[11/16, 6:31 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATOIN* PAGE 1 "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ihu jama'a, a kawo ɗauki!".Hayaniya da ihun mutanen gidansu ya ta tashe ta daga baccin safenta mai ɗan karen daɗi, ta ja dogon tsaki tana jan yaƙunannen bargonta don ta rufe fuskarta, wai ko za ta samu damar rage tasirin hayaniyar, gidansu gidan yawa ne, mai cike da hargitsi, sun saba da hayagaga mara dalili, sai dai ta yanzu ta fara zargin da dalilin, duba da yadda yara da manya suke ihun babu ƙaƙƙaunatawa, "Yekuwa jama'a! Salamatu ta faɗa a rijiya, ku kawo mana ɗauki!." Maganar Mama Karime ta daskarar da duk wata na'ura ta jikinta ta dakata da aiki na wucin gadi, a hankali ta juyo da kanta ta yi wa idanunta matsuguni a gefen shimfiɗar Mamanta, da fatan Allah Ya sa ba ita Salamatun ake nufi ba, duk da ta san babu wata a gidan mai irin sunata, nan ta ga wayam babu kowa a kai, ta tashi a firgice daidai sanda Nusaiba ta bankaɗo ɗakin da take tana haki tana cewa"Ke Nuratu, tashi babarku ta faɗa a rijiya!". Da wani irin hanzari ta fice a guje har sai da ta yi fatali da Nusaiban da ta kawo mita rahoto, maƙota har sun fara shigowa ana ta salati, ta yi tsalle da nufin faɗawa rijiyar don ta ceci Mama, ganin an tsaya kame-kamen yadda za a yi, kamar ba su ɗauki ran nata a bakin komai ba, Baba ban da salati ba ya yunƙurin taɓuka komai, aka cafe ta ana ba ta haƙuri, ta ɓarke da kuka tana kiran sunanta cikin fitar hayyaci, "Maaamaa!" Tsayin mintuna kafin Malam Haruna ya zo, wanda masani ne sosai a kan harkar haƙan rijiya, su biyu suka shiga, aka samu nasarar ciro ta, aka shimfiɗa tabarma aka zube ta aka shiga ba ta taimakon gaggawa, sai dai ta ƙi numfasawa, Baba ya ƙarasa ya kasa kunnensa a saitin zuciyarsa, sai ya ɗago ya ɗora hannu a ka yana cewa"Ƙalu inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, Salamatu ta tafi, ta tafi ta bar mu, an yi mana mutuwa ni da Nuratu!". Nuratu ta yi kanta a guje, tana jijjigata haɗe da gunjin kuka, amma ko motsi ba ta yi ba. Gabaɗaya gidan aka hau salati, wasu suna cewa ba ta mutu ba, a tafi asibiti, Baba ya hau faɗa yana cewa"To wane asibiti ana zaune ƙalau? Ni ƙaramin yaro ne da ban san mutuwa ba? Na binne uwata na binne ubana, na binne matata, na binne ƴaƴana huɗu sannan a ce ban san mutuwa ba, aradu Salame ko ba ta mutu ba na tabbata ba za ta tashi ba sai ta ƙarasa". Nan aka yi masa ca, ana nuna masa muhimmancin zuwa asibitin, abin takaici Baba sai ya zaro aljihun rigarsa duka biyun yana kaɗewa yake cewa"To wai da shekaruna zan kai ta asibiti? Ga shi dai ko ƙarfanfana babu a aljihuna". Ta sake fashewa da sabon kuka, nan wani maƙocinsu ya sunkuci Mama ya fice da ita, sannan Baba da sauran mutane suka mara masa baya, haka ita ma ta bi su ko ɗankwali babu a kanta, sai ƙanwarta ce ta cire hijjabin jikinta ta saka mata, ta bi su titi a guje, ta tari adaidaita sahu ta shiga, ya bi bayan nasu, a tare suka shiga asibitin ko ta kan kuɗin mai adaidaitan ba ta bi ba, shi ma bai tambaya ba ganin halin da take ciki. Bayan jira na ɗan lokaci aka tabbatar musu da rasuwar Mama Salamatu, Nuratu ta zauna a ƙasa dirshan tana gursheƙen kuka, ana ta ba ta baki, don Mama Karime ma ta ƙaraso asibitin, nan aka ja lissafin kuɗin asibiti da na ɗaukar gawa, wanda Baba ya ce ba shi da shi, sai karo-karo aka yi aka ɗauki gawar zuwa gida, sai ta shiga ɗaki ta zauna ta zama kamar mutum-mutumi sai hawaye da ta kasa dakatar da su, da ƙyar ƴan'uwan Mama suka ja ta zuwa kan gawar bayan an gama yi mata sutura, suka ce ta yi mata addu'a, kuka ta fashe da shi, da ƙyar ta iya buɗe baki cikin in'ina ta ce"Ma...Mama, Allah Ya yi miki rahma, Allah, Allah Ya sa can ya fi nan". Sai ta rushe da kuka, wata zuciyar tana raya mata Mama ba ta farinciki da addu'ar nan tata, saboda ta mutu tana tsananin fushi da ita, da ƙyar aka ja ta a ka mayar gefe, tana kallo aka fice da gawar, zuciyarta na tururi tana yi wa mahaifiyarta kallon ƙarshe. Ƙullin wainar siyarwar da Mama take yi, na yau sai ya zama na sadakar mutuwarta, Nuratu ta tuna jiya da daddare sanda take haɗawa, ko markaɗe da kanta ta kai, saboda tana fushi da ita, dama haka take yi idan ta yi mata laifi ba ta yarda ta taya ta aiki. Zuwa azhar ƴan'uwa sun cika gida, har an gama kuka an shiga hada-hadar rabon abinci, wanda Alhaji Hashimu ne ya kawo, ƴan gidansu har da masu faɗa a kan abinci, yayin da Nuratu kuma yawun bakinta ma ya yi mata ɗaci. Mutuwa ta yi mata yankan ƙauna, Mama ta tafi ta bar ta a gaɓar da take ƙishi da yunwar kasancewa da ita, a lokacin da ta fi buƙatar taimakonta da samun kusanci da ita, ta rasu tana fushi da ita, ba ta tsaya ta fahimci uzurinta ba, ba ta yarda da hujjojinta ba, idan aka ce baƙin cikin abin da ta aikata ne ya yi silar mutuwarta ba za ta yi musu ba, domin kuwa tun shekaran jiya da ta sanar da ita ƙaddarar da ta faɗa mata take cikin tashin hankali da ɗimauta, tana yin komai ne da ƙarfin hali, sannan a yadda Mama Karime ta ba da labarin yadda ta faɗa rijiyar ta san ba ta cikin hayyacinta ne, sannan Mama da asuba take fara suyar waina, amma a yau ɗin har gari ya waye ƙullin yana ɗaki ba ta fara ba, ita kuma sai wani shegen bacci ne mai daɗi yau ya ɗauke ta, cikin bargon da take kwance zazzaɓi yana nuƙurƙusarta, ta kai hannu ta dafa mararta tana tunanin yadda zan yi idan abun ɓoye ya fito fili, da wane ido za ta kalli duniya idan ta fahimci da ciki a jikinta na watanni biyu? Mahaifiyarta ma ba ta fahimce ta ba ballantana kuma duniya? Sai ta saki siririn kuka, don zuwa lokacin muryarta ta dashe sosai. Ƴan'uwan Mama da suke ɗakin sun yi iya yin su ta ci abinci ta ƙi, can bayan la'asar mata duk ana zazzaune, wasu suna shirin ɗora tuwon dare, sai ga Baba ya shigo, fuskar nan a dagule ya kalli Inna Asabe yayar Mama ya ce"Asabe yaya na ga ana shirin kunna wuta?" Ta ce"E abincin dare za a ɗora". Ya ce"Au! Wato kenan ku banza ta faɗi, kowa ya samu wajen fakewa ya ci abinci ko? Ɗan abincin sadakar da aka kawo mini don rage raɗaɗi tun da ba fita nema zan yi ba, a zage ni a gari a ce ban zauna karɓar gaisuwa ba, shi ne za ku saka abincin a gaba ku cinye, ku bar mu da tagumi ni da ƴar marainiyar Allah?" Sai ya zo tsakiyar gidan ya ɗaga murya ya ce"Kowa ya buɗe kunnenaa da kyau ya ji ni! Daga yau an rufe zaman makoki, kowace mace ta shuri takalminta ta tafi gidanta, gaisuwa ce an yi na gode, amma kar wacce ta sake zuwa gidana daga yau!". Mama Lami wacce ita ma matar Baba ce, ta taso tana cewa "Haba Malam..." Ya ɗaga mata hannu yana faɗin"Kin ga Lami ki kiyaye ni, ni na gama magana!". Sannan ya shiga ɗakin mai rasuwa inda aka ajiye kayan abincin ya dinga ɗibowa yana kai wa ɗakinsa, ya rufe da mukulli ya fice, nan mata aka dinga ƙananun maganganu, aka fara silalewa ɗaya bayan ɗaya. Inna Asabe ta shigo ɗakin tana cewa"Kaico! Amma wallahi wannan Iro an yi mara mutunci, yanzu ban da zub da mutunci a gidan mutuwar ma sai ya nuna halinsa? A kan abinci zai hana zaman makoki?" Mama Suwaiba ta ce"To ke za ki dinga ci da mutane idan kin ce su daina zuwa? Babu wanda bai san halin Iro ba, don haka wannan ba wani abun damuwa ba ne, ni kin ga tafiyata". Ta kalli Nuratu ta ce"Nuratu ki yi haƙuri ki bar kuka haka, Allah Ya yi mata rahma Ya zama gatanki". Sai ta gyaɗa mata kai alamar ta ji. Haka duk aka yoye aka tafi ana yi da Baba, ɗakin ya rage ita kaɗai, ta tuna jiya iyanzu tana kallon Mama zaune a cikin ɗakin, fuskarta cike da damuwa, sai ta fashe da kuka tana cewa"Allah Ya yi miki rahma Mama, amma kin bar baya da ƙura". Kiran sallar magriba ce ta fito da ita daga ɗakin, har jiri take yi saboda yunwa, ta tarar da Baba ya fito daga banɗaki, yana gyara tazuge, ya ce"Yawwa ke Nuratu, ɗazu Alhaji Hashimu ya zo, duk shi ya kawo kayan abincin nan ma, ya ce anjima zai zo ya yi miki gaisuwa". "To" Kawai ta ce, ta ɗauki buta ta fara alwala, tana tunanin da wane yaren za ta faɗawa Baba tana ɗauke da ciki a jikinta ya gane abin da take nufi? ******* Kamar kullum tana idar da sallar asuba, ta fito tsakar gida, ta fara kiciniyar kunna wutar gawayi, shayi ta fara dafawa sannan ta ɗora farar taliya, ta zauna tana ta fifita wutar ta ji kukan Aiman ƙaramin ɗanta ɗan wata biyar ya farka, tsakanin kukan da ƙwalla kiran da mijinta ya yi mata ba ta ma tantance wanda ya riga wani ba"Ke Hasana! Hasana". Ta tafi da sauri, ta shiga ɗakin tana raira ƴar waƙarta"Aiman ya tashi, manya sun tashi". "Ke dalla can kwashe shi ki fice mini!" Cewar mijin nata, ko a jikinta don inda sabo ta saba da halinsa na masifa, gabaɗaya shi kullum a zabure yake ba shi da lokacin nishaɗi tare da ita sai dai idan yana tare da yaransa ko kuma wayarsa, yaran da sai sun zama mutane yake fara son su, amma yaro indai ba ya tafiya ba ya magana to ba mutum ba ne a wajensa, ko kallo nai ishe shi ba, da safen nan idan tana can tana girki Aiman ya tashi, ta sha zuwa ta tarar ya dawo da shi falo, sauro suna ta cizonsa, idan kuma ta yi magana ya ƙure ta da zagi a gaban ƴaƴanta. Haka ta goya yaron, ta tashi sauran yaran Salim da Amir ta shiga yi musu shirin makaranta, sanda ta kammala komai bakwai da rabi har ta yi, don sai ta dafa musu indomi wacce za su tafi da ita makaranta baya sun ci taliya a gida, sai lokacin Nura ya fito cikin shirinsa na fita, ya buga uban wanka ya sha wani yadi daga gani ma yau ya fara saka shi, ya kafa hula, kamar mutumin kirki, irin wankan da ya sace zuciyarta ya yaudare ta da daɗin bakin sama mata rayuwar soyayya mai cike da farinciki, sai ga shi ya kawo ta baƙin gidansa mai cike da ƙunci ya kulle, ba ta da wani amfani a idonsa sai na bautarsa shi da ƴaƴansa, suka karya a tare, ya ɗauki mukullin babur ɗinsa ya haɗa kan yaran za su fita, ta ce"Me za a dafa anjima? Babu kayan miya a gidan". Ko kallonta bai yi ba, ballantana ta samu amsa, wannan yana ɗaya daga cikin halinsa wanda ta saba da shi, suka fice tana tunawa yaran addu'ar fita daga gida. Da rana ta dafa shinkafa da wake, sauran yajin nata ma kaɗan ne, ga shi ba ta da ko sisi ballantana ta ƙara barkonon, ƙarfe ɗaya yake ɗakko yaran daga makaranta, sai ya ci abinci ya koma kasuwarsa, wacce babu nisa da gidan nasu, dab da yaran za su dawo ƙawarta Ramla ta zo, ta ce daga kasuwa take shi ne ta biyo, ta zubo mata abinci, suna ta fira cikin nishaɗi. Tana jin ƙarar babur ɗinsa gabanta ya faɗi, don ba ta son ya shigo gidan tana da baƙi, don kar ya yi mata faɗa a gabansu har a san halin da take ciki, don ma dai ya san Ramla. Ya shigo da sallama, suka amsa, Hasana ta yi masa sannu, ya amsa idonsa a kan Ramla, wacce take kicikinar mayar da hijjabinta, ya kalli abincin da yake gabanta ya kalli Hasana ya ce"Ke wai Hasana wace irin mace ce mai taurin kai?" Sai ta sha jinin jikinta ta sunkuyar da kai ƙwalla har ta kawo idonta, ya ce"Sau nawa zan faɗa miki ki daina dafa mai da yaji a cikin gidan nan? Ta ya zan dinga yin cefane mai kyau kina nunawa duniya gidana babu rufin asiri? Nama ya ƙare ba za ki sanar da ni ba?" Ita dai ta yi shiru cike da takaici, don rabon da ta ga nama tun na babbar sallah. Ya kalli Ramla ya ce"Wannan ƙawar taki don Allah ki dinga yi mata faɗa, wai idan kana da shi ba ka ci ba me za ka yi?" Ta ɗan yi murmushi ta ce"Gaskiya kam ba ta kyautawa". Ya ce"Tsakani da Allah fa! A ce za ka yi baƙuwa ka dafa garau-garau, alhalin ba babu ba ce, Ina zuwa". Sai ya fice. Hasana ta sauke ajiyar zuciya, suka cigaba da taɓa fira, kafin ta tashi za ta tafi, ta rako ta tsakar gida, sai ga shi ya dawo da ledoji a hannunsa, ya ce"A'a Ramla kike ko wa? Ba dai tafiya za ki yi ba". Ta ce"Tafiya zan yi baban Salim". Sai ya miƙa mata ledojin ya ce"Ga wannan balangu ne da lemo, wallahi mai kaji bai fara gasawa ba, ba zai yiwu a zo gidana a ci garau-garau ba, alhalin Allah Ya hore mini". Hasana ta san Ramla da kwaɗayi, ai kuwa babu musu ta karɓa har tana rusunawa, ta yi masa godiya. Ya ce"Maman Salim bari na koma kasuwa, yau ba na jin yunwar ma". Baƙinciki ya hana ta cewa komai, ta rufe ƙofar gidan, ta koma ta zauna tana jin zafi a zuciyarta, zuwa yanzu ta fara zargin Nura aljanun son mata gare shi, babu damar ta yi baƙuwa ya ƙyalla ido ya ganta sai ya ruɗe ya yi ta kaiwa da kawowa, yana siyayyar ƙarya wacce ita ba ya yi mata, ƙawayenta sun sha faɗa mata mijinta ya bi su gidansu yana son su daga haɗuwa a gidanta, wasu ma matan aure ne, sai dai idan ya bi su hanya su faɗa masa ba, shiyasa yanzu sam ba ta son ma ta yi baƙuwa mace indai ba ƴar'uwarta ta kusa ba ce, group ɗinta na makaranta duk ta fita saboda yadda ake yi mata habaici a fakaice kowa ya san mijinta na mamajo ne. 08028966015 [11/17, 9:28 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 2 Nura ya jima kafin ya dawo, sai da ta shiryar yara suka tafi islamiyya, sai ga shi ya shigo yana haɗe rai, Hasana da zuciyarta take a zafafe bayan ya zauna ta kalle shi ta ce"Baban Salim yanzu haka daga gidan su Ramla kake ko?" Sai kuwa ya haɗe gira ya fara zabure-zaburen borin kunya yana cewa"Ko kuma uwarta ba! Wai ke Hasana me kika mayar da ni ne? Yanzu rainin naki na lura kullum gaba yake yi ba baya ba!". Hasana ta ce"Ai na fi kowa sanin halinka shiyasa na faɗa, idan ba haka ba meye na siya mata balangu, bayan rabon mu da nama a gidan nan tun watandar sallah?" Ya fara jinjina kai, ya ce"Laifina ne, wallahi laifiina ne, saboda na fitar da ke kunyar ƙawarki ko?" Ta ce"Ka fitar da kanka dai, ko kuma na ce ka shigar da kanka, don na tabbata ko ba daga gidansu kake ba, to za ka je". Ya ce"Ai ke ba ki da hankali, bai kamata ma na biye miki ba". Ya juya zai fita, ta ce"Ka tsaya na kawo maka abincinka". A fusace ya ce"Ba zan ci ba". Ya fice yana ta mita da borin kunya. Ba ta wani damuwa ba, saboda Nura ya sabarwa da zuciyarta irin wannan ƙuncin, ta ci abinci ta yi wanka ta ɗauku wayarta, tana kunna data ta ga Ramla online, ta ɗaga mata hannu, ta ce"Ya kika je gida?" Ramla ta ce"Lafiya ƙalau, na gode fa sosai, kin gan ni nan ina cin balanguna hankali kwance". Hasana ta tura mata stikar dariya. Sannan ta ce"Yau kin samu ɗan rakiya ko?" Ramla ta ce"Mijinki yana da kirki wallahi, kin ga har gida ya kawo ni fa, ku dai Allah Ya taimake ku, mu ga mu a gida ba karatun ba, ba auren ba, aure mai daɗi wai har faɗa ake miki don nama ya ƙare ba ki sanar ba" Ta haɗa maganar da emojim dariya da mamaki. Hasana ta ce"Hmm! Ke dai Allah Ya ba ki na gari, auren wuri ba shi ne kwanciyar hankali ba, dace a gidan auren ko da an samu jinkiri shi ne". Ramla ta ce"Hakane" Sai ta kashe datar, dama ta so ta san Nura ya kai ta har gidansu ne ko a hanya ya ajiye ta, tun da ta ji ya kai ta tana da tabbacin zai koma, sai dai za ta zubawa Ramla ido ta ga za ta kawo mata labari ko za ta karɓi mijin nata, tun da har ga shi tana yabonsa, sannan ta ƙosa da zaman gidan dama, da wannan tunanin ta kai yammaci, sai dab da magriba ta tashi ta dafa farar taliya, don har yanzu bai aiko mata kayan miyan ba. Ana idar da sallah ya shigo, ya ce ta kai masa ruwan wanka, bayan ya gama ya zo falo ya zauna,yana ta faman danna waya, ta kawo masa taliyar, ya buɗe ya yi tsaki, ya fara ci, duk rabin hankalinsa a kan waya yake, haka kawai ta zargi da Ramla yake chart, ta ɗauki tata wayar ta kunna data, sai ta ga Ramla ba ta online, ta sauke ajiyar zuciya, amma har lokacin tana fargaba, ta rasa ya za ta yi ya daina janyo mata abun kunya irin haka, ana fara sallar isha'i ya tashi zai fice, yana cewa Salim"Sai na dawo". Salim ya ce"Daddy ina za ka tafi? Don Allah ka zauna yau kar ka fita". Ya yi dariya yana ɗaga Amir sama ya ce"Ai dole na fita, idan na zauna a gidan me zan yi Salim? Zuwa zan yi na gyara wasu abubuwa". Salim kuwa da surutu ya ce"Wani abu?" Ya ce"Kai yaro ne Salim, ina zuwa kar ka yi bacci ka ji?" Ya gyaɗa masa kai, Nura ya fice yana kiran waya, idan ya yi irin wannan fitar sai