[10/12 à 13:05] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽 Na *Chamsiya Laouali Rabo* ```{MRS SADAUKI}```💫✍️ *FCWA* ☀️ *SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊 ___________________________________ 01 A duniya akwai wata babbar illa wacce ba kowa ke fahimtar illa ba ce sai wanda abin ya faru da shi kamar dai ni da duniya ta yi juyin waina da ni. Farinci;kalma ce da ban san me take nufi ba ballantana na more ta,na taso cikin matsin rayuwa mai cike da ƙalubale da rikitacen al'amari wanda da ace ba a kaina hakan ta faru ba da ko shakka babu ba zan taɓa yarda kan cewa Uwa na iya cutar da Ƴar da ta tsugunnai ta haifa ba. Sunana Janiki,ƴar asalin ƙasar Yuganda ce a wani ƙauye da ake kira da Norobi,ƙauyen ya shahara wurin bai wa al'ada haƙinta.Ni ce ta farko wurin iyayena,sai ƙannaina uku Ayo mai shekara goma sha bakwai,sai Sarah mai 13years sai kuma ƴar autarmu Natasha mai shekara goma.Dukkansu baƙaƙe ne sai ni ɗaya tal ke fara sol kamar zabaya,da wannan jama'ar ƙauyen suke tsokanata da ƴar fara mayya.Tun ina da ƙanannun shekaru ake kirana da haka har zuwa yanzu da nake cikin shekara ta ashirin da biyar. A hankali nake wanke kwanukan da zan zuba abincin rana,ina rera waƙoƙin da ake koya mana a Coci.Saukar dundu na ji a bayana kafin ashar ta biyo,“ to daƙunanna haihuwar asara,kin kama kwanuka kina shafa kamar mai yi wa jariri wanka sai sun sauko daga makaranta ba ki gama ba ko?” muryar Mama ce wacce a kullum nake fargabar jin ta. Jikina na kyarma na ce “ na kusa ida wa Mam...” ko rufe baki ban yi ba ta gwaɓe mini haɓa tare da shure ni da ƙafa tana mai cewa “ don ubanki kar ma ki gama zauna nan ki yi ta shafar kwanukan in ƙannan ubanki ne” ban ce komai ba sai sauri da na ƙara ina mai ci gaba da tsiyayar da hawaye,ina gama wanke wa daidai ƙannaina na shigowa su duka ukun a tare kowacce riƙe da jakar makarantarta. Kamar wasu jarirai haka Mama ta soma tarairayar su tana tambayar su makaranta, sai washe baki take tana fara'a kamar ba ita ce ta gama haɗe mini fuska tana zagina haɗi da dukana ba. “Shegiya mayya ta wani zubo mamu shegun ƙattin idonta tana kallo,ba za ki je ki fidda abincin ba sai na kare miki ƙafa?” Mama ta faɗa a lokacin da na shagala ina kallonsu,sumi-sumi na wuce zuwa mafada.Kamar yadda na san kowa shi ɗaya yake cin abinci haka na ɗauki kwanuka ina zuba abinci har na fidda shi duka,haka na jera kwanukan kan ƙaton faranti na kai gaban Mama. Nan kowacce ta ɗauki nata ni ma na ja nawa tare da komawa gefe na fara ci kenan sai ga Sallamar Hajiyar Lubabatu ƙawar Mama wacce a duniya in akwai wacce ta tsane ni bayan Mama to ita ce ta biyu. Ina ƙoƙarin sunne kai don gudun mugun kallon da za ta watso mini,amma sai ta shammace ni ta sakar min murmushi har da tsarabar furuci mai daɗi. “ Ah ƴata Jakini abinci ake ciki?” ta faɗa . Da sauri na gaishe ta “ ina wuni Tanti?” “Lafiya lau alhamdullah” ta amsa kafin su soma taɓawa ita da Mama,can kuma suka miƙe suka shiga ɗaki.Da wannan damar yasa na matsa kusa da ƙannan nawa ina mai cewa “ yawwa ku koya min karatun” Ayo mai mugun hali ta miƙe ta shige ɗaki,sai Sarah ce ta fara koya min duk da ba a rubuce ne ba amma ina fahimta sosai. “Janiki ashe har yanzu kina ta ƙoƙarin koyon karatu?” Hajiya Lubabatu ta faɗa bayan ta fito na tsawon lokaci da suka ɗauka ita da Mama a ɗaki.Na ɗan saki murmushi tare da jinjina kai,ta ƙara yin ƙasa da murya ta ce “ yawwa ki daure ki koya kin ji ai ana son mace ta waye ta fannin karatu,in kina so ma zan turo malami na Musamman don koy...” maganar ce ta yanke saboda fitowar Mama. “Kin ga fa Ayo ce da rigimar da ta saba ashe ta ji hirar da muka yi” Mama ta faɗa tana murmushi kafin ta janye Hajiya su nufi ƙofar fita da alamu rakiya za ta yi mata. Ina nan zaune sai ga Ayo ta fito tana hararena,wanda kuma ban san dalilin haka ba sai da Mama ta dawo. “To Janiki sai a fara shiri lokacin aurenki yayi,yanzu nan Hajiya Luba ta zo min da shawarar arziki kuma na yi amanna da ita” sai kuma ta yi shiru tana kallona kamar yadda ni ma ita nake kallo. “Ai kin san babban ɗanta Aliyu ko?” Mama ta tambaye ni,na jinjina kai tare da sunne kai ina jin zuciyata na mugun bugawa da sauri. “To da shi muka yanke shawarar haɗa ki aure,tun da dama ba wani karatu kike yi ba sannan ba saurayi ne da ke ba” Mama ta ƙara faɗa .Idona ne suka kawo ruwa,na ɗaga kai dakyar na ce “ Amma Mama tsoho ne fa,ya kai shekara arba'in duka-duka nawa nake?” “Yanzu na haifo ki Janiki!” ta faɗa cikin ƙaraji kafin ta ci gaba da yi min masifa “ wato kin samu zai rufa miki asiri ya aure ki shine za ki wani tsiro min da wani iya yi,a'a ba tsoho ne ba shine tuwo tashi ki bani wuri” ta yi min wata uwar tsawa tare da kai min duka. Da mugun sauri na tashi na shige ɗaki,kan katifa na haye na ci kuka sosai har na gode ma Allah.A haka na samu bacci ya ɗauke ni,haniyar mutane ce ta tashe ni da bushe-bushe. “Me kuma ake yi a gidan?” na tambayi kaina,shigowar da Abba yayi ce ta bani amsar tambayar hannunsa riƙe da alawa da goro.Bakinsa kamar gonar auduga tsabar murna,miƙo min yayi kafin ya ce “ kuɗin an gani ana so ne aka kawo miki Janiki,ina taya ki murna ke ma za ki je ɗakinki?” “Duk yaushe aka tsara wannan ban sani ba? Yanzu fa na kwanta bacci” na yi furicin ina duba tsohuwar agogon ɗakinmu sai na ga ƙarfe wajen biyar har da rabi na maraice alhalin lokacin da na kwanta duka-duka ƙarfe ɗaya ne. Abba bai wani damu da tashin hankalin da na shiga ba ballantana ya bani amsar tambayar da na jefo,kawai ya ajiye goro da alawar ya fice.Ban iya fita ba saboda har yanzu ina jin hayaniyar mutane da saura ba su watse ba,sai bayan gari yayi duhu ne gidan yayi tsit sai a halinsa kawai.Dakyar na je na yi wanka na sauya kaya na zauna tare da rabka uban tagumi ina tunanin zuciya ‘ yanzu dai gaske Umar za su aura min? Mutumin da kullum fuskarsa a haɗe take bai fara'a ? To shi ya ce yana sona ko shi ma dole za a yi masa?’ maganar Mama ce ta katse min tunani “ ki tashi kin yi baƙi” gabana ne ya bada rasss..... [11/12 à 02:37] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽 Na *Chamsiya Laouali Rabo* ```{MRS SADAUKI}```💫✍️ *FCWA* ☀️ *SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊 ___________________________________ 02 “Ba.baaa...ƙi kuma Mama?” na jefo mata tambayar muryata na ɗan rawa ,ƙwanda ta kai min ga kai tana cewa “ munafuka kamar ba ta son auren ,tashi don ubanki ki je suna jiran ki” Wani kallabi na jawo na ɗora a kaina kafin na fita,a cikin rumfa na gan su a zaune kan kujera sun tsurawa ƙofar ɗakinmu ido. Dakyar na aro nutsuwa na gaishe su“ ina wuninku?” “Lafiya lau amaryarmu” suka amsa su duka biyun lokaci guda,a fakaice na ƙare musu kallo suna sanye cikin dogayen kaya amma babu wanda ya ɗora hulla duk da ƙwan fitilarmu bai da wani haske sosai amma hakan bai ɓoye min ganin kamanninsu da Aliyu ba. “To mu za mu wuce dama mun zo gaishe ki ne,kasancewar ɗazu dandazon mutane yayi yawa ba mu samu muka gan ki ba ” ɗaya ya faɗa ,kafin su miƙe dukkan su. “To na gode” shine abin da na faɗa ina mai shigewa ɗaki ba tare da jiran sai sun tafi ba ko kuma tunanin yi musu rakiya. “Har sun tafi?” Mama ta jefo min tambaya,na gyaɗa mata kai ta ce “ mene ne suka kawo miki?” “Babu komai Mama ” na faɗa a sanyayye.Ta ja tsuki kafin ta ce “ wannan shegen sanyin halin ki bar shi tun yanzu,don gidan yawa za ki je sannan mijinki babban mutum ne wanda kullum cikin yin baƙi yake dole ki yi tunanin zama da shi.Yanzu su baƙin kin basu ruwa ma?” Cikin na dube ta na ce “ Mama ruwan me za su sha su da ba wani abinci suka ci ba?” ludayin miya ta jefo min aka yi rashin sa'a kuwa ya same ne ga ƙwandar ƙafa,na saki ƙara tare da soma yin hawaye.Nan Mama ta rufe ni da balbalin bala'i da masifa sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shiru. Haka na rakuɓe can jikin gini ina shafar hawaye,ƙafar kuma tuni ta ɗan kumbura tana min zugi. Tausayin kaina ne ya kama ni,ina daga gefe ina kallon ƙannaina suna lesson tare da yin hira jefi-jefi a tsakanin su amma ni tamkar wata mujiya sun maida ni gefe. ‘ Allah ke da magani,da wannan masifar ta Mama ai gara na yi auren na bar mata gidanta ’ na faɗa a zuci kafin na kwanta kan tsohuwar ledar ɗakin sai baccin wahala. Washegari kamar yadda Mama ta sunnanta mini a kowacce safiya zan miƙe na haɗa wa ƴan makaranta abincin safe haka na tashi tun da sauran duhu na fita zuwa madafa.Dakyar na samu wutar ta kama,na ƙara wanke tukunyar kafin na ɗora kan murhu na zuba ruwa. Garin ɗan wake na ɗauko na zuba kayan haɗi na kwaɓa,kafin na je na share tsakar gida tasss.Ko da na gama tuni tukunyata ta tafasa,sai da na wanke hannuna sosai kafin na jefa ɗan waken sai kuma na shiga yanka albasa da sauran abubuwan da zan soya mai da shi. Ba ni na ida aikin ba sai ƙarfe bakwai da wasu mintina,sai na hau kuma wanke kwanuka.Ina nan a zaune ƴaƴan takarda suka fito duk kowacce ta yi wanka ta shirya. “Janikiii?” Mama ta ƙwala min kira,jiki na ɓari na tafi a guje don amsa kiran hakan ya tuna min da ciwon ƙafata sai na tsangale ƙafar ina mai raba ta da ƙasa.“ Mama ga ni ?” na faɗa ina yamutsa fuska saboda zugin da ƙafar ke yi min,“ daga nan bakin ƙofa za ki tsaya ?” ina jin haka na san da akwai matsala amma na daure na ida shiga,kamar jira take ta kai min duka tana mai cewa “ da kika girka abinci ubanki ya kawo shi da za ki ce ba za ki zuba musu ba? Har da wani zaginta kina yi mata gorin cewa kin kusa bar musu gidansu” Ina jin haka sai na ɗaga kai na dubi Ayo don kuwa na tabbata ita ce ta ja min sharri,ina hawaye na fito na shiga madafa na zuba musu abin karyawa na kai musu. Wanke-wanken da na ƙare cikin kuka kenan,da za su tafi don tsokana har da ce min ta yi “ ƴar aiki mun tafi makaranta” ban kula ta ba sai Sarah ce ta shigar min ta hanyar bangazar ita Ayon. Bokiti na cika da ruwa na je na yi wanka,ko da na fito sai na tarar da robar da na ajiye ɗan wake a tsakar gida alamu ya ƙare. ” Mama ina nawa?” ita ce tambayar da na yi ko da na shiga ɗaki don yunwa nake ji jiya ban ci komai ba na kwanta,duk da ba mu yi girki ba amma su sun ci wanda aka tarbi baƙi da shi. “ Ba ki ci ba ne? To ya ida ” ta bani amsa tana mai ci gaba da cin nata wanda ta baɗe da yaji sosai har sai da yawuna suka tsinke.Ban ƙara cewa komai ba na je na buɗe jakar kayana na ɗauko mai na shafa kafin kuma na fita zuwa ƙofar gida.Kan dakali na zauna ina magana ni ɗaya “ Yesu kana dai ganin halin da nake ciki amma ka yi shiru,sai yaushe ne zaka amsa kokena?” sai kuma hawaye suka zubo min,na duƙe kai ina mai ci gaba da kukan haɗi da ɗaukar wata tsumagiya na soma wasa da ita ina yin zane. Inuwa na gani kai gare ni,da wani mugun sauri na ɗago kai sai muka yi ido huɗu da wani kyakkyawan saurayi.Ya sakar min murmushi kafin ya miƙo min hankici,ban karɓa ba sai farin hannunsa da ƙure da ido ina kallon yadda jijiyoyin hannunsa suka fito sharrr da su tsabar hasken fatarsa. Kan fuskata ya jefo min hankicin ya kuwa rufe ta ruf,da mugun sauri na lumshe ido tare da buɗe ƙofofin hancina ina shaƙar ƙamshin turaren da ke kan kyakkyawan farin ƙyallen. Can kuma na sa hannu na cire shi daga kan fuskata,sai dai wayam ban ga saurayin ba.Waige-waige na soma ko Allah yasa na gansa sai dai tsit layin yake babu kowa ,na miƙe tsaye ina mai cewa “ to ina kuma ya tafi? Amma ai bai kai ace har yayi nisa ba” sai kuma na maida dubana ga ƙasa inda sawun takalminsa ya fito raɗam har da wasu harufa,kamar wata zarariya haka na soma bin sawun takun takalmin ina tafe ina mamaki har na zo hanyar fita gari.Sai kuma na yi tsaye ba tare da na ƙara taku ɗaya ba,na ce “ cab! Ashe ba ɗan ƙauyen nan ba ne ai wannan da gani ma sai a babban birni” sai kuma na juya zan koma,abin mamaki sai na ga nisan komawa can gida ba kamar tafiyar ba.Sai ma a lokacin na yi da na sanin abin da na yi don da wuya har zuwa wannan lokaci ace Mama ba ta neme ni ba.Na kwashe sama da minti talatin ina tafiya kafin na isa gida,sai na tarar Mama ba ta nan sosai na ji daɗin haka kawai na shige ɗaki tare da kwantawa saboda muguwar gajiyar da na ji ta saukar min. A firgice na farka jin sautin muryar Mama tana zagina tare da jefo min tambayar da ta hantsila hanjin cikina “ ina abincin da na ce ki yi kafin na dawo?” Ido na shiga zarowa saboda ni na kasa tuna lokacin da muka yi da ita na yi girki,ga ƴan makaranta kuma sun yi tsaye sun zubo min ido da alamu sun kwaso yunwa. “ Don ubanki ba magana nake yi miki ba? Ina dambun da na ce ki yi?” Mama ta faɗa tana zuba min dundu a baya,cikin azaba na ce “ yana madafa cikin tukunya” a yadda na yi maganar cikin haƙiƙanin gaskiya ƙila shi ya saka Mama fita,ni kuwa da na san ban yi komai ba sai na ƙara tsurewa na zauna zaman jiran ta dawo na karɓi hukunci. “ Ke Ayo kika ce ba ta girka komai ba,je ki madafa ki zuba kan babban kwano a ci gaba ɗaya” Mama ta faɗa bayan ta dawo ɗakin.Sam ban yarda da abin da ta ce ba sai da Ayo ta shigo da dambu yana ƙamshi,duk suka kewaya suka soma ci suna santin yayi daɗi.Ni kuwa ido na tsura musu tare da yin saƙo ina ta son tuna lokacin da na yi dambun,“ Janiki ina kika samu kifi?” tambayar Mama ta katse min tunani,murya na ɗan rawa na ce “ Abba ne ya aiko da shi” Cike da masifa ta ce “ don baƙin hali irin naki shine kuma kika saka shi a miyar dambu?” “Na rage saura yana madafa” na sake sharo wata ƙarya ba tare da na san dalili ba,da wani irin sauri Ayo ta miƙe ta je ta ɗauko Kifin nan kuma suka shiga ci ban sani ba daɗin kifin ne ya shagaltar da su suka kasa ganewa kifi ƙwaya ɗaya sai ci suke ya ƙi ƙare wa ko yaya. Amma ni kam na lura da hakan,sai ya zamana tsakanin ƙaryar da nake yi tana zama gaskiya da kuma wannan abin al'ajabi wanne ya kamata na fi jin tsoro...... [13/12 à 08:05] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽 Na *Chamsiya Laouali Rabo* ```{MRS SADAUKI}```💫✍️ *FCWA* ☀️ *SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊 ___________________________________ 03 Abu dai kamar a mafarki ya tabbata gaskiya ne duk abubuwan nan da ke faruwa.Bayan sun ci sun ƙoshi suka ture Kifin wanda har yanzu kamar yadda Ayo ta ɗauko shi yake ko kaɗan bai ragu ba,“ ga shi nan ki ci ba don halinki ba” cewar Mama tana watso min mugun kallo. Dakyar na iya ɗaga ƙafa na je na ɗauki kwanon da kifin yake ciki na fita can tsakar gida,kasa ci na yi sai aukin tunani da na fara. ‘ To duk wannan wa ya ajiye shi? Ko dai saurayin ɗazu? To in haka ne wane ne shi? Ko aljani?’ sai kuma na waro ido a take kuma na ji wani tsoro ya mamaye ni. Ƙugin da cikina yayi shi ya fargar da ni da yunwar da ke ƙumshe da shi tun safe ban ci komai ba.Haka kawai na ji ban iya cin abin da ban san waye ya ajiye shi ba.Can madafa na kai na ajiye shi sannan na fita zuwa maƙwabta gun ƙawata Rahila,na kuwa yi sa'a ummarta ba ta gidan don sosai ta tsani ƙawancen namu duba da yadda na zama mujiya a cikin ƙauyen babu mai ƙaunar ya raɓe ni. “ Laaa! Wai ke ce? Yanzu kuwa nake shirin zuwa gidanku na kai miki ɗan malele da na yi” Rahila ta faɗa cikin fara'a.Na saki murmushi na ce “ kamar kuwa kin san tun safe ban ci komai ba” Nan take yanayin fuskarta ya canza ta ce “ ba ku yi abincin ba ne ko kuwa yau ma hana miki suka yi?” Na ce “ bani da na ci na ƙoshi na baki labari” ba ta musa ba haka miƙo min shi cikin kwanon mai murfi,na buɗe tare da zauna wa na soma ci . “Akwai sauran yajin ne ki ƙara min?” na tambaya,ta je ta kawo min kafin ta ce “ wane labari ne za ki bani?” ban ɓoye mata ba na labarta mata batun ɗan waken da Mama ta hana min har zuwa aljanin saurayin yau da kuma abubuwan mamakin da suka faru. Rahila ta ce “ ki ce gamo kika yi da aljani na ƙwarai,kin san da cewa ita ma Asabe ta taɓa ganin wani ɗan albarka har ya taimake ta ?” Na waro ido na ce “ wai kuma aljani da gaske?” Maimakon ta bani amsa sai ta canza zancen da “ jiya wai bushe-bushen mene ne aka ta yi gidanku? Na so na leƙa amma Umma ta hana” Nan take na ji abincin ya fita raina,na fidda hannuna tare da sunne kai.“ Mene ne wai?” Rahila ta tambaya da sauri. Dakyar na bata amsa da “ aure za su yi min da ɗan hajiya Luba aminiyar Mama” “Wai Luba ƴar bori ?” Na gyaɗa mata kai kawai,Rahila ta wani ƙara gyara zama ta ce “ cab! Wane daga ciki to? Ai na ga duk suna da aure” “Aliyu” na bata amsa . “Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” ta furta tare da yin shiru,sanin wannan furicin musulmi ba su yinsa ne sai in wani mummunan abu ya faru na yi saurin ɗago kaina na dube ta.Hawaye na gani tanƙam a idonta,hankalina sai ya ƙara tashi na shiga tambayar ta “ Rahila lafiya?” “Janiki har ƙiyayyar da Mama ke yi miki ta kai haka da har ta yarda ta aura miki mahaukaci?” ta yi furicin hawaye na silalo mata. Na daki ƙirji na ce “ mahaukaci kuma?” Ta jinjina kai ta ce “ wane ne bai san Aliyu nada taɓin hankali ba? Tun bayan dawowarsa daga mission ya haukace an ce wai ƙarar alburushi ce ta taɓa masa kwanya,amma wai a hakan Mama ke son haɗa ki da shi?” Jikina ne ya hau rawa kamar wacce aka zubawa ruwan ƙanƙara har sai da Rahila ta riƙe ni gam,“ na shiga uku Janikiii?” ta furta cike da tashin hankali.Da sauri kuma na ture ta tare da miƙewa tsaye ko hannu ban wanke ba na fita a guje zuwa gidanmu . Cak na tsaya ganin Hajiya Luba zaune dirshen kan tabarma ita da Mama suna tsara yadda bikin zai tafi har da zanen kayan katakai. “Ke lafiya don ubanki kika wani shigo a firgice kamar mai figar ruwa?” Mama ce da wannan furicin ,hakan ya bai wa Hajiya Luba damar ɗagowa ta dube ni. “ Ƴata Janiki ƙaraso ki duba da kanki ki zaɓi kalar gadon da za a yi miki ” shine abin da ta ce ,kamar mahaukaciya haka na ƙara kwasa a guje na fita a tsiyace.Gudu nake ban tsaya ba sai da na kai bayan gari sannan na samu wuri na zauna na haɗe kai da gwiwa na soma kuka kamar raina zai fita. Tsawon lokaci ina a haka kafin na ji tsayuwar mutum a kaina,ban wani damu ba na ci gaba da kukana. “ Ke ba ki gajiya da kuka?” na tsinkayo sautin muryarsa,da wani mugun sauri na ɗago na dube shi .Saurayin ɗazu da safe ne,yayi wanka ya sauya kaya sai baza ƙamshi yake. Ruwa ya miƙo min a gora ya ce “ ungo wanke fuskarki sai ki goge ta da wannan ” ya haɗo min har da sabon hankici.Kamar wacce ya yi wa asiri haka na karɓa na buɗe murfin gorar,ina soma wanke fuskata sai na ji duk wata damuwata ta gushe.Na lumshe ido ina mai ci gaba da watsa ruwan da nake jin su tamkar ruwan tsarki da father na Coci ke bamu labari. Ina buɗe ido yanzu ma wayam ban gansa ba,“ to ko dai aljanin ne kamar yadda Rahila ta ce?” na tambayi kaina a fili kafin na miƙe na kama hanyar gida. Kiciɓis muka yi da Hajiya Luba a ƙofar gida,ta dubi fuskata kafin kuma ta maida idonta ƙurrr kan hankicin hannuna.Yadda ta ƙure shi da kallo yasa ni ma na kai dubana,sai na ga a tsakiyarsa an zana masa wani hatimin masarauta. Da sauri na jimƙe shi ina mai cewa “ har za ki tafi?” ta sakar min murmushi ta ce “ eh ai mun gama zaɓen komai” sai kuma ta raɓa gefena ta wuce .Na bi ta da kallon mamaki,sai na ga ta waigo muka haɗa ido da sauri na shige cikin gida. “ Tun da kin dawo daga yawon gantalin sai ki zo ki fidda masara a ruwa ki je ki kai niƙa,yau tuwon laushi za a yi” Mama ta faɗa tana mai ci gaba da ƙirga kuɗin hannunta,na kuma yi imanin cewa Hajiya Luba ce ta bata. Sai da na je can ɗaki na adana hankicina biyu har da na ɗazu kafin na zo na soma aikin da aka sani.Bayan na fidda masarar na je na kai niƙa na dawo sannan na hura wuta,na ɗora tukunyata sannan na soma tankaɗe garin. Haka na yi aikin ni ɗaya ko ijin wuta babu wanda yayi min har na gama,na je na yi wanka . Ana kiran sallar magrib Abba ya shigo a gajiye ,ni ɗaya kawai na gaishe shi ya amsa kafin ya ce “ ki kai min ruwan wanka” “Toh Abba” na faɗa tare da fita na kai masa,kayan da ya cire kuma na ɗauko na fito da su don na wanke Mama ta tsayar da ni. “ Me za ki yi musu?” “Wankewa zan yi” na bata amsa. “Kin manta gobe Lahadi? To ki ajiye su zuwa gobe da safe sai ki haɗa da na yaran duk ki wanke” “Amma Mama gobe akwai zuwa Coci” na faɗa murya na ɗan rawa don ban son yin abun da za ta hana ni zuwa wurin bautar Ubangiji. “Gara da kika tuna min Kirista ta ƙwarai ai ni kin san bani sallah sai ke” Da sauri na sunne kai saboda a duniya ina tsoron mugun kallon Mama,na gwammaci ta dake ni a kansa.Haka ina ji ina gani na mayar da kayan,da kowa ya fara cin abinci ni kasa ci na yi saboda tunani biyu na farko na mahaukacin da zan a haɗa ni aure da shi don na san Rahila ba za ta taɓa yi min ƙarya ba,na biyu kuma sai aljanin saurayi.A haka bacci ya ɗauke ni tun wuri,hakan kuma sosai na ji daɗinsa don tun kukan zakara na farko na tashi na fita na zuba ruwa a manyan robobi tare da fiddo kaya na hau wanki. Ƙarfe takwas na yi na ajiye wankin na je na hura wuta na ɗora ɗumamen tuwo,sannan na so na ci gaba da wankina ina yi ina waƙoƙinmu na Kiristoci. Yunwar da nake ji ya sa na zuba ɗumamen na soma ci da sauri-sauri ina yi ina kallon kayan da suka rage ina addu'ar Allah sa na ida kafin ƙarfe goma ta yi lokacin zuwa Coci. “ Shegiya ɗiyar asara bayan haɗiya tuwo babu abin da ta iya,ji kamar ƴar yunwa yadda take cin abinci ” Mama ce ta faɗa wacce sai yanzu ta tashi daga bacci ta ɗauki buta ta shiga banɗaki. Idona ne ya soma zuba kamar wacce aka zuba wa barkono sai na ji tuwon ya fita raina haka na ajiye shi na wanke hannu na ci gaba da yin wankin. Bayan ta fitowa sai ta ɗora daga inda ta tsaya ta ci gaba da zagina tana aibanta ni har da ce min irin tsiya irin masifa da dukiyarmu ba ta tare komai ba. ‘Wace dukiya Mama ke magana?’ na tambayi kaina a zuci sai dai ban da mai bani amsa haka ta gaji ta bari don kanta. Zuwa ƙarfe tara da rabi tuni na gama wanki,amma dole na jira ƴaƴan gwal suka yi wanka sannan ni ma na yi daga ƙarshe.Dukkanmu shirin zuwa Coci muke har da Abba ,kaya masu kyau duk muka saka kuma iri ɗaya.Ta wannan fannin ne kawai zan ce muke kusan ɗaya da su Ayo,domin duk lokacin da Abba zai sayi kaya to iri ɗaya yake saya mana mu duka huɗun hakan yasa duk kayanmu kusan iri ɗaya ne sai in Mama ce ta ɗinka take banbanta mana wasu kuma su kaɗai take saya ma banda ni. “ Hodar me za ki shafa?” Mama ta katse min hanzari,sai na ajiye na dinga kallon yadda Ayo ke cancara kwalliya amma ni babu damar in yi.Haka na haƙura ,har mun fito tsakar gida Mama ta tsiro da wata sabuwar fita “ wai dama ba ki wanke nawa kayan ba?” Ƙyafƙyaf da ido na yi ina kallon ta kafin na dubi Abba,ai kuwa ya tare min faɗa “ Sulvi ki bari in muka dawo ta wanke wai yaushe ma kika fara bata wanki ban sani ba?” ba ta basa amsa ba ta cillo baki gaba kafin ta rufe ɗaki. Duk muka fita ,taxi Abba ya nemo mana muka shiga aka kai mu babban Cocin garin namu.Tuni ya cika da mutane haka muka je duk muka zauna kan kujeru,muna sauraren waƙoƙin da aka kunna kafin Father ya shigo duk muka miƙe muka gaishe shi.Ya bamu izinin zama kafin ya soma yin wa'azi daga ƙarshe kuma muka miƙe muka ɗora hannu a ƙirji tare da rufe ido muka soma yin doguwar sallah kamar yadda muka saba.Bayan haka kuma ya nemi cikin yara wanda zai rera masa sabuwar waƙar da za mu yi a sallar ƙarshen shekara,na ɗaga hannu don kuwa tuni na hardace ta. “Janiki matso,zo nan ki yi mana” ya faɗa yana murmushi,na tafi da sauri na je gaban mutane ya miƙa min sifika na soma rera ta kamar dama can ni ce na tsara ta,komai daki-daki nake yinsa.Tunk mutane sun fara yin kuka saboda kalmomin da aka yi amfani da su na ban girma da shugabanmu Yesu Almasihu.Cikin masu kuka har da Mama ,da Father ya cire Cross ɗin wuyansa ya saka min aka shiga taɓi nan ma ta zo ta rungume ni karon farko da ta nuna wa duniya ni ɗin ƴarta ce kuma kamar ta yi alfahari da hakan .Sai na ji zuciyata ta yi min sanyi wani daɗi ya rufe ni,na ƙanƙame ta gam ni ma ina hawaye. Ita ce ta ja hannuna muka koma wurin zamanmu, autarmu Natasha sai taɓa Cross ɗin take tana murmushin jin daɗi,bayan an tashi daga darasi sai muka fita aka soma cin girkin rana wanda Coci ke shiryawa duk ranar Lahadi. Da muka fito kowa sai nuna ni yake yayin da wasu iyayen ke yi wa ƴaƴansa huɗuba da su dage su zama kamar ni.Cross ɗin Father aba ce mai matuƙar muhimmanci, wannan yasa kowa ke sha'awar ina ma shi ne.Bayan cin abinci duk a soma watsewa,muka fito bayan Abba ya nemo taxi Mama ta ce “ Za mu wuce gida Mamy don ganin ko lafiya yau ba ta zo Coci ba,dama mun jima ba mu je” Jin an ambaci sunan Mamy yasa da sauri na ce “ Ni kuma zan koma gida na yi wankin kayanki” ta jefo min wani mugun kallo ta ce “ in ma dai don ki saci kuɗina na jiya ne kin yi ga banza na san ko nawa ne,kuma a tare za mu je” tana gama faɗa ta shige taxi su ma ƙannaina haka,dole ni ma na shiga aka kai mu gidan mala'ika wacce na gwammaci matsatsin Mama kan nata.Muna isa su Ayo suka shiga gidan a guje suna ƙwala kiran sunanta,ni kuwa ina daga baya na yi tsaye ina kallon yadda take wani shafarsu kamar jarirai tana murmushi muna haɗa ido kamar ta ga mugun abu ta gimtse fuska ta yi kicin-kicin har sai da Mama ta juyo ta dube ni. “Ina wuni Mo...m ” sai kuma na kasa ƙarasa wa tuna gargaɗin da ta yi min na kar in ƙara kiran sunanta ita ba Kakata ba ce.Ba ta amsa ba sai ma masifa da ta hau yi “ me kuma wannan abar ta zo yi Sulvi?” ta faɗa wa Mama cikin masifa. “Dama yau ne Father ya cire Cross ɗin wuyansa shine na ce bari na zo ita ta nuna miki ” Mama ta faɗa cikin sanyi,saboda duk masifarta da mugunta da baƙin hali to Momy ta dame ta ta shanye don dama can ita ta gado. “To shi ne me? Cross ɗin ce ban taɓa gani ba?” Momy ta tambaya cikin masifa. Ayo ta ce “ ta wuyan Father ce wann...” ta katse ta da cewa “ to shi Father Yesu ne? Ni dai gaskiya Sulvi ba ki kyauta min ba na faɗa miki sarai ina baƙin cikin ganin mayyar nan saboda ita na kamu da hawan jini,a duk in na yi tozali da ita kuma in bai tashi ba sai na yi ciwon zuciya .Na bar zuwa gidanki saboda kar na gan ta na jaza wa kaina masifa,da kuma na hana ki kawo min ita shine kika wani kwaso ta yanzu kika kawo min in ma bindiga zuciyata za ta yi ke ko oho” Tun da Momy ta soma masifa na tsure ta da ido ina kallo yayin da hawaye ke yi min zuba,na rasa daga ina wannan ƙiyayyar ta samo asali amma yau ji na yi ina so na sani .Hakan yasa na je na zube gaban Momy tare da tambayarta “ me yasa kika tsane ni? Me yasa sai ni kaɗai kawai ? Su su Ayo me suka fi ni da kike son s...” sauran maganar ce ta maƙale min jin saukar langa a kaina a zafafe Momy ta bani amsa da “ na saba! Ki dube ki sannan ki dube su kin ga kun yi kama ne?” Duk da uban zugin da goshina ke yi bai hana sauke idona kan ƙannan nawa ba ina kallo,tabbas ta yi gaskiya ba mu yi kama ba ta ko wace siga sai dai ko kaɗan tunanina bai kai ya hango gaskiyar da take son nuna min ba.Ina shirin yin magana Momy ta soma yin wani numfashi kamar za ta shiɗe da alamu ciwonta ne ya tashi...... [15/12 à 05:36] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽 Na *Chamsiya Laouali Rabo* ```{MRS SADAUKI}```💫✍️ *FCWA* ☀️ *SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊 ___________________________________ 04 Hankalin kowa a wurin tashe yake,ya tabbata dai hawan jinin Momy ya tashi.Bakinta sai fitar da kumfa yake,tuni Mama ita ma ta biyo sahuna ta soma kuka.Dakyar na yi jarumtar fita na taro mai taxi,ai kuwa ina zuwa tuni gidan ya cika da maƙwabta a haka na daure na je na shaidawa Mama mai taxi na waje.Momy irin matan nan ne masu ƙiba, wannan yasa sai da wajen mutum shidda suka ciciɓe ta zuwa ƙofar gida,dakyar suka cusa ta a taxi suka wuce asibiti . A ƙofar gida na tsaya ina kallon taxi ɗin har sai da suka ɓacewa ganina. “Duk laifinki ne mai baƙin jini,mayya kawai da ba ta da halin ƙwarai.In Momy ta mutu sai dai ki bar gida don wallahi ba za mu zauna da ke ba muna ji muna gani ki kashe mumu Mama don na san ita ma baƙin cikin ganinki ba zai bar ta ba.Yanzu da kika yi tsaye nan ƙofar gidan ubanki ne?” Ayo ce ke yin magana,ta wani zo ta yi tsaye a gabana tana zagina. Ƙanwata ce,amma banda ikon ko da ɗaga murya ne a kanta ballantana na dake ta.Ban ce mata kanzil ba na kama hanyar gidanmu,tunani kawai nake na tushen ƙiyayyar nan amma ban iya samun hujja ko da ƙwayar zarra ba ce.A haka har na isa gida,nan ɗin ma a rufe