata mari. Da sauri ta rik'e kuncinta tana kallonsa da mamaki. Dama ya saba mata haka, tasan da dad'ewa ba wani k'aunarta Y Abdullah yake ba. Zata bud'e baki tayi magana, ya riga ta cewa. "Ke wacce irin marar hankali ce?, shashasha kawai k'azama, dube ki da'aAllah, kina tafiya kamar ba mace ba, babu natsuwa ko kad'an a tare dake" Wasu hawaye masu zafi ne suka soma gangaroma Hauwa, tana jin zuciyarta na k'ara tsanar Y Abdullah duk da wata zuciyar tata na bala'in sonsa da birgeta. Ta sake jin saukar maganar sa yana cewa. "B'ace min da gani a nan wajan" Jiki a sanyaye ta rab'asa ta wuce tana goge hawayen dake mata zuba. Tana shiga da gudu taje ta haye cinyar Momy dake mata dariya sai murnar ganin juna suke, harta manta da abunda Y Abdullah yayi mata ma. Abba dake kallonsu ya a murmushi ya ce. "Ah ah Hauwar Abbanta, baki ga Abban naki bane, Momynki kawai kika gani ko" Da sauri Hauwa ta mik'e taje inda Abba yake ta rungumesa tana cewa. "A'a Abba duk murnar ganinku ne yasa ai" Wani tsaki Nahna dake gefe, ta saki k'asa-k'asa tana bin Hauwa da wani kallon banza. Inna ma murmushi take tana kallonsu cike da sha'awar ahalin nata. Tashi Hauwa tayi ta ce. "Momyna bari naje na cire uniform nazo" Zata wuce ta gefen da Nahna ke zaune ko ci kanki bata ce ba, kuma ta ganta itama, amma Hauwa ta k'ara kame kanta domin idan raini ne Hauwa ta tsane sa, shi yasa ko kallon inda take batayi ba, Momy na sane dasu zatai magana Inna ta rigata cewa. "Wato har yanzu baku daina wannan gabar a tsakaninku ba ko?" Momy ta amshe da cewa. "Ai Inna ba mai matsalar nan sai Nahna ita ce mai wulakancin, kuma wallahi idan ta sake saina ci mata mutumci wallahi" Inna ta ce "Ai itama harda Hauwar, idan ita bata tanka mata ba, ita tayi mata mana, tunda dama ai ta girme ta, dan ni gaskiya bana son irin abunda ke faruwa a tsakaninsu, kuna jini d'aya amma bakwa jituwa da juna" Abba yayi gyaran murna yana ma su Hauwa nasiha da akan su so jununsu, amma Nahna bana jin nasihar Abba tayi tasiri a tare da ita, domin Abba na fita waje Nahna ta ce. "Momy amma please yau zamu koma gida ko?" Dak'uwa Inna tayi ma Nahna tana cewa. "Ungo nan kinji Nahna, ashe kece marar mutumcin dama?, to a nan zaku kwana, ko zaki koma ke kad'ai ne?, ai ga hanya nan bismillah............ *RAYUWAR MAKARANTA* *©Zahra Royal Star* Page 8 *Government Secondary School Rimaye Katsina State Nigeria* A hankali Hauwa ta mik'a hannunta ta amshi Report d'inta. A hankali Malamin ya bita da murmushi yana kallon y'an class d'in ya ce "A first term d'inmu ga wacce tazo ta d'aya a cikin ajin nan, dan haka ku tafa mana please" Gaba d'aya ajin ne ya d'auki tafi, murmushi mai sanyi kawai Hauwa ta saki tana komawa ta zauna akan kujera. Tofa tunda Mlm ya fad'i haka, wasu daga cikin y'an class d'in suka fara bin Hauwa da wani kallon uku saura wasu hassada ce cike da cikin nasu. Duk K'awayen Hauwa sune suke bi mata a report d'in, Atu tayi na biyu, Hadiza na uku, sai Ammama na hud'u Fatee na biyar, sai ko su Asiya da Hafsat dake bin bayansu. Abunda ya k'ara jan wasu y'an surutai a cikin ajin kenan, wasu ma cewa suke ai Malamin dake basu Report d'in saurayin Hauwa ne, sonka kawai aka nuna ba wai adalci akai ba. Asiya dake tafiya da Hafsat bayan an sallami kowa an raba report anyi hutun sati uku, kowa na tafiya a k'asa d'alibai cike da farin cikin hutun da akai masu. Asiya ta kalli Hafsat dake cika tana batsewa ta ce. "Amma gaskiya an cuce mu wallahi, ace duk class d'inmu a rasa su waye za'a ba na d'aya dana biyu har zuwa na biyar, sai masu biye ma wancan yarinyar mai iskokai a saman ka?, wannan abun da kinji kin san wallahi son kai ne kawai aka nuna mana" Tsaki Hafsat taja tana cewa. "Ke nifa na tsane ta wallahi, ta fara tare mana wani abun da mu ya kamata mu fara samunsa ba wai ita ba, da sauran rukuninta, dole ne sai na ja mata kunne, dan naga sai wani shewa suke kamar da gayya ma" Tana idasa fad'ar haka tayi gaba inda take hango su Hauwa suna tafiya ita dasu Ammama, Asiya na faman kiranta amma ina tayi gaba, idonta ya rufe da masifa. Su Hauwa suna cikin tafiya kawai suka ga an Sha gabansu. Da d'an mamaki Fatee ta kalli Hafsat, ta d'an harareta dan itama haushinta take ji ta ce. "Ke kuma Malama miye haka?, muna tafiya zaki wani zo ki tare mana gaba, bama son k'auyenci fa" Wani mugun kallo Hafsat ta jefama Fatee tana nunata da yatsa ta ce. "Keee kinga rufe min bakinki a nan wajan, mai warin baki Kawai, ki daina ganin kunyo na farko a cikin class d'inmu, idan banda wannan shashashar dake d'oraku tana baku satar amsa, ku kun isa ku goga damu ne?" Hafsat ta k'are maganar had'e da nuna Hauwa tana wani mata kallon banza Hauwa ta rik'e k'ugunta tana k'arema Hafsat kallo a tsanake, Atu zatai magana Hauwa tayi saurin sa hannunta ta rufe bakin Atu Tana d'an harararta ta ce. "Karki sake ki ce komai, dan tsaf na sanki yanzu zaki b'ata mana lamarin" Ta sake juyowa wajan Hafsat dake tsaye. Zuwa can saiga Asiya ta iso. Hauwa ta d'an taka ta matsa kusa da Hafsat sosai kamin ta nunata da yatsa ta ce. "Ya ma sunanki ne baiwar Allah?" Wata uwar harara Hafsat ta dankara ma Hauwa ta na jan dogon tsaki ta ce. "Ba'a sani ba, wata k'ila ko sunan Gyatuma ne dani ba..... Bata idasa maganar ba taji wani gigitaccan mari tasssss, wadda ya kusa sa jinta da ganinta daina aiki. Da mugun sauri Asiya ta nuna Hauwa tana huce ta ce. "Kutumar uban nan Kaii, shine zaki mare ta?, ke wace ce?" "Ni uwar da ta haife ta ce, baki ji miye ta ce bane daga k'arshe?" Hafsat dake rik'e da kuncinta cikin jin rad'ad'in marin da ta ji shi a bazata, take kallon Hauwa da d'unbin mamaki. A zabure Hafsat ta kai hannunta domin rama marin da Hauwa tayi mata, kamar k'iftawar ido taji an rik'e tsintsiyar hannunta. Ido cikin ido Hauwa