*MAHAUKACIN SO* 💞 Na Autar Marubuta ______________________________________ *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< Babu editing Page 1 & 2 Wani mutum ne magidanci kakkaura zaune cikin wani tafkeken falo ,jarida ce bisa hannunsa yana karantawa. Wannan mutum ba kowa bane face Alaji Muktar mazaunin kaduna Mutum ne mai kudi bana wasa ba . Wata dattijuwa ce ta shigo falon, kallo guda zaka ga babu wahala jikin wannan tsohuwa. Tsayawa tai ta zuba masa ido tana kallon shi . Bayan ya lura da ita ne , ya yi sum-sum ya cire gilashin dake fuskar shi yana aje jaridar . "Hajjiya lafiya kuwa."? Ya yi wa dattijuwar tambayar Kawai tsaki tai tare da juyawa ciki tana cewa. "Duniya ce ." Alaji Muktar ya yi murmurshi yana cewa. "Hajjiya ke nan ." Kallon hoton dake falon dakin take kamar zai motsi a yadda take gani , sake kura masa ido take tana kallon dayar matar da suke tare a cikin hoton da suke matukar kama da juna . Wata mata ce ta katse mata tunanin data fara da cewa. "To Mama zan tafi Allah ya jikansu Allah ya bada hakurin rashi." Sannan Mama ta dawo hankalinta tana kallon wannan matar tana cewa. "To mun gode Zuwaira , Allah ya bada lada." Kana matar ta fice Mama ta kalli Nasir dake tsaye da jaririya a hannunsa yana jijjigata ta ce . "Sannu Nasir da raino , ai idan suka zo suka dauketa sai ka huta ." Rai ya hade mata yana cewa. "Haba Mama , ni fa baza a basu wannan yarinyar ba , kawai kar ma su zo." Mama ta kalli autarta Ummi dake gefenta suna hada idanu. Sannan ta koma ta kalli Nasir tana cewa. "Kamar ya baza a basu ita ba , yarinya jaririya kai ne zaka shayar da ita ."? Nasir ya yi ajiyar zuciya tare da shigewa cikin daki ba tare da ya ce komai ba . Gidan Mama ke nan mutuniyar kirki wacce tun shekarun baya mijinta ya rasu, kana kanwarta wacce suke tare ita ma Allah ya yi mata rasuwa, sai Mama ta zamo ita ka dai , sai 'ya'yan ta da Alaji ya bar mata Ibrahim, Nasir, sannan Ummi Wanda a kwana uku da suka wuce ne babban dan nata Ibrahim da matarshi Allah ya yi musu rasuwa, sanadin hatsarin mota. Wanda suka tafi suka bar jaririya yar karama mai suna Laila . Sai dai tunda a kai rasuwar yau har kwana uku Nasir yaki bawa dangin matar jaririyar , ya ce ita kawai yake gani yaji dadi tunda babu yayanshi Ibrahim.. Wannan ke nan Yana zaune a falo jaririyar sai kuka take , ya tashi ya dauko fidarta dake cike da madara ya fara dura mata , har ta fara sha , amman tasake bingirewa da kuka . Ya mike tsaye ya dauko ruwa ya bata , sannan tai shiru ya fara yi mata waka yana jijjigata da cewa . "Lailo, Lailo rigima, Lailo Lailo rigima, kukan ya isa haka ." Tai shiru ta tsura masa idanu , yanayin wata rawa da yayi mata ya sa ta sake fashewa da kuka . Sai ya cigaba da jijjigata yana mata wannan wakar . A lokacin Mama ta shigo , ta kalli Nasir cikin takaici tana cewa. "Wai Nasir mene kake yiwa yarinyar nan , saboda taurin kai ka basu yarinyar nan amman ka ki , kullum kuka a cikin gidan nan , yarinya jaririya duk ta rame ta yi baki , to wallahi bazan yadda ba sai ka basu yarinyar nan." Nasir ya yi ajiyar zuciya yana cewa. "Haba Mama dan Allah, ni zan kula da yarinyar nan idan ku baza ku iya ba , babu inda zan kai ta ." Mama cikin fada ta ce . "To ai ka basu su shayar da ita ko , idan kuma kana da nonon da zaka bata naji ." "Haba Mama, Laila fa watanta biyar a duniya, ai ta kai lokacin yaye , ni wallahi na yayeta babu wanda zai shayar da ita ." Mama tai shiru tana kallon Nasir domin takaici ya sa ta rasa abin cewa. A lokacin wata kawar Ummi ta shigo , ta durkusa da gaida Mama . Sannan Nasir ya sa jaririyar shi a baya ya goyata . Washe gari Wajejen hantsi wata dattijuwa zubin masu fada tana zaune a tsakar gida , Tsinke ne a hannunta tana sakace, ta jefar da tsinke tare da tsaki da fadin . "Bahijja, Bahijja." Tai kiran tana tura kanta cikin dakin da Bahijjan take . Bayan Bahijjan ta amsa ne , ta fito tare da zama gaban mahaifiyar tata tana cewa. "Gani Inna na yi zatan ma bacci kike yi." Inna ta ce . "Shiryawa zaki mu je mu dauko wannan yarinyar idan baso suke su kashe taba . Ita Maman Nasirun fin karfinta ya yi da baza ta ce ya bada ita ba , ya bayar ." Bahijja tai ajiyar zuciya me zafi tana cewa. "Dan Allah Inna kibar musu ita." Inna ta ce . "Lallai ne Bahijja, ai daga ke har Nasirun babu wanda yasan zafin haihuwa, shi ya sa baku damu ba , Kuma wannan yarinyar Laila ai nima jikata ce , ina da iko da ita , dole zan je na karbota mu anan akwai wanda zai shayar da ita ." Ta karasa maganar tare da mikewa tsaye ta shige daki , da nufin shiryawa domin zuwa gidan Mama. Anan kuwa Nasir yana zaune a falo sai kwalawa Ummi kira yake yana fad'in "Wai har yanzu ba a gama wankan ba ne ."? Ummi ya yi mata kiran yafi a 'yarga , harta gaji ta dena masa magana Ita ma Mama dake zaune a falon ko kula shi ba tai ba , Kamar ma bacci take son yi A lokacin Ummi ta shigo rike da Laila a hannunta an san ya mata kaya masu kyau . Sai suka ji ana kwankwaso kofar falon . Nasir ya mike ya karbi Laila a hannun Ummi yana cewa. "Je ki duba ." Mama kawai taji dariya ce ma ta kamata . Ya zauna tare da Laila a hanunshi , Ummi ta nufi kofar tare da budewa . Inna da Bahijja ne , hakan ya sa cikin sakin fuska Ummi ta musu iso zuwa cikin falon . Amman yadda Ummi ta kula furkar Inna babu annuri ko kadan , musamman yadda taji ta ratsa tsaki da ta ga Nasir. "Sannunku da zuwa Inna , ku ne a gidan ."? Mama ta fada yayin da take gyara musu gurin zama . Zama suka yi , Bahijja ta gaisa da Mama cikin far a Sannan Nasir ya kalli Inna yana cewa. "Inna ina kwana ." Ya mutse fuska ta yi sannan ta ce . "Lafiya lau , kawota ." Ta mika hannu, Nasir ya kalli Mama kamar bazai bada Laila ba sannan ya mika mata . Murmurshi Mama ta yi tana kallon furkar Inna da babu annuri tana cewa. "Ya mutanen gidan suke , ya karin hakuri." Inna ta kalli Mama tana cewa. "Hakuri kam muna ta yi , tunda ga shi mun zo mun ga yarinya jaririya duk ta canza , saboda wahala . Shi ya sa na taso domin yau zaku bamu ita." Inna ta aje maganar tana kallon Nasir "Tafiya da ita kuma ."? Nasir ya tambaya Inna ta maida masa da amsa da cewa . "Ehh ko zaka hana ne ubanta ." Nasir ya mike tsaye tare da cewa . "Amma ai na ga mu ne dangin mijin yarinyar nan , dan haka mun fi kowa iko da ita." "Wallahi idan ka ce zaka min rashin kunya zan kwashe ka da mari anan wajen ." Inna ta maida masa Mama ce tai ajiyar zuciya tare da kallon Inna tana cewa. "Ki yi hakuri Inna, ai abin bai kai haka ba , za a baku ita ." "Mama kamar ya za a basu ita , a kan me ."? Mama ta kalli Nasir cikin fushi tana cewa. "Idan ka sake samin baki a magana sai na bata maka rai ." Inna ta kalli Ummi tana cewa. "Shi ga ki debo mini kayanta ." Mama tai saurin dakatar da ita da cewa . "Ba sai an yi haka ba Inna in Sha Allah gobe da kai na zan zo na kawo muku Laila, in Allah ya yarda ." Nasir yaji wani abu ya tokare masa zuciya "To shi ke nan Allah ya kai mu goben , muna jiran ku." Inna ta karasa maganar tare da mikawa Ummi jaririyar tana kuma tashi tsaye "Haba ! Ko ruwa baku sha ba zaku tafi ." Mama tai magana tana kallon Inna , yayin da ita ma Bahijja ta mike tsaye "Eh zamu tafi muna da komai a gida, sai naji ku goben ." Tana gama fade ta fice Bahijja tabi bayanta... Autar Marubuta ✍️ 07040805269 WhatsApp only *MAHAUKACIN SO*💞💞 Na Autar Marubuta *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< ________________________________________ Babu editing Page 3 & 4 "Haba Mama dan Allah, hakurin ki ne ya sa matar nan take mana haka , basa da wani iko da Laila, domin a yanzu bata da wani uba da ya wuce ni ." Nasir yayi maganar cikin bacin rai Mama ta ce . "Nasir bana san tashin hankali, dole gobe zan mayar musu da yarinyar nan, idan ya so tai shekara biyu sai su dawo da ita , ba shi ke nan ba ." Nasir ya ce . "Nima zan iya rainon shekara biyun ai , gaskiya babu inda za a kai ta ." Mama ta mike tsaye cikin bacin rai tana cewa. "Kai mahaukacin ina ne wai Nasir, to wallahi gobe dole za a basu yarinyar nan ko kana so ko baka so , baki daya shekarun naka nawa suke , tunda aka haifi yarinyar nan ka haukace mana a gida . To Allah ya kai mu goben zan kawo karshen komai ." Tai tsaki ta shige daki. Nasir ya karbi Laila a hannun Ummi, yayin da wasu hawaye suka zubo masa . Har dare yayi Nasir yana cikin takaicin gobe ta yi . Domin duk wata mafita ya duba domin ganin an bar masu Laila a gidan amman ya rasa yadda zai yi . Haka da dare ya yi Ummi da Mama suka shige daki da Laila suka kwanta , shi kuwa Nasir yana falo zaune ko abinci ya kasa ci . Washe gari da safe Wajejen hantsi Inna na zaune tana hutawa tana tunanin yau za a kawo mata jikarta Anan kuwa Ummi tunda Allah ya sa ta kula cewa Laila bata nan hankalinta ya tashi , ta duba duk gidan amman bata ga Laila da Nasir ba Hakan ya sa ta tashi Mama a bacci take fada mata Nan ita ma hankalinta ya tashi matuka "To kira shi a waya mana , ko ya tafi kai musu ita ." Mama ta fada Ummi ta ce . "Wallahi Mama wayarshi a kashe tun d'azu." Mama tai ajiyar zuciya tare da fadin "Oh ni Nasir ina ka shiga ." Ta fita ta nufi dakinsa, koda Mama ta kula da yanayin dakin sai ta ga kamar Nasir ya debe kayansa Da sauri ta koma dakin su ta duba kayan Laila, ta ga riga guda biyu ce kawai a cikin akwatitinta "Innalillahi Ummi ba dai Nasir guduwa ya yi da yarinyar nan ba ." Ummi taji gabanta ya fadi , ta kalli Mama da cewa ."kamar ya Mama me kika gani wai ." Cikin tashin hankalin nan Mama ta kara mata da cewa . "Na duba dakinsa kayanshi basa nan , kuma dubi kayan Laila." Cikin faduwar gaba Ummi ta sa hannu cikin akwatin ta ga rigunan Laila guda biyu sai wata takarda da akai rubutu da fensir a ciki . Da sauri ta dauki takardar tana zaro ido tana kallon Mama "Shi ne ya aje takardar ko , karanta muji ." Ummi cikin jin tsoron abin dake cikin takardar ta zura mata ido da nufin fara karanta wa . "Mama ku yafe ni , ni na tafi da Laila, sai wata rana karku neme ni , kar kuma ku d'aga hankalinku , idan da rabo zamu gana watarana babata . Sako daga Nasir." Abin da Ummi ta karantowa Mama ke nan Mama hannayenta guda biyu ta dora a kai cikin tashin hankali tana cewa. "Innalillahi wa inna'laihir raji un. Yanzu abin da Nasir zai mana ke nan , wannan wanne irin mahaukacin yaro ne . Innalillahi wa inna'laihir raji un." Mama ta sauke hannayen kasa tare da zama a bakin gado cikin wani yanayi Dogon numfashi Ummi taja , sannan ta aje shi cikin matukar takaici da tunanin irin abin da Nasir ya aikata musu "Yanzu ni me zance zanin aro ya bata ." Mama ta fada tare da fara kuka Ummi ta durkusar da gwiwowinta kasa a gaban Mama , sannan ta dafa kafar mahaifiyar tasu cikin rarrashi ta fara magana. "Dan Allah Mama ki dena wannan kukan , in sha Allah duk inda Yaya Nasir ya je da Laila zasu dawo." Cikin sabon kukan takaici Mama ta ce . "Yi shiru Ummi kar zuciya ta buga , yanzu ina zansa rai na idan wannan zancen ya fita." Ummi ta durkusar da kai kasa , yayin da wasu hawaye suka gangaro mata , domin tasan tabbas abin da Nasir ya yi ba abin da kuda zai bi bane , dole Mama ta shiga tashin hankali. Har wajejen 12 na rana , su Mama suna cikin wannan tashin hankali, duk sun kira wasu daga cikin 'yan uwa , da suke tunanin Nasir zai je amman babu labari. Anan ita ma Inna sai mita take yi, har Bahijja ta gaji da ji "To yanzu dan Allah Inna yaushe garin ya waye , ai tunda suka ce zasu kawota , zasu zo ai ." Inna ta maida mata da cewa . "Shiru kike ji makad'i ya fad'a rijiya ai , gaskiya abin ya ishe ni haka ." Bahijja tai ajiyar zuciya tare da gyara zaman yaron dake kafarta mai kimanin shekaru biyar da haihuwa A lokacin wata 'yar Innan ita ma ta shigo gidan me suna Rabi . Yaron mai suna Mahmud ya tashi daga kafar Ummi da gudu ya nufi Rabi , ita kuma tasa hannu ta dauke dan nata sama . Murmurshi Bahijja tai tana cewa. "Lallai Mahmud ka kyauta ." Mahaifiyar Mahmud ta ce . "To kinga lefinshi , dan gatan babanshi .". Ta karasa maganar tana kallon Inna da cewa . "Inna har yanzu basu zo ba ne ."