na tarar da shi dole na zauna kan dakali na ci gaba da yin kuka. Ƙamshin turarensa ne ya fara kawowa hancina farmaki kafin shi ya bayyana a gare ni.Banda zarrar ɗagowa na dube shi,haka na ƙurewa inuwarsa da ido ina kallo hawaye na masu ci gaba da yi min zuba. “ Janaki !” na ji sautin muryarsa mai kamar busar sarewa,na lumshe ido ina jin zuciyata na tsananta bugu.Haɓata ya ɗago wannan yasa na buɗe ido taram cikin nasa,ya sakar min murmushi kafin yasa hannu ya miƙar da ni. “ Zo mu je ki ga wani abu” ya ƙara faɗa tare da yin gaba,kamar wacce ya tsafe haka na take masa baya.Mun yi ƴar tafiya kafin mu ɓullo cikin wata gonar mangoro,sai a wannan lokaci ya juyo ya kama hannuna ya zaunar da ni kan wani ƙaton icce shi ma ya zauna. “ Me yasa kike kuka?” ya jefo mini tambayar. “Babu komai ” na basa amsa. “ Ki zama jaruma a ko yaushe,yin kuka a kowane lokaci yana taɓa lafiyar ido” “To zan bari” na furta ina sunne kai.Ya miƙe ya je ya ciro mini wani ƙaton mangoro sannan ya jawo ruwa a guga ya wanke shi sannan ya miƙa min “ ki sha” na karɓa tare da ɗora haƙorana akan mangoron na soma sha. “ Wane ne kai?” na samu kaina da furta wa . “Prince Mahadi ” ya bani amsa tare da juyowa yana kallona,muka ƙure juna da ido. “Amma ba nan garin kake ba” na sake faɗa. “ Ɗan Nijar ne ni ” ya bani amsa kai tsaye,sai na waro ido na ce “ Nijar fa? To me ka zo yi nan ?” “Wurin ki na zo mana” Na ɗan saki murmushi jin wani zance,na ce “ kafin nan mene ne dalilin zuwan ka ƙasarmu?” Sai da yayi min wani kallo mai kashe ruhi kafin ya ƙara jaddada maganarsa “ na ce miki wurinki na zo” Kai na sunne ban ƙara cewa komai ba,sai ya kamo hannuna na ɗago da sauri ina kallonsa.Shi ma tsakiyar idona ya kalla na ɗan wani lokaci kafin ya lumshe su ya ce “in baki wani labari?” Ina kallon kyakkyawar fuskarsa na basa amsa da “ eh ina so” Sai ya soma da “ labarin masarauta ne,akwai wani Yarima da duk cikin ƴaƴan sarki ya fi sonsa,ba wai don bai da ƴaƴa maza ba a'a shi ɗin sunan mahaifinsa ya ci daɗindaɗa kuma wannan Yarima ya kwaso kaf halin Sarkin na rashin girman kai da girmama al'umma.Wannan abu shi ya jafowa wannan Yarima baƙin jini a wurin saurin danginsa waɗanda suke uba guda da shi.Kwatsam Yarima wata rana sai ya bar Masarautarsu ya je wani gari domin cika umarnin mahaifinsa na taimakon al'umma ba tare da sun nemi haka ba,magautan Masarauta sai suka fara tsara hanyar da za su bi su kawar da Yarima ba tare da ya sake saka ƙafa a Masarauta ba.Shi kuwa a ɓangaren Yarima haka ya dinga zagaye duniya yana bi gari-gari yana bada taimako har ya zo wani ɗan ƙaramin gari ,su kuma al'ummar yankin nan babbar matsalarsu ita ce rashin ruwan da za su sha. A nan Yarima ya soma fafutukar ganin ya samo hanyar da pampon ruwa zai tsaya a kowanne gida da ke cikin yankin.Aiki ne mai matuƙar cin kuɗi,wannan ya saka bayan kuɗin mahaifinsa shi ma dole ya ƙara da nasa.Kafin soma aikin sai da yayi wa mutanen garin bayani tiryen-tiryen, shugabansu ya amince aka soma yin aikin.To nan ne fa su kuma al'ummar suka dinga bada gudunmawarsu ta hanyar dafa abinci suna kaiwa ma'aikata,irin haka ne kwatsam sai Yarima ya ga wata baƙar mace kyakkyawa wacce ya ji ta kwanta masa a rai” yana kawowa nan sai ya buɗe idonsa,da sauri na sunne kai cike da kunya don tun ɗazu shi nake kallo. Sai yanzu na lura ashe tun ɗazu hannunmu na cikin na juna,na so na janye hannuna sai kuma na tsinkayi muryarsa “ ba ki so na ci gaba da baki labarin ne?” “Ina so amma ka sakar min hannu” “Ta ya zan baki labarin to in na saki hannun naki?” ya faɗa ,ni kuma na dube shi cike da mamaki kafin na ce “ ta hanyar riƙe hannuna shi labarin zai badu?” kai ya jinjina min ,ba tare da ya sakar min hannun ba ya ƙara lumshe idonsa a karo na biyu sai ya ci gaba da cewa “ soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Yarima da ƴar baƙar budurwarsa,sama da watanni biyu kenan kullum in ta kawo abinci sai ta zauna sun yi ta hira.Sannu a hankali ma sai abincin da take kawo wa iya shi ɗaya ke ci,ganin haka sai ta soma bai wa wata muguwar ƙawarta labari wacce ita kuma ta bada gudunmawa baƙar shawara shine su dinga zuba masa maganin mallaka da wanda zai hura wutar sonta a zuciyarsa,don su duk a tunaninsu ba zai aure ta ba.Ƴar baƙa ta bi gurguwar shawara,kullum tana kai wa Yarima abinci,adadin kwanakin kawo abinci adadin yadda magani ke aiki a jikinsa.Kan kace wani abu Yarima ya kamu sosai,kin san ƴan magana na cewa duk inda mugun so yake to sha'awa ce ke yi masa sanɗa.Sai Yarima ya soma bijiro wa ƴar baƙar budurwarsa da muradinsa da farko ta ƙi yarda a ƙarshe kuma ƙawarta ta bata shawarar kawai ta amince ta yadda in yayi devirgin nata ba zai taɓa suɓuce masu ba.Ita kuma babu wani tunani ta amince suka soma keɓewa da Yarima,tun daga wannan lokaci kuma suka fara tatsar shi kuɗi ita da ƙawarta.Kafin kuma su farga Yarima ya bar gari saboda kiran ujila da ya samu cewa Sarki bai da lafiya,bai san gidansu budurwar ba,sannan ita duk tsawon lokacin nan ba ta da wayar hannu haka ya bar ta cikin halin ƙaƙanikayi domin kuwa tana ɗauke da ciki har na wata biyu.Babu jimawa ta soma laulayi,wanda hakan yasa mahaifiyarta ta gane da ta tambayi ba'asi ne ta koro mata bayanin cewa ciki na Yarima ne.A al'adar garinsu duk wacce ta yi kuskuren ƙin kai budurci a gidan mijinta ta zama abar kwatance,to ina kuma ga cikin shege? Hanyar da suka samu mai ɓullewa ita ce aura mata wani saurayi da yake nacin sonta amma mahaifiyarta ba ta so saboda talaka ne.Shi kuwa so hana ganin laifi ya aminta da auren bisa yarjejeniyar ko da ɗaya rana kar ya taɓa nunawa abin da aka haifa banbanci tsakanin ƴaƴan da za su haifa a gaba.Ya riƙe alƙawarin da ya ɗauka,sai dai kash shi wannan ciki da aka haifa na farko yarinyar ta banbanta da sauran ƙannanta...” da wani mugun sauri na fizge hannuna yayin da jikina ya ɗau kyarma,na miƙe tsaye ina kallonsa kamar yadda shi ma ɗin ni yake kallo. Ko ƙaramin yaro aka baiwa labarin nan zai fahimci komai ballantana ni da nake cikin hankalina.Da gudu na bar wurin ko waiwaye babu har na shigo cikin unguwarmu,daidai ƙofar gidanmu na yi tsaye dafe da zuciya. A buɗe na tarar da shi,hakan yasa na shiga kamar wata munafuka aka yi sa'a kuwa Abba da ƙannaina duk suna zaune cikin rumfa yana yanka musu kankana. Ɗaya bayan ɗaya na soma kallonsu,dukkansu kama suke da Abba kana gani ka san ƴaƴansa ne. Kamar wata mahaukaciya haka na wuce ɗaki ko gaishe da Abba ban yi ba,madubi na ɗauka na soma ƙarewa farar fuskata kallo wacce ke ɗauke da zankaɗeɗen hanci har baka,ga gashin gira wanda yake baƙi ƙirin kamar na wanda ya ƙawata manya idona.Laɓana pink ne sirara,a hankali kuma na ture kallabina kyakkyawar sumata ta bayyana baƙa ƙirin da ita wacce tsabar yawanta yake sa ban yi kitso sai da na wanke na naɗe ta a tsakiya sai ya zama kamar na yi acuci maza.Karon farko da na ji sha'awar baje ta amma sai ban yi haka ba.Da gudu kuma na sake fita zuwa gidansu Rahila,aka kuma yi sa'a ummarta ba ta nan yau ma. Ɗakinta na shiga na yi tsaye gaban ƙaton madubinta sannan na warware gashina na cire ribob ɗin.Nan ya zube a gadon bayana da na jawo shi ta gabana har ya wuce ƙirjina,sumar kaina tana ɗaya daga cikin sirrin da Rahila ba ta san da zamanta ba . Tana tsaye tana kallona cike da mamaki tun shigowar da na yi ban mata magana ba sai yanzu. “A cikin ƙabilu wace ƙabila ce kika san masu yawan gashi Rahila? Dubi gashina kamar aljana har ya kusa taɓo mazaunaina ” na faɗa cikin rawar murya idona da ba su gama bushewa ba suka daɗa kawo ruwa. “Fulani ne,sai kuma buzaye” ta bani amsa kai tsaye. “Amma a Yuganda ba mu da ƙabilar nan,wacce ƙasa ce mai irinsu?” “Sai in ko Nijar kin san suna da kusan duk ƙabilun da kika sani,amma wai da gaske gashinki ne dama ba hulla gashin doki ba?” ta faɗa tare da zuwa tana shafawa.A garinmu kusan ƴan mata suna saka hullar gashin doki,don haka ba sabon abu ba ne ko da a ce na fita a haka. Maimakon na ba Rahila amsar tambayarta,wai kawai na toshe kunnuwana ina jin amon muryar Prince Mahadi suna yin gwaro da kalaman Mama wani sa'in yadda take tsare pampon ruwa ta yi ta zagi tana cewa “pampon tsiya,pampon ƙaddara ban ga amfanin kawo ruwa a wannan gari ba dama a haka aka bar mu muka ci gaba da ɗebo su a rijiya” wani sa'in kuma ta kan ce “ duk in na ga pampo takaici nake ji,sai na ji kamar duk na bi kowanne gida na cire shi” Wata uwar ƙara na saki na soma shure-shure rabin hankalina dai ya gushe amma ina ganin wasu abubuwa.Yadda Rahila ta ruɗe ta fita waje da gudu sai ga ta sun dawo da Abba,da lokacin da ya kiran pasto ya zo yayi min ruƙiya yana karanta abubuwan cikin Bible. Na yi tsit ina jan ajiyar zuciya,Abba ya kamo hannuna muka koma can gidanmu.Ya zaunar da ni kan kujera yana kallo,cike da tausayi ya ce “ Janiki tun yaushe kike da Aljanu ban sani ba? Sun taɓa taso miki?” Kai kawai na girgiza masa,su kuwa su Ayo sai kallona suke .Abba ya fita ya kawo cefane,ya miƙa mata ya ce ta yi girki . “ Abba ni ban iya ba” ta faɗa . Cike da masifa ya ce “ ki koya” sai kuma ya fice daga gidan. Bokiti na cika da ruwa da kuma buta uku na shiga banɗaki na yi wanka na wanke dogon gashina wanda a ƙa'ida sai wata-wata nake wanke shi.Ban bari ya wani bushe ba na yi parking nasa tare da laulaya shi ya tsaya tsab kamar tayar mota. Cefanen na karɓa na ɗora mana girkin dare,duk yadda na so na cire tunanin Prince Mahadi na kasa .Na yi wa kaina tambayar ” kenan ni shegiya ce ba da aure aka haife ni ba?” ya fi shuren masaki. Ban gama girkin ba har sai da aka yi kiran sallah,haka na zuba musu sai Ayo ta kawo wani kwano ta ce “ ki zuba wanda za a kai asibi” ba tare da na ce komai ba na karɓa na zuba. “ Shi ne ko jikin Momy ba za ki tambaya ba saboda mugun hali” ta faɗa tana mai ficewa,na bi bayanta da kallo ko kaɗan ban ji haushinta ba saboda a gidan ubanta nake ni nawa mahaifin a tsallake mahaifiyata yayi ya bar ta tun ina ciki. Na goge ƙwallar takaici ina jin tsanarsa na ɗarsuwa a zuciyata,bayan na fidda abincin na kai kwanukan can ɗaki na jera.Na miƙawa Sarah da Natasha nasu suka fara ci uwar iya yi kuma ta ɗauki na ƴan asibiti ta wuce. Kan shimfiɗa na kwanta tare da yin lamo,na ma rasa wane tunanin zan yi. Sallamar Rahila na ji a tsakar gida,da sauri na tashi zaune ina amsawa tare da bata izinin shigowa. Bayan ta shigo ta zauna sai ta miƙo min wani ƙaton kofi na roba mai murfi ta ce “ kunun madara ne na san kina sonsa shine na yi miki,ki sha tun da zafinsa ƙila ma ba ki ci komai ba” “Na gode” na faɗa tare da buɗewa na soma sha a hankali,yayi daɗi sosai hakan yasa na sha rabi sannan na ajiye.Rahila ta dafa ni kafin ta ce “ don Allah ki cire damuwa a ranki,kin ga ba isashiyar lafiya ce da ke ba” “Na gode sosai Rahila” na furta ina goge ƙwalla. “Ya Salam! To kuma mene ne na kuka? Ina Mama?” “Tana asibiti , Momy babu lafiya ” “Ok to ni zan koma gida kar Umma ta neme ni” har zan yi mata rakiya amma ta hana ni. Bayan fitarta ne na bai wa su Sarah sauran kunun suka sha,ni kuma na ci gaba da tunanina har bacci ya ɗauke ni. Washegari tun safe na tashi na yi aikin gida kamar kullum,suka ci abinci kafin su wuce makaranta Abba ma tuni ya fita kasuwa.Kayan da na wanke jiya na kwashe na ninke su sannan na sakawa kowacce a jakar kayanta,na Abba ma haka.Sai kuma a lokacin na ɗauko na Mama na wanke,bayan na gama komai na fita na zauna kan dakali da tunanin Prince Mahadi zai zo sai dai wayam sai duban hanya nake shiru. Taxi ce ta tsaya ƙofar gida,Mama ce ta dawo fuskar nan tata kicin-kicin kamar wacce ta dawo daga zaman makoki.Ni kuwa sosai na yi kewarta duk da kuwa tana takura min amma sai na ji gidan yayi min girma da ba ta nan. Na miƙe da saurina na ce “ sannu da zuwa Mama ” kanzil ba ta ce min ba ta wuce ciki,na take mata baya. “Jiƙa-jiƙar mene ne nan kika yi? Don iskanci wannan har wanki ne? Haka ake wanke kaya duk ba su fita ba sai uban datti? Don ubanki zo ki kwashe su ki ƙara wankewa” Shine abin da ta ce min tana hararena,na sunne kai na amsa da “ to” ta wuce ciki ni kuma na kwashe kayan haka na ƙara tsoma su a ruwa na wanke ba don ba su fita ba sai don tsiyar gumin Mama da ba ta ƙaunar ta gan ni zaune ina hutawa. Daga can cikin ɗakin ma ban tsira ba sai saƙon zagi take jefo min tare da aibanta farar fatata da ɓakar kala mai hasken tsiya da bai tare komai ba. Ni dai banda hawaye babu abin da nake yi,ban ga dalilin da zai sa a kama ni da laifin da ba ni ce na aikata ba.... [17/12 à 08:08] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽 Na *Chamsiya Laouali Rabo* ```{MRS SADAUKI}```💫✍️ *FCWA* ☀️ *SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊 ___________________________________ 05 Sati guda currr Mama ta ɗauka tana azabtar da ni da yunwa,ba wai ba ta bani abincin ba ne a'a sau ɗaya tal nake da damar cin abinci a wuni a maimakon sau uku.Kuma wanda ake bani ɗin ba wani ba ne,ƙarin haushi kuma ni ce ke girka musu abincin wani sa'in ma ita Mamar sai na yi mata nata daban saboda juna biyun da ya bayyana gare ta mai kwaɗayi. Yau ta kama asabar,gobe kuma ranar zuwa coci in na tuna da goben zan kai wa abin bautar tamu kokena a ɗakinsa har wani sanyi nake ji yana ratsa ni. Tun wuri na yi dukkan ayyukana har da wankin kayan ƴan gidan,sannan na yi musu girki.Ina zaune gefe ina kallon su suna cin girkin rana,shinkafa da miya ce na yi musu sai ƙamshin kifi take. “ Ko a zuba miki tun yanzu?” Mama ta jefo min tambayar,na jinjina kai alamun eh.Sai ta ɗauri wani ƙaramin faranti ta zuba min tare da turo shi gabana tana zagina “ don ubanki gobe ma ki sake yi min laifi,azabar da zan yi miki sai ta fi wannan.Kuma ki bar kallona da shegun idanun naki masu kama da na aljanun ruwa ” Ban ce mata komai ba na ɗauki abincin na fara hannu baka hannu akushi,ko minti biyu cikkake ban ɗauka ba na cinye kuma ban ƙoshi ba.Sai na soma kallon su Ayo da har yanzu suke cin abinci suna hira hankali kwance,ni kuma yatsuna na soma siɗewa ina jin hanji cikina na yin ƙugi alamun dai abincin bai ishe su ba. Mama ta tashi ta ɗauki buta ta shiga banɗaki,da sauri Sarah ta cika hannu ta zuba min a farantina har sau biyu.Jikina har rawa yake wurin soma ci. “Tukunyata kika buɗa kenan?” Mama ta faɗa cike da masifa,na girgiza mata kai.Uwar masu mugun hali ta ce“ cikin namu ta damtsa ta ƙarawa kanta” Mama ta sa hannu ta buge farantin abincin ya juye ga ƙasa,ta dungure min kai ta ce “ ke da baki jin kunya abincin ƙannan naki za ki ci?” Sarah ta ce “ Mama ni fa na zuba mata na ga ba ta ƙoshi ba” Da sauri Ayo ta ce “ ƙarya ce Mama Janiki ce ta ɗeba da kanta kin ga sawun ƙaton hannunta ma” Da harara Mama ta bi ni kamar idon za su faɗo kafin ta shige ɗaki,ni kuma da sauri na kwashe abincin na je wurin pampo na wanke shinkafar.Yunwa ce ta saka ni na ci haka nan,sai kuma na sha ruwa na fita na zauna kan dakali. Tunanin abubuwan da Mama ke yi min na soma,hawaye suka zubo min na ce “ ban san me zan yi don na faranta ranki ba Mama da tabbas sai na yi shi” sai kuma na goge hawayen kafin na ci gaba da cewa “ duk kai ne ka ja min da ace ba ka kusance ta ba da tabbas ba za a samu cikina ba,na tsane ka! Ban sonka!” na furta kamar ina gaban shi mahaifin nawa. Idona na ji an rufe min ta baya,na saki ɗan murmushi na ce “ Rahila ce” da sauri ta buɗe min idon tare da dawowa gabana ta yi tsaye. “ Kukan mene kike?” “Babu komai daga ina kike da tsakar rana?” “Umma ta aike ni na karɓo ɗinkunanmu,bari na nuna miki ” Rahila ta faɗa tare da ajiye ƙatuwar ledar kan dakali ta buɗe ta soma nuna min ɗinkunansu kala uku ita da Mamarta duk zanuwan iri ɗaya ne gwanin sha'awa. Ban san lokacin da na ce “ kin ji daɗinki Rahila ke Umma na son ki” Ta ce “ haba Janiki wace irin magana ce wannan? Ke ma ai Mama na son ki kawai dai don kuna da yawa ne shi yasa kike ganin kamar tana nuna banbanci ni kuma kin ga ni ɗaya ce kawai mace ga Umma” Na girgiza kai na ce “ wannan bai isa yasa Mama ta ƙi ni ba,kullum tana hantara ta.Kin ga mu bar hira nan zuciyata na ƙara ciwo” “Ya maganar aurenki?” Na taɓe baki na ce “ har yanzu dai Hajiya ba ta sake zuwa ba” “Shi Aliyun ya zo?” “A'a fa,Rahila ga Umma can ta leƙo ki je kar ta yi miki faɗa ” na faɗa ,da sauri kuwa Rahilar ta tafi saboda in ka ga Umma na yi mata faɗa to a kaina ne kawai kwata-kwata ba ta so ta gan mu tare. Ni ma tashi na yi na koma gida,masarar tuwo na fidda a ruwa kafin na je ɗaki don karɓo kuɗin niƙa.Mama tana kwance na kira sunanta,shiru ba ta amsa ba sai a na biyun ta tashi da ta yi min wata uwar tsawa har sai da na firgita. “Na ce mene?” “Kuɗin niƙa” na bata amsa. “Saboda kuɗin niƙa sai ki tashe ni ina bacci? ” “Ki yi haƙuri ban san bacci kike ba” na faɗa tare da fita waje,Ayo wacce suke exercices ita da sauran ta tuntsire da dariya kafin ta yi min gwalo sai ta miƙe ta shiga ɗaki. Babu jimawa ta fito tare da cillo min kuɗin niƙan,na duƙa na ɗauka tare da zuwa na ɗauki robar masarar na fice.Ina isa mashin na tarar da layi,na ajiye nawa kafin na koma can nesa da mutane na zaune.Idona suka ciko da hawaye,tunanin shan maganin ɓera ya zo min a kwanya na mutu kowa ya huta. “In kin gama kukan ungo ki ci” na ji muryarsa kamar daga sama,na ɗaga na dube shi kafin na dubi abin da yake miƙo min.A take yawuna ya tsinke,hannu na rawa na karɓa ba tare da jira ba na soma ci. Ya ja ajiyar zuciya tare da zama kusa da ni,bai ce min komai ba har sai da na ci rabin abin da ya kawo min wanda ban san taƙamaimai mene ne ba amma a tsakiyar akwai niƙaƙen nama. Gorar ruwa ya miƙo min na karɓa na sha,na yi ajiyar zuciya tare da dubansa cikin ido. “ Shikenan sai kika gudu kika bar ni?” ya faɗa . Na sunne kai kafin na ce “ da gaske wannan shi ne tarihina?” Ya saki murmushi mai sauti ya ce “ eh sosai” “Amma kai ya aka yi ka sani?” “Saboda ba ki san ni ba shi yasa har kika yi wannan tambayar,amma ni da nake yarima mai jiran gado jinin masarauta ai wannan ba abin mamaki ba ne?” “Kenan tsafi kake?” na samu kaina da tambaya.Bai ce komai ba ya miƙe tsaye,“ ina za ka je ?” “Zan koma gida mana” kafin na kai ga cewa komai mai yin niƙa ya kira sunana na waigawa don na amsa masa kawai ban farga ba Prince Mahadi ya ɓace. Niƙana na je na ɗauka tare da biya sannan na wuce gida,ragowar abincin da ya bani sai na kaiwa Natasha ta karɓa cike da murna ta shiga ɗaki. Ina tsaka da hura wuta Mama ta shigo madafar ta yi tsaye kaina,“ gidan uban wa kika samu gurasa da nama?” Gabana ne ya bada wani rasss ,na dubi Mama kawai ina zarar ido ga kuma Natasha gefenta tana cin abincin. “Da ke nake!” ta ƙara faɗa a dake tana haɗe rai. Murya na ɗan rawa na ce “ bani aka yi ” “Na sani ai,uban wa ya baki shi nake son sani?” Idona ya kawo ruwa na ce “ sadaka aka ban” ban rufe baki ba ta shure ni da ƙafa tana cewa “ almajira ce ke ballantana a baki sadaka? Wato daga jin za a yi miki aure shine kika fara biyar maza? ” nan ta rufe ni da duka kafin ta ce “ taso ki biyo ni don ubanki sai na duba ki” haka na tashi ina kuka na bi bayanta har banɗaki. “ Ki cire pant ɗinki na duba ki” ta faɗa ,jikina ne ya ƙara ɗaukar mazari yayin da kukan da nake ya ƙaru na buɗe baki da niyyar yi mata rantsuwa amma marin da ta sauke min yasa na yi yadda ta ce.Na rumtse ido gam,ina jin kamar zuciyata za ta fashe tsabar baƙin ciki yadda Mama ke duba ni har da gwada saka min yatsa ta yi kafin ta fita ta bar ni nan cikin banɗaki ina marayan kuka. Sai da na yi mai isata kafin na miƙe na fito,Ayo ta bi ni da kallon tausayi kafin ta je kusa da Mama tana cewa “ Mama kin san halin Janiki ba za ta taɓa aikata abin da kike zargi ba,kuma sam hakan da kika yi gaskiya bai dace ba” “Ki rufe min baki ko na ci mutuncinki,so kike na zuba mata ido ta je ta lalace?” Mama ta faɗa . Madafa na shige ban ƙara jin abin da suka tattauna ba,haka na yi musu girkin duk raina a dagule.Bayan na gama na ɗumama ruwa na je na yi wanka,amma duk da haka zazzaɓin da nake guje ma sai da ya saukar min.Haka na je na shige ɗakinmu na kwanta kan katifata na duƙunƙune na soma rawar sanyi,har aka kira sallar isha'i ban fito ba.Ina jin muryar Natasha na cewa ga lemu da ayaba da Abba ya kawo amma ban iya ɗaga kai na dube ta ba ballantana na karɓa,tana fita kuma Ayo ta shigo tana tambayata. “ Janiki ba ki sha ne?” dakyar na buɗe fuskata na ce “ banda lafiya ” sai ta matso kusa da ni ta zo ta ɗora hannunta kan wuyana kafin ta fita.Babu jimawa shi ma Abba ya shigo kafin ya ce na tashi ya bani magani.Haka ya ɗebo ruwa a kofi ya bani na sha cike da tausaya wa ,sai dai kamar ma an ƙara wutar ciwon sai abin ya ƙara ƙamari.Da gudu na fita na soma kelaya amai kamar raina zai fita,na zube nan cikin rumfa ina jan numfashi. Ina jin Mama na masifar ita dai ba da kuɗinta za a kai ni asibiti ba,amma a haka Abba ya fito yasa na wanke baki ya kai ni asibiti.Ina tsoron allura hakan yasa sai da ya riƙe ni sannan aka yi min,bayan mun dawo ne na samu na ci ayabar sai na kwanta na lumshe ido babu jimawa bacci ya ɗauke ni. Washegari na yi ranar tashi,ko da na farka har sun share ɗakuna da kuma tsakar gida.Girkin ma sun ɗora,haka na je na gaishe da Mama da Abba shi kaɗai ya amsa ita kuma banda saƙon mugun kallo babu abin da ta yi min. “ Munafuka yanzu da aka gama aikin gida ai ga shi can ta fito,kuma wallahi ba za ki je coci ba gida za ki zauna” na tsinkayo furicin Mama ina ƙoƙarin shiga banɗaki.Daga nan ina jin yadda Abba ke cewa “ daga yau ba ta yi aikin ba shikenan ta zama munafuka? To nan gaba ayyukan gidan raba su za a yi ita da sauran danginta su rinƙa yi a tare,wankin kaya kuma kowa ya wanke nasa” Ina jin Ayo na cewa “ Abba mu da muke zuwa makaranta” “Ai ba ku yin ta maraice sabka guda kuke yi,don haka in ta yi aikin safe ku sai ku yi na maraice ke da Sarah.Ita ma da zarar an bani kuɗina zan mayar da ita makarantar ta ci gaba da karatunta” “Auren fa?” wannan karon Mama ce ta yi maganar. “Aure ai bai hana karatu” “Amma dai ka san yanzu ta kusa shekara goma da barin makaranta ko? To wane aji za a saka ta?” “Daga inda ta tsaya za ta ci gaba,ai shi karatu bai da girma ko ke yanzu kika ce kina son komawa sai na mayar da ke” Abba ya faɗa cikin tsokana. Daidai nan na fito daga banɗaki sai na ga Mama na murmushi muna haɗa ido kuma ta gimtse fuska tare da kawar da kai.Ni kuwa ji na yi kamar na je na rungume Abba tsabar farin ciki,dama can mugun hali na Mama yasa na bar zuwa makaranta kawai don na kula da su Ayo ita kuma ta fice wajen kasuwancinta wanda a ƙarshe jarin ya karye ta zauna gida. Abincin kari muka ci,yau na ci na ƙoshi saboda a gaban Abba ne.Bayan haka aka soma shirin zuwa Coci ni ma na shirya kuwa sai dai yau ba kaya iri ɗaya muka saka ba saboda banda irinsu su da Mama sai suka yi anko. Da muka fito fuskar Abba ta nuna bai ji daɗin yadda aka ware ni ba,amma sai bai ce komai ba muka fita waje har muka shiga taxi Mama ba ta yi ƙorafin don me na biyo su ba. Da muka je can coci sai na hangi Momy,gudun fitina yasa na zauna a nan gaba yayin da su kuma suka je can wurin ta.Da lokacin yin sallah da addu'a yayi haka na lumshe ido na ta kai kokena wurin Yesu cike da yaƙini.Bayan nan aka soma gwajin fasaha ,tambayoyi ne akan rayuwar Yesu duk wanda ya sani sai ya ɗaga hannu ya bada amsa,yau ma kamar waccan satin na fi kowa bada amsa wanda a ƙarshe har Father ya buƙaci na je can kan dandamali. Lasifika ya bani tare da cewa na bada tarihin Yesu,ai kuwa haka na soma zayyanowa har ina haɗawa da wasu baitoci.Liƙen kuɗi aka soma yi min kamar ba gobe,Sarah ta zo tana tattare min har na kammala shi ma Father sai da ya bani kyauta ta musamman tare kuma da yin selfie da ni. Bayan an tashi dukkan kuɗin da na samu sai na miƙawa Abba ,ina ganin Mama kamar ta fashe da alamu ta ji haushin haka.Da muka isa gida kuwa Abba ya sake jaddada alƙawarinsa na mayar da ni makaranta,a ranar ya sayo min uniform da kuma Books da duk abin da zan buƙata. Washegari sai da na yi aikin da na saba yi kafin na yi wanka na shirya.Mama dai sai cika take tana batsewa amma wannan bai hana Abba kai ni makaranta ba,duk da ina da shekaru dayawa hakan bai dame ni ba musamman da na ga akwai wanda suka kai ni da girman jiki.Ina da ilimina dama,hakan yasa sosai nake fahimtar abin da ake koyawa wasu kuma dama tuni Sarah ta koya min su.Kamar a mafarki nake jin kaina haka na yi shawagi a filin makarantar da muka fito shan iska,abinci ma kasa ci na yi saboda shauƙi har muka taso na nufo gida. Ina shigowa Mama ta ce “ sai ki ɗauki cefane ki ɗora girki tun da baƙin ciki ya rufe miki ido sai da kika koma makarantar” ban ce mata komai ba na ɗauki cefanen sai da na cire uniform na je na hura wuta ,babu jimawa na haɗa jalob ɗin taliya.Na sauke tukunya na shiga wanka,bayan na fito na ɗauki kasona wanda Mama ta zuba min na ci na wanke hannu ba don na ƙoshi ba.Amma na share tare da ɗauko kayan makaranta na soma dubawa,sallamar Hajiya Luba ta saka gabana faɗuwa.Kamar yadda na yi tunanin kuwa zancen auren ne ya ƙara kawo ta inda take shaidawa Mama ranar juma'a za kawo lefe kenan sai ta sanar da dangi waɗanda za su tarbi kaya.Tun kafin ta fita kuwa Mama ta soma kiran wayar na kusa da ita tana sanar da su za a kawo lefen Janiki,har wani murmushi take tana nuna tsantsar farin ciki wanda ni kuma tuni zuciyata ta aminta Mama ba za ta taɓa yin farin cikin akan abin da zan amfani da shi ba sai dai in wanda zai cutar da Ni ne..... [19/12 à 04:41] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽 Na *Chamsiya Laouali Rabo* ```{MRS SADAUKI}```💫✍️ *FCWA* ☀️ *SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊 ___________________________________ 06 Shirye-shiryen kawo lefena bai sa na ƙi zuwa makaranta ba,sai dai sam na kasa nutsuwa na yi karatun yadda ya kamata.Tsorona guda shine kar bayan auren mijin da za a aura min ya hana ni karatu, wannan na samu Abba na kai masa kokena ya kuma alƙarwanta min abu ne da ba zai taɓa faruwa ba. Ranar juma'a ce suka tsayar don kawo lefe,yau ta kama Alhamis tuni kuwa dangin Mama sun cika gidan sai gyaran kayan da za a yi miya da su gobe suke.Abin da ya fi ban mamaki kuwa bai fi yadda na ga ana jiƙon ruwan lalle ba,wanda a al'adar garinmu ranar da aka ɗaura aure kawai ake yi wa amarya wanka da su.Amma sai na yi shiru na ja bakina,ina rakuɓe na kasa cin komai sai ga Rahila ta shigo.Kusa da ni ta zauna,kamar yadda ba na farin ciki da wannan auren ita ma haka. “ Ashe har da ɗaurin duk za a yi a goben?” Rahila ta faɗa ,sai na yi rau-rau da ido amma na kasa cewa komai yayin da ita kuma ta ci gaba da cewa “ an ce gobe bayan sallar juma'a za a ɗaura a masallaci,irin na shari'ar Muslunci za a yi tun da wai mahaifinki ma musulmi ne” sai a lokacin na lumshe ido kafin na maimaita kalmar “ musulmi?” cikin wata irin murya Rahila ta ce “ eh wai! Kenan Abba ba shi ya haife ki ba?” na buɗe idona hawaye na masu surnano min na dubi Rahila da kyau na ce “ ni ma ban sani ba,ƙila hakan ne.Amma ke wa ya faɗa miki?” “Umma na ji suna yin hirar ita da ƙanwar Hajiya Luba ” ta bani amsa,sai na sunne kai ina wani irin huci.