take kallon Hafsat ta ce. "Ai wallahi Uban kuturu yayi kad'an bare na makaho, ke kin isa na tsaya ki mare ni?" "Ni kuma kika mare?, ai na rantse da sarkin mulkin Allah yau sai na rama mari na wallahi" "Hhhh au haka dan Allah?, sai ki mare ni mu gani, ai mari na mare ki, kuma na mari banza, domin da baki tab'a min uwa ba, da bazan mare ki ba, ki sani iyaye ba abin wasa bane, daga yau ki sake tab'a iyayen wasu, wata k'ila ni na miki da sauk'i, akan abunda zaki tarba a gaba, idan kika tab'a Iyayen wasu, ki iya bakin ki Malama, kije gida a koya miki tarbayar iya magana, da alama har yanzu akwai rashin tarbiyya a tare da ke, akwai kuma ciwon hassada dake d'awainiya dake, to shi dai ciwon hassada cinye aiki yake dan haka Malama Hafsa kike ko wacece ma dai sai a taka a sannu" Tana gama fad'ar haka ta rab'a ta gefanta ta wuce tana ce ma su Atu "Kai please ku taho mu je, domin kun san ana Jira na a gida yau zamu wuce Kano, ni kad'ai suke jira, karma wannan mugun ya gaji da Jira na naje yayi min wata muguntar tashi" Bin bayanta sukai suna mamakin Hauwa a yau, domin sun san da y'an jan fad'ar na kai da yau Hafsat ta ci ubanta har da Uwar. Asiya cike da takaici ta dubi Hafsat dake had'iyar zuciya kamar zata mutu haka take ji tsabar haushin kanta da take ji, da tsanar yarinyar can Hauwa. "Sai da na ce miki kwata-kwata bai kamata ki tare ta a nan ki ce zaki ci mutumcin ta ba, da kin bini a sannu zan gano mana hanyar da zamuyi maganinta, amma gashi ta baki kunya a gaban jama'ar makarantar nan, kin b'ata abun wallahi". Kuka kawai Hafsat ta saki tana cewa. "Ai wallahi bata ci banza ba, na rantse da Allah banzan yarda ba, saina rama wallahi. Amma yanzu mi kike tunanin zamuyi mata ne?" "Karki damu, daina kukanki kawai ni nasan matakin da zamu d'auka, kawai ki bari a dawo hutu" "Shikenan Allah ya kaimu a dawon" Da haka suka ci gaba da tafiya Suma. Atu da Ammama ne har suna had'e baki wajan cewa. "Amma gaskiya yau ba k'aramin birgeni kikai ba Hauwa" Kallonsu ta d'anyi da mamaki kamin ta ce. "Tofa yau kuma, to akan mi?" Atu ce ta amshe da cewa. "Kawai yau d'in ne kinyi aiki da hankali, bakiyi fad'an naki kamar yadda kika saba ba" Dariya Hauwa tayi tana cewa "Ai ko idan haka ne, karma kuyi saurin yanke hukunci, domin ba hankali nayi ba, idan ma shine kuke tunanin nayi, domin wallahi sa'arta d'aya su Momy na Jira na, zamu tafi Kano, amma da babu mai jira na a gida wallahi saina tsaya munci uban juna ni da ita, sai na nuna mata ruwa bafa sa'an gwando bane, har yanzu ina a matsayin Hauwar da kuka sani a'ato ba canzawa nayi ba" Wani tsaki Atu taja tana tab'e baki ta ce. "Ai dama ni na sani, ai barin hali sai mutuwa, Allah dai ya shirye ki" Ammama ta amshe da cewa "Ke ni fa ta wani b'angaran bana ganin laifin Hauwa, saboda mutane idan kana barinsu suna maka duk abunda suka ga dama, tofa ka bani ka shiga uku, amma idan kaja masu birki dole su ja su tsaya" Da irin wannan firar suka rabu da juna kowacce tayi hanyar gidansu, suna cewa zasuyi miss d'in juna saboda hutun da akai, da hakan suka rabu. Atu ce k'arshe zata bi layin gidansu ta d'an tsaya tana ce ma Hauwa. "Y'an birnin Kano, a dai mana tsaraba please, kar a sake a dawo mana hannu rabbana a'ato" D'an bugu ta kai mata a hannu tana cewa. "Ke dai kika sani, tsaraba kuma banyowa" "Karda Allah yasa kiyo jarababba kawai" Dariya suka saki a tare cike da kewar juna suka rabu. Hauwa na sayo kai d'akin Inna taji Y Abdullah na jan wani tsaki yana ce ma Inna. "Wai Inna wannan yarinyar taki har yanzu bata dawo bane?, anya kwakwalwar yarinyar can ba tab'in hankali kuwa, kwata-kwata bata da natsuwa fa" Wani kallo Inna take ma Abdallah, hannunta ta ware tana cewa. "Abdallah Ungo nan, Jikar tawa ce mai tab'in hankali?, ka kiyaye ni Abdallah wallahi, kaga wancan wadda ya fita shin..... Da sauri Abdallah ya tashi yana matsawa inda Inna take yasa tafin hannunsa yana zaro ido waje ya ce. "Haba Inna, ya da haka Kuma, yi hakuri ba sai kin idasa ba, haba mai ran k'arfe" Y'ar dariya ta saki tana harararsa ta ce. "Ke ni sakar min baki ja'irin yaro kawai, yarinyar da Mat..... Tashi yayi da sauri ba shiri yana toshe bakinsa yana cewa. "Ni dai Inna sai had'uwa ta gaba gaskiya, na fita zuwa mota ina waje ina jiransu, idan sun shirya ta dawo, wannan magana da kike ta zarowa Inna, sauran wa'incan Yaran suji, suma raina ni" Ya k'are maganar had'e da ficewa daga d'akin da sauri. Inna ta d'aga murna yadda zaiji ta ce "Da ka tsaya mana d'an rainin wayo" Yana fitowa ya ci karo da Hauwa da ta gama jin duk abunda suke cewa, taso ace taji abunda Inna zata fad'a daga k'arshe, ta kasa gane ina maganar ta dosa, duk inda ta d'ora ta sai taga batai ba. Allah ya so wannan karon basu yi k'aro ba, dan basa waje tayi ya wuce yana jefa mata wani kallo, ita dai tunda ta gaida sa bata k'ara gigin masa magana ba. Nahna ta fito daga uwar d'akin Inna, tana wani lumshe idonta had'e da wani yatsine fuska ta kalli Inna dake dubanta ta ce "Wai Inna ita wannan yarinyar bata dawowa ne haka, dole ma sai mun tafi da ita ne, a barta inda tafi wayo mana" "Ke kinci ubanki yanzu nan wallahi, kaga ja'iran Yara, kowa ya taso Hauwa dai Hauwa dai, haba dan Allah ku barta ta huta mana ta shak'ata" Zata k'ara magana Hauwa ta shigo ko kallon inda Nahna take Hauwa batai ba, sai ma wani siririn tsaki da Hauwar taja mata. "Yawwa ga y'ar albarkar nan ma ta zo" Momy da ta idasa sallar k'arfe d'aya saboda da tafiyar da zasuyi tayi sallarta, danta ga har sha biyu da rabi tayi, shi yasa kawai tayi sallar, dan sallar zata iya riskarsu kan hanya ne. Ta fito daga d'akin tana cewa. "Kinga NahNah zan sab'a miki, dallah tashi kije kiyi sallah kizo ki shirya muyita tafiya. Y'ata Hauwa kema tashi ki Shirya ko mun d'auki hanya, kar dare yayi