? Inna ta dauke kanta , dariya ce taso kama Bahijja, domin wani abin idan Inna tai yana matukar bata dariya . Kallon Inna tai tana cewa. "Inna ke fa kina da jikoki , da zaki bar musu Laila, kinga Mama bata dasu ." Kawai Inna ta fashe da kuka tare da face majina da gefen zaninta tana cewa. "Allah ya jikanki Batula , Allah ya miki rahma , saboda ita nake son rike wannan jaririyar. Allah ya jikanki Batula." Duk sai jikinsu ya yi sanyi , yadda suka tuna 'yar uwar su . Bayan sallar magari ba Mama ta dukufa da addu'a , Domin har yanzu babu labarin Nasir Bayan Mama ta idar da adduarta, ta kalli Ummi da ke gefe ta yi tagumi ta ce . "Kira kanin mahaifin ku Alaji Bashir, kiji wanne hali ake ciki ." Cikin mutuwar jiki Ummi ta nufi daki domin dauko waya . Washe gari "Zancen banza , zancen wofi , kamar ya Nasir ya bata tare da Laila."? Inna tai maganar cikin masifa , Bahijja dai tai shiru , hakan ya sake ingiza Inna tana cewa. "Ai zancen duniya ba ya buya , tun jiya abin ya faru amman baza su iya sanar damu ba , Allah wadaran sirikai irin wannan wallahi Aikin banza aikin wofi ." Ta sake kallon Bahijja da ita ma abin ke dukanta tana cewa. "To yanzu wanne hali ake ciki , shi kanin baban nasu Bashir me ya yi akai ."? Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 *MAHAUKACIN SO* Na Autar Marubuta *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< ________________________________________ Babu editing Page 5 & 6 A daren yau ma kuka Mama take ta yi , carbinta na hannunta Ummi ce take rarrashin ta da cewa . "Mama ki yi hakuri dan Allah, kinji abin da malamai suka ce , suna cikin koshin lafiya , kuma kin san Baba Bashir zai cigaba da kokarin ganin Nasir ya dawo , ki dena kuka ." Mama cikin wannan kukan ta ce . "Ki bari kawai Ummi , Nasir ya yi abin kunya , kiji irin maganganun da mutane suke yi , ba kuma sa duba cewa Nasir kanin mahaifin Laila ne , amman wasu har cewa suke yankan kai zai shiga da ita , wannan wacce irin masifa ce ." Ta sake fashewa da kuka . Bayan wata daya Anan cikin wani babban gida kuwa , Alhaji Usman ne zaune a falonsa yana wasa da wata yarinya me kimanin shekaru biyu, yarinyar kuwa sai dariya take ta yi abinta A lokacin matarshi ta shigo tana murmurshi da cewa. "Alaji ke nan fatiman ce dai sai wasa ake da ita , kamar baza ka fita office ba ." Dariya ya yi yana daukar yarinyar bisa kafarsa yana cewa. "Wato Hajjiya wannan yarinyar tamu Fatima , tafi min komai , idan ina tare da ita duk wata damuwa mancewa nake da ita ." Hajjiya ta ce . "Hmm Alaji ke nan ." Alaji Usman ya sake fadin . "Allah dai ya raya mana ita , ta taso cikin daula da rikon amana da sanin ya kamata." Ta ce . "Ameen ya Allah, kamar dai halin babanta." Alaji ya yi dariya. Inna ce nan zaune a cikin daki , Bahijja ce ta shigo sanye da kayan makaranta . Zama ta yi kusa da Inna tana cewa . "Wash Allah na gaji Inna." Inna ta kalleta da cewa . "Ai ana rana , amman yau kun taso da wuri ." Bahijja ta ce . "Wai Inna mancewa ki kai muna jarabawar fita ne ." Inna tai dariya ta ce . "Au haka ne fa , to Allah ya taimako." Bahijja ta ce . "Ameen Innarmu , daman yau ina son naje gidan Aunty Rabi ." "To ai shikenan Allah ya kaimu." Cewar Inna Sannan ta kara da fad'in "Ohhh ni duniya, har yanzu babu labarin Nasir ko."? Bahijja ta ce . "Ummmm Inna ke nan ." Inna ta rufe da cewa . "To Allah ya kyauta, abin ya wuce yadda muke tunani.". Bayan shekaru biyu biyu Mama ce a zaune a tsakar gida tare da carbi a hannunta, ta kalli Ummi dake gefenta ke danna waya tana cewa. "Wallahi babu abin da zancewa kanin mahaifin ku Alaji Bashir, sai fatan alheri. Ki dubi irin wannan kayan dakin da ya yi miki , wallahi sai dai godiya , ai da wani ne bazai yi ba ." Ummi ta kalli Mama ta ce . "Uhmmm! Haka ne Mama. Ya rike mu da gaske , sai dai mi fatan Allah ya bamu ikon biyanshi ." Mama ta ce . "Haka ne , Allah ya bada lada , sauran kwana goma fa , kamar yau aka sa bikin nan ." Ummi ta sunkuyar da kai tana murmurshi, yayin da Mama take sake cewa . "Ga Bahijja yanzu ta kusan shekara a dakin mijinta ." Ummi ta ce . "Haka ne ." Anan gidan Alaji Usman kuwa Shi ne tsaye a cikin falo , yana bude murya yana cewa da matarshi . "Wai haryanzu baki shirya fatiman ba ne , na ga alamun kina son na makara ." A lokacin matarshi ta fito rike da hannun Fatima wacce aka shirya tsaf da kayan makaranta tana cewa. "A yi hakuri mana Alhaji, ai gamu mun fito ." Ya rike hannun yarinyar tasu ya yi waje , yayin da yarinyar ke kallon mahaifiyar tata tana cewa. "Bye-bye mommy.".. ...... Bayan wasu shekaru Kasaitacciyar budurwa ce kwance kan gadonta tana hutawa, domin ko alamun bacci babu a tare da ita . Wayarta ta jawo a gefe kai tsaye ta nufi wata number da kai saving da My fa Ta dannawa number kira , bugu daya , wata mace me dadin murya ta d'aga tana cewa. "Hello Fatima ya kike ya mommy."? Fatiman ajiyar zuciya tai tana cewa. "Wallahi Fa'iza lafiya lau , daman ina son mu hadu ne ." Daga can bangaren wacce aka kira da Fa'iza ta fara cewa . "Ba damuwa Fatima , zan zo in sha Allah." Ta karasar maganar da yaren masu jan kunne (turanci) Bayan sun kammala wayar , Fatima na saukewa wani kiran ya shigo mata , wanda ya matukar faranta mata rai , ba kowa bane face muradin aurenta Abdallah. Anan gidan Mama kuwa, bayan shekaru masu yawa babu abin da ya canza a wannan gidan , idan ka cire wasu shekaru a can baya da Mama ta kasa gane kanta sanadiyar shigowar Nasir cikin gidan babu zato babu tsammani A yanzu haka duk suna zaune a falo , a kan carpet suna karyawa . Nasir ne ya kalli Laila da duk hankalinta ke kan wayarta yana cewa da ita . "Laila bana hanaki danna waya ba , lokacin cin abinci."? Baki ta turo gaba kamar mai shirin kuka , sannan ta kalli Mama ta ajiye wayar a gefe ,kana ta maida hankalinta ga abincin dake gabanta "Uncle N , ina so naje gidan Aunty Ummi." Laila ta yi maganar tana kallon Nasir Shima kallonta yayi sannan ya maida mata da cewa . "Ki bari sai gobe zan kai ki ." Laila ta ce . "Tom Uncle." Mama dai bata ce dasu komai ba Wannan ke nan , shekarun baya da suka wuce Mama tana zaune da rana cikin gidanta , sai taji sallamar Nasir ya shigo , hakan ya matukar tada hankalinta sosai , domin tare da Laila ya shigo a hannunsa, lokacin tana da shekaru uku , Babu abin da Mama ta iya cewa a kan wannan lamarin , domin tunda Nasir yasa kafa ya fice da Laila tana jaririya, bai dawo da ita ba saida ta shekara uku . Mama kawai kuka ta fashe dashi mai matukar taba zuciya, mutanen gari kuwa kafin kace komai sai gari ya dauka ga Nasir can ya dawo shida Laila Haka Alaji Bashir Shima ya sami labari , bayan ya zo ya ganewa idanunsa ya matukar fitar da bacin ransa da takaicin sa ga Nasir, domin har wani zance yaso ya fitar da zaisa Nasir ciikin mugun yanayi, amman Mama ta hana shi . Tashin hankali aka yi sosai kafin komai ya dawo daidai , ita ma Inna da guntun bala'inta tazo , ta juyewa Nasir In takaice muku zance Mama harda hawan jini sai da ta watanni babu lafiya , kuma tai matukar fushi da Nasir Lokacin da Nasir ya so kare kanshi yake basu hakuri, tare da tabbatar musu ba ya son a dauke Laila a gidansu ya sa yayi wannan abin , domin sam baya son a raba shi da jaririyar yayan nashi . Sai dai babu wanda ya amshi uzurinsa , domin ba abin da za a kama bane Nan Inna ta sake tada jijiyoyin kai , a kan dole sai an bata Laila, Yadda Nasir ya ga Mama na matukar fushi dashi yasa bai ja dasu ba Sai dai bayan sun dauki Laila, abin bai musu dadi ba , domin kullum kuka babu wanda take kira sai sunar babanta Nasir, haka ta rame ta lalace babu wanda ta saba dashi sai Nasir. Hakan yasa dole suka dawowa da Nasir yar shi Bayan wannan ya faru sai komai ya fara lafawa , domin Nasir yayi matukar nadama , hakan yasa Mama ta yafe masa . Har yake bata labaranin yadda ya kula da Laila Nan ne aka sanyata makaranta, ta fara wayo Shi kuma Alaji Bashir bayan Shima ya huce , ya bawa Nasir aiki. Sai Mama taji duk farin cikinta ya dawo , domin a halin yanzu Laila ta gama makaranta. Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 MAHAUKACIN SO 💞 Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page. 7 & 8 Nasir ne zaune a cikin office dinshi , yayin da abokin shi Umar ya kawo masa ziyara Wayar Umar ta fara ringin, ya kalli wayar dake bisa teburin aikin Nasir da yakan iya ganin me kiran Sannan ya kalli Nasir yana cewa . "Mutuniyar ka fa ke kira. Dan Allah ka bawa yarinyar fuska , wallahi tana san ka ." Nasir kawai yaja tsaki tare da jan bakinsa yayi shiru Hakan baisa Umar jin haushi ba , ya sake cewa dashi . "Yanzu dan Allah to sai yaushe ne za kai aure, dukkan abokanmu sun yi aure , amman kai ko a jikinka , bayan ga yarinyar nan Batula na son ka kamar zata mutu." A lokacin Nasir ya maida masa da cewa . "Ni fa duk wani aure baya gabana , kuma babu yarinyar da nasa gaba , kawai sai na aurar da Laila tukun ." Umar kawai ya yi ajiyar zuciya. Anan kuwa Fa'iza ce kwance kan gadon Fatima, yayin da Fatiman take gefe bisa gadon a zaune "Har yanzu dai kin ga Abdallah shiru ." Fatima tai maganar tana kallon Fa'iza, murmurshi na yake Fa'iza ta yi tare da kauda kanta gefe . A karo na biyu , Fatima ta sake bude baki cewa. "Ai na ce masa bani da wata kawar data wuce ki , domin kawancen mu ya koma 'yan uwan taka ." Murmurshi Fa'iza ta kuma yi , kafin ta ce . "To ni wallahi da baki kira ni ba , yaushe muka gaisa da Abdallan ? Ko sati biyu ba ai ba , da naje shopping na ganshi ." Fatima ta maida mata da cewa . "Amman shi ya ce kun dade baku hadu ba , yana son ku gaisa." Fa'iza ta ce . "Ai shi ke nan ." Lokacin ne wayar dake bisa hannun Fatima , ta fara ringin Hakan yasa ta yin murmurshi tana cewa. "Kin ga kiranshi , ya zo ke nan .". Tana karasa maganar ta dauki kiran . Bayan ta gama ne ta fita , yayin daba wani dadewa tai ba ta bugo wayar Fa'iza tare da sanar mata ..... Wani tsoro Fa'iza taji duk ya kamata , jikinta kuma duk ya mutu, haka ta tashi ta nufi babban harabar gidan su Fatima inda suke tare da Abdallah Dogo ne sosai kalar hutu, da gani yaron manya ne , duk da ba fari bane . Haka Fa'iza ta karasa gabansu tare da cewa. "Assalamualaikum masoyan juna ." Murmurshi Fatima ta yi , yayin da Abdallah ya amsa mata da cewa. "Wa'alaikis Salam aminiyar sarauniya ta." Ba tare da Fa'iza ta kalli fuskar Abdallah ba ta sake fad'in. "To ya kazo , ya kawar tawa." Wani murmurshi me kyau da jan hankalin Abdallah ya yi sannan ya maida mata da cewa. "Lafiya kalau Fa'iza, amman wato yadda alakarku take da fateema abin yana matukar burge ni , rayuwar ku abin birgewa." Dariya Fatima da Fa'iza sukai a tare