“Mahaifinki Balarabe ne wai,kuma fari ne tasss kamar ke,sai yanzu ni ma nace ai sai larabawa irin wannan gashi naki tubarkallah ” “ Kaina yana ciwo Rahila ki taimaka min da magani” na furta tare da yin kwanciya. “To bari na je na siyo” tana fita na je na buɗe jakar kayana na ɗauko hankicin da Prince Mahadi ya bani na soma goge hawaye da shi ina shaƙar ƙamshinsa.Ba ta wani jima ba ta dawo ta kawo min maganin,na karɓa na sha sai kuma duk muka yi shiru. Mama ta shigo ta dube ni kafin ta ce “ Rahila ko kuna da buƙatar yin wani ɗan shagali ne?” “A'a Mama” ta bata amsa. “To ki yi mata ko dilka ne kafin gobe a yi mata lalle,kitso dai kam sai dai ta zauna da gashinta don babu ƴar wahalar da za ta kitse mata wannan tulin gashin” Mama ta faɗa tare da jefo wata baƙar leda.Rahila ta ɗauka tare da buɗewa sai ta kalle ni kafin ta ce “ kayan gyaran jiki ne,bari na haɗa sai ki shafa a dukkan jikinki” kanzil ban ce mata ba har ta ɗauko wani ƙaramin kwano ta haɗa kayan sai da suka yi kamar minti goma kafin ta matsa min na tashi na shafa. Wani tsohon zanena na ɗaura zuwa ƙirji kafin Rahila ta soma shafa min dilkan a kaf jikina.Sai da na yi kusan awa ɗaya kafin ta je ta kai min ruwan wanka,dakyar na iya fita saboda idon mutane.Bayan na fito daga wanka haka suka ta yaba yadda na ƙara kyau,ita kanta Rahila haka ta yi tsaye tana kallona kafin ta taɓe baki ta ce “ wannan ɗan tsamin ran ko an yi dilkan ma ai ga banza” “In ma dai iya tsamin ran ne kawai da sauƙi,in ɗayar maganar ba ta tabbata ba” na faɗa kamar zan yi kuka.Rahila ta ja numfashi kafin ta ce “ to da yake an ce iya ƙarar alburushi ne ya taɓa masa ƙwaƙwalwa,ƙila haukan ba yadda muke tunani ne ba” “Sani dai sai Allah ” na faɗa kafin mu soma yin hira jefi-jefi.Da Rahila ta tafi gida sai na ji kaɗaici ya ƙaru amma haka na daure,sai wuraren magrib su Ayo suka shigo gidan ashe wurin kitso da lalle suka je .Abin da na fahimta hatta su sun san gobe ake ɗaura min aure amma ni banda darajar da za a sanar da ni. Natasha ta zo ta faɗa jikina tana nuna min kitson da aka yi mata har da duwatsu,yadda take murna da nishaɗi sai na ji sanyi a raina. “Hum! Sai wani murmushi take kamar wani auren ƙwarai” Ayo ta faɗa wacce ita ma ta yi kitson da lalle,na ɗaga kai na dube ta kawai ban ce mata komai ba.Sai ta ja tsuki ta fita,Sarah ta matso tana cewa “ ki bar kula ta,so take ta ɓata miki daren aurenki ki kwana da baƙin ciki” “Mu ga kitson naki ke” na faɗa na yi kamar ban ji me ta ce ba,ta cire hullar kanta na gani.Da na ga kitson sai na ji ina sha'awar ganin gashina a kitse sai dai kuma na yi saurin cire hakan a raina sanin abu ne da ba zai yiyu ba,rabona da kitso tun ina ƙarama shi ma dunƙule biyu ne Mama ke yi min sai ta yi ƴan tsoraye a sama. Ina nan zaune aka kawo min abinci har da ruwan da zan sha,na tsurawa abincin ido ina kallo yau ce rana ta farko da aka taɓa yi min wannan gatan sai na saki ɗan murmushi tare da jawo kwanon na soma ci .Ina tuna gobe ne fa aurena sai na ji ya fita raina ba don ban jin yunwa ba sai don fargaba.Ƙawayen Mama da da danginta na ta ci gaba da yin hidima kafin ɗaya daga ciki ta kawo min wani tsimi ya fi kalar biyar,ban san na mene ne ba amma dai na yi biyayya na sha sauran kuma ta miƙa min ta ce na dinga sha har ya ƙare sai kuma wasu ƙullinka gari da kwalin madara su ma ta faɗa min yadda zan sha,ɗaya ne ta ware daga cikinsu ta ce “ wannan dole sai bayan sallar magrib za ki sha” kai kawai na gyaɗa tare da amsa. Bayan fitarta ne na jawo sabuwar ƴar ƙaramar trollyn da na ajiiye domin saka abubuwana,na zube duk magungunan sannan na kwanta ina ta ci gaba da wahalar da kwanyata da tunani iri-iri.Duk gari yayi tsit ba ka jin sautin komai sai na karnuka,tuni kowa ya samu wuri ya kwanta amma ni sam bacci ya ƙauracewa idona.Haka na yi ta juyi ina jin kamar na tashi na fita amma sai na haƙura na ci gaba da bulaye a tunani a haka ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba. Washegari hayaniyar mutane ce ta tashe ni tun asubah,kasancewar akwai waɗanda suka kwana gidanmu akwai kuma musulmi daga cikinsu.Daga inda nake kwance nake kallon yadda wata ke yin sallah cike da nutsuwa tana karanto wasu abubuwa da ban san na mene ne ba,har ta kammala ina kallon ta .Na ja ajiyar zuciya,ina sha'awar musulunci suna burge ni musamman in sun yi shigarsu ko ina a rufe. “Ki tashi ki yi wanka,ki shafa dilka sannan kuma ki turare jikinki da wannan kafin mai lalle ta zo” Mama ta faɗa cike da sanyin murya,na dube ta sai na ga duk ta yi wani iri amma ban tambaye ta dalili ba na tashi na yi yadda ta ce . Ko da na yi wanka na biyu tuni wacce za ta yi min lalle ta zo,doguwar riga na saka na zo na zauna kan tabarma kafin a soma sai da aka bani kunu mai zafi na sha. Kusan awa huɗu ana yi min lallen kafin a ida, jefi-jefi muna taɓa hira da mai lallen har muka yi ɗan sabo. Wuraren ƙarfe ɗaya na rana Abba da abokansa tuni sun taru da kuma dangi Mama maza.Tun a lokacin na soma jin gabana na faɗuwa,ina jin ƙarar cirawar motoci na sunne kai ina jin kamar zuciyata za ta fasa allon ƙirjina ta faɗo.Kamar minti talatin haka sai kuma ga su sun dawo ,wani maroƙi kuwa ya soma shela “ An ɗaura aure ya ɗaru,Aliyu Jafar ya zama mijin Janiki Al Haris ” Duk da ina cikin tashin hankali bai hana ni maimaita sunan ‘ Al Haris ’ a zuciyata ba,wato sunan mahaifina kenan,don dai shi Abba sunansa ba haka yake ba . Mata biyu ne suka ja ni zuwa banɗaki,kan wata kujerar katako na zauna bayan na cire doguwar rigar jikina kamar yadda suka ce.Haka suka yi min wanka da ruwan lalle,sai a lokacin kuma aka wanke min sumar kaina tasss har da saka min turare.Sai waƙe-waƙe suke har aka gama,sabbin kaya aka saka min haka ma takalmi sannan aka luluɓa min wata dara sabuwa dal aka fito da ni sai guɗa ake ta ko ina. Ɗakin Mama aka kai ni har kan gadonta,wanda yau ne kawai zan ce na zauna shi.Banda kuka babu abin da nake yi,yayin da ƴan uwanta ke yi min nasiha gefe guda kuma Mama ce hakimce cikin shigar sabbin kaya sai amsar kuɗin biki take. Dakyar na iya buɗe fuskata aka ɗauke mu hoto kafin na koma can ɗakinmu.Abun farin ciki sai na tarar da ƴan makarantarmu sun zo duk da kuwa ban gayyace su ba na san ji suka yi.Sai na ɗan saki raina muna hotuna,Rahila ita sai wuraren ƙarfe biyar ta shigo gidan ta rungume ni muka hau kuka sai da muka yi mai isarmu sannan muka yi shiru.An ci an sha amma ni kam ko miyar bikin ban lasa ba,mun yi hotuna ni da ƙannaina kafin motocin ɗaukar amarya su zo. Tuni kuwa an sa na yi wanka an fitar min da kayan da zan saka,ban yi kwalliya ba sai dai Rahila ta yi min kalba guda biyu ta zubo min su a gaba.Haka aka zo aka ja ni aka kai ni gaban Abba da Mama don neman gafara da kuma yi min addu'ar fatan alkhairi akan sabuwar rayuwar da zan fara .Idona cike da hawaye nake kallon Mama wacce zuciyarta ta karye take goge ƙwalla,haka aka rufe min fuska tare da ja na zuwa waje har muka shiga mota kuka nake. Babu wani nisa sosai da gidanmu,ko da muka isa ɗakin SURUKATA aka kai ni.Ana buɗe min fuska na ji wani ƙamshi marar daɗi ya daki hancina,ban sani ba iya ni ɗaya ce ke jinsa ko kuwa har da sauran mutane.Ni dai kam na matsu a fitar da ni,haka Hajiya Luba da danginta suka yi ta yin addu'a kafin a miƙar da ni zuwa ɗakina kamar yadda ta ce.Fuskata aka sake rufewa sannan aka ja ni izuwa can,ina zaune kan gado tare da dangina da kuma na shi mijin da aka aura min kafin abokan ango su shigo amma shi banda shi har suka gama karanto addu'o'insu bai zo ba haka suka fita dangin Mama na ta tsiyar gumin ƙin zuwan ango. Sannu a hankali duk suka watse suka bar ni,ina zaune a takure tare da tunanin wacce irin tarba zan samu a wurin mijin da haɗa mu aka yi ba soyayya ba na ji sallamarsa kafin kuma ta Hajiya Luba . Abin da na fahimta ita ce ta rako shi a madadin abokansa kamar yadda al'ada ta tanada. “Ki buɗe fuskarki mana” Hajiya Luba ta faɗa a daidai lokacin da na ji sun yi tsaye kusa da ni.Hannuna har rawa yake wurin bin umarninta,ina buɗe fuskar muka haɗa ido da Aliyu ,dogon namiji ne haka yana da ƴar ƙiba ba sosai ba fuskarsa sam babu walwala kamar ba ango ba.Da sauri na sunne kai ina jin zuciyata na ƙara ƙarfin gudunta,kamar wani yaro Hajiya Luba ta ce “ ka zauna kusa da ita” ko bakinta ba ta rufe ba kuwa ya zauna dab da ni har muna iya jiyo sautin numfashin juna. Aka ƙara yin sallama aka shigo,da muryoyinsu na gane su wato ƙannan Aliyu ne waɗanda suka taɓa zuwa gidanmu.Su ma ɗin da alamu kamar uwar ke juya su yadda ta so duba da yadda komai sai ta ce sannan su yi,amanar Aliyu suka ban kafin su ajiye ledoji sai suka fice su duka ukun muka yi sauran ni da shi. Kamar kurame haka mu ka zauna na tsawon lokaci kafin ya je ya rufo ƙofofin ɗakin ya dawo.Wata ƙofa na ga ya shiga can kuma na ji motsin ruwa ,da ya fito kamar wani mala'ika ya ce “ ki je mu yi alwala za mu yi sallah” sautin muryarsa kaɗai ya tsorata ni amma na aro jarumtar cewa “ Ni Kirista ce” “Daga yau kin fita daga wannan sahun ki tashi” ya faɗa cikin bayar da umarni. Wani tausayin kaina na ji,don kuwa ko giyar wake na sha ba zan yi masa muso ba.Jiki na rawa na sauka na shiga toilet ɗin,sai na tsaya ina kallon pampon tsaye don gidanmu babu shi. “Me kike yi wai?” “Ban iya ba” na basa amsa,ya kuwa shigo ya nuna min yadda zan yi kafin mu fita.Ban san inda ya samo dardumar ba,haka ya shimfiɗa muka yi sallah bayan mun gama ne ya jawo ledar tare da bani umarnin na ci a tsorace na ci na ƙoshi kafin kuma ya bani wani umarnin na wanke baki. Ina fitowa daga toilet na nufi gado zan kwanta saboda mugun baccin da nake ji,“ keee!” ya wani tsayar da ni,na juyo muna facing juna. “Da wannan kayan za ki kwanta?” ya tambaye ni yana mai tsure ni da ido ,kafin ya ja tsuki ya je ya buɗe wani trolly ya ciro min wasu kaya shara-shara.Haka na yi tsaye ina jujuya su,ina son ce masa ban iya saka su amma mugun kallon da yake watso min yasa a dole na shiga toilet na saka su sai dai fa na kasa fitowa. Ya buɗe ƙofar toilet ɗin yayi tsaye yana kallona shi ma ya canza kaya,na sunne kai kawai ina hawaye.Mun fi minti biyar a haka kafin ya zo ya ja hannuna,kamar wata ƴarsa haka ya ɗora ni kan bed yana yi min wasu abubuwa da suka jawo maganin da aka bani jiya da yau ya soma aiki,kayan baccin da ya bani ma ya cire rigar ido kawai na rumtse ina jin takaicin yadda yake kalle ni ta hasken ƙaton ƙwan lantarkin ɗakin.Ban fargaba ya raba ni da komai sai a lokacin kuma na buɗe ido nan na yi tozali da shi ashe shi ma bai da sutura,a yadda na ga halittarsa kamar ta ƙaramin yaro yasa gabana faɗuwa rasss ashe akwai sauran mamakin da zai ban a gaba.Ƙoƙarin shigata ya soma,ko minti ɗaya ba a yi ba na ga ya koma gefe wai har ya gama ban san lokacin da na tashi zaune ina kallonsa ba sai mayar da numfashi yake kamar wanda yayi wani abun ƙwarai,rigarsa na sa na goge ƙazantar da ɓata min jiki ina ƙoƙarin sauka daga bed ɗin ya wani jawo ni ya rungume sai a lokacin kuma ya kashe ƙwan lantarki.Mugun riƙo yayi min kamar ƴar kaso wannan yasa ban ma gwada ƙwatar kaina ba,wani irin tausayin kaina ne ya ƙara luluɓe ni duk da na san an rina tun da har Mama ta yarda in aure shi amma ta hana wa ƴar gaban goshinta.‘ A haka zan zauna da shi ,ga baƙin rai da son iko,ga ƙaramar halitta ga kuma saurin inzali? Da wane zan ji ni Janiki? Wacce irin lukutar ƙaddara ce wannan ka ɗoro min ya abun bauta? Shin dama ka yi ni ne don kawai na yi ta baƙin ciki ina zubar hawaye?’ da ire-iren waɗannan zancen zucin na samu bacci ya ɗauke ni kafin kuma na farka cikin wata lukutar masifar,hannuna har rawa yake wurin danna maɓalin wuta.Haske ya kawo ɗakin,na dafe ƙirji tare da aron kalmar musulmi na ce “ Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” na dafe ƙirji ina kallon yadda shimfiɗar aurenmu wacce ta yi shaɓe-shaɓe da fitsarin Aliyu . Daga nan zan tsaya duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank , sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 *Na gama free page* in ya zama Complete kuma 1k ne farashinsa. [21/12 à 08:37] MRS SADAUKI: My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Free 07 Hawaye ne suka soma yi min zuba, ‘ wannan wacce irin lukutar masifa ce mijina na fitsarin kwance ga kuma rashin lafiyar gamsar da iyali? Gaskiya abin yayi yawa shege da hauka sam ba zan iya auren ƙaddarar nan ba,da wane zan ji da ƙunci rayuwar da ya addabi ruhina ko da faman fitar da kafita kowacce safiya kamar mai yaron goye?’ Duk wannan tambayoyin na yi su ne a zuci ,yayin da na koma gefe ina kallon Aliyu wanda ke kwance cikin fitsarin sai sharara baccinsa yake da alamu ma sanyin lemar bai dame shi ba. Toilet na shiga na cika bokiti da ruwa na soma yin wanka,don ban saba yi da shower ba. Babu neman izini kawai na ga mutum shi ma ya shigo cikin toilet ɗin,da sauri yunƙura zan miƙe don kuwa ban ga dalilin da za mu yi wanka a tare ba.Ya cabko ni ya riƙe ni gam ko ƙwaƙwaran motsi ban iyawa,ƙoƙarin haɗe bakinmu yake ni kuwa na ƙi yarda saboda bai brush ba yanzu ya tashi daga bacci. Wani gigitacen mari ya ɗauke fuskata da shi wanda ya sani ganin taurari,tuni fitilun idona sun ɗauke hankalina ya gushe na wucin gadi.Ƙazamin bakinsa na ji kan nawa yana kissing ɗina,ya haɗe ni da bango yana yin abin da ya so da gangar jikina.Banda wani zaɓi banda na yin kuka,sai da ya gaji don kansa kafin ya janye jikinsa daga nawa ya soma yin magana. “Zo na nuna miki yadda ake wankan tsarki” ban ce komai ba,na dai zuba masa ido ina kallon yadda yake yi kafin ya bani umarnin yi.Har sai da na gama sannan ya ce “ ki yi alwala to irin na jiya ” jikina na rawa na yi sai sannan ya miƙa min towel na ɗaura. Da muka fito bayan mun saka kaya ya ja mu sallah,muna idawa ya miƙe yana hararena. “Na shiga uku ni Janiki yanzu kuma me na yi ?” na yi tambayar ina mai tashi tsaye. Cike da masifa ya ce “ ita katifar can uban waye zai fitar miki da ita?” “Yanzu zan yi” na faɗa tare da isa bakin bed ɗin na kwashe zanen gadon,sai da na ja ajiyar zuciya ganin ashe ba a fitar da ledar katifar ba sam fitsarin bai kai gare ta ba. Bokiti na ciko da ruwa na saka towel a ciki ina matsewa ina goge ledar daga nan kuma na shiga toilet na wanke zanen gadon . Ko da na fito har ya shirya cikin kakinsa na soja,sai na ji tsoronsa ya ƙara huda ruhina ya samu matsuguni.Fuskar nan tasa a murtuƙe ya ce “ abincin breakfast” murya na rawa na ce “ to” na faɗi haka ne gudun fitina sai na ɗauki bokitina na je na buɗe ƙofa.Allah yayi sa'a na ga igiyar shanya a tsakar gidan,sai na je na shanya zanen kafin na yi tsaye ina tunanin inda zan samo masa abincin . Gidan na soma ƙarewa kallo har na fahimci ɗakin hajiya Luba,a hankali na soma cira ƙafata har na isa .Sallama na yi har sau uku ba a amsa ba,ina kutsa kai na ganta zaune ta luluɓe dukkan jikinta da jan ƙyalle a gabanta kuwa wata ƙwarya ce cike da nono. Da sauri na juya zan fita don ina kyautata zaton ba ta gan ni ba duba da idonta da suke rufe,ina fitowa na yi kiciɓis da wata matashiyar mata.Ta sakar min murmushi ta ce “ amarsu! Fatan an tashi lafiya ya gajiya biki ya kuma baƙunta?” “Lafiya lau an gode Allah, please ina zan samu abincin breakfast?” na faɗa . Wani kallo ta yi min mai cike da ban mamaki kafin ta ce “ au! Har yanzu ba ki ɗora girkin ba?” “ Ban san ma inda madafar take ba” na faɗa a sanyayye ,ta ce “ ok biyo ni” haka na take mata baya muka shiga wani ɗan lungu ai kuwa sai ga wata ƙatuwar ƙofa ta saki murmushi kafin ta ce “ ga kitchen ɗinmu,duk abin da kike buƙata za ki samu.” Na marairaice murya na ce “ amma don Allah me zan dafa masa ban san me ya fi so ba” Wata irin dariya ta yi kafin ta ce “ ai mu nan gidan girki ɗaya ake yi na kaf ahali,sannan Hajiya Mama ce ke zaɓar abin da za a dafa.Yanzu ai na ga daga ɗakinta kika fito,ba ta sanar da ke me za ki dafa mana ba?” Na girgiza kai na ce “ ai ba mu yi magana ba” “Ki je to ki tambaye ta” Na sunne kai saboda har ga Allah ni dai tsoron komawa nake,“ ko kawai ki yi wainar ƙwai mai haɗi da fulawa na ga yau asabar kusan ita ake yi ” “Yawwa ki taimaka min na yi please ” na faɗa cikin sigar roƙo,nan ta amince ta soma sauko abubuwan buƙata haka ta dinga ja na da hira na ga alamu ba ta da wuyar sabo sai dai akwai shishigi sai bugun cikina take tana son jin yadda muka yi daren farko. Ban dai ce mata komai ba sai wainar da muke ta yi,“ wato kunya kike ji? Hum! Ai gwara ma ki cire ta don kaf gidan nan ni ce kawai zan saki jiki da ke,matan Umar ƴan ɗaukar kai ne ” ta faɗa tana wani kafe ni da ido . Na murmursa na ce “ har yanzu ba ki sanar da ni sunanki ba. “Binta ne sunana,ke kuma Janiki ko?” na gyaɗa mata kai ina mai cewa “eh haka ne,yanzu in mun gama girkin ya za a yi da shi? Kowa za a zuba masa nasa?” “A'a akwai ɗakin cikin abinci,can babban falon Hajiya Mama ” ta bani amsa. Cikin wani irin dogon faranti babba irin sosai ne muka zuba wainar kafin ta nuna min hanyar da zan bi na shiga falon cin abinci.Tun da na doshi ƙofar zuciyata ke tsananta bugu har na buɗe na shiga,babban falo ne sosai mai ɗauke da capet ja shi ma babba ne don ya cika ɗakin.Babu table ballantana kujerun cin abinci,sai wasu abubuwa masu kamar pilow da aka zagaye wurin da shi.Daidai tsakiya na ajiye farantin ina mai duba kowane bango da ke ɗauke da hotunan Hajiya Luba ,yadda duk idonta suke ƙurrr sai abin ya baka tsoro don tamkar tana kallonka za ka gani. Ina nan tsaye duk mutanen gidan suka soma shigowa mata da maza da kuma yaran gidan ,amma banda Aliyu .Cike da ladabi na soma gaishe su suna amsawa kafin Hajiya Luba ta shigo sanye cikin wata alkyaba kai kace sarki ko matarsa,abin mamaki sai na ga duk sun miƙe tsaye suna wani sunne kai to ni dama a tsayen nake babu buƙata kenan. Ido kawai na zuba mata ina kallo,a yanzu da nake tsaye a nan sam ba Hajiya Luba ƙawar Mamana ba ce nake gani wata ce ta daban mai abin ban mamaki. Yadda ta zubo min idonta cikin nawa har ban san lokacin da ni ma na bi ayari ba na sunkuyar da kai. Ta saki murmushi mai sauti,ban sani ba su ma sun ji shi ko kuwa ni ɗaya ce oho. “ Ƴata Janiki je ki yi wanka ki canza kaya,sannan ki cewa Aliyu ya zo fadar cin abinci in ji ni” Hajiya Luba ta faɗa ,na amsa da “ to Hajiya ” sai kuma na nufi ƙofa fita,ina jin lokacin da ta ce “ kowa ya zauna” Ko da na shiga ɗaki na tarar da Aliyu ya cika fam kamar zai fashe,har sai da ya ban tsoro . “Ina abincina?” ita ce tambayar da ya jefo min. “Yana..yana can ɗakin cin abinci kuma Hajiya ta ce ka je can fada tana nemanka” na basa amsa tare da yin wuf na shige toilet,a tsanake na yin wanka na fito cikin sauri na shirya saboda wata uwar yunwa da nake ji. Ko da koma can sai na ga Aliyu zaune kusan Hajiya fuskar nan tasa har yanzu a muturƙe,rasa inda zan zauna na yi sai na je kusa da Binta na yi zaune ina sakar mata murmushi na buɗe baki zan yi magana kenan Hajiya Luba ta yi min wata uwar tsawa “ Janikiii???” na zabura tare da dubanta,yayin da na ga duk sauran sun sune kai banda Aliyu da ke jefo min mugun kallo.Murya a dake ya ce “ a nan babu mai magana sai ya tambayi izinin Hajiya Mama,kuma ki sauke wannan shegun idon naki ƙasa” Ai kuwa ko baki bai rufe ba na yi ƙasa da kai. Cikin muryar gadara take cewa “a jiya mun samu baƙuwa a gidanmu,kowa ya san a gidan nan Aliyu ne babba wannan yasa daga yau na naɗa matarsa shugabarku wacce za ta dinga kula duk abincin da za a dafa,a madadin ni na dinga faɗa ita za ku dinga tambaya a duk lokacin da ranar girkin ɗaya daga cikinku ya zagayo.In kuma nata ne to ita ke da alhakin zaɓar abin da take son dafawa.A ƙarshe kuma ina sake gargaɗar ku akan lamarin da bai shafe ku ba,ban son bin didigi da tambayar juna sirrin da bai dace ba” tana gama faɗar haka sai ta buɗe faranti abincin,tare da bada izinin kowa ya ci. Kallo ɗaya na yi wa wainar na ga alamun canji,amma banda hujja ko kuma wata ƙofar da zan ce an saka magani .Haka na soma ci kamar kowa,har muka ida kowa ya watse amma Hajiya Luba ta tsayar da ni. “Janiki yaushe kika fara yin sallah? Wa ya baki wannan izinin?” ta jefo min tambayar tana shafar ƙafafuna,sai na ɗaga kai na dubi Aliyu ba tare da na ce komai ba. Ta haɗe rai ta ce “ daga yau kar ta sake yi,ka bar ta da addininta ban son jin komai kuma daga bakinka” kai ya jinjina alama ya ɗauka,kafin ta maido hankalinta a gare ni ta ce “ kar ki wani damu ƴata Janiki, Aliyu yayi kuskure da ya tursasa ki kan yin addininsa amma komai ya wuce,gobe ma zan sa ya kai ki Coci ki yi bauta ga Ubangijinku” Na saki murmushi na ce “ na gode Hajiya ” duk a tunanina soyayya ce ta jawo haka ashe cutata ce ta yi,wani kofin zinare ta miƙo min mai cike da nonon shanu ,kamar wacce ta shekara ba ta sha ruwa ba haka na ji ƙishi da sauri na karɓa na kafa kofin a bakina.... Ki daure ki biya kuɗin karatu Hajiya a yi tafiyar nan da ke. My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [22/12 à 21:39] MRS SADAUKI: My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Free 08 Wani irin abu ne na soma ji yana ratsa ruhina yana shiga,tamkar wacce aka juye wa tunani na wani ɗan lokaci haka na jin kwanyata ta yi wani lummm tare kuma da yin wani sauti kamar an buga ƙwai ga dutse. Na ware idona a hankali kan SURUKATA wacce take yi min gizo kamar mutum kamar wata halitta. “ Ƴata Janiki ?” ta kira sunana cikin wani sauti tamkar mai yin raɗa. Sam ban motsa bakina ba,amma tabbas na ji a jikina na amsa da “ da na'am Mama” sai dai sam wannan ba furicin bakina ba ne,ƙila ruhina! “Tashi ki je ki kwanta na san kin gaji,Aliyu yi mata rakiya zuwa ɗaki” ta faɗa tana wani murmushi . Ya amsa da “ to Hajiya Mama” kafin ya miƙe ya ɗauke ni cak ya ɗora kan kafaɗa,sai ya zamana kaina ya sunne ƙasa yana reto.Idona ne suka soma nuna min wasu abubuwan da ke luluɓe a ɓoye a ƙarƙashin jan capet ɗin falon cin abinci,sai dai na kasa tantance na mene ne abu ɗaya na riƙe shine an ƙawata da wurin da jini. A hankali Aliyu ya kwantar da ni kan bed ɗin,tamkar wata jaririya sabuwar haihuwa haka nake lumshe ido ina kuma ɗan buɗe su da zumar tantance wacce duniya nake sai dai sam na kasa . Wani bacci mai kamar ido biyu ne na soma yi,gani nan ina gudu cikin daji yayin da wasu mutane masu rabi mutum rabi doki na take min baya a tsiyaci.Sosai nake gudu ina waiwayen su,suna dab da damƙo ni Prince Mahadi yayi min iyaka da su ta hanyar diro wa daga sama kamar wani aljani.A nan take kuma suka yi baya suka gudu,yayin da shi kuma ya jawo ni ya haɗe ni da ƙirjinsa. Numfashi na yi ta saukewa saboda gudun fanfalaƙin da na yi,ya hura iska kan fuskata kafin ya matso da tasa fuskar dab da tawa kamar zai sumbace ni sai ya min raɗa a kunne “ ki tsaya ki lura da kyau,sannan ki kula da kanki” yana gama faɗa min haka na farka ina haƙi.Abun mamaki har zuwa yanzu ina jin wannan yanayin in mutum yayi gudu,maƙoshina ya bushe ƙamas .Na diro daga gadon,ina fitowa falo na yi kiciɓis da Hajiya Luba. “Har kin tashi ? Ga ruwa na kawo miki ” ta faɗa cike da kulawa,hannuna har rawa yake na karɓi kofin na shanye ruwan tass ta ƙara tsiyaya min wasu na shanye,sai da na yi kofi huɗu kawai ƙishin ya gushe. “ Halan kin kwanta da ƙishi ne? Ko kuma mafarkin shan ruwa kika yi?” Hajiya Luba ta yi min tambayar tana wani kafe ni da ido. Mafarkin da na yi tsaf ya dawo min a kai,amma sai na zaɓi na ɓoye mata na ce “ dama...dama ina da yawan shan ruwa ne” “Ok to ki kula sosai ba kowane ruwa ne ke maganin ƙishi ba” “Me kike nufi Hajiya?” “Babu komai,je ki yi wanka ki fito ki ɗora girkin rana” ta faɗa tare da ficewa. Can ciki na koma na shiga toilet,bokiti na ajiye tare da buɗe ƙaramin pampo sai na ɗauki soson wanka na zuba sabulu na soma cuɗa jikina.Ina saɓa fuskata da sabulu sai na ji tamkar wani na kallona,da sauri na sa ruwa na wanke fuskar ina gwalar ido.Babu kowa kawai tunanina ne ya bani hakan.A gaggauce na ida na fito,cikin sabbin kayana na lefe na zaɓi doguwar rigar atamfa na saka.Tunani na soma a kan abin da ya rage a ɗakin nan amma sam na kasa tunawa,trollyn da aka zuba min kayan kwalliya na buɗe na shafa mai da turare kafin na fita can kitchen. Tsaye na yi ina kallon uwar garar da ke cike da store ,ina mamakin duk me ake yi da su har haka kamar mai wani gidan marayu.Ban san me zan dafa ba,kawai sai na yanke shawarar bari na je na tambayi Hajiya . Yin sallama ba ta cikin tabi'ata,wannan yasa yanzu ma ina isa ɗakinta kawai na kutsa kai.Kusan daskarewa na yi saboda tarar da Hajiya da na yi zaune kan wani tsumma ,kan kafaɗarta kuwa wani tsuntsu ne manyan ido jajaye . Na ɗan ja da baya da nufin fita,amma sai na ga tsuntsun ya buɗe baki yana magana amma muryar Hajiya Luba ce ke fita. “Ƴata Janiki,matso mana ki zauna a gefena” ta faɗa . Jikina ya ɗau kyarma,na ce “ dama abin da za a dafa na zo nem...” ban ida kai ƙarshen maganar ba wannan tsuntsu ya tashi sama bai dira ko ina ba sai tsakiyar kaina.Daga nan kuma ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na gan ni kwance kan gadano,duk yadda na so tuna abubuwan da suka faru kuma na kasa.Abu guda na riƙe na je kitchen zan yi girki amma kuma ban yi ba. Aka buɗo labule,Aliyu ne ya shigo fuskarsa kamar kullum a murtuƙe.Kakin sojansa ya soma cirewa ni kuma na zuba masa ido ina kallo.A siffa ga namiji har iya namiji sai dai raggo ne a shimfiɗa,ga kuma fitsarin kwance. Na shagala sosai a kallonsa sam ban ga lokacin da ya zo gabana yayi tsaye ba,sai saukar muryasa da na ji “ ke ba ki san ki gaida mutane ba ?” “Ka yi haƙuri” na faɗa da sauri,ya ja tsuki kafin ya shiga toilet.Bayan ya fito ne yake cewa “ Hajiya Mama ta ce bayan fitata kin zame jiki kin faɗi a kitchen,shin dama kina da cutar farfaɗiya ne?” Shiru na yi ina tunanin ‘ to yaushe hakan ya faru ban sani ba? ’ “Ta ya kuwa za ki sani tun da hankalinki ya gushe” ya bani amsar tambayar da na yi wa kaina a zuci,cike da mamaki na ce “ ni fa ban yi magana ba” cikin ido ya kalle ni kafin kuma ya juya ya soma kimtsa wa . Na dafe kai ina jin can ƙasan zuciyata kamar akwai abin da ba normal ba,amma sam an ƙi bani damar yin tunani ballantana ma na san gaskiyar abin da ke faru. Daga can bakin ƙofa Binta ta yi sallama,da sauri na tashi na fita.Ta saki ɗan murmushi kafin ta ce “ ku fito lokacin cin abincin dare yayi” “To ga mu nan” na faɗa tare kuma da zancen ‘ kenan har dare yayi?’ “Mu je” na ji muryarsa tare da wani jan hannuna kamar wata ƙaramar yarinya. Muna fitowa sai na ga duhun magrib ne kawai ya keto amma kamar wasu kaji wai abincin dare za a ci. Har muka shiga falon cin abinci bai saki hannuna ba,wannan karon kusa da Hajiya Luba ya zaunar da ni shi kuma ya zauna gefena sai ya zamana sun saka ni tsakiya. Da ido kawai Hajiya Luba ta dube ni amma abun mamaki sai na ji sautin muryarta tamkar da baki ne ta yi maganar. “Ki buɗe kwanon abincin ki bai wa kowa umarnin ci” shine abin da idon nata suka faɗa min. A hankali na kai hannuna tare da buɗe ƙaton murfin,nan tururi da ƙamshin naman kaji ya cika wurin da kuma na wainar shinkafa.Na aro murmushi na yaɓawa fuskata mai cike da mamaki na ce “ kowa ya ci ya ji dadaɗan girkin da na yi mana,fatan za ku ji daɗinsa sosai” Duk suka yi murmushi kuwa kafin a soma ci,ni ma cike da zumuɗi na soma ci saboda yunwa da na kwaso.Bayan mun gama ci Hajiya Luba ta ƙara bani wani umarnin na kawo jus,haka na miƙe na fita zuwa ɗakinta. Da na shiga ɗakin duhu ne da shi ɗif,sai dai abun mamaki duhun bai hana ni ganin komai na ciki ba tamkar safiya.Ban wani damu ba tun da ni dai burina shine na ɗauko abin da aka aiko ni don shi,wannan yasa jus ɗin kawai na ɗauka na koma can haka na rarraba wa kowa kafin na koma wurina na zauna na sha. Muna gama sha aka kira sallah,sai duk suka fita wannan karon har da Aliyu.Ni kuwa tamkar wacce aka riƙewa mazaunai haka nake ji sam ban yi ƙoƙarin tashi ba ma. “Ungo ki sha” Hajiya Luba ta faɗa tana miƙo min kofin nan na ɗazu,na karɓa na shanye tass kamar jira kuwa ake sai na soma jin duk abubuwan da ni ɗazu sai dai na yanzu na ga wani banbanci shine yadda kawai na kwanta shanɗam kam capet. Ba bacci nake ba,haka kuma ba zan ce idona biyu ba .A takaice dai ina tsakanin duniyoyin biyu,ina kallon lokacin da Hajiya Luba ta miƙe tsaye ta soma zagaye ni tana faɗar wasu ɗalasimai kafin kamar almara ta soma yi wa ruhina magana. “Fito zuwa gare ni,zo ka yi min hidima ,lokaci yayi da nake ta faman jira” ta faɗa tare nuna tsakiyar ƙirjina,tamkar yadda ƙasa ke tsagewa haka na soma ganin gangar jikina na buɗewa kafin wani abu mai kama da inuwa ya fito,wanda ba komai ne shi ba sai ruhina..... Littafina na kuɗi ne,ki ɗaure ki biya 500 Hajiya via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [24/12 à 08:16] MRS SADAUKI: My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Free 09 Tamkar a mafarki dai ruhina ya fita daga gangar jikina ya je gaban SURUKATA ya zube,yatsan hannunta ta tsaga nan jini ya soma tsirta haka ta soma shayar da ruhina shi na wani lokaci kafin kuma ta basa umarnin ya je ya koma inda ya fito. Yadda in mutum ya suma in an zuba masa ruwa yake zabura haɗi da jan numfashi da ƙarfi,to ni ma hakan ce ta faru da ni bayan ruhina ya dawo cikin gangar jikina. “Ƴata Janiki kin tashi?” Hajiya Luba ta faɗa ,wacce a yanzu na gan ta zaune kusa da ni.Kai na gyaɗa mata ba tare da na ce komai ba,don ji na yi kamar na rasa tunanina. Ta saki murmushi ta ce “ tashi ki je ɗakinki zan aiko miki da magani domin magance ciwonki” ba tare da na san wane ciwo take nufi ba na tashi na fita zuwa ɗakina. A falo na tarar da Aliyu yana waya da dukkan alamu kuma da Ogansa ne duba da yadda yake magana cikin ladabi.Har zan wuce bedroom amma yayi min alama da hannu a kan na je.Sam jikina bai da wani ƙwari tamkar zan faɗi haka na je na tsaya a gabansa,ya jawo ni tare da ɗora ni kan cinyarsa.Yana waya yana yawo da hannunsa a jikina can ya ajiye kafin ya maido hankalinsa gare ni,wani irin kallo yake min kamar mai son ya isar min da wani saƙo.Ina ganin ya matso fuskarsa gare ni na yi saurin lumshe ido,ai kuwa abin da na yi tsammani ne.Sumbata na yayi ta yi haɗi da romance ,ba tare da neman izini ba kwatsam aka shigo ɗakin.Da sauri na zabura na tashi ina raba ido,ita kuwa Hajiya Luba kicin-kicin ta yi da rai tana wani kallonmu kamar ta ritsa kwarto. “Hajiya Mama ko da abin da kike buƙata?” Aliyu ya faɗa a kunyace ba tare da ya tashi ba. “Sai in ina buƙatar wani abu zan shigo ɗakinka Aliyu? Tun yaushe ka yi min iyaka da shigowa ba tare da na sani ba?” Hajiya Luba ta faɗa ,amon muryarta na fitar da hucin baƙin ciki. “Ki yi haƙuri Hajiya ba haka nake nufi ba,dama ai ko ba ki shigo ba yanzu zan je na sanar da ke zan je mission jibi ” Aliyu ya faɗa . “Ai ban ga alamun za ka je ba ɗin,ke kuma uwar me kike jira da kika yi min tsaye ko banda ikon yin magana da ɗana sai a gabanki?” wannan karon sosai fushinta ya fito,jikina na rawa na nufi bedroom ba tare da na ce mata komai ba. Kan gado na zauna ina haƙi kamar wacce ta yi gudu,wani abu nake ji tamkar zan faɗi.Dukkan jikina ya ɗauki rawa,murya na ɗan rawa na ce “ Aliyuuu!” da ƙarfi na yi maganar ta yadda zai ji. Ai kuwa ya shigo a guje yana cewa “ me aka yi?” “Zan faɗi jiri nake ji” na faɗa tare da tashi tsaye ,yayi saurin tallabo ni .Hajiya Luba ta shigo tana cewa “ dama maganinta na zo kawo mata ungo ka bata ta sha” ta faɗa tare da miƙa masa wata kwalba,Aliyu ya zaunar ni sannan ya dangwalo maganin da yatsansa ya saka a bakina kamar ƙyaftawar ido haka na ji komai ya dawo normal.Na ja wata ajiyar zuciya,cike da tausaya wa Hajiya Luba ta matso kusa da ni tana mai cewa “ ki kwanta ki huta Ƴata Janiki, Allah ya baki lafiya.Ki riƙe maganin nan wurinki duk lokacin da kika ji wannan yanayi to ki dangwale shi da yatsa ki sha za ki samu sauƙi” “ Na gode sosai Mama ” na furta cike da jin daɗi. “Aliyu ina ga ya kamata a ɗaukar wa da Janiki ƴar aiki wacce za ta kula da ita da kuma yi mata hidima,ciwon nan nata bai son yawan motsi da zirga-zirga ” “To Hajiya Mama ” ya furta kafin ya miƙa min kwalbar maganin.A tare suka fita shi da ita,ni kuma na kwanta kan gadona tare da rungume kwalbar a ƙirji. Na saki wani murmushi na ce “ wai Janiki ce za a ɗaukar wa ƴar aiki, na gode abun bauta da ka nuna min ranar da zan yi farin ciki” sai kuma na yi shiru na koma zancen zuci ‘ to yanzu a haka zan zauna da Aliyu ba tare da mun mori rayuwar aurenmu ba? Ko ya san bai da lafiya? Ƙila kuma shi wannan saurin inzalin bai ɗauke shi matsala ba don ban ga ya nuna alamun damuwa ba’ sai kuma na ji tausayin kaina. Ina nan kwance ya shigo, trolly ya jawo ya soma zuba kayansa yana yi yana waiwayena har ya gama ya zo yayi tsaye kai gare ni ya tsura min ido.Duk sai na ji na tsargu,ga kuma wani tsoronsa da ya dirar min lokaci guda. “Ki tashi ki yi wanka ki canza kayan nan zuwa na bacci ” ya faɗa yana furzar da huci.Ba tare da na ce masa komai ba na sauko,har zan wuce amma sai ya riƙe min tsintsiyar hannu.Wani irin kallo ya soma aiko min kafin kuma ya sakar min hannun,da sauri na shige toilet ina mamakinsa ko me ya shiga kansa yau. Bokiti na tara a pampo kafin na soma yin wankan,ana buɗe ƙofa na san da shi ne.Ko juyawa ban yi ba haka na ci gaba da yin wankan a takure ina jin idonsa gare ni.Na jawo towel zan ɗaura yayi saurin fizge shi daga hannuna,daidai kunnena ya min raɗa “ ina so mu yi wanka tare” ban kai ga yin magana ba ya buɗe shower ruwan suka zuba gare mu.Na ja wani numfashi saboda sanyin ruwan ina shirin guduwa ya riƙe ni gam tare da juyo ni muna facing juna,“ mene ne?” yayi min tambayar a dake .Idona suka kawo ruwa na ce “ ban so na jiƙa gashina” sai ya sa hannu ya cire hullata wacce ko bacci bai raba ni da ita yayi cilli da ita. Gashina da na laulaye na yi masa naɗin tayar mota ya warware tare da cire ribob ɗin,ido ya waro ganin sumar kaina.Kamar wani sakarai ya soma shafa ta yana jan ta cike da mamaki,yana tallabo fuskata na lumshe ido. Wanka muka yi cike da salon romantic,yadda Aliyu ya tafi da ni cikin shauƙi da tausasawa kamar ba shine na jiya ba da yayi ta yi min tsawa.Yadda ya manne ni a ƙirjinsa yana sauke min huci a kunne shi ya fi ɗaga min hankali,kamar wata ƴar baby haka yayi min wanka.Karon farko da na ga soyayya gun ɗa namiji don ban taɓa yin saurayi ba,bayan ya gama yi mana wankan muka ɗaura towel har zan taka da ƙafata amma sai ya ɗauke ni.A zuci na ce ‘ ka ga wani sabon salo’ kan bed ya shimfiɗe ni,yana shirin warware min towel na ce “ ka rufo ƙofa” “Na ru..fe ta ca..cccan falo ” ya faɗa muryarsa na rawa,haka kawai na ji tausayinsa saboda tsantsar buƙatuwa da na hango cikin ƙwayar idonsa amma na san ba za a je ko ina ba saboda bai da wani ƙarfin. Ido kawai na lumshe tare da yin shiru ina karɓa saƙonsa,ko ta ina yake min sumba jikinsa na yin rawa.Ɗumin hawayensa ne suka sa na buɗe idona,da dukkan alamu ya ji takaicin yadda yanzu ma da ya so kusantata kawai komai ya tsaya cak babu biyan buƙata.Fuskarsa na tsure ina kallo ,kyakkyawa ne shi duk da yana baƙi hakan bai ɓoye kyawun nasa ba.Ya koma gefe tare da kai hannu ya kashe ƙwan lantarki,ɗakin sai yayi duhu. “Zahra!” yayi furicin ,ban amsa ba don ba haka ne sunana ba.Ya jawo ni ya maido ni kan ƙirjinsa tare da cewa “ shine kika yi shiru?” “Ni sunana Janiki” na faɗa . “Ban sonsa ne shi yasa na zaɓa miki sunan Zahra shi ya fi yi miki kyau,tun da kin ga kai tauraruwa ce” “ Zahra na nufin tauraro?” na tambaye shi. Ya ce “ eh mai mugun haske ma kuwa” “Kenan ni tauraruwa ce?” na sake jefa masa tambayar.Shiru yayi kafin can ya ja numfashi ya ce “ eh ” “Saboda me?” “Me yasa kika aure ni?” shi ma ya jefo mini tambayarsa.Sai na kasa cewa komai,hasken ɗakin ya kunna kafin ya ƙara maimaita min tambayar yana kallon cikin idona a dole na amsa masa da “ Mama ce ta ce na aure ka” “Hajiya Mama?” Na girgiza kai na ce “ a'a Mamana” “Kafin su aura miki ni sun yi miki bayani kaina ba?” “Wane bayani?” “ Komai!” ya faɗa tare sake kashe hasken,ina jin yadda bugun zuciyarsa ke tafiya da sauri-sauri. A hankali na ɗan janye daga jikinsa kafin na juya masa baya,amma kamar wani ƙaramin yaro haka ya zo ya ɗora min ƙafarsa ɗaya tare da zagaye cikina a dole dai ya mayar da ni cikin ƙirjinsa.A haka muka yi bacci kafin lemar fitsarinsa ta tashe ni,na janye jikina da sauri tare da kunna hasken ɗakin shi ma ya farka sai muka fara ƴar kallon-kallon kafin kuma ya sauka ya je ya shiga toilet.Ni kuwa tsaye na yi ina kallon gadon da yayi shaɓe-shaɓe da fitsarin,a yau maimakon takaici sai na ji tausayinsa.... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [26/12 à 09:10] MRS SADAUKI: My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Last free page 10 Zanen gadon na cire ,sai na dubi ƙofar toilet da nake ta jin ƙarar zubar ruwan shower da alamu wanka ne yake don dole sai wankan tun da uban fitsarin nan da ya shashaɓa min.Ganin ba zan iya jiransa har sai ya fito ba kawai na yi niyya fita waje na ciko bokiti da ruwa na goge ledar da ke kan katifa.Ba tare da wani tunani ba na suturta jikina kafin na je na buɗe ƙofa na fita tsakar gida.Wani irin mugun haske ne na jar wutar mai kamar ta murhu ya min maraba,kaf tsakar gidan ya ɗauki kalar ja yayin da sararin samaniya yayi baƙi ƙirin kamar bayan tukunya sai giza-gizai ke gudu . A tsorace nake kallon giza-gizan masu kamar zanen fuskokin mutane,na toshe kunnuwana saboda wata gurɓataciyar murya da ke rera waƙa cikin wani kiɗa marar daɗin sauti kamar ana kiɗa goge. Baya-baya na soma da na ƙasa na darewa tana tsagewa kamar yadda in an yi girgizar ƙasa za ka ga wuri na ɓaɓarewa.Ihu nake son yi amma tamkar wacce aka riƙewa murya na kasa,hatta motsa ƙafafun haka na kasa gusawa saboda yadda nake jin tamkar an ɗinke fatata da kuma ƙasa. Wani haske ne ya tawo daga sama kamar tauraro ya hankaɗa ni na yi baya tare tashi sama ban dira ko ina ba sai cikin ɗakina,yayin da kuma ƙofar ɗakin ta bada ƙiiii tare da rufe kanta. Na dafe saitin zuciyata ina jan numfashi kafin na tashi dakyar na koma bedroom,sai na tarar tuni Aliyu ya fito daga wankan yana tsaye kan dardduma yana Sallah.Toilet ɗin na shiga na ciko bokiti da ruwa na goge ledar tare da saka wacce ta ɓace cikin bokitin,tun a cikin daren na wanke ta sannan na yi wanka na fito.Har yanzu yana kan dardduma ,kayan jikina na saka sannan na shimfiɗa wani zanen gadon.Can ƙarshen gado na hau na kwanta ,abubuwan da suka faru yanzu da na fita suka faɗo min a rai. ‘ To wannan ɗin duk na mene ne? Ko dai gamo na yi?’ sai kuma na watsar da tunanin don banda wanda zai ban amsa.Ina nan kwance shi ma ya zo ya kwanta tare da kashe hasken ɗakin.A tsorace na tashi na ce “ Please ka kunna haske tsoro nake ji” “ Zo nan ” ya faɗa tare da jawo ni cikin ƙirjinsa,ido na rufe ruf ina jin zuciyata na bugawa da ƙarfi.“ Me ya tsorata ki?” ya tambaye ni. “Babu komai kawai ban son duhu ne” na basa amsa. “To ko ma mene ne ba zai taɓa zuwa nan ba don cutar da ke muddin kina kusa da ni” ya faɗa tamkar ya shiga raina ya ga abin da nake tsoro. Lamo kawai na yi ina sauraren bugun zuciyarsa,a hankali yake dadaɓa ni alamun na yi bacci.Na yi murmushi ina tuna can gidanmu yadda nake bacci ni ɗaya,ga shi kuma yanzu na samu abokin kwana duk da auren ba mai moruwa ba ne amma da ɗan sassauci kan rayuwata ta gida. Kalamansa ne suka katse min tunani inda yake cewa,“ Zahra na san ba ki sona an aura miki ni ne bisa dole,sannan kuma yanzu da aka kawo ki sai kika ƙara tsanata saboda larurar da kike tarar ina da ita.Ki yi haƙuri da sannu za ki saba za ki ga kamar ma yana ɗaya daga cikin aikin da kika fi so na wankin kayan fitsarina,abu guda na sani kina da lada don ni mijinki ne sannan aure dukkansa bauta ce.Allah ne ya ɗora min babu yadda na iya,ba wai zaɓina ba ne duk da farko abin ya addabi ruhina har ya taɓa aikin da nake saboda ina tsoron yin bacci a cikin abokai na yi fitsarin kwance.Shawarar Mama ce da nake bi nake ganin canji,ita ce ta ce min kar na damu da duk halin da zan samu kaina Allah bai ɗorawa bawa abin da ba zai iya ɗauka ba,sannan in na je can mission inda zan yi bacci cikin mutane na saka a raina ba zan yi fitsarin ba,kuma kin san abun mamaki hakan take faruwa fa sosai nake jin daɗi” ya ƙarashe maganar yana sakin murmushi mai sauti yayin da kuma yake shafa gadon bayana. “Amma kuma sai in ka zo nan gida ne kawai fitsarin yake dawowa?” na samu kaina da tambayar shi. Ya bani amsa da “ eh! Amma ko a gidan ba kullum ba ne nake yi” “Ita kuma ɗayar matsalar fa?” na tambaya a kunyace,shiru yayi bai bani amsa ba sai da aka ɗauki lokaci kafin ya ce “ wace matsala kenan?” “A'a ko ɗaya ,zan yi bacci” na faɗa jin yana son raina min hankali wato fitsarin kwance kawai ya ɗauka a matsayin matsala shi rashin kusantata da ya kasa yi ba matsala ba. “Zahra don Allah kar ki guje ni kin ji?” ya faɗa yana wani ranƙwafowa kamar mai leƙen fuskata.Na turo baki gaba kafin na ce “ kar ka damu Janiki ba ta taɓa yin farin ciki ba dama,ina tabbacin cewa sanin zan iya zama da kai suka haɗa aurenmu” na yi furicin hawaye na surnano min. Hasken ɗaki ya kunna tare da yin zauna ,sosai nake jin idonsa a kaina duk da na juya masa baya. “Ki bani labarinki” ya faɗa . “Aliyu ba ka jin bacci ne halan?” na faɗa cike da takaici. Ya ce “ me yasa ba ki jin kunyar faɗar sunana gatsal? In banda Hajiya babu wanda ke kirana da shi kai tsaye” “To ai sunanka ne” na basa amsa a takaice. “Kenan ba zan samu alfarmar da za a kira ni da wani sunan ba?” ya faɗa ,ni kuma na yi banza da shi.Tun ina tunani har bacci ya ɗauke ni, washegari ko da na farka ban gansa ba.Wanka na je na yi na canza kaya sannan na share ɗakina da kuma kewayena na kunna turaren tsinke. Ina tsaka da goge ledar ɗaki sai ga sallamar Binta,bayan mun gaisa ne take tambaya ta “ me za a dafa?” Tsuru-tsuru na yi mata don ban san me zan ce ba,a yadda ma na ga duk ranta a haɗe babu fara'a sai na ji kuma duk babu daɗi. “Ban san dalilin da yasa Hajiya ta baki muƙamin nan ba,alhalin kaf gidan nan ni ce mace ta farko da aka fara aurowa.Amma an bai wa ƙanƙanuwar yarinya damar juya mu hum!” Binta ta faɗa tana wani kallona. “Ki yi haƙuri Binta ki dafa duk abin da kike so” na faɗa murya na ɗan rawa.Ta ja tsuki kafin ta fice na bi bayanta da kallo,ina nan tsaye sai ga Aliyu ya shigo sanye da kayan gudu da dukkan alamu daga motsa jiki yake. “Barka da warhaka!” na faɗa ,ba tare da ya amsa ba ya wuce har can bedroom da takalminsa na gudu waɗanda suka ɗauko ƙasa.Haka na ƙara bin wurin na goge,ko da na shiga ciki na tarar tuni ya soma wanka. Bakin gado na zauna ina kallon ƙofar toilet ɗin,babu jimawa ya fito ɗaure da towel a ƙugu muna haɗa ido na sunne kai. “ Ki zo ki fitar min da kayan da zan saka,sannan ki fara shirin zuwa Coci don da wuri zan ajiye ki na wuce wurin aiki” ya faɗa cikin dakakiyar murya,da na ɗaga kai na dube shi kamar ma ba shi yayi maganar ba. Na miƙe na tsaya gaban drower kayansa,yadda na gansu jere ras sai na rasa wane zan ɗauko masa. “Wane kake so?” na tambaye shi tare da juyowa ina kallonsa. “In har na faɗa miki to mene ne amfanin zaɓar min ɗin da kika yi?” ya faɗa wannan karon cikin taushin murya har da wani zuwa a bayana yayi tsaye kamar mai shirin rungumo ni. Hannuna har rawa yake wurin ciro masa wasu kwat baƙaƙe da kuma rigar ciki blue.“ Ka sa waɗannan za su yi ma kyau” na faɗa ina dubansa,ya langaɓar da kai kafin ya ce “ kin tabbata?” na gyaɗa masa kai. Ya ce “ ni fa baƙi ne” “Duk da haka za su yi ma kyau” na faɗa sai ya karɓa ya je ya ajiye su bisa gado sannan ya soma shiryawa,ni dai ina gefe ina kallonsa har ya gama. Na ce “ saura turare ko?” ya ɗan yamutsa fuska ya ce “ yau ban son jin ƙamshinsa”sake da baki na yi ina kallonsa. Sai na yi saurin fita falo jin muryar Hajiya Luba ,“ ina kwana Mama?” shine abin da na fara faɗa da na je,ta amsa cikin sakin fuska kafin ta ce “ ina Aliyu?” “Yana ciki shiryawa yake” “Yau ba ki yi wanki ba ne?” ta jefo min tambayar da ta bani mamaki,na ɗan dube ta kafin na ce “ yanzu zan yi” “Na zata ko tun jiya kika yi cikin dare” ta ƙara faɗa tana ƙanƙance ido.Na girgiza kai, sai ta wuce bedroom ɗin ta bar ni nan tsaye ,babu jimawa suka fito ita da Aliyu tana gaba yana biye da ita a baya har suka fice . Sosai nake mamakin wannan kusanci nasu don ba haka take da sauran ƴaƴanta ba,a haka na je na yi shirin tafiya Coci.Direct kuma sai na fita zuwa ɗakin cin abinci,a zaune na tarar da su tana basa wasu magunguna da ke jere cikin faranti zinare. Na samu wuri na zauna,babu jimawa kuwa mutanen gidan su ma duk suka zo don tuni Binta ta kawo abincin breakfast. Bayan kowa ya zauna na tsawon kamar minti biyar haka , Hajiya Luba ta ce “ ƴata Janiki ki bada izinin cin abinci mana ” Sai na ɗaga kai na dubi kowa,Binta ta yi kicin-kicin da rai alamun ba ta so ba .Amma haka na bi umarnin Hajiya na buɗe kwanon,yau ma wainar ce irin ta jiya da ɗan mamaki na dubi Binta sai na ga tana murmushi da ban san na mene ne ba,sai dai ko kafin na ɗora ayar tambaya Hajiya Luba ta rige ni “ yau ɗin ma wainar aka yi?”kana jin amon muryar za ka fahimci ranta ya ɓace . “Janiki ce ta ce na yi,sai da na faɗa mata mu nan ba kasafai ake yinta ba amma ta ce babu ruwana ai ita ke da damar zaɓar abin da za a dafa ” Binta ce ta yi saurin faɗar haka,nan kuwa Hajiya ta wani maido dubanta gare ni.A tsorace na soma i'ina ,“ dama...dama” sai kuma na yi shiru tare da sunne kai ina hawaye,don a duniya babu abin da na tsana kamar a yi min ƙazafin abin da ban yi ba. Ruwan hawayena na ɗiga kan capet sai kawai wani iska ya tashi labulaye suka soma tashi sama yayin da kuma hotunan Hajiya duk suka faɗo ƙasa,a can waje ma kana jiyo ƙarar faɗuwar abubuwa,duk sai hankali kowa ya tashi muryar Hajiya har rawa take wurin cewa “ ki yi haƙuri Janiki ki bar duk wannan abubuwan” Ina ɗago fuskata Binta ta fasa uban ihu tare da dafe wuyanta muryar dakyar take cewa “ ki..kikiki yi haƙuri wallahi sharri na yi mata” Tana faɗar haka na ja sanyyyar ajiyar zuciya,nauyin da na ji ƙirjina yayi ma duk ya ɗauke.Kamar kuma almara haka komai ya tsaya cak,ni sam ban fahimci cewa saboda raina ya ɓace ne hakan ta faru ba. Hajiya Luba ta ja wata ajiyar zuciya kafin ta ce “ to kowa ya ci abinci” nan muka soma ci,bayan mun gama kowa ya fita yau ma yayi saura mu uku sai dai ba ta bani komai na sha ba sai ƴar nasiha da ta soma yi min. “Ƴata Janiki ki dinga controling fushinki ,sannan ba komai ne yake sa mutum ya fitar da ɓoyayyar siffarsa ba” Ba tare da na fahimci abin da take nufi ba na ce “ to Mama” Ta saki murmushi ta ce “ Aliyu tashi ku tafi” Haka muka miƙe muka fito,sai da muka koma ɗakinmu duk muka yi brush kafin mu fita can waje inda motarsa take,duk da ba irin waccan ba ce ta miliyoyin kuɗi amma tana da kyau sannan duk garin ba za su wuce su biyar ba masu motar hawa. Gidan gaba na shiga ya ja ni zuwa Coci,har muka isa bai yi min magana ba.Har can ciki ya shiga da ni,ya samu wuri yayi parking kafin kuma ya juyo ya dube ni.Da sauri na sunne kai,ya kamo hannuna tare da cewa “ ki kula da kanki sosai kin dai ji abin da Hajiya Mama ta faɗa ko?” na gyaɗa kai tare da buɗe murfin na fita,cak kuma na tsaya ina kallon abubuwan da can farko ban ganinsu ban ma san lokacin da Aliyu ya bar wurin ba. Idona ne na soma jin suna wani irin zafi tare da sauya kala suka koma baƙaƙe ƙirin,inuwar mutum na gani ina ɗago kai muka haɗa ido da father. “Janakiii?” ya faɗa hankali tashe kafin ya riƙo ni,ido na rumtse gam jin tamkar ya jona min wutar lantarki.Amma a haka ya ja ni zuwa can ciki ya zaunar da ni,“ ina Cross ɗin da na baki?” ya jefo min tambayar ,sai yanzu na tuna tun bayan da aka sa na cire ta ranar da za a yi min lalle ban sake ganinta ba. “Tana ga Mama” na basa amsa.Bai ce komai ba ya fita,babu jimawa kuma ya dawo tare da miƙa min wani kofi ya ce “ ungo ki sha” na karɓa kuwa ba tare da na tambaye shi ba na sha,ko minti ɗaya ba a ɗauka ba na soma jin ana yi min motsi cikin ciki ta ko ina kafin na ɗuka na soma kelaya amai.Sosai na yi mamakin yadda na yi aman baƙaƙen tsutsotsi kuma duk da ransu sai motsi suke. Hankalin Father sai na ga ya ƙara tashi,ya tsure ni da ido na wani lokaci kafin ya je ya ɗauko wata kwalba mai kamar turare ya fesa cikin aman da na yi nan fa na ga abun almara yadda wurin ya kama da wuta har sai da komai ya ƙone ƙurmus wutar na tsayawa kuma aman ya ɓata. “Ban san cikin me kika jefa kanki ba Janiki,amma tun ranar da kika rera waƙar nan na ga wata ɓakar inuwa mai tsaurin ido na biye da ke.Tabbas inuwar nan na da ƙarfin tsafi tun da har ta iya shigowa cikin coci a kuma ɗakin bauta” a cikin kalamansa babu abin da na fahimta,kuma kafin na kai ga tambayar shi sai ga motar Aliyu ta sake dawowa da sauri na je gare shi. Gidan gaba ya buɗe min na shiga,ba tare da ya ce komai ba ya figi motar a tsiyace.Muna isa gida kamar wacce ta yi laifi haka ya wani fincike ni zuwa sashen Hajiya ,muna shiga a falon nata a yanayin da na ganta kawai na fahimci da tabbas na aikata mata wani babban zunubi wanda kuma take shirye da ɗaukar tsatsauran mataki a kaina.Daidai nan free page ya ida duk mai son ci gaba sai ya biya kuɗin karatunsa. My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ 01 ‘ Lokacin da muna yara,da zarar an ce MAFIYA kawai abu guda kwanyata ke bani ƙungiyar shan jini ce mai sa a yi kuɗi.Amma yanzu da na girma,na kuma tsinci kaina a ciki sai na fahimci cewa MAFIYA na nufin cikar muradi. Sunana HAROON matashi ne ni ɗan kimanin shekara talatin da takwas a duniya,maraya na uba ,shalelen mahaifiyata.Na taso cikin matsin rayuwa ta talauci kafin kuma na tsinci kaina cikin daula...... ' “Haroon sakatariyarka ta ce yau ba za ka fita ba ko zan san dalili?” muryar Ammy ta katse mini ɗan taƙaitaccen tunanin zucina wanda kusan lokuta da dama nake zama haka kawai ina bai wa kaina labarin kaina. Na saki murmushi ina kallon sanyin idaniyata abar alfaharina,“ ban jin daɗi ne Ammy shi yasa,amma kar ki damu ciwon kai ne kawai” “Kamar ya kar na damu ? Ciwon kan ne kake faɗa ƙaramin abu? Jira ni ina zuwa” ta faɗa tare da yin gaba. Na bi ta da kallon ƙauna,Ammyna kenan uwa ta gari wacce a idonta sam ba na girma kullum tamkar ƙaramin yaro haka take ɗauka ta.Ina nan zaune ta dawo hannunta riƙe da wata tasa da kuma ƙaramin towel,na lumshe ido lokacin da ta soma tsoma towel ɗin a ruwa tana matse shi sai kuma ta dinga dadanna shi a kaina.Cikin ikon Allah na ji ciwon kan yayi sauƙi,“Ammy ya isa haka je ki huta mana ban san yaushe za ki daina ɗawainiya da ni ba,kamar wani ƙaramin yaro dai sai ririta ni kike” na faɗa ina mai riƙe hannunta mai ɗauke da towel ɗin. Ta dungure mini goshi cikin faɗanta da ta saba yi min ta ce “ sai ranar da ka kawo matar aurenka a gidan nan.Wai HAROON yaushe za ka yi aure ?” Da sauri na miƙe ina mai cewa “ aure! Aure dai kullum shine zancenki Ammy,duka nawa nake?” “Yanzu na haife ka” ta bani amsar da ta saka ni dariya,sai kuma na ce “ kar ki damu zan nemo miki suruka kafin ƙarshen shekarar nan in sha Allah!” na furta ina mamakin furucina na ƙarshe da na ambaci sunan maƙagina,wanda a ƙalla zan kai shekaru biyar da muka yi hannun riga ni da umarninsa.Yanzu haka ambaton sunansa sai da na ji maƙogorona yayi min wani zafi,halshena kuwa tamkar an saka reza ne an tsaga shi. “Allah ya nuna mini wannan babbar rana, Ubangiji yasa ina da rai albarkacin Manzon Rahama Ya Rabb ka dubi Harunana ka basa mata ƴar aljanna mai haska duk wani duhun gidansa” ita ce addu'ar Ammy gare ni,ban ko amsa ba na yi gaba abina. Ina fitowa harabar tsakar gida direbana yayi saurin tashi tare da nufar motar da a yau ita ce zan shiga.Da kansa ya buɗe mini gidan baya na zauna,sannan ya ja motar. Hanyar babban ofis ɗina ya ɗauka amma na yi saurin dakatar da shi.“ Ka ga kai ni wurin da zan ɗan shaƙi iska yau ban ra'ayin aiki ko kaɗan ” na faɗa don haka kawai nake jin yau raina a dagule babu daɗi ga wani irin bugawa da zuciyata take. Gudu yake da ni amma hankalina ba ya ga hanya na lula sosai cikin tunani,ƙiiiii ya ja wani uban burki sai a lokacin na dubi gabana.Wata kyakkyawar budurwa na hango tana tsallakar da yara ƴan makaranta,yayin da duk ababen hawa suka tsaya suna jiran sai yaran sun gama wucewa. “Yi haƙuri yalaɓai bari na canza hanya” cewar direba ,da sauri na ce “no ! Jira” ido kawai na tsura mata yadda take ta zulumniya cikin ƙaton hijabinta ,yayin da hannunta kuma wanda ya sha jan lalle ke faman kamo na yara. Ido na lumshe sa'ilin da ta game dukkan hannuwanta alamun godiya ,ban san mun bar wurin ba sai da na ji direba yana cewa “ba don Malam Zainab ba ce da ƙila mutanen nan ba su tsaya ba sai an samu waɗanda za su ce sai sun wuce” “Ka san ta ne dama?” na samu kaina da tambayarsa. Yayi ƴar dariya ya ce “to wane ne zai ce bai san Malama Zainab ba,yarinyar da duk shekara ita ce ke cin gasar musabaƙa ta duniya.Makarantar can ma gwamnati ne ya buɗa mata ita da sunanta,yalaɓai in ka ji yadda ɗalibanta ke yin larabci kai kace ƙyanƙyasar Saudiya ce uwa uba ita in tana yi.Zaƙin muryar.....” “Ya isa haka juya ka mayar da ni gida” na yi saurin katse shi saboda bugun zuciyata da na ji sai ƙara hauhawa yake.Muna isa gida ko wani burki mai kyau bai yi ba na yi saurin fita daga motar ba tare da na jira ya buɗe min ba. Ammy na falo ta ga na shigo a hargitse,ta yo kaina tana tambayar lafiya amma ban bata amsa ba na haye step ina taka shi bibiyu yayin da ita kuma ta mara min baya tana faman kiran sunana.Ina isa ɗaki kuma na rufe shi gam da key,ga ƙofar na jingina ina sauke numfashi kafin dakyar na ƙarasa na je na zauna kan kujera ina kallon kaina cikin baƙin madubin da shine silar canza rayuwata daga jiya zuwa yau.A zahiri ni mutum ne complet,amma a cikin madubi ba komai ne ba face ƙwarangwal ba tsoka saboda da kaina na sayar da ruhina ga MAFIYA......... [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA* 02 Karon farko kenan da na yi da na sanin shiga MAFIYA,a tsawon shekarun da na yi a ciki na yi su ne cikin farin ciki.Hawayen takaici nake yi yayin da ƙwarangwal ɗin da ke cikin madubi ke ƙyartata dariya,ita ƙwarangwal ɗin nan ba kowa ba ne face Ni,inuwata ce ko kuma na ce ruɓaɓen ruhina.Daga can bakin ƙofa ina jin Ammy na buga wa tare da kiran sunana amma na kasa tashi ,zuciyata ta yi rauni ba zan iya tsayuwa gabanta ba na shaida mata alƙawarin da na yi mata na samo matar aure ne ya cika sai dai kuma baƙin ruhina da farin ruhin kyakkyawar budurwar nan sam ba za su iya zama a inuwa ɗaya ba saboda rayuwar da ta rage min ƙalilan ce. Wayata ce ta ɗauki ruri,ina dubawa na ga sunan Oga.A dole na ɗaga,“ ka zo muna da meeting ɗin gaggawa” shine abin da ya faɗa kafin ya kashe. Jiki babu ƙwari na miƙe na shiga toilet na wanke fuskata na goge ta da towel sannan na fito.A bakin ƙofa na ga Ammy idonta sun yi jawur,na sakar mata murmushi na ce “ kar fa ki damu kan ki zan nemo wata tun da wannan ɗin ta fi ƙarfina” “Wa kenan?” “Budurwar da na gani yanzu da muka fita,kin ga Ammy kar ki damu zan cika miki alƙawarin da na ɗauka” ina gama faɗa na soma tafiya,ta biyo bayana har muka sauko ƙasa sannan ta ce “ ƴar wace ce ita da har ta fi ƙarfin ka?” “Ba kowa ba ce kawai malamar makaranta ce” na bata amsa,“ mi sunanta?” Na juyo muna facing juna sannan na bata amsa da “ zan fita yanzu in na dawo za mu yi maganar” “Allah tsare ka ya maido mini kai lafiya” Dakyar na amsa da “Amen ” .Ina fita na karɓi key ɗin mota,don in magana ta shafi Oga ban bari a yi draving ɗina.Tuƙi nake amma idona ita suke hasko min,dakyar na samu na kai kaina can inda muka saba meeting ɗin. Tuni mutane sun fara taruwa,na samu wuri na zauna muka ɗan soma cacabke wa da sauran members.Sai da kowa ya hallara sannan wurin yayi tsit,Oganmu sai a lokacin ya miƙe ya soma jawabi.“ Kamar yadda kuka sani wannan Association ɗin namu yana da tsari,ba a shiga kudin sirrin kowa hakan ne yasa wasu informations ɗin ba mu samunsu kai tsaye ta yadda za mu fahimci daga ina suka fito.Sai dai sosai dakarun bayar da kariya suke iya ƙoƙarinsu wurin ganin babu wata ƙungiya ko baƙin haure da za su kawo mana hari.To yau ma ɗin mun samu labarin cewa wani mummunan al'amari na tunkaro ƙungiyarmu ,kune ƴaƴanta kune kuka san yadda kuke gudanar da rayuwarku don haka ku nutsu ku yi nazari a cikinku babu wanda ya tsokano faɗa ko kuma yayi wani kuskure wanda bai dace da tsarin ƙungiya ba?” Oga na kawowa nan da zancensa sai duk ya soma bin mu da ido ɗaya bayan ɗaya. Ko kaɗan ban kawo a raina cewa malam Zainab da na soma jin ƙaunarta ita ce matsalar da Oga ke magana a kai ba wannan yasa sam ban ma nuna damuwa ba.Har aka gama meeting babu wanda ya ce ga wata matsala sai Oga ya sallami kowa.Har zan fita ya tsayar da ni,sai da ya kalli tsakiyar idona kafin ya ce “ HAROON ka shekara biyar a cikinmu” “Ai na sani Oga” na faɗa don ban ga amfanin sanar da ni ɗin ba. “Eh tuni ne na yi ma don kar ka shagala” ya faɗa yana ƙara yi min kallon nan da ke sa mutum ya tsargu,shiru kawai na yi masa.Can ya ce “ kana iya tafiya” na jinjina kai. Bayan na fito daga can direct wani gidan shaƙatawa na tsaya Park,wuri ne da iyaye suke kawo yaransu don shan iska da kuma buɗe ido.Karon farko da na ji sha'awar ajiye yara,yadda suke wasa gwanin ban sha'awa sai ya sake tuna min da Malama Zainab.Hoton fuskarta nake gani a kan fuskar duk iyayen da ke wurin,sai nake ganin tamkar ma a nan ita ce ke kula da su.Na ɓata lokaci sosai kafin na bar wurin,ina draving ina tunaninta har na isa gida.Cak na tsaya bakin ƙofa ganin Malama Zainab ɗin tare da Ammy a zaune.Na girgiza kai tare da dariyar kaina a zuci na ce ‘ HAROON ka haukace tun da har a cikin gidanku Malama Zainab kake gani ’ sai na yi gaba har na hau step ɗin farko sai na tsinkayo muryar Ammy na cewa “ HAROON zo ku gaisa da malamar da za ta dinga koyar da ni karatu” Da sauri na juyo sai muka haɗa ido da ita amma ta yi saurin kawar da kai,tamkar wani gumki haka na tsaya ina kallon ta .Sanye take cikin pink ɗin hijabi,tafin hannunwata a waje suke ta riƙe litattafai da su.Kamar wani sakarai haka jan lallen yatsunta ya ja ra'ayina har ban san lokacin da na taka can inda suke a zaune kan salon ba,“ mu ga littafin da za ku soma” na faɗa tare da kai hannuna zan karɓa amma wani azababen suraci da ban san na mene ne ba ya daki hannuna da bala'in sauri na yi baya har ina shirin faɗuwa. “Yi sannu mana,Malama miƙo min na basa” cewar Ammy ta karɓo littafan ta miƙo min sai dai sam na kasa amsa saboda wani irin haske da nake ganin yayi min katanga da littafafan.Na girgiza kai na ce “ a'a Ammy ba sai na gani ba” sai kuma na nufi step da mugun sauri na haye can sama,ina shiga ɗaki na ƙargame shi da key ina jin wani tsohon ilimina na baya na dawo min.A nan take a inda nake na fahimci wani abu,ina cikin fushin Allah mai tsanani ta yadda har har littafai masu kalmomin saninsa suka yi min tawaye suka haramta gare ni........ MRS SADAUKI ce 💫✍️ [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 03 Duk yadda na so nuna wa zuciyata ruwa ba a sa'an kwando ba ne amma sam sai ta yi min bore ta ƙi aminta akan muradinta.Soyayyar Malama Zainab ɗin dai ta zaɓa ,duk da tunanina ya ƙi bata haɗin kai wannan bai canza zane ba.Dakyar na cira ƙafafuna zuwa toilet,kayana na cire kafin na shiga ƙarƙashin shower na buɗe pampon duka.Ruwa suka soma jiƙa ni,sanyinsu na rantsa sumar kaina ina jin wata ƴar nutsuwa na sauko min.Rabon da na ji yanayin buƙatar mace har na manta,zan iya kai wata biyu haka ban yi lalata da ƴar kowa ba amma yau soyayyar Malama Zainab ta motso mini da tsimin. Pampon na kashe ba tare da na yi wankan sabulu ba,towel na ɗaura a ƙugu kafin na fito ina tsane gashina da ɗan ƙarami.Bayan na gama na saka ƙananun kaya na fashe jikina da turare kafin na sauko ƙasa ,sai na tarar tuni ta tafi sai Ammy kaɗai zaune a falo tana duba littafi. Na ƙaƙalo murmushin dole na ce “ Barka da yamma uwa ta gari” Ta ɗago ta ɗan dube ni na wani lokaci kafin ta ce,“ meke damunka HAROON ? Ina ce ganin Malama Zainab zai sa ka nutsu amma sai na ga saɓanin haka” Kusa da ita na zauna kafin na ce “ wai aka yi kika nemo ta? Ko dama kin san ta ne?” “To wane ne bai san Malama Zainab ba duk Yamai? Na san ta mana har gidan marayun da take kula da shi ina zuwa duk ƙarshen wata” Na ɗan saki murmushi,taimakon al'umma yana ɗaya daga cikin halin kirki na Ammy.Duk wata ƙungiya mai kula da marayu sun san ta sannan ba wata ɓoyayya ba ce a garin Yamai don kusan duk wani abu da ya shafi Islam sai an kawo mata takardar gayyata irin taron ci gaban addini da sauransu,amma ko kaɗan ban yi tunanin ta san Malama Zainab ɗin ba. “Bayan fitarka ne na tambayi direba sai yake sanar da ni,shine fa muka je har can inda take na nemi alfarmar ta dinga zuwa tana min karatu a gida ” Ammy ta faɗa murmushi kan fuskarta. Ita ɗin tana da son Addini sai dai ba tada yawan karatu,kuma samun ilimi na ɗaya daga cikin burinta sai dai ta karaya ne tana ganin ai shekarunta sun ja. “To Ammy sai ku yi ta karatun,yaushe da yaushe za ta zo?” “Duk bayan sallar magrib in sha Allah,zan dinga aika direba ya ɗauko ta in kuma ta gama sai ya mayar da ita” “Amma iyayenta sun bari?” “Eh sosai,ai a gabansu na nemi alfarmar shi fa mahaifinta gani yayi ma kamar zunubi ne ƙin yarda da abin da na roƙe su ɗin.Iyayenta ƴan mutumci ne kamar dai ita” ta ƙarashe zancen fuskarta na canzawa,da sauri na kamo hannunta ina mai cewa “ mene ne kuma Ammy? Don Allah kar ki tuna shi,kar fa ki manta kin yi mini alƙawarin haka” Kai ta jinjina mini kafin ta ce “ zan shiga ciki sallar magrib ta gabato zan yi wanka” sai kuma ta miƙe,na bi bayanta da kallo kawai.Ina nan zaune mai aiki ta kawo min abubuwan motsa baki,ko kallon ta ban yi ba na soma ci ina tunanin abar ƙauna.Na kurɓi lemun zoɓo kafin na miƙe na fita harabar gidan,mota na shiga na ƙara ficewa. Ban yi nisa ba kuwa aka soma kiran sallah,amma ban wani damu ba na ci gaba da tuƙina har na isa inda nake tunanin zan samu macen da za ta sama min nutsuwa. Daidai wurin bada hannu na tsaya,almajiran suka fara miƙo min robobinsu duk da kuwa gilashin motata a rufe yake ruf.Dayawansu ba za su wuce shekara ashirin zuwa da uku ba,ganin ban buɗe ba yasa duk suka tafi sai ɗaya ce ƴar jaraba ta tsaya .Sai a lokacin kuma na yi ƙasa da madubin motar,cikin daƙiƙa biyar na ƙare mata kallo fara ce ita amma dauɗa ta saka ya disashe sannan irin kamar Fulanin nan na daji. “Alhaji ka taimaka mini ina son kai Mamana asibiti ne” ta faɗa cikin marairaice murya. “Nawa ne farashinki? ” na samu kaina da furta wa,ido kawai ta zuba min da alamu ita sabuwar zuwa ce ba ta san tabi'ar nan ta ban manda na baka gishiri ba. “Za ki bi ni mu je in kina son na baki kuɗi” na faɗa a karo na biyu,sai na ga tsoro ya bayyana a fuskarta.A hankali na soma mayar da madubin motar amma ta yi saurin dakatar da ni ta hanyar saka hannunta daga sama ,sai na ƙara yin ƙasa da shi. “In mun je da gaske za ka bani kuɗin?” ta jefo mini tambayar cike da yarinta. Kai kawai na jinjina mata,sai na ga fuskarta ta faɗaɗa da murmushi.Gaban mota na buɗe mata kafin na yi mata key,tuni gari ya ɗauki duhu sai hasken fitilun kan hanya.Gudu nake sosai ta yadda ta soma yi min magana cikin tsoro “ don Allah Alhaji ka yi haƙuri kar ka sayar da ni ” Na ja tsuki ban tanka ta ba,sai dai na rage gudun motar sai ta saki ajiyar zuciya.Gidana na kai ta wanda babu kowa a cikinsa hatta mai gadi ban sa ba,a waje na yi parking duk muka fito.Na buɗe gidan na shiga sai na ga ita ta tsaya bakin ƙofa,“ki shigo” “A'a ba sai na shiga ba ka ɗauko kuɗin ka bani” tsabar takaici ban san lokacin da na wani jawo hannunta da ƙarfi ba na shigo da ita ciki tare da rufe gidan. “In kika ce ihu ko kuka za ki yi min zan sayar da ke ɗin tun da haka kike so” na faɗa tare da yin gaba,a dole ta take min baya har cikin falo.Na kunna wutar ko ina sannan na haɗe rai tare da nuna mata toilet na ce “ ki shiga ki yi wanka” jikinta na kyarma ta shiga ɗin,sama da minti goma amma ta ƙi fitowa sai na mara mata baya ina shiga na ja wani uban burki zuciyata ta soma bugawa fat! Fat! Fat! Sakamakon ganin Oga cikin shigar kayan yarinyar da na ɗauko a mota. Waige-waige na fara sai dai babu ita sai shi ɗin dai,kamar ƙyaftawar ido yarinyar ta dawo normal ta soma magana amma muryar oga ce ke fita. “ Tun da na soma meeting ɗin yau hankalina yake kanka,wato a fuskar kowa na lura da damuwa saɓanin kai.HAROON ka fara soyayya faɗa mini wace ce ita?” yana gama faɗa sai ya ɗauki siffarsa ta namijin kayan yarinyar nan suka zube a ƙasa sai nasa kayan jajaye masu kamar jini. Kasa furta komai na yi,don in na ce in yi magana ƙarya ce zan faɗa kuma tsaf zai gane.To mene ne ma abin yi wa mutumen da yake da ƙarfin power ɗaukar siffar mace? Shirun dai ne ya fi alkhairi a gare ni. Kafaɗata ya dafa sai na ji wani zuuut,sai muka ɓace daga cikin toilet zuwa daularsa wacce kusan a can muke taro masu muhimmancin sosai ko kuma in wani sabon members ya shigo.Ban fita daga wannan mamakin ba na ji na yi sama cikin iska kafin kuma in ji ni gammm,bayana ya bugu da bango yayin da hannuwana kuma aka banƙare su tare da ɗaure su da kacar tsafi. “Babu soyayya a tsarin ƙungiyarmu,amma kai ka karya doka! Zaɓi biyu zan baka ko dai ka sadaukar da budurwar da kake so,ko kuma na aika ka ɓoyayyar duniya yanzu nan tun kafin wa'adin shekarunka su cika” Ido na rumtse gam,a cikin zaɓin biyu babu mai sauƙi a gare ni.Shekara biyar ta rage mini a doron duniya kamar yadda muka yi yarjejeniya a ranar da zan sayar da ruhina,an bani shekaru goma na rayuwa a wannan duniya kafin na isa ɗayar,a cikin goman kuma na yi biyar saura biyar suka rage mini.‘Wane zaɓi zan ɗauka?’ na tambayi kaina a zuci....... [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 04 “Wato soyayyar da kake yi mata har ta kai ka kasa sadaukar da ita kai tsaye shi ne ka tsaya shawara? Hahaha! Ōgāfōr̃!” Oga yayi lafazin ƙarshe cikin Yaren matsafa a nan take kuma na ga tile ɗin ɗakin na darewa wata jar turɓaya na bayyana kuma sai girrrr kake shi tamkar ƙatuwar tirelar ɗan danƙarau mai yin gina. A inda nake can sama ɗaure a jikin bango nake kallon duk abin da ke faru,gidan ƙasa ne ya bayyana sai a lokacin kuma kacocin hannuna suka kwance kansu yayin da na soma yawo cikin iska ina kaɗawa kamar wata leda. Wasu ɗalasiman tsafi Oga ya soma kafin ya ce “ je ka ɓoyayyar duniya ka yi ziyara na tsawon kwana uku,in ka fito daga ciki sai ka bani zaɓin ka” rufe bakinsa ke da wuya na soma ji na ina yin ƙasa har na shiga dogon ramen mai ɗauke da wata daular . Ina shiga ciki komai ya soma komawa normal ya ɗinke,sai da na ja wani numfashi sa'ilin da na ji ƙafafuna sun dogane da ƙasa. Baƙar ƙofar na kalla ta gabana wacce nake da tabbacin ita ce za ta sada ni da ainahin abin da ake kira da ɓoyayyar duniyar.Na shagala sosai ina kallon ƙofar tare da tunanin da na san ba zai fishe ni dare ba,kawai sai na ji ƙiiiiii ƙofar ta buɗe da kanta. Ido na tsura ina jiran ganin wanda zai fito,amma sai na ji wata murya na cewa “ Barka da zuwa duniyar Ruhaniya ” ban amsa ba haka ban gusa daga inda nake ba . Sai na ji an kamo dukkan hannuwana biyu ana jana amma ban ganin masu jan nawa,a dole na soma taka ƙafata har muka bi ta ƙofar nan a take kuma ta rufe ji kake gammm.Duhu ne ya turniƙe wurin,sai a lokacin kuma na ga inuwar masu jaye da ni saboda wani jan haske da goshinsu ke fitar wa kamar wuta. Ci gaba suka yi da ja na izuwa ciki,matakala muka soma takawa muna daɗa yin can ƙasa.Har muka ainahin duniyar,nan ɗin ko ina da haske tamkar goshin azahar haka. Duk masu bi suna wuce wa na soma duba,dayansu siffar mutane ce da su yayin da sauran kuma suke ɗauke da sifofin dabbobi iri-iri. Irin inuwar nan gani ta waɗanda suka yi min iso,a zuci na ce ‘ ko su waye su?’ “Dōr̃ānī! Masu kula da shige da ficen duk al'ummar nahiyar nan.Ko da wasa wani ya tsaya hutawa dangane da aikin da yake yi za su hukunta shi ne” na ji muryar ɗazu ta faɗa wacce ta tarbo ni tun a bakin ƙofa. Saitin inda murya ta fito na duba,sai na ga yanzu ana ganinsa da kyau sai dai muninsa ma ba zai bari ka ci gaba da kallonsa ba. “Amma kuma ƴan Adam ne?” na tambaya. “Duk faɗin nan babu mai ruhin bil'adama sai kai ,duk waɗanda ka gani da irin siffarka to mutum ne da rigar aljan.Bima'ana gangar jikin ce ta mutum amma ruhin aljani ne a ciki” “To ya ake hakan tana faruwa?” na sake jefo masa tambayar. “Mutanen da suka sayar da ruhinsu ga MAFIYA ,bayan wa'adin shekarun da aka ɗibar musu ya cika za a aiko da su izuwa nan.Ruhikansu za su dinga yin bauta ,yayin da gangar jikinsu kuma aljanai za su ɗauke ta su dinga amfani da ita.” yana kawo wa nan sai yayi shiru yayin da ɗaya abokin aikin nasa ya ɗora da cewa “ dayawan jinnu na son ganin kansu a duniyar bil'adama sai dai babu damar yin haka don ba za su iya bayyana da siffarsu ba,wannan ya sa suka ƙulla yarjejeniya da manyan masu ƙungiyoyin asiri da su dinga sayar musa da gangar jiki” “To mi za su yi da ita?” na yi tambayar cikin zaƙuwa zuciyata na bugawa jin ni ma abin da ke shirin faruwa da ni kenan nan da wasu shekaru.Sai da suka ƙyalƙyace da dariya kafin su yi haɗin baki wurin cewa “ duk wanda ya sayi gangar jikinka in yana so zai iya shiga duniya yayi yawo,wasu ma har auren bil'adama suke yi ” Tsoro ne ya kama ni,sai nake ganin tamkar in na dawo da zama a duniyar nan aljanin da ya sayi gangar jikina zai iya zuwa ya cutar da Ammyna. “Amma wanda ya sayar da ruhinsa ga MAFIYA shin zai iya karɓe shi kuwa? Ina nufin akwai wata hanya da mutum zai bi ya rushe waccan yarjejeniyar ta farko sai a kafa masa ta biyu?” duk shiru suka yi suna kallona,na gyara tsayuwa tare da matsawa can gaba ta yadda za mu yi facing juna na ce “please ku sanar da ni” “Eh to ba za a rasa ba,sai dai sharuɗan suna da tsauri sosai” Duk da ban ji su ba haka na ji raina ya ɗan sanyaya har sai da na sauke ajiyar zuciya da kuma ɗan guntun murmushi ko ba komai zan samu damar da zan yi rayuwa da abar ƙaunata. Muna nan tsaye wata rundunar wasu inuwoyi ta zo wuce wa,inuwar siffar mutum ce da ita amma babu gangar jiki. “Ka ga wannan shine ruhi! ” ya faɗa. “Amma suna jin magana?” na tambaya,babu wanda ya bani amsa sai yin gaba suka yi har na soma take musu baya suka ce “ kar ka biyo mu,tuni mun gama aikinmu yi maka iso da kuma amsa tambayoyinka” “To amma ina zan je?” na yi tambayar cikin ɗaga murya,ko juyo wa ba su yi ba ballantana su bani amsa a haka suka ɓacewa ganina.Sai a yanzu ma ne na ji mugun tsoro ya shige ni fiye da na farko,haka na soma bulaye a ƙatuwar duniyar ina kallon abubuwan ban mamaki har na isa wani wuri inda ake yi wa wani aski.Duk suka ɗago suna dubana kafin su fara ƴar kallon-kallon,ɗaya daga cikinsu ya ce “ wane ne kai?” Ba tare da wani tunani ba na basa amsa da “ Ni bil'adama ne!” ko ida rufe baki ban yi ba suka yi min caaaa kowa na faɗar ra'ayinsa“ a'a ni zan ɗauka! ” “A'a wannan fa gangar jikin tawa ce! ” “ kai kana da wajen biyu fa ka bar min kawai” Ido kawai na rumtse ina rawar jiki,jin ana rigima akan gangar jikina wacce Allah ne ya halitta min ita amma saboda wata buƙatata na butulce wa rahamarsa na sayar.Ina cikin haka ne sai na soma jin canjin yanayi,ina ware idona sai na koma fanko wato ruhi babu gangar jiki.Da ido nake kallon yadda ake faɗan shiga gangar jikina wacce ta zama tamkar riga mai haɗe da wando............ Talla! Talla! Talla!!!! Set d'in gyaran gashinmu na dauke da * Shampoing don wanke gashi * Man ganshi da zai taimakawa gashin wajen k'ara tsayi * Man gashi wanda zai cire miki kwarkwashi/dandruff/Pellicules * Garin ambunu da zai hana karyewar gashi * Man karkar da zai taimakawa gashi wajen k'ara bak'i * Garim amrfit don sakawa a hamata ta kasance cikin kamshi * Man coco na asali don gyaran fata +22780416252 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 05 Ni da gangar jikina amma banda iko da ita wannan lokaci,ban ma san taƙamaimai ya zan yi na mayar da ruhina a cikinta ba ko kuwa sun maido min ita.A yanzu da nake gantali cikin iskan ɓoyayyar duniya sai na fahimci a cikin MAFIYA ni ba kowa ne ba fa ce ɗan ƙaramin jinjiri ashe ban san komai a kanta ba. Dōr̃ānī kamar yadda aka sanar da ni sunansu tun shigowa ta nan,irinsu ne su biyu suka zo suka ƙwace gangar jikina daga hannun aljanan kafin su miƙo min . “Ka shiga gangar jikinka sannan ka koma duniyarku tun da wa'adin da aka ɗebar ma ya cika,ka yi kwana uku cicif ” Tsakanin furucinsa na cewa na yi kwana uku alhalin ni dai a lissafina ba zai wuce na yi minti talatin ba,da kuma tunanin yadda zan mayar da gangar jikin nawa a ciki sai na rasa wane zan yi. “Ka mayar mana za mu mayar da kai” ya ƙara faɗa . “Ban san ya zan yi na mayar da ruhina a ciki ba” na basa amsa. Suka kalli juna kafin kuma su haɗin baki wurin cewa “ kai ɗin ba ahalin MAFIYA ba ne?” Na jinjina kai na ce “sosai ni ɗin ɗana ga Mafiya amma ban san ya ake yin duk abubuwan nan ba” ban rufe bakina ba na ji sun soma karanta wasu ɗalasima wanda na yi imani na tsafi ne.Wani girrrr na soma ji,gangar jikina na haɗe wa da ruhina ban san ta yaya hakan ta faru ba amma tabbas yanzu na dawo HAROON ɗina. Na ja ajiyar zuciya lokacin da suka ja ni izuwa can wajen ƙofar fita,na kasa haƙuri na ce “ amma ɗazu kamar na ji ka ce wai har na yi kwana uku a nan,sai nake ganin kamar minti talatin ne ko zuwa da biyar haka” “Lokacin nan ba iri ɗaya ba ne da na duniyarku,duk minti goma ɗin ku matsayin kwana ɗaya yake a nan” ban kai ga ƙara yi masa wata tambayar ba suka cillo ni waje. Ta hanyar da na bi na shigo nan ta haka na koma,a gaban idona yanzu ma can saman ya tsage kamar wata leda marar nauyi haka na tashi cikin iska na fito har tsakar fadar Oga ,tile ɗin ya koma ya ɗinke kansa. Ɗaya bayan ɗaya nake kallon members ɗin ƙungiyar tamu,da dukkan alamu sun shirya wa fitowar tawa kamar yadda nake tsammanin Oga ya sanar da su komai. A cikin abin da bai fi minti biyu ba na ga wani sabon abu wanda can farko ban taɓa ganinsa ba,ba komai ne bai sai shatin Cross a goshin kowa na member ƙungiyar sannan a ƙasan Cross ɗin kowanne daga cikinsu yana da alamun lamba,wasu 9,wasu 18 da dai sauransu.Ban yi nauyin baki ba wurin cewa “ Oga lambobin mene ne nake gani a goshi mutane?” Bai bani amsa ba sai jin shuuu na yi,wani ɗan madaidaicin madubi ne ya zo yayi tsaye a gabana,ba wai wani ya riƙe shi ba a'a shi ke riƙe da kansa.A ta cikin madubin na hango hoton fuskata,wannan karon da tsokarta irin ta ƴan adam ba ƙwarangwal ce ba.Lamba ɗaya(01) na gani a tsakiyar goshina kuma ni ma ina da zanen Cross ɗin,ina gama gani madubin ya ɓace daga gabana. Sai a lokacin Oga ya soma magana,“ Barka da shigowa wani level daga cikin MAFIYA! A can farko ba kowa ne kai ba face costumer mu,amma a yanzu kana level 1 sannan kamar yadda ka nemi alfarmar janye yarjejeniyar mu ta farko domin kawo wata sabuwa,mun karɓi kokenka.Sai dai kamar tun can farko yanzu ma zan sake jaddada maka cewa kowanne tasiri yana da farashi,ina nufin yanzu shekaru biyar ɗin da suka rage maka a duniya za ka iya ƙara su domin yin doguwar rayuwa” yana kawo wa nan sai yayi shiru tare da nuna mini kujera na je na zauna kamar sauran. Zamana kan kujerar sai na ji tamkar ba normal kujera ba ce amma na dai yi shiru kawai ina jiran ƙarin bayani. “ HAROON ?” Oga ya kira sunana,na ɗaga kai na kalle shi sai kuma na je zan mayar da shi ƙasa amma ya hana ni ta hanyar ce mini “ tsakiyar ido za ka kalle ni sannan ka sanar da ni ka gani a ciki” Har sai da na ɗan ƙanƙance idona don ƙara samun tabbacin abin da nake gani shin gaskiya ne ko kuwa? “Mi kake gani?” ya jefo mini tambayar. “ Maƙabarta!” na basa amsa. “Ka san me ake yi a can?” “Eh na sani Oga!” “Yawwa madallah da kai HAROON tabbas alamu sun nuna kana yunwar ƙara tsawon rai” cewar Oga kafin ya nufi allon da yake yi mana rubutu ko nace darasi.Wani suna ne ya rubuta mai harafi bakwai wanda tuni na soma tambayar kaina ‘ mene ne kuma alaƙarmu da sunan?’ ashe kuwa amsar na kusa. “ HAROON ko tashi ka karanta mana abin da ke rubuce a nan” Oga ya umarce ni. Na tashi tsaye kamar yadda ya buƙata kafin na karanta “ likafani ” “Ƙwarai kuwa likafani ne kamar yadda ka karanta ɗin,ka yi daidai ina fatan kuma aikin da za ka yi da shi shi ma ɗin ya zama daidai” “Aiki kuma Oga?” na tambaya cike da tsoro,duk kowa ya kwashe da dariya sai da suka yi son ransu kafin Oga ya umarci kowa yayi shiru.Fuskarsa babu alamun wasa ya dube ni yana cewa “daga lokacin da wa'adin shekaru biyar ɗinka ya cika to za ka dinga farautar likafanin sabuwar gawa domin luluɓa shi a jikinka ka kwana da shi,ta wannan hanyar ce kawai za ka ci gaba da rayuwa a wannan duniyar akasin haka kuma za ka koma inda ka fito yanzu.Na sanar da kai ne tun yanzu don ka zamana cikin shiri,abu na biyu kuma da ƙungiya ke buƙata a wurinka shine tsofin takalmi na yara ƙanana.Kowa zai iya tafiya meeting ya ida” yana gama faɗa ya bi wata hanya ya shige yayin da kowa ya watse ya bar ni cikin zullumi. Dole dangin na ƙi ce ta saka ni fitowa ni ma,sai yanzu na tuna inda na bar motata wato can tsohon gidana.Taxi na shiga aka kai ni can amma abun mamaki babu motar a nan,a dole na ƙara shiga wata taxi ɗin na nufi gida. Tun a bakin ƙofa na ga kallon da direbana ke yi mini,kamar zai yi shiru sai kuma ya kasa ya ce “yalaɓai yanzu ko minti ɗaya ba a yi ba na ganka da baƙaƙen suite fa kuma ga shi har ka canza kaya” Na haɗe rai na ce “wato sa ido kake yi min?” “Yi haƙuri yalaɓai” ya faɗa yana rusunawa. Ina shiga cikin falo na ci karo da Ammy ita ma idon ta waro tana cewa “ HAROON canje-canjen kayan na mene ne? Ko don ka burge Malama Zainab ne? Hahaha! Wannan kayan fa kamar ma sun yi datti,waɗancan ɗin dai sun fi yi maka kyau” Murmushi kawai na sakar mata ina cewa “ina zuwa” sai kuma na haye can sama,ina buɗe ɗakina na hangi irina sak yana ƙoƙarin shiga madubina. “Dakata!” na faɗa da sauri,ya juyo muka haɗa ido amma bai saurare ni ba yayi wata suka cikin madubin tamkar wanda ya shiga ruwa haka ya nitse ciki tun ina ganin inuwarsa har madubin ya dawo normal........ Assalamu alaikum,mata da ƴan matan garin Agadas.CHAFA'ATU MAKE-UP fitacciyar kuma jajirtaciya mai koyar da kwalliya iri-iri.Ta yi tattaki tun daga Nigeria ta zo nan Nijar a garin Agadas domin horar da masu buƙatar koyon kwalliya,ɗaurin kallabi.Wannan horar wa da za a yi za ta kwashi kimanin sati biyu ,kuɗin koyo jika ashirin ne (20.000f).Ga masu buƙatar ƙarin bayanin za su iya kiranmu kai tsaye ta wannan lambar 88584336 ,ko kuma ku tuntuɓe mu lambarmu ta WhatsApp 09041604348 . [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 06 Gaban madubin na je na soma shafa shi tamkar wasu ruwan Teku haka na ji hannuna ya nitse a ciki.A kullum cikin ganin sabbin abubuwa nake tare da madubin da ni ne da kaina na saye shi,maimakon da na saka hannuna na ga ya nitse na fiddo shi a'a sai na gwada shigar da dukkan gangar jikina. Hazo-hazo na soma gani a cikin sabuwar duniyar da na tsunduma kaina,ban ganin komai sai wani abu da ke zuba kamar dusar ƙanƙara .Idona na soma ƙanƙancewa nan na hango gobena,ga ni tare da Malama Zainab har da yarinyarmu.Wani daɗi ya wanzu a zuciyata,ina son ƙara samun wani bayanin amma daga can waccan duniyar nake jin muryar Ammyna a kunnena raɗau.Da sauri na fito ina mamakin ‘ dama ana iya shiga cikin madubi ? ’ Sai kuma na watsar da tambayar na nufi ƙofa na buɗe murmushi kan fuskata. “ HAROON ka fito mana ko ka manta yau rana ce ta musamman a gare mu?” Ammy ta faɗa tana murmushi tare da gyara min zaman rigata ta sama. Sai yanzu na lura,kayan jikina sun sauya daga waɗanda na shigo da su zuwa irin mai kama da ni da ya ɓuya cikin madubi. ‘ Wane abu ne zai faru mai muhimmanci haka?’ na yi wa kaina tambayar a zuci,yayin da kuma na samu amsar tambayar kuma a cikin kwanyata “ yau za ka sanar da Malama Zainab kana son ta,shine alƙawarin da ka yi wa Ammy ” Shiru na yi ina tunanin ‘ ta ya aka yi nake jin muryar mutum na yi min magana cikin ƙwaƙwalwa? ’ Nan ɗin ma wata amsar aka bani “ saboda yanzu ka fita daga matsayin 0 ka koma level 01 ,kana da buƙatar ɗan kariya mai baka rahoto akan abubuwa da dama, waɗanda suka faru da kuma shawara wurin yanke hukunci” Ajiyar zuciya kawai na sauke ina kallon Ammy tsakiyar ido,“ ya dai? Kar ka ce min dai tsoro kake ji?” Ammy ta faɗa ,na girgiza kai na ce “ mu tafi ga ta can har ta iso” Da mamaki Ammy ta ce “ ta ya aka yi ka san ta iso?” sai ta ja kumatuna. Abin da na fahimta wannan ɗin sam ba furcin tunanina da niyyata ba ne, mataimakina ne ya furta ba ni ba.Amma sai na yi saurin cewa Ammy “ saboda ina mugun ƙaunarta shi yasa a duk in tana kusa da ni ina jin sautin zuciyata na canza wa” Ammy ta shiga yi min dariya kafin ta kama hannuna kamar wani ƙaramin yaro muka fito. Ina taka step ina kallon Malama Zainab wacce ke zaune tana duba wani littafi,yanayin nutsuwarta da cikar kamalarta sun fi komai burge ni a tattare da ita. Ammy ce ta yi sallama,da sauri ta ɗago tana amsawa tare da gaishe ta. “Lafiya lau Malama ya gida ina kuma iyayenki fatan duk kuna lafiya?” “Alhamdullah suna gaishe ki ma” ta faɗa cikin rawar murya tana sunne kai,cikin ƙwaƙwalwata na ji muryar nan na ce mini “ kar ka cika kallonta hakan fa zai sa ta fasa son ka” Ammy ta ɗan zungure ni,na dube ta sai ta yi min alamu kan na yi wa malamar magana.Na yi gyaran murya na ce “ uhum! Hajiya ko na ce Malama na gode sosai da kika karɓi wannan aiki na koyar da Mamana karatu muna godiya...” sai kuma na yi shiru, Ammy ta gusa ta bar falon tana harare na tare da yi min alama kan na zauna kan kujera .Abin da Ammy ba ta sani ba iya wannan tsayuwar ji na nake a takure,tamkar wanda ya shiga wurin da babu iskan shaƙa na san kuma hakan bai rasa nasaba da ƙarfin imaninta. Ɗan nesa da ita na yi,sai na ji abin yayi dama .Na sauke ajiyar zuciya kafin na ce “ Malama Zainaaab?” a hankali ta ɗago ta dube ni muka haɗa ido,sai na ji wani ƙuna tamkar ta watso min barkono wannan karon ni ne na sauke idona ina rayawa a zuci ‘ tabbas da matsala! Yarinyar da na kasa haɗa ido da ita ta yaya kenan za mu yi aure har mu haihu? Ko dai duk abubuwan da na gani cikin madubi ƙarya ne? ’ Ɗayar muryar mai min magana cikin kwanya ta ce “ sam wannan ba ƙarya ba ce,tabbas za ka aure ta sannan ku samu yara sai dai saurin yiyuwar haka na tattare da kai akwai abubuwan da ake buƙata ka yi kafin har ka cimma ƙudirinka in ka ji kana iya wa tun yau za ka soma” Tun da na soma jin maganar na yi shiru har aka ida kafin na sake tambayar muryar ‘ ta yaya kenan? ’ “Ta hanyar sato farin tauraro daga jikin wani bil'adama mai sakaci,tabbas da tauraronsa za ka yi amfani domin biyan buƙatarka” ina gama jin amsa na saki murmushi ,ina ɗago kai sai na kama Malama Zainab na satar kallona. Na sakar mata murmushi yayin da ta yi saurin miƙe wa tana cewa “ zan koma ina da ɗalibai da zan yi wa karatu” “Ok jira na kira Ammy ” na faɗa tare da zuwa ɗakin Ammy,tana gani na ta miƙe tana cewa “ komai ya tafi daidai? Ka furta mata ɗin kana son ta?” Na yi murmushi mai sauti na ce “ A'a Ammy amma mun samu kusanci sosai ina ga ita ma tana sona ” “Wato ba ka furta mata ba? Mtsww !” ta ja tsuki tana harare na tare da ficewa,duk sai na ji babu daɗi na take mata baya. Da murmushinta mai tsadar nan take sanar da Ammy uzurinta,“ HAROON ka sauke Malama a makaranta” “To Ammy ” na furta ba tare da na san yin haka babban kuskure ne a rayuwata ba.Har kusa motata Ammy ta yi mana rakiya,ita ce da kanta ta buɗe wa Malama Zainab gidan gaba.Dakyar na shiga na zauna na yi wa motar key,numfashina sai barazanar tsaya wa yake ba don komai ba sai don na yi kusa da farin ruhinta. Ina tuƙi ina haƙi kamar wanda yayi tseren doki,zuciyata ji nake tana matse wa tana takurewa wuri guda .Hancina kuwa tamkar wanda aka matse sam babu daɗi ,iya ta baki kawai nake samu ina sheɗawa.Tun ina daurewa har na kasa,ina ƙoƙarin tsayar da motar kuma wayar Malama Zainab ta hau ruri ƙira'ar Sheikh Aliyu Jabeer ce inda yake karanta suratul yaseen. “Yiiii!” na soma kyarma yayin da na kusa sakin sitiyarin motar ina,idona kuwa wani baƙin abu kawai nake gani da alamun lantarkin nasu ne yake dab da tsayawa.Hannunta na ji kan nawa on daidaita tsayuwar motar sai dai kafin wannan zuciyata ce ta tsaya cak da bugawa ........ Ga masu son fara yin payment ga detail nan ,500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 .Ki tura kawo sai ki turo min evidence sai na saka ki group. Talla! Talla! Talla!!! Set d'in gyaran gashinmu na dauke da * Shampoing don wanke gashi * Man ganshi da zai taimakawa gashin wajen k'ara tsayi * Man gashi wanda zai cire miki kwarkwashi/dandruff/Pellicules * Garin ambunu da zai hana karyewar gashi * Man karkar da zai taimakawa gashi wajen k'ara bak'i * Garim amrfit don sakawa a hamata ta kasance cikin kamshi * Man coco na asali don gyaran fata +22780416252 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 07 Cikin ikon Allah Malama Zainab ta yi nasarar tsayar da motar wuri guda,sama-sama nake jin sautin muryarta tana kiran sunana haɗi da girgiza ni “ HAROON ! HAROON ! Please ka tashi ! Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! ” ta furta kafin ta fita ƙila don neman taimako. Fitarta yayi daidai da dawowar bugun zuciyata,na buɗe murfin motar na soma kelaya amai kamar raina zai fita.Ta zagayo tare da yin tsaye tana kallona,sai kuma ta je za ta tsallaka titi tana mai tsayar da mai sayar da ruwa .Manta wa na yi da halin da nake ciki na yi wani uban tsalle na jawo ta baya don kauce ta daga motar da saura ƙiris ta kaɗe ta. Tamkar yadda in boom ta fashe take ɗaga mutum sama ta cilla shi gefe haka ce ta faru da na jawo Malama Zainab,sai da muka yi sama ni da ita kafin mu faɗa can gefe kaina ya bugu da dutse yayin da ita kuma ta faɗo kan ƙirjina gaba ɗayanta.A wannan karon babu wani jinkiri ruhina yayi nisan zango daga wannan duniyar na fita daga hayyacina ban ƙara sanin abin da ya faru ba. A ruɗe Malama Zainab ta tashi daga jikin HAROON idonta na kawo ruwa,mutanen da ke bakin hanya ne suka matso.Ita ɗin ba wata ɓoyayya ba ce a garin Yamai wannan yasa cike da girmamawa suka fara tambayarta ba'asi. “Yayana ne ya faɗi ne kansa ya bugu” ta faɗa cikin kuka ganin kan HAROON sai jini yake zubarwa,wasu samari suka taimaka mata suka saka shi a gidan baya yayin da ita kuma ta hau mazaunin direba ta tuƙa shi zuwa wata asibiti ta kuɗi. Da isar su aka karɓe shi,duk da kuwa ba tada kuɗi a hannunta amma sai ta nuna musu katin ɗan ƙasarta cikin ikon Allah ma wasu sun santa.Abu na farko da aka soma yi wa HAROON shine tsayar da jinin kansa aka naɗe da bandeji,cikin ikon Allah kuma numfashin nasa ya dawo normal sai dai yana buƙatar hutu. Sai a lokacin kuma ta kira mahaifiyarsa ta shaida mata ,babu jimawa kuwa sai ga Ammy.Ita ma kukan ta soma sai ya zamana babu mai rarrashin wani,ita sai faman faɗin “ HAROON kar ka mutu ka bar ni,kai kaɗai ne farin cikina a duniyar nan” Ita kuma Malama Zainab cewa take “ duk laifina ne,da ace ban yarda ya sauke ni ba da ƙila hakan bai faru ba,saboda son kasancewa da shi yasa na aminta oh ni Zainabu na ga ikon Allah! ” sai kuma ta fashe da kuka. Bacci nake mai kamar mutuwa, sama-sama nake jin sautin kukansu a hankali na ware idona ba tare da na buɗe su tarau ba.Ta ƙasan gashin ido nake hango yadda masoyana biyun ke kuka,sai na shagala yadda manyan idon Malama ke tsiyayar da ruwa ,pink leɓenta kuma duk ya jiƙe da yawunta yana rawa.Yatsun nan nata masu ɗaukar hankalina sai shafar hawaye suke,na dafe gefen kaina da ke sara min kafin na kira sunan Ammy.Da sauri ta matso kusa da ni tana cewa “ ka tashi? Mi kake ji? Ina yake ma ciwo?” Murmushi na sakar mata tare da nuna mata saitin zuciyata da kuma yi mata alama da Malama Zainab,wacce ta yi tsaye tana kallona hawaye na bin kumatunta yayin da fuskarta ke ɗauke da ɗan murmushi. Ammy ta ce “ za ka same ta in sha Allah kar ka wani damu” sai kawai na lumshe ido ina tuna abin da ya faru da ni, a daidai lokacin da mugun iskan nan mai ƙarfi yayi cilli da ni kaina ya bugu da dutse ɗigon jinina na farko ya ɗiga ga ƙasa Oganmu na gani a can gefe a tsaye yana kallona,bai samu damar ƙaraso wa inda nake ba sai da Malama Zainab ta ɗan yi nesa da ni,abin da na fahimta shi kansa yana shakkarta.Hakan kuma sai yasa na ƙara jin mugun sonta da ƙaunarta sun ƙaru a Wani farin abu ya saka min a inda kaina ya fashe kafin ya ɓace wa ganina. Dakyar ta iya cewa “ ya jikin naka?” Ammy ta ce “ bari na kira likita” sai ta fice. Sai a lokacin na amsa mata “Da sauƙi! Na gode sosai” Ta ɗan dube ni cikin ido kafin ta ce “ babu komai!” sai kuma duk muka yi shiru ,ni na ƙure ta da ido yayin da ita kuma take satar kallona lokaci-lokaci .A haka Ammy ta shigo ita da wata nurse,awon tension ta yi min kafin ta ce “ ka gyara zan yi ma allura ga cinya” “Ga cinyaaa ?” Malama Zainab ta faɗa da sauri duk muka kalle dukkan mu ukun sai ta yi saurin wayancewa ta ce “ ina nufin wace irin allura ce za a yi ga cinya? A yi ga hannu ai zai fi” Nurse ɗin ta ce “ saboda cinya ta fi tsoka,in ga hannu ne za ta iya yi masa zafi” “Bai komai ai shi namiji ne,ki yi masa ga hannun kawai tun da dai ana yi” ta faɗa cike da kishin da ita kanta ba ta san ya fito ba,Ammy dai sai murmushi take. Hannun rigar na cire sannan nurse ɗin ta yi min allura ga damtse,ni aka caka da allurar amma Malama Zainab ce ta yi ƙara har da rumtse ido. Nurse ɗin ta yi dariya tana mai cewa “ ah Madam irin wannan tattali haka ? Ko duk don kar a yi miki kishiya ne?” “Wace irin kishiya kuma ? Ai ...ai ba mij...” sai kuma ta yi shiru ƙila yadda muka haɗa ido da ita ne yasa ta kasa idawa. “Zuwa an jima za a sallame ku in Dr ya hau aiki,sannan akwai gwaje-gwajen da aka yi ana jiran result” nurse ɗin ta faɗa kafin ta fice. “Ni ma zan tafi Mama,am...ina nufin Hajiya Allah ya bada lafiya” shine abin da ta faɗa kafin Mama ta yi mata rakiya. Suna fita Oga ya bayyana a cikin ɗakin fuskar nan tasa kicin-kicin,kamar zai fashewa da kuka ya ce “ ina mai yi maka gargaɗi akan ka bar sheɗaniyar yarinyar can.Sam tarayyarku babu alkhairi a tattare da ita,sannan ina so ka yi gaggawar barin asibitin nan kafin ta kwaso zugar ɗalibanta su zo duba ka” Sam ban yi mamakin ganin nasa ba,amma na fi mamakin yadda yake so na bar asibiti alhalin banda lafiya.“ Amma Oga me yasa zan tafi? ” “Za ka iya jurar addu'o'in da za su yi ita da zugar ɗalibanta? Kai ka rasa wacce za ka so sai babbar maƙiyiyarmu? Ko ba ka san manyan sheɗanu sun yi tirrr da halinta ba? In banda karatun littafinsu babu abin da ta iya,a haka ne kake tunanin haɗa wuta da ruwa wuri guda?” “Ina son ta!” na furta kai tsaye ba tare da shakka ba,“ dole ka rabu da ita” “Zan zauna da ita Oga,kai dai kawai ka zuba min ido” bai kai ga bani amsa ba Ammy ta shigo. “ Da wa kake magana HAROON ?” ta tambaye ni. “A'a ban yi magana ba Ammy ” “Yanzun nan kafin na shigo na ji kana magana fa” “To ƙila ko dai a ɗaya ɗakin ne” “Ok to .Ka ga Malama Zainab na son ka ko? In sha Allah zan je can gidansu ni da Kawunka ” sam ban ɗauki maganar da wani muhimmanci ba na miƙe na shiga toilet saboda yadda na ji marata ta ƙulle,kamar jira ake ina shiga toilet ɗin na ga an zagaye ni na zamana a tsakiyarsu.Duka mutanen na gane su ahalin ƙungiyarmu ne,ban san da wane Siddabaru suka yi amfani wurin ɓatar da ni ba sai kawai na tsinci kaina a wani gun daban. Cikin faɗa Oga ke faɗa “tun da ka ji za ka iya sai ka zo a ƙaddamar da kai ta yadda za ka samu power da yawa,sannan waccan abar ka sani lokaci guda ne kawai za ka iya kusantarta wato in tana period” Cike da mamaki nake kallonsa kafin na ce “wannan ai ƙazanta ce! Ta ya zan kusanci matata da jinin al'ada?” “Ba kada zaɓi” Oga ya faɗa yana matsowa kusa da ni hannunsa riƙe da wata ƴar tasa ,yatsana manuniyar ya kama ya sa reza ya tsaga shi nan jinina ya soma zuba cikin tasar nan har sai da ta cika duka.Ya ajiye tasar sannan ya saka wani abu ya rufe wurin da ya tsaga sai jinin ya tsaya. Daga nan wani ɗakin sirri dukkanmu muka shiga ,ni dai ban san da zamansa ba amma su sauran da alamu sun saba shigowa.Komai na cikin ɗakin baƙi ƙirin yake sannan an yi masa adon zanen Cross da jan penti,gaban wata aba mai kamar halittar duniyar sama Oga ya je ya tsaya jinina da ke cikin tasa ya dangwala a yatsa ya shafa daidai bakin halittar ,wani irin girrrr na ji a yatsan nawa kafin kuma a sannu wani abu ya game dukkan gangar jikina.A gabana dukkan members ɗin suka dinga dangwalar jinina da yatsa suna lasa da alamu ma kamar daɗinsa suke ji saboda yadda kowa ke ta ƙoƙarin ganin ya fi ɗan uwansa sha.Bayan nan sai Oga ya ja mu izuwa wani katafafen capet duk kowa ya zauna amma ni ya hana ni,na buɗe baki da niyyar tambayarsa don me banda ni,kawai na ga abokan ƙungiyarmu sun shiga yin aman kuɗi sabbi dal da su wani irin tsoro ya kama ni har ban san lokacin da na saki ihu ba. My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 08 Tun da uwar da ta haife ni ban taɓa ganin inda mutum ɗan Adam yayi aman kuɗi ba sai yanzu,tamkar wasu ruwa haka takardun kuɗin ke fito wa daga bakin kowanne members har sai da suka kusan cika ƙaton capet ɗin.Ni kuwa banda kyarma babu abin da jikina ke yi,a nan take a inda nake tsaye kuma na ƙaryata fassarar da na yi wa sunan MAFIYA daga “cikar muradi ” zuwa “tsafi da shan jini”. Ashe ban kai maƙura wurin mamakina ba sai da na ga kuɗin na ware kansu suna yin dunƙule-dunƙule na 100k ,kamar ƙyaftawar ido suka jeri rasss a hakan kuma kowace takardar kuɗi ta san wanda ya amayar da ita . “ HAROON wannan ɗin duk kuɗinka ne!” Oga ya faɗa yana murmushi haɗi da bubuga gefen kafaɗata. Na ce “ duk me zan yi da uban kuɗin nan?” Sai duk suka hau yi min dariya,can suka tsagaita Oga ya ce “ ka manta akwai aiki jajur a gabanka? Ko da kanka za ka dinga bin maƙabartu kana ciro likafanin?” “Wane irin likafani kuma?” na tambaya cikin tsoro. Oga ya haɗe rai ya ce “ wanda zai taimaka ma ka yi tsawon rai nan gaba,ko ka manta ne?” Murya na rawa na ce “ ban manta ba amma Oga ai sai nan da shekara biyar ko?” “Bayan wannan akwai wasu sharuɗan! Kowanne ƙarshen wata za ka samo mana jinin period na budurwa,kar ka tambaye ni ta yaya .Ka fara tunanin hanyar da za ka bi ka kawo na wannan watan don yau muna ashirin da uku ga wata” Wasu irin yawu na haɗiye masu mugun ɗaci,ido kawai na tsura musu da alamu ko a jikinsu sai harakar gabansu suke suna saka min uban tulin kuɗin a jakakuna. “Amma Oga ina zan ajiye kuɗin nan? ” “Bisa kaina” “Ka yi haƙuri in na je da su gida Ammy za ta zarge ni ” Ran Oga ya ƙara ɓace wa ya ce “ HAROON ka fita idona,kana yawan matsa min da zancen Ammynka in ba ka yi sa'a ba kai ne za ka yi silar mutuwarta ” Gabana ya bada rasss jin wata lukutar masifa,amma na kawar da tsoron gefe na ce “ wannan shine babban kuskuren da za ka yi kuwa a duniya shine taɓa Ammyna,duk duniyar nan banda tamkar ta.Kar ka manta silar ta ne a yau nake cikin wannan ƙazamar rayuwar,Ammyna ita ce komai nawa in babu ita ban ma ga tsiyar da zan yi a duniya ba” duk wurin tsit yayi suna kallona shaye da mamaki,na sani sarai yadda duk ake tsoron Oga ni ma ina tsoronsa amma ba zan juri a taɓa Ammyna ba ko kaɗan ai gwara ya yanki fatar jikina ya fi yi min sauƙi. Ban taɓa ganin Oga cikin fushi irin haka ba sai yanzu,tako ɗaya yayi ya isa inda nake idonsa sun kaɗa sun yi ja sosai. “Ōgāfōr̃!” furucinsa kusan tsinke igiyar da ke saita mini numfashi yayi,na riƙe hannunsa tare da roƙonsa “ please Oga kar ka hukunta ni ta hanyar kai ni ɓoyayyar duniya” sai dai da alamu roƙon nawa a banza ne wai an tsikari kakkausa.Tuni ƙasa ta soma darewa ginin cikin ƙasa ya bayyana,idona na zubar da hawaye na tashi cikin iska kafin na yi nitso cikin dogon ramen a haka ƙasa ta rufe da ni ruf sai gani tsaye a gaban baƙar ƙofar nan a karo na biyu. Yau ɗin ma Dōr̃anī ne suka buɗe min ƙofar tare da yi mini iso a ciki,sai dai fa wata jahar suka kai ni ba nan fara isa ba. “Wannan karon kuma wane laifin ka yi mai yawa har Oga ya ce a kai ka sashen bauta ?” ya tambaye ni. Ƙin basa amsa na yi sai ma tunanin yadda zan yi na fita na soma,“ fatan dai ba wani sirrin ƙungiyar ka fitar ba?” “Ban fa iya surutun nan yau ka bar ni da abin da ya sha min kai” na faɗa cikin masifa,daidai nan muka iso wata duniyar mai cike da abubuwan ban mamaki mutum da jikin maciji,ko kifi,ko doki,mage mai ƙafa ta fi ɗari,ko kuma mage da kan mutum.Maciji mai magana,kare da shan sigari. “Ina ne kuma nan? Me zan yi a nan?” na tambaya a firgice,banza suka yi da ni sai tafiya suke ina take musu baya har muka isa gun wasu tsofi. “Ina ka samo mana ɗan saurayi kuma?” ɗayar tsohuwar ta faɗa tana wani kashe mini ido,yayin da wasu biyun suka taso suka soma shafa ta da sauri na soma ture su ina son guduwa. Dōr̃anī ya ce “ ladabtar da shi za ku yi,shi ɗin yana da muhimmanci ga uwa MAFIYA don haka kar ku taɓa lafiyarsa” Yana gama faɗar haka duk suka ɓata rai waɗanda ma suka yi min ƙawanya sun gusa daga jikina,su ma Dōr̃ānī tafiyarsu suka yi. Wacce ta fi su tsufa duka ita ce ta miƙe tsaye ta ce “ ɗan samari biyo bayana ” Dole dangin naƙi haka na take mata baya zuwa wani sashe mai cike da yana don ta cikinta ma muke bi muna wucewa,mun ɗan yi tafiya sosai kafin ta ja ta tsaya. “Ruhinka nada ƙarfi sosai ta yadda har yanzu Octoba ya kasa karɓe shi duka duk da kuwa ka sayar da shi,uhum! Amma me yasa kake fusata shi haka? Ka san mene ne za a yi maka a nan ɗin?” tsohuwar ta tambaye ni. “Mene ne zan yi a nan ɗin?” na tambaye ta tare da share duk sauran zancen da ta yi. “Matso kusa ka gani” ta faɗa ,na ɗaga ƙafata na isa gare ta abun mamaki sai na hango duniyarmu ta Bil'adama.Wasu abubuwa ta dinga furta wa nan gidaje da ababen hawa suka dinga wuce wa kamar mai yin tariya har ta isa ga asibitin da aka shimfiɗe ni. Wani irina na gani zaune kan gado Ammy na ɓare ayaba tana basa yana sha,gefe guda kuma direbana ne ya ƙura masa ido yana kallo. “Ko ka san me yasa waccan mutumin yake kallon mai kama da kai?” tsohuwar ta tambaye ni. “Eh saboda ba haka nake zama ba,sannan in zan ci abu da hannun dama nake riƙe shi ba hagu ba.Ban cika son mutum ya ƙure ni da ido yana kallo ba” ina gama faɗa sai na ga mai kama da ni ɗin ya mayar da ayabar a hannun dama yana cewa “ Ammy har yanzu hannun ga nawa ciwo yake,kai kuma lafiya ka tsare ni kana kallo? Fita ka ban wuri” Direbana ya miƙe da sauri da ya kai bakin ƙofa sai da ya sake waiwaya wa,nan ɗin ma sai da ta tambaye ni “ me yasa ya waiwaya?” “Saboda yi wa mutum tsawa da hantara ba tabi'ata ba ce” na bata amsa kai tsaye. “To da zarar ka koma duniyarku ya zama dole ka kashe direban can” Sai da na dafe ƙirji na ce “ saboda me?” “Amsar na wurinsa” tana gama faɗa ta wani kamo hannuna muka yi suka tare da sauka can doron duniya mun iso bakin kwalta na ja na tsaya,ta wani ja hannuna tana mai cewa “ kai gara iya ruhinka ne kawai a nan gangar jikinka na can sama” Haka motoci ke ratsawa ta cikinmu ba tare da mun kauce musu ba,wani gidan cin abinci muka je.Da murna take cewa “ tsawon lokaci kenan da ban shigo duniya ba ,ina son abincin nan ya kamata in nemi gangar jiki na shiga ta yadda zan ji daɗin abinci” “Ta ya kenan?” ba ta bani amsa ba ta je jikin wata budurwa wacce ke tsaye jikin mota ita da saurayinta,a gaban idona tsohuwar ta shige jikin yarinyar.Ta ja hannun saurayin suka zauna ta yi odar kaji da lemun kwalba,“ yau sai na baka mamaki zan cinye dukkan kaji biyun nan” budurwa ta furta wanda a baɗini esprit ɗin tsohuwar nan ne.Aka kawo kaji biyu ta cinye su tasss ta sha lemun kwalba,tana gamawa ta fice daga jikin nata ta zo daidai inda nake tsaye tana dariya “ na tsani soyayya,yau na yi silar raba su” sai kuma ta ja ni muka tashi cikin iska muka koma can inda muka fito,gangar jikina na gani a tsaye tana zaman jirana sai dai ban san ya zan yi na koma ciki ba........ My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank,DM +22795045822 .Saura page biyu na gama free page kafin nan zan yi discount ga mai so ya biya 400 sai ya tura min shaidar biya ta WhatsApp. Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 09 Wannan tsohuwar ce ta nuna min yadda matsafa ke yi wurin fitar da ruhinsu daga cikin gangar jiki da kuma yadda ake yi a koma. Cike da jin daɗi na isa inda gangar jikina take a tsaye kamar saƙaƙo,yadda ta koyar da ni ɗin da shi na yi amfani na koma ciki.Daga nan sabbin abubuwa ta soma koya min,irin yadda zaka juya tunanin mutum,kashe mutum ba tare da kaca masa wuƙa ko bindiga ba,yadda za ka cutar da wani normal mutum ba tare da shi kansa ya san an cuce shi ba. Daga wannan kuma sai ta soma yi min wani bayani da ya tafi da ruhina. “ HAROON ita duniyar MAFIYA da kake ganinta kowanne members yana samun power ne daga aikin da yake yi,wato iya yawan sacrifice iya adadin yadda ƙarfin ikonka zai ƙaru.Samun power ƙwaya ɗaya ya fi a baka miliyan ɗari,saboda su kuɗin za su ƙare ita kuwa power zaka iya sarrafa ta sosai ta yadda za ka samu dubban abubuwa marar ƙirguwa.Ka ga ko ita wannan wacce kake so ko? To tabbas kana iya yin galaba a kanta muddin dai ka samu power dayawa.Bari na nuna maka wani sirri na musamman da ba kowa ya san da shi ba” sai kuma ta miƙe ta ɗauko wani tandun kwalli ta miƙo min.Na karɓa ina dubanta,ta ce “ shafa shi da idonka sai ka sanar da ni me ka gani” Ban musa ba sai kawai na bi umarninta na shafa kwallin ga dukkan idanuwana,sanyi ne ya ratsa su kamar na ƙanƙara wannan ya sa na ɗan lumshe su.Ina buɗe su kuma na yi tozali da tsohuwar matar nan ta zama tamkar lagwami duk jikinta tattakaken ƙwarangwal ne babu kyawun gani. Ta ce “ wannan kwallin yana taimakawa wurin gane taƙamaimai asalin mutum da kuma niyyarsa a kanka,sannan zai ƙara ma ƙwarjina ta yadda babu wanda ya isa ya kalle ka cikin ido ciki kuwa har da Ammynka”sai ta yi shiru na wani lokaci kafin ta ɗora da “abubuwan da suka fi kawo maki a Mafiya sune mata da ƙananan yara,sai kuma mahaukata.Kowanna daga cikinsu da tasa rawar da yake takawa,in kana son a kowace irin jarabawa ko sabga taka ka yi nasara to da buƙatar ka yi sacrifice na ƙaramin yaro da bai balaga ba...” da sauri na katse ta da tambayar “ amma saboda me?” “Saboda ƙwaƙwalwa yaro a wanke take babu komai cikinta na tunanin wata matsala,sannan zuciyarsa ma haka fara ce fesss babu baƙin cikin kowa .Bakinsa kuwa gaskiya ce tsagwaron ta,irin haka ne zaka samu wasu mutanen da daɗin baki in sun yi magana sai ka ji tasu ta fi ta kowa” “Su kuma mata me yasa ake son sadaukar da su?” na tambaya. Ta yi wani murmushi kafin ta ce “ akwai wanda ya fi mace wuyar sha'ani a duniya? Ita fa kamar sawun keke take baka gane gabanta ballantana bayanta ,wannan ya saka Mafiya ke da buƙatar mata.A sassan jikin mace akwai waɗanda in aka yi tsafi da su aikin ya fi kyau ,daga ciki akwai al'aurarta da kuma mamanta,abu na ƙarshe kuma shine ana yi mata wankan ƙaddamawar sai namiji yayi amfani da ita irin haka ne ke janyo farin jini da dukiya mai tarin yawa” Na jinjina kai na ce “ su kuma mahaukata fa wane dalili ne?” Kai tsaye ta bani amsa da “ a gaskiya sabbin members na MAFIYA waɗanda suke son yin kuɗi sun fi amfani da mahaukata,dalili kuwa shine shi hauka launin cuta ce da ke zuwa daga ƙwaƙwalwa wasu ta jinnu ce wasu kuma haka aka haife su da ita,to ita kanta wannan launin cutar tana da matuƙar muhimmanci a mafiya tana sa member ya ji gamsuwa fiye da in da mutum mai hankali ne ka kusanta” Shiru na yi ina nazari,abin da na ƙara fahimta game da Mafiya wani rikitacen al'amari ne marar kyau.Duk abu na ƙwarai a wurin su ba mai kyau na ne sai gurɓatace,“ to amma yin mu'amala da mace yayin jinin al'ada fa me yake ƙarawa?” na jefo mata tambayar. “Yin haka tamkar rufe ƙofofin taurarin ita macen ne,sannan duk wasu lamurranta za su iya kwaɓe mata yayin da shi kuma namijin rayuwarsa ta ɓoyayyar duniyar za ta yalwanta ” Kasaƙe na yi ina zancen zuci ‘ kenan so ake duk na disashe taurarin Malama Zainab?’ “Bari ka ji HAROON ,babu abin da sheɗanu suka fi ƙauna irin warin jini musamman na al'ada yana da matuƙar muhimmanci a duniyarmu” “Wane irin sheɗanu kuma?” na tambaya kamar wani gara. Sai da ta sheƙe da dariya kafin ta jefo min tambayar ta saka zuciyata tsananta bugi,“ kai a tunaninka kai mutum ne? Bani amsa kai mutum ne?” shiru na yi na kasa cewa komai. Ta ci gaba da cewa “ ka sani tun ranar da ka kwashe kayanka a gaban Manzo ka fita daga sawun mutane,kai sheɗani ne HAROON !” ta faɗa cikin wani sauti wanda ya saka yanar da ke yaɓe ta ko ina ta soma kaɗawa kamar ana iska. “ Tashi ka bani wuri” ta faɗa cikin fushi,da sauri na ce “ na fita na je ina? Ki yi haƙuri amma ni ban ga abin ɓacin rai ba” ina gama rufe baki ta ja hannuna ta matso ni kusa a nan take madubina da ke can gida ya bayyana a nan. “Wannan ita ce siffar mutum? ?” ta tambaye ni tana nuna ƙwarangwal ɗin da ke cikin madubi ,na girgiza kai na ce “ a'a ba mutum ba ne fatalwa ce” Madubin ne ya ɓace ita kuwa sai ce min ta yi “ ai HAROON gwara fatalwa da kai,saboda kai sheɗani ne na musamman.Wai ma mene ne dalilin Oga na zaɓar ka alhalin ga dukkan alamu baka san muƙamin da ke jiran ka ba?” “Muƙami?” na maimaita. Dōr̃ānī ne ya shigo yana mai cewa “ lokacin komawar ka yayi” haka na bi bayansa muka fita. Sai da ya kai ni wani sashe aka yi min wanka da wasu korayen ruwa sannan na ci na sha kafin yayi min rakiya zuwa bakin ƙofa.Yau ɗin ma kamar kullum haka ƙasa ta dare na fito sai dai fa wani uban canji na ji,jin kaina nake yana hayaƙi yayin da kuma zuciyata nake jin tamkar an yi min musanyar ta,sauran tausayin da ya rage min ya kau a yadda nake ji ko wuyan jinjiri zan iya murɗe wa ya mutu.Ban gama mamakin kaina ba sai da na ga sauran members sun miƙe suna gaishe ni cike da girmamawa,yayin da shi kuma Oga yayi kicin-kicin da fuska haɗi da nuna min wata kujera da aka ƙawata ta da ado.A yau sai na yi wa Oga dubin uba mahaifi wanda kuma ban san dalilin yin haka ba,zuwa na yi na zauna nan ɗin ma wani sabon canji na ji amma dai na yi shiru ina ta nazarin komai daki-daki. “Daga rana irin ta yau na wakilta HAROON matsayin mataimakina wato shugabanku,in ba ni ga wuri shi zai ɗaukar matsayina sannan duk wani hukuncin ƙungiya da za a zarta ko ya shige muku duhu shine zai bada umarnin ƙarshe” Oga na gama faɗa suka shiga taɓa min kafin ya sallame su wurin ya zamana sai mu biyu kawai. “Wannan ɗin duk na mene ne Oga?” na samu dakyar na tambaya. Ya bani amsa da “ tun da aka kafa ƙungiyar nan kai ne na farko da ke iya maida min martani, wannan yasa na baka wannan muƙamin kana iya tafiya” ban sake ce masa komai ba na soma yin tsafin da zai kai ni inda mai kama da ni yake,aka yi katari kuwa yana cikin mota direba na tuƙa shi. Bayyana ta cikin motar yayi daidai da lokacin da direbana ke ƙara saita madubin gaba na mota,yayi ƙara tare da sakin sitiyarin motar sai a lokacin ɗayan ya ɓace saura ni.Na tashi da sauri na tsayar da motar tare da zama gefensa,direba ya dafe zuciya yana kallona kafin da sauri ya maido dubansa gare ni sai na fahimci tabbas ya ganmu mu biyun duka. Na saki murmushi na ce “ shi yasa bin didigi da ganin ƙwaf bai da kyau,duk yawan sa idon bai yi maka ba sai da ka nemo yadda za ka yi ka tantance shin mu biyu ne ko a'a .To ka tuƙa motar nan izuwa wani wurin cin abinci na ga alamun har da yunwa kake ji daga nan sai na aika ka barzahu” “Yalaɓai don Allah ka yi haƙuri!” ya furta tare da ƙoƙarin fita sai dai tuni na ƙargame dukkan ƙofofin yayin da kuma na saka motar ta soma tuƙa kanta da kanta ....... My is only 500 via2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 saura page ɗaya na gama free page in sha Allah. Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ Last free page 10 Ni kaina ban san taƙamaimai ina ne motar za ta je ba,gudu take tamkar aljani ne ke tuƙa ta.Cikin abin da bai wuce minti biyu ba har mun fita daga cikin garin Yamai mun shiga ƙasurgin daji sai a lokacin kuma motar ta tsaya cak tare da buɗe kanta.Na fito zuciyata na sake azalzala banda wani buri baya da na kashe direbana wanda har izuwa yanzu bakinsa bai gushe da bani haƙuri ba.Finciko shi na yi da sauri ya zube kan gwiwansa tare da kama ƙafafuna ya ce “yalaɓai ka yi mini rai ,na yi maka alƙwari zan kasance bafaɗenka mai yi maka hidima.Zan zama tamkar Kare da mai ikonsa,ka yarda da ni zan yi maka duk abin da kake so amma kar ka kashe ni ina da buruka masu tarin yawa da nake son cikawa kafin na bar duniyar nan!” Cikin ƙaraji na ce “ Illiya ka tabbata duk abin da nake so za ka yi shi?” “Eh yalaɓai koma mene ne zan yi” ya amsa mini cikin haƙiƙanin gaskiyarsa. “Za ka zama mataimakina kamar yadda ka ce akwai ayyuka masu tarin yawa da za ka yi min,in ka kuskure kuwa ka sani daidai yake da fitar numfashinka ” “Na gode sosai yalaɓai” ya furta tare da tashi har yanzu jikinsa bai bar rawa ba,haka muka shiga mota na lumshe idona ina jin wani matsayi ya hau kaina saboda na fara samo wa ƙungiyarmu member sannan duk wani wanda ya shigo ta sanadiyar ka to a ƙarƙashin kulawarka yake kamar yadda doka ta tsara. Ko da nake buɗe ido sai na tsinci kanmu a tsakiyar babban titin Yamai,na ɗan saki murmushi na ce “ Illiya na tambaye ka mana” “Eh yalaɓai ina ji tambaye ni” ya faɗa murya na rawa. “Matanka nawa?” “Matata guda yalaɓai da kuma yaronmu ɗaya” ya bani amsa a tsorace. “Zuwa gobe ka kawo min ita a babban ofishina ina son ganinta” na faɗa cike da gadara. “Yalaɓai ai ba ta yi makaranta ba” “Yaushe na ce ma zan ɗauke ta aiki ?” na yi masa tambayar a tsawace. Ya ce “ka yi haƙuri yalaɓai” Na juyar da kai ina kallon titi har muka isa gida,ina fita sai da na tsaya ina ƙarewa Illiya kallo gajere ne shi baƙi yana da ƴar ƙiba amma ba sosai ba,idonsa irin na munafukan mutanen nan ne masu son sanin sirrin wani. “Yalaɓai na faɗa ma zan yi duk abin da ka ce,ka yarda da ni ” ya faɗa cikin tsoro,na shafi sajena kafin na ce “in ma ba ka yi ba ai ka san meke jiran ka! Sannan duk faɗin duniyar nan ba za ka taɓa ɓoye min zan lalubo ka” ina gama faɗa na wuce ciki. Yau Ammy ba ta falo ban kuma nemi na san inda take ba kawai na shige ɗakina,wanka na soma yi kafin na fito ɗaure da towel.Kai tsaye kusan madubina na je na tsaya,ina son sanin abubuwa da dama game da MAFIYA wacce a yanzu garɗinta nake ji.Kamar wanda zai shiga ɗaki haka na yi na ratsa ta cikin madubin na shiga ciki,yau ɗin ma kamar waccan lokacin yanayin duniyar hazo-hazo ce sai dai hakan bai hana ni ganin abin cikinta ba.Wani aji na gani inda aka rubuta “TSAFI DA MATSAFI” babu wani tunani ai kuwa na je na tsaya sai na ga wata malama a tsaye tana koyawa wasu karatu,ba tare da neman izini ba na je na zauna ina kallon darasin . Tana gamawa kuma sai ga wani shi ma malamin ya bayyana kamar daga sama,kamar wani rediyo kuma ya soma yin magana. “Sannu Matsafana da kuma Mayuna!A yau za mu gano abokiyar sufi da muka fi so wato: cat da turanci,wacce a Hausa za mu kirata da mage ko kuma ƙuliya.Wannan halitta ko da yaushe tana da alaƙa da sihiri da mayu.Za ku ga a gidajen Mayu,matsafa ko malaman tsibo suna ƙawata shi da mage ko kuma ƙuliyoyi wanda normal mutum zai ɗauka iya soyayya ce kawai amma yanzu zan muku gwanjon sirrikan.Bari mu fara da labarin da zai burge ku!” sai ya tsaya da magana tare da soma yin rubuta a ƙaton allon da ke cikin ajin. # Cat da Bokaye: Tsohuwar ajiya a cikin kundin Labari na ƙarni biyu. Shine abin da ya rubuta kafin ya soma yi mana bayani dalla-dalla. “Tsawon ƙarnoni, ƙuliyoyi sun kasance abokan bokaye. Masarawa sun bauta musu a matsayin alloli. Indonesiya sun yi imanin cewa ƙuliyoyi na iya gani fiye da mayafi. A takaice, abokanmu na sirri sun fi dabbobi kawai. Abu na gaba shine : # Ikon Sufanci na Mage A naku hange me yasa mayu suke son kyanwa sosai? ” Mr Zulu na kawowa nan sai ya tsaya yana tambayar mu,wato ya bamu damar tsoma baki a ciki kamar yadda malaman makaranta ke yi. “ HAROON ko za ka faɗa mana dalili?” ya jefo min tambayar,duk sai hankalin kowa ya dawo kaina. Na ce “Domin suna da ƙarfin ikon sihiri” Yayi alama da babban yatsansa irin na jinjina kafin ya ce “ba shakka! HAROON yayi gaskiya a cikin halittun da duniyar Ruhaniya ta aminta da su mage nada kaso casa'in na ƙarfin tsafi yayin da sauran halittun kuma nada ƙarancin rinjayen.Daga cikin quality ɗin mage akwai: * Hankali, Cats suna jin kuzari da ruhohi mara kyau. Mafi dacewa don kiyaye gidanku.Ma'ana a duk lokacin da wani mummunan abu zai faru cikin gida mage tana sani kuma za ta iya kare mamallakinta daga wata cutar wa ita abin ya same ta. * Kariya :suna tunkuɗe mugayen ruhohi da munanan kuzari.Daga lokacin da mugu ya shigo gida zai ji ya kasa zama a ciki saboda wanzuwar ƙuliyar. * Warkarwa : Tsaftace su yana da tasirin warkewa, cikakke don rage damuwa.In mutum na cikin wata damuwa ta dalilin yadda yake mu'amulantar magensa zai iya samun sauƙi daga abin da ya shige masa. Sannan ku sani bayan wannan ɗin akwai wani ɓoyayyen sirri a tattare da kowacce mage.Abu na gaba da nake son ku sani shine TASIRIN LAUNI,kowacce mage da kuke gani da nata tasirin sannan ba haka kawai ake mallarkarsu ba sai an cika sharuɗa.Amma kafin nan bari na sanar da ku tasirin kowacce daga cikinsu. Kowane launin yana da ma'anarsa ta sihiri da tsafi. _Baƙar fata: Yana nuna kariya da sihiri. Saɓanin camfi suna kawo sa'a. _Fara: Yana wakiltar tsarki da waraka. _Grey: Yana jawo hikima da hankali. _Ja: Yana jan hankalin sa'a da kuzari. _Tiger: Yana wakiltar sassauci da daidaitawa, cikakke don lokutan canji. Zan tsaya a nan sai wani lokaci ” Mr Zulu ya faɗa tare da yin ɓaton dabo.Ina zaune dai cikin mamakin wannan lamari sai ga kuma wani tsoho shi ma ya shigo ajin tare da rakiyar dog.Na gyara zama don jin wane darasi ya zo mana da shi kawai na tsinkayo murya Ammy na faman kiran sunana,a dole na tashi na fito abun mamaki har yanzu jikina na ɗigar da ruwa kamar yanzu ne na fito daga toilet. Ƙofar na buɗe ina ƙirƙiro murmushi na ce “ Barka da maraice Ammy!” Ta dube ni da kyau kafin ta ce “ HAROON wai meke damunka ne? Ka dawo daga aiki amma ba za ka zo ka gaishe ni ba? ” “Yi haƙuri Ammy na gaji ne sosai,kaina kamar zai tsage haka nake ji shi yasa na soma yin wanka.Amma kina zuciyata ” na yi ƙaryar ciwon kai saboda shi ne abin da ke sa hankalin Ammy gusashe wa a duk lokacin da ta kama ni da wani laifi ni kuma ina gudun ta yi min faɗa . “Tun yaushe ka fara jin ciwon kan?” ta faɗa hankali tashe,na ce “ bai wuce minti goma” ba ta ce komai ba da sauri ta fita sai kuma ta dawo da ruwan ƙanƙara da towel,kamar ƙaramin yaro haka ta zaunar da ni ta soma yi min tausar kai har sai da na ce mata ya daina na bar ji.Wata irin wawuyar ajiyar zuciya ta sauke wacce har sai da na ɗora ayar zargi da tambaya na ce “ Ammy me yasa hankalinki ke tashi in nace kaina na yi min ciwo?” Ɗan daburcewa ta yi kafin ta ce “ ka saka kaya ka sauko ƙasa na yi maka girki mai daɗi” tana gama faɗa ta fice,na bi ta da kallo ina cewa “ tabbas akwai wani ɓoyayyen sirri da Ammy take ɓoye min” haka na miƙe na kimtsa sannan na sauka zuwa ƙasa. Ammy ta zuba min abinci amma na kasa ci,ta zauna kusa da ni tare da soma bani a baki tana mai cewa “ zama da yunwa bai da kyau yana haifar da cutar olser,ka yi niyya ka yi aure HAROON ko hankalina zai kwanta na san matarka za ta kula da kai” ban ce mata komai ba sai murmushi. Da sauri na juya bayana jin kukan mage yau a gidanmu ,magen fara ce sol ko tabo ɗaya ba tada kuma dumul-dumul da ita kana gani ka san ba ta da yunwa. “Ammy ina kika samu mage?” na yi tambayar ina kallon magen sam na kasa ɗauke idona a kanta . “Ka jira yanzu mai ita ta shigo ” cewar Ammy tana dariya,babu jimawa kuwa sai ga wata kyakkyawar budurwa fara tas da ita har da wani ƙaton baƙi a goshinta na sallah .Sallama ɗauke da bakinta sannan kuma ta gaishe da Ammy,kafin ta soma kiran sunan magen “ Mira! Mira! Zo mana” kamar uwa da ƴa haka magen ta je da gudu wurinta,ita kuma ta duƙa ta ɗauke ta kafin ta zo ta miƙawa Ammy key ta ce “ ga shi in Mama ta zo ki bata ni zan koma makaranta” Ammy ta karɓa ita kuma ta fita,da sauri na yi jarumtar tattara nutsuwata na share zancen magen na ci abinci. Kiran sallar magrib aka soma,“ HAROON je ka yi alwala ka wuce masjid ni zan shiga daga ciki” cewar Ammy,a dole na amsa mata da “ toh” sai kuma na fita can harabar gidan. Da hannu na yi wa Illiya alama da ya zo,da sauri ya ajiye butar da yake alwala ya zo jikinsa na rawa .