mana akan hanya" Da to Hauwa ta amsa ta tashi, ta shige, uwar d'aki, tana cire kayanta ta shiga toilet na cikin d'akin tayi wanka, tana fitowa ta shirya a gurguje tayi sallah, ta gama dama akwatinta har an kai sa mota. Itama kwata-kwata bata son tafiya tabar Innarta shi yasa yau d'in kwata-kwata bata wani jin dad'in yanayin. Tana Jin sadda Nahna ta shigo tayi sallar itama, koda ta idar tana d'akin, nan ma ba wata magana sukai ba, ta rasa mi yasa basa jituwa da juna. Komi Hauwa ta tuna jin muryar Abba ta fito da sauri tana cewa. "Yawwa Abba, kasan na nawa nayo a school?" "A'a d'iyata, yanzu nake cewa kina ina ne, dama abunda nake so na tabbaye ki kenan dama. Matso na gani Y'ar tawa na nawa Tayo" Da saurinta Hauwa ta matsa da zumud'i tana damk'ama Abba report d'in nata. Nahna da ta fito yanzu ta tsaki wani tsaki can ciki yadda ba wadda yaji ta tana maganar zuci. "Yo na nawa zatai fa?, idan banda na k'arshen class, karatun k'auye har wani karatu ne" Kamar Hauwa tasan miye Nahna ke kitsawa ranta. Ta d'an matso saitin da take tana kallon yanayin fuskarta yadda take wani tab'e baki tana b'ata fuska. Tana jin lokacin da Abba ke cewa. "Wow wow My daughter, gaskiya dole na baki kyauta domin kinyi k'ok'ari sosai ki ce first class fa mashaa Allah" Abba ya idasa fad'ar haka cike da tsananin murmushi akan fuskarsa da murna, Momy ma amsa tayi tana yabawa sosai. Hauwa dake tsaye kusa da Nahna a hankali ta d'an duk'a dai-dai tsawon Nahnar domin Hauwa ta fita tsawon k'afa ta ce "Ohhh sai gashi kuma nayo abun kirkin da baki so ji ba, karfa kiyi tunanin makarantun k'auye abun banza ne, no ba'a nan take ba Aunty Nahna, idan mutum Allah ne ya basa kwakwalwa, to a ko ina yayi karatu bazai tab'a dakushewa ba, wannan daga Allah" Da wani mugun sauri NahNah ta waigo tana kallon Hauwa da mugun mamaki. Ubanwa ya gaya mata zancan zucin da take yi ne, ko dai aljanu ne da ita?. Hijab har k'asa Hauwa tasa tayi mata kyau sosai tasa ruwan k'asa. Nahna zatai magana taga su Abba sun mik'e sunama Inna sallama gaba d'aya suka fita har Innar domin masu rakiya, har ita Hauwa sai ta take masu baya, dole tasa Nahna yin shuru ba dan ta so ba, itama ta bi bayansu. Kamar yadda suka zo a mota d'aya haka Abba ya shiga gaba Abdallah na driving, sai Momy a baya da Hauwa da Nahna. Hauwa kamar tayi kukan rabuwa da Inna, amma ta d'an matse hawaye a b'oye ta shige mota, Inna sai tsiya take mata, wai dama so take ta tafi ta barta ne............. *RAYUWAR MAKARANTA* *©Zahra Royal Star* Page 9 *No. 14 Audu Bako Way, Nassarawa GRA, Kano Nigeria* A gajiye suka shigo gidan, dan haka suna shiga Parlon gidan, Nahna tayi saurin haurawa sama dan ko kallon inda Hauwa take batai ba. Momy ta kalli Hauwa ta ce. "Hauwa ki haura sama kema ki d'an watsa ruwa, kamin a fito cin abincin dare" D'an yamutse fuska Hauwa tayi tana cewa. "Nifa Momy dama Abba baiyi mana d'aki d'aya da Nahna ba wallahi, bana son abunda zai b'ata min rai" D'an murmushi ta saki tana matsuwa kusa da Hauwa ta d'an dafa kafad'ar ta ta ce. "Abunda yasa Abbanku ya had'a maku d'aki d'aya shine, tun kuna Yara dama ra'ayinku ba d'aya bane, Nahna ta cika rawar kai da yawa, ke kuwa kin cika rashin ji, halinku kwata-kwata bai zo d'aya ba, bama ku zama waje d'aya bakuyi fad'a ba, shine mu kuma nida Abbanku muka yanke hukuncin a had'a maku d'aki d'aya kowacce da gadonta, ko mun samu ku d'an had'a kanku, amma duk laifin na wajan Nahna, idan bata daina halin nan nata ba wallahi zan d'au mummunan mataki ne a kanta" Da sauri Hauwa ta girgiza kai ta ce. "Ko kad'an Momy karma kiyi mata komai, wata rana k'ila ta gane abunda take ba dai-dai bane, zan zauna a d'akin namu, amma.... Sai kuma tayi shuru. D'an k'aramin murmushi Momy ta saki, tana cewa. "Amma idan tayi miki ki rama, karma kiji kunyarta, ni na saki tunda ta riga ta zubar da girmanta, amma Hauwa kuyi k'ok'ari ku so junanku ke kuma idan tayi miki wani abun ki rink'a hakuri da ita kinji D'iyar albarka?" Murmushi Hauwa ta saki itama ta haura saman tana d'aga kanta alamar taji kawai. Momy ta bita da kallon tausayi, ita yarinyar tausayi ma take bata. Abba daya dad'e a tsaye daga sama, ya sakko ta b'an garansu ya ce. "Momyn Yara ko dai zan sa a raba masu d'aki ne?" "No Karka raba masu please, nafi so su fahimci juna, su so junansu, bana jin dad'in rashin jituwarsu fa sosai" Momy ta k'are maganar fuskarta ba walwala ko kad'an. D'an murmushi ya saki yana kallonta ya ce. "Ki daina damuwa kinji, ai Yara ne har yanzu, duka suka wuce shekara goma Sha hud'u, to nan gaba zasu daina ne insha Allahu" D'an murmushin itama ta sakar masa ta ce. "Hmm Yara fa ka ce?, shekara sha hud'u sune Yaran?, dama dai y'an shekara goma ne, sai na ce masu yarinta ke damunsu, idan basuyi hankali a yanzu ba sai yaushe?" "Momyn Yara kenan, wallahi har yanzu Yara ne, yanzu fa suke shirin shiga JS3 fa karatun naso da saura ma, kofa secondry yanzu suka soma ta, ki bari kiga sadda Hauwa zata tare a gidan D'anki lokacin Zaki gane sun girma amma ba yanzu ba" Da sauri Momy ta rok'o hannun Abba taja shi suka zauna akan kujerar parlo. D'an murza hannunsa tayi cikin hannunta tana kallonsa, kamin tayi magana ya rigata cewa. "Ya dai Matar Abba?" Ya fad'a da murmushi kwance akan fuskarsa, domin yasan abunda zata ce masa. D'an turo baki tayi domin ita Momy indai a gaban Abba ne ji take kamar Yara suke har yanzun. Murmushi ya k'ara fad'ad'a akan fuskar Abba yasa hannunsa ya d'an ja mata hanci yana cewa. "Ke matar nan baki tsufa ne wai?, mi ya faru? fad'a min ina jinki" "Kasan abunda nake so na fad'a ai" "Noo fad'a min da bakin ki" Sauk'e ajiyar zuciya tayi kamin ta d'anyi k'asa da muryarta tana cewa. "Abbansu Hauwa, abunda nake so na ce shine, mi yasa Hauwa idan ta gama secondary bazata