da juna , kana Fatima ta maida masa da fadin. "Ai ni Fa'iza ta wuce komai a guri na , domin rikon amana da matukar mutunci, ta yadda ranta ya baci idan na wani zai yi fari , haka kuma ..." Fa'iza ce ta dakatar da ita da cewa. "A'a wannan ai kowa yasan halinki ne , ke mutuniyar kirki ce , ko rabin ki ban yi ba." Abdallah ya yi dariya cikin wani yanayi mai kyau , sannan ya kallesu yana fad'in. "Abin naku abin birgewa." Sannan Fa'iza ta kalli Fatima tana cewa. "Bari na shiga ciki, sai kin shigo , Abdallah sai anjuma." Su kai sallama sannan Fa'iza ta nufi cikin gidan. Allah-Allah Fa'iza take ta shiga ciki , domin ci take kamar kafafunta baza su dauketa ba , bayan ta karasa dakin Fatima, ta fada gado cikin wani yanayi ta rushe da kuka mai gwanin ban tausayi. Anan gidan Mama kam Tana zaune cikin falo suna kallo da Laila, Nasir ne rike da jakar office ya turo kofar falon. Bayan ya yi sallama ya sami daya daga cikin kujerun falon ya zauna. "Mama sannu da gida ." Nasir ya fada Mama ta maida masa da fad'in. "Sannu Nasir da hanya ." Kana Laila ta kalleshi tana cewa. "Uncle sannu da zuwa ." Ya maida mata da cewa. "Yawwa." Sannan ya maida hankali ga kallon da suke , lokaci guda kuma yana cewa. "Mama Allah ya sa dai ba tuwon kikai mana ba ." Mama ta ce . "Hmm." Ba tare data kara cewa dashi komai ba , bai damu da hakan ba ya kalli Laila yana cewa. "Yawwa ke Laila, wai mene hadinku da Mahmud ne , na ga kwana biyu abin bana gane masa ." Cikin mamaki Mama ta kalli Nasir tana cewa. "Kaji mini yaro , Kamar ya mene hadin su , ba d'an uwanta bane ." Kawai Laila ta kwashe da dariya mai cike da bayyana matukar kyanta Yadda Nasir ya ga tana dariyar ne yasa yaji farin cikin sa ya karu . Mama ce ta bude baki tare da cewa. "Ai kai ta zamanka , har Laila ta yi aure , kana nan a gida tunda abin ba ya damunka." "Hhhhhhhhhh. Mama ke nan ai bazan aure ba , sai na aurar da Laila, domin bazan bar rayuwar Laila ta shiga garari ba." Mama ta ce . "Ai shi ke nan , sai ka zauna har lokacin barina duniya ya yi , ban ga yayanka ba ." Dariya Nasir ya kuma yi yana fad'in. "A'a wallahi Mama babu inda zaki in sha Allah." Mama tai murmurshi tana cewa. "To zaka ci abincin ne ko zancen za kai ta yi." Nasir ya ce . "A'a Mama mu dai cigaba da zancen , domin tabbas sai me sa'a ce zata aure ni , kuma me sa'a ne zai auri Laila, Kuma idan na shigo gida na ganku tare da Laila sai naji duk damuwa ta ta tafi, shi ya sa Laila tunda ta ga ma secondary kawai ta zauna , domin bana so ta cigaba da karatu maza suna biyo mini kyakykyawa ta.".. "Dan Allah ka yi min shiru Nasir.". Mama ta fada Yayin da Laila ta kuma dariya . "Sai surutu kake yi tunda ka shigo, ka je kaci abinci ma ya gagara." Nasir ya yi ajiyar zuciya tare da murmurshi yana cewa. "Mama ke nan." Laila ce ta kalleshi da cewa. "Uncle N na kawo maka abinci ne." Shima ya kalleta ya maida mata da cewa. "Karki kuma ce min Uncle ko Uncle N, Yaya Nasir kawai." Yadda Laila ta ga alamun da gaske yake ya sa ta cewa. "Tom." Sannan Mama tai dariya tana cewa. "Ai ni lamarin ku dariya yake ban , ai kuma Baba ya kamata ki rika ce masa ." Dariya Nasir ya yi yana cewa. "A'a Baba kuma Mama, kina ganin had'ad'd'en saurayi." "To ai irin yadda kai wahala da Laila tana karama, idan tace baba ai batai laifi ba." Nasir ya ce . "Haba Mama mene na tone-tone kuma." Dariya Mama da Laila su kai , Mama tana cewa. "To mene Laila bata sani ba ,ai an bata labarin komai ." Duk ka suka kwashe da dariya Nasir na cewa. "Allah sarki duniya." Anan cikin gidan Inna kuwa , bayan shekaru masu yawa, tana nan yadda take , idan ka cire wata yarinya jikarta Farida da aka kawo mata suke zaune tare Inna na zaune taji sallama, tun ba a shigo ba hakan ya faranta mata rai ta fara nuna farin cikin ta , domin ta dau murya. Wani had'ad'd'en saurayi ne sanye da kananun kaya , rike da mukullin mota ya shigo . "Sannu da zuwa Mahmud, angon Laila in sha Allah." Inna ta yi maganar cikin farin ciki, yayin dashi kuma dukkan hakoransa suka bayyana yayin da yake dariya. Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 *MAHAUKACIN SO*💞 Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 9 & 10 Guri Inna ta sama masa ya zauna yayin da suka gaisa cikin raha da girmamawa take tambayar mahaifin nashi da mahaifiyarshi Rabi Nan ya tabbatar mata duk suna lafiya "To Inna ina Faridan ta shiga ne ."? Mahmud ya tambaya Inna cikin sakin fuska ta ba shi amsa da cewa. "Tana islamiyya , ba a ta so ba ." Mahmud ya ce . "To Masha Allah." Su kai shiru na wasu sakanni, hakan yasa Inna cewa. "To ko daga wajen Lailan kake ." Sarkin dariya, ya yi dariya yana cewa. "A"a daga gida nake , gurin ki na zo kawai ." Inna ta ce . "To ai ka kyauta, amman ya kamata ka biya gidansu Lailan." "To ai Inna Baban nata ne kamar ba ya son zuwa na fa ." Inna ta ce . "Kamar ya , wai Nasir, duk tsiya Laila jininka ce ai bai isa ya hanaka zuwa ba , gara a samu a tura kawai , idan ma wani yake son bawa ya fasa." Mahmud ya yi murmurshi yana cewa. "Haka ne Inna, amman kina ganin ban yi wuri ba ." "Babu wani wuri da ya yi , tunda dai ta gama makaranta tun -tuni , to me ake jira kuma." Mahmud ya ce . "Haka ne ." Haka su kai ta hirarsu , lokacin da ya tashi tafiya ya debo kudi ya bata , sannan ya hau motarshi ya koma . Suna cikin tafiya a mota , Laila ta kalli Nasir yayin da suka hada ido sukai wa juna murmurshi Ajiyar zuciya Laila ta sauke , kana ta kalli Nasir tana cewa. "Uncle ina da.." Ba tare da ya bar ta ta fadi abin da take so ba ,ya katseta da cewa. "Laila bana ce ki dena cemin Uncle ba ." Murmurshi tai tare da hadawa da dariya tana cewa. "Ni Uncle gaskiya na saba , ka barni a hakan ." Shima yayi dariya yayin da yake murza kan mota ya ce . "To shi ke nan." Murmurshi ta kuma masa tana cewa. "To Uncle yaushe za kai auren hankalin Mama ya kwanta." Zuciyar shi yaji wani bugu yana fita da ya kasa gane dalilin sa Ba tare da ya kalli fuskar Laila ba ya fara cewa da ita. "Laila ba ko yaushe ake samun so na gaskiya ba.so abu ne mai wahalar da zuciya da kuma rayuwa, zan yi aure Laila karki damu ." Kallonshi tai cikin sakin fuska tana cewa. "To Uncle wace zaka aura , zan so ganin wannan ranar ." Murmurshi ya mata , a sa'ilin da yake shan kwanar gidan Ummi yana cewa. "Ki samo mini wacce ta dace Laila." Cikin far a ta sake cewa dashi . "A kwai kyawawan mata da zasu dace da kai Uncle." Kallonta ya yi tare da katseta da cewa. "A'a bana son kyakykyawa Laila, wacce take da kyan zuciya kamar ke, take da hankali da tausayi kamar ke Laila." Sunkuyar da kai ta yi tana murmurshi, kana daga bisani ta dago tana cewa. "Uncle dina ke nan , duk kasa naji kunya ma , ni bansan so ba Uncle, amman ina gani ina kuma ji a littattafan hausa, so guba ne me karya zuciya Mai hana sukuni idan ba kai dace ba , sannan kaddara ne da ba a sanin lokacin da yake bibiyar mutane." Dariya Nasir ya yi tare da cewa. "Wato haka kika san so ke nan , karki mamaki idan kika ga komai ya faru a sanadin so ." A lokacin ya bude kofar motar ya fita , kana Laila ta bishi da murmurshi tana fad'in "Allah sarki Uncle dina , Allah ka ba shi mace ta gari , ka faranta rayuwar shi , shi ne komai na , kunnuwa na maganar shi kawai suke ji ." Ta wajen gilashin motar ya matso kusa yana cewa da ita . "To zaki fito ne ko kuwa." Dariya ta yi kawai ta bude murfin motar ta fita , kana ya tasa ta gaba suka shiga gidan Ummi kanwarshi. Sallama Laila ta fara yi a cikin falon , yayin da taci karo da wani karamin yaro yana zaune yana wasa. "Sultan ina maman naka ." Laila tai maganar yayin da ta dauki yaron a hannunta. "Sannunku da zuwa." Ummi ta turo labulan falon tana fad'i "A she Aunty Ummi kina nan na yi zatan Sultan kika barwa gidan." Dariya ta yi sannan ta kalli Nasir tana cewa "Yaya Nasir ka zauna mana." Nasir zama ya yi kamar yadda kanwarshi ta bukata "Aunty Ummi khairat bata zo nan ba ke nan ." Laila ta tambaya Ummi ta kalleta tana cewa. "Ta zo tana ta zaman jiranki har ta tafi." Laila ta zumburo baki tana kallon Nasir da fad'in. "Wallahi duk uncle ne yaja , tun dazu nake cewa ya taso mu taho." Nasir ya yi dariya yayin da ya kara da cewa. "To ba sai na kai ki gidan nasu ba , ko ba wannan kawar taki kanwar soja ba ." Kafin Laila ta ba shi amsa Aunty Ummi ta fara magana. "Wai ba ku ce min Mama kalau take ba , bamu gaisa ba , sai wani zance ake kuma ." Dariya Laila ta yi kana ta kalli Aunty Ummi, lokaci guda kuma tana gyara zaman Sultan dake hannunta yana wasa , tana cewa. "Mama tana lafiya kalau , ta ce a gashsheki sosai da sosai da jikokin nata ." "To Masha Allah." Abin da aunty Ummi ta fada ke nan Sannan Yaya Nasir ya maida mata da cewa. "To ina yartawa ne kuma Mama na." Aunty Ummi ta ce . "Au wai Mommy, tana makaranta." Laila ta ce . "Mai sunan Mama ai akwai son makaranta." Aunty Ummi ta kalli Laila tana cewa. "Na yi zatanfa da Mahmud ma zaku zo wallahi." Kawai Yaya Nasir duk ya canza ya koma wani yanayin daban Murmurshi Laila ta yi kana ta ce . "A'a Uncle ne ya kawo ni ." Kawai Yaya Nasir ya tashi tsaye , sannan ya karbi sultan a hannun Laila tare da mikawa Ummi shi , Fuska babu annuri ya ce . "Tashi mu tafi." Duk mamaki ne ya rufe su da ganin Nasir ya canza musu a wannan yanayi "Tashi mu tafi na ce ." Ya sake jefawa Laila maganar mai tafe da umarni "Hakan ya sa Laila ta mike jiki a sanyaye "Haba dai Yaya Nasir, daga zuwa kuma , ko gaisawa ba a gama ba , ko ruwa baku sha ba zaka ce zaku tafi." Aunty Ummi tai maganar tana nuna rashin jin dadinta a zahiri Ba tare da Nasir ya ce da ita komai ba , kawai ya nufi kofar fita kana yana fad'in. "Sai wani lokacin." Ya fice Da sauri Laila ita ma ta zura takalmi tana cewa da Aunty Ummi. "Zan dawo wani lokacin Aunty." Tabi bayanshi da gudu gudu Ajiyar zuciya Aunty Ummi tai tana cewa. "Ikon Allah, Yaya Nasir fa sai a hankali ." Anan kuwa bayan Fa'iza ta fito daga lecture ta sami guri ta zauna. Babu dadewa sai ga Fatima ita ma fito daga tata lecture din Kai tsaye in da tasan tabbas zata sami Fa'iza nan ta nufa Aiko tana karasa ita ma ta sami guri kusa da Aminiyar tata ta zauna tana cewa. "Washh Fa'iza, gaskiya yunwa nake ji ." Fa'iza ta kalli Fatima cikin murmurshi tana . "To sai muje muci abinci ai ." Kafin Fatima ta maida mata ne kiran waya ya shigo mata Wani murmurshi Fatima ta saki tana kallon Fa'iza. Hakan ya tabbatar wa da Fa'iza cewa Abdallah ne ke kira . "Hello Abdallah." Abin da Fatima ta fada ke nan ba yan ta kara wayar bisa kunnenta Fa'iza tai ajiyar zuciya tare da kauda kai gefe , amman hankalinta na kan wayar da Fatima ke yi Yanayin yadda taji Fatima na maganar soyyaya ya sa idanun Fa'iza suka kada sukai jajir lokaci guda kuma kanta ya fara ciwo. Mikewa tai tsaye tai nisa da inda Fatima take tana share hawaye Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 *MAHAUKACIN SO* Na Autar Marubuta *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>< ________________________________________ Babu editing Page 11 & 12 Bayan Fatima ta gama wayar ta hangi Fa'iza can nesa da ita , hakan yasa ta mike tsaye ta nufi wajen Fa'iza Fatima na karasa wajen ta , tai ajiyar zuciya tana cewa. "Wai nan kika taho."? Fa'iza juyowa tai da murmurshi mai ciwo tana cewa. "Eh ." Lokaci guda kuma tana kokarin boye idanunta na kuka . "Kuka ki kai Fa'iza, mene ya faru ."