“ Ga ni yalaɓai” “Yarinyar nan da ta fita yanzu Mai mage wace ce ? Ka san ta ne?” na tambaye shi . Ya ce “ Eh yalaɓai Salima ce ƴar gidan Yakubu soja tana karatu a babbar jami'a ne” “Ina son ta ne,ka san yadda za ka yi ta yarda da hakan” na faɗa kai tsaye. “Amma yalaɓai Malama Zainab fa?” Har sai da ƙarar rawar zuciyata ta motsa jin an ambaci sunanta,na saki wani murmushi na farin ciki kafin na ce “ ita wannan ta musamman ce” sai kuma na bar shi nan na koma ciki. ILLIYA POV Bin bayan HAROON kawai yayi da kallo yana mamakin wane irin rikitacen mutum ne shi,a haka ya koma yayi alwala ya je masallaci.Har aka yi sallar isha'i yana ta tunanin hanyoyin da zai bi ɗin ya sanar da Salima,da kuma ya tuna zancen Yalaɓai na ya kai masa matarsa gobe sai hankalinsa ya ƙara tashi.Haka dai ya samu ya fito daga masjid ɗin ya je bakin hanya ya samu taxi ta kai shi can gidansa,yau ko motar bai tafi da ita gida ba kamar yadda ya saba. Yana shiga kuwa ɗansa Abdul ya rugo yana tara masa hannu,sam ya manta bai shigo da komai ba kamar yadda ya saba musu ba.”Yi haƙuri Abdul na manta ban sayo ba ka bari har zuwa gobe” yana gama faɗa yaron ya fashe da kuka,hakan ya jawo hankalin matarsa Mariya ta fito tana kallon mijinta ta fahimci ba ƙalau ba,gaisuwar da ta yi masa ma dakyar ya amsa. Ruwan wanka ta kai masa,haka ya je yayi ya fito ya zo ya shige can uwar ɗaka ya rabka uban tagumi. “Baban Abdul” ta faɗa cikin Hausarta da ba ta dafu ba. Ya zabura ya ɗago ya dube ta,sai kuma ya haɗe rai ya ce “ lafiya kike wani kirana haka?” “Kai dai zan tambaya lafiya duk ka bi ka sauya haka?” “Mariya haka ya dace a tarbi miji in yana cikin damuwa? Ko abinci fa ba ki bani ba” ya faɗa wannan karon ya sassauta murya.Ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ ka yi haƙuri bari na kawo ma” sai ta fita ta je ta kawo masa.Ya ce “ ina Abdul?” “Ya gaji da kuka har yayi bacci ” ta basa amsa tare da zuba masa abinci a plate ya karɓa ya soma ci yana ƙare mata kallo,bafulatana ce ita kyakkyawa ba ta da ƙiba hakan yasa ƙirjinta har yanzu a cike suke kuma tsaye daram . “Lafiya kake ta ƙare min kallo kamar yau ka fara gani na?” “Kin san ke ɗin ce kullum kyau kike ƙarawa” ya faɗa tare da kashe mata ido ɗaya yana murmushi,ita ma dai ta ɗan saki ranta ta soma yi masa surutunta da wannan ta ɗan sassauta zuciyar Illiya har suka yi bacci,amma tsakar dare ya tashi a firgice saboda mummunan mafarkin da yayi.Sam kasa komawa yayi sai yayi zaune yana ta saƙa da warwara har garin Allah ya waye,suna tsaka da cin abinci kiran HAROON ya shigo wayarsa,gabansa ya faɗi rasss haka yayi ta kallon kiran har ya yanke wani ya sake shigowa amma shi ma ya ƙi ɗauka sai ana uku ne yayi ƙarfin halin tashi ya fita can tsakar gida sannan ya ɗaga idonsa na kawo ruwa ya ce “ yalaɓai ina zuwa yanzu nan zan kawo ta” yana gama faɗa kuma aka kashe kiran daga can ɓangaren.Illiya ya goge ƙwalla kafin ya dawo ɗaki,Mariya ta kafe shi da ido sai dai bai bata damar yin magana ba ya ce “ Ogana ne bai da lafiya yanzu nan aka kira ni,tashi ki saka hijabinki mu wuce” Ganin yadda mijin nata ya shiga tashin hankali yasa ta bi umaninsa kawai,Abdul ta kimtsa ta goya shi sannan suka fito bakin titi ya tsayar musu da taxi ya faɗa masa sunan babban kamfanin da za su je. HAROON Da abu uku na kwana daren jiya,na farko soyayya da ƙaunar Malama Zainab,na biyu kuma son mallakar magen Salima,na uku kuwa shine son ganin matar Illiya . Wannan yasa gari na wayewa na yi wanka na shirya,shayin Ammy kawai na sha kafin na fito sai kuma na tarar Illiya bai zo ba na yi tunanin don kar ya cika umarnina ne ya ƙi zuwa wannan yasa na soma jera masa kira domin yi masa gargaɗi sai kuma ga shi ya bani tabbacin zai kai ta. Ɗaki na koma na ɗauko key na mota,da kaina na yi draving na isa can kamfanina.Ko sauraren gaisuwar mutane ban tsaya ba na shige ciki,babu jimawa kuwa sai ga Illiya ya shigo shi da matarsa wacce idonta ƙurrr a kaina masu cike da mamaki da tambayoyi. Kujeru na nuna musu ,ta kwance goyonta kafin ta zauna shi kuwa Illiya ya ma kasa zama da alamu jira yake ya ji dalilin zuwan nasu. Rigar rashin mutumci na sake yaɓawa kaina kafin na ce “ Illiya karɓi yaron nan ku fita waje ina son yin magana da ita” jikinsa na rawa ya ɗauki yaron da tun da muka haɗa ido da shi ya soma kuka,Illiya ya je bakin ƙofa ya waiwayo yana kallona na banka masa harara da sauri ya fice ina mai ganin ƙwalla na zubo masa. Daga inda nake zaune na baiwa ƙofar umarnin rufewa,da sauri ita matar Illiyan ta juya tana kallon yadda key ke murɗa kansa handle kuma na motsi.Tana juyowa ta gan ni a zaune kan table gabanta har ƙafafuwanmu na gugar na juna,cikin ido na dube ta na ce “ ki cire hijabinki” Idonta ya kawo ruwa amma na san tabbas ba za ta iya musa min ba,haka ta cire shi nan na yi arba da siffarta mai ɗaukar hankali.Rabon da na yi mu'amala da mace har na manta, wannan yasa jikina ya ɗau rawa har ban san lokacin da na kai hannuna na zuge zip ɗin rigarta ba.Nan na yi arba da ainahin surarta,hawayenta da suke ɗiga sam ba su dame ni ba haka na yi mata sintiri ina shafar dukkan sassan jikinta.Daf da zan cimma burina na ƙarshe na ji sautin muryarta mai kamar tafasasshen ruwa,cak na tsaya ina sauraren amon muryarta wanda kuka ya gurɓata shi “ ka sani ni ma mace ce mai daraja kamar uwar da ta haife ka! Yadda baka son wani ya keta mutumcinta haka ni ma yarona da ke can waje yana kuka bai son a keta nawa” da sauri na yi baya ina dafe zuciyata ina kallonta ta soma mayar da kayan jikinta.Daidai nan na gama page na kyauta mai so sai ya biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 .Kawai ki tura in na zo zan saka ki group,wacce ta san ba biya za ta yi ba ta yi wa girman Allah kar ki yi min magana. Littafin MAFIYA labari ne ya cakuɗe da true life da kuma wanda na ƙirƙirar,sannan wannan duk shimfida ce ba mu ma shiga cikin zallar labarin ba. Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 11 Tun da nake babu wata ƴa mace da na taɓa rabawa da kayanta kuma ban kusance ta ba sai wannan.Har ta kai bakin ƙofa na dakatar da ita “ keee!” ta wani juyo a firgice jikinta na rawa,idona na kafe ta da su ina son sanin ko tana ɗauke da wani sirri ne na daban amma ban gansa ba.Na dafe goshina cike da takaici kafin na kwashi kayana na shige Toilet,gaban shower na je na tsaya na buɗe shi duka ruwan na soma sauka a kaina tsohuwar rayuwata ta baya ta fara zuwar min kamar wanda aka kunna wa video. Wannan labari yana ɗaya daga cikin mafi ruɗani da na samu. Yana da gami da madubi. Ba wai kawai kowane madubi ba, amma ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da ake ganin suna ɗaukar wani abu fiye da kawai tunaninsu. A ƴan shekarun da suka gabata, na ci karo da wata kasuwar kayan gargajiya a wani gari da nake wucewa.Kasancewar ni ɗin direban babbar mota ne,ina son yawo a cikin waɗannan wuraren koyaushe suna samun abubuwa masu ban sha'awa tare da labari. Ina zagawa wani tsohon madubi ya kama idona tamkar mayen ƙarfe. Yana da ban sha'awa, tare da firam ɗin katako da aka sassaƙa, an ƙawata shi da ƙira. Wani katon madubi ne, kusan girmansa kamar ƙofa, ga fuska kamar ya ɗan dusashe da shekaru. Dillalin kayan tarihi ya gaya mani cewa wannan madubin ya fito ne daga wani tsohon gidan da aka yi watsi da shi kuma ya kasance a wurin shekaru da yawa, ba tare da wani ya so ya saya ba. Ya ce wasu mutane in sun ga wannan madubin suna cewa “yana tattare da damuwa” ba tare da sun iya bayyana dalilin da ya sa ba. Tabbas, a matsayina na mai son abubuwan bazata da na ban mamaki sai na yanke shawarar saya. Na kai shi gida da tunanin zai dace da duniyata. Tun daga ranar farko da na rataye shi, na ji wani abu mai ban mamaki. A duk lokacin da na wuce nakan ji kamar tunanina yana kallona ta wata hanya mai ban mamaki. Ba kamar wani tunani mai sauƙi ba, amma kamar wani sigar ni a cikin madubi yana kallona ta baya, ko da kuwa bayan na kawar da kaina. Da farko na ɗauke shi a matsayin gajiya ce da na yi, tunanina kawai hankalina ne ke wasa da ni. Amma da yawan kwanakin da suka wuce, wannan jin yana ƙara tsanantawa. Abin da ya fara damuna da gaske shine lokacin da na lura cewa tunanina yana motsawa. Wata rana da yamma, ina wucewa gaban madubin , sai na ga tunanina ya ɗan juya kaina kafin in yi haka. Tsawon daƙiƙa ne kawai, amma a fili yake. Har na yi gwaji, ta wurin tsayawa a gaban madubi ina motsi a hankali. A wani lokaci, tunanina ya lummm a gabana ya kasance da dabara irin ya ɗan jinkirta abin da na yi . Na fara firgita sosai, amma na gaya wa kaina tabbas tunanina ne. A daren nan na yi bacci a kan kujerar falo, kuma madubin yana can hangen nesa na. Da tsakar dare na tashi ba zato ba tsammani, sai na ji wani yana kallona lokacin da na buɗe idona, sai na ga inuwa a bayana a cikin madubi, kamar a mafarki amma gaske ne. Na juyo ba zato ba tsammani sai dai ba komai babu kowa a cikin ɗakin .Zuciyata ta fara bugawa ba zato ba tsammani na sake duba madubin, kuma wannan lokacin ya fi muni,inuwar ba ta da kyau, yana can a cikin tunanina can tsakiyar madubi amma ba a cikin ɗakin ba. Ita wannan inuwar irin siffata ce da ita amma jikinta duk ko ta ina jini ne ke fita,yadda na ƙure ta da ido ita ma haka take kallona babu motsi. A yadda ake son na fahimta wannan na cikin madubi ni ne da kaina kamar yadda kowanne mutum in ya tsaya a gaban madubi zai ga kansa,amma ni nawa ya sha banban da na sauran.In na yi motsi shi na cikin madubin bai motsa wa yana nan a daskare kamar saƙaƙo,in kuma ni na tsaya ɗam ba tare da na yi wata alamar motsi ba sai na ga shi ya motsa. A firgice na bar ɗakin a wannan ranar ban dawo ba sai da safe. Washegari, na yanke shawara mai tsauri. Na rufe madubin da farar ƙatuwar zanen gado. Tun daga wannan lokacin, ya kasance a can a ɓoye. Amma kuwa duk da na rufe shi har yanzu ina jin kasancewarsa. Wani lokaci ina tsammanin ina jin ƙararrakin hayaniya suna fitowa daga wajensa kamar surutu da sautin faɗuwar wani abu kamar tasa ko kuma an cilla dutse a rijiya. Kamar wanda aka yi wa dole haka kuma na ƙi fitar da madubin,na ci gaba da rayuwa da shi har wata baƙar rana ta zo wacce ba zan manta ba.Ina kwance ina baccin bayan la'asar aka kira ni a waya Ammyna ta zame jiki ta faɗi babu hannu babu ƙafa ga kuma zuciyarta ta kumbura.Ko wanke fuska ban yi ba na ɗauki makullin mota,a ƙa'ida sai jibi zan yi jigilar dabbobi kamar yadda tsarin yake in na zo asabar sai kuma ranar Laraba zan koma can gida Agadas.Kwana ɗaya da wuni na yi a hanya kafin na isa,direct kuma asibitin da aka sanar da ni take na nufa,a yadda na tarar an banzatar da Ammyna sai na ji takaici ya rufe ni don babu wata kulawa ta musamman tsabar wulaƙanci ma kan tabarma take ba a gado ba. Ba ta iya yin magana ,bakinta ya juye yawu na yi mata dalala,motsin kirki ma ta iyawa sai idonta da ta kafe ni da su masu cike da rauni da neman agaji a gare ni. A wancan lokacin da na tambayi nurse dalilin ƙin bai wa mahaifiyata taimako yadda ya kamata sai ce min ta yi “ sai kun biya kuɗi na gwaje-gwaje,na gado,da kuma alluran da za a dinga yi mata tausar ƙafarta da ta sandare ” ƴan kuɗaɗen da na samu waɗanda sun kasance na uban gidana ne da su na yi amfani na bayar aka ba Ammy gado ,sannan da taimakon da ba a rasa ba.Dandanan goshinta ya fara fitar da zufa sai bacci,ganin haka sai yasa na wuce can gidanmu domin yin wanka.Mahaifina na tarar wanda shine silar duk halin da Ammy ke ciki,kayan jikinsa na tarar yana haɗawa da alamu garin zai bari. Ina kawo daidai nan na kashe shower saboda a duk lokacin da nake tuna rayuwata babu gaɓar da na tsana irin ta Abbana.Cike da takaici na kimtsa na fito na zauna kan kujera,ina jin tabbas ya zama dole na mallaki matar Illia direbana. ILLIA POV Babu wani tashin hankali da ya taɓa shiga wanda ya wuce wannan,babban takaici ne yau ace ya miƙar matarsa ta aure ga wani namijin da yayi imanin cewa imani bai wanzu a ƙirjinsa ba ballantana ya sa ran ba zai keta haddinta ba. Kamar wani marayan uwa da uba haka ya takure jikin katanga ya rungume Abdul gam a ƙirjinsa wanda tuni ya gaji da kuka yayi bacci,ido kawai Illiya ya ƙura wa ofis ɗin HAROON tunani iri-iri na ta zuwar masa .Ya san halin Mariya da tsoro tun a tashin farko za ta sallama kanta ko da kuwa bai yi amfani da tsafinsa ba.Yana nan jibge kamar kayan wanki ya ga ta buɗo ƙofa ta fito,da sauri ya nufe ta yana cewa “ me yayi miki?” ba ta basa amsa ba ta karɓe ɗanta ta yi gaba.Ya take mata baya yana kiranta,duk mutane na kallonsu amma ta ƙi tsayawa haka suka dinga yin tafiyar ƙasa su biyu har suka isa gidansu duk da kuwa uban nisan da ke da kwai. “ Mariya mene ne haka? Ina tambayar ki amma kin yi shiru” Illiya ya faɗa bayan sun shiga ɗaki. Ta dube shi da idonta da suka yi jajur tsabar kuka ta ce “ abin da ka kai ni dominsa shi yayi! Wato Illiya ban taɓa sanin cewa baka ƙauna ta ba sai yau amma ka sani wallahi na gama aurenka!” sai kuma ta wuce can uwar ɗaka ta soma haɗa kayanta. Shi kuwa zaman ƴan bori yayi jin HAROON wai kusance ta,kukan baƙin ciki ya soma yi kamar ransa zai fita yana da kishi sosai amma yau yana ji yana gani an ɗauki abunsa mafi daraja an tozarta shi .Wata irin tsanar HAROON ce ya ji ta ɗarsu a ransa,ya ƙudiri aniyar zai yi masa aiki amma kuma tabbas shine ajalinsa...... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 12 Cike da takaicin Illiya da matarsa na dawo gida,ina shigowa da sanyi idaniyata na fara cin karo wato Malama Zainab.Cak na tsaya a bakin ƙofa jin zazzaƙar muryarta na fitar da sautin karatun Alqur'ani wanda ya zama barazana ga ruhina,ji nake tamkar an watsa mini ruwan zafi. Tamkar Ammy ta san halin da nake ciki ta dakatar da ita da karatun ,“ Malama gobe in sha Allah mu ci gaba ga HAROON nan ya dawo,ƙaraso ku gaisa ” Ammy ta faɗa tana murmushi,sai da na je na ɗauki gorar ruwa mai sanyi na sha sannan na ƙarasa wurin su. Ammy na fara gaishe wa kafin na zuba wa malamar ido,ta ɗago a hankali ta ce “ ya ƙarfin jikin?” “Ai na ji sauƙi” na bata amsa ina mai ci gaba da kallonta,da dukkan alamu kuma ta tsargu da hakan don sai wani takure jikinta take. “Ka zauna bari na kawo ma wani abu” Ammy ta faɗa tare da nufar kitchen,nesa da Malama na zauna ina son tantance ta amma sam babu wata ƙofar tauraronta da ke buɗe wacce za ta bani damar ganin sirrin ruhinta. Na ja ajiyar zuciya na ce “ ya aka yi yau kuka fara karatu da wuri haka?” Kamar mai tsoron magana ta ce “ ina da wani aiki mai muhimmancin ne bayan sallar magrib ɗin” “Mene ne shi?” Sai da ta ɗan ƙara sunne kai kafin ta ce “ dama... Dama wanda aka yi mana baiko ne ya d...” sauran maganar ƙarar fashewar gilas ta maƙale ta. Ammy ce ta yi ɓarin lemun zoɓo,hankali tashe kuma ta bi ta cikin kwalbar tana mai cewa “ an miki baiko?” “Eh tun shekaru uku da suka wuce ni da Sheikh Ali,ba ki dai ji ciwo ba ko Ammy?” ta ƙarashe da tambayar Ammy wacce ta zuba min ido,ƙila mamakin ganin ban wani razana sosai ba ko na tayar da hankali. “Allah sa alkhairi,je ki direba ya mayar da ke” Ammy ta faɗa tare da zubewa kan kujera yayin da ita kuma Malama Zainab ta fice.A hankali na tashi na tsuguna a gaban Ammy na kamo ƙafarta da ke zubar da jini.Kwalbar na cire sannan na ɗauko ɗan akwatin da ke da kayan magani na shafa mata tare da naɗe ƙafar da bandeji. “ Ka kuwa ji abin da Malama Zainab ta faɗa ?” “Eh Ammy na ji” “Shine kuma baka ce komai ba?” “Ammy a kullum fa ke ce da kanki kike min nasihar cewa duk wanda ya yarda da Allah to komai nasa zai zo da sauƙi,kin ga kar ki damu Malama ba ta da wani miji da ya wuce HAROON zan je har gidan nasu na fallasa mata sirrin zuciyata ” Ammy ta shafi sumar kaina tana wani ɗan murmushi kafin ta ce “ haka take yarona” na miƙe tare da sakar mata murmushi sai kuma na nufi step,a cikin kwanyata na soma jin ana yi min magana “ HAROON lokaci yayi da za ka fara amfani da powerka domin sato taurarin mutanen kirki,ta wannan hanyar ce zaka samu Malama Zainab ” Kamar wani zararre na tambayi kwanyar tawa “ ta ya kenan zan soma?” “Je ka fara yin wanka tukunna,sai ka je madubinka zai sanar da kai” Haka kuwa aka yi,bayan na yi wanka na je na shiga cikin madubina.Direct ajin nan da ake koyar da karatu na shiga,yau ma Mr Zulu ne ke darasi akan allo yayi zanen baƙar mage mai jajayen ido yana kuma yin bayani. “Baƙar mage , waɗanda galibi ana lulluɓe su cikin sirri da camfi, koyaushe halittu ne masu ban sha'awa, musamman a duniyar mayu da ayyukan sihiri. Baƙar mage a zahiri suna ɗaukar kuzari mai zurfi, kariya da sihiri. A cikin wasu al'adun arna da sihiri, ana ganin baƙar fatar mage a matsayin mai kula tsakanin talikai, mai tsaro na ruhaniya. Ya ƙunshi ma'auni tsakanin haske da inuwa, bayyane da ganuwa. Wataƙila wannan duality ne ya sa bokaye da matsafa suka zaɓi baƙar mage tamkar abokan hulɗa masu mahimmanci a cikin aikin sihiri. Suna kawo hikimar dare da ikon kewaya wuraren ruhi na ɓoye. A cikin gogewar kaina, baƙaƙen ƙuliyoyi sun kasance sau da yawa jagororina da masu kare ni a lokutan canji ko haɓakar ruhaniya. Suna tunatar da ni cewa inuwa ba abin tsoro ba ne, amma illa fahimta. Suna ɗauke da sihiri mai hankali amma mai ƙarfi a cikin su, ƙarfin canzawa wanda ke ingiza mu mu wuce fiye da kamanni don rungumar ɗaukacin halittarmu. Baƙar ƙuliya kuma alamun sa'a ne a wasu al'adu, suna kawo albarka da kariya ga waɗanda ke maraba da su cikin gidajensu. Kasancewarsu na iya zama abin tunatarwa akai-akai game da sihirin da ke kewaye da mu, yana ƙarfafa mu mu kasance a buɗe kuma mu yi maraba da mutane wanɗada ba mu sani ba da gaba gaɗi. Shin kun taɓa haɗuwa da su a cikin ayyukanku ko rayuwar ku ta yau da kullun? Menene ma'anar waɗannan sahabbai masu ban mamaki a gare ku? ” Hannu na ɗaga hakan yasa ya ce “ ina jin ka HAROON ” Na ce “ ta ya za a yi mutum ya mallaki ita baƙar magen? Sannan mutum ɗaya zai iya ɗaukar ƙuliyoyi biyu a lokaci guda don yin aiki da su ko kuwa sai ƙwaya ɗaya kawai aka yarje masa?” Mr Zulu ya bani amsa da “ a'a in kana so duk launinkan ƙuliyoyin da muka lissafa zaka iya aiki da su muddin dai zaka iya ciyar da su.Bari na faɗa muku wani sirrin iya ƙuliyoyinka iya ƙarfin tasirin alƙalumanka,mai son baƙar mage ina da su da yawa na sayarwa ga su nan na kawo” ya faɗa tare da buɗe wani tsohon akwatin ƙarfe .Cike yake da jariran baƙaƙen ƙuliyoyi duk idonsu kuma jajur suke ,nan fa duk kowa ya soma cewa yana so ganin kamar za su ƙare yasa da sauri ni ma na isa gaban akwatin don zaɓar tawa.Akwai ƙwaya ɗaya wacce ta banbanta da sauran ta fi su girma haka yanayin fuskarta ma kicin-kicin yake babu fara'a. “Wannan nake so” na furta tare da kai hannu na ciro ta,Mr Zulu yayi min kallo kafin ya ce “ HAROON ka tabbata ?” Ba tare da tambayar dalilin da yasa sai ni kaɗai ya yi wa tambayar ba na ce “ eh yalaɓai ita nake so ” ya saki ɗan murmushi kafin ya ce “ shi yasa Oganku ya ce kai ɗin na musamman ne taurarinka masu matuƙar ƙarfi ne” ni ma murmushin kawai na sakar masa,magen hannuna ta yi wani zillo ta ruga da sauri na take mata baya kawai sai na tsinci kanmu a wajen madubi a tsakiyar ɗakina. Da ido nake kallon magen wacce ta haye bed ɗina ta yi min ƙuri da ido,da sauri na nufe ta na ɗauko ta na rungume.Sai yanzu na lura ashe namiji ne muzuru,kansa na soma shafawa na ce “ daga yau sunanka Tony” daga bakin ƙofa aka soma buga wa tare da kiran sunana “ na'am Ammy gani nan zuwa” na furta tare da tashi na buɗe mata,da faɗa ta soma “ HAROON me yasa kake son zama da towel,to in ka shirya ka fito ina son ganin ka” har za ta tafi sai kuma ta yi saurin juyowa tana kallon gadona,sai na kai dubana na ce “ Tony ne fa” “Yaushe ka fara son ƙuliya ban sani ba?” “Na sosa ƴar ƙeya kafin na ce zan yi miki bayani daga baya” Ta fice,ni kuma na rufe ɗakin.A tsanake na shirya na ɗauki Tony muka sauka ƙasa sai wani kuka yake “minyau!” Ammy ta ce “ Laure zuba ma magen nan abinci ƙila yunwa take ji,kawai haka nan ka kama ka rufe ta a ɗaki” Tony ya wani zille ya bi Laure mai aiki can kitchen,wani tsohon plate ta samu ta zuba masa abinci tana masifa ƙasa-ƙasa “kawai don mugun hali ka rasa magen da za ka kawo cikin gida sai baƙa mtsww!” ta ja tsuki,ƙafa ta sa ta bugi Tony ya tsaya yana kallonta “ ni bari kallona shegiya da wasu ido nata kamar mayya” sai kuma ta fito. Na dube ta na ce “ kin zuba masa abincin?” yau ne karon farko da na taɓa yi mata magana saboda ni da ƴan aikin gidanmu gaisuwa ce ke haɗa mu ita ma sai na ga dama na amsa. “Eh ga ta can tana ci” ta bani amsa. Na ce “ namiji ne ba mace ba,sunansa Tony ” “Sai kace dai wani mutum yalaɓai ai duk ƙuliya da sunan mace ake kiranta” Laure ta faɗa cike da jin haushi tana mai ɗaukar kwanon abincinta ta kama hanyar fita tana gunguni ƙasa-ƙasa sarai kuma kwanyata ta sanar da ni abin da ta ce. “Tun da baƙin hali gare mu don muna da kuɗi da kuma jiji da kai ki je an sallame ki daga aikin” na faɗa cikin ɗaga murya,da wani mugun sauri ta juyo tana kallona kafin ta zo da gudu ta zube a gabana tana bani haƙuri,tsakiyar idonta kawai na kalla na fahimci Laure irin mutanen nan ne waɗanda akan kuɗi babu abin da ba za su iya yi ba,sannan tuni hassada da baƙin ciki sun gama gurɓata ruhinta.Jin daɗina guda da Ammy ta gusa ba ta falon,na saki makirin murmushi na ce “ zan maido ki aiki zan kuma ƙara miki da wani wanda ya fi wannan albashi na san za ki iya ” Ai kuwa ta washe baki tana cewa “ sosai yalaɓai in dai zaka bani kuɗi” Na ce “ yawwa yarinyar nan Salima ƴar gidan Yakubu soja kin san ta ne?” Ta ƙara washe baki ta ce “ Salima mai mage ko? Ai har gidansu Hajiya ke aikina” “Yawwa a kanta nake son baki aiki” “Koma mene ne zan yi Alhaji in dai zaka bani kuɗi” “Ok za ki iya tafiya,gobe zan faɗa miki bayanin aikin naki ” ta miƙe ta tafi da ƙarfin gwiwarta,sai lokacin kuma Tony ya fito daga kitchen yayi tsalle ya ɗare kan cinyata na soma shafa bayansa ina jin wani irin daɗi na mamaye ni. Ina nan zaune sai ga Illiya ya shigo fuskarsa kawai na kalla na fahimci damuwarsa,ya zo ya gaishe ni tare da zama kan capet idonsa suka fara tsiyaya. “Ai zata dawo ba za ta iya barin ka ba,sai dai ka sani ban janye ƙudirina ba ya zama dole na ɗanɗani zumarta” na furta ina cije leɓena na ƙasa. Da sauri Illiya ya ɗago yana cewa “ yalaɓai dama baka kusance ta ba?” Na kawar da kai gefe ina kallon cikin idon Tony da nake tsintar wasu abubuwa a ciki. “Yalaɓai wannan muzurun fa?” Illiya ya jefo min tambayar da tasa na maido dubana gare shi na ce “ faɗa min Illiya ta ya aka yi a kallo ɗaya har ka san muzuru ne? Kana da wankin ido ne ko yaya?” Ya ɗan washe baki ya ce “ yalaɓai lokacin baya fa na ɗan taɓa aikin tsibo sai kuma na bari saboda kusan haukata ni jinnu suka yi” “Ita ma matar taka da tsafi ka aure ta kenan?” “A'a wallahi auren soyayya ne ko rubutu ban taɓa bata ba” “Ya ake samun costumer Illiya ? Ina nufin malaman tsibo ta wace hanya ce za su bi domin ganin sun samu mutane da yawa?” “Ta hanyar shiga gidan rediyo da tv,ka yi musu alƙawarin aiki kyauta ne sai buƙata ta biya sannan mutum sai bayar da abin sadaka” Na saki murmushi na ce “ to ka shirya min zama da manyan ƴan jaridu da kuma wasu mutanen da za su bayar da shaidun ƙarya akan na yi musu aiki ya ci sun zo godiya” Ya saki baki yana kallona kafin ya ce “ yalaɓai kuma bayar da magani zaka koma?” Na haɗe rai na ce “ tashi ka bani wuri,ka yi abin da na ce su kuma mutanen da zaka samo ka sanar da su zan biya su ne” da saurinsa kuwa ya tashi,ni kuma na kai baki na sumbaci Tony don wannan dubarar daga gare shi ta fito. Bayan sallar la'asar kuwa sai ga mutane sun cika gidanmu,gefe guda ƴan jaridu biyu ne sai bayan na gama bayanan ƙarya kan cewa ina warkar da dukkan cututtukan duniya sannan mutane suka soma faɗin abubuwan alkhairin da na yi musu,na biya masu gidan rediyo da tv domin yi min talla da kuma lambar wayata da za a kira ni.Su kuma masu shaidun ƙarya Illiya na baiwa kuɗi ya raba musu,kuɗin da ace sun san sune ajalinsu to da tabbas ba za su karɓa ba amma ƴan magana na cewa kwaɗayi mabuɗin wahala...... NB:Ina ƙara yawan free page ne,niyyar kaina. My book is only 500 via2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 Talla! Talla! Talla!!! DULLAHZ CAKES AND MORE 💕 Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu, Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki, Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884 Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884 Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884 Call:09111648884 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 13 Washegari,afujajan Illiya ya shigo ofis ɗina ko neman izini bai yi ba. “Yalaɓai ya haka? Dukkan mutanen da suka bada shaidar ƙarya a kan kai malamin tsibo ne sai ɗauki ɗaiɗaya mutuwa take yi musu” Da wani mugun kallo na dube shi na ce “ au! So kake na bar su da ransu daga ƙarshe su tona min asiri? ” “Yalaɓai kisan kai fa ne jinin wajen mutum goma” ya faɗa hawaye na zubo masa akan kumatu waɗanda suka sa na ji zuciyata ta yi mugun sanyi don tsabar daɗi,don a yanzu in ga mutum cikin baƙin ciki shi fi faranta min rai. Ido na lumshe ina tuna yadda Tony yayi amfani da madubin tsafina ya dinga tsotse jinin duk mutanen da na bai wa kuɗi,sosai hakan ya ƙara mini ƙarfin power ta yadda a wannan karon har na yi nasarar toshe bakin Ammy ta yadda duk abin da zan yi ba za ta ga abunsa ba ko kuma ta yi min magana. “Yalaɓai ciki fa har da mace mai ciki ” Illiya ya faɗa cikin gwanjin kuka,na buɗe ido jin furucinsa .Na ce “ ya zancen Salima ka kuwa fara wani shiri a kai?” Ya saka idonsa cikin nawa yana zancen zucin da nake jinsa raɗau kwanyata na karanto min shi,‘ dama duk rashin imanina akwai wanda ya fi ni ? Anya akwai zuciya a ƙirjin yalaɓai? Wato duk wannan iftila'in da ya jefa mutane shi ko a kwalar rigarsa?...’ Tunanin nasa ne na katse ta hanyar cewa “ wani abun jin daɗi ma daga cikin wannan lamari shi ne kuɗin za su ci gaba da yawo a doron duniya,kuma iya masu son zuciya ne kawai za su je hannunsu haka kuma zan ci gaba da amfani da tataccen ƙarfin jikin mutane domin inganta gobena.Illiya ina so ka sa a ranka babu abin da ba zan iya yi ba yanzu,don haka kar ka kai ni bango yin haka ban kwana ne da rayuwarka.Je ka yi aikin da na saka,ka tabbatar Salima ta kasance cikin tsaronka sannan duk wani motsi nata ka sanar da ni” Ba tare da ya ce komai ba ya juya zai tafi,na tsayar da shi “ mene ne sunan matarka?” Ya juyo da sauri yana kallona tambayar ‘ me za ka yi da sunanta?’ shimfiɗe akan fuskarsa.Na ƙara haɗe rai ina juya idona zuwa na mage,murya na rawa ya ce “ Mariya ” na sakar masa murmushi,shi kuma ya fice. Kan kujera na zauna ina tunanin hanyar da zan ɓullowa mijin da Malama Zainab za ta aura,wanda alƙaluman tsafina sun tabbatar min da tabbas auren babu fashi .Na ja tsuki ina jin takaici,kukan Tony na ji ƙarƙashin kujerar da nake zaune.Na duƙa na ɗauko shi na ɗora shi kan table,jikinsa na fara shafawa tare da soma yi masa magana ina neman shawara “ Tony a daren jiya na yi bincike akan Malama Zainab kuma an nuna min sai ta auri mijin nan nata,ban so ya kusance ta ya zan yi?” “Turen aljani za ka yi wa mijin,tun da ita tana tsare iyakokin Ubangiji sosai babu ta hanyar da jinnu zai shiga jikinta.Amma kamar yadda ka yi bincike haka ni ma a jiya na yi bincike kan shi Sheikh ɗin,duk da yayi karatun addini amma fa bai amfani da shi in taƙaice ma dai fuska biyu ce da shi har da giya yake sha” Tony ya faɗa min da idonsa amma raɗam nake jin sautin murya na fita daki-daki.Tsabar murna ban san lokacin da na ɗauke shi na rungume tare da miƙe wa tsaye na soma yin rawa,“ ashe babban sirri ne da mage baƙa har haka? Hohoho! Wato shi yasa Tony ka kasance na musamman abin da ban saka ka ba yi kake yi domin sauƙaƙe min aiki” Tony ya ce “ yalaɓai ka manta a daren jiya ka yi min sacrifice? Ai muddin zaka bani jini abin da zan yi ma sai ka yi mamaki” sam ban damu da cewa illata rayuwar wasu babbar cutarwa ce ba na ce “ in dai jini ne Tony kar ka damu”. Ina nan zaune Illiya yayi min waya kan cewa Salima ta tashi daga makaranta,kuma shine ya kai ta gida da sunan ya rage mata hanya.Duk wayar da nake Tony ya buɗe kunnuwa yana saurare,bai ce komai ba ya fita da gudu.Na saki murmushi don na tabbata kuwa wani aikin ne zai yi min,wayata da key na ɗauka tare da ficewa . Ina draving ina tunanin surar Mariya matar Illiya ,na lashi leɓena na ƙasa ina mai cewa “ ko fyaɗe ne sai na yi miki muguwa!” a haka na ƙarasa gida.Ina shiga na ga Salima a zaune kan kujera tana taya Ammy saƙar kayan sanyi,na saki wani murmushin jin daɗi ganin Laure ta fito daga kitchen hannunta riƙe da kofin zoɓo ta kai wa Salima. “Ga wannan ki sha Madam yana ƙara gani musamman gare ku masu kallon zare” Laure ta faɗa amma kafin Salima ta kai ga amsa Ammy ta ce “ Laure miƙo min ganin zoɓon nan har maƙoshina ya bushe,je ki kawo wani” Da sauri na ƙarasa ina cewa “ haba dai Ammy ya za ki ce haka? Ita fa wannan baƙuwarmu ce ita ya kamata a fara karramawa,kuma kin ga ke kina da mura.Laure je ki kawo wa Ammy marar sanyi,ki dinga kula don Allah ko ta ce ki bata abu mai sanyi kar ki biye ta” Laure ta miƙa wa Salima kofin,za ta ajiye shi ita ma na tari numfashinta “ Hajiya ƙyanƙyamin mu kike shine ba za ki sha ba?” da sauri ta girgiza kai ta ce “ a'a wallahi bari na sha to” sai ta kai kofin bakinta har sai da ta sha rabi sannan ta ajiye sauran.Laure na fitowa na yi mata nuni da ido kan ta tafi da ragowar wanda Salima ta ajiye,ai kuwa tana miƙawa Ammy nata sai ta ce “ bari na ɗauke sauran kar ya zuba ga capet” “Laure wane irin abu ne wannan? Ta sha abu ta ajiye shine za ki tafi da shi? In kuma tana son ƙara sha?” Ammy ta faɗa cikin faɗa ,a doli Laure ta ajiye kofin tana kallona ta koma kitchen. Hira suke tsakanin Ammy da ita Salimar ni kuma ina gefe ina danna waya,hannun Ammy na gani ya ɗauki kofin zoɓon ban san lokacin da na ce “ Tonyyyy!” ban ida rufe baki ba ji kake Ammy na salati haɗi ƴar ƙara tuni Tony ya saka bindinsa ya buge kofin daga hannunta ya faɗi ƙasa ya zuba a ƙafarta. Laure ta fito tana tambayar lafiya,na soma shafa bayan Tony da tuni ya zo ya ɗare cinyata kafin na ce “ zo ki tsabtace wurin nan please ” Jikinta na rawa ta zo ta goge wurin da ya ɓace ita kuwa Ammy sai faɗa take,a ƙarshe dai na tashi na bar wurin na koma part ɗina.Ta cikin madubina na ga hanyar da Tony ya bi ya bai wa Laure maganin da ta zuba a zoɓon Salima,ya ajiye mata shi ne a kitchen da kuma ƴar guntuwar takardar da yayi bayani daki-daki. ★MALAMA ZAINAB Matashiyar budurwa ce ƴar kimanin shekara ashirin da bakwai a duniya,ta mallaki hankalin kanta.Duk wata cikar halitta da ƙima da ake nema wurin cikakkar mace mai ƙima duk ta mallake su.Mace ce ita wacce ta riƙi bautar Ubangiji matsayin abu na farko a rayuwarta,duk sauran abubuwa suna biyo wa baya ne.Tausayi,kyauta,jinƙai su ne suka luluɓe duniyarta suka ƙawata kyakkyawar fuskarta mai cike da hasken ni'imar imani.Tun da take ba ta taɓa soyayya ba,duk da kuwa maza dayawa sun nuna ra'ayin haka amma ita ba ta ji wanda take so ba.Sheikh Ali ya kasance cousin nata,tun da ta tasa ya ga tana da addini ya ɗauki son duniya ya ɗora mata tare kuma da zage dantse wurin nuna mata abin da zai kawo ci gaban karatunta.Wannan yasa ba tare da wani tunani ba ta amince za ta aure shi har aka yi musu baiko,bayan haka ne ya tafi Misira wurin karatu.Tun da ya tafi kuma ba wata gamsashiyar waya suke ba kasancewar shi da ita ɗin duk ba su da wani isasshen lokaci.Kwana biyu da dirar shi a ƙasar Nijar ya nemi a yi walimar aurensu,wacce kuma tuni aka soma shawarwari tsakanin ahalin biyu kafin shi ma angon ya nemi su keɓe domin tattaunawa. Ko da ta fito daga gidansu HAROON direct gida direba ya ajiye ta,zuciyarta cike da fargabar abin da take gudu take kuma zato kar ace gaskiya ne wato tana son HAROON . Ɗakinta ta shiga ta yi wanka ta canza kaya,bayan ta yi sallar magrib sai ta shafa mai.Tana nan zaune tana saƙa da warwara Innarta ta shigo tana cewa “ Zainabu ki fito ga Ali nan ya zo” Sai da gabanta ya faɗi,amma ta daure ta ce ” to Inna gani nan” sai kuma ta miƙe ta zaɓo wani farin hijabi ta saka tare da fesa turare marar ƙamshi. Sai da ta yi jarumta sosai sannan ta ƙaƙalo murmushi ta yaɓawa fuskarta mai cike da damuwa.Da sallama ta fita falon,yana ganin ta ya kafe ta ido ko ƙyaftawa bai yi.Ta zauna ƙasan capet ta ce “ ina wuni Imam?” “Alhamdullah malamata fatan kin wuni lafiya?” ya faɗa ba tare da ya janye idon nasa a kanta ba,cike da tsarguwa ta ce “ Imam babu fa kyau kallon mutum haka” Yayi murmushi mai sauti ya ce “ haka ne ! Amma kar ki manta saura ƙiris ki zama tawa na yaye duk wani hijabin kunya a tsakaninmu” Ba ta ce komai ta miƙe ta je ta kawo masa ruwa da abin da Innarta ta gyara mata domin tarben baƙon.Tana zuba masa ruwa ya kafe hannunta da ido,nan take jikinta ya soma yin rawa ta ɗaga kai ta banka masa wata muguwar harara. Ya ja ajiyar zuciya ya ce “ sai da na ji wani yarrr ” ruwan ta ajiye masa ya ɗauka ya sha,sannan ta zuba masa abinci har da su cewa ta zo su ci amma ta ƙi. Bayan ya gama ne ya ce “ Malama Zainab yau muna wace rana?” Ta basa amsa kai tsaye da “laraba” Ya ce “to rana irin ta yau kin shiga lalle da yardar Allah,sai a yi ɗaurin aure juma'a,taron biki kuma asabar” Shiru ba ta ce komai ba sai ma duniyar tunani da ta lula,ranar farko da suka soma ganin juna da HAROON ,yadda suka yi baya ta faɗa kan ƙirjinsa,yanayin yadda yake kallonta cikin tako da kuma salo,yadda yake mata murmushi... “ Zainab ?” Sheikh Ali ya katse mata tunanin,a ɗan firgice ta ce “ na'am HAROON !” “Haroon kuma?” ya tambaya da mamaki,sai ta diririce ta soma kame-kame,ita ɗin ba ma'abociyar yin ƙarya ba ce shi yasa ya gane. “Kar ki yi min ƙarya Zainab,wane ne HAROON ?” Ba tare da ta basa amsa ba ta tashi da sauri har da ɗan gudunta ta shige ɗakinta tare da faɗawa kan bed ta fashe da kuka....... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822. Ki zo ki yi payment domin a yi tafiyar nan da ke, wannan karon salon na daban ne salo ne da ban taɓa yin irinsa ba. BONUS! BONUS! BONUS!!! Ina makaranta kuma ma'abotan son littafan soyayya ko kuma na tsafi? To ku zo MRS SADAUKI ta yi muku gwanjon Books ɗinta akan farashi mai sauƙi,duk book ɗin 500 za ta bar muku shi ne a 300 kacal,wanda kuma yake 700 ko sama da haka za ku same shi a 500 kawai .Me kuke jira kawai ku tuntuɓe ta WhatsApp +22795045822. Domin ku kwashi garaɓasar. [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 14 Sai da Zainab ta ci kuka ta ƙoshi sannan ta shiga toilet.Tana shiga ƙarƙashin shower tunaninta ya soma nuna mata ga HAROON nan tsaye tare da ita suna wanka tare da wasanni irin na ma'aurata.Murmushi ne yayi nasara bayyana a kyakkyawar fuskarta wacce a ɗazu take shimfiɗe da baƙin ciki.Tamkar wata zautata haka take murmushi na wasar ruwa da niyyar nan HAROON ne take watsa ma su haɗi da yi masa shagwaɓa.Towel ta ɗaura ta fito ,sai ta tarar da Inna zaune bakin gado.Ta ƙara sakin ranta kafin ta ce “ Inna?” “Ungo wannan ki sha,su kuma waɗannan ki dinga zuba a abinci kina ci yaji ne” cewar Innar tana mai miƙa mata kofi.Karɓa ta yi ta zauna tare da yin Bismillah ta soma shan madarar har ta shanye,sai da Inna ta ƙarara jadadda mata kar ta saki ta yi wasa da su kafin ta fice.Ita kuwa tsaf ta shirya cikin riga da wando na bacci ,ta yi sallar isha'i sannan ta zauna ta soma duba takardun jarabawar da ta yi wa ɗalibanta.Sai dai sam hankalinta ya kasa kwanciya sai aukin tunanin HAROON ,wayarta ta ɗauka ta kira Ammy bayan sun gaisa sai ta yi shiru.Can dai ta ce “ ina HAROON ?” “Yana ɗakinsa,ko na baki shi?” “A'a turo min dai lambarsa” sai kuma ta yi saurin kashewa tana dafe saitin zuciya haɗi da waro ido.“ Zainab mi kika yi haka?” ta tambayi kanta,ƙarar shigowar saƙo ta ji da sauri ta duba sai ta ga lambar ce aka turo mata sai da ta yi ta kallon lambar kafin ta yi saving da “ NAWAN” sai ta ɗora love daga ƙarshe. Data ta kunna tana addu'ar Allah sa yana WhatsApp,tsawon lokaci kafin a nuno mata lambarsa mai ɗauke da hotonsa da Ammy su duka biyun suna murmushi.Da sauri ta ɗauki hoton sai ta yanke daidai nasa kawai ta tsura masa ido can kuma ta rungume wayar tana mai jan numfashi.Duba takardun da ba ta yi ba kenan ta je ta haye bed,MP3 ɗinta ta kunna ƙira'ar Sudais ta soma tashi tana biyar karatun tana kallon hoton HAROON a haka bacci ya ɗauke ta. Washegari sai da ta tsarkake jikinta kafin ta gabatar da sallah saboda mafarkin da ta yi.Bayan ta gama ta yi shara da gyaran ɗaki sannan ta ɗumama abincin kari,sai kuma ta je ta yi shirin makaranta.Cikin ƴar ƙaramar kula ta zuba abincinta kafin ta yi wa Inna sallama,sai da ta zo bakin titi sannan ta samu abin hawa .Tana isa makaranta ɗalinta suka fara gaishe ta ita kuma ta wuce cikin aji,sai a lokacin ta ci abincinta cike da tunanin mafarkinta na jiya.Sai da ta yi da gaske sannan ta hakice tunanin HAROON daga ranta ta gabatar da darasi wanda shine ya zama na ƙarshe.Tana komawa gida aka shafa mata lalle,don dole ta haƙura tuni kuma aka fara shirye-shiryen biki kamar yadda abin ya zo mata a bazata haka su ma dangin da abokai amma duk da haka sai da aka fitar da anko.Har aka kawo lefe aka yi ɗaurin aure ko sau ɗaya Sheikh Ali bai kira ta ba haka ita ma ta share shi ko saƙo ta kasa tura masa.Yanzu ma da ake ta hidimar biki babu abin da take sai tunanin da ya daɗe da aurenta,na masoyin da igiyar aure ta yi mata iyaka da shi .Da zarar ta tuna cewa yau ɗin nan wani zai karɓe budurcinta sai hawaye su yi ta mata zuba,mutane kuwa tunaninsu kukan rabuwa da Inna ne kasancewar ita ɗaya ce tal ta rage musu a duniya duk ƴan uwanta sun rasu tun suna jarirai. Har aka yi kiran sallah magrib Malama Zainab na kuka,da aka ce ta je ta yi wanka domin shirin kaita ɗakinta ji ta yi kamar ta fasa ihu ta yadda kowa zai fahimci tsananin damuwar da ta luluɓe sirrin zuciyarta. Da ta yi wankan sai da ta yi sallar isha'i sannan mai kwalliya ta soma yi mata simple make-up ba irin tarkacen nan ba.Doguwar rigar less fari sol ta saka sannan ta ɗora alkyaba sama a haka ma sai da aka ƙara ɗora mata darar amare.Sai da aka yi hotuna da bidiyo da abokan arziki kafin a ƙara yi mata wata nasihar,daga nan aka ja ta zuwa can waje inda motocin da ango ya turo suke jira.Banda kuka babu abin da Malama Zainab take yi amma hakan bai hana aka kai ta ɗakinta ba,har aka gama addu'a kuma ba ta buɗe fuskarta ba.Nan mutane duk suka watse yayi sauran ƙawarta guda tal Hafsat wacce sai yanzu ta samu damar yi wa Zainab ɗin nasiha “ kukan nan ya isa haka don Allah! Abin da muke ta jiran ranar nan amma ta zo sai kuka kike” Malama Zainab ta buɗe luluɓin ta ce “ Hafsat tsoro nake ji,wallahi zuciyata kamar za ta fashe don fargaba don Allah ki taimaka min ki bani shawarar da zan yi amfani da ita wacce za ta hana Sheikh ya kusance ni” Shiru ta yi kafin ta ce “ caɓɓɓ! Batu wuya,gurguwa da aure nesa! Amma kin san wannan ba mai yiyuwa ba ne,wallahi sai ya kusance ki sai in magani bacci za ki basa ya sha” da sauri Malama Zainab ta ce “ yawwa ko hakan yana yi,don Allah je ki karɓo min ” sai ta zuge zip ɗin jakarta ta bata kuɗin,sai da Hafsat ta yi ta juya kuɗin kafin ta fita ta je ta siyo mata sai a lokacin hankali Malama Zainab ya kwanta.Babu jimawa kuwa ango ya shigo tare da rakiyar abokansa,bayan sun gama tasu nasihar Hafsat ta bi su don su sauke ta gida. Ido Sheikh ya tsura wa Malama Zainab wacce tun da suka haɗa ido sau ɗaya ta sunne kai.Ya ja wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar ado da kyawu” Dakyar ta amsa masa da “ wa'aleykum Salam!” sai hawaye shaaa,ya kamo dukkan hannuwanta ya sauko da ita daga bed ɗin yana mai cewa “ mu je ki yi alwala” “Ka bari zan yi ni ɗaya” ta furta,sai ya bar ta ɗin ta shiga toilet ta ɗauro alwala bayan ta fito shi sai ya shiga.Da sauri jikinta na rawa ta ɗauko maganin baccin ta je buɗe ledojin da ya shigo da su ta zuba maganin cikin lemu sai dai aka yi rashin sa'a tuni Sheikh ya fito daga toilet ya ga kwalbar sirop ɗin kuma ya fahimci na mene ne.Yayi saurin komawa toilet ɗin ya bata lokacin da za ta yi rashin gaskiyarta ta gama. Yana fitowa a karo na biyu ya sakar mata murmushi kamar bai ga komai ba,ya ja su sallah bayan nan yayi musu addu'o'i ya miƙe ya ɗauko ledojin da sauri ta karɓe ta ce “ bari na zuba mana” bai ce komai ita ta ɗauko plate da kuma kofinan shan ruwa. Da ta zuba haka ta daure tana cin kazar shi kuwa tunani ne fal zuciyarsa ‘ mene ne ribar Zainab in ta bani maganin bacci? Wato ba ta son na kusance ta sai kace ba sadakina na biya na aure ta ba .Ko dai tsoro ne take ji? A'a ba shi ba ne inda shi ne da tabbas da magiya da kissa irin ta mata zata ɓulo min’ yayi tambayoyin duk a zuci amma ya kasa samo amsa,ya ƙure ta da ido lokacin da ta cika masa kofi da lemun ya karɓa a nan take kuma ya tuna da sunan HAROON wanda y'zuciyarsa ta yanke masa tabbas saurayinta ne. Kofin ya kai bakinta yana mai cewa “ namijin kirki shine wanda ke fara shayar da matarsa kafin shi ya sha” “A'a ka sha ni ma zan sha ai ga nawa nan sai na gama ci na sha” ta faɗa tana zarar ido, Sheikh ya saki murmushi ya ce “ in dai ba ki sha to ni ma ba zan sha ba sai da na sha ruwan pampo” Malama Zainab na jin haka ta yi saurin karɓa ta sha ,da tunanin can su yi ta baccin su biyu .Shi kuwa Sheikh haka ya tsura mata ido har sai da ta shanye tass,ta cika masa kofi ta ce “ saura kai” ya laƙace mata hanci ya ce “ ai ni bana shan kayan zaƙi saboda suna da illa, dama dai wayo na yi miki ” Tamkar wacce cutar sanƙarau ta kama haka ta sandare ta kasa motsi sai idonta da ke tsiyayar da hawaye tana da na sanin haƙa wa ramen muguntar da a ƙarshe ita ce ta faɗa .Ba a ɗauki lokaci ba ta ji fitilun idonta na disashewa,sai a lokacin ta miƙe da hanzari ta shiga toilet ta wanke fuskarta duk don kar bacci ya ɗauke ta sai dai ina tuni ta soma jin jikinta ma na saki.Da sauri ta fito kamar wata makauniya tana lalube, Sheikh ya je ya kamo ta tare da ɗora ta kan bed yana mai cewa “ shi yasa aka ce in za ka gina ramen mugunta ka gina shi gajere” sai kuma ya soma cire mata suturar jikinta.Sai da yayi mata zirr kafin ya cire nasa,jikinsa har rawa yake wurin ƙoƙarin haura gadon sai dai cak ya tsaya saboda yadda idonsa suka fara nuna masa ba daidai ba.Malama Zainab yake gani ta rikiɗe masa ta koma lakaɗeɗen maciji sai wani haske take fitarwa...... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️ LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️ *Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo (MRS SADAUKI💫✍️) *Lambar waya:* +22795045822 *FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️* Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation. _____________________ 15 Jikin Sheikh Ali ne ya ɗau wata irin muguwar rawa ganin amaryarsa wacce aka kawo masa yau ta rikiɗe ta zama lakaɗeɗiyar macijiya sai wani kaɗan bindi take. Da gudu ya dawo falo ba tare da ya tsaya ɗaukar ko da wando ba ne,ɗakinsa da ya ware tun can a matsayin baraya ya shiga.Duk uban sanyin da ake zufa ce ke yi masa tsiyaya,tunani ya soma kamar wani zautace haɗi da suratai.“ Aljana ce aka kawo mini ko kuwa Jinnul ashiq ne da ita banda labari? Kaicona ni Ali ,ni kam banda rabo a duniya duk yadda nake mararin ganin wannan daren amma ya zo min ta wata mummunar siffa? Ai kuwa ba zan zauna da ke ba wallahi dole ki tafi gidanku” sam bai rumtsa ba haka yayi ta zagayen ɗakinsa yana tubka da warwara. ★HAROON Tun bayan da Salima ta sha lemun zoɓon nan sai ya zamana a kullum kafin na fita aiki sai ta shigo gidanmu.Haka za ta yi ta kallona amma ta kasa yin magana,gefe guda kuma Laure mai aiki na ci gaba da bata maganin da Tony ya ajiye a kitchen. Yau ma kamar kullum ina zaune ina duba takardun da nasa aka buga min irin wanda in kana son ganin likita patients ke cira,da sallama Salimar ta shigo.Ammy ba ta falo sai ni kaɗai,ido na zuba mata sai na ga ta soma kyarma yayin da bakinta ke ta rawa.Na fahimci kalmar so take son furta mini amma ƙarfin zuciyarta ya hana ta faɗa ,ni kuwa ta wannan hanyar ce kawai zan cimma ƙudirina a kanta. Idonta ne ya soma kawo ruwa,da sauri na kawar da kai gefe ina jin wani haushin ta .Sai ta fita a guje tana kuka,na ja tsuki tare da tashi na fito na shiga ɗakin da na ware domin duba maras lafiya da kuma masu son a yi musu aiki. Kamar yadda na tsara sai ranar asabar kawai zan dinga yin aiki,yayin da kuma Iliya direbana zai dinga karɓar kuɗin ganina sai ya bai wa mutum takardar shaida. Yau ce ranar farko da zan soma kamar yadda na sanar a sanarwar da nasa aka yi,amma mutane ne masu mugun yawa suka taru.Ɗaya bayan ɗaya suke shigowa ,in na karɓi receip/reçu ɗin hannun mutum ni ne zan sanar da shi sunansa da kuma matsalar da ta kawo shi .Dukkan bayanin kuma Tony ne ke sanar da ni komai,yanzu ma layi ya kawo kan wata budurwa da ta shigo.Ta miƙa mini takardar hannunta na karɓa ina dubawa “ sunanki Shukuriya,kina son a yi miki aiki kan Salele don ya saki matarsa ke ya aure ki saboda ba ki son kishiya sannan shi ma ya faɗa miki bai da tsarin yin mata biyu saboda bai da cikakken lokaci a matsayinsa na soja” na faɗa ina mai kallon ta,a zahiri fuskarta ce nake kallo amma a baɗini ruhinta ne abin dubana.Sam ba ta da mutumci ga kuma muguwar zuciya,uwa uba rashin imaninta yayi ƙasa sosai.Bayan na gama ganin qualitynta sai na saki murmushi,yayin da kuma muryar Tony ke ce min “ HAROON wannan ɗin ma ka riƙe ta gam da alamu za ta kawo ma ci gaba a tafiyarka ” “Eh haka ne malam,shine abin da nake so amma nawa zan bada?” ta tambaye ni tana wani sunne kai.Zama na gyara ina jawo tasar da na zuba ruwan tsafina na soma shafa su,sai na ce “ kina da hoton shi saurayin naki?” “Sai dai a waya kawai” ta bani amsa,na ce “ nemo ki miƙo min” da sauri kuwa ta miƙo min wayar don hotonsa ne kan screen.Saitin tasar ruwan na kara hoton tamkar mai yin scanning nan take zanen hoton ya zauna raɗam kan ruwan,cikin abin da bai kai minti biyar ba na gama kwashe duk wasu bayanansa. Na ɗago na dube ta na ɗan wani lokaci kafin na ce ,“me yasa kika yarda da shi har kika basa kanki? Cewa yayi zai aure ki ko? Yana son ki? To duk ƙarya ce kawai yana wasa da hankalinki ne,jikinki kawai yake so.Amma zan yi miki aikin da sai ya aure ki,fatan za ki bi duk sharuɗan da zan gindiya miki?” “Eh malam in dai zai aure ni koma mene ne zan yi” “Ina so ki kawo min maniyinsa” na faɗa . Ta waro ido tare da cewa “ ta yaya malam?” “Abu mai sauƙi,in za ku yi mu'amala ki saka condom ta mata ko kuma shi ki basa ya saka kin gane dai ko?” “To malam zan yi,sai me kuma?” “Shi kaɗai nake buƙata za ki iya tafiya,in kin samo shi ko yau ne ki dawo” na faɗa ta yi godiya tare da fita,wasu suka ci gaba da shigowa a cikinsu babu wanda na yi wa aiki sai dai cutarsu da na yi ina kwashe taurarunsu ina adanawa kaina domin ƙarin power a haka har dare yayi. Ina shigo wa falo Ammy ta soma yi min sannu tare da addu'ar ci gaba akan aikin alherin da na soma yau.Ko abinci ban ci ba na shiga ɗakina,madubina na ga yau yayi kicin-kicin da fuska alamun akwai matsalar da ke tunkara ta. Tony na duba na ce “ mene ne wannan?” sai kuma na yi tsaye gaban madubin. “Ana shirin kai abar ƙaunarka ne gidan Ali” Tony ya bani amsa,wani ɓacin rai ne na ji ya sauko min na ce “ fatan ka yi duk abin da ya dace?” “ Kar ka damu na aika masa da aljani mai juye hasken ido” Na saki murmushi,kafin na shiga na yi wanka.Kamar wata tv haka na zauna ina kallon idon Tony waɗanda suke fitar da wani jan haske ta cikinsu ne nake ganin duk abin da ke wakana.Tun daga ƴan kan amarya har lokacin da Malama Zainab ta zuba maganin bacci da yadda shi Sheikh ya fita a guje babu kaya jikinsa,raina fari ƙal tsabar murna haka na jawo Tony na rungume tare da ja mana blanket. Tunanin Malama Zainab ne ya addabi ruhina,yayin da muguwar sha'awarta ta yi min kamun kazar kuku.A haka dai na samu bacci ya ɗauke ni sai dai bai yi nisa ba na ji ana kiran sunana. “ HAROON ? HAROON ?” a hankali na soma buɗe idona da suka yi min nauyi,ban gani sosai amma ita muryar tabbas na san mai ita sai dai na manta a ina. “ HAROON za su kashe ni,ka cece ni HAROON ban bar gida ba don cutar da ku sai don na zaɓa wa kaina rayuwa mai inganci ” muryar ta sake faɗa ,a wannan karon zumbur na miƙe ina kallon madubina wanda hoton Abbana ya fito raɗau kuma yana motsi idonsa suna zubar da hawayen jini.Ko kaɗan ganinsa a cikin wannan hali bai sa na ji tausayinsa ba sai ma tuna min da yayi da tsohuwar rayuwata ta baya a ranar nan wacce na tarar da shi yana haɗa kaya ban manta ba abu na farko da na ce masa shi ne “ Abba ina kuma zaka je da kaya?” Ya juyo a zabure kafin kuma ya haɗe rai ya ce ,“ zan tafi na yi nesa da ku,zan auri yarinya sabon jini wacce zata kula da ni.Wacce ta san darajata da ƙimata,wacce duk abin da na nemo na bata ba ta raina wa sai ma dai ta ƙara da nata kuɗin.Na gaji da zama Ammynka,mugun halinta sai ƙara yin gaba yake,ta hana ni na ƙara aure na ƙi hannuwa shine ta tsiro da faɗuwar ƙarya wai jininta ya hau.To can ku ƙarasa rayuwarku ni ma zan yi tawa ” Cike da takaici na ce “ duk ƙoƙarin da take yi na yin ƴar ƙaramar sana'a domin ciyar da kai ba ka gani ba? Abba a wannan yanayin ne za ka ƙara aure? Ka manta nan gidan haya ne muke? In ka aure ta ina zaka kai ta?” “Ita ai ba matsiyaciya ba ce irin uwarka,ita shahararriyar ƴar kasuwa ce mai ji da kanta .Ga tsafta ga gayu,ga cima mai kyau ka ga sai an jima ni zan tafi” “Abba ka sani muddin ka bar gidan nan ka fita daga sawun masu rai a wurina” na faɗa sanin yana mugun sona.Amma ga mamakina sai na ji ya ce “ wannan ta fi nono fari a wurina” yana gama faɗa ya fice ya bar ni ina zubar da hawayen takaici. Yanzu ma gumin hawayen ne ya dawo da ni daga duniyar tunanina,na dubi Abba da ke haɗe hannuwa yana roƙona yafiya.Ban ce komai ba haka kuma ban motsa ba,Tony da ke kan jikina yayi tsalle ya kai wa Abbana farmaki a gaban idona ya kafa haƙoransa ga wuyan Abba . Na zabura na sauka daga bed ɗin,sai dai ko kafin na isa ga madubin duk hotunan suka ɓace ya dawo normal.Duk yadda na yi ƙoƙarin shiga ciki kuma abu ya cuttura,daga can bakin ƙofa na ji ana buga min ɗaki .Ba tare da na tambayi wane ne ba na je na buɗe,Ammy ce tsaye duk jikinta rawa yake da alamu a tsorace take. “Ammy lafiya kika fito da tsakar daren nan?” na tambaye ta. “ Tsoro nake ji HAROON ,yau ashirin da biyu ga wata Yulin ” “Eh mene ne ?” “Zagayowar sallar Lugnasad ” ta faɗa tana kuka,“ Ammy ni ban fahimci komai ba” “Ai dai kanka bai ciwo ko?” ta faɗa tana tallabo fuskata,na ce “eh bai yi” sai ta ja ajiyar zuciya kafin kuma ta juya ta fita tsaye na yi cike da mamaki,tabbas na ƙara yarda Ammy na ɓoye min wani sirri. Ɗakin na rufe tare da jingina jikin ƙofa,ina shirin rufe ido na ga saukar Oga tsudum.Da sauri na isa gare shi ina cewa “Oga kai ne a daren nan?” Fuska ya ƙara haɗewa kafin ya ce “ HAROON na taɓa wasa da kai?” “A'a Oga” “Amma mene dalilinka na ɓoye min gaskiyar kai wane ne?” “Ban gane ba Oga me kake faɗa haka?” “Dubi madubinka” ya faɗa tare da yi min nuni da shi,na kai idona nan na yi arba da wata siffa marar kyawun gani kai tsaye za a kira shi da aljani ko kuma dodo.Tsaye yake cikin iska yayin da wata mata ke yi masa kirari wutar na ɓulɓulowa ta ƙasa . “Wace ce ita?” na tambaya. “Amsar da nake son ji kenan daga bakinka,ita ɗin ahalinka ce maganar da nake yi ma yanzu rigima ce muke don ta ce kai ɗin nasu ne ” Oga ya faɗa . Na girgiza kai na ce “ban taɓa shiga ƙungiyar asiri ba” “Abbanka fa?” Oga ya jefo min tambaya,na ce “ba na tunanin yana ciki,domin kuwa da ace haka ne da talauci bai yi wa duniyarmu ƙawanya ba ,har ta kai ga Abba ya guje mu ya koma wurin wata mata wacce ba Ammy ba” “Yanzu na fahimta, wannan ɗin matar mahaifinka ce! Ita ɗin baya ga tsafi da take kuma ƴa ce ga ƙungiyar asiri,mahaifinka ya bayar da jininka matsayin sacrifice .Ya zama dole ka nemo mafita tun cikin daren nan,sannan ka tambayi ita Ammynka ta baka labarin ainahin abin da take ɓoye ” yana gama faɗa ya fice.Na dafe goshi ina shirin shiga toilet sai madubina ya soma fitar da wani haske,da mugun sauri na dafe gaban goshina saboda wani abu da na ji ya caki wurin kamar mashi sai kuma na zaro ido ganin kamar giftawar Malama Zainab,can kuma mijinta ya bayyana hannunsa riƙe da lakaɗeɗen belt.Da mugun sauri na isa bakin madubin,na kai yatsana manuniya na dakatar da mijin nata ta hanyar furta kalaman tsafi sai ya zube nan a yashe kan tile. ★MALAMA ZAINAB Tamkar gawa haka ta yi ta sharar bacci,ba ita ta farka ba sai ukun dare.Kanta ta soma jin yana ciwo,ta tashi dakyar ta zauna.Duk abubuwan da suka faru ne suka soma dawo mata daki-daki,sai ta duba jikinta sam babu alamar an yi amfani da ita amma kuma ga jikinta babu sutura.Toilet ta shiga ta yi wanka tare da ɗauro alwala,ta saka jallabiya tana shirin ƙabarta sallah ta ji ihun Sheikh Ali,da sauri ta fito ta soma tafiya har ta isa cikin ɗakin nasa sai ta tarar ashe mafarki ne yake. “Subahanallah Sheikh lafiya kake?” ta faɗa tare da ɗan bubuga gefen gadon,daidai nan ya tashi suna haɗa ido da ita ya tashi tsaye tare da kwaɗa mata mari ko kafin ta tambayi dalili ya rufe ta da uban duka.Dole dangin naƙi ce ta sa ta fito a guje,shi ma Sheikh ya ɗauki belt ɗin da ya gani kan gado ya biyo ta a tsiyace sai dai aka yi rashin sa'a kafin ya isa gare ta ya ji wani abu mai kamar tartsatsin wuta ya naushe shi .Yayi ƙara tare da faɗuwa timmm a ƙasa,hakan ya jawo hankalin Malama Zainab ta juyo sai kuma ta ga abin da ke faruwa ta dawo da sauri tare da zubewa tana kiran sunansa “Sheikh? Sheikh Ali ?” sai dai shiru bai ko motsa ba saboda babu numfashi a tattare da shi,ta ɗora hannu saman kai tana mai cewa “innallilahi wa'inna ileyhi raji'un!” daga wannan page ɗin ba zan sake fitar da wata ba,duk mai son ci gaba za ta biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ta turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 Mu haɗe a PAID group 🤗 NB: daga lokacin da ya zama Complete 1k ne farashinsa.