tare a gidan mijinta Abdallah ba?, idan yaso a gidan nasa sai tayi karatun na gaba please Abban Yara karka ce a'a" Ta k'are maganar had'e da d'an k'ara murja y'an yatsun hannunsa dake cikin nata. D'an sauk'e lumfashi kad'an yayi kamin shima ya ce. "Ba wai nak'i bane, amma nafi so yarinyata tayi karatu sosai, bana so aje akaita matarsa ta nemi mai da ita shashasha, amma ya kike gani" D'an murmushi ta sakar masa ta ce. "Ko kad'an Lubna bata isa mai da Hauwa shashasha ba, shi yasa ma hankali yake kwance domin nasan halin yarinyata, bata barin ta kwana, bana shakkar zamanta tare da Lubna Abban Yara" "Uhmmm" Kawai Abba ya ce yana d'an zare hannunsa dake cikin na Momy ya d'an mik'e yana kallon saman silin d'in parlon, kamin ya ce. "Abunda nake hangowa daban da naki, amma shikenan nima bana jinta, amma fa dole Y'ata ta fara karatu kamin ta tare a gidansa, bana so abunda zai kawo mata cikas akan karatunta. Sai nake ganin kamar karatun zai bata wahala a gidansa, kamar fad'an auran Abdallah a kanta zai iya kawo mata matsala a cikin rayu.... Da sauri Momy ta mik'e had'e da katse sa wajan cewa. "A'a karka fad'i haka Abban Yara, kayi masu fatan alkhairi kawai Abban Yara, domin ni harga Allah na gaji da jiran gawar shano a wajan Lubna, domin wannan matar bata tsoron Allah, bana jin dan yanzu zata bari ta haihu, idan ka lura so take ma ta fara juya min Yaro, ni kuma wallahi bazan zuba ido na gani na kyale ba, dole ne na nemar masa mafita, hatta Yarinyata Hauwa bazan barta a haka ta shiga gidan Abdallah ba kariyar Allah a jikinta, dole ne nasa a rink'a sadaka a Masallaci ana sauk'e al'qur'ani mai girma, saboda mata na sanmu da zafin kishi, babu abunda wasu daga cikinmu bazasu iya yi ba, saboda kishi. Da zarar an sanar da ita babu haukan da baza tai ba" Abba ya murmusa, ya fara hawa sama yana cewa. "Hakane Momyn Yara, ki hawo sama ki d'an watsa ruwa akwai gajiya" Bin bayansa tayi kamar yadda ya ce. A b'angaran su Hauwa ko, tana shiga ta iske Nahna na shirya kayanta a cikin waduruf tana yi tana jin wak'a. Ganin ta shigo yasa Nahna tab'e baki tana binta da wani kallo. Ko inda take Hauwa bata kalla ba bare tasan ma miye take. A hankali ta matsa inda tata waduruf d'in take, had'e da gadonta dake gefen damarta, zama tayi kansa, kamin ta d'an mik'e da yake tana da kaya a gidan, sai kawai tasa akwatinta a cikin waduruf d'in bata wani fiddo kayan dake ciki ba, sai wadda ya zama dole zatai anfani dashi a yanzun. Cire hijab d'inta tayi tana niyar tashi ta nufi toilet d'in d'akin nasu, kawai taji an jawota ta baya. Da sauri take duban Nahna da tai mata aika-aikar. "Ke kuma lafiya dallah can?" Cewar Nahna. Wani kallon uku saura kwata, Hauwa ta jefama Nahna kamin ta ce. "Ban gane ba Malama, ina ruwanki dani Kuma?, wani abun nayi miki ne?, zaki wani zo da kwasassun k'afafunki ki wani jawo ni" Wata uwar harara Nahna tayi ma Hauwa tana cewa. "Gani nayi daga shigowarki, kin wani d'ibi hanyar toilet, kuma na tara ruwan zafi na, zanyi wanka, fatan dai ba Kashi za'a mana a toilet d'in ba ko?, domin dai nasan y'an K'auye ba abunda suka iya sai Kashi da cin tsiyar masifa" "Hmmm" Wani murmushin mugunta Hauwa ta saki, shi yasa a shirye tazo dai-dai take da Nahna wannan zuwan wallahi. D'agowa tayi ta kalleta sama da k'asa tana nunata da yatsa ta ce. "Au haka?, au ashe fa ku y'an gayu ne bakwa Kashi da fisari da tusa ko?, saboda kune shafaffu da Mai ko?, ki matsa ki ban waje na wuce Nahna" Rik'e baki Nahna tayi tana cewa "Keee ni kike kira da sunana gatsal haka kawai?" "Au so kike na ce Aunty Nahna ko?, to kija girmanki tukunna sai ki dawo na ce miki auntyn, domin yanzu girma ya riga da ya fad'i, shi dama mutumci Madara ne idan ya zube baya kwasuwa" Zata sake wata maganar Hauwa ta fisge hanunta ta shige toilet d'in, ta kuma rufe k'ofar toilet d'in da k'arfi. Da sauri Nahna ta matsa bakin k'ofar toilet d'in tana cewa. "Na rantse da Allah ki fito, karki tab'a min ruwan wanka na Hauwa, zanyi rashin mutumci wallahi" Ko tak Hauwa bata sake ce mata ba. Hakan ya k'ara hassala Nahna, sai b'ab'atu take a k'ofar toilet Sai da Hauwa ta d'au lokaci sosai kamin ta bud'e k'ofar toilet d'in ta fito. Lokacin da zata fito ran Nahna idan yayi dubu ya gama b'aci. Bin ta tayi da kallon na tsananin mamaki, tashi tayi tsaye tana nunata da yatsa ta ce. "Kan Uban nan kayyasa, au wankan kika yi da ruwan zafin da na tara?, ai ko baki isa ba wallahi" Nan d'in ma ko inda take bata kalla. Nahna toilet d'in ta shiga, can sai gata ta fito tana sakin tsaki tana cewa. "Ai na d'auka wankan kike baki taran wani ruwan ba, da na rantse yau sai kin gane shayi ma ruwa ne" Ta idasa maganar tana shegewa toilet d'in. Murmushin mugunta Hauwa tayi tana d'an d'aure wani abu a leda tana yi tana cewa. "Zaki ci ubanki ne yau wallahi, ke ce zaki gane shayin ma ruwa ne yau" Zama tayi ta shirya a tsana ke ta shafa mai tasa kayan bacci, domin har bakwai na dare tayi da y'an minti na, shinfid'a abun sallah tayi ta gabatar da sallar da ake binta. Tana sallame sallar taji ihun Nahna daga cikin toilet da sauri ta mik'e ba shiri sai kuma ta tuntsire da dariya tana tafa hannayenta tana cewa. "Yanzun za'a fara wasan, ai dani kike zancan, duk wadda ya ci tuwo dani to miya yasha" Tana rufe bakinta taga Nahna ta fito daga toilet da gudu sai soshe-soshe take tana buri a k'asa sai kiran "wayyo Allah na shiga uku na, k'aik'ayi ko ina na jikina, dan Allah ki taimaka ki sosa min wayyo na bani na shiga uku" Mi Hauwa zatai idan ba dariya ba, harda kwanciya domin ganin yadda Nahna ke kiran ta bani ta sha uku, yadda take wage baki tana ihun azo a taimake ta. "Wayyo wayyo wayyo Momy kina ina ne?, dan Allah kizo ki sosa min, wayyo k'aik'ayi ko ta ina jikina, ji nake kamar zan mutu, na shiga