? Fatima tai maganar tana fuskantar Fa'iza "A'a ba kuma nai ba Fatima." Fa'iza ta maida mata da amsa Murmurshi tare da ajiyar zuciya Fatima ta yi tana kuma cewa. "Wai ba kuka ki kai ba , dubi idanunki fa ." Fa'iza ta sunkuyar da kai kamar wata yarinya tana murmurshi. "Dan Allah me yake damunki Fa'iza, akwai abin da kike boye mini." Fatima ta fada tana rike hannun Fa'iza. Hakan ya karyawa Fa'iza zuciya, kawai ta fada kafadar Fatima tana kuka mai gwanin ban tausayi. "Ya Allah." Abin da Fatima ta fada ke nan cikin mutuwar jiki Cikin wannan kuka Fa'iza ta fara cewa. "Babu abin da yake damuna Fatima, kawai dai kwana biyu na kan yi kewar mommy, ta tafi ta barmu cikin damuwa, duk duniya bata min dadi Fatima, rashin mahaifiya babban abu ne." Fa'iza ta aje maganar tana shekar kuka. Murmurshi Fatima ta yi tare da d'ago Fa'iza daga kafarta tana cewa. "Haba kawata , rasuwar mommy ta girgiza mu , amman a halin yanzu adduar mu kawai take bukata. Dan Allah ki yi hakuri ki dena wannan kukan , Allah ya gafartawa mommy." Ta karasa maganar tana sharewa Fa'iza hawaye da hankicin dake hannunta Murmurshi Fa'iza tai tana cewa. "Haka ne Fatima na gode ." Fatima ta mika mata makullin motar dake hannunta tana cewa. "Yau ke zaki tuka mu , karbi ." Fa'iza ta amsa tana dariya. Nasir ne a tsaye bakin mota tare da Batula Batula tai murmurshi tana kallon masoyin nata tana cewa. "A gaskiya na yi matukar farin cikin ganinka a kofar gidan mu ." Yaya Nasir ya yi murmurshi yana cewa. "Batula ke nan , to idan banzo gunki ba , gurin wa zan zo , ke ce fa wacce nake burin aure , uwar yayana farin ciki na , kaf mata banga ta biyunki ba , wallahi Batula ina san ki ,so na gaskiya babu yaudara." Wani farin ciki ne ya lullube zuciyar Batula, wai yau Yaya Nasir ne ke mata wannan zance Cikin zabura Batula ta farka a baccin da take , sakamakon ruwan sanyi da taji an watsa mata . Tana ajiyar zuciya Batula ta farka , lokaci guda kuma tana kallon wacce ta watsa mata ruwan Ba wata babba bace domin Batulan ma ta girmeta . "Asararriya , har yanzu baki tashi kin yi wanke-wanke ba , to uban waye zai miki , wallahi kika bari na fadawa Daddy sai ranki ya baci ." Tana gama maganar ta fice Ajiyar zuciya Batula tai tana murmurshi da cewa. "Daman mafarki nake Nasir bai zo ba ." Tai ajiyar zuciya A lokacin Khairat ta shigo dakin tare da sallama Batula na ganin kawartata tai murmurshi ta ce . "Khairat ke ce."? Khairat tai murmurshi tana cewa. "Eh wallahi , zan biya gidansu Laila shi ne nace bari nazo mu gaisa." Ta karasa maganar tana kallon yadda duk jikinta ya jike da ruwa "Rahma ce ta watsa miki ruwa ko , ai naga fitarta da kofi." Batula tai murmurshi mai ciwo tana cewa. "Wata rana sai labari ai khairat, yanzu ina iyayena suke , haka kowa zai bar duniyar ai ." Tsaki khairat ta ja tana cewa. "Kullum haka ki ke cewa Batula, yanzu a ce kanin mahaifin ki wai bazai iya rike ki da mutunci ba , matarshi ta wulakanta ki yarshi ma haka , sannan shima bai barki ba ." Murmurshin nan me ciwo Batula ta sake yi kana ta kalli Khairat tana cewa. "Ai da babu abin da zan dana biki naje naga Nasir ko zan ji dadi ." Khairat tai dariya tana cewa. "Ke fa sai a hankali, yanzu ko islamiyya bakya zuwa , Yaya Nasir kuma Allah ya waiwayo da hankalinshi gare ki ." Batula ke nan yarinya me kalli da nutsuwa, duk da ba sa'arsu khairat ba ce , amman suna tare da juna cikin aminci, sakamakon haduwarsu a islamiyya Batula ta dade tana wahala a rayuwa, domin tunda Allah ya yi wa iyayenta rasuwa ta fara fuskantar rayuwa a gidan kanin mahaifin ta . Wanda komai wulakancin da suka debo kan ta suke zubeshi. Sai dai Allah ya jarafci Batula da san Yaya Nasir, domin babu abin dake faranta mata rai face ganin hotonsa ko wani jinin shi . Duk da cewa har yau yaki bata fuskar da zata nuna masa soyyayar da take masa . Ni ko nace Yaya Nasir a duba maraicin Batula mana🤔 Anan kuwa Yaya Nasir yanzu ya dawo daga aiki Tun kafin ya shiga gidan ya tabbatar wa da kansa tabbas sun yi baki , cikin far'a da sakin fuska ya nufi ciki, Duk da bai san wanne suka zo ba "Assalamualaikum." Nasir ya yi sallama cikin falon ya yin da yake raba idanu Rabi ya gani mahaifiyar Mahmud zaune a doguwar kujera, kana Laila tana kusa da ita , sai kuma Mahmud din a kusa da Laila wato dai duk kujera guda. Sannan Mama a gefe fuska cike da far'a "Wa'alaiku mussalam Nasir." Rabi ta amsa ita ma cikin far 'a Murmurshin yake Yaya Nasir ya yi , sannan ya samu kusa da Mama ya zauna yana cewa da Rabi . "Yau ku ne a gidan namu , sannunku da zuwa." Ya karasa maganar yana murmurshin da bai kai zuci ba "Ina wuni Yaya Nasir." Mahmud ya fada Sai da Yaya Nasir ya d'aga kai ya kalleshi sannan ya amsa masa Sannan ita ma Laila ta kalleshi tana cewa. "Sannu da dawowa Yaya." Ya d'aga mata kai , alamun ya amsa "Ina wuni Aunty Rabi." Nasir ke nan Rabi ta maida masa da fad'i. "Lafiya lau Nasir, ya gida ya aiki . Ya wajensu Ummi." "Lafiya lau suke ." Aunty Rabi ta maida masa da cewa . "To Masha Allah, ai Mahmud ne ya dameni , in zo in ga Laila, sai kace ban taba ganin ta ba ." Ta karasa maganar tana kallon Mahmud da cewa. "To mun zo hankali ya kwanta ." Dariya Mahmud ya yi tare da kallon Laila dake kusa dashi cikin matukar yanayin shaukin soyyaya. Duk a kan idon Yaya Nasir da ke murmurshin yake mai ciwo . "Ai in sha Allah Mahmud, Laila matarka ce." Yaya Nasir yaji maganar har cikin kansa yayin da Aunty Rabi ke fada "To Allah ya tabbatar da alheri, tuwo na mai na ke nan ." Mama ta fada cikin murna . Kawai da saurin gaske Yaya Nasir ya mike ya shige dakinsa Nan su kuwa suka cigaba da hirasu , yayin da Yaya Nasir ya kan iya jiyo su daga daki . Bayan Mahmud ya dau mahaifiyar tashi sun tafi.. Sannan Yaya Nasir ya fito falon ya zauna cikin matukar mutuwar jiki. "Uncle baka ci abinci ba har yanzu ." Laila ta fada tana kallon shi Kawai kau da kanshi yayi gefe ba tare da ya ce komai ba Laila ta kalli Mama, Mama kuwa bama tasan abin da ake ba , domin ta shagala da jan carbin dake hannunta "Uncle lafiya kuwa."? Laila ta sake masa shishshigi🤣 Agogon hannunshi ya kallah kana ya yi ajiyar zuciya. Kamar kuma bazai kalli Laila ba , sannan ya juyo gareta yana cewa. "Kina son yaron nan Mahmud." Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 13 & 14 Ajiyar zuciya Laila ta yi , kana ta kalli Uncle din nata tana cewa. "Yaya ni ban za bawa kai na kowa ba , duk wanda ya dace dani daga gareka nake jiranshi." Murmurshi Yaya Nasir ya yi, sakamakon yadda yaji abin da bai yi zatonsa ba Kawai ya mayarmata da cewa. "Jeki kawon abincin." Anan kuwa Abdallah da Fatima ne cikin mota , suke tafe a hanyar zuwa gidansu Fa'iza "Gaskiya fa kina son Fa'iza da yawah." Abdallah ya yi maganar ga Fatima yana murmurshi Ita ma Fatima murmurshi tai tana cewa. "Eh wallahi, haka nima take sona Dear, wallahi rayuwar Fa'iza abin tausayi ne , zan yi komai dan farin cikinta." Murmurshi Abdallah yay yana sake cewa. "Hmm ai na gani , gashi zamu shopping kin ce a biya a daukota. Nima ai ina san abin da kike so ." Murmurshi Fatima tai tana kallon masoyin nata Yayin data duba fuskar wayarta tana duba wani sako da ya shigo mata . "Karki manta yau muna da ganin likita." Hawaye ne suka ciko mata idanu , ta kalli Abdallah tana cewa. "Ina matukar kaunar ka Abdallah." Abdallah ya juyo yana murmurshi yayin da take ganin wannan hawaye. Bai iya cewa da ita komai ba , domin ji yay baki da ya ta karya masa zuciya. Fatima tai murmurshi ta fice sa'ilin da ya yi parking daidai kofar gidansu Fa'iza Kallo ya yi ta binta dashi har ta shige ciki Kana yayi murmurshi da ajiyar zuciya yana cewa "Allah sarki baiwar Allah Fatima ta, kyakykyawa mai hankali, ya Allah ka bani ita a kaddarata." "Fa'iza tashi , tashi." Fatima tai maganar tana janye malullubin da Fa'iza ta lulluba . Ta tashi zaune tana cewa. "Kai Fatima na tashi to mene." Dariya Fatima tai tana cewa. "Ki fito , ina ta kiran wayarki, Abdallah ne a waje zai kaimu shopping." Wani faduwar gaba Fa'iza taji ya ziyarce ta dajin sunan Abdallah "Abdallah kuma." Fa'iza ta nanata "Ehh tashi-tashi-tashi." Ta fada tana jawota , kana tasa kai waje tana cewa. "Ki sauri ki fito muna waje." Yadda Fa'iza take a wannan tsayen kawai ajiyar zuciya tai , ba tare data motsa ba "Aminiyata ce Fatima, bani da kowa bayan ke , tabbas bazan rusa mana alaka ba Fatima ko zuciyata zata fashe." Ta karasa maganar tana jawo wata doguwar rigarta mai launin marun gami da yellow Cikin sauri ta fara shiryawa Domin zuwa ta same su a waje . Tana fita kofar gida ta fara hangensu daga cikin gilas din motar , sai farin ciki suke abinsu Murmurshi tai sannan cikin nutsuwa ta fara takawa wajensu Murfin motar baya dake a bude nan ta shiga tana cewa. "Soyyaya ruwan zuma." Abdallah ne ya juyo yana mata murmurshi kafin ya ce komai Fa'iza ta sake fad'i. "To ina zamu ne ." "Zamu je Abdallah ya siyo mana abayoyi ne Fa'iza." Fatima ta bata amsa murmurshi Abdallah ya yi kana daga karshe kawai ya dore da dariya. Anan kuma Laila ce ita da wani had'ad'd'en saurayi a cikin falonsu . Bayan sun gama gaisawa da Mama, kana Mama ta shiga ciki ta barsu "Wato Laila tunda naje America, duk rayuwata babu dadi na yi matukar kewarki sosai fatan dai alkawarin mu na nan ." Saurayin mai suna Usman ya yi maganar A daidai lokacin Yaya Nasir ya nufo cikin falon Hakan yasa ya dakata sakamakon muryar Laila da yaji tana cewa. "Nima na yi kewarka sosai , amman har gashi kayi shekaru da yawa a America, gaskiya ban yadda ka damu dani ba , ko nema na baka taba yi ba ." Laila tai maganar cikin shagwaba Zuciyar Yaya Nasir ce ta sake karyewa a take a wannan wajen Cikin rashin ya ke cewa . "Usman ne ya dawo ."? Ya yiwa kanshi tambayar "To Laila auren mu shi ne zai tabbatar da irin kaunar da nake miki, amman ko rana daya babyna bata wucewa ba tare dana tuna ki ba ." Usman ya sake fada cikin soyayya Murmurshi mai jan hankali Laila ta yi sannan ta bude baki da niyyar cewa wani abu. "Assalamualaikum." Yaya Nasir ya shigo da sallama ya tari numfashinta. Sallamar ta amsa masa cikin far'a Kana Usman ya zamo daga kujera yana gaida Yaya Nasir Babu wani salo ko shauki Yaya Nasir ya amsa gaisuwar Sannan ya shige ciki. "Laila ko dai har yanzu Yaya Nasir yana fishi dani ne , ai yanzu na shiryu na gyara halayena Laila." Laila tai ajiyar zuciya domin ganin Uncle din nata a haka duk bata ji dadi ba Shi kam Uncle dakinshi ya shige ya zauna , Domin tabbas sam bai ji dadin ganin Usman ma . A lokacin baya Usman ya shigo rayuwar su da matukar son Laila , duk da cewa uncle baya son kowa ya kusanci Laila komin mutuncinsa kuwa. Sai Uncle yayi amfani da yadda Usman yake takadiri kuma mara ganin girman mutane ya raba shi da Laila. Soyyayar Laila ita ce ta gyara Usman har ya shiryu ya zama mutum , domin a halin yanzu shi yake rike kasuwancin mahaifin sa Alhaji Shehu shanshani , mutum ne mai matukar dukiya. A halin yanzu sam Uncle ba ya jin dadin dawowar Usman. To za mu ji yadda zata kaya tsakanin wannan mutane. Shin ko Mahmud ne zai auri Laila ko Usman ko wani daban . Muje mu tambayi Uncle kawai, Laila 'yar gwal ce .😝 Domin kuwa duk wani saurayin Laila Uncle baya son shi🤔 Yanzu mene ai bun Usman da Mahmud Uncle? Tom ba dai musan me Uncle yake nufi ba , mu dai mu sha bikin shalele 😆 Ga kuma bangaren Fa'iza da Fatima Ga kuma Batula To dai alkalamin Autar Marubuta ne. Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 15 & 16 "Haba dan Allah khairat, wai sai Uncle ya min fada ne , wallahi mun yi yawo sosai , duk na gaji." Laila ta fada cikin mita "Ke wallahi Laila munguwar matsala ce dake , Uncle Nasir da ba ya bari kina fita , shi ne yau kin fito amman sai mitar jaraba, ai gara ai miki auren ma , ki zaman gidan da hujja ." Dariya Laila ta kwashe da ita yayin da suke hada kafad'a da kafada suna tafiya Laila ta ce . "Aure manya , ai saina aurar da Uncle tukun." Da sauri khairat ta kalli Laila tana cewa. "Allah sarki harkin tuna mini Batula, wallahi Laila tana son Uncle sosai ." "Wai wace wannan Batulan kina yawan fada mini ita , kuma Uncle yana santa ."? Cewar Laila Khairat ta ja wo hannun Laila su kai wani lungu tana cewa. "Zo muje gidansu ki ganta , wallahi tana san Uncle." Wata gajiya ce ta sake rufe Laila da ganin yadda khairat tajata wannan waje . Hakan ya sa ta fincike hannunta tana cewa. "Wai duk ina kika san wannan wajejen, ni fa ba kowacce zan bari Uncle ya aura ba , sai wacce ta isa ." Khairat kawai taja mata tsaki Gidan Alaji Muktar Yana zaune ya yi tagumi , kawai yana tunanin irin yadda yayan da ya haifa suke ta mutuwa, a lokacin da yake bukatar su . Duk wacce danta ya mutu sai ya saketa , yana cikin wannan yanayin ne wata matarshi Hadiza ta shigo falon Zama tai kusa dashi tana cewa. "Alhaji lafiya kuwa." Ba tare da ya ce da ita komai ba ,kawai ya zaro wata takarda a aljihunsa ya mika mata . Faduwar gaba taji dasss Hannunta na rawa ta amsa tana budewa. "Innalillahi wa inna'laihir raji un Alaji ni zaka saki , innalillahi 😭." Kawai ta fara kuka , ya mike ya bar mata falon . Ana cikin haka sai ga uwar gidan nasa Hajjiya Ma'anatu ta shigo Tana kallon Hajjiya Hadiza da takarda a hannu tana kuka ta ce . "Innalillahi wa inna'laihir raji un Hajjiya Hadiza sakin ne ko, shi ke nan sauran ni , tunda daman Allah ya yiwa mahaifiyar shi Hajjiya rasuwa shi ke nan tamu ta kare ." Hajjiya Hadiza ta sake fashewa da kuka . Anan kuwa Batula ce zaune kan kujera tana wanke-wanke Ta yi nisa sosai kadan ya rage mata ta gama , sai ga sallamar su Laila Sai da Batula ta fara zuba musu wannan murmurshi nata kana ta amsa sallamar cikin farin ciki Suma cikin far'a suka karaso kusa da ita. Kafin wani ya bude baki ya ce komai , sai ji sukai wani "Shamm" Wasu uban kayan wanki wata mata mai zubin hajjiyoyi ta zube a kan Batula dake wanke-wanke. "Uban me kike har yanzu baki gama ba , to ga wanki nan , maza ki gama ki dora girki sannan ki fara ." Cikin biyayya Batula da amsa da "To Mommy." Kana wacce ta kira da mommy ta juya ta koma ciki Murmurshi Batula ta sake yi musu tana cewa. "Khairat ki dauko wa Laila abin zama mana." Ta karasa maganar tana kallon Laila da duk jikinta ya yi sanyi "A'a! Ke da kike aiki tafiya zami ." Laila ta fada cikin nufar hanyar fita . Bayan sun yi sallama khairat tabi bayanta Tunda suka fito Laila bata ce komai ba haka ma khairat, kowa yana sake-sake cikin ransa "Wai ita Batulan aiki take yi a nan gidan , kinji harta sanni ." Laila taiwa khairat maganar cikin sanyi Murmurshi khairat tai tana cewa. "Allah sarki Batula, yadda take son Uncle ba dole tasan ki , kin gan ta wallahi tana shan wahala , nan fa gidan yayan babanta ne , iyayenta sun rasu."... Nan khairat duk ta bawa Laila labarin Batula na abin tausayi da yadda take son Uncle A karshe duk tausayin Batula ya rufe zuciyar Laila Fa'iza ce tsaye gaban mudubi sanye da rigar da Abdallah ya siyo musu ita da Fatima "A gaskiya rigar nan ta yi kyau Abdallah." Fa'iza ta fada a cikin zuciyar ta, yayin da take sake juya jikinta tana ganin rigar Wayarta dake ringin yasa tai saurin juyawa ga wayar Kana ta zauna bakin gado tare da daukar wayar tana karawa a kunne da cewa. "Hello Rabin Raina Fatima." Daga can bangaren taji muryar Fatima tana cewa "Wallahi bana son fada miki wannan zance a waya kizo dan Allah." Ajiyar zuciya Fa'iza tai kana ta maida mata da cewa. "Gaskiya 'a'a Fatima." Ba tare da Fatima taji haushin hakan ba , cikin sabon farin ciki ta sake cewa. "An yi mana baiko da Abdallah, ashe dadi sun tsai da magana." Yadda kasan an yi ruwa an dauke, duk Fa'iza sassan jikinta suka dena aiki Sai bugun zuciyarta da yake yi kamar zai fito "Uhm wai da gaske." Fa'iza ta fada yayin da wasu zafafan hawaye suka zubo mata Cikin farin cikin dai Fatima ta tabbatar mata da wannan lamarin mai dadin ji . Bayan sun gama wayar , kawai Fa'iza tai murmurshi tana fad'in. "Fatima Allah ya tabbatar da alheri, Allah ya baku zaman lafiya da Abdallah." Ta rushe da kuka mai gwanin ban tausayi Farin ciki ya cika zuciyar Fatima, tana zaune cikin falonsu da wannan farin cikin ne mahaifin ta ya shigo , Sakin fuskar shi ya yi sosai ga yartashi guda kamar rai Zama ya yi yana fad'in. "Me ake yi ne me sunan Mama, kin sha magani ko." Shalelen baban nata baki ta zumburo tana cewa. "Daddy wai shi likitan nan ya yi ta bani magunguna, ni ban sha ba na gaji." Zaro idanu ya yi yana fad'in. "A'a yi hakuri mana 'yata, ai lafiyarki ita ce kwanciyar hankalina dana mahaifiyar ki , daure mana ai kin kusa samin lafiya in sha Allah." Murmurshi Fatima tai tana cewa. "To Daddy na , amman kafin bikin mu da Abdallah daddy ina so ka kai ni Umara , daddy idan da hali hadda Fa'izata." A lokacin mahaifiyar Fatima ta shigo tana cewa. "To masu Daddy." Ta karaso ta zauna Murmurshi Alaji ya yi yana fad'in. "Shi ke nan Fatima, zaku je in sha Allah karki damu." Cikin farin ciki ta mike tsaye tare da cewa. "To Daddy bari naje nasha maganin." Ta wuce cikin farin ciki Murmurshin Hajjiya tasa tana cewa. "Fatima ke nan , Allah ka bawa wannan yarinyar lafiya." Ajiyar zuciya Alaji Usman ya yi kana ya fara da cewa. "Wallahi Hajjiya ciwon yarinyar nan yana damun rayuwata, zan so ace Allah ni ya sanyowa wannan ciwo na zuciya a maimakon Fatima, wallahi zuciyata kullum bata samun nutsuwa idan na tuna da halin da take ciki." Cikin rarrashi mahaifiyar Fatima ta fara cewa da mijin nata Alaji Usman. "Haba Alaji! Ai shi bawa kowa da irin tashi kaddarar, muma irin tamu ke nan , ya jarafce mu da yarinyar da muka fi so , to mu yi tawakkali kawai mu gode masa , tunda gashi dai tana samun lafiya. Kuma ka ga Abdallah da danginsa zasu kula da yarinyar nan , dan sun san halin da take ciki kuma suna santa ." Alhaji Usman ya dukar da kai kasa ya d'ago yana fad'in. "Haka ne , badaban Fatima na son yaron nan ba , kuma auren sa zai faranta mata, da gaskiya ni bana son tai nisa damu , amman farin cikin ta shi ne namu." Hajjiya ta ce . "Haka ne." Anan ma Alaji Sani Shanshani ne zaune cikin wani furgitaccen had'ad'd'en falo. A gaskiya ciki da wajen wannan gida ya matukar haduwa ba a magana. Gefe guda kuma ga wata Hajjiya can da gani babu tambaya matarshi ce Sannan wasu 'yan mata su biyu masu kama da juna , suma zaune a kujera kowacce tana danna wayarta Sallamar dansu ce ta sa suka kalli kofar shigowa falon Yayin da hajjiyan ta amsa sallamar "Usman ina aka je ne."? Mahaifiyar shi Hajjiya ta masa tambayar Yana sosa keya ya karaso ya zauna yana fuskantar mahaifin sa Murmurshi mahaifin nasa ya yi yana fad'in. " Lafiya kuwa, meke tafe da kai ."? Satar kallon Hajjiya Usman ya yi sannan ya dukar da kai kasa lokaci guda kuma yana sosa keya "Daddy a kan maganar Laila ne." Murmurshi gami da dariya Alaji Sani Shanshani ya yi Sannan ya kalli matarshi yana fad'in. "Ai ni nasan akwai magana." Sannan ya koma ya kalli Usman yana fad'in. "Ai Usman a matsayin ku na 'ya'yana , bazan gaza muku a kan komai ba, tun daga lokacin da kowannen ku ya fara numfashinsa na farko a wannan duniyar, idan akwai wanda ya nemi abu daga gare ni ya rasa ya sanar dani." Ya kalli sauran yayan nasa Sannan ya cigaba da cewa . "In sha Allah zaka aure ta , bari daman ita ce sanadin shiryuwar ka , ai alhamdulillah." Su kai dariya Yayin da hajjiya ke cewa. "Sai a kawo mana ita mu ganta , domin kullum kiran sunan ta ake tun kana America." Usman ya yi dariya da cewa. "Za ta zo kuwa mommy." Anan gurin aikin Nasir kuwa. Tashinsa ke nan ya shiga mota da nufin tafiya gida Muryar kanin mahaifin sa Alhaji Bashir yaji tana kiran sunan shi Da sauri ya fito daga cikin motar zuwa waje , yayin da ya durkusa yana gaida Alaji Bashir. "Wai meke damunka ne Nasir, duk ka rame haka , ko akwai wata damuwar a gida ne ban sani ba."? Alhaji Bashir ya yi maganar cikin saurin baki kamar yadda ya saba . *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 17 & 18 Murmurshi Yaya Nasir ya yi , kana cikin girmamawa ya fara cewa. "Wallahi babu komai , komai lafiya lau." Alaji Bashir ya ce . "To ai shi ke nan Allah ya rufa asiri , ka gaida Maman." Yana gama maganar ya juya cikin bugaggiyar shaddarshi da malum-malum ya koma ciki Yayin da Yaya Nasir yake cewa. "Zata ji in sha Allah." Sannan Yaya Nasir ya sami damar shigewa mota . Anan kuwa Mama ce zaune ita da Laila, gama cin abincin su ke nan , domin ko kwanukan basu kwashe ba , wani ma da sauran abinci a ciki Laila wayarta ta aje gefe , ta kalli Mama tana cewa. "Mama Uncle ya taba baki labarin Batula."? Mama ta maida mata da cewa. "Wace kuma Batula." Laila tai murmurshi sannan ta ce . "Mama budurwar Uncle ce , tana son Uncle sosai , wallahi Mama rayuwar ta abin tausayi sosai , iyayenta duk sun rasu tana shan wahala." Mama ta maida mata da fad'i. "Allah sarki." A lokacin Nasir ya bankado labulai ya shigo tare da sallama Kusa da Mama yaje ya zauna a kujera yana ajiyar zuciya Ido suka hada da Laila, hakan yasa ta ce dashi . "Sannu da zuwa Uncle." Ya ce . "Sannunki ke ma ." Ido suka sake hadawa a karo na biyu, Laila tai murmurshi tana sunkuyar da kai "Uncle kana lafiya kuwa."? Laila ta tambaya "Duk ka rame sosai ." Murmurshin ciwo Uncle ya yi , sannan ya ce . "Alaji Sani Shanshani jiya da kanshi ya zo a kan maganar auren ku da Usman." Laila ta zaro idanu cikin mamaki Kafin ta ce komai Uncle ya cigaba da cewa. "Amman bazan bari ki auri Usman ba bai dace dake ba Laila." Laila ta sunkuyar da kai Mama ce ta mike tsaye cikin bacin rai tana cewa. "Nasir wannan abin ya ishe ni , lokaci ya yi da zaka bawa Laila miji ko ka barta ta zaba, tunda ka nuna mana kafi kowa iko da ita . Domin bazan zuba ido yadda kaki aure ba , ka zaunar da Laila ita ma a cikin gida, abin ya isa haka ." Wani furgitaccen zafi Yaya Nasir yaji a zuciyarshi , domin ya lura da batun Mama babu wasa a ciki "Ko Usman ko Mahmud, duk wanda Laila take so , ka aura mata, wannan abin ya isa haka tom." Ta shige daki Cikin yanayin damuwa Laila ta kalli Nasir, babban tashin hankalin data gani yasa duk tunanin ta ya rude Hawaye ta gani bisa idanun Uncle sun zaru suna shirin zubo . Kawai ya mike ya fita kafin a kai ga wannan lokacin Ajiyar zuciya ita ma Laila ta sauke me zafi tana kallon kofar da Uncle din nata ya fice , duk ta rasa me yasa ta damu yanzu haka , kuma tausayin Uncle duk ya kamata. Yaya Nasir ya na fita gidan Umar ya nufa kai tsaye . Shima Umar ya yi mamakin ganin Uncle a wannan lokacin da bai saba zuwa ba Babu korafi Umar ya masa iso har falo suka zauna. Shi kan shi Umar ya fuskanci Yaya Nasir yana cikin damuwa "Abokina lafiya, tunda ka zauna kai shiru , ko wani abun yana faruwa ne ."