ya kai sha biyu har ƙarfe ɗaya, kullum sai ta yi bacci yake dawowa. Zuwa takwas da rabi yaran sun yi bacci, ta yi musu shimfiɗa a falo, ta yi musu addu'a, sannan ta rufe falon ta shige ɗaki, ƙofar gidan dama kodayaushe a rufe take, sai dai idan ya dawo ya saka mukulli ya buɗe, dayake tana da nauyin bacci ba kullum ba take jin dawowar tasa ba. Ta sauke Aiman daga bayanta ta kwantar, ta yi masa addu'a, sannan ita ma ta yi, babu jimawa bacci ya ɗauke ta, haka take yi kafin ƙarfe tara ta yi bacci, saboda babu ɗan fira. Yayin da Hasana ta saki baki take sharara bacci, shi kuwa Nura yana fita masallaci ya tafi sallar isha'i, bayan an idar ya hau babur ɗinsa ya tafi gidan su wata Hafsa, wacce ya karɓi lambarta tun shekaran jiya da ta zo shagonsa siyan kayan kwalliya, tun a ranar ya so zuwa, amma yana da wasu alƙawuran, sai yau layi ya zo kanta, Ramla ma ya je ganin gidansu ne kawai amma sai zuwa jibi zai koma. Fira sosai suka yi da Hafsa, wacce bai ɓoye mata yana da mata da ƴaƴa uku ba, sai dai ya faɗa mata sam bai yi dacen mace ba, Hafsa ta ce"Ikon Allah, amma dai auren wuri ka yi, wallahi ban yi zaton kana da aure ba". Ya yi wani murmushin ƙasaita ya ce"Wallahi da aurena, kawai dai tsabar tsafta ne da kula da kai, sannan kin san idan mutum yana cin guminsa yadda ya kamata ya ci mai kyau ya sha mai kyau, dole za a gan shi tsaf". Hafsa ta ce"Hakane" Don ita ta tsani kishiya, ba za ta iya auren mai mata ba, ta yi soyayya da masu mata wajen su uku, duk mammaƙo gare su, ba sa ɓarin kuɗi saboda hidimar gidansu ma ta ishe su, sai dai shi wannan ta ji yana zancen yana cin mai kyau. Nura ya ce"Wallahi Hafsa a hakan ma da kika ganni don ma dai ina da matsala ne a gidana, ban yi dace da mace ba, kin san ita rayuwa idan ka yi dacen mace ta gari wacce ta haɗa komai kamar dai ke ɗin nan, to fa har wata ƙiba kake yi". Hafsa ta ce"Kuna samun matsala da ita kenan". Ya ce"Idan kin ji matsala ɗaya kenan, matsaloli ne da yarinyar nan birjik wallahi, kin ga dai irin kayan kwalliyar da nake siyarwa, amma wallahi sai na yi wata ban ga hoda a fuskarta ba, kuma duk order da na yi sai na dara kai mata ta zaɓi kaya kafin na kasa a kasuwa, ɗinki duk wata sai na yi mata ita da yara, amma indai kin ga ta saka sabon kaya to fita za ta yi, nama a firji sai dai wani ya tarar da wani, amma idan ta kwaɓa girkin kare ma ba zai ci ba, gaskiya mata kuna da matsala, yawanci ku ne kuke saka mazanku ƙara aure". Hafsa ta ce"Wasu matan dai, amma ni yaushe zan samu mijin da zai yi mini komai na ƙi faranta masa?" Ya ce"To Allah Ya sa kakata ce ta yanke saƙa". Ta ce"Hmm! Idan da gaske kake ba". Ya ce"Kamar ya?" Ta ce"To ai na ga haka kuke masu matar nan, yawancinku kuna zuwa wajen zance ne don ku rage dare ba don aure ba, sai an ce ku fito sai ka ga wani matarsa ta fi ƙarfinsa, wani kuma gidan nasa ma da ƙyar ake cin abinci sau uku a rana, ba shi da halin ƙara auren, ni fa shiyasa ban fiya sauraron mai mata ba". Nura ya yi wata dariya ya ce"Baby Hafsa kenan, kin sanfa akwai maza, akwai muna maza, wallahi ni kam namiji ne a gidana, na fi ƙarfin gidana, sannan idan da yunwa a gidana a jikina za ki gani". Hafsa ta ce"A jikin matarka dai, ko tana da matsalar gyara jikinta na san tana cin abinci ta ci ko ba daɗi". Ya ce"To ni dai ki gwada ni ki gani, na tabbata ba za ki yi nadamar ɓata lokacinki ba". Ta ce"Zan yi bincike dai". Haka suka dinga fira, yana ta kushe Hasana, da ƙarairayi, don rabon davya ɗauki hoda ya ba ta kyauta har ta manta, ita yanzu sam babu kwalliyar ma a gabanta tun da ko ta yi ba ya ganin ƙoƙarinta ballantana ya yaba, sai dai idan ta yi wanka ta shafa hodar da man leɓe, don kanta ba dai don miji ba. Sai ƙarfe goma ya bar wajen Hafsa, ya zarce majalisarsu ta bakin titi, ana ta fita sai sha biyu ya koma gida, ya buɗe ya shiga, ya saka sakata, ya tura ƙofar falon ya shiga, yana haska yaransa, ya gyara musu kwanciya, don ɗaya ya ɗorawa ɗaya ƙafa, sannan ya shiga ɗakin, ya canza kaya ya hau gadon, ya haska Hasana da take ta sharar bacci, Aiman a kusa da ita, ya taɓe baki ya kwanta, a yanzu ba shi da burin da ya wuce ya ƙara aure, yana buƙatar ƴar sawalwala wacce dare yana yi zai ji yana ɗokin dawowa gida su sha soyayya, babu ciki babu goyo babu yaran da za a jira su yi bacci. ******* Ƙarfe takwas da rabi wayar Nuratu ta fara ƙara, ta duba ta ga lambar ce daga Saudiya, ta san Abdul ne mai kira, don yana aron wayar mutane ya kira ta idan ba ta hau online ba, saboda ba kasafai yake saka kati ba, Abdulmalik mutum ɗaya da take gani a matsayin sanyin idaniyarta bayan mahaifiyarta, ta san bai ji rasuwar da wuri ba shiyasa bai kira ta ba, ta ɗauki wayar da sallama, ya amsa, sannan ya ɗora da faɗin"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!". Nan ta ji wani sabon rauni ya taso a zuciyarta, ta fara kuka, ya ce"Ashe Mama lokaci ya yi" Sai ta kasa magana. Ya ce"Ki yi haƙuri Nuratu, duk mai rai mamaci ne dama, Allah da Ya ɗauke ta ya fi mu son ta..." Cikin kuka ta ce"Yaya Abdul ina buƙatar Mama a rayuwata, ina buƙatar uwa, yanzu da wa zan zauna a wannan bahagon gidan namu mai cike da takaici kala-kala?" Ya girgiza kai kamar tana ganinsa ya ce"A'a kar ki sake faɗar haka, Mama ba ta yi gaggawa ba, mu ma wataƙil yau ko gobe ne, duk mai rai gawa ne shi a tafe. Sannan Allah Yana sane da yanayin gidanku Ya ɗauke ta ɗin ya bar ki, sai mu bar hakan a matsayin wata jarabawar rayuwa Allah Ya ba mu ikon cinyewa". Hawaye mai zafi suka fara tunkuɗo juna daga idonta, Yaya Abdul ɗinta ne kaɗai mai mai da damuwarta tasu su biyu, sai dai wannan ƙaddarar da ta afka a dare ɗaya ta dalilin inganta rayuwarsa, sai dai tana zargin hatta shi Abdul ɗin ba zai iya karɓarta ba, da wane idon za ta kalle shi idan ya gane tana da ciki? Ina zai saka kansa a ranar? Ta fi kowa sanin zafin kishin shi, shiyasa yake tsaye tsayin daka a kan ƙananun buƙatunta wanda ba su gagare shi ba, ko wannan tafiyar da ya yi dominta ne, yana can yana bauta don ya tara kuɗin aurensu, kuma ya samu jarin da zai riƙe su, don su yi rayuwa mai inganci. Suna cikin waya ta ji muryar Baba yana ƙwalla mata kira, ta yi saurin cewa Abdul"Ina zuwa ka ga Baba yana kira". Ya ce"To ki yi masa gaisuwa, anjima zan sake kira". Kafin ta fito Baba har ya bankaɗo labulen yana cewa"Wai uwar me kike yi ne da kika share ni?" Ta fito jiki ba ƙwari tana cewa "Gani nan Baba". Ya ce"Ga Alhaji can a zaune, sai ki je ku tattauna". Ta ce"To". Ta bi bayan Baba, ta tarar da Alhaji Hashimu tsaye yana danna waya, ta tsaya tana kallon fuskarsa da wayar ta haska, babban mutum ne zai doshi shekara sittin, sati biyu kenan da haɗuwarsu, ya kawow malamin makarantarsu sadaƙar da yake kawowa duk wata, ya ganta, a ranar sai ga Malaminsu wato shuganan makarantar ya zo har gida wai an aiko shi, ya zo neman alfarma, ya faɗa mata Alhajin yana sonta, kuma matansa uku, nauyi da kunyar Malam Isma'il bai hana ta faɗa masa tana da wanda take so ba, don haka Malam ya samu Baba ya faɗa masa, a ranar Baba faɗa kamar zai ari baki, ya ce dole kuwa ta manta da kowa ta aure shi matuƙar da gaske yake, duk kuwa da kafin Abdulmalik ya bar ƙasar nan sai da iyayensa suka zo suka yi magana akan bayan shekara biyu zai dawo sai a yi auren, a lokacin Baba murna ya dinga yi, saboda yana ganin Abdul zai tara arziƙi kafin shekara biyun, amma bayan zuwan Alhaji Baba har yana cewa"Wane shirmen banza ne ki zauna jiran wanda ya tafi Saudiya? Ai sai ya shekara goma bai dawo ba, idan ya dawo ma ya ce kin tsofe ya samu wata ya aura, don haka ba za a yi wannan shashanci da ni ba". Mama ta yi iya yinta don a bar zancen Alhaji Baba ya kafe, tijarar safe da ban ta dare da ban, har ƙarar Mama ya kai wajen yayyunta tana hurewa ƴarsa kunne, shi ne ta ce kawai Nuratu ta haƙura ta aure shi, to a nan ne fa ta sanar mata zancen cikin jikinta, wanda ta same shi silar taimakon Abdul. 08028966015 [11/18, 1:06 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 3 "Barka da fitowa". Muryar Alhaji Hashimu ta dawo da ita nutsuwarta. Ta ce"Ina wuni". Ya ce"Lafiya lau, sannu Nuratu ya haƙuri?" Ta ce"Da godiya". Ya ce"Allah Ya yi mata rahma Ya sa aljanna makoma, sai ki yi ta haƙuri kin ji ko?" Ta amsa da amin, suka yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce"Kin ci abinci dai ko?" Ta yi banza da shi, ya sake cewa"Me kike son ci? Kar damuwa ta saka ki zama da yunwa, sai ya haifar miki da wani ciwon, na zo miki da abinci ki daure ki ci". Ya ƙarasa yana miƙa mata babbar ledar da take hannunsa, ba ta karɓa ba, kuma ba ta ce komai ba, sai hawaye da suke ta gudu a fuskarta. Ana haka sai ga sallamar baƙi gidan, suka wuce su a zauren bayan ta gaishe su, sarai ta gane Umma ce mahaifiyar Abdul, tare da abokiyar zamanta, sai ƙanwarsa, su ma kuma sun gane ta, don da fitila a hannunsu suka shigo zauren, gabanta ya dinga faɗuwa, saboda tana fargabar Abdul ya ji labarin an ganta da wani, ga shi mutanen da ba ta isa ta ce masa ƙarya suke yi mata ba ne suka ganta, duk hankalinta ya yi cikin gidan, ta ce masa"Zan shiga gida". Ya ce"To Allah Ya ƙara afuwa, ga wannan ki karɓa ki ci, da kuɗi a ciki ko za ki yi wata buƙatar, sannan duk abin da kike buƙata don Allah ki sanar mini, babu abin da ba zan ba ki ba, Allah Ya ji ƙan Mama Ya sa ta huta". Ta amsa da amin, ya ba ta ledar ta karɓa ta yi cikin gidan, ta samu su Umma a tabarmar da ke tsakar gida tare da su Mama Asabe, suna mai da yadda mutuwar ta kasance. Ta duƙa ta sake gaishe su, suka amsa suka yi mata gaisuwa cike da tausayawa, Mama Karime da ta ƙyalla idonta a kan ledar ta ce"Kina zaune ke kaɗai a ɗaki, sai mutuwar ta dawo miki sabuwa ai, ki wuce ɗakina ki kwanta, bari na aika a samo miki ko kunu ne". Ta ce"To" Ta shiga ɗakin nata. Sai Zainabu ƙanwar Abdul ta tashi ta bi bayanta, Khadija da Hannatu suna kwance a ɗakin, ta zauna tana ajiye ledar, Zainabu ma ta zauna ta miƙa mata ledar da ke ƙunshe a hijjabinta tana cewa"Yaya Abdul ya ce na kawo miki" Sai ta ɗakko wayarta ta danna ta kunna mata voice, sai ga muryar Abdul ɗinta ta bayyana, daidai inda yake cewa"Nuratu ga saƙona nan, jikina ya ba ni ba ki ci komai ba wunin yau, na yi nisan da zan ba ki wata kulawar da ta dace, amma ga ƙanwata nan a madadina, idan a baki kike so sai ta ba ki, don Allah ki ci wani abun". A nan maganar ta ƙare, Zainabu ta miƙa mata ledar, bayan ta ciro yougurt ta buɗe ta matso ta kai mata baki, Nuratu ta yi guntun murmushi ta ce"Wato Zainabu biye masa za ki yi ko?" Tana dariya ta ce"To ai ni ƴar aike ce". Nuratu ta karɓa ta fara sha, ta sha kusan rabin jarkar, daidai sanda su Umma suke cewa Zainabu ta fito su tafi, Nuratu ta ji cikina ya fara hautsinawa, yawu ya taru a bakinta, da sauri ta fita tsakar gida ta fara kwarara amai, suna ta yi mata sannu, Zainabu tana cewa daga shan yougurt, Mama Asabe ta ce"Ƙila don ta jima ba ta ci komai ba ne, sannu Nuratu kin ji" Ta gyaɗa kai, ta gyara wajen ta koma ɗaki, su kuma suka yi musu sallama suka tafi. Tana shiga ta kwanta, a kan sallayar da take wajen, Mama Asabe ta shigo tana yi mata sannu, ta ɗauki yogurt ɗin tana cewa ke ma ai ba za ki sha abu mai sanyi ba yanzu, tun da ƙila rabonki da abinci tun jiya, ta ce da Kadija"Dije tashi ki siyo mata kunu, ko ruwan bunu a wajen Mati mai shayi". Nuratu ta ce"Gara ruwan bunun Mama". Khadija tana fita, Mama ta janyo ledar wajen Zainabu, ta ga wani yougurt ɗin ne, da lemuka biyu, sai shawarma guda biyu, ta janyo ta wajen Alhajin, ta fara cin karo da ƴan ɗari biyar biyar a dunƙule, ta faki idonta ta soke su a zani, ta duba sauran kayan, har da kayan shayi, da biredi da manyan biskit ga kuma kaza da lemo babba, ta jinjina kai ta ce"Lallai ana gatale ki Nuratu". Nuratu saman ɗakin kawai take kallo, ta yi nisa a duniyar tunani, Mama ta ce"Wai ni kam dama babanki bai raba ki da Abdul ɗin nan ba?" Nuratu ta ce"Mama ni fa wannan Alhajin dole sai dai ya haƙura". Mama ta ce"Hmmm! Yaro man kaza, lallai kina da ƙarancin hankali Nuratu". Ana kawo shayin Mama ta ɗakko kofi ta haɗa mata mai kauri, ta sha, sannan ta ci shawarma guda ɗaya, ta ba su sauran, kayan shayin da biskit kuma ta ɗauka ta tafi ɗakinsu, Mama tana cewa ta kwana a nan ta ce a'a. Ta shiga ta zauna, kawai sai ta fara kuka, ga ta yau za ta kwana ita kaɗai babu Mama, wayarta ta yi ƙara, ta duba ta ga Abdul ne, ta ɗaga a sanyaye, ko gaisawa ba su yi ba ya ce"Nuratu wane ne wanda kuke tsaye ɗazu?" Ta sauke numfashi tana lumshe ido, da tunanin ta inda za ta fara yi masa bayani. Ya ce"Kar ki yi mini ƙarya". Ta ce"Wani ne, sunan shi Alhaji Hashimu, yana sona ne, ya fara zuwa sati biyu da suka wuce..." Ya katse ta da faɗin"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!" Sai ya kashe kiran ba tare da ya ce komai ba. Ta bi wayar da kallo, ta so ya tsaya ta ƙarasa, ta yadda za su fahimci juna, dama ta sani za a yi hakan, ga shi ba ta da katin kiran wata ƙasar, sai ta kunna data, ta kuwa ganshi online, ta yi masa voice ta faɗa masa komai tun farkon haɗuwarsu, ya duba bai ba ta amsa ba, ta yi ta jira har ta gaji, ta kashe data, ta saka sakata a ɗakin ta kwanta, tana jin wani abu mai kama da tsoro tare da kewar mahaifiyarta, sai ta kasa baccin, sai hawaye da suka ƙi tsaya mata. Haka ta yi bacci rabi da rabi, saboda kewar mahaifiyarta. Da asuba bayan ta idar da sallah ta kunna data, duk yawan saƙonnin da suke tururuwar shigowa na Abdul kawai ta kai hannu ta buɗe, "Ba zan fahimce ki ba Nuratu sai na kammala bincike a kanku. Fatana dai kar ki manta da alƙawarinmu, ke kaɗai ce macen da nake ƙauna da fatan aurenta duk duniya Nuratu, kar ki butulce mini". Abin da ya rubuto mata kenan, a maimakon ta ji daɗi irin yadda ta saba a yau sai zuciyarta ta yi rauni, ta fara hawaye. Ta koma ta kwanta tana jin yadda gidan nasu ya kaure da hayaniya, da alama har kowa ya cigaba da sana'arsa kenan, kwana ɗaya bayan mutuwar mahaifiyarta, kodayake idan ba su cigaba da nema ba, waye zai ba su abin da za su ci? Sai a lokacin ta ɗan samu bacci ya ɗauke ta sama-sama, Mama Karime ce ta shigo ta tashe ta, ta tashi zaune tana gaishe ta, Mama ta amsa tana cewa"Sannu Nuratu, kin karya?" Ta girgiza mata kai alamar a'a. Mama ta ce"Fito ki karɓi koko da fanke ga shi na rage miki". Ta ce"Idan da ruwan shayi dai zan karɓa". Ta tashi ta bi bayanta, tana jin yadda sanyi yake ratsa ta, saboda zazzaɓin da yake jikinta. Ƴan'uwa da maƙota ɗaiɗai ana ta shigowa ana yi mata gaisuwa, daidai lokacin Abdul ya kira ta, ta faɗa masa zazzaɓi take yi, ya ce zai turo abokinsa ya ɗauke ta su tafi asibiti, ta ce a'a ya bar shi, ya ce to zai turo Isa ya duba ta, Isa shi ma abokinsa ne, yana da chamest a ƙasan layinsu, ta ce kawai ya bar shi za ta sayi maganin zazzaɓin, suka yi sallama, saboda ba ya son jan magana. Suna gama wayar ta tuna jiya Alhaji ya ce da kuɗi a ledar nan da ya ba ta, sai ta ɗakko ta dudduba, ba ta ga alamar kuɗi ba, sai ta raya ko mantawa ya yi bai saka ba, ta san halin gidansu da sata, amma yanzun ba ta kawo wata ce ta ɗauka ba, to idan ma ɗaukar aka yi, ita yanzu ba ta su take yi ba, ta koma ta kwanta. Wajen azhar tana zaune tana cin abincin da ƙanwar Mama ta kawo mata, sai ga Isa ya zo da leda har da ruwa wai zai saka mata, Baba yana ƙofar gida Isa ya gaishe su, ya shige, don haka ya biyo bayansa, daidai sanda Nuratu ta fito tsakar gida. Baba ya ce"Kai yaro lafiya wajen wa ka zo?" Ya ce"Baba aiko ni aka yi zan duba Nuratu". Baba ya ce"Ikon Allah! Kai kuwa yaro wane hamshaƙin ne ya aiko ka?" Ya ce"Abdul ne saurayinta". Baba ya ce"Ka ce dai tsohon saurayinta, to wuce ba ta buƙata, sannan ka faɗa masa kar ma ya sake asarar kuɗinsa a kan matar da ba ta shi ba, ni na riga na ba da ƴata ga wanda ya dace, lokaci kawai muke jira, ba don mutuwar nan ba ma, da a cikin satin nan za a tsayar da rana". "Ok" Isa ya faɗa yana juyawa ya fice