uku wayyo wayyo All...... Ta kasa k'arasa maganar jin wani mugun k'aik'ayi ata bayanta, da sauri cikin fitar hayyaci tasa hannun nata a baya zata sosa wajan, can taji wuyanta ya d'auka jikinta ya k'ara d'aukar wani mahaukacin k'aik'ayi wadda yafi dana da, da take ji, ihu ta k'ara saki don k'arfinta. A rud'e kamar da gaske Hauwa ta sauka k'asa bayan ta gama tikar dariyar tata, Nahna na ganin yadda take mata dariya da yadda ta kasa bata taimako tasan ba wadda yayi mata wannan shegiyar muguntar sai Hauwa. "Momy!! Momy!! Momy!!" A rud'e Momy ta sakko tana cewa. "Innallihi Hauwa miye na wannan kiran har kinsa gaba na ya fad'i Fisbilillahi?" "Momy Ina Abba?" "Abbanku ya fita Masallaci" Zata sake magana Momy taji yadda Nahna ke ihun neman taimako. Da sauri Momy ta zaro ido waje tana dafe k'irjinta ta ce. "Subhanallahi mi ya faru Hauwa mi ya faru da Nahna?" Gaba Momy tayi a mugun rud'e domin ihun da Nahna keyi na fitar hankali ne hakan ya k'ara rud'a Momy sosai, dan har tana tun tube wajan shiga d'akin. Hauwa da ta rufa mata baya, suna shiga d'akin Momy tayi saurin runtse idonta tana cewa. "Subhanallahi ke Nahna miye haka?, babu fa sutura a jikinki, miya shiga kanki haka ne?" "Wayyo wayyo Momy ki taimka min ki sosa min, ko ina na jikina k'aik'ayi yake min". Da sauri Momy ta matsa kusa da ita tana tallafo ta a jikinta ta fara sosa mata ko ina na jikin nata da har yayi jawur tsabar kartarsa da Nahnar keyi. Momy a rud'e ta ce. "Wai mi kika shafa ma jikin naki ne?". "Wallahi Momy ban sani ba, daga watsa ruwa a toilet" "Innallihi wa'inna alaihir. Hauwa d'akko min wayata na kira doctor yazo" Da mugun sauri Hauwa ta k'ara sauka k'asa ta d'akko wayar, ko kad'an bata ji wani tausayin Nahna ba, gobe ma ta sake gaya mata maganar banza. Tana kowawa Momy har hannunta na kyarma wajan danna number doctor. Ba'a b'ata lokaci ba Doctor ya iso shima hankali a tashe, domin tunda ya taho Momy ke k'ara faman kiransa kamar zata tada gari, sai uban kira take masa. Da kyar tasa ma Nahna wata riga marar nauyi har yanzu soshe-soshe kawai take harda su kuka yanzu domin yanzu da ta sosa zafi ma take ji, domin duk ta karce jikin nata. A tare Abba da doctor suka shigo gidan, inda Abba yayi mamakin ganinsa, ya tabbayeshi ko lafiya?, wani ne ya kirasa a gidan, bai da labari. A tak'aice Doctor yayi masa bayanin da Momy tayi masa shima. Ai ko hankali a tashe shima Abba ya haura sama wajan d'akin su Nahnar. Abba na shigowa ya matsa kusa dasu yana cewa. "Wai mi ya kawo mata wannan susar jikin haka?" "Abban Yara nima ban sani ba wallahi, haka na zo na tadda ta, nima Hauwa ta kira ni fa na zo na ganta a haka" Juyawa yayi inda Hauwa take tsaye harda su kukan munafurci take yi da hawaye kamar gaske ya ce. "Hauwa mi ya sami y'ar uwarki?" "Abba nima ban sani ba wallahi, kawai ni dai ta zo ta shiga toilet har tana gaya min cewa y'an K'auye k'azamai ne basa wanka, dan taga banyi wanka ba sai ita, shine fa ta shiga da wata bak'ar leda wai ko k'awarta ta bata ko sabolo ne zatai wanka dashi, k'ila shine yasa ta jin k'aik'ayin" Duk irin halin azabar da Nahna ke ciki hakan baisa ta kasa gane mi ye Hauwa ke shirin k'ulla mata ba, nan ta k'ara tabbatarwa kanta cewa tabbas Hauwa ce silar sata a wannan halin da take ciki, tabbas ta rantse da tsarkin mulkin Allah sai ta rama bazata tab'a barin Hauwa ta ci bulis ba. Nahna tana kuka tana susar jikinta ta ce. "Wallahi Abba ba abunda nasa nayi wanka dashi, kawai watsa ruwa nayi, amma ban san miya kawo min k'aik'ayin ba nima". Ta wutsiyar ido take ma Hauwa kallon zamu had'u ne, itama Hauwar kallon ina jinranki ta aika mata dashi. Da kyar dai aka samu Doctor yayi mata wata allura tasa ta bacci had'e da kashe k'aik'ayin. Inda doctor ya k'ara masu jawabin cewa, akwai abunda ya sa mata k'aik'ayin nan, ba wai haka nan kawai ya same ta ba, akwai abunda ta shifa ma jikin nata.......... *Hi Masoya book d'in RAYUWAR MAKARANTA, karku shagala da yawa fa, domin book d'in RAYUWAR MAKARANTA yanzun ne tafiyar tashi ta soma, na kud'i ne akan raina d'ari hud'u ne kacal #400, zaka iya turo kud'in ka ta wannan account number d'in*. 👇 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank. Sai ka turo shaidar biya ta wannan number d'in👉08130479973 *RAYUWAR MAKARANTA* *©Zahra Royal Star* Page 10 *list free pages* *No. 12, Kawo Bos Stop Kano Nigeria* A gajiye ya shigo gidan, yana d'an sauk'e lumfashi kad'an. Turus yaja ya tsaya yana bin parlon da kallon cike da tsananin mamakin Lubna. Miye take har yanzu da ba'a fito an gyara parlon ba?, ko ina kaca-kace yake. A hankali ya taka ya nufi darning table shima dai a hargitse yake, baya jin ma tayi wani abinci. D'an dafe cikinsa yayi yana jin yadda y'an hanjin cikinsa ke masa k'ugin yinwa. Ransa idan yayi dubu ya fara b'aci, ransa na soya ya nufi sama, inda yake jiyo tashin kid'a kad'an kad'an yana fitowa. K'aramin parlonta ya nufa yana tura k'ofar ya ci k'aro da ita zaune tana danna waya tana cin biskit daga ita sai wata y'ar riga iya gwaiwa, ko d'ankwali babu akanta, tana zaune ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, tana cin biskit da su samosa, hankalinta kwance parlon ma yayi kaca-kaca. Motsin da taji ne yasa da sauri ta mik'e tana kallonsa, d'an sauk'e lumfashi tayi tana dafe k'irjinta ta ce. "Ohhhh wayyo ashe Kaine ka dawo?, harka bani tsoro fa" Wani kallo da ta ga ya jefa mata yasa ta d'ansa hannunta tana sosa keyarta, takowa yayi har inda take yana binta da kallo, tabbas ita gata tsaf k'amshi ne kawai ke tashi a jikinta, jikinta gyare yake, tana da tsaftar jikinta amma bata da tsaftar mahalinta. Da kyar ya iya bud'e baki tsabar b'acin rai ya ce. "Yanzu Fisbilillahi Lubna kin duba gidan nan kinga yadda ya koma?, ko ina kaca-kaca, sai ka ce ba