? Yaya Nasir ya kauda kai tare da ajiyar zuciya "Hmmm." Abin da Umar ya iya fada ke nan Hakan yasa Yaya Nasir ya kalli Umar ya fara cewa. "Mama ce ." "So take na aurar da Laila." Murmurshi Umar ya yi yana fad'in. "Laaa kaji wani zance me dadin ji , alhamdulillah Masha Allah, ai Mama wannan abin da tai shi ne daidai , domin baka da niyyar aurar da ita ." Cikin sauri da mamaki Yaya Nasir ya kalli Umar dake kusa dashi Cikin farin ciki Umar ya sake jaddada masa da cewa. "Wallahi wannan ya yi , a cikin Mahmud da Usman, nasan Laila zata so daya ." Da sauri Yaya Nasir ya mike tsaye tare da wata ajiyar zuciya Idanunsa suka canza kala "Wallahi Umar bana son aurar da Laila ga kowa, idan naji ko naga wani na binta da sunan soyayya sai naji duk na tsane shi , bana son rabuwa da Laila Umar, ban shiryawa hakan ba." Ya karasa maganar yana rike rigar Umar kamar mai shirin zarewa. Tsoro ne ya rufe Umar da ganin yadda Nasir yake . Kawai Nasir ya yi murmurshi ya sake shi sannan ya kama hanyar fita ba tare da yace komai ba "Ikon Allah." Umar ya fada yana bin sa da kallo Bayansu Fatima sun fito daga lecture, kawayenta sai matukar farin ciki suke da jin yadda aka sanya bikinsu da Abdallah Fa'iza tana cikin class a zaune, domin tunda aka fita bata fita ba , ko zuwa duba Fatima ba tai ba ko sun fito Durkusar da kai tayi bisa benci Babu kowa cikin ajin , daga ita sai wani dalubi da yake karatu a can bayan benci Wata me suna Maryam ce ta shigo ajin yayin da take kallon wannan dalubi da cewa. "Munaf. Sannu da kokari." Ya amsa mata da "sannu Maryam." Kai tsaye gun Fa'iza ta nufa , yayin da take kiran sunanta tana kuma kokarin d'ago mata kanta sama Cikin jajayen idanu Fa'iza ta d'ago "Maryam ya akai ." Maryam cikin rike haba ta fara fad'i. "Haba Fa'iza, wai meke damunki, duk sai ramewa kike yi , haba dan Allah mene ne ."? "Babu abin dake damuna Maryam." Fa'iza ta maida mata da amsa Ba tare da jira ba Maryam ta sake maida mata da cewa. "Gashi idanunki sun yi jah , alamun kin yi kuka , ai shi ke nan , idan tayi wari maji ." Dariyar da bata kai zuciya ba Fa'iza ta yi Sannan ta ce . "Ina Fatima."? "Fatima tana can tana ta nemanki fa , bata san baki fito ba ."..... Fatima ce zaune kan gado tana kallon hotonta dana Fa'iza Murmurshi tai tana shafa furkar Fa'iza, sannan ta fara cewa. "Ban san meke damunki ba , wani abu ya dade yana damunki amman kin ki sanar dani ." Zama ta gyara tana sake zumin din hoton ta cigaba da cewa. "Aminiyata har a aljanna, ina kaunarki Fa'iza, in sha Allah zan yi kokarin sanin meke damunki, tun da baza ki sanar dani ba ." Ta karasa maganar tana kallon saman dakinta kamar me yin wani Nazari . "Wannan wanne irin rashin mutunci ne da cin fuska , yanzu yarinyar nan Laila kina ji wai yaron gidan Alaji Sani Shanshani zasu bawa." Inna tai maganar bisa wayar dake hannunta ta kara a kunne "Mene ne Alhaji Sani yafi mijin Rabi ? Tsabar cin mutunci, to wallahi wannan lamarin ba a a yi shi ba ." Daga can bangaren Bahijja cikin muryar girmamawa ta fara cewa da mahaifiyar tata "Dan Allah Inna ki yi hakuri abi wannan lamarin a sannu , yanzu haka ma ba haka zancen yake ba ." Cikin wannan fada dai Inna ta sake fadin "Kamar ya ba haka zancen yake ba , wallahi naje gidan naci mutuncin Nasir din , tunda ba shi data ido ." Bahijja ta sake fad'in "Ni dai dan Allah Inna ki hakuri, karki je gun Nasir da wannan maganar." Inna ta ja dogon tsaki tare da kashe wayar tata Anan kuwa Batula ce ke girki ta kunna wayarta Tana sauraran wakar hamisu breaker mai taken "So Ne." "Banza jaka kin damu mutane da waka." Juyowa Batula tai tana kallon Rahma dake fada mata wannan maganar Batula kashe sautin ta yi kana ta cigaba da abin dake gabanta "Ai wallahi bari daddy ya dawo , zan fada masa Musa me gyaran takalmi yana son ki gara kawai a aura masa ke mu huta ." Da sauri da tashin hankali Batula ta kalli Rahma tana cewa. "A'a dan Allah Rahma, karki fadawa Daddy wannan maganar, Musa ba san shi nake ba , kuma daddy zai kama zancen ki ." Cikin maraici Batula ta karasa maganar "Hhhhhhhhhh to ai taimakon ki zai , banda shi waye yake son ki , can zaki talauci ya kashe ki banza ." Tasa kai Batula tai saurin riko rigar Rahma, hakan yasa Rahma ta dakata tana kallon ta cikin zafin rai "Uban me zan miki kika riken riga kazama kawai." Ba tare da Batula ta damu dajin wannan maganar ta Rahma ba ta fara cewa... *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta _______________________________________ Babu editing Page 19 & 20 "Kar ki fadawa Daddy, Musa kowa yasan ba ilmi ne dashi ba ." Rahma tasa hannu ta doke hannun Batula, taja tsaki sannan ta wuce Kawai hawaye Batula taji ya zubo mata Anan kuwa Alaji Sani ne yake yin waya ,yadda ranshi yake a turbune bai canza ba ya fara cewa. "Haba Akilu, to ita wannan yarinyar yar gidan waye, da zaka ce an nemeta a garin nan an rasa, bayan na fada maka ina tafiya a titin babbar unguwa ta taalakawa na ga yarinyar, sai da nai ta jira ko zanga inda ta shiga amman ban gani ba , gaskiya ka sake kokari Akilu ka zo min da labari mai dadi ." Yana gamawa ya aje ajiyar zuciya tare da cewa. "Gaskiya wannan yarinyar tamin , lokaci guda san ta ya kamani, tomm Hajjiya kishiya na tafe a gidan nan." Ya yi maganar shi kadai yana tunano yadda yadda ya ga wannan yarinyar, sai abin yake faranta masa rai . Sakamakon yau asabar babu inda Uncle yaje , tun wajejen hantsi yake a falo , har zuwa wannan lokacin da rana ta kusan faduwa. Idan har kasan Yaya Nasir, to yanzu idan ka ganshi zaka iya cewa ba shi bane. Duk da cewa shi ba mitum bane mai kiba , amman yana da matukar kyan gani Lokaci guda kuma yanzu duk yabi ya lalace , tunda Mama ta fara maganar auren Laila. Wayarshi tana gefe kusa dashi , yayin da shi kuwa yake kwance a kujera. Laila ce ta fito daga dakinta sanye da hijab ta karaso gabanshi "Uncle dan Allah me yake damunka , ko abinci har yanzu baka ci ba ." Uncle ya kauda kai gefe kamar bai ji maganar tata ba . "Uncle magana nake ." Kallonta ya yi cikin wani yanayi na isa yana cewa. "Tashi ki bani guri ." Ta kalleshi tana sunkuyar da kai da ajiyar zuciya Mikewa tai ta juya zata koma inda ta fito Taji muryar Uncle Nasir yana cewa. "Babu abin da yake damuna Laila." Hakan yasa ta juyo ta koma ta sake zama , Shima Yaya Nasir ganin ta zaune ne ya tashi zaune. "Uncle bani da kamarka a duniya, haifata ne kawai baka yi ba , idan nagan ka cikin wani yanayi bana jin dadi ko kadan , dan Allah Uncle idan a kan aure na ne ka dena damuwa, bazan auri kowa ba , sai wanda ka zaba mini koda bana san shi ." Nasir ya yi murmurshi mai ciwo , sannan ya ce . "Karki damu Laila, ina miki kaunar da bana son kowa ya rabe ki , amman akwai alamun lokaci zai raba mu ." Mama ce ita ma ta fito rike da carbi a hannunta ta samu guri ta zauna. Laila ta kalli Uncle cikin zumudi tana cewa "Yawwa Uncle, shi ne baka taba fadan komai a kan Batula ba ko." Wani dasss Yaya Nasir yaji ya dakar masa zuciya Ya kalli Mama da sauri Ba tare da Laila ta dubi yanayin da yake ciki ba , ta cigaba da cewa . "Gaskiya Uncle tana san ka , naji kuma an ce ko saurararta baka yi ." "Marainiya ce fa Uncle, wallahi tana shan wahala." Ajiyar zuciya Yaya Nasir ya sauke tare da cewa. "Nima ai maraya ne , sannan ke ma haka , babu wani soyyaya a tsakani da wannan yarinyar Batula, kin ga Laila ki dena maganar ta ." Kafin Laila ta bude baki tai magana Khairat ta turo kofa ta shigo tana sallama Abin da ya basu mamaki ganin Batula biye a bayanta "Wow Uncle, ka ga Aunty Batula 'yar halak." Laila ta fada ta tashi da gudu tana rungume Batula Yaya Nasir ajiyar zuciya yayi yana kauda kai gefe Mama cikin far a ta kallesu tana cewa "Auu wannan ne Batulan."? Mama ta aje maganar daidai da inda Batula ta zube gaban Mama tana gashsheta Nan Mama ta gaisa da Batula cikin sakin fuska, wanda hakan ya yiwa Batula dadi "Yaya Nasir ina wuni ."? Khairat ta fada bayan sun gaisa da Mama Ita kuwa Laila Sam bakinta ya kasa rufuwa , ta tsaya a kansu ta kasa zama "Ina wuni Yaya Nasir." Batula ta fada cikin sunkuyar da kai "Lafiya." Ya fada a takaice "Gaskiya Uncle kun dace sosai da juna .". Laila ke nan ta fada yayin da Yaya Nasir ya hade ransa Mama dariya ta yi kana ta mike tsaye tare da shiga ciki Kujerar da Mama ta tashi Laila ta zauna a hannunta tana magana cikin shauki "Ke khairat taso mu bar musu falon." Kafin khairat ta tashi Uncle ya mike zai fita "Uncle baku gaisa ba fa." Laila ta fada Dariya ya yi kamar me jin kunya kafin yace komai Khairat da Laila suka fita Kamar abin arziki Uncle ya koma ya zauna Hakan yasa Batula ta d'ago kai tana cewa. "Kayi hakuri Yaya Nasir , na zo ban sanar da kai ba , wallai ina cikin damuwa kala-kala , ganin ka ne zaisa naji sauki , shi yasa nazo tunda baka iya zuwa inda nake ." Wani takaici Yaya Nasir yaji ya turke masa zuciya Ya kalleta cikin zafi yana cewa "Ki dena yaudarar kan ki Batula, babu wani soyyaya tsakanin mu , babu yarinyar da nake so , hasalima bansan ya ake jin soyyaya ba , ya kamata ki sani bana san ki , kar kuma ki kuma zuwa inda nake babu abin da zaisa na soki har na aure ki ." Ya tashi ya fita Ajiyar zuciya mai zafi Batula ta sauke Gaff da kuka , zuciyar ta na mata zafi Lokacin Khairat da Laila suka shigo Wani murmurshi na yake sosai Batula ta jefa musu "Har an gama soyyayar Aunty."? Cewar Laila cikin tsokana Baki khairat ta tabe tana cewa. "Ki dubi wannan fuskar tata kice wani an sha soyayya. Laila Yaya Nasir fa baya san Batula maganar gaskiya ke nan ." Murmurshi Batula tai duk da bata ji dadin maganar ba "Inji waye 😏, shi kuwa yake sona , ina kaunar Yaya Nasir Laila, kaunar da bansan daga ina take zubowa ba." Ta aje maganar tana rike hannun Laila fuska da hawaye Zafi Laila taji a zuciyar ta , ta kankame hannun Batula tana cewa. "Uncle mijinki ne Aunty Batula kar ki damu dan Allah." Murmurshi Batula tai tana cewa. "Allah ya sa ." Matukar tausayin Batula ya sake rufe Laila "Kira Mama mi sallama mu tafi." Khairat ta fada tana mikewa tsaye. Fatima ce ta fito daga wanka , gama sa kayanta ke nan , Fa'iza ta shigo tana cewa. "Wai dan Allah tun yanzu zaki tafi , ki bari sai anjuma mana ." Harara Fatima ta jefa mata yayin da take sanya man lebe ta ce da Fa'iza. "Ai dole ki fadi haka , tunda kwanan da nayi ma bai miki ba ,ke fa Fa'iza sau daya kika taba kwana a gidanmu." Ajiyar zuciya Fa'iza tai kafin ta ce . "To ai naga nan da can din duk daya ne , amman ina nan zan zo na kwana karki damu ." Fatima tai shiru yayin da take kallon babban madubin dakin tana kallon irin yadda tai kyau Yadda Fa'iza ta lura da ita ne yasa tai murmurshi tana cewa. "Wayyo kyau , ka ga amaryar Abdallah, gaskiya baby kin yi kyau ." Dariya Fatima ta sake yi tana cewa. "Wato dan ki wayantar da zancen da muke ko , ai shikenan." Fa'iza mikewa tsaye tai tana rike hannun Fatima cikin kauna ta fara cewa. "A"a Rabin Raina Fatima, babu abin da yake damuna, to idan ina tare dake mene zai dame ni , bari ma gashi kullum kina samun lafiya, ai wannan kadai ya isa ." Murmurshi Fatima tai tana fad'in "Alhamdulillah, to tunda haka ne gaskiya kawai ki shirya Abdallah ya aure mu tare domin ban shirya rashin ki ba ." Cikin sauri da firgita Fa'iza ta saki hannun Fatima lokaci guda kuma ta fara dariyar da Fatima bata gane ba . "Haba dai , ai ni Abdallah ya min kauyenci , sai dai ke shalelen babanta." Cikin tsokana