daga gidan. Nuratu da duk ranta ya gama ɓaci, ta ce"Haba Baba..." Ya ce"Buhun ubanki! Ba ki da lafiya shi ne ba ki faɗa mini ba? Duk duniya yanzu kina da wanda ya fi ni ne?" Ya ja tsaki, ya ciro waya, ya yi danne-danne ya kara a kunne, can ya washe baki ya ce"Wa alaikumus sallam, Alhaji ina kwana?" Alhaji dake zaune tare da matarsa tana zuba masa abinci ya amsa da"Lafiya lau Baba, ya ƙarin haƙuri?" Baba ya ce"Da godiya. Wallahi Alhaji dama mutumiyar taka ce dama babu lafiya, wallahi zazzaɓi jiya ba mu yi bacci ba, shi ne na ce to bari a sanar maka..." Alhaji ya ce"Subhanallah! Bari yanzu zan aiko sai a ɗauke ta a kai ta asibiti". Daga nan sai Baba ya dinga jera godiya, har yana rusunawa kamar yana gabansa. Ya kalli Nuratu ya ce"Tafi ki shirya, zai aiko a kai ki asibiti yanzu, ai ke dai Allah Ya dubi maraicinki da ya kawo miki wannan bawan Allah mai karamci". Nuratu da ta shiga tashin hankali, ta marairaice ta ce"Baba ɗan zazzaɓi ne fa, ni ba sai mun je asibiti ba". Baba ya ce"Ai ke shashasha ce, har ki samu mau jiɓantar lamarinki amma ki tsaya shashanci, maza shirya". Ta shiga ɗaki, ta zauna, sai ta fara hawaye, ta san manyan asibitocin nan da ƙirƙire-ƙirƙire, tsoronta ɗaya kar a ce za a yi mata wani gwajin da zai fallasa sirrinta. Babu jimawa Baba ya shigo ya ce ta fito su tafi, yayarta Rahma ƴar Mama Karime tana tsakar gida Baba ya ce"Ke Ramatu wuce ki raka su". Har da saurinta ta sako hijjabi, suka fita, Nuratu tana jin kamar ta ce ba za ta je ba. Har da buɗe mata murfin motar, ta shiga ya ja suka ɗauki hanya. Dab da asibitin ta ga wani babban chamest, ta ce"Bawan Allah kawai ka tsaya ka siya mini magani a nan, ba dole sai an je asibiti ba". Ya ɗan yi jim, sannan ya ce"To Hajiya ai ni umarni nake bi, sai dai na tambayi Alhajin, duk yadda ya ce". Ta ce"To ka faɗa masa jikin da sauƙi sosai, magani ma ya isa". Ya faka motar, ya ɗakko waya ya kira Alhaji, ya yi masa bayanin da Nuratu ta yi, Alhaji ya ce kawai ya wuce su tafi asibiti, idan ma maganin ne su ba ta a can". Ba ta sake cewa komai ba, har suka ƙarasa asibitin. Tun kafin zu je Alhaji ya yi magana da likita, don haka kai tsaye direban ya rakata inda ya kwatanta masa, ta zauna a kujera sai raba ido take yi, hannunta yana dafe da mararta ta cikin hijjabi, gani take kamar likitan yana kallonta zai gane tana da cikin. Ya tambaye ta me yake damunta? Ta ce"Zazzaɓi ne kawai kuma ya riga ma ya sauka tun a hanya". Ya ce"Ma sha Allah! Amma Alhaji ya ce ko abinci ba kya ci, ya ce a saka miki ruwa saboda ki samu ƙarfin jikinki, sannan zazzaɓin ƙila malaria ce, za mu yi miki gwaji mu gani". Ƙirjinta yana ta dukan uku-uku ta ce"Likita, ni fa ina jin ƙarfin jikina, kawai ku ba ni magani ya isa". Likita ya yi murmushi, don ya sabada mara lafiya mai gardama, ya ce"Ki yi haƙuri Hajiya, a yi miki yadda ya dace kawai". Ya tura su wani ɗakin, wajen wata nurse, ita ta ɗibi jininta, sannan aka saka mata ruwa ta kwanta gabanta yana ta faɗuwa, tana ayyana ƙila yau ce ranar ƙarshe cikin ranakun farincikinta na gidan duniya. A ɓangaren likita bayan sun fita sai ga kiran Hajiya Laila, uwar gidan Alhaji, suka gaisa ta ce"Doctor yarinyar da aka kawo daga wajenmu me yake damunta?" Ya ce"Yanzu dai za a duba, zazzaɓi ne take yi, sai rashin ƙarfin jiki, an tafi saka mata ruwa". Ta ce"Ok, don Allah kar ka bari ta tafi, sai ka samu adireshinta ko lambar waya, ka ajiye mini account deteils ɗinka". Ya ce"An gama Hajiya godiya nake". Suka ajiye waya. 08028966015 [11/20, 9:35 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 4 Sakamako yana fitowa likitan Hajiya Kubra ya fara kira, ya sanar mata yarinyar ciki ne da ita na sati tara, sai kuma malaria. Hajiyar ta yi murmushi ta ce"Idan ka tashi sanar masa ka ƙara da cewar tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki". Likita ya amsa, amma a zuciyarsa yana ta auna yiwuwar hakan, domin babban laifi ne, har a cikin aikinsu, sannan yana gudun Alhaji ya bincika ya gane ba haka ba ne. Har allurar bacci Alhaji ya sa aka yi mata, don ta samu hutu, ba ta san tsayin lokacin da ta ɗauka tana bacci ba, ta dai farka ne kawai ta ga Mama Karime zaune a kan sallaya, gefen gadon da take kwance, gabanta ya faɗi, ta tashi zaune, har an cire ƙarin ruwan, Mama Karime ta ce"Sannu Nuratu kin tashi?" Sai ta kasa amsawa, kallonta dai take yi, tana son karantar fuskarta, don ta samu wani haske a kan zargin da take yi na fallasar sirrinta, sai dai ba ta ga komai a fuskar Mama ba, ta ce"Mama ba su sallame ni ba?" Ta taɓe baki ta ce"Jira suke ki tashi, amma ke wannan gadon asibitin ai a yanzu sai ya fi yi miki daɗi fiye da gidanku". Gabanta ya faɗi, tana rabon ido ta ce"Mama saboda me?" Ta ce"Saboda cikin jikinki, da ƙyar aka fitar da babanki daga asibitin nan, don cewa ya yi sai ya kashe ki, da tuni sai dai ki farka ki ji ana man Rabbuka?" Bugun zuciyarta ya tsananta, tuni tsoro ya dirar mata, ba ta sake shiga tashin hankali ba sai da Mama ta cigaba da faɗin"Babban abun damuwar ma asirinki ya tonu, don na san zuwa yanzu maganar nan ta fantsama cikin gari, tun da a gaban Zainabu aka yi komai". "Innalillahi! Me ya kawo ta?" Ta tambaya tana sakin kuka. Mama ta ce"Ta je gida kai miki abinci, aka faɗa mata kina asibiti, dama lokacin babanku ya ce gado aka ba ki, na ce ya kamata na bi ki, shi ne ta ce mu tafi tare, shigowarmu ke da wuya, muka samu ana kokowa da babanki. Nuratu kin ba mu mamaki, ba ki kyautawa Salamatu ba". Ta ƙarasa a raunane. Ta kifa kai a cinyarta ta rushe da kuka, shikenan asirinta ya tonu, abin da take ta ɓoyewa yau ya fito fili, tunani take yi yanzu ya za ta yi? Wane bayanin za ta yi musu su fahimce ta? Da wane idon za ta kalli Abdul? Sannan idan ta faɗa masa dalilita zai yi mata uzuri kuwa?" "Ina wayata?" Ta tambayi Mama. Ta ɗakko ta miƙa mata, ta danna ta ga ƙarfe takwas da rabi na dare, ta sakko daga gadon, ta shiga banɗaki ta yo alwala, ta fara jero salloli, lafin ta idar Mama ta zuba mata abinci, ta miƙa mata tana cewa"Wannan abincin duk Alhaji ne ya aiko miki, wallahi Nuratu kin yi asarar miji kamar shi, don kuwa shi ma zuwa yanzu ya samu labari, ai da mutunci ma, idan wani ne na tabbata korar kare zai sa a yi mana daga asibitin". Nuratu ta fara cin abincin a hankali, tana hawaye. Mama ta cigaba"Idan kuma Allah Ya tarfa wa garinmu nono sai ki ga duk da hakan bai janye ba, tun da wasu suna sane ma suke auren karuwa, saboda huce takaici ta wani ɓangaren". Sosai surutun Mama ya dame ta, saboda tana ruguza mata lissafin da take yi ta tafkawa a zuciyarta. Fatanta dai a ce yau a asibitin za ta kwana, indai lissafin da ta yi yanzu ya tafi daidai, to a tasha za ta kwana, washegari ta bar garin. Ƙarfe tara da ƴan mintuna, sai ga direban ɗazu da ya kawo su, ya shigo ya ce"Hajiya za mu tafi, in ji Alhaji". Nuratu ta ce"Sun sallame ni?" Ya ce"E". Ya kwashi kanukan abinci ya wuce gaba. Mama ta ce"Sai ki tashi mu wuce, ƙiyamarki ta tsaya cak yau". Wani sabon kuka ya zo mata, duk nuƙu-nuƙun da ta tsaya yi don Mama ta yi gaba, abun bai yiwu ba, haka ta saka ta a gaba suka shiga mota, a ciki suka tarar da Alhaji Hashimu, sai kunyar duniya ta rufe Nuratu, duk da ba son shi take yi ba, amma ba ta so a ce zai yi mata kallon mara tarbiyya ba, haka motar ta yi tsit har suka ƙarasa gidan. Baba da abokansa biyu suna zaune a ƙofar gidan, ya taso da sauri ganin motar Alhajin, sai dai Nuratu tana fitowa ya gimtse fuska, yana huci. Wani mugun haushinta yake ji, gabaɗaya ta canza masa lissafi. Suka shiga daga ciki, a zaune Alhaji ya ce su tsaya, Nuratu za ta wuce ya ce ita ma ta tsaya, ta dawo ta tsugunna kanta a ƙasa tana hawaye. Baba ya ce"Don Allah Alhaji ka yi haƙuri, wallahi da na san da wannan badaƙalar a jikinta da ban yi maka alƙawari ba, ɗan yau ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba!". Alhaji ya ce"Na sani, kuma a yadda na samu labarin tarbiyyar Nuratu na san wannan ƙaddara ce, kar ku damu, ni tsakani da Allah nake son yarinyar nan, musamman yanzu da wannan ƙaddarar ta faru da ita, na san rayuwarta za ta iya shiga garari, saboda Baba ni na ji na gani, zan aure ta na kau da ido a kan komai, da an cire cikin shikenan". Baba ya fara jero godiya har da kukansa, Alhaji yana cewa "Babu komai". Sannan ya yi wa Nuratu nasiha sosai, tamkar tsakanin uba da ƴarsa, har ta ji a ranta wannan mutumin ƴaƴansa sun yi sa'ar uba, ba kamar ita ba, ya ƙara da roƙon Baba kan kar ya ce zai dake ta, ko wani hukunci, addu'a ita ce kaɗai mafita, daga haka ya tafi, ita ma ta shiga gida, ta saka sakata a ɗaki, duk bugun da Baba ya yi ba ta buɗe masa ba. Ba ta taɓa zaton mutumin nan zai ce zai aure ta a hakan ba, ta san auren nasa rufin asirinta ne, amma ya za ta yi da soyayyar Abdul ɗinta? Sai ta ɗakko wayarta, ta yi masa sallama ta whatsApp, yana online bai duba ba har tsawon mintuna, sai ta danna voice, sai dai ta kasa cewa komai, har tsawon sakan goma, sai ta sake shi a hakan ya tafi, wannan karon da wuri ya duba, bai ce mata komai ba, ta ajiye wayar ta kwanta. Can tsakar dare kuma ta tashi ta fara haɗa kayanta a wata tsohuwar akwatin Mama, wanda ta bar mata ita, kayanta ne dama a ciki, ta saka komai ta ajiye ta tsaf, sam ba ta runtsa ba, kiran sallar farko a kunnenta, ta fito a hankali, tana jan akwati ta fice daga gidan a hankali, ta karo ƙofar, ta fara sauri don gudun wani ya biyo bayanta, tafiya mai nisa ta kai ta tasha, ta tarar da tsirarun mutane, ta zauna ta fara hawaye tana fatan Allah Ya sa a karɓe ta a inda za ta je, sannan ta samu buta, ta yi alwala ta yi sallar asuba wanda har an kusa idarwa. Ta faɗawa kwandasta Kaduna za ta je, aka saka ta a motar, ta yi zaune tana jira ta cika, zuciyarta tana ta dukan uku-uku. A daidai lokacin ne kuma Mama Asabe ta leƙa ɗakinta, ta ga ba ta nan, nan ta hau cikiya a tsakar gida, kowa ya fito ana jajantawa. ******** Misalin ƙarfe goma Nura ya kira Hasana a waya, tana ɗagawa ya ce"Ke maza ki buɗe wannan ɗakin ki share shi tass! Gani nan zuwa". Ta san dai ɗakuna uku ne a gidan, ciki da falon da take ciki, sai kuma falle ɗaya, wanda take saukar baƙinta, da kuma keken ɗinkinta a ciki, ta san shi yake nufi, amma hakan bai hana ta tambayarsa ba"Wane ɗakin?" Ya ce"Wannan wace irin tambaya ce? Ɗayan ɗakin nan dai, da kike saka shirgi, ba na so na zo na tarar da komai a ciki". Ta ce"To saboda me? Yanzu ina zan kai keken nawa?" Ya ce"Wannan kuma ya rage naki, idan za ki kai shi bola zan taya ki". Ya kashe wayar. Ta zauna tana mamakin me zai saka a cikin ɗakin? Ta san halinsa yanzu sai ya zo ya fara yi mata hayaniya, don haka ta tashi, ta fito da komai, ta share kamar yadda ya ce, ta janyo ƙofar ta koma ɗakinta, can anjima sai ga shi yana shigo da kaya, katifa ce madaidaiciya, da kayan kallo, har da ƙaramin firji, ta cika da mamaki, tana tsaye ya fara shiga da kayan yana ƴar waƙarsa, da alama yana cike da nishaɗi, ganin ko kallo ba ta ishe shi ba, sai ta shige ɗakinta, tana jira ya gama ta ji bayanin da zai yi mata. Ai kuwa yana gamawa ya ƙwala mata kira, ta fito tana amsawa, ya ce"Shigo mana". Ta shiga tana ƙarewa ɗakin kallo, ya ce"To yanzu saurana sif, zan sa a yi mini sif mai biyu ƴar madaidaiciya haka, wacce zan zuba kayana a ciki, kin ga komai na zai zauna lafiya, idan zan fita na rufe ɗakina shikenan". Da mamaki ta ce"Kamar ya ɗakinka? Au wai nan turaka ce ka ware kenan?" Ya ce"Ai ya wuce wai, ni na gaji da yadda nake bacci rabi da rabi, yara su hana ni bacci su hana ni sakat, tsakar dare a farka a yi ta kuka, don haka na ware ɗakina". Hasana ta ce"Baban Salim kenan! Kuma ban da abunka na ga dai yaran nan naka ne, sannan abu ba na farko ba, ba na biyu ba ai ya kamata zuwa yanzu a ce ka saba, kuma ma yanzu don ka yi hakan ai ba shi zai hana ka jin kukan Aiman ba, tun da dai ka san ba zan zo na kwana a nan na baro yaro ƙarami mai shan nono ba, dole da shi zan dinga tahowa". Nan take fara'ar fuskarsa ta gushe, ya ce"Ki taho ina? Wai kina nufin saboda na ware ɗaki sai ki kwaso jiki ki biyo ni? Kenan ma na gudu ban tsira ba! A'a ba zai yiwu ba, ki yi zamanki da yara, ni duk sanda na buƙace ki zan kira ki, amma gaskiya ba don mu tare mu biyu na ware ɗakina ba". Ta ce"To shikenan!" Ta juya ta fice, ranta bai so ba, sam ba za ta samu nutsuwa ba, saboda zarginsa da take yi ne zai ƙaru sosai, haka kawai ma tsakar dare farkawa take yi ta ga ba ya ɗakin, sai ta ji shi a tsakar gida yana waya, ko ta gan shi a falo yana vedio call, sai ya ganta ya yi tsaki, ya koma ya kwanta, to ina ga kuma ya ware ɗakinsa shi kaɗai? Tabbas zai ci karensa babu babbaka kenan, ta san ba ta isa ta ja da shi ba, amma kuma za ta yi iya yinta ta saka masa ido, don ganin bai kauce hanya ba, don haka ta ayyana bacci da ido ɗaya ya kama ta. Haka ya wuni yana shige da fice, ya saita kayan kallo tsaf, dama akwai babbar setilait a tsakar gidan, tun da risibarsu ta lalace take ajiye kawai, bai kai musu gyara ba, yanzu sai ya sa aka saita da sabuwar risibar da ya siyo, firji ma nasu ya lalace bai kai gyaran ba, don ya ce ya gaji da gyarawa suna lalatawa, ita kuma a ganinta tsufa ya yi, tun da tun na aurenta ne, shekararsa takwas kenan. Ya ɗakko yara daga makaranta, suna zaune suna cin abincin rana, yake cewa"Ma sha Allah! Ɗakina ya haɗu, yanzu mun yi magana da wani kafinta, zuwa jibi sif ɗina za ta zo, sai na samu ɗan kafet, na saka a tsakiyar ɗakin, ina ga ma sai na sayi senta tebur". Hasana ko kallonsa ba ta yi ba, saboda takaici duk ya ishe ta. Ya cigaba da cewa"Yadda tsarin gyaran ɗakin zai kasance, da safe idan na gama shiryawa, ina zaune ina karyawa, ke kuma sai ki shiga ki gyara, idan zan fita na rufe abuna, salun-alun karatun yankan jaki". Har yanzu dai ba ta ce komai ba. Sai ya ajiye kofin hannunsa yana haɗe gira ya ce"Wai ni Hasana me kike nufi ne? Ya ina magana kina manna mini hauka? Ko hassada kike yi da ɗakin nawa?" Ta ce"Hmm! A kan me zan yi maka hassada? Kawai dai gani na yi tsarin kamar bai yi ba, a ce kana da mata ita tana ɗakinta, kai kana naka, wai sai ranar da ka kira ta? Ka manta sai ka yi wata ba ka kira ni ba?" Ya ce"To mene ne? Ke ba hutunki ba ne ba ma? Ki sake a ɗakinki, na sake a ɗakina". Salim Ya ce"Abba wane ɗakin?" Gwab! Hasana ta buge bakin yaron, tana cewa"Ban hana ka saka mana baki a magana ba? Waye sa'anka a nan?" Sai kuwa Nura ya hartsuƙo kamar zai dake ta, yana cewa"Kar ki sake ki ƙara dukan shi, saboda ya tambaye ni? Da ke yake? Ba ki iya komai ba sai shirme!". Ya tashi yana ɗaukar mukullin babur ɗinsa ya fice zuwa tsakar gida, yana kiran Salim ɗin, ya je ya buɗe masa ɗakin suka shiga, sai da ta ga za su yi lattin islamiyya sannan ta leƙa tana cewa"Ku zo ku tafi makaranta". Salim Ya noƙe kafaɗa yana cewa"Daddy ni yau ba sai na je ba". Hasana ta ce"A kan me? Ai kuwa ya zama dole ka je!". Nura ya ce"Ƙyale shi, ƙila ya gaji ne". Ta juya ta koma ɗaki, tana jin sanda suka fita, ya siyo musu biskit ya dawo da su, tana zaune ranta a ɓace, saboda ta gaji da yadda yake ɗaurewa yaran akan rashin son karatun addini, ya ce"Ki biya musu karatun, tun da ba su samu zuwa ba". Ko kallonsa ba ta yi ba, ya fice daga gidan. Ta ja kunnen yaron ta murɗe tana cewa"Idan ka girma za ka gane ba gata yake yi maka ba!". Ƙarfe sha biyu na dare, Hasana ta kasa bacci, tana tunanin me Nura yake yi a halin yanzu? Ya yi bacci, ko yana ta waya da ƴan mata? Tunanin ya kasa barinta, don haka ta tashi, ta saka hijjabi, ta buɗe ƙofa a hankali ta fito, ta je daidai windon ɗakin ta leƙa, ta kuwa hango shi zaune ya yi ɗaiɗai a kan katifa, yana ta danna waya, wani abu ya zo ya dunƙule mata ƙirji, kamar ta buga masa ƙofar, sai kuma ta ga me ma za ta ce masa? Ta daɗe tana kallonsa ba tare da ya sani ba, sannan ta juya ta koma ɗaki, ta kwanta, sai ta ji ɗakin ma yau ya mata girma, gadon ya yi mata faɗi, duk da dama yawancin