mace a gidan" Turo baki tayi gaba ta ce. "Dama fa na mance na fad'a maka mai aikin tawa ce aka ce wai aure za'a mata a can K'auyensu, shine yau da safe ta tafi na sallameta, zuwa gobe ko jibi za'a kawo min wata daga gidanmu" Wani kalar abu yaji ya tokare masa mak'oshi. Wato dai gidansu ake d'aure mata gindin komiye ma take masa a cikin gida. "Ke yanzu bazaki iya tashi ki gyara gidan ba, har sai an kawo wata y'ar aikin?, ke kina ganin rayuwa zata tafi a haka ne?, komai ace sai anzo anyi miki, to gaskiya na fara gajiya da abunda ke faruwa a gida na, idan Zaki canza ki canza tun kamin ranar nadama ta riske ki, tun Kuma kamin na d'au mataki akan ki" D'agowa tayi ido cikin ido ta ce. "Ban gane miye kake k'ok'arin cewa ba honey?, kamar ya ranar nadama ta zo min?, abunda nake har wani abu ne marar kyau?, nifa na ce maka ko a gidanmu komai yi min ake, to dan haka bazai yuwu ace nazo gidan aure na ba, ace bazan huta ba a'ato, mai aikin nanma fa ba kaine ke biyanta, to miye na abun fad'a? Dan yau kawai kazo kaga gida a haka" "Haka zaki ce ma ko?" Ganin tayi shuru tana kallon k'asa tana wata jijjiga yasa shi d'an shafa sumar kansa ransa ya gama b'aci sosai. Tafiya ya somayi tana nufar k'ofa domin fice mata daga parlon, idan ya ce zai ci gaba da yin magana komai yana iya faruwa, zai iya mata abunda zatai dana sani har k'arshen rayuwarta, shi yasa kawai yayi saurin ficewa daga parlon, dan idonsa sunyi jawur jijiyoyin kansa sun tashi sunyi rud'u-rud'u, to komai na iya faruwa idan bai bata waje ba. Shiga yayi d'akinsa shima dai kamar yadda ya barsa a haka yazo ya iske sa, hatta gadon daya barta kwance akansa, ba'a gyarasa ba yadda ya barsa a haka ya zo ya same sa. Ransa ya k'ara b'aci sosai amma a haka ya haɗiye b'acin ransa, ya fara rage kayan jikinsa, da kansa ya fara gyara gadon, domin bazai iya kwanciya d'akin a haka ba, da kansa ya d'an gyara d'akin, gyaran da yayi ba wani yi masa yayi ba, ya shiga wanka, shima toilet d'in sai ya wanke sa sosai har sau biyu, yana tausayin kansa ace yana da mata amma yake duk wannan aikin, amma yasan abunda zai mata dole ne ma Hauwa tayi saurin tarewa a gidansa, koda su Abba basu amince ba, idan ba haka ba kuma zai je ya k'ara wani auren ne, domin ba zai zauna mace d'aya ta rink'a sa masa ciwon kai ba. Fitowa yayi daga toilet d'in bayan ya gama wanka, ya shirya tsaf yana d'an tunanin ina zaije ya sami abinci?. Idan ya ce zai tafi GRA, unguwarsu dare ya d'an fara, da sauri ya d'akko wayarsa ganin k'arfe takwas da y'an minutes yasa shi d'aukar key d'in motarsa ya yanke hukuncin can zai tafi, ya ci abinci a wajan Momy kawai, duk da yasan tabbas sai ta tabbaye shi dalilin zuwan nasa. Da d'an sauri ya sakko k'asa ganin Lubna a parlon k'asan yasa shi k'ara shan mur ko kallon inda take baiyi ba ya nufi k'ofar waje. "Honey ina zaka je kuma cikin daren nan?" Lubna ta k'are maganar da d'an k'arfe ganin ya fice ko waigowa baiyi ba, bare tasa ran zai bata amsa. Zama tayi kan kujerar parlon tana tab'e baki. *No. 14 Audu Bako Way, Nassarawa GRA Kano Nigeria* A hankali Momy ta kalli Hauwa dake tsaye wajan Darning table suna zaune har Nahna da ta d'an samu sauk'i, sun fito cin abincin dare. Nahna sai cika take tana batsewa so kawai take ta samu ratar da zata rama abunda Hauwa tayi mata, tama rasa miye zatayi mata domin rama abunda tayi mata. Maganar Momy ta katse mata tunanin data lula inda taji tana cewa. "Hauwa ki zauna mana, ko abincin da akayi baiyi miki ba, ki shiga kitchen ki dafa wani abu" Da saurinta kuwa ta ce. "Eh gaskiya Momy bazan iya cin wannan abun ba" Abba daya kai lumar abinci a bakinsa ya had'e abincin dake bakinsa ya ce. "Y'ata Sakwara ce fa, da Miyar agusi" "Eh Abba ni ban cika cinta ba gaskiya" Kallon Abincin Hauwa tayi gashi dai yaji naman kaza harda ma ganda zak'o-zak'o a cikin Miyar, amma ita dama can Sakwara bata wani dameta ba, bata cikin jerin abincin da ta take so. A hankali Momy ta dafa ta ta ce. "Yawwa tunda hakane kije kitchen ki dafa ko indomi ce, tunda kinga dare ya riga da yayi" "To Momy tama ishe ni Indomin" "Yawwa to je ki dafa" Nufar kitchen d'in tayi tana murnar cin Indomi domin Allah ya sani tana son Indomi, bare idan tayi mata dahuwa ta gani ta fad'a. Nahna dake zaune ta saki wani murmushin mugunta tana hango ta inda ya dace ta rama abunda Hauwa tayi mata, murmushi take tana girgiza kai domin ta hango muguntar da zatai mata. Suna zaune suka ji sallamar Abdallah. Da d'an mamaki Momy take kallonsa ganin yadda ya zo ya zauna akan Darning table d'in, ya kalli Nahna yana cewa. "Ke zuba min abincin nan yinwa nake ji dama" Abba daya gama yanzu yana niyar mik'ewa ya ce. "Ahh ahh Abdallah miye kazo yi a gida irin wannan lokacin?" "Wallahi Abba naje gida ne sai na iske har yanzu jikin Lubna ba lafiya, bata ko iya dafa abinci ba yau, shine yasa na zo nan na ci, domin kasan bana son cin abincin saidawa" Amsawa da kai kawai Abba yayi ya fice daga wajan Darning table d'in ya haye sama abunsa. Momy ta d'an hararesa tana cewa "Nifa wallahi Abdallah ban wani yarda da kai ba, indai akan matar nan taka ce, komi sai ka rink'a wani k'areta" Abincin da Nahna ta zuba masa ya jawo ya d'an soma ci, sai kuma ya ce . "Momy da gaske fa nake" "Hmmm Abdallah kenan, ai shikenan a juri zuwa rafi dai, wata rana tulu zai fashe ai" Tana k'are maganar ta tashi itama, tabi bayan Abba sama. Suna zaune su biyu sai ga Hauwa ta fito daga kitchen d'in, bata gama dafa Indomi d'in ba, jin muryarsa yasa ta fitowa, amma ko kallonsa batayi ba ta haye sama dan wani fisari da ta ke ji ya rik'e mata mara. Yana kallonta ta wutsiyar ido harta haye sama, babu hijab a jikinta, daga ita sai wata dogowar rigar bacci har k'asa, amma duk da haka yana iya hango albarkatun jikinta wadda Allah