ta aje maganar Dariya kawai Fatima tai , ba tare da tace komai ba ta dauki Jakarta ta rataya.. Dariya Fatima ta juyo tana yi , "Jiya na tashi sallah da dare ina ta tashin ki baki tashi ba ." Fatima tai maganar tana sanya agogo a hannunta "Hmmm , wallahi Fatima kawai bacci ne yaja ni , kuma kaina sai ciwo ." Fa'iza ta mayar mata Da sauri fateema ta fara cewa. "Daman haka zancen yake ai, kullum ciwon kai , saboda kina da damuwa baza ki fadan ba ." Fa'iza ta ce . "Hmmm". Update kullum ne ,idan ta kama sau biyu a rana . amman ga wa 'yanda suke bukata. *MAHAUKACIN SO* farashin sa kan N300 kacal Ga masu bukata su tura kudinsu a 7040805269 Fatima Abdullahi Ismail opay digital services Sai shaidar biya a 07040805269 Bana son kati🙏 *MAHAUKACIN SO*❤️ Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 21 & 22 Baiwar Allah kamar kullum, yanzu ma wanke wanke take yi , Allah Allah take ta gama ta yi shirin zuwa islamiyya Jin muryar Rahma tai a bayanta tana cewa. "Ke kizo daddy yana kira." Ta juya ta koma ciki Da sauri Batula ta mike tana share hannunta ta nufi inda suke zaune suna kallo Sallama ta fara yi kafin ta shiga ciki Duk da babu wanda ya amsa ta nufi kusa da mahaifin Rahma ta zauna tana sunkuyar da kai . Kamar saukar aradu ta ji yana cewa. "Wannan yaron Musa, ya zo neman auren ki , kuma daman yanzu Rahma take fadan kina san shi ." Da sauri da tashin hankali Batula ta d'ago kai tana kallon shi "Daddy ba haka bane , kasan Musa ko asalinsa ba a sani ba kuma .." "Ke rufe min baki ." Baban Rahma ya fada "Ke da zaki farin ciki kin samu miji , kina ganin ko ita Rahma bata sami irin shi ba ." Kuka Batula ta fashe dashi tana fad'in "Wallahi Daddy bana san shi ." "Tashi ki tafi ki bani guri , ni nasan abin da ya dace ." Baban Rahma ya fada , yayin da matarshi taja tsaki tana cewa "Karyar banza, idan bamu aura miki shi ba , waye me son naki ." Batula ta fita tana tare da tarin damuwa a fuskantar ta. Abincin safe suke ci , wajejen karfe 10, sakamakon yau Yaya Nasir bai fita aiki ba, kana garin an tashi da sanyi, yasa suke ta bacci abinsu. Sallamar Alaji Bashir ne yasa Mama sanya mayafi bisa kanta, lokaci guda kuma tana amsa sallamar Laila ta kalli Uncle din ta tana murmurshi "Shigo Alhaji Bashir." Mama tai maganar tare da canza wajen zama . "Assalamualaikum." "Sai yanxu kuke karyawa ke nan , an gayu." Laila tai dariya Gurin da Mama tai masa nuni da ya zauna , nan ya zauna tare da aje babbar wayarshi da mukullin motarsa "Baba ina kwana."? Laila ta fada ta na kallonshi Cikin saurin baki kamar yadda ya saba ya maida mata. "Laila lafiya kalau ." Sannan shima Nasir ya mika masa gaisuwa Yana gama amsar gaisuwar Nasir ya fara gaida Mama cikin far'a Tare da tambayar yanayin sanyi da aka fara shiga Nan Mama ta tabbatar masa komai da kowa lafiya. Sannan ya ce ."To Masha Allah haka ake so ." Shiru suka yi na wasu sakanni Sannan Alaji Bashir ya kalli Mama yana cewa. "Wato abin dake tafe dani, ba komai bane face Inna mahaifiyar babar Laila ta zo ta same ni ." Yaya Nasir da sauri ya kalli Mama, suka hada ido sannan Mama ta koma tana kallon Alaji Bashir "Ta sanar dani cewa, kai Nasir zaka bawa Laila yaro mara tarbiya , alhalin ga Mahmud can yana san ta . Kuma sannan ma kai waye a wajen Laila, bayan ni ina raye , da har zaka ba wani Laila, ba tare dana sani ba ." Yaya Nasir yaji zuciyar shi tai wani irin bugu suka hada ido da Laila Laila tai ajiyar zuciya ta mike tsaye tare da nufar dakinta "Ke Laila zo nan , ina zaki ." Alaji Bashir ya fada , sannan Laila ta dawo ta zauna Ajiyar zuciya Alaji Bashir yayi , sannan ya cigaba da cewa. "Ni bazan aurar da Laila ga wani ba , amman kasan cewa har yau bakai aure ba , sannan naga alamun Laila ma zaman gidan kake so tayi , domin ina samin labarin komai ." "Tom na baka lokaci daga yau, ka tsayarwa da Laila mijin da zamu aura mata , kuma na baka wannan damar ne domin yadda ka kula da Laila da yadda kuka shaku." Mama ta ce . "Wannan gaskiya ne , nima abin da nake so ke nan ." Alaji Bashir ya ce . "Yawwa wannan shi ne abin da ya kawo ni, domin Hasana yata kanwar Laila yanzu tana dakinta, Kuma kaima ya kamata kayi aure zuwa yanzu ." Matukar tashin hankali ya bayyana a furkar Yaya Nasir Ajiyar zuciya yayi ya kalli Alaji Bashir yana cewa. "Alaji abin da yake faruwa, har yanzu ban sami wanda zan aurawa Laila ba , Kuma wallahi da zarar an yi maganar auren Laila sai duk hankalina ya tashi ." Alaji Bashir ya mike tsaye tare da cewa. "Na dai baka lokaci, da zarar ya kare ni zan aurar da ita ga Mahmud." Ya nufi hanyar fita tare da sallama da Mama. Zumbur shima Nasir ya mike tsaye, duk su Mama ya basu tsoro Hanyar fita ya bi kai tsaye gidan Umar ya nufa babu ko takalmi a kafarshi. Dake babu nisa tsakaninsu sosai , cikin babban tashin hankali Yaya Nasir ya nufi gidan Umar. Umar na kokarin shiga gida, ya hangoshi yana tahowa, sai da ya zo gaff da Umar, Umar ya fara murmurshi tare da cewa. "Ka ga angon Batula." Lokaci guda yana kallon kafarshi da ya lura babu takalmi Kafin Umar ya sake maganar Yaya Nasir har ya juya ya sake nufar hanyar gidansu. "Kai lafiya kuwa, ko dai wani abin ne yake faruwa a gidan ."? Umar ya tambayi kanshi yayin da yake hangen Yaya Nasir dake komawa gida cikin dafewar kai Da sauri Umar ya shiga gida, da nufin ya dauko wayarshi ya bi bayansa. Laila ta mike ta koma kusa da Mama cikin matukar tausayin Uncle dinta ta fara magana. "Mama me yake faruwa da Uncle ne, yanzu fa ko takalmi babu ya fita , kullum sai ramewa yake ." Mama ajiyar zuciya ta sauke , sannan ta ce da Laila. "To nima ta ya zan sani Laila." Rufe bakin Mama ke nan Uncle ya shigo , kai tsaye kuma ya nufi dakinsa. Shima sai ga Umar ya shigo tare da sallama "Auu Mama nayi zatan wani abin ne yake faruwa, na ga Nasir cikin wani yanayi , shi yasa na biyo bayanshi ." Mama ta ce "Ummm ! Kai ma dai ka fada Umar, gashi nan daga maganar auren Laila ya koma haka ." "Bari na shiga dakin nashi ." Umar ya fada tare da nufar kofar dakin Koda Umar ya shiga , Yaya Nasir yana zaune bakin gadonshi ya dafa kanshi . Haka ya amsa sallamar Umar ba tare da ya d'ago ba . "Me yake faruwa ne Nasir."? Umar ya yi masa tambayar yana zama a gefenshi Hakan bai canza komai ba daga Yaya Nasir Sai bayan wasu sakanni sannan ya d'ago kai yana cewa "Ni ne fa na raini Laila Umar, ni ne fa ." Sai wasu hawaye sharrrr suka zubo masa "Tabbas ya kamata Laila tai aure , amman akwai ciwo a zuciya ta , bana son rabuwa da Laila , Umar in takaice maka zance ina MAHAUKACIN Son Laila , so na aure , da zamu rayu tare da juna har abada.".. Umar cikin tashin hankali ya damke masa baki , domin kar su Mama suji wannan kazamin zance . Lokaci guda gumi ya ketowa Umar *MAHAUKACIN SO* Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 23 & 24 Yaya Nasir ya wurgar da hannun Umar gefe, Cikin buguwa kamar dan maye ya koma ya kwanta. Wani das das das zuciyar Umar take bayarwa , ya kalli Nasir dake kwance cikin rashi yana cewa. "Wai daidai naji kuwa? Ko dai Nasir ya haukace ne , an ya kuwa abin da ya fada haka naji."? Ya aje ajiyar zuciya me zafi, kana da ya lura yayi bacci Ya nufi hanyar fita. "Ahh Umar tafiya zaka yi ne." Umar ya ce . "Eh Mama." Sannan shima ya fice kamar furgitacce Laila ta kalli Mama tana cewa. "Wai Mama baki ga Yaya Umar gumi yake ba , bayan sanyin da ake yi Ko dai fada sukai da Uncle."? Mama kawai ta ce mata "Ummm." Fitowar su ke nan daga harabar makaranta, suna jiran Abdallah. "Fatima da kin zo mun hau nafef kawai mun tafi Abdallah ya bata lokaci." Fatima cikin wasu idanu ta kalli Fa'iza sannan ta ce . "Fa'iza akwai abin da ya rikeshi , kuma yanzu zaki ganshi , gashi kaina yana matukar ciwo sosai , zazzabi nake ji Fa'iza." Murmurshi Fa'iza tai tana rike hannun Fatima, yayin da motar Abdallah tasha gabansu . Tun dazu Batula take zaune a falo tana jiran fitowar yayan babanta da take kira da daddy Domin wajen minti 30, ke nan tana zaman jiranshi Sai da aka sake kwasar minti biyar sannan Alhajin ya fito tare da matarshi. "Au ke Batula kina nan ashe." Ya fada yayin da yake lunkuma wani naman kaza a bakinsa . Sannan sai ga ita ma Rahma ta shigo rike da wannan naman a cikin plet, Sai da ya cinye wannan naman na bakinshi tasss , sannan ya kalli Hajjiya yana cewa. "Ita kun bata naman ko."? Rahma da sauri ta maida masa da cewa "Daddy ai idan taci nama wai zuciyar ta ke tashi." Tai maganar tana mata gwalo Kawai Batula tai murmurshi "Kaji yar baiwa shi ke nan Musa ya huta da siyen nama." Alaji ya fada Wani bakin ciki Batula taji ya turnike mata zuciya, Yadda Rahma tai mata sharrin bata cin nama bai bata mata rai ba , kamar yadda Alaji yanzu ya ambato sunan Musa mai gyaran takalmi. Shanyewa tai kawai tai shiru , sannan Alaji ya fara da cewa . "Batula abin da yasa na kira ki , ke kamar yar cikina ce , domin ke yar kanina ne Abubakar , mutum ne mai biyayya, kuma daman an ce mutuncin ya mace gidan mijinta." Tunda Batula taji wannan batu tasan inda ya nufa Hakan yasa suffar ban tausayi ta sake kamata "Jiya magabatan Musa sun zo mini , kan neman aurenki ." "Amma na ce su jira ni zasu ji daga gare ni , fatan dai kin shirya auren yaron nan , domin mutumin kirki ne , zai rike ki da mutunci, sauran gadon mahaifin ki dake hannuna sai ai miki kayan daki dasu ." Murmurshin mai matukar ciwo Batula ta ajiye sosai , domin yadda wani bakin ciki ya tsaya mata a zuciya yasa ta dole tayi wannan murmurshi. Duk da haka ba tai kasa a gwiwa ba , ta kalli yayan babanta tana cewa. "Daddy akwai wanda nake so , amman wallahi ba Musa ba ne , ka bani dama domin ..." "Ke dallah yi shiru, yana magana kina magana ko ."? Mahaifiyar Rahma ta fada Rahma ita ma ta dora Da cewa . "Karya take yi ma daddy babu wani wanda yake santa ." Alaji ya cigaba da cewa "Ai baza ai haka ba Hajjiya ,." Ya koma ya kalli Batula yana cewa. "Na baki kwana uku , ki kawon shi yaron da kike so , idan har ya cancanta to zan aura miki shikenan." Zumbur Batula ta mike cikin farin ciki tana cewa. "Na gode daddy Allah ya saka da alheri." Ta mike ta fita . Rahma tana jan wani tsaki . Tsabar farin ciki Batula ta rasa yadda yadda tai , amman lokaci guda ta kame tare da tunanin yadda zata kawo Nasir gaban Alaji , to tabbas wannan babban lamari ne, Amman ta yanke shawarar shiryawa ta nufi gidansu khairat. Fitowar Nasir ke nan zai tafi wajen aiki , ya kalli Mama sannan ya ce . "Ina Laila ta shiga kuma Mama."? Mama ta maida masa da amsa tana cewa. "Taje gidan kawarta ne ." Sannan Mama ta sake kallonshi tana cewa. "Ka ga yadda ka rame kuwa Nasir,duk ka lalace jijiyoyi ta koina haba Nasir meke damunka ne ." Yaya Nasir ya yi murmurshi sannan ya ce ."Mama ta ke nan , babu abin dake damuna, bari naje na dauki Umar mu tafi office." Yasa kai yana murmurshi Bayan Yaya Nasir ya isa gidan Umar, Umar ya fito suka tafi , sakamakon motarshi na wajen gyara . Suna tafiya cikin mota , Umar bai iya cewa da Nasir komai ba , domin kawai tunanin irin maganar da yaji yayi yake yi , "Shin wai gaske ne ko dai bai ji daidai ba , ta ya Nasir zaka ce kana son Laila." Umar yake maganar cikin ransa yayin da take kallon Nasir ta gefe . "Umar kana lafiya kuwa. Tunda muka fito kayi shiru ."