daren da bacci suke raya shi, amma duk ranar da ba ya nan tana jin babu daɗi. 08028966015 [11/20, 3:36 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee PAGE 5 Washegari da safe Hasana ta gama haɗa abun karyawa, tana shirya yaran, Nura ya shigo yana cewa"Ki je ki gyara mini ɗakina". Ta yi kamar ba ta ji shi ba, ya sake cewa"Hasana magana fa nake yi". Ta ce"Ni fa wannan raba ɗakin ba lallai ya zama maslaha ga rayuwar aurenmu ba, saboda haka ya kamata a sake sabon tsari". Ya tsaya yana kallon ta da mugun mamaki, ita kuwa da ba kallon shi take yi ba, ballantana ta lura da yanayinsa, ta cigaba da faɗin"A gaskiya sai dai ni ma na koma can ɗin, idan saboda Aiman ne, ni zan dinga yin shimfiɗata a ƙasan katifar mu kwanta". Takaici ya ma hana shi tsayawa jayayya da ita, dogon tsaki kawai ya ja, ya ce"Allah Ya raba mu da jahilci". Ta ce"Ni ce jahilar!?" "Duk yadda kika ɗauka haka nake nufi!" Ya faɗa yana jan kwanon abincinsa. Ta shige ɗaki ta yi zaune a bakin gado, ta rasa ta hanyar da za ta bi ta daƙile wannan sabuwar badaƙalar da yake son ƙullawa, sam ba ta yarda da shi ba, ta san bayan uzurin da ya kawo mata, dole yana da wata manufa ta raba ɗakin nan da ya yi. Haka suka gama karyawa suka fita tare da yaran, ya kulle ɗakinsa yana mamakin sabon hali na raini da take son tsiro da shi a zaman nasu. Da azhar da ya ɗakko su daga makaranta, yana shigowa fuska a murtuke, ya ɗauki tsintsiya ya share ɗakin, sannan ya haɗa ruwan mopping, har ya fara zuciya ta ciyo shi, shaiɗan ya yi zuga, ya fito a fusace, tana cirewa yaran unifom ya ce"Ke Hasana wai me kike nufi ne? Ɗan iska kika mayar da ni ko yaya?" Ta ce"Kamar ya?" Ya ce"Ta ya za a ce ga ki a gida ni zan share ɗakina? Mene ne amfaninki!?" Ta ce"Ka fi kowa sanin amfanina". Ya ce"Ki je ki gyara mini ɗaki Malama, ku mata sam ba ku da tunani wallahi, ba dole ma mutum ya ƙara aure ba? Hmm Allah dai ya hore, zan huce takaici tabbas". Hasana ta yi murmushin takaici ta ce"Ai wallahi ni na fi so ma ka ƙara auren, ta nan za ka san haƙurin da nake yi da kai". Ya ce"Ki kwantar da hankalinki, ai in sha Allah aski ya zo gaban goshi, wallahi da wannan siyayyar da na yi, kuɗin aure zan kai, to kawai na fi so lissafin komai ya tafi daidai shiyasa na jinkirta, amma kar ki damu indai aure ne dole zan yi shi". Ta ce"Allah Ya nuna mana". Ya yi ƙwafa, ta fice ta shiga ɗakin, ta ga wayarsa a kan katifa, ta raya ƙila mantawa ya yi, ta yi saurin ɗauka, sai dai da pasaword kuma ba ta san mene ne ba, ta yi ƙwafa ta ajiye ta, ta gama gyara ɗakin ta fito. Ta same shi a falo ta ce"Yanzu haka za mu dinga ganinka kai kana yin kallonka mu ko oho?" Ya ce"Tun da haka kika zaɓa ba!Na gaji da kai gyaran kayan kallo wallahi". Amir ya ce"Don Allah Daddy a gyara mana". Salim ya ce"To ai sai mu dinga yi a ɗakin Daddyn". Bai ce komai ba, ta kawo musu abincin rana suka fara ci, Nura ya yi kamar cokali uku ya taɓe baki ya ce"Abinci ma ba za a nutsu a yi shi ba, Allah Ya kyauta". Hasana ta yi kamar ba ta ji shi ba, don ita ma ta san gishirin ya yi yawa, ta manta shaf ta zuba, dab da za ta gama girkin ta ƙara zubawa, don haka ba ta da ta cewa. Ya sake tsaki ya ce"Wannan abincin dai ci kar ka mutu kawai, an zabga wa mutane gishiri a abinci" Ya sake tsaki. A fusace ya ce"Ina ta magana...!" Ta ce"To me kake so na ce? Ku maza dama haka kuke, sai mace ta yi daidai sau dubu, ba za ku tabe ta ba, amma idan ta yi ba daidai ba sau ɗaya sai kun yi ƙorafi, hannuna ne ya kufce na saka da yawa". Ya ce"Hmm! Gaskiya na yarda, duk wanda ya mutu da mace ɗaya shi ya ga ƙarshen wulaƙanci, gida biyu maganin gobara, Allah dai Ya kai damo ga harawa!". Ba ta sake bi ta kansa ba, har ya gama ya fice. Yau da daddare da wuri ya dawo, hakan ya sa Hasana ta raya a ranta ƙila yau ɗin ya kira ta, amma sai ta ji shiru, don ko leƙo su ma bai yi ba, tana jin lokacin da ya saka sakata a ɗakin, bayan ya gama uzururrukansa, kamar awa ɗaya a tsakani ta tashi ta sakko daga gadon, ta kalli agogo, sai yanzu goma ta yi, ta manta rabon da ya dawo gida kafin ƙarfe goma, sai dai idan ana tsananin sanyi, ko kuma da damuna. Ta saka hijjabi, ta fito a hankali kamar jiya, ta leƙa ta windo, ta ga ɗakin da hasken tv ga kuma sauti alamar ya kunna kallo, amma yana kwance a katifa waya kare a kunnensa ga murmushi shimfiɗe a fuskarsa, da alama yana cike da shauƙi, takaici ya rufe ta, duk abin da Nura yake yi mata na ɓacin rai, har yanzu tana ƙaunarsa, soyayya ce aka sha ta nuna wa sa'a kafin aurensu. Ta gama yankewa a zuciyarta sai ta hana shi sukuni, don haka ta koma ta wajen ƙofar ta fara ƙwanƙwasawa. Nura da ya nutsa a kofin soyayya da wata wacce ya yi mata laƙabi da baba Leemat, sosai ya yi mamakin wannan bugun ƙofar, da ya dawo sai da ya duba ƙofar Hasana ya ga a rufe, kuma ya santa da baccin wuri, ya ce da baba Leemat yana zuwa, ya katse kiran yana haɗe gira ya ce"Wace?" Ta ce"Ni ce". Ya zo ta buɗe yana cewa"To ya aka yi, ni har na fara bacci ma?" Za ta kutsa kai ciki, ya ɗan tare yana cewa"Wai mene ne?" Ta ce"Akwai wani film da nake kallo a bollywod, shi ne na ce tun da akwai wuta ga ka, ka dawo da wuri bari na zo na ci albarkacin turakar Oga". Ta ƙarasa da murmushi. Sai ya matsa ta shige ta zauna, ta canza tasha, amma gabaɗaya hankalinta yana kanshi, wayarsa tana ta kawo haske ya ƙi ɗauka, can dai ya tashi ya fice daga ɗakin, ya tura ƙofar ɗakinta a hankali ya shiga, ya haska ya ga Aiman ya baje yana ta baccin shi, ya ji fanka, ya kai hannu ya fara jijjiga shi, yaro kuwa ya fara mutsu-mutsu, sai ya tashe shi ya zaunar, ai kuwa ya fara ƙananun kuka, ya yi saurin ficewa daga ɗakin. Ya koma nashi ɗakin yana cewa"Na ji kamar kukan Aiman". Ita ma ta jiyo sama-sama, don haka ta tashi, ta ce"Bari na ɗakko shi". Ya ce"Ina? Kin ga Malama ki yi kwanciyarki kawai, saboda ni ma bacci nake ji". Tana fita ya mayar da sakata. ********* Baba ransa ya kai maƙurar ɓaci, ya kai ya kawo a tsakar gida rungume da hannuwa a bayansa, ya ma kasa cewa komai. Can Mama Karime ta ce"Malam ba fa shiru za ka yi, kamata ya yi a bi sahunta tun kafin ta yi nisa". Sai kuwa ya zaburo kamar mai jira, ya ce"To a gidan uban wa zan nemo ta? Ni dai na san abu ɗaya, yanzu Nuratu baƙinciki da hassada kawai take yi mini, wallahi saboda ta hango ɗan abin da zan samu a jikinta shiyasa ta yi mini haka, amma babu komai". Ya shige ɗakinsa. Ita kuwa Nuratu motarsu tana harbawa titi, ita ma ta harba duniyar tunanin makomarta, sam ba ta hango haske a gobenta, ta san babu ta yadda za a yi Abdul ya karɓi uzurinta, fatanta ya yarda da ita ko da ba zai aure ta ba, ita ta yarda ta sadaukar da mutuncinta don farincikinsa. Sai dai idan bai aure ta ba, wa zai aure ta ya kalleta da mutunci? Gani take shi ma Alhaji Hashimu da ya yi alƙawarin aurenta ya yi maganga ne kawai a cikin mayen giyar so, bayan auren ba lallai ya riƙe ta da daraja ba, sannan yana da mata har uku da yaran da ba ta san adadinsu ba, ta tabbata wasu sun girme mata, yanzu ya za ta yi idan suka ji ta yi ciki a waje kafin auren? Anya gori zai bar ta ta zauna lafiya? Da wannan tunane-tunanen fal zuciyarta aka ƙarasa Kaduna, kowa ya sauka, ta samu babur ya ƙarasa da ita unguwar da za ta je, sai da ta kai ƙofar gidan sannan ta fara fargaba, ta san dai wannan tafiyar ba gudu sunanta ba, don inda ta zo ɗin ba mafaka ba ce ba, kawai ta zo ne saboda ƙwaƙwalwarta ta samu hutu, kuma zuciyar Baba ta yi sanyi, don idan ya tashi yi mata hukunci ta samu sassauci. Ta kai hannu tana ƙwanƙwasa get ɗin gidan, sai da ta buga sau uku, sannan daga ciki aka tambaya waye, ta ɗaga murya ta ce"Ni ce". Babu jimawa aka buɗe, wata mace ce wacce za ta kai shekara ashirin da bakwai ta buɗe, ta ɗan saki fuska ta ce"Nuratu" Tana kallon tsohuwar akwatinta. Nuratu ma ta ɗan saki fuska ta ce"Anti Nawwara". Ta matsa mata, ta shiga jaye da akwatin, Nawwarar ta yi gaba tana binta har zuwa falo, ta zauna, ita kuma ta ƙwala wa mijinta kira"Honey!". Sai ga shi ya fito, yana gyara agogon hannunsa, ya yi turus ganin Nuratu, da mamaki ya ce"Nuratu, ke ce kuwa?" Sai idonta ya kawo ruwa, ta ce"Ni ce, Yaya Kabir ina kwana". Bai amsa gaisuwar ba, ya ce"Amma dai ba lafiya ba ko Nuratu?" Nawwara ta ce"Ina fa lafiya? Ko sadakar ukun babarta ba a yi ba, ka ga ta yo nan ai ka san akwai matsala". Ya ce"Mene ne ua faru Nuratu?" Sai ta fashe da kuka. Nawwara ta ce"A'a yi haƙuri, ta huta tukunna, kafin nan zuciyarta ta yi sanyi ma". Ta ja hannunta, ta kai ta ɗaki, ta zaunar a bakin katifa, ta koma kitchen ta haɗo mata shayi da biredi, har ma da sauran dankali da suka rage, ta kai mata, ta ce"Maza ki ci". Dayake gidan ba baƙonta ba ne, sai ta fara tashi ta yi wanka, ta canza kaya, sannan ta ci abincin, ta ɗakko wayarta, ta kunna data, saƙonni suka gama shigowa tass babu na Abdul, hawaye ya sakko mata, ta san yana can cikin ƙunci, ta yi masa sallama a rubuce, ba ya online, babu jimawa kuma ta ga tik biyu, alamar ya hau, ya duba saƙon nata, sai ya fara typing, tana ta fargabar abin da zai rubuto, har ya gama ya turo, "Wannan shi ne sakayyar soyayyata a gare ki ko? Na gode Nuratu, Allah Ya saka da alkhairi". Abin da ya rubuta kenan, sai ya bi bayansa da stika ta namiji yana kuka sosai. Ita ma kukan ta fara, ta danna viice ta ce"Na san ban cancanci ka saurare ni ba, amma don Allah ka daure ka ji bayanina, ba don halina ba, na yi komai ne saboda cika maka burinka, rayuwarka ta inganta". Bayan ya saurara ya tura mata emoji na mamaki, ta sake yin voice ta ce"Don Allah ka yi haƙuri, ka fahimce ni, na fi kowa shiga ƙunci sanadin wannan kuskuren da na yi". Ta typin ya ce mata"Cikin wane ne? Kar ki ba ni amsar da za ta wuce kalma uku, don ba ni da lokacin sauraron tsarinki". Sarai ta san halinsa, tun da ya ce haka, idan ta ba shi amsa akasin yadda ya buƙata, zai iya yin blocking ɗinta, don haka ta rubuta masa "Agent ɗin da ya yi maka hanyar tafiyarka ne" Ta tura masa. Abdul yana karantawa, ƙirjinsa ya doka da ƙarfi, ya fara karanto innlillahi wa inna ilaihi raji'un! Ya fara tunanin yanzu a kan shi ta ba da kanta ga wani banza? Nan ya tuna ranar da yake tunanin abun ya faru, da abokinsa Usman ya ce masa, ya ganta ta fito daga mota tare da Agent ɗin nan, amma Abdul fir ya ce ba ita ba ce, sannan a ranar mutumin ya kira shi ya yi masa alƙawarin tafiya. Ya kashe data yana mamakin irin _zuciyar mace_. 08028966015 [11/21, 11:35 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 6 Shiru bai ma sake kunna data ba, ballantana ta ji hukuncin da zai yanke, ta sake tura masa saƙo, ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, ni ban ce dole sai ka aure ni ba, kawai dai ka yarda ba yaudara ce ta saka na yi haka ba, ba kuma son abin duniya ba, kawai na yi ne saboda na taimake ka". Ta ajiye wayar tana tuna ranar da ya zo ƙofar gidansu, jikinsa a mace, yana faɗa mata Agent ɗin ya ce yau ce rana ta ƙarshe, idan bai kawo kuɗin nan ba, babu shi a tafiya, sai dai ya sake nema a gaba, abokansa uku duk sun biya, shi ne kaɗai ba shi da shi, ga shi mahaifinsa yana zaune a gida, jinya ta saka shi a gaba, a ƙa'ida ya kamata a ce yana asibiti, amma yanzu yana gida sai maganin Hausa ake ta banka masa. Ya ce"Nuratu macuta sun yi yawa a ƙasar nan, a gabana ya cikewa mata biyu, kuma ina zargin sun ba shi kansu ne, ɗayar ma buduruwa ce, tsananin rayuwa ya sa take son tafiyar, na ga bayan ta fito ta tsaya tana kuka, ita da ya kamata ta yi farinciki, ni kuma da nake namiji kuɗi ne kaɗai zai fitar da ni, na rasa yadda zan yi, ba na so tafiyar nan ta kufce mini, domin na san haka ke ma za ki kufce mini". Nuratu ta ce"Allah Ya kiyaye, wallahi ba zan taɓa kufce maka ba Yaya Abdul, zan jira har ka samu aiki". Ya yi guntun murmushi ya ce"Wa ya san nan da shekara nawa za a samu? Ai ni ma ba zan so tauye miki rayuwa ba". Ta ce"Yanzu babu wata hanyar?" Ya ce"Ba ni da komai wallahi, kin ga babata duk ta siyar da kayan ɗakinta, akan tafiyar nan idan ba ta yiwu ba akwai damuwa". Haka suka dinga tattaunawa, ƙarshe da zai tafi ta ce ya ara mata wayarsa za ta yi kallo, dama yana ara mata, don haka ya miƙa mata ya tafi. Ta shiga ɗaki ta yi zaune da wayar tana tunanin mafita, kafin ta bi shawarar zuciyarta ta ɗauki lambar Agent ɗin, shi ne wanda suka yi waya na ƙarshe, ta saka a wayarta, ta danna kira, ya ɗauka suka gaisa, ta ce"Ni ƴar'uwar Abdul ce". Ya ce"Wane Abdul?" Ta ce"Abdulmalik, wanda kuka yi waya ɗazu, wanda bai samu ya cika kuɗin tafiyarsa ba". Ya ce"Ok ya aka yi?" Ta ce"Dama ina son mu haɗu, akwai alfarmar da zan roƙa idan zai yiwu". Ya yi mata kwatance, Allah Ya taimake ta Mama ba ta nan don haka ta saka hijjabi ta tafi. A bakin titi ta tsaya, ya turo aka shiga da ita, ta shiga har ofishinsa, ta zauna ta gaishe shi, ta sake yi masa bayanin kanta, sannan ta ɗora da faɗin"Abdul yana cikin matsalar rayuwa, shi ne babba a gidansu, ga mahaifinsa ba shi da lafiya, don Allah ka taimaka masa ya samu tafiyar nan, daga baya sai ya biya ka". Ya ce"To ƴan'mata ai haka tsarin yake, mu babu ruwanmu da ƙarfin matsalar mutum, kamfani ne, dole yadda aka tsara ake yi". Ta ce"To amma me zai hana ka ɗauke ni a nan ɗin ko na shara ne, sai ka dinga riƙe albashin nawa da haka har ya biya ka?" Ya yi ɗan murmushi ya ce"Wannan lokaci ya ƙure masa ai, yau ce kaɗai damarsa, ni kuma ba zan yi masa aiki bashi ba". Idonta ya kawo ruwa, ta karaya sosai, ta tashi tana cewa"Shikenan na gode". Har ta kusa fita, ya kira ta, ya nuna mata kujera ta zauna, ya ce"Ya kuke da shi?" Ta ce"Yayana ne". Ya ce"To indai da gaske kike son taimakonsa, ai kina da abin da za ki taimake da shi" Ya ƙarasa yana yi mata kallon ƴan bariki. Ta ce"Inda ina da shi, da ban zo neman alfarmar nan ba". Ya ce"Idan har za ki amince mu tsallaka wancen hotel ɗin na kusa da mu, cikin mintuna za ki taimaki yayanki". Gabanta ya faɗi, ta ce"Amma sai wannan kaɗai?" Ya ce"E, idan kin duba ai ba wani abu ba ne mai wahala, saboda idan ya tafi zai yi miki alheri fiye da yadda kika yi masa, ƙila ma idan aurenki ya zo shi ne zai yi miki kayan ɗaki, sannan kamar kin taimaki iyayenki ne". Ta ce"Zan yi shawara". Ya ce"No, ki je kawai, na faɗa miki yau ne last". Ya ɗauki waya ya yi danne-danne ya kara a kunne, ya ce"Wannan list ɗin ku cire sunan Abdulmalik Ibrahim, zan tura muku sunan da za ku saka a kai". Hawaye ya zubo mata, ta ce"Don Allah Oga ka taimake mu, zan dinga kawo maka kuɗin a hankali". Ya ce"Ki je kawai, ba shi da rabon tafiyar". Ta tuna wane ne Abdul da yadda yake ƙaunarta, sai ta ga ya cancanci har sadaukarwar rayuwa ta yi masa, don haka ta ce ta amince, nan take suka fita, suka je Nuratu ta miƙa kanta, babu shawara babu tunanin ta tafka kuskure, ta manta wane ne namiji, ba ta tunanin ba kowane zai iya yi maka halakci har ƙarshen rayuwarku ba. Shigowar Nawwara ce ta katse mata tunani, ta kai hannu ta share hawayen fuskarta, Nawwara ta ce"Ki fito falo yana jiranki, fita zai yi". Ta tashi ta bi bayanta. Ta zauna kanta a ƙasa, Kabir ya ce"Nuratu me ya kawo ki? Ni ma gobe nake shirin tafiya gaisuwar fa, aiki ne ya yi mini yawa". Sai ta fara kuka, Nawwara ta ce"Ɗan'uwanki ne, tun da kika zo wajen shi na tabbata kina da yaƙinin samun sassaucin damuwarki, saboda haka bai kamata ki ɓoye masa komai ba" Sai ta tashi ta shiga ɗakinta, don ta ba su waje. Nuratu ta kasa faɗa masa komai, sai kuka da ya ci ƙarfinta, ƙarshe ya ɗauki waya ya kira Babanta, wanda ke a matsayin ƙanin uba a wajen shi, wato dai ɗan wa da ɗan ƙani suke da Nuratu, amma Allah Ya haɗa jininsu sosai, har ma ya so ta koma gidansa da ya yi aure, sai Mama ta hana, sai dai ta je hutu ta kwana biyu ta dawo gida. Suka gaisa da Baba, ya ƙara yi masa gaisuwa, sannan ya faɗa masa ga Nuratu ta zo tana kuka, ta ƙi faɗar komai. Baba da yake kwance a ɗakinsa abun duniya ya ishe shi, ya miƙe zaune yana cewa"Alhamdulillah! Gidanka ta zo ashe?" Ya ce"E ga ta nan". Nan Baba ya kwashe komai ya faɗa masa, Kabir ya yi mamaki sosai, saboda duk cikin ƴan gidansu ya fi ganin nutsuwarta, ya shiga yi mata faɗa, tana ta kuka, ƙarshe ya tambaye ta wane ne ya yi mata haka? Nan ma dai ta ƙi faɗa, don takaici ko sallama bai yi wa matarsa ba ya fice daga gidan, a waje Baba ya sake kiransa ya ce lallai-lallai gobe ya sako Nuratu a mota su dawo, ya ce masa da kansa ma zai kawo ta. Haka ta wuni a ɗaki, duk yadda ta so Abdul ya fahimce ta abu ya ci tura, babu kalar bayanin da ba ta yi masa ba, amma yanzu ya ma daina duba saƙon, kuma yana online. Shi kuwa a ɓangarensa shi kaɗai ya san halin da zuciyarsa take ciki, yana da matuƙar kishi, musamman a kan Nuratu da ya yanke a ransa da ita kaɗai zai rayu, ya kasa ganin da gaske halakci ta yi masa, ballantana ya yi mata sassauci a hukunci, abu ɗaya kawai yake yawo a kansa, Nuratu ta yi masa butulci, kuma zuciyarta ba mai kyau ba ce, yana tunanin da aurensu ma za ta iya aikata hakan, da sunan taimako. Amma ta duniya za ta kalle shi da iyayensa, idan aka ji domin shi ta aikata? Saboda haka zai yanke wani hukunci, zai aure ta na ɗan lokaci, daga nan duk wanda zai ji tarihinta a bazawara zai santa, kenan ba za ta samu wata matsala ba a duk yadda mijin da za ta rayu da shi ya same ta. Ya kira mahaifiyarsa a waya, ya tausasa murya, ya fara roƙonta yafiya, ya yi mata shimfiɗar ƙaddara, sannan ya faɗa mata kafin ya tafi shaiɗan ya shiga tsakaninsu da Nuratu, har ma tana da cikinsa, mahaifiyarsa ta shiga tashin hankali sosai, ta san idan ta sanarwa mahaifinsa zai iya ƙarasawa, don haka ta faɗawa ɗan'uwansa, wanda yake waliyin Abdul ɗin, duk faɗan da aka yi wa Abdul ya yi haƙuri ya jure, a ganinsa wannan ne halakcin da zai yi wa Nuratu kawai, ya rama wa kura aniyarta. Haka ƙanin babansa ya je wajen Baba da daddare ya faɗa masa halin da ake ciki, Baba ya dinga sababi, don dama Abdul ɗin kaɗai ya zarga, tun da ba ta kula kowa bayan shi, nan ya rarrashe shi, ya ce Abdul zai turo sadaki a ɗaura auren cikin satin nan, idan ya dawo sai ta tare, nan Baba ya ce bai yarda ba, su je kawai Allah Ya isa, amma ita Allah Ya rufa mata asiri, tana da miji. Washegari Kabir ya saka Nuratu a gaba suka dawo, nan suka zauna da Baba a gabanta yake sanar masa Abdul ne ya yi mata ciki, kuma ya ce zai aure ta. Ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, sai ta rasa farinciki take ciki, ko akasinsa? Ashe Abdul zai jiɓanci lamarin nan, har ya amsa laifin da ba nashi ba? Ta babbata ita da Abdul ruhi ɗaya ne a gangar jiki biyu, ashe ya nuna fushi ne kawai saboda ya hora ta, sai ta ji kamar ta fita daga duka damuwar ma. Kabir ya ce"To Baba ai ta kwana gidan sauƙi, dama wanda ya dama kunun ai shi ya kamata ya shanye, kuma suna son junansu, tun da ta ga za ta iya jiransa sanda ya bushi iska ya dawo sai su tare". Baba Ya ce"Ai ba a nan gizo ke saƙar ba!". Nan ya ba shi labarin Alhaji Hashimu, ya ɗora da faɗin"Ka ga shi ya ji ya gani, sannan babba ne mai hankali, ba kamar Abdul ba da ƙuruciya, bar ganin shi ya yi aika-aikar, tsaf zai wulaƙantata a hakan hakan, shi kuwa wannan mai rufin asiri ne, wulaƙanci mai kuɗi ya fi na talaka sassauci a zuciya, ko banza dai a gidansa za ta fi ƙarfin komai, sannan yanzu ta riga ta san daɗin namiji, ba lallai ta nutsu ba, ƙila ta cigaba da shashancinta shi yana can, tana kwasar zunubi, kuma ni ina ma zargin tilas za a yi masa, idan ya ƙi dawowa ya zan yi da ita?" Kabir ya ce"To gaskiya da wannan ma, indai shi Alhajin ya ji ya gani, ina ga gara ma kawai ta aure shi ɗin, shi Abdul mu bi shi da Allah Ya isa kawai". Baba ya ce"Yawwa ɗan gari, ashe ka gane". Nan suka gargaɗe ta akan kar ta sake ta amsa auren Abdul, wanda ta kalli maganar a wani abu da ba zai taɓa yiwuwa ba, domin tana ganin indai har sun yarda Abdul ne ya yi aika-aikar kuma suka zargi zai iya wulaƙantata bayan aure, to shi Alhajin waliyyi ne da zai ƙyale ta? Ta saka a ranta ba ta da mijin da ya fi Yaya Abdul ɗinta. 08028966015 [11/21, 6:01 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 7 Yau kuwa kafin Nura ya dawo Hasana ta ci kwalliyarta, wata ƙaramar rigar bacci da ta daɗe ba ta saka ba, ita ta ɗakko ta saka, ta fesa turare, ta zauna tana jiran dawowarsa. Yana dawowa ya shiga wanka, kafin ya fito ta tafi ɗakin nasa ta haye katifa ta zauna, har da kunna kallo, ya fito daga wanka yana tura ƙofar ɗakin ya ganta zaune tana yi masa murmushi, ya haɗe rai ya ce"Lafiya?" Ta ce"Lafiya ƙalau, an dawo lafiya?" "Ƙalau" Ya amsa a daƙile. Ta ce"Dama fira na zo taya ka, na ga ka dawo da wuri, ga wannan ɗan abun taɓawa ne". Ta ƙarasa tana miƙa masa ɗan kwano mai ɗauke da ilokar da ta yi da rana. Ya yi tsaki ya ce"To wace irin fira cikin daren nan?" Ta ce"Fira dai irin wacce kake yi a majalisa, na yi zaton ka fara dawowa da wuri ne saboda ka ba ni lokacina, mu dinga fira muna tattaunawa game da rayuwarmu da ta ƴaƴanmu bakiɗaya". Takaici ya ishe shi, shi kam ashe ya gudu bai tsira ba, yanzu haka daga wajen ƙawarta Ramla yake, kuma sun yi da ita za su yi vedio call su sha fira, sai ga shi ta kwaso jiki wai ta zo su yi fira, ya saka kaya ya nemi waje ya kwanta, ta ce"Baban Salim, ba ka sha ilokar ba". Ya ce"Ki ajiye zan sha". Ta ce"Ni kuwa Baban Salim sai na ga malaman makarantar yaran nan kamar sun fara shirme, sai a kwana uku ba a ba su home work ba". Ya yi kamar bai ji ta ba, ta ce"Ni dai kamar na je na ji dalili, saboda...." A fusace ya katse ta da faɗin"To tashi ki tafi! Wannan wace irin takura ce haka, na dawo gida kaina yana ciwo ba za ki bar ni na huta ba, wannan ai masifa ce! Ka ware ɗakin ma ba ka tsira ba!". Ranta ya ɓaci, ta ce"Allah Ya huci zuciyarka, ni dai ban ga abun faɗa a nan ba". Ta tashi ta fice ta janyo masa ƙofar. Ya je ya saka sakata, yana tsaki, a ransa yana ayyana sai fa ya taka mata burki a kan shigo masa ɗaki. Hasana ta zauna a kujerar falonta, tana tunanin yadda za ta yi, har ga Allah ba ta son mijinta ya zama ɗaya cikin masu lalata tarbiyyar yaran jama'a ta waya, ta taɓa ganin chart ɗin banza sau ɗaya a wayarsa, har ta kasa shiru ta tare shi da maganar, ya yi mata kaca-kaca, daga nan ya saka key a wayar yake kuma taka-tsan-tsan da ita, tun daga nan take zarginsa, ko don yawan son matansa dama dole ta kasa yarda da shi, ta san sarai bai daina chart ɗin banzan ba, ballantana yanzu da ya ware ɗakinsa zai ci karensa babu babbaka, sai a ce mace ba ta jan mijinta a jiki, shiyasa yake yi da wasu matan ta waya, to idan da ba ta ja shi a jiki ba, yanzu ta yunƙuro za ta gyara zaman, don kayan baccinta da ta daina sakawa duk ta fito da su, kuma ya ƙi ya ba ta dama. Ta jima tana wannan tunanin sannan ta tashi ta sake fita cikin sanɗa, ta leƙa shi ta windo, ta hango shi, zaune yana kallon waya yana magana fuskarsa ɗauke da murmushi, ta koma ɗaki ta ɗakko panadol da ruwa a kofi, ta je ta fara ƙwanƙwasawa. Nura yana jin daɗin firarsa, ga iloka yana rakawa da ita kawai ya ji bugun ƙofa, sai da ya zabura, sannan ya ce wa Ramla yana zuwa. Ya tashi ya je ya buɗe yana cewa"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Hasana kaina fa ciwo yake yi, na samu bacci da ƙyar kin tashe ni". Ta ce"Dama magani na ga ya dace na kawo maka". Ya karɓa, ya mayar da ƙofar ya rufe, ta koma ɗaki ta yi addu'a ta kwanta, tana jin zafi a zuciyarta. Da asuba ta idar da sallah ta ɗan kunna data, kamar an yi mata umarni ta shiga status ɗin Ramla, ta ga ta saka "Jama'a namiji ya ware turakarsa fa duniya ne, mace tana can sake da baki tana yawun bacci, shi yana caskalewa" Ta haɗa da emojin dariya. A na gaba kuma ta saka"Auren mijin wata akwai lada". Nan take Hasana ta ji ta tsargu, kamar ta wuce sai kuma ta kasa, ta dawo ta ba ta amsa a kai, ta ce mata"Ƴan'mata kenan, ku dai dinga tuna yadda ake caskalewar da ku, an caskale da na gidan fiye da haka, kuma kar lokacinku ya zo ku yi mamaki" Ta haɗa mata da dariya. A na biyun kuma da ta ce auren mijin wata da lada, ta ba ta amsa da "Musamman mai cefane da nama". Wajen azhar da Ramla ta duba saƙon, ta ce mata"Ke dai ƙawata ku riƙe mazajenku da kyau, amma tabbas duk wanda ya kawo kanshi wajena sai na tatike shi". Hasana ta ce"Ku dai bi a hankali, wani sai bayan auren za ki san ko wane ne". Daga haka suka taɓa fira, aka bar wannan zancen. Da rana yana cin abinci ta ce"Don Allah baban Salim kayan kwalliya nake so, hodata ta kusa ƙarewa, ina son siyan humra ma, kuma underwears ɗina duk sun tsufa". Ya ce"Mata kenan, ku fa babu ruwanku da halin da ake ciki, a nemo a ba ku kawai, ana ta abinci ke kina ta wasu tarkacen da ba su zama dole ba". Ta ce"Hmm! Ai tarkacen ne yake kwasarku ku je ku dinga rawar ƙafa a wajen matan waje, waɗanda ba kyau suka fi ni ba, na ji an ce ma an ce har wannan mai awarar ta bakin kasuwa ita ma son ta kake yi, wannan dai zubar da aji ne wallahi, ka rasa wa za ka so wannan kucakar? Wannan uban kurkur ɗin ne fa ya kwashe ka, amma ka faɗo wallahi". Ya ture abincin yana nuna ta da yatsa ya ce"Ke ya ishe ki haka! Saboda tsabar raini ni za ki saka a gaba da zancen banza sai ka ce wani ɗanki? Ba mai awara kaɗai ba har mai dankali ma son ta nake, wannan mai gurasar ma yau zan je wajenta, ko za ki hana?" Ya tashi yana cewa"Kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, ina da kuɗin auren, kuma Allah Ya ba ni damar ƙarawa za ki hana ne? Idan na ga dama ma mai ƙosai zan auro wallahi, ta zo kuma idan kika yi wasa ta fi fada a wajena!". Ta ce"Au kai har wata fada ce da kai?" Ya ce"Da babu da ba a biyo ni da ilokar toshiyar baki ba".Ya fice daga gidan, yana ayyana dole ma fa ya tattara ƙaryar nan ya tsayar da mace ɗaya ya aura. ******** Ta yi wa Abdul saƙo ya kai biyar bai ba ta amsa ba, amma ya saurara, duka haƙuri take ba shi, tare da alƙwarin za ta jira shi ko shekara nawa ne. Da daddare Alhaji Hashimu ya zo, Baba yana rawar jiki ya zo ya kira Nuratu, tana jin haushi a ce wai mahaifinta ne ɗan aiken saurayinta, ta fito suka gaisa, ta sunkuyar da kai, ya ce"Ya ƙarin haƙuri?" Ya ce"Da godiya". Ya ce"Ya jikin naki?" Ta ce"Na warware". Ya ce"To ma sha Allah!Mun yi magana da Baba, gobe za a kai ki asibiti sai a cire cikin, bayan sadakar arba'in sai a saka rana ko wata biyu ne, zuwa lokacin na kamalla ginin inda zan saka ki". Ta ce"Amma Alhaji Baba bai yi maka bayani ba?" Ya ce"Na me?" Ta ce"Shi saurayin nawa da abun ya faru sanadinsa, ya ce zai aure ni, kuma har an gama magana da Baba". Ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce"Amma bai faɗa mini ba". Ta ce"To zai faɗa maka". Suka yi shiru na ƴan sakanni, sannan ta cigaba"Alhaji na gode da ƙaunarka gare ni, sai dai ina so na faɗa maka ni Abdul shi kaɗai nake so, gaskiya duk wanda ya aure ni ba shi ba, zai iya yin nadama a gaba, saboda ba zai taba samun nutsuwa da ni ba, kai babban mutum ne mai mutunci, kuma kana da ƙima a idona, ba zan so yi maka abin da na tanadarwa namijin da ya yi gangancin aurena ba, saboda haka don Allah Baba ka kama girmanka, kai baban wasu ne, ba zan so yi maka ba daidai ba, tun da ba zan so a yi wa nawa uban ba, na gode sosai Alhaji". Daga haka ta juya za ta shiga gida, ya ce"Ɗan tsaya Nuratu". Ta dawo, ya ce"Na ji duk bayaninki, kuma na fahimce ki, ita rayuwar aure ba a yin ta da tilas, kamar yadda kika ce na kama girmana, na kama in sha Allah, dama ni na zo da ƙauna ne, da kuma niyyar taimako duba da ƙaddarar da ta same ki, yanzu zan janye batun soyayya, zan kuma yi wa Baba bayanin da zai fahimta, idan har kina buƙatar wani taimako ƙofa a buɗe take za ki iya tambayata, a matsayina na mai tallafawa marayu. Sannan goben za a je cire cikin" Daga haka ya juya ya fita, ta shiga gida jiki a mace, amma sai ya kasa faɗawa Baba yadda suka yi, saboda ba ya son haɗa ta da mahaifinta. Washegari da safe direba ya zo ya ɗauke ta, tare da wata yayarta, suka tafi asibiti, gabanta yana ta faɗuwa, tana jin kamar ta gudu, a hannun likitan farko dai ya damƙa ta, da alama shi ɗin amintaccensa ne, shi da kansa ya yi mata allurar zubar da cikin, sannan ya ba ta gado. Bayan ya kammala ya kira Hajiya Kubra a waya ya sanar mata. Zuwa yamma komai ya kammala, cikin ya fita duka, aka sallame su direba ya mayar da su gida. Tun kafin su ƙarasa likita ya kira Alhaji suka gaisa ya ce"An kammala aikin cikin nasara". Ya ce"To Alhamdulillah!". Likita ya ce"Sai dai fa akwai wata matsala". Ya ce"Ta mene ne?" Likita ya ce"To ban sani ba ko ka san yarinyar tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki". Gaban Alhaji ya faɗi, ya kaɗu sosai da jin kalmar nan, ya ce"Ok babu damuwa, na gode". Ya katse kiran, nan tausayinta ya ƙara kama shi, ya kuma raya a zuciyarsa lallai yaron nan ya cuci Nuratu, ko ta san tana da cutar a jikint? Da ya yi tunanin sanarwa Baba, sai kuma ya ga tun da yaron ne zai aure ta gara ma ya bar zancen don kar abun ya yi wa Baba yawa, ya tausaya musu sosai, ya kuma gode Allah da aka gano hakan, bai aure ta ba ya sakawa matansa. A ranar da daddare ya je ya kai kayan abinci da yawa, sannan ya kai wa Nuratu kayan shayi, da fruit, ya haɗa mata da kuɗi, ya zauna da Baba ya ce masa"Baba haƙiƙa na so na taimaki Nuratu ta hanyar aurenta, to kuma sai aka samu wata ƴar matsala wacce ba zai biyo na ƙara aure nan kusa ba, saboda haka ka yi haƙuri ni na janye zancen auren, idan ta samu miji kawai ka aurar da ita, sannan ina ba ka shawarar indai wannan yaron da ya yi mata abun ya amince zai aure ta, to kar ka ƙi, domin shi ne ya fi cancanta". Baba jikinsa ya yi sanyi ƙalau, ya ce"Amma Alhaji wannan wace matsala ce?" Ya ce"Matsalar iyali ce, na yi iya yina na ga abun ba zai yiwu ba, ka yi yadda na ba ka shawara kawai". Ya ɗakko dubu hamsin ya ba shi, ya ce ya ƙara a jarinsa don kula da iyali. Baba ya dinga godiya, har da ƙwallarsa, ya bi Alhaji da kallo cike da jajantawa Nuratu na asarar da ta yi. 08028966015 [11/23, 12:44 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 8 Baba yana shiga gida ya shiga ƙwala wa Nuratu kira, ta fito gabanta yana faɗuwa, ya ce"To yau dai burinki ya cika, Alhaji Hashimu ya fasa aurenki, sai ki je ki auri yaron da ba a san ranar dawowarsa ba ma". Ta ji sanyi a ranta, ba ta ce komai ba, har ya gama faɗansa ya fice. Tsawon sati ɗaya tana fama da Abdul ya ƙi sauraronta, sai dai ya duba saƙonta ya yi shiru babu amsa, har ta gaji ita ma ta ƙyale shi zuwa sanda zai huce, sai su sasanta. Wasu daga cikin ƴan'uwan Mama sun gane ta yi ɓarin ciki, saboda duk da Baba ya hana zaman makoki, suna zuwa kullum su ga Nuratu, su kuma taho mata da abinci, don haka ba ta ɓoye musu ba, saboda ta san dole zancen ya fita gari, ko ƴan gidansu za su iya fitarwa, ballantana kuma ƴan'uwan Abdul, ƙanwar Baba sai ta gyara mata jiki daidai gwargwado, bayan sun yi mata faɗa da nasiha. Bayan kwana arba'in da mutuwar Mama, zuwa yanzu har ta fara sarewa da lamarin Abdul, domin kuwa har yau bai saurare ta ba, ta yi nacin da magiya iya iyawrta ta gaji, don haka ta zuba masa ido, a kwana arba'in ɗin nan ita kaɗai ta san halin da take ciki na ƙunci, kullum a ɗaki take wuni, don kunyar fita waje take yi, gani take kowa yana ganinta zai gane ta zubar da ciki, idan an yi abinci ana miƙo mata, wataran duk su biyun su ba ta, wataran mutum ɗaya ta ba ta, wannan duk albarkacin kayan abincin da Alhaji ya kawo ne, don a baya Baba bai damu da cefanen gidansa ba, sai dai kowacce mace ta yi sana'arta, ta ci da ƴaƴanta, shiyasa Mama ma ta kama sana'ar waina kafin rasuwarta, ga shi yanzu har an ɗora Khadija a kai, dama tare suka yi Candy da Nuratu, kuma babu maganar miji, ballantana cigaba da karatu. A cikin satin da aka yi arba'in, sai ga Baba ya zo cikin gida da zancen gobe iyayen Abdul za su kawo sadaki a ɗaura aure, zuciyarta ta dinga dokawa, sai ta nemi farinciki ta rasa, ba ta taɓa hasashen