ya zuba mata, yadda kasan ba Hauwa y'ar shekara sha hud'u ba, kamar wata babbar mace haka ta koma masa a idonsa, yadda take hawa benen jikinta na girgiza taku d'aya biyu sai jikinta ya motsa, yadda take hawa benen da d'an sauri abun kallo ne, shi sai yanzu nema yake k'are mata kallo, Hauwa na da wani irin jiki na ban mamaki, wadda duk k'aryar namiji da jin kansa sai ya kalleta ya sake kallo. Motsin Nahna ne ya katse masa hanzari da tunanin daya afka, Wani tsaki ya saki jin motsin Nahna da ta tashi ta nufi kitchen da saurinta. Wani haushin kansa ya fara ji, duka nawa Hauwar take da har zuciyarsa ta fara kwad'er ta masa ita?, ba komai yaja masa hakan ba sai Lubna duka laifin ya d'orasa akan Lubna, idan badan ita mi zai sa ya kalli wancan yarinyar. A wajan Nahna tana shiga kitchen d'in tayi saurin bud'e tukunyar da Hauwa ke dafa Indomi da ita, ruwan Indomin har ya fara tafasa, tasa magi da komai sai kwai da ta aje daga gefe da alamar soya Kwan zatai, ba wai dafawa ba. Da sauri ta jawo Gashiri dake cikin leda, ta bud'e. Sai da ta cika hannu dashi ta zuba a cikin ruwan Indomin dake tafasa, tana zubawa tayi saurin rufewa ta maida gishirin inda yake, da saurinta ta fice ta k'ofar baya dake kitchen d'in ta nufi lanbo dake bayan kitchen d'in, idan ta tashi shigowa ta shigo da k'ofar gaba, dan karma ayi zargin ita ce tayi aika-aikar. Abdallah yana tashi baima kowa sallama ba yana gama cin abincin nasa ya fice daga gidan gaba d'aya. Hauwa da ta sakko k'asa tana satar kallonsa a lokacin da ya tashi yana nufar k'ofa. Sai da ta bari ya fice kamin ta idasa sakkowa ta nufi kitchen da sauri, domin tasan yanzu ruwan Indomin ta ya tafasa. Tana zuwa ko ya tafasa kamar ance tasa chokali ta d'an d'ebo ruman Indomin ta d'akko magi ko idan magin Indomin bai ji ba ta k'ara ta d'an d'ebo ruman ta kai bakinta, da wani irin sauri ta furzar dashi, tana tab'e bakinta girgiza kai ta farayi ita dai iya saninta ai bata sa gishiri ba, to waye yayi mata hakan?, bata yarda ba ta k'ara d'ebo ruman ta kai baki, nanma jau taci uban gishiri yayi yawa. D'an tsayawa tayi tana kallon ruwan dake tafasa har yanzu tama kasa magana, sai can ta saki wani shegen murmushi, girgiza kai ta farayi tana sauk'e ruwan Indomin ta zubar dashi ta wanke tukunyar ta sake maida wani ruwan tasa farin magi da wani magin Indomin, yana sake tafasa ta d'akko karas da girinbis da ta yanka ta dafasu daban tun d'azo tasa su, tasa Indomin minti kad'an ta sauk'e, tana a tsaye bata k'ara barin kitchen d'in ba, tana gama dafuwar Indomin, ta sauk'e ta juye ta a filet ta soya kwai daya ji al'basa da d'an jajjage kad'an da ta sa masa, tana idasa soyasa ta juye sa a saman Indomin. Fitowa tayi ta nufi sama, bata buk'atar zama akan Darning table ta ci abincin yanzu, so take ta tabbatar shin Nahnar ce tayi mata wannan abun ko kuwa?. Tana shiga d'akin taga babu Nahna zama kawai tayi dan tasan duk inda taje tana nan shigowa d'akin. Tana gama tunanin zucinta kuwa sai ga Nahna ta shigo d'akin tana dariyar mugunta. Da sauri ta tsayar da dariyar tata tana kallon Hauwa dake cin Indominta hankali a kwance, sai saka luma take yi. K'ara ware idonta tayi wai ko dai bata gani ne sosai ba, again dai gani tayi Hauwa sai cin indominta take har wani lumshe idonta take. Hauwa na kallon yanayinta ta wutsiyar ido, kuma tuni ta harbo jirginta tuni tasan ita ce kennan tayi mata hakan?. "Hmmm" Kawai Hauwa ta saki tana girgiza k'afar tana yi tana cin Indominta. Ganin fa kamar zata gane akwai abunda ta shirya mata, yasa Nahna kame kanta tana wani basarwa taja tsaki ta zauna akan gadonta tana latsa wayarta. Ta wani maze yadda kasan bata aikata komai ba. Washe gari da safe, kamin kowa ya tashi, Hauwa ce ta fara tashi, ta gyara ko ina na gidan, domin basu da wata y'ar aiki, duk aikin gidan Nahna ce keyi idan babu school, idan akwai kuwa zata tashi tunda safiya ita da Momy suyi aikin su, kamin gari ya gama wayewa sun gama har abincin safe, haka suke yi, shi yasa ma Hauwa ta saba da aikin irin na gidan, domin duk hutu a nan take yinsa, ko can Rimaye ma wajan Inna tare suke aikinsu suma, Inna b'ata tab'a barin Hauwa a sangarce ba, shi yasa komai ta iyasa bata jin wahalarsa, haka ma Nahnar itama Momy ta hureta da ayyukan gidan. Hatta abincin safe Hauwa tayi sa a safiyar. Nahna na sane tak'i tashi, domin tasan yau Momy baza ta fito da wuri ba, tasan suna nan sune zasuyi aikin, shi yasa tabar Hauwa ita d'aya tsabar mugunta da son kai. Hauwa ko tana sane da abunda ta shirya mata yau da safen shi yasa bata tayar da ita ba, da ba komai itama tasan bata aikin nan ita d'aya, amma Nahna harta manta da ta ma Hauwa wani abu. Hauwa bayan ta gama ta shigo d'aki, hannunta rik'e da wata y'ar roba dake cike da man gyad'a, murmushi ta saki ganin yadda Nahna ke sharar baccinta harda su fitar da munshari. Dai-dai inda Nahna zata taka idan ta tashi ta zuba man gyad'an, tana gama zubawa ta rufe robar ta maida kitchen. Koda ta dawo toilet ta shige kawai tayi wanka da sauransu. Bayan ta gama ta shirya ta d'an zauna tana jiran tashin Nahna da ta hakimce akan gado. Can ko sai gata ta mik'e tana sakin hamma harda wata mik'a ta saki tana bin Hauwa da wani kallo na uku saura kwata. Murmushi kawai Hauwa ta sakar mata, wadda yasa Nahna saurin tsarguwa. Anya ba wani abu Hauwa ta shirya mata kuwa?, take tabbayar kanta. Girgiza kai tayi kawai ta mik'e domin nufar toilet, sai dai taku d'aya biyu tayi, tayi taga-taga zata fad'i ihu ta saki tana son kamu wani abu karta kai k'asa amma ina ji kike rigijahhh, ta fad'i wani marayan kuka Nahna ta saki da ihu tana saurin dafe k'ugunta daya bugu sosai harda k'afarta ta dama. Mi Hauwa zatai idan ba dariya ba, sai da tayi son ranta kamin ta mik'e ta fice ko ci kanki bata ce ba