? Yaya Nasir ya fada yana kallon shi . Murmurshi kawai Umar yayi , kafin ya ce . "Ai kai za a tambaya Nasir, duk ka rame ka lalace, kamar wanda cuta ke cinsa ." Duk yanayin fuskar Uncle ta canza , ya kalli Umar, sannan ya maida hankali ga tuki yana cewa. "Lokaci ya yi da zaku san Laila rayuwa ta ce , duk da cewa kaji na fada shekaran jiya, kar kai tunanin ba na cikin hayyacina." Umar ya ji gabanshi ya sake faduwa da sake jin maimaicin wannan babbar zugar maganar daga Nasir. "Wai dan Allah Nasir kan ka daya kuwa , magana ake ta Laila kai ne ubanta , babu aure a tsakaninku, dan girman Allah kai shiru da wannan maganar, idan kuma wasa kake ka dena kar zuciya ta , ta buga . Wannan zancen kasan girmansa kuwa."? Da babban tashin hankali Umar ya masa maganar. Yaya Nasir ya aje ajiyar zuciya sannan ya ce . "Babu aure ka ce tsakani da Laila, tabbas ina son Laila Umar, Kuma wannan zancen dole ya fita waje, domin Laila tare zamu kasance." Hadiyar yawu Umar ya yi yana cewa. "Innalillahi wa inna'laihir raji un. " Tafiyar dactor ke nan ya gama duba lafiyar Fatima, sakamakon yadda bata jin dadi , Alaji Usman duk yabi ya tashi hankalinsa Fatima na zaune tare da mahaifin ta , sai ga Fa'iza ta fito daga dakin Fatima sanye da Jakarta a hannu . "Ba dai tafiya zaki ba , bayan mun yi dake anan zaki kwana , Kuma kin sanar a gida ." Fatima tai maganar tana kallon ta . Kawai Fa'iza tai dariya tare da juyawa tana cewa. "Daman so nake naji bakinki." Dariya Alaji yayi sannan Fatima ta tai saurin dakatar da Fa'iza da cewa . "Fa'iza ko zaki shiryawa Abdallah wani abin , ya ce mini zai zo yau ." Fa'iza ta juyo tare da cewa. "To ranki ya dade." Fatima tai murmurshi. Fa'iza na komawa dakin ta aje jakar tare da murmurshi tana cewa. "Fatima ke nan . Abdallah manya Allah ya kawo ka ." Matukar tashin hankali Umar yake ciki ,domin samm ya kasa fahimtar wannan zancen na Nasir baki daya , Idan yayi tunanin abin da yasa Nasir yake ramewa ke nan , Kuma yaki bawa Laila kowa ta aura, sai ya ga kamar gaske son Laila ya ke kuwa Amman Umar sai yayi tunani sosai , sannan ya koma ya tuba , domin lamarin tabbas ya yi muni sosai . *MAHAUKACIN SO* Na Autar Marubuta ________________________________________ Babu editing Page 25 & 26 Khairat da Batula ne a zaune, bayan Batula ta gama zayyanawa khairat tarin damuwa da yadda sukai da Alaji mahaifin Rahma. "Amman gaskiya Batula wannan lamarin babba ne , yanzu ta ya har Uncle zai yadda da aureki , cikin kwana uku har yazo gidan ku , Tabb." Khairat ta fada cikin gano matukar wahalar abin . Batula ta amsa da cewa. "Haka ne khairat, wallahi sai yanzu nima hankali na ya tashi, amman ya zanyi idan Musa shi ne kaddara ta ." Ta aje maganar tana kuka , duk sai zuciyar khairat ita ma tai sanyi , amman haka ta fara rarrashin ta , duk da ita ma khairat bata da wani kwarin gwiwa. "Assalamualaikum." Laila ta shigo dakin kharait tare da sallama Ita ta amsa sallamar ciki murya mara wadatuwar kuzari "Ahh me zan gani haka , Aunty Batula mene ya faru kike kuka kuma." Laila tai maganar tana durkusawa a gabansu. "Mutuwa aka yi ne khairat."? Laila ta sake fada. Sai da khairat tai murmurshi sannan ta ce . "Babu wata mutuwa, maganar auren ta ne, yayan babanta yace ta fito da miji kwana uku ko ya aura mata Musa, kuma kinsan Yaya Nasir take so . Sai kuma sauran matsaloli da baza a rasa ba ." Cikin rarrashi Laila ta fara cewa. "Haba Aunty Batula, dan Allah ki dena kuka , kuma in sha Allah da ikon Allah zaki auri Uncle dina , wallahi Aunty Batula zan yi duk yadda zan domin ki aure shi ." Murmurshin farin ciki Batula tai tana cewa. "Wallahi da burina ya cika Laila, da kuwa dukkan bakin cikina ya yaye." Laila ta ce . "Karki damu anuty." Murmurshin jin dadi ita ma khairat tai sannan ta fara cewa. "Ka ga yar gidan Uncle, daga ina haka ." Laila ta ce . "Hmmm daga gidan su Sadiya , kinsan yau ne Usman zai zo muje gidansu." Dariya khairat tai tana cewa. "Eh wannan gaskiya ne kuwa , ka ga amaryar Usman, sirikar Alaji Sani Shanshani." Duk suka kwashe da dariya. Sannan khairat ta sake kallon Batula tare da cewa. "To ya maganar jarin ya baki baban Rahman." Baki Batula ta tabe tana cewa. "Tab! Ni na ce ma ko a kudin gadona ne ya bani , amman yaki, bazai banba , bai bani da cikakken hankali, kuma wallahi ina son bude shagon atamfofi da takalma ko salun ne ma." Khairat tai murmurshi, yayin da Laila ta kara da "Ummm Auntyna Batula." Fa'iza ta gama shirin tarbar Abdallah tsaf,domin babu dadewa Sai ga Abdallah ya zo , sai da ya kwashi gaisuwa wajen Alaji da hajjiya sannan tare da yi musu ya mai jiki, sannan ya samu damar isa inda Fatima da Fa'iza suke . Tafiya suke cikin mota , babu wanda ya ce da kowa komai , sai dai kowa sake-saken shi yake a zuciyar shi. Fargabar Umar kar Nasir yaje gida ya bayyana Mama wannan zancen, domin tabbas yadda ta tsufa sai ya kasheta kasheta lokaci guda, tunanukan da Umar ya ringayi ke nan , Ganin Nasir ya kusan kawoshi gida yasa shi fadin . "Mu wuce gidan naku domin madam bata nan ." Ba tare da Yaya Nasir ya bashi amsa ba ya cigaba da tafiya a mota, yayin da yake kara gudu . Cikin kankanin lokaci suka isa gidan, Umar kamar yadda tun tuni ya saba ya fada cikin gidan yana sallama. Sannan bayan Nasir ya aje mota , shima ya shigo . Zama sukai a falon , lokaci guda kuma suna hada ido da juna . Umar ya yi saurin kauda kai gefe, wanda yayi daidai da fitowar Mama daga dakinta. "Auu kun dawo ke nan , Umar sannunku da zuwa." Umar ya amsa da . "Sannu Mama da gida." "To bari a kawo muku abinci ai kunsha rana ." Ta shige da nufin kawo musu Ajiyar zuciya Yaya Nasir ya sauke me zafi, kamar me shirin fara magana , amman ya yi shiru. "Nasir me zai hana ka dau hutu , kaje kaduna dangin Mama ai zaka huta ko." Umar ya yi maganar kamar mejin tsoron Nasir. "Ni yanzu babu wani hutu da zan je , anan ma ina hutawa ne ." Lokacin Mama ta gama aje musu abincin sannan ta samu guri ta zauna. "Mama ina Laila ne, tunda na shigo banji motsinta ba ." Uncle ya tambaya Mama ta kalli kofar dakin Laila kana ta ce . "Tana can tana shiryawa , ko ka manta yau Usman zai zo ya kaita gidansu." Da sauri Nasir ya mike tsaye, shima Umar yayi saurin mikewa. "Lafiya kuwa, kaji min yara ."? Mama ke nan Umar ya yi murmurshin yake tare da komawa ya zauna. Lokacin Laila ta shigo sanye da babban dogon hijabi , "Yau kika ce Usman zai zo Laila."? Ta kalli Nasir da fad'in. "Eh Uncle yama taho." Ya koma ya zauna kamar wanda aka cirewa laka. Ba tare da Laila ta dubi hakan ba ta fara cewa. "Uncle dina dan Allah ina neman alfarma a gunka , dan Allah." Ta karasa maganar tana durkusawa "Tashi -tashi , hau kujera ki zauna.kin fi karfin haka lailata, ke rayuwa ta ce kuma babu abin da zaki nema ki rasa." . Ta mike ta zauna, Mama ta ce . "Iko sai Allah, shakuwar Laila da Nasir." Ba tare da Laila ta sake jiran komai ba ta ce . "Uncle dan Allah ka dubi rayuwar Batula, ka share mata hawaye, ta nuna ka matsayin wanda zata aura, Uncle dan Allah ka aurota ta zamto matarka, tana cikin wani hali." Idanunta cike da ruwa ta karasa maganar Mama taja dogon numfashi, Umar kam lokaci guda ya rasa tunanin sa , domin ganin Nasir ya tsaya yayi jimmm yake tunanin irin amsar dazai bayar Murmurshi mai cike da karfin hali Umar ya yi . "Sannan ya ce . "Masha Allah." Nasir ya kalleshi Wayar Laila ce ta fara ringin Babu ko shakka Usman ne , hakan yasa ta mike cikin mutuwar jiki, Mama ta tashi ta nufi dakinta Ganin Laila ta fita ne , yasa Umar fad'in. "Dan Allah Nasir ka nutsu, kasan abin da zakana fade, ni wallahi idan ka bude baki zakai magana ba karamin tsoro nake ji ba , karkaji yadda zuciya ta ke zafi, gaskiya wannan ba Nasir din dana sani ba ne." "Umar kanajin abin da Laila tace kuwa, Batula fa, bayan ba wanda nake son rayuwa da ita sai Laila, gaskiya lokaci yayi da ya kamata kowa ya sani." Tsakiyar kan Umar ya sara , sakamakon jin maimaicin wannan zancen "Shin dan Allah Nasir ina ilminka, dole ne na kaika wajen malam ya sake tabbatar maka babu aure a tsakaninku, haba Nasir." Cikin kasa-kasa da murya ya yi maganar Lokacin Laila da Usman suka shigo nan Usman ya gaidasu Nasir ya mike tsaye tare da fad'in. "Tare zamu tafi, kaima Umar idan zaka je ka taho, zan kai Laila gidan , ni banma san dalilin da yasa wani sai taje gidan ku ba ." Ya yi tsaki ya dau mukullin motarsa ya fita . Aiko haka aka tafi, motar Usman a gaba sannan Uncle da Laila a tasu motar Haka suka isa gidan wannan shahararren mutum me kudi. Tabbas Uncle sun ga karamci sosai, haka kowa na gidan suka gaisa da Laila cikin farin ciki. Sai dai babban tashin hankalin da Alaji Sani Shanshani ya sami kanshi Laila ita ce yarinyar da ya ke ta neman ko yar gidan waye, domin tunda Allah yasa ya ganta kwanaki hankalinsa ya kasa kwanciya , tabbas son Laila yake bada wasa ba , sai dai kaf a cikin su babu wanda ya kula da irin yadda mahaifin Usman wato Alaji Sani hankalinsa ya tashi, bayan yaga Usman dansa ita ce yarinyar da yake burin aura. Tabbas zamu ga yadda za ai da wannan MAHAUKACIN so. A wannan tsakiyar daren Alaji Muktar ya tashi yana ta rusa kuka . Haka har ya tashi matarshi Hajjiya ma'anatu. "Lafiya lafiya kuwa Alaji."? Ta masa tambayar tana share idanunta na bacci . Cikin wannan kukan ya fara cewa. "Tabbas Allah abin tsoro ne Ma'anatu, yanzu bani da komai sai tarin dukiya kawai, bani da farin ciki bani da sukuni , haka Allah ya yi wa Hajjiya rasuwa tana shirin ganar dani hanya me kyau, na zama butuulu abin gudu abin kyama, rayuwa ta babu wani kyau a cikinta." Ya sake rushewa da sabon kuka Duk sai tausayinshi ya kama Hajjiya, karon farko data fara ganin kukan sa . Kafin ta ce dashi komai ya cigaba da cewa. "Allah ya jikanki uwata, Allah ya jikanki Hajjiya, kullum gobe na kike son ta gyaru, gashi yanzu na girma, tsufa ya fara cimmin Hajjiya innalillahi wa inna'laihir raji un 😭." "Tabbas lokaci ya yi da zan gyara kuskure na, ya Allah na tuba , ya Allah na tuba ." Ya kwanta kafar Hajjiya Ma'anatu yana sake rangada kukanshi Farkawar Fatima ke nan , ta tashi da niyyar yin sallar darenta kamar kullum yadda ta saba , Haske ta kunna cikin dakin tana kallon Fa'iza dake ta sharbar bacci . Murmurshi Fatima tai tana cewa. "Bari na yo alwaala kema tashin ki zan Fa'iza." Ta karasa maganar yayin da kanta yayi wata sarawa Hakan yasa ta koma bakin gadon ta zauna,tana dafa kanta , Ta bata wajen minti biyar sannan ta mike tsaye tare da shiga bandakinta dake cikin daki Babu bata lokaci ta dauro alwala, sannan ta shinfida sallaya , Kana ta nufi bakin gado tana lissafin baza ta iya wannan sallar a tsaye ba "Fa'iza." Fatima ta fada da niyyar tashin Fa'iza a bacci . Kafin ta sake bude baki ta kira sunan Fa'iza , taji muryar Fa'iza ba tare data farkaba tana cewa. "Shi ke nan Abdallah, son ka ne kaddarata, amman kafi dacewa da Fatima, babu yadda zan yi ." Cikin tashin hankali Fateema ta durkusa gaban Fa'iza dake bacci Bisa idanunta ta ga hawaye jeri-jeri . Ajiyar zuciya mai zafi Fatima ta sauke tare da fad'in. "Abdallah kuma."🤔 To masu karatu alhamdulillah Masha Allah nan na kawo karshen free page na wannan labarin nawa mai suna MAHAUKACIN SO. Ga masu son jin yadda kowanne sashi na wannan littafi zai kasance kofa a bude take Koda yaushe masu bukatar cigaba da karanta wannan labarin, suna iya biyan kudinsu ta wannan hanyar 👇 7040805269 opay Fatima Abdullahi Ismail Shaidar biya 07040805269 300 naira only 🙏