aurenta da Abdul zai zo ta wannan yanayin ba. Matan na shi suka tambaye shi za a yi biki ko ita Nuratu za ta yi ƴar walima? Ya ce babu wani taron banza da za a yi, a wannan auren na larura, da an ɗaura aure a masallaci shikenan, shi babu wani gayyata da zai yi ma. Duk da haka sai da suka kira ƴan'uwan babarta da na Baban suka sanar da su, washegari misalin ƙarfe biyu na rana aka ɗaura auren Nuratu da Abdulmalik a kan sadaki naira dubu hamsin, duk da an ce babu taron sai da ƴan'uwa na kusa suka zo, ƴan'uwan babarta suka auno shinkafa kwano biyu aka dafa kowa ya ci, an yi sa'a Baba ya zo ya damƙa mata kuɗin sadakinta, ta ajiye a gefe tana kuka, yayar babarta ta ce"Kawowa za ki yi a adana miki, wannan uban naki tsaf zai biyo ya ce ki bada". Wata ƴar'uwarta ta ce"Kamata ya yi a dinga juya su, ƙila zuwa sanda zai dawo ta tare su isa a siya mata katifa mai inganci". Duk suka yarda da shawarar. Nan suka tambaye ta batun lefe,ta ce ita ma ba ta sani ba, suka hau faɗa suna cewa wannan ai rainin wayo ne, babu lefe kuma ya ba da sadaki dubu hamsin? Ai arahar ta yi yawa, ita dai ba ta ce komai ba, domin ta san ita ce ta ja komai, a ganinta Abdul ya yi mata halakci ma da ya yarda zai aure ta, ya kuma ɓatawa kansa suna a duniya, don haka ba ta da ta cewa, zuwa magriba kowa ya kama gabansa. Da daddare sai ga Baba ya shigo yana kiran Nuratu, ta zo ta tsuguna, ya ce"Ina kuɗin sadakin? Ai sai ki kawo gobe a siyo miki katifa". Ta ce"Baba ai na za ta sai ya dawo". Ya ce"Au dama nufinku auren kawai aka ɗaura, na siyar da akuya kuma za ta cigaba da cin dangata? To wallahi ba zai yiwu ba, ko dai ya kama miki haya, ko ki tafi can gidan iyayensa ki tare, ni dai tun da na aurar da ke, to ya zama dole na gani a ƙasa, me za ki zauna ki yi a gida, da aurenki? A'a ba za a yi wannan shashancin da ni ba!". Nuratu jikinta ya yi sanyi, har ta fara hawaye, ta kuma kasa cewa komai. Baba ya ce"Ni shiga ki fito mini da kuɗin, na kama gabana!". A raunace ta ce"Ƴan'uwan Mama sun tafi da shi, su ma katifar za su siyo mini yau". Sai kuwa Baba ya rafka salatin da har mutanen gidan suka fito, ya ce"Yanzu ni na haifi ƴar, babu shegen da ya san cinta da shanta, har ta kawo moro, a ce ni ban kai a yi shawara da ni ba a kan sarrafa sadakinta!? Saboda tsabar rainin hankali! To maza shige mu je ki karɓo su!". Mama Karime ta ce"A'a Malam, wannnan fa ba wani abun tayar da jijiyar wuya ba ne, ni na tabbata mutanen nan ba za su cinye mata kuɗi ba". Mama Asabe ta ce"Wannan gaskiya ne, kuma su ma suna da haƙƙi a kanta, bai kamata a ce don an ba su kuɗi ka je ka karɓo ba". Ya ce"Cikinku nan akwai wacce ta siya mata wani abu na gudunmawa? Ko za ku bayar nan gaba? Ku fita harkar ƴata, babu ruwanku da tsarina!" Ya kalli Nuratu"Ke wuce mu je!". Dama da hijjabi a jikinta, sai ta wuce ya bi bayanta, suka tafi, suna zuwa ƙofar gidan ya tsaya, ta shiga a sanyaye, Mama tana ganinta ta ce"Nuratu! Lafiya kuwa cikin daren nan?" Ta fara kuka ta faɗa mata yadda suka yi da Baba, ta ce"Ai dama na san ba zai bar wannan kuɗin ba, ai shikenan dole a bi yadda ya tsara, kunya ce dai za a sha ta daga baya". Ta ɗakko kuɗin ta ba ta, tana cewa"Ki yi haƙuri da duk abin da za ki gani Nuratu". Ta karɓa ta fita ta miƙa masa, sai da ya ƙirga su cif sannan ya saka a aljihu suka tafi, a hanya ma yana ta sababi yana cewa zuwa gobe ya ba su, dole su zo su san inda za ta tare. Ta idar da sallar isha'i ta kasa tashi daga sallayar, gabaɗaya rayuwar ta yi mata zafi, ta rasa inda za ta saka ranta, a gaskiya ba ta son zaman gidansu Abdul, gabaɗaya ɗaki uku ne a gidan, na iyayen ɗaya, na Abdul da ƙannensa maza ɗaya, sai na ƙannensa mata, yanzu a ina za a saka ta kenan? Ba gara ma a bar ta a nan ɗakin babarta ba, idan ya zo ya dinga turo mata da kuɗin abinci. Da shi ya kamata ta yi shawara, amma ya ƙi sauraonta sam, ba ta da mafitar da ta wuce ta sake tuntuɓarsa, don haka ta ɗakko wayarta, ta kunna data, yawanci datarsa a kunne take, sai dai idan ya ji shigowar saƙo ya duba, ta same shi online, ta yi masa sallama, tare da stikar hawaye, ya duba bai ce komai ba, ta yi masa voice ta ce"Assalamu alaikum, Yaya ina wuni? Fatan kana cikin ƙoshin lafiya, a yau burin nan namu na tsawon lokaci ya cika, mun zama mallakin juna, sai dai kuma abun ya zo mana akasin hasashenmu, wannan yana rubuce cikin ƙaddararmu, ya kamata mu karɓe ta, Yaya tun da an cire cikin nan don Allah ka manta da komai, wannan ya zama tarihi, a tunanina soyayayyar da muke yi wa juna ta yi ginuwar da wannan ɗan saɓanin bai kai ya rushe ta ba, ina ƙaunarka har gobe angona". Ya saurara bai ce komai ba. Ta sake cewa"Yaya ya ka tsara bayan auren nan? Yanzu zan zauna a nan gidanmu ne, ko haya za ka kama mini?" Sai ta ga ya fara typing bayan ya saurara, tana ta zumuɗin ganin me zai rubuto, sai ta ga ya ce"Ni na ba wa kura ajiyar nama? Kin san maza sannan kuma na kama miki haya? Mtwsss" Ya ƙarasa da tsaki. Hawaye ya sakko mata, ta ce"Ko kowa na duniyar nan zai zarge ni, ban taɓa tunanin har da kai ba Yaya, tabbas na yarda a yanzu duniya ba ta da tabbas, na gode da komai, sannan zan ɗauki ƙaddarar zama da kai a duk yadda ka tsara zaman namu". Sai ma ya kashe data ba tare da ya sake cewa komai ba, sabon kuka ya zo mata, ta rasa da wa kuma za ta yi shawara, wa zai saka Baba ya yarda ta yi zamanta a gidansu? Ta ya za ta fara zama a gidan su Abdul, bayan ko shi kansa bai damu da ita ba, ballantana ya tilasta wa ƴan'uwan shi kula da ita? Ta samu kanta da kiran lambar Yaya Kabir, ya ɗauka suka gaisa, ya ce"Amarya, dama ina da niyyar kiranki, ɗazu Baba ya ce an ɗaura". Sai ta fara kuka ba tare da ta ba shi amsa ba. Ya ce"Nuratu, akwai wata matsalar ne?" Ta ce"E Yaya". Nan ta faɗa masa duk yadda Baba ya tsara, amma ba ta faɗa masa wulaƙancin da Abdul ɗin yake yi mata ba, ta ɗora da faɗin"Don Allah ka cewa Baba gara zamana a gidanmu, can gidan nasu ban ga inda za su ajiye ni ba, kuma ni ba zan iya zama gidan haya ni kaɗai ba". Yaya Kabir ya ce"To zan yi masa magana in sha Allah! Ki daina damuwa". Suna gama wayar kuwa ya kira Baba, yana jin wannan wata dama ce ta zo masa wacce zai cika muradin da ya daɗe a zuciyarsa, bayan sun gaisa da Baba ya tambaye shi, Nuratu ta tare? Baba ya ce"Ina fa? Babu ma mai zancen tarewar, ni dai zuwa gobe na ba su, ko ba su zo ba zan tura ta, ta tafi can gidan iyayen nashi". Kabir ya ce"A'a Baba kar ka yi hakan, ni a ganina kamar Nuratu za ta takura a can ɗin, me zai hana ta zo nan gidana ta zauna kafin a tsayar da maganar yadda za a yi?" Baba ya ce"To indai za ta je ni ai ba ni da wata damuwa, ta tattara ta tafi". Ya ce"To zuwa gobe zan turo mata kuɗin mota sai ta taho, kamar za ta fi samun nutsuwa a nan ɗin". Suka yi sallama Baba yana ta godiya. Sannan ya kira Nuratu, ya fala mata yadda suka yi da Baba, ta ce"Amma Yaya har tsawon wane lokaci zan zauna?" Ya ce"Har sanda zai dawo ƙasar mana". Ta ce"Amma Yaya babu takura kuwa?" Ya ce"Wa za ki takurawa? Ni da nake ɗan'uwanki ko matata wacce tun tuni take sha'awar ki dawo gidanta da zama?" Ta yi shiru. Ya ce"Babu wata matsala, sai dai ko idan kin fi son zaman can gidan nasu, don ban ga alamar Baba zai yarda ki cigaba da zama a nan ba, idan kuwa ya yarda to nan gaba abinci ma sai ya gagare ki, ki dai yi tunani, idan kin amince ki turo account na saka miki kuɗin mota, idan ba ki amince ba sai ki sanar mini, daga haka ya katse wayar. Nuratu ta zauna shiru tana tunani, ta san matarsa tana da hal mai kyau da son mutane, sai dai kuma wannan fa dogon zama ne, tana tunanin anya kuwa abun zai ɗore ba za ta ƙosa da ita ba? A zuciyarta dai ta ji ta amince, amma a yanzu a ƙarƙashin ikon mijinta take, saboda haka dole ta shawarce shi, ko ma a ce ta nemi izininsa, don haka ta kunna data ta yi masa sallama, ta rubutu ta ce masa"Yaya ina ta magana ka ƙyale ni, Baba ne ta ce bai yarda na zauna a gida da aurena ba, to ni ma ban goyi bayan ka kama mini haya ba, ko don ka samu nutsuwa a zuciyarka, amma na san gidanku babu inda zan zauna, ba wai na raina ba ne, kawai ba zan ji daɗin zaman ba, tun da zan takurawa ƙannenka, to yanzu dai an ce na nemi izininka na koka gidan Yaya Kabir da zama, har zuwa lokacin da za ka dawo. Ka amince?" "Ki je duk inda za ki je, sai dai ina tunasar da ke, ki ji tsoron Allah!" Amsar da ya ba ta kenan, sai ta tura masa godiya. Daga nan ta kira yayar babarta a waya, ta sanar mata halin da ake ciki, ta ce mata indai ta ga ana neman kai da ita ta dawo gidan kawun Hadi ta yi zaman ta, shi yayan Mama ne, Nuratu ta ce babu damuwa za ta je ta gwada zaman ta gani, idan da takura za ta dawo, ta yi mata nasiha sosai a kan ta kama kanta ta riƙe mutuncinta, sannan ta mu'amalanci kowa cikin mutunci, ta dinga kamawa Nawwara aikin gidanta. Suna gama wayar, ta turawa Yaya Kabir account lambar, nan take ya turo mata dubu goma, ta tura masa godiya. Kabir ya sauke ajiyar zuciya, yana jin wani kaso na nauyin da yake ɗauke da shi a zuciyarsa tun lokacin da ya ji Nuratu tana da ciki, ya ragu, ya ce"Yanzu za a fara yaƙin". LITTAFIN ZUCIYAR MACE NA KUƊI NE A KAN NAIRA 500 KACAL, ZA KU IYA FARA BIYAN KUƊIN KARATUNKU DAGA YANZU TA NAN 8028966015 Sadiya Abdulrazaƙ opay bank Shaidar biya ta nan 08028966015 [11/23, 12:45 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 9 GIDAN NURA Zuwa yanzu Hasana ta saba da kwana ita kaɗai, ta yi nacin da za ta iya har ta gaji ta watsar, wataran haka za ta je ta ce masa ba ta da lafiya wai ko zai zo ya kwana a ɗakinta, amma bai taɓa yin hakan ba, sai dai ya ba kawo mata magani ya yi tafiyarsa, yanzu ko ta buga masa ƙofar ma ba ya buɗewa, washegari idan ta yi masa maganar sai ya ce shi ya yi bacci a lokacin, alhalin tana kallon shi ta windo. Daga baya sai take kunna datar ita ma, ta dinga tura masa stika ko ƙananun kalmomi irin su i love you, i miss you, sai ya duba ya yi banza da ita, wai ita a nufinta abin da ƴan'matan suke faɗa masa kenan, ita ma sai ta koya ta dinga yi, da haka har ta samu hankalinsa ya dawo kanta, ya ƙyale su, amma daga ƙarshe sai ya kafa mata dokar chart ɗin dare, ya ce duk inda aka idar da sallar isha'i ya ganta online sai ya hana ta chart ɗin ma gabaɗaya. Haka ta zuba masa ido yake ta shagalinsa, a tsawon kwanakin nan sau biyu ya kira ta ɗakin nasa, tana tunawa a farkon aurensu Nura ba ya taɓa kwana uku bai kira ta ba, amma yanzu sai ya yi sati uku har fiye da haka ma bai kira ta ba, to ita kanta ta san a yanzu babu wani gyara da take yi, saboda gani take asarar kuɗi ne, uwa-uba ma ba ta da kuɗin gyaran ne, a da bayan ya yo mata cefanen komai wataran haka kawai idan kasuwa ta yi kyau yakan ɗauki dubu ɗaya ko biyu ya ba ta, amma yanzu ta manta ma rabon da kyautar kuɗi ta shiga tsakaninsu, ko data Husainarta ce take saka mata, da kyautar katin waya. Sannan zuwa yanzu ta yarda Ramla ita take yi wa habaici, ta gane da gaske mijinta yana soyayya da ita, abun yana yi mata ciwo sosai, indai wata ƙawarta za ta zo, ko kuma ƴan'uwanta to fa sai sun ba ta labarin Nura yana son wata wacce ta sani, ta rasa me yake damunsa, kamar wanda baki yake bibiyarsa. Daga baya ma Ramla sai ta saka a ka mayar da ita group ɗinsu na makaranta, ta yi habaici tana ba da labarin mijin wata ƙawarta ya maƙale mata, a ba ta shawara ya za ta yi da shi? Hasana sai dai ta yi shiru, don ta san ba laifinta ba ne, komai shi ne ya ja mata.Ta taɓa tambayarsa ina Ramla? Ya fara faɗa yana cewa"Wannan wace irin tambaya ce?" Ta ce"To ai na ji labarin kun jone da ita, kuna soyayya, kuma ita da kanta ta faɗa mini". Ya ce"To an yi ɗin, Hasana ki ɗauki mataki don Allah!". Ta ce"Babu wani matakin da zan ɗauka, kawai dai zan ba ka shawara ne, ya kamata ka riƙe mutuncinka, ni ma kuma ka sama miji aji a cikin jama'a, ana ta zagina a gari saboda wannan halin naka na son mata, wai da me na rage ka ne don Allah? Ka sanar da ni matsalata sai na gyara..." Ta fashe da kuka. Duk da jikinsa ya ɗan yi sanyi, amma ya danne bai nuna ba, ya ma tashi ya bar mata ɗakin, shi dai bai ga wata matsala ba saboda yana kula mata, ai namiji mijin mace huɗu ne, yana da ra'ayi da burin auren mata huɗu idan har ya samu dama, saboda haka ba ta isa ta hana shi ba. Daga baya ta yanke hukuncin jan hankalinsa don ta gane wace kalar mu'amula yake yi da mata a wayar? Sai ta saka Husainarta ta aiko mata d sabon layi, saboda akwai ƙanin mijinta wanda yake siyarwa, ta saka a wayarta, ta saita sabon whatsApp da shi, ta nemi lambar Nura ta yi masa sallama, ya amsa suka gaisa, ya ce bai gane mai magana ba, a rubuce ta ce"E dama ba ka san ni ba ai, yanzu dai nake ganin lokaci ya yi da ya kamata ka san ni, saboda ka daɗe kana azabtar da zuciyata da soyayyarka, burina ko yaya ne na samu matsuguni a zuciyarka, wanda za ka dinga tuna ni ko da sau ɗaya ne a sati". Sai ya tura stikar murmushi, ya ce"Ikon Allah! Da farko dai ya sunanki?" Ta ce"Sunana Suhaila, kuma a kasuwa nake ganinka, wallahi kana burge ni sosai, na daɗe da samun lambarka, amma sai na yi ta jujjuya ta, na kasa yi maka magana, saboda a zotona za ka yi wulaƙanci duba da ganin yadda ka haɗun nan kake da aji, na ji an ce ma mata ba sa gabanka, shi ne nake ta fargaba". Nura ya yi murmushi ya ce"Wannan dalilin ai ba shi zai saka mutum ya yi wulaƙanci ba, sai dau idan dama can halinsa ne, ita mace ai ba abar wulaƙantawa ba ce, mace abar riritawa ce da tarairaya, kuna buƙatar kula ta kowane fanni, wannan shi ne burin da na ci a kan matar da zan aura har tsufanmu". Ta ce"Kenan yanzu ba ka da aure? Zan so a ce ni ce zan samu wannan kulawar". Ya ce"Ina da aure har da yara, sai dai wancen burin nawa yana neman zaɓa tarihi, saboda wata kidahumar mace Allah Ya haɗa ni da ita, wallahi sam ba ta san kanta ba, ballantana ta san mijinta". Kalmar kidahuma ta daki zuciyar Hasana ba kaɗan ba, nan take ranta ya yi baƙi, sai ta ji kamar ta yi voice ta faɗa masa ita ce, sai dai kuma ba wannan gaɓar take nema ba, don haka ta daure zuciyarta suka cigaba, ta ce"Ikon Allah! Yanzu duk wannan haɗuwar taka ba ka yi dacen mace ba? Amma ai kai ya kamata ka canza ta, ka mayar da ita yadda kake so ku zauna". Wannan karon voice ya yo, yana ƴar dariya ya ce"Malama Suhaila kenan, wato ba ki san wace ce matata ba, shiyasa kike zaton za ta canza hali, yanzu haka zancen da nake yi miki fa kin gan ni kwance a ɗakina ni kaɗai, na kasa bacci saboda tsananin buƙatarta nake, amma na kirata ta ƙi zuwa, yanzu ya dace a ce mace ta dinga nisa da ɗakin mijinta wai sai sanda ya kira ta?" Hasana ta daskare da mamaki, sai ta kasa riƙe hawayenta, ashe dama haka Nura yake tona wa aurensu asiri? Kuma ma duk bin ta yake yi da sharri, indai har wacce ta fara yi masa magana yau bai santa ba, bai san inda take ba, zai saki jiki ya dinga tsara mata wannan ƙaryar, to ina ga wacce ya saba da ita har ma yake zuwa gidansu? Yanzu haka yake faɗawa Ramla ma? Tabbas dole ta raina ta. Ta share hawaye ta ɗauki wayar, sai ta ga ya turo mata stika, tana buɗewa ta ga mace ce da namiji rungume da juna suna bacci, ta daure ta rubuta masa"To ko ni ɗin na zo na taya ka baccin?" Ya tura mata dariya ya ce"Da gaske ba za ki ji tsorona ba?" Ta ce"To tsoron me?" Ya ce"Ai za ki zo ne matsayin mai ɗebe mini kewa". Ta ce"Hmm, za ka same ni fiye da matarka, kwatanta mini gidan naka yanzu zan zo". Ya ce"Ki dai gwada ta waya don na yarda idan kin zo ɗin za ki iya taɓuka abun arziƙi". Sai ya turo mata wani vedio, tana buɗewa, ta yi saurin kifa wayar, ganin blue film ne ƙarara, ta dinfa maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!", ta kashe wayar duka ba tare da ta ba shi amsa ba, sai ta samu kanta da fashewa da kuka, ashe irin mijin da take aure kenan? A daren nan da ƙyar bacci ya ɗauke ta, da safe har ta makara, sai da ya tashe ta, har da faɗansa yana cewa"Wannan wani sabon salon ne kuma salon yara