bare ta ce mata sannu. Tana fita Nahna ta kai dubanta a inda take zaune, hannunta ta d'ago jin wata lema-lema a inda ta fad'in. D'an murja hannunta tayi jin maik'o a hannun nata, ganin mai ne aka zubar a wajan, yasa Nahna sakin tsaki tana rik'e baki a fili ta ce. "Wato dai Hauwa ta gane abunda na yi mata kenan jiya?, shine itama ta rama yanzu kenan?. Idan fa banyi da gaske ba wannan aljanar yarinyar sai ta kassara ni, gara na yarda muka man yak'i na, na rabu da ita harta koma inda ta fito shegiyar kamar aljana wallahi" Ta k'are maganar tana dafa bango ta mik'e da kyar tana yatse ne baki wata y'ar k'ara ta saki, tana dafe k'ugunta had'e da runtse idonta, tana jin yadda k'ugun nata ke mata wani zafi. K'afar tata ma da kyar take dangyasa ta, da kyar ta lallab'a ta shige toilet tayi wankata ta fito domin shiryawa. Tana cikin shiryawa taji wayarta na k'ara alamar kira. D'an kallon wayar tayi, wayar da da kyar aka bar mata ita, k'arama ce, y'ar ta rik'ewa a hannu. Ganin Aunty Lubna ce ke kiran yasa tayi saurin d'auka, domin suna shiri sosai da Lubnar. "To Aunty insha Allah dana gama breakfast zan tahu gidan naki" Abunda naji Nahna ta fad'a kenan ta sauk'e wayar. A k'asa ko Hauwa na zaune su Abba da Momy suka fito. Momy ta kalli gidan yadda yayi tsaf dashi sai tashin k'amshi yake ta ce "Wow Mashaa Allah, hala D'iyata ke ce da wannan gyaran ko?, nasan dai wancar malalaciyar bazata iya wannan aikin ba" Murmushi ta saki tana cewa "Momy ina kwana fatan kun tashi lpy?, Abba ina kwana?" Cike da kulawa Abba ya amsa. Ta k'ara kallon Momy ta ce. "Eh Momy amma harda itama mukayi ai, har breakfast ma mun gama tun d'azo" Kan darning table d'in suka nufa Momy na cewa. "Ke Hauwa ki fad'a min gaskiya?" Murmushi kawai Hauwa tayi tana zuba masu abunda ta girka. Itama ta zauna suka fara ci a tare. Zuwa can sai ga Nahna ta sakko anyi wanka anci gayu. Zama tayi akan Darning table d'in tana gaida su Abba da Momy. Momy ta kalle ta tana cewa "Ke kuma wannan gayun fa?" Sosa kanta Nahna tayi tana cewa. "Momy dama Aunty Lubna ce ta kira ni, wai tana so naje gidanta yau" Tab'e baki Momy tayi tana cewa "To zaki je, amma keda Hauwa zaku tafi" Da sauri Nahna ta ce. "Nida Hauwa kuma?" "Eh ko baza'a je da ita d'in ba?" "A'a Momy ni ban ce ba" Nahna ta k'are maganar had'e da d'an sosa k'eya, ganin wata uwar harara da Momyn ta aika mata da ita. Hauwa zatai magana Momy ta d'aga mata hannu ta ce. "Ke ma kimin shuru, idan har ba so kike na soke mata tafiyar nan ba gaba d'aya, dan har in ba tare zaku je ba, to wallahi itama bazata je ba" Abba dake zaune ya ce. "Idan sun tashi tafiya Isa driver ya kai su mana shikenan" "Eh dama shine zai kai su, ya dawo da su kuma" Momy ta k'are maganar had'e da mik'ewa a tare ita da Abba, har waje ta rakasa domin zai wuce Company. Tana dawowa zata haye sama ta ce. "Idan kun gama ki kira Isa driver ya mik'a ku, saura kuma kije kisa ku kai dare kinji" Nahna da ta ji haushin zuwa da Hauwa ta ce. "A'a Momy baza mu kai daren da baki so ba insha Allah" "Yayi kyau" Kawai Momy ta ce ta haye sama. Tana barin wajan Nahna ta watsama Hauwa wata uwar harara tana zuba abincin ta fara ci, tana sakin tsaki. Dariya Hauwa ta saki tana mata haibaice tana cewa. "Ohhhoo dai a haka za'a ganni a barni, zama dani dole, K'anwar nak'i, ko ank'i ko an so" "Hmmm tsmwww" Kawai Nahna ta saki, danta yima kanta al'k'awarin bata sake tankama Hauwa, karta sake mata wata muguntar ta nakasata a banza, yanzu ma da kyar ta lallab'a ta sakko karsu Momy su gane ta fad'i, da kyar ta d'aure har sai da ta gasa jikin nata bare k'ugunta inda ta bugu. Hauwa ta fara tashi tana niyar barin wajan suka ji k'arar kiran waya, kallon wayar sukai a tare ganin wayar Momy ce ta bari akan Darning table d'in, ganin sunan Inna yasa da sauri Hauwa ta mik'a hannun ta d'auki wayar. Kiran ta d'auka da zumud'i tana k'arawa a kunnanta. Dai-dai lokacin Kuma Abdallah ya shigo parlon. Abunda aka fad'a a cikin wayar ne yasa ma Hauwa sakin wani dogon salati, had'e da sakin wayar jikinta na d'aukar rawa, wasu hawaye suka fara mata zarya, jikinta ne ya k'ara d'aukar rawa, ta tafi luuuu zata fad'i, da mugun sauri Abdallah yayi tsalle ya tarbeta a jikinsa, nan take ta zube a jikinsa a sume. Nahna ta mik'e tana zare ido hankalinta yayi mugun tashi, daga ita har Abdallahn. Miye aka gaya ma Hauwa ne da ya sa ta shiga wannan hali?. Jikin Nahna har yana rawa hannunta na kyarma ta mik'a hannunta domin d'aukar wayar da Hauwa ta saki a k'asa, Abdallah ya rigata kai hannusa ya d'auki wayar. Har yanzu Hauwa na jikinsa a sume, hankalinsa a mugun tashe yake ya ma kasa kara wayar a kunnansa, sai magana ake daga cikin wayar ga dai sunan Inna sun gani, amma ga muryar namiji na fitowa daga cikin wayar..... *To aka ce laifin dad'i k'arewa, a nan na kawo k'arshen Free pages, har yanzu masoya ba'a fara komai ba, a wannan book d'in, yanzu ne ma tafiyar ta soma akwai rikice a gaba. Shin miye ma aka gaya ma Hauwa ne daya sata suma haka?, wai tsayama mi zai faru idan aka sanar da Hauwa akwai auran Abdallah akanta ne?, wacce irin rigima za'ai idan Lubna tasan Abdallah nada mata a wani wajan, kuma y'ar uwarsa ta jini?, kaiii jama'a akwai fa kallo, akwai rigima akwai sark'ak'iya, akwai sauran kallo, akwai sauran rikici wadda zato bai zata ba a wanga book. Ku dai kawai masoya book d'in RAYUWAR MAKARANTA mu had'u a paid book insha Allahu* Hi Masoya book d'in RAYUWAR MAKARANTA, karku shagala da yawa fa, domin book d'in RAYUWAR MAKARANTA yanzun ne tafiyar tashi ta soma, na kud'i ne akan raina d'ari hud'u ne kacal #400, zaka iya turo kud'in ka ta wannan account number d'in. 👇 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank. Sai ka turo shaidar biya ta wannan number d'in👉08130479973