su makara?" "Ba ni da lafiya ne" Abin da ta ce kenan kawai, wani irin mugun haushinsa take ji, ji take kamar ta kama shi ta shaƙe, ta tambaye shi me yasa yake zaune da ita ba zai sake ta ba? Ta je ta kunna wuta, sai dai tunawa da kalmar kidahuma ya sa ta fara hawaye, idan ya tashi wulaƙancinsa har jaka yana ce mata, amma a jiya fa wata yake faɗawa ita kidahuma ce, tabbas ta san duk wacce zai auro nan gaba ba za ta kalle ta da mutunci ba. "Kukan me kike yi?" Ya tambaye ta yana yamutsa fuska. Ta ce"Na ce maka ba ni da lafiya". Ya ce"To Allah Ya sawaƙe, sai ki yi ƙoƙari ki dafa shayi, bari na siyo biredi". Ya fita, ta bi bayansa da kallo, tana tuna wannan ƙazamin vedion, wa ya san adadin matan da ya turawa shi? Wa ya san adadin yawansu a wayarsu, lallai wata wayar za ta iya yi wa mutum jagora zuwa jahannama, haka ta dafa shayin, suka karya, ta shirya yara, tana yin komai a sanyaye, yana taɓa aljihunsa ya ce"Ga shi ba ni da kuɗi da kin tafi asibiti". Ta ce"Ciwon kai ne, zan sha magani yanzu". Ya ce"Allah Ya sawaƙe ya fice". Wajen ƙarfe goma ta kunna data, ta gan shi online, zuciyarta tana ba ta shawarar ta ajiye layin nan, tun da har ta san wane ne mijinta, ta samu abin da take so, wani ɓangare na zuciyar kuwa zugata yake yi, a kan ta cigaba don ta gano iya waya abun nashi ya tsaya ko zai yarda su haɗu a zahiri? Ta fi yarda da wannan don haka ta yi masa sallama, sai da ma ya duba chart ɗin baya har farko, sannan ya tuna ta, saboda yawan matan da yake chart da su, ya amsa ya ce"Matsoraciya jiya sai kika gudu ko?" Ta ce"La ba fa guduwa na yi ba, wayar ce ta mutu, caji ya ƙare, ban ma kai ga ganin me ka turo ba". Ya ce"Kin bar ni da kewarki, har da mafarkinki na yi". Ta ce"Daga haɗuwa?" Ya ce"Ai haɗuwar ce ta yi daɗi shiyasa, yau za ki rage mini dar ko?" Ta ce"Me zai hana? Ni fa da gaske nake, ka ga ni ban saba ta waya ba, a ina za mu haɗu?" Sai ya tura mata dariya ya ce"Kamar gaske". Ta ce"Tun da ba ka shirya ba shikenan mu bar zancen". Ya ce"Wai ke ba kya yin voice note?" Ta ce"Ai ni kurma ce, ba na magana kuma ba na jin komai". Ya tura stikar dariya ya ce"Ban yarda ba, sai ranar da na ganki a zahiri". Ta ce"To yaushe zan zo taya ka kwana?" Ya ce"Yau". Ta ce"Za kuwa ka gan ni, da gaske fa". Ya yi dariya. Ta ce"Zan zo ƙarfe sha ɗaya daidai, saboda haka ka koma gidanka da wuri yau". Ya ce"Allah Ya kawo ki, zan shirya miki abubuwan mamaki kuwa". Daga haka ta kashe data, ta tashi ta ɗora girki, a ranta tana ayyana tabbas yau ɗin kuwa za ta je, ta fito masa a mutum, don ya san ta gane badaƙalar da yake yi a wayarsa. Da ya zo cin abincin rana ba ta nuna komai ba, sai dai sam ba ta da walwala, da daddare yana dawowa ya gama komai ya shiga ɗakinsa, ta kunna data, ta ga saƙonsa ya shigo, yana ce mata"Kyaun alƙawari dai a cika, yana jiranta". Ta ce"Ka tashi ka buɗe ƙofa yanzu za ka ji na turo na shigo". Ya ce"Na buɗe". Ta ce"Ba ka buɗe ba, ina kallonka fa, kana kwance a katifa da gajeren wando bulu". Ya yi ƴar dariya ce"Kuma wallahi kin canka". Ta ce"Na ce fa ina kallonka, yanzu na ƙaraso ƙofar ɗakin zan ƙwanƙwasa, ka buɗe, amma don Allah ko a yaya ka gan ni kar ka ji tsorona, wallahi ni mai sonka ce". Ya ce"Kai Suhaila kenan". Hasana ta buɗe ƙofarta a hankali, ta fito, ta fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Nura da ƙarfi, gabansa ya faɗi rass, ya ce"Wane ne?" Ta tsaya da bugun ta rubuta masa cewar"Ni ce mana, ya kake haka, ko na shigo ta saman ɗakin?" Sannan ta cigaba da bugawa. Nura bai san sanda ya yi wulli da wayar ba, ya fara karanto duk addu'ar da ta zo bakinsa, ya yaye zanin gadon da aka shimfiɗa a katifa ya lulluɓa, yana ta addu'o'i. LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 500 KACAL! ZA KU IYA FARA BIYAN KUƊINKU TUN YANZU TA NAN 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay bank Sahaidar biya ta nan 08028966015 [11/24, 1:16 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY PAGE 10 Jin shiru ya sa Hasana ta leƙa shi ta windo, nan ta hango shi ya naniƙe bango kamar ƙadangare, dariya ta zo mata, amma ta daure ta riƙe ta, ta matse murya tare da dakushe ta tamkar ta tsohuwar da ta gaji da duniya ta ce"Kai yaro kai fa ka ce kyaun alƙawari a cika, mu ba ma karya alƙwari, kai yaro yanzu za mu ɗage ka, kai da katifar mun kai ka tsakiyar sansanin karuwan aljanu, zan nuna musu masoyina, a can za mu rage dare na zo maka a matsayin matarka kamar yadda ka ce". Wani irin hautsinawa kayan cikinsa suka fara yi, ya yi adungure ya diro daga katifar, ya buɗe sif ɗinsa ya shige lokar ƙasa yana tsananta addu'arsa. Hasana ta sake cewa"Sakan ɗaya na ba ka, ka fito daga sif ɗin nan idan ba haka ba, zan rufe ta da mukullin garƙam na kakana na goma sha tara, babu wanda ya isa ya buɗe sai bayan shekara ɗari da saba'in". Kafin ta rufe baki, sai ga shi ya faɗo daga ciki kamar an jefo shi, ya kalli gabas da yamma, ya fashe da kuka yana cewa"Na tuba, wallahi na tuba don Allah ki yi haƙuri?" Ta ce"Me ka yi kake tuba?" Ya ce"Ni ɗan iska ne wallahi, amma daga yau na daina ba zan ƙara ba". Ta saki wata muguwar dariya ta ce"Yanzu kana nufin ka haƙura da rage daren?" Da sauri ya ce"E wallahi, dama ƙarya nake yi, ban san ma yanda ake rage daren ba, ki yafe ni". Ta ce"Ni sunana Aljana Salsabilatul-silsilatul-sakafilatul-salwaisus, ya na ce sunana?" Nan Nura ya ruɗe ya fara jero baragada, S kawai kake ji tana tashi, ga shi kuma yana kuka". Hasana ta kasa daurewa ta yi nesa da ɗakin, ta yi dariya a ciki-ciki, sannan ta daidaita kanta ta dawo ta sake buga ƙofar, ya zabura, yana ba da haƙuri, ta ce"Yi min shiru, munafukin banza!" Daidai nan kuma ta fara jiyo kukan Aiman. Ta ce"Ka ci sa'a, yau muna da mitin namu na ƙungiyar karuwai, amma ka sani zan dawo gobe domin mu tattauna game da ƙuntatawar da kake yi wa matarka, da sharrin da kake yi mata, sannan duk chart ɗin cikin wayarka ka tabbata ka goge su, ka goge whatsApp ɗin duka mun haramta maka shi har abada, tun da tarbiyyar yaran mutane kake ɓatawa". Ya ce"To zan goge, na ma goge wallahi, ni da charting har abada Kaka". Ta ce"Kai yaro, bar ganin muryata haka kake ce mini Kaka, ni matashiyar aljana ce, shekaruna ɗari uku da ashirin da uku, kawai ina yi maka kalar muryar da kunnenka zai iya ɗauka ne". Ya ce"To na gode, na gode". Ta ce"Gobe zan dawo mu tattauna, sannan duk wanda ka ba wa labari, to ka tabbata ka furta kalamanka na ƙarshe kenan, domin daga ranar zan fansar da harshenka ga saurayina, ba za ka sake magana da bakinka ba. Yanzu ka tashi ka yi ta tsallen kwaɗo har sai gari ya waye, idan ka fito kafin kiran sallar asuba, sai dai ka ga kanka a tsakiyar barikin aljanu". Ta leƙa ta windo ta gan shi yana ta tsallen kwaɗon har da kama kunnensa kamar a makaranta, ta buga ƙofar ɗakin da ƙarfi, Nura don tsoro har sai da ya faɗi, sannan ya tashi ya cigaba da yi, ta yi wani irin abu da muryarta, sannan ta tafi cikin sanɗa ta buɗe ƙofar ɗakinta, ta shiga, ta hau gadon ta ɗauki Aiman, ta fashe da dariya, ashe ita tana da maganin Nura ta tsaya take ta shaƙar takaici? Har ta fara hasashen azabar da za ta ba shi gobe, tabbas sai ta huce takaicinta. Haka ta kwanta bacci ranta fes. A ɓangaren Nura kuwa, ya kai awa biyu yana ta tsallen kwaɗo, yana yi yana addu'a, ya gaji matuƙa, amma tsoro ya hana shi tsayawa, ƙarshe dai da abun ya ishe shi, sai ya yi shahada ya daina yi, ya rarrafa ya kunna kayan kallo, ya nemo tashar da ake yin karatun Qur'ani, ya manta rabon da ya saurari Qur'ani sai yanzu da yake neman tsira, ya zauna yana bin karatun duk da ma bai iya surar ba, a haka har asuba ta yi, bai runtsa ba. Yana jin fitowar Hasana za ta yi alwala, amma tsoro ya hana shi fitowa, ya ce"Hasana!" Ta amsa tana tahowa ɗakin. Ya ce"Don Allah samo mini buta da roba mai faɗi haka, alwala zan yi, ki haɗo da fo ma". Ta ce"Subhanallah! Baban Salim karyewa ka yi ne?" Ya ce"Dalla idan ba za ki kawo mini ba ki faɗa mini!". Ta ce"A'a ni ba ni da fon da ƙato zai hau, ga dai buta nan" Ta miƙa masa butar hannunta da roba ta fice. Can dai ya yi shahada ya fito, ya yi alwala ya tafi masallaci, sai da gari ya waye sosai sannan ya dawo, yanzu tsoron ɗakin yake ji, wayarsa kuwa bai kula ta ba, sai da suka gama cin abinci, gabansa yana faɗuwa ya ɗauka, ya goge whatsApp ɗin duka, ya saka a aljihu ya fita, a kasuwa ma jikinsa duk a sanyeye, haka ya dawo cin abincin rana Hasana tana lura da yanayinsa, da zai fita ya ce"Yau kar ki rufe ƙofar nan, a nan zan kwana". Ta ce"A nan za ka kwana kuma? Kai kuwa me ya yi zafi?" Ya ɓata rai ya ce"Ban sani ba! Ko ni da gida za ki yi mini iyaka ne?" Ta ce"A'a, amma dai da mamaki, a ce wai kai da kake kora ta kuma yanzu za ka baro lafiyayyen ɗakinka ka zo nawa, gaskiya da wata a ƙasa". Ya yi banza da ita, ya fice. Ana yin sallar isha'i, Hasana ta garƙama sakata a ƙofarta, ƙarfe takwas sai ga shi ya dawo gidan, gabansa yana ta faɗuwa, ya ga abincinsa a ƙofar ɗakinsa, ya je ya fara ƙwanƙwasa ɗakin Hasana tare da kiran sunanta, tana ji ta yi banza da shi, ya dinga bugawa, ƙarshe har Salim da Amir yake kira, ya ji shiru, sai ya kira ta a waya ta ƙi ɗagawa, abun duniya ya ishe shi, shi bai taɓa jin haushin wannan nauyin baccin nata ba kamar yau, ya zauna a tsakar gida duk da gabaɗaya gidan ma tsoro yake ba shi, Hasana ta ɗakko wayarta ta rubuta mata saƙo, ta ce"Ko ka tashi ka shiga ɗakinka mu tattaunawa ko kuma mu yi sama da ƙoƙon kanka yanzu". Sai da gabansa ya faɗi da ya ji shigowar saƙon, ai kuwa yana karantawa ya tashi a guje ya nufi ɗakin Hasanar yana ta bugawa haɗi da addu'a, Hasana da take ta dariya, ta sake rubuta masa"Muna kallonka kana buga ɗakin baiwar Allah, nan muka aike ka?" A guje ya je ya buɗe ɗakin nasa ya shiga, yana ta addu'a. Ya tsugunna kamar ɗalibi a gaban Malami, ki mai laifi a gaban jami'an tsaro, ya fara cewa"Don Allah ki yi haƙuri ki yafe ni, wallahi na tuba". Hasana ta buɗe ɗaki ta fito, karaf a kunnensa, sai kuwa ya daddage yana ƙwala mata kira cikin kuka, "Hasana! Hasana don Allah zo ki cece ni". Maganarsa ta guntse jin an buga ƙofar ɗakin da mugun ƙarfi, ya yi tsalle ya haye katifa yana "Wa innahu Sulaimanu". Hasana ta fara irin muryar jiya ta ce"Wato matar taka da kake cuta ita za ta zo ta cece ka ko? To fitsari ta fito, kuma mun juya mata ƙwaƙwalwarta mun mai da ita ɗaki, sai kuma wa za ka kira?" Da sauri ya ce"Babu, wallahi babu wanda zan kira". Ta ce"Me yasa kake chart ɗin banza da ƴaƴan mutane?" Ya ce"Ƙaddara ce, amma na daina wallahi, har abada". Ta ce"Mun gama da wannan shafin, to me yasa kake ƙuntatawa matarka? Kake zaginta idan ka je zance wajen ƴan'matanka?" Ya ce"Babu komai wallahi, na daina". Ta ce"Bayan ƙungiyar karuwan aljanu, ina cikin ƙungiyar masu ladabta bil-adaman da suke ƙuntatawa matansu, saboda haka zan ɗauke ka na kai ka can ofishinmu na aljanu masu kare haƙƙin matan bil-adama! A tarihin sama da shekara dubu, babu bil-adaman da ya shiga ofishinmu ya fito da rai" Cikin tashin hankali Nura ya fara"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Don girman Allah ku yi haƙuri, wallahi na daina, daga yau ba zan sake yi mata komai ba, zancen ma na daina zuwa". Ta yi wata dariya ta ce"Muna sane da abubuwan da kake yi mata, ba ka ba ta kayan kwalliya, amma kana ba wa matan waje, kwanaki ta tambaye ka me kake so ta dinga yi don ku zauna lafiya, ka ƙi faɗa mata, ta ce ka ba ta kuɗi ta sayi ƙananun kaya nan ma ka ƙi, haka kawai sai ka fara yi mata masifa, sannan kuma ba ka ba ta ɗan kuɗin kashewa, kuma duk baƙin da ta yi sai ka ce kana son su, hakane? Ka raba ɗaki, ka hana ta dinga biyoka" Da sauri ya ce"Hakane, hakane wallahi wannnan duk halina ne, amma na tuba yanzu". Ta ce"Sannan sai ka yi wata ba ka kira ta ba, to idan ba ka buƙatar mace mu za mu turo maka aljana shafumuleratu, ta shafeka". Da sauri ya ce"Ku yi haƙuri don Allah! Wallahi zan gyara zan daina". Ta ce"Kenan da kana sane? Matan waje kake bi ko?" Ya ce"A'a wallahi ba na bin kowa, basir ne da ni". Ta ce"Mun ba ka wata ɗaya ka nemi magani!" . Ya ce"To, zan nema, gobe zan siyo". Ta ce"Ina kuɗin auren da ka fara tarawa? Yanzu sun kai nawa?" Ta tambaya, don a cikin satin ta ji wata ƴar'uwarsu ta ce kuɗin aure ma zai kai. Ya ce"Dubu hamsin ne dama za a kai ranar Lahadi, amma yanzu idan kun ce na fasa shikenan". Ta ce"Ba mu ce ba, amma wannan kuɗin ka ɗauke su ka ba wa matarka ta sayi underwears da kayan kwalliya, kuma ka ba ta haƙuri ku gyara zaman aurenku, sannan daga yau kullum za mu na kawo maka ziyara, idan muka zo muka ganka kana bacci kai kaɗai, sai dai ka farka ka ganka sansanin karuwan aljanu, daga yau ka kira matarka ku dinga kwana tare, ko ba ka ji ba!?" Ta ƙarasa da daka masa tsawa, wanda da ace a nutse yake ma tsaf zai iya gano muryarta. Amma da yake ba ya cikin hayyacinsa da sauri ya ce"Na ji, wallahi na ji, kuma zan yi duk yadda kuka ce". Ta ce"Idan ka yi haka ka taimaki kanka, daga gobe mu fara ganin canji". Ya ce"To, to,na gode". Ta buga ƙofar da ƙarfi, Nura ya kwanta ya lulluɓa yana ta salati. Da yake shi bacci ba a cin bashin shi, haka Nura ya dinga kokowa da shi, har dai ya samu wahalallen bacci ya kwashe shi, sau biyu yana mafarkin aljanu, sai ya farka a razane ya cigaba da addu'a. Yana jin kiran sallar asuba ya fito, ya yi alwala ya tafi masallaci, da ya dawo ɗakin Hasana ya wuce, ya shiga ya zauna a kujera ya yi shiru, ta gama azkar ɗinta, ta tashi ta fita don kunna wuta, da ta ɗota ta dawo ɗakin ta zauna ta ce"Baban Salim lafiya kuwa?Na ga ka fito da asubar nan". Ya sauke numfashi ya ce"Babu komai yanayi ne kawai". Can ya nisa ya ce"Dama ina son mu yi magana ne mai muhimmanci". A zuciyarta ta ce"An zo wajen". Ya ce"Ina so mu haɗu mu gyara rayuwar aurenmu ne dama,duk abubuwan da nake yi miki zan daina in sha Allah! Ke ma sai ki ɗan gyara wasu abun, ki guji ɓata mini rai, ina so mu samu zaman lafiya". Hasana ta ce"To Alhamdulillah! Ni dama baban Salim ai tun tuni nake so mu yi irin wannan zaman, kai ne ka ƙi fahimtata, in sha Allah ni ma zan dinga kiyayewa". Ya ce"To, me da me ma kika ci mini za ki siya kwanaki?" Ta ce"Ban ce zan sayi komai ba". Ya ce"A'a kin ce za ki canza underwears mana". Ta ce"Ai ka ce ba ta shi ake yi ba". Ya ce"Kuma yanzu ba gyara zama ake yi ba? Anjima zan ciro kuɗi na ba ki, sai ki siyo duk abin da kike buƙata". Ta ce"To na gode, Allah Ya saka". Ko amin ya kasa cewa don takaicin fitar da kuɗin yake yi. Haka kuwa aka yi, ya je ya ciro kuɗi, sai ga dubu hamsin kash ya kawowa Hasana, ta nuna farincikinta sosai kuwa, shi kuma jiki a mace, ta ce"Ni akwai wata hoda da Husaina take nema, ta ce za ta turo maka hotonta ta whatsApp". Gabansa ya faɗi tunawa da whatsApp ɗin, ya ce"Ta tura miki kawai ki nuna mini, ni na daina chart". Ta ce"Ikon Allah, saboda me?" Ya ce"Ba komai kawai na gaji ne". Har zai fita ya dawo ya miƙa mata mukullin ɗakinsa ya ce"Yawwa daga yau ki dinga kwana a ɗakina, babu amfanin raba ɗaki yanzu, tun da mun fahimci juna". Hasana ta ce"Oh! Baban Salim kana ta kashe ni da mamaki fa, ina godiya". Ya ce"Ki godewa Allah kawai". Ya fice, babu jimawa ya dawo da tarkacen magani, ya ce"Ungo wannan maganin basir ne ki dafa mini". Ta karɓa tana daurewa saboda dariyar da ta zo mata, ita da ya ce basir ne da shi ta yi zaton ma ƙarya yake yi, kenan ya san da cutar amma ya ƙi neman magani, sai da ya ji uwar bari. Ta ce"Baban Salim basir ne ya same ka?" Ya ce"E" Ya fice ba tare da ya jira ta ce wani abu ba. Ta dafa magani, da ya dawo da daddare ya kafa kai ya kwankwaɗa, ana idar da sallar isha'i ma ya dawo, ta kuwa ci kwalliyarta, cikin rigar bacci, tana ta jan shi da fita yana mazewa, da yaran suka yi bacci, sai ta ɗauki Aiman suka tafi ɗakinsa, shi dai addu'a ya yi ya kwanta, saboda baccin da yake idonsa, ita kuwa sai da ta yi kallo sannan ta kwanta, suka kwana lafiya ƙalau. LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 500 KACAL! 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay bank 08028966015 [11/25, 8:33 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE* BY SADIYA ABDULRAZAƘ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation) https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY Marubuciyar Wani auren Iya ruwa Da walakin... Wutar ƙaiƙayi Matar shige Alhakin so Mataccen buri Mukullin nadama Akwai ragi ga wanda ya sayi littafaina guda biyu ko fiye da hakan 08028966015 PAGE 11 Washegari misalin ƙarfe goma Nuratu ta haɗa duka kayanta a akwati, ta yi sallama da ƴan gida, Baba ya zaunar da ita ya ce"To Nuratu, kin ga dai duk wanda ya janyo ka jikinsa shi ba maƙiyinka ba ne ba, saboda haka dole ki bi umarnin Kabiru shi da matarsa, yi na yi, bari na bari, kar ki sake na ji an kawo wani ƙorafi a kanki, wallahi sai na saɓa miki, kuma sai dai ki nemi inda za ki zauna, ba dai gidan nan ba, ba zai taɓa yiwuwa na aurar da ƴa kuma ta zauna min a gida ba, ban da kin zaɓawa kanki haka ai da tuni kin auri mutumin arziƙi kina can ɗakinki hankali kwance, yanzu kuwa sai ki yi ta zama, ƙila ma har ki tsofe a gida bai dawo ƙasar ba, Allah Ya kyauta!" Kalaman da suka raba ta da Baba kenan, saboda haka ta tafi jiki a mace. Ana kiraye-kirayen sallar azhar Nuratu ta sauka a gidan Kabir, lokacin ba ya gida, Nawwara ta tare ta da murnarta tana cewa"Babbar baƙuwa ta ƙaraso, kodayake ma yanzu kin zama ƴar gida, sannu da zuwa". Ta ce"Yawwa Anti na gode". Ta yi wanka ta yi sallah, tana cikin cin abinci sai ga kiran Kabir, ta ɗauka ta gaishe shi, ya ce"Kin raho?" Ta ce"Ai har na ƙaraso ma". Ya ce"Ma sha Allah!". Bayan ta gama ta fito falo, suna ta fira da Nawwara, nan take faɗa mata ta samu aikin koyarwa a wata primary, tana zuwa kullum daga ƙarfe bakwai zuwa ƙarfe biyu, Nuratu ta taya ta murna, Nawwara ta ce"Kin ga yanzu ke kaɗai za mu dinga bari a gidan kenan, sai na dawo". Nuratu ta ce"Ai babu komai, Allah Ya taimaka". Nawwara ba ta taɓa haihuwa ba, saboda tana da matsala a mahaifarta, suna zaune lafiya da Kabir, kuma tsawon shekarun da suka yi bai damu da matsalar rashin haihuwarta ba, mafi yawan lokuta ma shi ne yake nuna mata muhimmancin yarda da ƙaddara, yana kyautata mata da ba ta kulawa daidai gwargwado, sai dai akwai wata ɓoyayyiyar hallayarsa wacce hankalinta bai kai kanta ba, ballantana ta yi nazari, ba ta taɓa sanin Kabir mane min mata ba ne, saboda yana yin komai cikin tsari, sannan ba mai tsananin da za ta yi saurin ganewa yake yi ba. Sau uku tana ɗakko wata yarinyar cikin ƴan'uwanta, domin ta zauna a gidan ko za ta samu ta rage kewar zaman kaɗaici, sai yaran sun zo suna murnar zaman gidan, daga ƙarshe sai su rikiɗe su ce su ba za su zauna ba, duka su ukun ba ta gano dalilin barin su gidan ba, Kabir ba ya iya ɗauke kansa a kan mace, ƙananun yaran nan su uku duk ya gwada masa halinsa, amma bai samu cikar muradinsa ba, wannan halin nashi ne yake korar su daga gidan, dangi duk an sani, ana kallonta a fanko, domin har mahaifiyarta ta sani, amma ta ƙi faɗa mata, kuma ta hana a faɗa mata, sai dai ta taka mata burki a kan sake ɗaukar wata yarinya da sunan riƙewa, ta ɓoye mata ne saboda ta zauna lafiya da mijinta, sai dai tana yawan yi masa addu'ar shiriya, saboda Kabir yana da kirki, yana girmama murane, wannan halin ne kawai matsalarsa. Da daddare bayan ya dawo sun gaisa da Nuratu, ya tambaye ta ta taho da kayan lefenta? Nan ta sanar masa ai bai yi mata lefe ba, sai kuwa ya hau faɗa yana cewa"Me yake nufi kenan? Wannan fa ya samu dama da yawa wallahi, ga cutarwar da ya yi miki kuma saboda samun sake lefe ma ba zai yi ba? Ki ba ni lambarsa". Gabanta ya faɗi, saboda ba ta so wani ya gano Abdul shi kansa ba son auren yake yi ba, ta sunkuyar da kai ta ce"Yaya ba haka ba ne, ka san bai daɗe da tafiya ba, duka wata biyu kenan, yanzu ma albashin wannan watan ne fa ya ba da sadakin, ya ce gaba zai yi mini lefen". Ya taɓe baki ya ce"Allah Ya kyauta, wannan auren amma sam inda an bi shawarata da an bar shi". Nawwara ta ce"A'a ka daina cewa haka Honey, tun da suna son junansu komai zai daidaita". Ya ce"Tashi mu je na samo miki kaya, na san nakin duk tsofaffi ne". Nawwara ta ce"Mu je na raka ku, dama ina son siyan wani curry". Ya ce"A'a rubuta mata dai ta ɗakko miki, kullum sai kin fita ko gajiya ba kya yi?" Ganin ta canza fuska kamar ba ta ji daɗi ba, ya yi murmushi ya ce"Ke wai ba ki gane me nake nufi ba ne? Ni dai ki tafi ki yi wannan shirin naki mai gigita ni, kawai ina dawowa na gan ki a turaka, ya fi miki wannan fitar". Ta yi murmushi tana faɗawa Nuratu sunan curryn, suka tafi tana cewa sai sun dawo. A hanya yake ce mata"Yanzu ke Nuratu kina tunanin nan da shekara nawa mijinki zai dawo?" Ta ce"E to, da zai tafi cewa ya yi shekara biyu zai yi, yanzu tun da an yi auren ƙila ma ba zai kai hakan ba". Ya yi murmushi ya ce"Kuma ke za ki iya riƙe kanki har tsawon shekara biyun?" Ta ce"To Yaya ka ce zan zauna a gidanka ai, idan ma an kwana biyu zan iya komawa gidan yayan babata, sun ce na koma can, sai na jira sanda zai dawo, idan kuma babu dama sai na fara wata sana'ar na dinga yi wa kaina komai". Ya ce"Nuratu kenan, ni fa ba wannan riƙe kan nake nufi ba, ai bai kamata mace ta dinga ciyar da kanta ba, ballanatana ma irinki wacce ta haɗa komai da najimi zai so". Ya gangara gefen titi ya faka motar ya kashe ta, ta kalle shi da alamar tambayar dalilin tsayawar, sai ya kafe ta da kallon da ya saka ta tsarguwa da kuma faɗuwar gaba, ta kau da kai daga kallon shi, a bazata ta ji hannunsa a kan nata, ta kalle shi da sauri, sannan ta kalli hannun nashi, a hankali ta zare hannunta, don ba ta manta wane ne shi ba a wajenta, shi ba muharraminta ba ne, ko ba ta da aure haramun ya taɓa ko da hannunta ne, ta ce"Yaya mene ne?" Ya ce"Wato Nuratu akwai maganar da nake son mu yi da ke mai muhimmanci, shiyasa na nemi mu fita mu biyu". Ta yi shiru tana sauraronsa. Ya ɗan yi shiru yana jujjuya kalaman da zai furta, sannan ya ga kunyar mara kunya ai asara ce, don haka ya fara magana kai tsaye"Nuratu wani auren ana yin shi ne kawai saboda rufin asiri da neman kamala a idon jama'a, kin gan ni a haka kamar ina samun cikakkiyar nutsuwa da matata, amma a baɗini ba haka abun yake ba, wallahi Nawwara sam ba ta san zaman aure ba, don dai ina da haƙuri ne kawai shiyasa har muka kai haka, dama can maleji nake yi, ballantana kuma yanzu da ta fara fita koyarwar nan, idan ta dawo ta yi girki dare ya yi, da na matso kusa da ita za ta fara ƙorafi, tana cewa ita fa duk a gajiye take, cikin kwanakin nan lamarin ya dame ni, ina tsoron na kasa jurewa. Nuraru na san a yanzu kin riga kin san maza, wannan mara kirkin mijin naki ya cuce ki, ya lasa miki zuma a baki". Ta dai yi shiru tana so ta ji ƙarshen zancen, ta gama sakankancewa so yake ya saka ta, ta nemi saki a wajen Abdul, don ta samu wanda zai aure ta su yi rayuwa mai inganci, sai dai tana nazarin me yasa zai sanar da ita matsalar iyalinsa? Kabir ya cigaba da faɗin"Nuratu ke ƙanwata ce, na san ba za ki kasa taimakona ba, wannan alaƙar da nake son mu ƙulla ni da ke sunanta taimakon juna, domin za mu dinga yin abin da Hausawa suke cewa ban gishiri, na ba ka manda". "Yaya alaƙa?" Ta tambaya da mamaki. Ya ce"Alaƙa mai ƙarfi ma kuwa, ina roƙon wannan alfarmar a wajenki Nuratu, mu dinga ragewa junanmu zafi, tun da ke kin saba da maza kuma yanzu babu damar samun su, ni kuma ga yanayin matata, kin ga ke ƙanwata ce, kuma matar aure, babu wanda zai kawo wani tunani mara kyau a kanmu, amma ya kike gani?" Ƙwalla ta cika idonta taff, ta ma rasa me za ta ce, gabaɗaya ya ɗaure ta da jijiyoyin jikinta. Ya ce"Na yi miki alƙawarin duk watan duniyar nan zan dinga ƙirga dubu ashirin ina ba ki, na tabbata kafin mijinki ya dawo kin haɗa kuɗin kayan ɗaki, kin ga ba ganewa zai yi ba, tun da dama can ya gama lalube ki, ya kike gani?" Tuni hawaye suka wanke mata fuska, ta rasa wane irin zamani ake ciki wanda mutane ba sa jin tsoron Allah, ba sa yin taimako domin Allah, indai wanda ke da matsayin ɗan'uwanta na jini zai so lalata rayuwarta to ina ga Agent wanda ba su haɗa komai ba? Tambaya take yi wa kanta wai meyasa maza suka mayar da kansu tamkar ƴan taure? Kabir ya kalli agogo a wayarsa yana cewa"Lokaci yana tafiya, na san maganar tana da nauyi, amma zan ba ki dama ki yi tunani, za ki samu ci da sha, har ma sutura a gidana, babu abin da ba zan yi miki ba, duk abin da kike buƙata kawai ki sanar da ni, sannan wannan ba wani abu ba ne mai wahala, da safe idan ta tafi gantalin koyarwarta, ni kuma sai na dawo gida, kamar ƙarfe goma haka, mu samu ko minti talatin ne". Ta ce"Yaya Kabir mayar da ni gida". Ya tashi motar yana cewa"Mu je ki yi siyayyarki, ki zaɓo kayan bacci ma su kyau". Takaici ya hana ta cewa komai, har suka ƙarasa babban shop ɗin, duk yadda ya yi da ita, fir ta ƙi fitowa daga motar, sai shi ya shiga ya siyo mata kayan, wanda yawanci riga da wando ne da riga da siket na roba, sai atamfofi kala uku, da ƙananun abubuwa, irin su towel, soson wanka, brush, da saitin man shafawa da subulai, haka dai kaya rigijib ya kawo mata, sai ta kasa yi masa godiya tun da zuwa yanzu ta fahimci ba don Allah yake yin komai ba. Da suka dawo gida sun tarar da Nawwara a falo, ta yi mamakin ganin shi ne ya ruƙo kayan ba Nuratu ba, sannan ba ta ce komai ba, ta wuce ɗaki, shi ma sai da ya ji ƴar fargaba, Nawwara ta ce"Lafiya kuwa, na ga ranta a ɓace?" Ya ce"Wallahi wani ne ya biyo mu wai yana son ta, na faɗa masa matar aure ce, to shi ne fa a mota har da kukanta, tana cewa ban da ƙaddara da tana tare da mijinta ai da wani bai ganta ba ma, ballantana ya ce yana sonta". Nawwara ta yi murmushi ta ce"Nuratu kenan, ni dai ban ga abun fushi a nan ba". Ya ajiye kayan, ta ɗauka ta buɗa tana cewa"An samo curryn?" Ya ce"To ina ma ta bi ta kan wani curry, lokaci ɗaya fa ta birkice kamar mai aljanu". Nawwara ta ce"To Allah Ya kyauta". Ta kwashi kayan ta miƙa mata, ta tafi ɗakin mijinta. Nuratu ta zauna tana ta tunanin mafita, indai wannan manufar ce tabsaka Yaya Kabir ya nemi ta zo ta zauna a gidansa, to kuwa gara ma ta zauna a gidan su Abdul ɗin, ba ta fatan ta sake aikata wani kuskuren a kan wanda ta yi, zina babban bala'i ce, ga shi ta sanadin aikatata sau ɗaya ta shiga masifar da take neman yi wa rayuwarta juyin waina cikin baƙar tanda, lallai gidan Yaya Kabir ba wajen zamanta ba ne, ya zama wajibi ta tattara ta koma inda ta fito. Bayan ta gama shirin bacci, sai ta ɗauki wayarta, ta kunna data, ta yi wa Abdul sallama ta gaishe shi, sannan ta ce"Na sauka lafiya tun ɗazu, da fatan kana cikin ƙoshin lafiya". Yana dubawa sai ta ga ya fara typin, daɗin zai kula ta da kuma fargabar abin da zai rubuto suka dira a zuciyarta lokaci ɗaya, yanzu har tana fargabar jin furucinsa a kanta, saboda ba ya faɗa mata magana mai daɗi. "Ke da waye yanzu a ɗaki?" Abin da ya rubuto kenan. Ita ma rubutun ta yi masa ta ce"Ni da kewarka ne, ka san gidan babu yara, ni kaɗai ce a ɗakin da aka sauke ni". Ya ce"Za ki iya yi mini vedion kanki a halin yanzu?" Ta ce"Gaskiya ba zai yi ba, saboda wayar babu flash". Ya ce"To gobe da safe ki yo mini vedion jikinki, ban ce ki saka kaya ba, saboda ina buƙatar ganin halal ɗina ne". Sai da ta ji gabanta ya faɗi da ta karanta, ta sake maimaita karantawa, ta yi mamaki, tun da ta ga yana ta nuna rashin damuwarsa a kanta, sannan ma ta lura kamar dole ce ta saka ya yarda da aurenta, amma har a ce yana jin kewarta da ta kai har yana neman ganin ko da hoton jikinta ne?" Ganin ta duba saƙon ba ta ce komai ba, ya sake rubuto"Ko ba zan samu ba?" Ta rubuta masa"Allah Ya kai mu goben". Ta ma rasa ta ina za ta fara wannan abun da ba ta taɓa yi ba, amma ta sani a yanzu Abdul mijinta ne, wannan ba haramci ya nemi ta aikata ba, sai dai tana jin nauyi kuma ta ga abun banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Tana cikin duba saƙonni sai ga saƙon Yaya Kabir ya shigo, stika ce ya turo mata ta mace da namiji rungume da juna, sannan ya yi gajeren rubutu ya ce"Zan kwana da kewarki". Don takaici ba ta san sanda hawaye ya sakko mata ba, ta kashe data ta kwanta tana jin zuciyarta babu daɗi, ga kuma rashin nutsuwa a tare da ita, ta san a yanzu idan ta ce za ta koma gida ba ƙaramin yaƙi ta ɗakko ba tsakaninta da Baba, da haka ta yi bacci kanta a cushe. Washegari da sassafe ta ji motsin Nawwara, ta fito ta gano ta a kitchen, ta shiga ta gaishe ta, sannan ta fara taya ta aiki, suna gama komai ta koma ɗaki, sanda suka fito karyawa Nawwara ta zo ta kira ta, ta ce"Anti sai anjima zan karya". Saboda ko ganin Kabir ma ba ta son yi. Bayan sun gama karyawa Nawwara ta leƙo tana ce mata "Za mu tafi" Ta ce"To Anti, me za a dafa muku kafin ku dawo?" Ta ce"Ki dafa duk abin da kike ra'ayi, sai mun dawo". Ta ce"A dawo lafiya". Bayan sun tafi, ta fito ta ci abinci, ta yi wanke-wanke, ta share gidan ta gyara komai tsaf, maganar Abdul tana maƙale a zuciyarta, don haka ta tashi ta yi wanka, ba ta ji a zuciyarta za ta iya yin vedion kamar yadda ya ce ba, don haka ta yanke za ta saka rigar bacci, sai kuma ta tuna ba ta da wata rigar bacci, rigunanta marasa nauyi ma duk sun tsufa sun ji jiki, ba za ta iya yi wa miji kwalliya da su ba, ta tsinci kanta da duba ledar kayan da suka siyo jiya, ta kuwa ga kayan bacci kala uku, ciki har da wata riga ta net mara kirki sosai, sai ta saka ta, ta ɗauki kanta a hoto, ta kunna data, da saƙon Kabir ta fara cin karo, da alama tun jiya ya turo, don cewa yake yi"Na zo na taya ki bacci?" Ta yi tsaki, ta shiga lambar Abdul ta yi sallama ta gaishe shi, sannan ta tura masa hoton da ta ɗauka yanzu, yana dubawa ya ce"Mene ne wannan?" Ta ce"Ba zan iya yin hoto babu kaya ba". Ya ce"Amma za ki iya ba wa wanu kanki ai ko? Kuma vedio na ce, sannan ina son ganin fuskarki sosai a vedion". Ta sauke gwauron numfashi, sai dai ta kasa cire rigar, don a ganinta rigar nan ta jikinta da ita da babu duk ɗaya suke, ta yi vedion a haka da rigar, ta tura masa. Tana turawa ta ajiye wayar tana jin babu daɗi, duk da ba haramun ba ne, sai can anjima ta ɗauki wayar domin ta ga amsar da ya bayar, ƙirjinta ya yi wata mummunar bugawa ganin kamar mutum biyu ta turawa, da sauri ta kalli lambar Yaya Kabir wanda har saƙon ya nuna blue tik alamar ya gani, ta miƙe tsaye tana ɗora a ka, ita ta ma manta da ana delete saboda yadda kanta ya ɗauki zafi, salati kawai take jerowa, wajen minti biyar kafin ta dawo cikin nutsuwarta, ta zo ta goge da sauri. Kabir wanda daɗi ya gama rufe shi, don wannan alama ce da take nuna ta gama amsar tayinsa, tuni ya tura shi zuwa laptop ɗinsa don ya more kallo da kyau, saboda haka ko da ya ga ta goge bai wani damu ba, sai ma stikar godiya da ya turo mata. Shi kuwa Abdul a na shi ɓangaren, yana kallon vedion zuciyarsa tana tafasa, wani kishi ne yake azabtar da zuciyarsa, a fili ya ce"Nuratu in sha Allah wannan vedion sai ya zama silar shigarki ƙunci na har abada, wannan vedion sai ya hana ki zaman aure, sai kin dawwama a gida kin tsufa kin mutu babu aure, babu ɗa babu jika, wannan ce hanya ma fi sauƙi da zan rama cin amanar da kika yi mini" . LAST FREE PAGES! To mutanena mu numfasa a nan, ko kun hango girman matsalar da Nuratu ta jefa kanta kuwa? Shin da gaske Abdul zai iya take ƙauna ya aiwatar da furucinsa a kan wacce ya fi so duk duniya, ashe ƙauna tana rikiɗa ta zama ƙiyayya? Yaya Kabir zai yi da wannan vedion? Shin zamanta a gidansa zai yi tsayi ko na ɗan lokaci ne? Na ba ku satar amsa? Nura zai yi ta aure-aure a wannan labarin, amma a ƙarshe ya zamansa da Hasana zai kasance? Akwai tarin ƙadarori a kan Nuratu, ku dai kar ku bari a yi babu ku, da ɗarinki biyar ki sha karatu. 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay bank Shaidar biya ta nan 08028966015